*TMWB2K001* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj Kamar wasu zakaru haka suka tsaya a bakin hanya suna kallon juna. Shi Sadiq ya Rufe kwayan idanuwansa ammh da ya bayyanasu da rauninsa ya bayyana, sakamakon Tahir da ke kallonsa cikin takaici da wani irin bakincikin da bai taba tsintar kanshi aciki ba. har gwara ace Mutuwa a kayi da wannan Danyen Hukuncin da Sadiq ya yanke ma Rayuwarsa. Tahir bakinsa ne ya yi nauyin da ya kasa mgana shi kuma Sadiq ba shi da kalaman da zai kare kansa a lokacin. Har abokan aikinsa da ya gayyato Anas da Mudansir ba yan zariya ba ne dukkansu yan cikin garin kaduna ne. Zuwa suka yi suka ba shi hannu suka yi musabaha tare da yi masa murna. Duk da auran nasa ya ba su mamaki lokaci d'aya haka, Sannan ba kamar sauran aurarrakin da suka saba zuwa ba ne wannan sai ya zame musu kamar Dabam. Ammh kamar yadda Sadiq ya yi musu gim da fuska Haka Tahir ya kallesu ya watsar shi ko hannun bai mika musu ba sai ya koma jikin Bangon gidan Baba Tanko ya jingina bayansa lokaci d'aya ya hard'e hannayensa a kan kirjinsa ya na hangen Sadiq yan Tsirarun mutanen da ba su watse ba suna ta faman yi masa Allah ya sanya Alheri cikin su harda Isuhu duk da shima ya yi mamakin faruwar auran da gaggawa haka kuma shi Adda bata fad'a masa da wani daurin aure ba ta kuma tabbatarsa masa Amma da Hasiya zai Dauko ya kawomata ammh ganin abunda ya faru sai yasan dole Lissafin ya sauya. Bai jira sauraran Habiba ba ya hau mashi ya koma Samaru. Ya bar su Sadiq a kofar gidan Baba Tanko Tsaye mai afkuwa ta riga ta afku shiyasa Sadiq ya ji gabadaya duka kalaman bakinsa sun kare shi kuma Tahir kafafunsa ne suka yi sanyin da suka kasa Daukansa ballatana yasan mafita bayan sun fito daga wajen da aka daura auran da har Abada ba yajin zai iya goyama Sadiq baya akan wannan Shirmen nasa. Suna nan tsaye sai ga Adda Fati da Habiba sun fito tun daga nesa ta ke kallon Sadiq wanda ya coge a tsaye duka Hannayensa suna cikin Aljihun wandonsa kansa kuma na kallon kasa bazaka iya Fahimtar a wani yanayi yake ciki ba. Ita kanta mamakin bai gama Sakinta ba tunda yaran Baba Tanko suka shigo da labarin Daurin auran Hasiya bata tsinke da Lamarin Amma ba sai da Baba Tanko ya shigo shima ya ke fad'in Daurin auran da kanshi. Har Adda Fati tayi subutan baka tace masa"Da wa aka daura ma Hasiya aure Baba.? Kai tsaye ya kalleta kafin yace"Da wanda uwarku ta aiko ki da shi mana" Daganan sai Adda Fati ta Fahimci Tsakiyar labarin da Karshe. Farkon ne yanzu kad'ai ya rage ta sani shi kuma Amma ke da Hakkin da zata fidda kowa acikin Duhu. Sanda ta kariso wajen ta na so ta yi mgana ammh itama sai bakinta ya yi mata nauyi kawai sai ta Rausayar da kai ta na fadin"Mu je ko? Ta yi gaba Sadiq ya taka ya bi bayan Habiba wacce sai ta juyo ta kallesa ta koma kuma ta kalli gabanta ta kasa yi masa mgana shima kuma ya kasa ko sakar mata fuska yadda ya saba. Tahir ne bai bi bayansu ba Sadiq ya juya ya na kallonsa kafin yace"Tahir.". Tahir ya kallesa kai tsaye batare da ya taso ba, Ballatana kuma ya yi masa mgana. Sadiq yasan daman haka zata faru zai Fuskancin Turjiya ta hannun Tahir. sai dai gwara Turjiyansa bayan Komai ya faru da Turjiyansa kafin hakan shine babban matsala tunda ya tabbata bazai taba barinsa ya cika wannan ladan na taimako ba. Sai da yaje da kansa ya riko hannunsa Sannan ya biyosa. Suna tafe har bakin Titi Adda Fati ta sake tsaida musu abun hawa kamar na dazu suka sake shiga sai Samaru har kofar gidan su Hasiya. Wannan karon da suka sauka Sadiq ya biya kudin adaidaitan. Sun iske Ana ta loda kaya a budaddiyar motar da Isuhu ya kawo saura ma kad'an a gama. Sadiq ya manta da zencen ta shin su Amma shi kuma Tahir dariya ce ta kusa kamashi ya zata kayan auran Hasiyan ake lodawa sai ya kalli Sadiq ya na fad'in"Gusau za'a wuce da kayan auran ko Shinkafi? Sadiq ya kallesa cikin mamaki shi kuma ya na dariya ya nuna masa motar kayan. Sadiq ya yi tsam bai yi mgana ba Tahir kuma kai ya girgiza kafin yace"Na kasa gane abunda kuma muka sake dawowa nan muna yi a tsaye." Sadiq dai bakinsa gum bai yi mgana ba Tahir sai k'ak'alan mgana ya ke Sadiq ya tankasa ya yi masa bore. Adda Fati ko ta na shiga gidanmu matan gidammu suka yo mata caa fad'i suke yi ashe kuma an Daura Auran Hasiya? Cikin sakewa ta ke amsa musu da cewa Eh ko dai na munafunci ne suna ta fatan Alheri. Ta na daga labulen dakin mu dukkanmu muna inda ta barmu labarin da muka samu baisa mun iya dagawa daga in da muke ba. Amma ce dai ke ta zirga zirganta sai Inna Talatu da tare da ita aka rika fita da kaya ita da yara zuwa waje. Amma na ganinta ta washe baki ta na fad'in"Fati ya aka yi ne? Adda Fati tace"Amma su na waje" Da Sauri Amma tace"To to..! Ni ta kallah kafin tace"Ramatu ku je dakin Maman boy ke da Hasiya. Zan kira ku daga baya." Ina jin haka kamar Daman ina kan kaya ne na mike Zumbur  dauke da Hanifa domin ba ni da idanuwan da zan iya kallon Assadiq a daidai wannan lokacin. Dakin Maman Boy muka shige ni da Ramatu da dukkammu muka kasa yi ma juna mgana. Ita dai sai kallona ta ke yi ta na mirmishi ta kasa mgana ni kuma sai tunani da ya cika min kaina a raina nake ji Amma ta so kanta in dai tunaninta ne wannan bai kamata saboda jin dad'in ka kai ka jefa rayuwar waani cikin wahala da ukuba hakan ba daidai ba ne. Bamu san yaushe suka shigo ba an d'an juma sannan Adda Fati ta leko tace mu zo dakim Amma ni da Ramatu. Daman da Hijabi a jikina tunda kayanmu gabadaya an had'a su waje d'aya sai dai nawa akwatin Amma ta hana a fita da shi ta na jin dadi tace kayana a bar su tukunna ba da ni zata tafi ba gidan mijina zan zauna in sha Allahu. Hanifa ce ta tashi sai na ari zanin Maman Boy na goyata Ramatu kamar zatayi min mgana sai kuma ta fasa ammh ina ganinta ta na kunshe Dariyanta. Itace gaba sannan ni ita kuma akaji sallamanta ni dai a saman lebena sallamar ta tsaya kuma har muka shiga na samu waje na zauna ban yarda na dago fuskata ba. Kusa da Ramatu na rabuke kamar wata marainiya. A sace na kalli mutanen Dakin Adda Fati sai Adda Rukayya Hamma Isuhu da bansan yaushe ya shigo ba. sai Habiba da Inna Talatu ban kalli Barayin Assadiq ba ammh naga kamar ba shi kad'ai bane ne zaune akan Dauduma daga gefen Amma. Muna zama Amma tayi gyaran murya kafin ta fara fad'in"Hasiya tun jiya ki ke tambayata me na Tattauna da Abubakar ko? Sai alokacin na Dago kaina ina kallonta a jiyan ne zuwa da Safe na ke neman karin bayani ammh daga dazu zuwa yanzu ba na bukatar wani karin bayani. Sai dai ban ce mata komai ba na maida kaina kasa ina wasa da yatsun hannayena acikin Hijabina. Amma ta cigaba da fad'in"Bayan Hasiya ina so kowa anan ya zama Shaida kan mganata. Nasan zuciyarku na cike da Tunanin ta ya ya haka ya faru? mganar gaskiya ni ce na kira Abubakar da kaina na kuma kwance masa komai na labarin Rayuwarmu da Halin da Hasiya ta tsinci kanta aciki sannan ni ce nan na yi masa tayi auran Hasiya batare da Tunaninsa ko cewarsa ba." Nasan kowa ya kalli Amma alokacin ban da ni saboda nasan daman za'a zo wajen ai tatsuniyar gizo daman bata wuce ta kok'i in ba Rokomsa ta yi ta ina Rayuwata ta dace da Rayuwarsa? Sai dai na jira ta gama ne duk da ta na mahaifiyata bazan fasa gayamata gaskiya ba abunda ta yi son kai ne sannan ba ta yi daidai ba. Ba wanda ya tambayeta dalilinta na aikata haka da kanta ta cigaba da fadin"Rauni irin na uwa ita ta sakani aikata haka. Hasiya yata ce na santa fiye da kowa acikin ku. Abubuwa da dama sun faru da ita a kananun Shekarunta wanda ba da son ranta ba ne ina son Hasiya ina kuma kaunar itama ta samu natsuwa da ingantattaciyar rayuwa a gidan auran ta kamar yadda yan'uwan ki suka samu, wannan Kwad'ayin yasa fara ganin Abubakar da Natsuwarsa da Hankalinsa yasa rauni irin na uwa batare da wani Tunani ba na yi masa tayi auran ki Hasiya." Amma ta karishe fad'a muryanta ta fara rawa alamun kuka. Sadiq ya dago ya na kallonta mganarta a jiya ta na dawo masa. Ya tausayama Rayuwar Hasiya matuka duk da ya ji labarin a bakin Tahir sai dai shi ba yadda ya Dauka ba ne. Yaji duniyar ta tsaya masa Lokacin da Amma ta durkusa a gabansa ta had'a Hannayenta waje d'aya ta na kuka ta na rokomsa da ya rufa mata asiri ya auri Hasiya. Alokacin kallonta ya yi a tsorace kafin yace"Aure kuma Amma? Meyasa zaki ce na auri yarki Ahalin baki sanni ba bakisan komai a game da ni ba? Amma ta bude baki cikin kuka ta na Fad'in"Bansan ka ba Abubakar ammh wlh tallahi naji lokaci d'aya ka shiga raina ina ji kuma ajikina bazaka taba cutar da Hasiya ba." Sadiq ya dad'e ya na kallon Amma ajiyan ya na tunanin ita ko meyasa zata yi haka? Cikin Sarkewar murya yace"Ba ni da kowa sannan ba ni da komai da me zan riketa? Sannan in dai a wajena ne ba zata samu kyakyawan rayuwar da ki ke mata fata ba, Saboda ni d'an makaranta ne ba ni da komai sannan ban mallaki komai ba Amma" A lokacin Amma ta fad'i wasu maganganu da suka sanyaya masa jiki da su ne silar da suka saka ya amince ya taimaki uwar da ke bukatar taimakonsa indai yasan Darajan Mahaifiya. Kafarsa ta kama ta rike lokaci d'aya ta na fad'in" _Ka ciyar da ita da abunda kaci Abubakar, Sannan ka Tunfatarta da ita da abunda ka tufatar da kanka, sannan ka ijiyeta a inda ka ke Rayuwa  Ba rayuwar Kud'i ko dukiya Nake son Hasiya ta yi ba. a'a ina mata Fatan rayuwar natsuwa kwanciyar Hankali mai Dorewa har Abada._" Ya na wannan Tunanin ita kuma Amma na warware musu yadda tattaunawarsu ta jiya ta kaya tsakaninta da Abubakar. Tahir na kallonta ji ya ke kamar ya tashi ya fita domin gani ya ke kamar Tatsuniya ta ke faman maimaita musu sannan ji ya ke kamar ya bude baki ya gayamata Sadiq ba maraya ba ne da yasa ta yi wasa da rayuwarsa Abun alfaharin wani kyakyawan Ahali ne sannan dan gata ne da bai Chanchanci auran kaskanci kamar yadda ta cutar da shi wajen aura mata zabiyar bazawaran yar ta ba. Amma ta share hawaye da Haban zaninta ta na fad'in"Ba na so na tafi da Hasiya garin mu  saboda nan ne ta saba da shi fiye da ko'ina sannan zata fi sakewa in ta na ganin yan'uwanta a kusa da ita da wannan dalilin yasa na Roki Abubakar da ya aureki Hasiya sannan ki yi hakuri ban nemi jin ta bakin ki ba duk da addini ya baki wannan damar ni na yanke miki Sadakin ki da kaina nace ya bada Dubu talatin mun yafe komai Daga bangaransa. Na tara ku ne ku zama shaida sannan na raba minti saboda Mutanen da ke zagaye damu suma su shaida hakan. Isuhu ma naji dadi da ya zama shaida wanda da ni da shi zamu iya gayama Adda abunda ya faru wanda bata sani ba ni zan bishi mu tafi na bar Hasiya Hannun mijinta Abubakar da na ke da yakinin zai rike min ita bisa gaskiya da Amana. Sannan na barta hannun ku Inna talatu Ramatu Fati da Rukayya Hasiya ta ki ce Amanarta da kula da Rayuwarta duka suna Hannun Allah ne kuma suna hannunku. Ku kular min da ita don Allah tunda kuna gani Rayuwarta ba ta yi daidai da irin kyakyawan Rayuwar da ku ka samu ba." Sai kawai Amma ta fashe da kuka wiwi. Adda Fati ma ta fara tayata Inna Talatu ne ta ke fad'in"Ki yi Shuru Aisha in sha Allahu kyakyawan Niyarki ta Alheri bazata tafi a banza ba. Hasiya kuma kada ki damu ki kaddara kina tare da ita in sha Allahu." Amma ta gyad'a kai cikin muryan kuka ta kalli Sadiq da Tahir da kansu ke kasa kamar ba sa wajen tace"Abubakar ga Hasiya nan. Ka rike hannunta ka da ka saketa har abada. Ka zame mata bango wanda zai kareta ga duk wani abun k'i, ka zame mata tudun Dafawa Abubakar ka kare rayuwarta ga dukkan wani barazana. Nasan Hasiya bazaka taba samun matsala daga bangaranta ba zata zauna da kai ta yi hakuri da kai sannan zata yi maka biyayya har karfin iyawarta Allah ya baku zaman Lafiya tare da zuru'a mai albarka a Tsakanin ku." Tahir a saman lebensa yace ba Ameen ba Sadiq kuma sai ya samu kansa da amsawa acikin ransa. Inna talatu ta bude murya ta na amsawa da Ameen Ameen. Amma Adda Fati ta kallah kafin tace"Kayan Hasiya na jere su na wuyan ki Fati na bar komai a hannunki." Adda fati ta jinjina kai kafin tace"In sha Allahu Amma." Adda Rukayya ta sake kallah kafin tace"Rukayya ke ce Babba. Ki rike girmanki ki ja yan'uwanki ajiki kada ki manta bayan su baki da yan'uwan da suka wuce su, Ki zama Alkaliya mai adalci a tsakanin kannen ki, ki yi hakuri da su don Allah bayan ba ni ke zaki cigaba da Bibiyan lamarin su. Sannan kada ku manta da Dangin babanku ku bisu ku yi zumumci da su ko da su baza su yi zumumci da ku ba hakki ne ku a kan ku ku yi zumunci da su." Adda Rukayya kanta na kasa tace"In sha Allahu Amma" Amma ta juya ta na kallon Ramatu Lokaci d'aya ta na fad'in"Ramatu ba sai nace miki komai ba. kinsan matsayinki a rayuwar Hasiya basai na yi miki wata mgana ba, nasan zaki yi komai domin ganin Farinciki a rayuwar Hasiya nagado miki sosai Allah ya saka miki da Alheri ya Dauwamar da zaman lafiya a tsakanin ki da mijinki." Ramatu ta amsa da cewa"In sha Allahu Amma Ameen nima nagode." Kowa sai da ya yi mgana a dakin nan ban da ni da kaina ke kasa ko motsin kirki ban yi ba. Amma ta kalleni na wani Lokaci kafin ta kira sunana ina Dagowa ta ga hawaye suna bin kumatuna alamun kuka naci a zaunenan da na ke. Cikin mirmishi Amma tace"Hasiya baki ce komai ba? Ajiyar rai na Sauke kafin nace"Amma me zan ce? Kin riga kin yi abunda baki shawarce ni ba, gaddama ko saba Umarninki ba Halina ba ne ammh wannan karon na kasa yi miki biyayya. Na kasa jin auran nan a raina Amma na kasa." Ba Amma kad'ai ba hatta Sadiq da Tahir a tare suka dago suna kallona. Ni ko idanuwana na Runtse sai hawaye Sharr cikin kuka nace"Nasan rayuwata cike ta ke da tarin kaddarori ina cikin Tsaka mai wuya Amma, Kinsan na sani aure ba shi ne mafita a cikin Rayuwata ba. Nayi auran nan na farko me na tsira da shi bayan saki da Tozarci? Ban karaya ba na sake yin wani auran shima me na Tsira da shi bayan Sakin wulakanci da Tozarcin da ya biyo baya Amma meyasa kuma zamu kara koma gurbin da muka san karshensa? Kin so ni kin yi son kai Amma kin jefa Rayuwar sa cikin Rayuwata Alhalinsa kinsan karshen hakan daidai ya ke da asaran dukiya da asaran lafiya da wani abunda wannan karon bamu san me zai Faru ba." Na karishe fad'a cikin kuka Amma da Sauri ta mike ta na fad'in "Hasiya.." Cikin Daga murya nima na mike ina Daga mata hannu Lokaci d'aya ina Fad'in"A'a Amma. Wannan karon baki yi daidai ba. Kin so ni ki ki shi, Kuma Hadisi ne kyakyawa ka so ma Dan'uwanka abunda ka ke so ma kanka. Amma na riga nace na gama aure a duniyar nan indai ta sanadina Rayuka zasu rika baci suna shiga mawuyacin Hali wlh na Hakura na Hakura Amma." Bansan lokacin da naji wani irin kuka ya fito daga kasan raina ba sai gani kawai suka yi na zube a kasa ina wani irin gunjin kuka domin kafafuna ne suka daina daukana da ya sa dole na bi zabinsu na zube a kasa. Kuka na ya tada Hanifa da ke bayana da Sauri Adda Rukayya ta yaye hijabina ta saukota duk ta had'a zufa. Kokarin kamani su ke in tashi naki Amma sai ta fashe da kuka ta kasa mgana. Cikin kukan na d'ago muka Had'a ido da Assadiq. da rarrafe na karisa gabansa cikin fitan hayyaci nace"Ka yi ma girman Allah ka sakeni ASSADIQ. ka da ka kara minti d'aya da aure ne a tare da kai  ka tsira da rayuwarka don Allah. Ka gani bazan damu ba, Salisu ma ranar da aka daura ma aure ya sakeni ammh duk da haka bai Tsira ba yana nan yana jinya Abubakar ma sai da komai na shi ya kare sai da komai na mahaifinshi ya kare duk saboda Dalilina ka sakeni ni ba kamar sauran matan da zasu samu kwanciyar Hankali ta sanadin aure ba ne ni Hasiya na yarda Annoba ce sannan gobarace ni duk inda na shiga sai naci Dukiya ko na taba lafiya." Na karishe fad'a ina wani irin kuka Amma ta dakamin Tsawa lokaci d'aya ta na fad'in"Hasiya lafiyan ki kalau kuwa? Cikin kukan na cigaba da fadin"Amma me yasa kika yi min haka batare da sanina ba? Kina so ki dauwama kina ganina cikin kunci ? To wannan auran ne zai sakani cikin kuka kamar yadda sauran suka zo suka kare haka shima wannan zai kare kamar ba'a yi ba." Wannan karon Adda Fati ce ta zo ta kamani ta na fad'in"Hasiya wani irin mganace wannan? Ta ke fad'a itama kamar ta yi kuka ina kallonta fuskata har ta koma jajur Saboda kuka nace"Eh mana da kun bar na zauna da rayuwata da ya fiyemin auran nan shine ke jawomin komai, in ban auri kowa ba wazai ce nayi sanadiyar rasa lafiyan wani? Balle ace an rasa dukiya!? ni rayuwata ba tare da kowa ba ta fiyemin kowacce Rayuwa da ki ke yi min Fata Amma." Zuwa Lokacin har Ramatu kuka ta ke yi Hamma Isuhu ne ya yi jarumtar rikeni  yana kiran sunana da karfi ammh ina kuka kawai na ke yi ina fad'in"Assadiq ya sakeni yanzu ba na bukatar auransa a kaina." Amma ce tace Ramatu da Adda Fati su fitar da ni daga Dakin haka suka Rikeni ina kuka ina kururuwa suka fita dani daga Dakin daman matan gidanmu suna fara jin kuka suka yi Dafifi ana son jin gulma. Suna ganin an fito da ni suka yayyame mu suna tambayan ba'asi ba wanda suka tanka suka shige da ni Dakin Maman Boy. Ramatu rikeni ta ke yi ta na Fad'in"Hasiya don Allah ki yi shuru" Na kasa domin komai da ya faru da ni tundaga farko ne ya ke dawowamin da kuncin acikin raina na kasa Sarrafa kaina. Kawai sai na Rungume Ramatu ina Fadin"Ramatu kamar na mutu haka nake ji. Gwara mutuwata da wannan rayuwar" Baki ta Rufemin ta na Fad'in"Kada ki yi sabo Hasiya ki bari don Allah kin ga jama'a hankulansu ya dawo kan ki." A tsakar gida kuwa Adda Fati sai shan Tambayoyi ta ke yi har da masu cewa ko wani abu ne ya samu angon? Ita dai ta ma kasa mgana ta sulalane ta koma Dakin Amma ta isketa ta na ta kuka Inna Talatu na faman lallashinta har Adda Rukayya ta kasa tsaida kukanta. Adda Fati Sadiq ta kalla da kansa ke kasa kanzil bai ce ba Tahir ne ke kallonsa a ransa ya na Tunanin shi ko Sadiq ya na da zuciya a kirjinsa kuwa? Duk yaji irin wannan bakaken kaddarorin ammh bai iya furtama yarinyar nan saki Lokacin da ta bukata ba? Shifa ko alama bai Tausaya musu ba su san su na da matsala meyasa suke kokarin gayyato wani cikin rayuwarsu? Wannan abunda suka aikata ba Adalci  acikinsa sam itama yarinyar ai tasan gaskiya abunda aka aikata akwai cutarwa acikinsa. Hamma Isuhu ya ji hon din mai Mota yasa ya fita da sauri ganin haka yasa Adda Fati ta kalli Sadiq ta na fadin"Amma yau zata koma garinsu gabadaya. Mganar Hasiya kuma kayan Dakinta suna hannuna kana da inda za'ayi mata jere ne yanzu.? Tahir ya kalleta kamar zai yi mgana sai ya fasa ya jira Sadiq da ya kawo kansa yasan mafitarsa. Kai Tsaye cikin natsuwarsa yace"Yanzu kam babu ammh za'a samar in sha Allahu. " Adda Fati tace"Shikenan daman in tambaya ya za'ayi ne zaka tafi da itan ne? Tahir ya yi tsam yaji amsar Sadiq yaji bai ce komai ba, kawai sai shi ya kalli Adda Fati ya na fad'in"Mu tafi da ita mu ijiyeta a ina? Bamu da inda zamu sauketa dakin da mu ke ciki Falle d'aya ne da ni da shi muke kwana aciki." Tahir ya fad'a cikin jin Haushi Sadiq yasan Halin Tahir aka cigaba da mgana sai kuma ya sauya zencen yasa da Sauri yace"Zata iya zama a wajen ki na wani lokaci kafin na sama mata muhallin da zata zauna? Ya fad'a lokaci daya ya na kallon Adda Fati wacce ta kalli su Amma sai suka gyada mata da yasa ta jinjina kai kafin tace"Shikenan bakomai. ga lambata in ka samu wajen sai ka sanar da ni akan Lokaci." Ba muau ya fiddo karamar wayarsa ya mika mata ta saka masa lambarta shi kuma ya kirata saboda ta ga Lambar sai ko ga kira ya shigo wayarta dake cikin jaka ta Dauko ta na Fadin"Bari na yi Saving din lambar." Bai ce komai ba ta na cikin Adana lambar Isuhu ya leko ya na fadin"Amma ya kamata mu tafi yanzu Direban ya matsa dare ya ke gudu." Jin haka yasa Amma tace"Hakane to bari na fito" Jin haka yasa Sadiq ya mike shi da Tahir a sanyaye yace"Allah ya tsare hanya Amma." Amma ta mike ta na gyara Daurin zaninta Lokaci daya ta na fadin"Ameen nagode sosai Allah ya jikan magabata. Allah ya yi muku albarka." Tahir ta kallah taga sai wani cin mgani ya ke cikin dan mirmishi tace"Shi  wannan abokin naka baya mgana ne? Sadiq ya kalli Tahir kafin yace"Ya na yi ammh ba sosai ba." Amma bata damu ba ta jinjina kai ta na fadn"Allah ya taimake ku. Allah baku yarda zaku yi ya kuma rabaku da Sharrin duniya da Mutanen cikinta." Sadiq ne kadai ya amsa da Ameen banda Tahir duk tare suka fito daga Dakin Amma na ta ce ma su Maman Boy tafiya ta tashi fa. Sadiq da Tahir kofar gida suka tafi suka Tsaya Sadiq na son ganin Tafiyar Amma shi kuma Tahir tsoro ya ke ji kada ya tafi ya bar Sadiq shi kad'ai domin ya fara jin Tsoron mutanen nan shiyasa bai tafi ba ammh ba domin haka ba Tuni bai san inda dare ya yi mishi ba Allah dai ya isa ba kowa ya Cucesu ba sai Sadiq haka kurum yau ya hanasu su kwanta su huta ya kawosu inda kwata kwata ko a Tsari Rayuwarsu bata yi daidai ba. Har Dakin Maman Boy Amma ta biyoni ta dafa kaina ta yi min addu'a daga karshe ta mike ta na fad'in"Allah yaga kyakyawan niyyata Hasiya. ina miki Fatan alheri da samun ingantattaciyar rayuwa a gidan auran ki in kin huce ki ka nemi sai na yi miki nasihan da uwa kan yi ma yarta a lokacin da zata je gidan mijinta." Daga haka ta fice ina jin Ramatu ma ta fita tasan ko tace na tashi bazan tashi ba jin irin kukan da na ke yi. Yan gidanmu da makota na kusa da na nesa duk sunzo sallama da Amma Allah Sarki Sabo suna ta kuka itama ta na kuka Adda Rukayya kuka Adda Fati ma haka, Habiba ko ta makale Amma ta na ta kuka Dakyar aka Rabasu sai cigiyata ake yi ana fad'in Ina Hasiya? Maman Boye ke ta fad'in"Ta na chan ta nata kukan a daki ita kad'ai" Maman Salihi ta karbe da fad'in"Abu biyu ne ya had'e mata ga Aure ga tafiyar Amma." Su kadai dai suke kid'an su suna rawan su Adda na ta kuka ba su bi ta kansu ba. Gaba Amma ta shiga ita da Hamma  jama'a na ta daga musu Hannu. Motar na wucewa Tahir ya fizge Hannun Sadiq suka nufi hanyar dakin su Sadiq na binsa a baya ya na mirmishi ya ke fad'in"Sake ni ba guduwa zan yi ba Tahir Yusuf Daura." Tahir yace"Tunda ka iya aure batare da sanin kowa ba to shima ka gudun abu ne mai sauki a wajen ka" Sadiq sai da ya yi dariya har Fararan Hakoransa suka bayyana. Cikin kwarin gwiwa yace"Ba inda zan gudu Tahir. Tahir bai sake masa hannu ba sai da suka Danganta da Dakinsu ya saka hannu daya ya bude kwadon dakin ya tusa kansa da Sadiq ciki ya maida koda ya Rufe. Ya cire riga da wando ya bar kanshi Dagashi sai gajeren wando. Wayarsa ya Dauko ya na Fadin"Sadiq ko ka saki yarinyar nan yanzu ko Billahillazi na kira Umma na fad'a mata duk abunda ke faruwa." Ya fad'a ya na kallon Sadiq ido cikin ido Tunda ya zare bakin gilashin da ya sanya. Sadiq ya yi zuru ya na kallon Tahir yanzu in yace zai yi wata mgana Tahir ba burga ya ke yi ba, zai iya aikata abunda yace din. Kuma hakan daidai ya ke da ruguza duka Tsarinsa lallaba Tahir yanzu shine a gabansa kafin yaji da Hasiya Daga baya. Mikewa ya yi shima ya zare Rigan jikinsa daga shi sai Farar Vest. Cikin kwantar da Murya yace"Tahir na fad'a maka taimakonta zan yi. Da zarar na inganta mata rayuwa Zan SAKETA da gaske." Tahir ya kallesa cikin shakku kafin yace"Zaka saketa ka ce ko? Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Eh zan saketa Ammh ba yanzu ba? Tahir ya katse shi da cewa"Har na tsawon wani Lokaci? Sadiq ya yi shuru kafin ya sauke ajiyar rai ya na fad'in"Ban sani ba ammh dai nasan auranta ba kamar Sauran aure ba ne Tahir tabbas zan rabu da ita ko saboda Ahalina." Tahir yace"Me yasa ba yanzu ba? Sadiq yace"Haba baka ganin halin Tsaka mai wuyar da na shiga ne? So ka ke na saketa yanzu na karya zuciyar Uwa mahaifiya ka duba mana Tahir." Tahir ya yi dariyan Takaici kafin yace"ka faranta ma uwar wata rai kai kuma ka bakanta ma taka uwar kenan? Sadiq ya girgiza kai ya na Fadin"Tahir zauna mu yi mgana" Tahir nace ka zauna don Allah." *Janafty* *17/01/2024* *TMWB2K002* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj K'in zama Tahir ya yi sai da Sadiq da kansa ya saka hannu ya ja shi da karfi ya zaunar da shi. Shima ya zauna a gabansa ya tankwashe kafa suna Kallon junansu. Sadiq ya kalli Tahir ya na warware hannunsa lokaci d'aya ya na fad'in"me ka ke son sani yanzu? Me kuma ka ke bukatar a yi? Tahir ya shaki iskan Takaici kafin yace"Abunda na so ayi lokaci ya riga ya kuremin. Abunda na ke bukata kuma na riga na sanar da kai tun farko" Ya fad'a cikin cin mgani, Sadiq ya murmusa Allah kad'ai yasan Halin da zuciyarsa ta ke ciki ammh bai rasa kwarin gwiwa ba niyarsa ta Alheri bata bar shi ya ji ya yi Nadama ba. Cikin sanyin murya yace"Me ka ke bukata Tahir? Wata uwar Harara Tahir ya sakar masa kafin yace"Bansani ba. Ka fi kowa sanin abunda na ke bukata. Ka sake yarinyar nan domin kasancewata abokinka kamar yan'uwa muka dauki juna. Bazan jure ina ji ina gani ka jefa rayuwarka cikin Halaka ba." Sadiq ya yi saurin cewa"Ba Halaka ba ne Tahir taimako na yi." Cikin kufuluwa Tahir yace"Wai ka na ta cewa taimako, hala dole kai Allah ya wajabta ka taimaka musu? Meyasa sai kai? Mazaje nawa ne a gari ba'a neme su ba sai kai? Sadiq sai ya kasa mgana ganin haka yasa Tahir ya cigaba da zazzaga masifa da kuma alwashin ko Sadiq ya saki Hasiya ko ya kira Umma ya Shaida mata komai tundaga fari. Sadiq ya yi shuru bai yi mgana ba illah agogon hannunsa da ya kallah kafin yace"Mu yi sallah sai mu cigaba da mganar" Ya yunkura zai mike cikin zafin Nama Tahir ya maida shi zaune lokaci d'aya ya na fadin"Ba inda zaka je sai mun gama mgana Mallam" Sadiq ya kallesa cikin mamaki kafin yace"Tahir sallah na gaba da mganarmu." Shuru Tahir ya yi jin ya fisa gaskiya ganin haka yasa Sadiq ya mike ya na fad'in"Mu yi sallah yau ina da Lokacin ka kaji." Ya fad'a ya na yar dariya, Dariya ya girgiza kai bai kara mgana ba. Sun riga sun makara  shiyasa a gida suka yi sallar su abinci ma ba wanda ya nema hatta ko Tahir da baya wasa da abinci, suna idar da salla ko Addu'a Tahir bai bari Sadiq ya yi ba yace su cigaba da maganar da suka fara. Sadiq ya koma ya gyara zama yasan ai yau sai Allah tunda ya shiga Hannun Tahir ya bani wai barawo a hannun mata. Cikin Sarewa yace"Fad'i abunda ka ke so ayi Tahir." Tahir yace"Meyasa ka ke so ka nuna kamar bakaji me na fad'a tun farko ba ne? Sakin ta na ce ka yi ko? Sadiq ya yi shuru ya na kallon Adon Darduman gabanshi kafin ya dago ya na kallon Tahir cikin muryan Kaushi ya ce"A'a Tahir nace maka zan saketa ammh ba yanzu ba." Tahir yace"Me ye hujjar ka? Sadiq yace"Ba na sanar da kai ba, na tausayama rayuwarsu ba su da kowa sai Allah ka na fa gani kuma kaji me dan'uwan mahaifinta ya ke gayamin su kansu sun gujesu in na saketa a wannan Lokacin zan kara fasa gurbin bakinciki a rayuwarsu" Tahir ya yi saurin taran shi da cewa"Dangin mahaifinsu sun gujesu kai kuma waye na su da zaka Rumgume su Sadiq? Sadiq ya sauke numfashi kafin yace"Tahir kuka fa matar nan ta rika yi mini. Bazan iya juran ganin Uwa ta na kuka saboda matsalan da zan iya mata mganinta ba, Ita bukatar ta Rayuwar Hasiya ta inganta shiyasa na amince da bukatar ta ammh ni kaina ina da nawa tsarin akan haka." Tahir ya kura masa ido bai basa damar mgana ba ya cigaba da fad'in"Ba son raina ba ne na yi wani abu batare da sanin iyayena ba Tahir. Da farko na so na sanar da su sai na fasa sanin ba wanda zai goyamin baya shiyasa na yanke wannan hukuncin." Tahir yace"Naji ka yanke hukunci mafitar da zata bulle da kai fa batare da auran nan ya je kunnen su Umma ba? Sadiq yace"Kai zaka ba ni wannan Mafitan Tahir" Tahir ya ware ido kafin yace"Ni kuma? Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Eh Tahir saboda kai kad'ai ne na kusa danin da yasan da Labarin auran nan mafitan bangaranka shine ka yi Shuru da bakin ka har Abada ka da wani yasan da wannan mganar.". Tahir ya yi shuru bai ce komai ba ganin haka yasa Sadiq ya dafa kafad'ansa ya na fad'in"Don Allah Tahir in ka yi min wannan taimakon ka gama sama min dukkan mafitan da na ke hange." Tahir ya sauke Numfashi kafin yace"Kasan dai abunda zaka sani na aikata ko? Sadiq yace"Na sani mana, niyyata zaka duba kai ma sai ka dubi ta ka niyar na taimakon  abokin ka." Tahir yace"Naji kai kuma mafitan bangaran ka fa? Sadiq ya gyara zama ya na Fad'in"Mafitan bangarena shi ne har lokacin da zai cika na saketa ba wanda zai sani nan da zuwa wata shidda lokacin mun gama Hidimar kasarmu nan zariya ne dagani har kai ba Tushen mu ba ne tafiya zamu yi mu koma Mahaifarmu." Tahir ya kura masa ido ya na neman karin bayani Ganin haka yasa Sadiq ya cigaba da fad'in"Sai dai kafin nan nayi alkwarin inganta rayuwarta da ilimi tare da jari mai karfin da ko bayan na saketa abun bazai dameta ba sosai." Shuru suka yi dukkansu kamar masu nazari kafin Tahir yace"Har yanzu baka samar ma kanka wata mafitar ba" Sadiq cikin mamaki ya kallesa kafin yace"Kamar wacce mafita kenan? Tahir ya gyara zama ya na fad'in"Ka manta kace ta zauna gidan yar'uwata kafin ka sama mata Muhalli? mafitan in da zaka ijiyeta batare da kowa ya sani ba na ke mgana." Sai gabad'ayansu suka kalli juna cikin nazari na wani Lokaci kafin Sadiq yace"Zamu samo wannan mafitar daga baya." Tahir ya ciji lebensa kafin yace"Na kasa aminta da wannan al'amarin Sadiq. Kai ne ka auri bazawara wace auranta biyu fa ka sani." Sadiq cikin Halin ko in kula yace"Kada ka fara duba wannan Tahir, Annabin mu da bazawara ya fara ya auri Nana Khadija ya na Saurayi dan Shekara ashirin da Biyar a duniya ita kuma ta na da Shekarun arba'in a lokacin. Ka ga da ba'a auran bazawara da Allah bai umarci Annabin Rahma salallahu alaihi wasallam da ya auri Nana Khadija ba.' Tahir ya tare shi da fad'in"Yanzu sunna na wa kaga mutane na takewa Sadiq? Sadiq yace"Wannan na su tsarin ne ina so na gayamaka auran bazawara ba Haramun ba ne, Kuma ka sani Annabi shine Jagoranmu abunda ya zo mana da shi ko ya aikata ko Sahabansa suka aikata shine abun koyin mu." Tahir sai ya kasa mgana ya koma ya na kallon Sadiq kafin yace"Ko ka fara son yarinyar nan ne Sadiq? A kaikace Sadiq yace"Wata yarinyar? Tahir na gatsine yace"Zabiyar ka ko nace yar bazawarar amaryan ka." Sadiq ya jinjina kai ya na mirmishi kafin yace"Sunanta Hasiya Tahir." Tahir ya dage gira ya na fad'in"Ni kuma ban san sunanta ba." Sadiq ya kallesa batare da ya yi mgana ba Tahir yace"in ka fara sonta ne ka fad'amin domin naga akan lamarinta kafi kowa zakewa ne" Sadiq ya yace"In na fara son nata zan gayamaka Tahir ammh yanzu na gayamaka ba mganar so a tsakanina da wannan yarinyar ka gane? Tahir yace"Zan gane nan da wata shidda in sha Allahu." Sadiq ya bi Tahir da kallo mai ya Daukesa ya na Tunanin zai karya alkwari ne?zai ko ba shi mamaki in sha Allahu. Sun yi shuru kenan wayar Sadiq da ke gefen Tahir saman gado ta hau Ruru da sauri ya dauko masa ya duba mai kira cikin zaro ido yace"Umma. umma ce ke kiran ka." Sadiq cikin natsuwa ya mika hannu ya karbi wayar ya na fadin"To sai me in Umma na kira? Daman ta saba kirana." Daga haka ya daga kiran lokaci d'aya da sallama bayan ya saka wayar a amsa kuwwa yadda Tahir zai ji. Dagachan bangaran Umma ta amsa sallamarsa cikin fara'a kafin tace"Auta ka na lafiya ko? Jiya ba mu yi mgana ba yau ma haka." Sadiq na shafa kanshi yace"Na yi uzurori ne jiya da yau Umma kuna lafiya? Umma tace"Lafiya lau ya aiki? Ina Attahiru? Sadiq na kallon Tahir da ya kafesa da ido yace"Ya na nan lafiya Umma ina Abba.? Umma na mgana yaji Muryan Innani ta na fad'a sai cewa ta ke yi"Kaji min kisisina wajen salamatu ni fa na Dauko kafata nazo nace ta kiramin Magajin gida mu gaisa ammh ta tsaya ta na wani uban labari da shi, don Allah ni dai kin ga ba ni shi mu yi mgana." Ta fad'a ta na kokarin warce wayar Hannun Umma daidai Lokacin da Umma ke fad'in"Auta ga Innani." Kai ya dafe sanda Innani ta amshi wayar ta na fad'in"Ina kwana Magajin gida? Shikenan ka manta da ni ko mema na baka yi ba? Cikin mirmishi yace"A ina zan neme ki? Kina da waya ne? Innani tace"Wani bakin Munafukin ne yace ba ni da waya? Kaji mutane da son had'a fad'a in sulaimanu yaji ai ransa bazai yi masa dadi ba yaga ya siyamin waya ammh ana chan ana yamad'id'i da ni ba ni da waya" Sadiq na kunshe Dariyarsa yace"To ai ke kikace an Dauke miki waya ki ka yi ta tsine tsine." Innani ta Rafka dogon Salati kafin tace"Ni kuma? Yaushe na ce an sace min waya? Oh ni duniya da tsufana ammh har yanzu ba'a daina bi da kulli ba to ta Allah ba ta mutum ba, Ni dije dashen Allah ne na gagara wlh." Sadiq ya kwashe da dariya kafin yace"Kedai ki ka sani. Sai ki fad'i mgana ki ce baki fad'a ba." Innani ta sassauta murya ta na fadin"Allah dai ya rabamu da yan Uba kaji Magajin gida.' Cikin Annushuwa ya amsa da Ameen zencen Innani ta cigaba da yi masa da ta tambayi Tahir yace ga shi a gabansa. Ya mika ma Tahir suka cigaba da shan Hira suna shan Dariyan Innani da wayar ta dawo hannun Sadiq ne Innani tace"ka ganni yanzu wajen mamanka na ke yi ni Shashena ba kowa sulsana ta fara zuwa boko ba mai d'ebemin kewa." Sadiq yace"Ki zauna da Umman sai ku rika yin hira." Innnani ta tabe baki kamar ya na ganinta batace komai ba daga gani akwai mgana a bakinta. Sanin haka yasa Sadiq yace"Yaushe ki ka dawo? Na dauka chan zaki mutu sai dai muje jana'iza." Innani ta saki baki kafin tace"Kaji wani mugun baki kuma? Ni da mutuwa ai sai na aurar da ya'yan ku kai da Sulsana." Sadiq ya kyakyace da dariya kafin yace"Kina da son duniya Innani ina Laifin ki ga auran namu na ya'yan mu kuma kina kabari za'ayi." Innani ta yi gum Magajin gida ne ba Halin ta yi masa masifa. Jin yadda ta yi shuru yasa yasan gabda ta ke da fashewa da kuka, yasa cikin barkwanci yace"Ya kika baro su Mallam zakarin? Jin haka yasa Innani ta gyara zama ta na bashi labaran abunda ya faru achan ta karishe da fad'in"Kai dai bari magajin gida kamar kar in dawo. Ammh ya na iya sulaimanu da matansa sai kira suke wai yaushe zan dawo? Saboda ma a nuna min iyakata aikamin akayi da mota akace in ni bazan dawo ba na turo su sulsana zasu fara zuwa makaranta abunan ya yi min ciwo matuka ni fa saboda Salamatu naje kamar ya' na Dauketa ita kuma kaga a uwa ta Daukeni ko ba Haka ba.? Sadiq yace"Hakane Innani kin Sada zumunci Allah ya baki lada" Innani ta washe baki ta na fad'in"Ameen Magajin gida, ai da na dawo sun sha masifa nace ina Dalili kun dameni na dawo sai kace Nono zan ba ma shi Sulaimanu din mutum ya girma da iyalansa ammh baza'a bar ran Tsohu ya huta ba, chan wlh ana kula da ni naci na sha mai kyau mu yi ni muna Hira da Zakari gwanin ban sha'awa nan ko sai zama a katon gida kamar mayya Sulsanar da ke tayani zama an yi min nunafunci itama Sulaimanu yace Boko zata yi ai shikenan maji dai ma gani wai an Tura uwar amarya biko." Sadiq duk halin da ya ke ciki sai da ya Biye ma Innani ya na ta cin dariya daga karshe suka fara Diraman sai ta zo zariya daman bata taba zuwa ba Dakyar ya lallasheta akan zai zo ya tafi da ita sannan ta Hakura. Sun fi awa biyu suna Hira sai da kudin wayar Umma suka kare shi kuma yaki kira daman ya gaji Innani ce fa Lamarinta sai Allah. Suna gama wayar alwala suka yi zuwa masallaci ba su dawo ba sai da suka yi isha'i. Bayan sun dawo ba su nemi abinci ba Ruwan zafi Tahir ya dafa musu suka sha Tea saboda ya warware musu ciki. Sadiq dai ya shiga uku da Tahir sai ya yi kamar yana goyon bayansa sai kuma ya Turje har ya gaji da basa mgana ya kyalesa duk da ya na da kyakyawan yakinin Tahir bazai iya Tona masa wannan Sirrin ba. Washegari kuma da wuri kowannen su ya isa inda ya ke Hidimar kasarsa Sai dai ba Sadiq kad'ai ba hatta Tahir kowa ya fahimci wani abu na Damunsa ya rage kazar kazar. Shi ko Sadiq duk da daman ba shi da Hayaniya sosai shima an Fahimci ya na cikin Damuwa. Abokansa na wajen ne da sukaje masa Daurin aure suka so su fasa mgana ya rokesu da Allah kada wani yaji Labarin ya yi aure ba su nemi sanin ba'asi ba sukace in sha Allahu sun bar mganar a tsakaninsu. Ya dauka al'amarin wasa ne sai da ya Faru sannan yasan abun ya wuce Tunaninsa. ******* Yau na kwana daya a gidan Adda Fati kwana ba irin wanda na saba ba Tunda achan baya in bata da lafiya na kan je har na kwana da ita. Ammh yau kwanan da na yi ya bambamta da sauran tunda na kwana ne a matsayin matar aure wacce igiya uku kwarara ke kanta. Tun bayan tafiyar su Amma mu ma mu taho gidan Adda Fati gabadaya har da su Ramatu. Ni dai ban samu damar sallama da matan gidanmu ba saboda kukan da na ke yi a Lokacin, ammh ina jin sanda Su ke ta fad'in in na tashi tarewa a gayamusu zumunci bazai taba yankewa ba. Tunda muka zo na shige dayan dakin nata na cigaba da kukana Ramatu ta ba ni baki har ta gaji Inna Talatu ma ta gaji tace su rabu da ni har da zafin tafiyar Amma kamar kuma ta sani duk shi ya dameni a baya itace karfin gwiwana yanzu ta yi nesa da ni wa zai Tsayamin in dan na kasa? Abunda na ke tunawa kenan ina Tunanin wazai tareni in wata guguwar ta tunkaro ni, su ba zasu gane ba ne ina gujema kaina wani abun da zai iya zuwa ya Dawo ne an yi daya ba'a ji da dad'i ba an sake yi nan ba'a rabu cikin mutumci ba meyasa baza'a hakura ba? Ko abinci ban iya sakama cikina ba ina jin da su Ramatu za su tafi suka shigo suka min sallama ban amsa su ba kuma dukkansu sai dare suka tafi suka barni gidan Adda Fati ni da Habiba. Inaga da mijinta ya dawo ne ta warware masa komai shine ya biyoni har dakin ya na ta bani baki da lallashi mganarsa guda d'aya ta saka jikina ya yi sanyi in da ya ke fad'in"Hasiya ki yi hakuri duk abunda kika ga ya faru ko zai faru da sanin Allah, Sannan ka da ki yi fushi da Amma ita uwa duk abunda zata aikata walau mai kyau ko mara duk saboda d'anta ya kasance cikin Farinciki ne ko da ita zata Dauwama acikin kunci  to ina so ki sani Amma ta zabi Farincikinki fiye da nata Hasiya." Wad'anan maganganun yasa ya hakura da kuka na tashi na je waje na kama Ruwa Adda Fati ta sakamin ruwa a kettle na yi wanka na rama sallolin da kai kaina sannan ta had'amin Tea na sha Sosai domin sai a lokacin naji wata irin mahaukaciyar yunwa ta tasomin hade da ciwon kirji. Allah yasa cikin kayana da su Adda Fati suka tahomin da shi akwai Omeprazole shi na sha na samu na kwanta sai barci. Har ina makara Sallar asuba Saboda gajiya shiyasa ko da na tashi Fuskata ya yi jajir sannan ta kumbura saboda kuka ammh kuma na daina kuka sai dai ba Annuri ko kad'an a fuskata. Ban fita ko Falo ba Adda Fati da Habiba daman tare muka kwana suka Biyoni har ciki da abun karyawata. Dakyar na bude baki na gaisheta ta amsa lokaci daya ta na zama a gefena. Habiba ta kallah ta na fadin"Ki yi sauri Baban Hanifa na jiran ki sun fita tare da Hanif" Ko da ban yi tambaya ba naga amsar Tambayata tunda naga Habiba na saka Uniform din makaranta kenan har sun sanya mata makaranta. Sai naji dadi a raina ina kallonta ta shirya sannan ta yi mana sallama bayan ta Dauki jakar makarantar ta ta fice. Koko da kosai ne Adda Fati ta yi kuma nasha kokon da yawa kosan nan naci kad'an saboda maiko. Adda Fati ta fita ta bani waje ni ce da nagama na kwashe komai zuwa tsakar gida na isketa ta na wanke wanke kunya da kuma ba Halina ba ne ganin ana aiki ina zaune yasa na Tsugunna ina tayata da Dauraya. Ta yi ta yi na barshi nace mata ta bari zan yi sai ta kyaleni. Tunda muka fara batamin mgana ba nima ban yi mata ba ga shi ina so na tambayaeta na kasa Dakyar nace"Amma su sauka lafiya? Adda Fati ta juyo ta na kallona kafin tace"Lafiya lau suka sauka jiya da Daddare mun yi mgana ta wayar Adda. Da safe ma ta sake kira tace na gaisheki." Mirmishi na yi ban ce komai ba ganin haka yasa Adda Fati tace"Hasiya ki yi hakuri ki yi ma Amma uzuri ta na cikin Halin da bata da wani zabi ne." Idanuwana sun tara kwallah nace"Shine zata amince  ma wanda bata san komai a kanshi ba ya aureni? Ni ba ma wannan ba nafi Tunanin makomar tasa Rayuwar" Adda Fati tace"Allah zai tsare Hasiya sannan ina da kyakyawan yakinin Abubakar zai bambamta da Sauran in sha Allahu." Daganan ban kara mgana ba har muka gama wanke wanken. Ni na share wajen na had'a da Tsakar gidan na share tas sannan ta ce ga ruwan wanka nan a gawayi in zan yi wanka ba musu na juye na yi wanka. Na sauya kaya sai na kara jin dadin jikina. Tare muka yi ni da ita, na dai tayata da sauran aikace aikace sai la'asar Adda Rukayya tazo sannan ne Adda Fati ta kirani ta na min bayanin Amma ta bar wasu kudi a hannunta tace a karamin da duk abunda na ke so. Kai tsaye yace"Adda ku siya duk abunda kuka ga ya kamata. Ammh ku sani ko kun siya kun kaini da su haka zaku je ku dauko su." Kalamai na suka kara sanyaya musu jikin da har Adda Rukayya ta tafi ba su karamin mganar Tarewa ba. Sai ga shi a hankali na sake a gidan Adda Fati Amma ce dai ban bari mun yi mgana ba sai dai Adda Fati na shaidamin ta na gaisheni a bakinta na ke jin Adda ma ta yi ta fad'a wannan gaggawa na Amma bai yi ba sam. Nima abunda na gani kenan so ta ke a fara kirgamin aure daga biyu zuwa uku har sama ammh in ba haka ba meyasa ta matsa ma kanta da sai na yi aure a Lokacin da ban shirya ba? Ni ba kaina na ke ji ba domin ni na riga na fidda rai da wata rayuwar jin dadi ASSADIQ na ke ji shine Bakuwar Rayuwarsa zata shiga gagari tunda ya had'u da tawa Rayuwar. Sai da na kwana biyar a gidan Adda Fati sannan Ramatu ta dawo wannan karon ita da Nura ne shima ta gama gayamasa komai duk maganganunsa Nasiho ne da ban baki to me zan ce? Baza su taba hango abunda na ke hangowa ne tunanina ya tafi kuma shi wannan auran ko ta ya ya zai kare? Na zura ido dai ina son ganin ta ina komai zai fara kuma ta ina zai kare. Ranar ma ina jin su na mganar Tariyan tawa ita da Adda Fati abunda ke bani mamaki ina su ka ga Assadiq din? Mutumin da tun ranar bamu kara jin Labarinsa. Bansani ba har Adda Fati ta yi ma Jummai Dillaliya magana Sannan ta bama Adda Rukayya wasu kudaden zata siyamin kula da sauran su Filet da ba na su sosai. Sai da na yi sati gidan Adda Fati sannan Hankalinta ya fara tashin jin Abubakar shuru. Ko yau da Safe da suka yi waya da Amma sai da tace ko ta kirasa ne? Amma tace kada ta kirashi ta bari zai nemata da kansa in ya shirya. Rashin ji daga barayin Abubakar ya sa sai gwowiyinsu ya yi sanyi daga shirin Tarewata. Ni dai yadda ba su gayamin ba haka na nuna ban gane komai ba. A cikin raina ina fatan Allah yasa ya tseratar da Rayuwarsa ne daga Rayuwata. Ko acikin raina bazan damu ba domin ya tafi ya barni ba zan fi son hakan na fi damuwa da tashi Rayuwar fiye da tawa Rayuwar da ta riga ta Gurbace. Wasa wasa sai ga shi ina son kwashe Sati biyu a gidan Adda Fati ba wani labari daga Abubakar ni kuma jin Shuru yasa har na fara maida jikina tunda na fara samun natsuwar zuciya. Ramatu ma ta damu bata kwana bata kira Adda Fati suna kuskus dai nasan kan mganar ne ni ko acikin raina Fata na ke yi Allah yasa ya yi nesa da Rayuwata. Har acikin sallata ina rokon sa Allah yasa Assadiq ya yi nesa da Rayuwata kada ya dawo cikin Duniyata balle wani abu ya sameshi sai naji na fi Tsausayinsa fiye da Abubakar da Salisu. Adda Rukayya da Ramatu suna ta sintiri a gidan Adda Fati in ba su zo ba za su kira waya har acikin zuciyata na ji dadin chanjin da nagani a tare da Adda Rukayya. Akwai wani al'amarin da mutane suka kasa ganewa shine in mace ta auri mugum miji ya kan rab'a mata wasu daga cikin Hallayansa. Halin mijin Adda Rukayya ba shi da kyau ya tsani asara sannan ga daukan zuga tunda ya nuna baya son muna zuwa gidansa ita kuma ta na son shi sai ta ke ganin a irin rayuwar da muke ciki shine Rufin asirinta sai daga baya ta gane bayan shi mu ma rufin asirinta ne, shiyasa ta zabi da ta kamashi mu ma kuma ta rikemu gam in bai so mu rab'esa ita da ta ke Dolenmu ita zata zo in da mu ke. Ranar da na cika kwana ashirin a gidan Adda Fati suka yanke shawaran Kiran Abubakar ita da Adda Rukayya ta kira Ramatu ma suka yi shawara. Bata gayama Amma ba ammh sun yi mgana da Adda sai Fada ta ke yi ta na fad'in"In auran bazai yuyu ba ya saketa mana Hasiyan ta dawo gabansu ta zauna." Da wannan Tunanin Adda Fati ta kwala masa kira da yammah. Lokacin suna Daki tare da Tahir suna shawaran yadda za'ayi. Bai gane lambar ba tunda ranar ya manta bai yi saving ba sai da ya dauka suka gaisa ta yi masa bayani sannan ya gane da sauri ya saka wayar a amsa kuwwa yadda Tahir zai ji komai. Adda Fati cikin sanyin murya tace"Abubakar Lafiya ko mu ka jika Shuru ba kira ba wani bayani? Sadiq ya kalli Tahir shima ya kallesa ya na yarfa masa hannun alamun ina Ruwana sai kaji da su kai da ka kira ruwa. Da sauri Sadiq yace"Lafiya lau ina ta wani shiri daga bangarena ne kinsan abunka ga talaka." Adda Fati tace"Mun sani wlh daman mun ji shuru ya yi yawa ne, sai nace bari na kira naji ko lafiya sannan mu ji yaushe ne Tarewwar? Ko nace ka samu in da zaka ijiyetan? Sadiq ya sauke numfashi kafin yace"Zan kira ki zuwa gobe abunda ake ciki zan sanar da ke." Adda Fati tace shikenan sai ta jisa da haka suka rabu. Ta na kashewa Tahir yace"Af daman zaka auri yar mutane ne kazo ka kwanta a gida? Sadiq yace"ba kai ne kace zaka sama min mafitan inda zata zauna ba." Tahir ya yi shuru kafin yace"Eh yanzu mafita itace gida zaka siya ko? Sadiq yace"Gida kuma? Ai sai ace ina da kudi haya dai ko zamu kama mata? Tahir yace"Oh hakane to a kama mata hayan ammh ba a inda aka santa ko aka sanka ba wani waje Dabam da muhallin ku." Sadiq ya kalli Tahir cikin karin bayani shi kuma ya gyara zama ya cigaba da fadin"Hikimar haka shine Rayuwar da zata yi kafin wata shidda itama kanta Sirri ce Sadiq." Sadiq ya yi shuru kafin ya jinjina kai yace"Na aminta da mganarka. Tunda har na sallameta ba na so ta san wani abu ko kad'an a kaina Tahir." Tahir yace"Shine mganata ka ga ko dole mu samo wani waje na Dabam" Sadiq ya yi shuru ya na nazari Tahir yace"Ka bar komai a hannuna a malaman makarantar da na ke Hidimar kasa akawai wani da ya ke Dillancin gidaje da Filaye zan yi masa mgana gobe naji yadda za'a yi." Sadiq ya sauke Numfashi kafin yace"Komai ka yi sa a goben tunda ka na ji sanda nace gobe zan kirata." Tahir yace"Kada ka damu in dai da kudi a hannunka za'a samu ko ciki da Falo ne ina Laifi." Sadiq yace"Kudina sun yi kasa ammh zan yi ma Abba waya.'" Da haka suka bar mganar akan gobe Tahir zai bincika musu gidan da Hasiya zata zauna nesa da inda aka santa ko aka san su saboda suna son komai ya kasance cikin Sirri ne kamar yadda Sadiq ya tsara tun farko. *Janafty* *TMWB2K003* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641 Washegari kan mganar suka rabu da Tahir ya na ko zuwa makaranta ya nemi Hambali ya yi masa mganar, nan da nan yace kada ya daamu za'a samu duk da ya sanar da shi ba sa bukata a nan samaru sai dai wani waje na daban. To an samu kafin mu su tashi daga makaranta sai dai ciki da falon da ya nema ne ba'a samu ba, sai dai Safecanten mai daki da kitchen a had'e kuma a Hanwa ne aka samu gidan. Sabon gida ne ma yanzu ne ake son a fara ba da hayan gidan mai dauke da Dakuna hud'u a shekara dubu dari da Hamsin Da Tahir ya nace sai mai ciki da Falo kad'ai Hambali ya gayamasa gaskiya yace irin d'akunan nan na Haya suna Wahala ga irin wanda aka fi saurin kamawa a irin anguwan waje wajen gari gwara kawai su karb'a. Bai ce masa komai ba sai dai yace masa in za su karb'an zai kirasa a waya sai da ya dawo gida ya jira Sadiq ya Dawo sannan ya sanar da shi Halin da ake ciki. Nan take Sadiq yace ba komai su kama wannan d'in. Tahir ya kallesa shekesheke kafin yace"Ka na da dubu dari da hamsin din ne yanzu? Sadiq yace"Akwai kudi a hannuna mana da na so na yi ma Abba magana sai kuma na fasa kasan akwai kudin alawuna na ba duka nake amfani da su ba, Tunda koda yaushe Abba na Turamun kudi sai na yi amfani da shi." Jin haka yasa Tahir ya yi shuru bayan  ya kira Hambali yace su same shi a bakin Titi tare suka dumguma suka tafi ganin gida kuma Alhamdulillah Tsarin ya yi ma Sadiq sosai sai dai ya so da wasu a gidan Tunda shi kam ba zuwa zai yi ya zauna a inda ta ke ba ko Saboda Halin rayuwar nan da muke ciki. Da ya yi ma Hambalin mgana shi kuma yace kada su damu duka d'akunan uku an kama daman wannan ne kad'ai ya rage kuma amare za'a saka nan da wata daya. Sai Sadiq yaji dadin haka domin a na shi Tsarin ba Tsarin ya zauna a nan gidan Tare da Hasiya. Karya suka yi ma Hambali da cewa wani dan'uwan Tahir ne ya yi aure shine suke duba masa gida shi kuma bai Damu ba ya na kan sana'ar shi ne Daman shi ya samo musu gida Saboda shi suka sani shi kuma suka bama kudin Hayan gida na Shekara cur. Sai yamma suka dawo shiyasa Sadiq bai samu damar kiran Adda Fati ba sai da Daddare yace mata ya samu wani waje duk da kudinsa bai kai ba an yi masa ragi. Sun rabu akan gobe da Safe tunda Tahir CDS zashi kuma sai ya fara biyawa Fada sai Sadiq ya rokesa kan ya raka Adda Fati ta ga gidan ya na masifa ya na komai ya amince shiyasa Sadiq ya fara tafiya ya barshi Tunda shi nan kafin akai kwangila za shi. Lambar wayar Tahir ya turama Adda Fati shima ya bata na shi ammh Tahir bai kirata ba sai itace ta kirashi duk da taso suje ko ita da Rukayya ko Ramatu sai taga tafiyar ta su ta Safe ce sai ta yanke shawaran in taje taga gidan daga baya sai ta kai su. Tunda ita ta na Sabongari ne a pizzet suka had'u da Sadiq ya saka complete kayan Bautar kasar sa sama sama suka gaisa suka samu abun hawa sai Hanwa. Suna zuwa daman already makullin gidan na hannun Tahir shi ya Bude mata sannan ya bata key d'in Dakin lokaci d'aya ya na fad'a mata Shi zai tafi ne kada ya makara ganin saurin da ya ke yi yasa ta yi masa uzuri ammh ba tun yau ba ta Lura da Tahir din ya na da Basar da Mutane. Alhamdulillah ta duba daki babu abunda babu ga shi sabon waje gidan ma ya  burgeta sosai ganin ba su da yawa ta kuma san in dai zama ne na gidan Haya Hasiya tasan kalubalensa zata kiyaye in sha Allahu. Ta jima ta na duba Dakunan sai da ta kirga kofa saboda Labule tun kuma ta na gidan ta kira Adda Rukkaya ta fad'ama ita kuma tace sai gobe zata zo su yi mgana. Cikin Farinciki Adda Fati ta dawo duk da bata gayamin inda taje ba ammh ta na cemin zata fita da Sassafen nan jikina ya ba ni wani abu. sai ko ga shi ta na waye waye ta na ba da Labarin Tsarin wajen da zan zauna tabbacin chan taje da Safe kenan. Ina jinsu da Rana suna mgana da Adda sai kuma aka bama Amma suka cigaba da mganarsu. Tashi na yi na shige ciki domin maganar sam bata burgeni meye amfanin bad'i ba rai? Suna rawan jikin tarewar da ina da tabbacin bazai Daure ba sai wani abu ya Biyo baya. Ai ni ina ganin abu ganin idona wajen su Adda Fati bayan hidimar kayan Dakina sai kuma suka Turomin Ramatu da magungunar gyara akan sai na sha sai suka bani dariya. Auren Abubakar na farko ne na yi wannan rawan jiki ammh ko na Salisu Fargaba bata barni na saki jiki na yi wannan Shaye shayen ba. Wannan ma na Tubure nace bazan yi ba da naga sun fara matsamin kawai sai na fashe musu da kuka ina fad'in"Nace ba na so ko? Haba ku kyaleni mana duk abunda ku ke yi ina sane ban yi muku mgana ba meyasa ni ku ke so ku tursasani aikata abunda ban yi ra'ayi ba. Wlh kuka matsamin zan yi tafiyata in da har Abada bazaku kara ganina ba." Jin kalamaina yasa suka shafamin Lafiya suka cigaba da Shirinsu duk azatona Amma zata zo tariyata saboda nayi kewarta sosai Fushin Abunda tayi min yasa ko a waya ban yarda na yi mgana da ita ba. Ashe bansani ba tace bata zo ba Adda ce zata zo kad'ai. Ina da labulai na tun na gidan Abubakar na kofofi da yawa Shiyasa a auran Salisu ban siya ba wannan karon ma wankesu a sake yi aka goge sai dai sun karamin kayan kitchen da abubuwan da baza'a rasa ba. Adda Rukayya kuma ta yi mana Atamfa mu h'udu da zamu ci yinin Tarewa da shi, Ramatu kuma ta yi min kayan maggi da sauran kayan Dake dake. Sannan mijinta Nura ya aikomin da Dubu talatin ban rikesu a hannuna ba na mikama su Adda da su suka yi amfani suka siyamin less da material sai Hijabai da takalmi sai dan kunne, tunda kayan nawa duk sun ji jiki. Salisu bai yi min kaya ba daman da Niyar in muka yi aure zamu je kano da ni da shi na zabi kayan da na ke so. Bansan ko shi Sadiq din ne ya saka musu rana ba naji suna fad'in Ranar jumma'a za su yi bikin Tariyar nawa ni har mamaki na ke yi su har wani Tunanin yin biki suke a auran da ba su da kyakyawan tabbaci a kan shi. Inna Talatu ita ta zame mana uwa a lokacin Tunda ba Amma Adda kuma bata zo ba tukunna. Adda Fati ta kira Baaba Ta lagos suka yi mgana sai tace Baba tanko ya yi mata mganar an d'auramin aure. Sai kame kame ta ke yi ta na fad'in ta jima bata zo garin ba ne ammh in ta zo zata zo su gaisa da Amma, nan ne ma Adda Fati ke sanar da ita komawar Amma wajen Adda Sai kunya duk ta kama Baaba ta kasa mgana. to gwara ita ta na yi mana sako in muka kirata mukace ga wani abu ya taso. Ba wai mganar sako ba dukkansu suna da karfin da bayan rasuwar Baba zasu duba bayanmu ammh ina ba su yi ba wasu ma cikin su sukan manta damu gabadaya. Irin su Baba Jibril na kaduna shi kila in na ganshi sai naga kamarsa ne da Dangin Babammu kila na ganeshi ammh daga matansa har ya'yansa ban ko san ko d'aya bani da masaniya ko su Adda sun san su barin ma Adda Fati da tafi mu bin su da son zumumci da su. Goggon kona fa ta na kusa ita da Baba Tanko ammh har ina manta rabon da na gansu da idanuwana ballatana iyalansa har gwara Baba Saminu ya na zuwa duba Amma duk da ba na duban da ya kamata ba ne na zuwa da ganin ya muka kare ne kuma ya gama mganganunsa ya shuru takalminsa ya kara gaba ko sisi bazai iya taimaka mana da shi ba. Adda Fati da kanta taje gidan Baba Tanko ta kai masa minti bikin Tariyar da ita da Adda Rukayya da Ramatu suka had'a hannu za su yi taron bikin. Sannan taje har gidan Goggon kona itama ta kaimata ita sai ta fara fad'an Laifin Amma ce itace ta yanke zumumci da su sai anan ma ne Adda ke Sanar da ita Amma bata garin nan ta koma Wajen Adda da zama gabadaya. Ni in da duk sun yi shawara da ni baza su yi min wannan gayyar ba. gayyar da bata da wani amfani illah ma daga baya ta zame min Tozarci. Har yan gidanmu da muka taso Adda Fati ta aika Habiba ta kai musu suna ta murna daman sun rasa ina zasu samu cikon Labarin. Habiba tace ta na zuwa suka Rufeta da Tambayoyin ina angon? Ya na nan lafiya? Sun gama Ammana aure na ba Alheri ba ne ni kaina tun ina sauraran jin ta ina kuma wannan karon kaddaran zata kwankwansamin ammh har lokacin ya gabato ban ji wata mgana sabanin shirin da suke yi ba. Ranar laraba suka je suka yi min jere sai dare suka dawo Ramatu ce ta isheni da Labarin kyan gidan kai Tsaye na kalleta kafin nace"Me kyan gidan zai kare min acikin rayuwata Ramatu? Haka gidan Abubukar ma kuka ce ya na da kyau na Salisu ma ammh kuma karshen mai ya faru? Sai ta kasa mgana ni kuma har cikin zuciyata na kalleta nace"To shima haka wannan zai kare a banza. Shiyasa ki ka ga ban tusa kaina ba nayi baya ina ta kallon ku Uhm.! Ku nafi Tsausayi saboda halin da zaku shiga in kuka ga kun kaini cike da Fata na sake dawo muku a karo na uku." Sai Ramatu ta kasa magana kawai sai ta tsaya ta na kallona cikin mutuwar jiki. Tayi kokarin kalaman bakinta su yi tasiri sai na dakatar da ita cikin mirnishi nace"Ramatu wannan karon kalaman ki baza su iya tasiri a gareni ba, me jiya ya yi ballatana yau? Ba bu abunda ya sauya ko da yaushe abu d'aya ya ke faruwa.' Tunda na fad'amata haka sai bakinta ya mutu ammh duk da haka sai da tamin mganar Kitso da kunshi Tsaraban Harara ta samu. Sai dai ban tsira ba domin washegari Alhamis Adda ta Dira ganinta ita kadai yasa sai da na tambayeta ina Amma sai ta harareni kafin tace"Daman kin damu da ita ne tunda ta tafi ko a waya baki taba gaisheta ba? Sai na kasa magana sanin ban kyauta ba, Adda ta gyad'a kai kafin tace"Aisha ba saboda komai ta aikata haka ba sai Saboda Rayuwarki ta inganta Hasiya. Kila yanzu bazaki gane hakan ba sai nan gaba ammh ina miki Fatan ki gane da wuri kafin Lokaci ya kure miki." Duk sai ta kashemin jiki zuwanta yasa ban kara gaddama ba saboda ta na da Zafi tace sai ta min dukan Tsiya ita ba irin Jari ba ne ballatana ta rika lallabani. Dole kanwar naki na Tsife kaina Ramatu ta rakani aka yi min wankin kai Kunshi kuma wata makociyar Adda Fari tazo ta min tamin na salatif na kwana da shi wayewar garin juma'a kuma ta yi min baki a hannuna na zane. Adda tazo min da Gumba wanda za'a sha da madara ban yi musu ba na karba da ta damamin na sha. Habibu mijin Adda ya yi kokari shi ya bada abincin Sha'anin wanda suka siya kuma sai Adda tace su bar min na gara tunda bazasu kaini haka ba. Na dauka na gama tara mutane Lokacin aurena ashe na manta cewa wasu ko don tafiya da abunda ya faru suna zuwa. Duk yadda na so kada na nuna Ina Farinciki da wannan auren su Adda Fati ba su barni ba sai da suka saka na yi wanka na shirya Ramatu ta min kwalliya. Abun mamaki duka matan Baba Tanko da na Baba Saminu sun zo su gambo da wuri suka iso saboda kada a yi wani sin din basa wajen. Goggon kona sai da yammah ta zo ammh wasu cikin ya'yanta sun zo da Rana. Bata ji kunyar yima Adda Mganar Amma ta raba zumunci da su ba ita kuma Adda ta same su ta yi musu wankin babban bargo ta rufe da fad'in"Aisha ta bi ku gajiya ta yi ta kyaleku. kuma har a wajen Allah ba ta da wani laifi ku ne kuka ki ta ku ka k'i ya'yanta duk da su d'in Dolen ku ne. Yau an wayi gari Zumunci ya lalace d'a sai wanda na Haifa ya'yan dan'uwa ba D'a na ba ne, Kwata kwata baku kula da su ba a banzace ku ka bar su suna wahala saboda canfin ku na karya da ba ku da tabbaci." Kasa mgana suka yi tunda ba su da gaskiya barin ma Goggon kona daman ance gaskiya ai sunanta gaskiya kuma daga kinta sai bata. Kunya suka ji? Ko kuwa daman suna son ganin abunda zai faru ne yasa suka tsaya har yamma. Na saka kaya kala uku a ranar ina cirewa gabda mangariba Adda Rukayya ta saka na sake wanka na saka less din da Farin Hijabi naji ana ta mganar ya kamata azo a tafi dani kada dare ya yi. Nayi ta kallon al'amarin ina mamakin ko motoci goma aka kawo sai sun cika wasu ba su samu waje ba. Saboda duka matan gidanmu da muka taso sun zo har da makota kuma suma sun ce da su za'a je kai Amarya. Har sai da nayi sallar mangariba ban ji wata mgana ba ina kan sallaya ina nirmishi ni kad'ai mirmishin da yafi kuka ciwo a cikin raina ina Tunanin kamar na Salisu za'ayi kila ma kafin na kai ga tarewan komai zai iya faruwa. Wayar Sadiq Adda Fati ta yi ta kira a kashe hankalinsu gabadaya sai da ya tashi sun rasa mafita Kuma bai kamata su je su kaini batare da susan wani Hali Shi mijin nawa ya ke ciki ba. Mutane nata zaman jira shuru ga Duhu ya shiga Adda Rukayyace ta fita ta na ce musu kowa ya tafi gida Amarya angonta yace zai zo ya Dauketa da kansa sai gwiwa duk ya yi sanyi. Su gambo dole suka tafi ba'a samu an karisa ganin abunda zai wakana ba matan gidanmu ma ba'a son rai suka tafi ba Ammh sunce daga baya zasu kaimin ziyara. Zuwa karfe 8 na dare kowa ya watse daga su Adda sai Inna Talatu sai Ramatu har Goggon kona ta kwashi Tsufanta ta kara gaba. Ni ina ciki ban fito su kuma suna falo suna fama da tararradi. Ramatu ta kalli Adda Fati da ta ke ta faman kiran wayar Sadiq a kashe cikin mutuwar jiki tace"Har yanzu baki same shi ba? Adda Fati tace"Wayarsa a kashe." Adda Ta numfasa kafin tace"Ina sha Allahu lafiya lau. Ku yi tunani ba ku da ko Lambar abokinsa ne? Sai a Lokacin Adda Fati ta tuna da lambar Tahir da Sauri ta mike ta na fad'in"Na tuna ina da lambar wannan abokin na shi." Da sauri kowa ya washe baki Inna Talatu tace"Maza ki kirashi." Da Sauri ko Adda fati ta kira lambar Tahir ta shiga har ta kusa katsewa sannan ya daga kiran. ****** Lokacin Da kiran Adda Fati ya shigo wayae Tahir ya na kishingid'e ya na chart ne Sadiq na kwance gefensa barci ya kwashe shi yau yini ya yi a wajen aiki ya dawo a gajiye da yasa barci ya kwashe da wuri suna Hira ne ma shi da Tahir. Har ga Allah sun ma sha'afa da mganar Tariyan Hasiya Basu san kan al'amarin ba sun zata ma basai ma an kira su ba Shiyasa ba su yi tunanin wani abu ba. Tahir ba shi da lambar Adda domin ba shi da alaqa da ita ballatana ya adanata shiyasa har ya daga wayarsa suka gaisa bai gane wacce ke mgana ba. Cikin Muryansa yace"Bangane wa ke magana ba? Adda Fati tace"Fati ce yayar Hasiya." Har ga Allah kwana biyu nan Tahir ya fara dawowa cikin Hayyacinsa da Halin Tsaka mai wuyar da Sadiq ya saka su ya fara mantawa da wata Hasiya tunda Sadiq baya masa mganarta shima ba ya yi masa. Kai tsaye yace"Na'am bangane ba wata Hasiya? Ya fad'a kai tsaye sai Adda ta kasa mgana su kuma su Ramatu sun Tsorata sun zata wani abu ne ya faru suka fara tambayanta ko lafiya Hankali ta she. Ba su kadai ba ni kaina ina makale a jikin kofar dakin gabana na fad'uwa. Bana son wani abu ya samu Assadiq in hakan ta faru ta sanadina bazan tab'a yafe ma kaina ba. Adda Fati ta hadiye miyau kafin tace"Sadiq na lafiya kuwa? Na yi kiran wayarsa a kashe ko ya manta yau ne nace masa Hasiya zata tare." Sai da ta fad'i haka ya tuna da gagurumin tarnakin Bala'in da Sadiq ya jefa rayuwarsu a ciki. Cikin mamaki yace"Ta na chan gidan ne yanzu? Adda Fati tace"A'a ina dai tambayan Sadiq ya na lafiya? Tahir yace"lafiyansa kalau ya kwanta ne bari na yi masa mgana." Daga haka ya yanke kiran Lokaci daya ya na shurun Sadiq da kafa. Fad'i ya ke yi"Mallam ai sai ka tashi Shigen Tausayi ya sa ka jefamu a masifa ba ka ga ta barci ba Sadiq." Sadiq ya motsa lokaci daya ya Bude idanuwansa ya na kallon Tahir kafin yace"A gajiye na ke Tahir ka bar ni na Huta don Allah.". Tahir ya kwashe da dariya kafin yace"Ina kaga ta wani Hutu? Amaryan ka Hasiya na chan na jiran ka." Kamar bai jisa ba sai kuma ya mike Zumbur ya na fad'in"Me ka ce? Tahir yace"Yanzu wannan yayar nata ta min waya suna tambayan ka ko lafiya ka ke kuma da sakon Amarya na chan na jiranka" Sadiq ya dafe kansa kafin yace"Na manta daman yau jumma'a ne?. Tahir baka tuna min ba." Tahir ya balla masa Harara kafin yace"Ni kuma a suwa da zan tuna maka? Kai da abun ya shafa ka manta sai ni karan kad'a miya." Mikewa zaune Sadiq ya yi cikin kasala ya na fad'in"Duk dai ba wannan ba yanzu ta na ina? Tahir yace"Oho ina na sani sai dai ka kirata kaji." Sai alokacin ya duba karamar wayarsa yaga ta mutu daman ya kwana Biyu bai sakata a chaji ba. Wayar Tahir ya amsa ya kira Adda Fati daidai Lokacin da zukata suka samu natsuwa jin Babu abunda ya faru da Sadiq. Ta zata ma Tahir ne sai taji muryan Sadiq tambayanta ya yi sun kai Hasiyan chan gidan ne? Adda Fati tace a'a ai ba su yi da shi zasu kaita ba. Kansa ya dafe kafin yace"Ku yi hakuri na Shafa'a ne sannan wayata ta mutu ba chaji. ina ne in da ku ke sai mu zo mu dauketa? Nan Adda ta rarrataba masa kwatance tace in ba su gane ba su kirata. Suna yin sallama ta kalli su Ramatu ta na fadin"Alhamdulillah ba abunda ya same shi yace mu yi hakuri ya sha'afa ne wayarsa ce ta mace ba chaji ammh yace gasu nan zuwa." Gabadaya suka sauke ajiyar zuciya ni kaina da na ke labe sai da na sauke Numfaashi ina jin gudun zuciyata na Daidaita. Sad'af Sad'af na koma daki na zauna ina maida numfashi. Sadiq ya sha fama da Tahir domin da Farko yace shi ba mai sake fitar da shi da Daddaran nan ya gaji. Sai da Sadiq ya yi ta rokonsa sannan ya tashi ya Shirya suka Rufe daki suka tafi. Ba yan gari ba ne kuma basa yawo shiyasa suka sha wahala kafin su gane gidan Adda Fati sai da Mijinta ya fita bakin hanya ya tarosu. Saboda Sauri kananun kaya ne dukkansu a jikinsu gwarama Sadiq ya Dora Jaket a saman riga da wandon jikinsa. Har Falon Adda Fati Habibu ya yi nusu Jagora in da su Adda ke zaune suna jiransu. Dukawa suka yi suna gaishesu Sadiq yafi nuna jin kunya Tahir ko aransa cewa ya yi kunyar me tunda ba surukansa ba ne. Adda ta jima ta na nazarinsu kafin ta yi mirmishi tace"Duk da bansan surukin namu ba ina da tabbacin mai kunyar nan ne" Adda Fati na mirmishi tace'Shine Addan mu" Sadiq ta kallah kafin tace"Abubakar ga Addammu yaya ta ke a wajen Amma." Sai a lokacin ya dago ya kara kallonta sai kuma ya ga tsantsan kamarsu da Amma cikin sanyin murya yace"Sannu da zuwa. Amma na lafiya? Adda tace"Ta na lafiya bata zo ba ammh tace sakon fatan alherinta na tare da ku a koda yaushe in sha Allahu." Da kai ya amsa mata Tahir kan kiris ya rage bai tashi ya zauna ba tunda yaji kafafunsa sun gaji da Tsayawa. Adda ce ta fara yi ma Sadiq tambayoyin sana'ar da ya ke yi. Su ka kalli juna shi da Tahir kafin yace"Ina bautar kasa ne da d'an alawun da suke bamu na ke buga bugata namu dai irin na talakawa." Adda ta jinjina kai kafin tace"Allah ya tallafa Naji suna fad'in kai d'an shinkafi ne nan ta zamfara ko? Sadiq ya gyada mata kai alamun hakane ya Dauka nan Adda zata tsaya ammh sai ta cigaba da fadin"To bayan iyayenka sun rasu a hannun wa ka ke a chan shinkafin? Sadiq ya kalli Tahir karo na biyu shima ya kallesa. Adda na ganin haka tace"Ina fatan ba damuwa ko? Kasan aure na bukatar haka an yi abun cikin gaggawa akwai bukatar ka gabatar ma da Ahalinka Hasiya." Sadiq ya had'iye wani miyau kafin yace"Eh eh zan kaita in sha Allahu." Adda tace"Baka amsa min tambayata ba? Wajen wa ye ka girma bayan ka rasa iyayen ka? Kamar Subutan baki Sadiq yace"Hannun kakata. Eh hannun kakata na girma." Adda ta murmusa kafin tace"Dakyau. allah ya baku zaman lafiya bayan an kwana biyu sai ka kaita taga Dangin ka. Allah ya baku zuru'a masu albarka nasihata itace ka rike Hasiya da Amana don girman Allah kada ka bari rayuwar Hasiya ta shafi zaman Lafiyan ku. Canfi ba gaskiya ba ne komai kaga ya faru daga Allah ne." Sadiq ya dago ya na fad'in"Wannan bazai taba zama matsala ba in sha Allahu. Kowa yasan ba bu mai yi sai Allah.". Adda taji dadin jin haka sai ta yi hamdala itama ta aminta da zabin jari yaron akwai hankali. Ramatu ta kallah kafin tace"Ki je ki taho da Hasiya. Dare na yi" Da Sauri ta mike zuwa Dakin Habiba na ciki da tashigo daga baya. Ban jira tamin magana ba na mike Ramatu ta saka Habiba ta Dauki karamin akwatina ita kuma ta rike Babban. Ina gaba suna bi na a baya muka fito falon ban kalli kowa ba gaban Adda na Durkusa. Ta Dafa kaina ta na sakamin albarka kafin ta mike ta na fad'in su tashi su rakani. Allah yasa ba su sallami mai adaidaitan da ya kawo su ba, har kofar gida suka rakani Adda da Inna Talattu suka sanya cikin adaidaita Sadiq na gefe Tahir kuma ya shiga gidan gaba. Adda ta kallemu lokaci daya zuciyarta ta aminta wannan ne mijin Hasiya wad'anda ta aura daga Farko suna cikin Kaddaranta ne. Cike da kwarin gwiwa tace"Hasiya ki yi hakuri da mijinki ki yi masa biyayya iya karfin ki, ki zauna da shi ki lallaba yanayin da ku ke ciki. Ina miki Fatan samun ingatttaciyar Rayuwar da mahaifiyarki ta ke miki Fata ina kuma rokon Allah ya barki a gidan auran ki sai mutuwa." Kaina na kasa ban yi mgana ba ina ta wasa da hannuna acikin Hijabina. Inna talatu ce ta jaddamin na yi addu'a kafin na shiga dakina. Da kaina na amsa musu Ramatu da su Adda na ta daga mana hannu muka bar kofar gidan Adda Fati. Tunda muka dauki hanya ba wanda ya yi mgana Tahir ne aka kira a waya ya yi mgana sai da ya gama sannan ya juya ya na kallon Sadiq da ke zaune gefe daya hankalinsa na wajen kallon Hanya nima ina gefe a rabuke. Karamin tsaki yaja bai yi mgana ba shi ya rika yi ma mai adaidaitan kwatance har gidan. Daman Ramatu ta sakamin key din gidan a hannuna muna sauka na mikama Sadiq yasa ka hannu ya karba" SShaf mun manta da kaya sai da mai adaidaitan yace ga kaya sannan ya sauke mana. Ban tsaya jiran komai ba na sunkunci babban akawatin Tahir shi ya yi gaba ya na bud'e gidan. Sadiq ya kalleni cikin Duhun anguwan ammh hasken Fatata ta Haske masa fuskarsa. Cikin sanyinsa ya mika hannu ya Dauki karamin akwatin Lokaci daya ya na fad'in"bani akwatin ta yi miki girma." A hankali ya fad'a wanda ina da tabbacin Tahir bai jisa ba. Ba musu na mika masa ya dauka daidai Lokacin da Tahir ya Bude get din gidan Tahir na gaba ina bin bayansa shi kuma Assadiq na bayanmu. Wannan karon ma Tahir ne ya Bud'e dakin sai da ya dawo daga baya ni na fara shiga da kafar dama tare da Bismillah. Sannan Sadiq yabi yo bayana Tahir dai a waje ya tsaya bai shigo ba. Kamar anguwan ba wuta dakin ya yi duhu sai da ya sauke kayan hannunshi sannan ya yi amfani da Fitilar wayarsa ya haska mana Dakin. Saman kujeruna tun na auran Abubakar na zauna saboda sai naji duk na gaji. Sadiq yasan Tahir na jiransa bai Tsaya kallon Dakin ba yace"Zan tafi sai zuwa gobe ko? Ai sai na ware ido ina kallonsa ina kuma ya ke nufin zai tafi ya barni a wannan gidan ni kadai ko'ina Duhu ga shi bani da waya ballatana Fitilar hannu. Bai ga razanan da na yi ba ne yasa ya jiya zai fice ya na fad'in"Gobe zan zo in sha Allahu." Ai bai gama fita ba nayi saurin biyo bayansa bai ankara ba sai ji ya yi kirjina ya bangaji bayansa. Lokaci d'aya na rirrike masa sagalen hannunsa ina fad'in"Don Allah kada ka tafi ka barni, Ina. Ina jin tsoro bazan iya kwana ni kad'ai ba." Da dan hasken Fitilar wayarsa ya ke kallon Fuskata, ko'ina na jikinsa na wani amsawa da yadda Hasiya ta rikeshi gam ta na rawan jiki. *Janafty* *TMWB2K004* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641 Da sauri ya matsa baya saboda kaucema rikon da Hasiya ta yi masa. Cikin yanayinsa yace"Me zai same ki? Ba komai kada ki damu" Nayi kwalkwal da ido cikin bayyana tsoro na nace"Wlh ina jin tsoro." Sai ya yi tsaye kawai ya na kallon Fuskata ta cikin duhun dakin Tunanin mafita ya ke yi mganar gaskiya bazata iya kwana ita kad'ai ba shima da fari ya yi tunanin haka. Kuma zaman shi tare da ita baya cikin Tsarinsa. Gyaran murya ya yi kafin yace"Kin ga ne? Gobe zan zo yau din ma saboda ina da wani uzuri ne yasa bazan kwana anan ba." Kai tsaye nace"To ka tafi da ni in da zaka kwana don Allah." Sadiq ya ware ido ya na kallon Hasiya ya na shirin mgana yaji muryan Tahir daga waje na fad'in"Kasan fa mai adaidaita na jiran mu a waje. Ga shi dare ya yi." Jin haka yasa batare da ya yi magana ya kama hanya zai fice ina ganin haka na yi zaraf na bi bayanshi. Ya na fita sai yaji ni a bayansa Tahir ko kallon mu ya yi cikin mamaki kafin ya samu zarafin mgana Sadiq ya juya ya na kallona. Cikin sanyin murya yace"Ba tafiya zan yi ba" Jikina na rawa nace"Don Allah kada ku tafi barni a gidan nan ni kada'i. Bazan iya zama ba ina jin tsoro." Na fad'a ina kara kallon wagegen gidan na saba da kwana a daki falle daya tare da Amma da Habiba. Sannan na saba rayuwa cikin mutane bazan iya kwana a gidan ni kad'ai ba. Tahir da Sadiq suka kalli juna kafin Sadiq ya sauke numfashi cikin sigan lallashi yace"Kinga Hasiya koma ciki magana zan yi da Tahir." Sai naji kamar ban yarda da shi ba. Kada na shiga ciki kuma su tafi su barni na shiga uku. Kif kif ta  idanuwana na rika yi na kasa shiga ciki kamar yadda yace. Ganin haka yasa Tahir yaja Hannunsa suka koma daga bakin get din ina hangensu. Sai na samu salama ganin ba tafiyar za su yi ba. Ammh na kasa komawa cikin dakin tunda akwai Duhu ko Tafin hannunka baka iya gani. Suna dagachan nesa da ya ke kuma ban kasa kunnuwana ba shiyasa ban jiyo mganganun na su ba. Kuma dai sun yi kasa da murya kamar wasu munafukai. Cikin rage sautin murya Tahir yace"Me ye wannan zabiyar matar ta ka ta ke nufi? Bazata iya kwana ita kada'i ba to so ta ke ka taya ta kwanan kenan? Sadiq ya yi shuru ya na wani nazari akwai hakkin kula da komai na Hasiya a kanshi yanzu aurensa sunan shi aure ko da wani Tunani a ka yi sa. In ya barta a cikin gidan nan wani abu ya sameta me zai ce ma mahaifiyarta da yan'uwanta? Har a wajen Ubangiji ma ba shi da abunda zai kare kansa hakkinta zai kamashi. Shiyasa ya kalli Tahir kafin yace"Tahir ba ni da mafita. kaga dai yanayin anguwan nan sannan ita kadai ce kuma macece akwai hatsari mu tafi mu barta ita kad'ai" Tahir ya dage hanci kafin yace"I see. to yanzu me ka ke so a yi? Sadiq yace"Zan tsaya na kwana kai ka tafi sai mu had'u gobe in Allah ya kaimu." Tahir ya kalli Sadiq a cikin Duhu baya ganinsa sosai ammh ya na ganin Duhun Fuskarsa. Cikin mamaki yace"Kace me?  nan zaka kwana tare da wannan yarinyar? Tahir ya fad'a ya na nuno Hasiya. Da Dauri Sadiq ya rike hannunsa ya na fad'in"Ka yi a hankali mana. So ka ke taji abunda mu ke fad'a? Ya fad'a ya na juyawa ya na kallona sai dai bai fahimci ko naji ko ban ji ba tunda a lokacin Tahir ya daga Sautinsa. Ni kuma ban ji su ba, na ga dai kamar an nuna ni tunda akwai hasken farin wata da ya raba tsakiya da kwata shiyasa sai duhu ya mamaye hasken farin watan. Tahir ya rausayar da Murya kafin yace"ammh kasan kwana a tare da yarinyar nan baka saka shi cikin Tsari ba ko? Sadiq yace"Na sani ba shi cikin Tsarin mu. Ya zama dole ne shiyasa ammh ai daga yau ne zan san abunda zan fad'a mata da zai saka na yi nesa da kwana tare da ita." Tahir ya yi shuru kamar bazai yi mgana ba. Ganin haka yasa Sadiq ya dafa kafad'ansa ya na fad'in"Da gaske na ke yi maka bazan bari a samu wata matsala ba." Tahir ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Shikenan bari na tafi." Sadiq yace"Ok sai da safe kenan? Tahir ya kallesa kafin yace"Abubakar." Cikin mamaki Sadiq yace"Na'am Attahir." Tahir ya had'a hannayensa ya na fad'in"ban da Kusanta, Ban da kusanta Abubakar." Sadiq ya yi saurin cewa"Kusanta? Cikin Sigar tambaya. Tahir yace"Eh kusanta nace kada ta ribace ka tab'ata kasan an ce in namiji da mace su ka keb'e su kadai to shed'an ne a tsakanin su." Sadiq sai a lokacin ya fahimci in da Tahir ya dosa baki ya hangame kafin ya rike Haba yace"Haba mana Tahir. Me yasa zaka yi irin wannan Tunanin fisabillahi? Tahir yace"Dole na yi tunda komai naka ya na zuwa ne batare da sanar da ni ba gwara na ja maka kunni yin haka tamkar ka fallasa sirrin da ka ke son Rufewa ne." Sadiq yace"Na sani  ni har ga Allah saboda taimako na auri Hasiya ba domin wani abu daga jikinta ya na Burgeni ko ni sha'awa ba. Ba bu wannan tunanin kwata kwata a raina." Tahir yace"Uhm! Irin ban yarda ba jin haka yasa Sadiq yace"Ko zaka zo mu kwana tare ne sai ka cire shakku a kaina? Tahir ya juya ya na fad'in"A dakin mata da mijin ne zan kwana? Sadiq ya yi dariya har sai da tayi sauti. Shi ya raka Tahir har kofar gida ya na daga jikin Gate din ya shiga adaidaitan suka wuce. Sannan ya dawo cikin gida da kansa ya sakama get d'in sakata. Sannan ya dawo in da na ke tsaye duk sauro sun cijemin kafa ammh tsoro ya hanani komawa daki. Gaba ya shiga ya na kunna Fililar wayarsa lokaci d'aya ya na fadin"Mu shiga ciki" Jin haka yasa na bi bayanshi har zuwa cikin Daki muna shiga ya juya ya Rufe kofar da sakatan sama da kasa. Mun tsaya dukkanmu a tsakiyar falon kowa na saka wani acikin ransa. Ni sai alokacin nake nazarin dakin shi kuma tunanin me ye abu na gaba da zai yi ya ke yi? Bai kuma sani ba gashi ya manta bai tambayi Tahir ba. Kallona ya yi kafin yace"Ki na jin yunwa? Kai tsaye na girgiza masa kai alamun a'a ina ji ya sauke numfashi kafin yace"ke ki kwana aciki ni zan kwanta a falo." Ban yi mgana ba ya duka ya dauki akwatina babba ya shiga ciki ni kuma sai na dauki karamar na bi bayansa. Shima cikin an gyareshi da Gado da wardrope duk da dai karami ne sai madubi kawai aciki. Gefe ya saukemin akwatin batare da ya kalleni ba ya juya ya na fad'in"Sai da safe." Gani nayi zai fita ya barni cikin Dubu sai jin takuna ya yi a bayansa da Sauri ya juyo ya na kallona. Kai na kasa nace"Duhu ba filita a nan." Wayar hannunsa ya kallah karamar wayarsa ne kuma layinsa ne na gida babban wayar tasa  ba ya wani abu da ita ya barota a gida. Wayar ma ba chaji sai buga battery low take yi don ma yar alkwari ce sai ta mutu sau nawa da ya kunna zata kawo sai kuma ta jima bata mutu ba. Gudun matsala yasa ya kashe Sim din a cikin wayar sannan ya mikamin ya na fad'in"Ki yi amfani da ita." Ba musu na saka hannu na karb'a ina Fad'in"Nagode.' Ficewa ya yi zuwa falo ni kuma ya bar ni nan tsaye ina tunanin mafita. Daman ban tsammaci zamu kwana waje d'aya ba tunda ga yadda auran namu ya kasance. Dole na nemi mafita hijabin jikina na cire marata ta daure shiyasa na tura kofar da na gani a cikin bedroom din. Ina tunanin nan ne bayi ina shiga ko naga Tioler ne mai kyau. Sai dai ba ruwa kad'an ne bai wuce na alwala ba. Sai da na yi tsarki sannan na fito Allah yasa na yi sallolina a gidan Adda Fati da na shiga uku ina zan samu ruwa a daren nan? Ko kakkabe gadon ban yi ba, na hau daga gefe na kwanta ina maida numfashi bayan na rufi da Hijabina Saboda halin da na ke ciki ban yi ma Tunanin sauya kayan jikina ba. Fililar wayar a kunne na barta ni wayar ma ban da riketa da na yi a hannuna ko latsata ban yi ba Tunda ba tawa ba ce. Ko add'an  barci ban yi ba Gajiya ce ta da rashin barcin da ban samu ba kwana biyu suka taru suka min Rubdugun da yasa wani barci mai nauyi ya kwasheni. Ban farka ba sai da gari ya waye tangararan. Bansan meyasa shi bai tasheni ba ammh ko da na farka haske ya cika Dakin wayarsa kuma ta mutu cikin dare ina chan ina barci ban sani ba. Na kwanta ko motsawa ban yi ba yasa wuyana ya kage ina kallon gefe na mike na shiga makewayin da sauran ruwan da na gani abotiki na da ya zama kankara saboda sanyi na yi amfani da shi. Ruwan ma bansan dad'ewarsa ba saboda ina tunanin tun na wanda su Adda Fati suka yi amfani da shi ne da suka zo danki. Hakanan na fito bansan ina ne gabas ba daidaitawa kawai nayi lokaci d'aya na saka Hijabi bayan na shimfid'a d'an kwali na tada sallah ammh a karkace tunda wuyana ya kage. Na jima bayan na gama sallah na kasa fita falo sai na fara tunanin ko ya tafi ne? Tunda ban ji ko motsinsa afalon nan ba. Tashi na yi da Hijabin jiya da kayan jiya na leka falon ta labule sai na ganshi kwance saman kujera ya na barci ya hard'e duka hannayensa saman kirjinsa. Fitowa na yi a sannu sannu gabansa na tsaya ina kallonsa barcinsa cikin natsuwa numfashinsa na sauka Daya bayan Daya. Fuskarsa na ke kallo kamar ya na mirmishi bansan ma yaushe ya bude ido ba sai gani nayi kawai ya mike zaune Lokaci d'aya ya na fad'in"Da damuwa ne? Cikin muryan barci, Da sauri na matsa baya naji kunya sai dai na juya kaina azaban wuyana ya isheni bansan Lokacin da na dafe wuya na ina fad'in"Wash." Da Sauri ya mike ya na fad'in"Lafiya? Me ya faru? Ina rike da wuya na nace"Na kwanta kan wuya na ne da na tashi kuma sai ya ke min ciwo." Kallona ya yi kafin yace"Oh sannu ki bar tabawa zai bari" Da toh na amsa masa kafin na rankwafa ina gaishesa. Ya amsa cikin dan kamewa hasken garin ya leka ta window ya gani kafin ya juyo ya na fadin"Rana ta yi karfe nawa? Na jujjuya naga babu agogon falon ganin haka yasa yace"Waya ta." Ina jin haka na gane da Sauri nace"Ta mutu inaga ba chaji ne." Kafin ya sake mgana na juya da sauri ammh sai da na rike wuyana saboda zafi Ciki na koma na Dauko masa wayarsa na basa shi kuma ya karb'a ya kunnata sai ga shi ta kawo. Ya na kallon wayar yace"Karfe 8 saura. Me ki ke bukata ina so na tafi ne." Sai na rasa ta cewa ni me zan ce ina Bukata? Bansan me da me suka kawo ba tunda tare muka zo ko kitchen d'in ban leka ba. Ganin ina tsaye yasa tunanin ya Duba kitchen saboda kada ya tafi ya barni da yunwa wani abu ya faru ya shiga uku. Kitchen din ya shige batare da ya yi min mgana ba nima ban bi bayansa ba. Ina nan tsaye ya fito ya na fad'in"gas din ba Refilling zan je da shi a yi miki Relling ina dawowa yanzu." Sai da ya yi mgana sannan na juya ina kallonsa har ya Dauko gas din. A dawo lafiya na yi masa shi kuma ya kimkima ya fita da yake ma karami ne 5kg ne. Bayan fitan sa na jima tsaye ina ta jujjuya wuyana sai daga baya na koma ciki na dauki akwatina na sauya musu muhalli na kakkabe gadon duk da bai yi datti ba na gyara dakin na Share tare da falo. Sai alokacin na shiga kitchen din naga Har da kayan abinci rabin buhun shinkafa da taliya da macaroni duka kwali. Sai magyada da manja,garin tuwo da shinkafar tuwo. Kayan maggi da kayan dage dage irin su kuka da kubewa sai manshanu da Adda Ta zo min da shi da zata zo. Sai sabbin kololin da Adda Rukkaya ta siyamin sun yi kyau sosai duk da bani da wasu kayan arziki sun yi min danki kuma ya yi kyau. Kitchen din ma karami ne sosai shiyasa ya cinye kayan har da ragowan Fili. Cikin Lokaci na gama komai bayi ne ban wanke ba, saboda ba ruwa kuma gashi ina so nayi wanka. Sai na saka takalmi na bude kofa na fita Tsakar gidan ina Dubbawa. Nice a falt din farko sauran uku suna bayana sannan Famfon gida ya na ta wajen dakina ne. Kamar wasa na kunna sai ga ruwa ya zo na yi ta mamaki sai da na daga kaina naga tanki ammh kuma ina mamaki kenan suna da wuta? Da na kara bin wajen da kallo naga ga wayoyin wuta ne da suka shigo ta gidan mahad'in puse na kowani flat. Ganin na samu ruwa yasa na zage na koma Daki na Dauko botikai na a Makewayi na rika cikawa da ruwa ina kaiwa kitchen a babban bambina na ruwa na rika zuba ruwan har da sai na cikata sannan na koma na fara zuba ma babban bambin da ke makewayi. Na dauko botikin karshen kenan muka ci karo da shi ya shigo Dauke da gas din da Babban leda a hannunsa. Dukkammu sai muka tsaya muna ma juna kallon kallon. Ni kayan jikina me tun na jiya ammh na nade zanin sama na kuma ma kaina Daurin gammo saboda Diban ruwa rabi na duk na jike sai yararin ruwa na ke yi. Kamar kuma sai naga ya na yar dariya. Sai na Tsargu da sauri nace"Am, Ba ruwa ne a makewayi shine da na fito naga gidan akwai ruwa shine shinre..." Bai bari na karisa ba ya wuceni zuwa Dakin ya na fadin"sannu da aiki." Kunya ta kara kamani cikin sanyin jiki na bi bayanshi baya falon ya shiga kitchen da sauri na shige cikin Dakin kada ya fito ya ganni. Abunda bansani ba yana leke na ta kitchen mamaki ya ke da siraran hannuwana da kafafuwana ashe ina da karfin Daukan botiki haka? Ledan da yazo da ita a kitchen ya barta ya fito falo yana jirana ni kuma ganin na jike yasa na kwabe da ruwan sanyin nan nayi wanka. Da na fito ban ko shafa mai ba na bude babban akwatina ina kokarin Daukan kayan da zan saka duk da kayan ba su da wani yawan kirki. Kamar wasa naji ana kiran sunana sai na tsagaita da abunda nake yi na kasa kunni sai naji Muryan ASSADIQ ya na fad'in"Ha..Si.. yaaa." Da Sauri na amsa da Na'am. Ban tsaya saka kayan ba daman akwai zanin leshin a jikina da na yi wanka sai kawai na nemi hijabi na saka na fita falo. Yana tsaye daga bakin kofa na zo ina fad'in"Ga ni" Kallon kafafuna ya yi da ya gansu suna Digan ruwa cikin gargasan gashin jikina. Kai tsaye yace"Tunda kin jike ki yi wanka mana" Nima kai tsaye nace"Na yi wanka" Baki ya bude kafin yace"Da ruwan sanyi? Da kai na bashi amsa, Kai ya jinjina kafin yace"Baki tsoron sanyi ya kamaki? Maimakon ki saka ruwan zafi." Sai na kasa mgana kaina na kasa. Bai damu ba yace"Kin iya kunna gas? Da kaina na amsa masa kafin nace"eh na iya Adda Fati na da shi" Kai tsaye yace"Ok sai ki yi amfani da shi ki rika girki, Ni zan tafi kinsan abunga ga takala ina buga bugan neman abunda zan rike kaina tare da ke" Ya dakata ya na kokarin had'a karyan da zai gayamin. Dakyar ya cigaba da fad'in"Ina da wani megida da ke shigo da kayan wuta shi na ke bi muna kasuwanci, wani Lokacin sai dare sosai na ke dawowa kuma kinga nan ya yi nisa da inda na ke hidimar kasata shiyasa zan rika kwana in da na ke kwana da Fari." Ya dagata ya na nazarin yadda na karb'i mganar. Kamar yadda ya sani ne a tsarace na kalleshi kafin nace"Ba anan zaka rika kwana ba kenan? Sai ya ji nauyin yace eh ammh ba shi da zab'i cikin karfin hali yace"Eh ammh zan rika zuwa lokaci bayan lokaci ina Dubaki." Kai tsaye na kallesa kafin nace"Ni kad'i zan rika kwana? Na fad'a idanuwana na cikowa da kwallah ya kasa kallona saboda kada Tausayina yasa ya bata tsarinsa. Kansa na gefe yace"nan da sati daya mai flat din kusa dake zata tare kada ki damu zaki samu abokan zama." Kasa mgana nayi kirjina ya cika da Tambayan kaina daman ana aure haka? Miji bazai kwana agidansa ba sai dai a wani waje? Ganin ya na shirin tafiya ne yasa nace"Fitila.. b" Da sauri yace"Na siyo miki ta na cikin kaya a kitchen." Da sauri na Sauke ajiyar zuciya. Ya fita daga cikin daki ya na kallona kafin yace"Ki zo ki kulle kofar gida." Ba musu na saka takalmina dake nan wajen na bi bayansa har waje. Sai da ya fita sannan ya juyo ya na kallona. Kad'an ya rage ban saki kuka ba kwayan idanuwana sun nuna masa haka. Cikin sanyinsa yace"kada ki rika barin gidan a b'ude, sannan har dakin ki ma ki rika Rufewa. Kada kuma ki kuskure ki bude kofa ga wanda baki sani ba kin ji ko? Da kai na gyad'a masa saboda bakina ya yi nauyin da na kasa mgana. Har ya juya zai tafi sai kuma ya kara jiyowa ya kalleni kafin yace"Hasiya." Ina kallonsa nace"Na'am" Kai tsaye yace"Ki kula da kan ki." Kaina na maida kasa kafin nace"To" Ina ganinsa ya wuce da yaga na tsaya kallonsa sai ya yi min alama da ido da na Rufe get din. Jikina a sanyaye na Rufe ai da gudu na koma daki na shige na maida kofa na Rufe. Na waiga hagu da dama ba wani motsin mutim bansan Lokacin da na zauna a kasan tayels din dakin na Rushe da kuka ba kewar Amma ya cikamin zuciya. Sai da nagaji ba mai lallashina na hakura daki na koma na samu doguwar rigar atamfa na saka kayan da na cire kuma na shanya a saman kofar makewayin. Cikina naji ya tamke nasan kuma na yunwa ne tunda tun jiya rabona da abinci. Kitchen din na shiga da ledan da ya Shigo na ci karo na budeta naga kayan Tea ne aciki sai Buredi. Sai Filita sabuwa mai irin na Chajin nan, sai kudi 2k aciki yan dubu Sabbi. Mirmishi na yi a fili na Furta "ASSADIQ.." Kayan Tea din na saka su cikin dirowan kitchen din, Gas din kuma na sama ma wajen zama zan kunna. Sai kuma naga ba ashana sai idona ya raina fata, sai da na kara duba kayan da ya shigo da shi naga ashana sannan na kunna gas din na dora ruwan zafi cikin karaman tukunya na jira har ya tafasa na kashe gas din na samu karamin kofi na shiga na had'a tea na yanki buredi na fito falo na zauna kan kujera ina sha. Gabadaya kadaici ya dameni ga shi ni ba waya ba sai yau na karajin takaicin da a baya Amma ta matsamin sai na siya waya na ki bin shawaranta. Da ace na siya da yanzu na kira su mun yi mgana. A zatona su Adda Fati za su zo min ammh sai ga shi har yamma ko kare ban gani ba sai dai haushin na makota masu manyan gidaje. Sai dai na zauna nayi zuru tunanin duniya sun rufeni ina tunanin shi kuma wannan auran nawa ya sunan shi? Kila shi kuma ahaka zai kare shima. Sai dare na samu na Dafa taliya da mai da yaji tunda ba ni da kayam miya sannan ban ga ko almajiri ba ballatana na samu yaron aike. Sai da dare ya yi na kara raina kaina a firgice na kwana kuka na sha har barci ya kwasheni shiyasa na tashi da Fuska duk ta yi ja. Sannan ga sauro duk sun cicijeni ba maganin sauro. Babu kuma wayar da zan samu na kira ko Adda Fati Allah Sarki ashe mutane Rahma ne. Ni kadai acikin wannan gidan har na tsawon kwana Hudu ko kafar dakina ba na fita komai aciki na ke yi. Barci duk sama sama ne kuma a firgice ko motsin iska naji ya taba get haka zan fara rawan jiki da na zuciya. Ba Labarin Assadiq ba labarin su Adda sai ranar da kwana biyar da Safe sai ga Ramatu Ashe ta jima ta na buga get ban ji ba ina wanka sai da ta zagaya ta bayan gida wajen falt dina ta rika kwalamin kiran sannan na jita. Na fita naje na bude mata kofa haka na Rumgumeta ina murnan ganinta. Ranar Ramatu tamin yini ina ta korafin ba su kara nema na ba. Ramatu tace"Saboda menene zamu nemeki? Haka kurun ango na armaci mu takura masa" Kallonta kawai nayi na kasa bude baki na fad'a mata tun washegarin da suka kawoni wannan gidan ban kara ganin Assadiq ba ammh sai naji na kasa gayamata gaskiya. Har kuma tambaya ta yi ina ya ke? Nace mata ya fita ba da dadewa ba. Ta shiga ko'ina ta na min murna tunda muna da ruwa. Yini muka yi hira bayan na yi mana girki mun ci ina goye da Noor kamar ta barmin ita. Ashe Adda ta koma Shekaranjiya shine ba wanda ya neme ni ya sanar dani. Ramatu ke fad'amin matan gidanmu na son zuwa suna ta ma Inna talatu mgana. Da sauri nace"Don Allah su zo ina son ganin su." Ramatu ta yi dariya ba ta yi mgana nasan zata ce saboda kad'aici ne ba dadi. Da wayarta na samu na kira Adda Fati ina rokonta da Allah tazo tace ba yanzu ba sai nace to ta turomin Habiba ta zo min da kayan miya bani da shi jin haka yasa tace sai gobe zata zo in ta dawo daga makaranta. Sai mangariba Ramatu ta tafi kuma ni na rakata har bakin titi na ga anguwan sosai ba wasu yalwar jama'a sosai sai da ta samu adaidaitan sannan na dawo gida. Washegari gari wajajen la'asar sai ga Habiba da Hanif sun kawomin kayan miya mai yawa. Da sun so tafiya da wuri na rike su sai shidda na barsu suka tafi. Yanzu neman mutane na ke yi ido a Rufe ban samu ba. Sai da ranar da na cika Sati da wuri Adda Rukkaya ta zo min yini ba ta jima da zuwa ba sai ga Inna talatu da matan gidammu. Duk da gulma ya kawosu haka na rika washe bakinsu ganinsu naga jama'a. Ba inda ba su leka ba sannan ba su ga wani alaman wahala ko damuwa tare dani ba sai mamaki suke yi. Sai dai sun ta tambayana ina angon? Ana so aji labari ni kuma naki ba su wani dama da zasu fahimci wannan karon abubuwan sun sha Bambam. Sai yammah suka tafi Adda Rukayya ta riga su tafiya saboda mijinta. Ta kawomin kalolin maggi da su korin kamshin girki. Ta tambayeni ba matsala nace mata ba wata matsala. Nasan suma a firgice suke ba sa son su kara jin wani abu kuma ya faru. Ni kuma ba na so na tada musu  hankali ai da na fad'u musu wannan karon ba irin na sauran ba ne. Har na kwana goma ban kara saka Assadiq a idona ba duk sai na damu. In har ya sakeni ne gwara ya fad'amin da wannan zaman da na ke yi ba wani a tare da ni. Sai kuma daga baya na fara Tunanin ko wani abu ya faru da shi ne bansani ba? Ina cikin wannan firgicin ne da yammah naji ana buga gida. Da sauri na saka Hijabi na fita jikina na rawa na Dauka ASSADIQ ne ashe ba shi ba ne. Saboda rudewa ko tambayan waye ban yi ba na bude get. Sai kawai na ci karo da wata mata yar babba haka. Tamin mirmishi na yi mata ni na fara gaisheta ta amsa cikin sakewa kafin tace"Mun kawo kaya ne" Cikin mamaki na kalleta ban samu zarafin mgana ba tace"Yarmu ce zata zauna a d'aya daga cikin flat din gidan" Ina jin haka kamar an min bushara da gidan Aljannah Da sauri na bata hanya ina fad'in"Sannun da zuwa." Shigowa ta yi ni kuma na leka ina ganin motar kaya cike da kayan su kujeru da gado sannan na Rufe get din. Matar na da fara'a ita ta gayamin ita ta fara yin gaba da motar kayan sauran matan suna hanya a daidaita za su zo yanzu ma surukin na su take jira ya kariso ya bata makulin dakin tare da yaran da zasu taimaka a kwashe kaya.. Jin haka yasa na ce ta shigo dakina ta yi tamin godiya kuwa. Na kaita har dakina ta zauna na bata ruwa. Na zo na zauna ta na min hira irin matan ne masu shigen surutu. Daga zuwanta har sunan Amaryan ta fad'amin Fatima ana ce mata Ummi. Har ta kayan dakin da aka siya mata sai da ta lissafa min. Sannan ta gayamin ita kanwar babanta ce a saudiya ta ke zaune tazo ne. Ni ban tambayeta ba ammh har ta fesamin Ummi ta gama Digree d'inta anan Abu zaria. Koyarwa ta ke yi a wata makarantan Secondary a sabon gari. Surukin na su kuma ma'aikacin gwammati ne a nan zariya. Cikin jiran awa dayan da tayi ne fa duk ta sauke min wannan labarin. Ni ko ina zaune ina jinta Eh a'a sai ko mirmishi. gidan haya mai tara jama'a da Mutane kala kala. *Janafty* *TMWB2K005* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan. Sai da Surukin na su yazo da yaran da zasu kwashe kayan zuwa cikin gida sannan ta min sallama ta fito daga dakina ni dai ban fito ba. Ammh naji ba jimawa sauran tawagan da tace suna hanya suma suka iso, na leka ta window na gansu Rurututu kamar a nan ake yinin biki kusan zazzagawa akwai kara. Duk ina cikin daki naji an fara shigowa da kayan dakin cikin gida ba gulma ba na mike na saka gwiyoyina saman kujera ina leken su. Kaya ne na alfarma ma su kyau burin kowacce macen da ta isa har aka kira mangariba ba su gama shigo da kayan nan ba shiyasa na koma daki na Dauro alwala na yi sallah. Ina kan darduma naji ana kwankwasamin kofa na tashi da hijabin jikina na fita na bude sai naga wannan matar da ta ce min sunanta Zainab. Washe baki ta yi kamar yadda nima na washe mata sannu da gida ta min kafin tace in ba damuwa na san musu butoci suna so su yi sallah. Ganin suna da yawa yasa na dauko musu botiki karami na zubo musu a ruwa aciki na bata buta guda biyu ta na min godiya. Chan kuma sai gata ta dawo min da botikina da butocina ta kara cewa na san mu su ruwan sha. Kitchen na shiga na samu katon jug dina na zuba ruwaan tunda nima shi na ke sha ba ni da pure water duk da akwai dubu biyun da ya bar mun ammh yaron ma da zan aika babban aiki ne. Na cika musu shi na had'a musu da kofunansa guda hud'u na kawo mata ta karb'a ta na fad'in sun gode. Cikin yanayina nace"Ku yi hakuri ba ni da pure water" Sai ta yi dariya kafin tace"Bakomai kin ji" Har ta juya ina shirin Rufe kofata ta juyo ta na fadin"Nace ki fito mana ki zo ki ga yanayin jeren namu kinsan ku ne yaran zamani sai mu gama kokarin mu ku ce bamu yi daidai ba." Kamar tasan nagaji da zama ni kada'i da Sauri na fito ina amsa mata da toh. Akwai key din kofar ta baya shi na cire na Rufe kofar na bi bayanta sai min hira ta ke yi. Muna shiga sauran matan suka bi mu da kallo ni kuma na gaishe su suka amsa cikin sakewa itace naji ta na musu bayanin anan gidan na ke. Gani mai hankali Ummi zataji dadin zama dani. Ina jinsu suna ta min godiyan ruwa, falon ga kaya nan zube ina ga ciki ne kanfintocin ke had'a gadon wata mata na gani ta na salla a kasa acikin raina sai naji ban kyauta ba meyasa ban basu Darduma ba? Gefe na koma na tsaya ina kallon abubuwan da su ke yi, ban san me ya tsaidani ba ammh naji gwara na zauna cikin mutane da na koma daki ni kad'ai kamar wata mayya. Gani na tsaye yasa matar nan tajani kitchen wai nazo na rika nuna musu yadda zasu jera kayan kitchen d'in, aiko zuwa na ya yi amfani da sun mata barna duk sun fara yaaga mata wasu kwalayen kayan sai da nace musu su bar su a kwalayensu in ba haka ba in ta jima ba ta yi amfani da shi ba za su lalace. Muna kitchen din suna ta aiki nima ina taya su babu bambamcin da Falt dina komai iri daya ne har girman ni da ya ke ba ni da wasu kaya yasa dakin nawa bai cika ba ammh ita ko da ta ke da kaya da yawa waje ya cika Damkam. Har sun gama gyara ciki sun fito falo bamu sani ba, sai da wani cikin samarin nan ma su kwashe kaya ya shigo ya na fad'in"Wacece Hasiya a nan? Mu muna kitchen shiyasa ba mu ji ba su kuma ba su dauka ni ce Hasiyan ba sai suka ce ba Hasiya anan wajen. Sai da ya fita ya kara dawowa yace matar dakin nan dake kusa da nan ake tambaya mijinta na jiranta. Muna cikin aiki wata yar matashiya ta leko ta na kiran sunana. Cikin mamaki na juya ina amswa da Sauri tace"Au daman ke ce Hasiyan? Sai na gyad'a mata kai. Da sauri tace"To ki je ga mijin ki chan ya dawo ya na jiran ki." Sai naji abun wani barambarakwai namiji da suna Hajara. Idanuwana na zuba mata har ta fice daga kitchen sai naji kamar ban ji daidai ba. Hajiya Zainab ce tace"To maza mana kije kada ya gaji da jira ransa ya baci." Jiki na a sanyaye na yi mata dariya na wuce suka bi ni da kallo. Ban dauka da gaske ba ne sai da na fita na ganshi tsaye a kofar dakina ya jingina da kofar, sanye ya ke cikin kananun kaya riga da wando. Hannunsa daya akwai Ledan d'ayan kuma ya tusa cikin Aljuhun wandonsa. Hasken gen din kusa damu ya haske Fuskarsa domin ni dai inaga tunda nazo gidan nan sai cikin dare suke bamu wuta kila ta lalace ne ko suna gyara. Kafafuwana kamar baza su daukeni ba haka nake takawa zuwa gareshi. Tunda na fito yasan nice saboda yanayin jikina da ya gani. Idanuwansa na kaina har na kariso gabansa cikin sanyin muryata nace"Sannu da zuwa." Bai amsani ba illah cigaba da kallon Fuskata da ya yi cikin d'an hasken da ke wajen. Ni kuma na sadda kaina kasa ina faman tura hannuna cikin Hijabin jikina. Ajiyar rai ya sauke ganin ina Lafiya domin har ga Allah tunda ya tafi baya cikin natsuwarsa. In ya ce zai zo ya dubani Tahir ya hanashi ya fara fad'in hakan ba shi cikin Tsarin su ba shi kuma Tsoro ya ke ji kada wani abu ya samu yar mutane ba shi da ta cewa. In kuma yace Tahir din yazo su je sai yace bazai je ba shima kuma ba inda zai je. Yau din ma Tahir din bai sani ba ya Sulale ya taho saboda ya gaza samun cikakiyar natsuwa. Numfashi ya sauke kafin yace"A tsaye zamu gaisa? Jin haka yasa da sauri na fito da hannu na mai dauke da key din dakin ya matsa baya na bude dakin hannuna na rawa. Ni ce a gaba sannan ya bi yo bayana dakin da Dubu ban kunna Fitila ba. Shi ya kunna hasken wayarsa sannan na samu damar ganin fitilan saman kujera na karisa na kunna haske ya cika Dakin dayake tunda na Fahimci basa barin wuta da rana sai na ke sokata a chaji kafin na kwanta zuwa Safe ta cika da Chaji. Bai jira ni na zauna ba ya samu waje ya na kallona Lokaci daya ya na fad'in"Zauna mana." Ba musu na zauna kujeran da ke yamma da shi. Ledan hannunsa ya sauke a gabansa kafin yace"Kina lafiya ko? Sai na kasa amsa masa da baki kai kawai na gyad'a masa. Cikin natsuwarsa yace"Kin tabbata? Sai na dago ina kallonsa kafin na yi mirmishin yake ban yi mgana. Shi kuma sai ya yi tsam saboda Sai yaga kamar wani kallo na yi masa na irin baka kyautamin ba. Baya so ma ya na kallona Tausayi na ke ba shi mganar gaskiya. Shuru na wani lokaci kafin yace"Naga mutane a gidan ne sosai." Cikin muryata nace"Eh wacce zata tare a dakin chan suka kawo kayan daki" Jinjina kai ya yi kafin yace"Good akallah zaki samu yar'uwan zama" Sai na gyad'a masa kai alamun hakane. Daganan muka yi shuru har na tsawon mintina goma ba wanda ya kara mgana. Wayarsa ya duba yaga kafin ya Dago ya na fadin"Lokacin sallar isha'i ya yi zan tafi ina so na tsaya a masallaci na yi sallah." Da idanuwana da suka cika da Ruwa na kallesa kafin na samu zarafin magana ya mike tsaye ya na fadin"Ba abunda ki ke da bukata in zan dawo sai na taho miki da shi? Sai na samu kaina da fad'in"Bakomai." Kudi ya ciro cikin Aljihunsa yazo har gabana ya ijiyemin tare da ledan nan ya na fad'in"Ki rike a hannun ki kin ji ko? Bansa ta ina raunin ya nuna kansa ba sai ji nayi hawaye na bin fuskata. Shima hawayen ya gani ya sa ya dakata da mgana jikinsa a matukar sanyaye yace"Hasiya Lafiya? Me ya faru? Da sauri na saka hannu na share hawaaye na kafin na kira sunansa. "ASSADIQ.." Yadda na kira sunan shi cikin karyewan Sauti ne yasa sai da ya samu kanshi da dukawa a gabana ya na kallon cikin kwayan idanuwana yace"Menene? Ko baki da lafiya ne? Kai na girgiza masa kafin nace"Yau ma tafiya zaka yi ka bar ni? Sadiq yaji kamar an kwarara masa ruwan sanyi saboda yadda jikinsa ya yi wani sanyi kalau. Hucin zafi ya fitar daga bakin shi kafin yace"Hasiya ba na gayamiki yanayin aikin nawa ba? Nan ya yi min nisa da wajen aikina ne sannan muna yawan tafiye tafiye ne ni da ubangidana." So na ke ya kalleni ne ammh ya kasa kallona cikin idanuwana kansa na kallon kasa ne kwata kwata ya ki yarda ya had'a ido da ni. Ganin haka yasa na kasa bud'e baki na yi mgana saboda ba ni da abun cewa. Shi kuma nauyin jiki yasa ya kasa tashi ji ya ke yi kamar bai kyauta ba yana ji kamar wannan tsarin na shi ba tsari ba ne mai kyau. Hakkin Hasiya na kanshi in ya aikata mata ba daidai ba Allah zai tambayeshi. Bazai iya bude baki ya gayamata cewa auran su ba kamar yadda ta zata ba ne ya kasa yi ma Amma gaddama ne yasa ya karb'i auranta bazai iya gayamata cewa kafin ya gama Hidimar kasarsa nan da wata shidda sakinta zai yi ba. Da sauri ya mike sai da ya juya mata baya yace"Ki yi hakuri zan rika zuwa ina dubaki Lokaci bayan Lokaci. Kuma ma ba ga shi kin samu abokiyar zama ba? Bayansa na bi da kallo kafin nace"Hakane." Jin na amsa shi yasa ya juyo ya na Fadin"Zan tafi. Ki kula da kanki in ban zo gobe ba jibi zan zo in sha Allahu." Da toh na amsa masa ya fara tafiya ya na fadin"Taho ki kulle kofar.". Ba musu na mike rike da kudin da ya ijiyemin a saman jikina har zuwa bakin kofa ya na fita ya juyo ya na kallona ni kuma ina rike da kofa kamar zan yi kuka. Ganin haka yasa ya Rausayar da kai ya na fadin"Babu fa wani abu ki rika addu'a in zaki kwanta sannan ki rika Rufe kofarki kada ki bude ma wanda baki sani ba ok? Jinjina masa kai na yi shi kuma sai ya zura hannayensa cikin Aljihun sa gabadaya kafin yace"Sai da Safe." Nima na bi shi a sanyaye da Sai da Safe. Har ya juya ya fara tafiya ina Tsaye bansan Lokacin da na kira sunan shi ba"ASSADIQ.." Da Sauri ya juyo ya na kallona cikin mamaki. Dawowa ya yi kofar dakin ya na fadin"Menene? Kaina na kasa nace"Na koma wajen su? Cikin mamaki yace"Wajen su wa? Da hannu na nuna masa dakin da ke gefena da mu ke jin hayaniya. Bi na ya yi da kallo cikin nazarina kafin yace"A'a ki zauna a dakin ki kin ji ko? Saboda ya na tsoron kada naje su gane yanayi na su tambayane ni nw fad'amusu mijina baya kwana a gidan tunda muka tare. Duk da rai na bai so ba ammh sai na Hakura tunda yace a'a bai tafi ba sai da yasakani na koma ciki na Rufe kofa sannan ya fita daga gidan ya na sauke numfashi. Karfi da yaji halayensa na so su gurbace Sanadin haduwarsa da Hasiya ya fara karya da kumbibiya ya fara kokarin zama munafukin Namiji. Ni ko ina kulle kofata ciki na shige na Dauro alwala na yi sallar isha'i sama sama nayi addu'a sannan na fito falo na duba ledar da yazo da shi tsireni mai uban yawa da yaji kuli da albasa da kokumba sai kyalli ya ke yi ga shi da zafi inaga da zai taho ya tsaya a siya. Sai kuma Lemun fanta da maltina masu sanyi suma. Miyau na har ya na tsinkewa ko samun daman Dauko Filet ban yi ba na zauna na fara ci sai da naji cikina ba waje daman ban yi girki da rana ba Taliya dawake na dafa da Dadddren jiya ita na Dumama da Safe da ta ragu ne na ci da Rana. Na rage kusan rabi na kulle shi a ledan na kai kitchen na boye ban sha ruwa ba Maltina nan na shanye duka na yi gyatsa na koma na jingina da kujera ina maida numfsshi. A bun ka ga wanda ya ci ya koshi sai naji na fara jin barci sama sama sai na tashi na haye saman kujera na kwanta ba jimawa sai barci. Bansan na jima ina barci ba sai da naji bugun kofata kamar a sama na tashi a firgice kuma a tsorace. Tashi na yi naje na bud'e sai naga Hajiya zainab matar nan masu danki. Ashe sallama za su min sun gama zasu tafi sannan ta dawo min da jug dina da Kofina. Na karb'a cikin murya barci muka yi sallama da juna har ta na cewa a gaida megidan rashin sani bata san ni kad'ai ce acikin dakin ba. Maida kofata na yi na kulle saboda barcin da ke idona nan falo na ijiye jug din na shige ciki na kwanta ko kayan Jikina ban cire ba. Washegari ma ban tashi da wuri ba, barci na sha sosai sai wajen goma na tashi, ban dafa komai ba Sauran tsiren nan na du'mama a tukunya na ci na sha Lemu fanta duk da ina da Ulcer ma naji ina Sha'awan lemum shiyasa na sha. Da rana kuma Macaroni na Dafa jalop guda daya, naci ni kadai a gida sai da yammah wasu matan suka kara zuwa sun kawo wani kaya ba su jima ba dai suka tafi. Kuma har dakina suka shigo muka gaisa na ba su ruwa suna ta min godiyan Dawainiya. Wata mata acikin su ta kalleni ta na Fad'in"Ai ba ma zata wuce sa'an Ummi ba." Ta gefenta tace"Nima haka nace acikin raina." Su naji suna hiran su na ko a baya an daga bikin ne suna ta fad'in ba ga shi har Lokaci ya yi ba satin nan ne bikin da Daurin aure. Acikin raina murna na ke yi kamar wacce za'a kawo wata yar'uwata. Ko bakomai zaman kadaici bazai kasheni ni kad'ai ba. Assadiq yace gobe ko jibi zai dawo ammh Shuru bai dawo ba ni ko har ina ta tsammanin shi. Na fara tunanin meyasa bazai kwana anan ba? Hujjar da ya ba ni ba hujja bace mai karfi tunda muna gari daya ne ba wani gari ba ne zuwa wani gari ba. Indai ko hakane ya na da dalilinsa na yin haka, kila ko ya na gujema hakanan ne saboda Canfin da ke kaina. In dai ko zai cigaba da tsira da lafiyarsa gwara nesa nesa da kusa kusan nan da baya haifar da d'a mai ido. Tunanin haka yasa na cire abun a raina na rika zirga zirgata. ina kewar yan'uwa mussaman ma Amma ina so na kirata mu yi mgana na roketa ta yafemin domin na tabbata gatan da ta yi min ban da ita ba wanda zai iya yi min wannan gatan. ***** Sadiq kunyar kallon Hasiya ya ke yi shiyasa ya kasa komawa. Gefe d'aya Tahir na gayamsaa in ya cika zuwa za'a zo a samu matsala. Wanda samuwarta bazai haifar masa da d'a mai ido ba. Ya nuna ma Tahir ba wanda ya san shi anan ballatana yace ya na tsoron kada labari ya kai gusai. Shi kuma Tahir ba ma wannan ne Tunaninsa ba yasan tunda nan din babu wanda yasan daga ina suke abokan karatunsu d'ai d'ai ku ne yan zariya duk yan wasu jahohin ne. Gwara ma shi za'a iya sanin wanene shi ammh Sadiq tun farkonsa ba mai iya nuna kansa ko shi waye bane. In ba na kusa da shi ba balle ka Fahimci wanene shi ba. Shi Tsoron sa d'aya Kada Sadiq ya cigaba da shigema zabiyar yarinyar nan ta ribacesa ya fara sonta ko wani abu ya shiga tsakaninsu ta Bata masa Rayuwa. Domin shi har ga Allah ya aminta da Mganar mutane akan Hasiya ballatana da yaji daga bakin iyayenta da yan'uwanta. Ba rami fa ba abunda zai kawo mganar rami gwara dai tunda ya Riga ya kai kansa to a samu hanyar da zasu rabu lafiya shine kawai taimakon da zai iya yima Sadiq ya saka masa da Tarin alherinsa garesa. Shi kuma Sadiq a lokacin ya zama wani ga shi nan ne abunda ya aikata ba da sanin iyayenshi ba ya fara Damunshi shiyasa duk abunda Tahir sai ya kasa masa musu, duk da yana jin Tausayin Hasiya fargabansa kada ciwo ko wani abu ya sameta cikin Dare ba bu wani a kusa da ita gida ita kad'ai, fargabansa ta ragu ne ma da yaga dakin kusa da ita mutane za su shiga da Sauki sauki zata rika jin motsin mutane. Yanzu haka Dari dari ya ke da kiran Abba ko Umma sai yaji kamar suna kallonsa da abunda ya aikata batare da sanin su ba ko yarda ko kar ya yarda yaci Amanar iyayenshi da ya iya aikata babban al'amari batare da saninsu ba. Baisan me ya shiga kansa ba har ya amince da auran Hasiya ba sai dai komai ya faru sannan ya dawo hayyacinsa. Shiyasa ya rage kiransu a waya sai dai su su kirashi suma baya tsawaita mgana da su hakama Sauran Sisters dinsa kowa ya Fahimci yanzu Magajin gida ya sauya ya rage sakin jiki da su su sha hira ko a waya ammh sun masa uzuri Tunaninsa aiki ne ya yi masa yawa tunda ya kusa gama Hidimar kasar na shi.. Ya gama tsara yadda abubuwa za su cigaba da kasancewa gwara ya siyama Hasiya karamar wayar da zata kiran yan'uwanta ta na rage kewa kafin ya yi natsuwar da zai san irin taimakon da ya yi niyar yi mata na inganta Rayuwarta kafin su rabu. Sannan shima zai rage fargaban ko wani abu zai sameta zai rika kiranta yana jin lafiyanta. Sannan kuma in wani abu ya same ta ko ta na bukatar wani abu zata iya kiransa. Shi kad'ai ya yi wannan tunanin shiyasa bai aiwatar ba sai da ya tambayi Tahir shawara. Shi kuma sai yace shawaran tasa ta yi ya siya mata waya ammh sai ya gargadeta. Sadiq ya kallesa cikin mamaki kafin yace"Gargad'in me? Tahir ya gyara zama ya na fad'in"Kada ta fallasa sirin zaman ku ga yan'uwanta ko kawayenta. Saboda in sukaji zasu dora ayar tambaya akan motsinka da kuma Dalilin ka." Sadiq ya yi shuru kafin yace"Hakane to ta ya zan ce mata kada ta gayama kowa? Tahir yace"gayamata zaka yi kai tsaye." Sadiq ya yi shuru bai yi mgana ba ya na Tunani Tahir yace"Kada dai ka gayamata mganar rabuwar ku yanzu sai mun kusa komawa gida tukunnah Lokacin ka bata taimakon da kace kaga bazata damu ba sosai." Shi dai Sadiq bai amsa ma Tahir ba ammh kallonsa ya yi da mamaki yana jinsa ne kawai in yace wai bazata damu ba in suka rabu. Aure sunan shi aure ko ya ya yake kuwa kuma saki ba shi dad'i ko da a fatar baki ne kuwa. Da kansa yaje pizzet ya siya karamar waya Tecno dubu takwas tare da layi ya kuma yi mata Rigister bai kai mata ba sai da ya chaja mata ya saka mata lambarsa a wayar ya kuma yi saving da sunan da ta ke kiran shi ASSADIQ. Ranar asabar da daddare ya je ya kaimata da tare da Tahir za su zo sai kuma yace ya fasa sai in zai koma da Rana ido na ganin ido sai su tafi dare. Har Sadiq na zolayansa da cewa ya gane wayonsa girkin Amarya ya ke so yaje ya ci. Tahir ya sheke da Dariya kafin yace"girkin wata Amaryan?  Su Amarya sun ji jiki. Wannan yarinyar bazata dafa abinci na ci ba." Sadiq ya kallesa kai tsaye kafin yace"Tahir ba sunanta yarinya ba. Hasiya sunanta." Ya fad'a ya na hade rai Tahir ya kara sakin Dariya kafin yace"Angon karya na Hasiya. Angon gaskiya na Sultana." Ya na yi masa wannan shakiyancin ya fita ya barsa. Sai da ya tsaya a hanya ya samu jam'in sallar isha'i sannan ya karisa koda yaje ya iske gidan cike da yammata ga shi akwai wuta. Ya na ganin haka yace an kawo amaryan kusa da Dakin Hasiya kenan. Lokacin da yazo dakina ya na bude tunda wasu daga cikin yanmatan Amarya sun shisshigo dakina wasu nan ma suka yi sallah iyayen ana kawo Amaryan ba jimawa suka tafi. Hajiya zainab ce tace ma yan matan in suna Bukatar wani abu su yi min mgana. In ka ganni sai kace nima ina cikin yan bikin ne sabon materil dina na saka Doguwar riga bakina a washe saboda ganin mutane, Allah ya gani na saba zama cikin jama'a shiyasa na ke murna da wannan sha'anin. Bansan zai zo ba har wata na tambayana miji na ya na gari? Sai nace a'a ya yi tafiya ban jima da bata amsa ba suna kuma zaune afalo in da suka yi sallah ni kuma ina kitchen na Dora Taliya jalop ganin baki kada su ce ba na girki ina da Rowa. Ban ji sallamansa ba ballatana shigowarsa dakin ni dai fitowa falo na yi naga ba yanmatan nan sai shi ya na zaune ya na latsa wayarsa. Cikin mamakin ganinsa na yi masa sannu da zuwa ya amsa. Ruwa a jug naje na debo masa sai da na kawo sannan ya kalleni ya na fadin"wannan wani ruwa ne? Kai tsaye nace na nan gidan nan ne. Bude baki ya yi kamar zai yi mgana sai ya fasa ya tashi ya fita. Ba jimawa sai ga shi ya dawo da ledojin pure water wajen guda Biyar nazo zan karbesa ya matsa gefe ya na Fadin"Kaji min yarinya ke yaushe zaki iya? Jin haka yasa na matsa baya ya shiga kitchen ya sauke ruwan. Sai yaga ina girki ya fito ya na kallona Lokaci daya ya na fad'in"Girki ki ke yi? Da kai na amsa ban yi magana ba Mirmishi ya yi kafin yace"Ki ce yau zan ci girkin Amarya." Dariya na yi ina Rufe fuskata da Tafukan hannuna. Wuceni ya yi ya na fadin"Rufe kofa ki zo ki gani." Ban kawo Tunanin komai ba naje na Rufe kofa na dawo. Na gansa da kwalin waya kirana ya yi nazo gabansa na zauna ya mikamin kwalin ya na fad"in"Ga wayarki nan" Ido na zaro kafin nace"Eh..'" Dariya na bashi sai da Fararen Hakoransa suka bayyana Cikin kwarin gwiwa yace"Taki ce ni na siya miki." Sai gani kan kafafuna bakina kamar zai yage. Na warce kwalin wayan ina dubawa cikin murna nace"Ka siya min waya? Ni? Da kai ya amsamin kafin yace"Bud'e ki gani." Rawan jiki yasa na kasa budewa sai da ya karb'a ya bude min ya fiddomin wayar ya kunna min ita ya mikamin Bakina a washe na karb'a ina dubawa dai na kalleshi na koma kuma ina kallon wayar bakina ya kasa Rufuwa. Ya yi min abunda na ke so alokacin da nake tsananin bukatar waya. Na kallesa ya na min dariya ganin yadda na kasa Rufe bakina. Gira ya dagamin kafin yace"Kin samu ta kiran Amma da su Adda Fati. Zaman kadaicin ya kare ko? Idanuwana suka ciko da kwallah kawai sai na duka ina fadin"Nagode sosai Allah ya saka da alheri ya kuma kara budi." Ya amsa da Ameen lokaci daya ya na saka Hannu ya dagoni Tsaye ya na fadin"To baki latsa wayar ba." Ai ya na cewa haka na koma na zauna na fara latsa wayar ina shige shige. Gefena ya zauna ya na fadin"Kin iya sarrafa wayar ko? Cikin murna nace"Eh mana Abubakar ya taba siyamin irin ta kafin auran mu." Sai da na yi mgana na Tuna a gaban wa na ke. Idanuwana a sanyaye na dago ina kallonsa shima ni ya ke kallo. Ammh sai naga ya basar da mgana da fadin"Na saka miki lambata in kina bukatar wani abu ki kirani na saka miki kudi a wayar." Ya dakata kafin ya cigaba da fad'in"Sannan sai ki kira sauran yan'uwan ki ko? Da kai ma amsa masa na kasa Rufe bakina. Ya rasa ta inda zai faramin mganar ne yasa ya yi shuru ni kuma ta duba wayata ina murna kamar an sani a Aljannah. Kamar daga sama naji ya na fadin"Hasiya kin taba fad'a ma wani ba anan na ke kwana ba ne? Na girgiza masa kai Lokaci daya ina fadin"A'a." Ina ji ya sauke ajiyar rai kafin yace"Yauwa. Kada to ki sanar da kowa kin ji ko? Ko Amma ko sauran yan'uwan kin ji ko? Wannan sirrin auran mu ne" Sai da na yi masa mirmishi kafin nace"In sha Allahu ba wanda zai ji." Numfashi ya saki mai karfi na samun salama. Ina kallonsa nace"Na kira Adda Fati? Kai tsaye yace"Kira ta mana ki na da lambarta ne? Sai na gyada masa kai jiki na rawa da Hannuna na saka lambarta na kirata ta na dauka taji murya na tace su Asee asee an yi waya kenan nace mata eh. Hira muka sha na manta da shima afalon ballatana girkin da na dora sai da ya fara kauri ni ban ma ji ba shine yaji ya yi min mgana ina chan muna hira da Adda Saboda murna har Mijinta sai da nace ta bashi mu gaisa. Shi ya rigani isa kitchen din ya kashe gas din ya na fadin"girkin Amarya ya yi kauri" Kunya naji da yasa na kasa mgana. Sai da na sauke tukunyar na bude yaga uban abincin da na Dafa ya kama baki ya na fadin"Hasiya ina zaki kai wannan abincin? Kai tsaye na kallesa ina fadin"Bazaka ci ba? Kuma zan zuba ma yan kawo amarya har yanzu ba'a kawo musu abinci ba." Sai ya kasa musamin cikin yanayin mganarsa yace"To zubamin kad'an tafiya zan yi." Yau sai naji ban damu da tafiyarsa ba. A filet na saka masa da ruwa na kai masa falo. Kuma abun mamaki ya ci kadan ya rage ya sha ruwa ya mike yace min zai tafi sai ya kara zuwa. Ni kuma sai nace ya tsaya mu fita tare na mika musu abincin Shi ya Daukamin kulan abinci ni kuma na Dauki karamin baho inda na saka musu ruwa da filet da cokullaya. Har bakin kofar dakina. Shi ya karbi key din ya Rufemin dakin ya na fad'in"Kada fa ki zauna achan da kin kai musu ki dawo dakin ki " Da Toh na amsa masa. Naso ya bani kulan ammh yaki har sai da ya rakani har kofar dakin Ummi sannan ya mikamin na tare hannuna guda d'aya na karb'a da mukullin dakin nawa saura kadan robar hannuna ta fad'i ya yi saurin tallafewa ya na fadin"Kin gani ko? Daman nace bazaki iya ba." Wasu yan matan Amarya ya gani su biyu a kofar dakin suna kallon mu suna zaune. Cewa ya yi su zo su taimakamin bazan iya ba ni ko fadi na ke yi wlh zan iya. Cikin ido ya kalleni kafin yace"Bazaki iya ba SIYA.." Sai na kasa yi masa gardama dukkansu suka taso d'aya ta karbi kulan d'aya ta karbi Roban sai alokacin nagane wad'anda suka shigo dakina ne. Bai tsaya ba ya juya ya na fadin Sai da Safe. Nima na amsa masa da Sai da Safe. Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da Ciwan sanyi duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086 *Janafty* *TMWB2K006* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj *BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA DEE*! *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Gaban ayu*. *Hakkin daka gangariya*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. *Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* *Ana dafa GIMBIYAR KAZA da tattabarun garari*. Bayan ya  b'ace ma  ganin mu ne har ma ya bude get ya fita daga gidan. Budurwan da ke kusa da ni ta kalle ni ta na fad'in"Ba shi ne mijin ki ba? Cikin mamaki na kalleta sannan na gyad'a mata kai na alamun eh. Sai naga sun kalli juna da ta kusa da ita kafin ta kara kallona ta na fad'in"Oh na gane kina da abokiyar zama ne ko? Kura mata ido nayi cikin mamaki ina so na fahimci dalilin tambayan nata sai da ta ambaci abokiyar zama na Fahimci bakin zaren. Dan daure fuska na yi kafin nace"A'a me ki ka gani? Yanayin yadda nayi maganar ne yasa tace min bakomai. Ina gaba suna bayana har cikin Dakin Ummi sai da muka kwankwansa wata yarinya ta zo ta bud'e mana. Nasan kawai sun yi shuru ne ammh suna da tambayoyi fal acikin su. Ni kuma na datse su ne saboda nima bani da amsar tambayan na su in kuma suka matsa zasu san abunda bai kamata su sani ba. Sai a lokacin naga Ummi Amarya tunda har cikin bedroom din ta na shiga yan'uwanta da kawayenta suna ta min godiyan abinci da Dawaniya. Hakane din ne baza mu wuce sa'annin ba sai dai ganin farko da na yi mata na Fahimci ba kamar ni ta ke ba. Ita ta na da wayewa sosai da Bud'ewar ido sannan rayuwarmu da muka taso ba daya ba ne da ni da ita. Ban wani jima a dakinta ba na musu sallama na koma dakina saboda ina zumudin na koma daki na kira Ramatu da Sabuwar wayata tunda itama na Haddace lambarta. Ina ko komawa daki na dauko Sabuwar wayata raina fes na saka lambar Ramatu na kirata. Nayi murnan jin muryata sannan taji dad'in jin na samu wayar da za su rika samuna. Mun jima muna ta hira da ni da ita har gwarancin Noor nace ta sakamin ina so naji. Gajiya inaga tayi dare ya yi yasa ta fara Hamma ta na fadin"Ke wai mijin ki baya nan ne hala? Bansan me nace ba sai ji nayi bakina yace"Eh." Da mamaki Ramatu tace"Eh kuma? Ke kad'ai ne yanzu a wannan gidan Hasiya? Da sauri nagyara mgana ta da cewa"Ya na nan abokinsa ne yazo suka fita tare. Yanzu zai shigo." Sai Ramatu ta sauke Numfashi kafin tace"Oh na zata baya nan nace ko yaje kauyen su ne? Ni dai daganan ban kara mgana ba na samu muka yi sallama da ita. Ban hakura ba na kara kiran Addan Fati nace ta turomin Lambar Adda Rukayya da Adda ina so na yi mgana da Amma. Karamin Tsaki Adda Fati taja kafin tace"Baki da Hankali ko Hasiya? Kinsan karfe nawa ne yanzu? Sai da ta fad'a na duba agogon wayarta naga goma ta wuce. Jiki a sanyaye nace"Sai da Safe." Bata amsamin ba ta kwashe wayarta, sai na koma na lafe kan kujera ina cigaba da danna wayar tawa yau ban ji na wani damu ba. Sabuwar wayar ta Daukemin Hankali na sosai. Ina cikin Saving din lambar su Adda Fati na shiga cantact sai kawai naga Lamba da sunan ASSADIQ.! nayi jim ina kallon Lambar sai na samu kaina da murmusawa. Ranar na jima ban yi barci ba game na rika yi a wayar sai da idanuwana suka fara yaji na ijiye wayar na yi shirin kwanciya Washegari ma Ummi ni ta roka na saka musu ruwan zafi sannan na ara musu kofinan da suka sha tea nima ba kayan kitchen din gareni sosai ba abunda na ke da shi na ba su. Ranar kamar a gidan mu ne bikin Saboda duka Danginta nan suka zo da rana aka kara gyara daki. Nima ba laifi ban wani zauna adaki ba ina dakin Ummi ina ganin abunda suke yi da rana ma Hajiya zainab tace kada na Dafa abinci daga gidan su Ummi za'a kawo abinci. Lafiyayyar Jalop harda Nama suka Diba'rmin a kula mai yawa shi naci da rana har na ijiye na dare. Da yamma kafin kawayenta da sauran yan'uwa duk sun watse sauran ne da suka Rage ango ya kawo mota har da Ummi suka dauketa zuwa gidan Surukanta, ammh kafin su tafi sai da Hajiya zainab tace ga Ummi ne mu zauna lafiya da juna nace mata in sha Allahu. Ni dai ina ganin haka na shige daki na kulle na dauro alwala na yi sallar mangariba sannan na dauko wayata na kara kiran Adda Fati na kara mata Tuni lambobin da nace ta Turomin. Sai tace bari ta bama Habiba ta Turomin ba jimawa Sai ga lambar Adda da ta Adda Rukayya. Jikina na rawa na kwashe Lambar Adda na saka a cikin wayar ita na fara kira har sai da ta kusa katsewa sannan Adda ta dauka da sallamanta cikin Hausanta da ta had'e da Harshen Fullanci. Cikin Zumudi na kira sunanta da Adda. Bata gane ni ba sai da nace mata Hasiya ce sannan ta gane muryata. Cikin shakiyanci tace"Au Hasiya ce? Kin gama Fushi da uwar taki kenan kin kira? Sai na kasa mgana kunya ta kamani cikin sanyin murya nace"Ku yi hakuri Adda." Bata damu ba tace"Yar nema. Ga uwar taki tunda yanzu kin gane muhimmancinta." Nasan tana mikama Amma wayar ta fice daga d'akin ina jin muryan Amma ta na kiran sunana. "Hasiya." Sai kawai na sakar mata kuka ina Fad'in"Amma ki yafe min don Allah." Mirmishin nan nata ta yi min kafin tace"Baki yi min laifin komai ba Hasiya. Ban kuma rike ki a raina ba nasan komai daren dad'ewa watarana zaki kirani ki godemin." Ina sharen hawaye nace"Ki yi hakuri Amma." Amma tace"Nace kada ki damu bakomai yanzu dai ki fad'amin kina Lafiya? Ina Abubakar ina Fatan ba wata matsala ko? Cikin Sanyin jiki da na Murya nace"Lafiya kalau mu ke Amma." Ina jin Ajiyar zuciyar Amma kafin tace"Alhamdulillah daman ni na sani akwai wani lokaci da zai zo mutane su gane babu mai yi sai Allah." Ina gyad'a kaina kamar ta na ganina nace"Amma ki ga fa babu abunda ya samu Assadiq wannan wayar ma shi ya siyamin ita jiya." Amma na dariyan jin dadi tace"Daman ai ke baki isa ki yi ma wani mutum arziki ba, balle ki yi masa Talauci kuma ke baki isa ki sauya rayuwar wani ba Allah kad'ai ke da wannan ikon Hasiya." Da sauri nace"Hakane Amma." Amma Nasiha ta cigaba da yi min ta na kokarin nuna min komai ma da ya faru a baya ba ni bace daga Ubangiji ne kamar yadda ta ke kara gayamin yanzu. Na kasa bude baki na gayamata kalubalen wannan auran sai naji bazan iya wargaza mata wannan Farincikin nata ba sai na yi shuru da bakina na saki jikina muna ta Hira. Cikin Shagwaba nace"Amma na yi kewar ki yaushe zaki zo na gan ki? Amma ta yi dariya kafin tace"Hasiya ki zauna lafiya a gidan auran ki. Ina nan watarana ke da Abubakar zaku zo ku gaisheni in sha Allahu." Sai na kasa ce mata komai sai na basar da wannan mganar da fadin"Amma kina jin dad'in zaman chan? Amma tace"Alhamdulillah hankalina a kwance nasan ya'yana suna cikin Tabattaciyar rayuwar da na yi musu fata." Jin Amma na lafiya yasa sai naji na samu natsuwa mun jima muna Hira ina ta bata labarin gidan da na ke ciki jiya an kawo wata amarya zamu zauna mu biyu yanzu kafin sauran su tare. Amma ta ta yi min fad'an na kama kaina nasan dai kalubalen zama a gidan Haya ji na yi kamar ban ji ba na gani nayi kamar ban gani ba sai na zauna lafiya nace mata in sha Allahu. Sai da aka kira sallar isha'i sannan Amma tace zata yi sallah nima naje na yi sallah sai alokacin muka yi sallama. Ban samu na kira Adda Rukayya ba sai da Safe kuma bata Dauka ba. Sai chan da rana ta kira muka gaisa tamin murna jin nayi waya tace daman rashin wayar nan ba dadi gwara dai a rika jin mutum ya zauna Shuru ba waya a hannunsa. Ba mu cika had'uwa da Ummi ba tunda ta na ta cin Amarci sai dai ranar litini mun had'u da Safe ta fito Diban ruwa nima haka. Muka gaisa cikin sakewa sannan da Rana ta kawo min Cincin da su Dublan da yawa harda Alkaki. Ban taba ganin mijinta ba sanda ya ke fita ina dakina kuma sanda ya ke shigowa ma ba na waje ina cikin Dakina. Sai dai ina jinsu suna ta baki maza da mata mazan ina tunanin abokansa ne suka zo ganin Amarya da yammah haka ko da Daddare. Matan kuma kawayen Ummi ne da yan'uwanta masu zuwa ganin daki da Rana. Ba jimawa ta fara girki ranar ma ni na san mata kayan miya tunda na nika shi na tafasa shi ya ma kusa karewa, na gayamata ta saka a kawo mata daga gida nan ba'a samun kayan miya to ina ma d'an aiken? Ko almajirai ni dai ban taba gani ba ko suna shigowa anguwan basa zuwa gidanmu. Ni na rika damun Adda Fati da waya ina mata shagwaban bata kara zuwa Dubani ba sai ga shi ta zo ita da yaranta gabadaya da Habiba suka min yini ita tazo min da kayan miya mai yawa har na Diban ma Ummi tunda itama da aka kawomata kayan miya da kayan lambu ta dibar min har kofar daki na tazo ta bugamin na bud'e ta bani na karb'a ina mata Godiya. Sannan na rakasu su Adda Fati Dakinta suka gaisa ta tarbesu hannu bibbiyu ta ba su ruwa da lemu ta na basu hakuri cincin ya kare  naace kada ta damu na wajen nawa da ban cinye ba na basu sauran sun ci. Ko da yaushe na shiga dakin Ummi sai naji kamar nawa ne Saboda ya Tsaru sannan koda yaushe cikin kamshin Turaren wuta. Sannan Ummi akwai Daukan wanka da gayu ni dai ta na Burgeni sosai. Da zamu tafi ta bama Hanif da Hanifa Dari biyu ta kuma rakomu har barandar Dakinta. Da muka koma Dakina Adda ta yi ta yabon Hallayar Ummi ta na min Fad'an mu zauna lafiya da Amana. Shinkafa da miya na yi mana muka ci muka sha sai bayan la'asar suka yi shirin tafiya. Da Adda Fati tace ina Abubakar sai nayi mata karyan ya na wajen aikinsa. Sai dai wani abu daya ya bata mamaki ita da Habiba suka kwashe kayan akwatina suka jeramin acikin wadrope ammh ko abunda ba'a so ba su gani na Miji na ba. Da Adda ta tambayeni sai na rasa me zan ce mata sai karyan ya kai wanki ta fad'omin nace mata da Safe ya kwashe ya kai wanki. Adda Fati har ta na ce min me yasa ni bazan kwashe na wanke masa ba. Nace shi yace ma barshi zai rika kaiwa ana wanke masa. Araina ko nace ina na ganshi ma? Na dai wanke sauran kayana da suka yi datti Tunda ya siyamin sabulun wanka da na wanki tun washegarin ranar da na tare. Tunda ya zo ya kawomin wayar nan bai kara zuwa ba, kuma a Waya bai wuce sau biyu ya kirani ba. Shima muna gaisawa yaji lafiyata sai yace min baya nan sun yi tafiya ne ammh in ya dawo zai zo. Ya tambayeni ba ni da wata damuwa nace masa Eh! Tunda ga ranar bai kara kirana ba nima ban taba gigin kiransa ba na cigaba da Lallaba Rayuwata a yadda kaddara ta zab'wmin. Jin dad'ina da Tarewar Umma in muka gama aikinmu zata zo dakina ko naje dakinta mu sha Hira da ya ke ta na da Surutu shiyasa duk wani Labarin da ya Danganceta ta na fad'amin da na Mijinta sannan in muka yi girki muna zuba ma junan mu. Ban tab'a bata labarin Mijina ko yanayin Rayuwata ta baya ba. Abu d'aya na taba gayamata da ta taba cemin hala ni buzuwa ce? Nace mata a'a Amma bafullatana ce Babanmu kuma Bazazzagi ne. A lokacin Dariya ta yi ta na fadin"Shiyasa sunan ki ya zama Hasiya kenan? Daman sunan Fulani ne." Ni kuma sai nace mata"Ba sunan Fulani ba ne sunan kanwar babanmu mai rasuwa na ci Hasiya." Daganan kuma sai ranar kawai tazo dakina mu yi hira tace min"bata taba ganin mijina ba ko matafiyi ne? Sai na samu kaina da ce mata Eh Saboda bani da mafita bayan wannan bata san komai a kaina ba. Ummi ta iya girken girken zamani Sosai ni kuma na fi iya na gargajiya. Tunda na saka Adda Fati zuwanta ta kawomin garin Damwake tunda na yi Ummi taci tace mijinta na son Damwake zan koya mata. Nace mata me zai hana? Shikenan sai muka had'a kanmu ni da Ummi in ta na girki na kan shiga in gani sai dai ko in mijinta ya na nan in baya nan tare mu ke yi ni kuma daman mijina baya nan ta kan kai dare a dakina sai Mijinta mai suna Muhammadu ya dawo sannan ta ke min sallama ta koma Dakinta. Bani da wata damuwa Rayuwa daidai misali mai sauki ni ke gudanarwa. Muna waya da Amma kullum tunda kudin da ya sakamin a wayar sun kai Dubu uku har lokacin ba su kare ba. Ummi kuma ta na da Sati biyu tace min zata koma aiki Tunda ta na koyarwa duk sai naji ban ji dadi ba Tunda mun fara sabawa. Sai dai ba ni da yadda zan yi tunda Saboda ni bazata fasa zuwa aikinta ba. ****** *KADUNA.* _Area: Malali_ 8:35pm. Zaune ya ke a falon gidansa mai cike da kayan alatu na more Rayuwa. Wata takarda ne a hannunsa ya na Dubawa. sanye ya ke da Riga da wando farare rigar bata da Hannu kamar na shan iska ne acikin gida. Babban mutum ne domin zai iya kaiwa kimanin Shekaru Hamsin da Takwas zuwa da Tara a duniya. Alhaji Jibril kenan ma'aikaci ne a Hukumar Nepa ta jakar kaduna wanda ya fi shekaru ashirin yana aiki a wajen. D'aya daga cikin ya'yansa ce ta yi sallama a kofar falon na shi ya amsa mata Lokaci daya ya na bata izinin Shigowa. Wata gajeriyar matashiyar Budurwa ta shigo wankan tarwada ta na sanye da Doguwar riga baka ta yane jikinta da bakin mayafi Dauke da faranti da nug a saman ya na Tiririn zafin Ruwan lipton din da ke ciki. Gabanta ta karisa ta ja karamin Tebur kusa da shi ta Dora a saman wajen. Sannan ta duka ta na fadin"Barka da Hutawa Baba." Cikin mirmishi ya na kallonta ya amsa mata da cewa"Yauwa sannu da kokari Zahra'u yar Baba." Kanta na kasa ta murmusa shi kuma sai ya ijiye takardan Hannunsa ya sunkuya ya Dauki mug din ya dan kurba sau biyu, kafin ya sake Dagowa ya na kallonta cikin jin dadi yace"Allah ya yi miki albarka Zahra'u." Ta amsa da Ameen Ameen Baba. Mikewa ta yi zata fice bayan ta yi masa sallama saboda Tsarinsa in ya na cikin Falonsa ya na Hutawa baya bukatar ganin kowa ko da kuwa Uwar ta su ce. Zahra'u ce kad'ai ta kan shiga Saboda ita ke hada masa Tea din da ya kan sha in ya na Hutawa kafin ya shiga barci. Kiran sunanta ya yi da"Zahra'u." Ta amsa ta na juyowa da sauri yace"Mubarak ya shigo kuwa? Girgizamai kai ta yi kafin tace"A'a Baba ammh ina jin duk inda ya ke yanzu ya na hanyar gida." Kai ya jinjina kafin ya yi mata alama da Hannu da ta tafi shikenan. Har ta kule ma ganinsa ya na binta da kallo. Kiran wayarsa ya katse masa tunanin da ya so ya fad'a. Ya na ganin mai kiran jikinsa na rawa ya Dauka ya na faman washe baki. Sun jima suna mgana kafin su yi sallama ya sauke wayar ya na kurama zanen kwalliyar cafet din dakin kallo. Wani tunani daki daki na shiga kansa Ya fara kasuwancin Shigo da gwala gwalai tun shekaru biyar da suka gabata kuma ya tara abunda bai Tara ba Tun fara aikin gwammatin sa. Bai san Alhaji Sulaiman Shinkafi ba sai ta sanadin wani abokinsa Alhaji Sheshe shi kuma Alhaji Sheshe sun fito daga mahaifa d'aya ne da Alhaji Sulaiman Wato garin Shinkafi. Ya san ya na da sha'awar kasuwanci da zai rika kawo masa manyan kudad'e saboda ya raina matsayinsa a yanzu sai ko Alhaji Sheshe da ya kasance abokinsa ne shi ya had'a shi da Alhaji Sulaiman har ya Bude masa ido a kan kasuwancin Shigowa da gwala gwalai. Tsawon shekaru biyar din nan suna Huld'ar arziki, Bai taba haduwa da iyalan Alhaji Sulaiman ba shima bai taba had'uwa da na shi iyalan ba. Sai dai yasan wasu mutane Biyu masu matukar Muhimmamci a rayuwar Alhaji Sulaiman. "MAGAJIN GIDA.." "INNANI.* INNANI da ita ta kasance mahaifiyace ga Alhaji Sulaiman, Sun jima tare ya na jin sunan magajin gida bai taba kawo ransa wannan magajin gidan D'a ne ga Alhaji Sulaiman ba sai a shekaran da ta gabata yasan ashe d'ansa ne sannan shine kwara d'aya tal d'a Namiji da ya Haifa sannan gatan Duniya yaron nan ya na da shi. Komai fa in za su yi sai yaji sunan Magajin gida kamar ma Alhaji Sulaiman ba ya iya yanke wani abu kan Dukiyarsa ko kasuwancinsa sai da Izinin Magaji gida. Bai taba ganin yaron ba ammh yasan matsayinsa ya wuce ya zauna ya na faman wani lissafi. Innani kuma ya fahimci Umarninta ne Umarnin Alhaji Sulaiman ya na sonta kuma duk abunda tace ta na so shi ya ke so. Alhaji Jibiril ya gyara zamansa sannan ya dauki ruwan zafin da aka kawosa ya kurb'a sau biyu kafin ya ijiye. Shuru ya yi kafin kuma Lokaci d'aya ya saki dariya mai kayatarwa shi kad'ai.. Lokaci ya yi da zai kara bunkasa kasuwancina. Lokaci ya yi da zai kara kusancin da Alhaji Sulaimam. So ya ke ya fisa ido a kan wannan harkan kasuwanci so ya ke nan gaba kad'an ya shahara da kudi fiye da Alhaji Sulaiman. Alhaji Jibiri mutum ne mai son kudi fiye da komai a duniya sha zumamu me baya rabar ka sai ya tabbatar da in zai karu dakai in yasan bazai karu dakai ba  to bazai yarda ya had'a inuwa da kai ba ko yan'uwan shi ne in yaga bazai karu da kai ba baya doguwar huld'a da mutum. Ko da wanda suka fito ciki d'aya ne kuwa in yasan sai dai ka karu da shi to mu'amula ta zumunci sai in dai kai ne ka rike zumumcin ammh shi bazai damu da shi ba. Mutum ne mai son abun duniya da ya gwammace son kudi fiye da komai. Alhaji Jibirl ne mai Daraja kudi fiye da komai a Rayuwarsa. Kud'i ne mutumcinsa su ne kimarsa in baka da kudi baka da wani kima ko Daraja a idanuwansa. Saboda kudi kuwa zai iya aikata komai a rayuwarsa. Alhaji Jibirl baya son asaran kudi ko ta na naira biyar ce in kuma asaran ta fara ji ya ke yi kamar ya Mutu saboda hakan. Acikin gidansa macen aure d'ayace Hajiya Murjanatu da ya'yansa guda Biyar mata uku namji biyu. Mubarak ne Babba sai Fathiha sai Zahra'u sai Kamal sai karamar su Fatima suna kiranta Bintu. Mubarak ya gama karatunsa ya na aiki ne da Kamfanin Dangote da ke kaduna sai Fathiha ta yi aure a garin kano sai zahra'u da ke shekara ta biyu  a kaduna State university sai kamal da ke karatu a Buk kano ya na zaune gidan yar'uwansa Fathiha. Autansu kuma Bintu ta na SS1 ne yanzu saboda tsakaninsu da Kamal akwai tazara mai yawa. Ko acikin gidansa daga matarsa har ya'yansa susan babansu na Daraja kudi shiyasa suma suke tayashi Daraja shi komai na gidan nan ya na kan tsari ne komai na abun bukata a Farkon wata zai siya in kuma wani abu ya kare ba'a isa ya fito da wani kud'i ba sai wani sabon watan saboda ya riga ya gama Budget din wannan watan ko rashin lafiya ne kuwa sai dai yace Hajiya Murjanatu ta ranta masa in sabon wata ta shiga zai biyata. Shi komai na shi akan Tsari ne in kuma ya kuskure ma tsarinsa sai dai a nemi wata mafitar. Bazazzagi ne gaba da bayansa uwa da Uba aiki ne da Sauyin Rayuwa ya maida shi Dan kaduna. Saboda makonsa yasa matarsa Hajiya Murjanatu kama sana'an saida kayan yara kuma Alhamdulillah ta na samu domin da shi ta ke Rufamana kanta asiri da ya'yanta. Tunda ko sha'anin yan'uwanta in bata neman na kanta sai taji kunya shi kanshi Alhaji jibirl din bai yi ma na shi ba ballatana na ta. Ita yar anguwan kabala ce nan aka haifeta kuma anan ta girma auran Saurayi da Budurwa suka yi tsakaninta da Alhaji Jibril. Saboda son kud'insa yasa bazai iya zama da mace sama da d'aya ba baya son kashe kudi ba gaira ba Dalili shi kan shi Dalilin nasa mai karfi ne shima in ya fita cikin Budget sai da ya jira sabuwar wata ta shiga. Ya na kurban Ruwan zafi ya na mirmishi Saboda ya hango cigaba sasai a hasashensa. Wayarsa ya Dauka bayan ya sauke kofin hannunsa saman teburin gabansa. Kiran ya yi sannan ya saka a kunne bayan an dauka suka gaisa kamar ba a yanzu suka gama waya ba. Cikin sauke Murya yace"Alhaji yanzu na yi wani tunani. Me zai hana mu kara fad'ada Zumumcim mu ta hanyar sanin iyalan juna? Mgana ake masa ta d'ayan bangaran ya na ta mirmishi da annushuwa. Daidai Lokacin da wani matashi ya yi sallama ya shigo falon. Hannu ya daga masa alamun ya na waya a yadda Mubarak ya ga Baba na mgana cikin Dariya da Farinciki yasan cewa wata harkace ta karuwa in ba haka ba haka Kurum bazaka gansa ya na Farinciki da Dariya haka ba. ****** In yace Hasiya bata ransa ya yi karya, sai dai ya na boye tunanin hakane Saboda Tahir. Tunda ya siya mata waya ba shi da ikon zuwa ya ganta sai Tahir yace ba ga waya ba in da matsala zata kirasa. In ya dawo daga wajen aiki haka zai kwanta ya na ta Tunane tunane hakikanin gaskiya har rama sai da ya yi saboda zullumi Gida ya ke so yaje ammh kuma kunya baza su iya barinsa yaje a wannan Lokacin ba. In ya gan su zai kara shiga damuwa cin amanan da ya yi musu. Sun kusa gama Bautar kasar su ba za su wuce wattani uku nan gaba ba. akwai bukatar kowa ya yi ma kansa tsarin da zai taimakesa anan gaba. Yana da Burin ya koma gida in ma karatun zai cigaba da yi bazai kara yi a Zariya ba sai dai ya sauya muhalli kuma nan gaba. Sun taba mgana da Tahir akan me zai fara yi bayan sun gama Hidimar kasar  su? Kai tsaye Tahir yace masa gida zai koma ko saboda Hajja sannan yan'uwansa daman sun matsu ya dawo gida, zai koma yaga abunda zai fara sannan kuma Zai taba siyasar yankinsu. Ba haka kurum Tahir ya ke karantar Siyasa ba, yana son siyasa shiyasa kaf Shafukansa na sada zumumta shi ne bin yan siyasa ya na musu comment da like karatu ya Dauke masa Hnkali daga Fad'awa siyarsa. Kuma ya na da tabbacin in Tahir ya samu dama zai shiga siyasa tunda ya na da Ra'ayi. Da ya tambayeshi mganar cigaba da karatu fa? Sai Tahir yace ko zai cigaba sai ya kama wani abun a hannunsa sannan. Shi ko ya na da Burin cigaba da karatu in sha Allahu kuma ya na da Burin ya samu aikin da zai Dogara da kansa baya so ya zauna saboda mahaifinsa na da kudi. Shiyasa duk inda aiki na ma su  irin karatunsa suke ya kan duba wajen sosai kamfanin da yake bautar kasa ma sun ce zasu daukesa aiki ammh bai amsa su ba saboda ba shi da Burin kara zaman zariya. Ya na Tunanin in ma Mastars dinsa zai yi sai dai ya je BUK kano ya yi chan bazai kara zaman zariya ba. Kuma Bazai ji dad'in zama ba Tahir ba. Wata zuciyar tace ga Hasiya? Sai ya ba kanshi amsa da cewa Hasiya sakinta zai yi ta koma wajen mahaifiyarta shima ya tattara ina shi ina shi ya koma Gusai gaban iyayensa Sultana na chan na jiransa. Ko a waya da ya kira Hasiya Sau d'aya da bai kara kiranta ba ya na da Dalili baya so ya cigaba da kiranta har ta Fahimci ya yi mata karya gwara su tsaya nesa nesa da juna kamar yadda Tahir din yace. Kuma sannan kunya yake ji in ya ganta ga Tausayinta sannan da kuma jin nauyin kansa da ya zama makaryacin karfi da yaji gabadaya wata Rayuwa ya ke yi ba rayuwa irin ta Abubukar Sulaiman Shinkafi ba. Yanzu Rayuwa ya ke yi a matsayin Assadiq maraya wanda ba shi da komai kuma wanda yaci Amanar iyayensa da karya sannan wanda ya kasa kula da Hakkin matar da ke kansa. Cikin wannan satin Tahir ya tafi Daura an kirasa Hajja ba lafiya har ta kai ga asibiti ya so ya bisa su tafi tare sai daga wajen da ya ke bautar kasa suna da wani aiki yasa ya barsa ya tafi shi kadai akan in ya samu Sarari zai biyosa sai su dawo tare. Duk sai kadaici ya kamashi ya saba komai tare suke da Tahir. Shekarun nan kusan tare suke sai ko in ya koma gida Hutu. Kwanan Tahir d'aya da Tafiya ranar dakyar ya yi barci ya na ta faman juye juye. Sai yaji Tausayin Hasiya ashe haka ta ke fama da kadaici bai sani ba? Batare da Tunanin komai ba ranar ta biyu daga wajen aiki Gidan Hasiya ya wuce Direct da Niyar zuwa ya Duba lafiyarta har acikin zuciyarsa. Baisan Allah da na shi nufin ya ke sarrafa namu zuciyoyin ba. Sannan abunda ke rubuce a zanen kaddaranmu bamu isa mu kauce masa ba. 🌿 Ina manyan mata masu MATSALOLIN rashin Ni'ima Ina sabbabin aure Wanda basu juku yanda Mai gida zai sume ba😂Ina wayanda zasuyi sabbin aure Nazo muku da magani SAHIHI ingantaccen TSIMIN TABAJE🤌🏽🥰😍 hmm uwar gida, amarya, tsoffin aure kuna Ina ko kuntsaya tsilla tsilla tohm maza kuzo nazo kusiya TSIMIN TABAJE 💃💃😂hajiya ta tunda kukaji na yaba wannan magani toh tabbas yakai inda yakai yanada matukar kyau, Yana saurin saukar da niima baya illa domin andafashine da saiwoyin da kuka San suna maganin dakyau... Hajiya ta 🙈wlh Mai gida zaiyi Santi zakiji dadi Kuma zakuzo ku godemun domin yanasa Gurin yayi dumi ya Kuma ciko miki da gaba Gurin Kuma zaiyi dadi zoyzoyy😂🙈💃Kuma duk afarashi kalilan akwai gorina 1k akwai galan, akwai jarka ga duk meso, hmmm duk Wanda yasha Sai ya Gode mun domin nice na baku tabbaci 💃😂kunsan banida burin daya wuce Inga anasaka Mai gida farinciki 💃😂🥰Toh kuzo kusiya zakuji dadi insha Allah Kuma Sai kun dawo.... muka hada miki maganin TSIMIN TABAJE sha'awa zaki koma kamar marka..game bukatar TSIMIN TABAJE ya kiramu tawa innan numbobin kamar haka *Location* *Zaria and kaduna* *but nation wide delivery* *for more details 07062349732 or 08143450259* 💃💃💃 *Janafty* *TMWB2K007* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan. Yau Danwake na yi da yaji mai manja, Ummi ba ta nan ta na makaranta karfe biyu ake tashi na rana kafin ta kariso gida uku ta yi wani lokacin kuma gida ta kan biya sai bayan la'asar ta ke dawowa. Yaji na cika ma danwaken nawa da yasa bayan na ci na kasa ta shi sai faman shi! Shi! Na ke yi saboda harshena da bakina ya nad'e da yaji har cikin kaina. Ta ko'ina zufa ke ketomin gabadaya rigar material d'in da ke jikina ya jike da zufa idanuwana sun yi jajir harta Fuskata ta nuna alamun na sha wuya. Zaune na ke kasan tayels din falona filet din da naci danwaken na gabana na kasa Daukewa harta ledan da na sha ruwa nan na watsar da shi ga Roban yaji da yar roban da na zubo manjan bayan na soya. Saboda kwazzaba danwake bai wuce guda ashirin na jefa ba, sha'awansa naji ina yi shiyasa na yi kad'an saboda ba na so ya kai min dare. Kamar daga sama naji ana kwankwasamin kofa agogon wayata na Duba dake gefe na, naga biyu da wani abu na rana sai a raina nace kila Umma ce ta dawo tunda in dai ta dawo sai ta fara bugamin kofa na leko mun gaisa kafin ta bude dakinta ta shiga. Shiyasa batare da tunanin komai ba na mike ina faman shan yaji Saboda Rud'ewa ko dankwali ban saka ba Kitson Shukun da ke kaina tun wanda Adda Fati ta min ne ranar da suka zo da na saka Habiba ta tsifemin na biki. Shi ma wannan din ya tsufa ballatana Sumana na da Santsi kitso ba ya Dadewa sai ya fara warware kanshi. Kai tsaye batare da tunanin komai ba na bude kofar lokaci daya ina fad'in"Ummi yau kin..." Sauran kalamai na sun makale ne samakon ganin abunda ban taba zata ba. Yana tsaye a kofar dakin sanye da riga da wando baki da fari da jaket a saman kayansa sai kafarsa sanye da Rufaffen takalmi na bakin fata mai kyau Sannan bayansa goye da jaka kamar ta yan makaranta. Hannayensa sanye acikin Aljihunsa kyam ya na kallona, sai naji na tsargu na kasa magana sai na fara sosa kai da Hannu guda d'aya mai kyau. Wanda ya yi dama dama da manjan sai na maida shi baya. Kunyar duniya duk tabi ta lullubeni cikin sanyin jiki da na murya nace"Sannu da zuwa." Daga sama har kasa ya karemin kallo kafin ya dan saki fuska kad'an Cikin maganarsa yace"Yauwa in shigo? Sai na gyad'a masa kai ammh bansan cewa na tsaya kyam na bake kofar shigowa ba. Sai da ya kara kallona sannan yace"To ba ni hanya ko Hasiya? Sai da ya fad'i haka sannan na yi gefe da Sauri ina kif kifta ido kamar mara gaskiya Sai da ya shigo sannan na kulle kofar na bi bayansa Lokaci d'aya ya na fad'in"ke haka ki ke bude kofa batare da kinsan wa ke miki knooking ba? Ya fad'a daidai muna karisowa Tsakiyar falon. Na kasa mgana ganin ya na bin inda na tashi da kallo cikin mamaki ya juyo ya na kallona bai yi mgana ba sai ma ya samu d'aya daga cikin kujerun falon ya zauna lokaci d'aya ya na sauke Jakar hannunsa. Ajiyar zuciya ya sauke na alamun gajiya ni kuma ganinsa da jaka sai na yi tunanin kila daga tafiyar da suka yi yake. A gaggauce na duka ina kwashe kayan gabansa cikin jin kunya da nauyi. Da akwai sauran danwake a Filet din yaji ya yi min yawa yasa ban karisa cinyewa ba. Filet din yabi da kallo sanda na ke mikewa cikin yanayin mganarsa yace"Danwake ki ka yi? Kai na gyad'a masa ban yi mgana ba kai tsaye yace"Zan ci. Ammh bari na dan watsa ruwa tukunna." Ina so nace masa babu ya kare ammh na kasa mgana. Ya mike ya na fad'in"Akwai ruwa a cikin Tiolet din? Da rawan baki nace"Eh ammh ba ruwan zafi bari na saka maka." Bai jiyo ba ya na nufar hanyar Bedroom din yace"Zafi na ke ji ruwan sanyi is ok a wajena." Daga haka ya wuce ciki sai a lokacin na samu damar Sauke numfashi. Kitchen na Rumtuma kwanukan wanke wanke tun jiya ban wanke su ba su na fara wankewa sannan na Sake dora masa ruwan danwaken. Sai alokacin na taba kaina naji ashe ban da dankwali a kaina da gudu na sake dawowa falon na Dauki Dankwali na Daura, sai alokacin naga ashe manja duk ya zuba a saman tayels din ga shi da haske ya bayyana. Da gudu na koma kitchen na jika Tsumma da ruwa na dan barbard'a omo na goge wajen. Sannan na dawo na kwaba garin Danwaken na jefa masa cikin mintina sai ga shi na gama komai har na kara gyara kitchen d'in. Nasan ya na san manja ammh ban yi gaban kaina ba nace bari naji Ra'ayinsa. Ammh har alokacin yaji bai bar auna min Rad'adi a saman harshena ba. Sai ga shi mura ta kamani ina ta faman jan majina saboda azaban yaji. Ina fitowa na gansa a falo zaune da waata na'ura akan cinyarsa ya na Dubawa. Daga nesa da shi na Tsaya ina fad'in"Manja zan saka maka ko Mangyad'a? Kansa ya dago ya na kallona kafin yace"Kinsan Ra'ayina ko? Sakamin manja" Sai na juya na koma a karamar kula na saka masa Danwaken sai na dauko masa Filet da cokali da ruwa. Manjan ma dabam na sako masa sai Roban yajin duk na jera a gabansa. Ina durkushen nace"yaji kada ka cika ya na da fad'a" Batare da ya kalleni ba yace"I see. Ko daga yadda kika jigata nasan ya na da fad'a." Sai da ya fad'an na kara bin kaina da kallo sai na kara yarda ma kaina a jigace nake. Sad'af Sad'af kamar barauniya na mike na shige bedroom da sauri. Ba Kasafai na ke kara yin wanka bayan na yi da Safe ba ammh yau ta kamani dole sai na kara. Nima kamar shi da ruwan sanyi na yi wanka naji dadi har raina da naga da Soson wanka na ya yi amfani. Da na fito daga wankan ban ko shafa mai ba na bude wardrope na Dauko Atamfa riga da zani na saka na Daura Dankwali. Sai na kasa fita falo Saboda kunya na yi zamana aciki. Zanina da na ke wanka da shi na gani an shayamin saman kofar Tiolet na tashi na taba sai naji da Danshin Ruwa. Sai nasan da shi ya yi amfani kila ya goge jikinsa tunda nikam ban tsaya Daura wani zani ba na fad'a wanka. Gajiya na yi da zaman cikin na fito salau salau kamar kazar da kwai ya fashe mata acikin cikinta. Hankalinsa na kan Na'urar gabansa da ya ke ta dannata sai nima yaja Hankalina. Kasa na zauna a kujeran da ke fuskartsa ina kallonsa hannunsa baya gajiya Tab! Tab! Kana jin karan abunda ya ke dannawa. Sai naji ya Burgeni abu kamar aljani bansan ya juyo ya na kallona ba, saboda shagala da kallonsa ina mirmishi sai ji na yi kamar daga sama yace"Kwashe kaya nan na gama tun daz'u." Sai na yi kamar na Firgita kafin na shiga Raba ido ina Fad'in"Eh." Bai kara kallona ba yana cigaba da abunda ya ke yi yace"Eh nace ki kwashe su ki kai kitchen.". Da sauri na mike na fara Tattarawa na mike na zuwa kitchen sai da nashiga sannan na duba naga yaci Danwaken da yawa kadan ya rage. Sai na ijiye masa sauran ina Tunanin kila anjuma zai bukace shi. Abunda ya bata na ke wankewa naji bude get da Shigowar mutum. Sai chan naji muryan Ummi kamar ta na mgana a waya ne. Ban jira ta bugamin kofa ba ina gama wanke abunda ya bata na kifesu a kwando na fito zuwa kofar dakina. Sai alokacin ya bi ni da kallo tun ba ma Siraran kafafuna ba. Ya na mamakin yadda na ke da karfi da Kuzari ashe abun ba daganan take ba. Ina bude kofar na ci karo da Ummi ta na saka wayarta a jaka. Cikin washe baki muka tarbi juna na yi mata sannu da hanya muka gaisa sannan ta karisa dakinta ta bude ta shiga ni kuma na maida kofata na kulle na dawo cikin Falon. Diri diri na yi tunda ni dai ban saba da shi ba, sai na yi tunanin na koma ciki na kwanta zuwa la'asar kafin ya tafi. Na kama hanya kenan naji ya na fad'in"Kin yi kawa ne? Sai na juyo ina kallonsa kafin nace'"Amaryan da ta tare ni kwanakin baya Sunanta Ummi." Jinjina min kai kawai ya yi batare da ya kara mgana ba ni kuma sai na yi wuf na fad'a ciki. Ban cika barcin rana ba saboda ban saba ba. Gwara ma kwanaki kafin na samu waya na kan kwanta na rasa na yi na yi ta tunanin rayuwa har barci ya kwasheni bansani ba. To yau ma hakane ya faru kwanciyata ba Dadewa barci mai nauyi ya kwasheni. Barcin da har akayi la'asar bansani ba shi kuma ba ma'abocin yin salla agida ba ne fita ya yi ya nemi masallaci ya yi sallansa ya dawo ya cigaba da aikin da ya ke wani aiki ne aka ba su daga wajen aikin su. Baisan barci na ke yi ba ya dauka na yi salla ban fito ba ne saboda zamansa a falon shi kuma sai ya samu kansa da Sakewa sanin ina cikin Dakin. In da yana chan dakin ne bazai iya wannan aikin ba kadaici da kewa duk zata addabeshi ya kasa yin komai. Sai da yaji ana ta bugamin kofa ne kuma yaga ban fito ba sannan ya tashi ya leka cikin Bedroom din yaga ina ta barci hankalina kwance. Bai tasheni a lokacin ba jin ana ta buga kofar yasa ya juya ya fita yaje da kansa ya Bude. Ummi ce ta kawo min abinci ta na ganinsa duk da bata taba ganin mijina ba amnh tasan ba wanda zai shigar min daki a wannan Lokacin in ba Mijina ba. Da sauri ta gaisheshi ya amsa da Lafiya lau bai kuma saki fuska ba. Cikin sauri Ummi tace"Hasiya fa? Kai tsaye yace"Ta na barci." Ummi sai ta mika masa kulan Hannunta ganin yadda ya wani Daure Fuska ta na fad'in"Ok ga shi na ta ne." Ba musu ya saka hannu ya karb'a Lokaci daya ya na fadin"An gode." Daga haka bai jira cewarta ba ya maida kofar ya Rufe a saman Fuskar Ummi da ta rike baki ta na bin kofar da kallo. A ranta tace Mijin Hasiya ba shi da Fara'a daga haka ta wuce ta koma Dakinta itama ta maido kofarta Ta rufe. Kitchen din ya shiga da kansa ya ijiye mata kulan, sai kuma ya tsaya ya na Dube Dube sai ya fahimci ta na bukatar cefane tunda ga yan kayan miyan nan ma duk sun bushe da ta shanya a kasa kuma ma ba su da yawa sosai. Fitowa ya yi daga kitchen din ya na wani nazari hakkin sa ne cafane da komai da komai ammh kuma shi bai san yadda tsarin zai tafi daidai ba. Wasu abubuwan bai san su ba tunda shi bako ne a harkan. Har sai da ya zauna sannan ya tuna da cewa Bai tasheni ba. Sannan ya kara mikewa ya koma Bedroom din daga bakin kofar ya tsaya bai shiga ba ya na kiran sunana a Hankali. A cikin barci naji kamar ana kiran sunana ban tashi ba domin na Dauka ina cikin mafarki ne. Sai na juya har ina gyara kwanciya sai naji an ja kafata lokaci daya ana fad'in"Bazaki tashi ba? Sai alokacin na tabbatar da cewa ba mafarki ba ne. A sannu sannu na bude idanuwana sai ga shi fes a kansa ya na tsaye ya harde hannayensa saman kirjinsa ya na kallona, kara lumshe idanuwana na yi saboda har Lokacin barci ne acikin idanuwana. Ganin haka yasa ya kara ja min yatsan kafata ya na fadin"Tashi ki yi sallah mana." Kasa ta shi nayi sai naji gabadaya gabbaina sun saki sai na kara juyawa ina Umh.! Ammh na kasa ta shi batare da Tunanin komai ya saka hannunshi Guda d'aya ya Dago kaina sai gani zaune kan Duwawuna a saman gado ina raba ido cikin tsoro da mamaki. Kai tsaye ya kalleni ya na fadin"Kin yi sallah ne? Kai na girgiza masa ina sosa idanuwana alamun a'a. Bai kara mgana ba sai da ya juya zai fice sannan yace"Ki tashi ki yi salla" Kai tsaye kuma ya fice na bi shi da kallo na dad'e ina zaune kasala ta Rufeni kafin na rarrafa na sauko daga kan gado na fad'a Tiolet na dauro alwala sannan na zo na yi sallah. Bayan na idar sai na fara gyangyad'i saman Darduma har da jin jigina da jikin gado. Sai naji kamar Danwaken da naci ne duk ya bi ya kashemin jiki na kasa jin karfin jikina. Sai kuma wani barcin ya kara kwasheni bai dadi cike da mafarkin wai gani da Amma muna ta Hira. Shi kuma ya na falo aikin da ya ke ya Daukesa lokaci mai Tsawo kafin ya gama. Ya lekani ya ganni saman Darduma ina barci sai kawai ya yi mirmishi abunda yasa bai kara tadani ba ganina saman Darduma yasa yasan na yi sallah kuma shi a tunaninsa tsoro da kadaici baya barina barci shiyasa yau na ke ta yin na rana. Shiyasa bai tadani ba har aka kira sallar mangariba. Lokacin ya gama amfani da Laptop dinsa ya maidata jaka agogon Fatan dake hannunsa ya duba ya na auna Lokaci gwara yazo ya tafi kada dare ya yi masa ammh gobe zai Dawo Saboda ya yi min cefane abunda ba ni da shi. A toilet d'in dakina ya shiga ya Dauro alwala sai da ya fito sannan ya yi amfani da Ruwan hannunsa ya yarfamin a fuska da yasa Dole na mike zaune ina faman mutsakan ido. Cikin yanayin maganarsa yace"Kinga an kira sallar mangariba" Da sauri na waro ido cikin Muryan barci nace"Mangariba kuma? Na fad'a da Sigan tambaya. Mirmishi ya yi min yana maida agogon hannunsa Lokaci d'aya ya na fadin"Eh ki ta shi hakanan ki yi sallah kada ki koma barci ki bari sai kin yi sallar isha'i sai ki koma ki kwanta." Ban samu zarafin mgana ba naji yace"In na fita daga chan zan wuce sai gobe zan dawo" Har ya juya zai fice sai kuma ya juyo ya na fadin"Na manta ki rubuta abubuwan da ki ke so na cefane gobe zan zo kin ji ko? Kamar wata gaula haka na gyad'a masa kai. Sai ya fita daga dakin inaga yaji ni shuru ban biyosa ba me yasa ya kara lekowa ya ganni na zaune na kasa ta shi. Cikin mamaki yace"Ki zo ki rufe kofa zan tafi ne." Sai a lokacin na yunkura na mike jikina duk ya mutu, na bi bayansa salau salau. Har zuwa bakin kofa ya na rataye da Jakarsa ya fita sannan ya juyo ya na kallona inaga ya fahimci har lokacin barci bai sakeni ba ne yasa yace"kada fa ki koma ki kwanta baki yi sallah ba." Nace Toh ina Hamma, kai ya kad'a kafin yace"Sai da Safe." Nima cikin muryan barci nace"Sai da Safe." Sai da ya wuce sannan na maida kofata na kulle na dawo falo na zauna kan kujera ina faman lumshe ido. Sai da na bata lokaci a zaune kamar bazan ta shi ba sannan na tashi naje na Dauro alwala na zo na yi sallah. Kiran wayata ya fito da ni daga Daki zuwa Falo ina Dauko wayar naga shi ne ke kirana. Da Sauri na Dauka haka kurum sai naji gabana na fad'i. Kafin ma nayi mgana naji muryansa ya na fadin"Ina fatan kin yi salla ba barci ki ka koma ba? Sai da na amsa masa da kai sannan na Tuna baya gabana sai da na yi saurin cewa"Eh na yi." Shuru ya biyo baya kafin yace"Ki Rubuta duk abunda ki ke so kin ji ko? Sai na amsa masa da Toh. Yace sai da safe nima nace sai da Safe. To wayarce ta sa na watsartsake daga barci na fara game. Yau ko Amma ba mu yi mgana da ita ba, naa kira da Safe network bai sa na sameta ba. Bansan Ummi ta aikomin da abinci ba sai da na shiga kitchen na gani sai na samu tabbacin sanda ina barci ta kawomin shi kuma ya karb'a Dambun shinkafa ne da Zogale shi naci na sha ruwa na kwanta. Da safe da muka hadu a bakin Famfo bayan mun gaisa na mata godiyan abinci. Sai ta yi mirmishi kafin tace"Ashe megidanki ya dawo jiya? Da Eh kawai na amsa mata daganan sai na Datse maganar. Bani da takarda da Biro wajen Ummi na ara kafin ta fita na Rubuta masa abubuwan da na ke so na Cefane. Kayam miya me sai kayan lambu sai mangyad'a da ya kusa karewa sai kayan maggi su kenan na Rubuta masa. Sai flower saboda ina so na rika Dan sululu da wainar Fulawa. Ina da tabbacin zai zo tunda yace shiyasa ko kafin yazo na yi wanka na har da kwalliya na yi na saka Jan baki da Hoda da Kwalli. Sannan na Fesa Turare yau ma kamar jiya daga wajen aiki ya biyo ta nan ya iske na Dafa Shinkafa da wake da mai da yaji ammh shi sai na soya masa manja saboda yace min da shi ya ke so yaci. Ammh bai fara ci ba sai da ya yi wanka sannan ya zauna ya ci saboda Rana ta Daga yasa yace sai la'asar zai fita ina gani ya kwashe wayarsa ita kuma Na'urar yau na cikin Jaka bai Fito da ita ba A gajiye ya ke yasa a kan kujeran da ya ke zaune barci ya kwashe shi. Abun mamaki ana fara kiran sallar La'asar ya tashi. Takardan ya karb'a ya duba baice komai ba ya saka a aljihu ya fita zuwa masallaci. Bai gayamin dagachan zai wuce cefanen ba shiyasa da naji shuru sai nayi tunanin ko ya tafi ne? Ammh ya tafi kuma ya bar jakarsa a nan? Ashe cefane yaje ya yo sai ga shi da ledoji niki niki kuma kamar na sani ban rufe kofata ba. Dakyar ya bani Leda Biyu yace wai bani da karfi bazan iya ba. Ni ya na bani mamaki wai bazan iya ba? Kayam miya ne da kayan lambu sai abubuwan da nace. Sai kifi da Nama da ya siyo sai dankalin Turawa da na Hausa sai mangd'aya king na karamar Roba. Shi ya tayani muka jera komai a muhallimsa kifin da Naman yace na soyasu kada su lalace tunda bani da Fridge. Bansan bayason karnin kifi ba sai da naga bayan na wanke na fara Soyashi ya bar Falon ya koma bedroom dina har ya na Turo kofa. Sai da na shigo ya fara Toshe hanci ya na cemin na rufe kofar baya son karnin Kifi amai ya ke saka shi. Cikin mamaki nace"To kasan baka so meyasa ka siyo? Kai tsaye yace saboda ni baisan ko ina so ba. Sai naji raina ya yi wani haske jin haka yasa ina gama soya kifin daman naman na fara Soyawa na dake na goge kitchen din da omo har Falon ma na share na goge na kunna Turaren wuta na tsinke da na Rushi da Adda Rukkaya ta kawomin. Sannan Ummi ma ta dibar min nata yau bata dawo da wuri ba kila gida ta Biya. Ina so na yi wanka ammh ya na Dakin kuma in na shiga zai ji karni Saboda kayana da ni kaina ina karnin kifin ne. Sai kawai na fara greetin din kayan miya na Dora girki Shinkafa da Miya na Dora sai kuma na fara yanka kabeji da zan yi salat da tun tuni na iya shi a gidan Adda Fati. Ina kitchen din ya fito yace zai je masallaci. Ina jin haka na fito da Sauri sai dai ban zo kusa da shi ba daga kofar Kitchen din na Tsaya ina fadin"Ammh ba dagachan zaka wuce ba ko? Kai tsaye yace"Dagachan zan wuce me ya faru ne? Sai na samu kaina da marairacewa ina fadin"Don Allah ka dawo kaci abinci." Shuru ya yi kamar mai nazari ganin haka yasa na kara sauke murya ina fadin"Kaji ASSADIQ. Don Allah na ce in ka ci sai ka tafi." Kallona ya yi cikin ido kafin yace"Bazaki dauki Lokaci ba ko? Da Sauri nace masa In sha Allahu. Kad'a kai ya yi kafin yace"Ok." Sai da na tabbatar da ya fita sannan na Daka Tsalle. Sauri sauri na tsane shinkafar sannan na had'a miyar naje na yi wanka. Ina cikin salla ya dawo sai da na Idar sannan na saka kaya ko mai ban Tsaya shafawa ba. Ina fitowa daga ciki yace"ke nake jira kada dare ya yi na rasa abun hawa. Sannan garin kamar da Hadari." Ni kuma kai tsaye nace masa"Da wuya fa ayi ruwa kasan farkon damina." Bai ce min komai ba na shiga kitchen daman bayan na fito wanka na zo na Duba miyan naga ta yi sai na kashe gas din Daman tuni na wanke salat dina had'a masa na yi miyan daman nama na saka masa saboda yace baya son kifi ni kuma bazan saka masa abunda baya so ba. Ban dauka ba zai ci abincin da yawa ba sai naga kuma yaci ba laifi da ya tambayani ni bai ga na zubo nawa ba? Sai na ce masa ba yanzu zan ciba sai anjima. Ruwan gora na Dauko masa Tunda ya siyomin da lemun Fanta kanta d'aya kowanne. Kamar wasa sai iskan Hadari ya taso yana jin haka ya mike yace zai tafi sai me? Ba sai ga Ruwa ma su karfi ba dole ya dakata da Tafiya tun ya na zaton ruwa zai Dauke har ya Sare. Sallar isha'i ma shi ya jamu jam'i Saboda Ruwa bai samu fita ba. Kamar ranar da farko ni yace na kwana aciki shi kuma zai kwanta afalo. Sai nace masa akwai sanyi shi kuma yace kada na damu. Ammh ban barshi haka ba sai da na Dauko masa zanin gadona nace ya yi Rufa da shi. Ummi ma ruwa ya taresu ita da Mijinta ni dai har na kwanta banji dawowarsu ba. Kwana aka yi ana ruwa har asuba ana ta yafyaf na alamun ruwa. Shiyasa Sallar asuba ma shi ya kara jamana Jam'i. Samakon wekeend ne yasa bai yi Tunanin zuwa wani waje ba Bayan mun karya da Safe tunda shinkafar jiya yace na Dumama masa ita zai ci nima ita naci. Gani na yi ya na ta juya wuyansa kamar yana masa ciwo yasa nace ya shiga ciki ya kwanta ya mike Zuwa anjuma. Bai yi gaddama ba ammh yace sai ya yi wanka saboda sanyin gari yasa na saka masa ruwan zafi ya yi wanka sannan ya koma ya kwanta. Ni daman tun safe na yi wankana, abun da ya ke bani mamaki in dai yazo gidan nan to kashe wayarsa ya ke yi baya kunnawa ballatana ma akirasa. Kuma ya sha barci sai azahar ya tashi ya yi alwala ya tafi masallaci Ummi kuma da na fita har dakinta na kwankwansa naji shuru sai nayi Tunanin a gida ta kwana Saboda Ruwa sannan ga dare. Na dauka zai ce zai tafi da yammah ammh sai naji malamin ka shuru. Ina dafama abinci kuma yaci sosai sai da mangariba ne ya fita sallah yace min sai an yi sallar isha'i zai dawo. To har wajen tara bai Dawo ba sai chan ga shi ya Dawo da wata karamar jaka ashe kayansa ne aciki ya Dauko. Tunda ba shi da wanda zai sauya na jikinsa sun yi datti ba shi da wasu. Aiko ya na cire kayan washegari da Safe na wanke masa su tas na shanya. Bai ma gani ba sai da suka bushe na kwaso ina ninke masa. Fad'a ya yi min da wai hannuna da ba kwari ne zan iya wanki. Dariya na yi har sai da na rike ciki ina mamakin in ya na Tunanin Saboda yanayin jikina ya ke min kallon mara karfi. Wasa wasa tun ina saka ran Assadiq zai ce min zai tafi har na saki jikina. Daganan ya ke tafiya wajen aikinsa ya kuma dawo, an ce mutum rahma ne sai na fi walwala saboda zamansa tareni da ni shi kanshi kusan hakane baisan ya akayi kawai yaga ya na ta kwaso kayanshi zuwa gidana ba. Tundaga ranar bai kara komawa Samaru ba sai dai za shi wajen aiki. Sati daya cur muka kwashe tare kwanaki bakwai masu muhummamci matuka a wajena. ko da ba Daki daya mu ke kwana ba Assadiq ya na da kirkin sannan ya na da kyakyawan mu'amala. Ko aiki na ke yi ya na tayani sannan ya na nan ruwa dakina ya kare yaga na fara Dibowa daga waje ya faramin Fad'a wai na Dauki Almajiri mana nace masa ba Almajirai a barayin sosai. Shi da kanshi ya Tube ya cikamin ko'ina ranar ma ina wanki yace na kawo zai tayani da na hanashi yaki hanuwa sai nace ya yi min Dauraya da Shanya. Atsakar gida muka yi wannan Diraman da shi Ummi bata nan ta na makaranta, shi kuma ya shanyamin su tas sai nace mu had'a da kayansa mu wanke sannan ya amince. Ina mamakin yadda kowani aiki ya iya shi sai da na tambayesa ya yi min mirmishi kafin yace"Ni fa Tashin kauye ne sannan goyan kakane ba kuma goyen Sangarta ba." Har nake ce masa yaushe zai kaini na gaishe da Kaka.? Kai Tsaye yace ba yanzu ba ammh zamu je watarana. Ina lura da shi ko waya zai yi sai dai ya kunna wayarsa ya fice daga gidan sai ya gama wayarsa ya ke dawowa. Ban taba tambayansa ba sannan ban taba saka masa ido kan wasu al'umran da bai sakani aciki ba. A tunanina ko fita ya ke yi ya na mgana da Uban gidansa kila baya so yasan yana wajena. Har acikin raina ban kawo tunanin komai ba. Sadiq bai san Tahir ya Dawo ba sai ranar da ya cika sati a gidan Hasiya da yammah ya na kwance saman kujera ni kuma ina kitchen ina Kokarin yi ma na abincin Dare. Wayarsa tun safe ta na kashe babban wayar kuma ta na chan samaru ya barota. yaana kashe wayar ne saboda itace wayarsa da kowa ya san shi da ita akwai matsala in ya na barinta a kunne a kusa da Hasiya. Ya kunna ne zai kira Tahir saboda Shekaranjiya sun yi mgana ya tambayeshi yaushe zai dawo? Yace masa bai saka rana ba duk da Jikin Hajjan da Sauki har an sallamo su sun dawo gida. Tahir da yajisa shuru ya tambayesa sai ya yi masa karyan daga wajen da ya ke bautar kasa ne bai samu Sarari ba. Ya na kokarin kiran Tahir din sai ga wayar Tahir ya shigo. Hanyar Kitchen ya kallah kafin da Sauri ya tashi ya shiga ciki ya Daga wayan Ko sallamansa Tahir bai amsa ba yace"Kai dilla kana ina ne? Na dawo tun dazu ban ganka ba." Sai Sadiq yaji gabansa ya fad'i da Sauri yace"Arm eh ina wajen aiki ne gani nan zuwa." Tahir yace"Naga kuma bakwa kaiwa yammah? Sadiq yace"Ina hanya gani nan zuwa." Daga haka ya katse kiran. Sai yaji zufa na ketomasa kamar Abba ne ya kira shi. Bai tsaya ba ya fito daga Dakin Dole ya tafi yanzu bayaso Tahir ya Fahimci ga inda ya ke duk tsawon kwanakin nan. Bai ma yi tunanin Tsayawa Dibar kaya ba ballatana takalmansa da ke gidana Jakarsa kawai ya Dauka sai kuma ya yi mantuwa laptop dinsa kan kujera bai sakata aciki ba. Ina kitchen ya leko ya na cemin zai tafi yanzu. Cikin mamaki na mike ina fadin"Tafiya kuma? Yanzu? Ya na duba agogon hannunsa yace"Wannan megidan nawa ne ya kirani tafiyar gaggawace ta same mu. Zan kira ki a waya ki kula da kanki." Daga haka ya wuce lokaci d'aya yana cemin nazo na kulle kofa. Sai da ya fita ne na dawo naga Na'urarsa saman kujera kuma ya riga ya tafi, ni kaina duk jikina ya yi sauki Daman ban riga na Dora girkin ba ina gyara kayan miya ne. Sai na barshi na koma kawai na zauna na yi Tagumi. Shi ko Sadiq ya na zuwa ya yi ma Tahir karyan sun tsaya wani abu ne. Shi kuma Tahir bai kawo wani Tunani a ranshi ba. Hirar Hajja suka dinga yi da ciwonta har suka kwanta sai washegari ne ya Fahimci ya baro Na'uransa a gidan Hasiya. Kuma sai da Tahir ya lura ba bu ita da ya tambayi Sadiq sai yace a wajen aiki ya barota. Sannan suna saka takalman junan su Tahir ya Fahimci ba wasu takalman Sadiq. Cikin mamaki ya tambayesa. Wannan karon Sadiq sai da ya kusa ba da kanshi kafin karyan ya kai folish ya fad'o masa. Ammh duk da haka sai da Tahir ya so ya gane wani abu. *LAME NIG!* *KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*. *AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*. *KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA* *KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?* *KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?* *TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*. *BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.* *TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*. *KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*. *ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU* *Janafty* *TMWB2K008* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* *LAME NIG!* *KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*. *AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*. *KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA* *KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?* *KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?* *TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*. *BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.* *TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*. *KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*. *ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU* https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj *GUSAU.* Asabar, 10:50am. Yau asabar din karshen mako ne. Gidan Alhaji Sulaiman Shinkafi kamar yau d'in sun ta shi da Hidima ne sosai saboda za su yi baki daga Jahar kaduna. Abokin kasuwancin Abba ne zai zo tare da iyalansa gabadaya. Shima a gidan Alhaji Sulaiman su Umma sun yi ma yaran na su waya, suma duk za su zo wad'anda ke cikin garin kenan na nesa kuma ban da su. Tun safe Umma da Mama ke kitchen a shaahen Umma suna ta dorawa suna Saukewa, tare da taimakon ya'yan su Salima da siyama sai Sultana. Abinci kala kala su ka yi musu sai kuma lemuka kayan Snkas kuma Anty Surayya tace zata zo da shi. Anty Sa'in kuma tace zata yo pepe Chicken ta zo da shi. Ita kuma Sajida tace za ta yi Dambun Nama itama ta zo da shi. Tun misalin karfe takwas da wani abu na Safe Abba yace bakin sun taso suna kan hanya. Shiyasa suka fara aikin da wuri kada Bakin su iso kuma ba su gama ba. Bayan sun gama girkin daman Tuwon Shinkafa ne miyar agushi suka yi musu sai Farar shinkafa da miyar Naman rago. Sai jallof d'in Couscous da ta ji hanta da kayan lambu. Sai lemun kankana, sai kunin gyada da Kunin aya. Da farko Abba yace bakin a shashen Umma za'a sauke su ita kuma Umma taga ga bangaran Innani bai kamata a sauki baki a na ta Shiyar ba. Sai tace a kai komai bangaran Innani a jera a nan bakin za su sauka. Abba bai ce komai ba Mama ce ma taso ta yi mgana sai kuma ta fasa. Siyama da Sultana ne ma su kai abincin zuwa Shashen Innani da daman Tun safe Sultana ta gyara Bangaran sai tashin kamshin Turare ya ke na daki. Innani na zaune a kasan cafet a cikin Falonta sai faman kankaran Rake ta ke yi da wata karamar wuka, ta na sawa a baki tana mamula da hakoranta na roba. Ta ci uban Dauri ta Rufe kanta Ruf har kunnuwanta ga gilashinta da ya cika rabin Fuskarta. Atamfarta mai kyau ce super ce mai tsada, dinkin Riga da zani na su na Tsoffi. Ta na jin sanda suka shigo ta dago ta na kallon su ba'a a falon suka jera komai ba ciki suka shiga da shi. Innani ta gaji da shige da ficen su ta dago ta na kallonsu cikin takaici kafin tace"Nace lafiya ku kuma ku ke ta min Faman sintiri a shashena da Uban Safiyan nan? Siyama ce tace"Kai Innani Abinci fa muke shigowa da shi." Innani ta ce"Abinci kuma? Na waye? Siyama na Tura baki tace"Na baki ne." Innani tace"Bak'i kuma? In ji uban wa ya ce a kawo abinci nan? Sultana ce da ke bakin kofa tace"Innani Umma tace mu kawo nan." Sai Innani ta yi shuru kafin tace"Oho na zata kinibibin Suwaiba ne. Bakin sun iso ne? Sulatana ce ta tsaya ba ta amsa ba Siyama ficewa ta yi ta na kunkuni. Innani ta rakata da fad'in"Uwarki kika yi ma kunkuni ja'ira." Ita dai Sultana ta fice ta bar Innani na ta masifa ta na faman cewa Sulaimanu ya auro dangin Jaraba sun zo suna neman hanata zaman lafiya ita da gidan d'anta. Daman in dai wad'anan kalaman ne kusan duk wamda ke gidan nan ya Haddacesu daga bakin Innani. Kowacce bangaransu ta wuce domin su yi wanka su shirya. Salima daman ita suka bari zata gyara kitchen din Umma. Masu aikin su daman basa zuwa Weekend saboda suna gida sai ranakun Litini zuwa jumma'a da basa gida. Abba kuma ya fita ammh yace zai Dawo ba jimawa zai yi ba. Ko kafin sha biyun rana ta yi kowa ya shirya Umma wani less dinta ta saka mai Tsada dinkin Doguwar riga ita kuma Mama sai ta saka Shadda ita mai Dinkin Doguwar riga. Siyama kuma da Sultana shigar Maryam Epytian Abaya su ka yi.https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V kuma duka iri d'aya suka saka kalan pick ma su kyau da Tsari sun kuma yane kansu da mayafin Abaya. Ita kuma Salima daman iyayen iyayine wani material ta saka Dinkin Riga da sikat ne sun mata kyau sosai kamar wata black American Kuma daman Salima ta na da kyau sosai suna kuma D'iban kama daman da Sadiq. Zuwa kuma lokacin su Surayya duk sun iso suma tare da ya'yan su suma sun yi shigar alfarma kana ganinsu kasan ya'yam manya ne sannan kuma suna auran manyan mutane ma su Rufin asiri. Gabadayansu Bangaran Innani suka yada Zango tunda nan bakin za su fara sauka, Innani sai washe baki ta ke yi ballatana kowacce da yar ledanta na Innani ka na bata zata fara washe baki ta na zuba mu su albarka sannan har taja ya'yanka a jikinta. In kuma baka zo ka bata komai ba ta Dinga Hararanka kenan, in kaci sa'a ka tafi salin alim ba'a bika da gori ba. Sadiya Kaza guda ta soya ma Innani suyan da ta ke so, Innani ta saka mata albarka kamar me. Sa'ima Miya ta yi mata mai Naman sa, Sai ga Innani na fad'in ya'yan Suwaiba duka ya'yan albarka ne ya'yan mutumci. Siyama ta kalleta ta na mamaki, Dazu da Safe ta gama cewa ya'yan Suwaiba ya'yan Jaraba ne ammh shine Saboda abun duniya har ta sauya mganarta. Ai Innani in dai kana son Siye bakinta to toshe shi da abun duniya shikenan sai ka samu lafiya. Sha biyu da rabi da wani abu baki suka iso tare da Abba suka iso daman sanda Alhaji Jibril ya kirasa ya fito daga inda yaje zuwa gida shine kawai yace Direba ya tsaya a hanya su taho tare da su zai fi da kwatance. Suna shigowa Haraban gidan Abba ya kira wayar Umma yace su fito su tarbi baki ga su nan a haraban gida. Umma ta shaida ma Mama da Sauram yaran suka Dumguma gabadaya. Har da Innani da ta mike ta na Faman Dogara sandarta. Salima ta kalleta lokaci d'aya ta na fad'in"Innani ke kuma ina zaki je kina tafiya Dakyar? Innani ta kalleta kafin tace"Gidan uwarki zani. Ka ji min yarinya mara kunya? Ina ce baki nan na Sulaimanu ne ba bakin Suwaiba ba ko? Umma ce ta katse fad'an Innani da Riko Sandarta ta na Fadin"Kyaleta Innani muje ke ya kamata Daman ki Fara musu maraba." Innani na jin haka sai ta washe baki ta na fad'in"Yauwa salamatu yar albarka." Sauran gaba su ka yi Mama daman ta na jin Innani ta fara ambaton sunanta ta bata rai ta na Hararan Salima domin tasan ita ta ja mata zagi wajen Innani da daman bata taba fari a wajen wannan Tsohuwar ba. Umma ce ta tsaya ta na taimaka ma Innani suka fito tare. Duk suna Haraban gidan Abba ne sun Sarke Hannu da Alhaji Jibril suna gaisawa kowanne fuskarsa cikin Annuri da Farimciki. Dukkansu kuma suna Sanye da Manyan riguna kamar wad'anda za su je wani waje Daurin aure. Su Mama kuma Hajiya Murjanatu suka nufa cikin Sakin fuska suna yi mata maraba da zuwa. Siyama ne da Sultana suka tarbi su Fathihatu da Zahra'u Salima kuma na gefe ta na faman Danna wayarta sai dai ta na wani kare ma mutane kallo cikin irin takun ta. Mubarak na gefe shima ganin ba shi da aboki namiji a wajen. Sanye yake cikin shigar shadda Fara dinkin zamani kafarsa cikin bakin Takalmi na Fata mai kyau. Kansa kuma cikin Hula kube kalan aikin shaddar jikinsa mai baki baki. Muryan Innani ne ta karad'e wajen da Muryanta sanda suke karisowa ita da Umma. Cikin muryanta na Tsufa tace"To gani na iso ina shi abokin Sulaimanun ina so na ganshi da idona." Jin haka yasa aka bata Hanya Abba ya kalli Alhaji Jibril ya na yar Dariya yace"Ga mahaifiyata da na ke yawan baka Labarinta." Innani ga Alhaji Jibril abokin kasuwancina ne shekaru biyar da suka gabata." Innani ta washe baki ta na Fad'in"Ma sha Allah sannu Jibrulu sannu kaji? Ai sulaimanu akwai kirki ga mutumci da son jan mutane ajiki sannun ku da zuwa Allah ya yi muku albarka." Alhaji jibril cikin Ladabi ya ke amsawa da Ameen Ameem kafin ya Zube a kasa ya na gaida Innani. Ita kuma sai amsawa ta ke yi cikin waahe baki taji dad'in ganin yadda ya bata girma. Alhaji jibril ya gabatar da iyalansa ga Abba shima Abba ya gabatar da na shi iyalan a wajen Alhaji Jibril. Sai faman saka albarka ya ke yi Alhaji Jibril ya Dafa kafad'ar Mubarak da ke gefensa cikin mirmishi yace"Ga babban yaro na Mubarak." Abba ya ba ma Mubarak hannu suka yi musaba yana tambayansa karatu yace ai ya gama yanzu aiki ya ke yi. Innani ce taga ana ta tsayuwa ga shi ta gaji sai ta yamutsa fuska kafin tace"Wai nikam a tsaye zamu yi zumuncin? Haba ni na gaji tunda ba Dije soja sunana ba." Gabadaya sai da aka yi Dariya Alhaji Jibril da sauri ya rike Sandar Hannun Innani ya na fad'in"Mu je Innani na yi miki jagora." Innani ta washe baki ta na fadin"Allah ya yi albarka kaji Allah ya raya zuru'a." Ya na ta amswa da Ameen Ameen. Umma da Mama suna tare da Hajiya Murjanatu su ke bin bayan su Abba zuwa Bangaran Innani. Su Surayya kuma suna tare da Fathihatu wacce ke Dauke da Danta karami namiji sai Siyama da su Sultana da ke tare da Zahra da Fatima Batul. Kamal kuma daman ya na tare da Babansa ne. Salima ce ke baya ta na tafe ta na taku d'aya bayan d'aya wayace a hannunta hankalinta ma baya kan in da take takawa. Har sai da ta kusa cin Tuntube ta fad'i Mubarak da ke bayanta kamar ya na kirga takunta ya yi gaggawan tareta ta hannun hagu shi ya taimaketa daga Fad'uwa. Ido cikin ido suka kalli juna kafin Salima ta yi saurin janyen kallonta Daga gareshi ta na fad'in"Thanks." Kai ya gyad'a mata batare da ya yi mgana ba. Sai dai ya nuna mata hanya da hannunsa ta fara yin gaba sannan shi yabi bayanta. Ya na tafe ya na kallonta ya na mirmishi daga ganinta a ransa yace ta na da aji da isa. Afalon Innani a ka yada Zango Abba da Alhaji Jibril duk suna zaune a kasan Cafet ne gaban innani haka su Umma da Sauran yaran Salima ce ta zauna kan kujera ta na mai Dora kafa d'aya kan d'aya. Hankalinta na kan wayar hannunta. Gaisawa aka sake yi cikin mutumtata juna. Da kuma tambayan Hanya da Mutanen gida. Ruwa Umma ta ce su siyama su fara kawowa tare da Lemu saboda su fara sha su jika makoshi. Siyama da Sultana suka rika wannan Zirga zirgan salima na zaune bata ta shi ba, daman ita yar iyayi ce bata son aiki sosai sai ya zama Dole. Mubarak na gefe ya na kallon Salima ammh cikin takun da ba ta sani ba Haka kurum ya ke jin yarinyar zata yi daidai da Zabinsa sannan da Ra'ayinsa. Sultana ta kawo masa Ruwa mai sanyi har gabansa ya karb'a ya na fad'in"Thanks." Mirmishi ta yi masa shima sai ya maida mata da martanin mirmishin nata. Bayan sun sha ruwa sun natsa Abba ya duba agogon hannunsa yaa na fad'in Lolacin sallah ya yi su fara gabatar sallah tukunnah. Umma ta ja Hajiya Murjanatu bangaranta suka yi sallah bayan Abba da Alhaji jibril tare da Mubarak da kamal sun fita zuwa masallaci. Siyama da Sultana su ka ja Zahara'u da Fatima batul duk da ba sa'ar su ba ce sai dai salima in ma bata girme mata ba ammh halin Salima sai ita shiyasa suka ja Zahra'un a jiki, a nan Shashen Innani suka yi na su sallar. Su Anty surayya kuma suna bangaran Mama tare da Fathihatu. Sai da Su Abba suka dawo daga masallaci sannan aka zauna zaman cin abinci. Sultana da Siyama har da Salima suka Shimfid'a babbar Darduma a tsakiyar Falon Innani aka jera komai a samanta Sannan suka zagayeta kamar cin abincin Larabawa. Innani ce kusa da Abba da Alhaji Jibril sai Mubarak da kamal sai Umma da Mama da Hajiya Murjanatu. Sai su Anty surayya sannan su Siyama ne a karshe. Salima ce chan kusa da Innani ta Hannun Hagu, suna kuma Facing din juna ita da Mubarak duk sanda kuma ta Dago kanta sai sun had'a ido. Shiyasa sai ta kasa sakewa ta ci abinci sosai Sarver ur self ne kowa da kanshi ya sama ma kansa abunda ya ke so Innani ce Alhaji Jbiril ya zuba mata ta na ta saka masa albarka. Ba innani kad'ai ba batta su Abba sun ji dadin ganin irin yadda Alhaji Jibril ke kula da Innani tun zuwan su. Abba ya kallesa ya na fadin"Nagode Alhaji Jibril." Sai kawai ya kad'a kai kafin yace"Haba bakomai mahaifiyata ta rasu da jimawa ina kallon Innani kamar uwa ce a wajena." Sai Abba ya jinjina kai cikin kara ganin kirki da Dattakon Alhaji Jibril. Suna cin abinci sama sama suna d'an Taba Hira har suka gama. Wannan karon manyan suka kwashe koma zuwa bangaran Umma. Suka kuma ja Fathihatu tare da su, Siyama da Sultana suka gyara wajen sannan suka ce Zahra'u ta zo su tafi, sai suka koma Shashen Mama suka zauna. Salima kuma Dakinsu ta shige abunta bata ko zauna  a falon ba, inda su Siyama ke zaune suna taba hira ba. Mubarak kad'ai aka bari da su Abba afalon sai su Umma da ke chan gefe suna ta hira da Hajiya Murjanatu. Innani gyangad'i ta fara ta na zaune sai Alhaji Jibril yace ko zata shiga ciki ne ta kwanta. Innani na jin haka sai tace bakomai ba barci take yi ba kuma da gasken barci take ji ammh kada ta tashi a yi wata mgana bata sani ba ne. Kamar ko ta sani taji Alhaji Jibril na Tambayan Abba cewa bai ga Abubakar sadiq ba ko baya nan ne? Kafin ma Abba ya ba da amsa Innani ta yi zaraf tace"Magajin gida ai ya na chan wani gari ne ma Salamatu? Ta fad'a ta na kallon Umma wacce sai alokacin ma taji mganar. Cikin alamun tambaya tace"Waye Innani? Innani tace"Wai magajin gida ya ke tamnbaya nace ya ma wani gari ne? Umma ta yi mirmishi kafin tace"Ya na chan Zariya ya na Hidimar kasa Innani." Innani ta washe baki ta na fadin"An yi ko haka ya na chan zariya abun shi gidan sai ya yi ba dad'i da bayanan ka san shi ai na Innani ne in dai yana gidan ne to bai da wata uwa da ta wuceni nan ne wajen zamansa barci kawai ke kaisa bangaransa." Alhaji Jibril yace"Allah Sarki." A ransa ya na mamaki kamar Alhaji Sulaiman ace dansa ma ba'a waje ya yi karatu ba? Kuma wai ya na zariya ya na Hidimar kasa sai abun ya yi masa wani iri. Sai dai bai yi mgana ba kamar an tambayi innani ta tsinke da labarin cewa Magajin gida zai auri Sultana an kusa bikin ma. Abba ya kalleta cikin mamaki ba Halin ya yi mgana. Alhaji Jibril kuma da mamaki ya kalli Abba na neman karin bayani. Sai Abba ya gyara zama ya na fad'in"Sultana diyar kanwata ce da ta rasu nan ta ke wajena ita ce mu ke so mu had'a auran su da Magajin gida in sha Allahu." Alhaji Jibril ya had'iye wani miyau mai daci ya kasa mgana ita ko Innani fad'i take yi wata yarinya nan mai kokari da suke ta kai da kawo ita da yar uwar ta? Wata mara kaurin jiki doguwa haka ita adole sai Alhaji Jibril ya ganeta. Sai ya yi mata yake ya na fadin"Ma sha Allah wannan tunani ne mai kyau Alhaji Allah yasa muna raye." Innani da karfi tace"In sha Allahu ma muna raye za'ayi auran magajin gida da Sulsana." Alhaji Jibril ya Dukar da kai ya kasa mgana Umma ce ta juya ta na ma Hajiya Murjanatu bayanin had'in Auran Sultana da Magajin gida da ke chan zariya ya na Hidimar kasa ammh ya kusa gamawa ya Dawo gida. Abba kuma ya na ta ma Alhaji Jibril magana sau yaga kamar ya d'an Shiga damuwa. Cikin mamaki yace"Alhaji nace ko lafiya? Alhaji Jibril ya sauke Numfashi cikin Damuwar da ta bayanna har saman fuskarsa. Cikin wani irin sauti yace"Shikenan kawai Alhaji." Abba yace"Shikenan me ya faru? Ka fad'amin mana? Alhaji Jibril ya kara sauke Numfashi kafin yace"Alhaji mganar bata da amfani mu bar ta kawai." Shi kuma Abba ya Dage sai ya gayamasa ko wata mgana ce. Jin ja'in jansu yasa hankalin su Umma ya dawo kansu. Har da Innani wacce tace"Fad'i damuaarka Jibrilu kamar yadda ka Daukeni uwa haka nima na Dauke ka d'a kamar Sulaimanu." Alhaji Jirbril ya kalli Matarsa Hajiya Murjanatu itama sai ta kallesa cikin mamaki Saboda ta kasa gane ma'anar kallon na shi. Sai kuma ya koma ya sunkuyar da kansa kafin yace"Had'uwar kasuwanci ne ya had'amu da Alhaji Sulaiman ammh jinsa na ke yi kamar Dan'uwa na jini Shiyasa na yi Tunanin na kara karfafa alaqar mu ta hanya aurattaya a tsakanin ya'yan mu." Innani ta washe baki ta na fadin"To miye abun damuwa? Ga mu nan da yaran mata a gida sai shi dan wajen naka ya duba ga Salima da Siyama ni da zai ji shawara sai ya zabi Siyama Domin tafi yayar Hankali da natsuwa kunga shikenan ma sai a had'a bikin su rana d'aya da na magajin gida da Sulsana." Kallonta kowa ya yi ya na mamakin ko gama mgana Alhaji Jibril bai yi ba har Innani ta yanke mgana. Shi kuma Mubarak da yaji komai har ransa yaji dadi daman kuma kila Rabon auran shi da Salima ne ya had'a Abba da Baba suka san juna. Maimakon yaji Alhaji Jibril ya karbi mganar Innani sai kawai yaji ya na Fad'in"Ba Mubarak na ke mgana ba Innani ina mganar Yar wajena Zahra'u da d'an wajen ku Abubakar Sadiq." Sai falon ya Dau shuru kallo ya koma kan Alhaji Jibril. Innani ko ta na jin abunda yace ta wani yamutsa fuska kafin tace"Wani Abubakar Sadiq din da wata Zahra'un? Da sauri Mama tace"Magajin gida dai Innani da kika sani Sadiq." Innani ta rafka salati ta na tafa Hannu har da wani cire gilashinta ta kare ma Alhaji Jibril kallon sama da kasa sannan ta maida gilashin nata lokaci d'aya ta na fadin"Ammh kai a wani gari a ka haife ka? Ta fad'a ta na wani yamutsa Fuska Alhaji Jibril cikin Ladabi yace"Ni haifaffan garin Zariya ne Innani aiki ne ya kawoni kaduna har kuma na yi aure na tara iyalai." Innani ta wani tabe baki kamar taga kashi kafin tace"Ba shakka. Hala baka jin bayanin da na yi maka ba ne? Naga alamun baka gane bayanin namu ba ne bari na yi maka gwari gwari shi magajin gida da ka ke mganar a had'a shi da wannan Gajerar yar taka da matar sa wannan yar fara yarinyar Doguwa sulsana itace wacce zai aura ba domin ma Magajin gida yace a dakata ba ai da yanzu kila ma an samu Rabo." Kunya ta kama Abba da su Umma na kalaman Innani da suka yi Tsauri. Ita kuma Innani tunda taji yace yarsa ta san wannan gajeran ce tunda yar mai Tsawon da auranta har da ya'yanta. Hajiya Murjanatu ko bakinciki ne suka mata runbdgu lokaci d'aya yasa ta kasa mgana illah kallon mijinta da take yi cikin Tuhuma meyasa baban bintu ya ke raina mata wayau ne haka? Ta yaya zai yanke Hukunci kan yarsu ammh bazai sanar da ita ba. Sai da yazo ya yi mganarsa kuma ba ta samu karbuwa ba daga baya kuma cin zarafi na neman biyowa baya to cin zarafi mana Innani tace gajerar yarsa da kushen Halitta a lamarin kenan. Alhaji Jibril kuma ya kasa kallon matarsa ballatana su Innani ko da akazo wannan gabar bai ji ya karaya ba. Sai ma kara Rusuna kai da ya yi ya na fad'in"Ai shiyasa da naji haka na so na Binne mganar a rai ku ka matsa har sai na sanar da ku." Innani ta kallesa a rene  sai taji bala'in haushinsa take ji wato daman ba Domin Allah ya ke wannan ladabin ba saboda ya samu biyan bukata ne lalle aiko sai dai  ya bi wani sarkin. Mubarak kuma Mamansa ya kallah itama ta kallesa sai dai ba su da ta cewa a yanzu tunda ba su da wannan Hurumin. Abba ne ya yi Saurin cewa"Bakomai Alhaji Jibril na yaba da karamcinka. magajin gida kuma mijin mace hud'u ne bayan ya auri Sultana zai iya karawa da Ita Zahra'un." Innani na jin haka bata bari ma ya Rufe baki ba ta saka musu kuka mai had'e da ihu. Har da kurma ihun wayyo Allahta ta shiga uku. Abba da su Umma suna Rige rigen isa gareta domin jin abunda ya sameta. Ammh sai Innani ta cire gilashinta ta fara goge hawaye da Haban zaninta Lokaci d'aya ta na fad'in"Shikenan Sulaimanu shikenan zai saka a yi ma Susalana kishiya itama a kashe min ita kamar yadda aka kashe min kuluwata." Ta karishe fad'a ta na mai kara fashewa da kuka kamar wacce ake yankata. Umma ta kalli Abba shima ya kalleta Hajiya Murjanatu ta isa gaban Alhaji Jibril a sannu ta na fad'in"Me ka ke shirin aikatawa Baban Batul? Kallonta ya yi kafin kai tsaye yace"Abunda kunnen ki yaji miki Murjanatu." Da haka ya kauda kansa, Abba ko da su Umma suna ta faman lallashin Innani ammh taki daina kuka. Kara fad'i ta ke yi za'a kashe mata Sulsana kamar yadda kishiyoyo suka kashe mata Kuluwarta. Abba ya kalleta ya na fadin"Innani ki daina da Fad'in haka Hauwa fa lokacinta ne ya yi ba kasheta abokan zamanta suka yi ba fa." Innani ta dago da idanuwanta da bata wani gani ta zabgamasa harara kafin tace"Matsa ka bani waje kai me ka sani? Kai dai a yi sha'ani kawai ammh a ranar gobe kiyama akwai tarin Hisabai a gaban Ubangiji ko tawa da Shitu kad'ai ta isa b'ata lokaci." Mama ta so ta yi dariya ammh ta Daure ammh sai da ta juya baya ta na tarin karya. Abba ya jinjina kai kafin yace"Shikenan naji ki bar mganar na nan don Allah." Innani tace"Ta ya zan bar magana kana neman kace za'a yi ma Sulsana kishiya tun ma kafin ta shiga gidan? Sulaimanu anya kana so ka gama da duniya lafiya ban sallamaka ba.? Umma ta yi saurin taran Innani da cewa"Haba Innani bai kamata ba." Kawai sai Innani ta cigaba da kukanta shi kuma Abba kunyan Alhaji Jibril yasa yace"Innani addini fa ya bamu damar auran mata sama da d'aya Hudu ya ce mu yi in muna da Hali." Innani ta dago ta na kallonsa ranta bace tace"Wlh ko bayan raina a ka yi ma jikata Sulsana kishiya ban yafe maka ba Sulaimanu." Ba su Abba kad ai suka zaro ido ba hatta da Alhaji Jibril da Hajiya Murjanatu. Abba ya kalli Innani kafin yace "Innani.." Bai karisa ba ta katse shi da daga masa Hannu Lokaci d'aya ta na fad'in"Da wanda ya biya Sadakin da wad'anda suka zo daurin auran dukkan su Allah ya tsine musu ba su da albarkata kai har da shi magajin gidan inda ya sake ya yi ma jikata Kishiya ba ni ba shi har abada ni da shi uban kowa ya yi ta kansa." Ai ta na fad'in haka sai jikin su Umma ya yi sanyi su san ta gama mgana Tunda har magajin gida bai Tsira ba. Alhaji Jibril ya yi shuru ya na wani nazari kafin Daga bisani kamar an zabure sa ya mike zuwa gaban Innani ya Durkusa ya rike hannuwanta. Ita kuma cikin masifa tunda ba gani take yi ba tace"Waye wannan kuma? Da sauri yace"Ni ne Innani.". Sai da ta ji muryansa sannan ta Saurara ammh fa ya sha harara da tabe taben baki. Cikin Ladabi yace"Innani kada ki damu tunda baki so ba wanda zai yi ma Jikarki kishiya ko bayan ranki in sha Allahu" Ba kunya ba komai Innani ta washe baki kafin tace"Ko kai fa? Ka ga dai an riga an ba shi ita kuma dangi kowa yasani nace maka ma ba domin magajin gida yace a dakata ba da yanzu kila har da rabo." Alhaji Jibril yace"Bakomai Innani in Lokacin ya yi a sanar damu in sha Allahu zamu zo." Innani tace"In sha Allahu kuwa Allah ya yi albarka kada ka damu kaji ko? Ba domin Sulsana ba ce da Tuni mun amimce ammh kada ka damu ka Siyama nan da Salima wannan Saurayin d'an naka ya zab'i daya acikin su sai a yi had'in zumuncin ba shikenan ba." Alhaji Jibril yace"Shikenan ko Innani yadda kikace haka za'a yi" Innani ta washe baki ta shiga saka masa albarka. A daidai Lokacin aka fara kirayen kirayen sallar la'asar yasa mazan suka tafi masallaci matan suka yi na su a gida. Suna dawowa Alhaji Jibril yace za su tafi Abba yace ya zata kwana za su yi sai gobe yace yau zasu koma sai kuma wani jigon. Umma tace in sha Allahu suma suna nan zuwa tunda su sun fara zuwa saura su. Hajiya Murjanatu yake kawai take yi ammh abun na cin ranta ta kosa su bar gida taji Dalilin Baban Batul da na aikata musu wannan Tozarcin. Innani ko harda ita a masu rako ta na ta Allah ya shi albarka ammh ta tafka musu tsiya saboda son kanta. Umma ta ba ma su zahra'u kyatan Turaman atamfofi da Turare sai Batul da bama Takalmi. Mama kuma ta ba ma Fathihatu Kyautar Turaren wuta mai kamshi zuwan maiduguri. Kamal kuma Abba ya basa kudi da baisan adadin su ba shi da Batul. Karfe hud'u da rabi suka bar Haraban gidan Alhaji Sulaiman bayan Alhaji Jibril ya bama Innani kudi da yawa da su siyama duk ya rabama 5k kowacce ammh ban da Salima wacce ke cikin Shashen Mama bata ko Fito ba. Duk da Mubarak yaso ya kara ganinta ammh har suka bar haraban gidan bai ga ko mai kama da ita ba. Suna fita daga gidan ko anguwan Hajiya Murjanatu bata bari sun fita ba ta kalli Abba da ke gabam Mota Inda Mubarak ke driving tace"Baban Batul me nake jin ka aikata ne haka? Ko waiwayowa bai yi ba cikin Kaushin Murya yace"Murjanatu ba anan ya kamata mu yi wannan mganar ba. So behave u self kina gaban yaran mu ne" Sanin haka yasa sai ta danne mganar ammh abun na cin zuciyarta. Abun takaicin ma su ke da ya mace ammh su suke kai tayi ana musu wulakanci kuma tasan haka kurum Baban Batul bazai aikata haka ba sai yasan ya na hangen riban da zai samu akan hakan. Su Surayya kuwa sai bayan Tafiyar baki suka samu labarin abunda ya faru a falon Innani. Sajida ta yi karaf tace"Haba mama Umma ai gwara da Innani ta hana. Tsakani Allah ba na son ganin kananan yara da kishiya duk sai kiga abun ba tsari aciki." Daman Umma ke shaida musu yadda abun ya wakana a shashen Mama. Kowa dai sai tofa na shi ya ke Allah yasa Sultana na shashen Innani abunta in abun Innani kuma na kusa ta kwashe yadda akayi ta fad'a mata shi yafi komai ma sauki. Surayya ta kada kai kafin tace"Sadiq bai da Tsarin auran mace fiye da d'aya." Sa'ima tace"Ba shi da hayaniyar da zai iya ma wannan gaskiya wannan karon ina bayan Innani." Mama ta yi dariya kafin tace"Kai Innani akwai karfin hali wai har ta na cewa gajerar yarsa." Gabadaya suka saka Dariya Salima na gefen Umma tace"Ba karya ta fad'a ba yarinya is too short ta yi ma Bro gajarta da yawa yadda ya ke gint d'inan" Umma tace"kun dai yi son kai kamar yadda Innani ta yi kun so Sulsatana kun ki Zahra'u." Sa'ima tace"Umma daman ai so so ne ammh son kai yafi ko Surry? Surayya tace"To daman mu ai Sultana ce tamu yadda bazamu so a yi mana abokam zama ba sai dai in kaddara haka itama mu ke mata wannan Fatan" Umma tace"Ai shikenan mgana ta kare. Ammh fa Innani tace in ya na so a had'a zumuncin ne ga Siyama ga Salima wanman saurayin babban yaron nasa ya zo ya zaba acikin su." Mama ta kada  baki tace"Sai dai Salima domin siyama ta yi masa kankanta." Salima na jin haka tace"Mama wata Salimar? Umma tace"Salima Sulaimam Shinkafi.". Salima ta mike ta na Tura baki Lokaci daya ta na fad'in"Tab ni fa ba yanzu zan yi aure ba karatu zan yi.". Tafad'a ta na tura baki kafin ta bar Falon. Sa'ima ta bita da fad'in"Ki yi fatan Innani tace a'a in kuma tace Eh! sorry ki yarinya." Gabadaya suka kwashe mata da Dariya sanin Halinta da Ra'ayinta na sai ta zama ma'aikaciyar gwammati ko za ta yi aure. 🌿 Ina manyan mata masu MATSALOLIN rashin Ni'ima Ina sabbabin aure Wanda basu juku yanda Mai gida zai sume ba😂Ina wayanda zasuyi sabbin aure Nazo muku da magani SAHIHI ingantaccen TSIMIN TABAJE🤌🏽🥰😍 hmm uwar gida, amarya, tsoffin aure kuna Ina ko kuntsaya tsilla tsilla tohm maza kuzo nazo kusiya TSIMIN TABAJE 💃💃😂hajiya ta tunda kukaji na yaba wannan magani toh tabbas yakai inda yakai yanada matukar kyau, Yana saurin saukar da niima baya illa domin andafashine da saiwoyin da kuka San suna maganin dakyau... Hajiya ta 🙈wlh Mai gida zaiyi Santi zakiji dadi Kuma zakuzo ku godemun domin yanasa Gurin yayi dumi ya Kuma ciko miki da gaba Gurin Kuma zaiyi dadi zoyzoyy😂🙈💃Kuma duk afarashi kalilan akwai gorina 1k akwai galan, akwai jarka ga duk meso, hmmm duk Wanda yasha Sai ya Gode mun domin nice na baku tabbaci 💃😂kunsan banida burin daya wuce Inga anasaka Mai gida farinciki 💃😂🥰Toh kuzo kusiya zakuji dadi insha Allah Kuma Sai kun dawo.... muka hada miki maganin TSIMIN TABAJE sha'awa zaki koma kamar marka..game bukatar TSIMIN TABAJE ya kiramu tawa innan numbobin kamar haka *Location* *Zaria and kaduna* *but nation wide delivery* *for more details 07062349732 or 08143450259* 💃💃💃 *Janafty* *TMWB2K009* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* *BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA DEE*! *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Gaban ayu*. *Hakkin daka gangariya*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. *Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* *Ana dafa GIMBIYAR KAZA da tattabarun garari*. Kaduna. Da daddare. Hajiya Murjanatu tunda suka isa gida lafiya ta ke kokarin su kad'aice da Baban Batul domin su yi mgana ammh yaki bata wannan damar. Suna dawowa ya shige dakinsa ya kuma ce kada kowa ya zo ya damesa ya na bukatar Hutawa ne. Ko Tea dinsa na dare zahra'u ta kai masa, sai dare bayan ta sallami yaran ta isa dakin nasa tunda har Fathihatu a nan zata kwana sai gobe mijinta zai zo ya dauketa. Abun na cin ranta ta kasa fad'a musu Mubrak ne kad'ai ya sani shi kuma ba shi da tacewa kan abunda Baban na su ya riga ya aikata. abunda bata sani ba ne shi bai ga illar hakan ba sai ma ya ke ganin shi kila a gaba maganar Baban nasu zai iya zame masa alheri watarana. Ta isa dakin nasa da shirin barcinta ammh ta dora zani da karamin Hijabi saman kayan barcin jikinta. Ko da ta shiga ta iske shima ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya mai saukin kauri ya na zaune gefen gado ya dora kafafunsa saman gado. Sai kurb'an tea dinsa ya ke yi hankalinsa kwance. Ta na shigowa ta cire zanin da Hijabin sannan ta haura saman gadon ta zauna kusa da shi Lokaci d'aya ta na fad'in"Baban batul Me yasa ka ke kauce ma mgana da ni ne ? Ko saboda kasan baka kyauta ma yarmu ba ne? Kai tsaye ya kalleta cikin kaushinsa yace"Dama na yi mata wani abu ne da ban kyauta ba Murjanatu? Ta gyara zama kafin tace"Haba baban batul kai ma kasan abunda ka aikata bai kamata ba taya ya mu ke da y'a mace kuma sai ace mu ne zamu je neman aure da kanmu a hanamu sannan daga karshe a bimu da cin zarafi akan yarmu gaskiya Abunda ka yi bai dace ba" Ta fad'a ranta bace cikin d'an mirmishi ya kalleta kamar bazai yi mgana sai kuma yace"ke kike ganin abunda na yi a zuwan bai dace ba. Ni kuma ina ganin abunda na aikata a matakin wani babban nasaran da na ke fata nan gaba ne kad'an.". Cikin mamaki ta kallesa kafin tace"Bangane ba? Cikin mirmishi yace"Zaki gane ammh ba yanzu ba." Hajiya Murjanatu ta kura masa ido daman tasan halinsa kuma sai da ta zargi haka tasan baya kwansa sai da zakara. Cikin kufuluwa tace"Ni dai kada garin son abun duniyar ka ya kara saka ka ka yi tallar ya'ya na, ba rasa masoya suka yi ba ballatana a ci zarafin su.". Kamar abun arziki yace mata"To." Ita kuma jin haka sai ta cigaba da Fadin"In da ka nemi shawarata wlh bazama ta kaimu ga haka ba baban batul. Kowa ya tsaya iya matsayinsa ya tsaya iya abokin Huldar ka ta kasuwanci ammh ban yi sha'awar had'a zuru'a da su ba gaskiya." Kai Tsaye yace"kina da Hujja ne kan haka?. Rausayar da kai ta yi kafin tace"Ba matakin Rayuwarmu d'aya ba. Gwara kowa ya zauna a muhallin da Ubangiji ya so ya ganshi in za'a yi zumunci to a yi saboda lillahi shikenan Fakat." Kai ya kad'a kafin yace"Naji Salamatu uwata.'" Ya fad'a Hankalinsa kwance kamar ba mgana ya daba mata ba. Jin haka yasa sai bakinta ya mutu ta kasa motsi ballatana mgana. Shi kuma sai ya sauko daga kan gadon ya na fad'in"Ki ma shirya domin nan da Lokaci kad'an alaqarku zata fi karfin zumuncin da ki ke fad'a." Ya na gama fad'in haka ya wuce tiolet ya na mirmishin nasara. Ba zahra'u kad'ai ya Haifa ba ya na da wasu ya'yan in ita bazata iya kaisa ga Nasara ba ya tabbata Mubarak zai kaisa ga nasara watarana. Tsohuwar nan ta gama Haska masa komai sai yanzu ma ya ke Tunanin Mubarak din nw daidai da Tsarinsa. Baki sake Hajiya Murnajatu ta bisa da kallo har ya shige cikin makewayin. Tasan Halin shi wajen son abun duniya da biyan bukatansa ba shi da karaya ko Sarewa. Ta kuma san duk Saboda kudin da Alhaji Sulaiman ke da shi ne, ta na Tunanin akwai abunda Baban Batul ya ke hari. Hannayenta ta d'aga sama ta na fad'in"Allah ga ya'yana ka karemin su daga tozarcin duniya da mutanen cikinta." Ta na shafa addu'ar ya fito daga Tiolet din ya na mirmishi kamar yaji abunda tace ammh kuma ko a Fuska ko fatar bakinsa bai nuna mata yajin ba. Ranar haka suka kwanta kanzil ba wanda ya kara cema D'anuwansa ita ta na ta Tunanin wannan karon kuma me Baban batul ya ke shirin kara aikatawa? Shi kuma ya na ta tunanin mafitar da Hanyar da zata bulle da shi in har abunda ya ke Hasaahe ya tabbata. Daga ganin yadda fuskarsa ta cika da Annuri ta cikin Duhun dakin zakusan ya gama hango nasara mai tarin yawa a nan gaba kad'an. ******* *ZARIYA*. Tunda Tahir ya dawo bai kara barin Gefen Sadiq ba ballatana ya samu ya je gidan Hasiya. Wajen aiki ne kawai kowa ya ke zuwa inda ya cancancesa. In kuma suka tashi kafin ya samu ya biya gidan Hasiya sai Tahir ya kirasa a waya yace ya dawo gida ya na jiransa ba Halin kuma ya yi masa wata karyar balle ya samu yaje ya Dubata. Sai dai kullum da Safe in yaje wajen aiki ya na kiranta sau d'aya a rana Domin yaji Lafiyanta. Duk da ta tabbatar masa ta na lafiya ammh a kasan ransa sai yake jin wani iri da zama da Tahir sai yake jin kamar yafi samun annushuwa in ya na zaune da Hasiya. Har maganar Laptop dinsa ta yi masa yace mata in ya dawo zai zo ya Dauka. Bai samu kuma yaje ba sai da aka Rufe sati sannan ya samu ranar da Sassafe kafin ya wuce wajen aiki ya biya ya dauko saboda Tahir sai masa mgana ya ke yi ganin bai saba barin komai nasa a wajen aiki ba. Bayan laptop bai dauko komai ba, ammh kuma ko bayan ganin Na'uran Tahir bai daina bincikarsa ba kamar yana zarginsa da zama a wajen Hasiya. Bayan takalma ya lura ba wasu kayan Sadiq har da wata jallabiyansa. Kai Tsaye ranar da Safe suna shirin Fita wajen aiki Tahir yace"Wai ni ko ina jallabiyar nan taka na daina ganinta ne kwata kwata.? Sadiq na duke ya na Daure igiyan takalminsa na masu hidimar kasa da gwamamati ke ba su, yau laraba suna da CDS, Hatta Tahir shima shigar kayan su na Bautar kasa ya yi. Cikin Halin ko in kula Sadiq yace"Wata jallabiya kenan? Tahir yace"Wacce kace ka siyo ta a Saudiya sanda ku ka je tare da Innani." Sai a lokacin ya tuna da ita ta na cikin kayan da ya baro gidan Hasiya. Kasa mgana ya yi shi kuma Tahir bai damu ba sanin Halinsa daman kana mgana yaji kuma ya yi kamar bai ji ba. Sai kawai yaji yace"Ta bace." Cikin mamaki ya juyo daga saka rigar jikinsa ya na kallon Sadiq yace"Ta bace? A ina.? Ba zato kawai Sadiq yaji bakinsa na fad'in"Wajen wanki mana." Tahir cikin tantama yace"Wajen wanki kuma? Yaushe ka fara kai wanki kai da kace baza ka kara ba shi wanki ba.? Sadiq ya runtse ido na wani Lokaci bayason ya na karyan nan ba Halinsa ba ne ammh kuma ya zama Dole. Mikewa ya yi ya na fadin"Eh na ji na gaji ne sanda baka nan shiyasa na ba shi." Tahir ya gyada kai kafin yace"To ka yi masa mgana? Sadiq da sauri yace"Sharesa kawai ko an yi mgana ai ba ganinta zan yi ba kasan Halinsa zai ce zai duba ammh kuma shuru zaka jisa." Tahir yace"A'a da dai ka yi masa mgana yasan abunda ake ciki ko? Sadiq yace"Tahir ka bar mganar nan kawai kaji." Tahir kamar bazai yi mgana ba sai kuma ya jinjina kai kafin yace"Shikenan tunda kace haka." Sai kuma bayan sun gama karyawa zasu tafi Tahir ya duba ma'ajiyar takalmansu yaga har alokacin ba wasu cikinsu cikin Maganarsa yace"Wai baka karb'o sauran takalman ka wajen mai Foolish din ba ne? Sadiq yaji kamar ya kurma Ihu ya na rataya jakarsa ta baya yace"Naje an ce ya tafi garinsu.". Tahir ya mike ya na fad'in"What!? Sadiq ya fice daga dakin batare da ya kara ma Tahir mgana ba. Shi ko Tahir mamakin Sadiq ne ya kamashi duk da yasan Halinsa na rashin ba ma wasu abubuwan Muhimmanci. Ko a hanya ma Tahir korafi ya rika yi ma Sadiq na ya rika kula da kayanshi ko don yaga ya na da su da yawa shiyasa baya maida kansa? Sadiq ya kallesa kafin yace"To Tahir." So ya ke daganan mganar ta tsaya shiyasa yau yace su hau mashi. Kowa kuma sai ya nufi inda za shi. Ya na Office din su na yan Castelia Hasiya ta kirashi har gabansa ya fad'i ya zata ko wani abu ne. Sai da yaji tace Yaron Adda Fati ne ba lafiya ta na so taje ta gaisheshi in ya bata izini. Cikin muryansa ta sanyi da natsuwa yace mata duk inda ta ke son zuwa kada ta damu da sai ta tambayesa ya riga ya yi mata izini. Da tl ya tambayeta ko ta na da kudi? Sai tace akwai wanda ya ke bata bata komai da shi sai ta yi amfani da shi na abun hawa Da haka suka rabu da juna bayan sun yi sallama. Sadiq ya yini Tunanin rayuwar da ya saka kansa aciki wato wata rayuwa ya ke yi, wacce kowa yasan ba itace ainihin Rayuwarsa ba. Har ga Allah Saboda ya taimaki Hasiya ya aureta sannan saboda tsaida kuka da damuwa daga Idanuwan Uwa irin Amma. Har kuma a zuciyarsa kuma ya na da Niyar sakinta in zai koma gida Saboda rayuwarsa ta zariya dabam ta ke da Rayuwarsa ta gusai. Sai dai kuma da abun ya matso sai yake jin kamar in ya saki Hasiya bai yi mata adalci ba tunda tun farko bai kafa musu wannan sharadin ba. Sai yake jin girman abunda ya ke so ya aikata zai iya shafe Ladan Taimakon da ya ke tunanin ya yi mata. Duk sai ya kasa samun Mafita ya na cikin Tsaka mai wuya gaba kura baya Damisa duk iya hangensa da Tunaninsa ya kasa gano wata mafitan da zata bulle da shi bayan ya saki Hasiya ta kama gabanta shima ya koma in da Rayuwarsa ta dace. Gashi Sauransu bai fi wata uku ba suna zuwa hutu gida suka dawo sai na tafiya gabadaya. Ya kamata duk wani taimako da zai yi ma Hasiya ya gaggauta taimakonta cikin wannan wattanin kafin Lokaci yazo ya kure masa. Suku suku ya yini kamar mara lafiya duk wanda ya yi masa mgana sai yace kansa ke ciwo har gida akace ya koma ammh sai yace a'a saboda yasan ko ya koma banda Tunanin da zai addabesa ba abunda kuma zai iya tsinana ma kansa. Da ace Hasiya na nan ne sai yaje wajenta ya kwanta ya Huta ammh yasan tunda ta masa waya ya na da Tabbacin ta tafi in da tace zata je d'in. Kamar ya sani muna gama waya da shi cikin murna da Farinciki na shirya na tafi saboda zumud'in da na ke ciki na fara fitata a karo na farko. Gidan ba dadi Ummi na makaranta sai dai kuma akwai yan jere za'a kawo amarya a dakin da ke kusa da na Ummi zamu karu mu zama mu uku kenan. Ban kira Add Fati nace mata zan zo wajenta ba, Amma kawai na fad'amawa da muka yi waya da Safe. Itace ta tambayeni ko na nemi izinin mijina? Sai na ce mata baya gari. Ita ta matsamin sai da na kirasa a waya na tambayesa cikin ikon Allah kuma ya bani izinin zuwa duk inda ya kamata. Dubu biyu na dauka acikin kudin da ke hannuna Dubu shidda ne daman a hanya na tsaya na siyama yaran Biskit sannan na karisa koda naje ma Adda Fatin bata nan taje kai Hanif asibitin madarkaci ta yara Habibun ne kad'ai a gida sai da na zauna na jirata sannan. Sai dai ta dawo ta ganni kamar Daga sama ko da bata fad'a ba sannan taji Dadin ganina. Hankalina kwance sannan har kiba nayi, Hanif yaji sauki zazzabi ne da Mura na ba su Tsaraban su shi da Hanifa sai bayan azahar Habiba ta Dawo daga makaranta ta na ganina ta Hau ihu ta zo da gudu muka Rumgume juna. Adda Fati na gefe ta na mana mirmishi. Ranar ni na yi mana girkin rana har miyan tuwon dare ni na Daura mata, Sai kallona Adda ta ke yi ta na mirmishi ganina cikin natsuwa da walwala kuma hakan ya na nuna ina cikin kwanciyar Hankali a gidan aurena. Mun sha hira duk da rabin Hiran na Amma ce ina ta ma Adda Shagwaban ya kamata mu shirya muje mu Duba Amma, Adda Fati tace Amma tace kowaccen mu ta zauna gidan mijinta ta yi biyayyan Aure ita lafiyanta kalau. Ba ni da tacewa tunda nima haka Amma ta fad'amin ammh mganar gaskiya ina kewarta sosai ina kewar cinyarta in da na ke kwanciya naci kuka na har sai na koshi. Sai da biyar ta gota ne Adda Fati ta fara min mganar na zo na shirya na tafi gida. Ina Tura baki nace"Kai Adda kamar ki na kora na? Duba fa agogo shidda ma ba ta yi ba" Adda Fati tace"To kafin ki shirya ki fita ai shiddan ta yi kuma kinga in yamma ta yi wahalan abun hawa." Jin haka yasa Sai ban yi gaddama ba naje na shirya na fito ina ce mata zan tafi sai taje na jira Habiba ta Dawo taje siyomin kayan miya ne da zan tafi da shi. Sai na zauna saman Hannun kujera ina Fadin"Ina so naje gidan Adda Rukayya ina tsoro." Na fad'a cikin wani yanayi Adda Fati ta kalleni kafin tace"Kada ki je yanzu ki bari sai nan gaba." Kai na jinjina mata kafin nace"Shikenan gobe sai naje gidan Ramatu na yi mata yini." Adda Fati ta kalleni cikin mamaki kafin tace"Gobe kuma? Na gyada mata kai ina yar dariya cikin Harara tace"Baki da Hankali ne? Ai sai ki bari a kwana biyu ko Hasiya? Kai tsaye na fara bata labarin yadda muka yi da shi a waya yau da Safe. Sai ta jinjina kai kafin tace"Baya gari kenan? Da kai na amsa mata alamun Eh kai Tsaye ita kuma tace"To wani gari suke zuwa shida megidan nasa? Na yi shuru kafin nace"Wlh bansani ba Adda." Adda Fati itama sai ta yi shuru sai a lokacin ta fara wani tunani anya ba su yi kuskure ba? Ba su san komai fa da ya Danganci Abubakar ba kuma ba'a aure cikin Duhu. Ni kuma iya gaskiya ta na fad'a mata tunda bai taba fadamin ga inda suke zuwa ba, muna cikin hakane sai ga Habiba ta kawo min kayan miyan sai na mike ina ma Adda Fati sallama. Har kofar gida ta rakani har na fita sai ta saka baki ta kirani na juyo na dawo kai tsaye tace"Kun yi mgana da shi akan ya kai ki chan garin na su ki ga yan'uwansa? Shuru na yi kafin nace"Eh yace zamu je ammh ba yanzu ba." Adda Fati tace"Ba yanzu ba sai yaushe? Kai tsaye na kalleta kafin nace"Bansani ba Adda." Sai kawai ta girgiza kai kafin tace"jeki Allah ya tsare sai mun yi mgana." Da haka na wuce Habiba ta rakani na samu mashin tunda yafi sauki muka rabu ina ce mata ina jiranta wannan Satin ranar da ba makaranta. Maganar da Adda Fati tamin ya tsayamin arai nima kuma sai naga ya kamata zuwa yanzu nasan waye na ke Aure. Duk da auran namu bai gama cika matakin kowani aure ba, ammh dai akallah tunda an kwarari wattani ya dace ace yan'uwansa da suka Rage masa su san da ni. Irin yadda ta min mganar haka ma Ramatu ta min washegari da na je mata yini. Duk da ban fito na bayyana mata baya kwana a gida ba na, in kuna ya kwana to muna mabambamtan muhalli. Ammh itama ta nuna min zuwa yanzu ya kamata na san wanda na ke aure sannan kuma yan'uwansa suma susan dani. Da farko bana wannan Tunanin ammh sai da Adda Fati da Ramatu suka ankarar da ni sannan na ga cancantar haka. Na kuma kuduri niyar zan masa mgana ya kai ni garinsu naga Danginsa. Abun sai kuma ya fara Damuna acikin raina haka ma Adda Fati ita Damuwar nata ma guda biyu ne, na rashin sanin takammman Sana'an da Abubakar ya ke yi. Damuwar ta bayyanan mata har a saman Fuskarta har sai da Baban su Hanifa ya fahimci ta na da Damuwa sai ya tambayeta. Cikin damuwa tace"Baban hanifa Sai yanzu na fara tunanin anya bamu yi kuskusren biye ma Amma ba? Kai tsaye yace"Kuskuren mene? Cikin Alhini tace"kan mganar auran Hasiya da Abubakar. Ka duba ka gani bamu san komai a kanshi ba babban abun tunanin ma bamu san sana'arsa ba ya dai ce shi mutumin Shinkafi ne sannan karatu ya kawosa nan da kuma Buga bugar sana'a." Habibu ya yi shuru bai ce komai ba, ya na nazari kafin ya nisa yace" Yanzu me ne mafita? Adda Fati tace" Na rasa mafita kaina duk ya kulle mun yi mgana da Hasiya ta ce itama batassn ina ya ke zuwa sana'ar tasa ba, kuma maganar ya kaita taga danginsa yace ba yanzu ba to sai yaushe? Tunda an riga an zama Daya, ai yakamata ya kaita ta ga Ahalinsa tasan wanda ta ke aure." Habibu ya jim kafin yace" Nima da farko da naji mganar auran Hasiya sai da wannan tunanin ya fad'omin sai dai jin abun daga Amma ne yasa ban ce komai ba ammh mafi a'ala acikin aure mu bi dokikin da Annabi muhammadu salallahu alaihi wasallam ya sanar damu ya yin bada auran ya'yanmu sana'a da sanin mu'amala tare da sanin Ahali shine ginshikin aure." Adda Fati sai ta zabga Tagumi ta kasa mgana sai a yanzu ta tabbatar ma kanta sun yi kuskure Halin da Amma ta ke ciki na Tsaka mai wuya shi ya kaita ga yanke wannan Hukuncin da zai shafi rayuawar Hasiya gabadaya. Habibu ya dinga lallashinta da ta kwantar da Hankalinta ba abunda zai faru sai Abunda Allah ya so. Za'a bincika har chan shinkafin domin a san ko waye shi ammh yanzu dai Hasiyan ta fara matsamai sai ya kaita garinsu tasan Yan'uwansa. Da wannan shawaran na Baban su Hanifa ta kirani da Safe ta na gayamin na matsamai sai ya kaini chan Shinkafi na had'u da Danginsa. Ni dai sai na bita da toh kawai bani da wani zabi sai dai ta yadda zan yi masa mganar ne na rasa yadda zan yi. Kada yaga kamar na nuna zakewata da yawa ne. Adda Fati sai ta yi karambanin kiran Adda ta sanar da ita tunanin da ta yi Adda kuma ta bata goyan bayan cewa ya kamata a bincikan aure ba mganar wasa ba ce kuma tun farko da Amma ta yi shawara da ita baza'a yi auran nan sai su san waye Abubakar da abunda ya Dangancesa gudun auran wanda bai dace ba. Adda ce bayan sun gama mgana da Fati ta sanar da Amma komai da kuma yadda Adda Fati tace Hasiya zata matsa masa ya kaita chan shinkafi in ya nuna ba yanzu ba sai a tada wani yaje chan ya bincika ya gani. Amma na jin haka ta saci idon Adda lokacin da ta shiga makewayi ta kirani a waya ta gargad'eni kada na sake na matsama Abubakar kan maganar sai ya kaini garin su domin naga yan'uwansa na bari in har shi da kanshi ya yi min maganar sai na shirya ya kaini. Cikin mamaki nace"Amma me yasa? Ai ya na da kyau nasan komai game da shi" Cikin kaushin Murya Amma tace"In lokacin da yakamata ki sani ya yi zaki sani Hasiya. Kada ki matsa ma kanki kan sanin abunda ba'a so ki sani ba. Zaki iya zuwa kisan abunda zai iya hana ki zaman lafiya ki jira shi Lokaci da ya so ki san komai a kansa shi zai sanar da ke da kansa." Da wannan kalaman Amma ta katse wayar ta barni sake da baki sai maganganunta suka sarkeni na kasa gane inda ta dosa. Me ta ke nufi da cewa kada na matsama kaina da son sanin abunda ba'a so na sani ba? Ko ta san wani abun da mu bamu sani ba ne? Ita ko Amma ta yi hakane saboda d'inke wata baraka abunda Fatin ta saka Hasiya ta yi gaggawa ne kuma shi gaggawa aikin shedan ne in a auransu gaggawa ya shiga bai kamata a zaman su kuma gaggawa ya shiga ba, a bi komai a sannu in sha Allahu alheri ne zai faru sannan kuma zai faru a yadda Ubangiji ya Tsara Faruwarsa ne. Maganar Amma yasa na binne mganar acikin raina na kuma cire yakinin ko Assadiq ya zo bazan masa mganar Ahalinsa ba, na bi mganar Ammaa zan jira lokacin da ya kamata na sani zan sani. Ranar asabar aka kawo Amarya kusa da Dakin Ummi mai suna Fadila. Yar cikin samaru ne a irin gidajen ma su kudin anguwan. Fadila irin yamatan ne ma su kaud'i da Son karya sannan ga fariya da wulakanci tare da renin arziki. Mijinta ma'aikaci ne a CVN a Abuja ya na gini bai gama ba ne yasa ya kama Haya kafin ya kamallah gidansa. Fadila Farar mace ce Doguwa mai jikin mata ta na da kyau irin kyau mai Daukan ido sosai, iyayenta ma su kudi ne shiyasa kayan Dakinta ma sun taka na Ummi a komai da komai. Tun ranar litini da Daddare da muka shiga ni da Ummi ganin Daki na tabbatar ma da kaina Amarya Fadila bata karb'eni ba. Fuskarta ba Fara'a ta amsanin gaisuwa sannan ta na ta min kallon kasa kasa a wulakance. Ammh ta amsa ma Ummi cikin Sakewa ko ma daga ganin yan'uwanta duka Dakin Ummi suka yi mu'amalansu kafin su watse na Fahimci wani abu. Wannan rayuwar kwarya tabi kwarya ne in kana da shi sai ayi da kai in baka dashi kuma kai da banza duk d'aya ganin haka yasa ban kara shiga Dakinta ba. Kuma ta shiga Dakim Ummi sannan ta bata Su kayan Fulawa ammh ni ko abunda ba'a so bata bani ba. Ummin ce ma ta sanmin a nata sai ta boyemin da cemin Fadilan ce ta had'ama waje d'aya tace ta dibarmin aciki. shuru kawai na yi mata ammh mganar gaskiya ko a fuska wanda ya ke yi da kai zaka sani. ***** Har su Sadiq suka samu Hutu bai samu Sararin kara komawa wajen Hasiya ba sai ranar da zasu tafi. Tahir zai wuce Daura shi kuma zai tafi Gusai. Da safe sun gama shiryawa duk da ya na kiran Hasiya a waya lokaci bayan lokaci yana jin lafiyanta yasan bai kamata ya tafi batare da yaje ya ganta ba tunda zai jima kamar wata daya haka kafin su dawo. Ya rasa wata karya zai ma Tahir ya samu ya je ya dubata sai dakyar ya samu karyan zai je ya ciro kudi yanzu zai dawo sannan ya samu ya yi wuf ya fita yaje ya hau mashin. Da misalin karfe 9am na safe na Ranar jumma'a ya kwankwansa ma Hasiya kofa. Ina cikin barci naji ana Bugun kofa sai kuma kasala da barci yasa na kara komawa sai kuma naji wayata na Ringing cikin barci na lalubota kasan Filo ban ko Duba mai kiran ba kawai dauka na yi na saka a kunne. Sanyin muryansa ce ta Dake ni sanda ya ke fad'in"Ina kofar dakin ki." Da haka ya katse wayar ai sai na wartsake na Diro daga kan gado da Sauri dagani sai rigar barci tun ta gida ce duk taji jiki sai na Rarumi Hijabi na saka sannan na fito nazo na Bude masa kofar dakin lokaci daya ina Murza idanuwana. Yana Tsaye kofar d'akin sanye da Riga da wando ma su ruwan kasa ya sanya Jaket baka a saman kayan sannan hannayensa suna cikin Aljuhun wandonsa. Na fahimci ya na son tsarin wannan Shigar sannan koda wani Lokaci yana jin dadin sanya hannayensa cikin Aljuhun wandonsa. Hanya na ba shi Lokaci d'aya ina fad'in"Sannu da zuwa." Ba amsa ba sai da ya shigo ciki sannan yace min yauwa. A tsakiyar falon muka Tsaya bai ko Zauna ba ya juyo ya na kallona. Ni kuma ina shirin juyawa zuwa kitchen ko ruwa na kawo masa a tunanina daga tafiyar suke yanzu suka shigo garin "Hasiiyaa." Sai naji ya kirani cikin Taushin muryansa tsayawa na yi kafin na juyo ina fad'in"Na'am! Kai tsaye yace"Dawo nan gaba na." Ba musu na dawo gabansa na Tsaya ammh kaina na kasa ina wasa da Hijabin jikina da Hannayena da ke cikin Hijabin. Na wani lokaci ya tsaya ya na kallona ya rasa abunda zai ce min. Sai kuma chan ya nisa kafin yace"Jiya da Daddare muka dawo garin Hasiya. Kuma yanzu ma wata tafiyar ta kama mu yanzu." Kai tsaye na kallesa kafin nace"Yau? To zuwa ina? Sai da ya ja Numfaashi kafin yace"Zuwa Gusai." Mirmishi na yi kad'an kafin tace"Allah ya kiyaye hanya." Kudi ya fiddo cikin Aljihunsa ba zato kawai naji ya riko hannuna ta cikin Hijabin ya jawo shi waje karo na Biyu da Fatayen Hannayenmu suka kara had'uwa waje d'aya. Dukkanmu sai da muka ji wani yam! Dumin Hannuna ya gauraye da Sanyin hannunsa. Duk da yaji yanayin ammh bai maida kai ba sai ya sakamin kudin da ke hannunsa a cikin hannuna ya matse Lokaci d'aya ya na fadin"Ki kuka da kanki kin ji ko?. Sai na samu kaina da gyad'a masa kai ammh na kasa mgana. Hannunsa guda d'aya ya saka ya Dago habata lokaci daya ya na kallon kwayan idanuwana. Cikin wani yanayi yace"Akwai kayan abinci ba su kare ba ko? Kai na kara gyad'a masa ina so ya sakeni saboda ji na yi idanuwana sun ciko da kwallah suna shirin zubowa. Ba shawara da ni kawai naji hawayen sun fara gangarowa saman kumatuna. Wad'anda na rasa ko hawayen kewarsa ne ko na tafiyar da yace zasu kara yi ne? Shi kuma hawayena su suka kara sakashi ya shiga wani yanayi har ga zuciyarsa da niyar ya lallasheni ya jawoni jikinsa ya Rungumeni, lokaci d'aya ya na shafa kaina zuwa bayana da Sigar lallashi. Kansa ya kwantar saman kaina ya na fad'in"Sorry. Am sorry SIYA..!" Ya ke fad'a cikin wani irin Taushin murya da sigan kuma lallashi. Bansan ya akayi muka samu had'uwar gangar jiki ba, na dai ganni Tsamo tsamo a saman kirjinsa, ya na faman lallashina. Bansan cewa bayan haduwar gangan jiki mun samu na zuciya ba, sai da naji nima na bude hannayena da na jimke kudin nan na Rumgumesa ta baya Lokaci d'aya ina sakin kukana. Jin ina kuka yasa ya fara bubbuga bayana ya na fad'in"Shii.! Shii! Alamun na yi shuru mun jima a haka na lumshe a tsakiyar kirjinsa ina shakan kamshin Turarensa. Kafin naji ya dagoni idanuwana suna lumshe ne da hawaye ina ji ya saka Tattausan hannayensa ya sharemin hawaye lokaci d'aya ya na Fad'in"Ki daina kuka na baki tabbacin bazan jima ba zan dawo." Kai na kara daga masa shi kuma sai ya rike hannayena ya na kara fadin"Ki kular min da kanki za mu rika yin waya ko? Cikin muryan shagwaba da bansan yaushe na iya ba nace"To ba kai ba ka kirana ba." Da Sauri yace"Zan rika kiran ki in sha Allahu." Sai na jinjina kai kafin nace"Alkwari.! Mirmishi ya saki mai kayatarwa kafin yace"Cikawa.!" Ina shirin kara mgana wayarsa dake cikin Aljihu ta Dauki neman agaji da Sauri ya sakeni ya fito da wayar ya na ganin sunan tahir ya yi gaba lokaci daya ya na fad'in"Mu je ki rufe kofar zan tafi." Jikina a sanyaye na bi bayansa sai da ya fita sannan ya juyo ya na min mirmishi hannu ya d'agamin nima sai na Daga masa sannan ya juya ya tafi. Sai da naga Fitansa daga get sannan na rufe kofar na dawo falo na zauna ina Bude kudin hannuna. Bansan cewa ina kuka ba sai da naga saukan digan hawaye saman kudin hannuna masu yawa da bansan adadin su ba. Sadiq kuma ya na fita sauri sauri ya kara samun mashi ya hau ya koma Samaru ko da yaje Tahir ya gaji da jiransa sai masifa ya ke yi ya na fadin a ina ya tsaya? Kai tsaye Sadiq yace"Layi ne acikin bankin" Cikin mamaki Tahir yace"Banki kuma? Sadiq yace"Banki naje saboda ina da matsala da Atm dina." Da haka ya kashe bakin Tahir suka dauki jakunkunan su. Suka kulle dakin, sannan suka yi sallama da yan makaranta da suke tare da su. A tare suka je tasha Tahir ya samu motar katsina shi kuma Sadiq ya hau ta zamfara. Allah ya taimaki su Tahir motarsu ba ta kai awa ba ta cika shi ya fara yin gaba. Sadiq kuma sun bata Lokaci kafin motarsu ta cika duba da yanayin da mike ciki na Tsadar rayuwa mutane ba'a tafiye tafiye kamar baya sai wanda ya zame ma Dole. Suna tafe a Hanya Sadiq na kujeran Tsakiya ya na kallon gefen hanya ta wajen glass ammh Hasiya ce da kukanta ke gilmawa ta cikin Idanuwansa da Tunaninsa. Sannan dumin jikinta har a lokacin bai bar jikinsa ba sai ya ke jin kamar har alokacin ya na Rumgume da ita ne. Shi dai har suka isa zamfara ba komai acikin zuciyarsa da Tunaninsa sai HASIYA.! Ba wannan zumud'in da ya ke shiga in zai zo ganin gida. Sannan kunya da nauyi sun gama lullubesa kwata kwata zuwansa gusai wannan karon ya sha bambam da zuwan da ya saba yi a baya. *Janafty* *TMWBK2010* https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj *BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA DEE*! *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Gaban ayu*. *Hakkin daka gangariya*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. *Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* *Ana dafa GIMBIYAR KAZA da tattabarun garari*. Shi dai yasan ya sauka a tasha kuma ya samu mashin zuwa anguwansu. Bayan mai mashin ya saukesa ya biya shi kudinsa sannan ya dauki Jakarsa da ya zubo sauran kayan da ya ke son ya kyautar da su in zai koma sai ya tafi da wasu daga gida. Jikinsa ba kwari ya karisa jikin get din gidansu ya kwankwansa. Mallam Tajudeen ya zo ya bude karamar Kofar ya na ganin Sadiq ya washe baki ya na fad'in"Yallabai barka da zuwa." Ba wannan Annurin da zumud'in a Fuskar Sadiq yace"Mallam Tajudeen na same ku Lafiya? Ya amsa masa Lokaci d'aya yana kokarin karban Jakar hannun Sadiq. Shi kuma sai ya hanashi ya na dan mirmishi yace"Har gobe ni d'alibinka ne kuma mai biyayya a gareka." Ya na fad'in haka ya sawo kansa cikin Haraban gidan. Sai dai me? Gabansa ne ya yanke ya fad'in hango Abba da ya yi a haraban gidan Jingine jikin Motarsa. Yana sanye da Shadda har da babban Riga waya ya ke yi, sai faman daga Hannu ya ke yi lokaci d'aya ya na ta saba hab'an gefe da gefem Babban Rigansa. Kunya da wani irin nauyin jiki da na zuciya suka lullube Sadiq da ya sa kafafunsa suka kasa daukansa zuwa ga Abba. Cak ya tsaya ya kasa gaba ballatana baya sai kawai ya zabi ya tsaya domin ba shi da karfin gwiwan fuskanta Abba a daidai lokacin da yasan ya ci Amanarsu ya aikata babban al'amari batare da saninsu ko amincewarsu ba. Mallam Tajuddeen ya daga Murya ya na fad'in"Alhaji ga Magajin gida ya iso fa." Abba da ke waya yaji sanda Mallam Tajudden yace ga magajin gida ya iso. Da Sauri ya juyo ya na kallon Sadiq cikin wani yadi mai ruwan kasa shara shara har ana ganin shatin Vest din jikinsa. Sai dai ya na tsaye kansa a sunkuye kamar wanda ya yi ma Sarki karya. Da sauri Abba ya ba ma Alhaji Jibril hakuri da fadin"Mu yi mgana anjuma Alhaji magajin gida ne ya iso yanzu." Dagachan bangaran Alhaji Jibril yace"Au ya dawo ne? Shine ba Labari Alhaji? Abba ya yi dariyan jin dadi lokaci daya ya na kallon Sadiq yace"Kasan halinsa zuwan bazata ya ke mana ni kaina jiya mun yi waya da shi, ammh bai Sanar dani yau ya na tafe ba, ba ri na gansa zan kiraka." Daga haka ya katse kiran cikin Sauri ya fara takawa wajen Sadiq ya na Fadib"Abubakar..!" Dalilin da yasa ya dago kenan shima ya fara takawa zuwa wajen Abba suka had'u da Sauri Sadiq ya rankwafa ya na gaida Abba shi kuma sai ya Rumgumosa ya na fad'in"Maraba da magajin gida maraba da Shalelen Innani." Mirmishin ya ke Sadiq ya yi ya na kokarin kara sunne kansa yau dai Abba ya zama Surukinsa. Shi ko Abba bai ma lura da shi ba Rikesa ya yi ya na fad'in"Shine baka gayamin yau zaka dawo ba? Da ka fadamin da na tura maka Direba ya Dauko ka." Sadiq ya yi mirmishi kafin yace"Abba shiyasa ban gayamaka ba, meyasa da girmana sai na saka an bama wani wahala ya tashi daga Gusau zuwa zariya kawai domin ya Dauko ni? Abba yace"Ka isa ne kada ka manta kai magaji ne kuma shi Magaji ya na da komai." Sadiq ya yi shuru bai yi mgana ba ammh a ransa fad'i ya ke yi a gusau Sadiq ya ke magaji a zariya kuma Abubakar ya ke. Dafa kafad'arsa Abba ya yi kamar wani abokinsa sannan Lokaci d'aya ya karbi jakar hannun Sadiq ya na fadin"Ina Attahiru? Sadiq yace"Ya wuce Daura Abba." Abba ya jinjina kai ya na fadin"Allah Sarki." Sadiq ne yaga Abba na jansa zuwa Shashen Umma yasa ya kallesa ya na Fad'in"Abba ba fita zaka yi ba? Abba yace"Masallacin jumma'a zani Direba na ke jira yaje Dauko yara nan daga makaranta." Da Sauri yace"Abba to bari na shirya sai na tuka ka muje ko? Kallonsa Abba ya yi Lokaci d'aya ya na bubbuga kafad'arsa kafin yace"Da zan so hakan Magaji." Sadiq zame jikinsa ya yi daga na Abba Lokaci d'aya ya na karban jakar kayansa ya na fadin"Bani minti goma Abba." Ya fad'a ya na wucewa bangaransa, Abba ya bi shi da kallon kaunar da Allah kad'ai yasan iyakarta Tsakaninsa da Sadiq. Ya na da makulin Shashensa tare da key din dakinsu na zariya ya had'a waje daya ya na jin shashen a Rufe ya Dauko key din ya Bude ya shiga. Ko'ina Tsab kamar ya na nan ya Tabbata kullum ake gyara masa bangaransa Saboda Halinsa na zuwan bazata. Kayan hannunsa kawai ya ijiye ya shiga wanka saboda kada Abba ya gaji da jiransa. Abba ko Umma ya shiga kwalama kira daga Haraban gidan da karfi"Salamatu. Salamatu.." Da sauri ta fito a firgice ba ita kad'ai ba Hatta Mama itama sai da ta fito. Dukkansu a tsorace har suna had'a baki wajen fad'in"Alhaji lafiya? Ya na mirmishi jin dadi yace"Magajin gida ne ya dawo" Umma ta washe baki ta na fad'in"Auta na? Ya na ina? Abba ya nuna mata bangarensa da baki ya na fadin"Ya shiga ciki ya shirya yau tare zamu tafi masallacin jumma'a." Umma ta saki kayattacen mirmishi kafin tace"Auta ya kyauta ya dawo Lokacin da gidan gabadaya ya yi kewarsa." Abba yace"Barin ma Innani ko jiya sai dai tace wai magajin gida ko lafiyarsa lau? Sulaimanu bazaka je ka duba mana shi kagani ba." Umma ta yi dariya kafin tace"Ina ruwan Innani." Mama na gefe karamin Tsaki taja a ranta ta na mamakin yadda suka Damu da yaron da bai damu da ya zauna da su ba. Ta na jin haushin yadda Daga Umma har Abba basa iya boye kaunar Sadiq ko a gaban waye. Ballatana Innani da zata iya yin komai a kan Sadiq ciki har da Tozarta sauran ya'yan gidan gabadaya. Suna nan Tsaye sai ga jar mota kirar Vibe ta shigo gidan Direba ne ya Dauko su siyama daga makaranta. Motar na gama parking a Haraban gidan suka Firfito. Siyama ce kan gaba Sai Sultana kowacce dauke da Jakarta. Salima kuma na baya ta na yaukinta da ta saba. Wajen su Abba suka karisa ganinsu dukkansu a haraban gidan kamar wani abu ya faru. Direba ne ya kariso ya rankwafa Lokaci d'aya ya na fadin"Yallabai ka yi hakuri mun samu cunkoso ne a hanyarmu ta dawowa.". Abba ya saki kayattacen Mirmishi kafin yace"Kada ka damu garba Magaji ya dawo tare zamu tafi masallacin" Garaba ya washe baki ya na Fadin"Maraba maraba ina yi ma magajin gida maraba da dawowa." Siyama ta ware ido ta na kallon Umma kafin tace"Umma Yaya Sadiq ne ya Dawo? Umma ta gyad'a mata kai ta na yar Dariya ,Tsalle ta daka kafin ta saki ihu ta juya ta na fad'in"Sultana Yaya Sadiq ya dawo wayarmu tazo." Mirmishi kawai Sultana ta yi mata ba ta yi mgana ba. Salima ce ta saki tsaki kafin tace"Yara sai kun shiga SS2 ko za'a siya muku waya" Siyama ta balla mata Harara kafin tace"Ina ruwanki damu? Ke ai kina SS1 a ka siya miki, kuma lokacin muma bamu yi mgana ba." Salima da Saurin harzuka ta kalli Abba ta na fad'in"Abba ka ganta ko? Rashin kunya zata min" Abba na Dariya yace"Siyamar Abba ki kyale Salima kin ji ko? Yayanku zai siya muku waya in sha Allahu kafin ya koma." Mama ta tabe baki kafin tace"Ku wuce ku je ku cire kaya ku huta ko? Suka amsa mata da Toh. Sultana ce a baya su kuma sun yi gaba suna Rigimansu na sako zuwa Shashen Mama ita kuma ta nufi bangaran Umma. Daidai Lokacin Sadiq ya fito ya na kokarim saka links din Rigar shaddar da ke jikinsa mai ruwan Dark Blue dinkin zamani da Hula kube wacce ta hau saman aikin kayan sannan kafarsa cikin Budaden Takalmi Kalan brown sabo ne yau ya taba saka shi sannan agogon Hannunsa ma Brown ne na Fata mai kyau da yarari. Hankalinsa na kan Links din da ya ke Sakawa shiyasa bai ga su Siyama ba. Abba da Umma kuma kamshin Turarensa suka fara shaka shi ya sanar musu wanzuwarsa a wajen. Umma kallonsa ta ke yi cikin Alfahari. Sadiq na Dabam ne acikin zuciyarta duk da ba duka Rayuwarta ta yi tare da shi ba ammh akwai karfafan alaqa tsakaninta da Abunda ta Haifa. Abba ma cikin Tarin alfahari ya ke kallonsa ya na jin wani annuri acikin ransa da Allah ya ba shi Sadiq a lokacin da ya riga ya fidda rai da Samun magaji. Mama kuma kallonsa ta ke yi ta na auna kwarjininsa ba ta isa ta ce ga wani abu na rashin d'a da ya taba Had'a ta da Sadiq ba, bai taba nuna mata bambamci Tsakaninta da Umma ba, bai taba nuna bambamcin Tsakanin ya'yanta da ya'yan Umma ba. Zuciyarta ta kasa jin Haushinsa Saboda Tarin kyakyawan Dabi'unsa. Siyama da Salima sun shige Shashen Mama ba su lura da shi ba. Ammh Sultana ta ganshi shiyasa ta tsaya kyam ta na kare masa kallo Zuciyarta na Harbawa. Sai yanzu da ta kara wayau sannan ta had'u Da Sabbin kawaye a makaranta ta kara sanin muhimmancin Sadiq a Rayuwarta. Ba ta san ta Tsaya ta na kare masa kallo ba, ta shagala da alfaharin yanzu wannan Had'adden gayen na ta ne ita kad'ai tuni wani alfahari ya cika kirjinta tare da wani kaunar Sadiq da tun daman ta na cikin zuciyarta Boyewa ta yi, lokaci d'aya kuma kishi ya zo ya lullubeta na yadda zai fita har wasu matan su kalle mata abunta. Sultana bata gama Fahimtar kanta ba ammh ta riga ta tabbatar da abu d'aya. Ta na cikin Sahun mata ma su mugun kishi kishi ma na Hauka, ba ta kaunar taga wani ya rab'i da abunda ta ke so bata so ta kare rayuwarta a haka kamar yadda mahaifiyarta ta rasu ta bar duniya ta bar Baba da wasu matan kuma ya na cigaba da Rayuwarsa. Ba ta son ta yi aure ta rika rab'a mijinta da wata kamar Umma da Mama, ba ta son ta yi auri taga wata matar na haihuwa da mijinta da ta ke so bayan ita, ba ta son ganin ya'yanta sun taso kamar su Salima da su Anty Surayya ta fi son komai in ya kasance nata ne to ya zama natan har gaban Abada nata ita kadai da bazata taba sharing d'insa da kowa ba. Ta na cikin wannan Tunanin bata sani ba har ya gama saka Links dinsa ya Dago da kansa da su Umma ya fara cin karo suna masa mirmishi. Shima cikin sauri ya maida musu da martanin mirmishin nasu sai dai ya yi Saurin kauda kansa gefe saboda ya na jin nauyin Umma da Abba a kan abunda ya aikata ba da sanin su ba. Inda ya kai kallon nasa ne ya hango Sultana Tsaye kofar bangaran Umma cikin kayan makaranta goye da jaka a bayanta. Abunda ya ba shi mamaki abu d'ayane zuwa Biyu, na farko ta yi kiba kamar ba wannan siririyar yarinyar Sultana ba na biyu kuma kuresa da idon da ta yi yasan tare suka ta shi a karkashin Rufi d'aya ammh bai taba sanin Sultana da kallo haka ba. yarinya ce mai kunya da shuru shuru. Ya yi mamakin yadda ya ke kallonta ido cikin ido itama kuma ta na kallonsa bata Dauke idanuwanta ba. Bai dauke kansa ba sai da yaji Umma na kiram sunansa sannan ya Sauke Numfashi ya karisa ga Umma ya Rankwafa ya gaisheta. Ita ma kamar Abba Rumgumesa ta yi ta na fadin"Auta na ya kara girma." Ya na mirmishi yace"Umma ta kina lafiya? Ya fad'a ya na shafa fuskarta acikin ransa kuma fad'i ya ke Umma ki yafemin na yi miki Laifi. Cikin jin dadi Umma Ta rike hannunsa ta na fadin"Lafiyata kalau sai dai ina kewar Auta na." Kai ya kad'a kafin yace"Umma zan yi dogon Hutu wannan karon Autan ki zai dade tare da Ummansa." Umma ta washe baki ta na kallon Abba kafin tace"Da gaske Auta? Kai ya gyad'a mata sai kawai ta Rumgumesa ta na fad'in"Allah ya yi maka albarka Abubukar Sadiq" Ya amsa mata da Ameen Ameen shi da Abba. Sai a lokacin yaga Mama sakin Umma ya yi ya karisa gabanta ya Rankwafa ya na gaisheta ta saka hannu ta Dagosa ta na amsa cikin Sakewa. Jinjina kai ya yi Lokaci d'aya ya na fadin"Mama duk kuna lafiya ko? Mama tace"Lafiya kalau mu ke Sadiq ya zariyan? Ya amsa mata da Alhamdulillah, Abba ya duba agogon Silban da ke hannunsa ya na fadin"Zamu makara fa Magaji." Da Sauri yace"Mu je Abba." Key din motar ya mika masa ta kamfanin Toyota. Sadiq ya shiga gaba Abba na binsa a baya su Umma suka rakasu da Allah ya tsare. Ba su bar wajen ba sai da suka ga Fitan su daga gidan sannan kowacce ta nufi bangaranta. Umma bangaren Innani ta leka Allah Sarki ta iske ta barci ya kwasheta a kasa daga zaune sai ba ta tasheta ba ta koma bangarenta da Niyar in da idar da Sallah sai ta koma ta tasheta. Ko kafin su Abba su dawo masallaci Umma ke da girki Ranar ita da Sultana da Hajiya yar aikinta sun gama had'a komai na abincin rana. An kai na shashen Mama, Abba kuma da na Sadiq Umma tace akai bangaran Abba tunda tasan in suka dawo zasu zauna tare su tattauna. Na Innani ne Umma ta Umarci Sultana da dauka ta kai mata sannan ta tasheta ta yi sallah. Sultana ba ta yi niyar zuwa ba saboda tun jiya su ke fad'a da Innani daga jiya da Safe kafin su tafi makaranta ta shiga gaisheta sai tace ta kunna mata Tv tashar Larabawan nan. Ba musu ta zo zata kunna sai Tv ya ki yi ashe kan soket din ya lalace. Innani taji shuru ba'a kunna ba ta kara mgana Sultana tace ya lalace. Ai Innani bata jira taji me ya lalace ba ta fara salati ta na salallami da cewa Sulaimanu ya siya mata Tibi ammh Sultana ta lalata mata Saboda mugunta da keta. Ita kuma Sultana taji Haushi tace ba ita bace sannan ta daina ce mata muguwa. Ai ko Innani ta harzuka ta lalubo sandarta ta daidai Saitin Sultana ta Rafka mata sai a saman kafarta sai da wajen ya kumbura sannan bai isheta ba ta bita da Zagin cewa Albasa ba ta yi Halin Ruwa ba, ba Halin Kuluwa ta Dauko ba bakin Hali da mugunta na Ubanta shitu ta gado. Sultana na kuka ta bar bangaren Innani ta kuma yi alkwarin sai ta nemota bazata kara komawa ba jiya kam duk wanda ya shiga sai ta gayamasa Sultana ta lalata mata Tibinta Saboda muguntar da ta gada wajen Ubanta Shitu. Saboda Umma ce shiyasa ta kasa mata gaddama. Ganin ta na Tura baki yasa Umma ta yi dariya ta na fad'in"Ke da Kakarki taki kuma yau Sultana? Ba mai ji kan ku fa ke da Innani." Sultana ta kwabe fuska kafin tace"Muguwa fa ta ke kirana yanzu." Umma tace"Ki je ki kaimata zaku shirya ne." Ba ta da Halin yin musu sai ta yafa mayafin Maryam's Egyptain Abayan da ke jikinta mai kalan sararin Samaniya https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V +201123302418 Sannan t Dauki Farantin abincin Innani zuwa Banagaranta. Ta na shiga ta iske ta bata Falon ga dai Sandarta da gilashinta nan. Dankwafar da abincin ta yi a kasan Cafet din sannan ta saka kafa ta shure sandar Innani kamar itace da kanta ta Daketa. Innani da ke cikin Dakinta bayan ta idar da sallah taji motsi daga ciki ta wage Murya ta na fadin"Waye nan? Shuru ba'a yi mgana sai kawai Innani ta yi tsaki ta na fadin"Ko ma wani shegen ne kada ya yi magana. A fitar min daga daki tunda ba d'an wani ya gina min ba Ehe." Sultana na jin haka bata kara ko Second ba ta fice daga bangaren innani da gudunta. Innani ta ji gudun sai dai bata san ko waye ba kyafci ta yi kafin tace"Yanzu haka cikin ya'yan Suwaiba ne. Ina ga ja'irar nan ne Salima Mara kunya." Bata san cewa Yar gaban goshinta ba ce Sultana da suka yi fad'a. Sultana na komawa tace ma Umma ta kai mata Umma ta kalleta ta na Fad'in"Kin ta sheta ta yi sallar? Sultana tace"eh" Saboda in tace a'a Fad'a Umma zata yi mata.. Daman tare suke cin abinci da Umma suna zaune a tsakiyar falo Sajida ta kira wayar Umma ta Dauka suna mgana anan taji Umma na cewa Yaya Sadiq ya ce zai jima a wannan Hutun kafin ya koma haka kurum taji sanyi acikin ranta ko bakomai zata rika ganinsa Sosai ta na jin dadi. Abba da Sadiq suna dawowa masallaci suka yada zamansu a shashen Abba tare suka ci abinci suna ta Hira duk da yawanci Hirar ta Abba ne kuma hirar kasuwancinsa ne. Shi kuma Sadiq ya na ba shi amsa ya iya abunda ya sani duk da bai karanta kasuwanci ba ammh mu'amala da Abba da sanin wasu al'muransa yasa yasan wani abu da yawa akan kasuwanci. Sadiq ya gaggayama Abba wad'anda suka kirasa daga Shinkafi. Ciki harda Goggo Husai na mganar Yarta ta samu gurbin karatu a jami'ar Buk kano zata karanta low ta na Bukatar taimako. Abba ya kalli Sadiq kafin yace"Ita dai Husai bata jin mgana na fa gayamata ta yi ma yarinyar nan aure tunda y'a macece karatunta ba Dole ba ne." Sadiq ya kalli Abba kafin yace"Abba karatun y'a mace a wannan zamanin Dole ne, kamar yadda Namiji ya zama Dole ya yi ilimi domin ya Tsaya da kafafunsa haka itama mace zata yi wannan Ilimin domin ta tsaya itama da Kafafunta." Abba yace"Ita fa mace mutumcinta shine gidan auranta." Sadiq ya murmusa kafin yace"Ban ki mganarka ba Abba. Kowa yasan aure shine cikar kamala da Mutumcin y'a mace. Ammh kuma ka sani wannan kimar ba ta cika ta zama Daidai sai mace ta samu cikakken ilimin addini da na zamani saboda ita ce uwa kuma mata sannan yaya ce in ba ta da ilimi bazata gyara zamantakewarta ba Abba." Sai Abba ya yi shuru alamun ya na gamsuwa da mganar Sadiq. Ganin haka yasa Sadiq ya cigaba da Fad'in"Abba duk wanda ya ilimantar da Mace guda d'aya kamar ya ilamantar da duka Duniya ne gabadaya. Ka da ka kara fad'in wannan kalmar saboda kada ka fad'a gaban wani da ya ke ganin girman ka Abba, kada ka auna kai ya'yanka sun samu mazaje da wuri ammh ai sun cigaba da karatunsu a gidajen mazajen su yaki da karatun ya'ya mata a wannan zamanin Jahilci ne Abba." Da Sauri Abba yace"Hakane na bari. Za'a taimaka in sha Allahu sai kuma me? Nan ya shiga zayyana masa duk wayar da suka yi masa ya na makaranta kananun da zai iya musu mgani ya yi musu wad'anda suka fi karfinsu daman yace zai fad'a ma Abba. Nan take kuma Abba ya bashi Umarni a taimaka musu Sadiq da kansa ya rika kiransu yace su turo acct lambar da za'a sanya musu kudi. Zamansu bai tashi ba sai da aka Biya ma kowa Bukatunsa Alhaji ya sha addu'a Sadiq sai masa Fatan gamawa da Duniya lafiya suke yi. Sannan Sadiq ya rika yi ma Abba nasiha kan riko da zumunci Abba ya sunkuyar da kai domin yasan ba shi da wannan. Sadiq ya kallesa kafin yace"Abba yaushe rabonka da kaje shinkafi ka gaida yan'uwanka? Abba ya yi jim kafin yace"Ina jin tun zuwan da muka yi tare. Kasan ba na samun zama ne Magaji" Sadiq yace"Abba naji baka zama ammh waya fa? Itama ai ana zumuncin da ita ka ware Lokaci duk sati ka rika kiransu kuna gaisawa nasan a baya suna kiranka gajiya suka yi suka kyaleka. Abba ka sani Allah ne ya Umarcemu da mu Sada zumunci sannan yace mu yi zumunci da wanda bai yi damu ba, Sannan yace ya tanadi Aljannnah ga ma'abota sada zumunci wanda kuma ya raba zumunci ya barranta da Abunda Allah ya yi mana Umarni." Abba ya jinjina kai kafin yace"Hakane." Sadiq ya cigaba da fadin"Abba ka na da Halin da zaka taimaka musu da abunda Allah ya baka don Allah ka Sada zumumci da yan'uwanka sannan ka ja su ajikin ka bayan su baka da kowa yau ko mutuwa ka yi ba mu da wajen da zamu je mu sai wajen su." Abba ya fara matsan ido ya na Fadin'"In sha Allahu zan gyara, Daman Innani ce....!" Sadiq yace"Abba Innani akwai Rikicin Tsufa tare da ita. ka daina biye mata kai dai kayi abunda Allah yace ai ba komai in zaka yi ma yan'uwanka sai ta sani ba." Abba ya kad'a kai ya na fadin"Allah ya yi maka albarka Madallah da Nagartattacen d'a kamar ka." Sadiq bai bar shashen ba sai da Abba ya tabbatar masa da zai gyara zumunci da yan'uwansa in sha Allahu. Sadiq shashensa ya koma ya kwanta Saboda ya Huta. Sai ga kiran wayar Tahir ya na Dauka yaji sa ya na zaginsa tare da Fadin"Baka iya kira kaji ya Mutum ya isa ko? Sadiq na lumshe ido yace"Ka isa lafiya? Ya su Hajja? Tahir ya yi tsaki ya kashe wayarsa. Sadiq ya wancakalar da wayar gefe ya na mirmishi. Karaf sai ta fad'o masa a rai kuma ya yi alkwarin zai rika kiranta. Da Sauri ya ta shi zaune ya Dauko wayar ya nemo lambarta ya kira. Sai dai har ta katse bata Dauka ba sai ya kara kira nan bata dauka ba. Sai wata zuciyar tace"Ko dai ta na kitchen ne? Ko kuma ta na waje ba." Da haka ya koma ya kwanta ammh wayar na Hannunsa ya Kurama lambarta da ya yi Saving da SIYA ido. Ita ke mai gizo a fuskarsa tunata da ya yi kawai sai da yaji jikinsa ya Dauki Dumi. Hannunsa ya jimke ya lume kansa jikin Filo ya na jin kamar alokacin ya rika hannunta cikin nasa hannun Dumin hannunta na ratsashi har kwakwalwarsa. A haka barci ya kwashe shi sai Hudu Saura ya tashi ya sake yin wanka ya Saaka Saukakkun kaya. Abba ranar ya na gida bai fita ba, tare suka fita masallaci achan ma wani bawan Allah na neman taimako matarsa zata haihu a asibiti kuma za'ayi mata aiki. Sadiq yace ma Abba suma zasu taimaka kudin dake Aljihun Abba duka Dubun goma Abba ya ba da sai ga shi lokaci kad'an an had'a masa ya kai Dubu arba'in tunda akwai masu kudi irin su Abba sosai. Sai dai wasu ba zuciyan yi ne in kuma an yi dace da ya'ya irin su Sadiq a gefe sai su zama ya'ya nagari masu kai Mahaifansu ga Tudun tsira. Suna Dawowa Abba yace bayansa ke ciwo bari ya kira Umma ta Shafa masa mam zafi. Sadiq na jin Haka yace bari shi ya shiga bangaren Innani su gaisa. Da yaso ma yace su je ya shafa ma Abba ammh jin ya ambaci Hajiya Umma ya sa ya gane wannan karon ba'a bukatarsa Lokacin Umma ne. Kai Tsaye Shashen Innani ya shiga ba kowa shuru Falon nata. Sai dai ga Farantin abinci nan da ta gama ci ga gilashinta a wajen. Innani da ta shiga makewayi ta yi alwala tazo ta yi sallah bayan ta idar ta fara Laluban gilashinta bata gansa sai Sandarta. Sai ta fara bin bango ta na ta masifa fad'i ta ke yi"Kai Allah ya rabamu da abun nasara masu jajayen kunnuwa ba su da tabbas yanzu yanzu ace gilashi na ido na na nema na rasa? Tabbas watarana zan iya fad'i ma na nakasa kaina in dai da wannan gilashin na Dogara." Sadiq na falon ya na jinta sai da ya Murmusa. Da Dafa bango ta fito falon ta na Fadin"Bawa ace ya na tafiya ya na Lalube kai jam'a? Ga dai mutane a gidan ammh duk ba ma su mutumci ba ne sun barni ni kadai a katon wajen wato Dije ci kanki kenan." Kyafci ta yi cikin takaici Sadiq ya yi yar Dariya har Innani taji Sautinta. A zatonta cikin su Siyama ne a Fusace tace"Ko wace ja'ira ce uwarki dai ki ka yi ma dariya ba ni ba." Wajen gilashinta ya isa ya Dauko mata yazo har gabanta ya saka mata Lokaci d'aya ya na fadin"Kakata." Innani na jin Muryansa ta ware idanuwanta ta cikin gilashin ta na fadin"Muryan wa na ke ji kamar ta magajin gida? Sadiq ya kara taro Fuskarsa gabanta ya na fadin"Ko har yanzu baki ganin ne? Da Sauri ta saki Sandar hannunta ta Rikosa ta na sakin kabbara. Sai kuma ta fashe da kuka yasan Halinta yasa ya jata kan kujera ya zaunar da ita, sannan ya koma ya Dauko mata sandanta yazo ya zauna kusa da ita ya saka mata Sandar a Hannunta, lokaci d'aya ya na fadin"Innani gayamin waye ya tabamin ke a gidan nan yau mu raba gari da shi? Innani na faman goge hanci da Haban zaninta tace"Kana dai gani a wulakance nake acikin gidan nan ba mai dubani kamar mayya Sulaimanu ne in yazo da Safe kuma sai Dare kasan sa da Sabgogi., salamatu ce kuma yanzu itama ta Lalace suwaiba ta zugata, Siyama da Salima daman marasa kunya ne ba su da wani amfani Sulsana ce ke kula dani itama inaga uwarta ta zugata jiya da yau ko Kafarta ban gani ba." Sadiq na jinjina kai yace"Gaskiya ko in hakane ba su kyauta miki ba. To yanzu ya kike so ayi? Innani na jan Hanci kamar gaske tace"Yauwa Dan albarka daman nasan inda ka na nan hakan bazata Faru ba. Ni dai na gaji da zaman nan kawai ka tafi dani chan ina ne ma in da ka ke karatu? Sadiq ya yi Tagumi kafin yace"Wai Zariya Innani? Innani tace"Koma ina ne ka tafi dani su ci kansu in ina da amfani a gidan ai za su sani daga baya." Sadiq yace"To innani ta ya za'ayi na tafi dake zariya? Dama na yi aure ne sai na tafi dake gidana ki zauna in su ba sa sonki ni ina kaunarki." Innani na jin haka sai ta yi shuru shi kuma fadin haka yasa sai Hasiya ta fad'o masa a rai Innani ce ta katseshi da cewa'"Kuma fa hakane? Ko na jira in an yi auranka da Sulsana sai na koma gidan ku da zama? Kai Tsaye yace"Yauwa hakan ma zai fi." Innani ta washe baki kafin tace"Haka za'ayi ammh ka yi shuunka kada Sulaimanu yaji sai kaga yaji Haushi kasan mutum sai Allah." Sadiq yace"Sosai Innani ai ba wanda zai ji sirri ne tsakanin mu " Nan fa Innani ta gyara zama ta shiga basa labarin duk abubuwan da suka faru da bayanan harda Labarin Alhaji Jibril da zuwansu da maganar da ya zo da shi. Cikin mamaki yace"Ni kuma? Ina zan kai mata uku Innani? Sai da yaji Innani tace"Mata uku kuma? Sannan ya dawo hayyacinsa da Sauri yace"Ina Nufin Sultana ta isheni Innani." Innani tace"Kwarai ai na yi musu Fata Fata daga uban naka har abokin sa na kuma ce ko bayan raina ban amince ka yi ma Sultana kishiya ba. Kaganni nan ko ni da na ke jan wuya na sha wahala kishiya ballatana Sulsana da ta ke jinta kamar wata gaula kai sai da sukaji nace ko kai ne ka yi mata kishiyan da kanka ba ni baka sannan nace Allah ya tsine ma wand daura aur..!! "Innani.." Da sauri Sadiq ya katseta da kiran sunanta ya na kuma kallomta cikin mamaki. Dariya ta saka kafin tace"Ahto suma haka suka Tsorata da kalamaina ai sai kaji mgana ta mutu na dai ce ga mara kunyar nan Salima in suna so sai ayi had'in zumumcin da d'ansa da ya zo da shi wani Dan Saurayi haka a fuska dai kamar na Allah ba'a son abunda ke cikin ransa ba kuma." Innani na bayaninta ne ammh kwata kwata Hankalinsa baya kanta. Ya Fahimci Innani da gaske ta ke yi ba wasa ba ne a mganarta. Yasan tun ba yau Innani ta tsani kalmar kishiya da an fara mgana zata fara ba da Tarihi tun auranta da kakansu da wahalan da ta sha hannun Mahaifiyarsu Baba Sammani. Shi dai har ya bar shashen Innani bai gane wasu maganganunta ba. Siyama ce tazo ta na damunsa da mganar waya ce mata kawai ya yi za'a siya mata. Sun fara fad'a da Innani akan wai ta shigo mata Daki da takalmi ya samu ya Sulale ya barta. Har dare kuma Hasiya bata kirashi ba ko bata ga kiran nasa ba ne? Su na dawowa sallar isha'i duk suna Bangaren Innani shi yace ya gaji zai je ya kwanta shiyasa ba wanda ya matsa masa. Ya na koma bangaransa ya sake kiranta sai lokacin ya sameta. Hankalinsa ya kwanta da ya tabbatar da ta na lafiya. Ni ko da yanzu na koma rayuwar ni kadai in ba na ido biyu to ina barcin dazun ma ina barci ya kirani. Da na zo na gani kuma ma kirasa bansame ba. Har ina tambayansa sun sauka gusai lafiya? Ya ce min lafiya lau. Ban dauka zai jani da Hira ba sai naga ya jani da mgana duk da ina cikin Damuwa ammh lokaci kad'an sai ga shi na warware muna ta Hira. Mun fi awa d'aya muna mgana sai da ya fara Hamma sannan muka yi sallama. Da Asuba kuma wayarsa ya tasheni ba domin shi ba kila har sai na makara bansani ba ina chan ina barci. *LAME NIG!* *KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*. *AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*. *KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA* *KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?* *KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?* *TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*. *BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.* *TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*. *KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*. *ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU* *Janafty* *TMWB2K011* https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj *LAME NIG!* *KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*. *AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*. *KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA* *KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?* *KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?* *TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*. *BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.* *TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*. *KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*. *ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU* Baisan meyasa ya maida kiran Wayar Hasiya kamar Ibada ba, sai dai ya na d'ora haka akan mizanin alkwarin da ya yi mata na zai rika kiranta lokaci bayan Lokaci. Kullum da Safe in ya tashi Sallah sai ya kirata ya tasheta saboda ya Fahimci wani abu Hasiya kamar Tahir ne suna da Rauni bangaran Ibadunsu. Da rana ma zai kirata yaji lafiyanta haka da daddare ma kafin ta kwanta, duk da ba wata hira ke shiga tsakaninsu ba ammh a kallah ya na samun natsuwar zuciya na jin ta a koda yaushe. Gabadaya kansa ya cushe ya rasa ma wani Tunani ya kamata ya yi. Ko da ya yi tunanin ya sanar da su Abba sai wata zuciyar ta hana shi ta na fad'amai bai kamata ba. Ga yadda ya tsara tun farko gwara ya tafiyar da Tsarin a haka in kuma ya yi Tunanin Sauya tsarinsa to za'a iya samun wata matsalar da ba zai yi masa kyau ba. Tunda ya dawo bai da aiki sai zama a bangaransa Tunda ba inda ya ke zuwa da yammah ne ya kan leka wajen Mallam Tajuddeen su yi karatu. ko shashen Innani da ya saba zama yanzu ya daina zama Sosai da ya shiga sun gaisa ya d'an zauna kad'an zai tashi ne ya koma bangaransa. Shashen Umma ko bai taba zaman minti talatin ba gabadaya iyayen da yan'uwansa sun fahimci wannan zuwan nasa ya sauya ba ya son nuna Fuskarsa garesu ko ya zauna da su. Shi ko kunya ce da Nauyi yasa ya ke tsame kansa daga gare su ya na Tunanin kamar a fuskarsa zasu iya gane abunda ya aikata. Ya zauna ya yi tunanin taimakon da ya kamata ya yi ma Hasiya kafin Rabuwarsu, ya kasa tsaida mafita d'aya kuma abun takaici bai taba samun kyakyawan zama da Hasiya ba ballatana yasan abunda ta ke so. Ya yi tunanin ko ya maidata makaranta ne ta cigaba da karatun ta? Sai kuma yaga kamar ya zake da yawa ba shi da wannan kud'in yanzu Tunda ba aiki garesa ba. Ko kuma ya bata jari ta fara kasuwancin da zata rike kanta? To in yace haka wani sana'a zata fara? Sannan in ya saketa ina zata koma? Har Tunanin ya kara kama mata hayan gidan nan na Shekara biyu saboda ta samu inda zata zauna. Shima sai yaga wannan Tunanin ba abun da zai yuyu ba ne. Saboda yar Damuwar da ya ke ciki har Rama ya yi duk ya yi wani zuru Zuru, Saddiqa da ta zo daga Kebbi ganin gida da ta gansa sai da ta yi mgana a shashen Umma. Kallonsa ta yi lokacin da ya shigo bangaran Umma su gaisa ga yaran gabadaya duk sun zagayeta. Har da Innani da ya ke ta na yin Saddiqan saboda Hakurinta sannan sosai take ji da Innani sako akai akai zakaji tace ga sakon Innani. Sai da suka gama gaisawa sannan ta kallesa tace"Autan Umma ya naga duk ka rame ne? Gaskiya zaman ka a zariyan nan duk ya sauya ka kamar ba kai ba." Kansa kawai ya shafa yana Mirmishi bai ce komai ba, Sultana da ke gefe ta rika satar kallonsa ta gefen ido ta na so taga irin ramar da a kace ya yi. Kuma itama ta lura kwana biyu nan ba shi da walwala sannan ya yi d'an wuya. Umma da ke gefe ta kallesa kamar bazata yi mgana ba sai can tace"Ni kaina naga Auta duk ya chanza, ya rage shiga mutane ko shashen da ya saba Zama yanzu ya daina zama sai dai ya kule cikin shashensa shi kad'ai ni na rasa me ke damun sa wlh." Innani na gefe ta tabe baki ya na fad'in"Ba na yi mgana an ki saurarena ba, In ku ka ga Namiji ya fara wannan Tsirfe Tsirfe Aure ya ke so mace ya ke so kusa da shi." Gabadaya aka kallo Innani ita ko ajikinta ma Siyama ta kalli Sultana suka kunshe kai suna Dariya. Sadiq kuma ko kala bai ce ba ya mike kawai ya fita suka bisa da kallo. Umma ta ce"Kun ga ni ko? Ni har kuzarinsa ma ya ragu ko bai da lafiya ne? Innani ta yi tsaki kafin tace"Ina gaya muku ga matsalarsa kuna zencen wani ba shi da lafiya? Yo ba shi da lafiya mana Tunda aure ya ke so." Umma ta yi shuru ba ta yi mgana ba, tunanin ba aure Sadiq ya ke so ba zaton wani abu Dabam ke Damunsa. Saddiqa ce tace"To Innani ai ta kwana gidan Sauki? Ga kanwarmu a gefe sai a yi auran kawai ba shikenan ba." Innani ta gyad'a kai kafin tace"Ahto Gwara dai asan abun yi kafin lalurarsa tasa ta fi haka." Sultana sai mirmishi ta ke yi kanta a kasa Siyama ta yi ma rad'a a kunne sai ta tsunguleta. Suna ta dariya Salima na gefe ta kallesu cikin Harara, Siyama ta tura baki ta na fad'in"Ina ruwan ki damu." Salima sai ta yi karamin tsaki kafin ta mike ta shige dakin da Sultana ta ke kwana Saboda ta gaji da wannan Hayaniyar. Bayan Barin Salima Falon Saddiqa ta kalli Umma ta na fad'in"Umma baza ku duba mganar Innani ba? Auta duk ya wani susuce ko dai baya jin dadin zaman zariyan ne? Umma tace"Ai shi ya zabi chan Saddiqa mganar auransa da Sultana kuma an yi mgana kwanaki chan baya shi Sadiq din da kansa yace ba yanzu ba.." Saddiqa cikin mamaki tace"Meyasa Umma? Umma ta sauke Numfashi kafin tace"Kinsan Halinsa dai yace shi sai ya gama bautar kasa kuma ya samu aiki." Saddiqa tace"Wannan ba Hujja ba ne Umma, Abba na da muhalli da zai ije sultana ko da ace ma a nan gidan ne, kuma ya kula da su ba su ba ma har ya'yan su." Umma ta yi shuru kafin tace"Uhm ki na ganin Auta zai yarda ne? Saddiqa tace"Umma dole sa ya amince tunda ga shi nan ya fara rama a tsaye bari Abba ya dawo zan yi masa mgana." Umma dai ba ta kara mgana ba, Innani kuma na gefe ta na Taunan goranta da ta gama kankarewa. Bakam ta yi ta yi kamar bata ji ba Saboda lamarin gabadaya ya fara bata Haushi me ake jira? Wannan ai sai Allah ya yi fushi da su sun ki cika Umarninsa na had'a sunnar ma'aiki. Sadiq baisan da mganar Saddiqa na zata samu Abba da mganar ba. Ballatana Maganar Innani abunda yasa bai tanka ba yasan ba wanda ya isa ya yanke masa wani abu acikin Rayuwarsa batare da cewarsa ba. Ganin da ya yi har su Umma sun fara Zargin wani abu na Damunsa sai ya yanke shawaran tafiya Daura ya kwana Biyu wajen Tahir daman kuma zai je ya Duba Hajja tun ciwon da ta yi kwanaki bai je ya gaisheta ba. Sai ya fara shirin tafiya batare da ya fad'a ma kowa ba, Da Tahir kad'ai suka yi mgana duk da bai saka masa ranar da zai zo ba. Saddiqa ta dad'e bata zo gusai ba shiyasa zata d'an kwana Biyu a gida, Maganar da tace zata yi ma Abba basu samu zama ba sai dai sun yi magana da Surayya tace ta bari ta shigo gidan sai su yi mgana su san me za su fad'ama Abba in sun je gabansa. Shiyasa sai ta dakata da yi ma Abba mganar Ita kuma Innani ta Samu abunda ta ke so ta dinga mganar Daman ta fad'a ammh aka ki jin mganarta ga shi nan Magajin gida zai lalace a tsaye. Ita surayya ita ta kira sauran yan'uwan duk ta sanar da su, su daman sun ce Sultana su ke ji ganin ta yi kankanta da yawa ammh tunda abun ya zama haka sai ayi auran sai su reni juna a tare. Ana gobe Sadiq zai je Daura Daddare ya kira wayar Mama yace ta turo masa Siyama yanzu zuwa bangaransa. Siyama na jin haka ta ruga da gudu ta san kiran Yaya Sadiq samu ne yawanci. Tana zuwa yace taje ta kira masa Sultana su zo tare, Da sauri ta je Shashen Umma ta kira Sultana bakinta washe Allah yasa wayar ce aka siya musu. Tare suka dawo ya na zaune acikin Falonsa ga kwalayen wayoyi nan a gabansa na Samsumg guda Biyu. Suna shigowa Siyama ta kyalla ido taga wayoyi sai ta washe baki jikinta na rawa da bakinta. Dukawa suka yi a kasan cafet suka gaisheshi ya amsa kai tsaye kafin ya kallesu gabad'ayan su. Cikin kaushin murya yace"Kun san meyasa na kira ku? A tare suka girgiza kai, kwalin wayar ya Dauka guda d'aya ya mikama Sultana ta saka Hannu ta karba itama Siyama ya bata nata ta karb'a bakinta na rawa tace"Namu ne Yaya Sadiq? Kai ya gyad'a mata kafin yace"Naku ne Abba yace a siya muku." Siyama ta saka Ihu ta Rumgume wayar ta na fad'in"Thank u Yaya Sadiq mungode sosai." Kai ya jinjina kafin yace"Ku yi ma Abba addu'an Gamawa da duniya lafiya." A tare suka ce"Allah yasa Abba ya gama da duniya lafiya." Ya amsa da Ameen. Kafin ya cigaba da fadin"kowacce akwai layi acikin wayarta. Ba an siya muku wannan wayar ba ne domin shashanci saboda ta taimake ku akan karatun ku ne kun ji ko? A tare suka toh za su kiyaye. Kai Tsaye ya sallame su suka mike suna Murna suka fice ya bisu da kallo. Ranar gidan nan ya cika da Murnan Siyama karad'inta kad'ai ake ji. Bayan sun yi chaji haka kiran sauran yan'uwansu ta na fadin Siyama ce sun yi waya ita da Sultana. Salima na kallonta ta tabe baki ta na fadin"Siyama gaskiya ke yar kauye ce ji fa abunda ki ke yi? Siyama ta tura baki ta na fadin"Eh d'in naji." Sultana kuma ta na chaza wayarta abu d'aya ta fara yi Lambar Sadiq ta fara sakawa daman kuma ta Hadaceta a kanta, Kuma da ya ke an saka musu 2k katin waya shi ta fara kira. Shi dai yaga bakuwar lamba ta kirasa ya na Dauka kawai yaji Muryan Sultana ta na fadin"Yaya Sadiq ni ce Sultana ce." Cikin mamaki yace"Sultana.."? Mirmishi ta yi masa ta cikin wayar kafin tace"Eh ka yi Saving din lambata." Sai ya jinjinamata kai kamar ta na ganinsa, sannan suka yanke kiran a tare. Mamaki ya cika shi sai dai kuma ya share mamakin nasa ya yi Saving din lambar nata kamar yadda ta bukata da sunanta wato SULTANA. Sai da asuba suna hanyar dawowa masallaci ya fad'a ma Abba zai je Daura. Abba yace ga Direba sai ya kaisa, Sadiq yace baya bukata saboda ba yau zai dawo ba sai ya kwana Biyu. Abba ba shi da yarda zai yi Tunda yasan Halin Abunda ya Haifa. Sai da ya gama shirinsa ya fito da karamar Jakarsa ta baya sannan ya shiga ya yi ma Umma sallama itama sai ta rika masa Fad'an meyasa bai gayamata da wuri ba. Kansa na kasa yace"Umma ki yi hakuri." Umma ta kallesa kafin ta kira sunansa"Abubakar.." Cikin mamaki Sadiq ya Dago ya na kallon Umma kafin yace"Na'am". Cikin mamaki saboda bai taba jin Umma ta kira sunansa kai tsaye haka ba, ko ba ta ce Auta ba sai dai tace Saddiqu. Cikin idanuwansa ta kallesa tace"Me ke damunka ne kwana biyu nan? Cikin Sauri yace"Umma me ki ka gani? Hararansa ta yi kafin tace"Bansani ba! Ji yarda duk ka wani susuce ina maka mgana kana ce min me na gani." Sai ya yi shuru kawai ya sunkuyar da kansa na wani Lokaci kafin ya Dago ya na fadin"Umma ni fa ba abunda ke damuna" Umma ta kura masa ido shi kuma sai ya kauce ma kallonta saboda kada ta Fahimci ba shi da gaskiya daga cikin kwayan idanuwansa. Umma sai kawai ta kad'a kai bata kara mgana ba. Bata da komai da zata ba shi ya kai ma Kakar Tahir sai cikin Atamfofin da Saddiqa ta zo mata da shi ta dauko guda daya sai ta hado mata da sabon Hijabin cikin wad'anda ta dinka ma Sultana sai turaren wuta na Rushi da na Tsinke, har da na fesawa. Ta kawo ma Sadiq tace ya kai ma Hajja kakar Tahir tunda shi tafiyarsa da zuwansa ba ma wanda ya isa ya sani Kansa na kasa yace"Ki yi hakuri Umma." Bata kara mgana ba ta koma ta zauna ta na latsa wayarta sai da ya mike yace"Umma sai na dawo" Kai Tsaye tace"Allah ya tsare ka gaishe su." Har ya fice ta na kallonsa Idanuwan Umma ya ciko da kwallah a fili ta Furta"Me ke damun Auta na ne? Bata da wannan amsar ammh in dai maganar Innani gaskiya ne to zata ba da goyon bayan auran nan yanzu saboda ya samu natsuwa sannan kowa ma ya Huta. Bangaren Mama yaje itama ya yi mata sallama itama sai da ta yi masa Korafin tafiya ba sanarwa haka Sadiq? Itama Hakuri ya bata, ta ce bakomai itama ba ta da abunda zata ba shi shiyasa ta Dauko masa Dan kunne da Sarka da abun Hannu sai Sabulun wanka mai kamshi ta had'a masa ta ce ya kai ma Kakar Tahir, Saboda Itama Hajja na da kokari Tahir baya zuwa hannu Rabbana abubuwanan na Mutanen chan duk ta na ba shi yazo mu su da shi. Bangaren Innani ne karshen shiga chan ya iske Saddiqa suna Hira. Saddiqa kam sai da tace"Kai kam Sadiq baka da Dabi'a. In zaka yi tafiya ba sanarwa ba kyau fa irin wannan." Kallonta kawai ya yi bai yi mgana ba Innani kuma sai kawai ta mike tace bari ta shirya su tafi tare itama taje ta gaida Kakar Attahirun. Sadiq ya kalleta a karkace kafin yace"Ki je ina? Innani ba inda zan je da ke Wlh." Innani ta saki baki ta na kallonsa kafin tace"Magajin gida..!" Kai ya jinjina kafin ya juya ya na fad'in"Sai na dawo." Sai kawai Innani ta saka kuka ta na fadin"Shikenan ai Allah ya tsare ni dai kace Kakar Attahiru ta aikomin da aya ina jin dadinta." Dariya ta kusa kamashi sai da ya fita sannan ya yi dariyansa. Kai Innani ke baki ba hakori a  baki ammh kina ba da sallahun a zo miki da wani abu. Daman Abba ya sallamesa tun safen da kudi duk da yace masa ya na da kudi a hannunsa Abba ya kallesa kafin yace"Ko me ka zama a wannan Rayuwar Abubakar ni ne mahaifinka kuma har in koma ga Allah bazan daina maka Hidima ba." Kalaman Abba suka toshe masa baki ya kasa yi masa gaddama. Tasha yaje ya hau mota zuwa katsina daga chan ya samu na Daura. Tahir na wajen taron siyasan d'an majalisan su da ya fara bi Sadiq ya kirasa yace masa ya na ina ne? Kai tsaye yace ya na wajen Taron Siyasa. Sadiq yace"To ya zaka yi dani? Ga ni a dakin Hajja." Tahir yasan ba karya Sadiq ya ke yi ba sanin Halinsa. Da sauri ya baro wajen ya na zuwa ko yaga Sadiq zaune dakin Hajja suna ta Hira shi kuma ya na shan Fura. Tsaye ya yi rike da kugu kafin yace"Kai ammh banza ne ka kira kace yau zaka zo shine ya gagare ka.? Kai Tsaye Sadiq yace"Bani da kudi ne a waya." Da Sauri Tahir yace"Karya ka ke yi wlh." Hajja ta dago ta na wurga masa maficin Hannunta Lokaci daya ta na fadin"Tafi chan mara tunani ya taso tundaga gari mai nisa saboda kai ammh kana kiransa makaryaci kai dai Dahiru Allah ya shirya ka." Tahir ya bata rai ya na fadin"Hajja sunana Tahir. Tahir sunana." Hajja tace"Nace Dahiru Dahiru ko zaka Tsireni ne? Sai Tahir ya kasa mgana Sadiq kuma na shan Fura ya na Dariya. Shigowa ya yi da kafa ya Shuri Sadiq ya na fadin"Munafuki." Hajja ta mike ta fadin"Fitar min da takalmi daga daki ina Ibadata aciki." Jin yasa ya koma ya cire takalmi sannan ya shigo, ya zauna kusa da Sadiq ya na Hararan shi. Hajja kuma bakinta washe ta nuna ma Tahir abun arzikin da iyayen Sadiq suka aiko mata da shi. Ya karba ya gani shima ya yi godiya sun jima dakin Hajja suna ta Hira sannan suka koma Dakin Tahir. Sadiq ya yi wanka ya sauya kaya suka fita sallar La'asar dagachan Tahir yajasa suka shiga gari. Sadiq so ya ke ya samu ya kebe ya kira Hasiya yau da Safe kad'ai suka yi mgana ammh Tahir ya tsare ko'ina kuma baya so ya kirata a gabansa Saboda baya son wani surutu. Sai da Daddare suka had'u da yayyen Tahir a bangaren Hajja suna ta Hira. Sai da Hajja ta gaji ta fara gangadi sannan ta kora kowa dakinsa. Sadiq cikinsa ya cika yau har Danwake ya ci da Dambu wanda kanwar Tahir ta kawo masa. Sun gaji shiyasa suna kwanciya sai barci sai da safe bayan sun dawo sallar asuba sannan suka zauna suna Hira. Acikin Hirar ne Tahir ya kalli Sadiq ya na fad'in"Wani shiri gareka kasan fa mun kusa yin sallama da garin zariya? Sadiq na kwance ya yi shuru kafin yace"Wani shiri kuwa? Shiri ai na Ubangiji ne" Tahir yace"Nasani. Mganar yarinyar nan? Kan rabuwarka wani taimako zaka yi mata kafin haka? Sadiq ya mike zaune ya na fadin"Shine na rasa mafita har yanzu Tahir." Tahir ya yi shuru shima ya na Tunani, Kafin ya yi magana Sadiq ya kallesa yace"Da na yi tunanin na saka ta a makaranta ta cigaba da karatunta sai kuma naga wannan ba mafita ba ne" Tahir yace"Gaskiya ba mu da wannan Lokacin." Suka yi shuru gabadayan su kafin chan Tahir yace"to ka bata jari ta fara sana'a mana ina ganin hakan ma taimako ne" Sadiq ya yi shuru kafin yace"Nima na yi wannan Tunanin. To wata sana'a ka ke ganin ta dace ta fara? Tahir ya balla masa Harara kafin yace"Ina zan sani? Ni ce zabiyar matar taka? Sadiq yace"Sunanta Hasiya ba Zabiya ba." Tahir ya yamutsa fuska kafin yace"What Ever. Sai ka tambayeta kaji ta bakinta ni nawa shawara ne" Sadiq ya koma ya kwanta ya na Fadin"Nagode da shawara." Tahir yace"Godema Allah." Sadiq ya yi dariya kafin yace"In ka dawo gida wani abu zaka kama? Tahir yace"Ba ni da wani zabi yanzu. Yaya kasimu yace ya yi magana a babban Sakandirin nan ta kusa damu zan kawo takarduna, in na samu shikenan in ma bansamu ba zan cigaba da siyasa a sannu a hankali." Sadiq yace"Ban ji ka yi mganar cigaba da karatu ba? Tahir ya yi shuru kafin yace"Uhm karatu yanzu ai sai da kudi Sadiq in na samu yadda na ke so zan cigaba in sha Allahu." Sadiq bai ce komai ba, shima Tahir haka shi Sadiq sai ya yi kamar ya Fara Barci shi kuma Tahir sai ya cigaba da latsa wayar hannunsa. Kwana uku ya yi a Daura sannan ya koma Gusai yaje kuma ya iske wata Sabuwar mgana ta kara ta shi. Yan'uwansa mata sun yi taro akan mganarsa da Sultana. Kuma wannan karon Umma ta goya musu baya sun kuma samu Abba da mganar shi kuma yace mgana ta na Hannun Sadiq duk abunda yace shi za'ayi. Babu abunda ya ba shi Haushi sai wai ana mganar ko a nan shashen nasa za su iya zama da Sultana kafin ya samu aikin, Haushi ya kamasa ballatana da yaga gabadayansu sun had'u harda wad'anda ke nesa ma duk sun zo ko da suke gaba da shi ammh ai su mata ne ya na gaba da su a tsarin addini bai kamata su zo su zauna suce za su zama control a kan Rayuwarsa ba. Ranar da ya dawo da Daddare suka shirya taron a falon Innani, sai dai ya bari duka sun gama maganganun su, ya na zaune gefe ya na kallonsu su Hujjarsu wai ya fara damuwa kuma suna Tunanin in ya yi auran zai samu natsuwa da kwanciyar Hankali. Sai ya yi kamar yace musu shi ai ya riga ya yi aure sai kuma ya fasa. Fuakarsa ya had'e ba ko Fara'a saboda ya na da wani abu guda d'aya ba ya son ka rika tsallake Hurumin da ba naka ba sannan ya tsani a shiga rayuwarsa. Abun da yasa ya kasa mgana Har Umma ta ba da goyon bayan wannan karon Mama ma tace duka abun gidane to ba ta ga matsala in an yi auran yanzu ba, Innani daman Burinta kenan bakinta washe da wawulamta domin ta cire Hakoran Roban sai dasashi ba Hakora. Sadiq bai yi niyar mgana ba sai da Abba ya kallesa yace"Kaji duka bayanan yan'uwanka menene Ra'ayinka akan mganar su? Gyara zama ya yi kafin yace"Abba ni bansan kan wannan zaman ba, na riga na gama tsayawa a matsayata tuntuni." Surayya tace"Wata matsayar kenan? Kallonta ya yi ido cikin ido ya na mamakin Saboda kawai su shiga rayuwarsa yasa suka baro gidajensu suka zo nan su kwana saboda su yanke ma Rayuwarsa Hukuncin da suka ga dama. Cikin Maganarsa ta kai tsaye yace"Ai na fad'a muku ba yanzu zan yi ba sai nagama Bautar kasa na kama aikin yi kilama har na fara masters dina." Sai falon ya Dauki Shuru Abba ya juya ya na kalllonsu kafin yace"To kun ji na shi matsayar" Umma tace"Ammah Abban siyama wannan ba Hujja bace. Kana da kudin da zaka iya rike su da shi da Sultana har ya'yansu meyasa zai ba da Hujjar da sai ya samu aiki.? Sadiq ya kalli Umma kafin yace"Umma Kudin Abba ba kudina ba ne. Abba ne ya sha wahala ya tara kudin da guminsa kuma kada ku manta ba ni kad'ai ya Haifa, duk nan ya'yansa ne kenan ba ni kad'ai ke da iko akan dukiyarsa ba, Ya riga ya sauke Nauyin da ke kansa na ciyar da ni da Tufatar da ni, sannan ya ba ni Gudummuwa kan karatu ya sauke wannan Hakkin nasa, ko yau Abba ya Mutu komai da ya mallaka ba na wa bane ni kad'ai shima ya'yansa ya taramawa nima shiyasa na ke son ku barni na Tsaya da kafafuna kafin na Fara Tunanin Dauko wani nauyin a kaina." Surayya ta bude baki kafin tace"Sadiq ni fa banga wata matsala a nan wajen ba. Abba ma mai iya baka gida ne kyauta wanda zaku zauna kai da Sultana." A fusace yace"In ya bani gidan shi zai rika ciyar da matar tawa? Ko kuma ke zaki rika daukan Dawainiyar nata? Rashin kunya ba Halinsa ba ne yasa gabadaya suka Dago suna kallonsa da mamaki. Surayya ta nuna kanta lokaci d'aya ta na fadin"Ni ka ke gayama mgana haka Sadiq? Karamin Tsaki yaja kafin yace"Kowaccen ku nan ta na da nata tsarin rayuwar. Ku yayyena ne nasan kun girmeni ammh kuma wannan ba shi zai baku damar shiga rayuwata yadda kuka ga dama ba. Mgana ta guda d'aya ce sai na samu aiki aure na da Sultana zai ta shi in kuma kun matsa ne sai ta yi aure sai ku nema mata wani mijin ammh ba dai ni ba." Umma ta mike a fusace cikin tsawa tace"Abubakar.." Shima cikin Daga murya yace"Umma me yasa su kika saurare su ni kuma kika kasa Fahimta ta? Umma kallonsa ta ke idanuwanta na Cikowa da kwallah. Innani tace"Na shiga uku ni Dije me nake ji haka? Ta fad'a Lokaci daya ta na Dafe kirji sai kuma ta saka kuka ta na fadin"Wlh ko bayan raina wani ya Tada maganar auran magajin gida da Sultana ban yafe masa ba ko da kuwa Magajin gidan ne da kansa." Sadiq ya kalleta a fusace kafin yace"To in dai kina son kada in tada wannan mganar ki fad'a musu su dakata da wannan mganar, zan auri Sultana bayan na samu aiki Fakat mgana ta karshe kenan." Daga haka kawai ya fice a Fusace suka bi shi da kallo cikin mamaki. Umma ta koma ta zauna ta na fadin"Me yaa samu yaron nan ne? Mama tace"Ya jima ransa bai baci haka ba." Sajida tabe baki tayi kafin tace"Duk su Umma suka ja, su suka fara nuna masa cewarsa da Ra'ayinsa na gaba da na kowa har ta su kansu." Innani ta harareta kafin tace"Rufemin baki, duk ba ku ne kuka saka ya so yace ya fasa auran Sulsanan ba? To wlh ku ji dakyau abar mganar nan a bi abunda ya ke so saboda ba na so ya tada wannan alkwarin saboda haka Sulaimanu ka tsawarta ma da ya'yanka da matanka su fita Hanyar maganar Auran magajin gida da Sulsana a bari har Lokacin da ya samu aikin ko yaushe sai ayi auran ba shikenan ba." Baki su Surayya suka saki suna kallon  Innani wacce yanzu yanzu ta sauya mganarta. Tana ganin suna kallonta sai ta fashe da kuka ta na fadin"ko Aljanune suka shafi Magajin gida da ya ke tunanin fasa auran Sulsanan? Kuma ni dai nasan yana tsananin sonta." Abba ya yi mirmishi kafin yace"kada ki damu Innani ba wanda ya isa ya Tada wannan mganar." Sun cigaba da Tattauna mganar matan duk jikinsu ya yi sanyi barin ma Surayya abun ya Tsaya mata arai da Sadiq ya yi mata rashin kunya Saboda kawai ta yi mgana kan inganta Rayuwarsa. Sai ta fara wani tunani ko dai ko dai? Ta fara Tunanin akwai wani abu ke Boye wanda ba su sani ba. Umma ma ranta ya baci ammh sai ta Danne ta Lallashi ya'yanta. Har suna ikararin sun cire hannunsa a kansa yaje shi ya sani. Allah yasa ma su Sultana ba su a wajen da shikenan sai taji wannan Dibar albarkar da Sadiq ya yi musu. Gari na wayewa duk suka kama gabansu sai yan nesa aka bari irin su Suba'atu. Saddiqa ko fad'a ta dinga yi ta na ba ma su Umma laifi da cewa su suka sangarta Sagir suka nuna masa Tun farko cewarsa da Ra'ayinsa na gaba da na su in da tun farko sun nuna masa cewarsu na gaba da banzan Ra'ayinsa da yanzu duk Hukuncin da suka yanke bai isa yace a'a ba. Umma dai ba ta da bakin mgana Tunda tasan gaskiya suke fada. Abba kuma ya kashe mgana da cewa za'ayi auran Sultana Lokacin da Abubukar ya so kuma ya kashe mganar baya bukatar yaji an kara taso da ita. Sadiq yana shashensa Ransa duk ya baci meyasa su ke gaggawa ne? Ba su san matsalan da ya ke ciki ba ne shiyasa su ke kokarin kara sakashi cikin wata matsalar. Ba niyarsa ya yi musu rashin d'a ba sai dai ya yi musu hakane saboda su yi Fushi su fita da Rayuwarsa su barshi ya tafiyar da ita a yadda ya ke ganin ta yi masa daidai Kuma har ga Allah bai isa yace baya son Sultana ba sannan mganar tada alkawarin auran barazana ya yi ma Innani Saboda ita kad'ai ne makamin Nuclear da zai Harba ta isa garesu gabadayansu kuma ya yi nasara. Gabadaya sai yaji gidan ya fita kansa in yaje gaida Umma fuska Daure ta ke amsa masa Abba kad'ai suke yar dad'i da shi. Ita kuma Innani sai ta rika masa kukan ko bayan ranta in bai auri Sultana ba bata yafe masa ba. Ranar ta ishesa yace"To karki yafe min mana, ai ba ke kika haifeni ba ko Tsine min kika yi bazan lalace ba Innani." Ranar yini ta yi jan majina da an yi mgana sai tace"Makiya sun shiga tsakaninta da Magajin gida yau kiri kiri yace bata haifesa ba ko ta tsine masa bazai lalace ba." Saboda Halin da ya ke ciki kwana Biyu bai kira Hasiya ba sai Ranar asabar da Safe ya kirata har sau hud'u bata Dauka ba. Sai ya kyaleta bayan ya kwanta barci ya tashi sai ya kara kiranta sai ga shi ta Dauka. Sai dai kuma a muryanta yaji kamar ta yi kuka, cikin tashin hankali ya mike zaune ya na fadin"me ya same ki? Dagacham bangaran na kasa magana Saboda ko yaya na Bud'e baki zan yi magana kuka ne kawai zai tahomin. Kawai sai na ce masa"Bakomai." Kafin na katse wayar nan a tsakar Falo na zauna na had'a kai da Gwiwa ina ta rafzan kuka. Kalaman Fadila kawai na ke tunawa Lokacin da ta ce min ni Annoba ce sannan Gobara daga kogi maganinta sai Allah. Tun bayan zuwan Ummi gidan nan da kyakyawan mu'amalata tsakanina da ita bantab'a Tunanin watarana komai zai zama Tarihi ba sai da Fadila ta tare. Ashe abunda bansani ba Diyar kanwar mahaifin Abubakar kawar Fadila ce itace tazo gidan ta ganni ni kuma bansanta ba,ballatana nasan cewa zata fad'i wani abu a kaina. Ita ta kwashe komai na Rayuwata na baya ta gayama Fadila, daman kuma Tun farko jininmu ni da ita bai had'u ba da Ummi kadai ta ke huld'ar ni ko haduwa muka yi in na gaisheta sai ta ga dama ta ke amsawa bayan ta gama min kallon wulakanci. Bansan ta gayama Ummi komai ba harda ma da karin karya sai da naga Ummi taja baya da ni, ta daina shiga Dakina ballatana mgana da ni, in ta dawo makaranta Dakin Fadila ta ke shigewa. In na yi abinci na kai mata da Safe zan ganshi ta zuba shi a bola. Sannan in nazo zan shiga Dakinta sai ta yi wuf ta fito ta kare kofa ko tayi min karyan fita zatayi ko tace mijinta ya na gida. Kwata kwata daai ta sauya ba kamar yadda na santa ba. Sai abun ya Dameni na kira Ramatu na Fad'a mata sai ta bani shawaran na sameta na yi magana ko wani Laifi na yi mata? Tunda zaman tare daman ya gaji haka. Shine yau din bayan na gama abinci na zuba mata zan kai mata sai na same su kofar dakin Fadila suna zaune saman Cafet suna hira suna shan lemu gefe ga kololin abinci nan da alamu sun gama ci ne. Na yi musu sallama ba su amsani ba sai da na kara sannan Ummi ta amsa. Sannu da gida na yi musu sannan na mikama Ummi abincin. Kamar bazata amsa ba sai ta karba a gabana ta mike ta isa wajen zuba sharan Fadila a kofar dakinta ta Juye shinkafa da wakenan a bola. Sai raina ya baci na kalleta cikin mamaki kafin nace"Haba Ummi in bazaki ci ba ba sai ki gayamin ba, ai bai kamata ki zubar da abinci ba." Kai Tsaye ta kalleni kafin tace"Gwara na zubar saboda kada ma wani yagani yaci ya ci ma kansa bala'i." Baki sake na ke binta da kallo nan ko naji ta na zayyanamin har da fad'in an gayamata nice sanadiyar Mutuwar Mahaifina da Karayan arzikinsa. Sannan na yi aure aure mazaje biyu duka sai da na Talauta su d'aya ma zaman garin sai da ya gagaresa. Dayan kuma gabad'aya rayuwarsa ya kusa rasawa saboda ni. Dole ne su daina rab'ata kada suma wani abu ya same su. Maganganu na batanci da cin mutumci Fadila ta kalleni ido cikin ido tace ni Annoba ne kuma sunana Gobara daga kogi mganina sai Allah. Sannan tace shima wannan auran da nayi ba'asan waye na aura ba shima ana Tunanin wani bala'in ne gagarumi zai samesa. Ba na ganin gabana sanda na shiga daki sabida tashin Hankali da kuka, ina cikin kukan ne na samu kiran Assadiq. kamar bazan dauka ba sai naga ya na ta kira na, sai na Dauka ina kokarin boye Halin da na ke ciki. *BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA DEE*! *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Gaban ayu*. *Hakkin daka gangariya*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. *Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* *Ana dafa GIMBIYAR KAZA da tattabarun garari*. *Janafty* *TMWBK2012* https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan. Na jin sanda ya ke ta kirana da ta yanke kuma sai wani kiran ya biyo baya. Gabadaya na rasa tunanin da zan yi kwakwalwata ta tsaya cak a waje daya zuciyata ta cunkushen da na kasa Sarrafa kaina ballatana nayi Tunanin wani abu. Kuka na ke rerawa wanda ke fitowa daga karkashin zuciyata kuma ya ke amsar duka gangar jikina. Tabbas na yaudari kaina in ina Tunanin kwanciyar Hankali da na samu a gidan Assadiq mai Dorewa ce, kuma na shagala da yawa matukar nayi tunanin abunda ke shafan Rayuwata zai iya gogewa har Abada. Nasan duk abunda suka fad'a gaskiya ne ya faru a kaina sai dai abunda har yau bangane ba ne meke faruwa da Rayuwata ne? Anya ni mutum ce ko Aljanna? Amma tace ni ba mayya bace ammh meyasa abubuwa marasa dad'i basa tashi Faruwa sai abunda ya dangance ni ko ya matso kusa dani? A d'an ilimin da Allah ya bani na dad'e da sanin babu mai yi sai Allah sannan Amma ta fad'amin Allah ne kad'ai ke da ilimin sanin gaibu ba Mutum ba sannan ta sha zaunar da ni ta fad'amin ni ban isa na rike kaddaran wani a hannuna ba duk abunda ya Faru da Abubakar ko da Salisu daga Ubangijin sammai da kassai ne, sai dai ya kasance kowani abu na duniyan nan akwai sanadin to ni ce na ke kasancewa sanadin duka al'amuran su. Meyasa mutane ba su da Tunani ballatana saurin Fahimta irin ta Amma? Ko da ya ke sai na tuna da yar'uwata Adda Rukayya itama ba ta dad'e da daina kallona a matsayin Annoba ba, Mijinta kuma da Ahalinsa har gobe a bar gudu suke ganinaa. Cikin satin nan naje gidanta ko awa Biyu ban yi ba na dawo gida Saboda Mijinta ya dawo sun shiga ciki naji ya na gayamata bayason ina zuwa masa gida saboda ya na son rayuwarsa sannan ya na son ya tsira da arzikinsa. Bata ma san na fito daga gidan ba sai dai fitowa tayi taga na tafi har na kawo gida ina kuka na rasa ina zan Nufa Amma tamin nisa ballatana na samu kafad'anta na kwanta na sha kukana ta lallasheni sai na Dawo gida na kulle kaina acikin daki nayi kuka kamar raina zai fita. Ban taba tunanin cewa Fadila na da alaaqa da Ahalin mijina na Farko ba. sai yau da ta ke fad'amin wacce ta sanar da ita komai game da ni. Da dukkan zuciyata na ke kuka kamar raina zai fita a wannan Lokacin nayi Fatan Mutuwa ban san iyaka ba. Na duba na hango sai naga ai banga amfanin Rayuwata ba in dai zan kasance Annoban da ke illarta da Mutane to rayuwata ba ta da wani amfani Tunda in dai ina Raye sai na zauna da Mutane kuma na zama cutuwa garesu. Na auna yadda zan kashe kaina ta Sigogi da Dama ammh kuma na kasa aiwatarwa duk wanda ya fad'omin a rai sai naji bai kwantamin arai ba har Tunanin na Rataye kaina nayi sai kuma na fasa ina Tunanin ya Amma zataji in na kashe kaina? Sannan zan mutu kafira ce ranar gobe kiyama Allah ya sanyani acikin Wutan Jahannama. Tuna haka yasa na watsar da Tunanin kashe kaina na fara tunanin nema ma kaina mafitan da zata sakani nayi nesa da dukkan rayuwar mutane gabadaya. Tun wajen goma na Safe na ke kuka har aka kira sallar azahar ban daina kuka ba, abunka ga jar Fata gabadaya Fuskata ta kumbura ta yi jajir sannan kuma Idanuwana ma sun shige ciki kaina kuma sai saramin ya ke. Da na mike zan shiga tiolet na Dauro alwala sai da na Dafe bango saboda jirin da naji ya kwasheni. Hakanan na Dauro alwala na zo nan falo na shinmfida sallaya na tada sallah ina sallar nan ina kuka hawayena kuwa da an tara dan karamin Botiki tsab zai cika saboda yadda suke zuba ba Control. Bayan na idar na koma na zauna kawai na jingina da kujera, na kasa ma addu'a na kuma rasa irin addu'an ma da zan yi sai kawai na koma na yi shuru ina jin cikina na kugin yunwa. Daman jiya da Daddare ban yi abinci ba taliyar da na Daface tayi saura sai naci da daddare. Shine da Safe na tashi na Dafa shinkafa da wake ko ci ban tsaya yi ba na fita kaima Ummi, shine suka Fahimtar dani cewa ni Annoba ce maganina sai Allah. Ba ni da karfin gwiwan cin wani abincin bakina kuma ya yi takaf kamar wacce ta tashi jinya. Shiyasa ban yi wani yunkurin tashi na taimaki kaina ba, a raina nace in yunwa ce ta kasheni ban mutu kafura ba in dai ko hakane bazan kara cin abinci ba ballatana na sha Ruwa har sai Ubangiji ya Dauki raina domin na gaji da wannan rayuwar. Ina jin ana ta sake kiran wayata ammh yadda jikina ya nemi ya fara saki ne yasa ban ko iya jirgirtawa kusa da wayar ba, ballatana nasan wake kira a tunanina ko Adda Fati ne ban taba Tunanin Assadiq zai damu ba, ballatana har ya cigaba da kiran wayata a kai a kai ba. Wayar ta na yankewa naji ana bugamin kofa, ko ina iya tashi ma da karfin jikina bazan tashi ba domin Tunanina ya gama gayamin su Ummi ne sun dawo ne domin su kara cin zarafina kamar yadda suka yi a farko. Ina jin ana bugun da karfi sai kawai na kara fashewa da kuka. A fili na furta"Innalilillahi wani'inna ilaihirraju'un ni Hasiya yaushe zan huta daga wannan bala'in ne? Daga wannan sai wannan? Haka na ke fad'a a fili ina gunjin kuka lokaci daya ina had'e kaina a gefen kujera kamar wata marainiyar da ta rasa komai, Eh mana marainiyar ce mana tunda ba ni da Uba sannan ba ni da wani bangon abun jingina na. Kamar wasa sai naji kuma ana Buga kofar dakina kuma ana Kiran sunana. Shiyasa na mike a kasalance kamar zan fad'i, na nufi kofar dakin na bude da Niyar na yi shuru har su ummi su gama fad'in abunda za su fad'i su tafi. Sai dai kuma me? Ina bude kofar ban tsaya kallon wajen ba na juya baya na ina sharan hawayena. Sai jin tattausan muryansa na yi ya na fad'in"Hasiya me ya faru? Amma ce ciwonta ya tashi? Da sauri na juyo muka had'a ido Hudu da shi ban taba Tunanin ganinsa ba. Yana sanye cikin Riga da wando,Rigar Ash ce mai ruwan kasa sannan akwai Dogon Hannu,sannan sai bakin wando a jikinsa,sai karamin akwatin Trolley a hannunsa da jakarsa goye a bayansa. Na kasa mgana illah kallonsa da na ke yi wasu hawayen na kara ambaliya a saman Fuskata. Shi kuma daman ashe bugawar kofata da ya dinga yi da karfi ya fito da su Ummi Daga Dakunansu suna ta kallonsa ita da Fadila, shiyasa ya yi saurin shigowa cikin Dakin Lokaci d'aya ya maida kofar ya kulle. Ni kuma da gudu na koma falo na zube a kasa ina gunjin kuka, cikin tashin Hankali ya sauke akwatin hannunsa lokaci d'aya da jakar bayansa ya Nufeni. Duk a Tunaninsa wani abu ne ya samu Amma zuciyarsa na fatan Allah yasa ba ta rasu ba ne. Tun sanda ya kirani yaji ina kuka kuma yana ta kara kira ban Dauka ba sai hankalinsa ya tashi, Baisan ya akayi ba kawai ya fara shirya kayansa ba shi dai yaji ya kasa natsuwa abunda ransa ya kawo masa wani abu ya samu Amma ko na ciwo ko na Mutuwa. Yaji hankalinsa ya tashi, ya kasa samun natsuwa da sukuni, ya san cewa Hasiya ba ta da wani abunda ta ke kaunar bayan mahaifiyatan rasata ko wani abu ya sameta babban tashin Hankaline a gareta. Shiyasa ya shirya tahowa Zariya batare da shawara da ko zuciyarsa ba Ruhinsa ne kawai ke jansa zuwa ga Hasiya. Abba ma baya gida Umma ce kad'ai ya samu ya yi ma sallama itama sai da ta yi ta nanata tafiyarsa har dai ta kare ta baya ce zai jima a gida ba wannan karon? Kai tsaye yace mata daga wajen da ya ke hidimar kasa ne suka Kira shi, Umma dai ba yarda ta iya illa rakasa da addu'an Allah ya tsare. Innani da mama bai samu shiga bangaransu ba tsabar yadda ya matssu ya gansa a zariya suna mota ji yake yi kamar ya yi tsuntsuwa ya gansa a gaban Hasiya. A gabana ya duka cikin Damuwar da ta bayyana har a saman fuskarsa sannan ta nuna kanta a cikin muryansa, Cikin wani yanayi ya fara kiran sunana. "Hasiya.. Hasiya." Ina jinsa na kasa amsa masa saboda kukan da ya ke murkukusan raina a lokacin, ganin ban amsa kiran da ya yi min ba yasa ya saka Hannuwansa ya Dago Fuskata da ta kumbura ta yi jajir saboda kuka ya na kallona cikin sanyim murya yace"Me ya faru? Amma ce? Ya fad'a lokaci daya yana bubbuga kumatuna idanuwana na Runtse sai ga hawaye sharr, sun sake zubomin cikin shakewar murya nace"Amma na lafiya, ba ita ba ce ni ne." Daganan sai kawai sai na kara fashewa da kuka wannan karon harda Sauti kamar wata karamar yarinya. Cikin damuwa ya tarairayoni a jikinsa ya na fad'in"Me ya same ki Hasiya? Ko baki da lafiya ne? Ya ke fad'a ya na kokarim kama Fuskata da hannayensa duka Biyun ni kuma ina zillewa kokarina na koma kasan tayels din na kwanta na cigaba da kukana, shi kuma ya hanani sai Faman Rikeni ya ke yi, ya na kuma ta maimaitamin tambayan me ke damuna? Ko ba ni da lafiya ne? Dakyar na yarda ya rikeni dakyau a cikin jikinsa, sannan fuskata na cikin Tafukan Hannayensa cikin tashin Hankali a muryansa ya kira sunana "Hasiya.." Dakyar na bude kumburarrun idanuwana ina kallonsa cikin Muryansa mai cike da Sanyi yace"Gayamin me ke faruwa? Wani abu ne ya same ki? Ko baki da lafiya me? Sai kuma hawaye sharr, kamar an bude famfo, ina kokarin kara zille masa ya kara rikeni gam ya na fadin"Me ya faru Hasiya? Cikin kakkausan murya da alamu ya fara gajiya da jiran amsata. Sai da na bud'e idanuwana jajir ina kallonsa ido cikin ido sannam muryata a shake nace"ASSADIQ...." Sai kuma na kasa karisawa cikin kosawa yace"Menene Hasiya? Cikin kuka nace"Ka sake ni. Don Allah ka sakeni Assadiq." Gabansa ya yi wani Rugugu ya fad'i kuramin ido ya yi a ransa sai ya fara Tunanin ko dai nasan shirinsa ne na sakina nan da Lokaci kad'an? Yana wannan Tunanin na katseshi da cewa"Gwara ka sakeni saboda ina son ka tsira da lafiyarka. Ban taba jin fargaban kada wani abu ya samu wani ba irin yadda na ke fargaban kada wani abu ya sameka ba" Cikin ido muke kallon juna kafin yace"Me ya kawo wannan mganar kuma? Kwace jikina nayi na koma gefe na jingina da kujera ina kuka cikin kukan na fara gayamasa abunda ya Faru Tsakanina da su Ummi na karishe da Fad'in"Ba na son wani abu kaima ya sameka shiyasa gwara ka sauwake min ka yi tafiyarka ka rabu dani Tun kafin wani abu ya sameka. "Ba abunda zai sameni face abunda Ubangijina ya kaddaramin Hasiya." Haka yafad'a lokaci d'aya ya na kallona cikin Kaushin murya kafin ya taso daga inda ya ke yazo gabana ya zauna ya tankwashe kafafunsa kamar mai Daukan karatu wanda har gwiwar kafafunsa na dukan gwiwan kafafuwana. Cikin Kaushin murya ya bud'e murya ya kira sunana "Hasiya." Na amsa masa cikin dashewar murya kafin naji yace"Dago kanki ki kalleni ina so zan yi miki mgana ne, kuma ina so ki bude kunnuwanki dakyau ki Saurareni." Ya fad'a ya na kallona kai tsaye sannan Fuskarsa ba Fara'a ballatana a yanayin muryansa na Fahimci babu wasa acikin mganarsa. Dagowa na yi ina kallonsa ina mai Tattara duka hankalina garesa. Cikin Tattausan lazafi yace"Hasiya waye ya Hallice mu? Kai Tsaye nace"Allah ne ya Hallicemu? "Waye mahallicin sammai da kassai? Nan ma na amsa masa da cewa"Allah ne" Ya kara cewa"Waye Mahallicin Tsuntsaye da Dabobbi? Cikin mamaki wannan karon na kallesa sai na ga da gaske ya ke tambayoyinsa ba wasa a saman Fuskarsa. Ni kuma tambayar ce na raina musu ai ko yaro dan shekara uku yasan Allah da abunda ya ke tambayana. Shi ya katseni da fadin"Kin yi shuru" Da sauri nace"Duka Allah ne Mahallicin komai da komai da ke cikin wannan Duniyar sannan shi ke da Duniyar gabad'aya da abunda ke cikinta." Cikin jinjina kai yace"Good. To kinsan haka Hasiya meyasa ki ke tunanin ke ce ki ka yi sanadiyar rasa Dukiyar mijin ki na farko? Sannan me yasa ki ke tunanin ke ce da alhakin Jinyar mijin ki na biyu? Sai naji na kasa mgana na yi tsuru ina kallon kafafuwana ina wasa da yatsun hannayena. Ganin na yi shuru yasa ya cigaba da fad'in"In dan har kinsan Allah ne Ubangijin duniya da abunda ke cikinta to ya kamata ki daina bari Tunanim mutane na Gurbata naki Tunanin Hasiya. Duk Abunda ki ka ga ya faru da bawa daga Rabbil Izzati ne shi ke da ikon aikata duk abunda ya so a kuma Lokacin da ya so sannan wani abu bai isa ya samu Dan Adam ba, face abunda Allah ya kaddara masa cikin Kaddarorinsa." Maganganunsa sun shigeni matuka da suka sanyayamin jiki. Cikin nadamar tunanin da na yi na kashe kaina na Dago idanuwana da suka cika da kwallah ina kallonsa kafin yace"Ba ni na ce ba Assadiq mutane ne ke fad'in haka a kaina Tun kafin ma na girma. Ana zargin ni ce Silar karayan arzikin Baba sannan ni ce silar mutuwarsa sannan ni ce Silar lalacewar Rayuwarmu har da Ciwon Amma da bayajin mgani." Sadiq ya yi shuru ya na kallona ina ta sharan kwallah kafin yace"baki amince da amsarki ta farko ba kenan Hasiya? Da Sauri nace"Na amince wlh." Kai Tsaye yace"Ke musulma ce kin shaida Allah Ubangiji ne sannan Annabi Muhammadu salallahu alaihi wasallam Manzonsa ne ko? Nan na d'aga masa kai, cikin taushin muryansa ya cika da fad'in"Kin kuma amince da karban kaddara mummuna ko kyakyawa daga Ubangijin ko? Sai na kara gyad'a masa kai da Sauri ya rike hannayena cikin nasa hannayen muna masu kallon juna kafin cikin Muryansa mai yanayin kashe jikin mace yace" To ki sani wannan al'amarin daga Allah ne, sannan Faruwarsa kuma ta Sanadin ki, shine kaddara mummunan da ake mgana Hasiya, in kika yi hakuri zaki cinye Jarabawarki in kuma ki ka kaza to zaki fad'i daga wannan Gwajin da Ubangiji ke miki Saboda Auna imanin ki." Amma ta sha zaunar da ni ta yi min nasiha ammh mganganun Assadiq sun kara sanar da ni wani abu, sannan sun kara Budemin ido sosai na Fahimci Ubangiji shi ke da Alhaki da duka Rayuwar duniya da Komai da ke cikinta. Sai kawai na fashe da kuka ina Fadin"Allah na Tuba Astagfirullah na tuba Allah dazu fa har tunanin kashe kaina sai da nayi Assadiq" Ido ya bude da Sauri ya na kallona kafin cikin Daga murya yace"Ke baki da hankali ne? Kinsan hukuncin wanda ya kashe kansa ko? Wutar Jahannama Khalidina Fiha Abadan Hasiya." Jikina na rawa na kara Jimke hannuwan Assadiq ina kara fadin"Ai nace na Tuba bazan kara ba Assadiq." Cikin Kaushin Murya yace"Kada ki kara wannan Tunanin komai ya yi Tsanani mganinsa na wajen Ubangiji duk sanda wani abu ya so ya gusar miki Da tunani ki ambaci Allah shi zai kawo miki dauki a daidai wannan Lokacin kin ji ko? Sai na samu kaina da gyad'a masa kai ina zubar hawaye. Cikin muryan kuka nace"Ka yi hakuri." Cikin Tausayina da ya cika Kirjinsa ya Saki hannayena, sai ji na yi saman Fuskata ya na sharemin hawaye cikin sanyin murya yace"Ki daina kuka ba abunda zai faru sai alheri kin ji ko? Sai na samu kaina da gyad'a masa kai ammh hawaye na sun ki daina Fitowa da kwarmin idanuwana. Kawai batare da zato ko tsammani ba sai na kara tsintar kaina saman Kirjin Assadiq a karo na biyu. Lokaci d'aya hannayensa a bayana ya na Bubbugawa kad'an kad'an alamun lallashi da ban baki. Ni kuma na samu waje sai na kara baje kaina a saman kirjinsa ina shakan kamshin Turarensa da ya fara sanyamin natsuwa. Ban sani ba har barci barci naji na neman kwasata ammh yunwar cikina bata barni ba sai ji nayi cikina na kuka Kuwwyaahh..! Kunya ta kamani sai na fara kokarin Dago kaina sai ya sakeni jin na daina kuka. Ya na kallona yace"Cikin ki ke wannan kukan? Cikin kunya na daga masa kai da Sauri yace"kina da Ulcer sannan ki na zama da yunwa ko? Sai na kasa ba shi amsa saboda kunya illah fara kokarin mikewa da nayi, ammh sai jiri ya kwasheni da yasa na kusa Fad'uwa sai da ya mike ya tareni ya na fadin"Kin gani ko? Zaunar da nayi ya yi a kan daya daga cikin kujerun falon ya na fadin"Bari na sama miki ko ruwan zafi ne ya warware miki ciki" Cikin sanyin murya nace"Na dafa abinci ya na nan cikin tukunyar da ke kan gas." Bai kara cewa komai ba ya shiga kitchen din da kansa. Ni kuma ganin haka yasa na mike dakyar duk da ina ganin jiri na Kwashe jakarsa da akwatinsa da ke nan Tsakar daki na kai masa cikin Dakina. Ina fitowa muka Had'u da shi ya fito yana ganina yace"Ba na ce kada ki tashi ba? Da sauri nace"Kayanka na shigar maka da su ciki." Sai ya kalli inda ya watsar da kayan yaga ba su sai kuma ya Dawo da kallonsu kaina na cire Hijabin jikina karemin kallo ya yi yana ganin Ramar da nayi. Ni kuma ganin kallon da ya ke min yasa naji kunya na koma na zauna da Sauri ina Rarraba idanuwana kamar wacce ta yi karya. A saman kaina naji mganarsa" Gas bai kare ba ne har yanzu? Dagowa nayi ina kallonsa kafin nace"Ya kare ranar da Habiba ta zo na bata cikin kudin da ka barmin taje ta sakamin" Kamar zai yi mgana sai kuma ya fasa ya koma kitchen din. Daman Dubu goma ya barmin kayan miya kawai nake siya da shi sai gas din da ta cikomin, sauran kudin na nan cikin Wadrope dina. Gas din ya kunna ya saka Ruwan zafi sai da ya jira ya tafasa sannan ya Juye ya zuba min a wani karamin kofi. Ruwan Bombita ya had'amin na fara sha saboda ya warware min ciki tunda ina da Ulcer ba na shan Lipton. Sai bayan na sha ne na ji na Fara Dawowa daidai sannan ya zubomin shinkafa da wakem da na Dafa na ci shi kuma yace sai ya yi wanka da ya shiga ciki yaga ba Ruwa a bambon makewayi sai ya fito ya na tambayana ban samu almajirin da zai fara zubamin Ruwan ba ne? Nace masa ban samu ba ni na ke zubawa da kaina. Kai tsaye yace"Shiyasa duk kika rame salon muje gaida Amma ki sa tace ba na kula da ke." Mirmishi kawai na yi ban yi mgana ba ammh a raina sai da nace ita kanta Amma tasan tun chan daman ni Ramammiya ce. Assadiq da kansa ya zake ya rika Fita chan wajen Famfo da botikai ya na Dibomin ruwa da na gama cin abincin nace ya kawo botiki d'aya na tayasa sai ya hanani yace naje na kwanta na Huta. A lokacin a wajen Famfon ne kuma ina da Tabbacin daga Ummi har Fadila suna leken mu ta windunan su. Ya Dauko Botikai biyu a Hannunsa da Ruwa na matsa masa ya bani guda d'aya kai tsaye ya kalleni kafin yace"Ba na ce ki je ki kwanta ki Huta ba ne? Zan yi mgana ya Dakatar da ni da cewa"Ba na son gaddama ki je ki kwanta." Jin abunda ya fad'a yasa na juya shi kuma yabi bayana zuwa cikin Daki. A falo na kwanta yace na tashi na shiga ciki bani da yarda zan yi tashi nayi na koma ciki na kwanta. Daman ya gama cika na Tiolet sai na Kitchen ne ya ke cikawa. Kamar ko ya sani barcin nake ji ina kwanciya sai barci ban farka ba sai Hudu saura. Naga abun mamaki Assadiq bayan Ruwa Sai da ya sharemin daki tas ya goge kuma ya kunna Turaren wuta daman jiya da yau dakin bai ga shara ba, na iskesa har ya yi wanka ya sauya kaya zuwa jallabiya ya na falo a saman kujera ya yi barci. Kunyar duniya ta kamani da naga har kitchen ya gyaramin sai dai bai yi min wanke wamke ba na ga dai shima yaci abinci tunda ga Filet dinsa nan alamun ya ci ba da jimawa ba. Kunya ta saka na koma ciki nima na zuba Ruwa a botiki na yi wanka Tunda garin akwai rana. Sai bayan na fito wanka ne ina Daure da zanin wanka na Daure gaba ya shigo Dakin. Da Sauri na yi kasa da kaina ina Raruman Hijabin da zan sanya. Bansan ko ya kalleni ba muryansa naji ya na fadin"Zan yi alwala." Ni dai har sai da ya dauro alwala ya fita sannan na iya sauke Numdashin da na rike da Sauri na shafa mai na saka Wata Doguwar rigata na Atamfa. Daman na yi alwala sai nima na Tada sallah na idar kenan naji shigowarsa kamar ya shiga kitchen sai na tashi na leka sai naga Pure water ne ya siyo sai ruwan gora da bakin lemu katan daya sai Fanta ya na Dauka zuwa Kitchen. Da sauri na Fito bai sani ba ya Dauki Katan din bakin lemun zuwa Kitchen ni kuma sai na Dauki na Fatam na bi bayansa. Ya fito kenan muka kusa cin karo, da Sauri muka kalli juna kafin ya yi mgana na rigasa da cewa"Sannu da zuwa." Bai amsa ba abun Hannuna ya karb'a Lokaci daya ya na fadin"Yarinyar nan na Lura baki jin mgana ko? Sum sum na wuce zuwa Falo na samu kujera na zauna. Shima ya kai sannan ya fito da bakin lemu ya zo ya ijiye nima ya Daukomin Fanta ya bani na karb'a. Cikin dakin ya koma sai gashi ya Fito da karamar Na'urarsa ya koma ya zauna ya kunnata. Ya na aikinsa lokaci bayan Lokaci ya na shan lemunsa. Sannan sai ya kalleni ya kauda kai har dai yaga ban sha lemun ba ya min mgana sai na Dauka ammh na kasa Budewa duk ya na kallona. Bansan ya taso ba sai ganinsa nayi a gabana kawai ya mika Dogon hannunsa ya karb'a ya bud'emin sannan ya maidamin ya na fad'in"In nace baki da karfi sai ki ga kamar ban fad'i gaskiya ba." Baki na Bude kafin nace"Laa..! Bai barni na karisa ba ya saka hannu ya rike hannuna ya Tura lemun a bakina sai da na kurba sannan ya saki hannuna ya koma ya zauna da wani kallo na bisa, shi kuma bai kara kallona ba ya cigaba da abunda ya ke yi. Muna nan zaune yana aikinsa ni kuma ina faman kallonsa, Fanta kad'an na sha Saboda gas kada ya rika tasomin bayan na kwanta, Shi kuma Tas ya shanye coke dinsa sannan ina gani aka kira wayarsa kamar bazai Dauka ba sai kuma ya tashi ya na kallona ta gefen ido ni kuma sai nayi kamar ban gansa ba. Fita ya yi waje inaga ya yi wayarsa sannan ya dawo ya cigaba da abunda ya ke yi ganin yamma na yi ne yasa na tambayesa me zamu dafa? Ya yi shuru sai kuma chan yace kada na Dafa komai tukunnah. Bamu muka tashi daga falon nan ba sai da aka kira mangariba ni ce ma da nagaji da zaman na d'an kishigid'a. Sai da ya juyo ya ganni ne yace min na tashi na zauna an kusa kiran mangariba. Shi fita ya yi masallaci ni kuma sai nayi nawa a gida, bai dawo gidan ba sai bayan isha'i da ya dawo wanka ya Sakeni ya sauya kaya zuwa wani Saukakken yadi ni kuma yace na yi wanka zamu fita ne. Ban musa ba na shiga na yi wanka na sauya kaya zuwa wanda na dinka da Auran mu, na saka farin Hijabina shi ya Kulle Dakin muka fita. Bai gayamin ina zamu ba sai da muka hau adaidaita muka isa sai naga An Rubuta Usmaniya Restaurant. Karo na Farko da na Taba zuwa Restaurant a rayuwata kenan Dare ne ammh kamar rana mutane sai harkokinsu suke yi. Ga masu zuwa cin abinci nan birjit wasu irin mu wasu kuma su kad'ai. Zabin abunda zan ci ya bani sai na rasa me zan ci sai nace a bani White Rice da Miya. Shi kuma sai yaci chips da Maltina kawai ya ce ni bazan ci chips din ba? Sai na girgiza masa kai. Bai kara mgana ba sai ya yi mgana aka kawomin Ferfesun kaza sai da aka kawo naji kunya tunda muna cikin wani babban Falo ne ga mutane suma duk a zaune sai dai kowa ya na Harkan gabansa ne shiyasa nace masa bazan ci ba. Harara ya sakarmin kafin yace"Duka zaki cinye tunda ba asaran kudina zan yi ba." Ba wasa a mganarsa yasa na fara ci kad'an kadan. Lemun Holladian ya ce a kawomin tunda yaga ban cika shan masu gas din nan ba. Karshenta dai sai da kowa ya watse ya barmu ina ta cin abinci sannu sannu. Ga shi cikina ya cika na kasa cinye Ferfesun kazan shi kuma tuni ya gama yana gefe ya yi fuska a bunsa. Ganin haka yasa na kira sunansa"Assadiq." Juyowa ya yi ya na kallona bai amsa ba ganin haka yasa nace"Na koshi wlh." Zai yi mgana saurin na kara cewa"Wlh kalli cikina". Gani ya yi kamar ina kokarin Bud'e masa cikin yasa da Sauri ya mike yace mu tafi. Muna tare da shi ya ciro walet dinsa ya ba su wani kati kamar dai Atm ne suka cire kudinsu. Mun fito daga wajen kenan yana tafiya ina gefensa sai faman kalle kalle na ke yi ina kara kallon wajen chan garin kallon na ci Tuntube na kusa fad'uwa sai da ya tareni. Cikin Tsareni da ido yace"Me ki ke kallo haka? Cikin Sauri nace"Assadiq ina ne nan? Sai da ya sakeni sannan ya rikemin hannu muna tafiya zuwa bakin Titi yace"Kina jin ana cewa kango? Sai na gyad'a masa kai shi kuma ya Cigaba da fadin"Nan ne kango" Kara bin wajen na yi da kallo ina fadin"Wajen da na kyau." Bai yi mgana ba sai ma kokarin tsaida mana da abun hawa da ya ke yi. Mun koma gida tara da wani abu na dare gashi na koshi da yawa shiyasa muna komawa na yi shirin kwanciya shi kuma sai da ya kara yin wanka ni har mamakinsa na ke yi baya gajiya da wanka ne? A falo ya kwana kamar yadda muka Saba da Safe kuma shi ya fita ya siyo kwai na soya mana sanin bayason karni yasa na saka ma kwan kayan kamshi irin su citta da Tafarnuwa. Muka sha Tea tunda ya siyo mana Buredi mai taushi. Da rana kuma yace na yi masa Danwake da salat mai kwai shi na yi mana muka ci muka koshi Tuni na manta da su Ummi ban kara bi ta kansu ba Tunda ba na fita koda yaushe muna cikin Daki tare shima in ya Fita sai dai in za shi masallaci ko zai fita siyan wani abu. Da daddare kuma Tsire yaje ya siyo mana da Yourghour muka sha muka kwanta da Safe kuma ya je kasuwa ya narko min Cefane wannan karon bai siyo Kifi ba sai nama sai kuma ya Siyo naman kan rago yace na Dafa masa yana so, cikin Lokaci kankani na zage na Dafa masa mai romo da yaji kayan kamshi kuma yaci da yawa tunda ko Taliyar da na Dafa da rana bai samu ci ba da Daddare ma shi na Dumama masa yaci da Burrdi. Ni daman naman ganda bai Dameni ba ban ci wani da yawa ba, shiyasa ya kalleni yace"Yarinya baki san Dadi ba." Mirmishi kawai nayi ban yi mgana ba Zama na da Assadiq zama ne na Mutumtu juna yadda ya ke tafiyar dani kamar kanwarsa nima sai na Dauke shi da Daraja sosai. Koda yaushe muna tare da juna bamu cika Fira ba sai ta kama ammh yana tayani shara ko zuba ruwa banda girki ko wanke wanke domin yace bai iya ba ammh yana wanke bayi sannan in zai yi wanki ya had'a da nawa ya yanke dauraya kawai nake yi masa na Fita waje na shanya. Ranar ko na fita shanya muka had'u da Ummi ta kalleni nima na kalleta kamar bazan yi mata mgana ba sai kuma na Duba Wani abu da yasa na Juya na yi mata sallama ta amsa a yamutse daganan na koma na cigaba da Shanyar kayan mu ni da shi ta tsaya kam ta na kallona kuma nasan bayan Fadila ta dawo sai ta gayamata. Suna ganin mijina ammh kuma ba Fuskar da za su san wani abu akanshi kuma Assadiq ya gayamin tare suke sallah da mazajensu Ummi a masallaci anguwan nan. Ammh iyakarsa da su gaisuwa shikenan. Tun bayan auran mu sai wannan zuwan nasa suka taba waya da Amma tun bayan tafiyarta. Sun gaisa sosai yace mata zamu zo mu gaisheta tace mu yi zaman mu. Adda ce da aka bata su gaisa ta yi masa mganar ko ya sanar da Danginsa game da Hasiya? Sai yace mata Eh sun sani'. Sai Adda tace"To tunda sun sani yakamata ka Dauketa ka kaita taga Ahalibka suma su ganta" Sai ya amsa mata da Insha Allahu. Tun ina saka ran zai ce min zai tafi har na sakankance. Watarana in bamu jin dafa abinci sai yace na shirya muje mu ci abinci a waje Dalilin Assadiq na san wasu daga cikin Gidajen Abincin garin zariyan da abaya ban san su ba. Kuma in zaman shurun ya yi mana yawa sai yace nazo mu yi kallo sai ya kunna mana kallo acikin karamar Na'urar computer dinsa ashe akwai kallo aciki. Ba na Hausa ba ne Fina finan Sai dai akwai fassaran Turanci, shine ya ke min bayanin Abunda suke fad'i in muna kallo duk da Rabi da kwata ba na gane komai. Ammh kuma ina jin dad'in haka dalilon haka mun samu sakewa da Sabo da juna sosai. 🌿 Ina manyan mata masu MATSALOLIN rashin Ni'ima Ina sabbabin aure Wanda basu juku yanda Mai gida zai sume ba😂Ina wayanda zasuyi sabbin aure Nazo muku da magani SAHIHI ingantaccen TSIMIN TABAJE🤌🏽🥰😍 hmm uwar gida, amarya, tsoffin aure kuna Ina ko kuntsaya tsilla tsilla tohm maza kuzo nazo kusiya TSIMIN TABAJE 💃💃😂hajiya ta tunda kukaji na yaba wannan magani toh tabbas yakai inda yakai yanada matukar kyau, Yana saurin saukar da niima baya illa domin andafashine da saiwoyin da kuka San suna maganin dakyau... Hajiya ta 🙈wlh Mai gida zaiyi Santi zakiji dadi Kuma zakuzo ku godemun domin yanasa Gurin yayi dumi ya Kuma ciko miki da gaba Gurin Kuma zaiyi dadi zoyzoyy😂🙈💃Kuma duk afarashi kalilan akwai gorina 1k akwai galan, akwai jarka ga duk meso, hmmm duk Wanda yasha Sai ya Gode mun domin nice na baku tabbaci 💃😂kunsan banida burin daya wuce Inga anasaka Mai gida farinciki 💃😂🥰Toh kuzo kusiya zakuji dadi insha Allah Kuma Sai kun dawo.... muka hada miki maganin TSIMIN TABAJE sha'awa zaki koma kamar marka..game bukatar TSIMIN TABAJE ya kiramu tawa innan numbobin kamar haka *Location* *Zaria and kaduna* *but nation wide delivery* *for more details 07062349732 or 08143450259* 💃💃💃 *Janafty* *TMWBK2K013* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641 Ranar kawai yace na shirya muje gidan Adda Fati mu gaisheta nan da nan na fara Murna, bayan la'asar muka tafi muna hanya ya kalleni ya na fad'in"Haka zaki je baki rike musu komai ba? Sai nace"To me zan siya musu? Kallona ya yi batare da ya yi mgana ba, sai da ya ga mun zo wani shago yace mu tsaya ya fita da kansa sai gashi ya Dawo da Leda cike da Biskit da Chaculet da Sweets. Wani abu na bani mamaki game da Assadiq bayan kashe wayarsa da kuma rashin yin waya a gabana sai kuma yadda ya ke kashe kudi ahalin nasan ba shi da sana'a mai karfi asalima ya na karkashin wani ne. Kuma a yanayin kashe kudinsa bai yi kama da wanda ke karkashin wani abu. Duk da yace gwamnati na Biyansu ammh kudin da ya kashewa ya fi karfin kudin da ya ke da shi. Na kasa yi masa mgana ganin kamar ba Hurumina ba ne Adda Fati da Mijinta kamar su goyamu Adda Fati Bakinta yaki Rufuwa ita da Habiba da ta Dawo daga Islamiya. Tare suka fita masallaci da Baban Hanif suka dawo suna falo suna Hira ni kuma muma ciki muna Hira da Adda Fati ta na faman tambayana ya yanayim zaman mu? Nace mata lafiya lau ko matsalan su Ummi ban fad'a mata ba. Kallona ta yi kafin tace"Ya mganar zuwa dake chan garin na su? Sai na kasa ce mata ban masa mgana ba sai kawai nace mata yace zamu je in ya samu Lokaci. Adda Fati tace"Gaakiya ki takura masa ya kamata kuje ki ga yan'uwansa suma su ganki." Sai na jinjina mata kai alamun to ina jinta ta na ta min bayanin Fa'idar haka ciki har da Tunanin kada mu zo mu fara tara zuru'a. Sannan ta tambayeni ko a waya bai tab'a had'amu mun yi mgana da kakar tasa ba? Nace mata a'a bai taba bani ba araina nace shi wannan wayar tasa ma ai ban taba ganinta ba koda yaushe tana jikinsa. Achan falo ma haka Baban Hanif ya tasa Saddiq da Tambayoyi shi kuma ya na bashi amsa a takaice. Tambayar da ta basa mamaki shine da Baban Hanif yace"Wani aiki ku ke yi ne kai da megidan naka? Sadiq ya kallesa kafin yace"Gwari mu ke yi harkan gwari ne" Baban Hanif ya kallesa ya na mamakin kalamansa shi dai a jikin Sadiq bai yi kama da mai gwari aikin Wahala ba. Sadiq da ya Fahimci haka sai yace"Muna zuwa gari gari har kudu ma muna zuwa." Sai Baban Hanif yace"Allah ya taimaka shi megidan naka anan garin ya ke? Sadiq ya yi saurin cewa"A'a a chan kano ya ke." Tun kafin Baban Hanif ya watso masa wata tambayar ya mike ya na fad'in nazo mu tafi kada mu yi dare a hanya mu kasa samun abun hawa. Sai Baban Hanif ya tashi yaje kirana muna Tsaka da Hira da Adda Fati ya leko yace mijina yace na fito mu tafi. Hijabina kawai na saka na fito Adda nata Godiyar tsaraban yara. Har waje suka rakamu ita da Habiba da Baban Hanif. Da kafa muka taka har bakin Titi sannan muka samu Adaidaita zuwa gida. A hanya ya tsaya ya siya mana gashashiyar kaza da Madaran Holladian, muka koma gida muka ci sannan muka kwanta sai na lura kamar Assadiq yana cikin Damuwa yau ko kallon bai kunna mana ba ya kwanta ya rufe ido. Ganin haka nima sai na shiga ciki na kwanta. Sadiq ya dad'e bai yi barci ba ya na Tunanin wani abu tunda yan'uwan Hasiya suka fara damuwa da Sanin Danginsa yasan akwai matsala. Shi gabadaya ma yan'uwan nasa Fushi ya ke da su tun abunda ya faru kafin tahowarsa. Sun kikkirasa duka yaki Daga wayarsu, Umma ce kawai ya ke Daukan wayanta sai Abba sannan Sultana ma na kiran shi abun da ke ba shi mamaki sai ganin sakoninta ma su kama da na Soyayya da kulawa da ta ke Tura masa shi kuma bai tab'a kiranta ko sau daya ba. Yasan shi ne karami ne acikin su ammh yasan yadda Mata suke jan Ragamar bata gida in dai suka yi yawa a waje. Bazai bari su shiga rayuwarsa su takura masa ba, kowacce taje taji da gidanta da Mijinta da ya'yanta. Sannan ya fara lura da in bai jajirce ba Ko auran Sultana ya yi su za su rika Tafiyar masa da matarsa shiyasa ya Tauna aya domin tsakuwa taji Tsoro. Big sis ce ta Turo masa sakon ya yi hakuri ya kirata za su yi mgana shi kuma baya so Hasiya ta Fahimci wani abu Shiyasa sau tari ya ke barin wayarsa a kashe. Sun yi mgana da Tahir sau biyu kuma bai taba sanin baya Gusai ya na zariya ba sun yi mganar zasu dawo zariya Lokaci d'aya. Ya kwana da tunanin yadda zai tambayi Hasiya abunda ta ke so ta fara sana'a in ta samu jari so ya ke komai ya kare kafin yan'uwanta su gano abunda ya ke boyewa. Sannan Tausayinta ya ke ji shiyasa har alokacin ya kasa aiwatar da Tsarinsa. Washegari kuma Ramatu ta kirani tana gayamin Noor ba lafiya sai na gayamasa sai yace anjuma muje mu gaisheta Kamar zuwan Adda Fati da Yammah mukaje gidan Ramatu cikin sa'a muka samu Nura ya dawo suka  had'e da Sadiq suna ta Hira ni kuma muka kule ni da Ramatu ita kadai na fad'a ma yadda muka kare da su Ummi. Ramatu ta yi mirmishi kafin tace"Kin manta na taba fad'a miki gangariyan miji na nan zuwa gare ki Hasiya? To shine Sadiq ina da tabbacin shine wanda zai zama bango gareki har Abada Hasiya kuma shi zai zama kariyar  kuma wanda zai tayaki wajen karb'an duka Kaddarorin ki." Sai na kasa musama Ramatu saboda nasan gaskiya ta fad'a Assadiq mutun ne mai hange nesa da sanin Zahirin Rayuwa. Nan ma sai Dare muka koma gida sai da muka ci abinci shinkafa da wake da Miya da Salat, tare duka muka ci abinci da su muna cikin cin abinci ne Ramatu ta kalleni ta na fad'in"k'awata ba ni shawaran wani sana'a zan fara Abban Noor ya bani jari" Tun kafin na kalleta Assadiq ya kalleni domin yaji me zan ce, sai kuma yaji nace"To wani sana'a zaki fara? Kai Tsaye tace"Shine na ke nemen shawaran ki" Shuru na yi kamar me nazari kafin nace"kina da Fridge ko? Sai ta dagamin kai sai na cigaba da Fadin"To ki fara saida Ruwan sanyi mana ki gani? Ko kuma ki had'a da Suya milk in ya amsu shikenan." Ramatu ta yi jim kafin tace"Eh to zan gwada na gani kaji Shawaran Hasiya Abban Noor? Nura na gefe yace"Sai ki gwada ki gani Allah yasa albarka." Sadiq na gefe ya kalli Ramatu kafin yace"To ita ki tambayeta in ta samu jari wani sana'an zata fara? Ramatu ta kalleni nima na kalleta sai na nuna kaina ina fadin"Wai ni? Ta na Dariya tace"Hasiya mamman kona ba." Cikin daga ido nace"Tab ai in na samu wasu kudad'e yanzu dubai zani na Saro zannuwa da kaya dogayen Riguna da su takalma ina so na zama yar kasuwa Sosai." Ramatu ta yi dariya kafin tace"Lalle wa yahga Hajiyar Dubai." Nura ya kalli Sadiq kafin yace"To kaji sai ka Shirya ka kusa zama mijin Hajiya." Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba daganan sai aka Rufe mganar sana'ar muna gidan har wajen goma saura sannan suka rakamu muka tafi. Har na ma mamta mun yi wannan mganar sai washegari da rana ya kirani ya na zaune afalo. Bayan na zauna a gabansa ya Tattara natsuwarsa ya fara fad'in"Da gaske kina son ki fara kasuwanci Hasiya? Kai Tsaye nace"Sosai ina son na zama babbar yar kasuwa watarana" Cikin jinjina kai yace"Baki sha'awar ki cigaba da karatun ki ne? Sai na yi shuru ban yi mgana ba sai da ya kara maimaita tambayarsa sannan nace"In na samu damar haka bazan ki komawa makarantar ba." Daganan bai karamin maganar ba ni kuma sai na Dauka kawai ya Tambayeni ne saboda hirar da muka yi a gidan Ramatu. Shi kuma har ga Allah alkwarin da ya yi ya ke son cikawa in yace zai maidani makaranta lokaci ya kure sannan maganar kasuwancin da nace zan fara sai yaga kamar yafi sauki gwara dai ya fara bani jarin da zan fara kafa kaina kafin ya rabu da ni. A daran ya kunna mana wani Turkish Film muna kallo muna zaune a saman kujera na zaman mutum biyu. Na'urar na saman Cinyarsa ni kuma ina ta gefensa muna kallon tare. Gajiya nayi da Tura kaina, duk wuyana ya sage ganin haka yasa da kansa ya ja kaina ya Dora saman kafad'arsa. Muka bi juna da kallo shi ya fara Dauke idanuwansa kafin yace"Zaki fi jin dadin kallon a haka." Sai ban yi mgana ba na gyara kaina saman kafad'arsa. Ana cikin kallo kawai ni bansan ya akayi ba sai ganin nayi jaruman Film din namiji da macen suna kissing din juna. Gabadaya sai falon ya yi shuru daman ba Wuta kuma mun kashe Fitila ssai hasken kallon ne ke haska Fuskokin mu. Kura musu ido nayi ina kallonsu shima ta bangaransa kamar kuma an dasa idanuwana, shi ma kuma ya  kasa tariye wajen. Shine kuma a baya in dai yaga za'ayi irin wannan abun sai ya yi saurin Tariye wa zuwa gaba. Ammh yau kuma kamar an dasa Hannunsa ya kasa gaba ballatana baya ammh a cikin jikinsa ya na jin Saukan Numfashina wanda ya had'e da Dumin jikina ya fara sauya yanayinsa gabadaya. A tare muka d'ago muna kallon juna shi idanuwansa da wani ruwa ruwa aciki ni kuma idanuwana Tarai tarai sai dai sun fara kankancewa. Bazan iya sanin ta ina abun ya faru ba ni dai naji hannun Assadiq acikin hannuna ya Damke daganan bansan yadda akayi ba sai ganin bakinsa na yi Daf da bakina. Daganan kuma sai na tsinci kan mu da aikata abunda na cikin Film din da muke kallo suke aikatawa wato kissing kuma kissing din na baki cikin baki ne. Bansan yadda akayi ba ni dai nasan na fita Hayyacina shima Assadiq din jikinsa na rawa ya kama kaina ya Rike gam yana totsan bakina da Harshena kamar Allah ya aikosa Ba dadi nake ji ba sai dai tsoro da bazatan yanayin sannan da Zafin da Radad'in da Harshena zuwa bakina ya ke yi. Allah bai kwaceni ba sai dai muka ji karar fad'uwan abu sannan ya iya sakin bakina. Ashe Laptop din ce ta sha kasa ni kuma ina ganin haka na kwace jikina na ruga da gudu cikin d'aki na Rufe kofa kunyar duniya duk ta gama sauka a kaina. Kan gado na kwanta ina maida Numfashi ina kuma shafa bakina inda ya Dau rad'adi D'au saboda azaban tsotsa. Sadiq achan falo kuwa mamakinsa kansa ya ke yi me ya same shi ya kai shi ga aikata abunda baya cikin Tsarinsa? Laptop din ya Dauke ya kashe ya ijiyeta nan saman kujeran shi kuma ya koma ya kwanta ya na kokarin yaki da abunda yake ji na son kara jin Dumin bakin Hasiya acikin bakinsa. Duk juyawar da zai yi sai yaji kamar alokacin ne yake kissing dinta ya taba bakinsa yafi a kirga shi kad'ai kawai ya na ta Mirmishi in ya Tuna. Wannan ne Kiss dinsa na Farko a Rayuwarsa kuma ya zama wani na musamman. Da Safe kuwa wasan buya na fara yi da shi, shi ko a jikinsa ni kuma ba na ma iya Had'a ido da shi Saboda kunyar abunda ya faru jiya. Ai tundaga ranar ban kara marmarin ya kunna mana kallo ba, kwana biyu tsakani yace nazo mu yi kallo. Kai tsaye nace a'a bazan yi kallon ba yau. Cikin mamaki ya kalleni kafin yace"Ko kina tsoron kada a yi abun ran nan ne? Sai da ya fad'i haka na kallesa sai kunya ta kara kamani sai na juya sum sun na koma kitchen ina rarraba ido shi kuma ya bi ni da dariya Lokaci d'aya ya na fadin"Kizo mu kallah na yi miki alkwarin makamacin abun wanchan ranar bazai kara faruwa ba" Ina jinsa ban fito ba ganin naki zuwa yasa shima duk bai ji dadin kallon  ba sai ya kashe shima ya koma ya kwanta ya na mirmishi shi kad'ai. Ranar jumma'a da Safe Tahir ya kirasa yace gobe zai dawo zariya. Sadiq na jin haka yace"Ni kuma ina hanya." Tahir yace"Hanyar ina? Sadiq yace"Zariya" Tahir yace"Shine baka gayamin ba? Sadiq yace"Ina shirin kiran ka ne sai gashi ka kira." Tahir ya katse wayarsa da Tsaki ya bar Sadiq na Dariya. Jin Tahir zai dawo gobe yasa ya ce min gobe zasu yi tafiya shida megidansa, ai sai naji ba dad'i tunda kusan Sati uku muna tare da shi mun saba da juna a kusa da junan mu. Bani da yadda zan yi ni na had'a masa kayansa daman ya wanke sai dai ba guga Sai da Safe ya tafi bayan ya bani 5k nace masa akwai kud'i a Hannuna. Bai damu ba ya Rike hannuna ya sakamin aciki sannan yayi min kiss a saman goshi. Ni na rakasa har bakin kofa sannan ya karbi akwatinsa yace na koma daki. Sai naji kamar zan yi kuka cikin Muryan Shagwaba nace"Yaushe zaka dawo? Kallona ya ke yi ko Kiftawa ba ya yi, sai gani ya yi na fara hawaye ina Kif kif da ido. Sai kawai ya sauke akwatin hannunsa ya shigo cikin Dakin. Bansani ba sai ji kawai nayi ya kama kaina kawai ya had'e bakin mu waje d'aya. Wlh abun na ransa daman ya na so ya kara Kissing din Hasiya ko zai samu sukunin da ya rasa tun ranar da ya fara jin Damshin bakinta. Ban hanasa ba sai ma rike hannayensa da na yi ina ba shi Damar haka sosai. Kissing muka yi har na tsawon mintina goma sannan ya saki bakina, sai na koma na lafe a jikinsa ina maida Numfashi. Shima rumgumeni ya yi yana fadin"Zan dawo da wuri kin ji ko? In ma na dad'e zamu rika waya ko? Sai na gyada masa kai, dagoni ya yi ya na sharemin hawaye. Ina yi masa Bye bye ya na yi min har sai da na ga fitansa daga get sannan na koma na Rufe kofata. Kan kujera na zauna ina jin wani kewa na Rufeni har miyan bakina na Dangwalo ina d'andana miyan bakinsa tare da jin bugun zuciyata na karuwa daga yanayin da na sani a baya. ***** Ya na komawa dakinsu ya share ya gyara kafin Tahir ya dawo. Tahir kuma sai yamma ya shigo garin, Ganin Sadiq sai ya aminta da cewa tun jiya Sadiq din ya dawo kamar yadda yace. Sadiq na faman tambayan Tahir yaya ya  baro su Hajja? ya yi banza da shi ganin haka yasa sai ya kama kansa. Sai da Tahir ya yo wanka yazo ya na shiryawa sannan ya kalli Sadiq da ke kwance lokacin ma Tunanin Hasiya ya ke yi. Kai tsaye yace"Ammh kai dai baka da Kirki mun yi fa mgana da cewa rana d'aya zamu taho." Sadiq kamar bazai tankasa ba sai chan yace"A jiyan ne na sauya Ra'ayina." Tahir ya yi tsaki kafin yace"Sai kaje chan kaji da banzan ra'ayin ka." Sadiq bai ma jinsa hannunsa na saman bakinsa d'ayan hannunsa kuma ya yi matashi dashi sai mirmishi ya ke yi shi kad'ai. Tahir ya kallesa kafin ya ja wani Dogon Tsaki ya wuce wajen kayansa yana shiryawa sai kunakunai ya ke yi domin bakaramin haushin Sadiq yaji ba. Tunda ya dawo bai samu waya da Hasiya ba saboda Tahir kuma baya so yasan ya na waya da ita shiyasa sai Ranar litini da yaje wajen aiki ya samu ya kirata suka gaisa yaji lafiyanta. Sultana ce ke ba shi mamaki yarinyar nan ta maida turo masa sako kamar Ibada Good mrning da Good Night. Kuma yasan duk sata ake yi ta Turo masa shidai bai taba kiranta ba kuma yana da Dalilin yin haka Ahalin da ya ke ciki ne neman mafita game da Hasiya baya so kuma Sultana ta shiga Tunaninsa yanzu. Yana ta nazarin adadin kudin da zai bama Hasiya wanda zai riketa bayan ya rabu da ita. Yasan ba shi da matsalan kudi Saboda Duk wata Abba na saka mai kudi, sannan Sauran Sisters dinsa ma suna saka masa kudi sannan ga kudin da Federal ke biyansu na Bautar kasa duk da Shigowar Hasiya Rayuwarsa yasa ya kashe kudad'e sosai. Ya zauna da Tahir ya fad'a masa Hasiya kasuwanci ta ke so. Tahir ya kallesa kamar sakarai kafin yace"Lalle yarinyar nan bata da Hankali wa zai bata jarin da zata yi wannan kasuwancin? Sadiq ya Had'e rai kafin yace"Ni zan bata Tahir." Tahir ya kunshe bakinsa kafin yace"To ai sai ka bata. Ka dai tabbatar bayan ka bata ka Rubuta mata takardan sakinta, domin ko wata daya ne da kwanaki ya ragemana a garin nan." Sadiq ya kallesa bai ce komai ba ammh sai yaji kamar kwanakin ma suna kara gudu ne, a baya ya fi kowa kosawa da gama Bautar kasarsa ammh yanzu sai yaga kamar Kwanakin na Gudu ne ya manta shekara d'aya yanzu kamar kwana ce. In zai je duba Hasiya sai dai ya je bayan ya D'au Excuse daga wajen aiki sannan ya ke zuwa  ya Dubata. Wani abu da ya zame ma Sadiq jiki shine tsotsan bakin Hasiya. In ya kwanta har mafarki ya ke yi duk sai ya kasa sukuni, in ko ya samu yaje sai ya dan tsotsa ko kad'an ne ba da yawa ba. Ni kuma gabadaya ya sabar min da wannan abun Shikenan nima in bai zo ba na rika shafa bakina kenan ina jin wani kewa har cikin kashin jikina. In kuma yazo kunya ke sakani ba na zakewa ammh in ya fara sai na bashi had'in kai. Daga dai kiss baya ko taba kirjinaa sai dai ya Rungumeni kawai. Da na yi masa mganar naga ya na zuwa ne ko ya dawo garin ne? Sai yace min suna kawo kaya zariya ne, shiyasa ya ke lekoni saboda ya Damu dani. Sadiq ba tare da ya farga ba kwanaki suka zo suka yi ta tafiya kamar ruwa, sai gashi ana saura sati daya su kamallah Service dinsu. Duk sai hankalinsa ya tashi ya kasa sukuni a karkashin ransa kuma sai yake jin wani irin kasalan jiki. Acikin zuciyarsa kuma ya na jin wani irin nauyi da farko ya kasa gane komai sai daga baya ya Fahimci na kewar HASIYA ne. Ya riga ya gama Tattara kudin hannunsa da niyar zai bama Hasiya na jarinta da zata fara kasuwanci. A daran ana gobe zasu je Zonal office nan ciki  zaria su karb'i Takardan shaidar kamalla Bautar kasar su sannan daga nan kowa sai ya yi ta kansa. Shi kuma daman ma'aikatan da ya yi Bautar kasa sun nemi da zasu rike shi a matsayin cikakken ma'aikaci ya ki ce musu komai. Tahir kuma sai damunsa ya ke da ya saki yarinyar nan? Yasan rabuwa da Hasiya shine mafitansa shiyasa ya zauna ya yi Tunanin Rubuta mata saki ammh ya kasa ya yaga takarda sama da goma ammh ya kasa iya sakin Hasiya. Tunani kawai ya ke yi kamar bai yi mata adalci ba tunaninsa in ya Saketa wani hali zata shiga? Fasa Rubuta takardan ya yi kawai ya Fice tahir baya nan yaje karbo wanki Tunda suna ta had'a kayansu. A waya ya kira Tahir ya fad'amasa zai je ya kaima Hasiya kudin da zata ja jari da takardan sakinta. Yana jin sauke ajiyar zuciyan Tahir kafin yace"Shine mafita Sadiq." Daga haka suka yanke kiran. Da kanshi yaje banki ya ciro 150k daga acct dinsa ya saka a Aljihu ya samu mashi zuwa gidan Hasiya. Ni kuma mun yi waya da Safe na jisa wani iri da na tambayesa sai yace min baya jin dadi ne ban yi Tunanin ganinsa ba sai ga shi daman ya fi zuwa Lokacin da ban yi zaton sa ba. Tunda muka yi wannan fad'an da su Ummi na daina shiga harkan su na koma Rayuwata ni kadai iyakata in mun had'u na yi musu sallama Ruwan su su amsa ko kar su amsa ni ban Damu ba Hakkin zaman tare na sauke. Ina cikin Daki naji kooking na dauka Habiba ce domin na kira Adda Fati nace ta aikota ta kawomin kayan miya sai dai ina Budewa sai naga Assadiq ya na sanye da shadda Dinkin zamani kansa ba Hula. Ina masa sannu da zuwa bai amsa ba sai naga kamar ya yi wani zururu kamar mara kuzari. Kafin na kulle kofa naje falo na iskesa zaune kan kujera sai na shiga kitchen na Dauko masa Pure water. Ya karba' ya sha sai dai ya rage ya bani ni kuma na karishe shanyewa. A'a kawai sai naga ya kwanta sai na zata jikin ne nasa. Kusa da shi na Tsaya ina fad'in"Jikin ne? Kallona ya yi da Jajayen idanuwansa kafin ya Sauke numfashi. A tunanina sanyi yake ji sai na juya zan koma daki na Dauko masa Bargo sai jin muryansa nayi cikin sanyi ya kira sunana"Hasiya." Sai na juyo kawai sai ya mokomin hannu alamun nazo ni kuma sai na nuna kaina ina fadin"Ni? Sai ya gyad'amin kai kafin yace"Zo nan SIYA." yadda ya kira sunana yasa na kasa yi masa gaddama. Jikin sanyin jiki na fara takawa gabansa ina zuwa ya kara mikomin hannu sai nima na mika masa nawa. Ya kama hannuna ya jimke cikin nasa ya na kallona cikin wani yanayi yace"Yanzu in nace zan sake ki Hasiya ya zaki ji ? Sai gabana ya amsa Ras! Cikin kura masa ido nace"Zaka sake ni ne ASSADIQ? Yadda na fad'i mganar ne bakina na rawa kamar yadda zuciyata ta ke rawa. Su suka taimaka wajen kara Narkar da zuciyar Assadiq da baisan lokacin da yajawoni na fad'a jikinsa ba sai ji kawai nayi na fad'a kansa sannan shi kuma ya saka duka Hannuwansa Biyu ya kamkameni. Fadi ya ke cikin wani Raunin murya"Ba zan iya ba Siya. Bazan iya sakin ki ba, saboda ina ji a jikina in har na rabu dake kamar na sare wata gaba daga cikin jikina ne." Yanayin mganarsa kamar zai fashe da kuka Zuciyarsa naci ya na Bugawa Fat Fat! Kamar yadda nawa ke bugawa. Kawai sai nima na saki jikina na Rike shi sosai sai kuka kawai. Cikin kukan nace"Assadiq wani abu ne ya faru dakai? Assadiq in ka sakeni bazaka zama na farko ba ammh ka sani Sakin ka sai yafi sakin Salisu da Abubakar illata Hasiya." Kuka ya kwacemin sai naji tsoro a Tunanina ko wani abu ne ya same shi sai ya tashi daga jikinsa ina Tattaba jikinsa cikin firgice nake fadin"Kana lafiya kuwa? Hannuna ya rike ya na kallona ni kuma sai hawaye ina fadin"Ko megidan ka ne ya koreka daga aiki tare da shi? Wani irin Tausayi da wani abu yaji na Dannensa sannan jikinsa da zuciyarsa na jansa zuwa ga wani abun Dabam. Ni dai bansan yadda akayi ba sai ganina nayi na dawo kasa Assadiq ya zama yana sama na. Kiss ya faramin nima da ya ke na iya na fara maida masa martani. Cikin zafi zafi ya ke sumbatar bakina nima ina kara rikesa yau abun ya wuce kissing ya koma shafa sassan jiki, yau har kirjina sai da Hannun Assadiq ya kai wani irin nunfashi kawai ya ke sakarmin a gefen kunnuwana daman riga da sikat ne ajikina ya yi nasaran cire min Rigar ya na shafa duk inda Hannunsa ya kai saman fatata bakina ko ya fara Daukan Radad'i saboda Sumbata. Muna yi nisa domin ni kaina ya yi nasaran tafiya da Sauran Tunanina mukaji wani abu na Gir! Gir! Ashe wayace da ke cikin Aljihun wandonsa ta ke Virbration. Kamar bazai dakata ba sai kuma ya Tsaya sai da ya ciro wayar yaga mai Kira Tahir ne sannan ya dagani Shaddarsa duk ta yamutse. Ina ganin haka na mike nima cikin kunya na tattara rigata na Ruga cikin Daki ya bi ni da kallo. Sai da ya tabbatar da na shige ciki sannan ya Daga wayar bayan Tahir ya kara kiransa. Yana Daga Kiram Tahir yace"Ya ake ciki ne? Baka bata takardan ba ne na jika shuru." Cikin Shakewar murya Sadiq yace"na bata gani nan tahowa." Tahir yace"Ya naji muryanka kamar wanda ya yi kuka? Sadiq bai Tsaya sauraransa ba ya kashe wayarsa. Ya koma ya zauna ya na maida numfashi. Batare da Tunanin komai ba ya mike ya nufi cikin dakin. Allah yasa nayi saurin maida Rigata ina zaune ina tattaba bakina ya shigo da Sauri na mike zan juya shi kuma ya Rumgumeni ta baya. Ina jin saukar Numfashinsa ta gefen wuyana mun dauki Lokaci a haka sannan ya sakeni ya juyo dani muna fuskantar juna. Kudi ya Dauko daga cikin Aljihunsa ya kirga Dubu ashirin ya sakamin a Hannuna sauran kuma ya maida su Aljihu. Cikin sanyin murya yace"Ki rike a hannunki zamu yi Doguwar Tafiya ni da megida na ne." Idanuwana suka yi kwalkwal ammh na kasa mgana. Kiss ya yi min a saman goshina kafin yace"Ki kular min da kanki sai mun yi waya ko? Ban bashi amsa ba ya sakeni ya juya ya fita. Na kalli kudin hannuna kafin wata zuciyar tace min in bai dawo ba fa Hasiya? Ai jin haka yasa na kwashi Gudu na Bisa har ya kusa fita daga Falon Kiransa na yi cikin muryan kuka "ASSADIQ." Cak ya tsaya sannan ya Juyo ya na kallona da gudu na tafi na Rumgumesa sai kuma na fashe da kuka ina fadin"Don Allah kada ka tafi ka barni ka dawo komai dad'ewarka zan jiraka." Yana mai kara Rikeni ajikinsa yace'" Nayi miki alkwarin komai Daren Dad'ewa da kuma Tsaka mai wuyar da zan shiya zan dawo gareki HASIYAAASADDIQ." mun jima muna makale da juna sai da muka kara jin wannan gir gir din sannan ya sakeni lokaci d'aya ya sumbaci bakina sannan ya bude kofa ya fita. Nan na Durkushe ina kuka acikin zuciyata sai nake jin kamar bazai Dawo ba? Ko dai wani abu ne zai sameshi bai gayamin ba? Ammh na Firgita da maganar Sakin nan in da Assadiq ya sakeni da na shiga uku na lalace. Sadiq kuma cikin halin tsaka mai wuya ya fita, ya kasa iya sakin Hasiya sannan ya kasa aiwatar da abunda ya kaisa sai ma yaje ya aiwatar da abunda bai kaisa ba. Cikin wannan Halin ya koma Tahir kamar yana jiransa ya na shigowa ya mike ya na fadin"Ka sake tan? Sai da ya kallesa sannan kawai ya samu kansa da cewa"Eh..!" Tahir sai ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Alhamdulillah har naji sanyi. Ina fatan ba ta ga laifinka ba ko? Ya na kokarin cire rigar jikinsa yace"Bata gani ba asali ma sai da ta godemin." Tahir yace"Haba ai kayi mata hallaci ne." Ya fad'a ya na kallon Sadiq da Rigan sa a hannunsa da ta yamutse kafin yace"Wai hala kayi wasan kura ne? Sadiq ya juyo ya na kallonsa da idanuwansa da suka sauya launi cikin shakewar murya yace"Me yasa kace haka? Tahir yace"Rigar ce naga duk ta yamutse kamar wanda ya sha wasan kura" Sadiq ya kalli Rigan hannunsa abunda ya faru tsakaninsa da Hasiya na Dawo mai daki da daki. Cikin wata murya yace"Eh tabbas wasa rigar ta sha ammh wannan wasan ya fi karfin wasan kura sai dai na Mutum." Tahir ya yi galala ya na kallonsa kafin yace"Bangane ba." Sadiq na kokarin rataye rigarsa a Hanger yace"Ai  bazaka tab'a ganewa ba Tahir,  Saboda har yanzu baka girma ba." Tahir sai ya tsaya kawai ya na kallon Sadiq cikin mamaki tun ballatana da sai a lokacin yaga Sadiq din duk ya Sauya idanuwansa sun ji ja, sannan Jijiyoyin kansa sun mike Rad'au. Har yammah bai wani sake ba yadai kwanta kawai ya yi shuru ya na Juye juye. Tahir ya gaji da tambayansa meke damunsa ganin ya yi banza da shi yasa yace"Wai ka na damuwa saboda ka saki zabiyar yarinyar nan ne Sadiq? Sadiq ya taso ya na fadin"Ba sunanta Zabiya ba Her Name is Hasiya. Hasiya Tahir." Tahir sai ya Bude ido kafin ya yi mgana Sadiq ya mike ya na fadin"Tahir ka kyaleni don Allah.' Yana gama fad'in haka ya shuri takalminsa ya bar Tahir da sakin baki kafin cham kuma ya daga kafad'a alamun dai bai damu ba. Sai Dare Sadiq ya Dawo kawai gari ya shiga shine har kofar gidan su Hasiya da suka zauna kuma baisan meyas kaisa ba abu daya ya sani Hasiya na cikin zuciyarsa kuma Tunaninta da Tausayinta na neman ya hanasa Sukuni. Koda ya Dawo ba su shiga Harkan juna shida Tahir ba kowa sabgar gabansa ya yi, Sadiq kwana ya yi bai yi barci ba daga karshe ya tashi ya yi addu'an neman zabin Allah da asuba da ya tashi sai ya samu kanshi cikin Halin Janaba saboda ya yi mafarkin ya kusanci da Hasiya sai da ya yi wanka. Sannan wannan nauyin kirjin da rashin sukunin duk ba bu shi sai dai Tunanin Hasiya na manne acikin Zuciyarsa. Shiryawa suka yi cikin Complete kayan Hidiman kasa suka tafi Zonal office ba bata lokaci bayan karban Shaidar kamallawansu suka Tsaya yin Hotuna da abokansu masu Hidimar kasa. Sadiq ya fara baro Tahir a wajen Domin Tahir baisan hotuna kala nawa zai Dauka ba. Tahir yazo ya iske duk ya had'a musu kayan su yana ma shirin kyautar da wasu kayan girkinsu zuwa ga yanmakaranta da suke tare da su. Daman masu gidan tuni sun gayamusu zasu tafi duk da daman kudin su ya kusa karewa. Tahir yace yana son gas da katifan su sai Karamin Fridge. Sadiq ya kallesa Fuska ba Annuri kafin yace"Zaka iya jigilan Daukan su? Tahir yace"Me zai hana? Sai kawai Sadiq ya bar masa botikai ne da wasu kayan filets da kololi Sadiq ya kyautar da shi yan makaranta suna ta Godiya. Ga kayan abinci ma duk ya had'a ya basu ba su had'a komai ba face kayan sawan su. Sadiq duk ya rage wasu kayan sawansu saboda baya som Daukan kaya, Tahir ne mai akwatina uku Sadiq kuma Biyu sai jakar baya sannan akwai karama ta Hannu da ya sanya takalmansu wasu ma duk ya ba ma Tahir saboda ya tsani Tafiya da kaya. Sun yi sallama da yan makarantan su suka rakasu ma har bakin Titi suka samu adaidaita zuwa tasha suna Daga musu hannu Domin an yi zaman Amana A tashar yan karfe da ke garin Zariya Tahir ya samu Motar Daura shi harda katifa, Sadiq kuma ya hau ta Gusau. Bayan sun yi sallama da Tahir har yana cewa"Ka yi ma zariya kallon karshe domin ban Tunanin zamu kara Dawowa" Sai da Motarsu ta cika sun hau Hanya sannan Sadiq ya furta a fili" Ta ina zan yi ma garin Zariya kallon karshe tunda ina da wani abu mai muhimmanci aciki. Tabbas zan dawo. Zan dawo gare ki HASIYA..!" *BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA DEE*! *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Gaban ayu*. *Hakkin daka gangariya*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. *Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* *Ana dafa GIMBIYAR KAZA da tattabarun garari*. *Janafty* *TMWBK2014* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj Mata muntashi tsaye mu yaki infection (sanyi) Wani ciwone Mai nacin gaske Wanda idan kikayi wasa xaihanaki jindadin Aure Sannan maganin shi saikin daure da nacin shanshi Akai Akai toh kufito🤌🏽 KUSAI TSIMIN TABAJE DOMIN MUNA DAFASHINE DA INGANTATTUN SAIWOYI MASU AMFANI AJIKI DAKUMA LAFIYA, CIWON SANYI, SANYIN MARA, BASIR DASAURANSU INSHA ALLAH DUK WANI CIWO INDAE NA SANYINE ZAIZO KARSHE DA YARDAN ALLAH KIDAE KIDAURE KIDUNGA SIYAN TABAJE KIJEFI TSUNSTU GOMA DA DUTSE DAYA💃💃💃 Akwai infection Wanda yake nuna kanshi Akwai Kuma kurman infection Wanda baxaki San kinada shiba Amma yanacan yana Miki illa domin duk kyan Kayan mata baxakiga aikinsu ajikinki ba ko Kuma sumiki aiki bayanda akaso ba Anason duk bayan wata 1 mace tasha maganin infection sbd samun lafiyar jikinta Alamomin shi sune Fitar farin ruwa Kaikayin gaba/ko kuraje Jin zafi yayin sex Daukewar ni'ima Daukewar sha'awa dadai sauran su Kafin kifara Shan maganin mata yakamata ki fara Shan maganin infection Ina Yan mata Budurwa kema Yakamata kidinga Shan maganin infection Dan kariya da lfy ki karsai kinyi Aure infection ya Riga yamiki illa Baki saniba Allah y bamu lfy y karemu Ameen 🙏 *Gusau.* Har suka isa Gusau Tunanin Hasiya ne cunkushe acikin zuciyarsa. Tunaninsa da Hankalinsa gabadaya ya na kanta ne sai yake ji kamar gangar jikinsa ne ke cikin Mota Ruhinsa da zuciyarsa na chan wajen Hasiya ya baro. Sai yake jin wani iri a cikin jikinsa kamar mara lafiya kamar kuma wanda wani abu mara dad'i ya faru da shi, ko kuma wanda ya kwanta Jinya na wani dogon Lokaci. Adaidaita ya samu Daga tasha zuwa gida kamar Mallam Tajudeen ya sani ya na jin karan adaidaitam ya bud'e karamar kofa ya leko sai ya ci karo da Sadiq yana sauke kayansa da Sauri ya fito yana yi masa maraba da sauka. Shi ya taimaka masa ya rage masa wasu kayan zuwa cikin gida suna tafe suna gaisawa cikin mutumtatawa kamar yadda suka saba. Sadiq ya tambayi Mallam Taju yana fatan gida kowa lafiya? Sai mallam Taju ya Rusunar da kansa yana Fad'in"Kowa lafiya Ranka ya Dad'e." Sadiq bai ce komai ba ya cigaba da takawa zuwa bangaran Umma, sai dai me? sai ya Lura da bangaren Abba a  Bude ne sannan ga takalma nan a kofar falon tabbacin dai akwai mutane aciki da Sauri ya kai kallonsa kan haraban gidan inda Motocin gidan suke nan yaci karo da Motar Abba. Cikin mamaki ya kalli Mallam Taju ya na fadin"Abba na gida ne? Mallam Tajuddeen ya gyad'a masa kai kafin ya samu zarafin mgana Sadiq ya rigasa da cewa"Ok kila yau jumma'a shiyasa bai kara fita ba." Haka zuciyarsa ta basa shiyasa ya fad'a Mallam Tajudeen daman bai yi niyar fad'a masa komai ba shiyasa ya yi shuru ya na Rausayar da kai. Chanza alaqan tafiyarsa ya yi Daga Shashen Umma zuwa bangaran Abba. Yana sanye da kayan yan Hidiman kasa sai jakarsa ta baya da ta Hannu akwatunan kuma suna Hannun Mallam Tajudden da ke bin bayansa. Siyama ce ta fito daga Shashen Mama dauke da Faranti shake da Ruwa da lemuka, ta na fitowa taci karo da shi ai sai ta zaro ido cikin washe baki da karfi tace"Yaya Sadiq.." Ta fad'a lokaci daya ta na kwaso gudu har lemu na fad'owa daga cikin Farantin Hannunta. Dakatawa ya yi ya na kallonta cikin d'an mirmishi ya ke fad'in"Siya ki yi a hankali." Sai kuma ya ji wani Dam! Sunan da ya kirata da shi sai ya famo masa da Tunanin Hasiya. Har Siyama ta kariso gabansa Tunaninsa na chan Zariya inda ya fito sai da yaji karad'inta a saman kansa cikin Murna ta ke fad'in"Yaya Sadiq sannu da zuwa." Ta fad'a ta na kallonsa domin ba su taba ganinshi da kayan Bautar kasa ba sai yau sosai kayan suka zauna ajikinsa suka yi masa kyau. Mirmishi ya sakar mata kafin yace"Siyamar Abba kina lafiya? Cikin washe hakoranta tace"Lafiya lau Yaya Sadiq sai dai Abba ne ba shi da lafiya har Su Baba Sammani sun zo ma dubashi  yau." Cikin Tarin mamaki yace"Abba ba shi da lafiya? Siyama tace"Eh jiya ma aka sallamosa daga asibiti Innani nata kuka tun jiya." Bai kara tsayawa sauraranta ba ya wuce da Sarsarfa takalman kafarsa na kara taimaka masa wajen kara bayyana Takunsa na Gif! Gif!. Siyama ta bi shi a baya da gudu ita da Mallam Tajudden da ke Dauke da akwatinsa. Ya na Bud'e kofar Falon ya shiga tare da sallamansa cikin Kakkausan Muryansa. Gabadaya mutanen Falon suka Dago suna kallonsa shima cikin abunda bai gaza mintina biyar ba ya gama Nazarin mutanen dake cikin Falon na Abba. Umma da Mama ya fara cin karo da su suna zaune a kasa gefe, Abba na Tsakiyar Falon a zaunar da shi bayan an saka masa filo ya tokare bayansa sanye yake cikin jallabiya kansa ba Hula ya mike kafafunsa saman Italiyan Cafet d'in da ya yi ma Falon kwanya. Daga gefen hannun Damansa kuma Innani ce zaune da makeken gilashinta ta yi zaune rashe rashe gabanta wani katon farin botiki ta Dafe shi kamar ranta ne aciki ya ke daga chan gefenta daga saman kujera kuma Baba Saminu ne da Yaronsa Auwalu sai Goggo Husai itama da Lullubinta daga gefe. Chan bangaran hannun Hagun da su Umma suke kuma ya hango gabadaya Sisters dinsa mata har da masu nisan sun zo suma. Yaya Saddiqa ce kad'ai bata ciki inaga ita bata kai ga isowa ba kenan. Sai kuma ya hango Mallam Shitu Mahaifin Sultana da Matansa duka Biyu yana kyautata zaton tare suka zo da su Baba Sammani. Tsaye ya yi da jakarsa a hannu duk ya na kallonsu kamar yadda suma suke kallonsa Siyama ce ta karisa tsakiyar Falon ta na sauke Farantin Hannunta tace"Yaya Sadiq ne ya Dawo.." Mallam Tajudeen kuma akwatinan Hannunsa ya sauke anan bakin Falon sannan ya fice. Sallamar da ba su amsa masa ba ne yasa ya coge bai karisa shigowa falon ba. Sai da ya kara yin wata sallamar sannan suka amsa masa gabadaya cike da Mirmishi da jin dad'in ganinsa. Yan'uwansa mata suna kallonsa cikin alfahari ne ganin yadda Kayan Hidimar kasar suka amshe shi kamar domin shi kadai akayi kayan. Sultana na chan gefe kusa da Big Sis Anty surayya ta na leken Sadiq cikin alfahari da Muradi mai girma. Sai Annuri Fuskarta ke saki kamar taga wani zara acikin wata. Bai Saurari Sannu da zuwan da ke tashi a Falon ba ya fara da Sauke Jakar Hannunsa yana mai tafiya zuwa gaban Abba. Sai da ya duka ne sannan ya Sauke Jakar bayansa lokaci daya ya saka Duka Hannunsa ya riko Abba cikin Sanyin Murya yace"Abba me ya same ka? Wai baka da lafiya da gaske? Ya karishe fad'a ya na kara nazarin Abba kuma Tabbas ya shaida ba shi da Lafiya saboda yaga ya rame idanuwansa sun zurma. Abba ya kallesa cikin son kwantar masa da Hankali yace"Ba bu abunda ya Sameni Magajin gida zazzabi ne kawai da zirga zirga." Sadiq ya yi saurin cewa"Abba da rashin Samun Hutu ko? Sannan kuma baka da lafiya ba wanda ya iya Kirana ballatana nasan me ke faruwa? Ya fad'a ya na zagaye kallonsa acikin Falon Umma da ke gefe ta kallesa bata dai yi magana ba. Sajida ce ta yi karaf tace"Abba ya hana kowa ya fad'a maka saboda baya so a tada maka Hankali." Kallonta ya yi cikin nazarinta sai yaga ta kara kiba sannan komai na Fuskarta ya koma babba ta yi baki sai Uban kuraje. Sai da ya kara kallonta yaga Ciki ne da ita har ma ya tsufa tabe baki ya yi bai ce komai ba. Juyawa ya yi yana gaida su Baba Sammani suka amsa masa cikin Sakewa Auwalu kuma ya bashi Hannu suka yi musabaha shi da Mallam Shitu. Gefen Abba ya zauna har ya na matse Innani da ke zaune ashe barci ne ya fara D'ibanta ta na daga zaune sai gyangyad'i ta ke yi. Jin an tureta yasa ta Farka da Sauri ta na fad'in"Wani mara mutumcin ne ke kokarin Tureni kusa da D'ana? Ta fad'a ta na kokarin gyara zaman gilashinta domin taga wani ja'irin ne yazo zai shiga tsakaninta da Sulaimanu a wannan Halin da ya ke ciki. Ido ta rika zarowa ta cikin gilashin nata ta na kallon Sadiq shi kuma ya juya ya na gaida su Umma da Mama. Mama ta amsa cikin Fara'a Lokaci daya ta na fadin"Mu ka ganka da kaya haka Magajin gida? Ko zaman zariya ya kare ne? Sai da ya gyad'a kai sannan yace"Mun gama da Hidimar kasa in sha Allahu." Gabadaya Sisters dinsa suka Had'a baki wajen fad'in"Alhamdulillah..! Kallonsu ya yi cikin mamaki Surrayya tace"Daman na tsani Zariyan nan bansan Dalili ba wlh.". Sajida tace"Nima wlh kiga har wani Rawan jiki ya ke yi in zai koma zariyan kamar wani chan ne gidan su." Hararanta ya yi kafin ya yi mata wani kallon Sama da kasa sannan ya tabe baki yace"Malama ki ji da kanki don Allah.". Yadda ya yi mganar ne yasa sauran suka sakamata Dariya. Shahida tace"lil bro ba ka da kirki." Ta fad'a ta na Danne Dariyanta domin kowa yasan yadda cikin nan ya Saka Sajida wani munin bala'i. Ai sai ta fara kumburin baki ta kalli Umma ta na fadin"Umna kinga Sadiq ko? Ki gayamsaa ni ba Sa'arsa ba ce wlh." Umma ta harareta kafin tace"Bakin ki na ciwo ne? Ba ga ki ga shi ba ki fad'a masa sai kin aike ni? Sai Sajida ta kasa mgana ta koma ta na wani cika baki da Sadiq. Sadiq ko hankalinsa ma baya kansu yana kam Abba suna mgana kasa kasa . Muryan Innani ce ta karad'e falon cikin Masifarta tace"Wai muryan wa nake ji kamar ta magajin gida? Baba Sammani yace"Shine Innani ga shi nan a gefen ki." Da Sauri ta riko Sadiq shi kuma ya kwace jikinsa yasan fa ta ganshi ammh wai ta na nuna bata ganesa ba. Kawai ana zaune kalau Innani ta fashe da kuka ta na fad'in"Allahu Akbar Allah ya yi magajin gida akwai Rabon ganawa tsakaninka da Sulaimanu, gani nan tun shekaranjiya Rabona da barci makiya da magauta sun sako min Sulaimanu a gaba, Lafiyan Allah ya yi min sallama ya fita ammh sai dawo mana da shi aka yi rai a Hannun Allah fa, sannan ni ina ganinsa Sannan Jifan magauta ne ba yadda ban yi kada su kaisa asibiti ba Amma Salamatu ta fara zama Mutuniyar kawai ta Daukesa ita da Suwaiba suka kaisa asibiti chan ya kwana sai jiya suka Dawo min da shi , ni daman Tunda na Fahimci Laluransa na nemo masa magungunan Tsarin jiki na jika masa su, to duniya duk ta lalace Mutane ba Allah a ransu ballatana sun ganshi Bul bul da Shi jajir da shi sun yi Tunanin ya na da wani shahararren arziki ne ba su san Rufin asirin Allah ba ne za su kashemin d'ana da ba ni da kamarsa" Ta karishe fad'a har majina na Zubowa Sadiq ya kauda kai kafin yace"Meyasa baki kirani kin Fad'amin ba? Da Sauri Innani tace"Ta ina zan gayamaka? Yar wayar tawa daka siyamin an dakaleta ta daina yi kwata kwata, su kuma iyayen naka sun ce wai Sulaimanu yace kada a kiraka a Tada maka Hankali, ni kuma kasan bansan garin da ka ke masta ba ai da ka ganni nazo na gayamaka ni fa Daman abunda nake tunani gwara kazo ku gana da Sulaimanu kila akwai Wasiyar da ya ke so ya bar maka Tunda kai kad'ai ne magajinsa a wannan Duniyan" Cikin Mamaki Sadiq ya kalli Innani sai Faman jan majina take yi girgiza kai ya yi kafin yace"Waya fad'a miki Abba zai mutu yanzu? Ai sai kin rigasa Mutuwa ma in sha Allahu." Sai Innani ta yi gum da baki. Abba na gefe ya na yar dariya shi da su Umma kowa na Rufe bakinsa Tuna yadda Innani ta rika kuka ta na fadin gwara ita Mutuwa ta zo ta Dauketa akan ta Dauki Sulaimanu shi kad'ai gareta in ya Mutu bata san ya rayuwarta zai kare ba. Yanzu ma kara fashewa ta yi da kuka kafin tace"haka nace dai gwara ni mutuwa tazo ta Daukeni ta bar Sulaimanu, shi kadai gareni da ya Ragemin sanyin Idanuwana, daman shi da Kulawa kad'ai na Haifa to bakincikin wasu maketatan sun kashemin ita da bakinciki Allah dai ya isar min wlh bazan yafe ba.". Tafad'a ta na sharan Majina da Haban zaninta ta cikin gilashinta sai Faman Hararan Mahaifin Sultana ta ke yi shi da Matarsa. Baba Sammani ne da goggo suke ta bata hakuri ta na kara auna Allah ya isa bata yafe ba cikin gayya. Sadiq na jinta ya kasa mgana gabadaya a gajiye yake ga Hayaniyar Innani duk ya ishesa. Jinginar da kansa ya yi jikin kujeran da ke kusa da shi ya lumshe ido ya na jin ana Dirama da Innani akan sai ta bama Abba wani magani da ta jika cikin Botiki wajen kwana Biyu kenan wai maganin magauta ne sannan da Jifa. Umma ta Dake ta na gayama Innani illar shan wannan jike jiken da ba wanda yasan wasu itatuwa ne ma Innanin ta jika zata Dora ma Abba, shi kuma bai isa ya yi mata Musu ba haka ma su Baba Sammani suna mgana yanzu Innani sai ta iya cewa ina Ruwansu da sha'anin D'anta. Ilai kuwa Baba Sammani ganin ana ta Daga da ita ta Dake yasa cikin Lallashi yace"Innani tunda har an fara na asibiti ki bari zuwa gaba sai ya fara shan na kin" Ai sai Innani ta kallesa a Dage kafin yace"Kaji min wani Tsirfa da Iyayi ko shisshigi Tusa kai ba kwarjini, ina Ruwan ka da sha'anin d'a na da zaka rika Tsoma min baki ? Ba asibiti ba asibito dole zan gina Sulaimanu da maganin Tsarin jiki tunda har kuna gani magauta sun fara sako sa a gaba." Ta fad'a ta na wani kumfar baki Duk ta gama Tofe na kusa da ita da Miyan bakinta. Juyawa ta yi ta na neman wanda zata aika chan idanuwanta suka hango mata Sultana da Sauri ta ya fito da Hannu sai da ta zo gabanta sannan tace taje ta Dauko mata karamin kofi ta Tsiyayan ma Sulaimanu mganin nan. Sadiq duk yana jinta baya so ya yi mgana ne Hayaniyar Innani ba ta karewa daga an hanata wannan sai ta koma kan wannan. Sai da Sultana ta Dawo da Kofin Inanni ta cika shi da wani kalan mgani baki har ya na wani yauki yauki ta kalli Sadiq ta na fadin"Magajin gida d'ago min Sulaimanu dakyau ko bai sha ba, Dore zan masa tunda ni na kawosa duniyar nan ba wata ba." Bude Idanuwansa ya yi da suka Sauya Launi kafin cikin sanyin murya yace"Innani mu ga mganin" Da yake shine sai batayi gaddama ba ta mika masa ya amsa ya na gani da ya shinshina sai yaji ma yana dan tashi, da Sauri ya kauda kansa kafin ya yamutsa fuska ya na fadin"Innani wannan wani irin mgani ne ya na wari? Innani ta kallesa sai dai batayi mgana ba saboda magajin gida ne. Innani naji ta na gani Sadiq ya sa Salima da Siyama su Dauke maganin gabadaya suje su watsar da shi suka Dauka suka fita suna toshe Hanci Innani ta shaka kamar ta Mutu. Abba ko fadi ya ke Sadiq ya ba shi zai sha shi kuma kai tsaye yace"Abba in Innani na fama da rikicin Tsufa kai fa? To wlh ka sha wannan abun in ma baka da wata cuta tabbas sai ka samo ta." Kowa sai danne dariyansa ya ke yi, Umma ta yi mirmishi daman tasan maganin Innani mutum daya ne kuma Allah ya kawo shi a lokacin daya dace. Sadiq ya takarkare ya na  yi ma Innani bayanin ire iren wad'annan mgangunan da cewa ba wai yace maganin gargajiya ba su da kyau ba ne a'a ya na magana ne akan irin nata gaskiya ba shi da wata manufa in ma maganin zata samo masa taje wajen masana abun su had'a mata na su bawai tace ita zata had'a da kanta ba a ransa ma ya fara Tunanin Allah kadai yasan da wani hauka ne Innani ta Had'a waje d'aya ta jika. Kamar Innani ta Hakura ashe ba ta Hakura ba, kawai ji akayi ta saka Ihu da kuka ta na fad'in"Shikenan tunda Magajin gida ya zubar da mgananin da ta jika ma Sulaimanu saboda Magauta" Ta kalli Sadiq ta na fadin"Sulaimanu fa Jifan magauta ne ko bakwa ganewa? Mutane yanzu sam ba Allah a ransu tunda anga ya na dan fita Harkokinsa shikenan za'ayi masa Sanadin samunsa Tir mutane dai ba Allah acikin ransu." Sadiq ya kalleta cikin kaushinsa kafin yace"Ba Allah a ran mutane ko ke ce ba Allah sam acikin ranki ? Sai Falon ya Dauki shuru Innani ta yi kasake ta na jin Magajin gida. Cikin bacin rai yace"In kin san akwai Allah meyasa zaki rika Tunanin wai magauta ne suka jefi Abba? Wannan ai Tunanin wad'anda ba Allah ne a ransu innani." Innani sai ta fara juya bakinta kafin tace"Ni wlh akwai Allah a raina Kawai dai ina gaya muku gaskiyan yadda Mutane suka Lalace ne." Sadiq yace"Ke dai kika lalace da shigen rashin Dogara ga Allah. Kuma Allah ne baki sani ba sannan baki da Tauhidi Shiyasa bakisan Takwalli ba." Ya karishe fad'a cikin kaushinsa. Abba na kishingid'e yace"Abubakar kyale min uwa hakanan don Allah." Sadiq yace"Abba ka bari na sanar da ita wanene Ubangijinta domin na Tabbata bata san shi ba" Ba Innani kad'ai ba kowa da ke falon sai da ya bi shi da kallon mamakin kalamansa. Shi ko cikin Daga Sautinsa yace"Man Rabbuka? Ya fad'a ya na mai kallon Innani kai Tsaye, Innani ta fara kyafta kyafta idanuwanta ta cikin gilashinta ta kasa mgana. Cikin Karin d'aga Sauti Sadiq ya cigaba da fadin"Man Rabbuka wanene Ubanginjinka? Rabiyalahul Lazi halaQani, Warrabani bini'imatihi_ Ubangijina shine Allah wanda ya Halliceni, kuma  ya reneni da ni'imominsa. Bi'aiyi shai'in Ta'arufu Rabbuka? Da wani alamomi ka ke sanin Ubangijinka? Aarufu Rabbi  alamatil kasira, _ Ina Sanin Ubangijina da alamomi masu yawa, minal laili wannahara, Wa shamsu walqammar, Daga cikinsu akwai dare da yini,da Rana da wata. Man Halaqa samawati wal ardi, wa shamsu walqamara, Wanene ya hallaci sammai da kassai? Sannan da rana da wata? Alllah Shine  wanda ya hallici  kasa wacce muke tafiya acikinta, kuma ya Hallici sama wacce take sama, kuma ya hallici wata da Taurari  wa'inda  suke cikin  sama kuma ya hallicci  mutane da duwatsuna, da itatuwa da dukkan komai, Allah shi ya ke saukar da Ruwan sama kuma ya ke azurta bayinsa, kuma ya ke ba su lafiya,  kuma shi kad'ai yafi chanchanta da mu bauta masa." Ya na kawo nan ya dakata ya na kallon Innani tare da Fuskokin mutanen da ke falon. da alamu jikin kowa ya yi sanyi sannan an natsu ana Sauraransa. Cikin yanayin mganarsa ya yi ajiyar zuciya kafin ya cigaba da fad'in"Ba Innani kad'ai ba duk wanda ke falon da  ya ke tunanin wani Mutum ya isa ya yi ma wani mutum wani abun to ya sani ko nace dukkan mu mu sani, Allah shi kad'ai ne ke da duka Kaddarorinmu a Hannunsa, shi ya hallice mu shi ya ke sa ka Faruwar abu mara kyau a Rayuwarmu dogara ko yarda da cewa wani zai iya maka wani abu wannan Raunin Imani ne sannan Rashin Tauhidi da ikilasi ne ya kamata mu sani duk abunda ya Faru damu ko zai Faru damu a gaba da Sanin Allah wani ko wata ba su isa su yi mana Abunda Ubangijin sammai da kasai bai yi mana ba." Ya karishe Fad'a lokaci d'aya ya na mikewa Abba ya kallah kafin yace"Abba zan je na yi wanka sannan ban yi sallar azahar ba ta kwace min ina bisa hanya." Abba cikin wani jin dadi dake fitowa daga cikin ransa ya gyada masa kai. Jakunkununsa ya Dauka tare da Tura akwatinsa ya bar falon. Sai bayan Fitarsa ne Mallam Shitu ya Dauki kabbara Baba Sammani na tayasa cikin farinciki Mallam Shitu yace"Alhaji Allah ya yi ma Abubakar albarka Allah ya kara masa ilimi da kwanciyar Hankali." Gabadaya aka amsa da Ameen Ameen. Innani ko sai sharan kwallah ta na fadin"Astagafurullah Allah na Tuba." Ta ke ta fad'i ta kadai ta fada yafi sau goma ta na yi ta na sharan kwallah, Abba ne ke ta cewa ta yi shuru hakanan babu abunda zai faru. Shi dai Sadiq sai da ya yi wanka ya yi sallah sannan ya kwanta Saboda ya Huta. ya na so ya kira Hasiya ammh kuma ya kasa bayaso ya Kirata yajita cikin Damuwa ne shiyasa ya fasa kiranta. Sun dai yi mgana da Tahir yace masa ya Sauka gida lafiya, daganan ba su Tsawaita mgana ba suka yi sallama Tunda Sadiq baya cikin Mood din magana. Barci ne ya Daukesa sai gabda la'asar ya tashi ya shiga Tiolet ya Dauro alwala, ya fito da niyar shiga bangaran Abba sai ya ganshi sun fito tare da su Baba Sammani zuwa masallaci sai yaji dadin ganin jikin Abba ya warware. Tare sukaje masallacin sai bayan sun Dawo ne su Baba Sammani suka yi shirin tafiya Abba ya ba da Mota yace a kaisu gida tare da tarin Alherin da ya yi musu yaji dadi matuka da suka tazo suka zo suka gaishe shi duk da yace su barshi ba sai sun zo ba. Innani dai yau taji wa'azi ba ta yi mgana ba itace ma ke fad'in kada a manta da Hassu itama a kai mata  nata alherin Abba yace bazai manta da ita ba, jikartace ba lafiya suna asibiti yasa ma bata samu zuwa ba. Duk suna Haraban gidan sanda suka tafi suna ta daga musu hannu da Fatan Allah ya kiyaye hanya. Sadiq na gefe sanye da Riga da wando masu saukin nauyi, hannayensa duka cikin Aljihun wandonsa. Fuskarsa ba Fara'a saboda bai sake da abunda suka yi masa wanchan zuwan da ya yi ba Shiyasa ya yi fuska ko mgana suka yi masa sai yaga dama ya ke amsa su. Shiyasa da Surayya ta zo gabansa ta na fadin"Ni ka share ko? Na yi ta kiran wayarka bana samu sannan na Tura sako cewa ka kirani shuru." Yana cin magani yace"Banga sakon ki ba." Daga haka ya juya ya koma Bangaransa Abba kuma an kira a waya ne suka koma shashensa shi da Umma tunda a asibiti an ce yana bukatar hutu harda gajiya da rashin Hutu a jikinsa. Sanin bai ci abinci ba yasa Surraya tace Sultana da dafa wani abu mai Ruwa Ruwa ta kai masa ita kuma jikinta na rawa ta Shiga kitchen ta girka masa Faten dankalin Turawa da Hanta ta had'a acikin faranti da Ruwa da lemu da ta Dauka zata kai masa Sadiya tace ta dawo taje ta gyara Fuskarta. Sajida ta kara da ta fesa Turare kada taje bata tashin kamshi. Surayya ta tabe baki kafin tace"Sadiq din ne naga ya zama abunda ya zama Tunda ya fara bautar kasar sa a garin nan." Sajida tace"Eh mana sai wani cika ya ke yana batsewa ko wa ye zai daka? Sa'adatu tace"Duk ku ku kyalesa ya na shiga Hannu sai kun ji shuru" Dariya suka saka gabadaya harda tafawa, Sultana dai taje tayi abunda suka ce tayi ta sako wani sabon mayafinta Baki daman ta na sanye da Doguwar riga na material. Sanda ta shiga falon Sadiq na kwance kan Doguwar kujera ya Harde hannayensa a saman kirjinsa ga TV a kunne ammh kuma Hankalinsa ba shi nan ya tafi wani waje na Dabam. Sai da ta kara yin Sallama sannan ya ji ta ya Dago idanuwansa ya na amsawa. Bai tashi daga inda ya ke ba, sai dai ya na kallonta ta Sauke farantin gabansa. Ta duka ta na fad'in"Sannu da Hutawa Yaya Sadiq." A saman lebensa ya amsa yana kallon Sultana da yanayin yadda ta karya Murya ta na yi masa mgana. Kallonta ya ke a kasa kasa, saboda yana ganin yadda lokaci daya ta ke kara masa girma acikin idanuwansa. Abinci tace masa ga shi nan ta Dafo masa kai kawai ya gyad'a mata. Sai ta kallesa a sanyaye kafin tace"Ko na Zuba maka? Da sauri yace"Ba yanzu ba.". Daga haka ya yi shuru, ita kuma sai ta kasa tafiya kanta na kasa ta na wasa da Gefen mayafinta. Anty Sajida tace ta tsaya ta d'an jashi da Hira ita kuma ta rasa ta ina zata fara Shi kuma mamakin zamanta ne ya kamashi sai dai bai yi mgana ba ya Tsaya yaga iya gudun ruwanta.. Yana ganinta ta na satar kallonsa sai ta kuma basar mirmiahi sai da ya kamashi ta gefen bakinsa. Mikewa zaune ya yi Lokaci daya ya na fadin"Sultana akwai damuwa ne? Da sauri ta Girgiza masa kai alamun babu. Shuru na wani Lokaci ya Gifta kafin yace"Tashi kije in ina son mgana dake zan kira ki kin ji ko? Sai ta amsa masa a sanyaye sannan ta tashi ta fita ya bita da kallo har ta fice daga falon Numfashi ya sauke sannan ya koma ya kwanta yana Tunanin mafita. Ko giyan wake ya sha yasan bai isa ya gujema auran Sultana ba. Sannan Hasiya fa? Baya tunanin itama zai iya barinta a daidai wannan Lokacin Tausayinta ya ke ji Shiyasa ya kasa sakinta a lokacin da ya Tsara. Su surayya har suka bar gidan ba su kara ganin Sadiq ba suma kuma ba wacce ta nemesa Gwara ma su shahida yan nesa sum had'u da shi a bangaran Abba da suka Shiga gaishesa. Tsabar Wulakanci  ko gaishe su bai yi ba, Sajida da ta kwana a gidan ne ta kallesa kafin tace"Sannu yayanmu ina kwana tunda mu kafi karfi ka gaishemu duk da muna gaba da kai." Innani na wajen ta fara masifa ta na fadin"Kaji min cin mutumci namiji ai a ko'ina shine Shugaba in da Mutumci ku zaku rika girmamasa Tunda shi Magajin kowa ne." Mirmishin gefen baki kawai ya yi batare da yayi mgana ba. Sajida ta tura baki Innani tace tasan wacce ta yi ma haka wannan uwar mijin nata mai kama da Ruwan inyamurai. Ba sadiq kad'ai ba hatta su Umma sai suka yi dariya Sajida ta fita da ciki a gaba kamar ta kifa Saboda Haushi. Cikin Sati daya Abba ya warware ya fara Fita wajen kasuwancinsa. An sha baki dai har mutanen Gummi sai da suka zo duba Abba Mallam zakari Kakan su Sadiq duk da yana fama da jikinsa shima.. Da yazo sai da ya yi mganar Auran Sadiq da Sultana Umma tace tunda ya Dawo gida ba jimawa magana zata ta shi, tunda Sadiq yaji haka hankalinsa ya tashi yasan wannan karon ba shi da Hujja kare kansa. Ga Hasiya in dai ya kirata a waya da kuka suke Rabuwa ita gani take yi kamar wani abu ne ya same shi bai gayamata ba. Shi kuma bude bakinsa ya yi mgana daidai ne da fallasan abunda ke Boye. Alhaji Jibril yazo duba Abba kuma sun jima tare a bangaransa suna mgana. Yaje har Shashen Innani sun gaisa ya bata kudi ta na godiya da saka masa albarka sai a lokacin ya taba had'uwa da Abubakar Sadiq sai yaga ma ai ganinsa yafi jinsa natsuwa hankali dattako komai Sadiq ya had'a shi waje daya. Duk yadda ya so ya samu dama acikin kwanakin nan ya koma zariya bai samu ba, gabadaya Tunanin Hasiya ya hanashi sukuni, mafarkinsa itace in ma ya na farke ne ita ne. Ga shi Umma ta zaunar da shi tace ya kamata su fara Fahimtar juna da Sultana shi abun ma sai ya yi masa wani iri ya rasa ta ina zai fara ma. Sai dai duk da suna gida daya saboda cika Umarnin Umma ya kan kirata a waya yace ta kawo masa wani abu in ya na Bukata. Sai hakan ya farantama Umma a tunaninta Sadiq ya fara aminta da Auransa da Sultana nan kusa. Dakyar a Daddafe ya yi sati biyu a gusai ya yi ma su Abba karya Tahir bai jin dadi zai je Daura ya Dubasa. Da wannan Damar kawai ya tsinci kansa a zariya Saboda Hasiya. Yaje ya iskeni duk na Rame saboda kadaici da rashinsa. A tunanina wani abu ne munmuna ya same shi tunda ni an riga an canfani ina da Farar kafa da bakin Fenti. Da na ganni gani ga Assadiq bansan sadda na daga tsalle na Rumgumesa ba. Shima haka ya kamkameni yana jin wani farincikin da tunda ya koma Gusai ya rasashi. Ranar ko girki ban yi ba tare muka fita mukaje muka ci abinci, washegari kuma Tun safe har dare muna tare da juna bansan haka zuciyata ta shaku da Assadiq ba sai a lokacin nake jin araina zan iya shiga wani mummunan Hali in na rasaahi. Shima kuma hakan ne ya shaku da ni sosai, ballatana bakina da baya gajiya da saka bakinsa cikin nawa sannan Hannayensa basa gajiya da kara kaina a sassan jikina. Sai ga Shi daga kwana Biyu sai da ya yi hud'u sannan ya Dawo gusai bayan ya yi min cefane mai yawa kuma ya karamin wasu kud'ad'e ina kuka haka ya tafi ya barni. Shima din su Umma ne suka Damesa da waya yana Tunanin kada su ce zasu kira wayar Tahir komai ya Lalace. shiyasa ya koma ammh ba domin ya gaji da Hasiya ba. Yana komawa ko sati bai yi ba yaji Gusau ta fita kansa Burinsa da Tunaninsa ya koma Zariya ya zauna tare da Hasiya Duk ya gama Tunaninsa ya Hango cewa ba shi da wata mafita sai na bin abunda zuciyarsa ke muradi. Ba tare da sanin su Umma ba Abba kad'ai ya yi mganar da shi ya fara neman Gurbin Masters d'insa sannan kuma ya karbi tayin da kamfani Dismento Nigerian Limited da ya yi bautar kasar suka yi masa na aiki da su. Da wannan Damar ya samu cikakken Lokacin tafiya zariya, ammh sai yace ma su Umma wasu takardunsa zai karbo achan cikin makaranta. Kuma da hakan ya ke samun zama tare da Hasiya ko da wani lokaci. Bai fad'a ma kowa mganar karatunsa ba sai da komai ya kamallah sannan har kamfanin sun ba shi Accepted Letter aiki kawai zai fara da su. Umma najin batun komawa Zariya tace bai isa ba ya maganar sultana? Ba shi da mafita Tunda cikar Burinsa ya ke so sai yace A tsaida mganar auransu nan da shekara Biyu in ta shiga SS3 sai ayi bikin nasu. Da wannan mganar Umma ta amince da komawarsa zariya a karo na biyu. Innani kuma jin an saka Lokacin bikinsa da Sultana sai bata damu ba ita bata ma tsaya jin shekarun ba ta fara Murna ta na lissafin wad'anda zata gayyata. Sauran yan'uwansa mata ba su da Sanin abunda ke Faruwa sai da kanin nasu ya sake tattaraawa ya koma zariya sannan suka sani. Surayya ta ciji yatsa acikin jikinta kawai taji kamar Sadiq yana Boye wani abu kuma koma menene yana da nasaba da garin da ya nace ma zama. Ita kad'ai ta acikin ranta ta shirya sai tayi bincike akan Sadiq kada yazo wata ya samu achan ta na so ta sauyasa daga yadda ya ke tun farko. *Janafty* *TMWBK2015* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488.* Haba Babyn Habiby ya zaki zauna kina ta fama cutar infection, ke ce rashin sha’awa, ke ce jin zafi yayin tarayya, ke xche d’aukewar ni’ima, ke ce kai’kayi ki fitar farin ruwa da sauransu, an yi maganin asibiti da na gargajiya amma duka dai, tau share hawayenki ‘karshen matsalarki ta zo, da Honeydrops infection flusher ko cleanser pro sai kin yi dariya da godiya don zai wanke miki duk wata cutar sanyi. Akwai original sabaya ta gyaran breast su cicciko kamar baki shayar ba, akwai ta hips da mazaunai ki yi ma sha Allah ki samu kaya kema su miki d’as ki bar yawo da doguwar riga. Na ce ba a nan muka tsaya ba muna da hadaddun kaya irinsu sweeteners, tighteners and wetners na tashin kan oga, wanda zai miki tukwicin dole, ke ko kurma ne sai ya yi magana ranar, don sumbatu ki dai samu abun rufe mai baki gudun ma’kota. Muna nan a garin Sokoto muna aike kowani gari kowacce kasa cikin aminci da rahusa. Kuna iya danna link din nan domin yi mana magana Kai tsaye https://Wa.me/2348167888934 ko kuma a kira 08167888934. Sai mun ji daga gareku isassun mata. Tahir ya sha matukar mamaki lokacin da Anty Surayya ta kira shi ta na tambayanshi game da Sadiq. sai dai mamakin na shi yafi karkatane inda ta tabbatarmai da cewa yanzu haka Sadiq na zariya. Abun sai ya ba shi mamaki a iya Zaman da suka yi tare da Sadiq yasan ya na da Burin cigaba da karatunsa ammh bai taba ce masa ABU zariya zai dawo ba. yadai san sun taba maganar BUK kano ya ke da Ra'ayin zuwa ya yi masters dinsa. Tahir ya kara shan jinin jikinsa da yaji dalilin kiran da Anty surayya ta yi masa shine ta na tambayansa a zamansu a zariya bai fahimci wani Sauyi Daga Sadiq ba? Ta na tambayan yana da wasu abokai ne bayan shi? Ko kuma bai Lura ya fara soyayya da wata ba? Ko kuma dai wani abu da ya Fara Dauke masa Hankali? Tahir ya yi shuru ya kasa magana a zahirin gaskiya yasan Sadiq ba shi da wani aboki Amini kamarsa, sannan Labarin Hasiya ne boyayye ga Ahalinsa kuma yanzu ba bu ita acikin Rayuwarsa. Shiyasa kawai ya fad'a mata iya abunda ya sani game da Sadiq sannan ya tabbatar mata da cewa ko shi bai gayamasa ya koma karatu zariya ba. Tahir ya Boye maganar Hasiya saboda akwai Amana Tsakaninsa da Sadiq bazai iya fallasa sirrinsaba, in dai ba shi ya nemi hakan ba. Sun rabu akan zai bincika mata achan Zariya in da Sadiq ya ke zaune yanzu da kuma Halin da ya ke ciki domin tace ita fa bata yarda ba akwai abunda ya ke d'aukan Hankalin Sadiq a zariyan nan, sannan ta fad'a ta kara Fad'a Hallayar sadiq ta fara sauyawa. Tahir suna gama waya da Anty Surayya ya kira Sadiq bai Dauka ba sai da ya kara kira ne sannan ya Dauka yana fad'a masa yana aji ne in ya fito zai kirasa. Sai Tahir ya kara Tabbatarea duk da yasan Daman Anty Surayya bazata gayamasa karya ba Haka ya yi ta dakon kiran Sadiq ammh har Dare bai kirasa ba, sannan shi din daya damu su yi mgana ya kirasa sai sharrin Network yasa bai same shi ba, Tahir yaji kamar ya zama Tsutsu ya gansa a Zariya. Har wani Shamsu ya kira cikin yan makaranta da suka zauna tare da su yana Tambayansa ko Sadiq ya Dawo nan dakin ne again? Nan take shamsu ya tabbatar masa da cewa tafiyarsu ba Dadewa wasu yan makarantar suka kama Dakin nasu sai anan ya kara Tabbatarma da kansa cewa Sadiq ya Sauya Muhalli wannan karon. Shi ko Sadiq sam ya manta da Tahir suna gama Lectures ya tafi wajen aikinsa sai Gabda mangariba ya koma gida. Ya iske Hasiya ta gama girki ta share daki ya na tashin kamshi sannan itama ta ci gayunta kamar yadda ta fara sabama kanta acikin yan kwanakin da suke tare. Babban abun da ke sakashi cikin Farinciki ya fita da Safe ya dawo ya iske Hasiya na jiransa cikin Farinciki nan take sai yaji komai na Duniya ya gama samu in dai ga shi ga Hasiya ne. Baisan wani iri abu ne mai karfi haka yake ji a kanta ba abu d'aya ya sani Allah ya had'a zuciyarsa da ta Hasiya waje d'aya. Tun dawowarsa ya zaunar da ita ya fad'amata cewa yanzu tare zasu zauna Ya samu gurbin cigaba da karatu sannan kamfanin da ya yi musu hidimar kasa sun Daukesa a aiki a matsayin ma'aikacin su cikakke, Hasiya ta yi murna da Farincikin jin wannan Labarin barin ma da ya ce tare zasu zauna tare yanzu. Sai ya kasance sun fara shimfid'a wata Sabuwar Rayuwar da dukkansu ba su Shiryamata ba. In ya na da Shiga cikin makaranta da Safe ya kan fara shiga kafin ya wuce wajen aiki daman kuma sun riga sun san ya na masters dinsa kuma sun amince da hakan. In bazai shiga makarantar ba sai ya wuce wajen aikinsa in kuma ya Dawo gida suna manne da juna shi da Hasiya. Girki ma tare suke yi ya na taimakamata da Dauko wannan suna yi suna Hira, Dibar ruwa shi ya ke mata wanki ma damam ya saba tare suke yi, abinci ma yanzu a kwano daya suke ci, in kuma baya Bukata sai su fita waje su ci abinci, da Daddare kafin su kwanta za su yi kallo ko kuma ya kunna musu game a babbar wayarsa su yi, ko kuma ya yi ta mata Hira kala kala na Duniya duk domin ya sakata Farinciki. Yana waya da duka yan'uwanta da shi har da Amma, hankalinsu ya kwanta a zaton su da kyakyawan yakininsu Hasiya ta samu sukuni da zaman lafiya a gidan auranta. Amma ta fi kowa jin dadin haka In Sadiq yace za su zo su gaisheta sai tace ba yanzu ba, tafi bukatar su natsu su samu kwanciyar Hankali da zaman lafiya. Har gidan Adda Rukayya sun je tare ba dai su jima ba ne a gidan duk da ya Fahimci kamar ba su cika shakuwa kamar Adda Fati ba, bai matsa sai yaji wani abun ba, gidan ramatu kuwa sun je bai san iyaka ba har gidan Inna Talatu ta kaisa ya gaisheta ya yi mata alheri. Kwata kwata Sadiq ya sauya Rayuwarsa gabadaya kamar ba shi ba, abu daya me bai sauya ba kwanan da suke yi Dabam Dabam, har gobe ita ta na cikin Daki shi kuma ya na Falo ne. Wannan matakin kam Sadiq ya kasa Jarumtar ketare sa tukunnah. ***** Yau ma bayan mun gama cin Tsiren da ya fita ya siyo mana da kayan Fruit muka zauna saman kujera muna kallo a karamar Computers dinsa. Tun ba na Fahimtar fina finan har yanzu na Fara Fahimta nima. Sanye ya ke da Riga da wando ammh wando 3quater rigar kuma mai gajerun Hannu. Ni kuma na sanya wata Rigar barci na Doguwa mai kauri wanda Ramatu ne ta bani kyautar ta acikin kayan auranta Lokacin bikinta da ya ke a gida ban cika sakata ba, shiyasa bata ji wani jiki ba. Ina zaune kusa da shi sai na yi matashi da kafad'arsa kamar yadda ya sabamin, bamu jima da gama jera kayansa acikin Wardrope dina ba da ya karbo daga wajen guga har da nawa, Da ba su da yawa sosai. Na tuna muna cikin jeran kayan ya kalleni ya na fadin"Iya kayan sawan ki kenan ko kin bar wasu a gida? Batare da Tunanin komai ba nace"Su kenan fa, don ma Adda Fati tamin Dinki Lokacin bikin mu." Kai Tsaye ya kalleni ya na fadin"Daman an yi mana Biki ne? Cikin ido ya kalleni nima ina kallonsa nace"Na manta Lokacin Tariyan mu zan ce." Sai ya jinjina kai kafin yace"Kinga kuma nima akwai hakkin yi miki kaya a kaina fa." Kai Tsaye nace"Ni na yafe maka Assadiq" Da Sauri yace"Ni ban yafe ma kaina ba zan siya miki kaya masu yawa In sha Allahu." A lokacin da zan kara mgana sai ya had'e rai yace baya son gaddama shiyasa na yi gum da bakina. Ni yanzu bani da wata matsala sai wacce Ba'a rasa ba na yi kiba na kara Fari kamar bani bace wannan Hasiyar da ke Danwake a dogon gida da ke Samaru ba. Ina yawan Tuna yan gidanmu in naga su Ummi na min wani abu sai na girgiza kai kawai, ni wani irin nau'in makirci da Ukuban gidan Haya ne ban sani ba ko nace ban gani ba ai sai dai na ba wasu Labari. Sun gama yada min Habaici da karad'e anguwa da Sirrina shiyasa ba mai kulani ballatana ya shiga Sabgata. Nima sai na kama kaina in ba Dalili mai karfi ba ko fitowa waje ba na yi. Ni dai ina musu sallama da gaisuwa in muka had'u saboda Nasihan Assadiq da yace kada na Biye musu mu yi gaba da Juna mu sani Tunda Zama ya had'a mu waje daya ko da bazamu yi Huld'a da juna ba to ya zama Dole mu zama ma su yad'a sallama a tsakaninmu. Shi ya kara nuna min cewa kada na Damu da mganar mutane a kaina abu daya zan yi yakini acikin raina shine Babu wani mai yi face Ubangijin sammai da kassai. Zama da Assadiq na kara sani wasu abubuwan mutun ne mai Addini da Sanin ya kamata, ni kaina a gabansa gabadaya raina ilimi na ke yi, ya faramin karatun Qur'ani da asuba bayan ya dawo daga masallaci Domin ya Lura ina da Rauni ta bangaran sanin addinin ma gabadaya. Sannan ya yi min fadan in na idar da sallah ba na tsayawa na yi azkar ballatana na yi addu'a ni kaina nasan gaakiya ya fad'a kwata kwata bani da Dakewa kan ibada da addu'a. Ammh yanzu na fara Sauyawa ya sanar dani muhimmanci Addu'a da rike Allah Saboda duk bala'in da Mutum zai shiga in ka kad'aita Allah to shi zai sama ma mutum mafita. K'aruwan da na samu sanadin zamana da Assadiq k'aruwa ce mai yawan da bazan iya kirga su duka ba. Ni kaina nasan Assadiq ya shiga zuciyata da Duniyata gabadaya batare da na sani ba. Idanuwana na wajen kallon ammh sam Hankalina ya tafi wani wajen sai da naji wayarsa na Vibration Gir! Gir alamun ana kiransa kenan, na yi mamakin ganin ana kira wayarsa sanin da na yi cewa in dai muna tare bai cika barin wayarsa a kunne ba. Da Sauri ya Daukota daga gefe ya duba ganin Tahir ke kiransa yasa ya saci kallona ni kuma sanin baya barina ina sanin wasu abubuwan da suka Dangancesa batare da ya fad'amin ba yasa na kauda kaina kamar bansa ma ana kiransa ba. Taba Fuskata ya yi Lokaci daya ya na fad'in"Kin fara barci ne? Cikin kankance idanuwana nace"Eh na fara barci." Kai Tsaye ya kashe kallon ya Dauke na'urar daga saman jikinsa ya ijiye a saman kujera ya saka duka Hannuwansa ya Dagoni. Sumbatar goshina ya yi kafin ya dan Rumgumeni Lokaci daya ya na Fadin"To je ki kwanta ko? Sai na gyada masa kai ya na rike da Hannuna har cikin Daki. Ya gyaramin in da zan kwanta ni kuma na shiga tiolet na kama Ruwa ko da na fito ya na Tsaye yana jirana. Na hau gadon ya lulluba min zani a saman kafata ya na fadin"Ki yi addu'a kafin barci ya Dauke ki " Nan ma sai na kara Daga masa kaina har zai fita sai kuma ya Dawo da Dauri daidai fuskata ya Duko ya sumbaci labbana sannan ya juya ya fita daga dakin ya na fadin"Sai da Safe." Ina jin ana ta kiran wayarsa bai Dauka ba, sai dai ya na fita ya jawomin kofar dakin ruf ya Rufeni. Tunanina ya fara kai kawon abunda Assadiq ke boyemin wanda ban sani ba, Sai dai na bi mganar Amma da tace kada mutum ya matsa da sai ya san abunda ba'a so ya sani ba. Gwara mutum ya yi shuru ya jira Lokacin da aka so ya san wani abun Addu'an barcin nayi sannan na gyara kwanciya ba Dadewa sai barci. Shi ko ba a falon ya tsaya ba, sannan ba'a a tsakar gidan ba sai da ya Bude gidan ya fita waje sannan ya Kira Tahir da ya ke ta Uban kiransa. Tahir da ya gama Fusata ya na Daukan kiran da ya fara fad'in"Kai ammh dai dan wulakanci ne Sadiq." Sadiq yace"Da na yi me kuma Dahiru? Tahir ya kasa mgana Saboda Haushi Cikin Kufuluwa yace"Bansani ba. Nace bansani ba, ka manta kace zaka kira dazu?  Yanzu ma kira nawa na yi maka baka Dauka ba? Sadiq yace"Ina wani abun ne sanda ka kirani yanzu, dazu kuma ai na fadamaka uziri na ko? Tahir yace"Ah Lalle Sadiq me ka koma yi a zariya? Sadiq ya yi shuru kafin yace"Me kuwa? Karatu da aiki mana." Domin daman Tunda ya rika ganin Kiran Tahir a kai akai a ransa yasan yaji Labarin dawowarsa zariya. Cikin son sanin wani abu Tahir yace"Ammh shine baka gayamin ba Sadiq? Sadiq yace"Ga shi yanzu ina fadamaka." Tahir ya sauke Numfashi kafin yace"Anty Surayya ce ta kirani. Nan ya shiga gayamasa duk suka yi da ita. Ya karishe da fad'in"Sadiq ka tabbata ba domin Hasiya ka dawo zariya ba? Sadiq yace"Wata Hasiyar kuma? Akwai wani abu tsakanina da ita ne yanzu? Tahir yace"Babu, ammh kuma dawowarka garin shima baya cikin Tsarin da muka yi mgana dakai." Sadiq ya yi shuru kafin yace"Tahir aiki na samu, kuma tunda na samu wannan damar sai na kara wata damar na Cigaba da karatuna" Tahir yace"Shikenan ammh ka kula Anty Surayya tace ka sauya hali sannan ta Umarceni da na saka ido a kanka.". Sadiq cikin Halin ko in kula yace"To ka yi mata abunda ta saka baka da matsala da ni." Tahir na Dariya yace"Har da Labarin wannan Zabiyar na bata? Sadiq yace"Duk ka yi daidai ne." Tahir yace"Kace eh mana in ba Tsoro ba." Sadiq yace"Ni cikakken Namiji ne kuma Tsoro ba shi da Gurbi a wajen Cikakun maza Tahir.". Tahir ya sheke da dariya Lokaci d'aya ya na fadin"Namiji Maza! Sadiq ya yi mirmishi kafin yace"Tahir. Tahir mu kwana lafiya." Tahir ya yi saurin tare shi da fadin"To a ina ka ke zaune yanzu? Sadiq yace"Uhm nan kusa da kamfani mu na samu wajen zama saboda yafi kusa." Duk yadda Tahir yaso ya gano wani abu Sai da Sadiq yasan yadda ya yi suka Rabu Lafiya batare da ya gane wani abu ba. Sadaf sadaf kamar mara gaskiya ya koma Daki ya Rufe kofa, Hasiya ya fara lekawa yaga ta samu barci karisa shiga dakin ya yi ya shiga makewayi ya kama ruwa sannan ya fito ya sauya kaya zuwa jallabiya ya koma Falo bayan ya kara gyarama Hasiya kwanciya saura kiris ta fado kasa. Akan doguwar kujeran da ya saba kwana ya kwanta ya fad'a Tunani bayan ya yi matashi da Hannayensa. Tunanin makomar wannan Boyayyiyar Rayuwarsa nasa ya ke yi, ya na da tabbacin yadda Big sis ta fara zarginsa bazata yi kasa a gwiwa ba sai ta Binciko komai kuma Faruwan haka daidai ya ke da Tsarwatsewan komai batare da ya Shirya ba. Ya zama Dole ya yi wani abu saboda Dauke musu hankali daga kara munana zargin da suke a kansa. SULTANA ce ta fad'o masa a rai sai kuma yaga tabbas itace makaminsa a daidai wannan Lokacin. Da ita zai yi amfani ya nuna musu cewa bai sauya ba, bayan Rayuwar da suka san shi da ita bai yin wata Rayuwar da suke zarginsa a kai. Ya tuna tunda ya bar garin sau daya ya Kirata a waya, shima zai yi mgana da Umma me ya kira wayarta a kashe sai ya kira Sultanan yace ta kai mata. Tun daga kuma ranar bai kara Kiranta ba ammh yana ganin sakonta a kai akai duk da yasan duk sakata aka yi ta rika yi masa wad'anan sakunan iskancin. Sannan yaga maganarta a WhatsApp duk da shi sai ya yi sati bai bude data ba, shi kafafen sada zumunta ba su cika Damunsa ba Tahir ya yi har ya gaji da ya Fahimci baya Ra'ayi. Da wannan Tunanin ya ta shi, yau  wajen aiki zai je tunda bai da shiga makaranta. Shiyasa da wuri ya fita Tea kawai ya sha ya fita ya bar Flat din da ya Rage agidan  ana tarewa aciki. Sai da yaje wajen aikinsa ya natsu sannan ya kira Sultana bayan ya Duba Lokaci yaga sun isa dawowa daga makaranta. Sai ga shi Sadiq ya Daddage ya na yi ma Sultana Hira wanda ya ke da yakinin yan saka ido duk za su ji Labari kamar ya sani kowacce na yawan kiranta suna tambayanta kuna waya da Sadiq? Ranar sun samu Labari mai dadi ta sanar da su ya kirata sun sha fira. Daga ranar kullum sai ya kirata in ya na wajen aiki duk da dai hiran ta su ta karatu da Tambayan gida ne ammah tabbas Hasashensa ya yi tasiri. Surayya da kanta ta kirashi ta na yi mishi Tsiyan wai ya shiga hannu sai yadda suka ga Dama da shi. Dariya ya rika yi a ransa ya na fad'in na shiga hannu ko kun shiga Hannu. Har su Umma suna samun Labari kowa sai yaji dadi jin Sadiq yanzu ya nuna da Gaske ya na son Sultana. Sai kuma mganar komawarsa Zariya ta bar Tunanin kowa. Suka koma Binsu da Fatan alheri tare da kara koyama Sultana wasu Dubarun zamantakewar. Sadiq ya na waya da Abba sosai tare da Mutanen shinkafi ammh sai in baya tare da Hasiya saboda gudun Tautsayi ma kashe wayarsa ya ke da Zarar ya dawo gidan nan. Ana cikin Hakane Abba ya kirasa da Mganar Salima da d'an abokin kasuwancinsa Alhaji Jibril. Tunda Had'in da yaso na Sadiq bai samu ba ya ba ma Mubarak izini ya zo ya nemi d'aya daga cikin ya'yansa. Sadiq ya yi supporting mganar Sosai. Acikin kuma Satin Mubarak yazo ganin Salima bayan Abba ya Kira Umma da Mama ya sanar da su komai. Ba'a samu matsala ta bangaren kowa ba sai Salima ta fara compain din cewa ita karatu zata cigaba Tunda suna Zana jarabawar Fita ne daga Secondary, mama ta kira sauran ya'yan yan Dakin su, su Sa'ima suka shige da ita suna mata fad'an ta shiga Hankalinta ga Sultana nan kanwar bayanta zata yi aure ammh ita ta Samu tana wani iskanci. Duk yadda ta nuna bata so sai da suka Tursasata ta amshi mganar Mubarak. Har sakeena na fadin bata da Tunani ne? Ba gwara ta yi ta Riga sultanan aure ba ta na dai ji ta na kuma gani Sadiq din baya son auran Sultana ammh Uwarsa da yan'uwansa sun  kafe sai an yi saboda sun san amfanin su kuma da ba sa son Sadiq din ya auri wata Daga waje. Kananun manganganu suna ta tashi, Duk da ga junansu ba sa nuna yan Ubanci ammh akwai wannan kishin Tsakanin ya'yan da suka Had'a Uba d'aya a tsakaninsu. Salima ba ta da mafita illah na Amince ma Mubarak sannan da yazo suka samu Lokaci suka gana sai taga zata yi auransa domin shima 80% ya yi daidai da Ra'ayinta kamar yadda shima ta yi masa daidai Dari bisa Dari. Hajiya Murjanatu ba ta so wannan had'in ba saboda a cewarta ba Tsaran juna ba ne shi da Alhaji Sulaimanu kuma ta na da Tabbacin ba domin Allah zai had'a wannan auran ba Da nuna raahin amincewarta Har ikirarin sakinta ya yi, kuma shima Mubarak din ya nuna mata ya na so, sannan da shawaran yaranta da na yan'uwanta sai ta koma ta yi shuru kawai Tunda ba ta da ta cewa. Da kansa ya shirya yaje zariya wajen yan'uwansa ya fad'a musu cewa zai kira su in Lokacin neman auran ya taso. Hajiya Murjanatu ta na mamakin irin zumunci na gidan mijinta da babu ruwansa kowa da kowa, ita kanta ta jima Rabonta da garin zariya da sunan wani sha'ani. Suma ba sa zuwa ballatana matansu da ya'yansu hana rantsuwa ta san iyalan Alhaji Tanko da iyalansa, sai Goggo Saratu ita gwara ita ta na biyo dan'uwan nata. Hajiya Halima ta garin ikko kuwa ba su had'u ya kai sau biyar ba. Ita fa tun wani rasuwar kanin Babansu Zahra da akayi ta yawo da Cewar Dalilin yar da ya Haifa mai Farar kafa ce ta yi sanadiyar karayan arzikinsa da Mutuwarsa bata kara ganin Hajiya Halimar ba. Su kansu yaran na su ba su san kowa ba domin da wayan su bai wuce sau d'aya suka taba zuwa garin da wayaun su ba. In ta yi masa magana sai yace shi ya ji da aiki yara kuma suna karatu in tace ita ya barta ta rika zuwa sai yace a'a, rabonta da Zariya tun auran Diyar Kaninsa Saminu wajen Shekaru hud'u kenan. Ita ta na ma so ta yi masa mganar ya'yan dan'uwansu da ya rasu da yarinyar da akace ta na da Farar kafa sai ta manta Tunda dai ita bata kara jin Labarin su ba. Abun na ranta ya na dawowa da Daddare bayan ta Shiga masa sannu da zuwa ta kai masa ruwa. Ta na zaune gefensa ta ce"Maganar auran Murabak din yanzu ne? Ya na gyad'a kai yace"In dai suka Fahinci juna me zamu jira? Hajiya Murjanatu tace"Hakane to Allah ya tabbatar mana da alheri su waye zasu nemam auran? Kai Tsaye yace"Alhaji Tanko da Saminu mana ina da wasu yan'uwan da suka fi su ne? Mirmiahi ta yi kafin tace"Baka da shi kam tunda duk sun rasu, ya ma sunan wannan wanda ya taba rasuwa kace min Ya haifi wata yarinya mai Farar kafa sai da ta talauta shi kuma sannan ta yi Sanadiyar Mutuwarsa? Sai da ya sha ruwa Sosai sannan ya mikamata kofin ya na fadin"Mamman kenan ki ke mgana." Da Sauri tace"Yauwa shi, wai ina Labarin iyalansa da matarsa? Alhaji Jibril ya tabe baki kafin yace"Ina zan sani? ni dai chan kwanaki naji Alhaji Tanko na mganar yarinyar ta sake wani aure kuma wai ko uwar tasu ta koma garin su." Hajiya Murjanatu tace"Ina ne garin na su? Cikin karamin tsaki yace"Bafullatanan Ruga ce na manta sunan garin, yaran kamar su hudu ne ina ji sauran biyun sun yi aure ita mai Farar kafar ce akace auranta uku duk wanda ta aura sai ta talauta shi wani ma an ce dakyar ya rayu." Cikin Tsausayi tace"Allah Sarki ku ma da laifin ku ai hakkin ku ne ku Kula da su bayan kasa ta Rufe idanuwansa." Cikin zaro ido ya kalleta kafin yace"Uban waye zai Daukan ma kansa masifa ? Ko Tanko da suke uwa da Ubansu bai Daukan ma kansa ba ballatana wani, ke ana gayamiki yarinyar sai a Hankali kina wata mganar ta Dabam" Hajiya Murjanatu tace"ammh ai babu wata Farar kafa a addini Abban zahra Canfi ne da rashin Tauhidi." Kallonta ya yi daga sama har kasa kafin ya tabe baki. Zata kara mgana ya Daga mata hannu Lokaci d'aya ya na mikewa ya shige ciki ya barta nan zaune. Da kallo ta bisa kafin ta Sauke Numfaahi. A cikin ranta sai taji Tausayin wannan Yarinyar Allah kad'ai yasan Halin Tsaka mai wuyar da ta ke Fuskanta a wajen Mutane. Abu kamar wasa sai ga shi ya Tabbata acikin watan waliyan Mubarak suka je har Gusau gidan Alhaji Sulaiman suka yi ma Mubarak Tambayan aure. Su Baba Sammani suka ba su Salima a matsayim mata. Sai dai ba'a tsaida Lokaci ba tunda Mubarak na gini sai aka saka nan da Shekara daya da Rabi kafin na Sultana da Sadiq kenan. Alhaji Jibril ya fi kowa jin dadin wannan Labarin bakinsa har kunne ko Mubarak albarka. Alhaji Tanko da suka Dawo nan kaduna gidan Alhaji Jibril fadi ya ke yi"Jibo ina ka had'u da wannan Ahalin ma su kudi haka? Alhaji jibril ya yi dariya kawai bai ce komai ba. shi ko Saminu fad'i ya ke yi" ni dai ko akwai kanwarta sai Nasiru Shima ya nema." Alhaji Jibril ya yi dariya kafin yace"Shege saminu har yanzu baka Daina son abun duniya ba ko? Shima ya na dariya yace"Yaya kaima fa na sanka baka kwai sai da Zakara." Dariya ya Bushe da shi kafin yace"Ka sanni sosai Saminu." Suna wannan Hiran ne a falon Alhaji Jibril bayan sun dawo daga Gusai da labarin irin sha tara na arzikin da aka yi musu a chan. Su ko sauran yan'uwan Salima mata yan Dakin Umma da suka ji Labari sai sukace meyasa ba'a hade da na Sadiq da Sultana ba? Umma tace itama sai da ta yi wannan tunanin ammh ganin kamar Mama ta fi son a fara yin na Salimar Shiyasa bata ce komai ba. Suma tace su bi mganar da Fatan alheri kada su furta komai. Innani ko sai shiri ta ke ta na Murna zata aurar da jikoki uku alokaci d'aya ba ta ga ta zama ba. Duk abunda ta samu sai ta boye tace na Hidimar Bikin Magajin gida da Sultana ne, Sai kuma Salima tace masu kid'an kwarya har bakin get sai sun cika gida. su san ranta ya kai na ganin auran jikokinta. Ba ma wanda ya zauna da ita ballatana ya sanar da ita ba Rana daya za'ayi auran ba. ******* *Bayan wata biyu.* Wata biyun da ya yi daidai da wajen wata hud'u da Tafiyar Sadiq Zariya. Yaje dai Gusai sau daya ya kwana Biyu sannan a wannan zuwan sun yi tad'i da Sultana a bangaren Innani. Duk saboda kauda Tunanin su Umma kan Boyayyiyar Rayuwarsa kuma ya yi nasaran haka. A lokacin ita da Siyama suna jarabawar shiga SS2 ne. Ko ba'a fada maka ba in ka ga Sultana zaka san ta kara girma da wayau. Kuma ta na ji kanta ita watace Tunda ta na da Miji a hannunta irin Sadiq. Salima kuma Tuni ban so ban so ya kare soyayya ta mika tsakaninta da Mubarak da ta ke kira Habibina. A sannu sannu kuma suna ta shirin su Tunda har Mutanen shinkafi sun san da mganar auran. Innani ta matsa sai da Abba ya Kira Mallan Shitu ya sanar da shi komai kan mganar auran Sultanan. A cewarta kada ya je ya kwanta ya ki yin komai gwara dai yasan an yi masa kokari. Zuwan da Sadiq zai yi Hasiya ta saka ayi masa awara tunda karya ya yi mata da cewa zai je gaida Matan ubangidansa da ya yi aiki a karkarshinsa sannan yace zai biya kauye ya gaishe da su. Da tace masa zataje kai Tsaye yace mata ba yanzu ba. Sai bata matsa masa ba sanin Halinsa baya son gaddama. Ramatu ta kira tana gayamata zai je garinsu me zata ba shi ya kai ma kakarsa.? Sai tace zata yi mata awara zata kira Habiba sai tazo ta karba ta kai mata. Aiko ta yi awara mai kwai ta saka a wata Roba ta yi siling dinsa. Habiba ta kira tazo ta Dauka ta kaima Hasiya. Sannan ta kira tace ta had'o da Turare ta hada ma Kakar tashi da shi. Shi dai ya tashi tafiya ne ta ba shi abu a leda tace kada ya Bude sai ya isa garin. Kuma haka akayi sai da yazo ya Bude da takardan da ta Rubuta na Kaka ne. Assadiq yaji matukar dad i kuma ya saka aransa zai kaima Innani. Kuma haka akayi ita ya kai mawa yace daga wata yarinya ce mai kirki abokiyar aikinsa da ya ke yawan bata Labarinta. Innani ta hau washe baki ta na ta saka albarka har ta na tambayansa matar aure ce? Ya na mirmishi yace"Eh sosai ma." Nan Innani ta fara addu'a da Fatan zaman lafiya da zuru'a dayyiba. Shi kuma ya amsa mata da Ameen. To chan Shashen Umma yaga Roban wajen su Umma suna ta santi Innani kadan ta sam musu tace a saka mata a Firiza in kuma wata taci Allah ya isa. Da zai koma d'an kunnen mai Tsada ya siyama Hasiya a matsayin tukwaici shima Dan kunnen wajen Anty Sa'ima  ya siya Tunda ta na saida su. Sai ya siya biyu daya na Hasiya daya na Sultana. Ammh sai ce musu dayar na abokiyar aikinsa ce data aiko ma da Innani da awara da Turare. Har Umma na fadin hakan ya yi daidai, har ta had'a mata da Sabon Hijabi tace ya kai mata.. Bata san Surukarta ta aikamawa ba har Umma na tambayansa sunanta yace"ASIYA.!" umma tace Allah ya yi mata albarka. Da ya koma ya kaima Hasiya yace in ji kakarsa ta yi ta murna ta na Tsalle ya na yi mata Dariya. Baisan addu'an Innani ta karb'u  na Allah ya ba su zuru'a Dayyiba bq sai da yaji matsuwar kasancewa da Hasiya. Sannan kuma ya fahimci son Hasiya ya ke yi soyayyar da ta sa ya fara fad'a da Ahalinsa saboda ita. Kuma ya Fahimci ya yi nisa da bayajin kiran kowa a wannan Lokaci shi dai Burinsa ya kasance tare da Hasiya. Tunda ya Dawo ba shi da Sukuni gashi ya sabar mata in dai ya na gida ta na tare da shi. Ya rasa mafita ya duba kuma ya Hango sai yaga ai cutar da kansa ya ke yi. Hasiya matarsa ce ba laifi in ya ji Dadi da ita ko ya samu natsuwa da ita. Sai ya fara Romances da ni domin deb'e kewa akai akai ammh duk a banza kamar ma ya taso ma abun ne ko da yaushe da Ciwon mara ya ke kwana. Sai kawai ya zauna ya yanke wani Tunani da shawara. In dai zai yi Tunanin fara kasancewa Tare da Hasiya to ya zama Dole ya zama mai adalci a gareta. Kuma in dai zai yi mata adalci sai dai ya zauna tare da ita har  na abada. Kuma Faruwan hakan daidai ya ke da Fallasa abunda ya Boye. Ammh kuma in zai iya yin haka ya na da wata mafita guda d'aya. Duk da mafitan ta wani bangaren akwai Cutuwa ta bangaran Hasiya. Ammh kuma ba shi da zabi ne. Wannan mafitar ita kad'ai ce ta Rage masa kuma ya na Tunanin zai yi amfani da ita. A fili ya Furta "Am sorry HASIYA bani da Sauran zabi ne." *Janafty* *TMWBK2016* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V *LAME NIG!* *KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*. *AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*. *KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA* *KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?* *KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?* *TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*. *BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.* *TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*. *KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*. *ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU* Gabad'aya acikin satin nan sukuku ya ke, gani ya ke kamar abunda ya ke shirin aikatawa ba mai kyau ba ne. Kamar kuma ya so kansa da yawa. Sai dai Kuma ba shi da wata mafita ne tunda shima ya shiga tsaka mai wuya ne, wanda fitarsa wani mawuyacin Hali ne ba shi da mafita ne ballatana zabi Shiyasa ya zabi abunda ya ke ganin shine daidai matukar ya na son kasancewa tare da Hasiya. Sai ya so kamar ya yi mata mgana sai ya kasa gabadaya ba shi da sukuni Gulty din abunda zai aikata ya fara Damunsa Tun kafin ya aikata. Da ya so ya Hakura ammh kuma sai ya ke jin hakan kamar daidai ya ke da Rabashi da Numfashinsa Ya fara Son Hasiya tun ranar da ya fara ganinta tana rokonsa ya taimakama mahaifiyarta bai sani ba sai yanzu ya Fahimci haka. Matukar kuma ya na son kasancewa taee da ita sai ya bi hanyar da ya ke ganin ita ta dace, yasan ko a gaba Hasiya bazata Tsane shi ba Tunda komai zai aikata koma ya aikata Saboda Farincikinta ne. ***** Na dad'e da Lura da Assadiq ba shi da walwala acikin kwanakin nan, Saboda ya rage hira da bani Labarai sannan wasu abubuwan da muke kafin mu kwanta da Daddare irin su kallo ko fita yawo duk ya daina sannan Rikenin da ya ke yi a jikinsa shima ya daina ballatana wasannin da ya sabar min kamar dai ya na jan baya dani ne. Kuma na tambayesa ko wani abu na yi masa? sai yace bakomai gajiyan aiki ne kawai. Yau jumma'a ne da La'asar ya ke dawowa daga wajen aikinsa, tun bayan da na idar da sallah na fito Falon ina Dakon jiransa kamar yadda na Saba na tuna da Safe kafin ya fita yace na shirya in ya dawo zamu fita ina ta Murna a zatona wajen cin abinci zamu je ko kuna wayon zaga garin da ya saba fita dani. Sanye na ke da Atamfa Riga da sikat sai na Daura saukakken Dankwalina hoda na shafa da man baki, da wuri na gama abinci Farar Shinkafa da wake da Miya Tunda ina da kayan miya satin da ya wuce mun je kasuwa mun yo Cafane mai yawa. Ina jin an fara knookig din kofata na Mike da Sauri Farinciki ya cika zuciyata sanin da na yi Assadiq ne sai dai ina zuwa na bude sai da na Rage Fara'ata ganin ba wanda na yi tunanin gani ba ne. Maman Sulaihat ce matar da ta tare a falt din kusa da na Fadila. Yake na yi mata bata ma jira mun gaisa ba ta tureni kad'an ta shigo Cikin Dakin ta na fadin"Ina ce dai megidan bai dawo ba ko? Sai da na Rufe kofar sannan na biyo bayanta ina Fad'in"Bai dawo ba Mama." Saboda Mama na ke kiranta Tunda ta Haifeni ya'ya gareta zaka zaka zaka mata da maza, biyu mata biyu sun yi aure, sannan ta na da budurwa yanzu a gabanta da balaggagen Namiji. Ko da nazo har ta samu waje ta zauna ta yi rashe raahe ta na faman washemin Fararan hakoranta masu Dauke da hakorin makkanta ya na tashin kyalli. Kujeran da ke fuskantarta na samu na zauna ina gaisheta ta amsa cikin Fara'arta, ni har mamaki na ke yi yadda ta ke son shigemin Alhalin nasan su Fadila sun gayamata komai game dani Tunda tun bayan tarewarta suna hulda da ita, ita ma d'in ta na Huld'a da su. Abunda na lura da matar bata san ta girma ba, ba ruwanta da shigema yara sa'anin ya'yanta,  sannan ga surutu haka zata zo ta yi ta min surutu ta na dukan ruwan cikina kaza an yi kaza ni dai ban taba bata Fuska ba. Sau d'aya na taba shiga Dakinta itama matsamin tayi sai na shiga na Duba kaya bayan ta je kano ta dawo, da yake babbar yar kasuwa ne babu abunda bata siyarwa kama daga Atamfa leshi, materila, Dogayen Riguna na Hajiya Maryam's Eygptian Abaya +201123302418 Saboda ingancin su yasa ta ke sara a wajenta, ga takalma, zannuwan gado komai da kuka sani ba abunda bata siyarwa. Babbar yar kasuwa ce sosai to ta tab'amin matsamin na Shiga naga kayan na saka albarka Tundaga Lokacin ta cigaba da matsamin da cewa ban yi ma megidana tallah ba ne a yi mata ciniki. Yanzu ma bayan shigowarta mganar ta faramin cikin mirmishi nace"na gaya masa yace ba shi da kudi ammh in ya samu zaki jimu." Cikin yar dariyanta tace"Ai bakomai wlh waye baisan yadda Rayuwar nan ta yi Tsada ba yar nan? Ai mazaje na kokari wlh Allah dai ya saka musu da Hairan." Na amsa mata da Ameen hankalina na kan agogon wayata naga har Biyar Saura Assadiq bai dawo ba. Sama sama naji ta na fadin"Wai a ina mijin naki ya ke aiki ne? Naga da Sassafe ya kan fita? Kallonta na yi cikin mamaki kafin nace"Bansani ba." Cikin mamaki tace"Baki sani ba fa kika ce? Cikin son kauda zencen nace"Eh mana Tunda ban taba zuwa ba, na dai san yana aiki da wani kamfani ne." Jin haka yasa sai ta yi shuru ganin yadda na Had'e fuskata. Sai ta basar cikin tafa Hannu ta fara mgana da cewa"Ke yar nan na tab'a ki da Alheri sai naji wani Labari a bakin makotan zaman ki? Cikin mamaki na kalleta kafin nace"Wani Labari? Ai sai ta gyara zama kafin tace"Fadila da Ummi suka sameni har daki suna gayamin wai na kiyaye ki, kina da Farar kafa, kaza da kaza maganganu dai kala kala wai har suna fadin kin yi aure aure kina talauta mazan da kika aura har fa Wanchan yar fara ta na ce min na yi a sannu kada na Rabeki ki yi sanadiyar karayan arzikiina." Har ta gama mgana ina kallonta Daman ai nasan za'a rina sai naji raina bai baci ba. Cikin Sanyin Murya nace"Ai gaskiya suka fad'a miki" Sai ta wani tabe baki kafin tace"Wani gaskiyan, tuni na warware su dukkansu nace ni ba'a haka dani, kin gani nan wlh nasan Allah kuma ina da Ikilasi na kuma san Tauhidi na kuma san Allah ke yi ba wani ba tuni na zagesu na Fattake su yi ni har za su nuna min wannan mganar? Ni da kanwar uwata ta haifi yarinya sak irin ki itama duk wanda ta aura sai bala'ai su rika fad'a musu auranta Biyar wannan na Shiddan bai dad'e ba shima hukumar Costume ta kame kayan mijin, kuma wajen cucukun Fitowa da kayan sai dai komai na shi ya kare karkenta dai kannensa suka mata Duka suka saka ya saketa da cewar itace sanadin Faruwar haka jama'a ina zamu kai kan mu a wannan Rayuwar sam ba Allah a ran mu? Ta fad'a ta na wani rike Hab'a irin abun ya Dameta. Sai na kasa mgana a raina ina fad'in daman akwai mata ma su ire iren kaddara na? Kafin ma na tambayeta ta fara bani Labarin komai tundaga Tushe sai ga shi ina sharan kwallar Tausayin yarinyar nan sai naji ashe ni nawa mai Sauki ne, ta na fad'amin duk inda yarinyar nan ta zauna na Sati daya sai anga bala'i da Iftila'i. Ni ina ganin kaina ashe akwai wasu wad'anda suke Fuskarta mummunar Rayuwar da ta fi nawa, ashe ashe ni yar aljanna ce. Saboda yadda Hankalin mu ya tafi yasa bamu ji buga kofar ba sai da naji kiran wayata dake gefe. Da Sauri na Duba sai naga Assadiq ne ina rawan jiki na Daga. Cikin Dakushewar Murya yace"Ki na ina ne? Ina buga kofa baki nan ne? Da Sauri na mike ina Fad'in"Ina nan mana ban ji ba ne." Ganin na Nufi kofa yasa ta mike ta na fadin"Na shiga uku ba dai megidan ne ya dawo ba ko? Kai Tsaye nace mata shine ya dawo. Sai ta mike tana gyare gyaren mayafi ta na fad'in"An yi abun kunya ke kuma ba sai ki fad'amin ya na hanya ba." Ni dai bam kara kulata ba na nufi kofa na Bude ya na tsaye rataye jakarsa sai Wata Leda dake hannunsa. Ina kauce ma kallonsa na mika hannu zan karbi' ledan hannunsa ina Fadin"Sannu da zuwa." Hanani Ledan ya yi ya maida ledan bayansa ya na kallon idanuwana. Cikin mamaki yace"Me ya faru? Naga idanuwan ki sun sauya ne, ko kuka yi ne? Kafin na samu zarafin mgana Sai ga Maman Sulaihat ta na yar dariya yace"Sannu da zuwa." A dakune ya amsa mata ya na kallona cikin mamaki. Da Sauri nace"Ta shigo mu gaisa ne." sai ya  matsa ya bata hanya ta fita ta na cemin sai an juma. Sai da ta fita sannan shima ya shigo ni kuma na kulle kofar na bi bayansa. Ya na Tsaye a tsakiyar falon ina Shigowa ya mikamin ledan hannunsa Lokaci d'aya ya na fadin"Fruit ne ki yanka min" Da Toh na amsa kafin na karb'a, shi kuma sai kawai ya nufi hanyar cikin Dakin ya na kara fad'in"Zan yi wanka." Sai na bi shi da kallo kamar ba Assadiq ba duk ya sauya. Da ya ke sanin yanayinsa in ba da Safe ba bai cika wanka da Ruwan zafi ba. Kitchen na koma ina duba ledar hannuna, Kankana me da Ayaba sai abarba da lemu. Kara wankewa na yi na jera acikin Filet, sannan na had'a masa abincinsa da Ruwan gora, sai bakin Lemu daman shi ya ke sha shiyasa baya bari ya yanke mana. Ko kafin ya fito na had'a masa komai na shimfid'a masa Darduma a falo. Ya na fitowa sanye da Riga da wando saukakku ya zauna na zuba masa abinci bai ce min komai ba ya fara ci. Ina ta kallonsa da mamaki yadda ya kasa yarda mu had'a ido da juna. Sannan yau bai matsamin mu ci abinci tare ba cewa kawai ya yi naci abinci nace masa eh? Daganan bai kara mgana ba. Fruit din me ya Turamin gabana ya na fad'in"Baki ci ba." Cikin yake nace"Ai baka bani ba." Da mamaki ya Dago ya na kallona ni kuma Daman ya sabamin in dai irin su Fruit ne ya na bani a baki.. Ko abinci ne ma in muna ci tare haka zai ta cika Cokali ya na bani a baki. Bansan ko ya gane manufata ba ne yasa ya Dauko kankana ya nufi bakina da shi ni kuma na Bud'e ya sakamin. A haka har muka shanye gabadaya, ni na tattara komai na maida kitchen, ina mamakin me ya samu Asssdiq ne na gansa haka? Kwanukan da muka bata na Tsaya wankewa, da gyaran kitchen din shiyasa na bata lokaci. Ina fitowa falon na gansa kwance kamar yana waya, sai dai ya na ganina ya yi saurin katse wayar ya na lumshe ido kamar mai barci. Sai na nuna kamar ban gani ba , na wucewata ciki, na zauna ina jiran ko zan ji ya kirani kan mganar Fitarmu ammh sai naji Shuru. Na fita falo bansan iyaka ba ammh sai ya nuna kamar ya na barci kuma ina da Tabbacin idanuwansa Biyu. Da nagaji sai kawai na fito na Tsaya a kansa ina fadin"Assadiq mun fasa fitan ne? Shuru ya yi min, sai nayi Tunanin barcin ya ke yi sai na kyaleshi. Ammh ni kaina duk yanayina ba Dadi, Sai mangariba ya tashi ya tafi masallaci kuma bai Dawo ba sai bayan Isha'i. Ya dawo ya iskeni ina ta kuka wurjajan,Sai ya Rud'e Hankalinsa ya tashi daman ina zaune saman gado ne ina masa kukan Tab'ara. Sai ya tarairayoni a jikinsa ya na Tambayata me ya faru? Cikin Jan hanci nace"Ba kai ba ne." Da Sauri yace"Ni kuma Hasiya? me na yi? Cikin Tab'ara nace"To kace zamu fita kuma na Shirya ammh ka yi barcin ka ka kyaleni sannan kuma ma..." Cikin Sanyin murya yace"Kuma me? Ina kallonsa nace"Kuma kana da Damuwa ammh baka fad'amin ba? Cikin bude ido yace"Kamar ya? Wata damuwar? Da Sauri na tashi daga jikinsa ina fadin"Eh mana duk ka sauya sai ka yi ta abu kamar mara lafiya." Shuru ya yi ya kasa mgana ni kuma ganin haka yasa na koma jikinsa na Lafe ina fad'in"Don Allah in wani abu ne ka fad'amin? Saboda ni ne ko? Rumgumeni ya yi sosai a cikin Jikinsa kafin yace"A'a na gayamiki gajiyan zirga zirga ne fa." Na kasa yarda da mganarsa ammh kuma bazan iya masa gaddama ba. Lallashina ya dinga yi da Tattausan kalaman bakinsa har sai da na Dawo ina Dariya. Kallona ya yi kafin yace"Mun fasa fita yau sai Ranar monday kin ji ko? Sai na gyad'a masa kai. Ranar dai mun yi abunda bamu taba yi ba  shine kwana a muhalli daya sannan a waje d'aya acikin Rufi daya. Muna manne da juna yanayin da na so ya Dauwama har abada. Ranar asabar da Lahadi bai fita ko'ina ba sai masallaci kawai ya ke zuwa ya na Tare dani muna shan soyayyarmu. Cikin kwanakin biyun nan na saka su cikin Ranaku ma su daraja a cikin ranakun Aurena da Assadiq. Shi kamshi haka din ne a wajensa, har ga Allah yaso ya sauya Tunani ammh acikin kwana Biyun nan ya kara Tabbatar ma kansa ya na Bukatar Hasiya, itama Hasiya ta na Bukatarsa. Shiyasa kawai ya Tsaida Tunaninsa waje daya. A wayarsa ya shiga Goggle ya yi duk Binciken da zai yi, washegari Litini yace na Shirya da wuri zamu fita. Har ga Allah na zata gidan Adda Fati zai kaini, tunda ba mu saba fita da Safe haka ba. Hijabina mai ruwan kasa na Sanya har kasa, shi kuma ya na sanye da wani yadi mai milk dinkin mazan zamani da jakarsa rataye a gefen kafad'arsa Tunda yace zai shiga cikin makaranta. Mamaki ya kamani sanda naga mun zo wani asibit acikin sabon gari. Ni dai ina ta binsa da ido, domin da na tambayesa me muka zo yi a asibiti kai tsaye yace min"Gwajin jini za'a yi mana ni da ke." Sai na kasa gane ma'anar mganarsa  zan kara mgana sai ya min alamun da na yi shuru. Asibitin ba wata babba bace daga gani dai irin asibitocin kudin nan ne. Likitan ya nema aka masa iso Office dinsa, ni kuma ya bar ni a waje tare da Nurses yace na jirasa. Ya fi tsawon mintina arba'in da Shiga sannan sai ga shi sun fito tare da Likitan wani d'an gajere. Ya kalleni sannan ya kalli Assadiq ya na fadin"Is she d one? Sai ya gyad'a masa kai, sai naga ya tako mgana ya na fadin"Sannu Madam" Na amsa masa cikin yake, baya ya juya yana yi ma wata Nurse mgana cikin Harshen Turanci. Sannan ya kalleni ya na fadin"Madam ka bi ta" Sai yaga na yi wani fiki fiki da ido ina kallon Assadiq shi kuma ganin haka yasa da Sauri ya iso kusa dani ya na fadin"Kada ki daga Hankalin ki jininki kawai zasu d'iba domin gwaji" Sai ya nuna min damtsen hannunsa inda aka Danne da Auduga ina fadin"Nima kinga har sun dib'i nawa." Jin haka da kuma ganin da na yi shima ya na hannunsa sai naji Hankalina ya kwanta. Sannan a karkashin raina ina da yakini tare da Tabbacin Assadiq bazai taba cutar dani ba. Ya na rike da Hannuna har gaban Nurse din sannan ya sakeni lokaci Daya ya na fadin"Zan jira ki, kin ji ko? Gyada masa kai na yi, Nurse din ta yi gaba ta na fadin na biyo ta. Sanin da na yi Assadiq bazai taba cutar dani ba yasa na saki jiki na sannan na Natsar da zuciyata waje daya. Wani office muka shiga tace na zauna saman wani karamin gado, na zauna a darare ina kallon yanayin Office din, Sirinji naga ta na had'awa sannan ta zo da wani igiya na Roba tace na bud'e Hannuna na Dama  na bude na mika mata ta rike, sai ta Dauremin hannu da wannan igiyar, sai ga jijiyo sun bayyana a guda daya ta soka alluran ta zuki jinina sai da na Runtse ido saboda naji zafi, ta cire ta na min sannu, auduga ta sakamin a wajen tace na rike saboda Tsaida jinin. Na ko rike wajen gam saboda tun farko ni ba na son ganin jini sosai haka a gabana. A zato na an gama ammh sai naga ta fita tace min bari tazo ba Dad'ewa sai ga shi ta dawo da wata kwalba karama sai sirinji a gabana ta fasa kwalban ta zuga mganin cikin Sirinji, na zata wani abun zatayi sai naga ta kara nufoni cikin mamaki na bita da kallo ganin haka yasa ta na mirmishi tace"Allura tsaida jini zan yi miki Tunda naga kamar jinin bai Tsaya ba ne" Sai na Dukar da kaina ina daga audugan da ke hannuna naga jinin kad'an ne, sai na Dago ina kallonta Lokaci d'aya ina fadin"Ai jinin kamar ya Tsaya" Cikin Sauri tace"To ai har da na Rage radad'i ko baya miki zafi wajen? Kamar wata gaula haka na gyada mata kai sai ta min mirmishi kafin tace"To bari na yi miki yanzu zaki daina jin zafin" Ban gama mamaki ba naga ta yaye min Hijabi ta ce na gyara a Duwawu zata yi min ni dai kamar an dinkemin baki haka na mike na bata baya na ta d'an ja sikat dina kasa ta tsiramin alluran nan sai da na yi yar kara. Sai ta farablilayamin wajen ta na fadin"Sorry sorry Madam.." Ni dai nasan na koma na zauna sai kuma daganan na fara jin kaina na Juyawa, Ina ganin Nurse din ta fita ta dawo da wani abu Hannunta ta kariso kusa dani har kuma bayan ita naga wasu sun shigo dakin ammh bazan iya tantance fuskokinsu ba. Daganan ban kara sanin inda kaina ya ke ba sai misalin karfe Biyar na yammah. Na farka na gani kwance kan gado ba Hijabi a jikina sannan a gefen hannuna na Dama a wajajen Damtsena an sakamin Bandage an Rufe wajen, ina kokarin mikewa kaina naji ya saramin saboda yadda naji gabadaya jikina kamar ba nawa ba. Cikin tashin hankali na koma na kwanta ina mai Dafe kaina Lokaci d'aya ina fadin"Wash kaina." "Sannu Siya kin ta shi? Are u ok? Muryan Assadiq na ji a gefena da Sauri na juya ina kallonsa bansan ko yaushe ya shigo ba, ban kuma san ko Daman ya na cikin Dakin ba. Na kasa mgana sai shi ne ya kariso ya Rike hannuna mai lafiya ya na kara min sannu. Cikin mamaki na kallesa kafin nace"Me ya same ni? Jinin ne bai Tsaya ba? Ina kallon cikin idanuwansa na yi mgana ammh shi sai naga ya kauda kansa cikin Dashewar murya yace"Ya kike jin jikin ki yanzu? Cikin karin mamaki na bi sa da kallo, da Sauri na yi kokarin tashi, sai ya Rikeni ya tadani har ya na fad'in"Ki yi a Hankali kada ki fama Hannun ki." Sai a lokacin na Tuna da Raunin da naga an lullubeshi da Bandeji. Cikin karin mamaki na kara kallonsa ina fadin"Me ya faru dani? Me ye wannan a hannuna? Na ji ciwo ne ko?ina jin hannun ya yi min nauyi sosai." Ajiyar rai ya sauke kafin yace"Ki yi hakuri Nurse ce tace kina zaune saman gadon nan sai gani tayi kin fad'o, ashe fad'uwar da kika yi Allura ta cake ki a hannun ki, kuma wajen ya yi rami sosai sai da aka yi Dinke shine Dalilin da kika ga an saka miki Bandage kenan." Ina so na kallesa yaki bari mu had'a ido, ni abunda na ke so na tambayesa yaushe na fado daga saman gadon? Sai na shiga Tunanin abunda ya faru ammh na kasa tuna komai Ina shirin kara mgana sai ga likitan ya shigo ya dubani ya na min sannu. Har ya na fadin"Sory Madam ina ke miki ciwo? Cikin sanyin murya nace"Kai na sannan ina jin kasala." Sai ya juya ya na kallon Assadiq kafin yace"ba zata yi aiki da hannunta na Tsawon kwana uku ba, kada ka Damu zan baka mganin da zarar ta sha kan zai sauka sannan zata ji dadin jikinta." Assadiq sai ya jinjina kansa kafin yace"Ka tabbata ba matsala Dr? Dr. Yace"In sha Allahu kada ka damu." Ni dai bakina ya yi nauyi na kasa mgana ma har Assadiq suka fita da Likita ba jimawa ya Dawo. Shi ya taimakanin na saka Hijabina da takalmina muka fito. Nures na ta yi mana sannu ina ta wurga ido ko zan ga nurse din da dibi jinina saboda ina so na Tambayeta garin yaya na fad'o daga saman gado? Abun kamar hankali bazai Dauka ba. Sai da muka jira Assadiq ya karb'i wasu Takardu guda biyu da takardan mgani, sannan muka fita ya na rike da Hannuna har bakin Titi muka samu adaidaita sai gida. Muna zuwa shi ya shiga dani har daki ya na rike da Hannuna kuma muka ci sa'a ba kowa a tsakar gidan. Ni dai gabadaya jikina da kaina baya min dadi kwantar da nayi ya yi yace na bari ya fita yanzu zai dawo. Ya d'an jima sai ga shi ya Dawo da ledoji abinci ya siyomana jallop din shinkafa da kaza sai madaran Holladian mai sanyi. Bakina takaf naji ya yi min sannan hannuna naji kamar ba nawa ba. Ganin nace ba zan ci ba yasa ya Dagani cak ya Dora saman cinyarsa ya shiga bani a baki sai da na koshi. Gabad'aya fa na koma sai yadda ya yi dani Tunda kasalace ta Rufeni. Shi ya tattara komai zuwa kitchen ya kaini Tiolet yace zai min wanka. Na bude baki na Rufe na kasa mgana. Wai saboda kada na Fama Hannuna. Sai ga shi ya zage ya yi min wanka da Ruwan sanyi sai dai sun yi Dumi Tunda suna cikin bayi ne. Kunyar duniyar duk suka kamani ammh shi ko ajikinsa. Ya sani na Dauro alwala ya Daukoni cak a jikinsa ya kawoni kan gado. Shi ya shafamin mai,ya kuma sanyamin kaya sai dai na lura kwata kwata baya son kallon cikin Idanuwana. Saboda an riga an tada sallar a masallatai yasa bai je masallaci ba ya yi a gida ni kuma yace na yi a zaune in bazan iya Tsayuwa ba. Hakam kuma na yi bayan na rama azahar da la'asar din da suka Kubcemin sai na yi mangariba. Ranar ko Kofi bai bari na Dauka ba shi ya Dinga tarairayata. Dakyar na iya jiran sallar ishai ina idarwa sai barci Sai da asuba na tashi Lokacin da naji ya na shafa Fuskata da Hannunsa mai Dauke da Danshin Ruwa. A iya kimanin kwanaki ukun da Likita yace na Huta Assadiq shi ya rika yin komai, kafin ya fita wajen aiki har shara sai ya yi, sannan ya sama mana abun karyawa in kuma zai Dawo ya Taho mana da Takeway. Ranar kwana na hud'un da na Dage ni zan yi wanka da kaina Tunda na daina jin kasalan da ciwon kai, tunda ya bani panadol na yi ta sha. To a wajen wankan ne bandage din ya  cire kansa, na dade ina mamakin Hannuna Domin naga wani waje a dantse hannuna inda ke da tsokar nan ya yi wani abu a wajen. Kamar dai wani abu ya shiga wajen, sai dai na watsar da wannan Tunanin ne da Tuna ance har Dinki an yi min sai nayi Tunanin shaidar dinkin ne. Sai da na fito ne na nuna masa wajen ya Duba sosai sannan ya kalleni kafin yace"Ba ya miki zafi ko? Kai na gyad'a masa, sai ya yi mirmishi kafin ya sauke ajiyar rai. Bai gwadamin takardan gwajin ba sai da Daddare ya nuna min kuma ya yi min bayami. Yace Blood group dina ONegative ne sannan Gytoype dina AA ce. Shima ya ce min Bood groups dinsa O ne, Sannan Bangaran rukuni kuma AS ne shi. Ni duk ban wani gane nufinsa ba ma ammh sai na nuna masa na gane kawai  bayan na tambayesa me ye amfanin shi gwajin da muka yi? Kai Tsaye yace min"Saboda tseratar da kan mu da haihuwan ya'ya masu Dauke da wasu cutuutuka." Sai na gyad'a masa kai alamun na gane. Cikin Satin nan haka ya rika ji dani kamar Tsoka d'aya a miya, Ba mu sake fita ba sai da Sati ya zagayo yace na shirya muje yawo mu mike kafa, ban taba Tunanin cewa Assadiq ya shiryama Daran Ranar ba. Sai da muka zama Daya sannan abubuwan da suka faru suka fara zuwa kaina. Kofar doka muka je ya siyo mana gasassun kaji guda biyu da kayan Fruit, sai kuma madaran Holladian har ina masa mganar sai ya yi ta kashe kudi wajen siyan kayan kwalama. Sai kawai ya yi dariya yace min"Anthing for u my Wife." Mun dawo gida shi ya ciyar dani nima na Ciyar da shi, cikina har sai nace masa ya cika sannan ya kyaleni. Sai dai bai tsawaita Daren ba yace muje mu kwanta Tunda tare yanzu muke kwana. Ya matsamin sai na kara yin wanka ni ko na so na bi lafiyan gado saboda nagaji. Ammh sai ya hanani sai da na yi wankan nan na samu zaman lafiya shima ya shiga ya yo wankan. Koda ya fito har na kwanta kawai sai ji nayi ya Dagoni cak sai kasa ya Saukeni ya na kallona yace"Sallah zamu yi? Ina fiki fiki da ido nace"Sallar kuma? Kai Tsaye yace"Shafa'i da Wuturi ai bamu yi ba." Nasan in nace wani abu bazai yarda ba yasa ina Tura baki na koma tiolet na Dauro alwala koda na fito har ya saka Jallabiya ya shimfid'a sallaya. Sai kawai nima na saka Hijabi na bi bayansa. Mun yi raka'a Hudu a rarrabe sannan ya yi mana addu'a sosai. Na Dauka da ya rikeni ya fara Sumbatata ire iren wasaninsa ne da ya sabarmin sai nima na Saki jikina ina ba shi had'in kai. Ashe Assadiq ya sauya Tunani a kaina, ni dai na san ya daukeni sai kan gado ya kuma yi min Rumfa da Faffadan kirjinsa da babu komai da ya yi mana shamaki. Ni kaina yar rigar barcin jikina ya cire min ita fatarmu na gogan juna zukatan mu na Fitar da wani Sauti.Ras! Ras!. Ban taba Tunanin Assadiq namiji ba ne ne sai da ya maidamu abu d'aya sannan na kara jinjina mganar nan ta Hausawa da suka ce maza suna suka Tara. Ban ko sha wani abun gyara ba, na dai san ina shan Fruit da madara sai abun mai kyau sannan Hankalina na kwance inaga shi ya taimaka wajen kara ma Assadiq kaimu wajen samun Biyan bukata daga Jikina. Kusan mintina arba'in sannan naji ya kamkameni ya na fitar da wani Sauti mai kara, ni ko na yi wani yaraf ina jin gabbaina duka sun saki wlh naji azaba daga kasana domin rabona da Namiji Tun Abubakar, Salisu dai bamu kai ga ma wannan Sharad'in ba. Shi ya fara tashi yaje ya Tsarkake jikinsa sannan ya zo ya na tashi na, kunya suka sani na kasa tashi, ganin haka kawai yasa ya yi dariya ya fita falo shi ya bani damar tashi da Sauri ina Raruman Hijabina na fad'a makewayi na yi wanka. Ina wanka ina Runtse ido sannan ina Mirmishi, ni kad'ai ko sunan Assadiq na tuna acikin raina sai naji jikina ya yi min wani iri. Ashe kowata mace na Bukatar Sinadarin d'a namiji a tare da ita bansan haka ba sai da na kasance da Assadiq a wannan daran sannan na kara Tabbatarma da kaina Cewa Nima ina Bukatar Namiji. Har na fito na sauya rigar barci na kwanta bai Dawo dakin ba sai chan naji Shigowarsa. Sai nayi kamar ina barci ina jinsa ya hayo gadon ya lafe a bayana Lokaci daya ya Rumgumeni. A cikin kunnina ya ke min Rad'a cikin Sanyi da wani salama a muryansa yace"Nagode Siya. Yadda kika farantamin a wannan Daran kema Allah ya faratamiki kin ji ko? Kin motsi na yi sai ya fara min cakulkuli ai sai na bangare ina Dariya. Kunyarsa nake ji shi kuma ya san haka sai ya kyaleni ya koma ya kamkamni ya na sauke Numfashi. Ni na samu barci ammh shi ya kasa sai Tunane Tunane ya ke yi. Salama da natsuwa yake ji suna Shigarsa duk da farko shed'an ya so ya yi masa wasa da kyakyawan niyarsa. Shed'an na fad'a masa ta yi aure aure wasu sun rigasa sanin inda ya ke son sani yanzu. Ammh tunda ya kasance a wajen ya ji ya daina wani kokwanto Hasiya ta zama shi, shima kuma ya zama ita na Har Gaban Abada. Itace mace ta farko da ta nemi Sauya rayuwarsa, kuma ta yi nasara sannan itace mscen da ta san sirrinsa a yadda ya Sameta shi dai dari bisa Dari ta yi masa bai san ko in ya sake wani auran zai ji makin da ya bata ya ragu ba. Tun daga ranar Assadiq ya Bud'e anarcinsa ba kama hannun yaro. Wata irin rayuwa muke gudawar ta soyayya da kauna mai Tsayawa a zuciyar Masoya. Assadiq ya zama nawa nima na zama na shi ya maidani yar gata acikin mata kuma ya sa na fara Tunanin na yi ma Sauran mata zarra. "Hasiya zan kula da ke, zan zama bangon ki mai kare ki da dukan wani abun da zai kawo miki kunci ko Damuwa." Kalamansa kenan koda yaushe kuma na aminta da shi, Domin komai na Muradin ya'a mace Assadiq na yi min shi. Na kara kiba kularwar Assadiq yasa na bude har raman wuyana ya fara cikewa haka Ramatu ta rika fad'i Lokacin da tazo wajena. Adda Fati ta fi kowa farinciki ganin na samu kwanciyar Hankali Amma ma Dagachan bangaran ta na sanin Labarina Hankalinta ya kwanta. Adda Rukayya ma da tazo ta ganni sai da ta yi mamaki, saboda ni kaina nasan na sauya kamar ba wanchan Hasiyar ba. Yanzu ko su Ummi basa gabana Soyayyar Mijina ta isheni komai Tunda bai taba barina na yi kuka ba. Suma sun kula da haka sai suka shiga Taitayinsu. gwarama Maman Sulaihat muna shiri da ita tunda ita bata kyamaceni ba. *Janafty* *TMWBK2017* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* Haba Babyn Habiby ya zaki zauna kina ta fama cutar infection, ke ce rashin sha’awa, ke ce jin zafi yayin tarayya, ke xche d’aukewar ni’ima, ke ce kai’kayi ki fitar farin ruwa da sauransu, an yi maganin asibiti da na gargajiya amma duka dai, tau share hawayenki ‘karshen matsalarki ta zo, da Honeydrops infection flusher ko cleanser pro sai kin yi dariya da godiya don zai wanke miki duk wata cutar sanyi. Akwai original sabaya ta gyaran breast su cicciko kamar baki shayar ba, akwai ta hips da mazaunai ki yi ma sha Allah ki samu kaya kema su miki d’as ki bar yawo da doguwar riga. Na ce ba a nan muka tsaya ba muna da hadaddun kaya irinsu sweeteners, tighteners and wetners na tashin kan oga, wanda zai miki tukwicin dole, ke ko kurma ne sai ya yi magana ranar, don sumbatu ki dai samu abun rufe mai baki gudun ma’kota. Muna nan a garin Sokoto muna aike kowani gari kowacce kasa cikin aminci da rahusa. Kuna iya danna link din nan domin yi mana magana Kai tsaye https://Wa.me/2348167888934 ko kuma a kira 08167888934. Sai mun ji daga gareku isassun mata. *Bayan Shekara D'aya da Rabi.* ALHAMDULILLAH kawai zan ce acikin Shud'ewar Shekara d'aya da Rabi, wanda ya yi daidai da shekaru Biyu da wasu wattani da aurena da Assadiq. A zuwa wannan lokacin ni Hasiya Mamman kona na riga nasan Ubangiji ya gama yi mini dukkan wani gata anan Duniya. Ya bani rai da lafiya sannan ya bani kwanciyar hankali natsuwa da cikar Zatin aure a tare dani, sannan ya Turomin Namiji tamkar da Dubu ASSADIQ wanda ya kasance wani Kafad'a  da na kan saukar da kaina a samanta cikin kuka ko Dariya. In Dariya ne shi zai tayani mu Dara in kuma abun kuka ne shi zai taimakamin ya Sharemin hawayena. Zaman aure daman hausawa sun ce zo mu zauna ne sannan kuma sunce zo mu sab'a ne. Bazan ce ina cikin Farinciki dari bisa Dari ba akwai kananun matsalolin da ba su kai ma a fad'e su ba. Assadiq ya gama min koma a wannan Duniyan Tunda ya tsamo ni daga cikin kuntattaciyar Rayuwar da ni ke ciki ya raya zuciyata da abun kawa da Soyayya ya kuma nuna min nima kamar sauran mutane na ke wanda Ubangiji ya Hallice su tare da Tarin Ni'imominsa. Assadiq ya yi sanadiyar da na manta da Rayuwata ta baya gabadaya, na Fuskanci Farincikin da ke tare da Rayuwata yanzu Assadiq na sona sannan yana son Farincikina kuma Bukatuna daidai misali in bai fi karfinsa ba yana cika mun su. Ya maidani yar gata sannan yar lele wacce na zarce duka yayyena sa'ar miji da gidan aure. A wanchan Shekaran ne ya sakani na Zana Jamb daman SSCE na ta yi kyau bani da matsala duk da ya lura karatun bai wani Dameni ba ammh bai Damu ba ya zaunar da ni ya nunamin Muhimmanci ilimin ya'ya mata a wannan Rayuwar. Da taimakon kalaman karfin gwiwansa da Aljihunsa da kokarinsa na Fara karatu a Federal Collage of Education da ke zariya, da kuma Amincewarsa ko nace zabinsa na fara  karatu a kolejin a shashen Biology Computer. Da Farko ina ganin wahalan karatun ammh kuma Jajircewan Assadiq yasa na fara jin dad'in kasancewata cikin Daliban kalejin ta zariya mai Dauke da Dalibai mabambamta daga garuruwa a fad'in kasar nan. Duk abunda ban gane ba shi ya ke zaunar dani ya koyamin har sai na gane, sannan bangaren Computer bani da matsala babu abunda bai sani ba na Computer. Yanzu haka muna hutun karshen Shekara ne in mun koma zamu shiga NCE2. In muna da karatun Safe tunda Regular na ke yi tare muke fita, ya sama min abun hawa sai na wuce shima ya ke tafiya wajen aikinsa in kuma aka tashi na samu abun hawan da zai kawoni har gida ya na bani ishasshen kudin kudin mota tare da kudin kashewa har ma wani Lokacin in ce masa kudin ya yi yawa hararata kawai ya ke baya cewa komai. Duk abubuwan da suka faru na Farinciki ne a Rayuwata, Amma ta yi rashin lafiya mun je har gadan mallam Mamman tare da Assadiq ya gaida Amma da Adda, sai dai bai Kwana ba ya Dawo ya barni na kwana Biyu tare da Amma sai dai muka Dawo Tare da su Adda Fati. Sannan Itama Amma tazo garin Zariya sau daya ta Dubamu kwananta uku a gidan Adda Fati ta sauka. A zuwan ne ta taramu gabadaya ta yi mana Nasihan mu nemi Dangin Babanmu mu yi zumunci da su in muka ce zamu yanke zumunci Allah bazai kyalemu ba. Sai muka nuna mata, cewa ai suma basa neman mu sai ta fashemana da kuka da cewa in Aka je Lahira Mahaifin mu ita zai ma kaico tunda bata nuna mana Muhimmancin Ahalinsa ba, ta Horemu da kada mu Damu su basu neme mu ba, mu sani suna da Hakkin zumunci a kan mu kamar yadda mu ma mu ke da shi a kansu Ruwanmu ne in mun ga Dama mu sauke wannan nauyin. Da wannnan Nasihan nata yasa muka fara zuwa wasu sha'anin na su, ni saboda makaranta ma, ba kasafai na ke shiga ba, tunda Tun farko daman ina da wani bakin fenti da bakowa ke ina Rab'ana ba. Kuma asabar da Lahadi Tare da Assadiq muke cinyesu a gida da Fita siyon kayan kwalama a kantina kantina Zariya da Suya spots har sun gaji da gane kammanin mu. Restaurant kuwa sun samu bakin Aljihun Assadiq sai yadda suka yi da shi tunda na Lura shi Namiji ne mai son Fita irin wajejenan tare da matarsa. A lokacin ya siyamin kayan alfarma kala kala a wajen maman Suhailat da Dogayen Riguna takalma da Hijabai ba na shigar banza sannan duk wanda ya gani yasan ina cikin jin dad'i da kwanciyar Hankali ballatana da duk ya siyamin Dogayen Rigunan na wajen Maryam's Eyptian Abaya masu kyau da yarari. In na saka su sai na zama kamar balarabiyar kasar Saudiya Saboda Hasken Fata ta da ya karu tunda ina Samun ababen gina jiki, sannan abun mamaki na kara kiba na cika kamar bani bace wannan Hasiyar da kashi duk ya bayyana ajikina ba. Mun taba zuwa bikin Yaron Baba Tanko wanda yan'uwa da Dama da suka ganni sun yi ta mamakin ganina da Irin sauyin rayuwar da na samu su azaton su ina chan cikin Wulakantciyar Rayuwa ne. Har Baaba ta Lagos sai da ta yi maganar chanzatawata, Goggon kona kuwa ba kunya ta tambayeni wani miji na ke aure? Mirmishi nayi ban bata amsa ba, Sai Adda Rukayya ce  ta ba su amsa da cewa ma'aikaci ne kuma ya na karatu, nasan suna ta mamakin chanzata tare da mamakin ya aka yi na iya zaman aure kuma wani abu bai samu mijin ba? Tunda har suna tambayan shekara nawa da auran nawa ? Adda Fati tace shekaru biyu da wani abu. A fuskarsu sun kasa boye mamakin su, Baba Tanko da ya shigo ya ganni har na gaishesa bai iya gane ni ba sai da ya shiga ciki aka masa bayani sannan ya iya gane ni. Da ya dawo zai fita kai tsaye ya kalleni ya na fad'in"Hasiya ko ba ke ba ce Hasiya ba? Ina mirmishi nace ni ce Baba, kai tsaye yace"To to ammh nace bazaki jima ba zaki tafi ba ko? Nasan abunda ya ke tsoro shi yasa ban Damu ba na gyada masa kai. Kamar yadda yace ban jima ba na tafi ammh na yi ta sharan hawaye acikin adaidaita. Duk da haka ba kowa ya ke zama kusa da ni ba sai yan'uwana da suka zame min Dole, ban ga laifin Baba Tanko ba Tunda Har yau Mijin Adda Rukayya in dai ya na gida ban isa na shigar masa gida ba, in kuma na shiga sai dai in baya nan da na Fahimci zuwana na kawo ma yar'uwata matsala. Rabona da gidan tun wani zuwa da nayi ya tare kofar gida yace bazan shigar masa gida ba, na yi kokarin kada na nuna naji zafi ammh sai da na nuna hakan da na koma gida kuka na fashema Assadiq, shi ya yi ta lallashina ya kara Tusamin yakana da Iklasi acikin zuciyata ya kuma kara Sanar da ni cewa jarabawa ce in na yi wasa da Tauhidi to zan gaza har a wajen Ubangiji. Da nasihansa da shawarwarinsa yasa yanzu na daina damuwa da ire iren wad'anan kananun abubuwan. na maida Hankalina wajen karatunaa, ban dauka bayan Ramatu zan kara yin wata kawa ba sai ga shi Shigata kwaleji na had'u da Wata Safiya Ahmad, group d'in mu daya da ita kamar wasa sai ga shi mun saba har mun zama kawaye. Ita yar anguwan kaya ce sannan ita batayi aure ba, abunda yasa ma muka Saba ita ta fara muna ta na so na da kawa, sannan gata da Hankali da natuwa ga kokari, shiyasa sai na amimta da ita muke kawance da juna. Tasan ina da aure ta kuma san inda na ke zaune ammh bata san wani Labari a kaina ba. Assadiq kuma bai taba ganinta ba sai dai yakan ji sunanta a bakina, tunda baya zaman gidan sai weekend, saboda aiki da kuma karatunsa. Ko matan gidanmu yanzu ba na bi ta kansu kwata kwata duk da yanzu Ummi ce kad'ai Fadila sun tashi ammh kafin ta shin su sai da suka yi Rabuwar uwaka da Ubanka da juna ita da Ummi fad'a har da shigar mazajensu cikin maganar. Ranar da sukayi tsiyan ina gidan har da Dambe ina gefe ban ko rabasu ba, Maman Sulaihat ce ke raba su fad'an mganace ta tsegumi da kananun maganganu. Da cewar ita Fadilan Ummi ce taje gari ta na yawo da cewa wai ta na jin ihunta ranar Daren farkonta sannan ta ce kuma ta na jin ihun mijnta in suna kwanciyar aure. Wani Tudu wani ganganre Fadila taji Labari shine tazo ta tada bala'i daga gani dai ba gaskiya a lamarin Ummi Tunda tace itama Fadila tace mijinta ba shi da karfin mazantaka Tundaga yanayinsa wuyansa kamar marikin lema. Abu kamar wasa kamar abun Dariya, Sai ga shi sun had'u suna ta Tona ma kansu asiri,da mazajensu kuma daga gani suna zama ne su yi hirar, Dambe suka yi kace kace kamar wasu yara Maman Suhailat na ta ce min nazo mu yi rabo na yi baya, ni ba ma a wannan gidan ba na riga nasan irin wannan abubuwan na gidan Haya Tun zaman mu a garin Samaru. Su kansu kwanaki chan gidan da muka zauna da naje kwanaki gaisuwa Maman Salihi mahaifiyarta ta rasu Ramatu ta gayamin na biyamata muka ke gidan tare shine zuwa na Farko Tun bayan aurena. Gidan duk ya watse kaltume ta tashi ita da Maman Boy suma ance fad'a ce ta had'a su kaca kaca abun dai ba dadin ji ballatana gani, shiyasa na kiyayi kaina da mutanen da ke zama a gidan haya sannan na san duka Tarin kalubalen da mata ke Fuskata a zaman gidan Haya. Bayan Fadila ta tashi an saka wata wata ya'yanta Biyar, Sai Ummi ta koma kamar jaba saboda yadda ta ke Dari dari da mutane ba Halin kuma ni ta Dawomin bayan ta san abunda suka yi min duk da ta so hakan ammh kwata kwata ban bata Fuska ba. Saboda Sau daya maciji ke saran Mumuni, bazan kara saken da wata zata shiga jikina daga baya kuma ta Tozartani da kaddarata ba. Yanzu babbar waya ce ke hannuna ta kamfanin Infinix, sai dai har karamar wayar ta na Hannuna ita d'ayan layin ke ciki sai kuma ita ya siyamin Layin Airtel na ke amfani da shi Saboda makaranta sannan na ce masa ina son na Fara kasuwanci kuma ya bani goyon baya ammh yace na bari mu samu jari mai Tsoka Tukunnah. Ina zaune ne a wani yammancin Alhamis tunda muna Hutun makaranta ina Tunanin wani irin kalubale na taba fuskata a zamana da Assadiq?, Na duba na hango na kasa hango ko d'aya sai wata matsala guda daya da ta fara cin mu tuwo a kwarya. Abu na Farko  shine da gaske ne na Fara Fahimtar Assadiq na Boye min wani abu, duk yadda muka zama Rufin asirin juna  bai yarda a kirasa a waya ya yi ta a gabana ba, in dai ya na tare dani to wayarsa ta na kashe ne sai dai ko in ya fita daga gidan sannan yana yin wasu abubuwan marasa gaskiya.. Na fara Fahimtar bai gayama Yan'uwansa na kauye ya aureni ba, Tunda har yau bai taba had'ani da wani na shi ko a waya ba, Sannan na yi nayi har na gaji bai taba kaini garin su ba, daganan sai na fara Fahimtar akwai wani abu Tunda ai ya na zuwa ganinsu akai akai kuma yana kawomin Tsaraba yace Daga kakarsa. Ammh ya ki amincewa da ya kaini na gansu, har na gaji da tambayoyin su Adda Fati na zauna na Sharara musu karyar cewa ai ya kaini naje na ga Ahalinsa. In ma na Cigaba da matsamasa sai ya Sauya fuska kwata kwata ya nuna baya son mganar abun na Damuna, kada yazo mu fara tara zuru'a a samu matsala fa, tunda chan kwanaki na fara zargin ko ina da ciki ne ganin wattani uku ban yi batan wata ba ina Shirin yi masa mganar sai kuma naga Period dina daga kuma watan bai karamin Tsallake ba sai na watsar da Zargin cewa ina da Shigar ciki ne. A yanzu haka ko wata Daya Assadiq bai cika da Samun wani aiki a garin Abuja ba, ya tafi Sati uku bai zo gida ba mun yi mgana da shi yace min sai yagama sanin kan wajen gabadaya ko zai fara zuwa min weekend sai da ya barmin komai na kayan abinci da Ishaahen kud'i a Hannuna ko da wata bukatar ta taso. Sannan ya siya mota duk dai ba wata babba bace, Assadiq ya mallaki yar karamar motar hawa tun kafin ya samu wannan aikin na garin Abuja. Yadda abun ke damuna a raina yasa na kasa sukuni ga shi na yi karya ba Halin na samu Ramatu ko Adda Fati mu Tattauna. Ammh tabbas jikina ya bani akwai wani matsalan! Kuma ina da kyakyawan zato akan cewa yan'uwan Assadiq ba su san da ni a matsayin matarsa ba. ******** *GUSAU.* Asabar, 12:10pm. A gidan Alhaji Sulaiman Shinkafi a tsakiyar Falon Innani ne mata baje ana ta Bude wasu kayan alfarma acikin wasu Rantsatsun akwatina. Masu kawo kayan auren Mubarak ne daga Kaduna Yan'uwan Hajiya Murjanatu sai wasu daga cikin Dangin Alhaji Jibril daga Zariya. Innani na gefe da katon gilashinta sai faman washe baki ta ke yi ita da su Umma da Mama sai yan'uwan Mama da suma suna wajen. Sai kuma yan'uwan Saliman duka matan masu aure a garin suna wajen yan nesa ne ba su riga sun zo ba sun ce sai ana biki saura Sati daya zasu Fara sauka a garin. Yau ya rage saura sati Hudu Bikin Mubarak da Salima, shine suka kawo kayan aure akwatuna Shidda da ghana cike da kaya sai son barka. An yi musu abinci jallop rice da Chicken sai lemuka na kwali da wanda su Surayya suka had'a musu na kayan Itatuwa. Sauran kayan su Sanks kuma da za'a ba su su tashi da shi ya na chan gidan Surayya sun had'u da ita Amaryan tare da Siyama da Sultana sai Sajida da Saddiqa suka je suna kama musu sauran kuma suna gidan Abba da su aka tarbi maso kawo kayan auren. An gama Bud'e kayan an saka albarka Gabadaya sun ba da kudin Dinki Dubu Dari, Umma kuma ta maida musu Dubu Hamsun na Tukwaicin su. Nan suka Rantse ba za su karb'a ba Umma kuma tace sai sun karb'a suma kudin yabawa ce suka ba su. Falon dai na Innani ya yi albarka sai Hira ake da Shewa su Sa'ima na ta Daukan Video kayan Suna Rangad'a guda. Innani dai yau ba Masifa sai washe baki ta ke yi Allah ya kusa cika mata Burinta saura na Magajin gida da Sulsana Shikenan bayan ta gama ganin ya'yan su sai ta mutu daga baya. Baki na shirin tafiya bayan sun ci abinci sun yi salloli sai suka fara Haraman Tafiya. Umma taja Surraya gefe ta na fadin"Wai ina su Sultana ne? Shuru har yanzu basu kawo ba kada a yi aikin banza  naga suna shirin tafiya ne." Surayya ta Dauko wayarta Cikin Aljihun Doguwar rigar da ke jikinta na Shadda ta na fad'in"Bari na kara kiran su Umma." Daga haka ta fita daga Falon Innani ta koma chan gefe ta na kiran Wayar Salima ammh sai aka gayamata ta na amfani da wayar. Karamin Tsaki ta ja a ranta ta san Da angon Salima ke faman wayarta na kwazzaba, sai ta maida Akalan kiranta wajen kiran Sajida. Kira daya ana Biyu ta Dauka cikin magana a hankali Surayya tace"Sajida ya naji shuru ne? Zasu fa tafi" Da Sauri Sajida dagachan Bangaren tace"Laa gamu nan mun gama Saddiqa ce kinsan zata Tukami ta ci kayan Fulawa ta barke da zawo yanzu haka ta na Tiolet." Surayya tace"Subhanallah ku kariso sai tasha magani. Ku yi sauri don Allah ko kuma ku ba ma Su Siyama kudin adaidaita su hayo da kayan su kawo mana don Allah Sajida." Sai ta amsa mata da to shikenan sannan suka katse wayar. Tana juyowa suka had'e da Sa'ima da Sauri tace"Sun ce fa kada su yi yamma ga hanya ba kyau." Surayya tace"Wai Saddiq ce ke gudawa ammh nace su ba ma su siyama sakon su hayo adaidaita." Sa'ima tace"Asshaa. Allah ya sauwake." Tare suka koma cikin Falon Innanin, suka kara bama bakin baki da su d'an kara jira kad'an don Allah. Innani ta tabe baki kafin tace"Wai kuna ta su jira su jira to su jira Uban me Tunda sun kawo kaya an karb'a kuma tsakani ga Allah sun ci sun sha ai sai kuma ku bar su yi haraman tafiya in ba so kuke su kwana anan ba." Umma ce ta yi saurin cewa"Ai yanzu zasu tafi Innani." Harara Umma ta samu kafin a tab'e mata baki, Allah ya takaita abun bata kara mgana ba sai dai ta fara Rage fara'a s ta na ta yamutse Yamutsen fuska kamar taga kashi. Kafin su Siyama su kariso Surraya ta kira yafi sau biyar sai chan suka kariso Ita da Sultana Dauke da Botikai duk an yi rapping din su da Farin Salatif. Yan mata Biyu ne suna kuma Sanye da kaya iri d'aya, Doguwar itace Sultana ta na sanye da Atamfa mai Ruwan green shi yasa mayafin su ma kalarsa kenan ita kuma Siyama bata da Tsawo ammh kuma ta fi Sultana jiki. Da sallama suka shiga Falon Innani sai kallo ya koma kansu, har kasa suka gaida baki, su kuma suka amsa baki har kunne su a tunanin su d'aya daga cikin ce surukar ta su, Surayya da Sa'ima suka karb'i botikan da suka zo da shi suka Tura gaban bakin suna fadin na su ne. Ba damar suce bazasu tafi da shi ba Tunda sun ce domin su aka yi sai suka Fara Godiya. Sultana ce ta fara mikewa zata fita Saboda kallon da ake ta yi mata sai ta Tsargu, ita kuma Siyama har hankalinta ya tafi kan ganin kayan da akwatin da suka fara Daukan idanuwanta. Sultana na mikewa kanwar hajiya Murjanatu ta kalli Umma cikin Dariya ta na fad'in"Ma sha Allah nace Hajiya wance ce surukar tamu ko? Ta fad"a Lokaci d'aya ta na nuna Sultana da ke tsaye suna mgana da Surayyah. Kamar Innani daman ta sani kasa kunni daman ta na gefen su cikin zabura tace"Wace? Wai sulsana? Ta wani kyabe baki kafin yace"Ahir ba ita ce bace surukar taku wannan da kike gani jikata ce itama bikinta saura wattani kad'an ita zata auri babban Jikana magajin wannan gidan, shima domin kinsan magajin gida da kafiya ne yaki bari a had'a sha'anin ai da tare za'ayi, ita surukar taku da kike mgana zaku ganta wata figaggiya haka da iyayi da feleke wata doguwa haka dai to itace salimar ai bata shigo ba ne ko , ke Siyama ina kuka baro yar'uwan taku ce? Ta fad'a ta na Daga Murya, Umma dai sai ta bige da mirmishi. Matar ba ta damu ba ta yi ta fatan alheri. Umma ta amsa da Ameen ta na fadin"Bayan an yi na Salima da wattani biyu za'ayi na su. Sadiq din yaro na ne ita kuma Sultana yar kanwar megidan ne tun ta na karama ta rasa mahaifiyarta sai na karb'ota na riketa a wajena." Cikin jin dadi matar tace"Dakyau Tuwo na Maina. Allah ya nuna mana Allah ya sanya alheri." Duk yadda suka so su ga Salima ba su samu ganinta ba saboda sun ce yammah suke gudu ga nisa. Ita kuma tana gidan Surayya suna tare da su Sajida sai bayan tafiyar su suka Dawo gidan Saddiqa duk ta zurma Saboda gudawa sai da ta sha mgani. Nan fa suka baje ana ta kara ganin kaya ana yabawa da kokarin Mubarak da cewa ga shi ya gama gininsa sannan kuma ga kayan aure na gani na Fad'a, Salima na gefe ta na ta latsa wayarta Siyama na ta mata kwakwazon tazo taga kayan aurenta. Cikin Yamutsa fuska tace"Ke je ki yi ta gani, ni na san komai da ke ciki tun tuni." Sai falon na Innani ya Dau Ihu da Shewa sai taji kunya da ta ga sun had'a ido da Umma sai ta tashi da gudu ta fice Mama ta bi ta da cewa"Salima kenan an gama ni karatu zan yi." Dariya suka kara sakamata Sa'ima ko sai faman Turama su shahida ta ke cikin Family group din su na SS SHINKAFI'S. Inanni na gefe ta gaji da iface ifacen da suke mata a falo ta fara masifa ta na fadin"Wai meye haka? Kun zo kun cikamin Ihu a falona ku kwashi kayan ku don Allah ku ficemin a daki zan kwanta ne na Huta." Umma ce ta fara bata hakuri ta kuma Umarci su Surayya da suka kwashe akwatinan zuwa bangaren Mama. Innani na jin haka sai ta sauya mgana tace a kai cikin Dakinta sai Sulaimanu ya Dawo ya gani. Gudun fitinarta yasa akayi mata abunda ta ke so harta y'an ya'yansu Innani sai da ta tarkasu tace zata kwanta ne ba d'an jikan da zai Takura mata ita da gidan Danta. Sai taron ya koma Falon Umma har da Mama da Sauran yan'uwanta ana ta Fira da shewa. Alrady daman abinci da yawa aka yi  shiyasa sai ya zama ba su da yunwa. Shiryen shiryen bikin kusan duk an kamallah hatta kayan dakin Salima an gama siyan komai ba ma ita ba Har Sultana abu kad'an ne ya rage yanzu haka. Daman hausawa sun ce duk abunda aka sanyama Lokaci sai yazo, ga shi har auran Salima da Mubarak yazo, kuma cikin ikon Allah ya gama gininsa nan kusa da gidan iyayensa. Sannan kuma ya ce Salima zata cigaba da karatunta tunda Burinta ne. Kuma Saboda auransa ta b'ata Shekara daya gida a zaune bayan sun gama jarabawar SSCE. A yayinda yanzu su Sultana na First semester ne na SS3, ita da Siyama da yanzu suka kara zama manya yan mata wad'anda keranci Budurci ya gama kere su gabadaya. Da bikin Salima ya taso Umma da sauran yayyen Sadiq sun so a had'a auran nan Lokaci daya ammh yace daman Shi Tun farko bai ce za'ayi bikinsa Rana daya da Salima ba. Tunda shi Magajin gida ne sai aka yi masa abunda ya ke so. Da kuma Dalilin da yanzu ya na kula da Sultanan sosai yasa ba wanda ya taba wani Tunani. Suna waya sosai in dai zai zo daga Zariya yana siyomata tsaraba na kayan kwalliyar mata kuma yace in dai tana bukatar wani abu ta gayamasa zai yi mata. Kashe mata kudi ya ke tuni Abba da Umma sun daina mata wasu walwalahu Tuni Sadiq ya cike wannan bangaran. Shi kuma abunda ba su sani ba ya yi mata adalci ne, kuma ya na yin hakane saboda kada ya bada kofar da za'a fara Zargin boyayyiyar Rayuwarsa. Sauran yan'uwansa kuma sun masa uzuri da cewa ya fara aiki a Abuja a bari ta cewarsa ya samu natsuwa sannan ya Fahimci in da ya ke aiki kafin a yi auran na su. ********* *Abuja.* _EL-Rufa'i & Patners, 24 Aminu road Kano cresent Abuja Nageria._ Monday. Zaune ya ke acikin Office sabon office d'insa tunda yau litini aiki garesa kaca kaca, hankalinsa ya kasu kashi biyu ne daya na kan na'urar da ke gabansa d'aya kuma na kan wata Takardan dake gabansa. Sanye ya ke da Suit baki da Fari ya sasauta tektie dinsa saboda ya samu Saukin ayyuka. Ya na aikin ya na sakin mirmishi shi kad'ai da ya tuna wayarsu da Siya yau da Safe. Shagwaba ta ke masa ko yace kukan banza saboda ya sakamata rai zai zo mata weekend sai bai samu zuwa ba. Saboda akwai wasu ayyukan da ya tsaya yi, yasan kuma in yaje zariya bazai taba iya aikin nan ba in dai ya na ganin Hasiya. Kuma a yadda bai jima da fara aiki ba, bazai yi wasa ba ballatana aga kamar ya fara wasa da aikinsa. Kamar zariya gidan haya ya nema anan kusa da inda kamfanin su ya ke zaune. Tunda aikin ya zo masa ne bagatatan, ya jima da Tura CV Dinsa bai kuma taba saka ransa ba shi mutum ne mai amfani da duk abunda ke Hannunsa. Ya yi mamaki sanda yaga Sakon Email dinsu suna nemansa, kuma har yazo Abuja interviuw bai gama sakankancewa da zai samu aikin nan ba sai ga shi kafin ya Dawo ma sun bashi accpeted letter. Kamar kuma Sun san ya siya mota da kud'in da ya tara zai siya, da ya gayama Abba sai ya cika masa ya siya toyota kirar 406 da ita ya zo Abuja nan sannan achan Zariya da ita ya fara zirga zirgan zuwa wajen aiki da Shiga makaranta duk da yanzu Project ya ke yi ya ma kusa gamawa. A shekara daya da Rabin nan ya yi ta kokarin boye sirrin auransa da Hasiya, ya kuma tare duk wani hanya da wani zai Fahimci wani abu ciki harda yan'uwansa da Tahir shi kan shi. Yana cikin wannan Tunanin yana aiki Wayar Big sis ta katse shi. Dole ya ijiye komai ya Dauki wayarta suka gaisa. Mganar kayan auran Sultana ta yi masa Abba ya ba da miliyan Biyu a had'a mata kayan aure. Bai yi mamaki ba sanim Daman auren Sultana na gata ne a wajensa. Auran Hasiya ne ya yi shi da Guminsa. Kamar yace ta siya komai guda Biyu sai kuma ya fasa sanin abunda zai jawo sanadin subutar bakinsa. Cewa kawai ya yi su yi mgana da Sultana sai Surayya tace shima Abba yace a yi masa a kwatinsa. Dariya kawai ya yi yana kara jin Kaunar Abba a ransa. Shi yasa bai yarda ya kwanta Saboda mahaifinshi na da kudi ba. Abunda ya sani shine Abba ya tara musu kudi shima zai tarama ya'yansa Saboda yau in Abba ya fadi ya Mutu ba shi kadai zai gaji wannan dukiyar ba, ya na da Sauran yan'uwan da suma suna da Hakki a kan Abba. Dakyar ya aminta da karb'an gidan da Abba ya ba shi hakal malak a Million Quaters dake garin Gusai. Anan za'a saka Sultana kafin ya samu inda zai ijiyeta anan garin Abujan Ammh har acikin ransa a zariya ya ke da Niyar barin Hasiya saboda wasu Dalilansa. Itama ya na so ya had'a mata lefe duk da ya siya mata wasu kayan, ammh zai bari sai bayan auransa da Sultana tukunmah sai ya had'a mata da Jarin da zata fara sana'a da shi. Sannan rayuwar da ya ke yi ta Sirri duk ta fara isansa sai dai ba shi da mafita ne. Hasiya ta zama wani bangare na Rayuwarsa da har Abada bazai iya rabuwa da ita ba. Shiyasa duk mafitan da ya hango sai yaga gwara ya cigaba da yin Rayuwa guda Biyu a lokaci daya domin tsira da abunda ya ke so da Muradi. Tunda yanzu ya Fahimci ba wai mganar Tausayi ba ya na son Hasiya. Yana son Siya irin kauna mai zafin da zai iya aikata komai domin yaga ta na Kusa da shi har gaban Abada. Dalilinta ya samu natsuwa ta magidanta maza ma su aure, ko gida yaje haka su surayya zasu rika mganar ya kara kiba ya yi haske kamar ba shi ba. Shi kanshi yasan natsuwar aure na Dabam ne. Kuma Hasiya ce sanadiyar zamowarsa cikin wanman natsuwar da a koda yaushe bata gajiya da shi in yazo da bukatunsa zata killacesa har sai yaji ta ishesa. Ba zai ce baya son Sultana ba, ammh Siya ta mamaye kaso mafi rinjaye acikin zuciyarsa. Ya tuna kwanaki kad'an ya rage asirinsa ya Tonu kafin samun aikinsa na garin Abujan nan ne. Suka fita cin abincin daren da suka saba da Siya duk karshen mako. A wani  restaurant  dake zariya wani abokin karatunsa anan Abu ya gansu shi har ga Allah bai gansa ba. To da yake gayen suna mgana da Tahir ta facebook kuma yana da lambarsa nan da nan ya kirasa ya na Tambayarsa Sadiq ya yi aure ne? Tahir yace"A'a." Sai yace ai ya gansa da wata mace anan zariya kuma a yanayin da ya gansu kamar dai in ba mata da miji ba to ba'a fad'in d'ayan. Tahir ya yi mamaki sosai nan da nan ya kira Sadiq ya na tambayansa. Shi kuma sai ya tuna Fitansu, ammh sai ya nuna ma Tahir ba shi aka gani ba Domin shi bai ma fita ko'ina ba. Tahir kamar yaso ya Fahimci wani abu Tunda har alokacin Sadiq bai bari ya Fahimci inda ya ke zaune a zariya ba in yace zai zo sai yace ya na Gusau To da yake Yanzu Tahir ya yi karfi a siyasa Dan majalisan garinsu ya bashi Shugaban matasan garin Daura na kafafen Sada Zumunta. Sannan kuma ya Dauki nauyin Cigaban karatunsa a jami'ar  Alkalam da ke katsina. Kuma ya na koyarwa a wata makaranta Sakandirin gwammatin garin. Gabadaya dai baya samun zama Shiyasa bayan komawarsu gida bai fi sau biyu suka had'u ba sai dai ta waya suna mgana sosai tunda yawancin Tsarin Bikin Sultana Tahir ne Jagora. Ammh duk da haka sai da Tahir ya Tsaresa da tambayan ko dai bai rabu da Hasiya ba ne? A lokacin sai da gabansa ya fad'i cikin Basarwa yace"Wata Hasiya? Ni har na manta da ita ma, inaga kamar ta koma wajen mahaifiyarta ma." Tahir ya ce"Sadiq ka kula. ka sani in har kana wani abun ne ka Boyemin wlh Ramar da ta kwabe maka ba Ruwana Sadiq." Maganar tahir ta jima na mai yawo acikin kansa ya sani watan watarana bai isa ya Boye wannan abun ba. Watarana kowa zai sani. Sai dai ranar ce ya ke jin Tsoron zuwansa, tunda dai abu d'aya ya sani Ruwa da iska ba su isa su Raba  shi da Hasiya ba. Itama Matarsace da Aure ya ba shi ita. Ga auran salima ya na Tunanin yadda zai yi da Siya, wannan karon karyan Wajen aiki zai yi mata in yana so su Rabu lafiya saboda yaga ta fara Fahimtar ya na Boye mata wani abu. Ajiyar zuciya kawai ya ke saukewa a Jejjere kamar na wanda ya tashi jinya. Sai kuma ya koma kawai ya jingina da Kujerar da ya ke kai. Fuskar Siya ya ke gani ta na gilmasa, kirjinsa ya ke shafawa a fili ya Furta. "I MISS U SIYAAASSADIQ..." *Janafty* *TMWB2K018* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan. Sai da ya kwashe kimanin Sati Shidda a garin Abuja sannan daga Abujan Ranar al'hamis  ya fara sauka a Gusau, tunda ya fi masa sauki yaje Zariya daga gusau sannan Daga Zariya ya koma Abuja. Yaje Gusau lokacin Saura Sati Biyu Bikin Salima da Mubarak ya iske gida cike da yan'uwansa mata na kusa Tunda Bikin ya karato nan suke yini. Daman tunda ya dauki albashinsa na Farko ya yi wani Tunani a ransa. A wani kanti ya tsaya ya siya ma Abba Agogo mai Tsada da Hula Zanna Bukar sai Bakin Takalmi sahu ciki masu kyau da yarari sai Turaren maza mai kamshi. Sannan anan yaga wasu lesuka masu kyau guda biyu sai ya siyama Umma D'aya Mama guda d'aya, Innani kuma sai ya siya mata Atamfa mai kyau mai Taushi. Ya so ya siyama Siya wani abu ammh kuma sai da ya yi wani Tunani sai ya fasa, wani abu dake damunsa shine duk abunda zai gani na kwalliyar mata baya hasaso kowa aciki sai Siya, Sultana bata cika zuwa ransa ba. In ya yi tunanin kada in ya auri Sultana ya kasa adalci a Tsakaninsu sai wata zuciyar ta fad'a masa cewa Saboda Ita Sultana ta na da gata ne Hasiya kuma ba ta da kowa sai shi. Da wannan Tunanin na zuciyarsa ya kauda Tunanin bazai iya yi ma Sultana adalci ba. Duk da ya taso cikin jin dadi sannan bai tab'a neman wani abu ya rasa ba, duk da mahaifinsa na da kudin da yafi karfin komai a gidansa shima a matsayinsa na Namiji tilo kwara daya da iyayensa suka haifa ya na da Buri da Niyar kyautata musu da d'an abunda ya ke samu. Shiyasa tun ya na aiki da wannan kamfanin na zariya in dai zai je gusau baya zuwa Hannu Rabbana duk abunda ya gani a hanya sai ya siya ya kai gida, Abba ya sha fad'an cewa sunan Magajin gida da Innani ta saka masa ba iya suna ba ne, suna ne da ya ke binsa har jinin jikinsa. Ko Yan'uwan su na Shinkafi bai manta da su ba in ya samu ya kan Turama Auwalu kudi ta bankinsa yace ya ba ma Baba Sammani ya raba shi da su Goggo Husai. Ko wannan karon ma 50k ya Tura musu yace su raba a tsakaninsu, haka suka kira sa suna ta yi masa Godiya da Fatan Allah yasa ya gama lafiya sai dai su kira Abba su ce Sadiq ya yi musu kaza kaza da su ba su sani ba. Shiyasa har abadan Abba baya Nadamar Fifitar kaunar Abubakar acikin ransa domin D'a ne mafi soyuwa acikin duka ya'yan da ya Haifa. Sanda ya ba ma Abba abunda ya siya masa sai da idanuwansa suka ciko da kwallah cikin Tsananin Farinciki a muryansa yace"Allah ya yi maka albarka Abubakar, Allah ya albarkaci Samun ka Allah ya Tsare ka a duk inda ka ke Allah yasa a fi haka." Sadiq ya amsa cikin mirmishi Abba ya kara kallon kayan sannan ya jinjina kai ya na yar dariya. Shi alheri ya na da dadi, sannan kuma koda wanda yafi dangote kudi ne in ka yi masa alheri ya na so kuma zai ji dad'i. Umma da Mama suma suka yi ta saka albarka Innani ko kuka ta fashe da shi , albarka ko ya sha shi ya fi cikin kwando, Su Surayya ma suka ce sai ya ba su na su shi kuma yace suna da mazajensu. Sajida ce ta yi tsagal tace"Ko da mu ke da mazaje ai kai kanin mu ne zamu ji dad'i in kanin mu ya yi ma wani abun." Harara ya sakar mata kafin yace"Da ya ke son kudi ne ai muryanki sai ta fi ta kowa zak'i." Itama Hararan ta rama shi kuma sai ya saka mata Dariya ganin yadda ta kara zama wata cus da cikin jikinta ya girma. Maganar Si yan ma Sultana Anko Surayya ta fara yi masa, tace har ta waya ma ta tura masa guda biyu ne material na ranar jumma'a yinin Biki kenan sai Atamfa na ranar Daurin aure. Nan take yace yana so duka guda Biyu biyu, Cikin mamaki ta kallesa kafin ta yi mgana ya yi saurin cewa" na sultana d'aya dayan kuma zan siyama wannan abokiyar aikin tawa ta zariya sosai zama na da ita ta yi min kirki." Surayya ta yi mirmishi kafin tace"ASIYA..." Cikin mirmishi yace"Ita fa Big sis, ai har yanzu muna zumunci ko da na koma Abuja yanzu." Cikin gyad'a kai tace"Gaskiya ya kamata ka siya mata ta na da kirki sosai Da fatan zaka gayyaceta ta zo mana Biki" Da Sauri yace"Anya? Da wuya ta samu zuwa zan dai siyamata ankon in sha Allahu." Surayya bata damu ba, Tunda duk abunda Hasiya ke ba shi in yace mata zai je garinsu gida ya ke kawowa da sunan abokiyar aikinsa ce ke ba shi ya kawo ya riga ya nuna suna zumunci da ita sosai ita da Mijinta shiyasa kusan duk yayyensa sun san sunan Asiya a baki abunda yasa basu damu ba Sanin ta ba cewa ta na da aure. Innani ko ta sha saka ma Hasiya albarka domin har Tuwon madara ta sha yi ta aiko mata da shi, daman kuma Innani akwai son Abun Duniya. Shi ko Sadiq duk ya zurma su ne a Buhu ya Dinke Hasiya ya ke nufi ammh sai ya sauya ma Labarin Suna da Muhalli yadda kafin su Fahimci inda labarin ya dosa za'a Dauki Lokaci. Bayan ya siya musu nan take ya Turama Surayya kudin Tunda ita ta Daukon ankon, Sannan kuma Sakeena na Saida mayafai da Jaka ta matsa sai ya siyama Sultana, bashi da yarda zai yi yace a kirata ta zaba ita kuma Hasiya a ransa yace in yaje zai bata kudin ta siya hannun Maman Suhailat. Ba su barsa haka ba sai da ya Turama kowaccen su 2k da sunan za su saka kati har Salima, shi kuma yace tunda hakane harda Umma da Mama da Abba suma sai ya Tura musu Falon Umma ya cika da Ihu suna ta fad'in"Allah ya yi albarka karamin kanin mu." Umma na ta saka albarka Mama haka har ta na fadin"In sauran suka zo suka ji Labari zaka yi biyan ba shi." Kai Tsaye yace"Suma zan Tura musu Mama." Abba ko fad'a ya fara masa da cewa yaushe ya fara aikin da zai zo ya na wannan Hidimar? Cikin yar dariya yace"Abba bakomai ku yi ta saka mana albarka shikenan kawai mu ke bukata." Abba ya Dafa kansa ya na ta saka masa albarka. Ya baro Gusau Ranar Lahadi da Safe ne yace zai biya ta zariya yaga Superversor dinsa. Ya baro su Surayya za su je kaduna Jeren kayan Salima duk da yasan an gama siyamata komai ammh sai da ya kirata shashensa shi da ita ya tambayeta in akwai wani abunda ta ke so ta fad'a masa zai siya mata. A lokacin sai ta kallesa kafin tace"Yaya Sadiq Abba duk ya gama siyamin komai fa." Cikin yanayin mganarsa yace"Nasani wannan na Abba Dabam ni a matsayina na yayanki me kike so na Siya miki? Ke kanwatace kuma aure zaki yi na fara aiki ina so nima na yi miki wani abu Salima." Idanuwanta suka kawo kwallah ko acikin maza an sai antona za'a samu irin Yaya Sadiq, ko acikin yayyen sai an tona Dari kafin a samu kamarsa. Bata Bukatar komai, ammh Saboda yadda ya Damu yasa tace ya siya mata Frem d'in Ayatul kurusiyu. Cikin yanayin maganarsa yace"Kin tabbata? Sai ta gyad'a masa da haka ya sallameta to kafin ya tafi ya kira Surayya suka yi mgana ya Tura mata kudi yace ta siya ma Salima Frem mai kyau da Tsada. Ko iyayen ba wanda ya sani sai da Surayya ta siyo ta zo da shi. Kowa yasan waye Sadiq ammh kuma ya na kara girma Hallayarsa na Dattako suna kara bayyana. Ko da ace su Abba sun gama mata komai shi a matsayinsa na yayanta shima akallah ya yi mata wani abu. ******* Tun ranar asabar na yi ta saka idon ganin Assadiq ban gansa ba tunda shi ya fad'amin ya na tafe wannan Weekend din. Ranar jumma'a naje anguwan su Ramatu ta yi kitso da kunshi ammh har Ranar asabar ta kare bai zo ba da na kirasa zan fara masa kukan shagwaba sai yace ya na wani abu zai kara kirana. Bai kirani ba sai da Daddare ni kuma Lokacin na yi barci sai da Safe nagani. Daman ina jin haushinsa yasa ban bi bayan kiran ba. Komawata na yi na yi kwanciyata ina ta Tura baki, gabadaya ba na jin dadin zama ni kad'ai jikina da Zuciyata ya saba da Assadiq sabon da yanzu ya ke Cutar da ni. Chan cikin Barci naji ana ta kiran wayata na tashi da Sauri na d'auki wayar, Sai naga Assadiq ne da kamar bazan dauka ba sai kuma na Daga ina cin mgani. Cikin Tattausan Lafazinsa yace"Ina kofar dakin ki Madam" Zaro ido na yi kafin yace"Gaske ko wasa? Ya na yar dariya yace"Ki fito mana ki gani." Ai da gudu na Diro daga kan gado na watsar da wayar hannuna saman gado. Dagani sai Rigar barci na fita naje na Bude kofa sai ko na yi farin gani da Assadiq. Da gudu na tafi na Rumgumesa ina Murnan ganinsa shima rumgumeni ya yi a jikinsa ya na yar dariya yace"To kada ki ka damu mana Siya." Sai da ya fad'i haka na sake shi bakina har kunne ina yi masa sannu da zuwa. Jakar kayansa na karb'a sai ledan Hannunsa shi kuma sai yace bari ya shigo da Motarsa ciki. Daki na koma bayan na ijiye masa kayan acikin daki na sako Hijabi na fito. Ni na tayasa Bude get ya shigo da Mota na koma na Rufe shi kuma ya gyara parking ya kashe Motar ya fito muna Rike da Hannun juna har tsakiyar Falon mu. Rumgumeni ya karayi cikin wani irin Jan Numfashi yace"Na yi kewarki Siya." Nima ina kara nutsewa cikin jikinsa nace"Ni ma na yi kewarka.". Dagoni ya yi kafin yace"Kamar sau nawa.? Ina fari da ido nace"Zaka iya kirga nawa ne acikin Buhun gero? Ido ya zaro ya na dariya nima ina Tayasa nace"To kamar haka na yi kewarka." Ba tare da Tunanin komai ba kawai ya had'a bakin mu waje daya ni kuma sai na tallafeshi na fara ba shi had'in kai. Tun muna Tsaye har muka zube saman kujera. yanayinsa da na gani yasa na san abunda ya ke so. Cikin shakewar murya na kira sunan Shi"Assadiq..!" CIkin magagin abun yace"Uhm Uhm!" Da Sauri nace"ban fa yi wanka ba." Na fad'a cikin yar shagwaba. Bai Saurareni ba sai chan da na kara magana yaja Numfashi kafin ya mike Tsaye dani a jikinsa ya na fadin"ya ma fi dad'i Siya." Bai Direni ko'ina ba sai saman gado nan muka sha Sha'anin mu sai bayan mun natsa ne sannan muka yi wanka mu ka Tsarkake Jikin mu. Tare da shi muka shiga kitchen na yi mana abun karyawa. Dankali da kwai na soya sai kuma Tea da muka sha. Bayan mun gama shi ya tayani muka gyara dakin muka goge, wanke wanke kuma ni na yi ammh shi ya rika Dauremin ya na kai su muhallinsu. Muna gamawa kuma muka Dawo Falo saman kujera muna manne da juna muna Hiran mu ta ma'aurata. Tare mu yini muna shan Soyayyarmu, Sai sallar mangariba ne ya fita Sai da aka yi isha'i ya dawo Lokacin naci gayu na, na kuma saka masa Rigiman sai ya zo mun fita mun ci abinci a waje. Ba shi da yarda zai yi illah shima ya Shirya muka fita mukaje shan Ice cream sannan muka siyo kaza da Madaran Hollandian sai katan din Ruwan gora da na malt da ya siyamin sai da muka dawo ne ya bani Kaya Atamfa da Material yace na Kai Dinki. Sannan yace daga baya zai Turamin kudin d'inkin ta acct dina tare da kud'in mayafi da Jaka. 15k ya bani dubu biyar yace na Rike  Dubu Goma kuma yace na Turama Amma da ya ke ya kaini na Bud'e bankin Gt bank. Sai gani ina kuka ina masa Godiya jawoni Jikinsa ya yi ya Rungumeni ya na lallashina fadi ya ke" in ban yi miki ba wa kike da shi da zai yi miki? Kuma gaskiya ya fad'a bayan Allah da su Adda bani da kowa sai Assadiq. A daran nan mun sha Soyayya kamar za'a rabu da juna har Abada, ban fara siyan maganin Mata ba ammh ina shan Madara da su Fruit. Washegari da Safe ya wuce da Sassafe, ammh sai da ya shiga cikin makaranta yaga Superversor dinsa sannan ya Dauki Hanyar Abuja. Kud'in da yace na turama Amma Hamma Isuhu na turamawa nace ya bama Amma sakon Assadiq ne. Ta kirani a waya ta na ta saka albarka tace shima zata kirasa tunda ta na da Lambarsa ya na kiranta Lokaci bayan Lokaci su gaisa. Dinkina Telan Ramatu na kaima wa yanzu Tun bayan aurena ita na kaimawa ita kuma tace zata kai masa. Sai Santin kayan ta ke yi har ta Furtamin tace Assadiq ya iya zab'an kaya masu kyau da yarari. Da yake akwai kud'i a hannuna da su na yi amfani na Biya kudin Dinki, ina da komai na kayan abinci da abun amfani Assadiq bai taba barina na neni wani abu ba. Kuma ya na barin min kud'i in zai tafi ban da kitso ko kunshi sai in ina makaranta na Trasport ba na komai da su. Da yake telan bai da wasa, kwana uku Tsakani ya gama min dinki Ramatu ta kirani tace ya gama nace ta kwatanta masa gidana ya kawomin. To Ranar da ya kawo min Adda Fati tazo min yini ita da Habiba da yara sai suka ga kayan Itama ta rika Santi ta na fadin"Kai sun yi kyau Hasiya daga gani suna da Tsada." Na yi mirmishi ban ce komai ba Habiba ma sai yabawa ta ke yi ta Dauki Material din da aka yi min Doguwar riga mai kyau tace ta na so na Bata Adda Fati ta kwace a Hannunta ta na fadin"Baki da Hankali ne? Mijinta fa ya siya mata kinga ai ya na so ya ganta da shi ne." Tura baki Habibaa ta yi ni kuma sai nace ta Sha kuruminta zan siya mata in sha Allahu. Sai da Habiba ta Shiga kitchen ita da Hanif suna min wanke wanke sannan Adda Fati ke gayamin akwai biki a kaduna nan da sati daya da wani abu. Cikin mamaki yace"Bikin wa kuma? Kai Tsaye tace"Bikin Babban yaron Baba Jibril na kaduna mana." Sai da na yi dogon nazari sannan na iya Tuna wai ashe Kanin Babanmu ne Baba Jibril da ni na ma manta da shi kwata kwata a rayuwata. Cikin Tabe baki nace"Tab daman wai ya na nan? Ni fa inaga tun Rasuwar Baba ban kara ganinsa ba." Adda Fati tace"Kinsan ai ma'aikaci ne a garin kaduna chan ya ke shi da iyalansa" Cikin Halin ko in kula nace"to ke waya fad'a miki.? Adda Fati tace"Amma ta kirani ta fad'amin kuma tace lalle na yi muku mgana mu tafi tare da ku." Cikin jinjina kai nace"Kaji Amma da wata mgana to ita ina ta sani? Nasan dai ba zumunci suke yi da ita ba." Adda Fati tace"Tace da ta kira Baaba ta lagos ne ta ke fad'amata ta na nan zuwa bikin kin ji inda taji zencen." Hasiya ta yi shuru kafin tace"ita yanzu Amma daman dalilin da yasa tace duk ki saka mana lambobin su kenan? To Allah ya kyauta ni kan sai na Tambayi Assadiq in ya barni Shikenan in bar barni ba bazan matsa masa ba." Adda Fati ta ce"A'a ki dai nuna masa Muhimmancin zuwa kin ji ko? Gyada kai na yi ammh har a raina ba wai naji ina son zuwan ba ne. Amma ce ke bani mamaki wanda ya had'a ya raba tunda kuma su ka banzarta damu har da ita ma kanta ammh ta na yin waya duk tace Adda Fati ta saka mata lambobin su. Da na yi magana nace Allah fa ya Raba wannan zumuncin Tsakaninta da su Baba tanko. Bud'e bakin Amma sai tace"Allah ya riga ya had'a Hasiya Tunda ya bani ku." Daganan sai ta kashe bakin  kowa ciki har da ni kaina. A gidana Adda Fati ta Kira Adda Rukayya ta fad'amata itama bata wani Damu ba tace zata ma Baban Amna mgana in ya amince shikenan Ita Adda Fati nufinta sai ta tasamu mun tafi tare har ta na cewa Amma tace in muna da kudi mu Had'a wani abun mu je da shi. Cikin bacin rai nace"Nan fa d'aya ga zuwa ga na biki? Mu uwar me Baba Jibril d'in ya taba yi mana? Adda Fati da taga bazan gane ba sai ta Kira Amma ta fad'a mata ta kuma ce a bani waya ta dinga yi min nasiha da Fad'an cewa bamu isa mu sauya ma Tuwo suna ba. Dangin mu ne, ba mu da kamar su saboda haka mu shirya mu tafi a yi sha'anin damu kuma mu had'a wani abun mu kai mu dai mun sauke namu Hakkin da ke kan mu. Gum na yi ma Amma da taji hakane tace"Kin ji ko Hasiya? Bani da mafita illah na amsa ma Amma ammh har acikin raina ban yi ra'ayin zuwa ba. Shiyasa ko a waya ban fara gayama Assadiq ba mantawa ma nayi da zencen kwata kwata. Sai cikin karshen Satin Assadiq ya zo Tun Ranar jumma'a ni fa in ya na gari mantawa na ke da kaina ma ba wani ba. Sai ga Adda Fati ta kirani ta kara Tunanin Bikin wannan Satin ne dalilin da yasa kenan na gayamasaa. Shuru ya yi kafin ya kalleni ya na Fadin"Dama kuna da yan'uwa a garin kaduna ne? Sai naji kunya da Sauri nace"Eh mana Shi ke bin Babanmu da ya ke ma'aikacin gwammati ne chan ya ke zaune da iyalansa." Bai damu ba yace"Yaushe zaki tafi? Kuma ke da waye zaku tafin? Kai Tsaye nace"ni da su Adda Amma tace mu tafi, Adda Fati tace mu tafi Ranar jumma'a sai mu dawo Lahadi da Safe." Jinjina kai ya yi ya na Tunanin abun ya yi daidai kenan da bikin Salima. Daman yazo wannan satin ne sati na sama zai ce aiki ya yi masa yawa ba zai Samu zuwa ba. Saboda Gusau zai yi wannan Weekend din, sai kuma ga wannan mganar tawa sai kawai yaga komai yazo masa da sauki. Daman nasan bazai hanani ba Duk da shine karon farko da na yi tafiya Tun bayan auran mu bayan wajen Amma da naje sai wannan karon. Shi dai kawai yace na kula da kaina ne sannan yace wannan Satin mai shiga Daman bazai samu dawowa ba shikenan a raina nace ta kwana Gidan Sauki. Ranar Lahadi da rana ya tafi, muka rabu kamar kada mu rabu bayan ya bani kudi a Hannuna, na mota da na  Zirga zirga sannan ya cika alkwari ya bani kudin dinki da na mayafin Wajen maman Suhailat na siya takalmi da mayafin a raina nace kayan da Assadiq ya siyamin da su zan yi amfani a sha'anin kaduna. Adda Rukayya ta kawo Dubu Biyar nima na ba da Biyar Adda Fati ta saka Biyar sha biyar kenan tace mun je zata bama mai bikin. Ni na Dauka mu kad'ai zamu tafi ashe Adda ta kira gidan Baba Sammani da Baba Tanko wai in zasu wuce mu tafi tare aiko suna ji dani aciki duk suka zame a cewarsu wlh bazasu hau Mota daya dani ba mota ta kife da su duk su mutu ba. Ni bansan ma sun yi haka ba sai Ranar jumma'an da na zo gidan Adda tare da kaya zamu tafi Adda Rukayya ke fad'amin dariya kawai na yi kafin nace"Ashe ba su yarda da Allah ba  karyan Musulunci ma suke yi ashe." Kamar zan ce ma Adda Fati ta daina kokarin chusa kanta a cikin Dangin nan da basa son mu saboda bakin Fentina sai kuma kawai na kyaleta Tunda Assadiq ya koyamin takawa da yakana. Mu uku kad'ai muka tafi Adda Fati daga ita sai Hanif hakama Adda Rukayya sai Goyonta Yara an bar ma Habiba su ni kuma dagani sai jakata akwati daman a ta Adda Rukayya muka saka kayammu waje daya. Material din na saka sai na yi amfani da mayafi coffe mai kyau da shi. Sai na zama kamar wata Baturiya ballatana da na kara fari da kyau. Na saka d'an kunnayena na da siya wajen Yayar kawata Safiya Ahmad da ya ke ta na harkan Saide saide itama ta Online. Su kansu yan'uwana sun kalleni sun kara kallona har sun gaji sun Furtamin na yi kyau mirmishi kawai na yi a raina ina kara godema Allah sannan ina kara godema Assadiq domin a sanadinsa na zama Mutum kamar kowa. Tun muna gidan Adda Assadiq ke kirana yaji ko mun tafi nace masa bamu tafi ba sai ya fara min fad'a da cewa kada mu yi dare a hanya. Ni kuma sai nace masa ai yanzu Hanyar kaduna Lafiya lau an gama gyara ba wani cikowa ko wani matsala. Hankalinsa bai kwanta ba sai da ya Kirani nace gamu a tasha har mun shiga Mota zamu tafi, sannan hankalinsa ya kwanta ya yi mana Fatan sauka lafiya. Shi ko a daidai Lokacin da ya ke kirana saukansa a Gusai kenan ba jimawa Daga Abuja. Gida ya cika da mutane bakin Shinkafi kwansu da kwarkwata sai Bakin Gammi Ahalin Umma ga Bakin cikin garin Gusai Ahalin Mama. Ga Ya'yan cikin gida yan nesa da na su ya'yan irin su Yaya subai'atu da su Shahida, Wasu har da guzarin kawayen su da Dangin mazajensu da abokan arzuka. Kowani Shashi ya cika da Mutane Tunda Ranar suke taron Biki gobe asabar ana Daura aure za'a tafi da Amarya. Shashensa ma an sauki Mutane sai kawai ya tafi bangaran Abba ya fi Sarari bayan ya yi wanka ne ya Kira Sultana yace mata ya Dawo ta kawo masa abinci. Shine kafin tahowarta ya samu ya Kira Siya tunda ta na makale a ransa baya so su yi tafiyar Dare gwara su isa cikin Lokaci. Sun yi sallama kenan ya na zaune falon Abba gajiya duk ta kamasa har yanzu DogomnTuki bai gama zama ajikinsa ba. Dogon wando ne a jikinsa sai karamar Riga mai gajeren Hannu. Sanda Sultana ta yi sallama ta shigo bai yi niyar Dagowa ba sai dai kamshin da yaji ya shiga Hancinsa ne yasa ya Bude ido da Sauri ya na Bin inda kamshi ya fito da kallo. Sultance a tsaye a gabansa ta ci gayu Cikin Materila din yinin Biki hannayenta sun sha jajayen kunshi Ta kashe dauri ga shi an yi mata makeup wanda ya yi mata kyau sosai. Mayafinta itama Coffea ne ammh kuma karami ne. Hannayenta Dauke da Farantin abincin nasa da ruwa da lemu. Har ga Allah bai san ya shagala da kallon Sultana ba sai da yaji ta na masa Sannu da zuwa. Sannan ya farga da Sauri ya basar ya na gyara zamansa. Cikin shakewar murya ya amsa mata ya na satan kallonta kasa kasa ta na Duke tana zuba masa abinci. Sai da ta gama sannan taja Center table din dake falon ta Dora masa komai sai kuma ta kallesa cikin mirmishi kafin tace"Bismillah." Ba musu ya matso domin ko karyawa bai yi ba, mahaukaciyar yunwa ya ke ji. Ya fara cin abincin kenan ta zuba  masa ruwa a wani karamin kofin Tangaran ta na Shirin mikewa ya kalleta da Sauri ya na fad'in"Abba fa? Ban gansa ba? Cikin yanayin maganarta tace"Abba ya fita Tun Safe." Kai ya jinjina kafin yace"To miye na taro Biyu? Ba gobe  ne Daurin auran ba? Mirmishi ta yi kafin tace"Yaya Sadiq Ya Mubarak fa yace an ana gama Daura aure za'a tafi da Anty Salima" Sai da ya Cinye abincin bakinsa sannan yace" shine daidai ammh wannan taron duk shirme ne." Ita dai sai mirmishi ta ke yi baya so ta tafi Saboda kwaliyarta ta yi masa kyau. Sai ya fara hasaso irin kwaliyar a Fuskar Siya di'nsa. Har baisan sadda mganar zucci ya Fito Fili ba yace"Wow Beatufull." Saboda har ya hango kyan da Siya zata yi in da itace ta yi wannan kwaliyar. Sultana ko ta zata da ita ya ke ta Rufe fuska da tafukan hannayenta ta na Fadin"Thanks Yaya Sadiq." Sai a lokacin ya fahimci aikin da ya yi sai bai karyata kansa ba ya kalleta ya na fadin"kin yi kyau ya zama dole Abubakar ya biya tukwaicin wannan adon." Sai jin dad'i ta ke yi ta na masa wani Fari da ido lokaci daya ta na yarfa Hannu. Bai sallameta ba har ya gama cin abinci sai janta da Hira ya ke yi , anan kuma wajen ya tura mata 5k ta acct dinta yace Tukwaicin gayun da ta yi Sultana zuciyarta kamar Farar Takarda Saboda Haske. Ba ta bar Falon ba sai da Siyama ta kira wayarsa ya na Dauka bayan sun gaisa tace masa Sultana tazo yan makarantarsu zasu tafi. Dalilin da yasa ya sallameta kenan, ta koma cikin gida shi kuma saboda mata sun yi yawa bai ko yarda ya Fita ba sai chan da yamma da baki suka fara Raguwa yan gari. Sannan ya sake wanka ya saka Shadda mai Ruwan kasa, kayan da zasu saka Gobe Farare ne Tahir ne ya matsa masa shi ya Tura ma kudi ya siya musu shaddar tunda yace yasan inda zai kai musu d'inki. Sannan Abba ma ya dinka musu su biyu, sannan ya dinkamusu har da su Baba Sammani, da sauran yayen su maza matasa har da Baban Sultana Mallam Datti. Sai Dare Abba ya Dawo gidan a masallaci suka had'u da Sadiq sai bayan sallar Isha'i suka baro masallacin zuwa cikin gida. Sai lokacin sauran yan'uwansa suka gansa Shashen Innani ya fara Shiga gaida Mutanen Shinkafi. Da ya ga Innani sai da ya yi Dariya har ya na Rike ciki. Ga uban Gwagwaro da ta maka a kanta ga gilashi, sai kuma wani Uban mayafi mai kauri mai kama da Bargo da ta yafa sannan ga wata jaka kamar ta wamzamai tace na Tara kudin Biki ne ai ba'a zo a tafi haka ba kuma Hidimar nan dai Sulaimanu ya yi ba Suwaiba da Danginsa ba ahto gwara dai a rika yi ana Tausayama Sulaimanu. Abba na gayamasa maganar gwagwaro Innani sai da tace in ba'a nad'o mata ba  sai ran kowa ya baci sannan Dakyar ya hanata Dauko masu Kidan kwarya ammh tace bikin Sulsana da Magajin gida taga Uban da zai hana makid'a shigowa gidan nan Abba ba ya son Bid'a su ma walima kad'ai Amarya da kawayenta tare da yan'uwanta suka yi. A daram Sadiq har shashen Mama ya shiga ya yi mata Allah ya sanya alheri yan'uwanta suka fara zolayansa da Ango gaba tuna shima na shi kamar Gobe ne shi dai baya mgana sai dai ya yi mirmishi. Shaahen Umma ne yaji daman bai Shiga ba cike da yan'uwansa mata da kawayen Amarya da su Sultana. Ya na shigowa suka Dau Ihu suna Fadin"Ga angon Sultana Fari mai farin Aniya." Duk yadda yaso ya zille suka hanasa suka Takura masa sai sun yi Hotuna haka ya tsaya suka yi ta Daukan junansu har da Amarya Salima da ta sha kyau kamar ba ita ba. Daga karshe Sajida tace"Ku matsa ku bama Magajij gida waje shi da Amarya su sha Hoto." Hararanta ya yi bai samu zarafin mgana ba suka Turo Sultana gefensa suna Daukansu Hotuna suna Dariya. Sajida har wani Had'a jikinsu ta ke waje daya ya make hannunta ya na fadin"Sajida." Dariya ta yi masa har da gwallo sai ya rasa yadda zai yi da ita. Karshe dai har rike kugun sultana sai da suka saka ya yi da ya gaji ne ya hade rai yace"Kai nagaji." Surraya tace"Bakomai akwai na gobe mai Hoto na nan zuwa." Shi dai sulalewa ya yi ya gudu sai a bangaren Abba yaga Umma suka gaisa Hidima ta yi musu yawa. Sai da Safe ya samu zuwa ya gaisa da Iyayen Sultana wato Matan Mallam Shitu kenan. Rana  bata karya sai dai Uwar Diya taji kunya karfe Sha biyu da Rabi na rana aka Daura auran Salima Sulaiman Abubakar Shinkafi da angonta Mubarak Jibril Mamman. Akan Sadaki mai Daraja. A masallacin kusa da su In da Abba ke sallah aka Daura auran. Daurin auran da ya sami Hallatan manyan baki kama daga abokan kasuwancin Abba yan anguwa, Mutanen Shinkafi dangin Umma da Mama Mazajen ya'yansa da Sauran su Sai Tawagan Ango daga Kaduna suma gayya Guda bayan Tawagan Uban ango shima sai wanda dai ya gani. Sadiq daman Shigar Farare suka yi shida Tahir da sai ana gabda ma Daurin auren ya iso garin Sadiq na mamakin Tahir komai yace ba shi da Lokaci kamar majalisan Dinkin Duniya. Daga nan reception din da Abba ya shirya suka je suka yi, Dagachan angwaye suka rigasu dawowa saboda Daukan Hotuna da Had'a Hadan Tafiya da Amarya. Hayaniyar gidan ta ishi Sadiq shiyasa yace ma Tahir su zauna a Restaurant din nan su Huta. Ga shi ya na son Kiran siya ba Dama, Tun jiya da suka yi mgana ta gayamasa sun sauka lafiya. Basu baro Wajen ba sai da Abba ya kirasa yace yazo gidan yan'uwansa na nemansa za'a tafi da Amarya. Koda ya zo duk suna haraban gidan ga Motoci ne birjit na tafiya kaduna. Hotuna suka yi har da su Umma da Abba da Mama da su Baba Sammani. Har da su Goggo Husai. Su Mallam shitu da wasu sauran jama'an ana gama Daurin aure kamar Mota Biyu suka koma Shinkafi. Salima ta sha kuka daman Nasiha tuni Abba sun yi mata sauran yan'uwanta ma ba'a bar su a baya ba. Da har ance a kaita bangaren Innani sai aka ji ta na masifan a fitar mata daga Shashenta zata kulle ne kaduna garin gwamma zata je kai amarya. Kuma wlh duk sai da aka fita ta saka wata yarinya kanwar Sultana ta saka mata kwad'o a kofar falonta. Kuma saboda matam baban Sultanan ne yasa tace zata rufe shashenta. Tunda suka zo Bikin nan Innani ke bala'i ta na Habaicin wani Hisabin dai sai a lahira. Sai gata da jakarta Tun na saudiya nan, ta cikata da kaya ta ci Atamfarta ta yinin biki zanin nan a kauri ga uban Daurin da ta Guma a kanta ga gilashi ta na tafiya ta na Dingisa sanda. Ba wanda bai yi Dariya ba a yi mgana kuma tafara tsine tsine. Abba da su Umma sun yi sun yi Innani ta yi zamanta kai Amarya  tace Uban kuturu ya yi kad'an sai taje gwara taje ta saka ido Bikin jikarta ne. Sadiq da aka so ya yi mgana wannan karon bai yi ba da kansa ma ya saka Innani a motar amarya yace ta je ta Raka Salima dakinta. Umma zata yi magana ya kalli su Sakeena ya na fadin"Ku kula da ita in kun isa chan." Sai kowa ya gyada kai Innani ko sai lekowa ta glass ta ke ta na kwararama Sadiq addu'a. Daga Siyama, Sultana sai kawayen salima guda biyu a dakin Umma kuma Sadiya da sa'adatu Sai Sajida, Dakin Mama kuma Sakeena da Saliha da Shahida Sai Umma sai Kanwar Mama sai Goggo Husai da matar Baba Sammani, sai matar Baban Sultana da Innani bata ga shigar ta Mota ba da tace tace in taje Allah ya tsine mata. Sa'ima da Surayya da Suba'atu sai gobe zasu taho da sauran mutane da wasu kayan. Karfe Biyu da wani abu na Rana Motocin Amare suka Dauki Hanyar kaduna. Daman Alhaji jibril tun daga Wajen Reception suka wuce. Suna tafiya ba Dadewa Tahir yace zai tafi  sadiq bai damu ba yace a sauka lafiya. Shima bai ma san tafiyarsa ba bangaransa ya koma ya na kiran wayar siya ammh bata Dauka ba, sai ya yi Tunanin kila ta na cikin Hayaniya ne ****** Ni ko ba biki ne ya yi biki ba da yasa ban ji kiran wayar Assadiq ba. Wayar ta na cikin Jaka kuma Adda Fati na bama ajiyar Jakar da Safe kuma basa nan suna makota gidan suke wai aikin abinci. Ita da Adda Rukayya ni dai nace ba na jin dadin na yi kwanciyata Dakin Zahra'u. Yaran gidan ma sai da muka zo na san su wlh, da ya ke kuma ba son mutane suke yi ba Daga yan'uwan matar gidan kad'an sai mu Dangin megidan Daga Zariya. Ita naji ma ana fadin a gidansu take nata taron ita uwar bikin, gidan sai bai wani cika ba sai mutane kad'an masu Shigowa. Abinci ma a wani waje aka Dafa sai dai aka kawosa a dafe kawai aka fara ci. Na samu sakewa kad'an Tunda matar gidan ta na da Kirki ita da ya'yanta Yan zuwa Bikin ne marasa Mutumci wato ya'yan su Baba tanko da Baba Saminu daga Zariya. Ina ga ko ba su so mu zo ba ne bansanin mu su ba, ni dai tunda na samu Zahra'un ta jani Dakinta sai Washegari na fito. Hajiya Murnajatu sai godiyan kudin da Adda Fati ta bata ta ke yi mana. Bata gane mu ba sai da Adda Fati ta yi mata bayani sannan ta gane mu. Shi ko Baba Jibril din ban san ko ya gane mu ba, mun dai gaisheshi da Safe da suka Shigo gidan suna gabda Tafiya Daurin aure. Angon ma daga nesa na ganshi ni ko a Hanya muka had'u bazan iya ganesa ba. Su zahara'u sun yi sha'aninsu sun yi gayyar kawayensu ba laifi, sai bayan La'asar Su Baba Jibril suka dawo ni kuma sai a lokacin na yi wanka na Saka Atamfata. Tunda sai da na jira su Adda Fati suka Dawo kayammu na wajen su. Su ne ke shiga cikin yan'uwa ni kam sanin bakin fenti na yasa na ke sahale kaina a gefe. Ina dakin zahara'u in nagaji da kwanciya na mike da ya ke ina al'ada ba na sallah Shiyasa. Ina ji da yammah ana karadin Saukan Amare daga Gusai ban fito ba. Sai bayan mangariba Adda Fati ta leko tace nazo muje Za'a raka Amarya gidan ba na son zuwa sai nace su je kawai ba na jin dadi. Har ga Allah ban so zuwa ba sai da Fathihatu ta shigo Daukan abu ta ganni kwance cikin Fara'a ta min mgana ko lafiya? Nace mata lafiya lau sai kawai tace na tashi mu karisa gidan Amarya. Na kasa yi mata musu sai na tashi na saka mayafi, jakata ce har yanzu ta na Hannun Adda Fati na ganta a hannunta sanda tazo min mganar tafiya raka Amarya. A motarta muka tafi ni da ita gidan duk ya watse sai kalilan duk jam'ar na gidan Amarya. Ashe ba Nisa tafiya kad'an muka yi sai gamu mun iso gidan a waje ta faka Motar sai a ka kirata a waya, ta tsaya ta na mgana sai tace na Dauki wata karamar kula muje gata nan zuwa. Sai na yi gaba saboda sha'ani sabon get din gidan ya na Bude ne ina Turawa na shiga. Haraban gidan akwai haske tar kamar an kuna gen ne ko kuma kila wuta ne domin naga anguwan ko'ina da haske. Ina shiga gidan na rasa ina zan nufa Tunda Kofar falon da na gani kamar a Rufene kuma ina jin hayaniya daga ciki. Bansan ta inda Tsohuwar nan ta Bullo ba ganinta kawai na yi a gabana, yadda ta ke dogara sandar hannunta ne yasa na tabbatar bata gani. Kamar kila Motsi taji sai ta fara fadin"Waye anan ne? Cikin mirmishi nace"Ni ce iya." Innani ta yamutsa kafin tace" ni sunana Innani yar nan nace ko cikin yan'uwan mijin ki ke ne ko? Sai na amsa da Eh da Sauri tace"Taimaka min ki Dubamin gilashina karfen nasara ba Tabbas daga Fitowa ai na sha iskar Ubangiji ya na fuskata ya fad'i daganan ne na nema na rasa." Da toh na amsa mata ta na nuna min inda tabi da sandarta ni kuma na Duka ina Dubawa sai ga shi na ganshi kusa da kofar falon. Na dauko mata na goge mata na karisa gabanta na saka mata shi fuskarta ina fadin"Iya ga shi nan na gano miki." Innani jin gilashi a Fuskarta yasa ta kara gwale ido ta na kallona. Nima ita na ke kallo abun mamaki Irin kayan da ke jikinta nima shi ne ajikina. Kafin mu samu Zarafin mgana dagani har Tsohuwar da tace sunanta Innani wata mata ta fito da Sauri. Ta na Dube Dube ta na ganin mu sai ta Sauke Numfashi. Da ya ke na juya baya bata fuskata ba sai ta kariso ta na fadin"Saliha ashe Innani na tare da ke? Na tsorata da na Duba ciki ban ganta ba." Juyowa na yi muka had'o ihu hudu da ita sai da mukaji wani iri. Kallona ta ke yi nima ina kallonta cikin mamaki. Innani ce ta tabe baki kafin tace"Wata Salihar? Yaran da tunfa muka zo ban kara ganin su ba, wata yar mutumci ce ta taimakeni kin ji yar nan Allah ya yi albarka." Ta fad'a ta na Dafa kafad'ata, Umma ta kalleni ta kara kallona nima na kalleta sai kuma na sunkuyar da kaina ina gaisheta ta amsa cikin Sakewa kafin tace"Ayya to mun gode" Da kai ma amsa mata Hannun Innani ta kama suka wuce ammh ta waiwayi ta kalleni nima kuma ina ta kallonta har suka shige cikin Falon. Kila ta na mamakin kayan jikina ne, ni kuma Muryanta ne naji ta yi kama da na wacce na sani. Sannan kamminta ne ya yi kama da na wanda na sani Ammh na kasa tuna komai. Sai kawai na Cigaba da Tsayuwa ina jiran Wacce muka zo tare. bazan iya Shiga gidan ni kad'ai ba Tunda bansan kowa ba. Mata muntashi tsaye mu yaki infection (sanyi) Wani ciwone Mai nacin gaske Wanda idan kikayi wasa xaihanaki jindadin Aure Sannan maganin shi saikin daure da nacin shanshi Akai Akai toh kufito🤌🏽 KUSAI TSIMIN TABAJE DOMIN MUNA DAFASHINE DA INGANTATTUN SAIWOYI MASU AMFANI AJIKI DAKUMA LAFIYA, CIWON SANYI, SANYIN MARA, BASIR DASAURANSU INSHA ALLAH DUK WANI CIWO INDAE NA SANYINE ZAIZO KARSHE DA YARDAN ALLAH KIDAE KIDAURE KIDUNGA SIYAN TABAJE KIJEFI TSUNSTU GOMA DA DUTSE DAYA💃💃💃 Akwai infection Wanda yake nuna kanshi Akwai Kuma kurman infection Wanda baxaki San kinada shiba Amma yanacan yana Miki illa domin duk kyan Kayan mata baxakiga aikinsu ajikinki ba ko Kuma sumiki aiki bayanda akaso ba Anason duk bayan wata 1 mace tasha maganin infection sbd samun lafiyar jikinta Alamomin shi sune Fitar farin ruwa Kaikayin gaba/ko kuraje Jin zafi yayin sex Daukewar ni'ima Daukewar sha'awa dadai sauran su Kafin kifara Shan maganin mata yakamata ki fara Shan maganin infection Ina Yan mata Budurwa kema Yakamata kidinga Shan maganin infection Dan kariya da lfy ki karsai kinyi Aure infection ya Riga yamiki illa Baki saniba Allah y bamu lfy y karemu Ameen 🙏 *Janafty* *TMWBK2019* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641 https://chat.whatsapp.com/I7uxPXgtPKBHnVQjaEbRlE Na dad'e tsaye bayan shigewar matar nan da tsohuwar da ta kira kanta da Innani ciki kafin Fathiha ta shigo. Ganina tsaye yasa ta rike baki ta na fadin"Kina tsaye? Me yasa baki shiga ba? Mirmishi na yi mata ammh ban yi magana ba sai ta yi gaba ta na fad'in"Muje." Ni kuma jin haka sai na bi bayanta har zuwa cikin kayattacen Falon Amarya da yaji komai na kayan more rayuwa masu kyau da inganci. Sai dai me? A falon ma duk da akwai wasu daga cikin yan'uwan uwar ango akwai na Amarya aciki ma su sanye da irin kayana. Mamaki sai ya kara kamani suna kallona nima kamar yadda na ke kallon su, cikin mamaki Sa'adatu da ke falon ta kalleni ta na fadin"Laa Sadiya ga irin ankon mu? Ta fad'a ta nuna ma wata da ke kusa da ita wacce ke latsa wayarta. A tare suka kara kallona kafin ma na yi mgana Fathihatu ta kalli kayan jikina kafin tace"Laa iri d'aya kuwa ni ban lura ba." Sadiya tace"Yar'uwan ku ce? Fathihatu ta gyad'a ta na fadin"She is a Cousin." Sannu dayar tace min ta farkon kenan Sadiya nima na amsa mata da Sannu, dayar wayarta ta cigaba da latsawa. Wurga ido na fara yi ina neman su Adda ban gansu a falo ba sai na Fara Tunanin ko sun koma gida ne. Sai wata cikin dangin Ango tace sauran suna d'ayan dakin suna ta sallah. Sai Fathihatu ta jani zuwa Dakin da Amarya ta ke ciki tunda ga Hayaniya nan muna jiyowa. Ni ban shigaba daga kofar dakin na mika mata kular hannuna nace zan fara shiga wajen su Adda Fati sai ba ta musa ba ta karba ta bude kofa ta shige ciki ni kuma sai na shiga Bedroom din da ke kallonsa. Ammh fuskata cike da karin mamaki ni ba na kayan da ke jikina naga wasu yara Biyu mata sun fito daga Bedroom din Amarya da irin material din da na saka Jiya sakin baki kawai na yi ina kallonsu, sai ace wannan shima kawai had'uwa ce? Irin Atamfar d'aya fa harda Material din ba bu wani bambamci. Sai wata zuciyar tace Hasiya Abun nasara ai ya na da iri da yawa da wannan Tunanin na shiga dakin da su Adda Fati ke ta salla su da sauran mutanen da suka zo daga gidan Baba Jibril. Ina shiga Adda Fati ta fara tareni Adda Rukayya na sallah, Cikin mamakin ganina tace"ke da wa ki ka zo? Cikin basarwa nace"Ni da Fatihatu ta matsamin sai da na Biyota." Adda Fati tace"Ta kyauta damn yanzu nake tunanin mu koma gida, jakarki na Hannuna ana ta kiran wayarki ina Tunanin mijin ki ne." Ta fad'a ta na mikamin Jakar na amsa ina kokarin Bude Jakar naji Diyar Goggo Kona ta na kallona tace"Hasiya Atamfarki iri d'aya da ta dangin Amarya da suka yi anko." Sai na kalleta batare da na yi mgana ba, Adda Fati ce ta kara kallon kayan jikina kafin tace"Eh mun gani sai da Adda Rukayya ta yi mgana tace iri d'aya da na Hasiya." Ni dai ban Tsaya sauraransu ba na cire wayata acikin jakata na sake mikama Adda Fati jakar na fice daga dakin daidai Lokacin da na ke duba Calls din wajen 20missed call kuma duka Daga Assadiq. Ba a falon na tsaya ba saboda Hayaniya sai na fita zuwa Haraban gidan na samu chan gefen wajen tankin ruwa sannan na kira Assadiq sai naji line Busy da alamu ya na nema ne sai na d'an dakata. Sai ko ga kiran shi ya sake shigowa da Sauri na d'aga kiran rabon mu da waya Tun jiya da yammah da muka iso kaduna. Ina Dagawa yaji muryanta sai ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Siya ina ki ka shige ne? Kinsan kira nawa na yi miki baki daga ba? Zan kira Adda Fati na nemi lambarta a wayana sai kuma na rasata." Ajiyar zuciya na sauke kafin nace"Wayar na cikin jakata karama, kuma bata wajena ta na wajen Adda Fati, ita na ba ma ajiyar jakar tun safe." Shima ajiyar rai ya sauke kafin yace"Hankalina ya tashi Sosai dazu na samu salama Tunda kina lafiya." Daganan sai ya cigaba da fad'amin yadda ya yi kewata na yinin ranar gabadaya ni kuma kamar an yi min wani abu na kasa yi masa Fara'a haka Kurum na ke jin raina ba Dadi. Muna cikin wayar ne wata mata tazo gefena itama da irin Atamfar jikina ta na mgana a waya itama. Sai dai ni na rigata gama Wayar Tunda dagachan bangaran Assadiq na ji kamar ana mgana sai ya yi saurin ce min zai kara kirana ya kashe. Dagowa na yi ina kallonta bata da wani Tsawo fara ce ammh ba Sosai ba ta na kuma d'an jiki kad'an na Hutu da jin Dadi. In zama girmeni da kad'an ne ko kuma mu zo Tsaran juna ni da ita. Ashe ta gama wayar itama sai taga ina kallonta sai ta yi min mirmishi nima sai naji kunya na maida mata martanin mirmishi. Ni sai nake ganin su, da wad'anda na gani a falon nan da ita din suna kama da wani Fuska da na sani har matar nan da Tsohuwar nan a raina ina jin kamar ni dai yanayin fuskarsu kamar nasan wani ko wata da yanayi mai kama da na su. Har ta wuce sai ta kara dawowa ta na kallona kafin tace"Allah sarki ga irin ankon mu." Nima sai na yi mirmishi kafin nace"Eh nima ina gani nace komai iri d'aya." Dariya ta yi kafin tace"To ai kamfani bamu kad'ai ya bugamawa ba. Sunana Saliha ke fa? Ta fad'a ta na bani hannu alamun mu gaisa nima sai na mikamata nawa hannun muka sarke. Cikin maida mata martanin mirmishinta nace"Ni kuma Hasiya." Sai ta Bude baki kafin tace"Hasiya? Ko dai Asiya? Cikin yar dariya nace"Hasiya dai domin shine sunan yanka na." Sai ta Rausayar da kanta kafin tace"ko? Abunda yasa kika ji nace haka nasan sunan Hasiya ai Asiya ne" Mirmishi na yi mata ban ce komai ba ita kuma sai ta kara kallona kafin tace"Ni yayar Salima ce Amaryan da muka kawo, Ina aure a Ibadan ya'yana biyu, Sha'anin nan ne ya kawoni da zarar an gama zan koma Ibadan." Nima sai na samu kaina da fad'in"Ni ma ina da aure ammh ban haihu ba, kuma ni a matsayin diyar yayan mahaifin Ango ne daga Zariya muka zo." Cikin Fara'a Saliha tace"Ma sha Allah naji dadin had'uwa da ke Hasiya kina da Fara'a" Nima cikin dariya nace"Kema haka sannan ban kai ki fara'a ba." Gaskiya na fad'a ta na da Fara'a ni kuma haka Kurum taji ta Burgeni. Sai ga shi mun samu wani Dutse da ke wajen mun zauna muna ta Hira ni da ita. Har ta na fad'amin ta gama Degree dinta ammh  bata aiki sai dai kasuwanci ta ke yi, nima na sanar da ina yanzu na fara karatun nawa ina shekarar ta Biyu ne in muka koma Hutun karshen Shekara. Ban tambayeta ba da kanta ta fad'amin akwai nisa Daga Ibadan zuwa Gusai in dai ba Jirgi ta Biyo ba sai ta kwana a hanya. Ni kuma sai nace mata ai yanzu in ta tafi sai ta jima bata zo ba ko? Cikin yar dariya tace"Wane ni? Ai zuwa ya kamani in dai da rai da lafiya nan da wattani uku akwai Bikin kanin mu Sadiq, da kanwarmu Sultana da ya ke diyar kanwar Abba ne kuma nan ta girma cikin gidan mu." Sai na jinjina kai kafin nace Allah ya  Sanya alheri. Ina so ta na tambayeta Tsohuwar nan da Matar da na gani yan'uwan su ne?ammh sai na kasa yi mata mgana. Sai dai a raina na yi Tunanin Tabbas tare su ke yan'uwan Amarya ne. Mun jima muna ta Hira har aka kira Isha'i sai tace ko zan yi sallah ne? Kai Tsaye nace mata ba na sallah itama ta na Dariya tace mun yi anko. Sai kawai mu ka cigaba da Hiran mu, sai aka kira wayarta ta dauka ta na magana naji dai ta na ambaton sunan Mama, da Umma sai kuma naji sunan Innani a bakinta. Sai da ta gama wayar sannan ta kalleni ta na fad'in"Mamanmu ce, ta na tambayata ya innani, kakarmu ce fa irin rigimamman tsoffin nan ne wai sai ta zo Abba ya yi ya yi da ita tace sai ta zo." Sai na yi mirmishi nace"Na ganta ba wata tsohuwa mai gilashi ba sannan itama da irin Atamfar jikin mu ko? Saliha tace"Itace a ina ki ka ganta? Sai kawai na yi dariya na fara bata Labarin had'uwar mu, sai da ta yi Dariya kafin tace"Umma ce ta zo ta Dauketa domin tunda muka zo muka bar mata wahala da ita, Sadiq da shi kada'i ne ya isa ya hanata zuwa wannan karon da kansa ya sakata a mota, to waye zai dauki Innani daga karshe ta rika tsine masa kwata kwata bata san abun arziki ba." In ta ambaci sunan Sadiq sai naji gabana ya fad'i ko don sunan Mijina ne oho? Saliha sai bani Labarin Kakarsu Innani ta ke yi, ni kuma ina ta shan Dariya sai naji ina sha'awar zama da ita, saboda ni bansan dad'in duka zama da kakkani ba. Ta na cikin bani Labarin ne wasu yanmata Biyu suka fito suma Haraban gidan. Ina ji Saliha ta kira sunaayensu Siyama da Sultana ta kira su da Hannunta. Sai ga shi sun kariso gabanmu ganina da Saliha kila shi yasa suka gaishemu dayar wacce bata da Tsawon ta fi Fara'a Doguwar kuma sam ba ta yi min Fara'a ba. Kai tsaye ta kallesu kafin tace"Sai ina? Siyama tace"Shago zamu fita nema  Amarya ta aike mu mu siya mata Coke mai sanyi." Saliha tace"Shine sai kun fita? Ta kira shi Mubarak din fa? Siyama tace"Ta kira sa wayarsa baya shiga." Saliha bata damu ba ta kalleni ta na fadin"Kinga kanwar tamu da zata auri kanin namu nan" Ta fad'a ta na nuna mara Fara'an nan, Sai Siyama da tace kanwarta ne itace auta a gidan su. Mirmishi na yi musu Siyama ta kara gaisheni wacce aka kira da Sultana ce kwata kwata naji bata kwantamin a rai ba kamar yadda itama gani Daya ta yi min taji ban burgeta ba saboda Farin fatata har shiga ido ya ke yi. Sai ma ta kauda kai kawai ta na wasa da gefen mayafinta. Ina jin Saliha na gaya musu ni kanwar Mubarak ce cousin muke, Siyama ce har suka bar wajen ta na Fara'a Sultana kuma ko kad'an banga Fara'a a Fuskarta ba. ita kanta Salihar sai ta ce min haka take wani Lokacin ta yi ta kunci kamar an yi mata wani abu. Sauro suka Damemu da ya sa muka tashi muka koma cikin gida. Ammh kafin mu Rabu sai da muka karb'i lambar juna Tunda na gayamata ba anan zamu kwana ba. kuma gobe da Safe zamu koma zariya. Dakin Amarya ta wuce ni kuma sai na wuce dakin da su Adda ke ciki na iske sun shirya ni suke jira. Da ya ke ba nisa a kafa muka taka zuwa chan gidan, na gaji so kawai na ke na kwanta daman Dakin Zahra'u na ke kwana Gyara jikina kawai na yi na kwanta, su Adda Fati suna dakin da aka sauki sauran yan'uwansu na Zariya. Na yi mamaki har gari ya waye ban kara ganin kiran Assadiq ni kuma ban kirasa ba, da Safen bamu koma gidan Amarya ba muka yi shirin tafiya Adda Fati na wani mganan mu jira a tafi gabadaya nace to ni dai zan yi gaba sai sun zo. Jin haka yasa tace to mu tafi mun yi sallama da Hajiya Murjanatu tace kafin mu tafi mu shiga mu gaishe da Babanmu tunda hayaniyar Daurin aure bai sa ya san da zuwan mu ba. Ni dai har ga Allah ban yi niyar zuwa ba ammh bani da mafita. Abun mamaki tare da ita mukaje bai ganemu ba sai da ta yi masa bayani sannan ya ganemu ya dago ya na kallonmu kai Tsaye yace"To to cikin ku wacece mai kashin Tsiyan nan ne? Sai Adda Fati da Adda Rukayya suka kasa magana. Hajiya Murjanatu tace"Haba Abban Zahara'u wannan wani irin mgana ce? Kai Tsaye yace"Maganar gaskiya ne Murjanatu akwai mai kashin Tsiya acikin su ko ba da ita kuka zo ba ne? Kaina na kasa na kasa mgana ammh naji wani abu mai daci ya Tokaremun zuciya. Ganin su Adda Fati sun kasa mgana yasa na dago ina kallonsa nace"Ni ba ni da kashin tsiya, ni Mutum ce kamar ka  kuma Baiwar Allah da ya Halliceni tare da Ni'imominsa." Sai shima ya Tsaya ya na kallona kafin ma ya samu zarafin mgana naja jakata na fice daga falon ina kokarin maida kwallata. Ko ajikinsa sai ma ya zakud'a kafad'a kafin yace"ance ta yi aure kwanaki in ji dai shima mijin bata nakasa shi ba ko? Adda Rukkaya tace"Suna zaune lafiya." Sai ya yi mirmishi kafin yace"Dakyau, Ina ita mahaifiyar taku? ko ta na chan garin na su ne da akace ta koma? Adda Fati tace"Eh ta na chan tace a gaisheku da Fatan Allah ya ba da zaman lafiya" Cikin jinjina kai yace"Ameen ku gaida Gida" Da haka ya Dauki wayarsa da ake ta kira tun dazu. Su Adda Fati suka fito jiki a mace Hajiya Murjanatu ta rasa ina zata saka kunyarmu. Su Adda Fati ne suka Tsaya tabasu abun Rabo na jaka da kofi sai kayan Fulawani ni a bakin Titi muka had'u da su, kuma har muka isa tasha muka Hau mota ba mu yi ma juna magana ba. Gidan Adda Fati muka sauka ni da ya ke ba na sallah ban Tsaya ko cin abinci ba na had'a kaya na wuce gida nace naci achan, ba su hanani ba ganin yanayina sai da na koma gida naci kuka na har na godema Allah. Sai da yammah Saliha ta kirani tace ga su sun zo gidan ba ta ganni ba. Murya a chunkuse nace mata mun Dawo Zariya tun dazu. Jin muryata wani iri yasa tace lafiya? Ni kuma sai na ce mata ina Mura ne fatan samun sauki ta yi min tace suma sai gobe za su koma Gusau sauran ne da za su zo daga gusau mota ta lalace musu a hanya sai da yammah suka iso. Fatan sauka lafiya na yi musu sannan muka yi sallama. Na zauna na yi ta Tunanin inda mutanen da na had'u da su a kaduna suka min kama da wanda na sani ammh na kasa ganewa. (Da ya ke Yan gidan su Assadiq ba su da mugun kama da juna, Gwara ma yan Dakin Mama ita suke Debo suna yanayi da juna akan dakin Umma Sadiq ne ma ya ke kama da Surayya kamar kwabo da kwabo). Sai a daren muka yi mgana da Assadiq shima dai ji na wani iri sai da ya yi mgana sai nace masa mura ne. Sai yace kila iskar Mota ce tunda na gayamssa tun dazu muka dawo. Matsamin ya yi na siya magani na sha na kwanta na amsa masa da toh. Washegari dakyar na iya rarrafa jikina na yi share share tunda dakin ya yi kura jikina nake jin ya na min wani iri sannan Jinin da na ke yi a kallah kwana Biyar sai ga shi har Sati bai Dauke ba. Sai na fara Tunanin kamar ba lafiya ko shi ya ke sakamin kasala ban sani ba ko abinci na rage ci da ga Tea da Safe sai Dare na Dafa Indomie. Yau din ma Tea na sha da Safe zaman kadaici ya isheni mun yi waya da Safiya Ahmad da Safe tace mun kusa komawa makaranta. To daman Assadiq ya bar min karamar Computer dinsa Saboda makaranta shi kuma sai ya siya Sabuwa kuma da ya ke muna yi a makaranta sannan shima ya Koyamin sai ya kasance na iya Sarrafata yanzu. Duk da ya maida komai na shi cikin Sabuwar da ya siya bayan ya goge komai aciki fina finai Kawai ya barmun sai karatun Qur'ani. Sai ni kuma na saka Safiya da ta zo ta Turamin Abun karatun mu na Computer aciki. Tunda aka yi Hutu ban Daukota ba, kallo bai wani Dameni ba sai in Assadiq na nan ne mu yi tare, in kuma baya nan sai dai na gaji da danna waya ko na yi barci karatun Novel din ma da na fara yanzu na Daina bani da juriyan karatun ne kwata kwata. Na Dauko na kunna kenan sai hannuna ya kai kan wani Draft da aka saka SSSHINKAFI a jiki ban taba Lura da wajen ba. Ko sanda Take na Assadiq ba ko'ina ya ke shiga a gabana ba, wasu app d'in ma duk sai da ya san ya musu pin in ba shi ba, ba wanda zai iya shiga ciki. Kamar wasa sai na Shiga sai naga Wani Hoto ne guda daya a wajen akwai alam ya makalene ba'a goge shi duka ba. Kamar bazan shiga Hoton ba sai na Danna sai ga Hoton ya bayyana. Hoton da sai da ya sa na tashi da Sauri Cikin kif kifta idanuwana na mamaki da Al'ajabi. A cikin Hoton naga mata Biyun da na gani a kaduna, sannan har da Saliha aciki da yaran matan da ta nuna min Siyama da Sultana. Sai wasu kuma da sun kai su goma sha a Hoton sun saka kaya iri daya na wani bakin leshi da Fari, sun saka Assadiq a tsakiya shima cikin Fararan kaya harda babban Riga. Sai dai fuakarsa ta yi karama a Lokacin kamar Hoton ya jima ko wani sha'ani ko kuma sallah ne aka yi wannan Hoton. Na gefe da gefensa sun Dafashi gabadayansu suna dariya ga Fararen Hakoransu nan a bayyane da Mirmishi da Fara'a sai gashi na samu kaina da Kara zooming din Hoton domin na kara Tabbatar ma da kaina abunda na gani shin gaskiya ne ko ni ce ban gani Daidai ba? Sai ga shi na kara tabbatar ma da kaina abunda na gani zahiri ne acikin wannan Hoton. Sai da na kara kura ido sai na samu amsar kokwanto na tunanin da waye sukamin kama? Ina ganin Fuskarsu yanayi da na wanda na sani to ba kowa ba ne face ASSADIQ.! Na dimuace sannan na shiga wani yanayi da Tunanin su waye wad'anan a wajen Assadiq? Wani lungu daga zuciyata ta bani amsawa da cewa"Ba sa wuce Yan'uwansa." Sai kuma na ce a fili to ai yace ba shi da kowa sai kakarsa to wad'anan fa a ina ya same su?  Kamar ana min Wahayi naji bakina ya furta"Kenan Assadiq ya yi miki karya ke da yan'uwan ki." Tabbas hakane domin ko wanda baisan kama ta jini ba yaga Assadiq da wad'anan matan yasan suna da alaqaan jini mai karfi a tsskanin su. Na yi ta kallon Hoton nan ina sake Zooming ina kokarin gasgasta zargina zuciyata na Tunanin Assadiq bazai min karya ba? Wata zuciyar na gayamin ya yi min karya tunda har yau bai taba kaini ga wani nasa ba hatta ko kakar tasa da yace ita kad'ai ta rage masa. Lokacin da nake zaune ina wannan Tunanin, ashe ban sani ba na yi sharkaf da jini, sai da naji abu na bin kafata sannan na farga ko da na mike sai da naji tsoron ganin jini ya bata siket din jikina yar ya bata kujeran da na ke zaune sannan ya bata har kasan Tayels wanda ya gangaro ta kafafuna. Wannan tashin hankalin ya mantar dani Hoton da na gani na shiga cikin tashin hankali na shiga Tiolet na gyara jikina sannan na kwabe kayan Jikina na wanke su tas sannan na fita waje na shanya. Muka had'u da Maman suhailat itama ta na shanya ta yi wanki sai muka gaisa sama sama domin ba na cikin yanayin nishad'i, na koma daki da Sauri na goge kujera in da na bata da kuma Tayels din na wurgar da Tsumman da na goge da shi. Abun kamar wasa sai ga karaman mgana ta zama babba kwana nayi ina Zubar da jini, pad ya daina amsata na koma yaga zanina ina kunzugu da shi ammh duk a banza kafin safe sai da na cika baho da kayan da na bata har da zannuwan gado har katifan ma sai da ta baci. Hankalina ya tashi saboda Ina Tunanin jinana ya kusa karewa, ni ba Ciki gareni ballatana nace ko bari zan yi tuni har karfina ya kare ma fara ganin jiri jiri dakyar na iya wanke kayan da na bata na fita na shanya, daga baya da naga zanin ya daina Tarenin jinin duk inda na zauna sai na bata ina tafe ina yoyo da sauri na Daga waya na Kira Adda Fati a Lokacin ban yi Tunanin kiran Assadiq ba Sanin da na yi baya kusa kafin ya kawomin agaji na mutu. Cikin tashin hankali nace mata tazo gida yanzu, jin yanayina yasa tasan ba lafiya, ko da ta zo ta iskeni zaune ina kuka ga jini na ta bin kafafuna. Cikin tashin hankali ta rikeni ta na Fadin"Innalillahi Hasiya? Me ya sake ki? Ko bari kikayi? Cikin kuka nace"Bansani ba, daga al'ada ne jini ya tsinke min adda Tainakemi ki kaini asibiti kafin na mutu jini na ya kare." Adda Fati ta rakani Bayi na gyara jikina ta ninka wani Dankwali na yi Kunzugu da shi sannan na sauya kayan Jikina, ita ta Rufe dakin muka ta fi asibiti abun da ya kara ba ma Adda Fati tsoro tun muna adaidaita jini ya fara bin kafata kuma duk ya bata kayan jikina da Hijabina Asibitin musulmi ta kaini mun jima kafin mu ga likita don ma wai jama'a sun Tausaya ganin ina ta zubar da jini ga shi nan inda na zauna har ya na gangara. Ni dai nasan Adda Fati ta rikeni zuwa ofishin Likita, daganan bazan iya tuna komai ba, sai da na farka da misalin hudu na yammaci na gani kan gadon asibiti a wani daki ni kad'ai sai Adda Fati a Tsaye a kaina sai kuma Ramatu na zaune gefena ta na rike da Hannuna. Cikin Nauyin jiki da na ido na farka ina bin su da kallo suma kallona su ke yi ganin na Bude ido yasa Ramatu tace da Sauri"Adda Ina ga ta farka." Jin haka yasa ta kariso gabana ta na fadin"Hasiya." Amsawa na yi cikin dakushewar murya ina kokarin tashi ta kamani na tashi lokaci d'aya ta na fadin"Ki bi a sannu kada ki fama Hannun ki." Sai na bi hannun da kallo cikin mamakin ganin bandage a hannuna, sannan kuma na duba kafata ban ga jini na bi na ba, ammh daga kasa naji kamar an sayamin Audugan mata. Cikin neman karin bayani na kallesu kafin na yi mgana Adda Fati ta Bude kofa ta Fice ta na fadin"Bari na Fad'a ma Likita ta farka." Ramatu na rika tambayan me ya sameni? Ko jinina ne ya kare? Sannan miye ya sameni a hannu.? Ramatu bata amsamin Tambayata ko Daya ba sai ma wani kallo da naga ta na yi min kafin kawai tace"Uhm Hasiya kenan." Daga haka ta tsuke bakinta sai abun ya bani mamaki, Adda Fati ta dawo tare da likita ya duba ni sannan ya yi min Tambayoyin ya na ke ji nace ba komai ina jin jiri nace a'a? Ina jin zubar jinin yanzu? Nace ba na ji. Sai ya kalli Adda Kafin yace"Kada ku damu zubar jinin ya tsaya, daman kuma shi Inplant da zarar an ciresa ya na tafiya tare da matsalansa ne, Saboda ta samu karfin jikinta sai ku kwana anan da Safe sai ku tafi gida." Bayan fitan liktan ina so na yi tambaya ammh Daga Adda Fati har Ramatu ba su bani Fuska ba. Haka suka yi Fuska kamar ba su sanni ba, kudi kawai Adda Fati tace ko akwai a Hannuna nace suna banki. Sai na gayamata in da na ke ijiye Atm dina Ramatu tace zataje gida ta  dauko sannan tazo min da wasu kayan. Sai lokacin na lura da na jikina ba nawa ba me na Ramatu ne wad'anchan kenan sun lalace komawa na yi na kwanta ina Tunanin abunda ya sameni da bansani ba. Adda sam taki sakarmin Fuska, Ramatu ta je gidana sai ta wanke kayan da na bata sannan ta Dauko min zani da riga, sai pant guda Biyu sai ta dabo Ruwan zafi a fulas ita ta gayama Maman Suhailat ina asibiti ba ni da lafiya ammh gobe zan dawo gida. A hanya ta tsaya ta cire kudi ta siyo kayan marmari da Buredi, sanda ta dawo ina barci sai daga baya na Farka Adda Fati ta rakani bayi na yi fitsari sai naga jinin ya tsaya sai dai dis dis ya ke diga a saman Audugan. Tea Ramatu ta hadamin na sha Daman yunwa nake ji, sai kuma Kayan marmarin da na sha, yadda suka min gim nima sai ban kara mgana ba ina so nace ina wayata ammh na kasa tambayar su. Adda Fati ce ta kwana dani Ramatu ta koma gida Tundaga Noor. Da Safe ma sai dai ta same mu a gida Tunda da wuri aka sallame mu. Sai ga shi da kafata na shiga Daki na tare da Adda Fati, Maman Suhailt da Ummi sun shigo sun gaisheni. Adda Fati ta had'amin Ruwan wanka na shiga na yi sai dai tace na kula kada na Fama Hannuna. Bayan na fito na sauya kayan jikina , na saka pant da pad duk jinin kad'an Ya ke zuba ita kuma har ta had'amin Tea ta soyamin kwai. Kadan naci kwan Tunda bakina baya min dadi, sai ta bani mganguna guda biyu na sha wanda inaga aka Rubuta daga asibiti ne. Adda Fati ta share dakin ta goge ni kuma ina zaune saman kujera ina Tunanin karo na Biyu kenan a sakamin Bangade a hannuna kuma duka ba acikin yanayin Hankalina ba to me ke faruwa ne? Wajejen sha Biyu sai ga Ramatu, ta zo suka had'u da Adda fati suka zauna waje daya suna ta magana kasa kasa bana jin me suke fad'a. Wayata ce a hannuna ina duba kiran da na rasa Assadiq sau biyu ya kira jiya da Daddare, sai bai kara kirana ba Kila ya na Tunanin na yi barci ne. Gabadaya sai na Tsargu, na fahimci kamar da ni suke. Sai na tashi Zaune dakyau ina kallonsu cikin mamaki kafin nace"Adda, ramatu wai don Allah me ya ke faruwa ne ? Tun a asibiti na ke tambayar ku shuru baku ce min komai ba ? Adda Fati ta Kalleni kafin ta harareni tace"Gani mu ka yi tambayar taki ba ta da amsa, Tunda kinsan abunda kika aikata." Cikin mamaki nace"Bangane ba? me na aikata? Ramatu ta ce ka tsaye"Ki na so ki gayamana baki san abunda kika saka a jikin ba ne da ya sakar miki jini ba? Cikin wani karin mamaki nace"Wani abu kenan? Don Allah ku fad'amin bansani ba." Adda Fati cikin bacin rai tace"Hasiya da wayau ki da komai me ya kai ki? Baki taba Haihuwa ba me ya ja miki saka Tsarin iyali? Abun takaicin ma in za ki saka Tunda baki son Haihuwar yanzu sai ki saka na shekara d'aya ko Biyu ammh Saboda Rashin Lissafi har na Shekara biyar kikaje aka saka miki to Allah ne ya cece ki, sai da aka yi miki karamin Tiyata a hannun nan naki aka Cire abunda kika kai kan ki aka saka miki" Har alokacin Cikin Duhu nake cikin Sigar tambaya nace"naje aka sakamin mene? Kuma a yaushe? Adda Fati tace"Bana son Renin wayau Hasiya, inplant din da kika saka na Tsarin iyali na shekaru Biyar." Na bud'e baki ya fi sau biyar ina Rufewa Lokaci d'aya ina kallon Adda Fati cikin mamakin kalamanta. Cikin fitar hayyaci da Sigar tambaya na maimaita"Inplanta kuma? Menene shi? Ban gama Rufe baki ba Ramatu ta ballamin harara kafin tace"kin fi mu sanin koma menene shi tunda kika iya aminta kika kuma saka shi a jikin ki Hasiya, kin bani mamaki ban zaci haka daga gareki ba." A zahirance ne na ke kallon Ramatu, ammh a badini ba ita na ke kallo ba na lula wani Tunani na dabam Ina jin acikin fad'an Adda Fati sai na gano ma'anar abunda aka gani ajikina. Inplanta wani abu ne na tsarin iyali, to yaushe na saka bansani ba? Kwakwalwata ta shiga Tunanin a watarana, sannan da wani Lokacin har haka ta faru bansani ba? Kamar an nuno min ranar sai na fara ganin sanda mukaje asibiti da Assadiq da duka abubuwan da suka faru da Farkawan da na yi na samu kaina a irin yanayin da na samu a yau. Kwakwata ta fara had'amin abubuwa a cikin kaina sanda na fara a wanchan ranar naga hannuna da Bandage ce min aka yi wai na fadi na cake da allura yau kuma ana gayamin a wajen na saka abun Tsarin iyali.? To waye ya sakamin? Wata zuciyar tace"ASSADIQ mana.." Sunansa kawai da na Tuna sai da naji jikina ya fara rawa. tabbas Biri ya yi kama da Mutun na Tuna duk abunda suka Tattauna da likita a ranar ba'a gabana ba ne. Ce min kawai ya yi za'a Dibi jinina kuma da hayyacina aka Dibi jinina in lissafina ya yi daidai tabbas lokacin da Nures din tamin allura ta barci ce kuma a lokacin da na samu barcin ne da Umarnin Assadiq a sakamin abun Tsarin iyali a jikina batare da na sani ba. Tabbas haka ne abun ya faru wannan shine hakikanin gaskiyan mgana. Kaina na Dafe kafin na saki salati a fili cikin fitan hayyaci nace"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Adda Fati ta tabe baki kafin tace"Ke kika sani Hasiya ammh wannan abunda kika aikata abun kunya ne na gode ma Allah da mijin ki bai sani ba da bansan da wani ido zaki kallesa ba" Ramatu ta karbe da fadin"To mene ma dalilinta na rashin son Haihuwa tunda ita ba haihuwar ta taba yi ba? Kamar Ramatu ni ta ke tambaya acikin zuciyata nace"Saboda Assadiq baya sona. Sannan baya son ya had'a Zuru'a da ni." Sai na fara Tunanin abubuwa da Dama, na game da Assadiq rashin wayarsa a gaba na, da sauran alamomin rashin gaskiyarsa in na auna da Hoton da na gani sai na samu wata gaskiya Assadiq baya sona ya aure ni ne saboda Biyan Bukatarsa, kuma karya ya ke yi ya na da Ahali kilama har da iyaye. In hasaahena ya tabbata ba bu wani ta bangaran Ahalin Assadiq da yasan dani a matsayin matarsa. Rayuwarsa guda Biyu ce ta boyayyiya da ta Zahiri. Ta Boyen itace tawaa, Ta zahiri kuma itace na hoton da na gani. Sai kuma na Tuna Saliha ta gayamin kaninsu zai aure yi mai suna Sadiq. Wani Sadiq din ta ke nufi? Assadiq ko kuma wani Dabam? Bani da mafita illah na dora zargin komai a kaina. Saboda kada su Adda su fahimci Rayuwata ta kara gangara cikin Tsaka mai wuya. Sai kawai na fashe da kuka ina fadin"Ku yi hakuri, ni tsoro na daman kada na zo na Haihu ya'ya na su Fuskanci Rayuwar Tozarci da wukakanci da ni na Fuskata wlh shi na ke tsoro." Sai kuma kalamaina ya saka jikinsu ya yi sanyi barin ma yarda na ke kuka. Sai suka sauko da ga jin Haushina suka zauna suna ta bani baki da nasiha har na yi shuru na nuna musu komai ya wuce. Sai yammah suka tafi bayan Ramatu tamin girki daman na kosa su tafi, Suna tafiya na tashi naje na Dauko Computer na kara Bude wannan Hoton ina Kallo. Ban yi wata wata ba na Dauki wayata na Kira lambar Saliha sai a lokacin na fahimci dalilin da yasa Allah ya had'amu saboda nasan gaskiyan da ya kamata na sani kan Assadiq. Bayan ta dauka mun gaisa na ke tambayanta ta koma Ibadan? Sai tace ta koma jiya, kai Tsaye nace sai biki kenan? Tace sai bikin in sha Allahu. Ina daidaita yanayina nace"Ya sunan Angon ma? Cikin Fara'a tace"Abubukar muna kiransa Sadiq ko magajin gida." Sai na jinjina kai kafin nace"Kila na zo bikin in sha Allahu in dai kika gayyaceni." Cikin murna tace"Me zai hana? In sha Allahi zan sanar da ke in Lokaci ya yi, Gusai ba nisa daga zariya." Sai na yi mata yake kafin nace"In sha Allahu." Daga haka muka yi sallama ina Dauke hawayen idanuwana. Na tuna da kayan da na gani tare da su irin kayana ne kuma Assadiq ne yazo min da shi ammh sai yace a Abuja ya siya. In na kara hasaso wani tabbacin Kanwar Assadiq ce ta auri Mubarak yaron Baba Jibril kuma matan da na gani a kaduna tabbas na had'u da Ahalin Asssadiq ban sani ba. Kuma wannan Tsohuwar itace kakarsa wacce ya yi min karya da sunanta. In ko hakane ya yi kuskuren yi min karya, tabbas zan gano sauran gaskiyan abunda ya Boyemim Wannan alkawarina ne. *Janafty* *TMWBK2020* *TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488* https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan. Nayi kokarin yaki da abunda ke cikin zucuyata game da Assadiq, saboda ba na so ya fahimci na fara sanin wani abu game dashi wanda ya boyemin bai so na sani ba. Ya yi ta kirana a waya ban dauka ba adaran sai da safe na dauka muka yi mgana, ko a muryanta bai Fahimci wani abu ba, ballatana a saman Fuskata duk da baya ganina. Kafin ma ya yi korafin rashin Samu naa a waya na yi masa karyan da cewa wayar ce ban ganta ba tun shekaranjiya ashe ta fad'a kasan gado sai da Habiba ta zo ta kama min muka Daga katifan sannan muka gani. Sai ya sauke ajiyar zuciya na samun salama Tunda ya tabbatar ina lafiya kuma wani abu mara dadi bai sameni ba. Tunda lokacin muka cigaba da wayarmu lafiya lau ni da shi kamar baya, bai dawo a satin ba sai na sama ya dawo min Weekend, na yi kokarin kada ko a saman Fuskata ya Fahimci na san ya sakamin Inplant duk hanyar da zai gane wani abu ban bari ya gane din ba. So na ke na ba shi mamaki kwatakwacin irin mamakin da shima ya bani, Ban damu saboda bai Fad'ama Ahalinsa game dani ba, ammh ni meyasa ya yi min karya ni da Yan'uwana game da shi? Kuma meyasa ya ke zaune dani Domin Biyan bukatunsa na Rayuwa ba domin ya na sona ba. In na tuna haka sai naji na Raunana har na fara kuka ban sani ba, ina Tunanin Rayuwata ta fita cikin Tsaka mai wuya ashe ashe bansani ba Zata kara shiga cikin wani Tsaka mai wuyar ne wanda ban taba shiga irinsa a baya ba. Duk abunda na saba na tarbarsa sai da na yi masa, kitso ne ban yi ba sai dai na gyara kaina na yi kunshi, a makotan mu akwai mai kunshi Shiyasa bani da matsala, sannan na yi masa girken girken tarba kuma naci kwalliyata kamar yadda na saba. Sai dai duk yadda na so na saki Jiki da shi na kasa kamar baya, da nake jin Matukar kosawa kasancewa da shi a lokacin naji komai ya fita kaina. Shi kanshi ya Fahimci wannan karon ban yi zumudin zuwan shi ba sannan ban yi masa rawan jikin da na saba yi masa a shimfid'a ba, ban kuma nuna na yi kewar kasancewa da shi ba kamar yadda ya rika gayamin lokacin daga ni har shi muka samu natsuwa. Da ya neme ni ban hanashi kaina ba, Saboda in na hanashi zai zargi wani abu Tunda ban taba yi masa gaddama ba ni mai tallafinshi ne in dai ya zo da Bukatarsa. Shiyasa na ba shi had'in kai ammh ba Dari bisa dari ba, abunda bai sani ba yana kasancewa da ni ina Sharan hawaye tunda nasan daman ya ijiyeni ne saboda na zama abar Deb'e masa kewa sannan ina Tunanin wata kila nan da Lokaci kad'an zama na da Assadiq zai zama shud'adden Tarihi kamar yadda na Abubakar da Salisu ya kasance a Rayuwata. Sai da muka Tsarkake jikin mu sannan muka sake komawa muka kwanta duk yadda na so na makale masa a jiki kamar yadda saba a baya na kasa sai na koma gefen gado na lafe ina maida Numfashi. Sai jinsa na yi ta bayana ya kwantar da kansa a saman wuyana ya na leken Fuskata sai na yi Saurin Runtse ido alamun na fara barci. Yar dariya ya yi ya na Jan Hancina kafin yace"Siya fushi ki ke dani Saboda ban zo miki wanchan satin ba ko? Ban ce masa komai ba ya cigaba da Fadin"Ki yi min afuwa Siya ta, kinsan yanayin aikin namu, sannan ga nisa in nace duk sati na rika dawowa akwai gajiya acikin Lamarin, ammh ina nan ina kokarina Dauke ki zan yi na maida ke kusa da ni in sha Allahu." Ina jinsa a raina nace ji karya ba Sai dai kila Sultana ka ke nufi. A fili ko dan motsawa na yi kafin nace"Ni ba fushi na ke yi ba, Barci kawai na ke so." Jin haka yasa ya juyo dani muna Fuskantar juna kafin yace"Kin tabbata.? Sai na gyad'a masa kai cikin sanyin murya nace"Na tabbata." Saboda ina so ya kyaleni, ban san kuma wata Doguwar mgana sai ji na yi ya rumgumoni a jikinsa ya na fadin"Nan ne wajen barcin ki kin sani ko? Sai na gyad'a masa kai, kaina ya kwantar saman Kirjinsa lokaci d'aya yana shafa sumar kaina zuwa bayana. Runtse idanuwana nayi kamar mai barci ammh ba barci na ke yi ba. Kamar yadda shima ba barcin ya ke yi ba ya lula cikin Tunanin mafita. Da gaske ya ke yi ya fara Tunanin neman Muhallin zama a Abuja. Kuma in dai ya samu to da Siya zai tafi domin ya na Azbatuwa saboda rashinta. Sultana kuma ta zauna a Gusai ya rika zuwa ya na ganinta. Barci ne ya kwasheni ban sani ba, shi kuma sai da Dare ya Tsala ya samu barci. Da Safe sai da na bari mun tashi mun karya, mun yi wanka ni kuma na gama Share share da goge goge, ya na zaune saman kujera ya na aiki a laptop dinsa na dauko nawa na zo kusa da shi na zauna. Bai damu ba ya Dauka wani abu zan nuna masa na bangaran karatuna. Hankalinsa na kan abunda ya ke yi yace"Kun kusa komama makaranta ko? Kai Tsaye yace"Eh Monday ta sama." Na fad'a ina Nuno masa Hoton nan sai da na kallesa sannan nace"Assadiq su waye wad'anan da nagan ku kun yi hoto tare? Da Sauri ya Dago ya na kallon Abunda na ke Tura masa, Sandarewa ya yi a zaune kamar ruwa ya cinyesa. Duk da Safiya ne sai da naga ya fara zufa sannan rashin gaskiya da Razana ya bayyana Kuru kuru a saman Fuskarsa Sai na yi mirmishi kafin nace"Abokan karatun ne ko? Da Sauri yace"Eh Eh, tare muka yi karatu da su a zariya." Cikin kallonsa nace"Ayya sai kuma naga kamar a gida kuka Dauki wannan Hoton? Hala gidan daya daga cikin su ne? Da Dauri yace"Eh.! Eh." Sai ya kasa mgana da Sauri ya karb'i Computer a hannuna a gaba ya latsa Delete ya goge shi. Cikin mamaki na kallesa kafin nace"Me yasa ka goge min? Kai Tsaye yace"Ba shi da Muhimmanci ne." So na ke ya kalleni ammh ya kasa duk ya Daridice alamun rashin gaskiya Muraratun Kamar zan yi mgana sai kuma na fasa, ina ganinsa ya na ta kara Dube Dube a cikin Computer Tunaninsa ko kila akwai wani abun da in nagani zai Tsarwarsa komai. Ban nuna masa na Damu ba, ko na nuna na Fahimci ba shi da gaskiya. Yadda ya kasa samun natsuwa yasa na kara Tabbatar da Zargina. Tashi na yi na bar masa falon ganin yadda gabadaya ya rikice ya kasa aikin gabansa sannan ya kasa iya kallon Barayin da na ke saboda kunya da nauyi. Assadiq bai taba kawo ma ransa da cewa Hasiya ta had'u da yan'uwansa a kaduna ba, Shiyasa sai ya yi Tunanin tunda ya goge Hoton ba lalle ta Zurfafa Tunani a kansa ba, ballatana har ta gano wani abun ba. Ya so ya kama kanshi Sanda yaga Hoton ne tambayar da na yi masa ita ta bashi Tabbacin ban Fahimci komai da ya Danganci Hoton ba. Abunda bai sani ba na Dinkesa ne a baibai kamar yadda shima ya jima ya na Dinke ni. Har ya gama Weekend dinsa ya tafi Ranar Lahadi da yammah ban kara nuna masa wani abu ba, abunda ya kara bani mamaki ko kafin Tafiyarsa sai da ya nemeni kuma na bashi Had'in kai sai bayan tafiyarshi na zauna Ina Tunanin haka Assadiq zai ta moran jikina a banza ni ya so ka shemin Rayuwa ya hanani haihuwa. Shi kuma zai yi auransa da Matar da ya ke so kuma Danginsa ke so ta haifa masa kyakyawan Zuru'an da ya dad'e ya na fata. Ni kuma ko Oho rayuwata bata da wani amfani ban chanchanci samun wani abun Farinciki a Rayuwa ta ba Tunda Kaddarata ta zo a haka, sannan ina Dauke da Bakin Fentin da zai iya shafar Rayuwata kila har bayan Mutuwata. Na yi kuka kamar raina zai fita kukan da ya zame min sana'a a kwanakin nan ga shi ba ni da bakin mganar da zan iya taran wani na yi masa mgana, Wannan al'amarin abunda ya shafi Rayuwata ne ban zan so na zame ma yan'uwana Damuwa a koda yaushe ba. Na yi Tunanin Ramatu sai kuma na Fasa Tuna itama na yi mata karyan, naje garin su Assadiq naga Ahalinsa ni ma kuma sun gani, yanzu ban isa naje musu da wata mgana ba. Amma ce na yi Tunanin kira sai da kuma na Kirata na kasa gayamata abunda ke damuna. Sai kawai na Bige da ce mata"Amma in bawa ya shiga matsanancin Damuwa  sannan ya rasa mafita wani irin mataki ya kamata ya Dauka? Sai Amma tace"Matakin da zai Dauka shine na Dogara ga Allah, ya maida Lamarinsa ga Ubangijin Sammai da Kassai, ya kaskantar da kansa a gabansa ya Rokesa mafita Allah shi Kowa ne in nace kowa ina Nufin kowa da komai shi ke samar da mafita da warwara al'amuran mu cikin gaggawa in ya so hakan Hasiya, ko kuma ya jinkirta al'amarin har zuwa Lokacin da zai Ribanya maka kyakyawan Tanadin da ya yi ma bawa." Da kalaman Amma na yi amfani na maida lamarina a wajen Ubangiji, na Dage da Ibada ba rana ba Dare na yi kuka na roki Allah in har aurena da Assadiq akwai alheri aciki Allah ya Daidaita al'amarin da kansa, in kuma babu Alheri Allah ya sa ya sahalemin cikin kwanciyar Hankali ba sai Rayuka sun baci ba. A haka muka zo muka koma makaranta, sai hakan ya rage min Damuwa na dage da karatuna gefe daya kuma muna tare da Safiya Ahmad. Assadiq bai zo ba sai bayan Sati uku, a kuma zuwan ne ya biya min kudin makaranta sannan ya bani kudin Handout da sauran Bukatu da zai tafi ya Turamin 50k yace na ijiye a acct dina, bayan 10k din da ya bani a Hannu yace min na zirga zirga ne. Duk da ina addu'a ammh muna taba juna a waya ni da Saliha so na ke kada Lokacin Bikin ya bace min a lokacin ne na ke so na kara tabbatar da abunda na ke Zargi a kan Assadiq. Abu kamar wasa sai ga shi mun kulla Zumunci da Saliha ita ke fad'amin ma yar'uwanta Sajida ta haihu a Gusai ammh bazata samu zuwa ba, sai biki Saboda ya yi nisa da ya ke mun yi Saving din Lambar juna muna ganin Statue din junan mu. Anan naga ta Dora Hotunan Taron suna na yan'uwanta da aka yi a Gusai. Wani Hoto da yaja Hankalina Shine wanda Maijegon tare da wata ta rike Jajarin a Hannunta Fuskarta da yanayin mirmishinta kamar Assadiq. Sai da na yi Tagging na Tambayeta"wannan ma yar'uwarki ce Saliha? Sai tace"Yes Big sis kenan itace Babba a gidanmu Sunanta Surayya itama anan Gusau ta ke aure" Wannan Hoton har Daukansa na yi na rika Zooming ina ganin abun mamaki. Ina da Hotunan a Assadiq a wayata wasu tare mukan Dauka wasu kuma shi ya Turamin na rika Dubasu ina mamakin ga kammani nan Zahiran da suka kara bani Tabbacin abunda na ke Zargi. Sannan kuma in ban manta ba a lokutan baya ya sha fad'amin sun tafi aiki da Megidansa Gusai kenan Gusai ne anihin mahaifarsa. Saboda kara samun Tabbaci yasa na Tambayan Saliha da cewa su yan wani gari ne? Ma'ana assalin su, kai Tsaye ta ce min su Asalin Mahaifinsu mutumin Shinkafi ne. Kawai a raina sai nace shikenan Hujjoji masu karfi sun kara tabbatarmin da wad'anan matan da ma had'u da su a kaduna sune Ahalin Assadiq da ban sani ba. Sai na Kudira a raina mamakin da zan ma Assadiq bai taba zaton zan iya basa wannan mamakin ba. Na kudiri wani niyya acikin Raina Niyar daga ni sai Ubangijina suka sani. Zan shayar da Assadiq mamakin da ya shayar da ni, kila ma nawa mamakin yafi gigitasa fiye da nawa. ******* Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah, ga shi har sha'anin bikin Assadiq da Sultana ya kawo saura Sati uku, dukkan Shiryen shiryen sun gama kamallah a nan garin Gusai. Tuni har an yima sultana Jerenta da kayan alfarman da Abba ya siya mata, a kuma jera mata su a cikin kayattacen gidan da Abba ya mallaka ma Assadiq Hakal makal. Sannan Surayya ta gama had'a akwatina Guda takwas shake da kayan alfarma, sai wanda ya gani kaya na gani na fad'a na ya'yan gata. Ta bangaram matan sun fi shirye shiryen Bangaren Ango Sadiq kuma sai in ma Tahir ya kirasa ne ya ke Tunawa da zencen auran. Shi dai ya na gefe sai abunda aka kirasa akace masa ya ke amsawa. Shi dai bai zira jikinsa ba, sannan bai yi baya ba. Tunda auran gata Abba zai yi masa, sai ya kudira a ransa zai ba ma Sultana kudin gyaran jiki da kwalliya sannan shi yanzu Fafutukarsa na Kudin da zai bama Siya ta siya kaya ne bisa adalci Tunda ita bai yi mata Lefe ba. Kudin da ya ke Turamata ta acct dinta sun kai yanzu Kimanin dubu Dari biyu da wani abu ya na so su kai uku ne yace ta Dauka ta siya abubuwan da ta ke so. Sannan ko mganar kayan angwanci Big sis tace Abba ya ba da kudi an had'a masa akwati guda, sannan Tahir ya yi masa wasu, ko katin Biki na waya da na Hannu Tahir ne zai yi komai Yana Abuja Tahir ya kirasa kan mganar inda za'a Daura aure saboda Buga kati, shi kuma ba shi da Say akan haka duk da suna mgana da Abba da Umma sosai Sisters dinsa ma suna yawan Kiransa, ita kanta Sultana ya na Kiranta ammh kuma sai ya tuna da Siya sai goma ya Kirata kafin ya Tuna da Sultana ya kirata. Ce ma Tahir ya yi ya bari in ya yi mgana da Abba zai kirasa ya fad'a masa. Sai dai ya yi ta kiran Abba bai Sameshi ba  har zuwa Dare sai ya Kira Umma ya yi mata zencen. Ita kuma ta warware masa Halin da ake ciki saboda kara Abba yace a shinkafi gidan Mallam Shitu Mahaifin Sultana za'a Daura aure. Ammh Innani ta Daka Tsalle tace Uban kuturu ya yi kad'an in kuma Sulaimanu ya Dage to ita dai ba da yawunta ba, ga shi Abba ya kira ya Furta Kowa ya sani ya rasa yadda zai yi da Innani. Sadiq na jin haka ransa ya baci da innani a satin Zariya ya so tafiya saboda ya cikama Siya kudin nan, ammh sai ya sauya Tsari washegari jumma'a Gusai ya tafi, yasan wacece Innani kan wannan mgamar sai ta yi Sanadiyar da Rayukan wasu bayin Allah za su baci. Ya kuma je ya isketa a na daru da ita ammh tace ba'a isa ba sai faman Zagin Mallam Shitu ta ke yi ta na kawo wasu labarai marasa Tushe ballatana makama, baiwar Allah Sultana sai kuka ta ke yi abun da zafi a rika zagin mahaifinka a kunnen ka. Su Umma sun gaji da mgana Daga karshe Innani ta had'a da su ta Zage daman kwanaki sai da ta yi kan kayan Dakin Sultana, wai shima sai an yi masa mgana ya kawo wani abu Tunda Ubanta ne shi, kuma an yi masa kokari an riketa na Shekaru sha ba tare da sisinsa ba. Kuma sanda Mallam Shitu ya zo a gabansa Innani ta rika mganganun har ta na yi masa gori, abun ba dadin ji, kuma Tsakani ga Allah ya kawo kudad'e ya bama Abba sai yaki karb'a yace ko Hauwa na da rai Sultana yarsa ce har gaban Abada, ammh Innani ta rika bala'i ta na masifa. An samu wanchan mganar ta wuce ga wannan kuma ta tsiro da shi. Sadiq Abba ya fara samu ya yi ma mganar bude bakin Abba sai yace"Magajij gida Innani uwa ce a wajena kuma akwai Rikicin Tsufa a tare da ita, gwara ku tayani lallabata mu Rabu lafiya." Sadiq na jin haka yasan Abba ya tsaya a matsayar Innani Tunda har ya na mganar zai samu Baba Sammani ya gayamasa yasan yadda zai yagama Mallam Shitu Saboda yana jin kunyarsa. Sadiq na jin haka yasan sai ya samu Innani ya fito mata ta bayan gida. Sai da ya bari dare ya yi ba kowa a shashen nata sai ita kad'ai yadda zai ji dadin yi mata abunda ya shirya. Kamar ko ya sani batare da ya tambayetaa ba ta fara rattaba masa Labarin abunda ya faru har ta na fad'in"Yo ni za'a kawo ma iskanci? Yarinya tun ta na jarriyarta Sulaimanu ya yi wahala da ita sai yau Rana Tsaka a wani ce gidansa za'a je daura aure in ya isa shegiya na ke, ai na ce in dai chan za'a je ni Dije ba da yawuna ba." Kallonta kawai ya ke yi cikin tattaro mganar bakinsa, Cikin kaushim murya yace"Daman gidan Ubanta nan ne a hakku a daura mata aure." Innani ta yi galala ta na kallonsa kafin tace"me ka ke nufi Magajin gida? Kai Tsaye yace"Abunda na ke nufi a shinkafi za'a daura auran nan a kuma gidan mahaifin Sultana." Innani ta ballamai Harara kafin tace"Au to daman turo ka suka yi ko? To wlh wannan karon ba wanda ya isa nan gidan Sulaimanu nan za'a Daura wannan auran naga Uban da ya isa ya ce Ba haka ba." Sadiq yace"Ba isa ba ne Innani, Sai dai ki sani matukar kika dage sai anan za'a Daura auran nan ni kuma wlh Tallahi kin ji na rantse miki da Allah zan fasa auran Sultana kuma da gaske na ke yi." Sai Innani ta yi shuru ta kasa mgana, shi kuma ya kura mata ido ya na kallonta ganin ta yi shuru yasa ya cigaba da fadin"Ke shikenan bakya yafiya? Ki rika afuwa Innani Domin ke kam baki san Tarin laifukan ki wajen Allah ba, da Allah baya yafiya ma da Tuni An dade da shafemu a wannan Duniyar, ya kamata ki Sassuta ma kanki wannan kiyayyar in ba haka ba zaki Mutu ana murna da Mutuwarki." Sai kawai Innani ta Fashe da kuka ta na Fadin"Ai shikenan na bar mganar ka gayama Sulaimanu na hakura aje a daura auran a shinkafi wlh na bar mganar har Abada." Jinjina kai Sadiq ya yi kafin ya ce"Dakyau naji dadin haka , Ni ina so in kin mutu Ranar Lahira ki Rabauta kakata, na baki wani kissar da zai taimaka miki wajen cire jin haushin wani a ranki? Bai bata Damar mgana ba ya Cigaba da fadin"A zamanin Annabi muhammad Sallahu alaihi wasallama, watarana ya na zaune acikin masallaci Tare da Sahabbai kawai sai Annabi yace ga dan Aljannah nan zai shigo, Sai Sahabbai suka yi shuru tare da kurama kofar masallaci ido su ga waye zai shigo. Sai ga wani bawan Allah ya shigo cikin masallaci kuma bayan Shi ba wanda ya kara shigowa, sai abun ya ba ma Sahabbai mamaki da jin abunda Annabi yace, na cewa shi d'in d'an Aljanmah ne, sai cikin Sahabban Annabi wani ya bishi gida yace ya ba shi masauki na kwanaki sai ya bashi da niyar ya rika ganin wani irin Ibada ya ke yi da Tun a Duniya Annabi yace shi dan Aljanna ce, sai yaga duk tsawon kwanakin da suka yi tare ko sallar Dare ba ya gani yana yi ban da kamsil salatu a ranar na uku ne wannan Sahabin ya sameshi ya gayamasa abunda Annabi ya gayama su game da shi, Dalilin da yasa ya zo wajensa saboda yaga wani irin Ibada ya ke da har tun a duniya Allah ya bashi Aljannah. Sai wannan bawan Allah ya yi Kabbara sau uku kafin yace" bai san har yakai haka ba, abu d'aya kawai ya sani Tunda ya ke bai taba kwana da wani a ransa ba duk abunda aka yi masa nan ta ke yake yafewa kwana yake zuciyarsa wasai ba kowa acikinta" Dan dakatawa Sadiq ya yi ya na kallon Innani da ta natsu ta na ji harda jan Doguwar kabbara."Allahu Akbar" lokaci daya ta na faman sharan kwallah. Sai Assadiq ya sauke ajiyar rai kafin yace"To kisance mai yawan yafiya Innani domin masu yawan afuwa Samakonsu na wajen Allah" Da Sauri Innani tace"Allahu Akbar Wlh na yafe ma kowa Allah Sarki. na yafe ma kowa ni yanzu shima Shitun na yafe masa duniya da Lahira Magajin gida ni yanzu zuciyata wasai." Sadiq yace"To ina fatan bazaki kara tada wata mgana ba.? Da Sauri tace"In sha Allahu Magajin gida kai dai Allah ya yi maka albarka kawai." Ya amsa da Ameen, Shikenan magana ta Mutu, sai dai su Abba sukaji sabon zencen Innani da kanta tace ko Bikin ma in chan za'a yi sai su kwasa su je gabadaya chan Abba yace nan dai za'ayi Sha'anin Daurin auran ne dai za'ayi achan. Duk da bai fito ya fad'a ba kowa yasan aikin Magajij gida shine kawai Maganganunsa ke sa ka Innani Ladabi da Nadaman Dole, kafin kwana Biyu ta koma gidan jiya. Ranar lahadi ya koma Abuja Da Safe ya tafi da cewa sai a satin biki zai dawo, sai da ya koma sannan ya Kira Tahir ya gayamasa ga inda za'a Daura auran Shima Tahir yace hakan ya yi daidai bisa adalci. Duk Abba yaki karban komai sai da Mallam shitu ya aiko masa da Buhuhunan shinkafa da gero da masara yace ya karb'a ba Saboda sultana ya ba shi ba domin Allah ya ba shi sannan ya karb'a bayan Sadiq ya saka baki. Ya so kwarai kudin da zai bama Siya su kai 300k ammh abu ya ci tura Tunda Big sis ta ishesa da kiran ya turo da kudin gyaran jikin Amarya da kudin kwalliya daman bata san yana da Niyar bada wa ba. Dubu 100k ya Turama Surayya, ita kuma ta cire 30k ta turama Surayya Dee marubuciya mai Saida saiwowin Gudiyo, da ya ke ita Surayyan ta santa tana tsiyan Littafanta har suka Saba sosai ta yi mata ragi sosai ta had'a mata ma su kyau da inganci duk da daman kayanta suna da kyau sosai. Daga Kano aka saka a mota sai Gusai Surayya ta karba sakon cikin murna nan da nan tabi Tsarin mgangunan suka Fara dura ma Sultana a cewar su sai sun gigita Kanin nasu yaji ya Ciji yatsan tsaikon da ya tsaya Tuntuni bai yi aure ba. +234 803 277 3332 Sun yi anko, wannan karon Less da Atamfa, da suka damesa da kiran ya Turo kudin ankon Sultana yace ba shi da kudi su a matsayinsu na yayyenta mata su siya mata mana. Shi kuma Duk Tattalinsa na Siya ne itama ya na so ta siya kaya masu yawa na alfarma a kallah ko da ba su kai na Sultana ba itama dai ta shaida Tunda bai yi mata lefe ba. A tsarin da ya tsara daman aa satin da Bikinsa ya rage sati daya da Sultana zai je zariya, satin Biki kuma ya je Gusai daman kuma ya Rubuta takardan hutun Sati daya na auransa in ya yi sati Biyu a gusau sai ya koma Abuja ya yi daya sannan yaje Zariya yaga Siya duk da yasan zai mata laifi ammh ba shi da mafita ne. ******* Shi baisan duk na san bikinsa da Sultana ya matso ba tunda muna mgana da Saliha tace min ta na nan tafe cikin Sati mai shiga in sha Allahu. Sanda yazo ya na fad'amin zai jima a Gusai  kafin yazo ban nuna masa na Damu ba. Sai dai na yi matukar mamakin da yace min kudin da ke acct dina 256k na Dauka na siya kayan sawa ya so ya yi min lefe na alfarma ammh kuma bashi da kudi ammh ko yanzu bai cire rai ba a gaba in ya samu zai siyamin duk abunda na ke so. Sai na fara hawaye shi ko ya Dauka na Kukan Farimciki ne nan kuwa a cikin zuciyata na wani irin kishi ne da Tunanin kudin fad'ar kishiya ya kawomin. Ina ganin Hoton Sultana a kwanakin nan Tunda Saliha na yawan sakata ta na Tagging da Amaryan Magajin gida, gwara ita yar gatace kowa na santa ni fa bani da kowa a baya sai Allah. Assadiq bani ya ke so ba jikina ya ke so Sultanace abar son sa kuma itace uwar ya'yansa. Ko kuma nace ita ya zab'a ta zama uwar ya'yansa bani ba. Na yi ta masa godiya ina sharan hawaye, shi kuma sai ya Rumgumeni ya na fadin"Shii ki daina kuka Siya in da ina da shi kasuwar duniya zan kai ki ki dauki duk abunda kike so domin na nuna miki kin chanchanta a wajena kuma matsayin ki ya zarce yadda ki ke Tunani ko hasashe." Kallonsa na ke idanuwana na tara kwallah kafin nace"Ka tabbata ka na so na Assadiq? Gyadamin kai ya yi kafin yace"Kina da Shakku me a kan son da na ke yi miki SiyaAssadiq? Sai na kasa mgana sai kuka, kawai sai na Rumgumesa ina fadin"Ban damu ka so ni ba Assadiq, ammh ina rokon ka ka ji tausayina watarana ka Tsaya a baya na, ka zame min bango abunda zan jingina in ji sanyi a raina." Cikin wata irin murya yace"in sha Allahu bazan taba barin ki ba, ki saka a ranki ko da kowa zai gujeki ni Assadiq ina tare da ke har Abadan." Ko da karya ya ke fad'amin sai naji zuciyata na yaudarana da cewa Assadiq na sona ba shi da zabi ne. Ni da kaina na had'e bakin mu waje d'aya ina Sumbatarsa. Sannan ni da kaina na gayyacesa kan gadon mu muka gudanar da sunna, sannan ni da kaina na ja ragamar duk abubuwan da suka faru. Ya yi ta sakamin albarka kamar zai lasheni, kafim ya tafi sai da ya siyamin kayan abinci sannan ya yi min Cefane. Mganar kaya kuma na shawarcesa da cewa ko na siya wajen Maman Suhailat ne? sai yace kudina ne na yi duk abunda ya kamata. Jin haka yasa bayan tafiyarsa na Kira Adda Fati na gayamata ita da Ramatu har Amma sai da na kira. Ita Adda Rukayya tace ne akwai kawarta mai saida kaya zata yi mata mgana, ammh sai Amma tace tunda makociyata na saidawa ba'a haka na yi mata cinikin yafi na kai wajen Tunda an zaune lafiya. Nima sai na aminta da Shawaran Amma shima da na kirasa na gayamasa abunda Amma tace sai ya yi mirmishi yace"Madallah da Amma Madallah da Uwar da ta haifi Hasiya matar Abubakar Sadiq." Sai ya bani dariya a kalamansa na san shima ya aminta da na siya Hannun Maman Suhailat. Haka ko a kayi wajenta na siya, da ya ke ta na kaya ta fito min da su na zaba da takalma, mayafai hijabai, da Tamfiofi da lesuna  sannan sauran kudin kuma na Rage muka shiga kasuwa da Ramatu na siya akwatina Guda Biyu sai Inears, sai Dankunneye jaka Biyu na siya wajen maman sulahait nafi siyan kaya tunda sune na ke da karancin su a hakan ma na godema Allah, tunda Assadiq ya siya min wasu a baya. Wannan zirga zirgan yasa na manta da Kudurina na zauna na yi Tunanin ya na da kyau na aikata abunda zuciyata ke Umurtana kuwa?. Sai naga kamar in nayi hakan ban kyauta ba, gwara na Tsaya a iya matsayina kada naje garin neman gira na rasa idanuwana. Saboda haka yasa na daina Duba Status din Saliha Tunda har kirana ta yi tace min ta zo garin, ta na kara min Tuni tunda nace mata zan zo mata Biki. Ranar Al'hamis ma ta kara kirana sai kawai nace mata ba na jin dadin jikina zai yi wahala nazo, duk sai bata ji dadi ba ta ce har ta fad'ama sauran Sister's dinta zan zo mata biki. Kenan har ta ba su labari? Abunda ban sani ba tuni har sun san ta na zumunci da yar'uwan mijin Salima. Har ita Saliman ta gayamata ta yi ta mata kwatancena sai tace bata gane ni ba. Har Safiyar Jumma'a ban bari zuciyata ta Rinjaye ne ba, sai da rana da na yi kiran Assadiq bai Dauka ba, Tuni kishi ya Rufemin ido zuciyata ta bani ya na chan tare da Amaryar so wacce ya ke so. Kawai sai na kwanta ina ta kuka ni kadai bani da mai lallashina sannan na Bude wayata naga Hotunansu Saliha sun ci gayu daga inaga Abu suka yi ga shi nan duk sun saka kaya iri daya. Amaryan ta sha kyau har tagaji da kyau kamar ita ta yi kanta. A raina nace Dole Assadiq ya so Yarinyar nan saboda kyakyawace ajin Farko gata yar yarinya karama. ***** Ranar Daurin aure. A garin shinkafi aka Daura auran Abubakar Sadiq da Sultana, Abba ya  ba da auran Sultana Mallam Shitu kuma ya karb'an ma Sadiq. Daurin auren da ya samu mahallata ma su yawan gaskiya Tahir duk sai da ya gayyato abokan karatunsu na Zariya har da su Jb da Mb da suka zauna Daki daya Cikin makaranta. Wasu ma Sadiq ya manta da su Ammh Tahir bai manta da su ba. Abokan kasuwancin Abba duk sun hallata mazajen su Surayya Harda Alhaji Jibril da ya zama na Hannun Daman Abba shi da Mijin Salima Mubarak. Sannan yan'uwan Mallan Shitu da abokan arzuka duk sun hallata har da wasu daga cikin cllasmate din su Sultana da Siyama. Hatta da Dangin Umma da Mama sun Hallaci wannan Daurin auran. Bayan an gama daurin auran daman daga Gusai sun taho da abinci wad'anda za su koma Gusai suka Tsaya suka yi sallah suka ci abinci a nan gidan mallam Shitu. Wadanda zasu koma daga nan aka Raba musu Takaway mai tsire da Lemuka. Sadiq ba shi da wasu abokai Daga Tahir sai Jb sai Mb sauran duk sun tafi, Jb ma daganan ya wuce kano Mb ne kawai sai Tahir, Tahir ma yayyensa duk sun zo ammh daga shinkafi suka wuce Daura Hajja da matan su kasim suna Gusai ana cin Biki da su. Saboda matsalan hanya  Karfe uku suka baro shinkafi zuwa Gusai Abba da Mutanensa sun riga su yin gaba su Surayya suna ta kiran Assadiq yazo ga mai Hoto ya zo shi fa ake jira. Ango na ta fama da Babban Rigar Shadda mai ruwan kasa, takalmimsa baki da hularsa dara kalan aikin jikinsa agogon hannunsa ma baki ne, Cikin kayan da Abba ya Dinkamasa ne Tahir ma  Babba rigane a jikinsa kamar shine angon. Duk da a saman Fuskarsa ya na Fara'a ammh daga kasan ransa damuwa ne damkam aciki sai ya ke ji kamar ya ci Amanar Siya me yasa bai fad'a mata gaskiya ba Tun farko? Shi dai ya ke kawai ya ke yi, ammh kuma ya rasa sukunsa kaddara ta riga fata daman chan Allah ya Rubuta masa Hasiya da Sultana su ne matansa anan duniya. Ba shi da wani Tsumi ballatana Dabara hakan wani kadararren Lamari ne daga cikin littafin kaddaransu Wato Launil Mahafuz. Sun iso Gusai biyar da wani abu na yamma, daman a Hotel ya sauke su Tahir tunda suna garin tun jiya, ya so su koma ta chan ammh kuma Tahir yace su Surayya sun matsa. Sai suka wuce gidan suna zuwa gidan cike da Mutane duk suna Haraban gidan ana ta Daukan Hotuna. Amarya ta saka wani irin leshi mai kyau da yarari kalan Deep Blue, an yi mata kwalliya sannan ta yane kanta da Neat mai sharara takalmin kafarta ya na da tsini Rigar jikinta Fitted gown ne ta kamata sosai daga kasa ta na sharan kasa. Wuyanta da Hannayenta Gold ne, ta sha jan lalle da ya kara fito da kayanta, su kuma su Surayya suma leshin a jikinsu, ammh na su fari ne da gold ajiki,suma sun yi kyau kuma sun sha kwalliya har ta su Umma ma Less din ne sai da su kalan nasu  Dabam. Innani ma less din ta saka ta ci Uban Dauri kamar wata Bayarbiya. Suna shigowa tunda suka hangosa suka Dauki Ihu suna fadin"Ango ya sha kamshi." Suka jasa zuwa inda Sultana ta ke daman suna ta faman daukan Hotuna ne, Umma ta koma ciki wajen mutane Mama ce a ke Dauka da ita, itama kiranta aka yi, Sai Innani ce da duk Hoton da za'a yi sai ta shiga mai Hoto na Dauka wasu na Dauka ta waya. Daga gani wannan sha'anin babban sha'ani ne da ke ji da shi acikin gidan. Tun da naji ana ihun kiran Ango ya sha kamshi na sauko daga kan Barandar Mama da ni ke Tsaye Tun dazu bayan Saliha ta matsamin na fito za'a yi Hoto. Lokacin da gidan suka samu Labarin an Daura aure sai suka cika gidan da Gud'an Farinciki ni kuma alokacin sai naji kamar kafafuwana sun kasa Daukata saboda yanayin da na ke ciki, sai naji kamar zan fara Nadaman zuwa na tun yanzu. Na fito ne na kara tabbatar ma da kaina Shin Assadiq ne nawa ko wane ne wanda ban sani ba!? Sai dai Lokacin da na Fara takawa  inda suka cika ana Ta hotuna. Ina sanye cikin Sabon leshina dinki Riga da zani mai Ruwan madara ne sai mayafina Gold dake saman kafadata. Saliha taso a yi min kwalliya nace mata bana bukata ammh su dukkansu sun yi kwalliyarsu. Sai da naji kamar an fizge zuciyata daga zuciyata a lokacin da na yi Tozali da Assadiq gefen Sultana ya rike mata kugunta ana ta Daukan su Hoto. Kura musu ido na yi, ina kara neman Tabbaci kada ya zamto idanuwana ne suka faramin gizo ko ba na gani Daidai ne. Sai dai har wajen mintina goma abu d'aya na ke gani sai na kara samun Tabbacin tabbas ASSADIQ ne MIJINA  Kuma sannan MIJIN SULTANA.! Idanuwana sun fara tara Ruwa jiri na ke gani, kaina naji ya fara saramin sai naji duniyar ta fara juyamin. Kawai sai na juya na fara tafiya kaina na kasa sai naji naci karo da mutum da Sauri na Dago cikin sanyin murya ina fadin"Sannu ban kula ba n.." Sai maganata ta makale lokacin da na ci karo da Tahir. Tabbas nasan shi Tahir ne abokin Assadiq da na fara sanin su tare duk da yanzu ya ijiye gemu na ganesa. Waya ya ke yi kuma kamar ya na cikin gaggawa ne da yasa bai Tsaya ba kawai yace min"Bakomai." Ya wuce sai na bi shi da kallo cikin mamaki. Kila bai gane ni ba kamar yadda na ganesa, Gidan naji kamar ya fara juyamin sai na kama hanya zan fita ina sharan hawaye. Sai sai ji na yi Saliha ta rikoni ta na Fadin"ina zaki? Taho mu yi Hoto tare." Sai da nayi Dubaran goge kwallata ina yi mata ya ke, ina shirin nace mata bazan shiga Hoton ba sai da ta jani, sai dai muna zuwa wajen itama Yan'uwanta suka jata za su yi family Picture gabadayansu mata Amarya da Anko na Tsakiya. Kamar an Dasani sai gani Tsaye ina kallon Assadiq ba na ko kiftawa kamar kuma ance ya kalli barayin da na  ke sai muka had'a ido da shi. Bansan ko wani irin Hali ya shiga ba ammh ya samu Daukewar Numfashi da Tsayawar gudun jini na wani Lokaci. Ni kuma da na Tabbatar da ya gani sai na sakar masa mirmishi, mirmishin da ya fito da zubar kwalla daga Idanuwana. Ba wanda ya Lura da inda Sadiq ya Kurama Ido sai Tahir. Cikin mamaki ya kallo in da ya ke kallo sai kawai ya gani. Da farko bai gane ni ba, Hasken Fatata  ya fara Tona ni a wajensa. Cikin mamaki ya kara ware idanuwansa kafin yace"HASIYA.? A fili cikin mamakin ganina. Ya juya ya na kallon Sadiq sannan ya juya shima ya na kallona. Da Sauri Tahir ya karisa wajen Assadiq ya jawo hannunsa ya na fadin"Ku ban aron ango na minti biyar." Su Sajida suka fara masa caa ya na yake yace mgana za su yi yanzu zai Dawo. Kamar rakumi da akala haka Tahir yaja Sadiq gefe da yaji kamar Duniya ta Tsaya masa cak. Cikin Fitan hayyaci Tahir yace"Sadiq ka ga abunda nake gani kuwa? Sadiq na kallona yace"Me ka gani Tahir? Tahir yace"Hasiya mana zabiyar matar da ka saka ita nagani mana, ga ta chan ko ba ita ba ce? Ya fad'a ya na nuna masa ni da ni ke tsaye ina kallonsu. Cikin sanyin jiki da na zuciya Sadiq yace"In dai kai ma kana ganin ta to da gaske itace. SIYA ce." Tahir ya Dafe kansa kafin yace"Innalillahi akwai matsala, akwai matsalan" Kaawai sai ya Juya da Sauri Sadiq ya Rike masa Hannu Lokaci daya ya na fadin"Ina zaka? Me zaka yi? Ya fad'a cikin Rawan murya. Da Sauri Tahir yace"Zan je na sallameta ne zan gayamata ta tafi don Allah nan ba Muhallin zuwanta ba ne" Da Sauri Sadiq ya kara Rike masa Hannu Cikin Muryansa da Firgici ya fara Disasar da ita yace" Muhallin zuwanta ne Tahir Tunda Gidan Iyayen MIJINTA NE." Tahir ya kallesa da Sauri Cikin Bude ido da baki, jinjina masa kai Sadiq ya yi ya na jin mutuwar jiki da na zuciya yace "HAR YANZU HASIYA MATATA CE TAHIR." Bakin Tahir sai ya fara barin Makauniya ya yi sama ya yi kasa lebensa na sama da kasa har Numfashinsa yaji ya Sarke ya na bin Sadiq da kallon ko ya fara Hauka ne. Sakin Hannun Sadiq ya yi sanda yaga na Juya ina sharan kwallah da zafinsa ya biyo ni har Babbar Rigarsa na Hard'esa. Baki a hamgame ya na Rufewa ya na Budewa haka Tahir yabi Sadiq da kallo ya kasa Motsi. Sahida ce ta hangosa suna chan suna Hotuna a zatonta ya gaji ne zai gudu da Gudu taje ta Rikosa ta na fadin"Big sis zai gudu fa." Kafin ka me? suka Yayyamesa suna masa Ihun yau Ranarsa ce sai ya gaji da Hoto. Ya na leken Hasiya sai yaga kuma ya nemeta ya rasa so ya ke ya yi mgana ya kasa haka suka jasa suka maida shi kusa da Sultana. Dage ya ke yi da kansa Ya na son hango ta ina Siya ta bi? Ya na da Tabbacin ita ya gani ba Aljannah ba. Surayya ce ta zo kusa da shi ta na gyara masa kai tace"kai daina mana Salon Daukan Hoton yan zariya." Dariya suka saka masa gabadaya shi ko gabadaya Hankalinsa baya jikinsa. Yaga wajen Siya da Tarin Tambayoyinsa. Ta ya ya aka yi ta san nan gidan? Waye ya kawota? Me ta sani a game da shi? Tahir kuma ya na nan Tsaye a wajen da Sadiq ya barsa kamar an dasa shi Kwakwalwarsa na faman maimaita masa kalaman Sadiq. "HASIYA MATATA CE HAR YANZU." KO dai Sadiq ya zare ne? Baya cikin Hayyacinsa ne zai kira matar da ya saka da matarsa? Sai wata zuciya tace to in bai saketa ba fa? Sai da yaji wani irin Gif a saman kansa in dai ko Hakane Sadiq ya cika Babban Mahaukaci. Ni ko ina nan acikin Haraban gidan banfita ba, bayan wata mota na samu na Labe ina Danne bakina. Kada a jiyo kuka na , kasa na Durkushe kafin na saki bakina na fashe da wani irin kuka, kukan rashin madafa da ganin abunda baka taba zato ko tsammani ba. Duk da tarin Hujjoji sun Tabbatar min da gaskiyan waye Assadiq ganin da na yi da Idanuwana ya fi komai Tarwatsa Rayuwata. Nan ne gidan su Assadiq. Matar da na gani a kaduna itace Mahaifiyarsa. Mutumin data gani yau da Safe Abba shine mahaifinsa gidan nan kuma cike ya ke da Ahalinsa da yar'uwansa. Ni miye matsayina? Assadiq da abokinsa sun gani gwara Bakina alaikun na sulale na bar gidan nan tun kafin abunda ke Boye ya bayyana wanda bayyanarsa bazai yi ma kowa dadi ba, kuma rashin jin Dadin sai ya fi muni a kaina. Da Sauri na mike ina waige waige da Mayafi naa na saka na Rufe fuskata na bi cikin jama'a na isa bangaran Mama In da Saliha ta saukeni a Daran jiya da na iso. Dakin da muka kwana jiya na shiga duk suna haraban gidan ba kowa a bangaran Mama har na Dauko karamin akwatina na fito Kaina cikin mayafina ina rike da karamar jakana ina kuka da Hawaye shabe shabe na fice Daga gidan su Assadiq. Ashe Tahir ya ga fita ta, suna tare da Mb da yazo ya same shi cikin wannan Halin Dimuwan. Ce masa ya yi ya na zuwa da Sauri yabi bayana domin so ya ke kara jin Tabbacin abunda Sadiq ya gayamasa Daga bakina. *K'arshen littafi na biyu, Zamu cigaba da littafi na biyu bayan mun je Hutun kwana Biyu* Nagode madallah da Masoyan Janafty. *Janafty*