[7/11, 3:57 PM] +234 706 160 2791: GIRMA YA FADI 1 KAUYEN GWARZO, 1988 Sunan da na taso da shi tun ina karama shine Zaynab Aliyu Gwarzo. Asalin mahaifina mutumin garin GWARZO ne da ke cikin jihar Kano da ake kira Malam Ali Mai Almajirai. Malam Ali, sananne ne a ciki da wajen kauyen Gwarzo da ya shahara wajen ba da maganin cututtukan da suka shafi aljanu daga Alkur’ani mai tsarki. Bayan magani da yake bayarwa yana karantar da dubban almajirai, kuma fitaccen manomi ne, makiyayi. Ya mallaki manya-manyan gonaki guda biyar, tirken dabbobi zuwa tsintsayen gida irin su kajin gidan gona, agwagi, talo-talo, jimina, gada, zabbi, akuyoyi da sauransu. Haka nan Malam Ali mutum ne mai cikar mutunci da tsananin kyauta, duk wanda ya kwana ya tashi a garin Gwarzo ya san da hakan. A garin Gwarzo baki dayanta Malam Ali fitacce ne da ake matukar girmamawa gami da ganin kima da mutuncinsa. Daga inda duk ka ce kana neman gidan Malam Ali, za a ce da kai “Mai Almajirai?” Daga ko’ina a cikin garin Gwarzo za a rakoka har dakalin gidan Malam Ali Mai Almajirai. Matan Malam Ali na aure uku ne, amma cikinsu babu wadda Allah ya baiwa haihuwa sai uwargida Inna Dubu da ta haifi Umar-Faruk shi kadai ya tsaya. Sai da ta yi haihuwa tara duk mutuwa suke tun suna jarirai wato (wabi). Daga Inna Dubu sai Inna Rakiya, sannan Innata, Rabi. Rabi matar Malam ta karshe Buzuwa ce fara sol, ita ce mahaifiyata kuma a hannunta na taso. Asalin auren Innata da Malam ya samo asali ne daga kawo ta neman magani, kasancewar Malam mutum mai ta’ammali da mutane daban-daban daga ko’ina cikin kasar Hausa da kewayen ta, manyan ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa da ‘yan boko da manyan ma’aikatan gwamnati kan zo neman taimako wajen sa a kan harkokin su, kuma suna ganin nasibi na hakika cikin taimakon sa, daga garuruwa daban-daban ana kawo marasa lafiya wadanda ya ware musu sashe guda a gidansa. Ya kan bada lakani na kasuwa, cututtukan da suka dami bil’adama, musamman wanda ya shafi aljanu zuwa cututtukan yau da kullum. Hakan ne yasa kullum za ka ga kofar gidanmu cike da motocin zamani wannan ya shiga wancan ya fita. To hakan ce ta hada shi da Alhaji Sani Buzu, shahararren dan kasuwar fata kuma dan siyasa daga garin Yamai ta kasar Niger. Ya zo Kano ne musmaman domin nemawa ‘yarshi maganin tabin aljanu da ta samu, tare da kanwarta Nuratu. A cikin Kano ne ya samu labarin Malam Ali ta hanyar wani abokinsa dan kasuwar Niger zuwa Kano, wanda shima ya sha zuwa amsar taimako hannun Malam Ali. Alhaji Sani bai san kowa a Kano ba, karewa ma ko zuwa bai taba yi ba sai a kan lalurar Rabi. Akwai kauna sosai tsakanin shi da ‘ya’yanshi biyu Rabi da Nuratu, wadanda mahaifiyarsu ta mutu ta bar mishi, tun rasuwar ta bai kara aure ba. Ya kawo su Rabi Kano da zummar neman magani ne kawai. Malam Ali, ba wai warkar da mahaukata yake ba, illa in lalurar kankanuwa ce ta kuma shafi aljanu bata gagararshi, ya kan raba mutum da su cikin ‘yan satittika daga ayoyin Alkur’ani mai tsarki. Ya kawo Rabi da kanwarta Nuratu gidan Malam Ali tsayin sati biyu ana yi mata magani, anyi sa’a lalurar tata karama ce, cikin lokaci kankani Malam Ali ya raba ta da su. Don farin ciki Alhaji Sani ya ce ya fadi komai yake so in dai bai fi karfin sa ba shi ko ya yi mishi. Budar bakin Malam Ali sai cewa ya yi, ai ko baka bani komai ba ka bani auren Rabi Mana? Ya fiye mini duk abin da za ka bani, bana karbar ladar aiki sai sadaka a inda ake da bukatar ta. Jikin Alhaji Sani ya yi sanyi, don bai taba kawo ma ranshi bukatar da Malam Ali zai nema kenan ba, da ko kusa bai fara wannan subutar bakin ba. Hankalinsa ya tashi matuka, yaran da basu ma taba zuwa Kano ba, ko kalmar “zo” da Hausa basu sani ba, gashi daya ba ta iya rayuwa sai da ‘yar’uwarta, akwai kauna da shakuwa ta hakika tsakanin Rabi da Nuratu. A can Yamai suna tare ne da mahaifiyarshi, yana sa ran yin aure cikin wannan shekarar kamin ayi zaben da yake nema a Jihar su (Damagaram). Ya yaba da rayuwar Malam Ali da iyalinshi, ko kadan bai raina musu ba, suna cikin suttura da cima mai kyau da rufin asiri, amma ita Rabin yake ji ko za ta amince, da yadda zai tafi da Nuratu babu Rabi. Abin mamaki da aka tuntubi Rabin farat daya sai ta amince, wannan ba karamin abin mamaki bane, domin a haife Malam Ali ya haifi ukun Rabi. Ita ko Nuratu ta ce kafarta kafar Yayarta wato ba za ta bi Baban ba. Shima Malam Ali ya yi alkawarin rike Nuratu tamkar Faruk har auren ta. Alhaji Sani bai tafi ba sai da ya yankawa Malam Ali sadakin Rabi ya biya. Allahu Akbar! Ashe karshen rayuwar sa kenan, sallamar shi kenan ta har abada da ‘ya’yansa Rabi da Nuratu. A kan hanyar shi ta komawa gida Niger, cike da zullumin bayanin da zai yiwa mahaifiyarshi da ‘yan’uwansa a kan auren da ya yiwa Rabi babu saninsu babu yardarsu, cikin jinsin da ko a tunani basu taba yin na tsintar kansu a ciki ba, a kasar da basu ko sani ba, jirginsu ya fadi a wani tsauni kafin a kai Niamey, babu maganar mai rai a ciki. Ni dai na taso bani da labarin NURATU. Gidanmu cike yake da ‘ya’yan riko, domin kowacce cikin matan Malam tana rikon ‘ya’yan ‘yan’uwa, don haka gidan Malam Ali da albarkarsa ba za ka ce ba a haihuwa ba. Na tashi tashin gata kuma tashin sangarta, kasancewata auta, wadda ba ta zo ba sai bayan haihuwar Faruk da a kalla shekara goma sha biyu, bayan ni kuma ba a samu wata ba. Don haka suke kira na “Kyauta” wato Kyautar Allah. Inna ta Rabi kadai ke ce dani “Abu” shi ko Malam “Zaynabu-Abu” ne baya ragewa. Bayan Inna Dubu Innar Faruk Inna Rakiya ba ta haihu da Malam ba, ‘ya’yan kanwarta ne take riko. Rayuwarsu cikin mutuntaka da sanin ciwo kai ce, domin kowacce cikin su ta mallaki hankalin kanta, babu rashin jituwa ko kadan a tsakaninsu. Dukkan su sun hada ‘ya’yan ‘yan’uwa da almajiran Malam sun rungume a matsayin ‘ya’yansu, sai dai a kan ce wane dan dakin wance ne, wance ‘yar dakin wance ce. Akwai Yaya Halima da Inna Dubu ta rike shekarun baya ne aka yi auren ta, Lami da Laure da Inna Rakiya ta rike suma duk Malam ya aurar dasu sun haihu a gidan mazajensu. Ina da shekaru goma Ya Faruk ya kammala sakandire, inda duk za shi ka ganshi rike da hannuna, ko me ya ci a waje sai ya rago mini, idan makaranta ya je ya dawo sai ya kawo min tsarabar rake, gurji, gyada da makani. Ina son Yayana Faruk, domin halayen sa dake burge kowa. Da fari dai Faruk shiru-shiru ne, miskili na kin karawa, da wuya ka ga yana hira in ba dani ba ko Rabi, haka da wuya ka ga ya daga ido ya dubi mai shigowa sai dai ya amsa masa sallama ba tare da ya dago ba. Akwai aminci da mutunta juna na hakika tsakanin Ya Faruk da Rabi, ta yadda duk wata damuwar Faruk Rabi ta sani, komi nashi da ita yake shawara, haka duk wata ajiyar shi mai muhimmanci a dakinmu take, kai ba za ka ce kishiyar Mamansa ce ba. Halin dattaku irin na Ya Faruk daban yake da na kowa cikin gidan, yaro ne a zahiri, amma halinshi na manya ne, tun ina yarinya a ban san komi ba, na san Faruk kyakkyawa ne, dana kan karkace kai in bata lokaci ina ta kallon sa, shi din bai sani ba. Idan ya juyo muka hada ido sai ya ce, “Kyauta yaya ne kike kallo na?” Mai hazaka da mai da kai, kuma mai nasara a kan duk abin da yasa gaba. Faruk tun yana shekaru goma ya haddace Alkur’ani, haka har girmansa da shigar sa babbar makaranta bai daina zama yana daukar karatun buzu ba wajen Malam. Faruk ne mai taje min dogon gashina tun ina shekaru uku, ya kallabe shi kalba biyu, hagu da dama, shi yake zabar min kayan da zan sanya, ya kuma goya ni a bayan keken sa ya kai ni makaranta, in an tashi ya je ya dauko ni dai-dai da rana daya bai taba gazawa ba. In Innata na mun wanka, sai ya girka kujera ya zauna yana azalzalarta ta daina cudawa da karfi, fatar Abu bata da kwari, ba kya gani ja ce ne? Inna sai ta tsage jini ya fito? Rannan ya ce, “Inna Rabi daga yau kada ki sake yiwa Abu wanka ni zan dinga yi mata, don na lura wallahi da gayya kike cudawa da karfi, ba kya tausayin fatar Abuna”. Rabi ta yi dariya ta kira Malam ta ce ya raba wannan rigima ta Faruk. Malam ya ce, “Faruku namiji baya yiwa mace wanka ka yi hakuri. Daga yau babu mai kuma yiwa Zainabu-Abu wanka da soso”. Tun tasowata na san Innana Rabi na fama da wani bakin ciki na shekara da shekaru, wanda in har ya ciwo ta, takan shiga daki ta yi ta kuka. A irin wadannan lokutan, Faruk kadai ke iya tausarta da kwantar mata da hankali. Na kan gansu suna ta kus-kus, na ita damuwar da ke damun Inna Rabi, wadda yawan shekaru da yanayin rayuwa bai taimaka ba ko kankani wajen gusar mata da wannan damuwar ba. Ta kan ce da ni, “Kyauta rayuwa abin tsoro ce, haka zuciyar mutum sau tari makiyarshi ce. Ta kan umarce shi ga abin da ta san ba dai-dai bane kuma Allah ya yi hani da shi. Ki guje ma sharrin zuciya, kuma ki tsarkake zuciyar ki, daga sabon Allah komai kankantarsa. Ki nisanci ZINA, ki kiyaye al’aurarki, mutum da kike gani abin tsoro ne, musamman wanda kika taimakawa, dama kuma Annabi (S.A.W) ya ce, “Ka ji tsoron sharrin wanda ka kyautatamawa”. A wadannan shekarun, bana damuwa da irin wadannan kalaman nata, kamar yadda bana fahimtar komai a cikinsu, domin hankalin bai isheni ba. Abinda na sani ko kuma na fahimta kawai shine, Inna Rabi rayuwarta daban ce da ta sauran matan Malam, komi baya faranta mata. Haka mafificiyar kaunar da Malam ke gwada mata, bata burgeta. Tana da wani mummunan kullaci a kan mutane da al’amarinsu, haka gaba dayan rayuwarta cikin kunci take. Sau daya na taba ganin ta tayi dariya a tun tasowa ta, wato ranar da Faruk ya ce ba ta tausayin fatata. Kokarin Malam da Faruk a kullum shine farin cikin Rabi da farin cikina, amma hakan baya hanata zubar da hawaye a yawancin lokuta. Duk wata kulawa ta uwa da uba kusan in ce na same ta ne daga Ya Faruk, yana sona, yana kulawa dani tamkar ‘yar da ya tsugunna ya haifa. Haka nan komi nawa mai muhimmanci ne a awurin Faruk, shirme ne ko akasi. Ire-iren mutanen birni da ‘yan boko da kan zo wurin Malam, ba zan iya iyakance alhairan da nake samu daga garesu ba, kullum cikin sabbin kaya, kayan wasa, sabbin dinkuna, kayan zaki da kayan kwalam nake saboda farin jinin da Allah ya yi min. Wasu kuwa kan ce kyawuna ne yake sayo min farin jinin, kowa ya ganni sai ya tanka, ya kuma tambayi Malam game dani, don ko a farcen kafa bamu yi kama ba (komi nawa irin na mahaifiyata ne) tamkar ta yi kaki ta tofar. Amsar da Malam ke bayarwa a kullum shine, nayo Innata ne, wadda take Ba’abziniyar Niger. Ni kaina na san ni da Inna ta daban ne a cikin gidan, haka muke wal! Sai ka ce tocilan don haske a cikin jama’ar gidan, ko kuma ka ce wata ne a cikin taurari. Sai dai abin da yake matukar burge ni da rayuwar gidanmu shine, ba za ka taba ganin an nuna wariyar launin fata ba, da ni da su Indo da Hafsisi da su Dubu ke riko, duka su Inna Dubu sun dauke mu daya ne babu banbanci. Sai dai Malam da Ya Faruk a kullum, a komi kuma a ko’ina, su kan nuna nice ‘yar gaban goshinsu. Halin Innata da irin rayuwar ta kam ya riga ya zame min jiki, har baya damuna, ba ni kadai ba haka duk kishiyoyin ta babu mai nuna damuwa da yanayin rayuwar ta, don in da sabo sun saba. Sai ta wuni ba ta yi magana ba sai bin kowa da ido, haka kullum daren Allah cikin yi min nasihohi da tsoratarwa a kan ZINA take. Ni a lokacin ma ban san mene ne zinar ba, ban gama tantance ma’anar kalmar zinar ba. Abin da na fahimta kawai shine; zina wani abu ne da Innata ke matukar kyamata, kuma wani abu da Allah ya yi kakkausan hani da shi. Na alkawarta ma raina zan guje shi, kamar yadda take gargadina a kullum, zan nisanceshi, kamar yadda Allah ya yi hani da shi. Akwai sanda ta ce min, “Kyauta da ki yi zina, gara mun mutuwarki da rayuwarki”. Da hankali ya fara zuwa min sai na samu kaina a mai tambayar kaina, shin mene ne shi wannan zina, da Inna ke damuna da zancensa? Me ke damun Innana ne? Meye dalilinta na yi min hasiha kadai a kan zina? Shin zina shine kadai abin da Allah baya so? Tambayoyi ne da ke min yawo a kwanya, tun ina mitsitsiyata, suke neman tarwatsa min kwakwalwa tare da wargaza min tunani. Don haka ban san sanda na samu Ya Faruk a dakinsa ba dake a zaure, a wani maraice, hannuwana dafe da kaina dake neman tsagewa gida biyu saboda ciwon barin kai guda (migraine) da nake yawan fama da shi, sakamakon tarin tambayoyi da damuwoyin da na kimsawa raina, suke addabar kwakwalwata, suka kuma fi karfin shekaruna. Na damu kwarai da wannan al’amari da Innana ke damuna da shi. Na zauna a masangalin kujera kwaya daya tak dake dakin, na yi tagumi da hannuwa bibbiyu na rasa abin da ke min dadi. Ya Faruk ya aje jaridar da yake karantawa ya juyo ya zuba min ido sosai cikin nazari, “Kyauta meke damun ki? Na lura a ‘yan kwanakin nan ba kya cikin walwala, kina ta ramewa kamar kudin guzuri, akwai damuwa kwarai cikin kwayar idanunki, ki gaya min mana. Idan baki gaya min damuwar ki ba wa za ki gayamawa?” Na saki sassanyan numfashi na ce, “Ya Faruk idan na tambaye ka za ka gaya min gaskiya tsakanin ka da Allah?” Cikin mamaki ya ce, “Abu, na taba gaya miki abin da daga baya kika bincika kika taras ba haka bane?” Na girgiza kai da karfi, “Baka taba ba Ya Faruk, don haka na san yau din ma gaskiyar ce dai za ka gaya mini. Wani al’amari ne da ya shige mini duhu yake sa ni cikin tunani da neman sani”. Na yi shiru cikin duban yanayinsa da ya zubo kyawawan idanunsa masu sheki yana kallo na. Na sarda kai cikin kunya da matsanancin jin nauyin abin da zan fada, domin duk da ban san ma’anarsa ba, na san ba abu ne mai kyau ba, ba kuma abu ne da ake son a dinga fada ba. Bai nuna kosawa ba har sai da na bara don kaina, na ce, “Shin mene ne ZINA da a kullum Inna Rabi ke gargadi na a kanta?” Na tabbata bai zaci tambayar da zan yi mai ba kenan, mamaki karara ya bayyana a fuskarsa. Ya ce, “Ita Innar ce take miki fada a kan hakan? Ba ta san ke yarinya ce ba? Gaya min gaskiya dai ina kika san wannan kalmar?” Na ce, “Wallahi Allah Inna ce take fada”. Na sake dukar da kai na warware masa wa’azin Rabi gareni a kowanne dare. Na kare da cewa, “Na rasa gane me take nufi, na rasa gane illar shi wannan abu. A da abun baya damuna, amma yanzu ya dame ni. Ba ta bari na in yi barci kullum “Abu, kada ki yi zina”. Shin ZINA shine kadai alkaba’in da Allah ya yi hani da shi?” Ya Faruk ya sunkuyar da kai yana kallon yatsar kafarsa, cikin dabara ya dauke siraran hawayen da suka cika mishi ido. Ya dade bai dago ba, cikin nannauyan tunani. Ya dago bayan wasu mintuna, ni kuwa na tsattsare shi da ido, ya yi murmushi irin mai kwantar da hankali, kamin ya soma yi min magana cikin tattausar murya. “Zina ba shine kadai aikin haramun da Allah baya so ba, sai dai yana cikin su. Kin ga babban haramun shine “shirka”, amma Inna Rabi na miki gargadi a kan zina ne kasancewar ki ‘ya mace, babu wuya an yaudare ku a wannan fannin, kasancewar zuciyar ku (delicate) wato rarrauna ce. Ta san ba za ki yi shirka ba, kasancewar ki rainon musulmi, kin kuma tashi cikin musulunci. Amma za ki iya yin zina, wadda take zigar shaidan ce da rudin zuciya, mai kuma jefa ‘ya’yan da aka haifa ta hanyarta cikin wata irin wahalalliyar rayuwa da bakin ciki tabbatacce. Abin da ake nufi da zina shine, yin rayuwa irin ta ma’aurata alhalin babu aure tsakanin ki da shi wannan namijin. Zina babu wuya an aikatata, amma jin dadin dake cikinta na dan lokaci ne, bakin cikin dake cikinta da abin da take haifarwa har abada ba zai gushe ba. Kamar misali idan wani ya aure ki bayan kin aikata ita zinar a waje, har abada ba zai taba ganin kima da mutuncinki ba. Hatta Bature da ya kawo mana ita, ya kuma yi sanadiyyar yaduwar ta cikin al’ummar mu, a cikin philosophy ya kira ta ‘dynamic pleasure’, wato jin dadi mai wucewa ya barka da bakin ciki mara karshe. Kin ji dalilin da yasa Inna Rabi ke nusarsheki a kanta”. Na ce, “To Ya Faruk me zai sa take tunanin ni din zan aikata Zina? Tunda ita ba ta taba yin zina a rayuwarta ba. Gaba daya rayuwarta tun daga yarinta har girma, ta kare ta ne a cikin bautar aure. Na kuma sha jin Malam na cewa, ‘abin da iyaye suka yi a kuruciyarsu shi ‘ya’yansu suke maimaitawa, wato barewa ba ta gudu danta ya yi rarrafe…..” Ya yi hanzarin katseni ta hanyar girgiza kai da cewa, “A’a, zamani ne ya sauya Abu. ‘Ya’yan yanzu bama koyi da iyayenmu sai da Bature. Da muna koyi dasu da abubuwan da ke faruwa a yau basu faru ba. Kuma Da a yau ka haife shi ne amma halinsa a duniya yake daukar abinsa. Ki kiyaye nasihar Inna Rabi Abu”. To a haka rayuwarmu ke tafiya, cikin rufin asirin Allah da tarbiyya ta gari. Lokacin da Ya Faruk ya zana jarrabawar fita sakandire, lokacin ne ni kuma na zana ta kammala firamare wato (Gwarzo Special) da nake zuwa. Malam mutum mai hanyoyin ma’aikatan gwamnati da dama. Akwai wani almajirinsa wanda ya tashi a gidansa, a yanzun kuma yake Farfesa a Jami’ar Danfodio wato (UDUS). Asalin dangantakar Malam da Proffessor Sa’idu shine, an kawo mai shi almajiranci daga wani kauye a Katsina. Da Dagacin yankin Gwarzo ya nemi da a kai yara makaranta, a wancan lokacin babu waanda Malam ya tuna ya kuma yiwa sha’awar yin boko kamar (Sa’idu-Baki) yadda sauran almajirai ‘yan’uwansa ke kiran sa kenan saboda bakar annakiyar daudar shi. Ya fi kowa datti cikin almajiran, haka ya fi kowa kazanta, inda duk ya wuce warin dauda da zarnin fitsari kawai za ka ji, amma haka nan Malam ke son shi fiye da sauran almajiran, don a cewarsa; Sa’idu duk ya fisu hankali. Kullum ya je makarantar bokon ya dawo abincinshi na nan cikin kwano Rabi ta ajiye mishi, sai kuma yai mata ‘yan aike da ba a rasa ba. A yadda Ya Faruk ya gaya mini, Inna Rabi ma na son Sa’idu, kuma da yake yana da cutar (ulcer) sai ba ta wasa da abincinshi, ko ba ita ce da girki ba in Sa’idu bai samu abinci ba sai ta daura mai tukunya ko ta jika mai garin rogo ta zuba zuma a ciki ta ba shi, haka duk ‘yan tsummokaran yaran gidan da Malam ke riko in sun tsufa ba ta suke ta bawa Sa’idu. Da sallah kuwa babba da karama, sababbi take dinka mishi, haka in zai je kauyen su Bindawa za ta hada mishi tsarabar Gwarzo niki-niki ya kai wa Innarshi da kudin motar zuwa da dawowa. Shima in zai dawo duk tsarabarshi ta Katsina su Aya da sauransu duka na Inna Rabi ne, don haka a bakin jama’ar gidan, Sa’idu dan dakin Inna Rabi ne. To ilimin boko dai babu matsayin da baya kai mutum a rayuwa, don bayan sakandire gaba dayan karatun Sa’idu a waje ya yi shi da taimakon gwamnati da ke daukar dawainiyar karatun dalibai a wancan lokacin. Yau Sa’idu-Baki shine da matsayin V.C watau (Vice-Chancellor) Proffessor Sa’id Salisu Bindawa, na Jami’ar Danfodio baki daya. Kuma anyi sa’a shi Sa’idun irin mutanen nan ne da basa manta alkhairin da aka yi musu komi kankantar shi. Balle shi yana ganin Malam da Rabi, matsayin wani tsaninshi na duk abin da ya zama a rayuwar shi, tunda iyayen da suka haife shi kasa rike shi suka yi saboda talaucin su da rashin dogaro da kai, suka turo shi almajirancin da ya zame mishi gata ba tare da sun kara bi ta kan rayuwar shi ba, sai dai shi ya neme su. [7/11, 3:57 PM] +234 706 160 2791: Sai ta sa kuka a hankali tana cewa, “Ni ban ce kada Abu ta yi karatu ba, amma duk makarantun Kano a rasa wadda za a sai an tsallaka na Sokoto? Bana son Abu ta gusa daga kusa dani ne ko ya ya, ina tsoron abin da ka je ya zo. Bana son abin da zai bata ran Abu, bana son abin da zai illata mutuncinta. Duk wannan kaunar da take mishi ai don ba ta san shi din wane ne ba, wane irin azzalumi ne? Kai ma ka sani da daga ranar ba ta kara ganin sa da GIRMA. Ina kokarin in kare GIRMANSA a idanun ta, in kare nata a idanun duniya, amma su basa gani, ai shi kenan, ga ku ga Abun nan ka ba shi ya tafi da ita, sai dai duk abin da ya biyo baya daga baya kar ayi kuka dani”. Ta fita tsakar gida ta bar mishi dakin. Wayewar garin wadda ta kasance Juma’a sai ga iyalin Farfesa, wato matan shi guda biyu sun zo da kansu, ya turo su kara baiwa Inna Rabi hakuri ta ba da Abu. Uwargida Haj. Sa’a da Amaryar ta Haj. Azumi, dama dai tuntuni babu shiri tsakanin Haj. Sa’a da Innana, gaba ce mai tsanani a tsakaninsu, don haka tana shigowa ko dakin Innar ba ta kalla ba dakin Inna Dubu ta shiga. Tana tafiya kai a sama, kai a dage kai ka ce wata matar shugaban kasa ce ba matar Sa’idu ba. Nima dai tuntuni Allah bai hada jinina da Haj. Sa’a ba, saboda girman kanta, mace ce mai dagawa da yawa, na tsani mutum mai girman kai da wulakanta talaka, to ita kuma halin ta kenan, ko ruwan gidan bai isa ta sha shi ba, da ruwan ta na roba take zuwa a bayan mota da sunkin abincinta cikin foil-paper, in ta ji yunwa sai ta je motar ta ci, ta sha, sannan ta dawo. Tabarmar gidan kuwa babu wadda ta isheta zama, sai dai ta zo da katuwar darduma mai laushi irin ta zuwa picnic din nan ta baje a dakin Inna Dubu, ta kishingida suna kwasar hira da yake ‘yan’uwan juna ne. An ce asalin ta ma a nan gidan Innar ta rike ta, Malam ya aurawa Farfesa, amma da yake Hajiyar birni ce shi Farfesa bai san hakan take yi ba in ta zo garin. Yawanci za ka samu wanda tushen sa talaka ne futuk in Allah ya yi mishi arziki rana daya, shi ke yin irin haka, ba wanda ya tashi ya kuma girma cikin arzikin ba, kamar amarya Hajiya Azumi kenan. Mace ce mai saukin kai, faram-faram da daraja kowa da zama ko mutunci ya hada ta da shi. Hajiya Azumi tamkar kawa take da Rabi, don basu fice tsararrakin juna ba, in da akwai wani da ya shafi Farfesa da Inna Rabi ke kulawa to Azumi ce, ina mamakin hakan, tunda kuwa ko ‘ya’yan da ta haifa ita Azumin basu tsira daga kiyayyar Innar ba (su Iftihal), amma ita in ka gansu suna hira rimi-rimi sai ka rantse da Allah Ya da Kanwa ne. Wannan na daga dalilin da yasa Farfesa Baba Sa’idu ya turo ta ga Inna Rabi, don ya san tana ganin mutuncinta fiye da na kowa nashi. Sun nitsa da hirar duniya Hajiya Azumi ke gaya mata makasudin zuwan nasu takanas nata ne, ta ce, “Ashe ni ba zan iya rike Abu tamkar su Aziza ba Rabi? Na yi mamaki da Alhaji ya ce dani wai ke kika ki amincewa da zaman Abu tare damu, wallahi kin ji na rantse Iftihal kullum ba ta zance sai na Abu, haka dan’uwanta, ba yadda za a zauna a mike bai ambaci Abu ba. Ba fa dauke miki ita zamu yi kwata-kwata ba Innarmu, duk hutu tana nan a dakinki. Kaunar Baban su Aziza da Abu Allah ne ya hada ta, mai zai sa ki kasa ganewa? Ba a san me Allah zai mai da Abu a nan gaba ba, a dalilin karatun nan har al’umma su amfana da ita”. Inna ta yi murmushin da bai kai zuci ba, ta ce, “Ni abin naku ku da mijinku ya daina bani haushi ya koma bani mamaki”. Azumi ta ce, “Mamakin me kuma Innar Abu?” Ta ce, “Mamaki mana. Yar daya jallin jal da Allah ya bani kun sa mata kahon zuka, kun dage sai kun rabani da ita duk da bataliyar ‘ya’yan da Allah ya baku, saboda hadama ko saboda mene? Ku daina cewa don Abu ta yi karatu za ta je gidan ku, kawai ku fito fili ku ce kuna so ku kwace ta ta zauna tare da ku, in makaranta ce har Sokoto ce za ta gayawa Kano karatu?” Azumi ta yi dariyar cin nasarar ganin ta fara samo kan Innar, ta ce, “Ayya Innar Abu! Ke din ce kin iya haihuwa, Abun taki abar so ce ga kowa, ga fara’a ga farin jini, yarinya ce mai shiga ran mutum farat daya. Idan aka samu irin su Abu suka yi ilimi mai zurfi suna da matukar amfani ga al’umma, su kuma zamo ababen alfahari ga iyaye. Ba kya gani komi nata, nutsuwar ta da takun rayuwar ta daban ne da na sauran yara? Ki daure ki bamu Abu, da yardar Allah na tabbatar miki ba za ki yi dana sani a kan hakan ba”. Shima Faruq tunaninsa daya ne da na iyayen dakinsa, don dai baya son Inna Rabi ta kullace shi ne kamar yadda ta ji haushin Malam da ya sanya baki. Yana ganin in an bar Abu a kauye, ba ta dandani rayuwar birni irin ta su Iftihal ba, ba ta kuma yi karatu mai tsada ta goge irin Aziza ba, an tauye mata hakki, duk kyawun nan nata da yalolon bakin gashinta maras gyara, a kauye za ta kari rayuwar ta, watakila ma a dauka a baiwa wani gardin kauyen yadda aka yiwa su Halima. Shi kuwa mai farin ciki ne da duk wani ci gaban kanwar sa tilo. A dan zaman da ya yi na shekaru biyu da iyalin Farfesa, sai ya rika tambayar kansa shin su rayuwa suke, ko ko a daji suke? Rayuwar gidan Vice-chancellor Proffessor Sa’idu Bindawa, a bar kauna ce a bar sha’awa, a bar so ga kowa. Irin rayuwar nan ce maras takura da rashin sanya ido, kowa ya yi abin da ya zaba ma rayuwar shi kamar a Turai. Wannan na da nasaba da zaman da sukai na shekaru goma a kasar Ingila inda shi Farfesa ya yi karatu tun daga digirin farko har PhD, inda dukkan su suka fara karatu. Ba rikici ba hargitsi, babu tsana balle tsangwama a tsakanin ‘ya’yan su. Ba wai dukiya ce ta yi yawa ba, ko facaka ake da kudi, illa rayuwa ta rikakkun ‘yan boko ziryan, komi akwai isasshe, ga kan kowa a bude ilimi ya wadaci kowannen su. Hajiya Sa’a ma’aikaciyar gidan talabijin ce na (NTA), inda ita kuma Azumi take (gynaecologist) a General Hospital na Sokoto. Gidan Proffessor yana cikin Jami’ar Usman Danfodiyo, wanda ya fi gaba dayan gidajen Malaman Jami’ar kyau da tsari kasancewar shi gidan V.C baki daya. Inna Rabi dai sun taru har Malam sun tattamketa da jijiyoyin ta, musamman ita Haj. Azumi. Duk wata hujja da Innar ta kawo ta soketa, ta ce ba ta amince za ta iya rike mata Abu kamar yadda ta dauki Innar Uwar ta ba. Malam Ali ya dubi wadannan kasaitattun mutane, basu kyamaci nashi ba sai shi? Ba wannan yake ji ba, illa tattalin mutunci da martabar Zaynabu Abu, wanda muddin ta gusa daga kusa da shi da Rabi, ba mamaki ya FADI a nan gaba. Abin da suke ta mummukin sa a tsakanin su shekara da shekaru ya fito duniya ta sani; GIRMA YA FADI! To amma shi kansa zai so Abu ta yi ilimin da watarana zai ganta haka a kasaice kamar su Hajiya Azumi, ko ko ta rika taimakon al’umma kamar yadda Sa’idu ke yi ta fannoni da dama, ba wai ta hanyar kudi ba kadai. A yau matasan da ke neman aiki a garin Gwarzo in dai har suna da takardun nasara masu kyau (graduates) na diploma ne ko NCE, ko ko babban digiri, wurin shi suke zuwa ya hada su da Sa’idu, kamin dan lokaci za su zo suna gode masa, suna sanar da shi an samar musu aiki da albashi mai tsoka. Haka masu neman gurbi a jami’o’i saboda yadda gurbin karatun jami’a ya zama a wannan kasa tamu, sai ga masu iyaye a gindin murhun. Almajiran Malam da Sa’idu ya ya samarwa gurbi a jami’o’i ba za su kidayu ba, don haka al’ummar Gwarzo kullum cikin amfana da Sa’idu suke, tare da shiwa Malam Ali albarka saboda ci gaban da ‘ya’yansu ke samu a dalilin sa. Haka matasa wadanda Allah bai basu daman yin karatun ba, yana hadasu da gwamnati su samu taimakon sana’o’i na dogaro da kai. Wannan dalilin da wasu da yawa da ba zasu fadu ba, ya karfafa shi da ya barsu su je da Abu, to amma bai yarda a yiwa Abu aure nan kusa ba, sai ta mallaki hankalin kanta, ta san WACE CE ITA? To ga ‘yan bokon, wannan ai ba wani abu bane da har sai Malam din ya fada, su dama basu da burin da ya wuce ayi ta bokon har a kure shi in ana kurewa. Da wannan ZAINABU-ABU ta koma Sokoto, gidan Baba Sa’idunta. *** ZAYNABU-ABU MAI TAGWAYEN SUNA! A duk yadda dan Adam ya samu sauyin rayuwa ko y ya ne, imma ta fannin abinci, suttura ko muhalli, ya kan samu sauyin zuciya dana surar gangar jiki gaba daya. To hakan ce ta faru dani a gidan Baba Sa’idu. Duk da irin sabuwar rayuwar da na budi ido na samu kaina a ciki, hakan bai hana ni tuno gida ba da wadannan mutane guda biyu; Malam da Inna Rabi. Sai kuma na samu kaina da jin haushin kaina mai tsanani na wautar da na yi na amince da zaman gidan Baba Sa’idu, bayan a da shine babban burin rayuwata, wato na ganni kusa da Baba Sa’idu. Dalilin kuwa shine, kwata-kwata tsarin rayuwarsu ya sha banban da tawa, da irin rayuwar da na taso a cikinta. A ganina irin wannan rayuwar bata dace dani ba; ‘yar mallam jikar mallam. Rayuwa wadda babu Allah ko daya a cikin ta sai rayuwar tsurar ta. Sai a kwana a wuni ba a ambaci Allah ba, balle a ja carbi, sallah ma ba kowa ke yi a kan lokaci ba, balle ayi maganar jam’i, don shi Baban ma kwata-kwata baya zaman gidan. Idan ya tafi cikin makaranta tun karfe takwas na safe sai shida na yamma yake dawowa cikin gidan, haka nan kullum yana bisa hanyar meeting ko seminar a Abuja ko Lagos da sauran manyan birane. Ban taba ganin mutum (busy) irin Baba Sa’idu ba, bautawa bokon yake da karfinsa, lafiyarsa, lokacinsa da aljihunsa, yayin da jami’ar Danfodiyo ke kara bunkasa da samun ci gaba (inaudiably) a dalilin kwazo da sadaukarwa irin nasa. Rayuwar gidan rayuwa ce da ke sawa mutum ya manta da Allah, da irin tarbiyyar da ya taso a cikin ta saboda jin dadin da ke cikin ta, sakaci da rashin kwaba ga ‘ya’yan su, abin har ya so yayi yawa. Duk da haka ina kokari naga cewa ban kaucewa tarbiyyar Rabi ba da koyarwar Mallam. Hakika duk wanda yasan rayuwar Malam Ali da iyalansa, itace rayuwa a bar koyi. Babu abinda suke bari ya shagaltar dasu daga bautar Allah da kiyaye sallah. Kuma babu shakka shima Baba Sa’idu a wurin su ya samu wannan tubalin na kiyaye sallah, domin ya kan ce mun tana hani daga aikata alfasha da aikin munkari. Irin yadda su Iftihal suka ga bana wasa da sallah, ko me muke yi da zarar lokacin sallah yayi zan tsame kaina har sai na bada farali, shine sanadiyyar da suma suka dage, duk sanda nayo alwala suma zasu mike su dauro alwala, wannan ba karamin fa ranta ran Haj. Azumi yake ba. A ranar dana zo Aziza bata nan tana porthercort hutu gidan Antinta Isaita kanwar Haj. Azumi, Iftihal kuma tana makaranta. Bazan manta ba zugum nayi, na zubawa akwatun kifaye da ban taba gani ba ido (aquarium) kifaye nata gudu a ciki masu ruwan kumfar zinare cikin mamakin ilmi da fasaha na bature, wanda yayi tunanin ya zabo kyawawan kifi masu rai, ya zuba cikin wannan gilashi. Haj. Azumi ta umarci Gaddafi (Gambon su Aziza) kuma autan ta, da ya rakani dakin su Aziza, in yi sallah inyi wanka in kwanta in huta, don kuwa ba karamar tafiya muka kwaso ba ta yini guda cur. Da nayi wanka na canza zuwa doguwar rigar shadda ruwan makuba, da aka yiwa dinkin babban riga. Haj. Azumi ta kira ni muka ci abinci tare, ni da ita da Ghaddafi, tana mun hiran shirmen Gaddafi cikin sugar Jan ra’ayi na da sake dasu, ga yadda na lura ta fi son Gaddafi fiye da su Aziza, ko don shi kadai ne namiji ban sani ba. Cikin murmushi kuma ta ce, “Abu ya ya? Za ki zauna dani ne ko ko wajen Hajiya Sa’a za ki zauna wurin su Faruq?” Ni kam cikin dan lokaci Hajiya Azumi ta saye ni kaf da kirkin ta, ganin ta nake tamkar Inna ta, gata dai ba wata babba ba sosai, ga kuma kissar zama da mutane, komi nata da na ‘ya’yanta burge ni yake, yadda take nan-nan da ni sai ka ce ba ta taba haihuwa ba. Ban san sanda na ce, “Ni dai da ku zan zauna, waccan matar bata dariya”. Ta yi dariyar jin dadi ta ce “Ni kuwa zan gwada miki kauna Abu, ba za ki yi kewar Inna ba insha Allahu. Tuni an sanya ki makarantar su mutuniyar ki, da zarar Azzy ta dawo jibi da yardar Allah za ku fara zuwa”. Cikin kwanaki biyun shakuwa mai tsanani ke shiga tsakanina da Mama (yadda ake kiran ta a gidan) hatta abinci tare muke ci, in za ta tafi aiki sai ta sanyamu a gaban motar muje in an sauke ta sai direban ya dawo damu. Fadin murnar da Iftihal ta yi da zuwana ma ba zai fadu ba. Ranar lahadi da Mama ba ta da aiki daukarmu ta yi ta kai mu wajen wankin kai, ta yi mun sayayya mai yawa. A ranar ne kuma Aziza ta dawo. Farkon ganina da Aziza ban san cewa ba Iftihal ba ce, saboda kamannin su (identical twins). Yara bula-bula dasu kamar hura su ake sai ka ce balloon, da gani duk na girme su sosai, cikar hutu suka fini. Azizah ce take tambayar Hajiya Azumi wai ni wace ce? Ta ce, “Anti-Abu kenan, Yayar ce Azizah”. Ta kyakkyabe baki kamar za ta yi kuka cike da kishi ta ce, “ita ma ‘yar ki ce?” Ta ce, “Yata ce mana”. Ta sake cewa, “To amma ai ita fara ce mai gashi irin na Indiyawa”. Ta tuntsire da dariya ta ce, “Ke kuma baka ce mai gashi irin na Katsinawa!”. *** Mafari kenan da sunan (Anti Abu) ya bini a bakin su Azizah har yau inda nake. Makarantarmu jeka-ka-dawo ce ta Gwamnatin Tarayya (Federal Govt. College). Alkawarin da Baba Sa’idu ya yiwa Rabi bai karya ba, a hutunmu na farko ko kwanaki biyu bamu yi da hutun ba ya hada mu da direba ya kaimu Gwarzo. Su Iftihal sun fini dokin zuwa Gwarzo, ba don komi ba sai don jin dadin zaman garin da ita Iftihal ta yi a zuwanta na farko, take kuma bai wa ‘yar’uwarta labari, musamman gidan gonar babansu. Inna ta ji dadin yadda ta ganni, har ta kasa boye mamakin ta. Ta ce, “Kyauta ke ce kuwa???” Ni kaina na san na yi kiba, haskena ya kara fitowa, nutsuwar nan da ta sanni da ita tana tare dani ba abinda ya canza ba kamar su Azizah ba, sai ma abinda ya karu. Na ji dadi da ba ta nuna wa su Azizah kyara a kan idona ba, illa dai dakinta ne ta kulle alamun ba za su shiga ba. A cikin kunne na na ji sanda tasa kara tana ture warin takalmin Iftihal da ban san ya a kai ya je kofar dakin ta ba, tana kunkuni tana cewa, “Allah kai mana tsari da ire-iren zuri’ar Sa’idu, ka kare Abuna daga dattin zina”. Gaskiya a zamana tsawon watanni uku kacal gidan Farfesa na yi hankali gami da wayewa fiye da nawa na da, don haka maganar Inna ta tsaya mun a rai. A kullum gidan gonar Baba muke wuni, can ake kai mana abinci. A lokacin su Hafsisi da Indo ma sun zo hutu daga Kabo, duk tare muke yawon. Kauyancinsu da gidadanci na baiwa Aziza matukar dariya, don komi suka gani a jikin su ko suka ji sun fada wanda basu sani ba sai sun tanka. Inna take tambaya ta Faruq kwana biyu bai zo ba. Na ce, “Nima tunda na je gidan ban ganshi ba, an ce karatun ne ya yi masu zafi, shi yana (attachement) ne a Abuja da (Federal Revanue) yayin da Imran ke yi da (Company SIWES) a Kaduna. Da zamu dawo aka hado mana tsarabar Gwarzo rankatakaf! Azizah mai son man shanu ce da madarar shanu sabuwar tatsa, wadda ba ta kai ga zama nono ba. Ita kuwa Iftihal ta fi son a ba ta korai da ludaya na duma masu zane mai kyau, duk haka Inna Dubu da Rakiya suka hado masu, daga Inna Rabi ko a sauka lafiya basu samu ba, sai Abunta ta hadawa shatara ta arziki, don haka cikin dabara na diba cikin tawa tsarabar data hadamin na basu na ce in ji ta, ko don wanke damuwar da Azizah ta shiga kan yadda Innar ta karbe su. Ita ko Iftihal ba ta ma kula da ita ba don ba ta dauke ta cikakkar mai hankali ba. Karfe takwas na daren ranar a Sokoto ta yi mana. A zamana gidan Baba Sa’idu abinda na lura na faruwa cikin gidan shine, Mama mace ce mai kishin jaraba, ita ko Hajiya Sa’a mulki da ganin kyashi ne cike da ranta, ba ta son Abban ya yiwa kowa wani abu sai ita sai ‘ya’yanta wadanda dukkaninsu maza ne su hudu, in ka dauke Imran da yake babba duk yara ne, fitinannu masu dan banzan raini. Kusan duk rabin albashin Farfesa a karatunsu yake karewa. Za ka yi mamaki in ka ji cewa yaro karami kaman Jauhar kudin makarantar shi naira dubu dari da hamsin ne (per-term), amma duk da haka ba ta gani, kullum idonta na kan na Hajiya Azumi da ‘ya’yanta guda uku, sai kuma ni da yanzu aka kara mata. Tun zuwana gidan suke damawa, kowacce tana haba-haba da miji don neman zama mowa. Shi ko Farfesa irin mugayen ‘yan bokon nan ne da biro da takarda ya fi komi muhimmanci a gare su. Ba shi da lokacin ire-iren gutsiri tsoman da ke faruwa a gidan, don haka ko da Hajiya Sa’a ta kawo mai korafin wai Azumi ta zuge ni in zauna a wurin ta, sai cewa ya yi, “Har nawa Abun take da za a zugata? Ki kyaleta ta zauna dasu tunda da su tafi sabawa, ko cikin maza kike so ta zauna?” Faram-faram ta tashi, tun daga ranar Hajiya Sa’a ta kulla ta dani, ‘ya’yanta Jauhar, Hassan da Rufa’i take gaya musu wai ni BARAROJI ce Buzayen Daji su daina zama kusa dani. Daga ranar fa suka diba wai Maman su Iftihal ta zo da Bararoji. In abinci suke ci na zo zan gifta sai Jauhar ya tsartar da miyau ya ce, “Tir! Me za ayi da kazame?” Tun abun baya damuna har na soma share hawaye, musamman ranar da Hassan ya kwararo amai da na wuce shi yana cin abinci. Iftihal ce ta gayawa Mama, ta yi mamaki sosai, ta yi ta lallashina ta ce in yi hakuri za ta fadawa Abba. Su ko su Azizah ganin kwana biyu Maman ba ta dauki wani mataki ba, su Jauhar kuma basu fasa abinda suke ba suma suka shaka. Da daddare an hadu ana cin abinci kaman yadda yake a al’adar gidan, Rufa’i ya faki idon Abba ya tofa mun miyau a cikin plate dina, Jauhar ko ya tsartar gefe, ya ce, “Hassan gaskiya da aka ce Bararoji babu wanda ya kai su kazanta, ka duba ka ga yadda take mixing mayonnaise da margerine cikin farar shinkafa”. Suka tintsire da dariya. Abban ya dube su suna ta dariya, ya ce cikin mamaki, “Ku kuma ina kuka samo Bararoji?” Duk suka yi tsit! Ya buga tebir da karfi ya kara maimaita tambayarsa, kowannen su mara ta cika fam da fitsari. Azizah ta yi kwafa ta ce, “Abba Hassan, Rufa’i da Jauhar ai BARAROJI suke ce da Anti Abu, in sun ganta su tsartar da miyau ko suyi aman abin da suka ci, in tana cin abinci su tofa miyau a ciki”. Farfesa jikinsa har tsuma yake, muryarsa na rawa ya ce, “Ai ban ga laifinsu ba, ga inda suka samu daurin gindi nan”. Ya nuna Hajiya Sa’a da ta sunkuyar da kai. Ya koma mazauninsa yana kaduwa kamar mazari kamin ya yi murmushi ya ce, “Sai ki nemi wani gidan kuwa, amma ba gidan Sa’idun Malam Ali ba!”. Ba ita kadai ba hatta Mama ta kadu da wannan hukuncin na Abba. Hajiya Sa’a saboda takaici ba ta san sanda ta ce, “Ban gane ba, Abu ta fimu iko da gidan nan kenan?” Ya girgiza kai don tabbatar mata tambayar ta ita ce amsar ta. Ta ce, “Aikin banza! Su da gidan ubansu? Ba Bararojin ba ce karya suke? Da dai ba a san asalin balbelar bane….” Kamin ta karasa ya soma kwallo da su Hassan a cikin falon, cewa yake, “Fice min a gida, Hajiya Sa’a, sai na neme ki”. Idanun Hajiya Sa’a suka firfito kuru-kuru, hankalinta ya tashi saboda irin dukan da yake yiwa su Hassan kamar ba mai rai yake bugu ba, da kyar Mama ta yi waje dasu bayan sun bugu, ko ina a jikinsu ya amsa ya haye ya yi suntum. Ta mike ta fice, dakinta ta shige ta kulle amma ba ta je ko ina ba. Abba ya rantse ya yi rantsuwa da Allah, “Wanda duk ya sake ce da Abu BARAROJI a cikin gidan nan sai dai ya nemi wani Uban ba ni ba, kun ji ko ‘ya’yan iska?” A ranar Mama da ‘ya’yanta kamar sallah, Abba ya wulakanta Hajiya Sa’a da ‘ya’yanta, su Iftihal kamar a rungume Abba kan su ya fasu, su a dole Abba ya fi son su da su Rufa’i. Azizah har kwarya-kwaryar liyafa ta shirya, inda ‘yan dakin Hajiya Sa’a su kai kwanan bakin ciki da takaici. **** [7/11, 3:57 PM] +234 706 160 2791: Ai jin haka Innana ta yi hanzarin zuwa ta kamo kofar dakinta ta bame da mukulli, wato (Iftihal ba za ta shigar mata daki ba). Ba don yarinya ba ce kuma ba ta kawo komi a ranta ba, da ta gane abin da Inna ta ke nufi. Sai Inna Rakiya ta dauki kayan hannunta ta ce, “Muna maraba da Iftihal Basakkwata”. Ni da ita muka yi dariya, yayin da na yi wata asirtacciyar ajiyar zuciya. Da alama Iftihal yarinya ce mai saurin sabo da kuma wayewar kai, gami da karbar rayuwa a duk inda ta tsinci kanta. Kafa ta nade tana cin gyada, tana bani labarin Aziza (twin- sister) dinta. Ba ta daddara ba ta sake kallon gefen da Inna take, ta ce, “Innar Abu sammun rogon nan da kike tsamewa, hadawa nake da gyadar”. Inna ko kallon ta ba ta yi ba, yayin da kirjina ya shiga luguden uku-uku. Tsoro na Allah tsoro na kada Iftihal da ta zo yau din nan ta fahimci cewa gabar da Innana ke yi da Babanta itama ya shafe ta. Idan rogon Innar ya amsa mata, to ita ma Innar ta amsa. Ta sake maimaita tambayar ta na Inna ta ba ta rogon. Budar bakinta sai cewa ta yi, “Ai ba ubanki ne ya saya ba!”. Na yi saurin kai hannuwa na dafe kai, cikin wasu hawaye da suka ciko idona. Inna Dubu ma ranta ya baci da wannan halayya ta Inna ta. Ta zo tana dibar rogon cikin roba tana cewa, “Bari ta ci kasona, ai ni mijina ne ya saya idan ita ba Ubanta ne ya saya ba!”. Tana fadi ne cikin dariya, domin gusar da damuwar da fuskar ‘yar yarinya Iftihal ta shiga. Watakila ba a taba yi mata irin wannan gwasalen ba a rayuwarta. Ta kawo rogon ta dangwarar mana, tana cewa da Iftihal, “Ke ci ki rabu da ita, ba ta jin Hausa sosai, ba ta fahimci me kike cewa ba”. Ta ce, “Abu ma ba ta jin Hausar? To wanne yare suke ji?” Ta ce, “Abu ta fita jin Hausa, ita faransanci take ji irin na kasarsu, ai kin sani ko?” ta ce, eh na sanshi, ana koya mana a makaranta, Abu ina ce ce kasar ku?” Na yi dan diri-diri na rashin sani, don kuwa ni ban san da wata kasa ba banda wannan da muke ciki. Inna Rakiya dake gefe ce ta ce da ita, “Niger!”. Malam da Baba Sa’idu ne suka shigo, suna hirarsu irin ta wadanda suka aminta da juna. A yau ban yi gigin yin tsallen taren Baba Sa’idu ba, kamar yadda na saba. Duk da kankantata na san ba abinda Innata ta tsana kamar ta ganni a jikin Baba Sa’idu, don haka na yi ma kaina alkawarin na daina, daga ranar da hakan ya janyowa Baba Sa’idu wulakancin da bai taba gani ba. Sai muka russuna mu duka muna gaishe su, ni ina gayar da Baba ne, Iftihal na gayar da Malam. Murmushin jin dadi ya bayyana a fatar bakin Baba Sa’idu, yayin da Malam ke ta tsokanar Iftihal da amaryarsa. Ya ce, “Yanzu-yanzu zai kwashe kayan dakin Rabi ya sanya ta, don ita ta tsufa ita ko gata nan sabuwa gar a leda”. Iftihal tana ta dariya, ta ce, “Baba Malam ka ce da Abu ta rakani in ga gari don in ba Aziza labari”. Malam ya ce, “Maza Abu sako takalmanki ki raka amaryata gidan gonar Babanta, ki kaita har gidan Halima da Safiya, ki gaya musu diyar Babanku ce”. Muna tafe tare da Iftihal tana ta yi min hira, wadda duk rabin maganarta Turanci ne ba duka nake fahimta ba, amma ita ta kasa gane hakan ta hutar da bakinta, ni dama tuntuni Allah bai dauran yawan magana ba. Da alama yarinya ce mai surutun tsiya, fadi ba a tambaye ka ba. Takaicin al’amarin Innata a kan Baba Sa’idu ke damuna, abin har ya wuce kansa ya shafi ‘ya’yan cikinsa? Rabona da su Iftihal tun suna kanana da suka zo da babarsu wadda abin mamaki ita suna shiri da Rabi, sabanin uwargidan da suke narka matsananciyar kiyayya. Shin har yanzu lokaci bai yi ba da ya kamata in san duk musababbin wannan? Tambayar da Iftihal ta jefo min ta sake jefa ni a cikin rudani, “Abu Innarki na da tabin hankali ne?” Nayi gaggawar juyowa na dube ta tamkar ta soka min mashi a kahon zuci, amma na kasa ba ta amsa, don ban san me zan ce mata ba. Gaskiya ne al’amuran Innata sun fi kama da na masu tabi hankali, kuma a yadda kowa yake biyar da ita a gidan, ba a dauke ta cikakkar mai hankali ba. Kishiyoyinta basa kishi da ita, basa takaicin duk gwasalen da take musu. Mijinta bai dauki yanayin rayuwarta da muhimmanci ba, balle har ya damu da hakan, binta kawai ake da yadda take so, don a zauna lafiya. To amma ni ba zan taba yarda da cewa da ake wai Innata na da tabin hankali ba, musamman in aka yi la’akari da irin kalaman da ke fita a bakinta na hankali da sanin yakamata ne. Illa in ce yanayin rayuwa ne ya mai da ta hakan, ya sanya ta daina kaunar kowanne dan adam sai mu da muka zame mata dole. Na kan tambayi kaina don me kiyayyar ta ya fi yawa a kan Baba Sa’idu? Me ya yi mata? Me yasa ta tsane shi fiye da kowa a duniya? Me yasa kome zai mata don ya faranta mata baya burgeta? Tunda nake ban taba ganin mutum mai kirki, karamci da mutuncin Baba Sa’idu ba, kamar yadda ban taba ganin mutum mai arzikinsa ba!. Na daga kai na yi duba ga Gidan Gonarsa makeken gaske, dabbobin dake ciki dukkaninsu farare ne sol. Girman gidan gonar kadai ya isa a gina gidaje biyar manya-manya, ba tare da kowanne ya gogi dan’uwansa ba. Ita kanta Iftihal sakin baki ta yi galala! Tana kallon Agwagin ruwa farare kal sama da dari na yawo a cikin tafki, fararen Tantabaru rainon Ingila na tashi daga wannan daki zuwa wancan. Fararen Babba-Da-Jaka dika-dika goye da ‘ya’yansu cikin jikkunansu, fararen Dawaki kosassu na ta haniniya tare da harba kafafunsu cikin koshin lafiya, fararen kaji (buloras) wadanda ba za su kidayu ba, haka kwaikwayen da suka sassaka mutum goma ba za su iya kwashe su a yini daya ba. Idan ka nutsa cikin gidan gonar sosai fararen ragunan Sudan ne buka-buka masu manyan kahonni suma cikin fili guda. Wannan ba zai burgeka ba sai ka ga fararen Balbelun dake shawagi cikin wayar da aka zagaye su. Ga kuma Tinkiyoyi da ‘ya’yansu suma farare sol-sol kai ka ce kullum sai an yi musu wanka, sun fi guda dari cikin fili guda. A can wani katon fili ‘zebra’ ne (jakin dawa) guda uku manya-manya masu zanen fari da baki. Babban swimming-pool cike yake da fararen kifi (salmon) manya da kanana, kai ka ce a (Dambatta-Dam_ kake. Iftihal bakinta ya kasa rufo da mamakin wai na ce wannan duk na Babanta ne. Ta daga kai ta yi duba ga Dawisu korra sharr dake ta shawagin su bisa doguwar katangar ginin kai ka ce katangar gidan Zoo ce saboda tsayi. Sun zubo dogon bindinsu kasa, wasunsu kuwa sun bude shi cikin nuna baiwar kyau da Allah yai musu dai bai yiwa wata dabba ko wani tsuntsu a duniya ba. Ma’aikatan wajen sun tsinko mata kayan marmari nunannu, sun wanke sun zubo mata a cikin kwando a matsayinta na bakuwarmu da ba ta taba zuwa ba, kuma diya ga Baba Sa’idu. Amma ta kasa sha, extremely puzzled! Sai tambaya ta take wai Baba shekaru nawa ya kwashe yana assasa gidan gonar nan? Wannan ai ya fi karfin a kira shi gidan gona sai gidan Zoo! Na ce, “Kin taba ganin gidan Zoo da babu zaki babu damisa? An ce Baba tun yana sakandire ya fara assasa gidan gonar da ‘yan tsirarun dabbobin da Malam ya bashi, amma bata fara habaka ba sai dawowar shi karatu daga Turai”. Ta ce a sanyaye, “Amma Baba mai yasa bai taba gaya mana yana da wannan gidan gonar ba?” Na girgiza kai na ce, “Ba zan sani ba, mai yiwuwa yawan abubuwan da ke kansa su suka mantar da shi ga yin hakan. Don shima sai ya zo garin nan sau uku bai zo nan din ba, duk albashin ma’aikatan ta hannun Malam yake basu”. Akwai shuke-shuke na kayan marmari musamman guava, Roman, fasa-dabur, inibi, tuffa, lemun zaki, ayaba, cashew da abarba. Muka debi iyakar iyawarmu a leda, daga nan muka tafi gidan Yaya Halima. A nan muka yi sallar magariba muka ci abinci. Na yi zaton Iftihal ba za ta ci ba, musamman da yake tuwon dawa ne miyar kuka, amma ita ce mai cewa a karo har tana side hannu. Yaya Halima ta ba ta dakakken yajin daddawa mai dadi da ta ce tana so. A kan hanyar mu ta dawowa gida Iftihal tace, “Shin Abu mai yasa Innarki ba za ta bari Baba ya tafi dake ba a sanyamu makaranta daya kamar yadda Babba ke so ba? Muma mun gama firamare, JSS 1 za a kai mu. Kinga ga Ya Faruk ba za ki yi kewa ba, za ki ji dadin zama da Mamarmu, don tana sonki”. Na yi sauri na ce, “Innata ma na sona, Iftihal ba za ta amince ba”. Na yi gaba abina na barta a baya. A kwanaki biyun da muka yi tare da Iftihal mun shaku sosai. Wasu halayen ta ne guda biyu, suka sa ta shiga raina; batasan mene ne girman kai ba, kuma ba ta dauki kanta a bakin komai ba. Duk wanda ta ga Babanta na so tana girmama shi. Da za su tafi mun sha kuka, ta rantse ba za ta tafi ta barni ba a barta a nan mu zauna tare. Sai da Malam ya yi mata alkawarin in Allah ya yarda WATARANA Zaynabu-Abu gidansu za ta koma baki daya, sannan ta hakura suka tafi. Inna na daga gefe ta ce, “Me kake nufi da da wannan alkawarin? To kada Allah ya yarda! In ma wani mugun nufi ne kuke da shi a kaina da Zainabu, kaida Sa’idun naka, to Allah ya fiku. Bani da kowa sai shi, don haka da shi na dogara. Na kuma tabbata zai fiddani da Abu daga kutunguila da sharrin Sa’idu”. Muna bakin motar Baba Sa’idu yana kara yi mun nasiha a kan muhimmancin kula da sallah a kan lokacin ta. Ya ce, “Zaynabu in kika kyautata sallarki, dukkan aiyukanki za su kyutata. A kullum ki yi kokari ki fi karfin zuciyarki, kada ki yarda ta fi karfinki. Ki kiyaye wadannan tsokokin guda biyu ‘harshe da zuciya’. Idan kika iya musu za ki iya ma dukkan rayuwarki. Idan suka yi kyau, dukkan al’amuranki za su yi kyau. Ki ci gaba da yi ma Innarki biyayya, kada ki taba yarda da kallon da ake mata na cewa ita din ba ta da hankali. Idan akwai mai hankali a duniya to ita ce, tana da kirki tana da alhairi yanayin rayuwa ne ya maida ta hakan. Kada ki yarda da yin mu’amala ko yaya take da namijin da ba muharramin ki ba, har sai kin san kanki, har sai kin san ke din WACE CE? Kada ki dinga sa abubuwa a ranki har su dameki kamar Innarki, ta fiya kullaci! Domin hakan lahani ne ga lafiya da kwakwalwa. Jeki gida Allah ya bamu alkhairi”. Na juya ina tafiya sannu-sannu, har na kai bakin kofar gida na sake juyowa, shima Baban bai shiga motar ba kallona yake. Na dawo da sauri, da na tuna ban yi masa addu’ar da na saba ba, na ce, “Baba Sa’idu Allah ya kaika lafiya”. Ya ce, “Amin Zayanabu, Allah yai miki albarka….”. Muna dagawa juna hannu ni da Iftihal direba ya ja suka tafi. Ban koma gida ba sai da na ga bacewar su cikin rairayi da kurar da ke bisa hanya. Dawawo ta kenan har zan shiga dakin Inna, amma jin muryar Malam yana ta fada yasa ni dakatawa ba don na so ba. “Kin dauka har yanzu Zaynabu yarinya ce ne? Irin abubuwan da kike nunawa Sa’idu a gabanta zai sanya ta sanya ma kanta ayar tambaya. Abu anyi shi ya wuce shekara da shekaru ya wuce amma kullum sabo kike mai da shi. Rabi kullum kina girma amma kina mai da kanki baya, idan don kin ga ba ta yin magana ne kike yi masa hakan a gabanta, ni na gaya miki wataran za ta tambaye ki dalilin haka, me za ki ce mata? Allah ma muna mishi laifin da ya fi wannan ya yafe mana, balle ke mutum dan adam? Wace ce ke da ba za ki yi afuwa ga wanda ya saba miki ba? Inda Allah baya yin afuwa a garemu, da tuni bai nade duniyar ba saboda dimbin sabon da ke cikin ta? Ina jiye miki ranar da ABU ZA TA JUYA MIKI BAYA A KAN SA’IDU, wannan a rubuce yake! Don haka ki sanyama ranki salama….” Na yi hanzarin juyawa na koma soro ina ta yarfe gumi da hawaye. Ni ZAINABU ABU wace irin rayuwa ce wannan? Babu ranar Allah da za ta fito ta fadi, ba’a yi musayen yawu a kaina ba. To ni din WACE CE? Kenan ba daya nake da sauran ‘ya’ya su Hafsisi ba, tunda kuwa ban taba jin an samu sabanin ra’ayi a kansu ba. Kai ba wanda yake zancensu cikin gidan, kowa ya bude baki ZAYNABU…. KYAUTA… ABU.. ... “Kada ki dinga sa abubuwa a ranki har su dameki tamkar Innarki, domin hakan lahani ne ga lafiya da kwakwala….”. Na tuna nasihar Baba Sa’idu, don haka na yi kokarin mantawa da wannan tunanin kada ya zamomin lahani ga kwakwalwa. Sati biyu a tsakani sai ga Ya Faruk ba zato ba tsammani. Ai kuwa na kwashi murna ba ji ba gani, na rasa ina naka-saka ina naka-aje da shi don farin ciki, inda duk yasa kafa cikin gidan nan nake mayas da tawa, na like masa tamkar cingam. Shima cike yake da farin cikin ganina, ya kara kyau da tsayi, ga wani irin gogewa da yake yi, jikinshi ya koma irin na Iftihal, mai santsi da taushin gani. A dakin Inna Dubu muke, na kwanta lamo aikinsa, cikin karamar murya na ce, “Ya Faruk Iftihal ba ta baka sako ka bani ba?” Ya ce, “Ta bani mana, fara kawo salala!”. Murmushi na yi, “Salalar me kake so?” Ya ce, “Ki daina wannan son jikin kamar mage, musamman kwanciya a jikin maza, ba kowa ne na gari ba, wani maye ne wani dan iska ne…”. Ba ni kadai ba hatta Inna Dubu ta ji kunyar maganarsa. Ta ce, “La’ilaha illallahu!…..” Amma shi din ko a jikinsa, iyakar gaskiyar shi ya fada zuciyarshi sak! Cikin sanyin jiki na tashi daga jikinsa na koma can gefen Inna na takure, duk raina ya baci. Bai kara bi ta kaina ba ya jawo jakarsa ya bude ya fiddo damin littattafan yara (junior readers series) na Turanci guda hudu ya miko mini. (An African Night Entertainment, Akin Goes To School, Suger Girl, da The Boy Slave). “Ga shi in ji ta”. Ya kuma fiddo wani takalmi (cover) rufaffe baki mai tsinannen kyau cikin kwalinsa, shima ya turo mani duk in jita. Ya sanya hannu ya fiddo ‘yar takardar littafin memo ta sha zanen shudayen furanni, ita ma ya miko mani. Na bude cikin zumudi, ga abin da ta rubuta layi daya kacal. “Abu plz, come soon”. Shi kansa Ya Faruk ya lura duk dokin zuwansa da nake, ya sagar min da gwiwa, don kuwa tunda na kwashi shirgina na haura kafa na yi dakinmu bai kara jin duriyata a gidan ba. Da daddare ya saba ni nake kai mishi abinci har dakinsa, amma yau sai Zulkiflu ne ya kai masa, domin Inna Rakiyar da ta kwashe tuwon ta yi kiran duniyar nan na yi kamar ban ji ta ba. Ganin Zulkiflu ya kawo mai abinci, ya tabbatar Abu dai fushi take yi. Ya yi cilli da jaridar da yake karantawa ya miqe ya shigo cikin gidan har dakin Innata. A lokacin ina cin tuwo, sai kawai yasa hannu cikin tuwona yana ci, na lura cin nasa har da mugunta ne, domin kan na kai loma daya ya kai uku gunduma-gunduma, nan da nan ya cinye mun tuwon. Na tsame hannuna na koma gefe ina ta kumburi, sai ya fita ya dawo da roba da sabulu gami da ruwa a buta. Ya soma wanke min miyar kukar. Inna ta ce, “Mulki sai mai shi”. Ya ce, “Kwarai, wannan Princess Diana ce”. Ban san sanda na yi murmushi ba. Ya ce, “To ko ke fa? Baki ga yadda kika yi kyau ba, da wannan murmushin naki mai narka zuciya, da wannan fararen idanun naki irin na Princess Diana, da wannan yalolon gashin naki irin nata. Na rantse da za ta ganki sai ta ce ke kanwarta ce. Duk namijin da Allah ya ba shi ke a matsayin mata, ya yi mai baiwa da rabin addininsa. Ga dai kyau ga kyan hali, ga hankali da addini. Ga Alqur’ani a cikin kanki. Ga ki da daukar rayuwa da sauki ban san ki da zuciya ba. A kullum kina auna abubuwa a mizani na hankali, ki yi hukunci wanda ya dace, ban san yaushe kika koma bin son zuciya ba….” Na toshe mishi baki cikin dabara ya cire hannun yace, “Is o.k, mun shirya ko Abuna? Taso maza muje ki gaya mun abubuwan da kika gabatar da bana nan, da kuma shirye-shiryen ki na tafiya babbar makaranta. Duk ‘ya’yan kirki suna makaranta sai ke ‘yar gatan Innarta da Ya Faruq”. Ya juya ya fita, Inna na ta mamakin mu. Da gudu na juya na je na sako bantena, na dora doguwar riga a kai, na daura karamin hijabi, na bishi muka fita waje muka zauna a kan dakalin kofar gida. Garin babu hasken lantarki sai na farin wata na daren goma sha hudu. Taurari birjik sun mamaye sararin samaniyar Subhana, sun kara haskakata. Da yake bayan isha ne duk almajiran Malam sun shiga gari bara, don ba duka Malam ke iya ciyar dasu ba saboda yawansu. Na sanya hannu na lalubo ‘yar akwatuna daga cikin bantena, Ya Faruq na ba na ce, “Ga amana, ka ajiye min. Domin Baba Sa’idu ya ce kada in sake in bari Inna ta kyautar min da zobban nan, a nan gaba za suyi mun amfani”. Cikin mamaki Ya Faruq ya soma kiciniyar bude akwatun, wani haske da ya fito ya dallare mana idanu ba shiri ya mayar ya rufe, daga inda nake ina iya juyo irin bugun da zuciyarshi ta shiga yi da sauri da sauri. Ya sake budewa domin tabbatarwa ya fiddo daya yana juya shi a hannunsa, hasken wata da taurari na kara masa walkiya. Ya ce cikin shakakkiyar murya, “Shi…… Baba Sa’idun… ne ya baki wannan da kansa Abu?” Na ce, “Allah shine, nima da fari na ji tsoro. Amma ya ce kar in sake in bawa Inna, to ni kuma na gaji da boyon su kullum tare dasu nake barci, har bandaki dasu nake shiga, shi yasa na matsu ka dawo”. Ya ce, “To ai nima wannan ya fi karfin in ajje shi wurina ‘sapphire’ ne (shudin yakutu) komai na iya faruwa. Shima Baban ban da abinsa bai dace da ya baki wannan ba yanzu, haba! Sai dai in kai banki”. Na ce, “Banki kuma Ya Faruq, ba kuxi ake ajiyewa a banki ba?” Ya ce, “Wannan ya fi karfin kudi, ya fi karfin zinari da diamond. Ana ajiye (valuable goods) wato kaya masu daraja a banki”. Ya yi shiru cikin tunani mai zurfi, da alama kanshi ya yi zafi. Can ya ce, “Gaya mun irin hirarrakin da kuke da Baba Sa’idu?” Na gaya masa irin nasihohin da yake yi mun ne kadai a kan sallah, sai irin wulakancin da Inna na ke mishi. Na ce, “Abin yana damuna Ya Faruq, shin me yasa Inna ta tsani Baba Sa’idu ne? Me ya yi kullum yake cewa ta yafe mishi tana wulakanta shi?” Akwai alamun rudewa sosai a tare da Ya Faruq, ya rasa amsar da zai bani, daga bisani ya daure ya ce, “Ban san yaushe kika koyi sanya ido a kan abin da bai shafeki ba. Ba tare kika tashi kika gansu ba Abu? To ki bisu da yadda kika gansu, nima ban sani ba. A yanzu haka Farfesa ya turo ni ne da wani al’amari mai girma wanda ban san yadda zan yi in shawo kan Innarki ba, don Malam ba matsala bane sai ita din mai tsatstsauran ra’ayi sa rashin kaunar duk wani al’amari daya shafi Baba Sa’idu. Ya turo ni ne da zungureriyar wasika zuwa ga Malam da ita Inna, kan su bada ke in tafi dake, an samar muku makaranta keda su Ifty. Amma sanin kanki ne wannan ba karamin aiki bane ya hada ni dashi, tunda shima ya buga ya kasa balle ni? Sannan Inna Rabi na ganin mutunci na fiyeda kowa, ina tsoron abinda zai zubar da wannan mutuncin, ya rana na kaunata a zuciyarta. Saidai na gamsu da hujjojin da ya bayar.” Daidai nan Malam ya karaso ya tadda mu, wani almajirin sa Matt ya rikon masa leda, da alama irin tsira da balanghiga gu da ya saba kawo mana ne duk dare, yana murmushi yace “yaya dai? Wa da ‘yar kanwar shi ana shawara ne?” Muka yi murmushi dukkanmu tare da sunkuyar da kai kasa. Yace “ku tashi mu shiga gida, bana son zama cikin hasken farin watannan, yana gadar da ciwo”. Muka mike muka shiga gidan gabadaya, shi da Malam suka shige turakar Mallam din, nikuma nayi daki na kwanta. Inna na bisa sallama tana ta sallah, wannan al’adarta ne na duk daren juma’ah kwana take sallah. Ta kan ce, “wanda ya bari du iya da Kyale-kyalenta ya rudest, ya manta da ambaton Allah da yawa ita tuba a gareshi, haqiqa yana cikin rafkanannu. Don haka nima ta koya min, har yabi jinin jikina. Sau tari na kan bita muyi ta yi, har sai kafafuna sun sare, yawun bakina ya bushe. A can dakin Malam me suka ce – me suka ce oho! Was he gari da asuba hi dai naga fuskar Malam babu annuri. Bayan yayi sallar asubah gari yayi Dan shaawa! Haka, misalin karfe shidda na safe ya shigo dakinmu. Inna na bisa sallaya tana lazumi har zuwa lokacin ba ta mike ba, ni kuma ina kwance bisa gado bayan da na ida sallah ban iya na koma ba. Na dai rufe ido ne kawai cike da tunanin al’amuran rayuwa masu rudarwa, su sanya zuciyar mutum cikin wani hali na rashin sanin tabbas da rashin jin dadin rayuwar ko ta yaya. Ba a rasa ci ba, ba a rasa sha ba, ba a rasa suttura ba amma zukatan al’umma babu dadi. Wannan ita ce hakikanin rayuwar da ke faruwa a cikin gidanmu. Da alama Malam bai san idanuna biyu ba. Ya ce, “Rabi’atu na zo miki da umarni ne ba yardarki nake nema ba. Ki yi duba izuwa rayuwarki, tun daga farkon ta har karshen ta cikin kunci take. Kina nufin a haka za ki kare ta? Wannan hukuncin da kika yanke na tsanar Sa’idu da al’amarinsa ba shi zai sa ba, ba kuma abin da zai rage sai dai ya kara dagula rayuwar Zaynabu. Ki yi hakuri ki ba shi ita ya sanya ta a makarantar, tunda BAKI FISHI IKO DA ITA BA! In kin dauki al’amuran rayuwa da sauki, watarana sai labari, za ki ga kamar ba a yi ba. Ke baki bar zuciyarki ta huta ba, ita yarinya kin hanata amfani da damar da Allah ya bata ta yin ilimi, wanda zai zamo gata ga rayuwar duk da ta tsinci kanta a gaba. Ya gaya mun hujjojinsa cikin takarda, kuma na gamsu. Ya yi alkawarin duk hutu Abu za ta zo nan tare da Faruku, in ta kare hutun sai a zo a tafi da ita. In kin sanyata a daki kin kulle me za ki yi mata itama me za ta yi miki? Ki duba ki ga duk tsararrakin ta sun wuce ta a karatu, shekarunta goma sha biyu, amma har yau ba ta fara sakandire ba sai yaushe? Sai shekarun karatun sun wuce mata? Su Hafsisi duk bana za su shiga aji uku na sakandire, amma ita ki kama kina mummukewa a daki haba Rabi! Ni mijinki ban ji dadin ki ba, abokan zamanki basu ji dadin ki ba, haka ‘yarki hakuri take da ke, duk da ta san babu wata uwa a duniya mai hali irin na tata uwar. Wannan kaunar da kike wa Abu wace iri ce tunda kuwa ita ba ta ganta ba? Wannan ba so bane, kwarar ta kike yi….. in gaya miki gaskiya in baki barta ta bishi ba za ta kullace ki, ko da ba ta gaya miki ba. Kuma IDAN NURATU CE BA HAKA ZA TA YI BA..…!!!.” [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Wata irin rayuwa ya yi mai ban tausayi da rashin galihu, amma a komi Malam Ali da mai dakinsa sun tsaya mishi. Ko taron iyaye da ake yi a makaranta Malam ne yake wanke kafa ya je a matsayin mahaifinshi da ya rasu tun bai yi nisa da karatun ba. Haka ranar taron iyayen yara Rabi ke shan lullubi ta je matsayin mahaifiyar shi, duk da idan ka dube ta za ka san a haife ba ta haife shi ba. Don haka a girman Sa’idu, da ci gaban da aya samu a rayuwa, baya da kamar Malam da Inna Rabi. Ka’ida ne duk karshen wata ya zo duba su, ya cika su da abin arziki kamar don su kadai yake nema, baya ga tarin iyalin da yake da shi a can Sokoto. Na taso cike da dokin, ranar zuwan BABA SA’IDU, wadda a kullum take lissafe cikin kaina. Ba don komai ba sai don na san ranar duk da ya zo, to ni ranar take sallah. Sabbin dinkuna da kayan ‘ya’yan gayu da yake kawo mini kamar shago za a bude mini, cakulet da biskit kamar (super-market) din su gare shi, don haka duk hakorana suka cinye da zaki suka gwaigwaye kamin in soma famfara, sabbin littattafai da sabbin uniform wannan duk wata ne sai ya sake mini, don haka nake daban a cikin yaran gidan dama garin Gwarzo baki daya, babu ‘yar gata kuma ‘yar gayu kama na. Ga kuma kyawun sura. Ribbon kuwa Baba Sa’idu dozin-dozin yake saya mani kala daban-daban. Ya Faruk ya zauna ya jera min su reras a kaina, in zamo kamar wata ‘yar Turawa, sai ka rantse da Allah Baba Sa’idu bai san ciwon kudinsa ba in dai a kaina ne. Allah ne ya hada jininmu da wata irin kakkarfar kauna, sai dai babban abin da ke bani mamaki, yake kuma sanyaya min jiki shine, duk wannan hidimar da Baba Sa’idu ke min, ko kadan baya burge Rabi, haka ko sau daya koda wasa bata taba sanya hannu ta taba kayan da suka fito daga hannun Baba Sa’idu ba. Kwankwalatin lemu ne da ni guda talatin, a karkashin gadon Rabi me fameka, kullum sai in ciri daya in jefa a kofi, ranar da suka kare kenan ita ce ranar zuwan Baba Sa’idu. In ina wannan kirgen, Rabi kallona take kawai, sai dai ba ta magana, na san tsabar takaicina ke hana ta magana. A raina sai in ce, “Inna ai ke rayuwarki sai ke, tunda Malam da Ya Faruk ma basa burgeki, shi Baba Sa’idu wane ne da zai maki gwaninta?” Ni dai haka nan nake son Baba Sa’idu saboda kirkinsa, saukin kai da haibarsa, ba shi da girman kai ko kadan, haka yadda yake sonmu ni da Ya Faruk yake kuma janmu a jiki, ko ‘ya’yan cikinsa basa samun hakan. Tun karatun sakandire ya so ya dauki Ya Faruk ya koma gidansa ya yi karatu a can Sokoto, Ya Faruk ya ki don a lokacin babu wani babban da namiji a gidan kusa da Malam sai shi, sai ko yanzu da manyan almajiran Malam su Lawal da Harisu suka tasa. Baba Sa’idu Malam ya dankawa alhakin nemawa Faruk gurbi a Jami’ar Ahmadu Bello, inda Faruk ya jima yana burin shiga, sai dai shi Farfesa so yake Faruk ya je UDUS don ya zauna kusa da shi, don haka ba tare da shawara da Faruk ba, a can Danfodiyon ya nema masa gurbi mai kyau, inda za ya karanci (computer-science). Dole Faruk ya koma gidan Farfesa kwata-kwata, sai bayan watanni uku-uku yake zuwa mana hutu. Na yi kewar Ya Faruk ba kadan ba, na yi kewar kulawa da kaunar sa, na yi kewar komai nashi, domin shi Yaya ne mai karamci da nuna kauna, mai muhimmanta zumunci da kyautata shi, mai gudun duk wani abu da zai zubar da mutuncina da na mahaifinmu. To amma ni kaina ina son ya yi karatun, kasancewar sa babban burin rayuwarshi. Ya kan ce yana so ya zamo mutun irin Baba Sa’idu, yana sha’awar duk wasu halayen shi banda abu daya, yana son ya zama mai hidima da iyayenmu da al’umma kwatankwacin Baba Sa’idu. Kwaikwayon halayen Alhaji Sa’idu dole ne ga duk wani mutum da ya san ciwon kansa, mutum ne wanda ilimi, daukaka, da duniyar da Allah ya ba shi basu sa ya manta alkhairin da wasu tsirarun mutane su kai mishi ba, he’s really a model! Kullum cikin hidima yake da Malam da almajiransa, da lafiyar shi, aljihunsa da karfinsa a gwamnati, amma ko kadan wannan baya burge Inna Rabi. Kai ni sai da na fara wayo ma na lura inda wanda Innana ta tsana da gani a duniya, take kuma kyamatar abin hannunshi, to Baba Sa’idu ne. Daga sanda ta ji rurin motarshi a kofar gida, kasancewar karar motar shi daban take da ta duk sauran motoci masu zuwa wurin Malam, domin ba ta da kwaramniya sai dai ka ji wani irin suuuuu! Kawai, to za ta shige dakinta ta bame da sakata, har ni ba ta kara nema na sai ya tafi, don ta san inda duk yake cikin garin to ina nanike da shi yana ta haba-haba dani. Yau da dare har mun kwanta na tuna ban saka kwankwalatin zuwan Baba Sa’idu a kofi ba. Sadaf-sadaf na sauko daga gadon, kada motsina ya tada ita. To amma duhun dare bai sa na ga kwankwalatin ba, don haka na kunna aci bal-bal na zarosu daga kasan gado. Abin takaici abin bakin ciki, sai na taras baki daya an hade min su wuri guda baki dayansu, bayan sun kusa karewa. Na tabbatar Inna ce da ta zo shara dazu ta sharo su daga kasan gadon ta hade su waje guda. Kenan wannan watan ban san takamaiman ranar zuwan BABA SA’IDU ba. Sai nasa kuka, ina yi ina karawa har da shessheka. Gunjin kukana ya ta da Inna Rabi, ta zuro fararen kafafunta kasa daga gadon ta ce, “Kyautar Allah me ya faru?’ Cikin kuka na ce “Bayan kece kika hade mun kwankwalatan ZUWAN BABA SA’IDU???”. Ta yi shiru na lokaci mai tsawo, na dauka zagina za ta yi ko ta rufeni da duka, ko me ta tuna? Sai ta yi ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, “Ki yi hakuri Kyauta, ban sani ba na hade miki, amma gobe ba zan kuma ba”. Muka koma barci, amma har garin Allah ya waye idanuna basu rintsa ba, zuciyata ba ta bar tukuki ba, haka ban bar yin nannauyar ajiyar zuciya ba, yadda na ga rana haka na ga dare, na kuma tabbata ita ma Innar ba ta yi baccin ba sai juyi a kan gado. Kwanaki biyar da yin hakan, ina durkushe a bakin ramin da na haka don wanke allona a ciki, misalin karfe biyar na yamma, allo na nake wankewa don shiga sabuwar sura. A gefe toka ce a cikin dan kokon ludayin duma da zan shafe allon da ita kamin in sake yarfa wani sabon rubutun. Ina diban ruwa daga cikin kwarya ina wanke allon a hankali tamkar mai wanke jariri, na tallabeshi da hannuna na hagu cike da tunanin Ya Faruk dake Sokoto, kowacce wainar yake toyawa? Na yi murmushi ni kadai a raina ina kwatanta Ya Faruk a cikin babbar makaranta, na tabbata nan ba da jimawa ba zai bada mamaki. Domin ko da nike yarinya kankanuwa ‘yar kimanin shekaru goma sha biyu, na san samun maza irin Yayana, ba abu ne mai sauki ba. Faruk ko a cikin tsararrakin shi daban ne a komai, haka yake da aji na musamman, sannan jarumi ne ko ta yawan kunyaryakin da yake nomewa Malam, wanda aiki ne da almajirai goma majiya karfi ke yi. Shi ba wani mugun kyakkyawa bane amma namiji ne ta kowanne fanni, kuma baiwarwakin da Allah yai mishi suna da yawa, har ba zan iya lissafasu ba. Kasancewar shi da namiji guda daya amma Malam bai taba takaicin rashin ‘ya’ya ba. Ya kan ce, “Faruk daya ne tamkar da goma! Da haihuwar yuyuyu, gara daya kwakkwara, ta kowanne fanni yana alfahari da Umar-Faruk….!! Ban ji karar (horn) din mota ba ko kadan, nayi nisa a cikin tunanina, illa takun Baba Sa’idu na GIRMA da nutsuwa, da ya bakunci kunnuwana. Yana kwarara mana sallama da wankakkiyar muryarsa tamkar wani balaraben Madina, saboda yadda muryar shi ke fita tar-tar. Ita kanta Inna Rabi na san ba ta zaci zuwansa a wannan lokacin ba, kasancewar ranar Juma’a ce ba Asabar din karshen wata da ya saba zuwa ba, wannan tabbas ne, da tun kan ya shigo ta shige dakinta ta rufe. Da na wulwula allon na yar sai a kan gadon bayan Inna Rabi dake gefe tana barar gyadar miya, ji kake tim! Ba kuma tare da na san aika-aikar da na aikata ba na yi tsalle na rikeshi ina “Oyoyo Babana!” Mikewa daya Inna Rabi ta yi sai ji na yi tana fizgata tana cewa, “Gafara ki bawa mutane wuri”. Shi kuma cikin ladabi ya russuna rike dani tamau yana “Allah ya baku hakuri Inna, Inna Allah ya huci zuciyarku”. Ta ce, “Sakar min ‘yata na ce Sa’idu, na yi ma kama da wadanda kudi ke rudinsu, a yaudare su? Da zuciyar ba ta huce ba da na kawo yau ne?” Kanshi a duke, cikin tsananin girmamawa da kaskantar da kai, ya ce, “Bani da kudin da za na yaudareku dasu Inna!!! Har gobe ni almajirinku ne dake neman albarkarku, dake neman abin da za ya sanya a bakin salatinshi daga tukunyarku. Hakurin nan nake dada badawa, wanda har abada ba zan daina ba, ko da yawun bakina zai kare. Dukkanmu ‘yan Adam ne da bama sama da aikata KUSKURE, ‘yan adam ne da shaidan ya yi alkawarin janmu ga ba dai-dai ba, kamar yadda ya ja Ubanmu Annabi Adamu Alaihis Salamu. Amma da ya roki Ubangijinsa, sai ya yafe mishi bai barshi ya rafkana ba. To Ubangiji ma kenan yana afuwa a garemu balle ku mutane?” Ta fiddo fararen idanunta ta zube su a kanshi za ta fara lailayo ire-iren ashariyar da ta ke narka mishi kenan Malam ya shigo gidan rike da tazbaha yana ja, ya ce, “Subhanallahi! Rabi’atu meye haka? Me zan gani haka? Saketa mana, karyata za ku yi?” Ni kam sai kuka nake ganin Baba Sa’idu yana kuka, abinda ban taba gani ba. Ta sake ni bayan ta ja wani mikakken tsaki da wasu dunkulallun hawaye da suka biyo kumatunta, ta shige dakinta. Bammm! Ta danno kofa, muna ji bayan sakata da ta sanya har kuba tasa ta kara kulle dakin. Allah kadai ya san halin da take ciki a yau. Haka ya ci gaba da durkuson bai dago ba. Malam ya samu wuri ya zauna yace, “Sa’idu lokaci ya yi da kai da Rabi za ku fuskanci gaskiya, ku daina aiki da karya, lokaci ya yi da za ku fuskanci abin da ya dace, wannan rayuwar ina za ta kaimu? Meye amfaninta?” Ya dago ya dubeni yana murmushi. “Yanzu cikata in aike ta tukunna”. Baba Sa’idu ya cikani, ba tare da ya dago ya dubi Malam ba. Ya ce, “Maza Zaynabu-Abu a samowa Sa’idu ruwa a randar Inna Dubu”. Na ruga da gudu dakin Inna Dubu amma kamin in shiga sai da na rabe na share hawayen idanuna. Na ce, “Inna kawo sabon kwanon shan ki a bawa Baba Sa’idu ruwan randarki”. Ta ce, “Abulle ‘yar gidan Sa’idu, ko dai kema can Sokoton za ki bisu ne wajen Yayanki?” Na yi murmushi domin ta yi mun susa a inda ke min kaikayi, na ce, “Ai kema kin san Inna ba za ta bari ba. Tun yaushe Baba Sa’idu ke cewa in bishi muje Sokoto a sani a makarantar su Iftihal, in na fadawa Inna tasa ludayi ta bubbuge min baki”. Ko kamin na iso sun gama maganar Innana sun koma ta karatun Faruk da amfanin gonar Baba Sa’idu dake nan Gwarzo. Isowana duk suka maido hankulansu gareni suna min murmushin su mai cike da kauna. Tsakanin Malam da Baba Sa’idu na kasa tantance wanda ya fi kaunata, dukkaninsu abu daya nake gani cikin kwayar idanunsu tun ina jaririya. Na russuna na mika mishi ruwan randar Inna Dubu, garai-garai da shi, ga sanyi kamar na firinji, duk gidan shi muke sha, abin kamar karama, ruwan randar Innar Ya Faruk ya fi na randar kowa sanyi, gardi da ratsa zuciya. Don haka ne kowa ya zo cewa yake a debo mishi ruwan randar Inna babba, ban da Ya Faruk mai son na Inna Rabi. Ya kan ce shi ta fi mishi ta kowa sanyi, duk da a zahiri ba hakan bane, illa kasancewar shi wani mutum mai son faranta mata a koyaushe, da kokarinsa na gusar mata da bakin cikin dake damun zuciyarta, amma duka a banza, wai kirari a gidan kurame. Baba Sa’idu ya ce, “To Zaynabu ni za ni koma, yau ban kawo miki komai ba saboda nima tafiyar ban shirya mata ba. Na je taron ‘convocation ’ ne a nan cikin Jami’ar Bayero, na ga don me zan koma ban biyo ba tunda gani a cikin Kano?” Na ce, “Babu komai Baba Sa’idu, Allah ya kaika lafiya”. Ya ji dadin addu’ar da na yi mishi. Ya kamo hannuna ya ce, “To meye sakonki ga yayanki da su Aziza?” Na washe dukkan hakorana ina fara’a, don jin dadin ya tuna min da Ya Faruk wanda dama ke makale cikin raina. Na ruga da gudu dakin Inna Dubu inda na boye kullin (awara da yaji) da Innar ta soya dazu, kasancewar shi mai son ta. Haka kawai yake sayo waken suya (soya-bean) ya kawowa Inna Rabi ya ce tayi mishi Awara, ya yi ta ci yana dangwala yaji yana santi. Wani zubin ya kan ce, “Amma dai ana hadawa da kwai ko Inna?” Sai ta yi murmushi ta ce, “Eh, ana hadawa amma kwan wake”. Na dawo da gudu na kawo mishi, na ce, “Ka kai mishi wannan”. Bai damu da maikon da ya mamaye ledar ba ya karba ya sanya a aljihun farar sassalkar shaddar dake jikinshi da a kalla ta ba naira dubu talatin baya. Ya ce, “To ina na su Aziza?” Na sunkuyar da kai ina murmushi na ce, “Ai basu sanni ba, kuma su ‘yan gayu ne basa cin awara”. Daga shi har Malam dariya na basu. Ya ce, “Wa ya gaya miki haka? Kada in kara jin haka, dake dasu duka daya kuke, sai ma ke da kika fisu. Ke da kike da haddar Izfi talatin a cikin kanki, su ko ko izfi biyu basu haddace ba, wawaye ne kurum! In zan dawo zan kawo miki su suyi sati tare da ke, ki dinga koya musu irin karatun nan naki mai dadin sauraro, mai kira’ar ‘yan Aljannah (warshu), kin ji Zaynabu?” Na ce, “Na ji Baba Sa’idu. Allah ya kaika lafiya”. A ranar sai a dakin Inna Dubu na kwana, don Inna na har washegari ba ta bude kofar ba. Kayan abincin da Baba Sa’idu ya zo mana dasu su doya da dankali, da safe Inna Dubu ta kasa ta kaiwa kowacce kasonta kofar dakinta. Inna na bude kofa ta ci karo da tsarabar Baba Sa’idu, ni kuma ina gefe ina rubutuna a allo da ban samu jiya na yi ba saboda zuwan Baba Sa’idu. Sai gani na yi ta samu fanteka tana jida tana fita dasu tana kaiwa almajirai. Tana dawowa ta hango katon din taliya da na kayan shayi a gefe, suma ta kinkima ta je soro ta rabar. Daga matan gidan har ni babu wanda ya yi mamaki, kamar yadda babu wanda ya daga ido ya dube ta, don in da sabo mun saba ganin abin da ya fi haka. Akwai sanda ta zuba turamen Holland da ya kawo musu da sallah cikin masai, ta gidan gabadaya, ranar ne ta ga bacin ran Malam irin wanda ba ta taba gani ba, Inna Dubu ce ta gayamasa, yace, “Wannan almubazzaranci ne, kuma masu almubazzaranci iyalan shedan ne. In bazata daura ba to ta bayar, amma ba za ayi wannan almubazzaranci a gidansa ba”. A dan tsukin na dage da addu’ar Allah yasa in ci makarantar sakandiren da nake so wato GGSS Kabo, ba don komi ba sai don su Hafsisi ‘yar dakin Inna Dudu da Indo dake can aji biyu ‘yar dakin Inna Rakiya, mun shaku dasu sosai, musamman Hafsisi da take kusan tsarata, shekaru biyu kawai ta bani. A satin Ya Faruk ya zo, amma ba jimawa zai yi ba don basu yi hutu ba. Na rasa inda zan sa raina in tsaida murnar, haka shima. Yayo min saye-saye masu yawa har da sabuwar jakar makaranta da wata na’ura mai koyar da harshen Turanci. Na ce, “Ya Faruk ina ka sami kudi haka, kai da kake karatu?” Ya ce, “Karatun ma ai don ku nake yin shi Kyauta, haka komi nawa naku ne. Kada ki damu da wannan alawus din dalibai ne da ire-iren kudin da Farfesa yake bamu ni da Imran wanda ni bana bukatarsu, saboda ci da shana da makwancina duk a gidansa yake. Iyalin Farfesa mutane ne masu karamci da suka san hakkin dan adam, suna kyautata mani sosai, haka shima Abban komi bai banbanta ni da Imran”. Na tambaye shi ko wane ne haka? Ya ce, “Shine babban dan Farfesa tare suke karatun. Ya ce, “Imran mutum ne mai kirki da dadin mu’amala, yana da saukin kai kamar Farfesa, I would like you to meet him even once (zan so kwarai watarana ki hadu da shi ko da sau daya ne). In kika zauna da shi wuni daya, za ki so ci gaba da zama da shi muddin rayuwarki”. Yawan labarin Imran da Ya Faruk ke bani, na irin rayuwar shi da yadda yake tafiyar da ita, sai na samu kaina da son ganin sa. Bayan wata guda jarrabawarmu ta fito, inda na ci makarantar ‘yammata ta gwamnati dake garin Gashuwa ba inda na so in samu ba. Muka yi ta kuka ni da Hafsisi, sai Malam ya ce, “Me ya yi zafi? Bari Sa’idu ya zo gobe in da abin da zai iya a kai, a maida ke Kabon”. Baba Sa’idu bai zo ba sai a sati na sama, saboda ya yi tafiya zuwa Brunei. Muna bakin motarshi ya miko min wata ‘yar akwati kankanuwa mai tsananin kyau, ya ce, “Ga tsarabarki Zaynabu”. Na karba cikin mamaki ina juyata a hannuna, cikin raina ina raina ‘yar tsarabar a zuciyata, tunda kuwa akwatu ya saba ciko min da kaya a duk sanda yai tafiya irin wannan. Da kyar na bude akwatin cikin gidadanci. Wani haske ne ya dallare min ido, musamman da yake a cikin rana ne. Duk da karancin shekaruna a lokacin jikina ya yi sanyi, na san ko yaya ne wadannan zobba guda biyu ba karamin abu bane. Kuma a matsayina na ‘yar Malaminsa kawai, ban kai matsayin da zai mallaka min wannan abu mai daraja ba. Ya lura da rashin kuzarina, ya kamo hannuna muka shigo soron gidan, almajiran Malam na ta gaishe shi yana yi musu kyautar shi da baya gajiya. Sai da suka dauke kafa ya ce dani cikin murya kasa-kasa “Ko me Inna za ta yi dake, kada ki bari ta yi kyauta da zobban nan naki. Ba gwal bane, ya fi zinare daraja, kusan rabin abin da na mallaka ne. Ki kula dasu sosai, a nan gaba za su yi miki amfani”. Sun dade suna magana da Malam, inda ya yi mishi zancen makarantata. Kai tsaye ya ce, “Ai tuni ya yanke shawarar tafiya dani Sokoto, ya sanyani makaranta tare da su Aziza in ba haka ba, ba zamu taba shakuwa ba”. Malam ya shiga girgiza kai yana cewa, “Ba zai yiwu ba, Sa’idu, na ce ba zai yiwu ba. To a barshi a hakan!”. Ya tashi ya karkade babbar rigarsa ya barshi a nan a duke a kan buzu. Ya fi awa daya a hakan kamin ya mike ya shigo gidan. A lokacin Rabi na bakacen masara a fai-fai, ko kallon shi ba ta yi ba, ya russuna a gabanta ya ce, “Barkan ku da yamma Inna”. Ba ta fasa abin da take ba, haka ba ta dago ido ta dube shi ba sai bakacenta take cikin kwarewa, tana huro mai dusar masara a fuska, kai ka ce da sassaken dutse yake magana. Ina tsugunne a gefe abin yana mun ciwo a rai, na kasa daurewa sai na sa kuka. Na yi niyyar in je in kama hannunshi in mikar da shi daga wannan durkuson da ya yi kamar na mai neman gafara a gareta, kada gwiyoyinsa suyi ciwo, amma tsoron abin da za ta ce dani ya hanani. Daman a daren jiya ta ce mun, “Idan abin duniyar da Sa’idu ke kawo mana ne yasa nake neman juya mata baya, to za ta mika ni gare shi mu tafi, kuma ko a lahira kada in ce na santa”. Wannan tunani da na yi ne yasa nayi hanzarin shiga daki na kwanta a dandaryar kasa, nayi ta kukan tausayin Baba Sa’idu. A ganina duk wulakancin da Inna ke masa shi yake jawowa kansa da yake shiga sabgarta, tunda ta nuna ba ta ra’ayi meye dole zumuncin? Ko bashi da uwa a duniya ya dace ya fita sabgar Inna Rabi, tunda ba ita ke raba wuta da aljanna ba. Haka na yi ta faman mummuke ‘yar akwatun zobunana cikin bante na (dinkakken siket mai hade da shimi da ake dinkawa a kauye). Don na tabbata muddin Innata ta ga wannan akwatu, to sunan ta badaddiya, koda kuwa a ce za ta sayi duniyar ne da abinda ke cikinta. Na matsu matuka da zuwan Ya Faruk, na yi matukar damuwa da zuwansa. Abubuwan nan sun addabe ni, na kuma tabbatar babu mai amsa mini duk duniya in ba Faruk ba. Shi kadai ne zai tsaya ya fidda ni duhu, ya ganar dani al’amuran Innana da suka fi karfin hankalina. Ina zaune bisa kujera ‘yar tsugunne ina cin magarya, yayin da Innana ke kiciniyar daura sanwar dare bayan ta sauke rogon da ta dafa. A gefe Innar Faruk ke surfen gero, Inna Rakiya da Zulkiflu wani yaro da take riko suna tuyar gyada marau-marau da take sayarwa. Daga zaure almajiran Malam ne suka rude da karatu kamar sa tsaga gidan, cikin muryoyin su daban-daban, da surorin su daban-daban, ba mai jin na wani. Inna ta dan juyo ta dube ni ta ce, “Yau ba a zuwa karatun ne Kyauta-Abu?” Na ce, “Rubutun da na yi nake jira ya bushe Inna”. Wata yarinya da ba ta kai ni ba, ta yi sallama cikin sassanyar muryarta ta shigo, hannuwanta duka biyu rike da ledoji, jikinta da fuskarta kamar an wanke a inji sumul-sumul da ita kamar tarwada abin sha’awa. Gaba daya muka amsa mata banda Inna da ta juyo ta kalle ta, ta juya ta ci gaba da abinda take. Na mike da sauri na amshi ledojin hannunta ina yi mata sannu da zuwa, muka zauna bisa tabarma, sai zare ido take na rashin sabo. Inna Rakiya ta ce, “Kamar Azizan Sa’idu, ‘yar wajen Hajiya Azumi, ina abokiyar tagwaitakar taki?” Ta ce, “Ba Aziza ba ce Iftihal ce, Aziza tana Porthearcourt”. Inna Dubu ta ce, “Ikon Allah, kamar taku ce har ta baci, wa zai iya banbance ku banda iyayen ku?” Ta yi murmushi da dan bakinta mai kyau. Jin an ce diyar Baba Sa’idu ne sai na yi ta kallonta, nan da nan na ji ina kaunarta. Dan mai kaunarka, ai abin kaunar ka ne. da gani babu tambaya, ko daga yanayin fatar jikinta da irin kayan da take sanye dasu, tana kuma yanayi da Baba Sa’idu da irin Hausarshi ta Sokkotawa. Cikin murmushi na ce, “Dama ke ce Iftihal?” Ta gyada kai tareda cewa, “Wa ce ce Anti-Abu?” Na kai duba na ga Innana wadda ko juyowa bata kara yi ba. Inna Rakiya ta zuba gyada da ruwan sha a babban kwano ta kawo mata tana nuna ni, “Ita ce Zaynabu Abu, ‘yar’uwarki gata nan”. Wani uban kallo da Inna ta juyo ta yarfa mata kadai ta san ta yi laifi, ta yi karambani, ta yi ba dai-dai ba. Amma ita din sai ta yi murmushi cikin bagararwa ta kara da cewa, “Ga Innar Abu nan tsugunna ki gaishe ta Iftihal”. Ta kai gwiwoyinta kasa ta ce, “Inna ina wuni?” Sai da ta yi kamar ba za ta amsa ba, can dai ko me ta tuna? Ta daga mata hannunta na dama ba tare da ta juyo ba. Banda dai ina tsoron Inna, da na tambayi Iftihal ina Baban yake? Sai na buge da ce da ita, “Ya Faruk yaushe ya ce zai zo ne?” Ta ce, “Ai sun tafi Bindawa shi da Ya Im, amma ina jin ya ce daga can nan zai taho, kullum yana zancen ki, yana cewa zai kawo mu wurin ki, koyaushe kuma sai ya yi tafiyarsa. Yau ne da na ji Baba zai zo na ce zan biyo shi tunda Aziza ba ta nan, shine ya taho dani”. Inna Dubu ta wanke min dattin raina da cewa da ita “To ina kika baro Baban?” Ta ce, “Yana zaure tare da Malam din nan gidan, amma ya ce komawa zai yi, nice zan kwana tare da Abu, idan zai koma jibi zai zo mu tafi”. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Mafari kenan da wannan ya sayo min tsana mai tsanani a wurin Hajiyar su Hassan da iyalanta, sai da na gwammace dama Abba bai ji al’amarin ba. Tsakanin mace da mijinta sai Allah, bamu san ya a kai suka shirya ba, mun dai gansu kuma sun hade abinsu. Amma Mama ta ce take jin Imran (dan lelen Abba) ne ya yi waya ya ba Abban hakuri. Na sha kimantawa raina ko ya Imran yake? Yadda abin ya bayyana a gareni shine, duk gidan kowa na son Imran, babba da yaro kowa bakin shi baya daina ambaton (Ya Im) kamar yadda na ji suna kiran sunan a takaice. Na san zai zamo mai kyawun sura kamar su Hassan, mai kyan hali kamar Baba Sa’idu. Tun ban ganshi ba na san dole ganinsa ya fi jin sa. Iftihal kan ce; “A duniya ba mutum irin Yayana Abu!”. Na tambayi kaina mai yasa shi din suke son sa, basa son kannensa su Hassan? Me yasa zai kasance na daban din, kamar yadda suke ikirari? Abubuwa da yawa kan sa a so mutum, muhimmi shine halayensa. A ganina ni ya dace in fadi cewa ba mutum irin Yayana Faruq amma ba su ba. Na kan so Ya Faruq in kaunace shi, kauna irin ta su Iftihal ga Yayansu, saboda halayensa. Faruq mutum ne mai tsarge gaskiya komi dacinta, ko da hakan na nufin ya bata maka ne, hakan ba zai dame shi ba in har ya gaya maka ita wannan gaskiyar. Ba ya shiga abin da ba ruwan shi, baya da karya, baya da daukar duniya da zafi. Babban abin da yake burge ni da shi shine, addininshi da gudun sabon Allah, a ko da yaushe yana kokarin fin karfin zuciyarshi a kan abinda take so, musamman idan ya fahimci wannan abun ba alhairi bane a gare shi. Idan kuwa aka juya ta bangaren halitta, to su Faruq sune ‘maza’ da za a kira su da wannan sunan suyi gaggawar amsawa a ko ina. Ga tsayi ga zati, irin wadanda kowacce mace za ta yiwa kanta burin mallakar su. Tunda na taso a rayuwata bani da abin tsoro irin MAGE, na tsani mage, ina tsoron mage tun ina mitsitsiyata. Idan na ga mage na kan firgita ne ko in kwalla kara. Idan kuwa ta hada yankwalallen jikinta da nawa, na kan suma ne ko in fita hayyacina, in yi ta firgita a yayin barci. Wannan dalilin ne yasa duk son kiwon mage da Malam ke yi ya hukura. Rannan muna dawowa makaranta a motar yara (school bus), dama kullum sai an fara dauko su Hassan da suke da nisa, sannan a biyo ta makarantar mu a debo mu. Mun dauko hanyar gida Hassan ya ce, “Wai Rufa’i baka san magen gidan su Na’im ta haifi ‘ya’ya har guda goma ba? Suna nan baka gani ba in suna boxing abin sha’awa”. Jauhar ya ce, “To su sammana man ko guda uku ne muyi kiwon su?” Rufa’i ya ce, “Ka ga ko Hajiya na son missa, don da tana da (Laura) da ta mutu ne ba ta sake samun wata ba”. Hassan ya juya ya ce da direba, “Maza kamin mu shiga gida juya kaimu gidan su Na’im”. Tuni Shehu direba ya cika aikinsa. Ban san sanda na fashe da kuka ba na ce, “Don Allah don Annabi Hassan kada ku amso ‘yar mussan nan”. Rufa’i ya ce, “To ‘yar iko da gidan Uban wasu, idan Malam mai almajirai ne ya sayi gidan sai ki hana mu zuba mage”. Hassan ya ce, “Bar ‘yar banza, mai bakin baki irin na karuwai. Tunda an hana mu ce da ke BARAROJI to SADAKA-YALLAH ce??? Suka bude motar da kafa fut! Suka shige gidan mataimakin Abban su. Basu dade ba sai ga kowanne dauke da farar babyn mage, in ban da mazari ba abinda jikina yake. Suna shigowa suka watso su jikina. Da na kwalla wata azababbiyar kara sai da suka razana dukkansu, na mimmike ba ko kwakkwaran motsi balle kyakkyawan numfashi. Iftihal tasa kuka ta ce, “Ai ga shi nan kun kashe ta, wallahi sai na fadi ma Abba”. Shi kansa Shehu direba ya tsorata, ya ja motar da gudu yana cewa, “Ku dai Hassan baku da kirki wallahi”. Yana sanya hancin motar cikin gate din dai-dai lokacin da Faruq ya yi parking karamar Honda Prelude ta Imran, suka fito a tare, dukkaninsu sanye da kanyan NYSC, bakin Abia, zuwan su garin kenan. Azizah ce ta fara fitowa daga motar a rude tana kiran “Ya Im!”. Shi ko Faruq ido yake warawa ya ga bullowar Abun shi, ya ga wane GIRMA da wane irin kyau ta kara, wane irin sauyin rayuwa ta samu a tsayin lokacin da ya yi bai ganta ba? Kullum, cikin sabani suke, sau tari duk sanda suka zo Sokoton daga Abia, wanda kwata-kwata ma zuwan su uku cikin shekara daya, za su tarar su kuma anyi musu hutu suna Gwarzo, sanda suke Gwarzon su kuma sun dawo Sokoto abin dai kamar shiri, amma ya faru ne cikin ikon Allah. Kuma gareni sai ya zamanto rayuwa da su Iftihal ya debe min kewar Faruq din kusan kashi saba’in cikin dari. Azizah ke fadin “Ya Im, su Hassan sun zubawa Anti Abu mage ta sume mana a motar”. Gaba daya Imran da Faruq suka yo motar, Imran ya riga Faruq dauko ni. Wannan shine karo na farko da ya daura idanun shi a kan Abun-Faruq, Abun-Baba Sa’id. Maimakon ya yi sauri, tafiya yake dauke da ita a hannun shi tamkar wanda ya taka kaya, ko ko wanda kwai ya fashewa a ciki. Ganin irin tafiyar da yake yi ne ta marasa kuzari ya sanya Faruq karbe Abun daga hannunshi zuwa dakin Mama. A ransa yana cewa, “Ashe Imran duk wannan physique nashi ragon maza ne, mace wannan kamar ‘yar shilla ya kasa daukar ta”. Mama ce ta yayyafa min ruwa na farfado tana shafa kaina tana zagin su Hassan kaman ta ci babu. Farfadowa na yi ina makyarkyata, hawaye na tsiyaya ta gefen idona, fadi nake ina maimaitawa, “Mage ce fa a cikin jikina Mama”. Ta aza kaina bisa cinyarta ta ce, “Ba wata mage, sai ni sai Ya Faruq, gashi nan ya zo”. Ni ko na dage, “Gata nan fa a hannun su Hassan har guda uku wallahi….” A ranar dai daga ni har Mama da su Imran babu wanda ya kwanta da wuri, don da na rufe ido barcin ya fara fizgana zan farka a firgice ina kiran mage. Washegari Imran ya tattara magen ya sanya a buhu ya ba Shehu direba ya ce ya mai da inda suka karbo. Ai kuwa a ranar su Hassan sun sha tafka da belt, sunyi kuka da majina, daman Imran ba daga nan ba (very-disciplined-brother). Duk hakan bai ishe shi ba sai da ya sanya su duka cikin store ya kulle, ya hana masu aiki basu abinci tun safe har yamma. Hajiya Sa’a ba ta san me ake yi ba sai yamma lis ta dawo aiki. Ta yi murna da zuwan Imranan ta da kammaluwar bautar kasar sa, suka barke da hirar yaushe gamo irin na Da da Uwa a babban falon ta. Ta nemi su Hassan ta aika su kawo mai lemu, ya ce, “Ai suna (store) ya kulle su”. Ta ce, “Dalili?” Ya yi kwafa cikin takaicin su da ya ki sakin sa har zuwa lokacin, ya ce, “Sun san yarinyar nan ‘yar Malam ba ta son mage suka watsa mata maguna ta suma, har yanzu ba ta san inda kanta yake ba”. Ga mamakin shi sai ta buga tsaki ta ce, “Shine me? Gidan Uban su ta zo, ban ga dalilin da za ta takura su ba ta hana su yin abin da suke so. In ba ta son magen ta koma gidan Ubanta mana? Sallamamme kawai ka san me ake a cikin gidan ne? A kan Buzuwar nan aurena da ubanka ya kusa mutuwa, da sai dai ka dawo ka nemo ni a kauyenmu, in baka sani ba in gaya maka dalilin cewa da ya yi in tafi kenan kwanakin baya da na gaya maka a waya don sun ce da ita BARAROJI, ko ka bude min yara yanzu-yanzun nan ko in sabar maka wallahi”. Ba musu Imran ya bude su Hassan domin dai shi mutum ne mai biyayya da baya saba umarnin iyayen shi ko ya ya ne. Ya samu Faruq a dakinsu yana cin abinci, ya zauna bakin gado ya dafe kai ya rasa abin da ke mai dadi, anjima kadan ya yi tsaki ya girgiza kai duk sai ya ba Faruq dariya. Ya ce, “Kai Imran ya ya za ka yi when you become a father? (in ka zama uba) baka san sha’anin yara bane?” Imran ya sake yin tsakin ya ce, “Ni ba wannan ke damuna ba, maganganun Hajiya ne ban ji dadinsu ba, ban gane inda ta dosa ba. Ita fa babba ce, da ya dace ta dauki kowa nata ne a gidan nan, duk da dai na san ita mai nuna son ‘ya’yanta ne, amma saboda Allah su Hassan basu yi laifin da suka cancanci a hukunta su ba?” Faruq ya dafa kafadunshi cikin murmushi “Common dear, don’t talk about this matter again, plz…” Shima sai ya share zancen bai kuma yin shi da Faruq din ba, to amma sai ya rika jin nauyin Faruq din ta yadda zai ga mahaifiyarshi a matsayin maras tunani, ga Faruq din shi bai dauki al’amarin wani serious ba ma. Kwana biyu na warware case din mage ya wuce, sai dai cike nake da tunanin mene ne BARAROJI mene ne SADAKA-YALLAH? Wannan tambaya ce da ta dade tana cina a rai, na kuma rasa wanda zan yi mawa, don haka da na ga abin ya fi karfin tunanina, dole na yakice shi karfi da yaji. Imran dogo ne baki kakkaura, sai dai bai kai tsayin Faruq ba, amma ya fishi kauri da fadin kirji (physique), yana da kyakkyawar sura sosai, ya aje zagayayyen gashin baki dan siriri wanda ya tafi ya hade da kauraran zagayayyun lebban shi masu sulbi. Yana da hakora masu haske, jerarru kuma masu sheki. Komai nashi attractive wato mai daukar hankali ya dube su ko da bai yi niyya ba. Kallon yanayin fatar jikinshi kadai ya isheka kimanta irin hutu da jin dadin da yake ciki, haka idanunshi za su nuna maka tsantsar ilimin da ke cikin su. Ba a fiya son mace mai kamun kai ta fiya sanya idanun ta sosai a kan maza irin Imran ba, domin ba wuya za a aikata zinar ido. Wanda kuma shi abin ya zo ne da halittar shi ba wai da gangan yake yi ba. Yana da yawan amfani da karamin gilashi (medicated) ba don lalura ba sai don kara karkon idanu, haka nan Imran baka raba shi da cin biskit din nan na alkama (hob-nobs), yana da fada sosai kamar barkono, amma in ka fahimce shi ya fi ruwan sha saukin sha, raini ne baya so. Shine babban da a ‘ya’yan Farfesa, sun haife shi a kasar England zamanin da shi Farfesa yake karatu, inda ya samu ilimin firamare da sakandire. Don haka ne in yana lallausar Turancin sa ba za ka so ya daina ba. Sai bayan haihuwar shi da kimanin shekaru goma, sannan aka haifi Hassan, Rufa’i ya biyo baya sannan Jauhar da dan karamin su Aliyu da Baban ya sanyawa sunan Malam Ali, suna kiran shi Haidar. Sai da ya fara aiki a UDUS ne ya auri Azumi, wadda take basakkwata usul, kuma diyar wani abokin shi Farfesa a nan Sokoto wai shi Dr. Isma’ila Taura, ya ganta ne ranar ba da shaidar (Degree) ga daliban shekararsu da matsayin da ta fito da shi ne (best overall student in MBBS) na shekarar su baki daya. Yana daukar lasifika abin da ya bude baki ya ce a filin taron shine, “Idan Azumi ba ta da aure shi V.C zai aure ta, wannan kawai shine kyautar da yake jin zai ba ta ya nuna kwazonta a duniya. Ba kuma tare da ya ganta ba, tsohuwa ce ko yarinya ce?” Gaba daya filin taron rudewa ya yi da sowa, masu ihu na yi, masu kabbara na yi da sanyawa abun albarka. Babanta ne ya shige mai gaba ya ba shi auren ta. Ita kanta ta san ba karamar sa’a ta yi a rayuwar ta ba. Imran da Faruk na tare tun daga farkon karatunsu na Jami’a, wato tun dawowar Faruq Sokoto, sun shaku sun kuma amince da juna, domin halayensu duk kusan daya ne, daman an ce wai sai hali ya zo daya ake abuta, wannan haka yake. Halayensu duk kusan daya ne, nutsuwar Imran daban take da ta sauran ‘ya’yan Farfesa, mutum ne da ya san ciwon kansa kwarai, yana adawa sosai da aqidun Malam Bature, yanayin rayuwar shi na Sokkotawan usli ne ziryan, hakan yanayin sutturarshi shadda ne, caftan ko babban riga a kullum, kai ka ce wani magidanci ne, da wuya ka ganshi da wani kaya ba shadda da hula ba, ra’ayinshi kenan. Bayan kammala karatun su sun samu an yi posting din su gari daya yin bautar kasa, wato jahar Abia, duk da ba fanni daya suka yi karatu ba, shi Imran ‘civil engineer’ ne. Sanda na kai aji hudu a sakandire duk wasu alamomin girma na ‘ya mace sun soma bayyana a jikina, da yake ban fara karatun sakandire da wuri ba, ni kaina na san na sauya wane shekarun baya. Abin nufi, halittar jiki da tsarin rayuwa. Zan iya kimanta shekaruna goma sha biyar a lokacin, mun yi sabo sosai da Imran duk da cewa ba zaman gidan suke ba suna fafutukar neman aiki. Ba zan manta da yadda sunan “Abu” ya bace min a shekarar ba, ta dalilin Imran. Ya dauko mu ne daga makaranta yana tuki ina gaban mota, ya ce, “Shin wai ke ya sunan ki ne?” Na dube shi galala! Baki a bude ciki da mamakin wai duk kiran nan da ake Abu-Abu bai san sunana ba? Wannan ai rainin hankali ne, don haka na juyar da kai ban amsa ba. Daga bayanmu Iftihal ta ce, “Kai Ya Im, da gaske baka san sunan ta ba?” Ya ce, “Gaskiya ban sani ba, na ji dai kuna cewa wani abu wai “ABU”, ni ko na san kyakkyawar yarinyar kamar wannan kallo daya za ayi mata a san ba sunanta Abu ba”. Gaba daya suka tintsire da dariya, ni ko na yi murmushi kawai. Ya kafa mun ido kamin ya mai da hankalin shi a titi cikin son karantar karbar da na yiwa zancensa. Na kalli can wani gefen daban, cikin raina ina cewa, gaskiyan Iftihal ne, gaskiya ne ba mutun irin Yayan ta! Komi nashi mai ban sha’awa ne, hatta furucinsa. Azizah ta ce, “A school ma ba a ce da ita Abu sai Zainab”. Ya ce, “That is good, ZAYNAB, daga yau cikin ku kada wanda ya sake ce da ZAYNAB (ABU)”. Wannan shine mafarin al’amarin. (Takori). **** Na kwanta a daren nan ina maimaita kalmar “ZAYANB” da Imran ya ambata, na fadi ya fi cikin carbi, amma ban ji na fadi dai-dai ba irin yadda shi ya furta. Na yi tunanin abubuwan da suka faru a ranar tare da Imran na kasa mantawa. Idanuwanshi suka sanya zuciyata cikin wani sabon al’amari da ban taba tsintar kaina ciki ba. Na yi kokarin in yakice Imran a zuciyata na kasa, inda duk na juya shi ke zuwa cikin idanuna. Na ji wasu sassa na jikina suna wani irin kaduwa da ban san na mene ne ba. Marana ya kulle tamau kamar zan yi fitsari, don haka na rarrafa zuwa (toilet) na yi ta kakalen fitsarin amma bai zubo ba. Na dawo daki na kwanta a dandaryar carpet, na ware fanka da A.C amma ban daina zufa ba. Wannan al’amari ya tsoratani, domin wani al’amari ne sabo a gareni da ban taba tsintar kaina a ciki ba, ban kuma san ko mene ne ba. Hawaye ya zubo min ina kallon su Azizah dake ta barcinsu cikin kwanciyar hankali, na rasa abin da ke min dadi, na rasa mene ne shi wannan abun, haka na rasa me zan yi ya gusar min da wannan sabon abu da nake ji cikin jikina har kuma cikin kwakwalwata. Wannan shine mafarin shigar rayuwata cikin gararin da har yau take ciki, cikin halin bakin ciki da dakacen ina ma ba a haifeni ba. Da ban hadu da Imran ba, watakila da rayuwata ta ci gaba da garawa a yadda take. Wato ba bakin ciki ba kuma farin ciki, sai godiyar Allah. Haduwata da Imran shine silar warwarewar al’amuran rayuwata da na Innana da suka shige min duhu, suke damun zuciyata tun ina kankanuwa. Har ila yau, Imran din ne sanadiyyar rushewar farin cikin rayuwata. Wata zuciyar ta ce dani, wannan al’amari da ke neman samuna ba alheri bane a tare dani, don haka in nemi tsarin Allah. Wannan ita ce tarbiyyar da iyayena suka dora ni a kai, wato duk wani abu da ya fi karfin iyawa ta, ya fi karfin sani na, ya fi karfin kariyata to in nemi tsari da kariyar Allah, domin shine mai iko a kan komi. Sai na mike ina layi na yi bayan gida, na dauro cikakkar alwala na yi (brush) na fito na suturce jikina na fara sallah, a cikin sujjada ta ina rokon Allah cikin yi masa kirari da ya yaye min wannan matsala da ya daura min a kan Imran, ya kawo sanadin da Imran din zai bar gidan gaba daya in huta. Washegari na tashi da azumin tadauwa’i a bakina, kasancewar ranar Alhamis ce dama na kan yi azumi litinin da alhamis. Wallahi sai na ji ni sawai, kaman an yaye mani. Na yi ta yiwa Imran boyo cikin gidan har aka sha ruwa, gani nake kamar idan ya kalli kwayar idona zai karanto abin da ke damuna game da shi, wanda ya hana mani barci daren jiya. Wannan ya faru ne tun ina da shekaru sha biyar a duniya. A daren Imran da Faruq na zaga gari cikin motar Imran din, Faruq ya ce, “Yau tun safe ban ga Abu na ba, na shiga sassan Mama ya fi sau biyar ban ganta ba, ina cikin damuwa wallahi”. Imran ya yi murmushin da shi kadai ya san dalili yin abin shi, amma bai ce komai ba. Ya yi parking a wani katafaren shopping complex suka shiga tare, shi Faruq ya dauka biskit din nashi zai saya da baya rabo da saye. Don haka shi ya yi wani barin can daban yana saye-sayen shi. Kafin ya zagayo inda Imran yake, ya ganshi ya cika kwando taf da kayan shafa na mata (designers) yana jujjuya kwalbar turaren cool-water watau (Davidoff) a hannun shi, turare ne mai sanyin kamshi na ‘ya macen da ta san sirrin da ke cikin turare. Sai daga baya ne ya dauki kayan shaving din shi da biskit din nashi na (Hob-Nobs) ya yi gaba ya bar Faruq da baki bude. Mamakin Faruq yaushe Imran ya yi budurwa bai sani ba? Ina ya je shi kadai ba tare da shi ba har suka hadun? Imran S. Bindawa, tamkar ya san me Faruq din ke sakawa a ranshi, sai ya yi murmushi ya kanne mai idon shi daya cikin tsokana, ya ciza lebbanshi masu sulbi, ya matso dai-dai kunnenshi ya ce, “Don’t be nervous mana (kada ka ji tsoro) ba kowa na sayawa ba face kanwata, ZAYNAB”. Ya yi gaba ya barshi nan yana mai son convincing zuciyarshi ta yarda da abin da take ji, amma zuciyar ta ki yarda, karyatawa take da cewa, ba ZAINAB ya ce ba ZUBAIDA. Da Imran din bai yi gaba ya barshi ba, da ya ji irin hautsinawar da ‘ya’yan hanjin shi ke yi, da kukan da akuyar cikinsa ke yi. Ya kuma ga kallon firgicin da ya bishi da shi da gumin da ke ta yankowa daga kowanne sako a jikinshi. Ya shiga gyada kai tamkar kadangare yana girgizawa, yana gayawa kanshi cikin lallashi cewa, ba da wani nufi Imran ya fadi kalaman shi ba, ba da wani nufi Imran zai yiwa Zainab kyauta ba, abin da yake kokarin fahimta ba shine ba. Zumunci ne kawai da alkhairi irin nasa, domin shi mutum ne mai alheri ga kowa ma ba Zaynab kadai ba. Abinci ake ci bisa makeken dining din gidan, to amma me? Imran idanun shi kyar bisa kyakkyawar fuskar Zainab, tana kai lomar ta a nutse ba irin su Aziza ba hannu baka hannu kwarya. Idan tana tauna kumatunta duka biyu da tsakiyar habarta lotsawa suke ciki sosai. Komi nata a yangace amma naturally ba wai tana sane take yi ba, yana tafiya ne da halittar Ubangiji. Sanye take da doguwar riga fara sol, ta matse dogon gashin kanta daga tsakiya da farin ribon ya sakko ya kwanta lamban bisa dogon wuyan ta kamar na barewa. Zainab a mike take sosai ga kuma alamun ‘mace’ dake neman bayyanuwa a jikin ta daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Ya kasa cin abincin sai ko juya cokali cikin farfesu? A bangarena, nima ba cin abincin nake yi ba, bugun da zuciyata ke yi a duk lokacin da na ga Ya Im, na yau har ya fi na kullum. Kaduwar da sassan jikina ke yi yanzu, wane na daren jiya. To a haka aka kare cin abincin ba tare da na ci wani abin kirki ba, haka tunda na dukar da kaina kasa ban dago ba. Idan akwai abin da nake son gani, nake kuma gujewa ganin nasa, to Imran ne. ba don komi ba sai don abin da hakan yake haddasa min a cikin gangar jiki da tsokar zuciyana baki daya. Karfe tara na dare ana falo har Abba ana kallon network news amma ni ina uwar dakinmu dukunkune cikin bargo, ga littafin assignment dina a gabana na kasa hassala komi sai fama da abin da ya dameni. Zan so in samu wani ya fassara mun ma’anar wannan abu dake damuna. Abin bakin cikin shine, ni bani da kawa, su Azizah duka yara ne na girme su, ni kaina ban san mene ne ba balle su da na kere sosai a shekaru. Kaduwar da jikina ke yi shi ya haifar mun da zazzabi da sarawar kai, haka abin da na dauka ciwon mara ke karuwa mini. Ga (assignment) din da na tabbatar in ban yi shi na bayar a gobe ba na rasa C.A dina na darasin physics, amma bai dameni ba kamar wannan ciwon Imran da Allah ya dora mini. Hawaye masu zafi suka soma biyo kuncina, na kara kudundunewa tamkar curin alkaki, haka al’amarin yana kara habaka a tare dani. Imran sanye da farar shirt (DKNY) da shudin wandon (Jeans) ya shigo falon, ya zauna ana kallon da shi ba don kallon ne ya kawo shi ba. Ya mike tsaye cikin damuwa ya zura hannunshi cikin aljihun bayan wandon shi kamar mai laluben wani abu, yana kallon su Azizah suna ta shewar su, ya hanga ya duba iyakar ganin shi bai ga mai rikirkita shi ba a ‘yan kwanakin nan. Cikin mamakin rashin ganin ta da yake cikin jama’ar gidan a dan tsukin ya ce, “Azzy ina Zaynab ne?” Iftihal ce ta amsa masa da cewa, “Tana can daki an ba ta assignment ta kasa shine take yi tana kuka”. Ya ce, “To ku baku taimaka mata in kun iya?” Iftihal da Azizah suka dubi juna suka kama baki, can kuma suka hadu suka tintsire masa da dariyar su ta ‘yan biyu mai ban haushi. Ya shaka, ya kulu, kadan ya rage ya yi kwallo dasu. “Mama ki ji Yaya Im don Allah, mune ma masu koya ma Zaynab karatu?” Mama ta ce, “Zainab ce malamar su Azizah ai, in ta iya su koya a wurin ta, in ba ta iya ba duk haka suke lalacewa”. Hajiya Sa’a ta kyabe baki, saboda neman fitina babu wanda ya sako ta cikin zancen su, amma sai cewa ta yi, “Ai tsiyar ‘ya’ya mata kenan duka tumaki ne, duk ba kwakwalwa sai ta shashanci”. Mama ta wani irin juyo ta dube ta, ta bude baki za ta yi magana Abba ya daga mata hannu ganin yadda yaran suke kallon su, ta yi shiru tana ciccika tana batsewa, kiris take jira ta yi kuka. Wannan dabi’ar Hajiya Sa’a ne, babu yadda za ayi a zauna da ita a tashi ba ta san abin da za ta ce wanda zai bakantawa Azumi ba, ko da kuwa ta cikin ruwan sanyi ne. Ita kuma Azumin ba hakuri, ba ta barin ko ta kwana da an tabo ta za ta hau suyi sama suyi ta yi kamar sa cinye juna. Shi kuma Abban ya zuba ma takarda ido yana rubutu kai ka ce dabbobi ne ya aje ko dagowa baya yi balle ya san suna yi. Ya kan ce cikin zuciyarshi mace daya ce ta ishe shi duba a duniya, mace daya ce ta isa ya daga ido ya dube ta ya ji sanyi a zuciyarsa kuma ta yi mai nisan da har abada ba zai kamo ta ba. Ta tafi da duk wata soyyarshi a kan diya mace. Don haka duk wata mace kallon ta kawai yake a dage, a kaskance, a hagunce, ma’ana ba ta da abin da za ta burge shi da shi har ya bata muhimmin lokacinsa a kanta. Sai zaman aure domin neman lada gami da kariyar kai daga dattin zina, da rainon ‘ya’ya wanda wannan daman dole ne. Ya dago ya dubi Imran idanunshi sun kada sunyi jazur da tunanin wani al’amari mai GIRMA da ya taba zuciyarshi, ya ce da karfi, “Dan Abba! Jeka koyawa Zaynab assignment”. (Kuskuren da iyaye ke yi kenan, musamman iyaye ‘yan boko da attajirai, kan dauki kebantuwar ‘ya’yansu mace da namiji baligai ba a bakin komi ba duk a cikin wayewar ne, wanda ko Annabi (S.A.W) ya fadi mana kebancewar mace da namiji, na ukun su shaidan ne, musamman ga ita Zaynab, da Abban ya yi tunani bai dace ya yi hakan ba, tunda shi da bakinsa ke yi mata nasihar mu’amala ko ya ya da namijin da ba muharraminta ba). Tamkar ya yi mai susa a inda ke yi mai kaikayi, da sassarfa ya nufo dakinmu. Har zuwa lokacin kwance nake kudundune cikin bargo ga littafin a gaban filon da na ta da kai da shi, idanuwana cike da hawaye amma basu kai ga zubowa ba. Daga bakin kofa ya dakata ya tokare a jikin kofar da hannunshi na dama kafafunshi na daga waje ya ce, “Zaynab mene ne haka? Cewa aka yi in baki iya assignment din ba korar ki za ayi daga makarantar?’ Shiru na yi masa tamkar da littafin yake magana, don ban san me zan ce masa ba. Shirun shine mafi alfanu. Ganin haka ya karasa shigowa dakin gaba daya, ya ce, “ki tashi na ce, ki tashi ki zauna Allah tun ban kwaye bargon ba”. Nan ma ba amsa, sai ido da na bishi dasu, luuu! Wadanda suka kankance suka yi jawur, tamkar an gumbuda musu barkono. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Ya yi tsai da ransa cikin son karantar me ke damun Zaynab? Ko me Zaynabu ke ciki? Ba tare da tunani ba kuma ya janye bargon ya wancakalar. Subhanallahi! Ba shiri ya mai da mun abuna saboda kananun (minis) da ke jikina. Ya juya mun baya da sauri cikin rawar murya yana fadin, “Ki tashi ki sa kaya in koya miki assignment din. Ki tashi tun baki yi sanadin da na idasa kai hannu gareki ba, wannan hawayen da kike zubarwa Zaynab ba zan iya jurarsu ba. Zaynab ya kike so in yi da raina? Kin hana mun ganin kyakkyawar fuskarki, kin haramta min jin lafuzan ki masu taushi, kin hana mun barci yanzu ma a ido biyun kina so ki mai dani wani zararre, haba Zaynab! Ke wace irin yarinya ce mara tausayi da halin ko in kula……..” Baki na saki galala! Ina jin abin da ko a mafarki ban taba yin na zan ji hakan daga Imran ba, ko a tunani, ban yi na wai Imran zai taba fadin hakan gareni ba even in my imaginations! To ko shima irin ciwon nawa ke damunsa? Bai san halin da nake ciki duk a kansa bane? Bai san duk wannan kukan ba na assignment bane na rashin abin da zuciya da gangar jiki ke so ne, wato shi YA IM, da nake ganin har abada ba zan samu ba. Still bai juyowa ba ya saki wata irin ajiyar zuciya ya ce, “To ni yanzu Abba ya ce in zo in koya miki karatu, me kike so in je in ce masa? Baki da lafiya ko-ko bakya jin magana?” Da sauri na lalubi jallabiyana na zurma, na daura mayafin ta cikin wani irin dauri maras fasali, cikin dasasshiyar murya na ce, “Ka yi hakuri Ya Im, bani da lafiya ne”. Da sauri ya juyo ba tare da ya yi tunanin nasa sutturar ko ban sanya ba, ya tako da sauri ya zauna a gaban gadona. Ya kai hannu goshina, “me ya same ki?” Wani irin shock ya same ni ya kuma taso da lalurar da ke kwance lumus cikin jikina. Jikina ya soma kyarma tun daga kai har yatsar kafata mazari nake. Ai Imran ba yaro bane, na san ya fahimci halin da nake ciki, sai ya yi azamar janye hannunshi a goshina ya ja da baya. Ya yi murmushi ya ce, “Zaynabu gaya mun irin ciwon da ke damun ki in ji ko zan iya maganin shi. Nima bani da lafiya amma nawa bai yi tsanani kamar naki ba. Kuma ni ina kokari a kullum in fi karfin zuciyata, in hana mata abin da na san ba alkhairi bane a tare da ita, in ce mata a’a, wannan ba dai-dai bane, bana biye mata domin sharrin dake cikin ta Allah ya yi yawa da shi. Sai ta kai ka garin DANA SANI ta baro, ita ba abin da ya dame ta. In yi hakuri in dauki kaddara, in roki Allah ya kawo mun sauki cikin al’amarina. Ni Imran da kike gani a duk sanda na ji zuciya na neman rinjaya na cewa nake, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’ouun!” Wallahi sai na ji matsananciyar kunyar shi ta saukar mun, na kuma shiga maimaita “Innalillahi…..” a fili da zuciyata. Wata nutsuwa ta musamman ta same ni, komi nawa ya koma normal, na sunkuyar da kai kasa cike da burin ina ma a ce…. kasar za ta tsage da na shige na huta da kunyar Ya Im, amma shi bai damu ba. Sharewa ya yi ya bagarar ta hanyar yin zaman direshan a gabana bisa carpet, yayin da ni nake zaune a gefen gado na zubo fararen kafafuna kasa, na tokare gefe da gefena da hannaye na biyu. Imran ya sunkuyo ya leka fuskata muka hada ido, ya sakar mun lallausar murmushinsa cikin son ganin na saki jiki na daina jin kunyar tasa. Na sanya tafukana na rufe fuska ina murmushi. Ya ce, “ZAY-NA-B”. Yadda ya kirayi sunan sai da tsigar jikina gaba daya ya kara tashi, ban iya na amsa ba. Ya ce, “Maza sauke hannuwanki daga fuskarki, kada ki sa in taba su”. Da sauri na sauke amma har yanzu ban bari mun hada kwayar ido ba. Ya ce, “Na ce ki gaya mun ciwon da ke damun ki, a kalla idan ban baki maganin sa ba zan baki shawara a matsayina na babba wanda ya fi ki shekaru. Idan kin barshi a ranki kin ki fadi, mai yiwuwa ne ya ci gaba da cutar dake ba tare da kowa ya sani ba, wanda a karshe hakan zai iya zamowa illa ga lafiyarki”. Ya yi shiru yana mai kokarin son mu hada ido amma na ki. Na yi tunanin dukkanin maganganun shi a kan hanya suke, ba wadda babu gaskiya a ciki. Don in ban mance ba Baba Sa’idu ma ya sha gargadi na a kan barin sanya abu a rai illa ne ga lafiya da kwakwalwa. To amma ni kaina wallahi ba na ce ga hakikanin abin da ke damuna ba, abin ya fi karfin bayyanuwa, ya fi karfin kwatance, ya fi karfin duk kokarin harshe na ya fassara shi. Unxpressable feeling kadai zan iya kiran al’amarina. Wanda in ban da ni da zuciyata da kuma Ubangijin da ya assasa mani shi a ruhi da gangar jiki, babu wanda ya san iyakar sa. Abin da na sani kawai shine, “I need Imran! I need Imran!! I need Imran a tare dani”. To amma idan na fadi mishi ai kamar na zubar da mutuncin kaina ne, na zubar da tarbiyyar gidanmu, duk da ban san wannan abun mene ne ba? Na san ba abun kirki bane, haka ba abin alheri bane kamar yadda ya fada mani. Don haka na kasa magana, tunda na fara tunanina bai katse ni ba. Ya yi nacin ya yi juyin duniyar nan amma na ki magana har ya gaji ya zuba mun ido da alamun ranshi ya baci, duk kuma sai na ji babu dadi. Wasu hawaye suka zubo min na sanya bayan hannuna ina sharewa. Ya mike zai fita ba tare da ya ce dani komi ba, har ya kai bakin kofa ba tare da ya juyo ba, ban san sanda na samu kaina ina mai cewa cikin rishin kuka “Ka yi hakuri Ya Im, mara ta ce take ciwo!”. Ya juyo a hankalce ya dawo, hannayenshi duka biyu cikin aljihunshi, ya dube ni sosai, na nutsar da kaina kas, kamar in ce, “Wayyo Allah!” Ya fi mintuna biyar yana kallo na kamin ya ce, “Al’ada kike yi ne ko zaki yi Zaynab?’ Da wata muhimmiyar kunya da haushin kaina mai tsanani suka taso suka kara lullube ni ban san sanda na fashe da kuka ba, yau tozarcin duniya na gama jin shi a rayuwata, da wanne ido zan daga in kuma duban Ya Im? Na wulakanta kaina na tozarta kaina na yi abin kunya. Imran ya ce dani kamar cikin tsawa, “Ba tambayar ki nake ba za ki sakar min sauti sai kin tara mana mutane a ka?” Na hadiye kukan gaba daya ji kake “mukut”, sai hadiyar rai nake tare da fyace majina da bakin dankwalina. Ya sake maimaita tambayar sa, wannan karon babu alamun wasa cikin maganarshi. Jikina na karkarwa na ce da shi, “A’a, ban ma jima da gamawa ba”. Ya yi ajiyar zuciya ya sassauta murya ya ce, “To meye abin kuka? Daga na tambaye ki don in san maganin da ya dace in amso miki sai ki bare baki ki fasa min kuka a zaci ma wani mugun abu nake miki, yanzu idan su Azizah suka zo suka ga irin wannan kukan da kike kamar na fitar rai suka tambaye ki me za ki ce musu? Maza share hawayen nan ki mai da mood din ki, mu yi karatun tun ban sa kafar wando daya dake ba”. Na koma cikin nutsuwata, na share fuskata tas na dauko littafin na budo mishi aikin. Ya zauna gefena yana dubawa, ya ce, “An excellent handwriting! Zaynab haka kika iya rubutu?” Sai yanzu ne na yi murmushi, domin dai ni mutum ce mai son yin abin yabo a yaba mani, yana kara (encouraging) dina. Cikin dan lokaci Ya Im ya fahimtar dani abin da na kasa har ma da abin da ban sani ba, da dabarun cimma nasara a darasin ‘Physics’ da muke cin kwakwa a kan shi ni da su Azizah. Ji na yi in zamu kwana muna karatun ba zan gaji ba, don kuwa Imran ba dai hikimar koyarwa ba. Imran S. Bindawa cool ne, reserve! Ga wani lafiyayyen kamshi da ban taba jiba dake fita bakinsa (Albaan mouth-fresh) in yana magana. Sai nake tambayar kaina dama akwai wadanda Allah ya halitta da kamshin baki ne? Ko da yake in ban manta ba ai Iftihal ta ce Yayanta daban yake a cikin al’umma. A haka su Azizah suka shigo kwanciya suka tadda mu, karfe goma sha daya da rabi na dare, don su tuni har sun yi barci a falon taso su aka yi. Suka saki baki galala! Suna kallon mu don basu zaci har lokacin yana nan ba. To shi kuma sai ya bi duk ya daure fuska, ya buga musu tsawa ya ce duk su dauko nasu littafin. A take kowacce ta shiga taitayinta barci ya nemi inda ya fito. Karatu ya dawo sabo, ya hadamu gaba daya yana koya mana, bai kyale mu ba sai da ya tabbatar mun gane, ya bamu aiki muka gwada mai a kan idonshi ya gani, sannan ya fita ya ja mana kofa, ko kallon mu bai kara yi ba. Azizah tana ta korafin ita dai da Abba bai ce Imran ya koya min karatu ba, gashi nan yanzu ya jawo mana masifa sai ya mai damu wasu alhuda-huda, su kam sun shiga uku kenan. Iftihal dake ta fi kowa son Ya Im cikin gidan ta ce, “Ai ba zama zai yi ba, baki ji Abba ya samo masu aiki ba? Yanzu haka next week in ya tafi duk da fadan shi ke da kanki za ki yi kewar shi”. Sai na ji duk hankalina ya tashi, Imran zai tafi aiki, ina? Ni kuma ina zan sanya rayuwata? Kasancewana tare da shi a yau na wani lokaci mai tsawo, ya kawo sauki 50% cikin ciwon zuciya da gangar jikina, ya wanke wani babban kaso na ciwon shi dake damuna, ya kuma kara gina wani makeken al’amarin da ya wuce na jin shi a gangar jiki kadai, maimakon haka, sai ya shigo har cikin bargo da kasusuwana. Ni kaina na san yau idan na ce idanuwana sun ga barci, to wannan karya ne. cikin kowanne juyina IMRAN ne, cikin kowanne kiftawar ido IMRAN ne, cikin kowanne zama da tashi IMRAN ne, cikin kowanne kwanciya da mikewar kafa IMRAN ne, cikin kowanne mafarki da ido biyuna shi din ne dai kadai ya mamaye, ya babbake yayi babakere a ko ina, bai barni da ko sako daya da zan sanya tunanin kaina ba. Da safe na sanya (uniform) dina cikin sauri ne saboda makarar da na yi, su Azizah tuni sun gama suna diniing suna karyawa, wannan ya samo asali ne da rashin isasshen barcin da na samu daren jiya, bayan sallar asubahi kuma wani nannauyan wahalallen barci ya yi awon gaba dani mai cike da mafarkai na ni da Y Im cikin wata irin rayuwa mai dadi, da kyar Mama ta tashe ni. Na ja cambas na daura na juya a hankali ina kallon kaina a mudubi. Ban yi mamakin ‘yar zabgewar da na yi ba cikin ‘yan kwanakin nan da duniyar Imran ta sanya ni gaba. Banda su Azizah shiriritattu ne ya dace su fahimto sauyuka da dama a tare dani, to ita kanta Mamar su haka take, ko cikin dare ba ta rabo da call na emergency case, don haka ba ta samun nutsuwar da har za ta fuskanci kananun abubuwa kamar wannan. Na ci gaba da kallon kaina cikin mudubin, ba wata kwalliya na yi ba ban da mai da farar powder da na shafa, amma ni kaina ina alfahari da ‘yar zagayayyar kayatattar fuskata, wadda in ba son kai irin na dan adam ba, zan iya cewa alhamdulillahi, babu abin da Allah subhana bai kawatata da shi ba. Fararen idanu, giran ido kakkaura, dogon hanci da tsararren baki mai daukar hankali. Idan kuma aka yi maganar zubin halitta abin sai shukrah ga Maqagina, domin ko yaro dan shekaru biyar ba zai iya yi min kallo daya bai maimaita ba. Farina kuwa ba fari ne sol ba, ja ce ni kalar uslin Abzinawa na Damagaram. Ko a farce ba za ka ce na hada jini da Bahaushe ba, domin komi nawa har yatsun kafata irin na Inna na Rabi ne. Na dauki jakata (school bag) na rataya a kafadar hagu, nasa kai zan fita, Imran na sawo kai zai shigo sai muka yi karo garam, da goshinmu, kasancewar nima ba baya ba ce wurin tsawo zamu yi kafada da Imran, illa ya nuna min kaurin jiki. Na yi saurin ja da baya ina ta faman ba shi hakuri don ni har ga Allah ban ji tahowar shi ba, kasancewar shi mutum mai nutsatstsen taku, duk na gigice saboda yadda ya yi min jiya na dan fara shakkun sa, da alama dariya na ba shi. Ya ce, “Ni ne mai ba da hakuri Zaynab, kin kwana lafiya?” Kalaman shi sun matukar bani haushi, wannan rainin hankali ne, kuma kamar son jin halin da mutum ke ciki ne, wanda shi din ba zai maganta mini ba, ba sai ya kyale ni in ji da ciwona ni kadai ba? “Don haka maganar na kwana lafiya ko ban kwana lafiya ba, ba damuwar ka bane….” Magana nake a zuci, ban san cewa har ta fito fili ya ji ba. Ya yi murmushi kamar bai ji ni ba, ya sake matsowa gareni ya russuna ya dauko min jakata da ta fadi a dalilin karon mu ya miko mani, ya sake cewa, “Kin kwana lafiya Zaynab?” Wannan mugun mutum ne, bani da zabi ban da na daga mishi kai domin ya gama kashe mun jiki da fitinanniyar muryarshi. Ya ce, “Amma ni kin ga ban kwana lafiya ba, Zaynab saboda ke!” Ya ci gaba da mugun murmushin, yana magana ne kasa-kasa yanda in har akwai wani cikin dakin bayan ni dake kusa da shi, duk kasa kunnen shi ba zai ji abin da yake fadi ba. Na kyabe baki na ce, “Allah yai maka magani”. Dariya ya yi ya ce, “Ya yi mana magani baki dayanmu za ki ce Zaynab. Ba gara ni ba, amma ke maganin naki ai mai GIRMA ne, wanda ni kadai ke iya maganta miki, kuma ba zan yin ba, saboda ni mai hankali ne sabanin ke da kuruciya ke dawainiya dake”. Ya sake jifana da mugun murmushin, sannan ya miko min ledar da ke hannunshi, tuni na yi suman tsaye. Wani takaici ya zo ya tokareni a kahon zuci kamar in yi aman zuciya don bakin cikin maganganun da ya yaba mani. Bai kuma bani damar in yi magana ba ya juya yana cewa, “Ki yi maza ki tafi makaranta kin zauna nan kina shirme, tun baki tafasa ba kenan wannan in kika kara shekaru uku a gida ban san me za ki zama ba, gara Abba ya tattaraku da zarar kun kare makarantar nan ya ba wani mai tsautsayin sadakar ku. Balle ke Zaynab irin jarababbun matan nan ne wallahi (nympho), duk wanda ya aure ki ya shiga uku”. Ya juya zai fita yana mun dariyar keta, na ga idan na bari ya fice ban yi wani abu ba na fadi ba nauyi. Idanuna suka ciko da kwalla, bayan kadawa da suka yi suka yi jawur na ce, “IMRAN!” Tunda yake yaran gidan baki dayansu babu wanda ya taba gigin kiran shi da Ya Imran ma balle IMRANAN gabagadi. Iyakacin kowa YA EM, don haka ya hanzarta juyowa cike da mamaki ya dube ni, da na wulwula ledar da ya bani na maka masa, niyyata ta fasa mun wannan bakin dake tozartani, ta illata wannan halittar da ke jan zuciyata ga abin da yake goranta mun a kanshi. Amma sai ya yi saurin dukawa ledar ta wuce ta saman kanshi, kayan shafar da ke ciki kowanne ya yi nasa wuri. Na yi murmushi na ce, “Baka da abin da za ka bani Imran, kamar yadda baka da maganin da zai yi maganin ciwo na, don ‘yan mazan naka da kake tinkaho, bai yi isar da zai isar da jarababbiya kamana ba. Amma ka san ina da surar da in maza dari nake so a rana zan samu, kuma daga yau zan fara, Allah za ka yi nadamar wadannan kalaman da ka gaya min”. Na wuce shi nan dafe da lebban shi yana girgiza kai kamar kadangare yana mamaki na gasken-gaske amma ya kasa magana. Kan mu zo makaranta kiris ya rage in yi kuka a gaban su Azizah, amma na yi kokari na daure na cije ina ta kukan zuci. Hirarrakinsu ko daya ban tsoma baki ba, haka fuskana babu annuri. A cikin aji ana ta aiki, amma ni ban rubuta komai ba, ashe wai har aikin aji (class work) malamin ya bayar suka yi suka gama ni ban sani ba, na yi nisa a tunanin rashin mutuncin da Imran ya yi mani. Malamin yana bin kowa yana sa mishi hannu har ya zo kaina, ya ce, “Ke ina aikin naki?” Na yi firgigit na dube shi, a sannan ne Azizah da Iftihal dake bencin bayana suka shiga zungurina da nasu litattafan, na mika hannu ta karkashin bencin na karbo na fito masa da shi kamar daga jakata na fiddo. Kuskuren da na yi shine, duka biyun na hada masa wato na Azizah da na Iftihal na kuma ba shi ba tare da na duba ba. Ya karba yana dubawa duka biyun, ya daga murya ya ce da ‘yan ajin, “Wace ce Azizah Sa’idu?” Gaba daya aka nuna Azzy da ta yi tsuru-tsuru. Ya sake cewa, “Iftihal Sa’idu Bindawa?” Wata kabila Ngozi ta nuna Ifty. Ya nuna ni ya ce, “Wannan kuma fa ya sunan ta?” Aka ce da shi, “Zaynab Aliyu”. Ya ce, “To ku taso dukkan ku mu isa wurin principal, yau idan uban ku gwamna ne ya daure ni har sai igiya tai rara. Dabbobin banza ni za ku mai da shashasha! Na zo duniyar na kuma je makaranta tun kan ayi cikin uwarku balle ayi tunanin haife ta, shine za ku mai dani sakarai?” Su Azizah suka tsugunna a kasa suna ta ba shi hakuri har da hawayensu, don ba abin da suka tsana a rayuwarsu irin a kai su wurin shugabar makarantar a ce sun yi laifi, don ta san Baba Sa’idu farin sani a take za ta gaya masa. Ni ko ko gezau, don zuciyata ta riga ta kekashe da bakin cikin Imran da ya yiwa zuciyata katutu, don haka don an duke ni gani nake dukan ba zai shiga jikina ba ko da kuwa da bulalar karfe ne. Ya ga ni ban ba da hakuri ba, karewa ma wani gefen daban nake kallo kai ka ce ba dani ake case din ba, kuma dama shine (discipline master) din makarantar baki daya, kowa ya san Malam GG watu Garba Gumel a wurin mugunta babu na biyun shi duk fadin makarantar. Ya ce, “Su Azizah su koma su zauna, ni kuma in taso in biyo shi”. Ban yi musu ba na karkade rigata na bishi a baya, Iftihal ta biyo ni tana ta ba shi hakuri ya daka mata tsawa ya ce ta koma mazauninta, ya kuma sanya monitar ajin Suhaila ta yi mai gadinsu, idan suka fito ta kira shi a waya ta gaya masa. Tafi-tafi ina bin shi kamar jela, ina gayawa kaina na cancanci a hora ni, wauta ce tun farko ta hanani gane Imran ai ba tsarana bane da zan kallafa zuciyata a kansa, don haka kome GG da Imran suka yi min dai-dain su ne. Wani kazamin (student toilet) ya sani in wanke kana tafiya kana karo da busasshen kashi, zarni kuwa ba a magana. Hankalina ya tashi, na soma hawaye amma GG in ban da narka min zagi ba abin da yake. Cewa yake, “So nake in ga matsayin ubanki a garin nan, in tabbatar da cikar ki ‘yar masu kudi. Allah yasa ‘Yar Aduwa ne ya haife ki, da kike wannan bunkasar. Kin ganni nan duk kyawun mace da farar fatarta ba ta burgeni, ko da kuwa ta hurul-eeni ce. Ko dai ta yi karatu ko in bautar da ita, bautar da uwarta da ubanta basu taba yi mata ba. Ke ni ko a aljannah bana fatan Allah ya hadani da mace, ba don komi ba sai don cewa ita ba komi bace face fitina a doron kasa, balle irin ku masu narka-narkan…….sai ku lalata mutum in ba ana wulakanta ku ba….” Na daga idona a hanzarce da hawayena suka kafe karaf, na dubi GG din nan na ‘yan dakikai don ji nake kamar Imran ne yake gaya mun hakan. Ashe dalilin Ya Im kenan na wulakanta ni, kada in lalata shi? Dalilin shi kenan na gaya mun abin da zai bata mun rai in ji har abada bana son mu hada hanya? Sai na ji GG ya yi gaskiya, na shiga kada kai ina mai gasgata kowacce kalma dake fita bakinsa. Na duka na soma ture busassun kashi da tsintsiya, da wani amai ya taho min gabagadi sai na kwararo shi a kafafun GG kore shar da shi kamar atini, don rabona da abinci tun na safiyar jiya. Ji nake kamar hanjina nake amayarwa. Ya daka tsalle ya yi gefe yana kara zagina, ya ce, “Wallahi ba amai ba ko hantarki za ki amayar sai kin wanke toilet din nan fes, kamar tuwo na ya fadi in dauka, in ya so gobe a sallameni daga aikin gwamnati. Wannan ba abun damuwa bane ina da makekiyar gonar gado a Gumel, sai in koma gida in cimma sana’ar Uwa da Uba watau (noma)”. Ya kira wasu dalibai da za su wuce ya ce su dauko mai kujera, ya girkata can gefe daga nesa ya zauna yasa hankici ya toshe hancinsa, lokaci guda kuma yana wanke kafarsa da ruwa a gwangwani da na kwararawa amai. Haka ba yadda na iya na zage na wanke toilets dai-dai har guda shida, na kuma kwashe busasshen kashi na zuba a dustbin, sannan ya sani a gaba muka nufo ajinmu. Lokacin karfe sha biyu da rabi na rana ya rage awa daya a tashi. Na dauka shi kenan GG zai kyale ni, amma me? Ina sa kai zan shiga ajin ya juyo ya dakatar dani ya ce, “Haka za ki shiga musu aji kina warin kashi? Koma ki shanya kanki a rana har sai warin ya gushe tukunna, kneel down”. Na koma cikin rana na zube gwiwoyina idanuna a rufe. Tsayin awa guda da rabi sannan aka kada kararrawar tashi. Su Azizah suka rugo da gudu suka rungume ni suna tattabani suna tambayar abin da ya yi mini, ban ce musu komi ba illa hawaye da nake ta sharewa ina fyace hancina da ya toshe don azaba, suka tabbatar ba za su ji kalma ko daya a bakina ba sai suka hakura suka kyale ni. Muka zo gindin bishiyar dalbejiya inda muke tsayawa Shehu direba ya zo ya dauke mu, shiru-shiru bai zo ba har dalibai suka fara karewa. Su Azizah suka kulu matuka, ni kuwa ta kaina nake da kuguna da ya rike kamar zai balle saboda durkuson da na yi na awoyi da dama. Sai misalin karfe uku na yamma sannan muka hango hancin motar Abba (Vanquish), muka shiga ware ido cike da mamakin yau Abba da kanshi ya zo daukar mu, to ina Shehun? Ashe dan duniyar ne ka janye da motar da Faruq a kujerar mai zaman banza. Suka saki baki suna kallon ikon Allah, don ni har zuwa lokacin kaina a durkushe yake, tunda na yi musu kallo daya ban sake dagowa ba. Ya daka mana tsawar da ta firgitamu ya ce, “Da Allah malamai za ku shigo ne ko kuwa mu juya ku kwana a makarantar, ruwan wa? ‘Yan kauye kawai kun saki manyan bakunan ku kuna kallon mutane kamar baku taba shiga mota ba a duniya…” Faruk ya katse shi da cewa, “Haba babban Yaya ayi musu a hankali man da me za su ji? Da yunwar dake damun su ko da shanya sun da aka yi kamar kayan wanki, ko-ko da fadan ka kamar barkono bayan basu suka kar zomon ba….?” Ya ja tsaki “Tsut-tsut!” Kamar ya ci kansa don bala’i. Mu dai tuni mun nabba’a a bayan mota babu wadda tai magana, ya fizgi motar da gudun ta mai kamar na tashi sama, kan ka ce meye wannan sai gamu a gida. Kamin mu fita Ya Faruq ya dubi Azizah ya ce, “Ya ya ne Azzy, na ga mutuniyar tawa ba yada take?” Azizah ta dan saki ranta ta jinjina kai ta ce, “Kai dai bari Ya Faruq, wani mugun malami ne Allah ya hadata da shi yau ya zane ta ya sata kneel down a cikin rana wajen awa daya wallahi”. Iftihal ta ce, “Kai ina jin ba zane ta ya yi ba, wankin kashi ya sa ta. Baki ji ba yana cewa ya za ta shigo mana aji tana warin kashi?’ Haushin su ya ishe ni na bude motar fit na fice kamar guguwa, Faruq yana danne dariyar sa ya ce, “Asshah! Abu bai yi dadi ba, galleliyar yarinya kamar Abu na a ce an sata wankin kashi?” Imran ya daga murya da karfi yadda zan jiyo yana cewa, “Ai madallah, kai madallah, wannan malami ya burgeni. Yanzu haka ba ta karatu sai SOYAYYAH! Ai ni wallahi ya yi min dai-dai, da zan ganshi da na sa Abba yasa an kara mai girma zuwa principal din F.G.C baki daya. Me ake da yaron da ba zai tsaya ya yi karatu ba? Kuma ku shiga taitayinku wallahi don gobe insha Allahu zan je na neme shi mu kulla abota, in ba shi izinin duk wadda ta ki tsayawa ta yi karatu ya ba ta aikin kashi….” Ni dai ban juyo ba sai kuka nake, sai Faruq dake ta shan dariya kamar me. Su Iftihal duk a kumbure suntum suka fito cikin dana-sanin da basu gaya musu ba. Wannan wulakancin da Imran ya yi mani, idan da zuciyata mai hankali ce da ya isa a ce ta saduda ta fidda shi a cikin ta da duk wani al’amari da ya shafe shi. Amma ina! Abu kullum kamar ana kara iza shi. Tun daga lokacin ya daina kaf-kaf din da yake dani ya koma treating dina yadda yake horas da su Azizah. Duk wani wasa da shakuwa dake tsakaninmu ya janye shi, kullum sai fada kamar Babana. Kai ni ko Babana bai taba yi min bala’I da sababi irin na Imran ba, da abin da ya isa da wanda bai isa ba, haka takurar da yakewa su Azizah ya kara ninkata. Ya hana mu kallon talabijin balle kallon fina-finan India wai mun fara lalacewa. Su Azizah da basu san hawa ba basu san sauka ba mamakin su ya kasa boyuwa, suka kai karar shi wajen Abba kan ya takura mana ko music ya hana mu ji a radio wai duk a nan muke debo lalata. Ya sayo kasusuwan kira’ar Jabir ya rika sanyawa duk gidan. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Na runtse idanuna da karfi, wani sanyi ya ratsa zuciyata tare da yin wata irin kakkarfar ajiyar zuciya, amma na kasa bude idon. Babu shakka Ya Im ya yi min bazata, ya shammace ni ya kuma gigita ni. Na rasa da idanun da zan bude in dubi su Azizah. Wata irin kunya da nauyin su da ban taba ji ba suka taru suka yi min mayafi, na bushe a zaunen da nake. Su Iftihal kan su bushewar suka yi, kamar sassakakkun gumaka. Cikin mu babu wanda ya san fitar shi, sai bude ido mu kai muka ganmu a cikin mota, direba ya ja, ko uffan babu wadda ta yi kokarin cewa a cikinmu. Sai me? Mun fito break kenan muka ga motar Ya Im a kofar ofishin principal, aka aika in zo, wani irin kululuuu! Da cikina ya bayar ban san sanda na tsugunne a kasa ba na dafe cikina dake hargagi, ita kanta Iftihal a tsorace take, don dukkan mu munyi tsammanin karar Malaman mu ya kawo da Azizah ta ce suna bamu amsa. Na shiga na tarar ashe ba a nan gizo ke sakar ba, zuwa ya yi a kan makarantar ta yi mun iyaka da su GG da ke cewa suna so na, domin ni matar shi ce an daura mana aure tuntuni. In ka kalli fuskar nan mai bam sha’awa ta Ya Im, ta juye gaba daya da harbadadden kishi zuwa na wani mutum daban mai zuciya da razanarwa. Na yi hanzarin daga ido na dube shi, in tambaye shi dalilin shi na yi mun haka? Wata uwar harara da ya jefe ni da ita ba shiri na dukar da kaina kasa na mai da bakina na dinke na kasa cewa komai. Principal ya ba shi hakuri, ya kuma tabbatar mishi za a tsawatar don wannan dokar makaranta ce dama. Shi kuwa GG anyi neman duniya cikin makarantar ba a ganshi ba ya gudu, tunda ya ga motar Ya Im ya tsere don bai san yau da wacce ya zo ba. Na cika na yi famfam na fito ina hada hanya saboda takaici, wai me Imran ke nufi dani ne? Ya hana mun kurbar ruwa a duniya ko me? Saboda kawai ina zaman cin arziki a gidansu? Ya sanya ni cikin wani hali na matukar kunyar su Azizah, ban fita daga wannan ba ya zo ya lankaya min auren da Allah bai lankaya min ba. Inda na gode Allah daga Azizah har Iftihal babu wanda ta yi mun tambaya ko daya, domin dai su yara ne nutsattsu kuma wayayyu da basu faya mai da hankali a kan abin da bai shafe su ba. Na dawo gida ina ta fushi, da dare kowa yana falo amma ni na kasa fita, gani nake kamar su Azizah za su fadawa kowa abin da ke tsakanina da Yayan su, na ji ni duk na zama wata bare mara gaskiya kuma munafuka, ban san sanda hawaye ya zubo min ba, nasa bayan hannuna ina sharewa duk da haka Imran na nan like a zuciyata, haka komi da yake yi bayan bani haushi illa wannan abu da ya yi mun cikin su Azizah da ya hanani kurbar ruwa cikin gidan gaba daya, duk da na san ba halayyarsu ba ce fadar abin da ba a tambaye su ba. Shi din ne dai ya shigo Iftihal na biye da shi, ya ce, “Kin gani ko abin da na gaya miki, saboda na ce ina sonta a gabanku ta bi ta kuntatawa kanta ta hana kanta sakat, nima ta hana mini. Tunda na zo gidan nan Iftihal Antin nan naki ba ta barni na huta ba, sai garani take kamar gare-gare ko kuwa juyani ya waina a tanda. Ban san me take nufi ba, ban san me take so in mata ba da zai nuna ni Imran mai so da kaunar ta ne. na yi duk iya kokari na ta saurare ni ta kiya, wayar da na kawo dominta ta rufe ta toshe duk wata kafa da zan bi in nuna mata manufata ta alkhairi ce a tare da ita”. Ya samu gefen gadon da nake zaune ya zauna, ya kai hannu ya dago habana ya ga yadda hawaye ke ta gudu, ya ce, “Jibi ki ga Iftihal, shin dama kaunar da kuke wa Anti-Abun na karya ne, da take shakkar ku? Saboda ni dai na san in dai so ne Zaynab na sona, ba tun yau ba, tun sanda ta fara kirgen dangi take sona balle yanzun? Dama so nake ku yi karatu kuma an kare, ba sai aure ba Iftihal? Yau shekaru dai-dai har uku ina rainon Zaynab a cikin raina, ina addu’ar Allah ya bani tsawon ran da zan ga karewar karatun ku, in fiddo burin zuciyata na son mallakar ta. Ki taya ni rokon Zaynab ta amshi kokon bara ta ko na samu nutsuwa, ita ma ta samu damar karasa jarrabawar ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Amma meye amfanin wannan hali da take neman jefa kanta?” Na matsa can gefe na takure cike da wata sabuwar kunyar, kamar in daura hannu aka in ce “Wayyo Allah!” Iftihal ta yi tsaki ta ce, “Kema dai don Allah Anti Abu meye haka kike yi sai ka ce wata Illiterate (jahila), mu fa ba tun yau ba mun san Ya Im na son ki, har amanarki yake bamu in zai tafi to meye wannan mummuken da kike mana sai ka ce baki yarda damu ba? Kina tsammanin zamu so Ya Im ya auri wata fiye da ke ne? Kin yi kuskure. Ko ita Azizah da take yawan yi miki zancen Mami ina tabbatar miki don kawai ta ga hawayen ki ne da kukan da kike mana cikin dare, kin dauka barci muke?” Ta fita tana dariya. Na juya na harari Ya Im da idanuwana da suka kada suka yi jawur, ya rausayar da kai cikin yi min wani lallausan kallo mai nuna yes, abin da yake fadi da wanda ‘yar’uwarshi ke fadi haka yake har zuciyarsu. Cikin kuka na ce, “Don Allah mai yasa ka yi mun haka? Ni da bakina kataba jin na ce ina son ka? Wannan ma ai sharri ne kuma wallahi sai Allah ya saka mini…..” Dariya na ba shi sosai. Ya ce, “Kina bani mamaki Zaynab, abin da baki sani ba shine, duk wani motsinki a tafin hannuna yake. Kuma tun baki da wayo nake da wayo. Maganar kina sona ko bakya sona duk a barta, na ji ni nake son ki, kuma a yau na furta. Amincewar ki kawai nake nema ba wani abu daban ba, ina fatan ranar da kuka kare jarrabawa ranar ne za a daura mana aure, don ba zan koma ko ina ba Zaynab sai tare da ke a matsayin matata (by my side) Insha Allahu. Abin da ya wuce a bar shi a matsayin wanda ya wuce a fuskanci na gaba…..” Na dago cikin murmushin takaici na katse shi da cewa, “Kana manta da wa kake magana Ya Im, ba da Mami bane da Zaynab ne. Ka shirya shiga uku ne da kake marmarin auren jarababbiya kamana?” Da sauri kuma cikin murmushi ya ce, “Na shirya Zaynab, in ma sau goma-goma ne a rana duk za ayi miki, me ake da ‘yan mazan? Ke irin ki hudu ma idan ana ciki a rana a kuma haife za ku haife goma-goma a rana daya, in dai Imran ne mijin”. Ya kanne min idonshi daya cikin zolaya yana murmushin sa mai girgiza zuciyana, na kyabe baki na ce, “Ban ga alama ba, wai Liman babu Mamu…” Da sauri ya mike ya nufo ni yana kokarin cire riga ya ce, “Eye! Me kika ce Zaynab sake fadi ban ji sosai ba, bari in nuna miki ko waye Imranan nan da kike rainawa… wayon ki kadan ne haka maganganunki ko daya babu respect a cikin su. Ko da yake mantawa na yi ke din babbar mace ce ba karama ba, tunda tun kina karama babba ce, to babu laifi yau kin samu babban namijin da zai sa ki raina kanki….” Na ga da gaske yake tubewar zai yi, sai ‘ya’yan hanjina suka hautsine, na koma lallashi na ce, “Haba don Allah Ya Im, idan Mama ta zo fa? Allah ni wasa nake….” Ya ce (yana kara dosoni) “Wannan ne kuma baki isa ba, tunda ba matse bakin ki na yi kika fadi abin da kika fada ba”. Ya wancakalar da shirt din da ke jikinsa ya rage singileti fara sol. Na dauka da wasa yake ba cirewar zai ba, na cira kai a hankali na hango wani irin ingarman kirji lullube da muscles baibaye da lallausar gashi baki sidik nannade da gurayen karfi ta ko ina. Ban taba ganin babban mutun irin Imran ba, ban taba ganin Da namiji mai halittar GIRMA irin Imran ba. Na tabbata duk abin da ya fadi babu kuskure a ciki, zai iya yin abin da ya fi hakan. Ubangiji da ya halicce shi ya iya halitta, ya kyautata halittarsa yadda ta zamo mabambanciya da ta sauran maza kwatankwacin sa. Kenan tsarki da GIRMA sun tabbata gare shi. Ganin ya nufo ni gadan-gadan yana shirin cafka ta, na ce, kafa! Me na ci ban baki ba! Zuwa cikin toilet na murza key sai karkarwa nake saboda tsabar kaduwa. Ina jiyo shi yana cewa, “Karyar banza cika bakin wofi, da ki tsaya mana ki ga aiki da cikawa, ki ga in ana haihuwa a gobe baki haifewa Abba dan jika a gidan nan gobe ba!” A raina na ce, “Allah ya tsare ni da haihuwar SHEGE!” Ashe har ya fito ya shiga kunnensa, ya ce, “Na ji abin da kika ce Zaynab, ina mai tabbatar miki in baki amince da bukatata ba wato daura auren mu bayan kammala jarrabawar ki, za kuwa ki haifi SHEGEN! In yaso daga baya ayi mana auren mu rike abin mu ko ya kika gani?” Zaynabu dai baki ya mutu, sai Uban mazari da jikina ke ta yi kamar wadda ta yi gamo. Ya yi dariya shi kadai yana fita daga dakin yana cewa, “Yarinya baki san Imrana ba, watakila sai a (foot-ball field) watau filin saka kwallo, ranar Innar taki, Abban naki da Ya Faruq din naki basu isa su kwace ki ba. Kuma in gaya miki ke karamar jarababbiya ce, su manyan jarababbun tsayawa suke a doka kwallon don a ga hazakar kowa, in ya so mai sa’a ya dauka, ba gudu suke suna neman mafaka ba alamar weakness (ragonta) kenan”. Bani na fito ba sai da na ji muryoyin su Iftihal suna cigiyata a dakin za su kwanta, na kasa ko da shakar kwakkawaran numfashi don yanzu su Iftihal sun zame min surukai, na rasa yadda zan yi in iya hada ido da su. Sai na jiyo Iftihal na dariya tana gulmatawa Azizah, “Allah sarki Anti Abu! Ya Im ya takurata a gidan nan, Allah ni har tausayi take bani, dazu da muka shigo baki gani ba tana ta kuka abin tausayi, yanzu zaman falo ya gagareta tana tsoron ko zamu gayawa Mama ne”. Azizah ta ce, “Ke rabu da ita, gulma ce ita ma tana son sa, baki san duk ranar da na yi zancen Mami da kuka take kwana ba? Gaskiya in suka yi sa’ar yin aure, they’ll make a perpect couple, domin sun dace da juna. Sai dai kin san ba karamin abu bane a ce Hajiya ta amince, yadda take son Ya Im da auren Mami, amma daga Abba ba za su samu matsala ba”. Na ga dai in zan kwana cikin bayin nan su ba abin da ya dame su, ba kuma fita za suyi daga dakin ba hirarsu kawai suke. Karewa ma tare zamu kwana cikin dakin, to boyon har na yaushe zan yi? Sai na share ido na murje kunyar na fito, duk suka juyo suka dube ni kamin su kyalkyale min da dariyar su ta ‘yan biyu mai ban haushi. Ban ce musu komai ba na bi lafiyar gado na ja bargo har kaina. A sannan ne kowacce ta bi gadon ta suka kwanta suma. Dakin nau gadaje ne na ‘silver’ kanana guda uku, nawa ne a farko sai na Iftihal sannan na Azizah. Can anjima Iftihal da ta fi makotaka dani ta kwaye bargon da ta rufe kanta iya wuyanta ta ce cikin rada yadda Azizah ba za ta ji ta ba, “Anti Abu don Allah in ce wani abu?’ Na dauka tsokanata za ta yi sai na sha mur na ce, “Ki rike abunki bana son ji”. Ta yi shiru, can ta ce, “Am serious, don Allah ya ya so yake? Ina nufin ya ya za ki iya kwatanta son Ya Im a zuciyarki?” (Tana murmushi mara amo). Na lumshe ido na a hankali ina jin wata sabuwar kauna na ratsa zuciyata. Ni kaina na san son da nake ma Imran ba za ya kwatantu ba, ba shi da iyaka, kwakwalwata ba ta yi kaifin da za ta fahimce shi ba, harshena ba zai iya bayyna shi ba, domin ya fi yawan silin gashin kaina. Ta tabbatar ba za ta ji kalma ko daya daga baki na ba, (shiru ma amsa ce, amma ga mai hankali), sai ta hakura ta juya ta kwanta. Washegari ya kama asabar din karshen wata, kuma rana ce da muke sanitary watau kakkabe komi na dakin mu, mu fidda kaya masu datti mu cire yana, mu kintsa sif din mu. Wannan wani aiki ne da muka sanya kanmu bama son masu aiki suyi mana saboda baya gamsar damu. Imran yayi sallama a dakin ya shigo, turaren da ya fesa na (Gucci-Rush) ya bakunci hancinmu. Na lumshe ido zuciyana na girgiza domin ba karamin kyau ya yi ba, cikin bakar shadda ghalila. Mu kuwa ko wanka ba muyi ba. Ni sanye nake da doguwar rigar barci fara sol mai gajeran hannu, sai dai na daura zanen atamfa a kai, kaina babu kallabi, don haka murdaden gashin kaina ke dunkule cikin tufka guda a gadon bayana, rike da abin sharo yana ina sharowa. Su Azizah duk suka russuna suna gayas da shi, ya amsa yana cewa, “Zance na zo Azizah, ina fatan ban yi sammako ba?” Kunya ta kama su duka, suka dukar da kai suna dariya kasa-kasa, ta ce, “Gaskiya ka yi sammako, Anti Abu ko wanka ba ta yi ba”. Ya ce (idanun shi a kaina), “Kin san meye ne Azizah? In da kin san kyan da ta yi min a haka, da na ce ta daina wanka. Wannan Zaynabun dake tsaye gabana, ta fi mun duk matan duniya. Idan na daga ido na dubi wata mace, komi wankanta da kwalliyar ta sai in ganta kodaddiya a kan Zaynab dina. Wanka da kwalliya ba su ke sawa a so mace ba, wannan daga Allah ne. Don haka in kina tunanin hakan ki daina. Ina tabbatar miki in Zaynab za ta shekara ba ta yi wanka ba, ba zan daina sonta ba, ba zan daina ganin ta a matsayin wadda ta fi kowacce mace a idanuna ba….” Dariya suka yi suna kokarin ficewa saboda su dai basu saba jin irin wadannan maganganun ba, balle kuma daga bakin da suke matukar girmamawa. Ya ce, “Ku yi zaman ku ayi hirar da ku, watakila in ci arzikinku ta amshi kokon bara na, in kun tafi ko kallo na ba za ta yi ba. Ku taimaka ku tambaya min Zaynab, shin kalamanta masu tsada na sayarwa ne? Ko-ko kwalliyar da na yo mata ne bai burge ta ba in koma in sako?” Suka sa dariya gaba dayansu, nima kaina ban san sanda na murmusa ba, still ban juyo ba na ci gaba da abin da nake, kamar in ce da shi shin ba yanzu ka gama cewa ba kwalliya ke sawa a so mutum ba? Ya karaso ya amshi abin sharar a hannuna yana cewa, “Kawo nan in karasa miki ko kya zauna mu yi zance?” Ya dubeni cikin idanun shi cike da abubuwa da dama, na yi hanzarin zama a gefen gado saboda kafafuna dake neman kayas dani. Iftihal ta ce, “Hala baka taba zuwa zance wurin Mami ba?” Ya ce, “Eh, yes, ban taba ba, ita ne take zuwa”. Ta girgiza kai ta ce, “Ko da na ji”. Ya dube ta bayan ya aje sandar ya ce, “Me kike nufi?” Ta ce, “Na ga baka iya bane, duk da ban taba yi ba na san ba haka samari ke gayawa ‘yammatan wai sun zo zance gatse-gatse ba, abin babu ko dadin ji”. Ta zura da gudu Azizah ta rufa mata baya ita ma ta ce, “Gaskiya idan baka koyo zance ba, ba za a karbe ka ba”. Ya zauna a gefena na yi saurin rufe fuska da tafukana ina dariyar su, ya ce, “Da gaske ne ban iya ba Zaynab?” Na girgiza kai ba tare da na bude fuskar ba. Ya ce, “Wallahi ko ki bude fuskar nan ko in sumbaci hannun ki”. Da sauri na bude. Ya ce, “Ashe dai yanzu an san ni wane ne, da kar ki bude mana”. Na tsuke fuska gami da baki gaba daya, ya yi dariya ya ce, “Yi hakuri don Allah saki bakin kada fushin ki ya lahanta ni, ya jawo min asara ya dai-daita zuciyata”. Na yi wani irin murmushi a raina na ce, “Ni kuma fa? Da ka sanya tawa zuciyar cikin wata irin wahalalliyar rayuwa da wani al’amari mai wahalar bayyanawa”. Ya ce, “Zaynab don Allah?” Tare da rausayar da kai gefe tamkar marayan da ya rasa uwa. Na ga in ban yi da gaske ba mutumin nan zai yi galaba a kaina, sai na juyar da kai gefe ba tare da na ce komi ba. Ya sake kankan da murya ya ce, “Zaynab don Allah!” Wallahi na ji wannan kira har cikin kwakwalta ta, kaina ya sara,z uciyata ta yi wani irin bugu da karfi. Na kai hannu na dafe kai da kirji duka a lokaci daya. Roko nake kawai Allah ya kawo sanadin da Imran zai tashi ya rabu dani, in ji da abun da ya dame ni. Ya sake kaskantar da murya tare da sakkowa bisa gwiyowin sa, ya daura kai bisa gefen gadon ya sake cewa, “Don Allah Zaynab…” Duk dauriyar da nake yi abin ya ci tura, wai yau Imran dake wahalar da rayuwata ne yau ke roko na da gwiwoyinsa a kasa. Tsinkayen Anti Rose ya tabbata kenan. Ba zan iya jure ganin shi cikin wannan halin ba, ban san sanda na ce, “Me kake so Imran?” Ya dago da hanzari ya dube ni da idanunshi da suka kada suka yi jawur, ya ce, “Zaynab muyi aure shine kawai abin da nake so. Na san kema shi din kadai kike so, duk wannan turjiyar wahal da kanki kawai kike yi, ba kuma solution ne ga problem dinki ba, wanda ni na san shi ba tun yau ba. Illa in ce ke jaruma ce na kuma yaba da jarumtakar ki. Duk wasu experiment da na yi a kanki baki fadi ko daya ba. Wallahi Zaynab ba tun yau nake son ki ba, tun ranar da na fara ganin ki, na dauko ki a sume baki san inda kanki yake ba, tun baki mallaki komi ba. Na ci gaba da rainon son har kawo sanda kika fara zama mutum, na kuma yi nufin bayyana shi gare ki. A lokacin ne na fahimci kema kin kamu da sona, amma ba irin son da ni nake miki ba, naki ragagge ne wanda sha’awa ce ginshikin sa. Sai na yi tunanin idan na ci gaba da nuna miki son da ni nake miki, wanda ya sha bamban da naki ba mamaki wata rana ki rinjaye ni na afka irin nakin, muyi abin da ba dai-dai ba. Kuma a shekarunki na wancan lokacin hakan babban hatsari ne ga rayuwar ki. Na yi tunanin abubuwa da dama a kanki a wancan lokacin, musamman inda kika samo wannan al’amari, duk da tarbiyyar da kika taso a kanta, wadda iyaye da dama ke son ‘ya’yansu suyi koyi da ke. Babu irin zargin da ban yi ba a kanki a lokacin, musamman sani da na yi bakwa kallace-kallacen banza, ba kwa karatun banza. (Excuse me pls) a lokacin sai na ji na kasa yarda da ke, don sai na ga idan kin so ni nta wannan siga, kowa ma za ki so shi da hakan, musamman wanda ya fini. Babu kuma namijin da za ki nunawa hakan ya iya kawas da kai a kanki, ba yabon kai ba sai dai-daiku masu tsananin tsoron Allah, domin ba karamar baiwa Allah ya yi miki ba. Daga baya ne na fahimci abin a halittarki ne nature”. Na yi tunanin idan har da gaske nake ina kaunar ki, to abin da zan yi in nuna hakan shine in yi ignoring dinki, ba don na daina son ki ba, sai don in yi kokarin daura ki a kan sahihiyar soyayya, ba wadda za ta zamo nakasu ga rayuwarki da mutuncinki a idanuna ba. Ha horas dake ta hanyoyi da dama domin ki azabtu ki koyi kaunata, kuma alhamdulillahi na yi nasarar hakan. Duk wasu experiment (gwaji) da na daura ki a kai kin haye su, na san a yanzu kina sona, kina kaunata kwatankwacin yadda nake kaunar ki. Don haka Zaynab don Allah ki yi hakuri ki fasa duk wani ramuwar gayya da kike son yi a kaina. Ban yi da wata manufa ba illa don amfanin kanmu gaba daya. Ban yi don in wulakanta ki ko in tozartaki ba, illa don in samawa kaina kyakkyawan matsuguni a zuciyarki. Ki yi hakuri ki daina wahalar damu haka, we need each other Zaynab plz stop this childishness. Na gaji Zaynab, na yi hakuri na yi juriya kema kin yi, to ki hutar da zuciyoyinmu su samu abin da suke so, tun baki sa na rushe ginin da na dade ina yi ba”. Hawaye ne na ji sun fito min sur-sur, na yi azamar dauke su kada ya gani, amma ya ganin. Ya dawo gabana a kasa ya zauna dirshan, ya kama hannuna na dama ya rike cikin nashi, ya ce cikin karyayyar murya, “Kuka Zaynab, why? Idan akwai abin da ya bata miki rai cikin kalamai na ki dubi Allah ki yafe mani, ban yi da niyyar in bata miki ba, na fada maki gaskiyar abin da ke zuciyana ne domin wanke zargina da kike da wulakanta ki. Ban sani ba ko kina daya daga cikin mutanen da ke son a fada musu karya don a faranta musu. Na fada miki iyakar gaskiyata ne domin ki fahimce ni, ki tsayar da zuciyarki wuri daya….” A nan ma ban ce komi ba sai hawayen dake ta bilbilo mini. Ya yi duk iya kokarinsa don jin wata kalma daga bakina na ki cewa komai, sai hawayen dai da nake ta fitarwa ina sharewa kamar an sunce famfo. Daga karshe sai haka ya fita ya kyale ni yana cewa, “Na baki kwanaki biyu ki yi shawara da zuciyarki Zaynab, ba zan takura miki ba. Na kuma yi alkawarin yin biyayya ga duk hukuncin da kika zartas garemu”. Kuka nake ba don komi ba sai don farin ciki da bakin ciki duka a lokaci daya. Kuka nake na farin cikin zuciyata yau ta tabbatar da abin da take shakku a kan shi, yau ta same shi. Kuka nake domin bakin cikin ba zan iya auren Imran ba, domin tsira da mutunci da martabana da na iyayena. Kwanaki biyu duk hanyar da na san zan ga Ya Im ina kauce mata. Shima bai matsa da lallai sai mun kebe din ba. Za su yi ta hirarsu shi da su Ifty da Mama ba tare da na tofa ko uffan ba. Ranar lahadi ne da daddare ya ce in je in kawo mishi wayana, ba musu na dauko har layin da na cire na kawo mishi. Ya dubi Mama ba zato na ji ya ce, “Mama na kawo miki karan Zaynab”. Cikin son fahimtar mene ne tsakanin Imran da Zaynab din suke share junansu ta ce da shi, “Me Zaynab din ta yi maka dan Abba? A sanina yau shekaru dai-dai har shida babu wanda ya taba budar baki a gidan nan ya ce ga laifin Zaynab, ko ya ce ta bata mishi sai kai yau. Amma ban sani ba ko Zaynab din dana sani, mai kirki mai addini, mai girmama na gaba da ita da tsantseni cikin al’amuranta ta canza hali ne. tunda ni ba zama nake yi ba”. Ya yi murmushi ya ce, “Ba ta canza ba, tana nan a Zaynab dinta da kika sani. Cikin kyawawa halayenta sai ma abin da ya karu. Waya ce na basu kowa yana amfani da shi amma ita ta rufe nata, ko kunnawa ba ta yi ta raina kenan?” Ta girgiza kai da sauri ta ce, “A’a, Zaynab ba ta rainuwa, ko kiyashi ka ba ta a matsayin kyauta za ta ce nagode, Allah ya kara budi. Watakila dai akwai dalilinta na rufewar amma ba wannan ba”. Ta juyo ta dube ni tana murmushi, na sarda kaina kasa nima ina murmushi cike da jin dadin yabon da take yi mun. Ta ce, “Ina sauraron dalilin ki na rufe wayar da Imran ya baki Zaynab, don in yi hukuncin adalci a tsakaninku”. Na ce a hankali, “Mama firgita ni take, karar ta na damuna, musamman in ina barci”. Suka kyalkyale da dariya ban da Imran, kallona kawai yake cike da matsanancin so da kauna. A hankali ya ce, “Ai ana canza tune din, ko kuma ki sanya shi a silent ba za ya ke firgita ki ba, ko kuma ki sanya kiran sallah for your own convience”. Ranar litinin Allah-Allah nake mu fito paper in nemi Anti Rose, kuma da yake paper din Islamic Studies ne bana jin wuyar sa, nice farkon fitowa. Gudu-gudu sauri-sauri na bita hanyar fita ganin tana kokarin juya motar ta domin tafiya gida. Na daga murya tun karfina daga nesa ganin cewa duk saurina ba zan iya cimmata ba, na ce, “Anti Rose”. Ta dakata kamar tana nazarin ta inda kiran sunan ya fito, kana ta yi hanzarin juyowa ta dube ni. Lokaci guda ta kashe motar ta fito. Sai murmushi nake ita ma murmushin take min tun daga nesa. Tana karasowa inda nake kuwa ta ce (tana mai nuna ni da dan yatsanta) “Akwai daddadan labarin Imran a bakin Zaynab dina”. Ta kama hannuna har staff-room, babu kowa duk suna dakin jarabawa, muka zauna a kujerun dake fuskantar juna ta ce, “Hurray Zaynab, bani in sha”. Na yi murmushi na zayyane mata dukkan abubuwan da suka yi ta faruwa tun dawowar Ya Im, ban rage kalma daya ba. Ta ce, “Thank God! Na kuma gode miki da baki yi saurin amsawa ba. Hakan ma wani abu ne da zai kara miki matsayi a zuciyarsa. Ki ci gaba da kin amsa bukatar shi har sai kin koma gaban iyayen ki. Idan ya biki ya cika mai kaunar ki Zaynab, sai ki nuna mai matsayin ki na cewa ke talaka ce, kasa da shi. Kina gudun wulakanci. Idan ya ce ya ji ya gani yana son ki haka, Zaynab ki yarda da Imran ku yi auren ku, ina muku fatan alkhairi”. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Mun baro Katsina ranar Lahadi, kai tsaye muka zarto Kanon Dabo, yaro ko da me ka zo an fika, mai Dala da Gwauron Dutse, tushen Maguzawa ta Dabo tumbin giwa. Kwanan mu biyu a gidan Baba Sa’idu na Kano dake Sultan Raod sannan muka tattaro muka yo Gwarzo. In ba don idon Abba ba, da Hajiya Sa’a da iyalanta ba za su Gwarzo ba iyakacinta Kano, domin ita a gareta takura ne zaman kauye ai sai dole. Amma shi Abban baya ganin haka. Kar ku yi mamakin jin cewa Hajiya Sa’a ‘yar Gwarzo ce ‘yar kanwar Inna Dubu da aka rike a gidan Malam Ali, domin iyayen Dubu talakawa ne futuk amma duk sun rasu. Don haka Dubu ta daukota ta rike. Shi kuma Abban a rayuwarshi ba shi da kamar Malam Ali, a shirye yake kuma da ya bata da kowa in dai a kanshi ne, daga ‘ya’yan shi har matan shi ya sha gaya masu wannan. Don haka wannan lokacin take taka-tsan-tsan. Ita dama ‘yar dakin Innar Faruq ne, don haka can suka sauka da ‘ya’yanta. Ni da su Mam, ‘yan biyu da Gambo muna dakin Innana dake ta faman makale ni kamar ta maishe ni ciki. Yau abin da sauki tunda kuwa ban ga ta hana su Iftihal shiga dakinta ba, ko don ganin idon uwarsu ne, oho! Ko kuma ‘yan mutuncin ne a kanta? Na danganta hakan da dokin zuwana da take, domin na yi dadewar da ban taba yi ba har watanni shaida ban zo ba. Rabi da Mama sun barke da hirar yaushe gamo wadda duk rabinta labarin rayuwata ne da ke burge kowa, yake kuma baiwa kowa sha’awa a can Sokoto. Ta ce, “Zaynabu-Abu uwar addini ce, ban taba ganin yarinya Abida (mai ibada) irin Zaynabun ki ba”. Inna ta kara janyo ni ta rungume tana murmushi dadi ya cika ta. Don ba abin da take so a rayuwarta irin ta ji ana yabon Abun ta, Kyautar ta, Kyautar Allah (kamar yadda take cewa). Sai na samu kaina da kara godiya ga Allah da ya kare ni daga aikata ZINA, kamar yadda zuciyata da gangar jiki ke so, har suka so su ja ni. Wannan ya samo asali daga addu’ar da Malam yai min a sanda aka haifeni a al’aurata, domin kariya daga aikata zina. Aya ta ( ) cikin Suratul-Maryam. (Don haka iyaye a dage da kula da ita wannan addu’ar a yayin da aka haifi yaro, to insha Allah ba dai ya aikata zina a rayuwarshi ba). Na tabbata da na karya zuciyar Inna Rabi, fiye da wanda ta samu kanta a gaba dayan tsayin rayuwar ta, wanda ni ba zan ce ga shi ba. Da duk wannan kaunar da take mun, ta koma kiyayya, watakila irin kiyayyarta ga BABA SA’IDU. Sai na samu kaina a mai tambayar kaina, wannan na nufin BABA SA’IDU ya aikata ZINA ne shi yasa ta tsane shi? To da WA????? (Wa’iyazubillahi). Wama taufeeqee illa billahil aliyul azeem…. Kada Allah yasa tunanin nawa na banza ya zama gaskiya, kada Allah yasa tunanin nawa na wofi tabbatacce ne. ya Allah ka fitar mun da wannan mugun tunanin a zuciyata…. Allah ka dube ni, kasa tunanina ba gaskiya bane rudin shaidan ne. Ba abin da ke dadadawa Innana kamar ganin yadda nake girma da wani irin murjewa, kai ka ce irin Larabawan nan ne na Lebonon. Duk na fi ‘ya’yan Farfesa daukar ido da kwarjini, haka duk kalar kayan da nasa kyau suke min su kuma amshe ni kasancewata jajur, masu tsada ne ko akasi, kai ka ce don ni aka kirkire su. Ni Zaynabu-Abu shiru-shiru ce, bani da kwaramniya, kuma bana sonta. Da wuya ka ga ina magana in ba a kan abu mai muhimmanci a gareni ba. Sun baro Gwarzo bayan motarsu cike da tsarabobin da suka saba komawa dasu, wato kamar su man shanu, garewanin man gyada, kindirmo, madarar shanu, kwan kaji da na zabbi da sauransu. Wannan karon har kajin gidan gona ishirin Malam ya ba su Hassan, amma an fige an gyara ya kuma ba Haydar takwaransa dan maraki, Abba ya ce a bar shi a nan a kiwata masa. Ni da su Azizah bamu so rabuwa ba, don dai ina son samun lokaci da Innana ne su kuma sun kallafa ran su a son zuwa Porthearcourt, akwai tambayoyi da dama da nake son in yiwa inna, musamman a kan irin gore-goren da su Hassan ke mani a shekarun baya, wanda wancan lokacin karancin shekaru da rashin wadatar hankali bai barni na kuma waiwayarsu ba, sai yanzu da hankali ya zo mini nake ganin hakan tamkar wani barazana ne ga mutuncina a nan gaba. Mun kwanta ne da daddare, sauro ya gallabe mu, duk kuwa da maganin sauron da muka kunna da (Rambo) da na fesa, amma ni ko jin cizon suron bana yi balle in sosa, abubuwa ne da yawa ke damuna a zuci. Wurin karfe daya na dare na ja tsuka “Tsut!” don tuno shekarun baya. Ashe Inna Rabi barcinta ba wani nisa ya yi ba, ta ce, “Ke in wani abu ne ya dame ki, ba kya gaya mun? Haka kawai ki bi ki isheni da tsaki cikin dare”. Maimakon in amsa mata sai tsakin ne (by mistake) ya sake subutowa daga bakina, na ce, “Kai abin ne ma Inna na kasa ganewa wallahi”. Ta ce, “Can gidan Baba Sa’idun naki, fi sauran-Babanni ne kike da matsala ko-ko satittikan da za ki yi mana ne kike ganin kyashin su, kin baro A/C sauro na cizon ki? Abin da na guda kenan ai tun farko Kyauta na hana tafiyar ki hannun su Azumi, amma Malam bai saurare ni ba, saboda dukkanku baku dauke ni a cikakkar mai hankali ba sai SA’IDU. Sa’idu ya fini GIRMA a idanun ku, komi Sa’idu ya ce shine dai-dai, amma Rabi ai MAHAUKACIYA ce…..” Wasu hawaye suka balle min, na ce cikin rishin kuka, “Ki daina gaya min haka Inna, wallahi-wallahi a kowanne hali, a kowanne matsayi babu inda ya fiye mun dakin nan naki kwanciyar hankali. Babu inda nake ji na sake, freely, cikin walwala da kwanciyar hankali tamkar nan. Bani da wanda ya fiki, bani da wanda nake so fiye dake. Baba Sa’idu bai taba daukar ki matsayin maras hankali ba, ke ce dai kike zaton haka. Ya sha cewa inda mai hankali a duniya to ke ce, in da wanda zan dage wurin bin maganarsa to ke ce, in da wanda ta san ciwon kanta a duniya to ke ce. Abin da ke damuna kwata-kwata bai shafi abin da ke kike tunani ba. So nake in tambaye ki ashe mu ba Fulanin Gwarzo bane? Kuma meye BARAROJI? Mene ne SADAKA-YALLAH?????” Inna Rabi ta mike zaune a nutse ta yi murmushi. Ta mika hannu ta latsa makunun wutar lantarki dakin ya gauraye da haske, iare-iren wadannan gorarrakin ita ma ta sha su wurin kishiyoyinta a zamanin kuruciyar ta, ta kuma tabbata watan-watarana za a yiwa Abun ta. To amma ba ta zaci tun yanzu ba, ta dauka sai a gidan aure ko lokacin aure. Ba ta san daga inda ya fara fitowa ba, don haka ta ce, “Shin wa ke ce da ke hakan a gidan Sa’idu?” Na ce, “Maganar fa ba ta yau ba, tun farkon zamana dasu ne. kuma tun lokacin Baba ya saba musu basu sake ba. Ita Hajiyar ma yanzu ba ta shiga harkata kowa zaman kansa yake a gidan, babu mai shiga shirgin wani. Ita Hajiya Sa’a ta gayawa su Hassan suka samin kahon zuka a wancan lokacin, wai suna kyankyami na saboda mu BUZAYE ne, kazame. Su tofar da miyau, suyi amai wai BARAROJI babu wanda ya kaimu kazanta. Sai nake jin tsoron ko wani ciwo ne hakan abin kyama”. Inna Rabi ta hasala ta ce, “Ita Sa’ar har tana da bakin gaya mun haka? Tana da bakin ce dake SADAKA-YALLAH ba ta fadin babban? Koma meye ta ce a yanzu ai duniya ce, ita din kuma makaranta ce babu abin da ba za ka gani a cikin ta ba. Wanda bai zo ba ma tana nan tana jiran, kuma tarihi MAIMAITA KANSA yake, sannan kowa ya kwana lafiya shi ya so. Idan a yau na ga dama wallahi ba za ta kara jin dadi a rayuwarta ba, daga ita har Sa’idun da take takama da shi, domin GIRMANSU YANA HANNUNA, yau ne ko gobe in na ga dama sai in FADAR DA SHI, in ga karshen kudi da boko, wadanda basu da amfani idan babu mutunci a idon duniya. To amma ba zan yi hakan ba saboda wasu manyan dalilai, akwai ranar da dubunta za ta cika. Tara su nake daga ita har Sa’idun ina jiran ranar da wani a cikinsu zai wulakantaki, ina jiran ranar da zai nuna fifiko tsakaninki da ‘ya’yansa….” Sai kuma ta razana da ta fuskanci ko da wa take magana, Zaynabu ce ba Au ba, da cikakkar budurwa mai hankali take magana ba Kyauta-Abun d ata sani a baya ba ce,. Ta yi hanzarin gyara zancenta da cewar, “Zaynab mu ba Bararoji bane. Sune ‘yan kasarmu dake daji, mu ‘yan kasar Niger ne ‘yan uslin wani gari DAMAGARAM, amma iyayenmu da ‘yan’uwanmu duk a babban birnin Yamai (Niamey) suke zaune, har yanzu suna can. Mahaifinmu fitaccen dan kasuwar fata ne da ya yi fice a Niger, kuma mashahurin dan siyasa ne da ya rike mukamai da dama a gwamnatin Damagaram, wanda gab da rasuwarshi yake dan takara mafi rinjayen magoya baya da suka tsaya neman kujerar gwamnatin Damaragam. Duk dangina suna Niamey, ba fakiri ko daya, bamu taba yin talauci a rayuwarmu ba, bamu san shi ba ni da iyaye da dangi na gaba daya. Kaddarar aure da rabon haihuwar ki ya kawo mu Najeriya mu da mahaifinmu da kanwata NURATU da ta bata a hanuna. Batan Nuratu ne ya hanani komawa gida, ya hanani neman dangina har yau don ban san me zan ce musu a kanta ba, kuma rashinta ne ya tsomani a halin da har yau kike ganina a ciki ake min kallon MAHAUKACIYA ko TABABBIYA. Su kuma danginmu basu san inda muke ba, don mahaifinmu rasuwa ya yi a sanadiyyar hadarin jirgi a kan hanyarshi ta komawa gida, ya gaya masu cewar ya aurar dani ba da saninsu ba. Ki taya ni addu’a Allah ya bayyana min Nuratu, ni kuma na yi miki alkawarin a ranar da na ganta a ranar ne zan sadaki da danginki na wurin uwa. Sai kin raina zamanki da su Sa’ar da ke ce dake SADAKA-YALLAH, sai dai ki basu SADAKAR ki wuce. Idan kika shiga Niamey ko Damagaram kika ce kina neman wani da ya shafi iyalin MAINASARA KANGIWA, ko yaro kankani ya san wannan sunan. Ki yi hakuri ki kyale ta, akwai dalilin da yasa ba ta son ki, ba kuma za ta so kin ba har abada, illa ta boye hakan a ranta don amfanin kanta, amma ai……” Ta sunkuyar da kanta. Ta dade tana kallon kyawawan yatsun hannunta, can ta dago ta ce, “Ke Zaynab kada ki damu kanki a banza, da dangin Uba ai ake tutiya ba na Uwa ba, ko ta isa ta ce da Malam SADAKA-YALLAH? Ni ta fada ta more, akwai ranar da GIRMA ZAI FADI!” Na yi shiru ko kwakkwaran motsi bana yi, sauraron Innana nake da dukkan hankalina. Ta ga akwai alamun rashin fahimtar wasu abubuwa cikin kalamanta a tattare dani, sai ta ce, “Ke yi kwanciyar ki don Allah kada ki kara sa wannan shirmen a ranki, na ce dake da dangin Uba ake tutiya ba na Uwa ba. Kuma ni nan da kike gani, zaman jiran Nuratu nake, amma ba zaman soyayyar Malam Ali ba, ko zaman jiran Sa’idu ya dauko ya bani. Domin har yau Sa’idu bai yi arzikin da zai bani in mance takaicin da ya tusa mini ba, da rayuwarmu da ta gurbata a dalilin son zuciya irin nasa…” Da maganganun Inna na kwana ina taunawa ina cizawa, ina hurawa a cikin raina. Abubuwa da yawa na kasa fahimtarsu, I’m confused! Da maganganunta masu daure kai da caza hankali, illa na samu kaina a daukan ‘Diary’ dina na rubuta kalmar “MAINASARA KANGIWA” da wasu cikin kalamun ta da ban fahimta ba. Nake fatan duk ranar da Allah ya dawo da Ya Faruq zan sanya shi ya fidda ni duhun da ke cikin su. Hutuna na wannan karon a Gwarzo na ji dadin shi fiye da na ko yaushe, don muna tare da mutanena su Hafsisi. Ita Indo an sa mata rana da wani malamin su a can Kabon, ita ko sarkin rigima Hafsisi ta ki kula kowa wai ita Faruq take jira, shi kadai take so duk fadin duniyar nan, idan ba shi ba sai dai ta mutu ba ta yi aure ba. Na yi dariya har da fidda hawaye, na jinjina kai, na jinjina mata, don ni dai tunda nake da Ya Faruq dai-dai da rana daya ban taba jin ya ambaci wata ‘ya mace a duniya da sunan so ba, balle wata Hafsisi. Sanda muke aji hudu ne ma Azizah ta taba rubuta mishi leta wai tana son shi, in ta kare karatu ya gayawa Abba yana son auren ta. Tun lokacin ya kirata kamar abin arziki, ya kwakkwada mata mari ya ce kuma ba shi ba, ko wani daban ta sake cewa tana so sai ya gayawa Abba, in yaso a cire ta makarantar ayi mata auren da Shehu direba dai amma ba da shi ba. Tun daga lokacin ko da wasa Azizah ba ta kara shiga shirgin sa ba, shima kuma sai ya rage wasan da yake dasu duka. Na ce, “Hafsisi in za ki ji shawarata, ki samu wani mai sonki tsakani da Allah ki yi auren ki ya fiye miki alheri, don shi wannan Ya Faruq da kike gani ko zancen aure baya yi, kuma nan da shekaru biyu ma albarka ya dawo. Azizah ma bai karbeta ba balle ke?” Hafsisi ta kulu, ta kawon duka ta ce, “Me Azizar ta fini ban da Turancin banza, nima yanzu meye ban sani ba a Turacin?” Na ci gaba da dariyar da ta kara kular da ita, cikin zolaya na ce, “Turancin ma ba fa fiki ba”. (maganar da na zo ina dana sani da ban yi ta ba). Budar bakin Hafsisi sai cewa ta yi, “Ba wani nan, ai dama ba tun yau na san kin fi son su Azizah dani ba, saboda su masu kudi ne kuna samu a jikinsu kuna ci ke da Malam da Ya Faruq din naki. Duk kun ki mahaifarku kun je kun tare masu a gida saboda tsabar kwadayi. In dai don dan abin da ake ikirarin Malam ya yiwa Alhaji Sa’idu ne da yana karami, ai yanzu ya biya shi har da riba, tunda har Makkah ya kai shi sau ba iyaka. Kada dai kuke mantawa a kullum an ce, inda kwadayi…..” Ta murguda baki ta yi tafiyarta ta barni da baki bude. Maganganun Hafsisi sun haifar min da ciwon kai, na dade ina maimaita kalamanta a zuci. Babu shakk duk abin da ta fadi gaskiya ne, kuma kalamanta duk shigen na Innana ne. Sai na ji wasu dumammun hawayen tausayin kaina masu zafi sun digo a kan yatsun kafata. Mafari kenan da Hafsisi ta daina yi min magana, ta dauki gaba dani, ta shiga nuna kyashin ta dani muraran. Tun daga lokacin na ji Sokoto ta fice min a rai, na rika gudun cikar kwanakin hutuna. Na alkawartawa raina ko da na koma gidan Baba Sa’idu da na kare makaranta ko kwana daya ba zan kara ba zan dawo gida. Don haka a komawata wannan karon su Azizah sun ga sauyi da yawa, gaba daya na yi sanyi, na mai da kaina bare a cikinsu. Na daina amfani da kudin da Baba yake bamu sai dai in ajiye kawai. Shima don ina jin nauyinsa ne amma da na ce ya daina bani. Na rage cin abincin gidan, idan na ci da karfe biyu bana kuma ci sai dare, na daina karin kumallo, don a ganina duk hakan yana cikin kwadayin abin hannun su. Daga baya ma in an tashi daga makaranta sai na dinga shiga restaurant din makaranta in saya in ci, in mun dawo ba zan ci na gidan ba. (Na manta cewa shi kansa kudin da nake sayin ai daga aljihun Baban yake fitowa). Su Azizah dai na kallon ikon Allah sun rasa ta cewa, sai Iftihal ce rannan ta ce, “Anti-Abu dai ta zama waliyyah”. Ranar wata alhamis mun dawo daga makaranta, a harabar gidan muka tadda Hajiya ta yowa wata kyakkyawar budurwa rakiya, ga wasu ‘yammata uku suna takewa budurwar baya sun rike mata jaka, za ta yi shekaru ashirin da shida. Baka ce amma a goge take, ko ina a jikin nan nata sumul-sumul, ga sullubebiyar mota ta (end of discussion) baka sidik sai daukar ido take. Tsayawa fasalta sittirun da ke jikinta ma bata lokaci ne, sai jifa mu take da wani irin murmushinta kamar madara, da hakoranta kamar kankara. Ta yafito mu da hannu muka je ta kama hannunmu mu duka tana tambayar mu ya ya shirye-shiryen (WAEC). Mamaki ne ya kama mu na yadda akai ta sanmu har ta san jarabawa zamu yi. Hajiya ta shiga yi mata bayanin mu, wai wadannan Azizah ne da Iftihal (twin sisters) din Imran. Wannan kuma Abu ce kanwar Faruq. Ta ce, “Lah! Ke ce Abun Faruq Aliyu?’ Ta makale ni sosai a jikinta ta sake cewa, “Ina jin labarinki sosai a bakinshi, amma ban zaci haka kike da kyau ba kamar Baturiya. Dan’uwanki ya damu da ke sosai Zaynab, da wuya a zauna da shi bai yi zancen ki ba, ina taya ki murnar kasancewa ‘yar’uwa ga mutum irin Faruq Gwarzo”. Na lumshe ido wani dadi ya kashe ni. Kowa ya budi baki alheri yake fada a kan Ya Faruq, ban taba jin wanda ya aibata shi ba, dai-dai da rana daya. Haka duk wanda ya san shi in ya ganni zai ce ya sanni, Faruq yana yawan ambato na. wannan ne yasa har abada ban da mutum mai kimar Ya Faruq. Ta mikawa ta bayanta hannu ta miko mata jakarta, ta sanya hannu a ciki ta damtso kudi da ba ta san adadinsu ba, (American-Dollars) ta fito dasu tsurar su ta raba su gida uku, ta mika mana. Azizah uwar son kudi ta riga kowa amsa, har da mu aka rakata bakin motar ta, ta ja ta fita cikin wani irin ubansun tuki. Azizah ta buga tsalle ta yi cikin gida tana cewa, “Yanzu zan shirya in tafi canji, in Allah ya yarda sai na zama MAMI ABDULHADI”. Na samu kaina a maimaita sunan Mami Abdulhadi fiye da cikin carbi, na so in ji sunan a baya amma na rasa daga inda na ji shi. A dakinmu na ce da Iftihal “Wai ita wannan Mami wace ce?” Ta ce, “Baki san Adda Mami ba? Diyar Gwamnan Sokoto Abdulhadi Talata Mafara, budurwar Ya Im?” Wallahi ban san sanda na saki kudin da ke hannuna ba suka tarwatse a kasa, a take na ji na tsane su bana son ganin su kamar yadda na tsani wadda ta bani. Na ji haushin kaina da har na tsaya na kula Mami, wani kululu ya zo ya tokare min a makogaro ko miyau na kasa hadiya. Su Azizah sun dauka wai mamakin ita ‘yar waye ne ya kamani, don son kara burge ni da tabbatar min da Mami wace ce, Azizah ta zura da gudu dakin Mama ta zo da mujallar ‘OVASION’ da bama gajiya da kallo ta auren Aishah Babangida tana nuna min Mami cikin ‘yammatan Aishah, dama kuma na so in tuno inda na ga fuskar Allah ne ya mantar dani. Irin rudewar da Azizah ta yi a kan Mami sai na ji ina tausayin kaina, da burin da na daura a kan Ya Im. Yanzu idan ta san ni din ina son dan’uwanta ko ya ya za ta karbi al’amarin? Ni Zaynabu-Abu ‘yar Malam Ali, jikar Mamman Gwarzo, da bamu da komi sai tumaki, sai tsintsaye. Na fara fidda rai da Imran a karo na farko a rayuwata. Na san Imran ya fi karfina nesa ba kusa ba, wai wan ce ‘kwarya ta bi kwarya…..’ Anya maganganun Anti Rose za su taba zama gaskiya kamar yadda take ikirari? Kwana na yi a ranar nan cike da kishin Mami, ko rintsa ido na kasa, gami da wani azababben son Imran dake kara daidaita zuciyata. Sai dai wannan karon kam kauna ce ta hakika, da har nake jin ko ya ya ne, ko ya nake ba zan iya barwa Mami shi ba. Amma a dole washegari na shiga tirsasa zuciyar da ta fidda Imran da duk wani al’amarin shi a cikin ta. Ina nuna mata beke da illar dake cikin hakan, ina nuna mata Imran ba alkhairi bane a tare da ita, ina nusarsheta da cewa a kul, Zaynabu! Igiyar rakumi… ta yi nesa da kasa, tsira da mutunci…. ya fi tsira da kudi, abu mai yiwuwa shi ake yi ba mara yiwuwa ba, yaro tsaya matsayinka…. kada zancen ‘yan duniya ya rude ka, kai zai kai nya baro. Amma wallahi zuciyar nan mai laushi da kafiya (delicate but strong) ta ki amincewa, ita dai Imranan nan shi kadai take so by all means. Babu abin da ya dame ta da hujjoji na, ba ta san su ba, IMRAN kawai ta sani. Cewa take Zaynabu-Abu luv, have no boundaries….. A kwanakin biyun da suka biyo baya, duk rabin hirar su ta Mami ce da kirkin ta. Idan na ji ba zan iya jurewa ba, sai in tafi daki na ci kuka na ya isheni, in sa sabulu in wanke fuska. Kamar wata zautacciya, in saka wannan in kunce da wancan. Daga karshe na alkawarta ma raina ko Imran din nan ne autan maza na hakura da shi, don tsira da mutuncina da na iyayena. Duk wanda ka ga Hajiya Sa’a ta tashi ta rako gate da kafafunta, to tabbata ya isa, ta san shi din wani ne, za kuma ta samu wani abu a jikinsa, duk da babu abun da Allah bai mata ba ita da mijinta da ‘ya’yanta, ba ta da godiyar Allah ko kadan. Ko a jiya Imran ya aiko mata da sabuwar mota (Hummer Jeep) da gaba dayan albashinsa na wata da watanni, dama ya ci alwashin ita ne za ta fara cin gajiyar iliminsa, amma a yadda take nan-nan da Mami, sai ka rantse ba ta taba mallakar kwandalar kanta ba. A kwanakin da suka biyo baya ban kara yardarma zuciyata ta tuna Imran ba, na tattarasu shi da Mamin da al’amarinsu na zuba a kwandon shara. A yau muka fara zana WAEC da practical Biology, bamu muka fito ba sai karfe hudu na yamma. Kwakwalwata ta yi zafi, kaina ya yi zafi rau, ga yunwa, gajiya da nannauyan barci a kaina, wanda ban samu na yi ba a daren jiya muna ta karatu. Don haka mun shigo gida a gajiye lis, muna tafe muna hada hanya, ban lura da bakuwar motar da muka samu ba a harabar gidan. Muka isa falo kowacce na ‘wash-wash’, ni ko dafe nake da goshina, idanuwana a rufe nake tafiya a cikin falon. Ban ankara ba na ji na yi karo da mutum, kamin wani lafiyayyen kamshin turaren nan na (Boss-Intense) ya bakunci hancina. Na yi hanzarin bude idanuna da suka yi ciki sosai saboda yunwa da wahala, na dube shi yana murmushin nan nasa mai cike da ginshira, a hankali ya ce, “Ya… ‘yan makaranta ba a gani ne?” Wallahi sauran kadan in fadi a tsakiyar falon sakamakon kafafuna da suka kasa daukar nauyin jikina, saboda yadda Imran ya koma, in da dare ne ba za ki gane shi ba. Ya zama kato, ya zama ‘giant’ ya kara kyau na ban mamaki. Tsayayyun kafadun nan nashi ‘pysique’ na barazanar gabje maza biyar a lokaci daya saboda yadda suka kara habaka har da doro na musamman, na kasaitattun maza. Ya kara haske ba can ba ‘chocolate’, ya kuma kara murjewa, da gani za ka san naira ce ta zauna da gindinta. Lafiyayyen agogon ‘switch-blustery’ sai walkiya yake cikin lallausar fatar hannun shi, yana sanye da farar shadda kal kamar takarda, dinkin mazan Maiduguri. Na yi gaggawar ba shi hanya, ya yin da shawarar Anti Rose ta zo min cikin kaina kamar karatun sallah. Cikin halin ko in kula na ce, “Sorry plz, ban ganka bane na gaji ne sosai. Muna barka da zuwa”. Da daddare muna falo muna ta hirar pepermu ta yau, ya shigo yana balle links din hannun shi yana tambayar Mama ina abincinsa. Gaba daya muka rude mai da labarin zuwan Mami, muryata ta fi ta kowa karadi, ina kara kuranta kyawun Mami da kurzanta kirkin ta, duk sai ya sha kunu ya bi ya daure lallausar fuskar nan tam, alamun ba wargi. Amma bamu fasa ba, kamar ma zuga mu yake. Hajiya na gefe tana ta murmushin jin dadi, ta ce, “To kai ka ji ‘yan kannen naka ma sun yaba da ita”. Ya dago fuskar nan a murtuke kamar hadari, ya kulu iyaka. Ya hade giran sama da na kasa a take ya koma (previous IMRAN) mai gigita kannensa. Na yi mamaki da bai daka mana tsawa ba. Ya zube min manyan idanun shi a mamakance, ya ce cikin gatse da wata murya mai kama da ta mai ciwon makogaro, “Har da ke Zaynab, kema kin yaba da Mami?” Da sauri na gyada kai ina dariyar nan da Malam Bahaushe ke kira (yake), na ce, “Wallahi kuwa Ya Im na yaba, a very simple lady, ba ta da girman kai”. Ya sakar min hararar da ta kada min ‘ya’yan hanji, ya ce, “Tunda haka ne ki hadata da Faruq man, kin ga shima baya da girman kan, amma ni ta yi mun tsufa sai yarinya (sweet 16) zan dauka, yadda nake (fresh) din nan in na auri kaman Mami ‘yar (28) ai na ci baya……” Iftihal ta toshe baki kada dariyar da ta zo mata ta fito, Azizah da Hajiya suka daure fuska wato sun ga samu suna neman ganin rashi. Ni ko na yi tsuru-tsuru don duk maganar nan da yake idanunshi a kaina yake yin su, kamar da ni kadai yake magana a falon. Ya ci gaba da cewa, “Shin ma wai ita Mamin da ta zo ne ta ce muku na ce ina sonta? ‘Yar ajin su Faruq ce fa, daga kawai tana gani na ina zuwa wajen sa ta like min kamar kaska, amma ni wallahi bana ra’ayin bakar mace a rayuwata, ni baki ita baka, muyi ta haifar bakaken ‘ya’ya me aka yi kenan? Ko Annabi (S.A.W) ya ce in kai baki ne ka auri fara, in kai fari ne ka auri baka, sai ku haifi ‘ya’ya masu kyau. To kin ga shi Faruq fari ne sol, watakila za ya iya maneji da ita su jera kafada, ko ya ya Hajiyata?” Ta dunkule hannu ta sakar masa dakuwa, ta ce, “Ungo nan, babban banza kawai, ka tsaya kana irin wannan maganar da kannen bayanka ko kunya baka ji, sahorami, shashasha, kada ka auretan mana wa ya yi asara? Ka san dai ba za ta rasa mai so ba, don ba ta yi kama da ‘yan kananan gida ba”. Ya yi dariya ya ce, “Allah yasa Obasanjo ne Babanta ba Abdulhadi ba, barawon dukiyar al’umma, tunda ya hau kujerar Sokoto ko kwatami bai yiwa al’ummarmu ba, sai baitil malin mu da yake ta handamewa yana kaiwa kasar waje. Ku saurara nan da sati za ku ji shi a hannun EFCC. Don haka sai ku samo min ‘yar sabon Gwamna, tunda ku ke da idon zaben mata ni bani da shi. Amma wannan bana yi, bana so a kai kasuwa, kada nima ina kwance ina shan amarci na ga sammacin Farida….” Ta dauki filet din da ta gama cin gasasshen nama a ciki ta maka masa, ya kauce ya fice da gudu-gudun sa yana kara gaya mata, “Ko da yake Hajiya ki yiwa Hassan din ki kamun ta, gashi nan ya dauko tsawo kwanan nan zamu yi kafada da shi, in har da gaske surukuta kike so da ita”. Da haka Imran ya kashe zancen Mami a gidan amma ban da a zuciyata. Kullum Mami tana nan like cikin raina har mafarkinta nake anyi musu aure da Imran, sai dai ko alama ba wanda na bari ya gane halin da nake ciki. A wannan zuwan da Imran ya yi, gaba daya ya canza mana, ya dawo YA IM din sa, mai son kannensa da son kula su, ko da yake ma mu yanzu bama zaman gidan, kullum safe da yamma muna makaranta. Ni kuwa in na shige daki tun karfe shida na yamma bana kara fitowa balle mu hadu a hirar falo, zan fiddo littafina in tisa karatu sai gobe kuma, in sha lemo in ci biskit in yi kwanciya ta zuciyata kal babu wani Imran a ciki. Na danganta canzawar shi da dadewa da ya yi bai ganmu ba. Ya dauki annual-leave din shi ne na watanni uku. Allah-Allah nake mu kare jarrabawar in yi gidan ubana in huta da wahalar rayuwa, zancen zuwa jami’a da su Azizah ke yi babu shi a wajena, sam bana ra’ayi. A can falo Imran cike yake da mamakin rashin ganina a gidan, ya damu su Azizah da tambaye me nake yi a daki ni kadai, sai su ce a takaice “Karatu”. Ya ce, “Ku bakwa karatun?” Su ce, “Muna yi mana, amma bama iya irin nata. In ta yi (seat) dinmu daya muna kwafe”. Don haushi ya rasa mai zai ce musu, ya dade yana kallon su kamin ya mike ya rufe ido ya balbale su da fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, wai zai kai su ga hukumar makarantar ayi musu daurin shekaru biyar na (malpractice). Sai Azizah ta mere baki ta ce, “Wallahi Ya Im yadda ka je haka za ka dawo, don kuwa duk (invigilators) din samarin ta ne, har wajen zaman mu suke kawo mana amsa, ita ce dai ba ta karba, amma wallahi har principal saurayin ta ne. shima GG da ya sata wankin kashi yanzu in zai rabu da duk abin da ya mallaka zai yarda, in har Zaynab za ta daga ido ta kalle shi…..” Allah sarki, ba ta san yadda zuciyar shi ke tafasa da kalamanta ba da ko kusa ba ta fara ba, da wannan sabon abu da yake ji game da rayuwar Zaynab. Ya ga ba ta da alamun yin shiru balle tunanin dasa aya, idanunsa a rufe gam, ya nuna mata kofa cikin kakkausar murya ya ce, “Ku wuce ku bani wuri mutanen banza kawai tambadaddu, jakai, dabbobi da basu san ciwon kansu ba….” Ya kware ya shiga tari ba kakkautawa saboda takaicinsu da ya kasa amayarwa, suka fita suna yi mai dariyar kwarewar da ya yi, wai masifarsa ce ta kwarar da shi. Amma Iftihal gorar ruwan (eva) mai sanyi ta dauka a firij ta koma ta kai masa, daga nesa-nesa ta ajiye mai ta zura da gudu. Suka zo suna kyankyasa min yadda su kai, na ce, “Kan ku kuka tonawa asiri, idan ya gayawa Abba fa?” Mu karasa a littafi na 2 Takori