_____ *🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 1 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* **FARKO ** Tana fitowa daga dakin ta soma rera kuka kallon dakin da Mahaifinta ke kwance a cikin. Kafadarta taji an dafa tare da kiran sunanta. “Ummu Salma, kiyi hakuri Allah zai ba mu mafita.” Ko bata dago ba ta san Yaya Hadiza ce. Cikin kuka ta ce, “Yaya Hadiza abin nan da bakin ciki, Naira dubu goma tasa za mu koma da Baba gida a haka?” Yaya Hadiza ta kama hannunta. “Zo muje kafın Yaya ya fito mu ga ya za’ayi.” A harabar asibitin suka tsaya can in da ba kai kawon mutane, sai motoci da ke aje a gurin. Suka jingina da wata mota ba tare da sun damu da zafin da jikin motar ya yi radau ba. Yaya Hadiza ta ce, “Salma yanzun ke nawa ne a gurin ki?” Ta ce, “Jarin Awarata gaba daya Naira dubu ne da dari bakwai, kuma kin ga dai kullum in nayi za a samu dari bakwai, dari shidda. Da shi fa muke cin abinci, in kuma an kwashe an ba da ina zamu samu na cin abinci, har ma a kawo asibiti?”Yaya Hadiza ta numfasa, sannan ta girgiza kai. “Taba wannan jarin ba zai yiwu ba, sai dai bari Yaya Auwalun ya fito muji, kin san shi aikin shi na gidan Biredi sai karshen Wata suke ba shi albashi, in dai ba Allah ne Ya kawo mishi dan gyaran wuta ya yi ba.” Salma ta ce, “To Yaya Hadiza ke babu wani kokari da za ki yi?” Ta ce, “Salma me ya rage min yanzun? Sai fa Gadon da muke kwana a kai. Shi ma Baban Amira kin san dai ba wani karfi gare shi ba, sai ya fita ya nemo sannan za mu dora.” Salma ta hango Yaya Auwalu yana ta waige waige alamar yana nemansu. Ta ce, “Ga Yaya can. nasan tabbas mu yake nema. Yaya Hadiza ta ce, “Yaya Auwal!” Ta kwala -mishi kira, ya kalli inda suke, sannan ya nufo su Suka ci gaba da tattauna yanda za su samu kudi. Sa dai kusan minti talatin ba su cimma matsaya ba, zancen dai daya ne na kudi kuma ba su da shi. Daga cikın motar suka ji ana kwan-kwasa kofar, Salma ta zabura da sauri ta matsa gefe,sannan ta ce Yaya Hadiza matsa, wani mutum ne Ya fito daga cikin motar sanye da shadda mai ruwan kasa, kanshi babu hula. Kyakkyawa ne wankan Tarwada, fuskarshi babu annuri sam-sam. Hakan yasa gaban Salma faduwa. Ta ce, “Alhaji don Allah kayi hakuri ba mu san da mutum ba.” Ya kalli sashen cikin asibitin, sannan ya soma latsa wayar da ke rike a hannunsa, suna dai kallon shi ya karata a kunne ya soma magana. “Haba abokina! Ka fito mana ko in je in dawo ne tukunna?” Ya dan yi shiru, sai kuma ya ce, “To babu matsala, bari in dawo minti sha biyar.” Sai lokacin ya kalli Salma wadda idanunta suka kasa daina kallon shi. Ya ce, “Nawa ku ke nema don ci gaba da kula da Mahaifinku?”Salma ta zaro ido tana in ‘ina.Am… in…kudin da muke so?” “Samu nutsuwa mana yarinya, kin ga sauke numfashi tukunna.” Ya fada a hankali. Ya kalli Yaya Auwal. “Nawa ku ke bukata a yanzun?” Har suna hada baki shi da Yaya Hadiza gurin cewa, “Dubu goma ne dai yanzun.” Ya ce, “To cikinku wa zai bini ya amso? Don in na fita sai na kai minti sha biyar kafin in dawo cikin asibitin nan in dauki abokina.”Yaya Auwal ya ce, “To bari in bika, mun gode sosai Alhaji, Allah Ya saka maka da alkairi.” Hadiza da Salma ma suka yi godiya. Ya ce, “Kar ku damu, ku gode wa Allah.” Nafisa ta kalli Mahaifiyarta wadda take zaune bakin Gadonta, tana shafa mai. Ta ce, “Mama har yanzun ina shakkar yiwuwar aurena da Yaya Shatima.” Uwar ta dubi Nafisa, sannan tayi dan murmushi. “Yau ita ce rana ta uku da ki ka tambaye ni, ko in ce da ki ka fada min cewa kina shakkar yiwuwar aurenku, amma kin kasa fada min dalilinki na fadin haka. Nafisa ta dan kalli saman silin din dakin uwar, kamar wadda take son tuna abin da zata fada. Uwar ta gama shafa mai, şannan ta mike ta nufi gurin durowa tana duba kayan da zata saka. Nafisa ta ce, “Mama nayi la’akari ne da yanda ya ki ya zo gurina, ko ya kira ni a waya. Tun sakon da ya turo min cewa ina jin zan iya auren shi? Na ba shi amsa da cewa zan iya, shi ke nan fa.” Uwar ta ajiye kayan da za ta sa a kan Gadon, sannan ta zo ta zauna kusa da ‘yar, ta kai hannu ta dafa yar.”Nafisa zan ba ki shawara, kar ki sake ki saka wannan a zuciyarki, aurenki da Shatima kin san babu abin da zai hana shi faruwa sai in dayanku ya mutu. Kar ki manta Babanki da Babanshi uwa daya uba daya. Kuma su ne suka yanke su hada ku aure ba tare da neman izininku ba, fatana dai ki zama ‘yar zamani mai kula da abin da zai ja hankalin mijinki. Abin da za ki lura shi ne, Shatima matashi ne dan zamani, mai ilimi, mai kudi, mai kyau. Mata da yawa irin shi suke nema, sai kin dage kin zama jaruma sannan ne za ki zama ‘yarlele, ki dauke hankalinshi daga kan kowace mace.”Nafisa tayi murmushi, “Ni dama matsalata guda daya ce, ya zo mu fahimci juna.Maman ta ce, “Kin san kowane namiji yana da irin nashi ra’ayin, da kuma irin nashi salon. Kila shi nashi kenan irin wannan salon.” Nafisa ta ce, “Amma Mama kina ganin ba laifi ba ne in nayi masa sakon gaisuwar Juma’a ban yi laifi ba?” Ta ce, “Babu laifi, amma yana da kyau mace ta zama mai kama ajinta a gurin namiji, ba kowane namiji ba ne ya ke son a dame shi ba. Haka kuma ba kowane namiji ba ne ya ke son mace mara aji, shima yaja aji bare ke mace. Amma dai ki masa sakon sau daya a Juma’ar nan mai zuwa mu gani, daga yanda ya dauki abin za mu iya fahimtar wani abu.” Nafisa ta ce “To shi kenan Mama, na gode da samun uwa irin ki. Ina alfahari da samun ki matsayin Mahaifiya. Nasan duk duniya babu wanda ya kai ni dacen uwa tagari mai dora ya’yanta a kan turbar daidai. Bari in je in ci abinci har naji yunwa, da dazu na kasa cin komai, ko in ce cikin kwanakin nan na kasa cin komai.” Uwar ta ce, “Je ki ci kar ki damu kanki ko kadan.” Munnir ya kalli wayar da ke jone a jikin chajar motar, sannan ya kalli mai jan motar. “Abokina wayarka tana ruri fa. Mai wayar ya kai hannu ya dago wayar sannan ya kalli fuskar wayar, da sauri ya daga wayar. Ta ce. “Hello! Manyan kasar Nijeriya.” Ya ce, “Amna ba dai kin shigo Nijeriya ba?” Ta ce, “Ba ka kalli number din ba ke nan?” Ya ce, “Shi yasa ai na tambaye ki, saukar yaushe?” Ta ce, “Saukar kwana hudu da suka gabata. Ya ce. “Amma shi ne sai yau ki ke kirana?” Ta ce, “haka ma za ka ce? Har ma kana da bakin magana tunda ka baro Dubai sau daya rak! Ka kira ni. “Kin fi ni gaskiya Amna, amma ina da dalilin haka. Cikin satin da na dawo Nijeriya aka sace min wayoyina da Laptop dita, sai da na rasa lambar kowa sai wanda ya kira ni.Ban da haka ma littafin da ni ke ajiye abubuwana na rasa in da na saka, ke kuma kin ki kirana bare in samu lambárki.” Ta ce, “To yanzun dai yaushe za ka zo?” Ya ce, “Ban da wannan satin, satin da za mu shiga.” Ta dan yi shiru. Can ta ce, “Ko dai ka canja ni ne a zuciyarka?”Ya ce, “Matsayinki yana nan daram! Me yasa ki ka tambaye ni?” Ta ce, “Yanda naga kamar ba ka yi dokin ganina ba.” “In da kin san tarin ayyukan da suke gabana da ba ki fadi haka ba. Zan tsallake da dama ne fa in zo in gan ki, kin san sabon ma aikaci, ofishin da na samu cike yake da tarin ayyuka.” “Na gamsu, don tunda muke tare ba ka taɓa fada min karya ba.” Ta fada cikin kwantar da murya. “Na gode da lambar yabon da na samu a gurinki. In na samu lokaci zamu yi waya.”Ta ce, “Sai na ji ka.” Ya mika ma Munnir wayar tare da fadin “Maida min ita a caji.” Daidai ya karya kwana. Munnir ya amsa tare da fadin “Abokina wai me ya ke shirin faruwa ne?” Ya dago ya kalli Munnir, sannan ya yi murmushi. “Wallahi nima ban sani ba abokina, amma tabbas ina ji a jikina babban al’amari zai faru, kuma zai faru din. Nayi wani mafarki kwanakin baya, kuma naji a jikina mafarkin alkairi ne.” Munnir ya ce, “Allah Ya tabbatar mana da dukkan alkairi.” Ya ce, “Ameen.” Kofar gidan su Munnir ya sauke shi, sannan ya nufi gidansu da ke Kwarbai a garin Zaria. Damfareren gida ne mai girman gaske, wanda daga gani ka san ma su gidan da kunbar susa, kila ma da jibin sarauta. Ya nufi ɓarayinsu ya aje motar ya kwashi wayoyin shi ya nufi cikin dirkeken falon. Tana zaune a kan kujera Badi’a tana shafa mata man zafi a kafa. Ya zauna kan Dardumar da ke gabanta tare da fadin “Sannu da hutawa Hajiya. Badi’a ta tashi da sauri tare da fadin “Sannu da zuwa Yaya. Ya ce, “Sannu Badi’a.” Hajiya ta ce, “Sannu Shatima, har ka dawo?” *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300 idan kina bukatar cigaba ki turo kudin ta wannan account din👇🏻👇🏻* ```ACT > 3024960720 POLARIS BANK MOHAMMED UMAR ko ki turo katin Mtn ta wannan number 09068032427``` *Idan baki shirya ba kada kiman mgn ki bari sai kin shirya*_____ *🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 2 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Masu son a tallata masu hajar su ko ayi masu sharing link din group din su na kasuwanci zaku iya yin magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku akan farashi me sauki* Mun tsaya Munnir ya ce, “Allah Ya tabbatar mana da dukkan alkairi.” Ya ce, “Ameen.” Kofar gidan su Munnir ya sauke shi, sannan ya nufi gidansu da ke Kwarbai a garin Zaria. Damfareren gida ne mai girman gaske, wanda daga gani ka san ma su gidan da kunbar susa, kila ma da jibin sarauta. Ya nufi ɓarayinsu ya aje motar ya kwashi wayoyin shi ya nufi cikin dirkeken falon. Tana zaune a kan kujera Badi’a tana shafa mata man zafi a kafa. Ya zauna kan Dardumar da ke gabanta tare da fadin “Sannu da hutawa Hajiya. Badi’a ta tashi da sauri tare da fadin “Sannu da zuwa Yaya. Ya ce, “Sannu Badi’a.” Hajiya ta ce, “Sannu Shatima, har ka dawo?” Ya ce, “Na dawo Hajiya. Akwai aikin da zan yi “a gida ne.” Ta ce, “To, cikin laptop din taka za ka yi kenan?” Ya ce, “Eh.” Hajiya ta ce, “To bari in sa a kawo maka abinci daki, gashi kuwa abin da ka ke son aka yi. “Burabusko ke nan?” Ta ce, “Eh, kuma akwai farfesun kafar Sa, su zubo maka ko?” Ya ce, “To Hajiya bari in shiga ciki.” Ta ce “Badi’a!” da sauri ta iso ta ce, “Gani Hajiya.” Ta ce, “Kira min Uwa a kicin.” Shatima ya nufi sama in da dakinshi yake. Uwa ta iso falon cikin girmamawa ta ce, “Ga ni Hajiya.” Ta ce, “A shirya ma Shatima abinci.” Ta ce, “To Hajiya, kunun zaki za a zuba mishi ko zobo?” Ta ce, “Kin san shi fa in bani na hada da kaina ba ba zai sha ba, ku kai masa ruwa mai sanyi da lemon kwali kawai. Yayi nisa cikin aikin sa, Badi’a ta kwankwasa kofa. Ya ce, “Shigo.” Ta shigo da sallama ya amsa. Ta aje ta fita. Ya kalli abincin, tabbas yana son ci amma yanzun aikin nan ne a gabanshi. A fili ya ce, “Ina ma nayi aure da sai a ke bani a baki ina aikina.” Daf da kiran Magariba ya rufe komai ya ci abinci, sannan ya yi wanka ya fito. Lokacin da yaje Masallaci ana raka’ar karshe, don haka ya jone da su. Abin da ke ranshi shi ne in ya idar ya nufi Tudun Wada don kai gaisuwa ga Kakarshi, Mahaifiyar Babanshi. Kusan kullum sai ya samu sakon korafinta daga bakin Mahaifinshi, tunda shi kullum ya ke zuwa kai gaisuwa ga tsohuwar tasa. Daf da kwanar da zata kai shi gidan Kakar ya daga ido ya kalli gidan su Aliya, duk da yasan tarihi ya shafe babin Aliya, kuma ba zai sake ganinta ba yana da kyau ya kalli gidansu don kauna. A fili ya ce, “Alherin Allah Ya kai miki a duk inda ki ke Aliya.” A cikin gidan Kaka tana fadin tayi fushi, ace tunda ya dawo ba ta samu arzikin ya zo ya duba ta ba, ko sau daya ta ma gan shi taji dadi. Sai dai ya kira waya ya ce a bata. Ya ce yau gani na zo Kaka kiyi hakuri, yanayin aiki ne Kaka ina dawowa Gwamnati ta bani aikin nan. Na samu aiki jingim a cikin wannan office din, so ni ke in karkare da komai, in kuma fahimci komai.” Ta ce, “To shi ke nan ka wanke kanka. Har ina cewa ko har yanzun bakin cikin Aliyar da baka samu ba ne.”Ya ce, “Kaka ni fa na jima da sa ma zuciyata hakuri, ba kin zuga su Baba sun ce in auri Nafisa ba?” Ta ce, “In ji wa ke nan? Ni ban ma san lokacin da suka shiryo abin su ba, ni dai sun fada min kuma nasa albarka. Nafisa tana da hankali, kuma tana da ilimi.” Ya ce, “Kaka sai dai fa ina zaton zan auri mata biyu ne rana daya, ya ki ke ganin yiwuwar hakan? Ban taba yin shawara da kowa ba sai ke yanzun. יי Ta ce, “Shatima in kana bukatar sama da haka addini ya baka dama, ni ko iyayenka ba mu da ikon da zamu ja da haka. To da Aliyar za ka kara kenan?” Ya ce, “Wace Aliya kuma, na sani yanzun tayi ‘ya’ya sun kai guda biyu. Kaka ta ce, “To ai bata yi auran ba.. Tsaye Shatima ya mike tare da maimaita kalmar “Bata yi auren ba?” Kaka ta ce, “Ni kar ka fado min, tana nan gidan da suka ce ba za ta jiraka ba.” Ya ce, “Kaka cire batun wasa!” Ta ce, “Shi ke nan kowane lokaci ne ake yin wasa? Zancen gaskiya kenan. Amma zauna ka nusu sai Maryama taje gidan ta kira maka ita. Ya ce, “Ni fa in kin bar ni tuni Aliya tayi aure.” Ta ce, “Tana nan takan zo gaishe ni a kwanakin baya.” Ta daga murya.”Maryama zo nan.” Ta zo ta tsugunna ta gaida Shatima. Kaka ta ce, “Je ki kawo masa abinci da ruwa.” Ta kalli Shatima wanda ya yi nisa cikin tunani, ta ce, “Sai dai fa tuwo muka yi.” Ya ce, “Iye! Me ki ka ce?” Ta ce, “Abinci na ce.” Ya ce, “Ba zan ci ba Kaka, ban dade da cin abinci ba, ki aike ta ta kira min ita don in shaida Kaka. Ta ce, “To goga na Aliya, duk ka birkice, Maryama je gidan Alhaji Garba ki ce ina kiran Aliya.” Ta ce, “Wannan me aikin asibitin?” Kaka ta ce, “Ita.” Ya bi Maryama da kallo kamar ita ce Aliyar, sannan ya maido da kallonshi kan Kaka. “Naji kuma kin ce mai aikin asibiti.” Ta ce, “Eh, ai bayan tafiyarka Makarantar koyon aikin jinya ta shiga ta gama yanzun tana aikinta.” Ya mike ya nufi window yana leke tare da fadin “Naji kamar motsi ne.” kaka ta ce, “Ikon Allah sai kallo. To kuma fa in ka faye zumudi Nafisa jikata ce sai in saka takalmin karfe in murza kasa in ce ita kadai za ka aura.” Ya ce, “Kaka ai in har ta tabbata Aliya ta ce, “To akwai yiwuwar zan yi mata uku rana daya.” Kaka tasa dariya sannan ta ce, “Ashe zaka kafa tarihi a Zaria ” Sallamar Maryama suka ji, bai amsa sallamar ba amma ya ce “Ina take?” Ta ce, “Tana sallah, Mamansu ta ce in ta idar zata zo. Ya sake kallon Kaka ya ce, “In ko Aliya ce, ban san ma wane irin albishir zan yi miki ba a duniya da na ba ki kujerar Makka, sai dai babu kafar zuwa. Ta ce, “In ka yi niyya ai ko zuwana na karshe kan kujerar turi nayi aikina, Babanka ya biya askarawa suka yi ta dawainiya dani. Shatima ya yi murmushi, ni dai ki bar batun Makka, zan siyo mimiki kaji ayi miki farfesu mai laushi ki sha kayanki. Ta ce, “Aikin banza, don kaji kullum Babanka sai ya kawo min.” Ya ce, “To kan Shanu fa..?” Sallamar da suka jiyo ce ta hana Kaka maganar Www.bankinhausanovels.com.ng sai amsa sallama tayi. Shi ko kasa magana ya yi, ya lumshe ido yana tunanin yanda zai ga Aliyarshi. Tayi sallama a kofar falon, nan kaka ta amsa. Kanshi yana kasa, ta isa can gefen wata kujera ta zauna, sannan ta gaida Kaka tare da cewa. “An ce kina nemana, Allah Yasa lafiya?” Kaka tayi yar dariya. “Ga me nemanki nan.”Sai lokacin ta kalli gurin da mutumin yake, don da ta shigo hakika taga mutum amma ba ta tsaya dalle kallonshi ba. Ya dago ido suka kalli juna. Zumbur! Suka mike tsaye suka zubama juna ido. Shatima ya yi ta maza ya ce, “Aliya dama kina nan ba kiyi aure ba?” Ta sauke ajiyar zusiya, sannan ta sunkuyar da kai “Ina yini?” Ta gaida shi. “Lafiya lau.” Ya amsa. Kaka ta ce. “A tsaye za ku gaisa?” Ya kalli Kaka, sannan ya kalli Aliya. “Zo mu zauna can kujerar kada Kaka taji abin da zamu fada.” Aliya taja mayafinta ta rufe gefen fuskarta alamun kunya, zuciyarta kuwa fal murna. Gani take yi ma kamar ba gaske ba ne, wai Shatimanta ne a gabanta. Sai da suka zauna ta sake gaida shi. Ya ce, “Ya ya ki ka ji da ki ka ganni?” Ta ce, “Har yanzun bangama yarda cewa ba mafarki nake yi ba.” Yayi murmushi, “Ni mamakina ashe ba kiyi auran ba?” Ta ce, “Duk wanda suke son in aura ni kuma bana sonsu, sai wan Babanmu na Katsina ya ce su bar ni in zabi miji da kaina.To sai Yayanmu Aliyu ya kawo min form din School of Nursing, shi ne ma na maida hankalina a kan karatu.Ya ce, “Yanzun kin gama kenan?” Ta ce, “Eh, har na gama Practical dina, kuma na fara aiki a wani asibitin kudi da ke nan unguwar. Ya ce, “Shekarunmu nawa da rabuwa ne har da ki ka yi karatu ki ka gama?” Ta ce, “Shekaru uku fa da watanni kenan.”. “Hmm! Haka ne. Za ki iya tuna rabuwarmu ta karshe?” Ta daga kai kamar mai son tayi tunani. Ta ce, “Mun rabu ne wata ranar Asabar wadda ba zan taɓa mancewa da ita ba.Mun rabu kafin Asabar din a kan magabatanka zasu zo, amma maimakon haka sai na ganka da labarin wai Mahaifanka sun ce za ka tafi Dubai don kayo Degree na biyu. Ta lumshe ido kafin ta ci gaba da magana. “Ba zan iya misalta bakin cikin da na tsinci kaina a wannan ranar ba, domin a cikin gida ina fuskantar matsin lamba a kan in fitar da mijin aure. Na ce to, ka sa a zo a fadawa iyayena ko za su amince in jira ka. Washegari Lahadi ku ka zo kai da abokinka Munnir don neman yardar iyayena su bar ni in jira ka dawo, sai Mahaifana suka ce sam! Ba zan jira ka ba, aure za su yi min.” Ta sake yin shiru tare da sauke ajiyar zuciya, sannan ta kalle shi. “Haka ne?” Ya ce, “Ashe dai ba ki manta ba. Ni Yayanku Aliyu ma ce min yayi dama wani abokinsa yana sonki, shi yasa na yanke hukunci cewa yanzun kin yi ‘ya’ya biyu.” Tayi ‘yar dariya, “Duk sun zo na ce ban son Ya ce, “Ashe rabona ce, amma kina da su. kishiyoyi fa!” Ta zaro ido, sannan ta dube shi “Kayi aure ne?” Ya ce “Rana daya za a sa ku a lalle.” Ta ce, “Nasan kana zolayata ne.” “Zancen gaskiya kenan Aliya, ku uku ne. Bayan na tafi Makaranta cike da bakin cikin rabuwa da ke, sai Allah Ya hadamu da Amna, ‘yar asalin jihar Kano ce, tana da dangantaka da Masarautar Kano., Babanta mai kudi ne sosai. Amna ta birge ni da halayanta na kamun kai, da nutsuwa, haka yasa wasu dalibai ke surutun tana da girman kai. Gidan da take kusa da namu ne mu kan hadu lokuta da dama in Makaranta, ko in mun je sallah. zamu shiga Ni dai tana birge ni, kuma ina son mu ke magana. Sai wata rana nayi mata sallama ta amsa muka gaisa, na ce ita ‘yar Nijeriya ce a wacce jihar? Ta ce Kuno. Tun daga lokacin muka soma magana har soyayya ta shiga tsakaninmu, sai ma na gane son da take min ko kwatanshi bana yi mata. Har mun shirya batun aure da ita. Kasancewar zan rigata dawowa sai muka shirya zan jirata. Na rasa sadarwa tsakaninmu da ita sakamakon wayoyina da Laptop da barayi suka sace. Yau din nan ta kira ni ta ke sanar min dawowarta kasar.” Aliya ta danne kishinta ta ce, “To ka ce mu uku ne dayar fa?” Ya ce, “Nafisa jikar Kaka ce, ina ce kin santa ma?” Aliya ta ce “Dama kuna soyayya da Nafisa ne? nasan ta mana.” Ya ce, “Kafin in dawo iyaye suka kulla, yanzun su ba su san ma da batun Amna ba bare naki. Yanzu dai za mu gyarota da Kaka, saboda in ta yarda dole Baba ya yarda, shi kuma in ya cije dole Hajiya ta saki.” Aliya ta ce, “Tab!” Ya ce “Ba za ki iya ba ko?” Ta ce “A’a in ana auren mata dari Shatima ka aura ba zan ki ba, na dai tausaya maka ne.” “In kuma na samu ta hudu sai in cike kawai.” Ya fada cik zolaya. Aliya ta ce, “Ni dai yanzun ka fada min wa ka fi so?””Wadda ta fi sona.” Ya bata amsa a takaice tare da mikewa. “Bari in tafi ko, amma kafin nan ki tashi kije gida zamu yi magana da Kaka.” Ya mika mata wayarshi karama.”Sa min lambarki, ki ajiye da sunan da ki ka ga ya dace.” Ta saka lambar tayi shiru tana tunanin sunan da zai dace. Ya ce, “Ki zabi duk sunan da ki ka sa shi ne sunanki a bakina.” Cikin sauri ta rubuta (My Love) ta mika mishi. Ya amsa ya kalleta.My love?” Tasa hannu ta rufe fuska cikin jin kunya. Ya ce, “Zan kira ki da wannan sunan a gaban kowa ma, kuma ina son ke ma ki kira ni da shi a gaban kowa. Ya nuna mata hanya da hannunshi, “Je ki sallami Kaka.” Ta tsugunna a gaban Kaka ta ce, “Zan tafi gida.” Kaka ta ce, “Har kun gama hirar? To Allah Ya tabbatar muku da alkairi.” Har bakin falo ya rakata, sannan ya dawo gurin Kaka. Ya ce, “Kin ga abin Allah ko Kaka!” Ta ce, “Ai ni na zaci ita ce ta biyun.” Nan ya bata labarin Amna. Ya ce, “Goyon bayankı kawai ni ke nema.” Ta ce, “Shatima nemi komai gurin Allah. ni ai in hudu za ka yi ina murna, don bana son ragon namiji. *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427*_____ *🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 3 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427* *Masu bukatar a tallata masu hajar su ko link din group din su na kasuwanci suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku akan farashi me sauki* Mun tsaya Ya nuna mata hanya da hannunshi, “Je ki sallami Kaka.” Ta tsugunna a gaban Kaka ta ce, “Zan tafi gida.” Kaka ta ce, “Har kun gama hirar? To Allah Ya tabbatar muku da alkairi.” Har bakin falo ya rakata, sannan ya dawo gurin Kaka. Ya ce, “Kin ga abin Allah ko Kaka!” Ta ce, “Ai ni na zaci ita ce ta biyun.” Nan ya bata labarin Amna. Ya ce, “Goyon bayankı kawai ni ke nema.” Ta ce, “Shatima nemi komai gurin Allah. ni ai in hudu za ka yi ina murna, don bana son ragon namiji. Shatima mai sunanka gwarzo ne, mu hudu ya aje, ba dai rana daya ba. Amma tsakaninmu babu nisa. Duk ciki ni ce kararmu, yau ina abokan zaman nawa? Ina shi Maigidan namu? Duk sun amsa kiran Ubangijinmu. Mun zauna da dadi-ba-dadi, kuma an yi zaman mutunci, kullum ina yi musu addu’ar samun rahamar Allah, kuma. Allah Yasa tawa tayi kyau irin tasu. The de jah manch slara ar Tilb 2 Ya ce, “Amin Kaka.” Ta ci gaba da fadin, “Mata hudu ba matsala ba ne matsalar tana tasowa ne daga gurin namiji in ya kasa adalci a gidansa.” Ya ce, “Kaka ni ai renonki ne ko? In sha Allah zan yi ba zata.” Ta ce, “In dai sunanka Muhammad Ja’afar, kuma ka amsa lakabin ka na Shatima, to kuwa nasan kai gwarzo ne.” ******* Tun da aka soma yi wa Malam Adamu gashin kashi sai jikin ya soma sauki. Dubu ishirin da suka samu a gurin Alhajin nan ta taimaka musu sosai. Ummu Salma ta sauka daga cikin Adaidaita dauke da kwanukan samira tuwo da miya. Ta shiga cikin asıbitin da hanzarinta don kaiwa Mahaifanta tuwon da ta yo bayan ta gama suyar Wara, ta samu riba tayo cefane ta girko. Tana taka matakalar da zata hau sama in da dakin maza yake, sai ko kafarta ta zame, takalmin kafarta silifa mai soso ya taimaka gurin zamar da ita har ta kai kasa. Ba damuwarta faduwar da zata yi ba, damuwarta kawai kar abincin Mahaifanta ya zube. Sai dai ta makaro, domin tuni abincin ya tarwatse a kan siminti. Wata ma aikaciyar gurin ta soma yi wa Salma fada. “Ke da Allah can! Kin zo kin bata wa mutane guri da wannan kazamin tuwon naku, da Allah zo ki share shi.” Ta mike tana kukan bakin cikin asarar abincin iyayenta. Daidai lokacin da wata mai sharar asibiti ta iso. Wannan ma’aikaciyar tana ci gaba da yi wa Salma sababi. Mai sharar ta ce, “Irin kazantar da ku ke yi a gidanku shi ne kin zo kina yi mana a nan guri din?” Ta tambayi Salma cikin hausarta mara dadi. Salma dai sai kallon su take yi. Ma’aikaciyar ta ce, “Ba za ki kwashe mana warman kazantar a nan gurin ba? kalli wai wannan ne abincin da za’a ba mara lafiya. Ta ya ya zai warke yana cin irin wannan kazanta?”Cikin mutanen da suka taru a gurin suna kallo sai wata daga ciki ta ce, “Gaskiya bai kamata ku saka yarinya karama a gaba kuna mata ihu ba, ita ma ai ba za ta so ba tayi asarar abincin da Allah ne kadai yasan yanda suka samo shi Nan suka dawo kan matar, hayaniya ta soma yin sama. Tasa hannu zata dauki tuwo, sai ta ji an ce”Bari kar ki taba.” Tana dagowa sai taga Alhajin nan shi da wani a cikin jerin mutanan da suka taru a gurin. Ya ce, “Ina ma su yin sharar asibitin?” Matar ta ce, “Mu ne muke shara, amma ita ne ta kwashe wannan din da ta zubar.” Ya ce, “Zo ki wuce, ku ku bar shi in ba za ku kwashe ba.” har ta nufi sama ya ce, “Zo nan.” Ta nufo gurinshi, ya ce “Bimu daina kukan.” Ta ce,”To.” Tasa kasan hijabinta tana share hawaye. Ya ce.. “Kin gane ni kuwa?” Bayan sun je gurin mota. Ta ce, “Eh, na gane ka. Kai ne wanda ka taimake mu shekaranjiya.” Ya ce. “Sunana fa?” Ta sake kallonshi, sannan ta girgiza kai “Ban san sunanka ba.” Yayi murmushi, sannan ya ciro kudi a aljihunshi ya nuna mata wata hanya.”Ki bi nan ki dan mike za ki ga shagunan saida abinci, su wanke miki kwanukan sai ki sai musu abinci.” Hannu biyu tasa ta amshi kudin, tana ta godiya. Shima abokin yana cikin mota lokacin, ya ciro dubu daya ya ce, “Kara mata.” Salma tayi godiya, sannan ta mike hanyar da ya nuna mata cikin murna tana kirga kudin, dubu hudu ne cas! Duk da dubun abokin. Sakwara ta sai musu da miyar agushi, ta sai musu lemon roba da ruwan sanyi. Tana isa Innarsu ta idar da sallar La’asar. Ta ce, “Yau ba kasuwa ne hala muka ji ki shiru Ummu Salma?” Ta ce, “Ai nazo tun dazu ɓarewa ya yi. Nan ta basu labarin komai, sannan ta kawo sauran kudin ta ba Innarsu. Inna ta ce, “Ba na amsa duka ba Salma, bani dai dubu guda sai ki rike dubu biyun, ke da ki ke dawainiya da mu. Shi kuma Allah Ya shi masa albarka, ya saka mishi da alheri, ya biya masa bukatunsa shima.” Salma ta ce, “Amin Inna. Sai bayan Isha’i sannan Innarsu ta ce, “Maza ki zo Salma ki wuce dare yana yi.” Ta ce, “To Innarmu, bari in zo in je.” A bakin titi tana jiran mota, wata ma’aikaciyar jinya ta fito itama tana jiran mota. Salma ta dube ta cikin faduwar gaba, don tana zaton matar dazu ce da ta yi mata cin mutunci. Ta saci kallon matar duk da akwai duhu ta gane ba fuskar waccan ba ce. Dan Adaidaita ya zo wucewa, tare suka hada baki gurin fadin. “Tudun Wada.” Ya tsaya ya dauke su, ma’aikaciyar ta ce, “Ashe unguwa daya za mu?” Salma ta ce, “Eh, nan za ni.” Ta sake cewa, “Kin zo duba mara lafiya ne?” Salma ta ce, “Eh, Babana aka kwantar.” Ma’aikaciyar ta ce, “Allah Ya ba shi lafiya.” Salma ta ce, “Amin.” A zuciyarta ta ce, ‘Ashe dai ba duka Nurses din nan ba ne suke da wulakanci, da ko har na tsane su.” Alhaji Isa Shatima yana zaune a falonsa da misalin karfe tara da rabi, labaran kasa suke kallo tare da matarsa Hajiya Halima. Dukkansu Tea suke sha wanda suka maida shi al’adarsu duk dare Daidai wannan lokacin ya kalli wani daurin auran da aka gama nunawa na ‘yar. wani Minister daga cikin Ministoci. Ya ce, “Au! Hajiya Halima har na tuna.” Ta ce, “Ka tuna me?” Ya ce, “Da na je duba Hajiya yau da safe take fada min wata magana da na kasa ce mata komai.” Ta maido da hankalinta kanshi sosai. “Meta ce?” Ya ce, “Shatima wai mata uku zai aura…” Kofin hannunta ya kusan faduwa, sannan ta kware da ruwan zafin da ta kurba. Dan tari ta shiga yi har ta yi zaton asmarta ce zata tashi, sai sannu Alhaji ya ke yi mata. Kusan minti biyar sannan ta dawo hayyacinta. Idanunta jajir ta ce, “Amma dai wasa ya ke yi ko?” Alhajin ya ce, “Babu alamun wasa a fuskar Hajiya lokacin da take yin maganar.” Hajiya ta ce, “Hmm! Wannan hira ce ya ke yi. Ban da Shatima ina zai kai mata uku?” Ya ce, “Na fadi hakan sai Hajiya ta min gorin da na gwammace ban yi magana ba sannan ta saki zancen alamun an wuce gurin. Hajiya Halima tayi shiru tana tunani. Badi’a ta shigo falon zata dauki takardarta wadda tayi home work da rana. Hajiyar ta ce, “Badi’a zo nan, kira min Yayanku a samansa. Kammala aikinsa ke da wuya ya rufe Laptop din yana hamma, ya sani ba bacci ba ne yunwa ce ke damunsa, don bai ci komai da rana ba.Ya ji an kwankwasa kofa. Ya ce, “Shigo.” Tayi sallama ya amsa, ta ce “Hajiya tana kiranka Yaya.” Ya ce, “To ina zuwa Badi’atu.” Gabansu ya zauna ya gaishe su, sannan ya ce, “Gani Hajiya.” Ta gyara zama ta hanyar dora kafarta daya a kan daya, duk lokacin da tayi hakan ya san umarni zata ba da na dole, don haka sai ya sake nutsuwa don jin abin da zata zo da shi. Koda yake tuni ya soma hasashen abin da zata yi magana a kai, zancen auransu da Nafisa… Ta katse tunanin shi da cewa, “Yanzun Mahaifinku ya ke bani labarin wai za ka auri mata uku rana daya?” Ya sunkuyar da kai cikin mamakin har zancen ya riske su da sauri haka! Yana tunanin lallai da gaggawa lamuran za su ke zuwa masa. Ta ce. “Kayi shiru Shatima?” Ya sake sunkuyar da kai. Ya ce, “Haka ne Hajiya.” Ta ce, “Amma ka fita a tunaninka ko? Ya ya za ka yi da mata uku rana daya? Yaron ka da kai Shatima za ka dora ma kanka matsalar iyali da yawa furfura ta fito maka ko? To ka sani ban amince ba sam-sam!” ya dan gyara zama. “Hajiya duk al’amarin ya zo ne ba da shirina ba, sai da shirin Ubangiji. Kuma Hajiya shekaruna talatin da shida, ai ko na girmi yaro.Sannan addinina bai hana ni ba, Allah a cikin Alkur’ani mai tsarki ya fada mana cewa, mu auri mata biyu, ko uku, ko hudu. In ba za mu iya adalci ba sai mu auri daya. To ni kuma ina da tabbacin zan iya adalci, don ina alfahari da irin tarbiyyar da ki ka bani, adalcin da ki ka tsaya a kai ki ke yi ma kowa da shi muka dogara. Kuma shi ni ke kwatantawa a ko’ina, da shi kuma zan zauna da mata ko nawa ne. Ina son ki sa albarka a cikin wannan auran, albarkarki ita ce ginshiki Hajiya.” Ta ce, “Ai kai Shatima ko dan siyasa ya fi ka iya zance kuwa? Ni dai kaje kayi tunani a kai, rike mace ko guda daya ce sai jan namiji. Amma kai ka ce rana daya guda uku!” Ya ce, “Hajiya ki sa albarka.” Ta ce, “Yanzu dai ba zan saka ba, in kana son in saka sai dai ka duba a cikin ukun ka dauki guda daya, ka zaɓa in ma ba Nafisar ba ce dai wadda kafi so. Don ka san an ce so daya ne tak! Kuma mace daya ka ke wa a cikin ukun, don haka sai ka cire ta.” Ya kalli Mahaifin nashi wanda bai ce kala ba tun da suka soma magana. Ya ce, “Alhaji ba ka ce komai ba?” Ya ce, “Ba ni da ta cewa Shatima, duk abin da yafi alkhairi Allah Ya zaba, tunda ka samu daurin gindin Tsohuwa a ta gefena ka kai makura. Shatima ya yi murmushin nasara a ta wannan gefen. Hajiyar ta ce, “Ka je kayi tunani nan da jibi.” Shatima ya mike cikin rangaji tare da fadin “Badi atu ta kawo min abinci Hajiya.” ** Tunda Kaka taji sallama tare da kamshin kalolin abinci ta tabbatar cewa Hajiya Halima ta diro gidan, domin wannan ita ce shaidar farko da take fara alamta mata cewa Surukar arziki ta shigo gidan. Ta fito daga cikin dakinta tana dogara ‘yar sandarta mai kyau, wadda ta ke taimaka ma kafafunta wadanda suka yi rauni. Ta amsa sallamar cikin murna, ta zo ta zauna kan kujera. Hajiya Halima ta zauna kasa kan kafet. Badi’a da Maryama suka shiga jere kulolin da Hajiya Halimar ta zo da su. Suka sake fita suka shigo da sauran. Kaka ta ce, “Ba ki gajiya Hajiya Halima, kowane lokacin in za’a zo duba ni sai an zo min da abin tabawa. Allah Ubangiji yasa ke ma ‘ya’yanki suyi miki. Ga jarumin namiji nan Shatima, cikin matansa Allah zai sa wata ta miki fiye da abin da ki ke min. Hajiya Halima tayi murmushi bata amsa ba don nuna kara ga uwar mijin tata. Bayan sun gaisa ne suka shiga hirar duniya, Badi’atu autar Hajiya Halima, da Maryam yar gidan Hajiya Saude kanwar Baban su Shatima wadda ke gaban Kaka, sun kule a daki suna tasu hirar. Hajiya Halima ta kalli Kaka ta ce, “Hajiya sai kuma wannan mashirmancin ya zo da zancen zai auri mata uku rana daya, wannan ai labari yake yi. Dubi masu mace daya ma yanda suke fama a wannan zamani, ni dai na ce masa a’a ya dai zabi daya, in ma karin ne sai ya bari ya ga kamun ludayin zaman, in yaso can gaba ya kara.” Kaka dai ba ta ce kala ba, har Hajiya Halima ta kai karshe. Kaka ta ce, “Zubo min abin da ki ka zo da shi in lasa ko nafi samun abin fadi.” Dariya suka yi su duka sannan ta ce, “Farfesun kajin zan zubo miki, ko na kafar Sa? Sannan akwai kus-kus, ga kuma faten acca.” Kaka ta ce, “To fa! Duk a cikina? To zubo min faten sai ki sa farfesun kafar Sa din a ciki.”_____ *🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 4 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427* *08146017245 hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar* *Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀 4 *Kaza mekwai* 🍀🍀 5 *Zabo me zuma*🍀🍀 6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀 7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀 8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀 9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja* 10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn* 11 *Maganin nono. Sahihi* 12 *Maganin hips and bobbs* 13 *hodar. Ni I'ma koramar mata* 14 *nakasan Mara babban sirri* 15 *kafi jijjibi* 16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani* 17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Maman haidar Bata tsaya anan ba* *Tana Saida hijabai dayadikan su akan darashin sari yadika dila dilahijaban. Yan gayu sannan* *takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeni awannan number* 08146017245 🍀🍀🍀🍀🍀 Mun tsaya wannan mashirmancin ya zo da zancen zai auri mata uku rana daya, wannan ai labari yake yi. Dubi masu mace daya ma yanda suke fama a wannan zamani, ni dai na ce masa a’a ya dai zabi daya, in ma karin ne sai ya bari ya ga kamun ludayin zaman, in yaso can gaba ya kara.” Kaka dai ba ta ce kala ba, har Hajiya Halima ta kai karshe. Kaka ta ce, “Zubo min abin da ki ka zo da shi in lasa ko nafi samun abin fadi.” Dariya suka yi su duka sannan ta ce, “Farfesun kajin zan zubo miki, ko na kafar Sa? Sannan akwai kus-kus, ga kuma faten acca.” Kaka ta ce, “To fa! Duk a cikina? To zubo min faten sai ki sa farfesun kafar Sa din a ciki.” zubo mata ta bata sannan ta kwala ma Badi’atu kira, suka fito. Ta ce, “Ku je ku kawo ma Hajiya ruwa, sannan ku zo ku kwashe kulolin nan zuwa kicin.” Suka ce, “To.” Sai da Kaka tayi nak! Ta koshi, sannan ta kalli Hajiya Halima. “Zancen Shatima, ina son ki cire rashin yardarki da kin amincewarki, ki aje su a gefe. Ki bi da ido, sannan ki hada da addu’a. Shatima gwarzo ne ba irin mazanku ba, mutum ya zauna da mace daya kamar fasto.” Ta gyara zama sannan ta ci gaba, “Yanzu bari in yi miki wani lissafi, mata nawa Maigidanmu ya aura? Nasan kin samu labari mu hudu ne ko?” Hajiya Halima ta daga kai alamun “Eh.” Ta ci gaba da cewa, “Kowace mace ta haifi ‘ya’ya da yawa, babbarmu tana da goma sha daya, mai bin ta na da takwas, wadda ni ke bi tana da goma, cikinmu ni ce kadai me ‘ya’ya hudu. Babbanṣu ya kwanta ya mutu shekara biyu kenan, matarsa na nan a Kaduna da ‘ya’ya biyar. Ke naki mijin ‘ya’yanku uku daga shi Shatima sai Mustapha, sai ko Badi’atu, sai dan uwansa Baban Nafisa. Suma su uku ‘ya’yansu duka mata, Nafisa da kannenta biyu. Saude ce ma me ‘ya’ya shida har na samu aka bani Maryama. Tattara ki kirga min jikokin nawa duk guda nawa ne? Ta dafa kirjinta tare da fadin “Ni fa nan da ki ka ganni yanda Allah Ya halicce ni ina son zuri’a, naso a ce cikin ‘ya’ya mazan nan guda uku da Allah Ya bani naso in samu wanda zai gaji Babansu a ‘ya’ya, don sai da ya bar talatin da uku a duniya. Kuma Alhamdulillahi kin dai san komai ba sai na fada miki ba, cikin ‘ya’yan nan babu mai irin mukamin da babu. Akwai Soja, akwai Dansanda, ga yan kasuwa, ga Malamai na duka bangare biyun boko da Islamiya. Ga Sarakuna duk da dai wannan gado ne, don haka ina son ki bi Shatima da addu’a don ina ga shi ne zai zama magajin Kakanshi, dama sunansu daya. Ina so ki sa masa albarka a cikin duk lamuranki.” Ba ta da zabin da ya wuce mika wuya don tasan ma babu wani abu da zata fada har ya yi tasiri. Don haka ta ce “To Hajiya, Allah Ya shi albarka, ya zaba abin da yafi zama alkairi. Kaka ta ce, “Yauwa hali dubu rubutun dutse, dama ni nasan ke komai naki cikin sauki ne da fahimta, Allah Yayi miki albarka. Hajiya Halima ta ce, “Amin. To amma Hajiya an bincika sauran da ya ke son an ji ya’yan asali ne ko? Ta ce, “Ke dai ki kwantar da hankalinki, komai na jan namiji daban ne, burinmu dai ki bishi da addu a.Nafisa tana zaune a cikin lambun gidansu kan kujera irin mai lilon nan, sanyi da kamshin lambun yana kara ma zuciyarta nishadi. Ta lumshe ido tana kallon surar Shatima a idonta, cikin shiga ta kasaita da kamshi. Gaskiya tana matukar son Shatima har ma ba za ta iya misalta son ba. Tasa hannu ta dauki wayarta da ke kan cinyarta ta bankado hotonsa wanda tasa Badi’atu ta turo mata. Zuciyarta tana dadi in ta kalli fuskarshi. Lallai za ta tura mishi sakon gaisuwar Juma’a yanzun nan tun da yau take babbar rana. Message ta shiga ta soma tura masa sako kamar haka: Ya Allah Ya tsareka, Allah Ya tsare gabanka da bayanka, ya daukaki rayuwarka. Ya sa ka Cimma duk abin da ka ke nema. Allah tsare idonka, da kunnenka, da ji da ganin haram. Allah Yasa Aljanna ce makomarka. Barka da Juma ‘a. Ta karanta ya kai sau goma kafin ta runtse ido, gabanta kuma yana faduwa ta tura masa. A fili ta ce, “Allah kasa kar in yi da na sanin tura sakon nan. Abin da ya bata mamaki kuma bata yi tsammani ba shi ne, jin karar sako ya shigo wayarta. Bata ba tunaninta wahala ba, kawai ta yanke hukunci cewa sakon daga shi ne Cikin nutsuwa ta duba ga abin da ya ce: Zan shigo misalin karfe biyar ni da Aminina, zan kasance cikin farin ciki in na same ki a gida. Sannan abincin gidan Babana shi ne zai zama abincin rana na a yau. Ki húta lafiya. Tayi ta maimaita karanta rubutun. Ta dai fahimci yana nufin zai zo yau shi da abokinshi, amma ba ta gane batun cin abinci ba. Ta ce a fili, Bari in je gun Mama tayi min fassara.” Uwar ta gama karanta sakon sannan ta saki murmushi. To in ba ki gane ba yau a nan gidan zai ci abincin rana, nan ba gidan Babanshi ba ne? Nafisa ta ce, Har nayi tunanin haka, sai kuma na ce kila in yaci abincin rana a gidansu sannan zai zo. To Mama yanzun me za’ayi masa kenan? Ta ce, Ki binciko irin abincin da ya fi so mana koda gurin Badi’atu ne.” Da sauri ta dauki wayarta ta nufi dakinta. Badi’atu ta kira tana tambayarta irin abincin da Yaya Shatima yafi so. Kusan duk abincin gargajiya yana so, amma babu kamar burabisko. Sosai tayi kwalliya ta fesa kalolin turaruka, ta kame tana yawaita kallon agogo. Tsinken agogon ya sauka kan digon da ke nunas biyar daidai, kararrawar kofar falo tana bugawa. Cikin dakinta ta shige da sauri kar ya soma karo da kwalliyarta, ba birgewa ba ne. Hamida ta ce, Yaya Nafisa in ba su ba nefa ki ka boye? Ta ce, “Ke dai kije ki gani. Kunnenta na gurin taji Hamida na fadin “Sannun ku da zuwa. Sai da Suka gaisa da Mama sannan ta ce Hamida ta kai su lambu inda aka yi musu shimfida. Ta ce, “Mami zo ki cema Yayarku ga su Yayanku sun iso, sai ki je ki taimaka ma Hamida ku kai musu abinci.Cikin shadda doguwar riga mai ruwan goro ta nufi inda aka sauki bakinta. Tayi musu sallama suka amsa, ita da shi suka kalli juna cikin ido. Tayi murmushi tare da jan dan mayafinta ta rufe fuskarta alamun kunya Sannan ta zauna a kusa da dayan tuntun wanda ba a jingina da shi ba. tuntu uku aka saka a kan kafet din da aka shimfida. Cikin girmamawa ta gaishe su. Ya ce, “Sunana Muhammad Jafar Isa, lakabina Shatima. Wannan abokina ne sunanshi Munnir Khamis, dukkanmu muna aiki ne a karkashin Gwamnati. Nazo gurinki ne don ina son ki zama daya daga cikin matana. Da sauri ta dago ta dube shi, suka hada ido ya sakar mata murmushi. Bakinki da magana amma ki fara gabatar mana da kanki tukunna. Cikin’ son taja ra’ayinsa da muryarta ta ce, “Sunana Nafisa Musa Shátima kuma ni daliba ce a Jami ar Ahmadu Bello da ke nan Zariya.Ina cikin shekarata ta biyu. Sai dai abin da ban fahimta ba shi ne, ka ce zan zama daya daga cikin matanka, shin kana da wasu matan ne ko ko ya ya abin yake? Sallamar su Hamida ce ta sa shi yin shiru. Suka Aje kuloli da kofuna. Hamida ta dauki plate biyu ta soma zuba musu burabisko. Yace, Kanwata sa plate daya wa abokina, ni matata ce zata sa min in gani ko ta san cikin mijinta. Nafisa ta amsa ta zuba mishi komai ta jere a gabanshi. Bayan tafiyar su Hamida ne, Shatima suka soma cin abinci. Matso ki ci tare da ni. Ya fada cikin murmushi. Ta ce, “Ni naci tun lokacin da aka gama. Ya ce, “Ba ke ki ka girka ba ke nan? Ta ce, “Ni nayi, bai yi dadi ba ko? Ya ce, Bari in gama tunda babu kyau magana in ana cin abinci.” Ta dafa hannuwanta “Bari in tashi ku gama. Ya ce, “A’a zauna ina son ina cin abinci ina kallonki.” Ta zauna tare da jan mayafi ta dan rufe gefen fuska. Sai da suka gama ci da sha, sannan suka koma hira. Ya ce. Meki ka ce dazu? ta ce, “Batun matanka da ka ce zan zama daya daga ciki.” Ya ce, “Eh gaskiya ke ce ta uku. Ta zata zolayarta yake yi, don haka bata ji Komai ba sai ma ta ce, Ban san lokacin da ka auri Biyun ba, ko kuma mu ne ba a gayyata ba. Ai rana daya za’a daura da naki, kuma ina zaton ma hudu za’a daura duk da ban san wace ce dayar ba.” Ta ce, “Zan fi son mu aje batun wasa, ni da kai muyi zance na gaskiya.” Ya ce, Ai ke ce ki ke ganin wasa ne, amma babu wasa cikin zancena. Fuskar Nafisa ta canza launi daga fara’a zuwa kalar damuwa, shi kan shi ya lura da haka amma bai bi ta kan haka ba, sai ma ya mika mata karamar wayarsa. Ban yi saving din lambar ki ba da na amsa a hannun Badi’atu, ki saka sunan da ya dace, don da shi zan kira ki a gaban kowa. Ta amsa ta saka tayi saving da (Sweety). Ya kalla sannan ya dube ta. “Sweety! Har a gaban Mama da Hajiya, da Kaka, da su Baba? Tayi dan murmushi “Eh. Ya ce “To kema hakan za ki kira ni. Sun dauki lokaci suna dan tattaunawa, kafin a kira Magriba. Suka mike da zummar tafiya. Ya aje mata kudi ‘yan dubu dai-dai guda goma. Ki sai omo ki wanke kwanuka, abinci ya yi dadi.” Ta dube shi, “Haba dai, ka bar shi kawai.” Ya ce, “Ai ba ki tambaye ni ba. Tayi musu rakiya har gurin mota. Bayan tafiyar su tazo a rude gurin Mama. Ta ce, “Mama Yaya Shatima ya yi min wata magana da ta sa naji komai na duniya ya ishe ni, wai mu uku zai aura rana daya! Mama tayi ‘yar dariya, “Ina ga ba ki san tsokana ba ko? Wasa ya ke miki.” Hawaye suka soma zubowa daga idanunta. “Wallahi Mama babu alamun wasa a tare da shi sam-sam! Ta ce, “To bari Babanku ya shigo mu Ji, in dai zai auri wasu ai shi ne waliyyin shi. Yana Yana daga kwance ya kalli agogon wayarshi, sha daya ta gota. Ya danna lambar Amna, sai da tayi ruri ta katsee. Yayi murmushi, ya san kadan daga cikin jan ajin Amna. Ya sake kira, can ta daga muryarta can kasa ta ce, “Hello!” Ya ce, “Ba ki yi bacci ba Amna?” Ta cc, “Eh, ban yi ba tukunna, sai yau ka ke kirana? “Kiyi hakuri zan shigo gobe.” Ta ce, “Sai kuma ka daga zuwan, don gobe duka gidan ba mu nan.” Ya ce, To fa? Ina za ku haka har da ba za ku amshi bakuncina ba?” “Ni dai Umra zamu je da Mom, da Dad sai Sisters dina guda biyu. Amaryar Dad da sauran yara za su je (London) hutu. Ya sauke ajiyar zuciya, “Sai yaushe za. ku dawo? Ta ce, “Sati biyu zamu yi, ba dadewa zamu yi ba.” Ya ce, “Shi kenan. Don Allah ki sani cikin addu’arki.” Insha Allahu, amma dai zamu yi waya in mun sauka ko? Dole na, ina son wannan muryar taki sosai Amna. Ya fada cikin murmushi. Muryata kawai ka ke so ban da ni? Ke ma kin san fada bata baki, ina matukar sonki. Nima ina sonka da yawa, sai dai ina ja baya ne don ina ganin kamar ba ka damu da ni ba. Ya ce, Me yasa ki ke ganin kamar ban damu da ke ba?” Tayi yar dariya tare da sake matse wayar a kunncnta don dadin hira da shi. Ta ce Tun ranar da na kira ka ka ce zaka kira ni in ka samu sukuni, sai yau ka samu sukuni din? Ya canza kunne da ya manna wayar zuwa dayan kunnen don ya ji SOsai, saboda Amna bata magana da karfi ko. kuma ba ta son hayaniya. Wannan tsarin nata yana matukar birge Shatima. Ya ce, “Ba za ki gane ba, amma lokaci ya kusa da zamu zama tare. Ta ce, “Wane lokaci kenan?_____ *🏚️RANA DAYA🏚️* CHAPTER 5 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427* *08146017245 hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar* *Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀 4 *Kaza mekwai* 🍀🍀 5 *Zabo me zuma*🍀🍀 6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀 7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀 8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀 9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja* 10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn* 11 *Maganin nono. Sahihi* 12 *Maganin hips and bobbs* 13 *hodar. Ni I'ma koramar mata* 14 *nakasan Mara babban sirri* 15 *kafi jijjibi* 16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani* 17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Maman haidar Bata tsaya anan ba* *Tana Saida hijabai dayadikan su akan darashin sari yadika dila dilahijaban. Yan gayu sannan* *takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeni awannan number* 08146017245 🍀🍀🍀🍀🍀 Mun tsaya Tayi yar dariya tare da sake matse wayar a kunncnta don dadin hira da shi. Ta ce Tun ranar da na kira ka ka ce zaka kira ni in ka samu sukuni, sai yau ka samu sukuni din? Ya canza kunne da ya manna wayar zuwa dayan kunnen don ya ji SOsai, saboda Amna bata magana da karfi ko. kuma ba ta son hayaniya. Wannan tsarin nata yana matukar birge Shatima. Ya ce, “Ba za ki gane ba, amma lokaci ya kusa da zamu zama tare. Ta ce, “Wane lokaci kenan? “Idan mun yi aure mana, kin san fa bana son a dauki lokaci me yawa nan gaba.” Ta ce, “Ban san ya zan ji ba in aka ce yau gashi na aure ka, ina tsananin sonka Shatima.” Sun jima suna hira kafin suka yi sallama da alkawarin zai kira ta gobe kamar yanzun. Lamo ya yi a kwance yana tunanin cikin su ukun nan bai fi son Amna ba kuwa? Wata zuciyar ta ce, ‘Ina ka bar Aliya mai hankali da sanin ya kamata, ga kuma Nafisa itama ba baya ba…?” Da wadannan tunanikan bacci ya yi awon gaba da shi. ******** Tana tsaka da tuyar Awarar ta ga yara sun zagaye ta tana son ta sallame su gashi itacen duk danye ne, sai faman hayaki yake yi. Idanunta sun yi jajir, zuciyarta tana can gurin Mahaifanta tana kokarin ta kammala tayi abinci ta kai musu, sai taji Horn din mota a kanta. Da sauri ta dago ta kalli motar, ranta ya dan sosu, don ita dai tasan ba a kan hanya take tuyarta ba bare ta ce, amma masu motar nan sun nufo ta. Tasan dai ba siyan Awara zasu yi ba tunda bata taba ganin wani mai mota ya tsaya da sunan siyan Awara ba.Yaran suka kauce motar ta tsaya daf da kaskonta. Cikin tsananin tsoro ta mike tsaye tayi baya. Motar taja baya taje gefe tayi parking, ita kuma cikin sauri taje tana tsame Awarar da ke cikin man don kar ta kone. Tana ta sauri jikinta yana ɓari, tana yi tana kallon inda motar ta tsaya. Yaran da suka dare suka dawo don ta kunsa Awarar. Sai da ta zuba dayan a mai sannan ta shiga kunsa musu. Tana sallamar su ana bude motar, ta tsura ma gurin ido gabanta yana wata irin faduwa. Sai kawai taga Alhajin nan. Ba ta san lokacin da ta sauke ajiyar zuciya ba tare da hadiye miyau, sai ta ji ta dan samu nutsuwa. Ta mike tsaye ta dan risina ta dafa gwiwarta alamun girmamawa ta ce, “Ina yini Alhaji?” Ya ce, “Ba sunana kenan ba, lafiya lau.” Ya kalli kayan “Dama nan ku ke?” Ta. ce, “Eh.” Ta nuna wani ribabban gidan sama na kasa, ginin tamkar ya zubo in ya ji kwakkwarar iska. Ya kalli gidan na tsawon minti biyu, sannan ya dubi kayan suyar tata, sannan ya yi magana. “Salma me ki ke saidawa a nan?” Itama ta kalli kayan sannan ta dube shi da ‘yar fara’a. “Awara ce ni ke saidawa.”Ya ce, “Shi ne ki ke zama a nan gab da titi? Ba kya gudun mota ta kwace ta nufo kanki ta taka kamar yanda na kwatanta din nan?” Ta sake kallon gurin, kamar zata yi magana sai kuma ta fasa. Ya ce, “Nasan za ki ce ba ki hau titi ba, amma mota tana kwacewa, me zai sa ba za ki yi a cikin gida ba?” Ta ce, “Ai in ana yi a cikin gida ba su sanin ana masu siyan, sai dai in je talla, kuma Innarmu da Babanmu basa son in je yawon talla.” Ya ce, “Gaskiya ne. To ki dan kara ja baya kadan ko?” Ta ce, “To na gode.” Ya ce, “Ina zuwa nan unguwar layin can na sama shi ne gidan Kakana.” Ta kai kallonta inda ya nuna. Ta ce, “Layin Shatima ko?” Ya ce, “Ai nan ne gidan Kakana.” Ta dan zaro ido “Laahh! Nasan gidan, muna zuwa ranar Juma’a karɓar sadakar waina, ko shinkafa da wake.” Ya tsura mata ido, ta ce “Yanzun dai bana zuwa sai kannena.” Ya ce, “To ya jikin Babanku?” Ta dan fadada fara’arta “Ya samu sauki, har ma yana tashi zaune tunda aka yi mishi gashin kashi sau biyu. Kuma naku mara lafiyar ya samu sauki?”Ya ce, “Ai mu ba a kwance ta ke ba, Maman abokina ce muna kai ta gashin Kashi ne.” Ta ce, “Allah Sarki! Allah Ya bata lafiya.” Munnir ya leko, “Abokina zo mu tafi mana.” “To, Ya dubi Munnir, sannan ya dubeta. “Sai an jima, amma don Allah ki matsa a titin.” Ta ce, yanzun zan matsa.” Tana tsaye suka ja motar suka wuce, sannan ta zo ta kara komawa baya da kayanta. Shatima yana harba motar kan titi, Munnir ya kalle shi rai a hade. “Wai me yasa ká ke son shiga harkar yarinyar nan ne? ka tsaya kana magana da ita kamar wata sa’ar yin zancenka.” Ya kalli Munnir, “Laifi ne kenan don nayi mata magana ta tashi a titi?” Munnir ya ja tsaki. “Mene ne to na fada mata kana zuwa nan ga gidan Kakanninka, ga waye-waye?” Shatima ya yi murmushi, “Ni kaina ban san dalilin da yasa ni ke son shiga lamarin yarinyar ba, amma dai nasan ina tsananin jin tausayinta. Aliya tana tsifar kai da yamma ranar Lahadi, misalin karfe hudu. So take yi taje wankin kai don rana irin ta yau ne take samu tayi abubuwan da ba ta samu tayi ba saboda aiki.Wayarta ta soma ringing, ta dauka ta kalli fuskar wayar, gabanta ya fadi don ganin (My love) da ta yi. Ta jima tana jiran wannan kiran amma dole ta hakura don tuntuni ta san halin Shatima, ba ya daga cikin maza masu nacin kiran wayar budurwa ko mai son da yake mata. Ta daga tasa a kunne tayi sallama. Ya ce, “My love fatan kina lafiya?” Ta ce, “Lafiya lau, ina fatan kai ma haka?” “Hakan ne. Zan shigo bayan sallar Isha’i mu gaisa koda minti goma ne.” Ta ce, “Sai ka shigo, amma ina neman alfarmar a kara min yawan mintuna.” Ya ce, “To zan duba in gani. Kafin takwas na daren, Aliya ta sha wanka sai kamshi take yi, tana son in ya zo ta ce ya shigo ya gaida su Mamanta, don bata basu labarin shi ba kar su karya tata, tunda ko yaushe tsiya suke yi mata, wai ta tsaya jiran Shatiman da bata san duniyar da yake ba, bai ma san tana nan ba. Kannenta biyu suka yi aure bayan tafiyar Shatima, don haka tana shan gori a dangi. Lokacin da take shirinta, matar wanta da Mamansu sai zancenta suke wai wane ne kuma ya samu shiga haka? Ta lura amma sai ta share tamkar bata san suna yi ba, ta dai tsara zata basu mamaki ne. Wani yaro yayo sallama. ‘Yar Yayansu ta amsa. Ya ce, “Wai ana kiran Aliya in ji wani mutum a waje.” Yarinyar ta ce, “Kai Anti Aliya ake cewa.” Mamanta da ke bakin kofarta tana jinsu ta ce, “Ke Yusra ko! In ke Antynki ce shi Antynshi ce? Kije ki kira ta.” Aliya tana jin su. Yusra ta leka dakinta ta ce, “Anti wai ki zo in ji wani.” Ta ce, “Ki ce ina zuwa.” Ba ta tsaya ɓata lokaci ba tun da ta san cikin lokutanta ne zata bata. Yana jingine a gaban motarshi, ta zaci su biyu ne sai taga shi kadai ne. Ta jingina itama sannan ta gaishe shi. Fitilar kofar gidan ta haska su, don haka ta lura da kallon da yake mata, tunda ta fito. Ya ce, “Kin ganni sai yau ko?” Ta ce, “Ai nasan kana cike da tarin ayyuka da uzurori, sannan dole in koyi hakuri tunda nasan bani kadai ba ce ina da kannai.” Kalaman Aliya suka yi masa dadi, da alamu ita ce zata fahimce shi fiye da sauran, don ya lura Nafisa tana da kishi sosai. Ita ko Amna har zuwa yanzun shakkar fada mata yake, don baisan yanda za ta dauki abin ba.Yayi murmushi, “Tun-tuni shi yasa ni ke ganin ki daban a ‘cikin mata, haka ma sonki daban ne a zuciyata. Ta gyara tsayuwa, “Nima a gare ni daban ka ke a cikin maza, don haka da ba ka nan duk namijin da ya zo sai in ga tamkar mace ‘yar’uwata.” Ya ce, “Na yarda da ke tunda ki ka jira ni. Ke na fara so, ke ce za ki zama uwargidana.” Ta ce, “Kana ganin zan girme su?” Ya ce, “Za ki girme su, amma Amna kila kuyi sa’a, ko ki fi ta kadan.” Ta ce, “Kuma suma duk Sun san cewa a rana daya zamu yi aure?” Ya ce, “Nafisa ce ta sani, amma na lura ta damu. Ina ganin tana da kishi sosai. Aliya ta ce, “Sai lallashi tunda yarinya ce. To ita fa dayar?” Ya ce “Ita kamma na kasa fada mata, yanzun haka suna Umra da ‘yan gidansu, ina son sai ta dawo zan je mata da žancen. Aliya ta sauke ajiyar zuciya, “Amma sai in ga da za ka dan tuntuba mata ko a waya, ba wai ka fito mata da zancen ba, ka nuna mata akwai fa wata muhimmiyar magana da za ku yi in ta dawo, kaga zata yi ta lissafin wace magana ce? To in ka zo mata da zancen ba za ta ji komai ba, don kila ta hasashi abin da yafi haka.”Ya ce”To zan gwada haka. Ya su Mama? Ya kamata in shiga in gaishe su ko?” Ta ce “To bari in fada musu. Suna gama gaisawa da Maman su Aliya, Yayansu Aliyu yana shigowa, shi ne ma ya gane Shatima. Suka gaisa, da zai tafi ya aje musu dubu goma ya fito. Sun dan yi ‘yar hira sannan suka yi bankwana ya tafi. Shatima da Mahaifinsa sun dawo daga sallar Juma’a, Mahaifin ya ce, “Mu wuce gidan su Hajiya in ba ka da wani uziri, don ban samu damar zuwa da safe ba.” Shatima ya ce, “Babu uzuri Alhaji, ko ma akwai naka yana gaban nawa. Cikin jin dadi Alhaji ya ce, “Sai dai goron da na sai mata yana motata a gida.” Shatima ya ce, “Sai a sai mata wani yanzun da izinin Allah.” Sun samu gidan cike da jikoki ‘ya’yan Marigayi babban wansu sun zo daga Kaduna su uku, biyun na gida. Sai kannan Nafisa Hamida da Momi, ga ‘ya’yan Anty Saude. Shatima ya ce”Masha Allah, duk ‘yan hutun satin ne haka fal a gida?” Ta ce, “Eh, ga su nan har gidan ya yi dadi, da ko shiru daga ni sai Maryama.” Suka zauna suka gaisheta. Shatima ya bata goronta da Zuma. Ta dinga zuba musu godiya da sa albarka. Sannan ta ce, “Dama ina son ganinka, dazu da su Hannatu suka zo sai suke fada min wai saurayin Rahma zai zo gaishe ku gobe Asabar.” Alhaji ya ce, “Allah Ya kai mu. A can Kaduna ta samu saurayin ita ‘Rahmar?” Ta ce, “Ban tambaye su ba, amma in ya zo ai ku za ku ji komai daga bakinsa. Alhaji ya ce, “Haka ne.” Shatima ya ce, “Rahma ta gama karatun ke nan?” Kaka ta ce, “A’a, sauranta shekara daya. Ai yanzun in an samu miji ba a cewa sai an gama karatu, haka kuma tsakanin karami da babba ba a jira. Ita Madina ai ta gama karatun yanzun bautar kasa ta ke. Da Allah zai kawo mijin ai sai duk a hada su.” Alhaji ya ce, “Sosai kuwa. Yaran suka dinga zuwa suna gaida su Shatima. Maryama ta kawo musu waina da miya, Shatima bai ci ba don yasan ‘yan aiki ne suka yi. Amma Alhaji da ya ke yana son waina ya ci kayansa.Suna ta hira har a ka zo kan batun auran Shatima. Kaka ta ce, “To kai yanzu gida daban daban za ka aje matan naka ko kuwa?” Alhaji ya ce, “Yauwa, dama nayi wata shawara. Filayen da na raba musu shi da Mustapha da Badi’atu ya yi min ciko ya maido min da nashi sai in ba shi wani babban filina da ke Rigachikun, kawai ya yi ginin guri hudu shi da matansa kawai, ko ya ya ku ka gani?” Kaka ta ce, “Amma kuwa kayi tunani mai kyau, ko ko kai ya ya ka gani Shatima?” Shatima ya ce, “Ai ni Alhaji ka gama min komai, don ka ga na sami saukin zuwa Kaduna gurin aiki kullum, don da ina tunanin duk su zauna nan Zariya, ni kuma ina Kaduna sai su ke zuwa.” Kaka ta ce, “Hakan shi ne daidai.” Ya ce, “Kaka a taya ni godiya gurin Alhaji, sannan a nema min alfarma, a rubuta takarda na yarda zan ba da cikon amma sai nan gaba, don kudin hannuna zan tada ginin da su.” Ya ce, “Wannan hutun na karshen mako sai muje kaga gurin.” Ya ce, “Allah Ya kara girma da lafiya Alhaji, Allah Ya jikan Mahaifinku, ya raba ku lafiya da Kaka.” Suka ce “Amin.” Nan suka ci gaba da tattauna al’amuran da suka shafe su. ._____ *🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 6 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427* *08146017245 hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar* *Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀 4 *Kaza mekwai* 🍀🍀 5 *Zabo me zuma*🍀🍀 6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀 7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀 8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀 9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja* 10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn* 11 *Maganin nono. Sahihi* 12 *Maganin hips and bobbs* 13 *hodar. Ni I'ma koramar mata* 14 *nakasan Mara babban sirri* 15 *kafi jijjibi* 16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani* 17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Maman haidar Bata tsaya anan ba* *Tana Saida hijabai dayadikan su akan darashin sari yadika dila dilahijaban. Yan gayu sannan* *takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeni awannan number* 08146017245 🍀🍀🍀🍀🍀 Mun tsaya kullum, don da ina tunanin duk su zauna nan Zariya, ni kuma ina Kaduna sai su ke zuwa.” Kaka ta ce, “Hakan shi ne daidai.” Ya ce, “Kaka a taya ni godiya gurin Alhaji, sannan a nema min alfarma, a rubuta takarda na yarda zan ba da cikon amma sai nan gaba, don kudin hannuna zan tada ginin da su.” Ya ce, “Wannan hutun na karshen mako sai muje kaga gurin.” Ya ce, “Allah Ya kara girma da lafiya Alhaji, Allah Ya jikan Mahaifinku, ya raba ku lafiya da Kaka.” Suka ce “Amin.” Nan suka ci gaba da tattauna al’amuran da suka shafe su. Ya idar da Nafilfilinsa na dare ya zauna yana istigfari, sai ya tuna wannan lokacin a Saudiya tamkar rana ce, zai iya yin magana da Amna. Ya tashi ya ciro wayarsa a chaji ya kunna yana neman lambar da Amna ta kira shi shekaran jiya. Ya kira sau biyu bata daga ba, ya mata uzuri kila bacci take yi tunda ba kowa ne ya saba da zama har wannan lokacin ba. Ya sake kira kashi na uku, sai gashi ta daga cikin mayen bacci. Ta ce, “Hello honey!” Ya dan zaro ido, don bata taba kiranshi da wannan sunan ba, ta kan dai ce mishi ‘Dear’. Ya ce, “Honey kiyi hakuri na tashe ki a bacci ko?” Ta ce, “Ba komai, ya ka ke?” Ya ce, “Ina lafiya. Kina yi mana addu’a kuwa ki ke bacci?” Ta ce, “Ina yi mana.” Ya ce, “Wace iri ki ke min?” Ta ce, “Ta kara karfin soyayya har gidan Aljanna.” Ya ce, “Kin kyauta, amma ina son kiyi min wata tawa ta musamman. “Kamar wacce ke nan?” Ta tambaye shi. “Ki min addu’a in kin dawo duk abin da na zo miki da shi za ki amshe shi.” “Ban gane ba?” Ta fada da sauri.”Za ki gane in kin dawo, ni dai ina son ki daga hannu ki ce Ya Allah Kasa duk abin da Muhammad Ja’afar ya zo min da shi in amshe shi. Tayi dariya, “In ka zo da abin da ya sha kan tunanina fa?” “Ba zai sha ba in sha Allah.””Nayi alkawarin zan yi maka.” Ya ce, “Na gode. Yaushe za ki dawo? Na kosa in gan ki.”Saura kwana biyar mu dawo.””To ni in zo yaushe?” Ya tambayeta.”Ban da ranar da muka dawo, amma ka iya zuwa koyaushe.” Ya ce, “To washegarin ranar zan zo.” Ta ce, “Na gode da kulawa, kaje kayi bacci.” Ya ce, “Ranki ya dade.” Tayi ‘yar dariya sukayi sallama. Ta shiga kicin ta samu Mama tana girkin abincin rana, taje tá jingina da (Freezer) din da ke bayanta. Ta ce, “Mama da zan tafi Makaranta kin ce min za ku yi magana da Babanmu, wallahi ni fa yau ko a aji ban iya gane komai ba. Ina son in san gaskiyar abin da Yaya Shatima ya fada, tun ranar da ya kira Baba Alhaji ya ce masa yaje gurin Kaka a can zai ji gaskiyar magana, to wai bai je ba ne?” Mama ta kalli yarta cikin tausayi, “Bari Babanku ya dawo sai kuje gurin Kaka tare don kiji da kunnenki.” Ta ce, “Amma dai zance mafi inganci shi ne mu ukun kenan?” Ta ce, “A’a, ni na fada miki ban san komai ba sam-sam!” Ta ce, “Ai ko yau da dare zan je tare da Baba din.” Ya zuba ido yana kallon gurin zaman Nafisa, “Ina me wannan kujerar?” Mama ta ce, “Tana dakinta tana kunci.” Ya tsura ma Mama ido.Wane kunci kuma?” Ta ce, “Zancan auransu da Shatima mana, bad na fada maka tace ya fada mata su uku ne rana daya ba, ka kira Alhaji ya ce maka kaje gurin Kaka ka ji cikakken zance.” Ya aje cokalin hannunshi ya kurbi ruwa sannan ya mike. Dakin Nafisa ya nufa saboda duk cikin ‘ya’yansa babu kamar ta a zuciyarshi. Kwance ya same ta tana wasa da rigar wayarta, amma ga dukkan alamu tunaninta ba ya tare da rigar wayar, hankalinta yana can wani gurin.Ya tsaya a gabanta, sannan ya maida hannuwansa baya. Ya ce, “Nafisa!” Ta dago ta dube shi. Ya ce, “Me yasa ba ki zo cin abinci ba?” Ta ce, “Na koshi Babanmu.” Ya ce, “Ina son ki fada min damuwarki.” Ta dago ta kalle shi. “Babanmu ina son ka binciko min gaske ne Yaya Shatima mu uku zai aura rana daya?” Ya kalli ‘yarshi cikin tausayi, duk da kunya irin ta Nafisa amma sai da ta iya yi masa wannan magana. Ya ce, “Tashi muje gidan Hajiyar yanzun. Cikin sauri ta saka hijabinta. Kaka ta idar da sallar Isha’i tana jan carbi kafin tayi shafa’i da wutiri. Sallamar su ta jiyo, duk da bata san ko wane ne ba, ta raya a ranta ba za ta fito ba sai dai in na gida ne su shigo cikin dakin nata. Maryama ta shigo ta ce, “Kaka ga Kawu Alhaji nan.” Ta ce, “Kamar murya biyu naji.” Ta ce, “Eh, shi da Nafisa ne.” Ta ce, “Su shigo ciki.” Gabanta suka zauna suka gaisheta. Ta kalli Nafisa, “Dama kina nan?” Ta sunkuyar da kai. Kaka ta ci gaba da yuwa Nafisa fadan rashin son shiga jama’a, da rashin zumunci. Hakuri tayi ta baiwa Kaka.Alhaji Musa ya ce, “Hajiya kiyi hakuri, wannan halinta ne rashin son shiga mutane, kullum tana gida in dai ba Makaranta taje ba.” Kaka ta ce “Ita dai ta sani, ga shi nan za ki yi aure da kishiyoyi, zama ne za ku yi na wanda ya iya allonsa ya wanke ya sha…” Nafisa ta dafa kirji. “Dama gaske ne Kaka ba ni kadai Yaya Shatima zai aura ba?” Kaka ta ce, “Au! Dama bai fada miki ba?” Nafisa ta soma kuka. Alhaji ya ce, “Hajiya bai kamata a bar Shatima yana dan karamin shi ya auri mace sama da daya ba, zai hada ma kanshi damuwar da zata sa shi yayi da na sani.” Kaka ta ce, “Allah Ya raba shi da aikata da na sani, sunna fa zai yi, ibada ka ke fada min da na sani? Yanzun dai a takaice ka taso ‘yarka ne ka fada min cewa ya fasa auran ‘ya’yan wasu ya auri ‘yarka?” Ya sunkuyar da kai, sannan ya shiga ba Hajiya hakuri don ba a son ɓacin ranta saboda tana da hawan jini. Duk da haka Hajiya ba ta yi shiru ba sai da tayi masu tatas! Ta ce, “Ku kun kasa zama jarumai, kun amince ku mutu da mata dai-dai shi yasa kowanne zai zo yana fadin bai kamata ba, amma ba wanda ya kawo min aya ko hadisi da ta haramta masa auran.Ke kuma ko da dayar zai zaba ai ba ki ciki, saboda akwai yarinya Aliya ‘yar makotanmu ce, sama da shekaru uku tana jiransa. Don haka kin ga kema cikin ‘yan kari ki ke.Nafisa ta mike fuuu! Cikin kuka ta ce, “Kaka sai anjima.” Alhaji ya ce, “Bari mu tafi Hajiya.”Ta ce, “Ku gaida gida.”A mota yana ta lallashinta. Ta ce, “Baba ni dai kawai na fasa, na hakura.” Ya ce, “A ‘a Nafisa, kar ki ce haka, ki bari dai muje gida. Iyayen sun tasa ta a dakin Maman suna lallashinta, kan cewa tayi hakuri kar ta ce ta fasa, domin Kaka za ta yi fushi. “Kin san dai fushinta zai janyo babbar matsala.” Mama ta ce, “Ke da yake dan uwanki, Hajiyarsu ke tafi so, kuma kema kin san dole zai fi sonki saboda dangantaka.” Haka dai suka yi ta lallashinta har taje ta kwanta, amma ba don ta gamsu da maganar mahaifinta ba. Tun da ya isa kofar gidan gabanshi ya fadi, duk yanda yake zaton kudin su Amna daga ka kalli gidan kasan ya wüce yanda ya zata. Dama tun da ya taso daga Zariya waya suke yi har ya iso tangamemiyar kofar gidan tasu mai kama da kofar gari. Maigadi ya bude masa ya shiga. ‘Yan matasan samari ne suka tare shi. Ya fito cikin shiga ta alfarma, shadda ce gizna mai kalar kwai. Yayi matukar kyau da bakar hular da ya dora.Su ne suka jagorance shi zuwa wani kasaitaccen falo. Duk da suna da kudi ya tabbata su Amna sun fi su nesa ba kusa ba. Amna ta fito cikin doguwar riga English wears, sai dan mayafi karami da ta yafa. Tayi kyau matuka. ‘Yan gidan suna ta zuwa suna gaishe shi (kannenta). Dama ta fada masa ita ce mace babba a gidan, sai wanta namiji babba yana zaune a Ingila da matarshi da yara biyu. Amaryar Babansu ta zo suka gaisa, itama yarinya ce danta daya. Tayi masa jagora zuwa gurin Mahaifiyarta ya gaishe ta. An shirya mishi abubuwan ci da sha na zamani. Sannan sun yi hira sosai irin ta masoya, amma ya matsu ya fada mata cewa su uku ne.Ita ma a nata ran ta matsu ta san abin da zai zo mata da shi, wanda ya ce ta yi masa addu’a a kai.Ya kalleta da niyar maganar, sai ta riga shi da cewa, “Ban ji kayi maganar da ka sani in yi maka addu’a ba?” Ya cire hula ya ajiye, yasa hankici ya share zufar da ta ratso goshinsa a nan take. Sannan ya ce, “Ki min alkawari abin da zan fada ba zai raba mu ba?” Ta lumshe ido, muryarta can kasa. Ta ce, “Nayi maka alkawari ba zan barka ba.” Ya ce, “Na taba baki labarin Aliya budurwar da na fara yi nace ba za ta jira ni ba ko?” Ta daga kai tare da fadin “Na tuna. Ya ce, “To ashe tana nan tana jirana.” Ya tsura mata ido yaga yanda zata dauki maganar. Tabbas fuskarta ta canza, sannan tayi shiru ta kasa magana. Ya ce, “Kin yi shiru honey.” Ta dube shi “Me zan ce maka? Na fahimci ka sani in yi addu’a a kan cewa zaka min kishiya, haka ne?” Ya ce, “Kishiyoyi za ki ce dai, domin gida sun cire min Nafisa baya-bayan nan. Yanzun dai ku uku ne za a yi rana daya.” Ta tura kanta cikin cinyarta. Ya tausasa murya.”Kar ki damu Amna, wallahi ina matukar sonki.” Ta dago ta dube shi.”Nafisar ba ta dame ni ba amma na tuna yanda kayi ta bani labarin Aliya da soyayyarku. Nasan kafi sonta.” Ya ce, “Ni nafi sonki, saboda kin fi sona.” Haka ya yi ta lallabata har ta hakura, sannan ta ce ya yi shiru yanzun tukunna kada Mom suji ba za Su yarda ba. Ya ce, “Shi kenan na gode da hadin kanki.” Da zai tafi ya ba kannenta dubu goma sabbin ‘yan dari biyar-biyar, ya ce su sha alawa babu yawa. Ita kuma ta kawo mishi wasu ledoji guda biyu ta ce ga tsarabarsa, suka rako shi har mota, ta zuba ledojin a kujerar baya. Ya nufi dakin Hajiyar shi don ya gaisheta tare da yi mata sallama, ya kuma kwashi albarkar safiya ya nufi Kaduna gurin aiki. Ba ta falon ba ta dakin, don haka ya nufi falon Alhajin su. Ya same su har Badi’atu suna karin kumallo ita da kayan Makaranta a jikinta. Ya tsuguna ya gaida su. Alhajin yasa mishi albarka tare da masa fatan ya dawo lafiya. Ya kalli Hajiya ya ce, “Hajiya zan je aiki.” Ta ce, “Kafin nan wai kai ‘yammatan naka wadanne iri ne? ni dai ‘yata Nafisa na sani, kasan dai sai mun bincika asali.”Ya ce, “Hajiya Aliya ce wadda dai ki ka sani asalin budurwata, ko Kaka dai za ta ba ki labarin asalinsu. Ta ce, “To dayar fa?” Ya ce, “Amna ‘yar family din Alhaji Baita Nasidi ce.” Ga mamakinsa sai yaga Hajiyarsa ta dago daga kashingidar da tayi. Ta ce, “Wane Alhaji Baitan? Na Kano babban dan kasuwar nan?” Ya ce, “Eh.” Ta ce, ‘Yar kareren dangi ce ko?” Ya ce, “Hajiya ba karere ba ce, jikarsa ce, shi ya haifi Babanta Alhaji Ibrahim Baita Nasidi.” Tayi dan murmushi, “Lallai ka tabo babban gida.” Ya kalli Badi ‘atu “Je dakina a kan gado za ki ga wasu ledoji guda biyu ki kawo min, yi sauri. Ya kai karshen maganar yana kallon agogon hannunshi gudun yin latti (makara). Ta ce, “Yaya bari in bi ka ka sauke ni.” Ya ce, “A’a ina Dircbanki? Ta tafi tana cewa, “Wai sai ya kai Yaya Mustapha wani guri sannan zai kai ni. Bai ce komai ba ta fita zuwa dakinsa. Ta dawo dauke da ledojin. Ya ce, “Ba Hajiya nata tsarabar da Amna tayo min daga Umra.” Badi’atu ta soma zazzage kayan iyayen suna kallo. Ledar farko riguna ne masu kyau, dogon hannu da gajeren hannu. Sai gajerun wanduna irin na ciki guda biyu._____ *🏚️RANA DAYA🏚️* CHAPTER 7 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko ku turo katin Mtn ta wannan number 09068032427* *08146017245 hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar* *Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀 4 *Kaza mekwai* 🍀🍀 5 *Zabo me zuma*🍀🍀 6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀 7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀 8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀 9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja* 10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn* 11 *Maganin nono. Sahihi* 12 *Maganin hips and bobbs* 13 *hodar. Ni I'ma koramar mata* 14 *nakasan Mara babban sirri* 15 *kafi jijjibi* 16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani* 17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Maman haidar Bata tsaya anan ba* *Tana Saida hijabai dayadikan su akan darashin sari yadika dila dilahijaban. Yan gayu sannan* *takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeni awannan number* 08146017245 🍀🍀🍀🍀🍀 Mun tsaya Ta ce, “Yaya bari in bi ka ka sauke ni.” Ya ce, “A’a ina Dircbanki? Ta tafi tana cewa, “Wai sai ya kai Yaya Mustapha wani guri sannan zai kai ni. Bai ce komai ba ta fita zuwa dakinsa. Ta dawo dauke da ledojin. Ya ce, “Ba Hajiya nata tsarabar da Amna tayo min daga Umra.” Badi’atu ta soma zazzage kayan iyayen suna kallo. Ledar farko riguna ne masu kyau, dogon hannu da gajeren hannu. Sai gajerun wanduna irin na ciki guda biyu. Daya ledar takalma ne sawu ciki kala biyu, sai turaruka da agogo mai kyau a kwalinsa. Hajiya ta fadada fara’arta. “Lallai abu yayi, masha Allah.” Alhaji ya ce, “An zo gurin, irin wadda ki ke so ko? Ma su kumbar susa.” Ta cc, “A’a Alhaji, ai mu ma ba a tsiyace muke ba.” Ya ce, “Amma tunda a ka ambaci Alhaji Baita ki ke washe baki.” Shatima ya ce, “Badi’atu kwashe ki maida, amma ki bar ma su Hajiya turarukan.” Alhaji ya ce, “Kwashe masa abinsa kin san dai na maza ne, me za ki yi da shi?” Ya nufi hanyar fita yana fadin “Sai na dawo.” Hajiyar tana fadin “Allah Ya shi maka albarka, sai ka dawo. Badi’atu ta nufi saman shi tana fadin “Don Allah Yaya ka jira ni.” Shi dai ya tafi yana mamakin Hajiyarsa, a nasa sanin Hajiyarsa bata daga cikin mutane masu kwadayi. Ginin Shatima da ke Rigachikun ya kankama, domin aiki ake yi babu dare babu rana, ko’in ce ba-ji-ba-gani, Flat ne guda hudu aka yi su suna kallon juna, kowanne yana dauke da manyan dakuna guda uku, kowanne da bandaki.Sai makeken falo da kicin babba, sai sito da ke manne da kicin din. Akwai Baranda a gaban kowane gini, sannan ga fili ishasshe wanda zai dauki sama da mota goma. A tsarinshi yafi son sai ya kammala gininshi tsaf! Sannan zai tunkaro maganar aure. Yasan jan aiki ya dauko, komai sai ya yi uku kila ma hudu, don har yanzun yana ji a jikinsa ta hudu tana tafe. Ranar wata Asabar suna tsaye a harabar gidan nashi da yake gini, lokacin ana yin rafta ne. Munnir ya ce, “Gaskiya abokina kana matukar kokari. Dubi yanda aiki ya yi nisa sosai.” Shatima ya ce, “Ba a magana. Yanzu haka na soma tunanin shiga asusun su Hajiyata da Alhaji.” Munnir ya ce, “Ai ginin akwai shi da cin kudi. To yanzun kowace tasan da wata kenan?” Ya ce, “Duk sun sani, yanzu zan tsara ma kaina yanda zan yi hulda da su kafin lokacin auran.” Munnir ya ce, “Har da wani tsari da zaka yi musu?” Ya ce, “Sosai ma kaga dai zan dinga ziyartar su ne bayan kowane karshen wata sau daya. Sannan kuma zan ke kiran su sau biyu a cikin kwana goma. Zan ke tura musu katin waya na Naira dubu daya a duk sati. In nayi haka ba zan gundure su ba, suma ba za su gundire ni ba.”Munnir ya ce, “Kamar kiran da kace a waya sau biyu a kwana goma ya yi kadan Shatima ya ce, “Ba ni da wani aikin kenan sai nasu, kiran ma awa dai-dai ne.” Ya ce, “To in wata cikin su ta kira ka fa?” Ya ce, “In ina da abin yi ba zan daga ba, in bani da shi zan daga in ji dalili, in abin mai mahimmanci ne in saurara, in ko shirme ne in ce ina da abin yi.” Munnir ya ce, “To in wata tayo message fa?” Ya ce, “Zan karanta in na amsawa ne in ba da, in ko akasin haka ne in share.” Munnir ya yi ‘yar dariya, “Lallai mutumina kana yin abubuwan ka da tsari.” Nafisa tana kwance cikin bargo, da zazzabi ta dawo daga Makaranta. Duk da ta sha magani bata daina jin sanyin ba. mama tana gefenta tana yi mata dan fada cikin damuwa ta ce, “Haba Nafisa, duk kin sa kanki damuwa tun daga ranar da ki ka san maganar nan kin bi kin damu. Sai kin sa ma kanki wani ciwon sannan za ki ji dadi, shi fa ba zai fasa auren sauran ba, ke in kin je babu lafiya yaushe za ki yi wata gama a idonshi. Wayar Nafisa tana ta ruri, har sau biyu. Mama ta ce, “Ina wayarki ta shiga ne? ina jin kararta daga cikin bargon.” Ta ce, “Bar ta kawai kila Mufida ce A na uku Mama tasa hannu ta ciro wayar a kusa da filon da ta tada kai. Ta kalli wayar “Ai Shatiman ne ma ya ke kiran ki.” Ta tashi zaune da sauri ta amshi wayar, Mama tayi murmushi sannan ta fita. Nafisa ta daga. Ya ce, “Sweety ina ki ka shiga ina ta kira ba ki daga ba?” Muryarta can kasa tana kuma rawa irin ta marasa lafiya. Ta ce, “Yaya bani da lafiya ne.” Ya ce, “Subhanallah! Tun yaushe?” Ta soma shesshekar kuka. “Na kwana biyu.” Ya ce, “Shi ne ba ki fada min ba? haba Sweety! Ban so ba da ki ka yi haka, me ke damunki?” Ta ce, “Zazzabi ne.” Ya ce, “To kin je asibiti?”Ta ce, “Mama ta ce muje na ce a’a, ina shan magani a gida Ya ce, “Wa ya fada miki ana zama da ciwo? Ina Mama din. ki bata.” Ta yunkura ta tashi ta ce, “Bari in kai mata.” “Za ki iya tafiya amma ko?” Ta ce “Bari na kokarta.” Ya ce, “Ban ji dadi ba Sweety, na kira ki muyi hira sai kuma in ji kina ciwo?” Ta ce “Ga Mama din.” Ya gaida ta, sannan ya fara korafın ya ya za’ayi a biye ma Nafisa don ta ce ba za ta asibiti ba?Mama ta ce, “Kaga Nafisa rigima ce da ita, tun daga ranar da ta ji cewa su uku ne rana daya tasa ma kanta damuwa take wannan ciwon. Ya ce “Au! Dama wannan ne?” Ta ce, “Shi ne.” Ya ce “To shi ke nan Mama bata wayar muyi magana. Mama ta mika mata wayar, ta nufi daki tana “Hello!” Ya ce, “Sweety kin bani mamaki, kin san ya ki ke a zuciyata kuwa?” Dadi ya rufeta, ta kara shagwabewa. “Ni Yaya sai ina ganin don iyayenmu suka hada mu shi yasa ka ke share ni, kuma ka fi son su.” Ya ce, “Ni na fi son wadda tafi sona, ke ga shi ma har yanzun ban tashi daga Yaya a gurinki ba.” Ta ce, “To zan daina cewa, kuma Allah Yaya duk nafi sonka.” Ya ce, “Gashi kin sake fada bayan mun yi da ke sunan da zan kira ki da shi shi ne za ki kira ni. Cikin shagwaɓa ta ce “To zan ce.” Ya ce, “To ce ina ji.” Tayi ‘yar dariyar kissa. Ta ce “Sweety.” Ya ce, “Kai! Kin iya fada, dan kara in ji.” Ta sake fadi. Ya ce, “To na kashe Yaya din nan ko matata?” Ta cc, “Eh.” Ya ce, “Don Allah ki tashi daga ciwon nan kar ki zo ranar biki ba ki yi kyau ba. Ni fa kin san bana son mace ramammiya.Ta ce, “To ai ba ka kirana ne kuma baka zuwa.” Ya ce “Wannan ba shi ne yake nuna bana sonki ba, aikina yana da yawa, kullum fa Kaduna ni ke zuwa ina dawowa, ga aiki a gida, ga ginin ku da za ku zauna. Abubuwa da yawa.” “To amma za ka ke kirana?” “Duk lokacin da na dan samu sarari kamar haka zan kira ki, kuma zan zo yanzun dai kin warke?” Ya tambayeta cikin nuna kulawa. Ta ce, “Na warke.” Ya ce, “Yauwa sweety, duk lokacin da ki ka tuno ni kiji a ranki cewa ina tare da ke dari-bisa-dari.” Haka ya yi ta nuna mata sonsa har sai da ya tabbatar ta gamsu, ta kuma yarda yana yinta sosai. Tsawon awa daya kafin yayi sallama da ita. Washegari misalin karfe takwas ya dawo daga Masallaci ya shiga motarsa ya zauna don ya yi waya da Aliya. Daidai lokacin da kiran ya shigo wayarta an dace da zata duba kudinta, ta gama saka lambobi ta danna kenan kiran ya shigo, don haka ko ringing bata yi ba ya zama ta daga. Duk da taga sunan Shatimanta ne bata so haka ba, sai ka ce tana zaman jiranshi. Amma sai ta sa a kunne cikin kissa tayi sallama ya amsa, sai ta ce, “Laa! Wai kai dinne da gaske?” “Kina zaman jirana ne?” Ya tambayeta. “Ina yin mamaki ne a zuciyata ne naji cewa ina danna gurin amsa kira, nasa a kunne zan ji muryarka, lallai sona da kai wani abu ne na musamman.” Ya ce, “Nasan haka, ba ki bukatar sai kin tuna min shekaru uku kina jiran soyayya, ba abin mamaki ba ne don kin ji a jikinki cewa kirana zai shigo.” Ta ce, “To mu gaisa in ji lafiyarka.” Ya ce, “Ina cikin koshin lafiya, sai so da kaunarki da ke kara samun mazauni a zuciyata.” Ta lumshe ido. “Ni ko ina nan ina tunanin ya ya ka kare da ‘yar uwata, ko ta amince zata zauna, da mu din?” Ya ce, “Ai tunda ki ka bani wannan shawarar naje na gwada. Tayi sosai, na kara miki lambar yabo a cikin kaunarmu.” Ta ce, “Naji dadin haka.” Ya ce, “Ke kamar kya yin kishina, wasu kuma suna cewa kishi yana daga cikin so, haka ne?” Ta ce, “Ai kishin jahilci shi ke så wa ayi ta tashin hankali my love. Mu da muke Musulmi, gidan Manzon tsira (S.A.W) shi ne fitilarmu, kalar kishin matanshi zamu yi, kishin faranta maka tare da ba ka shawarwari nagari. Kuma don ina kishinka ba zan kauda kai ga abin da ka ke so ba, zan danne in so abin da ka ke so tsakani da Allah. Ina jin sauran matanka dani zamu zauna tamkar ‘yan’uwa.” Ya ji dadin kalamanta, har yace”Ke ta daban ce a mata my love, haka a zuciyata.” Taji dadi matuka. Suka ci gaba da hira har ta ke tambayar shi yana ganin auransu zai dauki tsawon wane lokaci? Ya ce, “Me yasa take tambaya?” Ta ce, “Ka san an ce me kwarmin ido da wuri yake soma kuka.” Ya ce, “Haka ne. Ni dai a tsarina sai na gama muku wurin zama, sannan in zo kan batun biki, don bana son a sa min rana mai tsawo. Komai-da-komai dai bana son ya wuce na da wata tara.” Ta ce, “Allah Ya nuna mana lokacin. To ammal kafin lokacin za a sa manya a ciki ko?” Ya ce, “Eh mana, da zarar sun gama bincike su za su zo ga manyanku, itama awa guda suka kwashe kafin suka yi sallama, Ita ko Amna yafi jin dadin yin waya da ita in yaje kwanciya, Don haka sai da ya gama komai na al’adarshi kafin ya kwanta sannan ya kira ta.Yau ya ci sa’a a kiran farko ta daga, bai san ma ta dagan ba sai da ya ji ‘yar muryarta ta ce, “Hello honey.” Ya ce “My honey kina lafiya?” Ta ce, “Kamar yanda ka ke.” Suka yi hirarsu irin ta so da kauna, bata kawo mishi batun sauran ‘yan matan ba, shima bai dauko mata ba. Tsawon awa daya yana yada manufarshi kafin suka yi bankwana. Bayan duk bincike sai a ka tura neman aure, babu inda aka samu matsala sai gidan su Amna, in da suka nuna a dan jira in sun gama bincike za su neme su. Bayan sati uku sannan suka ce manyan su dawo. Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne zai amso auran Amna, ya zama ko ina an ba shi. – Gininshi kuma ya kammala, amma fa asusun ya yi kat! Har sai da yayi aro gurin Babanshi. shi Gida dai ba abin da yake jira sai masu gidan. Gurin tsara sadaki aka samu bambanci. Baban. shi shi ne zai ba da Nafisa, ya murza gashin baki ya ce dubu dari ne sadakin ‘yarsa. Baban Nafisa mai amsar ma Shatima aure ya ce “Haba Yaya, a dai rangwanta.” Alhaji ya ce, “In suna so su bayar, ‘yarshi tana da ilimi. Haka Baban Nafisa yayi masa transfer ta dubu dari a nan take, abin gwanin sha’awa.Su ko gidan su Aliya hamsin suka saka mata, sai kudin gaisuwa ashirin, saba’in kenan. Amna kuwa dukiyar aure dari, sadaki kuma hamsin. Duk haka aka ba da, sannan aka tsaida lokacin aure wata sha biyu ishirin ga shi a lissafi sauran wata hudu kenan. A son Shatima kar a kai wannan lokacin amma an duba lokacin da za’a samu hutu mai tsawo kowane bangare suna cikin kasa kuma suna cikin jihar. Kamar yanda ya tsara a wata daya yake kai musu ziyara, ran Juma’a yaje gurin Nafisa. Sati yaje gurin Aliya Lahadi kuma yaje gurin Amna. Haka duk karshen sati yake tura musu kati na dubu dai-dai. Haka kuma yake kiransu sau biyu a kwana goma, Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne ya biya dukkannin sadakin. Anty Saude kanwar Baban Shatima ita ce ta dauki nauyin siyan takalman da za’a zuba musu duka. Don haka ya amso lambobin takalmansu ya kai mata, dama oder take yi. Aliya ta kan tura masa da sakon Juma’a bata mantawa, Nafisa na tura masa da sakon barka da safiya lokaci zuwa lokaci_____ *🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 8 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko ku turo katin Mtn ta wannan number 09068032427* *08146017245 hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar* *Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀 4 *Kaza mekwai* 🍀🍀 5 *Zabo me zuma*🍀🍀 6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀 7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀 8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀 9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja* 10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn* 11 *Maganin nono. Sahihi* 12 *Maganin hips and bobbs* 13 *hodar. Ni I'ma koramar mata* 14 *nakasan Mara babban sirri* 15 *kafi jijjibi* 16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani* 17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata* 18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Maman haidar Bata tsaya anan ba* *Tana Saida hijabai dayadikan su akan darashin sari yadika dila dilahijaban. Yan gayu sannan* *takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeni awannan number* 08146017245 🍀🍀🍀🍀🍀 Mun tsaya Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne ya biya dukkannin sadakin. Anty Saude kanwar Baban Shatima ita ce ta dauki nauyin siyan takalman da za’a zuba musu duka. Don haka ya amso lambobin takalmansu ya kai mata, dama oder take yi. Aliya ta kan tura masa da sakon Juma’a bata mantawa, Nafisa na tura masa da sakon barka da safiya lokaci zuwa lokaci. Amna kuwa ba ta mantawa da tura masa sakon murna da shiga sabon wata a duk lokacin da aka shiga. Tsarin kowaccensu ya birge shi Shatima yana da kaifin basira, da hikimar zama da jama’a, don haka yake ganin kamar cin tuwo ne ko shan ruwa zama cikin mata hudu ma bare uku. Shagali ake shiryawa a kowane bangare musamman gidan su Amna wadda ta kasance ita ce mace ta farko da za’a soma aurar wa a gurin Mahaifinta. Itama Nafisa ana ta shiri don ita ce ‘yar fari gurin Babanta, ga kuma dangi kowa na cin buri, Aliya kuwa suma suna shiri daidai karfinsu, bata shagali suke yi ba su, suna ta kayan daki ne a samu a yi mata gado seti biyu, ga kuma gara tunda sun san yana da hali da kyar in ba daki biyu za’a kai ta ba. Sannan gefen kayan gyara jikin Amare ko ina suna ta yin daidai karfinsu. Alhaji Isa Baban Shatima cewa ya yi ba zai ba Shatima komai ba ‘yarshi zai wa kayan Gado da kayan gara. Ya fadi haka ne lokacin da Shatima ya samu Babanshi da Hajiyar su a daki Baban nashi yana tambayar wace gudunmawa zai ba shi? Shatima ya ce, “Alhaji nima a dan duba min, Allah asusuna babu kudin kirki, gashi ko akwatuna ban siya ba.” Hajiya ta ce, “Amma jiya ka ce min Alhaji Murtala ya turo maka da dubu dari biyu ko? Yanzun ma nike fadawa Babanku.” Shatima ya ce, “To duk kowace ta min magana ashobe da za su fitar, Amna ce kawai bata min ba, itama nasan zata yi, shi ne zan raba musu wannan dari biyun.” Alhaji ya ce, “Ai kai dan dangi ne za ka samu gudunmawa, Murtala da duk cikin ‘ya’yan Mahaifinmu yafi kowa mako, amma shi ya fara baka gudunmawa har dari biyu.” Hajiya ta ce, “Ba dole kowa ya motsa ba tunda Babansu zai yi aure har mata uku rana daya. Shatima ya ce, “Alhaji ka min daí wani abu koda canza min mota ne.” Ya ce, “Au! Ka ma tuna min, Alhaji Nadabo ya ce kaje gidan motocinsa ka zabi wadda ka ke so.”Murna ta cika Shatima. Ya ce, “Amma gaskiya Baba Alhaji Nadabo ya yi min komai.” Hajiya ta ce, “Kuma fa ya ce duk ruwan da za a sha a biki na gora aje kamfaninsa na ruwa a debo. Allah ya saka mishi da alkhairi.” Suka ce “Ameen.”Shatima ya ce, “Allah Yasa mu ma abotarmu da Munir tayi kamar taku, shima yana da irin halin Babanshi.” Ya cc, “To ke Hajiya har yau ba ki fadi naki ba.” Ta ce, “Kai uban masu kudi da gata ka ke, nan da wata mai kamawa asusunka sai yayi kamar zai fashe. Don haka ni yanzun ba zan yi alkawarin komai ba sai nan gaba tukunna.” Ya mike “Shi kenan, bari in je in shirya yau Kano zani gurin Amna.” Hajiya ta ce, “Ka fa yi ma Badi’atu alkawarin zuwa da ita tun shekaran jiya take min zancen.” Ya ce “To ta shirya har da Munnir zamu je ni na ma manta da mun yi haka da ita.” Karfe biyu sun isa birnin Kano sun samu tarba sosai musamman Badi’atu wadda tayi kyau cikin riga da wando da mayafinsu ‘yan Dubai. Amna tayi murna da zuwan Badi’atu, ta hada ta da kanwarta Sumy don za su yi sa’annin juna. Tunda suka kebe ta shagulgulan da za su shirya. soma mishi zancen Ta ce “Mu fa tun ranar Laraba zamu fara biki.” Ta tashi ta dauko mishi katin wanda aka tsara shi da ruwan zaiba, jikinshi kuma ruwan jibi. Karamine kwarai katin sai shegen kyau kamar ka lika a jiki kayi ado. Ya karanta a ranshi ya ce tab! In ko shi zai ba da kudin shagalin nan za a samu matsala, don ba shi da su, amma dai bari ya jira ya ji abin da zata ce. Ta dube shi. “Katin yayi kyau kuwa?” Ya ce, “Sosai ma.” Ta ce, “Kamar guda nawa zan baka?” Ya ce “Tun da yanzu saura kusan wata biyu har da kwanaki, ki bari sai abin ya kara matsowa, kar in zuba a wani guri in manta.Kin san kaina kullum kara daukan hayaki yake yi, mata uku fa!” Ta taba baki, “Ni ina mantawa da cewa bani daya ba ce, ko su Mom dina ba su fada ma kowa ba sune kawai suka sani. Zan ajiye maka amma za ka zo min dai duka ko?” Ya ce Zan dai zo amma ba duka ba, kuma mu da abokanmu zamu shirya Dinner wadda za ku zo ku duka amma sai an kai ku.” Ta ce, “In lokacin mutane na sun watse zan je mana, amma in suna nan sai dai kayi hakuri don ba su sani ba.” To babu matsala, Allah Ya kai mu.” Munnir ma da ya ga katin sai ya ce, “Ni dai bari in rike wannan yayi min kyau.”Sumayya da suka je dakin su da Badi’atu, ta nuna mata ashobensu kala shida. Duk masu tsada ne kowane shagali da kalar da za a sa. Badi’atu ta ce, “Lallai ku kam har kun fitar, mu dai sai cikin watan nan da zamu shiga sannan za a fitar, Kanwar Babanmu ce zata fitar da su.” Sumayya ta ce “Mutum yaushe har ma an kusan gama bada wa. Yayar Babanmu tayo odar ba saidawa ake yi ba, har kawayenta duk an basu ne tare da katin biki.” Badi’atu ta ce “Tab! Duk wannan kuma za a ba mutum daya?” Sumayya ta ce, “Eh mana. Ita kuwa Amarya kin ga kayan da zata sa da biki? Akwati uku ne aka je Dubai aka dinko su, na biki ne kawai har ma da irin rigar aure dinnan zata sa.Tare aka siyo da kayan da shima ango zai sa a ranar da takalmi da komai. Badi’atu ta saki baki, har ta soma tunani tsarata kawai Summy ke yi Har suka soma shirin tafiya Shatima bai ji tayi masa zancen kudin komai ba, kamar yanda Aliya da Nafisa suka mishi da ya ziyarce su a ranakun Juma’a da Asabar. Kowace ta tambayi kudin ashobe, da kuma sauran shagulgulan tata zata yi da kawayenta Ya kalli Amna, “Ke ba za ki yi ashobe ba ne?”Ta lumishe ido, “Ai tuni sun cire abinsu, ni ai ba zan sa ba, sun kusan gama raba shi ma.” Ya ce, “To yanzun me ki ke bukata daga gare ni don shagali ko wani abu? Gara in sani tunda wuri kin san abin da yawa.” Ta ce “Ban gane ba.” Ya ce, “Kudin siyan ashobe da shagalin da zaku yi.” Ta girgiza kai tare da tabe baki. “Babu fa. Ni ban sani ba ko ana bada wani kudi na shagali ba.” Ya ce, “Shi kenan, in dai da wani abu sai muyi magana ko?” ta ce “To, babu matsala.” Ta ce, “Bari in je in kira Badi’atu din ko.” Ta samu Mom dinsu ta hada ma Badi’atu sha tara ta arziki, irin su kayan kwalliya, da na ci, kayan zaki, sai ko ashoben su kala shidan nan da na kai, sannan Amna ta ba da turare a kai ma Hajiya Hajiya kuwa tayi murma har taji cewa Amna ta kwanta mata a zuciya, a fili ta ce, “Harkar arziki da me arziki ake yin shi.” Badi’atu kuwa sai labari a ke baiwa Hajiya na abubuwan da ta gano, da kuma wanda taji. Hajiya ta ce, “Ai familyn Baita Nasiri sun fi da haka, masu kudi ne na wuce tunani.”Kamar yanda iyayen Shatima suka ce, hakan ce ta kasance. Ana shiga watan sha daya, iyayensa maza da mata wadanda suke uba daya da wadanda suke da dangantaka ta dan nesa. Sai kira suke Shatima ya turo da lambarshi ta account. Bayan haka suna kaiwa Kaka tata. Shatima ranar yaje gurin Kaka yana alfahari da sunan da suka sa masa. Ya ce “Kaka ‘ya’yanki sun yi mini komai, sun cika asusuna da kudi gaskiya na yarda da kalmar Hajiya ni ne dan masu kudi, kuma uban masu kudi.” Kaka tayi dariya, “Tun daga haihuwarka goshinka kazo, uwarka bata baka labari ba? Ran da aka haife ka Kakanka ya samu Sarauta, kuma ranar ne Sarkin Zazzau na wancan lokacin ya bai wa Kakan naka kujerun Makka har uku. Dama shi da matarshi ta fari sun je, don hakan sai ya bar mana muka je mu uku.” Shatima ya yi dariya, “Ki ce da arzikina aka haife ni?” Ta ce, “Sha Allahu…” wayarshi tayi kira, da ya duba Munnir ne. Ya ce, “Aboki ya ya ne?” Ya ce, “Na zo gida ba ka nan, gani tare da Telan da muka yi magana da kai.” Ya ce, “To ku jira ni gani nan gidan Kaka nazo yanzu zan fito.”Ta ce, “In kuma kuna sauri ka shiga ciki, Badi’atu ta dauko maka kaya a cikin Ghana most go a kusa da durowata sai mu sake haduwa.” Ya ce, “To, haka ma za a yi. Sai mun yi waya kenan.” Suna sallama ya mike, “Kaka bari in je.” Ta ce, “Kayi baki ne?” Ya ce, “Tela ne wani da aka ce ya iya dinki ga rikon alkawari, a Abuja yake aiki.” Ta ce, “To ka gaida mutanan gidan.” Daidai kwanar gidan su Salma Shatima ya rage tafiya, yayi fakin gefe sakamakon ganin gidan su yarinyar nan in da ta nuna mishi. Yaga mutane sun taru, wasu na alwala wasu na tsaye. Da ya kai duba kofar shiga gidan sai ya hangi wasu suna kici-kicin shiga da Makara. Ya fito ya jingina da motarsa, sannan ya harde hannuwansa a kirji, jikinshi a mace. So yake ya sani ko wane ne ya rasu a gidan. Duk da zuciyar shi ta raya masa cewa Baban ne ya rasu tunda shi ne ba shi da lafiya, amma wata zuciyar ta ce masa ba dole ba ne ya zama sai shi, tunda dukkan mai rai maniaci ne, haka kuma cuta ba mutuwa ba ce. Kusan minti talatin sannan aka fito da gawar, shima ya shiga sahun sallah. Da aka idar ya koma jikin motar ana ta wucewa ya hango mata sun fito Kofar gidan suna kuka, ga wata can ana ta rike ta tamkar zata bi gawar. Ya gano Salma ce, don haka ya tsallaka, bai damu da dinbin matan da ke gurin ba, yaje kusa da ita da kuma wadanda ke rike da ita. Ya ce, “Kanwata!” Ta dago ido ta dube shi. Ya ce, “Wane ne ya rasu?” Ta ce, “Babanmu ne.” Ta sake rushewa da sabon kuka. Ya ce, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Jikin ne ya tashi?” Ta ce, “Ai dama bai samu sauki ba muka dawo gida, saboda bamu da kudin da za a ci gaba da yi mishi gashi, da kuma siyan magani. Ya ce, “Me yasa ba ki neme ni ba?” Ta ce, “To ni ban san in da zan same ka ba, ko da ma na ce zan neme ka sannan naga kayi mana taimako daidai gwargwado. Ya ce, “Ina Mamanku fa?” Ta nuna cikin gidan, “Tana ciki.” Ya ce, “Muje in gaishe ta.” Ya dubi matan, “Ku sake ta.” Ya ce, “Kiyi hakuri kin ji? Yaya sunanki?” Ta ce, “Ummu Salma.” Ya ce, “Kiyi masa addu’a, ita yafi bukata ba kuka ba. Share hawayen ki Ummu Salma kin ji?” Tasa bayan hannunta ta share, sannan ya ce “Muje.Mutanen cikin dakin suka ragu, aka shimfida mishi wata tsohuwar dardumar sallah ya zauna. Ya bi dakin da kallo. Wani dan tsohon gado ne na karfe da ‘yar feleliyar katifa, sai gidan sauro da ke daure daga saman gadon. Tsakar dakin duk simintin ya fashe. Gefe kuma ga tebur mai dauke da kwanuka, da sauran tarkace. Salma ta katse shi da cewa, “Alhaji ga Innarmu din nan.” Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya kai duba gurin Salma, sannan ya kalli wadda ta ce Innarsu. Daga gani ba wai tsohuwa ba ce, amma wahala tasa ta zama tsohuwa. Ya ce, “Ina yini? Ya ya hakuri?” suka amsa ya yi addu’a ga mamacin ya kuma ba Innar tasu magana sosai. Salma ta ce, “Inna wannan shi ne Alhajin nan da ya taimake mu.” Nan suka yi godiya. Ya mike ya fito tære da ce ma Salma “Zo mu je.” Ta taho haka. Yace “Ki saka hijabinki.” Duk da tsufan da kayan jikinta ke da su, da mataccen hijabin da ke jikinta bai ji kyamar bude mata gidan gaba ya ce ta shiga ba. Ita ma bata ji tsoron shiga ba, don sai take kallon shi kamar wani daga danginsu. Ya harba motar kan titi, sannan ya dube ta.._____ *🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 9 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻👆🏻ko katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* Mun tsaya suka amsa ya yi addu’a ga mamacin ya kuma ba Innar tasu magana sosai. Salma ta ce, “Inna wannan shi ne Alhajin nan da ya taimake mu.” Nan suka yi godiya. Ya mike ya fito tære da ce ma Salma “Zo mu je.” Ta taho haka. Yace “Ki saka hijabinki.” Duk da tsufan da kayan jikinta ke da su, da mataccen hijabin da ke jikinta bai ji kyamar bude mata gidan gaba ya ce ta shiga ba. Ita ma bata ji tsoron shiga ba, don sai take kallon shi kamar wani daga danginsu. Ya harba motar kan titi, sannan ya dube ta. “Kayan abinci zamu siyo, nasan su aka fi bukata yanzun ko?” Ta dube shi idanunta suka kawo ruwa. Ya ce “A’a kar ki min haka. Ba na ce ki daina kuka ba?” Ta runtse ido sannan ta sauke ajiyar zuciya. Ya kai hannu gefenshi ya dauko ruwan gora ya mika mata, “Amsa ki sha.” Ta amsa ta bude murfin roba ruwan ta daga tana sha, bata san tana jin kishi ba sai lokacin. Tas! Ta shanye ta sauke goran tana rufe murfin. Ya dube ta “Kiyi hakuri kin ji?” Ta ce, “Na gode Alhaji.” Ya ce, “Sunana Muhammad Ja’afar amma an fi kirana Shatima. Cikin uku sai ki ke kirana da daya a ciki, na kuma tambaye ki an fi bukatar abinci ko?” Ta ce, “Eh.” Wani shagon kayan abinci suka tsaya, ya sai buhun shinkafa, Gero, da Taliya, da su mai da Magi. Ya biya suka koma. Lokacin an dawo daga Makabarta. Yaya Auwal ne suka kama suka shiga da kayan suna ta godiya. Ya ciro dubu biyar ya ba Salma ya ce, “Ki ba Inna wannan saboda cefane. In na dawo aiki gobe zan zo ko da dare ne. Ta ce, “To Alhaji mun gode.” Ya ce, “Bana ce bana son alhj ba.” Ta ce, “To in ce maka ya ya?”Yanda tayi maganar cikin muryar tausayi duk sai ya ji tausayinta ya karu a zuciyarshi. Ya ce, “Ki ce min haka to. Kada ki manta na ce, addu’a za ki masa ba kuka ba.” Ta ce, “To.” Ya shiga mota ya wuce. Salma tabi motar da kallo har ya bace. Sannan ta ce, “Allah Ya biya ka da gidan Aljanna.” Ta shiga gidan ta samu har an soma wanke tukunya za a dora girki. Ta kira Yaya Hadiza ta bata kudin ta kuma fada mata yanda suka yi. Tunda ya gama al’adun shi da ya saba yi kafin ya kwanta, bacci yake ji sosai. Amma yana kwanciya sai ya ji baccin ya kama gabanshi. Tunanin gidan su yarinyar nan Ummu Salma ya tuna yanda gidan yake a rube, kowane lokaci gidan zai iya fadowa a kansu. Yarinyar nan ya tabbata bata kai sa ar Badi’atu kanwarsa ba, kuma bai ga alamun tana zuwa Makaranta ba.. Sannan kai gaskıya yana bukatar taimakawa yarinyar nan sosai. Ya rumtse ido a cikin zuciyarshi, ya ce ya dauki alkawari tsakaninshi da Mahaliccinshi zai taimaki Umma Salma Zai inganta rayuwarta ta hanyar bata ilimi. domin daga ganinta. Ya tabbatar tana bukatar ilimi, tana son karatu. Gaskiya gobe zai mata tambayoyi. sai dai a rin wannan lokacin da yake tsakiyar hidimar auransa ba shi da halin yi musu wani gyara domin aiki ne ba karami ba. Haka lamarin yarinyar yayi ta damun sa ya kasa bacci har kusan Asubahi.. Washegari ya dawo aiki ya yi wanka ya saka farar jallabiya kar!, takalmi ma silifa yasa mai dan tudu ya kwashi wayoyinshi da makullin mota ya nufi kasa Da motar ya nufi Masallaci, da suka idar da Magriba ya nufi gidan su Munnir. Bayan sun gaisa ya ce, ya zo su shiga su ci abinci. Shatima ya ce, “Bana jin yunwa. Muje ka raka ni muyi gaisuwa.” Munnir ya ce, “Waye ya rasu?” Shatima ya ce, “Baban yarinyar nan da suke kwance a asibiti.” Ya kwatanta mishi. Munnir ya gane ya ce, “Allah Sarki! To bari in fada ma Fatima.” Ya shiga ya ce da matarshi sun fita sannan ya zo suka wuce Sai da suka yi Isha’i sannan suka karasa gidan. Da suka yi fakin suka tsallaka gurin ‘yan zaman makoki suka gaisa. Yaya Auwal ya tashi ya zo yana sake fadin “Sannun ku da zuwa Alhaji. Shatima ya ce, “Na kawo abokina zai yi musu gaisuwa. Shi ne ya yi musu jagora zuwa dakin Innarsu. Daga waje suka tsugunna suka gaisar da ‘yan ciki. Innar ta leko bakin kofa. Yaya Hadiza ta kwala ma Salma kira. Idar da sallarta kenan a dakin Baito, ta fito ko takalmi babu, ta ce “Yaya Hadiza gani.” Ta ce, “Dama su Alhaji ne suka zo.” Tayi saurin karasawa kusa da su, ta tsugunna. “Yaya sannun ku da zuwa.” Ya dube ta. “Salma ya karin hakuri?” “Da godiya.” Ta gaida Munnir shima yayi mata gaisuwa. Suka mike suka soma tafiya, Inna tana musu godiya. Ya waiwayo yaga Salma a tsaye, dama gidan da duhu, kila ma ba a taba saka wutar lantarki a gidan ba. Da wayar Munnir suka haska don su ga hanya. Shatima ya ce “Zo mana Salma. Munnir ya bude motar ya shiga, Shatima ya jingina da motar. Tazo ta tsugunna a gabanshi cikin ladabi. Ta ce. “Gani Yaya.” Ya ce, “Tashi Salma.” Ta mike. Ya ce, “Dama zan tambaye ki ne kina zuwa Makaranta? Ta ce. “Eh, ina zuwa Islamiyya.” Ya ce. “Boko fa?” Ta ce, “Tun da na gama J.S.3 ban samu damar wucewa ba.” “Saboda me?” Ya tambaye ta.”Saboda lokacin Babanmu ya soma rashin lafiya, ba ya fita neman abinci, ni ce ni ke nemo mana abin da zamu ci. In yi talla ko in soya awara a waje.” Ya ce, “Ba ku da wani Yayan? Wancan ba wanku ba ne?” Ta ce, “Yaya Auwal shi ne ke aikin gidan biredi ana biyanshi dubu tara a wata. Lokacin kudin maganin Baba yake biya, ba sa isa ma.” Shatima ya ce, “Yanzun ke ce ki ke ciyar da ku? Shekarunki nawa ne ma?” Ta ce, “Shekaruna goma sha shida, idan wannan Azumin yazo.” Ya ce, “Sha biyar da watanni.” Ta ce, “Eh.” Ya lumshe ido cikin tsananin tausayin ta. Can ya ce, “Salma!” Ta ce, “Na’am!” Ya ce, “Fada min taimakon da ki ke son in yi miki?” Ta ce, “Kamar ya ya? Ai kayi mana duk wani taimako, abinci muka fi bukata kuma ka ba mu.” Ya ce, “Ban da wancan, ke kanki ni ke son in taimake ki, taimakon da ba za ki manta ba, ina son ki nutsu zan bar ki zuwa ranar sadakar uku, yaushe ne?” Ta ce, “Juma’a.” Ya ce, “In nazo sai ki fada min, kiyi shawara da Innarku da Yayanki, ki dubi mene ne burinki sai in taimake ki a kai, kin ji ko?”Ta ce, “To Yaya, Allah Ya saka da alkairi, Ya baka duk abin da ka ke so duniya da lahira.” Ya ce, “Babu komai, ki koma gida.” Yana shiga mota Munnir ya ce “Gaskiya mutanan nan suna cikin tsananin bukata, dubi irin gidan da ‘yan Adam ke rayuwa, kuma suna da makota masu hali sun sani amma ba za su iya taimakonsu ba. Shatima ya ce, “Ai ba ka sani ba, su fa masu hali in za su yi taimakon nan sai dai su taimaki masu karfi ‘yan uwansu.” Haka suke tattaunawa har suka zo layin su Kaka. Ya ce, “Yauwa, bari mu shiga in fada ma su Kaka a rinka kawo abin sadaka gidan mutuwar nan. Munnir ya ce, “Haka ne. Allah Ya taimake mu.” shi kanshi Shatima yana mamakin irin yanda lamarin yarinyar nan ya hana shi sukuni. Har yaje yake ba wa Hajiyar shi labarin yarinyar da iyayenta. Hajiya ta tausaya, ta ce “Akwai masara a store, ko za ka sa a kai musu buhu biyu?” Ya ji dadin haka sosai. Ya ce “Gobe ne zan je, in na dawo aiki. Tunda gobe rabin rana ce zan dawo da wuri. Wani abu da ya yi ta bai wa Shatima mamaki yanda har sakon Aliya da ya shigo na Juma’ar yau bai sami damar budewa ba, kowane lokaci zuciyarshi tana can gurin tunanin yarinya Salma. Abin da yafi tsaya mishi a rai, ‘yar shekaru sha biyar ke rike da gida. Salma da ke kwance a tsakar dakin Baito kan yar tabarma, ta rufe kafafunta da hijabinta, nan take kwana kasancewar Baito bata da miji. Juyi kawai take yi tana tunanin maganganun Shatima, dole tayi nazari sosai a kan kanta kafin ta tunkari su Yaya Hadiza, burinta da yake magana a kai shi ne take tufka da warwara a kai. Ta sani tun da ta taso fatanta Allah Ya bata ilimi mai albarka, ta zama ‘yar Jarida ma aikaciya a gidan TV ko Radiyo. Tun lokacin da Mahaifinta ya farka. Duk da cewa makarantar Gwamnati take kullum sai ya bata Naira talatin zuwa Naira talatin dawowa, in da kudi har Naira dari yana bata don ta samu dan na kashi. Mamansu tana aikin gida, a gidan wasu masu hali, itama dole aikin ya tsaya saboda jinya. Tun daga lokacin Mahaifinta ya soma zancen aurar da ita, kullum sai ya fadawa Innarsu cewa shi ya tabbata ciwon shi ba na tashi ba ne amma yanason don Allah su aurar da Salma don ta daina wannan wahalar ta talla, za su ci abinci daga abin da Yaya Auwal yake samu. Tunda in an aurar da ita sai Umar da Sani kannenta su ko maza ne. Ko ranar da zai mutu sai da ya yi zancen aurar da ita, abin da ya tsaya mata a rai har da kuka ya yi lokacin da ya ke maganar. Tana wannan tunanin ne sakamakon zancen da Shatiman ya zo mata da shi. Dole ta aje burinta na karatu, saboda in ya dauki nauyin biya mata kudin Makaranta da takardu da komai, kudin mota na yau da kullum zata dora masa ne? Ita dai kawai zata ce abu dayan da ya ce ta zaba ta zabi ya aurar da ita ga Basiru saurayin da ya nuna kaunarsa gareta, ya yi mata kayan daki tunda shi ne burin mahaifinta. Washegari da safe kula guda katuwa aka kawo cike da waina daga gidan su Kaka. Salma tana jin mutane na ta yabon Hajiya Kakar su Shatima, suka ce duk in da aka yi rasuwa ko basu sanka ba sai sun kai. Salma ta ce ma Yaya Hadiza “Ai Hajiyar Kakar wannan Alhaji ce da ya ke taimakonmu, kila ma shine ya sa a kawo.” Bayan yan addu’a sun watse ta ce Amira ‘yar gidan Yaya Hadiza ta leka ta kira Yaya Auwal. Inna ta ce, “Mene ne?” Salma ta ce, “Alhaji ya bani wani zabi ne, shi ne ni ke so muyi shawara da ku.” Bayan sun hadu, Salma ta fada musu yanda suka yi da Shatima. Yaya Auwal ya cc, “Mc zai hana ki ce ya sai mana gida?” Ta ce. “Burina ya ce wai in zaɓi abu daya, ba wai namu ba. Kowa yasan bani da burin da ya wuce in yi karatu in zama ‘yar jarida. Sannan kuma burin Baba shi ne ayi min aure To ina son ku duba ku gani a cikin nan wanne zan zaba?” Yaya Hadiza da Yaya Auwal suka ce, “Ki zabi karatun.” Inna ta ce, “A’a in ba ku manta ba, zancen aurar da ita yana daya daga cikin kalaman Malam na karshe. A nawa tunanin tunda ga Basiru yana sonta, kuma yana da dan abin yin sa,sai a ce ya fito. Shi kuma sai ya taimaka ya yi mata kayan aure. Hadiza tace, “Haka ne, to ayi hakan. Yaya Auwal ne dai shi bai gamsu ba, amma ganin ita Salma ta yarda sai ya mika wuya shima.Salma tasan ita bata son wani Basiru, bata ma san kowa don ba hakan a gabanta. Tana bacci taji ana cewa ga buhun nan masara ana shigowa da su. Duk da ba ta fito ba tasan shakka babu Shatima ne. Yaya Hadiza ta leko dakin Baito. “Salma ki zo ga Alhaji ya aiko da buhun Masara guda biyu.” Ta fito ta samu su Inna suna tsaye bakin kofa suna godiya. Hadiza ta ce “Kai wannan bawan Allah Yana taimakonmu, Allah dai ya saka mishi da alkairi.” Salma ta ce “Ya tafi ne?” Yaya Auwal ya ce, “Yana waje cikin motarsa.” Ta saka takalmi ta fita. Gaban motar ta gani a bude, daga gani ta samu matsala ne, shi kuma yana tsaye yana waya. Ta tsaya daga inda take, tana iya sauraron abin da yake fadi. Ta fahimci da Bakanike (mai gyara) ya ke magana. Don taji yana cewa “Zafi take yi, kazo ka same ni a nan Tudun Wada…” Ya ci gaba da yi masa kwatance. Da ya gama ya tsallako suka tsaya a inuwa inda “yan zaman makoki suka watse. Ya ce. “Salma! Tace. “Na’am! Yaya.”_____ *🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 10 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son a tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* ```🧕🏻🧕🏻Ina kuke kasaitattun mata, Hajiyata kada ki bari ki zama bora agidan auren ki yi kokari ki tsuma kanki da ingantattun magunguna na gyaran jiki 07032895551🍉🍉🥥🥥``` ```Mun zo maku da ingantattun magunguna masu kyau da inganci akwai TABAJE mai kyau gangariya 5litres 5k 07032895551``` ```Muna da hadin Abulbulo, akwai Dan saudiya Hajiyata kada ki bari wannan hadi ya wuceki,dagajin sunan ABULBULO kinsan akwai aiki 4k ne kudin shi🙈🙈``` ```Akwai sa Buzu Kuwwa,muna da kafi Budurwa uku sai angwada akansan na kwarai``` ```🗣️🗣️🗣️Ina matan da mazajen su kebin matan banza to matso kusa Hajiyata Muna hadi na musamman duk macen da tayi amfani dashi mijin ta be karajin dadin wata mace, wannan hadi in kinsan kinada kishiya don Allah kada ki siyeshi 8k ne kudin shi🥥🍉``` ```Akwai dahuwar kaza gangariya sai kin gwada Hajiyata zaki bani labari🙈🙈 akwai Dan dakarawa ya matseki tsam ya kuma saukar maki da ni'ima, akwai kafi sugar, kwallin mata dan matsi daya tamkar da dubu kenan🍉🥥``` ```Akwai hadin Zama daram,munada miski mekyau original, akwai dahuwar kaza ta amare da uwar gida🐓🐓🐓 Akwai Sabulun infection ya matseki ya yi maki maganin infection,yasa wajen yayi sulbi Hajiyata``` ```Muna garin katsina Muna aikawa ko ina a fadin Nigeria har ma da makotanmu Niger 07032895551``` ```Sai angwada ake sanin na kwarai, amma don Allah idan baki shirya siya ba kada kiman magana 07032895551 muna bada sari game bukata🙏🏻🙏🏻``` Mun tsaya Salma ta ce “Ya tafi ne?” Yaya Auwal ya ce, “Yana waje cikin motarsa.” Ta saka takalmi ta fita. Gaban motar ta gani a bude, daga gani ta samu matsala ne, shi kuma yana tsaye yana waya. Ta tsaya daga inda take, tana iya sauraron abin da yake fadi. Ta fahimci da Bakanike (mai gyara) ya ke magana. Don taji yana cewa “Zafi take yi, kazo ka same ni a nan Tudun Wada…” Ya ci gaba da yi masa kwatance. Da ya gama ya tsallako suka tsaya a inuwa inda “yan zaman makoki suka watse. Ya ce. “Salma! Tace. “Na’am! Yaya.” Ta tsugunna ta gaida shi, ya amsa tare da fadin “Mike.” Ta mike tsaye tana wasa da gefen hijabinta. “Ya karin hakuri?” Ta ce “Alhamdulillah.” Ya ce, “Kin daina kuka ko?” Ta ce, “Ai tun da ka hana ni ban kara ba.” “Yauwa, ki dangana. Yanzu wace shawara ki ka yanke, ko in ee me ki ke so in yi miki?” Ta kalle shi tayi dan guntun murmushi, sannan ta sunkuyar da kai. Ya ce, “Ki fada ni na baki zaɓi kuma na dauki alkawarin ko me ki ke so zan miki, ko nawa zan kashe. Gidanku kuma naso ace zan gyara muku amma ina cikin shirin bikina.” Tayi ‘yar dariya “Aure zaka yi?” Ya ce, “Aure zan yi, za ki zo min ko?” Ta ce “Zan zo.’ Daidai lokacin Bakaniken ya sauka a Mashin. Ya ce “Ina zuwa, bari muyi magana da Bakanike.” Sun kusa minti takwas sannan ya bar shi yana duba motar ya dawo gurinta. Salma ta rasa yanda zata yi masa maganar. Ya ce, “To karatu ki ke so ne ki ka kasa fada?” Ta ce, “Karatu naso Yaya, amma dai akwai burin mahaifina a kaina, kuma har a ranar da zai mutu sai da ya maimaita yana kuka…Hawaye suka soma zubo mata, tayi kokarin Isayar da kukan sannan ta ci gaba da magana cikin raunanniyar murya mai cike da tausayi. “Naso in zama ‘yar Jarida a rayuwata, amma dole in shafe babin haka in yi aure kamar yanda Mahaifina ya bar wasiyya..” “Aure!?” Shatima ya katse ta cikin mamaki. Ta kalle shi fuskarta sharkaf da hawayè. “Aure Yaya.” “To dama kina da saurayi kenan ko?” Ya tambaye ta. “Akwai wani Basiru da yake sona.” Kanshi ya sake kullewa, ‘yar yarinyar nan tana soyayya! Ya kalle ta. “Tun yaushe ku ka fara soyayya da shi?” Ta ce. “Zai kai wata biyu dai yana zuwa gurina, tun ina zuwa Makaranta ya taba cewa yana sona na ce mishi karatu zan yi. Da na daina zuwa kuma sai ya dawo lokacin Baba ya soma zancen aurar dani sai na hakura na saurare shi. Ya ce, “To ke kina sonshi ne?” Ta ce, “Ni ban san wani so ba.” Tayi ‘yar dariya tare da rufe fuska. Ya ce, “Ban gane ba?” Ta ce, “Ni dai kawai in aure shi amma Yaya wallahi ban san so ba.” Ya ce “Misali ba ki tunanin shi? Ba ki son ganinshi da makamantansu?” Ta ce, “Yaya ni fa in ya zo yazo, in bai zo ba har mantawa ni ke Allah yayi ruwan tsirar shi.” Shatima bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba, domin yanda ta fadi kalmar ta ba shi dariya sosai. Ya ce, “Har akwai wani ruwan tsirar mutum? Lallai Salma kin iya magana. To kin ga ba son wannan Basirun ki ke yi ba.” Ta ce, “To ko bana son shi Yaya zan aure shi haka don in cika umarnin Mahaifina, kai sai ka yi min kayan daki ka aurar da ni kawai.”. Yayi shiru yana kallonta. Itama ta kalle shi, sai taji kunya. Ta saka tafin hannunta ta rufe fuskarta. Ya ce, “Mamakin ki ni ke yi Salma, yanzu in aka yi miki aure kin san ya za ki zauna a gidan mijin?” Ta kama gefen hijabinta ta rufe fuska, “Zan koya Yaya.” Ya ce, “Karatunki ya zama tarihi kenan yanzun?” Ta ce, “Ya zan yi, dole in hakura.” “Sana’ar me shi saurayin naki yake yi?” “Gyaran famfo, da kuma Achaba.”Ya sake kallonta cikin tausayi. “In kin samu wanda zai ba ki dama kiyi karatu, kuma ya aure ki za ki bar Basiru?” Ta ce, “Sosai ma. Ban san adadin farin cikin da zan yi ba.” Ta runtse ido “Allah Ka tabbatar min da haka.” Ta manta a gabanshi take, sai taji an ce “Ameen.” Ta bude ido da sauri, tasa hijabi ta rufe fuska. Ya ce, “Kina amsa addu’a ba ki san Yaya mijin yake ba?” Ta ce, “Ai ko wane iri ne in dai Musulmi ne shi.” Ya ce, “To zan je in yi shawara da shi in zai yiwu zamu zo da shi.” Bata ma lura da wani bakanike ya gama gyara har ya dana motar ya dawo ba, sai da taga ya tsallako ya ba shi makulli. Ya ce, “To zan tafi Salma, sai dai na zo.” Ta ce, “To me zan ce musu a gidan?” Ya ce, “Ki ce zan canza miki wani miji wanda zai bar ki kiyi karatu har ki cika burinki.” Ta ce, “Na gode Yaya. Dazu naji ka ce zaka gyara mana, ai haya muke yi.” “Haya? Wannan gidan ne ake haya?” Ya tambaya cikin mamaki. Ya kalli agogon hannunshi, “Bari in tafi zan zo.” Ta ce. “To sai anjima.” Tana tsaye har motarsh ta bace.Hajiya ta kira shi, yana dagawa ta ce Momiyo tana ta kiran ka ba ka daga ba.” Ya ce, “Ina tuki ne shi yasa, sai na isa Kaduna zan kira ta.” Ta ce, “To shi kenan bari in fada mata.” Momiyo karamar kanwar su Hajiya ce. Ita ce kuma za tayo masa odar akwatunan lefe. Sai da ya isa sannan ya kirata. “Anty Mamiyo kina ta kirana ina hanya, ka’idata in ina tuki kiran Alhaji ko na Hajiya kawai ni ke dagawa.” Tayi dariya, “Za ka fara daga na matanka kwanan nan.” Ya ce, “Su a wa? Za dai su san ka’idata a kwanannan.” Ta ce, “Maganar akwatuna ce zan tura maka online sai ka zaba, saboda gobe zan yi odar.” Ya ce, “Kowace a dauko mata kalar da tafi so. Ta ce, “Wace kala ce suka fi so?” Ya cc, “Ita dai Amna tun muna Makaranta tana son Lemon green, Aliya kuma na san tana son ja, Nafisa ce dai bari in kirata yanzun, sai kuma daya yarinya Kin san na samu ta hudu a kawo mata baby pink.” Ta ce, “Bana son wasa.” Ya ce, “Antywallahi babu wasa. Ke ce ta farko da ki ka san zancan nan, Ta ce, “Ka san me ka ke yi kuwa?” Ya ce “Don Allah Anty kiyi yanda na ce, kar ki manta baby pink, bari in kira Nafisa din.” Take ya kira Nafisa ya tambaye ta best color dinta ta ce purple Ya kira Anty Momiyo ya fada mata. Salma tana shiga gida ta samu su Innarsu tamkar ita suke jira, ta fada musu komai yanda suka yi ita da Shatima. Su Yaya Hadiza sun hau murna. Inna kuwa ta dira ta ce “Ba ta yarda ba, ko dai mutumin nan da biyu ya zo?” Salma ta ce, “Inna biyu kamar ya ya?” Inna ta ce, “To ni ban gane ba, daga taimako sai kuma ya ce zai samo mata miji?” Yaya Hadiza ta ce, “Haba Inna, ki kyautata zatonki a kansa.” Auwal ya ce, “Inna jikan gidan Alhaji Shatima ne fa, sanannu ne “Shi kenan, Allah dai ya zaba mana mafi alheri.” In ji Inna. Suka ce “Haka za ki fada Inna.” Momiyo ta daga wayarta ta kira Hajiya. Tana dauka ta ce, “Momiyo ki bari zai kira ki.” Ta cc, “Ai ya kira ni Hajiya, wai seti hudu za a kawo masa, wai ya samu ta hudun. Haka ne?” Hajiya cikin daga murya ta ce, “Abin hauka ne za a ce ya samu ta hudu! Kila dai ita Amna. za a kai wa saiti biyu, tunda kin ga tuwon girma miyarsa nama, a ce komai daya za’ayi?” Momiyo ta ce, “Ni fa ya nuna min da gaske yake amma dai kyaji in ya dawo daga bakinsa. Ai ni tunda a ka ce flat hudu ya gina na san da wata a kasa.” Hajiya cikin damuwa ta ce, “To maji-magani.” Suka yi sallama. ** Biki saura kwana ashirin da tara, ko ina kansu ya dau zafi, gobe yake son yaje gidan su Aliya da Nafisa ya kai musu makullan gida, don kowa yaje ya ga gida. Haka kuma yana son ya kai musu Amna, amma abin da yafi daga masa hankali yanda zai ga ya shigar da lamarin Salma ga danginsa, dole ya je gurin Munnir yanzun don ya fara samun goyon bayansa. Suna cin abinci a falon Munnir yana gefen fada masa abin da ke tafe da shi. Munnir ya aje cokali, ya ce “Ka ga abokina fada min kawai abin da ka ke son fada min. Shatima ya ce, “Kai tsaye ina son yin ta hudu da yarinyar nan Salma wadda Mahaifinta ya rasu. Da karfi Munnir ya ce, “Me ka ce?” Har sai da faisal danshi da ke bacci a kan kujerar da ke kusa da shi ya tsorata ya farka. Munnir ya dauki yaron tare da kwalana uwarshi kira. Fatima zo ki dauki wannan.” Ta shigo ta amshe shi tana cewa “Ya tsorata ne?” Munnir ya ce, “Magana ce nayi me karfi, shi ne ya fırgita.’ Ta ce, “Kana tunanin mata ukun sun yi maka kadan ne da har sai ka kara da wannan ‘yar babyn da bata fi ka haife ta ba, da a ce kayi aure da wuri. Wai me ke damunka?” Ya ce, “Lafiyata lau, kuma ba wai wadancan ba za su ishe ni ba ne, taimako zan yi ina jin Tausayin yarinyar.” Ya fada mishi duk yanda suka yi da ita.Munnir ya ce, “Ban ga wata matsala a cikin bukatar tata ba. Ka sai mata kayan daki ka aura mata wancan shi kenan.” Shatima ya ce “To karatunta fa?” Munnir ya ce “Kayi magana da mijin ya barta kai ka dauki nauyin karatun nata, kaga shi kenan ka huta da wasu surutai da zasu taso daga danginka, da kuma matanka.” Shatima ya ce, “Ban yi wannan tunanin ba, amma na riga da na fada mata cewa zan kawo mata miji wanda zai barta tayi karatu, kuma tayi murna. Munnir ya ce, “Ka ce mata kai ne?” Shatima ya ce, “A’a.” Munnir ya ce, “To kawai ka dauko batun wancan ka cire kanka.” Shatima yayi shiru tamkar mai nazari, har Munnir ya soma zaton shawararshi ta shiga har yana cewa kayi nazari da kyau abokina.” Sai yaga Shatima ya bude ido sannan ya kalle shi, ba wai na gamsu da shawarar ka ba ne, ina tunanin yanda za ayi fadan karshe ne tsakanina da su Hajiya. Don tabbatar da yarinyar nan tana cikin mata hudun nan da na gani a cikin baccina. Sai yanzu na luna ban fada maka ba, akwai wata a mafi Kankanta a cikin matan mafarkina, babu shakka Salma ce Tsaki Munnir yaja sannan ya ce, “Allah Ya taimaka.” Shatima ya ce, “Dama haka ka ce, tun dazu da yanzun mun kusa gidan Kaka.” Munnir cikin jin haushi ya ce, “Ni babu inda zan fita, bacci ma nike ji.” Shatima ya ce, “Gurin Kaka dole ka zo muje, In na samu goyon bayanta kowa dole ya lafa min. Sai dai ina ji a jikina, ba za ta ba da hadin kai ba itama. Munnir ya ce, “Allah Ya sa kar ta amince.” Shatima ya mike. “Don Allah tashi muje koda zugata kayi ka ji?” Abokina haka sai ya gaji da matsin Shatima ya tashi suka fita. Allah yasa bata kai ga shiga cikin daki ba, lokacin da suka yi sallama a falonta. Bayan sun gaisa Shattima ya shiga kame kame ya rasa ta inda zai bullo ma al’amarin. Ya ce, “Kaka nasan dai muna tare ko me nazo da shi, ba za ki kware min baya ba.” Hajiya ta ce, “Kayi magana kai tsaye ni bacci nike ji in shiga ciki, don ka taki sa’a yau a nan nayi sallah.”_____ *🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 11 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* ```🧕🏻🧕🏻Ina kuke kasaitattun mata, Hajiyata kada ki bari ki zama bora agidan auren ki yi kokari ki tsuma kanki da ingantattun magunguna na gyaran jiki 07032895551🍉🍉🥥🥥``` ```Mun zo maku da ingantattun magunguna masu kyau da inganci akwai TABAJE mai kyau gangariya 5litres 5k 07032895551``` ```Muna da hadin Abulbulo, akwai Dan saudiya Hajiyata kada ki bari wannan hadi ya wuceki,dagajin sunan ABULBULO kinsan akwai aiki 4k ne kudin shi🙈🙈``` ```Akwai sa Buzu Kuwwa,muna da kafi Budurwa uku sai angwada akansan na kwarai``` ```🗣️🗣️🗣️Ina matan da mazajen su kebin matan banza to matso kusa Hajiyata Muna hadi na musamman duk macen da tayi amfani dashi mijin ta be karajin dadin wata mace, wannan hadi in kinsan kinada kishiya don Allah kada ki siyeshi 8k ne kudin shi🥥🍉``` ```Akwai dahuwar kaza gangariya sai kin gwada Hajiyata zaki bani labari🙈🙈 akwai Dan dakarawa ya matseki tsam ya kuma saukar maki da ni'ima, akwai kafi sugar, kwallin mata dan matsi daya tamkar da dubu kenan🍉🥥``` ```Akwai hadin Zama daram,munada miski mekyau original, akwai dahuwar kaza ta amare da uwar gida🐓🐓🐓 Akwai Sabulun infection ya matseki ya yi maki maganin infection,yasa wajen yayi sulbi Hajiyata``` ```Muna garin katsina Muna aikawa ko ina a fadin Nigeria har ma da makotanmu Niger 07032895551``` ```Sai angwada ake sanin na kwarai, amma don Allah idan baki shirya siya ba kada kiman magana 07032895551 muna bada sari game bukata🙏🏻🙏🏻``` Mun tsaya Don Allah tashi muje koda zugata kayi ka ji?” Abokina haka sai ya gaji da matsin Shatima ya tashi suka fita. Allah yasa bata kai ga shiga cikin daki ba, lokacin da suka yi sallama a falonta. Bayan sun gaisa Shattima ya shiga kame kame ya rasa ta inda zai bullo ma al’amarin. Ya ce, “Kaka nasan dai muna tare ko me nazo da shi, ba za ki kware min baya ba.” Hajiya ta ce, “Kayi magana kai tsaye ni bacci nike ji in shiga ciki, don ka taki sa’a yau a nan nayi sallah.” Ya ce, “Ko kin shiga sai na bi ki. Dama dai ta hudun ce na samu, shi ne ni ke son ki sa ba ki a jone ta cikin bikin.” Ta hade fuska, “Kai bana son maida bara bana, an riga an wuce nasan tunda kayi uku ai dole zaka yi ta hudu, amma ka bari sai can gaba.” Ya ce, “Haba Kaka! Don Allah ni a hada rana daya, dama su hudu na gani a cikin gara kawai mafarkina.” Taja tsaki, “Mafarkin ka na banza tunda kai ba Annabi ba ne ba wani tabi’i ba ko Malami, har wani mafarki ke gare ka?” Munnir ya ce, “Shi ne nima na gani da anyi magana sai ya ce mafarkin shi.” Shatima ya dubi Munnir, “Haba abokina! Kai fa ka san komai.” Ya dubi Kaka, “Wallahi yarinyar Marainiya ce, na san ki da tausayi.” Ta ce “Ni har a fada min maraici, ni da ubana ya mutu tun ina ciki, uwata kuma ran da ta haife ni ta rasu?” Shatima ya ce, “To ni dai kiyi hakuri in Alhajina ya zo ki ce kin yarda. Ta soma yunkurin mikewa. Munnir ya yi saurin mika mata sandarta. Ta amsa tare da fadin “Na gode dan nan kaje gida gurin iyalinka ka fita batun wannan uban wautar. Shatima ya taimaka mata har cikin daki yana kara rokonta amma sam ta ki magana. Bayan ya sauke Munnir ya nufi gida. Bai zaci zai samu Hajiyarshi a falo ba tun da sha daya ta gota, bai ma lura tana nan ba sai da ya nufi samanshi ya ji ta ce, “Kai zo nan. Gabanshi ya fadi, don tun jiya ta fada mishi cewa tana son ganinshi. Da safe a gurguje ya gaishe su wai yayi latti, da yamma ma haka ya yi ta goce ma haduwarsu, yanzu kuwa an ritsa shi.” Ya zauna gabanta, “Gani Hajiya.” Ta ce, “Wai ka manta na ce ina son ganinka ne ka ke ta yi min goce-goce?” Ya ce, “A’a abubuwan ne, kiyi hakuri.” Ta ce, “Ni ban yi fushi ba amma zan yi “Ai matsawar ka kasa fada min gaskiya.” Ya ce, ” ban taba yi miki karya ba Hajiya.” Ta ce, “Mene ne gaskiyar zancan da Momiyo ta fada min, wai ka samu mace ta hudu, haka ne?” Ya ce, “Haka ne, dama da safe zan zo muku da batun.” Ya daure ya kau da tsoron shi ya fada. Ta ce, “To wannan karon babu hannuna a ciki, kaji na fada maka.” Ya ce, Hakuri za ki yi Hajiya, in na cike ai ba sauran in da zan saka wata ko?”Ta ce, “Tunda kai naga kamar Namamajo ne sarkin mata ai in ka hango wata zaka iya zuwa ka saki wata ka shigo da wata. Ya ce, “Haba Hajiya, kar ki yi min fatan haka. Ki daure ki sama abin albarka gaba daya.” Ta mike tare da fadin, “Ba zan sa ba, dama kai ni ke jira in ji tabbaci, in haka ne in ce maka ba da yawuna ba.” ta nufi dakin Maigidanta ta bar shi nan zaune turus ya rasa tunanin da zai yi. Ya mike yana rangaji ya nufi samanshi, zuciyarshi bata taba mai zafi irin wannan ba, gani yake kamar gara ya fasa auren sauran matan guda uku ya auri Salma kadai, domin ita ce ya dauki alkawari tsakaninshi da MahaliccinShi zai taimake ta. Ya kalli abincin shi, ya kauda kai. Ya nufi gadon shi ya fada. Ruf da ciki ya kifa kanshi a kan filo, rabin kan shi ya soma ciwo, ya rasa tunanin da zai yi. A haka bacci ya soma fizgarshi. Can kuma sai ya soma jin sanyi, yaja bargo. Abin kamar wasa sai jiki ya yi zafi. Haka ya kwana, yana jin agogonshi yana kiran sallah amma ya kasa tashi. Badi’atu tazo kawo mishi abin kari sai ta ganshi a bargo, yana ta rawar sanyi ta ce, “Yaya! Yaya!!” RANA DAYA Da kyar ya ce”Kira min Hajiya.” Da gudu ta sauka, tun daga benen take kwala ma hajiya kira. A falon Alhaji ta same su tana kokarin hada ma Alhajin shayi. A tsorace ta waiwayo ta ce, “Mene ne?” Ta ce, “Yaya ba shi da lafiya.” Alhaji da ke cikin dakin baccin shi ma ya fito da sauri. “Ba shi da lafiya kuma?” Badi’atu ta ce, “Eh, yana ta rawar sanyi.” Gaba dayansu suka nufi saman. Sun tsorata da ganin yanayin shi, domin gaskiya ba shi da yawan ciwo. A tare suka bude bargon, ya kanannade jikinshi yana ta bari. Alhaji ya kama shi ya tallafo mishi kai. “Babana me ke damunka?” Hajiya ta ce, “Badi’atu, maza ki taso Mustapha ya fito da mota, yi sauri.” Ta tafi da gudu. Uban ne ya tallafe shi suka sauka kasa zuwa mota. Alhaji ya koma ya cire malun-malun yasa jallabiyya ya dauki kudi. Asibiti mafi kusa suka je ana shiga dashi, Likitan baya nan. Alhaji ya hau fada, yana cewa wane irin Likita ne har yanzun bai zo asibitin shi ba. Nurse ta ce, “Yi hakuri Alhaji, bari a kira shi, gidan shi babu nisa. Sauran Nurses kuma suka sa shi a gado don yi masa taimakon farko. Sun duba shi suka sa masa ruwa tare da allura. Iyayan da Mustapha kaninsa suna tsaye a kanshi suna yi masa sannu har lokacin jikinsa yana rawar sanyi, gashi ba su rufe shi ba, kuma sun kunna fanka. Likitan ya shigo da sauri. Ya ba Alhaji hannu suka gaisa, Alhaji ya ce, “Haba Likita! Bai kamata ace ba ka fitowa da wuri ba, asibiti mai zaman kanshi a ce an zo babu Likita?” Ya ce, “Kayi hakuri Alhaji, jiya sai kusan karfe uku na dare na bar asibitin nan mutum uku muka yi wa tiyata. Ya isa gaban Shatima ya soma da bude idanunsa yana tambayar abin da ke damunsa. Alhaji ya ce, “To mu dai lafiya ya kwanta jiya.” Hajiya ta ce, “Ni da har magana mun yi da shi kafin ya kwanta din ma.” Likitan ya taba jikinshi ya ji rau da zafi. Ya dubi ‘su Alhaji ya ce, “Ku dan zauna a waje.” Suna fita ya cire ma Shatima ruwan sannan ya taimaka mishi ya cire rigar jikinshi. Shatima ya ce, “Sanyi ni ke ji.” Likita ya ce, “Kar ka damu, zaka daina ji yanzun.” Ya kalli Nurse din da ke tsaye ya ce mata ta kawo mishi wata allura, ya fada mata sunan allurar ta fita. Ya maida masa ruwan yana ci gaba da yi masa tambayoyi. Bayan an kawo allurar ya yi masa ita a cikin ruwan, sai ya ce “Kar ka damu gajiya ce da zirga-zirga, sai kuma rashin bacci. Yanzun za ka yi bacci ka huta a nan zuwa jibi zaka wartsake sarai.” Shatima yayi saurin kama hannun Likitan mai kokarin fita. Ya ce, “Likita don Allah ina son kayi wani taimako daya, nima dai taimakon zan yi. Likitan ya dawo ya tsaya. Shatima ya ce, “Ina son ka ce ma iyayena damuwa ce ke tare da ni, don haka kada suke yawan matsa min, kuma ka ce musu su tambaye ni damuwar don suyi saurin kauda min ita saboda zata iya haifar min da wani ciwo.” Likitan ya ce, “Amma kai Lauya ne ko?” Shatima ya yi dan yake tare da fadin “A’a.” Likitan ya ce “Ka iya tsara magana. Zan fada musu haka din tunda ba cewa kayi a ce kana da wani ciwo ba.” Ya leka ya ce, “Alhaji za ku iya shigowa.” Suka shigo. Allah Sarki, iyaye duk sun damu suji me ke damun dansu har suna hada baki gurin tambayar Likitan “Me ke damunsa?” Ya ce, “Akwai rashin samun ishasshen bacci, zirga zirga da gajiya. Sannan kuma akwai wata damuwa a tare da shi wadda ya ki fada min ita. Ya kamata ku san ta don kuyi gaggawar raba shi da ita, domin zata iya haifar masa da katuwar matsala.” Suka ce, “To Likita, zamu bincika.” Yana fita Hajiya ta ce, “Shatima me yake damunka ne ka boye mana?” Alhaji ya ce, “Haba Hajiya, ki bari tukunna ya samu sauki mana. Zai fada mana kuma za a magance ta.” Shatima na jin su ya yi lamo, a hankali naman jikinshi ya daina rawa, bacci ya kwashe shi. Labari ya watsu a dangi cewa Shatima yana asibiti. Nafisa ta samu labari, hankalinta ya tashi take ta fasa zuwa Makaranta ta ce “Mama ba zan jira ku ba, bari in je in ganshi.” Ita ce ta fara zuwa a cikin Amaren Shatima. Lokacin da ta zo Hajiya tana zaune a bencin kofar dakin da wasu kawayenta. Nafisa cikin kunya ta durkusa ta gaida su, ta kuma tambayi jikin nashi. Hajiya ta ce, “Da sauki, ki shiga yana dai bacci, Mustapha ma yana ciki.” Tana shiga idanunta na kanshi, yana kwance sambal jikin shi babu riga, tausayinshi yasa idanunta kawo ruwa. Ta kalli Mustapha.yaya me ya ke damunsa?” “Zazzabi ne kawai, kar ki damu. Da ya farka zai warware.” Muryarta na rawa ta ce, “Allah yasa haka. Allah dai ya ba shi lafiya.” Mustapha ya tashi daga kan kujerar da yake zaune ya ce, “Ki zauna.” Ta ce, “A’a da ka bar shi.” Ya ce, “Bari in dan fita in mike kafa ma. Ta zauna shi kuma ya fita. Ta tsura ma halittarshi ido, a ranta tana godiya ga Allah da ya zaba mata Shatima a miji. Tamkar ta kai hannunta ta dafa nashi, amma sai ta tsawaci zuciyarta don addininta bai bata damar yin hakan ba. Lokaci-lokaci mutane na shigowa duba shi su fita. Iyayen Nafisa suka iso har su Hamida. Dauke da kuloli da kalolin abinci da kayan shaye-shaye. Su kansu masu asibitin sun shaida cewa dan gata ne ya zo jinya asibitinsu, tunda ba a yi awa shida ba amma motocin da suka shigo ba a magana. Abokan Alhaji kawayen Hajiya ga kuma dangi. Haka nan sai waya ake buga ma Jama’a, ana fada musu Shatima yana asibiti. Nafisa ta ce ma Mustapha lokacin da ya dawo dakin Ban ga Munnir ba.” Ya ce, “Ai ko ina ga bai sani ba.” Nan take ya kira shi ya fada masa. Ashe kuwa bai sanin ba, ya ce yana ta buga wayar Shatima ba a daga ba. Mustapha ya ce “Duk wayoyinsa suna gida. Bari ma yaje ya dauko.” Ya fita ya fada ma Hajiya, ta ce yaje ya dauko ya samu missed call sama da talatin. Yana dubawa ne ma ya kira lambar Aliya da aka sa my love, ya fada mata. Ya kira sweety sai da ta daga ya ce, “Amna ce?” Ta ce, “Ni ce Nafisa.” Mustapha ya ce, “Ok.” Ya kashe ya samu ta Amna. Itama ya fada mata. Ta ce, “Me ke damunsa?” Ya ce “Zazzabi ne. Ta tambayi sunan asibitin ya fada mata. ya kira Kaka, Maryama ta daga, ya ce “Maryam ki ce ma Kaka Yaya Shatima yana asibiti. Kaka ta rude ta ce, “Maryama ta kira shi. Da ya fada ma Hajiya nan ta rufe shi da fada. Ta ce, “Wa ya ce ya fada ma Kaka?” Sai ko ga kiran Kakar a wayar Hajiya tasa Maryama ta kira. Tana dagawa ta ce, “Maza ki sa a zo a ďauke ni in ga jikin dan nan.” Hajiya ta ce “Da kin hakura jikin nashi da sauki.” Ta ce “A’a ban yarda ba, a zo a kawo ni. Jiya ban yi baccin kirki ba na rasa me ke damuna, ashe jikinsa ne.” Hajiya ta ce, “Shi ke nan gashi nan zai zo yanzun.” Ta kalli Mustapha, sai kaje ka dauko ta dan sarki a surutu da ka tada mata hankali.” Aliya tana asibiti lokacin da Mustapha ya kirata ya fada mata ciwon angonta, duk hankalinta ya tashi. Taso taje gida ta canza kaya amma zuciyarta ta fada mata ciwon da aka kwantar da mutum, kuma har aka kira ta aka faca mata gaskiya da matsala. Ta dauki uziri, sannan ta dubi kawarta Aisha ta ce, “Kina ga in tafi a haka?” Ta ce “Kijo mana ai kayan ki a goge suke tsaf!” Ta kira*🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 12 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* ```🧕🏻🧕🏻Ina kuke kasaitattun mata, Hajiyata kada ki bari ki zama bora agidan auren ki yi kokari ki tsuma kanki da ingantattun magunguna na gyaran jiki 07032895551🍉🍉🥥🥥``` ```Mun zo maku da ingantattun magunguna masu kyau da inganci akwai TABAJE mai kyau gangariya 5litres 5k 07032895551``` ```Muna da hadin Abulbulo, akwai Dan saudiya Hajiyata kada ki bari wannan hadi ya wuceki,dagajin sunan ABULBULO kinsan akwai aiki 4k ne kudin shi🙈🙈``` ```Akwai sa Buzu Kuwwa,muna da kafi Budurwa uku sai angwada akansan na kwarai``` ```🗣️🗣️🗣️Ina matan da mazajen su kebin matan banza to matso kusa Hajiyata Muna hadi na musamman duk macen da tayi amfani dashi mijin ta be karajin dadin wata mace, wannan hadi in kinsan kinada kishiya don Allah kada ki siyeshi 8k ne kudin shi🥥🍉``` ```Akwai dahuwar kaza gangariya sai kin gwada Hajiyata zaki bani labari🙈🙈 akwai Dan dakarawa ya matseki tsam ya kuma saukar maki da ni'ima, akwai kafi sugar, kwallin mata dan matsi daya tamkar da dubu kenan🍉🥥``` ```Akwai hadin Zama daram,munada miski mekyau original, akwai dahuwar kaza ta amare da uwar gida🐓🐓🐓 Akwai Sabulun infection ya matseki ya yi maki maganin infection,yasa wajen yayi sulbi Hajiyata``` ```Muna garin katsina Muna aikawa ko ina a fadin Nigeria har ma da makotanmu Niger 07032895551``` ```Sai angwada ake sanin na kwarai, amma don Allah idan baki shirya siya ba kada kiman magana 07032895551 muna bada sari game bukata🙏🏻🙏🏻``` Mun tsaya Hajiya ta ce, “Shi ke nan gashi nan zai zo yanzun.” Ta kalli Mustapha, sai kaje ka dauko ta dan sarki a surutu da ka tada mata hankali.” Aliya tana asibiti lokacin da Mustapha ya kirata ya fada mata ciwon angonta, duk hankalinta ya tashi. Taso taje gida ta canza kaya amma zuciyarta ta fada mata ciwon da aka kwantar da mutum, kuma har aka kira ta aka faca mata gaskiya da matsala. Ta dauki uziri, sannan ta dubi kawarta Aisha ta ce, “Kina ga in tafi a haka?” Ta ce “Kijo mana ai kayan ki a goge suke tsaf!” Ta kira Ya ce, “Ko kin shiga sai na bi ki. Dama dai ta hudun ce na samu, shi ne ni ke son ki sa ba ki a jone ta cikin bikin.” Ta hade fuska, “Kai bana son maida bara bana, an riga an wuce nasan tunda kayi uku ai dole zaka yi ta hudu, amma ka bari sai can gaba.” Ya ce, “Haba Kaka! Don Allah ni a hada rana daya, dama su hudu na gani a cikin gara kawai mafarkina.” Taja tsaki, “Mafarkin ka na banza tunda kai ba Annabi ba ne ba wani tabi’i ba ko Malami, har wani mafarki ke gare ka?” Munnir ya ce, “Shi ne nima na gani da anyi magana sai ya ce mafarkin shi.” Shatima ya dubi Munnir, “Haba abokina! Kai fa ka san komai.” Ya dubi Kaka, “Wallahi yarinyar Marainiya ce, na san ki da tausayi.” Ta ce “Ni har a fada min maraici, ni da ubana ya mutu tun ina ciki, uwata kuma ran da ta haife ni ta rasu?” Shatima ya ce, “To ni dai kiyi hakuri in Alhajina ya zo ki ce kin yarda. Ta soma yunkurin mikewa. Munnir ya yi saurin mika mata sandarta. Ta amsa tare da fadin “Na gode dan nan kaje gida gurin iyalinka ka fita batun wannan uban wautar. Shatima ya taimaka mata har cikin daki yana kara rokonta amma sam ta ki magana. Bayan ya sauke Munnir ya nufi gida. Bai zaci zai samu Hajiyarshi a falo ba tun da sha daya ta gota, bai ma lura tana nan ba sai da ya nufi samanshi ya ji ta ce, “Kai zo nan. Gabanshi ya fadi, don tun jiya ta fada mishi cewa tana son ganinshi. Da safe a gurguje ya gaishe su wai yayi latti, da yamma ma haka ya yi ta goce ma haduwarsu, yanzu kuwa an ritsa shi.” Ya zauna gabanta, “Gani Hajiya.” Ta ce, “Wai ka manta na ce ina son ganinka ne ka ke ta yi min goce-goce?” Ya ce, “A’a abubuwan ne, kiyi hakuri.” Ta ce, “Ni ban yi fushi ba amma zan yi “Ai matsawar ka kasa fada min gaskiya.” Ya ce, ” ban taba yi miki karya ba Hajiya.” Ta ce, “Mene ne gaskiyar zancan da Momiyo ta fada min, wai ka samu mace ta hudu, haka ne?” Munnir ta tambaye shi asibitin ya fada mata. yace, “Shima zuwansa kenan.” Ta ce, “In ta zo zata kira shi.” Shima Munnir ya samu asibitin cankas da mutane, don ma wasu suna tafiya. Ya tsugunna ya gaida Hajiya, kuma ya tambayi abin da ke damun aminin nasa, har ya kara da cewa jiya har sha daya saura suna tare lafiya. Hajiya ta.ce “Ikon Allah kenan! Ai baya bata da kadan, ko mutuwa ce ma haka ne, ka shiga yana bacci.” Ya shiga sun gaisa da Nafisa, yaje yana taba jikin abokin nasa sassan wuyanshi, ya ji jikin babu zafi, har yana zufa duk da fanka da kuma (AC) da suke ta aiki. Ya kalli Nafisa “Ke ce mai jinyar?” Tayi murmushi tare da sunkuyar da kai ta ce, “Ka zauna.” Zata tashi ya nufi kujerar da ke can gefe mai zaman mutum uku da yake dakin aminiti ne. Bai fi minti hudu da zama ba kiran Aliya ya shigo, ya daga. Ta ce, “Nazo bakin asibitin.” Ya ce, “To gani nan fitowa.” Shi ne ya yi mata jagora har gurin Hajiya, cikin kunya ta tsugunna har kasa ta gaida Hajiya da mutanan da ke gurin. Hajiya ta ce, “Munnir wannan kuma wace ce?” Gaban Aliya yayi wata muguwar faduwa, don ta gane ita ce, mahaifiyar Shatima domin sun yi matukar kama. Munnir ya ce, “Hajiya Aliyan Shatima c Aliya ta saci kallon Hajiya don taga irin karbar da ta samu. Ta kuma gani don fuskar Hajiya ta yamutse, ta kuma kallon Aliya sannan ta ce, “Yana ciki.” Jiki babu karfi ta tura kofar tare da sallama ta shiga. Nafisa ta waigo don taga mai shigowa tare da amsa sallamar. Dukkansu gabansu yayi mugun faduwa da ganin juna. Sun san juna tunda Shatima sau biyu yana kai Aliya gidan su Nafisa a wancan zamanin da suka yi soyayya a baya. Nan da nan Nafisa ta hade rai tamkar bata taba dariya ba. Aliya ta lura da haka amma bata ki ce mata ina yini ba. Da kyar ta amsa, don ma Munnir yana ciki ne. Aliya taje kanshi ta tsaya, ta karanto addu’ar da tazo a Musulunci zaka karantawa mara lafiya. Sannan taje ta dauki folder din sa tana duba abin da ke damunsa. Ta kalli. Munnir, gajiya da rashin bacci ne ke damun abokinka kenan.” Ya ce Haka naji ana fadi.Ta dawo kusa da hannunshi, hannun ya kumbura. Ta ce, “A’a.” Ya motsa hannun ne?” Da alamu ruwan ba ya tafiya. Munnir ya taso da sauri ta duba sosai ta ce, “Tabbas ruwan nan baya tafiya. Nafisa ta fita da sauri kiran Hajiya. Aliya ta saka safar hannu da ke aje gurin da aka jera abubuwan amfanin da suke mishi aiki da su. Tazo ta soma cire ruwan ta sakale, sannan tasa hannu tana sabule allurar tun da ta cire. Ta ce da Munnir tunda an fi bukatar ya yi bacci, in ya farka sai a maida mishi ruwan.” Daidai lokacin Hajiya da Nafisa da Nurse suka shigo. Aliya ta kalli Nurse din ta ce “Na cire mishi ruwan don naga yafi bukatar bacci, na duba allurar da aka yi mishi.” Nurse din ta ce, “Haka ne, kin kyauta. In ya tashi sai a maida masa.” Aliya ta kalli agogo “Nan da karfe uku zai tashi, ko da mintuna.” Nurse din ta ce, “Haka ne” Nafisa ta tabe baki ta zauna. Hajiya ta juya ta fita. Nurse din ta ce “Ku ragu a dakin.” Aliya ta mike “Bari in je daga wajen.” Munnir ya ce, “To muje.” Nurse din ta ce, “Ke ya kamata ki tsaya tunda kin san yanda za a kula da shi.”Aliya ta ce, “Babu komai, ai an cire mishi ruwan.” Suka fito ta cire safar ta zuba a kwandon shara. Amna suna ta waya da Mustapha wanda yaje ya dauko Kaka. Yana kara yi musu kwatance yanda za su iso asibitin don sun shigo Zaria din. Domin Mustapha yana fada mata hankali tashe ta shiga gurin Anty Amaryar Babansu ta fada mata, don Mom sun tafi Dubai da China don hado kayan kicin na ita Amna din. Nan suka shirya zuwa duba shi, ita da Anty da kanwarta Sumayya. Amnarko bayan ta da ruwan gora zuwa kayan Tea da lemukan gora dana gwangwani Mustapha ya riga su isa asibitin, ya fito da kujerar Hajiyar da ake tura ta don bata iya yin doguwar tafiya. Har da Maryama suka zo suka taimaka mata ta zauna a kujeran, ya tura ta suka nufi cikin asibitin. Nan kowa ya tashi ana gaida ta cikin girmamawa. Hajiya ta tsugunna a gabanta tana yi mata sannu da zuwa. Ta gaida ta, Kaka ta tambayi jikin Shatima, ta ce, da sauki. Mustapha ya turata zuwa ciki.Tana ta fadin “Sannu dan nan, ciwo haka da gaggawa, jiya muna tare.” Nafisa ta durkusa ta gaishe ta. Mustapha ya fita da sauri sakamakon kiran da Amna ta masa cewa gasu sun iso. Ya same su a harabar asibitin. Yayi musu jagora. Amna sanye da doguwar riga dinkin Dubai, kalar ja da ratsin baki, ta yafa dan karamin mayafin rigar. Har gaban Hajiya ya kai su yana fadin “Ga Amna daga Kano amaryar Yaya. Ta gaban Aliya suka wuce, tunda taga Munnir ya tashi ya bisu ta zargi cewa wannan Amna ce. A fili ta ce, “Lallai kuwa Shatima ya hada mata.” Ta maida hankalinta don taga irin karbar da ita zata samu a gurin surukar tasu. Sai ta hanagi bakin Hajiyar har kunne, tana yi musu sannu da zuwa. Ta ce “Wace ce ‘yar tawa?” Sai Amna taja gefen mayafinta ta rufe fuska. Hajiya ta ce, “A’a na ganta masha Allah, to Munnir kai su ciki.” Anty Amarya ta ce da Mustapha suje da Sumy su kwaso abu a boot. Sumy cikin shagwaba ta ce, “Anty zamu iya kuwa? Akwai fa yawa.” Hajiya ta dubi Hamida kanwar Nafisa, da Maryama ta ce. “Kuje ku taya su. Amna tana shiga suka kalli juna da Nafisa. Amna ce tana shiga suka kalli juna da Nafisa.Amna ce ta fara kauda kanta,domin faduwar dataji gabanta yayi, tabbas wannan daya daga cikin kishiyoyinta ne.Anty ce kawai tagaida Nafisa tare da tambayar jikinshi.Amna tana tsaye tana karema Shatima kallo,so da kaunarshi azuciyar ta suka nunku. Uku da minti biyar Aliya ta sake dosar dakin dan tasan yana daf da farkawa. Tasamu Anty ta fito gurinsu Hajiya,ga kuma kayanan ana ta jibgewa wanda su Amna suka zo dashi acikin dakin Munir da Amna suna kan kujera Nafisa tana zaune inda take. Haka kuwa daidai lokaci yayi mika gami da salati yayi juyi kamar zai cigaba da bacci, sai ya ji gadon ba irin nashi ba. Ya dan yi shiru don son ya tuna ashe fa bashi da lafiya, sai ya bude ido ya kalli Hajiyar. Yayi yunkurin tashi, sai ya ji Munnir yace “Yi a hankali Shatima.” Ya kama shi ya tayar zaune. Mamaki ya cika shi ganin Aliya da Nafisa Ya ce, “Har an taso mutane haka Hajiya?” Ta ce, “To ai abokin kuka shi ake fadama mutuwa.” Ta nuno Amna wadda ke zaune tana danna waya tayi tamkar ba ta san suna yi ba. Ta ce, “Ga ma mutan Kano yanzu suka zo. Ya kai duba Amna ta dago suka hada ido. Ya saki dan murmushi “Har da ke honey?” Ta dago mishi yatsunta guda biyu alamun sannu. Ya ce, “Daga nesa? Ban amsa ba.” Nafisa ta cika tayi tam! Ya kalli Hajiya “Ina Alhaji?” Ta ce “Bari Mustapha su gama ya kira shi ya ce ka farka sai waya yake, bai dade da barin nan ba shi da sauran iyayenka.” Mutanan waje suka soma shigowa suna yi masa sannu suna fita. Ya ce, “Munnir ya ba shi rigarshi yasa. Ya ce zai yi fitsari. Munnir ya taimaka masa. Yanzun ba in da yake masa ciwo sai dai bakinsa babu dadi, jikinsa kuma babu karfi. Ya dan ci abinci kadan, Likitan ya shigo lokacin Kaka tana ciki tana ta yi wa ‘yanmatan nashi tsiya, wai sun kasa sun tsare. To ita ce dai me shi. Nafisa ban da kumburi ba ta komai. Aliya ce tayi dan murmushi ta ce “Ai ba zamu ja da ke ba.” sai lokacin Amna ta dago ta kalli Aliya,yanzu har da wannan a cikin matan da honey dinta ke so? Ita duk kallo take yi ko Malamar asibiti ce mai kula da shi, Likita yayi masa tambayoyi, sannan ya ce “In ya gama za’a maida masa ruwan da ya goce. Shatima ya ce, “Ka sallame ni in je gida aurena ya kusa.” Likita ya ce Sai ka huta nan da kwana biyu. Ko dama auren ne kasa a ranka ka ke neman ja za ma kanka wani ciwo?” Ya ce, “A’a Likita, waccan matsalar daban.” Kaka ta ce, “Likita kar ka sallame shi sai ya yi sarai. Yaron nan ya jaza min tun jiya bacci ya gagari idona, rabon da in fito kusan shekara guda da rabi, amma yau silar shi gani na fito.” Likita ya ce “Kaka ai ya taimake ki, fita tana kara lafiya, ki daure ki ke fita ko sau daya a sati.” Ta ce, “A’a ni ba in da zan je ko da ba mu saba yawo ba mu.” Hajiyar shi ta sake shigowa, bayan tayi ma wasu rakiya. Ta ce, “Shatima ga fa kaya nan da su Amna suka zo da shi, babu gurin ajiya sai dai a rabawa jama’a ko?” Kaka ta ce “Wai ni ana ta Amna har yanzu ba ku nuna min ita ba?” Shi da kanshi ya ce, “Ki duba duk matan gurin nan ki nunata da kanki.” Ta hau waige-waige. Amna ta ja dan mayafinta ta rufe fuska. Kaka ta ce, “A’a na ganta, to bude in gani kin kai ni kyau!” Nafisa ta mike fuu! Ta matsa. Aliya ta kalle shi, “Bari in maida maka ruwan in tafi gida basu sani ba, daga gurin aiki nazo.” Ya kalle ta, “Dama ke ki ka sa min dazu?” Cikin zolaya ya tambayeta. Ta yi dan murmushi. Ya ce, “Shi yasa ban ji zafi ba.” Ta dauki abin neman jijiya. Ya miko hannu yana murmushi yana kallonta cikin ido. Ta ce, “Ba wannan hannun ba ya kunbura, bai daina kallonta ba ya miko daya hannun. Ta ki su hada ido ta daure masa hannun, sai ya ce “Ash!” alamun zafi. Ta kalle shi da sauri, sai ya daga mata gira. Ta kalli su Hajiya da ke kallonsu, ta dauki auduga tana shafawa don jijiya ta fito, ta dauki allura ta tsira. Jini yana biyowa ta kalle shi. Ya sake kashe mata ido. Ta jona masa ruwan ta daidaita. Ta dube shi “Ka aje hannu da kyau, kada ya sake gocewa.” Ya ce, “To my love.” Ji tayi tamkar kasa ta bude ta shiga don kunya Ta kalli gurin su Hajiya, “Allah Ya kara sauki, zan tafi.” Suka ce “Ki gaida gida.” Kaka ta ce “Allah Yayi miki albarka, kai ka huta ga ma aikaciyar jinya a gida, in larura ta samu ba a fata ba sai an je asibiti ba. Aliya dai ta kalli Amna ta ce, “Ku gaida gida, an gode.” Amna ta dago kai ta dubi Aliya, da ido tayi alama tare da dan daga kai. Ta kalli Nafisa, “Sai anjima, Allah Ya kara sauki.” Nafisa taja tsaki, hakan ya ba kusan duk wanda ke dakin haushi har da Mamanta. Su Amna suka fita don yin sallar La’asar a Masallacin asibitin. Nan take Kaka ta shiga yiwa Nafisa fada, ta ya ya ‘yar uwarki tana miki sallama ki ka ja mata tsaki? Sai ta ce, “Kaka ina ruwanta da ni, ni fa ban kula kowa ba tunda nazo.” Shatima ya dubeta fuskarshi babu walwala, “Kije gida na gode kawai.” Mamanta ta ce, “Ai ita sakarya ce, shegen kishi ta dora ma ranta.” Hajiyarshi ta ce, “Nafisa ai dole kuwa ki koyi hakuri da danne kishi tun da Allah Yasa ba ke kadai ce za ki zauna ba.” Fuu! Ta fice ta nufi gida._____ *🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 13 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* ```🧕🏻🧕🏻Ina kuke kasaitattun mata, Hajiyata kada ki bari ki zama bora agidan auren ki yi kokari ki tsuma kanki da ingantattun magunguna na gyaran jiki 07032895551🍉🍉🥥🥥``` ```Mun zo maku da ingantattun magunguna masu kyau da inganci akwai TABAJE mai kyau gangariya 5litres 5k 07032895551``` ```Muna da hadin Abulbulo, akwai Dan saudiya Hajiyata kada ki bari wannan hadi ya wuceki,dagajin sunan ABULBULO kinsan akwai aiki 4k ne kudin shi🙈🙈``` ```Akwai sa Buzu Kuwwa,muna da kafi Budurwa uku sai angwada akansan na kwarai``` ```🗣️🗣️🗣️Ina matan da mazajen su kebin matan banza to matso kusa Hajiyata Muna hadi na musamman duk macen da tayi amfani dashi mijin ta be karajin dadin wata mace, wannan hadi in kinsan kinada kishiya don Allah kada ki siyeshi 8k ne kudin shi🥥🍉``` ```Akwai dahuwar kaza gangariya sai kin gwada Hajiyata zaki bani labari🙈🙈 akwai Dan dakarawa ya matseki tsam ya kuma saukar maki da ni'ima, akwai kafi sugar, kwallin mata dan matsi daya tamkar da dubu kenan🍉🥥``` ```Akwai hadin Zama daram,munada miski mekyau original, akwai dahuwar kaza ta amare da uwar gida🐓🐓🐓 Akwai Sabulun infection ya matseki ya yi maki maganin infection,yasa wajen yayi sulbi Hajiyata``` ```Muna garin katsina Muna aikawa ko ina a fadin Nigeria har ma da makotanmu Niger 07032895551``` ```Sai angwada ake sanin na kwarai, amma don Allah idan baki shirya siya ba kada kiman magana 07032895551 muna bada sari game bukata🙏🏻🙏🏻``` Mun tsaya Sai ta ce, “Kaka ina ruwanta da ni, ni fa ban kula kowa ba tunda nazo.” Shatima ya dubeta fuskarshi babu walwala, “Kije gida na gode kawai.” Mamanta ta ce, “Ai ita sakarya ce, shegen kishi ta dora ma ranta.” Hajiyarshi ta ce, “Nafisa ai dole kuwa ki koyi hakuri da danne kishi tun da Allah Yasa ba ke kadai ce za ki zauna ba.” Fuu! Ta fice ta nufi gida. Su Amna suna dawowa suka soma shirin.. tafiya. Shatima ya ce, “Ni dai ba ni ki ka zo dubawa ba.” Ta ce, “Waye ne nazo dubawa?” Ya ce, “Kin zo danna waya ne da zama a waccan kujerar.” Ta ce, “To ina zan zauna?” Ya nuna bakin gadonshi. “Ga guri nan.”Ai tafiya zamu yi, tunda ka ji sauki. Haka ma ya yi min dadi.” Ta fada cikin yake. “Ban gaji da ganinki ba.” Ya fada yana kallonta. Ta ce, “To kayi ta kallona na minti biyu.” Anty tayi dariya ta fita. Kaka ta ce, “Ikon Allah! Yaran yanzu ba kara.” Amna ta ce, “Kaka ban ce komai ba.” duk suka sa dariya, sannan suka fice. Rakiya gurin mota har da Hajiya. Zuwa washegari Shatima yayi sarai. Da safe iyayen sun zo duba shi, don Mustapha ne ya kwana. Ganin jikin nashi, shi ne ya ba su damar saka shi tsakiya suna tambayarshi wannan damuwa da Likita ya ce za su nesanta shi da ita. Shatima ya yi shiru. Hajiya ta ce, “Haba Shatima, kana son saka mu a cikin damuwa ko?” Yayi murya irin ta yaron da ke gaban iyayensa irin ‘yan gatan nan.Ya ce, “Ku bar shi kawai, ko na fada ba lallai ne ku amince ba.” Alhaji ya ce, “In kaga ba a amince ba to abin ya shafi addini ko mutuncinmu.” Shatima yayi shiru don dai ya dan kara ja musu aji. Alhaji ya ce, “Kayi magana mana Babana.” Shatima ya ce, “Wata yarinya ce ni ke son in cike ta hudu da ita su Hajiya suka ce a’a, kuma ni gara in fasa auran duk ukun nan in aureta ita daya. Yanda ni ke ji kamar zan rasa raina…” “Kai yi mana shiru!” Hajiya ta katse shi. “Na ce ban yarda ba da karin wani aure.” Shatima ya koma ya kwanta a hankali, bai ce komai ba.Alhaji ya dubi Hajiya, “Wai kin manta da zancan Likita ne?” Ya sake matsowa kusa da Shatima. “Babana ‘yar gidan wane ne?” Shatima ya ce, “Alhaji marainiya ce, ubanta ya mutu. Na yi ma Allah alkawarin kula da ita, aurenta shi ne zai fi bani damar lura da ita, domin zata kasance kusa da ni, in ko na barta na ce zan ke taimaka mata, kila wani lokaci yazo wani yanayi na daukaka ko akasin haka ya sani in manta da ita. Wannan ce damuwata, in har zan samu yardarku zan zama a cikin farin ciki mai dorewa.” Hajiya ta ce, “Ka san Allah…” Alhaji ya daga mata hannu tare da cewa “Kiyi min shiru.” Ya kalle shi, “Yaushe ka ke son aje zancen auren?” Ya ce, “In an sallame ni gobe ko zuwa jibi ne sai aje. ” Ya ce, “Shi kenan ka Kaddara cewa ka aureta an gama.” Ya kalli Hajiya, “Na haramta miki sake ďauko zancan nan in dai na isa.” Kwafa tayi sannan tasa kai ta fice daga dakin. Alhaji ya ce, “Kar ka damu, zata sauko da zaran na lallasheta. Zan sanar da Babanka Musa sai aje gidan iyayen yarinyar, sun san dai da kurewar lokacin ko?” Ya ce, “Sun sani.” Ya ce, “To ba ka da sauran damuwa in dai wannan ce. Yanzun dai zan wuce da Hajiya gida, ku ci gaba da zama da Mustapha in ta huce zata dawo.” Suna tafiya ya dauki wayarshi ya kira Munnir ya ce yana gurin aiki. Shatima ji yake kamar a sallame shi yaje yayi aikin da zai saka Munnir. Haka dai ya hakura har karfe biyar, Munnir ya taso. Ya ce “Don Allah yana son yaje gidan su Salma ya bata wayarshi zasu yi magana.” Munnir bai so ba amma ba ya son ya bata masa rai, tunda duk sun ji labarin abin da Likitan ya ce a kansa, ya tafi. Yana zuwa kofar gidan Yayanta yana fitowa. Suka gaisa, ya ce “Ina Alhajin yau?” Munnir ya ce, “Shi ne ya aiko ni, ina yarinyar nan?’ Yaya Auwal ya ce, “Umma Salma tana ciki, bari in kira ta.” Duk zatonshi Munnir ne mijin da Shatima ya ce zai kawo mata, har yana fada mata. “Kin gane abokin nan nashi? Ina jin shi ne zai aure ki. amma kije ki gani.” Tare suka fito, ta gaishe shi tare da tambayar Alhajin. Ya ce “Shi ne ma ya ce in nazo in kira shi za kuyi magana.” Ya soma kiran layin Shatima. Shi ko Yaya Auwal yana can gefe yana lura da su saboda tsaro. Shatima ya daga wayar Munnir ya mika mata tare da fadin. “Gashi.” Ta amsa tayi sallama. Shatima ya amsa. Ya ce, “Salma.” tace”Na’am! Yaya.” Ya ce “Ina Yayanki Auwal?” Ta ce, “Gashi can tsallaken titi.” Ya ce “Kira shi ki ba shi wayar.” Ta kalli gurin da Auwal yake suka hada ido. Ta yafito shi da hannu alamun yazo. Ya zo, ta ce “Yaya zai maka magana.” Auwal ya ansa tare da cewa “Alhajin ne?” Bayan sun gaisa ya ce, “Salma ta ce min haya ku ke yi ko?” Ya ce, “Eh haya ne Alhaji.” Shatima ya ce, “Ina wanda gidan ke hannunsa?” Ya ce, “Makocinmu ne.” Shatima ya ce, “Ina son ya samo muku wani gidan hayar za ku tashi a wannan gidan, ko ba ya nemowa?’ Auwal ya ce, “Yana yi.” Shatima ya ce, “To ina son duk yanda za’ayi gobe a samu gidan da zaku koma saboda za a zo neman auran Salma. Ka amshi lambata a hannun wannan abokin nawa, koda wayar wani ne ka kira ni ka fada min. Auwal ya ce, “To Alhaji, Allah Ya saka da alkairi.” Shatima ya ce, “Ba komai, ba Salma to.” Ya kalli Munnir ya ce, “Ka bani lambarsa.” Ta amsa ya ce “Sai ma na fada ma Yayanki ne zaku canza gidan haya kin ji ko?” Ta ce, “To Yaya.” Naji muryarka kana yin mura ne? Ya ce, “A’a na gaji ne, abubuwa sun yi min yawa ba ki ganni ba, zan zo.” Ta ce, “To Yaya amma yaushe ne za ka zo din?” Ya ce, “Ko jibi haka, kada ki damu ba Munnir wayar ta ce to sai anjima.” Ta mika ma Munnir tare da fadin “Gashi Yaya.” Ta dan durkusa ta bashi. Suna tsaye ya tafi, Auwal ya ce, “Muje ciki muyi magana da su Inna.” Auwal ya fada musu abin da Shatima ya ce.. Inna ta ce, “Kai ku tsaya! Ni fa ina tsoran wannan al’amari, kar fa garin son abin duniya mu sa kanmu uku! Yanzu in tsakani da Allah za’ayi ga inda aka ganta ba za a zo neman auranta nan ba?” Yaya Auwal ya ce, “Inna babu kyau munanan zato, mu fa ya ce mu nemo gidan hayar zai biya. Kuma manyan mutane ne za su zo kin ga ai mu ma ba za mu so su same mu a kaskance ba.” Yaya Hadiza ta ce “Inna yanzun dai a bar wannan zance a nemi índa za’a samu gida tunda dama kudinmu ya kare tun wancan watan. Masu gidan suna ta yi mana rashin mutunci. Salma ta ce, “Allah ne ya kawo mana mafita dama muna ta ya ya za a yi a samu dubu sha biyu da za a baiwa masu gida? Suka ce, “Haka ne kam!” Auwal ya ce “Ina ga ba zan yiwa Maigidan nan maganar wani gidan ba, gara in je in sa samu Bala dillali. Hadiza ta ce, abin da zance kenan, ba za’a rasa gida a hannunshi ba.” Ya mike “Ina zuwa ma dai ku gani, da zafi zafi a kan bigi karfe. Cikin sa’a Bala ya ce masa “Akwai gida guda biyu, daya na zaman mutum uku, daya kuma na zaman mutum biyu. Daki nawa za ku kama?” Auwal ya ce, “Daki biyu ma ya ishe mu.” Bala ya ce, “To me zai hana ku kama gidan can na kusa da ku, gidan dan kurma wanda ya saida Auwal ya ce Matsalar dai biya mana za’ayi kila kudin ya yi yawa ko?” Ya ce, “Dari ne da goma sai mu da za’a sallama.” Auwal ya ce, “A dai yi mana sauki mu gani.” Ya ce, “To magana daya dubu tamanin ne, sai mu kuma a sallame mu.” “To duk yanda aka yi zan same ka gobe.” Bala ya ce, “In kuma na wancan ku ke so daki biyu dubu talatin da biyar ne. Auwal ya ce zan fada masa duka. Haka kuwa sai washegari da misalin karfe goma Yaya Auwal ya kira lambar da ke jikin katin da Munnir ya bashi.. Shatima ya daga, ya ce Ni ne Auwal lambar Alhaji ce? Shatima ya gane ya ce, “Ni ne.” Ya kalli Mustapha da ke hada kayan su don Likita ya fita yanzun bayan ya sallame su. Ya ce, “Kaje waje. Bayan fitarsa Shatima ya ci gaba da magana. “Auwal ka samu gidan?” Ya ce “An samu alheji.” Ya fada mishi farashin su. Ya ce, “To ku kama naku kadai din zan ba abokina dubu dari ya kawo muku anjima, in da dan wani gyara sai kuyi.” Auwal ya shiga godiya, Shatima ya kashe.” Nafisa tana isowa asibitin suna fitowa. Ta ce, “An sallame ku ne? Suka ce “Eh.” Don haka tare suka juya. Da suka isa gida Hajiya ta ce “Kar ya hau samanshi, a bude masa falon Babansu saboda mutane za suke zuwa duba shi. Ya yi Transfer din dubu dari a cikin account din Munnir. Ya ce, “Ya cire ya kaima su Salma. Da ya taso aiki kuma ya ciro yazo ya yi sallama da Salma ya bata..Ranar kuwa suka biya kudin gidan aka ba su mukullin. Ranar suka share, washegari da safe, suka dan yi saye-sayen labule da ‘yar ledar kasa suka tafi suka gyara suka shiga. A daren ranar Alhaji da dan’uwansa Alhaji Musa Baban su Nafisa, suka zo gurin Shatima suka ce, “Batun wannan yarinya za a je gurin iyayenta. Shatima ya ce,. “Su bari sai washegari. Da yammacin washegari kuwa Shatima yayi fes cikin kananan kaya, in ka ganshi dole ya birge ka ya dauki makullin mota ya fita. Hajiya ta ce, “Ina zaka?” Ya ce, “Zan dan zaga gari ne, na gaji da zaman gida.” Ta ce, “To sai ka dawo.” Kai tsaye gidan su Salma ya dosa, cikin zuciyarshi yana son in ya zo gidan su nada ya tambayi inda suka koma. Cikin sa’a ma yana fitowa sai ya ji Auwal yayi masa sallama. Ya waiwaya ya bashi hannu suka gaisa, ya ce “Ai ina can naga wucewar motarka.” Shatima ya ce, “Ina ne gidan naku?” Auwal ya ce, “Baya ne kadan.” Ya ce, “To shiga muje. Ya ji dadin ganin gidan har ciki ya shiga. Su Inna da sauran ‘yan’uwansu da basu wuce ba suna ta godiya. Ya samu Salma tana wanke wanke ta saki tazo ta tsugunna ta gaida shi. Ya ce, “Salma nan yayi?” Ta ce, “Kai! Sosai ma.” Cikin mamaki tayi maganar. Ya dubi Inna, “Gurin wa za a zo neman auran na Salma, saboda anjima za sú zo?” Inna ta ce, “Gurin kanin Babansu ne a can Kofar kaura ya ke, in an ji lokacin da za su zo sai a je a dauko su da aminin Babansu nan makotan da muka taso.” Shatima ya ce, “Yau za su zo karfe takwas na dare Sannan kuma Inna bikin yau saura kwana ashirin da biyar.” Inna ta ce, “Kamar ya ya?” Ya ce “In sun zo iyayen namu za ku ji komai.” Ta ce. “To shi kenan, Allah Ya kawo su. Shi kuma Kawun nasu za a je a zo da shi.” Da zai tafi ya ce Salma ta zo, a zauren gidan suka tsaya. Ya kalleta yana murmushi. “Kin shirya aure nan da kwana ishirin da biyar?” Ta dan juyar da fuskarta cikin kunya ta kalli bango. Ya ce, “Kiyi magana.” Ta ce. “Zan yi mana.” Ya ce “To juyo ki kalle ni.”_____ *🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 14 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* ```🧕🏻🧕🏻Ina kuke kasaitattun mata, Hajiyata kada ki bari ki zama bora agidan auren ki yi kokari ki tsuma kanki da ingantattun magunguna na gyaran jiki 07032895551🍉🍉🥥🥥``` ```Mun zo maku da ingantattun magunguna masu kyau da inganci akwai TABAJE mai kyau gangariya 5litres 5k 07032895551``` ```Muna da hadin Abulbulo, akwai Dan saudiya Hajiyata kada ki bari wannan hadi ya wuceki,dagajin sunan ABULBULO kinsan akwai aiki 4k ne kudin shi🙈🙈``` ```Akwai sa Buzu Kuwwa,muna da kafi Budurwa uku sai angwada akansan na kwarai``` ```🗣️🗣️🗣️Ina matan da mazajen su kebin matan banza to matso kusa Hajiyata Muna hadi na musamman duk macen da tayi amfani dashi mijin ta be karajin dadin wata mace, wannan hadi in kinsan kinada kishiya don Allah kada ki siyeshi 8k ne kudin shi🥥🍉``` ```Akwai dahuwar kaza gangariya sai kin gwada Hajiyata zaki bani labari🙈🙈 akwai Dan dakarawa ya matseki tsam ya kuma saukar maki da ni'ima, akwai kafi sugar, kwallin mata dan matsi daya tamkar da dubu kenan🍉🥥``` ```Akwai hadin Zama daram,munada miski mekyau original, akwai dahuwar kaza ta amare da uwar gida🐓🐓🐓 Akwai Sabulun infection ya matseki ya yi maki maganin infection,yasa wajen yayi sulbi Hajiyata``` ```Muna garin katsina Muna aikawa ko ina a fadin Nigeria har ma da makotanmu Niger 07032895551``` ```Sai angwada ake sanin na kwarai, amma don Allah idan baki shirya siya ba kada kiman magana 07032895551 muna bada sari game bukata🙏🏻🙏🏻``` Mun tsaya Shatima ya ce, “Yau za su zo karfe takwas na dare Sannan kuma Inna bikin yau saura kwana ashirin da biyar.” Inna ta ce, “Kamar ya ya?” Ya ce “In sun zo iyayen namu za ku ji komai.” Ta ce. “To shi kenan, Allah Ya kawo su. Shi kuma Kawun nasu za a je a zo da shi.” Da zai tafi ya ce Salma ta zo, a zauren gidan suka tsaya. Ya kalleta yana murmushi. “Kin shirya aure nan da kwana ishirin da biyar?” Ta dan juyar da fuskarta cikin kunya ta kalli bango. Ya ce, “Kiyi magana.” Ta ce. “Zan yi mana.” Ya ce “To juyo ki kalle ni.” Ta juyo ta dube shi. Ya ce, “Kina sona?” Ta zaro ido cikin tsananin mamaki. Ta murtsuke idanunta wai ta ga ko mafarki take yi. Ta sake kallonshi a gabanta. Ta cce “Nasan kana tsokanata ne, ni ban fi yar wanke-wanken gidanka ba.” Ya ce, “Ni fa na tambaye ki ne kawai, kina sona?” Ta durkusa kasa, “Don Allah kada ka cutar dani, wallahi na dauke ka na musamman a rayuwata, na soma tsoron ka.” Hawaye suka zubo mata. Ya tsugunna shima, “Ba ki sona dai a takaice kenan ba za ki aure ni ba?” Ta dago ido, suka kalli juna hawaye suna sauka a kan kumatunta. “Ni ina sonki, kuma zan aure ki, kuma za ki yi karatunki har ma ki cika burinki na zama ‘yar Jarida. Ki ci gaba da daukana na musamman a rayuwarki, koda ba ki sona.” Ya mike tsaye. “Sai dai ke ce ta hudu da zan aure ku rana daya.” Ta mike tsaye, “Don Allah ka fada min wani zancen daban ba da wadannan zantukan na. zolaya ba.” Yayi murmushi, “Na tafi zan sake zuwa.” Nan ya bar ta tsaye tana al’ajabi. Ta jingina da bango, ba zan fada ma kowa wannan zancen ba, don na san ba gaskiya yake fada min ba. Ta share idanunta ta nufi cikin gidan ta ci gaba da harkokinta, tana jin su suna tattauna zancen dauko kanin Babansu. Ta ce a ranta ‘Ni dai zan ga ikon Allah!’ Daga nan gidan Anty Momiyo ya nufa, ta kai shi dakin da a kwatunan suke. Yayi murna da ganin su don sun birge shi. Ya ce, “Yanzun nawa ne cikona da Allah kai su yau, zuwa jibi a kai ma kowa kayanta.” Anty Momiyo ta ce, “Ai ba don ciwonka ba yau muka tsara za a kai kayan amma jibin ma ya yi. Ya ce, “Nawa ne ciko na?” Ta ce, “Hajiyar ku ta biya kudin ukunnan, tace ba za ta bada na karshen nan ba, shatima ya ce Au! Ta sai min ne? gaskiya ta min komai. To. ki cire kudin na Salma din, sai ki bata canji. Ta ce, Ta ce tuni na cire har ma nayi maka karambani.” Ta janyo wata Ghana most go wasu lesuka ne masu shegen kyau, ta ce “Ka gan su guda goma sha biyu ne kowacce guda uku. Ya ce, “Ai da kin bani kudina don na ba Hajiya kudin komai.” Ta ce, “Duk dai ba zai ki ba.” Ya ce, “Bari ma in je in samu Hajiyar muji ya za ayi?” Ta ce, “To muje da akwatunan mana. Ka dibi wasu nima in diba a mota ta muje ya ce “To.” Yasha mamaki da Hajiya ta fito da kayan da aka siya. Sai dai ta ce ita na mutum uku ne, sai, yasan yanda zai yi da dayar. Ya ce, To bari in bada kudi itama sai a kawo mata.” Hajiya ta ce, “Sam! Je kasuwa ka siya. Yayi shiru yana kallon kayan. Anty Momiyo ta ce, “Kana zuwa kasuwa za ka hada komai.” Ya ce, “Anty ku ne ku ka san kayanku. To ke don Allah in ba ki ki sai mata tace yawanci kayan nan ba ‘yan nan ba ne ba, lallai a samu irinsu ba. Amma ka kawo sai a duba.” Hajiya tana jin su kala bata ce ba. ya ce, “Zan yi miki Transfer cire mata kukan ta kija mata cikin akwatin ta kada kuma ta ce ban da ita marainiyar Allah. Take ya tura mata kudi don ta sai ma Salma kayan lefeb Lefen Amna a ka soma kawai kafin ranar sai da ya sanar da ita zuwan su Hajiya kuma sai da ta sa kayan Amna sun fi na kowa a cewarta babban goro sai magogin karfe. Suma sun samu sauka ta musamman sannan sun dauko tukuici mai tsoka. Washegari aka kai na Nafisa. Nan ma sun yi bajintar tukwici. Na Aliya ma an kai, suma sun ba da daidai karfinsu. Aka dawo ana ta tsegunguma. Salma kuwa cewa yayi a bari zai kai mata, don ya ji lokacin da Hajiyarshi ta kira Baba Alhaji Musa tana tambayar shi game da Salma, bayan sun dawo kai sadaki da kudin gaisuwa. Wai nawa suka bada? Ya ce, “Dubu hamsin suka ce kudin gaisuwa ashirin.” Ta ce,”Wai an binciki asalin yarinyar?” Ya ce, “Shi ya ce ya bincika.” Ta ce, “Yasan ‘yar matsiyata ce shi yasa baya so aje gidan, ai za a kai lefe, za’a zo min da labari.” Shi kuma yana falon bata san ya shigo ba, don haka sai ya juya. Ranar da za’a kai na gidan su Salma ya ce su bar shi shi ne zai kai. Hajiya ta ce, ai ko dole a kai. Ya ce, “Hajiya kiyi hakuri zan kai mata da kaina.” Alhaji yace, “Wannan fa al’ada ce, don haka ki har shi kawai.” ya kai da kanshi. Bayan ya kai ya baro gidan, Inna ta ce “Kai Hadiza! Ku lura da lamarin nan da kyau. Ba shi da dangi ne zai kawo lefe da kansa! ni fa ina tsoron in’kai ‘yata mahallaka da kaina?” Hadiza ta ce, “Ni dai ban tsorata ba, ai ba boyayyu ba ne. mu dai yanzun mu san ya ya zamu yi da wannan kudin, a sai mata gado da ‘yan kujeru.” Salma dai bata magana, domin har yau gani take ba’a ne duk da kayan da aka kawo masu tsada na lefe, da kudin dinki Naira dubu dari. Sun yanke a cire ishirin tayi dinki, tamanin a hada da saba’in a sai mata kayan daki da na aiki, tun dai daga wannan ranar har yau Salma bata kuma sa shi a idonta ba. Domin ko da ya kawo kayan lefe bata nan taje cefane, gashi har yau saura kwana goma biki cif-cif! Tun sassafe ranar Amna ta kira Shatima tana ce masa yau ‘yan gidansu za suje jere can Kaduna. Ya ce, “Ai tuni na ba da makullai ko?” Ta ce, “To honey ai ba wanda yasan gidan ka manta?” Ya ce “Au! Haka ne, to su biyo ta gidanmu sai su dauki kananina Mustapha.” Ya sauko kasa ya shiga gurin Hajiya ya sanar da ita. Ta ce, “To ai ba dan rakiya za’a basu ba, ka dau har da abinci.” Nan tayi waya in da ake yo musu abincin sha’ani, tasa ayi abinci na alfarma da kaji. Lokacin da suka iso daukar Mustapha har abin sha da na cin an shirya, suka kwasa suka wuce. Shatima ya ce musu za su ga plat guda hudu duk wanda suke so su zaбa. Na ciki suka zaba wai saboda tsoro. Mustapha dai yasha mamaki, domin sabon aiki yaga an tsiro ma gidan an canja fenti, sannan ga wallpaper irin na zamani an zuba a bangon tun ma kafin kayan su iso guri tsaf. An zuba kaya fadin su ma kauyanci ne, kayan kicin kuwa irin masu amfani da lantarki abin sai wanda ya gani. Dakuna guda uku kowanne an saka mishi gado na alfarma. Daidai da kayan bayi abin ba da labari. Hajiya ta ce, “Ni nasan za’ayi haka. Ai harkar manya ba karya.” Duk a ranar daí Ango yayi niyyar kai ma duk Amaran nashi da ke nan Zaria kudin walima shi da abokanshi. Abu daya ke damunshi yanda bai samu ya fayyace ma sauran Amaren cewa sun cika su hudu ba. Nafisa ita ce yake da yakini a kan cewa ta sani domin ta kira shi bai daga ba, sai tayi masa message cewa ya daga wayarta suyi magana, tana son tabbatar da abin da taji Babansu yana fada ma Mama. Ya ki dagawa sam! Ya sani sarai tana zaman jiranshi. Gidan su Aliya suka soma zuwa shi da Munnir da wani abokinsu Usman. Cikin sa’a kawarta Aisha tazo ganin lefe, sai suka fito tare. An gaggaisa sannan ya bata dubu talatin ya ce, kudin walima, sannan suka bata katina na daurin aure, sai na dinner din da zasu yi bayan an kai Amarya. Aliya tayi ta masa godiyar kudi har sai da ya ce, ta bari don Allah. Bayan barin su gurin ne abokan suke yabon halin Aliyan, suka ce daga gani tana da hankali kuma zai ji dadin zama da ita. Gidan su Nafisa suka tafi. Gabanshi yana ta faduwa. A harabar gidan suka tsaya. Ya kira ta a waya, har sau hudu amma bata daga ba. Yaje ya kwankwasa kofar falon. Momi ce ta bude. Ya ce, “Kira min Nafisa.” Ta ce, “To.” Sannan ta gaishe shi ta juya. Sun kusa minti hamsin har ran Shatiman ya soma baci, bata fito ba tana can Mama tana fama da ita a kan ta fito ta ki, sai da taga ran Maman ya baci sannan ta tashi ta dauki dan mayafin doguwar rigar da ke jikinta, ta saka takalmi mara tudu ta fita. Har ya ce su shiga mota su tafi sai ga ta ta fito kamar tana tafiya a kan kwai. Duk da cewa dare ne, kallo daya za ka gane ba walwala a tare da ita. Ta gaida su gaba daya a tare, Shatima bai amsa ba illa kallonta da yake yi tare da tunanin me ma zai ce mata? Munnir da Usman suka koma cikin mota. Ya cc, “Kudin walima da kati na zo ba ki.” Tayi shiru tana kallonshi. Yaje motar ya ce, “Ku bani katunanta.” Ya mika mata ta ce, “Ka bar shi, ni ba zan yi wata gayyata ba.”Ya ciro kudin ya cc, “To ga kudin walimar ko itama ba za ki yi ba?” Ta ce, “Eh ba zan yi ba.” cikin bacin rai ya ce, “Ok.” Ya wuce ya shiga mota ya ce, “Ku muje.” Nan suka bar ta tsaye sai kuma ta soma kuka. Tsakin da ya yawaita yi ne yasa Munnir tambayarshi abin da ya faru. Ya ce, yarinyar nan wai ni zata yi wa fushi? Ta ki amsar komai ita ta sani.” Munnir ya ce, “Nafisa tana kishinka da yawa ne.” Ya ce, “Ai wannan shirme ne ba kishi ba, tun kafin a zo zama zata soma haka?”Usman ya ce; “Ba dai ka ce zaka hadiyi Gatari ba?” Suka sa dariya. Shi dai Shatima bai ce musu kala ba. sai da suka hau titi sannan Usman da ke tuki ya ce, “Ina muka dosa?” Shatima ya ce, “Muje ku aje ni a gida.” Munnir ya ce “Salma fa ba za a kai mata ba?” Ya ce, “Zan kai mata gobe.” Washegari da sassafe da zai tafi aiki, shi ne ya tsaya a unguwar su Salma. Umar kaninta ya fito za shi siyan kosai yaga Shatima, shi ne ya nufe shi yana yi masa sannu da zuwa. Ya rusuna ya gaida shi, Shatima ya tambaye shi, “Salma fa?” Ya ce “Tana ciki.” Ya ce, “Kira min ita, ka ce tayi sauri zan tafi office ne a Kaduna.” Cikin sauri ya juya ya kira Salma da karfi. Ta fito daga kicin tana cewa, “Kai! Mene ne?” Ya ce, “Alhaji ne a waje, ya ce kiyi sauri yana jiranki.” Ta kalli jikinta, zanin tsoho ne gashi tana kauri. Tun da Allah Ya hada su yau ce rana ta farko da ta soma kallon jikinta don zata kiranshi. Inna ta ce, “Ki canza zani mana ga na Hadiza nan a kan kofa da ta manta jiya, ki daura mana.” Ta janyo shi ta daura ta zira hijabi ta fita. Numfashinta ya tsaya cak! Da ta ganshi tsaye jikin mota sanye da suit masu ruwan toka, idanunshi sanye da bakin gilashi. Ya ce “Iso mana, sauri nake yi.” Ta durkusa ta gaida shi, ya ce “Mike muyi magana.” tashi. Ya ciro katuna daga mota ya mika mata. “Ta “Na daurin aure ne kawai babu na dinner. Sannan ya bata dubu talatin “Wannan koda za ki yi walima da kawayenki.” Ta ce “Sun yi yawa Yaya.” Ya ce, “Haka na ba sauran.” Ta kalle shi zata sake magana ya ce, “Ki je gida ina sauri ne naga bakinki da magana, lokacin yinta yana zuwa amma ban da yau.*🏚️ RANA DAYA🏚️* CHAFTER 15 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya Ya ce “Iso mana, sauri nake yi.” Ta durkusa ta gaida shi, ya ce “Mike muyi magana.” tashi. Ya ciro katuna daga mota ya mika mata. “Ta “Na daurin aure ne kawai babu na dinner. Sannan ya bata dubu talatin “Wannan koda za ki yi walima da kawayenki.” Ta ce “Sun yi yawa Yaya.” Ya ce, “Haka na ba sauran.” Ta kalle shi zata sake magana ya ce, “Ki je gida ina sauri ne naga bakinki da magana, lokacin yinta yana zuwa amma ban da yau. Bai saurari abin da zata ce ba ya shiga mota, ta juya ta shiga gida. Biki saura sati daya aka je aka yi wa Nafisa jere itama. Aliya kuma washegari ana saura kwana shida. Duk kowace an yi mata bakin rabonta. Nafisa itama dakunan nan an zuba gadaje, sannan kicin da falo suma an yi babu laifi, don yafi na Aliya tsada ita gado biyu ne, dayan dakin aka sa katifa. Amma duk ba wadda ta kama kafar Amna. Ita ko Salma daidai wannan lokacin suna can suna ta ganganda yanda za a sai kaya. Gidan Gaje Dillaliya suka je in da suka samu gado da kujeru na hannu aka sake musu feshi, sai suka sai sabuwar kati fa da zannuwan gado. Sai kuma kayan girki abin da ba a rasa ba. Suna dan matsewa ne don su samu na siyan gara. Don ma Salma ta ba da kudinta na walima, ta ce ba zata yi walima ba tunda Babanta bai dade da rasuwa ba, babu wani taro da zata yi. A son Amna tun Laraba yaje mata, amma ya bata uzirin nasa shirye-shiryen da abokansa, ya ce tayi hakuri sai Alhamis zai zo ya kai har Asabar ya dawo saboda zata yi abubuwa da dama, ya dai halarci biyu. Ta ce, “To, babu komai.” Ko’ina ya kacame da shirin biki ba sauki. Ana ta shirya Amare ban da Salma, wadda tsimi kawai Yaya Hadiza ta bata, sai ci da kaza wadda ba a kawo ba ma. Su ko can Amna sai da tayi sati daya a gidan mai gyaran jiki. Haka- Nafisa har gida kullum mai gyara ke zuwa. Aliya ma dai ana ta dilka. Wata kawarta ke mata, saboda Amna aka maida daurin aure Lahadi, don su Kano sun fi daura aure ranar Lahadi. Tun Laraba suka fara da bikin gargajiya. Amna tasha kyau da kawayenta, washegari Alhamis suka yi ranar Larabawa, sun sha kyau ita da shi cikin shigar Larabawa. Haka abokansa sun je da yawa. Nan hotuna suka shiga zaga duniyar sama ana ta watsa su. Washegari Juma’a aka yi ranar Turawa. Sun fi kullum kyau don kayan da yasa a gidan su Amna aka sai masa. Bai ma san da su ba sai da aka kawo masa. Motar da aka dauke su sabuwa ce dal, an ce kyauta Babanta ya basu an jera mata balan-balan, gata mai tsada. bashi. Washegari Asabar yasa su taho da safe, amma ta roke shi ya bari sai da yamma saboda za suyi Kumbo. Can Zaria ma sun shirya kumbo din, kuma suna sa ran zai zo. Sai dai ita Nafisa bata so wannan kumbon ba dan sam bata gayyaci kowa ba, sai sauran sa’anninta na cikin dangi su ne suka raba katin, kuma suke shirya komai. Ko kudin da ta ki amsa Hafsa ce ‘yar gidan Anty Saude ta kira shi ya turo musu. Abin da ya kara ma Nafisa takaici yanda hotunan shagalin su da Amna yake ta ratsa wayoyin dangi ana ta labari. Bai baro Kano ba sai taran dare shi da tawagarsa. Ya shiga yayi wanka lokacin sha daya daidai. Yana kwanciya sako yana shigowa wayarsa. Shahida ce daya daga cikin ‘ya’yan kanin Alhajinshi, tana nuna mishi rashin jin dadinsu da yanda ya wofintar da nasu shagalin bai zo ba, ga kujerarshi nan babu kowa har aka tashi. Bái tura mata amsa ba duk da yana da amsar maganar, kuma ko yana gari bai zuwa. Ya fasa kwanciya ya sakko zuwa falon Hajiya, yana son yayi magana da Alhaji don a kasa daurin auren domin Kano na safe suke yi. Daidai kofar dakin Hajiya suna tsaye ita da Hajiya Azimi, tana cewa. “Babbar matsalata yanzun na ce miki wannan yarinyar da ya kutsota daga karshe. Nayi-nayi Alhaji ya daure masa gindi. Babu wani binciken asali ba komai, sai ka ce wani mara hankali. Kuma yanda na samu labari an ce matsiyata ne na karshe, kuma an ce kudi yake kashe musu na tsiya. Don haka ina son gobe kafin auran tunda unguwarku ce ki bincika min komai game da su, ni kuma ina son duk yanda za’ayi in hana wannan daurin auran. Yaron nan ba shi da hankali, an fada mishi da kowane gama-gari ka ke hada zuri’a, bare matsiyatan tilis.” Hajiya Azumi ta ce, “In don wannanne kar ki damu, ni da naji kin ce komai dare in na dawo in zo har na tsorata, nayi zaton ko wata gagarimar matsala ce. Ki kwantar da hankalinki, gobe tun safe zan fita da kaina in samo miki komai kafin goman safiya labarinsu ya nuna a gurinki.” Hajiya ta ce, “Ai ko kina da tukwici mai tsoka, na gode Allah Ya kara zumunci. Shi yasa na ce ki zo.” Shatima ya koma cikin mamaki, sam bai zaci Hajiyarshi tana da irin wannan mugun tunani ba, domin yaga suna kokari gurin taimakon na kasa da tausayin marashi. Ya zaci zata fi kowa murna in taji irin taimakon da ya shirya yi. Dama saboda talauci Hajiya ke gudun Salma? Shi kam ya sha alwashi in dai yana raye bai mutu ba, duk irin abin da zai faru goben nan sai ya zama mijin Salma. Allah bà zai ba su Hajiya ikon rusa raya sunnar Manzonsa ba. Tun da ya shiga dakinsa yake safa-da-marwa tare da tunanin yanda zai yi. Katin da suka buga na daurin auren kowanne da lokacin da suka saka. Na Amna sha dayan safe, na Aliya karfe daya bayan sallar Azahar. Na Nafisa Rarfe biyu da rabi, na Salma Karfe uku da rabi, sai walima karfe hudu. Lallai Hajiya tana da ishasshen lokacin da zata tarwatsa komai. Ya zari makullin motarsa ya fita. Kai-tsaye gidan su Salma ya nufa. Sha daya da rabi daidai lokacin su sun rufe gidan ma. Ya kwankwasa kofar, ya jima yana kwankwasawa kafin ya ji takun tafiya. Muryar Auwal ya ji yana tambayar. “Waye?” Ya ce, “Ni ne Shatima, wanda zai auri Salma.” Tsoro ya kama Auwal, kar dai mutumin nan fa mugu ne ta bakin Innarsu…ya ce, “Lafiya?” Shatima ya ce, “Lafiya lau, ka bude.” Auwal ya bude cikin faduwar gaba da addu’o’i a cikin zuciya. Shatima ya ce, “Yanzun zamu iya samun waliyin Salma?” Auwal ya ce, “To ban dai sani ba Allah yasa lafiya?” Shatima ya ce, “Ba an ce kanin Babanku ya bar ma aminin Babanku waliccin ba?’ Auwal ya ce, “Eh haka ne.” Shatima ya ce, “To muje mu duba.” Auwal ya ce, “Amma Alhaji lafiya?” Ya ce, “Muje za ka ji.” Sun kwankwasa Allah yasa shigarsa ke nan gidan ya fito. Shatima ya gaida shi, sannan ya gabatar da kanshi. Ya ce, “Alhaji lafiya?” Shatima ya ce,”Dama nazo ne saboda maganar daurin auren nan gobe, za a dawo da shi da safe saboda akwai wani daurin auran a Kano wanda za su tafi.” Waliyin Salma ya ce, “Wannan ba wata matsala, Allah Ya kai mu.” Shatima ya ce, “Amin. Karfe takwas na safe.” Waliyin ya ce, “Gashi dare ya yi bare aje a sanar da shi kanin Mahaifin nasu. Kai Auwal gobe da sassafe sai kaje ka zo da shi.” Auwal ya ce, “Babu komai, Allah Ya kai mu.” Suka koma, ya sauke Auwal a kofar gida, suka yi sallama. Sha biyu daidai ya koma gidan kamar ya shiga gurin Alhajinsu, sai kuma ya fasa. Ya daga wayarshi ya kira layin Alhajin. Bai zaci za’a daga ba, nufinshi ya bar missed call da asubahi yasan Alhajin zai neme shi. Alhajin ya katse mishi tunani da cewa, “Ya ya dai Babana?” gaban Shatima ya fadi, da wata zuciyar ta ce mishi in kuma suna tare da Hajiya fa? Cikin sauri Shatıma ya ce, “Dama ina son zamu yi wata magana ne, tunda ka shiga mu bari sai da Asubahi. Alhaji ya ce, “Ka gani ba za ka hana ni bacci ba, in ta sake-sake, fada min kowace magana ce.” Ya ce, “To ko in sakko ne kawai don tun dazu ni ke nemanka.” Ya ce, “Eh sauko, ina can tare da su Alhaji Amadi sun zo daga Sokoto, masaukin bakin Alhaji Nadabo muka kaisu, su da su Alhaji Na Allah duk sun iso. Shatima ya ce, “To gani nan.” Suka hadu a falo. Yayi ta waige-waige Alhaji ya ce, “Lafiya?” Shatima ya ce, “Bana son Hajiyarmu taji ne, don zata-ce komai sai in ce yarinyar nan. Dama mun canza lokacin da zamu yi walima ne da abokanmu saboda akwai wadanda za su koma garuruwansu a goben shi ne muka dawo da walimar baya, sai muka maida daurin auren Salman na safe karfe takwas.” Alhaji ya ce, “Babu damuwa, zan kira iyayen naka in fada musu, ana gama daurin auren natan sai a wuce Kano din kawai, tunda kila sai an kai tara a gurin ko ma fi.” Shatima ya ce, “Haka ne. na gode Alhaji, Allah Ya kara girma.” Ya ce, “Babu komai, kaje ka kwanta, zama ka iya bacci kuwa yau?” Alhajin ya zolaye shi.Shatima yayi ‘yar dariya. Ya ce “Shi yasa na baro masaukin abokaina nazo gida ko zan runtsa.” Ya ce, “To sai da safe.” Ya zauna bakin gado yayi shiru, gobe kamar yanzu ya zama Angon mata hudu, A fili ya ce “Allah Kasa wannan abin da na shirya ya yiwu, don ban san me Hajiyana ke shiryawa ba.” Idanunshi sun kasa runtsawa har kusan biyun dare, sai kawai yaga bari ya tashi yayi Ibada. Ya roki Allah sosai ya albarkaci auren nashi, ya ba shi ikon cinye jarabawar da ke cikin auran nashi, ya dora shi a kan matan nashi, ya kuma ba shi ikon sarrafa su. Ya dauki wayarshi bayan ya idar ya sake karanta sakon Shahida, yayi shiru yana tunanin kila ‘yan’uwansa suji haushinsa tunda ita Nafisa ‘yar dangi, daga ‘ya’yan yayin Alhajinsu sai na kannenshi sa’anninta. To bari kawai ya warware ma Shahida yanda suka yi da Nafisa kar su ci gaba da ganin laifinsa. Ya tura mata sako kamar haka: Ki tambayi ita Nafisa yanda muka yi da ita. Ta ce min ba za ta gayyaci kowa ba a ranar da nazo in ji tsarinta, don haka ban san kuna da wanı bikin da ku ke son in zo ba.Ya tura mata. Bugun kofarshi ne ya farkar da shi daga bacci, gashi har ya makara sallar Asubahi. Shida ya gani da ya kalli agogo. Cikin sauri ya nufi kofa. Badi’atu ta ce “Hajiya tana kiranka.” Ya ce “Ki ce na makara in nayi sallah zan zo.’ Wanka ya fada, da ya fito yayi sallah tun daga lokacin ya fara nuna shi ango ne. Gizna ce ya sha fara sol sai aikinta mai ruwan kasa da ratsin gwal.Aka soka hula kube takalmi. Turare kuwa yanda ka san zai yi magana. Ya sakko suka hadu a falo. Hajiya tana aiken Direbansu, ta tsaya tana kallonshi. Yayi mata kyau sosai. Ya ce, “Hajiya sannu da fitowa.” Ta ce, “Kai ne da sannu Ango, wannan irin wanka haka?” Ya ce, “Ai karamin wanka ne wannan sai ma anjima.” Ta ce, “To zo muyi magana mana.” Dakinta suka shiga ta ce, “Naji Alhaji yana cewa wai za a daura aure da safen nan?”*🏚️RANA DAYA 🏚️* CHAPTER 16 KARSHE BOOK 1 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya Wanka ya fada, da ya fito yayi sallah tun daga lokacin ya fara nuna shi ango ne. Gizna ce ya sha fara sol sai aikinta mai ruwan kasa da ratsin gwal.Aka soka hula kube takalmi. Turare kuwa yanda ka san zai yi magana. Ya sakko suka hadu a falo. Hajiya tana aiken Direbansu, ta tsaya tana kallonshi. Yayi mata kyau sosai. Ya ce, “Hajiya sannu da fitowa.” Ta ce, “Kai ne da sannu Ango, wannan irin wanka haka?” Ya ce, “Ai karamin wanka ne wannan sai ma anjima.” Ta ce, “To zo muyi magana mana.” Dakinta suka shiga ta ce, “Naji Alhaji yana cewa wai za a daura aure da safen nan?” Shatima yace “Na Kano ne?” Ta ce “A’a Idan da na Kano tunda asubahi fa naji yana ta waya wai saboda abokanka ko mene ne?” Shatima ya ce, “Ok, na Aliya ne za’a daura yanzun da safe, saboda ‘yan nesa, in mun yi walima za su tafi.” Hajiya ta fadada fara’a “Ayya, na gane. To ya za ayi da abincin daurin auran tunda ba mu san za’a zo da zancen ba?” Ya ce, “Ba akwai snacks da nama ba?” Ta ce, “Eh to, bari sai in sa a zuba a take away.” Ya ce, “Yauwa to sai su Munnir su zo su dauka.” Gurin abokansa ya nufa inda suka yi masauki, ya same su kwance wasu kuma suna danne dannen waya. Ya ce, “Don Allah ku tashi ku shirya daurin aure karfe takwas.” Nan suka shiga yabon kýan da yayi. Ya ce “Ko zama ba zan yi ba kar su yamutse.” Cikin zolaya ya yi maganar. Haka dai ya matsa musu har suka shirya wasu suka wuce gurin Hajiya don dauko abin da za a ci a gurin da abin sha. Sun je kofar gidan su Salma Karfe bakwai da wani abu. Babu kowa, Shatima yaje har kofar gidan ya yi sallama Auwal ya fito, yaga ko wanka bai yi ba. Ya ce, “Auwal kun manta ne?” Ya ce, “Muna sane, yanzun zan yi wanka.” Shatima ya ce, “Ka zo kawai ga abokina kuje da mota ku dauko kanin Baban naku.” Haka ya matsa musu aka tafi, shi burinshi kawai a daura auren nan, dama motocinshi uku duk suna gurin, da wadda a ka ba shi a gidan su Amna, da wadda ya zabo abokin Babanshi ya bashi. Da kanshi yaje gidan waliyyin ya fito dashi cikin shiri. Shatima ya dan ji dadi ya ce, “Dama nazo ne in ji ko ba ku manta ba.” Ya ce, “Ai lokacin bai cika ba ko?” Shatima ya kalli agogon hannunshi, “Eh saura minti talatin.” Ya ce, “Ba komai, shi Auwal ko ya tafi ya zo da dan uwan Baban nasu?” Shatima ya ce, “Na hada shi da abokina su tafi.” Ya ce, “Nan ma na sa an sanar a Masallaci, kuma da safen nan nasa an fadawa makota.” Shatima yayi godiya ya koma gurin abokansa, sannan ya ce “Munnir don Allah ka je ka taho da su Alhajin ku.”Munnir ya ce “Shatima wai me yasa ka kasa nutsuwa ne? kar ka manta ba wannan ne kadai auran da za a daura maka ba ko?” Shatima ya ce, “Ni dai burina a daura wannan, don shi kadai ne me matsala.” Munnir yayi tsaki, sannan ya wuce. Salma bata san ma wai an dawo da daurin auranta na safe ba, don ita ko kunshi bata yi ba, ta bari sai da rana tukunna. Umar ne ya shigo yana cewa “Mutane sun taru a waje.” Yaya Hadiza da wata kawarta itama lokacin sun zo za su amshi kudin cefane gurin Inna suje kasuwa, suka ga guri tam! Da ta shiga take tambayar Inna. Ta ce, “Ummi ni dai wannan lamari ina nan ina ta addu’a, jiya fa har mun kwanta ya buga gida, wai a maida daurin aure na safe.” Hadiza ta ce, “Insha Allahu alkairi ne.” Itama Salman sai lokacin taji. Hadiza ta dube ta, “Wai Salma kin tsefe kanki kuwa?” Ta ce, “Na tsefe da dare.” Ta ce, “To in an watse ki dauki wannan man da na ciro miki a akwati na shampoo din ki je shagon wankin kan.Ta ce, “To, kuma wadda zata min kunshin ta ce karfe goma zata zo.” Kawar Hadiza ta ce, “A fara yi mata kunshin mana shi ne mai wahalar.” Salma ta ce, “Nima haka naga zai fi.” Iyayen Shatima sun iso cikin zauran gidan aka sa tabarma suka zauna, sauran mutane suna waje. Guri fa ya cika tankam. Nan aka daura auren Salma da Muhammad Ja’afar Shatima. Ana gamawa abokan suka shiga raba-abin da suka zo da shi. ‘Yan unguwa kam sun shaida lallai Salma ta tako. Daga nan kai tsaye suka soma daukar hanyar Kano don karfe tara ta gota. Shatima ya ce, sai ya je gida ya canza kaya, Munnir ya jira shi. Bayan an ragu ya kira Auwal ya ce ya kira mishi Salma. Dogon hijabi tasa ta same shi a zaure. Ya kalleta cikin mamaki, ya ce “Salma ya ban ga kina kyalli kamar sauran Amaran ba?” Gabanta ya fadi, “Wai da gaske ka ke yi mu hudu ne?” Bata san lokacin da tambayar ta zo mata ba. Ya ce, “Wannan ce amsata.” Ta dan yi shiru, sannan ta ce, “Nima ban sani ba, kila don ban wanke kai ba ne sai anjima zan yi.” Ya ce “A’a su fa naga fuskarsu duk tana ta kyalli, ga kunshi, ke in ga hannunki.” Ta nuna mishi. Ya ce”Haba Salma! Me yasa za ki yi haka?” Ta ce, “Zan yi ai.” Ya ce, “Je ki shirya ki zo in kai ki gurin da za’a wanke miki kai.” Ta ce, “Yaya zan je Allah.” Ya ce, “Ai daga yanzun na koma miji ba Yaya ba, kuma ba a musu da miji.” Ta ce, “To.” Ta juya ta koma ciki ya fito, Munnir ya ce, “Ka zo muje don Allah kada lokaci ya kure.” Shatima ya ce, “Ai yanzun ma gurin gyaran gashi zan kaita.” Munnir ya ce, “Don iskanci ka bar ni in tafi tare da mutane ka tare ni.” Ya jeho masa makullin sabuwar motarsa, “Ga makullinka, bari in bi su Bello don a karshe ba zuwa zaka yi ba.” Shatima ya ce, “Ka bari mu bi jirgin karfe יי goma.” Munnir ya ce, “Goman dare ko? Duba agogonka kafin muje filin jirgin ma ai ‘yan daurin auran sun juyo, kaga ni bari in bi su sai mun dawo, don nasan kai ba zuwa zaka yi ba kana gurin wannan yar mitsitsiyar yarinyar.” Shatima yayi murmushi. Ya ce, “To Allah Ya tsare, amma ina mai tabbatar maka ina gabanka can zaka same ni.” Munnir bai sake magana ba ya shiga motar abokansu wadda da suka tsaya za su jera tare, ya ce, “Ku mu je wannan angon ba zuwa zai ba.” Salma ta sanar da Yaya Hadiza yanda suka yi da Shatima, Hadiza ta ce “Muje muji ta bakin Inna.” Inna ta ce, “Anya kuwa sa fita?” Wata kawarta ta ce, “Ai yanzu matarsa ce.” Hadiza ta ce, “Shi ne nima na gani.” Inna dai tayi shiru. Hadiza ta ciro mata jallabiya baka da mayafinta, sai takalmi mara tudu duk na cikin lefan, ta ce “Gashi ke ko wanka ba ki yi ba.” Salma ta ce, “Bari in dauraye jiki.” Suka bata turaruka ta fesa ta dauki saitin man da zata yi amfani da shi. Yana jingine a jikin mota, ta fito ta nufo shi. Ya bude mata gaba ta shiga ya zagaya ya shige. Ya dan dube ta bayan sun hau titi. “Bana son kazanta fa, amarya har yanzun bata gyara kai ba.” Ta ce, “Zan gyara dama, ni ban san da safe za’a daura auran ba.” Ya ce, “Amma ya ki ka ji da aka ce ya dawo na safe?” Tayi dan murmushi, “Ban ji komai ba.” Ya ce, “Har yanzun ba ki fara sona ba ko?” Ta dan ja mayafinta ta rufe fuska. Ya ce, “Ina jin ki.” Ta ce, “Ai ban san so ba ni. Ta yiwu ina yi maka.” Ya ce “To na baki lokaci ki soma sona kafin mu hadu, ki bincika ki san ya ya ake so? Ya ya so yake? Kuma mene ne so?” Ta kalle shi tayi murmushi ta ce, “To.”Katon shagon da ya kaita lokacin ma suke budewa. Ya ce suyi mata gyara me kyau amarya ce. Ya ji mamakin ganin gashin kanta mai cika da tsawo. Ya ce, “Dama kina da gashi haka?” Tayi ‘yar dariya. Duk da kiran da ake ta yi ma wayoyinsa bai ji ko da a ransa wai ya tafi ya bar ta ba, Hajiyar Shatima tana ta kai-kawo a cikin jama’ar da suka taru a gidan ‘yan uwa da abokan arziki, amma zuciyarta tana can gurin tunanin Hajiya Azumu.Wai ina ta shige ne oho! Ba ita ba labarin yarinya. Sai kusan goma da kwata sannan Hajiya Azumi tayi sallama a gidan. Hajiya ta mike da sauri tazo tana fadin, “Hajiya Azimi haka muka yi da ke?” Ta ce, “Muje daki da labari.” Can kurya suka shiga, Hajiya Azumi ta ce, “Hajiya da matsala katuwa, kuma gashi me afkuwa har ta afku.” Hajiya ta ce, “Kar ki ja min rai muje labari.” Hajiya Azumi ta ce, “Yarinyar nan sunanta Ummu Salma, iyayenta talakawa ne na tsiya har gidan da suka tashi sai da aka nuna min wanda suke haya. A cikin bikin nan Shatima ya sai musu gida suka koma saboda kada danginsa su gane tsiyar su.” Hajiya ta dafe kirji, “Ya sai musu gida?” Hajiya Azumi ta ce, “Har gidan na shiga. An ce barin kudi yayi musu ba kadan ba kuma ance abin sai wanda ya gani, kuma kullum yana gidan.” man Hajiya ta ce, “To wai yarinyar wani mugun kyau gare ta ne?” Hajiya Azumi ta rike baki tare da fadin “Wane irin kyau, ni da na ga yarinyar ma sai kunya ta kama ni, na soma tunanin ya ya aka yi ya ganta har ya ce yana so? ‘Yar mitsitsiya, figigiya ko nonon kirki babu, ke ina ‘yar aikinki Masa’uda!” Hajiya ta ce, “Kar ki ce min kamarta take?” Hajiya Azumi ta ce, “To ai Masa’udar ta fi ta cika ido. Hajiya ina ga asiri suka yi masa.”Hajiya ta soma zufa, “Lallai wajibi ne in kira Alhaji Musa tun kafin ma su dawo Kano.” Hajiya Azumi ta ce “Ki hana me? Ai lokacin da naje gidan an tashi daga daurin aure ke nan na shiga gidan nayi musu murna don dai in ga dil!” Hajiya ta zauna dabas! “Wai dama auran da aka daura da safen nan nata ne?” Hajiya Azumi ta ce, “Shi ne, kuma a gabana ya dauke ta a mota suka wuce…” Aliya da kawayenta guda biyu Aisha da Madina, sun tafi babban saloon don gyara gashin Amarya. Suna sauka a dan sahu suka bashi kudin, sai taji gabanta ya fadi. Ta kalli Aisha ta ce, “Kin ji wata wawuyar faduwar gaba da naji! Allah yasa alkairi ne.” Aisha ta ce, “Insha Allahu alkairi ne.” Madina ta kalli dankareriyar motar da ke kofar saloon din ta ce, “Dubi wata mota mai shegen kyau. Aisha ta ce, “Wai! Gaskiya motar nan tayi karshe a kyau.” Aliya dai bata yi magana ba duk da bata san motar ba, amma da ta kalli motar sai da gabanta yayi wata mummunar faduwa Cikin rashin kasala suka tura Kofar gilashin shagon, Aisha ta soma shiga sannan Madina. Ba su lura da cewa Aliya tayi mutuwar tsaye ba ne sai da Aisha ta waiwayo da nufin yi mata magana, ta zaci guri ta basu su fara shiga. ” Ta waiwaya ta kalli inda Aliyar take kallo, sai taga Shatima zaune ya tasa Salma an gama wanke mata kai ana tajewa da handrayer… Wash! Bari in tsaya a nan sai mun hadu a littafi na biyu don jin ya ya za ta kasance? Wane mataki Hajiya zata dauka? Ya ya Aliya zata yi da taga Shatima da Salma da ba ta san labarinta ba? Ya Amna zata amshi maganar Salma? Wane ma irin zama za’a yi? Wai wace ce ma uwargida? Wa ya fi so? Ku biyo ni.