[8/9, 07:57] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2 🏚️* CHAPTER 1 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya Ba su lura da cewa Aliya tayi mutuwar tsaye ba ne sai da Aisha ta waiwayo da nufin yi mata magana, ta zaci guri ta basu su fara shiga. ” Ta waiwaya ta kalli inda Aliyar take kallo, sai taga Shatima zaune ya tasa Salma an gama wanke mata kai ana tajewa da handrayer… Wash! Bari in tsaya a nan sai mun hadu a littafi na biyu don jin ya ya za ta kasance? RANA DAYA 2 Madina, ta ce “Shigo mana Amarya.” Hakan da ta fada shi ne ya janyo hankalin Shatima ga barin kallon gashin Salma, ya kalli inda ‘yanmatan suke. Zumbur! Ya mike da suka hada ido da Aliya. Da yake Shatima namijin duniya ne, sai ya shanye tsoron da ya tsirgo mishi da mamakinshi, sannan ya dan fadada murmushinsa ya ce, “My love kema kar dai gyaran gashi ki ka zo nan?” Ta danne tambayoyin da suka taso mata lokaci daya kusan guda biyar a kan wannan yarinyar da ta gansu tare. Ta dube shi da dan fari ta ce, “Eh, gyaran gashi nazo.” Ya ce, “Nayi zaton ke tuni kin gyara naki?” ta ce, “Ban samu lokaci ba ne, sai yanzun.” Ya kalli mai gyara gashin, “Wannan ma kiyi mata da kyau, don Amaryata ce itama.” Mai gyaran ta ce, “Amaryarka kuma?” Ya ce, “Eh, akwai wasu ma guda biyu.” Tayi dariya tare da fadin “A’a wasa ne.” Aliya tana son sanin wace ce wannan, don sai tana ganin kamar ta santa. Ko ‘yar’uwarsu ce? Ta dai san kanwarshi Badi’atu tafi wannan yanzun, don ko sanin da tayi mata a shekara uku baya, ta fi wannan cika ido. Amma bari taji daga gare shi. Cikin salo irin na mata masu wayo ta ce, “Nayi mamakin ganin ka a nan.” Ya ce, “Naga mamakin a fuskarki, amma mamakin me kike yi?” Ta ce, “Na zaci kana can Kano yanzun gurin daurin aurenka da ‘yar’uwata?” Ya ce, “Ban samu zuwa ba, saboda ‘yar autarku itama ta fito tsaf!” Ya fada tare da dafa kan Salma wadda aka gama gyarawa gashi aka daure. Daidai lokacin matar ta ce Aliya tazo ta zauna a soma yi mata. Amma ita Aliyar hankalinta yana gurin Shatima, tana son ji daga gare shi don ya sake daure mata kai. Ta ce, “Wai dama Badi’atu tana da kanwa ne?” Yayi murmushi, don sai yanzun ya fahimci bata gane ba. ya tuna ashe fa bai fada mata cewa akwai Salma ba. Ya ce, a ranshi bari yayi amfani da wannan damar yayi mata bayani, don haka ya ce, “Zo nan muyi magana.” Ya dubi Salma, “Jira ni simolinsu.” Yayi maganar cikin zolaya. Jikin motar suka tsaya. Ya ce, “Na manta ban fada miki batun Salma ba, yarinyar nan ina tsananin tausayinta. Na aureta ne don in taimake ta…” Aliya ta katse shi da cewa, “Kayi me?” Ya ce, “Na aure ta na ce.” Tayi shiru tana nazari, ya dan tsakura mata labarin Salma kadan, ya kuma sake tabbatar mata an fara daura aurensu da Salma kafin su wuce Kano. Aliya ta danne duk wani kishin Salma da ta ji ya taso mata. Ta ce, “Amma me yasa ba ka fada min ba? ko kana zaton zan ja da ikon Allah ne?” Ya tausasa murya. “Nayi kuskure, na san cewa ba zan samu matsala daga gurinki ba.” Ta kirkiro murmushi. “Ita ce karamarmu babbarmu ke nan ko me? Tunda naga aurenta aka fara daurawa. An ce wadda aka fará daura ma aure ita ce uwargida.” Ta kasa kunne don jin me zai ce. Ya ce, “Fadin Hadisi ko Kur’ani?” Ta ce, “Ina al’adar Malam Bahaushe ce.” Ya ce, “To ni a gidana ke ce Uwargidana.” Aliya ta ji dadi a zuciyarta. Amma sai ta danne. Ta ce, “Kar ka hada husuma, da dai ka bari an bi tsari.” Ya ce, “Tsari ya wuce, nawa. Ni zan tsara gidana, kije ayi miki naki wankin kan saboda lokaci na tafiya.” Ya shiga ciki ya biya kudin su duka, sannan ya ce ma Salma ta gaida Antynta. Ta russuna ta gaida Aliya da kawayenta, sannan ta fita. Ya dubi Aliya, “Bari in kai ta gida ko?” Aliya ta ce, “To sai anjima.” Yayi sallama kawayenta suka fita. Salma tana son taji wace ce wannan? Ya kalleta, “Bakinki yana son cewa wani abu ko?” Ta ce, “Me yasa ka ke gane haka?” Yayi murmushi, “Baiwata ce hakan. Ki fadi abin da ki ke son fadi.” Ta ce, “To wacece wannan din da ka ce in gaidata, ‘yar’uwarka ce? Itama tana aure yau ne?” Ya dan rage tafiya, sannan ya kalleta, “Tana cikin Amarena na yau. Amman ita ba a daura ba, sai an dauro na Kano. Ita ce zata zama uwargidanku.” Ta tsura mishi ido ta kasa magana. Yayi fakin a gefen titi, sannan ya kalleta. “Idanunki sun nuna rashin gamsuwa da zancena. Me yasa ki ke zaton maganata ba gaske ba ce?” Ta lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. Abin ne ni ke ji tamkar ba gaske ba.” Ya ce, “A zantukan da na fada miki, wanne ne ki ke ganin ya yi kama da ba gaske ba? Ko kuma wanne ne bai faru ba? Na ce zan aure ki, kuma na aure ki.” Ta ce, “Ni ina mamakin da ka ce mu hudu ne, mu hudun ne ban taba ji ba.” Ya ce, “To yau gashi ya faru da ke.” Ya kai yatsan shi ya lakuci kumatunta, “Ke ce kuma autar su. .” Ta ce “Ni na taba ganin wannan matar da kayan Nurse.” Ya ce, “Eh ita Nurse ce. Yanzun kin yarda ku hudu ne ko sai kun tare kin ga shaida?” Ta ce, “Yanzun dai ina tunanin mu biyu ne, in naga sauran sai in kara hakikancewa.” Ya tada motar tare da murmushi. “To nasan an jima za ki hakikance.” Ya sauke ta tare da yi mata sallamar sai sun hadu a gidan shi. ** KANO ** Can Kano ana ta hada-hadar daura aure, unguwar ta cika makil da manya kuma mashahuran mutane, maroka da makada abin sai wanda ya gani. An gama daurin aure lafiya, sai dai da dama sun so su ga angon musamman dangin Amarya wadanda ba su san shi ba. Haka ma cikin gidan su Amarya ya cika makil, Mahaifinta ya kira Mahaifiyar a waya. Ya ce, “Ku shirya Amna domin da ita za su wuce yanzun. Momi ta ce, “Suna kan shiri ne.” Motocin daukar Amarya da ‘yan rakiya tuni an tanade su, ba a jira wai gidan Ango su kawo motocin daukar Amarya ba, domin ita kanta Amaryar motocin ta biyu sabbi dal da aka bata a gudunmawa. A cikin daya aka dauke ta, dayan aka debo kawayenta, sai sauran dangi da suka jero cikin motoci na alfarma. Zariya suka dira, kamar yanda Hajiya ta tsara cewa duk matan da za a kawo su nan ne gidanta, suma suna da nasu biki da za suyi kafin a kai su gidansu, sai washegari ma sannan za a kai su. Gefen Alhaji aka sauki Amna, dama an gyare gidan ya sha fenti saboda bikin musamman, gefen Alhaji komai sai da aka canza. Ita da kawayenta ne a ciki kadai, Hajiya tasa an kai musu kayan ciye-ciye na alfarma da karamci. Don an ce tuwon girma miyarshi nama. Su dai maza suna gama hallaruwa suka shiga shirin daura auran Nafisa, a gidan Kaka aka daura shi, in da Baban Shatima ya ba da ta. Shatima yana gurin aka daura nasu da Nafisa, in da suka yi ta daukar hotuna da abokansu da kuma ‘yan uwa. Daga can suka wuce na Aliya, mutane sun sha mamakin wannan Ango mai mata hudu rana daya. Abin da ya ba Shatima mamaki yanda ‘yan jarida suke bin shi da son jin ta bakinshi, bai san kuma wa ya gayyato su ba. Sabuwar shiga ya sake in da suka tafi walima ta su ta maza zalla shi da abokanshi. Shahararren guri suka kama suka yi walimarsu mai tsari. Sun taso karfe shida saura na yamma, sai suka yanke shawarar suyi Magriba kafin su je daukar Amare, tunda duk nan dai gidan iyayen Shatima din za a tara su. Nafisa suka soma daukowa, wadda ta ci kuka ta gode ma Allah, sannan aka ɓanbare ta da kyar daga jikin Mamarta, aka sa ta a mota. Ita dakin Hajiyar aka kaita kai tsaye da kawayenta, hakan ya nuna ma kowa ita din ta gida. ce. Aliya kuwa gefen bakin gidan aka gyara, tare da bakin da aka sauka a gurin matsugunni, aka kaisu itama da nata kawayen sai dai su basu samu sauka kamar ta Nafisa ba, bare irin ta Amna. Shatima kuwa da shi aka je daukar Salma, tunda Hajiya ta karanta mishi wai gidan ta za a kai Amare kafin a wuce Kaduna, yake tausayin Salma. ba ta zo da kowa ce kawa ba, sai ‘yan uwa da makota. WaYan da suka samu labari, duk Amaryar da ta iso ‘yan uwan Hajiyar da Aminanta suke zuwa suna tarbar su zuwa in da aka yi musu masauki. Amman da suka iso da Salma babu wanda ya zo. har shi da kanshi Shatiman ya shigo gidan. Ya kira Anty Momiyo gefe, ya ce mata “Anty ga Salma fa, ita da danginta ba zan so a wulakanta yarinyar nan ba.” Anty Momiyo ta ce, “kana wucewa da ita, ya zama laifi a gurin Hajiya ka sani. Bari in tambayo ta muji yanda za’ayi. Suna falo suna shewa Anty Momiyo ta zo mata da batun da suka yi da Shatima. Hajiya ta mike cikin sauri, wai bata gayyar tsiya. > bari taje tayi musu zagin fitar arziki. Nan fa aka hanata, aka bata baki. Ta ce, “Bata da sauran masauki, in shi yana da in da zai sauke ta to ga gidan nan. Anty Momiyo ta koro masa abin da Hajiya ta ce. Ya ce mata babu komai Anty a kai ta samana kawai, ‘yan uwanta nasa su tafi.” Duk da haka sun rakata har dakin Shatiman, wanda sai an bi dai ta falon. Ko gaisuwa basu samu ba ‘yan uwanta bare ruwan sha, su dai suna aje ta suka ce sai sun zo goben don rakata dakinta. Sun wuce sun bar Salma tsuru zaune a bakin gadon Shatima, fuska lullube ta ci kuka ta gode Allah, tana ma kan kukan suka tafi. Shatima suna masaukin abokansa, sam ya kasa walwala, hankalinshi yana can gurin Salma, zuciyarshi ta ki nutsuwa, suna hira yana tsaki. Munnir ya ce, “Wai don Allah Shatima lafiya ka ke tsaki?” Ya ce, “Ina tunani ne, yarinyar nan Salma tana can cikin damuwa, koma ayi mata wani abin tun da na san ba a sonta Munnir ya zabga ma Shatima wata harara, sai ka ce irin yara kanana din nan, sannan ya ja dogon tsaki ya ce, “Ka san Allah har na soma tsanar wannan Salmar, duk ka bi ka zama wani soko a kanta.” Ya ce, “Munnir ba zaka gane ba ne, da dai na sani da na ce ma Anty Momiyo a hada ta da Aliya nasan zata kula min da ita.” [8/16, 21:02] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️* CHAPTER 2 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya Munnir ya ce, “Wai don Allah Shatima lafiya ka ke tsaki?” Ya ce, “Ina tunani ne, yarinyar nan Salma tana can cikin damuwa, koma ayi mata wani abin tun da na san ba a sonta Munnir ya zabga ma Shatima wata harara, sai ka ce irin yara kanana din nan, sannan ya ja dogon tsaki ya ce, “Ka san Allah har na soma tsanar wannan Salmar, duk ka bi ka zama wani soko a kanta.” Ya ce, “Munnir ba zaka gane ba ne, da dai na sani da na ce ma Anty Momiyo a hada ta da Aliya nasan zata kula min da ita.” Ya ce, “To ka kira mana ba ga waya a hannunka ba, ka dame mu da tsaki.” Shatima ya fita ya kira layin Anty Momiyo, sai a kira na uku sannan ta daga. Ya ce, “Haba Anty, kin ki daga wayata.” Ta ce, “Wallahi na gaji ne, na fara bacci.” Ya ce, “Anty don Allah Salma ita da wanene?” Ta ce, “Oho ban duba ba, ‘yan uwanta dai sun fito sun tafi.” Ya ce, “Ya ya za’ayi don Allah ki hada ta da Aliya.” Anty Momiyo ta ce, “Babu ruwana da Hajiyarku. Kowace Amarya an barta ita da kawayenta da danginta. Sai in je in ce tazo ta hadu da wata! Babu ruwana.” Ya ce, “To don Allah dan leka min ita Anty ba wai na raina ki ba ne.” Ta ce, “Sai dai in saci idon Hajiyar ka in duba don gaskiya ba da wasa take yi ba a kan wannan Salmar, zata saka kafar wando daya da duk wanda ya ce zai ko kalli inda Salmar take.” Ya ce, “A taimaka mini zan jira kiranki.” Kamar minti goma ta kira shi, da sauri ya daga ko ringing bata yi ba, har ya bata ‘yar dariya. Ta ce, “Dama zaman jirana ka ke yi?” Ya ce, “Wallahi.” Ta ce, “To ita daya ce a dakin, kuma sai kuka take, wallahi har ta bani tausayi.” Ya ce, “Anty ba ki bata hakuri ba?” Ta ce, “Au, ba ka ga kokarina ba, so ka ke sai na ja ma kaina matsala da ita kaga ni sai da safe.” Shatima ya zauna ya zabga tagumi suna ta hirarsu. Haushi ya hana Munnir magana. Sha daya saura, Munnir ya ce bari yaje gida. Ya zubawa Shatima makullan motocinsa guda biyu, tare da fadin “Ga wadannan ka rike zan tafi da dayar motar.” Shatima bai tanka ba. Munnir ya ja tsaki, “Duk ka damu mutane da zancen wata tsuntsuwar yarinya, ka dauki jarabar so ka dora mata. Shatima ya ce, “Kai ka ki saurarona ne bare ka gane dalilina, kaje kawai.” Munnir ya wuce. Shatima dai ya rasa sukuni, sai tunanin yanda zai fidda Salma a matsala. Har kusan sha biyu bai samu mafitar da ta wuce yaje gidan ba, duk da su Hajiyar sun nuna cewa zuwan shi gurin Amaran a yanzun ba tare da an yi budar kai ba kamar wani haramun ne bisa al’ada. Sha biyu da mintuna ya shigo da mota harabar gidan, ya kalli gefen baki inda Aliya take, sannan ya taka ya nufi falo. Babu mutane sai yara da suka yi bacci a kan kujerun falon. Amma yana jiyo magana daga gefen Hajiya, cikin sanda ya nufi samanshi. Salma wadda ta sha kuka fuskarta ta kumbura suntum! Kukanta da yawa, ta tuna Mahaifinta, ga rabuwa da Innarsu, da Yaya Hadiza, da Yaya Auwal, da Umar kaninta. Sannan gashi da a lamun bata samu karbuwa a wannan dangin ba, sannan gashi ba ita kadai gurin miji ba. Tana jin lokacin da Anty Momiyo ta bude kofa, cikin sauri ta dago ta dube ta, sai taga matar ta tabe baki ta juya. Hakan yasa ta sabon kuka ga makogwaronta ya bushe, tana bukatar ruwa. Sake bude kofar taji anyi, cikin sauri ta sake dago da kai suka yi ido hudu da Shatima. Wasu sabbin hawaye taji sun zubo mata, da sauri ya iso ya tsugunna a gabanta. “Salma, mene ne? An yi miki wani abu ne?” Yasa hannu ya dago fuskarta. “Subhanallahi! Haka fuskarki tayi? An dake ki ko?” Muryarta a dishe, tace “Ba a bige ni ba.” Ya ce, “Kukan me ki ke yi to, saboda ba ki sona?” Ta zuba mishi ido kawai tana kallonshi. Ya ce, “To share hawayenki, na tuna ke ba ki ma san so ba ko?” Ta daga kai alamun ‘eh’. “Na gano kukan da ki ke yi na rabuwa da Inna ne ko?” Ta daga kai. Ya ce, “To kada ki damu, zan dinga kawo ki a kai-akai kin ji?” Ta ce, “To.” Ya ce, “To yi murmushi.” Ta dan kirkiro shi tayi. Ya mike ya soma kwashe kayan shi da ke zube a kan gadon, duk sabbin da ya yi ta canji ne, sai kamshi suke. Ya ce, “Bari in rage miki kayan nan ko? Za ki ma iya kwana ke daya? Me yasa ba a bar miki kowa ba? kuma ke wai ba ki da kawaye ne?” Ta ce, “Su Yaya Hadiza sun ce an yi musu wulakanci ba za su zauna ba, ni kuma ban gayyaci kowa ba saboda Babanmu bai dade da mutuwa ba.” Ya dan yi jim! Don bai so abin da aka yi musu ba, amma sai ya kauda zancan da cewa, “Kina jin yunwa ko?” Sai lokacin ta tuna duk yinin ranar ba ta ci komai ba. ya matso “An baki abinci?” Ta ce, “A’a, yau ma bana zaton na ci wani abu.” Ya ce, “To ina zuwa.” Ya fita, ta sauke ajiyar zuciya. Taji dadin lallashin da ya yi mata. Mota ya zara ya nufi gurin saida kayan kwalam. Ya siyo Kaza da madara zalla mai sanyi da ruwa. Ya sake wucewa cikin sauri ya nufi samanshi. Sai dai wani tsautsayi, katsam! Hajiya ta fito da nufin zuwa saman don yin gargadi da barazana ga Salman da danginta in tare suke, sai kawai taga Shatiman yana bin kafar bene. Sororo ta tsaya tana kallonshi har ya wuce. Ranta yayi mugun baci, ban da gidan cike yake da baki ga su Amna da danginta, da sai ta yi tijara a cikin daren nan Ta gama yarda dari-bisa-dari cewa wadannan talakawan sun asirce mata da. Shatima bai san Hajiya ta ganshi ba, yana shiga ya same ta kwance ya ce, “Tashi Salma.” Ta mike zaune. Shi ne ya cire mata tsokar yana aje mata, ita kuma tana dauka tana ci tamkar irin dai yanda za ka yi wa karamin yaron da ka ke son ya ci abinci. Ya zuba mata tatacciyar madarar a kofi ta dauka tana sha. Sai da ta koshi tam! Sannan ta sha ruwa, lokacin ne ya duba agogonshi biyu saura minti shida. Ya ce, “Kai! Har dare ya yi haka? Bari in je in kwanta nima.” Ta ce, “Amma a cikin gidan nan za ka kwanta ko?” Ya ce, “A’a in da abokaina suke.” Ta ce, “Kada fa wani abu ya faru da kai…” Kwankwasa kofar suka ji an yi, gaban Shatima ya fadi, ya isa gurin kofar ya ce, “Wane ne?” Muryar Hajiyarshi ya ji ta ce, “Ka bude ka gani.” A fili ya ce, “Ya salam!” Ya bude a cikin tsoro. Ciki ta shigo sannan ta maida kofar ta rufe. Tana juyowa bai ankara ba sai jin saukar mari yayi dau!! Salma ta mike a tsakiyar gadon duk ilahirin jikinta ɓari yake. Hajiya ta wuce shi ta iso gurin Salma, cikin sauri ya nufo ya tsaya tamkar zai kare ta. Hajiya ta nuna ta “Ke! Kalli cikin idona kin ga alamar wasa?” Salma ta durkusa gwiwa biyu a kan gadon. Hajiya ta ce, “Ba ki da gurin zama a gidan dana, ki fada min ina ku ka je ku ka asirce min da?” Salma ta soma kuka, tare da fadin “Wallahi Hajiya ba ma zuwa gurin asiri.” Shatima ya ce, “Haba Hajiya!..” Ta dora yatsanta a kan lebe “Ka min shiru.” Ya ce, “Hajiya ina mamakin wannan fa ba halinki ba ne, ni na sani kina da tausayi.” Ta ce, “Na ce ka rufe min baki. Ta sake kallon Salma, “Zan sa a kama duk danginki a rufe min har sai sun karya asirin da suka yi wa dana. Kuma sai ya sake ki, sa’arki daya gidan nan yau da bakin alkairi bakin kunya, da sai na sa yai miki sakin wulakanci. Ina son ki sani zan zo har Kadunar kuma zan sa ya sake ki, kar ma kije da tunanin za ki shantake wai kin samu gurin zama. Sannan gobe ne bikina na nan gidan, da wasa kar ki sake ki fito bare ki bata min biki, na fada miki.” Salma bakinta na rawa ta ce, “Ba zan fito ba Allah, kiyi hakuri don Allah!” Tsaki Hajiyar taja “Ki ma fito ki gani.” Sannan ta juya kan Shatima.”Kai kuma fita muje, abin da ya sa ni ke raga maka don nasan ba yin kanka ba ne.” Ya ce, “Hajiya ni fa babu abin da aka yi min. Ta ce, “Ai ko anyi maka kai ba za ka sani ba. Da haka ka ke? Kai da ka ke tsayayyen namiji mai ji da kansa, gashi kan wannan duk ka zama soko, wuce muje.”Haka ta tasa shi a gaba har cikin dakin Mustapha kaninshi da ke can cikin harabar gidan, ta ce “Shiga nan ka kwanta.” Yana shiga Mustapha tuni sun yi bacci da shi da wani dan uwansu da suka zo biki, kan kujera ya zauna cikin tashin hankali da tunanin Salma. Ita kuwa Salma tana tasa shi gaba suna fita, ta sauko daga kan gadon tana kuka, ta samu can kusa da wata durowa ta shige sakon ta zauna. Kanta ya sake kullewa, lallai gaskiyar Inna ne da ta ke ta jinjina al’amarin auran nan, tabbas akwai dinbin da na sani a cikin duk abin da aka yi gaggawar shi, domin wata gaggawar daga shaidan take. Yanda Salma ta kwana zaune, haka shima Shatima zaune ya kwana, kowannansu cikin takaici tare kuma da rasa wane irin tunani ya kamata suyi.Da Asubahi Salma tana jin kiraye-kirayen sallah, har a ka shiga Masallaci. Ta yunkura ta tashi, tana rangaji ta nufi ko far da take zaton bandaki ne. Tayi alwala, ta kalli fuskarta a madubi, har yanzun a kumbure take. Ta zo ta yafa gyalenta da aka rufo mata, tayi sallah tana addu’a tana jin sanyi yana ratsa ta, kasancewar lokacin sanyi ne. Ga wani irin bacci da take ji tamkar na mutuwa. Kan gadon ta hau ta ja bargo ta kudundune, nan kuwa bacci me nauyi yayi awon gaba da ita. Shi kuwa Ango bayan sun fito Masallaci, yana son zuwa dakin abokansa inda suka yi masauki. Amma kuma yana son sanin halin da Salma take ciki. Ya nufi falo lokacin gari ya soma yin haske. Ya samu Hajiya ta saka ‘yan aiki suna ta gyaran falo da gida. Tayi kicin-kicin da fuska, kuma da kyar ta amsa gaisuwarshi. Ta ce, “Ina za ka nan?” Ya ce, “Badi’atu zan kira.” Ta ce, “Tana dakina tare da su Nafisa.” Ya tsaya. Ta ce, “Shiga mana ko ni zan kira maka ita?” Ya wuce falon Hajiyar kai tsaye. Duk ‘yanmatan Nafisa ‘ya’yan dangi ne nan suka kama gaida shi. “Sannu da zuwa Yaya.” Ya ce, “Ina Badi’atu?” Suka ce, “Tana cikin dakin Hajiya tare da Amarya Nafisa.” Yayi kamar ya ce su kira ta, sai kuma yasa kai ya shige dakin. Nafisar tana kudundune a gadon Hajiya cikin bargo, tana danna waya. Su Badi’atu suna kan gadon a gefen duk hira suke. Nafisa tayi maza ta tashi zaune jin muryar Shatima. Ya ce, “Badi’atu zo nan.” Suka kalli juna na lokaci. Rabon da su hadu tun ranar da yaje ba ta kati ta ki amsa. Shi ne ya fara dauke idanu daga kai, sannan ya ce, “Kina lafiya?” Ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin “Lafiya.” Sannan ta koma ta kwanta rigingine tare da jan bargon zuwa kirjinta. Ya fita tare da fadin “Zo Badi’atu.” Suka tsaya a babban falo. Ya ce, “Hau dakin nasa ki kwaso min wayoyina.” Hajiya da ke kallonsu ta windown waje, ta hangi Badi’atu tayi sama, ta ce, “Ke! Ina za ki nan?” Shatima ya ce, “Wayoyina zata kawo min.” Ta ce, “Oho!.” Ya ce, “Badi’atu zo.” Ta dawo, muryar shi kasa ya ce, “Don Allah Salma tana ciki ki duba min wane hali take ciki? In kin dawo ki same ni a dakin Mustapha.” Kusan minti tara, sannan ta shigo. Tana ba shi wayoyin shi kuma yana tambayar ta ganta? Badi’atu ta ce, “Na ganta tana bacci a kan gadon ka ta rufa.” Ya amshi wayoyin tare da fadin “Alhamdulillah.” Ya kama hannunta “Zo kiji Badi’atu. Don Allah ki min wani taimako.” Ta kalle shi cikin mamaki, Yayanta mai izza da isa yau kuma ita yake roko. Ta cè, “To mene ne zan yi maka Yaya?” Ya ce, “Ina son ki ke kula da Salma, in ta tashi don Allah ki dan debi abinci ki bata, duk abin da ya dace ki taimaka mata, ni kuma duk abin da ki ke so in an gama bikin nan ki fada min zan miki shi.” Badi’atu ta ce, “Ba sai ka bani komai ba Yaya, zan kula da ita insha Allah.” Ya ce, “Na gode kanwata.” Da ta tafi ya ji sanyi a ranshi, sannan ya kira layin Aliya, suka gaisa. Ya tambayi lafiyarta da ta mutananta. Ta ce, “Duk suna lafiya.” Ta ce, “Jiya ina daga window naga ka shigo, ka kuma fita ka dawo. Ka ban tausayi sai naga duk ka fada.” Ya ce”Ai naso in zo in da ki ke lokacin, Salma ce bata ci abinci ba, na fita na siyo mata.” Gaban Aliya ya fadi. Ta dake ta ce, “Ai da ka kira ni nan ga abinci sai yanzu ma na kwashe kayan.” Ya ce, “Tana dakina ita daya ce, ta bani tausayi, har kusan karfe biyu ina gurinta. Aliya ta sake danne kishinta tace, “Allah Sarki! Da ka rako ta nan sai mu kwana. Ya ce, “Babu [8/16, 21:11] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️* CHAPTER 3 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya dawo. Ka ban tausayi sai naga duk ka fada.” Ya ce”Ai naso in zo in da ki ke lokacin, Salma ce bata ci abinci ba, na fita na siyo mata.” Gaban Aliya ya fadi. Ta dake ta ce, “Ai da ka kira ni nan ga abinci sai yanzu ma na kwashe kayan.” Ya ce, “Tana dakina ita daya ce, ta bani tausayi, har kusan karfe biyu ina gurinta. Aliya ta sake danne kishinta tace, “Allah Sarki! Da ka rako ta nan sai mu kwana. Ya ce, “Babu komai, yanzun ma tana ta bacci.” Ta ce “Daya ‘yar uwar tawa fa ta Kano?” Ya ce, “Yanzun zan kira ta, in mun gama waya.” Ta ce, “To ka shigar da gaisuwata. Ya Nafisa?” Ya ce, “Tana lafiya, da na shiga gurin Hajiyarmu na ganta.” Ta ce, “To Masha Allah.” Bayan sun yi sallama ne ya kira Amna. Ta ce, “Honey sai yanzun ka tuna da ni ko?” Ya ce, “Kiyi hakuri honey, ban samu sukuni ba. Kina lafiya ke da duk mutanenki ko?” Ta ce, “Duk muna lafiya. Yaushe zan gan ka ke nan?” Ya ce, “Ai sai su Hajiya sun gama wannan bikin al’adar tasu, kin san wai ba dama in ganku sai an yi budar kai.” itaka Ta ce, “Yau ne za’ayi ko?” Ya ce, “Eh, ba ki bukatar komai ko?” Ta ce, “Hajiya tasa an yi mana komai.” Ya ce, “Shi kenan sai mun hadu?” Ta ce, “Eh, amma kana tunawa da ni kuwa?” Ya ce, “Haba honey, ko yaushe kina nan a raina.” Bayan sun yi sallama ya mike ya fita a ďakin, ya nufi gurin abokansa. Su Hadiza Yayar Salma kuwa jiki babu kwari suka isa gida, sai dai Hadizar ta hana a fadawa Innar don kada ta sake shiga damuwa. Sun ci gaba da shirin kai kaya a washegari kenan. Su ba su san ma za’a yi wani biki a gidan surukanta ba, sai da aka dauke ta. Sun za ci Kaduna za a kamar yanda ya ce musu lokacin da ya basu makullin gidan nata. Sun kammala siyan duk abin da suke ganin muhimmi ne a kai mata. gado da kujerunta mai zaman mutum uku, da guda dai-dai, sun sai katifa da kayan kicin wanda ya sawwaka. Sun siyo gara, Buhun shinkafa babba, da Taliya katon daya, sai dan karamin garin tuwo na Semovita. Sun hada da Mangyada da su maggi, sannan ta dan samu gudunmawa daga makota, ‘yan kofuna da dai dan abin da ba a rasa ba. Gidan su Aliya kam tun ana sauran ‘yan kwanaki suka kai mata kaya, don haka gara za su kai mata a washegarin. Sun yi mata kowanne bugu guda biyu, nufinsu daya su kai gidan Amarya daya su kai ma surukanta tare da kwanukan da ake ba dawa bisa al’ada. Badi’atu da sauran ‘yan uwa da suke tare da Nafisa tuni sun soma wanka suna sheka kwalliya tun bayan da suka karya. Shahida ta miko ma Badi’atu waya wadda ta fito wanka tana fadin, “Gashi har an gama yin Decorations din ko’ina da za’a saka mutane.” Ta amshi wayar tare da cewa, “Na manta ma ina mallakin wata wani kam.” Tana ganin Yaya Shatima ta zaro ido, tun da taga kiran ta tuna ajiyar da ya bata. Ta daga tare da fadin “Na’am Yaya!” Ya ce, “Kin kai mata kuwa?” Ta ce, “Yanzun zan kara dubawa don bata tashi ba.” Ya ce, “To kije da wayarki, zan yi magana da ita.” Ta ce, “To.” Ta fita taje kicin, duk babu wani abin kari. Ta shiga gurin Alhajinsu inda aka sauki su Amna. Su kam ga kayan karin nan sun ci naci sun bar na bari. Ta dauki Plate ta zuba dankalin Turawa soyayye da kwai da naman kaji. Ta dauki wani kofi ta zuba ruwan shayi, ta dauki madara da sauran kayan tea ta dora kan wani tire. Sumayya kanwar Amna ta ce, “Ba ki karya ba Badi’atu?” Ta ce, “Wata bakuwa aka yi.”. Ta aje can gurin kafar bene, sai da ta zo ta duba Hajiya suna can falonta da kawayenta suna tsara yanda za su gabatar da lamarin. Ta dawo da sauri ta dauka tayi sama. Tana zuwa ta samu Salmar zaune ta dauki sauran naman jiya tana ci. Badi’atu ta kalle ta cikin tsananin tausayi, ganin yanda idanunta suka yi jajir, sannan sun kumbura. Ta ce, “Ajiye wannan ki ci wannan.” Salma ta amsa tare da yin godiya. Badi’atu tayi masa flashing sai gashi ya kira. Ta ce, “Na kawo mata, gata ma.” Salma ta amsa. Ya ce, “Salma!” Ta ce, “Na’am!” Ya ce, “Kin tashi?” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “To ki ci abinci kiyi wanka.” Ta ce, “To, amma ba a zo min da kaya ba, tunda dama yau ne za su je min da kayan can Kaduna.” Ya ce, “Zan je in anso miki, zan ba Badi’atu ta kawo miki.” Ta ce, “To.” Ya ce, “Duk abin da ki ke bukata ki fada mata.” Ta ce, “To.” Ta ba wa Badi’atu wayar. Ya ce ma Badi’atu don Allah ta taimaka mata zai je ya kawo mata kayanta da zata sa. Badi’atu ta ce, “Insha Allahu zata yi.” Lokacin ya tafi gidan su Salma cikin sa’a dama suna son Auwal ya zo a kira shi batun motar da zata kai musu kaya Kaduna. Yaya Hadiza ce ta fito da Umar yaje ya sanar da ita zuwan nasa. Suka gaisa, ya ce a bashi kayan da Salma zata saka. Yaya Hadiza ta ce, “To.” Sannan ta ce, “Dama muna maganar motar kaya za’a tafi ayi mata jerene.Shatima ya ce, “To bari ya je zai aiko kaninshi Mustapha, ko ya kira Auwal ya amshi kudi sai a nemo mota don bai fito da katin shi na (A.T.M) ba. Badi’atu bata fito daga dakin ba sai da taga Salma ta ci ta koshi ta shiga wanka. Ta dawo ta debi kayan kwalliyarta lokacin ta tambayi ina Hajiyarta? Aka ce mata tana wanka. Ta ce, “Bari taje an aiketa in ta fito tana nemanta.” Can dakin ta koma inda ta samu ta fito. Ita ta zauna ta tsara ma Salma kwalliya, don haka kawai taji tana son Salman wai tana yi mata kama da wata Fatima kawarta Aminiyarta ce suna JS1 ta rasu. Salma ta ce, “Allah Sarki! Allah Ya jikanta.” Ya kira layin Badi’atu, ta sauko ta amshi kayan. Leshi ne mara nauyi mai kalar makuba da ruwan madara, ta saka shi, tayi kyau sosai. Badi’atu ta dauke ta hotuna kala-kala, ta ce “Zan nuna ma Yaya ne don yasan na cika alkawarin da na daukar masa. Salma tayi ta godiya. Badi’atu ta ce, “To, anjima in za a yi budar kai amma za ki canza kaya?” Salma ta dubeta cikin muryar tausayi ta ce, “Ai ba da ni za’ayi. Badi’a ta ce, “In ji wa? Kuma saboda me?” Salma ta ce “Hajiya ta ce ban da ni.” Badi’atu tayin shiru, don dama taji Hajiyar tana ta fadace-fadace.Mamakin halin da Hajiyar ta canza take yi, don iyaka saninta da Hajiyarsu ba muguwa ba ce. Ta samu Shatima a can waje Gate yana waya da Mustapha, wai in ya ciro kudin ya kai gidan su Salma. Da ya gama ta dube shi da murmushi. “Yaya wai duk cikin su kafi son Salma din nan ne?” Ya ce. “Me yasa ki ka ce haka?” Ta ce, “Naga kafi damuwa da al’amarinta fiye da na sauran.” Yayi murmushi, “Duk ba za ku gane ba ne. Kin gama abin da na sa ki?” Ta ce, “Eh, bari ma ka gani.” Ta ciro wayarta ta fito da hotunan Salma ta mika mishi. Yana ta kallon su cikin mamaki. Ya ce, “Amma kin yi editing ko?” Ta ce, “Sam! Ban yi ba.” Ya ce, “Ashe “yar small din tawa kyakkyawa ce.” Ya mika mata wayarshi, “Ki tura min su duka yanzu.” Ta ce, “To.” Tun sha biyu gidan ya soma dinkewa da manyan mata, don yau ne bikin Hajiyar karo na farko da zata aurar da danta, kuma zai auri mata uku, don ta ce su ta sani bata san ta hudun ba. An tsara gurin zaman amaran guda uku sai gurin da ango zai zauna da abokansa guda biyu. Sai rumfuna wanda jama’a za su zauna.Tuni wadanda aka baiwa kwangilar abinci sun kawo tare da wadanda aka dauko haya don su raba abinci, su ne za su ba kowa har abin sha. Sun tsara budar kan za’a fara shi karfe daya, don haka aka ce kowacce Amarya ana son ta shirya kafin lokacin. stil Hajiyar da kanta tasa aka kawo mai kwalliya. Amna a ka fara yi mawa, sannan Nafisa. Lokacin da ta zo gurin Aliya ta samu suna shawarar siyo mata audugar mata don taje alwala taga al’ada. Sai da ta gyara jikinta bayan Aisha ta fita ta siyo mata sannan aka zauna zaman yi mata tata kwalliyar. Duk kayan da suka saka a lokacin Hajiyar ce ta bada aka dinka musu tun kafin zuwan ranar. Duk da ba a auna su ba, doguwar rigar ta zauna ma kowa har tana jan kasa, kowace da kalarta. Koda yake sai da sauran suka zaɓa sannan aka kawo ma Aliya. Masu kidan ‘yan kasar Mali ne aka dauko, guri dai ya tsaru sosai. Mc abin magana ya soma fadin “A fito da Amare don ayi musu budar kai.” Salma tana jiyowa tamkar ta fito kallo. Lokacin ne Badi’atu tazo dauko ma Ango wasu kayan shi da zai sa shi ma. Ta ce da Salma “Ki fito kiyi kallonki, don Hajiya tana fama da mutane ba za ta gan ki ba.”Ta ce, “In wani ya fada mata fa?” Ta ce, “Ai babu wanda ya sanki bare ya fada mata din, ni kaina ai sai da Yaya ya aiko ni sannan na ganki.” Haka tabi Badi’atu cikin fargaba. Da suka fito harabar gurin shagalin bikin ta ce, ta shiga kujerun tsakiyar gurin ta zauna. Ta shige ta saje da Jama’a. Amna ce ta soma fitowa rigarta kalar bulu mai haske, an sha dogon takalmi, fuskarta rufe da wani mayafi da ke manne a jikin rigar. ‘Yan’uwanta ke yi mata jagora suna fesa mata abin kamshi har izuwa kujerarsu. Can sai ga Aliya itama, tata rigar koriya amma komansu iri daya. Da suka zauna kuwa zai yi wuya ka gane wannan wace ce, wannan wacece a cikinsu. Nafisa ce karshen fitowa ita kuma tata kalar siminti, sun yi kyau amma ita da ta zauna kasan ita ce karamarsu. Me abin magana ya ce, “Kai! Wannan Ango dangata ne, nan da shekara me zuwa ka cike ta hudu, duk shekara ka dinga kwasar jarirai guda hudu.” Aka sa dariya. Ya ce, “Yanzun ango muke jira, kafin ya iso ina ‘yan rawar nan su nishadantar da mu?” Nan fa ‘yan Mali suka shiga rawarsu mai ban sha’awa. Salma daga inda take zaune tana jin wasu mata suna musu. Wata ta ce, “An ce fa matan guda budu ne.” dayar ta ce, “Surutun mutane ne, su ukune. Ya dai so yin ta hudun Hajiyarsa ta hana.” Salma a ranta ta ce, “Gani ni ce ta hudun. Can Ango ya iso da gayyar abokai. Shatima ya yi matukar kyau cikin shaddar shi Gizna mai ruwan zuma. Hula da takalmi masu ruwan kasa kalar zaren Hula da aikin. Salma har mikewa tayi tana kallonshi, ya birge ta sosai. Sai da ‘yan bayanta suka ce “Zauna mana, kin tare mana.” Sannan ta zauna tana sauraron yanda matan gurin ke koda haduwar Angon. Shi kan shi mai abin maganar fadi ya ke, “Ga kasaitaccen Angon mu nan ya iso, kyakkyawan Ango ya iso sauran abokan suka je inda aka tanadar musu. Shi da guda biyu suka zauna a inda aka tanadar musu. Nan fa aka soma shirin budar kai, wata kawar Hajiya aka kira ta bude taron da addu’a, sannan aka bukaci Ango ya zo ya bude kan wadda ya zaba a uwargida. Abokanshi suka rako shi, ya zo gabansu ya tsaya. Nan ya dabirce domin ya kasa gane Aliya. Ya gane Nafisa don bata kai su girma ba, ya dan yi shiru, ya kuma tsura musu ido yana son gano Aliya. Da bai gane ba sai ya ce, “Aliya!” cikin sauri ta amsa, Ya ko sa hannu ya daga ‘mayafin fuskarta. Nan aka dauki tafi da guda. Aka ce danginta su zo su nuna cewa ita ‘yar dangi ce. Nan fa dangi suka yi tsuru-tsuru tunda ba su san da wannan irin lamarin ba. Abin da ke hannun su suka zo suka zuba mata, ba ma sabbin kudi ba ne, mutane sai kunkunai suke yi. Aka ce yazo ya bude ta biyu, ya zo ya bude Amna. Ita ma aka yi guda aka ce dangin ta su zo su fidda ta. Ruwan kudi suka shiga zazzage mata sabbi fil! Haka Nafisa. Salma da ke kallon ikon Allah ta ce, “Allah na gode maka da kasa Hajiya ta ce kar in fito, da wa zai zo ya fidda ni?” Daga nan sai aka ce Ango ya zo ya ba matanshi abin sha ko naci. ‘Yammata masu sanye da kaya iri daya su uku, su ne suka zo suka kawo wani dan tire. a rufe, daya da ‘yan kofuna guda uku, dayar kuma da hankici na share baki. Ta bude dan tire din, nakiya ce guda uku, ya dauki daya ya ba Aliya ta gutsura, aka yi tafi gami da rangada guda. Mai kofunan ta matso, ya dauka madarar shanu ce wadda ba a jima da tatsowa ba, ya kurba mata, sannan me hankici ta kawo ya dauka ya share mata. Duk su ukun hakan ya yi musu. [8/16, 21:35] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️* CHAPTER 4 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya Daga nan sai aka ce Ango ya zo ya ba matanshi abin sha ko naci. ‘Yammata masu sanye da kaya iri daya su uku, su ne suka zo suka kawo wani dan tire. a rufe, daya da ‘yan kofuna guda uku, dayar kuma da hankici na share baki. Ta bude dan tire din, nakiya ce guda uku, ya dauki daya ya ba Aliya ta gutsura, aka yi tafi gami da rangada guda. Mai kofunan ta matso, ya dauka madarar shanu ce wadda ba a jima da tatsowa ba, ya kurba mata, sannan me hankici ta kawo ya dauka ya share mata. Duk su ukun hakan ya yi musu. Shima haka aka umarce su su ba shi daya ta bashi nama, daya ta ba shi ruwa, daya ta ba shi tataccen ‘ya’yan itatuwa. Tsarin bikin ya birge mutane sosai, daga nan aka shiga daukar hotuna. Tsakiyar Aliya da Amna ya zauna, sannan ya rungumo su duka. Ya sake dawowa tsakiyar Amna da Nafisa, ya sake rungumo su. Sannan yayi da kowacce rungume da ita. Daga nan kuma aka shiga ci da sha na abinci. Ana cikin haka sai ga gara tazo daga gidan su Nafisa mota guda, kayan abinci da kuloli, da zannuwa, da shaddoji. Sai ga ta Amna ta linka ta Nafisa sau biyu, aka ce wannan ta iyaye ce, ta Ango an kai can gidan shi. Aliya ta rude, nan ta dauki wayarta ta yi wa Aisha kawarta text cewa taje gidan su ta ce a kawo garar nan, a basu duka har nata din. Can kuma sai ga shi an kawo, haka aka dire gara kashi uku. Salma ta sake yiwa Allah godiya da wannan rufin asiri da ya yi mata, ta ma daina jin haushin Hajiyar Karfe hudu biki ya tashi, aka ce da an yi sallah za’a kai Amare gidansu. Nan kowace Amarya ta koma gurinta don kimtsawa. Salma ma ta tashi da gudu don komawa samanta, wani abin mamaki har karo suka yi da Hajiyar a Halima Abdullahi K/Mashi kofar falo, cikin sa’a bata gane ta ba, sai ta ce “Wannan ‘yar waye haka ki ke gudu, tafi a hankali mana. Salma dama bata waiwayo ba, sai ta tafi saf-saf ta haye sama ta fada kan gado. Ko minti shida bata yi da shigowa ba, taji an turo kofar, a zatonta Badi’atu ce, don haka ta taso da ‘yar fara arta zata bata labarin karonsu da Hajiya, kawai sai taga Angonsu. Ta sauko cikin tsoro ta ce, “Don Allah Yaya ka fita, kar Hajiya tazo ta sake marinka.” Ya juya ya murda makulli, sannan ya dawo cikin tausayi. Ya ce, “Kiyi hakuri da zaman wuri daya, yanzun za ki fito, don yanzun za a kai ku.” Tayi murmushi, “Ai na fito. Badi’atu ta ce in fito in yi kallo. Naga kun yi kyau sosai da matanka.” Kalamanta suka sa tausayinta ya sake tsirga mishi. Ya ce, “Dama kina kallon mu shi ne ba ki zo .gurinmu ba?” Ta ce, “Tab! In zo in ɓata muku abinku! Hajiya ma zata yi fada.” Yayi shiru yana kallonta. Ta ce, “Kun yi kyau da ku ka dauki hoton nan, ashe gaske ne mu hudu ne? To a cikin su wa ka fi so?” Yayi ‘yar dariya, “Ke barda ke?” Ta ce, “Ai ni na sani ka tausaya min ne ba na cikin su.” Ya ce, “Ni dai kina cikinsu kuma nafi son duk wadda ta fi sona. Ta ce, “To wa ce ta fi sonka a ciki?” Ya ce, “Ban sani ba tukunna sai mun zauna.” Ya ciro wayarshi, “Kema ki zo mu dauka.” Ya zauna a kan kujera, bata ankara ba sai taji ya kamo ta ya dora a kan cinyarsa. Ya rungumota ya daga waya yana daukarsu. Wani abu take ji yana ratsa mata jiki, ta yunkura zata tashi, ya ce “Ki tsaya mu kara daya.” Ta ce, “Ya yi haka?” Ya yi dariya “To mu dauka a tsaye.” Ya sake kwantowa ta bayanta, ya matseta a jikinshi ya dauke su. Wayar ta shiga ruri ya daga tare da fadin “Munnir ya ce kazo mana mun fa idar da sallah.” Ya ce, “To bari ni in yi tawa in fito.” Ya shiga bandaki yayo alwala, a nan yayi sallah. Ya ce ta shirya. Ta ce, “Kayanta ne kawai da ta cire.” Ya bata wata leda ya ce ta sa a ciki. Ya fita ya bar ta tana sallah. Amna su ne suka fara tafiya saboda da motocinsu a hannu. Duk an kwashe Amaren saura Salma a sama. Shatima ya kira Anty Momiyo ya ce, “Ki ce ma Hajiya don Allah Salma a sama wai ga motar daukanta.” Halima Abdullahi k/Mashi Momiyo ta ce, “Tab! Ni na ma manta da ita, to ta ci abinci ko?” Ya ce, “Ban sani ba Anty, in kun yi ki sa ai kayi bayani.” Da sauri ta nufi gurin Hajiya, tana fadin “Hajiya ‘yar mutane a sama. Sai da Shatima ya ce a fito da ita sannan na tuna ko abinci bata ci ba.” Hajiya taja tsaki, “Nasan ba zai barta haka ba. Da zai ce a fito da ita wa zai fito masa da ita? Sauran ba danginsu ne suka fito da su ba! Ta sauko su wuce.” Hajiya Saliha ta ce, “Yanzun dai kin hana ayi wa yarinyar nan budar kai?” Hajiya ta ce, “Ai har abin da ya fi budar kai ita ya yi mata, domin jiya har biyun dare yana dakin.” Nan suka dauki salati, ita kuma ta nufi dakinta tana fadin “Ba ni da lokacin su.” Anty Momiyo da kanta ta hau sama, samu Salma tana zaune a kan abin sallah. Ta ce, “Au! Har da kaya ki ka canza? To taso ku je, kin ci abinci ko?” Salma ta ce, “Eh naci, domin na sakko kallo, da ana ba mutane nima aka bani na ci.” Anty Momiyo ta kalli Salma, “Lallai wannan yarinya ce, komai nata a kuruciya. Ji yanda take magana, iyakar gaskiyarta kawai take fada. Shatima yana tsaye Salma ta shiga bayan sabuwar motarshi, har ma sai da tayi mishi murmushi. Ya zo bakin kofar, “Ke kadai ce ko za a bi ta gidanku a dauki wasu?” Ta ce, “A’a, ai ina zaton fa duk suna Kaduna din gurin jere.” Ya ce, “Ina zuwa.” Ya shiga cikin gida ya kira Badi’atu ta fito. Ya ce, “Ke ba za ki ba ne?” Ta ce, “Zan je tare da su Anty Momiyo zamu je, in an tashi Dinner kuma mu dawo.” Ya ce, “Dinner da za’a tashi sha biyun dare, karfe tara za’a fara. Sai dai ku kwana. To ki zo ku zauna da Salma kuje tare, don Allah ki taimaka mata gurin kwalliya, don har da ita a dinner tunda wannan na abokaina ne.” Badi’atu ta ce, “To bari in kwaso kayan da zan yi amfani da su.” Shima ya koma gurin Salma ya ce, “Ina kayan da na ce ki dinka su za ki sa a Dinner?” Ta ce, “An dinka suna gidan mu.” Ya daga waya ya kira Auwal ya ce, “Ka amso min kayan Salma yanzun ka kawo min gidanmu.” Auwal ya ce, “Ai an tafi da Akwatunanta duka can Kaduna din.” Shatima ya ce, “Yauwa, hakan yayi.” Badi’atu tana fitowa suka kama hanya. Kowace Amarya tana gefanta da danginta suna kara kintsa mata guri, amma fa na Amna tun kafin ka shiga za ka hangi bambanci wanda iyayenta suka mata, har da wata Rumfa suka aje mata irin ta zamani kusa da na ginin don ta aje motocinta. Rumfar zata ci a kalla mota biyar. Sannan ga furanni na zamani da aka jera mata. Nafisa da taji ana labari, har ta zo iya wuya, wato ita don ‘yar masu kudi ce shi yasa yake bambanta komai. Haka da su Shahida suka shiga gurin Amna din suka ga duniya a tsire suka fito a rude suna labari. Suka ce, “Hatta fentinku na ciki ba iri daya ba ne.” Nafisa ta ce, “Ai ni na sani sai yafi sonta, kuna fadin ba dole ba ne ya zama haka. Salma kuwa suna tafe tana kallon ‘yan kauyukun da ke tsakanin Zariya da Kaduna, har tana tambayar Badi’atu “Nan ina ne?” Badi’atu ta ce, “Wai ba ki san Amarya shiru take yi ba?” Usman da ke gaban mota ya ce, “Ai wannan Amaryar ta daban ce.” Salma ta ce, “To kuma an ce tambaya mabudin ilimi ce.” Ya ce, “Haka ne.” Badi’atu ta ce, “Ba ki taɓa zuwa Kaduna ba?” Salma ta ce, “Tab! Ban taba fita daga cikin garin Zariya ba.” Suna shiga cikin Gate din gidan Salma ta bi gidan da kallo, har kofar falonta motar ta tsaya. Su Yaya Hadiza suka fito suka tare ta zuwa ciki. Badi’atu ta wuce neman gefen Nafisa, Salma tayi ta kallon ko’ina, har suna ce mata wai ba ta da kunya, tana leka ko’ina. Kujerun sun yi tsurut! A falon saboda girmansa, ga kujeru uku rak! Ta shiga dakin gadon yafi kyau. Sauran dakunan dai ba komai, sai dan tarkacen da aka sa mata. Kicin kuwa shima a rame. Amma dadi ya cika zuciyar Salma, tana ganin kamar babu macen da ta kai ta sa’a a duniya, wai nan gidanta ne. Kafin lokacin zuwa Dinner duk Amaran suna cikin shiri, domin Ango da kansa ya kira kowace ya ce ta zama cikin shi. Salma ce dai da bata da waya ya kira Badi’atu ya ce ta shiryata da kyau kafin karfe tara. Ya zaci Amna zata yi masa gaddama tunda ta ce, “in dai ‘yan’uwanta suna nan sai ya ji ta ce za su shirya da wuri. Salma tayi matukar kyau cikin riga da siket na pink din material. Kayan sun kama ta tsam! Duk da ba ta da kiba ko kadan, ‘yar singila. Badi’atu ta daura mata dankwali, sai tayi matukar kyau, tana ta kallon kanta a madubi. Mota daya aka so a dauke su, amma Amna ta ce a’a ita tana da motarta. Nafisa ta ce ba za ta zauna da kowa ba. Shatima ya kira Aliya a waya, ya ce za a dauko su da Salma ta ce ‘To.” Shahararren Hotel ne in da za’ayi Dinner. Hall din kuma mai kyau da tsari, ba’a bari kowace Amarya ta shiga ba, sai da suka zo su duka. Fuskar Nafisa tam babu fara’a, Amna kuwa zuciyarta cike da tambayar wannan wacece a cikinsu? A tare suka fito, shi ne a gaba sai Amna da . Aliya, Nafisa da Salma na biye da su, kowace da kalar shigarta. Kujerar su biyar aka zagaye tebur din da aka jere musu abin sha da tsotsa a kai. Can gefe ga dogon cake wanda aka yi surar mata guda hudu a jiki da namiji guda daya a tsakiyarsu. Bai zauna ba sai da yaga duk sun zauna, sannan ya fara nazarin inda zai tsoma nashi duwawun. Ya dauki kujerar shi ya sa ta tsakiyar Nafisa da Salma, sannan ya zauna. Amna da Aliya suka kalle shi, sai ya daga ma Amna gira, Aliya kuma ya kashe mata ido daya. Sannan ya ce, “Hasken fitila yana kashe min idone?” Aliya tayi dan murmushi. Amna ta dan saki fuska, sai dai shi ba don haka,,,,,,ba, yana gudun kar Amna ta tambaye shi wace ce Salma, sannan kuma zai ke kallon fuskar Nafisa wadda tayi murtuk da rai. Ma su kidan turanci ne irin wakar nan da ake yi cikin nutsuwa da sanyaya rai. Tun daga bude taro da addu’a har zuwa jawabin maraba da baki duk abokanshi ne suka yi. Abokai da ‘yan uwa suna ta zuwa suna daukar hoto da su. Daga nan aka zo batun yanka cake, duk suka je gaban cake din suka tsaya. Mai abin magana ya ce, “Wannan dangatan Ango ne, ga shi ga kyawawan matanshi. Yanzu za su saka hannu su duka don su yanka cake din su.” Duk suka sa hannu, Salma tsawonta bai kai ba don dogo ne. ya ce da Nafisa “Dan koma in da Salma take.” Salma ta dawo kusa da shi. Ta kara daure fuska, sannan ta koma. Da zata koma ta zauna nema, sai dai tayi ta maza ta cije. Duk da haka karshen wukar hannunta ya taba. Suka yanka ana yi musu tafi tare da murna. Me abin magana ya ce, “Yanzun Ango zai yanka cake ya ba kowacce daya-bayan-daya. Sannan suma su ba shi, yanzun zamu ga wadanne irin mata ya samu.” Shatima ya yanko ya soma baiwa Aliya, sannan ita ma ta amsa ta ba shi tare da risnawa, aka tafa. Me abin magana ya ce, “Uwargida mun gano cewa me ladabi ce, saura me bin uwargida.” Amnah kuwa daya Ya yanko zai bata sai ta amsa ta sa a bakinta, sannan ta kamo fuskarshi da hannuwanta biyu, ya gutsira a bakinta. Nan tafi da ihu ya cika gurin. Mai abin magana yana fadin wannan ta soyayya ce. Nafisa kuwa bayan ya bata da zata ba shi, har da hawaye don kishi. Me abin magana ya ce, “Wannan kuwa tana da tsoron Allah. Yanzu sai ‘yar autar Amare.” Salma ta girgiza kai cikin yanayi na shagwaba, tare da fadin “Yaya ba zan iya ba.” Ya rusuno da kunnansa daidai bakinta “Me ki ka ce?” Ta ce, “Tsawona ba zai kai ba.” Ya ce, “Zan taimaka miki.” Ta matso ta dan yanki kasan, ta kalle shi a zatonta zai durkuso ne tasa mishi, sai kurum taji caf! Yayi sama da ita, ya rike kugunta. Ta kalmashe kafafunta tamkar masu rawar turanci, sannan ta saka mishi a baki. Gurin ya dauki sowa. Maimakon ya dire ta sai kurum ya shiga juyi da ita. Guri kuwa ya dauki ihu da sowa. Sannan ya sauke ta, kowa ya koma mazauninshi, aka shiga ci da sha. Ba a tashi ba sai sha biyu da mintuna. Tun da aka dawo daga Dinner Salma ke zaune a barandarta, ga makulli a hannunta amma bata iya bude kofar ba, don tun kafin su Yaya Hadiza su tafi suka kulle suka bata makullin tasa a jaka. [8/16, 21:45] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️* CHAPTER 6 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya Yana gaida Hajiya, Mustapha ya shigo. Ya gaishe shi, Shatima ya ce “Don Allah Mustapha ka hada min duk kayana. Sannan kuma in an gama zirga-zirga ka dauki motar nan tawa ta da.” Dadi ya rufe Mustapha, ya shiga godiya. Hajiya ta ce, “Kafar yawo ta karu, ai dole kayi murna.” Mustapha yace Ai na huta, in na ari motarki, ko ta Alhajinma, sai a kira ni a ce dawo min da motata yanzun nan.” Ta ce, “Ai dai tayi maka amfani.” Ya ce, “Sai dai za ki dinga taimakawa da na mai ko Hajiyarmu?” Ta ce, “A’a wanda ya baka motar sai ya hado maka da na mai, ko kuma duk lokacin da zaka fita sai ka kira shi ya turo maka da na man.” Suka sa dariya. Bai baro Zariya ba sai da ya tabbata duk abokan shi na nesa sun wuce. Kusan karfe biyar ya shirya kayanshi a motocinsa guda biyu. Ya ce, Mustapha ya tuka masa motar suje, sai ya hau ta haya ya dawo. Yana cikin tuki ya tuna ashe fa zai bada abincin rana a gidansa, gashi tun da ya fito bai koma ba. A fili ya ce, “Lallai akwai kalubale na ciyarwa.” Yayi murmushi, tare da addu’ar Allah Ya taya shi. Gudu ya kara har Mustapha da ke biye da shi ya soma tunanin ko lafiya? Yana shiga gidan kai tsaye kofar Aliya ya tsaya. Bai bi ta kan Mustapha ba, bare kayan shi da ke cikin mota. Ya nufi falonta da sauri. Tazo ta bude tana yi masa sannu da zuwa, ya jiyo maganar mutane a ciki ya ce, “Kina da baki ne?” Ta ce, “Yan unguwarmu ne.” Ya ce, “Me ku ka ci? Na manta fa wai zan ba da abincin rana.” Ta ce “Ni dai naci biredi. Salma ma na ce mata tazo ta amsa ta ce akwai a gurinta.” Ya ce, “Ina zuwa, bari in ji sauran.” Daidai lokacin Mustapha ya karaso gurin su. Suka gaisa da Aliya, ta ce ya shigo. Ya shiga taje ta kawo masa cin-cin da ruwa, tana fadin gashi bani da komai, ni ko me zan baka? Tana ta haba-haba da shi. Shatima yaje gurin Amna ya zaci ‘yan uwanta suna nan. Amma sai ya ji gurin tsit! Ya shiga kiranta “Honey!” daga dakin da ke rufe dazun ta amsa da cewa, “Honey!” Ya shiga dakin a nan ya zama tamkar soko, domin dakin ya tsaru fiye da sauran dakunan. Ya kalleta a gaban madubi tana kwalliya, ya je ya tsaya a bayanta suna kallon juna ta madubi. Ya isa ya dafa kafadunta “My honey kin yi kyau matuka, wannan dakin ya dace da me kyau irinki.” Ta ce, “Honey wannan dakinka ne, shi yasa aka rufe shi. Ya ce, “Wai sun tafi ne? me ku ka ci da rana?” Ta ce, “Sun dafa Indomie.” Ya ce, “Kin tabbata ba su tafi da yunwa ba ko?” Ta ce, “A’a.” Ya ce, “To ke me ki ka ci?” Lokacin ne ya dora yatsun shi a kan lebunanta. Tayi dan fari “Ban ci komai ba, amma tunaninka ya kosar dani.” Ya kwanto a kan kafadarta fuskarsu suka daidaita. “Ina son ki Amna.” Ya fada cikin murya tattausa. Ta lumshe ido “Ina tsananin sonka mijina.” Yayi mata wata magana a kunne, tasa tafukan hannunta ta rufe fuskarta. Ya saketa yana dariya tare da fadin “Da gaske ni ke yi, bari in je in dawo.” Tabi kofar da kallo bayan ya fita, sannan ta sauke ajiyar zuciya. Tayi imani da gaske Shatima yafi sonta. Yana shiga gurin Nafisa, tana zaune a falo ta mike a kan kujera tana danna waya. Ta dago ta kalle shi tare da amsa sallamar kasa-kasa. ya zo ya zauna a hannun kujerar, yasa hannu ya dago fuskarta. “Haba Amaryata! Wai fushin me ki ke yi da Angonki?” Ta lumshe ido. “Bayan ba ka sona, don kaga su Alhaji ne suka hada mu.” Ya koma kan kujerar ya zauna, sannan ya janyota jikinshi. “Wa ya fada miki cewa bana sonki? Haba sweetyna, wallahi ina sonki tun kina Karama, ban dai taba fada ba ne. Allah Ya taimake ni su Alhaji suka yi min gata.” Tayi murmushi, “Har naji dadi.” Ya ce, “Kina jin yunwa ko?” Ta ce, “Ban ji yunwa ba, su Shahida ma sunyi-sunyi in ci indomie da suka yi na ce bana jin yunwa.” Ya kai hannu ya shafa cikinta, “A’a bari a samo miki wani abu. Me ki ke son ki ci?” Ta ce, “Abin da za ka ci.” Ya sumbaci kumatunta “To bari in je in nemo mana. Ya fito ya shiga gurin Salma. Bata ji shigowarshi ba, tana dayan dakinta wanda babu komai a ciki, tana kakkaɓe tsofaffin littafanta na Makaranta tun tana JS1 har zuwa 3. Ya ce, “Ke kuma me ki ke yi a nan?” Ta ce, “Ina duba takarduna ne ko da wanda zai min amfani. Ya ce, “To ajiye ki zo.” Ta same shi zaune a falo. Ta durkusa a gabanshi. Ya kama hannunta. “Zauna nan.” Zai dora ta a cinya ta ce, “Yaya bari in zauna a nan.” Ta nuna kujerar kusa da shi. Ya ce, “Nan za ki zauna.” Ta ce, “Wani abu ni ke ji.” Ta fada tare da rufe fuska. Ya kyalkyale da dariya. Cak! Ya daga ta ya dora ta kan cinyarshi tare da rungumeta. “Babyna kina jin yunwa ko?” Ta ce, “A’a.” Ya ce, “Aliya ta ce ta ba ki biredi.” Ta ce, “Bata bani ba, dama ina da wani ragowa na safe.” Ya ce, “Me za ki ci da dare in kawo miki?” Ta ce, “Ni fa komai ina ci, ko Rogo da dankali ne zan ci.” Yayi dariya, “Su ki ke marmari? Ta ce, “A’a wai naga su ne mutane basa so.” Ya dire ta sannan ya mike, “Bari in nemo mana abin da zamu ci.” Da ya dawo gurin Aliya, ya samu tayo wa bakinta rakiya’ za su wuce. Ya ciro dubu biyu ya basu, ya ce su hau mota. Suna ta godiya. Ya ce ma Aliya ta turo mishi Mustapha. Sun kwashe kayan cikin mota guda daya, ya ce “Hau muje.” Gidan abinci suka je suka siyo. Ya siyo har da su shawarma don ba lallai Amna ta ci abinci ba. Suna zuwa ya sallami Mustapha don kada dare yayi masa. Yana ba Aliya abincin duka ya wuce Masallaci nan kusa da su. Sai da yayi Isha’i sannan ya shigo. Ya ce ma Aliya ta fito da abincin nan ta shirya su don nan zai kira su duka aci, sannan yayi amfani da wannan damar ya hada kansu. Ta ce, “Hakan yayi.” Ya fito ya ce da Maigadi ya rufe gidan kawai. Sannan ya nufi gurin Nafisa don yafi tunanin zata fi ba shi matsala. Ya ce, ta zo sashen Aliya. Ta ko bata rai, sai yayi kamar bai lura ba ya fita. Yana shiga gurin Amna ta idar da sallah. Ya ce ta taso za suci abinci tare a gurin Aliya. Ta kalle shi “Mene ne?” Ya ce, “Gurin Aliya zamu je honey, saboda ina son in yi magana da ku.” Ta tabe baki, “Yi hakuri honey ban raina ka ba, amma gaskiya ba zan iya zuwa gurin wata ba.” Ya isa gurinta ya kama hannunta. “Haba honey, Aliya ta girme ku fa!” Ta ce, “Wannan ba matsalata ba ne, amma ba zan je ko ina ba.” Zai kara magana ta ce, “Honey banason muna yin jayayya please.” ya juya zai fita, ta ce “Yauwa honey, mene ne labarin yarinya ta hudu da muka je dinner da ita?” Nan take ya ji yawun bakinshi ya dauke. Ya dube ta. “Labarin yarinyar yana da tsawo.” “Gajarce min don in fita a duhu.” Ya ce, “Ita ce mace ta hudu, na aure ta ne don in taimaki rayuwarta, in cece ta, amma ba don so ba.” Ta tsura mishi ido, sannan ta daure fuska, “Auranta shi ne taimako na Karshe da zaka iya mata in ba haka ba za ta mutu?” Ya ce, “Honey shi yasa na ce miki labarinta mai tsawo ne.” Don ya kauda zancen ya ce “Zamu iya zuwa dakinki mu ci abincin?” Ta daga kafadu, “In kun ga dama ina yin maraba da ku.” Yana fita ya sauke ajiyar zuciya. Ya koma gurin Nafisa, ya ce “Tazo dakin Amna.” Salma ma ya same ta ta idar da sallah, ya kira ta. Ya je gurin Aliya, bai boye mata yanda suka yi ba, taji haushi… amma sai ta nuna ba taji ba. Ta ce, “Muje, durkusa ma wada ba gajiyawa ba ne, sai ka tashi da tsawonka.” Duk sun gigita da ganin falon Amna, Salma kuwa kasa shiru tayi ta . kalli Amnar wadda ta kwaso cokula ta zuba a cikin tiren da ke kan dinning din da za su zauna ta ce, “Anty gaskiya dakinki yayi kyau. Zamu iya leka sauran dakunan?” Aliya da Nafisa suka kalleta da sauri, har Nafisa ta kasa. dannewa taja tsaki. Amna cikin maganarta.can kasa ta ce, “Sosai kuwa, ku shiga ko ina.” Har Salma ta mike Shatima ya ce, “Jira mana aci abincin dama ya soma hucewa.” Salma ta dube shi, tare da fadin “To.” Tamkar Shatima ya sani Amna shawarma kadai ta ci sai madara. Nafisa ma kadan ta ci da alamu ita ba mai cin abinci ba ce. Duk da har da kishi da suka gama, ya ce su koma kan kujeru yana da magana da su. Ya ce, “wa zai bude musu da addu’a.” Salma ta cafke, don sun saba yin addu’a in anje gidan gaisuwa ko taya mura daga Islamiyarsu. Sai dai shi ne ya karasa addu’ar da fatan Allah Ya basu zama lafiya, ya hada kansu. Ya ce, To yana son sanar da su kamar yanda suka sani Aliya ce uwargida don ta dan girme su. Yana son su bata girmanta. Ita kuma yaja hankalinta da cewa tayi musu adalci, sannan ya ce dukkansu ga amanar Salma, yarinya ce kankanuwa yana son in tayi ba daidai ba su sa ta a hanya. Ita kuma ya ce ta bi kowa sau-da-kafa. Ya bukaci jin ta bakinsu. Aliya.ta ce, “Insha Allahu zata yi fiye da yanda yake so.” Amna ta lumshe ido cikin isa ta ce, “Zan kula.” Nafisa ta ce, “Naji, amma da ka ce ga amantar,wannam yarinyar shi ne ban dauka ba, don ba a rainon kishiya ko jaririya ce. Salma dai burinta a gama maganar ta kalli cikin dakunan gidannan, don haka da ya ce Salma ba ki ce komai ba? Ta ce, “Ni Yaya duk yanda ku ke so wallahi haka zan yi.” Kafin yayi magana ta ce, “An gama mu kalli dakunan?” Tausayin Salma ya tsirga mishi, yarinyar babu komai a cikin zuciyarta. Daga shi har matan ba su gabanta. Ya ce “Za ku gani ki bari a gama magana.” Ta ce, “To.” Ya ce, “Sai batun kwana, ni dai in sona ne in yi kwana daya a dakin kowaccen ku, amma ku ya ku ka gani?” Aliya ta ce, “Yayi.” Amna ma ta ce “Yayi.” Nafisa ta ce, “Ai dama sai hakan, don in ya wuce haka sai bayan wane lokaci za ka ga mijinka?” Ya ce, “Ke wai fadin to ne matsala?” Ya dubi Aliya, “Yau nan ni ke kenan?” Ta ce, “Haka ne. Suna tashi Salma ta ce “Zaku tafi ba mu gani ba.` Nafisa ta ce, “Ke bakauyiya sai kiyi ta kallo.” Aliya dai yi tayi kamar an kira wayarta, tasa a kunne ta fita tana fadin “Hello! Hello!! Salma kuwa sai da ta leka ko’ina, Shatima yayi mata jagora. Sai fadi take “Aljannar duniya!” Suka dawo falo inda Amna ta harde a kan kujera ta ce, “Anty guri ya yi kyau Allah ya kara arziki.” Amna tayi dan murmushi, sannan ta ce “Amin.” Suna fitowa Salma ta ce “Tsorona daya fa Yaya zan kwana ni daya yau, in aka dauke wuta zan firgita.” Ya ce, “Ba za a dauke ba in Allah Ya yarda, to a haske ki ke kwanciya?” Ta ce, “Sosai ma. Jiya sun dauke wuta Allah yasa Anty Badi’atu tana nan, na kankameta.” Ya ce, “Dama ke sarkin tsoro ce?” Ta ce, “Kai, Allah ko da ranar nan tsoro nayi ta ji.” Ya ce, “Muje in raka ki, kiyi addu’ar bacci babu abin da zai same ki.” Bayan ya sa ta ta rufe kofa, ya nufi dakin Aliya yayi wanka yasha sabbin kaya, ya dauki makullin mota ya fita. Kajin Amarci ya siyo da madara mai sanyi, da sauran kayan zaki, don ya lura Amna tana son shan zaki ko ya ce an saba musu da shan zaki. Kai tsaye gurin da motocin ta suke ya wuce, ya saka tashi. Sannan ya fito da ledojin ya nufi falon Amna. Yana shiga ya kulle kofar, don yasan ba zai fito ba sai gobe. Dakin da ta sanar da shi cewa nan ne nashi, nan ya nufa. Karan ruwan da ya ji daga cikin bandakin shi ne yasa shi tunanin tana ciki. Sai ma ya ga kayanta da ta cire a kan gado. [8/16, 21:53] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️* CHAPTER 5 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya kunnansa daidai bakinta “Me ki ka ce?” Ta ce, “Tsawona ba zai kai ba.” Ya ce, “Zan taimaka miki.” Ta matso ta dan yanki kasan, ta kalle shi a zatonta zai durkuso ne tasa mishi, sai kurum taji caf! Yayi sama da ita, ya rike kugunta. Ta kalmashe kafafunta tamkar masu rawar turanci, sannan ta saka mishi a baki. Gurin ya dauki sowa. Maimakon ya dire ta sai kurum ya shiga juyi da ita. Guri kuwa ya dauki ihu da sowa. Sannan ya sauke ta, kowa ya koma mazauninshi, aka shiga ci da sha. Ba a tashi ba sai sha biyu da mintuna. Tun da aka dawo daga Dinner Salma ke zaune a barandarta, ga makulli a hannunta amma bata iya bude kofar ba, don tun kafin su Yaya Hadiza su tafi suka kulle suka bata makullin tasa a jaka. Domin babu wanda yaje a cikinsu. Ranar dama yinin yunwa suka yi tunda ba a kawo musu abincin. ‘yan jere ba, wa ma yasan sun zo wani jere? Shi yasa suka ce ba za su je wata Dinner ba. Tana shawarar yanda zata yi, taga mota ta shigo. Taga abokan Ango ne suka rako shi, taje kusa da Munnir ta ce, “Yaya.” Ya waiwayo. “Lafiya ba tun dazu aka maido ku ba?” Ta ce, “Ban iya bude kofar ba ne.” Shatima ya fito a motarsu da ta shigo daga baya. Munnir ya ce, “Ango kazo ga Amarya ta kasa bude kofa.” Ya iso “A’a, Salma dama tuni kina nan? Ina su Hadiza?” Ta ce, “Sun tafi tunda muka zo wai suna jin yunwa ba za suje ba gurin Dinner.” Ya ce, “Subhanallah! Da yunwa suka tafi?”. Salma ta ce, “Eh.” Yaje ya bude mata sannan ya ce “Za ki iya kwana ke kadai?” Ta ce, “A’a, ina jin tsoro. Ya daga wayarshi ya kira Badi’atu, ta daga cikin yanayin bacci ta ce, “Yaya” Ya ce, “Dan fito gani a nan cikin harabar gida, za ki taya Salma kwana?” Ta ce, “To.” Da ta fito ya ce, “Yanzun daga dawowa har kin soma bacci?” Ta ce, “Na gaji Yaya.” Ya ce, “To ku shiga.” Badi’atu ta ce suje su kwanta don bacci take ji. Tare da Alkalamin Sai taga Salma ta kwanta da kayan jikinta. Ta ce, “Yaya zaki yi bacci da kaya masu kyau? Zama ki iya bacci da wannan kayan?” Ta tashi zaune a kan Gadon tare da fadin “Nima duk na gaji ne.” suka bude akwatin kayan ciki hade da na bacci. Ta ciro mata wasu kayan baccin ta ce tasa. Salma ta dago wasu irin masu shara-shara din nan. Dan wando ne da ‘yar riga. Ta ce, “Yanzun wannan ma sai a sa?” Badi’atu ta ce, “Me zai hana, ran da mijinki ke dakin ki za ki sa.” Salma ta ce, “Tabdijam! Wallahi ba zan iya ba.” Badi’atu ta ce, “Ke da za ku yi gasa!” Salma ta ce, “Ni ba ruwana.” Ta dago wata bireziya ta ce, “Dubi fa wannan ina zan kaita, duk kayan ciki sun yi min yawa.’ Badi’atu ta ce, “Ai ba a zata Karama ba ce shi yasa, kuma Yaya bai tambayo size din ki ba ne ko?” Salma tana dariya ta kalli kirjinta. “To ni me zan sa ma bireziya a nan, ban fa dade da farawa ba, da kirjina shafe yake. Kawai Anty Badi’atu ki kwasa.” Badi’atu ta ce, “Wai! Kar Yaya ya ji kina ce min Anty ba zan dauka ba, ki bár su nan gaba sai ki saka, masu tsada ne fa.” Salma dai ta dage sai da Badi’atu ta diba guda biyu pant biyu, don suma din sun yi mata yawa. Ta ce, “Amma ki fada ma Yaya sai ya sai miki daidai ke.” Salma ta zaro ido “Sai kuma in ce ya sai min pant!” Badi’atu ta ce, “To ba mijinki ba ne?” Salma ta ce, “Ni ba zan iya ba.” Haka kayan shafa Salma ta ba Badi’atu damar ta zaba, Sun jima kafin suka hau gado suka yi bacci. Nafisa tana ta juyi a kan gado, kadan-kadan tana jan tsaki, ranta kuwa wani kunci ne ke damunta. Ta tashi ta sauka a kan gadon tana kallon su Shahida, da sauran su suna bacci. Ta kalli gurin da Badi’atu take kwance. Yayanta ya kirata. Ina ya tura ta oho. Ta kalli madubi, taga yanda tayi kyau, ga lalle tasha, ban da gyara da aka yi mata irin na Amare, amma yau duk sun tashi a banza. Darenta na farko, daren da kowace ‘ya mace ke burin gani. Amma Angon yana can gurin wata. Hawaye suka zubo mata. Ranar dai bata runtsa ba sai da sanyin dare ya ratso, sannan ta kwanta bacci yayi gaba da ita. Ba za ka gane yanayin da Amna take ciki ba. amma dai da ka kalle ta za ka fahimci tana yin nazarin wani abu. Har yanzu bata samu amsar da zata ba ‘yan’uwanta ba a kan Salma. Domin ita kanta tana bukatar sanin wacece Salma. Kenan ita ma matarshi ce? Ta sani mata biyu suka yi magana duk da ita ne ta uku, kuma tayi iyakacin tunaninta don ta tuno ko ukun suka yi lissafi, amma bata tuna ba. In ko haka ne ya fara karya kenan? Lokacin da abokan Angon suka shiga dakin Aliya, ita daya ce zaune a falon ta rufe fuskartą. Sun dan yi wasa irin nasu na abokai, sannan suka yi addu’o’i da kuma shawarwari, suka yi bankwana suka tafi. Bayan sun ajiye mata abubuwa na al’ada. Ya ce, “Gobe fa za ku zo ku sake raka ni wani dakin.” Suka ce “Kayi kadan, mun yi maka wajibin sauran ya rage naka. Bayan tafiyar su ne yazo ya samu Aliya, “Tashi muje ciki.” Ya kalli kajin da abokanshi suka kawo ya ce, “Wannan kuma ya zan yi da su?” Ta ce, “Guda nawa ne?” Ya ce, “A’a ka bari kowacce randa zaka shiga gunta kaje a matsayin Ango da kajin ka da abubuwan da ake zuwa da shi na al’ada. Amma duk wadda ka ba yanzun ka fita daga dakinta zata ji babu dadi.” Ya ce, “Haka ne, amma kwana nawa ya kamata in ke yi a tsakaninku?” tayi dan murmushi, “Wannan ka bari sai da safe in ka tara mu, ko ba za ka yi mana nasiha ba?” Ya ce, “Zan muku mana, kin san fa har yanzun ban yi ma Amna zancen Salma ba, na rasa yanda zan yi.” Ta ce, “Kada ka damu, insha Allahu za ta fahimce ka.” Suka ci naman kazar sama-sama, sannan ya ce “Muje muyi sallah don godiya ga Allah tare da addu’ar neman albarkar da ke cikin aurenmu.” Aliya ta ce, “Kash! Ina fashin sallah.” Ta fadi tare da kallon fuskarsa. Ya kuwa canza fuska, sai taji hakan bai mata dadi ba, domin itama a burinta ta zama ita ce ta farko da zai kusanta a cikinsu. Ta sake kallon shi. “Don haka kayi hakuri.” Ya dan yi murmushin yake, “Haba ba komai, ai ba laifin ki ba ne.” Ta ce, “Ko za ka je gurin wata daga ciki?” Ya taso yazo ya rungume ta. “A’a ba gurin wadda zan je, na sani ko dukkanku ma kuna da larurar a yau.” Ta ce, “Ba zai zama haka ba insha Allah. Ya ce, “Na hakura zuwa gobe.” Haka suka rungume juna suka kwanta. Saboda gajiya, har makara ya yi. Shida ya farka, yayi sallah sannan yayi wanka ya maida kayanshi don bai zo da kaya ba. Yaga har Aliya ta hada ruwan zafi ta jera kayan karin kumallo, dama har da kayan tea suka shigo mai yawa, jiya da za’a rako shi daki. Ya kalla sannan ya ce, “Bari in leka sauran mutanan gidannan, bai kyautu in zauna yin karin kumallo ba tare da nasan halin da suke ciki ba. Ta ce, “Haka ne.” Har ya nufi gefen Salma, sai yayi tunanin zata ci masa lokaci da shirmanta, don haka sai ya juya zuwa sashin Amna. Sai da ya kwankwasa sannan wata tazo ta bude. Ya ce, “Ba ku tashi ba ne ni na tashe ku?” Ta ce, “Mun yi sallah, mun koma ne.” Ta juya zuwa dakin da ta fito. Ya leka dakin da ya ke zaton Amna tana ciki. Sumayya ya gani tana danna waya. Ya ce, “Har kin tashi sarkin chart?” Tayi murmushi, sannan ta gaida shi. Ya ce, “Ina honey take?” Ta kalli kan gadon “Gata can.” Sannan ta tashi ta fita. Yabi dakin da kallo, an zuba dukiya mai yawa. Ya kalli kan gadon tana kwance a tsakiyar gadon ta rufe jikinta da bargo, gashin kanta ya sauka a dokin wuyanta, tayi kyau da baccin. Ya matsa kusa da ita, ya saka yatsun shi na tsakiya, ya kwashe gashin ya maida kan filo. Sannan ya sunkuya ya sumbaci kumatunta. Tayi mika sannan ta sake gyara kwanciya, bargon ya dawo kan cikinta, sannan ta koma rigingine. Rigar baccinta bata da nauyi, don haka yana kallon kirjinta ta leshin da aka yi kwalliya da shi a kirjin. Tsigar jikinsa ta tashi. Ya juyo ya fita falo. Sumayya tana kan kujera ya ce, “Ashe tana bacci.” Ta ce, “Eh da ka tashe ta ai.” Ya ce, “A’a bar ta ta huta. Me ku ke bukata saboda karin kumallo?” Ta ce, “Bari in kira Antynmu.” Ta shiga wani daki ta kira kanwar Mamansu. Ya gaida ta cikin girmamawa, sannan ya ce “Anty dama ina son in ji me ku ke bukata?” ta ce tana zuwa. Suna da kayan tea da komai, biredi ne kawai. Sai gas da babu bare su soya wani abu. Ya ce, “Gas dole sai rana tayi, amma bari yaje ya kawo musu biredi.” Sumayya ta ce “Anty akwai abubuwa masu amfani da wutar lantarki a kicin din Yaya Amna. Ni dai zan gasa biredi kuma zan soya kwai.” Ta kalli Shatima. “Yaya ka siyo mana me yanka yanka.” Ya ce, “To Sumayya.” Daga nan dakin Nafisa ya shiga. Kaf! Din su suna dakin da Nafisar take, ya shiga suka yi ta gaishe shi. Ya duba bai ga Nafisar a cikinsu ba. ya ce, “Ina Amaryata?” Suka ce, “Tana wanka.” Ya ce, “Me ku ke bukata?”. Shahida ta ce, “Dama yunwa muke ji.” Ya ce, “Akwai kayan tea ne nan?” Momi kanwar Nafisa ta ce, “Sosai ma, gasu can a store.” Ya ce, “Bari in kawo muku biredi.” Hamida ta ce, “Yaya Nafisa kuwa bata cin biredi.” Ya ce, “To fa! Yanzu me zan kawo mata, me take ci?” Momi ta ce, “Ai naga akwai Indomie sai ayi mata.” Ya ce, “To bari yaje ya kawo musu biredi. In ta fito a ce, yana gaida ta kafin ya dawo. Ya shiga gurin Salma itama sai da ya Kwankwasa kofa. Tazo ta bude, ya kalle ta. Sanye take da kayan bacci, sun yi mata yawa. Sai gashinta da ya sauka a bayanta. Sannan ga abin risho a hannunta tana ta kici-kicin sawa da zabori, tasa daya tana fama da na biyu. Ya ce, “Mene ne wannan? Ta ce, “Abin risho ta durkusa “Ina kwana Yaya?” Ya ce. ne. “Lafiya. Na ce miki ni ba Yayanki ba ne ko? Yanzun me za ki yi da wannan?” Ta ce, “Zamu sa ruwan wanka ne, kuma zamu karya.” Ya ce, “Tashi daga tsugunno mana, ba ki da butar jona ruwa ne?” Ta girgiza kai, “Bani da shi.” Ya ce, “To ai babu kalanzir din da za ki kunna rishon ko?” Ta ce, “Babu.” Ya ce, “Kina da flask din ruwan zafi?” Ta ce, “Bari in duba.” Ta fito dashi a cikin kwalinsa ya ce “Ciro.” Ta ciro, ya amsa ya ce, “Bari in je sai Aliya ta dafa miki. Ina Badi’atu?” Ta ce, “Tana bacci.” Ya ce, “To ina zuwa.” Yaje gurin Aliya ya bata filas din ya ce, a sa ma Salma ruwan zafi a nan.” Ta ce, “To.” Ya ce, “Bari in je in siyo musu biredi.” Ya dauki makullin mota. Ta ce, “To amma wanda ba shi da kayan tea ga wannan da su Munnir suka shigo da shi.” Ya ce, “Su duk suna da kayan tea Salma ce kawai.” Ta ce, “To in ka zo sai ka kai mata. Da yawa ya siyo, kofar Amna ya tsaya ya ba Sumayya ta dibi wanda zai ishe su, itama Shahida ta dibar musu. Sannan ya koma gurin Aliya. Ya ce, “Gashi in za ta kara.” Ta ce, “Nasun nan ma ya yi yawa.” Ta bashi kayan tea har da ragowar kazar da suka ci jiya, ta ce ya ba Salma. Ya dubeta cikin jin dadi ya ce, “Allah Yasa yanda ki ke bani hadin kai da na zauna lafiya, sauran ma su bani.” Ta ce, “Za su ba ka insha Allah.” Ya kai ma Salma, sannan ya dawo suka karya suna ‘yar hirarsu irin ta masoya. Da suka gama ya ce bari yaje inda su Munnir suka kwana. Ta ce, “Har da Munnir aka kwana a nan?” Ya ce, “A wannan dare ina zai koma Zariya?” Ta ce, “To kaje musu da abin kari.” Ya ce, “A’a masaukin da suka sauka akwai gurin cin abinci, nasan yanzun sun ma karya. Kila tare za mu wuce Zariya da su in kwaso kayana.” Yana gaida Hajiya, Mustapha ya shigo. Ya gaishe shi, Shatima ya ce “Don Allah Mustapha ka hada min duk kayana. Sannan kuma in an gama zirga-zirga ka dauki motar nan tawa ta da.” Dadi ya rufe Mustapha, ya shiga godiya. Hajiya ta ce, “Kafar yawo ta karu, ai dole kayi murna.” Mustapha yace Ai na huta, in na ari motarki, ko ta Alhajinma, sai a kira ni a ce dawo min da motata yanzun nan.” [8/18, 09:54] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️* CHAPTER 7 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya Bayan ya sa ta ta rufe kofa, ya nufi dakin Aliya yayi wanka yasha sabbin kaya, ya dauki makullin mota ya fita. Kajin Amarci ya siyo da madara mai sanyi, da sauran kayan zaki, don ya lura Amna tana son shan zaki ko ya ce an saba musu da shan zaki. Kai tsaye gurin da motocin ta suke ya wuce, ya saka tashi. Sannan ya fito da ledojin ya nufi falon Amna. Yana shiga ya kulle kofar, don yasan ba zai fito ba sai gobe. Dakin da ta sanar da shi cewa nan ne nashi, nan ya nufa. Karan ruwan da ya ji daga cikin bandakin shi ne yasa shi tunanin tana ciki. Sai ma ya ga kayanta da ta cire a kan gado. A ranshi ya ce, “Wannan yarinyar wanka a gurinta ko kifi sai haka.” Ya cire hularsa ya ajiye a kan durowar da ke gefen gado. Tana fitowa daure da babban Tawul, ta rufa da karami tana goge jiki. Ya sakar mata murmushi, tare da cewa, “Koma kiyi alwala muyi wa Allah godiya.” Dan jim din da tayi sai ya ji tsoron kar dai itama bata sallah! Ya ce, “Kin ji ni kuwa?” Ta ce, “Ina tunanin kamar nayia alwala, amma bari in sake.” Shi ne yaja musu sallah suka yi raka’a biyu, ya dafa kanta yayi addu’o’i kamar yanda ya zo a sunna. Taje gaban madubi zata shafa manta wanda take shafawa in zata kwanta, ya zo bayanta, “Kawo in shafa miki.” Ta kalle shi ta cikin madubin, ya kashe mata ido daya. Tayi murmushi, “A fuska kadai zan shafa.” Ya ce, “Eh kawo.” Tamkar yana shafa kwai a kan kanta haka ya yi wa fuskar. Ya kalli ledar da ya shigo da ita ya ce, “Ina zuwa.” Yaje ya dauko plate da wuka da cokali mai yatsu. Ya samu tana saka rigar bacci. Ya ciro kajin da sauran abubuwan ciye-ciye. Ta kalle shi, “Me za ayi kuma? Ba dai cin abinci ba?” Ya ce, “A’a cin kazar amarci zamu yi.” Ta waro ido, dole ne cin kazar?” ya daga mata gira. Ta shafa ciki, “Gashi na koshi ne da yawa honey.” Ya cire rigarsa farar singileti kar ce a jikinsa, ya ce “Bari in ba ki kadan.” Ta hau tsakiyar gado ta zauna. Ya dauki tiren ya hau shima, yasa wuka ya yanko naman ya tsira da cokali ya ce, “Bude baki.” Sau hudu ta karba ta ce ta koshi. Ya bata madara, shima kurɓarta daya. Ya sauka yayi shirin bacci. Yana hawa gadon ya ce “To tashi in fada miki abinda zai biyo bayan kazar nan da ki ka ci.” Ta ce, “Ka kwanta ka fada min.” Ya kwanta, sannan ya dagota zuwa saman cikinshi. Ya kai hannu ya latse fitilar dakin. Ya fito daga bandaki, ya zo ya sake jan yatsunta. Tashi mana honey kiyi wanka muyi sallah. Da kyar ta sauko ya jirata tayi wanka da alwala. Shi ne ya ja su sallah, sannan suka koma kwanciya, ya janyota jikinshi. “Jiya kin hana ni bacci.” Ta ce, “Ka hana mu dai Honey.” Cikin shagwaba tayi maganar, suka rufa sai bacci. Kamar jiya ya shiga dakin kowacce ya duba lafiyarta tare da tambayar bukatarta. Su ukun kowacce tana bukatar Gas don dafa abinci. Salma kuma tana bukatar kalanzir tun da wuri ya ba kowaccen su abin da take bukata. Salma da Aliya ya siyo musu kayan abinci, kayan miya ne ya ce bai san ina zai samo ba. Ya tambayi Maigadi, ya ce a ba shi ya siyo. Aliya ce ta rubuta mishi kuma ya ba shi kudin mota zuwa kasuwar Kawo. Da aka kawo ta raba hudu, ta ba da na kowa. Kafın yamma duk ya sallame su. Ranar dakin Nafisa zai kwana, kuma washegari zai koma aiki. Itama dai yasai Kaji da sauransu kamar dai na Amna. Ya ji dadin darenshi da Nafisa, domin ta kasance mai shagwaba tare da kokarin faranta mishi, kuma da sassafe ta hada mishi abin kari. domin ya fada mata dan hutun da aka ba shi ya kare office zai koma. Tana rataye da jakar a kafada ta rike wayoyinsa, ta ce “Sweety muje in raka ka mota.” Ya ce, “To.” Suna fitowa barandarta ya ce, “Bari in duba yanda sauran ‘yan uwanki suka kwana.” Ta dan taba baki, tare da fadin “To.” Dakin Aliya ya nufa, wadda dama tana tsaye a windownta na falo tana hango lokacin da suka fito, kan ya Karaso ta koma cikin uwardaki da sauri. Taki amsa sallamar har sai da ya nufo dakin da ya san zai same ta a ciki yana kiran “My love!” Ta amsa daga ciki. Ya shiga, ta gaida shi tare da dan yatsina fuska. Ya ce, ” ba dai ba ki jin dadi Ba Ta ce, “Na kwana da ciwon ciki ne.” Ya ce, “Shi ne ba ki kira ni ba?” Ta zo ta dafa kafadarsa. “In na taso ka da wannan daren ina za ka neman magani, gashi mu baki ne a unguwar, sannan kuma na tuna kai da Amarya ne zan katse muku soyayya.” Yayi murmushi, “Komai soyayya ai ciwo ya fi komai.” Ta ce, “Na samu sauki har za ka fita office!” Ya ce, “Eh.” Ta ce, “Allah Ya ba da sa’a, Ya tsare mana kai, Ya saka samo mana halak.” Ya ce, “Ameen.” Ta rako shi har zuwa Barandarta. Nafisa ta kalli lokaci a wayar hannunta ya dauki tsawon minti tara a dakin Aliya. Ya nufi gurin Salma ya kwankwasa kofar don ya murda ba a bude take ba. Ya buga sosai sannan ta bude, daga gani bacci ta tashi. Ya shiga ta durkusa ta gaida shi. Ya amsa tare da tambayar kafiyar ta. Ta ce, tana lafiya. Ya mike yana tambayar ta karya kuwa? Ta ce, tun da tayi sallah bacci ya dauketa. Ya ce, “To akwai abinda take bukata?” Ta ce, “A’a.” Ya ce, “To zai tafi office. Ya koma yau. Ta ce, “To Allah dawo.dakai lfy ya bada sa’a.” Har ya fita ya tuna ya “Yau a nan zan kwana fa!” Shiru yayi yana kallonta yanda tayi tambayar cikin tsoro. Ya ce, “Naga kin tsorata ne.” Ta kirkiro yake, “A’a ban ji tsoro ba, sai ka dawo to.” Yayi ‘yar dariya,sannan ya fita. Nafisa ta kalli wayar, ya ci minti shidda ya zo zai je dakin Amna. Ya ce, muje tare da na fito zan shiga mota, tunda kin ga motar tana kusa da dakinta. Nafisa ta ce, je ka fito. Amna ma bata tashi ba, yana tsaye ta bude bayan yayi ta bugu. Kayan bacci ne a jikinta, zai shiga ta rungume shi, suna rungume da juna ya ce, “Zan tafi office.” Ta ce, “To sai ka dawo.” Ya sumbaci kumatunta sannan ya ce, “Zamu yi waya ko?” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “Kin ci abinci?” Ta ce, “Yanzun na tashi, ban san me zan ci ba, in da ka siyo shawarma din nan da nisa?” Ya ce, “Sai an fita unguwar nan, can cikin gari ne. Shi za ki ci?” Ta ce, “eh.” Ya ce, “To bari in tafi da Maigadi sai ya kawo miki. Allah Yasa dai suna da shi da safe nan.” Ta ce, “Amin.” Leda hudu ya bashi, ya ce ya mika kowane daki. Salma ta yini cikin damuwa da tunani tun da Shatima ya sanar da ita. Duk tsoronta tafi son ta kwana ita daya da ta ya zo dakin. Da rana ta dafa shinkafa dafa-duka, shirman da Salma tayi ta manta bakinta ne ita daya, ta shirga abincin fal tukunya. Yini tayi ci, bayan ta shake masa kula. Da dare ma shi zata ci. Karfe shida ya shigo, dakin Nafisa yayi wanka, itama sai da yaje siyo kajin amarci. Yana can ne ma ya ga kiran Amna. Cikin sauri ya daga. Ta ce, “Honey.” Ya ce, “Na’am honey ya aka yi?” Ta ce, “Ina jin yunwa ne, da rana ma banci komai ba.” Ya ce “Ba akwai danye ba kuma nasa muku Gas.” Ta ce, “Honey indomie kawai na iya dafawa, kuma ta gushe ni, kai kuma ba ka kawo min me aiki ba.” Ya kasa magana, can ya ce “To bari in zo gidan amma yanzun me ki ke son ki ci?” Ta ce, “Chips.” Ya ce, “Shi kenan.” Leda hudu yayo, ya kuma mika kowane daki. Lokacin da ya shiga gurin Salma tana zaune cikin kujera sanye take da riga doguwa baka da dan kwalinta. Har kafafunta ta zauna a saman kujera, zuciyarta cike da tsoro, fatanta kada ya ce zai bukace ta, domin duk wautar ta dai tana da labarin abin da ake yi in an yi aure. Bai lura da ita ba ya ce, “Salma!” Ta amsa, daga in da take ya waiwayo. “Dama kina nan?” Ta sakko tazo ta tsugunna a gabansa. “Gani Yaya.” Ya ce, “Amshi wannan ki kai ciki.” Ta amsa tare da cewa kicin zan kai?” Ya ce, “Daki dai ki kai tare da plate da cokali da kofuna.” Ta ce, “To.” Da ta aje bata fito ba, sai ta zauna a bakin gado cikin sake-sake. Ya ce, “Salma!” Ta amsa daga ciki. Ya ce, “Zo.” Ta tsugunna a gabanshi. Ya ce, “Kije gurin Nafisa ki ce ta baki jakata ta office.” Har ta kai bakin kofa sai ta waiwayo, “Yaya dakin da muka ci abi Anty Nafisa din?” Ya ce, “A’a na farkon.” A bakin kofar ta tsaya ta kwankwasa. Nafisa ta fito ta dan bude ta leko. Ganin Salma sai ta hada rai tayi, mata kallon sama da kasa. Sannan ta ce, “Lafiya?” “Yaya ne ya ce ki ba da jakarshi ta office.” Ta sake tabe baki, sannan ta juya. Salma da karambani ta shige ciki don kawai tana son ganin dakin. Cikin sha’awa take bin falon da kallo, har ma bata san Nafisa tana miko mata ba. Sai da ta ce, “Dalla ni karbi.” Da sauri ta kalli Nafisa. Cikin ‘yar fara’a ta ce, “Kema Anty dakinki yayi kyau wallahi.” Nafisa ta taba baki tare da fadin “Ni rike da Allah.” Yaya Shatima ya rasa wadda zai aura mata sai wannan abin?” Salma cikin sanyin jiki ta amshi jakar ta fita. A zuciyarta kuma tana cewa ita wannan bata san abin arziki ba.” ta shiga falonta bata ganshi ba in da ta bar shi ba. Ta dora jakar a kan doguwar kujera. Sannan ta leka dakin ta don ta ga ko yana ciki. Daga bayan ta taji sallamar shi ya shigo. Ta waiwayo, dama ka fita ne?” Ya ce, “Eh.” Ya shiga cikin dakin ya aje kayan hannunshi a kan gado. Ta kalli kayan da na bacci ne da kuma gogaggu kala uku. Ya ce, “Ina za ki sa min kayan nan?” Ta ce, “Ga akwatuna na nan an kwashe kayan an saka a sif sai waccan bababr ce kadai da kayan da suka min yawa a ciki. Ya ce, “Wane kaya ne suka yi miki yawa?” Ta ce, “Ga su can cikin akwati, wannan rigar ma ta jikina ai ta min yawa.” Ya kalli akwatin, cikin zolaya ya ce, “Dauko.” Ta ce, “Ba zan iya ba, rannan ma Anty Badi’atu ce ta sakko da ita.” Ya ce, “In daga ki ki dauko?” Taja baya, ba zan iya ba. Ya sauke akwatin a kan gado ya zauna a bakin gadon. Ya bude, kayan cikin ne ya gani. Yayi murmushi tare da daga wata bireziya, yanzun wannan tayi miki yawa?” Tasa tafin hannunta ta rufe fuska. Ya ce, “To wannan fa?” Ta bude taga pant a hannunshi. Da sauri ta juya baya. Ya ce, cire in gwada miki in tabbatar. Ta waiwayo ta zare ido cikin mamaki.” Ta ce, “Haba dai!” Ya daure fuska, ina wasa da ke ke ne! Laifi ne Inna ce ki cire ki gwada in gani? Idanunta suka yi rau-rau a lamun kuka. Ta ce, “Don Allah kayi hakuri Yaya.” Tamkar yayi dariya amma sai ya dake. Ya ce, “Ban isa ba ke nan ko?” Ta fara buga kafa tana fadin Yaya don Allah kayi hakuri ka ji.” Yanda take yin abin ya birge shi, dan shi mutum ne mai son shagwaɓa. Ya tura akwatin gefe, ya hau gadon gaba daya ya mike kafa. “Zan kirga uku in baki cire ba zan zo in cire miki. Kuma duk abin da ya biyo baya ba ruwana.” Ta ce, “Yaya babu kyau kallon tsiraicin wani, Allah haka Malaminmu ya ce Shatima ya sake daure fuska tamkar gaske ya ce, “Shi Malamin naku har da miji da mata ya ce?” Tayi shiru. Ya ce, “daya!” Da sauri ta cire dankwalinta ta jefar a kasa, tana kuka kasa-kasa. Ya ce, “Biyu!” Ta ce, “Wayyo! Don Allah Yaya kayi hakuri.” Ya ce, “Ina cewa uku zan taso.” Ta ce, “To bani wannan din.” Ya wurga mata pant da bireziyar. Ta dauki bireziyar ta zage zif din da ke makata zuwa kafadarta, ta soma saka bireziyar. Ya ce, “Ke! Ba wani wayo da zaki yi min. Cire ki ajiye rigar daban sannan ki dauki wannan ki gwada, kuma saura kiftawar ido goma in ce uku.” Da sauri ta cire rigar sai ta juya baya ta kuma kulle idanunta, sannan tasa hannuwanta ta harde, ta rufe kirjin. Dariyar shi ta kasa rukuwa sakamakon sikyat din da ta sa a jikinta, ta kuma daure da dankwali a kugunta, alamun yayi mata yawa sosai. Yayi dariya har da hawaye, ita kuma tana ta dan kukanta jikinta kuma yana ta ɓari. Ya ce, “Salma wannan siket din fa da ki ka daure kugu da igiya? Cikin kukan ta ce, “Ya min yawa ne, kuma bani da wani.” [8/18, 17:21] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️* CHAPTER 8 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya Ya ce, “Ke! Ba wani wayo da zaki yi min. Cire ki ajiye rigar daban sannan ki dauki wannan ki gwada, kuma saura kiftawar ido goma in ce uku.” Da sauri ta cire rigar sai ta juya baya ta kuma kulle idanunta, sannan tasa hannuwanta ta harde, ta rufe kirjin. Dariyar shi ta kasa rukuwa sakamakon sikyat din da ta sa a jikinta, ta kuma daure da dankwali a kugunta, alamun yayi mata yawa sosai. Yayi dariya har da hawaye, ita kuma tana ta dan kukanta jikinta kuma yana ta ɓari. Ya ce, “Salma wannan siket din fa da ki ka daure kugu da igiya? Cikin kukan ta ce, “Ya min yawa ne, kuma bani da wani.” Yanda tayi maganar ya sake ba shi dariya. A ranta kuwa cewa take, “Mugu kawai, dole ka min dariya. ” Ya ce, “To kwance wannan madaurin.” Ta ce, “In na kwance zai fadi fa Yaya.” Ya ce, “Kin juya baya kina min magana bana jin me ki ke fada. Bari in zo in juyo da ke.” Ta ce, “Yi hakuri Yaya, Allah zan juyo.” Ya ce, “To juyo.” Ta juyo. Fuskarta ya kalla sharkaf da hawaye, idanunta a runtse, hannuwanta a makale a kirjinta. ya tashi ya tafi a sannu, bata ji zuwanshi ba sai dai taji an ja dankwalin da ta kulle siket din, lokaci daya kuma ya warware. Da sauri tasa hannu ta riko siket din. Ya saki sabuwar dariya tare da fadin, “To ai kuma kin bude kirjin.” Ta tsugunna da sauri tare da fadin “Na shiga ukuna!” Yayi dariya sosai sannan ya shige bandakinta tare da fadin “Ki zo kiyi alwala muyi sallah irin ta ma’aurata.” Yana wucewa tayi maza ta saki siket din, sannan ta dauki rigarta ta maida. Ya fito ya ce, “Kije kiyi alwala.” Wuf! Ta shige bandakin. Taci kuka, a ciki sannan tayo alwalar. Ta samu ya maida akwatin ya ciro wata yasa kayanshi, sannan ya cire na jikin shi yana saka na bacci. Ta juya baya don lokacin da ta fito yana kokarin saka dogon wando a kan gajeren jikinshi, sannan bai kai ga sa riga ba. Ya kalle ta yayi murmushi. Sai da ya shimfida Darduma, sannan ya ce, “Kin juya baya kamar kin ga abin tsoro, ki sa hijabi ki zo muyi sallah.” Bayan sun idar ya ce ta dauko musu kajin Amarci su ci. Gabanta ya fadi, ta tuna da suka je kauyen Innarsu biki wanshekaren da aka kawo Amaryar suka je dakinta shi ne ta ke ba su labari, wai in ango ya kawo kaza da daddare amarya ta yarda ta ci, to ango zai ce ta biya shi. Sai Salma ta ce, “To kudi za ka ba shi?” Sai Amarya ta ce, “Tab! Kama ki zai yi yata wahalar da ke, kuma ko kina ihu ba zai bar ki ba.” Duk da Amaryar ba ta fayyace ba, Salma ta gane abin da take nufi. Ya katse mata tunani da cewa, “Shima abin tsoro ne cin kazar?” Ta ce, “Na’am!, a’a dama na tuna ne da abincin da ka ce in yi da kai.” Ya ce, “Kawo in ga irin shi ko kin iya girki.” Ta dauko har da goran ruwa da kofi, da ya ke yasa an kawo musu katan-katan na ruwa da lemon roba. Ya bude shinkafar, yayi dariya. Ya ce, “Ai ni bana cin shinkafa haka tsura, ba wani dan ganye, ba wake, ba komai. Kuma ina zan kai wannan abincin? Kin dauki kula irin ta can kasan saiti, babbar ciki, kin shake.” Yasa cokali ya dan tona, kamshinta sun hadu da warin lalacewar, ga wani kauri. Ya ce, “Salma ai wannan ma ya lalace. Sannan kuma gashi yana kauri.” Ya dube ta, “Ba ki iya girki ba ko?” Ta ce, “Ni dai ban san irin naku ba, amma a gida ni nake yi mana.” Ya ce, “Dan kadan za ki ke dafawa, kar kiyi la’aklari da yawan na gidanku. Fita da wannan ki aje da safe ki zubar, kin ga kin yi ta’adi. Zubar da abinci ba shi da kyau.”Ta ce, “Zan bar shi a bude, da safe sai in dindima în ci, da rana ma in ci.” Ya zaro ido. “Wa ya fada miki ana barin abin da za a ci ya kwana a bude? Ba’a fada miki ba Manzon Rahma (S.A.W) yayi mana umarni da rufe abincin mu da na sha in dare yayi sannan mu kashe fitilunmu. Ranar fa naji kina cewa ba kya iya bacci, sai a haske.” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “To dama kin daina, don ba shi da fa’ida. Maida ki zo muci wannan.” Duk da kamshin ya ishe ta amma bata jin zata ci wannan kaza ta mugunta. Ya ciro cinya ya ce, “Bude baki.” Ta tuno da zancen wannan Amarya, in da a hirar take cewa, “Har fa a baki za ki ga suna baki naman.” Cikin sauri Salma ta girgiza kai, “Na koshi, bari dai in ci dankalin nan da kwan.’ Ya tausasa murya cikin sigar lallashi, “Kin san muhimmancin kazar nan kuwa?” Gaban Salma ya sake faduwa, a ranta ta ce, “Na sani sarai, ta zalinci ce. Ya sake maimaita tambayar. Ta ce, “A’a.” Ya ce, “Kowace Amarya ana kawo mata a daranta na farko, daran ta na alfahari, kuma dole ta ci.” Ta ce, “To in bata ci ba me zai faru?” Ya kai bakinshi ya gutsira, sannan ya ce, “In bata ci ba Angonta zai ji haushi, kuma zata hadu da fushin Allah.” Tayi shiru, a ranta ta ce, “Kai! Ana cewa aure hutu ne, gaskiya babu wani hutu a cikinsa… Ta dube shi. “To in ta roki mijin ya yafe mata fa kuma ta roki Allah?” Ya ce, “Za su yafe amma mijin zai rage sonta.” A ranta ta ce, “Ashe dai ina da mafita. Ya ma daina sona ba rage so ba Ta dauki kwan ta ce, “Ni ga abin da zanci.” Ya ce, “Ke nan ba za ki ci kazar ba?” Ta ce, “Ka yafe min zan roki Allah Shima ya yafe min.” Yayi dariya, har ya kusa kwarewa. Ta bude ruwa da sauri ta mika mishi. Sai da ya sha sannan ya ce, “Ke ba Amarya ba ce yau.” Ta ce, “In dai don wannan kazar ne naji.” Ya ce, “To sai ki fada min me yasa ki ke gudun kazar ki ta daran farko?” Tayi shiru. Ya ce, “Ina jin ki, in ba ki fada ba zan matse bakinki in baki.” Ta ce, “An ce biya ake, ni kuma dai ba zan iya ba.” Ta tsura mishi ido taga yanda zai dauki zancen. Yayi murmushi mai sauti, “Biya kamar ya ya?” Ta ce, “Nima dai ban sani ba, amma dai haka naji.” Ya ce, “Gurin wa?” Ta ce, “Wata Amarya ce a kauye ta ce haka.” Ya daure fuska, “Ok! Dama kuna yin irin hirar nan mace take tona sirrin gidan mijinta?” Salma ta ce, “A’a ni ba ruwana.” fuskarshi a daure tam! Ya nunata da yatsa, “Ko da wasa naji kin ba da labarin abin da ke tsakanina da ke, ko maganar da muka yi, sai na bata miki rai, kina ji na?” Ta ce, “Wallahi ni ina jin kunyar fadi ma.” Ya ce, “Ci kazarki, ni ba sai kin biya ni yanzun ba, nan gaba dai kin biya ni ko?” Ta daga kai. Ya dauki wani yanki ya ce, “Bude baki to.” Ta amsa. Ya ce, “Ko ke fa! Kina ta wani boye kirji ashe ma babu komai.” Ta rufe fuska da hannunta daya. Ya ce, “Yanzun me da me kike so a nan dakin? Kin ga sauran suna da TV da Fridge, ke ko hita din nan kina bukata.” Ta ce”Ni dai in sona ne kawai a bar komai a sani a boko da Islamiyya.” Ya ce, “To shi kenan. Amma zan sai miki kettle na dafa ruwan zafi, don ki ke tashi da wuri kina hada min koda tea ne, kar in yi lattin gurin aiki. Kema in kin soma zuwa Makaranta kin ga za ki ke shiryawa da wuri.” Ta ce, “To Yaya.” Ya ce, “Ba za ki daina ce min Yaya ba wai?” Ta ce, “Ni ban san to abin da zan kira ka da shi ba.” Yayi murmushi, “Shi kenan, shima na daga miki kafa zuwa nan gaba. Ki gama ci kije ki wanke baki, sai ki kwanta don ki tashi da wuri ki min abin da ya kamata, don kar in yi latti ko?” Ta ce, “To Yaya.” Sannan hankalinta ya kwanta. Shi ko falo ya koma yana cewa na biye miki ina da aikin yi. Ya ciro Laptop din shi ya shiga aikinshi. Tabbas Salma ta birge shi, domin tana idar da sallar Asubahi yaga ta nufi kicin ta kunna Risho, domin shi a kan doguwar kujerar yayi kwanciyarshi bayan ya gama aikinsa. Har zai shiga ciki sai kuma yayi tunanin kada ta tsorata da shi in ta farka, bare yasa ta kashe wuta Ta ce, da ruwan zafi zai yi wanka? Ya ce, “Ai bayin akwai na’ura mai dumama ruwa.” Ta ce, “Ita bata sani ba.” Ya ce, “Zo ki gani.” Ya nuna mata inda zata kunna ruwan ya dahu, da kuma in da zata murda ya zo. Tayi ta al’ajabi, har ma tayi masa tambayar da ta bashi dariya, wai ba za a iya diban ruwan ba a hada shayi? Yayi dariya sosai, sannan ya ce, “Amma ina ki ka taba ganin an sha ruwan bayi?” Itama tayi dariya, ta nuna na’urar da ake tsarki da ita, “Wai wannan to mene ne amfaninta?” Ya ce, “To kin gá dai wannan ruwan zafin shi an yi shi ne saboda in ba ka bukatar ruwan sanyi, ko kuma lokacin sanyi. Shi kuma wannan na tsarki ne, in ka gama bayan gida ko fitsari, kin ga ba a bukatar buta.” Ta saki dariya, “Ka san ni wanka nike yi da shi abuna?” Ya ce, “Wanka?” Ta ce, “Na zata wancan na saman na ganshi da fadi na manya ne, wannan kuma na yara, shi ne na ce ni yarinya ce. Ta nuna jerin sabulun wankanta da ke saman kwamin wankanta, ta ce “Kaga wadancan ko? Anty Badi’atu ta jera min su, sannan ta nuna min amfaninsu.” Ya ce, “To ban da wannan me ki ke son sani?” Ta ce, “Shi kenan.” Ya ce, “To zo ki taimaka min in yi wanka?” Ta fita da sauri tare da fadin “Sai ka fito.” Yayi kyau cikin kananan kayan da yasa, ya ce “Ya ki ka ganni?” Lokacin da take aje masa kayan shayi. Ta sake kallonshi. “Kayi kyau Yaya, dama kai me kyau ne. Ya dauki flaks din ya tsiyaya ruwan zafin a kofi ya ce, “Sai dai sona ne da ba kya yi ko?” Tayi dariya, “Ni ai ba zan iya sani ba.” Ya ce, “Na ce ki nemo yanda ake so da mene ne shi kanshi son amma kin ki.” Ta ce, “Ban san ina zan nemo ba.” Ya ce, “Shima na daga miki kafa zuwa nan gaba.” Ta bude biredin sannan ta bude robar bluebond “In shafa maka?” Ya ce, “A’a, ko kina son in yi kato?” Cikin dariya ta ce, “Eh mana.” Ya ce, “Saboda me?” Ta ce, “Saboda bana son a ce kayi aure kuma ka rame.” hankali?” Ya ce, “Ashe wani lokaci kina da Ta ce, “Au! Da ni Mahaukaciya ce kenan?” Ya ce, “A’a ban ce ba, sai dai ke yarinya ce, baby ce ke.” Zata yi magana ya ce, “Ke kin dinga cin wannan din ko ke ma kin yi katuwa.” Bai lura da yana biye ma shirmen Salma, sai kawai yaga karfe bakwai ta gota. Ya ce, “Kai! Nayi latti.” Ya mike ya dauki Jakarsa, bata tashi daga inda take ba ta ce “Sai ka dawo to Yaya.” Hannu ya daga mata ya wuce. Motarshi ya nufa kai tsaye a ranshi ya ce zai kira su a waya in ya je office. Aliya da ke tsaye a jikin window din ta mamaki da al’ajabi ya cika ta. Me yasa yau da ya kwana a ďakin yarinyar nan ya makara? Sannan bai zo in da suke ba? Nafi ta kalli agogonta, “Bari ya shigo taga minti nawa ita kuma zai mata.” Tana ganin ta haka zata iya gane wadda ya fi so cikin su uku, domin tun a jiya ta gano matsayin waccan Mahaukaciyar yarinyar, don ita minti shidda ya dauka a gurinta. Sai dai har karfe takwas bai shigo ba, gashi ta kasa tashi ta nemi koda abin kari, sai wani bakin ciki da taji yana yi mata tukuki a zuciya. Amna ya soma kira don layin Aliya ya ki shiga. Ta dauka da fadin “Hello honey!” Ya ce, “My honey na makara office yau, ban shigo ba ina fatan kina lafiya?” Ta ce, “Ina lafiya zumana.” Ya ce, “Kin ci abinci ko?” Ta ce, “Yanzun na tashi, zan sha tea ne da Indomie yau.” Ya ce, “To ki sha da yawa. Ta ce, “Jiya mun yi waya da Mom dinmu, ta ce za a kawo min mai aiki yau ko gobe.” Ya dan yi jim, me hakan ke nufi, shi zai biya ‘yar aikin? Ta ce, “Hello kana ji na kuwa?” Ya ce, “Ina jin ki.” Ta ce “Kaga na huta.” Ya ce, “Haka ne, to sai na dawo.” Yayi shiru yana juya wayar hannunshi. Kenan ana nufin sai ya dauki ‘yan aiki hudu ko ko me? Ya juya ya shiga kiran layin Nafisa. A cikin dakinta ta jiyo karar wayar, ta mike tana dauka wayar tana tsinkewa, kiran ya sake [8/18, 17:28] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2 🏚️* CHAPTER 9 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya tun a jiya ta gano matsayin waccan Mahaukaciyar yarinyar, don ita minti shidda ya dauka a gurinta. Sai dai har karfe takwas bai shigo ba, gashi ta kasa tashi ta nemi koda abin kari, sai wani bakin ciki da taji yana yi mata tukuki a zuciya. Amna ya soma kira don layin Aliya ya ki shiga. Ta dauka da fadin “Hello honey!” Ya ce, “My honey na makara office yau, ban shigo ba ina fatan kina lafiya?” Ta ce, “Ina lafiya zumana.” Ya ce, “Kin ci abinci ko?” Ta ce, “Yanzun na tashi, zan sha tea ne da Indomie yau.” Ya ce, “To ki sha da yawa. Ta ce, “Jiya mun yi waya da Mom dinmu, ta ce za a kawo min mai aiki yau ko gobe.” Ya dan yi jim, me hakan ke nufi, shi zai biya ‘yar aikin? Ta ce, “Hello kana ji na kuwa?” Ya ce, “Ina jin ki.” Ta ce “Kaga na huta.” Ya ce, “Haka ne, to sai na dawo.” Yayi shiru yana juya wayar hannunshi. Kenan ana nufin sai ya dauki ‘yan aiki hudu ko ko me? Ya juya ya shiga kiran layin Nafisa. A cikin dakinta ta jiyo karar wayar, ta mike tana dauka wayar tana tsinkewa, kiran ya sake shigowa. Ta daga cikin daure fuska tamkar tana gabanshi. Ta ce, “An tashi lafiya?” Ya ce, “Lafiya lau, kin karya kuwa?” Ta ce, “A’a.” Ya ce, “Kan me sweety?” Ta ce, “Ba ka ki zuwa ba, kila ma kaje ka duba kowa ni ce ban da matsayin da za a zo a duba ni.” Muryarta ta soma rawa alamun kuka. Ya ce, “Haba Nafisa! Ki min kyakkyawan zato mana, tun yanzun za ki soma dora zargi a tsakaninmu? Gaskiya ban ji dadi ba. Na makara ne shi ne dalilin da yasa na tafi office na ce zan kira ku in ji lafiyarku.” Ta ce, “To kayi hakuri.” Ya ce, “Ya wuce, amma kar ki sake. Sannan ki nemi abinci ki ci.” Ta ce, “Zan yi yanzun.” Ya ce, “To babu kuma wata matsala?” Ta ce, “Babu komai, sai ka dawo. Kayi tunanina.” Ya ce, “Zan yi, kema kiyi tunanina.” Ta ce, “Kullum kana raina.” Aliya tana ta kai-kawo a cikin dakinta tsakanin kicin da dakunanta, abin karinta take dafawa. Taliya ta ke son ci dafa-duka ta manja, sai dafaffen kwai. Sannan tana son hada shayi, zuciyarta kuwa cike da son sanin abin da yasa har ita da take ganin ta kai a zuciyarsa bai iya zuwa ya dubata ba. Sannan tana son jin shin me ya faru jiya da ta ga rufe kofar Shatima bayan ya fito daga dakinta ya dau kaya, ta zaga gurin windown Salma ta baya, taji kukan Salma tana fadin “Don Allah Yaya kayi hakuri..” amma bata ji muryar Shatima ba duk da tasa kunne sosai. Kuma kukan na Salma yafi yi mata kama da kukan shagwaba fiye da kukan laifi. Karar wayarta da ke jone a chaji ne ya sa ta fitowa da sauri, don tasan Shatima ne, domin ta ware masa ringing dinsa na musamman. Tana dagawa ta ce, “Masoyina!” Ya ce, “Kin tashi lafiya abar sona?” Ta ce, “Lafiya lau.” Ta sauke ajiyar zuciya. “Na zuba idanu ban ji ka ba. Ya ce”Yau nayi latti ne my love, shi yasa na ce bari in ji ya ki ke, cikin bai kara ciwo ba ko?” Ta ce, “Bai kara ba, dama yana min haka ko a gida, wani lokacin cikin dare zai tashi.” Ya ce, “Kuma ba ki taba ganin Likita ba?” Ta ce, “Na gani sosai ma aka ce wai ba komai, zan daina lokaci ne.” Ya ce cikin muryar tausayi, “Allah Ya baki lafiya.” Ta ce”To Salma ta sha’afa ne bata tashe ka da wuri ba?” Tayi maganar cikin son ta ji kurilla. Ya ce, “Wannan baby din kin san sai dai ni in tashe ta, kuma kin san tayi kokari gurin bani abin kari da wuri, ni kaina ban san me yasa ni yin latti ba. Ta ce, “Soyayya ce tayi dadi.” Ya ce, “To, soyayyar ce gata nan kala-kala, kowacan ku da irin wadda take bani. Yau dai kina fes-fes ko? Don ke yau ne amarcin naki, kyalli na koya cika cif.” Tayi ‘yar dariyar tsokana, “Ai ko har yanzun ban yi fes ba.” Ya ce, “Haba dai, har ina cewa ke yau in mun zo me tazarce ne, dan watanni mu dauki baby.” Cikin jin kunya ta ce”Haba dai?” Yayi ‘yar dariya, “Sai na dawo ke dai ki sa mu cikin addu’a.” Ta ce, “To sai ka dawo.” Tana kashe wayar ta ce, “Allah Ameen. Allah Ka sa ni zan soma dire da a gidannan, kuma namiji yanda ni ke Yayarsu haka ma dana ya zama babbansu.” Aliya ta kammala karin kumallonta tana zaune shiru ta kasa kwashe kayan, tunda bata ji abin da take son ji ba a gurin Shatima, ya kamata ta bigi cikin wannan wawiyar yarinyar cikin dabara. Dan kwanan silba ta samu ta shake da taliyar, sannan ta saka kwai guda daya ta nufi sashen Salma. Salmar tana wanke-wanke a cikin kicin ta jiyo sallama hade da kwankwasa kofa. Ta dauraye hannu ta fito. Ganin Aliya sai ta saki fara’a “Sannu da zuwa Anty.” Ta saki fara’a itama “yauwa sannu kanwata. Na ce tun da ke ba ki zuwa gaida ni ni bari in zo mu gaisa.” Salma ta ce, “Lah! Ba haka ba ne Anty, ki zauna mana.” Aliya ta zauna a hannun kujera, tare da fadin “Ban sani ba ko an hana ki ne.” Ta ce, “Haba Anty, wa zai hana ni? An dai ce min ne kada na ke shiga dakunan kowa.” Ta tsugunna tana gaida Aliya. Ta amsa tare da fadin “Tashi ki zauna a kan kujera.” Ta mika mata, “Ga taliya ko kema abinci ki ka dafa?” Salma tasa hannu biyu ta amsa tare da fadin “Na gode, ba abinci na dafa ba, Biredi na ci.” Ta ce, “Ai bani iya cin biredi kullum.” Salma ta ce, “Ni ai duk abin da na samu bana tara.” Aliya tayi dan murmushi, “Kin huta.” Tayi dan kalle-kalle a dakin. Salma ta ce, “Kin ga nawa dakin bai kai naku kyau ba ko?” Aliya ta ce, “Ai wannan duk ba wata matsala ba ce, sannu a hankali za ki sai duk abin da ki ke so ko?” Salma ta zaro ido. “Ina zan samu kudi, ni dai na gode ma Allah Anty tunda na samu mijin daba irin gama-garin maza din nan ba.” Aliya taji mamakin kalamin Salma, har ma ta kasa boyewa. Ta ce, “Har kin san namiji me inganci?” Salma ta rufe fuska cikin kunya. Aliya ta ce, “Ashe kin iya soyayya shi yasa ki ka sa Angon naki ya makara?” Salma tayi yar dariya, “Ni ban san wata soyayya ba Anty, shima ya sani.” Ta ce, “To ai jiya ina jiyo ki daga dakina kina kuka.” Salma ta zaro ido tana kallon Aliya. Aliya tayi ‘yar dariya, “Ai ina ji kina kukan shagwaba, Yaya kayi hakuri.” Salma ta rufe fuska. Aliya ta harare ta, lallai abin da take zato haka ne. Ta ci gaba da fadin “Har zan shigo ceto na zaci laifi ki ka masa.” Salma dai tayi shiru. Aliya ta ce. “Ko wani abin ki ka yi masa?” Salma ta sake rufe fuska tare da fadin “Babu ruwana, ya ce kada in fada ma kowa.” Gaban Aliya ya fadi, tayi shiru. Can ta ce, “To ai ba zan fada mishi ba, ni na dauke ki kamar kanwata ne, duk abin da ki ka yi ba daidai ba zan nuna miki. Kuma shima ya bamu amanarki.” Salma ta ce, “Ni dai kiyi hakuri Anty, tun da ya ce kar in fada ma kowa.” Aliya ta ce, “Shi kenan. Juye ki bani kwanon.” Salma ta ce, “Ki bari in na wanke zan kawo miki, dama naga dakin kowa naki ne ban gani ba. Aliya ta mike, “To sai kin zo. Bayan ta koma sashenta, tana zaune a cikin dakinta tana ta nazari. Yanzu Shatima saboda rashin hakuri ga su su nawa sai da ya kula wannan ‘yar yarinyar saboda ja musu raini? Duk da ta ki fada alamu sun nuna akwai abin da ya faru tsakaninsu. Sai dai zata gwada kishin yarinyar ta gani kowane irin so take yi wa Shatima. Ba ta ki ace ita kadai ba ce da Shatima, kuma sannu a hankali da siyasa burinta duk sauran su zama a karkashinta, sai yanda tayi, sai kuma yanda ta ce. Salma ta gama komai, sannan ta janyo kofarta, ta dauki kwanon Aliya ta tafi kai mata. Ta same ta tana zaune tana kallon TV, don rana daya yasa aka saita musu TV nan su, aka kuma saka musu Tauraron Dan Adam. Salma ta shiga da sallama, Aliya ta amsa tare da cewa “Salma kanwar Anty.” Salma tayi murmushi, sannan ta tsugunna. “Sannu Anty.” Aliya ta ce, “Yauwa. Tashi ki zauna muyi kallo.” Ta kalli TV kasar Indiya take kallo. Sannan ta hau kujerar ta zauna. Salma ta dinga kallon falon, ta dubi Aliya wadda tana hankalce da duk motsin Salma da inda take kallo. Salma ta kalle ta. “Anty ashe kema haka dakinki yayi kyau?” Aliya ta ce, “A hakan? Ai ban kai su Amna ba nima.” Salma ta ce, “To ai kema babu laifi.” Aliyar ta mike “Zo ki ga dakunan kwanan.” Daki biyu da gado, daya kuma da kafet da katifa. Salma ta ce,”Wai duk dakunan da aka sa gado sauran wa ke kwana?” Aliya ta ce, “Babu kowa, amma in kayi baki ka huta sai su kwana, ko kuma yau in kun kwana a nan, gobe ku kwana a can.” Salma tayi dariya, “Ni in bakin nayi sai in shimfida musu Tabarma.” Aliya ta ce, “Kokari dai zaki yi kamar yanda na fada miki, ki dage ki sai duk abin da ba ki da shi, kiyi gado me kyau, sai ki cire wancan ki kai shi daya daga cikin dakin.” Salma ta ce, “Anty ni da ba sana’a ba, yanzun haka bani da Naira daya.” Aliya ta ce, “A wanda yake bamu mana. Salma ta dubi Aliya cikin. mamaki, “Wane kudi kuma?” Aliya ta ce, “Dubu dai-dai na kashewa da ya ke ba mu, shekaran jiya da jiya ya bamu.” Salma ta girgiza kai, “To kila ya manta ne, ko kuma zai tara min.” Aliya ta ce, “Wai kina nufin ke bai ba ki ba?” Salma ta ce, “A’a.” Aliya ta ce, “To amma kada fa ki tambaye shi.” Salma ta rike baki tare da fadin “Ni! Ba zan yi mishi magana ba, kila ku ya ga kuna da bukata ni ko me zan da kudi? Kuma nasan Yaya ba zai cutar da ni ba, da yaga ina da bukatarsu zai bani.” Aliya bata so haka ba, ta so a ce Salma ta nuna rashin jin dadinta a fili. Suka dawo falo, Salma ta ce, “Bari in je in kwanta bacci ni ke ji.” Aliya ta ce, “Ai gara kije ki kwanta tunda jiya bai bar ki kin yi bacci ba. Ta dan rufe fuska, “Kai Anty!” Sannan ta fice cikin kunya. Nan ta bar Aliya tsaye cikin takaici. Ta lura in ma ta tsaya bin ta Salmar nan haushi zata sha, gara ma ta koma yaki da manyan arnan. Amma zata bari ta kama Maigidan a hannunta. Haka Shatima ya ci gaba da zagaye dakin matansa, tare da kokarin ganin ya yi adalci a tsakaninsu. An turo ma Amna ‘yar aiki, ‘yar babba ce haka bazawara, kakarta ita ce ke aiki a gidan su. Amna taji dadin ta domin tana yi mata aikin gida tare da girki. Har Shatima ya share bai Tambayi albashin ‘yar aikin ba, sai kuma yaga rashin dacewar hakan. Ya tambayi Amna “To a kan nawa suka yi za ake bata, sannan zata ke dan taimaka ma sauran mata?” Amna ta ce, “A’a wannan ba wanda zata taimakawa, domin iyayena ne za su biyata. Za ka iya samo musu wasu babu matsala.” Hajiyarshi ta kira shi wata safiya, lokacin kwananshi goma da auren. Ta ce “To ‘Yallabai, yanzun an yi aure za ayi mana kaura, ko waya rabonka da kiranmu yau kwana uku. Na zaci ni daya ce, ashe har Babanku. To, in mun maka laifi ne tuba muke.” Cikin sauri ya ce. “A yafe min Hajiya, aiki ne kuma ga gidan har yanzu ban gama saita shi ba, amma zan shigo. Nayi kuskure, zan kira Alhaji yanzun nan.” Ta ce, “To ya batun zuwa gaisuwar Surukai? Sati daya ake zuwa bayan biki, kai kuma naji shiru, ko kun je?” Ya ce, “Tab! Wallahi Hajiya na manta, Munnir ma ya kira ni ya tuna min amma abin ya shige min. sai dai in Allah Yaso wannan satin da zai zo sai muje.” Ta ce, “To shi kenan. Su kuma sai ka debo su su zo ku gaida iyayenka da Kakarka ko?” Ya ce, “Wayyo Allah! Hajiya wannan shi ma dole ne? in bai zama al’ada mai karfi ba amin hakuri.” Ta ce, “Ba yanzun da sauri ba, a hankali ma sai ka zo da su.” Ya ce, “To shi kenan. Shatima ya kalli agógonshi, sha dayan dare sam bai so ya kai wannan lokacin ba, alhali yana dakin Nafisa, domin shi ya san korafi ta da mita, har bai so ya mata wani kuskure, don baya son tun yanzun ya fara nuna fushinsa. Kuma fita ce ta kama shi ta dole za su ga Gwamna. Daga can suka wuce bikin wani abokin aikinsu. Shatima ya mike tare da dafa na kusa da shi. “Abubakar ba zan iya jira a gama wannan Dinner din ba. domin iyalaina suna zuba ido.” Shima ya mike, “To ai dole nima in tashi tun da . [8/18, 17:36] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2 🏚️* CHAPTER 10 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya Shatima ya kalli agógonshi, sha dayan dare sam bai so ya kai wannan lokacin ba, alhali yana dakin Nafisa, domin shi ya san korafi ta da mita, har bai so ya mata wani kuskure, don baya son tun yanzun ya fara nuna fushinsa. Kuma fita ce ta kama shi ta dole za su ga Gwamna. Daga can suka wuce bikin wani abokin aikinsu. Shatima ya mike tare da dafa na kusa da shi. “Abubakar ba zan iya jira a gama wannan Dinner din ba. domin iyalaina suna zuba ido.” Shima ya mike, “To ai dole nima in tashi tun da kai za ka sauke ni a kawo, ka manta motana tana can gurin aiki?” Shatima yayi fakin ya fito, duk da yayi ma Nafisa sako ta waya cewa sun fito, amma haryanzun gaban shi yana faduwa. Ya kwankwasa kofar, kusan sau hudu, sannan ya kira layin ta sau uku, amma bata daga ba, ya saka makullin mota yana kwankwasawa. Ranshi ya soma ɓaci, domin yasan taji. Har ya fusata zai tafi mota ya shiga ya kwanta, don ba zai je dakin wata ba ya zama sabuwar matsala. Sai ya ji karar bude kofa. Ya waiwayo, ta bude ta leko fuskarta murtuk! Ya ce, “Saboda wulakanci kina jina ina buga kofa amma ki ka kasa zuwa ki bude min, na kira ki nanma ba ki daga ba?” Juyawa tayi, shi kuma ya bi ta ranshi ɓace. Ya shiga dakinshi, ita kuma ta wuce nata. Ya gama al’amuran rayuwarshi da ya saba kafin ya kwanta. Sannan yayi kwanciyarshi. Nafisa tayi tsammanin ya shigo ya roke ta, ko ya lallasheta. Sannan ya yi alkawarin ba zai sake yi mata irin haka ba, amma sai taji shiru. Ta tashi tayi ta kai-kawo.” Yayi rigingine idanunshi lumshe, yana nazari a kan halayan matansa din nan guda hudu. Bai ji shigowarta ba sai dai dan kukanta yaji, ranshi ya kara baci. Ya bude ido, sannan ya tashi zaune. Itama ta zauna. Cikin kuka ta soma korafi, “Ni kullum in dai girkina ne sai ka nuna rashin kulawarka kaina, ni nasan kafi son su a kaina, nasan ni ke sonka amma kai ba ka sona. Kana nuna min bambanci karara.” Ya daga mata hannu, cikin daga murya ya ce, “Wai ke ba ki da fahimta ne? ke kullum cikin korafi, bana turo miki message ba? Ke in dai ina dakinki bani da kwanciyar hankali. Ban san me zan yi miki ki yarda ina sonki ba.” Ta tsugunna ta hau kuka me karfi. Ya tashi ya koma falo ya kwanta. Nan ya kwana, da safe ya shiga dakin shi ya samu bata ciki, yayi wanka ya shirya. Bai ji motsinta ba ya leka kicin babu alamun zata hada mishi abin kari, don haka ya sabi jakarsa ya kai mota. Ya nufi dakunan sauran kamar yanda yayi tsammani. Haka ya samu Amna tana bacci, a cikin kwana ukun da ba a dakinta yake ba, bai taba samun ta ido biyu ba. Ya shafi kumatunta tare da sumbatar leбunanta. Ta bude ido. Ya ce, “Honey baccinki yayi yawa.” Ta yunkura ta tashi zaune. Nima ban san wane irin bacci nike yi ba honey ya zauna bakin gadon. Ta ce, “Baccina ya karu, sai in kai karfe daya fa ban ji na gaji ba.” Ya rungumota zuwa jikinshi. “Ko an samo mana baby me hana bacci ne?” Tayi dariya “Haba dai, lokacin al’adana bai kai ba tukunna. Kuma naga Anty Amarya ta gidanmu tana rashin lafiya sosai, tayi ta amai.” Ya kai hannu ya shafa damammen cikin ta, “Bani da ajiya ke nan?” Ta ce, “Babu, ina jin dai soyayyar da ka ke kashe ni da ita ne in kana gurina, sai in baka nan ta sani kasala.” Ya mike tare da cire ta daga jikinshi. “Bari in tafi kada nayi latti, ki tashi ki dan karya sai ki koma bacci, abincin safe yana da muhimmanci a gurin dan Adam.” Ta ce, “To.” Suka yi sallama. Yana shiga gurin Aliya ya same ta, kwance kan kujera tana kallo. Ya ce, “Kin yi abin kari kuwa don nan zan karya?” Ya fada tare da zama kusa da kafarta. Yasa hannunshi ya dafa kwafrinta. Ta kalle shi sannan ta mike zaune ta gaida shi. Ya amsa tare da nanata zancen abin kari. Ta ce, “Na zaci wasa ne.” Ta mike da sauri ta dauko flaks na ruwan zafi tare da jera masa kayan tea a gabansa.. Cikin sauri taje kicin ta soyo masa kwai zuciyarta cike da son jin abin da yasa bai karya dakin Nafisa ba, har wani bangare na zuciyarta yana addu’ar Allah Yasa fada suka kwasa, zata dan bigi cikin shi taji. Yana ci yana sa mata albarka, kuma a ranshi yana fadin Aliy matar rufin asiri ce.’ Ta ce, “Nafisa bata jin dadi ne?” Ya kalle ta, “Eh tun jiya jikinta ba dadi.” Gabanta ya fadi, a ranta ta ce, “Kar dai ciki ne?” Tayi murmushi “Allah Sarki, zan je in dubata.” Ya ce, “A’a kada kije, kin san ba kowa ke son sannu ba a ciwo.” Aliya ta ce, “Haka ne.” Nafisa tana daga cikin wadanda ba su son sannu. Ta ce, “Allah dai ya bata lafiya.” Sai da yayi tam! Sannan ya shiga gurin Salma. Tana zaune kan kujera, yau dai da kewar gida ta tashi, tun da tazo bata kara jin labarin iyayenta ba, kuma babu wanda yazo dubata. Bai zauna ba yana daga tsaye ta tsugunna ta gaida shi. Ya ce, “Yau kuma ya naga fuska babu annuri?” Salma ta ce, “Dama ina son kazo in ce maka ni zan je Zariya yau.” Ya ce, “Me ake yi a can?” Ta ce, “Ni dai ina son in ga su Inna ne gashi har an yi arba’in din Babanmu, kuma ban je ba.” hawayen da suka taru a ramin idonta suka zubo kan kumatunta. Ya tako zuwa inda take, yasa hankici ya share mata kumatunta ta inda ruwan hawayen ya bata. Ya ce “Kin ga nayi latti.” Ya fada tare da kallon agogon hannunshi. “Ki kwantar da hankalinki, in na dawo zamu yi maganar. Ni mun yi waya da Auwal jiya, duk suna lafiya. Me za ki dafa min yau?” Ta ce, “Duk abin da ka ce, bayan ko na dafa baka ci, sai ka ce ka koshi?” A ranshi ya ce, ashe tana sane. Ya ce, “Yau ba zan ci komai ba, zan ci naki ne amma ki min tuwo me kyau kar fa ya kone, bana son abu me kauri.” Ta ce, “Miyar me za ayi?” Ya ce, “Kubewa danya.” Yasa hannu a aljihu, ya ciro dubu daya, “Gashi ki sai abin da ba ki da shi. Ke baki da fridge shi yasa ni ke baki kudin nama, su kin ga suna dashi, ki ba Baba Maigadi ya siyo miki.” Ta ce, “To.” Suka yi sallama ya tafi. Nafisa ta tabbatar ita ce baya, don yana fita ta biyo bayanshi, taga shigarshi dakin Amna. Yau minti sha daya ma ya kwashe dakin ‘yar gwal dinshi kuma har minti sha uku. Itama Salma yau ta samu minti tara, gashi har latti yayi saboda ya duba lafiyar wadanda yake so a rayuwarsa. Kila ma ya fada musu cewa sun samu matsala ne tunda ko’ina ya kara lokaci fiye da da. Nan take taji zuciyarta tayi mata amanna da zargin ta. Don haka tasa sabon kuka ta shige uwar-daka. Aliya ta gama karinta, dama tuni ta kammala gyaran dakinta. Tayi wanka, riga da siket ta saka na atamfa bata daura dankwali ba, ta yafa gyale ta nufi sashen Nafisa, don tana son sanin ciwon da Nafisa din ke yi, fatanta dai ya zama ba ciki ba ne. Ta murda kofar ta shiga da sallama. Babu kowa a falon, sai da ta kare ma ko’ina kallo, a ranta ta ce, ‘Ashe itama an zuba Naira itama dai kujeru saiti biyu ne, sai dai na Amna sun fi tsada. Ta kalli gurin Dining, ashe itama dai tana da su, ta taba baki, sannan tayi sallama. Can Kasa Nafisa ta jiyo sallamar, ta tashi ta fito. Ganin Aliya sai ta hade ranta tam! Aliyar ta ce, “Ina kwana, ya jiki?” Nafisa ta ce, “Wa ya ce bani da lafiya?” Aliya ta ce, “Mijinki da ya zo ya karya a gurina, ya ce baki jin dadi shi ne nazo in ga ko zan iya taimaka miki da taimakon farko. Ran Nafisa yafi na da baci, ta ce “Fitar min a daki, kun ji dai da gulmarku ke da shi, kya fadi gaskiyar abin da ku ka tattauna, za ki zo kina wani wai kin zo duba ni, ja gulmarki ki fita.” Aliya ta fito jiki babu kwari, sai dai da taje daki ta nutsu tana nazarin maganganun Nafisar, ana ta tunanin Nafisar tana da cikin tabbas, kila bata son ya fada ne take zargin ko ya fada. Kila shima ta fada masa bata son a ji ne shi yasa ya ce kar taje ta gaida ta. Ran Aliya yayi matukar baci, in zarginta ya tabbata lallai shirinta zai rushe. Ta dauki wayarta ta shiga kiran Aisha. Ta daga tare da fadin, “Uwargidan Shatima, mai mulkin zuciyar Shatima da iyalanshi.” Aliya cikin sanyin jiki ta ce, “Hmm! Kawata ai wannan mukamin yana nema ya kufce min.” Aisha ta ce, “Da aka yi me?” Ta ce, “Nafisa, wannan ‘yar uwar tashi ciki gare ta. Aisha ta ce, “Ke fa?” Aliya ta ce, “Shiru, kuma duk ranar da yake dakina sai mun yi mu’amala da shi.” Aisha ta ce, “Abin Allah ke nan, to yanzun ke ya za kiyi?” Ta ce, “Shi ne na kira ki in ji ko da wata shawara.” Ta ce, “Kin sha kwayoyin nan masu daurayo mahaifa? Suna taimakawa kin sani.” Aliya ta ce, “Duk wata kwaya da na san zata taimaka min na siya nasha. Maigadi na rubuta na ba ya siyo min, don shima da ya gani sai dai na ce masa su ne ni ke sha.in cikina yana ciwo don nayi masa karyar ciwon ciki.” Aisha ta ce, “To ki jira kila nan gaba kadan ke ma ki samu. Ki dai yi kokari ne ki ga cewa kimarki bata girgiza ba a gurinshi.” Aliya cikin damuwa ta ce, “Ai na so ‘ya’yana su zama sune manya, dadin rike gida ke nan.” Aisha ta ce “Ba ki san in mace ta koma gurin miji yafi komai dadi ba, ko ‘ya’yanki ne kanana sai ki ga suna juya manyan don kaunarki ce zata shafe su, kuma dole a zauna haka. Dubi gidan Hajiya Rayya mana Maman kawarmu Sa’ida, ita ce ta biyu, amma dubi yanda take baza iko, ‘ya’yanta suna wadaka.” Aliya ta saki ranta har tayi ‘yar shewa, “Kuma fa haka ne. Su Sa’ida muna gama Secondary a ka kai su Umra, amma Tahir babban wansu an kasa biya masa kudin Makaranta. Aisha ta ce, “To ai yanzun shagon saida waya da gyaran waya ya bude. Su ko su Sa’ida suna Ghana, şun jima suna hira kafin daga baya suka yi sallama da cewa tayi ta addu’a. Nafisa tana kwance, tana jiyo sallar Azahar ana kira. Har zuwa yanzun bata karya ba, bakin ciki ta rasa inda zata saka kanta ace wai da miji ma ba ka da sirri, komai sai yaje ya fada ma kishiyoyi. Sallama ta sake ji da bugun kofa, tsaki taja tareda fadin “Wace munafukar ce kuma oho!” Tayi banza da bugun. Sai da ta jiyo an shigo falon ana sallama. Ta dauki muryar Anty Maimuna kanwar Mamansu da ke aure a cikin Jaji (Barikin Sojoji), mijinta soja ne. Cikin sauri ta fito da murna tana fadin, “Haba! Ni naji kamar muryar Anty, Anty sai yau?” Ta sauke ‘yar da ke hannunta, Nafisa ta dauke ta ta nufi cikin uwar daki tana fadin Anty shigo ciki kawai. Kan gado ta sauke yarinyar tana kallonta tare da tambayar “Ina su Hisham?” Antyn ta ce, “Yana Makaranta, ko ba Makaranta ba zan zo da ita ba. Nasrin din ma don dai taki zama ne. Nafisa ta ce “Gara ma da ki ka zo da ita na ganta.” Ta mike ta kawo mata ruwa da lemon roba. Ta ce, “Bari in dora abinci Anty, ina nan kwance ko karyawa ban yi ba.” Anty Maimuna ta ce, “A kan me za ki zauna da yunwa ga fuskarki ma duk a kumbure sai ka ce kin ci kuka?” Nafisa tayi rau-rau tare da fadin “Hmm! Bari Anty Maimuna, wallahi ina cikin wani hali a gidannan. Sai da nayi ta yiwa Mama mita a kan wannan auren ta ce ba haka ba, gashi yanzun tun ba a je ko’ina ba bakin ciki zai kashe ni.” Anty Maimuna ta zaro ido, “Fada min abin da ke faruwa don Allah, ke da mijin ko ke da kishiyoyi?” Nafisa ta soma kuka, “In su ne akwai wadda zan daga ma kafa ne? shi ne da kansa. kullum in dai yana dakina to fa sai sanda yaga dama zai dawo, in yi kwalliya in ta jiransa a banza. Karfe shida fa yake dawowa, amma ni jiya sai sha dayan dare. Nayi magana ya shiga fada min maganganu, har da yin yaji yana kwana a falo. Kuma gashi babu sirri, da safe yaje ya barbada ma matansa komai.” Ran Anty Maimuna ya baci, ta ce “To mene ne na zuwa ya fada musu don yaja miki raini?” [8/18, 17:44] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️* CHAPTER 11 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya yunwa ga fuskarki ma duk a kumbure sai ka ce kin ci kuka?” Nafisa tayi rau-rau tare da fadin “Hmm! Bari Anty Maimuna, wallahi ina cikin wani hali a gidannan. Sai da nayi ta yiwa Mama mita a kan wannan auren ta ce ba haka ba, gashi yanzun tun ba a je ko’ina ba bakin ciki zai kashe ni.” Anty Maimuna ta zaro ido, “Fada min abin da ke faruwa don Allah, ke da mijin ko ke da kishiyoyi?” Nafisa ta soma kuka, “In su ne akwai wadda zan daga ma kafa ne? shi ne da kansa. kullum in dai yana dakina to fa sai sanda yaga dama zai dawo, in yi kwalliya in ta jiransa a banza. Karfe shida fa yake dawowa, amma ni jiya sai sha dayan dare. Nayi magana ya shiga fada min maganganu, har da yin yaji yana kwana a falo. Kuma gashi babu sirri, da safe yaje ya barbada ma matansa komai.” Ran Anty Maimuna ya baci, ta ce “To mene ne na zuwa ya fada musu don yaja miki raini?” Nafisa ta ce, “Hmm! Ni yanzun ban san ma me zan yi ba wallahi.” Anty Maimuna ta ce, “Muje kicin din.” Suna girkin tare tana ci gaba da karanto korafinta. Anty Maimuna ta ce, “Gashi can nazo miki da wasu sirrika na mata, wata ke kawo wa barikinmu daga Maradi (Nijar). Kayanta masu kyau ne sosai, don akwai wata kusa da mu, mijinta kwallon dan neman mata ne na gaske, gata da yara biyu, amma baya ba su abin kirki, ba fa karamin Soja ba ne. Ai ko da na hada ta da matar nan, kin san Allah yanzu baya wannan yawon, kuma duk hakkinsu da ke wuyanshi yanzun yana saukewa, har da mota ya sai mata yanzu.” Nafisa cikin fara’a ta ce, “Ai ko zan ansa.” Anty ta ce “Amma fa suna da tsada, Allah Yasa dai kina da kudi.” Nafisa ta tabe baki, “Ina zan ga kudi? Kin san Allah sisi bai bani ba, ban san suba” Ta ce, “Zan biya miki wannan, gaba na san za ki zo da kudinki.” Nafisa ta ce, “Nawa ne kudin?” Tayi dariya tare da fadin “Kyaji in lokaci ya yi.’ Nafisa taji duk kuncin da ke ranta ya kau, sannan taji tana jin yunwa, dama dai burinta ta zama ‘yar gaba-gaba a gurinsa. Daidai wannan lokacin Salma ta fito gurin Maigadi zata bashi sako. Tana jin kunyar aiken dattijon wanda tasan zai haifi mijinta ma bare ita. Ta risina. “Baba dama sako ne zan baka.” Ya ce, “Alhajin ya fada min. Ta mika mishi dubu daya, “Kubewa danya ni ke so da kuma nama.” Ya ce, “Kubewa ta nawa?” Salma ta dan yi shiru, bata san ta nawa zata isheta ba, don haka sai ta ce bari in tambayo Anty.” Ta samu Aliya tana kallo, ta ce “Anty kubewar nawa zata ishe mu ni da Yaya?’ Aliya ta ce, “Ta dari daya ma kacal ta isa, yau kuma tuwo za ki yi?” Ta ce, “Ya ce yana son cin tuwo ne in yi mishi.” Aliya ta ce, “Lallai kuwa, sai ki dage kiyi shi me kyau yanda zai ci.’ Salma cike da wauta ta ce, “Hala ya fada miki bai taba cin abincina ba?” Aliya ta ce, “Ya fada min wai ba ki iya girki ba.” Ta fada cike da son tura ma Salma haushi. Salma ta saki dariyar wauta. “Ai yau zan bashi mamaki, zan yi tuwon da zai yi santi. Aliya ta taba baki, a ranta ta ce, “Wannan sokuwa ce, to sai ya ci tuwon in gani.” Ta ce, “In ko haka kike so sai ki sa kifi, kubewa danya tafi dadi da kifi.” Salma ta ce, “Haba?” Aliya ta ce, “Allah kuwa.” Salma ta ce, “Dama na gaji da cin nama. Kullum sai na sa kilo daya a dan abincina, kuma baya ci.” Aliya ta ce, “Ai gashi nan kin soma kyau.” Salma ta ce, “To bari in je in sa ya siyo min da kifin.” Aliya ta saki dariya bayan tafiyar Salma ta ce, “Shashasha. In ni ce ke bani da da, bakina ni kadai kullum a bani dubu daya ta kilon nama ai tarawa zan. Bai zama dole in ci ma nama kullum ba. Amma ba zan fada mata ba tayi ta dirkar namanta. Ta ba Maigadi kudi, ya siyo mata kifi da kuɓewa. Da ya dawo sai ya kawo mata kifi busasshe da kubewa, ya kuma bata canjin dari uku. Ya ce, ta ce kayi na mota Baba. Ya ce, “Eh har ma na sai goro na ashirin in nayi canji zan ba ki.” Ta sake daukar Naira dari ta ce, “gashi Baba ka kara, wancan ma ka bar shi.” Ya ce “To na gode.” Ya amsa. Har zata wuce ya ce, “Hajiya za ki ga na siyo miki kifi busasshe, Maigidan naku ba ya son danye. Domin waccan satin , Hajiya din nan ta karshe.” “Bani in sai mata.” Sai Alhaji ya ce, “Kada tayi abinci da danyen kifi don ba ya so. Salma ta ce, “To’na gode Baba.” Ta wuce ciki ta koma aikinta. Ta nutsu sosai ta zauna a gaban girkinta, ta gama ta kwashe a bakar leda guda biyu ta sa a kula. Sai ta saka sauran ta kai wa Maigadi, don kullum ita ce kadai ke kai mishi abinci, sannan ta dumama abincin ta na jiya ta taci. Da yamma tayi wankan ta tasa leshinta na akwati, don sabbin kayan ta ke ta mirtsika tunda ba a sako mata kayanta na gida ba, dama sun tsufa. Sai da yayi Ishsha ya shigo gidan don yaje yayi aski. Yana shigowa ya wuce wanka. Da jallabiya ya zo ya zauna zaman cin tuwo, tana budewa ta juye a plate. Ya ce, “Iye! Lallai yau zan ci tuwo.” Ta ce, “Naga kullum nama shi ne nasa maka kifi.” Cikin sauri ya ce, “Kifi?” Ta ce, “Bushasshe ne fa.” Ya ce, “Amma miyar bata yi karni ba dai ko?” Ta ce, “Har citta nasa don kada tayi karni.” Ta bude jikinta a sanyaye. “Ci kaji kuma.” Ya shaki kamshin, bai ji karni ba, don haka ya ce “To ba ni cokali.” Shi kanshi ya ji mamakin tuwon da ya ci. Tare suka ci da Salma har da suka rage ya ce tayi masa dumame da safe Ta ce, “Dama kana cin dumame?” Ya ce, “Ni da dumame nasan dadin tuwo ma, gidan Kaka in na kwana lokacin ina dan makaranta Kaka take yi min, sai ta ce dumamen gata, tasa min man shanu har da yaji.” Salma tayi ta dariya “Nima ina son manshanu. Ya ce, “To zai siyo muku.” Ta ce, “Ka ce zamu yi maganar zuwanmu Zariya.” Ya ce, “Bari in kira Auwal ya kai ma Inna ku gaisa, shi kenan?” Ta ce, “Allah Sarki, ka ce min zan je.” Ya ce”Ban ce haka ba fa, na ce ne in na dawo zamu yi maganar. Ta ce, “To yaushe za ni?” Cikin shagwaba take yin maganar. Ya ce “Sai kin yi kiba tukuna.” Ta ce, “Don Allah Yaya ina son ganin Yaya Hadiza ma.” Ya ce, “To ki bari sai kin kara kyau. Ta ce, “Ya za ka gane na kara kyau?” Ya ce, “Ai ina kallonki kullum.” Ta ce, “Me na kara?” Yace “Haske kadai ki ka kara, sai fatar ki da ta soma murjewa, Ta tashi ta dauko dari biyun ta ce, “Gashi canjin ka na tuwon.” Ya ce “Har da canji?” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “To ki aje min.” Ta ce, “To.” Ta tashi taje ta aje. Baccin Amna ya soma damun Shatima, domin yau da ya ke dakinta ma baccin take kwasa babu alamun zasu yi wata hira, shi kuma yana da bukatarta. Yayi ta tashinta da kyar ta tashi zaune tana zuga hamma. Ya ce, “Amna!” Ta dube shi idanu lumshe, ta ce “Umm, don Allah Honey bacci nake ji.” Ya ce, “Amna, ki tashi don Allah.” Ta kara cewa “Please, ka bar ni mana.” Ya ce, “Allah sai kin tashi.” Ya girgizata. Ta tashi, “Honey kaina ciwo yake yi, in ban yi bacci ba.” Ya ce, “To kin ci abinci?” Ta ce, “Bana jin yunwa, sai bacci.” Ya ce, “Kai ki tashi muje asibiti.” Ta ce, “Ni lafiyata lau, bacci ne kawai matsalata.” Ya bar ta yazo ya gama duk abin da zai yi kafin ya kwanta. Sannan yaje ya jata jikinshi ya kwantar suka ci gaba da bacci. Da kyar yasa ta tayi sallar Asubahi, don haka ya soma tunanin lallai babu lafiya. Ya kira Aliya a waya da safen yana tambayarta me yake saka mace yawan bacci? Aliya ta ce, “Dalilai da dama, ciki har da shigar ciki.” Ta ce “Wacece?” Ya ce, “Amna ce, yanzun ya za ayi a gane?” Ta ce, “Gwajin fitsari, tayi a wani abu ka kawo in gwada.” Da yake ranar Asabar ce ba shi da aiki, bai ko fito gaida saura ba, yana dakin ya sata gaba yana kallo “An ce tana da ciki.” Sha daya ta farka da yunwa, ya ce tayi wanka taji karfin jikinta. Ya ce”Me za ta ci?” Kafin ta fito yasa me aikin ta tanadar mata. tana ci zuba mata ido yayi. Ta ce, “In za ka ci muci mana.” Ya ce, “A’a ki ba babyna ya koshi.” Ta saki dariyar da ta sa ta ta kusan kwarewa. Ta cc, “In ji wa?” Ya ce, “In ji masu ilimin abin. Yanzun ma fitsari za ki bani in kai a gwada. Ta ce, “Wa zai gwada?” Ya ce, “Aliya kin san Nurse ce. Ta ce, “Wace ce Aliya kuma?” Ya ce, “Ta dakin farko.” Ta tabe baki “Oh, dama a nan gidan take? Ya ce, “Eh.” Ta ce, “Cikin matanka?” Ya ce, “Eh.” Ta girgiza kai “Ba wadda zan ba fitsarina, don ni ba tsararsu ba ce. Kuma bana dauke da wani ciki domin lokacin al’adata bai yi ba bare in tabbatar. Abin da na sani bacci lafiya ce, ina rama baccin da ban yi ba ne a baya lokacin ina Makaranta, da kuma lokacin biki.” Yayi murmushi, “Shi kenan muje asibiti.” Ta ce, “Wane irin asibiti, ba zan je ba.” Ya ce “Shi ke nan. Aliya tayi ta damuwa tana son jin me ake ciki da batun cikin Amna, ga na Nafisa. Koda ta kira Shatima cewa taji shiru bai kawo fitsari ba. Ya ce, “Ashe babu komai ta bar shi kawai.” Suna cikin hira ta gama cin abinci, sai taji zuciyarta na tashi. Ta ce, “Honey zuciya tana tashi, naci abinci da yawa.” Ya ce, “To kin taba jin haka?” Ta ce, “A’a sai a ‘yan kwanakin nan. Abin kamar wasa Amna ta shiga bandakinta tana sheka amai. Nan fa Shatima ya ce sai sun je asibiti. Ita kuma ta dage ai taji daidai da ta yi amai din. Yayi ta lallashinta amma ta ki. Ya kira Hajiayrshi ya kai mata kara. Nan take ta kira layin Amna, cikin sigar lallashi ta ce, “Amna ta yarda taje a dubata.” Ta ce, “To Hajiya.” Ta dube shi, “Ka ci albarkacin Hajiya.” Sai da suka yi sallar Azahar sannan suka shirya zuwa asibiti, doguwar riga ta saka da dan mayafinta, shi kuma yasha kananan kaya. Sun yi kyau abin su sosai A kan idon Nafisa da Aliya suka wuce. Kowaccansu da abin da ta kisima a zuciyarta. Cikin gari suka shiga, in da ya kaita wani asibitin kudi gwajin nan take kala biyu suka yi mata. Cikin sati uku da kwanaki ya bayyana. A gaban Likitan Shatima ya rungume Amna. A nan ya kira Hajiyarshi ya fesa mata. suna hanyar dawowa a mota Hajiyar ta kira shi. Ta nuna matukar murnarta da samun cikin, kuma ta ba ta shawarwari matsayinta na uwa. Amnar tayi godiya, suka yi sallama. Har suka kai gida Shatima na yiwa Amna sannu da zaran sun hada ido. Da ya tsaya da mota kuma bayan sun kawo gida, cikin shagwaɓa ta ce sai dai ya dauke ta. Ya ce, “In kullum ki ke son in dauke ki wannan abu ne mai sauki.” Kafin ta ce da wasa take yi har ta ji ta caraf a hannunshi ya yi sama da ita, yasa kafa ya rufe motar. Bai dire ta ko’ina ba sai a kan gadonta. Ya kira Aliya a waya ya fesa mata. Tayi murna sosai a wayar amma a can kasan zuciyarta takaici ne da damuwa. Ranar yana dakin har bayan Isha’i, sai da suka yi sallah yaga ta dan ci wani abu sannan ya lallabata tayi bacci, sannan ya fita bayan ya fada ma mai aikinta cewa ta kula da ita saboda dare. Dakin Nafisa ya nufa dama can yake, in san ranshi ne yaje ya duba Salma don bata da wayar da zai ji laifiyarta, amma baya son mitar Nafisa. Lokacin da ya shiga gurinta ba ta falo, dakin shi ya shige don ya yi wanka, bai neme ta ba ne don yasan yanda suka rabu. Haka ko ya shigo dubata a ranakun da ba ya dakinta gaisuwa ke hada su. To bai san irin tarbar da zata yi masa ba yau. Ya fito daure da Tawul ya ganta cikin kwalliya ta aje masa goran ruwa da kofi a gefen gado kamar yanda aka saba. Ya kalle ta cikin murmushi, a ransa ya ce, “Yau da akwai abin arziki.” Ta miko masa kayan baccinsa yasa, ya dube ta. “Turarenki yayi min kamshi sosai.” Ta fadada fara’arta. “Haba?” Ya ce, “Sosai ma, za ki sammin?” Ta ce, “A’a, za dai ka dinga shakar sa a jikina.” Yayi ‘yar dariya. “Hakan ma na gode.” Ta ce, “Muje ka ci abinci ko? Kus-kus ne nayi maka da fa-dukan shi, yayi dadi.” Ya ce, “Lallai kuwa kin ce yau in ci har in kasa tashi.” Suka yi dariya gaba daya. [8/18, 17:54] Ummi Tandama😇: _____ *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️* CHAPTER 12 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Mun tsaya Haka ko ya shigo dubata a ranakun da ba ya dakinta gaisuwa ke hada su. To bai san irin tarbar da zata yi masa ba yau. Ya fito daure da Tawul ya ganta cikin kwalliya ta aje masa goran ruwa da kofi a gefen gado kamar yanda aka saba. Ya kalle ta cikin murmushi, a ransa ya ce, “Yau da akwai abin arziki.” Ta miko masa kayan baccinsa yasa, ya dube ta. “Turarenki yayi min kamshi sosai.” Ta fadada fara’arta. “Haba?” Ya ce, “Sosai ma, za ki sammin?” Ta ce, “A’a, za dai ka dinga shakar sa a jikina.” Yayi ‘yar dariya. “Hakan ma na gode.” Ta ce, “Muje ka ci abinci ko? Kus-kus ne nayi maka da fa-dukan shi, yayi dadi.” Ya ce, “Lallai kuwa kin ce yau in ci har in kasa tashi.” Suka yi dariya gaba daya. Bayan ya gama da abincin kuma ya jinjina mata. Nafisa ta sha mamaki a kwanciyarsu, yanda ya tara da ita sau biyu a daran. Sannan da safe da yake Lahadi ce yana makale da ita sai gurin tara sannan ya tashi ya yi wanka. Tayi ta tabara wai ya gaji da ita ba za ta iya tashi ta shiga kicin ba. Ya ce “Zauna in shigar miki.” Shi ne ya hada musu abin kari, tayi wanka, tayi kwalliya suka karya. Ya ce, “To bari ya je ya duba lafiyar sauran Jama’ar gidan. Nan ne ta ɓata rai, wai haka jiya ai ita bai zo ya duba ta ba, kuma ta fito taga ya dauki Amna. Nan take ya dauke ta da yake Nafisa irin matan nan ne marasa kiba, sai dai tana da dan tsawo. Amma sanfurin jikinta, sanfuri ne irin wanda zai yi wuya tayi kiba ko me zata ci. Ya ce, “To dauka dai gashi na dauke ki ina zan kai ki? Ranta yayi dadi ta ce, “Ka kai ni dakina.” Ya dire ta kan gado, a kunne ya rada mata wata magana da ta sata fashewa da dariya, tare da saka kanta cikin filo. Yayi mata cakulkuli ya fita ya barta tana dariya. Sha biyu ya gani lokacın da ya kalli agogon falon Amina. Lallai yau hira tayi dadi tsakanin shi da Nafisa. Ya samu Amna zaune tsakiyar gado tana waya da ‘yan gidansu. A yanayin maganarta ya gane cewa ‘yan gidansu sun sani, ta fada musu kenan. Ya zauna suyi da wannan, wannan ya kira. Bayan ta gama ta dubi Shatima, “Su Mom suna gaida ka.” Ya ce, “Ina amsawa. Ya jikinki?” Ta ce, “Naji sauki.” Ya ce, “To kin yi karin kumallo?” Ta ce, “Eh, su fa suka tashe ni da kiran waya. Yanzu kam dole in tashi in yi wanka in karya don Direba yana hanya zai zo mu tafi.” Cikin mamaki ya ce, “Ina?” Ta ce, “Gida mana! Dad zai sa a duba ni na musamman. Shatima ya ce, “Ba ki fada musu cewa an duba ki a nan ba?” Ta ce, “Na fada musu, ka san Dad baya son wasa da lafiya.” Ta fadi tare da sauka ta nufi bayi. Shatima yayi shiru kanshi a daure, lallai wata sabuwar matsala kuma zata kunno kai a gidan shi. Shi ne mijinta shi ya kamata a nemi izininsa kafin a fada mata, shi ne ya kamata ya fada mata cewa Dad ya ce za ki je Kano a sake duba lafiyarki, amma sai gashi ita ce take bashi labari, babu wani neman izini. Jiki babu karfi, ya shige zuwa gurin Aliya. Yanayin da ta ganshi taso taji ko menene, amma ta san ba zai fada ba. Haka Salma duk shirmenta sai da ta lura cewa yau din yana cikin damuwa. Domin taga be tsokane ta ba. Ya dai miko mata kudin nama. Ta ce, “Me zata dafa?” Ya ce, “Tayi abinda take so. Gaba daya sai ya ji gidan yayi masa kunci. Dakin Nafisa ya nufa ya dauki makullin mota ya fita. Shi kanshi bai san ina ya dosa ba don yana bukatar shawara. Titin da zai kai ka filin bajakoli nan yasha kwana ya tsaya, saboda akwai karancin zirga-zirga a titin. Ya kifa kanshi a kan sitiyarin motar. Kamar minti daya ya dago, ya dauki waya ya shiga kiran layin Munnir. Babu jimawa Munnir ya daga, tun daga gaisuwa Munnir ya fahimci akwai matsala. Ya ce, “Ya ya abokina, naji muryarka wata kala?” Ya ce, “Akwai matsala.” Ya karanto mishi komai. Munnir ya ce, “Tabdi! To ai tun da wuri zaka yi maganin wannan matsalar ba sai ka bari tayi girman da zaka kasa magance ta ba.” Shatima ya ce. “Ta ya ya? Ni bana son ne a ce daga aure dududu ko wata biyu ba mu cike ba amma na soma kuno da matsala.” Munnir ya ce, “Kai da ka ke da basira ma, kayi kokari sosai fa, da harka tara mata guda hudu zuwa yanzun babu wata matsala ko wani korafi. Mace daya ma in ka aje in ba a yi sa’a ba kafin kuyi wata daya makota sun soma jin ku.” Shatima ya ce, “Ai kaina ya kulle, basirar tawa duk ta toshe, ka riga ni aure dai, ka san kuma yanda kowane Maigida yake takama da ikon gidansa.” Munnir ya ce, “Haka ne.” Shatima ya ce, “To sai a ce an tauye maka wannan ikon.” Munnir ya ce, “Abin da yafi kawai ka cije ka hana, ka ce ba ka bada izini ba, nasan dai za a dan samu fushi da sauransu kayi lallashi daga baya. In ko ba haka kayi ba, tabbaci hakika matsalar ta samu gindin zama. Shatima ya ce, “Haka ne, bari in koma gidan kawai da na fito ne nayi fushi a kan in sun tafi suma wuce Kano don ni.” Munnir yayi dariya. “Ai ka tsaya a namijinka nawa.” Shatima ya ce, “Har ina son in kira Hajiya itama in ji ta bakinta.” Munnir ya ce, “Kar ka sake kayi wannan kuskuren, domin zaka yi da na sani a gaba. Bari in fada maka wata magana abokina, duk rintsi kar ka sake ka sako iyayenka a cikin abin da ya shafi matsalar gidanka. Na farko zaka jona raini tsakanin Mahaifiyarka da matarka, domin ka san suma iyayenmu sai a hankali, basa so a ce kaza laifinmu ne, don haka sai kaga sun dora mu kan shawarar da mu zamu fitamma zamu cutar da iyalanmu. kuma kayi rashin sa’a a goyi bayan matar kai kuma kiri-kiri ka dinga cutuwa. Don haka kar ka sake ka zama mai kai matsalar cikin gidanka ga Mabaifiyarka, shi ke haddasa irin rikicin nan na tsakanin sirika da sarakuwa, wanda har yanzun an kasa cimna nasarar kawo karshen wannan lamarin shekaru masu yawa. Kawei abokina ka zama wanda kullum iyalansa suke ganin girman darajar iyayensa. Su kuma iyayenka kullum kana fada musu labari mai kyau, mai faranta rai daga iyalansa. Kai ko wata ce cikinsu ta kai kararka gurin Mahaifiyarka, in kaje kar ka ce ita ce ta min kaza da kaza, ka ce ayi hakuri zaka gyara.” Shatima ya ce, “Amma dai na gode da wannan shawara, in Allah Ya yarda zan kiyaye. Shi yasa a ka ce me shawara aikin sa baya baci, sai dai asirinsa ne a tone.” Suka sa dariya, sannan suka yi bankwana kowa ya kashe waya. Ya aje mota ya nufi dakin Amna. Tana zaune a kan Dining tana cin kwai da Tea. Ya kalleta, “Sai yanzun ki ke karyawa?” Gira ta daga masa alamun “Eh.” Ya ce “Me yasa? Ki daina wasa da abinci ba fa ke daya ba ce yanzu.” Ta ce, “Na gama hada abin da ni ke bukata ne, kar ya zo ya yi tajirana, ban dauki kayan sawa ko daya ba, don ina da kaya a gida a dakina. Ko lefena ma yana can…” Ya katse ta da cewa, “Ina wai za ki je ne kina ta fadin kar ya zo ya yi ta jiranki.” Ta cc, “Sau nawa zan fada maka cewa Dad ya ce a zo a tafi da ni.” Ya ce, “Amma Dad din bai fada min ba. Ya za ayi ki tafi ba tare da neman izinina ba Cikin mamaki ta kalle shi ya wani hade rai. Ta ce, “Dad dina fa na ce, ko ba ka ji da kyau ba ne?” Ya ce, “Naji ki sosai, amma tafiyarki kiran Dad din naki ikona ne ba ikonsa ba, don haka bisa ikona babu in da za ki je, ki kira shi direban a waya ki ce masa ya juya.” Ta mike a fusace, “Shatima kana son ka ce min za ka hada kanka da Dad dina? Shi ne fa ya haife ni ya raine ni, ya sani Makarantu mafi tsada a in da muke, har waje ya kai ni a can ka ganni ka ce, kana sona. To don Allah ka dawo cikin hankalinka bana son mu samu matsala, don… ihun murna da Summy ta shigo da shi, shi neya katse Amna daga zafafan maganganun da ta tanada don fesar ma mijin nata. Ta rungume kanwar tata, tare da nuna murnar ganinta. Sumayya ta kai hannu ta shafi cikin Amna tare da fadin “Na riga Dad taba Baby.” Amna ta saki dariya tare da tambayar ko sun yi muhawara ne? Sumayya ta ce “Ai ba su san na biyo dircba ba, domin Dad yacd babu wanda zai fara shafa Baby.”saishi Amna cikin dariya ta kalli Shatima, wanda ya harde hannu yana kallonsu. Ta ce, “Honey dubi son kudi irin na Summy. Bai ce komai ba, Sumayya ta dan risina “Ina yini Ya Shatima, ban ganka ba fa.” Ya ce, “Ai ba za ki ganni ba, idonki ya rufe.” Suka yi ciki suka bar shi nan tsaye.malala Kafın yayi wani tunani har sun fito, me aikinta dauke da dan karamin akwatinta. Sumayya da me aikin suka yi gaba, bayan ta ce “Yaya har da kai zamu?” Ya ce “A ‘a ina da office Summy.” Ta ce, “Yau Sunday.” Ya ce, “Gobe ni ke nufi nima.” Amna ta kalle shi, “Honey sai mun yi waya.” Ya ce, “Za ki tafi ba da izinina ba? Za ki tafi cikin fushin Allah da tsinuwar Mala’iku?” Amna ta ce, “Ni ban gane zantukanka ba, in ka gama fushin zamu yi waya.” Ta fice abinta. Bai fito ba har sai da ya daina jin sautin motarsu. Ya fito ya kulle dakin ya nufi dakin Nafisa. Kan kujera yaje ya zauna ya zabga tagumi. Nafisa ta zo ta zauna kusa da shi, ta dafa shi. “Lafiya kuwa?” Shatima ya ce, “Kanshi ke ciwo.” Ta ce, “Gashi babu magani a gidan ko za’a aiki direba ne ya siyo?” Ya girgiza kai tare da lumshe ido. “Gajiya ce da kai-kawo, in ya dan huta zai daina.” Ta rage TV sannan ta ce, “In baka guri ko?” Ya ce, “Ta zauna.” Ya janyo ta jikinshi suka yi shiru. Yana ta son ya danne bacin ranshi, yana karanta ma ranshi cewa ga wasu matan nan yana da su, me zai sa ya damu kansa da bakin ciki don ta tafi? Amma duk da haka ya kasa. Ya mike zumbur! Nafisa ta bi shi da kallo. Ya nufi dakin shi, ya canza kayan jikinshi zuwa shadda. Yasa hula da takalmi, yana saka turare Nafisa ta shigo. Ya ce, “Zariya zan je.” Ta ce, Lafiya kuwa?” Ya ce, “Lafiya lau.” Ta ce “To sai ka dawo.” Ya leka dakin Aliya, ya ca “Beri ya shiga Zariya ya dawo.” Ta ce. “Allah ya tsare hanya.” Ya isa gun Salma. Tana jin ya ambaci Zariya ta daka tsalle ta ce, “Yaya in zo muje?” Sai ya ji wani mugun bacin rai ya taso masa tamkar ita ce Amna. Ya shigo rai bace “Ina za ki zo muje? Don na ce za ni Zariya za ki ce ki zo muje, ni sa’anki ne? kin san me zan je yi ne? in ki ka kara yi min irin wannan sai na miki dukan tsiya!” Salma ta tsorata iya tsorata, jikinta sai kar karwa yake, tana mamakin dama haka Shatima ya iya fada? Tsaki yaja sannan ya fita. Tayi ta kuka, Tsonsa ya darsu a zuciyarta. Kai tsaye gidan su Munnir ya nufa, don ya kira shi cewa ga shi nan zai shigo Zariya ina zai same shi? Ya ce, Gida. A kofar gida suka tsaya don ya ce ba zai shiga ciki ba. Ya ba Munnir labarin yanda aka yi da yaje gidan. Munnir ya ce, “To fa! Ai shi kenan tunda an riga an yi.” Shatima ya ce, “Kar ka ji yanda raina ke baci, ni kaina ai zam fi so a ce suna kusa da ni ina ririta cikina. Amma nayi alwashi a zuciyata ba zan je ba har ta dawo.” Munnir ya ce, “In kayi haka ba laifi ba ne, amma kar kayi. Ka kira waya kuma kaje. Ta yiwu su basu da ilimin sanin mahimmancin aure, ko bambancin da ke tsakanin miji da kuma iyaye. A hankali za ka ke nusar da ita, har ta gane. Kai kuma ka kwantar da hankalinka, ka sani ma ko cikin sauran wata na da cikin?” Shatima ya ce, “Nayi ta kokarin in cire abin a raina, amma na kasa.” Haka dai Munnir yayi ta ba shi shawara kafin suka rabu. Yaje ya gaida su Hajiya, take tambayarsa “Lafiya da yamma?” Ya ce, “Lafiya lau, yaje gurin Munnir ne akwai abin da suka yi.” Ta ce, “Ina mai jiki fa, laulayi da sauki?” Ya ce, “Ta ma tafi gida dazun.” Hajiya ta ce, “Gida kuma?” Shatima ya ce, “Eh, ai za su dubata na musamman ne. Hajiya tayi dariya, “Kadan da aikin masu hali, shima dan zai ga gata.” Shatima dai ya ce, “Umm!” Ya mike yayi mata sallama. A hanya yayi Magriba. Koda yazo yayi fakin ya jima cikin mota yana takaici kafin ya fito. Har [8/19, 11:38] Ummi Tandama😇: *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️* CHAPTER 13 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* ya nafi dakim Nafisa sai ya tuna yau a gurin Salma yake. Ya juya ya nufi dakinta. Tana kan Darduma a can kuryar dakinta, tunda tayi sallah ta kasa tashi, ga faduwar gaba don lokaci-lokaci sai ta dafa Kirji. Matuka ta tsorata da fushin Shatima, har yana fadin zai mata duka! Tana jiyo sallamar Shi tsoro da fargaba suka hanata amsawa. Ya aje• hularshi a kan kujera ya nufi kicin. Ya dauko goran ruwa guda daya, ya zauna. Duk da babu sanyi da ya daga sai da ya sha fin rabi, sannan ya aje goran. Yayi ajiyar zuciya. Ya dauki wayarsa ya kira Nafisa, tana dagawa ya ce ta kawo masa jakarsa nan dakin Salma. Babu-gardama Nafisa ta dauko ta nufo dakin Salma. Da alamu wannan bacin ran na Shatima ya saka matan nashi, shiga taitayinsu, musamman Salma. Tayi sallama a Rofar dakin ya daga murya ya Ce Shigo mana, kin coge kamar wadda za a cinye ta." Ta shiga ta mika mishi tare da fadin "An lafiya?" Ba tare da ya kalleta ba ya ce, "Lafiya?" Ta wurga, ido tana kallon falon Salma, cikin mamaki duk da take ji a family ana cewa su Salma matsiyata Ne bata yi tsammanin tsiyar har ta kai haka ba. Ta taba baki tare da fadin "Uhum!" Ya dago daga kokarin da ya ke na ciro Laptop a Jaka ya ce, "Ya ya?" Ta girgiza Kai tare da sake kallon dakin ta ce, "Babu komai, ' Ya ce, "To kina iya tafiya. Ya fahimci dakin take ma wanna yatsinan. Salma da ke ciki tana jin su. Lokacin tana ta shawara a kan ta fito ko kar ta fito? Jin fitar Nafisa sai ta yi ta maza ta fito. Cikin tafiya tamkar Wahainiya ta nufi kicin. Ta dauko Tiren da ta jera kuloli guda biyu, daya farar shinkafa daya miya. Sai dan karamin kwanon silba da ta zuba naman yau farfesun shi tayi. Ta bude dan kwandon da ta yanka ganyen latas da kokumba, shima ta dora.Ta.zo ta dire tiren, kan ya zube ma saboda yanda jikinta ke Bari ta sauke daga tiren ta jere, ta koma ta dauko cokali da plate, da goran ruwa da kofi. Ta dago da niyyar tambayarshi ta zuba.mishi, sai suka hada ido. Cikin sauri ta sadda kanta har da dauke numfashinta. Domin ta zaci zai antaya mata mari ne. Jin shiru ta sake dagowa. Muryarta na rawa taCe. "Yaya in zuba maka?"Na koshi. * Ya fada a daKile. Da gudu ta mike kuma a rikice zata yi daki, tamkar ya kwashe da dariya sai ya dake yace.Ke" Kamar zata saki fitsari ta tsaya cak amma ta kasa waiwayowa. Ya ce, "Zo nan ki kwashe kayanki, ko nine zan kwashe miki?" •Ganin rawar jikin tata zubar da abincin a kofar kicin, da rasa me zata yi sai ta fashe da kuka. Yana kallonta yayi murmush: ya dauke kai Ta kwashe ta kai kicin, tazo ta haye gado ta kudundune. Lokacin ne Shatima ya samu dama har ya yi dariya sosai. Sai kuma ya ji zuciyarsa tayi masa sauki. Ya yarda da batun Likitoci, da suka ce dariya tana rage damuwa. Yana bude aiki zai fara, sai •yaga sakwanni a Emel din sa. Tun karfe uku sakon ya shigo cikin akwatinsa, suna da meeting a Abuja karfe tara na safe. Yayi hamdala da yaga sakon yanzu, da sai da safen zai gani. Dole Zai yi bukin din jirgin safe na karfe takwas.Salma bata yi bacci sosai ba, tana jin Shatima ya shigo har da gyara mata kwanciya. Tana jin shi yayi alwala ya tada nafila. Da asubahi ta tashi tayi sallah, ta fito zuwa kicin. Kan sallaya taganshi yana karatun Alkur'ani, irin dan Karamin nan. Taje ta dafa ruwan zafi, sannan ta soma suyar dankali kafin shida ta hada komai. Ta fito ta samu ya fito wanka yana cikin dakinta yana saka kaya. Tsam! Ya tsuke cikin suit bulu me duhu, rigar ciki bulu me haske. Tayi saurin dauke kanta lokacin da taga zai waiwayo. Ya iso gurinta, tayi saurin tsugunnawa tana fadin, "Ina kwana?" Ta dauke numfashinta jin bai amsa ba, kuma bata yi zato ba sai taji an kama kafadunta an mikar da ita. Idanunta a lumshe hawaye suna kwaranya. Cikin taushin murya ya ce, "Salma!" Ta bude idanunta a hankali, sunyi jajir. Ya ce, ' "Wai kukan me ki ke yi haka?" Cikin rawar murya ta ce, "Ban san ranka zai baci ba, jiya wallahi da ba zan ce zan bi ka ba. Ba zaton shi ta sulale Kasa kan gwiwarta. "Ka yafe ni don Allah." Ya zauna a kan kujera. "Tashi ba kiyi min laifi ba, jiya ne raina yana baci ba laifinki ba ne. * Ya dauki hankicin shi da ke gefe Ya share mata hawaye. Ya ce, "Tashi ki kawo min abin karin. " Ta ce, "Na kawo. " Ta juya don hada mishi shayi. Yana kallonta tun da ya hada shayi a gabanta, shi kenan kullum haka take hada mishi babu kuskure Suga da yake irin ta kwali yake amfani da ita ta san adadin da yake so. Ta mika mishi, sannan ta sa cokali me yatsu ta ciro mishi yankan Biredi guda,uku, tasa a cikin plate, sannan ta aje mishi kwai da dankali. Ya ce, "Sannu da Rokari, kina Koari sosai Ta dube shi "Na gode. " Cikin jin dadi ta nufi kicin don kammala kayan da ta yi aiki da su. Yana goge baki da 'yar takardar share baki. Ya ce, "Zan tafi Abuja. Ta dan ware ido cikin mamaki ta ce, *Kuma yaushe za ka dawo?" Yace "Yau insha Allah Ya nuna mata dubu daya a kan kujera, "Ga kudin namanki nan. " Ta ce, "To Allah Ya dawo da kai lafiya." Ya shafa kumatunta "Na gode. Ya fita ta koma kicin ta ci gaba da aikinta. Ya sallami sauran ya fita. Maigadi ya ce, "Alhaji yau motar babu lafiya ne?" Ya ce, "A'a zan hau Jirgi ne zuwa Abuja, yanzu zan dauki motar haya ne. YADDA ZAN FAHIMCI MUJINA Na daya, na fahimci baya cin danyan kifi, na biyu ba ya son a shiga huruminsa in yana cikin fushi, na uku yana son komai a gaskiya. Tayi murmushi da ta karanta, a fili ta ce, *Insha Allah sai na gama fahimtar halayensa. * Ta tashi ta maida littafin. Ta dauki kudin nama ta fita zuwa gurin Maigadi, sai aka kwankwasa Kofa Yaje ya bude, cikin mamaki sai ta hango Yaya Hadiza, cikin mura taje ta rungumeta. Ta dauki Amira don murna. Yaya Hadiza ta ce, "Duk cikin murnar za ki dauki wannan Katuwar yarinyar"?" Da gudu ta dawo ta ba Maigadi sako ta Koma. Hadiza ta ce "Kin gan mu sai yau ko?" Salma taCe Wallahi kullum ina ta kewar Inna, ya ba kuzo da ita ba?" Tace "Sai ta fita takaba sannan zata zo Suna ta hira, Hadiza tace "Kin yi fari kin Kara dan Tsawo, amma ba kiba. Salma ta Ce,kuma sai ina ganin kamar nayi Kiba." Ta ce, ' "Kin dai yi kyau, Kila Kibar sai nan gaba. Ranar ta yini har yamma suna hira. Ta ba Salma shawarar yanda zata dinga adana kudi maimakon cin kilon nama kullum. Ta ce, "Na dari uku ya ishe ki, sauran sai ki ke adanawa. Sai ki ga kin tara kudin da za a gyara miki daki, duk abin da babu a sai miki kafin Allah ya ba ki ciki ki haihu mutane su zo." Salma tace "Sai dai in tambaye shi in ya yarda, don bana son in yi masa rashin gaskiya, na kula ba ya son haka. Hadiza tace Ke amma sakarai ce ko? Ance miki maza suna son a rage musu kudin cefane ne?"' Salma tayi shiru a ranta tace *Don shawara na dauka, amma sai ya yarda, kawai wataran ya ganni da kudi ya ce ina na samo...?° Hadiza ta katse mata tunani da cewa, "Ke fa har yanzu sakara ce ko?" Salma ta ce, "Naji Yaya Hadiza, zan adana. "To ina ki ke zuwa kitso?" sai dai in dan kama da kaina in yi kalaba Ta ce Ai da yake ma gashin naki ba shi da zuciya, ko an yi banza da shi sai yayi ta hauka Salma ta ce Shi ko Yaya ma da na ce ina son " kitso sai ya ce ya fi son gashin a haka, sai dai in ina son a gyara min in mishi magana Hadiza "To shi kenan, kin ko fara zuwa Makaranta?" Salma ta ce, "Nasan ya na sane shi yasa bana mishi zancan Da za ta tafi, Salma ta ce "Gashi bani da kudi sai dari biyun Yaya da ya ce in aje masa, bari dai in debo miki biskit su Amira sa ke zuwa Makaranta da shi. Hadiza tace "'In kuma yazo yaga an diba fa?" Salma ta ce, "Nawa ne ya sai min har da alawa, shi baya cin irin su. " Hadiza tayi dariya tar da fadin "Yar gata Ta saka hijabi da nufin raka Hadiza har bakin titi. Hadiza ta ce "A'a babu ruwana, kin taba yin rakiya ne?" Salma ta ce, "Ban taba fita ko wajen Gate ba, Allah ina son in fita Suna cikin jayayya sai ga wata bakar mota. Shatima ya fito wani abokin aikinsa ya kawo shi. Ya fadada fara'arsa. "Sannu da zuwa, " Ta ce, "Yauwa Alhaji. Suka gaisa. Ya ce "Ba dai za ki tafi ba?" Tace "Wallahi zan tafi ne tun safe nazo. " Ya ciro kudi a aljihun wandonshi ya mika mata. "Ga shi ki hau mota. " Ta ce, "Da ka bar shi." Yace "A'a ki amsa, ni na ba ki." Ta amsa tare da godiya. Salma ta kalle shi, "Yaya zan dan rakata titi." Ba tare da ya kalleta ba ya ce, "A'a, ki koma daga nan. Ta tsaya cak! Ta mika ma Hadiza ledar hannunta. Ta ce, "Ki ce ina gaida Inna, ki bata dari biyar cikin kudin da ya ba ki. ." Hadiza ta ce, "Ko ba ki ce ba zan bata. Ta koma daki ta same shi a cikin dakin bacci, yana rataye suit din shi a jikin madubinta. Ya ce, "Wato za ki fita ba izini ko?" Ta ce, "Ban zaci zaka yi fada ba. Yace "To ko waye ya zo ban amince kiyi rakiya gaba da Gate ba. Ta ce, "To Yaya, insha Allahu. " Nan ma ta dauko littafin rubutunta, shima ta rubuta, har ya kalleta ya fito bandaki. "Me ki ke yi da littafin?" Ta ce, "Ina yin 'yan rubuce-rubucena ne yace "Yana da kyau haka. To me ki ka ba Hadiza din?" •Ta kalle shi "Ai bani da ko sisi, sai kudin ka dari biyun ka da ka ce in aje maka. Yace "Kuma a dakin ba ki da abin bata?" Ta girgiza kai tareda dan tabe baki, "Me gare ni Yaya, na dai ba; Yaranta biskit dina, tunda shi ai ka ce nawa ne ko?", Ya cc, "Eh." Tace "Ka ji abin da Ya Hadiza tace?" Ya tattaro hankalinga garè ta da tambayar. "Me ta ce?" Ta ce, "Wai in Rage siyan nama da yawa sai in tara kudin, wai in sai kamar ,na dari uku nace sai na tambayeka in ka yarda Yace to sauran kudin ayi me dasu? Wai in adana sai a siya min abinda bani dashi Yace to ai ta baki shawara ne ni bani da matsala da haka in kina ra,ayin rage cin nama kina iya yin hakan tace na gode yaya•Yayi murmushi, "Sarkin godiya. Gobe za a kawo form na Makarantar, ki. Ba ta san lokacin da ta buga tsalle ba har ta kai inda ya ke ta kuma rungume shi, tana fadin "Na gode Yaya. Yayi dariya, "Ki samu nutsuwa in fada miki." Ta durkusa a gabanshi, "To Yaya na nutsu." Ya ce Makarantar a nan Unguwar take kusa da titi, sannan maza ne da mata, in kin shiga ki kama kanki bana son kiyi abota da wadanda ba za ki karu ba, ki sa kai kiyi abin da ya kai ki." Salma ta ce Insha Allahu zan kiyaye." Ya ce "Ban ce musu ke matar aure ba ce, kin ga ke za ki [8/19, 11:57] Ummi Tandama😇: ____________ *🏚️RANA DAYA BOOK 2 🏚️* CHAPTER 14 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* kare mutuncin auranki." Salma ta ce, "Na gode • Yaya, Yaushe zan fara zuwa?" Ya ce, "Ina son nan da ranar Monday (Litinin)nake son ki soma zuwa insha Allah." Salma tayi ta godiya! Ranar ko baccin kirki bata yi ba, ta tashi tana ta kwatanta irin tafiyar da zata yi in zata Makaranta. Haka kuwa washegari sai gashi da form, da jaka, da takardu, da uniform kala biyu. Tamkar * sallah Salma taji, ya ce "Saura safa da takalmi. " TaCe Yaya duk kasuwa kaje ka siyo?" Ya ce "A'a Makarantar suke badawa. Takalmi da safa ne suka fadì kalar da za a siya." Sun je Makarantar an yi mata tambayoyi, in da suka gano tasan abubuwa sai dai bata jin Turanci. Da za su sa ta SS1 sai suka ce sai dai ta maimaita JS2. Salma, ba ta damu ba, ita ko JS1 ne bata da matsala. Ranar Litinin kuwa randa Salma zata fara zuwa Makaranta dama kwana tayi bata runtsa ba,gani take kafin gari ya waye za a tashi duniya. Tun kiran farko ta farka ranar ba dakinta yake ba, tayi wanka ta zauna jiran ayi kiran shiga *Masallaci, Ranar ko karin kumallo kasa yi tayi Riga da siket ne, siket din mai fadi kadan ya Wuce gwiwa. Amma suna saka wando baki irin damammen nan, sannan safarsu tana zuwa Kwauri daidai in da wandon ya tsaya, sai riga fara da farin karamin hijabi, siket din kuma ruwan hoda. Hakan yasa kayan suka yi mata matukar kyau. Ta taje gashinta ta kama shi. Ta kalli madubi, sai ta tuna wata Sajida a kusa da gidansu can Zariya, suma haka suke saka kayan Makaranta, ita da kannenta su hau keke kowa da nashi. Ita dai suna bata sha'awa tun da, amma Sajidar sai take musu dariya in taga sun fito suma za su tafi, sai take ce musu Almajiran Gwamnati. Tayi juyi a fili ta ce, "Sajida dama za ki ganni yau, nima Salma na hau layin dalibai masu neman ilimi Ta dibi biskit ta zuba a Jakar ta zauna jiran Yayanta ya shigo. Murmushi ya saki lokacin da suka hada ido, tayi matukar birge shi a cikin kayan Makarantar. Yana tsaye bakin Rofar ya zuba hannayenshi biyu cikin aljihu. Ta durkusa ta gaishe shi ya amsa tare da fadin "'Muje ko baby. » Ya fadì haka ne don tayi masa kama da baby Ta rataya jakarta a gadon baya, ta dauki makullin dakin. Ya miko mata kudin namanta. sannan ya bata wata dari biyar din yace Ki hau Mashin in an tashi, canjin kuma kiyi amfani da shi. Ta ce, "Yaya na dauki biskit ba sai nayi amfani da kudi ba." Yace, "Ki bar shi." Suka fito, ta mika mishi makullin, "Kulle min Yaya. " Ya amsa yana Nuna mata yanda zata yi, domin ba kullum ne yake nan ba.Ta dube shi "Bari na yi ma Anty Aliya sallama. " Ya ce "Yi sauri min ti daya da rabi. Dan gudu ta kwasa, tare da tsalle ya girgiza kai *Yarinyar nan da shirme bare taji ta a cikin uniform me saka dalibi Kiriniya. Ta samu Aliya tsaye a kusa da window tana leke. Salma ta rusna ta gaida Aliya, sannan ta ce sai ta dawo. Bata jira amsawarta ba ta juya don kar ta shiga lokacin da Shatima ya bata. Da dan tsallanta ta koma gurinshi. Ya tada mota zata hau baya, ya ce "Kina son ki nuna ma "Yan Makarantarku ni Direbanki ne ko?" Tayi dariya tare da komawa gaba. Da suka zo fita, ta mika ma Maigadi kudin nama. Ta ce, *Yau na dari biyar ni ke so Ya ce "To." Shatima ya kalleta "Za'a soma adana kudin ne?" Ta ce Ai na dari uku ni ke siya duk kwanakin nan, yau da kana dakina ne zan kara. Ya cE "Au! Yau ina dakin baby ne ko?" Tayi dariya, "Kullum kana dakina Yaya sai ka manta, " Ya CE "Lokaci zai zo da zan tuna. " Ta ce, "Allah ya kai mu." Ofishin Shugaban Makarantar •suka je, daga nan aka nuna ma Salma aji. Ta daga mishi hannu tare da fadin Bye-bye Yaya. " Cikin murmushi yace "Bye baby. A cikin ajin an nuna ta a matsayin sabuwar daliba, aka nemi da ta fadì sunanta. Ta mike ta ce, "Sunana Ummu Salma A. Bashir. Suka yi mata sannu da zuwa. Malamin ya nuna mata wata yarinya. "Ga waccan itama sunanta Ummu Salma, kije kusa da ita na hada ku kawance.Cikin sakin fuska ta kalli Salma, "Zo mu zauna." Cikin turanci tayi mata maganar. Salma ta kan ji amma bata iya maidawa ba. Umma Salma Sadi Dankasa ita ce Kawar da aka yi wa Salma, tana da kokari ga salo da iya yi, rawar kai kuwa ba a magana. Suna shiga falo Amna ta ce, "Ko'ina ya yi kura me aikin ta soma aikin shara. Ya ce mata "Bari ya duba Nafisa itama cikin ne. Amna ta tabe baki bata ce komai ba. Ya samu Nafisa kwance bata jima da dawowa dega amai ba. ya ce, "Aman nan yayi yawa, ko dai asibiti zamu je?" Ta ce, "Ba za ta iya tashi ba. " Ya dauki wayarshi, ya kira layin Likita ya fada mishi halin da Nafisa take ciki. Ya ce, "Ya zo asibitinshi da mota ya dauki Nurse ta saka mata ruwa, shine kawai abin da za'a iya yi mata. Ya CE "To." Haka ya dauki mota yaje ya kawo Nurse ta zo da komai ta hada ma Nafisa ruwa. Aliya da ke leke ta window ta ji haushin hakan, dama tana cike da takaicin yanda yake ririta Nafisar, ga Amna ma ta dawo. Ta dauki wayarta ta tura mishi sakon korafi. 'Haba my love, ban zaci za ka yi min haka ba, gani a gida sai ka dauko Nurse daga waje? Gaskiya ban ji dadin haka ba. Sakon na shigowa ya duba, guntun murmushi yayi bai damu ba yasan Aliya tana da fahimta, da ya yi mata bayani zata, fahimce shi. Sai da Nafisa ta samu bacci sannan ya kira Mama a waya yace Don Allah Hamida ko Momi wani ya zo saboda dare, yanzun haka ruwa ake yiwa Nafisa kari. Mama tace "Jikin ne har yanzun?" Ya ce, "Ciki ne da ita, sai wuya take sha, amai yayi yawa. Mama cikin murna ta ce, "Allah Ya bata lafiya. Hamida sai ta zo tunda itace ba ta zuwa Makaranta sun gama jarabawar fita.Yayi godiya suka yi sallama. Ya tafi dakin Aliya don fahimtar da ita. Tam! Ya same tacikin fushi, ya ce "Haba Aliya, keda ni ke gain kin fi su hankali, kuma za ki fisu bani hadin kai?" Tace "Ai ni gani nayi ilimina bai yi min amfani ba, in ba zan taimaki mijina da kuma abokan zamana ba. Ya kama hannunta "Na fahimce ki my love, amma kin san halinku na mata, nasan ba za ta yarda ki sa mata ba ne. Aliya ta ce, "To yanzun haka zaka sa mana ido muna matanka babu taimako a tsakaninmu, babu jituwa, ba za mu iya cin abinci kwano daya ba, gaisuwa ma ta gagara tsakaninmu, ko dan su suna jin su 'ya' yan wasu ne? Amma ni da Salma ai muna gaisawa, duk da sakarcin kuruciya irin na Salma ta fi min su tunda za'a gaisa. Ka iya tunawa fa ko makocinka ne Musulunci ya gindaya sharadin makotaka tsakaninku, bare matanka. Wannan fa aiki ne babba a kanka, domin kiwonmu Allah Ya baka, gashi za'a soma haihuwa a gidan tun yanzun gara kayi digin hada kan yaranka. Ya janyo ta zuwa jikinshi, "Ina sonki sosai gurin sa ni a hanya, ki taimaka min gurin hadin kan iyalina, ke ce ki ka fahimce ni. " Aliya ta dan ji dadi, yanda ya nuna mata. Salma kam bata da wata matsala, babu kowa da komai a gabanta sai karatunta, matsalarta daya in an bata assignment bata samun me taimaka mata in ta z0 gida, sai in ta koma Makaranta Salma Dakanta ta taimaka mata. Wannan Juma'ar an basu me wuya, gashi in sun je ranar Monday babu lokaci bare Salma ta taimaka mata don sai da ta bata shawara kan cewa Yayan da ke sauke ki ya dinga taimaka miki. Tace "Ba shi da lokaci ne amma zata mishì magana.Salma ta ce, "To ki fada a dinga biya miki lesson, ko a nemo miki Malamin lesson agida. " Salma tace "Bari zata yi masa magana. Cikin Nafisa me laulayi ne sosai, da tsarabar zan ci kaza, ba zan ci kaza ba. Domin wani abin ma sai an siyo shi tacì sai kuma ta sheka amai. Duk ta rame, ta kode abin tausayi kullum cikin Karin ruwa. Yanzun dole ta yarda Aliya tana saka mata ruwa, tun lokacin da Aliya ta dage a kan sai sun je ta duba Nafisar, shi kuma yana gudun kada Nafisar ta mata wulakanci ta ce ita dai suje. Da yake Nafisar ta kanta take yi sai bata yi wata masifa ba. Aliyar ta gyara mata ruwa ta ce, ta gode. Shatima ya ji dadì sosai. Tun daga ranar kullum sai ta-je gaida Nafisa, bare in ta lura Shatima ya shiga dakin. Amna kuwa ko ta shiga ta kan samu tana bacci, to da yake ba don Allah take zuwa ba, bata komawa sai kuma gobe in yana gida. Shatima zuwa yanzun ya dauki Aliya ya sata a wani matsayi mai girma. Har yana ganin ta kai yayi kowace shawara da ita, kuma yana ganin zata iya zama wakiliyarshi a wasu al'amura na gidanshi. Don tana da tsoron Allah, ga tsayawa a kan gaskiya da rikon amana. [8/19, 12:22] Ummi Tandama😇: ________ *🏚️RANA DAYA BOOK 2 🏚️* CHAPTER 15 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI* *Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki* Nafisa ta tashi zaune, ta ce Hamida ta saka mata pillow zata jingina. Ta ce "Hamida yanzun Karfe nawa?" Ta ce, "Tara na dare.Nafisa ta CE "Tabdi! Kin san wai me nike son ci?" Hamida ta yatsina baki ta ce, "A'a Ta ce "Zogala! Ji wata fitina, ni da bai dame ni ba Hamida ta ce "Ni yanzun ina za a samu wani zogala?" Nafisa ta ce, "Kira min Ya Shatima." Yana dakin Aliya daidai lokacin da wayar tayi ringing, ya zo daidai da lokacin da Salma tayi sallama a dakin na Aliya, hannunta dauke da littafin ta wanda za"a koya mata, Aliya ta amsa, sannan Shatima ya kalleta bayan ya dauki wayar yana duba suman. Zumbur! Ya mike tare da daga wayar ya ce, "Nafisa!" Hamida ta ce,"Ni ce, ta ce kazo* Ya ce, "To gani nan zuwa.Ya kalli Salma "Ya aka yi?" Tace, "Yaya dama assignment ne za a nuna mini." Ya kalli Aliya, "Duba mata don Allah, bari in je gurin Nafisa in ji Aliya tayi'yar dariyar yake tace "Sai ka dawo, don Allah ka ce ina yi mata sannu. Yana fita Aliya ta kalli Salma kallon sama da kasa irin kallon wulakanci da raini, ta ce "Aka yi sati da Lahadi duk ba ki tuna da assignment ba sai yanzun da ki ka ganshi a nan dakin? To bari in ja miki kunne, duk ranar da yake dakina na haramta miki zuwa. Salma ta ce, "Anty don Allah kiyi hakuri, ina ta tunanin yanda zan ma Yaya magana ne, " Aliya ta fizgi takardar tana dubawa. Salma ta ce " Anty bari ki ga yanda aka ce…. Aliya ta katseta da cewa, "Da Allah ni yi min shiru, ke ce za ki nuna min, tun kafin a haifi uwar me alli Balbela take da farinta." Salma ta ce, "Me ki ka ce?" Aliya ta ce, "Tun kina^yar mitsitsiyarki ni ke zuwa boko, kuma muke rubuta maths. Salma ta ce, "Yi hakuri." ." Don ta lura Aliyar tayi maganar cikin fushi ne. bata koya mata ba, saidai ta rubuta ta bata tare da cewa gashi nan ni bani da lokacin yi miki wani nune-nune. Salma taje daki tana dubawa cikin kokwanto,tana tunanin gaskiya da kyar in haka ne, amma zata je da shi Makaranta ta nuna ma Salma Dankasa Shatima ya shigo, "Ina Salman?" Ta ce, "Nayi mata ta wuce, yarinyar nan Allah Yasa dai tayi karatu, naga dan abin da ta kasa ganewa,ga takardarta duk ziro Ya ce, "To don Allah ki ke taimaka mata, sai a hankali.Aliya ta ce, "Har Lesson na ce zan ke yi mata." Ya ce, "To ai ko na gode. Yanzu ina zan samu zogala?" Ta ce, "Wake so?" Yace"Nafisa.Ce. Tace "Gashi dare ya yi. Amma ka tambayi Maigadi, in za'a samu danye sai a dafa mata yanzun ayi mata kwado. Ya ce, "Haka ne. Maigadi ya ce, "Can makotan suna da shi Sai gashi an samu, nan da nan Aliya ta zage ta dafa, ta cE "Sai kuma in da za a samu kuli-kuli Nan ma Maigadin aka sake tuntuba. Shi ya bazu cikin unguwa sai kusan sha daya saura ya dawo. Kura-Kura aka samo. Aliya dai aka zage aka daka, ta kwadanta mata. Nan ya dauka ya kai mata. Tasa a gaba kuwa tayi ta ci, cikin ikon Allah kuma sai gashi bata yi amai ba, Salma tana zuwa Makaranta, ta nuna ma Salma Dankasa, Salma ta ce "Wa ya yi miki?" Tace *Matar Yayana Salma ta ce, "To ba daidai bane. Ta dauko littafinta ta nuna mata. *Kin ga nIfa. * Salma mamaki ya cikata, amma ta share tace "Bari ta sake kwalewa sai tayi kafin Malaminsu ya iso." Amna cikin bacci taji karar wayar Shatima. Ta kalle shi yana ta bacci, da alamu yau ya gaji sosai,don sun je Abuja ne sai ma goma ya shigo gidan. Ta kai hannu ta shafa fuskarshi, "Honey ana kiran wayarka tun dazu." Ya bude ido da kyar, taCe "Ka gaji ko?" Ya ce, "Na gaji sosai." Yana daukar wayar daidai lokacin kiran ya tsinke. Yana dubawa yaga sau tara ana kira. "Nafisa!" ya furta da karfi tare da mikewa tamkar bai taba bacci ba. Amna ta dube shi, "Wai ina za ka?" Yace, "Nafisa, ina zaton jikin ne." Amna ta sakko itama bata yi mishi magana ba,illa dai taje ta murda makullin kofa ta cire key din tare da fadin, "Ba za ka fita ba. Na gaji da irin wannan abun, don ciki bai fi ciki ba. Saboda salo bata tashi kiranka sai ranar da ka ke dakina? Sau biyu tana yi min haka, ba zan bari tayi na uku ba, tunda naga abin nata yana neman ya zarme. Shatima ya ce, "Haba Honey, kin san fa cikinta ba irin naki ba ne. Ta ce, cikin mamaki, "Au! Dama akwai wani ciki na musamman ne wanda kayi mata shi ni baka yi min ba?" Ya ce "Ba haka nake nufi ba, nata cikin me yawan laulayi ne. Don Shatima ya kira. Hamida ta ce, "Tun dazun yake kira." Aliya ta ce "Bar shi kar ki daga har sai ya fito, in yana dakin wannan 'yar gwal din ba ya iya fitowa, yanzu dubi jikin baiwar Allahn nan amma ya wofintar da ita.Hamida ta ce "Allah nima abin ya bani haushi, na kira shi ya fi sau ishirin amma bai ko daga ba Da ya daga ya ce min yana zuwa shine fa shiru Aliya ta ce, "Sai ga shi ya kira ni wai inzo Hamida ta cE "Ai mun gode, Allah ya saka dabalkairi. Ai har Mamanmu na fada mata irin taimakon da ki ke mana.Aliya ta ce, "Ai yi wa kai ne. " Sai da aka kira sallar Asubahi sannan ta koma dakinta. Shi ko Shatima zama ya yi a kan durowar gefen gado, yana ta kiran layin Aliya, ita kuma ta baro ta can dakinta domin da ta Nafisa ya yi ta kira yana tambayar Hamida ko Aliya tazo? Tana fada masa cewa bata z0 ba. Bayan yayì sallah ya ce "To yanzun sai ki bude ni in dubo ta ko?" Ta Ce '"Ai ba yanzun ka ke zuwa ba. Ya cE "To yanzun kuma zamu iya samun matsala tunda gari ya waye Ta ce, "Mu samu mana, dama nasan ba zaka kula dani ba kaje ka rabo ni da gidanmu ina can cikin tattali kaje ka dauko ni." Ya ce, "Kin raina kulawar da nake ba ki? To kifada min abin da ki ke son in ke miki don ki tabbatar da ina kula da ke " Ya fada ranshi a bace. Ta ce "Ga shi ka kwana zaune kana dakina zuciyarka na gurin wata." Ta ce, "Yiwa kai ne dai,kuma bana fata kema wata rana in haka ta faru zaki ji dadì in ta hana ni fitowa in wofintar da ke?" Ta ce"Ni dai ba zan bude ba, dama ka shiga wanka in ba haka ba zaka yi lattin zuwa office." Ganin da gaske ba za ta bude ba, ya bi shawarar ta ya shiga wanka. Kan ya fito ta bude sai ya fita zuwa dakinsa ya hau shiri. Bai ko kalli karin da Ladi Mai aiki ta hada mishi ba, ya nufi fita. Kofar a damke take, ya waigo ta fito tana tsaye a falon. Ta ce, "Ga abin karinka. " Ya girgiza kai, "Bana jin yunwa. Ta ce, '"Ai ko ba za ka dakin wata ka karya ba. Ta soma hada mishi shayi, Har gurin Kofar ta Zota bashi. Ya amsa tare da fadin "In da ace za ki ke hada min ko shayin ne a duk ranar da nike dakin ki da na yi tasa miki albarka Ya kai Karshen maganar tare da kurbar shayin Da sauri ya watso shi domin suga ya ji har cikin kwakwalwar kanshi. Ya mika mata shayin "Ga abin ki, bude ni." Ta kalli agogo, duk abinka sai shida ta cika, Ya ce, "Amna har yanzun ina mamakin ki sosai, ashe kin iya mugunta har haka?" ' Ta ce, Na daina bari ana raina min wayo." Ya jingina da bango, "Shidar dai saura minti hudu. Ta ce,Inma minti daya ne sai ya cika." Ya samu Nafisa a yan da take, ya kira Likita ya ce zai kawo ta asibiti don fa jikinta ya yi laushi Likitan yace "Ko ka kawo ta babu abin da zamu ¡ya mata da ya wuce wannan ruwan. Amma zan fita zuwa asibiti, ka fito bakin titi in same ka sai muje in ga.jikin.Haka kuwa Shatima ya fita ya yi jiran kusan minti biyar kafin Likitan ya iso. Shi kanshi Likitan ya tausaya ma Nafisa, ya ba da wata allura ta tsaida amai, ya ce ayi mata a gani. Amma ciki irin wannan Kila sai ta kai wata biyar zata samu dan Salma tana ta jiran Shatima har takwas ta gota Ta fito taje dakin Aliya nemanshi. Aliya ta ce an fada miki nan yake?"Salma ta ce, "Ni wallahi yanzun bana tuna in da yake." Ta ce, "Yana dakin Amna. " Har zata wuce sai taga sun fito da Likita. Ta rusuna ta gaida su,sannan ta ce. "Yaya mun yi latti.Ya kalli agogon hannunsa. "Haka ne, ya ba ki tafi ba? Nafisa ce ba lafiya ban san lokaci ya tafi haka ba. Ta ce, "Anty ba lafiya, bari in dubata. Sun gaisa da Hamida, sannan tayi wa Nafisar sannu. Ranar latti taje Makaranta, sai da ya roka aka bude mata don har sun ce ta koma. ** Wata ranar Litinin misalin Rarfe biyu da minti bakwai. Salma ta sauka daga kan Mashin a bakin Gate din gidansu. Ta ba mai mashin kudin sai taga bakuwar mota zata shiga gidan. Maigadi yazo yana tambayar Direban gurin wa suka z0? Salma ta kalli Direban, kamar ta taba ganinshi a wani guri. Sun yi kama da Shatima kadan. Taji lokacin daga bayan motar an ce, "Uwar Maigidan ce Gaban Salma ya fadi, domin ko a ina taji muryar Hajiyar Shatima ba za ta manta ba. [8/19, 18:44] Ummi Tandama😇: _________ *🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️* CHAPTER 16 Karshen book 2 *BY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHI* Ta nufi cikin gidan gaba daya jiki a sanyaye,ta kasa bude kofarta,tabi motar da kallo har lokacin da taga motar ta tsaya daga cikin jerin motocin Amna da Shatima. Ta bude kofarta ta shige,kasa cire kayan jikin ta tayi na makarantar haka kuma ta kasa dora girki,sai da tayi ta maza ta kunna risho ta dora tafasasshen nama. Lokacin da su Hajiya suka shiga gurin Nafisa tana wanka,Hameeda tayiwa Mama da Hajiya oyoyo Aliya ta leko taga bakin Nafisa ne Dan haka sai ta yafa mayafi taje ta nufi wajen Nafisa da sigar duba jiki,tana shiga taga su Hajiya gabanta saida ya fadi tasan Hajiya ba kalar wasa bace, amma duk da haka saita cije ta zube ta kwashi gaisuwa a gabansu tana gaishe su yanda kasan zatayi masu sujada saboda girmamawa,Hameeda ne ta ajiye masu ruwa da lemu Aliya tace" Ya jikin Nafisa yau dai jiki da sauki? Hameeda tace "to gata nan ciki tana wanka". Cikin kissa tace "Masha Allah naji dadi sosai,tasha magungunan ta kuwa?". "Kinsan kuwa sai kinzo take sha,domin nidai nayi nayi da ita takisha" Aliya tace "to bari ta fito inna lallasheta nasan zatasha haka za'ayi tayi hakuri da ita bansan inda zan samu tsakin nan bane bare ayimata abinda takeso amma ga rama can maigadi ya siyo mana". Duk zubar da takeyi su Hajiya suna jin ta kuma sun yaba da maganganun ta musamman ma mahaifiyar Nafisa dan ance me da Wawa,Mama tace "Allah sarki kina dawainiya da Yarinyar nan Kullum Hameeda tana fadaman duk abinda ke faruwa har dare kina zuwa ki dubata." Hajiya tace "haka akeso aishi zaman aure dama zaman tare haka akeson babba ya kasance,ita Yar'uwar takufa? Aliya tace"Amna tana gurinta itama da sauki domin bacci takeyi,bari dai induba ta inaga yanzu ta tashi,Mama tace"Allah sarki kina dawainiya da wannan kiyi dawainiya da wancan kiyi da wannan Allah ya yi maki albarka. Aliya ta amsa da"ameen" ta fita cikin jin dadi ta nufi shashin Amna domin dai burin ta kawai ta shiga ne gurin kowa taga yadda yake,hakan ne zai bata damar kunna wutar da take bukata a wannan gida,ta samu Amna a zaune tana kallon T.v mai aikin ta kuma tana bare mata kwai a gefe akan filet. Tace "sannu da hutawa" Kallo daya Amna tayi mata,sannan tace"yauwa sannunta" ta maida kanta gurin T.v. Aliya tace "Hajiyan Shatima ne tazo tana dakin Nafisa tana bukatar ki,tace inzo inkira ki." Amna tace "Ina zuwa" Aliya ta juya ta fice. Tsaki kawai Amna taja banda Hajiya ce babu abinda zaisa taje wani dakin wata daga cikin su,dan kawai ta nunamana cewa tafison yar'uwarsu ne kowaye Nafisa tafi Oho..... Aliya na fita dakin Salma ta nufa ta sameta a jingine tayi jajjage. Tace "to gasu Hajiyar Shatima can kije ki gaidasu Maman Shatima ne,Salma ta danyi rau rau da ido cike da tsoro,tace "Aunty tsoro nikeji" "Tsoron wa.?" Salma tace Hajiya wallahi,Aliya ta"sai kace wata mayya,ta haifa maki miji gashi nan yanata kashe maki uban kudi amma kice wai kinajin tsoron ta". Salma tace "ba haka bane Aunty,ta taba man fada kuma ni ina tsoron fadanta. Aliya tayi murmushin mugunta a ranta tace yanzu ma wani fadan zan sake ja maki,ta dubi Salma tace to wuce kije ki gaisheta," Salma tace to bari in canza kaya in cire na makarantar nan. "Ta ya mutsa fuska jin cewa Salma zata samu canza kaya,inta cire kayan nan ai shikenan zata rage mata sauki ma har ta samu tseguntawa Hajiya irin kudin da ke kashewa Salma wadda abin ke damunta Kullum, Salma ta dauki dan mayafin jallabiyar ta tayafa tunda daga kanta babu dan kwali ta fito cikin fargaba ta nufi shashen Nafisa. Aliya ta shiga dakin ta dama ranar itace da Shatima kuma ta shirya mashi farfesun kaza yana wuta batama gama ba,sannan tayi dafadukan cos-cos da hanta,nan ta jerowa su Hajiya a katon tire ta shigo dakin Nafisa ta samu Salma tana rabe rabe a gefe ta kasa karasawa ciki,harda tsawar ta tace "muje mana kin wani rabe gefe guda." Hajiya tace"wacece?" Aliya cikin sigar son tura kiyayyar Salma ga surukar tasu tace "Salma ce uwar shanshanci". Hajiya ta gimtse fuska harma da Amna da Maman Nafisa da suke zaune, Salma ta tsugunna a gabansu kana kallon ta kasan a firgice take,Aliya ta dire tiren a gabansu nan kamshi ya daki cikin su,ta kalli Hameeda "kawo filet da cukula mana kisa". Salma cikin raunin murya tace sannunku da zuwa Hajiya,Mama ne kadai ta amsa "yauwa sannu Yarinyar nan". Ta kalli Nafisa wacce ke zaune saman kujera tace sannu Aunty ya jikin? Itama fuskar ta a daure tace "jiki da sauki" ta yunkura zata mike Hajiya tace koma ki zauna" Salma ta zaro ido tare da zama cikin tsananin faduwar gaba,ta tuno alwashin da Hajiya tayi sai tazo har kaduna tasa ankoreta,hawaye suka soma zubo mata... Muryar Hajiya ne ya katseta daga tunanin da takeyi "iyayen kine sukazo daga Zaria suka saki makaranta?". Cikin in inah Salma tace a'ah. Aliya tace "Ina sukaga halin sata a makaranta sunaji da abinda zasuci" Salma ta kalli Aliya a tunanin ta wannan maganar ta Aliya kamar tayine domin kareta a gurin Hajiya sai kawai taji Hajiya tace "Badai shi Shatima ne yasata ba?" Nafisa ta tabe baki "shiyasa ta mana Hajiya makaranta me shegen tsada" Aliya tace "tsada ai ba kadan ba ma tsadar,kusan dubu dari harda doriya" Amna ta kalli Aliya domin jin bakon lamari ita bata shiga harkar kowa batasan ma me akeyi a gidan ba. Hajiy tace "Eyyeh!" Aliya tace "to ai kudin shiga makarantar nan dubu saba'in da biyar ne banda kudin motar dawowar ta da Kullum sai ya bada dari biyar ga kudin namanta da komai da yake badawa dubu daya,"Aliya takai karshen maganar tanajin dadin tasamu abinda takeso. Hajiya ta kalli Salma cike da tsana tace hakane kudin makarantar dubu saba'in da biyar? Salma cikin rawar jiki tace "yanzu sun cike tamanin". Hajiya ta mike da sauri tana fadin "lallai kam sun cike tamanin wato ke yakeyiwa aiki kenan kullum rana ta Allah dubu daya da dari biyar a wata nawa zai kama? Jama'a kuyi mani lissafi? Da sauri Amna tace dubu arba'in da biyar kenan zai kama duk wata" Nafisa tace "Kan uba!! Muna zaune?" Hajiya tace "to aikoni dana haifeshi idan ya yi man haka nasan ya kai daa" Maman Nafisa tace "to shime yakaishi wannan batan basira? Wai rokon Allah da goge" Hajiya ta soma kiran layinshi ya daga tace "Ina gidanka Allah yasa ka kusa tashi" yace "insha Allahu nan da awa daya zan dawo" tace "saika iso" keda wayene? "Nida Mamanku ne Mustapha ne ya kawomu". Salma wacce sautin kukanta ya fara fitowa tace "don Allah Hajiya kuyi hakuri....."jifar da Hajiya tayi matane da karamin filon kan kujera ya hanata karasa maganar ta. Hajiya tacigaba da cewa "banason jin komai daga gareki Yar gidan masu asiri kawai,ai tundaga lokacin da yaron nan ya zoman tamkar zaiyi hauka akan wannan kazamiyar Yarinyar nasan aikin asirine. Ta kalli Maman su Nafisa ki tunafa be taba kwanciya a asibiti akan wata ba sai silar wannan Yarinyar dan nace bazai aureta ba ranar ya tashi a sankare idanuwa a kakkafe mukai asibiti" Duk matan nan suka kalli Salma cikin mamaki musamman ma Amna wadda take da matukar tsoron asiri. Nafisa tace "wai dama ciwon nan nashi yanada nasaba da itane?" Hajiya tace "inkinje gaba ma saiki fada daga nan abinda nayi mashi ya yi yawa kawai sai nasa ayiman tambaya wajen malamai can ne suka fadaman wai uwar tane tasa akayi masa asiri da sunan Shatima kuma an hada da naman bakar akuya da yawun bakinta da ruwan hawayenta aka bashi yaci,daf da bikin nan fa har gida sai da ya siya masu da sauri Salma ta dago tana fadin "wallahi Hajiya ba siya mana ya yi ba hayace,"Hayar..... Hajiya ce ta sake jifarta da wayarta dake hannun ta "karya zanyi maki kenan dan ubanki?" Aliya cikin sauri ta dauki wayar tare da fadin haba Hajiya wayarki kar tayi lahani mana. Hameeda wacce tausayin Salma ya kamata haka kawai taji ba gaskiya bane abinda Hajiya take fada ba,dan haka ta saci wayar Nafisa tayi cikin daki ta fada bandaki domin yin abinda ya dace. Aliya ta kalli Hajiya kiyi hakuri bari in zuba maku abinci. Sakawa Maman ku dan ni bazanci abincin nan ba sai anyita ta kare yau din nan. Nafisa tace"gwara ayita ta kare domin kada kowa ta yadda kiri kiri hmm" Aliya tace "aikuwa bayin kansa bane bakiji abinda akace bane" Amna wadda ta yadda da zancen nan dari bisa dari ta kalli Salma cikin tsana indai tana gidan nan kam nidai bazan zauna ba dan a gaskiya banason asirce asircen nan da akeyi. Hameeda ta kira sau uku kafin ya daga tace Yaya don Allah kazo gida yanzun nan ga Salma nan an tsareta su Hajiya ne" Gaban Shatima ya fadi ya manta da tsanar da Hajiya tayiwa Salma, yace "nagode Hameeda ganinan zuwa." Lokacin tashinshi beyi ba haka dole ya tashi yaje gida da gaggawa domin kashe waccen wutar wadda shedan ya rura a cikin sa ya dauki uzuri gaggawa ya fita bema san irin gudun da yakeyi ba kawai saidai ya ganshi a layinsu,yana parking lokacin Mustapha ya fito daga falon Aliya. Shatima ya nufi gurinshi "inasu Hajiya?" Mustapha yace suna falon Nafisa. Shatima yace "to bari inje mu gaisa" Mustapha ya biyoshi domin ya gama cin abincinshine.tun daga baranda yakejin muryoyinsu daya bayan daya. Hajiya tana fadin"ba bakin dan akuya ba ko bakin dan jakane kukayi asiri dashi yau sai kin bar gidan nan". Cikin kuka Amna take fadin"yanzu zan kira Dadyna nima yazo ya daukeni dan bazaiyiwu in zauna ba,Ina tsoron asiri". Nafisa take fadin" jiya nan fa saida nayi mafarki da ita gaskiya bazan iya tuno meya faru a mafarkin ba amma tabbas ita na gani,ni kaina idan tana gidan nan to wallahi Mama saidai mu tafi daku yau din nan." Mustapha ne yafara shiga hakanne ya hana Aliya magana taso tayi magana dan ta hangoshine a tsaye. Cikin tashin hankalin ya shigo cikin dakin gaba daya suka maida kallon su gareshi sannan kowacce ta shiga nanata abinda zata nanata, kowacce ta nanata abinda ta fada. Hajiya tace "duk kuyi shiru yanzun dai kai kazo ka zaba koni dana haifeka ko kuma iyalanka ko kuma wannan Yarinyar ita kadai? Ta nuna Salma wacce take durkushe tana cikin firgici da matsanancin tashin hankali,itama kallon shi takeyi cike da tsananin bukatar taimakon shi,idanuntane suka nuna shi kadai take bukata,shine taimako na karshe da takesa rai zaiyi wani abu akan wannan halin da take ciki. Hajiya ta katseshi da fadin "Zan la'anceka!!!..." Zan la'anceka!!! In ka sake kallon ta,kuma na baka nan da minti daya rak ka yanke hukunci.......... *Alhamdulillah anan muka kawo karshen littafi na biyu,a yanzu kuma labarin zai fara, akwai cakwakiya fah,anan kuma muka kawo karshen free pages idan kina bukatar 3&4 din littafin RANA DAYA ki turo kudin ki 300 ta wannan account number din👇🏻* ```ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925``` *Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana* *Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki*