AMANI Littafin SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI) takorikabara@gmail.com AMANI TARE DA NI, SUMAYYAH ABDULKADIR SHIMFIDA Safiyar yau wadda ta kasance Lahadi, an wayi gari da lullumin hadari mai hade da sassanyar iska mai dadi a gidan su Amani, wanda ke cikin rukunin gidajen GRA a birnin Katsinan Dikko. Kasancewar lokacin ya kasance lokaci ne na tsakiyar damuna, kada ka so ka ga yadda shuke-shuken dake harabar gidan suka bude ganyayyakin su suka yi korra sharr, suna bada kamshin furanni da bishiyu kala-kala, musaman da bada jimawa ana iskar sai yayyafi ya soma sauka, don haka iska ce mai dadi kawai take kadawa a gidan mai sanyawa alummar gidan nishadi, ciki harda Amani dake can upstairs, ta bude tagogin dakin ta iskar na tadda har cikin toilet din da takw wanka. Dai dai lokacin da aka tsuge da ruwan saman kamar da bakin kwarya. Amani ta fito wanka, daure da towel a jikin ta, ta karasa ta rufe tagogin ta don dakin ya soma jikewa, ta zauna gaban mudubin kwalliyar ta dan kasar Mexico mahadin furnitures na gogaggen katakon kasar waje dake dakin kamar dakin matar aure. Kamar yadda yake a aladar ta kullum, daga fitowa wanka sai ta bata lokaci tana kwalliya a zaune a kan stool, kamar mai shirin tafiya beauty contest in ka ga yadda take bata lokaci wajen tsantsara kwalliya kullum. To yau ma hakan ce ta kasance, Amani ta kwashe kusan mintuna talatin tana gyara fuskar ta da serene make-up, bakin nan ya dauki maikon wet lips na Elizabeth Arden sai sheki yake kamar ka sace bakinka gudu irin wanda ake kira kissable lips, ta shirya cikin wani dan shafal din swiss lace ruwan gwaiduwar kwai da feshin golden a jikin sa, duka wannan adon na karshen mako ne bana zuwa wani waje ba, koda-yake dama tun filazal ita maabociyar ado ce da son kyale-kyalen mata irin wanda ya wuce kima, musamman a renaku irin wadannan na karshen mako da take wuni a gida, don ita bata yawace-yawacen gidan kawaye ko bukukuwa don basu ishe ta kallo ba. An yi mata wani kyakkyawan dinki na zamani na doguwar riga wadda ta kama ta daga sama ta bude daga kasa sosai kamar (A shape). Kai da ganin dinkin nata kasan na yayan gata ne kuma ya ja kudi a jikin sa. Amani tana sakkowa daga matattakalar bene inda dakin ta yake a cikin gidan su, wata irin tafiya take yi kamar hawainiya, kamar bata son taka kasa, kuma kamar tsinin takalmin ta bai dame ta ba. Sakkowa take daga benen cikin takun ta na kasaita da rangaji irin na yan matan da ke cikin lokacin su, suka kuma yi katarin samun rayuwa ta gata da wadata, dai-dai da yadda suke buri ko suke son samun ta a duniya. Daga nesa sai tayi maka kama da matashiyar macen Dawisu saboda iya ado da iya baza tafiyar kasaita, koko zangarniyar dabinon da iskar hunturu ke kadawa sabida yadda ilahirin kyakkyawan jikin ta ke rangaji tana zuba kamshi. Kai Amani karshe ce a class da gayu karshen duk inda zaka iya kwatanta ta. A haka ta isa babban falon gidan su, inda ta tadda mahaifin ta yana aiki cikin wasu muhimman takardu da naura mai kwakwalwar bisa cinya (laptop) a gaban sa. Tun kafin ta gama sakkowa daga benen hankalin mahaifin ta Hon. Usman ya kai gare ta sabida karar takalmin ta mai tsinin dunduniya. Ya daga ido ya dube ta, sai ya sunkuyar, yana cigaba da danna naurar gaban sa cikin kwarewa, ita ta san baban ta Guru ne a computer da lissafi bay a taba yarda kwandalar sa ta bata cikin lissafin sa, in ma ka sace ta don kana maaikacin sa zai gane, kuma sai ka yi aman ta. Cikin sigar kirari kamar ba mahaifin ta da ya haife ta ba, sai ka yi tsammanin wani saan ta ne koko abokin wasan ta, Alhaji shiga fadin TA-FISU YAR GIDAN BABAN TA! Ya saki dariyar farin cikin ganin ta ba tare da ya dago ba, hankalin sa na bisa lissafin sa don kada ya bata kwandala, ya ce Ta-fi-sun Daddy an fito?. In ji Alhajin cikin kulawa, sai yanzu da ya kammala kirgen sa kaf! Sannan ya dago ya dube ta, ya kuma bata hankalin sa, bayan ya kashe naurar gabadaya, cikin murmushin kauna da kulawa cikin yan kananun firi-firin idanun sa masu kama dana yan China. TA-FISU-KIN FI SAURAN MATA! Ya kara fadi cikin kambama yar tasa, wadda a kullum ya dube ta surar mahaifiyar ta Jalan ke masa gizo, har kullum yana godewa Allah da wannan kyakkyawar halitta da ya bashi a matsayin diyar sa, yana godewa Allah da ta debo komai na Jalan bata ko dauko farcen sa ba, ji yake kamar ya lika ta a goshi don So da alfahari, banda Allah sarkin hikima da tsara halitta yadda yake so, wa zai iya hakan? Mai sanya mummunan mutum bakikkirin kamar sa ya haifi irin wannan kyakkyawar halitta? Ai sai Allah Al Khaliqu Sarkin kaga halitta a yadda ya ga dama, Ubangijin sammai da kassai. Mai sanya mummuna ya haifi kyakkyawa. Shi da kan sa Uban yau da ya dube ta sai da ya ce tsarki ya tabbata ga sarki Allah! Domin gani yayi gabadaya ta rikide masa ta koma mahaifiyar ta Jalan, sau tari har gizo take masa da Uwar ta, shi yasa har kullum yake kara kaunar ta, duk soyayyar da yake wa uwar ta kan ta ya koma. Har gobe bai auri macen da yake so yake darajjawa irin Jalan ba. A yau ganin ta yayi replica din Maman ta, wato kamar Jalan ce gaban sa shekaru ashirin a baya. Amma Amani har ta fi ta sheki da daukar ido, don nata kyan ya hadu da gyara da kyale-kyalen zamani mai tsada. Alhaji Usman Faskari, baki ne wuluk, tittirna, gajere, kuma mai dagaggen hanci da kananun idanu mitsi-mitsi kamar na yan birnin Sin. Kai babu wata suffa a jikin Alhajin da zaa kira kyakkyawa, a cewar sa shi yasa Jalan ta ki zama da shi duk arzikin sa. Jalan mai kama da matan Hurul-eeni don kyau. Ta sha ce masa firgita ta yake cikin dare, ya daina shigo mata daki in dare ya yi, ya dinga bari sai gari ya waye. Ta fannin halayyar Alhajin ma sai mu ce sai a hankali, domin dai a zahiri shi mutum ne mai mammako (marowaci) kuma mai son kan sa da yar sa kadai. Ya mallaki mahaukaciyar dukiya da shi kan sa bai san adadin ta ba, wadda ya mallaka ta hanyoyin duka yaki halaal, da ya ki haraam, tunda kuwa gogaggen dan siyasa ne na jiya ba na yau ba, wadanda suka dade suna ci da tada kai hadi da birgima cikin dukiyar alumma da sunan siyasa da cigaban alumma. A halin yanzu yana rike da shugabancin jamiyya mafi karfi, mafi shahara da farin jini a wurin alummar kasar Najeriya. Wato jamiyyar AC da aka fi sani da (Action Congress) ta kasa bakidaya. Ya iso ga matsayin shugaban jamiyya ne bayan ya rike manyan mukaman Siyasa da baza su lissafu ba, tun daga karamar hukumar sa ta Faskari, har zuwa matakin jiha, wato jihar sa ta Katsina, har zuwa halin da ake ciki yanzu da ake damawa dashi a Gwamnatin Tarayya. Cikin manyan mukamai na karshe-karshe da Hon. Usman Faskari ya rike har da Sanatan Katsina ta kudu sau biyu. Idan ka cire harkar siyasa da yafi bada karfi da yin kaurin suna a kai, don da ita aka san shi, da ita yayi ficce, har ila yau, shi din kuma babban dan kasuwar ketare ne (International Business Man) wanda koda siyasa ko babu ya riga ya haye tudun mun tsira. A can baya tun kafin ya haifi Amani har kasuwancin fidda Iron ore da aluminium ore yayi, wato exporting natural resources da ake hakowa a kasashen Afrika daban-daban irin Saliyo da Madagascar, yana da shahararrren kamfanin sa na kan sa a Katsina mai reshe a birnin tarayya, Abuja wato FASKARI INVESTMENT amma rayuwar sa tafi yawa a garin Katsina. Daga baya bayan Amani ta tasa ya mayar wa da kamfanin suna Amani Faskari Investment, kamfani ne na komai da ruwan ka a harkar shigo da kayan ginin gidaje dana sakawa a gidaje, ba irin kayayyakin da basa shigowa da su da suka shafi wannan bangaren daga kasashen ketare musamman kasar Faransa da kasar Mexico inda ya zuba mafi rinjayen hannayen jarin sa, har ta kai ta kawo rabin rayuwar Usman Faskari ya zama na yawo tsakanin Najeriya da Faransa da Mexico, komai na kamfanin sa kowa ya san daga kasashen nan France ko Mexico yake kawo su, wato daga makerar su sai kamfanin sa kadai, shi yasa baa fiya samun irin kayan sa a Najeriya sosai ba, abin nufi, kayan ginin kamfanin AMANI FASKARI INVESTMENT LTD sun fita daban. Kama daga kofofi, tagogi, tiles, marbles, da duk abubuwan ceramic da ake amfani dasu wajen ginin gidaje. Masu ginne-ginen estates da gidaje a Katsina da Abuja yawanci duk a kamfanin sa suke order. A halin yanzu, Alhaji Usman Faskari, wanda alumma ke kira Hon. Faskari, yana da shekaru hamsin da biyar amma in ka gan shi arbain zaka bashi sabida jin dadi da kula da lafiyar sa, bashi da wani buri da yasa a gaba yanzu irin diyar sa Amani da rayuwar ta, babban burin sa kullum shi ne farin cikin ta, jin dadin ta da walwalar ta. Hon. Usman ya wadata Amani fiye da kima, tun a kananan shekarun ta Amani ta san tafi sauran tsararrakin ta gatan aljihu dana Uba, ya kuma fifita ta ya sangartata wanda hakan ya shafi tarbiyya da muamalar ta da mutane, saboda ya jika ta da komai na jin dadi da bukatun rayuwa ba tare da ta yi maraicin mahaifiyar ta ba, wadda Amani bata taba gani ba ko a hoto, alhalin tana raye ba wai ta mutu ba. Iyayen ta sun rabu tun tana tsumman haihuwa, a cewar sa saboda munin sa ne Jalan ta ki zama da shi, wanda kullum take cewa yana firgita ta, a zahiri shi yake tunanin hakan, amma dalilai da yawa ne suka hana Jalan iya zama da shi, ciki har da halayen sa na kankamo da rowa, dama kuma auren dole iyayen ta suka yi mata da shi a dalilin ya saye mahaifin ta da dukiya. Tunda ta koma kasar su (Sierra Leone) bata kara dawowa Najeriya ba, wai da sunan ganin yar da ta Haifa ta tafi ta bari bata ko shayar ba, shi kuma bai kara bin bayan ta ba, bai ma san tana raye kota rasu ba. Sai ya maida hankali a kan rainon kyakkyawar diyar data bar masa wato AMANI, ya kuma maida kafatanin soyayyar da yake yi wa Jalan a kan ta, bai yarda ta nemi wani abu a rayuwar ta ta rasa ba, komai darajar sa, bai yarda ta yi kukan babu ba, ba ya ko tunanin ya dace ya aurar da ita haka, kullum kallon yar kankanuwar yarinya yake mata, yadda take shekaru ashirin a baya sanda yake goya ta da kan sa a bayan sa. Shi kan sa bai san iya son da ya kewa yar sa Amani ba, ko iyakar adadin abinda ya mallaka, kuma komai nasa da sunan tilon yar sa AMANI yake rubuta hakkin mallakar sa. Wato ita yake sanyawa hakkin mallaka a rubuce gaban lauyoyin sa. Wannan ne kuma babban abinda ya assasa bakar kiyayya tsakanin Amani da matar sa Hajiya Rabi, saboda ita bata taba haihuwa da shi ba. Kafin Hajiya Rabi ya auri mata kusan tara yana sakin su, duk ba a kan komai ba sai a kan rikon Amani, don sun kasa yi mata irin rikon da yake so na gaskiya da amana, kankanin laifi zasu yi, ya basu takardar saki in dai a kan yar sa Amani ne, da ya sakawa suna TAFISU. Yake mata kirari da Kin fi sauran mata. Haka masu aiki ma basu tsira ba, kullum cikin canzawa Amani su ake, saboda a cewar sa basa kula masa da ita yadda yake so. Wannan yasa Amani ta tashi yarinya sangartatta, hamshakiya, mai girman kai, mai yawan alfahari, mai raini ga mutane, kuma mai izzah da dagawa da son a bata girma koda kuwa mutum ya haife ta. Ga rashin tauna magana da kowa take Magana, har shi mahaifin nata kuwa wani lokacin bata masa magana da girmamawa, ka yi mata magana ta mayar maka da harara. Yadda duk magana ta zo bakin ta haka take furzar da ita ga kowa cikin raini da gatsali, bazata yi laakari da yawan shekarun da ka bata ba zata iya marin ka ko ta tofa maka miyau a fuska muddin ka shiga gonar ta. Sabida girman kai irin na Amani ko kawaye cikin tsararrakin ta bata da su domin ta raina ajawalin kowa, da an fara kawancen zaa babe, saboda ba kowa ke jure halin ta na raini da dagawa ba. Kawar ta daya ce da suka yi karatun sakandire tare a (Ulul Albaab Science Secondary School Katsina) wato Hamida Balewa wadda itama Baban ta tsohon dan siyasa ne, da ya rike har mukamin gwamna a jihar Baucin Yakubu. Hamida ta iya da ita da halin ta, don ta fi ta hankali da hakuri kuma tana son Amani kamar yar uwar ta, shiyasa suka rayu tsayin lokacin nan basu rabu ba, har zuwa yanzu suna tare a shekarar nan da suka kammala karatun Jamia tare a jamiar Tafawa Balewa. Har zuwa lokacin da mahaifin ta ya auri Haj. Rabi, ita da kan ta Amani ta roke shi ya rufe aure-aure daga kan Haj. Rabi saboda mutuncin siyasar sa, da kuma kasancewar tana son ya zama akwai mace tare da su, duk da dai in ya saki baya jimawa yake kara aurowa, kafin ya auri Haj. Rabi ya dade babu mata, don ta karshe ta kusa kashe Amani da duka don haushi sabida ta tofa mata miyau a fuska, ita kuma Haj. Rabi ganin inda raunin Alh. Usman yake wato (son a taya shi kula da Amani da taya shi soyayyar tilon diyar tasa), sai ta saka kaimi a kai, ta kama Amanin ta rungume a farkon zuwan ta, har fiye da kima, da ta gan ta zata hau rawar jiki da hidima da ita a gaban Alhajin, irin yadda Hon. Din yake so matar duk da ya aura ta yi wa Amani, Haj. Rabi ta shiga nuna mata soyayya har fiye da shi. Hakan yasa ta shiga ran Alhaji. Amma ba haka abin yake a zuciyar ta ba. Wannan ne yasa tayi dan nisan zango a gidan Hon. Usman, domin a kalla zuwa yanzu tayi shekaru kusan hudu a gidan su Amani, sauran matan da ya aura a baya babu wadda ta rufa shekaru biyu. Amma a zahiri Haj. Rabi ba wanda ta tsana data bude ido ta gani a duniya irin Amanin. Babban tashin hankalin ta ranar data fahimci cewa komai na dukiyar Alhajin sunan Amani yake bearing, mai nufin ya gama mallaka mata komai nasa, duk wadda zata zo sai dai ta jira dan tumunin takaba (idan ma ta yi nasarar dadewa a gidan kenan). Musamman hankalin ta ya kara tashi da likita ya tabbatar mata shekarun ta sun wuce na daukar ciki wato ta isa menopause ba matsalar haihuwa ce da ita ba yadda take zato. Haj. Rabi tana da yara biyu mace da namiji da tsohon mijin ta na baya. Ta aurar da macen, namijin kuma yana jamia yana hannun mahaifin sa a garin su Minna jihar Neja. **** ***** ***** Amani ta karasa saukowa daga matattakalar benen, ta karaso ta zauna a jikin mahaifin nata yadda ta saba duk girman ta, kai ka ce yarinyar goye ce a yadda take masa magana cikin shagwaba. Daddy, saboda Allah ba zaka daina kira na da sunan tsofaffi ba ko, bana son wannan Tafisun da kake kira na da shi, kullum sai na gaya maka ka bari bana so, amma ba dama ka ga na yi ado sai ka sake kira na da Tafisu-Tafisu. Amani ta fada cikin zumburo baki, tana kallon takardun da ya kammala sakawa hannu, sakamakon ganin sunanta baro-baro a kan takardar shaidar mallakar boutique na kayan sanyawa na mata mai suna AMANI COLLECTION. In bata manta ba tun shekarar data gabata Daddy yake shirye-shiryen bude mata boutique din nan, wato sai yanzu Allah yasa aka kammala kenan. Alhaji ya ce ba sunan da ya dace da ke irin Tafisu, saboda ai kin fi sun ne da gaske, ina nufin kin fi tsararrakin ki gata, kin fi sauran yaya gatan Uba, kin fi su komai tunda kina da Uba iri na, wanda ke tsaye a kan duk abinda kike so, da son tsaya miki kan duk mai son shiga hancin ki. Ya fada babu wasa a maganar sa, ita ta san Daddy yana nufin abinda yake fadi, a shirye yake ya tsaya mata a kan kowa da komai. Shi yasa itama bata hada kaunar sa da ta kowa a rayuwar ta. Hon. Usman Ya mika mata takardun yana fadin amshi ki duba Tafisu. Boutique din ki da na dade da yi miki alkawarin bude miki a nan Katsina ya kammala, yana nan a jerin shagunan Goruba Road, gobe sai kuje da MUKHY ki gani, idan da abinda bai yi ba, ko baa kawo ba, ko zaa canza cikin kayan da kika bada list aka yi odar su, sai ki fada masa, in ya so sai a kara yin sabuwar order, don yana da wata tafiyar dama nan da watanni biyu zuwa Mexico, ina saka ran zai shigo min da wasu samfurin marbles, sai ya karo miki abunda babu din. In yaso sai ku je tare ki gani, kina dubawa kina fada masa yana rubuta min komai a tsanake. Ai kuwa nan da nan fuskar Amani ta yi kicin-kicin, ta zama kamar hadarin da ya nausa ya yi gabas, ta yi mugun bata rai kamar bata taba fara a rayuwar ta ba, ta kirne kyakkyawar fuskar nan tata ta wani irin yamutse ta, fuskar ta a wannan lokacin sai ta koma masa exactly ta Jalan, wato mahaifiyar ta, idan kiyayyar ta ta motsa a kan sa; wata kwayar mace guda daya da ya taba so a rayuwar sa, kuma daga kan ta bai kara son kowacce mace ba, yanzun da Amani tayi hakan sai ya ga ta rikide ta koma masa Jalan har sai da gaban sa ya fadi sosai. Yanayin ta a irin wannan lokacin yafi kama da na yayan nan da baa kwaba, baa hantara, wadanda saidai iyayen su su bi abinda suke so ko basa so, fadi take cikin shagwaba, hassala da zumburo baki. Allah ya tsare ni hada hanya da shi, Allah ya raba gatari da saran kuka, shin Daddy sau nawa zan gaya maka ka manta ne? Magana ta gaskiya ka daina hada sabga ta da ta wannan mai cunkusashshiyar fuskar da halin sumumu-kasau din. Ina dalili mutum kullum yana faman kirnewa mutane fuska kamar malaikan daukan rai, alhalin da bazar su yake rawa? Mutum dan siriri da shi sai kafirin girman kai da bakin hali kamar na mutanen farko. Daddy yayi kasa da murya duk da yana son yin dariya amma ya hadiye, saboda yadda ta fitittike tana furzar da maganar zaka san an tabo fushin Tafisu, cikin lallashin yar tasa yake cewa. Uwa ta. Kullum ina gaya miki ki daina damuwa da yanayin fuskar Mukhtar cikin shaanin kasuwancin mu ko muamalar mu ta yau da kullum da shi, kowa da kika gani a rayuwa, yana da damuwa, mai yuwuwa damuwa ce a kasan ran sa take bayyana a kan fuskar sa, yanayin walwalar sa ko rashin ta ni ba zai shafi alaqa ta da shi ba, o neman kobo na because its obvious I cant do without him (a fili yake ban iya rayuwa sai tare da shi). Duk yadda yanayin halittar sa yake zan iya going da shi a haka, haka kema nake so ki fara, saboda babu mai iya yi min hidimar da yake yi min da jiki da kwakwalwa da lafiyar sa da zuciyar sa gabadaya hidimtawa dukiyata yake, haka Allah ya yi shi da rashin walwala, ba ke kadai yake yi mawa ba Tafisu. Kowa ma! Ki je office din mu ki gani, zan iya rantse miki ba wanda ya taba ganin dariyar sa. Kuma banda abin ki Tafisu, ina ruwan ki da faraar sa ko rashin ta? Amfanin da yake yi min, da rikon amanar sa a kan dukiya ta zaki duba, kafin a samu mai amanar sa da gudun duniyar sa da rashin zalama akan KUDI, zaa jima Amani. Na sha gwada Mukhtar ta hanyoyi masu tarin yawa da tawa hikimar da Allah ya bani ta testing mutane, amma ban taba kama shi da wani hali na son cuta min, ko yi min almundahana, ko munafurci ba. Hasalima amanar sa ce ta hada ni da shi ta hada wannan bond din mai karfi tsakani na da shi. Wanda ya wucde na ubangida da yaron sa nake masa kallon dan ciki na. A baya in kin tuna maaikata nawa nayi kafun shi, cikin su babu wanda bai cuce ni ba in one way or the other. Ban taba samun matashi nagartacce kamar sa ba, kuma kafin a samu yaro nagari irin wannan a zamanin nan abu ne mai wuya Tafisu. Inada dalilai na a kan son yaron nan, da bazaki fahimta ba. Ai ba komai yasa kika ga na jure masa yana bata miki rai da halayen sa ba, sai don in muka sallame shi kamar yadda kike so ba zamu taba maida asarar rashin sa ba, akwai maaikatan da kai kake amfana da su, ba su suke amfana da kai ba, ko me zaka biya sub aka iya biyan su. Ki saka Moukhtar Diffa a cikin jerin irin su. Saidai in ke zaki dinga yimin ayyukan da yake yi min din idan kika takura na sallame shi, which is impossible. A matsayin ki na mace ba zaki iya abinda Mukhtar yake yi min ba, irin su yawon kasashen ketare shigo da kaya da handling kamfani bakidaya, banda sauran wahalhalun da yake yi min (personally) a cikin gida, a kan dan albashin da bai taka kara ya karya ba, kuma cikin amana, girmamawa da tsantseni. Ga ilmin kasuwancin Allah ya bashi, ga kwakwalwa kamar kwamfuta, duk wata hanya da kika sani da zata maida min kobo ya koma dari cikin shekarun nan da suka gabata ina tabbatar miki daga Mukhtar ne nake samun Theory, tun zuwan sa gare ni ban san faduwa ba sai dai riba. Ya numfasa sannan ya dubi Amani wadda ke sauraron sa da kunne daya don kuwa hankalin ta na kan wayar hannun ta, bai damu ba don ya san tana jin sa, ya cigaba da fada mata cewa. Duk wata hanyar samun riba mai tsafta da kike gani yanzu a kamfanin nan shi ke kawo min ita. One impressive thing about Mukhy, baya taba waiwaye da cewa ina kwarar sa da dan albashin dana ke bashi kowanne wata, amma wallahi bai taba korafi ba, dan kuwa albashin dana ke biyan sa ko kusa bai kai kimar yawan ayyukan da yake min ba, da abinda yake nemo min, in aka yi laakari da cewa, ya mallakawa dukiya ta lokutan rayuwar sa baki daya, da kuma tarin fasahar ilmin kasuwanci dake cikin kan sa. Ko iyayen sa bai taba ziyarta ba tun zuwan sa hannu na. Kullum na yi masa maganar zuwa gida cewa yake Alhaji in na tafi wahala zaka sha, don ba lallai a bar ni in dawo ba. Kin san akwai wasu jinsin mutane da sam-sam basu san wani abu wai shi jin dadin duniya da da shagaltuwa da kyale-kyalen ta ba, irin wadannan mutanen su sai dai su taimakawa wani ya ji dadin shi kadai, ko ya samu duniyar shi kadai ya ji dadin, ba tare da sun raina dan abinda zai basu ba, to ina tabbatar miki Moukhtar na cikin su. Amani ta mike don zancen Mukhtar dinnan wanda ta laqabawa suna bare ka fi dan gida ya fara isar ta, ya gundure ta. Ta kuma san in ba ta bar wajen ba Daddy ba gajiya zai yi da bata labarin kirkin Mukhtar ba. Daddy ba zai sa comma ba bazai saka full stop ba kuma bazai gaji ba. Sai idan baka yi zancen Muktar Diffa a gaban Hon. Usman Faskari ba. Yanzun nan zaka soma jin nassi-nassi, maudhuI maudhui na kabakin alheri iri-iri daga bakin Alhajin a kan sa. Ta ce, Daddy, zancen ka ya shiga ta hagu, ya fita ta dama, ko me zaka ce a kan wannan yaron ni kam bai yi min ba, na tsani mutum mai iko, mai fadin rai da jiji da kai, alhalin shi din ba kowan kowa ba. Ta soma taka stairs don komawa dakin ta kada Daddy ya cigaba da gaya mata abinda ba shiga kan ta yake yi ba. Alhaji Usman ya yi murmushi, ko yaushe Amani zata fahimci banbancin human personality? kowa yadda Allah ya halicce shi ta fuskar personality, gashi har digiri ta yi a kan International Relation amma har yau ta kasa gane personality na halittar dan adam baya taba zuwa daya, wanda bai da alaqa da facial expression nasu, yace zo nan Tafisu, ya zaki tafi baki duba takardun Boutique din ba? Amani ta ce ba tare da ta tsaya ba Daddy in komai yayi maka, nima ya yi min, zan dauki maaikata da zasu kula da shagon mutum uku cikin yayan dan uwan ka na Faskari, da wanda ka ce tare aka shayar damu Kamilu yake ko Kamalu? Ka bar su a kauye suna noma da kiwo cikin wahala ka kama bare ka rike da daraja. Ni bani da lokacin zuwa wani boutique, ni dai in ji alert na shigowa kullum a ka yi ciniki, in sayi abubuwan da nake so shikenan. Cikin sauri Alhaji ya katse ta. Babu wasu yayan dangi da zaki dauka aiki a shagon nan kin ji na gaya miki, su zo su yi min rubdugu a kan dukiya ta da basu taya ni tarawa ba, in da na biye musu da hidimdumun su, da basa karewa, da yau ban tara abinda na tara miki ba. Ki dauki inyamurai da suka karanci kasuwaci suka kware da kula da shago su kula miki da shagon karkashin kulawar Mukhtar ba gayyar yan kauye ba, ko ki bar shi ya kawo maaikatan da suka dace da kan sa, don na san ba zai kawo na banza ba, ko wadanda basu gogu da harkar ba, ko marasa amana da zasu yi miki almundahana. Haushi da takaici ya kara kama Amani, na yadda komai na mahaifin ta sai ya dangana shi da wannan Mukhtar din yake samun aminci a zuciyar sa, wannan wane irin abu ne? Anya haka farin baabzinen nan ya bar mata Uban ta? Shi kadai ne mai amana a duniya a wurin Daddy, kamar wani dan sa na cikin sa, ga samari nan fal jinin sa yayan wan sa baya taimaka musu da komai, suna kauye suna gararramba, wau sun yi karatu babu aikin yi, kai bata taba jin tana kishin wani dake tare da mahaifin ta irin Mukhtar dinnan ba, wai har yafi yarda da shi a kan yayan dan uwan sa? Wadanda lomar abinci kullum sai sun fita sun nemo a kasuwannin kauye, wasu cikin su da yawa sun yi karatu mai zurfi musamman Kamilu, amma babu aikin yi, alhalin suna da kanin Uba mai wadata da gwamnati a hannu irin sa a kasar nan, amma gashi yana fadin a nemo inyamurai wadanda ba lallai su kasance musulmai bane a basu aikin yi a karkashin sa, su yan uwan sa a bar su cikin wahala, karkashin kulawar wani bare, wanda yafi jinin sa matsayi a wurin sa da ko asalin sa bai sani ba. Tana ganin tsayawa yi wa Daddy gyara a kan ire-iren kuskuren da yake tafkawa bata lokaci ne don ba dauka zai yi ba, ba kuma denawa zai yi ba tunda rowa, mammako, rashin yarda da wani ya amfana da shi, da rashin son nasa ya rabe shi halin sa ne zaunanne da ta dade da fahimta tunda ta soma hankali. Ita kuma duk da halin ta na raina ajawalin kowa saboda iko da mukamin data rayu cikin sa, da ganin kowa bai isa ba, Allah ya yi ta mutum ce mai yawan kyauta, da matukar son yan uwan mahaifin ta na kauye duk da talaucin su, tunda bata san na mahaifiyar ta ba. Wani abu mai kyau da zaa iya cirewa a halayen Amani shi ne abin hannun ta baya rufe mata ido sam, ke dai bar ta da facaka da kudi wajen kwalliya mai tsada da gasar hawa motar yayi. Ai kawai Daddy ka ce shi ka budewa boutique din ba ni ba, tunda shine mai ruwa da tsaki wajen gudanarwar sa gabadaya, bayan shi ya je Mexico ya shigo da komai, sai kawai a canzawa boutique din suna zuwa Mukhtar Collection. Amani ta fada cikin bacin rai ko shagube zaa ce? Kamar ba da mahaifin ta take magana ba. Tana mai tattaka matattakala don komawa dakin ta. Murmushi Alhajin ya yi, maimakon ran sa ya baci ya kwabeta a kan rashin kunyar da ta yi masa, amma sai ya buge da rubuta mata text message din lallashi da wayar hannun sa. Zuwa shekaru kadan a gaba, idan Allah ya raya mu, Tafisu zaki zo ki gode min, for making MUKHTAR DIFFA your Business Mentor, ranar da kika ga Mukhtar ya maida dan Boutique din nan naki ya rubanya zuwa PLAZA guda. Domin Allah SWA ya huwwace da ya halicce shi yayi masa hikimar maida taro ya koma sisi. Trust him my daughter, work with him for a while, give him a try as your business mentor!. **** **** **** Sai da Amani ta zo kwanciya ta ga wannan sakon na Daddy, zumburo baki tayi tana tunanin mutumin nan ba haka ya bar mahaifin ta ba. Yardar ta isa. Kaunar ta yi yawa. Ko shi ya haife shi sai haka. Iya shaidar arziki da zai iya masa kenan. Daddyn ta da duk wanda ta nuna bata raayi nan take zai yanke alaqa da shi ko waye kuwa, ko da zai kasance jinin sa ne, amma banda MUKHTAR DIFFA. Farin baabzinen data taso ta gani tare da mahaifin ta, yana rayuwa karkashin sa matsayin mataimakin sa, kuma yana tare da shi kullum a gida ko ofis. Dan asalin garin Diffa, ta kasar Nijar, wanda ko asalin sa basu sani ba har shi Daddyn kuwa, banda sunan garin sa da yake amfani da shi a gaban sunan sa DIFFA. Daddy dai ya dauke shi aiki ne da farko a dalilin haduwar jini kawai, ta sanadin wani halin amanar sa da ya bayyana gare shi, rashin zalama da rashin kwadayin abun duniya, in kana da wadannan halayen, tabbas zaka zauna lafiya da Hon. Usman Faskari tunda shi bay a so wani ya more shi ko yayi arziki da shi, sannan ga kyawawan kwalayen ilmi (educational qualifications) din sa masu nagarta, domin Mukhtar Diffa, ya fitar da kwalayen boko biyu masu darajar farko (B. Sc & M. Sc in Business Administration) daga jamiar Paris wato (Paris Saclay University). ***** ***** **** FARKON HADUWAR HON. USMAN DA MUKHTAR DIFFA Asalin haduwar su da Alh. Usman Faskari a wata tafiya da ya yi birnin Paris ne, lokacin da ya je shigo da wasu kayan assasa kamfanin sa na farko wasu shekaru kusan goma a baya. Cikin tsautsayi Alhajin ya yarda wallet din sa a cikin jirgin kasa, wanda ke dauke da dukkan katunan sa na banki daban-daban (credit cards), fasfo, ID cards, da duk wasu muhimman abubuwa da ake sakawa a cikin wallet. Bayan ya sauka daga jirgin kasan, ya shiga motar da zata maida shi masaukin sa ne ya lura babu wallet din sa a tare da shi, wadda ba katunan bankin sa kadai ta kunsa ba, akwai kudade (Euros) masu yawan gaske a ciki. Alhaji da kudi, ko sadakar dubu guda baya iya yi in ba ta hanyar siyasa ba. Yayi salati a gigice yana kara laluba aljihun sa yana gayawa direban da dauko shi su koma, ya yar da abubuwa masu muhimmanci su koma tashar jirgin kasa. Komawar da bata haifar da komai ba sai bata lokaci, domin train din tuni ya dade da barin Paris, ya nausa wata jihar dake gaba da Paris wai ita Bourdeaux. Ya dai bar report a ofishin jirgin kasan da wajen yan sanda. Hon. Ya shiga damuwa ba yar kadan ba a daren, domin a cikin wallet dinnan kusan duka sirrin rayuwar sa ne gabadaya. Ga tsabar kudaden da ke ciki wadanda ya fitar dasu daga banki ne da zummar zai yi amfani dasu wajen accommodation na tsayin zaman sa a kasar da cuku-cukun clearance na kayan sa har zuwa komawar sa gida. Damuwar sa tana karuwa in ya tuna identity cards din sa daban-daban na siyasa da na kasuwanci duk a cikin wallet din sa. Alhaji kamar ya zare. Amma ko minti goma bai yi da shiga masaukin sa ba ya samu kira a wayar sa, a lokacin yana kokarin revoking katunan sa na banki don kada a samu damar yashe shi. Duk da iya abinda ya mallaka ba wai a bankuna suka kare ba, yana da hannayen jari da kadarori masu yawa da kamfanin sa na FASKARI INVESTMENT LTD. Yana dagawa ya ji an yi masa sallama da hausar da bata fita yadda ya kamata, ko dai Francaise ya rinjayeta ko harshen Espanol, ko kuma abzinanci. Cikin ukun dai. Duk da haka a kan gane hausar idan aka saurara, kasancewar cikin nutsuwa mai kiran yake yin ta. Ina Magana da mai wannan layin ne? In sha Allahu kana tare da mai wannan layin Engnr. Othman Fass. Ya kasa furta sauran da accent din sa. Amma Alhajin ya gane yana son cewa Faskari ne. Sai ya karasa masa da cewa Eh nine Engnr. Usman Faskari. Alhmdulillah, ina zan sameka in baka wallet din ka yanzu? Na tsince ta a jirgin kasan da ya taho daga Bordeaux zuwa Paris. Na samu wannan lambar a jikin daya daga cikin identity cards din ka. Alhaji a zaune yake amma bai san lokacin da ya mike tsaye ba yana hamdala, yana hailala, ya gaya masa sunan Hotel din da yake, yace ya kira shi in ya zo reception. Cikin daren baa kwana ba saurayin ya zo hotel din, suka hadu da Alhajin. Ya dauko wallet din sa ya bashi. Ya tsaya har Alhajin ya bude ya duba sosai ya kuma kirga kudin sa ya ga suna nan cif, a jere yadda ya jera su, ko kwarzane basu yi ba, ya tabbatar ba abinda aka cire. Babban abun mamakin Alhajin, kudin sa na nan yadda ya bar su ko guda daya baa cire ba. Har yaron ya juya ya tafi, Alhaji Usman ya kasa daure mamakin sa. Sai ya bi bayan sa. Ganin cewa dan Afrika ne ga hausa kadan ya iya, duk da dai alamu sun nuna ba bahaushe bane Baabzine ko dai dan kasar Nijar ne, wato irin matasan nan na Nijar wadanda ke tahowa karatun boko kasar goyon su wato Faransa, daga Jamhuriyyar Nijar, kasancewar kasar Faransa ce ta goya kasar Nijar. Amanar yaron, exceptional personality, da kuma bravity din sa kai har ma da character da attitude din sa sun yi matukar impressing din sa. Alhaji Usman ya bi bayan sa da sauri yana fadin; Ya ka Da na, dakata don Allah, yaya sunan ka? Cikin halin sauri-sauri don kada ya rasa jirgin kasan komawainda ya fito, da koin kula irin nasa, kuma ba tare da ya juyo ba, cikin rashin sakin fuska da rashin annuri ya ce da Alhaji Usman, suna na Mukhtar. Daure ka tsaya ka ji Da na Mukhtar in maka godiya don Allah. Amma bai tsaya din ba sai tafiya yake, Alhajin kuma bai fasa bin bayan sa ba, yana rokon sa Allah Annabi ya tsaya ya bashi tukuici. Ya dan tsaya har Alhajin ya cimmasa, juyin duniya Hon. Usman yayi a kan ya karbi kudin dake cikin wallet din bakidaya don farin cikin taimakon da yayi masa, amma kyakkyawan matashin baabzinen ya ki, duk kuwa da cewa a lokacin neman kudin jirgin da zai koma Hong-Kong din China yake yi, saboda ya nemi wani aikin a can, kasancewar interview din da ya yi ta neman aiki da wani kamfanin turaruka a nan Paris din bayan kammala karatun sa, bai yi nasara ba. To na ji bazaka karba ba, na kuma gode da karamcin ka, na kuma yabawa nagartar ka, samun irin ka a cikin matasa is a blessing. Ka cigaba da wannan halin na taimako da amana zai kai ka har inda baka taba zato ba. Na sha gwada samari kamar ka, ban samu wanda ya san amana ba. Ni kuma mutum ne mai son mutane masu amana. Don ta yi karanci a wannan zamanin. Still fuska ba walwala ya ce na gode. Sannan ya juya da sassarfa ya bar reception din. Tafiyar sa kadai abin a bi da kallo ne, saboda taku yake da sassarfa, amma kamar na kasaita. Yaron ya tsaya masa a rai har wayewar gari. Don haka washegari ya kira shi da layin da ya kira shi jiya, suka gaisa. Alhaji Othman ne ko? Ya fada da kakkaurar muryar sa bayan sun gaisa. Ni ne Da na Mukhtar, ya ka je gida? Alhamdulillah ya bashi amsa. In ba damuwa ina so in zo in gan ka kafin na wuce gida Nijeriya gobe. Yace babu mishkilah, Allah ya kaimu, amma ka bari ni zan zo in same ka kasancewar daga Clermont-Ferrand City zan taho, bana so ka sha wahala har nan Baba. Murmushi Alhajin yayi yace na gode Da na sai ka zo, don Allah ina jiran ka. Lokacin da yayi masa waya yace ya taso a train daga Clermont Ferrand, Alhajin yasa aka shirya abinci na alfarma a dakin sa na hotel, dama kuma yayi sayayya ta sutturu masu tsada, agogon maza na (Swatch) da takalma da turaruka ga Mukhtar din, da niyyar ya je ya kai masa har gida a matsayin godiya, tunda ya ki karbar makudan kudin da ya barma shin. Wannan ya nuna ba karamar alfarma da haduwar jini Mukhtar ya samu a gun Hon. Usman ba. Kasancewar shi mutum ne mai tsananin kankamo, bi maana, ba kowa ke cin arzikin sa ba bayan tilon yar sa AMANI sai wanda rabon sa ya rantse, mutum ne mai rowa kwarai. Tsakanin sa da duk wani maaikacin sa albashi kadai, babu ihsani. Amma shi wannan yaron ya nuna masa akwai sauran masu amana da rashin kwadayi a duniya, sabanin daukar da yake yiwa kowa, cewa mutanen yanzu duk kwadayayyu ne masu neman gasashshen tsuntsu daga sama, shi yasa yake so ko yaya ya gode masa. Don yana yawan gaya wa Amani yanzu duk mutanen duniya makwadaita ne, shi yasa suke cewa ya fiya rowa, ya dauki kowa a irin dabiar da yake kai, wato son ci daga haram ko halak kamar sa. Sannan a ganin sa mutaen yanzu basa ganin kudi su kyale balle irin wadannan Euros dake dankare cikin wallet din sa. Ko a satin da wuce ya kori maaikata biyar daga kamfanin sa, da ya kama su da yi masa sama da fadi da wasu yan kalilan kudade. Bayan kuma kudaden ma bata suka yi cikin lissafi amma a hannun su. Ya iso kofar dakin ya danna kararrawa, Alhajin ya bude masa yana lale marhabin da shi, sanye yake da farar shirt an rubuta Fred Perry da bakin wandon CK Jeans. Dogon matashi, kakkarfa, farin baabzinen usli, mai wani irin sassanyan kyau, hancin sa kamar an sa ruler an ja masa shi an saka masa shi a tsakanin idanun sa, komai na halittar sa ya zauna a inda Allah Subhana ya ajiye shi, kamar shi ya zaba wa kan sa zati da kamala, ga wata lallausar suma da ta taru a saman goshin sa ta abzinawan usli, har ta dan kalmaso a kan goshin sa, ta maida shi tamkar Baindiyen nan mai farin jini (Shahrukh Khan). Alhaji ya bashi kujera ya zauna suka gaisa sannan ya nade hannun riga yace ya sauko kasa su ci abinci tare. Ko kadan rashin walwalar yaron da shan kamshin sa baya damun sa. Kamar ba zai ci ba, amma ganin Alhajin da an sa yayi serving din su a plate guda, sai ya kasa tankwabe kulawar wannan dattijon, wanda ke ta haba-haba da shi cike da kauna, sai ya sauko kasa ya kalmashe kafafun sa, suka fara cin abincin a plate daya. Suna ci, Alhaji Usman na hilatar shi da hira cikin dabara irin ta manya, har yaji abinda yake son ji, wato inda ya fito da kuma abinda ya kawo shi birnin Paris. Nan yake gaya masa cewa daga wani yanki na jamhuriyyar Niger ya zo nan, ana kiran yankin nasu Diffa Region, yau watan sa uku da kammala karatun digirin sa na biyu a nan kasar, daga jamiar Paris Saclay University. Ya gayawa Alhajin tun baya kammala masters din sa ya nemi ayyuka na wucin gadi har uku bai samu ba, kasancewar shi ba dan kasa ba, don haka zai koma Hong-Kong yanzu ya nema a can. An ce suna bada ayyuka sosai ga yan Afrika, shi neman na kan sa ya fito, ba yanzu zai koma gida ba. Kasancewar a lokacin kasar Nijar na fama da matsalar durkushewar tattalin arziki babu ayyukan yi ga matasa masu ilmi kamar sa a Nijar. Alhaji Usman ya tambaye shi ko me ya karanta da level din karatun sa duk ya gaya masa, cewa daga digirin sa har master first class ne. Alhaji Usman became highly impressed da jin hakan, sai kawai Alhajin ya ce, ina ma za ka iya zaman kasar Najeriya, da mun tafi tare na baka ragamar kamfani na, in ya so sai ka dinga zuwa gida kana ganin iyayen ka lokaci-lokaci, saboda ni din bani da Da namiji, sai mace tilo, ina neman mataimaki a kan harkoki na wanda zan iya ja a jiki na in sakar masa ragamar kamfani na. Na kuma yaba da halayen ka. Mukhtar ya ce ban taba zuwa kasar Najeriya ba Baba, amma ina jin labarin ta, kuma ina son aikin yi kwakkwara wand azan tsaya a kan sa da kafafu na, musamman wanda ya shafi kasuwancin kamfani, a nan buga-buga kawai nake babu permanent job ga wadanda ba yan kasa ba, ni kuma ba yanzu zan koma gida ba. Don haka zan bi ka in gwada in gani, idan naji dadin kasar, zan zauna, don bani da abun yi ko na koma Diffa. Kuma babu wanda ke jira na a can. Cikin mamaki Alhaji Usman ya ce ina iyayen ka? Nan da nan fuskar Mukhtar din ta wani irin sauya, ta rine ta yi jajir abin ki da farin mutum. Wani yanayi ya shiga na kokawa da numfashin sa da Alhaji Usman ya kasa karanta. Shi da kan sa ya baiwa kan sa amsa da basa raye kawai. Sai ya shiga yi musu addua ba tare da shi Mukhtar din ya ce masa komai a kan su ba. Amana ce ta hada mu, naji ina kaunar ka kamar dan da na haifa saboda halayen ka da suka burge ni, ina fatan wannan amanar tayi ta yado da yabanya a tarayyar mu. **** **** **** Mafarin zuwan Mukhtar Diffa kenan gidan su Amani, tarayyar da ta zamewa Alhaji Usman sanadin alkhairori masu yawa. Bai sakar ma Mukhtar ayyukan sa na sirri ba sai da ya cigaba da gwada shi iyakar gwadawa ta hanyar yawan aiken shi kai kudade banki, domin da farko kamfani ya kai shi, ya bashi ofis, a matsayin Chief Operating Officer (COO) ya kuma bashi gidan zama a kusa da gidan sa wanda babu nisa da kamfanin Faskari Investment cikin birnin Katsinan Dikko. Excellent Performance din da Mukhtar Diffa ya soma nunawa daga zuwan sa ya razana kowa, domin yana zuwa ya canza akalar komai zuwa na zamani, ya kawo sababbin innovations masu tafiya da zamani na yadda zaa bunkasa hanyoyin da kamfanin ke amfani da su wajen shigo da kayayyakin da kamfanin ke shigo dasu Najeriya daga Faransa da sauran kasashen Europe irin Mexico. Har ila yau, COO Mukhtar Diffa, ya kawo hanyoyin samun cigaba ga maaikata ta hanyar karawa maaikata sani da dabarun kasuwanci a zamanance, ta hanyar shirya (capacity building programs) iri-iri da yake shiryawa a kai-a kai ga kananan maaikatan Faskari. Ya tsame masu lalaci daga ciki ya kai su kasa, ya maye gurbin su da masu hobbasar cikin su. Ya kuma takura wa Alhaji a kan kara albashi da welfare din maaikata da yake kankamewa. Kan ka ce meye wannan hakan ya sayo ma Mukhtar farin jini gun kananan maaikata, ya kuma kara musu himma da maida hankali, sannan ya kawo conducive working atmosphere ga dukkan maaikatan Faskari Investment. Shi ba hausa ce ta ishe shi ba, amma da zuwan sa Katsina ba jimawa sabida cudanya da hausawa da maaikata a company, da kuma shi kan sa Alhajin da ke masa magana kullum da hausa don ya kware, a sannu bakin sa ya fara iyawa sosai, a hankali a hankali kuma accent dinsa na Francaise da abzinanci ya fara barin bakin sa sabida rashin abokin yi. Mukhtar Diffa, ya soma rikidewa yana koma wa zallan Ba-katsine, in ka cire nannadaddiyar sumar kansa da launin jar fatar sa da ke fallasa shi, matsayin kyakkyawan Baabzinen mutum dan hutu kuma dan zamani, hatta hausar bakin sa kafin shekara guda ta koma ta Katsinawa. ****** ****** ****** Sanda Alhaji Usman ya kawo shi gidan tana makarantar kwana aji daya a Ulul Albaab, ya dade a gidan ma bata san da shi ba, a lokacin Alhaji bai mayar da kamfanin da sunan ta ba, so ko ta zo hutu ba wani haduwa suke ba ko a ce bata san shi ba ko da ta hange shi, don bai cika zuwa gidan ba a Kamfani yake rayuwar sa, daga gida sai ofis, Mukhtar ko aboki bai da shi, sai Malam Tajuddeen mai gadin gidan Alhajin. Ranar da ya fara ganin ta wata asabar ce, direba ya dauko ta daga makaranta yana cikin motar Alhaji a harabar gidan yana jiran fitowar Alhajin zasu wuce duba wata gona da Alhajin ya saya a garin Bindawa, ji yayi yarinyar wadda fitowar ta Kenan daga mota tana zagin direban ta cikin daga murya wai yayi parking ba a kofar shifa falo ba, yana nufin da kafar ta zata taka har kofar falon ko yaya? Ga zakin murya cau ga zare ido kamar tana yi wa dan ta fada, shi kuma Malam Sirajo yah au rawar jiki yana bata hakuri tare da cewa Mukhy ne yayi parking a kofar falon yana jiran fitowar Alhaji, amma duk da yadda ya kwantar da kai ya bata hakuri data fito sai da ta tsarta masa miyau a fuska ta ce donkey, monkey, idiot! Mukhtar na shirin fitowa ya dauke yarinyar nan da mari sai ga Alhaji ya fito hanzari yan cewa yi hakuri Mukhy, ina jiran isowar TAFISU ne kada ta dawo bana nan an tafi dauko ta yana daga ido kuma ya gan ta cikin uiform din ta ta doso shi da gudu, Alhaji ya bude hannu yana Oyoyo! Da Tafisu na. Ta rungume Alhaji duk da ta fara kirgen dangi ma a lokacin suka yi ta murnar su kafin Alhaji ya ce mata ta shiga ciki, ya sa an shirya mata komai, gobe sabuwar matar da auro zata tare bazatayi kadaici ba wannan hutun. Direban data tsartawa miyau shi ya dauko jakar ta ya shigar mata da ita bayan yasa hankici ya goge fuskar sa, a ranar kuma ya ajiye aiki a gidan su Amani. Mukhy da Alhaji suka kama hanyar Bindawa, Mukhtar ke tukin Alhaji na gefen sa yana bashi labarin itace tilon yar sa Amani da yake bashi labarin tana makarantar kwana, ya ce ka gan ta Tafisu akwai rigima ga kyuya, nikadai nake iya mata. Ai komai nata na uwarta ta debo, yadda Jalan haka Tafisu take, kullum ina godewa Allah da bata debo kannina ba Mukhy dai tuki yake bai ce komai ba, amma a ran sa ya ce ai gara da kamannin naka ta debo, da wannan halin nata na rashin kunya, yar karama da ita da raina na sama da ita. Shi bai taba ganin rashin tarbiyya irin na yau ba. Imagine in shi ta yi wa abinda ta yiwa Malam Sirajo, wallahi sai ya mare ta, kuma daga ranar ko nawa ake biyan shi bai kara aiki a gidan su. Basu kuma kara haduwa ba har ta koma hutu, don shi ba wani zuwa gidan yake ba sosai, idan ba Alhaji ya neme shi a gida ba, duk harkokin su a kamfani suke yin su. Ya zama cewa in tazo hutu sau tari ya kan gan ta ko daga nesa ne, a harabar gidan ko a falon Alhaji, itama ta kan hango shi daga can saman balcony na saman benen ta, ko a falon Alhaji in suna ganawa ta sirri, wani lokacin ta kan shigo, in ta gan shi sai ta koma, bata taba gaishe shi ko yi masa magana ba, shi dai ko gaisuwa bata hada su tun da ya gane bata da kwalli a idon ta, sannan Alhaji baya kwabar ta, ta raina duk wani maaikaci na gidan, aka ce hanyar lafiya a bi ta da shekara, sosai ya kama kan sa, ko ya ganta zai bar wuri shima, don ya san zuciyar sa ba irin ta sauran maaikatan Alhaji bace, da suke iya shanye duk wani rainin ta da wulakancin ta saboda Alhaji. A haka suka rayu tsayin lokaci a gidan Hon. Usman, ko in ce tsayin shekaru, har Amani ta soma zama budurwa sosai, babu wata sanayya ko wani cordial relationship a tsakanin ta da Mukhy. Tana gama sakandire ba jimawa ta samu gurbi a Jamiar Bauchi, da taimakon Baban Hamida, suka fara karatun su ita da Hamida Hashim Balewa a ATBU, sai rayuwar ta ta koma Bauchi gabadaya, ko an yi musu hutun karshen zango ba koyaushe take zuwa Katsina ba saboda bata shiri da Haj. Laura ko kadan, wato sabuwar amaryar gidan su matar da Alhaji ya auro a lokacin, sai tayi zaman ta gidan su Hamidah sai dai shi Alhaji da kan sa yayi ta zaryar zuwa ganin ta, don harr aba su dambe aka yi kwanaki tuni Alhaji ya yanke shawarar sallamar Haj. Laura don itama kamrar sauran, ta kasa da Amani sabida rashin tarbiyyar ta. A haka Amani ta kammala jamia ta yi hidimar kasa duk a Bauchi din. Daga lokacin ne Alhaji ya maida Faskari Investment ya koma da suna Amani Faskari Investment ya maida hakkin mallakar komai nasa da sunan ta. **** **** **** Ta haura sama inda dakin ta yake tana gaya wa kan ta in har Daddy ya dage lallai sai Mukhtar ne zai taimaka mata wajen gudanar da tafiyar shagon ta, to kuwa zata hakura da shagon. Ita ta san kasuwanci ai ba sai mutum ya karanta shi ba ne zai iya tafiyar da abun sa, karatun ta na International Relation and Diplomacy ya ishe ta komai, kawai Daddy ya bar ta ya ga iyawar ta, ya daina underestimating din ta don tana mace, bata bukatar taimakon Mukhtar a dukkan shaanonin ta. Shi kuma Daddy abun nasa kamar wanda aka camfa, ko aka sihirce, from all indications, baya samun gamsuwa idan ba ya hada shaanin kasuwancin sa kowanne iri ne da Mukhtar din ba. Idan Mukhtar yana tsaye akan abu, ji yake kamar shi da kan sa ne ya tsaya ya kula da abun sa. Tsabar yarda da aminci. Don haka ta san ko me zata fada a yanzu ba zai yi tasiri ba, kowanne irin bore zata yi Daddy ba zai saurare ta ba, in dai a kan kada Mukhtar ya saka mata hannu ne a ragamar Boutique din ta. Tunda shi Ya riga ya yi amanna cewa komai nasa sai Mukhtar ya saka hannu ne zai tafi dai-dai. To ita bata son taimakon nasa a kan komai nata, a bar ta tayi irin tata iyawar da kokarin, a boko-akida irin nata what man can do, a woman can do better. Ta shaki iska cikin fushi sannan ta furzar ta bakin ta. Ba wanda zata gaya wa damuwar ta a kan mutumin nan ya fahimce ta sai Hamida Balewa. Aminiya daya kwal da bata da tamkar ta, duk da nisan gari da ya raba su yanzu, kullum suna tare a waya, hakannan suna ziyartar juna lokaci lokaci su yi kwanaki a gidajen juna, dama an ce garin masoyi ba shi da nisa. Zamantowar Hamida a Bauchi Amani a Katsina bai rage komai na karfin amincin dake tsakanin su ba. Har abinda ba zata iya gaya wa Daddy ba tana iya gaya wa Hamida kasancewar bata da yar uwa mace, musamman matsalar matar sa ta yanzu wato Hajiya Rabi idan ta saka ta gaba. Ta san Hamida mai fadin gaskiya ce a kullum, kuma mai yi wa kowa adalci. Duk da raayin su baya zuwa daya. Amma zata yi adalci tsakanin ta da Daddy a kan mutumin nan, ta kuma bata shawara ta gaskiya na yadda zata yi da zaman sa a gidan su. Wani banbanci dake takanin ta da Hamida shine an ce sai hali ya zo daya ake abota, amma ita Hamida kowa dake tare da su ya san ba halin su daya ba, haduwar jini ce ta mikar da abotar su domin Hamida Hashim, bata da girma kai, bata da dagawa sannan bata raina kowa duk da kasancewar ta diyar tsohon gwamna. Wayar ta ta dauka ta kira Hamida Balewa tana tsaye daga can saman balcony na sassan ta dake saman gidan su. Daga inda take tsaye tana iya hango duk abinda ke faruwa a yalwatacciyar harabar gidan nasu mai cike da korran shuke-shuke. Yaya aka yi mutuniyas? Kwana biyu ban ji duriyar ki ba, halan kin fara shirin tafiya Sierra Leone dinne? Hamida Balewa, ta fada bayan ta daga kiran aminiyar tata. Amani ta yi tsaki tana fadin Hamdy, ba ta wannan nake ba tukunna. Don wanda ke min binciken inda Maman nawa take ta karkashin kasa ya bukaci wasu kudade masu yawa a hannu na, wadanda ban san yadda zan fidda su ba a yanzu haka, ina nufin, ba zan iya fidda su ba tare da shaidanin nan ya ga alert ba, kuma tabbas zai gayawa Daddy a sanda ya gani din, idan kuma ya tambaye ni me nayi dasu bani da amsa don ya sha ce min in na zabi bin Mama na ko neman inda take, to tabbas in manta cewa ya haife ni, zai bar mata ni a kowanne hali na same ta, zai yafe soyayyar da yake yi mun komai girmanta, tunda bai rage ni da komai ba na duka soyayyar UWA da UBA. Actually har gobe ban san me yayi zafi haka tsakanin Daddy da Mama na ba, kuma ina so in sani, sama da komai ina so in ga uwata nima kamar kowa in ji dumin jikin ta tunda dai tana raye. Amani ta soma hawaye tana fadin Hamdy, I want to see my Mum, ko sau daya ne a rayuwa ta, koda a bukka take rayuwa a Sierra Leone din zan je gare ta zan kuma iya zama da ita, ba kuma don Daddy ya min komai ba, ko ya gaza da kulawa da ni ta wani bangaren, ba kuma don bana son cigaba da zama da mahaifi na ba, aah, shaukin soyayyar uwa da ban taba samu ba ke diba na, so nake kawai in gan ta a gefe na, nima in san cewa uwa da uba ne suka haife ni ba Uba namiji shi kadai ba . Hamida ta ce Da yardar Allah zamu je ga Mama bada jimawa ba duk inda take, amma bisa yarda da amincewar Daddy. Amma kamar yaya kike nufi in kika fidda kudi masu yawa daga account dinki Mukhtar din Daddyn ki zai ga alert? Amani ta numfasa tana fadin ba zaki gane ba Hamdy, Daddy na wani irin SMART ne, mutane ne ke ganin yana sangarta ni, yana min duk abinda nake so, baya hada kaunata data kowa haka babu abunda ya kai ni muhimmmanci a gun sa. Eh, hakane da gaske amma kuma bai yarda da sakin rayuwata sakaka in yi abunda na ga dama ba, musamman bayan haduwar sa da shaidanin mataimakin nan nasa, kullum sai kin gan shi da sababbin dabaru na kiyaye dukiyar sa. Zancen dana ke miki yanzu ko me nake so Daddy zai min, amma dole yaron nan ya sani, kuma yana saka ido sosai akai na da abinda nake kashewa kullum ranar Allah ta hanyar wannan fitinannen yaron, mai kwakwalwar huda-huda da ya hada account dina da lambar wayar sa (corporate account). Wallahi Hamdy na tsane shi bana ko son ganin shi, ba don komai ba sai don yadda Daddy ya daukake shi yake girmama shi, yake fifita shi da daukaka shaanin sa a kan kowa a gidan nan yanzu. Karo na farko kenan dana kasa samun abinda nake so a gun Daddy; wato yaki yi min abunda nake so kamar koyaushe na bukaci ya kori maaikacin da bai yi min ba, wannan karon ya nuna min bai iya rayuwa sai da wannan mutumin, ya shiga gabana da yawa a gun Daddy Hamdy, ko asiri yayi masa ni ban sani ba, Im extremely jealous of him!” Hamida ta soma dariya, dariyar da ta kara kular da Amani don ita tsakanin ta da Allah take fada mata damuwar ta, damuwar da tafi kowacce girma yanzu a gun Amani wato zaman MUKHTAR DIFFA tare da mahaifin ta Hon. Usman, Hamida ta hadiye dariyar ta jin Amani na kwafa, tana fadin Amani ki taka a sannu fa, ki bi abin a hankali, you are complaining too much about this guy, Kaman kina exaggerating abun ma, in ban manta ba duk ranar da kika kira ni complain din sa kike fara yi min, baki saka comma baki saka full stop, anya? Baki fa san inda rana zata fadi ba, shaaah! This dislike and hatered you have on him are beyond my understanding (kiyayyar ki a kan sa ta yi yawa har ta wuce fahimta ta) kuma na rasa dalilin ta, ina laifin mai son Baban ka, da taimaka masa kan dukiyar sa da shaanonin kasuwancin sa da zuciya daya irin wannan mutumin, calm, cool and reserve da shi? Ni wallahi ta koina ya yi min, kin ga dai daga nesa kawai kika taba nuna min shi last zuwa na KT, kuma ban ga fuskar sa sosai ba sai bayan sa yana shiga mota, amma ko daga tsayuwar sa da zatin bayan sa kadai mutum ya gani ya san Allah ya ajiye namijin duniya a nan, haibar sa da kamalar sa sun tafi da ni, da duk nutsuwa ta, kyawun sa ya tafi da Imani na na dade ban daina tuna shi ba. Ki ga min mutum kamar shi ya yi kan sa don kyau, ga iya daukar wanka, ga iya dressing, ga jan aji nna karshe, da iya takun tafiya, yana tafiya gib-gib tamkar basarake, ga wani special class (aji na musamman), na kasaitattun maza. Watakila saboda idon ki ya rufe da kishin sa da kiyayyar sa saboda son da Daddy ke masa ne yasa baki hango abubuwan da ni na hango a tare da shi ba.. Babu shiri Amani ta katse wayar ta, bayan ta lailayo ashar ta yarfawa Hamida. Haka kwana ta yi tana tsinewa furucin Hamida da Hamidar kan ta a zuciyar ta. Washegari tun da Amani tayi sallahr asubah bata koma barci ba, ta zauna bisa dardumar sallahr ta tana tunanin yadda zata yi ta fidda wadannan kudade daga corporate account din, wanda Daddy ya bude mata shi ne don ajiyar jarin kasuwancin ta kadai, ya kuma bude shi tare da sunan Mukhtar ne a matsayin Director kuma sakataren ta, sannan kuma mai kaso daya bisa uku na abinda ke cikin asusun, Hon. Usman yayi haka ne kawai ba don da gaske ya mallakawa Mukhtar din wannan kason ba aa, komai na Amani ne, ya yi ne kawai don Mukhtar din ya zama spy din sa a kan duk wani transaction na Amani da kuma sunan wanda ta turawa, ba don komai ba sai don ya san ta da almubazzaranci da saurin mika wuya wa mutane, shikuma ga shi da son abun hannun sa, bai yarda a ci da gumin sa ba. Tun bayan zuwan Mukhtar wajen sa Hon. Usman ya fito da wannan idea din, ta joining account din Amani da Mukhtar a matsayin corporate account na kasuwanci, yardar da ya yi masa mai yawa ce, don ko dan sa na cikin sa ba zai sakarwa sirrikan sa irin yadda ya sakar wa Mukhtar ba, yana jin takaicin almubazzarancin Amani don shi ko wane sisi da kowanne kobo abu mai daraja ne a wurin sa, kashe kudin Amani ya yi yawa, musamman ga dangin sa na Faskari, inda wani abu mai kyau guda daya tak cikin halayen Amani to kyauta ce. Amani tana da hannun kyauta wa na kasa da ita kasancewar bata san zafin kudin ba, abun duniya bai taba rufe mata ido ba kullum hannun ta a mike yake cikin yin kyauta ga wanda Alllah ya tsaga da rabon sa. Wani zubin tana sanin an cuce ta ko an dafketa wajen sayen abu, amma bata damuwa don Alhaji kullum kara tara mata yake. Babbar damuwarta a yanzu tana so ne ta turawa dan sandan cikin dake mata bincike a kan inda Mama Jalan take a kasar Sierra Leone. Dan sandan ya bukaci wadannan makudan kudaden da suka wuce hankali ne ganin yarinyar ta zama desperate a kan neman mahaifiyar ta, kuma ya ga alamar akwai kudin tare da ita sannan bata son shigar da kowa cikin maganar tasu. A karshe Amani ta ga cewa babu mafita fa dole sai Mukhtar ya ga debit alert dinnan, wanda ke nufin sanin Daddy, domin tabbas ne Mukhtar sai ya gayawa Daddy a irin amanar da ke tsakanin su cewa ta fidda miliyoyin kudi don ta san dalilin hadasu a account guda Kenan, don ko sau daya Mukhtar bai taba daukar wani abu a ciki ba. Don haka ta kai azahar a daki tana qulubi, tana bacin rai, ga shi dan sandan cikin wato DSS din da ke mata aikin ya tabbatar mata data tura masa kudin da ya bukatan a take zai turo mata adireshin Maman ta da ke Freetown wato babban birnin Sierra Leone. Kai har ma da lambar wayar ta ya ce duk ya samo. Amma sai ta fara biyan sa wadannan kudaden da ya kayyade mata tukunna. **** **** **** Abu daya da ta san bazata taba iyawa ba shine rokon Mukhtar alfarma, don tana ganin bai yi wannan isar a idanun ta ba. Ba don haka ba da ta roke shi ya yi mata alfarma ya rufa mata asiri sau daya a rayuwa, kada ya gawa Daddynta ta fidda 5 millions ta baiwa wani a boye domin ya nemo mata Innar ta. Idan Daddy yasa ta gaba da tambaya da kwakkwafi (query) tabbas zai gano shirin da ta ke yi ta karkashin kasa na son ziyartar mahaifiyar ta a boye. Tana cikin wannan tunanin wayar ta ta hau ruri. Ganin sunan Daddy a daidai lokacin da take tunanin sa sai da gaban ta ya fadi. Ta amsa a sanyaye. My Daddy! Daga can barin sa Hon. Usman ya ce Tafisu ki sauko falo na yanzun nan. Iya abinda ya fada kenan ya kashe wayar sa. Ta zura siraran kafafun ta cikin silifas din bakin gado sannan ta fita ba tare da ta canza kayan barci farare samfurin Calvin Klien da ke jikin ta ba. Falon Alhaji Hon. Usman Faskari, wani irin makeken falo ne wanda sai da ya ci saitin kujeru uku iri daban-daban saboda girman sa. Ya kawatu da kayan alatu da air condition ta tsaitsaye a kowacce kusurwa, komai na jin dadin rayuwa yaji a wannan falo mai kama da palace, din wani gwamnan kai ka ce babu ranar mutuwa a zuciyar mamallakin sa. Amani ta shiga tako matattakala tana saukowa daga saman benen ta tana tafiyar nan tata tamkar bata so. Kallo daya Mukhtar da ke zaune gefen Alhaji ya iya yi mata a lokacin tana saukowa daga stairs din, cikin takun nan nata tamkar na macen Dawisu mai ji da kasaita, ya yi maza ya sunkuyar da kai cikin jin faduwar gaba don bai taba yi mata kyakkyawan kallo ba, yau din ma kamar kullum, a sace ya kalle ta, amma ya ga surar jikin ta sosai a cikin kayan barcin, sai ya samu kan sa cikin jin takaicin wadannan sharasharan kuma bingilallun kayan dake jikin ta a matsayin ta na mace kuma Musulma a cikin mutane, domin kamar kanwar sa ya ke kallon ta. Har ga Allah Amani bata san da shi a falon ba ta riga ta saba gaida mahaifin ta da kayan barci in har tana son su gaisa kafin ya fita, kasancewar sa maabocin sammako. Tana cigaba da saukowar bugun zuciyar Mukhtar na dada karuwa, ba tun yau ba hakan ce take kasancewa da shi a duk a lokacin da ya hangi Amani ko daga nesa ne. Duk da dai wata kalmar fatar baki bata taba hada su ba. Amma Tafisun tun dawowar ta daga ATBU take yi masa kwarjini sosai. Tafisu na dauka tuntuni kin shirya jiran isowar Mukhy kike ya zo ku wuce ki duba Boutique din naki? Amani ta yi kicin-kicin da fuska cikin sakalci irin nata tace Daddy ai ba sai mun tafi tare ba, yayi gaba, tunda yana da mota a hannun sa, ni inna kintsa na gama breakfast na yi wanka sai in zo mu hadu a can. A zuciyar ta kuwa fadi take Allah ya tsare ni da shiga motar sa, Allah tsare ni hada hanya da shi. Don dai ita Amani fisabilillah bata yarda hakanan Mukhtar ya bar baban ta ba, tafi yarda da cewa asirin su na Diffawa yayi masa yake son sa irin haka, kada ta je itama ya hada da ita ya dinga juyata yadda yake juya Daddyn ta. Daddy ya ce cikin lallashi, amma kin san bana so kike tuki da kan ki ko Amani? Tunda duk kin kori direbobin saboda masifar ki sai ki shiryo Mukhy yana jiran ki ku tafi tare, ban yarda ki kara tuki daga yau ba, kada ki manta sau uku kenan kina yin accident din da sai na biya diyya ga wadanda kike bugawa mota ta baya, tunda tukin bai karbe ki ba, to a hakura da shi babu dole. Duk inda kike son zuwa ki kira Mukhy a waya ya zo ya kai ki. Amani ta hau tumami da kafa cikin shagwaba tana fadin "Ni gaskiya bazan daina tuki ba, da koyo akan iya Daddy. Kuma da haka ne zan kware da tukin". Hon. Yace "duk ba na ki ba, ina nufin for the mean time zuwa kafin ki koya din nake magana, daga yanzu duk inda zaki Mukhy na yarda ya kai ki. Shi kin ga bayan iya tuki na hankali, harda nutsuwa da sanin ciwon kai a tare da shi. Maza shiryo ki zo ku tafi kin ji Tafisu na? Bana son musu. TA FI SU KIN FI SAURAN MATA!. Ya fadi kirarin da ya san da shi yake lallashin ta, duk da tana cewa bata son kirarin amma sosai mahaifin nata yake ciyo kan ta da shi ta yi masa abu idan ta yi gardama, kamar wata karamar yarinya. Fuskar nan ta Amani kamar hadarin da ya nausa yayi gabas ya juya yayi yamma. Wato Daddy na nufin ita bata san ciwon kan ta ba kenan kuma bata da nutsuwa sai Mukhy din sa. A fusace ta juya zuwa hanyar data fito, bayan ta zabgawa Mukhtar wata hadaddiyar harara tamkar manyan idanun nata zasu fado kasa. Mukhtar wanda kansa ke sunkuye yana danna wayar hannun sa bai san tana yi ba, ya yi sallama da Daddy yana fadin zan jira ta a mota Daddy ya ce ka dai tabbatar da lafiyar motar da za ku hau din ko Mukhy? Kuma Amani zata so hawan wadda ka zabo din? Bata so tana tafiya a hanya mota ta samu matsala, kuma bata son dindimemiyar mota. Mukhtar ya dan cije lebe cikin jin takaici, ya ce Alhaji kai ka ce min farar Brabus ta fi son hawa, kuma ita na dauko, lafiyayyar mota ce. Yayi kyau, to sai kun dawo, kada ka manta ka yi tuki a hankali bata son gudu, ku dauko Hajiya a filin jirgi in zaku dawo, yau zata dawo daga Umrah da zarar kun gama da boutique din sai ku je ku dauko ta, na san kafin nan jirgin nasu ya yi landing don sai bayan azahar zasu sauka. Ba tare da ya ce komai ba yasa kai ya fita daga falon. Takaicin yadda Alhaji ke sakalta yarinyar sa ya fi komai bata masa rai. Amma shi ya isa yace wani abu? Shi yasa take ma mutane kallon hadarin kaji kallon kowa banza ne saboda ta san Alhaji ya daure mata gindin sakarci. Mukhtar Yafi karfin mintuna sittin zaune cikin motar yana jiran saukowar yar mulki Amani, har aka rufa awa guda da rabi babu Amani ko inuwar ta, tun yana duba rantsatstsen agogon hannun sa swatch' dama na motar as well, har ya gaji ya kishingida a kujerar direba, ya ware sautin radiyon motar yana sauraren waqar mutumin sa mai debe masa kewa a duk lokacin da yake tuki, wato fasihin mawakin nan Ba-sudane Mahmoud AbdoulAzeez. A rayuwar sa ba abinda ya tsana irin jira, to amma ya zai yi? Umarnin Alhaji ne, kuma in an bi salsala Amani itace kamar second Boss din sa bayan Alhaji. Dole yayi zaman jiran ta a mota, ta shanya shi iya yadda ta ga dama. Tun lokaci na farko da suka fara haduwa da Amani da ya fahimci dabiun ta na sangartattu ne kuma bata ganin kan kowa da gashi yake taka-tsan-tsan da shiga shaanin ta, yake kokarin kaucema haduwar su a yawancin lokuta, in kuma ta kure sun hadun baya yarda ya yi mata kallo na biyu, sabida yadda ta ke masa kwarjini da sanya shi faduwar gaba. Ga harara kala_kala da yake sha daga kyawawan idanun ta. Maigadin gidan Hon. Usman wanda tasu ta zo daya wato Malam Tajuddeen Bafillace, ya sha yi masa fatawar cewa, muddin kana son zaman lafiya da Alhaji, muddin kana son tafiyar ku tayi tsaho, muddin kana son fadar ka ta fadada a wurin sa kuma tauraruwar ka ta cigaba da haskawa a idanun sa, to ka kyautatawa mara kunyar yar nan tasa mai soyayyun idanu a tsakar ka. Shima ya yarda da hakan don idan ya zauna da Alhaji na minti biyar to hirar sa ta mintina uku cikin biyar din a kan tilon 'yar sa Amani ne da irin tanade tanaden da yake yi mata a rayuwa don baya so ko bayan ran sa ta sha wahala ko ta nemi wani abu ta rasa tunda bata samu soyayyar Uwa data dangi ba. A irin haka watarana ya taba gaya masa cewa ya gina mata estates har guda biyu ya kuma mallaka mata su da sunan ta, karkashin idanun lauyoyin sa a cikin Birnin Katsina da babban birni, Abuja. Watau AMANI FASKARI HOUSING ESTATES. Wadanda dukkansu ya zuba tenants 'yan haya duk shekara suna biyan Amani miliyoyin da shi kan sa bai san zai same su a jikin gidajen ba. Hakan ya sa dole ya bude mata hannun jari a kasar Mexico. Mukhtar ya kan yi mamaki a cikin ran sa, mugun mamaki don bai san ana haka ba, wai uba ne ke kaunar dan da ya haifa har haka! Wasu lokutan abun ya bashi sha'awa ko ya burge shi, don bai taso ya ga ana yin hakan a gidan su ba. Bai san dadin kaunar Iyaye ba. A nasu gidan ba'a san komai ba sai uwar riko sai 'yan ubanci, kishi tsakanin iyayen su mata, burin gado da horo mai tsanani da sunan tarbiyya, wannan itace rayuwar da ya taso ya budi ido ya ga ana yi a gidan su, wadda karfi da yaji ta koya masa zama independent. Shi ko alfarmar gaisawa da nasa mahaifin ba ya samu a sanda yake tare da shi, yana raye ba wai ya mutu ba kuma suna cikin gida daya. Amma sai ya yi wata biyar suna gidan da shi bai saka shi a idanun sa ba. Ko fuskar sa baya samun alfarmar gani. Wannan dan tunanin da ya mika a zaune, yasa kyakkyawar fuskar sa yin jajir, ta rikide zuwa yanayin ta na tun fil azal da aka san shi da shi wato yanayin sa na rashin walwala da kwantaccen bacin rai, irin bacin ran nan mai kwanciya a kasan idanun mutum, ya sauya ainahin kalar su zuwa brown, ya nuna zahirin rudanin da ke cikin zuciyar dan Adam. Wanda a duk lokacin da ya tuna mahaifin sa ko ahalin sa hakan ce ke faruwa da shi, ya ji yana son kara nesanta kan sa da Diffa many more miles away! If possible, har fiye da nisan da yayi da gida a yanzu, don Najeriya ba nisa da Nijar, zai fi son ya tafi can karshen duniya wato kasar China birnin Hong-Kong ya yi rayuwar sa a can. Matsalar guda daya ce yana jin dadin zama da Alhaji Usman don soyayyar Uba yake nuna masa irin wadda bai san da ita ba, bai san irin ta na existing ba. Shi kan sa yana mamakin soyayyar Alhajin gare shi a matsayin sa na bare a gare shi. Ba don haka ba da ya kara lulukawa cikin duniya ya kafa rayuwar sa a can. Dagowar nan da zai yi da zummar fita daga motar don zaman ya fara gundurar sa ya hangota tana takowa cikin rangajin ta na halitta, tamkar reshen bishiyar da iska ke kadawa ko kuwa Dawisun da ya baza adon halitttar sa yake tafiyar takama a doron kasa, sai kayi tsammanin beauty contest zata tafi. Ta yi kyau ba dan kadan ba cikin wani material lace kalar ja da ratsin baki, an yi mata dinkin riga da siket wanda aka tsaga kafar sa ta baya, babu mayafin arziki a jikin ta baya ga wani rakani gantalin cantitly sai daurin kai da ta kalmasa gwanin shaawa da dankwalin kayan kai bazaka ce ta hada jinsi da hausawa ba. In da abinda yafi bakanta masa rai a dabiun ta bai wuce rashin daukar mayafi da lullubi da muhimmanci ba, bai taba ganin ta da lullubi a kan ta ba balle a kai ga zacen hijabi ba. Amma shi waye da ya isa ya yi mata magana a kai? Zai iya yi wa Baban ta ya yi mata, amma ya lura Baban ma bashi da katabus a kan ta, tamkar itace uban shine yar, babban abinda yasa ya tsani Amani kenan. Duk halayen ta na sangarta, rashin ilmin zamantakewa da rashin sanin addini basa gaban sa, don ya san masu iya gyaruwa ne in ta samu uwa ko abokin rayuwa nagari, ba irin Hajiya Rabi ba uwar gantali uwar bisa titi wadda mijin ma baya gabanta irin kasuwancin ta da yadda zatayi ya bata kudi kullum, amma rashin girmama mahaifin nan nata da bata yi ko ta wajen magana yasa ya sallama mata, yana roka mata shiriya a kasan ran sa, don ya lura girman hannun namiji ce. Irin su Amani suna abu bisa kuskure ne ba tare da sun san cewa kuskure bane, saboda tun farko basu tashi ana kwabar su ko ana nuna musu girmama na gaba ba, aah, an raine su ne a bisa tafarkin duk abinda suke so dole su samu karkashin soyayyar iyaye masu duniya a tafin hannun su, irin mai samar da komai na bukatar rayuwa ga yaro ba tare da ya yi gumi ko ya fidda hawaye ba. A haka ta iso motar ta tadda shi, ta tsaya tana jiran ya bude ya fito ya bude mata yadda direbobin ta ke yi cikin rawar jiki, don da kunnen sa ai yaji Daddy ya ce daga yau shi zai dinga tuka ta which means yana matsayin sabon direban ta kenan. Amma Mukhtar sunkuyar da kan sa yayi, kamar bai san da tsayuwar ta a wurin ba ya dukufa danne- danne cikin tsaleliyar wayar hannun sa amma fa shi kan sa bai san me yake dannawa ba, saboda kwarjinin Amani mai bi har cikin bargon sa. Hey! Baka ganin mutane sun iso ne? Ko makaho ne kai? Mukhtar ya dago cikin slow motion ya zuba mata fusatattun idanun sa masu kama da an diga zaiba a cikin su. Nan da nan Amani ta daburce, bata san sanda ta bude kofar motar ta shige ba. Ta kuma rufe kofar motar da karfi. Ko gama rufe kofar motar bata yi ba ya ja motar, saura kadan ta rufe da kafafun ta. Wata irin shakkar Mukhtar ta soma shigar Amani, domin bazata iya fassara alamuran data hango fal cikin idanun sa ba. idanun cike suke fal da abubuwan da shi kadai ya san su, ga tarin damuwa da fushi da rashin walwala, sannan tuki yake amma ko kallo bata ishe shi ba. A rayuwa bata taba haduwa da namijin da bai yi mata kallon kwal uwar daka ba koko kallon kin yiwa sauran mata zarrah idan ta yi kwalliya sai shi wannan baabzinen. Koda take ce ma Daddy bata son sunan TA-FISU tana fada ne kawai, amma fa tana son sunan, domin yana kara mata alfahari da kyawun surar ta mai ruda yaya maza, wani lokacin har mata yan uwan ta (will not keep wishing they were like her). Yau ga ta ga namijin da bai yi mata kallo na biyu a duniya ba, ta saci kallon kan ta kadan, to kyawunta ne bai ishe shi daga ido ya kalla bane ko kuwa kwalliyar data cancada bata kai ta kawo bane? Ko kuwa shi din ma YA FI SAURAN MAZA ne? Kwafa tayi tace cikin yar rawar murya Malam ka rage gudu, baa gudu da ni a mota, I think Daddy ya gaya maka, drive with care. Yayi fumfurus kaman bai ji ta ba, maimakon hakan sai ma karawa motar sa wuta da yayi yana fadi cikin ran sa ai ni ba Daddyn naki bane, Mukhtar nake. Amani tayi kyacci, kamar ta ji me yake fadi a ran sa. Daddy ya san kai makaho ne kuma kurma ne sannan baka da seti ya saka ka tuka ni a mota? Sai lokacin Mukhy ya dan juyo a gicciye a dube ta, da idanun sa masu kalar silver, duban da sai da yasa hantar Amani da hanjin cikin ta karkadawa domin ta yi zaton kwada mata mari zai yi, don ko da bai yi magana ba ta san kallo ne na zazzafan gargadi ya yi mata, wato ta san irin maganar da zata dinga furta masa. He is not that stupid as she thinks. Suka isa Goruba Estate wato inda boutique din Amani yake. Nan ma jira take ya fito ya bude mata kofar mota ta fito amma ya bude yayi ficewar sa ya bar ta a zaune. Masu kula da wajen sai gaishe shi suke yi don su a tunanin su shine mamallakin shagon, sabida duk wani shige da fice shi ya dinga yin sa har komai na boutique din ya kammala, tankareren shagon yana daga jerin farko-farko na shagunan da ke cikin plaza din. Mai gadi ya kawo masa mukullan hannun sa ya bude ya shiga ciki. Da Amani ta tabbatar ba zai bude mata kofa ba sai tayi kyacci ta bude ta fito ta bi bayan sa. Ta tara shi fal a ranta har da karin gishiri da maggi na abubuwan wulakanci da zata gayawa Daddy ya yi mata, tana shiga shagon ita kanta ta girgiza da irin dukiyar da mahaifin nata ya narkar mata, takalma ne da jaka na mata na zamani na yayi da sittiru yan waje na yara da manya, shi kansa wanda ya zabo kayan ta sara masa wajen iya investing kayayyakin da zasu dauki hankalin kwastoma, a rashin sanin ta ba kowa bane dan mutanen Diffa ne amanar Alhaji Usman Faskari. Duk kushen ta da high taste din ta ta kasa kushe tsarin da Mukhy ya yi wa shagon nan. Ko da suka gama dubawa abubuwa kadan ta iya cewa a kara. Shi din ma rubutawa ta yi aka takarda ba da fatar baki ta gaya masa ba. Yayi gabas ita kuma ta yi yamma a cikin shagon don kada ma ta hada hanya da shi. Ta rubuta iya abubuwan da take bukata a kara sannan ta fice daga shagon ba tare da ta ce masa ta gama ba, shi kuma yana can zaune bisa wata kujerar roba a cikin shagon yana jira ta gama gatsine-gatsinen ta tana kallon komai tamkar ta ga kashi, nan kuwa can a kasan ran ta yabawa take yi komai ya yi mata, ta kuma jinjinawa fasahar wanda ya tsara shagon nan. Wasu kayan ma da aka zuba duk gayun ta bata san da irin su ba farkon shigowar su Katsina kenan. Da ta gama abinda zata yi mota ta koma ta shige ta zauna ta hau danna horn ji kake biiiiii..biiiii..kamar mai kiran kare. Yana jin ta ya yi kamar bai san tana yi ba, ya gama danne dannen sa a wayar sa ya mike ya haura zuwa upstairs na shagon yayi zaman sa. Ya rantse a kasan ran sa sai ya rama shanya shin data yi a gida cikin mota kafin ta fito. In bai manta ba ai jiran awa biyu kwakkwara yayi cikin mota yana jiran ta, to itama sai ta yi shi yanzu. Bakin ciki da bacin rai a wurin Amani abun baa cewa komai, data gaji da zama sai ta kira Daddy a waya yana dagawa ta hau kuka da balbalin masifa tamkar mai magana da kanin ta. Daddy kuwa cewa yake me ya faru ne Tafisu? Daga ina kike magana? Tace. Daddy daga cikin motar da wannan Dirty Human Being din ya shanya ni, tukun nama Daddy ka taba zaunar da shi ka gaya masa ko ni wace ce a wurin ka? Shi ba kurma ba shi ba makaho ba amma wallahi sun fi shi ji da gani, mutum dunkumkum sai kace dankali ba um ba um um sai bakar zuciya zaka hada hanyata da shi? Ko bude min mota fa bai yi ba, yanzu haka zaman sama da awanni biyu nake cikin mota har baya na ya fara ciwo. sai ta koma kukan shagwaba wanda Daddyn kadai take yi wa irin sa. Tace. Daddy in baka zo ka dauke ni da kan ka ba ba zai san matsayi na a wurin ka ba, idan baka kore shi ba dauka zai yi ni yar aikin gidan ka ce, babu wanda ya taba yi min wulakancin da mutumin nan naka yayi min. Amani ta tsinke da fada kamar tsinkakken carbi duk a kan kunnen Mukhy da bata ma san yaushe ya bude motar ya shigo ya zauna ba, bayan ya duba agogo ya tabbata awa biyu ta cika, kuma ko da take ma Daddy wannan balbalin kara fusata shi abun yayi because he respects Alhaji so much, ba zai iya jurar jin ana masa wannan rainin ba. Don haka ya fizgi motar a gujen gaske saida Amani ta zunkuda ta koma ta bugu da kujerar data ke zaune. Amani ta zuga salati tana cewa Daddy ka cece ni zai kashe ni Daddy ya ce bani Mukhtar din tace Daddy Allah ya sawwake ya taba min waya ya shafa mata bakin hali irin nasa abin nata sai ya koma baiwa Alhaji dariya, ya ce alright, bari in kira shi ya katse kiran nasu ya soma kiran Mukhtar. Yana ganin kiran Alhaji amma kuma yana tuki don haka saida kiran ya katse. Ya gangara gefen titi ya kashe motar sannan cikin nutsuwa ya bi bayan kiran Alhajin. A yadda ya tausasa murya ya kuma russunar da kai duk da Alhajin baya ganin sa sai kayi tsammanin da mahaifin sa ya ke magana, ya ce Alhaji muna hanyar dawowa kana son wani abu ne? Alhaji cike da damuwa ya ce No Mukhy, karar ka aka kawo min kala-kala, ka bi ta a hankali ka ji? Ka san wani lokacin haka take abu na yayan fari. Mukhtar ya saci kallon ta sai kumburi take kamar zata fashe ya ce Alhaji ai babu damuwa ina iyawa da ita, musamman da wani lokacin tana abu zayyal majnunah (kamar mahaukaciya), abinda bazan lamunta daga gare ta ba shine rashin kunyar da take maka, ka gaya mata ta dinga maka magana with respect irin yadda yaya suke yi wa iyaye, saboda kai ne gaba da ita ba ita ba. Idan ta cigaba da yi maka magana irin haka bazan kara daukan ta a mota ba. Alhaji ya ji dadi, ya ce Mukhtar kada ka damu da shirmen Tafisu ka ji? Ka san wanda baida mahaifiya a kusa sai ana masa uzuri Mukhtar yace ni ba zan yi ma ta uzuri da wannan ba, babu uzuri a cikin biyayyar iyaye, in dai a kan daga sautin ta sama da naka ne zan iya bubbuge bakin ta Alhaji Alhaji yayi murmushi yace to shariar taku ta fi karfin waya, ku dawo gida sai mu yi ta a zaune. Kuna ina yanzu? Yace muna hanya ko rabin isowa gida bamu yi ba. Ni gaskiya Alhaji a gate zan sauke ta, ni kadai zan je na dauko Hajiya, daga can ina da inda za ni Alhaji ya ji wani iri ya ce Mukhtar ban san ka da rashin kirki ba kada ka fara akan kanwar ka ya ce Alhaji sai ta daina yi maka fada zan yi kanwa da ita, in ba haka ba kowa ya yi rayuwar sa cikin gidan nan ba ruwan Yaya da kanwar, bani da zuciyar da zata iya daukan ana raina min kai. Daga haka ya kashe wayar sa Alhaji na fadin ka dai shigo da ita kada ka sauke ta a gate don Allah ba don halin ta ba. Duk abinda suke fada a kunnen Amani, mamaki da haushi ya hana ta ko kwakkwaran motsi, anya wannan mutumin bai taki komai ba? Yaya kana zaman yaron gida kake ma uban gidan ka Gadara irin haka shi kuma yana biye maka sai kace uban da ya haife ka? Amani ta saci kallon sa sai suka hada ido, ya kashe ta da harara, yana kokarin cire farin gilashin idon sa don ya sha round din da zai kai su unguwar su. Wani irin kyau ya yi a idanun ta mutum tamkar shi yayi kan sa, kai kace wani balaraben Madinah ne idan yana magana, tsafta da wanka sun kama jikin sa radam. Sai ta tuno alfarmar da take so yayi mata duk da ya bakanta mata rai yadda bata zato amma wannan ce dama ta karshe da zata iya rokon sa don ba haduwa suke yi ba, sai dai ta hange shi a harabar gidan daga balcony din ta yana shiga mota zai fita ko ya shigo gidan. Ko ya zo daukan Alhaji su fita. Ta rasa ta ina zata fara don kwata kwata babu fuska daga Mukhy, yama kara daure fuska tamau da suka hada ido don kada ta kawo masa wargi, ya lura da kallon kurillar da ta ke masa wanda ya wuce shariah. Shikuma baya son ko kalma guda ta hada shi da Amani don kada raini ya shiga takanin su irin wanda takewa kowa da ke karkashin ta. Ya Allah ya zata yi da wannan mutum mara sakin fuska? Sai kawai tayi kundumbala tace, Man, ina son fidda kudi ne daga corporate account dina? Mukhtar bai san cewa magana take da shi ba, ya dauka ma a wayar ta take magana da wani daban don haka ko juyowa bai yi ba. Amani ta daga murya da dan amo tace na tabbata kai ba kurma bane, but you are acting kamar baka ji! Sai yanzu ya san da shi ta ke, ya kuwa kara daure fuska yaci gaba da tukin sa. Amani sai ta fara hawaye don abun yayi mata ciwo mai yawa, baa saba yi mata irin haka ba, kowa na gidan girmama ta yake yi yana nan-nan da ita yana rawar jiki idan ta bada umarni, balle wanda ke matsayin yaron Baban ta ya yi mata irin wann funfurus din. Kuka ta soma yi sosai har da sheshsheka da fyace hanci, tace tunda dai na san kana ji na, halin ka ne shariya da wulakaci, to bari in fadi sako na, ya rage naka ka yi min alfarmar ko kada ka yi. Ina so zan cire kudi 5 million zan yi amfani da su bana son Daddy na ya tuhume ni, idan ka ga alert dinnan alfarma ce kada ka fada masa tunda dai kudi nawa ne, ba na wani ba. Mukhtar ya rage gudun motar ya dan juyo kadan ya saci kallon ta, sai kuka take tana fyatar hanci kamar wadda aka yi ma wani mugun duka, kada ya je ta daura masa sharri, don ya ji an ce masa mata makirai ne. Ya kashe motar gaba daya a gefen titi ya ce. Da ni kike? Amani ta ce aa da sitiyarin motar ka nake. Karo na farko da Mukhtar ya yi wani miskilin murmushi, ya ce to kai sitiyarin mota ana maka magana!. Amani ta kara rushewa da kuka tace Allah yasa ayi maka irin wulakancin da kake yi min. Allah ya hada ka da daidai kai, Allah ya sakawa mahaifina amana ta da ya baka kake ci don ka san ka asirce shi. Mukhtar ya bugi sitiyarin sa ya ce ban da muguwar addua ga wanda baki sani ba Maam, you will never know what a man like me is going through, I hate hayaniya, ki gaya min wace alfarma ce kike so? Bana son koke-koken banza me na yi miki? Wane kudi kike magana a kai? Kuma me zaki yi da su? Ban fahimce ki ba anymore. Amani ta dan ji dadi, at least hargagin ta ya sa ya kula ta, ta share hawayen ta da gefen mayafin ta, ta ce ba damuwar ka bane abun da zanyi da kudi na, kawai bana so Daddy ya ji ne, da ba zaka san ma na cire ba to kin san ba damuwa ta bane kuma bai shafe ni ba don me zaki sako ni ciki? An gaya miki ina shiga abunda baa sa ni bane? Ai kawai ki yi abinda kika ga dama nima in yi aiki na na daukar zance in kai gaba, tunda shi aka sa ni, ba sai kin saka ni cikin shaanin ki ba, mind your own business and leave me alone. Ya ja motar suka cigaba da tafiya Amani na gayawa kanta ta gara ta canza taku, tunda har kuka yana karya zuciyar sa ya saurare ta, ko baya so, ya bata amsa ko yaki Allah to zata rage izza tunda ta lura izzar ta ke tunzura shi ya ki sauraron ta. Tabbas yau ta gamu da wani sabon mutum a cikin rayuwar ta, wanda bata taba ganin mai hali irin nasa ba. Bawan Allah ko wa kake da suna? Na yi rantsuwa ba ta hanyar banza zan kashe kudin nan ba, kawai bana so Daddy na ya san da fitar su. Ta sassauta murya ta ce kayi min wannan alfarmar, ba don ni ba ba don hali na ba. Mukhtar ya yi mata kallon kin ishe ni haka kafin yace zan yi miki only in kin gaya min gaskiyar ko me zaki yi da kudin nan, bana backing munafurci da rashin gaskiya komai kankantar su, in kina da gaskiya ba zaki nemi a boyewa mahaifin ki wani abu da zaki aikata ba. Amani ta share ido da bayan hannun ta ta marairaice, sai ta dan bashi tausayi, ta ce wallahi ina da gaskiya ta, trust me, kuma ta hanya mai kyau zan yi amfani da su yanda ba zai gane ba, don bai san irin ciwon da na ke ji in naga kowa a jikin uwar sa ba. Ta cigaba da cewa Malam COO (Chief Operating Officer) ni din ban taba ganin uwa ta ba sai a hoto, ban rasa komai ba amma ina so in je gare ta, ba don kuma na raina kulawar Daddy na a kaina ba, sai don kowannen su matsayin sa daban a gare ni. Zuciyar Mukhtar ta dan yi laushi, laushin da shi kan sa bai zaci tana da shi ba, yafi zaton zuciyar sa tafi dutse tauri amma ashe akwai sauran tausayi a cikin ta, akalla ya gamsu, tunda ba shaye-shaye zata yi da kudin ba don tafi masa kama da masu banka kwaya, yace I will think over it. But remember always zaman Alhaji nake ba zaman wata Amani ba!. Maganar shi ta karshe bata yi mata dadi ba. Ta yi kuta ta ce kai a rayuwar ka baka da humanity ne? baka da concern? Baka da sabo da mutane kuma baka daukar kowa da muhimmanci sai Daddy? Ya murmusa kadan, har beauty point din fuskar sa ya lotsa ciki sosai yace ban san ta ba humanity din, concern kuwa ko maanar ta ban sani ba, mai yuwuwa sanda ake rabon su ni ina Diffa. Kin san ni dan Diffa ne, Diffa region, ta kasar Nijar. Amani ta kulu iya kuluwa, ta yaya ba zai dauki abinda ta gaya masa da muhimmanci ba bayan sirrin ta ne da bai kamata ma ta gaya masa ba? Zai bi ta da bakar magana bayan ta bude masa sirrin ta? Maganar mahaifiyar ta fa take masa, wadda bata taba gani ba, yana mata maganar wani garin su. Daidai lokacin da suka iso tangamemen gate din gidan su Amani. Dama bata son zuwa dauko Hajiya Rabi. Ba tun yau ba ta fahimci matar zal wajahaini ce (mai fuska biyu) a gaban Daddy kawai take nuna kaunar ta, a bayan idon sa kuwa kashi ya fi ta daraja a gidan nan. Shi yasa itama ta kama kan ta, sam bata shiga shaanin Haj. Rabi ko hanyar sassanta bata bi, ta kuma yi wa kanta alkawarin bazata bari Daddy ya sake ta ko ya san halin ta a kan ta ba, don ta gaji da aure-auren sa da ake faman kirga masa akan ta. Mace ta karshe da Alhaji ya saka wai ita Zaibi, ta fadi maganar data tsaya mata a rai har gobe ta kasa mantawa, kuma daga kanta ne ta kudiri aniyar hana Daddy kara sakin kowacce mata duk mugun halin ta. Gara ta bar su da halin su ta nemo tata mahaifiyar. Cewa matar ta yi ga gidan nan ta bar mata, karshen soyayya Alhaji ya auri Amani ya maye gurbin ta da ita. Don haka tun kafin ya gama daidaita parking ta soma kokarin bude kofar don ta fice kada ma ya ce suje dauko Hajiya Rabi tare, sai ta ji ta gadagau wato ya rufe ta automatically. Kallon tambayar dalili Amani tayi masa. Idanun ta fal hawaye. Mukhy ya daure fuska sannan ya shafa sumar kan sa ya ce da ita as a brother, zan hore ki da abu daya, duk rintsi kada ki kasance mai munafuntar mahaifin ki, domin mahaifin ki extraordinary Uba ne, musamman a kan ki, ban taba ganin uban da ke son yar sa irin son da mahaifin ki ke yi miki ba. Don haka bai cancanci ki boye masa komai da ya shafe ki ba. Mai zai hana ki same shi officially ki gaya masa damuwar ki, akan son ganin Maman naki? Im sure yadda Alhaji ke son ki da girmama lamarin ki ba zai ki kai ki ga mahaifiyar ki ba. Wane irin bincike ne saboda Allah har miliyan biyar? A kasa ake hako kudin? In gaya miki gaskiya an doki hancin ki, don an ga baki da wayau, kuma you are desperate, a kan bukatar ki, ni ki bar ni zan lallaba Alhaji ya kai ki gun Maman naki on koboless (babu ko sisin ki) ba kuma don ke ba sai saboda Alhaji ne ya haife ki. Wani kwayan mutum guda daya da nake matukar kauna da girmamawa. Alhaji da kan sa ya fi dacewa ya gaya miki inda take, ba sai kin bi ta karkashin kasa kin sha wahala ba Amani ta yi ajiyar zuciya tana jin wani irin relief na zagayeta a zuciyar ta, yau Mukhy kamar ba shi ba, yana magana ne ta hanyar bata dukkan attention din sa da concern as a brother, duk da ba kallon ta yake ba wayar sa ya ke dannawa a duka maganar da yake yi, amma kuma ya dauki zancen yanzu da muhimmanci, ba don komai ba sai don ya tuno tasa UMMAMIn. Yadda yake son Ummami da yadda yake son zama kusa da ita bai samu ba, ba don komai ba sai dalilin norms, culture and traditions irin na gidan su. Ya yarda rashin kulawar ta a tare da shi ne duk yayi mujazar matsalolin sa a rayuwa da a yau suka saka shi garanranba a duniya. Amani na bukatar tallafin uwa da gaske. Musamman a kan dabiun ta da tarbiyyar ta, kai har addinin ta ma yana bukatar gyara, in yayi duba da irin dressing din da take fita da shi da rashin kunya ga na gaba da irin tabarar data ke yi wa mahaifin ta. Amani ta ce I wish Daddy din zai saurare ni a kan damuwa ta irin yadda ka saurare ni yanzu, to ba zai saurare ni ba, ban san abinda ya raba su ba amma ko zancen ta baya so na yi masa, ya dauki gaba mai tsanani da mahaifiya ta yana fadin muddin na zabi zuwa gare ta to shikuma zai sallama mata ni ne. Ta share hawayen ta tace and I love my Daddy more than everybody, saboda da shi kadai na taso, da kaunar sa gare ni na budi ido. Ban san kowa sama da shi ba ko yan uwan mu na Faskari sama-sama na san wasu daga cikin su, bani da wa bani da kanwa. Cikin tausayi Mukhtar yace me yasa ba zaki neme su ba? Dangi da kike gani suna da matukar muhimmanci a rayuwar mutum, musamman ke da kike mace, daya tal a wurin iyayen ki, babu dan uwa babu yar uwa, it is your duty ki nemi dukkan su ki gyara gurbin rashin zumuncin dake tsakanin ku don hakika kina bukatar su, amma karkashin yardar mahaifin ki, dont ever try to hide anything from him no matter how bitter, ba abunda lallashi da ban baki ga iyaye bazai sa su yi maka ba. Jikin Amani yayi sanyi kadan, don ta sani bata lallashin Baban ta sam kullum sai rigima da rikici in tana son ya yi mata abu dole ya yi, a kan zuwa gun maman ta ne kawai da korar Mukhy daga gareshi kawai ya taba turje mata, tace cikin murya mai ban tausayi, ka ce zaka nemo min Mama na? Mukhtar ya ji wani iri a jikin sa da yadda tayi maganar murya na shaking, ya bude mata kofar yace cikin basarwa idan na lallashi Alhaji ya yarda ki je din, ni da kai na zan nemo ta, zan kuma kai ki duk inda take. Amani ta fita tana dan murmushi, a ran ta tana fadin ashe dai yana da dan kirki ko yaya ne, ga taushin murya, ga jan class, fuskar ce dai bata taba canzawa daga yanayin ta na rashin annuri da bacin rai. Tamkar wanda kullum ake yi wa mummunar bushara ko ake yankan naman jikin sa. Bai tsaya ta gama bacewa ba ya ja motar sa ya nufi airport don cika daya umarnin na Alhaji. Wato dauko matar sa. Ya dauko Hajiya Rabi suka kamo hanyar gida, a hanya tana ta mitar an bar ta a shanye a filin jirgi, baa zo daukar ta da wuri ba, mota ba tasa ba amma ya tafi yawon banza da ita yana kwambo a cikin gari gurin yammata, idan yana ikon sa da jin kan sa ya dinga tsayawa iya kan Alhajin da ya kawo shi ya kuma daure masa gindi yana baza iko a gidan mutane, kada ya kuskura ya shiga gonar ta. Ita warki ce daidai kugun kowa yanzun nan zata yi maganin mutum, ko Amani bata isa ta shanyata ba balle shi wani banza a banza. Mukhtar ya sunkuyar da kai yana jin ciwo a cikin ran sa, yau wata wadda bata ko kai matsayin mai gugar takalmin sa ba ke zagin sa haka, wai kwambo! Duk ba komi ya janyo masa ba sai zabar barin gida da independent life, an ce kuma a kowanne neman halal akwai challenges, ya cigaba da tuki bai ce mata komai ba. Ba tun yau ba ba sa ga maciji da Hajiya Rabi, ta fannin ta ba don komai bane sai don son da ta lura Alhaji na masa. Daga Amani sai shi a wadanda bata so ta bude ido ta gani a gidan nan, amma fa bata taba nuna hakan a gaban Alhaji ba. Kullum nuna masa take tana kula da Amani irin kulawar da uwa take yi wa dan ta, tana kuma son wannan yaro nasa mai hankali da amana da kullum yake yabo a gaban kowa. Shi kuwa Mukhtar ya san wacece Haj. Rabi sanin da ko Alhaji bai yi mata ba, shiyasa kawai ya ji baya son matar, wato ya san tana dan taba yawon barbada a waje don ba sau daya ba ba sau biyu ba ya taba ganin ta a hotels daban daban tare da wani mutum. Kuma har kofar gidan mutumin ya sha kawo ta. Duk da ba zai ce ga hakikanin abinda suke yi tare ba jikin sa yana bashi tarayyar banza ce don Alhaji yana da ciwon suga mai hana lafiyar auratayya. Yana ajiye ta ya juya ya koma Company, akwai muhimmin aikin da zai yi wa Alhaji amma tun shigar sa office din sa sai ya kasa zaune ya kasa tsaye. Mukhtar Diffa, ya hau safah da marwah, hannanyen sa biyu zube cikin aljihun farar shaddar da ke jikin sa. Ya rasa abinda ke tsaye a wuyan sa ya ki wucewa. Ya rasa meye ya tsaya masa a rai. Sai da yayi tsam da ran sa ya fafimci ba komai bane kukan Amani yake tunawa da shagwabar ta, da fyatar hanci cikin yanayin sakalcin ta. Sai ya ji wasu sassa na jikin sa suna respoding. Zuciyar sa na vibrating. Ya tuna matsananciyar damuwar da ke kwance kan kyakkyawar fuskar ta a kan son ganin mahaifiyar ta, sai ta kwadaita masa son ganin tasa Ummamin shima, kwarai ya gane da gaske take son ganin Maman nata, wasu abubuwan data yi a yau sun tsaya masa a rai, sun kasa bacewa, musamman kukan shagwabar nan nata is arousing something in him komai dakewar sa don bai taba ganin wanda kuka ya yiwa kyau irin Amani ba. Tsaki yayi cikin jin matsanancin mamakin kan sa, ya dauki kiran Alhaji da ya shigo masa a daidai lokacin. Ya ce Mukhy kana ina ne? Ina office Alhaji ya fada a kasalance. Alhaji ya ce to in ka kammala ka zo zamu yi wata muhimmiyar shawara. Kai bari kawai in gaya maka. Haka kawai ina zaune wani tunani ya zo min, ina son tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina. Mukhtar ya yi azamar rufe baki sannan ya bude, yana mai jinjina hadamar duniya irin ta uban gidan sa, me Alhaji yake nema kuma a siyasa da rayuwar sa bakidaya? A tunanin sa duk abinda dan adam ke nema a duniya Alhaji Usman ya gama samun sa, kamata yayi ya maida hankali ga kula da tarin dukiyar sa da neman lahira da aurar da wannan gansamemiyar sakaltacciyar diyar tasa, ba neman wani mukamin siyasa ba a yanzu, wand aba lallai yayi nasara ba, a fili ya ce Alhaji bari in zo kawai, wannan ba maganar waya bace. Yana tafe a hanya yana tunanin ta hanyar da zai bi ya lallashi Alhaji kada ya tsaya takarar nan, ba don komai ba sai don ya san mawuyaci ne alummar Katsina su zabe shi yanzu, don duk wani mukami da ya rike a baya bisa magudi ake bashi ba don alummah na so ba, sai don kasancewar yana da iyaye a babbar jamiyyah masu karfi a gindin murhun, jamaa basa son Alhaji Faskari ne saboda kankamon sa, da rashin jan talakawa a jiki sai ka ce ba dan siyasa ba. Wasu yan jaridar ma kan ce, HON. USMAN FASKARI; dan siyasar da ya rasa dukkan attributes da qualities na yan siyasa amma yana da saa a siyasa. Mukhy na tunanin karshen ta ya salwantar da dukiyar kamfanin sa a banza, wajen kamfen, kuma ya zo bai ci ba. Mukamin Sanata daban na gwamna daban. Mukamin gwamnatin jiha tabbas sai da soyayyar talakawa. A sanin sa ko Zakkah Alhaji baya iya badawa, har sai bayan zuwan sa gare shi, shi Mukhtar din, da ya tsaya tsayin daka da lallashi da nasiha a kan Alhajin, bisa dole ya sa shi ya dinga fidda zakka don tsaftace dukiyar sa. Sau tari, Mukhy kamar shine Ogan Alhaji subordinate, da wuya ya fadi abu Alhaji ya tsallake, don yayi amanna ba zai cuce shi ba, in Mukhy yayi magana akan abu, Alhaji baya iya tsallakewa saboda son da yake masa da yardarm da ya yi masa. Sanda ya iso gida Alhaji na tare da baki. Ya yi sallama ya shiga falon, Alhaji ya bashi iznin zama, Mukhtar ya gaida hamshakin mutumin dake tare da Alhaji, cikin ladabi y ace da Alhajin yace zan jira a karamin falo kafin ku gama Allhaji no Mukhtar, zo zauna, gara a yi shawarar nan tare da kai, you are part of me, samu wuri ka zauna. Mukhtar ya zauna bisa kilishi can gefen kafar Alhaji. Alhaji da bakon sa suna kan kujera, Alhaji yace Mukhy, wannan da kake gani shine aminina Alhaji Sadisu Talle, shugaban sabuwar jamiyyar data take tamu yanzu a farin jini wato PRC (Public Relation Congress) da ake wa lakabi da SAWUN GIWA. (ya take na Rakumi). Mun yi shawara da shi zan bar AC in koma PRC don AC bazasu yarda su bani takara ba. Sun riga sun tsayar cewa wannan karon yaro matashi mai jini a jika zasu baiwa takara. Suna cikin wannan maganar kafin Mukhtar ya furta komai Amani ta sauko daga upstairs da zummar wucewa kitchen (madafi), yunwa take ji, ga mai aikin ta Rakiya ta je kasuwa, sai idanun Alhaji Sadi suka sauka akan kyakkyawa Amani. Babu wanda ta gaisar a cikin su ta wuce zuwa kofar da zata kaita kicin, shi kan sa Alhajin yau sai da yaji kunyar wannan rashin tarbiyya ta Amani. Sabida matsayin Alhaji Sadi a wurin sa a ce yar sa ta wuce bata gaida shi ba, shi dama Mukhy baya layin ta. Data damo abinda zata sha wato quaker oat da madarar ruwa ta peak tazo zata wuce ta koma sama batare da tace musu uffan ba. Alhaji Usman ya yi jan wuya yace. Shin Tafisu baki ga Alhaji Sadi Talle bane zaki wuce baki gaida shi ba? Ta zumburi baki, kafin ta ce da Alhaji Sadi din ina yini? Ba tare da ta juyo ko ta durkusa ba, ko jira ya amsa bata yi ba tayi wucewar ta sama. Alhaji Sadi ya shiga yage baki duk sai ya dabarbarce ya rasa nutsuwar sa, sai mutsu-mutsu da baki yake yi ya kuma rasa abin cewa tun saukowar Amani falon ta tafi da imanin sa, yana tambayar kan sa ina Alhaji Usman ya samo wannan kyakkyawar diya haka? Babu kama ko ta farce shi da ita, ko adopting din ta yayi? Ya rasa yadda zai yi ya tambaya sabida Mukhy da ke zaune ya tsare shi da fusatattun idanun sa don ya gane canzawar sa da rudewar sa tun saukowar Amani. Shi Mukhtar takaici da haushin yadda dattijon ya kwalalo ido da baki yana bin Amani da wani mayataccen kallo har da hadiyar miyau yasa ya mike. Alhaji yace ya zaka tafi Mukhy bamu gama shawara ba? Yace Alhaji ban yi sallah ba ina zuwa. Nan kuwa ko zancen takarar Alhaji baya son ji, balle ya bar jamiyyar sa ta amana wato AC da ya dade a cikin ta ana damawa da shi. Kai shi bai ma yarda Alhaji Sadisu zai sa a bashi takara a PRC ba duk da matsayin sa na shugaban jamiyya, don ya san bashi da farin jini yafi yarda da cewa kudin sa zai ci ya wofintar da shi. Duk da cewa ba yau suke tare ba duk da banbancin jamiyya dake tsakanin su. Abota ce tsakanin su tun ta kuruciya. Ai Alhaji Sadi kamar jira yake Mukhtar ya bar wurin ya muskuta cikin kujerar sa bakin sa nata motsi yace shin Hon. Usman wannan kyakkyawar diya taka ce ko yar riko ce? Hon yayi dariya yace Amani ce fa, Amani Faskari, ita kenan yar daya jallin jal dana mallaka duniya da lahira. Sai a lokacin Alhaji Sadi ya hau tuna komai na Alhaji Usman yana bearing wannan sunan ne wato Amani Faskari, bai taba sanin sunan yar sa ne Amani din ba, don bai taba jin irin wannan sunan ba. Alhaji Sadisu ya shafa gemun sa da sajen sa yana murmushi yace ai kawai Hon. Ka ce ta zo gidan sauki tuwo na mai na, abu nawa maganin a kwabe ni. Ka bani auren ta ni kuma na maka alkawarin kujerar gwamnatin Katsina sau biyu, ko ana ha maza ha mata sai ka yi. Hon. Usman a matsayin sa na uban da bai taba jin wani ya tare shi yace yana son Amani ba, saboda kowa cewa yake tafi karfin sa saboda izzar ta da irin rainon da yayi mata, sai ya ji dadin maganar kwarai, ya ga cewa tabbas Alhaji Sadi zai iya da Amani ba tare da yace tafi karfin sa ba shi, tunda in dukiya da mukamin siyasa ne da take takama yana da su ne shima Sadi a cikin su yake dumu-dumu har ya dara shi komai yanzu, in ka dauke yawan shekarun sa da suka zarta nasa, da furfurar data soma samun muhalli tsilli-tsilli a saman kansa, sai ya ga cewa zai iya bashi auren Amani muddin zai taimaka masa ya zama gwamnan jihar su. Babban burin sa na yanzu kenan wato zama gwamnan jihar Katsina. Alhaji Sadi bai bar gidan ba sai da suka kulla yarjejeniya a rubuce da shi da Alhaji Usman cewa zai tsaya masa a matsayin sa na shugaban jamiyyar PRC a bashi takarar kujerar gwamna shi kuma kafin nan ya aura masa yar sa Amani. Ya so a yi maganar nan a gaban Mukhy, amma Mukhtar din tunda ya zame da sunan zai je yayi sallah ya ki dawowa. Haka kawai ya kasa jure mayataccen kallon da Alhaji Sadi ke bin Amani da shi, kuma in zaa kashe shi bazai ce ga dalili ba. Shi kawai yana ganin ba girman Alhajin bane. Basu kara haduwa da Alhaji ba sai washegari. Lokacin da Alhaji ya gaya masa yarjejeniyar da suka yi da Alh. Sadi washegari suna hanyar zuwa ofishin Alhajin, Mukhtar suman zaune yayi. Ya yarda neman Mulki yana fidda wasu dattijan a hankalin su. Ina Amani yar shekaru 20 ina tsoho dan shekaru 65 banda kwadayin Mulki da neman sa ido rufe irin na Honourable Usman? Kai bama wannan ba wani dunkulallen abu ne ya zo ya tokare shi a makogaron sa ya kasa cewa Alhajin sa komai, sai kawai ya maida hankali ga tukin da yake yi zuciyar sa na wani irin bugawa fat-fat. Alhaji Usman yace baka ce komai ba Mukhy, ko shawarar tawa bata yi bane? Na san ka da tsinkaye, amma nima ina da amfanin da zan samu a cikin auren, ai wato komai mutum zai yi a rayuwa yanzu ya fara hangawa ya auna ya gano ribar da zai samu a cikin sa. Kaga in ya auri Amani zai taimakamin na zama gwamna, zai tsaya min kan duk mai son taka ni a jamiyya, abinda na tsara shine sai in nada ka mataimaki na amma ko shi ban gayawa hakan ba, ka nemo mata kayi aure kai ma mu tara dukiya iyakar tarawa, mu Mulki Katsina tare, mu ci duniyar mu da tsinke, amma na yi rantsuwa ba mijin da zai ci min dukiyar Amani, don ita na tara mawa, komai nata zai koma karkashin kulawar ka da amanar ka ko da ta auri Alhaji Sadi. Hatta kayan daki ka ga ba sai mun yi mata ba gidan Alhaji Sadi duniya ne; babu abinda babu cikin sa. Kudin komai dana tanada don auren ta sai a kara jari dasu a boutique din ta ka ga dadin auren mai akwai kenan. Gashi babu mace yanzu tare da shi tun rasuwar uwar yaran sa bai kara aure ba, yaran bakwai duk sun manyanta, biyar daga ciki sun yi aure. Don haka Amani bazata yi masa rainon yara ba. Ya ka gani? Mukhtar Diffa dai ya zama mutum-mutumi a zaune. Tuki kawai yake ya rasa amsar da zai baiwa Alhaji. Bai san cewa ya bar hanyar da zata kai su company ba ya dauki wata daban da bai san inda zata kai su ba, har sai da Alhajin ya ankarar da shi, sannan ya koma da baya ya dauki hanya daidai. Da Alhajin ya takura sai ya ji ta bakin sa sai ya ce ni me zan ce Alhaji? Banda Allah yayi zabi mafi alkhairi?. Tunda kun riga kun rubuta yarjejeniyar a rubuce ai bani da say. Kome zan ce is too late. Sai dai naso ace Amani din da yardar ta aka zartar da komai. Saboda ina tsoron maka halin yaran zamani, kada ta baka kunya Alhaji. Yaran yau baa sha musu alwashi irin wannan. Shima sai a lokacin yayi wannan tunanin na cewa ba lallai Amani ta yarda ta auri Alhaji Sadi ba in aka yi laakari da yawan shekarun sa. A sanin da yayi wa Amani bata taba nuna tana shaawar a yi mata aure ba, tafi shaawar cigaba da rayuwar ta cikin hutu a gidan su, cigaba da tabara da wadaka da dukiyar mahaifin ta, ta hanyar yin kwalliya ta kece raini da sanya sitturu masu karshen tsada da hawa duk kalar motar data ke so wato yawan canza mota new mdel duk shekara, burin ta kenan. Rana daya azo a ce an bada auren ta ga tsoho abokin baban ta don cimma wani kuduri na siyasa, abin zai zo mata banbarakwai, shima ya san ya daukowa kan sa Dala babu gammo. Dama Amanin ga ta nan ga kamar ta wajen hankali da tarbiyya. Har suka iso ofishin Alhajin babu wanda ya kara magana a cikin su, Alhaji na cikin taraddadin yadda zai fuskanci Amani da maganar. Mukhtar da ke tuki na kokawa da numfashin sa dake faman kai kawo a tsakanin kirji da zuciyar sa. Kwana biyu a tsakani Alhaji na ta nan nan da Amani, ya rasa ta inda zai bullo mata da zancen Alhaji Sadi, ya tuna lokacin canza motar ta yayi bari ya nemo motar da take mafarki in yaso yace mata Alhaji Sadi ne ya kawo mata a matsayin goron na gani ina so, ga Alhaji Sadin ya takura yana so ya bashi izni ya fara zuwa zance. Ya san in bay a yi da gake ba zai sha kunya idan Alhaji Sadi ya tare ta da zancen kafin shi. Don haka yau dai yayi kundumbala ya kira Mukhtar falon sa. Suka zauna shi da Alhajin cikin dakin sirrin Alhaji, Alhaji Usman yace Mukhtar na yi abinda ya zo ya dame ni, har yanzu na kasa gaya mata zancen nan, jiya ta zo min da admission na son tafiya karatu a jamiar Queen Mary, ta ce tana so in yi mata iznin tafiya karatun digiri na biyu, ga Alhaji Sadi na maganar aure nan kurkusa, so yake in bashi izni ya fara zuwa ganin ta na rasa ta inda zan bullo mata. Mukhtar kamar yayi dariya ya dai gintse ya ce Alhaji Amani yar ka ce, me yasa kake shayin ta? Hakan bai dace ba ko kadan Alhaji yace rikicin ta nake tsoro, baka san ta bane, wanizubin kamar sarka take fadi ki rikice ta fannin rikici, sau da dama in ta rikice min kamar mahaifiyar ta take komawa, bana sanin ta ina zan shawo kan ta. Mukhtar na so ya ce ita siyasar dole ce da zaa saida farin cikin ya domin ta? A fili kuma yace Alhaji kamata yayi ka kirawo ta ka zaunar da ita ka gaya mata hujjojin ka kamar yadda ka gaya mini, na tabbata bayan rikicin, zata zo ta fahimta tunda dai kana son takarar nan, in ya so daga baya in ta gama rikicin zata yi biyayya, zan taya ka tausar ta. Da wannan shawarar ta Mukhtar ya dogara, washegari ya kira Amani, ya kawo takardar sabuwar mota da mukullin ta ya bata, ya ce Tafisu na ji kina korafin injin motar ki yana kara, nace bari kawai a sake wata, kafin ki zama Amarya. Amani ta karbe mukulli da murna tace My Daddy like no other, godiya nake, kamar ka san na dade ina son Lamborghini, Allah ya bar mini kai Baba na yace ai yau kyautar ba daga ni ta fito ba, daga Alhaji Sadi ne, ai kin san shi ko? Wannan abokin nawa da yazo satin da ya wuce? Amani ta ce ni kuwa na san shi, wannan mai katon cikin kamar kwaryar kindirmo, da idanu kamar na soyayyar gyada, yana kallon mutane tamkar mage ta ga bera. Alhaji ya kama baki yace Amani ban san ki da cin zarafin na gaba ba, shi da ya gan ki ya yaba da ke ya nemi auren ki cikin girma da daraja a hannu na da alkawarin zai tsaya min sai inda karfin sa ya kare in samu takara. Idan na samu kujerar ai ke zaki fi kowa morewa da jin dadi. Amani tayi sakale! Tana kallon bakin Alhaji tana cewa a ranta ko Daddy ya fara shaye-shaye ne? A fili tace Daddy ban gane komai cikin maganar ka ba, wace Amanin? Ni? Kuma takarar me ka ke magana? Alhaji ya sassauta murya cikin lallashi ya shiga yi mata bayanin yarjejeniyar su yadda zata fahimta. Sai Amani ta sunkuya ta rike ciki ta daddage ta hau zuba dariya tana cewa, Daddy! Dariya ta ci karfin ta in ta tuno kamannin Alhaji Sadi, har ya fi Daddyn ta muni da tsufa, da kyar ta tsahirta dariyar ta ce wato Daddy kawai kace ka sayarwa da abokin ka yar ka Amani bisa yarjejeniyar siyasa, to wallahi ko shugaban kasa zai tsaya maka ka samu bazan aure shi ba. Ai ba mijin aure na rasa a duniya ba, da sani na nake korar su, don lokacin aure na bai yi ba. Duk duniya ban ga mijin da zan iya so ba Daddy, mai yiwuwa ma baa haife shi ba, saboda ba kowa zan iya aure ba sai wanda zuciya ta take matukar so. Alhaji ya ce Amani kada ki yi min rashin kunya, tsakani na da Alhaji Sadi amana ce. abota ce ta kwarai, yafi karfin ya nemi alfarmar auren ki in hana shi. Amani da yake kunyar ta ragagga ce sai cewa tayi Daddy ka rage son duniya, na rantse da Allah ba don abota ka amshi wannan maganar ba sai don son Mulki, ka manta cewa (power is transient), ammma farin cikin yar ka guda daya (has to be eternal), ban san me kake nema kuma a duniya ba, da zaka mayar da ni hajar siyasar ka. Ta soma kukan ta na halitta na shagwaba kamar marainiyar da aka fadawa mutuwar iyayen ta, na yau har da sheshshekar kukan gaske. Kukan da ya fi komai dagawa Alhaji hankali. Cikin kukan ta ce wallahi Daddy bana so, bazan aura ba, ta yaya recently na gaya maka na samu admission ina so ka yi min izni in wuce Masters dina zaka kawo wannan maganar? Alhaji ya soma fusata yace to in ke kika haifi kan ki sai ki tafi Masters din mu gani, magana na gama, na baiwa Alhaji Sadi auren ki, don kin ga ina sakar miki da yawa shi yasa kika raina ni, karatu kin gama shi daga kwalin digiri ba kari, dama ana ta cewa na barki babu aure. Amani ta mike tana cewa to Daddy sai ka zaba ko ni ko abokin ka, idan aka takura min kan maganar nan na rantse zan sha poison in mutu ka huta, da dai in auri wannan mummunan tsohon. Gaban Alhaji ne yayi mummunar faduwa, exactly irin kalaman da mahaifiyar ta Jalan ta furtawa nata mahaifin a gaban sa, ranar da ya bashi auren ta. Kuma tabbas ta sha poison din bayan haihuwar Amani, bashi da tabbacin tana raye ko ta mutu, don tun ranar da ya kai ta asibiti ya damka wa mahaifin ta takardar sakin ta, bayan ya dauke jaririyar yar sa, bai kara waiwayar ta ba, a dalilin ta dade tana kunsa masa bakin ciki mai yawa saboda kawai ita kyakkyawa ce shi ba kyakkyawa ba. Allah wadaran masu aure don kyau, Alhaji ya fada a fili cikin tuno dararen da suka shude tsakanin sa da Jal'an. Allah yasa kada Amani ta yo halin mahaifiyar ta tarihi ya maimaita kansa tsakanin ta da Alhaji Sadi Talle, don shi aure da Alhaji Sadi ya riga ya gama zartar da hukuncin yin sa ba zai fasa ba. Amani ta wuce zuwa sama ba tare da ta san halin tunanin data jefa mahaifin ta a ciki ba. Ya dade a zaune a wajen yana tunanin mafita ko ta inda zai bullo mata ta yarda da auren Alhaji Sadi, ba abinda yake hangowa kansa sai gashi a kan kujerar gwamna, ya tuna Mukhy ma yace zai taya shi lallashin ta, da wannan tunanin ya shiga bayan gida toilet na dakin sa domin ya yi wanka ya kwanta, yana sanya kafa cikin kwamin wankan ya zame ya fadi a ciki, wata irin muguwar faduwa da ta yi sanadin kai Alhaji Usman asibiti cikin daren, Allah ne ya kawo Haj. Rabi dakin taji karar da ya saki, ta fado bandakin tana salati. Maigadi da mai ban ruwan shukoki ta kira suka kinkimi Alhaji suka sa a mota, Malam Tajuddeen ya tuka motar suka yi asibiti da shi. Sai da suka isa asibitin Malam Tajuddeen ya kira Mukhtar. A gigice Mukhtar ya zo asibitin, shi yasa hannu ya biya komai likitoci suka soma baiwa Alhaji taimakon gaggawa. Zuwa safe babban likitan da ke duba Alhajin ya tabbatar ma Mukhtar Alhaji ya samu stroke wato rabin jikin sa ya daina aiki. Kasancewar dama yana da hawan jini da suga masu tsanani. Mukhtar ya saka fuskar sa cikin tafukan sa ya na ambaton innalillahi wainna ilaihi rajioun. Tabbas dan Adam ba a bakin komai yake ba. Jiya jiyan nan suna tare da Alhaji lafiyar Allah yana kasafta yadda zasu ci duniya da tsinke da kudin talakawa idan ya zama gwamna yau a ce rabin jikin sa ya mutu? Amani tana gida bata san abinda ke faruwa ba, tun dare take waya da Hamidah tana kuka tana gaya mata Daddy ya daina son ta, zai aurar da ita auren dole ga tsoho, kuma saan sa saboda siyasa. Tace Hamida na tabbata ba zugar kowa bane wannan aikin annamimi Mukhtar ne, don ni Daddy bai taba yi min zancen aure ba, na tabbata shi ya zuga shi tunda yanzu baya jin maganar kowa sai tasa, kuma na tsole masa ido a gidan yana so a kawar da ni ya ji dadin cuta ma uba na. Ta fyace hanci ta ce Hamdy na shiga damuwa don ban ga alamar Daddy da wasa yake maganar nan ba, kamar auren da yake son yi min din is based on political aspiration din sa. Hamidah yarinya mai hankali tace "wato Bestie ba zaki daina tsanar bawan Allan nan ba babu gaira babu dalili? Zato zunubi ne, how sure are you shi ya zuga Daddy? Ke da kan ki kin ce is based on his political aspirations sai ki cire Mukhtar a ciki tunda shi ba dan siyasa bane. Ba lallai ya zama Daddy bai da ra'ayi sai nasa ba, kamar kina exaggerating alaqar tasu. Sabida kin damu da shi, kuma ba kya son sa". Amani ta saki tsaki tace "na damu da shi a gidan wa? Ai ni kawai so nake ya bar gidan mu" Hamida tace "ki ji da matsalar ki ta auren tsoho ki kyale bawan Allan nan ya sarara" "shawara zaki bani ko zagi na za ki yi Balewa?" Hamidah na dariya tace "duk wanda kika zaba shi zamu yi" ta ce "to shawara ta gaskiya nake so ki bani" "shawara ta itace ki yi wa mahaifin ki biyayya whatsoever hujjar sa na aurar da ke ga abokin sa, wanda yayiwa iyayensa biyayya baya taba tabewa. A karshe ina so ni da ke duka muyi istikhara mu nemi dacewa da zabin Ubangiji ba abinda zuciyar mu tafi karkata ba". "Menene istikhara!" Amani ta tambayi Hamidah. "Sallah ce ta nafila da Annabi SAW ya koyar ta neman zabin Allah kan kowanne al'amari da sulusin dare" Hamidah ta gaya mata yadda zata yi. Ta kuma daure ta yi din. Ita da kan ta tayi mamaki ganin cewa zuwa washegari data tashi sai taji ta wasai babu damuwa a dalilin istikharar data yi. Har jira take Alhaji Talle ya zo yayi mata bayanin dalilin sa na kutsowa rayuwar ta. Da abinda yake nufi da Baban ta, na cewa wani suyi yarjejeniya sai kace an gaya masa ita hajar sayarwa ce. Mai aikin ta ce ta kwankwasa mata kofa. Tana budewa a fusace tace "lafiya da sassafe haka kike damuna da bugun kofa?" Rakiya ta karya wuya ta langabe cikin lallashi ta ce "kiyi hakuri, Haj. Ce tace in gaya miki ki fito ku tafi asibiti Alhaji na can babu lafiya". Gaban Amani yayi mummunan faduwa, abinda ya zo ran ta shine irin rabuwar da suka yi ita da Daddy din daren jiya, kada dai shi ya saka a ran sa har ya kwantar da shi rashin lafiya? In haka ne kuwa zata yi masa biyayya iyakar iyawar ta ba Alhaji Sadi ba, ko kuturu ya kawo ya aura mata zata yi biyayya da dai a ce wani abu ya faru da Daddyn ta a kan ta. Sabida gigicewa a haka ta fito da kayan barci a jikin ta, sai Rakiya ce ta biyo ta da mayafi bakin mota. A yadda ta ga Mukhtar zaune a reception din asibitin ya hada kai da gwiwa, yayi jajawur abun ki da farin mutum ainun, hatta idanun sa sun yi jawur ya tabbatar mata condition din na Alhaji ba mai dadin ji bane. Ita ta sani ko Uban sa sai haka, a irin halin da ta gan shi a ciki. Suna hada ido ya sunkuyar da kai, ta karasa da sauri tana tambayar sa me ya samu mahaifin ta? Mukhtar ba baki sai ido ya bi ta da shi. Ta koma ga Haj Rabi tana tambaya. Babu wata damuwa a tare da ita tace "sun ce ya samu stroke ne, barin jikin sa ya shanye, Amma zasu dinga yi masa gashin kashi har ya samu lafiya". Daidai lokacin da aka gangaro Alhajin a kan gadon marassa lafiya aka bashi daki na musamman. Amani ta rasa inda zata tsoma ran ta, sai kuka take yi a dakin. Haushin ta ya ishi Mukhtar yace "ko ki yi shiru ki yi masa addu'a, ko ki koma gida" ta galla masa harara da jajayen idanun ta tace "Uban ka ko nawa?" Ya ce "to zage ni" ta yi tsaki ta ce "in aka zage ka din me za'a yi?" Kai tsaye yace "banida lokacin ki yanzu, amma ranar da kika kuskura kika zagenin, zaki ga me za'a yin". Haj Rabi ta yi salati tace "Amma ku kuwa an yi sakarkaru, ta yaya mutun yana kwance rai kwakwai mutu kwakwai kuna neman dambe da juna a kan sa? Ku kuma irin naku hankalin kenan maimakon ku dukufa yi masa addu'a?" Mukhtar ya juya ya fita daga dakin ya bar su. Amani ta nufi Alhajin da sauri ta kura masa ido yana barci kamar ba abinda ya faru da shi. Hawaye fal idonta ta soma magana. "Daddy in dai a kan auren da kake son yi min ne ka saka kan ka a wannan yanayin na roke ka ka tashi mu tafi gida, na amince ka aura min duk wanda ka ga dama, don Allah Daddy". Kuka ya ci karfin ta. Haj Rabi tace "toh? Ashe ke kika jawo masa? To ta Allah ba taki ba ban shirya yin takaba yanzu ba, in bai tashi nan da sati daya ba wallahi sai dai ku sallame ni don ban shirya yin takaba yanzu ba". Amani ta juyo ta dube ta da fusatattun idanu ta ce "in kika kara shiga sha'ani na sai na karawa wannan katon bakin naki tsini, ina ruwan ki da ni? Ko ina shiga sabgar ki? In ni na jawo masa Uban ki ko nawa? Ko kin haifa masa ko gunduren kashi ne? Ba tumunin takabar kike jira ba me kike so in ba shi ba?" Haji. Rabi ta kama baki, tace "ke mara kunya, wadda bata ganin mutuncin kowa, na fi karfin ki yimin diban albarka don uban ki nake aure, shashasha da bata san komai ba sai sangarta da rashin kunya". Likita ya shigo dakin ya na cewa "haba! Haba bayin Allah. Yaya zaku tsaya kan mara lafiya kuna daga murya? To daga yau mun yafe zuwan ku. Mukhtar kawai muka yarda ya zo har sai ya dawo gida". Amani da ta riga ta zo wuya, ga haushin Mukhtar ga na Haj Rabi ga kuma na wannan likitan yanzu. Ta ce "idan uban ka ne shi sai ka hana ni zuwa in gani" likita ya juya ya fita kafin yarinyar ta soma kai duka, ya fara tunanin tanada aljanu amma na rashin kunya da rashin tarbiyya. Ta yi tsaki tana fadin "Daddy zan sa a dauke ka daga rubabben asibitin su ka ji? Jidda zan kai ka a duba ka sosai. Get well soon my Daddy". Ta sunkuya ta sumbaci goshin sa, ta gyara masa rufuwa da bargo duk Alhaji na barcin allurar barci bai san me suke yi ba. Waje ta fito tana tunanin abun yi, tana neman mataimaki da zai taimaka mata wajen fidda Daddy saudiyyah. Amma Mukhtar shine yafi dacewa da ya taimaka mata din gashi ta gama caccakar sa ta masa gorin Uba. Da sanyin jiki ta hau neman sa a reception amma bata gan shi ba. Bata san ma shi a lokacin yana can yana cuku_cukun samun visar tafiya da Alhaji kasar Faransa ba. Ya gayawa Haj. Rabi niyyar sa ita kuma tace bazata jinya ba, saidai Amani ta je. Ko kwai bata ajiye masa ba bazata jinyar shanyewar jikin sa ba, alhalin ko tumunin takaba bai rubuta a bata ba komai na Amani ne. don haka ta karata da uban ta ita kadai. Mamakinta ya kusa kashe Mukhtar a tsaye, to dama ya bata hakkinta ne a matsayin ta na matar Alhajin. Amma Shima baya so ta bi shi don baya jin zata yiwa Alhaji kulawar data kamata, wannan aikin sai namiji kakkarfa. Yana tsaye a gate din gidan suna magana da Malam Tajudden yana gaya masa maganar zai tafi Abuja da Alhaji don Nemo visar tafiya asibiti a Paris. Amani ta shigo gidan tare da Malam Audi Mai baiwa shukoki ruwa wanda shi ya tuka su zuwa asibiti. Tajudden ya juya ya dan kalle ta sai yace da Mukhtar din ka sanar da Amani?" Yace "kaima ka san wannan yarinyar bata cikin 'yan shirgi na saboda rashin kunyar ta. Dazu har zagi na ta kusa yi fa Tajudden". Malam Tajudden ya dafa kafadar sa cikin lallashi yace "ka yi hakuri ka manta, na sha gaya maka sai kayi hakuri da ita in dai kana son albarkar Alhaji. Daure ka gaya mata saboda hakkinta ne ta sani, son samu ma ku tafi tare ta zama a kusa da mahaifin ta duk sanda ya bude idon sa ya ganta don itace sanyin idaniyar sa". Malam Tajudden ya karasa inda Amani ke kokarin fitowa daga mota yace "ran ki ya dade Malam Mukhtar na son magana da ke, a kan lafiyar Alhaji ne" Amani ta dalla masa harara tace "shi kurma ne? Ko Kai ne bakin sa? Bana son kinibibi bace min da gani". Mukhtar ya karaso wurin yana cewa "in kika sake alaqanta ni da rashin ji sai na buge bakin ki, wannan dattijon bai haife ki ba?" Ai kuwa Amani ta fusata fiye da farko tace "ka fita hanya ta don ni ba tsarar yin ka bace, mai kama da jan kosai kawai" ya kusa ya buge bakin nata ya tuna mace ce, ya kuma yarda Amani tayi fama da juvinile deliquency a shekarun kuruciyar ta, wadanda suka mika mata har zuwa yanzu da take shekaru ashirin. Bata ganin kan kowa da gashi. Har ta wuce shi ta tuno maganar asibitin Alhaji sai ta dawo tana sosa keya tace "for your information inaso zan kai Alhaji asibiti a Jiddah don ban yarda da kwarewar wannan asibitin da ka kai shi ba". Mukhtar ya hadiye haushin ta yace "France zan kai shi" tace "a wane dalilin zaka kai shi inda ban sani ba?" "Saboda ni Dan sa ne idan baki sani ba, daga yau ki sa a ran ki ba ke kadai ya haifa ba uwar tutiya da uban da bata iya masa biyayya" "to ban yarda ba Jidda zamu je. Akwai asibitin da suke duba shi a can, tun ina karama can yake zuwa". Musu ya kaure tsakanin Muktar da Amani, a karshe ya ce "wait pls, wai in aka bar ki kika kai shi Jiddan zaki iya jinyar sa ne? Alhaji fa yanzu komai sai an masa har wanka da tsarkin lalura, kina mace me zaki iya kulla masa? Na fada miki ki sakar min komai kawai, don ba abinda zaki iya kullawa". Idanun ta fal hawaye, don ta tsani a dinga nuna mata gazawa don tana mace. Shima Alhaji haka yake mata, komai tace zata yi sai yace Mukhtar zai yi don ita mace ce, shi yasa take kishin sa da cewa he snatched away her father's love from her. Mukhtar ya ga ta rasa ta cewa a wannan gabar, sai ya juya zai tafi ya bar ta a wurin. Sai ji ya yi ta ce da siririyar muryar ta mara amo. "To ka shirya tafiyar da ni, in ba haka ba hankali na ba zai kwanta ba in bana tare da shi, ban kuma san halin da yake ciki ba". Mukhtar ya daga gira ya ce "alright. Yanzu kika yi magana Ma'am". At long last. Mukhtar Diffa ya sake yin nasara a kanta. ***** ****** ***** Kasancewar Mukhtar, Alhaji da Amani duk suna da 'Schengen Visa' yasa basu sha wahalar gama shirin fita da Alhaji zuwa Birnin Paris ba. Inda tun kafin su zo Mukhtar ya gama yi musu kowanne tanadi ta yanar gizo da asibitin Hôpital Saint-Louis dake tsakiyar babban birnin kasar na Faransa wato Paris. Ranar Lahadi suka daga zuwa Paris daga birnin tarayya tare da Alhaji wanda zuwa lokacin yana cikin hayyacin sa sai dai baya iya motsa kowacce gaba ta barin daman sa. Tuni asibitin na Hôpital Saint-Louis sun shirya musu dakin da Alhaji zai yi jinya. Babban daki ne na alfarma ciki da falo a rukunin dakunan physiotherapy department. Daga zuwan su kuwa bayan Mukhtar ya gama settling bill din asibitin, likitoci na musamman suka fara yi wa Alhajin dukkan kulawar data dace da masu irin lalurar sa. Mukhtar da Amani dambe ne kawai basa yi kullum saboda sain sa, don a kan baiwa Alhaji madara ko tea ma kadai kullum sai sun yi fada. Kowanne yace shi zai yi. Mukhtar a hotel ya kama nasa dakin wanda ba shi da nisa da nan da asibitin. Amma kullum tun safe har dare yana dakin majinyacin, shi yake yiwa Alhaji alwallah, wanka, tsarki da komai. Tare da taimakon ma'aikatan jinya maza. Rannan Amani har da kukan ta, tana fadin duk ya kwashe ladan ya bar ta. Bayan ita ce da uban shi dan karo ne. Mukhtar ba kasafai yake tanka mata ba amma a sanda ta fadi hakan sai da ya kusa yin murmushi, amma ya shanye abinsa, kada ma ta ga murmushin sa, a ran sa ya ce na ji din. Dan karo kore dan gida kenan!. Shi ya san da ace gorin Uba na tsiro, da yanzu babu masaka tsinke a jikin sa sabida gorin Amani na Alhaji ba Uban sa bane. Wani zubin yafi gane yayi mata banza wanda hakan yafi kona mata rai, har gara ya amsa mata su yi wa juna wankin babban bargo yadda suka saba tun a gida ta fi ganewa da samun biyan bukata. Duk fadan nan da suke yi kullum Alhaji na jin su, don wani lokacin har sai ya daga musu hannun sa mai lafiya alamar yana rokon su yi hakuri su bari. A ran sa ya rasa dalilin wannan rashin jituwa, gashi yanzu duka burin sa ya taallaka a kan mayar da su abokan rayuwar juna wato su zama maaurata karkashin inuwar aure shine kadai burin sa na karshe a duniya. Kuma abinda zai bashi kwanciyar hankali a yanzu, tunda ya yarda yanzu kam ya nakasa, ba ya jin kuma zai sake tashi a kan kafafun sa nan kusa yadda yake jin jikin nan nasa. Sannan Alhaji babu baki. A kwance yake kawai yana karbar treatment amma yana hankalce da duk wani takun sakar Mukhtar da Amani mai saka shi a damuwa, don shi ba haka yake son gani daga gare su ba, so yake ya ga Mukhtar na kula da Amani kamar yadda zai kula da kanwar sa ta jini. Ita kuma ta dinga respecting din sa tamkar Yayan ta. hakan kawai yake so daga gare su. Kullum Alhaji na hango kujerar gwamna daga nesa a idanun sa, sai ya ji wani bakin ciki ya rufe shi. Tun farko me yasa ya jawowa kan sa maganar siyasar nan? Bayan duk daukakar da ya dade yana samu a siyasa karkashin jam'iyyar Action Congress? Watakila da bai kawo zancen ba da duk bai fada a damuwar data yi masa wannan sanadin wahalar ba. Ya dade da sanin conditions din sa na hawan jini da sugar Amma ya zo ya saka damuwar aurar da Amani a ran sa har ta kassara shi. Alhaji Sadi din bai san suna yi ba, ko irin abinda zancen auren da yayi sanadi ya janyo masa yanzu. Bakin Alhaji ya karkace baya iya magana amma kwarai ya ke so ya gayawa Mukhy maganganu da yawa masu matukar muhimmanci ciki har da son ya kira masa Alhaji Sadi Talle a waya don ya warware yarjejeniyar su. Ya hakura da kujerar gwamnan, yanzu ta lafiyar sa yake, zai baiwa Amani dama ta koma karatun da ta ke so a Jamiar da ta ke mafarkin zuwa wato Queen Mary University of London har Allah ya bashi lafiya idan ciwon sa na tashi ne. Idan kuma ba na tashi bane zai yi kokari ya cika umarnin da zuciyar sa ke bashi akan rayuwar Amani dungurungum, wadda yake ganin shine kadai mafita ga rayuwar ta da tasa! Wadda ba zai taba bari ta rushe ta hanyar fadawa hannun mijin da ba zai rike masa ita da so da kauna da amana ba, da kuma kiyaye mata dukiyar da ya karar da shekarun rayuwar sa yana tara mata ta hanyoyi daban daban na yaki halak da yaki haram, duk don ta ji dadi kada ta sha wahalar duniya. Wanda ta kowacce fuska ya san Alhaji Sadi Talle bai cikin wannan tsarin na rukunin mutanen da ya ke yi wa rayuwar Amani wannan tanadi. To wa ya dace? Zuciyar sa a take ta halarto masa da kyakkyawar amsa cewa ba wanda ya dace da zama mijin Amani wanda zai cika dukkan wadannan attributes din da yake so a tare da mijin Amani, ya zame mata garkuwa kuma mijin marainiya, ya tallafi dukiyar ta da gaskiya, ya kuma saita dabiu da tarbiyyar ta da bai samu damar yi ba sabida tasirin son da yake mata kamar Mukhy din sa. Wato yaron sa kuma mataimakin sa Mukhtar Diffa. **** ****** **** Kamar yadda yake ga cutar stroke saidai a ji sauki ba dai a warke sumul kalau gaba daya a lokaci guda ba, to hakan ce ta faru da Alhaji Usman Faskari da aka fi sani da Hon. Faskari. Yau satin su guda kenan a asibitin. Ya ji sauki a cikin jikin sa don yana gane duk wanda ke kan sa ya kuma fara magana amma bata fita sosai, yana zama in an jinginar da shi a jikin filo, daga baya Mukhtar ya samu hanyar da zai dinga jin abinda ke ran Alhaji, wato ta hanyar rubutu da hannun sa mai lafiya don baa iya gane abinda yake fada. Mukhy yayi sallama ya shigo dakin asibitin da Alhaji ke jinya hannayen sa rike da ledoji na sayayyar abinci da yayo musu, a kalla likita ya ce zasu yi wata guda anan kafin a basu sallama, Amani dake zaune dai- dai kan Alhaji ko ta amsa sallamar tasa. Ta maida hankalin ta ga hirar da ya samu tana yi wa Alhaji cikin kunnen sa. Wannan abu bai yi wa Alhaji dadi ba, yayi burun-burun din maganar sa duka basu gane me ya ce ba amma Amani ta gane fada yake mata kan kin amsa sallamar Mukhtar, tayi mirsisi kamar bata gane me Alhaji ke nufi ba, sai Mukhtar ya ajiye ledojin da ya shigo da su akan bed side, daya a gaban Amani, ya karasa gaban Alhaji ya kama hannun sa yana tambayar sa kome yake son cewa? Alhaji yayi masa alama da ya bashi biro, Mukhtar ya dauko jotar da suke magana ya bashi tare da biro, Alhaji yayi rubutu ya mikawa Amani, da ta karanta zumburo baki tayi don Alhaji cewa ya yi bai ji dadi ba da bata amsa sallamar Mukhtar ba, amsa sallama ga musulmi wajibi ne. Ta ce to Daddy in dai amsa sallamar wannan mutumin ce zan shekara ban amsa ba, tunda shima ba ya amsa tawa. Mukhtar yayi dan murmushin da ya kara masa kyau, ya matsa gaban Alhaji yace Alhaji ka ga kuma ni sayayya ma na yo mana har da ita, wai ni mai kanwa, amma ko nagode na tabbata ba zata ce ba. Amani tayi maza ta ce Daddy ka fada masa kada ma ya kara sayo komai da ni, kada ya kara alaqanta ni da shi, bamu hada jini ba bamu hada komai ba, idan ina son abu na san inda zan je na sayo ba shi kadai ya san hanya a garin nan ba. Mukhtar ya ce a ran sa kin yi da dan halak. Amma saboda ganin damuwar da ke kan fuskar Alhaji sai bai tanka mata ba, amma ya ji haushi sosai da wannan gorin nata na basu hada jini ba basu hada komai ba, dama kullum ta tashi rashin mutuncin ta ta kance masa dan karo, ai Alhaji ba uban sa bane. Sayayyar kayan ciye-ciyen snacks din McDonalds da ya yo mata da ya lura su take son ci kullum, bata da cin abinci sai su, ya dauke ledar daga gaban ta ya kaiwa nurses din da ke kula da Alhaji, bayan duk kamshin pizza ya gama cika ta, ya tado tsohuwar yunwar cikin Amani. Amma sabida ki-fadi irin nata tabe baki kawai tayi. A ran ta kamar tayi kuka, a kufule ta ce to da ka fita da abincin ni me zan ci? Ya ce ai na dauka kin san hanyar inda ake sayowa? Alhaji kan sa sai da ya harare ta don yana jin duk yadda aka yi. Mukhtar ya zauna yana cin shawarma yana korawa da sassanyan lemon tuffaha bai kara kula ta ba. Yadda yake taunar sa gentle-gentle ma kadai abun shaawa ne ba zaka gaji da tsayawa a gefen sa kana kallon kyakkyawan bakin Mukhtar ba. Ta yi kwafa ta mike don ta dauro alwalar sallahr azahar, amma me? Sai ta ga bakon watan ta ya zo, ga shi bata yo guzurin kunzugu daga gida ba. Ta rasa yadda zata yi, ta kasa fitowa daga toilet din, don ta san bada jimawa ba zata soma staining jikin ta. Gashi yanzu ta gama cewa kada ya kara sayo mata komai ta san hanya, kuma da kunya yanzu shi ba mijin ta ba ba komai ba ta aike shi sayen kunzugun mata. Da taga cigaba da zaman a toilet zai sa har jinin ya soma naso, cikin shagwaba irin tata sai kawai ta fashe da kukan da ta san yana rikita Alhaji. Daga Mukhtar har Alhaji ba wanda bai jiyo kukan nata ba, Alhaji har gaban sa sai da ya fadi don ya dauka wani mummunan abun itama ya faru da ita a toilet din, tunda shima tsautsayin da ya same shi a toilet ya same shi. Inkiya da buruntun magana ya hau yi wa Mukhtar da hannun sa mai lafiya a kan don Allah ya duba masa ita ya ga ko menene, shi Mukhtar kunya ce ta kama shi, ta yaya zai bita toilet alhalin ba matar sa ba ce ba kuma kanwar sa ba? Sai yanzu ya ga rashin dacewar tahowar su ba tare da sun lallaba Haj. Rabi an taho har da ita ba, don sau da yawa in ya shigo dakin sai dai ya koma in ya ga Amani ta baza dogon sassalkan gashin kan ta tana tajewa babu mayafi a jikin ta, wannan gashi yana matukar kidima Mukhtar, ita kuma ta kasa sabawa da barin lullubi a jikin ta, kamar yadda take yi a gida a nan ma haka take rayuwar ta babu takura saidai shi ya takura ko ya rufawa kan sa asiri ya fice in ya kasa jure kallon ta, sabida dalilai na shariah, ita kuma idan ta zauna da lullubi duk sai ta ji ta takura don bata saba ba, shi da kansa ya gaji ya yi mata magana jiya da kakkausar murya a gaban Alhaji ya ce mata ki dinga saka lullubi a kan ki idan ina nan. Me yasa ke baki san duk wani ya kamata bane? Me yasa Baki gudun fitsarin shaidanu a kan ki? A lokacin zumbura masa baki kawai ta yi bata tanka masa ba. Bata san cewa wannan zumbura bakin ba karamin kyau yake yi mata ba, ya kara fiddo zahirin kuruciyar ta a fili, ko ina ruwan Mukhtar da lullubin ta da zai nemi takura mata? Lullubi zata wuni tana yi saboda shi ko me? Shi waye dinta? Me ye gamin ta da shi baya ga kasancewar sa maaikacin Baban ta wanda ya dace a ce respect yake bata? Wannan mutum akwai wuce gona da iri in ji Amani. Ko an gaya masa don shi ta zo jinyar? Ko zaman sa ta ke yi a asibitin ba zaman jinyar mahaifin ta ba? Abinda ta fada a ranta kenan ba tare da ta tsinka masa ba wai aka ce kulawa ma yabawa ce. Mukhtar ya san yanzun ma in aka bibiya abinda take yiwa kukan nan bai kai ya kawo ba, sangartar ta ce kawai don bai ji alamar faduwa ko makamanciyar ta ba. Alhajin ba lafiya ma ba zata bar shi ya huta da shagwabar ta ba. Amma yadda ya ga Alhaji ya shiga damuwa sai tausayin sa ya kama shi, wannan ya tasa ko fitinanniya, ya mike zuwa kofar toilet din ya na kwankwasawa ya ce ke lafiya? Ki fito menene? Amani ta rasa abunda zata ce masa, dole ta share hawayen ta fito tana tafiya kamar a kan dan yatsan ta ko wadda kwai ya fashewa a ciki, Mukhtar ya hau kallon wannan tafiya kamar ta mai koyon tafiya ya rasa me take ciki haka? Ita kuma bata ce masa komai ba don ta san da kunya kuma ta aike shi wannan hidimar, bayan gwaleshin data gama yi yanzunnan, sai ta dauki Jakarta ta fita da sauri don ta taimaki kanta. Allah ya taimaketa a nan cikin asibitin ta samu akwai pharmacy, ta sayo pad ta dawo ta sake shigewa toilet wannan karon da gudu-gudu ta rufe, bata ko kula tambayar da yake yi mata ba daga inda yake tsaye harde da hannuwa a kirji. Are you okay? Tayi masa banza. Ba karamin haushi ta bashi ba da share shin nan data yi, ya kudire a ran sa bazai kara shiga shirgin ta ba har su koma gida. Alhaji ya so a ce yana da baki, ya yi sulhun alkhairi tsakanin Mukhtar da Amani, baya son wannan rashin jituwar tasu wanda zaman su waje daya tsayin sati biyu bai saka sun shaku da juna ko sun daina kyarar juna ba, su daina hamayyar nan mara dalili da shi take sakawa a damuwa da tantamar cikar burin sa a kan su. Shi dai kullum kunnen sa sain sar su ke tada shi daga barci, idanuwan sa basa ganin komai cikin idanun su sai tsanar juna, da rashin jin dadin zama da juna da hantara da kyarar juna. Bai taba jin sun yi maganar arziki a tsakanin su ba tun zuwan su asibitin, ko sentence daya balle a je ga batun gaida juna. Basa amsa sallamar junan su sai a cikin cikin su. Babu mai ragawa dan uwan sa. Gara shi Mukhy yana rage uzzura mata a dalilin kaifin idon Alhaji. Data fito daga toilet ficewa ta yi ta bar musu dakin ta koma reception din asibitin ta zauna a kujera nesa da jamaa ta kira Hamida Balewa. Hamida ta ce mutuniyas ina kika shiga ne? kwana biyu ban ji complain din dan Alhaji ba Da 'yar damuwa a muryar tace tana asibiti tare da Daddy a France, Daddy na ya samu stroke Hamdy ki yi masa addua na san ke mai addua ce mai yawan sallah ce da tsayuwar dare Hamida ta shiga juyayi, a karshe ta jajantawa aminiyar ta, ta ce ke da Haj. Rabi kuke jinyar kenan? Wani mikakken tsaki ya fito kai tsaye daga bakin Amani, tace cikin dan daga murya kema kin san ko da waye, ko baki tambaye ni ba, ni da waye kuwa banda bare ka fi dan gida, yana nan ya hana ni sakat, ya hana ni samun ladan uba na, masifar yau daban ta gobe daban, ke sai ki rantse da Allah yana da gadon Daddy ko tare Alhaji ya haife mu, tare kuma yake so mu rayu dole, ya shiga komai na gidan mu yayi kane-kane ya fi ni iko da uba na yanzu sai ta kama matsar kwallah, Hamida tana so ta yi dariya sabida wannan sakalci na Amani, amma ta san Amani bata cikin mood din da take bukatar a yi mata dariya, don tsakanin ta da Allah take sharing mata damuwar ta, don bata da inda zata je ta fada ta ji sanyi, wannan Mukhy! Ya addabi aminiyar ta, ita kuma haka nan yake burge ta, bata ganin laifin sa ko kankani, da kullum Amanin ke nanatawa, wanda duk ciki in ka saurareta zaka fahimci ba komai ke damun ta ba sai kishin son da mahaifin ta ke ma Mukhtar din. Hamida ta nisa tace kin san Allah Amani, idan har na isa in baki shawara ki dauka to ki koma girmama Mukhtar, ki kaunace shi matsayin dan uwan dake taimakawa Daddyn ki, ki bashi gurbin Yayan da baki da shi, ku zamawa Alhaji Yaya da kanwar sa. I'm sure duk da ban sani ba Alhaji haka yake so ya gan ku, musamman a yanzu da bashi da lafiya ku biyu ne a kans a kuke jinyar sa. Idan ya bar miki jinyar bazaki iya ke kadai ba dole sai namiji dan uwan sa idan ana maganan stroke. Kuma kin ga wannan fadan da kuke ta yi a kan idon Alhaji yana saka shi a damuwa musamman cikin yanayin da yake a yanzu, shi fa Daddy in na fahimta saboda Allah yake son Mukhtar din nan. Hayagagar ki bata isa tasa ya kore shi ba, da zai kore shi da tuntuni ya kora don gudun bacin ran ki. To fadan da yafi karfin ka hausawa suka ce ka maida shi wasa, sai ka zauna lafiya. My friend I want you to stay cool and healthy, kada Mukhy yasa jinin ki ya hau, zuciyar ki ta buga a banza ya yi wa Alhaji da kan sa asara. Ta karasa cikin dariya ta kuma yi maza ta kashe wayar ta. Amani na kururuwar sai tagaya mata me take nufi da hawan jinin ta ta ko bugawar zuciyar ta zata zamo asara ga Mukhtar. Meye manufar ta? Hamida nata dariya ita kadai ta tura mata text. Ga abinda ta rubuta mata. kan ki ake ji kullum a kan sa, kin hana kan ki zaman lafiya saboda shi, watch your actions over him, you care too much for him, listen to your heart and understand the actual feelings. -Yours Hamdy. Amani ta kusa zagin Hamida, ta kira ta back yafi sau biyar Hamida ta ki dauka, kamar ta yi hauka ita kadai wai Hamida ta zageta, zagin da baa taba yi mata irin sa ba, ta rasa wanda zata ce ta saurari zuciyar ta a kan sa sai Mukhtar? Me zata saurara din banda bugun zuciyar ta dake karuwa kullum a kan bacin ran da yake sanya ta kullum? Hamida daga inda take sai murmushi take yi rike da wayar hannun ta, ta dubi fuskar wayar kamar Amani take kallo tana mata murmushin karfafa guiwa, haka kawai ta samu kan ta tana ma aminiyar ta shaawar auren Mukhy din nan, duk da kasancewar sa a karkashin mahaifin ta, ta shiga yi ma Amani adduar samun daidaiton raayi da fahimtar juna tsakanin ta da wanda take ganin ya shige gabanta. A ganin Hamida ba wanda zai iya da ita da halayen ta duk duniya sai wannan Mukhtar din, da tun yanzu yake juya Amani wanda hakan ke nuna zai iya jarumtakar zama da Amani da dukkan halayen ta, ta san zama da Amani sai jarumin mutum, duk kawayen su na makaranta babu wadda Amani bata yi fada da ita ba itama don ta zame mata kamar 'yar uwa ne ko sun yi fada ita da kanta Amanin zata zo ta nemo ta su shirya. A ganin Hamida babu mai iya auren Amani ya juya ta sai jarumin namiji saboda izzar ta. Ta kuma yabawa Mukhtar wajen jure rayuwa kusa da Amani alhali kullum tana kyarar sa da gori kala-kala. To amma Alhaji ya riga ya karbi maganar abokin sa ta kuma ce mata ta yi masa biyayya a kan maganar Alhaji Sadi, yanzu kam ta fi mata shaawar auren Mukhtar yaro dan uwan ta mai halin manya. Zata dukufa taya Amani adduar samun zabi mafi alkhairi a matsayin ta na aminiya ta kwarai. Miji wanda zai taimaka ya saita musu hankalin ta, tarbiyyar ta, addinin ta da nutsuwar ta. Wadanda duk ta rasa a dalilin rashin tashi gaban mahaifiya. Sanda ta koma dakin maghriba ta kawo kai, Mukhtar na yima Alhaji alwallah zai yi sallah yadda yake yi daga kwance, sai ya tabbatar Alhajin ya tada sallah sannan ya shiga ya dauro tasa ya fito, sai ya tadda Amani ta ja ledar nashi abincin tana ci ba kunya ba tsoron Allah fuska tamke, an ce yunwa ba kanwar uwa bace. Girgiza kai yayi ya shimfida dardumar da yake sallah a kai ya tada sallah a gefen gadon Alhaji. Ko da ya idar da sallah bai ce mata don me ta ci masa abinci ba, ya san dama in yunwar cikin ta ta kama ta zata ci ne kullum haka take masa, ba don komai ba sai don kada tace ta gode a duk lokacin da ya sayo masu abinci. A haka sauki ke ta samuwa ga Alhaji Usman, bakin sa da ake ta gasawa ya fara fidda magana sosai, likitocin sa sun ce duk bayan watanni shida zasu dinga zuwa check up, duk da tafiya da kafafu bata samu ba don haka suka ce Alhaji zai dinga amfani da wheelchair. Watan su guda kenan suna jinyar Alhaji amma ba abinda ya canza a alaqar su. Yau suka sauka a gida Mukhtar na turo Alhaji a wheelchair inda Haj. Rabi taje ta taho dasu daga filin jirgi tareda sauran ma'aikatan kamfanin Faskari. Kowa ya zo falo ya jajantawa Alhaji yayi masa sannu da dawowa. Malam Tajuddeen shi ya gaya musu zuwan Alhaji Sadi Talle uku bai samu Alhajin ba, yace kuma layin Alhajin da yake da shi baya tafiya, sun gaya masa Alhaji asibiti yaje babu lafiya, ya ce duk ranar da suka dawo Malam Tajuddeen ya sanar da shi. Ba Alhaji ne kadai fuskar sa ta sauya ba har da ta Mukhtar. Amani tunda ta haura sama ta bar su bata kara saukowa ba. **** **** **** Washegari kuwa tunda safe Alhaji Sadi ya zo cikin rantsatstsiyar motar sa Acura, kai da ganin irin kwalliyar da ya caba cikin sassalkar shadda fara kal, zaka san ba dubiya kadai ya zo ba har da zance na saurayi ga budurwa don fara kafa gwamnatin sa. Mukhtar baya gida yana company don gudanar da ayyukan da suke jiran sa duk da cewa yana rage ayyukan sa daga can asibiti ta kwamfuta wadanda sakataren sa ke tura masa, musamman in Alhaji na barci, zaka same shi yana aiki cikin kwamfuta yayin da zaka samu Amani na harkokin ta cikin wayar ta cikin dakin ba ya ko daga ido ya dube ta, amma a zuciyar sa ya na takaicin ace mace bata da abun yi sai shiga social media, babu lazimi sam babu karatun Alqurani, Amani fa ko addua take son yi sai dai ta roki Hamida tayi mata don a cewar ta bata iya hana idon ta barci, kuma Hamida ta fi ta juriyar tsayuwar dare. A hakan da yake yi ya samu ya rarrage ayyukan kamfani da yawa ta yadda yanzu da ya dawo ayyukan basu cude masa ba, ko da yake yanzu ayyuka sun karu masa tunda shi yake gudanar da duk wanda Alhaji ke yi da kan sa a lokacin da yake da lafiya. Aka yi wa Alhaji Sadi iso falon Alhajin, bisa umarnin Alhajin. Yana shiga ya ga Alhaji cikin wheelchair a zaune yana kallon talabijin. Alhaji Sadi ya ce Ya salamu sallim, ashe ciwon babba ne haka? Yanzu da wadanne kafafu zaka yi takara? Kai bana jin ma jamiyya zata yarda in tsayar da mai shanyayyen barin jiki kan kujerar gwamna tunda ba ni kadai ke da jamiyyar ba. Sannan ya zauna gefen sa ya bashi hannu yana fadin sannu, sannu yaya jikin naka? Kana iya magana dai ko? Alhaji ya ji ciwon wadannan maganganu na Alhaji Sadi, amma ko a fuskar sa bai nuna ba, sai yayi murmushi yace ai ba sai ka gaya min na zama mara amfani ba yanzu, nima na sani, na kuma yarda duniya da dan Adam duka ba a bakin komai suke ba, yau ne kake mutum gobe zaka iya zama rabi gawa ko duka gawa, na yi kurakurai masu yawa a rayuwa ta dana ke neman yafiyar ubangiji a yanzu ba takara ce a gaba na ba, tuni na dade da janyewa. Yanzu zan maida hankali na ne akan ibadah da neman guzurin lahira da nemawa diya ta kyakkyawan Future. Da kyau. In ji Sadi Talle, wannan tunani ne kayi mai kyau, amma ina fatan ba zai shafi yarjejeniyar mu ba. Ka fadi duk abinda kake so daga gare ni in yi maka, koda tsayar da wannan balaraben yaron naka ne na ga alamun sa jajirtacce ne kuma namijin duniya ne ko daga takun sa, yana da leadership appearance, amma bayan ka bani auren Amani, yau da shiri na na zo don muyi ganawa ta musamman da ita. Alhaji yayi murmushi ya ce yadda na fasa takara haka na fasa aurar da ya ta, zan bata yancin ta ne na tafiya karatu ta kuma kawo duk wanda take so da kanta na aura mata, ko da kuwa kai din ne, don haka a adalci irin nawa, na baka damar ganawa da Amani yau, ka ji raa yin ta a kan ka, ka nemi soyayyar ta, in ta amince zan fi kowa farin ciki tunda ba yau muke tare ba na san baka da matsalar da zaa hana ka aure. Idan kuma Amani ta ce bata yarda ba sai kayi hakuri ka nemi wata. Ina Mukhtar ina tsayawa takarar gwamnan Katsina shi da ba ma dan kasar Najeriya ba? Baabzine ne fa! Alhaji Sadi sai ya rasa abin cewa, amma tabbas ya ji dadi da Alhaji ya bashi damar ganin Amani. Ya dauki wayar sa ya kira Amani, da kyar ta daga cikin magagin barci, ta fara korafi Daddy ka san gajiyar da ke jiki na kuwa ka tashe ni da safen nan? yi hakuri Tafisu, sauko yanzun nan amma kisa mayafi don na san ki da shirme. Kafin ta ce komai ya kashe wayar sa ya barta da mamakin ko lafiya yake fadin tasa mayafi? Saboda ya ji Mukhtar din sa na korafi shine shima yau ya koya, wato duk inda takurawa take sai Mukhy ya nemo mata ta hanyar juya kan baban ta da irin raayoyin sa na akida. Tana mitar tana komai ta saka Abaya da mayafin ta da silifas din bakin gado, tana saukowa suka hada steps da Haj Rabi saura kadan Hajiyar ta bangaje ta, Amani ta kauce. Haj. Rabi ta ce ji mana? Amani ta dan dakata da sauka daga steps din ba tare da ta juyo ba. Haj. Rabi ta tako ta iso bayan ta ta soma magana cikin zafin murya. Jiya na nemi saki a gun Baban ki don na fi karfin yi wa mai shanyayyen jiki takaba ko jinya, ni ba gado ba ba komai ba, ya ce magana tana hannun ki, ke kika hana shi sallama ta da tuni ya sallame ni. To don uwar ki ke kike aure na da zaki hana a sake ni? Da sauri Amani ta girgiza kai don bata taba jin wanda ya zagi uwar da ko gani bata taba yi ba sai yau, wadda duk da bata san ta ba, zuciyar ta cike take da kaunarta. Haj. Rabi ta cigaba da cewa. idan kin haifu cikin Usman da Jalan yau ki sa ya rubuta min shika uku, idan kuwa kin ki, in kun ki ji ba kwa ki gani ba. Don wallahi sai na saka masa filo a hanci na karasa shi, ko in saka masa shinkafar bera a abinci ya ci ya karasa, kuma dole a bani tumunin takaba. Amani bata iya ta karasa jin maganganun Hajiya Rabi masu neman fasa mata kwanya ba, ta wuce falon Alhaji da sauri. Ta fado dakin cikin gigita tamkar an jefo ta. Zata yi magana ta ga Alhaji Sadi a zaune, ai kuwa fushin ta ya kara ninkuwa, ta juya za ta koma. Alhaji ya ce Tafisu bakon ka Annabin ka. Ba don jikin ta yayi sanyi ba ta dawo ta zauna, sai don bata son kunyata Baban ta a idon Sadi Talle. Ta daga ido tace me kake so a wajena Malam? Alhaji ya soma gurgura kujerar sa mai tayoyi ya koma cikin dakin barcin sa ya bar su a falon. Babu kunya babu tsoron Allah fuskar sa kamar gonar auduga ya ce me kuwa na ke so ban da soyayyar ki Amani? Wadda nake fatan ta kai mu ga aure nan ba da jimawa ba? Amani ta yi kuta, ta ce ina maka kallon Babana ba don haka ba da na ce an yi furfurar banza, ka so hada ni rigima da Babana Allah ya fi ka, yana zaman zaman sa ka sa shi a damuwar data kai shi ga faduwa, wani ya baka aure na ka bashi takara shin Katsinar taka ce? Halan bai gaya maka cewa ta lafiyar sa yake ba yanzu ba ta sayar da yar sa ba? Aikin banza aikin wofi to bana son naka, ko a kafa aka daura min kai zan kunce in zura da gudu Alhaji Sadi ya ce ke mara kunya! Ya ishe ki haka, kada kimin gorin halitta don duk muni na ban kai na uban ki ba. gara ni ina iya auren shi kuwa me yake kullawa matar sa sai dai ta je waje. Don haka kada ki sake ki zage ni yanzu in tattaka ki a wurin nan. Sai gani suka yi an daga labulen dakin an shigo da sallama. Mukhtar ya bayyana a falon cikin bakaken shirt da wando na NEIMAN MARCUS, sumar nan nannadaddiya ta sha gyara da Argan Oil tayi lub a kan sa har ta sauka kadan a kan wuyan sa. Amani na ganin shigowar sa, bata san me yasa ba, sai taji duk wani rauni na duniya ya rufto mata, ga bakin cikin aj Haj. Rabi da tsoron kalaman ta, ga na wannan mutumin, ji tayi tamkar wani savior ya zo gabanta don ya kawo mata dauki, kawai sai ta mike ta nufi Mukhtar da azama ta rungume shi ta fashe da kuka mai karfi. Mukhtar ya kusa suma a tsayen da yake, sai kawai ya tsaya kamar an kafe shi a bakin kofar ya rike Amani dake kara neman mafaka a kirjin sa, yana kokarin zamewa tana kara rike shi, sai ya ga abin kamar a cikin mafarki amma duk da haka ya iya saita kan sa. Tsawa ya daka mata ya ce sakar ni nace, bana son sakarci. Cikin jin kunya ta cika shi tana kuka tana nuna Alhaji Talle. Ka roki Alhaji ya yi min iyaka da su, shi da Haj. Rabi, ka roki Alhaji kada ya kara bawa mutumin nan damar gani na, tunda ya zage shi ya ci mutuncin sa. Alhaji Sadi ya yi tsaki ya tashi ya fice daga gidan. A ran sa yana cewa ba don albarkar abota ba sai yayi wa yarinyar nan asiri ta rasa mijin aure. Mukhtar ya zuba hannayen sa duka biyun a Aljihu, ya zuba ma Amani ido tana ta kuka, ta cigaba da cewa ka fada ma Alhaji na bashi wuka da nama ya aura min duk wanda ya ga dama amma ban da wannan mutumin kuma na yi masa lamuni ya saki Haj. Rabi. Ka rokar min shi ya gaya min inda uwata take, na yi alkawarin maido masa ita gidannan ko tana so ko bata so. Amma ban yarda ya kara auren kowa ba in dai don siyasa ne ya hakura tunda bashi da lafiya. Tausayin ta ya tsirgawa Mukhtar har cikin ran sa, amma Mukhy da taurin rai irin nasa juyawa ya yi zai bar dakin ba tare da ya ce mata komai ba. Amani ta tsanan ta kukan ta tana cewa ka taimake ni! Mukhtar saida ya dafa kofar ficewa ya juyo ya dube ta, da idanun sa da suka kada suka yi jazir, ba abinda yake gani sai Amani zaune da Alhaji Sadi suna zance, in the first instance ta san bata son shi me ye na saukowa kasa har ta kebe da shi? Sai don ya zage ta zata zo masa da wasu zantuka da basu shafe shi ba? A fusace ya ce me yasa sai ni? Me yasa sai ni zaki aika na gaya wa Alhaji sakon ki? Baki da baki? Baki fi ni kusa da shi ba? Ko ko ni dan aiken ki ne? Mtsw! Yasa kai ya fice daga falon, zuciyar sa da gangar jikin sa da Amani ta makalkale suna vibrating. Kai tsaye mota ya dauka ya bar gidan zuwa nasa gidan da Alhaji ya bashi wanda babu nisa zuwa na Alhajin. Mukhtar yayi rigingine bisa makeken gadon dakin barcin sa ya na tuhumar kan sa akan me ke faruwa da shi haka? Me ke addabar zuciyar sa? Me ke saka zuciyar shi cikin jin zafin Amani, don kawai ya gan ta kebe da Alhaji Sadi? Shin abinda yayi mata anya ya kyauta tunda yau ta zubar da makaman yakin ta ta nuna masa da gaske taimakon sa take bukata??? Why is he so harsh on her??? Duka baya da amsar ko daya, don haka ya ci gaba da tuhumar kan sa yana nemo hujjar kare kan sa daga tuhumar da ya samu zuciyar sa na yi wa kana sa da kan sa a kan Amani. **** ***** **** **** Amani da zazzabi mai zafi ta kwana, don bata iya ganin Daddyn ta ba sai a washegari. Shi da Mukhtar suna balcony Mukhtar na bisa fararen kujerun roba da aka zuba a wurin suna Magana, Alhaji na zaune cikin Wheelchair din sa. Da alama sensitive magana suke yi domin Alhaji har share hawaye yake yi da hannun sa mai lafiya. Abubuwan da yake gaya wa Mukhtar yau ko Amani bai taba gaya wa ba. Yana gaya masa tarihin sa ne da kauyen da ya fito wato Faskari da yadda duniya da dukiya suka rude shi yayi abondoning dangin sa ko ziyara baya kai musu balle ya taimake su, bayan dukkan su talakawa ne na gamu kashe mu masu tsananin bukatar taimako. Yace Mukhtar ban san halin da suke ciki ba yanzu, bani da masaniyar suna raye ko sun mutu sun bar yayan su na garari cikin babu, ban tashi tuna cewa ban tafiyar da rayuwa ta dai dai ba sai yau dana nakasa, ina kuma son su yi min wani amfani wato daura wa Amani aure. Gaban Mukhtar ne ya yi bugawar dakikai masu yawa, kan sa ya wani irin sara. Ya dauka Alhaji ya janye kudurin sa na aurar da Amani ga abokin sa? Ya tuna rokon da ta rika yi masa jiya a kan ya taimake ta ya roki Alhaji ya fasa bata so, ko cikakken sauraro bai yi mata ba sabida a wajen sa Amani ba mai cikakken hankali bace. Shi kan sa Alhaji, sai da yayi noticing canjawar da fuskar Mukhtar tayi. Mukhtar bai ce komai ba a kan duka abubuwan da Alhaji ke fada masa, Alhaji ya cigaba da bashi labarin rayuwar sa inda ya ce. ***** ***** **** ASALIN HON. USMAN FASKARI Na fito daga garin Faskari ta Jihar Katsina, mu uku ne a wajen mahaifin mu, mu biyu cikin mu guda ni da Malam Idrisu. Dayar mace ce uwar ta daban wato kanwar mu Sahura. Malam Idrisu yana da bataliyar Iyali domin kuwa matan sa uku kowacce tana da yaya maza da mata sun haura goma. Sahura an yi mata aure a garin Funtua. Ban san adadin yaran da ta haifa ba. Asali na fito birni ne neman ilmin boko, sabanin yaya Idrisu da yafi maida hankali akan sanaar mahaifin mu wato Dukanci. A rayuwa ta ina da burin in tara kudi, in kuma auri kyawawan mata in cika gida dasu,duk da ana yawan cewa ni mummuna ne Idrisu ya fini kyau. Nayi makarantar koyon kanikanci a garin mu Faskari, da mahaifin mu ya rasu sai nayi wa yaya na da kanwar mu Sahura sallama na ce na tafi karatu birni. Mahaifiyar mu a lokacin bata tare da mahaifin mu tana aure ne a wani gari Kaita. Duk dai a cikin Katsina ne. A wannan lokacin samun gurbin karatu a jamioin Najeriya ba abu ne mai wahala ba, saboda gwamnati neman masu yin karatun take yi ruwa a jallo. Na samu gurbi a Katsina state Polytechnic inda nayi HND dina a fannin Engineering, daga nan na samu gurbi a Jamiar Bayero ta Kano, naje nayi digiri na na farko akan Architectural Engineering. Na dawo Katsina na fada harkar siyasa. Na shga siyasa da kafar dama, amma hakan bai hana ni shaawar kasuwacin kayan gine-gine ba wanda akan sa nayi karatu na. Alhaji Sadi Talle aminina ne tun na kuruciya a lokacin shi yana kasuwanci da kasashen Africa. Shi ya sakani cikin harkar fitar da Aluminium Ore da Iron Ore daga Sierra Leone zuwa kasar France. Kasuwanci ne wanda yayi mana sanadin samun arziki mai yawa, wanda idan zamu dawo sai in saro kayan gine-gine daga can in taho dasu kasar Najeriya. Cikin dan lokaci Allah ya saka min albarka a cikin nema na. Na soma tunanin wasu hanyoyin kasuwancin daban-daban har na samu na kafa kanfani na na farko wato Faskari Investment, amma duk da haka ban bar siyasa ba. Cikin irin tafiye-tafiyen da muke yi ni da Alhaji Sadi ne zuwa kasashen Africa muka shiga Freetown wato babban birnin Saliyo, wannan karon mun zo ne musamman neman matar da zamu aura, don mun jima muna shaawar auren kyawawan matan da ke wannan kasa. Abokin kasuwancin mu da muka dade tare shi ya gaya ma na hanyoyin da ake bi a nemi aure a wannan kasa, yace yayan attajiran kasar basa auruwa ga bako sai yayan talakawa, wadanda iyayen su ke cikin yanayi. Shi ya hada mu da mahaifin Jalan wanda manomi ne a garin, kuma talaka ne sosai, tun a hoto naga Jalan kuma tayi min dari bisa dari, na cika mahaifin ta da dukiya mai yawa ba tare da yayi shawara da ita ba ya daura mana aure, ya kuma ce in dauke ta in tafi da ita. Shi kuma Alhaji Sadi ya auri wata Jenaba wadda ita ta zame masa uwar yayan sa. In takaice maka labari Mukhtar, ban sha ta dadi ba a hannun Jalan, domin bata sona ko kankani, ni na san saboda muni na ne, don babu abin da ban mata a rayuwa ba ita da iyayen ta, amma a cikin shekaru biyu da nayi tare da ita sau daya na taba morar sadaki na. A wancan lokacin ni kuma son da nake wa Jaian mai yawa ne, don har gobe babu matar da zan so kamar ta, duk matan da na aura bayan ta don na rufa wa siyasa ta asiri ne, amma ba don so ba ko neman yaya. Kullum gorin Jalan gare ni shi ne ba zata taba so na ba, domin tana da wanda tayi wa alkawarin aure, na yaudari iyayen ta da abin duniya. Da tura ta kai bango na daina sakar mata bakin aljihu na don na gaji da gorin da take yi min. Rana daya Allah ya bani saa a kanta kuma ranar ne muka samu rabon Amani. Koda cikin ya isa haihuwa ta tubure lallai in maida ta kasar su ta haihu a can, ni kuma da bazan iya barin ta ta koma kasarsu ba sai na dauko mata mahaifan ta suka zo nan Katsina muka basu muhalli a cikin gidan nan, nace su zauna da ita har sai ta haihu, domin kuwa Jalan tana ta min rantsuwa da barazanar ba zata haihu da mammunan mutum kama na ba. Ranar ne na fahimci Jalan saboda muni na take kina, in banda haka dame na rage ta da iyayen ta? Har Hajji na kai su duka, in banda haka kiyayyar ta tayi yawa a kaina sai na soma kankame aljihu na nima. San da ta shiga watan haihuwa Jalan ta ci shinkafar bera don ta kashe kanta. Allah ya so mahaifiyar ta da suke tare ta fahimta da wuri, muka kaita asibiti hankali tashe, likitoci suka yi mata tiyatar gaggawa suka cire Amani, ita kuma suka bata duk wata kulawar da ta dace. Tun da aka bani ya ta a hannu na, yar da aka ceto da kyar, naji na tsani Jalan, yau kuma na tabbatar ba zata taba kauna ta ba. Sai kawai na rubuta mata saki na baiwa iyayen ta. Na kuma basu kudin da zai ishe su koma wa kasar su da kula da lafiyar ta. Tun a aibiti da na rabu da su ban kara bi ta kansu ba har gobe. Wanda sai yanzu nake tunanin ban kyauta ba, don ban ma tabbatar da cewa Jalan ta rayu ba ko ta zarce, ban kuma san ya suka yi suka koma kasar su ba. Na dauki Amina wadda na sakawa sunan mahaifiyar mu na tafi Faskari da ita, garin da rabon in shige shi har na manta sai a dalilin siyasa wato lokacin da nake neman kuriar kauyen namu, Yaya na Malam Idrisu yana can da iyalin sa, har lokacin kuma da na fara karfi banyi kyan kan taimaka masa ba ko yayan sa. Amma da yake aka ce naka sai naka, yau da bukatar taimakon su ta kama ni haka na murje kunya na kai masa Amani nace ya baiwa daya daga cikin matan sa ta shayar min da ita. Amma bawan Allahn nan bai dubi hali na ba ya karbi Amani ya baiwa amaryar sa Maryama, ta hada da Kamilu dan da take goyo ta shayar da su. Maryama ba tayi shekaru biyu cikakku tana shayar da Amani ba ta rasu. Sai Malam Idrisu ya dauke ta ya maida rikon ta hannun kanwar mu Sahura dake aure a garin Funtua. Amma zuwa na Funtua na farko naga bazan iya barin Amani ta cigaba da rayuwa a wannan gidan ba saboda rashin tsafta da cikowa, gashi nifa bawai ina taimaka musu da komi bane kan rikon da suke yi mata amma nazo na raina kokarin Sahura. Na karbo Amani tana da shekaru uku na dawo da ita Katsina hannun matar da na sake aura, na daukar mata mai raino. Amma hankalin Hajara na kan yar kankanuwar yarinyar nan da yadda zata cutar da ita, shi yasa da na gane na saketa babu bata lokaci. Na sake aure, saina daina baiwa mata na hidimar Amani, na daukar mata mai raino daya kwakkwara mai suna Rakiya, na sata a makaranta mai tsada, na ke kuma kirata AMANI don boye sunan mahaifiya ta. In takaice maka ko Mukhtar, kafin Amani tayi wadannan shekarun nata na yanzu aure na goma, babu wadda na cika shekaru biyu da ita, don sun kasa kaunatar min yar nan, wadda soyayyar da nake yiwa mahaifiyar ta ce bakidaya ta koma kanta. Suma masu rainon kullum cikin canza mata su nake, Rakiya kawai na bari mai dafa mata abinci har gobe, har Allah ya raya ta ta isa kula da kanta. Ita ta roke ni in daina aure-aure in kuma daina korar masu aiki saboda ita, shi yasa muka dade da Haj.Rabi. To ka ji Mukhy, wanan shine labari na da ya ta Amani, a yau ina cikin damuwar irin dabiun ta da irin tarbiyyar da nayi mata, amma yaya zanyi? Ni da mahaifiyar ta Allah yayi ba masu rayuwa tare bane na tsayin lokaci, kuma ban kyauta ba da ban kara bibiyar rayuwar Jalan ba, su kuwa dangi na na Faskari wallahi sai dai Amani tayi masu kyauta amma ba dai ni ba, bana kai ta wurin su, amma ita tana kai kanta lokaci-lokaci bama tare da na sani ba. Ba yabon nawa ba, Amani ta fini kirki, ta fini son zumunci kai dai bar ta da sangartar ta wadda rashin tashi karkashin kulawar uwa ko wata shaqiqiya mace ta jiki yayi mata sanadin sa. Mukhtar ya jinjina kai ya shafe gumi daga goshin sa. A hankali yace Alhaji labarin ka akwai darussa mai yawa a ciki Alhaji, sannan akwai tarin kurakurai a cikin sa. Na farko Alhaji, ban yarda da abin da ka yarda da shi bana cewa Mama Jalan na kin ka ne saboda baka da kyawun suffa wannan ba haka bane Alhaji. Hanyar da kabi wajen auren ta bata dace ba, kamar ka sayo akuya a kasuwa ka kawo kasar ka ka ajiye ne, duk da mahaifin ta shi ya aura maka ita, akwai bukatar ka nemi soyayyar ta da fahimtar juna tsakanin ku, kafin akai ga maganar aure ba duka mata ake saye ba. Amma irin wannan auren dama baya wata kima tunda da bakin ka kace min akwai wanda take so da suka dade tare, har suka yi alkawarin aure. Don haka ka cire maganar wai don munin kane bata son ka, kuma Alhaji da bakin ka kace kana yi mata kankamo, mata da yawa musamman na kasashen Africa suna aure ne a inda zasu samu wadata da kwanciyar hankali fiye da na kasar su ta asali. Mu koma maganar dangin ka na Faskari, zan iya cewa kayi wa Yaya Idrisu da Sahura butulci da rashin daukar zumunci da daraja. Dukiyar ka ta rude ka ka wulakanta zumunci domin sun cancanci ace a irin wadatar da Allah yayi maka kamata yayi ace ka rungume su ka zama kaine komai nasu tunda kace basu da karfi. Muhimmin abin da zaka yi a yanzu Alhaji shine gyara tsakanin ka da yan uwan ka, neman yafiyar su, da janyo su a jiki, ka saka su a cikin niimar da Allah yayi maka. Alhaji yana girgiza kai yace haka ne, haka ne Mukhtar, In sha Allah zan gyara, gobe-goben nan ka shirya mana tafiya Faskari don Allah ni da kai da Amani da yardar Allah zan gyara komai. Mukhtar yace naji dadin jin hakan Alhaji, saura iyayen Mama Jalan da ita kanta ya kamata ka neme su ka sada su da Amani. Mahaifiyar ta na da hakki a kan ta fiye da wanda kake da shi. In ta mutu baka sada su ba sai Allah ya tambaye ka Alhaji, Amani (is desperate) ga son ganin mahaifiyar ta, har taso ta bi ta wata hanyar da baka sani ba don ta kai kan ta ga mahaifiyar ta ba don na hana ta ba, duk da togaciyar da kayi mata akan zuwa gare ta. Kafin Alhaji yace komai suka hango Amani na tahowa inda suke da hanzari da sassarfa, suka yi shiru suka maida hankalin su gare ta. Tana isowa ta nufi Alhaji ta zauna kasan kafafun sa ta saka kuka. Alhaji yace ni fa dadi na dake shagwaba da sakarci maras dalili, yaya zaki zo muna magana ki saka mu gaba kina kuka? Mutuwa aka yi ko dukan ki aka yi? Amani ta dago jikakkun idanun ta ta dubi Baban ta cikin ido ta ce Daddy sona ke ka saki Haj. Rabi, kuma kada ka kara auren kowa, ba zasu taba son ka saboda Allah ba, dukiyar ka kawai suke so Daddy. Muddin kuma suka fahimci ba zasu samu ba na rantse zasu iya halaka ka ko ni su sabauta ni. Daddy don Allah ka sake ta, ni zan kula da kai, na fasa zuwa karatun, zan kare rayuwa ta gaba daya cikin kulawa da hidimar ka da lafiyar ka, in dai ka yarda zaka rabu da Haj. Rabi kuma zaka fasa aura min Alhaji Sadi. Alhaji yace cool down Amani, duk me ya kawo wannan? Maganar auren ki da Alh. Sadi tana hannun ki yanzu, na bashi dama ne ya nemi soyayyah daga gare ki, wallahi in baki so duk amincin dake tsakanina da shi bazan miki dole ba. Haj. Rabi kuwa ai zaman ki take yi, ke kika hana ta tafiya tuntuni. Ni da ke cikin rayuwa a wheelchair yanzu, rayuwa ta bata mata bace yanzu. Ko dama saboda siyasa nake aure-auran nan amma tun daga kan Jalan na gama auren biyan bukatar rai da kauna. Share hawayen ki kin ji Amani? Gobe in sha Allahu zamu tafi Faskari da wuri zan maida ke cikin yan uwan ki na jini. Amma Amani ta yaya zaki iya kula dani alhalin kina mace? Da zaki yi min alfarma irin wadda baki taba yi min ba ki amince ki auri da na Mukhtar, ya zauna tare da mu, ku cigaba da kulawa da ni tare har Allah ya bani lafiya. Na hanga na duba duk duniya ban ga wanda zan iya baiwa auren ki ba sai MUKHTAR Amani, da shi kadai na amince in yi surukunta, kuma da shi nake son jini na ya gauraya, koda kuwa ace daga sama ya fado, wato ba yan Adam ne suka haife shi ba. Amani da Mukhtar a lokaci guda suka daga kai suna kallon-kallo, kallon son fahimtar ko me Alhaji ke nufi? Sun shiga rudani mai yawa dukkan su, amma Amani ta fi Mukhtar gigicewa. Mikewa tsaye ta yi zumbur tana kallon Alhaji a tsorace, kafin ta soma ja da baya, da kyar ta iya cewa, Daddy ai gara min Alhaji Sadin, da dai wannan mara mutuncin mara tausayin kuma mara jin kan mace. Gara min Alhaji Sadi bakikkirin mummuna da wannan mai kyan dan macijin. Gara min Alhaji Sadi tunda ba a karkashin uba na yake cin abinci ba, kuma yake min keta da Gadara ba. Na rantse da Allah gara in auri Alhaji Sadi sau dubu da wannan sumumu-kasau din wanda bai san darajata a wurinka ba, saboda takamar yana da fada a wurin ka. Tana gama fadin haka ta juya ta bar wurin da gudu-gudu, sauri-sauri babu inda ba ya kyarma a jikinta saboda dimauta. Mukhtar kuwa komawa ya yi tamkar mutum-mutumi a wurin, ko kwakkwaran motsi bai iya ya yi ba. Haka ya kasa dago kansa da ya sunkuyar saboda kunya. Ga mamakin sa sai ya samu kansa da jin kunyar Alhaji mai tsanani. A can wani sako na zuciyar sa kuma ya samu kan sa da jin dadin wannan tayi da yayi masa. Shi ma ya san ba ya kyautatawa Amani yadda duk maaikatan Alhaji ke mata, haka ba ya bata respect din da maaikata suke bata, kullum jin kan sa yake sama da ita, ba ya yarda da subordination, shi mutum ne da ba ya yarda da raini ko kaskanci, wannan kuma a cikin jinin sa ne na iyaye da kakanni. Maganar aure da Alhaji ya yi yanzun kuwa tsakanin sa da Amani sai ta kashe duk wani kuzarin sa, ta jefa shi a wani yanayi da bai taba shiga ba na zurfin tunani da mutuwar jiki. Maganganun Amani wadanda suka zamo raddi ga mahaifin ta, kuma zagi a gare shi ko kadan ba su dame shi ba. Fassarar da ta dade tana yi masa a zuciyar ta ne yau Allah ya matsi bakin ta ta fada a gaban sa. Da kyar ya iya mikewa tsaye lokacin da Alhaji ya ce ya tura shi a kujerar sa ya maida shi falo ya huta. Har suka yi sallama da Alhaji, bayan ya bashi magungunan sa na yau ya sha, Mukhtar sanyin jikin sa da bugun zuciyar sa basu koma daidai ba. Da kyar ya iya takawa zuwa gidan sa wanda bai da nisa da gidan Alhaji. Ko motar sa a gidan ya bar ta don ya san ba zai iya tuki ba. **** **** **** MUKHTAR Mukhtar ya yi kwance a tsakiyar lallausar gadon sa yana sake tariyo maganganun ubangidan sa Alhaji Usman Faskari, kauna ce zallah ya nuna masa wadda babu algus, kuma wani bare bai taba yi masa irin ta ba, kuma bai taba samun kwatankwacin ta ko daga iyayen sa da suka haife shi ba. Ya soma laluba lungu da sako na zuciyar sa don son gano stand din da ya ajiye Amani, a zahirin gaskiya wannan yarinyar ba tun yau ta ke fizgar zuciyar sa ba, ta dade tana saka shi a faduwar gaban da bai san dalilin sa ba, sai ya bar wa ran sa a cewa kyawun halittar ta da kwarjinin ta ne yake razana shi, yake sanya shi faduwar gaban, kamar yadda duk wani lafiyayen namiji bazai iya kauda kai a kan ta ba ba tare da ya ji zuciyar sa ta motsa ba. Ya sha zama a cikin dare yana tuno wasu abubuwa da suka shafe ta a duk lokacin da wata alaka ta hada su suka fita a mota tare ya kai ta wani wuri, bisa umarnin Alhaji. A irin wadannan lokutan kwana yake da tunanin ta a ran sa. Fitsarar ta, rashin kunyar ta, hararar ta da tijarar ta duk basu bace masa. Ba don murmushi yayi kaura daga rayuwar sa ba da yace wadannan halaye nata duk da baya son su, to fa hakika suna saka shi murmushi a yawancin lokuta. Amani Faskari, tana da babban alamari a tare da shi wanda ya dade da kasa ganewa. A yau da Alhaji da kan sa ya yi masa tayin auren ta ya shiga rudu, ya shiga dimuwa da tunani mai yawa, wanda hakan ya saka shi tono duk wasu tsofaffin feelings din da ya san yana ji a kan Amani; and he realized for himself cewa ya dade yana son Amani, in dai pleasant feelings din da yake ji a can kasan ran sa a kan ta shine SO, to ya dade yana ninkaya a cikin sa ba tare da ya ankara ba, har sai yau da tayin Alhaji da kan sa ya ankarar da shi, amma kuma halayen ta sun sa ba ta burge shi, kuma ba ya son ko daya cikin dabiun ta. Ya na son ta a kasan ransa a can wani lungu da bai taba dauka da muhimmanci ba. In ba haka ba me ya sa ko kadan ba ya son zancen auren ta da Alhaji Sadi? Me yasa ranar da Alhaji ya gaya masa ya bada auren ta ga Alhaji Sadi ya kasa barci a tsayin daren bakidayan sa? Me ya sa yake kishin ganin ta babu lullubi (mayafi?) ta fito waje ma'aikata maza na kallon ta, don duk lokacin da ya gan ta babu lullubi a gaban maza sai ya ji zuciyar sa kamar ta tarwatse. Duka wadannan alamu ne na So, don ba a kishi sai da So, sai dai son bai zo a muhallin da ya dace ya zo ba, wato Amani ubangida ce a gare shi, sannan ba ta da tarbiyya da cikar addinin da mutum irin sa za ya so ta, har yayi fatan ta zama uwar yaran sa. Ko ya aura ya kai gaban iyayen sa su karba cikin sauki. Ya taso a gidan da ba'a san komai ba sai mutumta Dan Adam, tsatstsaurar tarbiyyah ga 'ya'ya maza da mata, gidan rikon addini da dattaku, gidan da dan gida ba shi ne Da ba, gidan da DAN RIKO daidai yake da dan gida har wani lokaci ya fi shi sakewa. Amani Faskari ta dade da satar wani kaso mai girma a zuciyar sa, wanda zai iya cewa daga Allah ne kawai, ban da haka in kyau ne ya baro mata ma su amsa sunan mata da suka dame ta suka shanye a kyau, dukiya, ilimi da gatan da take takama da shi. Amma babu wadda ta taba saka shi a irin situation din da yake samun kan sa a duk lokacin da ya ga Amani. Something like miracle, (abin kamar karama) tana da wannan boyayyen tasirin a kan sa. Mukhtar ya shiga ambaton innalillahi wainna ilaihi rajiun, wannan wace irin masifa ce ke neman hawa kan sa? Ya yarda da auren Amani ya yi ya ya da ita da rashin kunya da rashin tarbiyyar ta? Wadda ba ya tunanin ko karatun sallah ta iya daidai. Above all aure a gare shi a yanzu na nufin komawar sa gida, wanda bai taba shiryawa nan kusa ba. In Alhaji ya dage a kan bakan sa na aura masa fitsararriyar yar sa wa zai karba masa auren? Tunda ya san babu kowa nasa a kasar Najeriya? Kodayake Alhaji ya dauka iyayen sa sun rasu ne, shi ya sa ba ya takura masa a kan zuwa gida, duk lokacin da ya ce ya je ya gaida dangin sa zai ce zai je ne ba ya so ya tafi ya bar masa ayyuka da yawa ya sha wahala, har Alhajin ya gaji ya daina masa maganar zuwa ganin dangin sa don ya dauka ma iyayen sa sun rasu. Yanzu kuwa da Alhaji ya bullo masa da zancen aure sai ya ji wani sako na zuciyar sa yana missing gida, yana kewar Diffa. Sama da komai yana kewar UMMAMIn sa. ***** ***** **** AMANI Zamu iya cewa yau Amani dan karamin kwancewar kai ne ya same ta a dalilin furucin Alhaji gareta. Wasu notuka a cikin kan ta ta ji sun kwakkwance tsabar rudanin da mahaifin ta ya jefa ta. Ta nufi cikin gida tana tafiya tana hada hanya, saura kadan su yi karo da Hajiya Rabi da ke kokarin hawa benen Alhaji. Ai kuwa ta bangaje Hajiya sai da ta kusa kai wa kasa don ba ta zaci bangazar ba, duk da ta ga Amanin ta taho a fusace kamar kububuwa, ta ce a ranta, mai yiwuwa ita da baabzinen Alhaji ne, don ta san shi kadai ya tsaya wa Amani a makogaro ta kasa fyato shi. Don ya fi karfin ta a gun Baban ta. Hajiya Rabi ta dafa bango kafin ta kai kasa, ta ce, Ni ki ka bangaje? Kwaya ki ka sha da ba za ki dinga lura ba kina tafiya kai a sama kamar zakanya? Ai ba ni na kar zomon ba, ko ratayar sa ba a ba ni ba, jairar yarinya tatacciya, mara kunya, goyon namiji. Amani ta sa kafa zata hau bene kenan, jin abin da Hajiya Rabi ta fada ya kara tunzura ta, da ma ya ya lafiyar Kura? Alhaji ya gama kaskantata da cewa zai bada sadakar auren ta ga yaron sa da ta fi tsana a duniya, wannan annamimiyar kuma ta ce mata goyon namiji? Bari ta nuna mata goyon namiji. Ta wawuri Hajiya Rabi ta maka da kasa, da ma Hajiyar ba ta da jiki sam, Hajiya ta zuba ihu amma ba wanda ya jiyo ta sai Rakiya mai aikin Amani. Ita ta zo ta rike Amani da ke huci kamar maciji ya sare ta. Rakiya ta shiga lallashin ta tana fadin, Uwar daki na mai abun alheri, Hajiya babar ki ce, a dinga hakuri, uwar ki ce kamar kowacce uwa tunda Alhaji na auren ta. Ki yi hakuri ki wuce sama, bana so ki karasa gawar da ba taki ba. Ko ba kya ganin babu tsoka a jikin ta? Me za ki dauka in kin dake ta? Amani ta soma hawaye, wanda ba ta san yaushe suka zubo ba, zafi biyu ne ya tarar mata, ta ce, Rakiya bar ni in zubar mata da hakora don ta fi tabbatarwa ni jaira ce, tatacciya, mara kunya, goyon namiji. Rakiya ta yi maza ta ce, Wane mutum? Wane ita ta yi miki wannan zagin duk inda alkhairi yake ga talaka kin iya shi, zagin data yi miki ba zai rage ki da komai ba tunda ba ya fitowa a goshi. Kowa ya san albarkacin ki ta ke ci da ta yi wannan dadewar a gidan nan. Da haka Rakiya ta samu ta lallashi Amani ta raka ta har dakin ta ta dawo sannan ta tada Hajiya da ke kuka tana fadin, yau sai Alhaji ya sake ta kafin mahaukaciyar yar sa ta karya ta a banza. Tana tashi wurin Alhaji ta nufa, lokacin Mukhtar bai dade da shigar da shi dakin barcin sa ba, shi kuma yayi masa sallama ya tafi gidan sa. Alhaji yana kakkabe filon sa zai kwanta, Hajiya Rabi ta fado dakin tamkar an jefo ta. Biro da takarda ta dauko ta kawo masa har kan cinyar sa ta ce, Sakar ni, na ce sakar ni, kafin in sa filo in danne ka wallahi. Ka haifi jaraba, ba tarbiyya ba ganin girman na gaba, in sha Allahu ita ce ajalin ka! Alhaji Usman ya ce, Innalillahi wainna ilaihi rajiun. Kawai sai ya karbi takardar ya rattaba wa Hajiya Rabi saki. Ya ce, Duk abin da ke sassan ki ki kwashe ki tafi da shi na ba ki, amma tunda ki ka muzanta Amani da mugun kalami irin haka na gama auren ki, da ma ita ta ke roko na in zauna da ke. Bakin halin ki babu wanda ban sani ba da yawon ta zubar da cin amana ta. A sauka lafiya Umma-ta-gaida-Assha. Amani da ta shiga daki duk da lallashin da Rakiya ta yi mata amma zuciyar ta ta kasa yin sanyi, sai tafasa ta ke yi abubuwa goma da ashirin, sai kawai ta hada kai da gwiwa a tsakiyar gadon ta tana rera kuka tamkar marainiya. Ko da yake ita da marainiyar da uwar ta ta mutu ta bari tun haihuwa ai ba su da maraba, don ko hoton mahaifiyar ta Alhaji bai taba nuna mata ba. A yau tana kewar mahaifiya ko yar uwa mace, ko dan uwan da za ta kai wa kukan ta, ko wani babba a dangi da za ta kai wa karar Daddy a kan kasksanci da tozarcin da yake shirin yi mata (a wurin ta). Aure da Mukhy shi ne mafi kaskancin abin da Daddy zai yi mata da ba za ta taba iya yafewa ba. Kuma ko sama da kasa za ta hadu, ba za ta yarda ba, za ta gudu kawai wajen mahaifiyar ta su neme ta su rasa, za ta cire kudade anyhow ta biya mai yi mata bincike kawai ya turo mata adireshi ta koma wajen mahaifiyar ta. Ta yarda yanzu Alhaji ya fi son Mukhy tsintacce a kan ta. To za ta bar musu gidan, gabanin bashi auren nata. In yaso Alhaji ya maido Mukhtar dakin ta na gidan sa ya zauna madadin ta karshen kaunar da zai nuna masa kenan bayan ta bashi sadakar auren ta. Hamida ta fado mata a rai, ta share hawayen ta dauki waya tana dialling lambar Balewa. Duk da ta san maganar Hamida kullum daya ce, ta dinga yi wa Daddy biyayya, yau ta san Hamida ko za ta tsokane ta to kuwa za ta taya ta bakin cikin masifar da ta ke neman tunkaro ta. Abokin kuka aka ce shi ake gaya wa mutuwa, duk da Hamida ba koyaushe ta ke taya ta kuka ba, wani lokacin ma laifi ta ke ba ta, ba ta iya boye mata komai da ya shafe ta saboda tsananin haduwar jinin su. Ba jimawa Hamida ta daga waya da sallama, sai Amani ta daddage ta bude murya da karfi ta fashe da kuka mai sauti, don da can mara sauti ta ke yi. Kafin Hamida ta ce komai, sai da ta fara toshe kunnuwan ta da yan yatsun ta, kada a fasa mata dodon kunne, sannan a hankali ta ce, MUKHY ne ko! Ita ta san Amani ba ta da wata matsala a yanzu da ta wuce Mukhtar. Har ta saba yanzu in Amani ta kira ta, to ta san Mukhtar ya kunso mata. Ita kuma ko kadan ba ta ganin laifin sa, ina laifin mai son Baban ka? Mai taimaka masa? Amani ta gyada kai kamar Hamida na kallon ta, ta ce, Shi ne Hamida, karewa ma yau komai ya kare, tunda Daddy ya ba shi sadakar aure na. Wata muguwar dariya ta kutsowa Hamida, ita da ma wannan so da Alhaji ke wa Mukhtar ta san karshen tika-tika tik! Ko dai Mukhtar da kan sa ya ce yana son kyakkyawar diyar ubangidan nasa, ko Alhaji ya hada da kan sa, don cikar kaunar da yake yi wa Mukhtar da kara janyo shi jikin sa har abada. Hamida ta yi dariya iya dariya, amma bayan ta kashe wayar ta. Sannan ta sake kiran Amani ta ce, Afuwan Habibty, network ne, na ji abin da ya faru, amma abu bai yi dadi ba, shi ko Alhaji mai yasa zai yi haka? Bayan ya san ba kwa jituwa? To amma ke yanzu a tunani da hankalin ki me ki ka yanke? Za ki yi wa mahaifin ki mai son ki, mai kaunar ki, mai tattalin farin cikin ki, mai hidimta miki iya rayuwar sa biyayya ne ko kuwa kasa za ki bada masa a ido? Maganar Alh. Sadi fa? Ina ta kwana? Amani ta yi maza ta ce, kada ki daure ni da jijiyoyin jiki na. Ai hakkin sa ne ya so ni ya kula da ni, amma banda auren dole. Da ne Daddy yake so na Hamida, yake kauna ta, yake tattalin farin ciki na da gudun bacin rai na amma banda yanzu. Idan har zaki lura da kyau zaki gane Mukhtar kadai yake so yanzu, tunda har yana fadin bai iya hada jinin jikokin sa da na kowa sai nashi. Ta sake rushewa da kuka, ta ce, Hamdy, ina cikin tashin hankalin da Allah kadai zai iya fidda ni. Tunda har Daddy ya yi wannan tunanin. Kin sani na ki jinin mutumin nan da duk abin da ya shafe shi, tun yanzu sai abin da ya ce ma Daddy, ina ga ya zama son inlaw din sa ko ya haifa masa jikokin da baya da su? Ai shikenan kuma Daddy cewa zai yi ba ni ya haifa ba shi ya haifa. Hamida na ta guntse dariya, ta ce, Fisabilillahi Habeebty me ye abun tashin hankali a wannan abun arziki? Cewa nake da tsoho zai aura miki saan sa? Da ki ka yi hakuri kika fawwalawa Allah kika kuma bashi zabi, nima kuma nayi ta taya ki da addua ba gashi Allah ya amsa ya dube mu ba? Shi da kan sa Daddyn ya fasa ba tareda rayuka sun baci ba, ya zabo yaro santalele ya baki, son kowa, yaro sabon jini mai ilmi da nagarta, kuma mafi soyuwa a zuciyar sa? Ai kawai Amani ki manta da wata kiyayyar ki maras hujja, maras madafa maras dalili face envy dake damun ki a kan sa, ki bawa Mukhtar dama ki san ko shi waye a wannan fannin, ta hanyar yi wa mahaifin ki biyayya. This man is a treasure!. Hamida ta karasa fadi kasa-kasa ba tare da ta san lokacin da kalaman suka fito ba, tana jin dan wani kishi-kishi a ran ta. Domin tun ganin ta da Mukhtar na farko ya tsaya mata a rai, ya kuma shiga zuciyar ta. Har Allah-Allah ta ke Amani ta kira ta ta bata complain din sa don ita haka nan abun yana saka ta nishadi. Wato tana son hirar Mukhy da Amani ke yawan yi mata duk da cewa bata arziki bace. Amma daga ranar yau insha Allahu ba za ta kara saka komai a ran ta a kan Mukhtar ba, sai fatan daidaita tsakanin sa da sahibar ta. A tata fahimtar sun yi balain dacewa da juna, kuma ita ma kamar Alhajin tana ganin ba wanda ya dace da Amani sai shi, ba kowa ne zai iya auren Amani ya kuma jure zama da ita ba. Sai mai jan wuya. Gara shi Mukhtar din, tunda ya san mutuncin mahaifin ta, mai yiwuwa kuma ya san duka halayen ta tunda ba yau suke tare ba. Don haka zai iya hakuri da jure zama da ita. Ban gane me ki ke kokarin fada min ba Hamida?. Hamida ta ce, Eh, ina nufin Mukhtar is a treasure ga duk macen da tayi saar samun sa a matsayin miji kuma abokin rayuwa, hes a rare gem, sannan gashi mutum na musamman a halayya da dabia mai dauke da dukkan attributes na cikar mazantaka. Ina nufin. mutum ne daya cikin dubu, wanda kafin ki samu kamar sa a wannan zamanin sai an tona. Kamata ya yi ki gode wa Baban ki for giving you this treasure. Amani ta yi maza ta katse ta da cewa, Ai sai ki zo ke a ba shi ke sadakar. Na yi rantsuwa duk yadda zan yi in fidda kudin nan daga yau zuwa gobe zan yi in komawa mai binciken nan ya ba ni adireshi da lambar wayar Mama na. Na rantse guduwa zan yi Hamida, da in auri yaron Baba na kuma wanda ban san asalin sa ba, sannan mai mugun hali irin na Mukhtar gara na gudu gun uwa ta ko a bukka take mu rayu tare. Dama can na ki tafiya ne sabida Daddy da tunanin kaunar sa gareni, amma yanzu na tabbata wallahi ya fi son bare a kaina. Hamida ta kama kai, cikin cewa, Ki daina rantsewa Amani, Uban da ya haife ka baya hada kaunar ka data kowa sai dai kawaici. Ba zan gaji da ce miki a kowanne alamari da ya tunkaro ki, ki dinga neman zabin Allah ba, hakan shine daidai, kullum ina gaya miki haka. Yanke hukunci cikin fushi kuskure ne babba, ki yi sallah rakaa biyu ki nemi zabin Allah ta hanyar istikhara da Annabi SAW ya koyar, idan Mukhtar alheri ne a gare ki da addinin ki, Allah ya sanyaya zuciyar ki ki karbi zabin mahaifin ki da hannu bibbiyu. Idan babu alkhairi Allah ya sa Daddy ya janye da kan sa, ba tare da kin bata da mahaifin ki ba. Amani ta ce cikin hargagi. Daman na san ba za ki taba bin bayana ba a nan, ke kadai ki ka rage min da zan ji sanyi daga gare ta. Ba irin bayanin da ban miki a kan waye Mukhtar din nan ba, da rashin mutuncin da yake yi min, kamar ba a karkashi na yake ci ba. Amma kin ki ganewa da gangan, kullum sai dai ki yabe shi, saboda farar fata da bakin gashin kan sa na rudar ki. Insha Allahu daga yau ba zan sake kiran ki in kawo miki kuka na ba, don na san ba za ki share min hawaye ba in dai a kan Mukhtar ne. Zan nemo mahaifiya ta da kaina in koma inda ta ke duk yanayin da zan same ta, na san ita ba za ta taba yarda a yi min auren dole da wanda ba na so kuma ba zan taba so ba, har duniya ta nade. Ta kashe wayar ta tana kuka ta bar Hamida da mutuwar jiki. Ta fara yarda da gaske Amani ba ta kaunar Mukhtar, ba yin kanta bane, tunda yau ta zabi ta koma gun mahaifiyar ta bayan duk gatan da Daddyn ta ya yi mata a rayuwa. Yau ta zabi ta bar shi. Ba ta san ya za ta yi ta ceto kawar ta daga fadawa fushin iyaye ba. Ko kadan Hon. Usman ba irin uban da yaya za su bijirewa umarnin su ba ne domin bai ragi Amani da komai ba, sai ma dai a ce soyayyar sa gare ta tayi yawa, har babu kawaici a cikin ta. Ta yanke shawarar tahowa Katsina don ta taimaki kawar ta, don da gaske tana kan dokin fushi wanda zai iya saka ta aikata da na sani ko ya raba ta da mahaifin ta dungurungum. A daren Hamida ta hau shirin tafiya Katsina a washegari. Amani ta manta shaf da maganar tafiyar su Faskari, kuma ba ta san Daddyn ta ya saki Haj. Rabi ba, ta bar gidan tun daren jiya. Ta kwana cikin mawuyacin hali da tunanin Daddy ya daina son ta. A daren ta cire wadannan kudade naira miliyan biyar, ba tare da tunanin komai ba, sai na son ganin mahaifiyar ta, ta tura wa mai binciken kwakkwafin ta. Ta tura masa shaidar receipt ta layin wayar sa, tana yi tana tuna alkawarin bogi da Mukhy ya taba yi mata na cewa shi da kan sa zai nemo mata mahaifiyar ta on koboless. Amma ya nemo din? Tun daga lokacin har zuwa inda yau ke motsi bai kara tada zancen ba, saboda ashe sun hada baki da Daddy za su nakasta farin cikinta ta hanyar aura masa ita. Allah Sarki rashin sani, domin kuwa ko a daren bayan ya koma gida, duk da halin da yake ciki ya rubuta cikin schedules din sa na gobe cewa daga Faskari zai saka Daddy a gaba da magiya da lallashi da ban baki irin nasa, ya yarda su wuce su kai Amani ga mahaifiyar ta. Ba zai yarda Daddy ya yi mata aure ba da sani da sanya albarkar Innar ta ba, in har tana raye. Wannan wani alkawari ne da ya yi wa Amani, da yake da kyakyawar niyyar cika shi, duk da rashin jituwar da ke tsakanin su. Ba ya daukar alamarin mahaifiya da sauki, ko don irin son da yake yi wa tasa Ummamin, wadda bai samu tata soyayyar ba shima, so he can feel for Amani, a kan rashin soyayyar uwa, wannan wani abu ne da ba ya son tunawa a yanzu. Cikin kurakuran da yake so ya taimaka wa Alhaji ya gyara ko hakki ya ragu a kan sa, har da kai Amani ga mahaifiyar ta. Kuma alhamdulillahi tunda ya yi saa Alhaji ya amince, a lokacin da nadamar abubuwan da yake aikatawa na kuskure ta zo masa. To amma me? A washegarin ranar da asubahi yana kunna wayar sa da alert din banki ya fara cin karo, mai nuna an cire kudi miliyan biyar, zuwa akawun din wani Balogun Sunday. A take ya gane me Amani ke shirin yi, da ya tuna maganar su ta rannan a mota. Mukhtar ya kama kai cikin mamakin taurin kan ta. Wato ta yanke hukuncin data ke ganin ya fi mata. Tafiya Sierra Leone ko ta halin kaka, da dai ta amince Alhaji ya hada ta rayuwa da shi, don su kula da shi tare a kan lalurar sa har muddin ran sa. A fili ya ce. “Why Amani? Gaggawa daga shaidan ne!. Ya kuma tabbata don ta guje wa auren sa ne da mahaifin ta ya furta ta yanke shawarar guduwa any how, ba ta kuma da inda za ta je da nisa in ba can din ba. A take ya kira Alhaji, wanda a lokacin yana sallar asubahi a kan gadon sa daga zaune kamar yadda yake yi. Ganin kiran Mukhy a daidai wannan lokacin ya san ba lafiya ba, sai da wayar ta tsinke ya kuma idar da sallah, sannan ya kira shi da kan sa. Alhaji ka kula da takun Amani, kada a bar ta ta fita, ka sa ta a gaba mu tafi Faskari tare da taki da ta so. Ta fidda kudin nan da na gaya maka tana son fiddawa don a nemo mata Maman ta. She is desperate Alhaji. A taimaka mata. Bayan ni da kai na na yi mata alkawarin ni zan kai ta da kaina, zan nemo adireshin daga gare ka. Na tsara in mun gama da Faskari, in roke ka mu bi jirgi zuwa Sierra Leone din mu dangana ta da mahaifiyar ta. Ta yanke wannan hukunci cikin fushi, don haka ka bi ta a hankali ka rarrashe ta mu tafi Faskari tare, sauran ka bar komai a hannu na. Alhaji ya nisa, ba ya son kai yar sa ga Jalan da iyayen ta, don ya san Jalan bata son sa, kuma bazata taba son sa ba, don haka bazata so jinin sa ba, amma ya ya zai yi da Mukhtar tunda ya dage ya tsaya wa Amani a kan hakan? Jalan ta taya shi rainon diyar sa ne ko ko ta taba tunanin ta tako ta zo ta gan ta ko sau daya? Ai ta san inda ta bar yar in dai ba kiyayyar da ta ke masa ce ta shafe ta ba, ya ci a ce ko sau daya ta waiwaye ta ta ga cewa ta rayu ko ta mutu? Alhaji ya manta cewa shi ya raba tsakanin uwar da yar tun ranar da ta kawo ta duniya, shi y araba wannan kaunar da hannun sa, ya bar Jalan a halin da ita ma ba shi da tabbacin ta wuce ko ta rayu, Hausawa suka ce, laifi tudu. Alhaji ya ce, Kada ka damu, I will take care of her kafar mu kafar ta zuwa Faskari, in ka ga ta je wani waje bayan Faskari, to sai tana a matsayin matar ka, bisa yardar ka da amincewar ka. Biyayyar da ka yi min da kyautatawar ka gare ni Allah ya ba ka masu yi maka kai ma. Allah ya sa Amani ta zamo alkhairi gare ka da addinin ka. Allah ya ba ku zuria masu irin halin ka, ba masu irin nata halin ba. Dan murmushin mamaki Mukhtar ya yi, yana so ya ce, Alhaji na furta maka na amince ne? Amma kunya ta hana shi cewa komai, don karamcin Alhaji gare shi ya zama abin kwatance, tunda har ya amince ya ba shi auren tilon yar sa ba tare da ya san asalin sa ba, ba tare da ya san iyayen sa ko wani nasa ba, ba kuma tare da ya ga mahaifar sa ba. Sannan ba tare da amincewar yar tasa ba, wadda kowa ya san ba ya son bacin ran ta amma a kan sa ya yarda ya bata wa Amani karshen batawa da kan sa. Ko don wadannan dalilan, da wasu da dama, sai ya ji ba zai iya badawa Alhaji Usman kasa a ido ba. Zai rike masa amanar yar sa da dukkan halayen ta ababen ki, da dukkan tijarar ta da rashin kaunar ta gare shi. Zai iya rantsewa cewa zuciyar sa ta dade tana son AMANI, ita kuma ba ta son sa da alaqar aminci dake tsakanin sa da mahaifin ta, wanda ya san shi ya fi komai sayo masa bakin jini, kishi da tsana a idanun ta. Alhaji ya soma kokarin kiran Amani bayan sun rabu da Mukhtar a waya. Tana kallon kiran Daddy nata shigo mata amma ta kai zuciya nesa ta ki dagawa har ta katse, ya sake kira. Amani sai hada kaya ta ke tana kuka, amma ba ta amsa ba. Alhaji ya kira Malam Tajuddeen ya ce masa a rufe gate kada a bar Amani ta je ko ina in ba tare da su ba. Daidai lokacin Mukhtar ya shigo gidan, misalin karfe bakwai na safe, suka gaisa da Malam Tajuddeen da sauran maaikatan gidan, ya wuce maadanar motoci ya fiddo wadda za su tafi a cikin ta ya zuba mata mai da kan sa, sannan ya ce da Ali ya wanke motar amma wajen ta ba cikin ta ba, sannan ya karasa sassan Alhajin. Da sallama ya shiga falon, Alhaji ya amsa ya ce, Yanzu nake so in kira ka ka je ka turo min AMANI, tana can side dinta a saman bene. Na kira na kira ta ki dagawa. Mukhtar ya ce, Alhaji ka fara yin wanka tukunna, ka karya kumallo, ka kwantar da hankalin ka, everything will be alright, in sha Allahu. Ya taimaka wa Alhaji ya yi wanka, ya fiddo masa manyan kaya ya saka, ya tambayi Alhaji ina Hajiya Rabi don bai ga ta kawo breakfast ba har yanzu. Alhaji ya ce, Na ba ta tikitin ta daren jiya ta tafi, tana barazanar danne ni da filo in ban sake ta ba, daga kan ta na rufe aure in sha Allahu, zan zauna cikin kujerar nakasa in nemi lahira ta, har zuwa ranar da waadi zai cika, kai dai ka rike min Amani da gaskiya, ka bunkasa mata dukiyar ta har Allah ya baku zurria. Dan ku ya girma ya gaje ka kan shaanin kasuwancin mu. Idan na samu wannan na gama samun duk wani farin cikin rayuwa. A wannan lokacin Mukhtar ya jona kettle ya hada wa Alhaji coffee mai zafi ya bashi yana sha, ya yi waya kitchen ya ce Rakiya ta shiryo karin kumallo ta kawo wa Alhaji, kuma ta kai wa Amani. Ta lallashe ta ta tabbatar ta ci ko kadan ne, don fita za su yi. Alhaji na kurbar coffee dinsa yana jin abin da Mukhtar ke ce wa Rakiya, sai ya ji wani irin dadi ya lullube ran sa. At least Mukhtar bai ba shi matsalar da Amani ta ba shi a kan hukuncin sa ba. Ya tabbatar wa kan sa ko Mukhtar ba ya son Amani, to fa ba zai wulakanta masa ita ba duk irin halin fitsarar ta, wanda a yau ya yarda rashin tashi da uwa ne ya janyo mata, ko wata kwakkwarar uwar riko a gare ta. Kuma duk hakan ya faru ne bisa kuskuren sa da munanan halayen sa. Tun farko me yasa ya rabo ta da Sahura? Don kada ta sha wahala da rayuwar kauye. Me yasa bai barta ta rayu a Funtuwa ta samu tarbiyyar data dace a hannun kanwar sa ba da cikakken ilmin addini wanda zai sa ta san muhimmancin iyaye da girman da Allah ya yi musu? Rakiya ta shigo ta kawo musu karin kumallo mai rai da motsi, sinasir ne da miyar ganye da ta ji naman talo-talo, sai kunun gyada fari sal mai gardi. Mukhtar ya cikawa Alhaji plate ya tura masa gaban sa yana ta yi masa hirar abubuwan da ke faruwa a company kwana biyunnan don dai ya samu ya dauke damuwar da ke kwance kan fuskar Alhajin. Amma sai ya ji Alhaji ya ce, Na yi maka izinin hawa sama, har dakin TAFISU. Ka je ka zo min da ita nan cikin lallashi mu ci abincin nan tare da ita. Mukhtar ya rasa yadda zai yi da wannan umarni mai nauyi a gare shi na ubangidan sa, amma ganin irin damuwar da ke kwance a fuskar Alhajin sai ya ce. To Alhaji, amma idan ta ki fa? Zan dauko ta a ka ne? Ka san fa babu shiri irin wannan tsakanina da ita. Alhaji ya ce, Da irin haka ne za ku saba da juna. Har watarana ku kaunaci juna. Yanzu Amani matsayin matar ka ta ke, shaidu kawai ya rage su shaida. Mukhtar duk sai ya ji maganar ta Alhaji wani irin banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Alhaji ya kira Rakiya a waya ya ce ta zo ta raka Mukhtar sassan Amani. Rakiya na gaba, Mukhtar na bayanta har dakin Amani. Ta kwankwasa kamar yadda ta saba yi wa Amani. Amani na can abu goma da ashirin ya ishe ta don har zuwa lokacin da ta tura wa Mr. Balogun kudi da awanni biyu babu adireshi babu lambar waya na Maman ta da ya turo mata. Ta yi ta gwada kiran wayar sa tun tana shiga yana kin dagawa har ta daina shiga kwata-kwata. Ko dai an daina amfani da layin, ko an kashe wayar gabadaya. Sai ta dora hannuwa bibbiyu a kanta tana son rusa ihu ko ta samu saidah. Sai ga Rakiya ta murda kofar ta shigo, jin ta yi ta kwankwasawar Amani ba ta ba ta izinin shiga kamar yadda ta saba ba, sai kawai ta shigo kan ta tsaye don ta ga ko lafiya. Amani ta zuba wa Rakiya idanun ta da suka yi jazir da bacin rai, tana kallon ta tamkar ita ce Balogun. Rakiya ta karyar da kai gefe ta ce, Afuwan uwardaki na, Alhaji Mukhtar aka ce na rako wurin ki. Alhaji da kan sa ya ce in rako shi. Kafin Rakiya ra rufe baki, Amani ta samu zarafin ci mata mutunci, ko kunduma mata ashar, Mukhtar din ya shigo dakin kan sa tsaye. Daga jikin kofa ya tsaya hannuwan sa harde da kirjin sa yana kallon Amani da yadda a cikin dare guda duk ta zabure ta fice a hayyacin ta. Rakiya ta juya ta fita har da rufo kofar dakin, tana fadin a fito lafiya Alhaji. Mukhtar kallon ta kawai yake daga sama har kasa, wani irin kallo da bai taba yi mata ba. Duk da cewa kayan barci ne a jikin ta gashin kan ta babu rufi, gashin duk ya tarwatse duk ya yi buyaya da shi kamar sabon kamun hauka, shi a idon sa gani ya yi kamar an kara mata kyau da kwarjini, duk da idanun ta sun jeme sun yi zuru-zuru din. Kallon-kallo aka tsaya ana yi tsakanin Mukhy da Amani, kallon da su duka suka kasa fassara yanayin sa yayin da Mukhtar ya ji wani abu mai kama da tausayi ya darsu a ran sa game da ita, ganin yadda duk ta sauya kamanni da appearance a kwana daya. Amma ya riga ya san Amani zuma ce sai da wuta ake iya sarrafa ta. Kamar ba zai yi magana ba don ya san kiris ta ke jira ta saki tantrum, amma sai ya tuna damuwar da mahaifin ta ke ciki a kan ta. Ya tuna rokon da ya yi masa a kan ya lallaso ta ta zo ta karya kumallo tare da shi sannan su wuce Faskari. Alhaji yana da hope na cewa, shi kadai zai iya hakuri da tilon yar sa, mai tarin nakasu a halayya da dabia, shi ya sa ya damka masa ragamar rayuwar ta ta hanyar da ta fi kowacce muhimmanci ga dan adam, wato aure. Kuma a istikharar da ya yi daren jiya shi kam bai ji yana kin alamarin nan ba, ya dai san zai sha wahala iyakar sha a hannun Amani, tunda Allah bai halicci zuciyar ta da kaunar sa ba. Mukhtar ya nisa, ya kira sunan Amani, ba cikin yanayin da yake mata magana da shi a baya ba, na nuna halin ko in kula da alamarin ta. Wannan karon akwai kulawa da dan lallashi acikin sautin sa. Ya ce, Ki sani cewa komai ya yi zafi ga bawa bai fi karfin Ubangiji ba. Iyaye suna gaba da komai a rayuwar dan Adam. Mahaifin ki ba yaron ki ba ne, ba kuma dan ki ba ne da za ki dinga yi masa duk abin da ki ka ga dama ba. Ya kira ki kin ki amsa kiran sa, kin bar shi a damuwa, anya Amani kina son gamawa da duniya lafiya? A hakan kuma ki ke so Allah ya ji tausayin ki ya hada ki da mahaifiyar taki? Alhalin shi din da ya maye miki gurbin ta ba ki tsaya kin kyautata masa yadda yake kyautata miki ba? Me ki ka dauki kan ki Amani da ki ka zabi yin fito-na-fito da mahaifin ki? Ni da bai haifa ba na zabi in masa biyayya a kan umarnin sa, don na san ba zai ba ni matar da za ta cutar da ni ba. Sannan yana cikin hali na rashin lafiya yanzu, wanda kyautatawa da tausasawa kadai yake bukata daga gare mu. Yau in aka ce babu Alhaji sai kin fi kowa zama abun tausayi, ba ki ga tsuntsu ba ki ga tarko, baki rabauta daga biyayyar uba ba, sannan uwar ma ba za ki san inda za ki gan ta ba. Na zaunar da ke na ce ki bi shi a hankali, ki bar komai a hannu na, amma ki ka yi kan gaban kan ki saboda ke ba ki da mafadi kuma ba ki yarda kina da na gaba da ke ba. Zan iya rantsuwa da Allah kan cewa yan damfara ki ka tura wa kudi, bayan na gaya miki kada ki tura, gaggawar ta mece ce tunda na ce ni da kaina na yi alkawarin kai ki ga mahaifiyar ki amma karkashin umarni da amincewar mahaifin ki? Yanzu ina adireshin da ki ka sayo miliyan biyar sai ki ba ni in gani. Kuka ya kubucewa Amani, ba kukan shagwaba ta ke yi ba yau, kuka ne na kubucewar azanci da tausayin kai. In ta ce maganganun Mukhtar ba su yi tasiri a zuciyar ta ba ta san ta yi karya. Da gaske Daddy ya wuce komai a gare ta, kuma bai cancanci reactions din da ta ke yi mishi ba, amma zabin da ya yi mata ne ba za ta taba karba ba, domin ya kaskantata, ya sayar da ajin ta ya zubar mata da ego din ta, muddin Mukhtar zai bai wa auren ta. Daga nan har kotun koli za ta je don neman hakkin ta a kan hakan, bazata taba yarda tayi auren kaskanci ba, auren yaron Alhaji mara asali, mai halayen da ta ki jini, wato musamman girman kai, da kin yarda a taka shi, ita kuma ta saba taka kowa da ke kasan ta, tunda ta yi kokarin riskar mahaifiyar ta don ta samu mafaka a gun ta abun ya ci tura. Tana ta kuka tana fyace hanci da share ido da gyalen ta, Mukhtar ya ce, Taso ki biyo ni, mahaifin ki na son ganin ki, in kuma kin ki tashi ko a ka ne zan dauke ki in kai masa ke, na rantse. A yadda ta ga idanun sa sun rikide cikin bacin rai ta san sarai zai iya aikata abin da ya furta, sai kawai ta mike, ta na so ta ce ya ba ta wuri ta canza kaya, amma ya kasa ya tsare a kofar dakin yana muzurai na ko ta wuce ko ya ciccibe ta. To ka je zan canza kaya. Ta fada a turbune, fuskar kamar wani kauye wai shi Durbunde saboda turbunewa. Mukhtar sai ya ga akwai bukatar ta canza kayan, bai kamata ta tafi har Faskari da kayan barci ba, sai ya juya yana fadin, Na ba ki five minutes, in ban gan ki a falon Alhaji ba da jakar fita unguwa da trolley din matafiya da kayan ki da zasu yi miki a kalla kwana bakwai a ciki zan dawo. Don tafiyar tamu ba mu san har yaushe za ta kai mu ba, tunda neman sulhu da gyara zumunci ne zai kai mu. Ya fice a dakin ya bar mata daddaddan turaren sa na sirnanawa a kofofin hancin ta. Tana kuka tana komai ta canza kayan jikin ta, ta sanya doguwar riga sannan ta yi maza ta yayibo mayafi ta jefa kaya kala uku da man shafawa da deo spray a trolley da yan sauran abubuwan bukatar ta. A gurguje ta rufo dakin ta fito kada ya kara dawo mata daki, don ko turaren sa ba ta son ji, balle ganin cunkusasshiyar fuskar sa mara annuri da rashin walwala. Sai da ya taimaka wa Alhaji ya gama kintsawa ya debar masa duk abin da zai iya bukata har nan da kwanaki bakwai kama daga magungunan sa da kayan sanyawa ya kai komai mota. Ya dawo kenan ya tadda ita a falon na Alhaji, da jakar tafiya a gaban ta. Alhaji na ta faman lallashin ta kamar shi ne yar ita uban, yana gaya mata duk abin da ta ga ya yi mata soyayya ce, idan kuma har ta zabi ta bijirewa umarnin sa ta hanyar tozarta shi a idon Mukhtar, to kuwa zai yi hakuri da duk son da yake mata ya sallama ta, zai kwace komai da ya mallaka mata ya kai ta wajen mahaifiyar tata su karata. Mukhtar ya yi kamar bai ji me Alhaji ke fada ba a karshe, ya ce, Alhaji komai ya kammala, mota an mata full tank an kuma wanke ta sai tafiya ya rage. Allah ya yi maka albarka Mukhtar, dauki kayan ta ka sa mata a mota, jakar hannun ma karba mata. Yar murmusawa ya yi, a ran sa yana fadin, Alhaji ke kara lalata yarinyar nan, ya karba mata jakar hannunta wato ga mijin Hajiyar Faskari ko? Ko Alhaji ba ya karba wa briefcase in za su fita balle wannan fitsararriyar. Tana jira ya daukar mata har jakar hannu kamar yadda Alhaji ya yi masa umarni, sai kawai ta ga ya dauki trolley dinta da hannu daya ya bar falon. Ita ta kai zuciya nesa ta dauki jakar ta rataya sannan ta turo Alhaji a kan keken sa. Ita da Mukhtar din suka yi kici-kicin saka Alhaji a mota, ya nade keken nasa ya saka a boot din motar. Gidan baya ta shiga ta zauna gefen Alhaji don tana ganin ta fi karfin ta jera kafada da Mukhtar a gaban mota, alhalin yana matsayin yaron Alhaji ko kuwa ta ce direban ta. Zuciyar ta ba za ta taba ba shi wani matsayi bayan wadannan ba. Alhaji zai yi korafin muhallin da ta zaba don zama sai gani ya yi Mukhtar ya tada motar, ko a jikin sa, shima baya so ya hada kafada da ita, ko ba komai ta kula da Alhaji a bayan motar wanda suka yi masa kujera ta musamman suka sanya mishi belt sosai. Kamar ya san a karkashin zuciyar ta ta so ya yi magana ta gaya masa mara dadi, ta gaya masa har abada shi yaron gidan su ne, kada wani zancen aure da Alhaji ya furta ya rude shi. Sai aka yi saa bai tanka mata ba, ya ja mota cikin tukin sa na nutsuwa, na kwarewa da kamala suka yi reverse, wanda ba haka ta so ba. Mukhtar ya sa a ran sa ba zai dinga biye mata ba yanzu kamar da, saboda jiya da ya yi wa Alhaji b.p ya ga ya hau sosai. In ta rasa wanda za ta yi wa rashin kunyar dole za ta yi shiru ta bar su su ji da abin da suka fuskanta yanzu, wato gyara tsakanin Alhaji da yan uwan sa. Malam Tajuddeen ya bude musu kofa tare da daga musu hannu yana fadin, a sauka lafiya. Mukhtar ya dan daga masa hannu shima, sannan suka fita gate din gidan. Sannu a hankali ya hau bisa kwalta, sannan ya soma shimfida gudu da su kamar zai tashi sama dasu, abin da ya san Amani ba ta so, wato gudu da mota musamman a babban titi irin wannan, baa cikin gari ba. **** ***** **** Suna tafe kan titin da zai shiga garin Faskari Mukhtar ya kunna karatun Alqurani mai tsarki ya kure a radiyon motar cikin Suratul Baqarah, duk yadda ta ke so ta yi masa korafin gudun da mota da yake yi da su albarkar wannan karatun da ya kure sai ta kasa, ta samu kan ta da nutsuwa tana sauraron ayoyin na karshe na suratul Baqarah da taji sun mata dadi, kasancewar ita bata saba sauraren karatu ba sai music. Mukhtar na tafe yana tambayar kan sa shin ko Amani ta taba yin islamiyya? Balle a je ga batun sauke Alqurani? Ya nisa, umh. A lokaci guda Alhaji na tuhumar kan sa da ka sa a ran sa da sakaci mai yawa da ya yi a kan tarbiyya da kuma upbringing din Amani in general. Ya tuna ko hizfi biyar ba ta da shi a kan ta, don tun tana karama da ya dauki wani bayerabe yake zuwa gida yana koya mata karatun Alqurani, da ta yi wayo ta kai munzali sai ta nuna ba ta raayin koyarwar malamin. Dole Alhaji ya sallame shi. Daga wancan lokacin kuma Amani ba ta kara shaawar tahfiz ba, dan wanda ta samu a gun bayeraben nan da shi ta ke karatun sallah har yau. Alhaji ya nisa yana fadi cikin ran sa, na yi kuskure mai yawa a rayuwa ta. Allah ka bani ikon gyarawa kafin ka dauki rai na. Allah ya sa Mukhtar ya rike min Amani da dukkan nakasun ta, ba tare da ya goranta mata tarbiyya, ilmin addini da goyon gatan da na yi mata ba. Yau ga shi ga dukkan alamu Amani na so na kasa lankwasa ta. Wa ya janyo komai? Alhaji ya kara kudirewa a ran sa sai dai Amani ta mutu, amma sai ya cika kudirin sa, in yaso ya wanke gawar ta ya fara kaiwa gidan Mukhtar kafin ya danganata da kushewar ta, amma ba ta da miji insha Allahu sai Mukhtar din sa. Idan ta bijire masa wannan karon zai ba ta mamaki. (Alhaji ya manta icce tun yana danye ake tankwara shi). Daidai lokacin da Mukhtar ya karya kan motar suka hau burjin da zai shigar da su garin Faskari, Alhaji na ta kallon garin iyayen sa da kakannin sa with nostalgia, yana kokarin tuna ko yaushe ne last shigowar sa Faskari? In zai iya tunawa daidai tun lokacin da yake nema kujerar sanatan Katsina ta Tsakiya yana neman kuriar karamar hukumar tasa. Da ya zo ya dan yarfa musu. Ya tuna lokaci na karshe da Yaya Idrisu ya kira shi a waya yana gaya masa Kamilu dan sa ya kammala karatu an turo shi hidimar kasa cikin jihar Katsina ko zai ba shi muhalli ya zauna a gidan sa yayi hidimar kasan? Yadda ya balbale shi da fada kamar kanin sa yana fadin ba ya son a zo a cika masa gida shi bai iya jaye-jayen yayan dangi ba. Ya tuna cewa uwar Kamilun ita ta shayar masa da Amani, ba don ita ba da bata rayu ba, ko sai da madarar gwangwani. Yau ga shi ya dawo Faskari babu kafafu sai dai a tura shi a keken guragu, rabin jiki ba ya aiki, kuma kai tsaye gidan Yayan nasa ya dosa, wato gidan su na gado, wannan abun kunya da kayan nadama har ina? Ita dai Amani da ke gefen sa tana danne-danne a waya, sai gani ta yi Daddyn ta yana hawaye, ya kuma bar su suna ta zuba akan kundukukin sa ba ya ko sharewa wasu na korar wasu. Idan ya kara tuna cewa uwar Kamilu ita ta shayar masa da Amani, amma shi ya kasa daukar ko Kamilun ne ya yi yan watanni tare da shi na hidimar kasa duk irin arzikin da Allah ya yi masa da girman gidajen sa a Katsina. Yailahi! Da wace fuska zai doshe su yanzu? Da wane azancin harshe zai nemi gafarar su? Ba tare da sun yi tunanin sai da lafiya ta kare masa ba ne ya neme su? Don in bai manta ba daga waccan wayar da suka yi da Baba Idrisu har gobe Baba Idrisu bai kara neman sa ba, ya rike talaucin sa da mutuncin sa, ya rike yayan sa a kauye ko birnin Katsina ya haramta musu shigowa don ma kada su nemi kanin uban nan nasu da bai san muhimmancin zumunci da girman zumuncin Allah ba. Alhaji shi ke nuna wa Mukhtar hanya har kofar gidan iyayen sa, soron gidan duk ya zube, kana iya hango tsakar gidan da duk abin da ke ciki duk da an kare da zangarniyar dabino da azara. A nan ya umarci Mukhy ya yi fakin motar, daga can hanyar masallaci Alhaji ya hango Yayan sa Malam Idrisu na tahowa, Mukhtar ya fito ya bude but ya fiddo kujerar Alhaji ya warware ta ya dauko Alhajin daga mota ya sanya shi cikin kujerar. Amani ta fito tana ta cin magani da yatsine-yatsine, har da zumbure-zumburen baki, ita ta tura Alhajin zuwa kofar gidan su, yayin da Mukhtar ya tsaya kici-kicin fiddo kayan su. Daga nesa Malam Idrisu ya hango su babu bata lokaci kuma ya gane Amani tare da wani farin balaraben mutum da bai sani ba. Amma dattijon da ke cikin kujerar wheelchair ko kusa bai kawo cewa kaninsa Usman ba ne. Amani ta jira rike da hannun kujerar har ya iso, sai a lokacin ya gane dan uwansa. Innalillahi wainna ilaihi rajiun. In ji Malam Idi, yana fadin, Me ya same shi? Me ya faru da shi haka? Zuciyar yan uwantaka! Tuni ya karbe shi daga hannun Amani, da kan sa ya tura shi zuwa cikin gida. Kai Isya je ka kasuwa ka kira Kamilu ya zo ya bude wa baki dakin sa su aje kayan su. Yaron da aka kira Isya ya zura da gudu yana waiwayen Mukhtar don ya dauka bature ne ko wani balarabe, fatar sa ta wanku da boko, ya karya hula damanga a saman kansa wadda ta dace da launin shaddah getzner lemon green da ke jikinsa, kai ba za ka ce haihuwar Africa ba ne shi ya fi kalar larabawa. Uwa, ku ne tafe? Sunan da yake kiran Amani, kasancewar sunan mahaifiyarsu ta ci, wato Inna Amina mai rasuwa. Amani ta zumburo baki, kafin ma ta furta wa Yayan uban nata gaisuwa ta alada sai da ta saki korafi irin na rashin kunyar da ta saba yi wa Alhaji. Za ka fara ko, daga zuwa na? Kira na da UWA? Shi ya ce min wani TAFISU kai ka ce min wani UWA, bayan ga suna na mai dadi na yanka. Dariya Malam Idrisu ya yi don shi a duniya yana son Amani, duk da halin ta kuwa, ya sa matar sa uwargida Talatu ta yi musu shimfidar tabarma karkashin katuwar dalbejiya da ke tsakar gidan. Mukhtar ya gaishe shi cike da girmamawa, ya gaida Baba Talatu, Baba Idi na son tambayar Amani inda suka samo kyakkyawan mutum haka, shi kuma ba balarabe ba, don ga hausa ras a bakin shi, amma ya fi damuwa ya ji yadda aka yi dan uwan sa ya koma rayuwa a wheelchair. Faduwa ya yi a bandaki, ka san yana da hawan jini, shine ya samu stroke. An fidda shi asibiti har kaar Faransa Allah bai sa ya mike ba. Amma yanzu a hakan da sauki sosai, tunda yanzu yana magana ras, yana kuma iya motsa duka hannayen sa. Baba Idrisu da Baba Talatu suna ta sallallami da jajantawa, tuni suka manta da halin Alhaji. Baba Idi ya ce sai a koma na Hausa, ya san inda ake maganin irin wannan lalurar ta hanyar gargajiya a garin Kaita. Wannan lalurar da suka samu Alhaji a ciki sai ta maida komai ba komai ba na laifukan Alhaji a gun su, don dan uwan ya damu sosai, tunda shi da ma ba wai yana kwadayin abun hannun shi ba ne, aah zumunci na Allah yake yi da shi, kuma kulawar sa garesu kadai yake bukata. Kafin dan lokaci Kamilu da yayyen sa biyu Jibril da Usama sun iso gidan, Jibril da matar sa da yayan sa hudu haka shi ma Usman da yaya biyu. Suna ta lale-marhabin da Baffan nasu, tare da jajanta lalurar da ta same shi. Alhaji sai ya fashe musu da kuka yana neman gafarar Baba Idrisu, yana kuma tambayar Sahura. Talatu ta ce, Gobe insha Allahu za ta aika mata ta zo daga Funtua. Nan aka shiga mayar da zance tsakanin Alhaji da Yayan sa Malam Idrisu, ko ya rike dan uwan nasa a baya, ganin halin da yake ciki da nadamar da ya zo da ita duk sai ya ji rikon na narkewa a ran sa. Duk da haka ya fito fili ya gaya wa dan uwan sa yadda yayi wasarere da zumunci bai kyauta ba, ba ya neman kobon sa amma dole ya kyautata zumuncin Allah muddin yana son gamawa da duniya lafiya. Alhaji har su Kamilu sai da ya bi daya bayan daya ya nemi gafarar su, ya tambayi kowannen su abinda yake ciki, suka gaya masa, cewa wasu cikin su kasuwa suke zuwa wasu gona wasu sun yi karatun NCE wasu har degree, sai Alhaji ce wadanda suka yi karatu a cikin su zai tafi da su a duba ayyukan da suka dace da su a kamfanin Amani, wadanda ba su yi karatun ba ma duk ba zai rasa irin aikin da ya dace da su ba. Baba Idrisu ya ce, Ai kam ba ka kwashewa duka ka barmu mu kadai, sai kananan yara. Ka dai dauki masu takardun bokon ka bar min sauran su ci gaba da kasuwa da gona. Alhaji ya ce, Mukhy, sai a binciki irin sanaar da suke yi din a nan a bunkasa ta, a ba su training a kai, sannan a ba su jari mai tsoka. Consider it done Alhaji. Abu dai ya yi dadi tsakanin Alhaji da dan uwan sa da yayan dan uwan sa. Sai washegari Sahura ta iso don amsa kiran da Baba Idi yayi mata tun jiya, Alhaji sai ya ga duk ta tsofe ta mokade saboda wahala, don mijinta ya rasu ya bar ta da yaya takwas. An yi sulhu cikin tausayin juna sun yafe wa dan uwan su, suka ce ba su taba kullatar shi ba ko don Amani da bata yada su ba ita, kullum addua suke masa koda kuwa sunan sa kadai suka ji an fada a kafafen yada labarai. Baba Idi ya ce, Ah toh ni ai ban damu ba, na sani ko ba-dade ko ba-jima za ka neme mu, tunda ba ka da wadanda suka fi mu. Kusan kwanan zaune suka yi ranar da Sahura ta zo ana ta maida zance da labarin juna. Alhaji ya ce, tunda Sahura ba ta da karamin yaro duk ta aurar da su, na karshen ma yana makarantar Alkalam a Katsina, to zai tafi da ita gidan sa ta zauna tare da Amani kafin wucewar ta gidan mijinta. Sahura, Baba Talatu da Baba Idi har suna hada baki wajen tambayar Alhaji cikin mamaki, Uwa ta samu miji ne? Don su kam basu ga mijin da zai iya daukar Amani ba. Alhaji ya gyara zama da filon da aka sa masa a bayan sa, ya soma warware musu tun ranar farko na haduwar sa da Mukhtar a kasar Faransa, da irin gudunmawar da ya bayar ga habakar dukiyar sa, amanar sa, halayensa, rikon addinin sa da irin gudun duniyar sa. Ya kare da ba su labarin zuwan Alhaji Sadi neman auren Amani, da sanadin samun lalurar sa da jinyar sa da Mukhtar ya yi a Paris, tare da Amani, halayen Amani da Mukhtar yake tolerating, har da ganewa da ya yi cewa Mukhtar zai iya da halaye da dabiun Amani marasa kyau har ya samu ta gyaru ko ba ta so, a dalilin ganewa da ya yi Mukhtar kadai ta ke shakka, kuma shi ke iya lankwasa ta ta bi raayin sa ko ba ta so. Wannan ne dalilin da ya sa ya yanke shawarar hada su aure duk da Amani ba ta so, domin auren su ne kadai zai dorar da kyakkyawar dangantakar shi da Mukhtar din. Yana so wannan ya zama wasiyya da ya bari ko da ta Allah za ta kasance a kan sa gabanin ya daura musu aure da hannun sa. Yan uwan nasa sun fahimta, sun kuma gamsu da hujjojin sa. Rashin kunyar Amani wa ta bari? Tun tana karama yi ta ke har ya zame mata dabia a girman ta. Mukhtar din kamar yadda Alhaji ya ce yana da dakakkiyar zuciya kuma ya san halin ta, sannan bai yi musu ba da Alhaji ya ce ya ba shi aurenta. Suna da kyakkyawan hope na cewa zai rike Amani ko don kaunar da ke tsakanin sa da mahaifin ta. Amma sai Baba Idi ya ce, Ka binciki asalin sa? Ka gana da iyayen sa? Ka san daga inda ya fito, kuma ina dangin sa? Alhaji yayi danjim! Kafin ya ce, Ai ni ko daga sama Mukhtar ya fado, wato bai da iyaye, ko tsintacce ne a kan bola na bashi auren Amani, shaidu ya rage su shaida. Ni zan masa waliyyi, kai ka yi wa yar ka Amani walicci, goben nan nake so in mun sauko sallahr jumaa lafiya a daura musu aure. Jiki na na bani ko ma daga wane tsatso Mukhtar ya fito tsarkakken tsatso ne. Tsatso kuma mai albarka. Zaka taya ni fahimtar hakan idan ka zauna dashi na kwana uku. Baba Idrisu ya ce, Duk da haka, bayan daurin auren dole ya dauki matar sa ya kai ta ga iyayen sa su sanya musu albarka, in basa raye to bazasu rasa dangi ba. Alhaji ya ce, Na fahimta, amma a halin yanzu na fahimci Mukhtar yana da damuwar da ta fito da shi daga gida wadda ta saka ko a yi masa zancen ya je gida ba ya so. Bana so na takura masa (for now), da cewa lallai sai ya koma gida zan aura masa Amani, zan ba shi lokaci har zuwa sanda shi da kan sa zai bukaci hakan a karan-kansa, ba abin da lokaci ba ya iya canzawa a rayuwar dan Adam, amma zan roke shi kamar yadda ka ce kan su je garin iyayen sa bayan auren ya gabatar musu da iyalin sa, don su san da auren sa, ba sai sun tara yaya ba sannan su je musu, wajibi ne mu san mun damka Amani a hannun dangin sa da kan mu, saboda gaba a ke hange da yayan da za a haifa. Baba Idrisu ya gamsu da wannan shawarar ta Alhaji. Sun tsayar cewa gobe Jumaah bayan saukowa masallaci za su daura auren Amani da Mukhtar. Alhaji zai ma Mukhtar walicci Baba Idi zai wa Amani. Baba Idrisu ya dage Alhaji ya bar Mukhtar ya biya sadakin sa da kan sa. Don da cewa ya yi sadakin ma shi zai biya masa. Daga Amani har Mukhtar ba su san wainar da iyayen suke soyawa ba, don sun basu wuri ne don su gana da junan su. Shi Mukhtar yana dakin Kamilu inda aka sauke shi, Alhaji dakin da Jibril ya tashi ya bari aka share masa. Amani tana dakin budurwar gidan da ba a yi wa aure ba mai suna Laure. Ta yi korafin cizon sauro, sai da Laure ta je ta sayo maganin sauro ta kunna mata. Nan ma ta ce ba ta son warin sa, a nemo na fesawa. Laure ta fara gajiya da iskancin Amani, ta ce sai ki koma dakin Baba Talatu, ni ba zan kara fita a daren nan ba. Amani ta ce, Aah, gara in yi maneji da nakin ya fi tsafta kada in je berayen ta da ke tsere a gaban mutane su gwagwiye min kafa. Washegari Baba Idi ya sa Baba Talatu ta yi karin kumallo mai kyau duk gidan, kunun tsamiya aka yi da lafiyayyen kosai, aka kuma hada da shayi da biredi, saboda Amani da ta ce ba za ta sha kunu ba. Baba Idi ya ce, Ki yi ta yi. Nan din dai shi ne asalin ki, sarkin iyayi da kidifiri, kuma saboda ke tuwon gero za mu yi anjima miyar kuka da daddawa. Alhaji ya yi dariya ya ce, Tafisu ce, don Allah a dafa mata mai maiko. Baba Idrisu ya ce, farin balaraben mijin ta ya ba mu na cefane ne? Tunda ya zo fuska ba walwala, sai tamke fuska yake yana muzurai kamar yaci babu, a yi mutum kamar mai fuskar shanu? Amani ta tashi ta bar wurin, saboda bakin cikin Baba Idi ya alakanta aure tsakanin ta da Mukhtar. A ran ta ta ce, Ah toh! Ashe ba ni kadai na ki jinin yadda yake da rashin walwala ba, mai nuna zuciyar sa ba humanity ba compassion a cikin ta ko kadan. Balle a kai ga zancen soyayya iri ta mata da miji. Amani ta kyabe baki, a fili ta ce Allah ya tsari gatari da saran shuka ba dai ni Amanin ba. ta ce a ran ta muna komawa Katsina za su neme ni su rasa. Wallahi ba zan zauna a aura min wanda zuciyata ba ta taba kauna ba, kuma har abada ba za ta taba so ba. Na bi jar fata da gudu da bakin gashi na tattake ba takalmi a kafata. Ana saukowa masallaci a babban masallacin jumaa na garin Faskari Baba Idrisu ya gaya wa Liman a dakatar da mutane, zai daura auren yar sa Amina diyar kanin sa. Tun wayewar gari ya karbi sadakin Amani daga hannun Mukhtar Diffa, wanda ke ji da ganin komai na faruwa kamar almara. Ya kasa gasgata cewa shi Mukhtar ne zai yi aure yau. Ya biya sadaki mafi albarka, wato mafi kankanta daga aljihun sa, wanda ya kasance gumin sa ne. Bai gasgata duka abubuwan da ke faruwa ba, wadanda yake gani kamar a mafarki, sai da ya ji an shafa fatiha, mutanen garin Faskari da suka halarci sallar jumaa a yau duka suka shaida daurin auren Mukhtar da Amani. *** *** *** Mu karasa a littafi na 2. Sumayyah Abdulkadir 07030137870 (whtsp only)