https://chat.whatsapp.com/LP1fwEwAkejETakHaD59VO *_Bismillahir rahmanir rahim_* *_KURMAN BAK'I_* *H U G U M A* PAGE 01 _Akwai saqonni masu tarin yawa a ciki,saidai kuma KURMAN BAQI ne me wuyar fassaruwa,ga duk me nisan zangon hankali da tunani zai tsinkayi hakan,DAN JAGORA NE ga mata,musamman masu KISHIYA,kuma hannunka me sanda ne ga masu sana'a data shafi labarin dake cikin littafin_ *NOTE:qirqirarren labari ne wanda ya dace da matsalolin da mata ke fuskanta a yanzu,komai dake ciki qirqirarre ne,idan ya dace da zahirin rayuwar wata to arashi aka samu* Zaune take zaman farar stool din dake ajjiye gaban dressing table din dakin. K'afarta daya kan daya tana kuma karkadasu da wani irin sauri. Kallo daya tak zaka yiwa fuskarta ka fahimci akwai zallar bacin rai mai mugun yawa shinfide a saman fuskarta,bacin ran da ko shakka babu yana yiwa zuciyarta wani irin fusga da kud'a me ciwo. Hatta da launin idanunta zuwa fuskarta sun sauya,abinda zai alamta maka kuka tasha bana wasa ba,da alamu kuma ba wani lokaci me tsaho ta dauka da gama kukan ba. Har cikin zuciyarta takejin wani irin masifa da tashin hankali suna sadakarta. Qoqari take tayi ta taushi zuciyarta amma kuma kamar hakan yana neman gagararta. Ita din tana cikin jerin sahun matan da basu iya cinye fushi da bacin rai ba tare da zukatansu sun furta ko sun furzar da shi ga dukka wanda yayi silar afkwarsu a wannan yanayin ba. "Idan ba damuwa don Allah zan dan fita yau din,amma bazan wuce awanni biyu ba zan dawo in sha Allah" Sautin muryar dake tashi sama sama ya ratso ta cikin windows dinta,ya kuma keta labulayenta ya isa ga kunnuwanta. Isar sautin muryar kadai ga kunnuwanta amma sai taji kamar an sakar mata guduma cikin tsakiyar zuciyarta. Tana da muradin jin amsar da wanda akayi maganar dominsa zai bayar,wannan ya sanyata miqewa zumbur ta kuma kai ga labulen ta yaye a zafafe. Fes take iya hango mutum biyun wanda ke magana cikin wata irin nutsuwa a tsakaninsu. Tsayayyen namiji ne wanda ke tafe da tsaho da kuma qibarsa gaba daya,wanda hakan ya bashi wani irin kyakkyawan murjajjen jiki da ya qara masa kyau da cikar zatin da kai tsaye ya isa ya amsa sunan NAMIJI. Duk kuwa da cewa shi din ba wani mugun kyakkyawa bane,amma sam sam bai hada koda hanya da kalmar MUNI BA. Baqi ne da bahaushe kan kira da wankan tarwada,wanda yayi wani irin kyau me cike da nutsuwa cikin wani lallausan yadi ruwan sararin samaniya a jikinsa. Ganinka na farko da shi zaka tabbatar da cewa shi din gwanine wajen iya murza hula da sanya sutura ta zauna a jikinsa,hakanan telansa ya qware qwarai da gaske gurin baiwa dinki haqqinsa,dukka wadannan abubuwa suna da cikin abubuwan da suka hadu suka qarawa SALEEM kwarjini da cikae kamala da kuma siffa. Matar dake a gefansa kuwa duka duka shekarunta ba zasu haura ashirin da takwas ba,idan tayi nisa da yawa ashirin da Tara zuwa talatin. Ita dinma baqa ce kamarsa,saidai nata baqin har yafi nashi gogewa,chocolate color ce sosai,mai matsakaicin tsaho,ba gajeriya bace,saidai kuma bata kai tsahonsa ba sam sam. Tana da manyan idanu masu matsaikatan girma,hakanan hancinta yana da tsaho da tudu. Komai nata matsakaici ne,itama tana da wani kyau na daban,wanda baiyi yawa ba. "Ina zuwa kenan?" Ya tambayeta yana duban fuskarta da murmushi ya subuce mata "Gidan aunty khadija mana" kai ya jinjina yana murmushi "A dawo lafiya Allah ya tsare" ya fada yana same fadada murmushinsa. Qaramar dariya ce ta qwace mata "Da sauri haka?,saboda kaji gidan aunty deeja ne?" Ido ya fiddo yana sakin wani murmushin "Ta yaya zan hanaki zuwa nan?,ai nasan ta samu ne" ya fadi qasa qasa. Siririyar dariyar da ta ajjiyeta musamman saboda shi ta saki,cikin salon nuna jin kunya tace "Ni bance ba,amma dai sirri ne" "I know,bance sai naji ba nima,Karki jima please" ya fada cikin tausasawa yana takawa zuwa muhallin ajiyar mota na gidan dake dauke da motoci gida uku kamar yadda iya adadin abinda zai iya dauka din kenan "Nasan ba ka son yin dare a waje daddynsu,ba zan kuma saba ba in sha Allah" dakatawa yayi da tafiyar ya waiwayo yana dubanta. Wani murmushi ne saman fuskarsa wanda ya sani bai isa ya hanashi fita daga fuskar tasa ba. Tattausan murmushin itama ta saki sannan tadan rausaya kanta cikin alamun jin nauyin kallon da yake matan. Tamkar an saya hannu an finciko zuciyarta daga qirjinta haka ZAINAB taji. Taji na zata iya qara koda second daya a tsaye tana kallon wannan abun ba. Sai ta saki labulen da sauri ta kuma juya da sassarfa tana rufar qofa zuciyarta na sake soyewa da wani irin zafi da radadi. Ya za'a yi mutumin da tun daren jiya ta rasa ganin walwala koda qanqani saman fuskarsa?,hatta da abincin darensa ma bai samu ci ba,ya kuma gaya mata baijin dadi ne a haka suka kwana amma shine yake rausaya da idanu da wani irin shu'umin kallo irin haka?. Bayan ko yau da safe a tsaitsaye ya shirya,ko fuskantarta suyi magana ya kasa yi,sai baya da ya juya mata,ya gama shirinsa a gaggauce ya fice?. Ta dauka ya jima da barin gidan ma,ashe yana tare da wannan makirar baqar matar tasa. "Allah ya bada sa'a,ya tsare mana kai,ya baka ikon nemo halak ka ciyar damu da ita,a dawo lafiya" idanunsa ya lumshe kadan,addu'arta tana masa tasiri har tsakiyar zuciyarsa. Wanann addu'ar na cikin jerin abubuwan dake faranta zuciyarsa duk safiya,ta kuma yi masa rakiya har zuwa shagonsa na kasuwa. Da fara'ar shimfide akan fuskarsa ya bude idanunsa yana motsa labbansa. Sai idanun nasa suka sauka akan zainab wadda ke tsaye tana numfarfashi nata idanun itama a kansa. Janye dubansa yayi daga kanta ya mayar ga RUQAYYA yana cewa "Ameen ameen,na gode qwarai,Allah yayi albarka" "Ameen" ta amsa masa tana shafa tafukan hannuwanta dukka biyun saman fuskarta,sannan tayi taku biyu taja baya daga kusa da zainab din,ba tare data dubeta ba saboda sanin cewa ko meye zata gani saman fuska da idanunta ba alkhairi bane,sai ta saka kai cikin gidan tana zarcewa sashenta. "Har ka warke kenan?" Zainab ta jefa masa tambayar kai tsaye tana ci gaba da dubansa, tambayar da tazo da salo ma titsiye da kuma son qure mutum "Dama ai ba ciwo nakeyi ba,nace dai miki bana jin dadi ne kawai,kuma kowa yana tsintar kansa a irin wannan yanayin"Ya fada yana janye dubansa daga kanta,baqinciki na lasar zuciyarsa. Ita sam kwata kwata ma kamar bata kishin kanta?,bata taba damuwa da ta sauya wasu abubuwa ba ko don ruqayya. Ruqayya din bata taba zamar mata abar kwatance ba,tafi bawa abu guda daya muhimmanci,sannan wannan abu dayan tafi bashi himma kima da darajar data zarce ace an bashi din. "Kaji dai tsoron Allah kada ranar qiyama ka tashi da shanyayyen barin jiki wallahi.....koda yake ba laifinka bane,kaci ka sha,duk da shima asirin ai yana tadda hali ne" ta fada a zafafe sannan ta juya abinta tana komawa cikin gidan da sauri saurinta. Bai dakata da kallonta ba har ta bacewa ganinsa,ya sauke numfashi mai nauyi ya zura key yana qoqarin bude motarsa yana girgiza kai hadi da jan wani qaramin tsaki. Ba abinda ke yawo a idanunsa sai rigar baccin jikinta wadda duk dalli dallin maiqo ne a jikinta,abinka da abu silk jirwaye da maiqo bashi da wuyar nunawa a tattare dashi. Iya tsaiwarta a wajen,qamshin jikin ruqayya ya baje ya koma inda ya fito,ba komai a wajen sai wani yanayi dake nuni da lokaci yayi da gangar jikin mutum ta fara buqatuwa zuwa ga wanka,wankan da yayi imanin koda za'a yishi to saifa idan ya dawo ko kuma yana dab da dawowa idan an tafka sa'a a ranar. Zuciyarsa cike da qiyasce qiyasce da juya al'amuran zainab ya tashi motarsa sannan ya sulale ya fice a gidan yana son daidaita nutsuwarsa kota halin qaqa. A nutse ta tura qofar parlor din nata da bata gama rufewa ba saboda tana sauri ta cimmasa ta gaya masa zata fita din a yau. Ko ina a gyare yake tsaf a killace,sai ka rantse bata da yaro ko guda ko kuma amarya ce,saboda sassanyan qamshin turaren wuta da burner din dake kunne take bayarwa. Gurin burner din ta isa ta kasheta,ta gama bata qamshin da takeso ta kuma biya mata buqatarta. Sassanyan qamshin da tasan saleem din yafiso a ko yaushe bata taba yarda ta rabu dashi,bata damu ba da ranar girkinta ne ko ba ita ke da girki ba,itadai burinta a ko yaushe wannan qamshin ya zamana shine abu na qarshe da ya shaqa dag wajenta don ya zama abokin tayashi tunata tsahon yinin da zaiyi gurin neman halal dinsa. A nutse ta buda daya daga cikin qofofin dake parlor din. Madaidaicin dakin yara ne me dauke da qananun gadaje guda uku,cikin dayan gadon yarinya ce ke kwance tana bacci. Sai data leqata ta tabbatar babu wata matsala sanann ta dawo a nutse ta rufe qofar,ta isa ga madaidaicin dining dinta me kujera hudu tana tattare plates din da ta gama breakfast. Yau duka tayi abincin karin tare da yara ta diba nata saboda tanason fita din,batason tsaiwa hada wani lokaci ya qurace mata. Tsaf ta gama hada plates din da cups din,zata debe ta wuce kitchen taji an banko qofar babu zato ba tsammani,abinda ya sanyata waiwayowa da sauri tana fadin "Hasbunallahu wani'imal wakil,waye haka?" Kanta tsaye ba tare da shakka ko tsoro ba ta ratso cikin falon tana kallon ruqayya. Kallo na tsantsar qiyayya da tsana muraran. A kaf fadin duniya batajin akwai wata halitta da zuciyarta ta tsana bayan ita. Idanunta ta kuma saukewa akan plates da cups din dake riqe a hannun ruqayya,wannan ya sake bata tabbacin eh lallai,bayan ya tsallake breakfast din data shirya masa a nan yazo yayi karin kumallo?. Ta hadiye wani abu me tauri da ya tsaye mata a wuya me mugun radadi,sannan ta watsawa ruqayya wani mummunan kallo. "Nice nan,zuwa nayi na gaya miki abinda kika kasa ganewa,tunda baki da tsoron Allahn da zai ganar dake hakan,inason ki sani ke din baki isa komai ba kamar yadda baki isa ki rabani da saleem ba,duk yadda kike ganin bokanki tsafinki da tsubbace tsubbancenki sunayin tasiri,wallahi baki isa ki raba alaqar da Allaj ya hada ba,kuma a juri zuwa rafi da tulu da diban ruwa,dole wataran zai fashe" tana kaiwa nan ta juya a zafafe tana jin inama zai yiwu ta rufe ruqayyan da mummunan dukan da zai sanya a rasa gane ainihin halitattarta. Duk kuwa da tayi imanin babu wani kyau dake rudar saleem tattare da ruqayyan,face zallar tsafi da tsubbace tsubbace,tunda dai indai ana batu na kyan fuska da hasken farar fata,ko kusa ko alama ruqayya bata isa ta matso koda gefanta ba,wannan abun shi yake sake bata tabbaci a ko yaushe iyawa da gogewa a bun malamai da 'yan bori suke sanyawa ruqayyan ke shan gabanta a zuciyar saleem,wanda dukkan me dogon nazari da tsinkaye koda ba'a gaya masa hakan ba shi da kansa zai fahimta. Kasa ce mata komai ruqayya tayi face binta da kallo data ci gaba da yi har ta bacewa ganinta. Taja numfashi sosai sannan kuma ta sauke tana rausayar da kai. Koda sau daya bata taba tsaiwa ta biyewa shirmen zainab ba,amma a yau abun yayi ta'azzarar da har ta samu qwarin gwiwar shigo mata sashe?. Karamin tsaki taja ganin qananun tunane tunanen matsalolin Zainab da basu taba qarewa cikin gidan ba suna neman bata mata lokaci,saita juya zuwa kitchen zuciyarta na sake fadada da tunani da mamakin halayen Zainab din. Me yasa har yanzu IDON ZUCIYARTA ya kasa budewa?,ta gaza fahimtar abinda ke gabanta a bayyane?. Da irin wadannan tunane tunanen ta kammala dauraye plates da cups din da wanke kowanne kwano da aka bata da abinci ya zame mata jiki a duk sanda aka gama cin abincin,ta goge ko ina da kitchen towel ta sakayo qofar. Tsaftataccen killataccen bedroom dinta ta buda ta shiga,ta kalli agogo,sai ta bude wardrobe dinta ta ciro mayafinta daya dace da da A shape din atamfar dake jikinta a dan gaggauce ganin lokaci ya fara ja,tanason taje ta dawo da wuri kafin yaran su dawo daga makaranta,don ta dade da yiwa kanta alwashin muddin ba wani babban uzuri ba ta daina barwa zainab su saboda wani dalili. Ta dakin yaran ta biya ta dauki baby fatima dake barci ta sakata a kafada sannan ta maida lallausan mini blanket din yariyar ya lullubeta ta fito. *FREE BOOK NE,KU SAKI JIKI KUSHA KARATU*😂😂🙌🏼🙌🏼🙌🏼 *_FOLLOW MY AREWABOOKS ACCOUNT_* *HUGUMA*👑 *_KURMAN BAƘI_* *H U G U M A* PAGE 02 Muhallin da ta tashi dazun a dakin shi ta koma ta zauna,har yanzu babu wani sassauci data samu ko qanqani,duk da cewa daga ruqayya har saleem ta barwa kowa a cikinsu saqo. Sam bata damu da tarin qazantar dake a sashen nata ba bare hankalinta ya dauku wajen ganin ta tsaftace shi,duk kuwa da cewa rana ta fara yi,kuma lokaci ne da ya kamata ace gurin ya kasance cikin kintsi da gyara. Ba abinda yafi damunta irin uban kudadenta data kashe,ta siya magunguna masu tarin yawa na mata,magungunan da aka bata tabbacin sunansu KAFI MALLAKA. Kuma muddin tayi amfani dasu ba saleem ba,duk wani wanda yake rayuwa da saleem ma zaya zama qarqashinta ikonta da zabinta ne. Sai gashi gaba daya daga kudin har maganin babu abinda ta amfana dashi,maganin da yake na kwana biyu ne,tayi asarar dare daya,saura dare daya ya rage mata,wanda bata da wani hope a kanshi,saboda bahaushe ma ya fadi juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta. Irin rabuwar da sukayi da saleem a yau bata tunanin zai nema wani abu daga wajenta a daren yau din,ita kuma batajin koda zatayi asarar kudin data zuba zata iya saukar da kanta ta nemeshi,muddin ba shine akayi katari ya saukar da kanshi ba. Koda bai bata haquri ba tana iya sallamawa,saboda kaf kudaden da ya basu ne saboda siyayyar sallah tasu data yara ta narka a ciki cike da yaqini da imanin zata maida mafiyinsu muddin tayi amfani da maganin. Kamar wadda aka tsunkula ta miqe da sauri,ta sanya hannu tana jawo locker din madubinta. Tarin ledoji ne da tarkacen da zakayi tsammanin qaramar bolar mahaukata ce dake cunkushe da karikice,wasu a leda,wasu a kwalaye,wasu a takarda,wasu ma saboda rashin gyara da kintsin gurin sun fashe sun barbade a cikin locker din. Da kallo tabi locker wani takaici yana sake ninkuwa a zuciyarta "Wai dame na gaza da har yau na kasa ture wannan baqar matar tasa?,dame ruqayya ta fini ne?" Ta tambayi kanta tana qarewa locker din kallo,tako ina bata wasa da gyaran HQ dinta,duk wami magani da zata gani ana tallatawa,ko taji labarin kyan ingancinsa da aikinsa a gurin qawaye saita tabbatar ta mallakeshi hankalinta yake kwanciya,amma har yanzu ta gaza samun nasarar da take hangowa kanta. Hannu ta saka ta dauko baqar ledar dake ajjiye daga gefe tana jan tsaki,kunceta tayi saman madubi,wasu qullukan garurruka ne da dunqulallun wasu abubuwa guda hudu. Daya brown daya baqi daya fari tas dayan kuma kore. Tsaki ta sake ja "Fiye da rabin ma da akace nayi inserting nasu ashe nayi,banajin wadan nan ragowar zasu samar min da abinda nakeso" ta qarashe maganar tana maida ledar ta qulle. Gwara ta samo wani abun da zai cikashe mata gibin da zata samu. Saman hautsinannen gadonta ta miqa hannunta,ta cusa shi qasan pillow dinta ta ciro wayarta. Kai tsaye data dinta ta kunna,sannan ta hau watsapp dinta. Tarin saqwanni ne suka shiga shigowa,duk da jiyan raba dare tayi tana chart kafin ta rufe tabi saleem din bedroom dinsa. Fitsarin da ya cika mata mara ya sanyata ajjiye wayar a gefan gadonta,sannan ta miqe da sauri ta tura qofar toilet dinta ta shige. Saman tiles din toilet din ta tsugunna ta kwata fitsarin. Sai ta dinga bin fitsarin da kallo saboda wasu launika da ya fito dasu da wani birtsi birtsi. Tsaki ta saki tana jin wani sabon bacin ran "Kalli yadda damshina da aikin maganin ke bi ta rariya a banza,haba,dole a yiwa saleem uzuri,akwai abinda ke shan kansa" ta fada a zuciyarta. Ko digewa fitsarin bata jirayi ya gama yi ta miqa hannu ta tari ruwan famfon dake kwarara ta yafawa wajen,ta sake miqa hannu ta tara ta yafawa gurin ba tare da ta sanya hannu ta wanke ba,ta miqe tana qoqarin maida pant dinta da uban danshin dake maqale a sumar dake mararta damqam,wadda a qalla kusan watanni biyu kenan cikin ta uku ba tare da ta samu aski ba. Sai a sannan ta lura da pant dinta da ya canza launi saboda kalolin magungunan matsi da taketa inserting tun yammacin jiya. Tsaki taja,ta fasa sakawa,sai ta zareshi ta jefa cikin bathtub dinta wanda ke dauke da kalolin pants da Braziers dinta da bata samu wankewa ba,ta tsartar da yawun bakinta dalilin rashin brush tana sakayo qofar toilet din cikin hanzari saboda kiran da taji ya shigo wayarta tana gudun kada ya tsinke bata daga ba. LIKITAR AURE sunan da ya fito kenan baro baro,wani mahaukacin tsaki da yafi dukka na baya ta saki "Ku******mar uba,aikin banza" ta fadi a fili takaicinta yana kasheta,sai tayi rejecting kiran ta shiga watsapp abinta. Shamsiyya ta fara lalubawa cikin jerin chats din dake dashboard dinta "Yauwa" ta fada da sauri tana gyara zamanta saman gadon ganin ta sameta a online cikin sa'a. Sallama ta danna mata,yana shiga yayi ticking blue "Ina kika shiga likita tana ta kiranki?" Saqon shamsiyya ya shigo. Ji zainab tayi ba zata iya jurewa typing ba,sai ta fara yi mata voice note "Yo me zanyi mata?,bayan asara tana dab da fadamin?,nayi amfani da komai da tace amma babu abinda ya faru tsakanina da saleem,hasalima tunda ya dawo daga kasuwa ya shiga dakinsa ya ajjiye jakarsa ya dawo parlor ya hau wasa da 'yan biyu,haka kawai naga kamar ya shigo ne da wani irin fushi,ana kiran sallahr magariba kuma tunda ya fita sallah bai dawo ba sai bayan isha'i,da na kawo abinci ma baici ba ya shige wanka abinsa,da ya fito kuma yace bayajin dadin jikinsa ne gaba daya,na juya yaqi cin komai,da na gaji nima sai na qyaleshi don ba wannan ne yafi damuna ba,kinsan wani rainin wayo?,na tafi naje na kwantar dasu hassana kafin na dawo sai zuwa nayi na tarar yayi bacci?,ya duqunqune a blanket,juyin duniya ya tashi ina da buqata wallahi ko juyowa baiyi ba". Zaman jiran shamsiyya ta gama ji ta bata amsa sai taga yayi mata tsaho,don haka ta fice daga inbox dinta ta fara duba charts. Saqon wani group dinsu da take masifar so mai suna MATAN NI'IMA shi yafi kowanne shigowa, group din yana matuqar sakata nishadi don tana qaruwa dashi sosai ta fannin magungunan mata,musamamman na turawa,wanda ita kanta ta sissiya wasu tayi amfani dasu,hakanan a boye ta siyawa saleem ta sassaka masa abun sha ba tare da ya sani ba. Tayi hakanne saboda sanin da tayi masa,baya qaunar ire iren wadan nan magungunan sam,duk abinda za'a ce masa magani ne na irin wannan fannin to baya ciki,ita kuma yadda matan keta comment a kansa ya sakata sha'awar gwada amfani dashi. Saqonnin ta fara bi a hankali,tun tana jin hirar na gundurarta kamar ta fice har ta soma daukan hankalinta _Maman mahbuba ya daren?,ya kikaji aikin maganin?_ _a fito mata a bamu feedback mana_ _hmmma ai abun ba'a magana,wadda bata gwada ba gaskiya an sha da ita_ Ire iren maganganun da suka sanyata zaquwa kenan,ta soma bin saqonnin da sauri sauri har ta gano bakin zaren hirar. Kai tsaye ta yiwa matar data fahimci a gurinta akaci kasuwar maganin magana ta private,sai taga ma jiranta ta karanta saqon bata lokaci ne,don haka ta sauka ta kirata direct call. Tana dagawa taji ta ambaci sunanta,abinda ya dad'ad'awa zainab rai. Wato tayi shaharar da sunanta ya tambara a group din kenan har ake iya kama sunanta kai tsaye?. Sama sama suka gaisa,zainab ta nema qari bayani akan magananin. Bayanin da matar tayi mata yasa taji ta gamsu d'ari bisa d'ari "Nawa ne kudinsa?,idan na turo kuma zan samu a yau?" "Eh akwai available,zaki samu,dubu ashirin da biyar,to amma tunda kece ansan saba da juna,ki tura ashirin,naki ne da na megidan duka zaku sha,na tabbatar saikin kawo wata ma". Nauyi taji kudin sunyi mata,saboda sosai tayi barnar kudin wajen likitar aure. Tun daga fallen zanin daurawa na magani data siya a wajenta da tarkacen kayan matsi a qalla ta barnatar da kusan dubu dari da talatin,abinda ya rage mata a hannun nata yanzun dubu ashirin ce,kuma zubin adashi takeso ta fara dashi,to amma hausawa sukace ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba,don haka tace "Ba damuwa zan baki address,a kawomin sai na bada cash" "Shikenan ba damuwa". Ranta fes taji kamar an sauke mata wani nauyi da yahau saman zuciyarta. Sai ta koma ma ta kwanta tana sake bin feedback na matan da sukayi amfani da maganin. Murmushi sosai ta dinga saki,tana jin cewa daren yau lallai zai zama na musamman,tana jin ma su hassana gurin ruqayya zata turasu,kuma ko taqi ko taso dole ta karbesu don ta samu ta sake sosai. Wannan kwanciyar ta kaita har azahar bata sani ba tana group din ana maida yadda akayi tana biye dasu,har ji tayi ya qagu maganin ya iso. Bata ankara ba sai kiran sallar azahar din taji ana qwalawa. Ta rafka salati tana miqewa hadi da bin dakin da kallo. Tun safe tana fama da qunci,ko brush batayi ba bare ta sakawa cikinta wani abu,bare kuma ayi batun gyara gidan da dakin saleem,ga yara suna kan hanya sun kusa tasowa a makaranta,bata dafa musu abincin da zasuci su wuce islamiyya ba. A gaggauce ta sauko ta fara da kwashe tarkace kayan dake warwatse a qasan bedroom din,tana yi tana qiyasta rashin mutuncin da zata tsiyaya a yau idan maganin ta ya iso. Bata jin zata dagawa ruqayya qafa ko diss,tabbas sai ta cusa mata kwatankwacin abinda take gani da ji a duk sanda take da saleem. Wani irin sabon riritawa kulawa tare da kuma tattali take gani a idanu da fuskarsa a duk sanda ya kwana sassan ruqayyan. Tayi imanin babu wani abu dake siyawa mace irin wannan soyayyar illa abu biyu. Kula da HQ da magungunan da zasu matseki gam ta yadda zai kiyayeki tare da dasawa zuciyarsa babu macen da zata kai darajarki ta wanann bangaren. Sai kuma hanya ta biyu da ba zata jurewa zirga zirgar wahalarta ba bayan ga wadda ta fita sauqi wato asiri. Imaninta yafi tafiya ga cewa asirinne,domin itadai bata taba ganun ruqayya ta siya wani abu waishi maganin mata ba,ko labari bata taba ji ba,to ta yaya macen dake zaune haka saket ba tare da kayan aiki ba zata samu irin wanann soyayya da kulawar indai ba ta hanyar tsubbu da asiri ba?. Ko kafin ta gama gyara dakin ta gaji tubus,ta watsar da tsintsiyar ta zauna gefan gadon tana jan wani tsakin wanda bata gajiya da yinsa. Ba abinda ta tsana a duniya irin aiki,a yadda ta hasaso rayuwar aurenta ta kuma tsarata shine taci ta kwanta kawai,komai saidai a miqo mata. Saidai ga tarin rashin sa'a sai gashi tayi katari da mutumin da sam sam bashi da ra'ayin aje me aiki cikin gidansa. "Duka duka ma me akayi?,yaran biyu rak?idan akwai buqatarta nan gaba sai a dauka din" wanann itace amsar da saleem ya bata lokacin da tazo masa da batun. Cikin tarin qailula,zallar son jiki da rashin son morawa kai komai sai gashi takai gefin la'asar bata gama komai ba. A dai dai lokacin driver ya dawo da yara daga makaranta,suka shigo fici fici dasu kamar kullum cikin nau'in jigatuwar da duk dalibi yake tsintsar kansa. *HUGUMA*👑 https://chat.whatsapp.com/HeRo2w8C8gdG0Et1lqafjk *_KURMAN BAƘI_* *H U G U M A* Page 03 Yara biyu ne a gaba suka fara shigowa,mace da namiji wanda dukkansu ba zasu wuce shekara goma da hudu ba. Macen itace babba sai namijin. Farare ne sosai kamar yadda yanayin fatar mahaifiyarsu zainab take. Daga bayansu sauran yaran maza biyu suka shigo. 'Yan biyu ne identical masu kama da juna sosai. Rirriqe labulen sukeyi suna shigowa a hankali da alama babu sakewa sam a tattare dasu. Tunda sukaga qofar maman nasu a kulle hankalinsu ya gaza kwanciya,duk da qarancin shekarunsu amma dai dai da rana daya basa qaunar su shigo gidan su samu mahaifiyarsu bata nan. Zainab daketa fadin tashin kintsa falon ta watsa musu harara "Shegu masu shegen baqin hali,duka duka shekarunsu basu wuce a qirga da yatsu ba amma sun iya nunqufurci da shegen gulma da sanabe irin na uwarsu" ta fadi idanunta a kansu kamar zasu fado,har yanzu tana jin dacin haifar yaran a dai dai lokacin da take ganin cewa itace da gida,a sanda dukka lissafinta ya gama bata ta gama mallakar saleem mahaifiyarsa da kuma danginsa,ta haifa masa abinda ya jima yana mararin samu wato 'YA'YA,sai gashi a dare daya ruqayyan ta gigitata da wata irin ba zata da bata shirya mata ba. "Don uwarku ku koma idan ba zaku shigo ba" ta fada cikin daka tsawa tana jan tsaki. Tsam al_hussain ya riqe hannun al_hassan yana mele baki alamun zagin data masa ya taba ransa. Yafi al_hassan zuciya sosai,sai kawai ya figi hannun dan uwansa suka fice zuwa babban parlor din da ya hade qofofin falukan da suka samarwa da kowaccensu sassanta. "Kinga shegen yaro?" Zainab ta fada cikin mamaki tana binsu da kallo. Tun yanzun yaran suke da wani irin hankali da saurin fahimtar abu,tana tunanin gaba zaiyi wuya basu zame mata tarnaqi ko alaqaqai ba. "Zakaci ubanka zanga ka dawominne" ta fada tana daga murya don ta tabbatar suna falon a zaune. "Mama yunwa nakeji fa gaskiya" babbar diyarta haneefa ta fada tana yamutsa fuska "Iyalan ci da baku da aiki sai cin abinci,yo nima banci ba tun safe,ki bude lunch box dinki ki cinye sauran abinda ke ciki kafin na gama kintsa gidan na dora" ta fada tana ci gaba da hidimar gabanta. Ita a yanzu ma bata abinci take ba,maganinta kawai take kasa kunne taji me delivery yace gashi ta afa ta tabbatar ya isa cikinta. Yunwa ba yau ta saba zama da ita ba. "Mama dumamen abincin jiya ne fa dama kika zuba mana,kuma wallahi tun kafin azahar shinkafar ta jiqe,sai abincinsu alhassan muka ci" "Kut" zainab din ta fadi tana dakatawa da abinda takeyi bayan ta waiwayo "Uban waye yace kuci musu abinci?,ban hanaku ba?" Ta fada cikin fushi tana kaiwa yarinyar mari. Tun ranar da yaran suka taba yabon girkin ruqayya a gabanta saleem ya tayasu taji ta tsani duk wani abinci da zai fito daga gurinta,duk kuwa da cewa girkin dare hadawa sukeyi,hasalima tare sukeci a babban falon gidan. Zagi ta shiga dura mata abinda ya sanya yarinyar sakin kuka ta miqe tana zubda jakar makarantar da flask din a wajen tayi dakinsu da gudu. Hakan bai hana Zainab ci gaba da masifa ba kamar zata ari baki,da da hali dukan tsiya zata yiwa haneefa din a yau,saidai ta tabbatar muddin ta taba lafiyarta kamar a kunnen mahaifinta,abinda kuma tasan bazai haifar mata da d'a me ido ba,tana son yau ta gyara wasanta ba zata bar wani abu na rashin jin dadi ya wargaza mata shirinta ba,dole yau tayi kaffa kaffa da komai. Dan qara speed na motar tayi hankalinta yana kan lokaci. Tasan tabbas zuwa yanzu yaran sun dawo,bataso hakan ba amma uzurin da ya riqeta dole ta gama kafin ta taho. Shigowar motar tata yaja hankalin yaran, suka watsar da abinda sukeyi suka rufo da gudu gurinta. Tana qoqarin bude murfin motar amma sun hanata saboda yadda sukayi tsaye a bakin qofar suna murnar ganinta. Murmushi ta saki tana dubansu zuciyarta na karyewa. 'yan awanni kadan tayi bata gidan,amma dukka hankalinsu ya tashi,ina ace yau mutuwa tayi ta barsu?. Cikin taqaitattun mintunan da ta qara bata nan yaran har sun fara fita a kamanninsu,sunyi wasa a farfajiyar gidan sun vodeyAllah,suit din uniform din tasu sun cikata da qasa da ruwa abinsu,kada ma kayan alhussain yaji labari. "Yanzu don Allah ba zakuji kunya ba ifti ta ganku a haka?,ummm?" Ta fadi tana dan duban yarinyar tata dake daure cikin wata jaka da aka maqale a seat din motar. Jikkunansu suka kalla kafin su qyalqyale da dariya. Alhassan yace "Momy ni jikina bai baci ba sosai,ni zan dauketa" "Allah momy na rigashi zuwa" alhussain ya fada yana qoqarin tureshi. "Duk ba wanda zan bawa 'yata,me yasa baku shiga gurin maman haneefa kun zauna ba?" Ruqayya tayi musu tambayar tana fidda jakarta tare da saka iftihal a kafadarta "Ba zaginmu tayi ba ta kuma yi mana tsawa" alhussain ya fada yana tura baki gaba. Waiwayawa tayi ta kalli yaron,har cikin ranta taji ba dadi,hakan yana nufin ko babu ranta ba zata iya riqe yaran ba kenan,ta kuma san irin salon zaginta,bata iya qanqanin zagi ba,fadan kullum sai sunyishi da saleem kenan,domin yace bazai lamunci zagin da take kuntumawa ba,ba zata lalata masa yara ba. "Aiki take kuka dameta,muje ciki ku cire uniform kuci abinci" sai ta saka yaran a gaba suka wuce cikin gidan tana biye dasu a baya da jakunkunansu. Bata samu nutsuwa ba sam sai da maganin ya iso,ta zauna ta farkeshi ta duba sannan tayi amfani dashi kamar yadda matar ta gaya mata. Sakin wani murmushi tayi tana saka dukkan lurarta ga jikinta,ta fara lissafe lissafen irin canje canjen da akace ta sanya ran zata ji "Hmmmm,yau da sabga,ruqayya yau zaki qunshi baqincikin da sai ya kusa ajalinki" ta fada a sarari tana dariya. Tabbas yau zata aiwatar da komai ne da gayya saboda ta qona ranta yadda ya kamata,ta fanshe tarin baqinciki da bacin ran da take qunsa mata kowacce safiya da irin baqin kinibibinta. Duk yadda taso taga ta kammala komai ko don ta faranta ran saleem din yadda yasan yafison yazo ya sameta amma ta kasa,jiki dukka da zuciyarta a haka suke,ta riga data saba,zallar son jiki kasala da rashin son yin aiki sun zame mata jiki,sai data bata lokacin da girkin ma bata dorashi ba sai la'asar liqis. Yadda ta kacame da aiki a kitchen din ya Sanya nylon din rigar baccin dake jikinta ta soma damunta,ga zafin kitchen din ga kuma rashin yin wanka. Gefe taja tana jan tsaki "Ni shi yasa duk ababen nan basu dameni ba,me za'a wani yi da rigar bacci" zareta tayi ta azata jikin qofar kitchen din,ta ja zanin jikinta tayi daurin qirji dashi taci gaba da juya miyarta wadda keta kamawa saboda yadda ta raba hankalinta gida biyu,rabi yana ga girkin rabi kuma yana ga wayarta da taketa bin charts na group dinsu dake sake qara mata qwarin gwiwa tare da samun tabbacin yau din daren zai kasance na musamman ne. A nutse ya isa da motarsa harabar da ya saba ajjiyeta,ya daidaita tsaiwarta sannan ya kashe motar yana furzar da iska daga bakinsa a mugun gajiye. Yau tunda ya fita bai zauna ba,ya gaji liqis yadda ya kamata,sunata zirga zirga tsakanin warehouse dinsu da shagunansa,ko abinci bai samu yaci ba,yunwa ce a kwance a cikinsa. Hannun rigarsa ya tattare yana duba lokaci,ana dab da kiran sallar magariba ne,duka duka bazai wuce mintuna goma sha biyar ba. Hannu ya sanya ya bude motar ya fito hannunsa dauke da ledoji,qarar rufe murfin motar yaja hankalin zainab dake kitchen,ta ajjiye ludayin miyarta da sassarfa ta fito daga kitchen din ta isa window din da yakw sadata da kowanne kallo da ya danganci harabar gidan. Kamar zuciyarta zata fado sanda yake nufar sashen ruqayya,abinda tafi tsana kenan a rayuwarta,duk kuwa da cewa ita dinma hakan yake musu,baya taba shallake sashenta idan ya shigo sai ya fara dubata sanann ya wuce wajen ruqayyan yadda al'adarsa take kenan duk sanda ya kasance kece da girki. A nutse ta sauke idanunta ga ledar hannunsa,tanaso tasan meye a ciki?,saidai duk iya qwaqwarta ta kasa tantancewa saboda ledar baqace me duhu babba da qarama. Sakin labulen tayi yana jan tsaki,ta waiwayo ga haneefa wadda suketa wasan guje guje,wasan guje gujen da ya qarasa hargitsa gyaran 'yar burum burum din da ta yiwa falon. Tsawa ta doka mata sannan ta narka mata ashar "Ga babanku can yayi sashensu alhassan,bishi ki ga me ya shigo da shi a baqar ledar hannunsa" yarinyar kamar ba zataje ba,sai kuma ta zumbura baki tayi gaba "Zakici ubanki da shegen rashin son aike" ta sake binta da zagin idanunta kamar zasu fado saboda harara,sai kuma taja qwafa ta wuce bandaki a gurguje tanason watsa ruwa kafin yakai ga shigowa. Wani sassanyan yanayi ne da parlor din wanda ko yaushe baya rabo da shi saboda tsaftar da ya kamashi. Komai na tsaftace ne akan tsari da sanin darajar muhalli. Sassauqar doguwar riga ce a jikinta ta wani yadi maras nauyi ruwan madara me haske sosai,kusan duk shigarta tana yinta ne bisa tsari da favourite colours na saleem din. Alhassan da alhussain na zaune daga qasan carfet saman qananun duddumansu,kowanne jallabiyya ne a jikinsa farare da qananun hulunan tashi ka fiya naci. Kyau yaran sukayi kuma duk wanda ya kallesu dole su bashi sha'awa. Sallamar uban ta sanyasu hankulansu yowa kansa,al_hussain shi ya fara yo gaba yana qoqarin karbar ledar hannunsa hadi da fadin "Abba sannu da zuwa" wadda suka furtata kusan lokaci daya da al_hussain dake daukema abban nasu pillow daga saman kujerar don ya samu wajen zama. A duk sanda ya sanya qafafunsa a sassanta yakan jishi tamkar cikin wani muhalli na daban yake ba'a cikin gidan ba. Sau tari yakan tambayi kansa da kansa "Me yasa ya qaro aure?" Wani lokaci zuciyarsa da kwanyarsa kanyi hadin gwiwar bashi amsar "Rabo". Kamar ko yaushe a yau ma amsar da ta bashi din kenan,wanda yayi dai dai da ajjiye kaskon turaren wutan dake hannunta,ta kuma sauko daga dining area din yana gyara zaman dankwalin kanta me sulbi tana fadin "Barka da warhaka" "Barka kadai" ya amsa mata yana bin su alhussain da kallo wadanda suka nade abun sallarsu suka wuce dakinsu. Hannun 3sitter din da yake kai zaune ta zauna itama,idonsa ya dawo dashi kanta lokacin da ta miqa hannu ta jawo gorar ruwa me matsakaicin sanyi ta zuba glass cup tana miqa masa. Sai da ya saki murmushi sannan ya miqa hannu ya karba,ya shanye tas sannan ya miqa mata cup din "Na rasa wacce irin baiwa ce dake da har kike gane yunwata da qishirwata ba tare da na furta ba" murmushin ta kuma sakar masa "Da kallo guda daya tak da zanwa idanunka na gama samun amsar komai" kai ya gyada cikin gamsuwa tare da jin matsayinta yana sake zarcewa wani madaukakin muhalli a zuciyarsa. Kullum wayewar gari sai ya godewa Allah da bai bawa shaidan galaba a kansa a shekarun baya ya ingizashin da zai zama sanadiyyar rasa ruqayya ba,inda hakan ta faru?,yanzu da a wanne gurbi yake a rayuwa?. "Amma,me yasa ba kowacce mace ke da wannan baiwar ba?" Idanunta ta dan janye daga kansa,jikinta ya bata inda maganarsa keson dosa,don haka tadan juya ido kadan "Ya danganta da yadd kika zabi ki fuskanci mijinki ko ki mu'amalanceshi,hakanan ya danganta da iya adadin lokacinki da kuma kulawar da kika bashi". "Sai yaushe zainab zata dinga fahimtar irin wadan nan abubuwan tayi koyi dake ta kuma canza?" Dauke kanta ta sakeyi a karo na biyu. Duk girman matsin da zaya shiga muddin akan zainab ne bata da sha'awar ta shiga lamarinsu,lamarin miji da mata sai Allah,duk yadda take gani a yanzun a wata ranar tana iya ganin sauyin hakan a tattare dashi,duk da cewa zuwa yanzu ta jima da mance wannan lamarin "Ba'a sassa na kake ba,kada maman haneefa taga ka jima da yawa" ta fada tana miqewa, miqewar da taja hankalinsa har ya gaza dauke dubansa daga kanta "Au korata ma kikeyi?" Ya jefa mata tambayar da kafin ta bashi amsa turo qofa da shigowar haneefa taja hankalinsu. Rarraba ido ta fara yi tsakanin fuskar abban nasu da ruqayyan. Har cikin ranta ruqayyan tana jin babu dadi. Yadda yanayin tarbiyya haneefa take a gidan,akwai sakaci na bala'i daga wajen mahaifiyar da bata cancanci zama uwa ba. Duk da haneefa ta girmewa su alhussain nesa ba kusa ba,amma akwai nisan tazara me yawa a tsakaninsu,tun daga hankalinta zuwa nutsuwarta. Tsuke fuska saleem yayi ransa na baci,a tsawace yayi mata magana *HUGUMA*👑 https://chat.whatsapp.com/HeRo2w8C8gdG0Et1lqafjk *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 04 "Halan baki iya sallama ba bare gaisuwa haneefa?" Ta tsorata ainun,don duk yadda yake sakewa da iyalansa amma sun sani,muddin ya dauki zafi da kai ko fushi to zakaji babu dadi "Sannu da zuwa abba,ina wuni?" Ta fada tana hade maganganun duka guri daya "Koma kiyi sallama" ruqayya ta fada a sanyaye. Sakin labulen yarinyar tayi ta juya zuwa waje,haushin tsawar da akayi mata tana cikata,tana ji a ranta maamantata ce ta jawo mata. Irin yadda taga su alhussain din sukayi haka tayi,ya amsa yana dauke kai,saidai cikin ransa yaci alwashi bazai dauki wannan sakarce sakarcen da yayi imanin laifin na Zainab ne,dole ya zauna da ita ya kafa mata sharudda da qa'idojin da zata yawaita tunawa kanta bazai dauki irin wanann ba. Ledar hannunsa ya miqawa ruqayya babbar "Ga mutanen naki" murmushi ta saki cikin jin dadi,kamar yasan a daren tana da buqatarsu,duk da al'adarsa ce tunda kayan suka zama abebadan shanta "Na Gode qwarai qwarai,kaima Allah ya faranta maka ya qara budi da wadata" "Ameen ya hayyu ya qayyumu, your prayers are my strength" ya fada yana dan lumshe ido. Idanunta ta kada masa tana murmushi,ya zare nasa idon da sauri yana yin gaba "Inda zan zauna n qara awa daya tak zaki cikamin kunne da magiyar na tashi na tafi yanzun kuma kina yin abubuwan da sun saba doka da qa'ida irin ta yau" dariya ya bata sosai,sai ta rungume ledar ta juya zuwa cikin kitchen don ta wanke kayan ta kuma adanasu cikin fridge. Shigowar haneefa ya sanyata dungure man data dauko zata shafa ta waiwayo tana bada hankalinta ga yarinyar. Tun kafin ya gama shigowa ta kasa jumurin jira "Me ya shigar musu dashi?,ina ledar?" Baki haneefa din ta tura alamun dake nuna tsiwa ta zauna mata sosai a jikinta "Ina zamana kin saka anyimin fada harda tsawa" "Ba wannan na tambayeki ba leda nake tambaya" ta fadi tana zaro idanu cikin takaicinta tana duban haneefar "Ya bata" ta amsa mata a a taqaice "Ya bawa wa?" Zainab ta fada tana zaro idanu cikin jin bala'i da tashin hankali "Mommyn alhassan" "Lallai yau an taro fitina a gidan nan,wallahi bazan dauki irin wannan abun ba" ta fada tana jin kamar zata dora hannu a kai ta rusa kuka. Tako ina saleem cikin jawo abubuwan da zasu kawo rudani a zamansu yakeyi,rashin adalci tako ina yake gwadawa rayuwarta,duk qoqarin da ita din keyi na ganin sun zauna lafiya ita kuma ta faranta masa. Tana tsayen da daurin qirjinta hannunta riqe a qugu ya tura qofar dakin hadi da sallama ya shigo. Kamar me ciwon wuya haka ta waiwayo da qyar tana amsa sallamar,bakinta zaka dauka ya cusa lomar biredi ne data hanata yin magana da kyau. Tuna fadan da ya gama yi mata yanzu yanzu ya sanya haneefa juyawa ta fice a dakin. A nutse ya qara takowa ciki yana karantar yanayin dakin. Mutum ne shi me wani irin qaqqarfar halittar jiyo qamshi ko warin abu,don haka a yanzun ma kusan abinda hancinsa ke jiyo masa sam baiyi daidai da abinda zuciyarsa keso da muradi ji cikin gidan sa ba. Mayar da dubansa yayi gareta,tana tsaye qerere tana binsa da kallon da baisan daga ina ta samoshi ba. Cikin daurin qirji,gashin kanta me tsaho da laushi ya samu guri ya cure abinsa saman kanta,wanda hakan ke nufin akwai dauda da rashin tajewa da ya zama silar wanzuwarsa a haka. Kauda idanunsa yayi,don idan da sabo za'a iya cewa ya riga ya saba. Cikin ranakun mako guda bakwai zaiyi wahala zainab din ta tsallake kwana biyu ba tare da ya ganta da daurin qirjin ba,walau da safe ko da dare kamar haka,ko yanzunma yasan qilan dashi ta wuni,bayan tasan babu abinda yafi tsana irinsa _Note:Da yawan maza sun tsani wannan al'adar,domin bata da wani alfanu sai canzawa mace yanayi,musamman idan ta hadu da nau'i na qazanta irin ta zainab,akwai wasu lokuta da mace kanyi daurin qirjin don jan hankalin miji,in a stylish way,ta yadda zaki daure bakin zanin a tsakiyar qirjinki kamar kin qulle abu,ki koma sassauto da zanin zuwa rabin qirjinki wanda hakan zai bashi damar gano pant da wasu sashe na breast dinki,bawai daurin qirji irin wannan na gargajiya mara ma'ana ba da fallen zani me dauda_ "Sannu da zuwa" ta fada da qyar a hakanma tana tausar zuciyarta ne gudun kada daren yau din ta sake tafka asara kamar yadda tayi a jiya "Yauwa,ya gidan ya yaran" "Lafiya lau.....mu ina tamu ledar?" Ta tambayeshi kai tsaye tamkar ita ta aikeshi. Daga kai yayi ya dubeta yana maimaita tambayar da tayi masan,qasan ransa mamaki yana cin ran nasa. Ya akayi tasan ya shigo da leda?,har yanzu bata daina wannan dabi'ar tata ba kenan ta shegen sanya idanu a shige da ficen kowa na gidan?. "Oh wadda kika aikeni da ita?" Dan sararawa tayi kadan,saboda amsarsa ta bata hasken inda ya dosa "A'ah,ni ban aikeka ba,wai saboda naga yara sun ganka da leda ya kamata suma ace an basu ko tunda suma 'ya'ya ne kamar kowa" ta fada tana murmushin yaqe. Takaici ya qumeshi sosai,wai ita a hakan fa ta qure dukkan iyawarta ta gaya masa magana me dadi kenan. Miqewa yayi daga dosana zaman da yayi saman stool dinta "Abinda yake ciki ba cimarki bane,fruits ne,ke kuma nasan babu daya a ciki da kike ci,itace me ta'ammali dasu kullum shi yasa nakai mata na dibarwa su haneefa,duk da su dinma sun koya ba lallai su iya shanyewa" ya bata amsar yana nufar qofa. Kallo ta bishi dashi tana tabe baki,a ranta tana jin kawai zallar mugunta ta sanya ruqayya ta sakashi siyo fruit din. Wannan shan fruit da cin ganyayyakin nata yana masifar qona mata rai,aikinta kenan kullum kamar wata raquma "Ni bazan zauna ina fama da 'ya'yan itace ba,nafi qarfin gaban nan,mu saidai mu rungumi qwaryar qwayoyi musha muyi tatil mu gigita mutum" ta fada qasa qasa tana shafe fuskarta da mai,koda ta gama kuma bata nemi powder ba bare turare ta fara laluben kayan da zata saka. A gajiye ya tura qofar dakin nasa da shirin fidda kayan jikinsa ya watsa ruwa ya wuce masallaci yayi aallar magariba. Cikin qasa sa second biyar dukkan wannan karsashin nasa da dokin ya fita a kansa gaba daya. Yadda ya fita yabar dakin da safe haka ya sameshi,babu wani abu da ya sauya. Hatta da comb da ya taje kansa kafin ya fita yana zaune abinsa dungurgur saman madubin. Numfashi ya zuqa ya kuma fesar zuciyarsa na wani irin tafasa. Ya sha gaya mata,a duk sanda qazantarta ta motsa taje ta qarata,tunda yayi iya yinsa,to amma ta tabbatar qazantar bata shafi komai nasa ba. Murfin qofar ya saki bayan ya jingine briefcase dinsa jikin bango ya koma da baya falo inda yabar yaran. Duban ledar da ya ajjiye musu yayi,sun gutsutstsura fruit din kawai sun barshi sai ma bata gurin da suka sakeyi. Daga khalil dake da shekara shida har haneefa din dake da shekara goma cikin ta sha daya rasa me hankali yayi a cikinsu. Alhassan da alhussain dake da shekaru takwas cikin ta tara ya tuna,a wadan nan shekarun nasu sun iya share guri suyi mopping fes,sun iya wanke wanke da wanke qananun undies dinsu na mamansu dana qanwarsu,a yawancin lokuta har fada yakan yiwa ruqayya,saidai ta langabar da kanta "Ka bari sunyi mana daddynsu,idan basuyimin ba wa nake da da zaiyimin,sannan wataranma fa suma mazan auren wasu ne,idan suka iya ai kaga har matan da zasu aura sun huta suma,wataran sayi karba a aikin gidan,ko kuma wata lalurar idan ta samu matayen ko?" Hanci ya lakace mata "A fakaice dai ni kike zagewa fa rukky" dariya ta saki tana riqe yatsunsa "A'ah wallahi daddy,rainon inna ne fa kai?,kaima ai koda bata koya maka aikin gida ba aita koya maka abinda yafi wannan muhimmanci,iya kula da iyali,zuciyar soyayya da tausasawa da kuma kyautatawa" yadda kalaman suka fita a bakinta sun sake ninka kimarta a zuciyarsa,sun kuma sanyashi yana sake jin nauyinta da kuma rashin son tuna wasu abubuwa da suka wuce a baya. "Kiramin mamarku" yace da khalil,bayan ya wuce ya kalli haneefa "Haneefa" "Daddy" ta amsa "Ki tattare wannan abinda kukaci din ki sakasu a fridge,sauran ki saka a shara,duk abinda bakuci idan na kawo ku daina lalatashi irin haka,saboda qannenki zasu gani su koya ne" "Tom" kawai tace tana miqewa cikin sakalci ta soma gyaran wajen,wanda kana gani kasan bata saba ba kwata kwata. Kanshi ya girgiza kawai ya koma bedroom din nasa. Tsaho wasu mintuna bata iso ba,har ransa yaso ya soma baci,sai kawai ya miqe ya soma rage kayan jikinsa yana dorasu saman wadanda ya ciresu da safe. Sai da ya kammala sannan yaji ta turo qofar,still da uban daurin qirjinta na dazu,ya rasa me takeyi tun shigarsa dakin da fitowarsa kawo yanzu da bata nema wani abun ta saka ba ta raba kanta da daurin qirjin nan "Gani" ta fada tanason nemo dakiya a ranta,saboda tun shigowarta ta gama gano abinda ya farun. Shaf ta manta da wani batun gyaran dakinsa gaba daya,tunda ta zauna yau qoqarin neman maganin da zaiyi mata aiki sharp sharp shi da ita takeyi,kuma ko yanzun alhamdulillah ta fara jin alamun hakan cikin jikinta,saura shi. Waiwayo yayi yana qoqarin hadiye bacin ransa ya dubeta,sai ya hangi khalil kusa da ita "Wuce falo wajen haneefa" yace da yaron,bacin ransa yana sake tasiri. Kwata kwata basu da tsarin shiga guri daga shi har 'yar uwarsa,ko ina ma suna iya bin iyayen ko su shiga ba tare da rarrabe dacewa ko rashin dacewar hakan ba,yau ya kawo qarshe kuma dole ya sanyata ta gyara ginin data bata,bazai bari suci gaba da girma akan haka ba. "Haka ya kamata dakina ya zama?" Ya fada yana tsareta da kallon tuhuma bayan ficewar khalil din. Hannu ta saka ta sosa kanta "Wallahi na sha'afa ne inata aiki tun safe" "Eh naga alama a gidan ai" ya amsa yana juyawa abinda ya shige bandakin. Bai iya wanka a ciki ba saboda Allah ya zuba masa tsantsami,sai daya zazzaga garin klien hypo da ruwan izal ya wanke toilet din fes da kansa sannan ya hada ruwan wanka. A gurguje yayi wankan saboda gudun qwacewar lokaci,saidai duk yadda yaso ya fita akan karin sai da lokacin ya kusa qwace masa,abu na biyu daya tsana ya rasa jam'i,yana fitowa ya zura jallabiyya kawai a gaggauce ya fice. Bazai iya tuna randa yayi missing sallahr magariba ba duk sanda yake sashen ruqayya,saboda komai da tasan yanaso tana tanadar masa kafin yazo ga buqatarsa. Akwai banbancin da tazara me dinmbin yawa tsakaninta da ita,yana dukka iyakar qoqarinsa ne kawai wajen kamanta adalci da boye hakan a mu'amalarsa da su gwargwadon iyawarsa,amma ko sau daya zainab din idanunta basa gani. A kullum zancanta daya ne zuwa biyu,ruqayya ta mallakeshi shi yasa sai abinda takeso ake gani,baya kamanta adalci a tsakaninsu duk da qoqarin kyautata masa da takeyi. Ya rasa wanne adalci take bida bayan wannan?,me takeso yayi mata?,da wannan tunanin ya isa masallacin ya zare takalmin qafarsa ya shiga. Bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i,don gaba daya bashi da wani karsashi da dokin zama a gidan gaba daya. Kallon takaici kawai yabi dakin dashi,ya kada kai yana wucewa ciki ya ajjiye abun sallarsa. Sanda ya dawo falon da niyyar zama ba komai dake kai kawo sai qaurin abinci,ya kalli kitchen din kaman zaiyi magana sai kuma ya sake dauke idonsa. Wannan na daya daga cikin dalilan da ya sanya kullum ta Allah muddin zai zagaya backyard na kitchen dinta sai ya taras da uban lalataccen qanzo,qudaje da sauran qananun qwari suna parade akai iya son ransu. Duk yadda zaiyi wajen kwatanta mata ta daina amma hakan ya gagara,a taqaice ma abicin store dinta shine yake fara qarewa cikin gidan. Bama abincin ba,zai iya cewa kusan komai ma. Kamar ko yaushe a nutse ta shirya cikin wani sassauqan riga da wando na pakistan masi taushi da hasken launi,dan qaramin mayafin da kayan yazo dashi mai qarancin kaurin da kana iya hangen gashinta dake gyare a matse cikin band ta lullubawa kanta,ta lakaci oil perfume dinta ta shafe jikinta da shi sannan ta soma nufar qofar dakin. Tuntuni saleem ya sanya haneefa ta kirayi yaran,har fateema iftee ta bisu. Su da yake yara ne ba kasafai suke damuwa da yanayin dandanon abinci ba,koda sun gane dinma ba wanda ke mata maganar don bata basu fuskar dauko zance su gaya mata ba. Cikin rawar kai da karsashi taketa kai kawon jera abincin saman table mat din da suke shimfidawa a qasa suci abinci. Yau din tana da hope tana kuma da mafi rinjayen yaqinin zata shayar da saleem din abinda baya taba samu daga gurin ruqayya. Hankalinsa na kan waya yana amsa kiran sanda take zirganiyarta. Maimakon qamshi ya zamana abokin rakiyarta a duk lokacin da zata gifta din saidai akasin hakan ya biyo baya. Duk da tayi wanka saidai za'a iya kiran wankan da jiqa jiqa kai tsaye,uwa uba ta hada gumi wajen kammala girkin waje daya,bata saka koda alum ba bare turare,sai rigar data cire jiya ta maida jikinta,a cewarta tunda dare ne kuma kwanciya zasuyi,ba sai tayi asarar ware wankakkun kayanta ba. Gumin ya cakude da tsumammiyar rigar wanann yasa wani abu me kama da qari qari ke tashi kadan kadan. Dai dai sanda ya gama wayar ruqayyan tayi sallama a tausashe. Ya kashe wayar ya ajjiye ta a gefe yana dan murmushi. Itama fuskarta a sake ta qaraso "Sannu da gida maman haneefa" ta fadi da zuciya daya "Yauwa" ta amsa mata saboda darajar idanun saleem din,sai dai a gajarce murya can qasa, zuciyarta na quntata da ganinta a gurin. A son ranta taso ya qyaleta ko da iya yau kadai ne suci abincinsu su biyu. Daga gefe ta zauna,sannan tayi masa barka da warhaka a tausashe. Idanunsa yadan lumshe yana amsa mata cikin kulawa,abinda ya motsa zuciyar zainab,sai ta dire masa plate din abincin tana guna guni qasa qasa. Tayi bala'in tsanar dressing din ruqayya,takanji inama tana da dama da kuma iko,da tabbas zata cinnawa sutturunta wuta ne su kama su qone qurmus. Tanaso tayi bore akan hakan,amma tasan koda tayi aikin banza ne wai harara a duhu,ranar data fara magantuwa akan hakan tayi qara wajen saleem amsarsa batayi mata da kyau ba "Nifa ban fahimci kwalliyar da maman alhassan ke shigowa da ita ba,bayan cin abinci akwai akace tazo tayi ba nuna ado ba" ta fada fuskarta babu digon walwala a kai,don ba abinda ke mata yawo a lokacin sai kallon da saleem yabi ruqayya dashi. Tasha jin ana cewa baqaqen kaya basa yiwa baqi kyau,amma yau ita da kanta ta qaryata hakan saboda yadda baqar atamfar tayi mata wani irin mahaukacin kyau "Kaman yaya?,dama ita tsafta tana da ranakun yinta ne a taki fahimtar?" Sarai ta fahimci kamar magana yakeson gasa mata,saita waiwayo itama tana dubansa tare da sake tsuke fuska "Idan taso ta zama agwagwa ma sarkin wanka,amma ta tsaya iya ranakun girkinta,ban shiga hurumin kowa ba,nima ba za'a shiga nawa ba" "Bazan taba ce mata ta daina kwalliya ba idan ma wannan shine burinki,kema idan zakiyi babu wanda zai hanaki,hasalima ina maraba da hakan kuma sai nafi kowa farinciki,haka siddan kinason zama qadangaren bakin tulu "sai ya wuce toilet ya barta kawai. "Kadangaren bakin tulu" tayita maimaita kalma,kasancewarta macace me bala'in tsarguwa da sawa rai abu. Wayarta ta dauko saboda ta kasa nutsuwa da abinda yace. Ta bude data ta shiga group dinsu ta kuma antaya tambayar bayan taqaitaccen bayanin abinda ya farun. Cikin qasa da minti biyar kalolin amsoshi suka dinga fitowa,kasancewar group din group ne da baya rabo da jama'a,amsoshin da kai tsaye suka fito mata da ma'anar abinda saleem din ke nufi. Wayar ta ajiye ta koma gaban madubi ta zauna tana duban kanta. Har rana wayau ta kasa gane me tayi wai da ya saka mata da tsanani yake mata kallon qazama,dame ruqayyan ta fita banda baqar fata?. *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 05 Ci gaba tayi da gunaguni,Kusan wannan dabi'arta ce,ta qware wajen mita da gunagunin mai da magana a ciki. Nata ta zuba daban,sai ruqayya ta saka hannu tayi bismillah ta dauki plate din ta soma zubawa tana fatar ta iya kai abincin cikin cikinta. Allah ya sani har cikin zuciyarta tana jin qyamar Zainab,saboda ita din macace da qazantarta bata boyuwa ko kadan. Mafi yawa duk farar mace qazantarta tafi saurin bayyana saboda hasken guraben boye datti da take dashi. Misali yatsu da faratanta zuwa duga dugi,zaka samesu a dafe ne ko yaushe,saboda bata damu data sanyawa qafarta lalle ba koda qanqani,hasalima duk sanda me lallen ruqayya tazo yi musu kallon sakarkaru takeyi su dukka,takan tabe baki tana juya kai da kafada,har cikin zuciyarta tana jin cewa ita dince mace cikakkiya. Kamar wata rana da tayi subutar baki bayan saleem ya gaza daure kyan lallen cikin dogayen yatsun ruqayya masu tsaho duk kuwa da cewa fatarta me dan duhu ce,amma sunyi ma yatsun nata kyau sosai,ya yaba irin yabawar da har zuciyarta taji dadin hakan,sai taji ko nawa ta kashe wajen yin lallen bata fadi ba "Uhmmm,bonono,ana gyaran badini malam wa yake ta zahiri?,an bar qofar gari babu tsaro amma an tafi ana gyaran cikin birni" a nutse ta daga kai ta kalli Zainab. Sau tari tana yawan sake mata magana,saidai ita har zuciyarta tana jin cewa bata da lokacinta,muddin ta biye mata kenan hakan yana nufin ita da ita basu da banbanci kenan. Ba kasafai ta fiya sakin jiki ko hira da saleem ba duk ranar girkin Zainab din. Don a gurin Zainab hakan ma duka laifi ne. Banda tsaiwar ruqayya da baiwa banza ajiyar zainab din,hatta da kwalliyarta bataso saleem ya gani,bayan ita din koda kwalli da zai nuna anihin zatin kyan mace bai dameta ba. Wani irin zaman cin abinci suke mara armashi duk randa ya zamana ita ke da girki,ruqayya na tafiya bisa tsarin hakanne bawai don tana tsoron zainab ba,a'ah......tun asali ita din macace marason hayaniya da kuma tashin hankali,tana da wata irin nutsuwa da hankali wanda ke sake fusgar saleem a tare da ita. Hatta da shi din da ya zama miji a gareta shekaru kusan shida kenan,kusan komai nata da wani irin aji takeyinsa da zai nuna maka meye ainihin ma'anar sanin ciwon kai. K'ididdigaggun lomomi yayi yaji abincin yakai masa ko ina. Yasan dama za'a rina,a lokuttan irin wannan yafi ta'ammali da fruit masu yawa da kuma damammiyar fura. Ko a yanzun ma aje cokalin yayi "Ina nonon da na aiko isma'il ya kawo?" ya fada yana zuba ruwa a cup "Ba'a dama ba" bai damu ba don ya saba da hakan "Dauko ki damamin inaso nasha" sai data cika bakinta da lomar abincin,kamar batasan meye dandanon dadi bisa harshenta ba sannan tace "Kamar fa yara sun shanyeta dazun,sun iso daga makaranta suna jin yunwa aiki yasha kaina,ban ankara ba" ruwan ya dakata da sha yana dubanta. Ba sau daya ba sau biyu ba yasha yaja mata kunne kan irin wannan dabi'ar tata "Sau nawa zan gaya miki ne zainab?,duk sanda yara sukayi amfani da abinda bace a ajjiyemin ki dinga daukan waya kina gayamin kafin na dawo gida na buqaci amfani dashi don na taho da wani?" Kai ta langabe tanason gwada kissar da taga sauran mata nayi,duk da can qasan zuciyarta fal take da haushi,komai fa ruqayya tana gani,kuma uwa uba a yadda take mace me jajircewa da gyaran kanta dukkan ire iren wadannan tirjiyar bai kamata ta dinga fuskantarsu daga saleem din ba "To gashi na musanya maka da zobo ko?,kayi haquri ka sha" ta fada tana miqa masa bayan ta zuba. Duk da ransa ya riga ya baci,amma ya sani abune mai bata rai qwarai mace tayi abu don saboda kai ka wofantar kaqi amfani da shi,don haka ya danne zuciyarsa ya amsa din. Sanda ya fara shi ji tayi kaman anyi mata bushara da aljanna,farincikinta ya gaza boyuwa har saman fuskarta "Lallai da alama yau bazanyi asarar kudina ba" ta fada cikin zuciyarta tana jin wani dadi yana ratsata. Duk yadda tazo taci abicin ya gaza wuce mata saboda zallar rashin ma'anarsa,dole ta ajjiye ta dauki wayarta dake ajjiye gefe tana fadin "Nidai zan wuce,sai da safenku" cup din ya dire ya miqe kaman yadda ya saba "Muje na taka muku" maganar ta fusgi zainab, fargabar kada yaje ya jima wani abu ya faru ya sanyata miqewa "Nikam dama kin tafi dasu haneefa wallahi" tayi maganar cikin son cusa wasi wasi a zuciyar ruqayyan "Ba school ne gobe?,nakega bacci ya kamata su kwanta ko?" Saleem din ya fada yana duba agogon wayarsa. Ido ta kanne masa guda daya,ta matsa dab dashi sosai suna gogar juna "Na maka tanadi ne dear,inason space" dan dauke kansa yayi gefe kadan ya kuma yi taku biyu baya kadan ya rabeta yana yin gaba idanunsa akan ruqayya wadda har tayi gaba abinta. Yana mamakin yadda gaba daya baki da jikinta baya cikin damuwar da zata zanya damuwarta a kanta,baisan dsga safe har zuwa dare me takeyi da zata gagara tsaiwa gyara jiki da bakinta ba "Suyi kwanansu a nan din" ya gadi yana qarasa ficewa. Qwafa taja tana dauke kanta daga bakin qofar,bata karanci komai a fuskar ruqayya ba dangane da maganar ds tayi,taso qwarai taga adadin tasirin da maganar tayi mata,taso ta kwana da abun ya hanata bacci, gobe da safe kuma taga sauyin da zai qarasa gigitata. Zaune yake daga gefan gadonsa,calculator da wasu qananun takardu ne a hannunsa yana lissafin kasuwa. Sallama zainab tayi cikin doki tana shigowa dakin bayan ta kora su haneefa dakinsu. Kai ya daga ya kalleta yana amsa sallamar,bai qara koda second biyu ba ya ajjiye kan nashi yaci gaba da aikinsa. Gaba gadi taci gaba da takowa cikin dakin da daurin qirjin da ta sakeyi bayan ta cire rigar data maqala a dazun. Har ta gama abinda zatayi ta wuce gadon ta sheme bai motsa ba yana qarasa lissafinsa. "Daddyn haneefa.....kai nake jira fa,ka ajjiye aikin ka tashi ka cire kayanka mu kwanta" ta fada tana daga kwancen. Kansa ya daga haushi da takaici yana taso masa,kamar wanda zasuyi aikin gini ko na kauda itace,tana magana gatsau ba wani salo me jan hankalin miji a ciki?. Idanunsa yakai kan qafafunta dake saman cotton bedsheet din nasa,wanda asali ruqayya ce ta siyesu har guda shida tace ga guda daya kyauta ta bashi,saidai kuma a duk sanda yake kwananta ne ire irensu take canza masa a bedroom dinsa dake sashenta. Ba komai a qafartata face baqi da datti kwance qasan tafin qafartata,ga kaushi da qananun faso da suka tsatsagata suka bawa datti muhallin zama me kyau. Daga saman singalalin qafarta kuwa shima kaushinne da fata kanyi sanadin busawar sanyi sanyi da kuma rashin bata muhimmanci wajen shafa mata mai akai akai. Da ya maida dubansa ga zanin jikinta kuwa,farin siririn layin dake qasan bakin kowacce atamfa dake dauke da sunan atamfar ya sirka laifinsa. Alamu dake nuna dattin atamfa da kuma neman agajin wanki da takeyi. Hannunta na ajjiye daga qugunta,fararen faratanta da babu digon Jan lalle ko baqi ko misqala zarratin na shimfide a jikinta. Sake gyara kwanciyarta tayi tana jin farinciki cikin ranta,kallon da yake mata sai zuciyarta ta fara qissimamata lallai maganin ke aiki a jikinsa. Eh zai iya cewa tunda ya zauna a gurin yakejin sauyin a jikinsa,saidai kuma a yanzun da yake kallonta ya rasa wani abu guda da zaiyi masa tasirin da zai shauqantu zuwa gareta. Tana murmushin haqoranta da suka komawa ruwan madara qarfi fa yaji suka bayyana,ta miqa hannunta tana sosai gashinta dake a cunkushe wanda yaci arziqi saboda zuwanta ta shafeshi da man gelo fes,abinda yasa yake fesar da wani qamshi mara dadi kenan "Yanzu kin gama shirin bacci kenan?" Idanunta ta fiddo waje "Eh mana,kai nake jira" ta fada tana murmushi dadi yana ratsata. Kansa ya mayar ga aikinsa yana jin buqata tana tasiri a jikinsa "Ki shiga toilet dina kiyi wanka ki fidda zanin nan,ki bude wardrobe dina akwai wata rigar bacci black and white,ki dauki black din. "Wanka kuma yanzu?,bayan tuni nayi wanka na?, gaskiya dare yayi" ta fada tana jin wata muguwar ganda da qyuya tana ratsata. Ita batasan me yake damun saleem ba,ya fiya zafafawa da yawa,shegen sanabe da tsafta kamar d'an kwad'i "Umarni nake baki" ya fadi bayan ya dago idonsa ya zube a kanta. Batason tayi asarar kudinta shine babban dalilin da ya sanyata ta jawo jikinta ta sauko ba don taso ba. Ya bita da kallo yana girgiza kai. Wanka ma na shiga dakin miji sai ance da mace tayi,wacce irin rayuwa ce a wannan. A sassan ruqayya shi ake sanyawa yayi wankana,amma a nan sashen abun yasha banban. Ko minti hudu batayi ba sai gata ta fito daure da maqalallen zanin da ya rasa na meye,ta qarasa wardrobe din ta ciro rigunan kamar yadda yace,ta farke baqar tana dagata sannan ta dubeshi "Daddyn haneefa,rigace wannan ko matacin koko?" "Shafa kiji" kawai yace mata saboda takaici,abinda yakeji cikin jikinsa zuwa yanzu ya fara haukata,sai ya fara tattare kayan aikin nasa yana zubawa a bedside drawer dinsa. "Nifa wadan nan rigunan banga wani amfaninsu ba,banda asarar kudi,abu kamar sange(ragar net),da kudin aka baka ka qaro maganin harka da baifi ba wannan me zata tsinana maka,bakaci a bakinka ba ba baka matsa a qasanka ba sai kuma ace tana da amfani" ta fada cikin qunaquni. Qunaqunin da tsaf ya jita amma yayi banza da ita. Sai data gama qananun mitocinta sannan ta saka rigar. Rigar tayi sama abinta,saboda bata bada hankalinta wajen daidaitata a jikinta ba,gurin breast curves din yayi sama breast din kuma yana a qasanshi. Gwanace gurin shan magungunan mata,amma sai bata taba lura da cewa breast na daya daga cikin abinda ke tafiya da hankalin saleem din ba,itadai can qasan shine muhallin harinta ko da yaushe. Duk wani lungu da saqo dake isar da saqo a jikin mace yayi qoqarin ya aika saqo can,saidai da ya cusa kai ko harshensa wani qaqqarfan abu ke ingizoshi waje. Yayi wani irin rudewa da gigicewar da shi kansa ya dinga tuhumar kansa abinda ke faruwa,saboda a yadda yasan jikinsa yanayin da yake cikin ya wuce dabi'arsa. Duk sanda aka koroshin sai zuciyarsa ta tunasar dashi BA RUQAYYA BACE. dole daga qarshe ya haqura da nufin aika zafafan saqonnin ya koma kan hanyar da itama zainab din ta baje take jira ya isa ga gurin,a wajenta duk wadan nan abubuwan da yakeyi din bata lokaci ne kawai,tafi ganewa kai tsaye a shiga karatun. A yadda komai ke tafiya ya saka farinciki a zuciyarta ya kuma tabbatar mata da lallai yau din taci kudinta. Saidai a gefen saleem tun yana fahimtar abubuwan suna masa yadda yakeso har ya fara shiga wani yanayi na mamaki. Buqatuwarsa ta yau ta wuce ta kullum,abinda bai taba tsintar kansa a ciki ba muddin yana tare da Zainab dinne. Lokaci da qa'ida daya kamata ace komai ya lafa yazo qarshe sai ya kasa dakatawa. A hankali jikinsa ya fara weakening bugun zuciyarsa yayi mugun linkuwa,abinda ya haifar masa da haki da wani mahaukacin gumi. Bazai iya cewa ga yadda akayi ba,shi dai ya samu kansa da yin wani dummmm,kafin daga bisani yaji kamar jijiyoyin jikinsa basa aiki,ya sulale a hankali yayi kwance a gefe yana fidda numfashi. A qalla ya kusa mintuna goma a haka,sam bata lura ba tana daga kwance ta sheme tana sakin murmushi hadi da kada idanu,lallai yau akwai babbar kyauta da zata samu daga wajen saleem. Komai ya gudanar cikin wani irin zafi da kalar buqatuwar da takeso kullum ta ganshi a ciki. A hankali numfashinsa ya fara dai daita saidai yanzu kansa bai sauka daga nauyin da yayi masa ba,hakanan gangar jikinsa babu wata gaba dake da qarfi ko kadan. Miqewa yayi ya zauna yaja jikinsa da qyar ya wuce bandaki,da kallo ta bishi tana gyara kwanciyarta murmushi yana sake fita a fuskarta. Har ya fito tana kwance,ya goge jikinsa da towel ya sanya baqin gajeran wando da singlet ya dawo gefen gadon yana takawa a hankali ya zauna yana bata baya. "Tashi" yace da ita. Wannan ba sabon abu bane,duk sanda mu'amala ta shiga tsakaninsu shike fama da ita akan ta tashi ta tsaftace jikinta,har yau har kwanan gobe kuma bata canza ba,koda alwala kadai sai yayi yaqi takeyi bare wanka da sai da safe ma wani zubin sannan ta rattaba sallarta ta kuma hau shirya yara zuwa makaranta,wannan ya zama silar da duk sanda wani abu ya shiga tsakaninsu sai yara sun makara a makaranta,koda su alhassan sun shirya da wuri kuwa,tunda tare driver yake kaisu. Wannan ya sanya tun hankalin ruqayya baikai ba har ta fahimci abinda ke jawo hakan,saidai koda wasa koda saleem din bata taba nuna masa tasan dalili ba har yau har gobe. "Ni gaskiya bazan iya tashi ba,haba kaman ba kaga rashin imanin daka yimin ba yau,alwalar ma idan Allah ya kaimu asuba nayi" ta fada tana wani narkewa. "Me kika bani na sha zainab?" Ya jefa mata tambayar ba tare da ya waiwayo ba. Ido ta fidda waje hadi da tashi ta zauna ba tare data shirya ba "Me kuwa zan baka daddyn haneefa,me ya faru?" Waiwayowa yayi yana dubanta da idanunsa da suka sauya launi saboda kansa da yakeji ya masa nauyi "Yanayina ya canza,ba haka nake ba" "Okay,inda a tattare da ruqayya ka samu hakan ba zakace komai ba,saini saboda ban cika macen da za'a ji haka tare da ita ba?" Sai ta fashe masa da kuka. Can qasan ranta tasan tabbas ta kusa jawowa kanta matsala ne kawai,dose din maganin qwaya daya ne amma ta saka uku,kuma taji suna shaqiyanci a group din tare da gargadin masu wuce gona da iri din irinta ko ita a yanzun bawai ta gama sauka bane,amm bataga ta bakin cewa komai ba gudun tabbatar masa da zarginsa. Zazzabi yakeji a jikinsa baya kuma buqatar wata doguwar hayaniya ko qorafi,don haka ya dauke kansa yaja jikinsa ya koma saman gadon yana rufa da blanket idanunsa a rufe yana ambatar ALLAH qasa qasa. *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 06 *****Kamar kowacce rana da zata karba girki,duk sanda ka ganta tana gyare gyare zaka tsammaci wata tafiya me nisa saleem din yayi yake shirin dawowa. Kusan komai na dakin sai ta tabashi,wani ta canza masa guri wani ta gogeshi wani ta sauyashi gaba daya. Kafin azahar sai ta tabbata komai na dakin ya sauya daga ainihin yadda saleem ya fita ya barshi. Sha daya na rana ta fito daga dakin bayan ta gama kintsashi. Qofar ta murda ta bude ta fito parlor dinta hannunta riqe da qaramin towel da tayi goge goge dashi. Alhassan da alhussain ne zaune sun sanya tv a gaba,sun wani nutsu har abun yaso nata dariya. Ta jima bataga yatan dake masifar son kallon cartoon ba irinsu "Yadda kuka nutsu kuna wannan kallon,kada ku yarda anjima nazo karban hadda naci gyaranku". Yare suka dago kai suka kalleta suna dariya,alhussain ne ya fara cewa "Ni ko yanzu ma mommy ki karba Allah na shirya" "Nima din ai na shirya yaro" alhassan ya fada. Take 'yar musu ta barke a tsakaninsu. Gaba tayi ta barsu a gurin,don irin wanann qananun rigingimun nasu a rana har bata iya riga adadin sau nawa sukeyi,saidai fadan baya nisa ake watsewa,shi yasa ba kasafai ta fiya damun kanta da rabo ba. Gaban fridge dinta ta qarasa,ta saka hannu ta bude tana ciro wata doguwar gora me kyau,sai ta azata saman Fridge tana kallon agogo da dan mamaki a fuskarta. Tun dazun take mamakin rashin jin motsin saleem,duk da bata son zurafafawa kanta da tunanin abinda ya hanashi shigowa dubasu tunda hakan ba sabonsa bane,tanata son kiransa ko tabi ba'asin jinsa shurun amma zuciyarta tana kwabarta. Batason abun rigima da fitina,ko kuma taje ta gano ko ta jiyo abinda zai motsa kishin da taketa qoqarin ganin ta mallaki zuciyarta a kansa. Sai da yadan huce sannan ta bude gorar,take qamshin kanunfari da sauran kayan qamshi suka cika gurin. Tun kafin takai bakinta yawunta ya tsinke,ingantaccen tsumi ne data zauna ta dafashi da kanta jiya da sanannun saqe saqi da danginsu rake mazarqwaila harma da zuma a ciki. Cup daya ta cikashi dashi ta fara sha a hankali. Idonta ta lumshe tana jin dadinsa har saman harshenta,sai data shanye a nutse sannan ta kife cup din wanda yayi dai dai da kwada sallamar Zainab,sannan kai tsaye ta danno cikin parlor din. Hannu ruqayya ta sanya ta dauke gorar tsumin nata tana qoqarin maidawa fridge,duk da ba wani abu bane don Zainab din ta gani ba,koda ta gani tasan ba lallai ta fahimci meye ba,to amma ita din mutum ce da ba komai take bari idanun kishiyarta yakai kai ba (hakan ba laifi bane,yana da kyau ki iya takunki wajen kishiya,ba komai kike bari tana sani naki ba,koda kuwa me kyau ne,akwai abubuwan da sukan zama tamkar wani sirri ne naki,kuma makaminki da kike naki yaqin cikin gidan tsakaninki da mijinki,barin kishiya tasan da wannan sirrin ko makamin tamkar wargazawa kanki da kanki shiri ne). Tuni idanunta suka kai din,tunda itan tana cikin jerin sahun matan da komai kayi suna da buqatar sani ko gani,amma tunaninta sai ya tafi ga wani abun daban "Ana nan ana fama da coca-cola" ta fadi qasa qasa. Bata damu da kallon da ta bita dashi ba,ta gyara zaman tsumin ta maida fridge dinta ta rufe tana amsa sallamar tata "Aron mopper zaki ban yara sun karya min tawa" ta fada tana riqe hannu a qugu. Sau tari tana mamakin Zainab har ba iyaka,duka yara biyu amma idan kaga barnar da ake a sashen nata zaka dauka wasu gayyar yara gareta. Duk tsananin baqin kishinta kuma bata kunyar aron abu daga hannun kishiya?,wani abu guda daya tal da ruqayya zata iya bugar qirji tace bata taba yi ba(zubda kaine aron abu a wajen kishiya,muddin ba wai ta kama bane ko ba yadda zakiyi,komai da kikasan zaku buqata keda yara siya ki ajjiye,gwara ke a ara a hannunki). Waiwayowa tayi ga alhassan ta sanyashi shiga store ya dauko mata,saidai sanda ta maido dubanta ga zainab din sai ta sameta tana sana'ar tata wato sanya ido. A duk sanda wani uzuri ya kaita ga shigowa sassan nata to ba zata taba fita ba sai ta yiwa parlor din nata kallon tsaf!,in sha Allah duk abinda ta gani sabo ko baqo sai tayi qoqarin siyan makamancinsa. Abun tun yana bawa ruqayya mamaki har ma sai ya koma bata dariya. "Nikam daddynsu lafiya na jishi shuru bai leqo ba?" Tambayar da tayiwa Zainab mugun dadi,sai ta waiwayo tana sakin murmushi "Angoncinne ya motsa,don da qyar na lallabashi ya fita sallar asuba saboda jiya bamu samu isashen bacci ba ni dashi duka,saboda tsabar duniya ta masa dadi harda wani guntun zazzabin shagwaba" Girma sosai maganar ta yiwa ruqayya,takai idanunta da sauri kan alhassan da alhussain iftee dama baccinta takeyi saman kujera. Allah ya taimaketa hankulansu gaba daya ya tafi kan cartoon din sosai,da alama kunnuwansu basuyi wannan baqin jin ba,sai ta daga ido ta maida dubanta ga zainab. Idanun zainab din fes kan fuskar ruqayyan tanason ganin bacin ran da ta qiyasta zata gani din,saidai ga mamakinta murmushi ruqayyan ta saki bayan ta tako zuwa sashen da take don ta kaucewa kunnuwan yaran jin abinda bai shafesu ba "Ayyah,kayya kiyi masa sannu,ai ban sani ba,bai kamata ace har wannan lokacin ba'a shiga an dubashi ba,amma ina nan shigowa na duba angon naki,irin wannan dattijon amarci ga shekaru ga kuma bar muku sudi?,da kin sani ai aikomin kikayi dasu haneefan,kinga ni lokacin nawa amarcin duk girman gidan nan daga shi sai ni,baccin shekara ma sai muyi babu me tashinmu". Baki Zainab din ta tabe,maimakon ran ruqayyan ya baci sai tata zuciyar ta soma motsawa "Ah ai kunsha bacci,shi yasa tsabar bacci aka dauka juya ya auro" "Sai kuma ga mazaje har guda biyu sun wanke sunan ummansu daga juya zuwa uwar maza ba" ta maida mata amsar tana tsuntsira dariya abinta hankali kwance. Baki yasan abinda zai furta saidai kuma bashi da masaniyar amsar da za'a bashi. Maganar ta sake tunzura Zainab din,sai ta juya tana ficewa a gurin "Ki bar mopper din a wajenki idan kin gama" ruqayyan ta sake fadi,saidai ko waiwayowa zainab batayi ba ta qara gaba. K'aramar dariya ruqayya ta saki,kwata kwata wautar zainab take gani,idan tasan halittar ta saurin fushi,tunzura da rashin iya cinye bacin rai,to ya kamata ta kiyaye shiga ko faro maganganun da amsarsu ba zasu mata dadi ba,ta dinga kame kanta da hana kanta da kanta shiga hurumin da bai shafeta ba,ke da aka yiwa tambayar me gida kurum saiki zaqe?,bayan kinsan zuciya da fuskarki duka basu da baiwar iya shanye bacin rai da maida komai ba komai ba "Kadanma kika gani,na fiki iya iskanci" ruqayya ta fada tana komawa ciki. Kitchen kawai ta shige abinta,ta canza shawarar shiga dubashi din,a maimakon hakan sai ta jawo wayarta ta tura masa tex tana masa sannu da jiki. Yana fahimtar ta qwarai,tasan ko iya tex din ya wadatar. Data tabbatar ya shiga saita bude fridge ta ciro lafiyayyen kifi mara wadatar qaya ta kwara masa ruwan zafi sannan ta fara aikin sarrafashi. Nau'in kifin da saleem yafiso ne,kuma ita din bata taba rabo dashi koda wanda ya siyo ya qare,tana siya da kudinta ta zuba a fridge din. Jin dadin hakan ya sanya duk sanda yazo yaga ta zuba din zai biyata kudinta harma wasu lokutan ya qara mata. Abun na masa dadi qwarai,saboda na gefin Zainab sau tari saidai yaga an zubda a shara ya lalace,don ba damuwa ta fiyayi da kunna Fridge din kayan miya ba kwata kwata,ko ta kwashe ta bayar kyauta don kawai tayi bajinta. Kafin ta gama aikin ta kira qanwarta "Kizo ku tafi dasu alhassan su kwana gobe sauka idan jikin abbansu yayi sauqi na samu fitowa saimu dawo tare,tun jiya dama na tambayar musu" ba jimawa ta iso gidan,saita sakar mata gyaran kitchen din,ita kuma ta wuce bedroom dinta. Wankanta wani abune da bata wasa dashi,kowanne lungu da saqo da tasan maboyar datti ce sai tabi ta qalqale,ramin cibiya,qasan mama duk da tana da baiwar tsayayyun mama,matse matsin mazaunai,matse matsin cinyoyi,bayan kunne harma da cikin kunnen da qasan mara. Cikin mintuna talatin ta fito fes cikin doguwar rigar atamfa chocolate color din fatartan nan tayi luf cikin qamshi da cream masu taushi,daurin dankwalin kuma ya zauna mata sosai a kanta. Sai da tayi sallar azahar sannan ta dawo parlor din. A falo ta samu anata daru da iftee tace itama sai taje,da farko sai ta qyaleta tanata saka turaren wuta a burner tare da jona humidifier dinta,har ta gama bata bar kukan ba yarinyar,duk da ba'a jima da dawowa da ita gidan daga yaye ba, dole ta hada mata kala dayan itama ta bisu din. Kitchen ta wuce,ta ciro dafaffiyar budurwar kazarta da tasha hadin saqe saqi,kazar da take dafata da hannunta da ingatantattun saqe saqi da kayan da suke bawa jiki garkuwa da lafiya su kuma magance ciwon sanyi. Dan dumamata tayi kadan sannan ta zauna a nutse ta fara ci hankali kwance saboda sashen nata ya dauki shuru. Minti goma sha biyar ta gama,sai ta wuce da kwanon kitchen,ta koma dakinta tayi brush sannan ta dawo ta sake mulke jikinta da turaren da ba kasafai take amfani da shi ba idan ba lokacin kwanciya bacci ba saboda yadda saleem din ke matuqar sonsa. Bata yafa komai ba sai wani dan siririn gyale da yafi kama da mayafin yara wanda ya dace da atamfar jikinta ta fito daga sashen nata ta ratsa babban falonsu da yaron dake musu aike aike cikin gidan tuni ya gama tsaftaceshi ya wuce sabgar gabansa,ta doshi qofar falon sashen zainab din. Tun bata qarasa ba take jiyo ifce ifcen haneefa da khalil,da alama ma fada sukeyi,don tana jiyo muryar uwar tana kwarara musu tsawa wanda sauran kadan ta barke da ashar,tana tuna cewa saleem din yana gidanne da tuntuni ta hadasu data maguzawa,tunda a cewarta ta lura sunfi ganeta. Duk da tayi sallama ba wanda ya jiyota,sun kacame da dambe. Ta sanya qafarta da hanzari don ta isa ta rabasu,saudai tayi kyakkyawan Katarin taka wani abu me danqo. Koda ta dube sai taga ashe tea ne aka watsar har ya fara kama gurin ya soma bushewa. Tsigar jikinta ta zuba,ta janye qafarta tana takata saman carfet din falon saidai a nan ma qasa ta cabo a qasan qafartata. Dubanta ta maida ga tafin qafartata kafin ta dago kai saleem da hayaniyar ta isheshi har ta tayat dashi a bacci ya fito a dakin. Dif sukayi kowanne na neman gurin buya,sai suka fara qoqarin barin parlor din. Bai lura da ita ba saboda baiyi tsammanin shigowarta ba,saidai sassanyan qamshin da ya gauraye parlor din yake shiga masa hanci ya sanyashi wara idanunsa a parlor din. Qamshine da a jikin mutum guda ya sanshi,qamshine da duk sanda ya jishi ya tabbatar zai samu wani irin tarairaya da soyayya me girma,qamshin dake nuni da zai shiga wata duniya me cike da tarin nutsuwa. Ido suka hada daidai da fitowar Zainab daga kitchen wadda ke mamakin me ya sanya haneefa da Kahlil din nutsuwa lokaci guda?. Sarai ruqayya ta ganta amma ko da ido bata nuna mata hakan ba,sai tafi maida hankalinta ga saleem din. "Zuwa nayi na tafi da ango,ban sani ba ko angoncin daka balle jiya ya hanaka gane hanya shi yasa har yanzu baka samu shigowa ba" ta fada a tausashe tana murmushi. Hannu yasa ya shafi sumar kansa,har yanzu baya jinsa ya koma dai dai,kuma har yanzun idan ya tuna jiyan ya kasa nutsuwa haka siddan ya koma haka,ba abinda zai iya dorarwa me shauqin da zaice yayi matuqar qayatar dashi da zai tsaya masa a rai,face wasu irin abubuwa da hancinsa ya shaqa. Idanunsa sun rufe ya zurfafa hancinsa cikin jikinta,abinda dama ba kasafai ya fiya yi ba,wannan din wani sirrinsa ne da ba mahaluqin da ya sani,ruqayyan kadai yake iya yiwa hakan,saboda yasan duk inda zai cusa hancinsa AMINCI zai tarar da marabta me kyau. Gaba daya zainab din ma a tsarinta ire iren wadan nan abubuwan bata lokaci ne,gwara a dinga tafiya zuwa ga babbar headquarter din gaba daya. "Banajin dadi ne" ya fada shima cikin narkewar da baima san yayita ba,kawai wani farinciki yaji yana saukar masa tamkar mutumin dake tsakiyar kogo me duhu masu agaji suka riskeshi don fiddashi hakanan yaji. "Ya salam" ta fada tana nuna zallar alhini a fuskarta tana kuma takowa da sassarfa zuwa kujerar da ya zauna din a kai,yanayin yadda take takun ya bawa qirjinta damar motsawa,wanda ya ciko yayi fam saboda baiwar aqirji da take dashi,uwa uba kuma tana using push off brazier don bahaushe yace idan kana da kyau ka qara da wanka. Ita kanta tana alfahari da baiwar beast da hips da Allah ya bata,ita din baqace ko ace wankan tarwada,zainab ta fita fari da tsahon gashi sosai,farin da a baya yaso ya zame.mata tarnaqi kuma kalmar da akaso ayita cusguna mata da ita. Bata taba mance lokacin auren zainab,zuciyarta ce kadai ta rage bata buga ba,amma hawan jini kashi kashi ta yishi. Hasken fata da tsahon gashi tayi imani kawai zainab ta fita,saidai ita kuma Allah sai ya qareta ta bangarorin da take da tabbas ta yiwa zainab rata me tarin yawan da bazata lissafu ba. A hannun kujerar da yake kai ta zauna tana duban fuskarsa "Habba amma ya kamata na sani ko?" Ta fadi a shagwabe tana tura baki gaba. Murmushi ya saki yana kauda idanunsa saboda ta fara tadoshi sosai "Am sorry" ya fada a taqaice saboda tsaiwar Zainab a wajen wadda kamar zata fashe "Alright,muje na qarasa wannan jinyar gaskiya,wannan amarci an cishi yadda ya dace,har ruwan dumi zan maka na gasaka da kyau,kaga nima sai naji dadin diban nawa tsumammen uwargidancin" ta qarasa maganar tana kashe masa ido daya hadi da cije lip's dinsa na qasa abinda ya sanya tsigar jikinsa zubawa. *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 07 "Ba inda zaije,bashi da lafiya,kuma har yanzu kwanana ne" a nutse ruqayya ta waiwaya ta dubeta sama da qasa,ta ganta wata harikicibayya cikin zanin wata atamfa da yayi musu waccan sallar,ta Zainab din ruwan madara ne,atamfar kudinta duk daya ta doshi dubu goma sha takwas amma cikin qasa da wata goma tata har ta doshi hanyar zama tsumma,ta rune daga milk ta koma brown brown da torches na dattin abubuwa mabanbanta,bakin zanin yayi leb'atu wani ya zarta wani yana lilo "Haba amarsu bakya laifi,baki lura bane azahar har ta gota?,ko kin manta ke kika tsara mana hakan dama?,kiyi haquri kwana biyu rak zan dawo miki dashi da kaina" ta fada mata tana murmushi dariyar daurin dankwalijta yake a jirkice yana kama ruqayya. Sau tari bata fiya jin kishin zainab cancan ba, saboda tasan bata da abinda zata kara da ita,saidai hali kawai irin na zuciya da kuma abinda takeso. Miqewa saleem din yayi yace "Minti daya" "A fito lafiya" ta amsa masa tana maida dubanta ga tv din dake aiki, wadda rabinta tayi baqi saboda yadda su haneefa suka ragargajeta duk girmanta kuwa,shi kuma yayi rantsuwar bazai canza mata wata ba,saboda bayan wadda ya siya musu ita da ruqayya ya sauya mata wata,wannan din shine karo na biyu kenan da yake sauya musun bayan ta farko. "Ba inda zashi,yana nan" zainab din ta fada tana juyawa tabi bayanshi dakin. Aikin da ya gagara bai gama jiya ba yake hada kan takardun nasa sai yaji motsinta,koda ya waiwayo ta fara zare t.shirt da zanin jikinta,ta fara takowa inda yake tana girgiza kafadunta "Mene hakan?" Ya fada a mamakance,take fuskarta ta sauya kamar yadda bata iya cinye bacin ranta ba "Ragowar haqqina nake buqata,kuma kaima aina lura bawai ka gama nutsuwa bane" Dariya ce ma taso kamashi,yadan kauda kai daga nan yana jiyo yadda smell na jikinta ya canza da alamu tana da buqatar tayi wanka amma ta kasa gane hakan. Abu na biyu kuma ya fahimci tana so ne tayi abinda zata batawa ruqayya lokaci,saidai kash bata iya durfafar miji da salon zai dauke masa hankalin ba tare dashi kansa yasan ya akayi hakan ta faru ba "Lokaci ya fice yanzun kema kin sani" "Eh amma hakkina ne ai a wuyanka ko?" Tsaiwa yayi yana kallonta kafin daga bisani ya girgiza kai yaci gaba da hada takardunsa. Maganganu ta shiga yi na bacin rai har ya gama,ya miqe tsaye yana zuba mata idanunsa abinda ya sanyata rage kaifi bakinta "Kiyi qoqari ki tabbatar ba wani abun kika zubamin jiya ba,don muddin na gano hakan kinsan sai na hukuntaki tabbas!" Ya qarashe maganar yana kewayeta ya fice,saboda yasha mata gargadi akan hakan,yayi dukkan abinda zaiyi ya koya mata hade haden vegetables din da ruqayya keyi masa da suke da matuqar amfani ga lafiyarsa da auratayyarsu,amma tsabar son jiki ta kasa tsaiwa ta dinga yi masa a kullum kamar yadda yake da buqatar ya dinga ci din. Har wani sakakken numfashi ya saki sanda suka isa sashen nata,wata ni'ima da nutsuwa suna saukar masa. Ruwa me dumin sosai ta hada masa kamar yadda tace,koda ya sanya hannu cirewa yayi da sauri yana dariya "Wai ashe da gasken kike gasanin zakiyi?,na dauka kin fada ne kawai saboda kishi?" Yadda ya rutsata da ido yana tambayarta sai abun ya bata dariya,ta murmusa tana qoqarin danne kishinsa da takeji yana cin qasan zuciyarta "Amma dai kafi kowa sanin ruqayya,idan tace eh tana nufin eh din,idan tace a'ah shima tana nufin hakan" murmushi ya saki yakai hannu yana shafar dukiyar fulaninta da yanayin dinkin da akayi mata ya fidda shape dinsu sosai. Har yanzun yanajin wannan yanayin a jikinsa,saidai hankalinsa na kwanciya idan ya tuna ya fado hannun da zai samu dukkan kowacce irin nutsuwa. "Naji sashen shuru ina duka yaran"ya tambayeta sanda take taimaka masa yana fidda kayan jikinsa don ya samu yayi wankan,har yau har gobe muddin tana free irin haka itace ke taimaka masa da wannan,hakama shirin muddin ta gama nata ayyukan "Na korasu gidan kakaninsu don nayi jinyar daddynsu da kyau" wafta ya kawo mata,ya jawo qugunta ya riqeta suna musayar numfashi. Idonsa cikin nata,hakanan duk wani fitar numfashinta sai ya hado da sassanyan qamshinta. Sai ya tuna wata rana irin hakan da ya gwada yiwa zainab hakan,daga qarshe da hannunsa ya saketa saboda bala'in rashin tsaftar baki,wanda hatta da numfashinta da irin wannan yanayin yake hadowa ya fito. "Wannan jinyar ta tsaye miki a rai ko?,to kada ki damu,kema yau ki daure ki jinyatani hakan mana" ya fada yana kashe mata ido daya. Hannu biyu ta sanya ta turashi baya tana dariya "To bismillah ko an gaya maka raguwa ce?,ai dai kafi kowa sanin wace ni" dariya ya saki yana kai mata cafka,sai ta zame ta fice,don sam ba zata yarda ya rabeta daga barowarsa sassan zainab ba,tafi son ya tsaftace jikinsa duk da fes yake,amma hakanan take da wannan kishin a zuciyarta. Kafin ya fito ta hada masa hadin salad na musamman,bricole,spinach,cocumber,parsley cabbage lettuce cornflower,ta yayyankasu ta wankesu da ruwan gishiri,ta diga masa mai kadan. Tuni ta haramta zuba maggi me yawa a abincinsa bare akai ga farin magi,don haka gishiri ta zuba mishi kadan da yaji wanda tasirinsa bazai fito ba bare ya dameka. Blender dinta ta jona ta markada kabewa dabino da kanunfari yayi laushi qwarai kaman yoghurt ta wadatashi da zuma. Duk inda ta gifta saita aje masa qamshinta,hakanan tasirin maganin jiya da bai bar jikinsa ba ya dinga tsomoshi. Sai data gama shirya masa komai sannan ta dawo ta zauna tana dubansa cikin wani lallausan kallo data aje kawai saboda shi,zata iya cewa duk duniya ba wanda ya taba ganin makamancin kallo irin wannan a idanunta saishi daya tal "Ga abinci ya kammala,ka fara tabawa kafin na dora girkin dare" kumatunta yaja yana murmushi "Emergency kika hadamin ne?,naga harda pumpkin smoothie" farrr tayi da idanunta tana murmushi "A'ah,ya za'a yi mu hadu muyita tara maka gajiya?,so nake kaci ka qoshi ka kwanta ka huta,qwarin jikinka ya dawo" mintsininta yayi kadan yana murmushi, muryarsa qasa qasa yace "Ban yarda ba,tunda kikace kin tafi gidan aunty deeja nasan there's something special yau,naga wani abu me zaqi zaqi ma a fridge dinki" idanu ta fiddo tana kallonsa "Sai kuma kasha?" Kai ya girgiza yana langabe mata shima "Dandanawa kayi nayi fa,Allah bansha ba" shagwabe masa tayi sosai kaman zata saki kuka "Amma dai daddynmu kasan ba kyau bincike dai ko?" Dariya ta qwace masa "Ni ruwa naje sha ba bincike nayi ba" ya fadi yana daga hannunsa sama duka biyun yana dariya "To nidai na yafe yau din,an baka hutu" ta qarashe maganar idanunta nakan labulen window dinta dake ta veranda din waje. Idan idanunta sun nuna mata gaskiya shatin tsaiwar mutum take hangowa,karon farko kuma taji zuciyarta tafi kakata da cewa zainab ce. Sau uku qanwarta da maqociyarta suna gaya mata Zainab din tana mata labe,amma bata taba daukan abun da muhimmanci ba tunda bata taba kamata ba. "Ni kuma ban yafe ba" ya fada yana matsa hannunta dake da wani sulbi da taushi. Tana sane ta saki wata shagwababbiyar qara idanunta nakan labulen "Allah dear......ka bari don Allah,tun ba'a yi nisa ba kada kasa na kasa komai" "Na bari,amma mu fara salla tukunna kafin muci abincin" "Yes sir" ta fada tana miqewa. Sai data fara wucewa kitchen ta fiddo sumammen ruwa ta juye a wata roba sannan ta wuce toilet ta shirya masa ruwan yadda zaizo da dumi bayan tayi tata alwalar ta kuma shimfida abun sallah sannan ta zarce kitchen din. "Na daina raga miki" ruqayya ta fada qasa qasa tana dariya mugunta hannunta dauke da robar ta dawo falon din. Sake gyara tsaiwarta tayi da kyau zuciyarta na sake tafasa da bacin rai. Ba zata bar wajen nan ba har sai taji uban me dame sukeyi tas a cikin falon. Gumin fuskarta ta goge tana jin kamar ta rushe da kuka. Babu ta yadda za'a yi ma ta yarda cewa ruqayya ba asiri ta yiwa saleem ba,don bataga wani abu guda daya da zaisa saleem din ya dinga wannan rawar jikin a kanta ba,bayan itace tafi cancanta da hakan. Ai bata dire tunaninta ba taji saukar ruwan qanqarar da ya kusa tafiya da numfashinta gaba daya. Ta taqarqare ta kunzuma ihu ta mance ma shaf da muhallin da take a tsaye. Da sauri ruqayya ta bankade labulen da qofar gaba daya ta fito tana salati "Jar uba!,ni kika jiqa da ruwan qanqara,wallahi tallahi yau ko sama da qasa zasu hade bazan yarda ba" ta fada tana gyara daurin qirjin da tayi a saman zanin atamfar jikinta. Wata dariya ta tasowa ruqayyan yadda tayi tsamo tsamo da ruwan har tana rawar dari,amma dai sake gyara masoyinta takeyi wato daurin qirji "Aike za'a tambaya,me kikeyi a nan gurin?" Tambayar data daukewa Zainab din wuta difff musamman da tambayar ta fado dai dai sanda saleem yake fitowa daga falon saboda ihun zainab din daya riskeshi har bandaki. Ido tahau rabawa, ganin yadda shi da ita gaba daya suka zuba mata ido suna sauraren amsarta sai tahau tafa hannu "Ni zaki yiwa wannan tambayar?,ko kin manta yadda gidan nan yake naki nima haka yake a wajena?,ko wucewar ma mutum bazaiyi ba saboda window din daki ne?" "Wucewar ce harda kujera?" Saleem ya sake jefa mata tambayar yana nuna mata kujerar data aje a wajen. Dif wuta ta dauke mata,yayin da shi kuma yaci gaba da kallonta yana hadiye wani abu me tauri. "Allah ya kyauta" ruqayya ta fadi tana kewayeshi ta wuce ciki abinta,ko babu komai ya gani da idanunsa,bata bude baki ta fadi ba bare ace sharri ne da yarfe irin na kishiyoyi. Batasan yadda suka qare ba,saidai har alwalarta ta bushe bai shigo ba,sai daga bisani ya shigo yana ware hannun rigarsa,fuskar nan cike fal da bacin rai,saidai bata bari hakan yaci gaba da damunsa ba ,don bayan sun gama sallar sai data tabbatar ta mantar dashi komai ta hanyar biye masa ya sauke sauran nauyin da Zainab ta dibga ma cikinsa ba tare daya sani ba,sannan ta shiriritar dashi suna wata daddadan hirar gado wadda ta musammance data warewa lokuta irin wannan. Lokutan da suka gama kasancewa da juna a lokaci irin wannan da babu kowa daga shi sai ita. Yanason irin wannan moment din da take creating musu,yana sakin jiki qwarai yayi sirrika masu tarin yawa da ita,suyi shawara da juna ta kuma sauke masa damuwar da yakejin duk duniya ita daya keda wannan power din. *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 08 GIDAN HAJIYAR MATA daya daga cikin jerin gidaje guda goma sha biyar kenan dake layin. Faffadan gida ne dake da soro makeke guda,yalwataccen tsakar gida dake da bishiyar mangwaro a tsakiyar gidan,sai dakuna guda biyar manya,wanda kowanne cike yake da kayan jere na alatu wadanda suka fi qarfin a zubasu a gida kamar wannan,duk da gidan fes yake,baya rabo da fenti da 'yan gyare gyare kodon saboda baqi dake yawan zirga zirga a gidan. Kusan duk sanda zaka shiga gidan zaka samu dakuna hudun nan a rufe,musamman uku daga cikinsu,har gwara dayan ana yawan budeshi saboda baqi dake zuwar mata. Daki guda kuwa kulli yaumin yana a bude,saboda shine ainihin ma'assasar neman kudi da dukka wata taqama na hajiya zeena din. Akwai masu aikin dake zirganiya daga dakin zuwa tsakar gidan sanye da riguna koraye masu dauke da tambarin HAJIYAR MATA musamman idan ta kammala hada magungunanta za'a yi packaging. Saidai ko su din akwai wasu kebantattun lokutta da bata barinsu shiga dakin har sai ta kamala hada magungunanta saboda boye sirrin kasuwa kamar yadda takance "Mutane ba amana,kasuwa ai sirri ce" Ko a yau din ma masu aikin nata na zaune a tsakar gida suna hirarrakinsu tare da jiran hajiyan dake dakin ta sallami baquwarta ta kuma gama hada magungunan nata su shiga suyi aikinsu,don yau din akwai kaya da yawa tace musu akwai matar da zata sara. Daga cikin fallen babban dakin da yafi kowanne girma mata ne zaune saman kujeru guda biyu,dayar kana kallonta kasan itace matar gidan,don kanta daurin ture kaga tsiya ne tayi,qwaiwayayyen gashinta ya bullutso ta qasan daurin,yayin da d'ayar ke sanye da hijabinta saidai ta sabashi saman kafada "Shi carwash din yanzun saidai botiki uku?,botiki biyar naso saboda zanyi sabulun tsarki dashi me yawa wallahi" "Masu nema ne sukayi yawa hajiya,kuma kalolin da za'a sakawa koren ne babu,ke kuma koren kike da buqatar yayi ko?" "Eh mana,yo banda abinki ta yaya za'a yarda sabulun magarya ne babu koriyar kala?" "Ba matsala zanyi qoqarin hada miki cikin satin nan in sha Allahu" "Shikenan,zan jalauta haka" ta fada tana ninke takardar lissafin nasu,ta jawo wata lalita a qugunta ta zuge ta lissafo kudade ta miqa mata "Gashi babu kare bin damo,idan kin kawo sauran koren na baki kudinsa iya shi kadai" kudin ta jujjuya a hannunta "Haba hajiya,na zaci zaki bani kudinsa shima kafin na kawo" "Kije kiyimin irin ta wancan lokacin ko?,saiji nayi kin bawa wata,to kar nake kallonki" "Karmuyi haka dake mana,duk zaman nan ace ba aminci tsakaninmu?,kudin nan fa kafin ki tashi a nan na tabbatar kin maida ninkin baninkin dinsu" daurin dankwalinta ta sake turowa gaba ta bararraje tana jawo wani farin botiki dake cike da garin masara me azabar fari da laushi da yasha tankada da kyau,hakan ya nunawa matar da take kira da saude ba zata cika mata din ba "Kinga miqomin botikin zumar can" dariya saude ta sheqe dashi "Zuma ko dafaffen sugar cakude da dan zaqi?(sweetner)" Baki ta tabe cikin nuna halin ko in kula "Koma menene ke kika sani,miqomin nayi nayi na hada,basira zata shigo sari tace akwai gidan sunan da zata je yau din" "Hajiyar mata hajiyar mata" saude ta fada gana dire mata botikin. "Ahto,meye amfanin sana'ar da babu riba,tunda dai sunyi imani kuma yana musu aiki aimu alhamdulillahi......ina fiddausi?,zoki hada dan matsin nan yasha iska kafin anjima" ta qwalawa biyu daga cikin amintattun masu aikin nata kira. Wani kwali ta jawo dake dauke da zanen mace babu komai a jikinta sai pant,an fiddo abinda zai nuna maka tallan abubuwan da zasu qara masa girma akeyi "Balle capsule dinnan ki watsa a hadin garin qara girman nonon can za'a kai niqa" "Kinsan sirrin kasuwa hajiya" saude dake dariya ta fada "Yo mu din na wasa ne?,ke kinga yadda mata suke wasoson garurrukana?,to kina sha zai fara aiki,su dama haka sukeso,wannan zai fara miki aikin da idan hadin Allah kikayi musu sai yayi wata uku mace tana sha bataga canji ba,yanzu zakiji an bata miki kasuwa ana cewa bashi da kyau,bayan shine me kyan,tsabar gaggawa ce dasu to kinga gwara kawai kayi musu abinda sukafi ganewa,wanann garin duk yawansa bazaikai jibi be qare ba" ta fada hautsina garin masarar dake cikin botiki,da niqan aya da saqe saqen da batasan adadin yawa da kuma dame dame ta game waje daya ba. A hakan garin masarar yafi yawa,ganin yayi haske da yawa saita debi garin kala me dan duhu ta watsa "Yauwa,sai a dauka tsabar soyayyar ayace da ta wadata" hajiya ta fada a ranta tana qissima yawan ribar da zata fitar a wannan hadin da tayi. *******A nutse ta kammala komai,hatta da abincin dare harda farfesun kayan cikin da saleem ya aiko daga kasuwa. Ta shirya tsaf cikin atamfar black prince me kyau data dace da kalar fatarta. Wani irin sassanyan dressing,ita din gwanace gun hada ado da yakan dace da kowacce kalar unguwa. Hannunta riqe da key din motarta ta fito babban falon gidan da zai wuce da ita harabar gidan. Sauka idanunta yayi akan sassan zainab. A rufe yake gam,ta kusa awa hudu da tafiya tuntuni. Aike ta dinga yo mata ba qaqqautawa akan ta fito su tafi,ita kuma ta aike mata ta tafi kawai ta taho. Hakanan al'adar zainab take,indai taji batun fita gurin wani sha'ani ko taro jikinta har rawa yake,ba kasafai ranar abincinta ke ciyuwa ta dadin rai ba idan ma ta tsaya tayin. Wani murmushi ya qwace mata data tuna wani abu,ta girgiza kai kawai tana isa ga motarta,tabbas ta yarda wasu matan basu da wayo kam. Minti talatin ya kaita unguwar,suna akeyi na 'yar qanwar mahaifiyar saleem din. Kana gani kasan gidan cike yake,don kuwa duk da gidan yalwatacce ne amma har ta waje kana iya hango zirga zirgar jama'a. Tunda ta ajjiye motarta ta fito taketa gaisawa da mutane cikin mutuntawa da ganin kima,can qasan zuciyarta mamaki yana dan mamayarta,tana sake gasgata cewa tabbas ME HAQURI YAKAN DAFA DUTSE HARMA YASHA ROMONSA. Mutanen da wasunsu a baya suka daina magana da ita,wanda ita tasan ba komai bane ya jawo hakan sai saboda zainab da saleem ya auro da suke ganin 'yaruwarsu ce sunfi kusa da ita akan ruqayyan,duk da tarin kyautata musu da ruqayyan keyi amma suka shafawa idanunsu kwalli,sai gashi lokaci yanata nuna kansa, gaskiya kuma tanta halinta bayan ta watsar da damuwar kowa ta maida hankalinta ga addu'a da mu'amala da kowa da zuciya daya. Gaisawa ta dinga yi da mutane,bata kuma zauna ba har sai data lalubi dakin da surukarta take da wasu daga cikin qannen hajiya din. Da sallama ta shiga cikin kamala da kuma kunyar da har yanzu batajin ta gushe a tsakaninsu,duk da irin abubuwan da suka faru a baya,da irin ababen da ita hajiyan tayi mata masu dimbin yawa dake da soya zuciya da saka me rauni ya tsani mutum. Taji babu dadi ta kuma koka matuqa da gaske,saidai ko sau daya bata taba jin ta tsaneta ko zata iyayi mata rashin kunya ba,saboda me?. A koda yaushe tana duban hajiyan a matsayin wani tsani na dukka matakin da tahau a rayuwarta,duk tsiya duk kuma inda za'a je a dawo itace dai ta haifa mata saleem din da zuciyarta ke matuqar so take kuma son ta kyautata masa wanzu tare ila yaumil qiyamati,ta bashi tarbiyyar da har ta burgeta ta kuma zame masa silar mallakarta,tana ganin wadannan dalilai kadai sun isa babban dalilin da hajiyan ta cancanci dukkan wani uzuri girmamawa da dagin qafa daga gareta. Sallamar ruqayyan yaja hankalin hajiyan. Sai ta far gyara zamanta cikin fara'a da kuma d'ari d'ari,kunya da nauyin yarinyar a yanzu takeyi "Maraba,qaraso ciki mana,na tambayeki abokiyar zaman naki tace kina gida kina girki" murmushi cikin jin nauyi ruqayya ta saki. Hukumullah ta fada a ranta,duniya juyi juyi,wai yau itace hajiya ke tambaya?,ita din da a baya hajiyan kan fadi cewa kada a sake zuwa mata da ita?,ita din da a baya take cewa ta gaji da ganinta,yadda ta ganta jiya haka zata ganta gobe da jibi ma?. Kauda wannan tunanin tayi,ta zauna saman pillow din da hajiyan ta tura mata ta soma gaidata cikin tsantsar ladabi da kunya. Amsawa tayi cikin kulawa itama,ruqayyan ta waiwaya ta gaida sauran 'yan uwanta dake falon. Waiwayowa hajiya tayi ga wata dake a tsaye "Lu'ubatu a kawo mata abinci ko?" A ladabce ruqayyan tace "Bari naga me jegon tukunna hajiya" "Gasu can acan dakin sun cikawa jama'a kunne da hayaniya" dan qaramin murmushi tayi tana miqewa. Tunda ta shigo take jin tashin hayaniya sosai a dakin,saita ratsa ta isa ga dakin. Za'a iya cewa a cike yake dakin,saidai girmansa ya sanya kowa ke zaune a sake ba tare da an takura ba. Hira suke qwarai ba qaqqautawa,zainab na daga cikin 'yan committee na hirar don da alama ita ke bayarwa ana amshewa. Sallamarta tasa hayaniyar ta ragu,sai idanu kuma sukayo kanta,wasu na amsa sallamar yayin da wasu suka buge da qare mata kallo ciki harda Zainab dake tunanin yaushe ruqayyan ta dinka atamfar nan?. Raliya dake zaune daf da zainab ce ta tabota murya qasa qasa "Kin ganta kuwa sai yanzu,lallai ita me aji" waiwayo zainab tayi sannan ta tabe bakinta "Tana can miji ya maidata jaka,sai data gama girki da gyaran gidan,kinsan ni duk ranar girki ne lallabani yakeyi,kada na gaji dare yayi ya kasa morar dadi,duk ran girkinta a wahala take qarewa,uban kayan ciki ya hadata da dahuwarsa,a dafa mana,mu koma mu kwashi banza ba tare da mun tsinana komai ba" ta qarashe zancan tana kwarara dariya raliya na tayata suka tafa ji kake fass. Dariyar tasu taja hankulan wasu a wajen,banda ruqayya data tattara hanakalinta ga dan jaririn fatima. Fatima mutuniyarta ce qwarai,zata iya cewa cikin dangin mijinta ba wadda suke dasawa da ita kamarta. Tana riqe da yaron tana duba ciwon idanun da fatiman tace kamar yaron yana yi. Batulu ce dake gefansu ta dubi zainab dake dariya saman fuska,amma qasan zuciyarta kamar an watsa garwashi,don sosai black prince din jikin ruqayya ta tsone mata idanu,sai wani sheqi takeyi da daukar idanu "Wato ke sauqaqqan girki ake baki ko?,sharp sharp" "Ashe dai kin gane" ta fada tana watsa mata wani kallo. Dariya batulu ta saki "Yo ni ai banga wani gata a nan ba,hasalima gani nakeyi kamar ya raina sanwarki ne da iyawarki,shi yasa yake dabara ya kawo ranar girkinta don yasan bazai bata kudinsa ba" da sauri ta waiwayo tana duban batulu,dama akwai 'yar tsama kadan tsakaninsu. Batulun irin matan nan ne da basu barin ko ta kwana,hakanan basu da tsoro "Eh,ai gaskiyar maganar kenan,sanwarta tafi taki dadi,ai na tabacin farfesun naki,hakanan nasha cin girkin anty ruqayya ko wajen hajiya kuwa" "Hajiya kuma?" Ta tambayi batulu "Eh,lokaci lokaci ai ruqayya nada qoqarin wannan aiken kam,sai aka dace hajiyan nason sanwarta" sosai maganar ta daketa,don bata taba tunanin kaiwa hajiya koda silin taliya ba a matsayinta na 'yar 'yaruwarta,hajiyan mada tudu biyu a wajenta,babarta kuma uwarmijinta,bata kuma san ruqayya tana yi ba,asalima ita din tana cikin matan da suke ganin kaiwa uwar miji ire iren wadan nan abubuwan ba komai bane sai tarin bautar da kai. Tunda dai komai saleem yana siya yakai mata ai ba buqatar sai an kai mata dafaffe koda sau daya a wata ma kuwa. Idan Allah ya kawota baqunta taci,idan batazo ba haramiyarta a kuma sauka lafiya. Ci gaba da hirarta batulu tayi suna gaisawa da ruqayya kuma cikin fara'a da sakin fuska. Sallamar basira ita ta katse sauran tunanin da Zainab keyi ta tattarashi ta watsar,farinciki kuma ya maye gurbin bacin ranta,ganin basira kawai ta tabbatar yau din akwai harka. Muryarta kuwa tafi ta kowa dagawa "Kaga basira me kayan harka,Allah ya barmu dake ki jima kina yi" mamaki yadan kama ruqayya,don ta tabbatar har yanzu su hajiya na zaune a falon,kuma tayi imani suna iya jiyo komai "Ai inata sauri hajiya zainab karki tafi" "Wa?,ni?,Allah ya kasheni musulma naga kayan harka na tafi ban kwasa ba,ke a banza nake zaune a gidan alhaji saleem?,banda wadan nan abubuwan da tuni boka da malam sun jima da tsigeni a gidan" ta fada tana tafa cinya gami da kallon gefen da ruqayya ke zaune a sace tana gogewa babyn idonsa da magani. Zaman dirshan basirar tayi ta kuma zazzage jakarta,take mata akayi caaa,na waje ma da basusan me ake ciki ba sai gasu da daya da daya suna gangarowa. Yawancinsu amare ne auren watanni masu haihuwa daya zuwa uku hudu. Yaran mata sosai da sukejin ludayinsu yana kan dawo suka cika cacim. "Duk wadda bata da kudi ma kada ta damu,har adashi inayi,sai na saka kowa a wassuf guruf" basira ta fada cikin jin dadi da farinciki. Tunda take fadi tashi da buge bugen sana'o'i bata taba cin karo da sana'ar dake da wani irin mugun farinjini da kawo zallar madarar kudi a nan take ba irin wannan sana'ar "Ni wallahi wanann nakeso,da alama aikinsa yafi na dukka magungunan nan" zainab da hankalinta ya dauku ta fada tana daga kwalbar dake cike da wani abu me danqo,an lullube kwalbar da wani rubutun hatimi da wani tsinke a maqale "Yana da kyau akwai kuma aiki,amma gaskiya duk nan ba kaya me tsadarsa,tafiyayye ne tun daga sakkwato" sai tayi qasa qasa da muryarta "Kinsan Allah daga gidan malamin aka karbominshi ana kawomin shi na jefashi a jakar nan na fito nayi nan,wannan ma na wata hajiya ne,idan kinaso zan yiwa malamin magana yayi miki naki hadin na musamman" a take Zainab taji qaunar maganin ta shigeta. Kai ta girgiza "Wallahi ko na uban waye saidai tayi haquri,bani da kudi amma ina da kayan kudi,zan bayar a barmin shi,nawa kudinsa yake?" "Fisabilillahi a bisa sauqi shi da wannan ruwan....." Ta fadi tana miqa hannu ta dauki wani ruwa da yasha gamje gamje harda su dan tsami da gishiri da sauran tarkace ya koma brown,tana zaune kuma idea din hakan tazo mata "Idan kika hada aikinsu yafi zuwa dai dai,ki bada dubu arba'in da biyar,amma wallahi tallahi na rantse miki da Allah har dubu sittin na karba a kansa" kai zainab ta girgiza tana juya maganin a hannunta "Ai kuma na yarda hajiya,ni dama ba kasafai nakeson maganin dari biyar dubu daya ba,ko a baki wani sassaqen bagaruwa ko sassaqen malmo ace wai ka dafa tsumi kasha,tsumin me?,kafin kiga aiki miji ya gaji da jin shuru maqatau?" Ta fada tana daga murya hadi da gatsine duk don ya isa kunnen ruqayya. Ta jita amma ta bawa banza ajiyarta,hasalima dariya ta bata,saboda a wajenta wannan hade haden da zainab ke yiwa kanta tabbas abar tausayi ce ita idan batayi da wasa ba. Kawai fargabarta daya kada ta kwaso abinda zata qunsawa saleem itama kuma ya sanmata. Cikin lokaci kadan hannun basira ya cika da kudi dumus,aka kwashe kaya tsaf sai ragowa. Idanu ta shiga wulgawa a dakin tanason ganin wanda bai siya ba taja raayinsa,don so take ta fita da kudinta gaba daya. Ruqayya ta hango sai ta dubi zainab daketa shirya kayayyakinta qasan jaka cike da farinciki. Tasan kishiyarta ce amma ita ba ruwanta neman kudinta takeyi,don haka ta dan daga murya "Hajiya azo a yiwa me gida gyara mana,kayanmu ingantattu ne sai an gwada akan san na qwarai" kamar ta dorawa Zainab guduma aka haka taji,ita basira zata yiwa haka?. Fatima dake zaune tana cin tuwo gefan ruqayya ce ta zunguri ruqayyan,ba tare data kalleta ba murya qasa qasa tace "Don Allah kema anty ki saya mana kiyi gyara" murmushi ta saka bata dubi fatima ba tace "Hajjaju Allah ya bada sa'a" kai tadan sosa "To amin,amma ko kudi ne baki dashi ai ina lamuni,idan kika gwada yayi aiki kya biya daga baya" https://chat.whatsapp.com/EKyzZCUEGyRAEGGAnTHmGF *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 09 Murmushin takaici ruqayya ta saki,gaba daya babu nutsuwa ga matar bare ka samu gamsuwar abinda take saidawa "Kiyi haquri banacin bashi,ma hadu wani jiqon idon da rabo" "Allah ya qara,mtsweew......banda rainin hankali na gama siyan kaya a wajenki saboda saiki tallatawa kishiyata,idan baki wasa ba billhuwallazi bazan qara siyan kaya a wajenki ba" zainab dake jibgawa basira harara ta fada. Ganin zatayi asara ba wan ba qanin saita tura dankwali gaban goshi "A'ah me yayi zafi?,idan ma kin ajiye yo ba kanki kika yiwa ba,itama da bata siya ba kanta ta yiwa" "Gwara data yiwa kan nata,indai itace zatayi miki cinikin maganin mata zaki daina cin abinci da kudin magani a duniya,banda taci kayan ganye taci nama da coca-cola batasan komai ba" Dariya muqarraban Zainab din suka saki. Sarai ruqayya taji,amma hankalinta yana kan fatima suna maganarsu. "Ba yunwa kika ce kinaji ba amma zaki balle magunguna ki fara sha?" Raliya ta fada tana kama haba idanunta akan fuskar zainab "Bana bori da sanyin jiki nifa,gobe nike da turaka gwara na watsa tun yanzu subi jikina,yunwa wannan ba matsalata bace,don bata hanani shan magani abuna" tana gama fadi ta fara tuttula na sha da dama sauran da suke na gari. Sallama aka sakeyi daga bakin qofar,na'ima ce wadda daya ce daga cikin family din nasu,kakanni suka hada dasu saleem,saidai ita babarta 'yar Maiduguri ce. Hannunta dauke da wata babbar jaka tayo sallamar,sallamartata kuma ta hade da qamshi wanda ya cika dakin lokaci guda. "Nima ga hajata ayimin ciniki bayin Allah" ta fada tana dariya tare da kutso kai cikin dakin. "Hajiya zee,a zazzagen bakin jaka" ta fada tana murmushi idonta kan zainab wadda tayi tatul da maganinta tana jin tabbas gobe zata sake jarraba sa'arta. Ko da saleem baiyi appreciating nata ba tayi imanin da taimakonsu take zaune a gidan,kuma yana jin dadinta ne,wannan ya hanashi asirin farraqun da ruqayya keta qoqarin yi musu ya kasa kamashi "Ai kinzo a makare hajiya niimatu,na cinye kudin jakata harda bashi ma a kaina" zainab ta fada tana basarwa,don batajin zata wani tsaya siyan turare bayan saleem ne yake siya musu,wanda yake siya dinma ita idan suka dameta kyautarsu takeyi,ko kuma idan tana da buqatar magani ayi ban gishiri na baka manda,ta bada su a bata magani hankalinta kwance "Aikodai ban makara ba,shi turare da kike gani shine mace ai,bari na bude miki su ko baki shirya ba kikaji qamshinsu saikin siya" "Allah fa ni bani siya,karma ki buden qamshinsu ya cikan ciki magani na gama sha yanxu" ta fada tana yamutsa fuska "Wayyo Allah ya baki lafiya,ko an gamu ne?" Na'ima ta fada tana dariya "In sha Allah kwanan nan za'a gamun dai" ta fadi tana dan washe fuska,don yanzu duniya kaf burinta shine ta samu cikin 'yan biyu maza kamar yadda ruqayya ta haifa,idan hakan ta kasance kuwa gida ya gama tabbata nata ne kaman yadda ta gama sakankacewa da hakan a baya. Ta danyi ciniki,wasu a dakin sundan sissiya,saidai ko kwatar wadanda suka siya maganin basu siyi turaren haka ba,wasu dai sun shanshana sun kuma yaba sun aje suna addu'ar Allah ya bada sa'a. "A'ah, aunty ruqayya?" Na'ima dake shirin barin dakin ta fadi don sai a sannan ta ganta "Hajiya na'ima inata miqo gaisuwa ai bakijini ba" ruqayyan ta fadi tana murmushi. Sauya akalarta tayi zuwa sashen da take zaune "Wallahi hankalin yayi gaba" ta fadi tana zama gabanta. "Bari kiga asararriya,duk gefen kama turaka babu ita,ta saki bishiya gaba daya ta kama ganye" zainab da dariya ke cinta ta fada tana tabo raliya. "An fara DJ" wata muryar mace data leqo ta fadi,take kuwa kamar ana jansu da majayi suka fara miqewa suna fita da kadan kadan,sai gashi dakin ba kowa daga ruqayya sai fatima dake canza kaya sai na'ima da batulu dake ninke kayan da fatiman ke cirewa. "Ga turare a siyawa yaaya saleem" na'ima ta fada tana murmushi. Murmushin itama ruqayya tayi "Ai dole na siya turaren nan,tun kina shigowa naji yamin qamshi" sosai na'ima taji dadi, ruqayyan nada wani irin karamci da bata taba iya kushe abinka. "Allah aunty?" "Allah,wancan da kika bani kyauta yamin dadi sosai,yanzu ma nake son dama na tambaya ko kinzo?" "Nazo anty ban shigo bane da wuri" na'ima ta fada tana fiddo mata da turarukan. Da gaske turarukan masu kyau ne sosai da tsananin qamshi,guda hudu manya ruqayya ta ware sai humra baqa da fara da kwalaccam sukayi total ta miqawa na'ima kudin. Tana ta qoqarin neman canji ruqayyan tace "A'ah ki riqe ki siyawa mutuniyata najma biscuit" "Har haka anty?,na gode sosai,Allah ya qara rufa asiri" "Ameen ba komai" (don Allah mu rage qanqamo,kowa baya banbararki ke ba'a morarki,motsi kadan kice dangin miji basasonki,sun tsaneki saboda Allah ya miki rufin asiri,ko miji yana wadataki,ba dole su tsaneki ba babu ihsani tsakaninki da kowa?,kowa idan abinsa ya taso saiki kama hannu ki rungume,kice sai ya baki zaki basu bayan kina da wadatar da ba lallai saishi ya baki ba?,karku manta,kyautatawa tana saka d'a ya zama bawa ba tare da ya sani ba,kyauta da ihsani tana saka soyayyarka a zuciyar mutane,Allah yasa mu dace)". "Ni anty wallahi banji dadin rashin siyan maganin nan ba,bakiga yadda su anty Zainab ke dariya ba da sukaga zaki siya turare" "Au haba?" Ruqayya ta fada tana dariya sanda take zuba turarukanta a babbar ledar da na'ima ta bata "Allah,dama sunata gulmar haka kike zaune sakaka,banda asirin ma da kikewa yaa saleem da tuni ya sakeki" "Hmmmm"batulu ta fadi kawai ba tare da tace komai ba,don itama abin yana bata takaici. Zainab ce 'yaruwarta,amma har ga Allah yadda takejin ruqayya a zuciyarta take kuma burgeta Zainab bata taba burgeta ba,tun zamanin 'yammatanci ma,saboda ko a sannn din Zainab din ta fiya rawar kai da zaqewa,ga shiga abinda shekarunta basu kai ace ta shiga din ba tun a lokacin. "Ashe ni ban cika mace ba amma ban sani ba,indai sai na siya irin wadannan tarkacen lallai ko bazan taba amsa sunan mace ba,Allah yasa kuma bakwa kwasar ire irensu " ta fadi tana duban idanunsu. Girgiza kai batulu tayi da sauri "Nikam bani da juriyar irin wannana abun ma,fruit kawai sun isheni" "Kefa?" Ta fada tana duban fatima. Dariya tayi a kunyace "To aunty mu duka duka yaushe muka shigo sabgar ma,haihuwar fari fa nayi yanzu" "To duk ku zauna" ta fada tana gyara zaman babyn dake kan cinyarta. Basu musa ba kuwa suka zauna din kowa yana bata hankalinsa "Fruit kadai basu wadatar dake ba batulu,haihuwarku uku,haka kema Fatima bazaiyiwu ki zauna haka ba,dukkanku don baku da kishiya ne shi yasa a yanzun ba zaku fahimci komai ba,saboda hankulanku a kwance suke,baku da maraba da mutumin dake dakin mamansa a kwance yana bacci" idanu suka zuba mata suna dubanta,sai ta saki murmushi tana gyada kai "Eh,a baya nayi tunani irin naku,bayan auro zainab naci gaba da rayuwata daga abincina sai fruit,sai a hankali na fara karantar canji daga wajen saleem. Ban rasa tsafta iya girki haquri ladabi da biyayya ba,hakanan bai taba muzantani da ki cusgunamin da gangan ba,amma a aikace ina lure da rawar qafar da yakeyi akan zainab,sai daga baya na gane cewa tabbas dukkan mace tana buqatar gyara,amma gyara wanne iri?,ingantaccen gyara da bai wuce qa'ida ko hankali ba,gyaran da ko meye zataci tasan me taci,kome zata sha tasan me tasha,Allah ya sakawa anty deeja da alkhairi,bazan taba mantawa da ita ba cikin babin rayuwata,itace mutum ta farko data fara dorani akan hanya. Ta tunasar dani hatta iyaye da kakanni suna amfani da magungunan gargajiya gurin gyaran diya mace,kamar bagaruwa,ganyan magarya da sauransu. Inno kakata ta gayamin,yadda muke samun qaruwa(yagewa) yayin haihuwa haka suma suna samu,amma saidai su basusan wani dinki ba,ana gyara mace ta koma fes da bagaruwa da sabulun salo ta hanyar tsarki da shiga ruwan bagaruwan. Na baku misali mana" "Muna jinki" suka fada a tare saboda yadda bayaninta ya fara musu dadi da tasiri "Zai yiwu ki siya mota ya zamana kullum kin hawa kina sabgoginki,ko engine generator kuna kunnashi kullum amma ba'a masa service?" Kai suka girgiza a tare alamun a'ah "Idan hakan ya kasance wataran ba za'a wayi gari ya tashi a aiki ko yana aikin dai amma lallabawa kawai akeyi ba baya bada abinda akeso?" "Tabbas" batulu ta fadi "To kamar haka yake a wajen mace,kiyi gyara saffa saffa da ingantattun itatuwa da abubuwa natural,karki tsaya a gyaran qasanki,ko ina na jikin mace yana buqatar kulawa da gyara,saidai kuma komai da zakiyi gyaran dashi ki tabbatar ingantacce ne. Shi kansa engine din idan aka yawaita yi masa service din da juyen mai haka ba gaira ba dalili ba tare da alamu sun nuna yana buqatar hakan ba me zai faru?" Kai batulu ta jijjiga "Gaskiya akwai matsala, za'a yita sakwarkwatashi ne ana raunata qarfinsa" "Wani notin ma idan aka kwance ba lallai a iya mayar dashi wajensa a daure,shikenan sai ya fara rawa,sanadin hakan sai wani gurin ya kuma saki" fatima ta qara dorawa "Yauwa,alhamdulillah,komai idan yayi yawa yana da illa ga jiki da lafiya,hatta natural ways din idan ka dauke 'ya'yan itatuwa da su basa yawa ga lafiya" "Gaskiya ne" batulu ta fada "Duk shan maganin matanki ko acan da ake hadawa saikin kiyaye wasu abubuwa sannan zasuyi tasiri,suma masu kyan ba daka ake shansu ba ai" "Kamar me da me?" Fatima ta fada tana komawa ta zauna "Yauwa,dole ki zama mai tsafta,babu ta yadda zaki tuttuli magani ki nemi kasancewa da me gida amma ko ina yakai hari sai a koroshi waje....." Bata qarasa ba suka sheqe da dariya su dukka biyun. D ido ta bisu tana son jin ba'asi,batulu ta yanke mata tunani "Kamar dai zainabunki?" "Banaso, ba'a gulmar 'yaruwata a gaba na" "Ita tayi taki ai,har ta taya a zageki" batulu ta fada tana tabe baki cikin jin takaicin sakarkarun halayen zainab. Murmushi ruqayya tayi "Taga zata iya ne" ta amsa a taqaice sannan ta dora "Abu na gaba ba yadda zakisha maganin mata baki da lafazin baki,ladabi biyayya haquri da juriyar zaman aure wanda sune jigon zaman ba wai maganin ba,shan magani kawai yana armasa auratayya ne da hanata ta gunduri abokin zama" "Gaskiya ne wannan,na yarda da haka" batulu ta fada tana jinjina kai "Sai kuma babban abun,mata ne ku ba kunyarku zanji ba........shan maganinki bazai taba miki amfani ba ba tare da kin iya sarrafa me gidanki a turaka ba,dole ki koyi salo da dabarun kasancewa da me gida sannan tasirin maganin zai fara aiki a jikinki,wannan dole ne,ba kuma kiyita gyara kanki shi bakya gyarashi ba indai akwai fahimtar juna da sauqin kai a tattare da shi" "Suma ana gyaransu kenan" fatima dake dan qunshe dariyar kunya ta fada "Eh,sosai ma" ruqayya ta fada tana kallonta "Kinga maggi?,kinga maggi?,yana bala'in taka muhimmiyar rawa wajen qarawa maza rauni,zaqi,maiqo,yawan yi musu ta'ammali da man gyada,shan sanyi,shan abubuwan da suke da sinadari caffeine da yawa a ciki,shan lemukan nan masu gas irin coca-cola da sauransu,ki yiwa miji natural drink kamar zobo,karkice zaki zuba tiara ko baby mix ko cola a ciki,ki dafashi natural da cocumber ginger cinnamon cardamom na'ana'a scent leave (daddoya) kanunfari da abarba,ki tace kisa masa sugar kadan yafi ki bashi wadan nan lemukan kaf dinsu,ku daina jibgawa mazanku magungunan qarfin maza,kashesu kawai kukeyi, za'a kai jallin da ba zasu iya tsinana komai ba muddin basusha wannan maganin ba,ke kanki idan kika ta'allaqa rayuwarki da shansu akwai matsala wataran zakiyi expire wallahi" dariya dukka ta basu,har itama suka saka ta dara(akwai hadin salad da na baku a last page,shima yana da matuqar muhimmanci wajen qarawa maza kuzari a turaka) "Eh mana,sanda kike da buqata kiyi service kiyi,service me ma'ana da hankali,ko meye na gyara zaki iya siyan kayayyakin a ganyensu ko asassaqensu guda ki dafawa kanki,idan ba zaki iya ba ki karba a gurin wadda kike da tabbaci a kanta hundred percent. ammafa kome zakisha indai ba zaki dinga ci kina qoshi ba akwai matsala, ba'a son ki dinga zama da yunwa,ko a abincinki ya zamana babu wani abu da zai qareki a lafiyar jikinki". "Amma matsi fa mata na sonshi Anty" murmushi ta kuma saki,mata da yawa sun halaka ta sanadiyyar matsi "Akwai natural ways shima" "A bamu anty" fatima ta fadi da sauri sai kuma kunya ta kamata. "Zaki samu sassaqen bagaruwa,kanunfari,bagaruwa sai magarya,ki tafasasu ki dinga shiga ciki idan ruwan ya huce,kunga duk a ciki meye me cutarwa?,meye wanda baku sanshi ba?" "Babu wallahi anty" fatima ta fada cikin gamsuwa "To kun gani,ku damu kanku da sabulun tsarki,bayan babu sabulun da yakai sabulun salo indai kin samu original din" "Gaskiya ne" batulu ta fadi "Allah yasa mu dace" ruqayya ta fada tana miqa batulu babyn "Zaki tashi muna qaruwa dake" murmushi ta saki "Muna gaisawa da hajiya na shigo banko zauna ba,kuma inason na leqa gidan umma binta,zan jira shukra zata kawomin su iftee zasu wuce gida dasu" "Anty kafin nayi arba'in zanzo gida na sameki don Allah a bani sauran sirrikan" "Saikinzo fatiti,kawai dafe dafen nama kala kala da zakiyiwa kanki,a baki da dadi a jiki da aiki ba wani sauran fargabar meye a ciki" cike da murna tace "Zanzo in sha Allah" "Qafarki qafata" batulu ta fada tana dariya "Duka sai kunzo" ruqayya ta fada tana murmushi. La'asar liqis ta baro gidan sunan tayi sallama dasu don ta qarasa gidan umma binta kamar yadda tace. Qanwace ga mahaifiyarta kuma a nan bayan layin gidansu fatiman take. Don haka cikin qasa da minti daya ma ta isa tunda a mota take. https://chat.whatsapp.com/EKyzZCUEGyRAEGGAnTHmGF *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 10 Hankali kwance cikin nutsuwar ta ta macen da tasan kanta ta tura kanta cikin gidan bakinta dauke da sallama. Sai da tayi sallama sau biyu kafin a amsa. Daga can cikin daya daga cikin dakunan dake hannun hagunka. "Da alama umma bata nan" ta fadi qasa qasa ta wucewa dakin da take jiyo ana amsa mata sallamar. Labulen ta dage tana sake jaddada sallamarta. Ido hudu sukayi da matashiyar dake zaune saman abun salla. Sanye take da hijab har qasa,baka ganin komai sai fuskarta da tayi wani haske dauuuu,irin hasken da kana masa kallon farko zaka san cewa ba natural haske bane. Hannunta da yanayin hasken fatarsa yasha banban da hasken fatar fuskarta na riqe da carbi tana ja daya bayan daya,bakinta yana motsawa mis mis da alamun wani abun take karantawa "Iskancin banza,ashe kina ciki kina jina naketa kwada sallama" ta fadi tana dan jifanta da harara hadi da zare takalminta ta shigo dakin gaba daya tana cewa "Yo wannan basai a shigo ayi muku sata bama?" Tayi maganar tana zama gefan kujerar guda daya dake dakin idonta akan matar. Hannunta ta dora saman bakinta alamar tayi shuru,sannan taci gaba da jan carbinta. Sasakai ruqayya tayi tana binta da kallo,sai kuma taja tsaki ta maida dubanta ga dakin. Kayan ado ne jere sama madubin,mayuka kala kala da turaruka,harda kwalabe da gwangwanayen supplement kala daban daban. Kan supplement din hankalinta yakai,ta miqa hannu daga inda take ta dauki wata zungureriyar kwalba dake dauke da syrup a ciki. Tun a rubutun farko ta fahimci maganin qara qiba ne,saita daga kai tana kallo fuskar matar dake zaune akan sallah. Tabbas,ta qara qiba qiba data jima tana mamakin ya akayi wasila siririya da ake tsokanarta da sunayen tsokana kala kala saboda rashin qiba lokaci guda tayi irin wanna qibar?. Mamaki ya hanata magana,saita mayar da kwalbar ta ajjiye dai dai sanda idonta ya gano mata wani tablet din dake nuna whitening yakeyi. Kai ta sake jinjinawa tana maido dubanta ga wasilar,dai dai nan ta shafa hannunta akan fuskarta da alama ta gama. "Ke kuwa me kika zauna yi har rana tana shirin faduwa bakiyi sallar la'asar ba?" "Haba ni da nake da tarin buqatu?,ta yaya zan bari sallar ta kufecemin? la'asar dinta liman yana sallamewa ina sallame tawa,wannan wani wuridi aka bani nakeyi" "Wuridi ko addu'a" "Duk daya ne ai" ta amsa mata tana ninke sallayarta "Addu'ar ce idan anayi ba'a amsa sallama?,nidai a iya sanina salla ce kawai ya haramta idan anayinta ayi magana" Ruqayya ta sake jifanta da tambayar "Ke wannan ba irin addu'ar da kika sani bace,wannan ta neman miji ce,yazo ayi aure nima na ganni a dakina na huta kamar kowacce mace" ta fadi tana zare hijabin jikinta t wurgar gefe,hakan ya sake bayyanawa ruqayya qibar da ta tsammata daga wasilar,saidai ashe hijabi ma ya rufe wani abun. Kasa shuru ruqayya tayi tana duban wasilan tace "Yanzu wasila wannan wacce irin qiba ce haka da uban fari da fuskarki tayi?,ga kunnenki duk kin bula kin cikashi da barima?" Gefen ruqayyan ta zauna tana daukar wayarta "Ba zaki gane bane,ke don kina dakinki asirinki a rufe,yanzun rayuwar sai da updating sai kina gyara,idon mazan a bude yake,saisu rainaka ko kiga wanda baikai ajinka ba yazo yace kai yakeso saboda rainin hankali" "Yanzu qibar da farinma kenan yayinsu akeyi" "Ke,qwarai kuwa,mace 'yar duma duma ai duniya ce,farar mace kuma itace alkyabbar mata,lantarkin gida,ajebo kalar hutu,sadakinsu ma daban yake,hakanan sunfi shiga" hangame baki tayi tana kallon yadda wasilan ke magana da confidence. Tare sukayi yammatanci da wasila,tunda can tana da surutu da rawar kai,amma yanxun kamar an qara mata da wasu sabbin halayen "Indai hakane kice mu da bamu samu mashinshini ba" "Da kenan,sanda kukayi aure ai duniya a kwance take,shekara bakwai zuwa takwas baya fa,kema ba yadda banyi ki goge baqar fatar nan ba kikaqi,ai gashinan kina zaune kina ji kina gani mijinki yaje ya dauko farar,wadda ma bata fiki komai ba" dariya wasilan ta bata yadda take nuna jin zafi da jin haushinta duk sanda akayi zancan zainab "Wai tsaya,kin manta bleaching haramunne?" "To ya za'a yi?,neman wanda zamu shige daga ciki kawai mukeyi?" "Tabdijan,wasila?,a haka?,kina abinda Allah bayaso amma ke kina neman ya dubeki?shaidanne fa yayi alqawari da kansa Allah ya fada mana cikin suratun nisa'i aya ta dari da sha tara,cikin alqawarin da yayi yace zan sanyasu su dinga canza halittar Allah,cikin canza halittar Allah wadan nan abubuwan suna daga cikinsu,kisha magani ki qara qiba,kisha magani don ki sirance bayan qibar ba matsala take kawowa ga lafiyarki ba,ki shafa mai kiyi haske ko ki shafa mai don kiyi baqi duk da mu an jarabci mutanenmu da son suyi haske ne kawai,duk da ana samu cikin turawa da yahudawa masu maida fatarsu baqaqe,duk me ya kaiki wannan wasila?" "Ina zuwa" ta fadi tana dagawa ruqayya hannu sakamakon kiran da ya shigo wayarta. Da kallo ruqayya ke binta da shi har ta gama amsa wayar tana gatsine gatsine hadi da amsa maganarsa da qyar. Wayar ta wulla gefe tana jan siririn tsaki "Sirikin namu ne?" Ta tambayeta tana ciro tata wayar daga jaka ta kirayi shukra taji yaushe zasu iso "Wa?,Allah ya kiyaye,sulaiman ne fa" tsayawa ruqayya tayi da abinda takeyi tana duban wasila cike da mamaki "Sulaiman dinne abun Allah ya kiyaye?,badai sulaiman wanda yazo duba umma sanda aka kwantar da ita a asibiti ba" "Shine,amma ke kinga mijin aure a nan?" Ta jefawa ruqayya tambayar tana kallonta "Ni kuwa naga mijin aure nagartacce ma,me sulaiman ya rasa?" Baki wasila ta tabe tana jawo carbinta ta saka a yatsarta ta fara ja tana cewa "Abubuwa da yawa mana,haba ruqayya kamar makauniya?,yana da rufin asirinsa yana da hali me kyau,amma gaskiya kamar bai qarasa irin mijin da nakeson aure ba" Mamaki ya qarasa kashe ruqayya "Amma yanzu bake na samu kina wasu wuridai ba duk akan Allah ya kawo miki miji kiyi aure ki huta ba?" "Eh amma mijin ai ba kowanne iri ba,irin sulaiman ina dasu sun kusa hudu,amma wanda yadanfi hakan rufin asiri nake nema,bance saimai shahararren kudi ba,amma ina laifin miji kamar naki saleem din,ke ba motar hawa gareki ba yanzu ke da kishiyarki?" Kasa cewa komai ruqayya tayi mamaki yana ci gaba da kamata "Kuma ma dazu dazu na dawo daga gurin wani bawan Allah,yayimin istihara ya gayamin aure na da isma'il babu alkhairi a cikinsa sam sam,mijina yana nan zuwa,dan kasuwa ne a kantin kwari,kinga kuwa ta yaya zan tsaya ina dagawa kaina hankali akan wanda nasan ba mijina bane" "Shi din Allah ne da har zai fadi abu ki yarda?" "Amma istihara ai ba qarya bace" "Wacce irin istihara yayi miki?" "Normal istihara da aka saba,carbi ya ajjiyemin yace na zabi daya,da na dauka na miqa masa ya karba na wasu mintuna sai yayi min bayani,babu qasa a wajen bare dai kice min duba ne" wasila ta fadi cikin gamsuwarta da abun. Cike da takaici ruqayya ke girgiza kai tana duban wasila "Wai duk yawon islamiyyar da muka dinga yi ina naki karatun yayi wasila?,dama haka annabi ya koyar da istihara?,suna fakewa da duba suna canza masa suna da istihara?,wallahi sai sunyi shari'a da annabi,ba wani wanda zai maka istikhara kai zakayi abarka da kanka,bayan kinyi sallar raka'a biyu zaki karanta *_Allahumma inni astakhiruka bi'ilmika,wa'astaqdiruka bi qudratika,wa'as'aluka min fadlil azeem,fa'innaka taqdiru wala'aqdir,wa ta'alam wala a'alam,wa'anta allamul guyub,Allahumma in kunta ta'alam anna hazal amra(saiki fadi buqatarki)kairul lee,fi diny wamu'ashy wa'aqibatu amry,fayassirhu ly summa barikhly ly fihi,wa'inkunta ta'alam anna hazal amra(saiki fadin abun),sharrully fi diny wamu'ashy wa'aqibatu amry fasrifhu anni,wasrifny anhu,waqduriliyal khairu haisu khana,summa ardini bihi) annabi yace ba wanda ya taba istikhara irin wannan bayan yaji ya gamsu da abun ya zartar da shi,daga baya kuma abun ya zame masa nadama,idan kayita kayi shawara da mutane nagartattu guda biyu akansa sannan ka zartar" . Kai wasila ta kawar tadan mele baki sannan ta dawo da dubanta ga ruqayya "Na gode da tunasarwa,amma na jima ina yin wannan ai,sannan shi kansa abinda ke faruwa jifana akayi,mutum kusan biyar suna gayamin asirin akayimin don kada na auru,ina da magauta da yawa da maqiya,duk wanda naje gurinsa cewa yakeyi a gaba aka sakoni" "Babu wanda yasan gaibu sai Allah,amma asiri gaskiya ne yana kuma iya kama mutum,saidai bisa amincewar Allah ne,ba wanda ya isa ya cutar dakai sai Allah yaga dama,akwai kuma ayoyi daga alqur'ani da tsafatattun hanyoyin warware sihiri da kuma kare kai daga sake kamuwa dashi,kamar cikin suratul a'araf......" "Duk fa inayinsu amma.....hmmmm" sarai ruqayya ta fahimci me takeson cewa,sai ta gyara zama "Eh bata karbu ba kikeson cewa?,ko kin dade kinayi ba nasara ko?,to bari kiji wani abu da baki sani ba,ita kanta addu'a tana da qa'idojin yinta da amsata.....indai zakiji a ranki addu'arki bata karbu ba to kin wargazata,indai zakiyi......" "Kinga rubutamin addu'o'in saina hada dasu" ta fada tana zaro biro da memo ta miqa mata,sannan ta miqe tana fidda kayan jikinta. "An kusa kiran sallah,akwai hayaqin da zanyi kada lokaci ya wuce,ina zuwa" ta fada tana daura zanin fallen atamfa tana fita a gaggauce daga dakin. Da kallo kawai ruqayya ta bita dashi,saita girgiza kanta takaici yana kamata,cikin qasa da minti biyu qaurin hayaqi ya risketa a nan inda ta barta a zaune. *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 11 https://www.mkdatasarvices.com.ng *MK DATA SERVICES* _ake magana_👇🏽👇🏽👇🏽 *_INA MASU SARIN DATA,BIYAN BILL KO SUBSCRIPTION KO MASU SIYAN DATA DIN MA KADAI DON AMFANIN KANSU?_* *_TO KU MARMATSO KU BANKI ARON HANKULANKU DON KADA AYI BABU KU!!_* *_GA WANI SASSAUQAN WEBSITE DON SIYEN DATA CIKIN FARASHI ME SAUQI DA RANGWAME_* https://www.mkdatasarvices.com.ng _Ga me neman qarin bayani ko magana dasu kai tsaye sai ya tuntubesu ta wannan number wayar_ 08038258489 *ARAHA SAUQI DA RANGWAME KAMAR AN BAKA A KYAUTA*🫰🏾🫰🏾 Tana saka kanta a tsakar gidan umma tayi sallama "A'ah,baqi mukayi?" Umman ta fada cikin fara'a. Tun asali ita din macace me kirki da qoqarin zumunci,saidai ubangiji ya jarabceta da dabi'ar son 'ya'ya. Irin matan nan ne da basa iya boye soyayyar yaransu,wannan ya sanya abubuwa da yawa da yaran zasu aikata ba kasafai suke iya tsawatar musu akai ko su hanasu ba. "Sannu da zuwa umma" ruqayya ta fada tana murmushi,a ranta tana jin dadi me yiwuwa umman yanzu data shigo ta taras da uban qauri hayaqin turaren ta yiwa wasila fada,iya zallar qaurin ta isa ta sanya ka samu matsala idan kana da cutar asma "Tun yaushe kika zo?,munyi sabani naje barka 'yar hannatu ce ta haihu" ruqayya na qaramar dariya taja kujerar 'yar tsugunno ta zauna kusa da umma da ita ta zauna saman kujerar bayan ta fidda mayafinta ta rataye jikin igiya "Ahhhh,umma hannatu ce yanzu da jika?,lallai rayuwa tana gudu" "Uhmm,kedai bari kawai,shi yasa yanzu gaba daya hankalina ha koma kan 'yar uwarku,ta samu itama tabar gidan nan,kada na mutu banga aurenta ba" umman ta fada cikin karyewar murya. Gyara zamanta ruqayya tayi "Umma kada ki damu,muddin kina mata addu'a akwai lokaci shi aure kaman haihuwa yake muddin yazo sai anyishi ba abinda zai canza,lokacinta ne kawai itama baiyi ba" baki umman tadan tabe kadan fuskarta fal alhini "Uhmmm,mutanene yanzu sun zama abinda suka zama,baka takawa mutum ba baka barar masa ba amma sai ya saka ka a gaba sai yaga bayanka,nidai tunda nake ban tana jifan dan wani da ko Allah wadai ba,amma ni tawa diyar ita kenam qwaya daya an hanata ta motsa" cira kai ruqayya tayi tana kallon umman,alamu dukka sun nuna itama ta yarda da cewa jifa aka yiwa wasila,itama nata idanun sun rufe da tarin kura kurai da dabi'u da ya kamata wasilan ta fara gyarawa saboda ta samu tsakaninta da ubangijinta yayi kyau ta yadda addu'arta zatafi shiga. Sau tari mune sila na rashin karbuwar addu'o'inmu,amma saimu danganta sanadin ga wani ko wata. "Don Allah umma kada ki saka wannan a ranki,hadisi ne guda daga ma'aiki cewa,idan da dukka mutanen duniya zasu taru don su cutar da kai,ba zasu iya cutar da kai ba sai abinda Allah ya rubuta a gareka,hakanan idan da dukkansu zasu taru don su amfanar da kai basu isa su amfanar da kai ba sai abinda Allah ya rubuta a gareka zai sameka" "Uhmm,kedai Allah ya rufa asiri kawai,ina kishiyar tawa da masu gidan nawa?" Kamar jira suke umman tayi tambayar sai ga sallamarsu,suna gaba yusra na bayansu. Da gudu suka qarasa shigowa kamar wadanda suka shekara basu ga mamar tasu ba. A jikinta suka zube iftee ta haye cinyarta "Ku dagani hakanan ku gaida umma" ruqayya ta fada bayan duk sun gama ifce ifcen. Daya bayan suka durqusa suka gaidata har ifteehal da take qarama. Umman ta amsa tana shafa kawunansu sannan tace "Allah ya nuna mana yaran wasila haka,da tuni itama nata yaran sunkai haka" "Lokaci dai umma" ruqayya ta fada tana wucewa bakin famfo don yin alwala. Tana fitowa ta ji umman na magana da waseelar,waseelan tana sake mata bayanin abinda malamin ya gaya mata "Wallahi umma da kin barni na tambayeshi,ya gayamin su waye da waye,na rantse da Allah duk randa aurena ya tashi kaf sai na tambayi sunansu,sai naci(ta dura ashar),kuma wallahi wallahi ba wanda zai moreni,ba wanda zaici arziqina,kada ma daga baya kice ai ya wuce na yiwa wance kaza na yiwa wance kaza,arziqin mijina nawa ne saike sai 'ya'yana da wanda naga dama" ta fada tana shanye ragowar rubutun dake cikin leda ta jefa ledar cikin kurfetunsu na girki "Ki barsu da mugun nufinsu,duk wanda yayi na gari kansa ai ko?". Sake cika da mamaki ruqayya tayi,gaba daya wasilan ta sake canzawa,duk wasu halaye da ruqayya tasan wasila dasu ta ninko wasu a kai wasu kima ta sauyasu gaba daya. Tana salla amma mamaki ya gaza barin kanta,ita wasila dake wannan zancan har ma tasan me kudi zata aura kenan da take zancan ba wanda zaici arziqinta. Kafin ta gama sallar wasila ta shigo dakin,ta nade saman katifarta tanata amsa waya,ko muryarta ma ba'a ji iya ji sosai saboda tsabar sanabe da langwashe murya. Waiwayawa kadan tayi ta kalleta sai kuma ta dauke kai tana ci gaba da lazuminta tana sauraron kusur kusur din wasila saboda bata iya jin muryarta sosai. A gaban umma ta fara wayar,sai daga bisani ta tashi,tana mamakin yadda take iya zance tsaf da saurayi a waya a gaban umman ko yayyenta,ba tun yau ba ta saba hakan dabi'arta ce. Dai dai sanda ta shafa addu'a wasilan ta saki siririyar qara "Da gaske don Allah?.....wow......bari na shirya" ta fadi tana katse wayar gami da saukowa daga katifar "Ki tayani murna 'yar uwa, iphon 13promax yanzun nan za'a kawomin ita" wasila ta fadi tana bude wardrobe dinta tana zubo da kayan ciki qasa. "Toooo.......isma'il dinne?" Waiwayowa wasila tayi ta zabga mata harara "A'ah sulaiman ba isma'il ba,kina da abun haushi wallahi.....wannan wani guy ne irin type dina wallahi" ajjiye carbin hannunta ruqayya tayi ta tallafe habarta "A'ah,amma yanzu kk ce baki samu wanda kikeso ba ko saboda jifanki akeyi" rigar atamfar ta zaro ta dawo gefan gadon ta zauna tana kallon ruqayya "Inason mutumin nan ruqayya,amma na masa maganar ya fito yakai sau goma har yanzu shuru,malamai biyu sun gayamin jifan da akeyimin ne yake hanashi turowa,shima yana shafarsa" kai tadan gyada "Kuma kin tabbatar yana sonki kema?" "Sosai,ke kinga hidimar da yakeyimin ne?,kuma inda baya sona ai da tuni ya tafi,wata nawa muna tare,munfi shekara fa". Shuru ta sakeyi tana nazari,duk da ita da wasilan tamkar ciki daya suka fito haka suka tashi,kuma ko yanzun dukansu suna iya yiwa juna katsalandan akan abinda ya shafi rayuwar daya,saidai zuciya da kuma shaidan batasan ta fiya challenging wasilan. "Au,bari na gayawa umma ta tura wani yaron ma ya siyo masa lemo" wasila ta fadi tana fita da sauri a dakin. Minti daya kacal ta soma jin muryar umman tana magana "Bazaiyiwu ba,tunda kinsan ko kin karba Bashir sai ya saka an maida masa,bayan uban fadan dazai hada ni dake yayi mana" "Don Allah umma ki manta da yaa Bashir,shi wallahi ya fiya tsanani,waini qaramar yarinya ce da zatayi abinda bai kamata ba?,nasan fa abinda nakeyi da hankalina,waya me tsada kamar wannan ina gani umma kice kada a kawo?, gaskiya kiyi haquri umma,yaa bashir dai tunda ba'a gidan nan yake ba sai naso ma zaisan wacce irin wayace a hannu na". "Nidai ba ruwana na gaya miki" "Haba umma,haba umma" wasila ta fadi tana buga qafarta,sannan kuma rai a bace ta dawo dakin. "Wasila" ruqayya ta kira sunanta "Inajinki" ta amsa mata tana zama gefan gadon "Abinda ya bashir fa yayi dai dai ne,sannan dadewa da saurayi da kuma yi miki hidima ba shine tabbacin ingancin halaye da dabu'unsa ba,hakanan ba shine tabbacin yana sonki ba,babu soyayyar data wuce mutum ya aiko gidanku ayi maganar aure tsakaninki da shi" "To amma meye hadin waccar matsalar da wannan,kawai sai ace kyautar wayar ma ba za'a karba ba,komai an maka izini kamar dan qaramin yaro?" "Kudin iphone 13ya isa fa ya kawo kudin aurenki harda sadaki fa wasila,mutuncinki suke kare miki" juyawa tayi kawai ta kwanta rub da ciki ba tare data sake cewa da ruqayya komai ba,sai qananun gunaguni data ci gaba da yi,kana ta jawo wayarta tahau yin waya. Tata wayarce itama tahau tsuwwa,koda ta duba sai taga saleem ne. A nutse ta daga tana daidaita muryarta tamkar budurwar da zatayi magana da saurayinta da suke sharafin ganiyar soyayya "Habibee,hala munyi dare ko?,ayi mana afuwa umma dince ban samu ba sai dana jirata" "Kada ki dami habibtee,nima ina komawa na fito,zan qaraso saimu dawo tare,da motarki kika fita?" "Eh da ita ne" "To sai na qaraso" "Allah ya kawomin kai lafiya" "Ameen habibtee" ya amsa mata. Ajiye wayar tayi tana fita gurin umma,ta sameta tsakiyar su iftee ta sakasu a gaba suna cin alkubus da miyar ganye,sunata zuba mata surutu tana biye musu. Sake gaisawa sukayi a nutse sannan suka shiga hirar duniya wadda kusan duka ta zumunci ne. Akwai zumunci sosai tsakanin mahaifiyar ruqayya da umman data kasance qanwa ga mahaifiyar ruqayya. Suna tsaka da hira kiran saleem din ya shigo wayarta, saita duba tana cewa da alhassan "Duba ko abbanku ne a waje,yace zai qaraso mu wuce gida tare" "Asshsha,kya barshi a waje,jeki shigo dashi mana"umman ta fadi,sai ruqayyan ta miqe ta fice. Tare suka shigo tana zolayarsa,yayi kyau cikin yadin voyel fari qal yana zuba qamshi "Kodai kodai anya kuwa?" Murmushi ne ma ya qwace mishi,ita ta tafi dashi saboda daurin data lanqwasa kanta,fararen idanunta kuma sun fito tarwai a hasken qwan lantarkin da ya haske gidan gaba daya amma ita tsokanarsa take qoqarin yi "Kodai me?" "Zance kaje ka biyo ta nan" ta fadi tana qaramar dariya me jan hankali saboda sautin da take bayarwa ma daban yake. Hakanan ita kanta ta saba,idan tana tare da saleem komai nata yakan canza,takan rikide daga ainihin ruqayyanta zuwa habibtee dinsa. Sosai umma ta tarbeshi,don kafin su iso ma ta masa shimfidar dadduma. Hira sukayi kadaran kadaham,don yafi sakewa da ita ma akan maama mahaifiyar ruqayya. Wasila ta saka ta zubo masa alkubus,amna kuma baici ba yace ya qoshi,don ba kasafai yakecin abinci a wani guri ba muddin girkin ruqayya ne. Ko kadan bayason yayi missing girkinta,gurin hajiya mahaifiyarsa kawai yake iya karbar abinci yaci indai tayi masa tayi ranar girkin ruqayyan. Koda zasu tafi umman ta juye masa abincin "Ku tafi dashi ruqaiya" umman ta fadi. A gurguje ruqayya ta leqa don yiwa wasila da bata sake ganin gilmawarta ba sallama,saidai bata cikin dakin,bata kawo komai ranta ba ta fita suka wuce. *HUGUMA*👑 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 12 Hannu ga miqa mata zai karba key din,sai ta langabe kai tana dubansa qasa qasa "Ranka ya dade yi zamanka kawai ka huta,yau ni zan tuqaka,nasan daka koma gida baka kai ga zama ba ka sake fitowa" shima nasa kan ya karyar "Allah ya taimakeki ayi haka?" Girarta ta dage duka biyun "Me zai hana?" "Lallai na cika dan gata" ya fada yana murmushi. A nutse take tuqin yana daga gefanta,har cikin jikinsa yakejin bambancin komai da komai ma tsakaninta da zainab. Ya taba zama irin haka yace Zainab ta tuqasu,budar bakinta sai tace "Tabdijan,kamar wata driver?,wannan ai aikinka ne" ta jefa masa key din,abinda ya jawo ya bata mata rai kenan shima. Yana da sauqin kai yana da daukar wasu abubuwan da yawan maza suke kallonshi a mazaunin raini,amma shi sam bai dauki hakan a bakin komai ba,saidai abu guda da baya iya dauka shine,ki kawo masa raini ko maganar banza ko ta rashin girmamawa gaban 'ya'yansa ko yaran da suke aiki qarqashinsa ko qannensa. Dabi'un Zainab wasu irin dabi'u ne masu daure kai da ban mamaki. Ya jima yana mamakin halayenta,saboda shi ko kadan ba haka ya saba gani ba daga wajen ruqayya. Bazai iya cewa ga wata rana guda daya da ta gaya masa magana gatsau kwatankwacin ta Zainab ba. Tsahon shekarun da suka dauka da zainab din duk wani abu da ya kamata yayi don gyara bakinta yanayin mu'amala da tsaftarta yayi amma a banza. Sau tari hajiyarsa ke haqurqurtar dashi daga kawo wasu qorafe qorafen,a danneshi duk da sunan 'yaruwarsa ce yayi haquri. Bai taba kawowa auren zumunci da nasa illolin ba sai yanzu. Wasu lokutan yakan tambayi kansa da kansa. Shin wai me yasa yayi gaggawar qara aure?,da ya tashi qara auren kuma me yasa ya auri Zainab?. Duk sanda yayi wannan tunanin sai yayi istigfari,don ya tabbatar Rabon haneefa da khaleel dake jikinta nasa ne,kuma dole sai ta haifa masa Kota halin qaqa. Farkon aurensu ya dauka zata daina zata kuma gyara,amma zuwa yanzu ya riga yayi giving up,saidai bazai gaji ba bazai kuma daina saitata ba,hakanan bazai iya jurar wasu abubuwan nata ba. Hira sukeyi mai dadi da armashi tsakanin shi da ita da yaran. Irin hirar da yayi tsammanin daga sanda ya kawo zainab din gidan ta gushe a tsakaninsu,saidai a'ah hakan bata faru ba,duk da akwai abubuwa da yawa da har yanzun tunda ruqayyan ta ajesu a gefe tsakaninta da shi bata dawo dasu ba. Abubuwa ne masu yawa da yayi missing dinsu sosai,ya kuma saba da su,bai kuma taba zaton zata daina ba. Duk da bata cusguna masa ko hanashi qara aurensa ba,amma hakan sai yake ganin kamar wani horo tayi masa me kama da turin mutuwa,kuma har yau har gobe idan ya dauko zancan ta daina kaza bata taba bari suyi maganar da shi. A wani suya spot yace ta tsaida motar,ya buda murfin yana kallonta yana cewa "Bari na siyo tashi watstsake" kunya ta kamata,saita kawar da kanta gefe tana murmushi. Hannu ya miqa ya mintsina gefen cinyarta kadan yadda ba zataji zafi ba yace "Kin ajemin saqo ne ai,kuma saqon ya isa inda ya kamata yaje...." "Please su alhassan fa" ta fada tana kare fuskarta da hanun nata,sai ya qara girgiza kai ya buda murfin motar yana ficewa. Waiwayawa tayi ta yiwa su alhassan daketa hayaniya maganar su rage hayaniyar tayi yawa,juyowar da zatayi kamar ance mata kalli gefenki. Kyakkyawan gani ta yiwa wasila zaune cikin farar motar dake daura da su. Tana zaune a gaban motar ta bada dukka attention dinta ga matashin saurayin dake zaune mazaunin driver shima yana dubanta. Chiffon gown ce a jikinta sai yalolon mayafin da ya dace da material din,kanta ba hula ba dankwali kana iya ganin gaban gashinta. Wani malolon abune ya taso ya tokare mata wuya,duk yadda taso ta hana kanta fita amma hakan ya gagara,saita waiwayo ta kallo alhassan "Kada ku fito ina zuwa" ta cire key din motar ta fita tana dosar motar. Daga baya baya ta tsaya tayi musu knocking,dukka su biyun suka leqo ita da saurayin,saidai kuma kamar yadda taso wasilar ce ta ganta sosai. Sosai fuskarta ta nuna mamakin ganin ruqayya da dan shock kadan,amma saita daure ta bude murfin motar ta fito "Ya na ganki a nan?" Wasilan ta tambaya "Ke za'a yiwa wannan tambayar ai wasila,umma tasan da fitowarki?" "A'ah don ba jimawa zanyi ba" haushi da takaici suka cika zuciyar ruqayya. Ranta idan yayi dubu ya baci "Yanzu don girman Allah hakan mutunci da martabar ahalinmu kika siya mana ko sarayarwa kikayi?" Ta mata tambayar hannunta goye a qirjinta. Hannu wasilan ta yarfar tana dan buga qafa "Kin cika matsala wallahi ruqayya,yanzun wani abun kikaga inayi?,kun hanani karbar waya na haqura,yanzu 'yar pizza da shawarma din ma da zan karba sai ace a'ah don me?" "Idan yaa Bashir ya ganki kuma kice masa me?" Ta tambayeta tana ritsata da idanu "Yayi miki fada kice an matsa miki ko?" "yanxu yanzu zan koma,don ma sun jima wanda muka saka order din wajensa bai kawo ba da bazaki sameni a nan ba bare akai ga yaa bashir" kai ruqayya ta jinjina cikin zafin rai,dai dai sanda saurayin ya leqo yana cewa "Baby zo mu wuce gashi an kawo" wani kallon bamza ruqayya ta watsa masa,sannan taja hannun wasila kai tsaye ba tare data tsaya saurarenta ba ta wuce mota da ita. Kaman qaramar yarinya ta bude mata seat din baya ta turata,itama ta koma mazauninta ta balbaleta da masifa. Tun wasilan na kare kanta har ta kasa cewa komai sai shuru da tayi tana bin ruqayyan da kallo "A irin wannan abun kinsan 'yan mata nawa ne suka rasa budurcinsu?,kinsan yammata nawa aka yiwa ciki wasu suka haihu?,kinsan cewa daga zarar kin daga qafa kin shiga motar saurayi baki da guarantee akaran kanki dama abinda zai sameki?,kuma ko meye ya sameki ke kika rattaba hannu akan hakan" "ki daina wannan batun mana haba,nace na daina" "Kindai fada yanzu,kuma tabbas kinsan maso abinka ai ya fika dabara ko?" "Don Allah mana ruqayya" inda taga wasila na kalla ta maida hankalinta,sai taga saleem ke tahowa,alamu suna nuna batason yaji zancan "Saina gaya masa ai kima daina wani boye boye" "Ki rufan asiri karku cinyeni,ki barni na dan karbo pizza din mana na saka rai" "Ko mayya ce ke saidai ki mutu" ruqayya ta fada tana tayar da motar kafin saleem ya qaraso ya bude ya shige. Baice komai ba sanda tace zasu aje wasila gida duk da yasan ba tare suka fito ba,mutum ne shi da ba akan komai yake magana ba musamman akan lamuran ruqayya,ya sani duk da dan adam ajizi ne amma komai tana yinsa ne bisa doron hankali da sanin abinda ya kamata. Sai da suka sauketa ta dauki tata ledar da saleem ya bata ta miqa wasilan taja motar suka wuce. *_ZAINAB_* Tunda ta isa gida ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda wani mugun kartawa da cikinta yakeyi. A iya tunaninta a gidan sunan yau duka bata ma wani ci cikakken abinci ba,saboda batason cikinta yayi cushewar da magungunanta zasu kasa samun matsugunni a cikinta. Duk da kartawar cikinta amma hakan bai hanata dage labule lokaci lokaci ba tana hangen gurbin da ruqayya kan aje motarta,har yanzu bata dawo ba,kuma yaran sun gaya mata ga abbansu can ya fita sanda suke shigowa gidan a tata motar. Koda ba ranar girkinta bane ta tsani taga saleem din sun fita da ruqayya,takanji zuciyarta kamar zata faso qirjinta. Tasha gwada su fita din itama dashi amma sai ya noqe ko ya kawo uzurin rashin kudin yanzun sai yace sai wani lokacin "Amma inda ruqayya ce ba wanda zaiji bari ya gani,saidai mutum kawai yaga ka shigo yi masa sallama,kuma lokacin da nake waje ai baka taba kawomin uzuri ba idan na buqaci mu fita,sai yanzun da ka gama cin moriyar ganga ko?" A lokacin tashi yayi sosai yana dubanta. Harshenta kullum a tsaye yake carrr kamar wadda ak yiwa gorin harshe. Yana mamakin tarin rashin hankali irin na Zainab din,a lokacin da take maganar kudade masu yawa ya kashe a ranar ya gyaro mata wayarta data barwa yara suka jefata a ruwa,ko awanni biyu ba'a cika ba amma take wannan qorafin "Itama duk sanda kikaga mun fita din cikin ribar business dinta ne,kinga baki da bakin yin qorafi,tunda dai tare na raba muku jarin nan,amma naki har yau bansan ina yake ba,bansan kuma taqamaimen abinda kikayi dashi ba" fuskarta ta bata sosai. Tayi mugu mugun tsanar ayi mata zancan ruqayya bare jarin da tamkar bakin wuta aka bata. Duk da tasan ina ta zuba kudin suka narke,amma baqincikinta yadda ta saka rai kudin zasu jawo ninkinsu amma sai abun ya tabarbare mata kudin yabi ruwa. "Ni ina ruwana da wani business dinta?,nidai abinda na sani kawai cikin gidan nan sam ba'a kwata adalci ba,inda kasan ba zaka iya ba da barina kayi gaban iyayena baka nuna duk duniya babu yani ka tattagoni ka kawoni gidanka ka hadani da makirar matarka me shegiyar kissa da kisisina wadda babu Allah a ranta" daga wannan maganar ta miqe ta fice daga bedroom din nasa, ficewar da bata sake dawowa ba sai da safe. Ko kadan bai wani damu ba,bajewa yayi abinsa yayi kwanciyarsa. Don a ranar dama tuwo tayi musu,miyar ta cika daddawa har tayi baqi warinta yayi yawa. Da zanin data gama madaqalar tuwon dashi ta shigo masa bedroom,ba niyyar wanka bare brush. Tunda ya kwanta bai tashi ba sai da safe,kullum dai baya gajiya da mamakin yadda kishi ke rufe idanun zainab din ta gaza koyi da abinda zai amfaneta. Horn din motar da taji ya sanyata miqewa daga kujerar da ta tattakure,zanin atamfar jikinta ne tayi daurin qirji dashi sai dankwalin data daure kanta shima dashi. Ko kadan bata damu da kayan jikinta masu tsada bane,idan ta dawo unguwa ta nema masu sauqin ta saka ba, hakanan zata wayi gari dasu taci gaba da sabgoginta,ita da cire zanin har sai ita a karan kanta ta tabbatar yayi dauda yadda ya kamata. "Umma ni bana hangowa" khalil da yabi ta qasan uwar ya fada yana tura kai jikin window din da zainab ta yaye labulen tana son ganin tare da waye ruqayya ta dawo?. Daidai sannan cikinta ya sake kartawa tasa hannu ya dafe amma duk da haka taqi gusawa daga wajen sai taga abinda takeson ganin. *HUGUMA*👑 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 13 https://www.mkdatasarvices.com.ng *MK DATA SERVICES* _ake magana_👇🏽👇🏽👇🏽 *_INA MASU SARIN DATA,BIYAN BILL KO SUBSCRIPTION KO MASU SIYAN DATA DIN MA KADAI DON AMFANIN KANSU?_* *_TO KU MARMATSO KU BANKI ARON HANKULANKU DON KADA AYI BABU KU!!_* *_GA WANI SASSAUQAN WEBSITE DON SIYEN DATA CIKIN FARASHI ME SAUQI DA RANGWAME_* https://www.mkdatasarvices.com.ng _Ga me neman qarin bayani ko magana dasu kai tsaye sai ya tuntubesu ta wannan number wayar_ 08038258489 *ARAHA SAUQI DA RANGWAME KAMAR AN BAKA A KYAUTA*🫰🏾🫰🏾 Sam ba wanda yama lura da tsaiwarta a gurin,don hidimar gabansu kawai sukeyi. Su alhassan suka fara fitowa sai ta miqa musu iftee tace suyi gaba ta duqa ta dauko musu sauran ledojinsu tunda ita ta bada tata tayi gaba tana cewa "Sai ka taho" saboda tasan zai fara da shiga sassan zainab ne. Labulen ta saka tana jan qwafa bayan ta gama irga ledojin hannun ruqayyan sannan ya nufo nata sashen,zamewa tayi ta zauna kan kujerar tana jiran shigowarsa ta kuma ga da me ya shigo matan. Da sallama ya shigo sashen,khalil dake tsaye har yanzu saman kujerar ya diro ya nufoshi da gudu yana kiran "Daddy" daukansa yayi ya daga sama yana dubansa "Ya rigarka yake a jiqe?" Ya tambayeshi yana tattaba gaban rigar "Lemo nasha" "Oya jeka cireta ka canza wata" ya fada yana ajjiyeshi. "Baki iya sannu da zuwa ba?" Ya fada yana saka hannunsa daya a aljihun rigarsa yana duban haneefa dake tattaba ledar da ya shigo da ita. Magana yayi me harshen damo,ya aika saqonne har zuwa ga Zainab wadda banda sallamar da ta amsa da qyar bata ko sake kallonsa ba "Au sannu da zuwa daddy" "Yauwa,daga yau kada ki bari na sake tuna miki,be a good girl hanee" "To daddy" miqa musu ledar hannun nasa kawai yayi,suka karba suka kici kicin budewa. Kasa daurewa tayi don ta tabbatar suka bude din saisun cinye abinda ke ciki,tadan ciza lebanta tana cewa "Kuka bude sai kunci ubanku,kun koma kamar agololin gida,sai a wuce da leda biyu uku ku sai a baku daya" sosai ransa ya baci,don zagin baiyi kama da yaran takewa shi ba "Ku dauka ka tafi dakinku dashi naku ne" ya fada yana kallon yaran. Da farincikinsu suka miqe suka cilla dakin nasu kuwa. Maida dubansa yayi kanta idanunsa suna nuna bacin ran dake kan fuskarsa "Daga yau ya zama rana ta qarshe da zaki zagarmin yara a gabana,duk randa kuma kika kuskura kika sake aikata hakan to ki kuka da kanki" yayi maganar yana nunata da yatsa. "A'ah wallah,na me?,bayan kun gama cin amanar tawa ka zagaye kaje ka daukota saboda ita bada qafafun yin tuqi ta dawo gida shine ni kuma yanzu zaka sauke a kaina?,bashi yiwuwa" ta fada tana miqewa,saidai kuma dole ta duqa saboda wani azababben gudawa da taji yana taruwa waje daya a cikinta. "Anci amanar taki,kema idan kin iya kici tamu" ya bata amsar a zafafe yana motsawa don barin gurin. Idanunta dake rufe ta bude ta bishi da kallo,wani abu ya tsaya mata a maqoshi,bataso maganar nan ta tsaya iya haka saboda takai maqura da abinda akeyi mata,rashin adalcinsa a kanta ya fara isarta,yanzun inda ranar girkinta ne yaje yiwa ruqayyan sallama yana iya kwashe minti talatin bai fito ba,amma ita gashinan ko zama baikai ga yi ba "Wanda ya cuci wani Allah ya saka masa" "Ameen" ya fadi ba tare da ya waiwayo ba,saidai cikin ransa yanajin tabbas zaiyi maganin wannan rashin mutuncin nata. Ransa a bace ya koma sassan ruqayyan,taga hakan saman fuskarsa amma sai ta share bata tambayeshi ba,ta shiga hidimar shirya masa abinci da kunna room Heather saboda dakin yadan qara yin dumi don yau din akwai alamun sanyi sanyi. Tasan koma meye tsakaninsa da matarsa ne,ita kuma wannan ba huruminta bane. Pyjama dinsa ta cire masa ta dawo gefansa ta ajjiye masa tana kallon fuskarsa,har cikin ranta tana jin ba dadi to amma meye nata a ciki?,duk wanda ya debo da zafi bakinsa ai. Daga kai yayi suka hada ido sai tayi saurin dauke nata idanun tana warware kayan data dauko. A hankali ya kama hannunta ya riqe yana kallon kayan. Tare ya siyosu ya ajjiye wasu a bedroom dinsa na sashen zainab,amma tuni wadanda ke sashen zainab din suka zama tarihi,don daga qarshe da kansa ya bayar dasu sakamakon komawar da sukayi basu da maraba da tsumma "Anya ko da gaske kike kin yafemin?" "Da akayi me fa?" Ta fadu tana dubansa fuskarta na nuna rashin fahimta "Abubuwa marasa dadi keta faruwa,tunda na auro Zainab na kasa jin dadin zama da ita ko na kwana daya ne,wasu abubuwan ban taba zaton mace tana iya aikatawa miji ba sai zuwanta gidan nan,idan kace zaka kai qorafi saika zama........" "Saika zama qaramin mutum,haka zaka ci gaba da haqurin" ta fada tana miqewa tsaye daga saman gadon ba tare data kalli qwayar idanunsa ba "Zainab kwata kwata......." "Please mana habeeb......" Ta katsi numfashinsa tana fadi qwayar idanunta carr cikin tashi "Banason naji please,inaso wannan daren,banason abinda zai batashi" kansa ya girgiza yana kallonta "Kinga bacin rai da damuwa akan fuskata amma baki damu kin tambaya ba,da abun yayimun yawa kuma nake gaya miki da kaina nan ma ruqayya ba zaki fahimceni ba?,ba zaki bani shawaran da zata zamemin fitila akan matsalata ba?" Wani murmushi me ciwo ne ya qwace mata,ta kauda kanta gefe tana tuna wasu abubuwa masu ciwo da suka wuce. Tana mamakin halin maza qwarai,mace zaki iya cinye daci da zugin radadin da namiji ya banka miki,amma shi bai iya dauke radadi da ciwo. Yana samunsa yanzun zai ɓara kowa sai yaji. Ta kusa minti biyu a haka ba wansa yace da dan uwansa wani abu,shi ya kafeta da ido ita kuma ta kawar da kanta tana kallon wani gurin na daban tare da qoqarin hadiye abinda takeji sannan ta waiwayo tana dubansa "Ka tashi ka canza kaya muje kaci abincinka" "Bazanci ba,ba wannan maganar akeyi ba" "Maganar da akeyi din ai bata da muhalli a gurina,ba hurumina bane" "Eh ba huruminki bane amma na sakaki a ciki". Ta lura da gasken gaske so yake ya tsomata a ciki,yanaso ya sanyata yin abinda taketa dannewa,sai ta saki kayan hannunta zatayi gaba tabar dakin amma sai ya damqi hannunta ya dawo za ita ya zaunar "Amma baicikin aikin mace ta sanyaya zuciyar mijinta?,shima bada shawarar laifi ne?" "Wacce shawara kake buqata?,sanda kake da buqatar shawarar ka nemeta ne?,ko ka manta sanda nazo da shawarar?,ka tuna abinda ka gayamin?,na cika kishi,duk zancan magauta ne kai baka da haufi akan yarinyar ka manta?,kana da tabbaci da yaqini a kanta so yanzun bai kamata kayi loosing wannan courage din ba,ba hurumina bane sulhuntaku ko na shiga maganarku ba,ko shawara ma ba dole bane na baka indai akan abinda ya shafi iyalinka ne,na roqeka ka fiddani daga sha'aninku" ta fada tana hade hannuwanta guri guda,qwalla na cika mata idanu,don tabbas ya taba Mata tsohon mikinta. Kasa cewa komai yayi,wannan ya bata qwarin gwiwar miqewa a nutse ta fita daga dakin. Tana jin mahaukacin kishinsa cikin kowacce gaba da sashe na jikinta amma ya gaza gane hakan,komai tana yinsa bisa qarfafawa kai gwiwa da kuma jagorancin addu'ar da kullum takeyi dare da rana akan Allah ya bata ikon mallakar zuciyarta,kada Allah ya bata ikon cutar da zainab ko kasa yiwa saleem biyayya,tanayi maamanta tana tayata,ta tabbatar wannan shine ginshiqi na farko da yayi mata katanga daga bin son zuciyarta. Binta yayi da kallo jikinsa a sanyaye har ta gama ficewa ba tare da ya iya dakatar da ita ba. Iska me zafi ya furzar daga hunhunsa yana maida bayansa jikin gadon ya kwantar yana tariyo abubuwan da suka shude shekarun baya. A lokacin da idanunsa suka rufe yaji duk duniya ba abinda yakeso ya gani illa d'an kansa. A baya tunaninsa sassauqa ne akan wannan,amma tasirin kalaman mahaifiya da na qanne yasa sannu a hankali ya jarabtu dason qara aure don ya samu haihuwa kamar kowanne cikakken namiji yadda ake gaya masa. Mahaifiyarsa tayi masa nuni da Zainab cikin 'yammatan danginsa. Farar fatarta da yawan iyayinta yasa yaji kaman zata dace da yanayinsa. Duk macen da aka yiwa kishiya tasan zafi da rudanin da zuciya ke fuskanta a wannan lokacin, ruqayyan ma taji haka,duk da nata za'a iya cewa ragaggge ne bayan tasan wacece Zainab din. Taso qwarai ta kwatanta masa amma a sannan suna ganiyar buga soyayyar da babu kama hannun yaro. Ko kadan babu nufin hanashi qara aure a tattare da ita,duk da inda ace zai fasa zataji dadin hakan,to amma taso ya bata dama wajen zabowa kansa da ita abokiyar zama ta gari,da hakan zata kasance da farincikinta ya qaru. "Kin cika zafin kishi ne kawai,amma duk wanda yace ga illar zee to saidai munafuki ko wanda bai mata farin sani ba,ita din bakiga yadda take maganarki ba,kuma an gayamin girmamaki take duk sanda kuka hadu a wani taro,to me ya rage me kikeso indai ba masifa da fitina ba?" Ya fada a sannan hannunsa riqe da wayarsa yana replying watsapp massages na zainab din "Ki cirewa kanki fitina da damuwa don Allah,ta kusa shigowa komai yazo qarshe ma" maganarsa ta qarshe tafi kowacce bata mata ranta,don zatayi gyara don ta sama masa nutsuwa da farinciki ga duk auren da zai qaro sai abun ya juye kanta?. Ita ta sani bawai alfahari ba,bata tsoron karawa da kowacce macce indai ba daga aljanna aka sauko da ita ba,to amma me?,saleem din ya sota matuqar soyayyar da ta tabbatar zai wahala wata diya mace ta samu kwatankwacinta. Banda maganar aure data taso yanzu bai taba wani abu don ya cutar da ita ko ya cusguna mata ba,wannan yasa take masa laluben macen da zai samu nutsuwa da ita,wadda itama ba zata daga mata hankali kota rabata da nata farincikin ba. To amma saboda idanunsa sun rufe,ya kuma yi nisan da bayajin kira bai hango abinda ta hango masa din ba ita. Bayan gama tuna dimbin laifuka da abubuwan da yayi mata na rashin kyautawa bai zaci dawowarta dakin ba a sannan. Sai kawai ya tsinci tattausar muryarta daga bakin qofa tana fadin "Daddy abincinka har ya gaji da jiranka,muma kaga dare yanayi kai muke jira" Da ya daga kai ya kalleta murmushi ne saman fuskarta kaman ba itace ta fita da fushi ba. Daya daga cikin abinda yake burgeshi da ita kenan,kuma guda cikin failure na zainab. Ita muddin ya bata mata rai sai ta bata masa,muddin tayi fushi ko ranta ya baci saita nuna ta kuma furta maka "Ko sai nazo na qarasa shiryaka ranka ya dade?" Ta fada tana rungume hannunta a qirji idanunta a kansa "Me yasa na damu na kasa juriya da qaddara,na shiga neman aure ido rufe?,don kawai ruqayya bata haihu ba?,yanzu ita ke da twins har da tsarabar diya mace guda,lallai rashin haquri da juriya na gaggauto mana da wasu abubuwa da lokacin riskarsu zuwa garemu.ma baiyi ba" yana gama wannan tunanin tana isowa,kaman jiranta yakeyi yasa hannu ya fusgota zuwa jikinsa,wanann sassanyan qamshin nata yayi ma hancinsa kyakkyawan maraba "Kiyi haquri da bata miki rai da nayi" "Nasan bakayi don kana sani ba,kayine saboda relief kakeson samu a sannan daga abinda kakeji,kayi haquri nima, wani yanayi ne da bana iya controlling kaina" "Laifi nane,amma bazan sake ba in sha Allah,zan fuskanci consequences din ni kadai" "Ya wuce fa,tashi ka shirya,yara har sunci nasu sun wuce". Ita ta taimaka masa ya shirya din,duk bayan sakanni sai ya jawota ya shaqi qamshinta. Har fargaba yakeyi daren qarshe a ranakun girkinta su fita,don gobe warhaka yasan makomarsa. K'arin abun mamakin koda da kudinsa ya siya turaren yace a saka masa iya dakinsa idan ma ita bata da buqata to fa bazai samu hakan ba,ya rasa dalili kamar me aljannun da suke gaba da turare. Da suka zauna alhassan ta aika kiran Zainab din "Jeka kira ummanku,kace tazo muyi dinner" amsa mata yaron yayi ya juya ya fice,ita kuma ta maida hankali wajen fara serving saleem. Tana zuba masan suna hira qasa qasa,yana bin hannuwanta dake jujjuyawa wajen zuba masa abincin da kallo saboda jan lallen da tasha tun shekaran jiya,an mata ratsin baqi a farcenta. Sau da yawa akan ruqayya ne baya yarda da cewar lalle baya kyau a hannun baqaqen mata,bai sani ba ko don yakan manta da kalar lalle idan ba hannunta ba?,don idan kaga Zainab din da lalle to kan tabbatar lallai akwai biki a dangi. *HUGUMA*👑 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 14 *_RUK'AYYAT GRAPHICS_* *_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_* *_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_* *_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_* LOGO INVITATION CARDS BANK STICKERS BUSINESS LOGO SAVE THE DATE P.O.S BANNERS BIRTHDAY CARD BOOK COVER DATA FLAYER BIRTHDAY VIDEOS VIDEO INVITATION AI PICTURES _KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_ *_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_* *RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku _KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_ https://wa.me/+2347084515410 _ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽 ________________________________ "akwai maganar da nakeson muyi,saidai bansan yadda zaku fahimceta ba" saleem din ya fada a tausashe yana jan plate din data ajjiye masa a gabansa don ya qagu ya fara cin abincin,iya qamshin abincin kadai ya isa ya sa ka zaqu kakai bakinka,kada ma ayi maganar farfesun kayan cikin da yaji spices. Zama tayi sosai a gabansa kaman zata koma cikinsa ko kuma an bata gadinsa tana dubansa da wani tattausan kallo. Idonsa ya lumshe ya sake budewa duka lokaci guda yana dubanta qamshinta yana kai masa ko ina "Uwargida sarautar mata" ya samu bakinsa da fadi. Wani shagalallen murmushi mai qaramin sauti ta saki tana watsa idanunta "Itace maganar da kace zakayi din?" Kai ya girgiza "Bansan ya akayi bakina ya subuce ba" "To ka gyara bakinka tun kafin umman haneefa ta iso,don nidai ba ruwana" "Laifinki ne hajjaju,irin wanann kallon na rantse tsaf zai hanani cin abincin nan,bari kiga tun baki cikamin cikina da soyayya ba" rausayar da kai tayi tana sake sakin siririyar dariyar. Itakam har abada koyon kyawawan dabi'un da zasuja hankalin miji ba shakka sun biyata,don ko yaushe suna wanketa ne a idanun saleem,koda bata sanyawa jikinta komai da zaija hankalinsa din ba,iya kallonta kawai ya wadatar. "Umara nakeson muje gaba daya,ni dake da hajiya sai zainab,to amma kudin hannuna basu cika ba,kudin tafiyar mutum uku ne ba kadan,kinga mutum daya bai samu ba" "Kai,kai ma sha Allah" ruqayyan ta fadi tana langwashe qafafunta "Amma naji dadi qwarai da gaske,Allah ya qara budi,inda duk allura ta fita Allah ya naidata dutse" "Ameen ameen,duka wannan addu'ar haka bayan baki da tabacin kina cikin masu zuwan?" Murmushi tayi masa me kama da harara "Zakaje,hajiya zata je,to meye ya ragemin?,kamar nayi rabin zuwa kenan,rabin kuma sai ranar da ubangiji yayi kirana" zamansa ya gyara yana jinjina kai,ko da yaushe maslaharta itace tasa,koda yaushe buqatunsa take sakawa a gaban nata(maza nason irin wadan nan matan),to shikam me yayi masa saura game da matar kirki?. "Amma sai hajiya tace ko ita zata haqura naje daku,ita wata shekarar idan da yawan rai tunda alhaji me rasuwa ya taba kaita hajji" Kai ruqayya ke girgizawa da sauri tana dubansa "Kai yanzun koda tace hakan sai kayi hakan?,da yake mu muka haifa mata kai?,sam ba za'a yi haka ba,mu ya kamata mu haqura din,mune qasa da ita,yanzun ni ko Zainab wani a cikinmu zaiso idan su alhassan da khalil sun girma hakan ta faru tsakaninmu da matansu?". Kai ya girgiza yana jin wani sanyi a cikin ransa,lallai ya samu mace ta garin da annabi ya suffanta,yana cikin mazan da suka shigo duniya a sa'a. "Wai da ina ganin zanyi mata gyaran gida ne kafin mu tafin shi yasa" "Dukka ta cancanta daddy,ta cancanci abinda yafi haka ma,hasalima inda zata buqaci ranka ka ciro ka bata baka saka mata da komai ba" ta fadu tana dubansa. Wata ajiyar zuciya ya saki yana jinjina kai cike da gamsuwa,wata irin daraja da kimarta suna linkuwa a ransa,ruqayya macace daya tamkar da dubu lallai ya shaida wannan. Takun Zainab taf taf shine yana hankulansu,suka waiwaya gaba daya suna dubanta. Idanunta akan ruqayya suke,ji takeyi kaman ta shaqota,taji komai a labewar da tayi,banda baqin hali da baqar zuciya da ya cakuda da baqinciki ai ita taso yiwa mugunta. Saudiyyan nan daga ruqayya din har hajiyan ai sunje,shine don tsabar hassada da qyashi me makon ita da tunda tazo duniya ba'a taba zuwa da ita ba tace a dauketa sai tace a barsu?. "Amma dai wannan shawarar ba komai a cikinta sai zallar rashin adalci da qyashi da hassada" Zainab ta fada fuskarta na nuna tsantsar bacin rai. Daga zaunen saleem ya daga kai ya bita da kallo. Tsaiwarta a gurin kawai ya canza atmosphere na wajen. Daurin qirjin nan ne dai na gado sai armless shirt daga ciki,qafafunta tsage tsage a waje kamar sunyi d'ai d'ai "Da akayi me?" Ya jefa mata tambayar. Cikinta ne ya juya abinda ya Sanya yawu taruwa a bakinta kenan,sai ta juya gefan hagunta ta fesar da yawun tasa bayan hannunta ta goge ragowar da ya bata mata baki. Da sauri ruqayya ta kawar da kanta gefe tana a'uziyya zuciyarta na tashi saboda tsantsami. Juyowa Zainab din tayi tana duban saleem "Ta yaya zakayi shawara da ita ita kadai,bayan ba ita kadaice matarka ba?,ba ita kadaice take da haqqi a kanka ba,sai nayi magana kuma aga na cika qorafi bayan adalcinne sam ba'a yishi ba?" "Ni kika tsayawa akai kina gayan ban miki adalci ba?" Yadda yayi mata tambayar ta bugar mata da gwiwa,amma rashin son gaskiya da jin tafi qarfin ayi mata fada sunyi mata katutu saita kauda kanta gefe ta fara halin nata wato gunaguni "Eh ai azzaluma ka tambaya gashi tana batun ni da ita duka mu rasa ku tafi kai da hajiya saboda tsabar muguntar kowama ya rasa,bayan ko hajiyarma ta taba zuwa ai,nice ba inda na taba leqawa a qa'ida......" Ta fada hannunta a qugunta ba tare data dubeshi ba. "Idan baki matsamin akai ba sai ranki yayi mummunan baci,sakara mara wayo" maganar ta girmi kunnenta don bai taba gwada fadin hakan ba "Um um daddynsu,ya isa don Allah" ruqayya ta fadi qasa qasa tana tausarsa saboda ta hangi fushin da ya fara tasiri a idanunsa "Ki qyaleni na fadi mata,naji ta fara sako batun hajiya ne,ta dauka yanzun daa ne da zan dauki iskancinta akan uwata,wanda kikayi a baya ma na kasa tsawatar miki istigfari nakeyi har yanzu" can qasan zuciyar ruqayya cewa kawai tayi uhmmmm. Zuwan Zainab gidan tana amarya ba ita ba,hatta hajiyan ta shuka mata iskanci kala kala,ba zaka taba zaton akwai wata alaqa ta jini tsakaninta da hajiyan ba,a lokacin bai cewa komai,shi yasa ruqayyan tayi qoqari ta kama mutunci sosai a lokacin (kira ga uwayen gidaje,ina qara gaya muku sau tari ku kike siyawa kanku daraja da mutunci a farkon zuwan abokan zamanku,kuma kuke basu fuska da qofar rainaku tun farko,ki watsar da ita da me gidan gaba daya ki basu space ki maida kanki busy a lokacin da suke ganiyar cin amarcinsu,hakan shine zaifi zame miki alkhairi akan sanya idanu akan duk wani motsi nasu,ranki zaiyita baci ne kina ganin abubuwan da babu lallai suyi miki dadi,ke kuma babu tabbas din zuciyarki zata iya jurewa). Wannan kame kan shine abinda ya jawo har yau duk iya iskancin Zainab da ganin ruqayyan ta tare mata gaba ta tare mata baya ba komai take iya tunkararta da shi ba. "To ai saika dauki mataki yanzu ma bata baci ba" ta fadi a zafafe,saidai gama fadin keda wuya wani zazzafan amai ya biyo baya. Dan janye jiki ruqayya tayi cikin mamaki,zubewar da taga zainab din tayi a wajen ya sanyata miqewa tana fadin "Subhanallahi lafiya?" Qarasowa tayi dab da ita tana qoqarin riqota,saidai wani yanayi dake tashi a jikinta ya sanyata matsawa gefe ta tsugunna tana mata sannu. Mugun galabaita ta fara yi,ita da saleem din suna tsaye a kanta. Wannan abun ya sake bawa zainab dama ta sake ragwabewa sosai ta narke kamar matacciya "Dauko mata hijabi mu tafi asibiti" tsam ta miqe tana juya yadda Zainab din ta sake gaba daga yin amai?. Eh tayi wani irin amai mai yawa a gurin amma baici ace ta sassake haka ba. Sau biyu tana sallama yaran basuji ba saboda sun qure qarar tv sunata kuma damben fada akan abun wasa,harda haneefa da ya kamata ace a shekarunta ba wannan abun yakeyi ba,ita ke kula ma da khaleel. Sanda suka farga da kallo suka bita baki sake saboda ba zasu iya cewa ga ranar qarshe data tako sashen nasu ba. Tunda ta shiga falon yanayin falon taji sam baiyi mata ba,haka ta dinga takawa cikin tsantsani don ko ina datti ne,bata tunanin jiya ya samu kyakkyawar shara,yau kuwa dama tunda tana sauri biki ya samu tayi imanin inda zata leqa kitchen dinta ko wanke wanke batayi ba. Kusan ginin nasu iri daya ne,wannan ya sanya bata sha wahalar gane inda bedroom dinta yake ba "Karki shigarwa ummanmu daki fa" haneefa ta fada tana kallon ruqayya. Sosai abun ya bawa ruqayya mamaki,ta juyo tana duban yarinyar. Har tasan wani kishiya kada ta shigarwa kishiya daki?, komai ma wai zama zainab takeyi da yaran ta gaya musu?. Hannu ruqayya ta saka ta yafitota tana murmushi "Zoki nunan kayan ummanki zan dauko mata zani da hijab,asibiti daddynku zai kaita" tsalle tayo ta sauko daga saman kujerar da sun jima da cin ubanta ta nufo ruqayyan ba tare da ta maida hankali ga batun zuwa asibiti ba "Zakisha wahala,dauko kayan ummanmu akwai wahala,don itama kullum saidai ta gaji ta dauko wanda ta gani ta mayar da sauran" bata cewa yarinyar komai ba tabi bayanta. Kusan idan ka ganta cikin dakin Zainab haihuwa tayi,rabonta da bedroom dinta tun haihuwar khalil. Tayi mamaki har fiye da zato na yadda ta zamu dakin nata a hargitse,hatta da shimfidar gadon a harmutse take,harda qasa qasa a kai,panties nata Brazier da cup harda spoon ma. Qasan dakin kuwa baja baja yake da karikice da bazata ma iya tsaiwa tantancesu ba. Dakin ba abinda yakeyi sai wani irin hamami hamami kamar warin dauda cakude da warin hammata. Bata sani ba amma qila tsabar tashi da jiki da hammatar Zainab din keyi da annakiyar da dakin yake da ita ne ya sanya a madadin qamshin turare... Nata turaren ya zama wadannan warika ne gud biyu. Bandaki shima na buso tashi gudunmawar qarni da zarnin ta qoofar bandakin dake a wangale. Gaba daya kayane jibge a rataye tun daga murfin sif din zuwa kan qofar bandakin,zannuwanta ne panties da riguna. Haneefa ce ta bude sif din hankalin ruqayya nakan wani tsadajjen turarensu data gani yashe a qasa an tattara kwalbar an shareta acan matse matsi mudubi,ta yiwu dazun da tana saurin zata fice ne ya fashe garin ta saka,ita kuma ba zata iya tsaiwa ba ta tattareshi gefe da zummar saita dawo,data dawo din kuma bata da lokacin bi ta kansa sai ranar da Allah yakai tsintsiyar shararta gurin. Zubowar kaya kawai ruqayya taji yiiiiiiffffff kamar an saki buhu. Gefe ta matsa da sauri adan tsorace,haneefa ta sheqe da dariya "Haka ummanmu takeyi kullum idan zata saka kaya,ki zabar mata saiki barsu a gurin saikin dawo,ko natayaki mu mayar" yarinyar ta fada hankalinta kwance cikin nishadi kamar me bada labarin abun arziqi. Tsaf ruqayya ta qarewa kayan kallo,tama kasa tantance meye da meye,don basu da maraba kwashen dilar kayan gwanjo "Ke da nace kaya aiba wanki za'a kai ba,ba kayan dauda ba wankakku asibiti zataje" baki ta saki tana kallon ruqayya "Ai sune wadannan,idan aka kawosu daga wanki watsasu mukeyi,idan muka cire kuma indai laundry basket dinmu ya cika sai mu ajjiye ciki idan an tashi kai wanki a kwaso,rannan ma daddy yace duka kayan ciki tsami sukeyi" ta fadi tana toshe hanci cikin son gwada yadda yayin a ranar tana dariya abinta don maganar har yau dariya take bata "Ya isa,ina hanaki fadin abu ko an tambayeki bare ba'a tambayeki ba,mu kwashe kayan mu mayar" tace da haneefan. Tana tilar kayan tana dauke numfashi da kau da kanta,haka ta dunga diba tana cusasu yadda ta gansu haneefa na tayata. Kafin su gama cikinta ya gama gurbata,da qyar ta iya gano zani da hijabi ta fito dasu a hannunta amma zuciyarta fal qyanqyami. A nan ta samesu,ta ajjiyewa zainab din kayan amma sai tayi talau alamun ba zata iya sakawa ba. Saleem dinne ya karba ya fara saka mata. Da ya gama saka matan ya riqeta suka fita farfajiyar gidan Zainab din tana layi kaman zata fadi. Kwanukan abincinta ta fara tattarawa tana daukesu a wajen kafin suma su fita a kanta. *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 15 https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39 *_Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_* ____________________________ Tana kitchen taji ya sake shigowa "Ki dauko mayafi muje mu kaita" waiwayowa tayi ta kalleshi,sai kuma ta kauda kai. Wani abune ke mata yawo a zuciya,ba zata taba manta wannan ranar ba,ranar da banda kiyayewar Allah babu abinda zai hana ta rasa ranta a abinda Zainab din tayi mata,bayan ta rasa ranta harma ta rasa ran abinda yake cikinta "Kuje kawai saikun dawo,zan zauna da yaran tunda dai ba za'a barsu haka gida ba kowa ba" ido ya zuba mata na wasu sakanni,har zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice. Koda ta gama kintsa kitchen din alhassan ta aika ya kirayi su haneefa suka dawo sashenta,sannan ta saka alhassan din ya kulle sashen zainab din,don yafi haneefa nutsuwa da hankali,sau tari banda tsaho da ta fishi zaka dauka shine babban. Falon ta dawo ta zauna lokaci lokaci tana duba wayarta,yaran suna kallon carton,saidai bari bari da su haneefa din keta sanyata,ba'a samu sauqin abun ba sai da khalil yayi bacci. Dole ta saka ya qure ac dinsa saboda yanayin da jikinta ke bayarwa da ya soma dumame motar. Yawun takaici kawai yake hadiyewa,ya rasa me Zainab ke buqata a rayuwa da zai sanya ta canza halinta. Wasu lokuta yakanji kunyar ace ita din matarsa ce,abinda bai taba ji ba dangane da ruqayya duk da sunfi dadewa da ita nesa ba kusa ba akan zainab din. Wani kuka take kwazara mishi babu dadin amo bare dadin sauraro,ita a haka dole kukan da zai taba ransa yaja hankalinsa,abinda bata sani ba zallar takaici ne ya qumeshi. "Wallahi na sake yarda da gaske asiri yana tasiri a kanka,na rantse da Allah ko kaffara bazanyi ba inda ruqayya ke wannan kukan da tuni ka rasa inda zaka tsoma ranka,amma ba komai akwai Allah" "Ba zaki rusuna ba kenan ki saita kanki ba" "Me nayin da har zan rusuna?,saboda kawai idan ba'a sonka idan ka fada ruwa ma sai ace ka tayar da qura?,kuma ko meye ya sameni ai ta sanadinka ne,duk inayine don na gyara kaina na samawarwa kaina 'yanci kamar yadda ruqayya ke dashi,don bana son kaucewa hanya nabi malamai". "Anzo gurin" ya fada a ransa,cikin zuciyarsa yana fatan ace shiriyarta ce tazo,sai ya sassauta tuqinsa yana duban titi "Ai baki kama hanya ba sam zainab,ke din ba makauniya bace amma ta wani fannin kinfi makaho makanta,ta yaya kike tunanin zaki kamo ruqayya a haka?,bayan kinfi kowa sanin abubuwan da takeyi wadanda suka kaita matsayin da kike hange?,duk da ina iyakacin bakin qoqari na na yin adalci a tsakaninku?" Kamar ta banka masa ashariya haka taji,ita da yayi mata misali ko kwatance da ruqayya gwara ya sakata a daki ya lallasata tayi dumamen jikinta "Wanne abu takeyi banda zallar kissa da munafunci da bin malaman tsubbu duk don ta mallakeka?,idanunka ya rufe ka kasa ganin gaskiya?,ni da kullum nake fadi tashin gyara maka shimfidarka amma qoqarina a banza yake kullum". Kai ya girgiza "Zaki bawa Allah tabbaci ranar qiyama akan qazafin bin malamai zainab,ki kiyaye harshenki daga fadar abinda baki da yaqini akai" kuka ta fashe masa dashi "Ehnnn,an tabo shalelenka ba?,muddin kana irin wannan akan ruqayya wallahi zaman lafiya tsakanina da ita har abada" ko ya waiwaya ya kalleta bai sakeyi ba,ya sani Zainab tayi nisan da bazata taba jin kira ba sai wani ikon Allahn. Sun samu sunga likita,amma yawan gudawar da takeyi yasa likitan yace zata kwana anan a saka mata drip,gudun kada suje gida cikin dare abun yayi worsening. Sosai ta sharbe masa tana ci gaba da koke kokenta da babu abinda suke qarawa saleem sai takaici. Don tuni likita ya gaya masa ya dinga sakata tana kiyaye shan magani barkatai "Magungunan nan basu da wata qa'ida ko doka,duk maganin da za'a shashi ba bisa qa'ida ba dole yayi illa" tuni saleem din ya fahimci maganin meye,ba zata daina halinta ba kenan duk da tarin gargadin da yayi mata?. Bai iso dakin da suka batan ba sai daya kira hajiyayye qanwar mahaifiyarta akan tazo ta kwana da ita sannan ya wuce dakin. Tanajin sallamarsa ta sharbe magashiyyan. Baibi ta kanta ba tsabar takaici,yaja kujera ya zauna kawai yana danna wayarshi. Ba dadewa hajiyayye ta iso,ya miqe yana bata gurin zama "Da kayi zamanka abinka" hajiyayye tace "Ah dama ke nake jira,tafiya zanyi ni" ido zainab din ta bude da sauri,taci alwashin yau kwanan asibitin zaiyi,shine abinda zatayi kawai wanda zai quntata ran ruqayya. Yunqurin amai ta fara yi na qarya,shi da hajiyayyen dukka suka qaraso,saidai babu wani abu data fitar don tuni aman gasken ya fidda komai daga cikinta "Idan na fita zan tsaya na yiwa nurses din magana,ko alluran tsaida amai din suzo suyi mata" ya fadi yana matsawa gurin saman kanta "Sai da safe zan sake shigowa,banajima zamu kai azahar bamu koma gida ba,Allah ya sawwaqe " ya fada yana fiddo kudi daga aljihunsa ya ajjiye gefan kanta cikin qoqarin danne bacin ransa kada duniya ta fahimci halin da suke ciki "Yanzu ko tausayin halin da nake ciki bakayi tafiya zakayi?" Ta fada da qarfi don hajiyayye taji harda matso hawaye "Banda abinki zamansa a nan ai bazaiyiwu ba,kuma me zaiyi miki shi da bashi ke cire ciwo ba?,jeka abinka gida,Allah ya bamu alkhairi" "Sai da safe" ya fadi yana ficewa. Kaman jira takeyi ya fitan ta miqe ta zauna sosai har cannula din hannunta na qoqarin gocewa "Banso kikayi magana ba, wallahi hajiyayye na fara gajiya da rashin adalcinsa,qiri qiri mutumin nan kiga abinda yakeyi,na rantse miki da Allah yau inda ruqayya ce zatayi kwanan asibiti bazai iya tafiya ya barta ba" kai kawai hajiyayye dake cire hijabinta ta daga ta kalli Zainab. Duk da tasan wasu abubuwan amma sai tayi kaman bata sani ba ta hanyar tambayarta "Saboda me?" "Saboda wani irin mahaukacin kula da yakeyi da ita da wani kulawa da na tabbatar ba ta domin Allah bace" "Ke ya akayi kikasan bata Allah bace zainab?" Hajiyayye ta fada tana jawo kujera dab da gadon Zainab din saboda su biyu ne a dakin,donma daya patient din tayi bacci abinta tuntuni,kuma abun mamakin ita kadaice babu dan jinya. Sake jan kujerar tayi baya kadan saboda yanayin da jikin zainab din ke bayarwa taci gaba da kallonta daga nesa nesa "Yo hajiyayye aiba irin wannan soyayyar a yanzu a wajen mazan wannan zamanin,kana gyara ma ya ka cika dasu bare baka gyara,nifa kullum cikin fuskantar matsala nakeyi da saleem,kyara gwasalewa,komai nayi banyi dai dai ba,komai nayi baya nuna wani jib dadi ko kuma wai na burgeshi,ni kuma a iya sanina macen da bata gyara HQ dinta ita ke fuskantar wannan matsalar,macen dake gyara take kulawa baji ba gani ai tafi qarfin ayi mata irin wannan tijarar,to ita ba wani gyara da takeyi matar nan,idan kuwa ba asiri ba banga ta yadda zata mallaki saleem ba" "A tunaninki?" Hajiyayye data gama sauraron soki burutsun zainab ta fadi tana dubanta "Hakane mana" zainab ta amsa mata kai tsaye "Sam sam" ta sake maida mata tana zama sosai idanunta cikin nata "Mun sani mafi rinjayen abinda ake kira da aure wannan abunne,to amma shi kansa baya tasiri baya kuma qayatarwa gami da jan hankalin d'a namiji saikin mallaki wasu abubuwan,tsafta,ladabi biyayya iya magana tattalin miji da tarairaya duka ina kika barosu?,ina kika baro iya girki?,ado da gayu?" "Duk basukai wannan muhimmanci ba hajiyayye,indai sune ke riqe maka miji me yasa saleem ya auroni idan ka cire matsalar haihuwa?,ita kanta haihuwar ba damun wani namijin tayi ba indai zai samu wannan gurin da kyau" ta fada tana qoqarin maida kanta ta kwanta,don kwata kwata maganganun hajiyayye basu samu matsugunni a ranta ba. Ta dade da sanin Zainab da kafiya da kafirin taurin kai,musu kuwa ba abinda yafi mata shi sauqi,tunda har bata da intention na ta fahimcetan to ba fahimtarta zatayi ba,zata batawa kanta baki ne,don haka tace "Gaskiya ne,hakane,amma akwai gaskiya daya da zan gaya miki,don Allah ki dinga qoqarin amfani da turare,sannan kodon zirga zirgar da kake wuni kanayi wankanki ki maidashi sau biyu" "Ke hajiyayye kin ganni nan,saleem bai taba cewa wani abu ba,turare kuwa mu ko munsa ko bamu saka ba mun wanku fes daga gurin kakanninmu,jikinmu baya komai in gaya miki,ki qyaleni na huta" "Hakka" tace da ita kawai tana tura kujerarta baya,ta dauki wayarta ta soma chart abinda.(hajiyayyen bazawara ce, mijinta ne ya rasu ya barta bata taba haihuwa ba,shekarunta kuma duka duka basu wuce arba'in da biyu ba). Idanunta ta rufe saidai maimakon tayi nazarin maganganun hajiyayye a'ah,asarar da zata tafka ta maganinta take qiyastawa indai shegen likitan nan ya riqeta bai sallameta ba a gobe "Aikuwa koda tsiya koda tsiya tsiya dai an sallameni gobe" ta fada tana muskutawa hadi da gyara kwanciyarta. "Me kika ce?" Hajiyayye ta daga kanta tana tambayarta "Ba dake nake ba" ta amsa mata don bata taba zaton zancan zucin da takeyi ya fito fili ba. Itama bata sake tambayarta ba ta maida kanta ga abinda takeyi. ********Dogon tsaki taja tana gallawa wayar ta data dauki ruri a karo na babu adadi harara "Kinsan fa ni banason irin wannan abun,waye yake kiranki da baki daga ba bare ki kawo masa uzuri?" Umma dake zaune a gefanta tana cin tuwon dare ta fada "Isma'il ne umma" "To ki daga mana?" "Haba umma,dame zanji don Allah?,da takaicin shegen yaron nan da na aika ya siyomin indomie yaje ya zauna koda nacin kiran wayarsa?" Side hannunta data gama cin tuwon umma ta farayi tana cewa "Duk dai ke kika jawowa kanki,inda tuwonki kikaci da ba yanzu bakinki alaikum ba,ba wanda yaji bare ya gani" "Allah ya sawwaqe,tuwon masara aisaidai a bawa gawata" ta fada tana kyabe baki tare da gyara zamanta tana ci gaba da hada sabbin syrup da supplements din gyaran jiki dana qiba data siyo jiya. Gefe kuma ga mayukan saka hasken fata suma data yiwa roba guda. Dai dai nan yaron ya kwado sallama ya shigo hannunsa da baqar leda "Kaci uwarka surajo,inda kasan dadewa zakayi uban me yasa ka karbarmin aike?" "Banason lamarin zagin iyaye na gaya miki malama" umma ta fada tana kwada mata harara "Layine a wajne wallahi da qyar akazo kaina" "To kinji ma" umman ta fada ta yunqura tana miqewa da kwanonta ta nufi kitchen. Jakar umma ta jawo ta zuge,daga can umman ta jiyo qarar zuge jakar "A'ah fa,ni ba zaki talautani a daren nan ba,na baki kudin indomie me kuma kike nema?" "Pepsi zai siyomin don Allah,sai kuma ashirin din dana masa alqawari,zan biyaki bashi na ansa" ta fada tana ciro kudin da sauri ta miqawa surajo din tana masa inkiyar yayi sauri ya fita. *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 16 *_RUK'AYYAT GRAPHICS_* *_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_* *_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_* *_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_* LOGO INVITATION CARDS BANK STICKERS BUSINESS LOGO SAVE THE DATE P.O.S BANNERS BIRTHDAY CARD BOOK COVER DATA FLAYER BIRTHDAY VIDEOS VIDEO INVITATION AI PICTURES _KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_ *_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_* *RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku _KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_ https://wa.me/+2347084515410 _ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽 _____________________________ Da gudu surajo ya cilla ya fice daga gidan,saboda yasan indai umman ta fito ta karbi kudinta to ya shiga uku gurin wasila. Hakanan 'yar naira ashirin dinsa shima ta shiga rububi. Umma na daga kitchen tana mitar halin wasilan na zabe zaben abinci "To wai umma idan bakiyimin ba waye zaimin?,kuma ai ansan banason tuwon aka tashi akayi mana,kinga kuwa bazan kwana da yunwa ba". Suna tsaka da wannan taqaddamar Surajon ya dawo. Tasa hannu ta karba tana cewa "Surajo me abun arziqi da na tsiya,yanzu dai sai gaka sharp sharp,to ga kudinka" ta miqa masa ashrin din. Hannu yasa ya karba yana cewa "Ana sallama ma sake a waje" fuska tadan bata "Waye?" "Isma'il ne" ya bata amsa dai dai sanda umma ke fitowa daga kitchen "Bawan Allah dan albarka,je kace tana zuwa kaji" juyawa yayi ya fice abinsa,yayin da fuskar wasila ta canza ta jawo ledarta tana budewa. Kallonta umma tayi "Nayi tsammanin zakije ki fara saurararsa kada abar mutum haka a tsaye?" "Ni yunwa nakeji wallahi umma,sai naci abinci tukunna,idan bazai iya jira ba ya tafi" "A'ah,kedai kiyi da jiki ki gama" umman ta fada tana kade gefan tabarmar da suke kai din ta sanya hijabinta ta tayar da sallar isha'i. Da gayya ta dinga laqai laqai harta gama,siririn mayafi kawai ta yafa saman doguwar rigar jikinta tadan sake shafa turare tayi hanyar soron. Haushin isma'il takeji,wannan shige matan da yakeyi,sai taga kamar yana nesanta ta ne da irin mazan da take sa muradi,yaqi ya gane yaqiyin zuciya kuma ya barta. Kansa a qasa yana danne danne a wayarsa,jin takunta ya sanyashi daga kai daga abinda yakeyi yana dubanta,sai ya saki qaramin murmushi yana fadin "Barkanki da fitowa ranki ya dade" "Yauwa,barka" ta fadi kadaran kadaham. Ita kanta tasan isma'il bashi da wata matsala ko makusa,amma an riga an gaya mata ba shine alkhairi a tattare da ita ba,kuma itama ta gamsu da hakan,tunda baikai arziqin da takeson mijinta ace yana da shi ba,yadda take da tarin magauta din nan,tanason ta auri mijin da idan ta shiga gidansa za'a san yes!,ta auri me arziqi,mijin da first night dinta zai bata kyautar mota,mijin da zata dinga zuwa umra da aikin hajji har sai ta gaji,mijin da zai dinga sauya mata kalar motocin da zata ji dadin takota ta shigo unguwarsu tana fankama da hura hanci,ta bule maqiya da mahassada da qura,ana kiran hajiya wasila tana kyautar sabbin kudi,dukka tasan isma'il bazai iya affording wannan ba,duk kuwa da tasan ci sha sutura da wirin zama duk ba zata raza ba,don bai rasa komai din ba,hasalima Lagos yake zuwa yayi sari na shagonsa me yawa. Ya siya fili kuma gini yakeyi me kyau,amma yace mata idan bai samu kammalawa ba har lokacin aurensu zai kama musu haya kafin ya kammala daga bisani sai su tare. Itakam babban abun kunya ne a gareta ace wai yau ita wasila.......wasila guda tana a gidan haya,me yafi wannan abun kunya?,duk wadanda duka sanya ido suga ya zaka qare suyi maka dariya suyi shewa son ransu kenan,Allah sitru buqui inji kishiyar me doro. Shi ya karba daddumar da ta fito da ita ya shimfida sannan suka zauna akai. Kusan fiye da rabin hirar shi yakeyi,har zuwa wani lokaci da yaga ta fara hamma da lumshe idanu duk kuwa da cewa duka duka baifi minti arba'in da zuwa ba "Yadai?" Ya tambayeta cikin kulawa. Fuska ta yatsina ta danja tsaki "Bacci nakeji,kuma ma dai yunwa ma nakeji,haka kawai umma tayi mana tuwo yau" "Subhanallahi" ya fada cikin dan gajeran nazari. Bayan dan shuru da ya biyo baya na sakanni sai kuma yace "Ai bai kamata ki kwana da yunwa ba seela ta" ya fada yana fiddo wayarsa a aljihu. Bugu biyu aka daga suka gaisa "Ina layin nan dake kallon gurinku........eh takeaway nakeso a hadamin me kyau.......yauwa komai da komao,ya miqo layin sosai sai yazo gaban wani gida me farin fenti ina daga ciki...... alright na gode" daga haka ya cire wayar a kunnensa ya maida aljihunsa "Ai da ka barshi wallahi" Ta fada kawai don jin baki "A'ah,ba za'a yi haka ba ai,so kike nima na kasa bacci?" Murmushi ta saki tana jin dadi a ranta "Yauwa ni da albishir mafa nazo miki,ga yunwa kuma kina ji,anya albishir din nan zai fadu?" Wata zaquwa ce ta kamata, zuciyarta na hasaso mata waya zai sauya mata "Fadi kanka tsaye yallabai,ai dukka kunnuwana suna tare da kai" "To shikenan yallabiya" ya furta cikin dan salon tsokana,yaza hannu ya tura hularsa baya sannan yace "Zuwa yanzu wasila ina gani lokaci yayi da zamu maida alaqarmu ta ainihin gaske,tunda iya fahimtar juna mun yishi tsahon shekarun da muke tare,ina so ki shaidawa umma,ta yiwa su kawu magana in sha Allah qarshen watan nan zan aiko da kudin aurenmu hade da kudin sa rana,kuma banason duka a wuce wata hudu in sha Allah ba'a yi bikin ba" tunda ya fara zancan ta zuba masa ido gabanta yana faduwa. Bata shirya auren isma'il ba bata kuma son ta rasashi tun yanzu,tafison koda zai tafi sai idan FAISAL ko wani kaman faisal din ya kawo mata kudin aurenta tasan ta kama dahir "Kudin aure kuma isma'il ka gama ginin ne?" Ta fada tana dubansa. Dan nazarinta yayi kadan "A'ah,yanzu ba magana ake ta gama gini ba,gini na yana da buqatar a zuba masa kudade da yawa,inason nayi abu me kyau me tsari,wanda duk wanda ya kalla zai san na mori nemana" Fuska tadan bata tana girgiza kai "Gaskiya nidai nafi buqatar ka kammala tukunna" "Wasila" ya kira sunanta kai tsaye a maimakon seela da yakan kirata da shi,abinda yasa itama tayi hanzarin daga kai tana dubansa "Ni na shirya aure magana ta gaskiya,sanann hajiya kanta kullum maganarta kenan nayi aure taga 'ya'yana kafin ta Allah ta kasance a kanta tunda ban rasa komai ba,hankalina nima yanzu ya karkata ga hakan,in sha Allah bazan wuce wannan lokacin ba tare da nayi aure ba,idan kin shirya nima na shirya" "Idan ban shirya ba fa?" Ta fadi a qasan ranta tana dan satar kallonsa gabanta yana sake tsananta faduwa. Isma'il shine saurayi kusan na biyar da haka ta taba faruwa a tsakaninsu. Abdullahi,abubakar,nasir da sagir ga kuma isma'il. Dukkansu sun tafi ne saboda samun masu kudin da take muradi a irin wannan lokacin,kamar hadin baki dukkansu sai zance ya fara nisa a tsakaninsu sai masu kudin da take buri su bayyana saisu rushe gwamnatinsu,sai bayan ta sallamesu ne saboda ganin wadan nan sai suma daga baya su fece su barta ba wan ba qanin. Tayi qunan rai a sannan ba dan kadan ba,tun daga lokacin ta yanke hukuncin ta daina sallamar standby din har sai ta tabbatar ta kama wadancan din,yanxu gashi ana neman kwatawa (Yan mata!,yan mata!,wallahi wallahi wallahi kuyi hankali,ku yiwa kanku karatun ta nutsu,a irin wannan yanayin da ake ciki babban arziqi ne ma ki samu wanda zaice yau so nake muyi aure,da yawansu ba aure bane a ransu,saidai suzo su hole da ke kamar uwa su ta haifa musu ke,da yawan 'yammata ba mijin aure suka rasa ba, a'ah.......MIJIN BURI MIJIN MAFARKI suke jira ko ince suke nema,kibar wahalar da kanki kina namena lallai saikin auri me kudi,wallahi wannan din da kika raina qila shine me kudin da kike burin amma kika wulaqantashi,Allah ya rubuta sai ya aureki zakuyi arziqin tare amma kika bijire saboda idanunki sun kulle, ba'a ce ki auri namijin da bazai iya kula dake ba,namijin d a baikai ajinki ba,tunda ko a musulunci akwai KAFAA'A wato dacewa da juna,amma ta yaya a gidanku ana kulawa dake da kwatankwacin kudin da sukakai dubu dari kice ke wanda zai kula dake da million d'ari kike nema?wanne irin buri ne wannan?. A qa'ida dai ba'a son ana kula dake a dubu dari ki auri wanda saidai ya kula dake da dubu goma,ko ina anason aga mace gidan mijinta yafi gidansu ci gaba,AMMA FA👂🏼👂🏼👂🏼 ba tarin dukiya ba. Albishirinku!!!!,akwai tarin dimbin matan da zaki gani cikin leshi na kece alfarma,motar hawa ta isa da qasaita,gold kowanne corners na jikinta bodyguard da sauransu,amma billahillazi la'ilaha illa huwa da zata bude miki cikinta saikin kwana kina sallah kina godewa Allah da ya barki a inda kike,shi aure bawai mutum me DUKIYA kadai ake nema ba,Inaaaaaa........'yar uwa nemi MAI ZUCIYA wanda ko matar da take Jin mijinta wani ne idan kuka jera da ita zatasan lallai kinfi qarfin raini,nemi mijin dake KISHINKI wanda bai yarda matarsa ta rasa komai ba,wanda bai yarda a raina matarsa ba,wanda zai maidake SHALELE kifi qarfin rainin kowacce mace,mijin da zai kula da lafiyarki sai inda qarfinsa ya qare,wanda ya damu da damuwarki me tsare miki mutuncinki da dukkan qarfi da iyawarsa,wanda zai dauki iyayenki tamkar nasa ya basu girma na musamman.ba mai tarin dukiyar da baki da tabbas din zaki cita cikin kwanciyar hankali ma kuwa?. Da yawan 'yammata basu shiga gidan aure sunsan meye ainihin ma'anar miji ME DUKIYA ba dame ZUCIYA wannan shike rudarsu. Akwai wani jin dadin da duk girmansa kome miji yake baki koda kullum million hamsin ce wallahil azeem idan yana miki wasu halayen ba zaki taba jin dandanonsu ba,saikin gwammace naira dubu goma yake baki yake mua"amalantarki cikin nuna qauna tausayi da girmamawa,don Allah qannena yayyena da sa'annina YAMMATA ku farka,KU FARKA,KU DAINA KORE MAZAJEN AURENKU SABODA HANGE DA NEMAN WANDA YA FISHI,Allah ya shiga lamuran rayuwarmu gaba daya 👏🏽👏🏽 *HUGUMA*👑 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 17 Tana tsaka da wannan nazarin akayi sallama qofar soron,isma'il ya miqe a nutse ya karbo saqon ya dawo ya zauna yana ajjiyewa gabanta "Kada ki damu,amma kije kiyi nazari,saidai am sorry to say....koda baki shirya aure ba in sha Allah zanyi aure a wannan lokacin,don haka kiyi tunani a hankali kina da sati daya cif,duk abinda kikaji zuciyarki bata kwanta da shi ba kada ki yanke shi,ki zabi abinda kikaji kinfi aminta dashi,zaman aure zamuyi wanda muke saka ran mutu ka raba,bawai aje a dawo ba" da wadan nan maganganun yayi mata sallama ta dauki ledar takeaway dinta ta wuce gida. Da farko jikinta yayi sanyi sosai,har ma ta dinga juya lamarin,wata salihar zuciya daga qirjinta tana gaya mata "Me zaki jira?,kin cika shekara talatin fa kenan wasila,ki yarda da isma'il kiyi aurenki ki huta,tunda bazai barki da yunwa ko a wulaqance ba" zuciyar dake da gamayya da shedan na tuna mata "Shi kuma faisal ya zakiyi dashi?,idan kika amincewa isma'il shi kuma faisal yana da niyyar aikowa kinga kin yiwa kanki asara,yanasonki Faisal yanason kuyi aure,akwai jifan da ake miki ne ansan da arziqi a jikinsa ba'a so ki shiga gidan hutu shi yasa,amma da tuni kin jima da zama matarsa" kai ta jinjina tafi yarda da shawara ta biyu. Su masu jifan nata qila an duba musu sunga wahala zatasha a gidan isma'il shi yasa basu maida hankali su rabasu ba,sun hango arziqi jikin faisal wannan dalilinne yasa sukafi maida hankali a kansa. "Bari kiga" ta fada ita kadai tana janyo wayarta,wata number dake dauke da sunan MALAM ta lalubo ta dannan masa kira. Sai data kusa katsewa ya daga,suka gaisa da kakkaurar muryarsa sannan ta fara masa bayani "Isma'il ya matsa malam,yanzu haka zancen turowa yakeyi,ni kuma tun kafin ma ka shaidamin babu alkhairi tsakanina da shi nafison faisal gaskiya,don Allah malam a taimaka asa faisal ya turo ko yayi maganar kafin isma'il ya dawo" kai ya jinjina,yanzun haka a buqace yake da kudi "To ai shi kansa faisal din ba maganar aure a ransa kwata kwata,saidai zamu bullo masa ta bayan gida,bazai wuce wata guda ba tare da ya aiko din ba" "To na gode sosai malam Allah ya saka maka da alkhairi" "Ameen........yanzuuuu ......akwai turare da zamu siya,daga Syria ake kawo wannan turaren,sai wasu duwatsu daga misra a cikin ruwa ake samo ire irensu" "Kamar nawa kenan ane buqata malam?" Dan shuru yayi sannan yace "To,ai wasila ke abar tausayi ce,dole me imani ya tausaya miki saboda irin jifa dake jikinki Allah yayi yawa dashi,ki bayar da dubu ashirin,abinda bai cika ba na cika miki cikin aljihu na" Taji dadi sosai,godiya ta dinga yi masa kamar ta durqusa,sukayi sallama ta kashe wayar. Ranta fes ta soma cin takeaway dinta,a yanzu tunaninta inda zata hada kudinne kawai,don ba komai takeson gayawa umma ba,wani abun sai ta doje akai,tafison kome zatayi tayi abinta kai tsaye ba'a kawo mata cikas ba. Wayarta ta jawo sai tayi tunanin tayi kiran faisal(sau tari dama wasu 'yammatan suna qarewa ne da kiransu,kafin ya kirasu sau daya sun kira biyar). Duka yau basuyi waya da shi ba,amma takan bashi uzurin cewa harkokinsa ne sukayi masa yawa. Har ta katse bai daga ba,sai data qara kira bugu biyu ya dauka. Ranta fes ta shagwabe masa,shima ya biye mata suka bata kusan awa biyu suna waya,don leqowar umma biyu amma bata gama wayar ba. Suna tsaka da wayar dai dai lokacin da tasan yafison hira da ita ta katse wayar,sai bayan minti kusan biyu ta kunna ta kirashi "Nayita trying kuma naji a kashe" "Uhmmm wallahi,qawata ce ta shigo,bikinta ya kusa,ta kawomin anko amma nikam gaskiya na gaji da yin ankonnan,nima burina yanzu ace yau nice na fitar da nawa ankon kamar kowa?" "Nawa ne kudin ankon?" Ya fada yana share maganarta ta biyu "Dawainiya baby?" "No,kada ki damu abinda kakeso kake wahaltawa ai ko" "Gaskiya ne" ta fada da wata siriryar shu'umar muryarta cikin son sake shigar da kanta zuciyarsa "Lace ne 20k,sai atamfa 10k" "Alright,to ba damuwa,zan saka miki 40k harda kudin dinki" "Wow.....Allah ya biya, godiya nake" a cikin ranta tana jin ta samu kudin da zata biya malam harda riba. Wannan abun da ya faru a ranta sai ta sake jin me zatayi da isma'il?,mutumin da qarshen kyautar bajintar da zaiyi mata itace 10k,itama sai bisa abu me amfani tare kuma da qwaqwqwaran dalili. Tun a daren ta yankewa kanta shawarar sallamar isma'il,indai aikin malam yayi kyau Faisal yana magana zatace a saka wata biyu ma,tasan daga umma har yayunta duk a shirye suke mijin dama kawai ake jira. ********Tun da tayi sallar asuba bata koma ba ta wuce kitchen don hada abincin yara da nasu da wanda za'a kaiwa zainab asibiti. Shima saleem din da ya dawo daga masallaci zama yayi saman abun sallah yayi lazumi da karatu kamar yadda ya saba,bayan ya kammala bacci yadan daukeshi. Koda zai farka ta kusa gama sallamarsu,don uniform kawai suke sakawa,ya shiga dakin ya iskesu kowa yana saka uniform dinsa. Alhassan ya gama iftee yake sakawa socks. Su alhassan suka fara gaidashi,ganin haka kuma sun hada ido da haneefa sai itama ta matso tana gaidashi. Gefe ya koma yana karantar kowa. Tare ya canza musu uniform da komai na makaranta,amma idan kaga nasu haneefan zakayi tunanin sai da suka shekara biyu sannan aka dinka nasu alhassan,a haka ma kuma wai a wanke suke. Yana daya daga cikin abinda yasa daraja da martabar ruqayya ke qaruwa a idanunsa,sau tari idan zai canza musu abu takance yabar nasu alhassan din tunda nasu baiyi komai ba, musamman idan ta fuskanci baya da kudi sosai a hannunsa. Saidai karamcinta yakan sanya bayan wani lokaci itama yayi mata kyautar wani abun da yake kaman madadi na wannan sadaukarwar da tayi (hakan yana da kyau,bawai kice don an yiwa kishiyarki ba koda miji yadan shiga yanayi kema ko a mutu ko ayi rai sai an miki ba ke ba ruwanki,a'ah.....zuciya fa tanason me kyautata mata,sannan duk abinda ke faruwa namiji yana ankare,saidai ba kowane zai nuna ba amma a qasan zuciyarsa yasan da hakan. Bugu da qari ke kanki idanma ba zaki iya haqura ba,akwai hanyar da hankali kwance zaki fanshe kudin ba tare daya ankara ba,kema kuma baki rasa wannan darajar ba cikin wayo hikima da dabara). Da dukka lunch box dinsu ta shigi,tuni haneefa ta biyewa khalil suka dinga doka tsalle bayan sun bude sunga meye a ciki. Rabon da suje da sabon girki har sun manta,sannan koda zasuje da shi dinma ina yaga dadi da haduwar wannan. Dubansa ya maida kanta ta duqa kadan daga tsaye tana gyarawa iftee hijabinta. Yadan lumshe ido,ko yaushe abinda zai sanya yaga kyanta cikin idanunsa takeyi. Rigar baccin jikinta me wani irin taushi da sulbi sabuwa ce, gray color me wani irin daukan idanu,tabi tattausar chocolate color din skin dinta ta kwanta sosai. Baya taba gajiya da kasancewa tare da ita,koda komai bazai hadasu ba ta jingina da jikinsa kadai yana shaqar daddadan qamshinta yana shafar soft skin nata kadai yana sakashi nishadi. Hular kanta tadan zame bata,gashinta duk da baikai tsahon na Zainab ba amma yafi na Zainab bashi sha'awa da qayatar dashi. Don kafin ta karba girki shekaran jiya taje aka wanke mata shi fes aka mata stretching don ba kasafai ta fiya ma sanya relaxer ba. Qamshin hair mist kawai yakeyi da hair oil. "Zauna ki huta" ya fadi yana amsar agogon iftee da take shirin daura mata. Dagowa tayi sai suka hada ido,ta sakar masa murmushi ganin yadda yake faman qare mata kallo,har albarkatunta dake cikin riga idanunsa sai da sukakai kai "Na gode" ta fada a tausashe taja baya tana zama. Dan murmushi ya saki,qamshin kanunfari na fita daga bakinta,sai zainab ta fado masa,ya tabbatar da itace tayi masa magana a irin wannan lokacin saidai ya kauda kai. Da kansa ya kadasu farfajiyar gidan wajen driver,sai da ya tabbatar sun fice sannan ya dawo gidan da dan sassarfa,don ta riga data tsomoshi. Tana qarasa gyaran falon ya sameta tsaye gaban tv. Ta bayanta ya tsaya ya rungumota jikinsa yana cewa "Aiba wani aiki,aiki kuma ya qare,aji da dan hajiya malam saleem" qaramar dariya ta qwace mata,don ya tuna mata da tsohon sunan da ake kiransa shekarun baya "Haba malam saleem,da safen nan?" "To me zan jira?,bayan jiya qwalele kikayimin,wai ina isowa na tarar kinyi bacci ko tausayina ma bakiji" ya fadi yana shafa kafadarta har zuwa tsintsiyar hannunta. Tsigar jikinta ce ta zuba wannan ya sanyata noqe kafada "Kuma kika saka wannan rigar don kawai daukan alhaki ko?" Ya sake fada yana juyo da ita tare da saka hannunsa ya fara balle bottom na rigar. Shigewa jikinsa tayi wannan ya bashi damar riqeta sosai suka wuce bedroom dinta dake a gyare fes don dama ba ciki suka kwana ba. Yanayin bedroom din ya sake qara masa shauqi qwarai da gaske,ya tsumu da turaren wuta qwarai,hakanan bata gajiya da yiwa bedsheets pillow case da blanket dinta kabbasa. (Ko da magani sai da tsafta,ko da gyaran HQ saida gyaran tukunya,gyaran lafazin baki iya mu'amala da gyaran muhalli. Koda wadannan sai kina updating yanayin position na auratayyarku,ba ko yaushe ki shirgice ki jibge kaman kayan wanki ba,KINSAN AMFANIN DIRTY TALK?KINA MASA KO SAIDAI 'YAMMATA A WAJE SUYI MASA KINA ZAUNE?IDAN KIKA GA KUMA AN MASA KICE WANE YA ZAMA DAN ISKA MAZINACI?,BAYAN KEMA KIN TAKA RAWA?,TURQASHI.....nauyinku nakeji amma zan bincina muku kadan cikin littafin nan ta hanyar data kamata idan na samu chance😄,ragowa kuma zai shige a littafin GUDUN ƘADDARA 2024 in sha in sha Allah. *HUGUMA*👑 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 18 ________________________________ https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39 *_Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_* ____________________________ Ita ta fara ankara bayan komai ya kammala,ta tureshi tana sauka a gaggauce daga gadon "Lokaci yana wucewa fa, za'a kaiwa maman haneefa breakfast" da kallo ya bita yana dan bata rai cikin sigar zolaya "Shine kuma zaki tureni?" "Yi haquri,kai dinne....."ta fadi tana qyalqyale masa da dariya sannan ta tura toilet din ta shige. Har ga Allah batasan abinda yasa yake sake maqale mata ba duk kwanan duniya,abu guda daya ta sani,duk da maganin gyara ingantattu da take hadawa kanta ko da ta siya gurin amintattun da tasan su waye?,zuciyarsu kuma a tsarkake take......bayan wadannan ta naqalci abubuwa masu yawa dake tafi da zuciyar saleem din. Ba ruwanta da abinda ke tafi da zukatan maza,ABINDA KE TAFIYAR DA ZUCIYAR SALEEM ne kawai a gabanta (maza sun banbanta,me yiwuwa abinda ke burge wancan ba shine abinda yake burge mijinki ba,ki karanci mijinki a karan kansa,saiki tsara yadda zaki tafi dashi). Yana lalace a gurin yana tuna yadda ruqayyan ke bashi gamsuwa ta kowanne bangare tare da hasaso matsayin Zainab a duk lokaci irin wannan. Zai iya rantsuwa koda ya samu zainab din a matse,amma baya samun nutsuwa da gamsuwar da ruqayya ke bashi. Ruqayya kawai yake kaiwa ziyara ya samu hanyarta ba wani tarkace da zai dinga kawo masa tsaiko,ba dattu da qananun abubuwa bisa hanyar. Ruqayya kadai tasan salon kalaman dake sanyashi yaji ana tsinka masa tunani,kalaman da koda baiyi niyyar kasancewa da ita ba ya dawo babu shiri,kalaman da koda cikin kasuwa yake ta furta masa su zaiji bashi da sauran burin da ya wuce ya dawo gida ya kasance da ita,kalaman da zaijishi tamkar an daukeshi daga duniyar da yake ciki zuwa wata ta daban (sune dirty talk,a hausance ana kiransu da kalaman batsa,Yake budurwa?,kina yiwa saurayinki su koda shi zaki aura?,❌❌❌❌,hakan babban kuskure ne,MIJI shi kadai ake gayawa maganganu na batsa,zaki samu tarin lada me dinmbin yawa,nasan zakice kai?,a batsar za'a samu lada?. Eh tabbas!!!,muddin ga mijin da yake da igiyoyin aurenki ne guda uku,BANCE SAURAYI BA!❌. BANCE WANDA KUKA KUSA KUYI AURE BA!!!❌❌❌. Su wadannan yin wannan maganganun dasu ba abinda yake gadarwa face zallar zunubi da tarun fushin Allah,UWAYEN GIDA DA AMARE KU BIYONI👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽) (Kowacce zuciya meson bin rudin shaidan ce da kuma son jin gard'in sabon Allah,dukkanmu abinda ke mana waigi ahine tairon Allah tare da tsoron haduwa da fushinsa a ranar gobe. Duk mace ko nakijij da kika basa sabon Allah,bawai don basa so bane,ko don ba zasu iya aikatawa ba,aah.....zallar tairon Allah ne yasa akewa zukata waigi daga aikata hakan. To a wannan zamanin wata fitina ta samemu,Allah S W T ya kawomu wani lalataccen zamanin da wai DIYA MACE BUDURWA DA AKA SANTA DA TSANANIN KUNYA DA KAMEWA, KUNYAR DA HAR AKE SUFFANTA KUNYAR MA'AIKI DA MISALIN KUNYAR BUDURWA saboda sanin tsananin kunya da kamun kai da duk wata 'ya mace budurwa ke da ita. Amma anzo zamanin da yarinya zata iya baje jikinta me tarin daraja tayi hoton tsiraicinta ta turawa wani,anzo zamanin da diya macen da magana ke mata wuya gaban d'a namijin da yake ba muharraminta ba amma yanzu zata iya baje baki suyi magana akan abubuwan da wata matar auren ko zaki saka kanta gabas ba zata iya fadinsu ga mijinta ba!!!. Idan kika ga chart dinsu da ita saikin kisa sumewa. Toke ladingo kina aikin me?,ke baki b'aro zantuka ba ga ladidi can tana ware miki tufka?,me take gaya masa da ke ba zaki murje kunyarki ki gaya masa ba,BAKI AKA FIKI?,KO IYA GAYAWA MIJI BATSA AKA FIKI?. Ita zuciya tana da so da kwadayin sabon Allah duk kamewarta,saidai tuna girman Allah da girman azabarsa zai sanya ka dinga tanqwarata kana hanata abinda takeso,ME ZAI SA BA ZAKI TAIMKAKESHI BA?. Idan ma irin wamnan charts din ke burgeshi kuna zaune a falo kowa da wayarsa amma irin charts din kukeyi ke dashi. A bedroom(kuyi haqiri ta kama na gaya muku ne,saboda akwai mata da yawa da idan kikayi magana dasu akan wannan zasuce miki wallahi basusan ma anayi ba,su kunya sukeji da sauransu) irin wadannan kalaman batsan da zaki dinga fitowa baro baro kina gaya masa yana bala'in qarawa musu karsashi da kuzari me azabar yawa,sau da yawa wasu guraren cikin littafi(nawa bansan na wasu ba) zakuji nace ya rada mata wasu kalamai a kunnenta da suka bata kunya/ko ta qunshe kanta/kota gagara tsaiwa/ko ta rada masa wasu kalamai da suka sanyashi sakin murmushi/ko ya qanqameta da sauransu,dukka irin wadan nan kalamanne da bazaiyiwu ka fito ka rubutasu baro baro ba sabanin yadda wasu marubutan ke rubutasun gayansu(muna musu fata da addu'ar Allah ya ganar dasu gudun kada rubutunsu yayi waiwaye bayan dogon zamani ya tadda yara da jikokinsu ya zame musu qaiqayi koma kan masheqiya ya ruguza ginin tarbiyyar da suke gani sun bayar). Kunyar me zakiji ke da suke halal a bakinki tsakaninki da mijinki?,KIN GWAMMACE WATA TAYI MIKI SHUKAR DA BA TATA BA?. Gwara ki tare ko ina,ki tare komai. Da masu farautar sun fara gaya masa zaiga meye sabo a ciki?,ai wance tana gaya min su(kuma bayan kin gama gayan masan kin kunna abinki ga magani a gefe zaki saukeshi,wadancan kuwa idan abun yazo da sauqi basu da abinda zasu saukeshi dashi ta hanyar data dace kaman ke) zaiga meye sabo a ciki?(idan ke zazzafa ce ma kin fisu iya tsara kalaman masu tayar da hankali zaiga bashi da sauran lokacinsu). Mu cire kunya game da mazajenmu ta wannan fannin don Allah,tako wacce siga mu dinga updating muna daidaita kanmu da zamani,KOWANNE NAMIJI DAN DUNIYA NE😂(ba ina nufin duka 'yan iska bane a'ah,amma kowanne namiji yanason rayuwa yana son holewa duk taurin kansa duk miskilancinsa) kada kiga mijinki ustaz ne ko shuru shuru kice ai wane ba ruwansa wallahi KI GWADA KI GANI ZAKISHA MAMAKI MUSAMMAN A OTHER ROOM sanda al'amura suka fara tafiya(DON ALLAH KARKICE KIN TSUFA,KO MISKILI NE wallahi za'a yi babu ke,namiji baya tsufa shikam wallahil azeem,me yasa idan sun auro sa'annin jikokinsu sai kiga sun zama tabararru kuyita zaginsa?😂,tana masa abinda ke kike ganin tsufa yazo ba zaki masa ba,bayan cikin bedroom dinnan daga ke saishi,ba'a taron assembly kuke ba....ku yafemin mommies👏🏽👏🏽😄). Wanda bakinsu haya shuru kuma bance ki bawa kowa labari ba bayan kin gwada,kiyita blushing abinki idan assignment dinki ya samu nasara😄,ki sake fidda wasu hanyoyin kuma a kanki,sai shawara da zaki iya baiwa ga kowacce mace ta tsaftataccen harshe ba tare da kin bankadawa kanki asiri ba. Allah ya dawwamar damu da mazajenmu,wadanda basu da aure ya basu ikon kame kansu ya hadasu da mazaje salihai nagartattu.👏🏽👏🏽 *Ruwan wanka me kyau ta hada ta fara wanka farko. Ta sake hada wani zata sakeyi,har ta dauko sabulunta yau kadai taji qamshinsa baiyi mata ba,ya tsaya mata a hanci da qirji,saita maida ta buda shower gel dinta ta matsa ta fara wanke jikinta. Ita dinma hakanan taji kamar wari wari takeyi mata,amma sai ta kauda kai cikin hanzari taci gaba da wankan tana Allah Allah ta gama. *********Tana zaune saman gadon asibitin bayanta jingine da bango. Tun a daren jiya kawo yau idanunta da hanakalinta yana kan matar da suka kasance su biyu ne a dakin. Matar da qyar take takawa cikin takatsantsan duk sanda zata shiga bandaki,amma jikinta da bakinta sun nuna ras take,hakanan babu wani me jinyarta koda mutum daya ne,sai wasu nurses guda biyu dake shigowa suyi hira su fice. Yadda suke magana da nurses din yasa ta fahimci kamar qawayenta ne,kuma cikin maganar tasu ta fuskanci kamar dinki aka yiwa matar,saidai kuma dinki wanne iri?,shine abinda hankalinta yafi karkata akai kenan taketa da kwadayin jin dinkin meye akayi mata?. Bata tashi fahimta ba saida nurse din tazo duba dinkin. Mamaki sosai ya kamata,iya saninta masu haihuwa akewa dinki a wannan wajen,to amma ita wannan ai sam bataga alamun ciki ko haihuwa tattare da ita ba. Hasalima batayi mata kama da matan aure ba,tafi mata kama da irin matannan 'yan duniya. Bata gushe ba tana ci gaba bin qwwqwafin matar,sai ta lura manyan wayoyi ne a hannunta,hakanan manyan kudade take fiddawa tana kashewa ko a jikinta. Tuni zuciyarta tayi nisa gurin son sanin wace matar?,wanne sirrine a tattare da ita?,tayita Allah Allah hajiyayye ta fita,don ta shirya tunkarar matar qila ta samu wani haske daga gareta. Cikin sa'a hajiyayye kuwa ta fita dubiya can ward na yara,da sauri ta sauka a gadon tana daura dankwalinta ta zura slippers dinta ta tunkari gadon. Tana kashingide tana danna iphone14 dinta hankali kwance,sai ta daga kai tana amsa sallamar zainab din tana binta da wani kallo. "Sannu ya jiki?" "Da sauqi" ta amsa ciki ciki tana ci gaba danna wayarta "Ni sunana zainab,kuma nice nake jinya a dakinnan" ta fada tana murmushi "Ayyah sannu" ta sake fada ciki ciki *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 19 https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39 *_Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_* ____________________________ Ta amsa ciki ciki tana maida hankalinta akan wayarta. "Tambaya ce dani idan bazaki damu ba" "Inajinki" ta fada ba tare data sake kallonta ba "Don Allah kiyimin taimako ki gayamin meye amfanin wannan dinkin da akayi miki bayan ba haihuwa kikayi ba?" Ta qarasa fada cikin d'ari d'ari tana dubanta. Wani kallon tara saura ta watsa mata,don itakam tunda ta zauna a gurin hamamin jikinta ya addabeta,batasan uwar da tasa ta kwaso jiki tazo zata dameta ba. Ta buda baki zatayi magana daya daga cikin qawayenta nurses suka shigo "Jimmy,ya dai?,baquwa kikayi?" Maida kallonta kan nurse din tayi "Ni bansan me yake damun mutane da shiga sha'anin da bai shafesu ba....." "Wallahi ba haka bane,ina cikin kaidin kishiya ne,mafita nake nema don Allah ki taimaka ki gayamin" ta fada gabanta yana faduwa,kada taqi mata bayani wannan damar ta subuce mata. "Malama me kikeso?" Nurse din ta fada cikin sakewar fuska "Dinkin da aka yiwa qawarki nakeso ayimin bayani" murmushi ta saka suka hada ido da jimmy din,sai ta jawo kujera ta zauna tana fuskantar zainab "Wannan dinki shine kankat a fannin matsi,babu wani magani da zaiyi miki abinda kikeso sama dashi,yanansake tsuke gaban mace ya maidata tamkar budurwa 'yar sha hudu" . Tuni jikin zainab ya dauki rawa,gaba daya hanakalinta ya daga,yanzun duk wayewarta a fannin matsi akwai wani abu da yayi saura wanda batasan da shi ba?,ashe duk wayewarta bata kai ba?,koda yake dai dama shi ilimi ance kogi ne. "Don Allah malama ki taimakeni,nima inason ayimin,wallahi akwai matsala,na rasa hanyar da zan mallaki hankalin mijina,duk wani abu da mace zata yiwa namiji don ta mallakeshi ta hanyar shimfida nayi amma a banza,komai kyan magani nayi amfani da shi bana ganewa,idan kinga ya nuna jin dadinsa to sanda ya fita hayyacinsa ne bazai iya mallakar kansa ba wajen nunan jin dadin. Ni nafiso koda ba ranar girkina bane hankalinsa ya zamana yana tare dani,yana d'okin dawomin,wasu matan naga har satar kwana akeyi a kansu,amma ni koda wasa bai taba yi ba,tunda muka cinye amarci shikenan. Mijina ya auroni yana sona,ya auroni kuma don ya samu 'ya'ya dani,ni na fara haifa masa yara,amma bayan haihuwata ina yayewa saiga matsiyaciyar da ciki,wai data tashi haihuwa saiga twince,ina sake haife na biyu saiga wani cikij still ta sake haihuwa itama,wallahi malama asiri ne,ko cikin data samu aita hanyar tsubbu ne, mace batasan gyaran HQ dinta ba,batasan komai ba......kunsan Allah na fita hasken fata nesa da kusa ba,ita ko irin dan man nan da ake gogawa a murtsike baqi bata sawa jikinta,ko gashi ma wallahi gashinta baifi rabin nawa ba...." Tana cewa gashi jimmy data saki baki tana kallon yadda take zuba ratata kamar an kunna famfo ta maida kallonta ga sumartata. Baki ta tabe,ko ita da take mace tsantsami ta bata ta yaya zata burge namiji?,aba a qudundune?. "Don Allah nurse ki gayan bakya tsuke guri baka damsasashi ta yaya miji zai soki?" "A'ah babu fa zee baby" nurse ta fada tana qarewa zainab kallo a fakaice dariya da takaici suna kamata "To kin gani.....yanzu yaushe za'a yimin dinkin?,kuma nawa ne?" Ido nurse din ta dan juya "Eh to,ke zaki zabi watanni,dinkin kuma na musamman ne ai,a qalla zaki ajjiye dubu tamanin haka,don idan akayi miki kuma shikenan keda neman maganin matsi har abada,shi kansa oga idan ya kawo ziyara kullum inajin saikin taimaka masa zai samu gurbi" Duk da kudin da nurse din ta cika mata yayi yawan da bata dasu amma kuma amfanin dinkin take dubawa. Fuskarta ta yalwata sosai da fara'a "To shikenan,yanzu dai bani da wannan kudin a hannuna,amma mai gidan zai tafi umra inajin nan da kwana goma ne ko sati biyu,yana tafiya da sati daya za'a yimin kafin nan na hada kudin,sannan ma zai kasance kafin ya dawo na warke,zansan yadda zanyi zan lissafa kwanakin yabar qasar nan cikin kwanakina,yadda idan ya dawo kwanana ne " "To shikenan,ba laifi " nurse din ta fada. Godiya sosai zainab ta dinga kwarara mata,tana ji a jikinta lokaci yayi na maganin matsalarta. Wannan karon indai ta samu yadda takeso hatta saleem sai ta garashi yadda takeso,ba kullum zai samu ba,don ta tabbatar muddin yaji yadda ta sake komawa sai abinda hali yayi. Bayan zainab ta wuce bandaki duban nurse din jimmy tayi "Amma dai talatu baki da imani,yanzu don Allah don Allah inake ina wani dinki bayan ke kanki kinsan ba'a nan akayi dinkinnan ba?,nazo ne kawai nan na warke saboda kawar da hankulan jama'a?" Gyara zamanta tayi tana dariya "Allah ne kawai ya kawomin rabona har gida, karba zanyi na kankareta na dinke abinda ya samu" "Amma dai da kin gaya mata gaskiya ina ganin da shi zaifi,taje ta fara gyara jikinta,baiiji irin samamin da take bugawa ba?" Dariya talatu ta kece da ita har sai data kama bakinta ta riqe gam bayan data tuna zainab din tana bandakin "ke ni Allah yasa ma na iya bankadata,don wallahi wannan da alama can wajen ma ba sauqi,danqari!" Ta sake fada tana dariya. Tabe baki jimmy tayi tana gyara zamanta "Kyaji dashi dai,ni mijinne ma nake ganin qoqarinsa da yake iya maaja din jikinsa da nata" "Ke qazaman matannan ai jarababbun maza ne,yo ita ai na tabbatar miki ko abinci ya hanata ba lallai ta damu ba akan ya hanata abinsa,shan HARKA MEDICINE ai yafi musu komai muhimmanci koda sallah bata fiya samun lokacinsu haka ba" baki ta sake tabewa "Lallai,irin wannan ba dole mu qadangarun bariki 'yan kwalta mu qwace musu maza ba,kiga mace kamar tsohuwar jaka a gidanta amma wai a haka take so ta mallaki miji?,wata macen ko ke bakya bata burgeki wallahi bare miji. Jikina talatu duk wata sai nayi masa gyara,gyaran fata kawai fa na dubu hamsin,a turarani,a qamsasa ni,to ta yaya maza ba zasu liqemin ba?,kazo nan kaji lumus,can qamshi can taushi,ka koma gida ka tarar da qamaya maya........Da anyi motsi mace take miki namiji bashi da adalci,namiji dan kunama ne,namiji bashi da mutunci,namiji batulu ne da sauransu,bayan ke kika siyawa kanki,habba.....muddin akwai mata irinsu zainab a duniya to kasuwar karuwai ba zata taba mutuwa ba" Dariya talatu ta saka "Yo yanzu wannan kika jera da ita ai cewa za'a yi 'yar aikinki ce" "Allah ya kiyaye,wallahi ko masu aikina basu isa su zauna da irin wannan qazantar ba" jimmy ta fada tana kyabe baki alamun mugun tsantsami ya kamata. Ranta fes ta koma gadonta,duk bayan mintuna biyu saita kalli jimmy ta sakar mata murmushi tare da yi mata sannu. Gaba daya jimmy ta gama tafiya da ita,jikinta ya bata tsabar yadda HQ dinta ke a gyare ne take juya gidanta, don da ganin kura taci mutum,yadda jimmy din keta wayoyi cikin isa da qasaita y tabbatar mata isassar macace ita a gidanta,kuma komai tace tanaso zataji nurse tayi sallama ta miqo tace inji wane,hakan kadai ya isheta amsa. Murmushi ya kubce mata,Allah ya nuna mata wannan ranar,ranar da saleem zai dawo tafin hannunta,dole ruqayya ta dandana kudarta yadda ya kamata. Tare suka jero shi da ita cikin asibitin,yana riqe da kwandon kayan abincin tana a gefansa. Kallonta yayi kadan ta gefan ido "Yane?,tunda muka shigo naga kinata faman toshe hanci?" Fuska ta yamutsa tana sake jan gyalenta zuwa hancinta "Warin asibitinne baiyimin ba,sai shigarmin hanci yakeyi yana damuna" ta fada tana jin har cikinta yadda yake hautsina mata 'yan hanji. "Sannu,ai ba jimawa zamuyi ba,nasan sallama likitan zaiyi" "Ba komai" ta amsa masa tana sake toshe hancinta da kyau. Sallamarsu ita ta farkar da ita daga saqar da takeyi cikin mugun zare. Tare suka daga kai da jimmy kowa ya amsa sallamar gwargwadon muryarsa. Fuska zainab din ta tsuke ganinsu tare,ranta ya raya mata ita ta riqeshi basu fito ba sai yanzu har qarfe goma. Qarasawa ruqayyan tayi ta jawo kujerar da hajiyayye ta tashi dazu a kai zuwa gaban gadon tana cewa da saleem "Bismillah" kwandon ya ajjiye "Kai haba,nifa namiji ne,zauna kedai" "Muna gaisawa zan baku guri ai,ka zauna kafijin dadin dubata" "Dubiyar kukazo ko wasan kwaikwayo?,ko baqincikin daka saba cusan na jiya da ba'a cusan ba aka biyoni asibiti a cusamin" zainab ta fada tana hade fuska kaman zataci babu. Bai dubeta ba yaja kujerar ya zauna,ruqayya ta matsa gaba kadan tana cewa "Sannu maman haneefa,ya jikin?,Allah ya mayar kaffara" "Gani me tulin zunubi ba,dole ki kiramin kaffara ga bijirarriyar musulma" ta maida mata cikin zafi. Kullum sai taga wata sabuwar suturar a jikin ruqayya,kullum walau a cikin gida ko a waje ruqayyan cikin ado da sauya suttura take. Tayi ado duk da baby kwalliya ko kadan saman fuskarta amma adon dake jikinta zaka tsammaci bawai asibiti zataje ba "Zunubi kam aikowanne bawa yana tattare dashi,saidai ka zama me neman yafiya wajen Allah" ruqayya ta maida mata tana takawa a hankali tana barin wajen don ji takeyi kamar amai zai taso mata "Idan baka zalunci bayinsa bafa" zainab din ta fada cikin son maida raddi "Ya isa haka,likita ya shigo?" "Eh ai bazai zauna jiran zuwanku ba,yace qarfe sha biyu zai sallameni idan likitan rana yazo" ta fada tana hade fuska. "Sannu" ruqayya tace d jimmy sanda ta isa daura da ita zata zauna a kujerar da take a wajen. "Yauwa sannu" jimmy ta amsa da fara'a sassanyan qamshin dake tashi jikin ruqayya na burgeta(qamshi fa yana jawo maka farinjini a wajen mutane tabbas,ku zama masu qamshi don Allah yan uwa mata😄). Haka kawai taji ruqayya ta burgeta,tuni kuma ta fahimci itace kishiyar da zainab ke qorafi akai "Kayyasa,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa ai" ta fada can qasan ranta. Tazarace mabayyaniya me dimbin yawa tsakaninta da ruqayya. Ko a yanzun taga dabbanci da hauka a wajenta. Sun iso ruqayya na tattalinsa duk da tare suka kwana,ke anzo dubaki ba wani feleqe ba komai,jiya baki wanka ba me makon yau kafin su iso ko fece jikinki ko yaji dadin kallonki amma kin zauna kamar tsumammiyar jaka,sun iso da kayan abincin ba gaisuwa ba ya ka kwana ba sannu ba godiya kin buge da qorafi ke 'yar sakin zuciya,kamar ke kikafi kowa zuciya,BA KISSA BA SIYASAR ZAMA DA MIJI BA TSAFTA BA MAGANA ME DADI amma tsohuwar ballagazar dinki take buqata ayi mata, tabdijan!,Allah yasa ranar farko ya balle matsiyaci!. Jimmy ta raya a ranta dariya na balle mata har sai data toshe fuskarta da pillow. Tunda ruqayyan ta fidda wayarta take danne danne abinta,ko sashen da suke bata sake kalla ba bare taga abinda ranta zai baci. Yanayin basarwarta da kawaicinta ya sake burge jimmy qwarai,ta tabbatar da wata ballagazar ce itama da tuni tana gabansu ta kafa ta tsare,zainab zata yita yin abu da gayya ita kuma nata ran yana baci. A hankali ta dafe qirjinta saboda taso mata da amai yayi. Jimmy daketa aikin jarida tsakaninsu ta kula da haka,saita aje wayar hannunta "Lafiya?" Dan murmushi ta sakar mata "Lafiya ba komai,na gode" "Kaman yunqurin amai naga kinayi,ga leda don kada yazo bagatatan ya bata jikinki" jimmy ta fada tana cire wata leda da aka siyo mata gasashen nama a ciki ta bata. Qamshin Naman da ya daki hancinta ya sanya tasowar amai din gaba daya,tasoma kwarashi cikin ledar. Qarar aman ya jawo hanakalin saleem da Zainab,saleem din ya miqe da wani irin gaggawa ya isota yana tallafeta. Zainab na zaune ko motsawa batayi ba,wani abu ne kadai ke yawo mata cikin kai "Ruqayya da amai?,tabbas amai na daya daga cikin manya manyan sign na samun cikinta,cikine da ita?,ciki fa!!" Ta fada cikin zuciyarta wani tashin hankali yana zarto mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa yanzun qafafunta. https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 20 _Wai Allah🤦🏽‍♀️🤦🏽‍♀️,da qyar na qwaci kaina nayi wannan,ayimin afuwa don Allah,zainabu na gaisuwa ga jama'arta😂😂_ Gaba daya sai ta koma kamar mutum mutumi,ta dinga binsu da idanu harta gama aman,jimmy da tafi kusa da ita ta bata ruwa ta kuskure bakinta,saleem ya karba ledar ya qulle ya yar. "Danqari!!,ana dara......." Zainab ta fada cikin zuciyarta wadda keyi mata suya "Inaga kamar akwai likita ko?,muje ya dubaki karmu wuce gida abun yafi haka" saleem ya fada cikin kulawa ganin yadda jikinta ya saki. "Allah ya sawwaqe" jimmy ta fada tana komawa gadonta "Ameen na gode" ruqayyan ta amsa mata tana fita a dakin. Batasan ya suka qare ba,ya kusa mintuna uku sannan ya fito suka wuce karban file. "Kinga irin zallar rashin adalcin da ake gwadamin ko?" Zainab da idanunta suka cika da hawaye tace da jimmy "Ummmm,na gani" ta amsa mata tana bata haushi saboda yadda ta karanceta,sam bata iya mu'amala da miji ba,maganganun data gaggasawa saleem kafin ya fita ta tabbatar inda wani namijin ne me saurin daukan mataki daga nan saidai tayi gidansu,kai koda a dadiro ko dandi ne tabbas ba abinda zahana ya lakada mata na jaki har dai an qwaceta. Amma maganganun da ya dasa mata a rai da me hankali ce ita ya kamata taji zafinsu ne ta kuma dauki haske. "Banda aikin asiri.....kazo dubaninamma idanunka ya rufe ba tani kake ba?,don kawai tayi amai?" "Ai aman kawai ne?,bashi kikeyi ba ke sanda aka kawoki asibitin nan?" "Eh amma ni harda gudawa" "Baiwar Allah ai ciwo ciwo ne ko?,sannan nifa a nan banga aikin asiri ba,kawai dai ta fiki sanin kanta ne da alama" kamar cakewar mashi haka maganganun jimmy suka tsaye mata a rai,ta zuba mata fusatattun idanunta tana kallonta. Banda tana tsoron kada ta yiwa kanta sanadin dinkin da za'a yi mata wallahi da sai ta gaggasa mata maganganu "Ban gane nufinki ba" "Maganata a bayyane take ai,baki iya kula da mijin ba,baki da lafazi baki da mu'amala,sannan ki kalli jikinki da nata daya ne?" Jimmy ta fada kai tsaye tana kallon cikin idanunta. Dif sukayi su duka, abinda ya kawo katsewar maganar tasu shigowar hajiyayye, jimmy ta dauke kai taci gaba da harkokinta. Bayan duka tambayoyi sai aka bata gwajin PT don alamu sun nuna hakan. Gwajin kuwa ya fito da sakamakon da ake zargi na juna biyu. A take akayi mata scanning don duba baby. Scanning din ko ya bada sakamako me ban mamaki. "Cikinki ai yayi wata biyu harda rabi ma,kuma dukkan wasu alamu sun nuna twince ne,matso ku gani" likitan ya fada yana zooming scanning din. Wani mugun sanyi jikin saleem din yayi,ya dinga jin tsoron Allah yana ratsashi,anya ruqayyan ba wani matsayi gareta wajen Allah ba da yakeson nuna masa ishara?. Duk wani gwaji anyi ance ruqayyan sam bata taba haihuwa,amma cikin hikimar buwayi gagara misali sai gashi yanata nuna ayoyinsa. Ita kanta a karan kanta sai ta dinga jin girman Allah da girman al'amarinsa yana sake shigarta,ta dinga tasbihi a gareshi tana jin zuciyarta tana tsinkewa "Ki yafemin don girman Allah,saboda bansan me ubangiji yake nufi da hakan ba" saleem ya fada yana tsugunnawa a gabanta harda hade hannayensa biyu "Na yafe maka fa,na yafe maka tuni,komai da ka gani muqaddarine daga Allah" ta amsa masa tana jin nauyin duqa matan da yayi. Kafin su dawo hajiyayye tayi parking kayansu gaba daya saboda anyi sallama,wanda inda ta biyewa zainab motar haya zasu tara su wuce gida ba tare da sun jirashi ba. Tanata kumbura tana wani babbankewa ta wuce gaban mota. Itakam ruqayya ma dariya ta bata,yanzun ita kuma me ya rage mata?,Allah ya mata komai na rayuwa da mace keda burin samun bakin gwargwado,saidai ci gaba da neman qari. A gidan duniya rashin zuriya ne damuwarta,sai gashi Allah ya wanke mata hakan y bata ya bata ya sake bata wasu. Koda suka wuce gida bangarenta ta wuce kai tsaye abinta saboda sam batajin qwarin jikinta,gaba daya tunda tayi aman kamar laulayin aka zuba mata,zainab kuwa suka wuce da hajiyayye nata sashen,wadda ta matsa ta biyota din,tunda daima tasan nan da dan kwanaki saleem din zai wuce umra shi da hajiya. Tace dai iya yau zata zauna din,idan ya tafin ta dawo. Tunda ta zube a kujerar falon nata take saqawa take kwancewa,gaba daya komai yana neman qwace mata,wannan cikin na jikin ruqayya ya zame mata qadangaren bakin tulu,ya akayi har ruqayya ta rigata samun cikin ita tana zauna?,bayan ta shigo ne don ta haihu?,don ta cika gida da 'ya'ya ta yadda gida zai zama nata sai yadda tace?. Duk yadda hajiyayye takai ga aiki sai data sare,da farko ta dauka lalurarta yasa sashen nata yake kaca kaca haka,saita zage ta fara gyarawa. Saidai sai data fara gyaran ta fahimci lallai shayi ruwa ne,don kuwa tsohuwa kuma tsumammiyar dauda ce danqare a sashen. Iya dakinta da kitchen ta gyara ta dawo ta zauna tana maida numfashi,ta dubi Zainab dake a jabe "Gaskiya magana ta Allah muddin ba zaki gyara wannan annamimiyar qazantartaki ba to kin shiga uku wallahi,aiki tun kana na marmari har ya koma maka na jaraba?,yanzu don manzan Allah uban panties da kika tara a bandakinki cikin bathtub na meye?, harda me jini a jiki fa?" "Don Allah kada ki qaramin tension akan wanda nake ciki,haba mana,ki barni naji da abinda yake damuna" "Kiji da abinda yake damunki nima zanji da nawa,don wallahi gida zan wuce,kuma ko ya tafi indai kinsan baki kwashe kayan qazantarki kafin nazo ba kada ki kirani" "Haba dan hajiyayye zo mana" zainab din ta fada tana sasaautowa,don tasan ba wanda tafiyarsu zatazo daya da ita sai hajiyayyen "Kiyi haquri raina ne a bace don Allah" "Sakeni" ta fada tana zare hannunta ta koma kitchen din tana qunqunin mita "Dadina dake shegiyar mita wallahi" zainab din ta sake fada tana jan tsaki hadi da hararar inda hajiyayye ta wuce,saita gyara zamanta tana ci gaba da qulla wadda take ganin zata fishsheta. Tunda ta zauna wajen ta gaza motsawa,gaba daya komai ji take ya dagule mata. Ba irin tunanin da bata saqa ba akan cikin ruqayya,har addu'a take cikin ranta "Ya Allah kasa zuwa gobe da safe ta hadu da mummunan tsautsayin da zai kawo sanadin zubewar cikin". Duk zaman da tayi a wajen ta rasa wanne zata kama?. Dagewa zatayi tayi ciki?,ko ta bawa banza ajiyar saleem din ta dage tayi ciki?,idan ta haihu sai a dinketa gaba daya?. Tafi gasgata wannan shawarar kuma tafi yarda da ita,don haka dab da magariba ta miqe daga wajen data jabe ba azahar ba la'asar,duk da yadda hajiyayye keta fama da ita ta miqe din,ta wuce bedroom dinta ta wawwatsa ruwa don sauri takeyi kafin ayi kiran sallah ya zamana ta fito kafin salim din ya shigo gurinta. A gurguje ta biya bashin sallarta,sannan ta bude locker dinta tayi hadin magunguna,tana ji a ranta zata sake dagewa da gyara,don ta shirya samun ciki a wannan dan tsukin,idan so samu ne ma kafin yakai ga wucewa umra. Wata rigar shadda ta saka,wadda wuyan da fadin yadanyi mata yawa saboda sanda akayi dinkin tana da ciki tayi qiba sosai,yanzun kuwa ta zazzage ta koma ainihin jikinta. Ko kadan bata fiya damuwa da sauyawar fadin rigar ba saima jinta sakayau da takeyi saboda wankan da take jin tayi,sannan kuma aka dace shaddar wankakkiya ce,duk da babu shaidar guga a jikinta ko na gamin gafara. Parlor ta fito ta samu hajiyayye tare da yaran tanata fama dasu wajen gyara musu yanayin cin abincinsu,yau sashen fes yake hakanan abincin yau da hankalinsa,saita hakimce saman kujera tana dakon shigowarsa,a hankali tana jin maganin yana mata aiki,cikin qasan ranta take fatan inama ace a wannan daren ta samu rabo itama?, tabbas a yanzu 'yan biyu sune burinta,kai idan da hali ma guda uku zata roqa,so take ruqayya ta tabbatar da cewa da gaske fa gida ya zama nata,qila hakanne kadai hanya guda daya da zata saka ta saduda. *Kuyi manage,mu hadu gobe in sha Allah,na gode da haqurin jirana* *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 21 Kusan tunda ya ajjiyesu ya fita yake fama da ciwon kai. A haka dai a daddafe ya zauna a kasuwar saboda lissafin shago sukeyi na qarshen sati,dole kuma akwai buqatar ya zauna din gudun rubuta kuskure. Sanda ya qaraso yaran suka baibayeshi suna masa sannu da zuwa. Bai taba shigowa gida bannu haka ba komai,duk qanqantar abu sai ya kawo musu tsaraban kasuwa(wannan halayya ce me kyau,tana qara danqon soyayya tsakanin iyaye da 'ya'yansu,iyayenmu na da zaiyi wahala kaga sun shigo gidansu haka,koda ma'aikata bare 'yan kasuwa). Kai tsaye ya kama hannun iftee suka wuce sashen ruqayya yana tambayarsu mamar tasu "Daddy tana kwance tun da safe,mommy kamar bata da lafiya" iftee ta fada cikin karyar da muryar "Batajin dadi amma zata warke very soon in sha Allah" ya fada yana murmushi. Sanda suka shigo ta gama alwalar sallar magariba dake gabatowa tana sanya hijabinta "Sarkin tsafta"ya fadi a ransa,duk da batajin dadi amma sashen fes yake kamar kullum. Fuskarta dauke da murmushin nan take dubansa "Sannu da zuwa" ta fada "Yauwa,ke za'a yiwa sannu maman wasu twince din in sha Allah" yaran tadan kalla ta gefan ido tana bude baki kadan "Daddy,bakaso na huta" "Hutun me?,me ya rage banda ki cikamin gida da yara,inaso na ganni da yara masu yawa Allah ma ya sani,sai gashi Allah ya qaddara zaki zama uwar 'ya'yana" "Uhmmm,yau kuma ni za'a baiwa wannan matsayin kenan" tayi maganar tana zura hannun hijabinta. Dan kallonta yayi sai ya basar,yasan gori takeson yi masa "Baki da mantuwa" ya fadi qasa qasa sanda yake zama hannun kujerar dake daura da ita,saita daga kanta,har zatace wani abu kuma sai ta fasa "Baka da lafiya" ta fada a hankali. Idonsa ya lumshe yana jin qaunarta har qasan ransa,ita daya ke da qarfin maganadisun iya karantar kowanne motsi nasa "Kaina" ya fada a taqaice "Subhanallah,daddy bakason shan magani,tsaya kasha magani don Allah" ta fada cikin nuna maqurar damuwa "Ki barshi idan na huta zan koma normal " kai ta girgiza cikin narkewa "Kada muyi haka da kai daddy,yanzun idan wanine yace hakan sai kayita fada,mu shikenan ba zamu kula da lafiyarka ba?,waye muke dashi mu da yaranmu sama da kai?" Idanunsa da ya zuba mata ya lumshe gami da sakin murmushi "Shikenan ranki ya dade" yadda ya kalletan taji kallon har cikin jikinta,idanunsa mada matuqar tasiri har yanzu ga zuciyarta. Ba jimawa ta dawo da maganin ta balla ta miqa masa hade da gorar ruwa,baikai ga sha ba saiga haneefa Ibrahim yana biye da ita suna raba ido. Koda basuce komai ba tasan turosu akayi suyi CID,don haka tana gama bashi maganin ta juya daki dasu,shi kuma ya waiwaya yana dubansu. Kallon shi kadai yasa suka gane laifinsu,suka koma da baya suna sallama,ya amsa yana miqewa,ruqayya ta qaraso da abun sallah "Na gode" yace yana yin waje "Wajibina ne" ta amsa masa tana shimfida abub sallar. Yana sallama da ita ya fara cin karo,sai cika takeyi tana batsewa hadi da kumbura. Yi yayi kaman bai ganta ba,yayi sallama yana saka kai falon. Hajiyayye ce ta amsa ta miqe tana masa sannu da zuwa,ya amsa yana zama cikin kujera,har zuwa sanda hajiyayye tabar musu gurin. "Sannu da zuwa" ta fada ciki ciki kamar wadda aka yiwa dolen faden "Yauwa,ya jikin?" "Ka damu ka sani ne?,tunda tunda ka tafi baka ko kirani ba,ka dawo kuma kaje ka zauna a wajen wadda ba girkinta bane" ta fadi cikin hasala. Idanu ya zuba mata kafin ya janyesu "Wannan qorafin idan da sabo ya kamata bakinki ya gaji da fadinsu,kullum ke kenan cikin qorafi akan na shiga ganinsu?,bayan ita ko sau daya bata taba qorafi akan shigowata wajenki ba?" "Eh dama mana ai bazatayi ba tunda tasan tana cutata" ta fada tana gyara zamanta da alama da gaske ta shirya tayita zabgo qorafin. Ganin hakan sai ya miqe tsam kawai abinsa yana wucewa bedroom dinsa,cikin ransa yana mamakin yadda yau sashen yake fes. Amma yana shiga dakinsa ya tabbatar ba itace tayi gyaran gidan ba,don bedroom dinsa yadda ya tafi ya barshi ranar data fita a girki haka ya dawo ya sameshi. Da hannu ya tattara tarkacen ya zauna gefan gadon yana jira maganin ya ratsashi. Tsahon wasu mintuna zuwa sanda yaji an fara kiran sallah ya miqe ya wuce toilet ya daura alwala sannan ya fito don wucewa masallaci. A inda ya barta a nan ya sameta ita da hajiyayye,dama ita din tun da batasan wai tabi miji daki ko ta kebe dashi idan ya dawo daga aiki ko wani guri ba,saidai ya qaraci gararambarsa ya gaji "Ki shiga ki gyaramin dakin nan" daga kai tayi ta kalli hajiyayye "Don Allah qarasa ladanki mana 'yar hajiyayye" ta fada tana karyar da murya alamun lallashi. Kai hajiyayye ta daga suka hada ido da saleem saita sunkuyar da kai. Bai dauka haukan Zainab yakai har haka ba da zata aika masa bazawara gyaran dakinsa. Wani kallo ya jefeta da shi ya saka kai kawai ya fita a sashen. Karfe goma na dare ta shiga bedroom dinsa, idanunta a kanshi yana zaune daga gefan gadonsa yana dan duba waya sama sama,shigowarta sai ya kammala abinda yakeyi din ya ajjiye wayar. Idonsa yadan lumshe saboda yadda yakeji yana dan sara masa,a hakan maganin da ruqayyan ta bashi ya sassauta akan lokacin da ya shigo gidan,sai ya maida bayansa yadan jingina da gadon bayan ya zame kadan ya kwanta a rabin gadon bayansa. Lokaci lokaci yana karantarta sanda take shige da ficenta abunta,ko sau daya bata nuna ta fahimci wani rashin lafiya tattare da shi ba,duk da ko abinci ma kadan yaci don ruqayya yau bata samu zuwa cin abincin ba,to shi dinma bakinsa ba taste shi yasa bai samu ci da yawa ba,kota wannan bangaren a nasa ganin ya kamata ta fahimci akwai abinda yake faruwa amma hakan bai samu ba. Ita kawai sabgar gabanta take,sauyawar miji ta kowacce siga bata daukeshi wani abu da za'a bawa kulawa ba. Ta nata bangaren Idanunta a kansa jifa jifa tana satar kallonsa,ranta da zuciyarta ba abinda suke raya mata illa sauyawarsa na da nasaba da son bijire ma buqatarta,ita kuma taci alwashin ba zata lamunci a danne mata haqqi ba,ire iren wadan nan abubuwan ma qila suna daya daga cikin sanadin da ya sanya ruqayya ta rigata samun wani cikin. Gadon ta iso ta zauna daga bayansa,zuwa sannan yaja blanket ya rufe har kafadarsa saboda sanyi sanyi da yakeji na alamun ragowar zazzabin jikinsa bai tafi ba "Ina da buqata" ta fada sankankan kamar me bada labari. Ya dade da sabawa da wannan halayyar tata,sam bata da wani salon nunawa me gida buqata data wuce wannan "Banajin dadi yau,nasha magani ina buqatar na huta" wani abune yazo yayi mata tsaye a wuya. Ji take zuciyarta kamar zata fashe "Eh,ai dama na fuskanci take takenka,to ko baka da lafiya nidai haqqina nake da buqata" waiwayawa yayi kadan ya dubeta da kyau "Kizo ki qwata idan kina iyawa" ya fadi cikin matuqar maqurar jin haushi. Mutum kamar dabba,ace ko da yaushe shi kam baisan dai dai da ba dai dai ba,yana takaicin yadda sam zainab bata gane lafiyarsa da lalurarsa indai ba kwanciya yayi magashiyyan ba,koda yaushe tata buqatar ce s gaban tasa. Bai gama wannan tunanin ba sautin kukanta ya karade masa kunnuwa,cikin muryar kuka take cewa "Ai dama na sani,koda baka fadi haka ba komai ya fito a aikace,ni nasan dama da gayya ka yiwa ruqayya ciki ni baka yimin ba,to nima ciki nake da buqata haihuwa nakeso,banda ma rashin adalci ni da nake gyaran nan aini yafi cancanta ace kafi maqalewa,ni ya dace ace ina da ciki,amna saboda anqi Allah anqi ma'aiki sai gashi me ciwo daban me shan magani daban,Allah zai saka min" tana kaiwa qarshe tana sauka daga gadon. Wani dadi yaji yana ratsashi bayan tayi zuciya ta fita a dakin,ko banza zai samu yayi bacci cikin salama,don haka ya sauko a nutse ya murza key ya rufe dakin ya dawo gadonsa yayi kwanciyarsa,idanunsa a rufe amma cikin zuciyarsa yana wassafa irin kulawar da zai samu inda ace kwanan ruqayya ne. *******A harzuqe ta tashi washegari,don ko dakin bata leqa ba bare ta gaidashi. Abunda ya sake dugunzumata kayan da tayi order tace tanaso da sunan kayan sallan yara da nata sun iso,saidai kuma babu kudin da zata biya ta karba don duk sun tafi. Ita daya ta dinga qullawa tana kwancewa,tasan tabbas dole kafin saleem din ya wuce umra zai nema ganin kayan kowa,ita kuwa abun kunya ne ruqayya ta fiddo nasu ita ace ba abinda ta da nata sunbi ruwa. Sai wajejen sha biyun rana ta shiga a tsaitsaye ta gaidashi,ta samu ya fito a wanka ma yana shiryawa,gefe guda kwanukan abincin data aika haneefa takai masa ne na safe,da alama ko tabasu baiyi ba bare yaci abinda yake ciki. Zuwa azahar ya fito da shirin fita ya ajjiye mata kudin cefane ya wuce. Qaramin tsaki taja sanda yake ficewa,ta dauki kudin tana juyasu sannan ta ajjiye. Daidai sannan kira ya shigo wayarta. Kiran raliya ne,abinda ya sanyata nutsuwa kenan ta kuma amsa kiran ba bata lokaci. Qasa qasa takejin muryar raliyar,don sallamarta ma kaman a jigace take "Me ya sameki ne raliya?,bana jinki sosai" "Hala bakisha magungunan gurin basira ba?" Raliyan ta tambayeta tana numfarfashi "Niko nasha don jiya ma kwanan asibiti nayi maimakon kwanan turaka" "Madalla,mun samu qarin shaida,ashe matar nan bugaggiyar macuciya ce?,kin ganmu yanzu haka gidanta muka nufa, billahillazi saita fito mana da kudadenmu,ashe ita ke hada abinta a gida da duk abinda taga dama" "Kan uba,lallai biri yayi kama da mutum,jiya da qyar na qwaci kaina raliya....." "Ai ba'a bori da sanyin jiki,ki fito kawai mu hadu mu wuce gidanta,saita fito mana da kudinmu" "Yanzu kuwa,mu zata gwadawa shegantaka?" Ta fada tana katse wayar. Tsam ta miqe,ta danyi tunanin wacce qarya zata yiwa saleem ya aminta da fitarta?,don tasan ko giyar wake tasha bata isa ta cewa saleem wai kudi maganin kayan matanta zata amso ba. Lokaci ta duba,wata zuciyar ta gaya mata har taje ta dawo ba lallai saleem ya dawo ba,tunda idan ya fita bai dawowa sai magarib,ita kuwa me zata zauna ma tayi har magariba. Idan tayi wuta takai yamma,don ruwa ruwa zata zubawa basira rashin mutunci ta bata kudinta ta wuce,ta samu ta sissiya wasu kayan da zata nunawa saleem. "Umma ina zaki?" Haneefa da tayi tsaye a gabanta ta zuba mata ido tana kallonta sanda take gyara zaman hijabin wuyanta ta fada "Ku zauna keda.khalil,ko farfajiyar gidannan bance ku fita ba,yanzu zanje na dawo" tura baki gaba yarinyar ta fara yi tana qunquni har uwar ta fice daga gidan. Bata ma iya isa gidan raliya ba ta tsaya daga titi yayi mata waya,ba jimawa sai ga raliyan tana tafiya iska na kadata,ta zabge lokaci daya da alama taji jiki itama yadda ya kamata. Ba wanda ya iya magana a cikinsu don kowa idonsa ya gane masa,sai me napep kawai da raliya ta tsare musu, raliyan ce ta bashi kwatance sannan suka hau tana daukan wayarta tayi kira ta kara a kunne "Rabi gamu nan akan hanya.....uhummm" ta fada tana yanke kiran. *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 22 Kusan dukansu a galabaice suke daga ita har raliyan,saboda ba wanda baiji jiki a cikinsu,wannan ya sanya ko hirarma sama sama suke tabata,har zuwa sanda me napep din ya ajjiyesu a qofar gidan. Zainab ce me qwari qwari a jikinsu,ita ta zaro kudin ta miqa masa yayi gaba. A qofar gidan suka samu rabi ita da wata,su dinma kana kallonsu kasan anji jiki "Mu shiga kawai,mu shiga" Zainab da takeji kudinta kamar sunfi na kowa yawa ta fada,ko banza tana saka ran samun koda rabin kudinne idan ma duka basu samu ba. Tun daga soron gidan zakasan cewa tsafta ta tattara kayanta tayi gabas da gidan,tako ina sunyi hannun riga basa hada hanya ba. Hatta da Zainab yau d'ari d'ari takeyi kada ta taka kashin kajin dake karakaina abinsu cikin soron. Sanda suka amsa sallama kuwa basira data karkace a gefen kwatar data raba gidan biyu tana dahuwar kaza sam bata jiyosu ba. Hasalima waqe waqe take abinta cikin nishadi gami da jin dadi,gefe guda kuma tana jin zuciyarta tayi fess,saboda dawa tayi nama,domin kuwa dubu sha biyar ta karba a dahuwar kazar da duka dukanta naira dubu daya ce,sai tarin tarkacen magungunanta da suke amfani dashi ita da yara da ta yiwa gamje gamje ta zuba suka bada taste mara dadi,wanda shi makamin da zata bada hujjar cewa kazarta tasha hadin maganin mata me inganci. Cikin rawar jiki da washe baki ta miqe tana musu sannu da zuwa,cikin ranta tana jin yau farar rana ce a tare da ita,don dukkansu ba wanda bata samu kudi dashi ba "Sannunku da zuwa customer,eh lallai magunguna sunyi aiki, emergency ya kawo wuta yadda ya kamata,sabon hadi kuka zo ayi muku kenan......ahayyeeeeee cassss,saini basira me gyaran turaka......" "Ke da'alla malama ki yiwa mutane shuru ko na zazzabgeki da mari,macuciya azzaluma,ke kisa kikeyi ma inajin,kin bamu abinda kadan ya rage kwananmu ya qare" baya basira tayi baki galala tana qarewa zainab kallo "Ban fahimceki ba me kike nufi ne baiwar Allah?" "Koma meye ki shiga ciki ki lalubo mana kudadenmu da dukiyoyinmu da kika karba billahillazi ko na lahira ya fiki jin dadi" "Ahto,don ba zamu dauki asara goma da ashirin ba,ba wan ba qanin?" Raliya da qafarta ke rawa saboda rashin qarfin jiki ta fada rai a bace ta biyo bayan abinda zainab ta fada tana kada hannu. Guda basira ta saki tana yarfa hannu gefe guda "Ni zaki shigowa gida ki yiwa barazana?,to anqi a baki dukiyar taku....nace anqi a baku din duk abinda zakuyi kuyi" bacin rai da kuma ganin samu da rashi duka lokaci daya yasa idanun zainab suka rufe,ta tunzura da maganganun izgilanci da rainin wayon da basira ta fara kwararo musu,sai kawai ta kaiwa basira duka. Cikin tsananin sa'a kuwa ta sameta a fuska,ji kake qummmm...... Wani razanannen ihu basira ta saki tana dafe da fuskarta "Da kin dauka da wasa mukeyi miki 'yar rainin hankali,maza wuce ki dauko mana kudadenmu tun ban canza miki kamanni ba" "Ni kika yiwa wannan dukan?" "Nayi miki kuma na daki banza" "Wallahi wallahi sai kinsan ba kowa ake tabawa a kwana lafiya ba" basira ta fada tana juyawa afujajan zuwa dakinta "Duk abinda Zakiya kiyi,ina nan ina dakonki,karki fito saida kudina" zainab din ta fada tana huci gami da jan kujerar tsugunno da basira ta tashi a kai tana ci gaba da hayagaga da kumfar baki. Har kusan minti biyar shuru babu batun basira suna tsaye carko carko suna maida magana a tsakaninsu. Rabi ce ta dubesu cikin qosawa "Ko zuwa zamuyi mu tafi matar nan ba ita ba dalilinta fa,kada muje ta shirya mana sharri" "Wallahi indai ba batan dabo tayi tabar gidan nan ba inda zan motsa sai kudina sun fito,ta gama zamanta ta fito ta sallameni koda kuwa ku tafiya zakuyi,ni na fita bariki wallahi" zainab ta fada tana tafa cinya,tana jin kamar ta jawo basira ta bata kudadenta. Ko minti biyar bata rufa da rufe bakinta aka bubbuga qofar gidan da qarfi,ta bude baki zatayi magana cikin fusata sallamar wata mace me gurbatacciuar hausa ta sauka a kunnensu. Gajeriyar macace sanye da kaki na 'yan sanda(uniform),baqa me fadi da qiba,tana takowa tinqis tinqis "Hajaju........hajaju woooo" ta fada tana leqe leqe cikin gidan "Madam,ganinan,bazan iya fitowa ba,ko tashi bazan iya ba,haduwa sukayi suka yimin dukan tsiya,kin ganni a yashe a daki" maganar ta basira dake kwance a daki ta sanyasu kallon kallo a tsakaninsu,suka kasa cewa komai,saidai kowa zuciyarsa ta cika da tsoro "Aeaeaeae........sune wadacan mata na sakar geda ko?" "Sune madam,sune" basira ta fada tana nishin qarya "Angama" macen dan sandan ta fada tana fitowa. Da daya da daya ta qare musu kallo tana muzurai idanunta a kansu "Ku wuce mu tafi lafiya Allah ko na saka muku karfi" tace dasu "Ina zaki kaimu madam?,me kuka mukayi?" Zainab tayi qarfin halin tambaya "Tambaya na ma kikeyi?,to wa yabaki izinin shigowa gida ku dadaki matar gida kuma ku zauna a ciki ba izininta?" "Mu bamu daketa ba,kuma hakkinmu mukazo karba" zainab ta amsawa matar "Hey shut up stupid,naga alama kin fisu kwarin ido......hey. ... Samuel shigo ciki" matar ta fada cikin dan daga murya,nan take saiga matashin dan sandan ya sako kai,ya kuma taimaka mata suka tasa qeyarsu zainab sai police station. ****Tunda yace mata zaizo ta kasa zaune ta kasa.tsugunne,kusan ta manta rabon da faisal yace mata zaizo gidansu,ko yanzun ma tafi gasgata cewa aikin malam ne ya ciyoshi,don kuwa tayi dahuwar borkono tsidugu da rubutu,ta saka wuqa a garwashin wuta me dauke da sunansa,hakanan tasa anyi hatimi wanda aka buda aka rubuta sunansa a tsakiya dukka dai gaba daya domin azalzalo zuciyarsa,sai gashi cikin nasara da bakinsa ya furta zaizo din,bayan yazo din kuma yace akwai maganar da zasuyi wadda jikinta da zuciyarta sunfi gasgata mata cewa magana ce ta aure. Cikin wancan satin data shaidawa isma'il bata aurenshi yayi haquri yace ba komai Allah ya hada kowa da rabonsa sai jikinta dukka yayi sanyi daga baya,har ta dinga ji cewa kamar tayi gwari,kamar bata kyauta ba,kamar tayi wata asara,amma yanzu faisal ya wanke mata zuciyarta fesss da zancan zuwansa. Kwalliya ta zauna ta dandasa 'yar ubansu,itama umma bata zauna ba,tana ta aike siyo drinks da sauransu. Ta tatse jakarta yau tas,don hatta kudin da yaa bashir ya bata dazun duka sun narke. Turaren da malam ya bata hadi da kwalli duka ta dauka tayi amfani dasu,da taga akwai sauran lokaci sai ta dauko carbinta ta zauna tana fuskantar gabas ta soma qarasawa don jiya bata samu kammalawa ba. Ba dadewa suraja ya shigo yace ana sallama da ita. Kafin umma ta amsa ita ta rigata,ta ajjiye carbinta ta dauki mayafinta da duka duka bai wuce ayi dankwali dashi ba ta yafa ta fito kai tsaye ta wuce umman tana cewa "Bari na shigo da shi" Wani sanyi ne ya sauka a ranta sanda ta ganshi a tsaye jikin motarsa yana danne danne, exactly irin mijin da takeso. Kallonta yayi yadan saki murmushi ta maida masa "Bismillah,ka qaraso" ta fada tana juyawa ciki ya bita a baya yana qare mata kallo,don sosai straight gown din jikinta ta fitar da shape din mazaunanta,uwa uba kuma a yanzun da tasha supplement na qiba ta sake cika,kai ba zakace itace wasila 'yar ficika da ake tsokana ba,don har nankarwa yanzu gareta(stretch marks). Idanu ta juya masa a shagwabe sannan ta miqe tana fadin "Ina zuwa" sai tayi cikin gida yayin da shi kuma ya bita da kallo. Bayason su rabu amma kuma bai shirya aurenta ba kwata kwata,yanason macen da tafi wanann quality,duk wasu alamu da zasu nuna budewar idanun mace akwaisu a tattare da ita,duk da a iya saninsa bata taba zina ba,amma wasu abubuwan nata suna nuni ne da qarancin tarbiyya. Bata zauna ba sai data jere komai,komai tanayi ne cikin gwalangwaso iyayi da sanabe shi kuwa yana biye mata. Hira suka shiga yi kadan kadan,komai a shagwabe take masa hadi da kashe ido da karyar da murya kamar ba zatayi magana ba,abinda yasa ya dinga jin feelings a kanta kenan. Sama sama yaci abincin,duk da baici da yawa ba amma hakan ya mata dadi,tasan indai ya shiga cikinsa magana ta qare,sai daya nutsa yana goge hannunsa da tissue sannan ya dubeta "Waseela,inaso muyi magana ta fahimtar juna ni dake" "Tun dazu nake jira naji maganar ai" ta fada tana sakin murmushi gami da gyara zamanta "Kome zan fada miki ki dauka muqaddarine daga Allah,kuma shine qaddararmu da ni dake,amma kuma abinda zan fada din bawai yana nufin yankewar mu'amala tsakanina dake ba....." Maganarsa ta qarshe ta sanyaya faduwar gaba,amma ta dake taci gaba da sauraronsa. "Wasila aurenmu ni dake bazaiyiwu ba,saboda yanxu haka kakata ta dage ta tada rigima harda kwanciya ciwo wai sai na auri naana 'yar qanin mahaifi na" wani mummunan faduwa gabanta yayi,qafafunta sukayi sanyi ta kasa cewa komai saici gaba da tayi da kallonsa "Kiyi haquri don girman Allah,naso qwarai ni dake mu kasance miji da mata don nayi miki irin gatan da ban taba yiwa kowacce mace...... Amma yanzu ma bata baci ba,ni dake inaso muci gaba da mu'amala,ko meye kikeso zan kashe miki zan kuma baki". Hawayen da batasan yadda suka samu bane suka balle mata,ta girgiza kai cikin alhini tana dubansa "Amma me yasa duk lokacin nan baka gayamin ba?,ka barni inata bulayi da zaman jiranka?" "Banason ranki ya baci ne,kuma da farko na dauka zanshawo kanta ashe abun yafi qarfina,kiyi haquri don Allah karkiga laifina" kasa ci gaba da zama tayi,hankalinta tashe kawai ta miqe tayi cikin gida,tana iya jiyoshi yana kiranta amma bata ko waiwayeshi ba,kiran da hatta umma ta jishi,don tana shiga dakin tana binta a baya itama tana tambayarta ba'asi,saidai kukan da takeyi ya sanya ta gaza bata amsa. **Da sallama ya shiga sashen bayan barowarsa sashen ruqayya kaman yadda ya saba. Adan zabure Khalil da haneefa suka amsa sallamar tasa. Idanunsa ya sauke a kansu sanda suketa qoqarin daga tv plasma din data fado tayi zaman dabaro a qasan tiles. Ko da bai tambaya ba yasan abinda suka saba ne suka aikata,wato rikito da Tv din wajen fadace fadacensu da basa qarewa,su biyu kacal amma zaka tsammaci sunyi su goma a sashen "Waye yayi wannan aikin?" Ya jefa musu tambayar yana tsaresu da ido "Wallahi shine daddy.......qarya takeyi daddy itace ni ba ruwana,turani tayi kai" dukka sai suka kama masa rantse rantse. Ransa yayi qololuwar baci,ya rasa wanne hukunci zaiyi musu?,yo su idan suna da laifi ma ai kaso mafi yawa laifin na uwarsu ne. Matsawa yayi gaba yasa hannu ua daga tv din,ransa ya sake baci da ganin yadda tayi kwatsa kwatsa "Ina mamar taku take?" Ya tambayesu qasan ransa yana mamakin ya za'a yi abu me girma irin haka ya fado ya fashe amma baka ji ba ballantana ka fito? "Ta fita tun da rana" Khalil ya fada kansa tsaye. Tsaiwa yayi cak yana dubansa "Ta fita kuma?,ina taje?" Ya tambayi yaran "Bamu sani ba,mudau tace mana mu zauna a nan yanzu zataje ta dawo". Wani mugu mugun bacin rai ne ya sauko masa,a duniya cikin manya manyan abinda ya tsana a wajen matarsa satar fita, saboda shike haifar da wasu matsalolin da mai yiwuwa ba zasu taba gyaruwa ba. TV din ya maida duk da shi kansa yasan ta tashi a aiki,bata barnar da sukayi bane bama yanxu a gabansa,inda zainab ta sanya qafa ta fita bada izininsa ba tunda rana gashi ana shirye shiryen kiran sallar magariba. Cikin bacin ran yayi alwala ya wuce sallar magariba yana sanya ran kafin ya dawo ta dawo,saidai ko sanda ya dawo din ba ita ba dalilinta,dole ya tasa qeyar yaran suka wuce sassan ruqayya,don kuwa har sun fara jin yunwa,sunce rabonsu da abinci tun da rana,abind aya sake dugunzumashi kenan. Mutum ne shi da yaqi jinin yunwa ko kadan,wannan ya sanya baya bari a hora kowa da ita,koda baisan mutum ba bare cikin gidansa kuma 'ya'yansa. Tana zaune tana lazumi,alhassan da alhussain harma da iftee na zaune suna cin indomie da sukace sunan sha'awa ta kunna musu qaramin electric da ta ajjiye dama don saboda su,don wani lokacin qananun dafe dafe sukan iyayi,yaran badai qoqari ba,dafa taliya haka,shinkafa fara,ruwan zafi ruwan tea,tun uban yana fada da qorafi har ya barsu. *_KURMAN BAƘI_* ⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 23 https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr *_Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,akwai bonanza time to time da nakeyi,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_* Sallamarsu ta amsa tana binsu da kallo cikin mamakin abinda ya shigo dasu dukka haka a tare "Ina zainab taje?" Ya tambayeta yana tsareta da kallo cikin salo na tuhuma. Idanu ta zuba masa na wucin gadi kafin tace "Bata tayi?" Ta amsa masa da salo na gatse,don ba wannan amsar taso bashi ba. Ya karanci ko mene a idanunta,maimakon yayi qasa sai yaji ransa ya sake baci,gaba daya kaman sun rainashi kenan ita da Zainab din "Kina cikin gidan nan amma abar yara su wuni da yunwa don wulaqanci?,ita ta saka qafa ta fice bata gayamin inda zata je ba,ke kuma kinsan suna cikin gidan a barsu a guri su kadai,yanzun inda ace sun taba wani gurin sun hadawa kansu gobara fa?" "Uhmmm.....Allah sarki" kawai tace dashi taci gaba da jan carbinta. Hakan data masa ya sake qular dashi,idan ta saba share masa da qin yarda suyi zancan da ya danganci zainab ai issue din yanzu ya banbanta da na ko yaushe ko?. "Kai alhassan,ku dauki abincin ku qaro muku ku wuce dakinku kuci tare dasu haneefa" "To daddy,alhussain dauko plate din,ke haneefa bari a zuba muku naku ke da iftee" sai yaja yaran suka wuce. Kallonsa ya maido kanta bayan yaran sun wuce "Dake nake fa" kai tsaye ta sake kallonsa,duba daya ya fahimci da yunwa ya dawo daga kasuwa,ita ya kwaso take kuma tunzurashi(muddin kinsan kina barin mijinki da yunwa......muddin kinsan kina barin mijinki yana jiranki saikin kammala abinci to billahillazi daga yau ki taimaki kanki ki daina,yunwa tana jawo fushi,shi kuma fushi mabudin dukkan sharri ne,hanyar da zaki mallaki zuciyar mijinki shine ki kula da cikinsa ki tsare masa shi) "Wai nikam ajiyarta ka bani?,ko munyi yarjejeniyar zata dinga neman izinina kafin ta fita?" "To amma ai kece babba cikin gidan ko?,meye amfaninki da har irin hakan zata faru yara su wuni da yunwa a sashen ba tare da kin sani ba?" Dan qaramin murmushi ne da bata shirya ba ya subuce mata,tadan girgiza kai kadan "Allah sarki,yau kuma ni ake baiwa girman ake bani muqamin na saka ido cikin gidan nan?,bayan togaciya sharadi da iyakokin da aka taba gindayamin a baya?, gaskiya ne.......to kayi haquri ranka shi dade,indai ba fitina kake nemowa ba kuma,yara dai bansan su kadai bane a sashensu,da babu i zaa yi na barsu da yunwa,kafi kowa sanin bada abinci ko dafashi bai cikin matsaloli na.......Abinci ne gashican an basu,ita kuma bansan ta fita ba bansan kuma ina taje ba,shikenan?" Ta tambayeshi tana tsareshi da idanu itama. Wani numfashi ya saukar,kamar bazai motsa ba sai kuma ya juya ya nufi qofa,tana kallonsa qasan ranta tana hadiye dariya da mamakin halin da namiji,kamar ba'a wannan falon ya zauna ya qidanya mata dokoki da sharadai akan matarsa shalelensa wadda dangi kaf suka aza tazo ta cika gidan da 'ya'ya ba,ta nunawa ita ruqayya cewa ita din cikakkiyar juya ce,kaman bashi ba yanzun ya taho da confidence dinsa zai kawo mata qabli da ba'adi. Tasan yunwa ce take sasaqarsa,ita kuwa tun a wancan zamanin da ya watsa mata qasa a idanu ta daina bashi abincinta muddin ba ranar girkinta bane,gashi kuma shi din ba gwanin cin abinci a waje bane. Har ya isa dab da qofa wayarsa ta dauki burari,ya dakata yana fiddo wayar,ya sake qufula sanda yaga sunan zainab din. Koda ya daga wayar saqon da ake gaya masa sai yaji ya girmimi kansa,dole bayan ya ajjiye wayar ya waiwayo yana duban ruqayya,don ita kadaice yakejin zata tayashi tallafar nauyin da zuciyarsa da qirjinsa sukayi. Matarsa ta aure?,matarsa ta sunna a kulle a station. Sanda yake gayawa ruqayyan ita kanta abun sai ya bata mamaki ya girmimi kanta "Me tayi har ya kaita police station?,yaushe 'yan sanda sukazo da ni da nake cikin gidan nan banji ba har suka tafi da ita?" Tayi tambayar wadda daga shi har ita basu da amsa "Wata rigima ya debo na tabbatar da haka" ya fada cikin gamsuwa "Babu lallai,kaidai ka bincika" "Wallahi ko kaffara bazanyi ba idan na rantse,nasan halinta ciki da bai,taimaka kizo ki rakani muje" da sauri ta kada hannunta "Wa?,ni?,daga qarshe zance ya juye ace ni na saka aka kulleta?,Allah ya tsare hanya a dawo lafiya" ta fada tana nade abun sallarta. Haka ya tsaya yana binta da kallo harta gama nadewa ta wuce daki gurin yaran. Yana tuqi a hanya zuciyarsa tana dada zafi,cikin mintuna qalilan ya isa police station din. Muryarta ya fara cin karo da ita suna sa'insa da wani dan sanda,fadi yake cewa "Banda aure dake wuyanki da saikin raina kanki,yanzunma kuma kici gaba da cikama mutane guri kiga idan ban saka su Monica sun sassaba miki kamanni ba" tasan yadda yake da zafi iya awannin da sukayi a wajen,don haka ta rage sautinta,saidai kuma bata fasa maganganun ba. Kunya baqinciki da takaici suka ishi saleem sanda ake karanto masa statement na dalilin zuwansu gurin "Maganin mata da shiga har gida su doki mace har dakin mijinta" ji yayi kaman zai mutu saboda takaici,wanne irin tonon silili ne wannan?. Banda darajar su haneefa da khalil babu abinda zai hanashi tafiyarta ya barta a wajen ta nemi me belinta,to amma yaran kawai ya tuna ya karbi belinta harda tararta da sukaci,saidai kuma suna fita farfajiyar gidan yace ta nemi gidan zuwa,kada ta sake ta dawo masa gida,yaja motarsa ya wuce abinsa. Sanda ya koma yaran duk har sunyi bacci a dakinsu,shi Khalil dama cikinsa yana dauka ya haye tattausan gadon alhassan, komai iri daya aka siya aka zuba musu,to amma rashin kulawa da rashin tsafta yasa yaran suke ganin dakinsu alhassan din kamar yafi nasu kamar nasu dakin wata aljannar duniya ne. Wanka tayi data tabbatar sunyi bacci,ta saka rigar material mara nauyi. Abinka da me yaron ciki sai taji tana son shaqar iskar waje,don haka ta saka qaramin hijabi a kanta,ta dauki qaramin littafin hisnul muslim da taketa qoqarin haddace wasu addu'o'i masu muhimmanci a ciki ta fita waje.(akwai addu'o'i masu tarin muhimmanci a ciki,kada ki zauna ace baki haddace kowacce addu'a ba 'yar uwa,akwai babban hatsari,kaman ka gina gida ne babu qofofi ko winduna). Bata jima da zama ba taji hon dinsa,yaron gidansu da bai tafiya sai 12 na dare shi ya bude masa ya sako motar ciki. Tana zaune har ya saita parking ya tako zuwa cikin gidan kai tsaye kuma ya nufo sashenta. Daga kai tayi tana amsa sallamar sa tare da nazarin ganinsa shi daya "Ya na ganka kai kadai?,ko ta wuce ciki?" Ta tambayeshi tana gyara zamanta cikin kujera. Kai ya dauke gefe guda "Me zanyi mata?,na karbo ta amma saidai ta wuce gidansu,don ni bazan iya zama da ita ba da wannan abun kunyar da ta jawomin" "Ban fahimceka ba,kaman yaaya?" Ta tambayeshi fuskarta a dan yamutse "Eh nace ta tafi gidansu" kai ta ya shiga girgizawa "A'ah, bazaiyiwu ba,ta tafi gidansu ta barwa waye yaranta?,haka kawai mace na gidanta ka sallameta?" "Au haka kawai ne ma?" "Eh mana,don tayi laifi?,waye baya kuskure?" "Ganganci ne wannan zallar taurin kai da rashin jin magana" "Hakanan zakayi haquri da ita,amma ba inda zataje,don ban shirya riqon dan kowa ba,koda nan gaba aure ka qara to ka saka a ranka mutu ka raba kai da ita,nima nawa ban gama wahalarsu ba" "Sai naga ta yadda zakimin dole" ya fada yana shirin wucewa sashenta "Bafa kwanana bane,kada ka shigarmin gida ka tayarmin da yara" ta fada tana miqewa tsaye. A zafafe ya waiwayo yana dubanta,yana jin kamar tanason tunzurashi ne,wai wacce irin macace ita?wasu matan suna murna suna jiran irin wannan damar?,amma ita ta samu tana tankwabewa?. Baikai ga cewa komai ba aka buda can qofar get aka shigo. Akwai wadatar hasken fitilu a farfajiyar,don haka kana iya gano zainab. Dakatawa yayi da shirin shiga ya nufota rai bace "Ba gida nace ki wuce ba?" "Kayi haquri don Allah,wallahi bazan sake ba, tsautsayi ne wannan ma" "Banason na sakejin komai daga bakinki,gida nace ki tafi" "Bafa inda zataje,waye baya kuskure?,sai ka zauna ka fahimceta ai,idan da hali a bata uzuri ko?" Shi da zainab din dukansu ita suka kalla,zainab din bata taba kawo zata sanya baki ko ta bata kariya ba,amma duk da hakan da tayi bataji ta burgeta ba "Wannan ba hukuncin ki bane ba kuma huruminki bane,hukunci na riga na yanke" "Eh haka ne.....to jirani nima na hado nawa kayan mu tafi tare" ruqayya tace tana juyawa zuwa cikin gidan. A yadda taga tayi maganar ya tabbatar tana nufin abinda ta fada din,ya waiwaya ya dubi ruqayya sake shigewa ciki ya kalli Zainab dake tsaye saroro "Ki wuce ciki,amma wallahi saikin gane kurenki don bazan lamunci wannan zubda mutuncin ba" baqinciki da farinciki ne dukka suka gaurayar mata lokaci daya,tabbas badon ita ko domin Allah saleem ya barta ta koma dakinta ba. Yanzun kamar ita ace albarkacin kishiya taci?,wanne irin babban abun takaici da abun kunya ne wannan?. Wannan abun yayi wata wawuyar tsaiwa a zuciyar Zainab,a daren ranar baccinta ragaggge ne,duk sanda ta juya sai abun ya fado mata,wutar qiyayyar ruqayya ce kawai take sake ruruwa a zuciyarta. To wai banda don a gallaza mata a tozartata me yakai saleem aurota yasan ruqayya nada wadannan qualities din?,wato amfaninta kadai a wajensa dai dai yake da machine na haifar yara?,eh mana......tazo ne kawai kenan don ta cike masa gibin haihuwa?,a yanzun kuma da haihuwar ta samu daga gurin ruqayyan sai komai ya sake zama wani iri. Ya akayi a komai sai ruqayya ta fita ne?,iya cikin jikinta kadai ya isa abunda yake hana ma zuciyarta da kwanyarta nutsuwa da kwanciyar hankali. A daren taji burinta na qarshe a rayuwa shine taga bayan ruqayya,ta tabbatar shine abinda zaya sama mata nutsuwa da kwanciyar rai. ******Cikin kwanakin gaba daya damuwa ta yiwa wasila yawa,duk idan ka ganta zakasan bata cikin nutsuwarta,faisal yayi mata dukkan wata bazata da bata taba kawowa ba. Da ruqayya kadai tayi zancan bayan ummanta,saboda da ruqayyan ta amince,don kowa kallonsa take a matsayin wanda zai iya zaka mata hannu a lalacewar maganar aurenta. Duk yadd kaso ga bawa wasilan shawara ba lallai tayi tasiri,don haka iya gwargwadon hali ruqayya ta lallasheta ne tare da bata shawarar dagewa da addu'a,duk da tasan babu lallai addu'ar tayi mata tasiri tunda ta riga ta raba qafa. Dan man da take shafawa kwana biyu ta aje saboda bacin rai,hakan ta fada qibar ta dan janye kadan. Cikin wannan lokacin yara suka kammala exams, za'a yi musu hutu,hakanan an gayyaci dukkan iyayen yara don su halarci makarantar za'a yi taron tafiya hutu da bada kyaututuka ga haziqan dalibai. Farko ruqayya cewa tayi ba zataje ba,tunda duka makarantar yaran nasu daya ne Zainab din ta wakilceta kawai. Saleem ne yace a'ah,dukkansu suje kawai,bataso zuwa din ba don cikin yazo mata da zaman daki zuwa falo,batason leqawa ko ina,amma hakanan dai tunda yace aje din ta kira wasila tace tazo suje tare tayi mata rakiya. Kowa a motarsa zashi,don haka koda ta tashi tafiya bata cewa Zainab din komai ba. Tunda ta lura ta dauki wata gagarumar gaba da ita tun daga ranar da tace zata bita suyi yaji tare,sai itama ta sake kama kanta fiye da baya,don a nata ganin meye nata a ciki?,fadanta dama tsakaninta da mijinta ne,abinda ya sanya harta sanya baki ma shine ganin za'a bar mata wahalar yara,wanda ba ita ta fara tarbiyyarsu ba,so batasan ta ina zata dauko gyara ba. *_ZAZZAFAN ALBISHIR GAREKU MASU KARATU_*😊😊 *NACE BA*👂🏼👂🏼👂🏼 *ZAFAFA BIYAR FA!* *SABUWAR SHEKARA CE!!!*2024😍😍 *Abun ba'a magana*🥰🥰🥰 *_KUSAN WADANNE ZAFAFAN LABARAN SUKA DAUKO MUKU?_* AMEENATU mamuhghee KWANKWASON JIMINA Miss xoxo TSUTSAR NAMA Billynabdul GUDUN K'ADDARA Huguma *_kedai ki shirya kawai hajiyata,abun ba'a cewa komai_* *_akwai zazzafar tattaunawa da zazzafar muhawara_* *HUGUMA*👑 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 24 *_Asalamu alaikum warahmatullah,barkanmu da warhaka_* *_Har yanzu dai ina nan ina ci gaba da sauke muku kabakin kaya masu tsananin kyau quality da kuma saukin kudi kamar a kyauta a HUGUMA CLOSET_* *_SARI KIKEYI KI SIYAR KEMA?,KO NA SANYAWARKU NE A JIKI?_* *_TO TABBAS BA GROUP DIN DA YAFI DACEWA DAKE SAISHI👍_* *_ki siya kayanki cikin farashi me sauqi,kaya masu quality kuma unique one,suzo su sameki fiye da yadda kike zato hankalinki kwance cikin aminci_* *GANI ANCE YA KORI JI*😊 Iftee na riqe hannun wasila suka fito daga sashen ruqayyan. Tayi kyau sosai cikin doguwar rigar wani material wadda take zuwa hade da mayafinta,yaron cikin jikinta ya qara mata kyan fuska da na fata gaba daya. Fes da ita qamshin sassanyan turarenta kawai takeyi. Hira Suke ita da wasilan,wasilan na qorafin kan case dinta da faisal "Nidai bansan lokacin da idanunki zasu bude ba wasila,bansan sanda zaki gane abinda ke gabanki ba,ai alamun qarfi yana ga me qiba,hakanan duk juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta,ya kamata ki bude idanunki da kyau wasila" baki tadan tabe,har yanzu tana jin ciwon abinda faisal yayi mata "Shi kuma isma'il gaba daya yama daina kirana" "To zaizauna ne kina wulaqantashi son ranki?, bazaiyiwu ba ai,Allah ya hada kowa da rabonsa,tunda dai ya baki dukkan dama" "A yadda ma naji wai yakai kudin aure" ta fada tana jin dacin abun har cikin ranta "Ato,kinga ya sawwaqa miki wahala ko?" Maimakon wasilan ta amsa sai sautin dariyarta da ya isa kunnen ruqayya dake qoqarin zura key ta bude motarta. Daga kai tayi tana duban wasilan "Ke kuma lafiyarki?,muna magana me ciwo da kuma muhimmanci kina kuma dariya?" "Qanwarki za'a tambaya lafiyarta daya?,don muhammadur rasulillahi da gaske haka zata je makarantar 'ya'yan nata?" Duk yadda ruqayya taso ta dauke kai kada ta kalli zainab amma saita kasa,yadda wasila ke sheqa dariya abinta ta tabbatar ba qaramin abu bane. "Subhanallahi" ta fadi tana dauke kanta da sauri kada zainab ta fahimci suna maganarta ne. Wata irin hautsinanniyar shiga tayi kamar wadda ke shirin fara aikatau din abincin biki. Sai data tausa kanta da kyau sannan ya hadiye dariyarta,ta jefi wasila da harara "Gulma ajali,to ina ruwanki?" "Ki barni Allah yau daya na bata shawara kada taje a haka ta zubdawa 'ya'yanta aji" caraf ruqayya ta kamo hannun wasila,domin kuwa tasan halinta sarai,'yar takife ce,tsaf zata iya tarar zainab din,tayi imani kuma abun bazai qare da kyau ba,wasilar 'yar rigima ce ta gaske,zainab kuma ba haquri ta tabbatar ba zata dagawa wasila qafa ba. "Ba ruwanki don Allah, shige mu tafi" ta fada tana turata gaba. Duk da haka bata fasa tiqa dariyarta ba har zuwa sanda zainab din tazo giftasu. Suna Hada ido da ruqayya ta saki wani mugun tsaki sannan ta barke da waqa tanayin gaba "Kanbalasti,don girman Allah ki barni na yagawa jakarnan dawa,wai ita a nan haka macace?" Wasila daketa dariyarta kamar ba gobe ta fada. "Nace miki dai ba ruwanki bakinta ne tayita yi" "Su kishi manya,ni da gwaigwai" wasilan ta sake fadi tana kallon qafafun zainab data rabasu tana niyyar shigewa mota "Nikam wannan matar ko primary ta gama kuwa?" "Bansani ba nidai" ruqayya ta fada tana tayar da motarta tare da qoqarin danne dariyar da wasila ke qoqarin sakata yi qarfi da yaji. Ta daidaita motar suna shirin fita dab da motar zainab din wasila ta sauke glass "Mata suna muka tara,a cikinmu wace zara tauraruwa acan a sama......" Daga haka ta fuske ta maida dubanta wani sashen na daban. Sarai zainab taji maganganun wasilan,kuma ta tabbatar da ita take,ba tun yau ba tasan halinta,wannan ya sanya sam basa shiri da ita,muddin tazo gidan ba kasafai ta fiya tafiya salamun qaulin wani abun bai hadasu ba. Mita ruqayya ta shiga yiwa wasila bayan sun fita a gidan "Ke kike jin tsoronta,ni so nayi ma ta kulani na wanke qazama,yo koni da nake ba wanda ya ajjiyeni tsigau nake ta yaya zan zauna a haka bare ina da miji?" "Amma kinfi kowa sanin halina,ta yaya zanji tsoronta?,tashin hankali ne kawai ni banaso,zaman lafiya kuma yafi komai dadi" "A wajen wanda yake sonshi ba" ba wani jin dadin jikinta sosai takeji ba,don haka taja bakinta ta kulle ta qyale wasila,saboda tasan ko meye zata fada ba lallai ta yarda ta dauka ba. Sanda suka isa makarantar harabar gidan ta fara cika da mutane. Tsaida motar ruqayya tayi tana cewa "Banajin qwarin jikina sosai,ba jimawa zamuyi ba zamu koma gida gaskiya" "Ba damuwa,nima din yau zanyi baqo" dan dubanta ruqayya tayi "Really?,Allah yasa shine mijin" dan tabe baki kadan wasila tayi "Toh.....gashinan dai,yaa bashir ne ya hadamu" ta fadi tana bude murfin motar. Da kallo ruqayya ta bita,itakam wani lokaci al'amarin wasila kamar wata me almutsutsai,duk wanda yazo yakai mijin aure a idon kowa amma banda a idanun wasilan,ko meye yake damunta oho?. Tunda yaran suka hangi ruqayyan suka fara murnar ganin ummansu,haneefa na zaune daga gefansu tana raba ido. Duk da ba wanu shekaru bane da ita ba can amma shigar zainab ta sanyaya mata jiki. Kowa cikin yaran yanata nuna ummansa da azamarsa da karsashinsa amma banda haneefa da ta sake noqewa,kwata kwata shigar ummantata batayi mata ba. Cikin lokaci qalilan aka fara gudanar da taro gadan Gadan,har zuwa sanda aka fara raba kyaututtuka. 'yan biyu makaranta wato alhassan da alhussain sun samu kyaututuka kala daban daban har kusan kashi hudu. Zainab na daga gefe amma tana bibiye da komai,kusan fiye da rabin hankalinta yana kan yadda komai yake gudana. Ta kasa kunne ta jirayi jin an kira koda Khalil da ta saka buri me yawa a kansa,har wani lokaci takan kirashi da doctor,amma har akayi aka gama shuru maqatau kakeji "Shegun yara,an koya musu shegen sanabe da iyayin masifa da iya mallaka" zainab dake zaune akan kujera ta fada tan binsu alhassan da harara. Da daya da daya yawancin yaran suke gabatar da abokansu ga iyayensu,tun zainab bata ankara ba har idanunta sukakai ga su haneefa. Zugar yuyar qawayenta ne ta jasu zuwa wajen ruqayya dake zaune tana magana da abokansu alhassan,duk da cewa kusan fiye da rabinsu ta sansu dama,don bata wasa da zabarwa 'ya'yanta abokai,hatta kuwa da iftee da take qanqanuwa a cikinsu (mu kula da kyau iyaye,mu kula,mu sanya idanu,tabbas abokai na daya daga cikin mutanen dake taka muhimmiyar rawa ga rayuwar yaranmu,kada kace ba komai don abokin yarona baya zuwa makaranta tunda yarona yana zuwa,kada kace ba wani abu bane don abokin yarona ya kwana ko ya yini da yunwa tunda dai nawa dan yaci abinci hakan bazaiyi affecting dinsa ba,kada kace ba komai don abokin yarona yana zagi ko gidansu ba tarbiyya ai basa haduwa ko yaushe bazaiyi affecting nasa ba,a'ah......sam wallahi,kiyi iya bakin qoqarinki tuquru,yadda kikasan danki bai rasa komai ba kuma yana kan turba ki tabbatar abokan 'ya'yanki ma haka,daga yaranki suka fara samawa rayuwarsu abokai to aikin tarbiyyar dake wuyanki ya linku, tarbiyyar ta zame miki double muddin kinason kiga daidai,kiyi naki kiyi na abokan yaranki,duk yaran da iyayensa zasuyi fushi donkin hukunta dansu ko kin masa gyara ko tsawatarwa ko tabbas ki nesanta yaranki da wannan yaron,Allah ya dafa mana yayi riqo da hannayenmu wajen basu kyakkyawar tarbiyya ameen summa ameen). Washe baki sosai haneefa keyi tana cewa "Ga mommy na nima,ku gaisheta" da murmushi ruqayya ke bin qawayen haneefan da kallo,saidai babu wanda yakai ga furta komai suka tsinci bankowar zainab tsakiyarsu. "Mommyn uwarki mommyn ubanki?,ina tasan ciwonki don******ubanki,annamimiya kema an koya miki annamimanci ne koko yaya aka soma?,ko sihirin ya fara biyomin ta kanku?" Zainab ke fada a tsawace tana kallon fuskar haneefa data ruqayya. Har wasila zatayi magana ruqayya ta damqi hannunta,ta jata suka miqe tsam tace dasu alhassan "Ku wuce muje hakanan,taro ya tashi alhamdulillah,'yan yara sai watarana,ku dage kuyi karatu ku yaqi jahilci kunji?,domin shi jahilci babban ciwo ne da yafi na hauka". Daga wannan bata qara ba tayi gaba bayan ta sanya su alhassan a gaba. Daga inda motarta take take tsaye tana qoqarin bude musu amma tana iya jiyo ashariyar da zainab din ta lailaya sannan ta fara tunkaro inda suke "Don annabi kada ki tashi motarman,ki bari na nunawa matarnan qaramar qwaruwa ce ita tunda ke ta shanyeki" "Ba zamu raba hauka a nan wajen ba,indai mukayi haka damu da ita din dukka daya muke kenan,ki barta idan ta haifu ta sameni cikin gida" daga haka ta tayar da motar tun zainab bata qaraso ba,wanda hakan ya sake qona ran zainab din taja burki a wajen tana huci,saidai kuma zuciyarta na gaya mata tsoro ruqayyan taji ta gudu "Aiko baki tsira ba,yau sai na fanshe haushinki billahillazi,sai nayi sanadiyyar wannan matsiyacin cikin da ake feleqe a kansa" tana gama fadin haka cikin zuciyarta ta durfafi motarta,haneefa dake binta a baya idonta da ruwan hawayen takaici saboda yadda taga qawayenta da wasu mutane da sukayi saura a wajen na kallonta tabi bayanta "Kinga fa umma sai kallonki akeyi" ta fada tana kyabe baki cikin tabara. Tana waiwayowa batayi wata wata ba ta tsinketa da mari hadi da ingizata cikin motar "Kece sila da kika raina uwarki sai uwar wasu,sai nayi maganinki wallahi zakisan da waye kike magana" itadai yarinyar bata amsa ba sai kuka da take gurzawa cikin motar kamar wadda aka tsinkewa rai. "B kowanne lokaci bane ba kuma ko yaushe ne idan kishiya tayi miki abu kike tanka mata ba,ba kishiya ba hatta dashi mijin da kike zaman domin shi,yawaita tankawa kishiya akan ko meye tayi miki yana sanyawa ta rainaki,ta gane lagonki,ta kuma fahimci abinda bakiso da abinda yafi qona miki rai,wanda wadannan kuma sune makaminta da zata yita yaqarki dasu tana hanaki sukuni. Sa'insa ko tankiya yawan maimaitasu ba abinda yake haifarwa face jawo raini da zubewa girman babba. Duk mace idan taso tana iya siyawa kanta kwarjini da martaba a idanun kishiya,ita zainab da kike gani,har yanzu batasan mene yake mugun bata raina ba,har yanzu babbankiya takeyi saboda naqi bata wannan damar,har yanzu duk sanda zatayi iskancinta bata isa ta shigo sashe na ba iyakarta farfajiya,kuma har yanzu bata isa ta saka hannu a kaina ba,har kwanan gobe kuma akwai fadan da bata iya tsaiwa mu yishi,har yau har gobe kuma akwai abinda yake hurumina ne cikin gidan,ita ko shi ba wanda ya isa ya taka,idan na zartar saidai kawai su gani a qasa,koshi bazaice komai ba bazaice kuma don me ba,itama tun tana damuwa har ya zamar mata jiki. Ko zage zagen da takeyi yanzu ai sai dana bada baya bawai cikin idanuna ba. Idan kinso kina iya saiwa kanki wannan martabar,wanda tun farkon kawo kishiya zaki siyeta,ki girmanki da mutuncinki,kada ta sameki kina haukan kishi,ki nutsu ta sameki me cikakkiyar nutsuwa,ki yawaita addu'a da roqar Allah ya haskaka fuskarki a idanunsu ita da mijin,sannan kiyi fatan Allah ya baki mijin da yasan darajarki,don gwargwadon yadda ta shigo taga miji yana qimantaki gwargwadon yadda zata fahimci muhimmancinki,koda baya baki martaba shi da ita ajesu a gefe ki kama kanki,ki ki aikata musu a aikace ba ta hanyar magana ba cewa kefa kinsan kima da mutuncin kanki,ko baya qaunar Allah dole yayi biyayya koda bai shirya ba,musamman idan ke din ma'abociyar addu'a ce,me tsarkakkiyar zuciya,wadda baki zaluntar kowa kina qoqarin fita haqqin kowa" shuru wasila tayi jikinta ya sake,zuciyarta kuma na juya kalaman ruqayya. Tabbas tun suna qananuntasan ta fita hikima,ba komai bala'i da masufa yake baka shi ba. Hirarsu ta duniya sukaci gaba da yi wadda cikinta a yau wasila taji tana qaruwa. A nutse take musu tuqi har suka isa gida. Taso ta saka motarta ciki amma saita lura da motar zainab wadda aka yiwa wani banzan parking,so babu hanyar da zata shiga din,don haka ta tsaida motar ta fito tana cewa wasila "Bari naga me ya faru,idan ta matsar da motar ki shigo min da ita ciki,fitsari nakeji sosai" "Yauwa nima yau na dan dana kafin Allah ya kawo mana me siya mana muma" wasila ta fada cikin zumudi tana komawa seat din da ruqayya ta tashi a kai. Tana shiga farfajiyar gidan ta tambayi yaron gidan nasu ya aka ajjiye mota a haka?. Cikin dan rusunawa yace "Ummansu haneefa ce,nima nayi mata magana da nufin ta gyara ko bata lura bane ta zageni tace yau a haka taga daman ajjiyeta" dan jim ruqayya tayi tana gyada kai,sai ta koma da baya ta yiwa wasila magana "Ki ajjiyeta nan qofar gida ku fito ku qaraso ciki" "Me yasa?" "Haka dai nace" ta amsawa wasila tana dawowa ciki idanunta akan motar zainab har ta wuce sashenta. *_ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTANKU NA SHEKARAR 2024_* *_ZAZAFAR SOYAYYA ME SANYAYA ZUCIYA CAKWAKIYA GWAGWARMAYAR RAYUWA DA TATABURZA_* *_ZAZZAFAR MUHAWARA CIKIN KEBANTATTUN COMMENTS GROUPS NAMU,MUHAWARA ME SANYA NISHADI DA QULLA ZUMUNTA (ZAFAFA FAMILIES)_* *ZABABBUN LITATTAFAN NAMU SUNE KAMAR HAKA* *AMEENATU* Mamuhghee *KWANKWASON JIMINA* Miss xoxo *TSUTSAR NAMA* Billynabdul *GUDUN K'ADDARA* Huguma _TURK'ASHI!,KADA WANNAN DAMAR TA WUCEKU_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING ZAFAFA BIYAR*❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥 *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 25 Ranta a bace ta soma sauya kayan jikinta,cikin ranta tana tunanin abinda Zainab keso a tattare da ita. Ta gama kintsawa ta dawo falon don su bude kyaututukan yara kafin daddynsu ya dawo,abundai bai yiwa wasila ba har sai da ruqayyan ta sake magana da ita "Wooo wasila!......abinda tayin kina nufin ba wani abun ta taka ba a qasa?,idan kare yana haushi ai baka kulashi,ka barshi idan ya isa ya kawo maka cizo mana ya gani?,mai gidan ai zai dawo ko?,zaiga kuma komai,kanta ta haqawa rami ai ba ni ba" daga wannan ta watsar sukaci gaba da sabgar gabansu. Tafi awa tana sauraren ta jiyo ruqayya ko wasila ko wani nata yana maganar ta janye mota ko abinda ya danganci haka,ta rantse da Allah yau din sai tayi mata wankin babban bargo,saita basu mamaki(ni kuwa nace hmmm,bayan wanda kike basu😂),haka ta qaraci tanadin masifarta ta haqura ba tare kuma data janye motar ba. Tunda akace mata daddy yana kiransu a falon tsakiya tasan ba lafiya ba,tunda ya saba duk wadda ba girkinta bane yana leqawa ya sameta har sassansa su gaisa bayan ya shigo gidan sannan ya wuce sashen me girki. Ta gama alwalar magariba kenan duk da akwai sauran lokaci,sai ta qarasa gaban madubi ta tsane fuskarta ta shafa lotion kadan sannan ta shafa powder,sannan ta qara mulke jikinta da oil perfume ta fito. A tsaye ta samesu shi da zainab din tana riqe da qugunta. Ta dauki idanunta daga kanta kamar bata ganta ba ta zagayeta ta tsaya daga damansa "Daddy yada haka a tsaye?,ka zauna mana kaman ba cikin gida muke ba?" "Ba ruwanki da tsaiwarsa ko zamansa tunda ba ranar girkinki bane wannan ba huruminki bane" banza ta baiwa ajiyarta ta janye masa pillow din dake kan kujerar tace "Have a seat please daddy" tayi maganar a sanyaye cikin tausasawa ta yadda har tsakiyar zuciyarsa sai da yaji wani sanyi ya saukar masa,ya kuma shiga kokwanton maganganun da zainab din ta tare shi dasu bayan yabi ba'asin me yasa akayi wrong parking,ga wata motar kuma a qofar gida basa tsoron yara su kakkarceta. A nutse ya zauna din yana sauke numfashi can qasa,rashin ganin fuska daga kowannensu ya hana zainab din ta sake cewa komai,saidai ta qulu iyaka "Me ya hada zainab da ke da wasila?" Yayi tambayar calmly "Wani abu tace ya faru?,nidai a iya sanina bansan komai ba,ko magana ta fatar baki basuyi ba bare ace ma wani abu ya hadasu" "Dole kice haka mana,ki sakata tana sakarmin baqaqen maganganu tana min kallon raini,to wallahi kashedint......." "Ke da Allah malama dakata,da mijina muke magana ba dake ba,idan kuma kin gwammaci nayi magana dake din to daidai nake dake,ki kiyayeni ki fita idona don ni ba sa'ar yinki bace.......shashasha mara kunyar qarya da wofi ke duk tsiyar da kika shuka kina da bakin yin magana inda ace ke din me kunya ce?,kina nufin inda na barki da wasila zaki tsira ne?, wallahil azeem da wannan rashin kunyar da kika tsaya kina yima baki isa ki yita ba" "Ya isa ruqayya......" "Ai ba dogon magana na fito nayi ba dama,ka jawa matarka kunne,taci gaba da ji da abinda ya dameta,don ni bani da lokacinta ina da masu jimin da ita idan hakan ta kama" tana gama fada tayi gaba abinta "Kaji ko?,tabbacin ita ta sakata tayimin diban albarka" "Ya isa haka da Allah" saleem ya fadi cikin gajiya da soki burutsun qorafe qorafen zainab din. Tayita zuba idanu ruqayya ko zataji wani abun ya sake tasowa amma taji shuru,batasan yadda suka qarke ba,don ko abinci ma ranar cewa tayi bata ci,qememe taqi fita,saima tayi kwanciyarta ta tura yara. Koda ya shigo da kansa ma laga laga tayi tace masa batajin dadi haka ya koma. Wannan ya bata ran zainab,don ta shirya abubuwa masu yawa a zaman cin abincin amma ruqayya taqi bata wannan damar,don tun daga ranar ma sai ta janye zaman cin abinci,idan ta gama zata shirya musu ta koma sashenta,idan ya shigo zaiyi qorafi takance yau batajin dadin cikinta ko qamshin abincin ya cika mata ciki ba zata iya ci ba don zata iya amai. Sai ya zamana duk ran girkin ruqayyan suna gama cin abincin yake tattarawa ya wuce sashen ruqayyan sai kuma da asuba idan ya shigo tayar dasu sallar asuba. Yadda taga hankalinsa kamar yana sake karkata ga ruqayyan ya tashi hankalinta matuqa,ta kasa zaune ta kasa tsaye,hankalinta ya kasa tsaiwa guri guda. Hatta dasu haneefa yanzun duka sukeci a wajenta,ta kasa zama da kowa lafiya saboda tana ganin ubansu kamar baya yi mata adalci. Komai da yasan zasu buqata ya kammale waje daya kafin tafiyarsa,mutum ne tsayayye wajen kula da hidimar iyali da buqatunsu,ya danqawa kowacce adadin abinda zata buqata na cefane da hidimar gida,don ba zasu dawo ba sai ranar jajiberin sallah. Tuni zainab tayi nisa wajen hada kudin dinkin da za'a yi mata,ta zabge fiye da rabin kudaden da saleem ya bata ta sakasu a lissafin. Ta riga ta tsara abinda zata diba cikin kayan abincinsu ta saida ta sake hada wasu kudaden masu kauri,wannan karon sam ba zatayi wasa ba,tanason sanda saleem ya tsoma qafarsa a qasarnan ya dawo hannunta,ya koma mata bita zai zai,tanason ranar daya dawo dakinta daukacin al'ummar gidan su shaida,muryarsa tayi kururuwar da kunnuwan ruqayya zasu jiyo,ta gogewa idanunta dukka wani sauran bacci da ya rage mata,bayan wayewar gari kuma taci karo da gagarumin sauyin da zai ruguza duk wata kissa tata da take taqama da ita. Tanason ruqayyan ta zame masa kamar namiji dan uwansa,duk sanda zasu kasance da juna ya dinga jinta tamkar abincin da babu maggi ba gishiri,tayi imanin indai wannan buri nata ya tafi a haka komai zaizo mata a yadda takeso. Ana ya gobe zasu tafi ta yiwa wasila waya tazo ta tayata zama,saboda yanayin laulayi,kuma tayi imanin ba wanda zai iya zama da halin Zainab dai dai da halin nata sai wasilan,saidai ta sanya ta bawa umma wayar cikin zolaya take cewa umma "Zan dauke miki auta har zuwa sallah,amma ki jawa auta kunne wallahi kar tazo ta zaka kishiya ta babbakani" Dariya umman ta dinga yi,saboda tasan barkwancin wasila da ruqayya baya qarewa. Da daddaren ranar cikin girkin Zainab yake,wanda a washegari inda yana qasar nata girkinne. Tsaf ta shirya qananun jakankuna data masa qananun siye siye da tasan zaya buqata a can,ta kuma yi masa packaging na qananun snacks da ba zasuci masa guri ba ire iren wadanda tasan yana so. Bata jima da fitowa a wanka,don wani dogon bacci tayi,har ya shigo nemanta ya fita ma bata sani ba. Wata sabuwar doguwar riga ta siya me sulbi cikin ribar business dinta. Sunyi nacin rigar ita da zainab sosai,shima kuma yaso siya musu don tayi masa kyau amma wasu hidimomin suka shigo ciki sukayi gaba da kudin rigunan kusan 60k. A lokacin har sabani suka samu shi da zainab akan hakan,tace ya sanya musu rai dama dai baiyi niyyar siya musu ba. Wannan kalmar ta qona masa rai matuqa da gaske,saboda shi din duk wanda ya sanshi yasan me fada da cikaawa ne,muddin kaga bai cika ba to akwai babban dalili. "Bari naje gurin daddynsu muyi sallama,don shida na safe sun fita a gidan nan" "Okay bari nima na amsa wayar wannan dan anacen" ta fada tana miqewa. Kai ruqayya kawai ta girgiza,dole tayi bakin qoqarinta adan zaman nan da zasuyi da wasila ta canza tunaninta. Yana daga cikin bedroom dinsa yana hada kaya zainab na zaune a gefe tana qara masa wani sabon lissafin,don so take kota halin yaya ta sake samun wasu kudaden da zata maida asarar da basira ta janyo mata,ta hada kudin dinkinta tsaf,ta kuma fidda kudin hidimar gidan dai daya bayar. Sallamar ruqayyan ta ratso har dakin,ya amsa yana bata izinin shigowa,saidai dan tsayawar da tayi tana gyarawa haneefa assignment dinta na islamiyya ya bawa zainab damar yin magana "Ya muna daki zakace ta shigo mana fisabilillahi?" Bai kalleta ba yace "Bedroom dina nace ta shigo ba naki ba,ke shigarki nawa bedroom dina na sashenta?,kin taba ji tayi qorafi?" Tasan magana ya yaba mata,lokacin amarcinsu idan taso tsiya ma tana tuburewa ne tace tsoron sashenta takeji a nan zata kwana,wani lokaci saidai yabar mata nan din su kwana a bedroom din ruqayyan. Haka taci gaba da faruwa har sai ranar da ruqayyan ta gaji tayi maganinsu sannan aka samu sauqi. Da sallama ta shigo,idon zainab ya fara sauka a kan rigar jikin ruqayyan. Tashi daya fuskarta ta sauya,ta gane rigar sarai,tashi daya zuciyarta ta bata saleem ya zagaye ya siya mata,ko kuma ya bata rabin kudin a bayan idonta. "Aiki kake da kanka" ruqayya ta fada tana murmushi sannan taja stool ta zauna tana masa barka da dare. Cikin kulawa ya amsa duk da yana takatsantsan,yasan tsaf zainab din zata jawo wani maganar da rayuka duka zai baci. Tana so ta saka masa hannu a gyaran kayan amma tana gudun magana,don duk hirar da sukeyi zainab din na wajen,ita bata tanka ba ita kuma bata fita ba,hakanan bata tayashi da komai ba. Ta dan jima suna hirarrakinsu sannan ta miqa masa ledojin "Gashi daddy ba yawa" ita da ba ita aka bawa ba amma ta riga saleem din sanya idanunta akan ledar cikin son bin diddigi da tantance meye a ciki. *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ HUGUMA PAGE 26 "ma sha Allah,me muka samu?" Ya fadi yana dan murmushi. Murmushin itama tayi cikin salon tsokana "Gani ya kori ji ai daddy duk da babu yawa" . Ledar ya qaraso ya dauka,har sannan idanun zainab na akai tana son ganin qwaqwaf. "Kin gama komai ai,dama sauran abinda ya rage naketa tunani ban siya ba sai gashi kin kawomin,Ma sha Allah,ma sha Allah,Allah yayi albarka na gode qwarai" ya fadi yana buda kayan sosai. Tsam zainab ta miqe tsaye tana maganganu qasa qasa kafin daga bisani tace "Wannan ai cin fuska ne,me ya hana sanda ya shiga gurinki tun dazun ki bashi har sai da kika biyoshi gabana saboda tsabar iyayi da son nunawa?" Kallon tsaf ta yiwa zainab din,tana da amsoshin maida mata masu tarin yawa,to amma idan ta tuna gobe xai tafi ya barsu tare,kome zasuyi dashi zai tafi a tsaye cikin ransa sai kawai ta kauda kai ta bawa banza ajiyarta,ta kuma miqe a nutse tana dubansa "Zan wuce daddy,saida asubar?" "Alla ya tashemu lafiya maman twince" "Na gode abban twince" ta maida masa tana murmushi ta gota zainab din "Au aina dauka kwana zakiyi da sai na tattara nabar muku dakin" "Hakanma ba laifi bane tunda mata kuma uwar gidan saleem nake" ta amsa mata ba tare data waiwayo ba tana qarasa fita a dakin. Amsar tayi masifar qona mata rai,ga sunan da ya kirata dashi na maman twince sai take ga kamar gatse yakeyi mata,wannan ya hadu ya sakata rushewa da kuka. Tamkar baya ma dakin gaba daya,ko gezau baiyi ba bare ya nuna yasan da wanzuwarta ita da kukanta a wajen,ko sau daya tak bai daga kai ma ya kalleta ba bare ta sanya ran zai tanka ta Hankali kwance yaci gaba da hada kayanshi,har sai data gaza don kanta "Ko bakayi haka ba dama nasan ka gaji da zama dani matarka ce a gabanka,twince kuma itama ba ita baiwa kanta ba,wanda ya bata nima shi nake fatan ya bani" saita miqe ta bude zaninta tana bar masa dakin. Bai motsa ba har ta fice sannan yabi qofar da kallo,shi kansa da yake namiji yana mamakin sokonci da dolanci irin na Zainab din,mijinki zaibar qasa a gobe maimakon ki tattalashi ku rabu lafiya amma inaaa.......baki ya tabe,ko kadan fushinta da bar masa daki ba wai wani baqon abu bane a wajensa,qauracewar zainab daga gareshi ya riga ya saba da hakan tunda dadewa(karki soma hora mijinki da irin wadan nan abubuwan,hanashi kanki don ya bata miki rai da sauransu,duk sanda ya saba da hakan zai zame masa jikine har ya dinga jin hakan ba komai bane,kuma muddin kina hakan tabbacin baki cika mace bane,ba kuma ki iya horo ba). Tunda ta tashi sallar asuba ta kirayi wayarsa kamar tasan zainab din bata kwana a dakin ba. A lokacin ya idar da sallah yana shirin shiga wanka kenan,ta gaidashi cikin kulawa ya amsa mata "Ka shirya ne daddy?" "Waye zai shiryani tunda ba wajenki nake ba,komai da kaina nakeyi banga ma me shirin ba bare na saka rai" "Uhmmmm" kawai tace dashi don tuni ta fuskanci inda maganarsa ta sanya gaba. Bata fiya jan zancan zainab ba a tsakaninsu don haka tace masa "Idan ka gama shiryawar kayi min magana mu fito rakiya" "Alright" ya amsa mata har cikin qirjinsa yana jin kewarta. Yayi imani inda a bangarenta tafiyar ta riskeshi gata babu kalar wanda bazai gani ba. Koda ya fito dakin shuru sai ya kasa jurewa,ya daga waya ya sake kiran ruqayyan "Har me?" "Na kusa gamawa,ki kawomin manki zan shafa" "Daddy mai kuma?,ina umman haneefa akwai gurinta" "Naki nace ki kawomin" dan jim tayi tana kallon agogo,kaman yayi safiya da yawa ta shiga mata sashe,to amma tunda shi ya kira ba damar masa musu. Man shafawar nata ta dauka wanda tasan daman time to time yana shafawa shima suna sharing. Har zata gifta kitchen wani tunani ya fado mata,tasan ba lallai ta bashi wani abun da zai sanyawa cikinsa,don haka ta tsaya ta hada masa black tea a gurguje ta fito masa dashi. Sanda ta isa shi ya bude mata qofar ta wuce ciki,har ya kammala shirinsa saidai singlet ne kawai jikinsa da boxer,tana gama ajjiye kayan ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam yana sauke ajiyar zuciya. Jikinta ta janye gefe tana noqe kafada "Umman haneefa fa" "Ba wani umman haneefa,gari ya kusan yin haske,a qa'ida ma an shiga ranar girkinki ai......i missed you a lot ruky na" ya fada yana lumshe idanunsa. Murmushi ta saki,duk sanda ya kirata da wannan sunan yana tuna mata da wasu abubuwa masu dadi da suka shude a tsakaninsu. Duk da tana daddojewa amma haka ya jata sai data tayashi shiryawa "Kayi haquri ba ranata bace,kaima kanka kasan da cikin hurumina kake ko......" sai tayi shuru kawai tana girgiza kai "Yanxunma ai ni nakine ko?" "Ni da wata,dole kuma a fidda mata haqqinta" ta amsa masa kai tsaye tana duban idanunsa,sai yadan kau da kai. Sau tari idan tayi wata maganar yana jin ta daureshi ne da jijiyar jikinsa ko kuma magana take maida masa a fakaice(uta tsarguwa fa ba dadi maganar gaskiya 😂😂😂😂). Abinda ya daure mata kai har ta tayashi ya kammala shiryawa ba zainab bare motsinta "Daddy ka tasheta,bai kamata ace bata nan gurin ba yanzun,zan jiranka a waje" ta fada tana yin wuf ta fice don tasan idan bata haka ba zai tsaidata ne,kuma idan zainab din ta ganta ranta ba zaiyi mata dadi ba. Ballantana ita da ba haquri ne da ita ba ki dauke kai akan abubuwa. Da sallama ya tura qofar dakin,sai ya hangeta magashiyyan tana bacci abinta Jamar dazun mai mata knocking yace ta tashi tayi sallah ba. Takaici ya kamashi ta miqe tana hada rai ita ala dole jiya an mata laifi. Dankwalinta da ya cire ta jawo tana daure kan nata dashi sannan ta fara saukowa daga saman gadon da nufin shiga bandaki "Tsaya ni wucewa zanyi don n gama shiryawa,sufyanu yana waje yana jirana zamu dauko hajiya" "Allah ya kiyaye sai ka dawo" ta fada har yanzu fuskarta ba walwala tanason ya gane cewa lallai yayi laifi "Ki kula da yara ki kula da gida,banda fita barkatai don Allah,ko meye ya taso ga waya nan a shaidamin" "To" ta fada bayan ta tura baki gaba. Har ya juya ya dakata "Kinsan dai har yanzu akwai case dinki kan tarkacen magungunan nan........kuma baki manta da sharudan da na aza miki ba?........ kiyi qoqari ki kiyaye,ki zauna a hakanki ni bana buqatar wani gyara indai na magani ne,akwai gyararraki da yawa da ya kamata ayi amma ba wannan ba" ranta ya sake baci,tana matuqar jin haushin taji yace basai tayi amfani da komai ba hakan da take ya gamsar da shi,yo ita din goyon mahaukaciya ce da zata biyewa dadin bakin namiji?,tana da kishiyar irin ruqayya ai bataga ta bacci ba,zama bai ganta ba "Sai na dawo" ya sake fada yana saka kanshi waje "To" tace masa a cunkushe tana tura bandaki ta wuce ciki tana abunda tafi qwarewa akai wato qunaquni. Baiga alamun yaran sun tashi ba suma,yasha mata fadan tashinsu sallar asuba amma a banza,yo itana bata tashi ba sai anyi fama ina ga yaran. Tashinsu yayi yasa sukayi alwala suka watstsake sannan yayi musu sallama ya fito. A farfajiyar gidan ya samu ruqayya ita dasu alhassan,har iftee ma na maqale a gefe, dukansu sanye da jallabiyyar da ya siya musu ne saboda sallar asuba. Kusan tare yaran suka gaidashi,ya tsugunna gabansu yana amsawa hadi da jawo iftee dake maqale da qaramin hijabin dake nuna tare akayi sallar asubar da ita ya rungumeta yayi kissing nata yana amsawa hadu da tambayarsu yadda suka tashi. Duka suka rankaya har bakin gate din,ya hanasu fita saboda yayi sassafe da yawa,dukansu suka hada baki wajen masa addu'a har ana rige rige tsakaninsu da umman tasu,hatta da iftee, addu'ar da basu daina ba har zuwa sanda motarsa tabar qofar gidan ta dauki hanyar ficewa a layin. Sosai tafiyar saleem ta bawa zainab daman yin al'amuranta a tsanake,komai nata sai ya ninka fiye da na baya,qazanta sai abinda yayi gaba,don kuwa tana iya shafe kwanakinta biyu cur bata duqa tayi shara ba,kamar yadda wanka ya tafi hutu a tattare da ita. Abinci kuwa ba ita ba hatta yaran za'a iya cewa horon yunwa take musu,don saidai su shiga sassan ruqayya suci,wasila tayita mita don takaicin zainab takeji kamar kamar me amma hakanan ruqayya ke cewa ta basu ba komai bane,lada zasu samu. Da wannan damar zainab tayi amfani ta riqe 'yan kudadenta ta siya magunguna ta adana wanda zatayi amfani dasu bayan anyi mata aikin,sauran 'yan canji ta duba ma haneefa atamfofi a 'yan pieces ta siyawa khalil gumama da pieces na shadda aka dinka masa duka a zuwan kayan sallarsu. Ba wani takalmin arziqi bare jaka mayafi da sarqoqi da ubansu duka ya fidda kudinsu,nata kayan kam ba tasu take ba,don ta tsara gaya masa cewa an sace a wajen tailor dinta,shikenan hankali kwance. Tuni sun tsara da nurse din satin farko da aka kama azumi za'a yi mata dinkin,a lissafinsu kafin ya dawo ta warke sumul muddin zata kula da wajen tana tsaftaceshi da shiga ruwan zafi. Wannan ya sanya ta tura neman me zama da ita,bata samu ba sai safina ta samo 'yar wan babansu. Ba yarinyar taso ba,saboda basu cika jituwa can can ba saboda banbancin halaye dake garesu. "Ni umma yarinyar ta fiya tsaurin ido,ga shegiyar kafiya da taurin kai" "Eh amma ita kadai zata iya da aikin gidanki,don bata da son jiki ko kasala,da qyar fa nasha kanta ta yarda,kinsan abdurrahimu baya barinsu zuwa ko ina su kwana,sun riga suma da sun saba,yanzu ma a qila wa qala ake" "Shikenan,ki lallabata tazo din,don azumin bana da alama zai bada kashi" a haka sukayi sallama da umman nasu. ********Ranar da aka sauke azumi na uku ne,bayan an gama shan ruwa kafin akai ga tayar da sallar asham ruqayya ta shiga dakin d wasila ta sauka. Da sallama ta shiga ta sameta saman dadduma,dakin ya kaure da qamshin turare,sai wasu mayuka dake zube ta budesu tana hadasu guri guda. Guri ta samu ta zauna suna yiwa juna sannu,don wasilan ba laifi idan taso akwai aiki. "Nikam tunda aka fara azumin nan kamar baki da walwala sosai" dubanta wasila tayi kai tsaye sannan tace "Bazan boye miki ba,wata jarrabawa ce ta shigo min rayuwa,kinsan zaid?" "Zaid?,zaid?,wanne?" "Abokin yaa bashir wanda ya tafi madina karatu satin da aka fara bikinki?" "Oh.....ya zan manta da yaa zaid da ya kawo me lecture ranar wuni na" "Exactly......ya dawo nigeria ruqayya,shi zuciya ta kuma ya jarabtu da so,nayi addu'a nayi addu'a amma ba abinda ya canza,naje wajen malam yacemin lamarin akwai rikitarwa,amma yace zaiyimin aiki a kansa cikin satin nan ya gani idan akwai alkhairi" "A irin wannan watan wasila?" Ruqayya ta tambayeta cikin tsananin tashin hankali kwance a fuskarta,abinda ya Sanya jikin wasila yin sanyi ta bita da kallo. Sassauta fuskarta tayi ruqayyan ta zamo ta zauna gaban wasila "Wasila,wasila......babu wata addu'a da zakice ba zaki iya yiwa kanki da kanki ba sai wanine zaiyi miki,muddin kikaga kina addu'a kina ganin kaman bata karbuwa cikin daya biyu ne,kodai kin saka shakka a ranki game da addu'ar kin sawa ranki bata karbuwa,ko kuma kin saka gaggawa lokacinki yana tafe amma saboda gaggawa irin ta dan adam ya sanya kike ganin har yanzu shuru" "Wasila" "Na'am" "Kinsan Allah da kansa yace yana kunyar bawansa ya daga hannu ya roqesh ya hanashi abinda ya roqa?,kinsan ko sau daya kikayi addu'a zuciyarki tayi rawa akan cewa wannan addu'ar bata karbu ba to tabbas kin jawowa addu'arki matsala,annabi S A w yace kuyi addu'a kunajin yaqinin ta amsu cikin ranku,koda bakaga haka a zahiri ba ka sanyawa ranka cewa ta karbu din" shuru wasila tayi tana jinjina kai *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* 27 *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ PAGE 27 "Ba wani wata dake cike da falala sama da wannan watan,dama ce a gareki ki tsaya ki roqi Allah,basu isa su sanya Allah dole ba,ba wanda ya isa ya sanya Allah ya baki abinda bai cikin rabonki ko qaddararki,indai suna da wannan power din me yasa su basu canza qaddarorinsu ba?,me yasa basu zama masu arziqin da zasufi qarfin zama a soro ko jeji suna saurarar buqatun mutane?,kinsan cewa duk matar data taka taje wajen boka ko dan duba,duk da yanzun an canza musu suna nason zuciya da son rai,ana kiransu da malamai ana kiran DUBA da ISTIHARA,muddin mutum zai gaya miki wani abu da yake a boye,kaza ne zai faru,kaza ne yake faruwa,kaza ne zai faru,siyo kaza siyo zakara siyo akuya rago ki yanka kiyi sadaka,daka borkono qona abu kaza binne abu kaza to SALLARKI TA KWANA ARBA'IN BLANK TAKE EMPTY TAKE cikin littafin ayyukanki,kuma kin sani na sani sallah itace abu na farko da ake fara dubawa cikin ayyukan bawa,idan tayi kyau sauran ayyukan sun karbu,idan ka samu matsala tun daga nan ba zaka wuce bama bare a tafi duba ragowar ayyukanka. Awannan lokacin a cikin mata akwai macen da bata rufa kwana arba'in bataje wajen wani malami akan wata matsala ba,kinga a qididdigar lissafin ayyukanta bata da sallah,ki gayan ran qiyama meye marabarta da ARNE?,tunda duka guraben sallarta sun xama empty silar zuwanta gidan malamai yan duba yan tsubbu da yan bori?" "Wasila,duk abinda kikaje wajen malami yace miki zaki sameshi kuma kika sameshin,wallahi wallahi ba malaminne yayi sanadiyyar samun da kikayi ba,dama can Allah ya rubuta zaki sameshi,kuma da kinyi haquri bakije ba kina zaune a dakinki rabonki zai taddoki ta halastacciyar hanya ba tare da kin sabi mahaliccinki kinje wajen dan duba ba,wata ne wannan da ake ninka ladan ayyuka,ki zage kiyi addu'a kawai tsakaninki da mahaliccinki shine yafi". Sosai jikin wasilan yayi sanyi,kamar dai hankalinta ya fara kaiwa wani wajen daban. *********Yammacine lis lokacin da mata da yawa suka fara nisa wajen sauke abincin buda baki hadi da qoqarin kammala gurin da za'a yi buda bakin. A daidai sannan Zainab na cikin labor room na asibitin cikin matuqar farincikin matsalarta zata kawo qarshe. "Kinyi inserting wani abu ne?" "Ai kullum cikin matsi nake,waye zai zauna yaga zama?,mazan nan ka gyara ma amma baka tsira ba ina ga ace baka gyara ba?" "Gaskiya ne,hakane" nurse din ta fada can qasan ranta tana dariya da mamakin Zainab din. Har ta gama hada duk waji scissors da sauran tarkace Zainab din batayi ko gezau ba "Ki shiga toilet ki wanke abinda kika saka din kizo mu fara" "Toh nurse" ta fada da rawar jiki tana wucewa bandakin. Bayan ta fito ta zare pant din ta ajjiye sannan ta haye gadon ta bubbuda qafafu kamar yadda nurse din ta umarceta sanda take qoqarin balla razor din da zata kankareta biyu "Subhanallahi,meye haka don Allah?" Nurse din ta fada ganin irin cunkoson go slow din da gurin ya tara "Me kenan?" Zainab din ta tambaya "Tashi ki sauka kiyi aski,wannan ko inda zan dinke mikin ai bazan gani ba" ta fada tana jan tsaki qasan ranta tare da yin Allah wadai da son kudi itama irin nata. A gaggauce ta saisaye ta dawo ba wani cikakken baiwa wajen kulawar tsafta yayin aski,nurse din itama ta kula da hakan amma ganin itama a gaggauce take da ayin sai kawai taja kujera ta saka face mask ta fara aikinta. Sai da aka fara din ta gane Allah daya ne,don zata iya cewa batasan azabar stitches ba don bata taba qaruwa wajen haihuwa ba. Kafin a gama tayi wujiga wujiga,sauqinta daya ta taho da safina wadda batasan me za'a yi ba,tadai ga kawai Zainab din ta shige labor room. Magashiyyan ta kwanta ta kasa motsawa,tana jiyowa ana kiran sallah musulman cikinsu suna tafiya buda baki,ita da azumin Allaha a bakinta amma ta kasa koda kurbar ruwa saboda wata irin azaba dake ratsata kamar ta cire dukka gwiwoyinta zuwa cibiyarta. *_G I D A_* Komai sun kammalashi kamar yadda suka saba kafin ayi kiran sallah alhassan da alhussain da sukakai zuminsu daidai da na kowa na zube na jiran kiran sallah wasila na musu dariya Haneefa da khalil ne suka shigo daya yana biye da daya "Kuzo nan" ruqayya da fitowarta kenan daga daura alwala ta kirasu "Wasila zuba musu abinci banajin gidan nan Zainab ta wuni" "Iyalan ci,tunda ba'a gaya miki za'a fita ba basai ki qyalesu ba" "Ki bari mana wasila" ruqayyan ta fada tana dubanta. Bata sake cewa komai ba ta miqe ta nufi kitchen. Gaba daya safina ta kasa tantance me yake faruwa har sai bayan shigarta dakin taji nurse din tana jaddadawa Zainab dokoki. Mamaki ya kamata,itadai tasan ba haihuwa tayi ba bare ace qaruwa tayi,hasalima ko ciki bata dashi,to amma meye hadinta dinki?. Gabanta yadan fadi data tuna wata hira da taji wasu mata sunayi,kenan itama tabi sahun matan dake zuwa a diddinkesu kawai saboda su bawa namiji wani abu ba tare da suna duba makomar lafiyarsu ba?. Sanda duka isa gida tamkar 'yar shayi haka ta riqe zainab,takaici ya sake kamata sanda suka isa sassan Zainab din,komai ba bisa kan qa'ida ba,ta tabbatar kuma tsohuwar qazanta ce ba ta jiya ko yau ba. Tun tana aikin tana daurewa harta magantu "Wai bakwa shara bakwa wanke wanke ne?,kun taba mopping sashen nan kuwa?" Harara Zainab dake fama da azabar radadi ta balla mata "Ban sani ba,ku me yasa kuka fiya magana ne keda hajiyayye,hala gulmata kuka zama kuyi saboda kalamanku iri daya ne da nata" "Ba wani gulmarki,inama muka hadu ni?,abunne ya bani mamaki,tunda dai da nazo na leqa sashen anty ruqayya mun gaisa naga ba haka nata sashen yake ba,hakanan farfajiyar gidan nan fes yake ko ina da ina,to sai naki sashen ne zai zama haka?" "Zanci mutuncinki safina,ki wuce ki bani guri" ta fada a hasale. Baki safinan ta tabe tayi gaba,ba tun yau ba ta sani Sam zainab din bata qaunar a gaya mata gaskiya ko qanqani. Sam ruqayya batasan abinda yake faruwa ba,tana can sashenta tana sabgar gabanta,babban abinda yafi damunta kada tasha azumi,kuma Allah ya taimaketa tana samu tana gwadawa wasu lokutan. Tsananin son jiki da zallar qazanta ya sanya zainab bata iya shiga ruwa da kyau kamar yadda nurse din ta umarceta,tunda akayi dinkin tafi ganewa ta jabe a zaune a falo,ta lalace tsakanin kallon tv da chart kamar ba azumin ramadan akeyi ba. Tun safina ta murje idanunta,duk wanda yayi ba daidai ba tsakanin khalil da haneefa ubansu takeci,don tace ba zatayi wahalar banza ba,ta sha wahala kafin ta samu tadan kintsa sashen,duk da ba komai ya koma yadda ya dace ace ya kasance din ba,amma ba laifi sassan ya shiga saiti kaso sittin cikin dari,don wani abun idan ya baci baya gyaruwa. Sau tari idan dinkin ya dameta da qaiqayi sosa abinta takeyi,ko tayita mutsu mutsu har sai ta sosheshi,idan kuma yana radadi bankada zaninta takeyi ta kunna qaramar fanka. Sannu a hankali gurin ya fara rurucewa yana sakin wani irin ruwa,amma sanda taga ruwan a pant dinta sai murna ta kamata "Bayan matsi har ni'ima wannan dinkin yake saukarwa, Alhamdulillah" ta fadi farinciki yana kamata. Batayi wani yunqurin komawa asibiti ba,don nurse din ta gaya mata ta sallameta tunda ta gaya mata ruwan dumi zata dinga shiga,zaibi jikinta basai tazo dubawa ba. Tayi hakanne saboda dokar asibitinsu kora ce ga duk wanda yayi irin wannan,saboda hakan tamkar ya shiga a matsayin cin amana ne da zamba. ********Karfe sha biyun dare ta kammala salllolin darenta da basa wuceta a wanann watan,dukka tana yin addu'o'inta ne akan samun gamawa da duniya lafiya,zaman lafiya a gidanta da mijinta,da shiryuwar yaranta da yaran musulmai gaba daya. Sau biyu takanci abinci,irin wannan lokacin da kuma lokacin sahur shine take samu abincin ya riqeta sosai,tana yawaita shan kankana duk suna cikin abinda ke sauqaqa mata azumi(ga mace me ciki dakeson yin azumi ba tare data wahala ba,ta yawaita shan kankana tana taimakawa sosai). Har ta zuba abincin a dining saita dinga jin kamar sheshsheqar kuka a dakinsu iftee,ajjiye abincin tayi ta juya zuwa dakin. Wasila ce saman abun sallah sanye da hijabi take kuka kariris. Girgiza kai ruqayya tayi ta qarasa shigowa "Lafiyarki wasila?,da daren nan?" "Na shiga uku na shiga jarabawar da bansan yaya zanyi da ita ba,ruqayya ki taimakeni,anya ina da sa'a a rayuwata?,anya ina da rabon yin aure?" "Me ya faru?" Idanunta da sukayi jajur ta daga "Dazu na biya ta gida muna magana da yaa bashir saiga yaa zaid yazo zasu fita,sai naji yana gayawa umma zasu bincike ne kan yarinyar da zaid din zai kaiwa kudi bayan sallah......na rasa yaa zaid shima ruqayya don Allah ya zanyi?" "Malamin naki da kikaje gurinsa daxu ya gaza kenan?,ina tarin alqawuran da yayi miki?,ina mijin daya fasalta miki yace zaizo shi zaki aura?" Sak wasila tayi,don bata taba tunanin ruqayya ta ramfota ba "Kin yadda yanzu sa zancena kan cewa dukkaninsu maqaryata ne?,kin yarda da maganata akan cewa ba zasu iya ba?,me yasa suka gaza baki abinda kike da muradi tuntuni sama da shekara goma kina yawo a tsakaninsu?" Qas da kanta wasila tayi hawaye suna zuba "Na miki tambaya mana" kai kawai ta iya gyada mata "Yanzu misali kece mutum yana qarqashinki,kece cinsa shansa tufafinsa,iliminsa lafiyarsa,ke hatta rayuwar da yakeyi yau idan kikace bakiso zata yanke,amma duk kina bashi wadannan abubuwa,shi kuma yana iqirarin yana sonki saidai kuma baya iya miki biyayya,idan kince yayi gabas yamma yakeyi,idan kince yayi yamma kudu yakeyi,dare da rana haka ne,zaki iya ci gaba da bashi dukkan abinda yakeso daidai da wanda yake binki sau da qafa?" Kai ta girgiza alamun a'ah,sai ruqayya ta gyara zamanta "Sama da haka kikeyiwa Allah ta'addanci shin kin sani?,ya baki lafiya wadda bai bawa bayinsa miliyoyi da suka fiki yi masa biyayya,ya baki ilimi hankali ya kyautata surarki wadda bayinsa masu yawa da suka fiki binsa bai basu ba,kome kikeso ya baki shi kyauta ba da kudinki ba,amma ya shata miki wasu layuka 'yan kadan yace kada ki tsallake sai kikayi kunnen uwar shegu dasu. Kinsan cewa qarya kadai da kikeyi tana iya hanaki samun duk wani alkhairi a rayuwarki?,SHAFA MAI DON KIYI HASKE da magungunan qarin qiba da kike sha kinsan su kadai taka hurumi da dokar Allah ne?,SAKA FARCE KO AJJIYE FARCW A HANNU,QARIN GASHI DAMA KO MEYE da kikeyi bakisan haramun bane?,ba mijinki ba,ko waye zaki yiwa da sunan ado HARAMUNNE HARAMUNNE HARAMUNNE,kuma billahillazi la'ilaha illa huwa yadda annabi yace meyi ba zatashiga aljanna ba bazataji qamshinta ba,idan duk duniya gatanki ne ba wanda ya isa ya sanyaki shiga aljanna,bare uwa uba zuwa wurin malami ko dame yake aiki muddin zai gaya miki abinda yake gaibu ko abinda yake a boye,don wasu suna rudarku da ajjiye qur'ani da litattafan addini da rawani da carbi" "Nima tunda nake ban taba shiga jeji ko zuwa gurin wani malami me kayan shirka ba sai wanda na ganshi da litattafan addini........" "Suma mushrikai ne,suna sanya litattafannne saboda ado su jawo hankalin mata masu sauran imani,duk duniya ki gayamin WAYE YASAN GAIBU?,sai Allah shi daya sai kuma annabawa yakan sanar dasu cikin abinda yayi niyyar su sani,SANIN GAIBU SAI ALLAH....... *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 28 ________________________________ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ _____________________________ "mu'amala dasu bata qarawa bawa komai face cire masa imani da yaqini da ubangijinsa,ta fidda maka dukka wani hasken tauhidi,ta cire maka wani ginshiqi cikin ginshiqin imani wato yadda da qaddara me kyau da mara kyau,wasila.....ki kiyaye dokokin Allah sai Allah ya kiyaye duk wani abu da kikeso,kiyi kishin Allah sai Allah yayi kishinki,ki gwada wasila da iklasi da tsarkake niyya,wallahi wallahi wallahi Allah bazai baki kunya ba bazai bani kunya ba" sai ruqayya ta zare hannunta a hankali daga cikin na wasila tana kallon tsakiyar idanun wasilan wadda sannu a hankali maganganun ruqayya taji suna samun wani matsugunni me kyau a ranta,irin matsugunnin da basu taba samu daga gareta ba. Washegari da safe da hannunta ta tarkata duk wasu abubuwa da tasan tana ta'ammali dasu ta qona,irinsu jan farce nail polish,ribbon din attachment,shi kansa gashin da ake mata kitso dashi,ta cire sarqa qafa uban barimomin kunnenta,magungunanta da duk wasu takardu na rubuce rubuce da malamanta suka bata sukace tayi amfani dasu, supplement dinta na qarin qiba da haske dukka ta tattarasu ta qonesu. Bata cewa ruqayya komai ba,saidai ruqayyan taji dadin hakan ta kuma tabbatar da cewa lallai komai yana da lokacinsa,yau dare daya wasila taji nasiharta?. Ko bayan sun gama buda baki a ranar saita kalli ruqayya "Me dame kike ganin ya kamata na riqe a yanzu?" Sosai ruqayya taji dadin tambayar,ta saki murmushi "Muna lokaci na amsa addu'a,ki riqe istigfari ba kuma iya a baki kawai ba,duk sanda kikayi istigfari din kiji har zuciyarki kina yine saboda neman yafiyar ubangiji akan zunubanki,kuma kina yine saboda samun kusanci da Allah,ki yawaita ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astgis,Allahumma rahmatika arju,fala takilni ila nafsy darfata ainin,wa'aslihi li sha'ani kullahu la'ilaha illa anta,sai uwa uba kuma shakundum salatin annabi muhammad S A W ko shi kika riqe da istigfari sun isheki komai basai kinje gurin kowa ba,amma akwai babban abu muhimmi guda daya wanda da yawan mutane basu sanshi ba....." "Menene shi ruky?" Wasila tayi tambayar tana kallon fuskar ruqayya "Husnul kulq wato kyakkyawar mu'amala" "Kaman yaya?" "Ma sha Allah" ruqayya ta fada tana gyara zamanta "Ubangiji yana masifar kishin bayinsa,duk yadda kikai ga ibada da kusanta kanki da Allah muddin baki da mu'amala me kyau tsakaninki da mutane bayin Allah to za'a iya cewa ibadarki ta tashi a banza" idanu wasila ta fidda "Kaman yaya?" "Yauwa,zan baki wata kissa,watarana annabi S A W yana zaune da sahabbansa,sai akazo wucewa da gawar wata mata,sai sahabbai suke fadin irin halayen matar,macace me azumi ga ibada ga sadaka ga kuma tsaiwar dare,amma maqotanta basu tsira daga cutarwarta ba,sai annabi yace wajabat,wato tabbata akanta,da sahabbai suka tambayi ma'aiki akan hakan sai ya shaida musu ta tabe,yar wuta ce,kinga azuminta da ibadarta basu amfaneta da komai ba tunda bata da mu'amala,sau da dama mutumin da yake da mu'amala me kyau da mutane yana iya samun rahamar Allah bayan ya mutu koda kuwa shi din me yawan zunubi ne,sai yaci albarkacin kyautata zamantakewa da bayin Allah" sosai jikin wasila ya sake sanyaya,tayi shuru tana nazari,matan yayyenta duk da tana kyautata musu amma suna yawan kuka da halinta,kamar ruqayyan tasan me take tunani ta sake cewa "Abinda ka raina sai kaga ranar gobe babban abune a wajen Allah,ki zauna da kowa lafiya da kyakkyawar zuciya" "In sha Allah" ta amsa mata a sanyaye. Tun daga ranar komai na wasilan ya canza,hatta da magana me yawa ta rage duk da ita din gwanar surutu ce,ko yaushe zaka sameta da counter a hannu,koda ta sha'afa an fara doguwar hira zata koma istigfar dinta da salatinta. Sannu a hankali sai ta dinga jin wata nutsuwa tana saukar mata irin nutsuwar da tunda take yawan bin gifan malamai suke bata wurdodi bata taba jin makamanciyarta ba,dukka damuwarta akan zaid sai taji tana gushewa,tsananin tunanin zaid da takeji kaman zai zautar da ita sai ya fara raguwa a ranta,tana iya wuni ba tare data tunashi bama. Har a ranta kuma takejin zata iya daukar kowacce qaddarar rayuwa da zata sameta,samun zaid ko rasashi,taci gaba da addu'ar samun nagartaccen miji kadai wanda zai zamewa rayuwarta alkhairi. *_ZAINAB_* Ko sau daya bata taba kaiwa hankalinta ga yadda dinkinta ya dinga zarewa zaren yana ficewa ba tun baikai ace ta warke ba,ranar da taga zaren farko ta yanke abinta tana murnar "Dinkinnan yayi mugun saurin warkewa,ga zare nan ya fice da kansa?, gaskiya ina da sa'a" tsananin qazanta ya hanata jin tashi tashin da wajen ya farayi. Abun tun safina bata fara jinsa ba har ta fara yi mata complain,sannu a hankali itama ta fara ji saidai kadan kadan,sai kawai ta bagarar ta azawa ranta qaranta amfani da ruwan dumin da akace tayi amfani dashi da takeyi ne ya jawo haka. Wannan ya sanya kullum sau daya a rana zata cika baho da ruwan dumi ta shiga ta fito,a hankali ta soma jin qaiqayi,qaiqayin da yasa ta sake imanin dinkinta warkewa yakeyi fes,abin yayi mata dadi saboda yazo ne dai dai sanda ya rage saura kwanaki biyar saleem ya dawo. ******Zuwa lokacin ta fara jin sauqin laulayinta sosai,tana iya wasu abubuwa da yawa da kanta,hakanan azuminta taba bakin qoqari taga takai,sam bata sanyawa kanta irin son jiki na matan yanzu ba,wadanda daga ciki su da azumi sunyi hannun riga,idan ya sake zagayowa kuma suce shayarwa,wata shekarar kuma an samu wani cikin,sai ka wayi gari da yawa yawan mata suna wasa da ibadar azumi,wanda babbar masifa ce muke jefa kawunanmu,muna kuma kwashewa yaran albarka don ta silarsu muke fakewa da qinyin azumin. Tsaf wasila ta tayata sukayi kwalemar sashenta,don kada su jigata duka sai ansha ruwa sukeyi. Gwanar tattali ce ita,kuma uwa uba tana Sana'a,gashi cikin watan da ciniki yake yawaita,don haka cikin ribarta da abinda ta tattala din tayi siye siye,kusan tafi rinjiyar da komai ga gyaran dakin saleem din,burinta ya dawo ya samu komai ya banbanta da sanda ya tafin. Tun daga bedsheet blanket dinsa zuwa qananun underwears na ciki da curtains na dakinsa. Kwanaki biyu ya rage ya dawo ta kirayi me qunshinta ta ta zuba mata jan lalle ita da iftee,aka yiwa wasila itama a mazaunin qunshin sallarta,bayan ansha ruwa taje akayi mata wankin kai,take gashinta ya qara tsaho da sheqi ta hadeshi cikin ribbon gwanin sha'awa. *_ZAINAB_* Kusan tunda lissafin kwanakin dawowar saleem ya fara matsowa nata dokin ya ninka na kowa saidai ana iya cewa dokin banxa tunda nata tunanin yasha banban da na kowacce mace me hankali. Gaba daya tafi karkata tunaninta wajen neman magungunan mata da zata sake tsuma kanta da kanta a cewarta,dai dai da gyaran sashen ba abinda ta iya tsinanawa banda dakin saleem din data gyara a daddafe,tana gamawa ta sharbe a wajen,bata sake motsawa ba har sai da safina ta tasheta bayan ansha ruwa. Da dan hanzarinta taso miqewa,saidai hakan ya gagara kwata kwata saboda wani mugun riqewa da qugunta yayi. "Wayyo na shiga uku" ta fada tana dafe qugunta hadi da ware idanu. "Lafiya?" Safina ta fada tana kallonta,don ita kanta zuwa yanzu ta fara gajiyawa da abubuwa da yawa na Zainab,Allah Allah take mijinta ya dawo ta tarkata ta barsu "Mugun ciwo marata takeyi" ta fada tana yarfar da hannu "Sannu,ki daure ki tashi saikisha ruwa kisha magani" ta fada tana kallonta. Ta jimaa haka kafin ya saketa,ta miqe tana dafawa da qyar ta isa bandaki. Saman tiles ta tsugunna zatayi fitsari duk da yadda safina ke masifa idan ta wanke toilet din duk wanda ya mata fitsari a qasa. Maimakon ruwan fitsari sai ga jini yana fita da wani butaci butaci "Kaddai period ne yazo?" Ta tambayi kanta da kanta bayan ta gama fisarin. Cikin ranta ta gamsu shi dinne,saidai kuma yadda taji jini yana bin jikinta sai abun yadan bata mamaki "Koma meye kafin nan da ranar da zai dawo na gama period din nan,duk da ba haka naso ba amma ba matsala" ta fada a ranta tana duba tsummokaran da take period dasu,don kudin always dinta na watan shima ta sakashi a layin kudin magani. Tana sakawa ba dadewa ya jiqe,sanda ta fiddo tsumman yawan jinin da wari warin da yakeyi yasa ita kanta ta yamutsa fuska,a ranta tana tunanin maganin da ta shane da asuba bayan ta gama sahur. Wasu tsumman ta ninka sukayi tudu sosai sannan ta samu yadan zauna a jikinta. Bata wani jima dashi ba shima taji ta fara leaking,sosai hankalinta ya fara tashi da ganin yadda take bleeding. Daga daren zuwa safiya ita kanta tasan ta zubda jini sosai,cikin zuciyarta kawai taji taqi yarda ko gamsuwa da zubar jinin, zuciyarta ta shiga raya mata akwai wata a qasa,don haka ta jawo wayarta ta kirayi raliya abokiyar shawara. Sun jima suna waya da raliyan,kuma dukka maganganun data gaya mata sun zauna sosai a rai da zuciyarta,ta gamsu da maganar raliya,lallai ba makawa asiri ne,jifanta akayi,kuma ba kowa bace da wannan aikin sai ruqayya,da alama ta lura da shirin da taketa yi da gyaran HQ dinta don sake samun fada a wajen saleem,lallai kam wannan karon ba zata bari ba,koda bata taba bin malamai ba a wannan karon saita taba ruqayya don ta nuna mata ba tsoronta takeji ba,ba kuma wai finta sanin hanyar gidan malamai tayi ba,sai ta sanya an zubda cikin da take taqama da shi,sannan kuma ta sanya a saka mata warin jaba ta yadda ko dosota saleem bazaiyi marmarin yi ba,idan yaso ita da itan dukka su rasa ayi mutuwar kasko. Tana saman kujera tana faman kada qafa hadi da lissafin dokin rano safina ta shigo falon. Kallon safinan tayi sama sama ta sake maida hankalinta ga lissafinta,itama safinan bata bi ta kanta ba ta samu waje ta zauna tana cewa "Ba wani gyara ne da za'a yi umman haneefa?" Dan maida kanta kadan tayi ga safina "Gyaran me?,wani abu ya lalace ne a gidan nan?" Kai ta mirgina cikin takaici amma ta danne don har ga Allah tanason ta gyara din "A'ah,ba babansu haneefa saura kwana biyu ya dawo ba?,banga kin canza komai ba" "Me kuma zan canza?,dakinsa ne na shareshi yana kulle babu me shiga" haushi ya sake kamata,ko ita da take budurwa ai tasan abinda idan mace tayi zai dadadawa miji matafiyi "Haba ke kuma anty Zainab don Allah,share daki wani abune?,dakinma da daga shara ko goge goge bakiyi masa ba?,bakiga momynsu alhassan ba?,bakiga har qunshi akazo akayi musu ba?,ta wanke kanta ta gyare sashen har curtains naga ta canza......" "To baqar munafuka" zainab ta fada tana gyara zamanta hadi da ajjiye wayar hannunta a gefe "Da alama idan nayi baccin rana satar jiki kikeyi ki shiga wajenta ko?" "Kinsan inda zan shiga idanunki biyu ma shiga zanyi.....ita tsafta ai bata boyuwa hakama akasinta,ko kai makaho ne kazo gidan nan ka zauna zakasan matar tana da tsafta,don ko ta sashenta kazo giftawa zakaji qamshin sashenta daban yake,kwalliyarta daban haka sutturar da yaranta suke sawa ma atsaftace take" *_Mu hadu anjima in sha Allah new page_*😊 *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE_ *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 29 https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz *_Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_Hanzarta kiyi joining group dina domin samun kaya masu tsananin kyau da quality akan farashi me sauqi,siyan d'aya d'aya na cikin gida ko kuma sari kikeyi?, AKWAI RAGI DA DAMA TA MUSAMMAN DAGA WAJEN MASU SARI,KAYANMU MU MUKE KAWOSU DAGA TURKEY DA CHINA_* *_Akwak bonanza da nakeyi time to time na kayana idan dama ta samu_* "kin gama?" Zainab ta fada tana tsire safina da ido,safinar bata damu ba ta dora da fadin "Kina ganin kamar maganin mata kad'ai shine sirrin mallakar miji?,wallahi ba anan take ba,shi maganin mata shima ba kowanne iri ba ingantacce amintacce wani ciko ne na kwaskwarimar halitta ga d'iya mace tunda hausawa sunce ko kana da kyau ka qara da wanka,wani namijin kome zakiyi masa ba zaki burgeshi ba matuqar baki da tsafta baki da kalami baki da ladabi da qanqan da kai,wani namijin kuma muddin baki iya abinci ba babu abinda zakiyi ki burgeshi don a nan tasa jarabawar take,bawai gyaran can ciki bane yake mallaka miki miji,inda shine kadai yake mallakawa mace miji da mata da yawa basu mallaki mijinsu ba,gyara ba qarya bane kuma gyara abune me kyau,amma komai idan akayi na hankali yafi tafiya da kyau. Daidai da mace 'yar uwarta matar nan momynsu alhassan tasan yadda zatayi magana da ita me kyau da kyakkyawan lafazi,ni da nake yaruwar kishiyarra bata tabamin mugun kallo ko maganar banza ba,amma kefa shekaran jiya ina kallon yadda kika debi qannenta kika watsar da sukazo gidan nan shan ruwa,harda waqe waqe da qananun maganganu,duk ba siyawa kai raini bane?,kin taba ganin mu tayi mana haka?,kosu raliya da suke zugaki kin taba ganin tabi ta kansu su da haukarsu?,abu daya takeyi wanda yakeyi da ita a cikinmu tayi dashi harma ta fiki sonmu,wanda bayayi da ita tafi banza banzatar dashi wannan kuma nima yayimin banga laifinta ba sam sam" "To qaramar 'yar iska,yaushe akay dafen bare garin ya waye?,har yaushe kika girma?,yaushe kikazan irin waxan nan abubuwan na masu aure safina?" "Ni ba 'yar iska bace,zama da mata masu hankali yasa nayi karatun da banzo wajen ba kuma alhamdulillah yana amfanata" "Inaaa,saidai idan barbada kika fara safina" zainab tafada tana mirgina kai hadi da jin takaicin maganganun safinar data daukesu basu da maraba da zagi "Indai tsafta ce karuwanci to na fara karuwancin......' safina ta fada don ranta ya fara baci,ya daga bada shawara zainab din zata jefeta da mummunar kalma irin haka? "yasin matar nan na tabbatar wallahi pant dinta yafi brush dinki tsafta,don haka idan zaki qwaci mijinki da tsafta iya girki iya kalami.ladabi da biyayya tamkar ki kwanta ya takaki to...... don nidai banga ta inda mijinku ya rageku ba bare ace bai cancani a bishi ba" "To ko aurensa zakiyi ki shigo mu goga kafada?" Zainab din ta fada tana miqewa cikin nuna kishi. Dariya safina ta bushe dashi "Bazan iya goga kishi da mommyn alhassan ba,don nasan kamota da zama kamarta sai mace tayi da gaske" ta bata amsa da magana me harshen damo tana wucewa dakinsu "Fito ki koma gidanku tatacciyar mara mutunci" "Ko baki fada ba,aini na gama zama,ladan dana samu ma Allah ya amfanashi haka". A haka suka rabu da safina walle walle,tayita surfa ashar tana zagi bayan tafiyar safinan,don sai daga qarshe ta zauna ta faffasa maganganunta sannan ta fahimci zaginta ma ashe tayi a fakaice. Duk da ta sauke azumi saboda jinin da taketa zubarwa wanda a nata tunanin period ne amma taji jiki kafin ta gama ayyukan da safinan keyi,daga qarshe dai ranar ungulu komawa tayi gidanta na tsamiya,don bata iya gama aikin ba tayi jiqa jiqa yadda ta saba ta samu waje ta kwanta saboda wani irin weak da jikinta yayi duk a sanadin jinin da take zubdawa me yawa. *****Qarfe takwas na daren jajibirin sallah jirginsu saleem ya sauka. Dai dai lokacin da ruqayya ke kai kawo tsakanin falo da dakunan baccinsu don ganin ta wadata gurin da turaren wuta. Idan ka kalleta saita burgeka,saboda tayi kyau cikin dinkin wata lallausar atamfa da aka zuba mata doguwar riga. Daurin kanta ya zauna das,lallen dake hannu da qafafunta sun yiwa hannuwanta da suka qara taushi da haske kyau saboda cikin dake jikinta wanda ya fara turowa gaba. Duka yaran suna wajen wasila a daki anata faman fidda kayan da za'a saka a gobe idi. Yaran shadda tayi musu fara qal harda babbar riga iri daya da saleem data sanya aka zuba masa shima aiki a babbar rigar zatayi masa ba zata da ita a matsayin gift dinta na dawowarsa. Suna jin qarar tsauwar motar suka diba da gudu kowa na rige rigen isa farfajiyar gidan,dama kuma kunnuwansu dama suna farfajiyar gidan tunda sukaji an tafi dauko baban nasu. Garin wannan saurin suka yarda iftee,ta tsala kuka kuwa abinda ya dakatar dasu ya kuma ja hankalin ruqayya ta iso wajen. Harara daya tayi musu kaman yadda ta saba kowannensu ya shiga taitayinsa "Ku koma ku zauna" ta fada a dake,tilas kowa ya koma saman kujera ya zauna idanunsa a bakin qofa suna daukin ganin abban nasu. Godiya yayi ga Allah sanda ya shaqi iskar gidan,saidai kuma ya cika da mamakin abinda ya hana yaran fitowa musamman su iftee da ba kasafai koda yana gari suke missing zuwa tarbarsa ba. Kayansa ya bawa yahaya qaninsa yace ya wuce dasu sashen ruqayya shi kuma ya saka kai sashen zainab tunda yasan a sashen ruqayya zai sauka,abinda ke dada faranta ransa kenan tun a jidda kafin su taso,yasan zai sauke dukka wata gajiya tasa,zai kuma huta da kyau qwarai fiye da yadda yakeso. Yana sallama Khalil da haneefa suka yo kansa da gudu ya hadasu ya rungume yana amsa oyoyo dinsu. A sanyaye zainab dake zaune dafaan a wajen saboda jinin da ya fara bata zaninta bata samu ta tashi ba saboda wayar da sukeyi da raliya akan maganin da za'a amso mata na tsaida jinin data laqabawa suna jinin jifa,ta sauke wayar gabanta yana faduwa,saboda duka a lissafinta sai washegarin sallah zai dawo,kafin sannan suka ta samu ta saita komai,don taci alwashin ko na minti daya ba zata barwa ruqayya shi ba wai don tana cikin jini,sam ba zata bari ba,idan ma tayi ne don ta shawo kanta ita daya,kuma idan kwana biyun nan taci bulus,wani girkin da zata karba zata fara shine ta kuma qareshi cikin ciwo da tashin hankali hadi da jinin bari in sha Allahu,don ta qwaqule duk abinda yayi mata saura ta bayar ayi mata aiki akan ruqayyan. "Lafiya kike?ko azuminne?" Ya tambayeta yana kallonta saboda yadda ta koma wata iri gaba daya. Yaqe tadan sake masa kadan tanason kauda hankalinsa daga kanta "Azuminne na bana ya bada wahala" "To ya za'a yi?,ita dama aljanna ai ba'a samunta da sauqi kana daga kwance" ya fada yana zama saman kujerar yana mamakin yadda yaga qazantar sashen tadan ragu, cikin ransa yana fatan koyi takeyi da ruqayya tana rage wasu abubuwan. Ya danyi mintuna dasu yana basu alawoyin daya riqo kafin ya miqe "Inajin basusan na shigo ba,bari na qarasa ciki na huta" kai ta kawar tana jin zafi har cikin ranta yadda ya dawo dinnan a wajenta ya kamata ace ya huce dukka gajiyarsa,idan da hali ma kada ya tuna da wata ruqayya. Har yaran sun bishi ta kirasu,ta danqara musu ashar tace su zauna a nan. Hakanan suka dawo suka zauna gwiwa a salube,shikam baima sani ba tunda already ya fita. Haneefa ce data gaji da mutsu mutsu tace "Wannan zama kaman a birsin" tayi maganar kuwa akan gaba,don tana sauke maganar ta ta kai mata kyakkyawan duka a baki harda fuska,ta tsanyara ihu kuwa yarinyar tana dafe da fuskar "Don ****** ni zan dinga fada kinamin musu?,to zakisha wahala don wallahi mugun duka zan dinga miki daga yanzu" miqewa tayi tana kururuwa hadi da banka kuka har ta shige dakinsu. Kallon takaici zainab ta bita dashi har sai data shige dakin,taja qwafa tana maida hankalinta kan waya. Ci gaba da satar kallonta khalil yayi,don shima sashen nasu sam baya masa dadi,kamar gobe ba sallah ba,amma daxun da ya shiga wajensu alhassan sai yaji lallai da gaske gobe sallah. Gajiya yayi da zama ya miqe shima yabi bayan haneefa yana cewa "Ni wallahi dama momynsu alhassan ce ta haifeni,mu ko kayan sallar namu ma tsofaffi ne inajin" ya fada yana fadawa dakin da sauri don kada ta samu nasarar dukansa. Baki bude tabi qofar da kallo,anya ruqayyan bata fara taba mata yara ba?,anya sharrin nata bai gangaro mata kayan yaranta ba?,koma meye anzo qarshen maganar ai ba zata qyale ba sam. Kallo daya ya yiwa ruqayyan wata qaqqarfar ajiyar zuciya yaji ta subuce masa,tayi masa kyau iya kyau,gold Julius Holland din jikinta kamar saboda ita akayi wannan design din,yaran na lullube da shi amma hankalinsa yana kanta. Koda suka kebe bata gajiyar jikinsa yake ba,so yake kawai ya samu kaiwa ga kyakkyawan jikin da ya samu kyakkyawar kulawa da gayu me cike da nutsuwa da kuma cikakkiyar tsafta. Duk da gajiyar da ya sauke mata amma hakan bai hanata qoqarin ganin komai na abincin idin gobe ya kammala ba,daga qarshe tun farko farkon dare ya tsareta a daki yace tazo ta tayashi baccin gajiya,tana cikin jikinsa yana zuqar daddadan qamshinta har bacci yayi awon gaba dashi,wannan damar ta samu ta zare jikinta ta rufeshi da kyau ta fita suka qarasa komai ita da wasila sauran suka barwa washegari. *_WASHEGARI_* Sunyi fes abinsu shida alhassan da alhussain harda iftee da itama akayi dinkin shaddar da ita. Idan ka ganshi zaka dauka sabon angone,duk da a wajensa ya furta mata haka yake jinsa kamar sabon angon,duk sanda ya kalli kayan jikinsa tun daga sanda ya sanyasu kawo yanzu tun daga harshe har zuciya bai daina saka mata albarka ba. Yasan nawa ne price na shaddar data siya masa har yadi kusan goma,ya kuma san tsadar aikin data bayar akayi masa don kawai ta faranta masa. Duka kan iyalinsa ya hada suka wuce sallar idin saboda falalar dake cikinta,harda ruqayya wdda dama bata fashi duk shekara,indai bataje ba saidai idan bata da lafiya. Kusan sau uku yana aike kan zainab ta fito amma tace bata zuwa,tuni ta hangosu ta labule,kuma shigarsu kadai ta cusa mata tarin takaici da baqinciki. Shin idan tace zataje dinma me zata sanya ita?. Har suka fice idanunta suna kan haneefa da khalil wanda shigarsu ta banbanta data yaran,ta lura da yadda saleem din ya tsaya yana kallonsu hadi da jefa musu tambaya,yayi kaman zai shigo sai kuma taga ya fasa,ta sauke ajiyar zuciya,don ta tabbatar zaibi ba'asin kayan jikinsu ne. Sanda suka fice gidan sai ya zamana saura ita kadai,yau sallah don haka tayi niyyar itama tayi kwalliyar kece raini,saboda gobe tun da safe iwar haka zata matsa kambunta ta karbi miji. A duk sanda ta tuna haka ta Kuma tuna ta shiryawa hakan don wajen da ake abun dominshi nata a matse yake gam sai taji farinciki ya kamata,saidai kuma yadda jinin daketa zuba yaqi daga qafa abun yake sake daure mata kai,amma tana d hope don raliya ta gaya mata yau din bayan idi zata aiko mata da rubuta da.magunguna,kuma an bata tabbacin muddin dai asiri ne akayi mata awa hudu kacal zataga ya dauke. A gurguje tadan gyara falonta da bedroom dinta don tanason kafin su shigo tayi adon da zai cusawa ruqayya haushi don basu da nisa da masallacin idin. Hankali kwance ta soma cire kayanta don yin wanka a gurguje duk da tsummokaran jinin data jiqa wanda bata samu tsaiwa ta wankesu ba. Qunzugun ta zaro wanda ya jiqe sosai da jini,zarowar tasa yayi dai dai da fitar wani mummunan wari da ya sanyata kauda kai. *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 30 *_RUK'AYYAT GRAPHICS_* *_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_* *_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_* *_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_* LOGO INVITATION CARDS BANK STICKERS BUSINESS LOGO SAVE THE DATE P.O.S BANNERS BIRTHDAY CARD BOOK COVER DATA FLAYER BIRTHDAY VIDEOS VIDEO INVITATION AI PICTURES _KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_ *_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_* *RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku _KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_ https://wa.me/+2347084515410 _ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽 Daga ita har saleem babu wanda yake da tabbacin meye ya sameta,illa dai ta taimaka masa ya canza mata zani da riga,sannan yasa qarfi ya ciccibeta yana me dauke numfashinsa saboda abinda yakeji ya isa mota da ita. Zataso taje ta canza kaya ta kuma jefa wani abun a bakinta saboda azabar yadda zuciyarta take tashi,to amma yanayin da Zainab din ke ciki bazai bata dana ba,don haka tana a tsaye a nan tasa alhassan ya amso mata slippers da hijabi ta zura tabi saleem motar. Har suka isa asibitin Zainab matagugu take na matsanancin ciwon mara,dukkansu sannu suke binta da shi,saboda sunyi tambayar duniya bata cewa da kowa komai ba,dama ita ruqayya bata zurfafa a tambayar ba gudun jin abinda zai tayar mata da hankali ko maganar da zata bata mata rai. Duk da cewa ranar sallah ne amma asibitin a cike yake,akwai tarin masu ziyara da kuma tarin marasa lafiyar da Allah ys jarabta da ciwuwwuka. Sashen emergency na asibitin ne suka amsheta da gaggawa,saboda duk da kasancewarsa private amma babba ne,suna da tarin kayan aiki qwarai da qwararrun ma'aikata. Koda suka shiga da ita dakin marasa lafiya ita da saleem din zaune sukayi suna dako. Tana ankare da saleem din da ya kasa zama,sai dan tattaki da yakeyi kadan kadan daga hauni zuwa dama. Ba jimawa ya qaraso inda take ya zauna dab da ita,ta daga kai ta kalleshi suka hada idanu "Kina da masaniyar wani abu akan ciwon nan na zainab?" Ya yiwa ruqayyan tambaya muryarsa a raunane. Yau din sai taji ba zata iya bagarar dashi ba kaman yadda ta saba a duk sanda ya sako mata zancan zainab "Bansani ba,bansan komai ba,yadda ka ganta yanzun haka na ganta" shuru ya danyi,sannan yaja iska ya fesar "Jikina yana bani koma meye yana da alaqa da ta'ammali da gurbatattun magungunan matan da batasan ingancinsu ba anyhow" dubansa ruqayya tayi da sauri sai kuma ta sauke kai batace komai ba. "Ina wadanda suka kawo Zainab!,kuna ina!,bawan Allah kune?,ku taso maza maza!" Nurse din data leqo cikin daga murya da alamu na kiran gaggawa ta daga musu hannu tana fada. Ruqayya bata motsa ba saboda tana ganin ba huruminta bane ta shiga din,amma sai saleem ya kalleta "Taso muje" zata musanta ya saka hannunsa ya jawota sukayi ciki. Kukan Zainab suka fara cin karo dashi wadda ke maqure saman gado tana gunza kuka,sai nurses guda biyu a gefe da suketa magana cikin bacin rai da metron daya. Hankalinta yayi mugun tashi da taga tare suka shigo da ruqayya,sai taji kamar ta bankawa wajen wuta a tashi ba tare da anyi maganar komai ba "Malam ya akayi kabar matarka ta rube don girman Allah?,a haka kuma kake iya mu'amalar aure da ita?" Daya daga cikin nurses din ta fada bacin rai yana bayyana qarara saman fuskarta. Wani kallo ya watsawa matar saboda rainin hankalin da yaji qarara cikin tambayarta,shi zai riqa yawo ne da zainab duk inda zashi yana kula da gabanta?. Metron din data fuskanci kamar ranshi ya tabu da maganar saita dagawa nurse din hannu sannan ta dubi su saleem "Bismillah ku zauna" "Harda kishiyar tawa?" Ta zabura tana fadi.duk da radadin da take ciki. Dukkansu suka zuba mata ido,nurse din nan dai wadda da alama zafi gareta tace "Bakison kishiyar taki tasan me kike ciki kikayi wasa da gabanki?" "Ya isa hadiza" metron din ta sake fada. Zama sukayi gaba dayansu,metron ta kallesu "Alhaji a gaskiya duk da mu ma'aikatan lafiya ne,muna kuma ganin abubuwa kala kala amma case din matarka ya tashi hankalinmu,al'aurar matarka idan bai rube ba to yayi lalacewar da bashi da maraba da rubewa,akwai dinki a jikinta wanda bai samu kulawa ba,an barshi sasakai har ya gama farkewa gaba daya" "Na shiga uku dinkina!" Zainab ta fada tana dora hannu saman kai kaman ma ta manta a inda take. Idanun saleem da ya juyo ya watsa mata su wanda zuwa yanzu sun sauya launi sune suka ankarar da ita,ta kuma tuna ta yiwa kanta barna zata tonawa kanta da kanta asiri. Wannan abun kawai da tayi ya tabbatarwa da saleem ta aikata din,ta kuma yi komai ne tana sane,don haka ya maida dubansa ga metron "Bayan ya farke kuma da alamu infection sunbi sun shiga ciki yadda sukaga dama saboda rashin tsaftar gurin,sannan da alamu akwai abubuwan da ake yabawa wajen da basu cancanci zama a wajen ba,jinin kuma dake zuba a jikinta wannan gaskiya zan turaku zuwa ga doctor nur,tana nan a hawa na farko,amma dai ina addu'a abinda nake hasashe Allah yasa ba shine ya sameta ba" "idan ma shine ticket din data yankawa kanta kenan" ya fada qasa qasa muryarsa dauke da maqurar bacin rai. "Idan kun gama ganin Dr nur din zatayi magana damu tabbas,amma dai yanzun na tabbatar ba wanda zai iya ganinta a haka sai an fara maganin d'iwa da jinin dake fita a jikinta,idan sun tsaya ma sannan a fuskanci ainihin ciwon da yake jikinta da farkakken HQ din da ya riga ya bude sosai tunda an sake yagashi an dinke kuma ba'a dinke dai dai ba" kaman ta sake dora hannu a kai ta zunduma ihu dajin bayanan nurse din,yanzu ita daje beman tsukewa saboda lalacewa saita bude budewar da tafi ta baya yawa da muni?. Bai sake cewa komai ba kaman yadda ruqayya ta buga tagumi jikinta a mugun sanyaye,tamkar itace cikin matsalar, zallar mamakin zainab ne yake sake mamayeta,yanzun ita saboda kishiya da miji harta aminta ta cutar da kanta har haka?,yanzun gashi cikin su uku waye a ciki?. Duk zaman bin layi zuwa shiga wajen dr nur da sukayi saleem baice ta tafas ba,duk da irin ciwo da radadin da zuciyarsa ke masa wannan wanne irin tonon silili ne Zainab din ta jawo masa,har dinki taje akayi mata?,ta bankada al'aurarta ba tare da saninsa ba?,macece namiji ne waye yayi mata oho?. Tun daga shigarsu tsantsami ya kama dr nur kasancewarta me tsananin tsafta,saidai salon iya aiki yasa ta jure illa facemask data saka. Kai kawai take jinjinawa bayan ta gama gwaje gwajen da suka dauki lokuta sunayinsu "Kin samu cutar CANCER ciwon daji na bakin mahaifa wato CERVICAL CANCER" "CANCER kums likita?!" Zainab din ta fada a mugun gigice,gigicewar da ba ita kadai tayita ba hatta da ruqayya sakamakon ya girgizata,bare saleem da ya dasu a gurin bakinsa ya gaza furta komai. Kuka da tumami Zainab din ta farayi cikin matuqar razani da firgita, duk yadda dr nur taso tasha kanta tayi shuru amma ta qiya,har saida bakin saleem ya budu ya daka mata tsawa. "Ki tashi ki mata bayanin dame dame kika cusawa gurin ya zama haka?" "Tana inserting wani abune?" Dr nur ta tambaya tana duban saleem cikin ranta tana hango banbanci qarara tsakaninsa da zainab din qasan ranta tana fadin "Aure me hade hade" don ko kusa ko alama babu daidaituwar aji tsakaninsa da ita. "Zakiji a bakinta,inajin har fitsarin jaki sawa takeyi" ya fada yana miqewa don ya tabbatar Allah ne kadai yasan me dame Zainab din tayi. Yasha ganinta yasha kuma hanata tare da gargadinta sau babu adadi amma bataji ba. "Yallabai haquri zakayi ka zauna mu fuskanci matsalar nan a tare" Dr nur da itama ta fuskanci asalin fusata daga wajensa ta fada "Na gama da matsalarta ni,na gama fuskantar matsalarta,yanzun matsalarta tatace,Allah ya bada mafita" galala zainab din tayi tana jin asalin tashin hankali yanzu yana ratsata. Kadadai ace iqirarin da yasha yi mata wanda ita bata daukeshi a bakin komai ba a sannan a yanzu ne wa'adinsa zai cika?. "Don girman manzan Allah kayi haquri ka dawo ka zauna", ruqayya da tayi tsaye a bayansa ta fada a tausashe. Ta hadashi da babban bango kuma dan gatan Allah wanda bazai iya tsallakewa ya qetara sunansa ba,don haka ya dawo yana shirin zama,ita kuma tayi qofa zata fice don ta gaji da jin wannan tashin hankalin "Ke kika dawo dani dole ki zauna kema" saleem din ya fada a kausashe. Juyowa tayi tana kallonsa "Ita meye nata a ciki dama?,banda ma son a tozartaka ya za'a yi kishiya ta dinga jin sirrin ciwonka?" Zainab ta fada cikin muryar kuka. Wani kallon banza saleem ya watsa mata "Ke kikaso,ita aji nata mana" . Kasa dawowa ta zauna ruqayya tayi,tana daga tsaye jingine a bango kanta a qasa cikin tashin hankali. Tiryan tiryan zainab ta rattabo bayani da bakinta,abinda ya tashi hankalin kowa a wajen,ruqayya tsigar jikinta ta dinga tashi sai ta bude qofar kawai ta qarasa ficewa ba tare data jira umarnin saleem ba. Motarsa ta koma ta zauna tana maida numfashi,abu goma da ashirin,ga tashin hankali ga tashin zuciya,saita kwantar da kujera tayi kwance kawai tana maida numfashi. Kusan awanni biyu cur sannan taji shigowar saleem din motar,har tayi bacci ta farka,ta miqe ta zauna tana duban fuskarsa da babu alamun walwala a tattare dashi. Kiran waya yakeyi don haka batace dashi komai ba har aka daga,sai a sannan ta fahimci yayan zainab yakewa magana yana shaida musu tana asibiti an bata gado,a taho dame kula da ita "Subhanallahi me ya sameta" "Zatayi muku bayani idan kukazo" abinda yace dashi kenan. Baice komai da ita ba bayan ya gama ya tashi motar ne kawai suka wuce gida. Itama sai taja bakinta tayi shuru. Ranar gaba daya sukuku ya yita,damuwa ce fal ransa da bacin rai zallah,da akazo diban kayan zaman asibiti na zainab din ya sanya haneefa ta debo kayansu ita da khalil. Yarinyar nata murna ta debo din,saidai duk cikin kayan babu wani na arziqi,sai baya ruqayya tasa aka kaisu aka sake wankewasu fes. Bata sake masa magana ba sai washegari da safe da zata shiga kitchen hada musu breakfast "Yaushe zaka fita asibitin zan hada musu da abinci" "Ba yanzu ba,idan kina da me zuwa ki bayar yakai" ta danyi mamaki don ba haka yakeyi ba duk sanda wata ta kwanta asibiti ita ko zainab din "Ba damuwa,zan samu na kammala da wuri sai na fita nakai" "Ban aikeki ba" ya fada, koda ta dakata tana neman ba'asi blanket yaja ya lullube kansa abinsa ya juya mata baya. Kwana uku tayi tana aike musu da abinci,a rana ta ukun sai bayan qarfe goma na dare ya shigo gida. Tana zaune batayi bacci ba don ta kasa,saboda ba sabonsa bane yin dare a waje,ta kuma kikkirashi amma bata sameshi ba. Tunda tayi masa sannu da zuwa ta tabbatar akwai matsala babba tattare dashi. Har zuwa sanda sukazo kwanciya ta dubeshi "Gobe inaso naje na gano jikin zainab in sha Allah " "Ba zaki ba" ya fada a taqaice yana gyara pillow dinsa. Ranta tadan bata kadan "Me yasa kake haka ne?,ko yaran aika bari su ganta ko?" "Ce miki akayi ana ganinta?,ko salon idan kinje kin dawo ki ishi mutane da koke koke?" Ya fada yana tuna yadda likitan dake kan dubata a yanzun yayi masa bayanin irin illar da ciwon yayiwa jikinta da sassan mahaifarta,ransa yana baci kuma idan ya tuna yadda sam bata rusuna ba saima zagin ruqayya da takeyi duk da alkhairinta gareta da yadda ta hana kanta zaune kullum cikin girkin safe rana da dare. "Karki sakemin wannan maganar,hasalima mamanta ta nema mata saki tace sakacina yasa ta shiga halin data shiga din na kuma bata sakinta,na biya kudin abinci da jinyarta gaba daya,so ba wani abu da ya rage kuma" idanu sosai ruqayya ta fiddo gabanta yana tsananta faduwa "Sakifa kace saleem,matar tana saman gadon jinya har zaka yanka mata takardar saki?" Ta qarasa fada muryarta na rawa,cike da tsoron zargin da mutane zasuyi a kanta "Ji nan ruqayya" shima ya kama sunanta kai tsaye sannan ya zauna yana dubanta sosai "Me daki shi yasan inda yake masa yoyo,duk da ke matatace kuma gida daya muke akwai abinda bai kamata ki sani ba ba kuma zaki sani ba,kuma koda mamanta bata nema mata saki ba dama xamana da ita ya qare. Kinsan sau nawa mukayi case din magunguna da ita?,a gaban mamanta a gaban mamana?,mamanta ita ke goya mata bayan cewa dole ne tayi gyara saboda ke!,maganata ta qarshe tsakanina da ita kafin na tafi saudiyya akan maganin ne,ni da ita mukayi yarjejeniya duk randa na sake ganin wani abun daya danganci wannan tarkacen nata ko meye ya biyo baya kada tayi kuka da kowa sai kanta,ke ina hanaki gyara!,ban taba hanaki ba,saboda me?,saboda nasan duk abinda zaki sanyawa cikinki ko ki sakawa qasanki bazai taba lafiyarki ba,bazai taba tawa lafiyar ba,kinsan sau nawa tarkacen maganin da zainab takeyin amfani da shi ya cutar dani?,kinsan banda ina da sauran numfashi a gaba da tuni zuciyata ta samu matsala?,da tuni na mutu ba zancena akeyi ba saboda abubuwan da take sakamin a abinci da cikin abun shana?,wani abun yakanyi sati yana tabani,kina lura da wasu lokutan sai girkinki yazo ya fita ban nemi komai daga wajenki ba?,kinsan dalili?,ta sakamin wani abu a abincina ko a jikinta da nima ya tabani kuma banason na shafa miki wani matsalar da idan nayi hakan tamkar zalunci ne a wajenki,shekara nawa ana haka?,sauran dabi'unta ke zaki bawa wani labari,duk abinda ya kamata nayi don samun daidaito nayi amma ya tashi a banza,banaso banaso ki sake cewa wani abu akan wannan" "Bazan sake cewa din ba,amma kuma idan bera nada sata daddawa ma da warinta" ta fadi masa kai tsaye tana dubansa "Nace karki sake cewa komai,saikin sake fada din?" Yayi mata maganar ta sigar tambaya. Akwai maganganu da yawa a ranta da kuma rashin dacewar da take gani na sakin zainab tana asibiti,amma bacin ran da ta gani da kuma tsoron shigar shidan al'amarin saita janye qafafunta ta sauka qasa kawai. *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_KURMAN BAK'I_*⚫⚫⚫ *HUGUMA* PAGE 31 *_YOU ARE ALL INVITED TO MY BUSINESS GROUP_* *MASU SARI DA MASU SIYAN D'AI D'AI DUK KUZO MU JONE,SIYAYYA CIKIN AMINCI DA KWANCIYAR RAI* https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz Idanunta cike fal da wasu irin qwalla masu zafi take juya takardar sakin dake hannunta. Wani irin zafi radadi da bacin rai ne ke kai kawo a ranta a duk sanda ta kalli takardar,duk da kuwa mamanta ta bata yaqinin cewa ita ta qarfafa ya saketan "Wa ya gaya miki kana zafafawa akan miji tare da nuna masa sai dashi zaka rayu?,gwara ki qwaci 'yancinki yasan cewa ba dole sai dashi ba" "Tabbas na yadda da maganar bahaushe da yake cewa namiji dan kunama,namiji buhun qaya,namiji TABARMAR QASHI" ta fadi maganar a sarari. Gyara zama raliya da tazo dubata take kuma zaune a gefanta tayi,jiki da gwiwarta dukka a sage,ciwon da ya sarqafi zainab din ba qaramin ciwo bane,kamar yadda ba da wasa yake gigita rayuwarta da lafiyarta ba,tayi wani irin bushewa ta qanjame,saboda lamarin cutar cancer ba qaramin ciwo bane me qanqanin illa "Ko meye zaki fada akan namiji bazan musa miki ba,tunda gashi qiri qiri zahiri mun gani ni dake,banda butulci irin na da namiji?,kome kikayi kuma ko me kika zama ai ta silarshi ce,ta dalilinsa ne,inda baki aurensa ai da ba zaki saka komai a jikinki ba,komai don ki burgeshi kikayi ko" raliya ta fada cikin tsananin jin zafi itama kafin ta sake dorawa "Ni wallahi na sare da lamarin namiji,na daina wahalar da kaina sabodashi,tunda duk fadi tashin maganina wai bai hana bawan Allahn nan hango wata macen ba,har yana shirin miqa sadaki ban sani ba......". Sallamar safeena ita ta saka sauran maganar katsewa,kusan taji duk abinda suke cewa saboda ta tsaya daga famfon tsakar gidan daura alwala. "Kuyi haquri ba labe nayi muku ba,na tsaya daura alwala naji duk abinda kuke fada" waiwayawa tayi ga raliya "Daina gyara ai bai ganki ba anty raliya,keda za'a kawowa wata dole kiyi gyara ai,amma gyara na hankali,wanda duk ko meye zaki ci ko kisha ko kiyi seat bath kinsan ingancinsa ba gamje gamje ba......anty Zainab kiyi haquri,saki yana da ciwo akan kowacce mace,amma kusan fiye da rabin matsalolinki kece kika assasu, idan silar dirkar magani baji ba gani yaa saleem ya sakeki,to tabbas ba shine babban jigon faruwar hakan ba,akwai wani dalili behind it" idanu zainab ta zubawa safeena "Kin dade kina wannan maganar safeena amma yau Ina da sha'awar saurarenki" kujera taja ta zauna gaban zainab "Na taba gaya miki amma a sannan gani kike gaibu ne,maganin mata wani ciko ne da kwaskwarima a wajenmu kamar yadda ake mana bitar zaman aure duk wata a islamiyya,amma ba shine jigo ba,sam sam bashi zama jigo,zaki iya fin kishiyarki da shansa amma ta fiki a wajen miji saboda ta fiki tsafta,ta fiki iya tarairayar miji,ta fiki iya girki,ta fiki lafazi,ta fiki iya tarbar baqi,ta fiki kula da miji a daki......duk gayyar wannan abubuwan kina tunanin maganin mata kadai ya isa ya qunshesu?,sannan koda kin hada dukka wadannan abubuwan kina nufin har abada miji bazai bata miki rai ba?,ba zaku samu sabani ba?" Tambayar ta sanyayar da jikin zainab da raliya,kunya ta kamasu na yadda yarinyar qanwar bayansu ta fisu hangen nesa. **********Da tsohon cikinta wanda ya shiga watannin haihuwa take takowa zuwa gaban wasila dake zaune a gefan gadon dakin. Sanye cikin laffayar amarci data lullube jikinta tsaf,sai fuskarta dake kallon ruqayyan har zuwa sanda ta miqa mata cup din data tsiyaya wani abu a gora "Karbi ki shanye" ba musu tasa hannu ta karba. Sanda takai bakinta zaqin mazarqwaila da sauran tarkacen saiwoyin dahuwar tsumi masu dadin qamshi suka ziyarci hancinta. Tsaf ta shanye ta miqa mata cup din tana cewa "Wai dama kina amfani da irin kayayyakin nan?" Murmushi ruqayya ta saki tana ajjiye cup din "Indai kinga bana amfani dasu to ina cikin irin wannan yanayin na samuwar juna biyu" "Amma nayi mamaki" wasila ya fada tana dubanta. Wani murmushin ruqayya ta kuma saki "Kema kina cikin sahun wadanda suke min kallon bana shan komai bana amfani da komai sai fruit?" Dariya tadan saki "To ai iya abinda nake gani kenan" "Daga yau na wanke miki tunaninki,har maganin mata ina siya,amma ba kowanne magani ba maganin da ya amsa sunansa,gumba,daka, tsumi zuma duka,amma kinsan a hannun wa?" Kai ta girgiza "AMINTATTUN MATA wadanda nayi imanin sunsan kansu,sunsan me zasu bamu musha......sannu abu na biyu basai kin fito kina cika baki kina kurin ke kina Shan maganin mata ba,duk inda ake zancan maganin mata kina kan gaba,duk inda aka zauna saikin nunawa duniya ke ayuce,babu kalar maganin da baki sani ba,ba kuma wanda baki taba gwadawa ba,kai har na bature......kinsan duk matar dake amfani da magungunan mata na bature tausayi take bani?" Ruqayya ta qarshe fada a sanyaye "Kaman yaya?" "Har sai na tsaya miki bayani ma wasila?,zainab bata isheki izina ba,babu tabbacin ranar da zata koma mace kamar kowacce mace,ki gayamin da cushe cushe da shaye shaye me ya amfana mata?,shi kansa na gargajiyan ba'a ce ki dawwama a kansa ba,baci ba sha me kyau sai azabar kwankwadar magani......dukkan magani yana tasiri cikin jiki ne idan anacin abinci ana qoshi,ana tsafta ana kula da kai,wata matar ko shaving bai dameta ba amma tasan kowanne kalar magani,ta yaya zaki tara dakarun qazanta,mafakar infection sannan kice kinaso magani ya miki aiki?,ta yaya baki iya salo salo na kasancewa da miji a turaka ba,baki iya aika 'yan aike ba,baki da tsafta baki da kalami kuma kice maganin da kikai amfani zai yiwa miji tasiri?,qaryarki tasha qarya,ki gwada ki gani,ko ranar da bakisha magani ba muddin kinsan salo salo na faranta ran maigida,da kalolin auratayya zaki gigita miji fiye da gigitawar da magani zaiyi masa" "Amma ke muguwa ce,wai duk wannan abun kike amfani dasu amma kikabar mutane na miki wani kallo na daban?" Murmushi ruqayya ta saki "Meye amfanin macen da bata da aji wasila?,aiki zama me aji ko cikin 'yanuwanki mata bare gaban miji,uwa uba kuma ace kina da abokiyar zama hauka ba naki bane,dole ki kame kanki,sannan duk dadinki da miji karki fasa addu'ar zaman lafiya me dorewa a tsakaninku" dukka hannun ruqayya wasila takama ta riqe "Alhamdulillah,nidai na rabauta da malama kuma 'yaruwa,lallai na yarda mukewa kanmu asarar tagomashin alkhairin ubangiji,bazan taba mantawa dake ba ruqayya,kinban shawara na riqe addu'a,gashi cikin wata shida Allah ya juyan lamarina,ya bani miji wanda yafi su zaid da faisal,lokaci daya Allah ya sakan soyayya da nutsuwa a raina,ya mantar dani komai,koda na samu Ahmad nayi baccin nutsuwa irin wanda ban taba yin irinsa ba,tunda a baya da na samu saurayi nice zaryar gurin malamai,a duban da alkhairi?,a duban me hali ne.....kinsan me?" Kai ruqayya ta girgiza tana dubanta,har cikin ranta tana jin dadi yana ratsata,ba ranar data fi mata wannan farinciki yau wasila ta saitu ta sanadinta "Wallahi ban taba zuwa da buqatata sunce komai lafiya ba,kullum sai sun qirqiri abinda zasu gayan da zai daga min hankali,ya kuma sanyani gobe na dawo,ko na nemo kudi na bayar koda ban shirya haka ba,koda bani da komai,ke idan sukaji kwana biyu shuru ma wasu sukan kirani suce sunga taurarina suna canzawa,akwai alamun matsala,ashe qarya ne,ashe matsalata tsakanina da ubangiji na ne, ashe da gaske qananun laifukan da bawa yake rainawa suna iya zama silar nesantashi da cikar burikansa,ashe suna babbar matsalata,na hada Allah da wani wajen neman biyan buqatata" ta fada cikin rauni,raunin da ya sanya ruqayya dafa kanta "Kici gaba da godewa Allah kici gaba da istigfari kuma......" Sallamar haneefa ta katsesu "Shigo" ruwayya ta bata umarni tana jin dadin yadda ta soma canza yaran,duk yadda take tunanin zata sha wahala da dabi'unsu bata sha din ba,kuma ba komai bane tayi imanin addu'a data dinga yi tana neman taimakon Allah yayi riqo da hannayenta akan sha'anin yaran,sai gashi Alla ya mallaka mata su cikin watanni shida kacal komai yana zuwa mata a sauqi "Gwaggwo ce tace idan kun gama ku fito ku ake jira" "Gamu nan" ta bata amsa saita juya ta fice a nutse yarinyar kamar ba ita ba "To amarya yau sai kwanan gidan Ahmad" "Ina fatan na sameshi mafi alkhairin namiji fiye da yadda nake zato" ta fada da dan rauni a muryarta "In sha Allah" ta amsa mata tana kamata ta miqe. _BA'ACE KADA KISHA MAGANIN MATA BA, BA'A CE KADA KIYI GYARA BA,KIYI GYARA SOSAI AMMA GYARA ME KYAU,GYARA ME INGANCI,KOME ZAKISHA KISAN ABINDA ZAKI SHA,BA KASAFAI AKA FIYA SON YIN INSERTING BA SABODA MATSALA TA INFECTION DAYA ZAMA RUWAN DARE,IDAN YA ZAMA DOLE KIYI DIN KIDAN MEYE ZAKI MATSA A GABAKI,LAFIYA DAI GABA TAKE DA KOMAI,TSAFTA IYA GIRKI IYA KALAMAI IYA KULA DA SHIMFIDAR MIJI TSARE MASA MUTUNCINSA DUKIYARSA DA TARBIYYAR GIDANSA DUKKA GABA SUKE DA KOMAI,KI ZAMA ME ADO IDAN NACE ADO ADO NA SOSAI,KARKI ZAUNA A FIKI A KOMAI,KAMAR YADDA WACCAN TAKE MACE KEMA MACACE KAMARTA,ALLAH YA BAMU DACEWA,KURA KURAN CIKI YA YAFE MANA_ _MASU MAGANI KUJI TSORON ALLAH KU INGANTA SANAARKU KUYI MATA ADO DA GASKIYA,IDAN KUN GYARA TA KUN KYAUTATA SANA'A CE ME KYAU, SANA'AR GYARAN SUNNAR MA'AIKI,KOME ZAKI SAIDA KI TABBATAR DA HALASCIN SAIDASHI DA AMFANI DASHI_ *_KIRA GA AYARIN MASOYANA,MU HADU DAKU CIKIN LITTAFINS NA GABA ME SUNA (GUDUN K'ADDARA),BAZANSO KU KARANTASHI TA BAYAN FAGE BA,SABODA ZANSO KASANCEWARMU TARE DAKU CIKIN COMMENT GROUP DINA KAMAN YADDA MUKA KASANCE DAKU A KURMAN BAQI,KI BIYA KUDINKI SABODA KIYI JOINING DINMU NIDA MASOYANA DON NUNA HAQIQANIN SOYAYYARKU A GARENI,INA GODIYA MATUQA DA GASKE A GAREKU_* 400 ne kacal Zafafabiyar din guda hudu 1200 601947 *_TAMMAT BIHAMDILLAH_* *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_