[5/26, 4:11 PM] Khaleesat Haiydar💖: *If you should come across this post plss say a prayer for my late Father, Allah Ubangiji ya ji ƙan sa ya gafarta masa da duk musulman da suka riga mu gidan gaskiya, Allah ya sa mutuwa hutu ce a garesu, Allah ya yafe masu kurakuransu, Allah ya sa idan tamu ta zo mu cika da imani...*😓 *Greetings to my Lovely Mom, continue being the strong woman you are now and always, Allah Ubangiji ya iya maki Maman Papi*💖 _Here is MAYRAAH lovely fans, i assure u it's gonna be a whole banger, shey you trust my pen_ Bani da intention din fara rubutu a wannan watan, Cause i had july in mind, but the pressure from my lovely fans is something else day by day, so let enjoy ourselves and refresh our brain with Mayraah... 💖💖 _MAYRAAH_💖💖 By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 "Maheer ga wannan ka ajiye a account dinka...." Cewar Alhaji Mahmud kenan yana mika ma matashin dake zaune parlon bundle din kudin dake hannunsa, Maheer ya mike ya karasa ya amshi kudin daga hannun mahaifinsa yana jujjuyawa ya koma ya zauna, sai kuma ya ɗan sosa keya yana murmurshi yace "Toh Allah ya sa kar in hada da su wajen tawa hidimar" Hajiya Hajarah ta girgiza kai tana ɗan murmushi cikin sanyayyen muryarta tace "To ai kun fi kusa da ita...." Alhaji Mahmud na kallon budurwar dake zaune kasan carpet warce bazata wuce shekara ashirin da biyu ba yace "Allah Ubangiji ya sanya alkhairi My Daughter" Ita dai kanta na kasa tana wasa da gefen karamin mayafin dake kanta bata ce komai ba, Hajiya Hajarah tace "Toh tashi ki tafi ki kwanta...." Sai a sannan ta dago manyan idonta tana kallon iyayen nata tace "Sai da safe" Alhaji Mahmud da Hajiya Hajarah suka amsa tare wajen cewa "Allah ya tashe mu lafiya" ta kalli sauran yayyinta maza dake babban parlon su ma tayi masu sai da safe daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita daga parlon, Hajiya Hajarah ta sauke ajiyar zuciya, a hankali tace "Alhamdulillah, Allah Ubangiji ya nuna mana wannan lokaci lafiya, Allah ya rufa mana asiri, ya hore mana ta yanda bama tunani..." Cike da mamaki Maheer ke kallonta amma dai bai ce komai ba, Tayi murmushi tana kallonsa don ta gane nufinsa, tace "To kai wa ke ta kai zan aurar da auta and only daughter" Alhaji Mahmud yace "Rana daya aka sa da naka ai bawan Allah" Maheer was a bit surprise yace "Ohh ai ban sani ba, to Allah ya kai mu da rai da lafiya" Usman da Umar dake zaune parlon suka amsa da "Ameen ya Allah" Mikewa Maheer yayi, yayi ma parent din nasa sai da safe ya tafi sama, sauran kannensa duk suka bi bayansa, Umar ya shige Bedroom dinsa dake nan downstairs... Tana tsaye walk way da zai yi leading zuwa Bedroom ta jingina da bango, Maheer ya karaso yana kallonta ganin hawaye idonta da mamaki yace "What happened?" Kamar jira take ta fashe da kuka ta durkushe nan kasa, Usman ya karaso wajen yana kallonta yace "Me ya faru?" Cikin rawar murya take kallonsa tace "To ni yanzu aure za a min er yarinya da ni yaya?" Usman ya bi gefen Maheer yayi wucewarsa dakinsa, Maheer ya duka yana facing dinta yace "Wa yace maki aure za a maki, hutu kawai za ki je na ɗan lokaci ki dawo, ai we can't do without ur food in this house" Ta fara goge hawayenta a hankali tana kallonsa, Maheer na murmushi yace "Toh amma dai naga ke kika kawo mana mutumin nan gidan nan ba wani ya kawosa ba ko?" Ta kalli kudin hannunsa sai kuma ta mike tace "To amma dai ka bani kudin nan in sa a account dina kar kaje ka kashe min, i don't trust you with money...." Buda baki yayi yana kallonta da mamaki, da sauri ta bar wajen tana dariya, ya gyada kai yayi hanyar dakinsa..... Ta gama shirin kwanciya kenan wayarta dake gaban mirror dinta ya fara ring, karasawa tayi ta dauka tana kallon screen din, ganin me kiranta tayi picking ta kai kunne tare da sallama can ciki, cikin cool voice dinsa ya amsa, a hankali tace "Good evening sir...." Calmly yace "Evening Mayraah" kamar yana ganinta ta sunkuyar da kai don sai da gabanta ya fadi jin yanda ya kira sunanta, yace "Are you done with ur Defense slide?" Tace "A'a ina son ka fara duba min ne sai in ci gaba" yace "Ohk, that is thoughtful of you...." Shiru duk suka yi, bayan few seconds yace "Ya su Ammi?" Tace "Suna nan lafiya" Yace "Maa sha Allah, zan yi tafiya gobe, so zan kwanta da wuri, ko akwai maganar da za ki min" ta girgiza kai a hankali tace "Aa... Allah ya tashe mu lafiya" Yace "Ameen, good night" Daga haka ya katse wayar, ta kalli screen din nata wayar, tabdii... wato nufinsa ita zata fara masa maganar kudin da aka kawo shi bazai mata ba, ta langwabar da kai ta ajiye wayar tayi addu'a ta shige cikin duvet ta kwanta. Washegari da safe karfe takwas Mayraah ta shigo parlor, Ya Usman ne kadai zaune dining area yana breakfast, ta karasa tana tsaye bayan daya daga kujerun dinning din ta gaishesa, yayi mata kallo daya ya amsa yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Shiru duk suka yi, yana ci gaba da shan shayin gabansa, can tace "Me yasa naga kake breakfast da wuri bayan ba kotu zaka ba yau" Ba tare da ya kalleta ba yace "Zan yi tafiya ne" Ta gyada kai, a hankali tace "You look cute" Ya daga ido ya kalleta babu yabo babu fallasa, ta wara masa ido tace "Yes" Ammi ce ta fito daga kitchen ganin Mayraah tsaye dining area tace "Baki da lectures ne yau Mayraah?" Mayraah tace "Ai yau asabar Ammi" Tana fadin haka ta zauna daya daga kujeran dining din tana kallon Usman tace "Yaya can i join you?" Ya matsar mata da flask din kusa da shi zuwa gabanta da kayan shayin, Kafin karfe sha daya na safiyar ranan makota suka dinga tururuwan shigowa gidan yi ma Ammi Allah ya sanya alkhairin an kawo kudin auren Only and last daughter dinta.... Duk da arzki irin na Alhaji Mahmud bai yarda yayi nesa da anguwan da aka haifesa ba, don bayan haifarsa da aka yi a nan, nan din dai kuma ya fara rayuwa da Ammi bayan sun yi aure duk da locality din anguwan don duk yaku bayi irinsa ne dwellers din area din, a nan anguwan Allah yayi ma iyayensa rasuwa Mayraah na da shekara biyu, wanda kusan samun Mayraah ne ya bude ma Alhaji Mahmud kofofin arzkinsa bayan wani bulaguro da suka yi zuwa Yola garinsu Ammi sakamakon yanayi na rayuwa gashi babu me taimako kowa na fama da kansa, a lokacin Maheer is just 10 years Usman kuma 8, Ammi na goyon Umar that was almost 3 years sannan, basu tafi da yaran ba gudun kada suje su sha wahala a yola tunda babu takamaiman abun yi, Aka bar Maheer wajen Mahaifiyar Alhaji Mahmud a sannan da ranta, Usman kuma wajen Hajja Mahaifiyar Ammi warce ita ma ke garin kano, suka tafi da Umar kawai, watansu goma a Yola kwatsam sai ga Mayraah, daga nan kuma wani ikon Allah cikin kankanin lokaci kasuwancin da Alhaji Mahmud ke yi na kai kaya kasar Cameroon ya fara bunkasa kamar wasa, kan kace me ya zama millionaire a yan watanni kadan... Shekaran Mayraah biyu suka sake dawowa garin kano don zuwa sannan Naira ta zauna sosai, A nan kano cikin unguwan da aka haifi Alhaji Mahmud ya gina dankareren gidansa da na iyayensa, wanda kaf area din babu gidan da ya kama kafar tasa, a ko da yaushe zaka tarar da almajirai, yara, maza har da mata masu deban ruwa don famfo kusan biyar Alhaji Mahmud yayi a kofar gidan don kowa da kowa su amfana tunda ana wahalan ruwa sosai a area din, ga sadaka da yake yi duk ranan laraba da Juma'a, wannan dalili yasa kofar gidan baya rabo da jama'a a ko da yaushe, Mayraah na da shekara 6 kakanninta na wajen uba duk suka rasu a shekara daya. Mayraah na kitchen tana wanke utensils da aka yi amfani da su wajen yin breakfast ta jiyo wato makociyarsu Maman Shafa tana cewa "Ikon Allah, sati biyar aka sa kenan, ki ce dai rana daya da na Maheer...." Ammi tace "Ehh hadawa kawai aka yi ayi taron lokaci daya" Maman Shafa tace "Kai abu yayi kyau wllh, to Allah Ubangiji ya sa ayi da mu, Allah ya kai mu lokacin lafiya..." Ammi tace "Ameen Ya Allah" A sanyaye Mayraah ke wanke wanken don ita bata san date din da aka sa ba banda yanzu da take ji a bakin Maman Shafa, haka kawai taji dama a fasa auren nata yanzu a bar shi next year ko upper year, by then she will be 23. Bayan ta gama wanke wanken ta tafi dakinta, kwanciya tayi gefen gado ta rasa me ke mata dadi. Bayan magrib duk suna dinning da Abba da Ammi sai Ya Usman da Umar suna cin abinci, Maheer ne kawai baya nan, Ammi na kallon Mayraah dake ta juya abincin gabanta ganin ta ki ci, tace "Meye haka kike yi da abincin nan Mimi?" Mayraah ta daga kai ta kalleta, Abba ya maida attention dinsa kanta shi ma, Mayraah ta ɗan yi murmushi a hankali tace "Ammi kinsan dazu da yamma na ci abinci, kawai na ji yanzu bana jin yunwa" Ammi tace "Toh idan baza ki ci ba ki rufe za a ba almajirai" Mayraah ta dau wani plate ta rufe abincin ta mike ta bar dinning area din tana tafiya a hankali, dakin Yaya Maheer ta nufa, ta samesa kwance yana waya da fiancee dinsa, Mayraah ta zauna saman wani single chair dake dakin tana kallonsa, ya mike zaune yace "I will call u back dear" bayan ya katse wayar ya kalleta yace "Ya aka yi?" Ta sauke idonta daga kallonsa, a hankali tace "Yaya na ji kamar bana son inyi auren kuma" Lokaci daya hawaye ya kawo idonta ta ci gaba tace "Sai gabana yayi ta faduwa, may be ba yanzu ya kamata inyi auren ba, i am still little...." Yace "Addu'a za kiyi ta yi, it's always like that Mimi, fargaban barin su Ammi kawai kike, but this is the right time da ya kamata kiyi aure, u are in ur final year in school" Ta kallesa cikin rawan murya tace "Toh ni dai kawai a bar ni in fara gama karatun gaba daya since i am almost done" Maheer ya kalli wayarsa da ya fara ring yace "Mayraah, za mu yi magana gobe kin ga waya nake" Mikewa tayi a hankali ta nufi kofa ta fita daga dakin... Bayan ta gama shirin kwanciya wajen karfe tara na dare wayarta ya fara ring ta jawo wayar tana kallo, sai kuma ta daga ta kai kunne tayi shiru, sallama yayi mata ta amsa tace "Ina yini" Yace "I told you i was traveling today, but u chose not to call all through..." Zaro ido tayi, sai kuma ta marairaice tace "Kayi hakuri sir, na manta ne...." Yace "To kinyi kokari!" Ranan litinin da safe Mayraah na zaune cikin department dinsu tare da kawarta Hamida da wata Coursemate dinsu Amira, tun dazu suke tsokanarta wai amaryar next month, ita dai handout din hannunta kawai take dubawa pretending bata san da ita suke ba, a ranta kuma she is regretting telling Hamida, don tun ranan da aka kai kudin ta kirata ta gaya mata don bata da kamar ta a kawaye... Daga wani bangare na Department din clique din wasu yan mata ne in their early thirties su uku a zaune, Farar cikinsu ta gyara zama tana kallon kawayenta biyu Aisha da Amina with shock written all over her face tana sauraron abinda suke gaya mata, Aisha tace "Wllh Surayya ce taji Hamidah na ta tsokanarta da suka shigo department shine ta zo ta gaya mana, amma kar ki ce mana baki da labari, mu nan muna ta jiranki mu sha labari" Amina ta rike haɓa tace "Ikon Allah, wato baki ji ana zancen a gida ba kenan? To ko dae karya ne" Badiyyah da ta ji wani zufa na keto mata ga wani sanyin dake shigarta duk lokaci daya, ta girgiza kai cike da karfin hali tace "Kinsan naje weekend gidan yayan Babana a Bichi, yanzun ma daga can na taho makaranta...." Sai kuma ta mike ta dau jakarta tace "Bari kawai in tafi gida" Tashin hankalinta kwata kwata bai boyu ba, Amina da Aisha suka hada baki wajen cewa "Toh Lectures din fa?" Aisha ta kara da cewa "kinsan fa yanda attendance dinsa yake, kuma saura minti kadan karfe goman yayi..." Ko sauraronsu Badiyya bata yi ba ta nufi hanyar fita department din da sauri, Mayraah ta bi ta da kallo don sai a sannan tayi noticing dinta, Hamidah tayi kasa da murya tana kallon Mayraah tace "Hope tasan an kai kudin aurenki?" Mayraah tace "I don't know" tana fadin haka ta mike ta ajiye ma Hamidah jakarta tace "Zan yi alwala in dawo" Hamida tace "Saura fa minti bakwai, yanzun nan zaki ga ya shiga class fa" Mayraah tace "Bazan jima ba" Daga haka ta bar wajen da sauri zuwa inda zata yi alwala, ko minti biyar Mayraah bata yi da barin wajen ba sai ga lecturer din, Hamidah ta mike da sauri ta tafi inda suke sallah a department din ta tadda Mayraah ta tada sallah, tuni student suka shige lecture hall sanin wanene lecturer din not because he is strict or he have problem, but because of him being a principal person, Hamidah da Amira ma tuni suka shiga Hall din suka nemi wajen zama. Yana ta tsaye gaban rostrum dake hall din, ya jira har student din suka yi settling, idonsa na kan roll din da su Hamida ke zaune amma saboda glasses da yake sanye da baza kace ga direction da yake kallo ba, the class became absolutely silent in just few seconds, kowa kuma idonsa na kan lecturer din, after about a minute ya gaishesu gaba daya sannan ya fara abinda ya kawosa ajin, wasu student biyar maza da mata ne suka karaso bakin kofar hall din da sauri, sai dai basu yi gigin shigowa ajin ba sanin rules dinsa, kallonsa kawai suke with pleading eyes, bai ce masu komai ba ya ci gaba da bayanin da yake ma class din, ganin they are distracting ya kalli wani student dake front roll zai ce masa ya kulle kofar kawai ya hango ta, da sauri ta kauda kanta ganin direction dinta yake kallo, Ya dae ci gaba da lecturing dinsa, bayan some minutes ya kalli wa enda ke gaban kofa yace "Fine! You can come in, but no attendance for u all" godiya suka dinga masa suka shigo class din, ita ce karshen shiga, taki yarda ta kallesa ya bi ta da kallo ta cikin glasses dinsa, ta nufi wajensu Hamida don sun ajiye mata seat ta zauna, ya ci gaba da bayanin da yake, Hamida tayi kasa da murya tana kallon Mayraah tace "Dama nasan dole a shigo tunda da ke a ciki" Ita dai Mayraah bata ce komai ba ta ciro littafinta da biro ta fara rubutu, duk wani student da suka zo daga baya ya bar su sun shiga ajin sai dai fa basu da attendance kamar yanda ya ce. Karfe sha daya da minti arba'in ya gama lectures dinsa ya fita daga hall din. Wani Coursemate dinsu me suna Bashir ya nufo Mayraah yace "Hajiya Mayraah mu bi bayanki mu tafi mu basa hakuri mana, wllh bani da attendance dinsa wannan semester din, kuma duk wanda bashi da attendance dinsa baya test kun sani" Mayraah ta daga kai ta kallesa ta ɗan buda ido tace "Ni kuma?" Sai ga sauran student din duk sun karaso wajen ta suna mata magiyan tayi masu jagora zuwa office dinsa, Mayraah ta ajiye biro din hannunta tace "Ni ma fa bani da attendance din nan, kuma me yasa sai ni zan bi ku" Duk suka hada baki wajen cewa "Saboda kece assistant class rep mana" Ta ɗan yi murmushi tace "Tun yaushe na ajiye maku wannan post din" Hamida tace "Ba wani ke dae kawai ki tashi ku je" Ganin yanda suka takurata, sauran yan ajin na taya su yasa Mayraah ta mike tace "Toh mu je, idan ya koro mu ai shikenan ko" Haka nan suka tisa ta a gaba su kusan goma sha biyu zuwa office dinsa dake sama, Dr M-Abdallah shine sunan dake rubuce saman kofar office din, duk yanda suka yi da ita ta yi Knocking ta fara shiga ki tayi, ta koma gefe tace "Haka kawai ya koreni, wani dai yayi sallama idan yace a shigo sai duk mu shiga" Bashir yayi Knocking hade da sallama, sai da yayi masa izini sannan ya bude kofar ya shiga, Dr Musharraf na kallonsu a bit surprise yace "What happened?" Mayraah dai na makale jikin kofa wanting to hear him say get out, gaba daya student din kuma ita suke jira tayi magana, can dai ta ɗan kallesa a hankali tace "Sir hakuri muka zo baka don Allah a bamu attendance mu rubuta, we are sorry for coming late" Sai da ya fara sauke idonsa, sai kuma ya matsar da laptop din gabansa ya ɗan kalleta yace "I see... Ke ce mouthpiece dinsu kenan." Sunkuyar da kanta tayi, Bashir da sauran student din suka ce "Sir don Allah ayi mana hakuri, baza mu maimaita ba in Allah ya yarda" Dr Musharraf ya dau attendance sheet din gabansa ya mika ma Bashir, Bashir ya karasa da sauri ya amsa yana masa godiya tare da sauran daliban, Dr Musharraf yace "You can sign the attendance outside" Ko rufe baki bai yi ba Mayraah ta juya ta fita daga office din da sauri don dama a makale take jikin kofa, Bashir na signing ya mika mata ta amsa ita ma tayi, ta ba warce ke kusa da ita, har ta fara sauka stairs zata koma gun su Hamida wayarta dake hannunta yayi vibrate alamar shigowar message, duba wayar tayi... "Stay behind" shine content din message din, jingina tayi da stairs din kamar zata yi kuka don bata so haka ba, can dai ta koma daya bangaren corridor din stairs din ta tsaya, tana ganin Coursemate dinta duk suka sauka kasa bayan sun rubuta attendance din, babu kuma wanda yayi noticing dinta a cikinsu a hankali ta fara tafiya zuwa office dinsa, tana isa kofar ta kwankwasa a hankali, jin bai amsa ba ta yi sallama, sai da taji ya amsa sannan ta shiga ba tare da ta kallesa ba ta kulle masa kofar, kallonta kawai yake, tana tafiya slowly ta isa gaban table dinsa without looking at him ta ɗan risina tace "Good morning sir" Calmly yace "Mayraah" ta ɗan kallesa, sosai gabanta ya fadi taji ta kasa ci gaba da tsayuwa, bata san sanda ta zauna kan daya daga kujerun dake facing dinsa ba amma bata bari sun kara hada ido ba, yace "Why were you late to my class?" Ta girgiza kai tace "Sallah naje yi" Bai ce mata komai ba, bayan few seconds yace "Look at me" Da kyar ta dago ta kallesa suka hada ido, da sauri ta daura goshinta kan table dinsa tana jin wani sabon kunyansa da bata san dalili ba ita ma, ɗan murmushi yayi bai dai ce mata komai ba, ganin taki dagowa bayan kusan 40 seconds yace "Shikenan... Idan baza ki dago ba tashi ki tafi" Kamar jira take ta mike da sauri har tana tuntube ta nufi kofa ya bi ta da kallo, kafin ta fita yace "Sai ki nemi wanda zai duba maki Defense slide dinki" Da sauri ta juyo ta kallesa ta marairaice tace "Don Allah kayi hakuri" Yace "Toh dawo" Ba musu ta dawo tana sinne kai ta zauna, yace "When next ku ke da lecture yau" Tace "Sai 2" Yace "Ohk, kin zo da laptop din ki?" Ta girgiza masa kai, yace "Turo min slide din naki ta Email yanzu" Tace "Toh" Slide din ta shiga nema a wayarta zata tura masa, shi ko sai kallonta yake, can a hankali yace "Kwana nawa su Ammi suka gaya maki anyi fixing?" Sosai gabanta ya fadi, taki dago kanta balle ta basa amsa, maganar da take ta fatan kar yayi mata kenan, yayi murmushi yace "Look Mayraah...." Still taki dago kanta sai ma hade rai da tayi, yace "Toh tashi ki tafi" Da sauri ta kallesa tana buda manyan idanuwanta ta marairaice tace "Duba maka slide din nake fa Sir" Murya can kasa yace "I love you" sunkuyar da kai tayi har da rintse ido, kawai jin kamshin turarensa tayi sharply hakan yasa ta bude ido da sauri ta gansa a gabanta, ta fara kiciniyar mikewa tsabar rudewa ta harde kafa sai ga ta a kasa, ya koma baya da mamaki yace "Meye haka kike yi, do u want to injure ur sef?" Tuni ta mike tsaye kamar zata yi kuka tace "Na tura maka sir" ya duka yana kallon kafafuwanta to be sure bata ji ciwo ba, sai kuma ya mike yace "Ta fi kiyi wucewarki, gobe ki kawo min hardcopy uku na slide din" Da sauri tace "Ok Sir" Sai kuma ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, zaunawa yayi saman kujeran da ta tashi yayi letting out sigh, wondering if she will ever change, ya ga kamar kullum abun ta kara gaba yake. Karfe daya da 'yan mintuna Mayraah na zaune tare da su Hamida a class suna jiran lokacin next lecture dinsu yayi taji wayarta yayi vibrate, dauka tayi ta duba taga sako ne ya shigo, bude message din tayi tana kallo, "Ina jiranki a parking space" shine abinda ta gani a rubuce, ta kalli su Amira da Hamida ta mike tace "Ina zuwa yanzu" Bata jira cewarsu ba ta nufi kofar fita, Mayraah na isa parking space ta karasa har inda ya ajiye lafiyayyen motarsa wanda babu tantama yana ciki a zaune, zagawa tayi ta daya side din amma bata bude motar ba har sai da ya bude daga ciki sannan ta shiga ta kulle motar, maimakon ta kallesa sai ta fara wasa da Hijab dinta, ledan eatry dake back seat ya dauko ya mika mata ta ɗan kallesa sannan ta amsa tace "Nagode" Yace "Duk sanda kika gama lectures ki kirani, am going home now" Ta gyada masa kai, yace "Sai anjima" Bude motar tayi ta sauka tace "Allah ya saka da Alkhairi" Ta kulle masa motar ta nufi cikin department ya bi ta da ido. Badiyya na isa gida ko sallama babu ta shiga parlon kakarta, hankali tashe ta jefar da jakan hannunta tare da siririn mayafinta, Hajja kaka dake zaune parlon ta bi Badiyya da ido tace "Ke kuma lafiyar ki?" Badiyya ta zube gabanta ta fashe da matsanancin kuka, Hajja ta yi saurin dauke kopin kunun dake gabanta tace "Subhanallahi, lafiya Badiyya? Wani abun suka maki a can Bichin?" Cikin kuka sosai Badiyya tace "Wai Hajja da gaske an kai kudin auren Mayraah?" Hajja na kallonta da mamaki tace "Kudin Mayraah? Ina ruwanki kuma da wata Mayraah, yarinyar da ko ga maciji bakya yi da ita, kudi kuma ai yau kwana uku kenan da kawowa, shawara kika so ayi dake kafin a amsa kudin ne ko ko?" Badiyya ta daura hannu a ka ta kara rushewa da kuka tace "Amma Hajja na taɓa ce maki ina son mutumin fa amma kika bari aka amshi kudin nan, wayyo na shiga uku na lalace" Hajja ta koma baya a firgice tace "Anya kanki daya kuwa Badiyya? Me ya sameki haka? Ina ruwanki da mutumin da bai ce yana son ki ba? Ba ga ki da samarin barkatai na banza da na kirki ba, meye sai na Mayraah zaki sa ma ido fisabilillahi? Me yarinyar nan ta tsare maki a duniya ne?" Badiyya tace "Wallahi sai dai ita ma kar ya aureta duk mu hakura..." Hajja ta matsa daga kusa da ita a tsorace tace "Lallai ban san baki da hankali ba sai yau, ita er uwar taki kike ma baƙin ciki kiri kiri babu sakayawa Badiyya?" Mikewa Badiyya tayi tana kuka tace "Ni ba er uwata bace, babu abinda na hada da ita" Daga haka ta shige dakinta da sauri, Hajja ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya tace "To Allah ya sa ki gane, idan ba haka ba ai sai ki zama masifa da annoba a al'umma, ni dai ban taɓa ganin haka ba tun zuwana duniya...." WhatsApp Via 07087865788 No phone call pls, just WhatsApp. [5/27, 11:56 AM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖 By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 2..... Mayraah na zaune parlor tana danna wayarta wajen karfe biyar da rabi na yammacin ranan aka bude kofar parlorn, tana daga kai taga Hajja ce ta shigo da sallama rataye da jakarta, Mikewa tayi ta nufeta tana murmushi ta amshi jakar tace "Hajja sannu da zuwa" Hajja tace "Yauwa Mayraah, kwana biyu shiru baki je min ba, ko duk karatun ne" Mayraah tace "Dama wannan weekend din nake son zan je in sha Allah Hajja" Hajja tace "Toh Allah ya kai mu, ina Amminki?" Mayraah tace "Tana daki bari in mata magana" Daga haka ta tafi sama dakin Ammi, Hajja ta zauna a parlon tana gyara yafin gyalenta, ba a dau lokaci ba Ammi ta sauko tana ma mahaifiyarta sannu da zuwa, Hajja tace "Yauwa sannu, ya gida ya yaran?" Ammi tace "Alhamdulillah" Mayraah ta tafi ta dauko ma Hajja ruwa, Ammi na kallon Hajja tace "Ba ku zo tare da Badiyyan ba ko bata dawo Bichin ba har yanzu?" Hajja tayi kasa da murya tace "Wace Badiyya, Badiyyar da ta zama abar tsoro Hajarah, dalilin zuwa na kenan ma yanzu haka" Ammi da sai da gabanta ya fadi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Me kuma tayi Hajja? Ai da kin kirani ma na je ba sai kin taho da yamman nan ba" Hajja dai ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba tana bin Mayraah da kallo har sai da ta ajiye mata abincin da ta debo mata, Hajja tace "Ai da baki zubo min abincin ba ma, a koshe nake Mayraah" Mayraah tayi murmushi tace "Aa ki dai ci ko kadan ne Hajja" Daga haka ta bar masu parlon ta wuce sama. Ammi dai sai kallon Hajja take tana jiran jin me Badiyyan ta kuma yi, lamarin Badiyya na damunta don iya bakin kokarinsu suke yi a kanta amma abu sai gaba yake, dama tunda Mayraah ta zo ta sanar mata zuwan Hajja ta san ba lafiya, don Hajja sai tayi shekara ma idan ba da wani dalili me girma ba baza ta zo masu gidan ba, Hajja ta kara sauke ajiyar zuciya ta labarta ma Ammi yanda suka yi da Badiyya dazu da safe, Shiru Ammi tayi tana kallon Hajja da mamaki sosai, gaba daya ta ma rasa abinda zata ce tsabar yanda lamarin ya birkita mata lissafi, Hajja na girgiza kai tace "Yanzu da za ki bi ni mu koma gida sai kin ga abun ba kyau, tana can ta cika gida da kuka har sai da mai gadi ya kasa hakuri ya leko yana tambayar ko lafiya, sai nace masa bata jin dadi ne, har zuba mata abinci nayi na kai mata dakin wai duk don in fita hakkinta amma wllh bata ci ba, abun ya isheni na rasa yanda zan yi shine nace bari in zo ko hadani da Maheer za kiyi mu koma ya zane er banza, don in nace Usman sai ya iya ji mata ciwo" Ita dai Ammi ta kasa cewa komai, can dai ta dauke idonta daga kallon Hajja, Hajja tace "Ba shiru za ki yi ba Hajara, idan ba ke din ba wa zan je in tunkara da wannan magana" Ammi ta sauke ajiyar zuciya, cikin sanyin murya tace "Ai da zai yarda shi bawan Allahn da sai ayi auren da ita kawai Hajja, in dai hakan zai sa hankalinta ya kwanta, ita kuma Mayraah tayi hakuri Allah ya fiddo mata da wani" Hajja ta hade rai tace "Amma ban san baki da hankali ba Ammi, in zo neman mafita gunki ki dankaro min wannan magana ba dadin ji haka, ce maki aka yi abinda na zo ki gaya min kenan, wato ina ma goyon bayan taɓaran da Badiyya tayi kenan, ni zaki yanko ma lafiyayyen baƙar maganar nan..." Da sauri Ammi tace "Aa wllh ba haka nake nufi ba Hajja, baki fahimce ni bane...." Hajja ta katse ta tace "To bari kiji ba komai ya sa na zo na sameki na gaya maki ba sai don ayi ma lamarin tufkan hanci tun wuri a taka mata burki ta dawo hayyacinta, in ma akwai wani abu dake damunta a kanta ne sai a nemo mai magani ya cire mata, amma ta yaya zaki yi furucin cewar Mayraah ta hakura ta bar mata? Ina ruwan Mayraah da katuwa Badiyya can, shi yaron dama ita yace yake so ne da zaki ce haka?" Ammi tayi murmushi tace "Toh me zance Hajja, yanda fa Mayraah take 'ya ta, haka Badiyya ma 'ya ta ce, abinda zan so ma Mayraah shi zan so mata..." Hajja tace "Kwarai kuwa er ki ce, don ke kika sha Mama kika sakar ma uwarta, kuma yau nasan da Rukayya na da rai ai Badiyya bata isa ba" Sai kuma Hajja ta fara matsar kwalla tace "To duk mutuwa ce ta ja hakan, ke kuma idan kina cewa Mayraah ta hakura gani nake kamar kin mayar da Badiyya bare ne, don da er ki ce ai zaki mata hukuncin da ya kamata ki taka mata burki baza kiyi wannan furucin ba, banda lalacewar zamani yaushe ma za ki ce haka, ai hukuntata ya dace kiyi don wannan babban kuskure ne" Ammi tace "Kiyi hakuri Hajja, ki bari Maheer ya kusa shigowa yanzu, sai ku tafi gidan tare" Hajja tace "To ya dai fi, idan ko ba haka ba ni sai ince ta tattara ta koma can wajen dangin ubanta a Bichi bazan iya wahala ba, kai ba ma Rukayya ba hatta ubanta da ace yana da rai yau da sai ta gane kuranta, to mutuwa ce me tonan asiri, sai dai mu ce Allah ya gafarta masu" A hankali Ammi tace "Ameen" Ammi ta mike tace "Mu je sama kiyi alwala magariba ta gabato" Hajja tace "Aa gaskiya, son samu ne ma ni bana son Mamuda ya dawo ya sameni gidan nan, bar ni inyi sallan a nan, Maheer din na shigowa mu tafi kawai" Duk yanda Ammi tayi da Hajja bata yarda ta hau sama ba ta shiga bandakin dake nan parlor zata yi alwala.... Hajja na zaune saman darduma, Ammi da Mayraah na kitchen Ammi na hado ma Hajja abinci, Maheer ya shigo gidan da sallama, mikewa Hajja tayi da sauri tace "Yauwa ɗan albarka mu tafi ka kai ni gida dama kai nake ta jira tun dazu" Maheer yace "Ikon Allah yaushe kika zo Hajjaju?" Hajja tace "Ban jima ba, mu tafi kawai dare yayi kar Mamuda ya dawo ya sameni" Bata jira cewarsa ba ta nufi kofa da jakarta a hannu, Ammi ta leko parlon tace "Don Allah Hajja ki tsaya ki ci abinci gashi nan yanzu zan kawo, shi fa Alhaji sai tara zai shigo yau ya tafi daukan karatu" Hajja tace "Banda lalura tsohuwa kamar ni me zan fito yi warhaka ina galantoyi a titi ko wacce tsohuwa na killace a gida Ammi? kawai in anyi niyyar bani abincin a zuba min ko a leda ne in tafi gida, Allah ya amfana" Ammi tasan ko me zata ce ma Hajja bazata yi convincing dinta ta tsaya ta ci abincin ba, hakan yasa tace "Toh bari a juye maki a Cooler Hajja" Mayraah tace "Hajja zan raka ki sai mu dawo tare da yaya Maheer tunda shi zai kai ki" Hajja ta juya ta kalleta, Ammi tayi saurin cewa "Aa baza ki je ba, baki ganin dare yayi" Hajja tace "kyaleta mu je kawai sai su dawo tare, abinda a mota za su kai ni su dawo" Ammi na kallon Mayraah tace "Tafi ki juye abincin a cooler...." Mayraah ta koma kitchen, Ammi ta nufi inda Hajja take tace "Hajja da dai ki bari naji tace ran sati zata je gaisheki ae..." Hajja tayi wani murmushi tace "Nasan kin fadi haka ne saboda Badiyya ko? amma kin manta ni babba ce Ammi, ai bazan ma Maheer magana a gaban Mayraah ba, tunda tace zata ki bar ta kawai mu je ba komai" Maheer dake kallonsu yace "Me Badiyyar tayi?" Hajja tace "Ka bari mu je gidan sai in maka bayanin komai" Karfe takwas da yan mintuna Maheer ya isa gidan Hajja, Mayraah dake zaune gaban motar ta sauko ta bude ma Hajja back seat sannan ta dau abincin suka wuce cikin gidan, a nan parlor ta ajiye warmer din ta zauna... Hajja ta ja Maheer zuwa dakinta, nan tayi masa bayanin abinda ya faru dazu da safe tsakaninta da Badiyyah, Hajja ta kara yin kasa da murya tace "Ka ga ai taki fitowa taga wa enda ma suka shigo gidan ko da barayi ne, kuma tana nan dakin har yanzu ga takalmanta can bakin kofa, don haka ni ban san kan komai ba ban san me ya shiga kanta ba, hankali na yayi mugun tashi me babban suna" Maheer was totally speechless ya dinga kallon grandma din tasa, wato iskancin yarinyar nan gaba ma yake karawa maimakon ya ragu, Hajja tayi narai narai da ido tace "To ai ba shiru zaka yi ba" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Amma Hajja bai kamata ki bari Mayraah ta biyo mu gidan nan ba ai..." Hajja ta daga hannu tace "Aa to kai da uwarka kamar akwai munafurci a lamarinku, ni fa wllh duk daya kowa da kowa yake a gu na, babu abinda ya isa ya lalata mana zumunci, don me za ku dinga abubuwa haka kamar Badiyyar da Mayraah wasu bare ne?" Maheer ya mike ya fita daga dakin ya bude kofar dakin Badiyya, ta juya ta kallesa daga kwancen da take, lokaci daya ta kauda kai tana gyara kwanciyarta ganinsa, ya shiga dakin ya kulle yace "Ke dama rashin hankalin naki da rashin tunaninki ya kai haka?" Badiyya ta wani murtuke fuska taki cewa komai, ya gyada kai yace "Zan yi maganinki, Allah ya kai mu gobe" Daga haka ya fice daga dakin, ta bi sa da wani harara sai kuma ta ja tsaki. Sallama kawai yayi ma Hajja yace sai gobe zai dawo, a hankali Hajja tace "Toh Allah ya kai mu" Yayi hakan ne don baya son Mayraah ta fahimci komai don kiris ya rage ya cire belt ya zane Badiyya a dakin barin yanda ta wani juya masa baya saboda rainin wayo, Mayraah ta shiga dakin Hajja don mata sallama bayan da Maheer ya fito, Hajja tace "Toh Mayraah, Allah ya kai mu ran asabar din ina nan in zuba ido" Mayraah tace "In sha Allah, Na leka dakin Aunty Badiyya dazu naga kamar bacci take idan ta tashi kice ina gaisheta" Hajja tace "To zan gaya mata, sai da safe" Suna barin compound din Mayraah na kallon yayan nata dake driving tace "Yaya is anything going on?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Like?" Ta ɗan buda ido tace "Kawai dai nayi sensing kamar wani laifin Aunty Badiyya tayi ko?" Yace "Ai da kin shiga dakin kin tambayeta" Mayraah ta zaro ido tace "Tabb" Ya kawar da zancen ta hanyar cewa "Yanzu dai wasa wasa in less than 5 weeks zaki bar mu Mimi" Marairaice masa tayi tace "Ni bana son kana ce min haka yaya" Yayi er dariya yace "Toh ma dai su waye kawayen amaryan ke da baki da wasu kawaye??" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace "Ko Badiyya?" Nan ma dai murmushi tayi tace "Wannan ai senior sis dita ce" Yace "But.... Musharraf din yasan Badiyya ne?" Mayraah ta kallesa, sai kuma tace "Muna department daya kuma ai dole zai san ta yaya, beside he is our level co-ordinator" Maheer yace "Ohk suna mutunci saboda ke kenan?" Mayraah ta langwabar da kai tace "Not at all, ai shi kasan bai fiye magana da mutane a department din ba, most especially ladies, and sau biyu kawai yake zuwa a sati, Monday and Tuesday" Maheer yace "Amma tana zuwa office dinsa gaishesa tunda ai Cousin dinta yake so..." Mayraah tayi murmushi ta girgiza masa kai tace "Ba a shiga office dinsa haka nan, sai dai class rep ko assistant class rep, ko kuma idan shi ya kira ka" Maheer bai sake ce mata komai ba don dama kawai so yake ya fahimci wani abu, bayan few minutes Mayraah tace "Yaya nan ne hanyar gidansu Aunty Haseenah ko?" Maheer ya gyada mata kai yace "Yeah" Tace "Toh don Allah mu biya mana in gaisheta since she is back, kasan ni ban taɓa ganinta ba fa sai dai mu yi magana ta waya kawai" Yace "That is because she is schooling in Abuja, amma yanzu ai ta gama and ranan friday in sha Allah zan kawota gida ta gaida Ammi, zaki ganta physically ranan" Mayraah ta marairaice tace "Don Allah yaya kilan zata ji dadi idan ta gan ni yanzu" Ya kalleta yace "I haven't freshen up, daga fa wajen aiki nake" ta kai hancinta jikinsa perceiving his scent ta lumshe ido tace "Wallahi kamshi kake kamar yanzu kayi wanka yaya, you are smelling nice" Dariya yayi, ta langwabar masa da kai tace "Pls mana yaya" yace "Ohk then, let me call her" Daukar wayarsa yayi, yayi dialing number fiancee din tasa, yana fara ring ta daga, yace "How far?" Tace "Few Miles..." Ya ɗan yi murmushi yace "Ohk ina hanya, me zan taho maki da shi?" Tace "Really? Amma kace sai gobe" Yace "Naji ina son ganinki kuma" Tayi murmushi tace "To ba sai ka kawo min komai ba dear, ka manta gobe kace za mu je shopping?" Yace "Sure... in few minutes za ki gan ni in sha Allah" Tace "To Allah ya kawo ka my love" Yana katse wayar Mayraah ta kallesa tace "Ni dai ina son voice dinta" Murmushi Maheer yayi yace "Ae na kanwata yafi nata dadi" Mayraah ta washe hakora feeling so happy, Cikin minti sha biyar suka iso kofar gidansu Haseenah, mai gadi ya bude masa gate ya shiga katon compound din yayi parking sannan ya kirata a waya, tana dagawa yace "Ina parking lot" Tace "Ohh wai baza ka shigo ba Baby, ga shi har na ajiye maka fruits a parlor" Yace "I won't be taking anything, kawai zuwa nayi in gan ki in wuce ba dadewa zan yi ba" A hankali tace "Toh gani nan fitowa Baby" Bayan wani lokaci sai ga ta ta fito, Mayraah ta dinga kallon dressing din da tayi na kananun kaya da suka mata kyau sosai, banda a hoto bata taɓa ganinta ba sai yau, Shi kansa Maheer kallonta yake daga cikin motar har ta Karaso, tana isowa kuma ta bude front seat, turus tayi tana kallon Mayraah, Mayraah ta sakar mata murmushi ta sakko daga motar tace "Dama ni ce nake son in gaisheki Aunty..." Daga sama har kasa Haseenah ke kallonta, Maheer yayi saurin introducing din Mayraah yace "Lil sis dita ce, Mayraah! kuna gaisawa through phone call, kuma kin santa ai a hoto, ko baki ganeta ba?" Haseenah na gyara ɗan gyalen wuyanta ta juya ido tace "Ohh i see, na gane" Mayraah ta sauke kanta tace "Ina yini Aunty" Haseenah ta koma gefe ta tsaya jikin motar tana taunar gum din bakinta tace "Lafiya lau" Maheer ya sauko motar ya zagayo yana kallon Haseenah yace "Daga gidan Grandma dinmu mu ke shine ta dage sai na kawota ta gaisheki" Haseenah tayi murmushi wanda iyakarsa lips dinta tace "I appreciate" Ita dai Mayraah na tsaye bata sake cewa komai ba, Maheer yace "Ohk then, sai na shigo gobe" Haseenah tace "Toh Allah ya kai mu, na tura maka sako via WhatsApp dazu" Yace "I will check" Ya kalli Mayraah yace "Shiga mota mu tafi" Mayraah ta kalli Haseenah tace "Sai da safe Aunty" Haseenah tace "Yauwa" Daga haka ta shiga motar, Maheer ya zaga ya shiga motar shi ma, tuni Haseenah ta juya ta nufi cikin gida babu wani kwakkwaran sallama, bayan sun bar layin Maheer na kallon Mayraah da tayi shiru yace "Do u need anything?" Girgiza masa kai tayi without looking at him, a wajen siyar da fruits ya tsaya ya siya ma Ammi fruits sannan suka kama hanyar gida, yana parking a compound Mayraah ta sauka daga cikin motar rike da Ledan fruits din ta wuce cikin gida, daukan wayarsa yayi ya shiga kiran Haseenah, tana dagawa yace "Haseenah why did u act that way toward my sister? Ko kin zata ɓare ce ita? Get this in ur head she is my sis, and I cherish her more than u can imagine, I don't joke with her or her matter, me yasa zaki yi min treating kanwata haka??" Haseenah dake sauraronsa tace "Ohww waow, Ai ni na zata Cousin dinka ce, sai bayan kun tafi na tuna ta, ashe last born dinku ce ko??" Boiling from inside yace "Ita kuma Badiyya da kike kawance da wacece a wajena??" Tace "Come off it pls Maheer, i see no concrete reason why u should raise ur voice at me akan kanwarka, Badiyya ai kawata ce we did the same boarding school here in kano, she was my roommate and frnd then, nasan Badiyya kafin in san ka, banda ma taki karatu ai da yanzu ita ma ta kammala masters dinta just as i...." Cikin daga murya ya dakatar da ita yace "Dole in gaya maki ban ji dadin yanda kika yi welcoming kanwata ba Haseenah" Haseenah tace "Wai tun ba ayi auren ba kanwarka ta fara hadamu kenan kake nufi ko me? So kayi in doka tsalle da na ganta in fara ihu ko yaya kake so in yi?" Katse wayarsa kawai yayi ya jinginar da kansa da kujeran motar trying so hard to calm himself down, har cikin ransa yake jin zai iya hakura da auren Haseenah duk da bikin nasu bai wuce saura wata biyu ba don babban bacin ransa a duniya a taɓa Mayraah. Mayraah na zaune gefen gado a dakinta tana studying wani handout aka bude kofar dakin, daga kai tayi tana duban wanda zai shigo, Maheer yayi sallama ya shigo cikin dakin ya tsaya daga bakin kofa, Mayraah ta kalli agogo tace "Yaya baka kwanta da wuri ba yau" Yace "Yeah, hope u are not angry at Haseenah's attitude?" Mayraah ta wara ido sai kuma tayi murmushi tace "Ohh that.... but ai bata min komai ba yaya, kawai bata yi expecting dina bane shi yasa, it's fine" Yace "What time is ur lectures tomorrow?" Tace "8am in sha Allah" Yace "Allah ya kai mu" Daga haka ya juya ya fita daga dakin, zai kulle mata kofar tace "Good night" Yace "Allah ya tashe mu lafiya" Kulle mata dakin yayi ta ci gaba da karatun da take. Washegari har Mayraah ta gama shiryawa zata tafi makaranta bata ga Ammi ba which is very unusual, mai aiki kadai ce a kitchen tana hada breakfast, hakan ya sa ta tafi har bangaren dakin Ammi tayi sallama bakin kofa, sai da Ammi ta amsa mata sannan ta bude kofar ta shiga, kwance taga Ammi saman gado, ta karasa da sauri ta zauna gefenta tace "Ammi ko baki da lafiya ne?" Ammi ta mike zaune tace "Ehh na ɗan yi zazzaɓi ne cikin dare amma da sauki yanzu" Da damuwa Mayraah ta kai hannu jikinta tace "Baki sha magani ba kuma?" Ammi tace "A'a Abbanku ya ma Maheer magana tun cikin daren ya ban magani na sha, ai na ma ji sauki Alhamdulillah" Mayraah tayi shiru tana kallonta, da damuwa sosai tace "Ammi u look stressed" Ammi ta cire duvet din jikinta tana kallon agogo dake nuna karfe bakwai da rabi tace "Ki tashi ki tafi kar ki makara Mayraah" Mayraah ta girgiza mata kai a hankali tace "A'a ni bazan je makarantar ba Ammi, zan zauna in kula da ke, ina maganin da ya Maheer ya baki in gani" Ammi tace "Bana son shashanci nace maki naji sauki ki tashi kiyi tafiyarki" Mayraah ta marairaice mata tace "Allah Ammi bazan iya tafiya in bar ki ba, don Allah ki bari gobe zan je, yanzu ki gaya min inda ke maki ciwo" Ammi tace "Kinsan idan Abbanku ya fito dakinsa ya ganki baki je makaranta ba zai maki fada ko?" Mayraah tace "Zan ce masa bani da lectures yau, don Allah ki gaya min yanda kike ji yanzu" Ammi tace "Ba abinda nake ji, kuma babu inda ke min ciwo kawai bacci nake so inyi sosai" Mayraah tace "Bari in kawo maki shayi ki sha sai ki sake shan magani ki kwanta" bata jira cewar Ammi ba ta nufi kofa, Ammi ta bi ta da kallo har ta fita, lokaci daya hawaye ya kawo idonta ta koma a hankali ta kwanta trying hard to control her self amma ta kasa, dole tayi kokarin composing kanta kafin Mayraah ta dawo dakin, ba a dau lokaci ba sai ga ta da cup din shayin, sai kuma da ta tabbatar Ammi ta sha kafin ta fara duba magungunan da ta gani gaban Mirror, ta ajiye wani daga ciki tace "Baza ki sha wannan ba..." Maheer ne ya shigo dakin yana kallonta yace "Bazata sha wanne ba?" Mayraah ta juya ta kallesa tace "Analgesic..." Yace "To sannu Aunty Nurse da tafi Dr" Mayraah tayi murmushi tace "Ni dai ban ce na fi ka ba" ya karaso ya duka gaban Ammi yace "Ya jikin Ammin?" Ammi na kallonsa tace "Alhamdulillah na ji sauki" Yace "Toh Allah ya kara lafiya" A hankali Ammi tace "Ameen" Kallon Mayraah yayi yace "ke ba 8am kika ce kina da lectures ba?" Mayraah tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau" Ta mika ma Ammi maganin hannunta da ruwa a glass cup, bayan Ammi ta sha maganin Maheer ya mike ya fita, A hankali Ammi tace "Mayraah tashi kije ya ajiyeki makaranta" Mayraah ta girgiza kai ta dau cup din shayin da Ammi ta rage tace "I will stay with you and make sure u are fine Ammi, bazan iya tafiya in bar ki baki da lafiya ba" Daga haka ta fita da cup din da Ammi ta sha shayi zuwa kitchen, ta ajiye cup din a sink tana kallon Usman dake hada coffee a kitchen din tace "ina kwana yaya" Yace "Lafiya" juyawa tayi ta fita ta koma wajen Ammi. Haseenah ta shigo Bedroom dinta rike da tray din lemo da cupcakes ta ajiye tana kallon Badiyya dake zaune tayi tagumi tace "Ke ba a ganinki sai idan abu ya sha maki kai ko? Yau sati na nawa da dawowa Kano amma ko sau daya baki taɓa takowa kin zo inda nake ba" Badiyya ta daga kai tana kallonta tare da sauke ajiyar zuciya tace "Ina cikin tashin hankali Haseenah, kuma bani da wanda zan gaya ma da ya wuce ke" Haseenah ta zauna tace "Allah ya rabamu da tashin hankali, gaya min menene ya dame ki kawata?" Badiyya tace "Ina wannan lecturer din namu da nake baki labari?" Haseenah ta juya ido tace "Ke samarin naki ai yawa ne da su, wanne a ciki?" Badiyya tace "Level co-ordinator dinmu mana, yawanci yanzu ai labarinsa nake maki a chat" Haseenah tace "Ohh, wannan da kika ce kike karanta a whole textbook a Library saboda course dinsa?" Badiyya tace "Allah maki albarka shi fa...." Haseenah ta dakatar da ita tace "Bari dai in fara baki nawa labarin, ba jiya sai ga Maheer ya zo nan da wannan cousin din naki bayan magriba ba, ni fa dama tun ma ban ganta physically ba naji bata min ba, ko gaisheni zata yi a waya idan Maheer ya bata da kyar nake amsawa haka kawai naji na tsaneta, sannan na lura favorite dinsa ce yana ji da ita, magana daya biyu sai ya sakota yayi misali da ita, daga haduwar mu jiya da ita har fa sai da muka samu matsala da Maheer a kanta, to in gaya maki tun jiya rabon da Maheer ya kira wayata akan ban doka tsalle da na ganta ba, har yanzu na kasa daina mamaki wai Maheer ne zai iya yini daya curr yaki kirana abinda bai taɓa min ba tun da dating dinmu yayi karfi, meaning yana fushi da ni akan gantalalliyar yarinyar kenan" Badiyya tace "Haseenah ki bar duk wannan ki ji damuwata don tafi taki wllh... Haseenah lecturer din nan dai ya turo iyayensa few days back an kawo kudi har an sa ranan bikinsa da Mayraah ina can Bichi ban san abinda ke faruwa ba, wllh Haseenah kullum da son mutumin nan nake kwana nake tashi nake yini, saboda shi na maida hankali a Nursing Science har nake coping, wai gashi yanzu cousin dita yake shirin aure ba ni ba alhalin ni ya fara noticing a department din ba ita ba, kafin ya ma mutum tambaya daya ya min uku a Class, na shiga uku wllh ji nake kamar zuciyata zata buga in huta, rabona da abinci tun jiya da safe Haseenah" Sai kuma ta fashe da kuka sosai, Haseenah ta rike haɓa cike da mamaki tace "Ikon Allah, to ke garin yaya kika bari har suke dating juna bayan kina sonsa, me yasa baki taka mata burki ba tunda kince tana shakkar ki sosai" Badiyya tace "To wllh daga ita har shi munafukai ne, ni ban ma taɓa ganin munafukai irin su ba, ko kallon juna fa baza ki ga suna yi a department din ba, ita ma ko kallon inda yake bata yi, kai ya sha koranta idan tayi lattin zuwa ajinsa sannan bai taɓa yi mata tambaya a aji ba, kinsan idan lecturer na ji da student zaki ga yana yawan yi masa question a class, to i am among the students da yake yi ma question, wllh baza ki taɓa cewa akwai abu a tsakaninsa da Mayraah ba komin abunki in har dai ba shegen lura ke gare ki ba kamar Asma'u don ita ta fara ankarar da ni, kin san tana da Asthma din karya ita Mayraan, to ranan sai tayi pretending Asthma dinta ya tashi a class wai an goge ƙura kusa da ita, kuma lectures dinsa mu ke yi, u need to see the care and attention she got from him that day, lectures din da bamu yi ba kenan, ya kai ta dai office dinsa ya dubata har da bata magani, shi da baya sake ma yan mata fuska, wasu student din ma sunce shi ya mayar da ita gida ranan, to bayan haka kuma ni ban sake ganin ya kalli inda take ba a department din balle ya mata magana, ko sunanta ban taɓa jin ya kira ba wllh, Haseenah baki ga yanda na ke karatu ahead of this guys lectures ba tsabar sonsa da nake kuma don in burgesa, duk wani textbook din course dinsa sai na san yanda na takura a siya min a gida, tambaya kuwa idan yayi a class ina daya daga cikin masu bashi amsa, ni ban taɓa sanin ina da ƙwaƙwalwa ba sai da nayi arba da mutumin nan, kokarin da yaga nake yi ne ma ya sa fa ya fara noticing dina a department din lokacin muna level two 1st semester...." Haseenah dake danne dariyarta tace "Noticing dinki as how?" Badiyya tace "Like idan yayi tambaya sai ki ga yana kallona ko zan bada amsa tunda ina yawan basa amsan duk tambayoyinsa, a haka dai ranan bayan yayi tambaya na bada amsa ya tambayi sunana a gaban kowa da kowa a ajin wllh...." Kawai sai ta fashe da kuka saboda wani abu da ya tsaya mata a makogwaro, Haseenah ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh ke tun daga sannan zaki yi using privilege din ai" Badiyya dai ta kasa cewa komai sai kuka, Haseenah tace "Toh ita kuma cousin din taki ta yaya har suka fara soyayya baki sani ba" Badiyya na share idonta tace "Shine har yau nake son sani, don yanda kika san statue haka take a class ba um ba um um, infact clique din nata ma kauyawa ne yan ghetto fa wa enda da kyar ake biyan tuition fee dinsu per session, haka zaki gansu da Hijab zumbula zumbula wata er kauyen waratallawa ce fa kawarta a department din ana kiranta Hamidah, to a haka zaki gansu sun samu kujera can bayan class sun zauna ba um ba um um sai yan idanuwa kamar mayu, ni kuma dama front seat nake zama duk ranan da muke da lectures dinsa kinga dole dole ya san ni ko bana answering question balle ni kadai ce mace me bashi amsa a kaf ajin" Haseenah tace "To daga tambayar sunan naki ba abinda ya sake shiga tsakaninku?" Badiyya tace "Wa yace maki? Ai duk inda muka hadu a makarantar na gaishesa to haka zaki ji yace how are you *Badiyyah*, kaff matan department din babu sunan warce yake kira kai tsaye sai ni, ke kya ce shi ya rada min sunan, har fa haushina wasu yan matan suka fara ji a department saboda yanda yake amsa min gaisuwa" Haseenah tace "Ni ko zan so in ji yanda suka fara soyayya da cousin din nan taki" Badiyya ta share hawayen da yaki tsaya mata tace "Kilan da na yarda na zauna gidansu kamar yanda Ammi ke takurani da zan fahimci wani abu, amma ni rainin hankalin Maheer da Usman ne bana so, barin ma Usman din nan, shi yasa naki zaman gidan wllh, shi dama Umar ba ruwansa" Haseenah tace "Kin ga mu tashi mu tafi gidansu Zaliha bazata rasa shawaran da zata bada ba, ni kam gaskiya ban san me zance ba, da ma dai ba a kai kudin bane, amma wannan ai zance yayi nisa" Badiyya ta mike tace "Tashi mu je don Allah" *Har na fara hango maku littafin nan fans, baza ku gane ba*😁 07087865788✍🏻 Pls no phone call [5/27, 8:25 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖 By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 3.... Musharraf ya ajiye glass din parfait din hannunsa yana kallon dattijuwar matar dake zaune opposite dinsa a parlon yace "But Mami is that really necessary? Ni kin san i know nothing about kayan amfanin mace" Mami dake danna wayarta tace "Ai kai da ita za ku tafi, ta fi kowa sanin abinda zata fi bukata, kaga kuwa it's necessary..." Musharraf yace "For how many days kenan za ayi siyayyan, naga ba abu kadan ake siya ba, gaskiya Mami ni kin san fa...." Sai kuma yayi shiru ya jinginar da kansa da kujera yana kallon mahaifiyar tasa ganin kamar she isn't even listening to him, Mami ta daga kai ta kallesa ta cikin glasses din idonta tace "Na san me?" Yace "Mami why not taje da driver din gidan nan su yi siyayyar sai ta sa Nikab" Mami tace "Saboda a garin gaɓa gaɓa ake ai da iyayenta za su bari ta bi driver siyayyan lefe" Ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Mami kinsan every nook and cranny din kano akwai frnds dina bana son a gane min mata tun before marriage" Mami ta masa wani kallo tace "To sannu me mata, shopping din da a kwana daya duk za a yi a gama shine za ka hadu da each and every frnd dinka na cikin kano?" Yayi kasa da murya yace "Mami amma me yasa su Aunty Ruma'isa baza su hada kayan akwatin ba? Naga ai duty dinsu ne yin hakan" Mami tace "A yanda ka ki zabinsu shine za su hada maka lefe? Or are you dreaming? Yaushe rabon da ka ga Ruma'isa ko Sajida a gidan nan? Hatta Aunty Halima ta dauke kafa a gidan nan ai for long" Musharraf dake ta kallonta da mamaki yace "Oh really?" Mami tace "Don haka ka sanar ma yarinyar ranan asabar sai ku je ku siya abinda duk take so na kayan akwatin ta, dama da Baby ko Fatima suna nan su za su yi, ni kuma bana son stressing any of my frnds in daura masu wahala" Musharraf yayi shiru, can ya ɗan kalli Mami da har ta maida hankalinta kan abinda take a wayarta yace "Mami or should i send her the money su hada lefen a can gidansu?" Mami ta mike tace "Do what suit you sweetheart" Daga haka ta bar parlon, ya bi ta da kallo.... Mayraah ta ajiye wayar hannunta a gefen gado, lokaci daya duk mood dinta ya canza, bayan kusan minti biyu ta kalli Maheer dake kallo cikin system din sa, kamar zata yi kuka tace "Yaya" Ya daga kai ya kalleta yace "Oh har kin gama wayan" Tace "Wai kasan me yake ce min?" Maheer yayi pausing kallon da yake paying attention to her yace "No" tace "Wai za mu je siyayyan lefe tare, is it done that way plss?" Maheer ya buda ido yace "Of course, ko Haseenah tare muke zuwa siyayyan lefe ai...." Mayraah ta kara hade rai ta jingina da gadon ta rungume hannunta tace "Ni dai bazan iya bin sa ba" Maheer yace "Why?" Tace "kunya nake ji" Maheer ya buda baki, sai kuma yace "Ke fa bush gal ce Mimi, ai yanzu haka ake yi, kinga u will be privileged to chose whatever u want, komai na box din choice dinki zai zama ne" Ta marairaice tace "Yaya baza ka gane ba wllh kunya nake ji" Yace "To ki tafi tare da wata kawarki mana idan har ya amince" A hankali Mayraah tace "Hamidah?" yace "Good, ku je tare da ita" Tayi shiru, can kuma tace "Ohk i will tell him, sannan kuma wai zai kai ni in gaida Maminsa next week, is it done that way?" Maheer yayi dariya yace "Ni ba ranan friday din nan zan kawo Haseenah ta gaida Ammi ba" Mayraah tace "Yaya wllh ni dai kunya nake ji, i can't face his mum" Maheer yace "You have to my dear, it's good ya kai ki ki gaisheta, ta san surkarta tun ma kan ayi biki" Mayraah tace "Amma fa ina ga Ammi bazata bari inje siyayyan lefe da shi ba" Maheer yace "Haba zata bari mana, ai ana yin haka yanxu" Wayarsa ce ta fara ring ya dauka yana kallon me kiransa don rabonsa da ita tun da ya baro gidansu tare da Mayraah shekaranjiya, Mayraah da duk abun duniya ya dameta ta mike ta dau wayarta tace "Sai da safe yaya" Daga haka ta fita daga dakinsa ta koma nata... Bayan ta gama shirin kwanciya tayi dialing number Musharraf, katsewa yayi ya kirata, a hankali tace "Sir i have come up with an idea" yace "Ohk, i am all ears..." Tace "Pls za mu iya zuwa siyayyan kayan da Hamidah?" A takaice yace "No" zaro ido tayi tace "But why? She is my close frnd" Yace "I said No" ta wani turo baki tace "sai da safe" Yace "Sleep tight" Ko amsa masa bata yi ba ta katse wayar ta shige cikin duvet dinta. Washegari da safe har Mayraah ta tafi makaranta bata da walwala, kawai zulumin yanda za ta fita ita da Musharraf zuwa shopping din lefe ne ya cika zuciyarta, ko baccin kirki bata yi da daddare ba don abu kadan take sa wa a rai ya dameta, bayan sun fito daga second lectures dinsu na ranan wajen karfe daya da rabi Hamidah na kallonta da damuwa tace "Lafiyarki kuwa Mayraah, naganki duk wani iri yau" Mayraah ta kalleta ta ɗan yi murmushi tace "Kaina ke ciwo, yanzu ma gida zan tafi bazan iya jiran lectures din karfe 4 ba" Hamidah tace "Subhanallahi, Allah ya sauwake, mu je in raka ki, Allah sa mu samu Napep nan kusa, the sun is scorching" A haka suka fita daga department din, wani Coursemate dinsu ne ya nufo su yana kallon Mayraah yace "Dr Musharraf yace ki samesa a karkashin wancan bishiyar" Sosai gaban Mayraah ya fadi ta kalli direction din da Coursemate din ke nuna mata, da ɗan tafiya daga department dinsu amma ba sosai ba, Hamidah tace "To Alhamdulillah kin ga babu rabon mu yi dogon trekking zuwa gate, shikenan ki gaida su Ammi Allah ya sauwake" Mayraah ta kalleta tace "Ameen nagode Hamidah" daga haka Hamidah ta koma cikin department Mayraah kuma ta nufi inda ta hango motar Musharraf tana tafiya a hankali, tasan ya kikkira wayarta ita kuma a gida ta bar wayar.... Tana isowa gun motar ta bude front seat ta shiga ta kulle motar, kallo daya tayi masa ganin yanda yake kallonta ta dauke kai tace "Ina yini" yace "Why are ain't you picking ur calls?" Tana wasa da zoben hannunta tace "A gida na bar wayan" yace "Saboda me?" Tace "Manta sa nayi" ganin yana reverse tace "I am not done with today's lectures" Yace "Ko ba Dr Nura ba?" Ta ɗan kallesa bata ce komai ba, yace "To baza kiyi attending ba" Har suka fita daga school din bata ce komai ba, yana driving calmly yace "Saboda baki son mu fita mu biyu kadai shine kika yi introducing frnd dinki a fitan namu?" Ta ɗan daure fuska tace "Fitan mu? To ai ban gaya ma Ammi ba har yanzu, kuma idan tace bazan bi ka ba ai bazan bi ka ba no matter what, so i only suggested ko za mu je da kawata ba tare da nayi shawara da Ammina ba, in kuma Ammi ta hanani ai kaga babu inda zan je" Lokaci lokaci yake kallonta har ta kai aya tayi shiru, ya gyada kai yace "Ashe bayan shiru shiru har da rashin kunya kika iya ban sani ba" Ita dai bata sake cewa komai ba kuma bata kallesa ba, sai da suka kusa gida yace "Me za ki ci?" Ta juya suka hada ido sai kuma ta sauke idonta kasa tace "Nothing, thank you" Fruits ya tsaya ya siya a wani wajen masu fruit, suna isa kofar gidansu yayi parking yana kallonta ta dau jakarta tace "Kayi hakuri idan abinda na fada ya bata maka rai..." jin bai ce komai ba ta ɗan kallesa, murmushi yayi yana shafa beard dinsa a hankali yace "Ki shiga ki sanar ma Ammi zan shiga in gaisheta da jiki" Da sauri tace "Ai ta samu sauki" Yace "I know, shi yasa ma nake son shiga in gaisheta" Ta kasa ce masa komai, sai kuma tace "But..." Yayi kasa da murya yace "Do as i say Mayraah" Ta kauda kanta, bayan few seconds ta bude motar ta sauka ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gida. Bayan kusan minti biyar ta dawo tana kallonsa tace "Ka shigo" Kashe motar yayi ya sauka yana rike da ledan fruits din ya bi bayanta zuwa cikin gidan, a main parlor din gidan ya zauna, Mayraah ta tafi kitchen tana kallon Sabeera tace "Aunty Sabeera ki kai masa ruwa da lemo don Allah" Sabeera tace "To Hajiya" juyawa tayi ta fito daga kitchen din ta wuce sama ya bi ya da ido, ba a dau lokaci ba Ammi ta shigo parlon bayan sun gaisa da fara'a take tambayarsa mutanen gida, yace "Suna lafiya Ammi, ya jiki?" Ammi tace "Ai naji sauki Alhamdulillah" Yace "To Allah ya kara lafiya" Ammi tace "Ameen" yace "To zan koma, dama zuwa nayi in gaisheki" Ammi tace "To ko ruwan ma baka sha ba ai" Yace "Aa nagode Ammi, ana jirana ne" Ammi ta mike tace "Bari in mata magana, don Allah ka gaida umman ka, ina gaisheta sosai" Yace "In sha Allah" Ammi tayi masa godiya sannan ta wuce sama, fita yayi daga parlon, ko da Mayraah ta fita kofar gida bayan Ammi ta sanar mata zai wuce bata ga motarsa ba don har yayi wucewarsa, ta juya ta koma cikin gida. Ammi ta bude kofar dakin Maheer ta shiga da sallama, ya amsa yace "Baki kwanta ba Ammi?" Ammi tace "Ban kwanta ba" Karasowa tayi ta zauna kan kujera dake dakin tana kallonsa tace "Ka sake komawa gidan Hajja kuwa? Ina son sanin yanda ake ciki ne" Yace "Ko dazu naje har yanzu dai bata dawo daga Bichi da ta tafi ba" Ammi tayi shiru, can tace "Ya kake ganin za a bullo ma lamarin nan Maheer, ni duk kaina ya daure wllh" Da mamaki Maheer ya kalleta yace "Kamar ya kenan Ammi? Wai me yasa ake biye Badiyya ne..." Ammi ta katse sa tace "Marainiya ce Maheer, er kanwata ce duk yanda ku ke tunanin zan maku ita ma haka zan mata, wallahi abun ya tsaya min a rai, sannan bazan fifita Mayraah a kanta ba" Maheer yace "Don Allah Ammi ki bar wannan zancen, it's not even making sense sai kace wani wasan kwaikwayo, this is reality, abinda zai yiwu shi ake yi, ba ita wannan mutumin yace yana so ba, to don me za mu mayar da kanmu kananun mutane, don Allah ki bar issue din nan yayi sliding haka, ni wllh idan ta kuskura mu ka yi ido hudu da ita Allah sai na mata dukan tsiya tunda bata da kai" Ammi tace "Aa kar ka taɓa ta, tunda ku baku san meye maraici ba...." Maheer yayi saurin kauda zancen don ɓata masa rai ma yake, yace "Ammi gobe Haseenah zata zo gaisheki in sha Allah" Ammi tace "Toh, Allah ya kai mu lafiya" Yace "Ameen, and Mayraah ta sameni jiya da wata magana wai ita bazata iya gaya maki ba" Ammi ta maida attention dinta gaba daya kansa tace "Wace magana kenan?" Maheer yace "Gobe Saturday za su fita siyayyan lefe shine bazata iya gaya maki ba" Ammi tayi shiru tana kallon Maheer, bai bata daman cewa komai ba ya ci gaba "Kinsan ai yanzu haka ake yi, nima ba gashi tare mu ke hada kayan da Haseenah ba, so ba wani abu bane wannan" a hankali Ammi tace "To ai ban san ko Abbanku zai yarda ba" Maheer yace "Ni zan gaya masa da kaina, yanzu modern era mu ke, komai kuma tafiya yake da zamani" Ammi dai sai kallonsa take, yace "Kuma bikin na gabatowa zai kai ta ta gaida mahaifiyarsa, ni ba gashi zan kawo Haseenah gobe ta gaisheki ba" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "To dai duk ku gaya ma Abbanku ni ba ruwana" Murmushi yayi yace "Zan kirasa gobe da safe in sha Allah, naji yace next week zai dawo ko" Ammi tace "Haka yace" Mikewa tayi tace "Zan je in kwanta" Maheer yace "Allah ya tashe mu lafiya Ammi" Ta juya ta fita daga dakin ta kulle masa kofa. Washegari da ya kasance friday Mayraah bata je makaranta ba duk don tayi assisting Sabeera su yi girke girken da za a tarbi Haseenah, Fried rice ta yi da pepper chicken sai zobo drink da small chops, ganin da sauran time tayi cupcakes, babu abinda ke kara sa yayyinta maza ji da ita sai saboda iya girkinta, Mayraah is so perfect in making any sort of food, iya girki na daya daga cikin baiwarta, banda yanzu da ta shiga final year bata da time din kanta da kusan kullum ita ke ma Maheer girki, haka ma Umar dake bribing dinta tayi masa in dai yana gari, Usman ne kadai ko a jikinsa in an basa ya ci idan ba a basa ba ko kallo abincin bai ishesa ba, dama kuma ba wai suna wani shiri bane can da shi, Maheer ne favourite dinta sae Umar idan ya dawo, Wajen karfe sha biyu Ammi ta shigo kitchen din tace "Su Mayraah abun nema ya samu, wannan duk na Antyn taki ce haka" Mayraah tayi dariya tace "Abinci kala daya fa kawai muka yi Ammi" Ammi tace "To sannunku da aiki" Daga haka ta bar kitchen din. Bayan sallan juma'a Maheer ya iso gidan tare da Haseenah, tun suna hanya yayi ma Mayraah text yace sun taho, tana jin shigowar motarsa compound ta dau gyalenta ta fito ta tsaya balcony, shi ya fara sauka a motar sannan Haseenah ta sauko, sanye take da tsadadden atamfa an mata riga da skirt, sai mayafi medium size da ta yafa hannunta rike da jakarta, tayi ma fuskarta very light make up, tun daga nisa Mayraah ke hango gold din fingers dinta wa enda ke ta daukan ido, tayi kyau sosai ba karya, Mayraah ta sauka balcony din ta karasa har gun motar da fara'a tace "Sannu da zuwa Aunty" Maheer dai yayi gaba zuwa cikin gidan, ba tare da Haseenah ta kalleta ba tana taunar gum tace "Yauwa" Daga haka ta bar ta wajen tsaye ta bi bayan Maheer, Mayraah ta bi ta da kallo irin na mamaki, can dai ta bi bayanta tana tafiya a hankali, Mayraah na shiga parlor ta tarar har Haseenah ta zauna shi kuma Maheer ya haura sama, hada ido suka yi Mayraah ta dauke kai ta wuce sama ta tafi dakinta tayi kwanciyarta, bayan kusan minti ashirin aka bude kofar dakinta, ta yi saurin kulle ido don har taji kamshin turarensa, ya kulle kofar yana kallonta yace "Mimi" Ta bude ido da kyar kamar irin baccin nan take, yace "Why did u come upstairs?" Ta mike zaune tana murza ido cike da shagwaba tace "Yaya kaina ciwo yake tun safe kasan nake ta aiki fa, kuma da na shigo ban san sanda ma bacci ya daukeni ba" Yace "Ohk ki fito ku yi sallama i am taking her back home now" Mayraah ta marairaice tace "Yaya my head is so heavy, i am not feeling fine" Shiru yayi bai ce komai ba, can ya juya ya fita, komawa tayi ta kwanta, ba a dau lokaci ba ta sake jin an bude kofa ta juya, ya shigo cikin dakin ya ajiye mata paracetamol a bedside drawer da bottle water yace "Ki tashi ki sha, sai na dawo" Daga haka ya fita daga dakin. Maheer na ajiye Haseenah a gidansu tana shiga compound tayi dialing number Badiyya, Badiyya na dagawa Haseenah na buga kirji tace "Badiyya, ni wannan cousin din taki zata walakanta yau?? Ni zata ma kallon banza tayi wucewarta kamar ta ga kashi saboda naje gidansu?" Badiyya tace "Oh kin je gidan kenan yau?" Rai bace Haseenah tace "Wallahi wallahi da nasan abinda Maheer zai kai ni gidansu kanwarsa ta min kenan da ban je ba, babu abinda zai fara kai ni gidan komin tashin hankalin da za mu yi da shi, ita kanta uwar tasa kamar bata yi wani farin ciki da zuwana ba don ko minti biyar bata yi ba a parlon bayan mun gaisa tayi wucewarta sama aka bar ni daga ni sai TV da abinci a gabana kamar abinda ya kawo ni kenan" Badiyya tace "Atoh, shi yasa nace kice masa ba yanzu za ki je ba, kyau ace ina gidan kika zo" A fusace Haseenah tace "I feel so humiliated Badiyya, yarinyar da a haihuwan kaji na haifeta zata min wannan walakancin? Me aka yi aka yi ta?" Badiyya tace "Yanzu dai ki bari za mu yi waya jirana ake, nima ai yau zan koma gidan Hajja, Mayraah kuwa ko da ni Badiyyah ban auri Dr Musharraf ba ba fata nake ma kaina ba, to wllh sai dai taga wata can daban ta auresa amma ba ita ba, balle in sha Allahu ni ce matarsa, in Allah ya yarda.. " Haseenah tace "Ai wllh in har kika bari ta auri lecturer din nan ni na ma raina ajinki da capacity dinki, baki cika Badiyyan da duk muka sani ba in har hakan ta faru" Badiyya tayi murmushi tace "Ke dai za mu yi waya" Daga haka ta katse wayar. Ranan asabar kamar yanda Mayraah tayi ma Hajja alkawari karfe goma ta gama shirinta ta sauko downstairs don Ammi na parlor tare da Usman, Mayraah ta rakube jikin kujera tana kallon Ammi tace "Ammi na shirya" duk tunanin Ammi siyayyan za su je yi, ta kalli agogo tace "Ya zo ne?" Mayraah tayi jim tana tunanin yaushe tace ma Ammi Musharraf zai zo, can tace "Ammi ni fa gidan Hajja zan je" shiru Ammi tayi tana kallonta kafin tace "Ba naji ance za ku je siyayya ba, kuma me za ki je yi gidan Hajja" Mayraah ta ɗan ɓata rai kamar zata yi kuka tace "Ammi na mata alkawari zan je yau fa, kuma ma ai ba yanzu za mu yi siyayyan ba sai da yamma" Ammi tace "Aa ki hakura da zuwa gidan Hajja, ki bari ranan da baki da lectures sai mu je tare" Usman dake kallon Tv ya kalli Ammi yace "Saboda me?" Ammi tace "In zan je sai mu je tare kawai" Mayraah ta sunkuyar da kanta bata sake cewa komai ba amma abinda Ammi tace bai mata dadi ba, Usman yace "Ni ma ai can zan je yanzu, ki bari in ajiyeta sai mu dawo tare idan zan dawo tunda ni ba dadewa zan yi ba, i will be going to Zaria later" Ammi ta kalli Mayraah don har cikin ranta taji wani iri ɓata ran da tayi, Ammi tayi kasa da murya tace "To ku je tare, amma ki tabbatar kin biyosa idan zai dawo" a hankali Mayraah tace "To Ammi, Nagode" Kallon Usman Mayraah tayi tace "Yaya yanzu zaka tafi?" Usman ya kalleta yace "What is ur business?" Nan da nan Ammi ta hade rai tana kallonsa tace "Kai komai masifa bawan Allah" Mikewa Mayraah tayi ta tafi kan kujera ta zauna bata sake cewa komai ba, Ammi tace "To meye laifi ma don ta tambayeka banda fitinarka tayi yawa" Ya mike yace "To idan bata da lectures din sai ku je tare, sai na dawo" Mayraah ta zaro ido da sauri ta mike tace "Yaya don Allah kayi hakuri" tuni ya fice daga parlon, Ammi ta tabe baki tace "Bi sa ku tafi" Mayraah ta bi bayansa da sauri.... Tafiyar minti talatin suka yi suka iso gidan Hajja, tsabar ba dadewa zai yi ba a waje yayi parking motarsa suka gaisa da mai gadin gidan ya shiga ciki Mayraah na biye da shi, parlon Hajja cike yake da yaran makota sun shigo kallon cartoon, Hajja na ganin Usman tace "To duk ku tashi ku tafi jikana ya zo, maza ku tafi" Babu wanda ya motsa cikinsu kamar basu ji ta ba, Usman yace "Kai ba magana ake maku ba" lokaci daya duk suka mike suka fita, Hajja ta marairaice tace "Ni na gaji da wahala gaskiya, kaga da baka sa baki ba wllh baza su tashi ba, ko na koresu basa tafiya sun maida ni wata mara makabuli, kakanninsu na can suna hutawa ni kuma sai a zo nan a dameni a cika min parlor har da almajirai, tunda suka kyallara ido suka ga Badiyya ta fita duk suka shigo" Hajja ta zaro ido ganin Mayraah tace "Dama tare ku ke, sannunku da zuwa, ai ko kin cika alkawari" Mayraah na murmushi ta karasa ta zauna kusa da Hajja ta gaidata, Hajja ta amsa da fara'a tace "Ina Ammin taki" Mayraah tace "Tana gaisheki" Usman ya zauna yace "Ina kwana Hajja" Hajja tace "Lafiya lau ya aiki" Yace "Alhamdulillah" Bude kofar parlon aka yi sai ga Badiyya ta shigo, Usman ya bi ta da ido kamar zata wuce sai kuma tace "Ina kwana yaya Usman" Yace "Lafiya lau" Mayraah na kallonta tace "Ina kwana Aunty Badiyya" Tuni Badiyya har ta shige daki, Hajja ta girgiza kai murya can kasa tace "Na gaji da yarinyar nan, ko sallama fa bata min ba ta fita, yau da asuban fari naga tana ta hada akwatunanta na kasa hakuri na leka daki nace ina kuma zata, wai zata koma gidanku..." Sosai gaban Mayraah ya fadi tana kallon Hajja, Usman yace "Zata koma gidanmu tayi me?" Hajja ta rufe baki da sauri tace "Kul kar ka sake cewa haka, ba fa bare bace, yar uwarka ce ta jini, don tace zata koma gidanku ai ba wani abu bane, nasan babu abinda Mamuda zai ce kuma bazai hana ta zauna masa a gida ba, tun yaushe ake son ta koma can din don ku sa mata ido ta rage abubuwan da take amma fir taki, tunda yanzu Allah ya so mu don kanta ta dawo tace zata sai a bar ta ta tafi kawai, dama anjima nake son kiran Ammi" Usman yace "Karya take yi, akwai wani munafurcin da take kullawa, banda haka bazata ce zata dawo gidanmu ba" a fusace Hajja tace "O'o Allah mu yi mata kyakkyawan zato mana Usman" Usman yace "Allah ya kawo ta lafiya, dama zuwa nayi in gaisheki na kwana biyu ban zo ba, yanzu sauri nake zan tafi Zaria" Hajja tace "Ai ko nagode Allah maka albarka" Dubu goma ya ciro a aljihunsa ya ajiye mata, ta dinga sa masa albarka, ya mike yace "Ni zan tafi saboda ana jirana bani kadai zan je Zarian ba" Hajja tace "To maza kaje Allah ya tsare, ke Mayraah ai kina nan har gobe ko" Usman yace "Aa tare za mu koma gida yanzu" Hajja tace "Tare kuma? Saurin me take" Usman ya kalli Mayraah yace "Tashi mu je" Mikewa tayi tace "Hajja in sha Allahu zan dawo ni kadai" Hajja dai bata ce komai ba, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Wato Ammi ce tace kar ki zauna ko??" Usman yace "Ai ke dama kin iya zarge zarge a ranki" Mayraah tace "Bata ce haka ba Hajja, kawai akwai wani aiki da nake yi na makaranta ne" Ko rufe baki bata yi ba sai ga Badiyya ta fito da akwatunanta uku tana turasu, Hajja ta mike tace "Tafiyar kenan Badiyya?" Ba tare da Badiyya ta kalleta ba tace "Eh" Hajja tace "To ai kawai sai ki bi su Usman su ma gida za su tafi yanzu" Usman yayi saurin cewa "Wani Usman din?" Hajja ta kallesa baki bude, lokaci daya ta hasala tace "Wai me ku ka dau Badiyyar nan ne? Bare ko me? Er kanwar uwarka ce fa uwa daya uba daya, kwata kwata kun dauki tsangwama kun yafa ma yarinya marainiya ba uwa ba uba" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Usman ya fice daga parlon ita dai Mayraah ta kasa motsawa daga inda take, Usman ya leko parlon ganin Mayraah bata biyosa ba yace "Ke me kike jira Malama" Mayraah ta sauke idonta kasa ta nufi kofa, Hajja ta dau dubu gomansa da sauri cikin kuka tana mika masa tace "Gashi bana so ka kara fetur a hanyar Zaria" ko juyawa shi dai bai yi ba har ya fita, Mayraah dai sai bin sa take don bata son yayi mata masifa..... 07087865788 WhatsApp only. [5/29, 2:29 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖 By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 4.... Suna barin layin Mayraah na kallonsa a hankali tace "Amma Yaya Usman da ka daukota just for peace to reign" Usman yace "That peace should neva reign" Mayraah bata kuma ce masa komai ba ta jinginar da kanta jikin kujeran motar har suka isa gida, tsaye suka tadda Ammi a parlor waiting for them furiously, Mayraah na ganinta ta gane har Hajja ta kirata kenan, Ammi ta nufi Usman rai bace tace "Yanzu Usman abinda kayi ka kyauta kenan? Me zai rage ka idan ka dauko Badiyya a motar ka? Kai duk abin magana baka gudunsa? Inda Maheer ya fi ka kenan don da shi ne bazai taɓa yin haka ba, ko ransa bai so ba zai daukota" Usman ya nemi kujera ya zauna yace "Yanzu dai magana ta gaskiya abinda ya faru ya riga da ya faru sai dai kowa yayi hakuri Ammi, dama Allah ya rubuta Badiyya bazata hau motata yau ba" Yana fadin haka ya kalli Mayraah dake tsaye tana kallonsa yace "Go get me my box upstairs" Sama ta tafi zuwa dakinsa, ya mike yana kallon Ammi yace "Kawai zuwa fa zata yi ta dinga saka mutane magana ba wani abu ba Ammi" A fusace Ammi tace "Ina ruwanka? Naga ai ba gidanka bane nan din ko?" Ya nufi Mayraah dake saukowa rike da box dinsa ya amsa sannan ya dawo gaban Ammi yace "Ammi zan tafi ana jirana" Ammi tace "Amma gaskiya baka kyauta min ba Usman don wannan ba karamin magana ka ja min ba wajen Hajja" Yayi kasa da murya yace "Tafiya fa zan yi Ammi, ke da zaki min addu'a kice min Allah ya kiyaye hanya" Ammi ta maka masa wani kallo, ya koma ya zauna yace "Shikenan, sai a fasa tafiyar, bari in kirasu ince suyi wucewarsu kawai" Ammi tace "Ni ban hanaka tafiya ba, kaje... Allah ya kiyaye hanya, ya tsare, ya kai ku lafiya" Ya ɗan yi murmushi yace "Ameen" mikewa yayi ya dau box dinsa ya nufi kofa, Mayraah tace "Allah ya kiyaye hanya yaya" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga parlon, Mayraah ta nufi Ammi tana kallonta tace "Ammi kiyi hakuri, nima ban san me yasa yayi haka ba, kawai ta hau adaidaita sahu ta taho...." Ammi tace "Ni da ta zamar ma dole zan kira Abbanku in nemi izini in je in daukota ai" Daga haka Ammi ta wuce sama Mayraah ta bi ta da kallo..... Bayan fitar Ammi Mayraah ta wuce dakinta a sanyaye tana ta tunanin dakin da Badiyya zata ce zata zauna idan ta dawo gidan, don dakuna biyar ne a sama, Na Abba wanda ke hade da personal parlor dinsa, sai dakin Ammi still a bangaren Abba, sannan nata dakin, dakin Ya Maheer da Ya Usman duk a sama suke, dakuna uku ne downstairs, Na Umar, sai na mai aiki, da wani spare room, ta san Badiyya bazata zauna downstairs ba, don a da can baya idan ta zo to dakin Mayraah take zama, tayi ta mata abinda ta ga dama da nuna isa a dakin don ma Mayraah na da hakuri, she can't imagine staying in the same room with Badiyya again, bayan kananun issues dinta da nuna isa da gadara ga kuma rashin gyara waje, duk inda ta samu ajiye kayanta take babu nutsuwa, mayar da daki take kamar na mahaukata da tulin kayanta, she is soo unkept, Mayraah ta kalli wayarta dake ringing ganin me kiranta ta daga ta kai kunne, a hankali tayi sallama hade da gaishe sa bayan ya amsa yace "Baki je gidan Hajjan ba?" Mayraah tace "Mun je da Ya Usman, har mun dawo" Yace "Ohk, I will be coming over at 3pm, is that okay by you?" Ta kalli agogo sannan tace "Allah ya kai mu" Yace "Ameen, bye" Daga haka ya katse wayar, kwanciya tayi ta lumshe ido with many thoughts running her mind. Ba ayi awa daya da fitan Ammi ba Mayraah taji an murda kofar dakinta aka bude lokaci daya, juyawa tayi suka yi ido hudu da Badiyya tana turo Akwatunan ta cikin dakin, Mayraah ta mike tana kallonta a hankali tace "Sannu da zuwa" ko kallonta Badiyya bata yi ba ta karasa shigar da akwatunan ta fito dauko sauran bags dinta biyu, Mayraah ta sauka daga saman gadon ta dau wayarta ta fita daga dakin, lokaci daya mood dinta ya canza, dakin Ammi ta nufa ta sameta tana linke Hijab dinta, bayan ta kulle kofar a hankali tace "Ammi wai dakina Aunty Badiyya zata zauna?" Ammi tace "Dama ina zata zauna banda dakin naki, hakuri kawai za ki yi ku zauna" Mayraah ta sunkuyar da kanta, Ammi tace "Yar uwarki ce, don haka ki bi ta ku zauna lafiya, nasan dai baki da matsala" Da kyar Mayraah tace "Ni zan koma downstairs in bar mata dakin Ammi" Ammi ta mata wani kallo tace "A saboda na kawo maki bakuwa ko kuma na kawo maki bare cikin daki?" Mayraah dai bata ce komai ba, can ta juya ta fita daga dakin ta sauka downstairs ta zauna parlor, ta yi nisa tunanin da take taji Sabira na cewa "Hajiya a zubo maki abincin ne yanzu ko sai anjima" Mayraah ta daga kai ta kalleta tace "Ba yanzu zan ci ba" Muryar Ammi taji tana ce ma Sabira akwai bakuwa a sama ta zuba mata abinci ta kai mata, Ammi na gama gaya mata haka ta koma sama, Mayraah ta mike ta tafi bandakin dake parlorn tayi alwala ta fito, sama ta tafi don dauko Hijab dinta a daki, Badiyya na tsaye gaban press din dakin ta mayar da gaba daya kayan Mayraah gefe daya tana jera nata kayan, duk girman press din nan ta zabi ajiye kayanta tsabar rashin son zaman lafiya, Dama gaban mirror din dakin ma ta mayar ma da Mayraah kayan shafe shafenta da turarruruka gefe daya ita ma ta jera nata uban shirgin a gefe daya, ga jakunkunanta su ma duk ta jera a inda Mayraah ke ajiye bags dinta, haka shoes, Mayraah ta dau Hijab dinta ta fita daga dakin ta koma downstairs, tana idar da sallah ta kwanta kan doguwar kujera.... Vibration din wayarta ne ya farkar da ita daga baccin da ya dauketa, ta mike zaune da sauri ganin me kiranta tana kallon agogo dake nuni da karfe uku da minti sha biyar, daga kiran tayi daga daya bangaren yace "Hi.... I am outside" Ta zaro ido tace "Ohk pls ka bani like 20 mins..." Musharraf ya gyara zamansa a kujeran motar yace "Are you for real?" Tayi kasa da murya tace "Yeah pls" Yace "But na gaya maki ai karfe uku zan zo" Tace "I slept off, zan shirya ne yanzu" Yayi shiru, sai kuma yace "Ohk to kawo min ruwa" Tace "In ba me aiki ta kawo maka?" A takaice yace "No, thanks" Ta turo baki kamar yana ganinta, katse wayar yayi, ta mike tsaye ta sa hijab din da tayi sallah sannan ta tafi kitchen ta dau bottle water daya ta daura kan tray, glass cup ta dauka sannan ta fito daga kitchen din, to ma meye sai ta daura a tray? komawa tayi ta ajiye tray din kawai da glass cup sannan ta fito rike da goran ruwan... Tun da ta fito yake kallonta ta cikin motar don dama kawai sleeping face dinta yake son gani.... Ta bude motar without looking at him tace "Ina yini" Jin bai amsa ba ta daga kai ta kallesa ta ga kallonta yake, alama yayi mata da ta zagayo, ta kulle motar ta koma daya side din kafin ta karaso ya bude motar, yana kallonta murya can kasa yace "Dama kina baccin rana? Nurses don't sleep in the afternoon" Without looking at him tace "Sai Doctors?" ya jinginar da kansa jikin seat din motar yana murmushi yace "Yayanki ke baccin rana kenan" Da sauri tace "Aa ni yayana baya bacci da rana" Yace "Sai ni?" Murmushi me narkar da zuciya tayi bata ce masa komai ba, ya kafeta da ido, Da sauri tace "Sir lokaci na wucewa, ga ruwan" Ya sauke idonsa daga kallonta, kamar baxae ce komai ba sae kuma yace "Ki je kawai ki ma Ammi sallama ki zo mu tafi, ko shirin me zakiyi? Or baki yi wanka da safe ba ne" Ta zaro ido tace "Ni ce ban yi wanka ba kuma?" Yace "To je ki sallami Ammi kawai ki fito" Daga haka ya dau bottle water din hannunta yace "Thank you" Bata ce komai ba ta juya ta koma ciki, sama ta wuce zuwa Bedroom dinta, ita har ta mance Badiyya na gidan don tana shiga dakin da ta ganta sai da gabanta ya fadi, Badiyyar na zaune tayi dai dai saman gado ga plate din abinci a gabanta da malt, tana ta danna wayarta kamar bata san Mayraah ta shigo ba, Mayraah dai bata ce komai ba ta wuce bandaki, Badiyya ta bi ta da wani kallo, ba a dau lokaci ba Mayraah ta fito rike da sabulunta da shower gel sai towel, har ta fita daga dakin Badiyya bata daina bin ta da kallo ba, Mayraah ta tafi dakin Maheer ta shiga bandakinsa tayi wanka, ta wanke bakinta da mouthwash dinsa ta fito, Hijab dinta ta dauka ta saka bayan ta goge jiki sannan ta koma dakinta don daukan kayan da zata sa da duk wani abu da zata bukata, Badiyya bata fasa bin ta da kallo ba, bayan fitarta ta ajiye spoon din hannunta tana nazarin abubuwa iri iri.... Bayan kusan minti goma Mayraah ta fito daga dakin Maheer cikin shirinta, Hijab ne har kasa jikinta tana rike da handbag dinta ta nufi dakin Ammi ta sanar mata Musharraf na jiranta a waje, Ammi tace "Toh Allah ya tsare, sai a kula, kuma kar ki wuce karfe shidda, Abbanku ma yau zai dawo" Mayraah tace "Toh Ammi, Allah ya dawo da shi lafiya" Daga haka ta sauka downstairs, zaune taga Badiyya a parlon da plate din abincin da take ci, Mayraah ta kalleta tace "Sai na dawo Aunty Badiyya" Badiyya tace "Ina za ki?" Mayraah tace "Ana jirana ne a waje" Badiyya tace "Wa yake jiranki?" Mayraah da kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "Baƙo nayi" Daga haka ta juya ta bar parlon, Badiyya ta mike ta nufi window da sauri tana leka compound din gidan amma bata ga kowa ba, sai da ta ga fitar Mayraah daga compound din sannan ta fito har tana tuntube ta nufi gate tana leka kofar gida, sosai gabanta ya fadi ganin motar dake barin kofar gidan, Dr Musharraf! Abinda ta fada kenan a zuciyarta... Bayan sun bar layin Musharraf yace "A ina ake siyar da kayan ne?" Mayraah ta zaro ido tace "How will i know?" Yace "Ke ba er kano bace" Mayraah bata ce komai ba, Yace "kin yi shiru" A hankali tace "Kasuwa za mu je" Yace "Aa bazan je wani kasuwa ba, babu boutique ne irin na mata?" Murmushi kawai Mayraah tayi still bata ce masa komai ba, Idan tana masa wannan murmushin confusing dinsa take, ya gangara yayi parking gefen hanya, Calmly yace "Kin yi shiru" Mayraah ta sunkuyar da kanta tace "To me zan ce?" Yayi kasa da murya yace "Kinsan me zai faru Mimi?" Ta kallesa da sauri don Ya Maheer da Ammi kawai ke kiranta Mimi, ta girgiza masa kai, kana ganinta kasan she is uncomfortable, After few seconds of staring at her yace "I think it will be better in tura maki kudin kayan nan, ku hada a can gida, idan ma kudin basu isa ba sai ki sanar min" Sai a sannan Mayraah ta daga kai ta kallesa, A hankali yace "That will be better wife" Ita dai bata ce komai ba, Yace "Nawa account dinki ke iya dauka at a time?" Mayraah tayi shiru, sanin she might not even say anything yace "Ohk i will transfer 7M to you now for a start" Da sauri Mayraah ta kallesa ganin ya dau wayarsa tace "Kudin yayi yawa ai" Ya kalleta yace "Ba atamfofin dubu talatin talatin nace ku je ku siya ba Mayraah, and the 7M i am sending u is just for a start, sannan banda kudin Boxes a ciki da Abaya with jewelries, Mami ta riga tayi ordering dinsu" Mayraah bata kuma ce masa komai ba, Tana ganin ya fara danna wayarsa tayi saurin cewa "Seriously that amount is much" Ya kalleta for few seconds, sai kuma ya ci gaba da danna wayarsa, babu bata lokaci alert ya shigo wayarta, ta dinga kallon screen din wayar ganin 7M ya tura mata, can ta juya ta kallesa, ya jinginar da kansa jikin kujeran motar yana kallonta yace "Since we won't be going out for the shopping today kinsan me zai faru?" Ta ajiye wayarta tana sauraron abinda zai ce, Yayi kasa da murya yace "Akwai gidan Yayana da ya bani idan muna son zama ciki after the wedding, and i have my house da na gama wannan shekaran, sai kuma one of our houses, so i will be taking you to each and every one of them ki zabi inda ya maki" Ko rufe baki bai yi ba Mayraah tace "No, I don't think that will be possible, duk wanda yayi maka is okay, just drop me home now" Kallonta ya dinga yi, taki yarda su hada ido, lkci daya yanayinsa ya canza yace "Saboda ban yi deserving kiyi trusting dina ba?" Mayraah that is becoming uncomfortable ta girgiza kai da sauri tace "Ni ba haka nace ba, i just don't have choice duk abinda ka zaba is okay by me" Yace "No, ke zaki zaɓa ba ni ba" Ta kallesa da sauri ganin zai fara driving bata san sanda ta sakar masa kuka ba tace "Don Allah kayi hakuri ka maida ni gidanmu tunda baza mu je siyayyan ba" Da mamaki yake kallonta ganin hawaye a idonta kamar jira take, Bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da driving dinsa, Mayraah sai bin hanya take da kallo gabanta na faduwa tana jiran ganin inda suka nufa, ai bata san sanda ta sauke ajiyar zuciya ba ganin inda za su koma, suna isa kofar gidana bayan yayi reverse ta juya ta kallesa a hankali tace "Nagode" Ya gyada mata kai kawai, ta bude motar ta sauka tana kulle kofar ya ja motarsa ya bar layin ta bi sa da kallo, lokaci daya jikinta yayi sanyi, bayan few seconds ta juya ta nufi cikin gidan tana duba agogon wayarta dake nuni da karfe hudu da rabi. Ammi dake zaune parlor ta dinga kallonta tace "Wai har kun dawo" Mayraah ta zauna gefen Ammi tace "Kinsan me Ammi? Kawai cewa yayi it's better ya bada kudin mu siya kayan ba sai mun dinga yawon siyayya ba tare, so he sent me 7M" Ammi ta buda baki tace "Kika amsa?? Uban me za a hada maki na 7m Mayraah da zaki amsar masa kudade haka?" Mayraah ta marairaice tace "Wallahi nace masa yayi yawa amma yaki ji na Ammi, kuma wai banda boxes da Abaya and jewelries a kudin" Ammi dai ta kasa cewa komai, Mayraah dai sai kallonta take, can Ammi tace "To shikenan, Allah Ubangiji ya sanya alkhairi, shi kuma Allah ya kara masa budi" Mayraah ta sunkuyar da kanta, Ammi tace "Je ki canza kayanki mu je kitchen mu nema ma Abbanku abinda zai ci anjima, tun dazu nake nan nake nazarin abinda zan girka" Mayraah tace "To" Har ta mike zata wuce sama zuwa dakinta Badiyya ta fado mata, can ta juya a hankali ta kalli Ammi tace "Aunty Badiyya na sama ne?" Ammi tace "Aa wai taje amso littafinta a gidan kawarta" Mayraah dai bata ce komai ba ta wuce sama zuwa dakinta, tana bude kofar dakin ta dinga bin ko ina da kallo, ji tayi kamar tayi kuka, what is all this plss? kaya can, kaya nan, everywhere so littered with clothes kamar warce tayi sati a dakin, ta karasa ciki, within few minutes ta hada wasu abubuwanta da tasan zata bukata ta fice daga dakin ta tafi dakin yaya Maheer ta ajiyesu sannan ta cire Hijab dinta ta linke ta canza kayanta ta fita daga dakin ta dawo parlor... Sai kusan karfe shidda suka gama girkin Ammi ta fito parlor, Mayraah kuma ta hau gyara ko ina na kitchen din, Ammi na zaune parlor Maheer ya shigo gidan, bayan ya gaida Ammi ya wuce sama, Ba a wani dau lokaci ba ya dawo downstairs yana kallon Ammi yace "Ina Mimi?" Ammi tace "Tana kitchen" Ya nufi kitchen din, Mayraah na ganinsa tace "Yaya sannu da dawowa" Ya kulle kofar kitchen din yace "Me kayanki yake yi a dakina?" Mayraah ta marairaice tace "Yaya Aunty Badiyya ce ta dawo gidan nan, and she's already scattering everywhere in my room" Maheer yace "Yaushe ta zo?" Mayraah tace "Dazu" Yace "Shine kika cika min daki da kayanki? Me yasa baki kai dakin Usman ba?" Ta zaro ido tace "Kana son yayi min fling dinsu idan ya dawo?" Juyawa Maheer yayi ya fita daga kitchen din Mayraah ta ci gaba da abinda take. Ammi na zaune parlon Abba bayan ya gama cin abinci wajajen karfe tara, tana kallonsa tace "Yallabai dama nace sai ka dawo zan sanar maka, Badiyya ta dawo gidan nan da zama yanzu" Abba yace "To maa sha Allah, ai haka ake so, Allah yasa ta zauna wannan karan" Ammi tace "Ameen, sannan kuma kaga biki na ta karatowa ban ga kace a fara shirye shiryen komai ba" Abba yace "Wannan ai ba damuwa bane, a rana daya za a siya furnitures da duk wani abu da za a kai mata, so ko ana saura kwana biyu bikin ne za a iya yin wannan ko?" Ammi tace "Haka ne" Abba yace "Abinci kuma zuwa next week, za a kawo buhunhunan shinkafa da flour da su mangyada, taliya, manja da dai sauransu, duk a ajiye a store" Ammi tace "Toh Allah ya kara budi Yallabai" Yace "Ameen, akwai kudin saniya da raguna uku da na bada shekaranjiya, Usman kuma yace min zai siya lemo da ruwa da za a bukata na taro" Ammi tace "To maa sha Allah" Abba ya jawo wani envelope ya bude ya ciro wasu takardu ya mika ma Ammi ta amsa tana kallonsa tace "Na menene wannan din?" Yace "Wani Plaza aka min tallansa 2 weeks ago, to akwai wani business da nayi an samu kudi Alhamdulillah shine na yanke shawaran siyan wajen da sunan Mayraah, ki ajiye mata takardun gun yan uwansu" Ammi ta sauke idonta bata ce komai ba ta mayar da takardun cikin envelope din ta mike ta nufi Bedroom dinsa, Abba ya bi ta da kallo yace "Next one da sunanki za a siya, then Umar" murmushi kawai tayi ta shiga dakin. Wajajen karfe goma Mayraah ta shigo dakin Ya Maheer, yana zaune yana danna waya, ya bi ta da ido yace "Baki kwanta ba?" Tace "Ni fa a nan zan kwanta yaya, tayi occupy din ko ina" Yace "To ke tsoronta kike ji je da baza ki ce mata ta gyara zaki kwanta ba" Mayraah tace "Aa dama ni ba dakin zan kwana ba ai" Yace "You are disturbing me Mayraah ki tafi dakin Usman mana" Ta kallesa ta marairaice tace "To kai kaje ka kwanta mana he won't say anything, amma idan ni ce zai min masifa kai ma ka sani" Maheer bai sake ce mata komai ba ya ci gaba da danna wayarsa, ta lallaba ta kwanta karshen gadon kafin ya canza mind ya koreta, tana kwanciya babu ɓata lokaci bacci ya dauketa, Maheer ya dau wayarsa ya koma dakin Usman ya ci gaba da abinda yake, wajen karfe daya yaji yana jin yunwa, har ya kwanta yaji bazai iya jure yunwar ba ya tashi ya sauko downstairs, kunna fitilar parlon yayi ga mamakinsa ya ga Ammi zaune, ya nufeta da sauri yace "Ammi baki kwanta ba?" Ammi tayi saurin goge hawayen idonta wanda tuni Maheer ya gani, ya zauna yana facing dinta da damuwa yace "Ammi are you okay? Me yake faruwa ne" Ammi ta kirkiro murmushi tace "Sallah nayi shine na dawo nan na zauna" Yace "No, kuka fa kike Ammi" Ammi tace "Kukan rashin mahaifina da 'yar uwata sannan kanina, hakan har ya zame min jiki kai ma ka sani Maheer" Maheer ya kwantar da murya yace "Ammi addu'a kawai zaki dinga bin su da shi ba kukan nan ba, don Allah ki daina haka kar ki je wani ciwon ya shige ki" Ammi ta gyada masa kai tace "In sha Allah Maheer" Yace "Ki tashi kije ki kwanta" Tace "Kai me ka sakko yi" Yace "Abinci zan ci" Ammi tace "In ko baka daina cin abincin tsakar dare ba zaka ajiye tumbi ne" Yayi murmushi yana shafa cikinsa yace "Yau ne fa kawai Ammi, kuma kaɗan zan ci, bari ma in zubo ki ga" Daga haka ya mike ya tafi kitchen, ba a dau lokaci ba ya fito rike da plate din abinci, yana ci suna hira da Ammi a parlon, har ya gama, tare suka koma sama ganin ya nufi dakin Usman tace "Can zaka kwanta?" Yace "To tayi hijacking min dakin" yana fadin haka ya shige dakin Usman ya kulle, Ammi ta bude kofar dakin nasa a hankali ta kunna wuta tana kallonta, tana kwance tana bacci, Ammi ta karasa cikin dakin ta lulluba mata bargo a hankali sannan ta juya ta kashe wutan dakin ta fita ta tafi nata dakin. 07087865788✍🏻 WhatsApp only, no phone call ... [5/29, 6:36 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖 By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 5...... Washegari sai kusan karfe goma Mayraah tayi realizing basu yi waya da Dr Musharraf ba tun bayan da ya dawo da ita jiya, ta karasa wanke wanken da take yi a kitchen ta fito, Sabira ce kadai parlon tana goge goge, Mayraah ta wuce sama ta shiga dakin Maheer, tun karfe takwas ya fita aiki, yana fita kuma ta gyara masa dakin ta wanke bandaki, wayarta ta dauka ta zauna gefen gado tayi dialing number Dr Musharraf, har ya katse ba ayi responding ba, da har zata sake dialing kawai kuma ta fasa, ta daga kai jin an bude kofar dakin, Ammi ce ta shigo, Ammi ta karaso tana kallonta tace "Meye da dakin naki da kika yi hijira daga can yanzu?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Aa ba komai, kawai ina son Aunty Badiyya ta zama comfortable ne shi yasa" Ammi tace "To bana son haka, kuma kar in sake ganin haka, ki tattara yanzun nan ki koma dakin ki, kar ki sake cewa zaki kwana dakin Maheer saboda Badiyya na dakinki, as far as tana gidan nan to daki daya za ku zauna" a hankali Mayraah tace "Toh" Ammi tace "In ke tayi ma haka zaki ji dadi? Saboda ita ki ki zaman dakinki kamar ba er uwarki ba, naga dai ko cacan baki bai taɓa hada ku ba balle kice, to me ya janyo wannan abu haka? In kinyi hakuri duka duka ma kwana nawa ya rage maki a dakin Mayraah" Mayraah ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Ammi" Ammi tace "Ki tashi ki koma dakin ki" Daga haka ta juya ta bar dakin, Mayraah ta bi ta da kallo. A hankali Mayraah ta bude kofar dakinta ta shiga ciki da sallama, Badiyya dake shiryawa bata ko amsa sallaman nata ba balle ta kalli inda take sai ma wani tsuke fuska da tayi, Mayraah ta karasa cikin dakin ta ajiye wayarta gefen gado sannan ta shiga bandaki rike da shower gel dinta da towel, Badiyya ta bi ta da kallon gefen ido har ta kulle kofar bandakin, Badiyya ta wani taɓe baki ta ci gaba da shafa cream dinta, ko minti biyar Mayraah bata yi a bandaki ba wayarta da ta ajiye gefen gado ya fara vibrate, Badiyya ta juya tana kallon wayar, da sauri ta dauka tana kallon number jikin screen din don da Emoji aka yi saving maimakon suna, wayarta ta jawo tayi snapping screen din sannan ta mayar da wayar inda yake ta ajiye da sauri, babu bata lokaci ta haddace number sa tayi snapping ta shiga True caller don ganin number waye, Musharraf Abdallah taga ya fito, wanda sai da gabanta ya fadi ganin sunansa kadai, a sanyaye ta ajiye wayarta ta karasa shafe shafenta ta mike ta dau kayanta ta saka ta koma gefen gado ta zauna, tayi nisa cikin tunanin da take bayan kusan minti ashirin taji fitowar Mayraah daga bandaki, mikewa Badiyya tayi ta figi wayarta ta fita daga dakin, Mayraah ta bi ta da ido, ganin bata kulle mata kofar ba ta karasa ta kulle kofarta. Musharraf ya shigo parlorn Maminsa ya zauna opposite dinta yana kallonta yace "Gani Mami" Mami tace "Why ain't u picking ur brother's call?" Yana karasa buttoning din t-shirt dinsa yace "Bana kusa da wayan" Mami tace "To ka kirasa za ku yi magana" Musharraf yace "Ohk" daga haka ya mike, Mami tace "Ina kuma za ka? koma ka zauna ka kirasa yanzu, don nasan ba kiransa zaka yi ba" Musharraf ya kalleta yace "Mami sauri fa nake, ba ni nace maki zan kirasa ba" Mami tace "Musharraf" Komawa yayi ya zauna ya jinginar da kansa da kujera, Mami tace "Kira sa yanzu" Musharraf ya hade rai yace "Mami shi fa gayen nan baya taɓa kiran mutum haka kawai, i know there is definitely something annoying that he wants to say to me" Mami tace "Why don't u respect the fact that he is ur elder brother Musharraf?" Musharraf bai ce mata komai ba ya dau wayarsa yayi dialing number brother din nasa wanda ko saving dinsa ma bai yi a wayarsa ba, yana fara ring ya sa handsfree, Mami dai sai kallonsa take, sai da ya kusa katsewa aka daga from the other side, Musharraf yace "Good morning" Yayan nasa yace "Baka ganin kirana ne?" Musharraf yace "Eh yanzu naga kiran" Daga daya bangaren brothern nasa da ake kira da Daddy yace "Akwai personal discussion da nake son mu yi akan auren nan da zaka yi" Musharraf ya ɗan yi jim, sai kuma yace "Ina ji" Daddy yace "Ok, amma da farko ina son sanin ko kana da issue da Farrah ne?" Musharraf yace "Wacece haka?" Ita dai Mami kallonsa kawai take, Daddy yace "Farrah ce baka sani ba?" Musharraf yace "Oh, me yasa ka min wannan tambayar?" Daddy yace "At the first place.... Why did u decide to date somewhere else ga er uwarka that has all qualities also" Musharraf bai san sanda ya mike tsaye ba yace "Is that so? Since ni ban yi ba ai kai zaka iya yi a madadina it's still not too late, look yaya ni dama nasan there is nothing good da zaka kirani ka gaya min, and sorry to say bana son kowa ya kara sa bakinsa a lamarin aurena, not even you! Hatta su Aunty Halima babu ruwansu da matar da zan aura, i am not a kid da za ayi min zabin matar aure... Kai idan ka tashi auren sai ka auri Farrah ai ka ma fi ni saninta" Yana gama fadin haka ya katse wayar, Mami kam buda baki tayi tana kallonsa da mugun mamaki, ya juya ya fice daga parlon, Dama ita she is not in support of cewar sai ya auri cousin dinsa kamar yanda dangin ubansa suka dage, beside she is not even interested da wannan hadin da suke ta dagewa a kai, Allah kadai yasan me suka kira Daddyn suka tsara masa shine ya kirata da batun ita kuma tace ba ruwanta ya kira ɗan uwan nasa sun fi kusa, to dai ga yanda kiran ya karke a gabanta, Wayarta ne ya fara ring ta dauka ganin Daddy ke kiranta ta daga ta kai kunne, Daddy yace "Mami daga wannan moment din na cire baki a kan duk wani issue da yayi concerning Musharraf, he can go an do whatever he wish, sannan wllh bazan zo daurin auren ba ma, kudi da na kai masa gidansu yarinyar ma nayi da na sani, kawai na bata lokaci na shigo kano akan yaron da ya bi ya raina kowa...." Mami tace "Wani magana kenan kake yi Daddy, kana da kamarsa a duniya ne? Ni fa ban ga lafinsa ba, he is not a kid da za ace lallai lallai sai an zabar masa warce zai aura, kuma ai gaskiya ya fada kawai choice of words dinsa ne are wrong, a gabana ya kiraka ai, meye za su dage sai ya auri Farrah?" Daddy yace "of course nasan zaki yi supporting dinsa ne ai Mami, to sai yaje ya auri yarinyar da zai aura, amma ni kam bazan zo daurin aurensa ba tunda har ni yayi ma rashin kunya a waya" Mami ta tabe baki tace "Yana da wani ɗan uwan da ya wuceka ne da zaka ce baza ka zo daurin aurensa ba? Ni don Allah sai anjima kar ku ɓata min rai kai da shi" Daga haka ta katse wayar ta mike ta tafi wajen Musharraf, yana kokarin fitowa daga dakinsa tace "Ina za ka?" Ya ɗan kalleta yace "Zan fita ne" Mami tace "Musharraf shi yayan naka ka gaggaya ma magana babu kunya a gabana?" Musharraf yace "Mami ke baki ji maganan da yake min bane, he just love controlling me alhalin naji kunce da shekara biyu kawai ya girmeni, nasan ai bashi da girlfriend to don me bazai yi dating farrah ba su yi aure" Mami ta kamo hannunsa tace "I know they are wrong but ba haka ya kamata kayi approaching maganar da yayi maka ba, yayi deserving some respect from u, for peace kawai kamata yayi kace masa u are not interested shikenan" Musharraf yace "Mami ni fa as far as u are not against my marriage to babu wanda ya isa ya hanani abinda nake so, tun daga kan Daddy har su kawu da su Aunty Halima, nobody" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanzu ya batun lefen jiya baka ce min komai ba" Yace "I decided to give her the money su siya kayan" Mami tace "Nawa ka bata?" Yace "7M" Mami tace "Why not make it 10m?" Yace "Zan kara mata" Mami tace "To ka dai ce mata banda Abaya da akwati ko?" Yace "Yeah" Badiyya na zaune dakin Haseenah tana goge hawayen da yaki tsaya mata cikin rawan murya tace "Haka kawai kun sa in koma gidan ni ban ga amfanin komawata ba yau kwana biyu kenan, tun da naje dama ta tattara ta koma dakin Maheer, ba wani information da nake samu banda numbersa da nayi snapping dazu da ya kirata tana bandaki, kuma kinga ai tun dazu muke kira baya shiga saboda settings dinsa da ya saka idan baya da numberka bazaka samesa" Haseenah tace "Kilan Private line dinsa ne, amma babu ta yanda likita zai sa wayarsa a wannan setting din, definitely yana da wani layin da kowa ke samunsa" Badiyya ta jinginar da kanta jikin gado tana shessheka tace "Wllh na gaji Haseenah, wasa wasa fa yau saura wata daya bikin" Haseenah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni zaki gaya ma sauran kwana nawa bayan rana daya ne da nawa da Maheer, ai ko nima an cuceni wannan damuwar da aka sa ki, banda haka da yanzu ai har dake zamu yi ta shirye shiryen bikina, amma ace ana ta abu ba ke" Badiyya dai bata ce komai ba sai hawaye take, Haseenah tayi kasa da murya tace "Toh kece da gaddamar tsiya, Nan nan Zaliha ta kawo mana shawara shekaranjiya kince ba haka ba, wannan kadai ne fa option dinmu yanzu Badiyya" Badiyya tace "Ke ni fa bazan dau kudina in kai ma wani kato wai Malami ba, wa enda na kai a baya wani result din na gani? Duk karyace da cin kudin jama'a in gaya maki, da zan gaya maki nawa Malamai suka ci kudina a shekaru na talatin da biyu a duniya wllh sai kinyi mamaki, ke bari kiji tun ina 22 years nake bin Malamai amma har yau ban ga out come ba, don haka wannan karan ma bazan yi asaran kudina ba, bayan samari haka na dinga ba malamai kudi akan in hada common degree din nan amma dubi sau nawa ana Withdrawing dina from this university to another, ta dalilin wannan Dr Musharraf din ne na gano ashe ina da ilimi rashin maida hankali ne kawai, ai abun akwai mamaki ace wai ni Badiyya ke final year a Nursing Science, alhalin Microbiology ma na kasa shekarun baya" Haseenah tayi wani murmushi tana girgiza kai tace "Uhumm Badiyya kenan, wllh baki dai samu na kwarai bane kawai" Badiyya ta zaro mata ido tace "Ke na fa ce maki duk karya ce Haseenah, haka nan ake cewa ba a samu na kwarai ba amma ni nayi harka da Malamai sun fi 50 kuma idan gaskiya ce ace a cikin mutum hamsin babu na kwarai ko daya? Aa wllh ba da kudina ba wannan karan" Haseenah dai tayi shiruu, Badiyya ta kalleta tace "Ko ke kinsan wani Malami ne?" Da sauri Haseenah ta zaro ido tace "Ah haba dai, wane ni??? ina nake zuwa da zan san Malamai, kuma su waye kawayen nawa banda ku? Ban san kowa ba wllh, kawai shawara na kawo amma ni ba malamin da na sani" Badiyya na goge idonta tace "Shikenan nasan abinda zan yi" Haseenah tace "Me za ki yi?" Badiyya ta mike ta dau handbag dinta tace "Ke dai kawai ki zuba ido" Haseenah tace "Toh Allah Ubangiji ya sa a dace, yanzu yaushe zaku fara final exams din ku?" Badiyya ta nufi kofa tace "Wa ke ta wani final exams" Haseenah tace "Aa Badiyya kar fa kije kiyi 2-0 gwara ki samu ki kammala degree din nan naki successfully, shekara biyar fa ba wasa ba" Badiyya ta hade rai ta juyo tana kallonta tace "Ai sai dai Mayraah tayi 2-0 babu degreen babu miji, tunda har ta shiga gonata... Wallahi in dai ina numfashi i can go to any extent na ganin auren nan ya lalace, kuma lalacewar auren zai yi distablizing dinta har sai ta kasa final exams" Tana gama fadin haka ta fice daga dakin tayi banging kofar, Haseenah dai ta taɓe baki, haka kawai tace mata ga malamin da ke mata aiki har ya karkato da hankalin Maheer gareta wataran abu ya hadasu ta tona mata asiri a familynsu ta shiga uku, waye bai san Badiyya da tonan silili idan abu ya hadaku ba.... Sai bayan Magrib Badiyya ta shigo gida, Ammi na zaune parlor tare da Maheer, ta gaida Ammi, sannan Maheer ma ta gaishesa ciki ciki, zata wuce yace "Zo nan" tsayawa tayi, sai kuma ta juyo tana kallonsa, yace "In taso in sameki ne?" Dawowa tayi ta zauna saman kujera bata ce masa komai ba, yace "Daga ina kike?" Ta daure fuska tace "Daga gidansu Haseenah nake muna shirye shirye" Maheer yace "This should be the last day da zaki fita ki kai magariba a waje, nan ba gidan Hajja bane da kike fita sanda kike so ki dawo sanda kika ga dama, sannan gidan nan ba a fita anyhow without control we are not animal, this should be ur first and last warning" Tuni ta kauda kai zuciyarta na tafarfasa, tabdijam banda su Haseenah da Zaliha da suka ja mata a ina wannan mutumin zai ganta ya dinga yanka mata warning haka kamar er cikinsa, duka duka da shekara nawa ya girmeta?? Ita dai Ammi bata ce komai ba, Lokaci daya ta mike fuuu ta wuce sama, Ammi na kallon Maheer tace "Allah ya shirya mana ita" Maheer yace "Allah abunta har da iskanci saboda taga babu me ce mata komai, gashi Hajja ta gama lalatata, su kansu dangin babanta are not helping matters at all, da anyi magana sai kuce marainiya" Mayraah na zaune tana karatu a daki Badiyya ta shigo ko sallama babu, Mayraah na kallonta tace "Sannu da zuwa" Wani mugun kallo Badiyya ta watsa mata, daga nan ta hau tube kaya tana diresu kan gado, Mayraah dai ta ci gaba da karatun da take, Badiyyah na shiga bandaki Mayraah ta mike ta bar dakin, a stairs suka hadu da Maheer ta bi sa zuwa dakinsa kamar zata yi kuka tace "Yaya don Allah ka tayani yi ma Ammi magana ko downstairs ne in koma, wllh i can't stay in the same room with Badiyya, ko na mata magana bata kulani, and ta riga tayi occupying ko ina a dakin, ni tsoronta ma nake baxan iya kwana daki daya da ita ba, Ammi kuma tace dole sae na tsaya a dakin" Maheer yace "Leave Ammi alone, ki shigo nan kiyi duk abinda za kiyi, in few weeks time zaki bar mata gidan ita da Ammin ai" Yana fadin haka ya shiga bandaki, Mayraah ta karasa a hankali ta zauna gefen gado. Karfe bakwai na safe Mayraah ta fito daga dakin Maheer kafin Ammi tayi noticing a nan ta kwana, dakinta ta nufa da sauri ta buda kofar dakin a hankali ta shiga, bbu kowa cikin dakin tasan probably tana banɗaki, Mayraah ta fiddo kayan da zata sa yau don karfe tara take da lectures, zaunawa tayi tana jiran fitowar Badiyya amma shiru, ta kalli agogo ganin she is been sitting for 30min ta kalli kofar bandakin, ita dai bata ji an buda ruwa ko kuma dai wani alama da zai nuna mutum na bandakin ba, tana ta zaune bayan wani minti goman ta mike tana bin dakin da kallo, to ko dai bata bandakin ne, Boxes din Badiyyah uku ne ranan da ta zo gidan, yanzu kuma maimakon uku Mayraah sai taga biyu kawai babu na tsakiya, kallon gaban mirror tayi da sauri taga babu wasu turarruka da kayan shafe shafen Badiyya, nan ta lura hatta Charger dinta da power bank dake bedside drawer babu su, kofar bandakin ta nufa ta ɗan tura kafin ta leka ciki taga wayam, fita tayi daga dakin ta tafi dakin Usman don can Maheer ya kwana, knocking tayi sai da ya amsa sannan ta bude ta shiga, ta samesa kwance, ta karasa kusa da shi da sauri tace "Yaya Aunty Badiyyah fa bata gidan nan" Maheer yace "How?" Mayraah tace "Wallahi kuwa, yanzu naje dakin nama yi zaton tana bathroom ina ra jiranta sai daga baya nayi noticing babu jakanta daya a dakin" Maheer yace "To me zanyi kika zo kika tasheni" Mayraah tace "To ko gidan Hajja ta koma?" Maheer yace "Da ya fi mata dai" yana fadin haka ya gyara kwanciyarsa ya juya mata baya, Mayraah ta ɗan turo baki, can tace "Zan je in gaya ma Ammi" bai ce mata komai ba, hakan yasa ta mike ta fita daga dakin, Hankali tashe Ammi ta nufi dakin Mayraah bayan Mayraah taje ta sanar mata Badiyyah bata gidan, Ita dai Mayraah na tsaye bakin kofar dakin nata tana kallon Ammi dake bin ko ina na dakin da kallo har da bude press taga Badiyya ta kwashe kayanta, Ammi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ke yaushe kika lura bata nan?" Mayraah da gabanta ya fadi don bata son Ammi tasan ba a dakin ta kwana ba tace "Kawai ina tashi naga bata nan, ni na zata tana parlor ne at first" Ammi ta fice daga dakin ta koma nata dakin, wayarta ta dauko tayi dialing number Badiyyah taji a kashe, ta rasa yanda zata yi kawai ta kira Hajja, Hajja na dagawa bayan sun gaisa Ammi tace "Hajja Badiyyah ta je gidanki ne?" Hajja tace "Wacece kuma Badiyyah?" Ammi ta kasa cewa komai, nan taji dama bata kira Hajja ba, amma to duk ta rude, Hajja tace "Ban gane Badiyyar da kike nufi ba, bayan warce ke gidanki dama akwai wata Badiyya ne?" Ammi tace "To zan kiraki Hajja" Bata tsaya sauraron Hajja ba ta katse wayar ta ajiye kan gado ta fita da sauri zuwa dakin Maheer, ganin baya dakin ta tafi dakin Usman, Maheer da har ya ci gaba da baccinsa ya bude ido saboda irin kiran sunansa da Ammi take, ya mike zaune yana kallonta, hankali tashe Ammi tace "Maheer Badiyyah bata gidan nan fa" Maheer yace "Toh Ammi jaririya ce ita Badiyyar nan?" Rai bace Ammi tace "Wani irin magana kake gaya min haka, an tashi babu yarinya a gida kace min jaririya ce" Maheer yace "To nima haka na samu labari, kilan gidan kakarta ta tafi ba an mata fada jiya kan ta dawo da daddare ba" Ammi tace "To na kira Hajja kuma daga yanda take amsa min Badiyyah bata je gidanta ba" Maheer yace "Bichi ta tafi kenan" Da damuwa Ammi tace "Wayarta fa a kashe Maheer" Maheer yace "Don Allah kar ki wani damu kanki Ammi, Badiyya fa ba yarinya bace, inda baza a mata fada ba zata yi abinda ta ga dama ta tafi" Ammi ta kasa cewa komai, can ta juya ta fita daga dakin, Maheer ya koma ya kwanta... Wata dattijuwa ce tsaye kofar gidanta da wani bugujejen riga dake ta zamewa daga shoulder dinta, ga wani uban dankwali ta kima a kai hannunta rike da tsintsiya, fada take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, cikin daga murya take cewa "Sannan a karshe sae dae ince Allah ya isa tsakanina da ku, Allah ya saka min wannan cutata da sa ni magana da kuke ba dangin iya ba na baba, kuma ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba bishiyar nan ta girmi iyayen kakanninku, wllhi ban yafe ba har karshen duniya...." Wata mata dake wucewa da kayanta dukundukun tace "Baaba Ladi ina kwana, wani barnar aka maki halan" Mama Ladi ta juya tace "Sai ma kin tambaya?? yaran da kowa yasan Allah ya riga ya tsine masu albarka tun a nan duniya, yanzu don Allah ke a ina kika taɓa ganin an sha rake a karkashin bishiya Delu? Ba fa iyayensu masu zaman kashe wando a kauyen nan suka dasa bishiyar ba, nima gadonsa nayi gun mijina shi ma kuma gun iyayensa da suka gada wajen nasu iyayen ya gada, kinga kuwa ae ba banza bishiyar take ba, tun fa asuba nake aikin share wajen nan sae yanzu na gama, ai kinga an cuceni an ci amanata, sai cikin dare ko wani mahaluki ya tafi ya kwanta ya bai ma hakarkarinsa hakkinsu sai shaidanun yaran su hada daba karkashin bishiyata suna shan rake suna cin gyada, kuma in sha Allahu ƙara zan sa a zagaye min bishiyar da shi, sai in ga ta inda 'ya yan banza za su zauna karkashin bishiyar" Matar dake tsaye tana sosa kanta tana sauraron Mama Ladi tace "Ai ko kawai yanda kika ce ya kamata ayi, abi duk a zagaye wajen kawai da kara, sai dai fa wannan zai ci damin ƙara ba kadan ba tunda bishiyar tsamiyar kin ga ai tana da girma, kina yin haka kuwa kin yi maganinsu, kin ma huta da masu bi maki kofar gida kullum" Machine ne ya tsaya kofar gidan aka sauko rike da akwati, Mama Ladi tayi shiru tayi mitsi mitsi da ido tana kallon warce ta sauko daga saman machine din, can dai tace "Wacece wannan?" Warce ta sakko bata ko kalleta ba ta ja akwatin zuwa cikin er tsakar gidan, Matar dake tsaye tare da Mama Ladi ta washe rubabbun hakoranta tace "Baƙi aka yi daga birni kenan Baaba Ladi" Mama Ladi ta kalleta tace "Ke dai tseguminki yawa ne da shi Delu, nan kika gama bani shawaran banza wai in zagaye bishiya da ƙara kamar don ni kadai aka halitto bishiyar, to ai mugun halina bai kai haka ba da zan ki bari a zauna a sha iska in samu lada a karkashin bishiyata, kawai mata kiyi ta yawo kina doyi kina shiga hakkin jama'a, ke baki jin warin jikinki ne baiwar Allah, ke wari mijinki wari, aa to Allah ya mana tsari... Tafi ki ban waje munafuka" da sauri Delu ta yi gaba, Mama Ladi ta shige gidanta, haɓa ta rike tace "Wa ya maki kwatancen nan Badiyya?" Badiyya da har ta tube kaya ta watsar kasa tace "Nan din ne bazan gane ba Mama Ladi" Mama Ladi tace "Ai ko gaki nan kin kawo kanki tubarkallah, naga baki taɓa zuwa ke kadai bane sai da Hajja kuma kuna zuwa baki wuce awa daya kike wucewa ki bar Hajja tunda ita har sati tana iya yi a kauyen nan, ke sae kice baxa ki iya ba" Badiyya tace "Yanzu dai wanka nake so inyi, wannan garin naku zafi kamar oven...." Mama Ladi tace "To Hegen almajirin me debo min ruwan a rafi bai zo ba, amma akwai ruwan da na adana bari in kai maki kiyi wankan" Daga haka ta fita daga bukkar, Badiyya ta bi ta da kallo, katon drum da ta sa ma kwado ta bude ta dau bokiti ta cika da ruwa tace "Banda ke ma wa ya isa yasa in bude wannan ajiyar tawa, ruwan nan yafi wata shidda komin rashin ruwan da nake bana taɓa sa, sai dae rashin ruwan ya kasheni babu ruwana, nasan wataran zai min amfani, to yau ga amfaninsa" Badiyya ta fito da sosonta da Sabulu ta wuce ɗan karamin bandakin dake tsakar gidan bayan Mama Ladi ta kai mata ruwan, Mama Ladi tace "Allahu Akbar, wllh sak marigayiya, bana mantawa haka take zuwa ta min sati a garin nan tun ma bata yi aure ba, ita kadai ce bata kyamatar inda nake sae er uwata Hajja kaka, Allah dai ya ji ƙan Rukayyah, shi yasa komi na samu er ta Badiyya nake ajiye ma idan na samu me shiga kano in basa amana ya kai mata" Badiyya na fitowa daga wanka ta tarar Mama Ladi ta ajiye mata kunu da kosai, ta ɗan yi shafe shafenta sannan ta fara cin abinci don karfe biyu na rana ake nema, Mama Ladi har da shimfida mata sabon zanin gado a kan gadon karfenta, Mama Ladi ta dawo ta zauna gefenta tace "Ban ji kince er uwata Hajja tace ki gaisheni ba" Badiyya ta fashe da kuka kamar jira take, a gigice Mama Ladi ta saki kara tace "Wayyo Allahna, mutuwa Hajjan tayi? Na shiga uku na lalace, ta mutu ne?" Cikin kuka Badiyyah tace "Tana nan Mama Ladi ba abinda ya sameta, kawai dama na zo in gaya maki abinda ake min ne saboda an ga bani da kowa, anga Abbana da Ummata basu da rai" ta kare maganar tana kuka sosai, Mama Ladi tace "Subhanallahi me ake maki Badiyya, su fa mutane har yanzu basu gane rikon maraya akwai tsarkakkiya ba shi yasa da yawan jama'a wuta za su, wa yace masu ana ma marainiya haka? Yanzu basu san ta dalilinki duk sai su shiga wuta ba" Nan Badiyya ta gyara zama ta labarta ma Mama Ladi duk abinda ke faruwa, na karya da na gaskiya, wanda na karyar ma yafi yawa, Mama Ladi tayi shiru tana kallonta baki bude, can ta gyada kai a hankali tace "Tabbas Hajja ta kirani ta sanar min da wannan biki har nace idan Allah ya nufa in zo to zan zo, don gaskiya naci alwashin sai bikinki zan je garin kano don kece tawa, Ita kanta Ammin ta kirani ta sanar min da batun bikin na mata Allah ya sanya alkhairi kawai, ko ba komai hakan ma zan samu lada, to da naji har da na Mashir ne ma yasa na canza shawaran zanje bikin don Mashir nawa ne, ashe kwace suka maki suka makala ma ita meran, ikon Allah, mutane sun zama abinda suka zama a harkan rashin tsoron Allah... Amma Ammi ta bani mamaki ainun, wllh ta ban mamaki, ita Hajja dama bazan kullaceta ba tunda nasan Ammin ce ke juyata yanda ta so, Hajja bata jin maganar kowa sai ita ko don tana kulla mata shinkafa a leda ta kai mata ne oho, amma banda haka ko ita da bazata amince da wannan abu da aka maki ba, me aka yi akayi Mera kuma Allah na tuba? Ana nufin Mera ta fi ki matsayi wajen Ammi ko Hajja kenan? To ko dai cutar mantuwa ce ta kama su, kina er kanwarta uwa daya uba daya a maki haka akan Mera?" Badiyya dake ta kallon Mama Ladi tace "Ko dai baki gane wacce Mayraahn nake nufi ba?" Mama Ladi tace "Ni ko na gane warce kike nufi, ko ba er wajen Ammi ba? Ko ba wannan tsigalalliyar fara doguwa da hanci zarere kamar biro" Badiyya ta hade rai tace "Ita mana... Ita ce ta kwace saurayina za a masu aure yanzu haka saura wata daya" Murmushi Mama Ladi tayi ta rike haɓa tace "Ikon Allah, dama ance in da ranka zaka ga abubuwa iri iri, to gashi ko na ga wannan" 07087865788✍🏻 WhatsApp only. [5/31, 4:45 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖 By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 6...... Babu wanda ya kai Ammi shiga tashin hankalin disappearance din Badiyyah, Maheer dama ko a jikinsa ya shirya ya fita aiki wajen karfe tara, Mayraah ma shi ya sa ta tafi lectures, don ita ma hankalinta ya tashi ganin yanda Ammi ta damu sosai, gashi Ammi ta kasa gaya ma Abba abinda ke faruwa har dai ya fita wajen karfe goma, dama kafin ya fita ta nemi izinin zuwa wajen Hajja, yana fita kuwa ta bi bayansa zuwa gidan Mahaifiyarta... Hajja dai ta bi ta da kallo har ta nemi waje ta zauna sannan tace "Ke baki da aiki sae daga ma kanki hankali akan abinda bai kai ya kawo ba matar nan, waye bai san halin Badiyyah ba, yarinyar da nima ta sha min haka in tashi da sassafe in ga babu ita a gida, nace maki ki kwantar da hankalinki kin ki" Da damuwa Ammi tace "To Hajja naga na kira Bichi sunce bata je ba, ga shi har yanzu wayarta a kashe kinga kuwa dole in damu ai" Hajja tace "Yanzu haka tana wajen kawayen nan nata da basa gaya mata gaskiya, sai can yamma nasan zata tafi Bichin, haka nan take sai dai in mantawa kika yi, don haka ki kwantar da hankalinki kawai, in dai Badiyya ce zata aikata abinda yafi haka ma" Har kusan la'asar Ammi bata bar gidan Hajja ba, lokaci lokaci kuma take kiran layin Badiyya still sai ta ji a kashe, a takaice dai ranan ta kira Badiyya ya fi sau Hamsin, Hajja tace "Kin ga ki tashi ki koma gida yamma ya gabato" Ammi "Me zan girka maki kafin in tafi?" Hajja tace "Ga dai sauran girkin da kika yi da rana ai ya isheni har ma zan ba almajiri a ciki" Hajja bata rufe baki ba wayarta ya fara ring, ta dauka tana nuna ma Ammi screen din tace "Waye?" Lokaci daya Ammi ta sauke wani ajiyar zuciya ganin Badiyya ce ke kiran Hajja, Ammi tace "Ita ce" Hajja tace "Ahaf, taga daman kunna wayar kenan, Allah dai ya shirya mana ita kawai"' Hajja ta daga kiran tare da saka handsfree tayi sallama, daga daya bangaren Badiyya tace "Ina yini Hajja?" Hajja tace "Lafiya lau Badiyya, ina kika je duk kika bi kika daga ma mutane hankali haka?" Badiyya tace "Kawai na tafi Bichi, kuma zan yi sati zuwa kwana goma a nan kafin in dawo" Hajja ta buda baki tace "Makarantar fa Badiyya? Ba naji ance a matakin karshe ku ke ba? Wa zai maki jarabawan?" Badiyya tace "Kwana goma fa kawai zanyi in dawo ai" Hajja tace "To me yasa kika tafi babu ko sallama duk kowa ya bi ya damu, ko Ammin taki fa baki sanar ma tafiyarki ba duk ta daga hankali" Badiyya tace "Kawai ni Hajja bazan iya zaman gidan ba ana nuna min wariyar launin fata saboda iyayena sun mutu, Shi Maheer yayi ta min fada yana min tsawa kamar wani ubana kuma ko fuska baya sake min alamar dai bai ji dadin zuwana gidan su ba, ita kuma Mayraah saboda ni taki zaman dakinta ta kwashe duk wani abun amfaninta ta fita, kwata kwata ma ta daina kwana dakin kuma ko magana bata min tun da naje wllh, kawai dai alamar babu wanda yayi farin ciki da dawowata gidan, shi sa kawai na taho Bichi idan nayi kwana goma a nan na huta zan dawo gidanki, sauran kayana dake can gidan dama ki aika a kwaso min a ajiye nan gidanki" Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "To shikenan sai kin dawo, ina gaida mutan gidan gaba daya" Badiyya tace "Za su ji" Daga haka ta katse wayar, Mama Ladi dake dama fura tace "To kin ga haka ae ya fi kar tashin hankali yasa er uwata ta shiga wani hali in shiga uku" Badiyya dae bata ce komai ba ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayarta ta koma ta jingina da gadon karfe tana kallon Mama ladi, Mama ladi tace "Wai ya naga duk kin dawo wani iri" Badiyya dai bata ce komai ba, amma fa kana ganinta kasan she looks confuse.... Ammi kam tayi jigum tana kallon Hajja bayan ta ajiye wayar hannunta, ta ma kasa cewa komai maganganun Badiyya kawai ke mata yawo a kai, Hajja ta kyabe baki tace "Ki tashi kawai ki tafi gida, Allah ya sauwake, amma Mayraah bata kyauta abinda tayi mata ba, da bata yi mata haka ba, Su dama 'ya yan nan naki maza ni nasan ba son Badiyyah suke ba tun asali, dubi abinda Usman yayi mata ranan kamar wata mara galihu, kawai an maidata baren karfi da yaji, haka ae babu dadi, in su basu hada komai da ita ke kam ai dolenki ce..." Lokaci daya hawaye ya kawo idon Ammi jikinta yayi sanyi, Hajja tace "Ni ba kuka za ki min ba, ki tashi ki tafi sae anjima, amma ki gargadi Mayraah abinda tayi sam bata kyauta ba..." A hankali Ammi ta girgiza kai tana hawaye tace "Ni ban isa in canza maki tunaninki akan abubuwan nan dake faruwa a kwanakin nan ba Hajja, nasan akwai abubuwa da yawa a ranki da baza ki iya fadi ba, sannan nasan duk abinda zance maki bazai sauya tunaninki na cewar ina fifita Mayraah akan Badiyya ba, kuma ina ta kokarin gudun hakan amma abun ya ci tura, dai dai da second daya ban taɓa fifita Mayraah akan Badiyya ba Allah shine shaida...." Hajja ta dakatar da ita da sauri tace "Ke kin fi kowa sanin ba haka nake ba, Allah ya sauwake kuma in zama haka, ni babu komai ƙasan raina sai Alkhairi, ai ɗa na kowa ne bawa sai me shi, Allah dai ya rufa mana asiri duniya da lahira, in ma akwai wani zargi da kike yi a ranki da har yake damunki yau da kullum to ki gogesa, ba komai ke hanaki sukuni da aikin koke koke ba illa abinda kika dasa a ranki yake nukurkusan ki, ni ai ba yarinya bace, don haka ki tashi ki tafi gida kawai, yara kuma gaba dayansu Allah yayi masu albarka, duk daya suke a wajena babu banbanci har ga Allah" Har Ammi ta bar gidan Hajja jikinta a sanyaye yake, why is all this happening all of a sudden, duk kwanan nan bata samun nutsuwa ta rasa dalili, ta saƙa wancan ta warware duk ita kadai a ranta, tun dai da aka kawo kudin auren Mayraah, Ko da ta koma gida maimakon tayi scolding Mayraah kan abinda Badiyyah tace a kanta bata yi hakan ba, sai ma kara jan abarta da tayi a jiki tana kuma jin ta har cikin ranta.... Throughout satin tare Mayraah suka dinga zuwa kasuwa da very close frnds din Ammi guda biyu, kaya na gani na fada suka dinga siya mata na lefe masu tsada da quality, within period din kuma Dr Musharraf ya tura mata sauran 3M din, Ammi tayi ta mata fada me yasa zata bari ya kara turo kudi, wannan ai rashin godiyar Allah ne da kai kai inda Allah bai kai mutum ba, kafin sunday suka gama hada komai na lefe, Abaya da akwatuna ne sai jewelries kawai ba a siya ba.... Ranan litinin da yamma Musharraf ya tura driver dinsu ya je daukan kayan don a zuba su cikin akwati, bayan magrib Mayraah ta sauko downstairs sanye da hijab har kasa, Ammi ce zaune parlon da Usman, Mayraah ta karasa kusa da Ammi ta durkusa kasa tace "Ammi yana jirana a waje" Ammi na kallonta tace "To amma kar ki dade" Mayraah tace "Toh Ammi" Ta kalli Usman dake kallonta sannan ta mike, Usman yace "Me yasa shi bazai zo ido na ganin ido ba" Ita dai Mayraah bata ce komai ba, Ammi ta kallesa tace "Ai bai ma fiye zuwa da daddare ba" Mayraah ta juya ta nufi kofa kamar munafuka, Usman yace "Saura ayi isha kina waje" juyawa tayi ta kallesa, Ammi ta hararesa tace "Yi tafiyarki ki rabu da shi, wani ya hanasa dinga zuwa zancen shi ma..." Mayraah ta ɗan yi murmushi ta fita daga parlon. slowly take tafiya har ta isa kofar gidan, ta jingina da motarsa tana jiran ya sauko, sauke glass yayi lkci daya turarensa ya gauraya wajen, yana kallonta yace "I am not staying long, ki shigo mu yi magana...." Ba musu ta bude motar ta shiga sannan ta kulle ta jinginar da kanta da kujeran motar cikin sanyin murya tace "Good evening sir" Yana kallonta yace "Me yasa baki je school ba yau?" Ta ɗan yi shiru, sai kuma a hankali tace "I was having headache" Ya dinga kallonta, can yayi kasa da murya yace "Mayraah" Juyawa tayi ta kallesa suka hada ido, sosai gabanta ya fadi, shi ya fara sauke idonsa yace "Tell me... menene yake damunki? for almost a week u are moody, What's happening wifey?" Tana kallonsa da manyan idonta tace "Ba abinda yake damuna fa" Yace "Ur test scores were poor..." Mayraah ta dinga kallonsa tana nazarin wani test ma suka yi, sai kuma tace "Na Dr Garba?" Yace "Test nawa ku ka yi last week?" A hankali tace "Uku" Yace "You didn't perform well in all" Kasa cewa komai tayi, and at the same time she look disturb and sad, Ganin yanayin da ta shiga yace "Tell me, baki yi karatu bane?" Ta langwabar da kanta a hankali tace "Wallahi nayi" Yace "Kinga it's ur final semester Mayraah, u need to add in more effort... Idan akwai abinda yake damunki ki gaya min yanzu, feel free to tell me Baby" Cikin sanyin murya tace "Pls sir baza a iya barin bikin sai bayan na gama final exams ba?" Shiru yayi yana kallonta for almost 40 seconds, jin yayi shiru ta ɗan kallesa suka hada ido, kamo hannunta yayi ta janye da sauri tare da turo baki, yace "Me yasa kike son a bar bikin sai bayan final exams?" Tace "So i can concentrateq fully" Yace "No Mayraah, in 2 weeks time za ayi bikinmu in sha Allah, i know u are in ur final semester i will give u the whole time, I won't stress u, zan fi kowa son ganin kin fito da first class dinki, i promise bazan takura ki ba, naga kuma nema kike ki dawo 2.1, your performance is dropping terribly..." Mayraah dai bata dago kanta ba, yace "Idan ma kina son ki zauna gidanku bayan anyi bikin har zuwa sanda za ku gama exams din it's okay by me" Ta kallesa cikin sanyin murya tace "Toh ka bari in zauna gidan namu har in gama exams din" yace "Consider that done" Ta sauke kanta tace "Thank you so much" Ya sakar mata Murmushinsa me kyau underneath his breath yace "My pleasure" Tace "Yaushe za mu yi test dinka?" Yace "Gobe" ta dago da sauri tana kallonsa duk da ta san gobe ne amma tunaninta zae ɗaga masu, yace "I know u can do it Dear" Ta marairaice tace "Plss sir ka bar shi on Wednesday mana" yace "Ae bana zuwa Wednesday, beside i will be going to Abuja that day" tayi shiru tana kallonsa, ya shafa beard dinsa yace "Zan tura maki AOC, and u can forward to ur colleagues a group dinku na WhatsApp, kinga su ma sun ci albarkacinki kenan" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "To mun gode Sir" Yace "Sai bayan biki zaki daina ce min Sir din nan?" Ta ɗan saci kallonsa amma taki cewa komai, Ya lumshe ido ya bude, yace "Kinsan Friday za a kawo lefen ki?" Mayraah da sai da gabanta ya fadi tayi shiru bata basa amsa ba, yace "Yeah, on sunday sae in kaiki ki gaida Mamina with her sisters, they are all around" Mayraah dai ta kasa cewa komai, yace "We have just this week, daga next week bazan samu lokacin kai ki ba" Jin she is quiet yace "You are not saying anything Wife" Ta yi gathering courage tace "Allah ya kai mu lafiya" Ya kalli agogon wrist dinsa yace "It's almost time for isha, zan tafi yanzu" Washegari Mayraah na zaune class tare da sauran Coursemates dinta ko wanne da sheet of paper a gabansa da question paper, ita dai sai juya pen din hannunta take, she looks so confuse cause ta yi karatu jiya da daddare don sai da ta kai kusan karfe daya kafin ta kwanta, but ji tayi kamar bata bude handout din ba kwata kwata, ga wani ciwon kai da ya sa ta gaba, ta daga kai ta kalli Dr Musharraf dake tsaye hall din wearing a sparkling white shirt, baƙin glasses ne a idonsa so she can't tell where he is looking in particular, ta ɗan bi hall din da kallo, Zaune taga Badiyya tare da clique dinta ta dage sai kwafan na Amira take da gefen ido, tun last week rabonta da school sai yau, bayan kusan minti talatin Mayraah ta mike kawai ta linke takardanta, Hamida sai kallonta take da mamaki ganin fa bata ga tayi rubutu ba, ta dinga mata alamar ta tsaya kar taje tayi submitting amma tuni Mayraah ta nufi inda Dr Musharraf ke tsaye, tana kallonsa tace "Where can i submit sir?" Ya mika mata hannu ta basa takardan, zata juya ta bar wajen as if in a whisper yace "Wait" ta tsaya ba tare da ta kalli fuskarsa ba, bude takardan yayi yaga sunanta kawai ta rubuta sai course da code, ya dinga kallonta kafin ya mayar mata da takardan yace "Go back and sit my friend" Ta amshi takardan ta juya a hankali ta koma, Badiyya dake kallonsu ta wani tabe baki ta ci gaba da satan answers din Amira da gefen ido, kusan sai da duk yan class din suka yi submit suka fita har Badiyya da clique dinta, ajin ya rage few students sai Mayraah dake ta juya pen dinta, zuwa sannan dai ta samu ta tuna solution din second question din kuma ta rubuta, yana cewa 5 minutes more amsan number 1 ya dira kanta in full speed, within that 5 minutes ta amsa question din ta kusa cika fullscap, dama questions hudu ne, to ta samu ta amsa biyu, zuwa sannan su hudu ne kawai a ajin da basu gama ba, ta mike ta tafi ta basa takardan ta ya amsa yana kallonta, ta juya ta fita daga class din ya bi ta da kallo ta cikin glass... Gun Hamida ta nufa, Hamida ta mike ganinta tace "What happened, baki yi karatu bane Mayraah, ina ta daga maki script dina kiyi rubutu amma baki kalla ba" Mayraah ta sauke ajiyar zuciya tace "Kema kinsan bazan iya ba, but na samu nayi answering guda biyu...." Hamida tace "To Allah ya bamu sa'a gaba daya" Wani Coursemate dinsu Nasir ne ya nufo su, yana kallon Mayraah yace "Dr Mu'azzam na kiranki Mayraah" Mayraah ta ɗan buda ido tace "Ni kuma?" Yace "Eh" Ta kalli Hamida da sauri tace "Me na masa?" Hamida tayi dariya tace "Ke dai kije ki ji, ba munyi test dinsa ba last week, kilan he is impressed with your performance" Lokaci daya jikin Mayraah yayi sanyi don kaf department din nan babu wanda bai san Dr Mu'azzam da masifarsa ba, kusan kowa shakkarsa yake, babu wanda yake son encounter ya hada su, nan dai ta sa Hamida ta rakata sama zuwa office dinsa, Suna isa bakin kofar Hamida ta kara gaba ta bar ta da sauri kafin ma ya ganta, Mayraah ta sauke ajiyar zuciya gabanta na faduwa tayi knocking kofar office din a hankali, sai da ta sake knocking aka amsa sannan aka mata izinin shiga, ta bude kofar ta shiga ciki ta rufe yana zaune office din tare da wani prof wanda shi ma lecturer dinsu ne, lkci daya gabanta ya tsananta faduwa don tsoron encounter ya hadata da lecturers din department din nan nasu take, ta risina ta gaishesu gaba daya, cikin fada Dr Mu'azzam yace "Ke what is wrong with u this semester with poor performances up and down, wani abu yana damun kanki ne?" Mayraah ta hadiye wani abu da ya tsaya mata da kyar ta girgiza kai tace "No sir" ita ihunsa kadae gigitata yake, Prof Habibu yana kallonta yace "Madam sai a final semester dinki zaki fara wasa? Are you okay? Or do you have any family issues u are handling?" Cikin fada Dr Mu'azzam yace "If not that she is one of our best student i won't waste my time looking for her, to ina ruwanmu idan student ya zama unserious, Prof kasan shi fa student yana da mentality din cewar yana shiga final semester ya ma gama karatun gaba daya, sai yayi ta abinda yaga dama, ke me yake faruwa dake haka? Ko Dr Musharraf ne ke damunki da baki iya maida hankali a karatunki yanzu?" Mayraah ta kasa cewa komai kanta a kasa, Prof ya kalli Dr Mu'azzam a bit surprise yace "Wani Musharraf din?" Dr Mu'azzam yace "Dr Musharraf dai da ka sani, ae fiancee dinsa ce, ba a kai maka IV office ba?" Prof Habibu ya kara kallon Mayraah yace "Ohh dama ita ce zai aura? Maa sha Allah, naji rumors wai a department din yarinyar take ashe haka ne...." Dr Mu'azzam yace "Gaskiya da alama Dr Musharraf na damun yarinyar nan kuma zai sa ta samu matsala, ke bari in gaya maki idan baki yi wasa ba zaki dawo 2.1 ne with the way i am seeing ur performance this semester" Prof yace "Kira min Musharraf din yanzu" Dr Mu'azzam yace "Ai na masa magana da nayi marking script dinta tun ran friday, i even showed him the script" Prof yace "Gaskiya ya bar yarinya tayi graduating da first class dinta, har muna tunanin zata breaking mana record din department din nan after 15 years" Dr Mu'azzam yace "That is my main concern wallahi prof, first class that she has been retaining tun daga level 1 sai yanzu a level 5 zata yi wasa da shi" Dr Mu'azzam ya kalleta yace "Madam leave my office, gwara tun wuri ki maida hankalinki" da kyar Mayraah tayi masu godiya ta juya ta nufi kofa, lkci daya hawaye ya kawo idonta, ita kanta bata san me ke damunta semester din nan ba, abinda Musharraf din ma sae yayi sati biyu bai je gidansu ba sae dai su hadu a school ko kuma su yi waya, Tana kulle kofar office din sae ga Dr Musharraf, taki yarda su hada ido ta juya ta bar wajen da sauri, ya bi ta da kallo.... Ranan al-hamis Mayraah na dawowa daga school ta tarar an kai lefen Haseenah, akwatuna set biyu Maheer yayi mata wato 12 boxes, ita dai Mayraah tun kayan na gidan ma bata damu taga abubuwan da aka zuba ba, wasa wasa an fara shirye shiryen biki a gidan babu kama kafar yaro don duk wani abu da za a bukata na taron Abba ya siya ya jibge a store, ita duk ba wannan ba babban damuwarta sunday da Musharraf yace zai kai ta gidansu ta gaida Maminsa, da ta tuna hakan sai taji gabanta ya fadi, gashi gobe za a kawo nata lefen..... Mami ce zaune parlor tare da sisters dinta biyu Aunty Fatima da Aunty Baby dake zaune gefenta, sai su Anty Halima da Ruma'isa kusan dai su biyar ne ke ta fiddo da kayan cikin akwatuna set biyu me guda 7 each dake gabansu, Wasu dattijai mata biyu ma na zaune parlon, wanda daya yayar Dad dinsu Musharraf ce, daya kuma kanwar kakarsu, daya daga friend din Mami Hajiya Hafsah dake tsaye ita ma tana kallonsu Hajiya Halima tana ɗan murmushi tace "Ai ina ga ba sai an fiddo duk kayan nan gaba daya ba Hajjaju, maidasu bazai zama easy ba gaskiya, ga yamma ya gabato ga kuma drebobi na jiranmu a waje" Hajiya Halima ta daga kai tana kallon occupant din parlon gaba daya tace "To wai halan er gwal Musharraf zai auro da za a jibga mata wannan uban kaya haka tsadaddu kamar ɗan fashi? Shi bazai yi tanadi me kyau na rayuwarsa ba sai ya kare a zuba tsadaddun lefe ma yarinya? Ikon Allah! To ko fili ya kara cikin kadarorinsa ai ya karu karuwa ta har abada, amma duk a rasa wanda zai sa shi a hanya ya dinga wannan uban siyayyan? Da kyar idan kayan nan basu yi na Miliyan goma sha ba, da yake dama ita uwarsa duk harkar karya da nuna isa tana kan gaba gaba, banda haka ai ita me masa fada ne da taga yana jibga kayan nan ta tsawatar masa, Musharraf baya jin maganan kowa babu wanda ya isa ya saka shi ya hanasa a duk cikin mu, kuma ba kowa ke mara masa baya yake abubuwan nan ba sai uwarsa, ta dauki son duniya ta dora masa, duk ya bi ya raina mutane baya ganin kowa da gashi, yarinyar da aka ce a can wajajen kurnan ɗan asabe take kafin a karasa mil tara can hanyar Daura shine za a hada ma uban kayan nan? Local girl irin wannan ne za ayi ma wannan kaya fisabilillahi jama'a kuyi alkalanci fa?" Aunty Fatima da ranta ya riga ya gama baci tace "Gaskiya Aunty Halima babu abinda za a rage a kayan nan tunda babu sisin kowa a ciki, in ma akwai to nasan bazai wuce na mahaifiyarsa ba ko yayansa, don haka yanda kayan nan suke a nan haka za mu dauka mu kai su..." Aunty Halima ta mike a fusace ta dakatar da ita tace "Ke kar ki gaya min magana Malama, yanda kike ganin kuna da iko da Musharraf to mu mun ma fi ku iko da shi, bar ganin kunyi bake bake kan lamarinsa kun mayar da mu bare, to wannan karan bari kiji sai abinda mu dangin uba muka ce za ayi ba dangin uwa ba, ku kun gama playing part dinku kuma haka, wannan zancen aure ake ba na wasan yara ba don haka mune tsaye kyamm akan lamarin nan ko mutum ya so ko ya ki, kuma ni Hajiya Halima nace baza a fitar da duk kayan nan daga parlon nan ba sai an rage su tunda ba fashi da makami Musharraf din yake ba" Mami that was calming herself down tace "Yanzu ke meye ribar yin haka Hajiya Halima? Idan aka kai ma Farrah kayan nan dama ba da hannu bibbiyu zaki amsa ba?" Hajiya Halima tayi wani shewa tace "Of course da hannu bibbiyu zan amsa saboda Farrah tayi deserving dinsa, ita kuwa yarinyar da za a kai ma er talakawa ce bata yi deserving ba bata san value dinsu ba, iyaka ma ta walakanta su ta kashe su kafin shekara daya, ni nan da kike gani bana shakkar fadin gaskiya a ko ina wallahi ko a mutu ko ayi rai, yau da Yaya yana da rai ai shima bazai bar ɗan sa yayi wannan almubbazzarancin ba da sunan hada kayan aure, kayan auren ma na yar talaka" Tana fadin haka ta fara rage laces da atamfofin da suka fi tsada tana jefawa kan kujera a fusace, Aunty Baby ta rike haɓa tana ganin ikon Allah, Mama Harira warce ita ce yayar Abbansu Musharraf tace "Kinyi kuskure babba Maryam da har zaki bari yaron nan ya kashe kudi haka wajen hada kayan aure, yo wannan ko er gidan sarauta ai sai haka, banda an ware mu bama sanin duk abinda ke faruwa ai baza mu bar wanna abu ya kasance ba, don haka dole ne sai an rage kayan nan, kuma ko da mun kai kayan ba tare da an cire ko daya ba bana tunanin za su iya bamu tukuicin da ya kamata tunda naji Halima tace a Kurna yarinyar take, banda rashin tunani irin na Musharraf ina shi ina ita? Ga er uwarsa Farrah kowa yayi masa sha'awa amma yaron nan yaki, dama gida bai koshi ba a ina aka taɓa kai wa waje? To dai duk kece me babban laifi tunda baki nuna masa haka ba" Mikewa Mami tayi ta fice daga parlon ta wuce sama, Hajiya Halima da su Ruma'isa suka bi ta da harara, Daya dattijuwar Mama Karima tace "Sam abun dai babu tsari, an raina mu ba a dauke mu bakin komai ba, duk ku cire abinda ku ka ga ya kamata a cire ai ba er gwal bace" Friends din Mami gaba daya where speechless and shock, suka dinga kallon yanda Hajiya Halima da Rumaisa ke kwashe kayan lefen ba tsoron Allah, mikewa Aunty Fatima tayi ta bi Mami zuwa sama, zaune ta ganta a parlonta tana waya, Aunty Fatima ta rungume hannunta tana tsaye jikin kofa kana ganinta kasan she is boiling from inside ita ma, Mami tace "Ni bance ka kirasu ba Daddy amma wllh idan na tashi rashin mutuncina kare bazai dauka ba wllh, na gaji da abinda dangin babanku suke min, akan me? After so many years baza su bar ni in huta ba sai bibiyata suke da sharri?" Daga daya bangaren Daddy yace "Mami pls kiyi hakuri kar ki ce masu komai, ko kayan nawa suka cire ni zan tura kudi ayi replacing ko washegari ne sai a kai sauran kayan, and pls don't say anything to Musharraf kinsan halinsa" Mami tace "Wallahi na gaji, wannan ai cin mutunci ne da cin fuska a gaban kawayena fa" Daddy ya sauke ajiyar zuciya yace "Pls kiyi hakuri, everything will be okay in sha Allah" Musharraf yayi parking ya sauka daga cikin motarsa yana kallon machine (Bike) din da yayi zoom off leaving the security guy a tsaye da envelope a hannunsa, Musharraf ya karasa gun security man din yace "Na meye wannan?" Mai gadin yace "Yanzu wani me babur ya bani wai a kai ma su Hajiya" Musharraf yace "Okay" Daga haka ya amshi envelope din ya shiga cikin compound din yana unsealing dinsa ya ciro takardan ciki ya warware yana jujjuyawa, he was surprise to see rubutu jikin takardan, babu bata lokaci ya fara karanta content din, ko 30 seconds bai yi da fara karantawa ba yaji ya kasa ci gaba da tsayuwa, yayi saurin jawo farin kujeran dake kusa da dakin mai gadi ya zauna, lkci daya yaji zufa na taho masa, kan kace me har ya gama karanta content din takardan sai kuma ya fara kokarin apprehending abinda ya karanta, after few seconds of trying to apprehend yayi squeezing din paper din a hankali ya cusa a aljihunsa..... 07087865788 WhatsApp only [6/1, 2:56 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖 By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 7...... Mikewa Musharraf yayi ya fita gate din gidan da sauri yana kallon security man din yace "Daga ina yace maka yake? And me yace maka da ya baka wannan?" Security man din ya karaso wajensa da ladabi yace "Bai gaya min daga inda yake ba ranka shi dade, kawai mika min yayi yace in ba Hajiya" Musharraf bai kuma sauraronsa ba ya nufi motarsa ya shiga ya bar layin, mai gadin ya koma ya zauna.... Bayan kayan cikin lefe har da akwati hudu su Hajiya Halima suka cire wai babu amfanin a tafi da akwatuna goma sha hudu, guda goma ya isa, Ita dai Mami bata sake sakkowa downstairs ba don ma kada zuciyarta ya kasa hakuri ta biyesu, Mama Harira tace "To yanzu kayan nan da aka rage ya za ayi da su, nan din za a bar su?" Hajiya Halima tace "A bar su suyi me a nan Mama, shi me yan uwa mata barkatai a family, tafiya za ayi da shi a ba kowa hakkinsa" Kawayen Mami babu wanda yace masu komai, kowa dai ya zuba masu ido, suka gama abinda za su yi sannan aka kira drivers su shigo su dau akwatunan su saka su a mota... Mami na kallon Aunty Fatima da tace baxata je kai lefen ba tace "Ki yi hakuri ku je Fatima, ai ba don su za ku yi ba, in don ta su ne ai baza a kai kayan ba" Aunty Fatima tace "Wallahi yaya yanzu yawanci maza ne ma ke kai kayan ba mata ba" Mami tace "To sun ce su za su kai ya za mu yi masu, kawai kiyi hakuri ku tafi, kowa yayi da kyau ai don kansa, abinda su ma suna da baya" Aunty Fatima ta sauke ajiyar zuciya bata sake ma yayar tata musu ba ta dau gyalenta da handbag ta fita, su Goma sha uku suka tafi kai kayan a motoci hudu, wanda kusan tara duk dangin Abbansu Musharraf ne, Hajiya Halima da Cousin sis dinta me suna Murja sai kyabe baki suke a mota ganin hanyar da aka nufa, Murja ta rike haɓa tace "Yanzu duk fadin garin kano yaron nan ya rasa inda zai je neman aure sai outskirt din kano, ashe girman kansa duk na banza ne, ai ko na raina ajinsa yanzu" Aunty Halima dake taunar cingam tace "Atoh, ba uwar ce me mara masa baya yake abinda ya ga dama ba, ga su ga yar kauye ai sai mu ga yanda za ayi zaman" Ruma'isa dake gaban mota a zaune tace "Kuma ina me tabbatar maku auren nan bazai je ko ina ba tunda ba class dinsa zai aura ba, shi da yake nuna yana da taste ashe duk na banza, balle ma yanzu fa an daina auren mai kudi da talaka, kowa lane dinsa yake tsayawa, kwarya tabi kwarya, ina me kudi ina talaka a wannan zamanin?" Murja tace "Toh wai ma ina ya hadu da yarinyar nan tukun? Zan so in ganta kuwa" Aunty Halima tace "Har yau nima abinda nake son sani kenan, me ya kai sa kurna har ya ga yarinyar yace yana so" Ruma'isa tace "Can ta matse masa dai, mu dai za mu zuba ido mu ga yanda abun nan zai yiwu" Motar su Aunty Fatima da frnds din Mami biyu ne ke leading sauran motocin zuwa gidansu Mayraah don shi yaje kwaso kayan lefen daga can, bayan tafiyar kusan 40mins suka iso anguwan, Aunty Halima tace "Ikon Allah, nan ne fa anguwan Murja, cabb ko a mafarki ban taɓa tunanin da abinda zai kawo ni area din nan ba" Duk suka yi shiru ana bin ko ina da kallo cike da takaici, har dai suka ga motarsu ta tsaya kamar yanda sauran motocin ma suka tsaya, Hajiya Halima na kallon wani lafiyayyen gidan dake gefensu tace "Wannan kuma wani hau ya fada masa duk girman kano ya rasa inda zai gina tanfatsetsen gidan nan sai a nan.... Ikon Allah" Murja dake kallon gidan ita ma tace "Nima shi na saki baki nake kallo, wannan ai bai yi dubara ba dubi almajirai sun masa cirko cirko a kofar gidan, to yanzu dai ina gidan da za a kai lefen?" Sauka duk suka yi daga motar ganin sauran ma duk sun sauko, Mama Harira dake toshe hanci tace "Wai ina dreban da aka ce yasan gidan ne an bar mu tsaye a walakance duk sai doyi ya bade mu cikinmu ya kumbura daga kawo kayan aure" Dreban ya taho da sauri yana nuna gidan da su Hajiya Halima suka gama magana a kai yace "Nan ne gidan ai Hajiya" Bai rufe baki ba aka bude gate din gidan sai ga wakeken compound gari guda na kallonsu, Hajiya Halima ta kalli Murja sannan ta kalli Rumaisa, ko wannensu na zare ido, Mai gadin gidan yace "Motocin duk za su shigo, bismillahn ku sannunku da zuwa" Duka drivers din suka koma cikin motocin da nufin shiga compound din gidan, Hajiya Halima dai ta koma gefe ta tsaya, sai kuma ta kyabe baki tana gyara yafin gyalenta dake wuya, Aunty Fatima da kawayen Mami sai satan kallon reaction din dangin mahaifin Musharraf suke, bayan motocin sun shiga da kafarsu suka karasa cikin gidan, sister din Ammi da yan uwanta na kusa da nesa da kawayenta sannan ga neighbors ne cike gidan suna jiran isowar family din Musharraf, yanda gidan yake a cike kai kace taron biki aka yi, Tarba irinta girma da karamci aka ma dangin Musharraf a gidansu Mayraah, Hajiya Halima dai na zaune babu yabo babu fallasa tana taunar cingam ga akwatuna an zubesu a tsakiyar parlon, sai bin ko ina take da kallo don kam kana gani kasan Naira ta zauna daram, familyn Mayraah sai duba kayan suke sama sama ana yabawa, Hajiya Hafsah frnd din Mami ta bude jakarta ta ciro set din sarka da dankunne na gold har da zobensa, Aunty Halima da mukarrabanta suka saki baki suna kallon ikon Allah don basu san da shi ba, kuma ba a nuna masu ba, they were shock, Hajiya Hafsah ta ajiye set din gold din saman akwatin jewelries, makotan Ammi suka dinga maa sha Allah ana guda cike da farin ciki, sai cewa suke yarinya tayi goshi, Alhamdulillah, Aunty Fatima ta fiddo 300k a cikin jakarta ta daura kan akwatin zannuwa tace "Wannan kudin dinki ne, duk da an dinka mata duk kayan fitan biki suna cikin akwatin, sannan a duba abinda babu a wannan kayan a sanar mana" Hajiya Halima ta wani maka mata kallo, Mama Harira tayi caraf tace "Ai mu babu abinda bamu zuba a kayan nan ba, sai dai son rai...." Aunty Rumaisa tace "Lallai kam son rai, ina ganin in dai babu wani abu to mu za mu koma don daga GRA muke gaskiya" Aunty Halima ta mike tace "Shine kam, kar dare yayi mana a hanya cikin tsukakken lokon nan, ni sai naji kamar barin kanon ma muka yi gaba daya wannan uban tafiya haka" Babu dai wanda yace masu komai a parlon sai Maman Shafa makociyar Ammi da tace "Ai ko dai, dama idan mutum bai saba fita ba sai yaga nisar zuwa nan din, amma a jirgi ma ai ana tafiyar awa da awanni, loko kuma a haka muke zaune cikin kwanciyar hankali babu karya ba komai" Hajiya Halima ta jefa mata wani kallo ita kuwa bata ma san tana yi ba don yaba kyan wani tsadadden lace dake cikin akwati ta hau yi, Small Chop da snacks iri iri da pepper chicken da aka ajiye ma yan kawo kayan nan wani sai yace na gidan biki ne, ga manyan coolers din abinci iri iri da yaji naman rago, ruwa da lemo kuwa yayi park 150 da aka jera masu waje daya abu dai irin na girma, aka kuma dau 300k aka basu tukuicin kayan da suka kawo, Su Aunty Halima basu taɓa zaton haka ba, kuma kana ganin reaction dinsu kasan hakan bai masu dadi ba ko kadan, kamar ana cunkulinsu suka fita daga parlon drebobin da suka zo tare suka dinga fitar da kayan abincin ana sakawa a motoci, aka rakosu har bakin gate cike da mutuntawa har suka shiga mota suka bar anguwan.... Ruma'isa na kallon Aunty Halima dake gefenta tace "Ikon Allah, ashe dai ba er matsiyata bace" Ko kulata Aunty Halima bata yi ba, Mama Harira tace "Amma duk yanda aka yi ubanta kasungumin ɗan kauye ne wanda yayi aziki sama ta ka, banda haka bazai shigo wannan anguwa haka ya kera gidan nan ba kamar ance masa jeka ka gani" Rumaisa tace "Dama mana, irin yan kauyen nan ne fa da suka fito birni suka yi kudi babu zato babu tsammani, to ko wacece uwarta a cikin matan parlon oho...." Mami da sisters dinta suka bi Musharraf da kallo ganin yayi hanyar stairs without even noticing them a parlon, Mami tace "Musharraf" tsayawa yayi sai kuma ya juyo yana kallonsu kafin ya dawo cikin parlon ya gaishesu, duk tunanin Mami ya gano kayan lefen da aka rage ne ganin mood dinsa, har ce ma sisters dinta tayi kada wanda yayi masa maganar duk don a zauna lafiya, Mami tace "Ina ka shiga tun dazu?" Ya shafa kansa a hankali yace "Ina tare da frnds dina" Mami tace "Are you okay?" Ya daga kafada yace "Sure" Tace "Ban ga ka ci abinci ba?" Yace "Na ci" yana fadin haka ya juya ya wuce sama duk suka bi sa da kallo, definitely tasan akwai wani abu gaya mata ne bazai yi ba, Aunty Baby tace "To ko amaryar ta sanar masa babu wasu abubuwa a kayan ne tunda kince a gidansu aka hada kayan?" Aunty Fatima tace "By all odds ta gaya masa" Mami dai bata ce komai ba, don ma in da gaske yarinyar ta gaya masa ae abinda ta gani ta gaya masa. Musharraf na shiga dakinsa ya zauna gefen gado ya rike kansa da yayi masa nauyi, ya dade bai shiga irin wannan damuwar da ya shiga yau ba, he can't even think straight, duk yanda ya so saita tunaninsa hakan yaki yiwuwa, abubuwa iri iri ne ke masa yawo a kai, he is super confuse at this moment, me ke shirin faruwa haka, inda wani abu daban ne ya damesa haka da yayi sharing dinsa da Mami but not this, to me ma zai ce mata, how will she even react to this, tashi yayi ya nufi window ya tsaya staring into space babu ko kiftawa, yafi minti goma tsaye a haka kamar wanda ya tuna abu sai kuma ya juya ya nufi kofa da sauri ya fita daga dakin ya sauka downstairs, har sannan su Mami na parlon, bai kalli inda suke ba ya fita compound, gun security man din gidan ya nufa, Mutumin ya taso da sauri ganinsa, Musharraf yace "Ko da za a sake baka wani sako ka ba Mami or anybody in this house, ka amsa kawai ka ajiye ni ka bani, kaji me nace maka?" Security man din yace "An gama ranka shi dade" Juyawa Musharraf yayi walking slowly ya koma ciki, yana shiga Bedroom dinsa wayarsa na katsewa, ya karasa ya dauka yana duba me kiransa, miss call din Mayraah ya gani, ya dinga kallon screen din sai kuma ya zauna gefen gado yayi dialing numberta, yana fara ring ta daga, tayi masa sallama, ya amsa yace "How are you" Tace "Alhmdlh... yau ma kayi tafiya ne?" Gently yace "No" Shiru tayi na few seconds kafin tace "Are you okay?" Ya lumshe idonsa ya bude yace "Not really" Da damuwa tace "What's wrong?" Yace "I was so stressed today, i don't feel okay, i think i am getting sick" Tace "Kuma baka sha magani ba" Yayi kasa da murya yace "Give me prescription...." Tace "Ohk, i will send u via text message right away" Yace "Thank you" katse wayar tayi cikin few minutes sai ga text ya shigo wayarsa, ya shiga message din da ya ga ta rubuta kamar haka "No Drugs... Just stay relaxed, get enough rest.... I mean, sleep like a baby, and dream of me" Ya maimaita message din yayi sau uku, thinking if it's really coming from her or wani ne ya rubuta mata, ya dai yi murmushi, yayi mata reply kamar haka "Not when u are not by my side" Yana tura mata text din ya ajiye waya ya shiga bandaki feeling a bit relieved.... Ko da ya fito bandaki goge jikinsa yayi da towel ya shirya cikin pajamas dinsa, sannan ya kwanta saman gado ya dau wayarsa, ya ga tayi masa reply kamar haka "Let the count down begin from today...." Dialing numberta yayi har ya gama ringing bata daga ba, ya kuma kiranta still no response, and yasan she will neva respond. Ranan asabar, Ammi na dakin da ke cikin parlor tare da sister dinta Aunty Mariya, makota ne yan shigowa ganin lefe cike a parlorn babu masaka tsinke, yan uwan Ammi na nesa da na kusa da matan Brothers din Abba sai aminiyar Ammi Hajiya Safiyya su ma duk suna parlon zaune suna monitoring kayan tunda duniya ta dawo babu gaskiya, tun jiya Ammi bata samu sun yi wata maganar kirki da er uwarta ba warce take aure a garin kaduna, sai dai ita Allah bai taɓa bata haihuwa ba, ita ma jiya wajen karfe sha biyu ta iso gidan, kuma bazata koma ba sai bayan biki, dama su hudu Hajja ta haifa, Ammi, sai marigayiya Rukayya warce ta haifi Badiyya, sai kaninsu namiji da Allah yayi ma rasuwa kusan 8 years back ko aure bai yi ba, sannan Aunty Mariya warce ita ce autarsu, Aunty Mariya dake kallon Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah dai ya fishsheta don kam gaskiya ban ga mutunci tattare da dangin mijin nan da zata aura ba, abu babu arziki??" Ammi tace "Shi yasa abun ya dameni.... Ga Mayraah kin ga ba magana take ba, baza ta iya kwatan kanta ba, kar su je suyi ta cutar min da ita" Aunty Mariya tace "In sha Allah hakan ma bazai faru ba Ammi, komai zai zo da sauki, za mu yi ta taya ta da addu'a" Ammi tace "Hatta kayan fa ba iya su kenan ba, Ita Hajiya Safiyya ai ta sani don su suka hada kayan, sun cire abubuwa sosai daga cikin lefen nan" Aunty Mariya ta bude baki tace "Haba dai?" Ammi tace "Akwatunan ma da ta nuna min ya tura mata ta WhatsApp ai ba iyakarsa kenan ba, ke dai Allah ya rufa asiri ya sa gidan zamanta ne" Aunty Mariya tace "Ikon Allah, amma kamar babu dangin Mamarsa gun yan kawo kayan ko?" Ammi tace "To ban sani ba dai" Aunty Mariya tace "Ki kwantar da hankalinki Ammi, in sha Allahu gidan zaman Mayraah ne, babu me cutarta da izinin Allah tunda mijinta na sonta kuma yana da ilimi bazai bari a taka masa mata yana gani ba" Ammi tace "Allah ya sa hakan" Aunty Mariya tace "Kin sanar ma Mama Ladi bikin nan kuwa?" Ammi tace "Na gaya mata tun sanda aka sa rana, da har tace bazata iya zuwa ba kuma daga baya ta kirani wai ai bata san har da na Mahir ba tana nan zuwa" Aunty Mariya tace "Allah dai ya rufa mana asiri kar ta zo ta addabi jama'a ta wargaza mana taro" Ammi tace "Wallahi nima fargaban da nake kenan, da tace bazata zo da farko ba baki ga farin cikin da nayi ba wllh, ban son komai ya hadani da baiwar Allahn nan gaskiya, ni wllh da ta hakura mun yafe zuwanta" Aunty Mariya tace "Hajja za mu yi ma magana kawai su yi taronsu a gidanta don gaskiya abun bazai yi kyau ba idan baiwar Allahn nan ta sauka gidan nan" Ammi tace "To ki gaya ma Hajjan haka" Aunty Mariya tace "In sha Allahu, ai anjima Maheer zai je ya kawota ganin kaya zan mata magana idan ta zo, wai Badiyya fa? ba naji some weeks ago kince ta dawo gidan nan ba" Ammi tace "Uhm Badiyya taki zama wllh Mariya" Har kusan karfe sha daya na safe Mayraah dake dakinta taki fita ko nan da corridor saboda mutane taga Musharraf bai kirata ba, ta saba during weekend yawanci before 9 yake kiranta, sai da ta ga karfe sha daya har da minti goma sannan tayi deciding ta kirasa, ta dau wayarta dake Caji tayi dialing numbersa, har ya katse bai daga ba, ta dai ci gaba da karatun da take don on Monday suna da test har biyu, tana zaune kan darduma bayan ta idar da sallan azahar Aunty Mariya ta shigo dakin da sallama, Mayraah ta mike ta linke darduman da tayi sallah tana amsa sallaman Aunty Mariya, Aunty Mariya tace "Ki sakko ki debi abinci Hajiyata" Mayraah ta marairaice tace "Aunty mutane sun yi yawa a gidan" Aunty Mariya tace "Babu wasu mutane duk sun tafi sai imu imu, ki fito ki zuba abinci" a hankali Mayraah tace "Toh" Aunty Mariya tace "Ko kuma bari in sa Sabira ta kawo maki kawai" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Yauwa Aunty Nagode" Juyawa Aunty Mariya tayi ta fita daga dakin Mayraah ta xauna kasan carpet din dakin tana duban agogo dake nuna karfe daya da yan mintuna, har sannan kuma Dr Musharraf bai yi returning call dinta ba, or did he travel today? Ta kasa hakuri ta kara dauka wayar ta sake kiransa nan ma no response, or is he still sick, ajiye wayar tayi nan da nan taji she is disturbed da ta tuna yace mata baya jin dadi jiya, tana ta zaune har Sabira ta shigo mata da abincin ta ajiye mata ta fita, kasa cin abincin tayi, ta ci cokali biyu kawai ta rufe ta mayar gefe, ta mike ta kwanta kan gado, tana ta kwance bayan kusan minti talatin wayarta yayi vibrate ta dau wayar duk tunaninta shi ne sai ta ga Hamida ce, Ta daga bayan sun gaisa Hamida tace "Amarcy za mu zo ganin lefe da su Amina yanzu" a hankali Mayraah tace "Hamida baza ku bari gobe ba?" Hamida tace "Zaki fita ne?" Mayraah tace "Akwai mutane da yawa gidan ne, i won't be comfortable ko kun zo, ku bari idan an rugu zuwa gobe pls" Hamida tace "To Allah Ubangiji ya kai mu, ke har fa na amso anko na wajen tela, sai kin ga dinkin yayi kyau wllh in gaya maki, Amina ma sun amso nasu, saura lace din ne ba a karasa ba" Mayraah tace "Ohk shikenan" Hamida tace "In ji dai sun saka maki kayan fitar biki a akwati ko sai next week zai kawo maki?" Mayraah tace "Yace min an sa, ni kinsan ban ga kayan ba ma har yanzu" Hamida tayi dariya tace "Idan muka zo duk za mu gani tare" Mayraah tace "Allah ya sauwake, ni ce zan ga lefe da ku, ba wani lefen da zan gani" Hamida tayi dariya tace "Ke dai sai mun zo" Daga haka suka yi sallama, Mayraah ta ajiye wayar ta koma ta kwanta. Har tayi bacci ta tashi wajejen karfe uku da rabi Musharraf bai kirata ba, nan taji ta shiga damuwa sosai, bandaki ta shiga tayi wanka tayi alwala sannan ta fito, sai da tayi la'asar bayan lokaci yayi sannan ta sake kiransa, sai da ya kusa katsewa ya daga, Nan da nan ta hade rai kamar yana ganinta tace "Why are u not picking my calls since morning?" Yace "Ba na ce maki bana jin dadi jiya ba" cike da damuwa tace "Har yanzu? Did you go to the hospital?" Yace "Ban je ba" Tace "Toh wani magani ka sha?" Yace "Ban sha ba" Shiru tayi sai kuma tace "Baka da lafiya kuma baza ka sha magani ba?" A hankali yace "Babu maganin" Tace "Mami fa?" Yace "Tana gida" Da mamaki Mayraah tace "Kai kana ina?" Yace "Bana gidan" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Why are you answering that way?" Yace "How am i answering Mayraah?" Ta dan buda ido tace "Kana ina yanzu?" Yace "I need rest so i am not at home..." Tace "Nasani, cewa nayi kana ina?" Yace "Nan din da nake ma gida ne...." Tace "Ohk, now tell me how you are feeling" Yayi shiru, hakan yasa tace "Hello" Yace "Ina jin ki" Tace "Kayi shiru" Yace "I should tell u how i am feeling?" Tace "Eh" Yace "Ohk i am not feeling fine Mayraah" Da damuwa sosai tace "Don Allah ka gaya min how you are feeling, idan bazaka gaya min ba kuma ka aika wani da prescription ya siya maka magani ka sha" Yace "Wa zan aika?" Tace "Kai kadai ne a gidan wai?" Yace "Yeah" Tace "Amma me yasa zaka zauna gida ba kowa bayan baka da lafiya?" A hankali yace "U said i should get enough rest Dear, shi yasa na zo nan" Mayraah tace "Ni bance kaje inda babu kowa ba" Yace "Ohk ai ban sani ba" Tace "To yanxu ka ci abinci?" Yace "Wa zai bani?" Ta zaro ido tace "Since morning?" Shiru yayi bai ce komai ba, tace "Can i go out and get u some food now?" Bayan shirun few seconds yace "Ohk, with the drug" Mayraah tace "In sha Allah" Daga haka ta katse wayar. Mikewa Mayraah tayi ta ciro kayanta a press, within few minutes ta shirya ta saka Hijab dinta har kasa sannan ta saka Nikab, ta dau handbag dinta ta duba ciki to make sure her Atm card is inside, ta zura wayarta a ciki sannan ta fita daga dakin, tsaye tayi bakin kofa tana tunanin inda zata ce ma Ammi zata je, gashi ita in dai zata yi ma Ammi karya sai ta kamata don bata iya karyan ba ma, A hankali take tafiya zuwa Bedroom din Ammi gabanta na faduwa, tayi sallama a bakin kofar sai da aka amsa mata sannan ta shiga, Ammi da Aunty Mariya kadai ne a dakin suka daga kai suna kallonta, da mamaki Ammi tace "Ina za ki?" Mayraah tayi karfin halin karasawa kusa da su gabanta na ci gaba da faduwa sosai, ta durkusa kasa tace "Ammi zan je in siyo abu in dawo yanzu" Ammi tace "Me zaki je ki siyo?" Da kyar tace "Wani material na karatun mu" Ammi tace "Karya kike yi Mayraah, gaya min inda za ki dai" Mayraah ta marairaice tana tunanin inda zata ce mata zata, Aunty Mariya tace "Ko dai wajen kawayenki zaki?" Nan da nan idea ya zo ma Mayraah ta sunkuyar da kai tace "Ammi kiyi hakuri, wajen Hamida zan je" Ammi tace "Shine sai kin min karya tukun, kuma tun safe baki ce zaki gidansu Hamida ba sai bayan la'asar kina ganin gari na neman lullubewa da hadari, bayan kuma kinsan unguwansu da nisa sosai daga nan, ki bari kawai gobe idan Allah ya kai mu" Mayraah ta daga kai tana kallon Ammi with pleading eyes tace "Nayi alkawarin bazan dade ba Ammi" Aunty Mariya tace "Kawai ki bar ta Ammi tunda tace bazata dade ba, kilan shirye shiryensu za su yi, kawai dai kar ta wuce karfe biyar a gidan" Ammi tace "Wani karfe biyar, Allah sa zuwa biyar din ta isa gidan, can fa gaban unguwa uku ne, kuma ai ita Hamidan ya kamata ta zo, ba wai ta bi ta gidansu ba" Aunty Mariya tace "Ke dai kiyi hakuri ki barta Ammi, nasan dai Mayraah ba fita take ba idan ba kwanan nan ta canza ba, tunda tace sharp sharp zata je ta dawo kawai ta tafi, Allah ya tsare" Ammi dai tayi shiru, can tace "Amma me yasa baza ki bari gobe ba Mayraah?" Mayraah tace "Ina son inje yau ne don akwai reading material dina da zan amso wajenta ran monday muna da test kuma ban yi karatu ba" Ammi tace "Shikenan, Allah ya tsare, amma kar ki jima Mayraah kinga yamma tayi ga hadari, kina gama abinda zaki yi ki kira Maheer yaje ya dauko ki, kar ki wani ce zaki shigo adaidaita sahu" Mayraah tace "To Ammi nagode" Ammi tace "Kina da cash dai ko?" Mayraah tace "Eh" Ammi tace "Toh sai kin dawo" Mikewa tayi ta ma Aunty Mariya sallama sannan ta nufi kofa duk suka bi ta da kallo. 07087865788 WhatsApp only *Kiya kiya a zo ayi abinda ya kamata kar aji ni tsit kamar an aiki bawa garinsu, free pages har guda sha biyar nayi maku fa, to a zo a sallameni kar in koma gefe inyi shiru* 🙄 [6/2, 4:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖 By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 8..... Mayraah na fita gida ta fara tunanin abincin da zata siya ma Musharraf, sannan a ina ma zata samu abincin har ta siya, tayi deciding ta fara fita daga area dinsu tukunna don ba lallai ta samu eatry da zata siya masa abinci me kyau a nan ba, after leaving the area ta samu wani babban eatry ta siya masa abincin with bottle water da drink sannan ta fito, tana fitowa wayarta dake jakarta ya fara vibrate, ta ciro wayan tana duba me kiranta taga Ya Maheer ne, ta ɗan yi jim, yanzu fa kilan tana dagawa idan ta gaya masa abinda ta gaya ma su Ammi sai ya iya cewa ta koma gida, sarai ta san halinsa, taki daga kiran har ya katse, zata mayar da wayar cikin jaka sai gashi ya sake kira, bayan ta ɗan yi nazarin abinda zata ce masa sai ta daga ta kai kunne tace "Yayana...." Yace "Ina kike haka nake jin noises din vehicle haka?" Mayraah ta ɗan buda ido tace "Gidansu Hamida zan je yaya..." Yace "Hamida? Zaki je ko zaki dawo?" Ta ɗan turo baki tace "Zan je dai" Yace "Are you serious?? Since morning baki je gidansu Hamida ba sai yanzu that everywhere is busy? Almost five o clock now" Mayraah ta marairaice tace "Yaya ba dadewa fa zan yi ba" Yace "I see, yanzu kina ina?" Ta ɗan kalli inda take, sai tayi saurin cewa "Nima dai ban sani ba ina cikin adaidaita sahu amma nasan mun kusa, ina amso reading material dina zan juyo, we are having test on Monday" Yace "Ohk, amma baki ga hadari ba?" Ta kalli sama tace "Ba sosai ba, abinda ya ma fara washewa" Yace "Toh Allah ya tsare" Tace "Ameen, Me zaka gaya min ka kirani?" Yace "Wanted telling u kiyi min stirred fried spagh....." Mayraah tayi murmushi tace "Ai dama nasan girki zaka ce in maka, baka taɓa kirana sai in kana son in ma girki, but don't worry yayana idan na dawo zan maka in sha Allah" Yace "Take care, and do not stay long" Tace "In sha Allah" Daga haka ya katse wayarsa, ta ɗan yi jigum kamar me nazari, to ma dai tukunna a ina ma za su hadu da Musharraf ya amshi abincin, ko tambayarsa ma fa bata yi ba ta fito daga gida, sannan bata ma san maganin da zata siyo masa ba tunda bai gaya mata ba, Tana kokarin dialing numbersa sai ga kiransa ya shigo wayarta ta daga ta kai kunne, yace "Where are you?" Tace "Yanzu na fito eatry, wani Drugs zan siya maka?" Nan ya gaya mata drugs da zata siyo tace "Toh, amma ta yaya za a kai maka abincin da maganin? Dispatch rider?" Musharraf yayi shiru jin abinda tace, jin shirun yayi yawa tace "Hello?" Yace "Dispatch ridern zaki ba abincin da zan ci?" Ta ɗan hade rai tace "To ya za mu yi, do u have the strength to drive ka fito ka amsa?" A takaice yace "I don't have" Tace "To ai ni ban san inda kake ba, and beside i can't say...." Ya katse ta yace "I will send u d address of my location" ta buda ido da mamaki tace "Sae na je har can kake nufi?" Shiru yayi, cike da damuwa tace "Am i suppose to come to ur location?" A hankali yace "Toh shikenan ki samu dispatch rider din ki basa magungunan kadai ya kawo min" tace "Abincin fa?" Yace "Bazan ci ba, it is not proper for a dispatcher to deliver my food" Tayi shirun few seconds, a ranta kuwa tunani take, how is it wrong for a dispatcher to deliver someone's food? a hankali tace "Let me get the drugs, sai ka turo min address din location din naka, ina isowa unguwan sai ka fito ka amsa" Yace "Alright tnx" Katse wayar tayi, ta nemi nearest pharmacy ta siya masa magungunan da ya gaya mata, tun kan ta fito pharmacy din address dinsa ya shigo wayarta, bayan ta fito ta samu adaidaita sahu ta gaya masa inda zata sannan ta shiga, nan kuma gabanta ya dinga faduwa, what if ta hadu da any of her family members or relatives? tunanin hakan yasa gabanta ya tsananta faduwa and she became so uncomfortable, sae kusan biyar da minti talatin da biyar suka isa layin, mai adaidaitan yace "Nan ne unguwar Hajiya" Mayraah dake ta bin unguwan that is so quiet da kallo tace "Pls kayi hakuri yanzu zan mika sakon nan sai ka maida ni, ban ga alamar zan samu adaidaita sahu a nan ba" Yace "To, amma kiyi sauri kinga yayyafi ake" tace "To Nagode" Da sauri ta shiga dialing number Musharraf, yana fara ring ya daga, tace "I am at the street, ka fito ka amsa pls, mai adaidaita sahu yana jirana kar mu bata masa lokaci kaga an fara yayyafi" Musharraf yace "Ki basa kudinsa, zan ajiye ki gida" Ta wani zaro ido tace "I don't understand? Kai da baka da lafiya, pls i am going back together with the Tricycle" Yace "I will try and take you back Mayraah, bana son ruwan nan ya taba ki" Ta sauka daga cikin adaidaita sahun don she is not comfortable making call in front of the owner, A bit worried tace "Don girman Allah ka fito ka amshi abincin nan da magani in koma gida, wllh ce ma Ammi nayi zanje gidansu Hamida, da kyar fa ta bar ni, don Allah ni dai tsoro nake ji kar ayi finding out inda na je kayi hakuri ka zo ka amshi abincin in wuce gidanmu" Musharraf yace "Mayraah..." Kamar zata yi kuka tace "Ina ji" Yace "Ki sallami mai tricycle din nan nace, ba ni nace zan ajiye ki gida ba?" Tace "Am sorry I can't, kayi hakuri ka fito ka amshi abincinka in koma gida" Yace "Ohk" daga haka ya katse wayar, ta koma gun mai adaidaita sahun tana basa hakuri, tana ta tsaye jikin tricycle din duk da yayyafi da ake ba me yawa ba, sae ga Musharraf ya fito daga gate din dake opposite dinta, ita bata ma san nan ne gidan ba kawai sun tsaya ne ita da ɗan sahun, tun da ya fito take kallonsa, bata taɓa sanin he is this vast and broad ba sai yau, ko don bata yarda ta kallesa a school ne saboda kunya, bashi da haske a inda take, ma'ana tafi sa haske sosai amma kuma shi ba baƙi bane, duk hancinta kuwa ya fi ta, and he have got a very beautiful eyes with thick eyebrows that one can ever imagine, lips dinsa look so cute on his face, duk a cikin few seconds Mayraah ta kare masa kallon nan kafin tayi saurin dauke idonta, nan kuma taji gabanta na faduwa sosai, har ya karaso inda suke, da kyar tayi karfin halin cewa "Good evening sir, ga abincin da magani, i don't know if you will...." Kasa ci gaba tayi da mamaki ganin kudi yan dubu dubu da bata san nawa bane ya mika ma mai adaidaita sahun yace masa zai iya tafiya, Mai adaidaita sahu bai ko kalleta ba ya fara kokarin reverse da machine dinsa, Mayraah ta kasa cewa komai cause she became so confused and lost of words lokaci daya, da kyar ta kallesa tace "What is the meaning of this?" Yace "Ke baki da aiki sai yin musu da ni ko? ban taɓa ce maki abu kinyi direct ba sai kinyi musu, is that how u will be treating me after the marriage?" Kamar zata yi kuka tace "I told u i lied to my Mother about where i am going to, me yasa baza kayi considering dina ba sir, i did this because i was so worried about you" Shiru yayi yana kallonta, Lokaci daya hawaye ya cika idonta ita ma tana kallonsa, babu abinda ke kara karyar masa da zuciya sae hawayenta duk da Nikab din fuskarta he can see the tears in her eyes, yayi kasa da murya yace "I promise u in just 10 mins time zan maida ki gida Mayraah, i appreciate ur care and concern toward me, the rain is going to make u wet, mu shiga ciki in shirya sai in kai ki gida, kiyi hakuri" Tana goge hawayen idonta tace "I will wait outside, zan jira ka a nan" Yace "Bana son ki kara min musu, since ni nace zan kai ki gida, just do as i say" Yana fadin haka ya juya ya nufi gate din gidan da ya fito, hawaye ya dinga sauka idonta tana bin sa da kallo, nan da nan ta jika Nikab dinta, don ma babu kowa a Unguwan, bayan few seconds ta bi sa zuwa cikin gidan tana shiga gate din gidan ta zauna ɗan dakalin dake kofar dakin da aka yi ma Mai gadi, ya kulle gate din, ita dai sai kallonsa take gabanta na wani irin faduwa, dukawa yayi gabanta yana kallonta a hankali yace "Mayraah kinsan saboda ke na shiga wannan halin da nake ciki yanzu? Throughout yesterday night i couldn't sleep, ban taba shiga damuwa irin damuwar da na shiga daga jiya zuwa yau ba Mayraah, i am so disturbed" Kasa ci gaba yayi, yayi shiru yana kallonta, Maganganunsa suka dinga mata yawo a kai, ya shiga damuwa saboda ita kuma? As how? To me tayi masa? Dage Nikab din fuskarta tayi tana kallonsa for some seconds, can ta marairaice tace "Did i offend you in anyway? Ka gaya min don Allah ko wani laifin nayi maka, me yasa zaka shiga damuwa saboda ni?" Sunkuyar da kansa yayi bai ce mata komai ba, nan taji hankalinta ya kara tashi, cike da damuwa tace "Don girman Allah kayi hakuri ka gaya min sir, wllhi ban san me nayi ba, how did i offend you?" Nan da nan wasu sabbin hawayen suka ciko idonta, Yayi gathering courage, da kyar yace "Baki min komai ba Mayraah, baki taɓa min komai ba, asali ma u are the most nicest, Pious, gentle lady i have ever come across all my life, samun mace irinki sai an tona, i am always proud u accepted me after all the up and downs, ina alfahari da ranan da na fara haduwa da ke, amma ina son ki min wani alkawari Mayraah" Ta zuba masa ido tana kallonsa and he could see the confusion in her eyes, ya kamo hannunta yace "Ki min alkawarin duk runtsi, duk tsanani, no matter d situation no matter what is going to happen baza ki taɓa rabuwa da ni ba!" Mayraah ta kasa cewa komai, ganin yanda ya kafeta da ido tayi karfin halin cewa "Amma ban taɓa cewa zan rabu da kai ba, me yasa kake fadin haka?" Yace "Baza ki gane ba Mayraah, nasan baki taɓa cewa baki sona ba, but ban san ko zaki iya canza ra'ayinki at anytime from now, may be because of pressure or whatever, amma ina son ki sani as far as ni Abdallah ban ce zan rabu da ke ba kuma ban guje ki ba baki da hujjan bari na no matter what, i mean no matter anything Mayraah" Ta sauke idonta tace "I have no intention of leaving you, bani da wannan niyyar, ban taɓa irin wannan tunanin ba, ta yaya zan ce zan barka bayan aurenmu saura yan kwanaki? Me kayi min?" Ya ɗan yi murmushin karfin hali, yayi kasa da murya yace "I know u won't get it right Mayraah, amma ina son kiyi min alkawarin ko kafin bikinmu, ko bayan bikinmu duk wani abu da zance maki zaki amince da shi babu musu" Ta dinga kallonsa tace "Kamar me kenan sir?" Yace "Abun da ya shafi rayuwata da ke, kiyi alkawarin zaki yarda da duk abinda na tsara" Ta sauke ajiyar zuciya tace "Nayi alkawari, i will be obedient in sha Allah, in dai bai saɓa ma mahaliccina ba" Ya dinga kallonta, ta sunkuyar da kanta, A hankali yace "Sannan kiyi alkawarin duk runtsi duk tsanani, muna tare da juna daga this very moment har forever" Ta ɗan yi murmushi tace "In sha Allah" Yace "I love you Mayraah, and nothing can ever change my love toward you" Ta rufe fuskarta kan gwiwanta a hankali tace "Same with me" Yace "Ba ma sai na kai ki kin gaida Mamina ba again, after the wedding zata san ki" Mayraah ta dago tana kallonsa amma bata ce komai ba, yace "Give me just 10 mins yanzu zan fito sai in maida ke gida, nasan baza ki yarda ki shiga parlor ba, i know u have trust issues, kawai ki jirani a parking lot don kar ki jike da yawa" Yana fadin haka ya mike ya nufi cikin gidan ta bi sa da kallo, tasan har ranta tana son Musharraf, amma sai taji kamar yau an kara mata sonsa ne, bata daina kallonsa ba har ya shiga cikin gidan, ta kasa tashi daga inda take zaune duk da ruwan is just drizzling kadan kadan, kamar yanda ya fada bayan minti goma sai gashi ya fito rike da makullin mota, mikewa tayi da damuwa ta nufesa tace "Sir baka ci abincin ba" Yace "Sai na dawo bana son magariba yayi baki koma gida ba, tayi shiru tana kallonsa, ya bude mata motarsa dake parking space yana kallonta, karasowa tayi ta shiga cikin motar ya kulle mata, sai da ya fara bude gate sannan ya dawo ya shiga motar yayi driving dinsa out of the compound, ita dai sai bin sa da kallo take, har ya dawo motar bayan ya kulle gate din suka bar unguwan. Mayraah bata yarda Musharraf ya kai ta har kofar gidansu ba, shi ma kuma bai yi insisting ba, ta bude motar zata sauka kenan ta zaro ido, ta juya da sauri tana kallonsa tace "Nace ma Ammi zan amso handout wajen Hamida, i can't go in without Handout...." Bata rufe baki ba ya juya ya dauko wani material a back seat ya mika mata, sosai hankalinta ya kwanta, ta amsa tace "Thank you" Yana kallonta a hankali yace "Welcome" Bude motar tayi ta sauka tace "Sai da safe sir, Allah ya kara lafiya" Yace "Ameen" Sae da taga yayi reverse sannan ta fara tafiya zuwa kofar gidansu, sosai gabanta ya fadi ganin Usman zaune bakin gate din gidan, ta ma san ya ga saukanta daga motar Musharraf ganin yanda yake kallonta from head to toes, Tana isa gate din yace "Wa ya ajiye ki a mota?" Ta juya ta kalli bayanta taga tuni motar Musharraf ya bar layin, kin ce masa komai yayi, ya mike jin ana kiran magrib yace "Zaki gaya min motar waye bari a idar da sllh" Daga haka ya wuce cikin gida, ta wani tura masa baki ta bi bayansa zuwa cikin gidan, tana biye da shi tace "Yaya gidansu Hamida fa nace, to da ya kirani yaji ina can ne shine dama yana kusa da anguwan sai kawai ya maido ni gida" Usman ya juya yana kallonta, komawa baya tayi da sauri, yace "Yaushe kika koyi karya Mayraah?" Tayi narai narai da ido tace "Yaya i am not lying" Yace "Ohk bari a idar da sallah zan kira Hamidar" Ko damuwa bata yi ba saboda tasan bai da number Hamida, ya tsaya bakin tap dake compound din zai yi alwala ita kuma ta wuce cikin gida, Sai da ta fara zuwa dakin Ammi don sanar mata ta dawo, Aunty Mariya tace "Ai kam kinyi sauri" Ammi tace "Mahir din ne ya dawo da ke?" Mayraah tace "Aa ban ma ce ya zo ya daukeni ba" Ammi tace "Toh ki je kiyi sallah" Juyawa tayi ta fita daga dakin, Aunty Mariya tace "Wai ya batun gyaran jiki, tun fa ana saura wata biyu ake farawa Ammi" Ammi tace "Ni ba sanin yanda ake yi nayi ba, tunda dai Allah ya kawo ki ai sai duk ayi abinda ya kamata" Aunty Mariya tace "Toh naji tana zancen test, kamata yayi ace daga yau ma ta daina fita" Ammi tace "Matakin karshe fa suke yanzu, nan da sati shidda ma nake jin za su fara final exams" Aunty Mariya tace "Toh Allah ya bada sa'a, tare suke da Badiyya ko?" Ammi tace "Eh" Aunty Mariya tace "Kinga ai har yanzu bata zo ta gaisheni ba" Ammi tace "Zata zo" Washegari lahadi throughout Mayraah na daki tana karatu for tomorrow's test don bata son lecturers dinta su sake saka ta gaba, har bayan la'asar tana daki studying her handout, Aunty Mariya ta shigo dakinta tace "Mayraah ki sakko Hajja ta zo tana son ganinki" Mayraah ta mike ta dau Hijab dinta ta saka, ta bi bayan Aunty Mariya, Hajja na zaune parlor an shimfida mata wani carpet din ana ta fiddo mata lefen Mayraah tana ta saka albarka cike da farin ciki, ta ma rasa yanda zata yi don murna, Mayraah ta karasa ta zauna kusa da ita tace "Hajja sannu da zuwa" Hajja ta rungumeta tace "Lallai kin yi goshi Mayraah, Allah Ubangiji ya sanya alkhairi, Allah ya nuna mana na yan baya haka, Allah sa mijinki ne shi har aljanna" Sai a sannan Mayraah ta lura da Badiyya dake zaune kan kujera ta daura kafa daya kan daya kamar yar tasha, tana ta bin kayan da kallo fuskar nan nata babu yabo babu fallasa, wani daci take ji a makogwaronta tsabar hassada, Mayraah tace "Ina wuni Aunty Badiyya" Badiyya bata ko kalli inda take ba tayi pretending kamar bata ji ta ba, Hajja tace "Ke Badiyya, Amarya tana gaisheki" Sai a sannan Badiyya ta ɗan kalli Mayraah tace "Ohk, lafiya" Mai gadi ne yayi sallama dai dai bakin kofar parlon, duk aka daga kai ana kallonsa don baya shigowa parlon yau sai ga shi, wani akwati ne da aka yi yayinsa tun tale tale a lkcn su inna na yan mata ne a hannunsa, kana ganinsa kasan shi ma he is not comfortable shigowarsa parlon, Yana kame kame yace "Cewa tayi sai na shigo mata da shi, bakuwa ce aka yi" Muryar Mama Ladi suka ji tana cewa "To ko dai ba boyi boyin gidan bane? Ya zan baka kayana ka shigar min da shi gida ka dinga nokewa, kasan daga inda nake ne, ku haka ku ke yi a garin nan?" Sosai gaban Ammi ya fadi ta juya ta kalli Aunty Mariya da ita ma tayi shock, Hajja tace "lale lale, muryar wa nake ji kamar ta Ladi" Ladi tace "Ni ce mana yaya, tun asuba na biyo hanya ashe rubabbiyar mota na shiga abu ba arziki in gaya maki, tafiya daya biyu mota ta lalace, tafiya daya biyu ta fara wani ƙara tana hayaki, ni dai nayi ma dreban Allah ya isa, yanda motar take a rube haka shima wani rubabben tsoho ne in gaya maki, mu dai mun yi barka da muka shigo kano lafiya" Badiyya ta mike da sauri ta tafi ta rungume Mama Ladi cike da murna tana cewa "Sannu da zuwa Mama" Mama Ladi tace "Yauwa sannu Badiyya, ina Mashir din da na zo bikinsa?" Hajja na nuna Mayraah tace "Ai har da na Mayraah, amarya ne da ango ai a gidan" Mama Ladi tace "Wacece kuma Mayraah?" Mayraah na murmushi tace "Sannu da zuwa Mama" Tuni Ammi dake ta kirkiran Murmushi ta mike tace "Kin sha hanya Mama Ladi, sannu da zuwa..." Amsan Handbag dinta tayi tana kallon Aunty Mariya tace "Mariya maza yi mata shimfida a dakin can, ki kunna mata ruwa a bandaki..." Mama Ladi tace "Aa ni dakin saman bene za a kai ni in zauna" Ammi tace "To bismillah Mama Ladi" Sama ta nufa Mama Ladi na kallon Hajja tace "Bari in watsa ruwa in dawo mu gaisa yaya" Daga haka ta bi bayan Ammi, amma ta kasa hawa benen saboda ciwon kafa, Aunty Mariya tace "Kinga kasa zai fi maki fa Mama Ladi" Mama Ladi tace "Babu ruwanki" a haka ta daure ta fara hawa benen tana yi tana hutawa, sai da hawa benen ya dauketa kusan minti sha biyar..... 07087865788 WhatsApp only..... [6/3, 3:16 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖 _By khaleesat Haiydar_✍🏻 9..... Aunty Mariya na kallon Hajja tayi kasa kasa da murya tace "Don girman Allah Hajja in zaki koma gida kice mata ta bi ki ku tafi, kin dai san halin Mama Ladi" Hajja tace "Haba ai kwa bari ko kwana daya tayi ko Mariya, hanya fa ta biyo tun asuba" Aunty Mariya tace "Wllh tana wuce yau a gidan nan ina me tabbatar maki babu inda zata je har sai an gama bikin nan Hajja, ke kadai ce zaki gaya mata taji, kice mata baƙi sun fara yawa a nan kawai ta fito ku tafi gidanki" Hajja tace "Toh amma dai za a bari tayi wanka ta ɗan huta ta ci abinci tukunna ko?" Aunty Mariya tace "Aa dama ai sai ta ci abinci Hajja, ba yanzu nake nufi ba, ba sai in Maheer zai maida ke gida sai ki mata dubara ki tafi da ita" Hajja tace "Toh babu damuwa" Aunty Mariya ta mike ta wuce kitchen don hada ma Mama ladi abinci, mikewa Mayraah tayi ta wuce sama, Hajja na kallon Badiyya dake danna wayarta tace "ke sakko ki karasa zuge akwatin sarkokin nan kada wani abu ya ɓata masu a shiga uku, da ganinsu kasan masu tsada ne, basu yi kama yan kasar nan bane" A takaice Badiyya tace "Ban ga zan iya ba" Hajja ta buda baki tana kallonta, can tace "Toh Allah ya baki hakuri, abinda dai da yatsuna ni ba kuturwa ba, ai ni sai in rufe meye a ciki" Tana fadin haka ta mike tana kokarin rufe akwatin da kyau, Hajja ta ci gaba da cewa "Wani ma ba sai yace hassada kike ma kanwar taki ba, ji fa tun da ake bude kayan nan babu wanda kika yaɓa a ciki balle kice Allah ya sanya alkhairi kema Allah ya dora ki a danshinta, sai wani nukurci da murtuke fuska kike, wannan dai ba yi bane in gaya maki gaskiya, in zaki canza halin ki tun wuri ki canza wllh" Wani fitsararren kallo Badiyya ke ma Hajja kamar zata rufeta da duka, Hajja dai ko damuwa bata yi ba, ta koma ta zauna tana cewa "Dama duk wanda ma zai zo ba sai an sake fito masa da Gwal din ba, ido ba kyau, gwara a fada da baki ace gashi an sa gwal kawai shikenan...." Nan da nan facial impression din Badiyya ya canza jin Hajja ta ambaci gwal, gwal? Wato har da gwal a lefen, Hajja ta ci gaba tana cewa "Gwara a adana sa kawai, kar a sake fitowa da shi, ba a san zuciyar wani ba" Badiyya ta hadiye wani abu da kyar, tana sake bin duk akwatunan da kallo, yanzu har da gold cikin akwatin nan wai? Hajja ta kwalo ma Aunty Mariya kira, Aunty Mariya ta fito daga kitchen tace "Gani Hajja" Hajja tace "Dama cewa nayi kar a kuma fito da gwal din nan a nuna ma kowa don Allah" Aunty Mariya tace "Haba tun ranan da aka kawo kayan ba a sake fitowa da shi ba sai yau da kika zo ai Hajja" Hajja tace "To da kyau, hakan yafi, amma sai nake ga bai ma kamata a bar sa a akwatin ba, wani fa ba don Allah yake zuwa ganin kayan ba sai don ya tafka halin bera" Aunty Mariya tace "Ai ba ciki suke ba dama, na kai sama yana cikin jakata tun ranan, zuwanki ne yasa na fito da shi" Hajja tace "Toh madallah, gwara haka" Juyawa Aunty Mariya tayi ta koma kitchen, Ammi ta sauko downstairs tana kallon Badiyya tace "Badiyya tafi kitchen ki hado ma Mama Ladi shayi, tace shayi da kwai da bread zata ci, akwai full bread a kitchen ba a taɓa ba, sai ki soya mata kwai hudu, Madara da Milo kuma ki kai mata gwangwanin gaba daya, tana nan dakin Mayraah" Badiyya ta mike tace "Toh" Hajja tace "Banda abun Ladi cikin zafin nan me zata yi da shayi kamar shugaban mayu, ga dai tuwo da taushe me kyau anyi nima har na ci" Ammi tace "Gwara dai a kai mata, idan ya so anjima sai a kai tuwon" Badiyya ta nufi kitchen ta sanar ma Aunty Mariya abinda Ammi tace, Aunty Mariya tace "Ita kuma me zata yi da shayi da ranan nan haka?" Badiyya dai bata ce komai ba ta kunna gas zata daura ruwa, Aunty Mariya tace "Toh sai ki soya mata kwai, anjima idan za su tafi sai a zuba mata tuwon a Warmer su tafi da shi" Daga haka ta fice daga kitchen din, Badiyya har ta mance yaushe rabon ta kunna gas, kullum Hajja ce ke masu girki a gida, hatta ruwan zafin nan idan tana bukata yana cikin flask zata tarar Hajja ta cika mata dam, don haka babu hadinta da gas, ta bude fridge ta fiddo kwai hudu ta fasa, ta dau maggi cube biyu ta marmasa a ciki, ta saka gishiri, sai kuma ta dinga kalle kallen kitchen din tana tunanin sai kuma me za a saka a kwan? Ta nufi inda taga Scotch bonnet da albasa ta dau wuka ta fara yanka albasan, da kyar ta gama yankawa don sai hawaye take kamar an buda pampo alamar rashin sabo, ta zuba tarugun manya uku a blender da albasan ta markada su sannan ta juye a kwan ta kada da kyau, tunawa tayi bata sa curry ba tayi maza ta fara duba inda curry yake a kitchen din har ta gani sannan ta zuba a kwan, ta kara beating dinsa, minti biyar ta dauka tana soya kwan, sai da taga kamar konewa yake yi ta maza ta juye a plate, cikin few minutes ta gama hada komai a katon tray sannan ta fito daga kitchen din, Aunty Mariya tace "Sai kace me soya kwai crate daya Badiyya" Badiyya bata ce komai ba ta wuce sama tana murguda baki, tana shiga dakin Mayraah ta tarar da Mama Ladi zaune kasan carpet tana ta mulka Vaseline a jikinta da fuska, sai wani naso take kamar an tsomata a man gyada a fiddo, Mama Ladi tace "Sannu er nan, Allah maki albarka har da kwan aka soyo ko?" Badiyya tace "Ehh bari in dauko gwangwanin Madara da Milon" Mama Ladi ta washe baki tace "To yi maza" Badiyya na fita ba a dau lokaci ba ta dawo ta ajiye ma Mama Ladi gwangwanayen sannan ta zauna gefen gado tana kallonta tace "Wannan Vaseline din da kika lafta fa Mama Ladi?" Mama Ladi tace "To ai ji nayi kamar hunturu kar inje in fara bushewa kamar an tono ni a rami..." Badiyya tayi dariya tace "AC fa aka kunna maki ba wani hunturu ake ba" Mama Ladi tace "Au too, ni dai naji sanyi ba kakkautawa sai nayi zaton hunturu ake a nan" jawo cup tayi ta fara hada shayin, Badiyya ta dawo kusa da ita tayi kasa da murya tace "Mama Ladi kinsan me naji Aunty Mariya na ce ma Hajja?" Mama Ladi ta kalleta da sauri tace "Aa" Badiyya tace "Wllh wai ce ma Hajja tayi don Allah in zata tafi ta tafi dake gidanta su baza su iya da halinki ba gaskiya" A hankali Mama Ladi ta ajiye flask din hannunta tace "Ita Mariyar ce tace haka a kaina?" Badiyya tace "Wallahi, nufinta ke fitinanniya ce baza ki zauna masu a gida ba Hajja ta tattara ki ta tafi dake idan zata koma gida anjima, amma fa bana son ki ce masu komai, kawai dai idan Hajja tace ki tashi ku tafi kice mata a'a ke gidan biki kika zo babu inda za ki" Mama Ladi tayi mitsi mitsi da ido tace "Ka ji shegiyar da naci kashinta na ci fitsarinta, a lokacin fa gashin kanta yanda kika san hammatan ɗan iska ba kyan gani, gashi bata da aiki sai kirba kashi a wando ta bar ni da wanke mata, shine take fadin haka yau a kai na? Ni Mariya take cewa a kora a gidan nan sabida ta auri ɗan gwangwan ya kai ta makka?" Badiyya ta fara zare ido tace "Don Allah ni dai kiyi shiru, sirri na zo na gaya maki fa kina neman aji a waje, sannan na riga na gaya maki amsan da za ki basu idan Hajja tace ki bi ta, shikenan kawai ki bar zancen, don Allah kar ki ce na gaya maki wannan maganar Mama Ladi" Mama Ladi ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Sai kace wata yarinya zan ce ga abinda kika gaya min, ki tafi kawai ki hada min shayin, madaran cokali shidda zaki zuba min haka nake sha a gida" Badiyya ta hada mata shayin ta ajiye a gabanta, Mama Ladi ta yanko kwai ta kai baki, tana fara taunawa ta maza ta tofar kan farantin tana yamutsa fuska a gigice tace "Wani azzalumin ne ya min suyan kwan nan?" Badiyya tayi tsuru tsuru tana kallonta, Mama Ladi ta mike tace "Na shiga uku na lalace, Badiyya wace shegiyar ce ta soya min kwan nan a gidan nan?" Badiyya ta ɗan daure fuska tace "Me ya samu kwan ne wai?" Mama Ladi tace "Ki ɗan dana ki ji mana er nan, ga uban gishiri ga yaji, wacece tayi min wannan aika aikan, ko dai Mariyar ce?" Badiyya ta ɗan tabe baki tace "Me aikin gidan ce" Mama ladi tace "Mu je ki nuna min ita, to ko dai Mariyar ce ta sa ta tayi min wannan walakancin?" Badiyya ta zaro ido tace "Na shiga uku, don girman Allah ki rufa min asiri Mama Ladi, kar fa kije kice masu ga abinda nace in shiga uku, ke ba a sirri dake ne?" Mama Ladi tace "Yo ni ina ruwana da abinda kika zo kika gaya min, ki ɗan dana kwan nan kiji don Allah" Ammi ce ta shigo dakin tace "Kin idar Mama Ladi" Mama Ladi ta fashe da kuka tace "Ammi taho ki ga abinda mai aikinki ta soyo ta kawo min saboda ta ga ni ba er birni bace, amma abinda bata sani ba nima ai a birnin aka haifeni" da mamaki Ammi tace "Me aiki kuma, Badiyya ce fa na sa ta hado maki shayin ta soya kwan Hajja" Mama Ladi ta juya tana kallon Badiyya da mamaki, Badiyya ta wani dauke kanta, Mama Ladi ta rike haɓa tace "Ke a haka kike son ki kwace ma yarinya saurayi ko girki baki iya ba goɗe goɗe da ke? Idan ba mantawa nayi fa da shekara biyu ko daya Mashir ya girme ki, amma ace guzuma irinki baki iya sarrafa kwai ba, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to kinyi ma kwai wannan azababben suyan ina ga idan girki za ki yi me gaba daya? Aa Hajja ta cuce ki, me za ayi da mace da bata iya girki ba sai kwalliya a fuska a wannan zamanin, shi saurayin Meran me zai yi da warce bata iya girki ba?" Ammi dai na tsaye ta kasa cewa komai, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "Wallahi baki ji kwan ba kamar ba kwai ba Ammi, ni na zata flawa ce aka lafta ma tarugu da maggi da gishiri, ko sati biyu fa ba ayi ba matar nan taje har karaye ta sameni tana kuka wiwi wai Mera ta kwace mata saurayi gashi har za ayi aure kuma babu wanda ya dau mataki a kai kowa ya goyi bayan Mera, wllh ina ta tausayinta nace amma kun ci amanar Rukayya, kuma idan baku yi hankali ba sai wuta ta ci ku, har na kullaci Meran dazu tana gaisheni nayi mata banza ashe masharanciya ce Badiyya ban sani ba, nasan da Mera aka saka wannan suyan da tuni na kusa cinyewa ina neman kari, aa gaskiya Hajja ta cuci Badiyya, kuma nayi da na sanin goya mata baya da nayi da taje wajena" Mikewa Badiyya tayi ta nufi kofa fuuuu ta fice daga dakin kamar zata tashi sama, Mama Ladi tace "Muguwa kawai, Mijin Mera sai gani sai hange tunda ke makaryaciya ce warce bata iya girki ba" Ammi dai ta rasa ma me zata ce, wato karya Badiyya ta musu ta tafi bichi ashe Karaye ta tafi wajen Mama Ladi, Mama Ladi ta koma ta zauna tace "Gaskiya a fitar min da wannan azaban a kira Mera ta soya min kwan da zan iya ci" Ammi ta sunkuya ta dau plate din kwan tace "Kiyi hakuri Mama Ladi, yanzu za a kawo maki wani" Mama Ladi tace "Hakuri ai ya zama dole, munafukar yarinya wai Mera ta kwace mata saurayi, wani saurayin arziki ne zai aureta bata iya girki ba, wanda bai iya soya kwai ba ai babu abinda zai iya kuma a rayuwarsa har ya mutu" Ammi dai ta fita daga dakin. Bayan la'asar Hajja ta tafi sama har zuwa dakin Mayraah wajen Mama Ladi, Rabon Hajja da haurawa saman gidan zai yi shekara bakwai, tun wani rashin lafiya da Ammi tayi, Hajja na tsaye bakin kofa bayan ta shiga dakin tace "Ke Ladi tashi zaki yi tunda kin huta mu tafi gidana don nan baƙi yawa za su yi zuwa nan da kwanaki kadan, gwara mu je inda zaki sake babu takura" Mama Ladi dake kishingide jikin pillow tana sakace hakora bayan ta ci kaza tayi nak tace "Ko yaya?" Hajja tace "Kwarai kuwa, kinga ni ma gida zan tafi Maheer zai ajiye ni yanzu" Mama Ladi tace "Toh shikenan, a kira min Mariya ta zo ta dau min akwatina mu sauka kasa akwai dukiyana a ciki bazan ba yara ba gaskiya" Hajja tace "Toh bari in mata magana" Hajja ta juya ta fita, bayan wani lokaci sai ga ta ta dawo tare da Aunty Mariya, Hajja tace "Akwatinta zaki dauka a saka mata a mota za mu tafi gida" Aunty Mariya ta shigo dakin da sauri ta nufi inda akwatin yake ta duka zata dauka Mama Ladi tace "Munafuka algunguma wato daukar akwatin zaki yi, to babu inda zanje ina nan tunda ba gidanki bane balle na mijinki, har zaki je ki wani ce ma Hajja ta lallabani ta tafi da ni tunda gani barbadaddiya, to ina nan har sai an gama biki tunda ba wajen Hajja na zo ba, ke har kin manta irin azabar da kika min kina yarinya da zaki dinga kakkabi da ni? To wallahi babu inda zan je, ai ba gidanki na zo ba, babu wanda ya isa ya hanani zama gidan nan har sai bayan biki" Aunty Mariya was sooo shock, don kasa motsawa tayi a inda ta duƙa, Hajja tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wannan wani irin magana kike Ladi, a ina kika ji wannan maganar haka?" Mama Ladi tace "Badiyya ce ta zo nan ta gaya min, kuma wllh bazata maku sharri ba ji tayi an fada ne, in dai an ga na bar gidan nan to Mamuda ne ya koreni, amma ita kanta Ammin tayi kadan Al-qur'an, ai bikin jikokina biyu na zo Mera da Mashir" Tana kai wa nan ta juya masu baya ta ci gaba da kwanciyarta, Hajja dai ta kasa cewa komai balle Aunty Mariya da ta kasa dagowa kamar kasa ya bude ta shige, Ammi da ke kokarin shigowa dakin dama a kan kunnenta aka yi komai, ta juya sum sum sum ta bar wajen ba tare da ta bari an ma san tana wajen ba.... Hajja na saukowa parlor ta dau er jakarta tace "To da Alkhairi na tafi gida ni kam" Ammi dai na zaune kan kujera banda dariya babu abinda take, sai ga Aunty Mariya ta sauko kasa kamar wanda ruwa ya cinye tace "Wallahi wallahi sai na yi ma Badiyya abinda bata taɓa tunani ba, ba tace ita magulmaciya bace munafuka, Ni zata je ta hada da wannan matar?" Hajja tace "A dai dinga tunawa marainiya ce" Daga haka ta bar masu parlon, Nan Aunty Mariya ta hau shiga dakunan gidan ranta a bace tana neman Badiyya, Sabira tace "Ai Aunty Badiyya ta bar gidan nan tun dazu fa Hajiya" Musharraf yayi parking kofar gidansu wajen karfe shidda na yamma zai shiga ya gaida Mami don bai da intention din kwana a gidan ranan, throughout today wayarsa a flight mode ya bar sa yasan Mami ta nemesa har ta gaji, balle kuma Mayraah, duk yau ita ma basu yi magana ba, yanzun ma da ya taho gida ba kunna wayar yayi ba still, kawai baya son Mami ta daga hankalinta ne, Yana sauka motar ya nufi gate din gidan, ya amsa gaisuwan da Mai gadi ke masa without looking at him, zai shiga ciki Mai gadin yayi kasa da kai cike da ladabi yana biye da shi yace "Yallabai an samu akasi fa" Musharraf ya juyo da sauri yana kallonsa yace "Akasin me?" Mai gadi yayi kasa da murya kamar munafuki yace "Wallahi dazu Hajiya za su fita da Dreba sai ga dai wannan mutumin da ya kawo takardan nan wancan ranan...." Musharraf ya katsesa a rikice yace "Sai me ya faru??" Mai gadin da har ya tsorata ya fara kame kame, a fusace Musharraf yace "Malam ka gaya min ya aka yi??" Mai gadin yace "Wallahi a kan idonta mutumin ya bani irin wannan takardan na ranan nan, don dreba ya fito da motar kenan daga cikin gidan za su tafi... Shine Hajiya ta sauke gilashin mota ta amshi takardan a hannuna, kaga ai bazan ce mata a'a ba ranka shi dade" Musharraf da yaji wani zufa na keto masa yace "Ita da waye a motar??" Mai gadin yace "Aa ita kadai ce, ina jin Check up zata je" Musharraf bai sake sauraronsa ba ya shige cikin gidan da sauri, cikin few seconds sai ga shi a parlor, babu kowa a parlon ya haura zuwa bangaren Mami, a parlonta ya sameta da mai aikinta dake shiga tayata hira a kai a kai, Mai aikin ta mike ganin Musharraf ta gaishesa da ladabi sannan tayi ma Mami sallama ta fita, Musharraf yayi kokarin calming kansa down yana kallon Mami dake kallonsa ita ma, A hankali yace "Good evening Ma" Mami ta sauke idonta daga kallonsa tace "Evening, me yasa ka kashe waya tun safe?" Ya zauna saman kujera zuciyarsa bai daina bugawa ba yace "Ina hutawa ne yau" Mami tace "Okay" Daga haka ta mike ya bi ta da kallo gabansa na mugun bugawa, bedroom dinta ta shiga sai ga ta ta dawo rike da Envelope a hannunta tana kallonsa, kadan ya rage Musharraf bai samu heart attack ba a lokacin, don sai da yaji komai nasa ya tsaya for some seconds.... A gigice Aunty Mariya ta shigo dakin Ammi tana kallonta tace "Ammi dama baƙi na shiga dakin Usman ne?" Ammi da lokaci daya hankalinta ya tashi ganin yanayin kanwar tata ta mike tace "Me ya faru Mariya?" Aunty Mariya da zufa ke karyo mata tace "Kinsan a dakinsa na ajiye jakata da akwatina tun ran da na zo..." Ammi tace "To me ya faru? Ai babu wanda yake shiga dakinsa a gidan nan sai Maheer shima ba ko da yaushe ba" Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku Ammi ban ga zinarin akwatin lefen Mayraah da na saka a handbag dina ba na kai dakin dazu bayan da aka nuna ma Hajja" Sosai gaban Ammi ma ya fadi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aunty Mariya ta kasa ci gaba da tsayuwa ta zauna gefen gado tace "Yanzun nan na shiga dakin zan dau kudi a jakar naga babu kudin, kusan dubu talatin, nan na duba inda na ajiye zinarin da sauri, naga wayam babu an dauke har shi" Tana kai wa nan ta fashe da kuka sosai, Ammi tsabar confusion ta kasa cewa komai, Aunty Mariya ta mike ta fice daga dakin tana kuka tace "Waye ya mana wannan aika aikan...." *Start making ur payment before the end of free pages fans, kar a ji ni shiruuuu* 07087865788✍🏻 WhatsApp only [6/4, 7:47 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖 _By Khaleesat Haiydar_✍🏻 10..... Mikewa Musharraf yayi ya amshi Envelope din hannun Mami ya dake yace "What is it for?" Mami tace "Ka duba" Tana fadin haka ta zauna saman kujera tana kallonsa, a hankali ya ciro takardan cikin Envelope din ya warware yana karanta rubutun jiki, same content ne da wancan da aka fara kawowa, sai dai wnn an kara abubuwan da suka linka na farkon tsayawa a rai, Musharraf ya kalli Mami dake ta kallonsa babu ko kiftawa, zaunawa yayi side dinta yayi kasa da murya yace "And did you believe this Mami?? ke kin yarda da wannan takardar?" Mami dai kallonsa kawai take, can tace "Uhnn abun ne ai da mamaki da daure kai" Musharraf ya mike a fusace yace "Mami i swear to God wannan ba komai bane facce sharri, karya da hassada, daga ganin wannan rubutun kasan mahassadi ne yayi sa, beside dama ai babu wani auren da baya zuwa da kalubale barin idan shaidanu suka cika lamarin from every angle, all i know is that, koma wani mara aikin yi ne ya turo da wannan saƙon to yayi a banza, babu abinda hakan zai canza...." A hankali Mami tace "Musharraf" Kallonta kawai yake bai ce komai ba, Mami tace "Akwai abubuwan dubawa a lamarin nan...." Da mugun mamaki yace "Mami so u believe all this?" Mami ta girgiza kai tace "No ba wai nace maka na yarda bane my dear, kawai dai ina gudun abinda zai je ya dawo ne, this isn't a minor issue, sannan babu wasa a zancen aure don abu ne da ake son ayi sa na har abada...." Bai kuma ce mata komai ba ya bar parlon kamar zai tashi sama ya wuce dakinsa Mami ta bi sa da kallo, mikewa Mami tayi ta bi bayansa, bayan ta shiga dakin nasa tana kallonsa tace "Look Musharraf, bana son ka daga hankalinka, pray hard about it, Allah Ubangiji ya tabbatar mana da Alkhairi, and i pray this should be between me and you, ba sai kace ma kowa komai ba, Allah ya daura mu kan makiyanmu, no need to disturb ur self, i gat ur back" Musharraf ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, dama yasan Maminsa bazata taɓa juya masa baya ba, duk abinda yace mata ba haka bane, ita ma a hakan zata tafi a ba hakan bane, bata son komai yayi stressing din mata son dinta, because she loves him so dearly, he always reminds her of her late husband, shi yasa take jin sa har cikin ranta, and she can go any extent for him, mikewa Musharraf yayi ya kamo hannunta yace "Thank you for always believing in me Mami, and i appreciate ur support always" Ta sakar masa murmushi tace "Anything for you sweetheart" Ammi ce zaune dakinta sai Aunty Mariya da har a sannan ta kasa daina hawaye da ta tuna a hannunta zinarin nan yake aka sace sai ta kara rushewa da kuka, Maheer ma na tsaye dakin ya ma rasa abinda zai ce bayan Ammi ta kirasa ta gaya masa abinda ke faruwa, Ammi ta kalli Aunty Mariya tace "Wai baza ki rabani da wannan kukan da kike ba Mariya?" Aunty Mariya ta kara fashewa da kuka tace "Dole inyi kuka Ammi, ni fa aka ba abun nan a hannuna, kowa yasan ni aka ba ajiya, yanzu ta ina zan fara fisabilillahi? Waye yayi mana wannan aika aikan? sarkan kusan miliyan biyar, na shiga uku na lalace" Maheer yace "Yaushe Badiyya ta bar gidan nan?" Duk suka daga kai suna kallonsa, Aunty Mariya tace "Babu wanda tayi ma sallama kawai nemanta aka yi ko sama ko kasa" Maheer yace "To ita ta dauka" Ammi ta zaro ido tare da dafa kirji tace "Ka rufa mana asiri kada Hajja ta tsine mana Maheer, ta yaya zaka ce Badiyya ce ta dau zinari?" Aunty Mariya tayi shiru tana nazarin abinda Maheer yace, dazu fa da Hajja ta Kirata tana mata maganar zinarin Badiyya na zaune parlon, daga ita sai Hajja a parlor, kuma throughout today babu baƙin da suka hau sama banda Mama Ladi, Aunty Mariya ta mike tace "Wallahi babu tantama ita ce, don babu wani visitor da ya haura sama duk yau, Mama Ladi kuwa ko motsawa bata yi daga dakin Mayraah ba har yanzu" Aunty Mariya ta figi Hijab din Ammi zata fita, Ammi ta rikota tace "So ku ke ku jawo mana tashin hankalin da bashi da ranan karewa ne Mariya? Ta yaya za ace Badiyya ce ta dau zinari bayan ba ita kadai bane a gidan nan?" Maheer ya kalli Aunty Mariya yace "Ai kin ji irinta, ban san me yasa Ammi take haka ba, kuma wllh yanzu zan tafi gidan Hajjan duk inda Badiyya ta kai zinarin nan sai ta fito da shi wallahi idan ba haka ba in kakkarya yar iska" Aunty Mariya dake huci tace "Tare za mu tafi Maheer, sai dai duk abinda zai faru ya faru yau, idan ba tasan ta aikata rashin gaskiya ba ta yaya zata sidade ta gudu ta bar gidan ba wanda ya sani, yarinya shaidaniya kawai bayan gulma da munafurci ashe har da halin bera duk tana yi?" Ammi da hankalinta yayi mugun tashi ta fashe da kuka tace "Ni dai duk wanda ya fita da sunan zuwa gidan Hajja ya samu Badiyya da zancen zinari ban yafe ba koma waye" Daga Maheer har Aunty Mariya haka suka tsaya kallonta, Maheer yace "Toh Allah ya baki hakuri Ammi, yanzu dai gold din nan zai yi miliyan 5 ko ma fin haka, kuma babu ta yanda za a kai Mayraah gidan mijinta babu wannan gold din tunda su suka saka a lefe, don haka sai a san yanda za ayi" Ammi na goge hawayenta tace "Ba komai, ai anyi hotonsa a waya, Zan sa a shiga kasuwa a duba min sak irinsa, Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi" Maheer ya juya ya fice daga dakin, Aunty Mariya ta bi bayansa. Aunty Mariya ta bi Maheer har zuwa dakinsa ta kulle kofar, a fusace Maheer yace "Kinga exactly abinda kika gani yanzu Aunty? To kullum a haka ake, kwata kwata Ammi bata son ace Badiyya tayi laifi balle a hukuntata, idan kayi magana tace bata son Hajja ta kullaceta ne saboda wasu dalilan da ta bar ma kanta sani, Hajja bata da aiki sai lakaba ma Badiyya maraici wanda wannan mentality din ya riga ya makale a kwakwalwar yarinyar yanzu, an lalata mata rayuwa kawai, babu wanda ya isa ya hanata ko ya sa ta, iskancinta take zubawa yanda ta ga dama...." Aunty Mariya da zuciyarta ke tafarfasa tace "Ai kaga Malam Bahaushe sai Allah kawai, da mutum ya rasa iyayensa ko makamancin haka sai ayi ta binsa da wai maraya ne shi, wanda wnn kalmar ba karamin tasiri yake a zuciyar yaron ba, yayi ta amfani da shi yana iskancin da ya ga dama, dama shi Maraya saboda iyayensa sun mutu sai aka ce a sangartasa har a bar sa ya lalace?" Maheer ya zauna gefen gado yace "Toh baki samu labari bane kwanaki har cewa tayi ita idan ba lecturer din da ke neman Mayraah ba to ita fa sai dai ta mutu, tayi ta iskanci iri iri a period din Ammi da Hajja na biye mata, infact i am fed up with all this wllh, har bana son a nuna Badiyya a kirata da er uwata saboda mugun halinta da yayi tsamari, yanzu ai ya ci ace tana da tsayayye ita ma tayi auren nan, amma babu ko daya, kullum sai dai wannan ya zo ya dauketa a mota ya dawo da ita, wancan ma ya zo ya dauketa ya dawo da ita a gidan Hajja, kuma Hajja bata da bakin magana don rufeta da fada take kamar zata mata duka" Aunty Mariya tace "Yanzu dai ba Ammi tace taji ta gani kar a ma Badiyya magana ba ita zata siyo wani gwal din? To ai shikenan, ko ba komai ni dai hankalina ya kwanta" Tana kai wa nan ta fice daga dakin.... Haseenah ta rike haɓa tana kallon Badiyya tace "Yanzu ke baki ji tsoron wannan abun da kika aikata ba Badiyya? Kilan ba ana can gida ya hautsine ana neman zinarin nan" Badiyya tayi wani dariya hade da taɓe baki tace "Kuma babu wanda ya isa yace ni ne don Hajja kadai ta ishesu wllh" Haseenah tace "Gold din nan fa zai yi miliyan hudu kila Badiyya" Badiyya ta hade rai tace "Ni dai in zaki hada ni da masu siyar da Gold da kika sani a kasuwa ki hadani in kai abun nan su bani kudina, waye zai san na sata ne gwal din idan ba fada aka yi ba tunda dai ba waya bace balle ace za ayi tracking, kawai ce masu zaki yi Mummynki zata siyar amma reciept ya ɓata tunda kince sun saba ciniki da ke" Haseenah tace "Ai ni tsoron abinda zai je ya dawo nake Badiyya, what if daga karshe suka gano na sata ne in one way or the other kuma gashi nayi involving Mummy a ciki, kin fa san halinta" Badiyya tace "Wallahi ke shegiyar matsoraciya ce Haseenah, babu wanda zai tsaya wani bibiyan zinari, abun nan fa family issue ne su kansu baza su so ya fita waje ba, kuma Hajja bazata bada chance din da kowa zai zargeni ba, haba sai kace baki san Hajja ba" Haseenah tace "To nawa zaki bani a ciki yanzu don nasan halinki da kudi, dama in bai min ba to wllh bazan yi hanyar siyarwa ba" Badiyya ta gyara zama tace "Ai wllh kin fi ni son kudi Haseenah nawa ne kawai ya fito fili, yanzu dai in sun siya miliyan hudun da kike ta cewa zan baki 500k a ciki" Haseenah tace "Kan uban can, to ai ni ba er iska bace, ungo abinki kije ki siyar da kanki" Badiyya ta mata wani kallo, can ta kyabe baki tace "To naji zan baki 1M in dai miliyan hudun aka siya, in basu siya haka ba to wllh bazan baki haka ba, ai ba wani ya sato min ba" Haseenah tace "Za ma su siya hakan, wnn fa da kyar in bai yi gram 45 zuwa hamsin ba" Badiyya dai sai murmushi take, Haseenah tace "To wai yanzu kina nufin kin hakura Mayraah ta auri Lecturer din naku tunda kin tsira da gold?" Badiyya ta mata wani kallo tace "Na hakura?? Ashe ban cika Badiyyar ba kenan, wllh Haseenah in kika ga anyi auren nan to faduwa nayi na mutu murus, amma ina me tabbatar maki baza ayi auren nan da Mayraah ba matsawar in numfashi, ba boka ba Malam" Haseenah tace "To sai da ke za ayi auren kenan?" Badiyya tace "Aa ban ce da ni za ayi ba, ba sai an samu an lalata auren ba kafin in cusa kaina? Ai yanzu lalata auren shine babban aiki tukun... Akwai maganganu da yawa da nake son in gaya maki amma sai bayan naga an fasa auren don bana son soyayya dadi ya kwashe ki kije ki gaya ma Maheer ba tare da kinsan kin yi ba" Tana kai wa nan ta mike tace "Kin ga akwai wani gida da muke son zuwa yau din nan, mun fi sati muna kokarin gano gidan sai dazun nan da safe Allah ya sa aka gano, Haseenah tace "Wani gida kenan?" Badiyya tayi wani murmushi tace "Duk za a baki labari kwantar da hankalinki kawata, gidan ma ba daya bane ba biyu, gidaje kusan hudu ne, wallahi na kashe yafi dubu dari biyu wajen neman gidajen nan, yanzu haka bani da ko sisi a account dina, shi yasa nayi mugun farin ciki da samun gwal din nan" Haseenah na jijjiga kai tace "Baddieeeee" Badiyya ta wani juya tana dariya tana kas kas da chewing gum tace "Say it louder" Haseenah tace "Ai baki sani ba, ko da ace baki samo gold din nan ba na shirya daga dubu dari zuwa sama in baki contribution in dai akan ki lalata auren Mayraah ce, i will support u 100%, baki ga kullum follow up nake kan issue din nan ba, ai ba kiran banza nake maki ba kullum inji yanda ake ciki, A whole me fa Haseenah yarinyar da a haihuwan kaji na haifeta tayi ma walakanci of the highest order a gidansu daga wai an kai ni in gaida uwarta, ai har yau da wannan abun nake kwana nake tashi yayi min mugun ciwo wllh, sannan har Maheer zai iya daukan gaba da ni a kanta for days, Wallahi ko da wasa bayan aurenmu da Maheer wataran ta shirya tace ta zo wajen yayanta sai na mata abinda har ta koma ga Allah bazata manta ba kuma a gaban yayan nata, babu kuma abinda ya isa yayi wllh" Badiyya tace "Ke naki duk me sauki ne Haseenah, bari in je Baddo na ta jirana tun dazu, duk yanda ku ka yi da masu siyar da gold din ki kirani ki gaya min" Haseenah tace "In sha Allahu" Daga haka Badiyya ta fice daga dakin Haseenah, mayafi babba ta yafa yau gudun fadan Maman Haseenah don matar ta fiye takura a cewarta. Yau Wednesday Mayraah na class suna rubuta test din wani lecturer dinsu, invigilators sun kusa hudu a ajin suna invigilating dinsu, suna shiga da some minutes Mayraah ta gama answering questions dinta duk da mugun wahalan da question din suka yi, Badiyya na class din sai satan amsa take a tsorace ta cikin wayarta da ta cusa a cinyarta, kamar daga sama taji ance "Stand up" duk ta gigice har sai da wayar ya fadi kowa ya juya yana kallonta with shock a class din, lecturer din da ya kamata ya duka ya dau wayar sannan ya kwashe script dinta yace "Get out" Juyawa tayi da sauri ta fice daga class din duk aka bi ta da kallo, Lecturer din yace "You will come back for this course in sha Allah, so let me see weda u will have another partner" Masu kokarin satan amsa dama duk suka shiga taitayinsu aka yi jigum, lokacin submitting nayi Mayraah ta mike ta taje ta yi submit din nata sannan ta fita daga class din, fita tayi outside the department don taga ko Dr Musharraf ya zo makarantar amma bata ga Motarsa a parking space ba duk da tasan monday da Tuesday kadai yake zuwa kuma week din nan duk bai zo ba, gashi basa wani magana sosai a waya yanzu, yawanci ma a kashe zaka ji wayarsa wani lokacin, sai in ya kunna ne yake kiranta suyi few minutes su a magana kuma shikenan, wanda hakan na damunta sosai, in just 2 days time bikinsu, kuma daga yau bazata sake shigowa department ba sai bayan bikin, duk da suna da test har biyu on friday amma duk lecturers din sun daga mata kafa za su bata make up test idan tayi resuming, dama iya test din yau ne ya kawota makarantar, don haka ko su Hamida bata tsaya yi ma sallama ba ta nufi gate din makarantar don samun adaidaita sahu a waje ta wuce gida za ayi mata gyaran jiki.... Mami ta sakko downstairs jin hayaniyar da ya cika parlor alhalin ita dai tasan daga ita sai mai aikinta ne a gidan, da mamaki take bin su Hajiya Halima da Mama Harira da kallo, yau har da matar yayan Abbansu Musharraf da bata ko zuwa gidan don banda ita ma aka kai lefe, Mami tace "Lafiya menene yake faruwa haka?" Continue making ur payment before the end of free pages 07087865788✍🏻 WhatsApp only [6/5, 12:00 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖 _By khaleesat Haiydar_✍🏻 11..... Da daddare Haseenah na dakinta tare da kawayenta da cousins dinta ana ta hira, ba a ajima da gama zanzara mata kananun kitso ba, kitson kuma yayi mata kyau sosai kana ganinta ka ga Amarya, lalle ne kawai bata yi ba har sannan, bakinta yafi na kowa a dakin kamar dai ba ita ce amaryar ba, zuwa lokacin gidansu cike yake da jama'a da suka zo bikinta, kana ganinta kasan tana cikin farin ciki mara misaltuwa, ga wani uban rawan kai da take, wata kawarta Samira tace "Toh yanzu wai ya za ayi da kayan da zaki saka for dinner on Saturday? Ni wllh kawai don kince wannan din bai maki bane but seriously yayi kyau sosai" Haseenah ta wani yatsine fuska tace "Baby yace a bar wannan kawai, za mu je mu siya already made, so gobe in sha Allah zai zo mu tafi inda za mu siya as early as possible" Samira tace "Cabb zaku sha tsada kuwa...." Haseenah tayi er dariya tace "Yes we can afford it" Cousin dinta da zata kusa shekara 39 me suna Jamila tace "Banda ma zamani yaushe har zaki wani bi ango ana gobe daurin aurenku kuje siyo kaya, ai ace da ne tun ana saura sati biyu ko uku baza ku sake haduwa da shi ba sai dai a dakinki in an kai ki, amma yan matan yanzu ko a jikinsu babu kunya suke sabgar su" Haseenah taki kallon inda take kuma ta mata banza don shegen manyancen ta yafi ƙarfin ta, gashi dama ba wani shiri suke ba, Bata taɓa auren ba fa amma tsabar manyance tana maganar zamanin da, Samira ta mika ma Haseenah wayarta dake ringing, Haseenah ta amsa ganin Badiyya ce ke kiranta ta mike ta fita daga dakin ta kullo kofa tayi kasa da murya tace "Hello Badiyya ya aka yi?" Badiyya tace "Ke zan tambaya ya aka yi, ina ta kasa kunnuwa shiru ban ji feedback ba, ko baki kai kasuwan bane wai?" Haseenah tace "Sai bayan kin tafi na tuna fita fa zai min wahala Badiyya, kinsan jibi ne fa daurin auren, amma nayi ma shi customer din nawa magana yace zai zo har gida ya amsa gobe da safe, to idan ya zo zan san ta yanda zan fita in basa a kofar gida" Badiyya da hakan bai mata dadi ba tace "Gidan naku fa naga an fara taruwa Haseenah kada aje a samu matsala, kuma kinsan wllh wllh ba yarda zan yi ba ko" Haseenah tace "Haba dallah, yanzu haka maganar da nake maki ma jakar da na saka gold din gashi a makale a hammata ta, ko da wasa bazan bari inyi nesa da shi ba ai sai kace ban san meye a jakar ba" Badiyya tace "To don Allah ki takura sa har sai ya zo goben ya amsa nan ne hankalina zai kwanta" Haseenah tace "In sha Allahu, dama yace da scale zai zo a gabana zai auna, kinga yana gaya min price din zan kira ki ki turo account number" Badiyya tace "Toh shikenan Nagode" Daga haka suka yi sallama Haseenah ta koma dakinta. Maheer ya shigo dakin Ammi da sallama yace "Gani Ammi" Ammi tace "Idan ka bude WhatsApp dinka zaka ga na tura maka picture din gold din nan, don Allah kai ma ka taya ni bincikawa ko..." Maheer yayi saurin katse ta yace "Ta ina Ammi? Ni da ba kasuwa nake shiga ba ba sanin komai nayi a kan Gold ba wannan ai sai mata" Ammi tace "To shikenan, Hajiya Safiyya tace min zata shiga kasuwan gobe ta duba, dama wallahi Maheer kudin account dina ne basu wuce 3.5M ba, shine nake so don Allah idan bazan takuraka ba ko 1M ne ka ara min in sha Allahu babu jimawa zan mayar maka, in dai na samu 1M din nan nasan sauran bazai gagara ba da izinin Allah, bana son Abbanku yasan komai a kan wannan abinda ya faru ne don abun kunya ne a gareni, amma nasan zai bani in na tambayesa, Usman kuma ni bana son fitinarsa gaskiya, ina gaya masa sai abun nan ya dawo sabo fil wallahi, don haka ka rufa min asiri Maheer duk da nasan hidimar da kayi na kashe kudi a yan kwanakin nan, kayi hakuri ka ji" Maheer dake ta kallon Ammi dama ya innata abinda ya sa ta kirasa kenan shine ta fara kame kamen wai ya nemo mata irin Gold din a kasuwa, yasan ba dalilin kiran ba kenan tunda dai tasan shi ba kasuwa yake shiga ba, she just beat about the bush kafin taje main point dinta, ko kadan Maheer bai son duk abinda zai daga hankalin Mahaifiyar tasu, yace "Shikenan Ammi zan tura maku in sha Allah, Allah ya rufa asiri" Ammi tace "Ameen, Allah maka albarka Maheer, Allah ya sa 'ya yanka su maka biyayya yanda kake min, Allah ya kara maka budi" Bai wani jima a dakin ba ya fita... Washegari Thursday karfe tara da rabi Maheer ya fita gida zuwa gidansu Haseenah don kai ta su siya kayan dinner dinta tunda na farkon tace masa bata so, jiran kusan minti ashirin yayi mata a mota sai ga ta ta fito ta shiga front seat tana masa wani kallo tana blushing tace "Good morning Sweedy" Ya jinginar da kansa jikin kujeran motar yace "Nace maki akwai inda zan je amma kika bata min lokaci Madam" Ta wani karyar da kai tace "Ita fa amarya bata laifi Baby, ko ka manta ne?" Tada motar yayi suka bar layin, waje me shegen tsada ta kai sa za ta siya ready made din dinner wear din wanda tun a IG ta sa suka turo mata ta zabi wanda take so, kawai yanzu zuwa zata yi ta gwada in akwai ɗan wani adjustment da za ayi sai a mata nan take, shi dai bai ce mata komai ba har suka shiga Lounge din wajen, bayan some minutes aka yi attending masu, wani ubansun dress ya ga an dauko mata wanda ko ba a fada maka ba kasan sai aljihu ya girgiza, ta amsa tana wani murmushi aka yi leading dinta zuwa inda zata je ta gwada, Maheer ya sauke wani ajiyar zuciya a ransa yace ai ko za su yi bala'i da ita don in har kayan nan ya wuce 200 zuwa 250 to sai dai a fasa siya, ya dau ruwan da aka ajiye masu yayi sipping yana jiran jin price din kayan, wayar Haseenah dake cikin jakarta ne ya fara vibrate, ya kalli jakar dake gefensa sannan ya dauke kai, har dai kiran ya katse, sake kira aka yi nan ma dai bai yi attempting ya ga me kiran nata ba, sai da aka yi kira kusan sau hudu, sannan ya sake kallon jakar da mamaki, jawosa yayi kusa da shi ya bude ya ciro wayar, yana cirowa kuwa yaga wata babban sarka sai daukan ido yake can kasar jakan, ya sa hannu ya ciro sarkan yaga hade yake da dankunnensa da zobe, da ɗan mamaki yake jujjuya sarkan, wayar Haseenah da ke daya hannunsa ya fara vibrate, yana dubawa yaga Badiyya ce, sake kallon sarkan yayi kamar me observing din wani abu, da sauri ya ajiye wayarta ya dau nasa ya shiga WhatsApp ya shiga chat dinsa da Ammi yayi downloading image da ta turo masa jiya don dama bai yi downloading ba, he was sooo shocked ganin exactly sarka da dankunnen hannunsa ne a picture din, ya dinga kallon hoton gold din wayar tasa da na hannunsa, banbancin kawai wanda Ammi ta tura masa a case dinsa yake, wannan kuma ba cikin case yake ba, kamar wanda ya tuna abu yayi saurin mayar da wayarta cikin jakarta ya ajiye jakar inda ta bar sa, ya fara tunanin yanda zai yi da sarka da dankunnen hannunsa, da sauri ya zura a aljihun wandonsa, and it was very obvious zata iya lura da aljihun nasa, can ya mike ya kai wayarsa kunne kamar yana waya ya fita daga Lounge din ya fito harabar wajen, motarsa ya nufa still pretending he is making call ya bude motar ya boye Gold din a ciki sannan yayi maza ya koma ya zauna inda yake zaune, bayan few minutes sai ga Haseenah ta fito tana wani murmushi tace "Baby transfer the 600k for them mu tafi, masu lalle nasan suna can suna jirana dama nace sai ana gobe daurin aure zan yi so that it will remain clean har a kai ni gidanka" Ya sakar mata murmushi yace "That is thoughtful of you, dress din ya maki dai ko?" Ta zauna kusa da shi tace "Sure dear, i love it soo much" Nan take yayi transfer din, bayan sun yi confirming payment din aka bata package din kayan suka fito tare da shi tana sakale da jakarta.... Direct gida ya maida ta yace sauri yake ana jiransa daga haka yayi reverse ya bar layin, Haseenah ta ciro wayarta bayan ta shiga gate din gidan ta zaro ido ganin miss call din Badiyya har biyar, dialing din number me siyar da Gold tayi tace "Haba Hamisu tun daxu fa kai nake jira wllh" yace "Ehh Hajjaju gani a hanya ai" tace "Toh sae ka Karaso" Ta kira Badiyya tace "Dadina dake takura wllh, gashi nan yanzun nan na kirasa yana hanya, kinsan basa fitowa kasuwa da wuri ne yau, don Allah kiyi calm down ya a isowa zan kira ki" Badiyya tace "Gaskiya ni dai yayi sauri Haseenah, wllh akwai wanda zan ba 200k ne duk ya addabi rayuwata yana neman min tonon asiri" Haseenah tace "Nan da minti kadan yana isowa bayan ya auna zaki ji alert abinda kin turo min acc dinki kawai be patient Baddiee" A haka suka rabu Haseenah ta shiga cikin gidan tana sauri ta je ta nuna ma kawayenta classy and unique dinner dress din da zata saka, amma fa tayi mamaki da lokaci daya Maheer yayi payment din bai ce kudin yayi yawa ba don shi kam ba mai son fake life bane, a ranta tayi concluding yasan abinda yake jira eagerly ai dole ya biya kudin dress sharp sharp babu musu. Haseenah bata bari an fara mata lallin ba saboda Hamisu dake hanya, wajen karfe sha biyu ya kirata yace yana waje, ta dau jakarta ta lallaba ta fice daga gidan babu wanda ya lura da ita, tana zuwa inda tace ya tsaya ya jirata ta bude jaka tana kokarin fiddo gold taga wayam, da farko ta zata idonta ne ya nuna mata haka, ta kikkifta idon ta sake wangale jakar still taga wayammm, wani azababbun zufa ne suka hau keto mata tana gwale ido tace "Hamisu, duba min jakar nan ka ciro Gwal din a ciki ni na kasa cirowa" tana fadin haka ta manna masa jakar a hannu tana zare ido, Hamisu ya mayar mata jakar da sauri yace "Ke me jakar baki gani ba sai ni Hajiya" Zazzage komai na cikin jakar ta hau yi a kan titi a rikice amma babu gold bBu alamar Gold, da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku da Badiyya" Hamisu yace "Gaskiya Hajiya kin bata min lokaci ne kawai, ai da kin fara dubawa kafin ki kirani.... Gashi customers can na ta jirana na bar su na yo nan wajen ga Unguwan nisa, kawai ni bari in tafi kasuwa yanda ake ciki sai ki kirani" Yana fadin haka ya buga machine dinsa ya kara gaba. Kiris ya rage Haseenah ta saki fitsari a titin, ko ina na jikinta rawa yake tsabar tashin hankali, ta dai samu ta ruga cikin gida ta shige visitors toilet dake cikin compound tayi fitsarin, tana fitowa ta tafi can backyard din gidansu ta zauna zufa wani na bin wani a goshinta, ita ba abun tayi raising alarm ba asirinta ya tonu Mummy ta gano abinda ke faruwa, dazu fa kafin ta fita da Maheer sai da ta duba jakar yana ciki kuma tunda suka dawo bata ajiye jakar nesa da ita ba balle tace a dakinta aka dauke, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ko dai wajen siyan kayan ne aka mata sata da taje gwadawa?? Sai a sannan ta fashe da matsanancin kuka ta daura hannu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace me zan ce ma Badiiya" Ammi ta kasa motsawa daga inda take zaune tana kallon abinda Maheer ya ajiye masu saman gado ita da Aunty Mariya, Aunty Mariya ta mike a gigice tace "Ina ka samo wannan Maheer?" Shi dai bai ce komai ba ya koma gefe daya ya rungume hannunsa yana bin su da ido, Ammi ta kallesa tace "Maheer wannan daga ina? Ko sabo ka siyo ne?" Yace "Babu wani sabo, tsohon da ku ka sani ne dai" Ammi ta buda ido with shock tace "Daga ina??" Maheer ya ɗan yi shiru yana tunanin abinda zai ce masu don bai son fara painting Haseenah black wajen Ammi, he just have to cover her up in other not to create doubt tsakaninta da iyayensa, Aunty Mariya ta hade rai tace "Dallah ka mana magana ka yi wani shiru, where did u find this?" Ya shafa kansa yace "Ita warce Ammi bata son laifinta ta kai ma Haseenah ajiya, shine Haseenan ta bani dazu da naje gidan, Badiyya ta kai ma Haseenah sarkan ta ajiye mata" Ammi ta dafe kanta cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aunty Mariya kam buda baki tayi hangangan tsabar mamaki, Maheer ya juya ya fita daga dakin, Ammi ta fara hawaye tana girgiza kai ta kasa cewa komai, Aunty Mariya ta mike ta dau Gold din ta adana shi inda babu wanda hankalinsa zae kai wajen a dakin Ammi ita ma ta fita daga dakin. Mami ce zaune parlonta a sama tare da yan uwan mijinta maza su biyar, Kawu Mansur yace "Maryam da girmanki da hankalinki bai kamata kina biye Halima kuna maida maganganu haka ba, shi sa muka ja ki muka dawo nan sama dake ayi magana ta fahimta...." Mami dai wani direction din daban take kallo kawai zuciyarta na tafarfasa, Kawu Mansur yace "Tsakaninki da Allah Maryam me kika sani game da gidan nan da Abdallah yake neman aure?" Mami tace "Au ashe ma yan uwana ne kenan da har zan san wani abu game da gidan, ka ga fa Yaya Mansur yanda ku ka samu wannan labari sama ta ka to nima haka nan ya riskeni, yanda duk aka bi ku da Envelope nima haka aka kawo min nan, sannan ina ganin ai ba wani zai zauna ma Musharraf da yarinyar nan ba, ko ma menene tunda yace yaji ya gani yana so ina ga a bar yaron kawai, he is old enough to make decisions for himself, shi ma ai an basa takardan kafin ma a kai maku and he wasn't bothered about it...." Kawu Faisal na kallonta kasa kasa yace "Tunda auren wasan yara ne da har zai bude baki yace yaji ya gani ba? Mu kuma gamu a banza, To abinda ke da shi baku sani ba shine, bai isa ya yanke ma kansa decision kansa tsaye as far as mu iyayensa muna raye, don haka ba shi da wani say a wannan lamari sai abinda mu manya muka ce, in kuma bashi da manyan ne sai ki gaya mana yanzu mu ji...." Mami ta masa wani kallo kafin ta kai ga cewa komai Kawu Mansur yace "Yanzu dai duk ba wannan ba, wannan lamarin da ake ta cukuikuyawa abu ne me sauki wllh, mu fa muka kai kudin nan ba wasu suka kai mana ba, mafi sauki shine mu sake komawa gidan don a warware mana abinda ya shige mana duhu daga bakin iyayen yarinyar nan da suka amshi kudi hannunmu, ai ba sai an tsaya ana cece ku ce ba, ga best alternative kawai na kawo" Mami tace "Ohh da an san da haka za a zo nan a daga min hankali saboda an raina ni? To wallahi ku ja ma Halima da Rumaisa kunne idan basu fita harkata ba ina me tabbatar maku hukuma ce zasu min iyaka da su, nan ba da dadewa ba kuwa" mikewa Kawu Saleh yayi ya fita daga parlon sauran ma duk suka mike suka bi bayansa parlon ya rage Kawu Mansur kawai, Kawu Mansur yace "Yanzu dai kiyi hakuri Hajiya, duk abinda ake ciki za ki ji kira anjima, ko kuma in zo da kai na" Daga haka ya mike ya fita daga parlon.... Abbansu Maheer na Bedroom dinsu yana duba wasu takardu, dawowarsa kenan daga Abuja saboda daurin auren 'ya yan nasa da za ayi gobe, Ammi ta shigo dakin tace "Yallabai wai kayi baki fa" Abba ya kalleta yace "Daga ina?" Ammi tace "Maheer yace kamar dangin yaron nan ne Musharraf, yace su suka kawo kudi" Abba ya ajiye takardun hannunsa yace "Toh lafiya, Allah sa dai ba cewa za su yi a daga bikin ba" Ammi tace "In hakan shine mafi alkhairi ai babu yanda aka iya" Abba ya dau wayarsa ya fito daga dakin ya fito compound don a nan parlon baƙin yake, yana shiga parlon duk aka gaggaisa, Maheer ya shigo ya ajiye masu carton din ruwa da lemo, Abba yace "Ya shirye shiryenmu?" Duk suka amsa da "Alhamdulillah mun gode Allah" Abba yace "To Madallah" Kawu Mansur yace "Dama wata magana ce ke tafe da mu Alhaji, sai dai za mu so kayi mana uziri kuma ka fahimce mu, don ko kaine a shoes dinmu iyaka hakan kai ma zaka yi" Abba da yayi jim, can yace "Ikon Allah, to ina sauraronku Alhaji, Allah sa dai lafiya" Maheer dake kokarin fita daga parlon jin abinda Uncle din Musharraf yace sai ya kasa fita lkci daya jikinsa ya basa all is not alright, Alhaji Faisal ya ciro takardan aljihunsa ya mika ma Abba, Alhaji Mansur ma ya ciro ya mika masa, Alhaji Sale shima yayi haka Abba dae sae amsan takardun yake yana bin su da kallo cike da mamaki yace "Na menene wannan din?" Alhaji Mansur yace "Mu ma duk haka suka iso gidajenmu a yammacin jiya, ka duba ka gani Alhaji" Abba ya maida dubansa kan takardun baya ko kiftawa amma ya kasa duba ko daya ya karanta, Maheer ya karaso kusa da Abba zai amshi takardun Abba ya daga masa hannu, calmly yace "Zan duba" Yana fadin haka ya shiga duba content dinsu gaba daya, daya bayan daya yabi har ya gama karanta su, a hankali ya linke su duk ya ajiye gefensa yana kallon Uncles din Musharraf da suka zuba masa ido gaba dayansu, Abba ya ɗan kwantar da kansa jikin kujeran da yake zaune, trying all possible best to be calm yana kallonsu yace "Haka ne.... Duk abinda ke rubuce jikin takardun nan gaskiya ne amma banda abu daya zuwa biyu ..." Yana kai wa nan yayi shiru, Alhaji Faisal yace "To Alhamdulillah, sai dai fa Alhaji abu dayan nan zuwa biyu da kace is of no importance to us right now, don tun asali baka bi ka'idar da ya kamata ka bi ba while giving out the girls hand in marriage tunda kasan da wnn babban issue din a kasa, in other words an yaudaremu an kuma yi playing with our intelligence an mayar damu kananun mutane, sannan an cuci ɗan mu, a lamari na aure babu amfanin shigowa da rashin gaskiya cikinta saboda gudun abinda zai je ya dawo, domin haka muke son sanar da kai cewa a yanzu mun janye daga wannan auren da muka nema ma ɗan mu ake kokarin daura sa gobe, sadakinmu da duk wani abu da aka kawo gidan nan za mu aiko a amsar mana in sha Allah, gatan da ko wani uba zai yi ma ɗan sa kenan a issue irin wannan, mun bar ka lafiya Alhaji" Abba was speechless, har duk suka mike suka fara fita daga parlon, Maheer da gaba daya ya dinga jin maganganun Uncle din Musharraf kamar a mafarki yayi saurin daukan takardun da Abba ya ajiye a gefensa yana dubasu daya bayan daya, kallon Abba yayi, lkci daya ya duka nan gabansa hankali a tashe yace "Abba ban gane ba, what is all this? Me yake faruwa??" Abba ya kasa ce masa komai don yayi nisa tunanin da ya tafi, Maheer that is getting impatient don har wani zafi yake ji duk da AC dake kunne parlon yace "Don Allah kace min wani abu Abba, i am loosing my self, I can't stand this anymore, me ke faruwa?" Abba ya sauke ido ya kallesa, bayan few seconds ya fara magana Calmly yace "Haka ne.... Mayraah isn't my biological daughter Maheer, ba ni da Ammi muka haifi Mayraah ba, bamu san ta yaya ma aka sameta ba, mu dai kawai...." Kasa ci gaba Abba yayi, Maheer that was dumbfounded and shock ya dinga kallon Abba kamar ranan ya fara ganinsa it felt like mafarki yake kawai, bayan shirun kusan minti uku tsakaninsu, Maheer yayi karfin halin mikewa with breaking voice yace "Ni da Usman kuma su waye iyayenmu? If Mayraah isn't ur child then mu ma ba yaranku bane" Yana kai wa nan ya fice daga parlon Abba ya kasa ce masa komai... Mayraah ta mike zaune tana kallonsu Hamida dake ta harkan gabansu a dakinta, waya ne kare kunnenta suna magana da Musharraf da ya kirata ko minti biyu ba ayi ba yanzu, a hankali tace "I will call u back, i am not alone" tana fadin haka ta katse wayar ta fita zuwa corridor din dakunan, sake dialing numbersa tayi yana dagawa ta marairaice tace "But sir kasan bazan iya fitowa yanzu ba ai, they are people everywhere a gidan, i will be noticed idan zan fita" Musharraf yace "Plss Mayraah find a way da zaki samu ki fito it's urgent plss" She couldn't resist because of the urge in his voice, cike da damuwa tace "But are you okay sir?" Yace "No i am not" Tace "Ohk, yanzu kana farkon shigowa layinmu kace?" Yace "Eh" Tace "Toh i will be coming right away" Katse wayar tayi ta fara tunanin ta yaya zata fita gidan nan without being noticed, daga karshe dai she successfully found her self outside ba tare da an lura ita bace don Nikab ta saka, ko su Hamida basu son ta fita daga gidan ba, inda yace mata yayi parking ta nufa, taga Motarsa ta karasa ta bude front seat din ta shiga tana kallonsa da damuwa, kafin ta ce komai taga ya fara driving motar, da mamaki tace "Sir ina kuma za mu je?" Payments before end of free pages, to avoid going for break... 07087865788✍🏻 WhatsApp only, no phone calls pls [6/6, 4:38 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖 _By khaleesat Haiydar_✍🏻 Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga one and only Maman Khadee me sabon kasuwar dutse😁 (Aunty Zahrah) da Er ta Deejah me lamurje a ɗa kafin ta fara siyar da namijin goro yanzu, sai kuma me cikin shekara uku da taki haihuwa har yau har gobe (Matar Babana Ummu Nabila🙄) khaleesat Haiydar na maku fatan alkhairi a ko da yaushe😁 This page goes to you Zainurah Yazeed Ahmad, u are one of the die hard fan i am opportune to meet, Allah Ubangiji ya raya maki zuri'a, and i do appreciate u now and always dear, Allah ya biya maki bukatunki na alkhairi.... Sauran fans da suka yi patronizing dina even before in gama free pages wllh i really appreciate u people, ina maku fatan alkhairi duniya da lahira, Allah ya raya maku zuri'a, ya kara ma iyayenku lafiya da tsawon rai me amfani, Ameen. 12.... Mami was speechless, lokaci daya duk jikinta yayi sanyi, banda kallon Alhaji Mansur babu abinda take, Alhaji Mansur ya ci gaba yace "Don haka mun sanar masa za aje karbo mana duk wani kaya da aka kai gidan da sunan aure, kudin da muka kai kuma Faisal zai koma ya amso su" Mami ta girgiza kai cike da damuwa tace "Ba sai an amso komai ba Alhaji, mu bar masu ko don...." Ya wani hade rai ya dakatar da ita a fusace yana kallonta yace "Akan me zaki ce ba sai an amso komai ba? Mu bar masu saboda muna tsoronsu? Mutanen da basu san mutunci ba, mutanen da suka yaudaremu suka maida mu yan iska, ai basu cancanci ko tsinke a bar masu ba wlh, komai sai sun fito da shi idan ba haka ba hukuma ta rabamu da su" Mami dake masa wani kallo ta kasa jurewa tace "Ku ko ina sai kun nuna wannan halin naku na karanta? Idan shi wanda ya siya kayayyakin da kudinsa yace a bar masu fa?" Alhaji Mansur ya mike yace "Shi wanda ya siya kayan ya ci kaza kazansa, ai ba shi ke da iko da kansa ba, Kuma wallahi wallahi kin ji rantsuwan musulmi ko? To sai an amso kayan nan gaba daya, yanzun nan za a tura su Halima tunda dama su suka kai, don haka su za su koma su amso, aikin banza kawai" Yana kai wa nan ya fice daga parlon yana muzurai, tashin hankalin Mami ya kashi biyu yanzu ta ma rasa wani tunanin zata yi in particular, babban damuwarta na farko Musharraf, she don't know how he will take this and cope don ta ga yana son yarinyar, na biyu kuma ita a rayuwarta bata son taga an ci ma mutum mutunci, she detest that, babu tantama tasan an tara jama'a gidansu yarinyar nan, a haka su Halima za su je su gwada halinsu na rashin tarbiyya da rashin mutunci cikin taron jama'a, mikewa tayi ta dauko wayarta tayi dialing din number Alhaji Saminu wanda shine babba a family din and he resides in kaduna, kuma duk suna shakkarsa suna jin maganarsa, yana picking bayan sun gaisa ta fara masa bayanin abinda ke faruwa, ya katse ta yace "Duk na san da batun nan an kirani an gaya min komai, ashe kananun mutane ne makaryata, kinga kuma baza mu bari ɗan mu ya auro warce bata da asali ba, dama an san su waye iyayen nata ne to da sauki, kinga kuwa ai baza mu yarda a kawo mana irin wannan cikin zuri'ar mu ba" A hankali Mami tace "Haka ne, amma yanzu Alhaji Mansur ya bar nan wai za a tura su Hajiya Halima su je can gidansu yarinyar su amso kayan aure da aka kai, ni kuma naga hakan bai kamata ba tunda nasan wacece Hajiya Halima nasan kuma me zata je ta aikata a gidan, kasan cin mutunci bashi da dadi Alhaji" Alhaji Saminu yace "Shikenan shi Faisal da zai koma amso kudin auren sai ya karbo har akwatunan, zan kirasu in sanar masu kada a tura kowa in ba shi Faisal din ba" Daga haka yayi mata sallama ya katse wayarsa, Mami ta ɗan ji hankalinta ya kwanta don baza ta so a walakanta kowa ba a kan Musharraf, kara kiran layin Musharraf tayi for the countless time amma still a kashe, she felt so disturb and worried for him, ta zauna saman kujera ta dafe kanta.... Ammi ta kasa nutsuwa tun bayan da ta shigo parlon baƙi ta dalilin kiran da Abba yayi mata a waya, Abba ya bi ta da ido har ta nemi waje ta zauna tana kallonsa ita ma, da kyar tayi karfin halin cewa "Lafiya dai ko Yallabai?" Abba ya kasa ce mata komai ya dauke idonsa daga kallonta, nan taji hankalinta yayi mugun tashi don kana ganin Abba kasan he is not himself, Ammi ta kasa jurewa tace "Don Allah ka gaya min abinda yake faruwa Yallabai ko yaron cewa yayi ya fasa auren ne??" Abba ya kasa bata amsa don a duniya baya son duk wani abu da zai daga mata hankali sanin condition dinta, but he have no choice dole zata sani, Ganin yanda Ammi ta rikice masa yayi ta maza yace "Haka ne" Ammi was shock, ta dinga kallon Abba ko kiftawa babu, lokaci daya hawaye ya cika idonta cikin rawan murya tace "Kana nufin ya fasa auren?" Abba ya gyada mata kai, Ta fashe da kuka tace "Meye dalilinsu Yallabai? Sai ana gobe daurin aure an tara jama'a za su zo yau su ce sun fasa, me aka masu haka?" Kuka take sosai tana kallon Abba da ya kasa cewa komai don zuciyarsa ya gama karaya, he is just trying his possible best to be stable, yasan in dai ya sanar ma Ammi dalilin fasa auren nan sai ta fadi kasa yanzu, she won't be able to take it ya sani... Abba ya dake yace "Ya isa haka Hajara, dama Allah ya riga ya rubuta Mayraah ba matar yaron nan bace, shi yasa kika ga hakan ya faru ana gobe daurin auren, kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki, duk abinda Allah yayi mana dai dai ne kada mu masa butulci, sai dai bana son ki sanar ma kowa an fasa auren nan tukunna" Cikin kuka sosai Ammi tace "To me ya rage yallabai, gobe ne fa auren? Meye amfanin boye boye, ba gwara a sanar ma kowa ya kama gabansa ba? babban damuwata halin da Mayraah zata shiga idan ta samu wannan mummunan labarin don ban ga alamar ta sani ba..." Ammi ta kasa controlling kanta a parlon sai kuka take kamar ranta zai fita, Jikin Abba ya kara sanyi, he wish yaron nan bai sanar ma Mayraah ya fasa auren ba da kuma dalilinsa na fasawar don duk abu da ya taɓa Mayraah yasan shi ya taɓa, shi kansa bai san irin son da yake ma Mayraah ba, bai taɓa mata kallon ba shi ya haifeta ba, Abba yayi kasa da murya yace "Na dai ce maki kar ki ce ma kowa komai, kuma kin manta daurin auren biyu ne? Ai akwai na Maheer, so for now kiyi shiru don Allah, and pls ki kwantar da hankalinki ki koma ki ci gaba da sabgogin ki" Sai da Ammi ta ci kukanta na kusan minti biyar a parlon sannan ta share hawayenta ta mike a hankali ta fita a sanyaye, Abba da gaba daya tunaninsa ya dagule ya dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a ransa, waye wannan da yasan da batun ba su suka haifi Mayraah ba har ya je ya sanar ma family din Musharraf?? Waye yayi wannan danyen aikin, baya tunanin zai taɓa yafe ma kowa waye wannan, da zai san waye sai ya sa an dauresa even if da last card dinsa ne, asalin Mayraah abu ne wanda su kansu are still very surprise ta yanda suka ajiyesa babban sirri a zuciyoyinsu for almost 22 years now, ko da wasa basa tada zancen tsakaninsa da Ammi, sai dai in ya siya kaddara da sunan Mayraah ya bata ta ajiye sai yaga mood dinta ya canza don hakan na tuno mata da cewar ba fa su suka haifi Mayraah ba sannan Mayraah bata da gadonsu, ita ce ma ta kawo masa shawaran dinga siyan property da sunanta tun yarinyar na shekara sha biyu, duk sanda kuma Abba yayi hakan takan kwana ta yini cikin damuwa a zuciyarta ranan, ya san duk son da yake ma Mayraah bai kama kafar na Ammi ba, don Ammi ta dauki son duniya ta daura mata, yanda ta saka Mayraah a rai ko su Maheer bata saka haka ba, kawai Allah yayi Mayraah bazata sangarce ba saboda su Maheer da Usman da basu bada space din haka ba especially Usman that was so strict on her, Abba ya kasa ci gaba da zama ya mike ya dinga safa da marwa a parlon, shi dai yasan a garin Kano babu wanda yasan da cewar Mayraah isn't their Biological daughter, a takaice ma bayan shi, Ammi, Hajja, sai iyayensa kafin rasuwarsu, sai kilan ko Aunty Mariya babu wanda yasan da wannan secret din, ko da kuwa cikin abokansa da yan uwansa maza, Ammi ma yasan hatta kawayenta basu san ba ita ta haifi Mayraah ba, Abba ya kusa minti sha biyar yana zaga parlon, bai taɓa shiga damuwa da rudanin da ya shiga a wannan moment din ba, abu ne da ya zo unexpected kamar daga sama, Daga karshe ya dau wayarsa yayi dialing number Maheer, sai da ya kusa katsewa Maheer ya daga, amma bai ce komai ba, Abba yace "Kayi hakuri ka dawo mu yi magana Maheer, we need to talk pls" Abba bai jira jin me Maheer zai ce ba ya katse wayar, komawa yayi ya zauna yana ta sake sake a ransa har Maheer ya shigo parlon, Abba ya bi sa da kallo ganin yanda duk ya dawo wani iri a cikin ɗan kankanin lokaci, har ya samu far end of the parlor ya duka kasa ba tare da ya bari sun hada ido da Abban ba, Abba felt so guilty a moment din nan, in ma basu gaya ma kowa ba bayan wasu shekaru da suka ga Maheer ya mallaki hankalin kansa ai da shi sun sanar masa basu boye masa ba, Abba ya ma rasa ta inda zai fara, Shi dai Maheer ya sunkuyar da kansa bai yarda ya kalli Abba ba, kana ganinsa kasan ya shiga damuwa sosai ba kadan, it's something that hit him so hard kamar a mafarki, Abba yayi kasa da murya yace "Ina son ka fahimce mu Maheer, mun yi abinda muka yi ne for the Sanity of Mayraah, muna son ta taso like every other child cikin so da kauna, ta yaya za a so yarinya kamarta ta taso da damuwar ba mu ne iyayenta ba? How will she cope with that? Sannan wllh mu kan mance ba mu muka haifeta ba tsabar yanda muka dauketa...." Shi dai Maheer bai ce komai ba kuma bai dago kansa ba, Abba ya ci gaba yac "Maheer ban kiraka a yanxu don gaya maka yanda muka samu Mayraah ba, duk da nasan dole a yau ko gobe kowa zai san wacece *MAYRAAH* kuma ya aka yi ta shigo rayuwarmu har muka ga gwara mu boye ma jama'a, don yanzu babu wani batun boye boye kuma, amma Maheer ina son ka sa a ranka Mayraah isn't ur Biological sister, er uwarka ce kawai ita in islam, baya nan babu wani alaka ta jini tsakanin ku, kuma ka sani cewar da aure tsakaninku...." Maheer ya daga kai da sauri ya kalli Abba jin furucinsa na karshe, bai san sanda ya mike ba yana girgiza kai yace "Abba har abada babu aure tsakanina da Mayraah, kuma har gobe zan ci gaba da yi mata kallon kanwata ta jini ne warce muka fito ciki daya, bayan wannan bazan yi ma Mayraah wani kallo ba, she still remains my blood" Shiru Abba yayi yana kallonsa don gaba daya ya gama discouraging dinsa akan abinda ke zuciyarsa, bayan few seconds Abba ya sauke kansa kasa yace "Haka ne, And i am happy u said this..." Maheer yace "Kuma tunda aka fasa aurenta nima a daga nawa kawai, dan i won't have the rest of mind of getting married tomorrow bayan damuwar da nasan kanwata zata shiga" Abba ya girgiza kai yace "Baza a daga naka ba, in sha Allah gobe ne daurin auren ka babu fashi" Aunty Mariya ta dinga salati a rikice a dakin Ammi bayan Ammi ta kirata ta sanar mata abinda ke faruwa, Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, a saboda wani dalili yace ya fasa? Mun shiga uku" Cikin kuka Ammi tace "Ni dai kawai Alhaji ce min yayi an fasa amma ban san dalili ba" Aunty Mariya da har hawaye ya cika idonta tace "Da kyar in ba yan uwan nan nasa da suka kawo lefe ne suka lalata auren nan ba, kai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu ta ina za a fara Ammi? Ina Mayraah din, anya ma ta san abinda ke faruwa kuwa?" Hankalin Ammi ya kara mugun tashi da ta tuna Mayraah, ta yaya zata dau wannan lamari, Ammi ta kalli Aunty Mariya cikin kuka tace "Ban san ko ya gaya mata ba, amma dai sun cutar min 'ya ta, kuma Allah ya saka mata" Aunty Mariya ta share hawayen dake sauka nata idon ta mike ta fita daga dakin, can dakin Mayraah ta tafi ta bude kofar, ganin su Hamidah kadai ne a dakin tace "Ina Mayraah?" Hamidah tace "Kilan tana dakin Yaya Maheer, waya take yi ta fita saboda hayaniya" Aunty Mariya da jikinta yayi sanyi ta juya ta bar bakin kofar, dakin Maheer ta tafi, ta gansa shi kadai a dakin nasa zaune gefen gado ya dafe kai, Aunty Mariya ta karasa cikin dakin ta kulle kofar cikin damuwa sosai tace "Maheer amma me yasa suka ce sun fasa? Wani laifin aka masu ne?" Ya dago kansa yana kallon Aunty Mariya da idanuwansa da suka kada sosai yace "Aunty...." Sai kuma yayi shiru, Aunty Mariya dai ta kasa cewa komai ita ma duk zuciyarta ya karaya, Cike da karfin hali Maheer ya ci gaba yace "Aunty wacece Mayraah?" Sosai gaban Aunty Mariya ya fadi, ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, and u can see the shock a fuskarta, Bakinta na rawa tace "Ban gane ba Maheer, wani irin tambaya ne wannan kuma?" Mikewa yayi trying his possible best to control his emotions yace "Aunty dama ba Ammi da Abba suka haifi Mayraah ba?" Aunty Mariya bata san sanda ta nemi waje ta zauna ba don sai da taji zuciyarta ya tsinke, da kyar tace "Maheer? Where did u hear this from?" Maheer ya hadiye wani abu da kyar yace "Dalilin fasa aurenta kenan...." yana fadin haka ya fice daga dakin, Aunty Mariya ta dafe kirji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, mun shiga uku" Kasa kwakkwaran motsi tayi daga inda take zaune tsabar yanda ta girgiza, bayan kusan minti goma ta mike kamar warce ruwa ya cinye tana tafiya a hankali ta fita daga dakin, dakin Ammi ta koma ta bude kofar a hankali ta samu Ammi zaune gefen gado tayi tagumi hawaye sai sauka yake a idonta, Aunty Mariya ta tabbata Ammi bata san abinda ke kasa ba, kasa karasawa cikin dakin Aunty Mariya tayi ta juya ta fita, ta tafi dakin Usman ta dau Hijab dinta da purse ta fita direct sai gidan Hajja, tafe take hawaye na sauka idonta tana tausayin halin da Ammi zata shiga idan tayi find out dalilin fasa auren Mayraah, ba a ma maganar Mayraah din, to ta ina wannan boyayyen maganar da bai fi su hudu kawai suka sani bane ya fita? Waye ya fitar da wannan sirrin na shekara 22, haka ta dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un har ta isa unguwan Hajja bata sani ba sai ji tayi mai adaidaita sahun na cewa "Hajiya mun shigo layin" Tsabar gigicewa kawai ta sauka ta fiddo dari biyar ta basa ta karasa har karshen layin da kafarta, tana shiga parlon Hajja ta zauna nan kasa tana kallon Hajja da Mama Ladi dake gwada tsohon breziyar Badiyya tana baɓɓaka dariya kamar tababbiya ita a dole ta samu breziyar da zata sa da biki, dama Badiyya ba dai manyan kirji ba shi yasa Bra dinta yayi ma Mama Ladi ciff, Hajja na kallon Aunty Mariya ganin yanayinta tace "Lafiya Mariya?" Nan da nan wasu sabbin hawayen suka shiga sakkowa idanuwanta cikin rawan murya tace "Hajja an fasa auren Mayraah" Caraf a kunnen Badiyya dake shiryawa zata je gidansu Haseenah ta mata rashin mutunci don ta kirata har taji babu dadi bata dagawa daga karshe ma wayar sai ta ji sa switch off, Ba Hajja ba har Mama Ladi sai da ta mike tsabar gigicewa, Mama Ladi na zaro ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, aka fasa auren Mera?" Hajja da ita ma ta rude lokaci daya tace "Ban gane an fasa auren Mayraah ba Mariya, me ke faruwa?" Aunty Mariya ta fashe da kuka ta kasa cewa komai, Mami Ladi tace "Dama ana fasa aure haka kawai babu dalili? Ki gaya mana me ya faru aka fasa auren, ko wiwi mijin ya sha da zai ce ya fasa aure ana gobe daurin aure, Ga ire irena da suka zo daga wata uwa duniya saboda bikin nan, me yake nufi da mu kenan mun yi tafiyar banza? Ai zama bata gan mu ba mu tafi can gidan ayi komai a gabanmu, amma Allah ya tsine ma mijin nan albarka dai dai gwargwado" Hajja da ta kasa zaune ta kasa tsaye ta dau Hijab dinta ta nufi kofa, da ganinta kasan a gigice take, Mama Ladi ta figi mayafinta ta yafa kan breziyar jikinta ta bi bayan Hajja suka bar Aunty Mariya zaune sai hawaye take, Tsabar farin ciki Badiyya bata san sanda ta dare saman gado ba ta dinga tikar rawa tana karkade kirji, ta rasa inda zata saka kanta don murna, tunda ta fito duniya bata taɓa shiga farin ciki da murna irin na yau ba, Jin an banko gate alamar fitar su Hajja da Mama Ladi Aunty Mariya ta mike da sauri ta bi bayansu, Badiyya ta leko parlor bayan da taji shiruuu alamar babu kowa a gidan, takalmanta ta sa har wani ɓari jikinta yake ta tafi gidansu Haseenah tayi mata breaking news din nan me dadin ji, tana fita kofar gida ta hango Hajja, Mama Ladi da Aunty Mariya can saman layi sun yi nisa, sai da ta jira ta daina hangosu kafin ta canza hanya ta samu ɗan sahu direct sai gidansu Haseenah. Haseenah na zaune dakinta cikin kawayenta abun duniya ya mata yawa ta rasa tunanin da zata yi, gashi ko kawayen nata bata gaya masu abinda ke faruwa ba na ɓatan gold din cikin jakanta don cousin din nan nata Jamila na dakin, kuma in dai tayi magana a gabanta to kamar Mummy ta ji ne, Haseenah ta kalli agogo dake nuni da karfe biyar da rabi na yamma duk da damuwar da take ciki hakan bai sa ta rike cewar Maheer bai kirata ba tun bayan da ya ajiyeta dazu da safe, dama line biyu gareta, kuma Badiyya guda daya kawai gareta bata da dayan, da Badiyya ta isheta da kira sai ta cire sim din ta ajiye, Haseenah ta sauke ajiyar zuciya ta jawo wayarta tayi dialing number Maheer kilan in taji muryarsa hankalinta zai kara kwantawa, har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma no Answer, bude kofar dakin aka yi ta juya a tsorace don da taji an bude kofa Badiyya take expecting gani, ai ko taga Badiyyar ce ta shigo ba ko sallama kamar an hankadota, nan da nan Haseenah ta dake ta hade rai tana tunanin karyar da zata lafta mata, Badiyya na zuwa ta kamo hannun Haseenah bakin nan nata har kunne tace "Taho kawata labari da dumi duminsa..." Haseenah ta mike ganin farin ciki ne kaca kaca fuskar Badiyya ta bi ta suka koma dakin me aiki, da mamaki Haseenah tace "Lafiya naga kamar an maki albishir da aljanna wannan farin ciki haka?" Badiyya ta saki wani guda tace "An fasa auren Mayraah da Dr Musharraf" Haseenah ta zaro ido tace "Keee don Allah??" Badiyya tace "Wallahi kawata, yanzu Mama Mariya tazo gidan Hajja ta sanar mata" Haseenah tace "Alhamdulillah, Alhamdulillah, kai amma na taya ki murna wllh, what next kenan yanzu?" Badiyya tace "Sai in fara shooting shot dina, in gaya maki babu zancen aure dai kam, yanzu haka so nake in ga idanuwar er iskan nasan suna can sun kumbure" Haseenah ta rike haɓa tana kallon Badiyya lokaci daya kuma tana jinjina makircinta, Haseenah tace "Amma don Allah kawata ki bani labarin yanda kika yi wannan abun, ni fa na fara tsoronki yanzu wllh" Badiyya tayi wani dariyar bosawa tace "Breaking news kawata, dama nace bazan gaya maki ba sai nayi accomplishing mission dina, Ashe dai duk wannan abun da ake ba Ammi da Abba bane suka haifi Mayraah, Mayraah dai er tsintuwa ce mara asali warce kila ma cikin shegenta aka yi aka jefar da ita a titi, ni kuma tun da na samu information din nan shine na bibbi dangin Dr Musharraf na sa aka rubuta letter aka kai masu one by one, har gidansu Musharraf din an kai yayi sau uku, to kinji dalilin fasa auren" Shiru Haseenah tayi tana kallonta, lkci daya tana kokarin fahimtar abinda take ce wa, sai taji kamar ba hausa ma take mata ba, Badiyya tayi wani shegen dariya tace "Ya naga kin ƙame? to wllh shock din nan da kika shiga bai kama kafar nawa ba da na samo labarin wacece Mayraah, sai da nayi kwana hudu cikin shock da wasi wasi a raina, at first na ma kasa yarda in gaya maki amma daga karshe that is just it, wllh babu abinda Mayraah ta hada damu tsintattciya ce don ki ji ma in gaya maki, abinda yasa ban gaya maki ba tun a lokacin da na sani, ina tsoron kar kije ki gaya ma Maheer don hatta shi bai san cewar Mayraah ba kanwarsa ta jini bace kilan duk sai yau za su sani, Ammi da Abba suka boye wannan sirrin kusan shekara ashirin da biyu babu wanda ya sani ko da wasa" Haseenah da taji kanta na juya mata ta dafa Badiyya ta samu gefen gado ta zauna tana haƙi, Da mamaki Badiyya tace "Meye haka ke kuma? Duk shock din ne haka?" Haseenah da har zufa ya fara ketowa mata ta ko ina a jikinta tayi karfin halin cewa "Yanzu kina nufin da aure tsakanin Mayraah da Maheer?" Shiru Badiyya tayi tana nazarin abinda Haseenah tace, lokaci daya ta zaro ido after realizing what she said really made sense, Badiyya ta zauna gefenta da sauri tace "Kin ji ki da wata magana, shi yanzu Maheer don bashi da kai sai yayi sha'awar auren warce for 22 years yake ma kallon kanwarsa ta jini? Ta yaya haka ma zai faru? Ashe ma kenan sha'awar kanwar tasa yake duk ba a sani ba all this while" Haseenah ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku na lalace Badiyya, ni kika yi ma wannan abu ba wani ba, ni kika cuta ba kowa ba, ashe dama wnn ne yasa tun farko naji na tsani yarinyar nan ban san dalili ba" Badiyya ta tabe baki tace "Ke dai kin cika fitina wllh, yanzu baza ki daina wannan kazamin maganar ba Haseenah, ta yaya ma Maheer zai yi sha'awar auren Mayraah sai kace wani ɗan iska, ashe ma kenan ba kallon kanwa yake mata ba a gidan, misali ma idan ya zama ɗan iskan ai ita nasan ba er iska bace Mayraan, baza kuma ta taɓa amincewa da wnn tabargazan ba balle shi kansa nasan bazai yi hakan ba kawai silly thought dinki ne, kamar kece fa rana guda a tashi ace Sufyan ba yayanki bane kawai sai yayi sha'awar aurenki ko ke kiyi sha'awar aurensa? kinga ni don Allah kar ki lalata min farin cikina let me go home and know my next move" Tana kai wa nan ta mike ta fice daga dakin ita tsabar farin ciki ta ma mance da batun Gold a yanzu dai, Haseenah ta mike tsaye har sannan hannunta na daure a kanta ta dinga zaga dakin tana cewa "Na shiga uku na lalace, Badiyya ta cuce ni...." Tun Mayraah na dakewa tana masa magiya ganin tafiya kawai suke for almost 35 mins now a motarsa har dai ta fara masa kuka ta marairaice tace "Don girman Allah sir kayi min magana, why are you quiet? And where are you taking me to? Ba fa a san na fito daga gida ba, yanzu fa magariba zai yi" Har sannan Musharraf bai ce mata komai ba, driving dinsa kawai yake idanuwansa da suka kada na kan titi, gashi ba a hankali yake tafiyar ba, ita bata ma taɓa ganinsa a wannan yanayin ba, wannan yasa taji gabanta na ta faduwa ta kasa sukuni tana ta kallonsa hawaye na sauka idonta, duk wannan magiyar da take masa bai ma san tana yi ba don yayi nisa tunanin da ya tafi, yasan definitely bata san me ke faruwa ba har yanzu, idan kuma tasani she will get distablize and Depress, taji komai ya fita a kanta daga karshe ta karya alkawarin da ta daukar masa taki amincewa da shi, don haka kafin ma hakan ya kasance zai yi abinda zai sa she won't have any other choice then being with him forever, he will leave her with no choice sai na zama tare da shi as mijinta..... _Free pages otilor ya kare_🙅🏻‍♀️ *Masu bukatar continution na littafin Mayraah, mu hade a payment group na littafin, subscription for the book is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah* Ur evidence via👇🏻 07087865788 WhatsApp only. Kuma kun san dai together with you all we shall make this a blockbuster💣 kawai dai daga ni har ku muyi trusting alkalamina, it won't disappoint us in sha Allah, i am assuring u it's gonna be mind blowing😁 [6/10, 10:51 AM] Khaleesat Haiydar💖: Hajja na shigowa Bedroom din Ammi ta rafka salati ta fashe da kuka a rikice ta zauna kasan carpet tace "Allah mun gode maka da wannan jarabawar" Mama Ladi da tuni tayi cilli da gyalen da ta yafa tace "Toh wai na taɓa jin inda aka fasa aure babu wani dalili ni Ladiyo? Kamata yayi ai a turkesu su fada mana uwar me aka masu za su fasa aure, ko kuma kawai a kai su caji ofis a bi mana hakkinmu, da wani ido za mu kalli jama'an da muka tara?? Ko dai yan iska ne yaron da iyayensa? A kira mana Meran mu ji ko wani sa'insa ya hadasu da yaron ne, ko kuma a kai ni gidan ni inji dalilin fasa auren" Ammi dai tayi nisa tunanin da take don tayi kukan har ta gode Allah, wai a haka ma fa bata san dalilin fasa auren ba ina ga ta sani, Aunty Mariya dama bata bi su Hajja zuwa dakin Ammi ba don ganin yayarta cikin kuka na kara karyar mata da zuciya, Abba kawai take son gani don gaya masa kar ya sanar ma Ammi dalilin fasa auren nan for her mental health, gun Maheer dake zaune parking space ta tafi, he looks so heartbroken and sad, Aunty Mariya ta fi minti biyu tsaye amma ta ma rasa abinda zata ce masa kamar yanda shi ma bai ce mata komai ba kansa a sunkuye, parlon baƙi ta nufa daga karshe duk jikinta a sanyaye, tana sallama kuwa ta tadda Abba har sannan a ciki, shi kansa kana ganinsa kasan ya shiga damuwa ba kadan ba, Aunty Mariya ta zauna saman kujera nan da nan hawaye ya cika idonta tace "Alhaji ina ga da an boye ma Ammi dalilin fasa auren nan because of her health, kar a gaya mata don Allah" tana fadin haka ta fashe da kuka, Abba dai yayi shiru yana kallonta ya kasa cewa komai, bayan few minutes Abba yace "Ina Mayraah?" Aunty Mariya ta buda ido sosai, infact duk wannan abinda ake babu ma wanda yaje ya ga halin da yarinyar ke ciki, Aunty Mariya tayi karfin halin cewa "To Allah ya sa yaron bai gaya mata ba dai, i think tana dakinta tare da kawayenta" a hankali Abba yace "Ki dubo min ita" Mikewa Maheer yayi yana kallon Hamidah da ta nufo parking space din da yake zaune, tun bata karaso ba yace "Where is she?" Hamidah tace "Wallahi na duba upstairs gaba daya bata nan, har dakin dake downstairs she is not inside" Maheer ya buda ido yace "What?" Barin ta yayi wajen a tsaye ya nufi cikin gidan da sauri. Hankali tashe Maheer ke searching all of the house for Mayraah, har kiran wayarta yayi yaji switch off, Aunty Mariya da ta shigo ita ma a lokacin duk ta gigice bayan Hamidah tace mata ai Mayraah ce bata gidan, ita dai Hamidah was so confuse at this time don bata san abinda ke faruwa a gidan ba, bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo, babu fuskan wanda ya kalla ya wuce sama direct, Maheer ya bi bayansa yace "Wait, we can't find her in this house, she is no where to be found...." Usman da bai ma san abinda Maheer din ke cewa ba ya nufi parlon Ammi tun kan Maheer ya riskesa, yana bude kofar ya shiga yana kallon Ammi da ta daga kai tana kallonsa, yayi gathering courage yace "Su waye namu iyayen mu kuma?" Dai dai nan Maheer ya shigo parlon yayi gripping hand dinsa ya fitar da shi daga parlon, Ammi ta bi su da kallo as if trying to understand abinda Usman yace, can ta kalli Hajja da ita ma ta bi su da kallon mamaki, Mama ladi tace "Kamar yaya su waye nasu iyayen, ko dai wiwi suka bashi a kotun?" Ammi bata san sanda ta mike ta fice daga parlon da sauri ba, tsaye ta gansu corridor Usman ya hade kansa da bango Maheer was standing by his side looking confused as well, Ammi bata ce masu komai ba kamar yanda su ma basu ce mata komai ba, ta sauka downstairs Maheer ya bi ta da kallo, Aunty Mariya ta share hawayenta da sauri ganin yanda Ammi ta sauko downstairs tace "Ina kuma zaki Ammi?" Ammi bata ce mata komai ba ta fita, parlon da Abba ke zaune ta nufa, tana shiga ciki ta tsaya nan bakin kofa tana kallonsa tace "Boye min dalilin fasa auren Mayraah zaka yi?" Abba dake ta kallonta, ya ɗan sauke ajiyar zuciya, he knows she will definitely find out shi yasa ma da Aunty Mariya ta shigo tana ce masa kar a gaya ma Ammi yayi shiru don yasan wannan labarin kuma Allah kadai yasan iya inda ya tafi a yau din nan, gani yake har makota yanzu sun samu wannan labarin tunda ba a san ta inda ya billo ba, ya mike ya nufeta ya kama hannunta making her seat down kan kujera ganin she is palpitating, yayi kasa da murya yace "Ki kwantar da hankalinki Ammi, komai zai daidaita in sha Allah" Ammi na girgiza kai da kyar, hawaye na sauka idonta tace "Ka gaya min me ke faruwa, ina son ji daga bakin ka, menene yasa aka fasa auren Mayraah?" Abba ya dake yace "Allah ya ga zuciyar mu, bamu yi abinda muka yi don cutar da kowa ba, we did this out of our good heart, we only wanted the best for Mayraah, we didn't mean to be deceitful to anyone, Allah ya san intention dinmu...." Ya kasa ci gaba ya dinga kallon Ammi cike da tausayinta, he wish rana me kama ta yau bazai taɓa zuwa ba, the secret they kept for almost 23 years is now no longer a secret, ya dafa Ammi ganin she is more than shock, yace "Our main priority now is Mayraah, kada mu bari ta shiga damuwar da zai iya mata illa because it won't be easy mutanen da kake gani a matsayin iyayenka rana daya a tashi ace ba su ne iyayenka ba, she needs us the most in this trying time, and in sha Allah we will continue being the parent figure we are to her" mikewa Ammi tayi hawaye na sauka idonta a hankali tace "Zuwa yanzu duk an san ba mu muka haifi Mayraah ba kenan?" Bata jira cewar Abba ba ta juya zata fita daga parlon amma tun kan ta kai bakin kofar taga kofar da ma parlon na juya mata gaba daya, Abba ya nufeta da sauri... Mayraah ta dinga bin sa da kallo har ya kashe motar ya sauka, bata taɓa jin tsoro irin na wannan lokacin ba, ya zaga side din da take zaune ya bude motar, duk da yanda gabanta ke mugun faduwa ta marairaice cikin rawan murya tace "But i don't understand the meaning of this sir, ina ne nan ka kawo ni plss? This i almost 8pm, nasan ana ta nemana a gida" Tana kai wa nan ta fashe masa da kuka sosai, Musharraf dake ta kallonta yace "Kin zata son da nake maki iya baki kadai ya tsaya? An gaya maki na taɓa yi ma wata mace irin son da nake maki banda mahaifiyata? You think i have d strong heart to loose you just like that? You think bazan yi duk wani abu da zai sa in mallake ki ba?" The way he is talking kadai ya isa ya kara tsoratata, ita dai ta kasa cewa komai sai kallonsa take da manyan idanuwanta, kawai taga ya kamo hannunta ya sauko da ita daga cikin motar ya kulle, bugun zuciyarta ya tsananta she was so afraid of him a moment din nan, he doesn't look the gentle Dr Musharraf she knows, bin sa kawai take yana rike da hannunta, she don't think he is even okay, sai da ya fara kunna solar din gidan sannan suka iso entrance din parlon gidan, ta ga ya ciro makulli ya bude kofar, suna shiga ya sa ma kofar key ya zare, bata san sanda ta fashe masa da matsanancin kuka ba ta durkusa gabansa tana girgiza kai tace "Na shiga uku, sir don girman Allah tell me the meaning of this? Ina ce gobe ne fa daurin aurenmu, menene ya sa kuma zaka kawo ni wani waje da daddaren nan daga ni sai kai?" Musharraf ya girgiza mata kai yace "They are not prepared su daura mana auren gobe...." Yana fadin haka yayi hanyar dakunan dake parlon, Mayraah that was so confused ta bi sa da kallo zuciyarta na bugawa, gashi ya amshe mata waya ya kashe tun suna hanya, tayi zaman dirshan a wajen ta hade kai da gwiwa tana kuka cikin tashin hankali, ko dai dama ba sonta Dr Musharraf yake ba kawai yaudaranta yayi, sai kusan karfe takwas da rabi ya fito daga dakin da ya shiga, yanzu kam wani mugun tsoronsa take ji har cikin ranta, yana kallonta yace "Tashi ki je kiyi sallah" Ta kasa kallonsa tsabar tsoro kuma bata motsa daga inda take ba, yace "Ba ki ji me nace bane" Mikewa tayi zuciyarta na bugawa, ya nuna mata daki da zata shiga, kamar munafuka ta shiga inda ya nuna mata tana waigensa. Har Mayraah ta idar da sallah hawayen dake sauka idonta bai tsaya ba, ta takure waje daya saman darduman da take zaune wasu sabbin hawayen na saukowa idonta, what will she tell her parent and her brothers, ina zata ce masu ta je tun wajen karfe biyar har gashi yanzu tara ake nema na dare, kafin su zo nan tafiyar kusan awa daya da rabi suka yi a hanya, yanzu idan yace zai maidata gida ai sai wajen goma da rabi kilan za su isa ko sha daya, is he even ready to take her back home today? Tunanin hakan ya sa ta fashe da kuka sosai, bude kofar dakin aka yi, ta hadiye kukan da take ta koma baya a tsorace taki barin su hada ido da shi, ya shigo cikin dakin yana kallonta, ta sunkuyar da kanta hawaye wasu na bin wasu a cheek dinta ga wani faduwa da gabanta yake, ya duka dab da ita ya ajiye cup din fresh milk dake hannunsa a gefenta, he was just staring at her for almost a minute, cikin raunin murya yace "Saboda ina sonki yasa nayi haka Mayraah, wallahi i can't imagine me without you, ni kaina bansan irin son da nake maki ba Mayraah, plss kiyi min uzuri i only have this option...." Sai a sannan ta daga idanuwanta da suka yi ja tana kallonsa, kamo hannunta taga zai yi tayi saurin matsawa a tsorace without noticing d cup he kept by her side ta wuntsular da shi gaba daya milk din ya malale kasa, tun kan ya dagata har yayi soaking hijab din jikinta, yayi kasa da murya yace "I am sorry" Ta dake muryarta na rawa tace "Bana son kana taɓa ni don ni ba muharramarka bace" tana fadin haka ta juya masa baya duk da yanda gabanta ke faduwa, kallonta kawai yake, can ya juya ya fita daga dakin, Mayraah ta shiga bandaki da sauri ta cire hijab din jikinta, er doguwar riga ce a jikinta mara nauyi, ta wanke hijab din da detergent da ta gani a bandakin snn ta shanya inda taga towel a ajiye, har zata fito sai kuma ta koma ta dau towel din ta lullube jikinta da shi tana fitowa dakin ta gansa yana goge inda madaran ya zube, ta sunkuyar da kanta ta koma daya side din ta zauna kan carpet tana kallon agogon dakin, bayan ya gama goge wajen ya fita da mop din. Mayraah bata sake ganin Musharraf ba har kusan sha biyun dare, sau uku bacci barawo na sace ta tana farkawa a tsorace don babu kwanciyar hankalin yin bacci, ga duk tunaninta yana wajen Amminta, ko wani hali take ciki yanzu, daga karshe ganin karfe daya yayi ta mike a hankali ta nufi kofar dakin ta bude making sure bai yi ƙara ba, ta dinga bin corridor din dakunan da kallo, can tana tafiya a hankali ta shiga parlon gidan, a mugun tsorace da shock ta koma baya ganinsa kwance tsakiyar parlon idonsa a lumshe daga shi sai singlet with 3 quarter, ga empty kwalaben alcoholic wine guda uku a gefensa da roban fresh orange juice wanda shi kadae ne bai gama shanye wa ba, tsabar gigicewa bata san sanda ta karasa parlon ba don tabbatar da kwalban me take gani haka, ta durkusa ta dau kwalba giyan daya ta zaro ido tana karanta rubutun jiki, bata san sanda ta saki kwalban ba har sai da ya tarwatse tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" mikewa taga yayi zaune da sauri yana kallonta da jajayen idanuwansa, a guje ta tashi ta koma dakin da ta fito jikinta na rawa zata saka key amma taga babu key jikin kofar, ta durkushe kasa tana zaro ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku" Bude kofar dakin taga yayi ta mike da gudu ta koma can karshen gado ta fashe da kuka don tsoro ta kasa cewa komai ta hade hannuwanta biyu tana kallonsa, kana ganin idanuwansa kasan he is drunk amma kuma he is calm at the same time duk da tafiyar ma da kyar yake yi amma he is not staggering, saboda gigicewa Mayraah bata san sanda ta shige bayan labule ba da taga ya nufota tana cewa "Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri sir" Ya bude labulen ya janyota ta rirrike hannunsa cikin kuka tace "Nooo don Allah ka rufa min asiri sir, i am begging you pls..." Yayi hugging dinta cikin calm voice dinsa that is shaking yace "Kar ki bari a rabamu Mayraah, i don't know what will become of me, i...." Kasa ci gaba yayi, ita kuwa ko ina na jikinta rawa yake, ya jinginar da ita da bango underneath his breathe yace "Say something pls wife" Bakinta na rawa tace "Bazan bari a rabamu ba, i promise you, trust me" Yana kallonta da lumsassun idonsa yace "Can i kiss you pls?" Ta rike hannunsa ta wani zaro ido har sannan jikinta na rawa amma cike da karfin hali ta dake ta masa murmushi tace "Not now, u need to brush and freshen up first, i just caught u with bottles of wine isn't it...." Ya hade goshinsa da nata, da kyar yace "Orange juice was the last i drank..." Ai kam she could perceive the flavor of orange as he speaks, bata ankara ba sai jin bakinsa tayi a nata, she struggled to free her self amma ta kasa saboda irin rikon da yayi mata, hawaye ya dinga sauka idonta duk jikinta na rawa, bata kara gigicewa ba sai da taga ya fara canza salo, bata san sanda wani dakewa ya kuma zuwa mata ba tace "Ermm, i am very hungry pls sir, ina son in ci abinci kasan ban ci komai ba" Tana fadin haka kuwa ya saketa, she was still shaking don lokaci daya gaba daya yanayinsa ya canza, kamar me counting din words dinsa yace "Should... i.... get you some fresh.... Milk?" Ta gyada masa kai da sauri bakinta na rawa tace "Yes, yes yes plsss, i need it" Juyawa yayi ya nufi kofa, ta fara kalle kallen dakin, tana ganin ya fita ta nufi bandaki da gudu ta shiga taga babu key shi ma a ciki, sosai hankalinta ya tashi ta sake fitowa a gigice ta fita daga dakin, sauran dakuna uku dake corridor duk ta ji su a kulle an sa makulli, ta daura hannu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku, wayyo Ammi" Tana nan tsaye sai gashi ya taho rike da cup din fresh milk din, ta sauke hannunta ta hadiye kukanta da sauri trying her best to stay calm duk da yanda kirjinta ke heaving, ya nufota yana mika mata milk din, Mayraah ta amshi cup din tana kirkiran murmushi tace "Thank you so much, babu bread or chin chin?" Jingina yayi da bango alamar tsayuwar na neman gagararsa yace "Ba...bu" Ta hadiye wani abu da kyar tace "Ohk, let me sip it little by little don yayi sustaining dina" Yana kallonta da idonsa da suka dawo so sexy murya can kasa yace "Ohk, ok..." Dukawa tayi nan kasa ta zauna tana satan kallonsa ta kai cup din baki tana kurban madaran da taji sa kamar magani a bakinta, da kyar ta hadiye banda bugawa babu abinda zuciyarta yake, still bata fasa satan kallonsa ba taga shi ma ya zauna nan kasa yana facing dinta kamar zai hadiyeta saboda kallo, yau sai taji bata son kamshin turarensa dake kara mata sonsa a da, tunanin yanda zata janye hankalinsa daga abinda taga alamar yake son yi ta shiga yi don bata ga alamar kuka da pleading dinta zai canza masa wannan ra'ayin ba she just need to use her brain, shi ko bai fasa kallonta ba, Can dai dubara ya zo mata bayan ta kara kurban madaran a hankali tana kirkiran murmushi tace "But tell me sir, me yasa kake tunanin za a raba mu bayan kasan ina sonka sosai, kai ma kuma kana so na" Ya gyara zama kamar me rada yana maganar da daddaya da daddaya yace "Ba a son mu yi aure Mayraah, ance ba su Ammi da Abba bane suka haife ki, they said they are not ur Biological parent...." Mayraah ta sauke cup din bakinta tayi still tana kallonsa babu ko kiftawa jin abinda yake cewa, ya kalleta yace "Ko in kawo maki note din da aka dinga kawowa gidanmu akanki" Mayraah ta maida cup din milk gefenta tana gyada masa kai tace "Kawo min" Mikewa yayi taga ya shiga parlor this time around he is staggering alamar giyan ya fara hitting dinsa hard, ta bi sa da kallo babu ko kiftawa abinda ya fada na kai koma a kanta, bayan few minutes sai ga shi ya dawo ya zube mata Envelopes har hudu a gabanta ya zauna yana kallonta, Mayraah ta dauki daya ta bude da sauri ta fara karanta content din, ta fi minti daya tana sake nanata karatun kamar dai tana son fahimtar abinda ake nufi, can ta dau wani ta bude shi ma ta nanata yafi sau hudu, haka Mayraah ta dinga bi tana karanta duk takardun cikin envelope din, kana ganinta kasan she is confuse at this point, Musharraf ya kamo hannunta yana murzawa a hankali yace "Abbanki bai musa ba, yace haka ne, ba su ne suka haifeki ba, shine dangin babana suka ce bazan aureki ba don baki da asali, Mayraah even if u were born out of wedlock ni Musharraf bazan taɓa rabuwa da ke ba, ko ma wacece ke a haka nake son ki nothing can ever change that, Baby don Allah kar ki bari a raba mu, kawai mu yi rayuwanmu just i and you... we can go to Abuja a daura mana aure daga nan i will take you to Maldives mu yi rayuwarmu a can ki haifo min cuties kamar ki, i know my Mami won't be against that...." Mayraah ta zame hannunta a hankali daga nasa don duk abinda yake cewa bata ma san yana yi ba, kawai abun da ta gama karantawa ne ke ta mata yawo a kai tana sake nanatawa a zuciyarta, bata san sanda ta matsa daga kusa da shi ba tana girgiza kai tace "Noo, kawai dai ana son raba mu ne amma Abba da Ammi su ne suka haifeni they are my parent, it's all a lie" lokaci daya har hawaye ya cika idonta, Kawai gani tayi ya rungumeta a rikice yace "Yes love, karya suke yi, kawai suna son rabamu ne, plss don't let that, permit me to show u how much i love you today, tomorrow and forever..." Tashin hankalin Mayraah ya dawo sabo fil ganin ya dawo mata kamar wani zautattce, ganin abinda yake kokarin yi, ta dake tana gyada masa kai da sauri tace "Toh, to, to amma pls ka bari in yi wanka, kai ma kaje kayi wanka first...." _Double update for june 10_🎊 *Alhamdulillah, it's another June 10🎉🎊🎈 for me, Allah ya karo min shekaru masu albarka, Thanks for d well wishes fams, i appreciate u now and always, Allah ya saka da Alkhairi... Nayi discount for the book Mayraah yau, every other book nakan yi haka on every june 10, so you can pay just 300 naira into* 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah To gain access to reading the book till the end hankalinki kwance babu burden or hakki akan ki.... Ur evidence of payment via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah [6/10, 8:43 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah bata tsaya taji abinda Musharraf zai ce ba ta kama hannunsa duk da yanda gabanta ke faduwa ta nufi Bedroom da shi tana cewa "Zan saka maka warm water kayi wankan yanzu so u can feel much better" Bin ta kawai yake zuwa dakin yana kallonta babu ko kiftawa, suna isa bandakin ta kallesa tace "Wait for me here" Ba musu ya Jingina jikin kofar bandakin yana bin ta da ido, zuciyarta na bugawa ta karasa can ciki tana ɗan satan kallonsa sannan ta shiga tara masa ruwa a bathtub, har ta gama sannan ta juya tana kallonsa, a lumshe taga idonsa a yanda yake jingine da kofar, ta nufesa tayi kasa da murya tace "Kaje kayi wankan" Ya buda ido bai ce komai ba, bude kofar bandakin tayi a hankali ta fita sannan ta kulle, ta sauke wani ajiyar zuciya feeling a bit relieve now, sai kuma ta fara tunanin what next, da sauri ta fita zuwa parlor, nan ta hau dube duben makullin da ta ga ya zare sanda suka shigo gidan, amma babu shi babu alamarsa a parlon, lokaci daya jikinta yayi sanyi, ta zauna nan kasa hawaye cike idonta tana tunanin yanda zata yi to keep on distracting him daga intention dinsa, a sanyaye ta mike ta nufi wani kofa da ta gani a parlon, kitchen ta gani ta dinga bin ko ina da kallo, can ta nufi fridge ta bude, tsoro ne ya kamata ganin cike yake da alcoholic wine irin wanda ta gani a parlor sae orange juices, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, fitowa da wine din ta dinga yi tana ajiye su a sink with tears in her eyes, duk sai da ta bi ta bude su ta tuttular a cikin sink din ta bar kwalaben wajen ta fita daga kitchen din duk jikinta a sanyaye, corridor ta koma idonta ya sauka kan takardun da Musharraf ya dauko ya ajiye mata wani mugun faduwa gabanta ya sake yi, maganganun da ya gaya mata akan takardan ya dinga mata yawo a ka, wai an fasa aurensu saboda abinda aka rubuto a takardun nan, amma me yasa iyayensa za su yarda da wannan karyan da makirci, ta yaya bayan kowa yasan su waye iyayenta amma za a rubuto wannan karyan har su yarda, hawaye taji ya kawo idonta da ta tuna yace mata parent dinsa sunce bazai aureta ba, kenan dama gobe baza a daura masu aure ba? But did her parent know about what is happening? ta fi minti daya tsaye tana kallon takardun hawaye na bin kuncinta, can ta durkusa a hankali ta daukesu gaba daya, sae da ta sake karancesu sannan ta jefar wajen ta saka kuka, amma how will somebody just sit down and forge this lies har a yarda?? Ta hade kanta tana ci gaba da kuka a hankali, sosai taji zuciyarta ya mata rauni, Kakarin amansa ta dinga ji daga bandaki, ta daga kanta amma bata motsa daga inda take ba, jin shiru har bayan minti talatin ta mike a hankali ta leka dakin, kwance ta gansa nan tsakiyar dakin yayi ruf da ciki idonsa a lumshe, ta lallaba ta koma ta sake zama a corridor din tana jin zuciyarta na bugawa, yanzu ya zata iya idan ya sake riskanta a nan? ko da wasa wani yace mata Dr Musharraf na shan giya baza ta taɓa yarda ba, don bai yi kama da masu sha ba, he is too gentle and calm for this, mutumin da ko magana ma bai damesa ba how on earth zai zama mashayin giya??? ta fashe da kuka mara sauti don abubuwan yanzu sun taru sun dagula mata lissafi, maimakon taji tsanarsa ko kuma haushinsa sai taji kamar an kara mata wutan sonsa ne a zuciyarta, ita kanta bata san yanda aka yi sonsa yayi mata yawa haka a zuciyarta ba, a da ta san tana sonsa amma ba kamar yanda take jinsa har cikin ranta yanzu ba, kwanciya tayi nan corridor ta takure waje daya duk da sanyin tiles din, a haka bata san sanda bacci ya dauketa ba, cikin bacci ta ji warm hand din mutum a fuskarta dama a ɗar ɗar baccin ya dauketa, hakan ya sa ta farka a tsorace ta mike zaune tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" a gabanta ta gansa a duke yana kallonta, ta dinga komawa baya a tsorace duk jikinta na rawa, hannu ya nuna mata alamar tayi calm down, ita dai har ta manne da bango bata bari sun hada ido ba, cikin sanyin murya yace "I am sorry Mayraah" Sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, ya sunkuyar da kai yace "For good 6 years ban sha alcohol ba Mayraah believe me, that was my foregone habit, na daina tun bayan da na dawo daga America, i don't know what came over me yesterday, i felt i was loosing my mind" Kasa ci gaba yayi, ita dai kallonsa kawai take, bayan few seconds ya dago yana kallonta da idanunsa da suka kada yace "Damuwa yayi min yawa, ban san halin da zan shiga idan na rasa ki ba" A hankali Mayraah tace "Ur foregone habit?" Ya dinga kallonta kafin yace "Kin gansu da yawa a fridge ko? Billah na frnds dina ne ba nawa ba, ba ga dakunansu kin gani a kulle ba, we do spend our weekends together here, ni ne ma nakan dade ban zo nan ba, wllh nasu ne ba nawa ba" Mayraah dai tayi shiru bata ce komai ba, yace "Tashi mu shiga ciki ki kwanta" Sosai gabanta ya fadi amma bata nuna hakan ba, ta dake tace "Ina zaka kai ni daga nan kuma?" Yayi kasa da murya yace "Abuja, za mu je can a daura mana aure, daga can zamu fita kasar..." Mayraah ta sunkuyar da kanta tace "Ohk, but promise me baza ka taɓa ni ba har gari ya waye" Ya dinga kallonta babu ko kiftawa, can yayi kasa da murya yace "Idan na taɓa ki ma ai ni zan aure ki ba wani ba" Taji gabanta ya fadi amma ko da wasa bata nuna hakan a fuskarta ba tace "Then babu inda zan bi ka a daura mana aure idan har baza ka bari sai bayan an daura auren ba zaka zo kusa da ni, ko ka mance addininka ne?" Yayi kasa da murya yace "Yi hakuri Wife, i promise ko finger dinki bazan taɓa ba" Yana fadin haka ta mike ta nufi Bedroom din ya bi ta da kallo wani sonta na fizgarsa, saman gado ya ga ta kwanta duk da fa karfin hali kawai take don ita bata ma gama tabbatar da mayen ya sake sa ba, ya mike ya shiga dakin shi ma, pillow ya dauka ya ajiye a kasa ya kwanta, ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, a hankali yace "Can i take off the light?" Tace "No" Yace "Ohk" Juya masa baya tayi ita kanta tana mamakin courage din nan nata, sai dai fa har kusan karfe uku bata yi bacci ba sbda fargaba, kamar yanda shi ma yake ta juye juye bai yi baccin ba, Wajen karfe hudu ta juya ta kallesa taga alamar bacci ya daukesa, she needs to get the key of this house kafin ya tashi, ta sidado ta sauka daga kan gadon tana kallonsa, zaro ido tayi ganin makullin ya ajiye a gefensa, ta fara tiptoeing zuwa side din nasa trying her best not to make any noise, can dai ta tsaya tana tunanin ko dai ta kashe wutan dakin sai tayi stretching ta saman gado ta dauko, don yanzu tana zagawa da kyar idan bazai tashi ba tunda bata san ko yana da nauyin bacci ba ko bai da, hakan tayi daga karshe ta kashe wutan dakin ta hau saman gado ta koma side dinsa sannan tayi stretch din kanta ta dauko makullin, bata ankaraba kawai sai gani tayi ta rikito kansa, tsabar gigicewa tayi saurin jefa makullin saman gado tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Duk don kar yaji sound din makullin, shi ko ya mike zauna holding on to her yace "Baby are you okay?" Bakinta na rawa tace "I had a bad dream" ya mike zai kunna wutan dakin ta riko kafarsa da sauri tace "Noo, i switched it off, kar ka kuna plss, bana son hasken" Ya koma ya rikota yace "But are you okay?" Ta hadiye wani abu da kyar tace "Sure, i am fine, zan kwanta nan amma stick to our deal pls" a hankali yace "Ohk" Ta kwanta nan side dinsa gabanta na mugun faduwa, don tasan yana kunna wuta dole zai ga makullin da ta jefar kan gado, yace "In dauko maki duvet din ne?" Tayi saurin cewa "No thank you, kawai ka matsa can ka kwanta" A hankali yace "Okay" Tana jin ya matsa nesa da ita ya kwanta, ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, har aka kira asuba daga shi har ita babu wanda yayi bacci, fargabanta kar ya kunna wutan dakin in zai je alwala, ai ko tana ganin ya mike tace "Pls kar ka kunna min wutan" He was surprise don yayi zaton bacci take, a hankali yace "Ohk dear" Tana ganinsa ya kunna na bandaki sannan ya shiga, ta sauke wani ajiyar zuciya yana kulle kofar bandakin ta mike da sauri ta kunna wutan dakin ta dau makullin sannan ta dau Hijab dinta da ya linke mata tun jiya da daddare ta saka, da sauri ta fita zuwa parlor, kan centre table taga cash da bata san ko nawa bane, ta dau 5k a ciki jikinta na rawa ta nufi kofa ta bude da mukullin ta fita, har wani ɓari jikinta yake ta nufi gate din gidan ta dinga gwaggwada bunch din makullin hannunta har ta samu na gate din ta bude a hankali, sannan ta fita, kulle gate din tayi ta waje sannan ta jefa makullin making sure bai yi hanging a barbed wire ba har sai da taji faduwarsa a kasan compound, sauri sauri gudu gudu take tafiya tana waigen bayanta, can dai ta ga ta fito babban titi ga motoci sai wucewa suke, haka ta dinga sauri har ta fara ganin masu adaidaita sahu ta tsayar da wani ta shiga, yace "Ina za ki Hajiya?" Tace "Tasha" Yace "Toh" sai da taga sun yi nisa sannan tace "Don Allah ya ma sunan garin nan" Juyawa yayi ya kalleta, sai kuma yace "Amma dai ke bakuwa ce ko?" Tace "Eh" Yace "Ai naga alama, to Zaria ne nan" Ta buda ido sosai wato Zaria ma ya kawota, Mai adaidaita sahu na ajiyeta a tasha ta samu motar kano ta hau, nan da nan motar ya cika suka yi set off zuwa kano, sai a sannan ta sauke wani ajiyar zuciya hankalinta ya dawo jikinta, assuming bata yi duk wannan dubarun da tayi ba tasan Dr Musharraf bazai bar ta haka ba, kafin karfe bakwai da minti talatin sai ga su a cikin garin kano..... Babu wanda ya rintsa a gidan Abba daren ranan nan, ga Ammi jini ya hau sosai, don she is under medication a gida har da karin ruwa, zuwa sannan duk kowa yasan an fasa auren Mayraah sannan Mayraah ba er gidan Abba da Ammi bace, wajen karfe takwas da rabi jama'a duk sunyi cirko cirko a parlor har da baƙin da suka zo daga nesa da wasu makotansu Ammi, kowa dai duk jiki a sanyaye, duk da ba bacci Ammi take ba amma idonta a rufe suke ita kadai tasan abinda take ji a wannan lokacin, gani take kamar shikenan bazata sake ganin Mayraah ba har abada, Mama Ladi ta fyace majina cikin rawan murya tace "Ni wllh nasan annamimiyar da ta hada wannan bam din aka shiga wannan rudanin a gidan nan...." Hajja dake zaune tayi tagumi a parlon ta juya tana kallon Mama ladi, rai bace Hajja tace "Amma dai nace maki ki iya bakin ki Ladi, wannan wace irin rayuwa ce baki da aiki sai hada hutsuma cikin jama'a? Tun cikin dare kin ishemu kinsan wanene kinsan wanene, to ke a garin kano kike da zaki hakikance kinsan wanene, haba don Allah ki bari mu ji da daya mana, wannan fa ba karamin magana bane kuma kina ji Mamuda yace sai yayi Shari'a da koma wanene yayi mana haka" Mama Ladi ta mike tace "Tun jiya zan yi magana kike hanani magana Hajja, to wallahi ni dai da iyayenmu suka haifeni kema kinsan ba munafuka bace ni, kuma babu ruwana da harkan munafurci, a cikin ku akwai warce nace ma Badiyya taje wajena har tayi kwanaki biyar?" Duk kowa yayi shiru yana kallon Mama Ladi har Hajja don kam bata gaya ma kowa ba, cike da mamaki Aunty Mariya tace "Taje yin me a wajenki Mama Ladi?" Mama Ladi tace "Wallahi ina zaman zamana sai ga shegiyar yarinyar nan Badiyya kamar an jefota karaye, yarinya ta zo ta giggilla min karya wai ana nuna banbanci tsakaninta da Mera don an ga bata da uwa bata da uba, duk kowa ya tsaneta har saurayin da ke nemanta da aure ance ya hakura ya nemi Mera kuma har ya hakura gashi an saka ranansa da Mera, sannan sau dari idan Mariya zata kira sai dai tace a ba Mera baza tace a ba Badiyya waya ba, ni ko da zuciya ta debeni nace wacece Mera? meran da bamu hada komai da ita ba babu dangin iya ba na baba ko dai ita Ammin da Hajjan sun mance ne, nan ko na kwashe duk yanda aka samo Mera na gaya ma Badiyya da zuciya daya ba da zuciya biyu ba, ban san da er iska munafuka nayi tadi ba" Mama Ladi na kai wa nan ta fashe da kuka tace "To yanzu zan fasa kwan nan a gaban kowa, wllh wllh Badiyya ce ta lalata maganar auren nan daga dai na bata labarin wacece Mera da zuciya daya" Ammi ta bude ido ta mike zaune tana kallon Mama Ladi babu ko kiftawa, ita kanta Hajja kasa kwakkwaran motsi tayi tana kallon Mama Ladi, Aunty Mariya ta fashe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me yasa kika mana haka Mama Ladi?" Bude kofar parlon aka yi Mayraah ta shigo, tsaye tayi bakin kofar tana bin kowa da kallo kamar yanda duk aka yi still a parlon ana kallonta da shock, Mayraah ta nufi Ammi da gudu hankalinta tashe ganin drip a hannunta tace "Ammi... saboda ni ne?" Mama Ladi ta rushe da kuka tace "To da saboda waye? Banda mun sa ma kanmu salama ai har mu da sai kin ganmu da karin ruwan a hannu, Dama nace masu babu inda zaki je dole ki dawo garemu ko da bamu hada komai da ke ba, ko don halaccin da muka maki ai kya dawo, To idan ba jiya ba ke kin taɓa sanin cewar ba Ammi da Mamuda bane suka haifeki? Ko a bakin wanin mu kin taɓa ji? Kinga ai basu taɓa nuna maki banbanci tsakaninki da ainahin yaran da suka haifa a cikinsu ba, kuma soyayyar da suke maki yasa suka boye ma duniya ba su ne asalin iyayenki na gaskiya ba mu ma kuma muka ja bakinmu muka yi shiru muka taya su rufa wannan asirin banda yanzu da asirin ya tonu, amma gata kam ai babu irin wanda baki samu ba a wajensu Mera, da yawa wa enda ke gun iyayensu na asali ma basu samu gatanki ba wllh, ko su Maheer da suka haifa basu samu haka ba magana ta gaskiya, to don me baza kiyi la'akari da wannan ba zaki gudu ki bar mu cikin tashin hankali ki tauye mana baccinmu jiya, yanda muka ga rana haka fa muka ga dare, kuma da kika kama hanya kika gudu ina zaki je? Ke da baki da dangin uwa balle na uba" Mayraah da ko karasawa gun Ammin bata yi ba ta tsaya tana sauraron abinda Mama Ladi ke gaya mata babu ko kiftawa, lokaci daya ta dinga ganin parlon na juya mata ta dinga kallon Mama Ladi da ta dawo mata double double a ido, Ammi ta kasa daurewa ta hade kanta da kujera tana kuka sosai tana jin zuciyarta na mata zafi, Aunty Mariya ma kukan take don su duk tunaninsu Mayraah tasan asalin me ke faruwa daga bakin Musharraf, dalilin da yasa ta bar gida kenan jiya, Mama Ladi ta sharce majina tace "A nan bakin wani masallaci a cikin garin Yola aka yasar da ke ko cibiyarki bai fadi ba, a lokacin Mamuda na fama da baƙin talauci ya fito zai share masallaci ya jido ruwa kafin a fara fitowa sallan asuba ya ganki cikin yakunannen tsumma uwarki ta wurgar da ke ta kara gaba" Tsawa Hajja ta daka ma Mama Ladi ta mike tana huci tace "Ke mahaukaciyar wace gari ce Ladi?? maza dauko rubabben akwatinki ki kama hanya ki koma karaye tun raina bai gama baci ba...." Ko rufe baki Hajja bata yi ba suka ga Mayraah ta sulale nan kasa, dai dai shigowar Usman parlon yayi saurin karasawa inda ta fadi, tsabar rikicewa Ammi mance drip din hannunta tayi ta mike tayi kan Mayraah a guje, sauran mutanen parlon ma duk suka nufi Mayraah suna salati, Mama Ladi dai sai gwaggwale ido take a inda take tsaye..... Still on todays discount for the book Mayraah, pay 300 Naira into 👇🏻 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 To be included to group, discount ends today by 12am. Subscribe and read happily. Thank you. [6/11, 5:49 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer na zaune kan kujeran dake kusa da gadon dake dakin asibitin ya jinginar da kansa da kujeran idonsa a lumshe, Usman na tsaye jikin window din dakin yana danna wayarsa, lkci lkci yake daga kai ya kalli saman patient bed din da Mayraah ke kwance, she is being unconscious tun safe sai wajen karfe daya da wani abu ta farka, tana farkawa kuma babu bata lokaci aka mata wani allura shine har yanzu take bacci and this is almost 4pm, motsi yaga tana yi, ya saka wayarsa a aljihu ya nufeta, ya duka a bit closer to her yana kallonta, bude ido tayi a hankali, tana hada ido da shi ta fara kokarin tashi zaune, Usman ya rike hannunta yace "Do not injure ur self, akwai drip a hannunki" Bude ido Maheer yayi da sauri, lkci daya ya mike tsaye holding on to her yace "Are you okay Lil sis?" Mayraah dai sai kalle kallen dakin asibitin take, Maheer ya fahimci she is trying to recall things, ya maidata ta kwanta yace "Lay still, you will be fine in sha Allah Mimi" Bin su Mayraah ta shiga yi da kallo kamar ranan ta fara ganinsu, bayan kanta da yayi mata nauyi har kirjinta ma ji tayi yana mata wani azababben ciwo, dafe kirjin tayi tana son magana amma ta kasa, Maheer dake rike da ita har sannan yace "Kina jin ciwo a nan ne?" Kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta, yasan dole zata ji haka cause she had a terrible panic attack that triggered her Asthma, tun daga gida yayi kokarin reviving dinta har suka taho asibitin aka kwantar da ita giving her the necessary treatment, ya jinginar da pillow din kan gadon da bango sannan ya sa tayi resting a jiki yace "U will feel relieved in sha Allah" Usman ya koma inda yake ya tsaya yana kallonsu, Maheer ya bude flask din da Aunty Mariya ta kawo masu da kayan shayi don ko minti talatin bata yi da barin asibitin ba, yayi making din mata shayi ɗan kadan a cup yayi diluting da bottle water sannan ya mika mata a hankali yace "Ki daure ki sha ko kadan ne sai a maki allura for the chest ache" Bata ce masa komai ba don tayi nisa tunanin da ta tafi, ya zauna gefen gadon yana kallonta, sai da yayi gathering courage kafin a hankali yace "Mimi" ta dawo duniyar tunanin da ta tafi tana kallonsa, yace "Amshi shayin ki sha even if it's just a little" Sauke idonta tayi kasa without responding to him, wayarsa ne ya fara ring a aljihunsa ya ciro ganin Abba ne ke kiransa ya daga ya kai kunne, ya gyada kai yace "Eh ta tashi" Yana fadin haka ya kalli Mayraah yana mika mata wayar yace "Za ki yi magana da Abba" Girgiza masa kai kawai tayi ba tare da ta kallesa ba, ya maida wayar kunnensa a hankali yace "Zan kira ka Abba" Ajiye wayar yayi bayan Abba ya katse yana kallonta, ko bata ce komai ba kasan she is in pain, ya ajiye cup din shayin ya juya ya fita daga ward din don kiran likitan da ya amsheta to make some suggestions on more injections da za ayi mata ko zata samu relief gaba daya, Shi dai Usman na tsaye ya rungume hannayensa yana ta kallonta, ta daga kai ta kallesa suka hada ido, sai kuma ta sunkuyar da kanta hawayen dake makale idonta ya sakko fuskarta, jinginar da kai yayi da bango not knowing what to even say to her, he wish he could take away her pain and grief, Maheer na dawowa tare da likitan wayarsa ya fara ring ya ciro a aljihunsa ya ga Haseenah ce, ta kirasa yafi sau arba'in yau, tun da garin Allah ya waye take kira ko daya bai daga ba a kiran sai ma silencing din wayar da yayi ya bar sa a aljihu, ya bar likitan ya shiga ward din shi kuma ya tsaya daga corridor yayi picking din call din nata, babu ko sallama a fusace ta fara cewa "Yanzu Maheer fisabilillahi yau daurin auren namu guda tun da garin Allah ya waye ko message dinka ban gani a wayata ba balle kiranka? Sannan ban yi fushi ba ni ina ta kiranka amma still ka ki daga min waya alhalin nasan kana gani ba wai baka gani ba? Ko wace amarya ana daura aure angonta ke kiranta yayi mata albishir sannan yayi masu fatan zaman lafiya amma kai babu kira babu message sannan na samu labarin ko daurin auren baka je ba wajen cousins dina, Maheer ko ka mance yau ranar ka ce? Ka mance sau daya ko wani mutum a duniya yake experiencing wannan babban ranan?" Maheer dake ta sauraronta yace "Are you trying to tell me baki san kanwata na kwance unconscious a hospital ba all through today?" Haseenah ta wani hade rai tace "To waye zai gaya min tunda ni dai ba bokanya ba? Kuma ba a gidanku nake ba, how will i know??" Maheer yace "To banda Abba da yayi insisting a daura auren nan yau ban yi niyyar a daura auren ba, because bani da wannan nutsuwar seeing my sister on sick bed....." Haseenah ta zaro ido zuciyarta na tafarfasa tace "Ohh saboda kanwarka bata da lafiya shine ka so cewa a daga daurin auren mu yau Maheer?" Maheer yace "Ke malama kar ki wuce limit dinki, banda ni me biyayya ne ga mahaifina da baza a daura auren nan yau ba am telling you the fact, ta yaya za a daura min aure with my sister unconscious on bed?? If not for my father i don't think that would be possible" Haseenah was shock, don tsabar shock kasa ce masa komai tayi ta ji ya katse wayarsa... Shiga ward din yayi, likitan ya juya yana kallonsa yace "Dr za a shigo ayi mata wasu alluran yanzu, so pls let her take a little thing" Maheer yace "Toh mun gode Dr" Karasawa yayi kusa da ita ya dau shayin yana kallonta cikin kwantar da murya yace "Pls ki sha ko kadan ne Mimi" Girgiza masa kai tayi hawaye na taruwa idonta har sannan bata bude baki tayi magana ba, ya ciro handkerchief dinsa yana goge mata hawayen yace "Don Allah ki sha kin ji" Shi dai Usman na tsaye yana kallonsu, Maheer ya ciro wayarsa dake ringing, ganin me kiransa ya daga ya kai kunne, description din zuwa ward din da suke yayi a wayar sannan ya katse, yana ci gaba da lallabata ta sha shayin, amma taki ko amsa balle ta sha, sai lallabata yake ta sha, bayan few minutes aka bude kofar ward din, duk suka daga kai suna kallon kofar, Mayraah ta dinga kallonsa har ya karaso ciki, gun Usman ya nufa ya basa hannu yana kallonsa suka gaisa, Maheer ya mike daga gefen gadon da yake zaune, ya basa hannu suka gaisa yace "Ya me jiki?" Maheer yace "Alhamdulillah" Mayraah dai har sannan kallonsa take, Ya karasa kusa da gadon a hankali yace "Ya jikin?" Wasu sabbin hawayen suka cika idonta, bai san sanda ya dafa gadon ba murya can kasa yace "No plss, stay strong Mayraah, everything will be alright in sha Allah" Ta sunkuyar da kanta hawayen bai fasa zuba idonta ba, ji yayi kamar ya jawota jikinsa ya lallasheta yanda ya kamata don kukanta karyar masa da zuciya yake tun ba yanzu ba, Wata Nurse ta shigo ward din bayan ta kwankwasa kofar, tana kallon Maheer tace "Ta sha tea din?" Maheer yace "Not yet amma yanzu zata sha" Nurse din tace "Ohk za a mata allura ne i will come back in some minutes time" Tana fadin haka ta juya ta fita, Dr Musharraf ya kalli shayin dake ajiye gefensa a cup, ya dauka ya mika mata yace "Ki sha kadan za ayi maki allura" Ta daga kai ta kallesa, ba musu ta amsa ta kai bakinta a hankali, Maheer felt much relieved da ya ga ta amshi shayin, ya juya ya fita daga ward din don an fara kiran Asr, Juyawa Usman yayi shi ma ya fita, Mayraah ta bi su da kallo, bata san sanda ta ajiye cup din ba ta fashe da kuka, nan da nan hankalin Musharraf ya tashi yace "Plss ki daina kukan nan haka Mayraah, u had a panic attack..." Cikin rawan murya tana kallonsa tace "But where can i get my parent?" Musharraf da jikinsa yayi sanyi sosai yayi shiru yana kallonta, can ya zauna gefenta a hankali yace "Do not be an ingrate Mayraah, har a yanzu Abba da Ammi are your parent, and they will keep on being a parent figure to you" Sosai take kuka cike da rauni tana kallonsa, zuciyarsa ya karaya ya ma rasa abinda zai ce mata, ya jinginar da kansa da bango ya lumshe ido yana wishing he could take all her pains away, Nurse din ce ta dawo ward din rike da alluran da zata ma Mayraah tace "Hope ta sha shayin?" Musharraf ya mike ya dau cup din shayin ya kai mata baki yace "Pls take even if it's little za ayi maki allura" Ba musu ta amshi cup din a hannunsa ta fara kurban shayin da kyar, ya dinga encouraging dinta tana shan shayin har ta kusa shanyewa, daga karshe ta ajiye masa cup din tana girgiza kai tace "Zan iya yin amai" Ya dau sauran shayin ya ajiye kan overbed table dake kusa da gadon, sannan ya kalli nurse din da ta karaso kusa da Mayraah, juyawa yayi ya nufi kofa zai fita, a hankali yaji tace "Baza ka tafi ba ko?" Ya juya yana kallonta kamar yanda take kallonsa ita ma, yace "I will wait outside ta maki alluran" Mayraah ta gyada masa kai, ya fita ya kullo masu kofar ward din, nurse din na gama mata alluran bayan ta fita Musharraf ya koma dakin, hawaye ya gani idonta, da mamaki yace "Injection din kike ma kuka?" Ita dai bata kallesa ba kuma bata ce masa komai ba, ya dinga kallonta, kamar wanda ya tuna wani abu ya juya da sauri yace "An tada sallah, let me go to the mosque" a hankali tace "Will u come back?" Yayi shiru yana kallonta, can yace "Are you afraid of anything?" Ta girgiza masa kai tana share hawayen da yaki tsaya mata cikin sanyin murya tace "I am no longer comfortable" Shiru yayi bayan bayan few seconds yace "Am not leaving you" Daga haka ya juya ya fita, Ta koma ta kwanta maganganun Mama Ladi na mata yawo a kwakwalwarta kamar a lokacin take fadan su, Mayraah bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba tana jin zuciyarta na mata zafi sosai, bata san for how long she have been crying ba taji an bude kofar ward din, ta kulle idonta da sauri, muryar Maheer taji kusa da ita a hankali yace "Mimi" Still taki bude idon kai sai kace bacci take, Maheer ya ajiye fruits din da ya siyo mata outside of the hospital a kan overbed table sannan ya zauna kan Plastic chair yana kallonta don a tunaninsa bacci take, bayan some minutes Usman ya shigo ward din, yana kallon Maheer yace "I will be going home now to check on Ammi" Maheer yace "Ohk..." Daga haka ya fita daga ward din, Maheer ya ciro wayarsa dake vibrate, Tun yana sallah Haseenah ke kiransa, yaga calls goma tayi masa a mintunan da basu wuce 15 ba, ya daga kiran ya kai kunne, babu ko sallama tace "Maheer wai me kake nufi da dinner dinmu ne yau? Naga har anyi la'asar banji kace min ga abokanka nan zuwa da motoci ba" Maheer rasa abinda zai ce mata ma yayi tsabar takaici, Haseenah tace "Hello" Calmly yace "Ina jin ki" Tace "Ohh da kana ji na kayi shiru, wai ko ka manta munce babu African time ne? Nan da awa daya da wani abu fa ya ci ace duk muna can" Yace "Haseenah" Tace "Ina jin ka" yace "Kije ke da kawayenki da yan uwanki ku yi dinner din, i, my relatives, and my frnds won't be available" Haseenah ta wani zaro ido tace "What?? Ban gane me kake nufi ba Maheer" Yace "Abinda kika ji na fada shi nake nufi tunda ba wani yaren daban na yi maki ba, beside nasan Mumy da sisters dinta baza su rasa gaya maki halin da Mimi take ciki ba tunda sun zo duba ta wajen karfe daya ai" a fusace Haseenah tace "Wannan kai ta shafa Maheer don ni babu abinda ya sha min kai, kuma akan wata can bazan ɓata wannan day din nawa ba wallahi, abu dai da sau daya zanyi witnessing dinsa a duk rayuwata shine za ayi min haka? Naga dai ai ba kai kadai bane a gidan da dole sai kai zaka tsaya da ita a asibiti, don me ma wata tsohuwa a danginku bazata zauna da ita a asibitin ta kula da ita ba sai kai?" Maheer dake ta sauraronta yace "Mayraah din kike ce ma wata?" Ta fashe da kuka tace "Nace din Maheer, abinda duk labari ya gama bazuwa a duniya ashe babu abinda ku ka hada da ita er tsintuwa ce ba Ammi da Abba suka haifeta ba..." Maheer ya mike yace "You've successfully cross ur boundary Haseenah, wllh wllh kika sake furta wani kalma akan Mayraah a yau din nan zan datse igiyarki dake kaina, yanzun nan zan datse alaqar da aka kulla mana just some hours ago without second thought and no regrets" Haseenah that was soo shock and speechless ta buda baki tana sauraron abinda yake gaya mata a kunne, yace "Nonsense" Daga haka ya katse wayar, duk wannan abun Mayraah na jin su hawaye kawai ke sauka idonta. Bude kofar ward din aka yi Aunty Mariya ta shigo rike da basket me dauke da abinci a ciki, Maheer da har sannan xuciyarsa ke tafarfasa akan abinda Haseenah ta fada masa kan Mayraah ya nufeta ya amshi abincin hannunta yace "Sannu da zuwa" Aunty Mariya dake kallon Mayraah a sanyaye tace "Ta farka kuwa?" Maheer yace "Ta farka dazu, amma yanzu bacci take an mata allurai ne" Aunty Mariya ta zauna kan kujera duk abun duniya ya taru ya mata yawa ga Ammi ana tunanin za a taho da ita asibiti a kwantar da ita don jikin nata sai a hankali har yanzu, dafe kanta tayi a hankali tace "Sun je sun kwashe kayansu, in gaya maka abun ba mutunci Maheer, ban taɓa ganin matsiyata mara su kirki ma irin mutanen nan ba, sai kaga abinda suka mana wllh, don ma bakin Mama Ladi da wata makociyarku Maman Shafa bakinsu ba shiru yayi ba, abinda suka manta ne kawai su ma basu gaya masu ba, duk da su suka fara sakin maganganu, Mama Ladi ta fara dura masu zagi, abun dai ba dadi kai dai in gaya maka, zuga guda fa suka yo kamar yaƙi wai sun zo kwashe kaya, Allah ya rufa mana asiri an ga Gwal din nan da ban san ya za a kaya yau ba, don ba lallai ma su hakura muje kasuwa mu nemo ba tara mana jama'ar anguwa kawai za su yi, amma anya da amincewar iyayensa yaron nan ya nemi Mayraah kuwa Maheer? Alamu duk sun nuna dama tun farko they were not in support of the marriage kafin wannan abun ma ya billo" Maheer dai yayi shiru yana kallonta don ya ma rasa abinda zai ce, Aunty Mariya na girgiza kai cike da takaici tace "In the other way round ni sai naga kamar rashin auren ma shi yafi alkhairi da dai wannan tashin hankalin da na gani da idanuwana yau..." Bude kofa aka yi Musharraf ya shigo ward din, Maheer ya sauke kansa kasa codedly yace "Do not say anything, shi ne" Aunty Mariya ta juya tana kallon Musharraf don bata san sa ba, ya karaso ciki ya gaisheta da ladabi, a dakile ta amsa ta dauke kai, Musharraf ya ajiye ledan fruits din hannunsa, Maheer na kallonsa ya ɗan yi murmushi yace "Nima na siyo mata, amma naga bacci take" Musharraf yace "Ohk" duk wannan abun Mayraah na jin su kawai ta rufe ido ne kamar tana bacci, amma ita kadai tasan abinda take ji a duk jikinta most especially her chest and her head that is banging, Musharraf ya juya ya nufi kofa cause duk sai jikinsa yayi sanyi ganin yanda Aunty Mariya ta amsa masa gaisuwa ta dauke kai, Maheer yace "Amma ba tafiya zaka yi ba" Mayraah bata san sanda ta bude idonta da sauri ba jin abinda Maheer yace, amma ta daure bata bari ta juya ba balle su gane idonta biyu, banda bugawa babu abinda zuciyarta ya fara yi da sauri da sauri, Musharraf ya ɗan yi murmushi yace "Aa ina waje" Maheer yace "Ohk" Daga haka Musharraf ya fita ya kullo masu kofar, a fusace Aunty Mariya tace "To uban me ya biyota nan yayi mata kuma? Yau naga iskanci" Maheer ya kwantar da murya yace "Aunty shi fa bashi da laifi, dangin Abbansa ne suke ta wannan abun, ba shi ne yace bazai aureta ba, fin karfinsa aka yi a gida, kuma kinga ba shi da yanda zai yi tunda ga abinda iyayensa suka ce" Aunty Mariya ta wani ja tsaki tace "To me zuwansa nan zai kara mana da shi? Gwara kawai yayi tafiyarsa ni bana son ganinsa gaskiya, yayi tafiyarsa kawai ba a bukatansa ya bar mana er mu ta dawo hayyacinta cikin aminci, tun ban bude baki nayi masa magana ba ka sallamesa gaskiya" Maheer dai ya ma rasa abinda zai ce mata ganin yanda ta hasala, Ta ci gaba tace "Wannan ai rashin kunya ne ma, salon ta farka tayi arba da shi abu ya kara lalacewa" Maheer dake neman yanda zai kauda zancen yace "Aunty Hajja fa?" Aunty Mariya tace "Tun dazu in gaya maka ta daga hankali ita zata tafi Bichi banda hanata da aka yi, kasan Badiyyar ta gudu ta tafi can ai, to shine wai take son zuwa ta sanar ma dangin ubanta abinda ta aikata, mun dai hanata don yanzu ba wannan bane a gabanmu, yanda Mayraah zata dawo hayyacinta ta kwantar da hankalinta, ita ma Ammi Allah ya bata lafiya is our major concern now" Maheer ya girgiza kai a ransa yana tunanin abinda zai yi ma Badiyya da za su yi ido hudu da ita, Aunty Mariya ta mike tace "Bari in koma gida wajen Ammi Maheer, in dai ta farka don Allah ka kirani, Hajja ma na son a kawota nace ta bari sai ta farka, karya muka masu ba a barin kowa ya shiga inda take shine muka samu lafiya amma da jama'ar da za su cika asibitin nan ai sai Allah yau" Maheer bai ce komai ba ya rakata suka fita, Aunty Mariya na kallonsa tace "Abba ya zo?" Maheer ya girgiza kai yace "Tun dai wajen karfe biyu da ya tafi" Aunty Mariya bata kuma cewa komai ba har suka fito haraban asibitin, zaune suka tadda Musharraf a karkashin bishiya, Ya mike yace "Allah ya tsare Aunty" Aunty Mariya tayi kamar bata ji sa ba ta shige mota tayi wucewarta, Maheer sai duk bai ji dadi ba, ya nufi Musharraf yace "Let me make some calls, ka ɗan shiga ciki ba kowa" Musharraf yace "Ohk" Maheer ya zauna karkashin bishiyar, Musharraf ya nufi cikin asibitin, Maheer yayi haka ne don yana tunanin ko da ta farka idan ya bata abincin zata ci tunda dazu da ya bata shayi ta amsa a gun sa.... Musharraf na shigowa ward din Mayraah ta juya jin kamshin turarensa, ya karasa kusa da gadon yana kallon drip din da sai a sannan yayi rabi, yayi kasa da murya yace "Are you still feeling much pain in ur chest?" Ta girgiza masa kai, don tun da aka mata alluran taji ya ɗan mata sauki ba kamar dazu ba, ya ɗan kara gudun ruwan, sannan ya bude basket din da Aunty Mariya ta kawo ya bude warmer din abincin, irish porridge ne da yaji hanta sai kamshi yake, Duk da halin da Ammi take ciki hakan bai sa ta mance abincin da Mayraah ke iya ci in dai bata da lafiya ba, haka ta sa Aunty Mariya tayi mata sannan aka mata pepper soup din ƙoda, Mayraah dai sai kallon Musharraf take, ya dau plate ya debar mata abincin ya sa cokali a ciki sannan ya mika mata yana kallonta yace "Plsss ki daure ki ci ko kadan ne" Hawaye ya cika idonta sai a yanzu maganganun da yayi mata ranan da taje kai masa abinci da magani suka dinga dawo mata, she now understands why he said in dai shi bai bar ta ba bata da wani hujjan barin sa, wato tun ba yanzu ba yasan da wannan maganar shine yaki gaya mata, bata san sanda ta fashe da kuka ba ta hade kanta da pillow, Musharraf ya ajiye plate din hannunsa kan overbed table da sauri yace "Are you okay?" Ta dago tana kuka sosai tana kallonsa tace "Why did my parent abandon me? Where can i find them?" Musharraf yace "No Mayraah, don't be an ingrate like i said before, butulci zaki ma su Ammi da Abba? What is it that u lack from them as parents? Love? Care? Or what? Meye basu maki ba a cikin wanda iyaye ke ma 'ya yansu?" Cikin kuka tace "But i need to know my real parent, bazan iya ci gaba da kallon su Yaya Maheer as people that i am not related with ba, i can neva be comfortable any longer, all this years me yasa aka...." Kasa ci gaba tayi ta dinga kuka, Musharraf da duk jikinsa yayi sanyi ya dinga kallonta because he understands her feelings, yanzu jin ta zata dinga yi kamar bare a cikinsu, nothing will ever change that a zuciyarta, kamar fa yanzu ne ace masa ba Mami bace ta haifesa he can't even imagine that, ba ma shi ba, koma waye won't like to imagine that balle har ya faru a kansa, the shock, confusion and disappoinment kadai ya isa ya jefa mutum into depression, ta dafa hannunsa tana kuka sosai amma ta kasa maganar da take son yi masa, nan da nan ta sa idanuwansa suka kada yana jin kukanta har cikin ransa, yayi wrapping hannunsa cikin nata a hankali yace "I will neva let you down Mayraah, ki amince da ni mu je a daura mana aure somewhere else, i will give you all the love and care u deserve in this world, kuma na maki alkawarin i can use my last breathe wajen ganin kin hadu da iyayenki na asali" Ita dai ta kasa cewa komai kuka kawai take, Yace "Kin amince za ki bi ni?" Ta girgiza masa kai da kyar tace "Danginka basu so na even before finding out who i am, za su iya disowning dinka...." Katse ta yayi a fusace yace "For all i care, as far as ba Mami bace zata yi disowning dina, Mayraah a shirye nake da ko wani challenges da zan fuskanta saboda ke a rayuwar nan" Ta goge idonta tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Sai mu je ina?" Yace "Idan an daura mana auren we will sort that out" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, Musharraf yayi kasa da murya yace "Idan Maheer ya shigo u should let him know that u need ur Hijab, nasan zai ce zai je gida ya dauko maki kafin ya dawo i will find a way da za mu bar asibitin nan" Ko rufe baki bai yi ba aka bude kofar ward din, suka sake hannun juna da sauri, ya mike tsaye ya dau plate din porridge din yana mika mata, ta amsa, Maheer ya shigo ward din, ko minti biyu bai yi da shigowa ba Musharraf yace "Let me get something outside" Maheer yace "Ohk" Daga haka Musharraf ya fita daga dakin, Maheer ya karasa kusa da Mayraah dake ta juya abincin hannunta da spoon, she became so uncomfortable da ya dawo kusa da ita, ta ki yarda ta kallesa kamar wani stranger haka take jin sa, a hankali yace "Mimi" Ba tare da ta kallesa ba bakinta na rawa tayi karfin halin cewa "In.. ina son hijab zan yi sallah" Maheer da duk jikinsa yayi sanyi ganin how uncomfortable she is just because he is close to her, cikin sanyin murya yace "Mimi yayanki ne fa" Sai a sannan ta daga ido ta kallesa for the first time..... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur Evidence via 07087865788 ki biya ki karanta hankalinki a kwance bbu hakki. [6/12, 9:24 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer yayi kasa da murya yana kallonta yace "I know you to be a very strong lady Mayraah, kiyi hakuri... This is our destiny and we have to accept it with good faith, amma har yau har gobe u still remain our blood nothing can ever change that" Ita dai ta sauke kanta tana goge hawayen da ya fara sauka idonta a hankali, Ya zauna kan kujeran dake kusa da gadon cikin sanyin murya yace "Pls ki daina kukan nan yana taɓa ni, you know i hate seeing you cry lil sis, and tell me if you are feeling pain anywhere??" Ta girgiza masa kai ba tare da ta kallesa ba amma hawayen yaki tsaya mata, yanzu kenan ita ba jininsu bace kowa ya shaida, Maheer ya kamo hannunta yace "I think we can go home now, zan ci gaba da duba ki a can" Mayraah ta zame hannunta da sauri daga nasa sannan ta kallesa jin abinda yace, he felt somehow da tayi hakan, amma dai a hankali yace "Kilan idan Ammi ta gan ki she will feel much better too, kinsan bata da lafiya and taki a kawota asibiti, she is seriously sick" Mayraah ta sunkuyar da kanta, yace "Idan mun koma gida sai kiyi sallahn tunda babu hijab a nan" Ita dai Mayraah tayi shiru bata ce komai ba, yace "Let me go to the Dr's office yayi discharging dinmu" Ta bi sa da kallo har ya fita daga ward din, yana fita ko 5 minutes ba ayi ba Musharraf ya shigo, ta dinga kallonsa har ya karaso kusa da gadon yayi kasa da murya yace "I just finish speaking with My Mami tace in gaisheki da jiki, i told her baza ki iya waya ba...." Mayraah ta sauke idonta daga kallonsa a hankali tace "Yaya Maheer yace za ayi discharging dinmu yanzu mu tafi gida fa" Tana fadin haka ta fashe da kuka cikin rawan murya tace "How will i face them all after all this?" Da damuwa Musharraf yace "No Mayraah bana son kina wannan kukan it's hurting me, and keep in mind that they are still ur family and will remain ur family, ki gode Allah da ya sa hannunsu kika fada kika taso cikin aminci tare da su, and apart from love and care, they also gave u all the goodies of this life, u neva lacked anything tun tasowarki tare da su, they gave u quality education, they took u as theirs without second thought, tunanin haka kadai ya ci yasa ki cire komai a ranki and continue looking at them as ur own family and appreciate them, i only want us to go far away from everyone saboda nasan su kansu a yanzu baza su bari a daura mana aure ba after all this that happened, amma i have no intention in rabaki da su forever....." Bude ward din aka yi Maheer ya shigo ya karaso ciki yana kallon Musharraf da yayi shiru, Maheer yace "We are being discharged now..." Musharraf yace "To maa sha Allah, Allah ya kara mata lafiya...." It took Maheer not less than 10 mins ya kai duk abubuwan da Aunty Mariya ta kawo can parking space ya saka su a booth din motarsa, Musharraf ya cire mata drip din dake makale hannunta ganin kamar ta fada duniyar tunani yayi kasa da murya yace "Nothing about you can ever change in my mind, i still love you more than you can imagine Mayraah, get well soon so we can sort our self out, i think we shouldn't rush matters" Ita dai kallonsa kawai take, Maheer ya dawo dakin tare da Dr din da yayi discharging Mayraah, Dr din na kallonta murmushi kwance fuskarsa yace "I can see you are feeling much better now" Ta sunkuyar da kanta yace "Sauran injections dinki Dr Maheer zai dinga maki a gida ya ci gaba da baki duk kulawan da ya kamata" Dr Musharraf ya daga kai ya kalli Maheer suka hada ido, shi ya fara dauke idonsa, likitan ya ci gaba yace "Sannan ki cire duk wani abinda ya dameki a zuciya ba a san musulmi da haka ba kin ji, idan kina da damuwa ne u have ur brother's that care soo much about you, ki gaya masu duk wani damuwarki they will always be there for u from they way naga sun damu da lamarin ki..." Dr Musharraf ya juya ya fita daga ward din, Mayraah ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, likitan dai ya gama bata shawarwarin da ya kamata amma fa duk bata san abinda yake cewa ba tunda dai Musharraf ya fita, likitan ya kalli Maheer daga karshe yace "To ango, za ku iya tafiya da kanwarka... That's all i have to say to her, Allah Ubangiji ya tsare gaba, ya kara mata lafiya, kai kuma Allah ya baka zaman lafiya da amarya" Maheer yayi masa godiya sosai, likitan ya bar ward din, Maheer na kallon Mayraah dake kokarin sauka daga saman gadon ya karasa ya mika mata hannu da nufin taimaka mata ta sauka, ta dauke kai taki basa nata hannun har ta sauka, a hankali take tafiya don sai taji jikinta babu kwari, and she is still feeling a bit dizzy, yana biye da ita a baya suka fita daga ward din, tun da suka fito haraban asibitin take bin ko ina da kallo amma bata ga alamar motar Dr Musharraf ba balle shi, shi kansa Maheer shi yake ta dubawa da ido a compound din amma sai yaga motarsa ma bata nan hakan ya tabbatar masa ya tafi, Maheer dai bai ce komai ba har suka iso gun motarsa ya bude mata back seat yana kallonta, ta sunkuyar da kanta ta shiga ya kulle, lokaci daya hawaye ya cika idonta ta jinginar da kanta jikin kujeran motar, ya zaga ya shiga front seat ya tada motar suka bar asibitin, sai da suka hau saman titi yayi dialing number Musharraf, sai da ya kusa katsewa Musharraf ya daga, Maheer yace "Ka tafi ne Dr? I can't find ur car at the space provided for parking" Dr Musharraf yace "Yea, i received an urgent call shi yasa na tafi" Maheer yace "Ohk, muna hanya za mu tafi gida yanzu in sha Allah" Dr Musharraf yace "To Maa sha Allah, Allah ya tsare" Maheer yace "Ameen" Daga haka ya katse wayar, Mayraah dake sauraron conversation din nasu jikinta yayi sanyi sosai hawaye ya kasa daina zuba idonta, all through the ride babu wanda yace komai cikin su, kowa da tunanin da yake a ransa, sai da Mayraah taga sun shigo layinsu ta hade kai da gwiwa hawaye masu zafi na sauka idonta, yanzu kenan kowa a anguwan nan yasan wacece ita? Everybody now knows she is not the daughter of her supposed parent, kowa yanzu yasan ita bata da asali kenan, tunanin nan yasa ta fara jin numfashinta na sama, har Maheer yayi parking a compound bata san yayi ba, ya zaga ya bude back seat yana kallonta cikin sanyin murya yace "We are home Mimi" Ta dago kanta da kyar, ganin yanda take numfashi ya kamo hannunta da sauri yace "Are you okay?" Bai jira me zata ce ba ya sauko da ita daga motar yana kallonga da damuwa yace "Me yasa kike haka Mimi, kina son ki daura ma kanki wani ciwon ne? Why are you doing this to us pls?" Ya jinginar da ita jikin motar har ya ga numfashin ya fara dawo mata dai dai, ya hade rai yace "Why are you doing this plss Mimi?" Ta sunkuyar da kanta tana sauke numfashi a hankali, ya kama hannunta ya nufi visitors part saboda mutane na gidan har sannan kasancewar za a kawo Haseenah zuwa bayan Magrib tunda dai an daura aure babu abinda ya rage, Babu kowa babban parlon Maheer ya karasa cikin Bedroom din dake cikin parlon yana rike da hannunta, ya zaunar da ita gefen gado ya durkusa gabanta cike da damuwa yace "Don Allah Mimi ki cire duk wani abu da kika sa a ranki yake damunki, we all felt what u feel today, kamar yanda aka boye maki wannan abun mu ma haka aka boye mana, duk kusanci na da Abba bai taɓa gaya min wannan maganar ba, kuma so ne yasa suka mana haka Mimi, don Allah kiyi hakuri mu yi accepting fate din nan da hannu bibbiyu mu gode Allah, but keep in mind nothing can change the fact cewar ke jininmu ce har gobe har abada, you still remain our lil sis" Shiru tayi tana kallonsa hawaye masu zafi na sauka idonta, yayi kasa da murya yace "Say Alhamdulillah Mimi" Ta sauke idonta a hankali tace "Alhamdulillah" Maheer ya mike yace "Let me get u ur hijab kiyi sallah" Daga haka ya juya ya fita daga dakin, ta zamo kasa tana son ganin bata fashe da kukan da ya taho mata ba amma ta kasa, kuka take kamar ranta zai fita abubuwa iri iri na yawo a kanta, yanzu kilan da tun farko tasan fate dinta kowa yasan wacece ita da ba a fasa aurenta da Musharraf ba, amma saboda su Abba sun boye asalin wacece ita shi yasa duk abun nan suka faru, jin an bude kofar dakin ta daga kai tana kallon kofar, Usman ya shigo rike da Hijab dinta, suna hada ido ta sunkuyar da kai, ya karasa har inda take, after standing for like 20 seconds, ya duka gabanta ya ajiye mata hijab din yana kallonta, ita dai har sannan bata daga kanta ba, yayi kasa da murya yace "You say Alhamdulillah in all situation.... And that is among the etiquette of being a devoted muslim, but get this straight..., nothing can alter the fact of u being our sibling, we love u and will continue loving u the way we do forever, Ammi and Abba remains ur parent now and forever" Mayraah ta daga kai tana kallonsa, ya sa hannu ya goge mata hawayen idonta ya sakar mata murmushi yace "That's it, we love you no matter what" Ta sauke idonta kasa, yace "Ki shiga toilet kiyi alwala, it's almost Magrib, i will be going to mosque too" Yana fadin haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, tun farkawanta a asibiti sai yanzu tayi feeling a bit relieved daga damuwar da suka yi layi a zuciyarta, a hankali ta mike ta fito parlor ta shiga bandakin dake ciki don yin alwala. Mayraah ta idar da margrib bayan duk ta rama sallolin dake kanta tana linke darduman da tayi sallan Aunty Mariya ta shigo parlon, duk bata san Mayraah na gidan ba sai yanzu da Maheer ya sanar mata bayan ya dawo daga masallaci, dama Usman kawai ya gaya ma tun dawowarsu, Mayraah ta sunkuyar da kanta ganin Aunty Mariya, Aunty Mariya ta nufeta ta rungumeta cike da farin ciki tace "Welcome back home daughter, Maheer bai gaya min kun dawo ba sai yanzu, hope you are feeling much better now?" Mayraah ta gyada mata kai, Aunty Mariya tace "Toh Alhamdulillah, mun gode ma Allah, naga heater din bandakin nan baya yi bari in kawo maki ruwan zafi kiyi wanka ki canza kaya, ki ci abinci yanzu" Mayraah dake kallonta a hankali tace "Aunty, Ammi fa" Aunty Mariya tayi murmushi tace "Kina wanka in kin ci abinci zaki je ki dubata, yanzu bacci take" Aunty Mariya ta zaunar da ita kan kujera tace "Let me get you the hot water dear" Daga haka ta fita daga parlon, dai dai nan yan kawo Haseenah suka iso gidan a motoci biyu, da yake family din nata masu hankali ne sun san abinda ke faruwa ba a wani yi zugan kawota ba, don bai fi mutum bakwai bane suka taho da ita.... Aunty Mariya bata tsaya an amshi Haseenah da ita ba don duk hankalinta na kan Mayraah, tuni ta kai mata ruwan zafi bangaren visitors, ta surka mata ruwan da kanta a bandaki, dama ta taho mata da sosonta da shower gel da towel, bata bari kowa yasan Mayraah na gidan ba, bayan Mayraah ta shiga wanka ta sake komawa cikin gida ta dauko mata kayan sawanta da kayan shafe shafe, nan parlon ta ajiye mata don ta gani idan ta fito daga bandaki sannan ta sake komawa cikin gida hado mata abinci da shayi, she is so happy yanayin da ta ga Mayraah kamar ba ita dazu ba.. Mayraah ta fito parlon daure da towel tana kallon kayan da Aunty Mariya ta ajiye mata kan kujera da turarrukanta at the same time tana tunanin inda zata samu waya ta kira Dr Musharraf, bude kofar parlon aka yi ta juya taga Usman, lkci daya ya juya ya bi gefen Maheer dake bayansa shi bai kai ga shigowa parlon ba, Maheer ya bi sa da kallo ganin ya fito, bai dai ce masa komai ba ya shiga parlon shi ma, Tuni dama ta durkusa kasa tana zare ido, Maheer yace "Ohh sorry, finish wearing ur clothe" daga haka ya juya ya fita, ta kwashe kayan ta shige daki da sauri. Haseenah na zaune dakin da Hajja da Mama Ladi suke an shigo da ita ta gaishesu Aunties dinta uku na zaune gefenta, Hajja dai ta sa mata albarka sannan tayi mata nasiha irin ta manya a takaice, daga karshe tana murmushi tace "Allah kuma ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Allah ya sa gidan zamanki ne na har abada, Allah ya albarkaci auren...." duk yan dakin suka amsa da "Ameeen ya Allah" Mama Ladi ta ajiye kwanon tuwon da take ci tace "Sai dai kuma anyi biki duk bama cikin kwanciyar hankali muna cike da alhinin abinda ya same mu, don da an biye ta Mashir ma ɗaga bikin nan za ayi sai xuwa duk sanda Allah ya nufa, don bakina da nasa yace min lafiyar kanwarsa ta fiye masa wannan auren shi, ta yaya zai yi aure kanwarsa na gadon asibiti, mu dai muka ce ya rufa mana asiri kar ya maida mu kananun mutane a idon duniya ayi ta yamadidi da mu, magana ta zama biyu a kanmu, ga na Mera ga na Mashir" Sake baki Hajja tayi tana kallonta cike da takaici, ba Hajja kadai ba duk yan uwan Ammi da suke dakin haka suka sake baki suna kallon Mama Ladi cike da mamaki, Haseenah ma ta dinga lekota ta cikin mayafi tana jin zuciyarta na bugawa don ita kanta ai ya gaya mata makamancin haka a waya, wato ashe da gaske ma yake??? Mama Ladi ta dau ƙashin dake kwanon abincinta tana gwagwiya tace "Mu kanmu tun safe bamu gansa ba yana can asibiti da Mera, ko er farar shaddan biki da angwaye ke sa wa ma ban ga ya sa ba duk yau, yana ta yawo da wata jallabiya ruwan hoda ko guga babu sai daga baya nake samun labarin ko wajen daurin auren ma bai je ba, Yo banda uban nasa ma yace a taho dake yau a in don ta shine tarewarki ba yanzu ba sai sanda Mera ta farfado kin ga kuma ba rana kenan, ai yau kam mun ga jarabawa ganin idonmu, don haka nake baki shawara ki zama me kwantar ma mijinki da hankali akan wannan iftila'i da ya fada mana, ai kinsan an fasa auren Meran ko? To in gaya maki dazu matsiyatan dangin shegen da zata aura suka zo kwashe kayansu da suka kawo nan, da jefe jefe muka rabu da yan iska, nayi masu wankin soso da sabulu nace masu gayyar tsiya" Maman Shafa na kallon Aunties din Haseenah tace "Kamar baku je bangaren Ammi ba ko? Muje in kai ku nasan yanzu ta farka tunda anyi magariba" Tana fadin haka ta mike, Aunties din Haseenah da sai kallon Mama Ladi suke, har dai suka daga Haseenah suka bar dakin, Mama Ladi ta bi Maman Shafa da harara ta ajiye ƙashin hannunta cikin kwano tace "Wai ita kuma wannan katuwar dake yawo da kodadden zani da yagunannen hijabi wacece ita fisabilillahi? Naga sai shigar min hanci take da kudundune tun da garin Allah ya waye, banda taron biki me zai hadani waje daya da ita mata kamar almajira kaya duk a yamutse" Rai bace Hajja tace "Ladi ke yanzu baza ki saka ma bakinki linzami ba, wllh kar ki bari in maki koran kare daga gidan nan, kin isheni kuma haka tsakani da Allah, wannan wani irin bala'i ne baki gyara abu sai dai ki tabarbare lamari" Mama Ladi tace "Wai kiyi ta cewa zaki min koran kare yaya, ni fa gidan Mamuda nake ba gidan kowa ba, daga magana sai a juya min a fassara abinda nake nufi ta wata tsigar? Ko don anga ban haihu ba balle in aurar da jika?" Tana fadin haka ta fashe da kuka ta jawo mayafinta tana matsar kwalla ta mike ta fice daga dakin da kwanon abincinta. Mayraah na biye da Aunty Mariya suka shigo parlon Ammi, babu wanda ya lura da shigowarsu gidan don ta baya suka shigo ta bangaren Abba, Ammi na zaune kan darduma bayan Hajiya Safiyya ta cire mata drip din hannunta tayi sallah har ta idar, ta daga kai tana kallon Mayraah babu ko kiftawa don bata ma san sun dawo gida ba, nan da nan Mayraah taji hankalinta ya tashi don daga fuska zaka fahimci Ammi na jin jiki, ta karasa da sauri ta durkusa gabanta ta riko hannunta tace "Ammi are you this sick??" Ammi ta rungumota jikinta amma ta kasa cewa komai, kuka kawai Mayraah take a jikinta, Ammi ita ma hawaye ne ke sauka idonta, Babu wanda yace masu komai a dakin, cause bond din exactly irin na uwa da ɗan ta, Aunty Mariya dai na tsaye bakin kofa ta ma kasa karasowa cikin parlon duk jikinta yayi sanyi, Kwankwasa kofar parlon aka yi, Maman Shafa ta leko tace "Za a shigo da amarya wajen Ammi" Aunty Mariya tace "Ohk to ana zuwa" Aunty Mariya ta nufi Ammi da damuwa tace "Plss kiyi composing din kanki Ammi, za a shigo da Haseenah" Aunty Mariya na fadin haka zata janye Mayraah daga kusa da Ammi a hankali Ammi tace "Ki bar ta, su shigo kawai ba komai" Aunty Mariya da Hajiya Safiyya suka yi mamaki sosai don fa tun safe Ammi bata yi ma kowa magana sai dai ta bi ka da ido kawai, Aunty Mariya ta koma tayi masu iso har cikin parlon don dama an shimfida tsadadden carpet babba, Haseenah da Aunties dinta suka zauna, Mayraah dake makale jikin Ammi ta daga kai tana kallonsu, cike da karfin hali Ammi ke amsa gaisuwarsu da ya jikin da suke mata, Haseenah kuwa sai leko Mayraah take ta cikin gyale don sarai ta ganeta, nan taji bacin ranta ya ninku, wato saboda wannan er iskar aka yi bikinta kamar ana zaman makoki yau ko? Frnd din Ammi ce tayi ma Haseenah nasiha wanda Ammi zata yi mata, amma duk Haseenah bata san me take cewa ba don gaba daya hankalinta na kan Mayraah da tunani iri iri da take yi a kanta.... Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788.... In kinsan baki biya for subscription na littafin nan ba kiji tsoron Allah ki zo ki sallami jikar inna marainiya. *Assalamualaikum everyone... ina sanar da ku cewar muna saida samosa WRAPS masu gardi da crispy 50 pieces for 2000, Spring rolls wraps 50 pieces for 2800, i assure u Samosa and spring rolls wraps din masu kyau da inganci ne Plss patronize us via*👇🏻 09014996620 Thank you ❤️🙏 +234 901 499 6620 [6/13, 7:29 PM] Khaleesat Haiydar💖: Bayan fitarsu Haseenah da yan uwanta Mayraah ta daga kai tana kallon Ammi cikin sanyin murya tace "Ammi ko in maki shayi?" Aunty Mariya tace "Eh kawo mata" Mikewa Mayraah tayi Ammi ta bi ta da kallo har ta fita daga parlon, Hajiya Safiyya na kallon Ammi tace "Kin dai ga Mayraah Alhamdulillah ta samu lafiya, don haka kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki ki cire komai a ranki don jininki ya samu ya dawo dai dai" Da damuwa Aunty Mariya tace "Ai shine, just forget everything that happened we should face reality, there is surely reason for everything a rayuwar nan" Aunty Mariya na kai wa nan ta mike ta shiga dakin Ammi ta dauko babban duvet zata kai dakin da aka sauke su Haseenah da wa enda suka kawota.... Mayraah na kitchen tana dafa ma Ammi shayi da yaji kayan kamshi ga madaran gwangwani da ta juye ciki yanda dai tasan Ammi ke son ayi mata, ita kadai Ammi ta fi son tayi mata irin shayin, Absentmindedly ta ke aikin da tunani iri iri a zuciyarta, zuwa yanzu kuma ji tayi zuciyarta ya kasa yarda wai ba su Ammi suka haifeta ba, she is now just finding it hard to believe, ta yaya ma za a ace ba Ammi ce ta haifeta ba bayan ita kanta ta san irin son da Ammi ke mata, or are they pranking her? Ji tayi an bude kofar kitchen din, ba tare da ta juya ba ta gane wanda ya shigo don haka yake bude kofa a ko ina, daga baya kuma taji kamshin turarensa, bayan some seconds ta dan juya ta gansa ya dau plate yana zuba abinci, ta kashe gas din sannan ta dau tea pot din ta fara tsiyaya shayin cikin cup, ganin zai fita daga kitchen din ta juya ta kallesa suka hada ido sai kuma ta sunkuyar da kai tace "Don Allah ina son inyi amfani da wayarka" Yace "Yana daki" Daga haka ya fita ya kulle kofar, Mayraah ta ɗan yi goge goge a kitchen din sannan ta wanke hannu ta dau shayin Ammi ta fita, zuwa yanzu babu kowa a gidan sai baƙin da suka zo daga nesa, duk aka bi ta da kallo har ta haura sama and that made her so uncomfortable, yanzu kallon ba er gidan ba ake mata kenan, tana shiga parlon Ammi ta durkusa gabanta ta ajiye mata shayin tana kallonta ta zauna gefenta, cikin sanyin murya Ammi tace "Nagode" Maheer ne ya shigo parlon, ya zauna kujera yana kallon frnd din Ammi ya gaisheta, ta amsa da fara'a tace "Ango ka sha kamshi" Ya ɗan yi murmushi ya kalli Ammi yace "Ammi ya jikin" Ta dau shayin da Mayraah ta ajiye mata tace "Alhamdulillah" Yace "Allah ya kara maki lafiya" Tace "Ameen" Yana kallon shayin gabanta yace "Wannan kamar shayin Mimi" Frnd din Ammi tayi dariya tace "Ai kam yanzun nan taje ta yo sa a kitchen, ni ma kamar ince a tsammin" Mayraah ta kalleta tana murmushin karfin hali tace "Akwai saura bari in debo maki" Hajiya Safiyya tace "Aa zan je da kaina in debo, ke da ba lafiya gareki sosai ba" Mayraah ta sunkuyar da kanta tana wasa da darduman da Ammi ke zaune, Maheer dai sai kallonta yake, bayan few seconds yace "Kin ci abincin Mimi?" Ta daga kai tace "Na ci" Yace "Okay ina jiranki dakin Usman" Yana fadin haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita. Haseenah dake zaune kan gado da kawarta Zaliha dake mata magana kasa kasa ta fusata cikin daga murya tace "To wai ke sai ma kin bata bakinki sai kace baki san ni ba Zaliha" Kanwar mamarta Hajiya Farida dake zaune kasa inda aka masu shimfida da sauran sisters dinta ga abinci iri iri da aka dire masu ta daga kai ta kalli Haseenah rai bace tace "Wai ke wace irin mahaukaciya ce mara kamun kai kina daga mana murya a gidan surkai? Sannan ba nace ki dau mayafin nan ki rufe jikinki ba tunda ba daina shigowa suka yi ba, wato sai kin gama gwada ma kowa ke fitsararriya ce ko?" Haseenah ta hade rai tace "Aa ni gaskiya Aunty zafi bazai hallaka ni ba a banza, ai ba nan ya kamata a zo a jirge ni ba kamar wata mara galihu" Aunty Mama ta kyabe baki tace "To nima dai shi na gani, na zata in kin gaida surkar taki da kakarsa gidanki kuma za mu kai ki, amma sai naga an kawo mu daki anyi shimfida an dire abinci ga mayunwata, a ina ma aka taɓa haka? Aa ni ban taɓa ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, Aure duk ba wani armashi kamar auren dole, ni wllh sai nake ganin kamar ma ba wani sonta yaron yake ba ita ce kawai ke haukanta a kansa, atoh tunda gashi ya fi ba matsalar gidansu Muhimmanci a kanta" Aunty Farida dai ta tabe baki tace "Ba tace taji ta gani ba, mu kuma meye namu, kina jin abinda tsamurarriyar tsohuwar can ta gama fada a kunnenmu ai, me yafi wannan walakancin? Ga Salmanu bawan Allah da ya nace mata kememe yarinyar nan taki wai bai yi boko ba sannan ba shi da kyau da qualities din da take so, to wa ke ta wani kyan banza yanzu in dai mutum na da nera meye kuma wani kyau, duk shekara fa Salmanu sai ya je hajji har ma ya biya ma wasu, gashi ba wai zata zauna da kishiyar bane tunda har ya nuna mata ginin da yake mata zai ajiyeta ita kadai, kuma gidajensa sun fi biyar a garin kano, ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba yafi wannan da ta makalema arziki, shi wannan ina ga ubansa ne kaɗai ke da arzikin ma, duka duka nawa ne albashin likita" Bude kofar dakin aka yi duk suka yi shiru, Mama Ladi ta shigo tana rafka uban sallama, Haseenah ta fara kiciniyar yafa gyalenta ta rufe fuska da sauri, Mama Ladi na washe hakora ta dafe gwiwa tace "Sassannunku da hutawa fahh, in ji dai bakwa bukatan komai ko? Abincin ma idan bai isheku ba sai a kwaso maku sauran dama don ku aka girka, Ko katifa za a karo maku ku baje nan kasa?" Haseenah sai hararanta take ta cikin mayafi don har taji tayi mugun tsanarta, Aunty Mama na kirkiran murmushi tace "Aa hakan ma ya isa Babaa, mun gode sosai wllh" Mama Ladi tace "To bari a buda maku tagogi yanda iska zai shigo maku a wadace ba algus" Tana fadin haka ta tafi ta fara bude windows din har da net din jiki duk ta wangale sai ga su tsirara suna hango waje, duk suka dinga bin ta da kallo har ta gama ta fice daga dakin, Aunty Fauziyya ta rike haɓa tace "Anya tsohuwar nan na da lafiya ma kuwa, wannan ai sai sauro ya kashe mu kafin gari ya waye, ji wani shegen buda window fa da tayi kamar an sa ta, ga Ac a kunne meye na bude mana window" Aunty Mama ta ja tsaki ta mike ta tafi ta kullo windows din tana cewa "Wallahi in dai naga babu alamar kai ta gidanta gobe da safe to tafiyata zanyi ba da ni za a zauna gida nan har yamma ba kamar wata mara abun yi..." A hankali Mama Ladi ta bude kofar dakin da Hajja ke ciki tana lekawa don tun dazu da suka yi baram baram ta fita bata sake komawa dakin ba sai yanzu, ganin yanda Hajja tayi tagumi ya sa ta karasa ciki da sauri tace "Lafiya yaya da wannan uban tagumin? Naga jikin Ammin ai da sauki daga can ma nake yanzu haka har muka ɗan yi hira da ita, dake Meran na jikinta in gaya maki kamar ba ita bace ke kwance tun safe rai a hannun Allah, anya akwai shegen da zai iya raba Ammi da Meran nan kuwa naga wani azababben soyayya take mata, ba don ba don yarinya bace Meran ai da sai ince asiri ta ma Ammin" Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "Ladi ba nace maki haka kawai su Nura baza su ki zuwa daurin auren Mahir ba??" Mama Ladi tace "Wanene kuma Nura?" Hajja tace "Kanin mahaifin Badiyya mana wanda take wajensa a Bichi" Ladi tace "Aiho wnn guntun me hanci wargajeje dai da na sani?" Hajja tace "Ashe wai Badiyya zuwa tayi ta ce ma dangin mahaifin nata wai an daga bikin gaba daya sai zuwa bayan karamar sallah" Mama Ladi ta saki salati tana tafe hannu tace "Amma yarinyar nan anyi tantiriyar er iska" Hajja tace "Haba Ladi ki daina zaginta don Allah, shiriya za mu yi ta nema mata kawai, to na kasa hakuri yanzu na sa aka kira min lambarsa inji dalilin rashin zuwansa daurin aure sai yake sanar min gashi gashi abinda Badiyya tace masu ai, nayi salati hankalina ya tashi ainun, ban boye masa ba nan na labarta masa duk abinda ke faruwa da abinda ake zargin yarinyar nan taje ta aikata mana, yanzu gobe yace min da safe zai dauko Badiyyar su zo nan har da Garba yayansa" Mama Ladi ta saki baki da karfi tace "Wani zargi?? abinda kowa ya tabbata ya kuma shaida ita ce ta aikata wannan abu zaki ce zargi, wllh ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Badiyya ce ta aikata wannan zunubin, kuma gwara su taso keyarta ayi ta ta kare" a fusace Hajja tace "Gaskiya Ladi idan baza ki dinga yayyafa ma lamari ruwan sanyi ba to ki dinga jan bakinki kiyi shiru, ke duk wani fitina kin san yanda zaki tada shi a rayuwar nan?" Mama Ladi ta kyabe baki ta nemi waje ta zauna, Hajja tace "Sannan ni tsakani da Allah fargaban zuwansu da ita nake, kowa dai yasan yanda Usman da Maheer suka kullaceta abun ba kyau, kuma kinsan Usman dama tun asali ya tsaneta kada a zo da ita ya illata er mutane mu shiga uku...." Mama Ladi ta mike tsaye da sauri tace "Kin gan ki ko? To me kike nufi a takaice? A kyaleta a zuba mata ido kada a hukuntata kenan ta ci bulus?" Hajja tace "To hukuncin me kuma? Abinda aikin gama ya riga ya gama, kawai a dai ja mata kunne yanda ya kamata a gargadeta ayi mata jan ido, yarinyar nan fa marainiya ce, ba uwa ba uba" Mama Ladi tace "Ko daga kasa aka tonota karewar rashin uwa da uba sai an mata hukunci dai dai da abinda ta aikata don uwarta...." Bude kofar dakin aka yi Aunty Mariya ta shigo tana kallon Hajja tace "Gani Hajja" Hajja tayi kasa da murya tace "Ammin na iya lallabowa ta zo nan yanzu? Naga tana da baƙi kuma magana nake son maku" Aunty Mariya tace "Toh bari in je in gaya mata, zata iya zuwa ai" Hajja tace "Sannan har Maheer da Usman su zo" Aunty Mariya tace "In ji dai lafiya Hajja?" Hajja tace "Lafiya lau, duk dai ku zo" Aunty Mariya tace "Toh bari in masu magana" Daga haka ta juya ta nufi kofar, Hajja ta juya inda Mama Ladi ke tsaye tace "Ai kin ga gwara haka dai ko?" Wayam ta ga wajen... Mama Ladi na kallon Maheer da Usman tace "Don haka kashe wutan dakin kawai za ku yi kamar kun kwanta kada wanda ya fita wllh in da hali ma ina fita ku sa makulli, ni wallahi na ma fara zargin anya ba Hajjan bace ta turata ta aikata tsiyar nan? Aa gaskiya na fara tsoron Hajja kuma haka, dama tun asali an san na fita tsoron Allah tun muna yara" Usman da Maheer dai kallonta kawai suke, Maheer yace "Gwara da kika zo kika sanar min babu inda zanje" Mama Ladi tace "Atoh dai, dama shi Usuman tace azzalumi ne tun Badiyya na jaririya yake cutarta kiris ya rage wataran ya kasheta aka kama sa, Badiyyar da tsakaninsu bai fi wata 7 ba ko shidda, to ina ruwansa da ita kuma" Usman ya ci gaba da danna wayarsa dai bai ce komai ba, Mama Ladi tace "Dama shine nace bari in lallabo in zo in gaya maku kuyi ta kanku, babu gaskiya ko kadan a lamarin Hajja" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, tana fita Usman ya mike ya sa ma dakin key, ai ko haka Aunty Mariya ta zo ta gaji da buga kofar babu wanda ya bude mata cikin shi da Maheer, Mama Ladi na komawa daki Hajja tace "Ina kika je Ladi?" Mama Ladi na kallon Ammi dake zaune kasa ta sunkuyar da kanta tace "Fyace majina na tafi yi a tsakar gida daga nan na leka makota ina ta masu ban gajiya kin san haka ake yi" Hajja ta maida dubanta kan Aunty Mariya da Ammi jin sun yi shiru bayan ta gama masu jawabinta, can Aunty Mariya tace "Haba Hajja, yanzu kina nufin shikenan sai a zuba ma Badiyya ido tayi ta abubuwa baza a dau wani kwakkwaran mataki a kanta ba?" Mama Ladi ta kyabe baki ta tafi gefen gado ta zauna, Ammi kam hawaye ne ke sauka idonta duk da kanta a sunkuye yake, Hajja ta fashe da kuka tace "To ya ku ke so mu yi ne?? Badiyyan nan fa ba bare bace, jininmu ce babu yanda muka iya da ita, ai hannunka baya rubewa ka yanke ka yar, addu'a kawai za mu dinga mata Allah ya shirya mana ita" Mama Ladi tace "Amma dai anya Hajja ba ke kika aika Badiyya tayi mugun abun nan da tayi ba yanda naga kina ta kakkare zancen nan, kamar kina tsoron a tona maki asiri ke ma..." Hajja ta kalleta sai ta rushe da sabon kuka tace "Allah ya isa tsakanina dake Ladi, kuma asuban fari na yi ki dau akwatinki ki koma inda kika fito, bana bukatar ki a nan kuma, har abada kar ki sake dawowa inda nake" Mama Ladi ta mike ta nufi kofa tace "Jama'a sai su ce basa son gaskiya kiri kiri, kuma kiyi ta cewa in koma karaye in koma karaye to dangin uwa gareni a can ko na uba, daga dai aure ya kai ni can miji ya mutu ya bar ni yau shekara goma sha biyu, to ina ruwana kuma da wani karaye, Badiyya ce dai sai an mata hukuncin da ya kamata don ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba zata iya kashe mutum, ke kuma da kike daure mata kugu idan ba ayi hankali ba sai ta iya zama ajalinki, ni tsoronta ma nake yanzu wllh, duk wanda zai iya lalata aure babu abinda bazai iya aikatawa ba a duniya, kuma Mamuda ne kadai ya isa ya koreni a gidan nan" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, Hajja dai kuka kawai take, cike da karfin hali Ammi tace "Shikenan Hajja in sha Allah maganar nan ta wuce, babu me tada sa kuma, har su Maheer din zan masu magana, sannan kamar yanda kika bukata na maki alkawarin Mahmud ma bazai ji wannan maganar ba in sha Allah, Allah Ubangiji ya shirya mana ita" Hajja na share hawayenta tace "Ameen, Allah ya maki albarka Hajarah" Aunty Mariya kasa cewa komai tayi tsabar bakin ciki da takaici, can ta mike ta fice daga dakin, Hajja ta kalli Ammi tace "Ki tashi ki koma dakinki, Allah ya maki albarka, Allah ya baki lafiya ingantacce" Ammi tace "Ameen" sannan ta mike ta fita daga dakin, downstairs ta sauka don she needs to find a place tayi kukan nan ko zata ji sanyi a ranta, ta shiga dakin baƙi dake parlor ta tadda Aunty Mariya tayi tagumi, Ammi ta zauna dakin ta fashe da kuka tana girgiza kai tace "Shekara kusan ashirin da biyu kenan ake a haka, sau dayawa ina yin abinda nake ne don kada Hajja taga kamar ina fifita Mayraah da ban haifa ba akan Badiyyah da take jinina, don Hajja mahaifiyata ce nasanta ciki da bai, sai ku ga kamar ina goyon bayan Badiyyah a ko da yaushe amma ba a san duk don a zauna lafiya nake yin haka ba tunda gani za ayi na fifita Mayraah a kan er kanwata uwa daya uba daya, yanzu dai kinga yanda ta bi ta kakkare ta rufe wannan maganar ko?" Aunty Mariya da zuciyarta ke tafarfasa tace "Kuma wllh kada kice ma su Maheer komai, Allah ya kawo Badiyyar gobe da safe su fara ball da ita tun daga bakin gate" Ammi tace "Ki rufa min asiri Mariya, tun da tace in ja masu kunne gwara in ja masu babu ruwansu duk su zuba ido kawai, Allah shi yasan dai dai" Wajen karfe tara da rabi Maheer ya bude kofar parlon Ammi ya sameta zaune da Hajiya Safiyya ga plate din abinci a gabanta, yanxu kam she looks much better tun da gashi har tana cin abinci, ya zauna saman kujera yace "Ammi ya jikin?" Ammi na kallonsa tace "Alhamdulillah" Shiru yayi, yana son tambayar Mayraah amma ya kasa, can dai ya mike daga karshe ya fita, a stairs ya hadu da Aunty Mariya tana haurowa sama yace "Aunty Ina Mimi?" Aunty Mariya tace "Tana dakin Ammi" yace "Okay" Aunty Mariya tace "Wai ka ci abinci ma kuwa Dr?" Yace "Zan ci" Daga haka ya koma parlon Ammi, Bedroom dinta ya nufa direct ya bude kofar ya shiga, kwance ya sameta kan gado idonta a lumshe har ta fara bacci, ya karasa kusa da gadon ya zauna gefenta yana kallonta, hannu ya kai forehead dinta yaji her temperature is a bit high, ta bude ido da sauri suka hada ido, sai kuma ta mike zaune ta matsa daga edge din gadon ba tare da ta bari sun kara hada ido ba, yace "Kin ci abinci?" Ta gyada masa kai, yace "Ur injections and medicine" Ta girgiza kai tace "Aa maganin kawai zan sha" Yace "Ai maganin guda daya ne, kuma alluran ya kamata a maki" Mikewa yayi ya fita daga dakin, ba a dau lokaci ba ya dawo da ledan dake dauke da alluran da magani, tana kallonsa ganin ya fara hada alluran, tayi gathering courage tace "Zan yi alluran da kai na" Ya kalleta a bit surprise, Bata sake barin sun hada ido ba, Bayan few seconds ta sake cewa "Kawai idan ka gama hadawa ka bani inyi" Still shi dai bai ce komai ba, tun daga sanda ya zama likita har zuwa yanzu shi ke mata allura idan bata da lafiya, yawanci every month end sai yayi mata alluran cramps, ya ajiye syringe din bayan ya rufe sannan ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo, ita kanta duk jikinta yayi sanyi, Yana fitowa parlor ya kalli Hajiya Safiyya da yake nurse ce, yace "Mama ana jirana a waje yanzu, ga alluran da za ayi mata can na sa a syringe" Daga haka ya fice daga parlon Ammi ta bi sa da kallo, Hajiya Safiyya ta mike ta shiga dakin, bayan ta gama yi ma Mayraah alluran ta fito, sai a sannan Mayraah ta lura da wayarsa da ya ajiye bedside drawer, ta dauka tayi searching number Musharraf sannan tayi dialing, a kashe ta ji wayar, lokaci daya jikinta yayi sanyi ta ajiye wayar ta koma a hankali ta kwanta da tunani iri iri a ranta... Washegari wajen karfe tara da rabi Aunty Mariya ta shigo parlon baƙi da sallama duk aka amsa mata, kallo daya tayi ma Badiyya dake zaune kasa ta sunkuyar da kai kamar algunguma ga Hijab har kasa a jikinta, Aunty Mariya ta nemi waje a parlon ta zauna ta gaida yan uwan mahaifin Badiyya da kanwarsu Hajiya Murja dake zaune parlon, ko minti ashirin ba ayi da zuwansu gidan ba, dama Aunty Mariya sai da ta tsaya ta gama sallaman su Haseenah da yan uwanta with breakfast sannan ta shigo parlon bakin shi ma don kada Hajja tace bata je bane banda haka da ko keyarta baza su gani ba, Hajja na zaune kasan carpet tayi tagumi, Ammi ma na parlon a zaune, sai Maheer da zuciyarsa ke ta tafarfasa, shi kam Usman dama kin zuwa yayi, Mama Ladi kuma Hajja tace in ta shigo bata yafe mata ba, Alhaji Nura ya daka ma Badiyya tsawa rai bace yace "Baza ki bude baki kiyi magana ba kina bata mana lokaci" Ta fashe da kuka me karfi tana bubbuga kafa tace "Wallahi kawu nace maku ban san komai kan zancen nan ba, kaji har na rantse, ni babu wanda nabi na kai ma wani takarda, a ina nasan su? balle in kai takarda?" Kuka take sosai tana rantse rantse bata san zancen ko wani takarda ba ita, Alhaji Garba yace "To a ina kika samu labarin an daga aure har kika gaya mana?" Cikin kuka tace "Matar yaya Maheer kawata ce ita ta kirani take ce min an daga aurensu ni kuma sannan ina Bichi, kilan kawai bata son in zo bikinta ne, zuciya daya na yarda da abinda tace min ni kuma na gaya maku, amma ni ban kai ma kowa takarda ba, to ma a ina nasan gidajensu? in kuma ana ganin karya nake a kai ni gidajen da suka ce an kai masu sai su fadi ko ni ce na kai masu, kawai don an ga ni marainiya ce bani da kowa sae Allah" Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka har da kifa kai a carpet tana shessheka kamar ranta zai fita, Aunty Mariya tsabar mamaki ta kasa rufe baki tana kallon Badiyya, Maheer ji yayi kamar ya tashi ya tattakata a wajen ya rufeta da duka, Ammi kuwa dama bata dago kanta ba, Hajja na matsar kwalla tace "Ni dama ina ta tunanin ta inda za ace Badiyya tasan gidajen mutanen nan da suka ce an kai masu takarda, Badiyyar da kowa yasan babu inda take zuwa daga gidana sai Bichi sai gidan kawarta wato matar Maheer da aka daura aure jiya, don ko gidan nan wllh sai nayi da gaske take zuwa, amma to an bi ance ita ce ta dinga kai ma jama'a takarda...." Kowa dai yayi shiru a parlon, Maheer yayi da ya sanin zaman nan da ake yi da shi, he wish bai shigo ba, kuma banda bai son daga hankalin Ammi babu abinda zae sa yayi shiru a wajen, Aunty Mariya tayi saurin mikewa tace "Lahh na fa daura abu a kitchen Ina zuwa..." daga haka ta samu ta fice daga parlon don kar takaici ya kar ta..... Bata san yanda aka karke ba dai daga karshe sai ga Badiyya ta shigo main parlor Hajja na biye da ita a baya tana gaya mata dakin da su Haseenah suke, Badiyyah sai wani hade rai take tana kumbure kumbure, kuma ko gaida Aunty Mariya bata yi ba ta haura sama, sai a sannan ta sauke wani bayanannen ajiyar zuciya tana murmushi ta nufi dakin da su Haseenah suke tana bude kofar ta saki guda.... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 *Assalamualaikum everyone... ina sanar da ku cewar muna saida samosa WRAPS masu gardi da crispy 50 pieces for 2000, Spring rolls wraps 50 pieces for 2800, i assure u Samosa and spring rolls wraps din masu kyau da inganci ne Plss patronize us via*👇🏻 09014996620 location kaduna.... Thank you ❤️🙏 +234 901 499 6620 [6/14, 7:15 PM] Khaleesat Haiydar💖: Badiyyah na shiga dakin da su Haseenah suke bakinta har kunne ta gaida Aunties din Haseenah sannan ta ɗare saman gado ta zauna kusa da Haseenah da Zaliha tana kyalkyala dariya ta ba ma Zaliha hannu suka cafke, sannan ta juya tana kallon Haseenah ta rike haɓa tace "Amarsu ta ango, kin ga yanda kika yi kyau kike wani glowing kuwa? anya Maheer zai gane ki idan ya ganki irin wannan canji haka? Ke wai me ya samu wayarki ne nake jin sa a kashe duk sanda zan kiraki" Haseenah da ta hade rai ta sauke ajiyar zuciya tayi kasa da murya yanda Aunties dinta baza su jiyo ta ba tace "Badiyya duk ke kika ja bikina ya dawo kamar na wata gantalalliya mara galihu, ban taɓa ganin warce aka ma irin wannan auren da aka min ba ko a kauye, kawaye na sai dariya suke min a bayana saboda cika bakin da na dinga yi akan bikin nan, daga karshe wae ace babu wani occasion da aka yi, a whole of my wedding? gown din dinner da na ci burin sa wa ya tashi a banza a hofi, banda Zaliha dake tare da ni da depression ya kama ni wllh" Tana kai wa nan ta fara matsar kwallan baƙin ciki, Badiyya ta ɗan kyabe baki tace "Ni duk ba wannan zancen ba, ban ga kin turo min kudin Stuff din nan ba har yanzu abu kusan kwana uku yau fa" Haseenah tayi mata wani shegen kallo a fusace tace "Ai kya bari a fitar da ni daga gidan nan tukunna dai ko? Wato ina gaya maki matsalata irin ke bai ma shafe ki din nan ba alhalin duk ke kika janyo wannan abun dake faruwa, tun fa jiya har yau ban sa Maheer a ido ba a matsayinsa na mijin da aka daura min aure, ko damuwa ya gan ni ma kamar baya yi" Zaliha ta sauke ajiyar zuciya tace "Kema Badiyya yanzu ba lokacin wani magana bane, kwantar mata da hankali za ki yi before anything" Badiyya ta taɓe baki tace "To ba dai tace ta ji ta gani ba, duk yanda na so ta hakura da Maheer din nan Allah ya bata wani Haseenah taki fahimtata, don daga karshe ma gaba ta dauka da ni, ɗan uwana ne fa, kuma baza ta ce min ta fi ni sanin mugayen halayyarsa ba, kawai mu dai fatan alkhairi za mu maki... Yanzu dai naji Hajja na gaya ma Uncles dina zuwa nan da sha daya za a tafi kai amarya gidanta...." Haseenah tayi tagumi murya can kasa tace "Badiyya duk ba wannan ba, wllh tun shekaranjiya hankalina ya kasa kwanciya, bazai kuma taɓa kwanciya ba in har da yarinyar nan Mayraah, na kasa samun sukuni idan na tuna matsayinta yanzu...." Badiyya ta rike haɓa tace "Yanzu nake samun labari ashe dai ta dawo daga guduwan da tayi, in dai kan wannan karamar alhakin ce ki kwantar da hankalinki da kafarta zata sake guduwa na har abada kuwa, wai baki yi trusting dina bane, tunda har na san yanda na bi aka fasa auren da Dr Musharraf kinsan ai babu abinda bazan aikata ba, haba ashe shi yasa kwata kwata na tsaneta tun tana karama, dama babu abinda muka hada da ita er tsintuwa ce kawai warce bata da asali, wa ma ya sani ko cikin shege uwarta tayi ta haifeta sannan ta jefar da ita ta gudu, da gani kasan ba er halaq bace yarinyar, shine saboda rashin tsoron Allah har ake fifitata a kai na a family, ai kam wannan duk ya kare yanzu tunda na gano wacece ita" Sauka Badiyya tayi daga kan gadon ganin flask ta bude tace "Ni fa ko karyawa ban yi ba muka taho...." Aunty Fauziyya tace "Ai ko duk an fita da sauran kayan kumallon sai dai kije kitchen" Badiyya tace "Bari in hado shayin" Badiyya na fitowa daga dakin Aunty Mariya kuma na kokarin shiga don sanar ma yan uwan Haseenah yanzu za a tafi kai ta gidanta su shirya, Badiyya taki barin ta hada ido da ita tayi saurin barin wajen ta sauka downstairs, Usman ta hango zaune kan dinning area, lkci daya ta juya ta koma sama ta fasa zuwa kitchen din..... Kaya kawai Badiyya ta canza ta fess uban turare ta yi daurin ture ka ga tsiya tana taunar cingam, hannunta rike da Mayafinta da handbag suka fito daga daki tare da yan uwan Haseenah da ita kanta Haseenar dake sanye da lapaya ta rufe rabin fuskarta, sai da aka fara kai ta tayi ma Ammi sallama sannan aka kai ta dakin Hajja, Badiyya ta zauna kusa da Hajja kamar zata shige jikinta, bayan Hajja ta kara yi ma Haseenah nasiha yan uwanta suka fita da ita daga dakin, Badiyya ta mike tana kallon Hajja tace "Kinga ki bani makulli kawai, don daga can gida zan tafi bazan dawo gidan nan ba gaskiya" Hajja tayi kasa da murya tace "Aa Badiyyah, ke dai ki dawo don sai gobe za mu tafi gida gaba daya har Ladi, so nake in kara ganin yanayin jikin Ammi yau" Badiyya ta wani murguda baki tace "To ina Mama Ladin?" Hajja tace "Kilan tana can gantali gidajen makota, daga zuwa unguwan mutane ta shiga gida yafi a kirga yanzu haka" Badiyya tace "Gaskiya ni dai gwara in koma Bichi in har da ita za mu tafi gida, wai ba an gama bikin ba me kuma take jira?" Hajja tayi kasa da murya tace "Banda abun ki ai jiya aka yi biki Badiyya, nasan nan da gobe zuwa jibi zata koma ita ma" Badiyya ta juya ta fice daga dakin tana murguda baki... Aunty Mariya na kallon Mayraah dake dakin Ammi tace "Ni ma kaina ai ba zama zan yi ba, ana kai ta zan juyo" Ammi dake zaune dakin tana jin su tace "Ki bar ta kawai Mariya tunda tace baza ta ba, kinga ita ma ba dadin take ji ba ai, daga baya idan Allah ya nufa sai taje ganin dakin amarya" Aunty Mariya tace "To shikenan sai na dawo" Dama tayi insisting ne Mayraah ta shirya su tafi don bata son tayi feeling neglected duk gidan an tafi kai amarya babu ita, don yanzu kamar taki sakin jiki a gidan, komanta sanyi sanyi take kuma a dar dar kamar dai bakuwa, tuni duk gidan aka watse kai Haseenah dakinta, Mayraah damuwar ta ya kasu kashi kashi yanzu amma babban abinda yafi tsaya mata a rai shine yanda bata samun Musharraf a waya, tun wayewar gari ta kirasa ya fi a kirga da wayar Ammi amma sai taji wayarsa a kashe, tana gama kiransa dama take clearing kiran a call log kar Ammi ta gani tunda tana da numbersa... saboda yanda ta sa abun a rai har ji tayi kirjinta ya fara mata ciwo, tana kwance bayan azahar idonta a lumshe duk da ba bacci take ba Ammi ta shigo dakin, Ammi ta zauna kusa da ita tana shafa kanta a hankali tace "Bacci kike daughter" Mayraah ta bude idonta sannan ta mike zaune tana girgiza mata kai, Ammi dai sai kallonta take, Abba ne ya karaso cikin dakin, lkci daya Mayraah taji zuciyarta ya karaya bayan sun hada ido, amma tayi kokarin ganin hawayen da ya makale idonta bai taho mata ba, Abba ya karaso har kusa da gadon he couldn't even look at her in the eyes again, bayan shirun few seconds yayi karfin halin cewa "How are you feeling daughter?" Ta kasa amsa masa sai gyada kai kawai tayi don tana buda baki tasan zata fashe da kuka, Ammi ta kalli Abba a hankali tace "Bacci take ne, anjima in ta tashi sai ku yi magana..." Abba dai bai ce komai ba, bayan few seconds ya juya ya fita daga dakin, Ammi ta mayar da ita ta kwantar tace "Or you need anything?" Mayraah ta girgiza mata kai hawaye na gangaro mata, Ita ma Ammi tuni hawayen ya kawo idonta, Mayraah ta riko hannunta tace "Ammi kin sha maganin?" Ammi ta gyada mata kai sannan ta mike ta fita daga dakin tana goge hawayen dake zuba idonta. Bayan Magrib Mayraah na zaune dakin Ammi ta idar da sallah, zuwa sannan babu kowa gidan duk yan biki sun watse, Ammi na parlonta ita ma ta idar da sallan tana zaune kan darduma, Mayraah taji Ammi na cewa "Baka tafi gidan ba bawan Allah?" Muryar Maheer taji yace "Zan duba jikin Mimi ne" a hankali Ammi tace "Naga ma bata cin abinci yanzu, ko maganin cin abinci za a bata?" Maheer yace "Bari in tambayeta ko da abinda take so ne" Ammi bata ce masa komai ba ya karasa cikin dakin, tun da ya shigo Mayraah bata bari sun hada ido ba, ya zauna gefen gado yana kallonta don tunaninsa addu'a take saman darduman, jin bai ce komai ba ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, ta sauke idonta tace "Ina yini" Yace "Kin gama?" Ta gyada masa kai, yace "To tashi mu je ki fadi abinda kike so a siya maki" Ta ɗan kallesa tace "Ai na ci abinci" Shiru yayi yana kallonta, don komin abincin da ta ci bata taɓa ƙin bin sa ya siya mata ko ice-cream or shawarma in zai fita siya ma Ammi fruits da daddare, jin yayi shiru ita dai taki dago kanta tana ta wasa da fingers dinta, she was soo uncomfortable, a hankali taji yace "You are now trying to tell the world i am no longer ur brother Mimi, and u forgot i have been ur brother for good 22 years, me yasa kike son canza hakan yanzu?" Hawaye ya kawo idonta, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya dago ta, ta kwace hannunta tana hawaye, tsayawa yayi yana kallonta da mamaki, cikin rawan murya tace "Kayi hakuri" Ya ma rasa abinda zai ce mata, bayan few seconds a hankali yace "Mu je" Bata bari sun hada ido ba tana goge hawayen dake sauka idonta ta nufi kofa ya bi bayanta, suna fitowa parlor Ammi ta dinga kallonsu, yace "Ammi i want to get her something sai in dawo da ita yanzu" a hankali Ammi tace "Ka bar er mutane fa a gida Maheer..." Yace "Ai kawayenta suna nan, kuma sai naje ma zan maida su various houses dinsu" Ammi ta kalli Mayraah tace "To sai kun dawo Mimi" yana gaba ta bi bayansa suka fita daga parlon, mamaki bai cika Maheer ba sai da yaga all through the ride ko tari bata yi ba, Mayraah da har sai ya gaji da labarinta idan suna mota tare, sosai ya ji abun ya damesa yanzu, yayi parking dai dai wani eatry yana kallonta a hankali yace "Shawarma da me zan siya maki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Anything" Bayan few seconds ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido, yana dawowa motar ya ajiye mata abinda ya siyo mata sannan suka bar wajen, duk da hanyar da ta ga ya nufa da ita bata ce komai ba, bayan tafiyar kusan minti ashirin yayi parking dai dai gate din gidansa, wayarsa ya dauka yayi dialing number Haseenah tana dagawa yace "Tell ur frnds ina jiransu zan ajiye su gida yanzu" Da mamaki Haseenah tace "Ban gane ba, ina abokan naka? Kana nufin yanzun ma baza a siyi baki ba da sauransu?" Maheer yayi shiru kafin yace "Bakin wa za a siya?" A fusace Haseenah tace "Ni wallahi na gaji da walakancin da kake min Maheer dama ba sona kake ba ka aureni?" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, yace "No.... it's not like that Haseenah, kinga frnds dina yawanci a Abuja suke so duk sun koma saboda aiki, kiyi hakuri kawayen naki su fito in maida su gida, sannan su fadi nawa za a basu sai su turo account number" Cike da shagwaba Haseenah tace "Za ku yi magana da Zaliha idan sun fito" Yace "Alright" Daga haka ya katse wayar, juyawa yayi ya kalli Mayraah, if it was before yanda tayi shiru haka da ya ja hancinta amma yanzu kam bai yi hakan ba, yayi kasa da murya yace "Tunanin me kike?" A hankali tace "Bacci nake ji" Yace "Ohk, yanzu zan maida ki gida ki kwanta, hope kina shan magungunan da na siyo maki tunda baki son alluran?" Ta gyada kai tace "Ina sha" Yace "Ohk" kawayen Haseenah hudu suka fito daga gidan har da Badiyyah, Maheer ya hade rai ganinta, Zaliha ta bude front seat tana washe baki tace "Ango ka sha kamshi" Gaba dayansu suka yi turus ganin Mayraah gaban motar, barin Badiyyah da ta bude baki da mugun mamaki, Maheer yace "Ku shiga in ajiye ku gida, it's getting late" Zaliha ta kirkiri murmushi ta koma back seat tare da sauran frnds din nasu, Badiyyah ta zaro ido tace "Aneesah na baki wayata kuwa?" Aneesah tace "Aa" Da sauri ta juya ta nufi cikin gidan tana cewa "Lahhh ban ciro sa a caji ba kenan" Badiyya na tuntube ta koma dakin Haseenah, tsaye ta ganta gaban madubi tana gwada kayan baccin da zata sa tana murmushi, Badiyyah tace "Ke kinsan da wa Maheer yake a cikin mota kuwa?" Haseenah ta juya da sauri tace "Aa" Badiyyah tace "Wllh er tsintuwar nan muka gani zaune gaban motarsa, wato duk maganganun da muka maki kan cewar ki ja masa aji yau akan abubuwan da ya dinga maki a biki har kin watsar kin wani kwaso kayan bacci kin zube kina zaba ko? To ai shikenan" Sosai gaban Haseenah ya fadi jin warce Badiyya tace mata sun gani a motar Maheer, ta dinga kallon Badiyyah ko kiftawa babu, tuni Badiyyah ta juya ta fice daga dakin ta koma compound tana ma mai gadi sallama sannan ta fita kofar gida, still tayi bakin gate ganin babu motar Maheer alamar ya tafi ya bar ta. Wajen karfe tara da rabi Mayraah na tsaye a kitchen kusa da gas tana dafa ma Ammi shayin da ta saba yi mata, dafa shayin take amma gaba daya hankalinta baya jikinta, rashin samun wayar Musharraf ya dameta sosai don har wani zazzabi take ji yanzu, to ko dai he doesn't need her anymore because of who she is, tunanin hakan yasa taji hawaye ya kawo idonta, sai yanzu ta sake tabbatar da son da take ma Musharraf na gaske ne, tana kokarin zuba shayin a cup bayan ta gama taji an bude kofar kitchen din ta juya, sosai gabanta ya fadi ganin Badiyya ce ta shigo, Mayraah tayi saurin dauke kanta ta ci gaba da abinda take tana goge idonta zuciyarta na bugawa, dawowar Badiyya kenan gidan tun bayan da Maheer ya tafi ya bar ta, Badiyyah tayi wani dariya tana kallonta tana tafe hannu, can ta rike haɓa tace "Ohh wai Shege ya fi ɗan masu gida, to in ji dai yanzu kin gane cewar matsayina da naki ba daya bane a family dinmu, don ke ba kowa bace facce tsintattciya walakantacciya warce karuwar uwarta ta wuragar da ita a gefen masallaci! Banda ma rashin sanin wacece ke ai da baza ki fara soyayya da Musharraf ba don yafi karfinki nesa ba kusa ba, shima kuma ko a mafarki bazai so ya kula irin ki ba mara asali, dama ance rashin sani yafi dare duhu, ai irin su Dr Musharraf sai mu masu asali gaba da baya yan dangi yan gata ba wa enda aka jefar tun suna tsummam haihuwa ba...." Mayraah kasa juyowa tayi sai hawaye kamar an bude famfo, ihun da taji Badiyya ta kwala ne yasa ta juyawa da sauri, da kafa ya sa ya kwasheta sai ga ta rigijib a kasa sannan ya kulle kofar kitchen din, Mayraah ta tsorata sosai ga koma gefe tana kallonsa, tuni ya zare belt dinsa ya fara lafta ma Badiyya ta wajen kan belt din kamar an aikosa, Ihu Badiyya take iya karfinta tana kokarin tashi amma ta kasa tsabar yanda belt din ke shigarta ta dinga birgima kamar macijiya tana cewa "Na shiga uku na lalace, Hajjaaaa" Mayraah da duk ta gigice ta tafi kofar kitchen da zai yi leading dinka zuwa backyard din gidan zata bude ya daka mata tsawa yace "Kina budewa zan hada da ke" Makalewa tayi jikin kofar zuciyarta na bugawa tana kallon yanda yake dukan Badiyya ba kakkautawa, bude kofar kitchen din Aunty Mariya tayi a gigice don tana saukowa parlor ta fara jiyo ihu kamar daga kitchen, a sama kuma ba a jin komai, Badiyya na ganin Aunty Mariya cikin gigicewa ta dinga cewa "Wayyo Aunty ki shigo ki taimakeni zai kasheni, wallahi kasheni zai yi ki kira har da su Hajja da Ammi" Aunty Mariya na ganin abinda ke faruwa ta kullo kofar kitchen din tana murmushi ta koma parlor ta zauna, Sai da yayi mata lilis ya farfasa mata duk jikinta da belt har bata iya motsin kirki tsabar dakuwa sannan ya duka yana kallonta cikin husky voice da idanuwansa da suka canza launi yace "Ko kallon banza ki sake yi mata a gidan nan ki ga" Daga haka ya tsallaketa ya nufi kofar kitchen da Mayraah ke kokarin budewa ya hanata, da sauri ta koma gefe ta basa waje gabanta na faduwa, ya bude kofar ya nuna mata waje yace "Fita mu je" Ba musu ta fita da sauri, shi ma ya fita ya kullo kofar..... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 aji tsoron Allah a sauke hakkin marainiya😥 amma fa ba irin maraicin Badiyya ba🙄 [6/19, 12:43 AM] Khaleesat Haiydar💖: Badiyya ce ke rusa kukan azaba ga bakinta yayi suntum tana biye da Hajja dake rike da hannunta suka nufi kofa, Mama Ladi ta ajiye kwanon abincin hannunta tace "O'o Hajja ba haka zaki ce ba, yaran nan fa duk daya suke a wajenki, ni wllh abinda yasa hankalina bai tashi ba saboda nasan ba wani can bare bane yayi mata wannan mugun bugu haka, ɗan uwanta ne na jini fa, zuciya ce kawai ta debesa yayi mata wannan aika aikan, kai har ma da sharrin shaidan don ni nasan ba haka yayi niyya ba" A mugun fusace Hajja dake huci tace "Babu abinda ta hada da shi banda uwarsa da take kanwar uwarta, don haka kar ki sake ce masa ɗan uwanta Ladi" Aunty Mariya dai na makale dakin baƙi tana jiyo duk abinda ake a parlon amma taki fitowa, Mama Ladi ta kyabe baki ta jawo kwanonta ta ci gaba da tsotsan ƙashin hannunta tace "To ke yanzu da kika figeta haka a ina za ku samu abun hawa da talatainin daren nan, wannan ai sai mai adaidaita sahun ya tsorata ya zata barauniya ce ta tsere daga hannun jami'an tsaro.... Wai anya ma Badiyya ce wannan ko dai kawai haukanmu muke, ya za ayi daga ɗan duka baki yayi suntum haka kamar leben rakumi?" Mama Ladi na kai wa nan ta tuntsire da dariya har da kwanciya tana kyakyatawa tace "Hajja duka ne fa an riga an nakada mata shi babu yanda muka iya sai dai muce Alhamdulillah, komai Allah yayi dai dai ne, kawai hakuri zaki yi idan Allah ya kai mu gobe da asuban fari sai ki ja ta ku tafi duk inda za ku amma yanzu dai ku rufa mana asiri don kuna fita idan Allah ya sa ku ka hadu da yan sanda cikin daren nan duk bayanin da zaki masu baza su gamsu ba, cewa za su yi sata taje tayi aka mata haka...." Cikin kuka Hajja ta katse ta tace "In kwana su karasa kasheta Ladi? In kwana saboda gidan ubana ne nan din ko kuma gidan ubanta? Ae wllh da dai ni da Badiyya mu kwana gidan nan gwara ko titi ne mun je mun yi shimfida mu kwanta, kuma ba laifin kowa bane laifina ne don dazu da safe da ta bukaci in bata makulli da na bata da duk haka bazai faru da Marainiyar nan ba, sannan da ace nayi tafiyata tun safe naje nayi abinda zai fi min alkhairi a gidana da hakan bai faru da Marainiyar ba, ko dabba baza ayi ma wannan dukan da aka mata ba, ki dubi jikinta fa duk a farfashe, dubi bakinta fa, kafarta kuwa da kyar idan bata yi targade ba, yanzu idan dangin ubanta suka ce sai sun dau mataki akan wannan abinda aka mata ni na isa in hanasu? Ko barawo dai baza ayi ma wannan tsinannen dukan na rashin imani ba balle ita da ba sata tayi ba ba kuma ɗan mutum ta kashe ba kawai tsabar zalunci da zuciyar kafirci yasa aka mata haka, kuma in dai burin mutane ne cin mutuncin maraya su walakantasa to wllh wllh baza su wanye lafiya da duniya ba, sannan ko ma wanene ya mata wnn aika aikan Allah ya isar mata cikin gaggawa, babu yafiya tsakanin ta da koma waye, ni ma kuma ba yafe masa zan yi ba tunda amanata ce ita" Ammi dake tsaye parlon ta kasa cewa komai sai hawaye, gaba daya jikinta yayi sanyi, she is soo speechless, Mama Ladi dai sai fama take da ƙashin hannunta tana lullumshe ido tana kallon Hajja, Hajja ta figi hannun Badiyya dake dingishi tana rusa kuka har sannan, za su fita daga parlon, Ammi tayi karfin halin bin su tace "Don girman Allah Hajja kiyi hakuri ki bari...." A fusace Hajja ta dakatar da ita tace "Ba abinda zaki ce min, inyi hakuri in bari a kasheta ki huta 'ya yanki su huta? kuma kije ki rungumi warce zaki runguma da ta fiye maki Badiyya tun asali dake da yaranki, ai tun ba yanxu ba dama kike nuna baki hada komai da Badiyya ba, ni kadai ce dolen Badiyya a duniyar nan tunda ni na haifi uwarta...." Mama Ladi ta buda baki tace "Kaji wata magana kuma, to wai ita Badiyyar er gwal ce da baza a doketa ba, ni wani irin duka ne ban sha a wajenki ba ina karama duk da bani da uwa bani da uba a lokacin, kin dubi maraicina da kike nakada min duka? yarinya munafuka kawai mara tsoron Allah kiyi ta daure mata kugu, wato dai duk wannan tsiyar da ta tafka so kika yi a zuba mata ido saboda ga ta munafukar Marainiya ko? To wai ma uban waye ba maraya ba a zamanin nan na yanzu, ni iyayen gareni? Bakina fa da nata na bata labarin yanda aka samo Mera da zuciya daya wllh, sae ga labari a duniya an kasa a faranti ana ta yawo da shi, to wani marayan arziki ne zai yi wannan mugun abu? A marayun ma Badiyya er iska ce kawai...." Hajja tace "Ke ma Allah ya isa wannan kazafin da kika mata Ladi, in sha Allahu sai Allah ya saka mata, za kuma ki gani a kwaryar ki" Mama Ladi ta kyabe baki ta koma ta ci gaba da taune ƙashinta tana hararan Badiyya, Hajja tace "Kuma ina ce dai saboda ni kika zo garin nan ko? To ki koma inda kika fito ba a bukatarki, bana son ma kice zaki kara zumunci da 'ya ya na, ni da na zame maki dole kiyi da ni amma ba 'ya yana ba...." Hajja na kai wa nan ta fice daga parlon tana rike da hannun Badiyya, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "To ko dai wiwi Badiyyar ta banka mata ne" Ammi dai ta kasa ci gaba da tsayuwa ta zauna kan kujera tana kuka sosai, Mama Ladi tace "Ko ma dai waye yayi mata wannan jibgar Allah yayi masa albarka, kyau ace ma ya cire mata haƙora biyu na sama da na kasa ta dawo kamar mujiya...." Mayraah dai ta gaji da zaman parlon baƙi ga baccin da ta fara ji, she is been sitting for almost an hour now a parlon, ta kalli agogo dake nuna karfe goma da minti arba'in, sannan ta ɗan kalli inda yake kwance, waya yake amma duk da babu wani tazara tsakaninsu bata jin abinda yake cewa, she just notice he is on phone call, a hankali tace "Ina jin bacci Yaya" Ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya mike zaune ya katse wayar, after few seconds ya tashi, tana ganin haka ta tashi ita ma, ya nufi kofa ta bi bayansa, sai da ta fito parlon ya kashe Ac da wutan parlon sannan ya kulle kofar ya fara sauka porch din building din tana biye da shi, suna shiga main parlor din gidan suka tadda Ammi da Mama Ladi har sannan a parlor, ita dai Aunty Mariya daga karshe dama kwanciyar ta tayi a dakin baƙin ta fara bacci don bata da strength din fara lallashin Ammi, kallo daya yayi masu zai wuce sama fuskarsa a murtuke, Mama Ladi tayi saurin cewa "Yauwa Usuman don Allah nace gobe zaka kai ni gidan Mashir kasan ba dani aka je kai amaryarsa ba, daga shiga makota in fito na tarar wai an tafi kai amarya, kaga Mashir ae bazai ji dadi ba ace ban je ba ko? To ina gudun kar ya kullace ni shi sa gobe da sassafe zaka kai ni gidan" Usman yace "Allah ya kai mu" Daga haka ya wuce sama, Ammi ta bi sa da wani kallo shi kam yaki kallon ma inda take dama, Mama Ladi tace "Kya wani bi sa da harara, me yayi maki? Ance maki kowa ne baya son gaskiya kamar ke da uwarki?" Mayraah ta juya a hankali ta tafi kitchen don sake dafa ma Ammi shayin da take dafa mata dazu. Ammi na zaune Bedroom dinta da safe, waya ne kare a kunnenta cikin sanyin murya tace "Wallahi ban yi wani baccin kirki ba jiya" Daga daya bangaren Maheer yace "Pls ki kwantar da hankalin ki Ammi, in sha Allah zuwa anjima zan je can gidan nata, ke ba sai kinje ba tunda ranta ya baci haka" Da damuwa Ammi tace "Amma shi Usman bai duba halin da nake ciki ba ya kara dauko min wannan maganar bayan yasan halin Hajja? Me yasa bazai yi considering din condition dina ba?" Maheer yace "To kika san abinda tayi masa, ke dai kawai ki bar zancen, shi da ba shiga harkanta yake ba kika ga yayi mata haka ai kinsan dole da abinda tayi masa" Ammi tace "Ya wuce wannan abinda tayi a kan auren Mayraah? Bayan shi ai ba wani abu da ya hadata da shi na ga, burinsa kawai ya ga ya janyo min magana, shekarun baya haka yarinyar nan ta nuna tana sonsa ita in ba shi ba bazata yi aure ba, amma duk irin lallaba Usman da nayi daga karshe ai kaga abinda yayi mana gaba daya, shi yasa har yanzu Hajja ke kullace da shi ba kuma fita ranta abun yayi ba don har gobe cewa take saboda Usman taki tsayar da miji, sannan kwanaki kiri kiri ya daukota a motarsa ya ki, babu abinda Hajja ta manta bata gaya min a waya ba akan wnn abun da yayi, to yanzu kuma kaga irin dukan da yayi mata, haka kawai ya ja min magana wajen Hajja" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ni dai yanzu duk ki bar zancen nan ki kwantar da hankalinki Ammi, ki samu kiyi breakfast ki sha drugs dinki ki kwanta, in sha Allah anjima za mu yi magana idan na je gidan" A hankali Ammi tace "Naji Mama Ladi na cewa zata je wajen naku yau, to bana son inyi magana ita ma ta juya min zance ne yasa ban ce mata komai ba, amma ai bai kamata daga tarewar yarinya a fara mata sintiri ba" Maheer yace "Ai ba komai don ta zo Ammi, ita da ba garin take ba, it's okay" Maheer ya juya jin an bude kofar dakin nasa, Yace "Za mu yi magana Ammi sai anjima" Ammi tace "To ka gaida Haseenar" Yace "In sha Allah" Sai kuma yayi maza yace "Mayraah fa?" Haseenah tayi still bakin kofar dakin bayan ta shigo tana kallonsa, Daga daya bangaren Ammi tace "Yanzu ta fita" Maheer yace "Hope she is much better yanzu ko?" Ammi tace "We will talk later Maheer let me get some rest" Maheer yace "To sai anjima" Daga haka ta katse wayar, juyawa yayi yana kallon Haseenah da ta wani hade rai tana ci gaba da kallonsa yace "Kin tashi baccin?" Bata tankasa ba ta juya ta fice daga dakin ya bi ta da kallo, sai kuma ya mike ya bi bayanta. Aunty Mariya ta kalli agogo dake nuna karfe takwas da yan mintuna na safe sannan ta kalli Mama Ladi tace "Mama Ladi ai yayi wuri yanzu mana, ki bari ko zuwa karfe sha daya ne, da kyar in sun tashi bacci ma yanzu" Mama Ladi dake saka dankunnenta irin na yan hamsin da ake siyarwa a kasuwa ta juya tana kallon Aunty Mariya tace "Mariya ba fa gidanki nace zan je ba balle ki gindaya min sharadi da ka'ida, gidan Mashir nace a kai ni, to ke meye naki a ciki banda rakiya da nace ki min in kina ra'ayi? In kuma baki ra'ayi ki sha zamanki, Mu a garinmu fa duk inda karfe bakwai da rabi na safe yayi to kaje inda zaka ka dawo har ka huta...." Juyawa Aunty Mariya ta yi ta nufi kofa Mama Ladi ta bi ta da harara ta ci gaba da saka dankunnenta, Tana gamawa ta tafi dakin Usman sai da ta kwankwasa yayi sau goma sannan ya bude kofar yana kallonta daga sama har kasa, buda baki tayi tace "Kai kuma ya da bacci bayan nace maka za mu fita yau, ko ka manta ne" Yace "Za mu fita mu je ina?" Cikin daga murya tace "Yau naga jaraba, ban gaya maka zaka kai ni gidan Mashir ba?" Yace "Da sassafen nan zaki je gidan nasa?" A fusace Mama Ladi tace "Mu fa a garinmu war haka har mutum yaje yayi sabgar gabansa ya dawo gida" Usman yace "To bari in shirya, koma daki ki jirani" Mama Ladi tace "To ya dai fi, ina nan ina jiranka" Daga haka ta juya ta bar wajen, ya kulle dakinsa ya ci gaba da kwanciyarsa, haka Mama Ladi ta tafi parlon Ammi tana ta raba ido tana jiransa... Wajen karfe sha daya Usman ya shigo parlon Ammi da sallama, Mama Ladi na kallonsa rai bace tace "Amma Usman ko don yanda na takarkare na dinga kare ka wajen Hajja jiya bai ci ka walakanta ni haka ba yau, tunda nake ban taɓa zuwa anguwa karfe sha daya ba..." Usman yayi murmushi yace "Yanzu dai tashi in kai ki" Mama Ladi tace "Haba don Allah, wallahi ba don kai ne ba da na fasa wannan gantalalliyar tafiyar in huta ma raina, wannan ai walakanci ne kuma ni ba a walakanta ni in dauka gaskiya, har fa gyangyadi sai da nayi na tashi" Ita dai Ammi bata ce masu komai ba, Usman bai yarda ya kalli inda Ammi take ba tun asuba da ya shigo ya gaisheta ta amsa masa kamar bazata amsa ba, Aunty Mariya ta shigo parlon Mayraah na biye da ita a baya rike da abinci, Mama Ladi ta mike tace "To kaga Mariyar da nace zata rakani, idan ita ma ta canza shawara ne sai in ji yanzu muyi tafiyarmu kawai" Aunty Mariya tace "Tafiyar ne?" Mama Ladi tace "Atoh, sai yanzu ya ga dama, dama uwar tace da kyar ya kai ni da yake tasan halin abunta, tana cikin fadin haka sai ga shi ya shigo tunda ɗan halaq ne" Aunty Mariya tace "To bari in dauko mayafi" dakin Ammi ta tafi dauko mayafinta, Mayraah ta karasa gaban Ammi ta ajiye mata abincin hannunta a hankali tace "Ammi ga abincin" juyawa tayi ta kalli Usman tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau" Aunty Mariya na fitowa Mama Ladi ta dau katuwar jakarta wanda tace zata debo kayan gara ta rataye a kafada tace "Toh sai Allah ya mana dawowa kuma" Usman ya kalli Mayraah yace "Ke baza ki je ba?" Mama Ladi ta juyo tace "Atoh nace ta shirya mu je ta ki, ka santa da taurin kai tun tana yarinya, har Mariya sai da tayi mata magana kememe yarinyar nan taki, to me za mu yi mata?" Usman na kallonta yace "Dauko hijab dinki mu tafi" yana fadin haka ya nufi kofa ya fita, Mayraah ta juya ta kalli Ammi, Ammi tace "Tashi ku je" Mikewa tayi ta tafi dakinta, a parking space ta tarar da su suna jiranta, Aunty Mariya ta bude ma Mama Ladi bayan mota ta shige ciki sannan ita ma ta shiga, Mayraah ta karaso ta bude front seat ta shiga, sai da suka bar gidan Mama Ladi ta tuntsire da dariya har da kyakyatawa, Aunty Mariya ta saki baki tana kallonta, Usman kam ta madubi ya dinga kallonta, Tayi dariyar me isarta tace "Wai Usman me ya hadaka da Badiyya ne kayi mata wannan dukan mutuwan haka?" Kara tuntsirewa tayi da dariya har da kwanciya, Aunty Mariya bata san sanda ta fara dariyan ba ita ma don dariyar Mama Ladi ne ke bata dariya, Usman yace "Wacece kuma Badiyya?" Mama Ladi ta tsagaita dariyarta ta dago tana kallonsa, yace "Ai ban san ta ba" Mama Ladi ta kara tuntsirewa da dariya tace "Wallahi naji dadin abinda kayi mata, kawai inda raina ya baci da har take gane mutanen dake kanta, kyau ace bata gane kowa, ai jiya ka sha tsinuwa wajen Hajja" Usman na ci gaba da driving dinsa yace "Ina ruwana da tsinuwarta tunda ba ita ta haifeni ba" Mama Ladi tace "Atoh dai, nima shi na gani, ta dai kwasheta sun tafi ko yaya suka isa gida oho" Aunty Mariya tace "Amma me ta maka kayi mata wannan dukan Usman?" Usman yace "Ni wai wa yace ni na doketa? A ina muka hadu na doketa?" Mama Ladi ta kara fashewa da dariya tace "Nima dai haka nace, wa ya sani ko aljanin dare ne ya lallabce ta ake ta laka maka wai kai ne" Har suka isa gidan Maheer Usman bai sake cewa komai a motar ba, yayi parking a waje yana kallonsu ta madubi, Mama Ladi tace "Motar bazata iya shiga gidan bane?" Usman yace "Ai juyawa zan yi" Aunty Mariya tace "Ka juya kuma? Aa jiranmu zaka yi, duka duka minti nawa za mu yi" Mama Ladi tace "Ban gane minti ba Mariya, wai nufinki muna shiga mu fito kamar barayi?" Da mamaki Aunty Mariya ke kallonta, Mama Ladi tace "Ni dai ba ruwana, bude min mota in sauka...." Aunty Mariya ta bude motar ta fara sauka sannan Mama Ladi ta sauko, Bude motar Mayraah tayi ita ma ta sauka, Aunty Mariya tace "Kai baza ka shiga ba Usman?" Yace "Aa" Mama Ladi tace "Haba ya kake haka ne komai naka babu tsari, gidan yayan naka ne baza ka shiga ba ka sa masa albarka yayi aure, ko hassada kake da shi" Tuni Aunty Mariya ta nufi gate Mayraah ta bi bayanta, sau daya Aunty Mariya tayi knocking kofar shiga entrance din parlon gidan aka bude.. Maheer ya koma gefe da murmushi fuskarsa ganinsu yace "Sannu da zuwa Aunty" Aunty Mariya ta shiga parlon Mayraah na biye da ita tace "Sannu ango, ya gidan?" Sai da suka zauna parlon ya karaso ya zauna shi ma ya gaida Aunty Mariya da ladabi, ta amsa tace "Ya gidan" Yace "Alhamdulillah" Kallon Mayraah yayi suna hada ido tace "Ina kwana" Ya mata murmushi yace "Lafiya lau Mimi, ya su Ammi?" Tace "Alhmdlh" Maheer ya kalli Aunty Mariya yace "To ina Mama Ladin?" Ko rufe baki bai yi ba sai ga ta da Usman sun shigo parlon tana cewa "To kaga ai shi ma sai yaji dadi ka shigo" Maheer ya mike yana mata sannu da zuwa, Tace "Ina amaryar?" Yace "Bari in mata magana tana daki" Usman yace "Good morning" Maheer na kallonsa yace "Morning" Juyawa yayi ya bar parlon, Aunty Mariya ta kalli Usman da yaki zama ya tsaya bayan kujera tace "Kai kuma ya haka kamar Soja? In zama zama, in kuma fita fita" Ɗan murmushi yayi ya karaso cikin parlon ya zauna, Ba a dau lokaci ba Maheer ya dawo parlon yace "Tana fitowa yanzu" kitchen ya tafi ya kawo masu ruwa da drinks ya ajiye, for almost 15 minutes Haseenah bata fito ba, Mama Ladi sai hira take da Maheer tana basa labarin yanda aka samu wanda ya lakada ma Badiyya duka kuma har yanzu ba a san ko waye ba, shi dai Usman danna wayarsa kawai yake, Aunty Mariya dai sai zuba ido take taga fitowar Haseenah shiru har bayan minti ashirin, Can Mama Ladi ta ankara tace "To wai ita amaryar er wani sarki ce ita da zata shanya mu a nan kamar yan iska?" Maheer yace "Erm ina jin wanka take" Daga haka ya mike, Aunty Mariya ta tabe baki, dakin ya sake komawa ya sameta kwance tana danna wayarta, da mamaki yace "Haseenah wai baki ji abinda nace maki bane?" Haseenah ta ajiye wayarta ta wani hade rai tace "Haba don Allah daga kawo mutum ko 24hrs bai yi ba za a fara masa sintiri haka Maheer? Wani dan gidanmu ka ga ya zo gidan nan? Ai ko ba komai an san ina tare da gajiya sai a bar ni in huta ko na sati biyu ne tukun kafin a fara min zarya, amma ya daga tarewa kawai a fara zuwa min gida da safe haka" Kallonta kawai Maheer yake ko kiftawa babu, ya ma rasa abinda zai ce mata, bayan few seconds ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da harara, tun da ya fito Aunty Mariya ke kallonsa, bai yarda ya kallesu ba ya zauna yace "Tana bandaki ne" Mayraah dai na kusa da Aunty Mariya a zaune, Mama Ladi tace "Ai ko ita ce warce ta fi kowa kiba saɓar saɓar a duniya ya ci ace ta gama wankan ta fito haka, awan mu daya fa yanzu a nan a zaune, wacece wannan ka aura haka Maheer? Ko har an fesa mata daga karaye nake ne take kokarin kawo min raini?? Shi fa karayen nan ba kauye bace don ma ku ji in fada maku" Usman ya mike ya nufi kofa ya bar parlon, Mama Ladi tace "Tada motar ga mu nan fitowa yanzun nan Usman...." Maheer yyi kasa da murya yace "Mama yanzu fa zata fito, ae nasan wankan take ne" Mama Ladi ta mika masa jakarta tace "Oho ko ma canza fata take, ni dai gashi kwaso min gara in san inda dare yayi min" Maheer ya amshi jakar yace "Mama kin san yanda mata suke dadewa a bandaki fa, yanzun nan zaki ga ta fito" Bai jira me zata ce ba ya tafi kitchen din, Haseenah ta mike zaune daga kwancen da take tana nazari, to ko ba komai ai zata so taga wa enda suka zo gidan, hijab dinta ta dauka ta saka sannan ta fito parlon, da Mayraah ta fara hada ido, wani irin faduwa gabanta yayi da farko ta kasa karasowa, Mayraah ta dauke idonta, Haseenah ta karasa parlon tana tafiya a hankali ta zauna empty chair ta gaishesu kamar me ciwon baki, Mama Ladi na kallonta da kyau tace "Mijin naki bai gaya maki mu su waye bane halan?" Ta dan girgiza kai ba tare da tace komai ba tana ɗan juya ido, Mama Ladi tace "Toh kanwar kakarsa ce ni uwa daya uba daya, ita kuma wancan da kike gani kanwar uwarsa ce uwa daya uba daya, ta gefenta kuma kanwarsa ce, sai dai kawai akwai aure a tsakaninsu ne a yanzu ba kamar yanda kika sani ba a baya, yanzu abubuwa sun canza, duk da dama mu mun san da auren tsakaninsu su ne dai basu sani ba, amma kanwarsa ce halaq malak" Sosai gaban Mayraah ya fadi, sai dai na Haseenah ya fi nata faduwa, Mama Ladi ta ci gaba tace "Shine dama nace a kawo ni in ga gidan ɗa na in sa albarka, ba wai zuwa nayi takanas saboda ke ba, tunda ai na ganki a can gidan" Tana kai wa nan ta mike tace "Mariya zaga da ni in ga gidan mu yi wucewar mu" Ko gama mikewa Aunty Mariya bata yi ba Mayraah ta mike, Mama Ladi tace "Yauwa mu je har ke kika gidan yayan naki..." kitchen suka ga Mayraah ta nufa, Mama Ladi tace "Au to, ganawa zata je tayi da yayan nata, mu je Mariya" Haseenah ta dinga bin Mayraah da kallo zuciyarta na bugawa, Aunty Mariya ta bude wani spare room tace "Wannan dakin baƙi ne ina jin" Mama Ladi tace "Waiii gashi da girma kuwa, kinga ai ko hutu aka yi Mera zata iya zuwa nan tayi hutun ta idan can gidan ya isheta" Mayraah na shiga kitchen din Maheer dake ta deban chin chin da cokali yana saka ma Mama Ladi a jakarta ya juya, he was surprise to see her, ita kanta sai ta daburce ta fara kame kame tace "Dama, dama yaya ina son ka ara min wayarka ne" Maheer yace "Did u misplaced urs?" Ta gyada masa kai, yace "To anjima zan kai maki wani gida, wanne kike so?" Shiru tayi tana wasa da handle din kofar kitchen din, yace "Ohk nama san wanda kike so" Ta ɗan kallesa tace "To wanne?" Yace "Idan na kai zaki gani" Ita dai bata sake cewa komai ba, yace "Zo ki debar mata snacks din ban san yanda ake yi ba" Karasawa ciki tayi, ta amshi jakar sannan ta fara debo kayan garan tana zubawa a ciki, yana tsaye gefe yana jiran ta gama zubawa aka bude kofar kitchen din, Haseenah na huci cikin daga murya tace "I am not going to tolerate this Maheer" Maheer kallonta kawai yake, Mayraah bata ko dago ba ta dinga zuba ma Mama Ladi alkakin da take, Haseenah ta karaso cikin kitchen din jikinta na wani tsuma tsabar bacin rai ta ci gaba da cewa "Bazan dauka ba wallahi, bazan yarda wata banza da baku hada komai da ita ba ta dinga shigo min gida...." Sai a sannan Maheer yace "Kin san wani abu Haseenah? Za ki iya yi min rashin kunyanki, ki gaya min duk abinda ranki yake so in dauka, amma kar ki kuskura ki sa Mimi a rashin hankalin ki don a nan ne ranki zai yi mugun baci wallahi, ki cire Mimi a bakin ki" Cikin daga murya Haseenah tace "Do ur worst Maheer, nace do ur worst, ba Mimi ba Momo, na sa ta a baki din yi abinda zaka yi in ga, kuma karya nayi ne? Ko da abinda ka hada da ita banda kasancewarta er uwarka musulma? To wa ma yasan ko kafura aka haifeta, A yanzu dai Maheer babu wanda bai san wacece ita ba duk da ni ka munafurceni baka gaya min abinda ke faruwa ba da fasa aurenta da aka yi saboda rashin asalinta, to har gida ake samu na a gaya min duk abinda ya faru, kowa yasan bata da asali, er tsintuwa ce kawai warce ma ba a san ta hanyar da aka sameta ba" Kallonta kawai Maheer yake babu ko kiftawa, Haseenah na tafe hannu tace "In sha Allahu kuma sai ta zama abun kyama a al'umma, don dama irinsu ai abun kyama ne tunda a walakance aka yasar da ita, kai kanka sai kaji gwara ka saka makiyin ka a ido da ka saka ta a ido, sannan tun ma kafin haka sai ta fara nuna maku cewar ita tsintattciyar mage ce...." Haseenah na kai wa nan ta fice daga kitchen din tana huci, Sai bayan kusan second ashirin Maheer ya iya juyawa ya kalli Mayraah, kulle jakar hannunta take kokarin yi, duk da idonta a kasa yake but he can see the tears filled in her eyes, lokaci daya jikinsa yayi sanyi sosai, ya ma rasa me zai ce mata, ta ajiye masa jakan hannunta a kan cabinet ta nufi kofa ta fita daga kitchen din, har sannan su Mama Ladi basu fito parlon ba, Haseenah da ta kasa zaune sai safa da marwa take a parlon zuciyarta na wani irin ƙuna ta bi Mayraah da ta nufi kofa da kallo, har ta fice daga parlon, wani murmushi Haseenah tayi ganin har da hawaye a idonta, nan da nan taji ta samu nutsuwa a ranta ta nemi kujera ta zauna ta sauke wani ajiyar zuciya, Mayraah na isa kofar gida ta tadda Usman a tsaye jikin motarsa ya rungume hannayensa yana jiran 12 dot yayi idan yaga basu fito ba yayi wucewarsa, tun da ta fito yake kallonta, ganin yanayinta yace "Me ya faru?" Ta karaso kusa da motar ta kasa ce masa komai, lokaci daya kawai ta fashe da kuka, da mamaki yace "Ke meye haka?" Kuka kawai take kamar ranta zai fita, kalle kallen wajen ya fara yi yaga babu kowa, yace "Talk to me, an maki wani abu ne?" Still taki ce masa komai sai kuka, ya jawota gefensa yana kallonta yace "Baza ki gaya min me ya faru ba? Me suka maki a gidan?" Still taki cewa komai don kukan ma bazai bari tayi magana ba, ya dawo yana facing dinta yayi kasa da murya yace "Tell me what happened???" Ganin bazata yi magana ba ya bude bayan motar yace "Shiga ciki" juya masa baya tayi ta hade kanta da motar taki shiga tana rusa kuka, Cikin calm voice yace "Mimi...." Sai a sannan ta juyo ta girgiza masa kai cikin rawan murya tace "Ina son zan je wajen Ammi" Shiru yayi yana kallonta, can yace "To shiga in kai ki" shiga cikin motar tayi hawaye na sauka idonta, ya kulle motar sannan ya shiga front seat ya tada motar suka bar layin, sai da suka hau main road ya kalleta ta madubi, zuwa sannan ta daina kukan ta jinginar da kanta da motar kana ganinta kasan tayi nisa cikin tunanin da ta fada, bai ce mata komai ba har suka isa gida don bai son ya mata magana ta fara sabon kuka. Mama Ladi tace "Ahaf... Ai dama tun suna yara suka iya munafurci, Mera da Usman ba? Sam ai zuciyarsu ba kyau, to banda rashin kyan zuciya mu taho tare rimi rimi ana hira a mota daga karshe ku zame ku yi tafiyarku ku bar mu? To da babu Maheer din wa zai maida mu gida yau, wallahi da na sani ma jiya da ban karesa wajen Hajja ba, don irin dukan da yayi ma Badiyya ya ci ace yana self din yan sanda yanzu haka, da ya sumar da er mutane sai yace me?" Haseenah dake tsaye parlon tana ɗan murmushi tace "Kiyi hakuri Umma, kilan wani uzurin ne ya taso masu" Mama Ladi ta ɗan kalleta tace "Ke kuma wannan magana ai ta pamily ce ba sai kin sako mana baki ba, sun ga za mu ɓata masu lokaci ne yasa suka yi tafiyarsu tunda suna da abun yi" Daga haka ta nufi kofa, tuni dama Aunty Mariya ta fita daga parlon, Haseenah bata ko damu da abinda Mama Ladi ta ce mata ba don ita yau ranta fari tass, tana kallon Maheer da ya bi bayan Mama Ladi cike da shagwaba tace "Sai ka dawo baby, amma don Allah kar ka jima" Yace "Ohk in sha Allah" Daga haka ya fita daga parlon, Haseenah ta zauna kan kujera tana wani murmushi, ita ta ma manta rabon ta ji ta cikin nishadi irin yau.... Maheer na ajiye su Aunty Mariya, Mama Ladi tace "Baza ka shigo ka gaida baabarka ba bawan Allah?" Yana ɗan murmushi yace "Zan shigo anjima da daddare in gaisheta ae" Mama Ladi tace "Duk barin jikin ka koma wajen wancan kodaddiyar matar taka ce haka?" Yayi er dariya yace "Aa ni dai ban ce haka ba" Sallama yayi ma Aunty Mariya yayi reverse ya bar layin. Ko da ya koma gida Haseenah har tayi wanka sharp sharp ta bada tsadaddun turarrukanta a jiki sannan ta dauko wasu shegun kananun kaya ta saka, welcoming dinsa tayi tun daga bakin kofa ta rungumesa, yayi pecking dinta a goshi sannan ya karasa cikin parlon ya zauna, ita ma ta zauna kusa da shi kamar zata shige jikinsa tana kallonsa kamar mayya, ya kamo hannunta yace "What will we be taking for lunch" tana shafa beard dinsa tace "Abinda Babyna ya fi so" Yace "Ko muje eatry mu siya abinci?" Ta juya ido tace "Sure dear" Yace "To shirya mu tafi" Hijab dinta har kasa ta saka kan kayan jikinta sannan suka bar gidan, dama bai shigo da motarsa ba a waje yayi parking, duk ita ta zabi abinda za su ci, bayan sun bar eatry din yace "Zan biya gidansu Ahmad in bashi sako" Tace "Ohh bai koma Abujan bane shi?" Yace "Aa ya koma, kaninsa yace in ba zai je Abujan gobe" Tace "Ohk" Suna kusa gidan Haseenah ta kallesa tana murmushi tace "Kamar in shiga gida wllh" Murmushin yayi shi ma, don dole sai ka wuce gidansu kafin ka karasa gidansu Ahmad a layin gaba, saboda yawan zuwa gun childhood frnd din nasa da yake yi ne ma suka hadu da ita a unguwan, yana isa dai dai gate din gidansu yace "Ko zaki shiga ki gaida su Mumy kafin in dawo daga gidansu Ahmad din?" Ta zaro ido tace "Kai Baby dama ana haka?" Yace "Why not, ai kamar yanda kike yawan fada yanzu muna era din civilization and modernization" Tayi dariya tace "Kuma haka ne, to in ka dawo sai ka kirani in fito, amma fa zan ji kunya" Yana kallonta yace "Ba wani kunya baby, ki gaida su Mumy" Bude motar tayi tace "Alright sweet, amma kar fa ka dade don Allah" Yace "Ina mika masa zan juyo ai, kece ma zan ce ma karki ki fitowa da wuri ki shanya ni a nan" Ta sauka daga motar tana dariya tace "Haba ai ni bana ma sha'awan zaman gidan namu yanzu tunda na dandani zaman gidan ka, ae gidan miji daban ne" Kulle masa motar tayi tana masa kallon kauna tace "Sai ka dawo my hubby" Yace "Ohk, but ji mana" Har ta fara tafiya ta juyo tana kallonsa, ya gyara zamansa yace "Go inside and explain to ur parent where u lost ur virginity cause u didn't bring it to my house, after that they should do better akan tarbiya da manners din da suka baki don ya maki karanci, idan kin masu bayanin na farkon wanda shine main issue a nan, sa iya nemana in saka masu convenient lokacin da zan zo su min bayanin da kansu, that is idan ina da lokacin ma kenan, sannan a dawo batun rashin tarbiyyarki da manners dinki, wannan kuma ban san for how long zae dauka a koya maki ba, though my main concern ynxu is how and where u lost ur virginity i really want to know that from ur parent daga nan ne zan iya deciding fate din aurenki a kaina..... ita warce kika kira tsintattciya mara asali i can swear with my life virgin ce, she is intact, cause she is my mum's training, she is my training, i raised her since from when she was a toddler, kin ga kuwa ba standard din ku daya ba" Yana kai wa nan ya tada motarsa yayi zoom off ya bar ta tsaye a ƙame a wajen kamar statue ko kifta ido bata yi. MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 Plss ayi hakuri aji tsoron Allah a sauke haƙƙi..... [6/20, 9:01 PM] Khaleesat Haiydar💖: Haseenah ta dinga bin motar Maheer da kallo ko kwakkwaran motsi bata yi a inda take tsaye har taga ya bar layin nasu, bayan few seconds ta hadiye wani abu da ya makale mata a makogwaronta da kyar, gani take kamar fa mafarki take ba gaske ba, ta kikkifta ido ta bude still dai ta ganta tsaye a kofar gidan nasu, nan fa ta tabbatar ba mafarki bane da gaske ajiyeta Maheer yayi a gida, tayi karfin halin juyawa ta kalli gate dinsu dake a kulle, bata san sanda ta fara tafiya ba da sauri ta bar bakin gate din tana tafe tana harhade hanya kamar mara gaskiya, da hijab dinta ta dinga rurrufe fuskarta don kada wani a layin ma ya ganta ya ganeta, a haka har ta bar layin gaba daya ta isa bakin titi, zufa ne ke keto mata a goshi ga cikinta dake murda mata, sai a sannan ta daura hannu daya a kai cikin tashin hankali tace "Na shiga uku" tunanin inda zata nufa yanzu ta fara yi, Zaliha ta fado mata, sai kuma ta girgiza kai da sauri don tasan tana zuwa gidansu Zaliha yanzu dole su hadu da mamar Zaliha, matar da wuni tayi a gidansu ranan bikinta, gashi banda wayarta babu ko sisi a hannunta, gefen ta koma jikin wani shago ta shiga kiran layin Badiyya, har ya katse bata daga ba, ta sake kira tana addu'ar Badiyya ta rufa mata asiri ta daga kiran don ita kadai ce mafitar ta a yanzu, Badiyya na dagawa kamar warce ke cikin maye tace "Account din zan turo?" Sai a sannan Haseenah taji hawaye ya cika idonta, ta fashe da matsanancin kuka tace "Badiyya na shiga uku, don Allah kina ina yanzu?" Badiyya dake kwance bakinta yayi suntum ta mike zaune da kyar don duk jikinta ciwo suke mata wai a haka Hajja ta kai ta chemist an mata allura an bata magani, Badiyya tace "Me ya faru??" Cikin kuka Haseenah tace "Ni dai don Allah gaya min kina ina, in fara barin nan kafin wani da na sani ya gan ni, in ma Bichi kike sai in taho kawai yanzu" Badiyya ta zaro ido tace "To fa... To me ya fito dake? Jiya fa muka kai ki Haseenah" Haseenah ta rushe da sabon kuka tace "Ni dai ki fara gaya min inda zan sameki Badiyya" Badiyya tace "Ke ni fa gani a gida ba lafiya fa" Haseenah tace "Innalillahi, Badiyya kin dai san bazai yiwu in zo gidan ba kada kakarku ta gan ni ko, Badiyya gidanmu Maheer ya maido ni yanzun nan" Badiyya ta zaro ido tace "Gidan ku kuma? Garin yaya?" Cikin kuka Haseenah tace "Wallahi, yanzu haka gani a junction din gidanmu na rasa inda zanje, gashi ina tsoron kada wani ya gan ni, ko kuma wani ɗan gidanmu ya zo wucewa" Badiyya tace "To gashi ni bazan iya fitowa ba bakina yayi suntum baki ji yanda nake maganan ba ma, sannan duk jikina yayi tsami ko daga hannu da kyar nake yi wllh, da sai ince mu hadu a hotel, amma kawai yanzu ki samu adaidaita sahu ki taho idan ya so sai in lallaba in fito mu shiga gidan Maman Bala, wannan gidan dai da nake shiga in canza kaya wani lokacin in za mu fita" Haseenah ta gyada kai da sauri tace "To, to gani nan zuwa yanzun nan" Daga haka ta katse wayar ta tsayar da adaidaita sahu ta shige da sauri tana zazzare ido ta gaya masa inda zata. Suna isa layin Haseenah ta kira Badiyya, babu bata lokaci Badiyya ta daga kiran, Haseenah tace "Gani a kofar gidan, don Allah ki fito masa da kudi babu ko sisi a hannuna" Badiyya tace "Toh gani nan" Hajja da ta gama dama ma Badiyya kunu kenan ta juyo tana kallonta da mamaki tace "Ina kuma za ki Badiyya?" Da kyar Badiyya tace "Zan ɗan motsa jiki na ne ko zan ji dama dama, daga nan sai in shiga gidan Maman Bala" Hajja tace "Ki shiga gidan Maman Bala a wannan yanayin Badiyya, a'a da dai kiyi hakuri ki koma ki kwanta ga kunun na dama maki" Badiyya tace "Ke dai ba ruwanki, tunda kika ga zan fita ae zan iya ne" Daga haka ta fice daga parlon Hajja ta bi ta da kallo. Badiyya ta ba mai adaidaita sahu kudinsa tana kallon Haseenah da ke ta hawaye tace "To wai me kika masa haka? Ko da yake mu je gidan Maman Balan tukun" tana dingishi suka shiga gidan Maman Bala tare da Haseenah da ko lura da jikin Badiyya da bakinta bata yi ba tsabar tashin hankalin da take ciki, Dakin yaran Maman Bala suka shiga Badiyya ta zauna tana kallon Haseenah tace "Amma Maheer mahaukaci ne, me kika masa har yake da mind din mayar dake gida daga tarewarki jiya??" Haseenah ta zube kasa ta fashe da kuka sosai tace "Na shiga uku Badiyya, babban tashin hankalina kar ma Mumy ta samu wannan labarin, wallahi nasan kasheni kawai zata yi" Badiyya tace "To kin ki gaya min me ke faruwa, sae kuke kuke da kame kame kike, wani abun kika masa ne?" Haseenah ta hadiye wani abu da kyar tana nazari, ita dai tasan ko karen hauka ya cijeta bazata yi gigin gaya ma Badiyya da kowa yasan bata da sirri abinda ya sa Maheer ya maida ta gida ba, can dai tayi karfin halin cewa "Wai daga yarinyar nan Mayraah sun zo dazu da safe na nuna masa bana bukatarta a gidana shkkn fa Badiyyah, shkkn Maheer ya maida ni gida" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Badiyya ta rike haɓa cike da mamaki tace "Lallai yarinyar nan ta zama annoba a al'umma, saboda ita fa Usman yayi min wannan dukan jiya da daddare a gidansu, Allah Allah nake in samu kaina in san ta inda zan billo ma matsiyaciyar, yanzu kema a kanta aka maida ke gida??" Sai a sannan Haseenah ta kula da yanda halittar Badiyya ya canza gaba daya, amma da yake ba shi ne gabanta ba bata bi ta kan hakan ba sai kuka take, cikin shesshekan kuka tace "Badiyya ki taimaka ki gaya min yanda zan yi, gaba daya kaina ya ƙulle, wallahi kasheni yan gidanmu za su yi in suka samu wannan labarin, zuwa fa kawai yayi ya ajiyeni a bakin gate dinmu daga fita mu siyo abinci a eatry, ashe yasan plan din da ya hada min" Badiyya da taji zuciyarta na tafarfasa tace "Tashi mu shiga wajen Hajja, yanzun nan kuwa zata kira uwarsa...." Da sauri Haseenah ta rikota tana zare ido tace "Don girman Allah ki rufa min asiri bana son kowa yasan abun nan da ya faru banda ni da ke, na yarda dake ne yasa na zo har nan na sameki" Badiyya ta buda baki tace "To yanzu ya kike son ayi? In ba wajen Hajja za mu je ba ta kira uwarsa ni kinga da wani abu da zan iya yi a nan? Ai dole kuwa uwarsa tasan abinda yake faruwa" Haseenah ta girgiza kai da sauri tace "Aa gaskiya ni dai nace maki bana son kowa ya sani, let sort this out without involving anybody" Badiyya ta taɓe baki tace "Cabb, ashe kuwa baza muyi sorting dinsa ba har abada, an gaya maki suna jin maganar kowa banda na uwarsu ne? Ai in ba Ammi bace ta saka baki a maganar nan wllh Maheer bazai saurari kowa ba, ke ma dai da nacin ki sai da na nuna maki illan auren Maheer kika ki saurarata to yanzu ga irinta nan daga kwana daya ya koro ki gida" Haseenah na goge hawayen da yaki tsaya mata tace "Ni dai Badiyya ki min alfarma kar ki gaya ma kowa wannan abun, bari in kira Zaliha ta same mu a nan inji ita kuma shawaran da zata bada" Badiyya ta kyabe baki tace "To kuma babu abinda ya shiga tsakaninku??" Haseenah tayi kamar bata ji ta ba tana kokarin dialing number Zaliha. Wajen karfe uku da wani abu Mayraah na gyara Bedroom dinta don jiya da shekaranjiya duk a dakin Ammi take kwana, yau kuma dakin nata take son ta dawo, aikin kawai take amma ba wai hankalinta na kan aikin ba, tunani kala kala ne cunkus ke yawo a ranta, gaba daya ji take kamar zata yi zazzabi, the fact that nobody is even saying anything to her akan issue din nan dake faruwa ya sa taji ta fara tsanar kowa a gidan, they are all acting like everything is normal, babu wanda ke son tada maganar ko da wasa, it's more like an bar ta a duhu kawai babu wani bayani from anybody and that's beginning to hurt her deeply, ta goge hawayen da ya taru idonta ta tafi jikin window ta tsaya tana kallon waje, Then who is she? Menene asalinta? Why was she dumped right from birth? Me ye laifinta da aka yi abandon dinta tun daga haihuwa? Tunanin hakan yasa taji wasu sabbin hawayen na sauka idonta, bude kofar dakin aka yi, bata juyo ba ta goge hawayen dake sauka idonta da sauri, jin shiru bayan some seconds ta juyo a hankali don ganin wanda ya shigo, ya jingina da kofar dakin yana kallonta yace "Kukan me kike dazu a gidan Maheer?" Kamar baxata ce komai ba, sae kuma ta girgiza kai tace "Babu komai, i just saw my self crying" ya mata wani kallo yace "That's a lie" tayi murmushin karfin hali tace "Da gaske nake yaya, babu komai" Zai yi magana aka bude kofar dakin ya koma gefe, Aunty Mariya ce ta shigo tana kallonsa tace "Kai Mama Ladi na ta nemanka tun dazu fa" Ya hade rai yace "Kai, gaskiya this old woman is stressing me seriously, me kuma zan mata?" Aunty Mariya tayi dariya tana kallon Mayraah tace "Hajiyata ban ga kin fito kin diba abinci ba har yanzu, ko kawo maki zan yi" Mayraah tayi murmushin karfin hali tace "Zan zo in diba Aunty" Aunty Mariya tace "Better" daga haka ta juya ta fita dakin tana cewa "Kai kuma bari in je ince ma Mama Ladi kace tana damunka" Bai ce mata komai ba ya maida dubansa kan Mayraah yace "Je ki debo abincin" yana fadin haka ya juya zai fita tace "Yaya ka ara min wayarka don Allah" ya juyo yace "Ina naki wayar?" Tace "I lost it" Ya ciro wayarsa a aljihu ya ajiye mata gefen gado sannan ya fita daga dakin, ta karasa ta dau wayar ta zauna gefen gado ta fara dialing number Musharraf, a ranta ta fara addu'ar Allah ya sa ya kunna wayar yanzu, amma unfortunately aka ce mata a kashe, nan da nan hawaye ya cika idonta damuwarta ya karu a kan na da, what is happening? Baya son magana da ita ne yake kashe wayarsa kenan, Kwanciya tayi edge din gadon hawaye me zafi na sauka idonta. Karfe biyar Mayraah ta shigo parlon Ammi ta dalilin kiranta da ta yi, tun da ta shigo Ammi ke kallonta, ita kanta Ammin ta kasa samun nutsuwa har sannan a zuciyarta daurewa kawai take duk abin nan, Mayraah ta durkusa gabanta a hankali tace "Ammi ga ni" Ammi tace "Me za ki girka ma Abbanku?" Mayraah tace "In masa tuwo da vegetable?" Ammi tace "To je kiyi" mikewa tayi ta nufi kofa zata fita suka kusa cin karo da Maheer, ta koma gefe ba tare da ta kallesa ba tace "Sannu da zuwa" daga haka ta fita daga parlon ya bi ta da kallo kafin ya karasa ciki yana kallon Ammi dake kallonsu... Cikin awa daya da wani abu Mayraah ta gama girkin tunda ɗan kadan zata yi dama, Ta dawo parlon Ammi tace "Ammi na gama" Ammi tace "To sannu da aiki" juyawa tayi ta fita, Maheer ya mike yace "Bari in je masallaci in dawo" Ammi tace "Daga can ka wuce gida Maheer, ya zaka fara barin yarinya ita kadai a gida daga kai ta, ai zaka bari ko sati tayi tukunna" Maheer dai bai ce mata komai ba ya fita daga parlon, dakinsa ya tafi ya dau ledan da ya ajiye sannan ya fito ya tafi dakin Mayraah, tana tsaye jikin window tana kallon waje ya sameta, Mayraah ta juya jin an bude kofar dakinta, ya karasa ciki ya zauna gefen gado yace "Ga sakon ki Mimi" Tana kallonsa tace "Na mene?" Yace "Amsa ki duba" Ta sauke idonta sannan ta nufesa ta amshi ledan da yake mika mata, tun bata bude ledan ba ta gane waya ce, tana kallonsa da murmushin karfin hali a fuskarta tace "Nagode sosai yaya" Ya girgiza kai yace "That smile is fake" Dariya ya bata wanda bata san sanda tayi ba, tace "Allah da gaske naji dadi yaya" Yace "Toh kinga wannan is not fake" Murmushi kawai take ta bude wayar taga wanda yafi nata na da ne ma, a hankali tace "Nagode sosai, Allah ya kara budi" yace "Everything for my Mimi" shiru duk suka yi, bayan few seconds a hankali yace "And... sorry about what happened dazu a gidana Mimi, you know i will neva let that slide...." Da sauri Mayraah ta katse sa tace "Aa ni ai ya wuce a wajena har na manta ma" kallonta kawai yake, ta fara bude kwalin wayar, yace "Za a san min tuwon Abban?" Ta kallesa tace "Ohk amma halve, sai in ba Ammi sauran halve din, dama leda uku ne nayi" Yace "Toh bari in dawo masallaci, ki ajiye min a daki" Tace "Toh" Mikewa yayi ya fita daga dakin, Mayraah ta dinga kallon wayar bayan ta bude, sosai yayi mata kyau ba kadan ba and she is so happy about it, taga har da sim card ya siya mata, ta jona wayar a caji sannan ta ajiye kwalin ta tafi bandaki don yin alwala.... Bayan Magrib tana zaune kan darduma aka bude kofar dakin ta daga kai tana kallon wanda ya shigo, ya karaso dakin ya ajiye ledan hannunsa gefen gado, tana kallonsa tace "Ina yini" Yace "Lafiya lau" Tace "Ana ta kiranka a waya" Tana fadin haka ta mike ta tafi ta dauko masa wayarsa da ya bata tun da yamma, ya amsa ya juya ya fita, Mayraah ta dau ledan da ya ajiye mata taga kwalin waya ne a ciki, ta buda ido da mamaki tana juya kwalin, exactly irin wanda Maheer ya siyo mata dazu color ne kawai daban da wancan, ajiyewa tayi gaban mirror ta fita dakin ta sauka downstairs, abinci ta saka ma Maheer kamar yanda yace mata, ta kai dakinsa, zaune ta gansa dakin yana kallo a laptop, yayi pausing movie din ta karaso ta ajiye masa abincin a gabansa tace "A kawo maka tea ne?" Yace "No... thanks Mimi" Ta mike zata fita yace "Ke kin ci abincin?" Tace "Aa anjima" zata fita dakin sai ga Ammi, Ammi tace "Wai Maheer baka tafi ba har yanzu?" Maheer yace "Ammi wai korata kike ne?" Ammi tace "Eh koranka nake, wannan wani irin abu ne haka? Kai in kanwarka aka ma haka zaka ji dadi?" Ya kalli Mimi dake tsaye yace "Aa bazan ji ba gaskiya, bari in gama cin abincin in tafi Ammi" Ammi tace "Gaskiya bana son haka, kar ka sake zuwa min gidan nan kwana kusa, ya zaka fara barin er mutane ita kadai daga kai ta jiya? Don't u have conscience" Muryar Mama Ladi suka ji tana cewa "O'o Allah, O'o Allah, ba fa yarinya bace amaryar nan da zaki wani daga hankalinki haka a kan an bar ta ita kadai a gida Ammi, jiya fa da muka je na kalli idonta da kyau wllh ba yarinya bace, da kyar in ma bata girmi Mashir din ba, ni dai nayi ta mamakin a inda ya samota har yaji sha'awan aurenta, ke fa baki mata kallon da na mata ba jiya, don haka kawai ki ja bakinki kiyi shiru in baki san abu ba" Ammi dai bata ce mata komai ba ta juya ta fita daga dakin Mayraah ta bi bayanta, Mama Ladi na kallon Maheer dake cin abincin da Mayraah ta kawo masa tace "Kai ko kamar wanda aka ma rufa ido, maimakon ka samu yarinya er dai dai warce bata wuce Mera ba zaka kare da uwar mata haka Mashir? Ko kai baka ganta ba wani saɓar saɓar da ita sai uban mazaunai, kyan fuska kawai gareta fa shi ma kamar mai ta shafa, wannan haihuwa daya biyu zata sukurkurce ta fashe, don irin kiɓan kazantar nan zata yi da tayi haihuwa daya, wanda da ta gifta zaka ji doyi" Mama Ladi ta kyabe baki tace "Allah dai yasa kada Usuman yayi irin wannan zaben tumun daren, ya samu yarinya er dai dai abunsa kamar Mera" Murmushi kawai Maheer yayi yana cin abincinsa, Mama Ladi ta juya ta fice daga dakin. Sai da Mayraah ta fara zubo ma Ammi abinci ta kai mata parlonta sannan ta tafi dakin Usman. Ya ajiye wayar da yake yace "Ya aka yi?" Tana jan fingers dinta tana tsaye jikin kofar dakin tace "Thank you so much for the phone yaya, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen, any other thing?" Ta girgiza masa kai tace "Kawai godiya zan maka dama" Yace "Accepted Mimi" Tayi murmushi ta juya ta fita daga dakin. Da gudu Haseenah ta shige bandakin yaran Maman Bala jin muryar Hajja tana sallama a tsakar gida, Maman Bala ta fito tana amsa sallaman tace "Sannu da zuwa Hajja" Hajja tace "Allah sa dai nan Badiyya ta shigo Sahura" Maman Bala tace "Ehh gata can dakinsu Bala kuwa" Hajja ta nufi dakin, Badiyya ta hade rai tace "To ke Hajja meye na biyoni don Allah kamar wata er yarinya" Hajja tace "Ayya naga kunun har ya huce kin san flask din nawa ya fashe balle in juye maki a ciki" Badiyya tace "Toh ki tafi gani nan zuwa ni dai" Hajja tace "Toh" Daga haka ta juya ta fita, Haseenah ta fito tana zare ido kamar warce tayi ma sarki karya, Badiyyah tace "Yanzu da magariban nan kice zaki kama hanyar Zaria Haseenah, to wai ma wani waya kike da baza kiyi a gabana ba sai kin wani fita tsakar gida, in haka ne meyasa baki je wajen wanda ku ke wayan da baki son in ji ba, ina fama da kaina na fito saboda ke amma don munafurci sai ki wani dinga fita kina kus kus a saya" Haseenah ta marairaice tace "Wallahi ba haka bane Badiyya, duk bayanin da na maki nake yi a wayar da kika ga ina yi, Coursemate dita ce Fatiha fa" Badiyya dai ta kara kyabe baki ta dauke kai, Haseenah tace "Kuma ai da ban yarda dake ba bazan zo wajenki ba Badiyya, yanzu dai bari in maki transfer ki dauko Atm dinki ki cire kudin ki bani inyi maza in tafi" Badiyya ta mika mata hannu babu yabo babu fallasa tace "Haseenah bani sarkan nan da dankunne zanje kasuwan da kaina in siyar" Haseenah ta hadiye wani abu da kyar tace "Yana fa wajen me siyarwan account number kawai zan tura masa ya saka maki kudin wllh, hidimar bikin nan da ake ta yi ne yasa aka samu delay, yanzu dai don Allah gobe za mu yi maganar gold din ta waya, ki tashi muje ki ciran min kudi a account dinki inyi maza in tafi, zan tura maki dubu talatin yanzu" Badiyya na girgiza kai irin ba mutuncin nan tace "Gaskiya idan goben yayi da kaina zan je shagon me gwal din na gaji kuma haka, aban gold din ko kuma aban kudin" Haseenah tace "Ehh goben sai in baki kwatancen wajen mutumin ki je, ai sananne ne a kasuwan" Mikewa Badiyya tayi tana dingishi suka fita daga dakin Haseenah na biye da ita, Badiyya tayi ma Maman Bala sallama suka bar gidan, suna isa gate din Hajja Badiyya tace "Kinga kawai muje gun me POS din ki masa transfer ya baki kudin don ina shiga gida yanzu Hajja zata iya biyoni waje idan nace zan sake fitowa, kuma kince baki son tasan komai" Haseenah tace "Gaskiya kam, wannan sirri ne tsakanina da ke" Suna karasawa gun me POS Haseenah tayi transfer din aka bata cash, Tace "To sai mun yi magana Badiyya, ina isa Zaria zan kira ki" Badiyya tace "Amma dai wajen wa zaki a Zari'a ke da baki da dangin uwa balle na uba a can" Haseenah tace "Haba gobe fatiha zata sameni a Zarian ai, yanzu dai zanje gidan wata Coursemate dinmu ne tukun" Badiyya ta tabe baki tace "Toh Allah ya tsare" Haseenah tace "Ameen" Daga haka ta bar layin da sauri, Badiyya ta koma cikin gida, Hajja na ganinta tace "To kiyi sallah bari in zuba maki kunun" Badiyya ta taɓe baki ta zauna tana kallon Hajja tace "Hajja kin san matar Maheer ce ta zo muka shiga gidan Maman Bala kuwa?" Hajja ta kalleta tace "Matar Maheer? Wani Maheer din?" Badiyya tace "Wallahi kuwa in gaya maki, wai ya korata gida daga dai Mayraah taje gidan ta mata rashin kunya tace bazata dauka ba" Hajja ta dinga kallonta tace "Mayraah ta mata rashin kunya?" Badiyya tace "Wallahi nake gaya maki, ko gaida Haseenar ma bata yi ba da taje gidan tana ta abu Isa isa da gadara, shine Haseenah abun ya ɓata mata rai tace to gaskiya ita bata son haka ya za ayi ta shigo mata gida babu gaisuwa sai kallon walakanci, kar ki dada karki raga Maheer kawai ya dauketa ya maidata gidansu, shine fa ta shiga tashin hankali bata shiga gidan nasu ba ta yo nan hankali tashe" Hajja na tafe hannu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Badiyya tace "Ace Mayraah bata zama annoba ba? Dubi tashin hankalin da take hadawa a family dinmu duk tana neman tarwatsa kanmu ta lalata mana zumunci" Hajja na gyada kai a hankali tace "Wannan gaskiya ne" Badiyya tace "To wannan magana tsakaninmu ne dake, kar ki ce ma kowa komai babu ruwanki, kinga dai ni ga abinda ta sa Usman yayi min don ma Allah ya so da sauran kwanana a gaba, Aunty Mariya na ji tana gani bata kwace ni ba kuma har yanzu ai kinga bata zo gidan nan ba balle ta duba halin da nake ciki, ita kanta Ammin bata kira taji ya jikina ba kuma ya kamata ita ma ace ta zo ta duba ni ai, ai kinga duk babu wanda ya zo, balle Mama Ladi dake ta goyon bayan abinda aka min duk akan wata banza wai Mayraah, yanzu gashi sabon auren da Maheer yayi tana nema ta kashe masa, ai wannan badluck ce a family dinmu wllh, ashe dama babu abinda muka hada da ita shi yasa tun farko na tsaneta jinina bai hadu da ita ba, Ammi tayi ta fifitata a kaina komai ace Mayraah, a gabana Aunty Mariya zata kira sai dai tace a ba Mayraah...." Hajja dai bata ce komai ba tayi shiru, Badiyya ta tabe baki ta mike da kyar ta shiga bandaki... Washegari da safe Mayraah ta gama shiryawa don tana son shiga school ba don kowa ba sai don Dr Musharraf kilan zata gansa a school din, fitowa tayi zata sauka downstairs taje kitchen don hada ma Ammi shayi, babu wanda yasan zata school a gidan don dama so take sai ta kai ma Ammi shayi kafin tace mata zata je makaranta, a stairs ta hadu da Hajja dake haurowa, tayi murmushi ganinta tace "Ina kwana Hajja" Ko kallonta Hajja bata yi ba, Mayraah ta koma gefe ta bi ta da kallo in shock, Hajja ta nufi parlon Ammi ta bude kofar babu ko sallama, Ammi da Mama Ladi sai Aunty Mariya duk suka daga kai suna kallonta, shiga parlon tayi tana kallon Ammi da kyau tace "Hajara" Ammi ta kasa cewa komai ta dinga kallonta gabanta na faduwa don Hajja bata kiran sunanta kai tsaye sai dai ta kirata da Ammi, Hajja tace "Ina ce dai da yardata kika dau yarinyar nan kika rike har zuwa yau ko? Ina ce Mamuda ƙin amincewa yayi da farko, ni ce nan na karfafa masa gwiwa na rokesa Allah da annabi ya barki kiyi rainon yarinyar tun tana tsumma ko? To a yau nake son ki zabi ko ni ko yarinyar" MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 [6/21, 8:09 PM] Khaleesat Haiydar💖: Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga Sister Nafisat Sanda (Mom twins🥰) Allah Ubangiji ya raya mana twins mu taho biki Sakkwato muna daddaga shoulders😁 Hajiya Safiyya Usuman🤪 (Ummu Sultan) 5 gbosa for you, Allah ya karo arziki ki bude plazan kayan yara a titin anguwanku, Allah ya raya mana Noor in fara tara kayan kitchen 😁 My lovely fans ina maku fatan alkhairi for always being there for me, Allah ya raya maku zuri'a🥰 Mama Ladi ta saki salati ta mike ta dafe gwiwowinta tana kallon Hajja kamar ranan ta fara ganinta tace "Yau mun shiga uku, Me ya sameki haka Hajja? Ko dai ɓatan hanya kika yi ba nan zaki zo ba?" Hajja ta dakatar da ita tana huci tace "Kee babu ruwanki a maganar nan ki kama gabanki kar ranki ya baci Ladi, magana ce nake yi tsakanina da 'ya ta" Mama Ladi ta mike zumbur ta wangale hannu tace "Ba lafiya jama'a, to amma dai a yanzu ai kowa yasan ba Ammi ke da iko da Mera ba a gidan nan, sai dai in kije ki samu Mamuda dama bai fita ba, kije dakinsa ki samesa ki zazzage masa duk abinda ke ranki, haka kawai mata muna zaman zaman mu baza ki zo nan ki daga mana hankali ba gaskiya, ki tafi can dakin Mamuda kice ya maida Mera jikin masallacin da ya tsintota tunda shi ya tsintota ai ba Ammi ba, babu ruwan Ammi a wannan maganar gaskiya, ita umarnin mijinta ta bi take rike da Meran har yau don zaman lafiyanta da mijinta, in kuma kashe mata auren zaki yi ta koma gidanki to sai mu ce Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, don wannan hanyar kashe mata aure kika dauko" Aunty Mariya was speechless and shock, gaba daya jikinta yayi sanyi, ta ma rasa tunanin da zata yi balle tace wani abu, to in ma tana da abun cewan ba dai a gaban Hajja ba, don tsaff sai Hajja ta iya tsine mata, Ammi kam dawowa tayi kamar an dasa ta a wajen don ko kifta ido bata yi, that was the least she was expecting from Hajja, she was still finding it hard to believe Hajja ce yau ke fadan wannan maganan, is this really Hajja, her eyes where soo dry tsabar yanda maganar ya zo mata a bazata ita da hawaye bai da nisa daga idonta, kallon Hajja kawai take babu ko kiftawa, Hajja na kallon Mama Ladi tana nunata da ɗan yatsa take cewa "Nace ki cire bakinki a batun nan Ladi kada ki kai ni bango, ki cire bakinki a abinda ya shafi zuri'ata tunda baki da alkhairin da zaki fada, in dai har akan Mayraah abubuwa za su yi ta faruwa haka suna caɓewa a zuri'ata to na yanke shawara Hajara ta zabi ko ni ko ita kawai, ehh ta zabi ko ni ko ita Mayraahn, bazai yiwu a kan Mayraah a kusa nakasa Badiyya ba sannan har yau babu wanda yaje yace mana ci kanku balle ya duba halin da take ciki daga ku har shi munafukin da yayi dukan, bazai yiwu akan Mayraah 'ya yan Hajara su dau ƙaran tsana su dora ma Badiyyah ba, basu da makiyiya sama da Badiyya a duniya, sannan yanzu kuma a kan Mayraah banga dalilin da zai sa Maheer ya kora matarsa da duka duka kwananta daya a gidansa, wai fa duk saboda Mayraah, to ita Mayraahn nan duk abubuwan nan dake faruwa duk ta dalilinta alkhairi ce a garemu kenan?? ai a ganina an mata mai wuya tunda har aka riketa aka ciyar da ita kawo yanzu da tasan kanta, wani irin karatu ne bata yi ba gashi za a yaye su a jami'a kwanan nan, don haka bazan zuba ido in ga familyna na neman lalacewa akan wata da babu abinda muka hada da ita ba a duniya sai don zuciya irin ta musulunci da ya sa muka sakota cikinmu ba tare da mun kyamace ta ba, nayi hakuri na kauda kai, na nuna komai ba komai bane yau shekara ashirin da biyu kenan, tun daga kan yanda ake banzatar da Badiyya da lamarinta a kan yarinyar nan ma ai yaci ace na dau mataki, amma ban yi haka ba saboda zuciyar musulunci, don haka duk sanda Hajara ta yanke shawara sai ta zo gida ta sameni, Ko ni ko Mayraah, bazan mutu in bar baya da ƙura ba..." Hajja na kai wa nan ta nufi kofa fuuu ta fice daga parlon, Mayraah dake tsaye tun shigan Hajja parlon Ammi kuma duk ta jiyo abinda Hajja ke cewa ta juya da sauri ta nufi dakinta ta kulle ta jingina da kofa tana maida numfashi.... Sai a sannan hawayen tashin hankali ya kawo idon Ammi tana kallon Aunty Mariya da tayi tagumi tana furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a ranta, Mama Ladi na tafe hannu tana zare ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una lalacewa ta samu Hajja, dama Hausawa sunce ba farkon ba karshen, yanzu dama haka Hajja ta koma ni ina can Karaye ban sani ba?? me ya sami yayata ta lalace da mugun hali haka?" Tana kai wa nan ta fice daga parlon ta nufi dakin Usman, Aunty Mariya tayi karfin halin cewa "Ammi ki kwantar da hankalinki, nasan cikin bacin rai Hajja tayi maganganun nan she doesn't mean it har ranta...." Kasa ci gaba Aunty Mariya tayi hawaye na sauka idonta tana tausayin yayar tata, Ammi dai ta rike kanta hawaye na zarya a idonta tana jin zuciyarta na mata zafi, har sannan maganganun Hajja ne ke kai kawo a kunnenta, Aunty Mariya ta koma gefenta cike da karfin hali ta rungumota tace "Don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki Ammi...." Sai a sannan Ammi ta fashe da kuka sosai... Mayraah ta fi minti bakwai tsaye jikin kofar dakinta ta kasa motsawa daga wajen, her eyes were soo dry, lkci daya taji kirjinta yayi mata nauyi sosai kamar an daura mata ƙaton dutse, ta kasa ci gaba da tsayuwa ta lallaba ta koma gefen gado da kyar ta zauna hoping zata samu relieve din kirjinta da ya riƙe, bata ji ya mata saukin azaban da yake mata ba, daga karshe ta lallaba ta daure ta tashi ta tafi gun da Hijab dinta yake ta dauka ta sa, ta ciro Nikab dinta ma ta saka sannan ta dau handbag dinta ta nufi kofa, a hankali ta bude kofar don taji ana ta knocking din dakin Usman, leka corridor din tayi taga Mama Ladi tsaye sai bubbuga kofar Usman take ba kakkautawa, rufe kofarta tayi making sure it made no sound, ta jingina jiki tana jin kamar she is beginning to find it hard to breathe normal, bayan wani lokaci taji Mama Ladi a fusace tana cewa "Kai ya za a dinga buga kofarka ka ki tashi kamar me baccin mutuwa, wannan wani irin baccin asara ne Usman, ina ma ka ga ta bacci gida ya kacame ba lafiya ta ko ina" Mayraah taji Usman yace "Me ya faru?" Mama Ladi ta shige dakin tana cewa "Ba maganar tsayuwa bace ai" ya bi ta ciki sannan ya kulle kofarsa, Mayraah na jin haka ta bude dakinta a hankali ta fito, da sauri ta sauka downstairs ta fita compound, cikin few minutes sai ga ta a bakin titin gidansu, adaidaita sahu ta tare ta shiga bayan ta sanar masa inda zai kai ta... Duk da tafiyar da Mayraah tayi zuwa department din nasu ba wani me nisa bane, amma da kyar ta karaso saboda numfashinta da take ji yake sarke mata, she was so tired, bata karasa har bakin department din ba don ma kar wani ya ganta ya ganeta ta nemi karkashin wani bishiya me dauke da gossip chair ta zauna tana maida numfashi, she sitted there for 3 good hours, amma babu alamar shigowar ko daya daga 3 cars da yake zuwa makarantar da su, ganin it's almost pass 12 tayi karfin halin mikewa, zuwa yanzu ita kadai tasan me take ji a duk jikinta da kirjinta, ga wani jiri dake dawainiya da ita, tafi minti sha biyar tsaye bakin titin makarantar tana tunanin inda zata je, daga karshe ta tsayar da adaidaita sahu ta shiga ta sanar masa inda zai kai ta..... Bayan tafiyar kusan minti talatin mai adaidaita sahun ya tsaya dai dai inda Mayraah tace masa ta sauka sannan ta basa kudinsa, a hankali take tafiya zuwa gate din gidan, she leaned against the gate for almost 5 minutes kafin tayi knocking, gajiya tayi da kwankwasa gate din don babu alamar za a bude, bata ma san ko da mutum a gidan ba at first, she is soo tired and sick everywhere, kawai daurewa take ga rana me zafi, tana ta tsaye nan don ko inda zata zauna babu, don ma dai tun zuwanta bata ga kowa ba a street din and that made her more comfortable to keep standing by the gate, masallacin dake next street taji ana kiran sallahn azahar, ta jingina da gate din gidan ta rufe ido, ji tayi ana unlocking gate din after almost 15 minutes, ta gyara tsayuwarta ta koma baya da sauri gabanta na faduwa don bata ma san wanda zata gani ba, aka bude gate din at last, kallonta yake kamar yanda take kallonsa ta cikin Nikab din fuskarta, he looks so surprise and perplexed seeing her, ya bi street din da kallo da mamaki yace "Mayraah!" Ita dai bata ce masa komai ba ta sauke idanuwanta daga kallonsa, da sauri ya kamo hannunta zuwa cikin gidan ya kulle gate din ya dage Nikab din fuskarta yana kallonta, ganin yanayinta and how she is beginning to heave yace "Are you okay??" Girgiza masa kai kawai tayi, bai sake cewa komai ba yana rike da hannunta ya nufi cikin gidan da ita da sauri, ko karasawa entrance din parlor basu yi ba Mayraah ta fara ganin gidan na juya mata bata sake sanin inda kanta yake ba daga nan kuma. Maheer ne tsaye yana kallon Aunty Mariya sounding so pissed off yace "Aunty I think babu ruwan kowa da duk wani harka da ya shafi gidana ko matata, idan ma sakin Haseenah nayi it's my decision and i am old enough to make decisions for myself babu ruwan wani, ai ba wani ya bani shawaran aurenta ba so babu wanda zai bani shawaran yanda zan zauna da ita banda mahaifiyata ko mahaifina, ina ruwan Hajja da abinda ya shafi gidana har zata daura ma Mayraah? I don't think wannan ne kaɗai dalilin da yasa ta zo gidan nan tayi abinda tayi, there is definitely more to that, Kuma in har tace Ammi bazata kara rike Mayraah ba mu za mu riketa don kanwar mu ce har yau har gobe and this is our fathers house, beside ko gidana Mayraah zata zauna nobody is going to question that, dalilina kuma na maida Haseenah gida still remains between i and her, wannan tsakanina da ita ne babu wanda ya shafa, kuma babu ruwan Mayraah a mayar da Haseenah gida da nayi" Usman dai na tsaye ya rungume hannu fuskar nan tasa a murtuke tsabar bacin rai ko magana yaki yi, Aunty Mariya dai sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, gaba daya ta ma rasa abinda zata ce, tun dazu Ammi dai ta kama hanyar zuwa gidan Hajja and this is 12pm bata dawo ba, wa ya sani ko zuwa zata yi ta ce mata ta amince babu ita babu Mayraah din kamar yanda Hajja ta bukata, Mama Ladi na tafe hannu tace "Kai in fa za ku fito fili ku buda ma ubanku abinda ke faruwa ku fito, babu wani zancen nuku nukun da za a mashi wannan karan, Hajja ce ta zo har nan da sassafe ko tashi daga bacci bamu yi ba tace zata ɗaga ma Ammi mama idan bata sallama Mera ba ta shiga duniya, fitar Hajja ke da wuya aka nemi Mera ko sama ko kasa aka rasa alamar yarinyar ta ji duk abinda Hajja ta fada a gidan nan, iyakar maganar fa kenan, duk da nasan Mera dole ta dawo duk inda ta tafi tunda babu dangin uwa balle na uba a duk inda za ta, yarinta ce kawai yasa ta bar gidan nan amma nasan tana hango magariba zata dawo shi yasa hankalina bai wani tashi ba, wancan lokacin da ta gudu ai tana ganin babu sarki sai Allah sai gata ta dawo da asuban fari, wa ya sani ma ko a titi ta kwana ranan, to yanzun ma muna zaune za ku ga ta dawo wujiga wujiga wanda ke da dangi ma ya ya kare idan ya shiga duniya balle ita da aka tsinta bakin masallaci a tsumma, sannan a buda ma Mamuda cewa Badiyya ce ta ruguza auren Mera, in ma Shari'a zai yi da ita bismillah dama ya haifi lauyan da zai tsaya masa ai, ita kuma Ammi karshen biyayya idan ta dawo muga tana watsi da kayan Mera titi taga ita ma irin koran da Mamuda zai mata, ai Mamuda ke da iko da gidansa ba ita ko uwarta ba, ko shi da 'ya yansa kadai sun isa su rike Mera, sannan nima nan ban ki in riketa in samu lada ba, sai in koma karaye in tattaro sauran kayana in dawo kawai, Mariya kuma ku bar ganin tana matsar kwalla a nan muna barin parlon nan ita ma zata saɓa gyale ta bi bayan er uwarta zuwa gidan uwarsu duk kukan munafurci take yi a nan, a yanzu gatan Mera Mamuda sai ni da ku kawai" Ficewa Usman yayi daga parlon ya tafi na baƙi don Abba na can, zaune ya tadda Abba shi kadai a parlon, tun bayan fitar Ammi daga parlon zuwa gidan Hajja bai motsa daga inda yake zaune ba don Ammi bata boyesa masa duk abinda ke faruwa ba, bai taɓa tunanin abubuwa will turn out this way at the end ba, da sun san haka abubuwan za su kasance da har ita Mayraah din baza su boye mata wacece ita a garesu ba baza su boye mata ba su suka haifeta ba, iyaka su sakaya suce iyayenta hatsari suka yi suka mutu suka tsinceta ita kadai a motar, and sun yi bakin kokarinsu basu gano relatives dinta ba, da hakan suka yi tun farko da abubuwa sun tafi smoothly, all this while Abba avoiding din Mayraah yake don bai san da idon da ma zai kalleta ba, gani yake daga shi har Ammi failed her, they disappointed her don ta taso da mentality din su suka haifeta amma all of a sudden rana daya taji ba su ne iyayenta ba, she is going through all this because of them hakan na damun Abba sosai, yanzu ko nan gaba aka samu wanda zai aureta tabon nan na rashin asali bazai taɓa goguwa a tare da ita ba, kawai he is just acting like everything is okay but deep down him he feels so sorry for Mayraah and he regret their actions, ya ma ga kokarinta duk da yasanta to be a very strong gal tun tasowarta, to yanzu ga kuma wani matsalan da Hajja ta billo da shi, Ammi kuma duk duniya babu maganar wanda take ji bayan shi da yake mijinta sai Mahaifiyarta, and her mum first in everything.... quite alright ba don Hajja ba da gidan Marayu zai mika Mayraah shi da yan anguwan a ranan da aka tsinceta duk da yanda Ammi ta nace masa a lokacin ya bar mata ita amma yaƙi har sai da Hajja ta saka baki... Bayan wani lokaci Abba ya daga kai yana kallon Usman da ya shigo parlon, Usman ya nemi waje ya zauna, Abba dai bai ce masa komai ba, after few seconds Usman yayi karfin halin cewa "Yanzu a ina za mu samo Mayraah?" Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya calmly yace "Zata dawo, she will come back in sha Allah, babu inda zata je" Usman ya mike yace "But It's over 3 hours da fitar ta gidan nan fa, who knows the condition she is now??" Abba ya jinginar da kansa da kujera kamar bazai ce komai ba, can yace "Sit Usman" Usman ya koma ya zauna, Abba yace "Ga wata alfarma da nake nema gun ka Usman" Usman ya daga kai yana kallonsa, Abba ya nisa, cikin calm voice yace "Usman ina son hada aure tsakaninka da kanwarka Mayraah, i know u will protect her as ur sister, ur wife and as the orphan dat she is" MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 Ki sauke hakki kiyi karatu hankalinki kwance..... [6/22, 11:56 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mikewa Usman yayi da sauri yana kallon Abba cike da mamaki, tsabar yanda maganar Abba ya zo masa a ba zata kasa cewa komai yayi, can dai yayi gathering courage yace "In auri Mayraah fa kace Abba? Did you mean it? How? Mayraah da muka taso nake ma kallon kanwata Muharramata how zan aureta as wife? This sounds more like an abomination to my ears, it's weird, ta yaya zan auri kanwata da nake ma kallon uwarmu daya ubanmu daya kawai don abun nan ya faru? No pls tell me ta yaya Abba?" Komawa yayi ya zauna ya ciro handkerchief yana share zufan da ya keto masa a forehead, he looks so confuse, yana girgiza kai yace "No Abba, this isn't going to work, Mayraah kanwata ce har yau, har gobe, har abada, bayan wannan babu wani kallo da zan sake mata, kanwata ce ita ta jini...." Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "It's okay Usman, i understand you, but we all neva bargained for this, kawai abinda yasa na kawo shawaran nan naga abinda muke boyewa for many years an tonosa ta hanyar da bamu taba zato ba bamu yi tsammani ba, sannan duk wanda zai zo neman auren Mayraah ina da tabbacin tun daga waje za a tsegunta masa asalin wacece ita, my wish yanzu a rayuwa bai wuce ace Mayraah ta wuce gori ba, i want her to live like every other person, kuma nasan ku da na haifa kadai ne baza ku goranta mata asali ba, baza kuma ku kyamace ta ba, za ku riketa ne da amana ko da raina ko babu raina" Abba ya girgiza kai yace "I don't think there is any means da za ace za'a fara neman iyayenta or anything of such a yanzu because it's of no use, ko daga yanda aka yi dumping dinta a wajen nan a ranan ya nuna ba a bukatarta ne kawai, ba a kuma ajiyeta a wajen da niyyar ta rayu har wani ya dauketa ba, a'a an ajiyeta ne kawai ta mutu, ba kuma a jikin masallaci kamar yanda ku ka ji ana cewa aka ajiyeta ba, i don't know who created that rumors, kawai nasan that faithful day na fito kamar yanda na saba zan zuba ruwa a randunan masallaci kafin jama'a su fara fitowa sallahn asubahi, daga inda ake debo ruwan a wani rijiya ne, sai dai babu wani tazara tsakanin inda rijiyar yake da masallacin, a nan gaba da rijiyan aka nannadeta cikin zani har fuskantar sannan aka saka ta cikin kwali kuma aka rufe kwalin da plank ta yanda iskan kirki ma bazai shiga ba, kaga wanda ake son ya rayu ai baza ayi masa haka ba, kuma me imani bazai taɓa yi ma ɗan da ya haifa haka ba, kai koma ba ɗan da ya haifa ba bazai bari ayi ma wani haka ba, tabbacin koma wacece ta ajiyeta bata da imani, bata tsoron Allah sannan azzaluma ce don da niyyar kasheta tayi hakan, ina jan ruwa a rijiyar nan ina jin kamar kukan jariri amma na rasa a ina gashi kukan babu sauti sosai can kasa kasa ake jin kukan, kawai na bayar ko mage ce ke wannan kukan, har sai da nayi sahu uku da ruwan na kasa hakuri na fara duba wajen da torchlight ina neman inda wannan sautin kukan ke fitowa, in takaice maka nafi minti 10 ina dube duben area din daga karshe na lura da kwalin da aka ajiye nesa da rijiyar kusa da wani kwata na karasa na daga plank din, sai ga sautin kukanta sosai, i was shocked don dai anyi wrapping har fuskarta da zani, na kasa taɓa ta gashi babu kowa, duk ana ciki yawanci ba a tashi bacci ba don karfe hudu da rabi ma bai karasa ba a lokacin, tsabar yanda na zama confuse kawai na koma gida gun Amminku, ita ma tana bacci na tasheta nan na sanar mata abinda na gani bakin rijiya, babu bata lokaci ta sako hijab ta biyoni muka dawo wajen, har sannan kuma jaririyar bata daina kuka ba, Ammi bata yi wani tunani ba kawai ta cirota daga kwalin cikin tashin hankali ta warware zanin da aka yi wrapping dinta da shi, a lokacin sai Amminku ta fashe da kuka tana salati, don yanayin da jaririyar ya nuna ba a ma jima da haihuwarta ba tunda ko goge jikinta ba ayi ba, Ammi bata bi ta kaina ba tayi cikin gida da jaririyar nan a hannunta, Ni dai tsabar yanda mamaki da takaici ya isheni jikina yayi sanyi na koma bakin masallaci na zauna ina tunanin wacce azzalumar ce zata aikata wannan abun comfortably babu tsoron Allah a ranta, sannan duniya na kwance lkcn duk bamu san a haifi jariri a yasar shi ba, wannan yasa abun ya tsaya min, ya kuma tsaya ma mutane da yawa a rai, don kafin gari ya waye labari ya karade unguwa har ma da makota an tsinci jaririya a bakin masallaci kamar yanda ake cewa, da Ammi ta gyara yarinyar ta mata wanka sai da nayi kwalla, ita dama tun da ta dauko yarinyar take kuka, fara ce kal jaririyar, she was a cute baby kamar balarabiya, nan dai aka kai ta gun manyan anguwa aka fara shawaran yanda za ayi da ita, kowa dae na tsoron yace zai riketa don ba a san dalilin yasar da ita a walakance ba a bakin kwata, wasu suka bada shawaran a kai ta gidan marayu, a sannan ma gidan Marayun bai yi yawa ba kamar yanzu ina jin ma babu a garin sai anje wani gari, aka dai yarda akaita can gidan Marayun a harhada kudin mota, duk fa ba wai mun san yanda process din yake bane a lokacin sannan bamu sako yan sanda a ciki ba, nan na shigo gida na sanar ma Amminku shawaran da aka yanke akan jaririyar nan, Ammi ta sakar min kuka ta fara hadani da Allah ita dai a bar mata yarinyar zata rike, tunda a sannan Umar was almost 5 years kuma shi kadai ne a gabanmu, after much pleading and begging, har ta hadani da Hajja, Hajja ma ta saka baki a maganar babu yanda na iya ba don raina ya so ba manyan anguwa suka damka ma Ammi jaririyar nan, a ranan kuma tace min ita dai ta saka mata suna MAYRAAH, as at then we were leaving from hand to mouth, nayi ta kokarin nuna ma Ammi baza mu iya da dawainiyar jaririyan ba muma muna fama da kanmu a garin, gashi Ammi ta jima da yaye Umar babu ruwan Maman da zata ba yarinyar which means dole madara za a dinga siya mata kenan, a hakan ma yan anguwa sun harhada tsofaffin kayan yaransu an kawo ma jaririyan, har kudi aka hada da bai taka kara ya karya ba aka bamu, da shi muka fara siya mata madara, ni dai duk hankalina bai nutsu da rikon yarinyar ba kawai ina jin kunya Hajja ne, a ranan na fita naje kasuwa inda nake dako a biyani kafin in harhada yan kudadena in siya kaya marasu tsada in shiga Cameroon in siyar sai inyi wata daya ban gama hada kudin siyan kayan ba wani lkcn duk abinda na samu ma dole da shi za a ci abinci, that same day da muka tsinci Mayraah ina kasuwa from no where sai ga wani bawan Allah ya bani dubu goma daga kai masa kaya mota, imagine 10 thousand 22 years ago, ai kaga ba karamin kudi bane, nayi ta farin ciki na koma gida duk da ko minti talatin banyi da fitowa ba, a washegari sai ga wata dubu uku daga wata Hajiya ita ma na dau mata kaya zuwa mota, let me make this brief, tun daga sannan ba ayi ranan da zan fita ba a min kyauta ba, me yawa, ɗan kadan a haka dai kullum, nan na dinga saran kaya ina shiga Cameroon a kwana biyu uku kaya suke karewa tas ga riba wanda a baya sai inyi sati uku a Cameroon kaya basu kare ba, tun daga samun Mayraah hanyoyin arziki suka dinga bude mana ta ko ina, ta yanda bamu taɓa tunani ba a rayuwarmu, in less than few months ni kaina na tsorata da abinda na tara, nayi ta jin tsoro, haka ma Amminku wanda nasan da bata san halina ba tunani zata yi sata na fara, amma abu sai kara ci gaba yake, harkoki na ta bunkasa kan kace me kafin wata 12 muka tattaro muka dawo kano, kaga kuwa samun Mayraah alkhairi ne a garemu, kuma ko da muka dawo Kano barka kawai ake shigowa yi ma Ammi tunda shekaranmu daya a can muka samu Mayraah, tana wata sha biyu kuma muka dawo Kano, don haka babu wanda ya kawo cewar ba er mu bace Mayraah, ku kanku where very happy bayan dawowarmu don an sanar maku Amminku ta haihu tun bamu dawo ba.... Usman ya ɗaga kai yana kallon Abba jin yayi shiru, Abba ya nisa yace "Ko da wasa mu ma bamu taba zaton akwai randa za mu yi ma 'ya yan da muka haifa tayin auren Mayraah ba don duk daya muka dauke ku gaba daya babu banbanci, amma muna namu Allah kuma na nasa...." A hankali Usman yace "Yanzun ma hakan baxai faru ba Abba, we will continue being the brothers we are to her, for better for worst we will protect her and will always be there for her, babu wanda zai taɓa ta ya kwana lafiya, ko da yau ta samu wani da zai aureta kallon banza idan ya hadasa da ita balle har ya kai ga goranta mata asali zai gane she has a Barrister as a brother and 2 other elder Brothers, not even outsider ko na cikin gida ne yace zai takura Mayraah i in particular can go to any extent na kwatar mata 'yancin ta, i will take that personally i am assuring you Abba, don haka har abada babu aure tsakaninmu da Mayraah, she remains our blood sis" Yana kai wa nan ya mike yace "I want to excuse my self sir" Abba ya gyada masa kai, ya juya ya fice daga parlon Abba ya bi sa da kallo. Maheer ne tsaye dakin Ammi kansa a kasa duk da bacin ran dake tare da shi bai nuna a fuska ba but deep down him he is boiling and yana ta controlling kansa baya son yayi wani magana da zai kara hurting din Amminsa hankalinta ya kara tashi, gwara ya bar ta ma taji da wanda take ciki yanzu, Ammi dai sai goge hawayen da ya ki tsaya mata take maganar ma ta kasa ci gaba da yi, not long ago ta dawo daga gidan Hajja don ko minti sha biyar bata yi da shigowa gidan ba, after a 5 minutes silence tsakaninsu Maheer ya dago kansa yana kallon Ammi yace "Shikenan... Na kuma fahimce ki Ammi, for the meantime Mayraah zata koma gidana...." Ammi ta daga kai tana kallonsa, yace "Eh zata dawo gidana, a nan kuma zata zauna, Hajja don't have any say in this, ba kuma wai don Hajja zata hanata zaman nan gidan Abba bane yasa zata koma gidana don zamanta a gidan nan ma Hajja bata da say cause this is our father's house, ban san irin zaman da za ku fara yi da Mayraah ba idan ta ci gaba da zama a gidan nan shi yasa zan maida ta gidana, don haka gobe zan je gidansu Haseenah in daukota, duk sanda Hajja ta gane kuskuren abinda take kokarin yi fine, zan so ki rabu da ita lafiya, don haka ki ci gaba da yi mata biyayya...." Aunty Mariya ce ta shigo dakin da akwatinta, tana kallon Ammi cikin sanyin murya tace "Toh Ammi, ni zan tafi sai mun yi waya" Kai kawai Ammi ta gyada mata tana share hawayen da ya ki tsaya mata har sannan, Aunty Mariya ta kalli Maheer tace "Zan tafi Maheer" Sauke idonsa yayi yace "Bari in kai ki park Aunty" Fita tayi daga dakin ya juya ya bi bayanta, bayan ya kullo kofar Aunty Mariya na kallonsa cike da damuwa tace "Ku yi hakuri Maheer, kuyi hakuri da duk abubuwan nan dake faruwa, Allah zai daidaita al-amarin nan in sha Allah, sannan nasan Mayraah bazata yi nisa ba, duk inda ta tafi zata dawo a yau da izinin Allah, tunda Hajja tace in tafi gwara in tafi kawai" Shi dai Maheer bai ce mata komai ba, ta fara tafiya ya bi bayanta. A hankali Mayraah ta bude idonta, ta dinga bin dakin da take da kallo, kwance take saman gado an rufeta da lallausan farin duvet, ta mike zaune da sauri trying to recall where she is, and who brought her here, idonta ya sauka kan alluran dake kan bedside drawer da drugs, cikin few seconds komai ya fara dawo mata, ta cire duvet din jikinta zata sauka daga kan gadon taji kamar an soka mata mashi a kirjinta, dafe kirjin tayi da sauri feeling so much pain, dai dai nan aka bude kofar dakin, ta daga kai ta kallesa, tsaye yayi bakin kofar yana kallonta, can dai ya karasa yana tafiya a hankali ya isa har inda take ya zauna cikin sanyin murya yace "How are you feeling now?" Tun safe sai a yanzu taji kukan da ta kasa yi ya taho mata ta kasa controlling kanta, kamo hannunta yayi yace "Noo pls kar kiyi stressing kanki Mayraah, u need rest" Ta warce hannunta daga nasa cikin kuka tace "Saboda kasan wacece ni shi yasa kake avoiding dina yanzu kake kashe wayarka don baka son...." Dakatar da ita Musharraf yayi yana girgiza kai yace "That is the last thing i will do on earth Mayraah, and mind u tun kafin ke kanki ki san ko wacece ke na riga ki sani, kuma hakan bai sa naji kin canza a zuciyata ba, i switched off my phone for my mental health..." Tace "You are avoiding me because of ur mental health?" Yayi shiru yana kallonta kamar yanda ita ma ke kallonsa, daga fuskarsa kadai zaka gane ya rame, he doesn't even look normal, can ya juya yana kallon side daban yayi kasa da murya yace "Na ba Dr Maheer space ne ya gama maki duk injections dinki da aka yi prescribing, sannan ya kula dake kamar yanda likitan ya umarta, so i had to back off for my sanity" Kallonsa kawai Mayraah take, ya mike tsaye yana facing dinta, hawaye ne kawai ke sauka idonta tace "But that isn't enough to let u ignore me all this while, when u know i will need u the most during this hard time" A hankali Musharraf yace "Kinsan yanzu da aure tsakaninku da Maheer and Usman?" Kallonsa Mayraah take babu ko kiftawa, ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, ta fashe da kuka ta hade kanta da gwiwa, ba a dau lokaci ba ya dawo dakin da plate din abinci da ruwa, ya ajiye mata kan bedside drawer yana kallonta yace "Mayraah" Ta daga kai tana kallonsa hawaye na sauka idonta, zaunawa yayi kusa da ita yayi kasa da murya yace "I am sorry Mayraah.... u know i love you soo much, ina sonki fiye da yanda kike zato, amma the thought of Maheer made me sick for all the 3 days da kika ji wayata a kashe, i became insecure zuciyata na ta raya min abubuwa da yawa, kilan saboda abubuwan nan da suka faru Abba can just decide to get u married to Maheer or Usman, the thought of that nearly took my life this 3 days, Mayraah I can't imagine loosing u, i don't know what will become of me idan na rasa ki, kiyi hakuri ki yarda da ni mu je a daura mana aure, i promise to give u all the love in this life, i will protect you till my last breathe, u will neva regret trusting me" Mayraah na share hawayen dake sauka idonta a hankali tace "I have to because i have no option, a yanzu ina ga bani da kowa kuma bani da inda zan je, i am all alone in this life" Musharraf ya girgiza kai ya kamo hannunta yace "You are not alone Mayraah" Tana kallonsa cikin rawan murya tace "I don't know what is happening but i overheard my grandma telling Ammi to choose between i and her, she said....." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai, Musharraf ya jawota kusa da shi yace "It's okay Mayraah, baki ji ta bane da kyau, u misheard her, yanzu ki ci abinci ki sha magani, it's almost magrib" Yana fadin haka ya dauko abincin ya fara bata a baki, cokali daya ta ci ta girgiza masa kai da kyar tace "Bazan iya ci ba, my chest is aching" Yace "Bari in kawo maki shayi" Tashi yayi ya fita daga dakin, ta koma ta jingina da gadon all this while sai yanzu ta ɗan ji ta samu relieve, bayan some minutes ya dawo dakin da cup din shayi ya mika mata yace "I diluted it, babu zafi" Amsa tayi ta fara sha, ya dauko mata magungunan yana bude mata, tana gama shan shayin ta amshi maganin ta sha, yace "Zan je masallaci in dawo, kiyi alwala kema kiyi sallah" Ta gyada masa kai ya mike ya fita daga dakin.... Ko da Musharraf ya dawo Mayraah har tayi sallah, ya ajiye mata yoghurt da ya shigo mata da shi ya zauna yana kallonta yace "Are you feeling pain any where?" Ta girgiza masa kai, a hankali tace "But what will be the outcome of my final exams?" Yayi shiru yana kallonta, can a hankali yace "Shouldn't we get married first before thinking of that Mayraah...." Mayraah ta zuba masa manyan idanuwanta, bude side drawer yayi ya ciro wayarsa ya kunna yace "Let me make a call, if possible in ga ko za mu iya zuwa Abuja gobe..." Ita dai kallonsa kawai take, yana kunna wayan bayan ya gama booting kira ya shigo wayar, ya daga kai ya kalleta ganin me kiransa, hade rai tayi ganin Dr Maheer a gaban screen din...... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 [6/23, 8:19 PM] Khaleesat Haiydar💖: Har kiran Maheer ya katse Musharraf bai daga ba, can ya jefar da wayar kan gado ya hade rai yace "I see no reason why he should call me because u are missing, what does that mean?" ita dai bata ce komai ba, ta koma tayi lamo kan gadon tana kallonsa, Sake ringing wayar ya fara yi, Musharraf ya kalli screen din yaga Mami ce ke kiransa this time around, ya sauke ajiyar zuciya, sai da kiran ya kusa katsewa sannan ya dau wayan yayi picking ya sa handsfree ya ajiye gefen gadon yayi shiru, Daga daya bangaren Mami tace "Musharraf" A hankali yace "Good evening Mami" cike da damuwa Mami tace "Me yasa ka kashe wayar ka yau kwana uku kenan?" Shiru yayi bai ce komai ba, Mami tace "I am talking to you Musharraf" Musharraf yace "Ina hutawa ne" Mami tace "Kai kenan baza ka amshi kaddaran da Allah ya dora maka hannu bibbiyu ba kana matsayin ka na musulmi? baka tunanin nima kana saka ni cikin damuwa da sleepless night? Why will u just switch off u phones, Kasan adadin kiran da nake ma wayarka a rana kuwa?" Yayi kasa da murya yace "Am good Mami u need not to worry about me, i will take care of my self, nace maki kawai hutawa nake" Mami tace "Yanzu kana ina?" Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Abuja" Tace "To ka dawo gida Musharraf, hankalina baxai taɓa kwanciya ba idan ba gida ka dawo ba na ganka, it's not the end of life don an rabaka da warce kake so, dama can Allah ya riga da ya tsara baza ku yi aure a yanzu dai da ita ba, and there is always a reason for everything da kaga ya faru a rayuwar nan kuma Allah kadae yasan dai dai, so who are we to question him? sai kaga kilan Allah ya sake hadaku da ita nan gaba a inda bakwa zato, kuma in har matarka ce ko nan da shekara nawa ne babu abinda zae hana ka aurenta, be patient for now pls Musharraf, do not rush things, gaggawa na shaidan ne, ita ma if u have access na contacting dinta ka kwantar mata da hankali kada all the 5 years she spent in school ya tafi a banza tayi asaransa, nursing science is not a joke, she needs to graduate and get her cert, don a yanzu karatu na daya daga cikin gatanta a rayuwar nan, duk da foster parent dinta really tried for her ita ma ya kamata ace tana da abinda zata taimaki kanta da shi nan gaba without being too dependant on any one, idan tana da rabon ganawa da danginta a duk inda suke zata gana da su komin daren dadewa, everything is just a matter of time, don haka kuyi hakuri gaba daya, tun da har ka iya hakuri da rashin mahaifinka da kanwarka in a motor accident wannan ma Allah zai sa maka hakuri har yayi maku abinda yafi alkhairi daga kai har ita yarinyar, find a way to access her ku yi magana ta fahimta da ita, ka kara kwantar mata da hankali, do not be a coward son...." A hankali Musharraf yace "Thank you Mami" Mami tace "Plss gobe ka dawo gida ina son ganinka ka ji" Yace "In sha Allah" Tace "To maa sha Allah, ka ci abinci?" Yace "Na ci" Tace "Toh sai da safe, plss kar ka sake kashe wayarka son" Yace "I won't" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar, Musharraf ya juya yana kallon Mayraah da ta rufe fuskarta da pillow, gaba daya jikinsa yayi sanyi da maganganun Mami, ya koma inda take ya zauna kusa da ita cikin sanyin murya yace "Baby" Mikewa zaune tayi hawaye na sauka idonta tana kallonsa, nan da nan ta karyar masa da zuciya, he hate seeing her cry, cikin rawan murya tace "What Mami is saying is the truth, may be ba yanzu bane lokacin auren mu, kilan ba yanzu Allah ya rubuta za mu yi aure ba, dama tun kafin faruwan abubuwan nan ina ji a jikina kamar baza mu yi aure ba yanzu" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Kauda kai Musharraf yayi, bayan few seconds ya juyo ya kalleta.... Ta mike zaune tana share idonta tace "But i don't have anywhere to go to" Musharraf yace "Mayraah" Ta daga kai tana kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "I will keep on telling you not to be an ingrate, Ammi da Abba where the best of parent to you, basu taɓa failing dinki as parent ba, they raised u well, gave u quality education, protect you in whatever way they can, sun baki tarbiyyar da wasu dake tare da iyayen nasu ma basu samu ba, they gave u both Motherly and fatherly love, babu abinda kika rasa a rayuwar nan, ko da kika ji ina cewa mu je mu yi aure a wani wajen i don't have intentions of separating u from dem forever, komin daren dadewa za mu dawo, a yanzu nasan baza su taɓa bani aurenki ba bayan abubuwan nan da suka faru ni kuma zuciyata bazata iya jure hakan ba, you overheard our conversation with Mami, it won't be fair in bari 5 years dinki a university ya tafi a haka nan ba, kiyi hakuri baby, after ur final exams za mu je mu yi aurenmu, baza kuma mu dawo ba sai after u give me 2 beautiful kids like you" Kallonsa kawai Mayraah take, ya kamo hannunta a hankali yace "Yes dear, idan na tafi dake yanzu baki karasa karatun nan ba ban maki adalci ba cause zaki bukacesa a gaba it will be ur weapon against all odd in future" Hawaye na sauka idonta tace "A ina zan zauna in gama exams din?" Yayi kasa da murya yace "Gidanku, wajen Amminki da Abba" Ta kauda kai tana girgiza kai tace "Saboda ni ai bazai yiwu Ammi ta bijire ma mahaifiyarta ba, ta ce mata ta zabi ko ni ko ita, kaga bazan so abinda zai sa Ammi taki yi ma Hajja biyayya ba" Musharraf yace "Haka za kiyi hakuri ki zauna har ki gama exams din Mayraah, that doesn't mean ance ki bar gidan, Abba ma bazai yarda da haka ba, nasan Ammi ma komin me mahaifiyarta zata ce bazata so ki bar gidan ba bayan sun san baki da inda za ki, trust me Hajja doesn't mean all what she said duk da bansan me ya faru ba" Mayraah ta fashe da kuka ta kasa ce masa komai, cikin sanyin murya yace "Ki min alkawarin kuna gama final exams za mu tafi a daura mana aure Mayraah, ki min alkawarin baza ki canza ra'ayinki ba idan lokacin ya zo" Tana share idonta tace "Bazan canza ra'ayina ba sai in kai zaka canza naka, sai in kai ne zaka fasa aurena Sir" Yayi wani murmushi yace "The last thing i will do on earth is to deny u Mayraah, in kika ga ban aureki ba to bana numfashi ne, i am making you this promise" Wayarsa ne ya fara ring, duk suka juya suna kallon wayar, Maheer ne ke kira still, Musharraf ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yana kallonta, ita dai sunkuyar da kanta tayi, Musharraf ya dauko wayar, da sauri ta rike hannunsa cikin rawan murya tace "Me zaka ce masa?" Calmly yace "I know what to tell him" Daga haka ya mike ya nufi kofa ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, bayan some minutes Musharraf ya dawo dakin yana kallonta, Sunkuyar da kanta tayi, a hankali yace "Tashi mu je Baby" Ƙin tashi tayi kuma bata ce komai ba, ya karasa kusa da ita ya mika mata hannu, kauda kai tayi hawaye cike idonta ta sauko daga kan gadon tana kallonsa tace "What did u tell him?" Musharraf ya ɗan yi murmushi yace "You know I won't tell him u are in my house, so no need to worry" A takaice tace "I won't be worried even if u should tell him that" Daga haka ta dau yoghurt din da ya ajiye mata ta sha kadan sannan ta nufi kofa da sauran, ya bi ta da kallo har ta fita sannan ya sauke ajiyar zuciya, wayarta da ya ajiye a dakin ya daukar mata da magungunanta sannan ya dau makullin Motarsa ya fita, parlor ya sameta a tsaye, ya karaso inda take tsaye, ta kallesa tace "How comfortable are you in a dusty house?" Ya langwabar da kai yace "I was sick" Bata sake cewa komai ba, ya mika mata wayarta ta amsa sannan suka fita parlon, tana tsaye jikin motarsa bayan ya kunna to warm it up, ya zagayo inda take yana facing dinta yayi kasa da murya yace "I still want to remind u of how insecure i am with ur brothers Mayraah" Tana kallonsa a hankali tace "Insecure in what aspect?" Yace "Yanzu akwai aure tsakaninku" Da mamaki Mayraah tace "So u think ni zan iya auren daya daga cikin wa enda na taso nake ma kallon yayyina na jini? Mu yi aure da su as husband and wife or what? I don't understand" Tunanin hakan sai da yasa Mayraah ta fara jin wani sanyi na shigarta ta yaya ma hakan zai yiwu? How? tana girgiza kai tace "That's an abomination to me and them also" Matsawa tayi da sauri tana zaro ido ganin he is trying to lean on her, yayi hanzarin rikota onto him, tace "Meye haka?" Yayi kasa da murya yace "Not even a goodbye kiss Baby?" Kasa ce masa komai tayi, kawai wanda yayi mata ranan a gidansa ya fado mata, she wanted resisting this but he left her with no space for that..... Har suka bar unguwan Mayraah bata ce komai ba a motar, banda kamshin turarensa babu abinda ya cika mata hanci, kuma daga jikinta kamshin ke tashi, Bayan tafiyar kusan minti ashirin Mayraah ta gansu a area din makarantar su ya nemi waje yayi parking, still ita dai bata ce komai ba, ya jinginar da kansa da kujeran motar ya lumshe ido, bayan few minutes wayarsa ya fara ring, dauka yayi, yayi picking ganin Maheer ne ke kira, ita dai Mayraah idonta na kan titi, Musharraf yace "Yea sai ka wuce traffic light, i parked in front" Yana fadin haka ya Katse wayar ya juya yana kallon Mayraah da taki cewa komai har sannan, ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "Are you still angry Baby?" Ita dai bata ce masa komai ba, ɗan murmushi yyi caressing her hand a hankali yace "I am sorry Baby, u know i love you" Mayraah ce ta fara ganin motar Maheer, Musharraf na sighting dinsa ya dau wayarsa ya kirasa yace yayi parking kawai, juyawa yayi yana kallonta yace "I told him kina school, and i met u here...." Ta dauke idonta zuwa daya side din, yace "Za ki shigo school gobe?" Juyawa tayi ta kallesa, ta marairaice tace "Are you coming?" Yace "Sure" Tace "Ohk" ganin Maheer yayi parking Musharraf ya sauka daga motarsa, Maheer ya karaso ya basa hannu suka gaisa, ita dai Mayraah taki sauka daga cikin motar, Musharraf ya zaga ya bude mata motar yana kallonta, Tayi kokarin ganin hawayen dake taruwa idonta bai zubo ba ta sauko daga motar, Yoghurt din da ta bude ya dauka da ledan magungunanta ya mika mata, ta amsa ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Thank you" Musharraf ya kalli Maheer dake kallonsu, yayi feigning smile yace "I will be on my way Dr" Maheer yace "Thank you so much Dr Musharraf" Musharraf na kallon Mayraah yace "Take care of ur self" Daga haka ya zaga ya bude front seat ya shiga ya bar wajen, Maheer ya amshi ledan hannunta da drink yana kallonta yace "Mu je" bata yarda ta kallesa ba ta nufi motarsa tana share hawayen dake sakko mata, back seat ta bude ta shiga, ya shiga motar suka bar wajen, har suka yi nisa Maheer ya rasa me zai ce mata, ita dai sai goge hawayenta take da hijab din jikinta..... Mamaki ne ya cika Mayraah ganin inda ya kawota, bayan yayi parking a compound din gidan ya sakko ya bude mata side dinta yana kallonta, tayi karfin halin cewa "But me yasa zaka kawo ni nan yaya?" Yace "Nobody is at home" Shiru tayi ta kasa cewa komai, She knows he isn't saying the truth, lkci daya maganganun Hajja na dazu da safe ya fara dawo mata, to dama ta yaya Ammi zata zabeta akan Mahaifiyarta, shikenan Hajja ta rabata da Amminta kenan, shkkn bazata sake zama gidan da ta taso take tunanin gidan iyayen da suka haifeta ne ba, ta kalli Maheer dake kallonta shi ma ya kasa cewa komai don yasan ma tunanin da take, lkci daya duk jikinsa yayi sanyi, cikin rawan murya tana girgiza masa kai tace "Yaya bazan iya zama da Aunty Haseenah ba, kai ma kasan bata so na, ko in nemi favor wajen Hamidah in zauna gidansu har in gama exams?" Maheer ya kamo hannunta ya sakko da ita daga motar yace "Haseenah bata isa ta zama obstacle na zamanki a gidana ba Mimi, it's my house not her's, kuma dolenta ta zauna dake in dai tana son zama da ni" Mayraah ta fashe da kuka don yanzu kuma ganin abubuwan take kamar a mafarki, ta yaya ma za ace Ammi da Abba ba su ne suka haifeta ba, anya ba mafarki ma take ba tukun, why will they even say Ammi and Abba are not her parents, or are they pranking her?? Maheer ya kasa ci gaba da jure kukan nata ya rungumeta yana jin kukan nata har ciki ransa yace "Plss stop this Mimi...." Sai da tayi kukanta me isanta sannan ya dago kanta yana kallonta, he is just short of words, ya ma rasa wani kalma zai yi amfani da shi wajen rarrashinta, can dai yayi karfin halin cewa "Kiyi hakuri Mimi, we all never bargained for this...." Kai Kawai ta gyada masa, ya share mata idonta sannan ya kama hannunta suka shiga cikin gidan, ko parlor bai tsaya da ita ba ya tafi da ita dakin da yayi mata furnishing duk a yau, hatta kayanta ya kwaso mata daga can gidan with the help of Usman, Mayraah ta karasa cikin dakin ta zauna gefen gado tana goge idonta, duk ta ma gaji da kukan she's exhausted with crying, durkusawa yayi gabanta yace "Me zan siyo maki ki ci Mimi?" Tayi shiru tana kallonsa ko kiftawa babu, yace "Anything?" Ta gyada masa kai kawai, mikewa yayi yace "Toh kiyi wanka kiyi alwala kiyi sallah, i will be right back" Bata san sanda tace "Are you leaving me all alone with her?" Maheer ya girgiza kai yace "Ae bata nan, kuma ko tana nan babu abinda zai faru" Daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita.... Tun safe sai yanzu hankalin Maheer ya kwanta, don ko da suka fara waya da Musharraf ya sanar masa suna tare da Mayraah bai samu rest of mind ba har sai da ya ganta, yana driving zuwa inda zai samo mata abinci kiran Usman ya shigo wayarsa.... Mayraah ta gaji da zama ta mike a hankali tana kallon akwatunan kayanta dake dakin, bathroom ta shiga taga duk wani abu da zata bukata yana cikin bandakin, tayi wanka tayi alwala sannan ta fito daga bandakin, akwati daya ta bude ta ciro wani kayan da zata sa da hijab, sannan tayi sallan Isha.... Maheer na dawowa gida bayan yayi parking a parking lot wayarsa ya fara ringing, yana dubawa yaga Haseenah ce ke kiransa tun dazu take kiransa yaki dagawa, yayi ta kallon wayar daga karshe ya daga ya kai kunne, tun ranan da ya kai ta gida sai yau ya daga kiranta duk da kusan kullum sai ta kirasa yafi sau goma amma baya dagawa, daga daya bangaren Haseenah ta fashe da kuka cikin tashin hankali tace "Maheer yanzu zuwa gidanmu kayi ka tona min asiri akan abinda ni nasan ban taɓa aikatawa ba a rayuwata ta duniya? Maheer me kaje kace ma iyayena da suke ta kirana haka tun safe?" Maheer dake sauraronta yace "Haseenah dama da na ajiye ki kofar gidanku nace ki tafi wani waje daban ne?" Cikin kuka tace "Ta yaya kake tunanin zan iya shiga gida Maheer? Me zance masu idan na shiga? Did u even know who my mum is??" Maheer yace "Ina kika tafi?" Ta marairaice tace "I was confuse kawai na tafi gidan kawata, idan na shiga gida ban san me zan ce masu ba" Maheer yace "Bani address din gidan kawar taki in zo yanzu" Ta zaro ido gabanta na faduwa sosai, da sauri ta kauda zancen tana shesshekan kuka tace "Maheer ka gaya min me kaje kace ma iyayena ko hankalina zai kwanta? Wllh na kasa sukuni tun dazu, gashi na ki daga kiransu, what did u say to them?" Yace "Ohk, zuwa nayi nace masu ina neman alfarman su sanar maki kanwata Mayraah zata dawo gidana da zama saboda final exams dinta.... Na maki magana kin nuna ke baki amince ba, don haka shi yasa na zo har gida na sanar masu su da suka isa da ke, domin akan haka za mu iya samun issues a zaman aurenmu da ke wanda bai kamata ba, don kuwa yanxu haka bakya gidana" Shiru Haseenah tayi tana sauraronsa da mugun mamaki trying to understand what he is trying to say, can dai tace "Ban gane Mayraah zata dawo gidanka ba Maheer? Wace Mayraah din? Da can daga gidanka Mayraah ke zuwa makaranta?" Yace "Look Haseenah, i am not forcing you to stay under same roof with Mayraah, kawai dai nasan ke zan iya canza ki at anytime amma ita bazan iya canzata ba tunda jinina ce ita, kuma in har kina so na da gaske dole ki so jinina, don haka ni ba da gadara nake ce maki Mayraah zata dawo gidana ba, Aa alfarma nake nema a wajenki kanwata ta dawo gidana for sometimes don zata fara final exams dinta, in kuma kina ganin baza ki iya ba to bana jin zan iya ci gaba da rayuwa da warce bata son jinina, it's now left for u to decide, though it's request not command...." Haseenah da taji zuciyarta na tafarfasa amma tunda dai neman hanyan komawa dakinta take asirinta a rufe, ta dake tace "Atohh tunda ba kaina zata zauna ba ina ruwana da ita Maheer, ba fa kaina zata zauna ba" Yace "Glad u reason dat..." Ita dai tayi shiru tunani iri iri na yawo a ranta, Maheer yace "Kina ina in zo in dauke ki yanzu?" Tace "Gaskiya ban shirya ba, sai dai gobe" Yace "Allah ya kai mu" MAYRAAH Is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 [6/24, 6:01 PM] Khaleesat Haiydar💖: Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga our very own Barrister Inna (Aunty Fatima) Allah Ubangiji ya iya maki, ya raya maki zuri'a, ya kawo cinikin turaren wuta kaca kaca ki bude plaza a Gombe kina daddaga shoulders🥰 Lush and Scrumptious (The Mardiyya without letter R) da kawarta ICE, kuma na gaisheku da fatan alkhairi Allah ya kawo maku mazaje na gari, Sis Aisha Abba (Ummu Janan) i greet you and Baby Janan, Allah ya raya maki ita yayi mata albarka🥰 My lovely fans, i love u all as always, Allah ya iya maku💖 Mayraah na zaune kan darduma tun bayan da ta idar da sallahn isha bata tashi wajen ba tayi nisa tunanin da take ta ji an bude kofar dakin, da sauri ta juya tana kallon kofar, Maheer ya shigo da sallama rike da plate da ledan takeaway din abinci a hannunsa, karasawa yayi kusa da ita ya durkusa ya ajiye ledan ya ciro takeaway din ciki sannan ya juye a plate, ya daga kai suka hada ido ya sakar mata murmushi yace "Ur favorite" Ta sauke idonta tace "Thank you" Yace "Kinyi wankan?" Ta gyada masa kai, ya mike yace "Ohk bari in saka maki kayanki a press kafin ki gama cin abincin" Yana fadin haka ya mike ya nufi akwatunanta guda uku dake dakin ya bude guda daya, ta maida dubanta kan abincin gabanta ta fara ci a hankali, Absentmindedly take cin abincin da ko taste dinsa bata ji a bakinta, bayan wani lokaci ta juya taga ya bude wani akwatin with her inners inside, da sauri ta ajiye spoon din hannunta tace "Aa, ka bar min wannan zan yi da kaina" Ya juya ya kalleta yace "Ohk" maida akwatin yayi ya bude wani, ta ci gaba da cin abincinta, har ya gama jera mata duk kayan a press ko quarter din shinkafar bata iya ta ci ba, ya dawo kusa da ita yace "You are not eating Mimi, ko baki son shinkafan ne yau?" A hankali ta matsar da plate din tace "Na koshi" Yace "Ko in kawo maki Milo?" Ta girgiza masa kai tace "I am full" ya dau ledan maganin da Dr Musharraf ya siya mata ya fiddo su yana duba su, ita dai kallonsa kawai take, after examining the drugs ya ballar mata su ya mika mata yace "Take" ta mika hannu ta amsa sannan ta sha da ruwan goran dake gefenta, yace "Tunda baza ki ci abincin ba ni bani in ci" Daukan plate din tayi ta mika masa ya amsa, ta mike ta shiga bandaki zata wanke bakinta, Maheer ya juya yana kallon gefensa, Hijab dinta ya tsura ma ido for few seconds, can ya dauka ya kai hanci yana perceiving din scent din Hijab din, dai dai nan ta fito tana cewa "Yaya babu toothpaste a ciki" Shiru tayi tana kallonsa, ya ajiye hijab din da sauru yace "Oh ok bari in dauko maki yanzu" Yana fadin haka ya ajiye plate din hannunsa ya mike ya fita daga dakin, Mayraah ta karasa bakin gadon ta dau Hijab din nata ta kai hanci ita ma, ajiyewa tayi ta sauke idonta kasa ta juya a hankali ta koma inda take tsaye, can kuma ta sake komawa gun Hijab din ta dauka ta shiga bandaki ta saka a bucket ta zazzaga detergent dake cikin bandakin ta bude pampo, yana dawowa dakin ya kwankwasa mata bathroom din, ta bude kofar ta amshi toothpaste din sannan ta kulle, juyawa yayi ya dau abincin da ta bari ya fita daga dakin, Mayraah ta gama wanke bakinta ta dauro alwala ta fito, kwanciya tayi gefen gadon ta lumshe ido after so many thought that ran through her mind bacci ya dauketa, Wajen karfe goma Maheer ya shigo dakin, ya karaso kan gadon yana kallonta yace "Kinyi alwala kafin ki kwanta Mimi?" Kai kawai ta gyada masa idonta a lumshe, yace "To gyara kwanciyarki" Ta koma middle of d bed ta kwanta, ya rufa mata duvet yace "Don't forget to pray" Ta gyada masa kai, ya rage AC, ya kashe wutan dakin gaba daya sannan ya fita ya kullo mata kofar. Washegari da asuba Maheer zai tafi masallaci ya shigo dakin don tada ta, bai yi mamakin ganin ta tashi ba don a gida karfe biyar take tashi dama, ya fita zuwa masallaci, Mayraah na idar da sallah ta koma ta kwanta, for the past 4 days sai jiya tayi bacci sosai da daddare yanzun ma kuma wani baccin take ji kilan har da maganin bacci a magungunan da Musharraf ya bata, karfe takwas da kusan rabi ta farka, da sauri ta mike bayan ta tuna ai zata school yau, ta shiga bandaki don yin wanka, kafin tara da rabi har ta gama shiryawa, ta zauna gefen gado tayi jim tana bin dakin da kallo, babu abinda babu ciki, and it look beautiful, can dai ganin lokaci na wucewa kuma karfe goma take da lectures ta mike ta nufi kofa ta bude a hankali, main parlor ta shigo, ta dinga bin parlon da kallo, sosai parlon ma ya hadu yayi kyau, cream with touch of gold ne yawancin abubuwan parlon, ta kalli hanyar kitchen sannan ta nufi can, tana bude kofar ta gansa tsaye yana peeling Irish, ya juya yana kallonta yace "Good morning Mimi" A hankali tace "Good morning Yaya" Yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kin yi bacci sosai?" Ta gyada masa kai, yace "That's great" Karasawa tayi cikin kitchen din tace "Kawo in fere" Yace "Aa ke da baki da lafiya, kawai kije kiyi kwanciyarki i will serve u breakfast in bed...." Ɗan murmushi tayi wanda iyakarsa lips dinta tace "Ni dai ka kawo inyi zaka bata min lokaci" Juyawa yayi yana kallonta yace "Yunwa kike ji ne?" Ta girgiza kai tace "Aa, zan je school" Shiru yayi sai kuma yace "No Mimi, ki bari zuwa Wednesday, kin ga u are just recovering, kar ki yi stressing kanki" Tace "Pls ina son inje, I've missed a lot, and our exams is in 4 weeks time" bata jira me zai ce ba ta amshi peeler din a hannunsa ya sake mata ya koma gefe yana kallonta, ta fara fere irish din, juyawa yayi ya fita daga kitchen din, before 10:15 har ta gama ta soya kwai ta dafa ruwan shayi ta fito parlor da fried Irish and egg din, ganin baya parlon ta kai masa dinning ta ajiye sannan ta ja kujera ta zauna tana jiran shayinta ya huce, sai gashi ya shigo parlon, dinning area din ya karasa yana kallon plate din irish dinta wanda bai wuce kwaya biyar ba da karamin kwai a gefe yace "Meye wannan din Mimi?" Ta daga kai tana kallonsa, daukan plate din yayi ya juye abincin nata a nasa sannan ya kai middle of the parlor ya ajiye, ya koma ya dauko shayinta da nasa ya ajiye a parlon ya zauna yana kallonta yace "Dawo nan mu ci" Ta marairaice tana kallonsa, can ta kalli agogo ganin she is wasting her time ta mike ta tafi parlon ta xauna gefensa ta fara cin irish din, haka nan yayi forcing dinta sai da ta ci da ɗan yawa ta sha shayinta, 10:40 ya tafi da ita school din a motarsa.... Gaban department dinsu yayi parking yana kallonta yace "Yaushe za ku gama lectures?" Tace "4pm" yace "Ohk i will be here by 4" Tana kallonsa tace "Aa kawai zan samu me adaidaita sahu Yaya" Yace "Aa for today zan dawo in dauke ki" kudi ya ciro a aljihunsa yace "In case zaki ci abinci a cafeteria" Ta girgiza kai tace "Bazan ci komai ba" Yace "To amshi dai" karban kudin tayi tace "Nagode" Yayi mata sallama ya bar wajen, shiga department din tayi, tasan yanxu duk an shiga lectures, kawai ta tafi inda suke sallah ta zauna, shiru shiru ita dai bata ga shigowar Dr Musharraf ba har kusan 12, lokaci daya mood dinta ya canza gashi bata fito da waya ba balle ta kirasa, sai ga Coursemates dinta sun fara fitowa daga lecture hall, Hamidah na ganinta ta nufota da sauri tace "Lahh Mayraah, ashe kin shigo" Mayraah ta mata murmushi tace "Eh na shigo, Ya lectures din?" Hamida ta zauna gefenta tace "Alhamdulillah, na ma rubuta maki attendance, to me yasa baki shigo hall ba" Mayraah tace "Na ga time ya wuce ne shi yasa" Hamidah ta sauke ajiyar zuciya tace "Bari in nuna maki note din da muka yi, ya su Ammi?" Mayraah ta sauke idonta kasa tace "Suna nan lafiya" Da alama Hamidah bata son kawo ma Mayraah maganan aurenta da aka fasa shi yasa take ta kame kamen nuna mata note, ta ciro notes dinta ta mika ma Mayraah tace "Iyakar abinda muka yi kenan, nasan a yau duk za ki karance" Mayraah tayi murmushi ta amsa tana dubawa, nan sauran Coursemates dinsu suka nufo su ganin Mayraah, duk aka gaggaisa, babu dai wanda ya kawo mata zancen fasa aurenta, har suka shiga second lectures din ranan Mayraah bata da wani walwala balle sukuni, bata taɓa tunanin bazata ga Dr Musharraf a school ba yau, but he told her he will be coming, he didn't keep to his words, a haka dai suka gama lectures din wajen karfe hudu suka fito, sai da suka yi la'asar sannan Mayraah suka fito department din tare da Hamidah, Motar Maheer ta gani a inda ya tsaya da safe, Tana kallon Hamidah tace "Ya Maheer ya zo zai daukeni, mu je sai mu rage maki hanya" Hamida tace "Ai ko nagode" Tare suka tafi gun motar, Mayraah ta bude front seat, Hamidah ta shiga baya, bayan ta zauna ta gaida Maheer, ya amsa da fara'a yace "Ya lectures Hamidah?" Tace "Alhamdulillah" yace "How is preparation for exams?" Tace "Muna ta yi" Yace "To Allah ya baku nasara" Hamidah tace "Ameen mun gode" Mayraah ta kallesa ta gaishesa, ya amsa sannan suka bar gun, dai dai inda Hamidah zata samu adaidaita sahun anguwansu Maheer ya ajiyeta, ya bata 2k kudin ɗan sahu sannan ya kama hanyar gida tare da Mayraah, sai da ya fara tsayawa a hanya yayi masu takeaway din abinci sannan suka karasa gida.... Yana parking a parking space Mayraah ta dau ledan takeaway din ta bude motar ta sauka, shi ma ya sauka, yana kallonta yace "Haseenah is back" Sosai gabanta ya fadi sai dai bata ce komai ba, yace "Mu je mana" Ta fara tafiya ya bi bayanta har suka iso kofar parlon, ta bude kofar ta shiga da sallaman da tayi a ranta, Haseenah na zaune parlorn ta cakare dankwaki a kan doguwar rigar jikinta tana taunar cingam, tun da ta ji shigowar motar Maheer ta fito parlon ta zauna dama, Suna hada ido Mayraah tace "Ina wuni" Haseenah ta kalli Maheer dake bayan Mayraah a takaice tace "Lafiya" Mayraah ta ajiye ledan hannunta ta wuce daki, Maheer ya karasa parlon ya zauna yana kallon Haseenah yace "I dislike this gum u are chewing Haseenah, ke baki gaji da tauna chewing gum making that awful sound?" Mikewa tayi ta bar masa parlon ta yi hanyar dakinta kamar zata tashi sama, ya bi ta da kallo sannan ya mike ya bi bayanta, a daki ya ganta zaune gefen gado ta jefar da dankwalinta, yana kulle dakin ta fashe da matsanancin kuka tace "Maheer tun da nake ban taɓa ganin inda daga tarewar amarya da kwana uku za a kawo mata zankadediyar budurwa haka a ajiye a gida ba, yanzu kai a tunaninka adalci aka min? Wannan wani irin shiga hakki ne? Ko amarci na baza a bari in gama ci lafiya ba, da can kai kake rike da ita ko duk don a musguna min ne yasa za ace zata dawo gidan nan da zama, bikina haka nan aka yi sa a gantale saboda ita, ko daurin auren baka je, babu wani program da aka yi, sai yanzu kuma ka kawo min ita kace nan zata zauna" Tana kai wa nan ta fada kan pillow ta fashe da matsanancin kuka, Maheer yayi shiru yana kallonta, can ya sauke boyayyen ajiyar zuciya ya karasa kusa da ita ya zauna gefenta ya dagota, yayi kasa da murya yace "Kiyi hakuri Haseenah, that wasn't the plan wllh, kuma ban yi hakan don in shiga hakkinki kamar yanda kika ce ba, ban taɓa kawowa a rai Mayraah zata zauna gidana ba, abubuwa ne suka zo da haka, and Mayraah is only staying here for the meantime not forever, kiyi hakuri don Allah ki min alfarma ta zauna gidan nan zuwa wani lokaci, kinga zata taimaka maki wajen aikin gida, and Mayraah bata da matsala komai kika sa ta zata maki, pls albarkacin soyayyan da kike min kiyi hakuri ku zauna lafiya, her staying here is just for a while i promise u" Ita dai goge hawayenta kawai take tana wani cika tana batsewa, ya rungumeta yana shafa gashin kanta yace "Kin ji dear" cike da shagwaba tace "Shi kuma walakanta ni da kayi 3 days ago fa?" Yayi kasa da murya yana kallonta kasa kasa yace "Sharrin shaidan ne dear, i don't know what came over me that day, forgive me pls" Sai dab da magrib Maheer ya fito dakin Haseenah, da mamaki yake kallon ledan abincin da suka siyo daxu dake saman center table, juyawa yayi da sauri ya nufi dakin Mayraah, zaune ya ganta kan darduma da materials din karatu a gabanta, ta daga kai tana kallonsa, da damuwa yace "Dama baki dau abincin ba Mimi?" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, juyawa yayi ya koma parlon ya fara dauko plate a kitchen da goran ruwa a fridge sannan ya dau takeaway din ya nufi dakinta, Haseenah da ta fito parlon sanye da wata er dangalalliyar riga ta daura karamin towel a kanta ta bi sa da wani kallo tana kyabe baki, can ta ja tsaki, Maheer na shiga dakin ya duka gaban Mayraah ya zuba mata abincin, ba tare da ya kalleta ba yace "I am sorry Mimi, i slept off, ban san baki dau abincin ba" ita dai bata ce komai ba, bai bari sun hada ido ba ya mike ya fita daga dakin. Haseenah na zaune parlor tana danna wayarta Maheer ya fito daga Bedroom dinsu bayan yayi alwala, yana kallonta yace "Zan je masallaci, ke baza kiyi sallan bane kike zaune nan?" Ta langwabar da murya cike da shagwaba tace "Zan yi mana, Baby don Allah gasasshiyar kaza nake sha'awar ci" yace "A ina za a samo kaza yanzu?" Ta wani turo baki tace "Ai ka fi ni sani, kawai ka fita da motarka kayi parking a waje, ana idar da sallah ka tafi ka siyo min ni dai" Ya ɗan yi jim sai kuma ya juya ya koma daki ya dauko makullin motarsa sannan ya fita daga parlon, ta tafi window da sauri tana leka compound har ta ga ya fita da motarsa sannan ta dawo parlon, Zaunawa tayi ta dau wayarta ta yi dialing number Badiyya, yana fara ring kamar jira Badiyya take ta daga cikin fada tace "Wai ke Haseenah baki ganin kirana ne? Ban fa gane abinda kike nufi da ni ba ina ta binki ki bani kayana kin ki, kin fa san halina sarai Haseenah, ina ta bin ki a hankali kina raina min wayo ko? nace na fasa siyar da gold din nan ki bani kayana ko ana dole ne?" Haseenah ta katse ta tace "Ke dai baki da hakuri wllh Baddiee, gwal dinki dai na nan ki kwantar da hankalinki, kinsan dae bazan cuce ki ba kawata" Badiyya tace "Haba wannan ai ya fara zama rainin hankali, abu kusan sati daya yanzu kina ta yawo da hankalina, gashi bani da ko sisi a account sai da na siyar da zobuna na biyu na biya bashin da ake bi na sannan na samu kwanciyar hankali, sannan inyi ta kiranki ki ki daga wayata, ni dai yanzu ki gaya min kina ina?" Haseenah tace "Labari na kira in baki da dumi duminsa" Badiyya tace "Haba dai, Maheer din yaje Zarian ne?" Haseenah tace "Wani Zaria? gani nan a gidansa yanzu haka nake gaya maki har abu ma ya sake kankama, ashe dama da gaske kike da kika ce min Hajja taje ta kori Mayraah a can gidan?" Badiyya tace "Au da ke kin zata wasa ne, ae ina nan ina ta zugata duk abinda za ace mata kar ta saurara kowa, har Ammi taki saurara tace sai dai Ammi ta zabi ko ita ko Mayraah, Abba ma dazun nan ya bar parlon nan, kinsan shi ma yana respecting dinta sosai kuma yana jin maganarta, kuma baya son abinda zai daga hankalin Ammi, to duk da zuwan Abba har yanzu Hajja na kan bakanta, yanzu zancen da nake maki ba a san inda Mayraahn ma take ba, wa ya sani ko duniya ta shiga, kinga dama ni da ake ma kallon er duniya ai gwara ita ma ta zama er duniyar, Allah Ubangiji ya sa ta fada hannun uwar karuwai, Magajiya ake ce mata ko me? Ita dai, ko kuma Allah ya sa ta fada hannun ɗan iska yanda cikin kankanin lokaci zai lalatata yayi lagos ko tafa da ita, daga nan kin ga ta samu hanya ai, kawai fatana kenan Allah kada ya bata ikon fadawa hannun kirki, kuma Allah ya kara hankadata tayi gaba yanda ko waiwayo mu bazata sake yi ba, Musharraf kuma dama sai gani sai hange a gareta, tana ji tana gani zan auresa...." Haseenah tayi wani dariya tace "Wani duniya?? To ga Mayraah a gidana" Badiyya sai da ta mike tsaye daga kwancen da take tsabar shock, da wani irin mamaki tace "Gidanki kuma??" Haseenah tace "Wallahi kuwa nake gaya maki Badiyyah" Cike da confusion Badiyya tace "Gidanki fa kika ce Haseenah?" Haseenah tace "Karya zan maki ne? To ta ma rigani dawowa gidan in gaya maki, nima dawowa nayi na samu har ta tare a nan, ga daki an mata furnishing kamar amarya, an zuba mata komai a bathroom, ga kayanta ta jera reras a sipp" Badiyyah tayi mitsi mitsi da ido tace "Kan uban cannn, kuma kika yarda Haseenah???" Haseenah tace "Ohh ashe baki yi trusting dina ba kenan Badiyya, ae a halin da ake ciki yanzu dole in nuna na yarda, sannan in nuna kamar ba komai, dalilin da yasa Maheer ya maido ni cikin sauki kenan fa, ke kin zata haka kawai Maheer zai bi ta kaina kwana kusa? kinga dole nima inyi melo for now, amma hauka ake da Mayraah zata zauna gidana inyi shiru in koma gefe in zuba ido, yarinyar da na tsana tun ma ba a san wacece ita ba balle yanzu da nasan babu hadinta da Maheer na gano mara asali ce ita tsintattciya" Badiyya tace "Tabdijam, wato saboda ya nuna ma Hajja iyakarta shi yasa ya daukota ya maida ta gidansa kenan, ke kuma kika yi shiru kika amince saboda kina son a maido ki" Haseenah tace "Ke wai baki san komai dan siyasa bane Badiyya, yarinyar da duk duniya nake jin bbu warce na tsana irinta ne zan yarda mu zauna lafiya under same roof?? Inaaa ai kema kinsan bazai yiwu ba" Badiyya tace "Ya fara fita aiki ne Maheer din?" Haseenah tace "Naji dai yana cewa gobe zai je aiki" Badiyya ta gyada kai tace "To maa sha Allah, zan kiraki goben" Haseenah tace "To Allah ya kai mu, ai ina ga daga karshe duniyar ma zata gwammace ta shiga da dai ta zauna gidan nan" Badiyya tace "Aa tun yaushe, ke dai kawai mu yi waya gobe" Daga haka ta katse wayar, Haseenah ta dinga girgiza kafa tunanin ta inda zata fara na yawo a brain dinta, can tayi wani murmushi tana kallon hanyar dakin Mayraah tace "Zaki gwammace shiga duniya da zaman gidana" Tana fadin haka ta mike fuuu tayi hanyar Bedroom dinta ta shige ta kulle kofar. Wajen karfe bakwai da rabi Maheer ya shigo parlon, Haseenah na jin shigowar motarsa dama ta fito da sauri, da ido take binsa har ya karaso tsakiyar parlon ya ajiye leda daya, ta dinga kallon ikon Allah taga yanda zai yi da dayan, hanyar dakin Mayraah taga yayi, da hanzari ta sha gabansa tana masa wani kallo tace "Ban gane ba Maheer, ita ta aike ka halan? Meye wannan din zaka kai mata" Maheer ya hade rai yace "Hey Haseenah, do not start this with me, kina ganin zan ci abu ne in hana kanwata a gidan nan? Are you even okay? Kinga in kina so mu zauna lafiya ki cire idonki a duk abinda za ki ga nayi ma Mayraah, ina ta lallaba ki tun dazu kada ki bari inyi displaying my other side" Barin ta yayi wajen a tsaye ta bi sa da kallo baki bude, yana bude kofar dakin Mayraah yaji ta sa makulli, dama tun da taji fitar motarsa ta kulle dakin da makulli, ya kwankwasa kofar yace "Mimi open the door" mikewa Mayraah tayi daga inda take duke tana karatu, tun bayan da ta idar da sallahn magrib taji alamar cikinta zai fara mata ciwo, ta karasa ta bude kofar, mika mata ledan hannunsa yayi yana kallonta yace "Do you need any other thing?" Ta ɗan yi shiru tana kallonsa, sai kuma tace "I need sanitary pad" Yace "Oh.. ok" Juyawa yayi ya bar wajen, Mayraah ta mayar da kofar ta kulle da lock, Haseenah dake tsaye parlor har sannan ta bi Maheer da kallo ganin ya nufi kofa, tana jin sa ya sake fita da mota, ta zauna gefen kujera zuciyarta na tafarfasa tana kokarin calming kanta down, sai kusan 8 Maheer ya dawo gidan, Haseenah na jin shigowarsa gidan tun bai karaso cikin parlor ba ta shige dakinta ta rufe kofa, Maheer yayi knocking dakin Mayraah ta bude, ya mika mata ledan hannunsa yace "Akwai magani a ciki, i don't know ko zai maki naga yanzu baki son allura" Tace "Zai yi, nagode" Yace "Let me get u hot water" Ta gyada masa kai, kitchen ya tafi ya dafa mata ruwan zafin ya zuba a flask ya kawo mata har da cup, ta amsa tana kallonsa tace "Nagode yaya" Yace "Take care of ur self" Ta gyada masa kai, yana barin wajen ta kulle dakinta. Har dare ya tsala Mayraah bata yi wani bacci ba saboda ciwon mara, Maheer na kwance amma gaba daya tunaninsa na kanta cause yasan yanda cramps ke mata, ya kuma san wahalan da take sha, in da gida ne har ayi asuba ya dinga shiga dakinta yana dubata shi da Ammi, but now baya son issue da Haseenah dake gefensa, yana fita dakin nan yasan sai ta bi shi ya zamar masu bacin rai, haka nan ya dinga juye juye all his thinking akan Mayraah, kasa daurewa yayi daga karshe ya mike zaune yana kallon Haseenah dake baccinta hankali kwance, taba ta yayi yace "Dear...." Ta bude ido a hankali, ya kunna closet light din dakin, ta mike zaune tana murza ido tana kallon agogo dake nuni da karfe biyu da rabi tace "Baby lafiya, why are you awake?" Yace "Erm pls, i want you to check on Mayraah bata da lafiya, ni ina fita yanzu zaki iya maida shi issue" Tace "Bata da lafiya? Shi yasa ka kasa bacci? To me ya sameta?" Yace "Ban gane na kasa bacci ba, u have started again ko?" Tace "To nace me ya sameta?" Yace "Ki je ki dubata" Sauka tayi daga kan gadon da shegun kayan baccin jikinta zata fita daga dakin yace "Haka za ki fita?" Juyawa tayi ta kallesa tace "Wajen namiji zan je halan?" Yace "Plss cover ur body before going out Haseenah" ta wani kyabe baki ta dau zani ta daura sannan ta fita dakin.... Mayraah na durkushe a dakin ta daura kanta saman gadon wayarta dake gefenta ya fara vibrate ta jawo wayar da kyar ta daga ta kai kunne amma bata ce komai ba, daga daya bangaren yace "Kin samu kin sha ruwan zafin?" kai kawai ta gyada masa, yace "Har yanzu kuma baccin bai zo maki ba?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "You are not saying anything ko dai baccin kike ji Baby?" Kamar zata yi kuka tace "Aa" a hankali yace "I wish I can take away the pains for you" Ita dai bata ce komai ba don azaba ya isheta, yace "Ko za ki sake shan maganin" da kyar tace "Na sha sau uku ai" shiru yayi yana jin tausayinta har cikin ransa, cike da karfin hali tace "Ina zuwa" Yace "Aman ne dai?" Tace "Eh" Ajiye wayar tayi ta shiga bandaki da sauri, Haseenah ta gama zagayenta a corridor din dakunan bayan yan mintuna ta koma dakinsu tana kallon Maheer dake zaune, ta kashe closet light din dakin tace "Bacci take yi, kai ma sai ka kwanta kayi bacci" Bata jira me xai ce ba ta shige jikinsa.... Har karfe hudu Dr Musharraf bai yi bacci ba kamar yanda Mayraah bata yi ba, every few minutes xai kirata to check on her, har dai ya kirata around 4:45 yaga bata daga ba, nan ya gane bacci ya dauketa.... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 [6/26, 10:09 AM] Khaleesat Haiydar💖: Washegari da safe Mayraah ta bude idonta a hankali ta dalilin vibration din wayarta, ta mike zaune da sauri ganin gari ya waye kuma ko kiran sallahn asuba bata ji ba, jawo wayar tayi taga Musharraf ne ke kiranta, ta kalli agogon wayar dake nuni da karfe takwas na safe, har kiran ya katse bata daga ba, tayi tagumi tana kallon window din dakin tana jin ciwon cikin har sannan yana damunta sosai, bayan kusan minti sha biyar ta daure ta sauka daga kan gadon a hankali ta nufi bandaki, kafin karfe tara tayi wanka ta shirya, ta dau handout din da take karantawa jiya ta saka a jaka, kallon agogo tayi don makaranta take son tafiya, ta zauna gefen gado tana tunanin ta yanda zata fita ta hado shayi don ta sha magani, ganin lokaci na wucewa ta mike ta nufi kofa ta bude a hankali ta tafi parlor, babu kowa a parlon har ta nufi kitchen sae kuma ta dawo ta tafi window din parlon tana dubawa parking space, juyawa tayi ta karasa kitchen ta hada shayi sannan ta fito, tsaye ta ga Haseenah a parlor don tana jin kamar an bude kofa tayi maza ta fito, duk da yanda gaban Mayraah ya fadi bata nuna hakan a fuskarta ba, don kallo daya tayi mata ta dauke kai tace "Ina kwana" Haseenah dake tsaye sanye da rigan wanda da kadan ya wuce cinya tana kallonta da kyau tace "Ke sae ance kiyi shara da goge goge sannan za ki yi? hankalin ki bai baki abinda ya kamata kiyi first thing in the morning ba kina tashi? ko dai baki ga karfe nawa bane yanzu?" Mayraah na juya shayin hannunta da cokali courteously tace "Yayan bai gaya maki bana shara ba?" Sake baki Haseenah tayi tana kallonta babu ko kiftawa cause she wasn't expecting that, Mayraah ta girgiza kai a hankali tace "Ni ae bana shara...." Tana fadin haka ta juya ta bar ta a wajen ta nufi dakinta ta shiga ta kulle kofa, Haseenah ta kasa rufe baki, she couldn't believe her ears, What??? juyawa tayi ta nufi dakinta kamar zata tashi sama, yanda tayi banging kofar yasa Maheer farkawa ya mike zaune da sauri yana kallon agogo yace "Kin dubo Mimi? Ya jikinta?" Tun dawowarsa sallan Asuba yayi niyyar shiga duba Mayraah, amma Haseenah ta janye hankalinsa tun sannan da bacci ya daukesa sae yanzu ya farka, bai jira Haseenah ta basa amsa ba ya sauko daga kan gadon da sauri ya dau Jallabiyansa zai sa, Haseenah na masa wani kallo tace "Wace Mimin? Yarinyar da ta min rashin kunya yanzu kiris ya rage ta zageni??" Maheer ya juya yana kallonta yace "Rashin kunya kuma?" Kamar zata fashe da kuka tace "Wallahi kuwa dear, daga nace ta taimaka ta ɗan mana gyaran gida ni kuma in nema mana breakfast a kitchen, kawai ta zabga min wata uwar harara wai ance min tana shara ne da zan sa ta shara, ko baka gaya min ita bata shara ba, Maheer i was so shocked, yarinyar nan na fadin haka tayi wucewarta kamar zata bangajeni ta bar ni a tsaye, kai fa kace in zauna lafiya da ita shine har yasa duk na ajiye makaman yaki nace ta taimaka ta mana gyaran gida ni kuma inyi breakfast" Maheer ya karasa saka Jallabiyansa yace "Yeah she is Asthmatic bata shara, sannan bata duk wani aiki da zai yi triggering dinsa, idan me taya ki shara kike so sai a samar maki me aiki karama ta dinga maki" Yana kai wa nan ya fice daga dakin, Haseenah ta bi sa da kallo baki bude, dakin Mayraah ya bude ya shiga ya sameta zaune gefen gado, ya kulle kofar yana kallonta ya nufeta, Kallo daya tayi masa ta ci gaba da shan shayin da ke hannunta, ya karasa ya zauna gefenta yace "Mimi ya jikin? Hope u slept well?" Taki kallonsa tace "Ehh" Shiru yayi, cause kilan yanda ya santa ciki da bai Ammi ma bata santa haka ba, with the way she answered shows that she is angry at him, ya sosa kansa yana kallonta a hankali yace "Ai na shisshigo fa da daddare kina bacci" Ko kallonsa bata yi ba ta ci gaba da shan shayinta, ya ɗan yi shiru, can a hankali yace "Ohk am sorry Mimi..." Ta marairaice tana neman kuka tace "Kasan ai bazan iya bacci ba, kuma shine....." Kawai sai ta fashe da kuka, kame kame ya fara yana bata hakuri, yace "I am so sorry Mimi, i use to over sleep this days saboda aiki yana min yawa, yau ma kawai gani nayi asuba yayi" Ita dai taki cewa komai, yace "Baki ga bread a dinning table ba, bari in je in dauko maki" Yana fadin haka ya mike ya fita, dinning area ya tafi ya dauko mata bread da butter with knife ya dawo dakin, ta ajiye cup din shayin don har ta shanye, yana kallonta yace "Baki son bread din ne kika shanye shayin?" A takaice tace "Eh" Daga haka ta mike ta nufi well ironed hijab dinta ta dauka zata sa, da mamaki yace "Ina zaki?" Ta saka hijab din ta dau handbag dinta tace "School" Yace "Will u be able to cope in school?" Tace "Tunda nayi coping da daddare ai zan iya coping a school ma" Shiru yayi yana sosa keya, can ya kalleta yace "To bari in shirya sai in ajiye ki" Tace "Ina son in hau adaidaita sahu am late already" Yace "I promise i won't waste time" Komawa tayi ta zauna gefen gado ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, yana komawa Bedroom dinsu yaga Haseenah kwance kan gado tana shessheka, har zai shiga bandaki sai kuma ya tsaya yana kallonta yace "Saboda Mimi bata maki shara ba kike kuka?" Mikewa zaune tayi a fusace tace "Yarinya tayi min rashin kunya in gaya maka ka maida ni er iska? Maheer dama dawowa da ni kayi don kai da ita ku dinga walakanta ni a gidan nan? Kanwata ta kusan ta hudu ta min rashin kunya daga dai maganar fatan baki amma ka maida ni er iska?" Maheer na girgiza kai yace "Haseenah karya kike, rashin kunya is the last thing da Mayraah zata maki, i know her too well, ke dai ki nemi wani sharrin da zaki mata amma ba wannan ba, nasan politely zata gaya maki bata shara not rudely, i know Mimi" Yana fadin haka ya shige bathroom ya kulle kofa, wani murmushi Haseenah tayi tana girgiza kafa tana jin zuciyarta na tafarfasa, can tayi kwafa a hankali mike ta fita ta koma parlor, saboda Mayraah Maheer bai bata lokaci wajen shiryawa ba, ya fito ya shigo parlor, kallo daya yayi ma Haseenah ya nufi kitchen, tashi tayi ta bi sa, taga yana zuba ruwan zafi a cup, tayi kasa da murya tace "Baby aiki zaka tafi?" Yace "Ai na ce maki yau zan yi resuming" Sosai farin ciki ya cikata jin zai tafi aiki yau, amma sai ta ɗan hade rai tace "Ko sati daya baza su iya baka ba don Allah, daga aure kwana hudu sai ace ka koma aiki, a ina ake haka, why not ka dau leave kawai ko na sati biyu ne" Shi dai bai ce mata komai ba ya ci gaba da hada shayinsa, Ta marairaice tace "Gashi ban maka komai na breakfast ba, wallahi jiya na zata u were just pulling my legs da kace zaka aiki" Yace "No offense, gobe sai kiyi" Tana murmushi ta rungumosa ta baya tace "To Allah ya kai mu Babyna, amma ka gaya min what will i be cooking for dinner?" Yace "Cook anything" Ta kwanta a bayansa tace "Alright dear" Juyowa yayi suka fita kitchen din tare, a parlor ya zauna yana shan shayin, ita dai tana zaune gefensa yace "Dauko min makullin motata" Mikewa tayi ta nufi dakinsu, tana shiga kiran Badiyya na katsewa a wayarta, ta juya ta kalli kofan da ta rufe kafin ta daga da sauri, Haseenah tace "Yanzun nan ma shirin fita aiki yake, in the next 15 to 20 minutes kawai ki fito" Suna gama magana ta ajiye wayar tana murmushi, sannan ta dau makullin Motarsa da tsadadden turarensa da agogo dake gaban madubi ta fito zuwa parlor, ya mike ya amshi makullin ta fara fesa masa turaren tana cewa "You look cute sweetheart" Ya amshi agogon hannunta yana kokarin saka wa yace "Thank you" Shafa beard dinsa tayi ta marairaice tace "Don Allah Baby ka rufa min asiri kar ka kalli ko wace ya mace idan ka fita, sannan banda sakar ma patient mata fuska har ma da nurses plsss" Murmushi yayi da ya kara fito mata da ainahin kyansa, Haseenah ta kasa daina kallonsa, ya karasa saka agogonsa yace "Baki da matsala" Daga haka ya juya ta bi sa da kallo tana jin wani sabon sonsa, dakin Mayraah ta ga ya nufa, nan da nan ta hade rai har ta daina hangosa, Maheer na shiga dakin ya ganta durkushe bakin gado, ta juya jin an bude kofar dakin, ya karaso da sauri yace "Cikin ne?" Kai ta gyada masa da kyar, yace "You see, i know u can't cope in school Mimi, kiyi hakuri ki bari kawai zuwa gobe in kin kara samun sauki ki je" Cike da karfin hali ta mike tana girgiza masa kai tace "Aa ni zan iya" Da mamaki yace "Like this??" Jakarta ta dauka da wayar ta nufi kofa tana tafiya a hankali tace "Na ce maka zan iya" ya bi ta da kallo har ta fita sannan ya bi bayanta, suna fitowa parlor Haseenah dake tsaye har sannan tana jiran fitowar Maheer ta buda ido da mamaki ganin Mayraah cikin shiri, Maheer yace "Zan ajiyeta makaranta in tafi aiki" Da sauri Haseenah tace "Makaranta kuma Dear? Ba naji kace bata da lafiya ba? Maimakon ta zauna ta huta, me zata je yi a makaranta ita da ba lafiya ba" yace "Ta samu sauki ae" Haseenah taji kamar ta rusa ihu ta ma rasa abinda zata ce masa, Ita dai Mayraah ta karaso cikin parlon tana kallonta tace "Sai anjima" Daga haka ta nufi kofa, Haseenah ta bi ta da kallo, Maheer yace "Sai na dawo" Kin ce masa komai tayi tsabar bacin rai, shi dai ya nufi kofa ya fita, fuuuu ta juya ta koma dakinta. A hanya Maheer na driving wayar Mayraah dake kafarta ya fara vibrate, ya juya yana kallon screen din wayar, tayi silencing kiran bata daga ba, bayan tafiyar kusan minti goma Maheer yace "You are going to school because of him right?" Ta ɗan kallesa da mamaki tace "Why because of him?" Maheer yayi shiru yana ci gaba da driving dinsa, can yace "Toh mu tafi asibiti mana, don nasan ko kinje school babu abinda zaki yi sai kwanciya, i know how u behave during this period of the month...." Mayraah tace "Makaranta zan je i can cope" Bai sake ce mata komai ba har suka isa makarantar, yana isa gaban department yayi scanning parking area din da ido har ya hango motar Musharraf, kashe motarsa yayi ya jinginar da kansa da kujera, Mayraah ta juya tana kallonsa ganin bai bude motar ba, can dai da taga ba shi da alamar budewa tace "Yaya i am late fa" Tada motar yayi without looking at her ya fara reverse yace "Baza ki shiga school din nan yau ba Mimi, when I know babu wani lectures da zaki iya zama a class kiyi attending" Ta marairaice tace "No plss yaya, nace maka fa zan iya wllh" Bai saurareta ba ya ja motar suka bar department din, nan da nan hawaye ya cika idonta ta dinga kallonsa, shi dai bai kalleta ba har suka fita daga school din, ya dau hanyar asibitin da yake aiki..... Har suka isa asibitin Mayraah share hawayen da ya ki tsaya mata take, kiris ya rage ta fashe da kuka, bayan yayi parking ba tare da ya kalleta ba yace "Wajen Dr Musharraf za ki je ba lectures ba, if i may ask, do u still have any business with him?" Bai jira me zata ce ba ya sauka daga motar, ta fashe da kuka sosai, ya zagayo ya bude mata motar yace "Sauko" Ta hade rai ta sauko ya kulle motarsa, yace "Mu je" Tafiya ta fara yi yana biye da ita suka shiga cikin asibitin, gaba daya nurses din sun santa don banda yanzu da karatu yayi mata zafi a da asibitin is like her second home barin idan yana da aiki weekends, to a nan take spending weekend dinta ita ma, tayi composing kanta suka gaisa da nurses din gaba daya ta bar sa reception tsaye ta nufi office dinsa... Tana tsaye ya karaso ya bude office din ta shiga ciki ba tare da ta kallesa ba ta tafi inda take kwanciya duk sanda ta zo, hawaye kawai take a inda take kwance ga ciwon ciki da ya takurata sae juye juye take, kiran Musharraf ya shigo wayarta for the second time tun shigowarsu asibitin, ta mike zaune a hankali tana kallon screen din wayar, leka office din Maheer tayi da yake anyi demarcating inda take kwance da main office din, ta gansa zaune office chair dinsa yana attending to a lady with her baby, Daga kiran Dr Musharraf tayi ta kai kunne tayi shiru, Daga daya bangaren yace "Mayraah" Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace "Ya Maheer yace bazan je school din ba kuma" Shiru Musharraf yayi, bayan few seconds a hankali yace "Ohk" Shiru suka yi gaba daya, can Musharraf yace "Hope you are feeling much better now?" Ta gyada masa kai tace "Alhamdulillah" Yace "Allah ya kara lafiya, sai anjima" Nan da nan jikinta yayi sanyi wasu hawayen suka cika idonta, ta ji ya katse wayar, leka office din Maheer tayi ta gansa shi kadai yana rubuce rubuce, ta zabga masa wani harara kamar yana ganinta, dai dai nan ta ga ya mike ya nufo inda take, da sauri ta goge idonta ta koma ta kwanta ta juya baya ta rufe ido, yana isa wajen ya leka fuskarta yace "Mimi" taki bude idonta, yace "Ina jin ki fa kina waya not long ago" Mayraah tayi still jin abinda yace, sai a sannan ta tuna how sharp his hearing is, ta mike zaune fuskarta babu walwala, yace "Cikin na ciwo har yanzu?" Ta gyada masa kai kawai, yace "In maki allura?" Ta kallesa suka hada ido, shi ya fara dauke idonsa ya juya, sai kuma yace "Bari in kira Amina ta maki" Daga haka ya nufi kofa ya fita daga office din, sae da ya sa ta ɗan ci abincin da aka siyo mata sannan Nurse Amina ta mata alluran, ko minti ashirin ba ayi da mata alluran ba bacci ya dauketa, don dama ana mata alluran take ji kamar an zare mata ciwon... Tun da Maheer ya fita tare da Mayraah Haseenah ta rasa sukuni, tasan zuwa yanzu dai Badiyyah ta kamo hanya, kuma tana zuwa gidan nan tunda har Mayraah bata nan dole hankalinta zai koma kan zancen gold, gaba daya ta rasa yanda zata yi, daga karshe dai ta saka Hijab dinta ta fita compound da sauri, gun mai gadi ta nufa yana gaisheta ko amsawa bata yi ba tace "Malam ya sunanka?" Da ladabi yace "Musa Hajiya" Haseenah tace "Ohk, akwai wata mata da zata zo gidan nan at anytime, zaka ganta doguwa tana da haske, sannan bata kai ni jiki ba, to tana zuwa kace mata babu kowa a gidan kai kadai ne" Mai gadin yace "An gama Hajiya, in sha Allahu" Haseenah ta juya ta koma ciki, wayarta ta dauka ta rufe layin da Badiyya ta san ta da shi yanda tana kira zata ji switch off, sannan tayi dialing number kawarta kuma aminiyarta Salima, Salima na dagawa Haseenah ta saka wani uban shewa tace "Kawata ayyuka sun yi kyau fa ta ko ina in gaya maki" Salima tace "Kai haba, bani labari in sha" Haseenah ta gyara kwanciyarta tana murmushi tace "Wallahi in gaya maki ya dawo yanda kika san wani bita zai zai, kin ma san nawa ya tura min a account jiya da nace masa bani da kudi? Wallahi tunda nake da shi bai taɓa tura min irin kudin ba" Salima ta saki guda tace "To maza a ciko min kudaden mutane in kai masu" Haseenah tace "Kai wannan ai dole ne, don Allah wacece wannan me siyar da kayan nan??" Salima ta kwashe da dariya tace "Aa wallahi bazan fada ba, kinsan babu boye boye tsakanina da ke to nima wllh sarowa nake wajenta in ɗan yi mix sannan in daura nawa riban in siyar, yanzu in na gaya maki ai gun ta zaki nufa direct gashi nata shine sadidan haka kawai ki saka bawan Allah ya zama makale mata ki ja a koresa aiki, gwara dai ki tsaya iya nawa me mix" Haseenah tace "Kai kawata, wallahi ni ko biyanki kika ce inyi sai in biyaki ki bani numberta, fadi price in tura maki yanzu" Salima ta kwashe da dariya tace "Yanzu duk ba wannan ba, Hajiya cikon kudin Malam fa? Kinsan fa har da nasa aikin, ko kinji ya sake maki wancan maganar me muni?" Haseenah tace "Cewa ma yayi sharrin shaidan ne wllh, kar fa ki ji komai duk zan tura kudin casss, sannan akwai ma wani matsalar yanzu haka Salima, amma kinsan ance the wall have ears, don haka mu yi chatting kawai" Salima tace "Toh shkkn bari in kunna data" Katse wayar Haseenah tayi ta bude WhatsApp dinta. After sleeping all day Mayraah ta bude idonta a hankali ta dalilin hannun da taji a forehead din ta, suna hada ido ta mike zaune da sauri tana murza ido tana kallonsa, yace "How are you feeling?" A hankali tace "Alhamdulillah, ina yini?" Yace "Lafiya lau" Maheer ya karaso wajen nasu yana kallonta yace "Are you okay now?" Ta gyada masa kai, Usman ya juya ya koma kan kujera ya zauna, Maheer yace "Me za ki ci?" Usman yace "I will get her, idan mun fita, it's getting late now" Maheer yace "Ohk, baza ki shiga bandaki ba, za ku fita da Barrister" Mayraah ta kalli Usman, sai kuma ta sauko daga kan gadon ta dau handbag dinta ta nufi bandaki, zata iya daukan pad a gaban Maheer but not Usman tun tasowarta, Maheer dai ya bi ta da kallo ya koma office chair dinsa ya zauna, ko da ta fito daga bandaki Maheer kawai ne a office din, yana kallonta yace "Yana jiranki a mota" Ta marairaice tace "Ina za mu je yaya? Kasan bani da lafiya" Maheer yace "Ai ba dadewa za ku yi ba, zai dawo da ke soon" Ta ɗan yi shiru, sai kuma ta nufi kofa ta fita...... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence 07087865788 [6/26, 7:46 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na isa parking space din asibitin ta nufi motar Usman, ta bude front seat ta shiga ba tare da ta kallesa ba, ya tada motar suka bar asibitin, babu wanda yace koma cikinsu har suka yi nisa, Ita dai sai baza ido take ta ga inda zai kai ta, after many minutes ride ta gane inda suka nufa, nan da nan jikinta yayi sanyi sai take jin abubuwan da suka faru suna dawo mata sabo a zuciyarta, a cikin compound din gidan yayi parking ya juya yana kallonta sannan ya bude motar ya sauka, Mayraah ta kasa fitowa daga motar, gani take kamar za su ga Hajja a gidan, har sai da Usman ya zagayo ya kwankwasa motar yace "Za a sauko da ke ne?" Sunkuyar da kanta tayi ta sauko daga cikin motar ya kulle, sannan ya fara tafiya ta bi bayansa har suka shiga gidan, babu kowa a parlon, ta zauna kan kujera kamar wata bakuwa, Usman na kallonta da mamaki yace "Are you okay? Baxa ki tafi sama ki gaida Ammi ba?" Bata ce komai ba ta mike ta wuce sama tana tafiya a hankali, ya bi ta da ido, Mayraah ta kai minti biyu tsaye bakin kofar parlon Ammi ta kasa shiga ciki haka kawai take jin gabanta na faduwa har Usman ya hauro saman, bata bari ya karaso wajenta ba ta bude kofar a hankali ta shiga ciki tare da sallama, Mama Ladi dake zaune da kwanon abinci a gabanta ta tura kwanon ta wagale hannu tace "Lahh jama'a ga Mera, ga Mera" Mayraah suka hada ido da Ammi dake zaune parlon gefen Mama Ladi, Ammi ta kasa daina kallonta ko kiftawa babu, karasawa Mayraah tayi ta duka kusa da ita tana kallonta tace "Ina yini Ammi" Ammi bata bari sun sake hada ido da ita ba, ta jawota jikinta a hankali tace "Lafiya lau Mimi, ya jikin naki?" Mayraah ta sunkuyar da kanta tace "Da sauki" Mama Ladi dake ta washe baki tace "Haba gashi yarinya har tayi kyau tayi kumari ta kara haske da ta bar gidan nan na kwana biyu kawai, amma da duk an bi an sa ta a bakin duniya, baki yayi mata yawa ta ko ina sai hayagaga tsofaffi da yara suke da sunanta gashi ba a san bakin wani ba, wannan yace yeyeyen wancan yace yeyeyen, ba tsoho ba yaro" Ammi dai ta kara jan Mayraah jikinta kamar zata maida ita ciki, ji take kamar an yaye mata duk wani damuwa dake tattare da ita a moment din nan, she just felt a lot of strength da ta rasa na kwana biyu nan, ita kanta Mayraah felt relieved in Ammi's bosom, and for the second time tun faruwan abubuwan nan taji kawai ita bata ma yarda Ammi is not her mother ba, she just can't believe that, don ita dai a duniya bata da uwa sama da Ammi.... Usman na shiga parlon Abba ya zauna ya gaishesa Abba ya amsa yana kallonsa yace "Ya jikin nata?" Usman yace "Da sauki, tana wajen Ammi" Abba ya ɗan yi shiru, sai kuma ya nisa yace "Usman ta yaya kake ganin zan fara yi ma Mayraah magana ga me da asalinta ta yanda hankalinta bazai tashi ba? I really don't want to hurt my daughter, though she is already hurt, what if she is healing in sake dawo mata da zancen? yanzu kamata yayi ace kwantar mata da hankali za ayi giving her hope ba kara daga mata hankali da wannan issue din ba Usman, ko na ce zan mata magana ban san ta inda zan fara ba" Usman ya daga kai ya kalli Abba yace "Abba babu amfanin boye mata komai ga me da asalinta a yanzu dai don abinda zai faru ya riga ya faru, abinda ya sa she is this hurt is because ba a bakinku ta fara jin ku ba iyayenta bane, don haka bai kamata ayi shiru a ki ce mata komai ba har yanzu, dalilin abun nan fa yasa aka fasa aurenta Abba, as if that is not enough Hajja ta billo da nata matsalar which is uncalled for, to ta yaya za ayi mata shiru and we keep on acting like everything is okay whereas ba haka bane, shirun nan zai fi mata ciwo a kan telling her who she is a yanzu dai, you need to talk to her Abba, nasan ita Ammi bazata iya ba" Abba ya nisa yace "I will, amma i don't think zan bazan bude mata komai kamar yanda na bude maka" Usman yace "Abba just tell her everything once and for all, idan ma baka gaya mata ba zata ji a wani waje wataran tunda kaga yanzun ma a wani wajen ta fara ji" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "To bari mu dawo masallaci, it's almost Magrib now" Mayraah na zaune gefen Ammi dake kan darduma ta idar da sallahn magrib, tuwon da Ammi ta sa Sabira ta kawo mata take ci a hankali, Mama Ladi ta rufe akwalan akwatinta tace "Kala uku ma sun isheni zaman duniya ba na kiyama ba a gidan, banda ma dai Badiyya ta kwace Rigar Maman da ta ban ai ba sai na debi kaya har kala uku ba" Ammi dai bata ma san abinda Mama Ladi ke cewa ba don duk hankalinta na kan Mayraah dake cin tuwo a hankali, sosai taga ta rame kamar ba Mayraan ta ba, kuma kana kallon fuskarta zaka san akwai damuwa still a tattare da ita, Mama Ladi na kallon Mayraah tace "Wannan dai dakin da na zabar maki aka baki a gidan?" Mayraah ta daga kai ta kalleta sannan ta gyada mata kai, Mama Ladi tace "Ahau ai dama nace naki ne dakin, kuma girmansu daya da dakin Sasinar, kinga su suna daga can gefe ke kuma ga ki a naki gefen babu ruwanki da harkar matar don naga er iska ce ta bugawa a jarida" Ammi ta juya ta kalli Mama Ladi , Mama Ladi na zare mata ido tace "Kwarai kuwa er iska ce, ai ta min iskancin ne, naga kina wani kallona" Ammi dai ba abinda tace mata, Bude kofar parlon aka yi duk suka juya, Usman ya shigo da sallama yana kallon Mayraah yace "Ina jiranki a corridor" Mayraah ta kalli Ammi, Cikin sanyin murya Ammi tace "Why not leave it till around 10" Usman yace "Abba wants to speak to her" Ammi tace "Ohk, bari ta gama cin abincin" Juyawa yayi ya fita daga parlon, Mama Ladi tace "Ji jaraba kamar Allah Allah ma yake ya fita da ita daga gidan, anya da gaskiya cikin lamarin 'ya yan nan naki kuwa?" Ammi dai bata ce komai ba, Mayraah ta rufe abincin gabanta duk da ta dan ci ba laifi, Ammi tace "Baki cinye ba ai" Ta girgiza kai tace "Na koshi" Mama Ladi ta mike tana kokarin kinkiman akwatinta tace "Maza wanko hannu mu tafi" Ammi ta juya ta kalli Mama Ladi da mamaki, can dai tace "Abba ne fa ke kiranta Mama Ladi" Mama Ladi tace "Aihoo, to je ki dawo, ina nan ina jira" Mayraah ta wanke hannu ta fita, tsaye ta tadda Usman a corridor, ya maida wayarsa da yake dannawa cikin aljihu ya nufi parlon Abba ta bi bayansa, tun da ta shigo Abba ke kallonta, ta zauna kasan carpet cikin sanyin murya tace "Abba ina yini" Abba ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Lafiya lau daughter" juyawa Usman yayi ya bar masu parlon. Usman na dawowa parlon Ammi tayi masa turanci tace ya jirata waje zata masa magana, Mama Ladi dai tayi kishingide a parlon tana jiran dawowan Mayraah daga wajen Abba, Bayan yan mintuna Ammi ta mike tana kallon Mama Ladi tace "Bari in hada ma Alhaji abincinsa a kitchen" Mama Ladi tace "Toh ba laifi, maza je ki" Daga haka Ammi ta fita daga parlonta, can bakin stairs ta tadda Usman a tsaye yana jiranta, Ammi ta karasa kusa da shi da damuwa tace "Usman kana gani fa Mama Ladi ta hada akwati wai zata bi Mayraah gidan Maheer, abinda ya kamata fa shi ake yi, me zata je tayi gidan yarinya da aka kai ko kwana biyar ba ayi ba yau fisabilillah? Ita kanta Mayraah in sha Allahu kafin nan da sati biyu komai zai daidaita ta dawo gida, wllh ba da son raina take gidan Maheer ba i just don't have choice for now, ji nake kamar wani part of me ne baya tare da ni yanzu haka, kuma abinda yasa ma na hakura da zamanta gidan Maheer din nasan bazai bar ta cikin damuwa ba, to ga wannan tsohuwa wai ita lallai lallai sai ta bi Mayraah, ita Haseenar adalci aka mata? Wannan ai ba ma abinda hankali zai dauka bane, At the first place ma bai yi ace daga tarewarta an kai mata yarinya ba in dai adalci za a bi" Duk da Usman ya hango Mama Ladi da ta makale jikin bangon kusa da karfen stairs din bai ce komai ba har Ammi ta kai aya, Usman ya gyara tsayuwarsa yace "Toh yanzu ya kike son ayi Ammi?" Ammi tace "Kawai kace mata baza ka tafi da ita ba, iyaka tayi fadanta ta gaji ta kwanta, ko kuma kace mata Maheer din da kansa zai zo ya dau Mayraah, kaga sanda za ku fita ma bata sani ba" Murmushi kawai Usman yake yana shafa beard dinsa, Mama Ladi tayi wani tsalle ta fito sarari tayi mitsi mitsi da ido tace "Ashe dai ba Mariya kadai ta iya munafurci ba" Usman ya juya yana dariya ya sauka downstairs ya bar su wajen, Ammi tayi tsuru tsuru a tsaye, Mama Ladi tace "Amma wallahi kin ban mamaki, kuma naga dai ba gidan uwarki Hajja nace zan je ba gidan Mashir zan je balle ki min iyaka, kuma gidan Mashir kamar na je wallahi ban ga wanda ya isa ya ki kai ni ba ko a kafa zan nemo gidan, haka kawai bazan zuba ido wannan guzumar da ya ajiye a gida ta cuci Mera ba duk Allah ya kama mu tunda dai zuwa yanzu babu wanda bai san Mera marainiya ce da aka tsinta a bakin masallaci cikin kwali ba, sannan kiyi ta makala ma matar nan yarinya, wai an gaya maki matar Mashir yarinya ce? Ta fa girmesa don ma ki ji in gaya maki, ni tun a ranan da aka kawota daki ta gaishemu na dauka Bazawara ce kawai dai na ja bakina ne nayi shiru kada ace na cika surutu" a hankali Ammi tace "Kiyi hakuri ni ba haka nake nufi ba Mama Ladi" Mama Ladi tace "Kya dai ci kanki, gidan Mashir kamar naje wllh" Daga haka ta juya ta bar ta tsaye a wajen. Abba na kallon Mayraah dake ta hawaye ya dafa kanta yace "In sha Allah next week Maheer zai maido ki gida, Allah maki albarka" ta kasa cewa komai ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta.... Parlor Mama Ladi ta dawo ta zauna da akwatinta a gaba tana jiran fitowar Mayraah don tun da Usman ya fita Masallaci sallan Isha bai shigo ba, Mayraah ta sauko downstairs Mama Ladi ta mike tace "Dau akwatin mu tafi, yana can waje yana jiranmu har ya fita da mota" cikin sanyin murya Mayraah tace "Kitchen zan shiga" Mama Ladi tace "Wai ya ku ke abu kamar ba kwa kallon agogo, karfe takwas da rabi fa yanzu" Mayraah tace "Shayi zan dafa" Mama Ladi ta koma ta zauna tace "Da can da suka biye Hajja uban wa ke dafa mata shayin in ba gulma ba" Ita dai Mayraah ta shiga kitchen din ta kulle kofa, a hankali ta bude kofar baya kamar yanda Usman yayi instructing dinta ta fita sannan ta rufe, ta zagayo zuwa gaban compound ta nufi gate ta fita da sauri, yana cikin mota yana jiranta, ta bude front seat ta shiga sannan ya ja motar suka bar layin..... Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 [6/27, 8:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Usman yayi parking dai dai kofar gidan Maheer, sannan ya kalleta yace "Sae da safe" Tace "Yaya za ka kawo min jakar gobe?" Yace "Kiyi me da shi?" Tace "My handout is inside" Bai kuma cewa komai ba, ganin haka ta bude motar tace "Sae da safe" Yace "Allah ya tashe mu lafiya" Sauka tayi ta kulle masa motar sannan ta nufi gate, yana tsaye har ya ga shiganta compound din gidan kafin yayi reverse, Mayraah na tsaye bakin kofa tayi knocking a hankali ta koma gefe ta tsaya, jin shiru yasa ta sake kwankwasawa, bude kofar aka yi suka yi ido hudu da Haseenah, Haseenah tayi mata wani matsiyacin kallo tare da jan dogon tsaki ta mayar da kofar ta kulle da karfi sannan ta saka makulli, Mayraah bata san sanda ta taɓe baki ba, tayi unlocking wayarta dake hannunta tayi dialing number Maheer, yana fara ring ya daga yace "Kun dawo ne?" Tace "Ehh" yace "Ohk let me open the door for you" Daga haka ya katse wayar, sai ga shi ya fito parlor daga Bedroom, Haseenah dake zaune kan kujera ta bi sa da kallo har ya nufi kofar parlon, budewa yayi yana kallon Mayraah, sai da ta shigo parlon yace "Usman din ya tafi?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk zan baki spare key ki rike a wajenki" Haseenah dae sai girgiza kafa take tana kallon TV fuskarta babu yabo babu fallasa, Mayraah ta nufi dakinta ya bi ta da kallo yace "Ina jakar?" Tace "Ya Usman zai kawo min gobe" Yace "Ohk" Daga haka ta wuce dakinta ta kulle, Maheer ya ɗan kalli Haseenah ya zauna gefenta yace "Where is the black tea i asked you to make for me?" Bata ce masa komai ba, yace "Baby i am talking to you" bayan some seconds ta mike ta nufi kitchen ya bi ta da kallo, sae da ya ga ta shiga kitchen din sannan ya tashi ya tafi dakin Mayraah, tsaye ya ganta tana linke Hijab dinta, ya kulle kofar yayi kasa da murya yace "But why didn't u greet her Mimi?" A takaice tace "She shut the door in my face" Yayi shiru, ta gama linke Hijab dinta zata ciro kayan da zata canza taji yace "Amma da kinyi hakuri kin gaisheta..." Juyawa tayi tana kallonsa, ya ɗan shafa kansa yace "Kinga ai Aunt dinki ce Mimi and she deserves some respect" Mayraah tace "Is that why she should close the door on me? Did she think i want to be here too??" Nan da nan hawaye ya cika idonta, dai dai nan aka bude kofar dakin Maheer ya juya da sauri, Mayraah ta ajiye kayan baccin da ta ciro ta dau pad da inner wear dinta tayi shigewarta bandaki ta bar su wajen, Maheer na kallon Haseenah dake masa wani irin kallo yace "Har kin dafa shayin?" Ta watsa masa kallo daga sama har kasa ta bar bakin kofar, ya bi ta har zuwa Bedroom dinsu. Ko da Mayraah ta fito makulli ta sa ma dakin ta sa kayan baccinta ta kwanta, ko kadan bata bari abinda Haseenah tayi ya tsaya mata a rai ba cause that's not her concern for now, damuwarta yanzu dalilin da yasa Musharraf ya ki kiranta throughout today, dialing numbersa tayi, after ringing for a while ya daga, kamar yana ganinta ta hade rai tayi shiru, daga daya bangaren yace "Ya jikin ki?" Kamar zata yi kuka tace "Sae da na kira ne zaka tambaye ni?" Yayi shiru, kafin yace "I called, not reachable" tace "You didn't" yace "Yanzu dae ba an kula da ke kin samu lafiya ba?" Tace "Toh shikenan, sae da safe" Yace "Wait..." Bata katse wayar ba tayi shiru tana sauraronsa, yace "How are you feeling now?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kin ci abinci?" Tace "Na ci" yace "Ohk, good night" shiru tayi kamar bazata ta ce masa komai ba, sae kuma a hankali tace "Zaka zo school gobe?" Yace "Yau da kika sa na zo, kin zo?" Ta marairaice tace "Ae don bni da lafiya ne, amma gobe in sha Allah zan je" Yace "Allah ya kai mu, take care of ur self" a hankali tace "Sure" Daga haka ya katse wayar ta dinga kallon screen din. Washegari kafin bakwai da rabi Mayraah ta shirya ta fice daga gidan without anybody noticing her ban da Musa mai gadi, don bata ma ga alamar masu gidan sun tashi ba, ko shayin bata tsaya ta sha ba yau, ta isa har inda zata samu adaidaita sahun da zai kai ta makaranta, takwas dot ta shiga department dinsu, ita da Hamidah da wata Coursemate dinsu Amina suna zaune class don karfe takwas din suke da lectures, amma gashi har takwas da rabi lecturer din bai shigo ba, Hamidah na kallon Mayraah tace "Wai Badiyyah bata nan ne, na ga ta daina zuwa school long ago, ga exam is fast approaching" Mayraah tace "Ni ma ban sani ba kam, kilan tana Bichi, but nasan zata dawo tayi exams ai" Shigowan lecturer din ya sa duk aka nutsu a class din, Mayraah ta bude jakarta ta fiddo littafinta da pen, paying attention to their lecturer... Karfe goma da rabi suka fito daga lecture hall din, ta fiddo wayarta a jaka ta ga miss calls har shidda, uku na Maheer, biyu na Usman sai na Dr Musharraf guda daya, ta dinga kallon calls din, kawai tayi dialing na Dr Musharraf, yana fara ring ya daga ta gaishesa a hankali, ya amsa yace "Are you done with the lectures?" Ta zaro ido tace "How did u know i am in school?" Yace "Kawai na ji kamshin turarenki gaba daya department din" Bata san sanda tayi dariya ba ba tare da ta shirya ba, Hamidah dai na zaune kan gossip chair tana kallonta, ko Mayraah bata gaya mata ba tasan tana cikin damuwa cause it's obvious a fuskarta, Musharraf yayi shiru yana sauraron dariyan nata, can a hankali yace "Ina jiran ki a office now" tace "Sir zan ɗan yi karatu ne fa yanzu" Yace "Yauwa dama ina son in tambayeki, kin canza project supervisor ne ban sani ba?" Zaro ido tayi don ita ta ma mance da batun wani project, a hankali tace "Aa ban canza ba" Yace "Ok na zata kin canza, don naga mate dinki are almost done with theirs ke kuma har yanzu kina chapter 1" Da sauri tace "Aa wllh Chapter 3 ne" Yayi murmushi yace "Uhm i see" Ta marairaice tace "Amma sir ban zo da system dina ba" Yace "In kin gama karatun ina jiranki" Daga haka ya katse wayar. A hankali Mayraah tayi knocking din kofar office dinsa wajen karfe sha daya, sae da yayi mata izinin shigowa sannan ta bude kofar ta shiga, tun da ta shigo yake kallonta, ita kuwa kallo daya tayi masa ta karasa har inda yake ta sunkuyar da kai ta gaishesa da ladabi, ya mike offering her his seat yace "Ga wannan.... Naga kamar na gabanki basu maki ba" Murmushi tayi ta zauna kujeran dake gabanta a hankali tace "Ina kwana sir" Ya koma ya zauna underneath his breath yace "Lafiya lau.... how was ur night?" Ta kallesa tace "Good" Yace "Hope u slept well?" Ta langwabar da kai a hankali tace "Ai baka kira ba" Shiru yayi yana kallonta babu ko kiftawa, bai taɓa tunanin bond dinsu zai dawo haka da Mayraah ba, don kafin faruwan issues din nan har tunani yake if she will ever change ko da sun yi aure sai gashi yanzu she talks to him openly, she expresses her feelings unlike before da yake rasa gane kanta komai kunya, komai shiru shiru, Mayraah dai sai kallonsa take jin yayi shiru, ya sakar mata murmushinsa me kyau yace "To an hana in ganki jiya, and i was sad about that" Ta sunkuyar da kanta tace "Ai saboda bani da lafiya ne shi yasa yaya yaki ya bari in fita, kawai... An ban magani na sha shine nayi bacci har yamma" Yace "Am glad u are okay now, no pains" Tace "There is, but ba kamar jiya ba" Yace "To kin sha maganin?" Tace "Ban yi breakfast ba" Da mamaki yace "Why?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Ohk akwai abincin da Mami ta zuba min yana mota, kinsan every day in dai ina gida sai ta min breakfast kafin in fito, ni kuma bana ci, wani lokacin in ba cleaners or security...." Makullin motarsa ya dauko ya mika mata yace "Get the food, I don't even know what she prepared" Mayraah dai kallonsa kawai take, yace "Ko in je in dauko maki" tayi murmushi tace "Sir ni bazan iya cin abinci a school ba" Yace "Aa cewa za ki yi, sir ni bazan iya cin abincin gidanku ba" Mayraah ta zaro ido tace "Wallahi sir ba haka bane" zai yi magana aka yi knocking din office door din, Mayraah zata tashi yace "Is there anything wrong?" Ta girgiza masa kai, yace "To koma ki zauna" Komawa tayi ta zauna ta sunkuyar da kanta tana danna wayarta, yayi ma me knocking din izinin shigowa office din, daga bakin kofa ta tsaya bayan ta shigo a hankali tace "Good morning sir" Mayraah ta daga kai jin muryar warce ta ji sai dai bata juya ba balle ta kalleta, Dr Musharraf yace "Morning Badiyyah, how are you?" Tana makale jikin kofar tace "I am fine sir" Yace "You can come in" Ta karaso cikin office din tana tafiya kamar me tsoron taka kasa, ta tsaya ɗan nesa da table dinsa tana jujjuya textbook din hannunta tace "Sir dama plss tambaya nake son zanyi akwai abinda ban gane ba... I don't know if u will have the time...." Dr Musharraf yace "Ohk, is it pertaining to my course?" Ta gyada kai da sauri, ɗan murmushi yayi ganin kamar she looks nervous yace "Why are you tensed Badiyyah? You have all right to ask ur lecturer duk abinda baki gane ba, kawo textbook din in ga" Ta karasa har kan table din ta mika masa textbook din da ladabi, tuni fitinannen kamshinta ya baza office din, sai a sannan suka hada ido da Mayraah, Mayraah ta dauke idonta ta ci gaba da danna wayarta, Musharraf ya nuna ma Badiyyah kujeran dake kallon na Mayraah yace "You can sit" a hankali ta zauna edge din kujeran tana wasa da hannunta, sanye take da wani atamfa da dinkin yayi matukar yi mata kyau ya amshi jikinta, ga mayafinta da ta daura saman kai, hannunta kuwa ya sha lalle baƙi da ja da ya kara haska farar fatarta, light make up ne a fuskarta that made her look naturally beautiful, Duk a few seconds Mayraah tayi mata wnn kallon ta side eye, Dr Musharraf ya gama duba abinda Badiyyah tace bata gane ba sannan ya mike ya zagayo ta inda take zaune ya ajiye textbook din a side dinta yace "Now listen, so that u won't get confuse, ba wani abu me wahala bane" Badiyyah da taji kamshin turarensa ya cikata don dab da ita ya duka taji kamar ta sume a inda take a zaune, ko sanin abinda yake cewa ma bata yi ba, nan ya fara kokarin mata explaining din abinda tace bata gane ba, ita dai kallonsa take ko kiftawa babu, bata san haka gayen nan ya hadu ba sai yau da take kallonsa dab dab da ita, his nose, his eyes, his white teeth, his thick eyebrows, cute lips, the way he speaks fluently, and the best of all his cool scent me makalewa a hancin mutum, Subhanallah.... ji tayi kamar ta jawo sa ta rungumesa gam gam, bayaninsa kawai yake amma babu abinda Badiyyah take ji a abinda yake cewa, Mayraah ta mike rike da jakarta, Musharraf ya juya ya kalleta, makullin motarsa ya dauka ya bata yace "Gashi ki dauko stuff din" without looking at him tace "Aa zan yi picking call ne, i will be back" Daga haka ta juya ta nufi kofa ta fice daga office din, Musharraf ya jawo kujeran da ta zauna ya zauna a kai, yana facing din Badiyyah da ta riga ta gama narkewa a wajen, yace "Hope you get where i am heading?" Ta gyada masa kai da sauri, nan ya ci gaba da mata bayanin da bata ganewa ita kuma ta dinga kallonsa babu ko kiftawa.... Mayraah na sauka downstairs kiran Usman ya sake shigowa wayarta, dagawa tayi, a hankali tace "Ina kwana yaya" Yace "Baki ga calls dina bane?" Turo baki tayi tace "Yanzu muka fito lectures ai" yace "Me yasa kika ce in kawo maki jakarki kin san da sassafe za ki fita?" Tace "Ka kawo ne?" Yace "Fito department dinku ki amshi jakarki" Daga haka ya katse wayar, ta saka wayarta cikin jakan hannunta ta tafi inda zata samu Hamidah tace "Hamidah sai gobe in sha Allah" Hamidah tace "Lectures din anjima fa?" Mayraah tace "Kawai ki min attendance pls" Hamidah tace "Toh shikenan sai gobe" Daga haka Mayraah ta juya ta fita daga department din, ba ma kusa da department din nasu yayi parking ba, haka ta karasa har inda ya tsaya da kafa, ta bude motar tana kallonsa tace "Ina kwana" Ya dau jakarta ya mika mata, taki amsa, ta marairaice tace "Yaya don Allah ka ajiye ni gida" Daga sama har kasa yake kallonta yace "Kun gama lectures din ne?" Tace "Kawai na gaji, ina son in kwanta" bata jira me zai ce ba ta shiga motar ta kulle ta jinginar da kanta da kujera without looking at him, bayan few seconds ya tada motar suka bar school din, suna hawa main road ta ɗan juya ta kalli bayan motar jin aroma din abinci dake tashi, ledan wani babban eatry ta gani, can dai ta kallesa tace "I am even hungry" A takaice yace "Me too" Ta ɗan hade rai, sai kuma tace "Naga abinci a back seat fa" Ya jefa mata wani kallo yace "To naki ne?" Shiru tayi tana kallonsa, bata sake ce masa komai ba ta kauda kanta, wayarsa dake ajiye ya fara ring ya daga yace "I am on my way" after some minutes ride sai ga su a gate din wata makaranta wanda ke gaba da na su Mayraah, suna shiga school din bayan sunyi tafiya kadan ya juya yana kallonta yace "Will u wait for me under that tree?" Mayraah ta kallesa tace "No, i will follow u" Ya hade rai yace "Kika san inda zan je?" tace "To me yasa baka son in ganta ne Yaya?" Yace "Ki ga wa?" Ta langwabar da kai tace "Warce zaka kai ma abincin mana" Yace "You are not serious" Er dariya tayi tace "Dama yaya kana da budurwa ashe?" Ya tsuke fuska yace "Yaushe na fara wasa da ke" Ta rufe bakinta bata sake cewa komai ba, suna isa department din yayi parking, wayar da zai yi ma sai da ya sauka daga motar sannan yayi, ita dai Mayraah murmushi kawai take tana bin sa da kallo, baza ta manta ba few months back Ammi ta dage wai ai Usman bai da budurwa, saboda taga shi baya kawo mata waya su gaisa da budurwan yanda Maheer ke yi, shkkn Ammi ta saka a rai ai bashi da kowa, ita kuwa Mayraah ta dage ma Ammi kan cewar yana da ita kawai dai saboda shi introvert ne shi yasa ake ga kamar ba shi da, still dai Ammi bata yarda da Mayraah ba a lokacin, Mayraah wished daga nan wajen Ammi zata je ta kai mata news din nan, tunanin nan yasa lokaci daya jikinta yayi sanyi, ta jinginar da kanta da kujeran motar tana tunanin wannan sabuwar rayuwar tata, knocking din da taji ana yi ta side dinta ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fada, wata ta gani tsaye jikin motar tana mata murmushi, Mayraah ta bude motar tana kallonta, baza su wuce age mates ba da yarinyar, ita ma doguwa ce fara me kyau da ita, Mayraah ta sauko daga cikin motar tana mata murmushi kamar yanda yarinyar ma ke mata, yarinyar tace "Hi Mayraah, i am Maleeha, nice meeting you for the first time" Mayraah tace "Nice meeting you too Maleeha, ya lectures" Maleeha tace "Alhamdulillah, ya naki?" Mayraah tace "Same too" Maleeha tace "I have been longing in hadu dake sai yau Allah ya yi" Mayraah tace "Ai kam, i am happy to meet you" Maleeha tace "Barrister ya gaya min Nursing Science kike yi, ni kuma i am studying Biochem, final year student just as you" Mayraah tace "Maa sha Allah, Allah ya bamu sa'a gaba daya" Lokaci daya Mayraah taji tana son Maleeha har cikin ranta, Usman ya zagayo inda suke ya bude back seat ya ciro ledan da ya kawo ma Maleeha ya mika mata yace "Sai anjima" ta amshi ledan tana kallonsa, ya kalli Mayraah yace "Shiga mota mu tafi" Maleeha tace "Tunda i am done with lectures for today ka bar ta mana plss, so we can stay together, and know our selves better" Usman yace "Not today" Mayraah ta tuna fa yanzu dole gida zai ajiye ta daga ita sai Haseenah, bata san sanda tace "Ya Usman, i will stay... sai anjima zan tafi gida ba yanzu ba" Maleeha tayi murmushi tace "Anjima kawai zan sa drivern mu ya fara ajiyeta before dropping me home" Usman ya zaga ya shiga motarsa ya bar su nan a tsaye, ko minti goma bai yi da tafiya ba sai ga message dinsa ya shigo wayar Mayraah, ta bude message din tana karantawa kamar haka "Watch ur words" ta mayar da wayar cikin jakarta kawai, Mayraah bata yi regretting staying back tare da Maleeha ba cause she enjoyed both her company and her 2 frnds kuma dukkansu sa'aninta ne, bayan sun idar da sallahn asr a masallaci Mayraah ta ciro wayarta a jaka taga miss calls din Dr Musharraf har uku sai na Maheer biyu, wayar a total silence yake don haka bata jin kira sai dai ta ga miss calls kuma she like it that way, zata ajiye wayar sai ga kiran Maheer ya sake shigowa, tayi excusing kanta ta bar jakanta wajen Maleeha sannan ta fita outside of the mosque, a karkashin bishiya ta zauna bayan ta daga kiran, daga daya bangaren Maheer yace "Mimi me yasa baki responding to my calls?" Tace "Muna lectures dazu, yanzu kuma mun idar da sallah ne" Yace "Why did u leave home without waiting for me?" Tace "Saboda ban san sanda zaka tashi ba, kuma ina da lectures karfe takwas" Yace "Me yasa baza ki kira wayata ba, sannan kawai kin fita without taking breakfast" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Zan kawo maki abinci yanzu" Tace "Aa ni na ci abinci yaya" Yace "A ina kika ci abinci?" Tace "Ya Usman ya kawo min" Shiru Maheer yayi, can dai yace "Yaushe?" Tace "Da rana" Yace "When is ur lectures terminating?" Tace "Anjima" Yace "6 kenan?" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Eh" Yace "Zan zo in dauke ki" Tace "Ya Usman will pick me" Yace "Ohk, is that so?" Tace "Haka ya ce min" Maheer yace "Ok" Daga haka ya katse wayarsa ta turo baki, Mikewa tayi ta koma cikin masallacin. karfe biyar saura Maleeha ta kira Usman to tell him za su yi dropping Mayraah ba sai ya zo ba, yace "No Maleeha, ina hanya zan zo in dauketa" Maleeha tace "Toh sai ka zo" Suna karkashin bishiya gaban department din nasu Usman ya iso, tuni driver din Maleeha ya zo makarantar amma tana jiran Usman ya fara daukan Mayraah kafin ita ma ta tafi, Maleeha ta raka Mayraah har bakin motar Usman, suka yi sallama, tana kallon Usman tace "I will be going home too, nagode sosai Barrister" Yace "Ohk, a gaida su Umma" Daga haka ya bar department din, bayan sun fita makarantar yana kallon Mayraah ya wani hade rai yace "Hope u didn't talk too much?" Ta kallesa ta wara ido tare da dafe kirjinta tace "Did i use to talk much yaya?" Yace "Look Malama stop being silly.... Maleeha is my frnd, she is just a frnd kar ki yi zaton budurwata ce or anything of such, kanwar abokina ce ita, so mun saba da ita ta dalilin Hafeez, but we are only frnds da ita" Mayraah bata san sanda tayi dariya ba tace "Ae dama na san she is ur frnd, and nima zata zama frnd dina daga yanzu, and beside i never asked for all this explanation" Kallonta kawai yake, ta kallesa suka hada ido ta fashe da dariya, daure fuska yayi nan da nan ta kama kanta, imagine wai yau ya Usman ne ke taking time trying to explain to her what she neva asked for, ita bata ma san ya iya dogon bayani ba sae yau, wani dariya ya kara zuwa mata ba tare da ta shirya ba, shi dae driving dinsa kawai yake. Mayraah na shiga compound bayan Usman ya ajiyeta taga Maheer bai dawo aiki ba, kawai ta karasa ta zauna kan wani kujera da ta gani a parking space don bata jin zata shiga gidan, tana ta zaune a wajen har kusan karfe shidda sai gashi ya dawo, yana parking ya sauko daga motar, ta mike tana kallonsa tace "Sannu da dawowa" Da mamaki yace "Bata bude maki kofar bane yau ma?" Mayraah ta girgiza kai tace "Aa kawai iska nake sha a nan" Ya mika mata ledan hannunsa ta amsa, sannan ya nufi entrance din gidan tana biye da shi a baya, yana bude kofar parlon hayaki me kama da na turaren wuta da ya turnike ko ina na parlon ya ce masu salamu alaikum, Mayraah na ganin haka ta juya da sauri ta bar entrance din parlon, Ammi na saka turaren wuta amma wnn kam kamar ba turaren wuta bane don wani irin kamshi kamar na yan bori yake, Maheer ya bi ta da sauri yace "Hope u didn't inhale much?" Ta girgiza masa kai still walking away from the vicinity, parking space din ta nufa, shi dai yana biye da ita, ta zauna kan kujera ya duka yana kallonta yace "Kiyi hakuri ki ɗan zauna nan har ya fita, bata san baki so ba" Mayraah dai bata ce komai ba, ya mike ya koma cikin gidan, yana shiga parlon ya fara kwala ma Haseenah kira, ta fito daga kitchen sanye da wani atamfa tayi daurin ture kaga tsiya ga make up a fuskarta ta nufesa ta rungumesa tana taunar gum tace "Oyoyo Baby, sannu da dawowa my husband" Yana yamutse fuska yace "Wannan hayakin meye kika cika a gidan nan Haseenah?" Ta wara ido tace "Turaren wuta mana" Yace "Aa wannan ba turaren wuta bane gaskiya, kuma ba nace maki Mimi is Asthmatic ba? Because of this she can't come inside now" Haseenah ta hade rai tace "And so what? Saboda Mimi kana nufin bazan sa turare gida na yayi kamshi ba kenan?" Yace "Madam!! Ammi tana sa turaren wuta amma ba me hayaki irin wannan kamar anyi gobara ba, beside wannan wani awful smell yake fitarwa unlike wanda Ammi ke using..." Haseenah ta juya ido tace "Toh ni kalan nawa turaren wutan kenan, take it or leave it Maheer" Tana fadin haka ta bar sa tsaye a wajen ta nufi daki, kasa ce mata komai yayi, can ya juya ya fita ya koma wajen Mayraah.... Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 [6/28, 1:28 PM] Khaleesat Haiydar💖: Greetings to you Hajiya Bilkis (Mom Fa'iq, Maman Eesha) Allah Ubangiji ya ba Baba lafiya ya tashi kafadunsa, ya sa jinya ya zama kaffara Ameen, Hajiya Faty gogori i greet u too with respect Allah ya raya maki zuri'a ya kara maki kwanciyar hankali da farin ciki... Aunty Amina (Sis Amzaj) ina maki fatan alkhairi, Allah ya albarkaci zuri'a, ya raya min Mara Jiddah in sha baki.... Aunty Nurse (Damsel) kema na gaisheki sosai, Allah ya biya maku bukatunki na Alkhairi, ya cika maki duk burukkanki na rayuwa, Ameeen. Har aka kira Magrib Maheer na tsaye parking space tare da Mayraah da ke ta danna wayarta, ya dawo kusa da ita yana kallonta yace "Mimi let me check ko ya ragu sai mu shiga ciki" Ta daga kai ta kallesa, ya juya ya nufi parlon gidan, har a sannan da hayakin sai dai ba kamar da farko ba, ya juya ya fito ya koma parking space din yace "I think u will be able to manage, in kin shiga daki sai ki kulle kofa" Mikewa tayi ta fara tafiya, ya bi bayanta har suka koma cikin gidan, she held on to her breathe don bata ma son kamshin koma meye Haseenah ta ƙona a gidan, har wani hawa kai yake, tana shiga daki ta kulle kofar tana sauke numfashi, sai a sannan Maheer ya dawo parlor ya shiga toilet dake nan yayi alwala ya tafi masallaci, ko da ya dawo gidan Haseenah na kwance daki yana kallonta yace "Baki yi sallah ba Haseenah" A takaice tace "Nayi" zaunawa yayi gefenta yana kallonta, a hankali yace "I don't mean to hurt u Haseenah, is just that...." Kamar jira take ta fashe da wani shagwababben kuka tace "Wallahi tun ba aje ko ina ba na gaji Maheer, ta yaya ni da gidana kuma turaren wutan da zan sa inji dadi ace baxan saka ba? Shikenan sai in bar gidana ya fara warin ruma saboda wani dalili can?" Maheer yace "No ba ace baza ki saka turaren wuta ba Haseenah, kawai dai ki dinga sa wa da rana idan babu kowa a gidan, kin ga Mimi tana da Asthma, sannan nima hayakin idan yayi yawa yana damuna sosai, but kiyi hakuri" Ta wani daure fuska tace "Sannan kuma magana ta biyu a gaskiya bazan zauna da gandareriyar yarinya haka a gidan nan ba ace bata taimaka min da komai, inyi wanke wanke inyi gyaran kitchen, in share gida inyi goge goge, in wanke bathroom, sannan inyi girki, to wllh bazai yiwu ba ni ba boyi boyin kowa bace, ai ni ma ba lafiyayyar bace ciwon baya gareni...." Maheer dake ta kallonta yace "Yaushe kika fara girkin, in dai ba yau kika yi ba?" Ta masa wani kallo tace "Ae nayi din ne shi yasa nayi magana" Ya shafa kansa yace "Ohk, amma dai shara Mimi baza ta yi ba saboda condition dinta, so zata dinga maki gyaran kitchen sannan ta maki goge goge, har da girki in kina so" Haseenah tace "Sai kuma ta wanke duk bandakin gidan" Shi dai bai ce komai ba, Haseenah ta mike tace "Mu je inyi serving maka abinci, i cooked ur favorite" Yace "Let me take a shower first" Daga haka ya mike ya shiga bandaki ta bi sa ciki. A tare suka fito parlon bayan isha tana makale jikinsa, zuwa sannan ta canza kayan jikinta zuwa na bacci, dai dai nan Mayraah ta fito daga kitchen rike da cup din shayi, Maheer ya hau tura Haseenah da sauri daga jikinsa amma sai ta wani sake makalesa kamar za su dawo daya, Mayraah dai bata sake kallon inda suke ba ta nufi dakinta, Maheer da abun bai masa dadi ba yace "C'mon Haseenah, meye haka kike yi kina ganin yarinya??" Sai a sannan Haseenah ta sakesa tace "Wallahi babu wanda ya isa ya hanani cin amarcina yanda ya kamata, wannan ce yarinya?" Tana fadin haka ta manna masa kiss tace "Bari in kawo maka abinci Baby" Zaunawa yayi kan kujera yana shafa kansa yana kallon hanyar dakin Mayraah, sai ga Haseenah ta dawo parlon ta ajiye warmers din abincin ta fara serving dinsu a plate daya, sai bayan da ta gama zuba masu yace "Mimi ta zuba abincin ne?" Da sauri Haseenah tace "Ehh naga ta diba" which is a lie, saukowa Maheer yayi kan carpet, ya dau spoon, ita ma ta dauka suka fara cin abincin a tare, ba za dai ace abincin bai yi ba amma sai yaji it can never be compared with that of Mayraah, shi har yau ya kasa samun abincin da yayi masa dai dai da na Mayraah be it restaurant or home, hakan yasa yaji gaba daya abincin Haseenah bai masa dadi ba a baki, Haseenah tace "Ya ka ji abincin Dear?" Ya kalleta yana gyada kai yace "It's so good, it's delicious, ban san you are a good cook ba haka" Ta fara wani blushing tace "Anything for my hubby" Yace "Amma fa sai yanzu na kara fahimtar ki da kika ce aiki yayi maki yawa wifee, duk ke kadai kika yi girkin nan ga kuma gyaran gida?" Ta marairaice tace "Wallahi kuwa Dear ni kadai raina babu mataimaki" Yace "Kinsan me zai faru, tunda Mimi bata shara why not kawai ki bar mata girkin ita ta dinga yi tunda naga ta ɗan iya, U can't be stressing ur self this much...." Haseenah na girgiza kai tace "Aa ni zan dinga yi ma mijina girki, haka na taso na gani a gidanmu, saboda me zan bar wata tayi ma mijina girkin da zai ci gani da lafiyata" Maheer bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da tuttura abincin, bai ci ya kai spoon shidda ba ya ajiye cokalin yace "Kinsan da daddare bana cin abinci da yawa, i prefer tea" Ta hade rai tace "Baby ko dai abincin bai maka bane?" Ya zaro ido yace "Wannan abincin? Ai ko a babban restaurant sai haka wife, mata nawa ne yanzu ko Indomie basu iya dafa shi yayi kyau ba" Ta marairaice tace "To naga baka ci da yawa ba" Yana shafa cikinsa yace "I'm full, kinsan it's not healthy mutum ya ci abinci da yawa da daddare" Ita dai ta ɓata rai tana jujjuya spoon din hannunta, da sauri ya kawo wani labari duk don ta mance da batun abincin, daga karshe kuma ya bar ta da bashi labarin ya jingina da kujera yana sauraronta inattentively don duk hankalinsa na kan Mayraah, kawai bai san matsalarta shi yasa ya kasa tashi ya je dakin Mayraah din, ita kuwa sai labari take basa wanda duk bai ma san abinda take cewa ba kallonta kawai yake, wayarsa dake kan kujera ne ya fara ring, ya dauka yana duba screen din ya ga Usman ne ke kiransa, picking call din yayi ya kai kunne, bayan ya gama sauraron Usman yace "Me yasa baza ka shigo ba kai?" daga other side Usman yace "Sauri nake, kawai ta zo ta amsa ba sai na shigo ba" Maheer bai kuma cewa komai ba ya katse wayar, mikewa yayi Haseenah ta bi sa da kallo ganin dakin Mayraah ya nufa ta kyabe baki tare da jan tsaki kasa kasa, yana shiga dakin ya sameta zaune gaban madubi daure da towel tana shafe shafenta alamar fitowarta kenan daga wanka, tun da suka hada ido ta sunkuyar da kai ta kasa dagowa, she don't know why she felt soo ashame today, unlike before da bata jin komai, shi kansa sai ya zama uncomfortable ya ɗan fara kame kame yace "Usman yana jiranki a waje zaki amsa sako" Yana fadin haka ya juya ya fita, Mayraah ta dinga mamakin wani sako Ya Usman zai bata da daddaren nan, ta dai mike ta dau kayan baccinta ta saka sannan ta daura hijab har kasa a kan kayan ta fito parlor, tunda ta fito Maheer dake zaune shi kadai a parlon ke kallonta babu ko kiftawa, Tana karasowa tsakar parlon yace "Kina amsa ki shigo gida, do not exceed 2 minutes" Tace "Toh" Daga haka ta fita waje. Tana isa gun motar Usman ta bude front seat tana kallonsa tace "Yaya ina yini" Yace "Lafiya" Ganin ta tsaya bata shigo ba yace "A waje zan baki sakon? Or should i come down to give u?" Bata ce komai ba ta shiga motar ta rufe, ta juya tana kallonsa, ya dauko warmer dake cikin leda a bayan motar ya mika mata, ta amsa yace "Ammi tace a kawo maki" Mayraah bata san sanda ta wara ido ba tana murmushi tace "Nagode sosai, yaya wajen Maleeha zaka je ne?" Ya juya ya kalleta lkci daya ya hade rai yace "Ke yaushe na fara wasa da ke ne?" A hankali tace "Toh naga u look cute" shiru yayi yana kallonta, Tana murmushi tace "Idan can zaka je sai in raka ka" kamar warce ta tuna abu ta zaro ido tace "Lahh, Ya Maheer yace kar in wuce 2 minutes fa" Usman dake kallonta yace "Aiki ya baki a gidan da yace kar ki wuce 2 minutes?" Mayraah dai tayi murmushi kawai bata ce komai ba, Danna wayarsa ya fara yi a motar, ita dai sai kallonsa take, can bayan wasu mintuna yace "What did u need?" Tace "Kamar me?" Yace "Baki bukatar komai?" Tace "Ohk, cream, ya kusa karewa" Yace "Just that?" Shiru tayi tana tunani, can tace "Eh shikenan" Bai sake ce mata komai ba ya ci gaba da danna wayarsa, after another few minutes ba tare da ya dago ba yace yace "When is ur exams?" Tace "Saura 3 weeks" Mayraah dai kallonsa kawai take, can kuma yace "Are you comfortable staying in the house?" Tayi shiru, sai a sannan ya daga kai ya kalleta ya ajiye wayar hannunsa, ta sunkuyar da kanta tace "Yes" Yace "Ke" Ta kallesa yace "Gaskiya za ki gaya min, are you comfortable?" Tace "To ai ba a gidan nake wuni ba, ina zuwa school" Yace "If there is anything you let me know" Ta gyada masa kai, ya dau wani leda a bayan mota ya mika mata ta amsa, ko bata duba ba ta gane shawarma ne, tana kallonsa tace "Thank you" ya ciro Atm card dinsa da bai fiye amfani da bank din ba sosai amma kuma yana saka kudi ya mika mata yace "If u need anything, u can withdraw, will forward the pin to you via sms" Ta amsa still tana kallonsa tace "Thank you" yace "You can leave" bude motar tayi ta sauka tace "Sai da safe" Ya ja motarsa ya bar wajen, tana shiga compound taga Maheer tsaye a balcony, ta karasa tana tafiya a hankali, da ido ya bi ta har ta shiga parlor ta wuce dakinta... Mayraah ta linke Hijab dinta sannan ta zauna ta bude warmer din da Ammi ta bada a kawo mata, pepper soup din kaza ne da yaji kayan hadi, nan da nan aroma din ya cika dakin, tashi tayi ta saka hijab dinta ta nufi kofa, ta bude a hankali ta fita, zaune ta ga Maheer a parlor shi kadai, ta karasa kitchen ba tare da ta kallesa ba, ya bi ta da kallo, plate da spoon ta dauka zata koma daki nan ma ya bi ta da ido, Mayraah ta debar masa rabin pepper soup din ta kai masa parlon, yana kallon plate din yace "Shi ya siya maki?" Tace "Aa Ammi ce ta bashi ya kawo min" Amsa yayi yace "Ni da Haseenah?" Mayraah bata san sanda ta amshe plate din daga hannunsa ba tayi juyawarta ta koma daki ta rufe kofa, ya bi ta da kallon mamaki, bayan few seconds ya mike ya bi bayanta, Mayraah na kokarin juye naman cikin food warmer din ya shigo dakin, kallo daya tayi masa ta ci gaba da abinda take, ya ɗan sosa kai yace "Ok i am sorry, i was only asking Mimi ai ban sani ba" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ni kadai aka kawo ma dama ae" Yace "Ohk then" juyawa yayi zai fita, ta daga kai tana kallonsa, a hankali tace "To zan tsam maka amma a nan" Ya juya ya kalleta yace "Ohk" Ta sa masa naman guda hudu a plate ta mike ta kai masa, amsa yayi yana kallonta yace "In je parlor da shi?" Ta ɗan yi shiru sai kuma ta juya tace "Ohk" Yace "Thanks Mimi, good night" Fita yayi daga dakin, ta koma ta debi wanda zata ci, bata wani ci naman da yawa ba, ta ci shawarman da Usman ya siya mata sannan ta tafi bandaki ta wanke bakinta ta fito, ta kwanta kenan kiran Musharraf ya shigo wayarta dake gefenta, ta dinga kallon call din kafin ta daga ta kai kunne tayi shiru, Musharraf yace "Na maki laifi ne Dear?" Tace "Laifi kuma na me?" Shiru yayi, ita ma haka, can yace "Kiyi hakuri, in ma na bata maki rai unknowingly, may be i should have gotten the food for u my self, i am sorry Mayraah" lokaci daya ta ji jikinta yayi sanyi, yace "Dama kira kawai nayi in baki hakuri, sae da safe" kasa ce masa komai tayi har ta ji ya katse wayar, a hankali ta rufe idonta tana karanto addu'ar bacci, sannan ta ajiye wayar a bedside drawer ta rufa da duvet, amma for almost an hour ta kasa bacci sae juye juye take, daga karshe ta jawo wayar tayi dialing numbersa, yana dagawa a hankali tayi karfin halin cewa "I am.... I'm sorry too" Har kusan karfe biyun dare Mayraah bata kwanta ba kuma babu alamar bacci ko kiris a idonta, yau kam sun yi hira sosai da Musharraf a waya, they talk about so many things, basu taɓa dadewa a waya irin yau ba tun fara dating dinsu, she is just realizing Musharraf is different in many ways, kawai suna tare ne amma bata san abubuwa da yawa game da shi ba sai yau da yake gaya mata, he told her how he lost his father and his sister that was 13 years old in a car accident, how he cherish his Mami soo much, he gist her about his group of frnds da irin rayuwar da suka yi a kasan waje sanda suke karatu... har labarin Farrah da aka so hada shi da a family sai da ya bata, Mayraah enjoyed every bit of their conversation that night, wani taji tausayinsa, wani taji haushinsa, wani kuma ya bata dariya, wani ya bata mamaki, at the end yace "But trust me Mayraah, no matter who my frnds are back then, Billah ban taɓa zina ba, even this common kiss ni ban taɓa yi ma ko wace mace ba sai ke, i will gain nothing if i lie to you, ni ina da kyankyami sosai shi yasa sai in ji mace bata burgeni ko inji feelings na mace, but surprisingly that stop immediately after i met u, bayan ke kuma ni bana yi ma ko wacce mace kallon sha'awa, Alcohol kuma the weather in Canada lured me and some of our friends into taking it, muna fatan Allah ya yafe mana, mind you... har ma da peer pressure, though ni dai na sha wahala sosai kafin in saba da weather din Canada, amma billah tun bayan dawowata Naija na daina shan alcohol Mayraah, back in Canada ma sai inyi many weeks ban sha ba sai in na gani gun abokan mu, many of my friends basu daina ba har yau, i don't know what came over me da har na sha ranan da daddare a zaria, may be it's because i was loosing my self, Mami bata taɓa sanina da alcohol ba har yau...." Mayraah dai tayi shiru tana sauraronsa, Bayan few seconds yace "Now tell me how u felt the first day we met" Murmushi Mayraah tayi ta kasa ce masa komai, can dai tace "Some other time" Yace "Ohk, ina son kuma zan tambayeki...." Tace "Ina ji" Yace "I tot u once told me Badiyyah er gidanku ce or so" Tace "Sure...." Yace "But da safe da ta shigo office naga kun yi kamar baku san juna ba, why?" Mayraah tace "Ai mun riga mun gaisa da ita a downstairs... And wajenka ta zo a office ba wajena ba" Dr Musharraf yace "Ohkk then, it's already late, ki kwanta.... ni zan yi sallah" a hankali Mayraah tace "Ohk" yayi kasa da murya yace "Sleep tight my love..." tace "Thank you..." Daga haka ya katse wayar Mayraah ta lumshe ido. Washegari har karfe takwas Mayraah bata tashi ba don bazata school yau ba tunda Dr Musharraf yace mata bazai je ba, dama kuma friday ne, tana tashi wajen takwas da rabi ta ga miss calls din Ammi tun 5am, kiranta tayi yana fara ring Ammi ta daga, sun kusa 15 minutes suna magana da Ammi daga karshe suka yi sallama, Mayraah ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki, wanke baki tayi, tayi wanka sannan ta fito... Bayan ta gama shiryawa wajen goma saura taji anyi knocking din kofar dakinta, ta mike ta isa bakin kofar ta bude a hankali, Maheer ta gani tsaye, yana kallonta with smile on his face yace "Good morning Mimi" Tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau, how was ur night?" Tace "Alhmdlh" Yace "Yau baza ki school ba?" Tace "Eh" Yace "Ohk, fito ki debi breakfast" juyawa yayi ya bar bakin kofar ya koma parlor ta bi bayansa tana tafiya a hankali, zaune ta tadda Haseenah a parlor ga breakfast din da tayi ma Maheer a tsakar parlon tana kokarin hada masa shayi tana cewa "Baby special tea fa na dafa maka yau, bana jin ka taɓa shan irinsa wllh" ya zauna kan kujera yace "Really" Tayi er dariya tace "Sai ka dandana zaka gane..." Kamar ance ta daga kai taga Mayraah a parlon, nan da nan ta hade rai sosai, Maheer yace "A ina kika koyi dafa shayin?" Banza tayi masa tana saka cube din sugar a shayin, ya kalli Mayraah yace "Zauna mana Mimi" ta zauna edge din kujera tana kallon Haseenah tace "Ina kwana" Ciki ciki Haseenah ta amsa fuskarta a murtuke kamar hadari, Maheer ya sauka daga kan kujeran ya zauna kan carpet ya dau plate ya debar ma Mayraah irish din da kwai, sannan ya hada mata shayi me ƙauri, yace "Amma lectures ne baku da shi yau ko dai kawai zuwa school din ne baza ki yi ba Mimi" Mayraah tace "Kawai bazan je ba" Yace "Ohk sai kiyi karatu a gida, sauko kiyi breakfast" Mikewa Haseenah tayi fuuu ta wuce daki kamar zata tashi sama, Mayraah dai ta sauko kasa Maheer ya ajiye mata breakfast din a gabanta sannan ya fara hada nasa shayin da Haseenah ta bari, bayan ya gama hada shayin yace "Let me get my phone" Daga haka ya mike ya bi bayan Haseenah zuwa daki, Mayraah ta kyabe baki ta mike ta dau breakfast din ta kai daki ta ajiye sannan ta dau warmer din farfesunta na jiya ta tafi kitchen tayi warming, Maheer na shiga dakin ya kullo kofa yana kallon Haseenah cikin kwantar da murya yace "Me yasa kika taso Haseenah?" A mugun fusace tace "Bazan taso ba? Ta yaya zan sha wahala in tashi da asuban fari in mana girki ka debar ma yarinyar dake kwance tana bacci tun jiya da daddare?? Ko na ce maka ciki uku nayi ma breakfast din? It's just for me and you don ma kaji in gaya maka, Idan ba ma rainin wayo ba tsabar ka daure mata kugun ta raina ni yanda ta ga dama ta yaya ita bata tashi ta nema mana breakfast ba ni zan yi kuma ka debar mata?? Maheer tell me who does that??" Maheer yace "Amma fa jiya da na maki magana ce min kika yi kin fi so kiyi girkinki da kanki" Cikin daga murya tace "Toh sai nace maka har da ita zan yi ma girkin ko ita kuturwa ce da bazata nemi abinda zata ci ba a gidan? Maheer wllh na gaji da wannan walakancin daga yau na daina dauka sai dai duk abinda zai faru ya faru" Maheer yace "Ki daina daga min murya haka Haseenah, i am being patient all this days amma u are trying to push me to the wall" Ta mike tsaye tana huci kamar zata bangajesa tace "Har outside of the wall zanyi pushing dinka babu abinda ya sha min kai, wllh a duk duniya babu macen da zata dauki wannan abinda ake min in za a cire son zuciya, meyasa zan tashi da sassafe yarinya na bacci inyi wahala inyi breakfast ko bakina ban kai ba balle kai da nayi ma ka ci, zaka wani cika ma yarinya plate ka kwashi kwai ka lafta mata??? Duka duka irish din guda nawa na soya har zaka kwashe ka cika mata plate? Ko ita ta soya min??" Calmly Maheer yace "Toh ni bazan ci ba, ki cinye sauran tunda ba shi da yawa idan naje office zan nemi abinda zan ci, and you know what?? Gwara da haukanki ke tsayawa iya kaina Haseenah, don daga sanda kika yi gigin fara yi ma Mimi to za a ji kanmu gaskiya, ni za ki min inyi hakuri in shanye amma wllh kar ki kuskura ki ce za ki yi mata, ni ki ci gaba da min kawai i will endure, zan kuma ci gaba da baki hakuri" Yana kai wa nan ya dau makullin motarsa ya fice daga dakin ta bi sa da kallo baki bude.... Mayraah ta fito kitchen kenan da plate din kazarta da tayi warming, ganinsa a parlon tace "Yaya are you going to work?" Yace "Yea, u need anything?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Ko za ki je asibitin?" Gyada masa kai tayi, yace "Ohk, i will wait for you je kiyi breakfast dinki" Tace "Okay" Daki ta koma ya zauna parlor yana jiranta, Kuka wiwi Haseenah take a daki kamar ranta zai fita, yau kawai ji tayi da za a bata wuka wllh zata iya caka ma Mayraah ta huta, yanzu duk hakuri da ƙauda idon nan da take kamar yanda Salima tace ance tayi ya tashi a banza kenan, ita fa ba don umarnin Salima ba kilan da tuni tayi ma Mayraah duka a gidan duk abinda zai faru ya faru, amma ance ta bi komai a hankali, to tana ta kokarin kai zuciyarta nesa gashi yanzu rainin wayon da ake mata ma gaba yake yi maimakon baya, tana jin fitar motar Maheer a gidan ta fito da sauri tana huci ta shigo parlor tana leka compound ta tabbatar eh ya fita tunda taji ai yana cewa Mayraah baza ta makaranta ba, dawowa tayi ta koma kofar dakin Mayraah ta murda ta ji a kulle, kundume kundumen zagi ta fara tana jijjiga kofar kamar zata balla tana cewa "Shegiya tsintattciya mara asali ki bude kofar mana kiga ikon Allah yau, wallahi sai dai wata ba ke ba a gidan nan, hakurin da nake yi ya ci kaza kazansa, an daina hakurin daga yanzu, wallahi sai na canza maki kamanni ta yanda baza a gane ki ba yau" Bata fasa jijjiga kofar ba tana kundume kundumen zagi duk zaton ta Mayraah na ciki, kamar mahaukaciya ta fita daga gidan ta zaga bayan windown dakin Mayraah nan ma tana bubbuga glass din ta dinga cewa "Don kaza kazanki ki fito mana ki ga aiki da cikawa" Ta gama zuba haukanta ta koma ciki sai a sannan ta lura da babu takalmin Mayraah a bakin kofa, da sauri ta koma gun mai gadi tana tambayarsa ko Maheer kadai ya fita nan ya sanar mata ai har da karamar Hajiya, komawa ciki tayi ta baje a parlor ta dinga rusa kuka, wallahi Salimah ta cuceta da fa yanzu an wuce wajen, kilan da har an samar ma Mayraah wani wajen zama amma ba nan ba, daki ta koma ta dau wayarta ta kira Salima taji a kashe, ta zauna gefen gado tana kukan baƙin ciki da takaici, wata zuciyar ta raya mata to ko dai asibitin zata bi su ne, wani yace mata a'a a gida ya kamata ayi duk abinda za ayi a wuce wajen, ta share hawayenta tana nazari iri iri a ranta bata taɓa shiga bacin rai da baƙin ciki irin wannan ba, wayarta ne ya fara ring ta jawo da sauri a tunaninta Salimah ce, sai ta ga kawarta ce Zaliha, yanda take da Badiyyah haka take da Zaliha duk bata wani yarda da su ba bata gaya masu sirrinta, ta daga wayar ta kai kunne Zaliha tace "Meye duniya Haseenah daga aure sai kiyi watsi da mu ki canza layi?" Haseenah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ba haka bane Zaliha ina cikin damuwa da tashin hankalin da baza ki gane ba, kuma ban canza layi ba wani lokacin kashe wayar nake ko zan samu sassauci" Zaliha tace "Ikon Allah, me ke faruwa Haseenah? Kuma gashi da yau zan zo gidanki, shine ma nace bari in gwada layin ki yau" Haseenah ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Ke da wa za ki zo?" Zaliha tace "Ni kadai ce, yanzu haka ma na shirya wllh" Haseenah tace "Toh zan gaya ma mai gadi ya bude maki gate, sai kin zo" Zaliha tace "Toh shkkn, sai na iso" Haseenah na katse wayar ta fita zuwa gun mai gadi tace "Musa zan yi bakuwa idan ta zo ka bude mata gate" Yace "Toh Hajiya" Juyawa tayi ta koma ciki, wajen karfe sha biyu saura tana zaune parlor har sannan ta kasa shan ko ruwa, warmers din da ta ajiye na breakfast da tayi har sannan suna tsakar parlon taki kwashewa, knocking din kofar parlon ta ji anyi ta mike tana kallon agogo ta karasa ta bude kofar, sai da cikinta ya kusa shigewa cikinta ganin Badiyyah da Zaliha a tsaye bakin kofar.... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 [6/29, 9:05 PM] Khaleesat Haiydar💖: Badiyya ta yi wani tsalle ta finciko kwalar rigar Haseenah ta ja ta zuwa cikin parlon tana huci ta cire gyalen jikinta da handbag tayi cilli da su cikin daga murya tace "Fito min da gold dina kar in maki shegen duka, yau karyar ki ta kare kuma tunda har Allah yayi na shigo gidan nan" Zaliha ta riko Badiyya da sauri tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una meye haka Badiyyah? Dama abinda yasa kika dage mu zo kenan, dama abinda kika shirya kenan salon ki sa Haseenah ta fara min wani gani gani, ni wllh da na san abinda za ki zo kiyi kenan bazan yarda mu taho tare ba, meye haka don Allah" Duk da tashin hankalin ganin Badiyya da Haseenah ta shiga a lokacin ko da wasa bata yarda ta nuna hakan a fuska ba, sai wani dakewa da tayi tana kallon wani wajen daban, Badiyya na huci tace "Zaliha kin san tun yaushe nake bin matar nan ta ta bani kayana amma ta maida ni er iska er wahala? To wallahi ko ta fito min da gold din nan yau ko kuma in nakada mata shegen duka yanda mijinta bazai ganeta ba idan ya dawo, haka akwai daga abun arzki? Tana da gado na ne ko kuma akwai bashi ne tsakaninmu? Har kofar gidan nan na zo ranan mai gadi yace ba kowa a gidan kuma jikina ya bani tana ciki kilan Maheer ne kawai baya nan, sannan in dai na kirata sai in ji waya a kashe, duk sanda na ci sa'ar samunta kuma sai taki daga kiran, kin ga alamar rashin gaskiya kenan ko? to wallahi bazan yarda ba tunda ba uwarta ta min hustling gold din ba, don haka a yau ta bani kudina ko gold, idan ba haka ba duk abinda nayi mata ita ta ja ma kanta" Haseenah ta wani kyabe baki tace "To cikani in dauko waya in kira mai siyan gold din yanzu a gabanki, idan ya kama in hada ku ma sai ki amshi number sa kawai" Cikin daga murya Badiyya na jijjigata tace "Ina ruwana da me siyan gold da za ki hadamu? Saninsa nayi ko meye hadina da shi? kawai abinda na sani shine a bani gold dina ko kuma kudi, idan ba haka ba hukuma ta rabamu" Zaliha ta rike hannun Badiyya tace "Don Allah kiyi hakuri ki saketa ta dauko wayar tukun Badiyya, kin fi kowa sanin halin Haseenah fa, wllh Haseenah bazata cuce ki ba...." Da kyar Zaliha tayi convincing Badiyya ta sake Haseenah tana huci, Haseenah ta juya ta nufi dakinta, da farko niyya tayi ta kulle dakin da makulli tayi zamanta a ciki idan sun gaji da jiranta su tafi, wata zuciyar tace kai in dai Badiyyah ce sai ta iya zama har magariba a gidan in kuma hakan ya faru Maheer zai iya dawowa ya sameta, ta san tsaf Badiyyah zata iya mata sharri tace ita ce ma tace ta dau gold din, ita kam tsoron Badiyya take... Haseenah ta dau wayarta tana zaga dakin tana tunanin yanda zata yi, nan da nan idea ya zo mata tayi dialing number wani tsohon saurayinta da sauri ta shige bandaki ta kulle, babu bata lokaci ya daga yace "A'a Big gal an tuno da ni kenan yau" Haseenah tace "Wani big girl Biliya ina cikin tashin hankali, na kiraka ne ka taimaka min" Yace "To faa, kar ki ji komai Big gal fadi abinda ke tafe da ke kanki tsaye...." Cikin minti daya biyu ta gama yi masa bayanin duk abinda ke faruwa tsakaninta da Badiyyah sannan ta sanar masa plan din da take so su yi tare da shi, yace "Ba ki da case, ina jiran kiran naki" Katse wayar tayi ta fito daki da sauri, a bakin kofa suka kusa cin karo da Badiyya zata shigo dakin, Badiyya na mata wani kallo tace "Dauko wayar ce kusan minti biyar??" A takaice Haseenah tace "Aa Malama ki saurara min, mijina ne ya kirani na tsaya nayi attending masa, kuma ni kin ban mamaki da har za ki bar Zaliha ta ji tsakaninmu, na zata abotanmu ya wuce haka da ke" Bata tsaya ta saurari Badiyya ba ta fito parlor ta fara dialing number Bilyah tana tsaye, Badiyya ta karaso parlon tace "To Zalihar uwata ce ita da zan ji tsoron gaya mata abinda ke tsakaninmu da ke, da kin bani Gold dina ta yaya ma Zaliha zata ji kanmu har za ki ce na baki mamaki da Zaliha ta ji kanmu??" Haseenah ta kasa cewa komai jin abinda Badiyyah ke cewa, Zaliha dake kallonta tace "Ohh gani bare ko Haseenah? To ai shikenan bari inyi tafiyata" Haseenah ta rikota tace "Aa Zaliha ba haka nake nufi ba, ki tsaya ayi komai gabanki ki zama shaida" Har kiran da Haseenah take yi ya katse Bilya bai dauka ba, Badiyya ta fara girgije girgije tace "Heheee, let it not be what i am thinking Haseenah, don wllh wllh bazan yarda ba, ko da uban wa kike yawo sai kin bani Gold dina ko kudina" Haseenah ta sake kira nan ma bai daga ba, hakan kuma duk yana daga cikin plan din nasu, sai da ta kirasa sau uku sannan ya daga yace "Ke wai ya zaki ta damuna kullum da kira kamar wanda zai gudu ne?? Why are u disturbing me plss sai kace bamu saba harka da ke ba" Haseenah tace "Ni dai ka dawo kasar ko baka dawo ba?" Yace "Ban dawo ba, nace maki ina dawowa za a bada kudin ko, kina abu sai kace ban san ki ba baki san ni ba" Haseenah tace "Me shi ne ta takurani wllh, tana ga kamar na cinye mata kudi ko wani abu..." Bilya yace "Ita da aka samu za a siya stuff din nata babu reciept, wa ya sani ma ko sato sa tayi za mu yi taking risk mu siya saboda ke shine kuma zata yi ta takura mutane, wllh ko wa zata kai ma gold din nan bazai siya babu reciept ba, sannan ba pure gold bane wllh, kinsan gold din step by step ne to nata karami ne" Zaliha ta zaro ido jin abinda Bilya ke cewa, Haseenah tace "Kai dai babu ruwanka da wannan kudinmu muka sani kawai, nawa ne kudin ma kace?" Yace "Sau nawa zan ce maki miliyan daya da rabi za a siya, kawai account zaki ajiye ina shigowa kasar inyi transfer" yana fadin haka ya katse wayar, Badiyya da tayi mitsi mitsi da ido tace "Kan uba, shi gold din da kika ce min ya kusa miliyan biyar ne naji ake cewa miliyan daya da rabi, ni za a cuta??" Haseenah na kallonta da kyau tace "Ke bari kiji in gaya maki Badiyyah, an fa daina siyan Gold babu reciept a garin nan, wannan ma alfarma kawai ya mana saboda ni, kuma ni kudina na yin har wata daya biyu a wajensa, ko kwandala bai taba cinye min ba" Badiyyah ta girgiza kai tace "Inaaaa, bazai yiwu ba gwara kawai a bani Gold din na fasa siyarwa wllhi tallahi, in ya kama ma sai in sa abina inyi kwalliya kawai" Haseenah tace "Toh sai mu jira ya dawo kasar, ina jin Umra ya tafi, wannan wani irin rayuwa ne, Cousin dinki ya daura min pressure, tsinanniyar yarinyar da aka kawo min gida ta daura min pressure, kema yanzu ga shi kin zo da naki, ke da ya kamata inji dadi ta wajenki, wai ya ake son inyi ne??" Badiyya ta zaro ido tace "Ita Mayraahn kika bari take daura maki pressure?" Kamar jira Haseenah take ta fashe da kuka amma ba hawaye tace "Badiyya da za a bani wuka ina jin babu abinda zai hanani kashe yarinyar nan in huta, ban taɓa jin tsanar mutum kamar yanda na tsaneta ba, ki tambayi Zaliha ko da ta kirani dazu ai kuka nake saboda abun duniya ya isheni" Zaliha tace "Kwarai kuwa, kuma na gaya ma Badiyyar haka amma da yake bata da mutunci ji abinda ta zo tayi maki" Badiyya ta nemi waje ta zauna tace "To ai ni na zata duk zance Zaliha ke min, ban san da gaske bane, wai sai kika yi shiru kika zuba mata ido Haseenah?" Haseenah ta zauna kasa tace "To bari ki ji me kankat Badiyyah, yau breakfast na tashi tun asuba nayi mana ni da shi, wallahi gari na wayewa ya kwashe ya bata kun ga sauran nan ko taɓawa ban yi ba saboda takaici, yanda kika san zai yi worshipping dinta a gidan nan haka yake yi, gashi tayi mugun raina ni bata ganina da mutunci, babu gaisuwa tsakanina da ita, sannan ko cup bata dagawa a gidan nan komai ni nake yi, kuma in nayi girki ya kwasa ya bata" Badiyyah tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Wargi ma ai waje ya samu, da ace kin daidaici ranan da baya nan kin kama shegiya kin nakada mata shegen duka wallahi da kafafuwanta zata gudu ba sai wani yace ta tafi ba, ai ni na ma ga kokarinki da kike ta zaune da ita har yanzu under the same roof, kina fa koranta a gidan nan bata da inda zata je da ya wuce ta shiga duniya kuma, don har yanzu Hajja na kan bakanta wallahi, ko kiran Ammi sai nace ta daga take dagawa in ko na zugata nace kar ta daga to wllh baza ta daga ba, kin ga kuwa duk ranan da kika kori Mayraah bata da wajen zuwa a duniya" Haseenah ta marairaice tace "Wallahi dukan nayi niyyar mata yau naga ashe tare suka fita ina daki ina ta haukana, tun fa da ta zo bamu taɓa yini tare da ita a gidan nan ba, kullum sai taje makaranta, yau kuma naji tace bazata je ba daga baya kuma naga bata gidan kilan asibiti ya tafi da ita, kawai sun mayar da ni er iska a gidana, Babban tashin hankali na yanda kowa yasan da aure tsakaninsu yanzu, wallahi in na tuna hakan kasa bacci nake da daddare, har abinci sai in ji ya fita raina, kar wataran...." Kasa ci gaba tayi kawai sai ta fashe da matsanancin kuka, Badiyya ta rike haɓa tace "To bari ki ji har yau tana makale da lecturer din nan namu in gaya maki, Wllh jiya naje office dinsa na ganta ciki zaune yanda kika san office din ubanta, tana ganina kuma ta mike ta fita, ai ko sai da nayi minti ashirin a office din yana min bayanin course din da na kai masa nace ban gane ba, yanzu ran Monday zan sake duba wani topic in je in samesa a office again in ce ban gane ba a haka a haka har in shige masa, sai dai babban damuwata har yanzu bai taɓa tsayawa irin ya kalleni din nan ba, ko fuskata bai cika tsayawa ya kalla ba abinda ke gabansa kawai yake, sannan ganinta da nayi a office dinsa ya tsaya min a rai sosai kin ga kenan hakan na nufin basu rabu ba, to in basu rabu ba ta yaya har zai saurareni ni jama'a? Wllhi har da wannan yasa nace yau sai na san yanda nayi na zo na sameki tunda ke kadai ke bani mafita sai Zaliha, so nake ya rabu da ita kwata kwata ya ji ya tsaneta baya son ganinta, ta zama makiyiyarsa, ni kuma in shiga zuciyarsa farat daya" Haseenah tayi shiru tana kallon Badiyya, Zaliha tace "Tabdi, ai ko wannan dole sai an hada da Malamai, ta yaya zai ji ya tsaneta bata masa komai ba" Badiyyah ta juya tana kallon Zaliha tace "To ai malaman ne ni gani nake kudin mutum kawai suke ci wllhi" Haseenah ta sauke ajiyar zuciya tace "Nima dai haka nake gani, amma fa akwai wata kawata dake ta bani labarin wasu malamanta biyu ni dai nace Naira biyar dina bazai yi ciwon kai ba ba ruwana i am not interested, Malaman sun mata aiki akan wani mai shegen kudi a zaria da take so da aure, kuma aikin ya ci tun da yanzu haka maganar da nake maku ya saki matarsa, ita kuma kawar tawa saura sati biyu bikinsu har ta turo min IV... Kinga kuwa ai aiki ya ci" Badiyyah ta sauko kasa tace "Don Allah fa??" Haseenah tace "Wallahi kuwa in gaya maki, bayan nan still sun yi ma kawar kawar tawa aiki ita ma ta kori kishiyarta, yanzu daga ita sai yaranta a gidan, ga mota an mallaka mata" Badiyyah ta marairaice tace "Toh ko za ta hadani da su don Allah" Haseenah tace "Sai dai in kirata ta turo mana number, tunda ni dai nace mata i am not interested bata sake bin ta kaina ba, kinsan abinda mutum bai taɓa yi ba" Badiyyah tace "To don Allah ni dai kirata kawata, ni ban ki in kashe ko nawa bane in har zan mallaki Dr Musharraf" Haseenah ta mike tace "Bari in kirata don kinsan sirri ne, nima ta aminta da ni ne yasa ta gaya min, tana jin kawayena zan ba number sai ta iya hanani wllh don ba mutunci ne da ita ba" Badiyyah da har wani tsuma jikinta yake tace "Toh je daki ki kirata kawata" Haseenah ta shiga daki ta kulle kofa ta zauna gefen gado tana murmushi, shikenan yanzu za su wanye lafiya da Badiyyah ba wanda zai sake jin kansu, don number Malamin da ke mata aiki zata bata kawai, dayan Malamin kuma sai tace mata kawar ta hana numbersa saboda yafi iya aiki sai dai in ana son abu abi ta wajenta ita zata dinga gaya masa duk abinda yace kuma ta bada feedback, shkkn sai tayi using wannan opportunity din ta dinga ce ma Badiyya zata dinga bada kudin da haka da haka har ta ce mata kudin gold ya kare gun biyan malami.... Bayan wani lokaci Haseenah ta fito tace "Ohhh Mansura ko jaraba, da kyar ta bani number dayan Malamin in gaya maki, dayan kuma tace bazata bani ba don yafi iya aiki sannan ba ma wayar kowa yake dagawa ba sai manya manyan kasar nan, sai dai duk abinda nake so in gaya mata ita zata dinga masa magana sannan ta dinga feeding dina back, bata san ba ni bace kawata nake ma fafutuka" Badiyya tace "Wallahi na yarda, a ban number dayan, dayan kuma duk yanda tace ayi haka za ayi don ni yanzu mafita nake nema" A haka Haseenah ta ba Badiyyah number malaminta na Zaria, nan take kuma Badiyya ta shige dakin Haseenah ta kirasa tayi masa bayanin komai, sun kusa minti sha biyar suna waya sannan ta fito tana kallon Haseenah dake cin dankali da kwai ita da Zaliha, ta zauna gefen kujera a sanyaye tace "Haseenah yace in fara bada 150k for a start, ni kuma wllh ko dubu hamsin kudin account dina bai kai ba duk na biya bashi da kudadena" Haseenah tace "Tabb, a yanda fa Mansura tace min dubu dari uku yake fara cajin sa, ke ya ma maki da sauki kenan, shi kuma dayan malamin dama tace daga 500k zuwa sama yake fara cajinsa don aikinsa ba karya, ba irin malaman nan bane masu amsan dubu goma dubu ashirin su yi cefane a gida" Badiyyah ta hade rai tace "Gaskiya ki kara kiran me gold din nan ko dubu dari biyu ne ya fara turo min in biya ma kaina bukata, abu dai kusan sati biyu yau" Haseenah sai da taji dankalin ya makale mata a throat, can ta kalli Badiyya tace "Ai to baya kasan ne Badiyyah, yanzu abinda za mu yi zan baki aron dubu dari, sai ki ganganda ya zama 150k din ki tura masa" Badiyya ta washe baki tace "Yauwa kawata wallahi nagode sosai, shi yasa nake sonki bani da kamar ki, dama na ce masa nan da yamma zan tura masa" Haseenah tace "Zan maki transfer din kar ki ji komai" Badiyyah ta sauko kasa ta saka hannu tana cin dankalin ita ma tana jin ranta fari tassss, har ta fara hango kanta a gidan Musharraf a matsayin matarsa, tunanin hakan sent quivers all over her body, whatttt, murmushi kawai take ita kadai tana cin dankalin da kwai... Har bayan la'asar su Badiyya na gidan ba kuma su da niyyar tafiya, jikin Haseenah dai bai ga ta wanka ba yau, ta narko masu uban Indomie da kwai suka tashi da shi a parlon, plans iri iri ita da Zaliha ke kitsa ma Haseenah akan yanda zata yi maganin Mayraah a gidan har da bata shawaran ita ma ta ciro kudi ayi mata aiki kan Mayraah, Haseenah dake ta jin su tana masu kallon shashashai, ta girgiza kai tace "Aa gaskiya bani da kudin da zan ba Malami, bakina kadai ya isa ya sa Mayraah ta shiga duniya, dama can kuma ai a duniyar aka tsinceta" Su Badiyyah duk suka kwashe da dariya... Karfe biyar suka ji an bude gate din gidan, Zaliha ta zaro ido tace "Kaddai mai gidan ne ya dawo?" Badiyyah ta gyara zama tace "To sai me, ai ina ga daga yanzu sai dai yayi hakuri don kullum zai dinga ganina a gidan nan" Haseenah tace "Wallahi da kin kyauta kuwa, kyau ma ace kin kwaso kayanki kin dawo nan din da zama...." Badiyyah tace "Aa bazan kwaso kayana ba amma kullum kam zan zo, kuma bai isa ya hanani ba don wani bomb din zan kara hadawa wllh" Bayan few minutes aka bude kofar parlon Maheer ya shigo da sallama, bin parlon ya dinga yi da kallo don everywhere is so untidy, ga warmers din breakfast din safe ba a kwashe ba, ga tray din da suka ci Indomie har ya bushe, ga goran ruwa da lemo a yashe parlon, ga plate din su cin cin da alkaki, worst of all Parlon yayi wani dummm kamar babu ventilation don Ac a kashe yake, Zaliha na gyara mayafinta tace "Sannu da zuwa Dr" Yace "Yauwa sannu" Badiyyah ta dau cin cin daya tana ci tace "Ina wuni" Yace "Lafiya" Yana tsaye har Mayraah ta shigo Parlon rike da leda a hannunta, da ido duk ta bi su kafin tayi hanyar dakinta, Maheer ya kulle kofar shi ma ya wuce nasu dakin, Badiyyah ta kalli Haseenah tana zaro ido tace "Kan bala'i, kin ga kallon da tayi mana ta wuce kuwa?" Haseenah tayi murmushin takaici tace "To kullum haka take min a gidan nan Badiyyah" Badiyyah ta rike haɓa tana kallon Haseenah da mamaki, Zaliha tace "To kuwa komai ya kusa zuwa karshe in dai za ayi amfani da shawaranmu, ni dai yanzu ki tashi mu tafi Badiyyah yanzun nan zaki ji magariba" Badiyyah tace "Kawai kiyi tafiyarki, ni sai can da daddare, kilan ma zuwa za ayi a daukeni" Haseenah ta kalli Zaliha tace "Kema ki bari sai anjima mana" Zaliha tace "Wallahi kar in rasa abun hawa ne" Badiyyah tace "Kar ki ji komai in an zo daukata sai a fara ajiye ki" Zaliha tace "Nasan karfe nawa za a zo daukarki? Aa bari ku ga tafiyata yanzu" Sallama tayi masu ta dau jakarta Haseenah ta rakata bakin kofar parlor sannan ta dawo, Badiyyah tayi kasa da murya tace "Munafuka ce fa Zalihar nan, wllh ban so munyi wasu maganganu a gabanta ba, duk ita ce fa ta hada min plan din yanda zan zo in riske ki fa a gida, a gabana ta kiraki tace ga ta nan zuwa" Haseenah tace "Kaji shegiya, wallahi in dai kun yi magana da ita ko ta WhatsApp ki nuna mata ke kin ma hakura da ba Malami kudi yayi maki aiki zaki yi amfani da hikimarki kawai" Badiyyah tace "Ai ko haka zan yi, don ban yarda da ita ba, sai kinga yanda ta dinga zugani kan cewar kar in yarda in fito daga gidan nan yau sai da gold ko kudina" Haseenah tace "Kaji algunguma, to wllh bazan sake barin ta xo min gidana ba" Badiyyah tace "Da dai ya fi" Mikewa Haseenah tayi tace "Bari in je in ga sweetheart dina ko welcoming dinsa ban yi ba" Daga haka ta mike ta nufi dakinsu, Zaune ta tadda Maheer a dakin fuskarsa babu walwala, ta kulle kofa tana murmushi tace "Welcome back baby, ka dawo ka gan ni tare da baki" Maheer ya daga kai ya kalleta yace "Yanzu ke ko kunya baki ji ba yanda na tafi na bar ki haka na dawo na sameki a gidan nan Haseenah? Wannan wani irin kazanta ce? Are you not perceiving d odour coming out from ur body?" Haseenah ta hade rai ta dakatar da shi tace "Aa don't go there Maheer, kai yanzu banda tsabar sharri tun daga can ka jiyo odour dina? Kuma nace maka ban yi wanka bane yau?" Bai sake ce mata komai ba ya ci gaba da dannan wayarsa, ta juya ta fice daga dakin.... Ana kiran Magrib Maheer ya fito, ya bude kofar dakin Mayraah, karatu ya sameta tana yi, ya kulle kofar ya karasa parlor, har a sannan Badiyyah da Haseenah na zaune suna kus kus a parlon, kuma har lokacin basu kwashe kwanukan tsakar parlon ba, ya koma corridor ya bude kofar dakin Mayraah yayi instructing dinta ta kulle dakinta sannan yayi tafiyarsa masallaci, ko da ya dawo daga masallaci Badiyyah ce kadai zaune kan 2 sitter a parlor tana kallo, zuwa yanzu dai an kwashe kwanukan goran ruwa da lemo ne dai ba a kwashe ba, ta daga kai ta kallesa ta ci gaba da kallonta, zaunawa yayi kan 2 sitter din shi ma yace "Ya Hajja fa?" Sai da Badiyya ta kara kallonsa to be sure first, kafin ta ci gaba da kallonta tace "Tana lafiya" Yace "Kinyi resuming school din ko har yanzu kina nan kina gantalin ki?" Tace "Gantali kuma, ni ai kullum ina zuwa school" Yace "Ohk, kin dai ga final semester din ku ne you have to be very serious with ur studies, da alama yau ma yini ku ka yi a nan ko handout baki bude ba" Tace "Bayan ma bani da handout din duk ban san inda suke ba" Yace "A haka za ki yi exams din to?" Ta ɗan tabe baki bata ce komai ba, yace "To nawa ne handout din?" Kallonsa ta kara yi to be sure again, is this really Maheer?? can dai tace "Gaba daya fa kusan 15k ne, kasan handout dinmu akwai tsada" Yace "To tura min account dinki in sa maki kudin" Badiyyah ta kara kallonsa this time around with surprise on her face, Haseenah ce ta fito daga daki tayi wanka ta canza kaya sai baza kamshi take ta karaso parlon tana kallonsu ganin su zaune kujera daya suna kallon juna, Badiyyah tace "To ai ni bani da number ka" yace "Nima bani da taki" Yana fadin haka ya ciro wayarsa ya mika mata yana kallonta yace "Sa min numberki" MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 *Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake* [6/30, 7:58 PM] Khaleesat Haiydar💖: Badiyyah ta amshi wayar da Maheer ke mika mata ta saka numberta sannan ta mika masa tana mamakin wai yau Maheer ne da amsan numberta, is this for real?? Haseenah ta dauke kai daga kallonsu ta karaso parlon ta zauna babu yabo babu fallasa tana kallon TV, Maheer ya juya ya kalli Haseenah yace "Babu Dinner a gidan kenan?" A takaice tace "Breakfast din da nayi maka ma ai baka ci ba..." Yace "Ohk" Daga haka ya mike ya bar masu parlon, Badiyya ta zaro ido ta mike da sauri ta koma kusa da Haseenah ta rike haɓa tace "Kawata ki ji wani sabon salo wai Maheer da amsan numberta, wai nan fa duk so suke Hajja ta fara kula Ammi kamar da, sulhu kawai su ke so da ni fa" Haseenah tace "Atoh nima abun ya daure min kai" Badiyyah ta kyalkyale da dariya tana tafe hannu tace "Ai in dai zuga ne yanzu na fara, in aka ga na daina to babu Mayraah a familyn gaba daya" Da sauri ta ciro wayarta dake ringing tace "Yauwa gashi nan ya zo kawata, bari in tashi in tafi... " Haseenah tace "To sai yaushe kenan?" Badiyyah tace "Gobe asabar zanje Bichi wajen kawuna in masa karya akwai practical da za mu yi na final exams in amso kudi wajensa da zan cika ma malamin nan, kilan in dawo a goben, in kuma ban dawo ba sai Sunday in sha Allah" Haseenah tace "Toh shikenan za mu yi waya, duk yanda kawata suka yi da shi second Malamin zan sanar maki" Badiyyah na murmushi tace "To kawata nagode sosai" Mikewa tayi, Haseenah ma ta tashi ta rakata har bakin gate sannan ta dawo gidan, dakin Maheer ta tafi ta ga baya ciki, dama tun da aka kawota a dakinsa ta tare, nata kuwa sai jefi jefi take shiga ko in tana bukatar wani abu ko in zata yi waya, bata gansa cikin dakin nasa ba, ta leka nata nan ma baya nan, ta fito da mamaki ta tsaya corridor tana kallon kofar dakin Mayraah, babu tantama yana ciki tunda bai fita daga gidan ba, karasawa tayi ta kasa kunne amma bata jin komai, fita tayi daga gidan gaba daya ta zaga ta bayan window din Mayraah nan ma ta kasa kunne, ba abinda take gani kuma bata jin komai saboda window a kulle yake sannan curtains din ba a bude suke ba, nan da nan taji zuciyarta na tafarfasa ta dawo cikin gida, kawai ta nufi kofar dakin ta bude, Mayraah na zaune kan darduma with her handouts, shi kuma yana duke gabanta explaining something to her from the handout, duk suka juya suna kallonta, kallon sama har kasa ta dinga masu kafin ta juya ta bar bakin kofar dakin without saying a word, Maheer ya karasa bayanin da yake ma Mayraah yace "Hope kin gane yanzu?" Ta gyada masa kai, mikewa yayi zai fita ta daga kai ta kallesa, a hankali tace "Yaya dama..." Juyowa yayi ya kalleta yace "Dama me?" Ta sunkuyar da kai, ya dawo ya duka gabanta yace "Talk to me Mimi, dama me?" Ta daga kai tace "Dr Musharraf will be coming" Shiru yayi yana kallonta hakan yasa ta sunkuyar da kanta, can yace "Coming to where?" Murya can kasa tace "Here" Calmly Maheer yace "Me zai zo yayi?" Ta dinga kallonsa ta ki cewa komai, ya girgiza kai yace "I don't think there is any need ki ci gaba da kula mutumin nan Mimi, ba aure za ku yi ba, kawai kuna bata ma kanku lokaci ne, babu amfanin ku ci gaba da wani mu'amala after all that happened, don haka i see no reason da zai zo gidana....." Nan da nan hawaye ya cika idonta tace "To ai ba rabuwa muka yi ba yaya, beside...." Sai kawai ta fashe da kuka tace "Ni ina sonsa" Maheer ya dinga kallonta, mikewa yayi yace "To ki cire sa a ranki don baza ku taɓa aure ba, kamar yanda iyayensa suka ce basa son auren to kema naki iyayen haka, you both should stop deceiving ur selves and face reality" Kuka kawai Mayraah take tana kallonsa, ya hade rai yace "And all this is going to stop after ur final exams" Yana kai wa nan ya fice daga dakin... Mayraah ta kara fashewa da kuka, ta dau wayarta ta kashe gaba daya ta mike ta hau kan gado ta kwanta tana ci gaba da kuka kamar ranta zai fita, ta kai kusan karfe sha biyun dare tana abu daya daga karshe bacci ya dauketa. Washegari da sassafe ta tashi da kumburarrun ido, tayi wanka ta shirya ta dau wayarta ta saka cikin jaka ta fice daga gidan wajen karfe bakwai da rabi.... A hankali ta bude kofar main parlor din gidan ta shiga, kamar ko da yaushe babu kowa parlon ta wuce sama direct fuskarta babu walwala, tana shiga parlon Ammi suka fara ido hudu da Usman dake zaune sai Mama Ladi da ta bararraje tsakar parlon ga tuwo malmala biyu a gabanta tana ci da katon cup cike da shayi, Mayraah na shiga parlon ta fashe da kuka ta zauna kasa ta kife kanta da kujera tana kara sautin kukanta, Mama Ladi ta saki salati ta matsar da kwanon tuwon gabanta da shayi ta mike tace "Ahau dama ba nace maku zamanta daga ita sai Sanisa a gidan nan bazai yiwu ba amma ku ka maida ni er banza mara makabuli, jiya jiyan nan na gama gaya ma Ammi nayi mafarki Sanisa ta ma Mera dukan tsiya, wai kawai matar nan sai ta kira Mashir a gigice tana tambayar Mera shi kuma sai yace mata suna asibiti tare, daga haka ta shashantar da mafarki na, to gashi nan dai ya tabbata dama bana mafarki a banza, kiri kiri aka ki barin inje gidan in sa ido saboda an maida ni tsohuwar banza, to gashi nan dai ta mata tsinannen duka hankalin kowa sai ya kwanta" Tuni Usman ya mike ya nufi Mayraah ya duka gabanta worriedly yace "Mimi me ya faru?? me aka maki??" taki dago kanta balle tace komai sai rusa kuka take kamar ranta zai fita, Mama Ladi ta figi zaninta dake linke ta warware ta yafa a jiki tace "Ai sai mu kama hanyar caji opis don ba mu ga ta zama ba, abinda nake ta gudu kenan aka kasa fahintata dama tunda naji Sanisar kawar Badiyyah ce hankalina ya tashi don ai ance abokin barawo barawo ne, to shi shegen Mashir din yana ina ta maki wannan aika aikan?" Ganin Mayraah taki dagowa balle ta amsa uban tambayoyin da yake jero mata kawai ya kai hannu ya dagota ya zaunar da ita gefen kujera, Mama Ladi ta nufi kofa da gudu tana cewa "Ita kuma wancan da taje ta makale ma miji bari inje in kwankwasa masu su fito ba lafiya, abinda nake ta hangowa gashi ya faru" Usman dake ta kallon Mayraah da ke kuka ya duka gabanta cikin kwantar da murya yace "Calm down Mimi now tell me what happened, me aka maki? Ke da waye?" Ta kallesa tana goge hawayen dake sauka idonta cikin rawan murya tace "Yaya ne" Da mamaki yace "Yaya?? Me ya maki?" Nan da nan expression din fuskarsa ya sauya yace "Gaya min abinda yayi maki?" ta kara fashewa da kuka ta ki cewa komai, mikewa Usman yayi yana kallonta yana jin kukan nata na damunsa, Ammi ce ta shigo parlon da sauri Mama Ladi na biye da ita a baya tana cewa "Gaba daya fuskar ta kumbura, tana dingishi ta shigo mana, dama kuma ba nace maki nayi mafarki ba" Ammi ta nufi Mayraah ta kamo hannunta hankali tashe ta zauna gefenta tana duba duk jikinta tace "What happened daughter? Me aka maki a gidan?" Cikin rawan murya Mayraah tace "Yaya ne" Ammi da Mama Ladi suka hada baki wajen cewa "Yaya???" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Shi Mashir din??" Dai dai nan aka bude kofar parlon duk suka juya, Maheer ya shigo, Mayraah ta turo baki ganinsa ta kara shigewa jikin Ammi, Mama Ladi ta nufesa tace "Mashir daga ka auri er iska sai kai ma ka zama ɗan iska? Fisabilillahi ne ta maka zaka mata wannan duka haka yarinya marainiya??" Maheer ya dinga kallon Mayraah da ta rufe fuskarta jikin Ammi, can kuma ta mike ta shige dakin Ammi tana turo baki, Ammi ta dinga kallon Maheer tana jiran jin abinda zai ce don ita dai tasan bazai kai ma Mayraah hannu ba don bai taɓa ba, Usman ya bi Mayraah cikin dakin, zaune ya sameta kasan carpet fuskar nan nata a murtuke, yace "Me ya maki?" Cikin rawan murya tana goge idonta tace "Wai Dr Musharraf ne zai zo jiya ya hana sa..." Tana kai wa nan ta fashe da wani sabon kuka, Usman ya dinga kallonta babu ko kiftawa, kafa taga ya saita zai haureta ta bar wajen da sauri ta shige bandakin Ammi ta kulle, fita yayi daga dakin ya fice daga part din gaba daya, Mama Ladi ta nemi kujera ta zauna ta saki salati tana kallon Maheer tace "Aa to Mera ta zama abar tsoro, meye hadinta da mutumin da iyayensa suka zo nan suka ci mutuncin iyayenta? Kaca kaca fa mutanen nan suka mana ko furfura basu duba ba, to ko dai baku bata labarin abinda danginsa suka yi ranan da suka zo kwace lefensu bane?? Yanzu ko maza sun kare a duniya ita har zata tsaya ta kalli mutumin nan balle har ta sauraresa, ko don ba iyayen da suka haifeta aka yi ma cin mutunci ba shi yasa ko a jikinta? Kai ma dai Mashir har da naka, ai da shiru zaka yi mata ka bari mutumin sai ya zo har kofar gidanka kayi maza ka kira masa yan sanda su garkame sa, to in ba lalata zai yi ba meye zai wani dinga bibiyarta bayan an fasa aure, to ni dai ba ruwana" Ammi dake ta kallonsu, cikin sanyin murya tace "Mama Ladi amma da an bar ta, a hankali zata rabu da shi ba farat daya ba, mutumin kirki ne wallahi ba ruwansa...." Maheer ya dinga ma Ammi kallon mamaki, Mama Ladi tace "Kaji wata magana kuma ko? Wato muna nan muna babatu ashe ke kika daure mata kugun ta ci gaba da kula katon, kanin ubanta ne shi da bazata iya rabuwa da shi farat daya ba??" Ammi ta kalli Maheer tace "Plss take it easy on her, ka daina firgita min yarinya, ka taɓa ganin inda aka rabu farat daya? Allow her breathe plss" Tana fadin haka ta mike ta shiga dakin, Mama Ladi ta bi ta da kallo baki bude, Maheer dai na tsaye ya kasa cewa komai, can ya juya ya fita daga parlon. Karfe goma saura Usman ya shigo parlon Ammi Maheer na biye da shi, tun da Mayraah ta hada ido da su sau daya ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da danna wayarta, Maheer dai na tsaye bakin kofar, Usman ya zauna yana kallon Ammi, calmly yace "But Ammi, kamar bai kamata kiyi supporting din...." Ammi ta dakatar da shi tace "Plss bana son wannan maganar, kowa yayi abinda zai fishshesa, bana son a sake tada min zancen nan" Mama Ladi ta matsar da farfesun gabanta kamar zata yi kuka tace "Yau naga jaraba ni Ladiyo, meyasa kike haka ne Ammi, mata kiyi ta goyon bayan karya kamar uwarki Hajja, wannan wani irin dabi'a ce ku ka gada wajenta, yanzu so kike a zuba ma yarinyar ido ta lalace ta zama er banza, Abu ya taru ya mata yawa ga rashin sanin asali gashi ta lalace? Ina ruwanta da shi wancan katon da ya fasa aurenta in dai za ayi maganar gaskiya jama'a, ai tunda har babu maganar aure tsakaninsu to kilan da wata manufa yake bibiyarta, amma saboda sonta ya rufe maki ido kin kasa fahimta, to ni dae wllh ba ruwana" Ammi dai ta hade rai taki cewa komai tana kallon TV, Mama Ladi ta kalli Usman da Maheer tace "Kyau ace daya daga cikin ku ya aure er banza in ga ta tsiya" Daga Maheer har Usman sai da suka yi still a inda suke cause they never saw that coming from Mama Ladi, Mayraah ma taji komai ya tsaya mata jin abinda Mama Ladi tace, ita kanta Ammi felt somehow da furucin Mama Ladi, Tuni Mama Ladi ta maida kanta kan kwanon farfesunta kamar ba ita ta fada ba, mikewa Usman yayi ya nufi kofa ya fita daga parlon, Mayraah ta ɗan daga kai suka hada ido da Maheer dake kallonta, da sauri ta kauda kanta, Mama Ladi dai sai cin farfesunta take, Bayan few seconds Maheer ya sake kallon Mayraah, a hankali yace "Dauko Hijab dinki mu tafi" a takaice Ammi tace "Sai da yamma" sosai Mayraah taji wani relieve, Maheer ya juya ya fita daga parlon ya kulle masu kofa.... Bayan la'asar Mayraah na kwance dakin Ammi suna waya da Dr Musharraf, duk yawanci hirar tasu akan fast approaching exams dinta ne, yana bata tips on how to prepare for the final exams, a hankali tace "But sir unlike before, yanzu i am finding it difficult to apprehend idan ina karatu, sae in dade a handout daya ban gane ba" Dr Musharraf ya kwantar da murya yace "That's because kin sa damuwa a zuciyarki Mayraah, pls ki cire komai a ranki and read like there is no tomorrow, this is ur future, it will be sad ace kin samu issue, you need not to worry about ur project for now i will handle that, kawai kiyi concentrating a karatunki, in sha Allah zan baki AOC a courses dina biyu, and i will try and get from other lecturers too if that will be possible, i will write it down idan mun hadu school gobe sai kiyi sharing with ur cousin Badiyyah" Shiru Mayraah tayi jin abinda yace, Dr Musharraf yace "A gida daya ku ke da ita?" Girgiza masa kai tayi kamar yana ganinta, yace "Hello" A takaice tace "Aa" Yace "Ohk, but ta bangaren Abba ku ka yi relating ko bangaren Ammi?" Mayraah tace "We will talk later, ana kirana" yace "Alright dear, take care, zan kira ki Anjima" Katse wayar tayi without saying anything to him, ta sauka daga kan gado ta fita daga dakin. Bayan magrib Mayraah na zaune parlon Ammi dake mata combing dogon gashinta don dama Ammi ce ke mata always, Mama Ladi kuma ta shiga makota tun da yamma har sannan bata dawo ba, Maheer ya shigo parlon da sallama, zaunawa yayi ya gaida Ammi, Ammi ta amsa without looking at him, Mayraah tace "Ina wuni" Yana kallonta yace "Lafiya lau" Bayan few seconds ya kalli Ammi yace "Tare mu ke da Haseenah za ku gaisa Ammi" Ammi tace "To ka shigo da ita nan mana" Mikewa yayi ya fita daga parlon, ba a dau lokaci ba sai gashi ya dawo tare da Haseenah dake sanye da dogon Hijab, Haseenah ta zauna kan carpet ta sunkuyar da kai tana murmushi, Ammi tace "Aa tashi ki hau kujera mana Haseenah" Haseenah ta girgiza kai tace "Aa nan yayi Ammi, ina wuni" Ammi tace "Lafiya lau Haseenah, ya gidan?" Haseenah tace "Alhmdlh Ammi" Haseenah ta kalli Mayraah tana murmushi tace "Gyaran gashi ake Mayraah" Mayraah ta ɗan kalleta tace "Ina wuni" Haseenah tace "Lafiya lau, ya gida" Ammi ta dau hulan Mayraah ta sa mata tace "Tafi ki kawo mata ruwa Mimi" Mikewa Mayraah tayi ta nufi kofa, Maheer ya bi ta da kallon gefen ido, can ya mike shi ma ya fita daga parlon, Ammi na kallon Haseenah tace "Fatan dai babu matsala Haseenah" Haseenah ta girgiza kai tace "Lafiya lau Ammi, ba komai" Ammi tace "To maa sha Allah, haka ake so" Haseenah ta kara jingina jikin kujera tana ɗan laluban kasan kujeran ta cikin hijab dinta taji ko ina is sealed, kallon agogo tayi sai kuma tace "Zan yi sallah Ammi" Ammi tace "Toh shiga daki Haseenah" Haseenah ta mike jakarta na makale cikin Hijab dinta, don dama Hijab din ba me hannu ta saka ba ta wuce dakin Ammi, Tana shiga dakin Maheer ya shigo parlon tare da Mama Ladi da tayi kasa da murya tana masa magana..... Manage with this, am not too fine today. MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 *Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/1, 5:06 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya zauna parlon bayan ya shigo yana kallon Ammi ganin bai ga Haseenah ba yace "Ta sauka downstairs ne?" Ammi tace "Aa sallah take a daki" mamaki yayi don yasan sun yi magrib before leaving home, a ransa ya fara tunanin to sallan me kuma take tunda dai ko isha ba a kira ba, bai dai ce komai ba yayi shiru, Mama Ladi na kallon Ammi tace "Uwar daƙan naki ta shiga tayi sallah duk girman parlon nan?" Ammi tayi kamar bata ji ta ba don tasan Mama Ladi da ɓarin zance, Mama Ladi tace "Ikon Allah, to bari in je mu gaisa a dakin" Dakin ta nufa ta bude kofa a hankali ta shiga, salati Mama Ladi ta saki tana gwale ido, Maheer da Ammi duk suka juya suna kallonta da sauri, Mama Ladi na tafe hannu tace "To dai wani wajen daban ta kalla take sallah ba gabas ba, ita bata tambaya idan abu ya sha mata kai??" Ammi tace "Ai bata sani bane Mama Ladi" Maheer ya mike yana kallon Ammi yace "Idan Mimi ta shigo ki ce ta shirya za mu wuce" Daga haka ya fita daga Parlon, Haseenah na murmushi bayan ta katse sallan ta juya tana kallon Mama Ladi, tsabar yanda gabanta ya fadi sai da hannunta dake cikin hijab ya fara rawa, cike da karfin hali tace "Ban sani ba Mama, ina ne gabas din?" Mama Ladi ta nuna mata sannan ta koma parlor, kusa da Ammi ta zauna murya can kasa tace "Amma a zancen gaskiya bai kamata ki bari ta shigar maki daki ba, da sai a mata shimfida a nan tayi sallahn, duka duka yaushe ma aka yi auren har aka gama sanin halinta zaki tura ta dakin ki wai tayi sallah, kawai ni dai jikina bai yarda da ita ba tun ranan da na fara ganinta lullube a mayafi...." Mikewa Ammi tayi don bata son zancen tace "Ina zuwa Mama Ladi" Daga nan ta fita daga parlon, Mama Ladi ta kyabe baki tace "Ai shikenan, tunda an maida ni gantalalliya" Bayan isha za su tafi Ammi ta bi Maheer har downstairs tana tsaye kusa da shi tace "Maheer pls ka dinga bin Mimi a hankali, ka ga she is just recovering kar ka sake birkitata don Allah, in dai Musharraf ne pls kar kace zaka hanata mu'amala da shi, after all he is still her lecturer and she is still in school, it's none of their fault that this happened, kuma don an rabu ai baza a ki zumunci ba ko" Maheer dai sauraronta kawai yake ya ma rasa me zai ce mata, Ammi tace "Magana nake maka kayi min shiru" A hankali yace "Toh Ammi" Har mota Mama Ladi ta rakasu tana washe baki bayan Maheer yayi mata alkawarin zuwa ya dauketa ranan juma'a, sai tayi sati a gidansa... Haseenah sai hira take jan Maheer da shi happily bayan sun bar gidan bini bini kuma sai ta kyalkyale da dariya, ita dai Mayraah na zaune bayan mota tana danna wayarta, Maheer ya kalli Haseenah don dariyar nata ya fara yawa yace "Farin cikin meye haka kike ne?" Tayi wani dariyar tace "Na zo na gaida Ammi na ji dadi mana, ai tamkar Mumy nake jin Ammi a raina" Bai sake ce mata komai ba har suka isa gida, yana parking ta sauka daga motar, Mayraah ma ta sauko zata dau warmers din abincin da suka taho da shi daga can gidan, Haseenah tace "Kawo daya in taya ki da shi" Ba Mayraah ba har shi Maheer sai da yayi mamaki, Mayraah ta bar mata daya, ita ta dau dayan, a haka suka nufi cikin gidan.... Mayraah na office din Dr Musharraf washegari wajen karfe goma tana masa bayanin wani course dinsu dake bata tough time using her understanding, ko handout babu a gabanta but the way she is explaining in details zaka ce takarda na gabanta, kallonta kawai yake yana mamakin irin brain dinta, she is really intelligent he must admit, kwankwasa office din aka yi duk suka juya, ya tambayi waye suka ji muryar mace, nan da nan Mayraah ta gane muryan, yayi mata izinin shigowa ta shigo, lokaci daya kamshin turarenta ya cika office din, yau ma sanye take da atamfa riga da skirt sai mayafinta dake rataye kanta, ta gaishesa da ladabi tana sinne kai, ya amsa yana kallonta yace "Morning Badiyyah, how are you" Tace "Fine sir... Dama sir wani tambayar zan maka ne if u are less busy" Dr Musharraf ya kalli Mayraah da ta hau danna wayarta without raising her head, sannan ya kalli Badiyyah yace "Ohk, can you come back in the next 30 minutes?" Tana gyada kai tace "Sure sir, thank you" Ya gyada mata kai yana kallonta yace "You are welcome" Juyawa tayi ta fita ta kullo office din tana murmushi, Dr Musharraf ya kalli Mayraah yace "Go on dear, ina jin ki" Ta kashe wayarta without looking at him tace "I think a nan na tsaya, sai na ci gaba da karatun before going further, let me go and continue now" Yace "Haba sauran ma zaki iya mana, kawai ki ci gaba nasan ai kin karanta course din during test" Ta dau handbag dinta tace "I am serious nan na tsaya, yanzu zanje in ci gaba" Yayi shiru yana kallonta, sai kuma yace "Ohk, idan kin ga Badiyyah around the premises ki ce ta shigo" Mikewa Mayraah tayi ba tare da ta kallesa ba tace "Ohk" Daga haka ta fita daga office din. Tana sauka downstairs taji gaba daya makarantar yayi mata zafi, ta kasa zama cikin department din har sai da ta fita waje, rasa inda ma zata je tayi, ta zauna karkashin wani bishiya, kawai sai taji hawaye ya cika idonta, nan da nan ta goge da sauri, ta ciro wayarta a jaka, tun da suka yi exchanging number da Maleeha basu taɓa waya ba sai chatting, yau kawai tayi dialing numberta yana fara ring ta daga, bayan sun gaisa Mayraah tace "Kin shiga school ne yau?" Maleeha tace "Aa ina gida wllh" A hankali Mayraah tace "Ohk, i tot u are in School" Maleeha tace "Why not come over to our house ba wani nisa fa daga school din" Mayraah tayi murmushi tace "Aa next time" Maleeha tace "No plss, don Allah ki zo tunda kinyi niyyar mu hadu" Shiru Mayraah tayi, Maleeha tace "Pls ki samu mai adaidaita sahu sai in gaya masa address, muna nan tudun yola fa, kinga ai ba nisa sosai" Mayraah tace "Ohk zan zo" Cikin minti sha biyar Mayraah ta isa gidansu Maleeha, Maleeha tayi farin cikin ganinta sosai, suka shiga parlonsu, Maleeha da mai aikinsu kadai ne a gidan duk parent dinta sun fita aiki, gisting with Maleeha made Mayraah felt relieved taji hankalinta ya kwanta sosai, tana gidan har aka yi azahar, bata yi niyyar cin abinci ba amma sai da Maleeha ta tursasa ta ta ci, suna cin abincin Mayraah tace "Plss Maleeha kar ki gaya ma Ya Usman na zo gidanku yau fa" Maleeha tayi shiru tana kallonta, sai kuma tayi murmushi tace "Ai muna dadewa bamu yi magana da shi ba" Mayraah ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace "How?" Maleeha tace "Nothing.... he is just a frnd fa, Colleague din yayana ne, so i knew him through my brother, once in a while yana zuwa gidanmu" Mayraah tace "Wai ba soyayya ku ke ba?" Maleeha tace "At all, wai don coincidentally ya kai min abinci school ranan tare da ke? Yayana fa na kira ranan suna office tare sai nayi requesting abincin sai yayana yace he is busy, shi kuma sai ya kawo min amma wllh ba soyayya muke ba, ko chatting muna jimawa bamu yi ba" Mayraah was speechless, A hankali Maleeha tace "But i must confess to u Mayraah, i love ur brother amma shi bai san ina yi ba" Mayraah tayi murmushi tana kallonta tace "Then why not shoot ur shot dear" Maleeha tace "Hmmm, i am afraid" a hankali Mayraah tace "U need not to be Maleeha, zan so ace kun yi aure da yayana" Maleeha ta kauda zancen kawai ta kawo wani hiran. Karfe biyar saura Mayraah ta isa gida bayan ta bar gidansu Maleeha, tun fitowarta daga gidan gaba daya mood dinta ya canza, sai a sannan ma ta kara tuna cewar Dr Musharraf bai kirata ba all through, tayi kokarin yakice damuwar nan a ranta, bata ga motar Maheer a parking space ba bayan ta isa gida, ta zauna compound for some minutes don kawai sai taji bata son shiga gidan, kasa ci gaba da zaman tayi saboda damuwar dake tare da ita, taji kawai kwanciya take so tayi, mikewa tayi duk da yanda gabanta ke faduwa ta karasa balcony tayi using spare key da Maheer ya bata ta bude kofar parlon, zaune ta tadda Haseenah da Badiyyah a parlon duk suka juya suna kallonta, ta sauke idonta kasa ta cire takalminta a bakin kofar parlon zata wuce dakinta Haseenah ta mike ta sha gabanta tana mata wani matsiyacin kallo tace "Ke gidan ubanki ne nan din da zaki shigo mana babu sallama sannan ki saka kai zaki wuce daki kamar kin ga marasu asali zaune a parlon? Are you mad?" Mayraah dai tayi shiru tana kallonta, Badiyyah tayi wani dariya ta mike tace "Kinsan duk inda mara galihu yake to yafi masu galihu iya shege banda haka mu sa'anninta ne da zata wuce bata gaishe mu ba? wallahi na rasa jin kan me yarinyar nan take har yanzu bayan tasan mummunan history dinta, da nine ita da nikab zan dinga yawo a gari on a serious note, duk department yanzu an san bata da asali kuma Shegiya ce" Juyawa Mayraah tayi da zuman fita ta bar masu parlon, Haseenah ta fizgota a fusace ta cakumi hijab dinta tace "Don ubanki mu zaki yi walk out on muna maki magana ko dai codeine kike sha ne??" Mayraah ta dinga kallonta babu ko kiftawa, can tace "Pls take ur hands off me" Bata rufe baki ba Badiyyah ta wanka mata mari me kyau a fuska, Haseenah ta kara mata a other cheek din tace "Ni kike gaya ma i should take my hands of u? How dare u talk to me like that?" Badiyyah ta cire dankwalinta ta daura a kugu ta finciko Mayraah daga wajen Haseenah tace "Dama har yau ban fanshe dukan da Usman yayi min a kanta ba, so this is the rightful time, kamar yanda ya dokeni ake ganin ya doki banza babu wanda ya dau mataki kema yau haka zan dokeki in doki banza babu abinda zai faru wallahi...." Mayraah na jin haka ta fara kokarin cire Hijab dinta don baxata bari haka kawai Badiyyah ta doketa ba, Badiyyah tayi using wannan opportunity din ta shakota da Hijab din ta fara dukanta ta ko ina tana cewa "Yau sai dai wata ba ke ba wallahi" Haseenah ta koma gefe tana kyalkyala dariya tana kallonsu tana hailing din Badiyyah, Sai da Mayraah ta san yanda tayi ta fizge Hijab din daga jikinta ta fara retaliating dukan da Badiyyah ke mata, nan suka fara kokuwa suna kai ma juna duka ta ko ina, Haseenah ta ga alamar at anytime Mayraah zata iya kai Badiyyah kasa ashe Badiyyar ba wani karfi ne da ita ba, kawai Haseenah ta shige kitchen da gudu ta kunna gas ta dau fry pan ta zuba manja ta daura kan wuta ta yanka albasa ciki sannan ta cika wutan gas din sai da taga ya fara hayaki sosai kitchen din ya turnuke ita kanta tari take sannan ta fito da fry pan din parlor ta nufo inda suka damben, Mayraah taji numfashinta ya fara tsarkewa ta fara struggling to breathe saboda manjan da Haseenah ta fito parlor da shi tana zagaya su, Badiyyar ma tari take amma hakan bai hanata dinga kai ma Mayraah duka ba har sae da ta kai ta kasa duk da yanda taga numfashinta na kokarin daukewa bata fasa dukanta ba, Haseenah na ganin haka ta ajiye fry pan din hannunta bayan kujera ta gudu daki ta dau wayarta tayi dialing number Maheer yana dagawa ta fashe da kuka tace "Baby kana ina ne don Allah? Ka bar ko me kake yi ka dawo gida ba lafiya" Maheer da fitowarsa kenan daga asibiti ya rage sautin karatun Alqur'ani da ke tashi a motarsa yace "Me ya faru???" Cikin Muryar kuka Haseenah tace "Wallahi ina zaune ko minti ashirin ba ayi ba Badiyyah ta zo wai shekaranjiya ta mance charger dinta zata dauka, to zata tafi kenan sae ga Mayraah ta dawo ita ma zata shigo parlor, kawai sai Mayraan ta bangajeta a bakin kofa, ni dai kawai sai gani nayi suna dambe, daga haka kuma numfashin Mayraah ya fara sama sama...." Katse wayar Maheer yayi, Haseenah ta koma parlor da sauri, zaro ido tayi tana kallon Badiyyah da ta mike tana huci tana kallon Mayraah dake kwance kasa kamar bata numfashi, Haseenah ta dafe kirji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kamar bata numfashi fa Badiyyah" Badiyyah ta dau Hijab din Mayraah da sauri ta saka don tuni shegun kayan jikinta suka yage kaca kaca, ta dau handbag dinta da wayarta da gudu ta bar gidan, rikicewa Haseenah tayi ta nufi windows din parlon da sauri ta bude labule don hayakin manjan ya fita, ta kure fanka ta buda Ac sannan ta dau fry pan din shima da gudu ta kai kitchen ta zubar da manjan a sink ta fara wanke wanke, gaba daya a tsorace take, ta kara dawowa parlor tana kallon Mayraah that is lying almost lifeless a kasa, jikinta na rawa ta kara daukan wayarta tayi dialing number Maheer amma bai daga ba, da gudu ta tafi kitchen ta debo ruwa ta fara zuba ma Mayraah tana jijjigata, gaba daya ta tsorata ba kadan ba, ta fita a guje tana kwala ma Musa mai gadi kira tana cewa "Musa zo ka duba min kaddai mutuwa tayi" Musa na shiga parlon shima ya kasa karasawa ya dinga "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una" Tuni Haseenah taji hanjin cikinta ya kada ta daura hannu a ka ko ina a jikinta na rawa tace "Ta mutu ne Musa??" Dai dai nan Maheer ya shigo parlon, shi kansa bai san ta yaya ma aka yi ya iso gidan ba, dukawa yayi inda Mayraah ke kwance ya dagota yana kiran sunanta cikin tashin hankali, ganin she is unresponsive ya fara mata Chest Compressions da sauri, daga bisanni ya bude bakinta ya hade da nasa giving her mouth to mouth resuscitation, duk da tashin hankalin da Haseenah ke ciki sai da ta hade rai tana kallonsu ganin abinda yake ma Mayraah, nan da nan ta nemi fargaban da take ciki ta rasa, ganin bazata iya ci gaba da kallonsu ba ta fito balcony ta tsaya fuskarta a daure. Haseenah ta fi minti biyar tsaye a balcony taki shiga parlon, sai a sannan kuma ta fara addu'ar Allah ya sa Mayraahn ma ta mutu kawai, tana tsaka da wannan tunanin ne Maheer ya fito dauke da Mayraah ya nufi motarsa dake waje da sauri, Haseenah ta wani kyabe baki ta bi Mayraah da kallo ganin idonta a rufe suke ta fara wishing dinta mutuwa, can dai kuma ta bi su har kofar gidan da sauri, cike da damuwa kamar gaske tana yarfe hannu tace "Maheer hope she is breathing now? Hope kayi reviving dinta?" Ko sauraronta Maheer bai yi ba ya shige driver seat ya tada motar ya bar unguwan with speed, wani murmushi Haseenah tayi ta juya ta koma ciki tana ci gaba da yi ma Mayraah fatan mutuwa. Maheer na zaune ward din da aka kwantar da Mayraah wajen karfe tara na dare, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, kana ganinsa zaka san he is not himself, ba a jima da cire mata oxygen ba don breathing din nata ya dawo normal, lkci lkci yake tashi ya dubata a kan gadon, Usman ne ya shigo ward din, direct gadon da Mayraah ke kwance ya nufa ya tsaya yana kallonta babu ko kiftawa, Kamar yanda bai ce ma Maheer komai ba haka Maheer ma bai ce masa komai ba, ko minti ashirin Maheer bai yi da kiransa ya sanar masa da abinda ke faruwa ba, don ko Ammi bai gaya ma ba har sannan, after standing for almost 5 minutes yana kallon Mayraah, Usman ya juya ya kalli Maheer for the first time yace "Me ya kai Badiyyah gidanka har tayi mata haka?" Maheer dai bai ce komai ba, juyawa Usman yayi ya nufi kofa ya fice daga ward din Maheer ya bi sa da kallo. Usman na fita ko minti sha biyar ba ayi ba Mayraah ta bude idonta, Maheer ya mike da sauri ya duka kusa da ita ya kamo hannunta yace "Mimi how are you feeling?" Hawaye ya gani a idonta, lkci daya jikinsa yayi sanyi ya ma rasa abinda zai ce mata.... Badiyyah na kwance Hajja na gasa mata hannu da ruwan zafi sai ihu take duk ta cika gidan tana cewa wayyo mamana kamar gaske don babu abinda ya samu hannun, dama tana dawowa gida ta sanar ma Hajja karya zalla wai Mayraah ta rufeta da duka a gidan Maheer da kyar Haseenah ta kwace ta, daga dai Mayraan taga wannan lecturer din da ya fasa aurenta yana kula ita Badiyyar a school, ta dai yi fabricating lies ba kadan ba tayi feeding din Hajja da shi, wanda nan da nan Hajja ta kira Ammi tana vibrate, abinda ta manta ne kawai bata fada a wayar ba don in ance ma ta tsine ma Ammi ba mamaki, Hajja ta tafi ta dafo ruwan zafi ta hau gasa ma Badiyyah hannunta da tace ya goce, a cikin ihun da take ne take cewa Hajja ita Bichi kawai zata tafi, Hajja tace "Ki tafi ina a haka? Ae wallahi in har Hajarah bata dau mataki a kan wannan abinda aka maki ba sai dai ta nemi wata uwar kuma ba ni ba, saboda ta nuna min iyakata shine ta sa Maheer ya tafi da yarinyar gidansa, to wllh yau za ayi ta ta kare, su zabi ko ni ko yarinyar nan, ae ita ke da iko da Maheer ba shi ke da iko da ita ba...." Hajja na kai wa nan ta mike tana huci ta shiga daki zata dauko man zafin da zata shafa ma Badiyyah amma ta neme sa ta rasa, fitowa tayi ta dau gyalenta tace "Bari in amso man zafi nan makota in dawo" Badiyyah na ganin fitar Hajja ta mike da sauri ta shige daki ta dau karamar jakarta ta saka kaya kala biyu da kayan shafe shafenta ta zuge jakar har wani rawa jikinta yake don ita gani ma take kamar za a kira ace Mayraah ta mutu, da ta tuna yanayin da ta bar ta sae gabanta ya fadi, tana fitowa parlor ta nufi kofa zata bude aka riga ta budewa, duk a tunaninta Hajja ce amma tana daga kai taga ba haka ba, a cikin minti biyar zuwa shidda ya gama mata abinda ya kawosa ya bar ta kasa ko kwakkwaran motsi bata yi tsabar duka, ya fice daga parlon.... Maheer na tsaye kan Mayraah dake zaune kan gado wajen karfe goma, tun dazu yake lallabata ta gaya masa menene ya faru dazu amma taki cewa komai, a haka Usman ya shigo ward din ya same su, Maheer ya dinga kallonsa don ko ba a gaya masa ba ya ma san daga inda yake, Usman ya nemi kujera ya zauna as if everything is okay, Maheer ya kalli Mayraah dake kallonsa, sai a sannan ta bude baki a hankali tace "Aunty Haseenah ce da sis Badiyyah" da wani expression Maheer ke kallonta, can dai yace "Haseenah?" Mayraah ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, juyawa yayi ya fita daga ward din.... Haseenah na zaune parlor tana cin Indomie din da ta dafa, zuwa yanzu har ta gaji da addu'ar Allah ya kashe Mayraah, banda ma ta gigice ai da taga ta shiga comma kamata yayi ace ta dau throw pillow ta danne mata fuska da shi da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, ta kyabe baki tana cin Indomienta da soyayyen kwai, tun da taga har goma da rabi tasan Maheer ba lallai ya dawo ba kenan tunda kanwar uwarsa na kwance asibiti, tana cikin tunanin nan ya bude kofar parlon ta daga kai da sauri, ganinsa ta mike ta nufesa da damuwa tace "Baby ya jikin nata, har na gaji da kiranka a waya baka dagawa, kaga tun dazu sai yanzu na iya dafa Indomie zan ci...." Takardan dake hannunsa ya jefa mata ya juya ya fice daga parlon, ta dinga kallon takardan gabanta na wani irin faduwa, da kyar ta durkusa ta dauka ta warware tana duba content din, wani ihu ta fasa ta bi sa a guje tana cewa "Maheer ka sakeni saki daya kamar yaya??? ban gane ba Maheer, ni din ka saka?" Amma tuni ya shige motarsa ya bar layin, shi dai mai gadi sai zare ido yake. MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 *Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/2, 6:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya kalli agogon wrist dinsa dake nuni da karfe sha dayan dare sannan ya kalli Usman dake danna wayarsa yace "It's getting late, baza ka tafi gida ba?" Usman ya daga kai ya kallesa yace "I should be asking you that kai da kake da iyali a gida" Maheer yayi shiru bai sake ce masa komai ba, lkci lkci yake kallon Mayraah da ta koma bacci tun dazu, ganin har sha biyu Maheer ya mike ya dau makullin motarsa without looking at Usman yace "Sai da safe" Usman yace "Allah ya tashe mu lafiya" Bai ce masa komai ba ya fice daga ward din ya kulle kofar... Through out night din Usman bai yi wani bacci ba, he kept a close eyes on Mayraah dake ta bacci just to make sure is okay, karfe biyar saura na asuba aka bude kofar ward din ya daga kai ya ga Maheer ya shigo, Ajiye ledan hannunsa me dauke da hijab din Mayraah da toothpaste and brush yayi, sannan ya ajiye takalmanta a kasa kusa da gadon ya juya ya fita daga ward din, sai da aka kira sallah Usman ya fita shi ma. Da safe karfe bakwai da rabi aka yi discharging din Mayraah daga asibitin, suna isa parking space da brothers din nata taga ko wannensu da motarsa a nan, tsaye tayi gefe daya not knowing motar wanda zata shiga cikin su, Usman dai ya bude motarsa ya shiga ya tada ya bar su tsaye wajen yayi wucewar sa from the hospital, Mayraah ta bi motarsa da kallo sannan ta bude motar Maheer a hankali ta shiga ta zauna. Kusan a tare suka isa gida sai dai Usman ya riga su shiga cikin gidan, Maheer na gaba tana biye da shi suka shiga gidan, zaune suka tadda Usman a parlorn downstairs tare da Mama Ladi dake cusa lafcecen kwai cikin biredi tana dannewa, ga cup din shayinta a gefe tana cewa "Wallahi yanzu haka wai suna asibiti, ko wani asibiti ne oho, wa ya sani ko gantalinta zata je mota ya kade ta, tun karfe hudun asuba Ammi ta bar gidan nan har yanzu babu ita babu alamarta inji Saliba me aikinku, ni dai nace sai na ci na koshi kafin inje ko ina babu ruwana da lalacewa inje yunwa yayi min lahani ayi min hisabi da yan hanjin cikina ranan gobe kiyama" Shigowan Maheer da Mayraah yasa ta daga kai tace "Yauwa Mashir wai me ke faruwa haka ne? Saliba tace min Ammi tun asuba ta bar gidan nan" Maheer ya karasa ya zauna kan kujera yace "Sabira dai ko, ina kwana..." Mayraah dai tafiya take a hankali ita ma tana kallon Mama Ladi, Mama Ladi ta yagi kwai da bread ta kai baki tana cewa "Ni jiya da wuri nayi bacci bayan na ci abinci ban san kan komai ba wllhi, ita Salibar ke gaya min an kai Badiyyah asibiti" Bata rufe baki ba Ammi ta shigo parlon rike da basket din flask da kayan shayi, Maheer da Usman suka juya suna kallonta haka ma Mayraah da ta nufeta zata amshi basket din hannunta tace "Sannu da zuwa Ammi" Ammi bata ce mata komai ba kuma bata bata basket din hannunta ba ta wuceta ta karasa cikin parlon tana kallon Maheer da Usman tace "Ina jiranku a sama...." Daga haka ta ajiye kayan hannunta ta wuce sama, duk suka bi ta da kallo, har Mayraah da ke tsaye inda Ammi ta bar ta, Mama Ladi na kora bread dinta da shayi tace "Ko kudi za a harhada na trintment din Badiyyar tunda dai duk mun san dangin ubanta matsiyata ne, tun tana karamarta Ammi ke mata komai sai Mamuda da Hajja da ni, sai kuma ku da ku ka kawo karfi yanzu, ku dai je ku ji, iyaka ku bada dubu daddaya ta rabaku da kowa lafiya tunda ba wani ya aiketa ba...." Usman ya fara mikewa ya wuce sama, Maheer ya tashi ya bi bayansa shi ma, Mayraah dai ta kasa karasawa cikin parlon ta zauna, Mama Ladi ta mike ta dau shayinta da bread tace "To ya ma za a bar ni a nan sai kace wata bare..." Sai kuma ta kalli Mayraah tace "Zo ki dau min shayin nan mu tafi sama kar garin hawa benen nan in barar in shiga uku ance milo ya kare, duk an wani watse a bar mu kamar mun ci mutum" Mayraah da gaba daya jikinta yayi sanyi ta rasa dalilin hakan, ta karasa gun Mama Ladi ta dau mata shayin suka wuce sama a tare. Usman na shiga parlon Ammi ya ga Haseenah zaune kan kujera da hijab dinta har kasa sae counter din carbi a hannunta, duk da yayi mamakin ganinta ya gaisheta a takaice ya shiga dakin Ammi, Maheer ya shigo Parlon few seconds later, he was very very surprise to see Haseenah sitted in Ammi's parlor, ya dinga kallonta, suna hada ido ta kauda kanta ta wani daure fuska tana daddanna counter din hannunta, lkci daya yaji wani mugun ɓaci rai ya zo masa, but ya dai yi calming kansa down bai ce mata komai ba ya wuce dakin Ammi, tsaye ya ga Ammi bakin window duk tana jiran su, kallo daya Usman yayi mata bai ma karasa can cikin dakin ba ya tsaya daga gefen kofa cause her facial expression isn't giving, Maheer ne yayi karfin halin karasawa ciki yana kallonta shi ma, daga shi har Usman babu wanda ya iya bude baki ya gaisheta don basu ma ga fuskar yin haka ba, Mama Ladi ta shigo parlon Ammi Mayraah na biye da ita, buda baki tayi ta koma baya da sauri ganin Haseenah, cike da mamaki tace "Ke kuma daga ina matar nan? Ko dai ba da ke aka tafi jiya ba?? Ni fa na raka ku har mota, garin yaya haka na ganki a nan?" Haseenah dai ta sunkuyar da kanta tace "Ina kwana Mama" Mama Ladi ta nufi dakin Ammi tace "Yau ni naga ikon Allah" Mayraah bata bari sun hada ido da Haseenah ba ta ajiye Shayin hannunta a kasa sannan ta zauna kan carpet din parlon, tun da Haseenah tayi mata wani matsiyacin kallo ta kyabe baki ta kauda kai tana girgiza kafa.... Maheer yayi gathering courage yana kallon Ammi yace "Ina kwana Ammi" A fusace Ammi tace "Ban kwana ba, nace ban kwana ba..." Kallonta kawai Maheer yake yayi shiru, Ammi na nunasa cikin bacin rai tace "Before going into my main point ina son ka maida matar ka immediately first..." Maheer ya sunkuyar da kansa, Ammi ta masa tsawa tace "Are you deaf, ko baka ji na ne?" Ya dago kai a hankali yace "I have done that" Mama Ladi da ta shigo dakin ta buda baki tace "Wai me yake faruwa ne kike daga murya haka? Me ke faruwa ni Ladiyo? Wace matar za a mayar?" Ammi bata ko kalleta ba tana kallon Maheer tana gyada kai tace "Sai yanzu na fahimci inda Hajja ta dosa all this while, sai yanzu na gane abinda take son ta fahimtar da ni na kasa ganewa, i now fully understand Mimi is nothing but a nuisance in our midst now, she is beginning to cause nothing but chaos in this family, kai ka saki matarka da ko sati uku ba kuyi da aure ba duk a saboda ita, shi kuma ɗan uwanka ya sake komawa for the second time yayi ma Badiyyah dukan tsiya duk a kanta ba tare da yayi binciken abinda ya faru ba, a saboda yarinyar nan har yau mahaifiyata bata ɗaga wayata, ko naje inda take babu maganar arziki tsakanina da ita all because of Mimi, is that how she wants to pay us by destroying us? Toh all this is going to end now" Cikin daga murya Ammi tace "Maheer from today henceforth she is not staying in ur house any more, bazata sake zama a gidanka ba nace...." Maheer couldn't believe this is really coming out from Ammi's mouth, ji yayi kansa ya wani sara masa yana kallonta cike da karfin hali yace "Where will she stay then?" A takaice Ammi tace "I don't know, and I don't care Maheer, idan ma kai da Usman za ku dawo hankalinku ku dawo, baku hada komai da ita ba, i repeat babu abinda ku ka hada da ita in any way, she is not ur blood, and because of her bazan zuba ido zumunci ya lalace ba, Ita Badiyyar da ku ka mayar makiyiyarku ita ce dolen ku duk inda za a je kuwa, ita ce er uwarku ta jini, sannan baza ka taɓa hada matar da kake aure da ita ba, matar ita ce dolen ka ba ita ba" Usman ya dinga kallon Ammi da mamaki babu ko kiftawa, jin maganganun nata yake kamar a mafarki, Mama Ladi dai sai zazzare ido take duk da turanci yafi yawa a maganganun amma sarai ta fahimci komai, salati ta saki tayi zaman dirshan a kasa tana girgiza kai tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Hajaru yau kece kike wannan munanan kalaman akan Mera? Me suka baki kika sha a asibitin Hajaru, yau mun shiga uku mun lalace, ina ake son Marainiyar ta sa kanta taji dadi kenan?" Kawai sai ta fashe da kuka wiwi, Maheer dake ta kallon Ammi ganin zata fita ta bar masu dakin, a hankali yace "Ohk then, tunda kince babu abinda muka hada da ita, sannan ita din ba jininmu bace yanzu na yarda kuma na amince da hakan, as at before i was still doubting that, don bamu ji kin gaya mana hakan da bakin ki ba duk abubuwan da suka faru, it was hard for us to assimilate Mimi isn't our blood all this while, but after saying this today naji na yarda da hakan har cikin raina, saboda haka ni zan auri Mimi in samar mata gidan da zata zauna to bring an end to all this...." Juyawa Ammi tayi da sauri tana kallonsa kamar yanda Usman ma ya daga kai yana kallonsa, Ammi na kallonsa da kyau tayi wani murmushi tace "Ba da yawuna ba, in kuma gaban kanka zaka yi i assure u baxa ka taɓa ganin dai dai ba..." Juyawa Usman yayi ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Mayraah na zaune parlor kanta a kasa duk tana jin abubuwan da ake yi a dakin, banda murmushi babu abinda Haseenah take tana kallon Mayraah kasa kasa dom everything was clear kamar a gabansu ake yi, Mama Ladi dake rusa kuka ta mike tana kallon Maheer tace "Kawai ta hado kayanta mu tafi karaye Mashir, dama ka taɓa ganin inda barewa tayi gudu ɗan ta yayi rarrafe??" Bata jira amsarsa ba ta fice daga dakin ta koma parlor tana kallon Mayraah tace "Tashi maza ki tattaro kayanki" Sai a sannan Mayraah ta daga kai tana kallon Mama Ladi da manyan idanuwanta, cikin daga murya Mama Ladi tace "Baza ki tashi ba sai kin ga tana watsar maki da kayanki titi" Mayraah ta mike tsaye, Mama Ladi tace "Fita mu je, ai naga akwai sauran kayanki a gidan nan tattaro su gaba daya kawai ki zuba a akwatina" bin bayan Mama Ladi Mayraah tayi suka fita daga parlon zuwa dakinta, Mama Ladi ta bude inda sauran kayan Mayraah suke ta dinga kwasowa tana zubawa a akwatinta, ita dai Mayraah na tsaye tana kallonta kamar statue, Maheer ya shigo dakin looking so weakened and confused, Mama Ladi ta dago bayan ta gama cusa kayan a akwatin tana kallon Mayraah tace "Shikenan abinda zaki bukata kin wani tsaya kamar gunki kina kallona, ko baki ji abinda ke faruwa a gidan bane" Mayraah dai ta kasa cewa komai sai kallonta take, it seems like it's taking her too long to absorb the reality of what is happening, Maheer na kallon Mama Ladi a hankali yace "Tana da jarabawan da zata yi Mama" Yana fadin haka ya karasa ya kama hannun Mayraah suka fita daga dakin kawai, ita dai bin sa kawai take har suka sauka downstairs, Balcony ya fita da ita ya sa ta zauna, shi ma ya zauna ya rike kansa da yayi masa nauyi, gaba daya tunaninsa ya tsaya cak ganin abubuwan yake kamar a mafarki ya rasa wani tunanin zai yi, ita dai Mayraah kallonsa kawai take, can ya dago ya kalleta ganin yanda take kallonsa ya kama hannunta yace "Mimi" sauke idonta tayi ta amsa, yaji wani tausayinta har cikin ransa, seeing her dry eyes ne ya kara daga masa hankali don yasan taji duk furucin Ammi tunda kofar dakin a bude yake ya kuma san ita din me saurin kuka ce amma ynxu bbu ko digon hawayen a idonta.... Haseenah bata taɓa shiga farin ciki irin na yau ba ko aurenta da Maheer bata ji irin wnn mugun farin cikin ba, gaba daya ta kasa tsaye ta kasa zaune a part din Ammi don murna, babu kowa sai ita kadai a part din, aka bude kofar Parlon juyawa tayi da sauri ganin Abba ta sauko kasa tana sinne kai tace "Ina kwana Abba" a takaice ya amsa ya nufi dakin Ammi ya bude yaga babu kowa a ciki, fitowa yayi daga part din ya sauko downstairs ya tadda Ammi zaune a parlon fuskarta a murtuke, Abba na nunata da yatsa cikin bacin rai yace "Ke Hajarah, naga kamar baku san kawaici ba daga ke har mutanen ki, all this while ina ta bin ku a yanda ku ke so don kawai a zauna lafiya, to kun kai ni bango kuma yanzu i am not going to tolerate this nonsense any more, babu wanda ya isa ya gaya min yanda zanyi ko yanda bazan yi ba a gidana, it's my house not anybody's...." Ammi ta dakatar da shi tace "Ohh zagina da iyayena zaka yi akan Mayraah? No tell me zagina da iyayena zaka yi? Naga dai ba wani ya bani shawaran ince zan raini yarinyar nan har zuwa yau ba ko, ba kuma wani ya tursasa ni in riketa ba, sannan kai har kana da bakin magana yanzu? ka mance dauki ba dadin da muka yi da kai a kanta tana jaririya?" Abba yace "Duk wannan ke ta shafa, kuma baki isa saboda ke ko wani naki Mayraah taki zaman gidan nan ba, she remains in this house tunda ba gidan wani bane gidana ne, take it or leave it Hajarah babu inda Mayraah zata je...." Cikin tsawa Abba ya kare maganar, mikewa Ammi tayi tana wani murmushi tana kallonsa tace "Ohh i see, sai ka zabi ko ni ko ita, kuma tunda har aka billo min ta haka wllh wllh bazan ci gaba da zama da ita ba ko me zai faru kuwa, ai da can naga ba wani ya sa na zauna da ita ba, ynzun ma babu wanda zae sa ni in zauna da ita, don haka daga kai har 'ya yan naka da suka kai maka karata sai ku hadu ku zauna da Mayraah, su kuma su nemi wata uwar ba ni ba wllh" Daga haka ta juya fuuu ta wuce sama, Mama Ladi da ta sako da sauri jin hayaniya yayi yawa ta fashe da kuka tana kallon Abba bayan Ammi ta wuce sama tace "Kawai ka korata gida gun uwarta dake zugata su je can su karata Mamuda, ni dai ka gan ni nan babu ruwana bana goyon bayan rashin gaskiya tunda uwata ta haifeni wallahi" Abba da ransa yayi mugun baci ya juya kawai ya bar parlon, Maheer na jin duk yanda Abba suka yi da Ammi, likewise Mayraah dake gefensa, he never saw this coming, bai taɓa tunanin things will turn out this way ba, yasan Usman ne ya je ya samu Abba a part dinsa, ya kalli Mayraah dake ta kallon gate babu ko kiftawa, kawai ya jawota jikinsa, gathering every courage yace "Komai zai wuce Mimi" ta daga kai ta kallesa, sai a sannan ya ga hawaye a idonta, ya rungumeta lkci daya idanunsa suka kada shi ma, yana jin hawayenta na sauka jikinsa, cikin rawan murya yaji tace "Ina zan je yaya?" _If you are reading this book without payment u owe me 500 till forever_ MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 *Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/3, 9:26 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer was speechless and so weak, ya ma rasa me zai ce mata, lumshe ido yayi yana jin kukan nata har ransa, sai dai bai hanata kukan ba cause he want her to feel relieve ko yaya ne, sun fi minti goma zaune a wajen, ya dago kanta yana kallonta a hankali yace "Kiyi hakuri Mimi, komai zai wuce, u still remain our lil sis, we still remain together, babu inda za ki je, i know Ammi is not okay, bata san ta fadi duk maganganun nan ba" Kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta tana kallonsa, ya sa hannu ya share mata hawayen cikin sanyin murya yace "I assure you, that's not Ammi" ita dai kawai ta gyada masa kai, ya dagata suka tashi a wajen suka koma ciki, babu kowa Parlon ya wuce sama da ita zuwa dakinta, Mama Ladi na zaune tana tura bread dinta da kwai da sauri ga akwatinta a kusa da ita, tana ganin Maheer tace "Ina gama karyawa ka kai ni tasha Mashir, bazan iya ci gaba da zama ina kallon rashin imanin nan dake wakana ba, zan je ina da wani Malami a karaye, shi yake bani kaikayi koma kan mashekiya da dai itatuwan tsari, shi sa ka gan ni fess da ni da lafiyata, duk wanda yayi min mugun abu kansa yake komawa wllhi, to zan je in sanar masa abinda ke faruwa sannan ya taimaka yaga me ya samu er uwata Hajja, wa ya jefeta take abubuwa haka? don in na bar ta a haka wallahi wuta Allah zai ajiyeta, gwara in je tun wuri in nemo mata taimako, kai kana jin maganganun Ammi kasan zugota aka yi ba yin kanta ba, yaushe har bakinta ya bude zata yi wannan tabargazan, Aa wllh zugota aka yi kuma ba kowa zai zugota ba sai Hajja da tsinanniyar jikarta wanda sai ta kusa ajalinta, ke Hajja tsofe tsofe dake baza ki koma ga Allah ba sai kawai tayi ta hada bamm ke da jikarki Badiyya?? Ai ko zanje ko nawa ne in bada in ceto ta daga shiga wuta, ai ba kyau ace ina aljanna ita tana wuta, er uwata ce uwar mu daya ubanmu daya" Maheer dai bai ce ma Mama Ladi komai ba ya zaunar da Mayraah gefen gado yana kallonta cikin sanyin murya yace "Ki jira ni a nan" Ta gyada masa kai tana kallonsa ya juya ya fita, makullin kofar ya cire bayan ya fita ya kulle kofar ta waje, Mama Ladi ta rushe da kuka ta ajiye bread din hannunta tace "Toh nace masa mu tafi karayen dake yace zaki yi jarabawa, to shi jarabawan baza a iya kai maki karayen kiyi ba?" Ita dai Mayraah kallonta kawai take babu ko kiftawa amma bata ma san me take cewa ba, Mama Ladi tace "Toh ma jarabawan banza ba sai da kwanciyar hankali ake jarabawa ba, su ajiye maki duk randa kika dawo a baki kiyi mana, bari kawai in gama karyawa ya bamu kudin mota mu yi wucewar mu, ranan laraba da juma'a kadai Malamin ke shigowa karaye yafi zama a Maradi" Maheer na zaune parlon Abba tare da Usman ta dalilin kiransu da Abban yayi, they've never seen their father this angry kamar ba shi ba, he was really vibrating and raising his voice kamar zai ari baki, rai bace ya ci gaba yana cewa "In ma ta zauna gidan nan da Mayraah ko ta tattara ta tafi duk inda zata tafi i don't care, bata isa tace Mayraah bazata zauna a gidana ba, i am not tolerating that nonsense again, all this while na kauda kai nayi hakuri na bi su a yanda suke so, ba wai don ban san abinda nake bane, yanzu kuma babu wanda ya isa ya canza min tsarin gidana, Mayraah will keep on staying as comfortable as she was before in this house, babu wani wanda ya isa ya canza haka, duk wanda bazai zauna ba ya bar gidan" Daga Maheer har Usman were quiet, bude kofar parlon aka yi Ammi ta shigo, duk tana jin abinda Abba ke cewa tun daga part dinta cause he was raising his voice so high, tayi wani murmushi tana kallonsa da kyau tace "Ai ba sai ka zaunar da su kana ci min mutunci a gabansu akan Mayraah ba Mahmud, ga ku ga ta ai kai da 'ya yan ka sai ku zauna da ita ni kuma zan bar maku gidan" Abba yace "Ai ban hanaki tafiya ba, so ki tafi duk inda zaki, sai yanzu na kara fahimtar ke da iyayenki ba kwa son gaskiya, i repeat in dai kan Mayraah ce ki tafi duk inda zaki, she remains in this house tunda gidana ne nan din ba gidan uban kowa ba" Juyawa Ammi tayi ta fice daga parlon, Maheer ya ji kansa ya sara, Usman was also short of words, Abba na kallon Maheer strictly yace "Duk kayan Mayraah da ka kai gidanka ka kwaso ka dawo mata da shi gidan nan" Maheer yayi kasa da murya a hankali yace "Abba ku yi hakuri abun duk bai kai haka ba, yanzu Mayraah tana bukatar nutsuwa sosai, her final exams is in just 2 weeks time, i think it will be better ta zauna hostel don tayi concentrating...." Shiru yayi don gaba daya ya ma rasa yanda zai yi composing word din yanda zai yi making sense a kunnen Abba, bazai so ace Ammi ta bar gidan akan Mayraah ba, the issue is just taking another dimension, Abba yace "A gidan nan nace zata zauna ba hostel ba, all this years ai ba a hostel take karatun ba...." Usman ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yana kallon Abba yace "Abba wannan final exams ne, she needs all the concentration, with what is happening now bazata samu nutsuwa ba, plss ka bari ta zauna hostel har after the exams, it's just for 3 week" Usman ya fadi haka ne shi ma saboda exactly tunanin da Maheer yayi shi ma yayi, it won't make sense Ammi ta tafi saboda Mayraah, Strictly Abba yace "Nace baxata zauna a hostel ba a gidan nan zata xauna tayi exams dinta" Duk suka yi shiru suna kallonsa, ya juya yayi wucewarsa daki, mikewa Usman yayi ya fita daga parlon, Maheer ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, gaba daya ya rasa tunanin me zai yi. A hankali Maheer ya bude kofar dakin Mayraah ya shiga, tsaye ya ganta bakin kofar dakin, Mama Ladi ta mike tace "Kai ya zaka kulle mu a daki kamar barayi kayi tafiyarka, sannan anya baxa ka duba ƙwaƙwalwar yarinyar nan ba tunda dae naji ance kai likita ne, tun daxu fa nake mata magana yanda kasan da bebiye nake, ni wallahi ta ban tsoro kawai dakewa nayi" Maheer ya tafi dakinsa da Mayraah, after letting her sit, ya duka gabanta a hankali yace "Kina ji na Mimi" kallonsa kawai take, yace "Do you have any frnd or Coursemate dake hostel?" Mayraah tayi shiru tana kallonsa, yace "Say something Mimi" Ta gyada masa kai, mikewa yayi yace "Abba zae maki magana, tell him hostel kike so ki zauna for ur final exams" Daga haka ya tafi Parlon Abba tare da ita.... A tare Maheer da Usman ke kokarin su yi convincing Abba to let Mayraah be in hostel har bayan exams dinta, Abba ya nuna sam bai amince ta je wani hostel ba, ita dae Mayraah na zaune parlon duk tana jin su, Abba yace "Kuma kada wanda ya sake kawo min maganar hostel" Sae a sannan Mayraah ta daga kai tana kallon Abba cikin sanyin murya tace "Abba dama a can nake so in zauna inyi exams din, many of my Coursemates are also coming back to hostel till the final exams, i will concentrate more" A ranan da yamma Maheer ya maida Mayraah hostel nan kusa da makarantarsu bayan yaga Abba ya fita daga gidan don Abba na iya cewa sae ana gobe exams, shi kuma tun da Ammi ta fita gidan da safe hankalinsa yayi mugun tashi kwata kwata bai so abun ya kai haka ba, tare Mayraah zata zauna da kanwar wata colleague dinsa wajen aiki, ita yarinyar tana level 200..... ya sauko mata da duk kayanta da zata bukata tana kai wa cikin dakin sabuwar roommate din nata tana ajiyewa, all this while Maheer na tsaye jikin mota yana bin ta da kallo, kawai tausayinta yake ji har cikin ransa, he wish he can't take away all this sad moment for her, handbag dinta ta dauka lastly a motarsa, a hankali yace "Mimi" bata yarda ta kallesa ba, nan da nan yayi noticing hawayen dake makale idonta, dawo da ita yyi jikin motar yace "Mimi i trust baxa ki ce zaki je ko ina ba shi yasa na kawo ki nan, i trust you Mimi, i know 24/7 karatun exams dinki za ki yi a nan because ur 5 years over everything for now, pls Mimi do not betray my trust, kar ki bari zuciyarki yayi leading dinki zuwa yin abinda bai kamata ba, Ammi and Abba are still ur parent, we are ur brothers, in sha Allah all this will come to pass very soon, ki cire komai a zuciyarki kiyi concentrating kan exams dinki to make Abba and Ammi proud, kinga da kyar muka shawo kan Abba ya yarda ki dawo hostel idan wani abu ya sameki a nan mu Abba zae yi blaming, mu kuma muna son ki maida hankali ne yasa muka ce ki dawo nan, duk sanda kike son wani abu just give me a call.... Usman is on his way now with ur foodstuffs" ko rufe baki bai yi ba sae ga motar Usman, bayan yayi parking Maheer ya nufi motar tasa, ita dae tana tsaye tana kallonsu, babu abinda Usman bai siya mata ba na abinci barin wanda yasan ta fi so irin su junk food da drink, suna tsaye duk ta shiga da su cikin hostel din, Usman na kallonta bayan ta dawo yace "Meye babu a kayan?" Ta girgiza kai tace "Ba komai" yace "Ohk, if u need anything ki kirani" Ta gyada masa kai tace "Nagode" motarsa ya koma ya bar su tsaye da Maheer ya wuce, Maheer bai bar wajen ba sai kusan karfe shidda. Gidan Hajja ya nufa, bayan yayi parking a kofar gida sae da yayi sallan magrib a masallacin dake layin sannan ya shiga cikin gidan, ya kai minti daya tsaye bakin kofar Parlon don bai ma san me zai tarar ba idan ya shiga, can dai daga karshe ya bude kofar ya shiga da sallama, Hajja na zaune parlon ga Badiyyah kwance a gefenta tana mata fiffita tana jero mata sannu, Haseenah ma na zaune parlon tana zuba madara a cup zata hada shayi, kallon Ammi dake zaune kan darduma ta idar da sallah yayi, tana ganinsa kuwa ta tamke fuska, ya zauna kan kujera yana kallon Hajja a hankali yace "Ina yini Hajja?" A takaice Hajja tace "Lafiya lau" yace "Ya mai jikin?" Hajja tayi banza da shi, Haseenah ta kallesa tace "Ina yini" Yace "Lafiya" Ya sake kallon Ammi cikin sanyin murya yace "Ina yini Ammi?" Mikewa tayi ta shige dakin Hajja ta kulle kofa, Hajja dae ta kyabe baki ta ci gaba da yi ma Badiyyah fifita don ba wuta a gidan, Haseenah ta mika ma Hajja shayin da ta hada cikin ladabi tace "Bari in je inyi sallah Hajja" Hajja tace "Toh Allah maki albarka er nan" Haseenah ta ɗan yi murmushi tace "Ameen Hajja" Daga haka ta mike ta shiga dakin Badiyyah ta kulle kofa, Maheer yayi kasa da murya yace "Don Allah Hajja ku yi hakuri da abubuwan nan da suka faru, wannan duk sharrin shaidan ne ba wani abu ba" a fusace Hajja tace "Ae shaidaniyar na nan tare da ku, babu wani shaidan sae ita, daga abun arziki sae ya juye ya zama na tsiya? Kai tun da kake ka taɓa ganin ubanka da uwarka sun samu sabani har ya daga mata murya? To kaga kuwa ae shaidaniya ce yarinyar nan, a kanta kai har kasan ka saki matar ka ta sunna wanda duka duka yau sati nawa da auren, dubi er uwarka ta jini halin da take ciki duk a kanta, to wallahi da mun san haka gari zae waye in na bari Ammi ta riketa shegiya nake, da mutum na sanin gaibu wllh da babu abinda zae sa mu fara shigo da ita zuri'ar mu...." Maheer felt so bad akan accusation din da Hajja ke ma Mayraah, don nan da nan yaji zuciyarsa na tafarfasa, amma dae ya dake yace "Abinda zae faru ya riga ya faru Hajja, kuma Mimi bata ma gidan yanzu haka, tunda Abba ya ga ran Ammi ya ɓaci ya sa aka kai ta gidan kawu Lawali, so Ammi zata iya komawa gida yanzu don Allah ki bata hakuri Hajja" Hajja tace "Ba ruwana wallahi, ae rufe ido yayi ya ci mata mutunci a gaban surkarta duk akan yarinyar da muka tsinta da kyakkyawar manufa, da kuma yake zakalkalewa kan Mayraan ance maku yyi niyyar riketa ne da farko?? Har da ku a kwayewa uwar ku baya a kan wannan yarinyar?" Maheer yace "Hajja wannan duk ya wuce, ki ba Ammi hakuri ta koma gida don Allah" Hajja tace "Ni nayi mata laifi da zan bata hakuri?" Shiru yayi bai ce komai ba, can ya mike ya tafi dakin da Ammi ta shiga yaji ta sa makulli, dawowa parlon yayi duk jikinsa yayi sanyi, ya zauna yana kallon Hajja, Hajja tace "Babu abinda zaka gaya mata yanzu da zata saurareka, kawai ka dau matarka ku tafi gida sai da safe" a hankali Maheer yace "Amma don Allah ki kara bata hakuri, gobe in sha Allah zan zo da safe" Hajja tace "Dauki matarka nace ku tafi sai da safe, ka bar mu muji da abinda ya tsaya mana a rai" Tana fadin haka ta mike ta je kira masa Haseenah da ta shige daki, suna fitowa parlorn Maheer ya tashi ya isa inda Badiyya take kwance yana kallonta yace "Ya jikin naki?" Pretending tayi kamar tana bacci, ya kalli Hajja yace "Ko za mu tafi gidana tare da ita saboda in dubata har ta samu sauki?" Haseenah ta juya ta kallesa da sauri, Hajja tace "Taje tayi me a gidanka Maheer? Ba zuwa gidan naka da tayi bane yasa aka kusa illata min ita? Aa babu inda zata je nasan ko hada baki ku ka yi da ɗan iskan kanin naka ku karasa kasheta??" Yayi kasa da murya yace "Ki bar wannan zancen don Allah Hajja, wannan ai saboda lafiyarta yasa nace mu je da ita ba wani abu ba" Badiyyah dake sauraronsu, ta mike zaune tana wani mitsike ido tace "Zan je" Hajja tace "Zaki iya taka kafafuwan ne da kike cewa za ki je?" Tace "Zan daure" Ita duk saboda yin waya da Malamin da Haseenah ta bata numbersa yasa take so ta bar gidan, don tasan definitely Ammi a dakinta zata kwanta bazata ce zata kwanta dakin Hajja ba, shkkn yanzu kuma bata da privacy tunda Ammi na gidan ba damar waya, ga shi daki biyu kadai ne a gidan, sannan tun jiya da daddare yace ta kirasa kafin abun nan ya faru har yau kuma bata kira ba babu privacy duk da yanda take fama da kanta, don duk jikinta ciwo yake mata ba na wasa ba, ga kafafuwanta don dai likitoci sun ce ba karaya bane amma ita sai take jin kamar sun karye ne kawai, hannunta daya ma mugun ciwo yake mata aka ce targade ne shine aka gyara mata a asibitin ko amfani bata iya yi da hannun har sannan, tana kallon Hajja da kyar tace "Hajja ki sa min kayana kala uku a jaka" Hajja tace "Ba fa inda za ki je nace su je su karasa ki, ke wai baki da zuciya ne, ko da kudi idan aka ce ki koma gidan Maheer sai ki koma?" Badiyyah ta wani hade rai tace "To wai ke ina ruwanki Hajja, in zaki hada min kayan ki hada in kuma baza ki hada ba in tashi inyi da kaina" Haseenah dai na tsaye taki cewa komai, Hajja tace "Toh, Allah dai ya ga na fita hakkin ki, dama so nayi ki zauna nan in maki duk abinda ya kamata" Daga haka Hajja ta mike ta shiga dakin Badiyyah, ba a dau lokaci ba ta fito da jakar kayanta ya hada mata kala uku, Maheer ya amsa yana kallon Badiyyah yace "Zaki iya tashi ai" Da kyar ta mike tsaye tana dingisa kafafuwanta da suke mata azababben ciwo, ya kama hannunta suka nufi kofa yace "Sai da safe Hajja" Hajja dai taki cewa komai don har ranta bata so Badiyyah ta sake komawa gidan ba to amma ya zata mata tunda taki ji, can ciki Haseenah tayi ma Hajja sai da safe ta bi bayansu fuskarta babu walwala, back seat ya bude ma Badiyyah ta shiga da kyar da kyar tana washh washh yana mata sannu, ya ajiye jakar kayanta a booth, Haseenah ta bude gaba ta shiga ta zauna, shi ma ya shiga motar suka bar anguwan, sai da suka yi nisa yace "Me za ki ci Badiyyah?" Badiyyah da ta kwanta bayan motar kamar er yarinya ta marairaice tace "Ai bana iya cin abinci" Yace "Toh bari a siya maki kaza da yoghurt, kilan appetite dinki ya dawo" Haseenah ta juya ta ɗan kallesa, ya samu inda zai siya ma Badiyyah abinda yace, yayi parking sannan ya sauka daga motar, bayan wani lokaci sai gashi ya dawo da leda daya tal, ya bude back seat ya ajiye ma Badiyyah, nan da nan kamshin kazar ta gauraye mota, ya koma driver seat ya tada motar suka kama hanyar gida, suna isa gida a kofar gida yayi parking, duk tunanin Haseenah zai koma ne su ma ya siyo masu kazar, ya bude ma Badiyyah back seat ta lallaba ta sauko tana rike da ledan kazarta da yoghurt, ya ciro jakanta a booth, all this while ko kallo Haseenah dake ta bin su da ido bata ishesa ba, a haka dai suka shiga cikin gidan Haseenah na tafiya a hankali tana biye da su fuskarta a daure, ya bude ma Badiyyah wani spare room ba wanda Mayraah ta zauna ba, fuuu Haseenah ta shige dakinta ta zauna gefen gado ta cire hijab dinta don wani mugun zafi ta dinga ji, can dai ta kasa ci gaba da zama ta fito corridor ta gansa ya dauko plate da cup ya shiga dakin da Badiyyah take, da ido ta bi sa har ya fito daga dakin ya fice daga gidan gaba daya, mota ya shiga ya kama hanyar inda Mayraah take don tun dazu hankalinsa gaba daya na kanta, kaza ya siya mata da drink din da yasan tafi so me sanyi, yana isa ya tadda motar Usman a kofar gate din hostel din, Mayraah dake zaune kan wani dakali tare da Usman dake danna wayarsa ta bi motar Maheer da kallo, tun da Usman ya zo after magrib basu yi maganar da ya wuce na minti biyu ba ya fara danna waya, lkci lkci dai zai daga kai ya kalleta, ita dai kawai tana zaune gefensa tayi nisa tunanin da take har ta hango motar Maheer. MAYRAAH is 500 Via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 [7/4, 7:37 PM] Khaleesat Haiydar💖: Usman ya mike bayan Maheer yayi parking, ya kalli Mayraah yace "Sae da safe" Daga haka ya nufi inda motarsa take, ita dae kawai ta bi sa da kallo, Maheer bai sauko ba har sae da yaga Usman ya tafi sannan ya bude motarsa ya fito, ya nufeta ya zauna inda Usman ya tashi yace "Hope kin ci abinci" ta kallesa ta gaishesa, ya amsa yana mika mata ledan hannunsa, tana karba bayan taji abinda ke ciki tace "Yaya ya kawo min, but i will give my roommate this" Maheer yace "Ohk, me kika dafa?" Ta girgiza kai tace "Roommate dina ta ban shinkafa" yace "Kuma kin ci?" Duk da ko spoon biyu bata ci ba a shinkafar da Ummi ta zuba mata kawai sae ta gyada masa kai, ya mata murmushi yace "Good, gobe za ki shiga school ae?" Ta girgiza masa kai kawai, bai sake cewa komai ba, ita ma tayi shiru, Allah ya sani kawai daurewa take and she is trying to act she is okay, but deep down she is soo heartbroken and sad, gashi gaba daya ta kasa kuka ko zata ji sauki a ranta, tun kukan da tayi da safe bata sake ko digon hawaye ba har zuwa yanzu, ji take kamar hawayen nata sun ƙafe ne, babu irin tunanin da bai zo zuciyarta ba bayan sun ajiyeta dazu, da ta tashi zata yi abinda zuciyarta ke raya mata sae ta tuna da furucin Mamin Musharraf ta koma ta zauna a dakin, did she really want her 5 years to go in vain, idan ma ta bar shi ya tafi in vain din zata iya farawa daga farko kuwa? Ƙwaƙwalwarta zai iya daukan karatun nan gaba ma kuwa? All this thought ke sa wa ta kawar da abinda ke running a mind dinta, amma minti goma yayi kadan tunanin zai sake ringing a head dinta, ita kadae ce dakin don roommate din nata ta shiga school wai zata yi karatu, a haka kiran Usman ya shigo wayarta ta fita ta samesa, sae kuma Maheer da ya zo yanxu, ita kanta bata san she is this strong ba sai yau, firgit ta dawo daga tunanin da ta tafi bayan Maheer ya dafa ta cause magana yake mata amma bata san yana yi ba, ta juya da sauri ta kallesa, da damuwa yace "Mimi tunani kuma? I tot u promise me not to, i just caught u now" Tayi resting kanta a shoulder dinsa cikin sanyin murya tace "Yaya tunanin exams nake, i don't know where to start reading from, all the courses are bulky...." Maheer bai taɓa zama uncomfortable with Mimi leaning on him ba sae yau, ya kasa ce mata komai sae gyada mata kai kawai yayi, for almost 5 minutes babu wanda yace komai cikinsu, ita dae kanta na shoulder dinsa, can dai yayi karfin halin cewa "Erm naga kamar ba wuta hostel din ko? let me go and get u rechargeable flashlight yanzu in dawo" Ta daga kai ta kallesa tace "Yaya Usman ya kawo min with fan" Maheer yace "Good, yanzu za ki shiga ciki ki fara karatun ne? i will be calling u every now and then to know how far you've gone" A hankali tace "Ohk" yace "Good gal, go inside and start reading" Mikewa tayi tana rike da ledan da ya kawo mata tana kallonsa tace "Nagode yaya" Murmushi kawai ya sakar mata bai iya cewa komai ba, ta juya ta shiga ciki, sai a sannan ya sauke ajiyar zuciya, for some minutes ya kasa tashi a wajen daga karshe ya mike ya nufi motarsa, his intention was to be with her har zuwa 10 bai yi niyyar tafiya da wuri ba. Yana isa gida wajen karfe tara da wani abu bayan yayi parking ya shiga ciki, Haseenah na zaune parlon sanye da kayan bacci ga fruits da ta aika Musa ya siyo mata ta yanyanka ma Maheer ta rufe tana jiran dawowar sa, yana shiga parlon tun da ya lura ita ce a parlon bai ko kalli inda take ba yayi hanyar corridor ya bude dakin da Badiyyah take, Haseenah ta mike ta bi bayansa, tsaye tayi corridor din ganin dakin da ya shiga, Badiyyah na zaune ta kusa tashi da kazar da ya siya mata tana siɗe hannu yace "Baki bukatar komai?" Tace "Ba a kawo min ruwa ba" Juyawa yayi ya fita, ya wuce Haseenah dake tsaye ya tafi kitchen, Haseenah ta karasa dakin Badiyya tana kallon ciki, Badiyyah na lashe hannunta tace "Ke naga kamar yaya bai siya maki kazar ba ko?" Haseenah ta dinga jin zuciyarta na wani tafarfasa taki ce ma Badiyyah komai sai kallonta take, Badiyyah tace "Ga yanka daya nan ki shigo ki dauka" Sai ga Maheer ya bi gefen Haseenah ya shiga dakin ya karasa kusa da Badiyyah ya duka ya bude bottle water din ya zuba mata a cup ya dauka ya mika mata yana kallonta yace "Hannun ya maki sauki yanzu?" Ta wani marairaice tace "Har yanzu yana min ciwo wllh" Juyawa Haseenah tayi ta bar bakin kofar ta koma parlor ta zauna tana jin zuciyarta na tafarfasa..... Mayraah na zaune kan darduma da handout a gabanta tayi tagumi, tun tafiyar Maheer ta dauko handout din amma ko layi biyu ta kasa assimilating gashi yanzu har kusan karfe sha daya, gaba daya taji kanta ya tushe ga wani ciwo da yake mata, wayarta dake gefenta ya fara vibrate ta kalli screen din ganin Dr Musharraf ke kiranta tayi silencing kiran, yana katsewa ya sake kira nan ma ta kara silencing kiran daga karshe ta sa wayar a flight mode, ta tattara handout din ta ajiye gefe tayi kwanciyarta kan darduman, kuka take son yi amma ta nemesa ta rasa gaba daya, a haka roommate dinta ta dawo daga cikin school ta sameta kwance, Mayraah ta kulle ido kamar bacci take, bayan roommate din nata ta gama shirin kwanciya ta fara tashinta a hankali tace "Sis ki tashi ki hau kan gado" Mayraah ta bude ido tace "Ina son tashi inyi karatu ne anjima kadan ne" Ummi tace "Ki gaya min sanda kike son tashi zan sa alarm in tashe ki, kin ga kasa akwai sanyin tiles" Mayraah tayi shiru, can ta mike zaune a hankali tace "Toh Nagode" Komawa saman gadon tayi tana kallon Ummi ta nuna mata ledojin kajin da su Maheer suka kawo mata tace "Ki dauki daya naki ne, yayana ya kawo mana" Ummi tayi murmushi tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi, karfe nawa zan sa maki alarm din" Mayraah tace "Sha biyu da rabi" Ummi tace "To in sha Allah zan tashe ki lokacin" Mayraah tace "Nagode" sannan ta kwanta ta lumshe ido amma har karfe sha biyu idonta a bushe yake babu alamar bacci, sha biyu da rabi nayi Ummi da bata kai ga kwanciya ba tana revision ta fara tashin Mayraah, duk Mayraah na jin ta amma tayi shiru, daga karshe ta mike zaune da kyar, Ummi tace "It's time" Mayraah ta sauko daga kan gadon ta sake dauko handout dinta ta zuba masa ido kamar hoto, tana ta zaune har karfe biyu saura kawai daga karshe ta tashi taje ta dauro alwala ta dawo.... Sai kusan karfe hudu Mayraah ta kwanta kuma har a sannan ko line uku bata fahimta ba a handout. Ummi ce ta tasheta sallan asuba bayan ta idar ta koma ta kwanta, bata farka ba sai kusan karfe takwas da rabi, sosai kanta ke mata ciwo ta mike zaune da kyar tana bin dakin da kallo, Ummi ta gyara ko ina ta share har wanke wanke tayi, takarda ta gani gefenta ta dauka taga note Ummi ta bar mata kan cewar ga breakfast ta ajiye mata a warmer, akwai ruwan lipton ma a flask ita ta tafi school... Mayraah ta ajiye takardan ta dafe kanta, can ta jawo wayarta da ta sa flight mode tun jiya, bude wayar tayi ko minti daya ba ayi ba sai ga kiran Usman ya shigo, ta daga kiran ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Me ya sa kika kashe wayarki?" A hankali tace "Ina kwana?" Yace "Ko ba ki da caji ne?" Tace "Akwai, bacci nayi ne" Yace "To kar ki sake kashe waya malama" Cikin sanyin murya tace "Toh" Yace "Kin yi breakfast?" Tace "Yanzu na tashi" Yace "To yi breakfast din ki fito" Ta daga kai tace "Ina?" Yace "Waje... Kar ki wuce tara da rabi zan tafi aiki" a hankali tace "Toh" katse wayar tayi ta mike ta shiga bandaki, kafin karfe tara tayi wanka ta saka kaya, ta bude warmer din da Ummi ta ajiye mata taga irish ne da kwai, ko kamshin abincin bata son perceiving, ta bude dayan taga kazan jiya ne tayi masa kamar pepper soup, lipton kawai Mayraah ta sha ta saka hijab dinta ta fita waje, zaune ta gansa cikin motar, he was on suit, ya ajiye wayarsa bayan ya ga ta fito, ta karasa jikin motar ta bude tana kallonsa a hankali tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau, how was ur night?" Tace "Alhmdlh" yace "Kinyi breakfast din?" Tace "Nayi" Yace "Karatun fa?" Kai kawai ta gyada masa alamar tayi, ya ɗan yi shiru, ita dai kallonsa kawai take, can yace "Baki bukatan komai?" Tace "Ba komai" Yace "If there is anything ki kirani, zan je aiki yanzu" Tace "To Allah ya tsare" Yace "Ameen, sai anjima" ta gyada masa kai ta juya ta koma ciki. Maheer na kwance parlor idonsa a lumshe kamar me bacci amma ba baccin yake ba, yana jin Haseenah a kitchen tana ta soye soye tun karfe takwas, jin an bude kofa ya bude idonsa, Badiyyah ce ta shigo parlon kamar ba ita ke dingishi jiya ba, ta dawo garas abinta, ta ɗan sosa kai tace "Ina kwana yaya?" Yace "Lafiya lau..." Sai ga Haseenah ta fito daga kitchen da tray din breakfast tayi ma Maheer, kallo daya tayi ma Badiyyah ta dauke kai ta isa dai dai inda yake kwance ta ajiye duk da tun jiya bata ga fuskarsa ba tana murmushi tace "Honey ga breakfast nayi maka" Bata jira me zai ce ba ta bude cooler din ta fara debar masa irish din a plate, Badiyyah tayi hamma sannan ta nufi kitchen, tana shiga taga wayam duk Haseenah ta wanke kayan da taɓata, ta gama dube dubenta a kitchen din bata ga alamar breakfast ba, can ta fito ta dawo parlon tace "Haseenah ni ina breakfast din nawa?" Ba tare da Haseenah ta kalleta ba tace "Ni zan maki breakfast din da zaki ci? Baki san hanyar kitchen din bane?" Badiyyah ta wani hade rai tace "Ban gane ban san hanyar kitchen din ba, dama a gidan nake da zaki ce min ban san hanyar kitchen ba? ina bakuwa dani baza ki bani breakfast a gidan yayana ba kike nufi?" Banza Haseenah tayi mata ta ajiye ma Maheer plate din irish da kwai ga ketchup a gefe, ta bude wani cooler din ta zuba masa farfesun catfish da tayi, shi dai bai ce mata komai ba, ta langwabar da murya tace "Bari in dauko madara in hada maka shayin baby" Daga haka ta mike ta koma kitchen, Maheer ya kalli Badiyyah da tayi wani mitsi mitsi da ido tana huci tana bin Haseenah da kallo, sai da ya ga Haseenah ta shiga kitchen yace "Zo ki dauka ki je ki ci" Badiyyah ta taho da sauri ta dau plate din irish din da bowl din catfish ta tafi dinning area ta zauna, sai ga Haseenah ta fito, sake baki tayi tana kallon Badiyyah, can ta nufeta a mugun fusace tace "Ke Badiyyah ki shiga hankalin ki kar in maki rashin hankali, breakfast din mijin nawa kika dauka saboda baki da saiti?" Maheer yace "To ke ina ruwanki, ba dai ni na bata ba?" Badiyyah na tafe hannu tace "Kuma baki isa ki hana yayana ya bani abinda ya ga dama ba a gidan nan, ta ya ma zan zo gidanki saboda bakin hali ki hana ni breakfast kamar wata yar iska??" Maheer ya mike tsaye yace "Dauki breakfast din ki wuce daki" A mugun fusace Haseenah ta nufo sa tace "Ban gane ba Maheer?" Calmly yace "Kina nufin da yunwa zaki bar sister na ko kuma ance maki bare ce ita?" Badiyyah ta ja tsaki ta dau breakfast dinta ta wuce ta gaban Haseenah har tana neman bangajeta ta wuce daki ta kulle kofa, Maheer yayi wucewarsa daki shi ma ya bar Haseenah wajen tsaye baki bude kamar an dasa ta.... Wanka yayi ya shirya ya fito parlon, sai ga Badiyyah ta shigo parlon ita ma rike da kwanukan da ta shiga daki da su bayan ta siɗe tass kamar dama a yunwace ta tashi, tana ganin Maheer zaune parlor tace "Yaya aiki zaka tafi?" Yace "Ehh" Tace "Don Allah nima sai ka ajiye ni a school, yanzun nan zan shirya" Yace "Ohk har kin warke kenan" ta sinne kai tana murmushi tace "Ehh hannun kawai ke ciwo amma zan iya zuwa school din" Yace "To kar ki bata min lokaci" Haseenah dake zaune kan kujeran dinning ranta a mugun bace ta dinga bin su da kallo, gaba daya ta ma rasa wani tunani zata yi, Maheer na ta jiran Badiyyah a parlor har ta fito, daga ita har shi babu wanda ya kalli inda Haseenah take suka fita daga parlon. Yana ajiye Badiyyah a bakin gate din school din nasu ta kallesa da sauri tace "Aa yaya bakin gate kuma zaka ajiye ni baza ka shiga ciki ba? Da nisa fa department din namu" a takaice yace "Ana jirana a hospital ne" Tace "Toh shikenan" Sauka tayi daga motar ta rufe tana washe masa baki tana daga masa hannu alamar bye bye, ya gyada kai ya ja motarsa ya bar wajen, A ranta tace kai wai ashe dama haka yaya Maheer ke da kirki bata taɓa sani ba?? Ashe ya Maheer is this nyc? Ko da yake dama ita babu abinda ke hadata da shi kuma ko ta gaishesa da can ma yana amsawa, iyaka idan yaga tayi ba dai dai ba yace zai mata fada ita kuma shine bata so, Usman ne kawai ya tsaneta tun asali, kwafa tayi a ranta tana imagining ta tura ma Usman yan daba su rama mata dukan da yayi mata har sau biyu kenan, da sauri ta shiga cikin makarantar tana addu'ar Allah ya sa Dr Musharraf ya shigo school ta samesa a office, sai murmushi take... Maheer kadai yasan yanda yake tausasa zuciyarsa na ganin ya biye Badiyyah ita kuma har ta wani sake jiki da shi abinda ma ke kara ƙona masa rai kenan, da ta san irin mugun haushinta da yake ji da baza ma ta dinga biyesa ba, but babu komai za su ci gaba a haka he knows his target ae, hostel din da Mayraah take ya nufa don sun yi waya da ita not long ago tace bazata je school ba. Da yamma karfe biyar Maheer ya koma gida, har ya iso gidan ma bai sani ba don tunani iri iri suka cika zuciyarsa, ga damuwar Ammi da taki komawa gida duk da Mayraah bata gidan, Abba dama tun jiya da yamma ya bar kanon ya tafi ya ci gaba da harkokinsa ba tare da ya bi ta kan Ammin ba, ga Mayraah kuma da baya jin dadin yanda yake ganinta yasan she is just pretending to be fine karfin hali kawai take, but she look traumatized, he wish yanzu da ne da zai iya rungumeta ya lallasheta sosai ya kwantar mata da hankali amma that is not possible a yanzu kam, handout da tace masa ta karanta cikin dare ya amsa yayi mata tambayoyi bayan yaje wajenta da safe amma ta zuba masa ido kawai with no answer, if things should continue like this yasan zata samu matsala a makaranta, gaba daya yayi confuse ya rasa way out, parking yayi ya shiga cikin gidan, Haseenah na kwance kan doguwar kujera tana danna wayarta, sai ga Badiyyah ta fito daga daki tana kallonsa don ta ji shigowar motarsa, tana huci tace "Wai yaya fa Haseenah bata ma mutane girkin komai ba a gidan nan yau, tun da na dawo da rana babu abinda na ci, gashi yunwa nake ji yanzu...." Ko rufe baki bata yi ba Haseenah ta mike zaune tace "Ke kuturwa ce da baza ki shiga kitchen din ki dafa abinda za ki ci ba" A mugun fusace Badiyyah tace "Kee kar ki gaya min maganar banza a gidan yayana malama, nan din gidan mijina ne da zan dinga shiga kitchen anyhow?? Ba ke ce matar gidan ba, ai ke ya kamata ki dinga ma mutane girki su ci, ko ke a gidanku haka kika ga ake ma dangin miji??" Haseenah ta mike tsaye da sauri tayi mitsi mitsi da ido tana nunata da yatsa tace "Kar ki sake ki sako yan gidanmu a haukanki, kuma bazan yi girkin ba ai ba zamanki nake ba kuma ke din naga ba gurguwa bace da baza ki iya shiga kitchen kiyi girki ba" Badiyyah ta nufota kamar zata tashi sama tace "Ke ni fa ba Mayraah bace da kika rena wllh kika kawo min nonsense zan nakada maki duka a nan kuma babu abinda zai faru, ko kin ga na maki kama da Mayraah? Tun da yaya ya kawonu gidan nan jiya don ya dinga duba lafiyata naga kina bakin ciki, to naga dae ai ba gidan iyayenki na zo ba ko??" Da sauri Haseenah ta kalli Maheer dake tsaye yana kallonsu without saying anything, lokaci daya ta fashe da kuka ta dafe kirjinta tace "Maheer kana jin rashin kunyar da take min kayi shiru??" Maheer yace "Amma ke me ya hanaki girki kin san gidan da bakuwa? Ko dae baki san wacece ita bace in tuna maki?" Badiyyah ta wani karya kai tana girgiza kafa irin yesss din nan, Haseenah ta bude baki tana kallon Maheer with shock babu ko kiftawa, Maheer yace "To ita din ba bare bace, she have all right to ask for food from you in this house, dama don me aka auro ki? In case u don't know my family over everything Haseenah, dole kiyi girki ki bata" Cikin tsawa Haseenah tace "Toh bazan yi ba sai dai duk abinda zai faru ya faru, wallahi bazan girka ma katuwar banza abinci ba, wannan wani irin Fitina ne daga wannan sai wannan? Wani irin aure ne wannan" Badiyya tace "Sae dae uwarki ce ƙatuwar banza ba ni ba" Haseenah ta zaro ido tana kallonta, cakumota take kokarin yi a fusace, Maheer ya dakatar da ita yace "Keee respect ur self" Sai kuma ya kalli Badiyyah dake girgije girgije yace "Dauko Hijab dinki mu je in siya maki abincin" Da sauri Badiyyah ta koma daki ta dauko Hijab dinta, ko da ta dawo parlor taga Maheer har ya fita ya koma mota yana jiranta, Haseenah kuwa na tsaye ta kasa motsi saboda shock, sae zufa take a goshinta, she just can't believe it, Badiyyah na mata wani kallo tana juya ido tace "Yauwa wannan kudin gold din nawa da kika ce za a biya wannan malamin na biyu da shi na fasa, kawai a bani kudin gold dina ko inyi rashin mutunci, dama can ni ba ruwana da harkan Malamai kika wani tashi kika hada ni da Malami" Sai da gaban Haseenah ya fadi tsabar rikicewa da jin abinda Badiyyah ke cewa don murya a sama tayi maganar yanda in dai mutum na balcony ma zai jiyo ta, Haseenah ta dinga kalle kalle da sauri to be sure Maheer baya wajen zuciyarta na wani bugawa, tuni Badiyya tayi wucewarta ta bar ta nan a tsaye, kawai yau ta dawo gida cike da farin ciki don har numberta sai da Dr Musharraf ya amsa bayan ta samesa a office da wani topic a course dinsa amma rashin ganin abinci a gida ne kawai ya ɓata mata mood dinta gaba daya don ita bata wasa da cikinta, bayan tun da take bata taɓa irin wannan farin cikin da tayi yau ba wai a whole Dr Musharraf yayi requesting phone number dinta zai tura mata wani slide ta WhatsApp kawai Haseenah ta wani ɓata mata mood dinta.... Throughout this week was nothing but hell for Mayraah bata yi tunanin zata yi surviving har zuwa ran friday ba, sosai ta rame duk da kokarin da yayyin nata maza suke don a rana sai su zo wajenta sau biyu sau uku amma ta kasa samun sukuni gata nan gata nan dai ne kawai, ga karatu yaki tsaya mata a kai, she try all her best tayi composing kanta idan sun zo, amma suna tafiya zata koma gidan jiya, taji duniyar ya isheta komai yayi mata zafi, she just want to see her self far away, may be in a another world, kullum da wannan feeling din take kwana take tashi a ranta, amma da taji zuciyarta na ingizata ta aiwatar da hakan sai ta tuna final exams dinta.. Yau Sunday tana kwance ita kadai a daki Ummi ta shiga School karatu wayarta ya fara vibrate, ta jawo wayar taga Dr Musharraf ne, tun da ya kirata Tuesday, Wednesday, Thursday bata daga ba bai sake kiranta ba sai yau Saturday, tana ta kallon wayar har ya katse, ya sake kira, dagaws tayi ta sa handsfree tayi shiru, yace "Ki gaya min me na maki kike avoiding calls dina Mayraah? Yayyinki suka hanaki daga kirana ko?" A takaice tace "Saboda me za su hanani daga kiranka?" Yace "Toh gashi nan baki dagawa all this while, we were good, all of a sudden u stopped responding to my calls Mayraah, kin ga dole zan yi tunanin hanaki ɗaga wayata aka yi" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "It's not so, bani da lafiya ne" Da mamaki yace "Really? but i asked Badiyyah about u yesterday and she said u are fine kince a gida zaki dinga karatun ki" Mayraah dai tayi shiru, yace "Mayraah ki gaya min me yake damunki plss?" Tace "Ai na ji sauki" cike da damuwa yace "Pls ina son ganinki yau, where can i meet you?" Tace "Ai zan shigo school gobe" yace "Da gaske?" Tace "In sha Allah" yace "Amma kina karatun sosai kuwa, next week fa exams din ku" Tace "Ina yi, yanzu ma shi nake yi...." a hankali yace "Ohk in kyaleki ki cigaba kenan?" Tace "Yeah" yace "Toh zan kira ki anjima" katse wayar tayi ta ajiye ta ci gaba da kwanciyarta... Washegari karfe goma da rabi Usman ya ajiyeta a school, a parking space ta ga motar Dr Musharraf, Usman na kallonta bayan ta sauka daga motar yace "In kin gama ki kirani" a hankali tace "Ya Maheer yace zai zo ya daukeni" Shiru Usman yayi, sai kuma yace "Ok" ya ja motarsa ya bar wajen, ta shiga department din nasu, sosai gabanta ya fadi ganin Dr Musharraf na saukowa stairs tare da wani lecturer dinsu, tun da ta kallesa sau daya ta sunkuyar da kanta ta rasa dalilin da zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri, shi ma kallonta kawai yake ta cikin glasses din idonsa, ba tare da ta sake kallonsu ba ta gaishesu ta wuce, inda suke sallah a department din ta nufa tana tafiya a hankali, gabanta ya sake faduwa ganin Badiyyah zaune da kawayenta biyu tana basu labari duk sun cika wajen da muryarsu, Badiyyah ta daga kai tana kallon Mayraah da mamaki, ita wllh har ta manta da ita a duniya, mamaki ta dinga yi tana tunanin daga ina kuma take haka, dama tana nan ashe, can ta wani kyabe baki ta ci gaba da ba kawayenta labarin da take basu, da har Mayraah zata juya ta bar wajen sai kuma dai kawai ta zauna ɗan nesa da su ta ciro handout dinta tana kallo amma surutunsu duk ya cika mata kunne, Badiyyah tace "In gaya maku har karfe dayan dare we were chatting with him wallahi tallahi" Kawarta Aisha tace "Shi Dr Musharraf din?" Badiyyah ta kyalkyale da dariya tace "Wallahi nake gaya maki, bari ma ku ga" da sauri ta ciro wayarta ta shiga WhatsApp tana nuna masu chat dinta da Dr Musharraf, duk suka zaro ido da mamaki suka ce "Whatttt" Badiyyah dai sai murmushi take ta mayar da wayar jakarta, sai kuma ta fito da wani tsadadden foreign coffee a kwalinsa tace "Toh da yace min yana son coffee shine na dauko masa wannan coffee din a gidan yayana in basa, kun san yanzu gidan Maheer nake for almost a week now, shine ma ke kawo ni school yanzu, dama warce ta shiga tsakaninmu da su yanzu an koreta a gidan, familyn mu ya dawo dai dai yanzu, don haka sai kun ga yanda Maheer ke ji da ni a gidansa wllh tllh, sai ma da na gaya masa zan dauki coffee din kafin in dauka" Aisha ta zaro ido tace "Ke ga Dr Musharraf din na hango ashe ya shigo school din" Badiyya tace "Kai haba" Aisha tace "Wallahi kuwa na ganshi yana tafiya upstairs" Badiyyah ta ciro powder dinta da sauri ta shafa sannan ta fito da wani turare a kwalba ta shafa tace "Bari in kai masa Coffee powder din yanzu kawai" Sai da ta kusa taka Mayraah da gangan sannan ta bar wajen, ita dai Mayraah kanta na kasa tana jin duk hiransu, ta dai kafa ma takardan hannunta ido babu ko kiftawa...... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 *Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/5, 9:45 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah ta daga kai a hankali tana kallon wata Coursemate dinta da ta dafa shoulder dinta, Farida ta buda ido tace "Duk karatun ne haka Mayraah, have been talking to u since fa" Mayraah ta kirkiri murmushi ta ajiye handout din hannunta tace "Ayya ban sani ba Farida, ya kwana biyu?" Farida tace "Lafiya lau wllh, ya preparation din exams?" Mayraah tace "Alhamdulillah" project supervisor din su daya da Farida wato Dr Musharraf, dama su biyu kadai ne project student dinsa, Farida tace "Supervisor dinmu na kiranki, wani chapter kike yanzu ne? I submitted my chapter 4 just now" Mayraah tace "Ohk, ni ban yi submitting ba" Farida tace "Ohk yace ki je yana jiran ki" Mayraah tace "Toh" Tun barin Badiyyah wajen for almost an hour Mayraah ke zaune ita kadae a gun don kawayen Badiyyan ma tuni suka bar ta a wajen, bayan Mayraah ta maida handout dinta cikin jaka da wayarta da ta saka a Flight mode tun daxu, ta mike ta wuce sama bayan sun yi sallama da Farida don tace gida zata wuce. Office din Dr Musharraf Mayraah ta nufa, tana tsaye bakin kofa tayi knocking gently, sae da yayi mata permission din shiga sannan ta shiga ta kulle office din, shi kadae ne zaune office din amma ba kan office chair dinsa ba yana danne danne a laptop, ya daga kai yana kallonta, ita dai bata bari sun hada ido ba, kwalban coffee dake kan table dinsa kawai take kallo, ta isa har wajen table din ta tsaya kusa da kujeran dake facing din wanda yake zaune without looking at him tace "Good afternoon" Bai amsa ba ya cire glasses din idonsa yace "Na kira wayarki a kashe, so da ban ce a kiraki ba baxa ki shigo ba kenan, i think ko don saboda project dinki ma ai ba sai kin bari na kira ki ba" Shiru tayi taki cewa komai, Musharraf dai kallonta kawai yake, har sannan kuma bata bari sun hada ido da shi ba, bayan few seconds tace "Ana jirana, za mu tafi gida" Ganin bai bata amsa ba ta juya zata bar office din ya riko hijab dinta, bata san sanda ta warce ba ta juyo tana kallonsa da kyau tace "Kar ka sake pls" Ya mike yana kallonta yace "Are you okay?" Ta gyada masa kai furiously tace "I am very much okay, kawai nayi regretting relationship dina da kai ne tun daga farkonsa har yau, i just realized u are the reason i am going through all this, nayi da na sanin haduwata da kai...." Dr Musharraf ya koma ya zauna yana kallonta yace "Really?" Mayraah was trying so hard to control her self kar ta fashe da kukan dake cin ta tace "I regret everything...." A hankali Musharraf yace "I should be the one regretting Mayraah, ni aka yi ma damage so i should regret not you" Kallonsa kawai take zuciyarta na bugawa, can ta juya ta nufi kofa shi dai bai ce mata komai ba, har ta rike handle din kofar ta juya tana kallonsa with regret tace "I regret trusting you, i hate my self for believing in you har na kusa saɓa ma Allah, i will never forgive u for this...." Musharraf yayi kasa da murya yace "I don't understand, ni na sa kiyi saɓon Allah? How?" Hawaye cike idonta tace "Ae zuwa gidanka ma da abinda ka so yi min saɓon Allah ne" Yace "Na taɓa cewa ki zo gidana? Of course no, kawai ke kika ga ya kamata ki zo but ni ban taɓa ce maki ki zo ki sameni a gida ba...." Kallonsa kawai Mayraah take babu ko kiftawa, lokaci daya ta juya ta fice daga office din ta share hawayen idonta bayan haka kuma bata sake jin hawayen ya taho mata ba, ko minti daya bata kara a makarantar ba ta wuce hostel din da take, tana isa hostel din first abinda ta fara yi shine goge duk numbers din Dr Musharraf a wayarta bayan tayi blocking dinsa, ta shiga WhatsApp ma tayi blocking dinsa ta nan, kwanciya tayi gefen gado taji hawaye me zafi na sauka idonta kamar an bude pampo, kalmominsa na karshe ne kawai suka dinga kai komo a brain dinta, tayi da ta sanin zuwa ta samesa a gidansa, tayi mugun da na sani, she wish she neva did that, ta fashe da kuka sosai, tayi me isarta sannan ta mike ta dau wayarta ta shiga timetable din exams dinsu tana dubawa, don tun fitowar timetable din sau daya kadai ta duba, after checking the timetable ta fiddo complete handouts dinta ta jera su according to the timetable sannan ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito don an kira azahar. Karfe hudu da rabi Mayraah ta fito waje ta dalilin kiranta da Usman yayi, yana tsaye jikin motar ta karasa ta tsaya gefensa ta gaishesa, ya amsa yana kallonta yace "Ya kike?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kina karatun sosai?" Ta daga kai ta kallesa tace "Ina yi" Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Zan yi tafiya gobe zan je wani aiki, so i don't know how long zan tsaya a can kafin in dawo...." Mayraah tace "Toh Allah ya tsare, i will be fine in sha Allah" Yace "Sure?" Ta ɗan yi murmushi tace "In sha Allah" Usman bai wuce 30 minutes ba ya wuce, Mayraah ta koma cikin hostel, har ranta dama taji bata ma son kowa ya dinga zuwa wajenta daga yanzu she just want to be left alone, and she is happy Usman is traveling tunda shi bazata iya gaya masa she wants to be left alone ba, Maheer kuma dama zata iya masa magana without any fear zata ce masa tana son ta dinga karatun ta without distraction..... Daren ranan Maheer ya zo, Mayraah ta gaya masa abinda ke ranta, bai iya ya ce mata komai ba at first, ita dai tana ta jiran abinda zai ce, bayan wani lokaci yace "Haka kike so Mimi?" Ta gyada masa kai tace "Yea, i want to concentrate fully, za mu dinga shiga school tare da Ummi from morning till evening don inyi karatu sosai" Maheer ya sauke ajiyar zuciya, yau kam yaji da confidence dinta take magana kamar ta samu motivation from somewhere, a hankali yace "Shikenan, if that is what u want Mimi...." Bata ce masa komai ba and she was expecting taga ya tashi ya tafi, can ya juya ya kalleta yace "Amma ai zan iya dinga zuwa sau daya in ganki?" Ta girgiza kai tace "Aa yaya, i said i can take care of my self, even Ummi that is in level 2 babu wanda yake zuwa nan dubata kullum, and i am not a kid" Maheer dai kallonta kawai yake, can ya ɗan yi murmushi yace "To shikenan, nasan zaki kula da kanki Mimi, today is Monday, in sha Allah Wednesday zan zo in ganki, hakan yayi ko?" Ta ɗan hade rai tace "Aa yaya, i said i can take care of my self, I am not a kid" Bai kuma ce mata komai ba, ita ma haka, a ranta kuwa ta kagu ya tashi ya tafi ta wuce ciki abunta, she just hate the sight of everyone har cikin ranta, bayan few minutes yace "Shikenan zan tafi, i will be calling u Mimi" Tace "Thank you" Daga haka ta mike ta shige cikin hostel din ya bi ta da kallo.... Har ya koma gida jikinsa a sanyaye yake, kullum addu'ansa Allah ya kawo karshen wannan abun ko zai samu rest of mind, a kofar gida yayi parking don yana son zai je wajen Ammi bayan magrib, yana shiga cikin gidan ya zauna parlor, kamshin girki ne ya cika gidan alamar ana girki a kitchen, can dai ya mike ya nufi corridor, dai dai nan Badiyyah ta fito daga dakin Haseenah kusan a guje rike da turmin atamfa uku ta cusa a cikin leda, sosai ta tsorata ganinsa ta koma gefe tana gwale ido sai rufe bakin ledan take kar ya ga meye a ciki, da kamar bazai ce mata komai ba sai kuma yace "Kin dawo" Tana kame kame tace "Eh, dama, eh dama yanzun nan nima na dawo, ajiya na bata shine na dauko yanzu" Yace "Ohk" Daga haka ya bude dakinsa da yake kullewa da makulli ya shiga ya rufe, Badiyyah tayi saurin shigewa dakin da take ta bude jakarta ta saka turamen atamfar ta kulle jakar, ta zauna gefen gado tana sauke ajiyar zuciya. Haseenah ta gama tuwo da miyar vegetable da take ta juye komai a cooler ta fito daga kitchen din, zaune taga Badiyyah a parlor, ko sanin Badiyyar ta dawo bata yi ba don tun karfe uku take kitchen kamar me girka abincin mutane goma, sai yanzu biyar da rabi ta fito, Haseenah ta dake tace "Aa kin dawo ashe" Tun da Badiyyah tayi mata maganar kudin gold few days back ta ɗan fara sake mata sama sama tana kauda kai a abubuwa da yawa sai dai ita kadai tasan plan din da suka yi ma Badiyyah ita da Cousin sister dinta Ramlah, Badiyyah na tauna chewing gum tace "Yanzun nan na shigo ae ko daki ban karasa ba" Haseenah tace "Ko zaki dafa Indomie don tuwo ne malmala biyu ya sa in masa, nasan ke baki cin tuwo" Badiyyah ta hade rai tace "Ni nasan yanda ake wani dafa Indomie, kuma yaushe nace maki bana cin tuwo" Haseenah tayi wucewarta ta bar ta a wajen, bata so Badiyya ta dawo gidan bata gama girki ba, so tayi ace kafin ta dawo ta gama tayi maza ta shige daki da shi ai dai bazata ce tayi girki ta hanata ba, duk saurin da take wai ashe har Badiyyar ta dawo.... Haseenah tayi wanka sharp sharp ta fito daga dakinta wajen karfe shidda, har sannan bata san Maheer ya dawo gidan ba tunda bai shigo da mota ba, Badiyyah ta gani tsaye corridor tana kwankwasa kofar dakin Maheer, Haseenah ta koma gefe tana kallon ikon Allah thinking yaushe Maheer ya dawo, Maheer ya bude kofar yana kallon Badiyyah, Badiyyah ta wani narke murya tace "Yaya don Allah subscription zaka min, nawa ya kare kuma abu ake koya min a WhatsApp for my exams" Haseenah da zuciyarta ya hau tafarfasa ta dinga kallonsu da mamaki, wai dama Maheer ya dawo gidan nan, to ko dai tare ma suka dawo tana can kitchen bata sani ba, Maheer na kallon Badiyyah yace "Ohk, kamar na nawa kike so?" Ta washe baki ta jingina da bango tana wasa da hannun rigarta tace "Yaya ko na dubu goma ne kawai kayi min nagode" Maheer yace "Ohk, naga kin kara haske wani mai kike shafawa ne haka?" Haseenah taji brain dinta ya tsaya cak for some minutes, Badiyyah tayi wani er siririyar dariya tace "Wallahi dama yaya cream din ma ya kare da soap, haka ma turarena sun kare" Yace "Sai a siya maki ai, zan je gidan Hajja yanzu ki shirya sai mu fita tare daga nan sai mu je supermarket din..." Badiyyah na wani blushing tace "To yaya bari in shirya, nagodeee yayana" Daga haka ta shige dakinta da sauri, Maheer ya kulle kofar dakinsa duk suka bar Haseenah wajen a tsaye kamar an dasa ta, tsabar yanda abun ya bugi Haseenah a haka Maheer da Badiyyah suka fito suka sameta tsaye har lkcn kamar statue, Maheer ya wuceta without looking at her, Badiyyah ta kulle dakinta da makulli ta saka makullin cikin jakarta sannan ta yafa ɗan iskan gyalenta ta bi bayan Maheer tana kallon Haseenah tace "Kawata sai mun dawo" Haseenah ta bi ta da kallo har taga sun fita daga parlor, dakinta ta shige da sauri ta xauna gefen gado ta jawo wayarta ta fashe da matsanancin kuka tayi dialing number cousin sister dinta Ramlah, Ramlah na dagawa Haseenah ta kara rushewa da kuka sosai tace "Ramlah wallahi na gaji, na gaji, ji nake kamar xuciyata zai fashe Ramlah, sai yanzu na gane gwara min Mayraah sau dubu a gidan nan tun da ita bazata min wannan abinda Badiyyah take yi a gidana ba kuma shi ma bai wani kula Mayraan a gabana, Ramlah kin ga abinda nake gani a gidana kuwa?" Daga daya bangaren Ramlah tace "Dalla ba wani gwara, ke dai nace ki kwantar da hankalinki ba dai mu mun san abinda muka shirya ba?" Cikin kuka Haseenah tace "Tsoro nake kada tsinanniyar kakan nan tasa tace ya auri Badiyyah tun da an ga suna shiri yanzu, kar ita ma Badiyyar ta zo ta fara sonsa tunda ba hankali isasshe gareta ba, wallahi ina ji a jikina at anytime komai zai iya faruwa idan ban kawo karshen wannan abun ba cikin gaggawa, gashi har yau Maheer yaki kulani" Ramlah tace "Kin ga ni bana gida yanzu haka Haseenah, tun da dai nace ki kwantar da hankalinki ki kwantar da hankalinki kawai, auren nan sai kace bamu yi ba mun fito, Mun fa san kan ko wani tsiya, wallahi Badiyyah da kafarta zata bar maki gida yanda ita wannan mara asalin ma ta bar gidanki" Haseenah na shessheka tace "Amma fa na gaya maki yanda kakar nan tasu ke ji da Badiyyar nan, don ita ce ma ke control dinta wallahi, ni dai wallahi gwara min Mayraah a gidan nan da Badiyyah, Ramlah da na sani da ban hada Badiyyah da malamina ba, kullum da fargaban haka nake kwana nake tashi" Ramlah tace "Kinga ni don Allah zan kiraki in na koma gida" Daga haka ta katse wayarta, Haseenah ta dinga kuka a ranta tana tunanin menene yasa ita dai komai nata bai tafiya dai dai a rayuwar nan, daga wannan sai wannan, ga Maheer ya juya mata baya aure ko wata daya bai cika ba amma sai reto auren nata yake. Throughout daren yau Mayraah bata yi wani bacci ba kasancewar washegari za su fara exams, she is trying by all means taga tayi covering din course din da suke da shi da safe, ita kanta tasan she is not fully prepared for the exam, to amma ta rasa ta yanda zata yi karatun ya shiga kanta, it seems her brain is just weak, a haka dai ta shiga makaranta karfe bakwai da rabi for the exam, rabonta da makarantar tun last week monday, Mayraah ta nuna ma wani lecturer dinsu dake tsaye bakin hall din da za su yi exams ID card dinta sannan ta shiga ciki, seat din da ya nuna mata ta nufa, tana zaunawa sai ga Badiyyah ma ta shigo ta zauna kujeran dake gefen na Mayraah don nan aka nuna mata ta zauna, sai dai akwai ɗan tazara tsakaninsu, a haka aka fara raba masu answer sheet, kamar ance Mayraah ta daga kai taga Musharraf tsaye at the far end of the hall yana danna wayarsa, ta dauke kanta da sauri bata sake kallon side din ba, a haka har suka fara exams din, Mayraah ta dinga kallon questions din that look strange in her eyes, tunani ta fara yi ko dai ba handout din ta karanta ba, though the questions look familiar but she is just confuse, just few minutes da fara jarabawan Mayraah ta sunkuyar da kanta trying to calm herself down, ta lura Badiyyah na ta mutsu mutsu cikin Hijab, Mayraah ta kalli side dinta, sai da gabanta ya fadi ganin wayarta take lullubewa da hijab bayan ta ciro shi daga bra dinta, duk da how strict the invigilators where haka Badiyyah ta dinga satan amsa da wayarta cikin dubara tana yi tana keeping serious face, Mayraah gabanta ya dinga faduwa don in dai lecturer ya kamata to kora ne direct bbu wani corner corner, after like 30 minutes Dr Musharraf ya karaso gaban Badiyyah yana kallonta, tayi saurin cusa wayar tsakanin cinyoyinta, can ya ɗan kalli colleagues dinsa ko kadan bai son attention dinsu ya dawo wajen, hakan yasa ya ɗan fara zagaye zagaye a wajen, sai kuma ya tsaya dab da ita, yayi kasa da murya yace "Bring the phone Badiyyah" Badiyyah jikinta ya fara rawa, ta ciro wayar gabanta na mugun faduwa, kawai ya kai hannu ya karba without letting anyone notice them ya saka a aljihu ya bar wajen, Badiyyah ta sauke ajiyar zuciya, Mayraah ta bi Musharraf da kallo..... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake. [7/6, 4:52 PM] Khaleesat Haiydar💖: *I dedicate the whole of this page to MAYRAAH Conversation groups💖, ina yin ku irin 💯 din nan, Allah Ubangiji ya iya maku, ya biya maku duk bukatunku na alkhairi ya raya zuri'a* _Team Musharraf ina kara bamu hakuri, mu kwantar da hankalinmu komai zai daidaita, Team Maheer kuma su ci kansu babu mai ba yaji, Team Usumanu kuma kamar yanda muka kasa gane zuciyarsa su ma har yau bamu san zuciyarsu ba gaskiya, su dinga buda baki ko za mu gane inda suka dosa_🙄 Mayraah ta sunkuyar da kanta saboda hawayen da taji ya kawo idonta, bata taɓa shiga exams hall taji kanta so empty like today ba, ɗaga kai tayi after some minutes ta goge tears dinta, suka hada ido da Dr Musharraf dake kallonta, dauke kanta tayi daga direction din, Badiyyah dai sai kallon Mayraah take tana murmushi kasa kasa ganin sunanta da reg number kawai ta rubuta a booklet, yawanci idan suna exams in dai Dr Musharraf na invigilating zama yake yi colleagues dinsa su yi invigilating din, ko nan da can bai son zuwa, yau kam ya amshi attendance sheet going round to give each and every student to sign, har ya iso roll din da Mayraah take zaune, yana isa gabanta taki yarda ta dago kanta, ya ajiye mata sheet din attendance din kan booklet dinta, ya amshi pen dinta dake hannunta ya ajiye mata nasa, kallon pen din nasa ta dinga yi ba tare da ta yarda ta daga kai ta kallesa ba, can dai ta dau pen din nasa tayi signing attendance din, ya dau attendance sheet din ya bar wajen, lkci daya duk kamshin turarensa ya cika mata hanci, ta wani hade rai ta ajiye pen din nasa kawai kan booklet, dai dai nan wani lecturer dinsu ya karaso inda take ya tsaya yace "Are you not comfortable here?" Ta daga kai ta kallesa, a hankali tace "Yes sir" Yace "Ok let me change ur sit" Mikewa tayi ta dau booklet dinta da pen din Dr Musharraf ta bi bayan lecturer din ya kai ta har gaban hall ya nuna mata kujera da table dake kusa da podium ta karasa ta zauna, tana zaunawa ta bude booklet din sai ta samu kanta kuma da fara rubutu, 50 minutes da fara rubutunta ta gama abinda zata iya a questions din, zuwa Lokacin students sun gama sun fara fita class din, sai a sannan ta lura Badiyyah ma ta fita, ta hada ido da Musharraf that is sitting opposite to her, yana amsan booklets din wa enda suka gama, ta rufe booklet dinta ta mike ta tafi zata yi submitting, tana ajiyewa gabansa ya dauka ya bude, ita dai kanta na kasa tana jiran ya bata attendance tayi signout don yana hannnunsa attendance sheet din, after few seconds ya ajiye mata yana kallonta, pen dinsa dake hannunta ta ajiye zata dau nata da ta ga ya ajiye kan table yayi saurin daukewa, daukan nasa din tayi, tayi signing ta fice daga hall din, Hamidah na ganin Mayraah ta fito ta nufeta tana kallonta tace "How was the paper Mayraah?" Mayraah ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Alhmdlh" Hamidah tace "Toh Allah ya bamu sa'a" Mayraah tace "Ameen" Hostel Mayraah ta wuce bata kara ko minti daya a department din ba. Mayraah na kwance ita kadai a daki da yamma tana ta tunane tunane, zuwa yanzu tunani har ya zame mata jiki, tayi wannan tayi wancan, wani tayi murmushi, wani kuma taji hawaye ya cika idonta, wayarta ne ya fara vibrate, ta jawo wayar a hankali tana kallon screen din ta ga Maheer ke kiranta, da kamar bazata daga ba don dazu ya kirata bayan ta dawo hostel, can dai ta daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yace "How r u Mimi?" Tace "Alhamdulillah, ina yini" Yace "Bacci kike ko karatu?" Tace "Just lying down...." Yace "Ohk, na bada sako a kawo maki ki fita kofar gida ki amsa" Shiru tayi sai taji da ma tace masa tana school, yace "Hello" a hankali tace "Toh" Daga haka ta mike ta dau hijab dinta ta saka ta fita waje, tsaye tayi bakin gate din hostel din ganin Abba, bata san sanda ta nufesa ba da farin cikin ganinsa ta gaishesa, ganin yanda ta rame Abba yace "Kina cin abinci kuwa Mayraah?" Maheer dai na tsaye jikin mota shi ma yana kallonta, he is not happy with the way take ramewa kullum, tun shekaranjiya rabonsa da ita sai dai ya kirata a waya, yana bata enough space kamar yanda tace don tayi karatu, Mayraah na murmushi a hankali tace "Ina ci fa Abba" Abba bai gamsu da hakan ba ya kalli Maheer yace "I don't think she is comfortable here Maheer, ta dawo gida kawai" da sauri Mayraah tace "Abba exams ne fa, but ina cin abinci wallahi, karatun da nake yi ne shi yasa" Abba yace "Papers nawa ku ka yi yanzu?" Tace "On monday muka yi daya, muna da wani gobe Thursday in sha Allah" Abba yace "Sai kuma yaushe bayan na gobe?" Mayraah tace "Sai kuma Monday" Abba ya kalli Maheer yace "Idan tayi paper din gobe ta dawo gida for the weekend, bring her back home" Lokaci daya Mayraah taji gabanta ya fadi ita gaba daya bata ma son tuna gidan, da sauri tace "Amma Abba za mu yi practical a laboratory for Monday's paper, friday and Saturday duk za mu shiga school, ka tambayi yaya ya sani ai" Abba yace "Duka courses din nawa ne gaba daya?" Tace "Guda 6 with project" Abba yace "Toh za ku gama da wuri kenan" Mayraah dai ta yi murmushi kawai ta gyada masa kai, duk da dai intervals na 2 days ne for every course, Siyayya sosai Abba yayi mata Maheer ya fito mata da su daga mota ta shiga da su cikin hostel, minti sha biyar kawai Abba yayi suka wuce tare da Maheer, ita kuma ta koma cikin hostel, zaunawa tayi tana kallon handout din da ta ajiye gefen gado, tun jiya ta kasa bude handout tun da taga course din Musharraf za su yi, ba shi ba har course din nasa taji ta tsana har cikin ranta, wanda a da it's among her best... Sai can da daddare bayan tayi isha ta jawo handout din ta ɗan yi scrolling daga karshe kawai ta ajiye tayi kwanciyarta don ranta kara baci yake just scrolling through the handout... Washegari tana zaune hall din exam din nasu da booklet dinta da aka masu sharing suna jiran question paper, kamar ran Monday yau ma Badiyyah a gefenta ta zauna, ita dai ko kallon side dinta bata yi ba, wani lecturer dinsu ne yayi sharing masu question paper din don Musharraf din ma bai shigo ba, ta dinga kallon takardan questions din, tuni Badiyyah aka fara rubutu babu ɓata lokaci ana murmushi irin anyi karatun nan, Mayraah na daga kai after some minutes taga Musharraf zaune hall din, tayi saurin dauke kai ko da mistake bata sake kallon side din da yake ba, bata wani stressing kanta ba a exam din, she just wrote what she can cause bata ma yi karatun ba ai, an hour into the exams ta mike ta tafi inda zata yi submitting booklet dinta, kallonta kawai Musharraf yake ta cikin glasses din idonsa, zata yi signing attendance dake gabansa ya janye, ya amshi booklet din nata ya bude, ita dai taki yarda ta kallesa ta wani hade rai tana tsaye, rufewa yayi ya ajiye mata right in front of her yace "Go back" ta dau booklet dinta ta juya ta koma ta zauna fuskarta a daure, yawanci invigilators din close colleagues din Musharraf ne shi yasa nobody was against his action a lkcn, Mayraah ta rufe booklet din ta hade kanta da table ba tare da ta kara ko fullstop a abinda ta rubuta ba, kusan ita ce karshen fita hall din bayan duk Coursemate dinta har Badiyyah sun fita, ta tafi tayi submitting gun wani lecturer tayi signing out ta fice without looking at Musharraf da ya bi ta da kallo ta cikin glass, ba wanda zai ce ita yake kallo. Sauran exams din haka Mayraah tayi su ba yanda ta saba exams dinta ba, hakan ke kara daga mata hankali, ita yanzu she is not even after any first class kawai ta samu ko da pass ne ta tafi don ita kanta tasan bata abun arziki a exams din nan, komin dadewan da zata yi tana karatu sai ta ji bata iya rikesa a kai kamar da, nan da nan karatun yake bin iska, a haka har suka yi 5 exams, ya rage masu just last paper dinsu da za suyi on Friday, saboda wahalan course din sannan tasan bata da wani score me yawa a test yasa ta dage tayi karatu ba na wasa ba, ana gobe za su rubuta last paper din nasu tana kwance tana replying message din da Maheer yayi mata ta WhatsApp, bayan ta gama replying dinsa wani message ya shigo mata, ta bude message din ganin bata da number a contact dinta, Pdf taga an turo mata guda biyu with her name, ta bude taga complete project dinta ne from chapter 1 to end, daya pdf din kuma taga project Defense slide ne, tana fita daga cikin slide din taga message kamar haka "Print out 3 copies, 1 for ur Supervisor, 2 for ur project co-odinator, to be submitted to ur external supervisor.... submit ur Supervisor's copy on Monday 5:30pm prompt" Mayraah ta fita daga cikin message din ba tare da tayi reply ba ta ajiye wayar, time din da aka sa ne ya tsaya mata, ta sake dauko wayar ta bude message din tana sake kallon time din wai 5:30pm, tabe baki tayi ta jawo handout dinta ta ci gaba da karatun ta. Washegari da safe karfe goma Mayraah na zaune hall bayan an raba masu booklet suna jiran question paper dinsu, kowa ka gani a class din kasan a tsorace yake da last paper din nan, ga malamin ba shi da kirki, don Malamin da ya kirata office yana mata masifa ne kwanaki, a haka har aka masu sharing question paper, Badiyyah na zaune seat din da take zama tun fara exams din, yau ma Hijab ne har kasa a jikinta, Mayraah ta lura duk ranan da take so tayi expo ne take sako Hijab, ranan da bazata yi ba to mayafi take sakawa, 40 minutes da fara exams din Mayraah taga Badiyyah na ta mutsu mutsu cikin Hijab, ita dai rubutunta kawai take kafin ta mance abinda ke kanta tunda bata iya rike hadda for long yanzu.... Lokaci daya duk yan ajin suka juya jin wata lecturer dinsu da ta nufi Badiyyah da sauri tana bata instruction din ta tashi tsaye cikin tsawa, tuni sauran lecturers din maza dake Hall din suma suka nufo Badiyyah, Badiyyah dake ta zazzare ido tayi kasa da hannunta ta cukuikuye wani takarda ta jefar kusa da Mayraah, Mayraah ta zaro ido tana kallonta a tsorace, tuni lecturers din suka zagaye seat dun Badiyyah, a tsakiyan Booklet dinta suka ciro papers cike da rubutu an linkesu neatly, Badiyyah ta fashe da kuka a tsorace tana nuna Mayraah cikin rawan murya tace "Wallahi ba ni kadai bace har da ita, we were passing answers to each other wllh tllh" Lecturers din suka kalli Mayraah da ta zaro ido, wani ya karasa kusa da ita ya durkusa ya dau takardan da ya gani yana instructing din Mayraah ta tashi tsaye, nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah ta ma rasa abinda zata ce tsabar rikicewa, lecturer din ya warware takardan da Badiyyah ta jefa mata yana dubawa, tuni wani lecturer har ya yage envelope din mal-practice form jikinsa na rawa ya ciro biyu ya ajiye daya kan table din Mayraah, dayan kuma kan table din Badiyyah, wani student dake zaune bayan Mayraah ya daga hannu alamar zai yi magana yace "Wallahi sir jefo ma Mayraah takardan kawai tayi da taga an kamata, amma they are not together sir" Sai a sannan Mayraah ta fashe da kuka tana girgiza kai tace "Sir u can check d paper and my answer booklet if they correlate, wallahi i am not together with her" Wata security lady da ta ta karaso cikin Hall din ne tace "Malam naga fa duk abinda ya faru, ita wancan matar me satan amsan ce ta jefo ma yarinyar nan takardan nan da ta ga an kamata, i saw everything from outside.... Tun dazu nake noticing tana mutsu mutsu but i want to be sure with what she is doing first, sai gashi Malama ta kama ta, tun fara exams din nake mata kallon mara gaskiya shi yasa ban bar wajen da na tsaya ba" Still lecturer din bai yarda ba sai da ya bude booklet din Mayraah ya duba abinda tayi da wanda ke cikin takardan yaga babu hadi, sannan ya dauke mal-practice form din daga kan table dinta, Kuka kawai Badiyyah take don gaba daya an zagayeta sai ta cika Mal-practice form amma taki yarda ta cika, can dai ta daidaici kofa ta kwasa a guje kamar barauniya ta bar class din, Lecturer din da ta kamata ta dau pen ta cike mata form din don har ID card dinta na kan table ta bar shi, kowa a class din jikinsa yayi mugun sanyi da abinda ya faru, Mayraah ta ji gaba daya komai yayi Vaporizing daga kanta tsabar tashin hankali, har sannan jikinta bai daina rawa ba, Lecturers din suka ci gaba da invigilating dinsu bayan an cike ma Badiyyah mal-practice form kamar babu abinda ya faru, ba Mayraah kadai ba a lot of student sun kasa ci gaba da rubutun exams din barin kawayen Badiyyah, shkkn fa 5 years dinta ya tafi a banza kenan, don in dai aka bude sealed envelope din mal-practice form to magana ta kare kuma, Daga karshe Mayraah ta mike kawai don bata san kuma me zata rubuta ba ta tafi tayi submitting tayi sign out ta fita daga class din, har ta isa gida bata daina hawayen da take ba, don tasan da ba don wannan Coursemate din nasu dake bayanta da Security woman din nan ba Lecturers din nan ko me zata ce baza su taɓa sauraronta ba don marasu mutunci aka hada a class din dama, tana isa hostel ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya... Badiyyah na isa gidan Maheer bata ko kalli Haseenah da cousin dinta Ramlah dake zaune Parlon ba ta shige dakinta jikinta na rawa, ko handbag dinta bata dauko a exam hall din ba, don ma Allah ya rufa mata asiri yau bata kulle dakin nata da makulli ba tunda ba wani abun da zata boye a dakin, turamen atamfar da ga sato cikin akwatin lefen Haseenah dama har ta kai ma tailor dinta ya dinka mata, zaunawa tayi gefen gado tana share zufar da ke ƙeto mata har sannan gabanta bai daina faduwa ba, can ta kwanta ta lullube da bargo ta rufe idonta don har wani mugun sanyi take ji, ko tuna abinda ya faru bata son yi, gani take tunda har ta gudu bata cike form din ba to shikenan ta tsira, kuma fa Malamin nan yace lafiya zata gama exams har ma tayi passing duk courses din, to ya haka? Ya aka yi aka kamata bayan sai da yace baza a kamata ba ko da textbook zata shiga Hall din, taga dai kwanciyar nan baxae kara mata komai ba ta mike ta fito parlor, kilan in ta gaya ma Haseenah abinda ya faru zata fi samun sauki a ranta har a samo mata solution, Haseenah na ganin fitowarta tayi shiru, haka ma cousin sis dinta Ramlah, Badiyyah ta zauna gefen kujera har sannan gabanta na faduwa ta marairaice tace "Haseenah an kama ni da expo a school" Haseenah ta dafe kirjinta ta juya da sauri ta gwalo ido tana kallonta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, final exam din?? Garin yaya haka ya faru Badiyyah, ba kin ce min Musharraf din na baki Area of concentration ba?" Badiyyah ta fashe da matsanancin kukan tashin hankali tace "Wallahi an kama ni yau Haseenah" Haseenah ta gyara zama tace "Musharraf din na hall din kuma?" Cikin kuka Badiyyah tace "He is not among our invigilators today, Haseenah don Allah ki rufa min asiri ki gaya min ya zan yi? 5 years fa Haseenah" Haseenah tace "kai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ga shi makarantar nan naku basu da mutunci har Allah Allah suke su kama mutum da mal-practice don a basu buhun shinkafa da man gyada, yanzu form din suka ciro a envelope suka baki?" Badiyyah ta silalo kasa tana rusa kuka tace "Don Allah ki taimakeni Haseenah, wallahi ji nake kamar zan mutu, ban taɓa shiga tashin hankali irin yau ba, ki gaya min yanda zan yi don girman Allah Haseenah" Ramlah dake sauraronsu ita ma cike da mamaki ta gyada kai tace "Tabdi, ae in dai jami'a ce to kinyi asaran shekaru 5 din nan wllh, babu wani abinda za a iya yi in dai dumu dumu aka kama ki" Haseenah tace "Gashi she is almost 33 yanzu fa Ramlah balle a sa ran zata fara daga farko, sau uku ana koranta a University fa, wannan duk mun sa rai zata yi graduating da muka ga ta kai level 500, duk fa mate dinta masters garemu yanzu" Badiyyah ta marairaice tana kuka tace "Ni dae ko Malamin nan naki zan kira in gaya masa abinda ke faruwa ko da abinda zai iya yi min" Haseenah ta zaro ido tace "Wani malami na? Ni kin taɓa ganin nayi harka da Malami Badiyyah? Ai bana harka da malamai, ban taɓa ba wallahi, to albishirinki dama don naga kwana biyu kina wani daɗɗaga min kai a gidan nan ne yasa na fita harkanki na kyale ki, wallahi kawata ta kirani tace ince maki ki fita sabgar malamin nan da ta hadaki ɗa shi ashe mayaudari ne ba malami bane, ya damfari jama'a ya gudu da kudadensu ya bar Zaria...." Badiyyah tace "Mutumin da yayi min aiki na kuma ga aikin yayi ne za ace ma mayaudari? Kinsan yanda muka fara zama close da Dr Musharraf kuwa yanzu duk sbda aikin da Malamin nan yayi min? To ke abinda baki sani ba last week da nace zan je Bichi da na samu intervals after our 4th paper a school, to Zaria naje wajen Malamin don ma ki ji in gaya maki" Sosai gaban Haseenah ya fadi, a ranta tace shikenan ta banu ta lalace, ynxu Badiyyah taje har gun malaminta kenan a Zaria, Badiyyah ta wani kyabe baki tace "Kuma kallonki kawai nake xaki wani ce min malamin kawarki ne bayan ashe malamin ki ne da shi kike harka, to har hotonki na nuna masa kuma yace min ae ke loyal costumer dinsa ce, yace min kun fi shekara bakwai tare yana maki aiki" Haseenah ji tayi kamar kasa ya bude ta shige tsabar yanda ta gigice har hakan bai boyu ba a fuskarta sai zare ido take, Ramlah dae ta kyabe baki tana kallon Haseenah irin maganinta kenan, Badiyya tace "To ni duk ba wannan ne a gabana ba, bari kawai inje in kirasa kar lokaci ya kure in shiga uku, don in har aka kore ni a makaranta komai zai iya faruwa da ni wllh, har fa Dr Musharraf yace min zai min hanyar samun aiki a babban asibiti as a Qualified Nurse, kafin nan ni kuma nasan duk yanda na bi muka yi aure, kuma yace min fa har kasan waje za a iya daukata aiki" Tana fadin haka ta fashe da kuka ta mike ta wuce daki ta kulle kofa, Haseenah ta daura hannu a ka tana kallon Ramlah tace "Na shiga uku na lalace Ramlah, ban san iyakan me Malam Dauda ya gaya mata ba akan alakata da shi, na shiga uku na lalace" Ramlah na hararanta tace "Ba dai ke bakinki bai tsayawa waje daya ba komai sae kin yi surutu, maganinki kenan wallahi" *If you are reading this book without payment u owe me 500 till forever* MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 [7/8, 1:41 PM] Khaleesat Haiydar💖: Bayan Magrib Mayraah ta fito kofar gida ta dalilin kiran da Maheer yayi mata, har a sannan bata gama recovering daga shock din abinda Badiyyah tayi mata dazu a school ba, gaba daya a sanyaye ta yini ranan, ɗan shayin da take iya sha ma idan ta dawo daga exams yau duk bata sha ba, haka nan ta wuni sai dai ta sha ruwa, ta zauna inda ta saba zama duk sanda yayyin nata suka zo, Maheer dai sai kallonta yake, cikin sanyin murya tace "Ina yini?" Maimakon ya amsa sai cewa yayi "What is it again Mimi? You look disturbed" Cike da damuwa yayi tambayar, nan da nan hawaye ya kawo idonta, for almost 4 weeks now bai ga hawayenta ba duk da a sati hudun nan bai fi sau biyar ya zo wajenta ba, hankalinsa ya tashi ganin hawayen nata, yayi facing dinta a rikice yana tambayarta me ya faru, cikin rawan murya tace "They caught Sis Badiyyah with Mal-practice in exam hall today, shine da taga haka sai ta jefa min takardan da take expo din" Bai san sanda ya mike tsaye ba yana kallonta babu ko kiftawa, ta fashe da kuka tana goge hawayenta da hijab din jikinta, Da wani expression yace "Ta wurga maki takardan? Ta wurga maki as in how? And what happened afterward?" Ta daga kai ta kallesa a hankali tace "A security lady saw when she did that, da kuma Coursemate dina dake bayana, duk sun ga sanda tayi haka sai suka gaya ma lecturers din" Maheer ya sauke ajiyar zuciya ya koma ya zauna, bayan few seconds yace "Amma kin gama exams din Mimi?" Tayi shiru tana kallonsa, yace "Ko baki gama ba?" Cikin sanyin murya tace "I did what i can remember, amma fa yaya an cika mata Mal-practice form don ta bar ID card dinta ta gudu daga hall din, is there nothing they can do about that so that baza a koreta ba? Kasan expulsion ne fa idan an kama mutum yaya" Maheer ya mata wani kallo yace "To ke ina ruwanki in an koreta din? Da bata samu tayi implicating dinki ba shine kika samu bakin magana? What if babu wanda ya ga sanda tayi hakan kin zata ke ma baza a sa ki cike form din ba a kore ku tare? ni dama tun farko nace school is never for Badiyyah, ban san me yasa aka dage sai tayi karatu ba, going to school was neva her calling, kilan yanzu da aka koreta for the 4th time kowa zai hakura da cewar sai tayi karatu a fara nema mata wanda za a lallaba ya aureta" Ita dai Mayraah bata ce komai ba, yace "Nasan baki ci abinci ba" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya, ya mike yace "Mu je in siya maki abun da za ki ci" Tace "Ai Ummi bata dakin tana school, the door is open" Yace "Ba ta baki spare key din dakin ba, just close it, mu je mu dawo yanzu...." Mayraah ta mike ta wuce ciki ta kulle kofar sannan ta fito, zaune ta samesa cikin mota yana jiranta, ta karasa ta bude front seat ta shiga motar, har suka bar area din Maheer na jinjina abinda Badiyyah tayi a ransa, shi bai taɓa ganin shaidaniya in human form kamar Badiyyah ba she can go to any extent don yi shaidanci kanta tsaye, ya girgiza kai cike da takaici, can ya juya ya kalli Mayraah da tayi shiru tana tunani ita ma, yace "Wato tana ganin an kamata sai ta fita da gudu daga hall din?" Mayraah bata sanda tayi murmushi ba bayan ta tuna yanda Badiyyah ta gudu daga hall din, Maheer har ya mance rabon da ya ga murmushinta, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, he wish she will continue smiling like this forever, Mayraah ta kasa controlling kanta ta fashe da dariya tana kallonsa tace "Yaya u need to see how she jumped and ran out of the hall, Kuma fa first day da muka fara exam din wannan Dr Musharraf din ya kamata da waya tana satan amsa amma yayi covering dinta ya amshe wayar without anyone noticing" Maheer dake sauraronta yace "Akan wani dalili yayi covering dinta? He saw her with expo kuma yayi covering dinta wani irin lecturer ne shi?" Mayraah dai tayi shiru, Maheer yace "Toh ke me yasa ma ku ka zauna waje daya da ita at the first place?" Mayraah ta kallesa tace "Kawai tun first day da muka fara exam din naga ta zauna gefena, shine kullum take zama side dina" Maheer ya girgiza kai yace "Sai taje ta gaya ma wa enda suka dage sai tayi karatu abinda ta aikata on her final paper, it's better she go and learn tailoring in dai ba a samu wanda zai aureta ba yanzu" Mayraah tace "Ai kai ma zata gaya maka abinda ya faru yau" Yace "Saboda me zata gaya min?" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Ba ka maida ta gidanka ba yanzu, kaga kai zata fara gaya ma kafin kowa ma" Juyawa yayi ya kalleta da sauri, lokaci daya ya maida idonsa kan titi cike da mamakin yanda tayi tasan Badiyyah na gidansa, bayan some seconds yace "Wa ya gaya maki tana gida na?" Mayraah ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "To ai ba wani abu bane don tana gidanka tun da yar uwarka ce, she is ur blood" Maheer bai ce mata komai ba cause he don't want to talk about that again, yayi parking inda yake son siya mata abincin sannan ya juya ya kalleta, a hankali yace "Mu je" Ta girgiza kai tace "I will wait here Yaya" yace "Saboda me?" Ta jinginar da kanta jikin kujeran motar tace "I am tired" ya gyada mata kai yace "To me zan siya maki?" Tace "Anything" Bude motar yayi ya sauka, ya wuce ciki ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, ignoring din maganarta na karshe da yayi ya mata ciwo sosai, shirun da yayi mata ya nuna Yes Badiyyah blood dinsa ce. Karfe tara saura Maheer ya ajiye Mayraah a hostel, ta bude motar ta sauka rike da ledan abincin da ya siya mata, a hankali tace "Sae da safe" ya gyada mata kai yana kallonta don tun da suka baro wajen siyan abinci ta zama so silent, zata juya ta wuce ciki yace "Wait Mimi" juyowa tayi ta kallesa, yayi kasa da murya yace "How about ur project?" Tace "Na gama, on Monday zan yi submitting" yace "Ohk, kar ki kashe wayarki zan kira ki anjima" ta gyada masa kai sannan ta juya ta shiga ciki ya ja motar ya kama hanyar gida... Maheer na isa gida ya tadda Badiyyah kadai zaune a parlor, har ya shigo tsakiyar parlon bata sani ba don tayi nisa cikin tunanin da take, ta saka wancan ta warware wannan duk nan neman solution take ma chakwakiyar da ta jefa kanta yau, she just can't imagine ace yau da gaske an koreta a school, tare suke zaune da Haseenah a parlorn, amma Haseenah na jin shigowar motar Maheer ta ruga dakinta da gudu wai zata je tayi wanka don tun safe bata yi wankan ba, Maheer ya gyara tsayuwarsa yana kallon Badiyyah ganin alamar bata san yana tsaye kanta ba yace "How was ur exams?" Firgit ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, ta juya da sauri tana kallonsa, ta ɗan sosa kai tana murmushin yake tace "Sannu da dawowa yaya" Yace "Sannu, ya exams din?" A hankali tace "Alhamdulillah" yace "Shikenan kun gama kenan ko?" Ta gyada masa kai ba tare da ta bari sun hada ido ba, kana ganin yanda take muzurai kasan bata da gaskiya, yace "To Maa sha Allah, Allah Ubangiji ya baku sa'a, ya baku cleared pass gaba daya" Badiyyah dai taki cewa komai sai sosa kai take, dakinsa ya wuce, yana shiga ya kulle kofa.... Badiyyah ta mike ta wuce nata dakin ta shiga ta kulle ta zauna kasa ta fara shesshekan kuka ta daura hannu a ka, tun dazu ta kasa cin komai tsabar tashin hankali ko ruwa ta kasa sha, bata taɓa shiga damuwa irin na yau ba, ga Haseenah is not helping matters at all don duk shawaran da Badiyyah ta kawo a matsayin mafita sai Haseenah ta kyabe baki ta gwale shawaran tana girgiza kai tace ai fa nace maki ko da uban wa kike yawo kin riga kin koru a makarantar nan kawai, wannan kalman ke kara rikita Badiyyah ya sa tashin hankalinta ya ninku, gashi har yanzu bata samu Malam Dauda a waya ba balle ta gaya masa abinda ke faruwa, ta kirasa har ta gaji da kiransa, wayarta ne ya fara ring ta dauka da sauri taga Malam Dauda da take ta kira ne ya biyo ta yanzu, hannunta na rawa ta daga kiran ta kai kunne ta fashe da matsanancin kuka ta hau gaya masa abinda ya faru, daga karshe tace "Kuma Malam kai fa kace min ko da katon littafi na shiga babu wanda zai kamani, gashi da yan kananun takarda na shiga aka kamani" Sai da suka yi minti goma sha biyar suna waya daga karshe ta ajiye wayar bayan sun yi sallama, nan kuma ta fara tunanin inda zata samu dubu arba'in din nan da yace ta bada ayi aiki, ita dae ta shiga uku, ko dubu ashirin babu a account dinta yanzu haka, gashi yace tana turowa cikin daren nan zai fara aikin rufe bakin duk lecturers din dake nan sanda abun ya faru, hakan zae sa a kasa koran nata, zumbur ta mike ta fice daga dakin tayi hanyar dakin Maheer, ta tsaya jikin kofar dakin tana tunanin abinda zata ce masa, can dai ta kwankwasa kofar a hankali, dae dae nan Haseenah ta fito daga dakinta sanye da kayan bacci ta baxa uban turare a jiki, tana ganin Badiyyah ta hade rai ta tsaya tana kallonta daga sama har kasa, Badiyyah dai ko kallon inda take bata yi ba ta sake kwankwasa kofar dakin, bude kofar Maheer yayi ya kalleta sannan ya kalli Haseenah dake tsaye ta wani murtuke fuska, ya maida dubansa kan Badiyyah yace "Ya aka yi Badiyyah?" Badiyyah ta dawo gefensa ta langwabar da kai ta marairaice murya tace "Yaya dama don Allah akwai wani abu da nake son siya ne, kuma bani da kudi wllh" Yace "Ohk nawa ne kudin" ta sunkuyar da kai tace "Dubu hamsin" Yace "To zan tura maki" Da sauri ta kallesa ta wani washe baki tace "Nagode sosai yayana, Allah ya kara maka budi" Yace "Ameen" Juyawa tayi cike da farin ciki ta koma dakinta, Haseenah ta dinga kallon Maheer da yaki kallonta ya kulle kofarsa, kofar ta nufa a fusace ta bude ta shiga ta tsaya tana kallonsa tana huci tace "Maheer tun yaushe nake ce maka ina bukatar kudi kaki bani shine yanzu zaka dau har dubu hamsin ka ba ma wancan gantalalliyar da sae dae ta siya kwaya da kudin? dama da ni da ita wanene haƙƙinsa ke rataye wuyanka? wanene yafi cancanta ka ba ma kudi tsakanina da ita?" Maheer ya daga kai ya kalleta yace "Ita ma haƙƙin nata ya kusa dawowa wuyata gaba daya kamar yanda naki haƙƙin ke wuyata, daga sannan zaki ga ita ma ta cancanci a bata kudin" kallonsa Haseenah ta dinga yi babu ko kiftawa as if trying to understand what he meant by saying so, can dai tana stammering tayi karfin halin cewa "Ban fahimci abinda kake nufi ba Maheer" A takaice yace "Zaki fahimta nan ba da dadewa ba, dama bana son ki fahimta da wuri sae lokacin yayi" Yana fadin haka ya mike ya fita daga dakin ya bar ta tsaye tana bin sa da kallo kamar idanuwanta za su fito tsabar kidimewa. Daren ranan nan Haseenah bata yi baccin kirki ba, da tayi zata farka a firgice saboda mafarkin Badiyyah, daga karshe ma parlor ta dawo ta zauna, ita ba sallah ba balle salati, da asuba tana jin Maheer ya fito daga dakinsa, tsaye yayi corridor yaki karasawa parlon ganin wutan parlon a kunne, can dai ya ɗan leka ya hango Haseenah zaune tayi tagumi, tun da aka kawota gidan bai taɓa ganin ta tashi da asuba ba, ko ya tasheta tayi sallan asuba bata tashi, yawanci sai gari ya waye tar take sallan asuban ta, yana ganinta a parlon ya nufi dakin Badiyyah ya fara knocking kofar dakin, Haseenah ta daga kai da sauri jin yana kwankwasa kofar dakin Badiyyah, mikewa tayi tana lekan corridor din taga ya bude kofar dakin yana kallon ciki yace "Ki tashi kiyi sallah lokaci yayi" Haseenah ta koma kan kujera ta zauna da sauri, ita kanta bata san wani kalan abu take ji a ranta ba tun daren jiya, har wani heartburn ke damunta tsabar tashin hankali, Maheer ya fito Parlon yayi mata kallo daya ya wuce masallaci, ta mike ta hau zaga parlon tana jin zuciyarta na mata tukuki, maganganun da ya gaya mata jiya a dakinsa ne kawai ke yawo mata a ka, daga karshe ta shige dakinta tana wani murmushi. Karfe goma saura Badiyyah ta fito daga dakinta, baccinta tayi har da minshari daren jiya tun bayan da Malam Dauda ya bata assurance babu wanda ya isa ya koreta a makarantar, sanye take cikin riga da skirt sai ɗan figigin mayafinta da handbag alamar fita zata yi, Haseenah na zaune dining area abun duniya ya taru ya mata yawa tayi nisa cikin sake saken da take a zuciyarta na nema ma kanta mafita, bata san ma sanda ta fito parlor daga cikin dakinta ba har ta zauna kan dinning chair tsabar tunani, ɗaga kai tayi jin kamshin turare ya baɗe parlon, suka hada ido da Badiyyah, sai da taji wani mugun faduwan gaba, Badiyyah ta nufeta tace "Ina breakfast din Haseenah?" Wani bacin rai da takaici ya zo ma Haseenah har wuya ta dinga jin zuciyarta na wani tafarfasa tayi mata banza ta ki cewa komai, Badiyyah ta bude coolers da ta gani kan dinning taga babu komai ciki, ta wuce kitchen nan ma taga ko ruwan zafi Haseenah bata dafa a gidan ba, Badiyyah ta fito a fusace tana kallonta tace "Amma dai gaskiya baki kyautawa Haseenah, wannan ai mugunta ce da baƙin hali, yanzu haka kike son in fita ban karya ba kenan? mutum na gidanki amma ki dinga barin sa da yunwa saboda ke muguwa ce" still Haseenah ta mata banza sae girgiza kafa take, juyawa Badiyyah tayi a mugun fusace ta nufi corridor zuwa dakin Maheer kamar zata tashi sama, ta kwankwasa kofar tana jiransa ya bude, yana bude kofar tace "Yaya wai kana ganin yau ma Haseenah bata yi ma mutane breakfast a gidan nan ba ko? Haka jiya ta sa na tafi exam hall ban ci komai ba nayi exam din ina jin yunwa da jiri na gama na fito, yanzu kuma zan je gidan Hajja na je zan dau breakfast naga ko kunna gas din matar nan bata yi ba" Duk Haseenah na jin abinda Badiyyah ke cewa saboda cikin daga murya take maganar, Maheer ya fito daga dakin ya dawo parlor Badiyyah na biye da shi a baya, kallon Haseenah dake zaune dining yayi yace "Ke me yasa baki girka breakfast din ba?" Haseenah ta masa wani matsiyacin kallo tace "Ko kai yau baka isa in maka breakfast a gidan nan ba balle wata katuwa can" Badiyyah ta nufeta tana huci tace "Shi yayan nawa kike gaya ma magana haka saboda baki da tarbiya??" Haseenah dai taki ce mata komai don tana buda baki bata san kalan tereran da Badiyyah zata mata ba a wajen shi yasa tayi mata shiru tun daxu, Maheer na kallon Badiyyah yace "Ki shiga dakina ki dauko min makullin mota in ajiye ki gidan Hajjan, idan kin je can sai kiyi breakfast din" Badiyyah ta galla ma Haseenah wani harara ta bar parlon, Haseenah ji tayi kamar numfashinta zai dauke don takaici, wai Badiyyah taje dakinsa?? to ko Mayraah da ta zauna gidan nan bata taɓa tsayawa bakin kofar dakinsa ba balle ta shiga dakinsa, wasu hawaye ne suka cika idonta ba tare da ta sani ba, a haka Badiyyah ta dauko makullin motarsa ya amsa tayi ma Haseenah gwalo ta bi bayansa suka fice daga parlon, Haseenah ta fashe da matsanancin kuka ta zamo kasa ta zauna tace "Na shiga uku na lalace ta ina zan fara ni Haseenah" Maheer na ajiye Badiyyah kofar gidan Hajja ta sauka tana kallonsa tana washe baki tace "Baza ka shigo ku gaisa da Hajja da Ammi ba Yaya" Ya dake yace "Sauri nake" Daga haka ya ja motarsa ya bar wajen ta dinga daga masa hannu kafin ta shiga gidan cike da farin ciki, sai da ta tsaya jikin kofar parlon ta kasa kunne, Hajja dake zaune parlorn rike da cup din kunu tana kallon Ammi dake linke kayanta cikin akwati tace "Hakuri kawai za ki yi, ko don yaron nan Maheer, dubi yanda ya daga hankalinsa kullum sai ya zo gidan nan yaro ɗan albarka me gudun zuciyar uwarsa, ga kuma Umar da ke hanya gobe, kin ga bai kamata ya dawo ace baki gidan ba tunda shi bai san abinda ke faruwa ba har yanzu, gwara kuma da ba a gaya masa ba kar aje karatunsa ya samu matsala, amma wannan yaron naki Usman kam ki binkita ko canja maki shi akayi a asibiti gaskiya" Ita dae Ammi bata ce komai ba hada kayan nata kawai take, Hajja tace "Duk ɗan kwarai baxai banzatar da uwarsa yanda Usman yayi ba...." Ammi ta katseta tace "Yana fa kirana a waya ke ce dai baki sani ba Hajja" a fusace Hajja tace "Kiran banza kiran hofi, shi Maheer kiranki yake ba zuwa yake ba da yake yana son gamawa da duniya lafiya, kawai kin haifi jaraba kawai, azzalumin yaro, wllhi yana nan sae yayi mamakin matsayin da Badiyyah zata kai a rayuwar nan, kuma sae yayi da ya sanin duk abinda yayi mata, da na dauki duk jikokina daya a zuciyata amma yanzu kam kowa da matsayinsa wallahi, ko da wasa kada Usman ya nuna yasan Badiyyah wataran" Ita dae Ammi bata sake cewa Hajja komai ba, Badiyyah ta bude kofar parlon ta zube kasa ta rushe da kuka sosai ta kwanta, tsabar gigicewa sae da Hajja ta kusa zubar da kunun hannunta ta mike da sauri ta nufeta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, lafiya Badiyya, me ya faru" Ammi ma ta nufeta hankali a tashe, Cikin kuka Badiyyah tace "Hajja jiya za mu yi jarabawa a aji na manta na shiga da wani takarda a hannuna shine Mayraah ta kira wata malama a ajin tace mata gani can na shigo da satan amsa, kuma wallahi ba satan amsa bane wani takarda ne daban, yanzu an koreni a makarantar gaba daya Hajja" Hajja ta juya ta kalli Ammi da ta nemi waje ta zauna tana kallon Badiyyah da mamaki jin abinda take cewa, ita dai Badiyyah rusa kuka kawai take duk ta cika parlon da kururuwarta tana cewa ita fa an koreta a makaranta saboda Mayraah, Hajja tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ita Mayraahn ta maki wannan sharrin? kuma ke baki da bakin da zaki ce masu ba satan amsa bane a hannunki Badiyyah? Yau ga matsiyaciyar yarinya, sai yanzu na kara tabbatar da karin maganar nan na Hausa da suke cewa tsintattciyar mage bata mage, In da can suna mata kallon er uwarki a makarantar ke baza ki buda baki kice masu babu abinda kika hada da ita ba yanzu ba ma ta gidanku? Iyye Badiyyah?" Cikin kuka Badiyyah tace "Babu wanda ya saurareni wallahi Hajja, kawai korata suka yi" Ammi da duk jikinta yayi sanyi ta mike ta shiga daki tayi dialing number Maheer har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma no response, ta fi minti biyu tsaye parlon kafin ta dawo parlor, taga Hajja zaune ta cika famm kiris ya rage ta fashe, Ammi ta kwantar da murya tace "In sha Allahu ma ba a koreki ba Badiyyah, na kira Maheer ina jin ba ya kusa da waya da sai in ji yanda za ayi ko zuwa makarantar za ayi a samu malaman in ya kama ko nawa ne a basu su yi hakuri, kuma ke ma ai tun jiya kuna fitowa daga exams din ya kamata ki zo ki sanar da abinda ke faruwa" Badiyyah na shessheka tace "Gidan ya Maheer kawai na tafi shi kuma bai dawo ba sai da daddare sannan nayi bacci, shine yanzu da safe na zo nan" Ammi ta zauna tace "In sha Allahu za a san yanda za ayi, za a samu malaman" Duk da Ammi har cikin ranta take jin she have nothing to do with Mayraah anymore, ta dalilin Mayraah ta ga abubuwa marasu dadi da bata taɓa expecting a rayuwarta ba, ta dalilin Mayraah yau rabonta da gidan mijinta wata daya currr kuma har a lokacin ko bin ta kanta Abba bai yi ba, yanzun ma ba don Hajja da ta tilasta ta koma gida saboda Umar dake hanya ba ko shekara nawa za suyi ita da Abba a haka sai dai su yi, wai duk ta dalilin er da ba karamin jahadi tayi ba na rainonta tun tana tsumma, er da da farko kin amincewa yayi ta rike ta, shine yau saboda ita yayi mata wannan rashin mutuncin da girmanta da shekarunta, bata taɓa da ta sanin abinda ta aikata na alkhairi irin wannan ba, tayi da ta sanin don ko jin sunan Mayraah ma bata son yi, duk da wannan abubuwan amma deep down tasan Mayraah bazata yi abinda Badiyyah tace ba, dama can Badiyyah na da history din satan amsa a koreta a school, idan kuma ba satan amsa ba to point din ta will be very low har sai an koreta a makarantar, Hajja tace "Mu muka ga karshen taimako, dama ance ba kowa taimako ya ke amsa ba, mu kam bai amshe mu ba wallahi" [7/8, 5:15 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer na zaune parlon Hajja wajen karfe biyu da rabi na rana bayan kiran da Ammi tayi masa, duk tunaninsa gida zai maida ta kamar yanda dai suka tsara a jiya da ya zo gidan, don ba karamin kai ruwa rana akayi ba kafin Ammi ta yarda zata koma gida, at first she was reluctant don tace ita da komawa gidan Abba sai dai wani ikon Allah kuma, kusan kullum idan Maheer yaje gidan hakuri kawai yake bata ta janye vow din nan da tayi ta koma gida, yawanci ma abinda ke kai sa gidan Hajja kenan kawai ya ba Ammi hakuri har cikin ransa he is not happy da zaman gidan Hajja da take, gashi ba isassun dakuna, don ma Badiyyah na gidansa banda haka dole sai dai tayi sharing daki da bandaki da ita don yasan Ammi bazata dinga kwana dakin Hajja ba, to a jiya sai da Hajja ta saka baki har da nuna bacin ranta, wanda a baya idan yana ma Ammi magiyan ta koma gida sai dai Hajja ta kyabe baki ta kauda kai, wani lokacin kuma tace shi Mamudan ai bai biyota ba har yau balle ta kwashi kafa ta koma masa gida kamar bata da gata, to jiya dai kam Hajja ta saka baki kan Ammi tayi hakuri kawai ta koma don 'ya yanta amma ba don Mamuda ba, wanda hakan na nuni da ita ma abun ya fara isarta tunda Abba yaki waiwayansu balle ya biyo su har sannan, da yake Ammi na jin maganar Hajja kuma bata son duk abinda zai sosa ranta wannan yasa kawai ta yadda zata koma amma ba don ranta ya so ba sai don babu yanda ta iya, Shiru Maheer yayi yana kallon Hajja har ta kai aya rai a bace, Maheer ya ma rasa abinda zai ce tsabar mamaki, kullum sake mamakin mugayen halin Badiyyah yake, dama tun da ta kyallara ido ta ga ya shigo gidan ta saka kai ta fice daga gidan tunda tasan abinda ta hada, after few seconds Maheer ya girgiza kai very careful with his words kar ya tunzura Hajja ko ya bata ma Ammi rai yace "Hajja karya Badiyyah take gaskiya, jiya da na koma gida idonta biyu bata yi bacci ba don a parlor na sameta zaune har na tambayeta ya jarabawa tace min Alhamdulillah, amma ku nan tace maku ai tayi bacci kafin in koma gida, yanzu kawai abinda zai faru kamar yanda Ammi tace aje a samu Malaman sai mu je tare da ke ko Ammin ai suna wajen sanda abun ya faru sai su mana bayanin duk yanda aka yi a ajin, ae su baza su yi karya ba" Hajja ta katse sa tace "Ka ji ka da wata magana, zuwa za ayi a titsiye su kake nufi kenan, mutanan da za aje a lallaba su yi hakuri su bar ta ta koma ta ci gaba da jarabawanta kake so a je a kure, ai zuwa kawai za ayi a lallaba su ba wai a titsiye su ba, cuta ne an riga an cuceta kawai sae kuma neman mafita" Maheer ya gyada kai don bai son jan zancen yace "Toh shikenan, zan je makarantar ranan litinin in sha Allah" Hajja ta hade rai tace "Me ya hana baza ka je yau ba sae Litinin?" Yace "Yau asabar babu makaranta ai, sai Litinin din" Hajja tace "To Allah ya kai mu, amma ina lafiya za a kori yarinya da tayi shekara biyar tana wahala a makaranta ga uban kashe kudi" Maheer ya kalli Ammi yace "Za mu tafi ne yanzu Ammi?" A takaice Ammi tace "Ban shirya ba" Shiru yayi, sai kuma ya mike yace "Toh zuwa Anjima zan dawo" Ammi tace "Kar ka ba kanka wahala ban yi niyyar zuwa ko ina yau ba" Hajja tace "Aa ke kuma, anjima da la'asar kawai ya dawo ya kai ki gida tunda haka aka tsara idan ya so ranan litinin din sai yaje can gidan ya dauke ki ku je makarantar tare a ba Malaman hakuri, idan ma wani abu za a basu ko kaɗara na ne sai in siyar a basu" Maheer dai yayi masu sallama ya juya ya fita daga Parlon, shi dai ba kawai ya ji su ba ya kuma lallaba ya bar parlon ba tare da yayi masu musu ba, sun zata primary school ne da za aje a ba Malaman hakuri, motarsa ya shige ya bar anguwan, ban da yana da plan dinsa na barin Badiyyah a gidansa da yau ya koreta wallahi but there is still time. Da sallama Maheer ya shiga parlon Abba ta dalilin kiransa da yayi shi ma, don ko gida bai karasa ba daga gidan Hajja sae ga kiran Abba, hakan kawai yasa ya nufi gida maimakon gidansa da yayi niyyar komawa, tun shigowarsa gidan mood dinsa ya canza gaba daya don har bai son zuwa gidan saboda rashin Ammi da Mayraah, the house is soo empty without them, ya zauna ƙasan carpet ya gaida Abba dake duba wasu takardu, Abba ya amsa sannan yace "Yauwa kace Mayraah sun gama jarabawan ae ko?" Yace "Eh sun gama" Abba yace "Good, kaje ka dawo da ita da kayanta gaba daya yau" Maheer yayi shiru yana kallonsa shi ya so ace sai Ammi ta dawo kafin Mayraah ta dawo gidan, Abba yace "Ko kuna da wani plan da ku ka kulla kai da uwarka ne kake kallona haka?" Maheer ya sunkuyar da kansa bai ce masa komai ba, Calmly Abba yace "Wai ma tsaya tukunna in tambayeka, ana nufin ni a gidana bani da wani say sai abinda uwarka da danginta suka shirya? Yau ko ba Mayraah ba idan nayi niyyar kawo yara goma gidan nan akwai wanda ya isa yayi questioning dina akan haka? To a yau ba sai gobe ba nace ka dauko Mayraah ka dawo da ita gida tun da sun gama jarabawan" Maheer ya gyada kai cikin sanyin murya yace "Dama zan dawo da ita kamar yanda kace Abba, kawai nayi tunanin sai zuwa next week tun da basu gama project ba har yanzu" Abba yace "To yau nace ka dawo da ita ba next week ba, zata karasa project din a nan, wai ku kuna ma da imani kai da mahaifiyarka da danginta kuwa? That gal is an orphan, ta taso bata san kowa ba sai mu, all of a sudden this unforeseen circumstance came from no where, idan bamu ja ta jiki mun yi consoling dinta ba a wannan stage din depression ake son ta shiga at her young Age?? she neva bargained for this, ita haka Allah ya kaddara mata kuma babu bawan da ke wuce kaddararsa, wallahi Baabarka ta ban mamaki ainun, ba a taɓa disappointing dina irin yarda mahaifiyarka tayi disappointing dina ba, da wannan abun da tayi ma ni da Mayraah akan selfish interest dinta da relatives dinta wllh gwara ace asara nayi na miliyoyin kudi, ban taɓa expecting haka daga gareta ba ko a mafarki, kuma in har tana ganin ita bazata iya dawowa gidan nan don ta ci gaba da rike Mayraah ba to ta sha zamanta duk inda take, don ni a jiya na riga na auro warce zata zauna tare da Mayraah a gidan nan, na kara aure saboda Mayraah, da ban yi niyyar gaya maku ba sae dai ku gani da idonku amma ynzu na gaya maka zuwa anjima ita warce na auran zata tare in sha Allah, wannan ne dalilin da yasa nace ka dawo da Mayraah gida, ita kuma mahaifiyarka taje can ta karata for all i care, all this while da kaga na amince da zaman Mayraah a hostel saboda nasan bazai yiwu ta zauna ita kadae a gida ba ni na tafi sabgogina, kai kana gidanka Usman kuma bai gari, shi yasa kawai na hakura da zamanta a hostel...." Maheer ya dinga kallon Abbansa babu ko kiftawa, and u can see the shock written all over his face, kasa cewa komai yayi tsabar yanda ya girgiza, Abba yace "In kuma baza ka je ka daukota ba ni zan je in daukota da kaina a hostel din yanzu" Maheer ya mike still bai daina kallon Abba ba, he was speechless to ya ma rasa abinda zai ce, can ya juya ya fita daga parlon ya kulle masa kofa, sai a sannan yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Har ya fara sauka downstairs kawai ya juya da sauri ya sake komawa Parlon Abba, sosai hankalinsa ya tashi yana shiga parlon, Abba ya daga kai yana kallonsa, Maheer ya karasa ya zauna pleadingly yace "Abba don girman Allah kayi hakuri ka janye batun auren nan, wallahi yau Ammi tace in je in daukota zata dawo gida...." Abba ya dakatar da shi yace "Ohk ita kuma warce aka daura mana auren da ita jiya sai in saketa yau saboda mahaifiyarka zata dawo ko me kake nufi?" Maheer yayi kasa da murya cike da damuwa yace "Abba masalha fa ake nema..." Dakatar da shi Abba yayi yace "Bana neman wannan masalhar, da mutunci na da furfurata mahaifiyarka da danginta suka walakanta ni suka nuna ban isa ba duk akan son zuciya irin tasu, to ni ba karamin mutum bane Maheer, aure ne an riga an daura kuma yau matar zata tare na sa an mata furnishing dakin Mayraah, Mayraah kuma zata koma dakinka nan din ma na sa an gyara, kai kuma duk sanda ka zo da iyalinka zaku iya sauka Chalet din gidan, period, go and bring back my daughter home.... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 *Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake* [7/9, 9:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya jima zaune a parlor bayan ya sauka downstairs, gaba daya kansa ya ƙulle ya rasa wani tunanin zai yi, gashi da yamma yace zai je ya dauko Ammi yasan kuma in dai suka ji wannan abinda Abba yayi ba lallai Ammi ta yarda ya dawo da ita gidan ba, to amma me yasa Abba zai yi haka Ammi bata yi deserving haka daga garesa ba, rike kansa yayi, he is really confuse at this point don gaba daya he was short of idea, mikewa yayi a sanyaye, to wa ma zai gaya ma wannan maganar yanzu, Aunty Mariya ce ta fado masa ya fita compound yayi dialing numberta, tana dagawa bayan sun gaisa tace "Ka kai ta gidan ne Maheer?" Yayi wani ajiyar zuciya me cike da damuwa, duk da Aunty Mariya na kaduna sam bata jin dadin zaman da Ammi take tayi a gidan Hajja ta ki komawa gidanta for more than a month now, kusan kullum ita ke encouraging Maheer kar ya gaji da zuwa gidan Hajja ya dinga ba Ammi hakuri ta koma gidanta, ita dai fatanta ace Ammi ta koma dakinta a ko da yaushe addu'anta kenan, jin Maheer yayi shiru, Aunty Mariya da gabanta ya fadi tace "Ta canza shawara kuma ko?" Maheer ya girgiza kai a sanyaye yace "Aunty Abba ne ke sanar min ya kara aure.... He is just telling me now" a tsorace Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ya kara aure kamar yaya Maheer? Aure fa kace" Maheer ya kasa ce mata komai, cikin kidimewa tace "Ban gane ya kara aure ba, shi Abban ya gaya maka haka?" A hankali Maheer yace "Yanzu haka daga parlonsa nake Aunty, ya tabbatar min yayi aure jiya kuma yau matar zata tare sannan kuma ni ga yanda muka yi da Ammi kan cewar yau zan je in daukota, akwai fa matsala Aunty, Ammi gani zata yi kamar nasan da auren Abba na mata shiru kuma na tilastata ta dawo, ni kuma wllh he is just informing me now" Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wannan wani irin fitina ne daga wannan sai wannan duk Mama Ladi da Badiyyah suka ja mugayen abubuwan nan dake faruwa, yanzu ina Mayraah din? last time da na kirata tace min sauran masu 3 papers to ban sake waya da ita ba har yau, is she still in the hostel?" Maheer bai ma son ya furta ma Aunty Mariya kalman da Abba yayi wai zai kara aure saboda Mayraah don shi ma sai da abun ya dakesa, Abba look into his face yace zai auri warce zata rike masa Mayraah ya mance duk rikon da Ammi tayi mata kamar ita ta haifeta wanda ko da wasa su kansu basu san wacece Mayraah ba sai da wannan abun ya faru, kawai ya girgiza kai cikin sanyin murya yace "Sun gama on friday, yau kuma zan daukota daga hostel in maido ta gida" Aunty Mariya ta rasa abinda zata ce duk jikinta yayi mugun sanyi and she felt for her sister, ya da kuruciyarta ba a mata kishiya ba sai yanzu da ta fara ajiye surkai, nan da nan hawaye ya cika idon Aunty Mariya tana girgiza kai tace "Maheer this is seriously getting out of hand, yanzu sake blaming Mayraah din za su yi, dama suna ganin ta dalilinta komai ya dagule to ga uwa da uban dagulewa yanzu kowa zai gani, kaga shkkn sai su tabbatar da abinda suke tunani a ransu don yanzu ma cewa za su yi gashi Abban yayi aure duk a ta dalilin Mayraah, wannan wani irin fitina ce, me yasa Abba bai yi hakuri ba tun da yasan ba halin Ammi bane wannan, me yasa zai saka mata da haka bayan duk gwagwarmayar da suka sha tare a rayuwa, fisabilillahi sai da shekarunta zai kawo mata abokiyar zama saboda shaidan ya shiga tsakani??" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Maheer dai ya kasa cewa mata komai duk jikinsa yayi mugun sanyi, Aunty Mariya ta matsar da abincin da take ci don gaba daya ya fice mata a rai, hankalinta yayi mugun tashi da batun nan da Maheer ya kawo mata, ko ya Ammi zata dau wannan labarin, ita ma ji yanda taji balle Ammi, da ba don uwa uwa bace da sai tace duk Hajja ce ta ja ma Ammi, duk Hajja ta kara rikita wannan al'amarin haka, kuma Badiyyah ita ce babban silar faruwa komai, hawaye kawai take ta kasa magana tana jin zuciyarta na zafi kamar ita aka ma kishiya, suka yi shirun kusan minti daya ko wannensu da tunanin da yake a rai, Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Yanzu Aunty ki bani shawaran yanda za ayi, bana son Ammi taji haushina in anyway, gani zata yi i know everything, kuma in dai tasan da batun kishiyar nan nasan bazata dawo ba Aunty" Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya tana share hawayenta tace "Kawai ka bari gobe lahadi zan shigo da safe zan nuna kawai na zo bikina, idan ya so sai in rakata gidan, in mun koma gidan we will sort things out a samu ta fara komawa gidan dai tukunna, don tabbas kana maidata gida Anjima duk bayanin da zaka mata bazata fahimceka ba za ku ma taga kamar da hadin bakinka aka mata haka, ka bari kawai ni zan zo gobe in rakata mu koma gidan, kawai ka basu wani uzurin ko na emergency a asibiti sai kace gobe zaka je ka dauketa ka kai ta gidan" A hankali Maheer yace "To Aunty, Allah ya kai mu goben" Tace "Umar din ya iso ne?" Ya girgiza kai yace "Anyi delaying Flight din nasu gobe zai iso in sha Allah" Aunty Mariya tace "Toh Allah ya kai mu, ita ma Mayraah kar ka maidata gidan yau, it's better gobe ta same mu gidan ba mu sameta ba kilan abubuwan za su fi zuwa mana da sauki" Maheer ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "But Abba insisted sai na maidota yau fa Aunty, instruction din da ya bani kenan" Aunty Mariya tace "Just find a way out Maheer, kayi duk yanda zaka yi sai gobe zata koma gidan, zan kira ka anjima har kaina ya fara ciwo wallahi, wannan wani irin jarabawa ne astagfirullah" katse wayar tayi, Maheer ya fita daga gidan ya shiga motarsa ya wuce gida ransa duk a dagule. Mayraah ta saka hijab dinta ta fito waje ta dalilin kiranta da aka yi, yana tsaye jikin mota ya rungume hannunsa, ɗan murmushi tayi ta karasa kusa da motar tana kallonsa tace "Ina yini Yaya?" Yace "Lafiya lau, how was the final exams?" Tace "Alhamdulillah" yace "Saura project" Ta gyada kai tace "I am submitting on monday in sha Allah, yaya yaushe ka dawo?" Yace "Not long ago" Tace "Ya aiki?" yace "Alhamdulillah" Ta jingina da motar tace "Ya Maheer yace min yau ya Omar zai dawo, is he back?" Usman ya girgiza kai yace "Sai gobe in sha Allah, ki shiga ki dauko kayanki, za mu tafi gida" Sosai gabanta ya fadi nan da nan mood dinta ya canza ta kafesa da ido babu ko kiftawa, shi dai kallonta kawai yake, haka kawai Mayraah taji da ma kawai ita dai ta ci gaba da zama a hostel din in ma na har abada ne, she is tired with the way things are happening all of a sudden, bata awa daya kalaman Ammi na karshe basu fado mata a rai ba, wani lokacin ta ɗan yi murmushi, wani lokacin kuma taji hawaye na sauko mata, sai taga kamar tafi samun rest of mind zaman da take a hostel din duk da ba wai damuwanta ya yaye bane, a'a har yanzu tana cikin damuwan sosai ma but baza ta so ace ta koma gidan nan ba ko a mafarki, Usman dake ta kallonta as if reading her mind yace "Ko nan din gidanku ne da baza ki bari ba Madam?" Nan da nan hawaye ya fara zuba idonta, ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yayi kasa da murya yace "Za ki koma gida Mayraah, it's still ur home baki da wani wajen da ya wuce can, baki san ko ina ba sai can, as far as we are concern bamu da wata kanwa da ta wuce ke, Abba yace in je in dauko ki, ko gida ban karasa ba na taho nan, so go and pack only ur clothes ki bar ma Ummi duk wani foodstuff ki zo mu wuce gida" Mayraah ta share hawayen dake ta sauko mata cikin rawan murya tace "Amma yaya ban gama project din ba fa, don Allah a bari in gama" Yace "Abba yace zaki gama a gida, be a good gal and do as i say" Juyawa tayi a hankali ta koma cikin hostel din ya bi ta da ido, bayan wani lokaci sai ga ta ta fito da jakarta Ummi ta dauko mata akwatinta biyu, har sannan hawaye ya ki tsaya mata, ita kanta Ummi jikinta yayi sanyi don ta zata Mayraah zata tsaya har nan da sati biyu kafin su gama da internal and external defense dinsu, Usman ya bude masu booth suka ajiye boxes din da jakar, Usman na kallon Ummi with smile on his face yace "Thanks for accommodating our sister Ummi, Allah Ubangiji ya baku sa'an exams, hope kun yi exchanging contact" Ummi na murmushin ita ma tace "Ameen, eh mun yi exchanging" Yace "Maa sha Allah, God bless you" Daga haka ya zaga ya bude ma Mayraah front seat yana kallonta, ta daga kai ta kallesa tana share idonta, bai taɓa bude mata mota ba sai ranan, Maheer kam sai dai in ita ta bude ta shiga amma he is never tired of opening the car door for her, bayan ta shiga ya kulle motar ya zaga ya shiga driver seat Ummi ta dinga daga masu hannu har suka bar area din. Mayraah suna isa gida bayan Usman yayi parking ta bude motar ta sauka, haka kawai gabanta ke faduwa sosai, bata taɓa tunanin akwai ranan da zata shigo gidan da take ma kallon comfort zone dinta tun tana er yarinya ba ta dinga jin wannan faduwar gaban da feeling din kanta as a stranger, ya fito da akwatinta biyu bayan ya mika mata karamin jakar, shi kuma ya dau 2 boxes din suka nufi entrance din shiga gidan tana tafiya a hankali har sannan gabanta na faduwa, wnn ya sa ta fara addu'a a ranta har suka shiga parlon, gaba daya an canza fasalin parlon ba yanda yake a ɗa ba, parlon ya dawo sabo fil don har da sabon fenti aka yi, ga wani daddadan kamshin turare da ke tashi a each and every angle din babban parlon, turaren kuma babu hayaki ko kadan sai azababben kamshi me sanyaya zuciya, Usman ma dai ya ɗan yi jim a parlon don har a sannan yasan Ammi bata dawo gidan ba gashi rabonsa da garin kusan sati uku, yana ajiye Boxes din Mayraah wayarsa ya fara ring, ita dai Mayraah na rakube bayan kujera kamar bakuwa tana bin ko ina na parlon da kallo, kawai samun kanta tayi da tunanin she is not a member of this big house anymore fa, ita din bare ce kawai a cikin yan gidan, she is a total stranger yanxu ta kuma yi accepting haka, ta goge hawayen da ya taru idonta tana kallon Usman da ya ciro wayarsa dake ring, dagawa yayi ganin Abba ne, Abba yace "Ku kuka shigo yanzu?" Yace "Ehh" Abba yace "Ohk ku taho parlorna a sama" Usman yace "To" Katse wayar yayi ya kalli Mayraah yace "Meye kike yi haka kamar kin shigo gidan da baki taɓa shigowa ba?" Ita dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace "Mu je Abba na sama" Bin bayan Usman tayi suka haura sama, Mayraah ta dinga bin Corridor din da kallo don har nan ma anyi fenti, turaren wutan har sama, infact everywhere is soo cool sbda kamshin nan, tana biye da Usman har suka isa parlon Abba, Usman yayi sallama Abba ya amsa sannan suka shiga parlon, Abba na zaune Parlon rike da cup din shayi, Mayraah ta karasa ta zauna kasa kusa da shi tana murmushi ta a kallonsa tace "Abba ina yini" Abba yyi patting kanta yace "Welcome back home daughter, fatan kun gama jarabawan lafiya?" Mayraah ta gyada kai tace "Alhamdulillah Abba" Abba yayi murmushi yace "Maa sha Allah dear, Allah Ubangiji ya fiddo sakamako mai kyau in samar maki aiki a babban asibiti..." Murmushi Mayraah ta dinga yi don har ranta taji dadin wannan abinda Abba yace, Abba ya kalli Usman dake kallonsu yace "Ya gajiyan hanya barrister?" Usman ya dan shafa kansa yace "Alhamdulillah" Abba yace "Amma na hanaka tuƙin dare baka ji" Usman yace "Wajen 5 muka baro Kaduna, akwai matsala a hanya ne" Abba yace "Toh Allah ya tsare, a dinga kula dai da tafiyar dare pls" Usman yace "In sha Allah" Abba ya dau wayarsa yayi dialing number sannan ya kai kunne, ana dagawa yace "They are around" Daga haka ya katse wayar, ba a wani dau lokaci ba aka bude kofar parlon daga Usman har Mayraah suka daga kai don ganin wanda zai shigo, wata mace ce in her mid 40 ta shigo parlon da sallama, Usman dai sai kallonta yake haka ma Mayraah, matar ta zauna kan kujera cike da fara'a tace "Sannunku da zuwa" Usman ya kalli Abba, sai kuma ya kalleta yace "Ina wuni" Tana murmushi tace "Lafiya lau, barrister ko?" Yace "Eh" Ita dai Mayraah kasa ma gaisheta tayi ta kafeta da ido har sai da matar tace "Mayraah fatan a gama jarabawan lafiya?" Mayraah ta sauke idonta daga kallonta gaba daya she is confuse, can dai tace "Ina yini" Matar da fara'a yaki barin fuskarta tace "Lafiya lau dear, Allah ya baki sa'an jarabawa a fito da sakamako me kyau in sha Allah" Mayraah tace "Ameen" Usman dai yayi shiru, in ya kalli matar sai ya kalli Abba daga karshe dai ya mike da nufin barin parlon Abba yace "Aa zauna ai ban yi introduction ba" Usman ya koma ya zauna yana kallon Abba, Abba na nuna matar dake zaune yace "Sunanta Hajiya Amina, she is ur new aunt...." Usman ya dinga kallon Abba babu ko kiftawa haka Mayraah da ta jingina da kujera kamar idonta za su fito tana kallon matar da har a sannan take murmushi, Abba yace "A jiya friday aka daura mana aure da ita, few hours ago ta tare, she will continue taking care of the house and the people in it kamar yanda ake yi a baya, for more than a month now the house lack this, zata ci gaba da kula da duk wani welfare din gidan nan, kaga kamar kai da ka biyo hanya tun karfe biyar u need something to eat, so akwai abinci a kitchen yanxu haka, Mayraah ma kaga bazata sake zaman hostel ba akwai warce zata sa mata ido a gida ko da bana nan, ku ma bakwa nan, Umar dake hanya gobe bazai dawo gida babu kowa ba, ka gane ko...." a takaice Usman yace "Allah ya sanya alkhairi, let me take a shower" Yana fadin haka ya mike yana kallon Hajiya Amina ya ɗan yi bowing yace "You are welcome Ma" Tana murmushi tace "Thank you so much dear" Juyawa yayi ya fice daga Parlon ya ciro wayarsa yana dialing number Maheer, Abba na kallon Mayraah yace "Mu je ki ga dakin ki daughter" Mayraah da jikinta yayi sanyi kalau, ta mike da kyar bata sake yarda ta kalli Hajiya Amina ba har suka fita daga Parlon Abba ya kai ta har dakin Maheer yana nuna mata yace "This will be ur new room" shiga dakin kawai tayi Abba ya bar wajen ta kulle kofa, Mayraah ta jingina da kofar hawaye cike idonta ta fashe da kuka, she still can't believe this, kishiya Abba yayi ma Ammi? Did this also happen because of her? Dama tun barin ta gidan nan Ammi bata sake dawowa ba kenan, ita all this while tayi zaton Ammi ta dawo gidan, yanzu fa duk ta dalilinta abubuwan nan ke faruwa kenan, tunanin hakan yasa ta kara fashewa da sabon kuka ta sulale kasa tana jin komai na duniyar ya isheta why is all this happening for her sake, why??? me yasa abubuwa ke ta faruwa because of her. Har kusan karfe goma Mayraah na zaune bakin kofar dakin ko motsi ta kasa yi tsabar yanda ta kidime, taji anyi knocking kofa, da sauri ta mike tana kallon kofar ta goge hawayenta kafin ta bude, Hajiya Amina ta gani tsaye sanye da hijab har kasa, Hajiya Amina na kallonta cike da kulawa tace "Kin ci abinci kuwa?" Mayraah ba ta yarda ta kalleta ba a takaice tace "Na ci" Hajiya Amina tace "Ohk to, sai da safe kenan?" Mayraah tace "Eh" Hajiya Amina tace "Toh Allah ya tashe mu lafiya" Tana barin bakin kofar dakin Mayraah ta hade rai ta kulle kofar ta tafi can cikin dakin ta zauna hawaye na sauka idonta. Washegari Aunty Mariya ta nemi izini gun mai gidanta na zuwa kaduna urgently, yana barinta kuwa ta kamo hanya, karfe tara da rabi ta isa kano ta nufi gidan Hajja, tana shigowa parlon Hajja, Hajja tayi sororo tana kallonta daga sama har kasa, can tace "Lafiya?" Er dariyar karfin hali tayi ta karaso ta zauna, ita kanta Ammi kallon Aunty Mariya take don sai da gabanta ya fadi, Hajja tace "Tambayarki nake lafiya??" Aunty Mariya tace "Wallahi ba komai kawai mun zo wani biki ne na family din mai gidan, tun jiya ai nake kano kawai nace bari in maku surprise shi da ban sanar maku ba" Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "To kin zo a dai dai kuwa, sai ki raka er uwarki zata koma gidanta yanzu haka ma Maheer take jira na kirasa yace yana hanya, ko don saboda yaran nan gwara kawai ta koma dakinta baza a biye Mamuda ba, Umar din ma wai bai iso ba sai yau" Aunty Mariya tace "Kai Alhamdulillah amma naji dadin wannan labari wallahi ashe na zo a dai dai, dama abinda nake ta son ku gane kenan Hajja, ai ba saboda Alhaji Mahmud zata koma gidan nan ba ko don albarkacin 'ya yanta da yanda hankalinsu ke a tashe ya kamata kawai tayi hakuri ta koma" Hajja tace "Yanzun ma saboda su din ne ai ba wani ba, bazan so wannan yaro Umar ya dawo bata gidan ba babu dadi haka" Maheer ne ya shigo parlon da sallama he look so down kawai karfin hali yake kiran da Usman yayi masa jiya ya basa sleepless night bai taɓa zaton haka daga Abba ba, kawai sai ya dinga tausayin Amminsa, da mamaki yake kallon Aunty Mariya bayan ya zauna yace "Aunty daga ina haka?" Tayi murmushi tace "Daga sama" Yace "Kai amma nayi mamaki fa, babu wanda yace min za ki zo" Aunty Mariya dai ta ɗan yi dariyan karfin hali tace "To ai babu wanda na gaya ma" Hajja ta nuna masa jakan Ammi tace "Ga kayan can ka kai mota" Mikewa yayi ya dau box din ya fita daga parlon ya fita kofar gida ya bude booth ya saka, ya rufe booth din kenan, ya ga adaidaita sahu ya tsaya dai dai gidan, ya dinga kallon adaidaitan don ganin wanene a ciki sai ga Mama Ladi ta sakko da kwarababben akwatinta tana ce ma mai daidaita sahun "To kai yaro Allah ya sa ina da dari biyar din da kace, don wllhi daga ni sai dari da hansin na sauka kano, in zaka hakura ka amsa haka gashi...." Mai adaidaita sahun ya kashe machine din nasa yana kallonta yace "Ban gane ba baaba" Haseenah na kallon Badiyyah dake cin dankali da kwai tace "Ke don Allah Badiyyah?" Badiyyah tace "Wallahi nake gaya makiz ai sai da na bi duk yanda na bi na gano daga inda take zuwa exams, har hostel din sai da naje da nose mask in gaya maki, kuma wallahi kullum sai Maheer yaje wajenta sau biyar a rana, ashe wannan fitan daren da yake wajenta ma yake zuwa ke kina nan kin saki baki sai karfe goma ya dawo mana nan" Haseenah ta dinga kallon Badiyyah with straight face, kamar wasa yau Badiyyah ta tashi da cewar sai Haseenah ta bata kudin gold, da yake Haseenah ta san ta kan dubara tuni ta san yanda ta shashantar da zancen ta shigo da zancen Mayraah shine har da debo ma Badiyyah dankali da kwai da hado mata shayi, shine Badiyyah take bata labarin tasan inda Mayraan ma take yanxu haka, Haseenah tace "Kuma su Ammi sun sani???" Badiyyah tace "Nima fa jiya nayi binciken na gano, har yanzu ban gaya masu ba, so nake sai naje gidan anjima, to ai yau ma Ammin zata koma gida" Haseenah ta zaro ido tace "Da gaske don Allah?" Badiyyah tace "Wallahi, ai shi yasa kika ga Maheer ya fita can gidan Hajja zai je ya dauketa ya maida ta gida" Haseenah ta fara sosa kai tana kalle kalle, can ta kalli Badiyyah da ta cika dankali da kwai a baki tace "To dai gaskiya zan je gidan in taya ta kwalema tun da kinga ko ina dole zai yi ƙura yanzu" Badiyyah ta kalleta da sauri sai kuma tayi dariya tace "Ji neman kugun zama da sabon salo, ance maki babu me aiki ne a gidan??" Mikewa Haseenah tayi ta wuce dakinta da sauri sai ga ta ta fito sanye da doguwar riga da Hijab hannunta rike da handbag dinta, Badiyyah ta saki baki tace "Ina za ki?" Haseenah tace "Gaskiya can zan je in taya su aiki, ko ba komai ai Ammi kamar mahaifiyata take, kuma zata ji dadi idan taga na rigasu ma zuwa gidan na fara mata gyare gyare...." Badiyyah tace "Tabdi, to kin gaya ma Maheer din ne?" Haseenah tace "Ba sai ma gaya masa ba, ai Mahaifiyarsa zan je in kyautata ma" Badiyyah tace "Toh bari in sa kaya mu je tunda bani da inda zan je yau" Haseenah tace "To don Allah kiyi sauri" a haka Badiyyah ta mike ta tafi dakinta ta shirya ta yafa gyale ta fito suka kama hanyar gidan a cikin adaidaita sahu, Haseenah sai fatan ta riga su Ammi zuwa gidan take...... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 *Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/10, 9:17 PM] Khaleesat Haiydar💖: Duk yanda Hajja ta bi da Mama Ladi a kan kar ta bi su Ammi gida ƙin yarda tayi, don bata sake sauraron Hajjan ba ta sake fita da akwatin nata zuwa motar Maheer tana cewa "Ji min tsohuwa dai, to wajenki na zo da zaki ce min sae na zauna wajenki, bayan ni nasan me ya dawo da ni, ko kin zata yawon banza na zo yi Kano, kina zaune kara zube babu neman taimako babu komai sai surutu da isa da gadara, gashi da hannunki da bakinki kina neman tarwatsa zuri'arki" Bayan fitar Mama Ladi Aunty Mariya na kallon Hajja da ta cika tayi fam, ita a dole Mama Ladi baza ta bi su gidan Abba ba, Aunty Mariya tayi kasa da murya tace "Ae kafata kafarta Hajja baza ta zauna gidan ba in sha Allah, ko awa daya baxa mu yi a gidan ba za mu dawo nan tare da ita, haba ai yanzu kuma ba da bane da za ayi hakan" Ita kanta Aunty Mariya sae da taji wani iri da kalmarta na karshe, su kuma baxa su gane ma'anar yanzu ba ɗa bane da ta fada, Ita dai Ammi taki cewa komai a parlon amma sam ita ma bata son Mama Ladi ta bi su, shikenan ita danginta basu da zuciya kenan, me ma zai kara burgesu da gidan Abba, me Mama Ladi zata bi ta gidan su yi after all this that happened, Maheer dama bai bi ta kansu ba ya dinga danna wayarsa daga tsayen da yake kamar baya jin ma me suke cewa, haka kawai baza a dinga daura masa pressure daga wannan sae wannan ba, A fusace Hajja tace "In ban da ma rashin zuciya me kanwata zata sake koma yi gidan Mamuda, mutumin da har yau bai sake bi ta kanmu ba, wallahi in nace maku nayi farin ciki da dawowar Ladi garin nan to nayi ma Allah karya, sam bata da hankali bata da zuciya bata san inda ke mata ciwo ba, ta wani kwaso rubabben akwatinta ta kara dawo mana to me za mu mata??" Aunty Mariya dai tace "Ke dae Hajja kawai ki bar ni da ita nasan yanda zan bi da ita in sha Allahu" Aunty Mariya na kai wa nan ta mike ta dau handbag dinta, Hajja ta kalli Ammi tace "Ki tashi ku je Allah ya tsare" Ammi ta mike ta dau karamin jakarta tace "Ameen" Sai a sannan Maheer yayi ma Hajja sallama ya juya ya fita daga parlon, Mama Ladi na tsaye jikin mota tana ta jiransu sai ga shi sun fito, Mama Ladi tace "A saman motar za a daura akwatin Maheer?" Ya ɗan yi murmushi ya bude mata booth yace "Ai nan ba karaye bane da ake daura akwati a saman mota" Mama Ladi tace "Ƙul ɗan nan, wllhi karayen nan ba kauye bace" Shi dai bai ce mata komai ba ya dau akwatin karfen ya saka bayan motar ya bude mata kofar baya, ta shiga sannan Ammi ma ta shiga, Aunty Mariya ta shiga gaba, sai da suka bar layin Mama Ladi ta sauke wani ajiyar zuciya me karfi tace "Maganganu dai sanka sanka, babu dadin ji.... huhuhu" Babu wanda dai ya tanka Mama Ladi a motar, can ta kara sauke ajiyar zuciya tace "Mutum ba kyau, ku ji tsoron mutum, amma dai ba komai Allah ya kai mu gidan lafiya" Maheer na kusa gida duk jikinsa yayi sanyi, bai san yanda Ammi zata dau wannan lamarin ba, bai san yanda zata yi reacting ba, ita kanta Aunty Mariya tayi nisa tunanin da take, ita dai tasan koma meye bazata yarda ta bar Ammi tace zata sake barin gidan ba, she just have to let her stay by all means, tsoronta yanzu Mama Ladi tunda ba alkibla gareta ba kar ta kara ɓata abun ta rikita komai, Maheer yayi parking bayan mai gadi ya bude masu gate din gidan, nan bugun zuciyarsa ya fara tsananta, baya ma tunanin zai zauna gidan bayan ya ajiye su gwara kawai ya bar gidan duk ma abinda za ayi ya kasance baya nan, he is just tired of everything, ya kashe motar, Aunty Mariya ta fara sauka sannan Ammi, Mama Ladi ma ta sauko tana kallon Maheer tace "Fiddo min da akwatina Maheer, abubuwan ciki ba na wasan yara bane" Maheer ya bude booth din ya sauko da akwatin nata, Aunty Mariya da gabanta ke faduwa ita ma ta kalli Ammi da ta tsaya kamar tana jiran Mama Ladi tace "Ammi mu shiga akwai rana kamar ba safiya ba" da fara'a Ammi ta amsa gaisuwan Mai gadi da ya taho yana gaisheta cike da girmamawa, sannan ta bi bayan Aunty Mariya zuwa cikin gidan, Mama Ladi na biye da su a baya, shi dai Maheer na rike da akwatin Mama Ladi yana tafiya a hankali, Aunty Mariya na shiga parlon Ammi taga Haseenah da Badiyyah zaune parlon ko kadan ganinsu bai mata ba, Ammi ta karasa cikin Parlon ita ma, Haseenah na ganin Ammi ta zamo kasa daga kan kujera tana sinne kai tana ma Ammi sannu da zuwa tare da gaisheta, Ammi ta amsa da ɗan fara'arta, Haseenah ta gaida Aunty Mariya ma, Aunty Mariya ta amsa, Badiyyah ma duk ta gaishesu, Mama Ladi ce ta shigo parlon ta gwale ido tana bin ko ina da kallo tace "Nan gidan ne kuwa naga kamar ba nan ba fa, ko idona ne? auuu kamar dai fenti aka canza da kujerun gidan fa" Aunty Mariya na kallon Ammi a sanyaye tace "Ina makullin part din ki Ammi?" Ammi ta mika mata handbag dinta, Haseenah dai sai wurga ido take kamar warce tayi ma sarki karya, Mama Ladi ta cire gyalenta ta jefar kan kujera tace "Ina Salibar ta kawo min abinda zan ci" Aunty Mariya ta wuce sama jiki duk ba kwari Ammi na biye da ita a baya, Mama Ladi ta bi bayansu tana cewa "Salibar ta kawo min kumallon saman bene kawai, kai amma Mamuda ya kyauta yanzu duk saboda dawowar naki yayi wannan gyaran haka?" Haseenah na ganin sun haura sama ta mike da sauri za ta bi bayansu ita ma taji ance "Me kike yi a gidan nan Haseenah? Da izinin wa kika fito?" Strictly yake tambayar, Haseenah ta juya tana kallon Maheer da ya shigo parlon da akwatin Mama Ladi ta ɗan hade rai tace "Yan gyare gyare na zo taya Ammi mana Maheer, zuwa muka yi ni da Badiyyah mu tayata kaga baxa mu bar ta tayi aikin ba ai" Maheer ya wani hade rai yace "Zo ki fita ki bar gidan nan kar ki tunzura ni, baki da hankali ne zaki kwaso kafa without informing me kice kin zo taya Ammi gyare gyare? To ba a son gyaran naki, sae kece zaki mata gyara aka gaya maki, i am giving u 5 minutes ki bar gidan nan kada ranki ya bace wllhi" Ransa a bace yake maganar, Haseenah ta wani taɓe baki tace "To ai ba don saboda kai na zo ba Maheer, don in ta kai ne ma bazan yi ba wallahi, gani nayi kawai ya kamata tunda Ammi abinda take min ko Mumy sai haka, sannan da hankalina ni ba yarinya bace ba sai wani ya sa ni ba shi yasa na zo kawai, kuma naga Mahaifiyarka ce Ammin nan kyautata mata kawai na zo yi kamar yanda zan yi ma tawa Mahaifiyar, to meye kuma abun tashin hankali a nan" Bata tsaya ta sake sauraronsa ba ta wuce sama da sauri, Badiyyah dai sai tauna chewing gum take tana jin su a parlon, Maheer da yaji zuciyarsa na tafarfasa ya bi bayan Haseenah sama da sauri dolenta kuwa ta bar gidan nan, Badiyyah ta kyabe baki, to ita bata ma ga amfanin biyo Haseenah da tayi ba gashi bata da kudin motar komawa banda haka yanxun nan ma sai ta tashi tayi tafiyarta, ko minti ashirin basu yi da isowa gidan ba amma tun da suka zo basu ga gilmawar kowa ba ga ko ina tsit, har sama Badiyyar ta tafi ta murda kofar dakin Mayraah a hankali ta bude duk da tasan bata gidan, zaro ido tayi ganin wasu tsadaddun furnitures masu shegen kyau cikin dakin, zanin gadon saman katifar ma kadai abun kallo ne ga wani kamshi dake ta tashi a dakin, ko ina na dakin ya canza ya dawo sabo fil kamar na amarya, ga sabbin akwatina da ta gani, a ranta tace to kuma dakin waye wannan haka, har zata karasa ciki ta yi ɗan hali ganin handbag ajiye a dakin sai kuma ta tuna ta fa ga motar Usman a parking space, a hankali ta jawo kofar ta kulle tana tabe baki ta nufi bangaren Ammi ta murda kofa taji a kulle, sauka downstairs tayi tace ma Haseenah ai fa gidan daga Usman sai Abba tunda motarsu ne kadai parking space sai na Ammi da ake kai ta anguwa a ciki, Haseenah na kallonta tace "Kuma bangaren Ammin ba a bude yake ba?" Badiyyah tace "Ai fa kamar ta kulle ne ta tafi da makullin" Ko kadan Haseenah bata ji dadin jin haka ba, amma dai tayi shiru suna ta zaune parlon suna jira, a haka ne su Ammi suka shigo gidan suka same su. Aunty Mariya na bude part din Ammi suka shiga ciki gaba daya har Mama Ladi, Aunty Mariya ta kaƙƙabe masu kujerun parlon suka zauna, Mama Ladi na girgiza kai tace "Mutum mugun icce" Bude kofar Parlon aka yi duk suka juya, Haseenah ta shigo tana ɗan murmushi tace "Ammi akwai abun shara a nan kuwa?" Mama Ladi ta tsuke fuska tace "To sai aka yi yaya in akwai? Don Allah ki rufa mana asiri kiyi tafiyarki za mu share da kanmu, ko ni kadai na isa in share ai" Aunty Mariya da bata ji dadin abinda Mama Ladi ta ma Haseenah ba tace "To meye laifi don tace zata yi shara Mama Ladi?" Mama Ladi tace "Naga jaraba? Mariya taga sa'anninta a nan ne da zata shigo mana wai zata yi shara, ni fa bana son shisshigi wllhi, naga dai ke ba a kiraki ba, ba a kuma ce ki biyomu ba to menene wannan haka ....." Haseenah dai sai ɗan murmushin karfin hali take, Ammi tace "Kije kitchen ki dauko tsintsiyar Haseenah, suna nan kitchen" Juyawa Haseenah tayi zata fita suka kusa cin karo da Maheer, ko kallonsa bata yi ba ta bi ta gefensa da sauri ta wuce, shi kuma ya karasa ciki ya ajiye akwatin Mama Ladi ya juya ya bi bayanta, Mama Ladi na kallon Ammi tace "Wato ke me surka bari ki gwaleni a gabanta ko Ammi? To wallahi tunda nace bazata yi sharan nan ba bazata yi ba, ni kadai raina na isa in tsaftace parlon nam da daki" Mama Ladi ta mike ta kulle kofar ta dawo tayi kasa da murya tace "Toh bari kuji, naje waje yafi hudu a karaye da getso, an min maganganu iri iri ba dadin ji, kuma duk zan zayyanosu amma sae nayi kumallo, kai har suna wallahi an bani kuma za ku sha mamaki in kunji wa enda ke da sa hannu a cakudewar lamarin nan, sannan waje na karshe da naje bawan Allahn ce min yayi idan baki maida hankali kin dawo gidanki ba to wallahi zaki je ki tarar da abokiyar zama" Sosai gaban Ammi ya fadi tana kallon Mama Ladi, Ita kanta Aunty Mariya da taji wani mugun sanyi ya shigeta kallon Mama Ladi kawai take, Mama Ladi ta dafe gwiwa tana kallonsu tayi kasa da murya tace "Wallahi yau sati daya kenan da ya gaya min wannan maganar, to ina ta fafutukan hada kudin da zan bada a bani iccen da zan kawo maku da zai lalata duk wani mugun abu da bamu san kansa ba, kar fa ku ce wajen boka ko matsafa naje, aa wallahi ba ruwana da wannan harkar, irin malaman nan ne salihai masu tsoron Allah da basa shirka, kuma duk inda naje abu iri daya ake ce min, idan na ci na koshi duk zan Kasa komai a faranti, sannan batun Mayraah kuma....." Mikewa Ammi tayi alamar bata son wannan zancen ta dau handbag dinta ta ciro makullin dakinta zata bude, Aunty Mariya ta buda baki kamar yanda Mama Ladi ma ta buda baki suka bi ta da kallo har ta shiga daki, Mama Ladi ta kalli Aunty Mariya tace "Kin dai ga ko? To ba ruwana kuma, kin dai ga alamar uwar ta gama hure mata kunne kuma duk sun shiga sun zauna sun yi daɓas a ranta ko" Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta bi bayan Ammi, Mama Ladi ta bude jakanta ta dinga fiddo kullin magunguna kashi kashi tayi kasa da murya tana cewa "Dama tun da aka kawo yarinyar nan lullube cikin mayafi ranan hankalina bai kwanta da ita ba, ilai ga maganganu sun fito iri iri a kanta ashe gagaruman yar bin boka ce, shi sa na mata koran kare yanzu, bari dai inyi kumallo a debo min garwashin wuta za a ga fitina a gidan nan yau..." Ba a dau lokaci ba Aunty Mariya ta fito daga dakin Ammi ganin taki sauraronta don ma kamar bata bakinta kawai take, fita tayi daga parlon zata je dauko abubuwan da za su gyara part din da shi, ta hadu da Haseenah dake haurowa sama da sauri, tana ganin Aunty Mariya ta fara matsar kwalla tace "Aunty daga na zo zan taimaka ayi gyare gyare da ni shine Maheer ya dage sai na tafi gida har yana min maganganu marasu dadi" Aunty Mariya tace "To ke ya zaki fito babu izinin mijinki? Dama bai sani ba ki ka taho? To gaskiya ki koma gida tunda umarnin da ya baki kenan...." Haseenah ta kasa cewa komai, sai tayi da ta sanin yi ma Aunty Mariya magana da ta sani kawai direct Ammi ta tafi ta samu, Aunty Mariya har ranta taji dadin da Maheer yace ta tafi don duk wani abu da zai faru a gidan nan yanzu sirrinsu ne bai kamata ace daga shigowar Haseenah ta fara sanin komai kan gidan ba ko ana yin komai a gabanta, it's too early yaushe ma aka aurota, gaskiya hukuncin Maheer yayi mata dai dai don dama tun shigowarsu parlon sai da taji wani iri ganin Haseenah a zaune da Badiyyah, shikenan komai za ayi sai anyi a gabanta basu da sirrin kansu, Aunty Mariya na kallonta tace "Kiyi hakuri ki juya kawai ki koma gida ki bi umarnin mijinki, kuma aikin ma ai ba wani aiki bane ni kadai zan iya komai" Dai dai nan Hajiya Amina ta fito daga ɓangaren Abba that is at the very far end of the corridor sai ma ka kara corner idan ka kai karshen corridor din kafin ka shiga ɓangarensa, tun da Aunty Mariya ta hangota ta fahimci wacece ita, sosai gabanta ya fadi, ta maida dubanta kan Haseenah dake kallon Hajiya Amina ita ma tace "Ki tafi kawai nace, sai anjima" Haseenah bata ce komai ba, Aunty Mariya da ta ɗan fusata tace "Magana nake maki Haseenah" A hankali Haseenah tace "To Aunty amma..." Aunty Mariya ta dakatar da ita don bata son Hajiya Amina ta samesu wajen tace "Baza ki tafin dai ba kenan" Haseenah ta juya ba don ta so ba don ita kanta tana son sanin wacce mata ce ke tahowa daga can bangaren Abba, Aunty Mariya ta kasa ci gaba da tsayuwa don ji take kamar ita ce Ammi tsabar wani daci da take ji a ranta da wani bakin ciki, kawai ta sauka downstairs tun kan Hajiya Amina ta karaso, ita kanta Hajiya Amina da farko da ta hango Aunty Mariya tayi niyyar juyawa amma sai taga kamar hakan bai kamata ba duk da ba wai tasan ko wacece bace a tsaye, kuma Abba bai sanar mata da zuwan kowa yau ba, A haka dai ta karaso tana dab da isowa wajen kuma taga Aunty Mariya ta sauka downstairs kawai, hakan yasa ta karasa dakin da Mayraah take tayi knocking kofar gently, Mayraah na kwance idonta biyu tun dazu take ta jin kamar footsteps kuma ba na mutum daya ba amma ta kasa tashi balle ta fito ta duba, haka kawai gabanta ke ta faduwa tun asuba, yanzu kuma tsoro ne ya lullubeta, ana bubbuga kofar sai da zuciyarta ya buga sosai, ta mike a hankali ta karasa ta bude with throbbing heart, Hajiya Amina ta gani tsaye bakin kofar, Mayraah ta sauke idonta ta gaisheta, Hajiya Amina ta amsa mata da murmushi tace "How was ur night?" Mayraah tace "Alhamdulillah" Hajiya Amina tace "Kin ga breakfast a kitchen kuwa? Na so tashin ki muyi girkin tare da sade sai kuma na tuna exams kika gama kina bukatar hutu yanzu" Ita dai Mayraah kallonta kawai take with a neutral expression babu kuma alamar zata bata amsa, Hajiya Amina ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace "Is it too early ki saki jiki da ni daughter? Naga kina dari dari tun jiya, I have 2 kids Mayraah, twins... kuma su kenan Allah ya ban kafin babansu ya rasu! kin ma girme su they are just 15 years, ki daukeni kamar mum dinki daughter...." Mayraah ta ki cewa komai tana jin wani zafi a ranta, she still can't believe wannan matar kishiyar Ammi ce, she don't think she will ever like her, kawai kallonta take bbu fara'a a fuskarta, Hajiya Amina ta jawota bossom dinta tace "Take me as ur mother Mayraah, u will gradually get use to me" lokaci daya Mayraah taji wani mugun faduwan gaba bayan ta hango Ammi da ta fito daga part dinta, kallonta kawai Mayraah take kamar yanda Ammi ke kallon Hajiya Amina duk da she is backing her, a hankali Ammi ke tahowa this time around tana kallon Mayraah da Hajiya Amina, Mayraah bata san sanda ta kulle idonta ba zuciyarta na wani irin bugawa, Hajiya Amina ta saketa ta dago kanta tana kallonta tana murmushi tace "Je kiyi breakfast daughter sai mu girka lunch tare kafin Abbanki ya tashi bacci...." Karaf a kunnen Ammi, Mayraah ta hadiye wani abu da kyar ji take kamar kafafuwanta sun kasa daukarta, Hajiya Amina ta juya zata bar wajen suka yi ido hudu da Ammi da tayi still a inda take bata fasa kallonsu ba, sosai gaban Ammi ya fadi tana kallon Hajiya Amina babu ko kiftawa, Hajiya Amina na kallonta amma kuma bata san ta ba, don ko a hoto Abba bai taɓa nuna mata hoton Ammi ba, ta dai tace "Sannu, barka da safiya" Ammi bata amsa ba sai kallonta take kamar ta ga alien, hakan yasa Hajiya Amina ta bi gefenta ta nufi part din Abba kawai, da sauri Ammi ta bi ta da kallo kamar idanuwanta za su fito. Mayraah wished all this was nothing but a dream, she felt so weak and sick at the same time, nan da nan taji kamar zazzabi na neman lullubeta, tsabar yanda abun ya bugeta ta kasa ce ma Ammi komai sai kallonta kawai take, Ammi ta sake waigowa ta kalli Mayraah, Mayraah couldn't say anything, kawai Ammi ta juya da sauri ta koma part dinta, Mayraah ta kulle kofar dakin ta sulale kasa ta hade kanta da gwiwa hawaye masu zafi na sauka idonta, Mama Ladi ta bi Ammi da kallo baki bude ganin yanda ta shigo parlon da sauri kamar an korota, Ammi bata ko kalleta ba ta shiga dakinta, kawai Mama Ladi taga Ammi na fitowa da duk akwatunan ta daga daki wa enda bata je gidan Hajja da su ba, Mama Ladi ta gwalo ido ta mike tace "Ke meye haka? Ko su ma wanke su za ayi sun yi ƙura ne?" Sai a sannan taga hawayen dake sauka idon Ammi, Ammi taki ce mata komai ta dinga shiga dakin tana fito da duk wani kayanta, Mama Ladi ta saki salati ta fita da sauri ta je kiran Aunty Mariya, tare suka dawo dakin Aunty Mariya tace "Ammi menene haka kuma?" Ammi na girgiza kai hawaye na sauka idonta kamar an bude pampo tace "Na gama zama da Mamuda, na gama zaman gidan nan, ya aiko min da takarda ta bayan na tafi kawai" Aunty Mariya tayi karfin halin zama kan kujera don tasan babu tantama Ammi taga Hajiya Amina kenan, cikin sanyin murya tace "Babu inda zaki je Ammi, nan din gidanki ne, babu wata warce zata hanaki zaman gidan nan, babu warce za ki tafi ki bar ma gidan nan ko ki bar gidan saboda ita..." Aunty Mariya ta kasa ci gaba hawaye ya fara sauka idonta tana taya Ammi jin zafi a ranta, Cikin kuka Ammi tace "Ni Mahmud zai yi ma haka akan yarinyar da na ci wahala kanta tun tana cikin dattin haihuwa, ni zai ma wannan walakancin akan Mayraah? Maheer ya cuce ni wllhi da ya bari na tako kafata na dawo gidan nan naga wannan abun bakin ciki da takaici, da nasan abinda zan dawo in tarar kenan bazan dawo ba Mariya har abada kuwa, nayi da na sanin abubuwa da yawa a rayuwata, nayi da na sani wallahi, alkhairi na aikata ya zamar min sharri daga karshe" Kuka Ammi take sosai tana girgiza kai, Tace "Maheer ya san ubansa ya kara aure shine zai je ya takurani in dawo gidan nan? In dawo in yi me kuma? Me zan dawo in masu? Wallahi ya cuceni" Mama Ladi ta saki salati tana tafe hannu jin abinda Ammi ke cewa tace "Mamudan ya kara aure?? A ina kika ji wannan magana haka? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, aure fa??" Ita dai Aunty Mariya hawaye kawai take ta rasa abinda ma zata ce, Ammi ta ci gaba da fiddo sauran kayanta tana kuka, Mama Ladi ta rike kai tace "Huhuhu, ashe Mamudan ɗan iska ne dama bamu sani ba?" Sai kuma ta fashe da kuka tace "Duk Hajja ce ta ja maki wannan jaraba, kina zaman zamanki lafiya gidan mijinki ta zuga ki kika koma ɗan kuturun gidanta ku ka takure waje daya numfashi da kyar, babu wani alawance din da mutum zai sake ya bararraje komai a takure kamar gidan mayu shi sa nake gudun gidan idan na zo kano na gwammace in sauka nan, yanzu ga irinta nan ta cuceki ta sa an dankara maki kishiya kina can kin saki baki, dama an gaya min wallahi, kuma da kika wani kwaso akwati er iskar da ya auro zaki bar ma gidan kike nufi?" Kwankwasa kofar dakin aka yi, Aunty Mariya ta juya tana kallon kofar, can tayi karfin halin mikewa ta karasa tace "Waye?" Hajiya Amina tace "Ni ce" Aunty Mariya ta ɗan hade rai tace "Ana zuwa" Maida kayan Ammi ta dinga yi daki da sauri, tuni dama Ammi ta shige daki, Mama Ladi ma ta mike tana taya Aunty Mariya tura akwatunan da sauri duk da bata san ko wacece ba, Aunty Mariya ta fito bayan sun kai duk kayan daki ta bude kofar, Hajiya Amina ta shigo da sallama. MAYRAAH is 500 via 3276052019 FCMB Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 *Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/11, 8:55 PM] Khaleesat Haiydar💖: Hajiya Amina ta karasa cikin parlon ganin Mama Ladi sai bata zauna kan kujera ba ta zauna kasan carpet tana kallonta cikin ladabi tace "Ina kwana Mama" Mama Ladi dake ta kallonta daga sama har kasa ta kalli Aunty Mariya dake zaune kan kujera fuskarta babu yabo babu fallasa tana danna waya tace "Wacece wannan kuma kika bude ma kofa ta shigo mana Mariya?" Hajiya Amina ta ɗan yi murmushi tace "Sunana Amina Mama" Mama Ladi ta yamutsa fuska tace "Amina? Meye kuma Amina? Amina daga ina? Ko dai batan hanya kika yi? To ko dai korar Salibar aka yi aka canzo wata mai aikin Mariya?" Hajiya Amina ta kalli Aunty Mariya dake ta harkarta da waya tace "Ina kwanan mu" Sai a sannan Aunty Mariya ta dago kai a takaice tace "Lafiya lau" Mama Ladi tace "Kin san ta ne Mariya ta shigo mana kanta tsaye ko dai makota zata shiga tayi ɓatan kai? Ko Saliba aka canza" Aunty Mariya tayi pretending kamar an kirata a waya ta mike ta shige daki ta kulle kofar, dai dai nan aka Bude kofar parlon Usman ya shigo da sallama ya karaso ya zauna kan kujera yana kallon Hajiya Amina yace "Ina kwana" Hajiya Amina ta kallesa tace "Lafiya lau barrister" Daga haka ta kalli Mama Ladi dake ta kallonta daga sama har kasa kamar taga abun kyama ta mike tace "Mama bari in baku waje..." Daga haka ta nufi kofa ba tare da ta jira cewar Mama Ladi ba ta fita, Usman na kallon Mama Ladi da ta bi Hajiya Amina da kallo baki bude yace "Ina kwana Mama?" Mama Ladi ta dawo da kallonta kansa, sai kuma ta saki kuka ta rike kai tace "Yanzu Usman kai da nake ganin hankalinka ace har da kai a zuba ido ubanka ya dankara ma uwarka kishiya baka taka masa burki ba? Me zai yi da wata matar gashi da gandara gandaran samari a gida banda son rai da son zuciya irin nasa? Shekara kusan arba'in yana tare da uwarku bai mata kishiya ba sai yanzu kuma kuka yarda da hakan baku tada masa bori ba? Kuma don Allah a ina ya jajibo wannan mata haka sai uban mazaunai? Sannan saboda raini da duniyanci shegiyar sai ta biyo mu har nan daga shigowarmu ko minti daya ba mu yi ba? Ina ruwanmu da ita zata shigo nan idan ba munafurci ba? Ta ina Ammi zata fara kishi da wannan mata haka kamar karuwa, ko kai baka ga yanda take wani juye juye bane?" Usman dai ya mike zai fita Mama Ladi ta tashi da sauri tace mu je ka kira min uban naka, kace Mama Ladi daga karaye na sallama da shi. Duk yanda Aunty Mariya ta dinga kokarin kwantar ma da Ammi hankali tana bata baki Ammi bata saurareta ba don kamar dada tunzurata ma take, sai harhada komai na dakinta take waje daya tana kuka, daga karshe ma ce ma Aunty Mariyar tayi in ta sake mata wata magana zata mareta, hakan yasa Aunty Mariya ta ja gefe ta rasa kuma yanda zata yi ta tsaya duk jikinta a sanyaye, seriously Ammi ke hada sauran kayanta tana goge hawayen dake sauko mata. Mama Ladi na zaune parlon baki sai girgiza kafa take tana jiran taga ta inda Abba zai billo bayan ta aika Usman ya kira mata shi, bayan some minutes sai gashi ya iso chalet din ya shiga parlon da sallama ya zauna saman carpet ya gaisheta da ladabi, Mama Ladi ta fashe da kuka ta rike kai tace "Yanzu kai Mamuda shekaranku 40 da Ammi ba a taɓa jin kanku ba, ba a taɓa sulhunta ku balle a raba ku fada ba sai don wannan ɗan matsalar ya gitta tsakaninku sai ka mata sakayya da kishiya? kishiyar ma kamar daga Tafa ka aurota, Mamuda ka mance yanda Ammi ta zauna da kai kana matsiyacinka cin yau da kyar na gobe daban tsabar talauci, baka da ko kwandalan kanka alhalin masu kudi ne suka dinga sonta da aure taki amince masu ta makale maka kamar me bakin uwa? Ko dai ka mance yanda ta dinga kwana da yunwa ta yini da yunwa duk bamu sani ba tana ta rufa maka asiri a haka har ta haifa maka yaran nan cikin baƙar yunwa? Shine yanzu zaka saka mata da wannan tozarcin Mamuda?" Abba dake sauraronta yana kallon TV, ya ɗan yi murmushi ya girgiza kai yace "Baaba ban kara aure don in tozarta ta ba, na karo aure ne saboda babu yanda zan yi hakan shine kadai mafita a gareni da yarana, baaba a duk abubuwan nan da suka faru in za ayi alkalanci tsakani da Allah ke kanki kinsan na kauda kai nayi hakuri na kuma nuna komai ba komai bane...." Mama Ladi ta share hawayenta tace "Sarai nasan wannan, don juya ka suka dinga yi kamar sun samu waina, su ce wannan su ce wancan kuma kana ta bin su babu musu har na so inji haushinka wallahi" Abba yace "Yauwa baaba, na bi su yanda suke so a lokacin nan don a zauna lafiya, duk yanda suka ce haka ake yi, a tsarinsu na karshe ne naga bazan iya ci gaba da goyon bayan zalunci ba, na kuma nuna ma ita Ammin bazan yarda da haka ba shine ta debi kayanta ba fada ba komai ta bar gidan nan, baaba fisabilillah akwai wanda Mayraah ta sani a duk duniyar nan bayan mu?" Mama Ladi ta gyara zama tace "Ina fa?? Yarinyar da ku kanku baku san asalinta ba balle ita da sai kwanan nan ma tasan ba ku ne iyayenta ba" Abba yace "Kinga da farko Ammi ta nuna Hajja tace bazata sake rikon Mayraah ba, na danne zuciyata na nuna ba komai tayi ma mahaifiyarta biyayya kawai, nace Mayraah ta koma gidan kanina wato ɗan yayan mahaifina shi ma iyalansa suna nan garin kano shine dai yake legas, Maheer ya nuna gidan yayi nisa daga makarantar ta sai dai ta zauna gidansa kawai, duk aka amince saboda dai Ammi ta samu kwanciyar hankali gun mahaifiyarta, wannan duk bai isa ba sai gashi sun billo da wata maganar wai bazata zauna gidan Maheer ba sannan nan din ma Ammin bazata riketa saboda son zuciya irin nasu da rashin binkicen asalin abinda ke faruwa, ina ake son yarinyar ta tafi fisabilillah ga jarabawarta na karshe zata zana? ban da ni me hakuri ne wa za ayi ma haka a zauna lafiya Baaba? Yarinyar da tun tana jaririyarta ake tare da ita yanzu da girmanta a billo mata da haka don ma tana da strong mind? Ina ake son in kai ta to?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Ka ma yi kokari wallahi Mamuda don ba ko wani namiji bane zai dauki wannan iskancin ba zancen gaskiya, kuma Allah ya maka albarka yanda ka dinga bin duk abinda suka ce da farko kana ta kauda kai...." Abba yace "Auren nan kuma da nayi, nayi sa ne kawai saboda babu yanda zan yi, Baaba kema kinsan babu ta yanda za ayi kana tare da mace babu zagi ba cin mutunci ta tattara kayanta ta koma gidansu kuma mahaifiyarta na kallonta amma tayi shiru ta barta ta ci gaba da zama bata saka ta koma gidanta ba" Mama Ladi tace "Ita fa Hajja ka rufa ma kanka asiri ka daina sa ta a sabgar nan, don wllhi gobe ma nake son mu kai ta asibiti a duba mana kwakwalwarta don tsufan duk ya rikirkitar da ita abun dai ba kyau" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Na ƙaro aure ne saboda bazai yiwu ace Mayraah na gidan nan babu babban mace dake saka mata ido ba, sannan yayyinta duk ba gidan suke ba a ko da yaushe, in ma suna gidan to yanzu duk sun san su ba muharraman juna bane.... Kin ga ai abinda zai yiwu shi ake yi" Mama Ladi tace "Kul, kar ka sake cewa ka karo aure saboda Mayraah ka kara goga mata baƙin fenti a shiga uku, me ya kai ka fadan haka? kai dai kawai kace ka karo aurenka saboda baza ka iya zama babu mace ba, kai ni ban ma yarda cewar saboda wannan ɗan matsalar ka tashi kaje kayi wannañ gantalallen auren ba Mamuda, dama can kana da bazawararka a boye kuna tadinku, kar ka raina min hankali kawai" Abba yayi murmushi yace "Ko daya, hada ni aka yi da ita ma" Mama Ladi tayi mitsi mitsi da ido tace "To Allah ya tsine ma koma wanene ya hadaka da ita" Shi dai Abba bai ce komai ba, Mama Ladi tace "Kuma yanzu ka tashi mu koma can bangaren Ammi da bakinka ka gaya mata ka kara aure, don babu rashin mutunci ace namiji ya dankara ma mace kishiya babu saninta, ko mata dari zaka aura baka da sama da Ammi kaji in gaya maka, maza tashi mu je ka bata hakuri sannan kasan inda zaka kai kishiyar don baza su zauna gida daya ba suna gogan kafada da katuwar matar da ka auro, ai na ganta wata sandan sandan kamar er Ghana" Abba dai kallonta kawai yake, ta mike tana gyara yafin gyalenta tace "Ka tashi mu tafi nace ko" Ya ɗan yi murmushi don bai son yi mata musu amma ba don yayi niyyar hakan ba ya mike ya bi bayanta suka koma main house zuwa bangaren Ammi, Mama Ladi ta bude kofar taga akwatunan Ammi an sake fito da su parlon, Mama Ladi ta rike haɓa tace "Ji shashasha...." Abba dai ya nemi kujera ya zauna babu yabo babu fallasa, Aunty Mariya ta leko daga dakin jin muryar Mama Ladi tana ganin Abba ta hade rai ta koma cikin dakin Ammi, Mama Ladi ta shiga dakin tana kallon Ammi dake kulle last box dinta tace "Fito fito, hada akwatuna ba naki bane" Daga haka ta bar dakin, Ammi ta fito tare da last box dinta, tana ganin Abba cikin bacin rai tace "Me ka biyo ni nan ka gaya min kuma? Dama in kasan ba takardata ka kawo min ba ka tashi ka fita bana bukatar ganinka, takardan kuma in ma kaki badawa to za mu hadu a kotu ne" cikin tsawa Mama Ladi ta kunduma mata zagi tace "Takardan uwaki? Baki san gidan mijin shine rufin asirinki ba gode gode dake? A baki takardanki ki tafi ina wai? Ai yanzun ma kawai kin hada akwati ne a banza don in har na isa dake to babu inda za ki, kin dawo dakin ki kenan, don mu ba kananun mutane bane, kuma mu ba gantalallu yan iska bane" Cikin kuka Ammi tace "Wallahi ban dawo ba Mama Ladi don minti biyar bazan kara a gidan nan ba, Maheer ne kawai ya cuce ni ya takura rayuwata na dawo banda haka wallahi har abada ni da gidan, kuma a yanzu zan sake komawa inda na fito ya zauna da warce ya auro, idan nayi masa halacci a rayuwa zai sani wataran...." Mama Ladi tace "Kaji mahaukaciya, to wallahi ko Hajja bazata maki baki ya kamaki ba kamar yanda ni zan maki ya kama ki, tunda naji ance ranan gobe kiyama ma ni zaki gani ba Hajja ba, haka dai naji ance, don haka in kin isa ki fita gidan nan mu ga, tun farko da kin ji ta nawa ai da duk haka bai faru ba Ammi, kishiya kuma dama nace masa baza ki zauna da ita ba, in ma ta bar maki gidan ya kama mata haya ko kuma ke ki bar mata gidan ya gina maki wanda yayi ukun wannan, ai shi Mamudan ba ɗan iska bane yasan abinda ya kamata..... Karfe biyu saura Mama Ladi ta sauko downstairs daga part din Ammi duk ta hada zufa tsabar sulhun da take ta kokarin yi tun karfe sha daya take abu daya har yanzu da ta fito shi ma saboda lokacin sallah ne yayi Mamuda zai je masallaci, tana fifita da gyalenta cikin bacin rai tace "Tirrrr, tunda uwata ta haifeni ban taɓa kai wa warka ban ci abinci ba akan abinda bai shafeni ba, tun shayi da ɗan burodi da na ci da safe fa, ita kuma wannan mata Ammi Allah wadaranta, Allah wadaran hali irin nata, don wannan taurin kai ko a kafurai ba a samun me shi gaskiya, kai ko a dabba ma yanzu a daina samun masu taurin kai haka, ni ko nace in ta haifu cikin Sadiya da Ubale ta bar gidan nan taga tsiyar da zan mata wallahi, ita ko ɗan kuturun gidan Hajja bazai sa ta hakura ta zauna cikin rufin asirinta ba, mata sae kace kanwar shaidan don ma Mamudan me hakuri ne, to uban wacece ita da baza a ma kishiya ba ma dai tukun, kishiyar da rubabbiyar uwarta ce ta ja mata kowa ya sani, sam ni Ladiyo bana goyon bayan rashin gaskiya, abinda shegiyar amaryar da ke tafiya tinkis tinkis da duwaiwuka ba kanki zata zauna ba ina ruwanki da ita, to ni dai ba ruwana na daina asaran kudi na kan Ammi, in ma taki jin maganata ta koma kuturun gidan Hajja ni dai ina nan wallahi tallahi" Hajiya Amina ce ta sauko downstairs ita ma, Mama Ladi tayi tsit tana bin ta da kallo, Hajiya Amina tace "A kawo maki darduman nan ne Mama?" A fusace Mama Ladi tace "Ke ni fa ban ci komai ba fa sai ɗan burodi da shayi da safe" Hajiya Amina tace "Toh kiyi sallan zan hado maki abincin yanzu in sha Allah" Mama Ladi tace "Aa bari dai in fara ci don yunwar ta gigita ni wllh, kada inje sallan bai yi dai dai ba" Hajiya Amina tayi murmushi kawai ta shiga kitchen, Mama Ladi ta dinga murmushi ganin uban liyafan abincin da Hajiya Amina ta hado mata kamar wata matar sarki, babu abinda bata taɓa a abincin ba don sai da ta kusa cinye duk abincin tass, ta kwankwade shayi me ƙauri da ta hado mata sannan ta tafi bandaki tayi alwala tana cewa "Alhamdulillah" ko kafin ta fito Hajiya Amina ta shimfida mata dardumanta me laushi da kamshi, bayan Mama Ladi ta idar da sallah ta koma bangaren Ammi tana ta murmushi tunda ta koshi, har a sannan Ammi kuka take a parlor, Aunty Mariya na ta bata baki, Mama Ladi ta kyabe baki ta kishingida kan carpet tana sakace hakori tace "Mariya ga abinci can me shegen dadi Aminar ta dafa da zuka zukan kaji ki rufa ma kanki asiri kije ki deba ki ci kar ya kare, na ji tace har da na Umar Usman yaje daukosa a filin jirgi sun iso" Ko kallonta Aunty Mariya bata yi ba ta koma daki don tuni Ammi ta mike ta shige daki, Mama Ladi tace "Kishiya sai kace kanki farau, abinda na ga Aminar ma na da hankali da biyayya, ina laifin wanda ya mutunta naka, tun dazu take ji da ni a parlor, sai kinga liyafar da ta hada min na abinci ko iya cinyewa ban yi ba, to ni dai ba ruwana wllh..." Mayraah dake kwance ta daga kai tana kallon Hajiya Amina da ta shigo dakinta, mikewa zaune tayi tana kallonta, Hajiya Amina tace "Ko dai baki da lafiya ne Mayraah?" Mayraah ta girgiza kai tana murza ido don ko kallonta bata son yi tace "Bacci nayi" Hajiya Amina tace "It's almost 3pm ki fito ki debi abinci ki ci" kai kawai Mayraah ta gyada mata, ganin Hajiya Amina taki fita yasa Mayraah ta sauko daga kan gadon, har sannan taki yarda ta kalleta, Hajiya Amina ta bude kofar dakin ta fita Mayraah ma ta fito tana tafiya a hankali, ita kanta tasan she is not okay she is just trying to be fine, Hajiya Amina ta shiga nata dakin, Mayraah ta sauka downstairs, tun da tayi ido hudu da Ammi bata sake bude dakinta ba sai yanzu da Hajiya Amina ta shigo, bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo Umar na biye da shi da jakansa a hannu, Umar na ganinta ya ajiye jakarsa yana kallonta, can ya nufeta yana murmushi, duk da maganganun da Usman da Maheer suka masa na ringing a kansa hakan bai hanasa rungumeta ba kamar yanda ya saba duk sanda ya dawo, yace "Me kika dafa min Mimi?" Usman dai na tsaye yana kallonsu, Mayraah tayi murmushin karfin hali kawai ta kasa ce masa komai ya daga kanta yace "Are you sick?" Kai ta gyada masa tace "Amma da sauki" bata jira cewarsa ba ta nufi jakarsa ta dauka tace "Welcome back home bro" Daga haka ta tafi dakinsa dake downstairs, Umar ya bi ta da kallo sannan ya kalli Usman, zaunawa yayi kan kujera ya rike kansa, Mayraah na zuwa dakinsa wanda tun da sassafe Hajiya Amina ta gyara masa ta ajiye jakarsa sannan ta fito, bata sake kallonsu ba ta shiga kitchen, Usman ya bi bayanta, yana shiga kitchen din ta juya ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Kin shiga kin gaida Ammi?" Ta girgiza masa kai alamar A'a, ya ɗan yi shiru sannan yace "Yanzu me za kiyi?" Tace "Abinci zan zuba ma Ya Umar" Yace "Ke kin ci abincin?" Ta girgiza masa kai, yace "Debi naki kawai ki wuce daki, idan kin gama ci ki tafi ki gaida Ammi" Ta gyada masa kai, kasa cin abincin Mayraah tayi bayan ta deba ta tafi dakinta, can dai ta rufe ta mike ta fita daga dakinta ta nufi bangaren Ammi tana tafiya a hankali gabanta na faduwa, parlor ta bude a hankali kamar me tsoron taɓa handle din, tana shiga Mama Ladi dake ta zuba gyangyadi ta bude ido, gyara zamanta tayi da mamaki tace "Mera? wai dama kina gidan nan?" Mayraah ta gyada mata kai ta zauna kasa cikin sanyin murya tace "Ina wuni" Aunty Mariya da har a lokacin bata gaji da ba Ammi hakuri ba ita kanta tayi mamakin jin muryar Mayraah don ta ma mance ta tambayi Maheer ko ya dawo da ita, Ammi dake zaune gefen gado bata daina kuka ba ta mike ta nufi kofar dakinta ta saka makulli, jikin Aunty Mariya yayi sanyi ta bi ta da kallo, Mama Ladi ta kalli kofar dakin jin an kulle da makulli, taɓe baki tayi tace "Tashi kiyi tafiyarki in baki ci abinci ba ki samu Aminar kice ta baki abinci, ta girka lafiyayyen abinci me kyau, nima ban dade da gama ci ba" Mayraah dai sai kallon kofar dakin Ammi da taji an sa makulli take, Mama Ladi tace "Ko kin ci abincin?" Mayraah bata son taga hawayen da ya kawo idonta ta mike tace "Aa, zan ci yanzu" Daga haka ta juya ta fita ta koma dakinta, fadawa tayi kan gado ta dinga kuka tana jin zuciyarta na mata zafi... Babu yanda Aunty Mariya bata yi da Ammi kan ta gyara mata bangarenta ba don yayi ƙura Ammi ta ki daga karshe ta rufe Aunty Mariya da fada, Aunty Mariya ta ja bakinta tayi shiru.... Wajen karfe shidda Aunty Mariya ta fito rike da handbag dinta da akwatin Mama Ladi tana kallon Mama Ladi dake ta kallon TV a parlor ga bowl din fruits cike a gabanta tana sha, ganin Aunty Mariya ta washe baki, bata ko lura da akwatinta dake hannunta ba tace "Kin ga yanzun nan ta kawo min wannan Mariya, anya kuwa ba er kirki bace matar...." Aunty Mariya ta wani hade rai tace "Za mu koma gidan Hajja ne" Sai a sannan Mama Ladi ta lura da akwatinta dake hannun Aunty Mariya, ta ajiye slice din kankanan hannunta tace "Ajiya kika min a akwatin ne kika dauko min?" Aunty Mariya tace "Ae tashi za ki yi mu tafi magariba ya gabato" Mama Ladi ta matsar da bowl din gabanta kamar zata yi kuka tace "To gidan uwarki na zo da za ki ce in tashi mu tafi Mariya? Ko ina ruwanki da ni fisabilillahi idan ba neman magana ba?" Aunty Mariya tace "Yanzu Mama Ladi ko wani yace ki kwana gidan nan sai ki kwana bayan kin san abinda ke faruwa?" A fusace Mama Ladi tace "Aa ban san komai ba wallahi, wani sabon abun ya faru ne bani da labari? Ke ni fa ba yarinya bace Mariya da zaki kawo min raini zan ci uwarki la'ada waje wallahi, shi kansa Mamudan sai da ya tambayeni yace amma zan kwana biyu kafin in koma ko, nace masa to tunda yace haka bari in zauna zuwa kwana biyun kuma shine zaki zo min da rainin wayo da maganar banza, ina ruwanki da sabgata, gidan uwarki ko gidan mijinki?" Ajiye akwatin Aunty Mariya tayi ta fice daga Parlon ta bar gidan, Mama Ladi tace "Yau naga fitinanniyar yarinya kai, haka zan kama hanya in tafi in bar Ammin cikin wannan damuwan bazan zauna in dinga kwantar mata da hankali ba, sannan ga maganganu cike cikina da zan gaya mata game da tsinanniyar surkarta warce ni da kaina zan ja Hajja mu je gidan Mashir din da sassafe bayan na laka ma Hajjan karya Sanisar bata da lafiya rai a hannun Allah daga nan zan turketa ta fadi mugun abinda tayi da bakinta dama ga turarena da kasko na taho da shi a jaka, to ga dai na kishiya ya tabbata ko daga nan ai bai kamata a dinga shashantar da lamarina ba, ni ba boka nake bi ba Malaman gaskiya da suka san addini nake mu'amala da" Mama Ladi ta kare tana huci ta jawo bowl din fruit dinta tana sha..... Throughout ranan sai bayan magrib Maheer ya shigo gidan tun da ya fita da Haseenah da Badiyyah, dawowar da yayi yanzun ma don Ammi ta kirasa yafi sau uku tana son ganinsa ne amma da bazai zo ba, yana shigowa parlor ya tadda Mama Ladi da Hajiya Amina zaune parlon ga malmalan tuwo biyu a gabanta da miyan vegetable da yaji nama, Maheer ya karasa ya gaishesu, Hajiya Amina ta amsa, Mama Ladi tace "Ta zubo maka tuwon ne kai ma?" Maheer yace "Aa ai daga gida nake" Sama ya haura, direct ya nufi bangaren Ammi, zaune ya ganta a Parlon da Usman da Umar, alamar dai shi kadai ake jira, zaunawa yayi don tun dazu sun hadu da Umar a gidansa, sai da ma Usman ya fara kai sa gidansa har suka sanar masa abubuwan dake faruwa kafin su taho gida tare da Usman, a hankali Maheer ya gaida Ammi yana kallonta, duk wanda ya ganta yasan ta ci kuka ba na wasa ba ranan, Maimakon ta amsa gaisuwarsa sai cewa tayi "kun san dalilin kiranku nan?" Duk suka yi shiru suna kallonta, Banda Usman da kansa ke kasa, Ammi tace "To kun ga Mayraah?" Sai a sannan Usman ma ya daga kai yana kallon Ammi, ta girgiza kai as if counting her words tace "Babu ku babu ita har abada, ko magana ya sake hada ku da ita ban yafe maku ba, you 3 should just assume baku taɓa saninta ba, baku taɓa rayuwa waje daya da ita ba" Gaba dayansu kallonta suke babu ko kiftawa, da wani expression Umar yace "How Ammi? It's not her fault all this happen...." Tsawa Ammi tayi masa tace "Questioning dina zaka yi?" Yace "No, amma bai kamata ki ce haka Ammi ba, ni har yanzu zuciyata bata yarda ba ke ce kika haifi Mayraah ba to be sincere" Ammi ta mike tana kallonsa da kyau tace "To ba ni ce na haifeta ba Umar gashi ina gaya maka da kaina yanzu, ban hada komai da ita ba, don haka ina sake jaddada maku ko gaisuwa ya kara hadaku da Mayraah wallahi ban yafe maku ba gaba daya, sannan har yanzu ina kan bakata bazan zauna gidan ubanku ba, it's better ku samar min gida in koma don gidan Hajja ma bazan je ba" Tana kai wa nan ta shige Bedroom dinta. MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake. [7/12, 8:11 PM] Khaleesat Haiydar💖: Usman ne ya fara mikewa after almost 5 minutes ya fita daga Parlon, Umar ya mike ya shige dakin Ammi yana kallonta ya girgiza kai yace "Gaskiya ni bazan iya ba Ammi, zancen gaskiya kenan.... Me ta mana za mu daina kulata yarinyar da muka taso tare ku ka koya mana daukarta a matsayin little sister dinmu, me yasa tun a sannan baku sanar mana wacece ita ba sai yanzu da rana tsaka ku ce mana ba ku kuka haifeta ba, that not being enough kuma all of a sudden kice mu daina kulata, how will that be possible?" Ammi ta juya tana masa wani kallo tace "Kasan dama i am against ur coming back for this holiday ko? To kuwa zaka koma inda ka fito, in kuma kana da wata uwar da zata gaya maka kaji ne sai ka tafi ka sameta, get out Umar" Juyawa yayi ya fice daga dakin, ya bar parlon ma gaba daya banging the door behind him, Maheer ya bi sa da kallo ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, gaba daya ya kasa tashi a inda yake, Usman na komawa dakinsa ya dau jakarsa ya hada duk abinda zai hada a ciki ya fice daga gidan ba tare da yayi ma kowa sallama ba, Umar bai ma san action din Usman ba don shima yana shiga dakinsa dama jakarsa is already set, ya dauka kawai ya fice daga gidan trying to check if there is any flight to Abuja that evening with his phone. Sai da aka kira Magrib sannan Maheer ya tashi ya fita daga parlon Ammi, yana idar da sallah a masallacin layin ya shiga motarsa ya wuce gidansa. Daren ranan Mayraah bata yi baccin kirki ba, gaba daya taji gidan yayi mata zafi, sai kusan asuba bacci barawo ya sace ta kan darduman da ta kwanta bayan ta idar da sallah, washegari kafin karfe takwas ta shirya, kawai tana son shiga school ta nemi waje ta zauna ko zata ɗan ji sanyi a ranta, to gaba daya ta ma rasa wa zata ce ma zata tafi school yanzu, har cikin ranta taji tana tsoron Ammi ba kuma ta son ma ta hadu da ita, ta mike daga zaunen da tayi gefen gado ta dau jakar makarantar ta duk da jirin da take gani ta nufi kofa a hankali ta bude, kamar ko da yaushe yau ma Hijab ne har kasa jikinta, sauka tayi downstairs dai dai nan Hajiya Amina ta fito daga kitchen tana kallonta da mamaki tace "Ina kuma za ki?" Mayraah ta gaisheta sannan tace "Ban gama project dina ba zan shiga school ne in je cafe" Hajiya Amina tace "Toh ai baki karya ba, ga breakfast can na gama ki je ki diba" Sai a sannan Mayraah ta tuna throughout yesterday fa kamar bata ci komai ba sai ruwa da tayi ta sha kilan ma shi yasa take ta jin jiri yanzu, a hankali Mayraah tace "Toh" karasawa kitchen din tayi kawai ta hada shayi ta fito ta zauna dining ta na sha bit by bit, Hajiya Amina dake zaune parlon tace "Aa Mayraah ki je ki debi abinci, in baza ki ci Irish din ba akwai doya da kwai ki deba" Mayraah ta girgiza mata kai ba tare da ta kalleta ba tace "Bana iya breakfast da sassafe, idan naje school zan ci abinci" Hajiya Amina tace "Toh shikenan" Mayraah ta gama shan shayin ta mike ta kai cup din kitchen ta wanke sannan ta dawo parlor, Hajiya Amina tace "Abban ya san za ki school yau?" Mayraah ta gyada mata kai still not looking at her, Hajiya Amina tace "To transport fa?" Mayraah tace "Ya tura min" Hajiya Amina tace "Toh Allah ya tsare" Mayraah tace "Ameen" Daga haka ta fita daga gidan. Har Mayraah ta isa school bata sani ba don tayi nisa tunanin da take, har sai da mai adaidaita sahun ya juya ya kalleta don yana ta ce mata sun isa amma shiru kuma yaga idonta biyu ba wai bacci ko wani abu ba, Juyowan da yayi ne ya dawo da Mayraah daga duniyar tunanin da ta fada, ta fara kalle kallen inda suke sae kuma ta sauka da sauri ta basa kudinsa ta shiga cikin makaranta, nesa da department dinsu ta zauna har sai da karfe goma yayi sannan ta mike da kyar ta tafi cafe don yin printing copies din project din nata gaba daya, bata bar cafe din ba sai kusan 12, ita kanta tasan her Temperature is rising gradually, she is becoming so weak, ga wani ciwo da kanta yake, da kyar ta tako har department dinsu taga Motar Musharraf a parking space, ta shiga cikin department din ta tafi sama, sai da ta fara zuwa office din project co-odinator dinsu tayi submitting masa copy biyu da zata basa, sannan ta fito da copy daya zata kai office din Musharraf, tsaye tayi for few seconds bakin kofar kafin tayi knocking, sai da ya mata izini sannan ta bude kofar ta shiga ya daga kai yana kallonta, ita dai bata yarda sun hada ido ba ta karasa kusa da table dinsa still not looking at him ta ɗan risina tace "Good afternoon sir, i came to submit my project" Musharraf ya sauke idonsa daga kallonta after a minute ganin bazata dago kai ba, can kuma yace "When did i ask u to submit?" Shiru tayi bata ce komai ba, on a serious tone yace "I am asking u Madam" Still kanta a kasa tace "I can't remember sir" Yace "Ok i see, go and come back around 5:40pm" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa suka hada ido, lokaci daya ta dauke kanta ta juya ta nufi kofa, ya bi ta da kallo har ta fita ta kulle masa kofar sa. Mayraah na fita office din tana share hawayen da ya cika idonta ta sauka downstairs, ji tayi bata da strength din da zata ci gaba da zama makarantar har zuwa sanda yace, she is beginning to feel pain in all over her joint, nan da karfe biyar din da yace kusan awa biyar kenan fa, to ina zata je? In ma ta je masallaci zata takura masu sallah ne tunda kwanciya zata yi, Ummi ce ta tado mata, ta ciro wayarta a jaka bayan ta nemi waje ta zauna tayi dialing numberta, suna gaisawa cike da karfin hali tace "Ummi don Allah kina hostel?" Ummi tace "Wallahi ina school kinsan yau za mu yi final paper dinmu, kuma paper din 4pm ne, za ki je hostel din ne?" Mayraah tace "Eh na shigo inyi submitting project dina ne kuma supervisor din yace sae 5pm, to na gaji baxan iya zama school din har zuwa sannan ba" Ummi tace "To bari in zo department din naku in kawo maki key yanzun nan" A hankali Mayraah tace "To Nagode" Katse wayar tayi ta mayar jakanta, babu bata lokaci sai ga Ummi ta zo ta kawo mata makullin, Mayraah ta amsa ta mata godiya suka fita tare, Ummi ta koma department dinsu, Mayraah kuma ta wuce hostel, Mayraah na isa hostel din taji zazzabi ya rufeta, da kyar ta iya yin alwala saboda sanyin da ta fara ji, ta jira har lokacin sallah ya karasa sannan tayi sallah bayan ta idar ta kwanta ta rufa da bargon Ummi nan da nan bacci ya dauketa... A hankali Mayraah ta bude ido ta dalilin taɓata da taji anyi, da sauri ta mike zaune tana kallon Ummi, da damuwa Ummi tace "Baki da lafiya ne naji jikinki yayi zafi" Mayraah ta buda ido sosai tace "Karfe nawa pls?" Ummi ta kalli wayar hannunta tace "5:30" Mayraah tace "Innalillahi ban yi sallah ba, and i have to submit my project" Tana sauka daga kan gadon taji wani jiri ya debeta ta koma da sauri ta zauna ta rike kanta, Ummi ta rikota tace "You look very sick, kawai ki kira Supervisor din naki kice u are not feeling fine.... temperature dinki is so high" Mayraah ta girgiza kai da sauri tace "Aa zan iya" Daurewa tayi ta mike tana kallon flask din Ummi tace "Akwai ruwan zafi zan yi alwala" Ummi tace "Bari in daura maki" daga haka ta mike ta daura mata ruwan a kan gas, duk karfin hali kawai Mayraah ke yi amma duk jikinta ciwo yake mata, a haka tayi alwala ta dawo tayi sallah sannan ta dau jakarta tana kallon Ummi tace "Bari in je inyi submitting" Ummi tace "To za ki wuce gida daga can ne?" Mayraah ta gyada mata kai sannan ta mata godiya ta fita, ita kanta bata san da yanda ma ta iso department din nasu ba tsabar yanda take ji a jikinta, har a sannan Musharraf na school din don ta ga motarsa a parking space, the department was so quiet except for some few Lecturers dat are still around, alamar yau ba ayi exams din karfe hudu ba a department din or probably duk yan department din sun gama exams dinsu, hawa stairs kadai took her almost 7 minutes don sai ta huta take ci gaba da tafiyar, a haka har ta isa office din Musharraf tayi knocking, yana mata permission din shigowa ta shiga office din ta kulle kofar, wani mugun sanyi taji na shigarta saboda AC dake kunne, cike da karfin hali ta karasa gaban table dinsa taki kallonsa ta ajiye masa project work din nata kan table tace "Good evening sir" Shi dai kallonta kawai yake, ganin yaki ce mata komai gashi ta gaji da tsayuwar don jiri kawai take gani, ga sanyin da yasa ta fara shivering kawai ta zauna kan kujeran wajen, mikewa yayi ya zagayo ya zauna kujeran dake facing dinta yana kallonta a hankali yace "Are you okay?" Still taki barin ta hada ido da shi, he notice she is shivering, ya dau remote ya kashe AC din office din yana kallonta yace "Mayraah" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, and he saw how pale she look, mikewa yayi da sauri ya dafa goshinta ya hau jero mata tambayoyi without waiting for answer yace "Baki da lafiya ne? Your temperature is so high, have u been sick?" Duk da halin da take ciki ta wani hade rai ta cire hannunsa da sauri a goshinta, ta mike da nufin barin wajen ta ji wani dizziness tuni ya kamata ya zaunar da ita kan kujeran nan da nan hankalinsa ya tashi, still holding on to her yace "Tun yaushe ne baki da lafiya Pls??" Mayraah ta hade kanta da table bata ce komai ba, da sauri ya koma ya bude drawer dinsa ya ciro Blood pressure gauge ya dawo, ya duƙa gabanta ya kamo hannunta, janye hannun tayi nan da nan hawaye ya cika idonta amma ta kasa cewa komai, cike da damuwa yace "Pls ki bari in duba B pressure dinki..." Haka nan ta bari ya dubata, yayi unwrapping din inflating rubber cuff din da sauri ya zauna kujeran da ke kallon wanda take, a bit shocked yace "Subhanallah, ur blood pressure is beyond low, Baby what's wrong with you? Me yake faruwa?" Mayraah dai bata dago kanta ba hawaye ne kawai ke zuba idonta, Mikewa yayi ya dauko mug dinsa ya dauraye ya zuba ruwan zafi ya hada mata coffee drink ya ɗan yi diluting dinsa da bottle water ya dawo gabanta ya dagota yace "Drink this plss dear, it's a first aid, sae mu tafi hospital right away" Hannunta na rawa ta amshi mug din, ganin haka yaki sake mata ya fara bata coffee din da kansa, sae da ta kusa shanyewa ya kyaleta ya ajiye cup din, ya kashe fridge din office din ya sake curtain din windows ya dawo ya dau makullin motarsa amma sae ya tuna ba lallai ta iya tashi da kanta ba, assuming ba department suke ba he will definitely assist her, kawai ya fita office din hoping zai ga wani student mace or even a female Lecturer da zata rike Mayraah zuwa Motarsa, Dr Asma'u ya samu office dinta, ta biyosa har nasa office din bayan ya gaya mata abinda ke faruwa, ta dago Mayraah tana mata sannu suka fito daga office din har zuwa parking space tana rike da ita, back seat ta bude mata tana kallon Musharraf tace "Dr ko zaka jira in rufe office dina mu tafi asibitin tare?" Yace "Toh ba damuwa" Ta koma cikin department din, sannu kawai yake ma Mayraah da ta hade kanta da seat din motar, a haka Dr Asma'u ta dawo ta samesu da jakarta ta shiga back seat din ta dago Mayraah tana mata sannu, Musharraf ya shiga motar suka kama hanyar asibiti. Tun da aka yi ma Mayraah allurai aka sa mata drip take bacci, Dr Asma'u suna isowa asibitin bayan anyi admitting Mayraah dama ta wuce gida, Musharraf na ganin karfe takwas yayi kawai yayi deciding ya kira Maheer cause definitely yasan za a kikkira Mayraah a waya kuma jakar na office dinsa, he was even surprise da ya ga har a sannan Maheer bai kirasa ba tun da zuwa yanzu dai yasan dole za a san bata koma gida ba, Maheer na daga kiran bayan sun gaisa, Musharraf yace "Mayraah ce bata da lafiya anyi admitting dinta hospital since around 6:30...." Maheer yayi shiru, sai kuma a hankali yace "Subhanallah, bana gari but zan tura maka number Abbanmu right away, nima ban jima da kunna wayar ba kilan Abban ya neme ni bai sameni ba, let me send u his contact now" Musharraf yace "To ina jira" Babu bata lokaci Maheer ya tura masa number Abba, Musharraf yayi dialing bayan Abba yayi picking, ya gaishesa sannan yayi introducing din kansa tare da sanar masa dalilin kiran duk a lokaci daya, Abba yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, tun 6 ake kiran layinta no response...." Musharraf yace "Eh i think jakar nata na makaranta" Abba yace "Wani Asibitin ne?" Musharraf ya sanar masa, Abba yace "Gani nan zuwa yanzu, thank you" Daga haka ya katse wayar. Hajiya Amina ta fito daga dakinta sanye da hijab bayan Abba ya sanar mata Mayraah na hospital, sai ga Mama Ladi ta taho daga bangaren Ammi rike da kwanon abincin da ta ci zata kai kitchen, Hajiya Amina tace "Mama wai malamin makarantar su ya kira tana asibiti an kwantar da ita, yanzu Abban nasu ya kirani yake gaya min" Mama Ladi ta saki salati tace "Mun shiga uku, asibiti kuma, me ya sameta? to ke yanzu ina za ki da hijabi?" Hajiya Amina tace "Asibitin za mu tafi, yana waje yana jirana" da sauri Mama Ladi tace "Jirani in dauko gyale mu tafi tare kawai, ai hankalina bazai kwanta ba idan ban bi ku ba" Hajiya Amina tace "Toh zan jira ki a kasa Mama" Da sauri Mama Ladi ta koma bangaren Ammi, Ammi na zaune kan darduma a parlon, Mama Ladi ta ajiye mata kwanon hannunta ta figi mayafinta tace "To ga Mayraah can bata san inda kanta yake ba a asibiti rai kwakwai mutu kwakwai, yanzun nan aka kira daga asibitin aka sanar za mu tafi da su Mamuda" Ammi ta juya da sauri ta kalli Mama Ladi da har ta fice daga Parlon da gudu da mayafinta. Ko da suka isa asibitin har a sannan Mayraah bacci take, Musharraf ya mike daga kan plastic chair da yake zaune yana ma Abba sannu da zuwa da ladabi, kallo daya Abba yayi masa ya amsa ya karasa gadon ward din yana kallon Mayraah, Musharraf ya gaida Mama Ladi da Hajiya Amina da ladabi, Hajiya Amina ce kawai ta amsa, Mama Ladi ta dafe kirji cikin rawan murya tace "To me ya sameta ni Ladiyo? Ko dai hatsari tayi? Don lafiya ta fita gida" Abba ya kalli Musharraf yace "I want to see the Dr" Musharraf yace "Toh yana office Abba" Abba ya bi bayansa suka fita zuwa office din likitan. Har karfe sha dayan dare Mayraah bata farka ba, Hajiya Amina ta koma gida ta kawo mata blanket da kayan shayi da flask ta dawo, babu yanda Abba bai yi da Mama Ladi kan a maida ta gida sai Hajiya Amina ta kwana da Mayraah ba amma taki, Hajiya Amina na kallon Abba tace "To kawai ka tafi bar Alhaji" Da sauri Mama Ladi tace "Aa, bi shi ku tafi, ni kadai raina na isa in dubata, abinda duk 'ya yan mijina da jikoki haka na dinga wahala da su in aka kwantar da su a asibiti gashi gantalallun ko bin ta kaina basa yi yanzu, ai in da sabo ni dai na saba da jinyan jama'a a asibiti, kawai ku tafi kuyi baccinku ni ina nan" Babu yanda suka iya haka nan suka tafi gida leaving Musharraf behind duk da Abba yace masa ya tafi gida shi ma it's already late, Mama Ladi na kallon Musharraf bayan tafiyarsu Abba tace "To kai kuma bawan Allah ai mun gode kuma haka, ka kama hanya kayi tafiyarka Allah ya saka da Alkhairi, ko da wani abun da kake so a baka ne da ka kasa ka tsare ka ki tafiya?" Musharraf dake kallonta yayi mata sallama ya juya ya fita daga ward din, tace "Haba, kai ba saninka aka yi ba ba komai ba, daga kawo yarinya asibiti kawai sai ka makale cikin mu kaki tafiya, in ma wani abu kake so a baka ai da tun wuri kayi ma Mamudan magana ko er dubu biyar ce ya sallameka da shi" reception Musharraf ya koma ya zauna don bai jin zai iya tafiya gida, tun da Musharraf ya fita daga dakin Mama Ladi ta dau bargon da Hajiya Amina ta kawo ma Mayraah sabo fil da shi a leda ta fiddo shi ta warware ta shimfida kasa ta kwanta, ko minti biyu bata yi da kwanciya ba ta cika dakin da minsharinta. Wajen karfe sha biyu da rabi Mayraah ta farka, sosai kanta yayi mata nauyi ta kasa bude idonta gaba daya, ta mike zaune da kyar tana bin dakin da kallo, amma ta kasa sunkuyawa ta ga wanda ke minshari a kasa tsabar ciwon kai, a hankali aka bude kofar dakin Musharraf ya tsaya bakin kofar yana kallon Mama Ladi dake ta baccinta kamar a dakinta take, ya karaso cikin ward din bayan ya kulle kofar a hankali, ya nufi gadon yana kallon Mayraah da damuwa yace "Baby kin tashi? How are you feeling now?" Ta kasa cewa komai, bude flask yayi ya fara hada mata shayi me kauri sannan ya mika mata yace "Zaki iya rikewa?" Ta amshi shayin ya zauna plastic chair dake kusa da wajen yana kallonta, a hankali ta dinga shan shayin, ta sha me ɗan yawa ta mayar masa da sauran ya ajiye, ya dau magungunan da Dr din ya bari a dakin da za a bata idan ta farka, ya budesu ya bata ta amsa ta sha da bottle water, ganin tana disconnecting drip din daga hannunta yace "Me yasa kike cirewa?" Cike da karfin hali tace "Zan yi sallah" Yace "Ohk" Tashi yayi ya cire mata da kansa, sannan ya kamo hannunta ta sauka daga kan gadon a hankali, duk wannan abun Mama Ladi na ta buga minsharinta kamar kato na bacci, Mayraah na idar da sallah Musharraf ya maida mata ruwan, yana kallonta yayi kasa da murya yace "I am sorry Mayraah, i am sorry for everything" Ita dai bata ce masa komai ba, a hankali yace "You know i love u so much" Komawa tayi ta kwanta ta kulle idonta, bai kuma ce mata komai ba sai kallonta yake, har yaga alamar ta koma bacci. Musharraf bai bar dakin ba sai da aka kira sallan Asuba, kuma har sannan Mama Ladi bata farka ba, ya kamo hannun Mayraah dake bacci yayi pecking dinsa sannan ya fita daga ward din ya kulle kofar. Washegari da safe karfe bakwai Mama Ladi na zaune kan Bargon da ta kwana ta hada shayinta cikin Cup, Mayraah dai na kwance idonta rufe duk da ba bacci take ba, Bude kofar ward din aka yi Hajiya Amina ta shigo da sallama da basket din breakfast, Mama Ladi ta amsa sallaman, Hajiya Amina ta gaisheta da ladabi, Mama Ladi tace "Lafiya lau" Hajiya Amina tace "Ya kwanan takura" Mama Ladi tace "Wani kwana er nan? Ni ina naga ta bacci an bar min amanar yarinya, ke dai kawai ayi sha'ani, ita kam dai ta sha baccinta" Hajiya Amina tace "Allah sarki, dama gida zaki tafi yanzu ki samu kiyi wanka ki karya sai ki kwanta kiyi baccin ki huta" Mama Ladi tace "Aa ni ba sai na wani je gida ba, abinda in da sabo na saba, sae in iya kai wa wani daren a haka ma" Hajiya Amina tace "Toh bari in zuba maki abincin kawai ki karya" Mama Ladi tace "Yauwa to, dama yunwa nake ji" Karfe takwas Musharraf ya shigo ward din har yaje gida yayi wanka ya dawo, Mama Ladi na kallonsa tace "Yau naga bala'i sake dawowa kayi ɗan nan? Ba nace ka tafi mun gode ba" Hajiya Amina tace "Mama naji fa Alhaji yace malamin makarantarsu ne, shi ne ma ya kawota asibitin" Mama Ladi tace "Ayyoo to kai ba sai kayi bayani ba, wallahi na zata irin gayun nan ne masu zaman banza, naga sai sintiri yake kamar yana son a biyasa abinda yayi, ashe malami ne sannu kaji yaro" Musharraf dai murmushi kawai yake ya karaso, tana kallonsa tace "Ai tun da ka tafi ka bar mu wajen karfe sha biyun nan har yanzu a haka nake, hana rantsuwa dai na ɗan gyangyada" Musharraf ya dinga kallonta babu ko kiftawa. MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 *Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/13, 6:11 PM] Khaleesat Haiydar💖: Karfe goma saura Abba ya zo asibitin duba Mayraah, tana zaune kan gado da fruits a gabanta an sa mata wani drip din don wancan ya kare, Ta daga kai tana kallon Abba dake tambayarta ya jikinta tace "Da sauki Abba" Yace "Are you sure?" Ta gyada masa kai, yace "Toh Allah ya kara afuwa daughter" Mama Ladi tace "Yo jiya ina ma ta samu sararin shan kankana da su lemo, jiki ai yayi sauki Mamuda" Abba yace "Gaskiya ne, yanzu zaki tashi in maida ke gida kema kiyi wanka ki huta kiyi bacci Mama, ita kuma Hajiya Amina ta zauna nan da ita zuwa anjima...." Mama Ladi ta katse sa tace "Aa ai ba cewa nayi na gaji da jinyan ba Mamuda, ita Aminar ta koma kawai ko girki ne sai tayi ta kawo mana" Abba yace "Aa da dai mun tafi gida kin huta Mama" Mama Ladi tace "Na fa ce kar ku damu da wai ban yi bacci ba, na saba da irin wannan jinya a asibiti, idan Aminan ta kawo abincin anjima muka ci sai a maida ni gida inyi wanka, in ba a sallameta ba har zuwa dare sai a dawo dani nan wajenta" Abba yace "Toh shkkn" Hajiya Amina na kallon Mayraah tace "Allah ya kara lafiya dear, anjima zan dawo in sha Allah" Kai kawai Mayraah ta gyada mata, Hajiya Amina tayi ma Mama Ladi sallama sannan suka fita da Abba, Mama Ladi ta jawo sauran ƙwan da ke cikin warmer da Mayraah ta ki ci ta fara ci. Mayraah na kwance wajen karfe sha biyu da rabi ta kalli Mama Ladi dake shan lemon ɓawo tace "Mama, yaya ya zo ina bacci ne?" Mama Ladi tace "Waye kuma yaya? Mashir ko Usman?" Mayraah ta gyada mata kai, Mama Ladi tace "Yanzu lemon nan da nake sha nazarin da nake kenan a raina wallahi, ai baza su ce basu ji baki da lafiya ba kina asibiti tun da tun a jiyan da ake ta neman inda kika tafi har Mashir sai da Mamuda ya kira aji ko kin je gidansa Mashir yace a'a baki je ba, ai idan ya damu da sai ya zo gidan a daren da yaji ba a ganki ba amma wallahi bamu ga ko keyarsa ba, tun da garin Allah ya waye nake zuba ido in ga shi ko Usman sun zo duba ki shiru har yanzu ana neman karfe sha biyu, babu shi, babu Usuman din balle uwa uba kafurar nan don ni dai na fara tunanin anya Ammi musulunci take kuwa, kai kamar fa bata cikinmu yanzu gaskiya, ke ki ga fa sai wani bare can da kawai taimakonki yayi ya kawo ki asibiti ke ta sintirin shigowa duba mu kamar wasu marasu galihun dangi, jiya ma sai da na kore yaron wajen karfe sha biyun dare sannan ya tafi, kina ganin yau da sassafe kuma sai gashi, ga yaron kyakkyawa da shi kamar bafillatani ne ina ji, to daga shi sai Mamuda da sabuwar amaryarsa kadai ke zuwa mana, ma'aikatan asibitin ba sai suyi tunanin bamu da dangi bane" Ko rufe baki Mama Ladi bata yi ba aka bude kofar ward din ta daga kai da sauri, Musharraf ne ya shigo da sallama with basket of food, Mama Ladi ta gyara zama ta ajiye bawon lemon hannunta tana ɗan murmushi tace "Sannu da zuwa" Ya ajiye abincin ya gaisheta, ta amsa da fara'a tace "To wai ya ma sunanka ne?" Yace "Sunana Musharraf" Mama Ladi ta gwalo ido tace "Musharri? Sharri fa kace?" Mayraah ta kauda kai ta ɗan yi murmushi, Musharraf ya sunkuyar da kansa yace "Abdallah ake kirana" Mama Ladi tace "Ayyo, har hankalina ya tashi, to sannu da zuwa Audullahi, naji dadin yanda ka nuna ka damu da jikata daga taimako, Allah ya maka albarka" Ya ɗan yi murmushi yace "Ameen" Mama Ladi tace "Dama ina ta jiran wanda zai zo nima in ɗan samu in fita in ɗan motsa kafafuwana, tun jiya mutum na waje daya kamar gunki kada jini ya daskare min" Daga haka ta mike tana yafa gyalanta ta nufi kofa, Musharraf ya nufi Mayraah bayan ta fita yana kallonta yace "How are you feeling now dear?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ba inda kike jin ciwo?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "Mami ta bada abinci a kawo maki, zata zo dubaki nace mata ba sai ta zo ba" Mayraah ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Nagode" Hannu zai kai goshinta ta kauce da sauri, yayi kasa da murya yace "I just want to feel ur temperature" A takaice tace "Don't worry, i felt it my self minutes ago" Bai sake cewa komai ba ya zauna kan kujera, yace "Ammi bata nan ne? Naga ban kanta ba har yanzu" Mayraah ta gyada masa kai kawai, sai kuma ta kwanta ta juya masa baya don bata son zancen, a hankali Musharraf yace "Thursday za ku yi Internal Defense, but u need not to worry about that, external din ma kar ki damu i will sort it out, kina bukatan hutu sosai yanzu" Murya can kasa Mayraah tace "Thank you" shi dai kallonta kawai yake don har a lokacin bata juyo ba, ko minti biyar ba ayi da fitan Mama Ladi ba sai ga ta ta dawo tace "Toh Alhamdulillah na zaga har na dawo" Musharraf yace "To sannu da dawowa Mama" Mama Ladi tace "To amma na fa ji ana ta kiran sallah a masallaci" Mikewa yayi yace "Eh yanzu zan tafi" Tace "To maza ka tafi" yana fita Mama Ladi ta hau bude abincin da ya kawo, buda baki tayi tace "Kai kai kai, wannan abinci haka kamar a gidan sarauta" sai kuma tayi murmushi ta kalli Mayraah tace "Za ki ci ne?" Mayraah tace "Na koshi" Mama Ladi bata sake bin ta kanta ba ta dau plate ta fara zuba abincin ta tula nama ta koma ta zauna tana ci. Throughout ranan daga Mama Ladi, Hajiya Amina sai Musharraf idan ya shigo ne kadai ke tare da Mayraah a asibitin, wajen karfe uku na yamma 3 of her lecturers tare da Dr Asmau suka zo dubata a asibitin da ledan fruits, Mama Ladi sai sa masu albarka take bayan Mayraah ta sanar mata malaman makarantansu ne har suka tafi, Sai a sannan Mayraah ta koma ta kwanta da tunani iri iri cike fal ranta, she felt so relieved da ta tuna bata da wani issue na project da defense a yanzu kuma, she will just assume ta gama kawai. karfe uku da rabi Hajiya Amina ta koma gida don yin girkin dare ta kawo masu, sai bayan da suka fita Mama Ladi ta rike kanta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah wadaran Ammi, Allah wadaran kafirin zuciya irin nata, wato har 'ya yan ma ta hanasu zuwa kenan, magana na ta ci na ba daman inyi gaban wannan baiwar Allah dake ta hidima da mu a asibitin nan taje kawai ta raina mu, Kaiii a gaskiya Mamuda bai yi dacen uwar gida ba bazan ci amana in ki fada ba gaskiya" Ita dai Mayraah na kwance bata ce komai ba banda ɗan murmushi da tayi, Mama Ladi ta ciro wayarta da aka nannade da rubber band ta mika ma Mayraah tace "Kira min Mashir din" Mayraah ta kalleta, a hankali tace "Me za ki ce masa Mama, kawai ki..." Katseta Mama Ladi tayi a fusace tace "Ina ruwanki? Ke dai ba kawai cewa nayi ki kira min shi ba ki miko min" Mayraah ta amshi wayar tayi dialing number Maheer ta mika ma Mama Ladi da ta danna handsfree, sai da ya kusa katsewa ya daga, Mama Ladi bata amsa sallamansa ba tace "Mashir wai baka da labarin an kwantar da kanwarka tun shekaranjiya yau kwananta uku kenan a asibiti?" Maheer ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Ai bana gari" Mama Ladi tace "Baka gari? To shi Usuman shi ma baya gari da wannan farin yaron da ya dawo jiya?" Maheer yace "Gaskiya ban sani ba" Mama Ladi tace "Toh ko da baka gari ai sai ka kira kace a baka Meran kaji jikinta, yarinyar da aka kawo asibiti bata numfashi sai da kyar yau ta fara numfashi amma duk cikin kai da yan uwanka babu wanda ya zo dubata?" a hankali Maheer yace "Aiki naje ne Mama" Mama Ladi tace "To ba laifi" Daga haka ta ba Mayraah wayarta tace "Kashe min" Mayraah ta amsa ta katse sannan ta mika mata. Karfe shidda saura likitan ya shigo daki zai sallami Mayraah, Mama Ladi tace "Kar fa mu koma gida jikin ya kara rikicewa dafta, ni dai ina ga gwara a bari a ga zuwa gobe tukun" Likitan na murmushi yace "Jinin nata ya dawo normal Baaba, kawai magunguna zata ci gaba da sha, da kuma wasu cimar da zata maida hankali gun ci yanzu, duk na gaya ma Abbanta" Mama Ladi tace "Toh shikenan, amma ai uban bai san za ayi sallama ba yau, ga abinci can anje gida za a kawo mana kuma" Likitan yace "Bamu jima da gama waya da shi ba, yace zai zo bayan magariba ya tafi da ku gida" Mama Ladi tace "Atoh shikenan ba damuwa, Allah maka albarka" Likitan yace "Ameen Baaba" Ya maida dubansa kan Mayraah yace "Allah ya kara afuwa yan mata" A hankali tace "Ameen Nagode" Juyawa yayi ya fita, Mama Ladi tace "To kuma idan muka tafi wannan malamin ya kara kawo abinci fa, kar fa asa yaje yayi asaran abinci da sun bari can bayan isha'i a sallame mu" Mayraah dai kallon Mama Ladi kawai take, don tayi nisa tunanin da take bata ma san me Mama Ladi take cewa ba, Bude kofar aka yi Musharraf ya shigo Mama ladi tace "Kaga ɗan halaq yanzu nake maganarka nace kar kuma ka zo ka tarar bama nan, don za a sallame mu inji likita" Musharraf yayi murmushi ya gaisheta yace "Ai ina asibitin dama ban tafi ba" Mama Ladi tace "Allah sarki" karasawa yayi ya ajiye ma Mayraah jakarta na makaranta yace "Kin ji sauki sosai ko?" Ta gyada masa kai, yayi kasa da murya yanda Mama Ladi baza taji maganar ba yace "Can i come home in dubaki?" Sai a sannan Mayraah ta daga kai suka hada ido, tayi saurin sauke idonta tace "Gobe in sha Allah" Yace "Toh Allah ya kai mu" Tace "Ameen" Musharraf yace "Dr din yace min Abba is on his way zai kai ku gida yanzu, so ni zan wuce, and i need one favor from u pls Mayraah" Ta daga kai tana kallonsa, a hankali yace "Unblock me plss" Shiru tayi bata ce komai ba yace "Pls" Ta bude jakar ta ciro wayarta, yana kallonta tayi unblocking digit dinsa, a hankali yace "Saura Whatsapp" nan ma ta shiga tayi unblocking dinsa, ya sakar mata murmushi yace "Thanks" Daga haka ya juya yayi ma Mama Ladi sallama tace "Au har zaka tafi kai ma, toh mun gode Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen ya Allah Mama, Allah ya kara mata lafiya" Mama Ladi tace "Ameen, idan ya so ko gida ne zaka iya zuwa ka dubata kanka tsaye kaji?" Yace "In sha Allahu zan zo gobe" Mama Ladi na washe baki tace "To muna nan muna jiranka" Daga haka ya fita daga ward din, Mama Ladi ta dawo kusa da Mayraah tace "Ke ko dai sonki yake ne, wannan kulan da yake baki kamar ba banza ba wllhi" Mayraah ta girgiza kai tace "Aa ba haka bane" Mama Ladi ta koma ta zauna tace "To ke me kika sani, mu da muka ga jiya muka ga yau, Allah dai ya kawo sa goben ni zan bincikesa don bana son nuku nuku" Mayraah dai bata ce mata komai ba, ana idar da magrib Abba ya iso ya daukesu duk suka wuce gida. Suna isa gida bayan Abba yayi parking Mayraah ta sauka daga cikin motar, Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Jira za mu yi magana Mamuda" Abba yace "To Mama" Mama Ladi ta sauko daga motar tana kallon Mayraah dake kokarin dauko abubuwan da suka dawo da shi daga asibiti tace "Yi wucewarki ki kwanta duk zan kwaso su, ina kika ga karfin jidan kaya" Juyawa Mayraah tayi ta nufi cikin gidan, Mama Ladi ta koma kusa da Abba tayi kasa da murya tace "Mamuda kasan bayan ƙin zuwa da wannan matar tayi har 'ya yanta ma ta hana su zo duba baiwar Allahn nan a asibiti? Wannan wace irin rayuwa ce fisabilillahi?" Abba ya dan yi murmushi yace "Ina sane Mama, tasa ai Usman da Umar sun bar gidan nan yanzu haka basa nan" Mama Ladi ta saki salati tana tafe hannu, Abba yace "Amma zan dau mataki nan ba da dadewa ba in sha Allah, duk zan yi maganinsu har Maheer din" da sauri Mama Ladi tace "Aa don Allah kayi hakuri, nasan kayi hakurin nan kuma kana kan yi, amma don Allah ka ci gaba da yi sai kaga duk kamar ba ayi ba wllh, kaga ai ni bana goyon bayan mugun abun nan da suke, don haka sai kaji sanyi ta bangarena, ita kuma Ammi ka rabu da ita kar ka biyeta akwai ranan kin dillanci, su kansu mazan ka bar su su ci gaba da taya uwarsu goyon bayan rashin gaskiya su ma akwai ranan kin dillanci da ina masu kallon masu hankali ashe duk yan iska ne munafukai ace har Mashir yaki takowa ya duba marainiyar nan a gadon asibiti, amma ba komai, ita kuma Mera ni da wannan matar taka me hankali mun isheta a yanzu dai, kayi hakuri komai zai wuce in sha Allah" Abba da yayi shiru kansa a kasa yana sauraronta, ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh shikenan Mama nagode sosai" Mama Ladi tace "Yauwa Allah maka albarka, ka ci gaba da hakuri dan nan, duk me hakuri na tare da Allah" Ko da Mama Ladi ta shiga gidan dakin da Mayraah take ta tafi, nan taga Hajiya Amina har ta kai ma Mayraah abinci sama, Mama Ladi ta zauna kan darduma tace "Ni ma kawo min nawa nan kawai er nan" Hajiya Amina ta gaisheta tana mata sannu da zuwa sannan ta fita taje dauko mata nata abincin bayan ta ajiye ta fita. Hajiya Amina na kallon Abba bayan ta ajiye masa abincinsa tace "Alhaji ina da suggestion plss idan baza ka damu ba" Abba ya kalleta yace "To ina jin ki Amina" Ta ɗan yi murmushi tace "Alhaji ina ga fa kamar zamana a gidan nan ba mai yiwu bane with the way things are going, why not kawai ka bar ni in koma gidana kai ka dinga zuwa can din, idan kuma baka son zuwa gidana ne ko haya ne sai ka kama min ko da daki biyu ne Alhaji, ita kuma Mayraah zata iya dinga switching daga gidana zuwa nan gidan ta yanda uwar goyonta bazata kullaceni ba bazata kullaceta ba don yanzu koma waye gani zai yi kamar na zo ina shisshigin rabata da yarinyar ne which is not so, ina ga kamar wannan shine masalha kawai Alhaji, don a gaskiya abubuwa baza su daidaita ba haka sai dai su kara rikicewa, kaga ina dawowa gidan nan duk sons dinka sun bar gidan u just confirm that this morning, to saboda ni kuma kaga ai bai cancanci su bar comfort zone dinsu ba" Abba ya girgiza kai yace "Babu inda za ki Amina, u remain in this house, duk wanda bazai zauna saboda kina gidan ba ya tattara ya tafi duk inda za shi, as far as Mayraah is going to be comfortable bani da damuwa da haka, kowa yayi abinda ya ga dama gatan da suke da shi a yanzu dai ita bata da shi so my major concern now is Mayraah, kamar yanda nace su suna da gata ita kam bata da shi, zan bar su su yi duk yanda suke so....." Hajiya Amina tayi shiru bata sake cewa komai ba tana kallon Abba, har yau fa common gaisuwan nan Ammi taki bari ya hada su, iyaka ta shigo kitchen tayi abinda zata yi ta wuce sama babu annuri a fuska. A daren Mayraah na kwanciya ta kashe wayarta ta rufe har kanta da bargo amma har karfe dayan dare idonta biyu ta kasa bacci, tana jin Mama Ladi na ta minshari a shimfidar da Hajiya Amina tayi mata a kasa, Mayraah bata ji dadin kwanciyar da Mama Ladi tace zata yi a dakinta ba cause she needs privacy a wannan moment din. Mayraah na zaune kan darduma bayan ta idar da sallan asuba taji Mama Ladi na wanka a bandaki bayan ita ma tayi sallan, Mama Ladi na fitowa ta bude akwatinta wanda suna dawowa daga asibiti jiya da daddare taje bangaren Ammi ta daukosa ta ajiye a dakin Mayraah, Ammi bata tambayeta ya mai jiki ba ita ma bata ce mata ci kanki ba, iyaka ta amsa gaisuwar da Ammin ta mata ta fita daga bangaren, Mayraah na ta kallon Mama Ladi har ta gama saka kayanta, ta yafa gyalenta tana kallon Mayraah tace "Ko zaki leka kasa kiyi ma wancan matar magana ta kawo min kumallo don ina da inda zanje yanzu haka" Mayraah tace "Toh" tana fita dakin bayan some minutes suka dawo tare da Hajiya Amina ta ajiye breakfast din hannunta ta durkusa tana gaida Mama Ladi, Mama Ladi ta amsa tace "Lafiya lau wllhi ke dai, dama zan je gidan yayata ne in gaisheta shi yasa zan karya kafin in fita kada in fita ba komai a cikina" Hajiya Amina tace "Hakan ma yayi Mama, bari a hada maki shayin" Bayan Hajiya Amina ta hada mata shayin ta zuba mata abubuwan da tayi for breakfast a gidan ta mike ta fita, sai da Mama Ladi ta tilasta Mayraah suka yi breakfast din a tare, Mayraah dai shayin kawai take sha da kyar, har Mama Ladi ta gama ta mike tayi gyatsa ta dau katon handbag dinta tana kallon Mayraah tace "Zuwa karfe goma zaki ga na dawo idan na gama abinda ya kai ni, kina shan maganinki ki fitar ma Amina da kwanukan ki ajiye mata can kitchen ki dawo ki kwanta kiyi bacci abun ki kinji" Mayraah felt so much relieve tana kallon Mama Ladi a hankali tace "Toh Allah ya tsare" Mama Ladi tace "Ameen daga haka ta fita daga dakin" Mayraah na ganin fitan Mama Ladi ta sauko daga kan gadon a hankali ta shiga bandaki tayi wanka a gurguje, tana fitowa bayan ta shirya shima sharp sharp, ta nufi jakarta maidaidaici ta dauka, ta dau kwalayen phones din da Usman da Maheer suka siya mata kwanaki ta saka su a cikin jakar, sannan ta dau Atm card da Usman ya taɓa bata da nata Atm card din su ma ta saka a jakan, bin dakin ta dinga yi da kallo, ta shiga bandaki ta dau tooth paste da tooth brush dinta da sabulu da sponge ta saka su a Wani leda ta sa cikin karamin jakar, ta bude press dinta ta ciro iron hijabs dinta uku da dogayen riguna uku duk ta saka a jakan with few of her undies, ta dau perfumes kanana su ma ta saka a jakan sannan ta rufe jakar ta ajiye gefe daya, a hankali ta bude kofar dakin ta fita ta sauka downstairs tana kalle kalle, bata ji motsin kowa a kitchen ba, ta dawo sama da sauri ta dau handbag dinta ta rataye bayan ta sa charger dinta da power bank with lip gloss a ciki, sannan ta dau karamin jakar ta fita daga dakin gabanta na faduwa ta sauka downstairs ta nufi kofar fita, da sauri ta fice daga compound din gidan ta nufi bakin titi tana waige waige kamar munafuka ta samu adaidaita sahu yana tambayarta inda zata je tace "Tasha" sannan ta shiga da sauri. Hajja na kallon Mama Ladi da ta ki zama tace "Ke wa ya gaya maki wannan maganar Ladi?" Mama Ladi tace "Ka ji ki da wani zance kuma Hajja, nace maki Mashir din da kansa ya kirani tun jiya da daddare, shine naga kema ya kamata kije ki dubota idan ya so sai ki bar ni a can kawai ki dawo gida, babu wanda dae zai ce baki je ba, yace yan uwanta kawai ke zuwa dubata kuma hakan ba dadi, ki tashi kawai mu wuce ban sallami me adaidaita sahun ba yana jiranmu" Hajja tace "Subhanallahi, to yanzu asibitin da aka kwantar da ita za mu je kenan?" Mama Ladi tace "Aa yace a nan gida aka sa mata ruwa, ni dama ba sanin gidan nayi ba ke kwanaki naji kina cewa za ki gane gidan, Hajja lokaci na ta wucewa kada yaga kamar ban damu da damuwarsa ba ki tashi mu je don Allah tunda tun jiya ya kirani ya sanar min" Hajja tace "To bari in tashi, to ko laulayi take Haseenar?" Mama Ladi tace "Ni ma nafi tunanin hakan gaskiya" Haka nan Mama Ladi ta ja Hajja suka kama hanyar gidan Maheer a daidaita sahu, Mama Ladi sai girgiza kafa take a adaidaita sahun, abu biyu yasa ta zo ta tafi da Hajja, na farko so take duk tonan sili da zata tayi ma Haseenah a gidan da turaren da zata kunna ace a gaban Hajja za ayi komai taji yanda Haseenah zata tona ma kanta asiri da kanta, na biyu kuma dama ita bata san gidan ba dole sae ta samu mai kai ta wannan yasa ta zo ta tattago Hajja ta lafta mata karya wai Haseenah ba lafiya inji Mashir, Hajja ta kalli Mama Ladi tace "Duk na samu labarin abinda Mamuda yayi Ladi, ke kuma don baki da zuciya baki san inda ke maki ciwo ba kin je kin sake mike kafa a gidansa kin zauna, to in na isa dake Ladi daga gidan Maheer gida za mu komo tare baza ki sake komawa gidan Mamuda ba, sannan zaman da Ammi take yi yanzu haka a gidan bai san albarkacina bane don da ba don ni din ba da tun a jiya Ammin bazata kwana gidansa ba ni nayi mata magana ta waya, dama can yana da niyyar aurensa ya fake da wannan matsala amma babu komai, jiya na hana idona bacci ina me yi ma Ammi addu'an Allah yayi mata abinda yafi alkhairi a rayuwarta kuma Allah ya saka mata wannan zalunci da Mamuda yayi mata cikin gaggawa, kuma albarkacin wannan hawayen nawa da na zubar wllhi Ammi zata ga sakayyan abin nan da Mamuda yayi mata babu dadewa, ita kuma Mayraah idan har mu muka cuceta Allah ya saka mata duniya da lahira, idan kuwa ita ce ta cuce mu ta rikita mana zuri'ar ta lalata zumuncin mu to Allah Ubangiji ya saka mana cikin gaggawa wallahi, da Ammi tasan ta dalilinta Mamuda zai mata wannan walakancin wataran me zai kai ta rikonta? Ai sanin gaibu sai Allah" Mama Ladi dai ko kallon Hajja bata yi ba balle ta bata amsa, Allah Allah kawai take taga sun isa gidan Maheer. Haseenah ta fito daga dakinta kamar mahaukaciya tana bubbuga kofar dakin Badiyyah, Badiyyah dake bacci ta tashi da sauri ta bude kofar da mamaki tace "Waye haka?" Haseenah na huci tace "Badiyyah kin san ni, na sanki, tun wuri kada ma third party ya jiyo mu ki fiddo min atamfofina set bakwai da lace uku da shadda daya da mayafi kala uku, da jaka da takalmin su ma set biyu da kika dauka a cikin akwatin lefena, daga ni sai ke a gidan nan sannan kin san nafi kowa sanin halin ki ciki da bai, kin zata duk ban san kan kayana bane zaki min wannan gagarumin satar?? To wallahi shiga ki fito min da kayana kada in maki abinda baki yi zato ba kuma baza ki taɓa mantawa a rayuwarki ba" Haseenah dake ta mata wani shegen kallo daga sama har kasa tace "Amma ke shashasha ce dabba wllhi, fataran kayan sa wa kika ga ina yi da zaki min sharrin na taɓa maki gantalallun kayan lefenki? In taba maki lefe inyi me da shi, ni za ki yi ma kazafi a gidan ɗan uwana?" Maheer ya bude kofarsa jin hayaniyar tasu ya tsaya nan bakin kofar yana kallonsu hannunsa rike da wayarsa, Haseenah ta nufesa tana huci tace "Maheer tun wuri kace ma barauniyar kanwarka ibilishiya mara tsoron Allah a zuciyarta ta fiddo min kayan lefe na da ta sata, in tana ma wasu sata tana kwana lafiya to ni wallahi bazata min ta kwana yau ba ka dai ji na rantse" Ko rufe baki bata yi ba Badiyyah ta sauke mata wani lafiyayyen mari tace "Don kaza kazanki ni kike ce ma barauniya?" Haseenah ta dafe kuncinta with shock tana kallon Badiyyah baki bude, Badiyyah na tafe hannu tace "Gwara dai ni kowa yasan ba zuwa gidan bokaye da malamai nake yi ba a Zaria, malamin nan naki..." Haseenah bata ba Badiyyah daman karasawa ba ta cakumota nan suka fara dambe a wajen suna kai ma juna duka iya karfinsu, Maheer dai na tsaye yana kallonsu bai ko motsa a inda yake ba, kawai ya juya ya koma dakinsa ya kulle, dai dai nan aka bude kofar parlon da sallama, Hajja da Mama Ladi suka yi tsaye bakin kofar bayan sun shigo jin hayaniya ya cika gida, Mama Ladi ce ta fara hangosu Haseenah dake zabga dambe ta gwalo ido tace "Innalillahi, menene zan gani haka?" da gudu ta nufesu Hajja ta zaro ido ita ma jikinta ya dau rawa ganin yanda Haseenah ta saka kan Badiyyah a hammata kamar zata kasheta tana duka, Hajja ta bi bayan Mama Ladi a gigice tana cewa "Innalillahi kar ta kasheta Ladi" Ihu Badiyyah take tana cewa "Wallahi yau sai na tona maki asiri a gidan, sai na fadi duk mugun abubuwan da kike yi, Mama Ladi wallahi boka da malamai take bi in ma kun ce in kai ku gidan malamin da take zuwa a zaria sai in kai ku har can, don ta kai ni wajensa wai nima yayi min aiki, Malamin har ce min yayi asiri take ma surkarta ya bata wani asirin ta kai dakin Ammi don ta raba Ammi da Mayraah yanzu haka asirin na nan a dakin har yanzu, kuma wallahi gold din akwatin Mayraah ma ita ta sa na sato na kawo mata har yau taki bani kuma taki bani kudin....." Haseenah duk ta gigice da maganganun da Badiyyah ke yi har hakan yasa ta fara loosing stamina, wanda wannan ya ba Badiyyah dama ta dinga hade kanta da bango da mugun karfi sai kace an aikota, kan kace me sai ga jini kamar an buda pampo, Mama Ladi da Hajja ihu suke a tare kamar rubabbu suna salati amma sun kasa matsawa kusa da su, Ciwo ba na wasa ba Badiyyah ta ji ma Haseenah a kai don kan kace me jini ya malale corridor din kamar an yanka rago, Haseenah ta fadi kasa wajen a sume, Badiyyah sai zare ido take ganin kamar kwakwalwan Haseenah fa take hangowa, ihun su Hajja ne ya fito da Maheer daga dakinsa, tuni Badiyyah ta shige daki a guje ta saka hijab dinta ta dau wayarta da handbag ta fice daga gidan da gudu..... MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence via 07087865788 *Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/13, 10:08 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya mike ya nufi wani likita da ya fito daga emergency ward kafin yace komai likitan yace "Kai ne mijin nata?" Maheer yace "Eh ni ne" likitan yace "To mu je office" Bin bayan likitan Maheer yayi har suka karasa office dinsa, Mama Ladi da Hajja dai suna tsaye sai zazzare ido suke tun zuwan su asibitin kusan awa biyu da rabi kenan, Mama Ladi ta fashe da kuka bayan sun bi likitan dake tafiya tare da Maheer da kallo, ta rike kanta tace "Rabon ayi kawai, dama kuma ance sanin gaibu sai Allah, banda haka ni in nasan abinda zai faru kenan me zai fito da ni daga gidan Mamuda da sassafe ina cikin rufin asiri na? Wallahi ko koshi ban yi ba na fito ashe wannan fitinar ce ke kirana, Yanzu in yarinyar nan ta mutu ai har mu sai an kai kotu mun bada shaidan abinda ya faru, wai don ma Allah ya so ban karasa shiga ciki ba abun ya faru, da ya zan yi da raina yau ni Ladi, to wallahi da kyar in ba rataye Badiyyah za ayi ba in har wani abu ya samu matar nan, ni dai Allah ya so ban shiga parlorn ba" Hajja ta juya da sauri ta kalli Mama Ladi jin abinda tace, a fusace tace "Ke dai mugun alkaba'in ki yawa garesa Ladi, kuma bakin ki ya sari danyen kashi, ita Badiyyar kike ma fatan a rataye saboda shaidan ya shiga tsakaninta da matar Maheer, kawarta ce fa kowa ya sani, da gangan Badiyyah bazata ji mata wannan rauni haka ba, ko ke baki ga yanda matsiyaciyar matar ta shaketa a wuya ba da farko har sai da Allah ya ba Badiyyan sa'an bugata da bango, ni dama tun da naga Maheer ya daina walwala tun bayan auren sa da yarinyar nasan akwai lauje cikin nadi, har muka yi ta kumfan baki ya saketa akan Mayraah ashe matsiyaciya ce bamu sani ba, to ga dai maganganu tiryan tiryan a bakin Badiyyah kuma wllh ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Badiyyah bazata mata sharri ba, amma dai bari a gama da asibitin nan tukunna mu san ta kwatanci...." Mama Ladi na girgiza kai tace "Aa ba dai Mera ku ka mayar er iska ba mara galihu saboda bata da uwa bata da uban nunawa a duniya, mu je dai zuwa" Hajja ta mata wani kallo tace "Ke da kike wnn maganar kika san yanda muka reni Mayraan har zuwa yau Ladi? Ina ruwanki da Mayraah? To wallahi kar ki gaya min maganar banza kar ranki ya baci" Mama Ladi ta taɓe baki, ta ja bakinta tayi shiru bata sake ce ma Hajja komai ba tana girgiza kafa. Likitan ya zauna yana kallon Maheer yace "Ana bukatar za a mata karin jini, don tayi loosing blood sosai, but Alhamdulillah Allah ya takaita bai yi affecting inda muke tsoro ba at first da aka kawota, but the wound is so deep gaskiya daga gefen kanta ne sai kuma goshinta da shi ma taji ciwo, mun mata stitching anyi dressing din wound din, gefen fuskarta kawai gurjewa tayi , i think that's all, in sha Allahu muna sa ran zata farfado zuwa nan da yan awanni, yanzu kawai jinin za a kara mata, idan jininka da nata yayi dai dai to sai kaje lab yanzu for test a deba, in kuma bai yi ba za ka siya mata a blood bank din mu" Maheer yace "To in sha Allah Dr, Nagode sosai" Tare suka fita office din da likitan, kafin Maheer ya karasa lab din asibitin ya taho gun su Hajja yace "Za ku iya tafiya gida kawai, jikinta da sauki za a mata karin jini ne yanzu" Hajja tace "Inji babu wani mummunan abun da ya samu kan nata?" Maheer yace "Rauni ne kawai ta ji, amma likitan yace da sauki" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Waiii, amma Allah ya hore mata jini, yanda fa kasan an yanka saniya Maheer" Maheer bai tanka ta ba ya tafi zuwa laboratory, Mama Ladi ta mike tace "Kin ga tun da ba mutuwa tayi ba Hajja ki tashi mu tafi gida don ni yunwa nake ji yanzu haka daurewa kawai nake amma tun dazu cikina ke kugi..." Hajja tace "Mu dai babban fatanmu yanzu ta samu lafiya sai a san abun yi" Mama Ladi ta gyara yafin gyalenta ta fita daga asibitin Hajja ta bi bayanta... Karfe sha biyu saura Maheer na zaune dakin da aka kwantar da Haseenah da aka nannade kanta da tulin Bandage bayan an aske kusan rabin gashinta, ledan jini ne a hannunta, shi dai kallonta kawai yake maganganun Badiyyah na yawo a kansa, har a lokacin bai kira kowa a cikin yan uwanta ya gaya masu abinda ke faruwa ba, ya dai kira Ammi ya sanar mata Haseenah na asibiti not long ago, A hankali Haseenah ta bude idonta, Maheer dai sai kallonta yake daga inda yake zaune, suna hada ido tana kokarin mikewa da kyar tace "Maheer wallahi duk sharri Badiyyah ta min babu abinda ta fada da yake gaskiya" Maheer ya mike ya dakatar da ita yace "Na sani, you don't need to stress ur self koma ki kwanta" cikin rawan murya tace "Kasan halinta ae ko, wallahi karya kawai take min dama ta saba sharri iri iri, dubi sharrin da ta dinga bin Mayraah da shi, wallahi karya take min Maheer" Maheer ya mayar da ita ta kwanta yace "Duk na sani, do not worry ur self, u need rest" Haseenah tayi shiru tana jin kanta kamar ana buga mata guduma, Maheer yace "Bari in kira likita" Daga haka ya fita daga ward din, yana fita bayan few minutes sai ga wata nurse ta shigo ta karasa har kusa da Haseenah tana mata sannu, cike da karfin hali Haseenah tace "Nurse ji nake kan kamar ba nawa ba, yayi min nauyi nurse, ko dai bandage din da aka sa min ne?" Nurse din tace "Kiyi hakuri, zai maki sauki in sha Allah, sai a hankali zaki ji ya dawo dai dai, ki daina yawan magana kin ji" Haseenah dai sai hawaye take, Nurse din tace "Bari in dauko alluran da za a maki yanzu, mai gidanki ya fita samar maki abinda za ki ci kafin a maki alluran" Haseenah na son gyada mata kai amma ba dama saboda ya mata nauyi kan, cike da karfin hali tace "Ki ɗan ara min wayarki zan yi kira nurse" Nurse din tace "To ba damuwa" A aljihun uniform dinta ta saka hannu ta ciro wayarta ta mika ma Haseenah sannan ta juya zata fita, Haseenah tace "Don Allah ya sunan asibitin nan?" Nurse din ta gaya mata, bayan ta fita Haseenah tayi dialing number kanwar mum dinta Aunty Fauziyya, yana fara ringing Aunty Fauziyya ta daga, Haseenah ta fashe da kuka da kyar tace "Aunty ina asibiti" Aunty Fauziyya tace "Asibiti kuma? Subhanallahi, me ya sameki Haseenah? Wani asibitin kuma?" Nan Haseenah ta koro mata duk abinda ya faru tana kuka da kyar sbda azaban ciwon kai, Aunty Fauziyya ta mike tsaye daga zaunen da take tace "Kan bala'i, ita Badiyyar ce ta fasa maki kai? Kuma matsiyaciyin mijin naki ya kasa bugowa ya sanar mana abinda ke faruwa, wato ta fasa ma banza kai kenan? Wani asibitin kike yanzu?" Haseenah na gaya mata asibitin Aunty Fauziyya ta katse wayar, Haseenah tayi dialing number Aunty Farida ita ma sis din Mum dinta ce amma ta ji tana on another call, Cousin sis dinta Salma ta kira ita ma tana dagawa ta gaya mata abinda ya faru da asibitin da take, bayan ta gama sanar ma Salma sai ga kiran Aunty Farida ya shigo, Haseenah ta daga da sauri cikin kuka zata fara mata bayani cikin daga murya Aunty Farida tace "Fauziyya ta kirani ai ta gaya min komai, ga mu nan zuwa asibitin yanzun nan za mu ga uban da ya tsaya ma Badiyyah har ta maki haka" Daga haka Aunty Farida ta katse wayar. Ammi ta fito daga bangarenta bayan Maheer ya kirata ya sanar mata abinda ya faru, har zata sauka downstairs ta tsaya for few seconds, Mama Ladi dama ta gaya mata a dakin Maheer Mayraah take yanzu, kawai ta buda kofar dakin taga babu kowa ciki, hakan yasa ta sauka ta fita zuwa asibitin da Maheer yace mata aka kwantar da Haseenah, Ammi na isa asibitin ta kira Maheer ya fito ya shigo da ita ward din da Haseenah take, ko da wasa bai yarda sun hada ido da Ammi ba, ita dai Ammi na tsaye kan Haseenah dake ta juye juye tana wayyo Allah don Anaesthesia ya fara sakinta, gaba daya Ammi ta ma rasa me zata ce jikinta duk yayi sanyi ganin ashe ciwon ba na wasa bane ganin yanda aka nannade kan Haseenah da bandage wanda har ya fara staining sosai da jini, Bude kofar ward din aka yi sai ga Aunty Farida da Fauziyya da Aunty Murja warce cousin dinsu ce, sai kawar Aunty Farida sun shigo babu ko sallama fuska a murtuke basu ko bi ta kan Ammi da Maheer ba suka nufu gun Haseenah kamar wasu sojoji, Aunty Farida na huci tace "Kan bala'i, ita Badiyyar ce ta maki wanna aika aikan? Ita Badiyyar? To wallahi wallahi sai mun yi shari'a da ita, sai naga uban da zai tsaya mata a kano" cikin bacin rai Aunty Fauziyya tace "Wato ba don ke kin kira mu ba so suka yi sai kin mutu su kira mu su sanar mana mu xo mu dauki gawarki ko? Saboda 'yar su ce shine suke neman rufe abun ko? to wallahi sai mun ga uban da ya tsaya mata a kaf garin kano, mu je Farida, wallahi ko guduwa tayi ta bar kano sai mun sa an daure uwarta tayi mana providing dinta, ai ba kowa ake taɓawa a kwana lafiya ba" Aunty Murja ta kankance ido tace "Wallahi kasheta kawai tayi niyyar yi ko ince suka yi niyyar yi, uban me ta masu haka? wani irin family Haseenah ta fada haka?? Duka duka yau wata nawa da auren aka mata haka?" Ammi ta kasa cewa komai ta saki baki tana kallonsu da mugun mamaki, Shi kansa Maheer na tsaye jikin window yana kallonsu bai ce komai ba, Haseenah kuwa sai kururuwa take tana juye juye saman gado tana cewa wayyo Allah zata mutu, Aunty Fauziyya da Aunty Farida suka fice daga ward din Murja da kawar Aunty Farida suka bi bayansu, dama mijin Aunty Fauziyya babban dan sanda ne amma yana Abuja kuma daga kanon aka maida shi Abujan, tana fita ta kirasa a waya tana huci tace "Abban Ikram wallahi mun zo asibitin abun ba na wasa bane, ya wuce yanda muke tunani Abban Ikram, yarinyar tayi raga raga da kanta da kyar raunin bai taɓa kwakwalwarta ba zancen da nake maka yanzu haka, kuma abun takaicin har zuwa yanzu da muka zo asibitin babu shegen da ya kira mu ba balle su gaya mana abinda ke faruwa wato so suke su rufe case din mu kuma an cuce er mu an illata ta, ka kira division din da kace kawai muje yanzu a hada mu da yan sanda a bamu mota ai nasan gidan su yarinyar, wallahi ko ta gudu sai mun tafi da uwarta ta fito da ita" Haka nan duk suka shiga motar Aunty Fauziyya suka nufi police station, motar yan sanda guda aka basu, Aunty Fauziyya tayi ma motar yan sandan jagora har gidan Hajja a tata motar.... Mama Ladi na tsakar gida tana alwala tayi maza tayi sallah ta tafi gidan Ammi, Hajja kuwa na kitchen tana ta kokarin hada girki ta koma asibiti ko don saboda Maheer, yan sanda kusan biyar suka shigo tsakar gidan Su Aunty Fauziyya da Aunty Farida na biye da su a baya, Tsabar gigicewa sai da Mama Ladi tayi zaman dirshan a kasa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una" Aunty Farida na huci tace "Ina Badiyyar take?" Bakin Mama Ladi na rawa tace "Wallahi ni me aikin gidan ce, ga kakarta can a kitchen bazata rasa sanin inda take ba, ni ban san komai ba" Yan sanda suka nufi cikin gidan su Aunty Fauziyya na biye da su, Hajja ta saki murfin tukunyar hannunta bayan taga yan sanda tsaye kanta a kofar kitchen, tambayar da aka jefa ma Mama Ladi a waje shi aka kara jefa ma Hajja wato ina Badiyyah, Jikin Hajja na ɓari tace "Wallahi wallahi Badiyyah bata dawo gidan nan ba" Wani ɗan sanda yace "Amma ai kin san abinda ta aikata?" Hajja ta fashe da kuka tace "A gabana aka yi komai ranka shi dade, amma don girman Allah ku yi mata hakuri ku yafe mata wallahi marainiya ce yarinyar ba uwa ba uba, bata taɓa haka ba tunda take" Cikin daga murya Aunty Farida tace "Iyyeee wato marainiya, ita Haseenar uba gareta aka ce maki? To wallahi sai an dau mataki a kanta bata illata banza ba" Wani ɗan sanda na kallon Hajja yace "Kinga wannan kalman da kika yi Hajiya ya nuna cewar kin san inda yarinyar take ko kuma kina goyon bayan duk abinda take yi, don haka ki fito mu tafi station idan kika yi providing mana yarinyar sai a sake ki, kuma kina sake buda baki a nan za mu yi using din shi against you" Kuka sosai Hajja take jikinta na rawa tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, nace maku bata dawo gidan nan ba ku shiga duk inda za ku shiga a gidan nan ku duba ta, wallahi bata dawo ba, ku rufa min asiri tunda nake ban taɓa zuwa Caji opis ba" A fusace Aunty Fauziyya ta kalli yan sanda tace "Don Allah mu tafi tana bata mana lokaci officer, ta fa san inda yarinyar take sarai da hadin bakinta yarinyar ta gudu tunda tace ai tana wajen abun ya faru, don haka in mun je station din sai ta fadi inda yarinyar take sai a saketa" Haka nan Hajja ta saka Hijabi tana kuka yan sandan suka tisa keyarta zuwa tsakar gida, Mama Ladi dai sai wanke kayan da ta ga an jiƙa a cikin baho take ita a dole mai aikin gidan har aka fito da Hajja aka yi kofar gida da ita tana rusa kuka tana salati, gaba daya yan anguwa aka fito ganin motar yan sanda a kofar gidan Hajja sai ga kuma Hajja an fito da ita tana kuka wiwi an saka a motar yan sanda an tafi da ita, makociyar Hajja Maman Bala ta dau waya jiki na rawa ta kira Ammi ta sanar mata ga yan sanda sun zo da katuwar mota an saka Hajja a ciki an tafi da ita..... Ba karamin gigicewa Ammi tayi ba bayan Maman Bala ta kirata, ta fita ward din da sauri don Maheer yaje office din likita yana kiransa, A hanya suka hadu, ganin yanda Ammi ta rude Maheer yace "Ammi lafiya?" Ammi ta fashe da kuka tace "Yanzu Maman Bala makociyar Hajja ta kirani wai yan sanda sun zo sun tafi da Hajja Maheer" Sake baki Maheer yayi yana kallon Ammi with shock, ya kasa cewa komai, Tuni Ammi ta nufi reception tana kuka sosai, Maheer ya bi ta da sauri yace "To ina za ki Ammi" Ammi tace "Police station din zan tafi mana Maheer, su yanzu don basu da mutunci da tsufan Hajja za su tafi da ita station?" Maheer ya kama hannunta yace "To ai bamu san wani station din bane Ammi, ki kwantar da hankalin ki mu fara sanin wani station ne tukun" Ammi ta kasa ci gaba da tsayuwa ta zauna kujeran dake reception din tana kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, wannan wani irin fitina ne, wace irin yarinya ce Badiyyah? Meye wannan ta ja mana fisabilillahi?" Maheer that was so confuse ya ciro wayarsa yana tunanin wanda zai kira. Hajiya Amina na zaune parlor wajen karfe biyu Abba ya shigo da sallama, mikewa tayi bayan ta amsa tana kallonsa tace "Ka sameta a wayan Yallabai?" Abba yace "Ban sameta ba, wai tun yaushe ke kika lura bata gidan?" Hajiya Amina tace "Dazu wajen karfe goma na safe na shiga dakin ban ganta ciki ba duk tunanina ko tana bandaki ne, sai na koma na kwanta kawai, sai yanzu da aka yi azahar na tashi na sake komawa dakin inji ko ta ci abinci still ban ganta a ciki ba, shine na duba bathroom naga it's empty...." Da mamaki Abba yace "Kuma bata ce maki zata makaranta ba yau?" Hajiya Amina ta girgiza kai tace "Gaskiya bata ce ba Alhaji, kaga jiya da zata tafi makarantar ai ta gaya min, Kuma ina parlor da safe Mama ta fita balle ince tare suka tafi" Call logs Abba ya shiga na wayarsa ya ga ko zai iya gane number da Musharraf ya kirasa da shi jiya, yayi tracing calls dinsa har zuwa yesterday evening trying to recognize Musharraf's Number before calling, dai dai nan kiran Maheer ya shigo wayarsa, Abba da kamar bazai daga ba sai dai kuma ya daga, Hajiya Amina ta juya ta bar parlon ta koma sama, a takaice Abba ya amsa gaisuwan da Maheer ke masa, nan Maheer yayi kasa da murya ya sanar ma Abba duk abinda yake faruwa, Abba yayi shiru with surprise, can dai yace "Police station? To kai kana ina duk wannan abun ya faru? Sannan ina Badiyyar take har suka tafiya da Hajjar?" Maheer yace "Basu ganta bane ai Abba, shi yasa" Abba ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu wani station din aka tafi da ita Hajjan?" Maheer yace "Ban san division din ba, makota suka kira yanzu suke sanar mana" Abba yace "To bari dai ina zuwa...." Yana katse wayar yana kokarin kiran number wani abokinsa ɗan sanda sai ga Hajiya Amina ta sauko da wata farar takarda a hannunta da ta gani a dakin Mayraah tana kallon Abba babu ko kiftawa, Abba na kallon takardan yace "Na meye wannan?" Bata iya ta ce masa komai ba bata kuma fasa kallonsa ba, Abba ya karasa ya amshi takardan ya warware yana duba na menene.... [7/14, 6:16 PM] Khaleesat Haiydar💖: Karfe biyu da rabi Mayraah ta sauka daga mota rike da karamin jakarta tana bin park din da kallo, kowa hada hadar gabansa yake cikin hanzari don hadari ne sosai a garin, muryar dreba da taji yana tambayar ko bata da kaya ne a booth din mota ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi a inda take tsaye, ta girgiza masa kai ta nufi hanyar da ta lura nan ake bi a fita daga cikin tashar, tsaye tayi bakin titi tana makale da jakarta a dai dai sanda aka fara iska sosai ta dinga bin duk motocin da ke wucewa da kallo, yan adaidaita sahu sai tambayarta inda za ta suke, kan kace me aka fara yayyafi, ta fara dube duben inda zata raɓa kar ruwan ya jikata, wani shagon point of Sale da kuma accessories din waya ta nufa da sauri ta tsaya a ɗan rumfan shagon nan aka fara ruwa kamar da bakin kwarya, saboda karfin ruwan sai ya kasance da ma rumfan da take karkashi gwara babu, don ruwan har ya fara jikata, me shagon na ganin haka yace "Ki shigo ciki Hajiya, ai wannan jikewa zaki a wajen" Mayraah ta juya da sauri ta shiga shagon tace "Nagode" Kan plastic chair ya nuna mata ta zauna, ruwa aka yi sosai don sai kusan hudu da rabi ruwan ya ɗan tsagaita, me shagon har bacci yayi ya tashi, ita dai Mayraah na takure kan kujeran don wani sanyi take ji sosai ga gajiya da jiri da take ji, gaba daya tayi weak wanda ko ba a fada mata ba tasan symptoms din low bp ne, Mai shagon yace "Hajiya ko dai a tare maki Napep tunda ruwan ya ɗan tsagaita ki tafi gida, naga kamar sanyi kike ji, kuma babu alamar daukewar ruwan nan yanzu" Mayraah ta juya ta kallesa kamar baza ta ce komai ba, sai kuma a hankali tace "Ni daliba ce yau na fara zuwa garin ban san ko ina ba, ban san kowa ba, ina son zan kama gida irin na dalibai ne, to ban san ta yaya zan fara ba" Mutumin yace "Jami'ar nan da take gwagwalada?" Mayraah ta gyada kai da sauri, mutumin na gyada kai yace "Chabb ae ko gida wahala yake a garin nan sai shegen tsada, dama dai Suleja kika ce to can ma ni nake, business dina ne kawai ke fitowa da ni cikin gari, ni nasan yanda za a samu gida me kyau a suleja, sai dai kuma Sulejan yayi maki nisa zuwa gwagwalada gaskiya, ga tsadan kudin mota" Da sauri Mayraah tace "Aa in dai za a samu bai yi min nisa ba" Mutumin yace "Atoh in zaki iya shikenan, ina daga nan zan sa a bincika min gida a can, ai garinmu ne Suleja iyayena da matana duk suna can" A hankali Mayraah tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi, ka bincika min sai in bada kudin a kama min" Yace "In sha Allahu zan bincika a yau kuwa, amma dai yanzu makarantar zaki tafi? Kin dai ga garin kara lullubewa yake" Mayraah ta kalli sama da ya kara lullubewa tace "Eh tare min adaidaitan" Mikewa yayi ya fita cikin yayyafin ya samu adaidaita sahu sannan ya dawo yace "Ga can wani na tare maki har na maki ciniki da shi kudin kawai za ki basa" Ta mike tace "To nagode sosai" Yace "Yanzu lambar wayarki zaki bada a kira ki in an samu gidan ko ya za ayi?" Tace "Ai wayata ta mutu, goben dai zan zo in sha Allahu sai in ji ko an samu" Yace "To ba laifi, Allah ya kiyaye" Fita tayi daga shagon tana jin sanyi sosai ta tafi ta shiga adaidaita sahun da ya tare mata, bayan sun ɗan yi nisa Mayraah na kallon mai adaidaita sahun a hankali tace "Bawan Allah akwai hotel don Allah a unguwan da za mu je yanzu?" Yace "Kwarai kuwa, iri iri ma kuwa" Tace "Toh kai ni daya don Allah" Yace "Toh ba damuwa" Yana isa wani hotel yayi parking yace "Kinga ga wani nan, me kyau ne wannan naga yan mata na zuwa sosai" Mayraah na kallon hotel din tace "Toh Nagode" Ta sauka a daidaita sahun zuwa yanzu ruwan ya sake dawowa da karfi, tana kallonsa tace "Nawa ne kudinka" Ya fada mata ta ciro a handbag dinta ta basa sannan ta shiga cikin hotel din da sauri ruwa na jikata, a reception ta zauna bayan sun yi confirming payment dinta suka bata makullin dakinta ta wuce dakin, tana shiga ta kashe Ac din dakin ta kwanta ta rufa da bargo saboda sanyin da take ji sosai, har kusan magrib tana nan a haka gashi bata yi sallah ba, gashi tana jin kamar alamar cramps wanda hakan yayi mugun daga mata hankali, to yanzu ya zata yi ita kam, ta yunkura ta tashi ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta fara Sallah. Tun bayan da Abba ya gama karanta takardan da Hajiya Amina ta mika masa yake zaune parlor ya kasa cewa komai, ya furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya fi a kirga a zuciyarsa, ita dai Hajiya Amina na inda take a tsaye ita ma ta kasa cewa komai, daga karshe kawai ta juya ta bar parlon, kiran Maheer ne ya sake shigowa wayar Abba for the third time, Dagawa Abba yayi, calmly yace "Kana ina yanzu?" Maheer yace "Ni ina asibitin har yanzu, Ammin ma taki saurarata ta bar asibitin yanzu haka, ta ma ki jiran in tafi da ita a mota" Abba yace "Bayan kai babu kowa a asibitin?" Maheer yace "Eh yanzu wasu cousins dinta suka iso..." Abba yace "To ka taho gida yanzun nan" Daga haka ya katse wayar, Maheer didn't get dalilin da zai sa Abba yace ya taho gida yanzu bayan ga abinda ke faruwa, kawai dai ya tafi parking space din asibitin ya kama hanyar hoping all is well, Duk da rashin nutsuwan dake tare da Abba haka nan ya kira abokinsa wanda shi ma babban ɗan sanda ne, in brief ya sanar masa abinda ke faruwa, abokin nasa yace "Wani Division ne ranka shi dade?" Abba that was just confused don kusan Absentmindedly yayi masa bayanin yayi wani sigh yace "I don't really know" police officer din yace "To a wani anguwa abun ya faru, sai in kira division din anguwan with immediate effect" Abba ya fada masa anguwan da gidan Maheer yake, Officer din yace "Ohk, give me a minute" Daga haka ya katse wayar, Abba ya ciro handkerchief ya share zufar goshinsa ya mike ya fara safa da marwa a parlon yana sake nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarsa, sake duba takardan yayi for the countless time, kawai ya koma kujera ya zauna ya rike kansa yana kiran Allah a zuciyarsa, duk wannan abubuwan dake faruwa Abba bai taɓa jin haushin Ammi yanda yake jin haushinta yanzu a zuciyarsa ba, Bayan some minutes wayar Abba ya fara ring, ya duba ganin officer din ne ya daga, Officer din yace "Yauwa after making series of calls an samo division din yanzu, in sha Allah za a saketa sannan ayi sulhu a gida tunda Allah ya takaita ita warce aka ji ma raunin is responding to treatment, wannan family issue ne kawai dama a gida ya kamata a sasanta, Allah kuma ya kiyaye gaba" a hankali Abba yace "To nagode kwarai da gaske officer" Sallama suka yi Abba ya katse wayar ya sake mikewa yana zaga parlon, dai dai nan aka bude kofar parlon Mama Ladi ta shigo duk ta hada zufa, Abba dai kallonta kawai yake har ta Karaso cikin parlon tace "Mamuda yan sanda fa sun yi ramm da Hajja" Sai kuma ta fashe da kuka tace "Wayyo Allahna, wayyo Allah, Allah sarki yayata, wallahi da dai ni suka tafi da suka bar ta amma suka ki sauraron haka, da kafa na taho gidan nan Mamuda tsabar gigicewa ga yunwa ko gidan ban rufo mata ba, unguwan nan ya cika babu matsaka tsinke in gaya maka, sai ga Hajja a motan yan sanda, tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin irin wannan tashin hankali da bala'i ba sai yau, wai ace surkan jikanta suka dauko mata yan sanda kusan goma" Abba ya katseta don surutunta kara masa ciwon kan da yake ji yake, a takaice Abba yace "Nayi waya an saketa" Mama Ladi ta fashe da sabon kuka tace "Allah Ubangiji yayi maka albarka, in ba kai din ba wallahi sai dai ta kwana cikin barayi a self, tana kuka fa basu ji tausayin tsufarta ba suka dinga figarta har kofar gida, kuma ba kowa ya ja mata ba Badiyyah" Maheer ya shigo parlon da sallama, ya nufi Abba yana kallonsa ganin yanayinsa amma ya kasa cewa komai, Abba ya mika masa takardan hannunsa yana kallonsa ya girgiza kai sounding so pained yace "Ur mother failed me" Daga haka ya wuce sama, ita dai Mama Ladi sai zare ido take tana bin takardan hannun Maheer da ido, Sai da kan Maheer ya sara yana fara karanta first 3 lines din takardan kuma yaga writing din Mayraah, ya ji kafafuwansa sun kasa daukansa ya zauna kan kujera zuciyarsa na bugawa yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mama Ladi ta zaro ido a tsorace tace "Lafiya, takardar mecece Mashir?" Kasa bata amsa yayi ya rike kansa. Hajiya Fauziyya da mukarrabanta dake cikin mota za su koma asibitin da aka kwantar da Haseenah bayan ta tabbatar mai gidanta ya bada order din kada a bada belin Hajja sai an kama Badiyyah tukun wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin mai gidan nata ne ta daga tace "Abban Ikram muna hanyar asibitin yanzu haka, don Allah ka kara jaddada masu kada a bada belin matar nan sai an kamo matsiyaciyar yarinyar" Mai gidan nata yace "Ai ina jin fa kawai hakuri za kuyi ayi sulhu Fauziyya, don yanzun nan wani officer da nake jin nauyinsa don gaba ma yake da ni gun aiki kawai dai na fi sa sanin Officers dinmu ne ya bugo min wai surkar abokinsa ce ita matar da yan sandan suka kama, yana kuma neman alfarman a rufe case kawai aje gida ayi sulhu" Hajiya Fauziyya na huci tace "Ban gane ba Abban Ikram, kana nufin an doki er mu an fasa mata kai a banza kenan? Wai kai kaga uban raunin da ta ji mata ne kuwa? Ko don ban dauka a hoto na turo maka ba?" Yace "Na dai gaya maki, ayi hakuri a je ayi sulhu don gaskiya ina bala'in girmama Mutumin nan kuma ina jin nauyinsa, don haka ni har na kira Dpo din division din nace masa a saki matar kawai....." Cikin daga murya Aunty Fauziyya tace "In mun yarda shegiya nake, in mun yarda Allah ya tsine mana, wallahi baza mu yarda ba, a tura mu kotu kawai alkali yayi mana Shari'a...." Katse wayarsa yayi, Aunty Farida tace "Lallai Baban Ikram, a saketa fa yace??" Aunty Fauziyya na huci tace "Kyaleni da shi kawai, a tura mu kotu a kwatar mana hakkin er mu kawai, babu wani sulhu da za ayi a gida, idan ko ba haka ba idan ban kira Yaya Abdurrahman soja an kai Badiyyar barikin sojoji ba sun kakkarya mana shegiya ku ce ba ni bace......." Haka Ammi ta dinga yawon police stations tana neman Hajja, in ta hau wannan adaidaitan ta sauka ta hau wannan a haka dai har Allah ya kai ta division din da aka kai Hajja, Hajja na zaune gaban yan sandan sai zare ido take, tana hango Ammi ta fashe da matsanancin kuka, Ammi ta nufeta ita ma ta fara kuka, wata police woman tace "Ku tun dazu an kawo tsohuwar nan station amma babu wanda ya biyota kamar bata da gata kusan awa biyu kenan......" Ammi na kallonta cikin kuka tace "Tun dazu na fito wllhi, nayi ta duba stations don ban san wanda aka kawota ba, da muna gidan ai sai dai ko ni a tafi dani baza mu bar haka ta faru ba" Police woman din ta taɓe baki tace "To za ku iya tafiya kawai an rufe case din, wai ku je gida ku sulhunta kanku" Ammi tace "Toh mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Ammi ta kama hannun Hajja dake kuka har sannan saboda takaicin wai yau ita ce a motar yan sanda har police station, adaidaita sahu Ammi ta samar masu, ta dinga bata hakuri amma Hajja ta ki daina kuka don kamar ma dada tunzurata take, cikin rawan murya Hajja tace "Kar ma ki maida ni anguwan nan don yanxu ban san da idon da zan kalli yan anguwan ba wannan abun kunya har ina? Da tsufana da mutuncina a min wannan cin mutuncin Ammi, wallahi ko yarinyar nan kadai ta rage a duniya Maheer bazai zauna da ita ba" Ammi ta rasa ma me zata ce jin furucin Hajja na cewar kar a maidata gidanta, to yanzu ina zata kai Hajja, da ace da ne dama gidanta kawai zata tafi da ita amma yanzu ba da bane, tunanin hakan yasa hawaye ya kawo idon Ammi ta rasa tunanin da zata yi kuma, tana kallon mai adaidaita sahun kawai ta gaya masa unguwan Maheer tace "Can zaka kai mu kawai" kafin su karasa ta kira Maheer, yana dagawa tace "Kana ina ne?" Maheer da har a sannan ya kasa motsi yana rike da takardan da Abba ya basa cike da karfin hali yace "Gida" Ammi tace "Wani gidan, mu gashi muna hanyar gidanka da Hajja yanzu tace bazata koma gidanta ba, ya za ayi da makulli?" A hankali yace "A bude gidan yake" Ammi ta katse wayar, wato bazai ma tambayeta ya aka kare ba, a haka suka isa gidansa ranta a bace, babu wanda ya nuna concern din abinda aka yi ma Hajja daga shi har uban nasa, suna shiga parlon Hajja ta zauna kan kujera ta fashe da sabon kuka, cike da damuwa Ammi tace "Don Allah kiyi hakuri Hajja" Cikin kuka Hajja tace "Ni abinda ya ban takaici da aka ki bin ba'asin ma abinda ya hadasu tun asali, wllhi da muka shigo nan da Ladi shake Badiyyah matar tayi tana neman kasheta har Allah ya ba Badiyyar sa'a ta bugata da bango, da kuma Badiyyar bata yi haka ba da ta dade da mutuwa a hannunta wllh, yanzu da ita matar ce ta kashe Badiyyar sai ace yaya? Ban shiga uku ba idan hakan ta kasance me zance ma dangin ubanta daga sun bar min amanar yarinya? Ashe matsiyaciya ce matar Maheer duk bamu sani ba tace Mayraah kaza, Mayraah kaza, Mayraah ta zageta, Mayraah ta ci mutuncinta, Mayraah ta tara mata kawaye a gida ita da kawayen su yi ta shewa, bayan ni dai nasan ba tarbiyyar da muka yi ma Mayraah ba kenan, yarinyar da kowa ya shaida nutsuwarta amma azzalumar matar nan ta dinga mata sharri tana kawowa kunnenmu, to wallahi Maheer ya gama zama da ita har abada kuwa, muna zaman zaman mu lafiya ta shigo ta tarwatsa mana Pamily, ta lalata komai, ashe ita ce ibilishiyar cikinmu daga aurota ko wata uku ba ayi ba ta tarwatsa komai, idan an bibiya wllhi ita ta dinga zuga Badiyyar ma take ta kawo wasu mugayen maganganu kan Mayraah, don da ai ba haka Badiyyah take ba, to yaushe ma ta zauna dindindin a kano balle ta shiga sabgar Mayraah har tace ta mata wani abu, tsakaninsu fa gaisuwa kawai ba wani shiga harkan juna suke ba duk mun sani, suna zaune lafiya kuma, Tun a sannan sai abun yayi ta daure min kai don nasan Mayraah dai da na sani a baya ba haka take ba, amma sai nake tunanin canzawa tayi kawai don ta gano ba mune asalin jininta ba bari ta gwada mana halin ɗan Adam, ashe shegiyar matar Maheer din nan ce duk ta hada komai, duk ita ce ta hada fitinar nan ta rikita mana komai, to da yake Allah me gafara ne sai gashi cikin gaggawa asiri ya tonu tun bamu shiga hakkin Mayraah ba, to wallahi sai Maheer ya saki annobar nan, ya rubuta mata takardanta kawai a gadon asibitin ya bata ba sai ma anje da nisa ba, a duk duniya babu cin mutunci da ya wuce wanda dangin Haseenah suka min yau don har in koma ga mahaliccina bazan manta ba wallahi, da mutuncina da girmana wai yau ni aka saka cikin motar yan sanda" Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka ta ci gaba tana cewa "Wai fa a haka Allah ya rufa mana asiri an dauke Mayraan daga nan gidan bata kasheta ba, a yanda naga ta shake Badiyyah wllhi zata iya kisa matar, Allah dai shi yasan dalilin faruwan komai wallahi" Ammi dai kanta na kasa duk tana sauraron Hajja, lokaci daya hawaye ya kawo idonta, Hajja na share idonta tace "Duk ma abinda kika ma Mayraah ai er ki ce halaq malaq babu me ce maki don me tun da ba shi ya maki rikonta ba ya sha wahala da ita har zuwa yau, kuma 'ya bata fushi da uwarta koma me zata mata dole dai uwarta ce bazata canza haka ba, nakudarta ne kawai baki yi ba amma babu wanda ya kai ki sanin zafinta, ba kuma wanda zai nuna maki ya fi ki sonta daga 'ya yan naki har uban nasu, shi kuma Mamuda dama can da niyyar aurensa kece kawai baki sani ba, a yawace yawacensa ya samo Bazawararsa suke tadi ke kina gida kin saki baki, shine da ɗan matsalan nan ya faru yayi maza ya aureta ya fake da matsalar, ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba yana da niyyar auren ya dai rasa yanda zai gaya maki ne, ni fa ba yarinya bace" Ita dai Ammi bata ce komai ba kuma har sannan bata dago kanta ba, hawaye kawai ke zuba idonta, Hajja ta cire dankwalinta ta share hawayen fuskarta tace "A samo min ruwan zafi in je inyi wanka in hadiyi panadol, wallahi duk jikina ciwo yake" Ammi taji baza ma ta iya shiga kitchen din ba, banda lalura me zai kawota gidan matar Maheer har ta zauna, rabonta da gidan tun ba a gama gini ba almost a year ago da ya kawota ta gani, ta dau wayarta ta mike ta fita balcony hawaye na sauka idonta ta sake dialing number Maheer, yana fara ringing ya daga, sai da tayi controlling kanta sannan ta iya cewa "Ka taho da Mayraah" Duk da Maheer ya ji ta ya kasa ce mata komai, kuma yana dai dai gate din gidansa ta kirasa, bude gate din yayi Ammi na ganinsa ta katse wayar, zata juya ta koma parlor kira ya sake shigowa wayarta ta duba taga Abba ne ke kiranta, sai da gabanta ya fadi don wata daya kenan rabon da kiransa ya shigo wayarta, ta daga kiran ta kai kunne ba tare da ta ce komai ba. [7/15, 5:30 PM] Khaleesat Haiydar💖: Abba yace "Na kira ne in sanar maki burin ke da danginki ya cika a kan Mayraah, You and ur relatives have succeeded into pushing her, dama duniya ae kuke so ta shiga ko? To hakan ya faru sai ku zuba ruwa ƙasa ku sha..... amma ina son ki sani, idan wani abu ya samu yarinyar nan a duk inda take bazan taɓa yafe maki ba, i will never forgive u, duk halin da ta shiga ke da danginki ne sila saboda selfishness dinku, alhaki a kanku kuma ina me tabbatar maki Allah bazai bar ku ba....." Abba na kai wa nan ya katse wayarsa, Ammi dai ta ƙame a inda take tsaye as if trying to assimilate all what Abba is saying, after few second da katse wayar da Abba yayi ta juya a hankali tana kallon Maheer da ya iso balcony din, Har a lokacin bata cire wayarta a kunne ba, tana kallon Maheer ko kiftawa babu cikin karfin hali tace "Ina Mayraan?" Maheer bai yarda sun hada ido da ita ba ya mika mata takardan hannunsa, Ammi ta amsa da sauri tana duba takardan, lokaci daya ta juya ta koma parlor gun Hajja ta durkusa gabanta ta fashe da matsanancin kuka, Hajja ta gigice ta mike tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, lafiya? Me kuma ya sake faruwa?" Takardan hannun Ammi ta amsa a rikice tana jujjuyawa tace "Ko sakin ki Mamudan yayi??" Ammi dai ta kasa cewa komai sai kuka take uncontrollably, Hajja ma ta fashe da kuka gashi ita ba iya karatu tayi ba balle ta karanta takardan taga na menene, cikin tashin hankali tace "Ki bude baki kiyi min magana don Allah, sakin ki Mamudan yayi wai??" Ganin Maheer ya shigo Parlon Hajja ta nufesa da sauri jiki na rawa tana nuna masa takardan tace "Maheer takardan meye wannan din?" Maheer yayi shiru yana kallonta da farko, can yace "Mayraah ce ta rubuta" Hajja tace "Mayraah kuma? Na meye to?" Maheer yace "Ta tafi" Hajja ta zaro ido tana kallonsa tace "Ta tafi? Ta tafi ina?" Maheer bai bata amsa ba ya juya ya fita daga parlon ya koma balcony ya tsaya, Hajja ta dawo da sauri tace "Ina wai Mayraahn ta tafi Ammi?" Cikin kuka Ammi tace "Allah ya gani ko 'ya yan cikina ban gwada masu son da nake ma Mayraah ba, ban taɓa mata kallon ba ni na haifeta ba tunda Allah ya bani ita, kallon jinina nake mata, soyayyar uwa da ɗan ta nayi mata....." Ta kasa ci gaba saboda kukan da ya ci karfin ta, Hajja ta zauna kan kujera ta rasa abun cewa, can ita ma ta fashe da kukan ta daga hannu sama tace "Allah mun gode maka, wannan wani irin fitina ne ke ta billo mana ni Sadeeyah daga wannan sai wannan? Wa ta sani a duniyar da har zata ce ta tafi? Ta tafi ina? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya tsine ma wannan mata ta Maheer duk ita ta jagwalgwala al-amarin nan, muna zaman mu lafiya ya auro annoba ta tarwatsa mana farin cikin mu, yanzu ita kanta Badiyyar bamu san inda ta tafi ba bamu san wani hali take ciki ba, ga Mayraah ma wai ta tafi, ta wa ta sani da zata ce ta tafi?" A ranan Abba ya maida Hajiya Amina sabon gidansa da ya gama ginawa har yayi furnishing not long ago a Miller road, he wanted to take Ammi by surprise, don ko su Maheer basu san da gidan ba balle ita, kawai rana daya yayi niyyar ce masu su shirya za su fita kawai sai ya kai su gidan daga nan kuma sai tarewa ba lallai ma su koma tsohon gidan ba, don shi ma a yanzu yana son barin anguwan da ya taso ya koma area with full security ya zauna, tsohon gidan nasa kuma ya saka cousin dinsa da matansa uku don kar gidan ya kasance babu kowa, Chalet kuma dama wani makocinsu dake biyan kudin haya da kyar don yawanci shi ke biya masa kudin hayan ma duk shekara, to shi yayi niyyar ba ma chalet din da matarsa da yaransa su zauna, to a yanzu kam ya ji zaman gidan ya fita ransa, tafiyar Mayraah ba karamin daga masa hankali yayi ba da distablizing dinsa, he wish zata canza tunani ta dawo gida don bata da wani gata a duk inda ma zata je yanzu, ya kuma san he tried his best, yayi bakin kokarinsa na ganin she wasn't traumatized or felt dejected with all what was happening, yayi iya kokarinsa all through the Saga but all his effort prove abortive, yasan da Ammi bata mata abinda tayi mata ba koma me zai ci gaba da faruwa bazata bar gida ba, baya jin zai iya yafe ma Ammi da ahalinta gaba dayansu, ba don yaranta ba babu abinda zai hanasa tura mata text kar ta dawo masa gida don har cikin ransa yaji baya ma son ganinta, amma bazai yi hakan ba ko don albarkacin su Maheer, don haka gwara kawai ya bar mata gidan kawai, daga ita har yaran nata. Karfe bakwai da rabi bayan gari yayi duhu Maheer ya kai Hajja gidanta, Throughout hours din da suka yi gidan Maheer kuka kawai Ammi take regretting so many things, kana ganinta kasan ta shiga tashin hankali mara misaltuwa, she never expect things to go this way, ba kowa ya ja mata duk wannan abun ba sai Hajja da take kokarin ganin ta rabu lafiya da, pressure din Hajja duk shi ya ja mata wannan abu, she was only trying to please her mother in so many ways kar su samu matsala, Hajja kam ba bakin magana amma ta tsine ma Haseenah ya fi a kirga, ta rantse ta kuma rantse Maheer bazai ci gaba da zama da annoba, Abincin da ya fita ya siyo masu ma duk basu ci ba saboda babu kwanciyar hankalin ci, Maheer na maida Hajja gida ganin Ammi zata sauko daga motar Hajja ta kalleta tace "Ina kuma zaki kike kokarin saukowa?" Cike da karfin hali Ammi tace "Me zan koma gidan in yi Hajja? Babu amfanin komawata kawai" Sai kuma ta fashe da kuka sosai, Hajja tace "Ni kuma me zaki shigo min nan kiyi, ni fa ina ji a jikina babu inda Mayraah ta tafi in ma zaki kwantar da hankalinki, ki kwantar da hankalinki ki dukufa da addu'a ba ji ba gani wallahi zata dawo, babu abinda kukan nan zai kara ki da shi sai ma ki ja ma kanki wata cutar dama ke ba lafiyayya ba yanzu, kwanaki ma ba haka ta dinga yi ba da aka fasa auren kuma daga baya sai ta dawo, duk bacin rai ne da rashin madafa ba wai wani abu bane yasa tace ta tafi, tunda ita kanta tasan bata da inda za ta, bata da kowa da ya wuce mu, ai yarinya ce me hankali Mayraah, ina da tabbacin kilan gidan kawayenta ta tafi ta samu nutsuwa na ɗan lokaci, amma in sha Allahu zata dawo komin dare, ke kin taɓa ganin inda ɗa ya guji iyayensa komin laifin da suka masa? To ki sa ma ranki salama ki koma dakinki ki samu kuyi shawaran yanda za a fara cigiyarta a gun yan makarantarsu ke da mai gidan ki, wannan kawar tata da kika kira daxu ai ba ita kadai bace kawarta, kilan wajen wata daban taje, kar ki biye abinda Mamuda ya maki ki samesa a san na yi tun dare bai tsala ba, in sha Allahu Mayraah tana nan gun kawayenta, nima yanzu ina shiga zan buga lamban yan bichi in ji ko Badiyyah ta je can ko hankali zai kwanta, amma Mayraah kam nutsuwarta da sanin ya kamata ma bazai sa ta tafi wani waje ba, tana nan kusa da mu in sha Allah" Hajja na kai wa nan ta bude gidanta dake bude har sannan ta shiga ciki a hankali tana cewa "Wai ni yau da mutuncina da girmana aka kai Caji opis" Sai kuma ta fashe da kuka ta kulle gidan. Maheer ya bar anguwan bayan sun ajiye Hajja, tun dazu ko magana bai yarda ya hadasa da Ammi ba balle ya bata hakurin kukan da take, to me ma zai ce mata. Wajen karfe tara Mayraah ta farka daga baccin da take, it was still raining but not heavily, zuwa sannan zazzabi ne sosai jikinta, ta daure ta sauka daga kan gadon ta lallaba ta bude jakarta ta ciro wani hijab ta saka sannan ta dau Atm card dinta, tana tafiya a hankali ta bude kofar dakin ta cire makullin sannan ta fita ta kulle kofar ta sauko kasa, reception din hotel din ta nufa cike da karfin hali tana kallon receptionist din tace "Plss where can i locate...." Kasa ci gaba tayi ta dafe kanta, receptionist din ta zagayo inda take da sauri ta riketa ganin tayi baya zata fadi tace "Are you okay Madam?" colleague din receptionist din shi ma ya taho da sauri suna mata sannu, Mayraah dai gyada masu kai kawai, receptionist din ta karasa da ita inda kujera yake ta xaunar da ita kan kujera tana kallonta, sauran ma'aikatan wajen ma duk suka taho suka tsaya kan su, Receptionist din tace "Amma baki da lafiya ko?" Mayraah ta kasa bata amsa sbda sarkewa da breathing dinta ya soma yi, nan duk suka rikice aka fara mata fifita duk da sanyin gari, wata worker din wajen na cewa ko dai a tafi da ita asibiti don babu wani tanadi incase of such emergency a hotel din, Wani mutumi ne ya shigo Reception from upstairs zai fita waje, ya tsaya ganin yanda ma'aikatan hotel din suka taru waje daya sai fifita suke ma Mayraah, ya karasa inda suke yace "Hope all is well?" Wani ma'aikaci yace "Bata da lafiya ne muna jiran za a dauko makullin mota a tafi da ita asibiti" Yace "Subhanallah, why not mu tafi asibitin since i am with my car key, i am going out now" Yana fadin haka ya tsaya gaban Mayraah yana kallonta yace "Sannu, are you Asthmatic?" Mayraah bata ma san yana yi ba don zuwa sannan double take ganinsu gaba daya, da sauri ya kalli receptionist din yace "Ku fito da ita kawai, mu tafi asibitin" Yana fadin haka ya fita in a haste don tada motarsa dake parking space, receptionist din suka tafi da Mayraah motar tasa, ya bude masu back seat, ma'aikaciyar hotel din daya ce ta shiga motar tare da Mayraah za su tafi asibitin bayan ta amshi Atm din Mayraah dake hannunta kar ta yar, makullin dakin kuma ta ba colleagues dinta su mayar cikin hotel din, tuni ya ja motar suka bar haraban hotel din bayan an bude masu gate. Mutumin na driving din ya kira wani abokinsa yana dagawa yace "Hello Dr kana hospital ne?" Sai kuma yace "Ohk, to dama emergency ne, wata baiwar Allah ce bata da lafiya muna hanyan asibitin yanzu" Daga haka ya katse wayar. A hankali Mayraah ta bude idonta after an hour a asibitin, ido hudu tayi da receptionist din dake zaune ward din ana jiran tashin Mayraah don ta kira yan uwanta kafin ma'aikaciyar ta koma hotel bakin aikinta as instructed by the hotel manager, matar ta sakar ma Mayraah murmushi ta mike tace "Sannu fa" Mayraah ta mike zaune da kyar tana bin ward din da kallo, it's so big and clean, daga gani kasan ba karamin asibiti bane ko daga gadon da take kwance zaka gane hakan, Receptionist din tace "Bari in masu magana ince kin tashi...." Daga haka ta fita daga babban ward din, Mayraah ta bi ta da kallo, sai kuma ta kalli Cctv camera dake ward din, maida dubanta tayi kan drip da aka makala mata a hannu, dai dai nan aka bude kofar ward din ta daga kai da sauri, wani mutumi ne ya shigo tare da wani dake biye da shi a baya with white lab coat da stethoscope a wuyansa, ita dai duk kallonsu take har suka iso bakin gadon da take, mutumin da ya fara shigowa dakin ya ɗan duka ya dafa gadon yana kallonta yace "Baiwar Allah ya jikin?" Mayraah tace "Alhamdulillah naji sauki" Likitan ya karaso ya kara gudun drip din kafin shi ma ya kalleta yace "Hope you are feeling much better now?" Tace "Sure" Yace "To Maa sha Allah" Receptionist din tace "Manager yace ta kira yan uwanta sai ni in koma bakin aikina" Sosai gaban Mayraah ya fadi, likitan yace "Eh gaskiya ne, ai kun ma yi kokari for such hospitality" Sai kuma ya kalli Mayraah yace "Ki kira yan gidanku yanzu ki sanar masu kina asibiti" Da sauri tace "Ai wayar na dakin hotel din" Mutumin da ya kawota hospital ya ciro wayarsa ya mika mata yace "Za ki iya amfani da nawa" Sosai gabanta ya fadi, ta amshi wayar tana tunanin yanda zata yi, nan da nan dubara ya fado mata tayi dialing din layinta dake kashe ta sa handsfree, duk suka dinga kallonta jin switch off, a hankali tace "Number Abbanmu ne, bari in kira yayana" Daga haka ta sake dialing other line dinta nan ma aka ce switch off, Mayraah ta kalli receptionist din tace "Za ki iya tafiya, Nagode sosai, nasan zuwa anjima zan samesu a waya" Receptionist din tace "Toh Allah ya kara lafiya, ga Atm card dinki" Mayraah har ta mance da Atm card din, ta amsa tana juyawa tace "Nagode" Receptionist din tayi mata Allah ya kara lafiya, zata fita mutumin da ya kawo su yace "Ko za ki jira mu koma tare in 30mins time" Tace "Ayya, kar ka damu zan samu Cab idan na fita, kaga instruction din manager dinmu kenan, yace tana farkawa in dawo bakin aiki" Yace "To ba laifi" Daga haka ta fita daga ward din. Mayraah na gyara Hijab din jikinta a hankali tace "Naji sauki fa, kawai za a iya sallamata in biya bill din" Dr Khalil ya kalli abokinsa Ahmad kamar yanda Ahmad din ma ya kallesa, can Dr Khalil yace "Ae ba a gama baki proper medications ba, kuma kinga ko rabi drip din hannunki bai kusa ba" Mayraah tace "Ni fa i am okay, kawai jinina ne yayi kasa, but i am better now" Ahmad yace "Ohk then, ka sallameta Dr, sae kawai a rubuta mata drugs" Dr Khalil yayi kasa da murya yace "To ae kasan ka'idar hospital din nan...." Ahmad yace "To tace zata canza hospital, It's not ur fault" Dr Khalil yace "Ohk then" [7/16, 1:35 PM] Khaleesat Haiydar💖: Bayan rubuce rubuce Dr Khalil yayi discharging Mayraah, daga gefe kuma ya rubuta mata drugs a wani takarda ya mika mata yace "Ki siya wannan a pharmacy, Allah ya kara lafiya" Ta amshi takardan cikin sanyin murya tace "Thank you, nawa bill dina?" Ya nuna Ahmad dake zaune yace "Yayi clearing din bill din" Ta juya ta kalli Ahmad din kafin tace komai ya mike yace "Idan hotel din za ki koma nima can zan tafi yanzu, in kuma da inda zaki sai inyi dropping dinki it's already late now" Mayraah tace "Toh Nagode" Fita suka yi daga ward din likitan na biye da su, Mayraah ta dinga bin asibitin da kallo ganin na masu hannu da shuni ne don har da jajayen fata ta gani a asibitin, a haka har suka fito haraban hospital din, ruwan ya tsaya gaba daya amma ko ina yayi mugun sanyi, ta takure cikin hijab dinta har suka isa inda yayi parking motar sa, ta bude front seat ta shiga bayan shi ma ya shiga motar, sae da suka fita hospital din ta dinga jin wani yunwa ba na wasa ba, dai dai wani eatry tace "I want to get something here pls if u won't mind" yace "Ohk" parking yayi, ta bude motar ta sauka ta kulle masa sannan ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba ta dawo motar rike da leda ta bude ta shiga, sae a sannan ta tuna kanta kadae ta siya ma abinci fa, bayan ya fara tafiya ta ɗan kallesa tace "in siya maka ne?" yace "No, na ci abinci, thank you" Bata sake cewa komai ba, tana ganin pharmacy har zata ce ya tsaya ta siya maganin da aka mata prescribing sae kuma ta fasa da zumar zata siya gobe idan ta bar hotel din, suna isa bayan yayi parking ta sauka tayi masa godiya ta shiga hotel din ta bar sa a baya kamar ba tare suke ba, tsaye take a reception tana jiran makullin dakinta shi ma ya shigo, ana bata aka basa nasa ta bari ya fara tafiya sama, sannan ita ma ta wuce sama, nan taga ashe dakinsa na kallon nata ne ma, ita dae bata kallesa ba ta bude dakin nata ta shiga ta kulle kofar da makulli. Tun da suka dawo asibitin Mayraah ke kwance bata yi bacci ba, don tana shigowa daki kamar tare ta shigo da cramps, wanda a hospital ko alamarsa bata sake ji ba tun da ta farka har suka bar asibitin, tun tana daurewa ta sauko kasa ta sake koma kan gado, ta mike tsaye ta zauna har dai ta kasa ci gaba da jurewa, nan da nan ta fara fita hayyacinta, wajen karfe daya da rabi ta bude kofar dakinta ta fito ko sanin ta fito ma bata yi ba saboda ciwon yayi mata yawa, ta durkusa bakin kofar dakin da taga ya shiga ta kwankwasa da kyar, sae da ta kwankwasa sau uku sannan taji yana tambayar waye, cikin rawan murya tace "Ni ce" bude kofar yayi ganinta Durkushe ya koma baya da sauri yana kallonta, ta fashe da kuka muryarta na rawa tace "Don Allah ka taimaka ka kai ni asibiti" Kallon mamaki yake mata, ta hade hannunta tana kuka sosai tace "Don Allah kayi sauri, wallahi baxan iya ba kuma" Komawa daki yayi ya dauko makullin motar tasa ya fito, sai a sannan ta mike ta jingina da bango har sannan tana kuka, ya kulle dakinsa ya tafi nata ya bude, tana kallonsa ya shiga sai gashi ya fito da hijab dinta ya mika mata, amsa tayi ta sa da sauri, ya kulle nata dakin ma da makulli, a daddafe ta bi sa suka sauka downstairs ya mika ma yan reception din makullansu sannan suka fita tana biye da shi a baya zuwa parking space. Har suka isa asibitin Mayraah kuka take don ita kadai tasan abinda take ji, shi dai tun da ya mata sannu sau hudu ya ja bakinsa yayi shiru.... Dr Khalil ya fito ward din da Mayraah take yana kallon Ahmad dake zaune corridor din wards din ya jingina da bango idonsa a kulle yace "Hey wai bacci kake a nan" Ahmad ya bude ido yace "Really, karfe nawa yanzu?" Dr Khalil yace "Biyu ya wuce, Flight din naka na karfe nawa ne?" Ahmad yace "Karfe biyar" Dr Khalil yace "Nan dae da 3 hours" Ahmad yace "In sha Allah" Dr Khalil yace "Tayi bacci yanzu, i think zaka iya komawa hotel din kar kaje kayi missing Flight dinka, ita kuma zuwa safe za mu yi expecting yan uwanta, daga nan sai ayi discharging dinta don it's just cramps, But still idan baza ka takura ba mu je office dina ka kwanta zuwa 3:30 sai ka tafi hotel din daga can ka wuce airport" Ahmad ya mike yace "Ohk I will prefer that" Tare suka koma office din Dr Khalil Ahmad ya kwanta. Wajen uku da minti arba'in ya tashi daga baccin da yayi, bai ga Dr Khalil a office din ba, ya fita yana rike da makullin motarsa, sai da ya fara zuwa ward din da aka kwantar da Mayraah, kwance ya sameta idonta biyu, har ya karaso ya tsaya kusa da gadon bata ce masa komai ba, yace "Jikin da sauki?" Ta gyada masa kai, yace "Allah ya kara afuwa" Tace "Ameen, Pls ina Dr din?" Ahmad yace "U need anything?" Ta girgiza masa kai tace "Kawai ka kira min shi pls" Yace "Ohk, i will.... Kun yi magana da yan uwan naki?" Mayraah ta sauke idonta kasa, can tace "Ni iyayena ba garin nan suke ba suna Bauchi, admission na samu a nan" Yace "Ok.. ke student ce?" Ta gyada masa kai tace "This is my first time in Abuja, na samu admission a University ne, to kafin in samu hostel shine nayi lodging hotel din" Ahmad yace "Kin samu hostel din ne yanzu?" Still ta gyada masa kai tace "Ana kan processing din mun ne" Yace "Zuwa yaushe?" Tace "Nima ban sani ba, amma idan aka gama zan bar hotel din" Yace "Na gane, shikenan ni zan tafi Allah ya kara lafiya...." Tana kallonsa tace "Ameen, thank you" Yace "I will be checking out of the hotel idan na koma, so take care of ur self, Allah ya bada sa'an karatu" Tace "Ameen, Nagode" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, har parking space Dr Khalil ya raka abokin nasa yace "To yanzu sai yaushe kuma in ka tafi?" Ahmad yace "May be nan da 5 weeks bikin Humaira" Dr Khalil yace "Ohh haka ne fa, To Allah ya tsare" Ahmad yace "Ameen" Daga haka ya bude motarsa ya shiga, Dr Khalil ya koma cikin asibitin ya tafi ward din da Mayraah take, ya karasa kusa da gadon yace "Ya jikin yanzu?" Tace "Na ji sauki" sai kuma tayi kasa da murya tace "Pls is there anywhere i can get sanitary..... " Sai kuma tayi shiru" Yace "Ohk, give me a minute" Daga haka ya juya ya fita. Da safe breakfast lafiyayye aka kawo ma Mayraah kamar yanda ake ma sauran patients din asibitin, har ta mance rabon ta zauna tayi breakfast din kirki, sosai kuma ta ci abincin, tana gamawa ta koma ta kwanta, bayan sallan asuba Dr Khalil ya shigo ward din yana kallonta yace "Ko dai ba garin nan iyayenki suke ba? Naga har yanzu baki ce za ki kira su ba" Ta gyada masa kai tace "Ni student ce, na samu admission ne a University" Dr Khalil yace "Oh ok, amma ai ya kamata su san baki da lafiya ko" Ta girgiza kai da sauri tace "Aa bana son in daga masu hankali, jiya fa na zo garin" Yace "Really?" Ta gyada masa kai, yace "Daga ina?" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Bauchi" Ya ɗan buda ido yace "That's far" Kamar warce ta tuna abu kuma tayi saurin cewa "But my aunty is in Suleja with her husband" Dr Khalil yace "Ohk sun san kin taho Abuja kenan" A hankali tace "Sai nayi settling a hostel zan je wajensu" yace "Ohk that's good, ni zan tafi gida kin ga night duty nayi, zaki kira aunt din taki ne ta taho yanzu?" Mayraah tace "Ni fa na samu sauki, dama idan aka min allurai shikenan sai in ci gaba da shan magani kawai, i am feeling much better now" Yace "Kina nufin a sallameki kenan?" Ta gyada masa kai, yace "Are you sure?" Nan ma ta gyada masa kai yace "Ok then, are u still going back to the hotel?" Tace "Yes" Yace "Toh let me get u discharged sai in ajiye ki hotel din before heading home" Tace "To Nagode" Tare Mayraah suka fito reception da Dr Khalil, duk nurses din sai sallama suke masa da fara'a kana ganin haka kasan he is a free man, a haka har suka fito haraban asibitin, Mayraah dai sai kallon girman asibitin take because it is so beautiful and big, ambulances kusan biyar ne cikin compound din asibitin, sai da ta ga ya shiga motarsa sannan ita ma ta shiga, bayan sun bar asibitin yace "Ya sunan hotel din?" Shiru tayi tana son tuna sunan hotel din, yace "Ko kin manta?" A hankali tace "I can't remember" driving dinsa ya ci gaba da yi har suka iso hotel din yayi parking yana kallonta, duk da tayi mamakin yanda yasan hotel din haka dai tace masa "Nagode" yace "You are welcome Maryam" ta juya ta kallesa tace "Mayraah" yace "Sorry about that" bude motar tayi zata sauka yace "Anytime u are sick, you can come to the hospital ki ce kina neman Dr Khalil" Ta gyada masa kai tace "Thank you so much" yace "You are welcome" Daga haka ta sauka daga motar ta shiga cikin hotel din, tana shiga receptionist din da ta bata makullin dakinta tace "Wannan mutumin da ya kai ki hospital jiya ya biya maki kudin daki na sati daya" Mayraah ta dinga kallonta babu ko kiftawa, can a hankali tace "Toh Nagode" Daga haka ta wuce sama zuwa dakinta. Yanda Ammi taga rana haka ta ga dare, gaba daya ta rasa me ke mata dadi a rayuwar, gashi bata ji alamar Abba a gidan balle matar da ya auro, a yanda ta fahimta ma kamar ita kadae ce a gidan, da safe wajen karfe tara tana zaune kan darduman don tun dawowarta jiya bata shiga daki ba sai dai ta shiga bandaki ta dawo ta zauna kan darduman, ta daga kanta da ke mata azaban ciwo jin an bude kofa, Usman ne ya shigo Maheer na biye da shi, Ammi ta sunkuyar da kanta, Maheer ya zauna yana kallonta yayi kasa da murya yace "Ina kwana" Ammi ta kasa amsa masa wasu sabbin hawayen suka cika idonta, Usman ya zauna kan kujera shi ma yana kallonta a hankali yace "Ina kwana" Kawai ta fashe masu da kuka sosai, Maheer ya rufe ido ya bude cike da karfin hali yace "Don Allah ki bar kukan nan haka Ammi, addu'a kawai shine mafita, pls u are stressing ur health" Ammi ta katse sa hopelessly tace "Ta yaya zan bar kuka Maheer? I failed as a mother, I failed u all, i failed Mayraah, I wished i neva witness a day like this, gwara ace bana duniyar da wannan..." Kukan da take yasa ta kasa ci gaba, Usman na kallonta yayi kasa da murya yace "U didn't fail Ammi, mu kan mu shaida ne kan son da kika yi ma Mayraah, we are not in the position to question God akan abinda ya faru, dama haka Allah ya riga ya tsara babu dubaran da zai canza hakan, ki kwantar da hankalinki, in sha Allah Mayraah will be back home safe and sound, babu abinda zae sameta" Ammi dai kuka kawai take, Maheer ya mike yace "Let me get you tea" Daga haka ya fita daga parlon don yasan tun jiya bata ci komai ba, Usman ya ci gaba da kwantar mata da hankalinta don abun sai yayi masu yawa kuma idan Ammi ta kwanta ba lafiya, it's better su dinga lallabata suna kwantar mata da hankali. Da yammacin ranan Maheer na zaune wani eatry da goran ruwa a gabansa, ya fi awa daya zaune eatry din, ya kalli agogon wrist dinsa for d countless time dai dai sanda Musharraf ya shigo eatry din, Musharraf na hango Maheer ya nufi inda yake zaune, ya basa hannu suka gaisa sannan ya zauna kujeran dake facing dinsa, Maheer yace "Sorry nace mu hadu nan Dr ban san ko na shiga hakkin ayyukan ka ba, i am so sorry for the inconvenience this might have cause you" Musharraf yace "Never mind, i am all ears" Maheer na kallonsa calmly yace "Dr nasan Mayraah tana wajen ka, babu inda zata je da ya wuce wajen ka, don babu wanda ta sani sai kai, and tayi hakan sau uku kenan if i am not mistaken, but if i may ask pls idan kanwarka ce Mayraah zaka ji dadin wani saurayi ya dinga bata shelter ko yana hosting dinta saboda wani issue ya faru a gidansu?" Kallonsa kawai Musharraf yake, can yace "Ban gane abinda kake nufi ba" Maheer yace "Mayraah is missing since yesterday kuma babu inda zata je tun jiya har zuwa yau da ya wuce gun ka, you know her whereabout don haka kaji tsoron Allah, abinda baza ka so ayi ma kanwarka ba kar kayi ma kanwar wasu, at the first place ma in taje wajenka me ya kamata ace kayi as a responsible guy? That aside pls kai ba musulmi bane? Ta yaya ma zaka ci gaba da relationship da yarinyar da iyayenka suka ce baza ka aura ba in dai ba wata manufar gareka a zuciya game da ita ba? Meye amfanin relationship din da kai kasan will neva lead to marriage tsakaninku tunda iyayen ka sunce baza ka auri mara asali ba? Why not go ur way and leave the innocent girl alone pls?" Mikewa Musharraf yayi ya buga table din gabansu yace "You are talking bullshit, da nasan kirana kayi ka bata min lokaci baza ka gan ni a nan ba Malam" Daga haka ya juya ya bar wajen a fusace, Maheer ya bi sa da kallo har ya fice daga eatry din. Musharraf na shiga motarsa maganganun Maheer suka dinga masa yawo a kai zuciyarsa na bugawa, Mayraah bata gida tun jiya? To ina ta tafi? Since yesterday yake ta kiran wayarta switch off, har he was planning on coming to their house to check on her today, sosai kalman Mayraah bata gida tun jiya da Maheer ya fada yayi distablizing dinsa, da kyar ya iya jan motar ya bar parking space din eatry din yana tunanin to ina ta tafi, sosai yaji hankalinsa ya tashi, Maheer na fitowa eatry din ya kira Abba yace "Abba mun hadu da shi, ya ki saurarana, wanda hakan ke nuni da truly suna tare da Mayraah...." Abba da ke ta jiran kiran Maheer tun dazu yace "Turo min numbersa, i will get him arrested immediately, his parent were the root of every problem occuring now, i wil surely get him arrested a yau din nan har sai ya fito min da daughter na...." Maheer ya tura ma Abba number Musharraf, babu bata lokaci Abba yayi making few calls nan da nan aka fara tracking Musharraf..... [7/16, 8:10 PM] Khaleesat Haiydar💖: Musharraf na dakinsa bayan la'asar Maminsa tayi knocking, yasan ita ce but saboda damuwar da ya cika zuciyarsa ya ki tashi ya bude kofar, may be idan taji shiru zata yi tunanin bacci yake ta wuce kawai, continuously yaji take knocking din kofar, hakan ya sa ya ajiye wayar hannunsa da yake ta dialing number Mayraah amma switch off, ya mike ya nufi kofar ya bude yana kallonta bai dai ce komai ba, daga sama har kasa take kallonsa tace "Me kake yi a ciki nake knocking baka responding Musharraf?" Ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yace "Kawai na kwanta ne Mami, i want to get some rest" Mami ya dinga kallonsa, ganin damuwar dake fuskarta yace "Is anything wrong Mami?" Ta karasa cikin dakin ya bi bayanta yace "Mami wani abu ya faru ne" Mami ta juya tana kallonsa cike da damuwa tace "I should be asking u that Musharraf, tell me what are you hiding from me? menene ke faruwa?" Musharraf ya shafa kansa yace "Me ke faruwa kamar me fa Mami, kin ga anyi wani abu ne?" Mami tace "You are not saying the truth, tell me kai da waye ku ke da matsala? Menene kake boye min?" Ya ɗan buda ido yace "Matsala kuma? I don't have issue with anyone" Mami tayi shiru still looking at him kafin tace "Then me yasa police officers suka zo gidan nan nemanka yanzu?" Kallonta ya dinga yi cike da mamaki yace "Police officers kuma? I don't understand" Mami tayi kasa da murya sounding so disturbed tace "Kar ka boye min komai don Allah son, me yake faruwa?" Musharraf yace "Wallahi Mami ban sani ba..." Bai sake cewa komai ba ya fice daga dakin Mami ta bi bayansa tana kiransa bai tsaya ba har ya sauka downstairs, ya nufi kofar parlor ya bude, wasu mutane uku ya gani tsaye dai dai bakin kofar parlon, daya daga cikinsu yace "Musharraf Abdallah??" Musharraf yace "Yes, how may i help you?" ID card dinsa ya ciro don dukkansu ba uniform bane a jikinsu, Ɗan sanda na nuna ma Musharraf ID card din yace "You are under arrest" Juyawa Musharraf yayi ya kalli Mami dake tsaye bayansa, trying all possible best to calm her down yace "U need not to worry pls Mami, it's not something serious, zan bi su mu je" Mami da hankalinta yayi mugun tashi bata ko kallesa ba balle ta sauraresa tana kallon officers din tace "Pls wani division din ne?" Wani officer ya gaya mata, ta juya ta koma sama da sauri don dauko makullin motarta da gyale, Musharraf ya bi yan sandan har kofar gida zuwa gun motarsu, babu wanda zai ce yan sanda ne don motar ma me kyau ce suka zo da shi, nan suka kama hanyar station tare da Musharraf. Maheer na zaune asibitin da aka kwantar da Haseenah wajen karfe biyar na yammacin ranan, she is responding to treatment don har ta fara iya cin abinci a hankali, amma fa tana jin jiki don fuskarta ya kumbura suntum saboda azaban bugun da kanta ya sha, tun da abun ya faru shi dai bai ga mahaifiyarta ta zo asibitin duba ta ba, danginta ne kullum ke sintirin asibitin su kawo mata wannan su kawo mata wancan, kuma ko sun zo basa ce ma Maheer komai, ko Aunties dinta idan ya gaishesu basa amsawa fuska a murtuke suke wucesa shi kam ko a jikinsa don duk ya kagu a sallameta a asibitin shi ma ya sallameta zuwa gidansu don har ransa yasan bazai iya zama inuwa daya da Haseenah ba kuma, shi mamakin ma yanda aka yi har ya auri Haseenah yake kamar wanda aka yi ma rufa ido, ko da yake baka sanin halin mutum ai sai ka zauna da shi dama, he regret knowing her har suka kai ga aure, yana zaune haraban hospital din yayi nisa tunanin da yake don shi har a sannan gani yake Mayraah na gun Musharraf, infact bai ma yarda bata wajensa ba, few minutes ago Abba ya kirasa ya sanar masa anyi arresting Musharraf, so kawai yana jiran Abba ya sake kiransa yace masa Musharraf yayi admitting Mayraah na wajensa, yana wannan tunanin kiran Abba ya shigo wayarsa, da sauri ya daga, Abba yace "Akwai wanda ke tare da matar taka a asibitin ne ka taho Miller road ka sameni yanzu?" Maheer yace "Miller road, Ina kenan a nan Abba?" Abba yace "I will send you the full address" Maheer yace "To" Shi fa duk tunaninsa Abba baya kano da bai gansa a gida ba, though ya dai lura kamar Hajiya Amina ma bata can gida amma he was thinking tare Abba ya tafi da ita, mikewa yayi don Aunties din Haseenah na ciki tare da Haseenar ya shiga motarsa ya bar hospital din, address da Abba ya tura masa ya bi har dai daga karshe ya ga kansa a wani hadadden layi na manyan masu kudi, don duk gidajen wajen hadaddu ne na karshe, yayi parking a number gidan da Abba yace yayi parking yana kallon gidan wondering whose house Abba yace ya zo, bude gate din gidan aka yi bayan ya kira Abba ya sanar masa ya iso kofar gidan, ganin haka ya shiga ciki yayi parking, a compound ya tarar da Abba tsaye waiting for him to come in, ya sauko daga motar Abba yayi leading dinsa har zuwa babban parlon gidan shi dai Maheer na ta mamaki yana bin gidan da kallo, Maheer na shiga lafiyayyen parlon ya zauna yana kallon Abba yace "Abba whose house is this?" Abba yace "Gidana ne" Da mamaki Maheer yace "Gidanka kuma Abba? Gidanka?" Maimakon Abba ya basa amsa sai cewa yayi "Yanzu kawun nan matar ka suka bar nan, her paternal and maternal Uncles" Nan da nan mood din Maheer ya canza, Abba yace "Sun zo sun bada hakuri akan abinda ya faru...." Maheer ya girgiza kai trying his possible best to be calm yace "Abba gaskiya bazan iya ci gaba da zama da ita ba....." Abba yace "Maganar banza ma kake kenan, ni zaka mayar karamin mutum? Meye dalilin da baza ka ci gaba da zama da ita ba, anyi abinda yafi haka ma an koma an ci gaba da zama balle wannan abun da ya faru duk kwamacalar mata ne da haukan mata" Maheer ya kalli Abba cike da damuwa yace "Abba wai kaga abinda sisters din mahaifiyarta suka yi ma...." Abba ya dakatar da shi yace "Bana son jin komai, dama su mata ai abinda yafi haka ma za su aikata don haka babu ruwana da wannan batun, har mahaifiyar yarinyar yanzu sai da ta kira suka bani waya tace ayi hakuri, ta kuma ce za ta zo har gida ta bada hakuri sannan ita ma kakar taku zata je ta bata hakuri, kaga wannan na nuni da iyayen nata ma ba kananun mutane bane ai, balle ko da basu zo bada hakuri ba ban ga dalilin da zaka saketa ba, ita da ma aka ji ma mummunan rauni take asibiti..." Maheer ya dake yace "Amma Abba...." Abba ya dakatar da shi again yace "Maheer bana son gardama, a lokacin da aka ce maka ka dauke Mayraah daga gidanka ai baka yi gardama ba, sai nine ka raina? Wato ni ban isa in gaya maka ba" Maheer bai sake cewa komai ba ya jinginar da kansa da kujera yana jin zuciyarsa ba dadi, shi duk zatonsa a kan Mayraah Abba ke kiransa, ya zata an gano inda take ne shine Abba yace ya zo anguwan ya dauketa, ashe kawai bacin rai zai zo ya ji, Dai dai nan Hajiya Amina ta sauko downstairs Maheer ya dinga kallonta babu ko kiftawa, ta karaso parlon tace "Sannu da zuwa Maheer" Ya sunkuyar da kansa yace "Ina wuni" Tace "Lafiya lau" Sai kuma ta kalli Abba tace "Alhaji ya ake ciki, kun sake waya da yan sandan ne?" Abba yace "Sun ce inyi expecting call dinsu ko zuwa nan da magrib, so ina jira in sha Allah" A hankali Hajiya Amina tace "Toh Allah ya sa a dace" Daga haka ta juya ta koma sama, Maheer felt so bad at what he saw, wato dauko matar nan Abba yayi suka dawo nan suka bar Ammi ita daya a can gidan, lokaci daya duk jikinsa yayi sanyi damuwan suka taru suka cunkushe masa a zuciya, ga na Mayraah, ga Haseenah da Abba ke cewa lallai sai ya zauna da ita, ga kuma halin da Amminsa ke ciki, ga Abba na neman kaurace mata, cikin sanyin jiki ya mike yana kallon Abba, Abba yace "Mu je ka duba gidan, i finished it few months back ban dai gaya maku bane kawai" Maheer ya dake yace "Sai na sake dawowa Abba, babu kowa a asibitin, zan koma ne" Abba yace "Ohk, nima ina jiran kiran yan sandan ne idan sun kirani naji yanda ake ciki na dan samu nutsuwa to zan zo asibitin da Hajiya Amina ko zuwa bayan isha ne in sha Allah" Maheer ya ki ce masa komai ya nufi kofa zai fita, can kuma dai ya juyo yayi gathering courage yace "Abba ina ɗan son za mu yi magana in babu damuwa" Abba ya mike yace "Okay" Can babban compound din gidan suka fita, Maheer na kallon Abba yayi kasa da murya cikin ladabi yace "Amma kayi hakuri in maganata zata ɓata maka rai Abba, Abba i don't think Ammi deserves this from you...." Abba ya dakatar da shi yace "Ni nayi deserving abinda ta min? Ni nayi deserving walakanci da rashin mutuncin da ta min wanda gashi yanzu a sanadin selfishness dinta ban san whereabout din Mayraah ba? Maheer let me be frank with you, for now I can't withstand the sight of ur mother billahi, albarkacinku kawai ta ci ban ce mata kar ta sake dawo min gidana ba, tayi failing dina ta yanda bana tunani, assuming the issue is just between us bazan wani damuwa ba, amma ta jefa rayuwar yarinya karama a halaka, ko da ace yanzu Mayraah na gun shi saurayin nata da muke zargi mahaifiyarku bata cuceta ba? Don't forget ta dalilinta Mayraah ta samu guts din zuwa gidan saurayi for days now, duk ita ce silar duk abinda ya samu Mayraah in ma rayuwarta ya lalace to alhaki akan Ammin ku, da ace ita bata juya mata baya ba komin pressure din kakanku da ahalinta Mayraah bazata yi tunanin barin gida, tare da kai muka karanta wasikar da ta bari ai ko? So kar ka kuma ce min Ammi bata yi deserving abinda na mata ba, sabon gidan nan da kake gani ban taɓa tunanin ba ita ce zata fara shiga ciki ba don ita nake gina ma, so do not blame me for my actions, And mind you ni ba jahili bane Maheer nasan abinda nake...." Maheer dai kansa na kasa bai sake cewa komai ba amma zuciyarsa fal yake da tausayin mahaifiyarsa, he felt so really bad, Abba yace "So duk abinda ake ciki a station din i will call and let you know" Daga haka Abba ya juya ya koma cikin gidan, Maheer ya bude motarsa duk jikinsa a sanyaye mai gadi ya bude masa gate ya fita daga gidan. Karfe shidda da rabi Musharraf ya fito station Maminsa na biye da shi a baya, after few seconds Usman ya fito ya nufi motarsa, sai ga Abba ma ya fito bai ko kallesu ba ya nufi tasa motar shi ma, Mami ta bi Abba da kallo har sannan maganganunsa na mata zafi a rai, Maheer ne ya fito ya nufi tasa motar shi ma without looking at them, Mami na kallon Musharraf on a serious note tace "Look at me Musharraf" Musharraf dake saka agogonsa ya juya ya kalleta tace "Babu kai babu yarinyar nan har abada, ni ban san ai guardian din nata marasu mutunci bane marasu daraja...." Musharraf ya katse ta yace "To ba su Kawu Mansur da Aunty Halima bane suka fara masu rashin mutunci ba Mami" Tsawa Mami tayi masa tace "Ina magana kana magana? to wallahi idan kana son kaga bacin rai na Musharraf kar ka fita sabgar er mutanen nan" Da damuwa Musharraf yace "To Mami ina ma take yanxu? Ba ma sai an san inda take ba before all this, we should even pray she is safe" a fusace Mami tace "Oho that's not my problem, ni dai na gaya maka in ba fushina kake so ba babu kai babu ita har abada kuwa, in kuma bakina kake so to bismillah" Kallon Mami kawai Musharraf yake helplessly don bai taɓa ganin Maminsa so angry at him ba haka, truly Abba da Usman sun yi maganganun da ko ma wa aka gaya ma sai ransa ya baci, but shi duk wannan ba damuwarsa bane, matsalarsa kawai inda Mayraah take, Dai dai nan Yayan late father dinsa wato Hon Alhaji Kabir Saminu ya fito daga station din, escort dinsa dake haraban Police station din suka nufosa da sauri, Yana kallon Musharraf strictly yace "Kai..." Musharraf ya juya ya kallesa sannan ya sunkuyar da kai, strictly Alhaji Kabir yace "Babu kai babu er kananun mutanen can daga this very moment, ban da ma kai wawa ne mahaukaci meye zaka ci gaba da bibiyar yarinyar da bata da asali? Are you stupid? Kai mutuncinka ne yanzu police station da suka kawo ka? Wallahi ban da mahaifiyarka da ta hana da babu abinda zai hanani Shari'a da su, mutanen banza kawai mutanen hofi makaryata, su har suna da wani sauran mutunci bayan lamarinsu babu komai facce karya, da mutuncin ka kan wata yarinya can mara asali an kawo ka nan ana tuhumarka sai kace wani Kidnapper ko ɗan fashi, da ban tako tun daga kaduna na zo nan yau ba kana zaton ba cikin barayi zaka kwana a cell ba yau? To wallahi kashedi na farko da na karshe kenan nake maka babu kai babu er su ko da kai ne HOD din department din ba Lecturer din ta ba, nonsense" Shi dai Musharraf kansa na kasa ko sanin abinda kawun nasa ke cewa bai yi ba, don tunanin ta yanda zai fara neman Mayraah kawai yake a ransa, Alhaji Kabir ya kalli Mami yace "Tare kike da motar ki Hajiya" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Ehh da motata nake" Alhaji Kabir yace "Shikenan.... ni zan koma kaduna yanzu" Mami tace "Baza ka bari gobe ba Alhaji" Yace "Ina da appointment da yawa goben, so we will be heading to airport now" Mami tace "Toh shikenan, Allah ya tsare, a gaida su Hajiya da yaran" Yace "In sha Allah" Ko kallon Musharraf bai yi ba ya nufi inda motar sa yake with his escort, sai ga DPO ya fito yace "Honorable tafiyar kenan?" Alhaji Kabir yace "Ehh wallahi zan koma kd yau ne" Har mota suka tafi tare da Dpo din, wanda abokinsa ne for long, Mami ta nufi motar ta without looking at Musharraf, bin bayanta yayi yana tafiya a hankali, ya bude back seat ya shiga, ita dai bata ce masa komai ba, suna kama hanya Mami tace "In dai ban isa da kai ba Musharraf wallahi ka ci gaba da kula yarinyar nan, ni kuma zan nuna maka ba kai kadai na haifa ba" Shi dai bai ce mata komai ba ya jinginar da kansa da kujera abinda ya damesa daban, wato yanda zai fara neman whereabout din Mayraah. Kamar yanda Alhaji Kabir ya kasance abokin Dpo, haka Abba ma Dpo din childhood frnd dinsa ne, kawai aka sulhunta su a wajen don an duba call history din Musharraf don ganin when last ma suka yi communicating da Mayraah aka ga babu communication kwata kwata tsakaninsu for long banda just of recent da ya dinga kiran wayarta baya samu, kamfanin layin da Mayraah ke amfani shi sun yi confirming babu wayar da ya shiga tsakaninsu for more than a month now, sannan asibiti da Musharraf ya kai ta ma an bincika an gano ba shi kadai ya kai ba tare da Dr Asma'u warce ita ma lecturer dinta ce suka je asibitin, har Dr Asma'u sai da aka kira a issue din to confirm. Bayan Mayraah ta idar da sallan Magrib a dakin hotel din da take ta bude jakarta ta ciro wayarta tana jujjuyawa, ciro sim dinta duk biyun tayi, ta mike ta zubar da su a karamin dust bin dake dakin sannan ta saka hijab dinta ta dau Atm card dinta ta fito daga dakinta ta sauka kasan reception, bayan sun gaisa da ma'aikatan hotel din dake zaune reception din ta fita, tsaye tayi bakin titi tana jiran adaidaita sahu, har ta samu tace "Don Allah Malam nearest supermarket nake son ka kai ni" Mutumin yace "I no dey hear hausa madam" Turanci tayi masa ta gaya masa inda zata je, yace ta shiga, tana shiga bayan tafiya me nisa ya tsaya dai dai wani babban shopping Mall ta sauka ta ciro kudinsa ta basa sannan ta shiga ciki. Bangaren mayukam shafawa ta nufa don bata dau cream dinta ba a gida, ta dau cream din da shower gel ta koma side din turarruka tana zaba kamar ance ta juya...... [7/17, 6:50 PM] Khaleesat Haiydar💖: Da sauri Mayraah ta dauke kanta kafin ya kalli direction din da take tsaye ta bar wajen ta koma wani section din mall din gabanta na faduwa tana zare ido, wani lecturer dinta ne Dr Nasir which is a very good frnd of Musharraf don su biyu kadai ne young Dr's din department din nasu as at then, farko da Musharraf ya fara sonta yayi discussing hakan da Dr Nasir din ne, yawanci sai Dr Nasir ya kira ta office din sa as if zai yi mata tambaya ko kuma ya ce zai tura mata Pdf na handout in kuma taje office din tare zata gansa da Musharraf da baya ce mata komai a lokacin, nan kuma shi yake sa Dr Nasir din ya kirata office din kawai don ya ganta, that was 2 years back don tuni Dr Nasir ya bar department din nasu yana Uni Abuja yanzu, Mayraah duk ta rikice ta fara tunanin yanda zata bi ta maida kayan da ta zuba a karamin shopping cart dake hannunta don tana tsoron kar ace taje wajen biya su hadu da shi a can, da ta sani da ta fito da nose mask, cikin dubara ta ɗan sake leka section din da Dr Nasir din yake taga yana tahowa, da mugun sauri ta juya zata bar wajen ta ci karo da wata mata rungume da babynta, zaro ido Mayraah tayi tana kallonta ganin alamar bahaushiya ce matar tace "Don Allah kiyi hakuri...." Matar tayi mata murmushi tace "Ba komai" Ko rufe baki matar bata gama yi ba Mayraah taga Dr Khalil bayan matar rike da wata babyn mai kama da warce matar ta rike alamar dai yan biyu ne, Dr Khalil ya ɗan buda ido alamar yana son tuna sunanta yace "How are you" Matar ta juya ta kallesa, ita dai Mayraah duk a rikice take kar Dr Nasir ya zagayo ya ganta, kamar mara gaskiya tace "Ina yini" Dr Khalil yace "Lafiya lau ya jikin, hope kin ji sauki gaba daya yanzu?" Mayraah tayi saurin gyada masa kai, Dr Khalil ya kalli matarsa yace "Patient dita ce, dazu muka sallameta a asibiti" Matar na kallon Mayraah tace "Allah sarki, Allah ya kara lafiya" Mayraah na murmushin karfin hali tace "Ameen Nagode" Dr Khalil ya lura da how tensed Mayraah is don ta kasa tsaye waje daya kamar mara gaskiya, matarsa na kallon Mayraah tace "To sai anjima" Mayraah ta gyada mata kai da sauri ta bar wajen, Dr Khalil suka wuce tare da matar sa, wani ajiyar zuciya Mayraah ta sauke batan ta hango Dr Nasir can bakin entrance din mall din zai fita da sauri yana waya kuma babu komai hannunsa alamar kilan ya fasa siyayyan, har dai taga fitar sa, gaba daya sai ta dawo uncomfortable a mall din don gani take kamar zata sake haduwa da wani wanda ta sani, da kamar ta fasa siyayyan kawai ta koma hotel dinta sai kuma ta tuna ba fa ta da mai da zata shafa gobe, kuma har pad tana son siya with few junk food don ba ko da yaushe take jin cin abinci ba, kamar mara gaskiya haka ta dinga shopping din nata being very cautious, duk inda kuma taga alamar za su hadu da Dr khalil da matarsa sai tayi maza ta canza route dinta har dai ta gama picking few things da take bukata sannan ta nufi counter inda zata biya, tana hango Dr Khalil da wife dinsa tsaye wajen su ma sun gama siyayya sai taki biyan kudin kayan nata a nan, ta koma next counter din, Dr Khalil na gama biyan kudin abubuwan da suka siya, dai dai sanda aka zo kan Mayraah dake daya side din, tana kokarin bude handbag dinta ta ciro Atm card dinta ya mika ma mutumin Atm card dinsa da turanci ya ce masa ya cire kudin, Mayraah ta daga kai ta kallesa da sauri tace "Aa Dr kar ka damu, i will pay" Dr Khalil yace "Ai na riga ma basa card din...." Mayraah ta kalli matarsa dake kallonta, hakan yasa matar ta sakar mata murmushin karfin hali, Mayraah ta mayar mata da murmushin tace "To Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Tuni aka yi ma Mayraah packaging few abubuwan da ta siya ta amshi ledan, matar kadai tayi ma sallama ta fita daga mall din don su kayansu da yawa ba a gama masu packaging ba, Zainab ta kalli mijin nata tace "Kai kowa dai patient dinka ne Dr" Yayi murmushi yace "Amma kamar patient yan matan sun fi tsaya maki ko...." Tace "Not at all nasan halin ka ai, and i trust u" Yace "Double that trust girlfriend" Tayi murmushi tana kara rungume daughter dinta dake bacci. Washegari karfe goma saura Mayraah ta fito daga hotel room dinta bayan sun gaisa da ma'aikatan wajen ta fita ta tari adaidaita sahu tace masa tasha zai kai ta, ya tambayeta wani tashar, nan ta hau kalle kalle don bata san ma sunan tashar da aka sauketa shekaranjiya ba, can dai ta shiga tana kallonsa tace "Kai ni ko wanne" a traffic ta siya nose mask ta saka don bata son taking risk yau, luckily kuwa mai adaidaitan ya kai ta tashar da aka sauketa Shekaranjiya, ta sauka ta basa kudinsa sannan ta karasa shagon mai pos din ranan, yana ganinta ya gane ta, bayan sun gaisa yace "Har ina tunanin kilan kin samu gidan ne da na ji ki shiru" Mayraah ta ɗan yi murmushi ta zauna kan kujera tace "Aa ban samu ba, jiya ban ji dadi bane shi yasa baka gan ni ba" Yace "Allah sarki, Allah ya sauwake" Tace "Ameen, ka duba min gidan kuwa don Allah?" Yace "Kwarai kuwa an bincika har an samu biyu, duk wanda yayi maki a ciki shi za ki zaba" Tace "To ba damuwa, kuma nawa ne sai in tura kudin?" Yace "Toh Hajiya yanzu dai kowa yasan yanda duniya ya dawo babu gaskiya, daga haduwa da ni ba haka nan zaki yarda dani har ki bani dukiyarki ba duk da dai kowa yasan nan ne wajen neman abinci na, amma abinda ya kamata yanzu kawai zuwa can sulejan za mu yi tare da ke, bayan kin duba gidan kin ga wanda yayi maki sai ki bada kudin a baki makullin gidan" Mayraah tace "Aa ni kam ba sai naje ba, kar ka damu kawai a zabar min duk wanda aka ga yafi, but pls ya kasance da ruwa kuma da wuta a anguwan" Yace "Ai kar ki ji komai Hajiya ni ma bazan kai ki anguwan da zaki jigata ba don naga baki yi kalar wahala ba, wuta har sai kin gaji da shi, sannan babu matsalar ruwa gida me borehole aka duba maki" Mayraah tace "Toh nawa kudin hayan?" Yace "Toh amma ke irin gida me part part na haya kike so, ko kuma karamin self contain wanda ke kadai zaki zauna ciki?" Mayraah tace "Eh ni kadai nake so, bana son me mutane" Mutumin yace "Toh me daki daya suna bada shi akan naira dubu dari biyu da hamsin har agreement, in kuma daki biyu kike so har dari uku da hamsin ana bayar wa, dari hudu dai a takaice in da agreement, tsakar gidan ma zaki gansa ba lefi mota daya zata shiga ta zauna lafiya lau" a hankali Mayraah tace "To duk wanda dai aka samu ba damuwa" Yace "Amma fa gaskiya me daki biyun nan deal ne Hajiya, in dai da kudin kawai ki rufe ido ki amshe sa don anguwa ce me kyau akwai kuma jama'a kintsatsu ba laifi" Mayraah tace "To shikenan, a ina za a tura kudin" Yace "Ki saka a account dina don cash zan kai masu kar a zo ana dogon zance" Mika masa Atm card dinta tayi, don kudin ciki zai kusa 1.3 tunda babu abinda take da kudi ko Abba ya tura mata sai dai yayi ta zama a account din tunda su Maheer duk wani abun bukatarta su suke siyo mata, ya amshi Atm card din hannunta ta gaya masa pin tana kallonsa tace "Ka cire dubu dari hudu da talatin, sai ka rike dubu talatin din Nagode sosai" Godiya sosai mutumin yayi mata yace "Don dai kin ki ne Hajiya da akan idonki za ayi komai na gidan, har kudin in basu a gabanki" Tayi murmushi tace "Kar ka damu, don Allah ina zan samu sim card in siya?" Yace "Ai ina siyarwa" Ta ɗan yi shiru don tasan su suke ma layin register da kansu, can dai tace "Toh bani daya" bayan ya cire kudin ya mayar mata da Atm card dinga sannan ya dauko sabon layi ya mika mata ta amsa tace "Nawa ne?" Yace "Aa ki bar sa, ai ba tsada" tace "Toh nagode, sannan don Allah a can garin ana samun gado ko da ba babba ba?" Yace "Gado? Ko dai katifa irin ta yan makaranta?" Ta gyada kai tace "Shi" yace "Gaskiya can zai yi tsada, kyau a siya daga nan a kai can din kawai" Mayraah tace "Toh, zan tafi yanzu, ka bani numberka anjima idan na saka layin zan kira ka inji yanda ake ciki" Yace "Toh Hajiya" Ya rubuta mata number ta amsa sannan tayi masa sallama ta bar shagon, sai da ta fara biyawa wani karamin eatry ta siya snack sannan ta koma hotel din da take. Mayraah na gama cin meatpie din ta dau magungunanta ta tasha sannan ta kwanta tayi bacci. Bata tashi ba sai can kusan yamma, dauko wayarta tayi ta saka sabon sim card din taga layin ya hau, sai dab da magrib ta kira me pos din, bayan sun gaisa yace mata an biya kudin gidan, tace "To shikenan nagode" Yace "Ko gobe kika ce zaki tare in dai da abubuwan da zaki zuba a gidan ba matsala don sabon waje ne ba wani kwaskwarima da za ayi masa" Mayraah tace "Toh ba damuwa, goben zan zo in sha Allah" yace "To Allah ya kai mu" Maheer na zaune parlon Ammi da ya siyo ma abinci bayan magrib yana jiran yaga ta fara ci, har da magunguna ya kawo mata don dazu da safe tace masa bata jin dadi, a maganin ya hado mata har da na cin abinci da kuma wanda zai sa ta dinga samun isasshen bacci don kana ganinta kasan bata bacci, ga wani rama da tayi tun ma tana gidan Hajja, ganin har an kira isha Ammi bata da alamar fara cin abincin gabanta yayi kasa da murya yace "Ammi ki ci ko kadan ne ki sha magani pls, nasan fa tun safe babu wani abu da kika ci" Ammi ta kallesa cikin sanyin murya tace "Amma Maheer ina kake tunanin Mayraah zata har kwana uku yau, ba fa wanda ta sani Maheer, ba kuma inda ta sani, ko dai gidan radio da social media za a bada cigiyarta?" Maheer ya sauke boyayyen ajiyar zuciya ya kwantar da murya yace "Duk inda ma take tana cikin koshin lafiya in sha Allah Ammi, kuma addu'a kawai za mu ci gaba da yi har Allah ya karkato da hankalinta ta dawo gida, babu abinda zai sameta da izinin Allah, Mayraah ba ɓata tayi ba balle mu yi cigiyarta she just decided to leave, yanzu ko anyi cigiyar ma kamar muna kara tona ma kan mu asiri ne, ya mace ce ita ana saka cigiyar kowa da perspective din da zai kalli abun, gwara kawai mu ci gaba da addu'a kawai Ammi" Ammi ta share hawayen da ya sakko idonta bata ce masa komai ba, bude kofar parlon aka yi Mama Ladi ta shigo da plate cike da taliya da cup din shayi a hannun ta, Maheer ya daga kai ya kalleta yana nuna mata nata abincin da ya siya mata yace "Baza ki ci wannan din ba Mama?" Mama Ladi tace "Inji wa?? Ai sai can cikin dare idan na farka in sha Allah, taliya ce leda daya na dafa don tun da na sauka wallahi ban samu na ci komai ba, sai wani gantalallen biredi da ruwan shayi da na samu a kitchen Usuman ya bari" Daga haka ta zauna ta fara cin taliyar, Maheer ya ji dadin dawowan Mama Ladi don gidan babu kowa sai Ammi sai Usman da yake kwana gidan shi ma saboda Ammin, amma da safe kuma yake fita aiki, har Maheer ya fara deciding kiran Mama Ladin sai ga ta kamar an jefota dazu da rana lokacin ya dawo duba Ammi.... Maheer yayi nisa tunanin da yake sai kawai ganin Mama Ladi yayi a gabansa tayi kasa da murya tace "Ka sameni a palo Mashir" Maheer ya bi ta da kallo sannan ya kalli Ammi da har sannan taki cin abincin gabanta, ya mike ya bi bayan Mama Ladi suka sauka downstairs, kujera Mama Ladi ta nuna masa tace "Zauna ina zuwa" Ya zauna ya ga ta nufi kitchen sai ga ta ta fito da abun kwasan shara ta ajiye masa tana kallonsa, da mamaki yace "Wannan fa?" Mama Ladi ta wani kyabe baki tana murmushi tace "To a karkashin gadon uwarka na gani an makala sa yana ta reto, kasan ina sauka dazu ko zaunawa ban yi ba na fara kwaleman dakin duk na kwalkwale ko ina, to dai ga tsiyar da na gani karkashin gadon Ammi tana ta rayuwa kai in gaya maka Mashir, ni dai da naga duk a birkice take damuwa ya mata yawa ko nuna mata abun ban yi ba ma har yanzu, kuma wallahi dama ance surkarta ta ajiye asiri a dakinta...." Maheer dake ta kallonta ya katseta yace "Wa yace haka?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Gun bawan Allahn da naje neman taimako mana, kai baka ga abubuwan dake ta faruwa babu kan gado ba, ai mutum bai ga ta zama ba Mashir, har auren nan da Ubanka yayi wallahi an gaya min...." Maheer ya girgiza kai yace "Wajen boka kenan kike zuwa" Mama Ladi ta zauna kan kujera a gigice tace "Auzubillahi, don Allah ka rufa min asiri kar ka sa ni a bakin duniya Mashir, wani irin boka kuma? Ashe haka kake ban sani ba?" Maheer yace "Yanzu ke har yanzu baki hakura da zuwa gun mutanen nan da ke cinye maki kudi suna maki karya ba Mama? babu fa wanda ya isa ya maka abu sai Allahn da ya halicceka, in mutum ya sa wannan a rai to babu ta yanda za ayi masa mugun abu, ke kawai baki da aiki sai zuwa gun makaryatan banza marasu tsoron Allah" Mama Ladi ta saki baki tana kallonsa, a fusace tace "Kar ka sake gaya min maganar banza Mashir, kai wawa ne baka san komai ba baka san me duniya ke ciki ba, kuma laifina ne don wannan zancen ma ba da kai ya kamata in yi ba don kai ba sa'ar magana ta bace, tsinanniyar matar nan taka dai ita ta saka wannan mugun abu a dakin Ammi, shi yasa duk abubuwa suka cakude haka" Maheer ya kai hannu zai dau layan ta janye parkern da sauri tace "Rufa mana asiri, ni nasan inda zan kai sa, ni kaina bazan bari hannuna ya taɓa ba" Can dai yace "To meye manufar layan da aka sa kasan gadon kenan?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "A rabata da Mera ta tsaneta taji bata sonta kwata kwata, sannan kuma a tarwatsa mata gidanta ta dawo bora, kaga kuma yanzu tsakani da Allah wanne ne bai faru ba? Rabata da Meran ko tarwatsa gidan? Wai ma ina Mamuda don na tambayi Ammin tace min bata sani ba dazu" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ya koma can wani gidan da ya gina da matar" Mama Ladi ta gwalo ido ta daura hannu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wani gidan da ya gina? Amma ga dukkan alama matar ma matsiyaciya ce shaidaniya, zuwa kawai tayi ta mallakesa ta rabasa da Ammin, kai shegu dai sun yi yawa wallahi a duniya, yanzu ka gaya ma Ammin suna wani gida da katuwar matar?" a hankali yace "Ban gaya mata ba" a hankali Mama Ladi tace "To ka ja bakinka kayi shiru kar hankalinta ya sake tashi don naga ɓatan Mera ya gigitata gaskiya, kar ka kuskura ka gaya mata" Wayarta ta kunce a ɗan kyalle da ta cusa cikin hulan kanta ta mika masa tace "Kira min Mamudan" Maheer ya dinga kallonta, a fusace tace "Kira min shi mana" Amsan wayar yayi, yayi mata dialing number Abba sannan ya mika mata, ta amsa ta kai kunne, yana fara ring Abba ya daga, da karfi tace "Mama Ladi ce Mamuda..." Gaisheta Abba yayi, tace "Don Allah ina son ganinka yau na shigo garin" Yace "Toh sannu da zuwa Mama, zuwa gobe kenan idan Allah ya kai mu" Mama Ladi ta girgiza kai da sauri tace "Wani gobe? A yau nake son ganin ka Mamuda" Yace "Toh zan sa Maheer ya kawo ki inda nake" Mama Ladi tace "O'o ba ruwana gaskiya kawai ka shigo mota ka taho ina nan gidanka yanzu haka gani ni kadai zaune a parlor ba kowa" Abba ya dan yi shiru, sai kuma yace "To gani nan zuwa" tace "Yauwa ina jiranka" Daga haka ta katse wayar tana kallon Maheer tace "Ai kaga ni ba er banza bace da zan je in samesa a wani sabon gida bayan yayi watsin ruwan tsarki da 'ya ta" Shi dai Maheer bai ce komai ba. Maheer na barin gidan da minti arba'in Abba ya shigo wajen karfe tara da rabi kenan, Har sannan Mama Ladi na zaune parlon tana jiransa bayan ta gama cin abincin da Maheer ya kawo mata daxu, Abba na shigowa ya gaisheta da ladabi sannan ya zauna kan kujera yace "Ya hanya Mama?" A hankali Mama Ladi tace "Kai yanzu Mamuda so kake ranan gobe kiyama ka tashi da shanyayyen ɓarin jiki? So kake duk mu tafi aljanna kai kana wuta? Auren da har yanzu bamu gama na'am da shi ba a zuciyarmu shine har ka fara rashin adalci a cikinsa Mamuda? Ita Ammin ka gama cin moriyarta ta zama bola kenan yanzu kake nufi?" Sai kuma ta fashe da kuka tace "Ko me Ammi zata maka a duniya bata cancanci walakanci daga gareka ba Mamuda, balle baiwar Allahn bata taɓa maka komai ba sai biyayya da girmamaka tun kana talakan ka, sai yanzu don kaga ka rasa yanda zaka yi da kudi sai ka canza hali ka kasa hakuri da ɗan kuskuren da ta maka? Ko ka mance ɗan adam ajizi ne? Ammi ta taɓa maka wani gagarumin laifi duk zaman ku tare tsakaninka da Allah?" Abba yace "Yanzu tace maki na mata wani abu ne Mama?" A fusace Mama Ladi tace "Kayi mata mana, sai ta fada sannan za a san ka mata? don me za ka dau bazawarar da ka aura sama ta ka, ka kai ta sabon gida ku tare a can Ita kuma ku bar ta a nan?" Abba yace "Ai ni ban san tana gidan nan ba ma" Mama Ladi tace "Kai dai kaji tsoron Allah kaji tsoron kamun Allah Mamuda, wallahi kaji tsoron Allah ina gaya maka" Abba yace "Yanzu tun da nasan tana gidan duk ranan kwananta zan shigo gidan in kwana a bangarena" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Haba Mamuda, don Allah kayi hakuri.... wallahi ni kaina nasan Ammi tayi kuskure nasan bata kyauta ba amma duk sharrin shaidan ne, kai shaida ne mutuniyar kirki ce Ammi, babu sa wa babu hanawa, kar ka yi mata mummunan hukunci saboda wnn ɗan kadɗarar ya fada mata, wallahi kaddararta ce wannan, amma kai kanka kasan duk bamu fi ta son Mera ba, kayi hakuri ka dubi halin da take ciki ka ja ta jiki ka maida komai ba komai ba har Allah ya dawo mana da gantalalliyar yarinyar nan da ta tafi inda bamu sani ba dama kuma ta saba shiga duniya da er matsala ta faru, Wallahi Ammi na cikin mawuyancin hali yanzu a kan batar yarinyar nan, da wanne kake so ta ji, ga kishiya ka dankara mata Mamuda?" Abba dai yayi shiru bai ce komai ba, Cikin lallami Mama Ladi tace "Nasan ka da hakuri da kauda kai Mamuda, kayi hakuri yanzu ka tafi sama ka duba halin da take ciki sai ka ga ta samu nutsuwa a ranta, babu bawan da ke wuce kaddararsa wllhi, babu tsimi fa babu dubara sai wannan abu ya faru Mamuda" Abba yace "Shikenan Mama, zan duba ta" Mama Ladi tace "Yauwa ko kai fa ɗan albarka, ai haka ake son babba ya gaya ma yaro magana ya ji, ni wallahi ka gama min komai wannan mutunta ni da kake yi" Mama Ladi tace "Yanzu sai ka tashi ka tafi sama ka dubata, ni kuma zan je kitchen in nemi abinda zan ci kar yunwa ta kasheni" Mikewa Abba yayi ya wuce sama zuwa bangaren Ammi. [7/17, 10:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Washegari da safe Mayraah ta sake komawa gun me pos din a tasha, kamar jiya ma yau Nose mask ta saka don gaba daya a tsorace take da Abujan gani take kawai zata yi jamming wanda ta sani, wajen karfe goma da rabi ta isa shagon nasa, bayan sun gaisa yace "To yanzu zan bar yaron shagona ya jire min shagon sai mu kama hanyar sulejan ki ga gidan Hajiya...." Mayraah tace "Toh shikenan, nagode" Mayraah bata yi tunanin haka Sulejan ke da tafiya daga cikin Abuja ba, don har bayan minti arba'in bata ga sun isa ba, though is not as if she cares about the distance tunda babu abinda ma zata dinga shigowa garin Abujan tayi, at last dai suka iso garin Suleja ya tare masu adaidaita sahu suka tafi anguwan da yace mata gidan yake, anguwar dai ba laifi amma duk yawancin gidajen unguwan na average class ne har ma da lower class, suna isa gidan da aka kama mata bayan ya shiga da ita ko ina tare da wani agent sun nuna mata suka fito compound din gidan yace "Toh ya kika ga gidan ya maki kuwa Hajiya?" Mayraah da bata da choice kawai tace "Eh yayi" Agent din ya bata makullin gidan da reciept din payment ta saka a handbag dinta, bayan ya tafi Mutumin da ya kawota yace "Kin ga ai anguwan bata da hayaniya ko? Ga shi kuma a cike yake da jama'a" Mayraah tace "Haka ne, yayi kam" Yace "Kuma gidan kin ga sabo ne dal bai da matsala" Mayraah tace "Eh duk na gani, amma kasan abinda zai faru? Don Allah idan baza ka damu ba ina son in baka list din wasu abubuwa ka taimaka min ko a kasuwan garin nan ne ka siyo min, gobe nake son zan dawo gidan gaba daya" Yace "Toh babu matsala kamar me da me kenan kike bukata" Nan Mayraah ta zayyane masa duk abubuwan da zai siyo mata a kasuwa na bukatar gida har da kayan abinci, ta mika masa Atm card dinta yace "Aa Hajiya, da dai kawai ki min transfer" Tace "Kar ka damu, bana iya transfer ne shi yasa" Yace "Toh amma fa mantuwa gareni, kyau kawai muje kasuwan tare Hajiya" Ta ɗan yi shiru tana nazari, sai kuma tace "Toh shkkn mu tafi" Tricycle suka samu zuwa kasuwan. kafin yamma Mayraah ta siyi duk wasu abubuwan da tasan zata bukata a gidan tare da mutumin da yace mata sunansa Aminu, har gas da few kitchen utensils sai da ta siya, da labule da aka dinka masu sharp sharp a kasuwar suka siya da karafen labulen, wajen karfe biyar da rabi tana kallon Aminu bayan ya gama saka mata labulen karshe tace "Gaskiya Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen Hajiya, amma yanzu abinda zai faru ya kamata ki ɗan shiga makotanki ku gaisa su sanki ki ce masu ke daliba ce, yau kika dawo unguwan, kinsan yanzu yan sa ido sun yi yawa a duniyar kar su yi zaton ko zaman kanki kike a nan bayan basu san karatu ya kawo ki garin ba" Mayraah dai tayi shiru tana kallonsa, a hankali tace "Haka ne, zan shiga in sha Allah amma sai gobe idan na dawo nan din gaba daya, yanzu na gaji ina son mu koma Abuja ne in hutu sannan in harhada kayana na can" Yace "To ba laifi Hajiya, in dai da wani abu da kike bukata ko na aike koma na menene kawai ki buga wayata, in kin dawo nan din gaba daya har iyayena zan hada ki da su da matana duk da dai gaskiya anguwansu da nisa daga wannan anguwan, sai a dinga zumunci" Mayraah na murmushi tace "Toh shkkn, in na dawo din duk sanda kake da lokaci ko kuma in ka shigo garin sai ka hadani da su" Yace "In sha Allahu kuwa, Allah kuma ya baki sa'an abinda kika zo nema" A hankali Mayraah tace "Ameen nagode" Sai kusan shidda da wani abu suka shiga garin Abuja, Mayraah tayi tayi da shi ya tsaya ta ciri kudi a wajen wani me pos ta basa yace mata wllhi wanda ta basa ma ya isa saboda Allah yayi mata, taji dadin hakan har ranta, she really appreciate him, ta samu adaidaita sahu da ya maida ta hotel don duk ta gaji. The next day Mayraah tayi check out daga hotel din ko kwanakin da aka biya mata bai cika ba ta koma sulejan wajen karfe sha daya na safe, zaunawa tayi a gefen gadon dakin tana bin ko ina da kallo, tun barin ta gida sai yau kawai taji tunanin yayyinta ya cika zuciyarta, ita kanta tasan tana kewansu, this made her feel so down tun safe take jin ranta babu dadi, lokaci daya ta ba kanta courage ta shiga kitchen ta dafa Indomie wanda har ta mance rabon da ta ci Indomie, kamar yanda Aminu yace mata gidan kam da wuta don har suka gama abubuwan da suke yi jiya ba a dauke wuta ba yanzu ma gashi da ta zo ta tarar da wuta, ta jona wayarta a caji sannan ta saka hijab ta fito zata yi yanda Aminu yace mata, karamin gidan dake gefen nata ta fara kwankwasa gate din aka bude, matar gidan na kallonta daga sama har kasa tace "Sannu da zuwa" Mayraah tace "Ina kwana" Matar ta amsa still tana kallonta irin ban sanki din nan ba, Mayraah tace "Ni neigbor dinki ce, jiya na dawo wancan gidan..." ta fadi haka tana nuna gidan, Matar tace "Ayya, Allah sarki, bismillah sannu da zuwa baiwar Allah, ai ko naji yan anguwa sun ce an tare a gidan ni dai ban ga kowa ba, ashe kuwa da gaske ne" Mayraah dai ta bi ta har cikin gidan ta zauna kan kujera a karamin parlon ta kara gaisheta, matar ta amsa da fara'a tace "Sannu da zuwa anguwanmu, ya sunanki?" Mayraah bata san sanda tace "Ilham, sunana Ilham.... ni daliba ce ina karatu ne cikin garin Abuja, shine aka samar min daki a nan in zauna" Matar tace "Allah sarki, toh Allah ya baki sa'a Ilham, ai ko zaki ji dadin zama cikinmu wallahi duk bamu da matsala, ni ana ce min Maman Hanan, yanzu zan zaga dake duk sauran gidajen a san juna" daga haka ta mike tace "Bari in dauko maki ruwa ki sha sai mu tafi" Mayraah dai sai kallon yarinyar dake kwance da bazata wuce shekara 8 ba tana numfashi ta baki take, har matar ta dawo Mayraah ta kalleta tace "Bata da lafiya ne yarinyar can?" Matar ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi Hanan ba lafiya yau kusan sati daya ko makaranta bata zuwa, tun dazu ma nake ta goge mata jiki da ruwan sanyi don naji zafin yau na daban ne da sauran ranaku, gashi zazzabin baya sauka wallahi" Da mamaki Mayraah tace "Kuma ba a kai ta asibiti ba har yanzu Aunty?" Maman Hanan tace "Baban magunguna ya siyo mata a chemist ake ta bata, wanda ya fara siyowa har sun kare ya sake siyo wasu" Mayraah couldn't stop looking at the woman with surprise, a ranta tana mamakin me yasa wasu iyayen ke irin wannan sakacin ace yaro bai da lafiya critically amma sai a wani je chemist a siyo masa magani, mikewa tayi ta tafi kusa da Hanan din ta durkusa tana kallonta don ko rufe baki bata iya yi kamar warce mura yayi ma mummunan kamu, and she is breathing noisily, Mayraah ta bude bakinta tana duba ciki, lokaci daya ta mike tana kallon Maman Hanan tace "Ya kamata a tafi da ita asibiti yanzu Aunty" Da damuwa Maman Hanan tace "Ko?" Mayraah tace "Gaskiya, a nemo adaidaita sahu a tafi asibitin kar a bata lokaci" Wani irin numfashi Hanan din ta fara yi, Maman Hanan ta maza ta dauketa tana jijjigata tace "Haka fa take yi tun dazu sai numfashin yayi kamar zai dauke wllh sai ya dawo, bari in kira baban nasu" Mayraah tace "Mu je kawai asibitin idan mun je can sai ki kirasa" A tare suka fita gidan, Maman Hanan duk ta gigice ko kulle gidan bata yi ba suka nufi titi, Mayraah dai bata karbi yarinyar a hannunta ba, a haka suka samu adaidaita sahu, wani Asibiti nesa da Sulejan Maman Hanan ta sa mai adaidaita sahun ya kai su, duk tunanin Mayraah zata ga babban asibiti saboda taga wajen da ɗan tafiya daga suleja, kawai taga clinic, though ba laifi kamar clinic din sananne ne don taga patients da yawa amma bata tunanin the clinic is well equipped suna isa entrance din clinic din basu fara karo da kowa ba sai Dr Khalil yana kokarin fitowa rike da makullin Motarsa, kallon mamaki yake ma Mayraah kamar yanda ita ma take kallonsa da mamaki, Maman Hanan ta saki ihu don taga kamar numfashin er yayi sama bai sake dawowa ba, Dr Khalil ya saka makullin motarsa a aljihu da sauri ya amshi Hanan din a hannunta ganin condition din da ta shiga ya juya ya koma cikin asibitin sauran nurses suka nufosa, Mayraah ta bi bayansa da sauri har ta isa dai dai wajensa tayi kasa da murya tace "I think it's Diphtheria, symptoms din ne..." Da sauri ya juya ya kalleta, ya kalli yarinyar hannunsa, amma saboda babu lokacin batawa kawai ya shiga da ita emergency dake reception wani likita da ya fito office ya bi bayansa da sauri, Mayraah ta koma gefe ta tsaya Maman Hanan kuwa sai kururuwa take a reception din nurses na bata hakuri, Dr Khalil na shiga emergency din kawai abinda Mayraah ta fada yasa hankalinsa bai kwanta ba ya saka safar hannu, da few protections sannan ya fara gwaje gwaje, nan ya tabbatar da abinda Mayraah ta fada haka ne, Likitan da ya shigo wanda shine me asibitin shi ma ya koma baya closing his nose with nose mask ya buda ido sosai yace "Diphtheria, wannan sai dai a tafi da ita Abuja Dr.... Babu facilities a nan" Dr Khalil bai cire protective gown din jikinsa ba ya dau yarinyar ya fita daga emergency din, kawai ya nufi motarsa Maman Hanan ta bi sa a guje tana cewa "Ina za a kai ta Dr?" Ya kalli Mayraah dake tsaye ta kasa cewa komai yace "Ki taho da ita asibiti can Abuja" Daga haka ya shiga motar da likitan suka zuwa cikin Abuja, Mayraah har gajiya tayi da lallashin Maman Hanan a hanya har suka karasa Abuja, bata mance sunan asibitin ba wanda is so popular duk da asibitin masu kudi ne, suka hau adaidaita sahu ya kai su har asibitin, Sun fi minti ashirin zaune a katon reception din hospital din, bakaken fata da fararen fata sai kai koma suke a reception din, everywhere is just so organized kamar a kasar waje, suna kuma da lokacin zuwa duba mara lafiya ba anyhow ake shigowa ba, Mayraah ta kalli Maman Hanan for the countless time tace "Maman Hanan kiyi hakuri da kukan nan addu'a kawai za kiyi mata, in sha Allah zata samu lafiya kin ga nan babban asibiti ne" tausayinta kawai Mayraah take don ta san ko da an kwantar da Hanan to ko ita baza a bari ta zauna da ita ba sbda infection din is contagious, don su inda ake kwantar da masu cutar ma daban ne ba kowa ke shiga ba sae ma'aikatan asibitin, After another 20 minutes wata nurse sanye da cute uniform dinta ta nufosu tana kallon Mayraah da turanci tace likita na bukatarta a office, Mayraah ta mike tana kallon nurse din ita ma da turanci ta tambayeta ina office din, Nurse din tace "First floor, office number 1, Dr Khalil" Mayraah tace "Ohk" Maman Hanan ta mike da sauri cikin rawan murya tace "Tare za mu je?" Mayraah tace "Aa ki jira yanzun nan zan fito ai" Daga haka ta wuce sama ta isa har office number din da nurse din tace mata tayi knocking, sai da aka mata izini ta shiga, the office was large and organized, ko ina fes fes ga Ac a kunne, yana zaune kan office chair dinsa ya canza kaya alamar har yayi freshen up, ta karasa har front din table din ta zauna tana kallonsa tace "Dr ya jikinta?" Ya kalleta yace "Ina mance sunanki, pls remind me" A takaice Mayraah tace "Ilham" Yace "Ilham, how did u know it's Diphtheria?" Ta ɗan buda ido thinking of what to say sai kuma da sauri tace "Na taɓa koyon aiki a wani karamin asibiti" Yace "Really, kina da experience kenan in haka ne" Ta ɗan yi murmushin karfin hali bata ce komai ba, yace "Kin samu hostel din?" A hankali tace "Aa ina wajen aunt dina a suleja" Yace "What about ur parent" Tayi shiru tana kallon sa, kawai ta samu kanta da cewa "They are late" Ya ɗan sauke kansa sai kuma yace "Allah ya ji kansu" Tace "Ameen" Yace "But idan baki samu hostel ba ai akwai off campus da zaki samu cikin gari, isn't suleja too far for you? Yayi nisa fa zuwa school din" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yayi shiru da ya tuna ba fa kowa ake haifa da silver spoon ba barin ita da tace iyayenta sun mutu, probably bazata iya affording off campus ba, can yace "Wani course aka baki admission yanzu?" Mayraah ta rasa ma me zata ce masa, can dai "Microbiology" Ya gyada kai yace "That's good, i guess ur Aunty isn't financially stable ko?" Nan ma kawai tayi murmushi, ya sauke ɗan ajiyar zuciya yace "Mu kinga nan ba a daukan health workers sai da Qualified medical certification, infact ba mu da vacancy ma yanzu haka, we are dealing with just qualified medical staffs don wasu daga likitocin mu ma turawa ne da indians, so i will see if it will be possible in san yanda zan yi inyi attaching dinki ko during weekend ne as an auxiliary Nurse don ki samu ki dinga fending for ur self kar ki sakar ma mutane burden dinki su gaji da wuri" Mayraah kallonsa kawai take da mamaki and she couldn't believe her ears, aiki a babban asibitin nan?? can tace "Zan ji dadi idan ka min haka" Yace "But fa dole sai ta bayan gida zan yi maki wannan abun don we have strict orders a asibitin nan...." Mayraah tayi shiru tana kallonsa, Calmly yace "Kar ki damu, i will try my best zaki fara aiki a nan in sha Allah" Cikin sanyin murya tace "Toh Allah ya sa, but i am sorry about that admission da nace na samu da naje makarantar ba haka bane" Yace "I don't get you" Ta sunkuyar da kai tace "An ban admission din da dadewa ne, sai yanzu muka tara kudin makarantar ban san ashe ba a haka ba, da naje makarantar shine suka ce anyi cancelling admission din long ago" Yace "Subhanallah" Daga haka bai sake cewa komai ba, ita dai kallonsa kawai take, yayi kasa da murya yace "Kar ki damu Ilham, zaki fara aiki a nan, and the salary is good sai kiyi ta saving ki sake sabon jamb ki nemi wani admission din" Ta ɗan yi murmushi tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" Yace "Ameen" Da sauri tace "Plss ya jikin yarinyar??" A hankali yace "She is late already, before we could do anything" Mayraah da gabanta ya fadi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Yace "Ya ku ke da matar?" Nan da nan hawaye ya kawo idon Mayraah tace "Neigbor dinmu ce a Suleja" Yace "Sai hakuri, yarinyar ta rasu" Ta masa wani kallo tace "Shine tun dazu baka gaya min ba??" Mikewa tayi tana share idonta ta nufi kofa yace "Wait Ilham" Ta juya ta kallesa yace "Ce mata za kiyi nace ta bada number baban yarinyar ita kuma ku tafi gida a kawo ma yarinyar abinci, so i will communicate with the father, bama son ta hada mana commotion a nan" Cikin sanyin murya Mayraah tace "Sai dai nurses din su gaya mata ni bazan iya ba" Ya dau waya yace "I will tell dem now" Kiran nurses din yayi downstairs, Mayraah kuma ta fita a sanyaye. [7/18, 8:04 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na tsaye gefe wata Nurse tayi ma Maman Hanan bayanin da Dr Khalil yayi mata a waya na cewar ta bada number mai gidanta sannan ta koma gida ta dauko ma Hanan kayan sa wa, ko minti daya Maman Hanan bata kara asibitin ba bayan ta bada number mijinta bata bi ta kan Mayraah ba ta fita da sauri zata koma gida, Mayraah dai ta bi ta da kallo ciki da tausayinta, tana tafiya a hankali ta nufi kofar fita reception din ita ma, Dr Khalil ya sauko downstairs kenan ganin Mayraah zata fita ya bi bayanta har suka fito haraban asibitin yace "Na kira mijin nata suna hanya yanzu haka..." Mayraah ta gyada kai tace "Toh, Allah ya ji kanta, Allah ya basu hakurin rashi" Yace "Ameen, haka yawanci wasu mutanen suke sai yaro ya jigata ake kawo sa asibiti..." Mayraah tace "Na fa shiga gidan ne nayi insisting mu tafi asibiti amma bata da intention din kai ta asibiti don tace mijin ya siya mata magani a chemist" Dr Khalil yayi murmushi yace "Yanzu ina kika nufa?" Tace "Zan koma gida" Yace "Ohk, bari in baki transport naga ko jaka babu a hannunki" Sai a sannan Mayraah ta lura ashe empty handed ta fito, ta kalli Dr Khalil, sai kuma ta fara fidgeting fingers dinta tace "Wallahi ban ma yi noticing haka na taho ba, i was so disturb with the little girls condition" Yace "Sure haka ne, ai kema kin yi kokari" Ya sa hannu aljihu ya ciro 5k yace "Wannan ai zai kai ki gida" Ta ɗan risina ta amsa tace "Nagode sosai" Yace "U are welcome, yanzu idan na samar maki space a nan din how will i communicate with you?" Tayi shiru don ita ko haddace new number dinta bata yi ba, can ta kallesa tace "Ka bani complimentary card dinka sai in kira da number ta, new number ne, bani da shi a kai" Yace "Ohk, zan ba Nurse su kawo maki yanzu, take care of ur self" Tace "I will, thank you" Daga haka ya juya ya koma cikin asibitin ta bi sa da kallo, bayan some minutes sai ga wata nurse ta fito, ta nufo inda Mayraah ke tsaye ta mika mata complimentary card din Dr Khalil, Mayraah ta amsa tayi mata godiya sannan ta juya ta fara tafiya, after minutes walk saboda girman compound din ta iso babban gate din fita haraban asibitin securities din wajen suka bude mata gate din ta fita. Mayraah na komawa suleja taga maza cike kofar gidansu Maman Hanan ana jiran gawarta, mata kuwa sai shiga gate din gidan suke, jikin Mayraah yayi sanyi sosai ta bude nata gate din ta shiga don baza ta iya shiga gidan taga koke koken da ake ba. Mama Ladi na zaune parlon Ammi tana hada mata kwadon salad tana cewa "Ai tunda har yace maki ana bakin kokarin ganin an nemota kawai ki kwantar da hankalinki, ki cire komai a ranki Mamuda bazai maki karya ba tunda ba gantalalle bane shi, sannan yasan manya manyan mutane a kasar nan, ba gashi ana tafiya da Hajja gidan yan sanda ba sai gashi kawai waya yayi ko zuwa caji opis din bai yi ba aka sako Hajja, to tunda yace maki Mera ma ana ta bakin kokarin ganin an samota to muna nan dake zaki ga an samo ta an sakota w mota an dawo da ita gida" Ita dai Ammi kallon Mama Ladi kawai take, Mama Ladi ta gama hadin salad da take bayan ta cika kuli kuli sannan ta tura shi gaban Ammi tace "Kina fara ci zaki ji bakinki sakayau, daga nan kuma komai ma zaki iya ci don buda maki ciki zai yi" Ganin Ammi bata ce komai ba kuma bata dau salad din ba Mama Ladi ta hade rai tace "Ke ni fa na gaji da maki bauta kina maida ni er banza, kinsan inda naje na samo salaq din nan na kwadanta maki kuwa? anguwan naku duk na yaku bayi wani yakunennen salaq suke siyarwa duk ƙasa, sai da nayi tafiya me nisa na samo wannan wllh, duk kwantar maki da hankalin da Mamuda yayi bai ci ace kin hakura kin fawwala ma Allah komai ba, ita fa wannan shegiyar Meran ba yarinya bace duk mun sani, da gangangan ta mana haka kuma wallahi in muka ce baza mu yafe mata ba ta zaunu, don ta wahal da zuciyoyinmu ta cuce mu, ki saki ranki ki ci gaba da harkokin ki in taga kowa yayi banza da ita zata dawo gidan, amma yanzu tasan duk mun damu shi yasa taki dawowa take gana mana azaba" Ammi ta dau salad din ta fara ci a hankali, Mama Ladi tace "To ko ke fa, ga kaji can an kawo an cika a firiji ina jin Mamuda ne yasa aka kawo, anjima sai in farfesa mana muyi ta ci da bredi abunmu bakinmu alekum" Sallama aka yi kofar parlon duk suka juya, Badiyyah ce ta shigo cikin wasu matsattsun dinki ta rataye gyale a wuya hannunta rike da handbag ta karaso har inda suke ta zauna kan kujera tana kallon Ammi tace "Ammi ina yini" Ammi bata sake kallonta ba tana ci gaba da cin salad din hannunta a takaice tace "Lafiya lau" Badiyyah ta kalli Mama Ladi da ta saki baki tana kallonta, babu yabo babu fallasa tace "Ina yini" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Sannu jarabar duniya, wato har kin dawo daga yawon tamɓelen naki kenan kamar akuya, shegiyar marainiya annamimiya shedaniya me tarwatsa zumunci, to uwar me ya kawo ki gidan nan ko ance maki Hajjan tana nan ne, baki san hanyar kuturun gidanta bane kika yo mana nan?" Badiyyah ta wani hade rai tana hararanta tace "Ni gaskiya ki daina zagina Mama Ladi, me na maki? Ko meye ruwana da ke daga shigowata zaki fara zagina haka? Wallahi ki dena ina gaya maki" Bata rufe baki ba Ammi na nuna mata kofa tace "Tashi ki fita" Badiyyah ta kalli Ammi da sauri irin bata yi expecting haka ba, Mama Ladi kuwa ta rarumi spatula da ta gama hadin ƙwado ta jefa mata da karfi tace "Tashi ki fita shegiya guzumar banza kawai, shi sa gashi kin doshi arba'in har yau ba mashinshini saboda mugun hali" Badiyyah ta fashe da kuka ta mike ta fice daga parlon da sauri, Mama Ladi na huci tace "Wallahi ni na raina dangin Sanisa in har suka bari Badiyyah ta ci bulus, haka kawai ta fasa masu kan er su har ana hango ƙwaƙwalwa su kyaleta kuma, a ina aka taɓa haka kamar Sanisar bata da gata, ni Allah da na san gidan dangin Sanisar sai in tashi yanzu in je ince masu Badiyyah ta dawo amma in masu kashedi kar su sake cewa za su kama er uwata Badiyyar dai ta dawo su koma gidan za su ganta" Ammi dai bata ce komai ba sai cin salad din gabanta take Absentmindedly. Direct gida Badiyyah ta koma tana shiga parlon Hajja ta zauna kasa ta mimmike kafa ta fashe da matsanancin kuka tace "Dama sai da nace maki bazan je ba kika ce sai naje duba Ammi bata da lafiya, sai da nace maki wallahi bazan je ba kika takurani, daga dawowata kika dameni sai naje duba Ammi to wallahi duk zagina suka dinga yi ita da Ladi wai suke ce min shegiyar marainiya annamimiya, har da ce min na rasa mashinshini shekarata arba'in" Hajja dake zaune tana kallonta tayi kasa da murya tace "Har ita Ammin?" Cikin kuka Badiyyah tace "Ba ita ta fara ba ma ta koreni daga Parlon, ni wallahi kar wanda ya sake shiga harkata babu hadina da su tunda basa so na, idan ba haka ba zan zagi mutum ba ruwana" Hajja dai ta kasa cewa komai amma gaba daya ranta yayi mugun baci, can tace "Ki rabu da su kowa yayi na gari don kansa, amma na Ammi ya fi bani mamaki, ban yi mamakin na Ladi ba tunda ita dama mahaukaciya ce er iska" Badiyyah ta kalleta da sauri tace "Ita ce ma tace in tashi in fita in bata waje fa nace maki, wallahi Ammi ce ta fara" Hajja tace "Kawai tace ki tashi ki fita??" Badiyyah ta fashe da sabon kuka tace "Eh mana" Hajja ta dau wayarta a hankali tace "Kira min Ammin" Badiyyah ta amshi wayar ta yi dialing number Ammi yana fara ring ta mika ma Hajja, Ammi na share parlonta, Mama Ladi kuma na zaune ta daura kafa daya kan daya tana cewa "Kema sai ki ji kin kara jin kwari a jikinki ba wai ki sakar min komai kamar baiwa ba kina zaune gefe daya kan darduma kamar me takaba, ko mutuwa Mera tayi a yanzu ai ya ci ace mun fara saka ma ranmu salama mun fara hakura" Sai da Ammi ta daga kai ta kalli Mama Ladi da ta ci gaba da kallon tv ko a jikinta maganar da tayi, Ammi dai ta ci gaba da sharan ba wai don tana jin dadin jikinta ba kawai Mama Ladi ce ta tilasta sai tayi shara karfi da yaji, wayar Ammi ne ya fara ring, ta mike ta dau wayar Mama Ladi na kallonta tace "Waye?" Ammi tayi shiru at first, sai kuma a hankali tace "Hajja ce" Mama Ladi ta mike da sauri ta fizge wayar tace "Ina ake dagawa?" Ammi dai ta kasa cewa komai, a fusace Mama Ladi tace "Don Allah ki daga min kar ya katse" Ammi tayi picking call din, Mama Ladi tace "Salama alekum, yaya ina wuni" Daga daya bangaren Hajja tace "Ina Ammin?" Mama Ladi tace "Sallah take shine na daga, ya aka yi ne?" Hajja tace "Ban sani ba, halan wajenki Badiyyan taje da zaki ci mata mutunci Ladi?" Mama Ladi tace "Wacece kuma Badiyyah? Ayyo wai Badiyyah jikar ki? Wato don ba a bar ki kin kwana cikin barayi ba shine har bakinki zai kara furta sunan Badiyyah gatsal Hajja?" A fusace Hajja tace "Kar ki gaya min maganar banza Ladi, ke wace irin munafukar mace ce me hada fitina ne? Ki ba Ammi wayar ba dake zan yi magana ba" Mama Ladi tace "Wallahi bazan bata ba, in bata wayar ki kara daga mata hankali tunda in ta mutu ni nayi asara ba ke ba, ki bar mata taji da ɓacewar er ta mana Hajja, duk ke da Badiyyah fa ku ka dinga juya matar nan har ta kora er ta kwaya daya ta shiga duniya saboda son zuciya irin taku, gashi kun ja mata kishiya me diri har Mamuda ya dauke kishiyar sun koma dankareren sabon gidansa da ya gina ya bar ita Ammin a walakance a nan cikin yaku bayi Mashir ke gaya min jiya da daddare, wa ya ja mata banda ke da jikarki da tsinanniyar surkarta, Wallahi ban taɓa ganin uwar da bata son kwanciyar hankalin 'ya yanta ba irin ki Hajja, ko ni da ɓan taɓa haihuwa ba bazan yi wannan abinda kike yi ba Hajja, kuma in baki yi hankali da yarinyar nan Badiyyah ba wallahi zata sa a rataye ki muyi ta koke koke muna nema maki rahama wajen Allah" Hajja da ranta yayi mugun baci tace "Ladi ni kike gaya ma wa ennan maganganun? Ni Ladi?" Mama Ladi tace "Toh me na ce? Ni dai Allah ya gani ba rashin kunya na maki ba gaskiya nake gaya maki, haka kawai in ki gaya maki Allah ya kama ni, aa ba ruwana wallahi" Hajja tace "Ba komai, Nagode Ladi, ni dai kike ci ma mutunci haka ko? Ita Ammin ta sa ki gaggaya min wannan maganganun ko?" Mama Ladi tace "Wacece Ammi? Ammi da yanzu haka gata can Mashir ya sa mata ruwan drif, ni dai ba ruwana sai anjima ba rashin kunya na maki ba gaskiya ce dama ance daci gareta" Daga haka ta karasa gun Ammi da sauri tana mata alamar ta katse, Ammi ta katse wayar tana kallon Mama Ladi babu ko kiftawa don kalmar da tayi wai Mamuda ya dauke kishiya sun koma dankareren sabon gidansa ne kawai ke ta yawo kan Ammi, can a hankali Ammi tace "Sabon gida ya koma da matar?" Mama Ladi dake share zufar goshinta tace "Wa?" Ammi ta kasa cewa komai, Can Mama Ladi ta tuna maganganunta a waya, da sauri tace "Haba duk shirgata nake ko zata dawo hankalinta fa, ba nan Mamudan ya kwana jiya ba? Kawai na gaya mata haka ne don in gigitata ta shiga taitayinta ta kyaleki kiyi zaman aurenki lafiya, amma wannan Amarya ai ina jin tana gidansu yanzu haka tun da gashi daga zuwanta komai ya kara tabarbarewa, ai shi Mamudan ba wawa bane" Ammi dai bata sake cewa komai ba, Mama Ladi ta dau tsintsiyar ta ci gaba da sharan tace "Dama baki yi niyyar yi ba, tafi ki zauna kawai ni da kika mayar boyi boyi saboda daga kauye nake sai in ta yi ai tunda za a ban in ci in koshi" Ammi ta koma ta zauna amma zuciyarta ya kasa kwanciya da maganar sabon gidan da Mama Ladi tayi. Mayraah na zaune parlon Maman Hanan da yamma don ranan aka yi sadakan uku, zuwa sannan ma duk mutane sun watse sai yan uwanta, Sosai mutuwar yarinyar ya girgiza uwar gashi tun ita bata sake haihuwa ba shekarar yarinyar takwas, Mayraah ta kalli wayarta da yayi vibrate taga number Dr Khalil da ta kira dazu da safe ne da bai daga ba sai yanzu ya biyota, tayi silencing wayar tana kallon Maman Hanan tace "Aunty bari in shiga gida, sai gobe idan na shigo in sha Allah, sai ki basu takardan da na rubuta maki maganin a siyo maki ki sha zaki samu bacci in sha Allah" a hankali Maman Hanan tace "To Nagode Ilham, baki debi abincin ba kuma" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Na koshi wallahi, nima wanda na dafa ban cinye ba" Maman Hanan tace "Toh shikenan sai kin shigo goben" Mikewa Mayraah tayi suka yi sallama da mutanen parlon sannan ta fita ta koma gida, bayan ta kulle gate din ta shiga daki ta yi dialing number Dr Khalil, sai da ya kusa katsewa ya daga tayi sallama ya amsa sannan ta gaishesa, yace "Wa ke magana?" Tace "Ilham ce" Yace "Oh, Ilham sorry u called tun dazu, ina busy ne wllh" Tace "Ba damuwa, ya aiki?" Yace "Alhamdulillah, gobe ki shigo asibitin da safe kawai" A hankali tace "Toh" Yace "Yeah, in kin shigo sai ki kirani" Tace "To Allah ya kai mu Nagode" Sallama suka yi ya katse wayar, haka kawai taji gabanta na faduwa, ta zauna gefen katifa tana tunanin yanda zata fara aiki a babban asibitin nan cikin manyan health workers da suka yi shekara da shekaru a aikin, za ma ta iya kuwa? Anya ma zata iya tuna abubuwa yanzu don gani take kamar kanta baya ja, haka nan ta kwana cikin zulumi da tunani iri iri a ranta, gari na wayewa bayan ta shirya cikin doguwar riga ta saka hijab dinta har kasa da tayi iron, shayi kawai ta iya sha don duk a tsorace take, bayan ta gama ta dau nose mask dinta ta saka sannan ta dauki handbag dinta ta fita ta kulle gidan, sai da ta fara lekawa gidan Maman Hanan ta gaisheta ta tambayeta ko ta samu bacci, Maman Hanan tace "Ai kam na samu bacci sosai Ilham, Nagode fita za ki yi ne?" Mayraah tace "Eh zan tafi makaranta" Maman Hanan tace "Toh Allah ya tsare sai kin dawo" Daga haka Mayraah ta fita ta kama hanyar cikin garin Abuja, tana isa asibitin wajen karfe goma saura bugun zuciyarta ya tsananta ita kanta ta rasa me yasa ta zama so tensed haka, sau biyu ta kira Dr Khalil bai daga ba, ta zauna reception bayan ta gaida wasu nurses da ta gani, wata nurse na tambayarta ko tana da appointment da Dr ne, Mayraah ta girgiza kai zata yi magana sai ga Dr Khalil ya shigo Reception din, yana ganin Mayraah yace "Meet me at my office" Daga haka ya wuce sama ta mike ta bi bayansa zuwa office din nasa, bayan ta shigo ta gaishesa ya amsa yace "Zauna mana" Zaunawa tayi kan kujera tana kallonsa, wani leda ya dauko ya ajiye mata kan table yace "Ur Scrubs and shoes, Allah ya sa su maki" Mayraah ta dau ledan, Dr Khalil yace "Ya kamar kina tsoron ledan" Ɗan murmushi tayi tace "Aa" Yace "Zaki fara aikin yau ai?" Mayraah ta rasa abinda zata ce, ya nuna mata wani kofa a office dinsa yace "Ki shiga nan ki gwada scrubs din ko za su maki da shoes din" Ta gyada masa kai sannan ta mike tana rike da ledan ta nufi kofar da ya nuna mata ta bude ta shiga, bayan few minutes ta fito sanye da hijab dinta tana kallonsa tace "Sun yi" Yace "To me yasa baki bari a jikin ki ba kika cire, u are resuming work today" Mayraah dai kawai tayi murmushi ta koma ta zauna tana kallon sa, kwankwasa office din aka yi yayi izinin shigowa wata nurse ce ta shigo warce bazata haura 30 years ba ta gaishesa da ladabi, yace "Morning Hafsat, ga sabon staff dinmu zan damka maki ita yanzu, ki dinga guiding dinta pls, for now she is not working amma komai za ki yi you make sure tana kusa da ke tana gani" Nurse Hafsat ta karaso tana murmushi tace "To ba damuwa sir, in sha Allah i will do so" Yace "Transferring dinta aka yi zuwa nan ko da wani ya tambayeki...." Hafsat tace "In sha Allah sir" Dr Khalil ya kalli Mayraah yace "Nurse Ilham, follow your colleague zata nuna maki inda zaki saka scrub din ki" a hankali Mayraah tace "To Nagode" Daga haka ta mike tana rike da ledan ta bi bayan Nurse Hafsat suka fita, suna sauka reception din few nurses dake wajen suka bi su da kallo, Nurse Hafsat ta kai Mayraah changing room tace "You are welcome to be part of Us in this great hospital Nurse Ilham" Mayraah tana murmushi tace "Thank you" Mayraah na gama saka scrub din ta fito daga bandaki Hafsat tace "Waow kin ga yanda ya maki kyau kuwa kamar sai da aka auna ki kafin a dinka" Mayraah dai ta kirkiri murmushi, Nurse Hafsat tace "You look smart on this scrub" Mayraah was a bit comfortable cikin uniform din saboda me Hijab ne duk da karamin hijab ne, unlike yanda taga wasu nurses babu hijab sai scrub cap amma tana tunanin ba musulmai bane don Hafsat ma nata uniform din da karamin Hijab a kai, Hafsat tace "Wani makarantar kika yi?" A hankali Mayraah ta gaya mata school din da ta gama, Hafsat ta wara ido tace "Da gaske? Wani department?" Mayraah ta gaya mata, Hafsat tace "Lahhh, nima shi nayi ai, mun gama kusan 8 years kenan" Mayraah da bata son zancen tayi saurin cewa "Ayya, ina zan bar jakana yanzu?" Wata nurse ce ta shigo wajen ta kalli Hafsat sannan ta kalli Mayraah, can ta maida dubanta kan Hafsat tace "There is an emergency" Daga haka ta juya ta fita, Hafsat ta amshi jakan Mayraah da sauri ta bude wani safe ta saka ciki da ledan second scrub da takalmin Mayraah sannan ta kulle safe din ta ja Mayraah suka fita daga room din da sauri. [7/19, 12:06 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na zaune wani ward da babu kowa ciki ta daura kanta kan gadon idonta a lumshe, ga cup din Caffeine drink da bata shanye ba kan table dake kusa da ita, Dr Khalil ne ya shigo ward din tare da wani Dr Hamid, duk suka nufota Dr Hamid na kallonta yace "Why didn't u lie down?" Mayraah ta daga kai da sauri tana kallonsu don bata ji shigowarsu ba alamar bacci ya fara daukarta, Dr Khalil ya kalli cup din coffeen yaga rabi kawai ta sha yace "Me yasa baki shanye ba?" Ta girgiza masa kai a hankali tace "Ya isheni" Wata nurse ce ta shigo ward din rike da blood pressure gauge, Dr Hamid yace "Check the Bp again" Nurse din ta kama hannun Mayraah ta hau duba Blood pressure dinta, bayan ɗan lokaci da dago tana nuna masu tace "It's almost normal sir" Dr Khalil na kallon Mayraah yace "Ki kwanta ki yi relaxing zuwa anjima kadan" Mikewa tayi ta cire takalman kafanta a hankali sannan ta hau kan gadon ta kwanta, Dr Hamid ya juya suka fita tare da Dr Khalil, Dr Hamid na kallon Dr Khalil yace "When was she employed here? I have never noticed her, naga kuma babu vacancy, in ma akwai 'ya yan masu ƙasar suke ba ma ae" Dr Khalil ya ɗan shafa kai yace "Ai ina jin transfer aka mata..." Dr Hamid na gyada kai yace "But she is really good gaskiya, irin nurses da nake son aiki da kenan, tana da nutsuwa da composure wajen aiki she did all the sutures perfectly without waiting for directive, ba ko wace nurse ce zata iya ba, Intradermal suture fa, even Dr Balogun commended her" Dr Khalil na gyada kai yace "Nima na gani, i was also surprised, stress din aikin ne yayi weighing dinta down, dama kuma bata da lafiya tace min" Dr Hamid yace "She needs to work on her diet, and decrease her carbs intake, hypotension ai ba abu bane me kyau" Dr Khalil yace "Gaskiya kam" Mayraah na bacci wajen karfe shidda saura Dr Khalil ya shigo ward din da take, ya taɓa gadon da take kai ta bude ido a hankali, yace "How are you feeling now?" Ta mike zaune tace "I feel better" yace "Pls avoid eating lot of carb food Ilham, bai kamata jininki na kasa haka ba, more veggies to ur diet" Ita dai tayi shiru, yace "Yanxu yamma bai yi ba kice za ki koma Suleja? And I don't think it will be possible kullum kina komawa can kina zuwa nan, the distance..." Mayraah tayi saurin katse sa tace "Ai mun yi magana da Aunt dina da mijinta tun da kace zaka samar min aiki sai suka ce ko hostel na student ne sai in samu a nan Abuja in zauna saboda da nisa daga can garin ace in dinga zuwa nan kullum, duk sanda bana da aiki sai in je sulejan" Shiru tayi don ita kanta sai taji kamar maganar bai mata ba a kunnenta, shi dai Khalil kallonta kawai yake as if observing something, har ta tsargu ko ya gano karya take ne, gabanta dai sai faduwa yake ta sunkuyar da kanta, after few seconds of silence yace "Shikenan, amma at the first place da nace zan samar maki aiki ai kamata yayi ita aunt din ko Uncle dinki wani ya biyoki nan don tabbatar da hakan tunda yanzu kowa yasan yanda duniyar ta dawo, amma naga duk basu yi hakan ba" Nan gaban Mayraah ya tsananta bugawa cikin few seconds tayi cracking brain dinta ta samo abinda zata fada tana kallonsa tace "Ranan da muka zo da matar nan da yarinyarta ta rasu ai tare muke da aunt din nawa, ita komawa gida tayi ta bar mu, to nace mata nan asibitin ne...." Dr Khalil na kallonta yace "Even at that Ilham, amma ya ku ke da ita aunt din taki na Suleja? I mean dangantakar ku?" Mayraah taji hankalinta ya fara tashi, amma ta dake tana kallonsa tace "Kawai ta taɓa auren dad dina ne kafin ya rasu" Dr Khalil yace "Ur stepmom kenan?" Ta gyada masa kai tana kokarin sauka daga kan gadon alamar tambayoyin sun isheta, Dr Khalil yace "How about ur mum?" Ta wani kallesa a takaice tace "But i told u my parents are late" Ita kanta tasan she sounds pissed off, Dr Khalil yace "Dangin mamanki da babanki fa?" Tace "Dr... suna bauchi, admission din nan ya kawo ni Abuja ban san anyi cancelling dinsa ba, if not ni bani da kowa a Abuja ai sai stepmom dita a suleja" Dr Khalil na nodding kansa yace "Ohk i get, to bari zan kai ki inda zaki yi passing night din yau don yanzu yamma yayi kice zaki koma Suleja, amma ki fara kiran stepmom din taki ki sanar masu tukun, sai ku samu wani alternative din inda zaki zauna a Abuja" a hankali Mayraah tace "To" a ranta kuwa tunanin ina zai samar mata ta kwana take, kawai ita dai taji har ranta ta yarda da Dr Khalil don yawancin abubuwa idan yana yi ma kallon Maheer kawai take masa, kusan personality dinsu da halinsu daya, tun daga caring, tausayi, sannan he is also very free like Maheer, uwa uba kuma ta lura he is also observant just like Maheer, dole sai ta tsaya at alert incase ya mata tambaya ta jefa masa amsa babu bata lokaci yanda bazai sa zargin komai a ransa ba, Da sauri ta kallesa don har a sannan kallonta yake as if dai yana nazari, tace "To in kwana a asibitin kawai mana" Yace "Aa ai asibiti ba wajen kwana bane idan ba dole ba, kuma u need much rest, yanzu ki tashi ki dauko stuffs dinki, let me get my car key don i will still have to come back akwai surgery da za mu yi bayan magrib...." Mayraah tace "Toh" Sai da ya fita ward din sannan ta bi bayansa har a sannan kuma bata daina jin dizziness ba, awa biyu kawai tayi a theatre da wasu daga manyan likitocin asibitin har da wani ba indiye a cikinsu all trying to save the the lives of 4 people da suka yi mummunan hatsarin mota irin 'ya yan masu kudin nan, kawai daga taje mika wasu allurai da Matron ta bata ta kai wani likita ya tsayar da ita alamar bai ma san ranan ta fara aiki a asibitin ba, haka nan gabanta ya dinga faduwa duk da ko da suka yi clinical rotations dinsu back then in school she was one of the best student, but yanzu kam she is so nervous and afraid amma haka nan tayi composing kanta a wajen aka fara aiki da ita, Daga nan kuma bayan aikin awa biyu bata san sanda ta sulale kasa ba tsabar gajiya da dizziness shine likitocin dake wajen suka yo kanta da sauri. Mayraah na fitowa reception bayan Hafsat ta dauko mata jakarta da ledan uniform dinta tace "Allah ya sauwake Nurse Ilham, hope you are much better now?" Mayraah tace "Alhamdulillah naji sauki" Sauran nurses din dai sai kallonta suke kuma babu wanda dai yace mata sannu, Nurse Hafsat tace "Sae gobe kenan?" Mayraah tace "In sha Allah" Dai dai nan Dr Khalil ya sauko da makullin motarsa ya fita, Mayraah ta kara yi ma Hafsat sallama ta bi bayansa, nan ma duk aka bi ta da ido, suna barin hospital din bayan sun hau hanya Khalil yace "Amma a wani asibiti kika koyi aiki Ilham?" Sosai gabanta ya fadi tana kokarin tuna ko wani asibiti ta fada masa, ai ko nan ta kirkiro suna babu bata lokaci ta basa, yace "Wani gari kenan?" Ta ɗan kallesa tace "But i told u, a Bauchi nake" Yace "Yea na tuna, Shekara nawa kika yi kina koyan aikin?" Tace "Na ɗan dade fa" Yace "No wonder! but...." Mayraah taji gabanta ya fadi tana jiran jin but what, sai kuma ya karyar da kai ya fasa fadin abinda zai fada yace "Anyways it's fine.... u did a very good job dazu a theatre i was so impress kin ma fi wa enda suka yi karatun nurse din nutsuwa wajen aiki, you are so composed" Ta ɗan yi murmushi tace "Nagode sir" Yace "You are welcome" Bai sake ce mata komai ba har sai da suka yi tafiyar kusan minti ashirin ita dai sai bin cikin garin Abuja take da kallo, sai da suka shigo wani anguwa yayi horn bakin gate din wani gida aka bude gate din, ita dai har a sannan bata ji gabanta ya fadi ba ko kuma taji tsoro she don't even get the kind of trust she have for him daga haduwan sati daya da kwanaki, yana parking ya bude motar ya sauka ita ma ta sauka rike da ledan uniform dinta, wasu yara maza biyu yan shekara sha uku ne wanda da alama yan biyu ne ke ta ball a tsakar gidan suna ganinsa dayan ya dau ball din nasu ya rike a hannu a tare suka ce "yaya sannu da zuwa" Dr Khalil yace "Ba islamiyya?" A tare suka ce "Ai mun dawo" Gaida Mayraah suka yi ta amsa tana kallon kyawawan yaran, Dr Khalil ya kalleta yace "Mu je" Ba musu ta bi bayansa har suka shiga cikin parlon gidan, Wata elderly woman ce da bazata haura shekara 56 ba zaune parlon da mai aikin gidan suna hira, Khalil ya zauna kan kujera yana kallonta yace "Ummi ina wuni" Mayraah ta zauna kasa tana kallon matar da yace ma Ummi ita ma ta gaishta, Ummin tace "Aa tashi ki hau kujera mana" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Aa nan ya isa" Ummi ta kalli Khalil din tace "Ashe kuna hanya ma ka kirani kenan" Yace "Aa ko fitowa ban yi daga office ba, Ummi za mu shiga theatre after magrib zan koma" Ummi tace "To Allah ya bada nasara" Yace "Ameen" Ya kalli Mayraah yace "Ilham feel at home" Daga haka ya mike sai kuma yace "Ummi ya jikin Inna?" Ummi tace "Ai bacci ma take ina jin" Yace "Ohk, kilan sai gobe zan shigo" Daga haka ya fice daga parlon, Ummi na kallon Mayraah tace "Sannu da zuwa Ilham, ya aikin?" Mayraah na murmushi tace "Alhamdulillah" Ummi tace "Yace min suleja kike ko" Mayraah tace "Eh" Ummi tace "Suleja kam ai yayi nisa, sai dai ki nemi alternative, Karima ki kai ta daki ga magariba ma ya gabato" Mai aikin ta mike tace "To Hajiya" Wani daki da ba kowa Karime ta kai Mayraah, Mayraah ta shiga ta zauna gefen gadon dakin. Bayan isha Mayraah na dakin da aka sauketa, wata yarinya kyakkyawa da bazata wuce 11 years ba na cikin dakin ita ma sai labari yarinyar ke ba Mayraah da turanci, tun da yarinyar ta kyallara ido taga Mayraah shikenan bini bini zata shigo dakin, Mayraah na kallon yarinyar tace "Har yanzu ai baki gaya min sunanki ba" Yarinyar ta kyalkyale da dariya tace "My name is Fatima amma ana ce min Mimi" Mayraah ta gyada kai tace "Nice name..." Yarinyar ta dawo kusa da Mayraah tace "Aunty ke ya sunanki?" A hankali Mayraah tace "Ilham" Dai dai nan wayarta ya fara ring, Mimi ta mike da sauri ta dauko mata ta kawo tace "Aunty in kin gama wayar ki kirani" Mayraah tace "Toh zan kira ki" Daga haka yarinyar ta fita daga dakin, Mayraah tayi picking call din don Dr Khalil ne ke kiranta, bayan sun gaisa yace "Hope you are comfortable Ilham?" Mayraah ta gyada kai tace "Sure, Nagode sosai" Yace "That is my in-laws house" Mayraah ta buda ido tace "Ban gane ba" Yace "Gidansu matana mana, that's her mother" Mayraah was shocked ta ma rasa abinda zata ce masa..... [7/20, 7:06 PM] Khaleesat Haiydar💖: Washegari da safe Mayraah na zaune dakin da aka bata bayan tayi wanka amma ko leka parlorn gidan ta kasa yi, tun da Dr Khalil yace mata gidansu matarsa ne ya kawota jikinta yayi sanyi ta kasa samun nutsuwa har gari ya waye, Karime ce ta shigo dakin da sallama, Mayraah ta gaisheta Karime ta amsa da fara'a tace "Hajiya na kiran ki a parlor" Mayraah ta mike sanye da hijab dinta ta fita parlor, da ladabi ta gaida Ummi, Ummi ta amsa tace "Baza ki je aikin bane naga baki fito ba har takwas yanzu" Mayraah ta sunkuyar da kai tace "Zan je" Ummi tace "To ki shirya ki fito kiyi breakfast kafin nan driver ya dawo daga ajiye yara makaranta sai ya sauke ki asibitin" Mayraah tace "Toh Nagode" Daga haka ta mike ta koma dakin da ta fito, karfe takwas da rabi Mayraah ta sake fitowa parlor bayan ta shirya cikin uniform, tana fitowa Karime kadai ta tarar tana ta aikace aikace a parlon, Karime ta nuna mata dinning area tace "Ga kumallon naki can na kai maki" Mayraah ta mata godiya sannan ta karasa ta zauna, shayin ta hada, ta debi irish da kwai ta fara ci, ko bayan da ta gama breakfast din tana ta zaune parlor sai ga driver yana sallama bakin kofar parlor, Karime tace "Yauwa ga Dreban ya dawo, Hajiya ta shiga ciki ta kwanta tace ince maki Allah ya tsare" Mayraah ta mike tace "Toh nagode" Daki ta koma ta dauko handbag dinta da wayarta sai ledan scrub din ta sannan ta fito ta kara yi ma Karime sallama ta fita. Driver na ajiyeta bakin gate din asibitin ta sauka tace masa "Nagode" Yace "Allah ya tsare Hajiya" Daga haka ta shiga gate din asibitin. Kamar jiya yau ma haka Mayraah ta jigata a asibitin don daga shigowarta da safe wani Dr Balogun ya aika a kira ta zuwa theatre, ba kuma wani aiki tayi ba kawai surgical equipments suke kira by their names ita kuma babu bata lokaci take mika masu Instruments din, kuma ko sau daya bata yi mistake din ko daya ba, wani ma bata jira a tambaya take mika wa sanin function dinsa, 2 other senior nurses ne tare da likitoci biyu a theatre din giving them assistant, ba su suka fito theatre din ba sai bayan azahar, Dr Balogun na kallon Mayraah yace "Ur alma mater Madam?" Sosai gabanta ya fadi, sai ga wani Dr ya zo yana ma Dr Balogun din magana, sum sum ta bar wajen da sauri ta koma reception tana zare ido, Nurse Hafsat tace "Sai yanzu, sannun ku da aiki" Dai dai nan Wata nurse ta ajiye telephone din hannunta saman desk tana kallon Nurse Hafsat tace "Who is Nurse Ilham?" Nurse Hafsat ta nuna mata Mayraah, Nurse din ta kalli Mayraah ta sanar mata Dr Khalil na nemanta a office dinsa, Tun da Mayraah ta shigo asibitin basu hadu ba bata ma san ko ya zo ba ko bai zo ba, sai da tayi sallan azahar sannan ta tafi sama zuwa office dinsa, bayan ta shiga ta kulle masa kofa ta karasa har bakin table dinsa ta gaishesa, ya ajiye aikin da yake yi a laptop yayi mata izinin zama sannan ta zauna ta sake gaishesa ya amsa yace "You looked stressed, ai tunda kika bari Dr Balogun ya gano ki sai kinyi hakuri da shi, haka yake in dai ya lura nurse bata basa problem wajen aiki and she is composed kuma ta san abinda take shkkn duk zai yi aiki sai ya sa an nemo masa ita sai dai in bata duty ranan" Mayraah dai bata ce komai ba sai murmushi da tayi, yace "Nasan baki ci abinci ba ko?" Bai jira cewarta ba ya dau ledan takeaway ya mika mata, ganin bata amsa ba yace "Karbi mana" Ta sunkuyar da kanta tace "Bana son ina daura maka burden dina, i am suppose to get food my self ba wai ka siya min ba" Yace "Ki tambayi Nurse Hafsat in dai ban siya mata lunch ba to probably ban zo asibitin ba ko kuma bana duty ranan, i do this for most of the nurses, it's nothing a wajena" Mayraah ta amsa a hankali tace "To Nagode Allah ya saka da Alkhairi" Yace "Ameen, ya kika baro su Ummi" Mayraah ta kallesa da sauri, sai kuma tayi kasa da murya tace "Amma me yasa zaka kai ni gidan in-law dinka?" Yace "Bayan in-law nima mamata ce ai, bani da kamar ta a duniya...." Kallonsa kawai Mayraah take, yace "Ina da shekara biyar Mom dita ta rasu ta bar ni gun stepmom dina, i still remember vividly the maltreatment from my stepmom, yes it is still in my memory, duk abinda tace shi Dad dina yake yi ba shi da wani say may his soul rest in peace, dangin Mom dina sun so daukana a lkcn stepmom ta saka dad dina yaki amincewa su tafi dani, to cut everything short, Ummi that was our neighbor then ita ta daukeni ta kawo ni cikin nata yaran bayan tayi threatening stepmom dita zata kai ta kara kotu cause barrister ce, Babansu zainab ma haka, kowa na shakkar shiga sabgarsu a layin, even my dad couldn't confront her duk da gidan su Ummi was opposite to ours, few years later dad din nawa shi ma Allah ya masa rasuwa, Ummi and her husband are the reason i am who i am today, and after everything they gave me der daughters hand in marriage... though Zainab father is also late bayan aurenmu da shekara biyu..." A hankali Mayraah tace "Allah ya ji kansa, Allah ya ji kan iyayenka kai ma" Yace "Shi yasa naji tausayinki da kika ce min ur parent were late" Nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah, yace "Ya ku ka yi da aunt dinki about inda zaki zauna saboda aikin?" A hankali Mayraah tace "Dama tace kayi min recommending area da zan iya samun wajen zama a nan since mu bamu san Abuja ba kai kuma a nan kake" Dr Khalil na kallonta yace "Ohk akwai kudin kama wajen da zaki zauna din kenan?" Ta gyada masa kai, yace "Meye Budget din ku?" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Ai ban san nawa bane ake renting waje a nan" Yace "Nasan baki sani ba, amma nawa ku ke da shi a kasa don in san irin wajen da za a samar maki gidan" Tace "Like 300k yayi?" Khalil ya gyara zama yana kallonta da kyau yace "Yanzu akwai 300k din a kasa?" Ta gyada masa kai, kallonta yake ko kiftawa babu, hakan yasa ta sunkuyar da kanta, Yace "Ilham" Ta daga kai ta kallesa yace "Kuna da 300k din kama gida me yasa baki yi registration din admission da kika ce an baki ba?" Ta hade rai tace "I told u sai da aka tara kudin na taho, kuma da na zo naga an riga ma an rufe portal na registration har ma sun kusa fara exams, kaga ai dole za a soke admission dina" Dr Khalil yace "Wani makaranta ne? And where is the admission list?" Mayraah taji wani zufa na keto mata amma ta wani daure fuska, dai dai nan aka kwankwasa kofar office din ta mike da sauri kamar jira take tace "Kilan patient ne...." Yayi izinin shigowa sai ga wata patient da yake da appointment da ita ta shigo office din, tuni Mayraah ta fice daga office din nasa, gaba daya ta kasa samun nutsuwa a asibitin har aka yi la'asar, Dr Khalil na shigowa daga masallaci Mayraah ta ki barin su hada ido a reception din sai duba file din wata mata take a shelf, ya wuce sama, komawa tayi ta zauna a hankali tana Allah Allah karfe shidda lokacin da yan evening za su amshi duty yayi ta kama hanyar suleja komin dare kuwa, 6 nayi dot Dr Khalil ya sauko ita ko har ta fito daga changing room rike da jakarta, tana ganinsa ta wani hade rai taki yarda su sake hada ido, duk yana kallonta, makullin office dinsa ya mika mata yace "Get me my laptop and bring it to the parking space Nurse Ilham" Ta amshi makullin ya fita daga reception din, ko da ta iso parking space bayan ta mika masa laptop din yace "Ina za ki yanzu?" A takaice tace "Gida" yace "It's late ki ce zaki kama hanyar suleja yanzu, so kawai gidan Ummi....." Katse sa tayi da sauri tace "Aa ni bazan je ba gaskkya" yace "Saboda me?" Tace "Gidansu matarka ce fa" Yace "It's nothing, nace maki nima gidanmu ne, matata tasan wanene ni, ko dazu da muka yi waya da Ummi ta tambayeni ke, i told her anjima zaki je can cause nasan baki da inda zaki zauna nan Abuja yau din ma" it took more than 10 minutes kafin Dr Khalil yayi convincing Mayraah ya kai ta gidan surkarsa, duk jikinta a sanyaye ta shiga gidan kamar munafuka shi ko dama yana ajiyeta ya juya, Ummi na parlor da sister dinta Rabi'ah warce ita ma ranan ta zo, Mayraah ta zauna kasa ta gaida Ummi, Ummi ta amsa da fara'a tace "Ya aikin?" Mayraah tace "Alhamdulillah" Ummi tace "To maa sha Allah, yace min har yanzu baki samu wajen ba ko?" Mayraah ta gyada mata kai, Ummi tace "To in kin ga babu damuwa kiyi zamanki a nan mana sai ki dinga komawa gida weekend, ni dama da yace wai gida kike nema ki zauna hakan bai min ba kina 'ya mace, dama hostel ne cikin makaranta da sauki wannan, amma gida kam bai kamace ki ba" Mayraah dai kanta na kasa, Ummi tace "Sai ki ma iyayen naki bayani in sun gamsu ba wani takura sai ki zauna nan abun ki kina zuwa aikin ki, abinda in kin fita tun safe sai karfe shidda, weekend kuma sai ki je masu gida tun da naga Auxiliary nurses basu fiye aiki weekends a asibitin ba" Mayraah ta daga kai tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" Ummi tace "Ameen sai ki shiga kitchen ki debi abinci" Mayraah tace "Toh, nagode" Mikewa tayi ta nufi dakin da aka sauketa, Rabi'ah da ta bi ta da kallo tace "Ummi wacece?" Ummi tace "Bakuwa ce" Daga haka ta mike tace "Bari in je lokacin sallah yayi" Mayraah ta kai minti sha biyar tana nazarin zaman gidan da Ummi tace tayi, anya zata iya kuwa, though taga matar is very kind amma ita sai abun yayi mata wani iri a kai, shi ko tsoro baya jin kar su zargi wani abu ko ayi tunanin budurwarsa ce ita, kauda zancen tayi kawai a ranta daga karshe ta mike ta shiga bandaki. Da daddare Mayraah na daki Ummi ta shigo dakin tace "Ilham zo ki duba magungunan nan da Khalil ya bada aka kawo dazu bai bada prescription ba" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi ta bi bayanta suka fita zuwa wani daki, Wata tsohuwa ce zaune dakin kana ganinta kasan bata da lafiya, Mayraah ta zauna tana kallonta tace "Ina wuni kaka" Tsohuwar bata amsa ba, Ummi tace "Hajiya ba lafiya Ilham, duba magungunan ki ga" Da kyar tsohuwar ta bude baki tace "Kar ki sake sa ni a bakin duniya kice bani da lafiya Zuwaira, na kuma samu lafiyata babu abinda yake damuna yanzu, aniyar kowa ta bi shi" Ummi na kallon Mayraah tace "Ilham in kin bude maganin sai ki bata" Daga haka ta fita daga dakin, Tsohuwar na kallon Mayraah cikin rawan murya tace "Ke kiji rainin wayo, ita da 'ya yanta fa suka sa min guba yau sati uku kenan ina fama jiki yaki dadi, amma duk wanda ya zo sai tace masa Hajiya ba lafiyaa, sai terere take min" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Mayraah dai sai kallonta take ta ma kasa cewa komai, ta karasa buda mata maganin ta mike mata, hannu na rawa ta amsa ta dau cup din ruwa, Mayraah tace "Sannu, amma jikin da sauki ko?" Tsohuwar tace "Ke ba wani sauki, yanzu haka duk jikina ciwo yake er nan, banda yaron nan Halilu ɗan albarka ai da na mutu mushe a dakin nan, wai fa a haka an sa min gubar ban mutu ba sai ki ga ita wannan er figigiyar macen da suke ce ma Mimi tana lekoni tana raye raye da tafe tafe, su kuma yan biyun maza sai su zaga baya suyi ta buga kwallo kan windown dakin wai duk don kar in yi bacci, ke bari kawai abinda suke min a gidan nan wallahi kare bazai ci ba, Allah ya isa kawai, banda mutuwa me tonan asiri" Mayraah dai ta ma rasa me zata ce, Tsohuwar na matse kwallan idonta tace "Ga flask can ki tafi da shi ki dafo min wani ruwan zafin a kitchen ban yarda da wanda ke ciki ba tun dazu nake jiran shigowan Halilu ya dafo min wani ruwan shima shiru shiru gantalallen bai shigo ba yunwa nake ji kamar zan suma, ita ma munafukar me aikin gidan na daina yarda da ita duk bakinsu daya da yan gidan" Mayraah ta mike tace "Toh bari in dafo maki Kaka" Daga haka ta fita daga dakin, Tsohuwar tace "Gwara na kama bare kawai, in ma ta cuceni bazai min ciwo ba kamar na jikina" Mayraah na fitowa Ummi dake parlor da karime tace "Ikon Allah...." Karime ta kyalkyale da dariya tace "Ai kuma shikenan kun ƙulla da Inna tunda har ta yarda ki dafo mata ruwan shayi" Ummi tayi murmushi tace "To Allah shi kyauta, sai ki je ki dafo mata" Hajja na kishingide bayan isha a parlor tana kallon Badiyyah dake kwance ko sallan la'asar bata yi ba balle Magariba ga isha har anyi, daga gefenta kuma plate din abinci ne da Hajjan ta ajiye mata har ta cinye ta bar mata plate din a wajen, Hajja tace "Ke yanzu fisabilillahi Badiyyah ina ta magana tun dazu kin ki tashi daga kan kujeran nan, ga salloli a kanki, kima je kiyi sallan mana sai ki dawo ki ci gaba da latse latsen wayar Badiyyah" Badiyyah tace "Kai na shiga uku, ke Hajja nace maki bazan yi sallan nan bane da kika dameni haka, ina fa sane, ki bari in gama abinda nake a wayar mana tukun" Hajja tace "Kina jin ai gorin da suka maki ranan babu dadin ji, amma ni ko a jikina tunda nasan ba su suke bada mijin auren ba, ita Ladi dama makwadaiciya duk inda galmi galmi yake nan take makalewa, cabdi ta zo nan tayi min me tasan ni ba me kudi ba, ai in ma ta zo wallahi koran kare zan ma er iskar makwadaiciya, tunda bata da zuciya tayi ta zama gidan Mamudan...." Ko rufe baki Hajja bata yi ba aka tura kofar parlon duk suka daga kai, wasu maza ne su hudu suka shigo parlon, Hajja ta mike zaune a firgice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una me zan gani haka, daga ina ni Sadiya??" Badiyyah da ta gigice ta mike tsaye ita ma gashi babu daman gudu duk sun zagaye Parlon, Daya daga cikinsu ya sanar da cewa su yan sanda ne ya ciro ID card dinsa yana nuna masu sannan yace "Wata waya muka yi tracking muka gano tana cikin gidan nan" Badiyyah jiki na rawa tana nuna masa wayarta tace "Wallahi waya ta ce wannan ku duba ku ga" Wani ɗan sanda ya daka mata tsawa yace "Kar ki rena mana hankali ke, bayan wayar taki wani wayar ce a gidan nan kuma?" Badiyyah tana zare ido tace "Waya kuma? Sai ɗan karamin wayar kakata fa wllhi" Hajja dai salati kawai take ta kasa zaune ta kasa tsaye ko ina na jikinta na bari, Wani firgitattcen tsawa da police man din yayi ma Badiyyah sai da ta kusa sakin fitsari yace "Idan kika bari muka shiga muka dauko wayar da kan mu to baza ki ji da dadi ba" Nan suka sanar mata sunan wayar har da color din wayar Badiyyah ta hadiye wani abu da kyar ganin babu wasa fuskarsu ga wani har yana kokarin kai mata mari tace "Yana daki bari in dauko maku" Bin ta suka yi har zuwa cikin dakin ta dauko wayar wanda farashinta zai yi miliyan daya da rabi suka amsa a hannunta suka kado ta parlor, Hajja salati take har a sannan tana zaga Parlon babu wanda ya bi ta kanta aka saka Badiyyah dake rusa kuka a gaba suka bar gidan. Abba na zaune parlor tare da Mama Ladi dake cewa "Ni kaina Mamuda wallahi na gaji da koke koken nan da Ammi take ba dare ba rana kan yarinyar nan Mera, ka tambayi su Mashir babu abinda bana gaya mata don dai ta kwantar da hankalinta amma duk a banza, zuwa yanzu ya ci ace ko mutuwa Mera tayi Ammi ta sa ma ranta dangana kuma haka balle er banzan na can in an bibibiya hankalinta kwance tana sabgogin gabanta mu kuma ta bar zuciyoyinmu cikin walagigi, ni da ba don ma kar ku kullaceni ba da sai ince dama ance tsintattciyar mage bata mage, Mera ta nuna cewar lallai da gaske mu ba danginta bane shi yasa ta shiga duniya kanta tsaye ko duba irin kyakkyawan rikon da aka mata na shekara 23 bata yi ba duk ta mance wannan halaccin, to ni ko Allah ya isa na mata sai ya bi ta duk inda take wllhi, kuma haƙƙin Ammi bazai bar ta ba a dubi mugun damuwar da ta jefata ciki fisabilillah, to shine nake son baka shawara Mamuda anya baza ka dau Ammin nan ko Saudia ne ku je ku kwana biyu ba ko Allah zai sa ta samu salama a zuciyarta, ni wallahi tsoro nake kada ciwon zuciya ya kamata tunda dama tana da hawan jininta duk mun sani, kaga ban ma san zaka kawo min maganar ba ina ta son in samu lokaci in zaunar da kai ince maka gaskiya a duba lamarin Ammi ashe kai ma hakan na damunka bawan Allah" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan Mama, shawaran da kika kawo ma yayi gaskiya, in sha Allah zuwa nan da sati daya sai mu tafi Saudi Arabia kawai" Mama Ladi tace "Yauwaaa Allah maka albarka Mamuda, daga nan sai ku saka er banzan yarinyar a addu'a Allah ya karkato da hankalinta gida, ai gantalin ya isa haka kuma, ni dai kafin ku tafi dama kar ka manta kajin firiji sun kare, er mantinar ma duk Ammi nake juye ma a kofi in zuba mata madaran gwangwani duk sun kare su ma, kasan kuma babu dadi a tafi a bar gida babu isasshen kayan abinci" Bude kofar Parlon aka yi duk suka juya, Hajja ta shigo tana rusa kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mama Ladi ta mike tace "Mun shiga uku mutuwa Badiyyar tayi??" Cikin kuka Hajja tace "Yan sanda ne suka zo suka tafi da ita muna zaune parlor ba laifi ba komai, yaushe rabon ma da ta fita ko nan da gate Marainiyar" Abba da ya mike shi ma yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" [7/21, 2:40 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mama Ladi dake zaune Parlon Ammi ta maida cup din shayin gabanta gefe da sauran bread din da ya rage tana kallon Hajja da ta kasa daina kuka kamar ranta zai fita, ta marairaice tace "Yaya ki sa ma ranki salama don girman Allah, wallahi kukan nan naki ya sa na kasa nutsuwa in ci abinci in koshi duk hankalina ya rabu, tunda Mamuda ya ce zai yi duk iya bakin kokarinsa don ganin an sakota ai kema kinsan zai yi hakan, kwanaki da suka tafi dake ba waya kawai yayi aka sako ki ba ko kin manta ne...." A fusace Hajja tace "Ladi ki shiga hankalinki ki fita harkata kar ki sake cewa za ki min wata magana, ai da er ki ko jikarki aka shigo har gida aka dauke baza ki samu damar hada katon kopin shayi da bredi ki sa a gaba kina ci ba, rayuwa ce fa Ladi, kuma kowa yayi da kyau zai ga da kyau" Mama Ladi ta saki baki tana kallon Hajja da mamaki, can tace "Ka ji yaya da wata magana dai, sai in ki cin abinci ina jin yunwa saboda yan sanda sun tafi da Badiyyah?? ayi magana fa ta gaskiya domin Allah? Shi ciki ina ruwansa da abinda ke faruwa shi dai ba kawai a fita hakkinsa a sallamesa ba, ita kanta Badiyyar yan sandan baza su bar ta haka ba sai sun bata abinci a celf balle ni da nake gida, kaji fa yaya da wata magana jama'a, shi ciki meye nasa a wannan lamari da za a tauyesa?" Ammi dai dake Parlon zaune sai kallonsu kawai take bata ce komai ba, a fusace Hajja tace "Ga ki ga abinci Ladi... Kiyi ta ci ba komai rayuwa ce" Mama Ladi ta mike ta dauke shayinta da sauran bredi ta nufi dakin Ammi tana cewa "Ji min dai fadan rashin gaskiya kiri kiri wai kar in ba cikina haƙkinsa don an tafi da Badiyyah, a ina aka taɓa haka, ba sai mutum ya ci ya koshi zai samu karfin jajanta lamarin ba, ni dai ba ruwana" Daki ta shige don har Hajja ta bata mata rai, murya can kasa tace "Ina ruwana da wata Badiyyah ma dai tukun, ban da dai neman magana irin na Hajja, Mera ma da bamu san inda take ba bai sa mun hana cikinmu abinci ba balle wata Badiyyah da muka san inda aka kai ta" Ammi na kallon Hajja cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Hajja, tun da yace zai yi duk yanda zai yi in sha Allah a daren nan za a gama komai ta dawo gida, ki kwantar da hankalinki don Allah" Hajja na kuka tace "Toh Allah ya sa Ammi, Allah ya dubi maraicin yarinyar" Abba na zaune parlonsa Maheer ya shigo ta dalilin kiransa da Abban yayi, ya zauna kan kujera Abba na kallonsa yace "Wayar wani babban mutum fa yarinyar nan taje ta dauka babu batun bail yanzu haka, anya kuwa yarinyar nan kanta daya bata da wani mental problem?" Maheer yayi shiru yana kallon Abba yana jinjina abinda Badiyyah tayi a ransa, Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Gaskiya an ɓata rayuwar yarinyar nan kawai, abun nata sai gaba yake, ya kai har da dauke dauke yanzu take, ko kwana goma ba ayi ba taje gidan matarka tayi mata sata wanda ya kai su ga fada har ta fasa mata kai, yanzu kuma wayar mutane taje ta dauko me tsada aka yi tracking, wannan wace irin rayuwa ce?" a ran Maheer tunani ya shiga yi don ma Abba bai san duk adadin gurmin da ta hada a yan watannin nan ba, iya wanda kawai ake gaya masa ya sani, wanda da zai san har da sa hannunta wajen barin Mayraah gida da ma fasa auren Mayraah da ko bin ta kan case din nan bazai yi ba, dama shi tun da yaji an zo an tafi da ita ko bin ta kan issue din bai yi ba don abinda ya damesa ma ya ishesa, duk inda ma za a kai ta a kaita for all he cares ba kuma abinda zai tofa a lamarin, Abba ya kara sauke ajiyar zuciya yace "Sai dai zuwa gobe da safe kuma mu ga abinda hali zai yi, amma wannan ba karamin case bane gaskiya, don sun ce sai me wayan ya zo yana Abuja, to wa yasan sanda zai zo" Maheer yace "Allah ya kyauta" Abba yace "Ameen" Wayarsa dake ring ya dauka ya ga Hajiya Amina ke kiransa, Maheer ya mike ya fita daga Parlon, this past days kawai karfin hali yake yi, rashin Mayraah ba karamin taɓa sa yake ba, it's weighing him down sosai ba kadan ba, dare daddaya ne baya mafarkinta idan ya kwanta, downstairs ya dawo ya zauna ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido missing his lil sis, he misses her so badly, ya fi minti sha biyar zaune parlon ya ji muryar Mama Ladi ya bude ido yana kallonta, Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Ya ake ciki, inji dai Mamuda bai samesu a wayar ba su yan sandan" Maheer ya gyara zama a hankali yace "Wayar wani babban mutum ta dauke, ba ma batun bail yanzu maganar da ake" Mama Ladi ta gwalo ido tace "Wayar babban mutum? Eh lallai Badiyyah ta shahara sauran kawai ta fara yawo da makamai, nan ko kakar tun dazu ta ishi kunnemu da kuka wai da kyar ba sharri aka laka ma Marainiyar ba ni ko a raina ina ta tunanin anya Hajja ba bakinsu daya da Badiyyah ba kuwa? Da kyar fa in ba ita take kai ma kayan satan ta ajiye mata ba, sannan don girman Allah kai dai ka ja bakinka kayi shiru kar ka wani ce ma kowa ance babu beli wllh hanamu bacci tsohuwar nan zata yi daren yau don gaskiya yanzu haka ma bacci nake ji kada a shiga hakkina akan abinda bai shafeni ba, yanzu haka ina komawa sama shimfida zan yi in kwanta ince mata Mamudan bai dawo daga caji opis din ba" Daga haka tayi wucewarta kitchen zata kai cup din shayi.... Still wajen karfe sha daya Maheer na parlor Ammi ta sauko downstairs zata shiga kitchen ta hado ma Abba shayi, Ammi na kallonsa a hankali tace "Ita waccen dake asibitin an sallameta ne da na ganka a nan" Maheer ya girgiza kai yace "Sai gobe za a sallameta yan uwanta na asibitin, amma Ammi na so kawai taje gidansu daga asibitin don ina bukatar space, but Abba ya hana hakan ni kuma gaskiya i can't stand the sight of her a yanzu" Ammi dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta wuce kitchen kawai. Kamar kullum yau ma karfe bakwai na safe Mayraah ta fito daga daki bayan tayi shirin tafiya aiki, kitchen ta tafi ta dafo ma inna ruwan zafi don for 5 days now ita ke kai mata ruwan zafi da breakfast kafin ta fita aiki, Mayraah na shiga dakin ta ajiye mata ta gaisheta, Inna da bakinta ya bude ras tace "Lafiya lau, kin ga yau fes na tashi bana jin ciwo a ko ina alamar guban ya sakeni" Mayraah tayi murmushi tace "Haka ake so dama inna Allah ya kara maki lafiya" Inna tace "Ameen, ai da so suka yi ace na mutu su hade har gadona, ni da nasan komai" Mayraah dai murmushi kawai take tana hada mata shayin, Inna tace "Allah maki albarka ke dai, naji wai aiki kema kike a asibitin su Halilu ko?" Mayraah tace "Eh" Inna tace "Toh Allah ya baki sa'a, kuma Kinga yaran gidan nan ki bar sake masu fuska kar su raina ki yanda suka raina ni basu da mutunci kwata kwata ya yan jaraba ne ga uwar bata kwabarsu" Mayraah dai sai murmushi take tace "Bari inje kar inyi latti Inna" Inna tace "Toh maza ki tafi Allah ya tsare" Mikewa tayi ta fita, bata tsaya tayi wani breakfast din kirki ba don ka'idar asibitin karfe takwas ne, sallama tayi ma Ummi ta fita gidan, kwana biyar yau basu hadu da Dr Khalil ba sun je wani workshop Lagos, Ta fito daga wani ward downstairs wajen karfe sha daya Dr Balogun ya shigo Reception, tare da shi aka tafi workshop din, nurses dake reception suka hau gaishesa suna masa sannu da zuwa yace "The MD is around, so u have to compose ur selves...." Daga haka ya wuce sama, Smartly dressed in black suit with white shirt ya shigo Reception din hannunsa rike da laptop dinsa, Mayraah ta bi sa da ido, gaba daya nurses din suka dinga gaishesa da ladabi kamar sun ga wani prominent person, yayi wucewarsa sama bayan ya amsa a takaice without looking at any of them, Dr Khalil dai na biye da shi a baya holding on to his laptop too ya daga ma nurses din hannu, Hafsat ta kalli Mayraah dake kokarin ajiye file din hannunta ta dawo ta zauna tayi kasa da murya tace "Wai shi ne me asibitin?" Hafsat ta buda ido sosai tace "He is the managing director" Mayraah bata sake cewa komai ba, bayan few seconds ta sake kallon Hafsat tace "But he is a foreigner?" Hafsat tace "Wallahi ban dai sani ba, amma ya cika jaraba mutumin, and he is a no nonsense, kowa shakkarsa yake" Da sauri Mayraah ta mike bayan ta tuna akwai wata patient da Dr Hamid yayi assigning dinta ta sa ma ido, ward din ta nufa to check on the patient, bayan azahar Mayraah ta tafi office din Dr Khalil zata kai masa wani file, gaishesa tayi ya amsa yace "Ya kwana biyu, ya aiki?" Tace "Alhamdulillah, how was the trip?" Yace "So stressful, nan da wata daya za mu koma in sha Allah" Mayraah tace "To Allah ya kai mu" Yace "Ameen, just that you have to be very careful cause or Director will be around har zuwa next workshop kafin ya koma, don haka ki zama diligence kan aikinki kar ki bari encounter mara dadi ya hada ku it wont be funny, though bana wani jin ki tunda har Balogun yayi commending dinki" Mayraah ta zauna bata dai ce komai ba, yace "Ya su Ummi?" Tace "Suna lafiya lau" Yace "Ummi ta ban labari kun kulla kawance da Inna yanzu" Dariya Mayraah tayi, yace "To ki dai dinga bin a hankali kar ya kwabe maku" Murmushi kawai Mayraah tayi tana gyada masa kai, yace "Kin je weekend gida kuwa?" Tace "Na je" wayar kan desk dinsa ne ya fara ring, ya kalleta yace "MD na kirana, make sure kar ki tafi gida ki jirani i will drop you don nima zan je gidan" Tace "Toh" Mikewa yayi ita ma ta tashi suka fita office din tare, shi ya tafi last flour zuwa office din MD din, ita kuma ta sauka downstairs ta dau allurai a tray zuwa wani ward zata yi ma wata yarinya da aka yi admitting da safe, tana shiga ward din ta tarar Maman yarinyar na bata abincin da aka kawo masu na asibitin, sai da ta zauna ta jira ta gama bata abinci sannan ta mike ta fara hada alluran, bude kofar ward din aka yi Mayraah ta juya, sai kuma ta koma gefe tana kallonsu, MD din ne da Dr Khalil dake biye da shi a baya, Matar ta gaishesu MD din na kallonta yace "Hello Ma, is there any improvement?" Da turanci Matar tace har yanzu jikin yarinyar na zafi, sai zazzabin ya sauka sai ya sake dawowa, sannan yarinyar na zabura, MD ya kalli Mayraah dake tsaye gefe yace "Diagnostic procedure?" Haka kawai taji gabanta ya fadi ta dau file din yarinyar da ta shigo da shi ta fara budewa da sauri, lkci daya duk sai ta daburce, Dr Khalil ya amsa file din a hannunta yana dubawa ya sanar masa diagnosis din, Gyara tsayuwa yayi yace "Ita bazata iya dubawa ba sai kai" Dr Khalil yace "We have 19 more wards ahead Doctor" MD din yace "Therapeutic procedure?" Nan ma Dr khalil ya karanto masa within few seconds, MD din yace "Any medical History?" khalil ya sanar masa yana duban file din still, karasawa MD din yayi feeling the girls temperature ya duba ta da stethoscope din wuyansa, bayan few seconds ya kalli Mayraah a takaice yace "Give her the injections" Daukan alluran tayi ta nufi kusa da yarinyar zata yi mata amma sai abun yayi mata kamar bata taɓa yi ma kowa allura ba kamar ranan zata fara ga kuma kukan da yarinyar take ya gigitata, MD din ya kalli Dr Khalil a bit pissed off yace "Why is she so sluggish? Wannan ta san aikinta kuwa?" Dr Khalil zai amshi alluran ya dakatar da shi furiously yace "What for?" Mayraah ta masa wani kallon gefen ido bayan ta ɗan daure fuska, nan dai ta tsaida hankalinta waje daya tayi ma yarinyar alluran, ficewa yayi daga ward din Dr Khalil ya bi bayansa. Karfe biyar wata senior nurse ta sanar ma nurses dake reception da za su yi ma yan evening handing over cewar su jira akwai meeting, yan evening na zuwa to su yan morning za su shiga meeting din da director a meeting room dake cikin asibitin, the next day kuma kafin yan evening su tafi za su yi nasu meeting din. Mayraah ta fito daga wani ward Dr Khalil ya nufota yana kallonta yace "Kiyi tafiyarki gida kawai ba sai kin yi attending meeting din ba Ilham, beside he doesn't even have ur data for now sai na basa, after the meeting i will be coming back home too" Mayraah taji hankalinta ya kwanta don dama tun da Matron ta sanar masu da batun meeting ta rasa sukuni, ita in son samu ne ma bata son ko wani irin encounter ya hadata da wnn MD din har sanda zai koma, kawai taji kwata kwata bai mata ba she don't like him, he is rude and arrogant sannan ta ga alamar ya iya disgi, Ta langwabar da kai tana kallon Dr Khalil tace "Toh shikenan, sai ka dawo" Yace "Hope kina da cash dai?" Tace "Ehh ina da, thank you" Ko minti goma bata kara a asibitin ba ta dau jakarta ta tafi bayan taje tayi ma Nurse Hafsat sallama a injection room, tana fita nurses din reception suka fara kus kus a tsakaninsu ganin ta tafi bayan ance akwai all staff meeting, dama tun da aka lura da yanda wasu daga likitocin asibitin ke yaba mata shkkn aka fara mata hassada kiri kiri don wasu ko magana basa mata a asibitin ita kuwa ko sanin suna yi ma bata yi ba tunda ba wani surutu take ba ko hira, tsakaninta da su gaisuwa shi ma wasun su sai suyi kamar basu ji ba, asibitin da ko kwana goma bata yi cikakke da fara zuwa ba, hatta yanda Dr Khalil ke kiranta office da kuma yanda Dr Balogun ke interacting da ita ya tsaya ma da yawansu a wuya, wata nurse fa'iza tana kallon colleague dinta murya can kasa tace "Wato ita shafaffiya da mai bazata tsaya meeting din ba kin ga ta dau jakarta ta tafi, tabdi bata san MD bane, ta zata irinsu Dr Khalil da Dr Balogun ne ko Dr Hamid dake shining mata hakora, muna nan dake wallahi sai MD ya gane bata shiga meeting din ba, sai in dai basu hadu a asibitin ba wannan mayen, zan ga ko shi ma kwarkwasan zata dinga masa yanda take ma sauran likitocin, Allah Ubangiji ya sa ya disgata gaban kowa da kowa mu ga iskanci, ko su Dr Khalil din da Dr Balogun babu abinda za su iya yi in ba haka ba ya hada da su" Nurse Victoria tace "The thing tire me my sister, ke daga zuwanki sai wani feeling kanki kike kin zo kin samu mutane a waje ki dinga wani ciccin magani kina daga masu kai wai ke me kokari, who does that?" Nurse Bola dake jin su tace "Fatana kawai yana ganinta after all the meetings ya gane bata shiga ba, a nan zata ga ikon Allah" Suna hango Nurse Hafsat duk suka yi shiru. Mayraah na isa gida ta tadda Ummi zaune parlor tare da Zainab matar Khalil da kanwar Ummi warce ake ce ma Aunty Rabi'ah, tun zuwan ta gidan sai ranan taga Zainab ta zo, ta karaso ta zauna ta gaida Ummi da Aunty Rabi'ah sannan ta gaida Zainab din ma, kallo daya Zainab tayi mata ta kauda kai ta amsa, Mayraah ta mike ta shiga dakin da take, Sai da Ummi ta ji ta kulle kofa sannan ta kalli Zainab tace "Wannan wani irin amsawar walakanci ne Zainab?" Zainab tace "Walakanci kuma Ummi, ta gaisheni kuma ai na amsa" Aunty Rabi'ah tace "Wai Ummi har yanzu bata samu gidan bane, last week da na zo ce min kika yi gida take nema fa, wannan ko sabon gidan da aka gama ginawa take so ya ci ace ta samu yanzu dai" Ummi tace "Bata samu ba, kuma baza a samun ba ma" Aunty Rabi'ah ta kyabe baki tace "To Allah ya kyauta" Har bayan magrib Mayraah bata fito daga daki ba, cause impression din Zainab duk sai yayi weaken dinta gaba daya, Mimi ce ta shigo dakin tana kallon Mayraah tace "Aunty Ummi tace in kira ki" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi daga kan darduma ta fita zuwa parlor, Ummi kadai ce zaune parlon, Mayraah tace "Ga ni Ummi" Ummi tace "Naga baki debi abinci ba" Mayraah tace "Ina jiran ayi isha ne" Ummi tace "To ai lokacin ma ya gabato, Inna na tambayarki nace kin dawo kina hutawa ne a daki" Mayraah tayi murmushi dai dai nan aka yi sallama kofar parlon, Ummi ta daga kai tana kallonsa da mamaki tace "Aa... kai kuma daga ina haka? 5 weeks din kenan?" Juyawa Mayraah tayi gabanta ya fadi lokaci daya ta dauke kanta da sauri. [7/22, 12:58 PM] Khaleesat Haiydar💖: Karasowa cikin parlon yayi yace "Ina wuni Ummi" Ummi tace "Lafiya lau, ko dai dama baka tafi ba?" Ya ɗan yi murmushi yace "Ban tafi ba kuma? Bayan har vid call mun yi 2 days back Ummi" Ummi tace "To na gan ka ne kamar an jefo ka ai" Sai a sannan ya ga Mayraah da kanta ke sunkuye kamar munafuka, lkci daya murmushin dake fuskarsa yayi fading, kallon Ummi yayi ya sake kallon Mayraah, kamar tasan kallon nata yake ta daga kai da sauri tace "Ina yini" Still looking at her yace "Lafiya lau" Ummi na kallonsa tace "Bakuwa ce" Yace "Oh ohk" Barin parlon yayi zuwa dakin sa, yana shiga ya ciro waya yayi dialing number Ahmad. Gaba daya Mayraah ta kasa cin abincin da ta debo a kitchen, duk ta rasa wani tunani zata yi, shi ma wannan mutumin gidansu ne nan kenan? She still vividly remember his face, Maida abincin gefe tayi ta jinginar da kanta da gado tsabar yanda ta zama confuse. Ana idar da isha mai aikin gidan ta zo tace mata Inna na kiran ta, ta mike ta saka hijab dinta ta fita, babu kowa parlor ta shiga dakin Inna da sallama murya can kasa, sosai gabanta ya fadi ganin Zainab, Dr Khalil da shi mutumin da ko sunansa bata sani ba su ma suna dakin inna, ta karasa ta zauna kasa tana kallon Inna tace "Inna ina yini?" Inna tace "Lafiya lau, naji shiru shiru baki shigo kin zubo min sabon ruwa a flask ba shine nace ko kema kin fara canza hali ne, ko kuma yan gidan sun fara canza maki ra'ayi" mikewa mutumin yayi ya fita daga dakin, Mayraah tayi murmushin karfin hali tana kallon Inna tace "Bari in kawo maki" Zainab dai sai danna wayarta take, Mayraah ta dau flask din ta fita daga dakin, Dr Khalil ya mike ya fita Zainab ta bi sa da kallon gefen ido. Mayraah na kitchen bayan ta kunna gas zata daura ruwan flask din aka bude kofa, ta juya da sauri ya shigo yana kallonta yace "U told me admission kika samu a Abuja? Aikin me kuma kike yi a asibiti yanzu?" Kallo daya tayi masa ta dauke kai ta ci gaba da abinda take tace "Admission din bai yiwu ba" yace "Why did u change ur name from the Mayraah u said at the hospital to Ilham?" Ta kallesa tace "Kaga kai ma ba dai dai ka fada sunan ba yanzu haka, so sbda irin wannan issues din yasa ake kirana Ilham most of the time" Yace "Really?" Tace "Yeah" Yace "Ohk, welcome to our home Ilham" yana fadin haka ya juya ya fita ta bi sa da kallo, wani boyayyen ajiyar zuciya ta sauke ta ci gaba da abinda take, ko da ta je kai ma Inna ruwan zafin ta tarar har Zainab da Dr Khalil sun tafi gida, ita ta ga kamar ma shakkar matar tasa yake wai ko magana bai mata ba saboda Zainab din na wajen, Inna na kallonta bayan ta ajiye flask din tace "Kin ga jikana Ahmad ya dawo daga kasar turawa ko, to shi ne babba a gidan kuma sa'annin juna ne da Halilu, shima kuma Halilun ɗan gida ne duk da ba jininmu bane shi amma ya zama ɗan gida, sai wannan mata da ta bari tayi kiba dazu da kika shigo tana zaune can tana latse latsan waya sunanta Zainab yanzu haka tana da yan biyu mata, saboda yabawa da kyawawan dabi'un Halilu, marigayi ubanta ya ba Halilun auren Zainab, kinsan ni na haifi uban nata, Allah dai ya ji kansa, Bayan Zainab sai yan biyu maza Hassan da Hussaini kullum sai su zagaya bayan windan nan su isheni da buga kwallo wai kar in huta, sai figgiyar yarinyar nan Fatima bata da aiki sai raye raye, duk Zuwaira ce ta haifesu, in ma kika ce ba ita ta haifi Halilu ba to ranta baci yake" Mayraah dai sai kirkiran murmushi take don ta kagu ta bar dakin, daga karshe ta samu ta sulale tace mata zata je tayi wanka. Musharraf na kwance dakinsa da safe Mami ta shigo, yayi mata kallo daya ya kauda kai, mancewa ma yayi bai kulle kofar ba bayan ya dawo masallaci, ta karaso cikin dakin ta zauna gefen gado tana kallonsa tace "Musharraf" Ya kalleta bai dai ce komai ba, ta kai hannu forehead dinsa tayi kasa da murya tace "Yanzu baza ka cire ma kanka damuwar nan ba Musharraf kayi facing reality" Ya ki kallonta balle yace komai, ta sauke ajiyar zuciya tace "Ta shi mu je kayi breakfast" Mikewa zaune yayi ya matsa daga kusa da ita yace "Mami duk ke kika ja wannan abun, u caused everything, da kin bari mun yi aure tun wancan lokacin she wouldn't have gone missing now, yanzu wa yasan halin da take ciki a inda take" Mami tace "Musharraf ita 'ya mace komin rintsi ban ga dalilin da zata bar gidansu ba ko ince gidan da ta taso, bata da wani hujjan da zata ce ta bar gida, ni fa tunda yarinyar nan ta iya tsallaka kafa tayi tafiyarta har aka zo ana zargin ka akayi arresting dinka naji ta fita a raina bazan boye maka ba, who knows the life she's living now tunda ta gwammaci ta shiga duniya tayi rayuwarta..." Musharraf da yaji haushin furucin Mami har ransa yace "Mami kika san wani pressure yasa ta tafi? She is so young for all this that is happening to her, she can't think straight, so ake yarinyar ta kamu da depression, she is just 22 fa Mami" Mami tace "Ni dai in za ma ka cire ta a rai ka ci gaba da harkokin gaban ka is better u do so, don babu aure tsakanin ka da wannan yarinyar just put that in mind, in kuma har ka mance abinda guardian dinta suka mana a police station sai in ji, it's simple idan har zaman kasar ma baka so to ka tafi Canada ka samu Daddy...." Musharraf ya katse ta yace "Waye Daddy? Mami pls ki daina hadani da gayen nan, i have no business with him" Mami tace "Shi ɗan uwan naka zan daina hadaka da?" Musharraf ya sauka daga kan gadon yace "Ɗan uwana that is happy with what i am going through, he is happy with my downfall, ko sau daya bai taɓa kirana duk wannan abubuwan dake faruwa ba" Mami tace "To saboda me zai kiraka, kai kiransa kake Musharraf?" Bai sake sauraronta ba ya fice daga dakin. Maheer na zaune parlon Ammi yayi kasa da murya yace "Ammi yau za a sallami Haseenah daga asibiti, so Abba insisted in kawota gidan nan har ta karasa samun sauki" Hajja da ke zaune parlon hannunta rike da carbi ta dago da sauri tana kallonsa jin abinda yace, Aunty Mariya ma da ta zo jiya da mai gidanta da ya zo yi ma Hajja jaje ta kalli Maheer da mamaki, Hajja tace "Wani gidan? Wai ci gaba da zama da matsiyaciyar nan zaka yi kake nufi Maheer? Ko dai baka da kai ne? Ita Hasinar kake mararin dawowa da ita har zaka kawota gidan nan?" Ammi dai bata ce komai ba, Hajja ta kalleta ta hade rai tace "Ya kika yi shiru Ammi? Kema kin goyi bayan ta dawo ya zauna da er matsiyatan kenan tunda har kika yi shiru" Ammi ta kalli Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "Hajja ba daga ni bane, nima na so nuna ma Alhajin hakan amma yace lallai Maheer bazai rabu da ita ba saboda ɗan matsalar nan da aka samu, shi yasa kawai na hakura na ja bakina nayi shiru" Hajja na gyada kai tace "Eh lallai, dole kice ɗan matsala tunda ba ke aka kai Caji opis ba aka ci ma mutunci aka walakanta ba ko shi Mamudan, ae ni aka taɓa dama ba ku ba, karshen biyayyar da kike ma Mamuda naga sakayya ya maki da kishiya ai, ke uwar yan bin miji, wato baza ki iya nuna masa ke baki yarda ba an ci mutuncin uwarki shine kika yi shiru kika kyale hukuncin da ya yanke, to ba komai ai rayuwa ce" ita dai Ammi kanta na kasa, mikewa Hajja tayi tana kallon Aunty Mariya tace "Ni ai sai in bar gidan, dama banda lalura da damuwar da yayi min yawa ban san halin da yarinyar mutane ke ciki ba ga dangin ubanta sai zarya suke mana me zai zaunar da ni a gidan surki har zuwa yau, ai an san ba halina bane wannan, ki tashi mu je Mariya dama zuwanki kawai nake jira kuma jiyan baku iso da wuri ba" a hankali Ammi tace "Aa kiyi hakuri Hajja yanxu haka fa Alhajin suna hanya da Badiyyar mun yi waya da shi yace an gama komai in Allah ya yarda yau zata dawo gida an rufe case din" Ko rufe baki Ammi bata yi ba Badiyyah ta shigo parlon, Hajja ta saki salati ta fashe da kuka ta tafi da gudu ta rungumeta tana kiran sunanta, Ammi dai sai kallon Badiyyah take ganin yanda ta rame tayi bakikirin kamar ba ita ba, ita kanta Aunty Mariya sake baki tayi tana kallon Badiyyah, Hajja na kallonta daga sama har kasa cikin kuka tace "Sannu Badiyyah, sannu, Allah Ubangiji ya saka maki wannan abu da aka maki, Allah ya saka maki" Aunty Mariya tace "Allah ya saka mata fa kika ce Hajja? Yarinyar da ta dauke wayar mutane me tsada ne zaki dinga yi ma wannan addu'ar? Maganar da sai da na kai zuciyata nesa na iya sanar ma mai gidana saboda kunya, kuma ke nan har kullatata kika yi ban zo ba, sata fa Hajja? Gaskiya wannan ba karamin abun kunya Badiyyah ta ja mana ba ta ja ma kanta, me ta rasa da zata jefa kanta cikin wannan mummunan hali na satan kayan mutane?" A mugun fusace Hajja ta juyo zata yi magana sai ga Abba ya shigo da sallama, Hajja ta koma ta zauna tayi kasa da kai don dama da hijab dinta a jiki, Abba ya zauna ya gaida Hajja, Hajja ta amsa tana masa sannu da kokari, Aunty Mariya ta gaida Abba ya amsa, sannan yana kallon Badiyyah on a serious note yace "Ke bude kunnuwanki ki saurareni" Badiyya dake rakube jikin Hajja ta daga kai tana kallonsa yace "Kin ga sati dayan nan da kika yi hannun hukuma? To ya kamata ya zame maki darasi a rayuwarki, in har baki yi hankali ba a sati dayan nan to ko baza ki taɓa yi ba, da girmanki da hankalinki ban ga dalilin da zaki dau wayar mutane da sunan sata ba, me kika rasa da har kika ji sha'awar yin sata Badiyyah?" Hajja tayi kasa da murya tace "Mamuda kilan dai akasi aka samu, amma ni nasan halin Badiyyah wallahi sata ba halinta bane bata taɓa daukar min ko kwandala ba tun da ta taso" Tana fadin haka Badiyyah ta fashe da matsanancin kuka tace "Abba kawata ce fa ta bani ajiyar wayar ban san sato shi tayi ba" Abba ya daka mata tsawa yace "Wato bakin ki bazai mutu ba, da aka ce ki fadi inda kawar take kin fada a gaban yan sandan? Maganar banza maganar hofi, ke kika saci wayar ba kawarki ba" Aunty Mariya tace "Ai mara kunya ce, sam bata da kunya, don in har tana da kunya ma bazata bude baki tayi magana ba a nan, kuma dama duk inda makaryaci munafuki yake za a samesa da daukar abinda ba nasa ba, to kanki kika ja ma abun kunya wallahi ba mu ba, sannan ga record dinki na sata can wajen yan sanda" Hajja dai ta kalli Aunty Mariya ta gefen ido bata ce komai ba, Abba ya mike kawai ya fita daga parlon don shi case din ma kunya kawai ya basa kawai babu yanda ya iya ne yayi involving manyan mutane masu ganin girmansa, ace wai er kanwar matarsa ce tayi satar waya, satar ma a hotel kawai dai bai son bude zancen ne gaba daya sai dai yayi da Ammi but he is highly disappointed don a hotel Badiyyah tayi satar wayar, ga Maheer da Usman suka ki shiga case din suka bar sa shi kadai yana ta fama for one week, Aunty Mariya na ganin fitar Abba kafin Hajja ta samu damar ce mata komai ita ma ta mike ta fice daga parlon zuciyarta na tafarfasa, Hajja na kallon Badiyyah ta mike ta dagota tace "Tashi mu je gida kiyi wanka in samar maki abinda za ki ci, ba komai rayuwa ce, wanda bai zo ba ma jiransa yake" Ammi dai sai kallonsu take cike da takaici wai er late sister dinta ce haka, yanzu da Rukayyah na da rai Badiyyah ai bazata zama haka ba, Allah ya gani tayi bakin kokarin ganin ta ba Badiyyah tarbiyar da ta ba nata 'ya yan, tarbiyar da ta ba Mayraah ta so yi ma Badiyyah amma Hajja tayi ta intruding saboda son duniya da ta dauka ta dora ma Badiyyah don maraici, haka yasa Badiyyah ta daina tsoron kowa ta daina ganin kowa da gashi tunda tasan Hajja zata tsaya mata, ko kallon banza su Maheer suka ma Badiyyah sai Hajja ta ɓata rai, wani lokacin har Ammi hakan ke shafa don sai ta fita harkanta na sati da satittika duk don kan Badiyyah, wannan dalili yasa Badiyyah na cewa tana son Musharraf Ammi tace a hakura a bar mata tunda ita tasan wacece Hajjar, amma at the end duk da hakan bata fita ba, ta dalilin Badiyyah yau gashi babu Mayraah, tunanin hakan yasa hawaye ya kawo idon Ammi, shi dai Maheer ido kawai yake bin su da shi, Hajja na kallon Badiyyah tace "Baki da lafiya ne, naga kina layi? Ko dukanki suka yi a can?" Badiyyah ta marairaice tace "Jiri nake gani, kuma...." Da sauri ta rufe baki tana tsaye inda take kamar wata er yarinya ta fara kwararo amai Hajja ta gigice tana rike da ita tana salati, Ammi ta taso ta nufo su, Maheer dai sai kallonta yake babu ko kiftawa. Mayraah na zaune ita da Hafsat wajen karfe tara da rabi sauran nurses din na ta harkar gabansu attending to patients da suka zo allura, Hafsat tace "Ko energy drink ne ki amso Ilham don kar ki zama weak anjima, naga jinin naki ya ɗan sauka kadan da na duba, kuma akwai operation har biyar yau..." Mayraah tace "Ai ba da ni za a shiga theatre din ba..." Bata rufe baki ba Dr khalil ya shigo Reception din daga meeting room, tun safe da suka shiga meeting sai yanzu suka fito, MD ma ya shigo reception din ya wuce Dr Khalil dake gaisawa da patients, a takaice ya amsa gaisuwar nurses din zai wuce sai kuma ya juya kallon Mayraah, keenly yace "Hey, i didn't see u in any of the 2 meeting, are you a staff in here?" Nan duk nurses din suka maida hankalinsu kan Mayraah, wasu farin ciki fal cikinsu suna jiran jin me zata ce, Dr Khalil ya karaso yana kallon MD yace "Wannan satin ta fara aiki, kuma...." MD ya daga masa hannu yace "She should speak for her self pls" Yana fadin haka ya maida dubansa kan Mayraah a takaice yace "Madam me ya hanaki shiga meeting?" Mayraah ta nuna masa Dr Khalil a takaice ita ma tace "He have said it all" Ba MD ba, hatta Khalil was shock at her reply, Duk nurses din ma suka saki baki suna kallonta da mugun mamaki, Khalil ya dafa shoulder din MD yayi kasa da murya yace "I spoke to you about...." MD ya dakatar da shi yace "Meet me in my office" Daga haka ya wuce sama kamar zai tashi, Mayraah dai ko a jikinta don ko daga kai ta kallesa bata sake yi ba, Dr Khalil ya juya ya bi bayan MD din, Hafsat ta dawo gefen Mayraah tana zaro ido tayi kasa da murya tace "Ke Ilham why did u speak to him that way? Baya son raini fa? He is our boss Ilham" Mayraah ta kalleta tace "How did i speak to him, tambayata fa yayi kuma an riga an basa amsan tambayar da yayi min and he is still repeating the question" Wata nurse na hararanta tace "Kina wasa da aikin ki kenan yarinya, ko baki san shine MD din duk asibitin nan gaba daya ba, ke haka aka koya maki tarbiya a gidanku, kina ganin ya fara maki magana za ki mike tsaye da sauri ba wai ki zauna kina basa amsa ba cikin isa da gadara, who are you? Ke kamar kanki na hayaki daga fara aiki last week ko, to ina me tabbatar maki idan baki yi hankali ba yau shine karshen aikinki a asibiti nan ba dai MD kika ma rashin kunya ba, kin zata su Dr Hamid da Dr Balogun ne masu fasa maki kai wai kin iya aiki ko, to MD no go area ne, da kyar idan bazai yi firing dinki yau ba" Wata nurse din ta amshe tace "Ki kyale ta mana, yara duk sun je private University sun karbi Degree sun zo nan suna raina mana hankali suna maida mu bamu san me muke ba, to wa zata nuna ma iya aiki in ba karya ba" Mayraah dai bata ko kallesu ba balle ta basu amsa, infact kamar ma ba da ita suke ba, kai ita fa ba dole sai ta bar asibitin ta kama gabanta bata son isa da izza ga nurses ma sai raina mata hankali suke, abeg she can't, Can dai ta kalli Hafsat warce da alama duk jikinta yayi sanyi don a kaf asibitin hatta likitocin kaffa kaffa suke da MD har ma fararen fatan, Mayraah ta kalleta as if whispering tace "Wai shine me asibitin ne wannan jaraba haka?" Hafsat tace "Aa, but he is in charge of everything" Mayraah tace "To su waye masu asibitin?" Hafsat tace "Ceo din ba musulmai bane kamar ma ba yan kasar nan bane, but MD is the Managing Director cause he is good at what he does, kowa shi ya sani" Hafsat ta marairaice tace "Ni tsorona kar yace zai yi firing dinki kin ga ko tanka ki bai yi ba ya wuce sama yace Dr Khalil ya bi sa" Mayraah ta kyabe baki ta dauke kanta tana wasa da farcenta, iyaka ta koma Suleja abun ta tayi ta bacci ba shikenan ba. Dr Khalil ya zauna kan kujera bayan ya gama sauraron MD yayi kasa da murya yace "Look Dr, yarinyar bata san ka bane, and satin ta daya kenan da fara aiki a nan, pls pls consider..." MD ya dakatar da shi sounding so pissed off yace "Plss I don't want to see her in this hospital nace maka Khalil, bana son in sake sauka downstairs for any reason in ganta a asibitin nan seriously, banda kai waye kaga yake kawo health worker just like that inyi employing din sa ba tare da an bin proper procedure for the employment ba, ban ga CV ba, babu interview babu komai, infact ita ban ma kai ga ce maka komai kan employment din nata da ka min magana ba kawai ka sa ta fara xuwa aiki without my consent har ka bata uniform Dr, sannan yanzu from all indications naga rude workers ka fara kawo mana asibitin, so she should leave immediately pls, bamu da vacancy" Dr Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Kai matsalata da kai saurin hawa, ka ma ki tsayawa ka saurareni" MD ya mike ya buga table dinsa yana kallonsa da kyau yace "Bazan saurareka ba Khalil, she have to leave this hospital immediately ko in kira security yanzu su fidda ta" Murmushi khalil yayi yace "Kasan er wacece?" MD ya koma ya zauna calmly as if counting his words yace "I don't care" Khalil ya mike yace "Kayi hakuri ka bata second chance pls, ni kaina nasan bata kyauta ba but she seriously needs this job, nasan kai me hakuri ne don Allah ka janye batun bazata sake aiki ba, idan ya so i can tell her idan ta tafi yau she should stay back home har sai ka bata employment din fully kafin tayi resuming" MD ya mike yace "She should stay back home, i am not employing her at all, i mean my words" Dr Khalil ya juya ya fita daga office din ya sauka floor din da office dinsa yake, yana zaune office ya kira downstairs yace a turo masa Mayraah, ba a dau lokaci ba ta shigo office din nasa tana kallonsa, sai da ya mata izinin zama sannan ta zauna, a hankali yace "Ilham me yasa kika yi ma MD magana rudely?" Mayraah tace "Did my words sound rude? Ni wallahi ban sani ba" Kallonta kawai yake, ta sunkuyar da kanta, bayan few seconds Khalil ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yace "Yanzu ki tashi ki je office dinsa ki basa hakuri politely, and be careful with ur words pls Ilham, speak to him politely kice yayi hakuri kinyi kuskure baxa ki sake ba, talk to him remorsefully" Mayraah ta zaro ido tace "Office dinsa kuma?" Khalil yace "You have to Ilham, office dinsa na last floor" [7/22, 8:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mikewa Mayraah tayi ta fita daga office din Dr Khalil bayan ya bata direction din zuwa office din MD, jingina tayi da bango tana tunanin yanda zata fara zuwa office din nasa, in taje sai tace masa me? bayan few seconds ta fara tafiya zuwa last floor walking slowly, with direction din Dr Khalil ta isa har door din office din wanda bayan shi babu wani office a wajen, tana ta tsaye bakin kofar ta kasa knocking taji an bude kofar ta koma baya da sauri, wani Dr ne ya fito ta gaishesa ya amsa da murmushi ya bar mata door din a bude ya wuce, a hankali ta saka kai ta shiga office din that was extra large, it was damn chill ga kamshin freshner da ya hadu da sanyin office din, everywhere was so organize and tidy, ya daga kai yana kallonta don bai san ta shigo ba, sosai gabanta ke faduwa ta kulle masa kofar kafin ta karaso cikin office din a takaice yace "Get out and shut d door behind you....." Mayraah ta daga kai ta kallesa, lkci daya ta ɗan hade rai ta juya ta fice daga office din ta kulle masa kofar. Ko office din Dr Khalil bata koma ba balle ta gaya masa yanda suka yi, ta sauka downstairs kawai intention dinta tayi wucewarta gida a lkcn don ta riga tayi making din mind dinta bazata sake barin komai ya dameta a rai ba, gwara ta ci gaba da lallaba low bp din da ta samu all of a sudden, she will never allow anything weigh her down cause babu kuma abinda ya rage mata bata gani ba a rayuwar nan, zata tafi inda zata dau jakarta kenan wani Dr ya ganta ya kirata zuwa theatre room, duk nurses din reception suka bi ta da kallo wasun su na kyabe baki, Mayraah na shiga theatre din taga 2 nurses already a ciki, the theatre is already set for the surgery that was going to start soon, ta saka surgeon gown da hula tayi decontaminating hands dinta ta saka gloves with nosemask, bata dai san surgery din da za ayi ba, but she will just be assisting with surgical instruments don abinda likitan ya nuna mata kenan tun shigowar ta, after few more minutes tana juyawa taga MD ya shigo theatre din gabanta yayi mugun faduwa ta dauke kai da sauri don ma dai fuskarta da nosemask, wani Dr that will not be part of d surgery yayi assisting dinsa wajen saka protective wears sannan ya fita, MD ya wanke hannuwan sa, ita dai bata yarda ta sake dago kai ba tayi facing din instruments dake gabanta. Mayraah wished Dr Salim zata dinga mika ma instruments din gabanta not MD, babu yanda ta iya don shine kan surgery din, though su ma da nasu part din da za su yi playing, fatan ta dai bazai gane ita bace duk da bata barin su hada ido take mika amsa duk abinda ya bukata babu ɓata lokaci, after working for long, tsabar yanda ta fara gajiya taje zata maida wani instrument ta dau wani kawai ya fadi a hannunta, da sauri ta durkusa ta dauka ta mayar cikin sauran yan uwansa, ba shi MD ba har su kansu doctors dake wajen where took aback da abinda tayi, nan da nan tayi realizing mistake din gabanta ya fadi, maimakon tayi sterilizing wanda ya fadi sai kawai ta hada da sauran equipment din, contaminating them also, dole aka dauko wasu instruments din nan take don ta yi contaminating dinsu kenan, at last dai suka gama operation din successfully aka fitar da patient din zuwa ward, tana ta Allah Allah ta fita bayan ta cire gown din jikinta da gloves taji Husky voice din MD dake facing dinta yace "Where is ur theatre Hygiene?" Wani Dr ya mata alamar ta sauke nosemask dinta, tayi yanda yace a hankali tana kallon MD din ba tare da tace masa komai ba, sai a sannan MD yasan ita ce a theatre din, after looking at her from head to toes kawai ya fice daga theatre din zuwa office din Dr Khalil. Maheer ya fito daga office din likita da takarda a hannunsa yana kallon Ammi dake zaune da Hajja a reception, ga Badiyyah rungume jikin Hajja tana ta mata sannu, Hajja tace "Wai ba gado za su bata bane Maheer? Tana jin jiki fa, nasan ba komai bane illa cizon sauron inda marasu tsoron Allah nan suka kai ta" Maheer yace "Sun ce ba sai an kwantar da ita ba ya rubuta magunguna za a siya" Hajja tace "To allurai fa" Badiyyah ta marairaice da kyar tace "Ni bana son allura" Ko kallonta Maheer bai yi ba yace "Ku tashi mu tafi gida" Hajja ta mike ta dago Badiyyah, Ammi zata riko Badiyyan Hajja tace "Aa bar ta kawai ki ji da kanki tunda kema ba isasshen lafiyar gareki ba" A haka suka fita Maheer na biye da su a baya, suna shiga motar Hajja tace "Gida kawai za ka kai ni, na sa Mariya taje ta min share share ta daura girkin da zata kawo mana asibiti ban ma san baza su bamu gado ba" shi dai Maheer bai ce komai ba, after 30 mins of driving ya iso gidan Hajja yayi parking, Hajja ta sauka tare da Badiyyah Ammi zata sauka yace "Ammi we need to talk" Ammi ta kallesa sai kuma ta koma motar, Tuni Hajja ta shige cikin gida da Badiyyah tana mata sannu, Maheer ya mika ma Ammi takardan hannunsa, haka kawai Ammi ta ji gabanta ya fadi, ta dinga kallon takardan kafin ta amsa tace "Na meye" bata jira cewarsa ba ta fara warware takardan, sai kuma ta kallesa da sauri tace "Ka gaya min na meye ni ba ganewa zan yi ba Maheer" Ya sauke idonsa kasa yace "She is pregnant.... 4 weeks pregnant" Ammi da gabanta ya wani yanke ya fadi ta saki takardan ta jingina da kujeran motar tana zaro ido tace "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, ita Badiyyar??" Maheer dai bai sake cewa komai ba, nan da nan hawaye ya cika idon Ammi ta dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un jikinta na ɓari, gaba daya ta rikice a motar sai maganganu take daga karshe ta bude motar ta sauka kawai ta shige gidan Hajja cikin tashin hankali, Maheer ya ja motarsa ya kara gaba, Ammi na shiga parlor ta tarar da Hajja rike da Badiyyah da ta kirba amai nan tsakar parlorn, Hajja sai sannu take mata tana cewa "To nace a kwantar dake ance min ba haka ba, ya zan musu, tun dawowarku zuwa yanzu kinyi amai yafi a kirga gashi cikin babu komai" Mama Ladi dake zaune parlon sai yamutse fuska take tace "Yanzu fisabilillahi ita yarinya ce ma da zata sako amai daga tsaye? Ko yaro yaji amai ya san inda zai je yayi" A fusace Hajja ta dakatar da Mama Ladi tace "Ban gayyato ki gidana ba Ladi? Uban me ma ya kawo ki in ba neman magana ba, yaushe rabon da ki tako cikin gidan nan??" Ammi ta fashe da matsanancin kukan takaici tace "Kin cucemu Badiyyah, kin cuce mu...." Aunty Mariya ta fito kitchen da sauri tace "Lafiya Ammi? Me ke faruwa kuma" Ita kanta Hajja kasake tayi tana kallon Ammi jin furucin da take ma Badiyyah, Mama Ladi ta mike da sauri tace "Auzubillahi wani satan ta sake yi kuma?" Ammi na kallon Aunty Mariya cikin tashin hankali duk jikinta na rawa tace "Mariya ciki ne da Badiyyah har na sati hudu, Mariya ki gaya min ta ina za mu fara Mariya" Wani ihu Mama Ladi tayi tace "Ciki fa kika ce Ammi? Cikin ɗan mutum ko me?" Ko rufe baki Mama Ladi bata yi ba suka ga Hajja ta sulale kasa. Mayraah na fita daga asibitin bayan ta isa bakin titi inda zata je ta samu abun hawa taji wayarta dake jaka na vibrate, ta bude jakar ta ga Khalil ne ke kiranta, ƙin dagawa tayi ta mayar da wayar tana duba cash din jakarta taga babu ma cash din sai dubu daya don kusan kullum idan ta fito tana siyan Energy drink biyu wani lokacin har uku saboda low bp dinta sannan tana yin transport din komawa gida shi yasa cash din bai dade mata, nan ta hau dube duben ATM card dinta bata gani ba a jakar sai na Usman kawai, tunanin inda ta jefa nata ta fara yi, ko dai ta bar shi a daki ne can gidan Ummi the last time da tayi using dinsa ko kuma ya fadi ne bata sani ba, tunanin faduwan yasa hankalinta ya tashi, ta rasa yanda zata yi gashi yau dama bata yi niyyar komawa gidan Ummi ba Suleja kawai zata wuce abun ta, can dai da ta gaji da tsayuwa ta ciro Atm card din Usman tana jujjuyawa tana nazarin tayi amfani da shi ko kar tayi a ranta, wani me adaidaita sahu ta tare tace masa inda zata cire kudi take son ya kai ta, tana shiga bayan sun yi tafiyar like 15 minutes yace "Ga wani banki Hajiya" Ta kalli bank din tace "Mu je dai, bana son cire kudi a wnn bankin din" Haka yayi ta tafiya da ita suna ta wuce bankuna da dama sai tace su je wani, har dai mai adaidaita sahun ya gaji yace "Hajiya kudin ki fa yawa yake, kar mu je muna wallahi tallahi a hanya" Mayraah tace "Ba damuwa mu je zan baka ko nawa ne" Daga karshe dai bayan tafiya me tsayi tace masa ya tsaya, ta sauka tana kallonsa tace "Amma zaka yi hakuri in cire kudin in dawo yanzu" Ya wani hade rai yana kallonta, can ya kashe napep dinsa ya sauko yanda zai dinga ganinta da kyau yace "Ina jira" Shiga bank din tayi ta tafi ATM machine din, duk da yanda gabanta ke faduwa haka ta saka ta fara cire dubu goma tukun, ai ko ya ciru, bayan nan ta sa 50k shi ma ta cire sannan ta maida Atm card din cikin jakarta da sauri ta fito ta dawo gun mai adaidaita sahun ta shiga tace "Mu tafi" Yace "Mu je ina?" Tace "Inda zan samu motar zuwa Suleja zaka kai ni" Yace "To bani kudin kawo ki nan da nayi tukun" Dubu biyar ta kirga ta basa amma duk ta kagu su bar wajen, yana amsan kudin bayan ya ga nawa ne ya tada adaidaita sahun suka bar wajen, sai kusan Magrib Mayraah ta iso Suleja a gajiye ga yunwa da take ji don har wani juya mata kanta yake, bayan ta sauka a daidaita sahun da ya kawota anguwan nasu don yace bazai shiga layin ba haka ta fara trekking zuwa cikin layin tana tafiya a hankali, tun daga nesa take kallon motar da ta hango anyi parking few houses before her's babu ko kiftawa....... [7/23, 8:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Har Mayraah ta isa dai dai inda aka yi parking motar bata daina kallon motar ba, as if tana son tabbatar da motar waye, kasa ci gaba da tafiya tayi zuciyarta na bugawa ganin an bude kofar motar alamar wanda ke ciki zai sauko, idonta na kansa har ya sauko ya kulle motar ya rungume hannu yana kallonta without blinking, ta wani hade rai ta ci gaba da tafiya kamar zata tashi sama, zata wucesa yace "Ilham" a mugun fusace ta juyo tace "Me yasa kake bibiyata? And how did u get here??" Yana kallonta directly yace "Saboda tun daga first day din da Ahmad ya kawo ki hospital baki da lafiya na gano da yawa daga maganganunki karya ne, nasan karya kike tun a sannan, u never called ur people that very night da Ahmad ya baki waya ki kirasu, wasu nambobi daban da kika san basa amfani kika yi dialing, don har yau i have the 2 numbers na karba gun Ahmad kuma ina kira inji a kashe, wacece ke? Why did u chose to say all sort of lies about so many things to me? Take a look at ur self, baki yi kama da warce tasan wani abu wai shi wahala ba a rayuwa, baki yi kama da warce ta fito daga gidan da sai an tara kudin admission kafin ki taho makaranta ba, sannan a ilimin ki da wayewarki bazan yarda cewar baki san anyi terminating admission dinki kika taho Abuja ba, show me the admission list kin ki, wani school ne kin ki fada min, ke da kika tsaya tara kudin makaranta da kyar ta yaya ma za kiyi lodging hotel me tsadan nan, har kiyi ikirarin zaki iya kama gidan dubu dari uku a Abuja, so many unnecessary lies, kin ce sunanki Mayraah kin dawo kince Ilham u think i forgot, and worst of all ke kadai kike zaune gidan da zaki shiga yanzu not with anybody kamar yanda kika yi claiming cewar gidan stepmom dinki ne, har briefing dinki labarin rayuwata nayi duk don ki zama relax and tell me a little about ur self amma kin ki, ban san mission dinki a Abuja ba, amma baki yi kama da warce ta fito daga gidan da ba tarbiya ba, you look decent and well brought up, as a medical Dr na hango depression a idanuwanki, damuwa na daga cikin abinda ke contributing na low bp dinki.... Nayi kokarin ganin kin fara aiki a hospital din ko zai canza maki thinking dinki akan abubuwa da dama da ya shafi rayuwarki amma naga ba haka bane, and kin nuna u are not even after the job, u are not desperate about it, sannan u don't mind being fired, that aside kina da enough cash a tare da ke" Mayraah ta kasa ci gaba da kallonsa nan da nan hawaye ya cika idonta, kasa daurewa tayi ta hade kanta da motar ta fashe da kuka sosai, shi dai kallonta kawai yake, can ya sauke ajiyar zuciya yace "Zan je masallaci, ana kiran sallah, ki shiga ciki kiyi sallah, idan na dawo masallaci i will call u out" Kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta ta wuce sa ta karasa gate din gidanta ta ciro makulli a jaka ta bude ta shiga ciki, sai a sannan ya dauke kai daga kallonta ya karasa masallacin da ya ji ana kiran sallah. Mayraah na zaune kan darduma tun da ta idar da sallan magrib, har sannan ta kasa daina kuka don ya famo mata ciwon da ke cikin zuciyarta, bata taɓa sa wa a rai wai zata zauna ta gaya ma wani anything about her self ba, she just want to be, bata son tana tuna abinda zai dameta, juyawa tayi tana kallon wayarta dake vibrate, can ta jawo ta daga ta kai kunne, Dr Khalil yace "Ina jiran ki" Ta sauke idonta bata ce komai ba ya katse wayar, bayan few minutes ta mike ta linke darduman ta fita waje, tana tafiya a hankali ta karasa har gun motar yana zaune driver seat leaving the door open, hakan ya sa ta zaga ta bude front seat ta shiga ta zauna ba tare da ta kallesa ba tana fidgeting fingers dinta, shi dai kallonta kawai yake, can yace "Mayraah" Ta daga idanuwanta ta kallesa yace "Tell me who u are, me ya kawo ki garin Abuja" Nan da nan hawaye ya cika idonta, yace "Assuming i have any other intention toward u kinsan bazan kai ki gidanmu ba, ko ince gidansu matata, duk abubuwan nan da kika ga nake ta kokarin yi a kanki don bana son kije ki fada wani hali ne ba don komai ba, ni mutum ne me tausayi kowa ya sani so i have no bad intention toward u, don kin gaya min wacece ke iyaka idan naga da inda zan baki shawara sai in baki kuma bazan baki shawaran da zai cuce ki ba, idan kuma taimako ne da bai fi karfina ba sai in maki, trust me Mayraah" Ta goge hawayen dake sauka idonta ta gyada masa kai, a hankali tace "Sunana Mayraah Mahmud..." Ya gyada mata kai yana kallonta, tace "I was born and brought up in kano" Sai kuma ta fashe masa da kuka yace "Kin ga kiyi hakuri, be strong and tell me what u want to tell me" Nan ma kai ta gyada masa tana goge hawayen da ya ki tsaya mata.... Mayraah bata boye masa komai game da rayuwarta ba har zuwa ranan da ta bar garin Kano, she told him every single thing, shi dai Dr Khalil kallonta kawai yake cike da tausayinta, abu biyu kadai ne yaji tausayinta a kai a duk labarin nan da ta basa, na farko wa enda take kallo a matsayin iyaye tun tasowarta bayan shekaru 22 ta gano ba su ne iyayen nata ba, he can't imagine this great disappoinment, na biyu kuma fasa aurenta da aka yi saboda rashin sanin asalinta, shine kawai tausayinta da ya ji amma ita irin upbring din da ta samu ma mutane da yawa dake tare da iyayensu basu samu kwatankwacinsa ba, ta taso cikin gatanta da soyayya ta ko ina, she lived a comfortable life har zuwa sanda calamity din nan yayi befalling dinta, can ya tallabi chin dinsa yace "Mayraah" Ta daga jajayen idonta tana kallonsa yace "Ur story is not enough to leave home, baki ma Abbanki halacci ba, ita ma Ummin baki mata uzuri ba, da kin tuna irin soyayyar da ta maki tun baki san kanki ba na tabbatar babu abinda zai yi motivating dinki ki bar gida, sannan yayyinki maza su ma baki masu halacci ba" Cikin kuka tace "May be u are saying all this because u are not in the shoe, kowa zai dinga gani kamar it's easy but u promise u it's not, it's painful, i tried my best to be fine with them amma daga karshe kawai naga idan na ci gaba da zama zuciyata zata iya bugawa at anytime, i can't stand Ammi not talking to me a gidan bayan ba haka na taso take min ba, at the end su ma yayyin nawa avoiding dina suka fara yi ai, Abba did marry because of me...." Ta kasa ci gaba ta fara wani kukan, Dr Khalil yayi kasa da murya yace "Zaki koma gida Mayraah! dole za ki koma gida" Ta share idonta tana kallonsa tace "Bazan koma ba anytime now, idan kuma kace zaka takurani i am leaving Abuja.... i promise u" Da mamaki yake kallonta, can yace "To ke yanzu halaccin da zaki masu kenan? Kika san halin da suke ciki bayan barin ki gida?" Tace "Ba halaccin da zan masu ba kenan, i will never forget their good deeds and they still remain my parents har ko da yaushe, bani da kowa sama da su, kawai dai ina son in bada space ne zuciyar kowa yayi sanyi... Ina son komai ya dawo dai dai a family din, tunda ta dalilina kaga yanda abubuwa marasu dadi suke ta faruwa, i am the caused of everything, tun daga sanda aka fasa aurena abubuwa ke ta faruwa, i am blaming my self for everything" Dr Khalil yayi shiru kamar me nazari, can yace "Ya ma kika ce sunan yayan naki that is a Medical Dr?" Ta wani kallesa tace "I don't think that is necessary" Ya ɗan yi murmushi wanda iyakarsa lips yace "Ohk then, kin samu labarin fitowar result dinku na makaranta?" Ta girgiza kai a hankali tace "Bani da contact din kowa yanzu" Ya sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan" Bai sake cewa komai ba ita ma haka, and they were silent for almost 3 minutes kowa da tunanin da yake a ransa, A hankali tace "It's getting late, kuma zaka koma Abuja" Gyara zamansa yayi ya sauke ajiyar zuciya yace "Haka ne, amma don Allah ina son kiyi hakuri ki daina dawowa Sulejan nan kwata kwata saboda ke macece bai kamata ki kama gida ke kadai ki dinga rayuwa ciki ba, don't forget everyone is watching u, za a maki fassaran me zaman kanta...." Mayraah ta kallesa tace "How did u find out nan da nake?" Yace "Nace maki tun farko dama ni ban taɓa yarda dake ba ko na second daya, though confidently kike karyanki but facial expression dinki ke exposing dinki, ina me baki shawara next time ki daina karya bai yi fitting dinki ba kuma za a gano ki cikin few minutes...." Ta sunkuyar da kanta, yace "I came here through ur neighbor's Husband, yarinyar da ta rasu kwanaki a hospital, i had to trace the man's number, don ranan da za su zo daukar gawan yarinyar yayi ta kirana ban daga ba ina aiki, sai yayi min text message, so sai da nayi tracing text message dinsa sannan na samu number" Mayraah ta wani hade rai tace "To banda sa ido irin na mutane shine har yace maka ni kadai nake rayuwa a gidan nan?" Yace "Aa bai ce haka ba, ce min yayi according to his wife ke student ce a jami'a, weekend kawai kike dawowa yi a gidan" Mayraah bata sake cewa komai ba, Dr Khalil yace "And lastly yanzu idan na bar nan zan je gidan MD, i will beg him on ur behalf cause dazu bayan tafiyarki ya shigo har office ya sameni, ke da nace kije ki basa hakuri sai kika ki basa kika yi masa kerere a bakin kofa, why Mayraah..." Da sauri ta wani hade rai tace "Ta yaya zan basa hakuri bayan yace in fita daga office dinsa" Dr Khalil ya ɗan yi murmushi yace "Ai yana cewa ki fita baxa ki fita ba zaki fara basa hakurin cikin ladabi, not to just walk out don yace ki fita" Mayraah ta kauda kai, Dr Khalil yace "Ba aikin kike bukata ba sbda ke ba shi ne ma a gabanki ba shi yasa u won't mind ko kin rasa aikin da thousand of people ke nema, but i wont allow that happen sbda bana son ki sake zama Sulejan nan, ban ga alamar an maki tarbiyar da zaki zama me zaman kanta ba" Ita dai bata ce komai ba, yace "Ki shiga gida sai da safe, gobe ki shirya ki taho asibitin" A hankali ta bude motar ta sauka, sai da ya ga shigarta gidan sannan ya bar layin a ransa yana nanata sunan Maheer da ta ambata masa a labarin da ta basa, sai kusan karfe tara saura ya shigo Abuja, yana parking bakin gate din gidan MD wayarsa ya fara ring, yana dubawa yaga Zainab ce, murmushi yayi, yayi silencing wayar don yasan taga bai dawo bane yasa ta kirasa, ya lura da ita duk kwanan nan she is acting insecured akansa, ya gaisa da mai gadin gidan ya shiga, a parlor ya tadda MD with different textbooks a gabansa da laptop, Dr Khalil yace "Mun kusa fara ce maka professor fa mutumin nan" MD ya daga kai ya kallesa, Murmushi khalil yayi ya zauna yana facing dinsa yace "To ya ake ciki?" MD ya rufe laptop din gabansa yace "Next week fa zata shigo, ina ga her plan is to meet the workshop" Dr Khalil ya bude ido yace "Really, i tot kace makarantar da take lecturing za su yi commencing exams" MD yace "To haka dai ta ce min" Dr Khalil yace "Kace akwai ƙura kenan" MD ya daga kafada yace "Ita da Dr Ajay kenan, yaushe rabona da asibitin, ai ta sani" Dr Khalil yace "Lallai kam, MD alfarma na zo nema don Allah" MD ya kallesa, nan da nan ya hade rai yace "Ba dai maganar fitsararriyar yarinyar nan ya kawoka gidana ba" Dr Khalil ya girgiza kai yace "Wallahi kayi misperceiving dinta ne MD, she is so good sannan ta iya aiki" MD ya girgiza kai yace "Ban ga alama ba, wai ba ita bace ta kasa ba ma yarinya common injection ba a ward ranan, sannan muna aiki a theatre tayi contaminating mana equipments, how is she good, don Allah do not spoil my mood Khalil, kai ma kasan bamu da vacancy" Dr Khalil yace "Na sani, shi yasa nace alfarma pls" da mamaki MD yace "To ko dai budurwarka ce yarinyar nan?" Dr Khalil yayi dariya yace "Kai ma kasan daga Madam dita ai babu kari" MD ya ɗan yi tsaki yace "Wallahi i hate dealing with rude human beings, zaka takurani Khalil" Dr Khalil yace "Ka dai yi hakuri don Allah" MD ya kara jan tsaki, bayan few seconds yace "Ina CV dinta?" Khalil ya shafa kansa yace "Za a kawo" MD yace "Till then" Khalil yace "Don Allah kafin su Madam su shigo kasar nan ka bata aikin nan, kasan in suna nan it will be hard wllh" MD yace "Ka ma maida ni ban san abinda nake ba Khalil, ta yaya zan bada aiki babu CV?" Khalil yace "Ko Hafsat ba sai daga baya aka kawo ba, kuma me wuyar dama mutum yayi graduating ko" MD yace "Don Allah lokacin kwanciya na yayi, in dai yarinyar nan ne bazan bata aiki babu takardu ba, apart of takardu sai nayi interviewing dinta, kuma idan naga she is not fit for the job Billah sai dai kayi hakuri bazan bata ba kaji har na rantse, even after the interview idan tayi passing kenan she will be starting as an Enrolled nurse" Khalil yayi shiru yana kallonsa, can a hankali yace "Enrolled nurse kuma MD" MD ya fara tarkata textbooks dinsa da nufin barin parlon, Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh shikenan ba matsala, amma a fara interview din tukunna pls" MD yace "Then she should come together with an apology letter in 2 days time, gobe bani da lokacinta haka ma jibi, sai ta bari on Sunday kenan idan Allah ya sa na shiga Asibitin" Yana gama fadin haka yace "I will be going to Bed Khalil" Khalil ya ɗan yi murmushi ya mike yace "To shikenan, thank you sir, Allah ya tashe mu lafiya" Daga haka ya bar parlon. Maheer dake zaune dakin Usman sai kallonsa yake har ya rufe hand luggage dinsa, can Maheer yace "When did u see the debit alert?" Ba tare da Usman ya kallesa ba yace "Not long ago" Maheer yace "To yanzu ina za ka?" Usman yace "I contacted my account officer ya sanar min a Abuja ta cire kudin" Da mugun mamaki Maheer yace "Abuja?" Usman dai bai ce masa komai ba, Maheer yace "Yanzu Abujan zaka tafi da daddaren nan?" Usman yace "Yeah" Maheer yace "But... Ta yaya za ka fara tracing nata a garin Abuja that is wide??" Usman yace "Watch and see, i have been waiting for this day dama" Maheer ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, tun da Usman ya kirasa ya sanar masa Mayraah ta cire kudi a account dinsa yaji wani kwanciyar hankali ya zo masa don the silence is too much, shirun ne yasa duk hankalinsa ya tashi, but tunda har ta cire kudi ya nuna she is fine and doing well kilan kudin account dinta ya kare kenan, Maheer yace "But ya kamata ka fara zuwa gidan Hajja ka dubata har yanzu she is not saying anything, she is really shock" Usman ya kallesa yace "Wani abu ya faru ne da zan je dubata?" Buda baki Maheer yayi yana kallonsa don sarai yasan abinda ke faruwa duk commotion din nan da aka yi throughout yau yana sane amma yaki tofa nasa, Maheer ya mike ya dafa shoulder dinsa yace "Saboda Ammi zaka yi Usman, ni ma ba don Ammi ba i won't involve my self in this, yanzu haka can zan tafi, kayi hakuri mu je tare" Usman bai ce masa komai ba suka fita gidan a tare. Maheer ne ya fara shiga parlon Hajja da sallama Usman na biye da shi a baya, Hajja na kwance an sa mata drip sai bin kowa take da ido tana numfashi sama sama, Mama Ladi na gefenta sai fifita take mata ta tsuke baki, Ammi da idanuwanta yayi jajir ita ma tana zaune kasa har a sannan bata daina kukan da take ba, Aunty Mariya dai tayi tagumi, Abba ma na zaune parlon don ko minti biyar bai yi da shigowa ba su Maheer suka zo, Maheer ya karasa kusa da Hajja yana dubata, Mama Ladi ta fashe da kuka tace "Mashir ni dai da kawai a tafi asibiti a duba min er uwa da kyau, naga kamar karkacewa bakin nata yake kokarin yi, ita kenan gareni a rayuwar nan fa ka rufa min asiri mu tafi asibiti" Maheer yace "Ko mun je asibitin abin nan da nake shi za a mata, in sha Allah zata samu sauki" Shi dai Usman na tsaye bakin kofa, Abba ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Ammi for the first time yace "Ina Badiyyar?" Mama Ladi tace "Er iskar na daki in gaya maka Mamuda, wa ma zai bi ta kanta muna kokarin ceton ran er uwata wallahi ko sanin halin da take ciki bamu yi ba yanzu haka, kawai yanzu tunda zaratan mazan nan sun shigo kamata yayi su risketa a dakin da duka ta fadi uban da yayi mata ciki duk mu ji, tun dazu nake ce ma Ammi da Mariya su shiga su tambayeta cikin waye sun ki hankalinsu na kan lafiyar uwarsu" Abba ya sunkuyar da kai yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sai ga hawaye na sauka idon Hajja, Mama Ladi ta fashe da kuka tana goge mata hawayen da dankwali tace "Tun dazu a haka take, sai dai kawai mu ga hawaye na bin gefen idonta ni dai na shiga uku na lalace Badiyyah ta cucemu" Abba na kallon Maheer yace "Kira min ita" Maheer bai so wannan aiken na Abba ba, don shi kansa tun dazu bai sa Badiyyah a ido ba bai kuma tambayi isilinta ba ya ma zata ta gudu ta bar gidan, amma bai ma Abba musu ba ya mike ya tafi zuwa dakinta, bude kofar yayi ya shiga ya ganta kwance kasa kamar warce ta yi wata uku tana jinya da alama har yanzu ko ruwa bata samu ta kai baki ba, tana ganinsa ta rushe da kuka ta mike zaune da kyar tace "Yaya don girman Allah ka rufa min asiri ka bani magani in cire cikin nan" bata rufe baki ba ya sauke mata lafiyayyen mari yayi ball da ita yace "Ni kike ce ma in baki magani ki cire ciki?" Bude kofar yayi fuskarsa a murtuke yana nuna mata waje yace "Fita ki je ki gaya masu who is responsible kar in kakkarya ki" Jikinta na rawa ta fara rarrafe zuwa bakin kofar don ko tashi bazata iya ba, rakubewa tayi jikin pillar dake corridor din tana kallon mutanen parlon hawaye na sauka idonta, Abba da Mama Ladi sai Usman kawai ke kallonta, don Ammi kauda kai tayi haka ma Aunty Mariya da zuciyarta ke tafarfasa, Mama Ladi na nunata da yatsa tayi mitsi mitsi da ido tace "Allah ya isa tsakaninmu da ke Badiyyah, kaf zuri'a ba a taɓa dauko mana abun kunya ba sai a kanki, Allah ya isa bamu yafe ba, yanzu da wani ido za mu kalli yan ubanmu?" Sai kuma ta rushe da matsanancin kuka tace "Ba don mun zama daya da Mamudan ba shi kansa da wani ido za mu kallesa wannan abun kunya haka a pamily dinmu" Abba na kallon Badiyyah calmly yace "Who is responsible?" Ta kara makalewa jikin pillar tana zazzare ido kamar me nazarin abinda zata ce, Abba ya sake jefo mata tambayar still looking at her, ta daga kai a hankali ta kalli Maheer. [7/24, 7:34 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya wani hade rai ya daka mata tsawa yace "Baza ki bude baki kiyi magana ba kina bata ma mutane lokaci" Ta fashe da kuka a hankali tace "Wallahi Haseenah ce ta hada ni da shi ni ban san shi ba" Daga Ammi har Aunty Mariya basu san sanda suka juya da sauri suna kallon Badiyyah ba, Mama Ladi da ta gwalo ido tace "Wacece haka? Sunan fa matar Mashir naji ta kira ko dai kunnena ne jama'a? Sanisa dai da duka muka sani?" Cikin kuka Badiyyah tace "Wallahi ita ce ta hada mu, Malaminta ne shi yake mata aiki a Zaria" Salati Mama Ladi ta saki bayan ta ajiye maficin hannunta tana tafe hannu cikin kidimewa tace "Malaminta kuma?" Maheer kam kallon Badiyya kawai yake babu ko kiftawa kamar yanda Abba da Usman dake tsaye bakin kofa ma suke kallonta, Cikin rawan murya Badiyyah tace "Dama bayan an fasa auren Mayraah nace mata ina son Musharraf din ya dinga kulani, shine ta hadani da malamin wai ya iya aiki, shikenan mu ka fara waya da shi na fara tura masa dubu hamsin sai watarana yace in je Zaria zan amshi wasu turarruka da zan dinga amfani da shi, ni kuma sai nayi ma Hajja karya zan je Bichi sai na tafi Zaria wajensa" Tana kai wa nan ta kara rushewa da kuka, Mama Ladi dake ta zare ido tace "Sai aka yi yaya?" Cikin kuka sosai Badiyyah tace "Wallahi ni ban taɓa iskanci ba Haseenah ce ta hadamu da shi, kuma yace min shi ne ma yayi mata aiki har ta auri Ya Maheer, sannan ya bata asiri da ta kai dakin Ammi wai don Ammi taji ta tsani Mayraah, ita ma kuma ai tana zuwa wajensa a zaria sai da tayi aure ne ta daina zuwa wajen sa" Mikewa Mama Ladi tayi ta dafe gwiwa tana kallon Hajja da hawaye ke sauka ta gefen idonta tace "To Allah ya sa dai kunnuwanki basu samu matsala ba kina jin duk abinda marainiyar ki ke cewa, mu dai sai dai mu ce Allah ya isa lalata mana zuri'a da za ayi da shege, yau ga dai Badiyyah da cikin boka" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta rike kanta, Ammi ma kukan take sosai wani bakin ciki da takaici na taso mata a zuciya, ita dai Aunty Mariya shock ya sa ko motsi ta kasa yi a inda take zaune sai kallon Badiyyah take, shi kansa Abba kallon Badiyyah kawai yake ko kiftawa babu, can ya girgiza kai ya mike kawai ya fita daga parlon, Usman ya juya ya bi bayansa, Maheer ya kusa minti biyar tsaye parlon da tunani iri iri a ransa, can ya nufi kofa ya fita shi ma, Ammi ta mike ta bi bayansa da sauri har a sannan tana kukan takaici, tsayawa yayi har ta karaso inda yake cikin rawan murya tace "Yanzu Maheer ta yaya za ayi a cire cikin nan? Ya za mu yi yanzu ya fita Maheer?" Da mamaki Maheer ke kallonta yace "A cire fa kika ce Ammi?" Ta fashe da kuka tace "To me zance Maheer? da wani ido za mu kalli duniya? Wannan abun kunyar har ina Maheer? Badiyyah ta cuce mu, ta cuce mu wllh" Maheer ya girgiza kai yace "Ai in ma wani ya kawo shawaran a cire cikin ke me hanawa ne Ammi" Muryar Mama Ladi suka ji da karfi tana cewa "Ashe baki da kai Ammi? Ina maki kallon me ilimi ashe ba haka bane? Wani cikin za a cire? So kike Allah yayi fushi da kaf zuri'ar mu? Ga laifin zina sannan ga na zubar da ciki, to wallahi babu ruwana sai inyi ta kaina in fita daga zuri'ar nan in shiga duniya kamar yanda Mera tayi, babu zunubin shegiyar da zai shafeni ban ji ba ban gani ba, ai tunda taje ta yo cikin dole sai ta haifesa a ba Hajja ko kuma a baki ku yi raino don nasan Mariya bazata amsa ba, ni ma kuma ba ruwana wallahi, da ana canza ma tuwo suna wallahi a yau din nan da na canza pamily bakina alekum na koma wani pamilyn, yanzu zancen da nake maki wllh kunyan Mamuda nake ji tun dazu na kasa hada ido da shi" Ammi dai kuka take ta kasa cewa komai ta nemi dakali ta zauna, Maheer ya fita daga tsakar gidan kawai, a kofar gida ya tadda Abba tsaye alamar dai lamarin nan ya girgiza sa ba kadan ba, shi dai Usman na tsaye jikin gate din gidan har sannan bai ce komai ba, shi fa bai yi mamaki ba ko kadan yasan akwai ranan da za a zo wanna gaɓar in har Hajja ta ci gaba da biye Badiyyah to gashi nan kuwa an zo, Abba na kallon Maheer bayan ya fito yace "I won't decide for you Maheer, duk hukuncin da kaga ya kwanta maka a zuciya game da matarka zaka iya yankewa but... Ka tabbatar baza kayi hakan ba sai kana da kwakkwaran hujjoji da zaka gabatar ma danginta don Badiyyah ba abun yarda bace, a yau na gama sarewa da lamarinta sannan na zame hannu a duk wani abu da ya shafe ta babu ruwana, sannan zan gaya ma mahaifiyarku daga yau bana son Badiyyah ta sake takowa cikin gidana" Abba na kai wa nan ya shiga motarsa ya wuce. Mayraah na zaune kan darduma bayan ta idar da sallan asuba tana azkar dinta idonta a lumshe ta jingina da bango, wayarta ne ya fara ring ta bude ido tana kallon wayar cike da mamakin wanda ke kiranta by this time, Dr Khalil ta gani jikin screen din, ta sake duba agogo taga karfe shidda, picking call din tayi ta kai kunne hade da sallama, ya amsa yace "Good morning, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah, ina kwana" yace "Lafiya lau, i just want to let u know ba sai kin shigo hospital yau ba MD na da meeting, but just make sure karfe tara na yi ki tafi gidan Ummi mu hadu a can" Mayraah ta ɗan yi shiru, yace "Are u there?" A hankali tace "Eh ina ji" Yace "Good! Zan kira in ji ko kin tafi anjima nima sai rana zan shiga asibitin" Tace "Toh" Katse wayar yayi ya juya yaga Zainab tsaye kansa tana masa wani kallo, bai ma san ta fito parlorn ba, a fusace tace "To kar ta kuskura ta sake kai kafarta gidan mahaifiyata don wallahi zan mata rashin mutuncin da bazata taba mancewa a rayuwarta ba, ka nemi wani wajen da zaka kai ta amma in har tayi mistake din zuwa gidanmu yau din nan to zata ga ikon Allah, halan ita arniya ce da bata da iyaye har zata shigo garin Abuja namiji ya dinga accommodating dinta, kuma ko bata da iyaye ai bazata rasa yan uwa ba ko yawon bariki ta shigo yi a Abujan ne dama" Dr Khalil dai kallonta kawai yake ya ma rasa me zai ce mata, tace "Naga rainin hankalin ya kai rainin hankali yanzu, wato har kiranta kake da asuba ka gaya mata kar ta ma je asibiti saboda baza ka je ba, duk kwanan nan dama ina ta lura da take taken ka, ga wani gidan Ummi da ka tsiri zuwa kullum tunda ka kai ta can, an mayar da ni wata shashasha to my patient is finished, kuma ka sani babu yarda tsakanina da kai yanzu" Ya mike tsaye yace "Listen Zainab...." Ko sauraronsa bata tsaya tayi ba ta wuce daki kamar zata tashi sama, ya sauke ajiyar zuciya bai ma san yanda zai mata bayani ta fahimci babu komai tsakaninsa da Mayraah ba sae Kasancewarta er uwar sa musulma da baxai so ganin ta fada halaka ba, gani yayi ta fito daga daki da akwati kamar dama ta hada akwatin ta ajiye gefe abinda take jira kenan, da mamaki yace "Ina zaki Zainab?" Ko tsayawa bata yi ba ta bude kofa ta fice daga parlon, ya kalli dakin da twins dinsu ke ciki suna bacci, komawa yayi ya zauna don yasan ko ya bi ta tunda har taki tsayawa a nan ta sauraresa to a wajen ma bazata sauraresa ba sai ma dai kawai su tona ma kansu asiri, he definitely knows ba gidan Ummi zata ba gidan Aunty Rabi'ah zata dama ita ke zugata always. Tara da yan mintuna Mayraah ta fito daga gida bayan Dr Khalil ya sake kiranta yace kawai ta taho asibiti ba sai taje gidan Ummi ba kuma, wajen karfe sha daya ta shigo asibitin ta gaisa da nurses din da ta gani reception ta tafi sama zuwa office dinsa, hijab ne jikinta bata saka uniform ba, zaune ta samesa office din da twins dinsa sun cika sa da surutu shi kuma yana ta aikin gabansa, tun da ta hadu da su a supermarket ranan bata sake ganinsu ba sai yau don bata taɓa ganinsu gidan Ummi ba, ko kilan an kai su bata nan bata sani ba, ta karasa tana murmushi tana kallon kyawawan yaran tace "Su ma sun zo aiki yau ne Dr?" Shi dai kawai yayi murmushi yana ci gaba da abinda yake yace "Ya hanya?" Tace "Alhamdulillah" tace "Ya sunansu?" Yace "Fatima and Khadija, ana kiransu Ashnaah and Ashfah" Tace "They are so cute" yace "Dama zan fita, ke nake jira so u can stay with them here" Mayraah tace "Ohk, Maminsu fa?" Yace "Bata jin dadi ne" Mayraah tace "Toh Allah ya sauwake" Yace "Ameen" Yana kallon girls din yace "Za ku zauna tare da Aunty zan je in dawo yanzu kun ji? Ga cartoon zan kunna maku sai ku yi kallo, do not disturb Aunty" Ashnaah da Ashfah suka kalli Mayraah a tare, dukawa tayi tana masu murmushi ta kamo hannunsu tace "Hello cuties, yanzu Daddy zai dawo, i will keep u company" Dr Khalil ya dau makullin motarsa bayan ya sa masu cartoon a tv dake office din ya kalli Mayraah yace "Ga cornflakes dinsu da abinci a jaka if they need" Mayraah tace "Ohk" fita yayi daga office din zai tafi gidan Aunty Rabi'ah don ya kira Zainab ya fi a kirga bata daga kiran, Da ya kira Ummi kuma normally suka gaisa nan ya gane ba can taje ba kamar yanda ya zarga kawai sae bai ce ma Ummi komai ba, Mayraah bata san yaran are sharp haka ba, don cikata suka yi da surutu ta rasa wanda ma zata amsa cikinsu, bayan tafiyarsa da kusan minti talatin Ashnaah tace "Aunty i want cornflakes" Mayraah tace "Ohk" Ashfah tace "Me too" Murmushi Mayraah tayi ta tafi inda ya nuna mata jakar ta durkusa tana dubo cornflakes din a ciki, bude office din aka yi ta juya da sauri, sosai gabanta ya fadi ganinsa amma lokaci daya ta dauke kai ta ci gaba da abinda take, tana ji ya shigo office din yaran suka je da gudu suka rungumesa ya duka ya ba ko wannensu peck yana kallonsu yana murmushi yace "Where is papa?" Ashnaah tace "He is gone" Yace "And he left u 2 all alone?" Ashfah ta nuna masa Mayraah da ta mike tsaye, ya juya suna hada ido ya wani sha kunu kamar ba shi ke murmushi ba ya mike tsaye ya jefa files din hannunsa kan table din Dr Khalil, tayi gathering courage zata gaishesa taga har ya fice daga office din daga ita har yaran suka bi sa da kallo, tabe baki tayi ta zagayo ta mika ma yaran bowl din cornflakes da ta hada masu. Sai kusan azahar Dr Khalil ya dawo, duk yaran sun yi bacci ta kwantar da su kan kujera, yana shigowa ya ajiye car key dinsa ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta yayi kasa da murya yace "Me yasa baki gaida MD ba da ya shigo office din nan dazu, Why pls Mayraah?" Hade rai tayi tace "Ni gaskiya Dr bazan iya aiki a asibitin nan as far as wannan mutumin yana nan, ya tsaneni, how will i greet someone that just disappeared daga gani na, he is just too rude for my liking, sannan ya fiye nagging" Dr Khalil yace "Let me tell u something, in fa kina karkashin mutum dole za kiyi hakuri a rayuwar nan, mu ma nan duk hakurin mu ke, MD is nyc but he have anger issues sannan baya son wasa baya son raini, he is a man of principle, mun yi degree tare da shi ne shi yasa har muka ɗan saba yake daga min kafa a abubuwa da yawa" Da mugun mamaki tace "To asibitin sa ne nan din with his principality?" Murmushi Dr Khalil yayi yace "Ba nashi bane, amma he is the second in command, he is a braniac Mayraah yasan aiki sosai, i think his dad is also a Dr in the US yanzu haka, and he is an only son, dole sai kinyi hakuri da shi, ni ina maki sha'awar son ace kin zama staff a nan saboda zaki ga advantage din hakan nan gaba" Daukar jakarta tayi tace "Tun da ka dawo ni zan tafi" Yace "No, i spoke to him now, zai yi interviewing dinki, he is less busy a office yanzu" Sosai gabanta ya fadi tace "But i am not ready Dr" yace "Dole ayi inputing data dinki yau Mayraah, don gobe me asibitin nan will be around saboda next workshop da za mu je, kin ga idan bai baki employment din ba u are not a staff, sannan babu vacancy, and they will be none anytime soon" Mayraah da taji hankalinta ya tashi tace "To amma wani irin interview zai min, i don't have knowledge of how it is..." Dr Khalil ya katse ta yace "Just compose ur self, u are not dull Mayraah, i know u can do it" Bude drawer yayi ya ciro farin takarda ya mika mata yace "Apology letter, in kinje kin gaishesa sai ki basa hakuri da baki respectfully sannan ki mika masa wannan" Sake baki Mayraah tayi tana kallon takardan, can tace "Apology letter for what? Are we in secondary school?" Dr Khalil ya daure fuska yana kallonta, da tasan stress din da yayi going through yau duk a kanta da bazata ci gaba da stressing dinsa ba ita ma, first yaje shawo kan matarsa duk a kanta, secondly ko gamawa da matar tasa bai yi ba sai ga kiran MD babu abinda ya mance bai gaya masa a waya ba, yana shigowa asibitin yanzu yaje ya samu MD after almost 30 minutes of persuasion ya shawo kansa har ya yarda yayi mata interview din yau and she is here trying to complicate issues the more, Mayraah ta amshi takardan, on a serious note Dr Khalil yace "Mayraah ko zaginki yayi kice kin gode, kuma kar ki kuskura ki fito office din duk ma me zai ce maki" Ta ɗan yi murmushi kawai ta juya ta fita, ya zauna ya sauke ajiyar zuciya a yanda ya lura ma ta fi MD din girman kai amma bata sani ba, Mayraah na tafiya sama ta tsaya kofar office din MD din tana kallon sunan dake manne jikin kofar daga sama. [7/25, 7:04 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah tayi knocking din office din a hankali ta koma gefe ta tsaya, jin ba a amsa ba bayan some seconds ta sake knocking, Sai da tayi knocking sau uku sannan taji ya bada izinin shigowa, ta bude kofar a hankali suna hada ido tun kan ta saka kafarta cikin office din yayi saurin cewa "I am occupied Madam, leave and come back tomorrow 8am prompt" yana fadin haka ya ci gaba da sipping juice dake hannunsa yana operating laptop, kallonsa ta dinga yi babu ko kiftawa, a karo na farko tun barin ta gida Musharraf ya fado mata a rai, don last day da ta je kai masa project work dinta a office dinsa da yanda yace ta tafi ta dawo 5:30pm prompt ne ya shiga rotating a kanta, ganin bata bar bakin kofar ba ya daga kai ya sake kallonta ya hade rai yace "Are you daft?" Wani tsinannen kallo ta jefa masa, wanda hakan yasa ya ajiye juice din hannunsa ba tare da yasan yayi hakan ba cause he was taken aback by her reaction, tuni ta kulle kofar office din ta bar wajen fuskarta daure, har ta sauka second floor ta kasa kauda tunanin Musharraf da ya mamaye ranta wanda hakan yasa kuzarinta ya ragu, office din Dr Khalil tayi knocking ta shiga bayan yayi mata izini, da mamaki yake kallonta ya mike tsaye yace "What happened again?" Ta kirkiri murmushi tace "No, na samesa yana cin abinci ne, shine yace in bari gobe karfe takwas na safe idan Allah ya kai mu" Dr Khalil yace "Are you sure Mayraah?" Ta gyada masa kai tace "Da gaske fa, yace gobe da safe in sha Allah" Dr Khalil ya koma ya zauna yace "Ohk" Daukar handbag dinta tayi tana kallonsa tace "Na gaji, ina son in tafi" Yace "Toh ki gaida su Ummi, inna dai na gidan Baffan su Mimi, cousin din Zainab zata yi aure next week" Tayi murmushi tace "Allah sarki, pls idan twins sun tashi kace masu sai mun sake haduwa i will miss them" Yace "To zan gaya masu" juyawa tayi ta fita daga office din ta sauka downstairs, sallama tayi da Nurse Hafsat sannan ta fita haraban asibitin, zaunawa tayi karkashin wani bishiya ta ciro wayarta a jaka, a hankali ta fara dialing number Musharraf da ake samunsa not his private line dake kulle, tafi minti uku tana kallon numbers din ta runtse ido kawai ta goge ta maida wayar cikin jakarta ta mike walking slowly ta fita daga asibitin, tana taran adaidaita sahu ta gaya masa inda zai kai ta sannan ta shiga, after many minutes ride yayi parking inda tace ya tsaya sannan tace "Don Allah ka jira ni zan amshi sako ne sai ka kai ni wani wajen daban" Yace "Toh" Karasawa tayi ta shiga shagon Aminu, gaisawa suka yi da fara'a yace "Ya makarantar Hajiya" Tace "Alhamdulillah ya kasuwa?" Yace "Lafiya lau wallahi, kin ga na kwana biyu ma ban shiga Sulejan ba ni" Tace "Allah sarki, don Allah SIM card nake son zan kara siya" Yace "Toh wani network kenan?" Tace "Ko wanne, sai ka hada min da katin dubu daya" Dauko mata yayi ta ciro dubu biyar a jakanta ta basa tace "Ka saka katin waya da sauran canjin" Godiya ya mata sosai bayan ya amsa, tayi murmushi ta yi masa sallama ta koma cikin adaidaita sahun dake jiranta. Mayraah na sauka kofar gidan Ummi bayan ta ba mai adaidaita sahun kudinsa ta shiga gidan, Ahmad na zaune compound making a phone call, kawai ta ɗan masa murmushi not wanting to distract him ya bi ta da ido har ta shiga gidan, karime kadai ce a gidan bayan sun gaisa karime tace "Ai ko awa daya yan gidan basu yi da fita ba in gaya maki, kinsan aminiyar Hajiya ke aurar da er ta, to can Hajiya ta tafi da Mimi, gobe asabar ne daurin aure ranan lahadi kuma ayi taron biki, ina jin ranan lahadin za su dawo, Hassan da Hussaini kuma sun je gidan baffansu tare da Inna tun jiya, Baffan zai aurar da er sa satin nan da za mu shiga" Mayraah dake zaune parlon tana danna wayarta tace "Allah sarki" Karime tace "Ai gobe baki da aiki ko?" Mayraah ta daga kai ta kalleta ta ɗan yi murmushi, Karime tace "Sai mu je gidan bikin kawai tare, Hajiya ta ce in je gobe, ina jin bata san za ki dawo ba tunda mun san can Suleja kike weekend dinki" Mayraah tace "Zan je aiki goben in sha Allah" ta fada haka ne ba don tana da intention din zuwa asibitin gobe ba sai don kawai bata son bin karime gidan bikin, Karime tace "Allah sarki, to bari in zubo maki abinci" Daga haka ta mike ta shiga kitchen Mayraah ta bi ta da kallo, Karime zata yi shekara kusan arba'in da biyu, kuma ta fi shekara bakwai tare da Ummi sai dai taje ganin yaranta da iyayenta a kauyensu ta dawo don ta zama kamar wata er uwar Ummi, Karime na kawo mata abincin ta ajiye Mayraah tace "Nagode sosai" Karime tace "Kin ga da daddare ba sai mun yi girki ba, tun da akwai burodi kawai soya kwai za mu yi mu sha shayi don shi yallabai dama shayi yake sha da daddare" Mayraah dai ta ɗan yi murmushi ta dau plate din abincin ta fara ci, sama sama take biye karime da ta cikata da hira a parlon don duk ta kagu ta wuce daki ta saka sabon sim card da ta siyo, kiran la'asar ya sa Mayraah ta mike ta tafi kai plate din kitchen ta wanke sannan ta dawo ta tarar har Karime ta shiga daki ita ma zata yi sallah, Mayraah ta dau jakanta ta wuce nata dakin da take sauka a gidan, alwala tayi, bayan ta idar da sallah ta dau sabon sim din ta saka a wayarta, ganin ya hau ta loda katin, dialing din number Musharraf tayi da sabon Sim card din, tana ji ya fara ring sai da gabanta ya fadi, ta daura goshinta saman knees dinta har sannan zuciyarta na bugawa tana jiran ya daga, sai da ya kusa katsewa taji ya daga, shiru tayi shi ma yayi shiru bai ce komai ba, after few seconds taji ya katse wayar, murmushi tayi don tasan dama bazai ce komai ba in dai bai san number ba haka yake, sake dialing number tayi duk da a ranta tasan ba lallai ya sake dagawa ba ai kam har ya gama ringing bai daga ba, kawai ta kashe sim card din cikin wayar ta ajiye wayar ta kwanta. Mama Ladi ce zaune gefen Hajja dake jingine da bango tana zaune kan shimfidar da aka mata a parlonta wajen karfe biyar na yamma, Mama Ladi na washe baki tace "Alhamdulillah jiki ai ya fara kyau, gashi har kin kusa shanye shayin, tun jiya fargabana ta ina zan fara jinyarki idan shanyewar barin jiki ya sameki, wallahi hankalina yayi matukar tashi bazan boye ma kowa ba" Ammi dai na zaune parlon tana kallonsu, Aunty Mariya kuma na kitchen tana dama ma Hajja kunu, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "Ke fa nace maki ki tashi ki tafi gida kar Mamuda ya ga rashin hankalinmu ya sake tabbatar da mu kananun mutane ne, tun shekaranjiya fa kike nan ko mutuwa aka yi ya ci ace kin koma dakinki barin ma ga Hajja har ta fara tashi zaune ga kuma shayi tana sha, nima zuwa anjima in sha Allahu zan taho sai Mariya ta zauna tayi jinyar Hajjan da me laulayin can, don gaskiya bazan iya jure ƙarnin aman da Badiyyah take kirba mana ba, in tayi aman ƙarnin har nan malam, to a kan me, ɗa ba ɗan sunna ba ta dinga cutar mu da ƙarni, bazan iya ba wallahi" A karo na farko Hajja ta bude baki a hankali tana girgiza kai tace "A fitar min da ita daga gidana dama jira nake in gama shan shayin inyi magana, a tafi da ita duk inda za aje da ita, in ko ba haka ba in bi Mariya mu tafi kaduna ta sauke ni gidan yahanasu" Tana magana ne hawaye na sauka idonta, Mama Ladi ta saki baki tana kallon Hajja da mamaki, can tace "A fita da ita a kai ta ina Hajja? Ko dai baki gane wa nake nufi ba, Badiyyah fa nake magana, Badiyya guda fa taki" Hajja na gyada kai wani bakin ciki na kara tokare mata makogwaro tace "Ita Ladi, bazata kwanar min a gida yau ba ta tafi duk inda za ta, ni ma kaduna zan tafi gun yahanasu" Ammi tayi kasa da murya tace "To ina za ta Hajja? Da dai kin yi...." Dakatar da ita Hajja tayi cikin rawan murya tace "Wallahi tallahi bazan kwana da Badiyyah gidan nan ba yau kun ji har na rantse, dama ina ta addu'ar in samu karfin yin magana tun jiya Allah bai bani iko ba sai yanzu, to Allah ya isa tsakanina da ita, Allah ya isa, Allah ya isa wannan abun gorin da ta ja min har karshen rayuwata, duk soyayyar da na nuna mata saboda tausayin maraicinta duk jan ta jiki da nayi don kawar mata da maraici a rayuwarta sakayyar da Badiyyah zata min kenan, da haka zata saka min? ta cuce ni, ta ja min abun kunya, ta ja min abun magana, ta ja min abin gorin da har in koma ga mahaliccina...." Kasa ci gaba tayi saboda tarin da ta fara kamar zata shide tana gwalo ido, Mama Ladi tayi saurin mikewa tana kallon Ammi tace "Kin ga tun da tace a fitar mata da ita daga gidan nan bazata kwanar mata ba to gaskiya ki shiga ki temaka mata ta hada kayanta a akwati a dora ta motar Bichi ta tafi wajen dangin ubanta, haka kawai bakin cikinta bazai kashe min yayata ba in shiga uku, maza a fita da ita ba ruwana, ko kuma ni in je in hado mata tsummokaran nata da kaina" Hajja na kuka tana tari tace "Ku fita da ita ko ni in tafi, ku fitar min da ita nace" Mama Ladi ta nufi dakin Badiyyah da gudu tana cewa "Daga wannan tarin fa wani ake zare ran, wallahi ba ruwana Badiyyah ta zo ta tafi kar in rasa yayata" kwance Mama Ladi ta tarar da Badiyyah shame shame a kasa kamar mara galihu, ko bin ta kanta bata yi ba tana toshe hanci ta bude inda kayanta suke ta dinga kwaso su tana zubawa cikin akwatin da ta bude, Badiyyah sai bin ta take da ido tana sauke numfashi a hankali, tun shekaranjiya babu me bi ta kanta a gidan sai Ammi dake ajiye mata kunu a bakin kofar dakinta tayi tafiyarta, ji take kamar mutuwa kawai zata yi, komai ya dena mata dadi a rayuwar, Mama Ladi na gama cusa kayan cikin akwati tana kallonta tace "Tashi ki fita a samar maki adaidaita sahu ki tafi can gun dangin ubanki su yi jinya, mu ba yan iska bane duk ta sunna aka same mu, don haka baza mu yi jinyan cikin shege ba Allah ya tambayemu" Badiyyah ta mike zaune da kyar tashin hankali karara a kan jemammen fuskarta tace "Mama Ladi wallahi basa so na, ko a baya ba jin dadin zaman can garin nake ba don Allah ki rufa min asiri Mama Ladi" Mama Ladi bata sake sauraronta ba ta fito parlor da akwatinta, Ammi na tsaye tana kallon Hajja dake kuka hade da tari ta dage a fitar mata da Badiyyah daga gidan, Mama Ladi tace "To ni dai bani da karfin dagota Ammi ki je ki fito da ita ga akwatin nata na fito da shi, ko shatar adaidaita sahu ne sai a dauko mu biyasa ya kai ta har Bichi" Sai ga Badiyyah ta shigo parlon da rarrafe ta fashe da kuka tace "Don girman Allah Hajja ki ce ma Mama Ladi a bar ni nan bazan iya zaman Bichi ba basa sona ke ma kin sani" Wani rikicewa Hajja tayi ganin Badiyyah ta dinga tari da karfi tana nuna alamar a fitar mata da ita, Dole haka Ammi ta fita da Badiyyah compound don Hajja ta dena ganinta, Mama Ladi ta dauki akwatin Badiyyah ta bi su da shi, Badiyyah ta rike kafar Ammi tana kuka sosai tace "Don Allah Ammi kema kinsan bani da inda zan je, basa sona a Bichi, don Allah ku yi min rai Ammi" Ammi dai na tsaye ta kasa cewa komai, Mama Ladi na ajiye masu akwatin ta koma gun er uwarta Hajja tace "An fitar da ita yanzu za a daura ta a mota ya kai ta Bichin don Allah ki kwantar da hankalinki yaya" Hajja dake ta sauke numfashi da kyar Aunty Mariya na durkushe gabanta ta rike hannayenta biyu, cikin sarkewar murya tace "Mariya ki kai ni wajen yahanasu kawai" Aunty Mariya ta kwantar da murya tace "Hajja yamma yayi mu kama hanyar kaduna yanzu, ki yi hakuri gobe da sassafe sai mu tafi in Allah ya yarda" Mama Ladi ta zauna gefenta tace "Tafiyar yamma babu dadi yaya, gobe da asuba har ni sai mu je Kadunan in hankalinki zai kwanta da haka, idan ya so idan nayi kwana biyu sai in bar ki tare da yahanasun ni in dawo" Kai kawai Hajja ke gyada masu tana sauke numfashi, Ammi dai an bar ta tsaye da Badiyyah da akwatinta a tsakar gida ta rasa yanda zata yi, Aunty Mariya ta kira da wayarta dake hannunta, ba a dau lokaci ba Aunty Mariya ta fito tsakar gidan, ko kallon Badiyyah dake kwance ƙasan compound din tana rusa kuka bata yi ba ta karasa gun Ammi da ta koma gefe tana jiranta, Ammi na kallon Aunty Mariya cike da damuwa tace "Yanzu ya za mu yi Mariya?" Aunty Mariya tace "Ya za mu yi me Ammi?" Ammi tace "To ina za a kai yarinyar nan yanzu?" A takaice Aunty Mariya tace "Aa, ba dangin ubanta na Bichi ba, ko kin manta ne Ammi" nan da nan hawaye ya cika idon Ammi tace "Kar ki manta Mariya yau ace Rukayya na da rai...." Kasa ci gaba tayi saboda kukan da ya taho mata, Aunty Mariya dai tayi shiru nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta, cikin rawan murya Ammi tace "Hannunka baya rubewa ka yanke ka yar, ko mun ki ko mun so Badiyyah ta mu ce, er uwar mu ta jini ce ta haifeta gashi bata doron kasa yau ga halin da er ta ke ciki, kuma Allah ya gani mun yi bakin kokarinmu kan Badiyyah, i tried my best Mariya, my children tried their best also, ke za a ce ba a garin kike ba, Amma Allah yasan kokarin da nayi kan Badiyyah" kasa ci gaba Ammi tayi, Aunty Mariya ta goge hawayen idonta tace "Yanzu ya za mu yi yaya?" Ammi na hawaye tace "Wallahi ban sani ba, kin ga tace bata son ganinta ni kuma yanzu ba ɗa bane a gidana, i don't have that power anymore, ban san ko Mahmud zai amince Badiyyah ta koma can ba" Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni kuma kin san family house nake, bazan dau Badiyyah da ciki in fara kai ta gidana ba ya zame min abun gori gun facalolina da dangin mijina" Ammi na gyada kai tace "Haka ne, kawai yanzu daukarta zan yi mu tafi gida sai in ga yanda za mu yi da Mamuda" Aunty Mariya tayi kasa da murya tace "In har ya nuna bai amince ba ko jayayya kar kiyi da shi Ammi, ki nemi izini kawai ki kai ta Bichi gobe, nima goben za mu tafi da Hajja kadunan tunda tace baxata zauna nan ba, ga Mama Ladi tace za ta bi mu" Ammi tace "Toh shikenan" Aunty Mariya ce ta fita ta samo masu adaidaita sahu, aka saka akwatin Badiyyah a ciki, Ammi ta daure fuska tana kallon Badiyyah dake kwance a kasa tace "Tashi ki fita" Da rarrafe Badiyyah ta karasa gate din ta lallaba ta shiga adaidaita sahun, Aunty Mariya tayi ma Ammi sallama tana tsaye har adaidaita sahun ya juya ya bar layin sannan ta koma cikin gida. Ammi na isa gida dab da magrib ta sauka ta ba me adaidaita sahun kudinsa sannan ta sauko da akwatin Badiyyah ba tare da ta bi ta kanta ba ta shiga cikin gidan, Badiyyah ta sauko da kyar tana biye da ita a baya tana maida numfashi, Ammi taga motar Abba a garage alamar yana nan, Haseenah ce ta fito daga Chalet sanye da Hijab bayan ta leko compound jin an bude gate taga Ammi ce, ta sauka kasa ta karasa gun Ammi tace "Ammi sannu da zuwa" Ko kallonta Ammi bata yi ba tace "Sannu" Zata amshi akwatin hannun Ammi, Ammi ta ki sake mata tace ta bar shi kawai, tun shekaranjiya Haseenah ke gidan bayan an sallameta daga asibiti kamar yanda Abba ya umarce Maheer ya kawo ta gidan don tana ma gidan Badiyyah tayi wannan tonan sililin a parlon Hajja, kamar ance Haseenah ta juya taga Badiyyah ta shigo compound wujiga wujiga duk ta rame tayi baki, nan da nan Haseenah ta hade rai ta kauda kai, Badiyyah dake fama da kanta ko bin ta kan Haseenah bata yi ba ta shige cikin gidan da sauri don kwanciya kawai take son yi ga amai da ke taso mata, Haseenah ta ɗan yi jim, sai kuma ta bi bayansu zuwa main building din gidan ita ma, a parlor ta tadda Badiyyah ta kwanta, Ammi kuma ta haura sama, Lokaci daya ta ga Badiyyah ta mike da gudu ta shige bandakin dake parlor tana kakarin amai, bude baki Haseenah tayi da mamaki bayan ta bi ta da kallo, a hankali tace "Amai kuma??" Can dai ta juya da sauri ta fita daga parlon ta koma Chalet din da take. Ammi tayi shiru tana kallon Abba a sanyaye don maganganu kawai yake cikin fada inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, har ya kai aya, can ta sauke kanta kasa cike da karfin hali tace "Shikenan Yallabai kayi hakuri... kayi hakuri, goben sai in kai ta Bichi idan Allah ya kai mu" A takaice Abba yace "Da dai ya fi don bazata zauna a gidana ba i stand my words" Daga haka ya mike ya shige Bedroom dinsa Ammi ta bi sa da kallo wasu hawaye na sauka idonta, duk ya canza kamar ba shi ba, Abba da ko ɗaga mata murya baya yi idan yana mata magana a baya, abu ko bai masa ba idan tace haka take so to haka nan zai yi don baya son bacin ranta kwata kwata amma yanzu duk babu wannan, duk hakan na neman zama tarihi daga yan watannin nan da suka shude, he is now a changed person, tunanin hakan ya kara breaking heart dinta sosai, ta mike ta fita daga parlonsa ta koma bangarenta ta ci kukanta ta gode Allah..... Mayraah na kwance dakinta bayan isha Karime ta shigo da sallama tace "Hajiya Ilham ga can kwan na soya maki a kitchen sai ki yanki bredin da zai isheki ki debi ruwan shayi a flask ki bar ma yallabai sauran, ni zan shiga gidan makociyarmu in duba jikin er ta ta kone a kafa, to duk yau ban shiga ba" Mayraah ta gyada mata kai tace "In zan ci zan je in dauka" Karime tace "Toh sai na dawo" Mayraah ta bi ta da kallo sae kuma tace "Amma ba dadewa za ki yi ba ko?" Karime ta juyo tace "Toh akwai dae wani pim din hausa da ake yi duk ranan juma'a, wani lokacin in Ummi ta shiga ta kwanta da wuri na kan je gidan in kalla, kinsan duk an rufe tashoshin gidan nan saboda yan biyun nan maxa da yarinyar nan Mimi da basu son maida hankali su yi karatu sai kallo, to yallabai duk ya rufe tasoshin ba a kallon finafinai a gidan nan, ke baki ga tun da kika zo sae dai ki ga an kamo tashan labarai ba" Mayraah tace "Yanzu dai kallo za ki je yi kenan" Karime ta kyalkyale da dariya tace "Baxan boye maki ba shi zan je inyi gaskiya, karfe goma ake gama pim din, ana gamawa zan dawo in sha Allah" Mayraah tace "Toh... Shikenan, sai kin dawo" Karime tace "Toh kar dai ki bar kwan ya sandare" Daga haka ta fita daga dakin. [7/26, 7:51 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah ta sauko daga kan gadon da take kwance bayan tafiyar karime da kusan minti sha biyar, wayarta ta dauko ta bude second sim din da ta kashe tun dazu, ta zauna gefen gado tana ta kallon wayar as if contemplating to call him again or not to, after many minutes of thinking ta ajiye wayar a hankali ta mike ta shiga bandaki, wanka tayi ta fito, tana cikin dauko daya daga dogayen rigunan bacci da ta siya a Suleja cikin jakarta taji wayar ta na vibrate, ta dauko kayan baccin ta mike tana gyara daurin towel din jikinta ta karasa kusa da wayar tana duba me kiranta, sai da gabanta ya fadi ganin number Musharraf, ta zauna gefen gadon a hankali ta dau wayar tana kallo, har ya katse bata daga ba, ya sake kira nan ma bata daga ba har ya gama ringing, sake kira yayi this time around sai ta daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren ta ji yace "Pls who is this?" Ai bata san sanda ta zamo kasa ta zauna ba, she just realized she missed him so very much, ta kasa cewa komai zuciyar ta na bugawa, daga daya bangaren yace "I know u can hear me, pls say something...." Mayraah ta jinginar da kanta da gado a hankali tace "Good evening" Musharraf ya mike tsaye daga zaunen da yake yace "Mayraah" Shiru tayi bata ce komai ba, ya marairaice mata yace "Plss tell me kina ina Mayraah?" A hankali tace "Ina lafiya" Trying all best to be calm yace "I know, yes i know, amma plss ki gaya min inda kike trust me, tell me pls Mayraah, just trust me pls" Lkci daya ya birkice mata, Ta langwabar da kai tace "You don't worry about that" Yace "Nooo pls, Mayraah kin san halin da kika tafi kika bar ni ciki kuwa, not only me, ur brothers, ur parent, haba Mayraah, pls i am begging u ki gaya min inda kike, Baby don't u trust me?" Mayraah ta lumshe ido ta bude tace "I am somewhere far away, kar ka damu tunda ka ga na kira ka i am fine, and i just wanted to say hi...." A hankali yace "Mayraah" bude kofar dakin taji anyi ta juya da sauri taga Ahmad, kallonsa ta dinga yi don duk tunaninta idan ya ga yanayin da take zai fita sai taga ba haka ba, instead he is even walking in, dauke kanta tayi zuciyarta na bugawa tace "I will call you back" Bata jira cewar Musharraf ba ta katse wayar wondering dalilin da zai sa ya shigo mata daki duk da yanayin da ya ganta, she just tied a towel, gefen gadon ta ji alamar ya zauna, lkci daya ta juya ta kallesa tace "I am sorry, i want to dress up" Ya ɗan yi shiru yana kallonta, sai kuma ya buda mata hannu alamar what is there? Kasa motsawa tayi daga inda take zaune with shock amma taki nuna hakan a fuskarta, ko hijab dinta ta kasa yunkurin daukowa don dole sai ta tashi zata yi hakan, banda faduwa babu abinda gabanta yake gaba daya ta rasa wani tunanin zata yi a lokacin, silencing kiran da Musharraf yake ta yi mata tayi ta ajiye wayar a gefenta, kawai gani tayi ya dawo gabanta ya durkusa yana kallon idonta as if counting his words yace "I understand what u are going through Mayraah, Khalil briefed me earlier, it's sad and i get kin fito ne ki samu relieve by chilling away ur worries right? i love ur courage and braveness" Mayraah ta fara matsawa jikin gadon a hankali tana kallonsa babu ko kiftawa, a hankali tace "You are drunk" Buda ido yayi sosai yana gyada mata kai yace "Not much though, but how did u know? Ko kema kina sha ne?" Tayi murmushin da iyakarsa lips tace "Yeah" ya kara buda ido yace "Really?" Ta gyada masa kai tace "I won't mind some" Ya karyar da kai yace "Unfortunately I can't bring that home because of my Ummi, i drink only outside" Sosai gaban Mayraah ya fadi a tunaninta zai ce bari yaje ya dauko mata ne tasan na kwatanci, nan da nan hankalinta ya tashi, yayi kasa da murya holding on to her hand yace "Would u mind us spending the night somewhere...." Ta dake tace "Somewhere like??" Yace "Hotel, club, guess inn... And what have you" Tayi saurin gyada masa kai tace "Ohk, let me get dressed" Yayi kasa da murya yace "Thank you...." Bata yarda ta mike ba a gabansa, gaba daya idonsa na kirjinta, da sauri tace "Can u excuse me in shirya?" Yace "C'mon meye in kin shirya while am here" Daga ta zai yi ta wani fizge hannunta tace "Stop it" Ya mike yace "Ohk then" Jikin window ya koma ya tsaya ya rungume hannunsa yace "Ki shirya" Babu yanda ta iya haka ta mike tsaye, wani takaici ya tokare mata wuya, she was trying her best kar ta bari hawaye ya taran mata a ido, daukan kayanta tayi ta shiga bandaki ya bi ta da ido, sai a sannan hawaye ya fara sauka idonta ta jingina da bangon bandakin bayan few minutes ta saka kayan ta fito ta dau Hijab dinta ta saka, ta dau handbag dinta with her charger and phone, duk yana ta bin ta da kallo, without looking at him tace "I am done" har suka fita compound din gidan a motarsa Mayraah bata yarda sun hada ido ba, kamo hannunta yayi yana kallonta yace "or should we go for the hotel we met first?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ohk, but do u have an international passport?" Duk da tana da shi haka ta girgiza masa kai tace "Nop" Da mamaki yace "Why? Big gal kamar ki ace baki da International passport" Ta yi feigning murmushi bata dai ce komai ba, yayi kasa da murya yace "I will get you one if u don't mind, sai a maki visa ko na Uk ne don zaman kasar nan baya wani cire ma mutum damuwa a rai ga sa ido irin na malam bahaushe, u need to be far far away, i think next week zan koma i will try and see if we can make it together" Mayraah tace "Thank you" All through the ride shi yake ta surutunsa, ita kam tayi nisa tunanin da take suna isa hotel din kafin ya shiga ciki ta kallesa tace "Zan ɗan amso abu a mart din can na gaba, wait for me" Yace "Me za ki amso?" Tace "Chewing gum" Yace "Oh ok, bari in amso maki" Ta masa murmushi tace "Ai baka san irin wanda nake so ba" Yace "True" Bude motar tayi ta sauka ta kulle masa tana kallonsa tace "Not every girl that left home is a bitch, not every girl that left home is useless, don kaga na baro gida ba yana nufin ni er iska bace, kuma hakan ba yana nufin bani da tarbiya bane, i chose leaving home because of my mental health..." Tana kai wa nan tayi tafiyarta, sai a sannan wasu hawaye masu zafi suka dinga sauka idonta tana jin zuciyarta na mata zafi, ko waiwayawa bata yi ba har tayi nisa daga hotel din, tana isowa main road ta tare adaidaita sahu ta shiga ta gaya masa inda zai kai ta, har suka iso bata san sun iso ba don tayi nisa tunanin da take ga hawayen da ke ta saukan mata, sai da mai tricycle din yayi alerting dinta sannan ta sauka tana goge idonta ta basa kudinsa, tana shiga gate ta nemi kujera ta zauna, sai da tayi kukanta me isarta sannan ta ciro wayarta, missed calls din Musharraf ta gani ya fi goma, tayi dialing number Dr Khalil yana fara ringing ya daga, gaishesa tayi a hankali, ya amsa yace "Ya kike, ya gida?" Tace "Alhmdlh, are you at work?" Yace "Yeah ina night duty, Why do u ask?" Tace "Aa just want to be sure" Yace "Are you okay?" Wasu hawaye ne suka cika idonta kawai ta katse wayar, mikewa tayi taji ya sake kiranta bata daga ba ta shiga cikin asibitin, sau uku yana kiranta bata daga ba, tana shiga reception ta gaida nurses da ta gani ta haura sama zuwa office dinsa, wata nurse fa'iza ta mike da sauri ta tafi inda jakarta yake ta ciro wayarta ta fara kiran Zainab. Dr khalil na zaune still calling her line ta shiga office din ko knocking bata yi ba, yana ganinta ya mike yana kallonta, bata yarda sun hada ido ba ta zauna kan kujera, ya zagayo yace "Mayraah are you okay?" Bata san sanda ta fashe da kuka ba, ya iso gabanta da mamaki yace "Lafiya? Talk to me, me yake faruwa?" Duk da tambayoyin nan da yake jefo mata hankalinsa kawai ya tafi kan kila Zainab taje ta sameta ne a gida don not long ago ya kira Ummi tace masa tana gidan biki, ganin taki basa amsa sai kuka take ya duka gabanta yace "Plss talk to me Mayraah, an maki wani abun ne?" Bude office din aka yi duk suka juya, MD ne ya shigo, Dr Khalil ya mike yana kallonsa, Mayraah ta kauda kanta da sauri, tunda ya kallesu sau daya bai sake kallonsu ba ya ajiye files din hannunsa yana kallon Khalil yace "See me off" Dr Khalil yace "Ohk" fita yayi office din Dr Khalil na kallon Mayraah yace "I will be back right away" Daga haka ya fita daga office din ta bi sa da kallo tana goge hawayen dake sauka idonta. Dr Khalil na kallon MD bayan sun fita reception yace "Drivern ya iso ne?" MD yace "Ban kirasa ba, just drop me" Dr Khalil yace "Ni fa da na ga kayi dare na zata u will pass the night here MD" MD na mika masa makullin hannunsa yace "Ka taba ganin na kwana asibiti in ba dole ba?" Dr Khalil bai amshi makullin nasa ba yace "Sae dai mu je a motata ka bar naka a nan, tunda zan dawo asibitin" MD yace "Mu tafi a nawa sai ka dawo da shi, bazan iya jira sai kaje sama ka dauko key ba" Yana fadin haka ya bude front seat ya shiga, Dr Khalil ya zaga ya shiga driver seat, sai da suka bar asibitin Dr Khalil yayi dialing number Mayraah, tana dagawa yace "Nan da 30 minutes zan dawo in sha Allah, ki jirani" yana gama fadin haka ya katse wayar, MD dake kallonsa yace "Wato ita wannan mannerless teenager din budurwarka ce shi yasa ka dage sai ta samu aiki a asibitin nan ku jone salon ka daina maida hankali a aikin ka ko, sannan ita wannan er mitsitsiyar yarinyar har yaushe aka haifeta tayi degree? thank God ba aikin za a bata ba, kuma baza a taɓa bata ba as far as i remain the MD in here, sannan on a serious note bana son sake ganinta a asibitin nan, she is neither a staff nor a patient don haka ban ga dalilin da zata dinga shigowa ba, i will talk to the securities not to let her in from henceforth" Dr Khalil dai bai tankasa ba driving dinsa kawai yake. Bayan tafiyar Khalil da kusan minti arba'in Mayraah dai na zaune office dinsa ta jinginar da kanta jikin kujera tayi nisa tunanin da take taji an bude kofar office din ta juya duk tunaninta shi ne ya dawo, sosai gabanta ya fadi ganin Zainab ta shigo office din fuska a murtuke kamar an jefota, Mayraah ta sauke idonta daga kallonta, lokaci daya jikinta yayi sanyi, Zainab ta karaso har gabanta tana kallonta da kyau tace "Ke don kaza kazanki duk fadin garin Abuja baki ga maza yan iska mara mafada karuwai irinki ba sai mijina za ki makale ma? Baki ga matsiyata masu zaman kansu kaman ki ba sai mijina? To wai ma ke uban wa yace maki Khalil ɗan iska ne? ko kuma ance maki shi ma daga sama ya fado bashi da iyaye kamar ki? Don in har kina da iyaye ban jin zaki dinga irin wannan kazamin rayuwar da kike kamar sakakkiyar akuya a garin Abuja, baki can baki nan, baki gidan mutane, baki asibiti, baki hotel, baki Suleja da kika kama gida kike zaman kanki ko ance maki duk ban bincika ba? to bari ki ji wallahi wallahi ina ja maki kunne da babban baƙi ki fita harkar mijina, i am warning u ki fita harkar khalil, stay away from my husband kada inyi maki abinda baki taɓa zato ba a rayuwarki don wallahi ba mutunci ne da ni ba, ba ni da kirki wallahi, sannan in ba zina iyayenki suka yi suka haifeki ba to ki bar min gidan uwata ki kama gabanki ki je can ki ci gaba da rayuwar zaman kai da kike a suleja, mu gidanmu gidan tarbiya ne, sai ki wani dinga yawo da hijabi sumi sumi kamar ta kirki nan kuma lalata mazan mutane kike yi cikin Abuja, i am cutting you this first and last warning idan kuwa ba haka ba nace maki duk abinda na maki ke kika ja ma kanki, banza kawai karuwa me zaman kanta" Zainab na kai wa nan ta fice daga office din kamar zata tashi sama, Mayraah ta jinginar da kanta jikin kujeran da take zaune. Sai bayan awa daya Dr Khalil ya dawo asibitin, Mayraah na zaune yanda Zainab ta fita ta bar ta ya shigo office din, ya karaso yana kallonta bayan ya ajiye makullin motar MD kan table dinsa yace "Ki gaya min me ya faru Mayraah, why are you crying?" Shiru tayi har sai da ya dawo gefenta ya zauna leaving enough distance tsakaninsu yace "Pls say something, an maki wani abu ne kika shigo kina kuka daxu?" Mayraah ta kallesa sannan a hankali tace "Dama idan mutum ya bar gidan su yaje wani waje sai a fara masa kallon yana iskanci?" Tana masa tambayar hawaye ya cika idonta, Dr Khalil yayi shiru yana kallonta, ta fashe da kuka ba tare da tasan tayi hakan ba, tace "Ko dai nayi kama da warce take iskanci ne?" Dr Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Gaya min me ya faru?" Tace "No! answer my questions first" Dr Khalil yace "Mayraah, in our society today da kuma al'adan mu na hausa fulani duk macen da ta bar gaban iyayenta for whatsoever reason dole zata yi facing fiye da haka a rayuwa, kin ga wasu za su mata kallon warce tafi karfin iyayenta, wasu su mata kallon er iska warce idonta ya bude tunda an san dai tafi karfin iyayenta ne ya sa ta shiga duniya, don babu iyayen da za su ba ma er su go ahead ta tafi tayi zaman kanta, wasu za su mata kallon warce ke karuwanci, bazan boye maki ba Mayraah at first da na ga take taken ki nayi maki kallon warce ta zabi ta shigo Abuja tayi rayuwar shashanci ne, even the hotel u lodged in na sa maki question mark a lokacin, but at the same time u look innocent" Goge hawayen dake sauko mata tayi tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "Tell me what happened" Cikin rawan murya tace "Shi yasa Ahmad yake min kallon er iska har yake tunanin zan iya bin sa hotel mu kwana?" Khalil ya zaro ido yana kallonta, yace "Ahmad??" Ta fashe masa da kuka sosai, mikewa Khalil yayi ya ma kasa ce mata komai gaba daya jikinsa yayi sanyi Ahmad bazai taɓa canzawa ba kenan, bayan few seconds ya sauke wani ajiyar zuciya ya duka gabanta yana kallonta a hankali yace "Only this is enough for you kiji hankalinki ya koma gida Mayraah, mace in ba gaban iyayenta take ba kowa ma kallon da yake mata kenan to be frank.... You have given dem enough space na sati biyu yanzu, nasan duk hankalinsu ba a kwance yake ba na rashin ki" Mayraah tayi murmushin takaici tana share idonta bata son tace masa komai game da abinda matarsa ta shigo tayi mata bayan fitarsa, bazata so ta dalilinta happy family din su samu issues ba, tunani ne iri iri a ranta a lokacin, daren ranan a nan asibitin Khalil ya sa ta kwana, with d hope that as early as possible kafin zuwan MD zai je yayi dropping dinta, amma sai suka tashi da wani aiki da asuba tare da sauran likitocin asibitin, zuwa karfe tara Mayraah ta gama shawaran abinda zata yi a zuciyarta, tun cikin dare take tufka da warwara a ranta ko baccin kirki bata yi ba sai bayan sallahn asuba ta samu bacci ya dauketa, yanzu kuwa tana tashi ta tafi bandakin office dinsa ta wanke bakinta da mouth wash ta wanke fuskarta sannan ta fito ta dau Handbag dinta ta nufi kofa ta fita har sannan kuma su Dr Khalil basu fito theatre ba, tana sauka stairs tayi ido hudu da MD da shigowarsa reception din kenan da wasu turawa biyu sai bakin fata daya duk sanye da suit, a tare da su wata dattijuwa ce warce bata da maraba da halfcast coporately dressed in black suit with skirt da iyakarsa gwiwa, dai dai nan su Dr Khalil ma suka fito theatre da likitoci kusan hudu, gaba daya nurses gaida matar suke da ladabi, har ma da Dr's din tana amsa su cikin fara'arta da turancinta me cike da phonic, MD gaba daya attention dinsa na kan Mayraah bayan ya wani hade rai kamar bai taɓa dariya ba da ya hangota, wato a asibitin ma ta kwana kenan, Mayraah ta karasa saukowa downstairs ita ma ta gaida matar, Matar ta sakar mata murmushi tace "Helloo" Har tayi gaba ta sake juyowa tace "Are you a staff here young lady?" Mayraah ta ɗan kalli MD da ya kafeta da ido, a lkci daya ta kalli Dr Khalil taga ya nodding mata kai alamar ta ce eh, da sauri ta gyada ma matar kai kamar kadangariya, matar ta kalli baƙin mutumin dake cikin fararen fatan tace "Dr Yemi, you remember my Late moslem frnd Hajiya Amina?" Yace "Oh yes, Late Professor Amina, exactly i remembered Ma" Matar ta nuna Mayraah tace "Her replica, she just reminded me of her, may her soul rest in peace" Duk suka amsa da "Ameen" Matar tace "Ba don nasan yaranta ba kuma bata da karamar yarinya da nace ke yarinyar ta ce..." Mayraah dai sai murmushin karfin hali take tana kallon kyakkyawan dattijuwar don bata taɓa zaton tana jin Hausa ba sai gashi tayi hausa, amma Hajiya Amina da tace take replicating ya tsaya ma Mayraah cak a rai, to ko dai she is related to the Hajiya Amina tunda tace suna kama, MD na kallon Ceo din tasu da ladabi yace "Ma, You've stood for so long" [7/28, 6:22 PM] Khaleesat Haiydar💖: Da ido Mayraah ta bi su har suka haura sama da sauran Dr's din dake biye da ita za su rakata office dinta, Ceo din na hawa second stairs ta kara juyawa ta kalli Mayraah, sai kuma ta kalli MD dake bayanta tace "What is that her name again?" MD ya girgiza kai da sauri yace "I have no idea Ma'am" Ta kalli Mayraah tace "What did u say ur name is?" Mayraah da gabanta ke faduwa tace "My name is Mayraah" Ceo ta bude ido tace "Mary Ann?" Dr khalil yace "She is Mayraah Ma'am" Daga likitocin har nurses duk kallon Mayraah suke, MD dai bai sake kallon downstairs din ba, Ceo na gyada kai tace "She should meet me in my office, in 30 mins time" Tana fadin haka ta ci gaba da tafiya sauran likitocin na biye da ita, Dr Balogun yayi ma Mayraah thumbs up ya wuce sama yana amsa gaisuwan da take masa, Dr Khalil ya nufo ta ya mata murmushi yace "Good morning" Tace "Ina kwana?" Yace "Har kin tashi baccin?" Ita dai bata ce komai ba, yace "Kije office dina ki jira tunda tace ki sameta nan da minti talatin" Mayraah tace "Toh" Sama ta wuce, few of the nurses suka bi ta da kallo with enviousness and jealousy. Dr Khalil ya bude office dinsa kenan zai shiga wayarsa ya fara ring yana dubawa yaga MD ke kiransa, ya kalli Mayraah dake zaune office din ya karasa ciki yace "Yanzu za a kawo maki breakfast" Tace "Toh Nagode" Fita yayi daga office din zuwa office din MD, tsaye ya samesa office din yana jiransa, MD ya nufesa cikin fada yace "Kasan implications din da kake kokarin ja min kuwa yanzu Khalil? How on earth will i explain to the CEO that this silly gal isn't a staff here?? I told u bana son sake ganin yarinyar nan a asibitin nan you are taking me for granted, saboda tsabar bata da kunya an tambayeta if she is a staff tayi nodding kanta, waye yayi employing dinta? Wa ya bata aikin? Ko ka fara bada aiki ne a asibitin nan ban sani ba?" Dr Khalil ya nemi waje ya zauna yace "To avoid the complications u are talking about kawai kayi imputing data dinta a system yanzu MD a wuce wajen" a fusace MD yace "Never!! Bazan taɓa bata aiki a asibitin nan ba like i have already said, ko dole sai tayi aiki a nan? Ba ga asibitoci iri iri da zaka iya samar mata aiki ba, all my thought was that u will be contented with Zainab amma ashe ba haka bane, ka makale ma er cikinka kasa duk ta rainamu ko aikin bata samu ba, baza kuma ta taɓa samu ta wajena ba, watch and see" Yana kai wa nan ya fice daga office din, Khalil ya bi sa da kallo yana murmushi. Ceo na zaune babban office dinta wanda mutum sai yayi tunanin a kasar waje ne tana stamping wasu files MD ya shigo, tana ci gaba da abinda take tace "I won't be able to go round the hospital today because i will be leaving in an hour time, i have a meeting to attend, and when did u say the next workshop is in Lagos?" Da ladabi MD yace "In 2 weeks time Ma'am" Tace "Ohk, i think zan koma UK nan da kwana biyu saboda exams da yaran nan za su fara, I will be back before the Lagos workshop, Send me the names and details of all our staffs i have a little token for them, and lest i forget there will be a medical conference in the US, za mu je da staffs biyu...." Bata jira ya bata amsa ba tace "Where is the Lady i asked to meet me in 30 mins time? Did she hear me right?" Yayi kasa da kai yace "Erm... Ma'am, but" Daga kai tayi ta kallesa don duk wannan maganar da take kanta na kasa tace "Is there anything Aliyu?" Ya girgiza kai da sauri yace "No, i will get her right away" Daga haka ya juya ya fita daga office din. Mayraah na zaune office din Dr Khalil ta bude burger din da aka kawo mata with healthy toppings for breakfast sai black tea taji an bude kofa, juyawa tayi Dr Khalil ya shigo yana kallonta yace "MD yana kiranki office dinsa yanzu, pls and pls Mayraah be a good gal, i am hoping data dinki zai yi imputing, banda girman kai da kallon rainin wayo" Mayraah na kallonsa da mamaki tace "Girman kai da kallon rainin wayo kuma?" Dr Khalil yace "Yes kina da girman kai, sannan kin iya kallon rainin wayo amma duk baki san kina yi ba" Shiru tayi tana kallonsa don ita tunda take babu wanda ya taɓa ce mata tana da girman kai ko kallon rainin wayo, hakan kuma kamar yayi shock dinta, Dr Khalil ya zauna gefenta yace "The thing is that, ke girman kai shi ma MD girman kai shi yasa ku ka kasa jituwa... Halinku daya da shi i am telling u the truth" Mayraah ta hade rai tace "Aa ni ba halinmu daya ba, i am not rude and arrogant, sannan ina ba mutane value dinsu, shi kuma he is rude and at the same time arrogant" Murmushi Dr Khalil yayi yace "In gaya maki gaskiya? Da za ki hadu da MD a waje ba a asibiti ba wallahi za ki ga he is the most lovely person to be with, idan aka ajiye aiki gefe daya wallahi yana da kirki and he is a free minded person outside of work, kawai shi baya son raini ne kuma baya son wasa da aiki, he is always serious when it comes to his discipline, shi yasa za ki ga kamar bashi da kirki, ba haka bane yana da kirki sosai, ni baki ga yanda muke da shi ba? He is my very good frnd amma da zaran muna asibiti ajiye frndship din yake aside ayi abinda ya kamata, and i do respect him as my boss" Mayraah dai bata ce masa komai ba don in duk jikinta kunnuwa ne bata jin zata yarda MD yana da kirki ita dai. Dr Khalil yace "So now, go and meet him in his office, and be a good gal while in there" Mayraah ta mike tace "I have always been a good gal, just that yana da anger issues ne" tana fadin haka ta nufi kofa ta fita. Tana tafiya a hankali ta isa office din MD, tayi knocking ta jira har sai da yayi mata izinin shigowa sannan ta bude kofar ta shiga, sau daya ta kallesa ta sunkuyar da kai tana tafiya a hankali ta isa har gaban table dinsa, shi dai tun da ta shigo bai dago ba idonsa na kan laptop da yake operating, tace "Good morning sir" Bai amsa ta ba yana ci gaba da abinda yake, fingers dinsa da ya daura kan table ta dinga kallo, bayan few seconds ta daga kanta a hankali idonta ya sauka kan eyebrows dinsa, kallonsa take babu ko kiftawa, shi kam har sannan bai daga kai ya kalleta ba operating laptop din gabansa kawai yake, can dai ta sake gathering courage tace "Good morning sir" Still not looking at her yace "I am not deaf Madam, where is ur CV? And did u have working experience in anywhere?" Shiru tayi tana kallonsa, sai a sannan ya daga kai ya kalleta yace "Good! no CV, No working experience, shine saurayinki ya dage sai na baki aiki with pending CV saboda ance masa korean film muke acting a nan, ko kuma ance masa i am also mad like he is, mutane nawa ke da CV dinsu available amma basu samun aikin ba sai ke da naki is still pending, infact ni ban ma yarda kinje higher school ba, kuma may be ya manta ba a bama underage aiki a asibitin nan, cause i don't think u are up to 18, always coming here to inconvenience our Staffs and patient, to daga yau kar ki sake shigowa asibitin nan, i will talk to the securities to help u out immediately bamu da vacancy a nan, saurayin naki ai yana da connections me yasa bazai samar maki aiki a wasu asibitocin ba sai lallai wannan" Mayraah dai kallonsa kawai take, aka bude office din duk suka juya, Ceo ce da kanta ta shigo office din, MD ya mike da sauri ganinta yace "You need anything Ma'am" ta karasa tana mika masa wayar hannunta tace "Attend to them pls..." Amsa yayi ya daga ya kai kunne introducing himself immediately with his British accent, Ceo ta kwashe textbooks da ta gani kan table dinsa tace "Get urs pls" Sai a sannan ta kalli Mayraah da ta koma gefe ta tsaya kanta a kasa, tace "Ba ke nace ki sameni office ba?" Mayraah ta gyada mata kai kamar kadangariya, Gaba daya hankalin MD dake waya na kansu, Ceo ta mika mata textbooks din hannunta tace "Come with them" Mayraah ta amsa da ladabi sannan ta bi bayan Ceo din. Suna isa office dinta Mayraah bata zauna ba sai bin ko ina na office din take da ido, bata taɓa shiga office irin wannan ba sai sai ta gani a film kawai, kallon hoton ceo dake office din da wasu likitoci turawa ta dinga yi, Ceo na gama ajiye textbooks da ta dauko office din MD a library dinta ta dawo ta zauna ta nuna ma Mayraah kujera tace "Get sitted Mary Ann" Mayraah ta zauna kanta a kasa, ceo ta dau wayarta after few minutes ta mika ma Mayraah with a smile on her face, Mayraah ta amshi wayar tana kallon matar dake hoton, taga dai suna yanayi da matar amma matar ba fara bace, Ta daga kai ta kalli Ceo dake kallonta, Ceo tace "Did u see the resemblance?" Mayraah tayi murmushin karfin hali tace "Eh na gani muna kama" Ceo tace "Good, Her name is Amina, she is my childhood frnd, she is the reason i am where i am today, she was my God on earth...." Mayraah ta kifta ido jin kalmarta na karshe, can kawai ta hango gold rosary din dake makale wuyarta, Ceo tace "But she left so soon, Amina died 7 years ago, har yau har gobe ina jimamin mutuwar Amina da nake jinta kamar er uwata, her in-laws sent her to her early grave, they made marriage life difficult for her, they shattered her, har yau mijinta na nan Abuja" tissue din dake saman table dinta ta zaro tana share hawayen cikin idonta, jikin Mayraah yayi sanyi tana kallonta a hankali tace "Sorry about that ma'am" Ceo tayi murmushi tace "Thank you, zan hada ki da yaranta in sha Allah, i know they too will attest that u have a resemblance with Hajiya Amina, Abbakar is in Uk, Yusuf is in India, and Maryam is married in UK also, but they are all adopted, she adopted them tun suna yara from orphanage, ita Allah bai bata rayayyun 'ya ya ba, it's always one thing or another" jikin Mayraah yayi sanyi sosai ta kasa ce ma Ceo komai, har cikin ranta taji tana son tasan wa enda suka san Hajiya Aminar nan, a hankali tace "Don Allah zaki hadani da yaran nata?" Ceo na murmushi tace "Sure i will... You can leave now, tell MD to come over with the phone i took to him" Mikewa Mayraah tayi tace "Thank you Ma" Daga haka ta nufi kofa Ceo ta bi ta da kallo har ta fita ta kulle mata kofar. office din Dr Khalil ta nufa duk jikinta a sanyaye, ya ajiye wayarsa da yake ta kiran Ahmad yaki dagawa saboda yasan abinda ya aikata, ya mike yana kallonta bayan ta shigo ganin yanayinta yace "Ya ku ka yi da shi?" Mayraah ta zauna tace "Ka kirasa kace masa tace ya kai mata waya" Dr Khalil yace "Kin je office din nata ne?" Gyada masa kai tayi, yace "Shi ya turaki?" Ta girgiza kai tace "Ta sameni ne a office dinsa" zagayowa yayi ya dawo inda take yace "To ya ku ka yi da ita?" Mayraah tace "Kawai ta nuna min hoton matar da tace ne" Yace "Kuma kinga kuna kama?" Ta daga kai ta kallesa tayi masa nodding kawai, Dr Khalil yayi shiru with different thoughts running his mind kamar yanda ita ma tunani iri iri ke yawo a ranta a lkcn, can yace "Tace zata hada ku ne?" Nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah a hankali tace "Ae tace ta rasu" buda ido yayi sosai, can yace "To yaranta fa?" Mayraah na goge idonta tace "Tace zata hadamu" Khalil yace "Ita matsalarta shiririta ta da shauninta yayi yawa, yanzu tana iya kama hanya in ta tafi sai bayan shekara za mu ganta a kasar nan" Mayraah dai sai kallonsa take, yace "Amma ki kwantar da hankalinki kafin ta koma dai in tana ganin ki she will be remembering definitely" Mayraah tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Zan wuce gida" Yace "Wani gida?" Ta daga kai ta kallesa, ya sauke idonsa yace "Zaman kan naki zaki koma Sulejan ki ci gaba da yi?" Ta wani kallesa, calmly yace "Mayraah" shiru tayi bata amsa masa ba, yace "Kamar yanda nace maki jiya, it's high time ki koma gida yanzu, you've given them enough space nasan yanzu komai ya daidaita in sha Allah" Mayraah ta girgiza kai tace "I will go back when i know it's right to do so" Da mamaki Dr Khalil yace "Abinda Ahmad yayi maki har yanzu bai zame maki darasi ba kenan, to let me tell you, ba Ahmad ba kowa ma kallon da zai maki kenan, don duk mace me mutunci ko gunduwa gunduwa da namanta iyayenta ke yi baxata bar gabansu ba, kuma duk warce kika ga ta bar gida ta tafi wani gari to babu wanda ya isa ya canza kallon er iskan da mutane za su dinga mata, ba ga su nan muna gani a Abuja ba sun tsallake sun bar gida sun dawo nan suna ta iskancinsu" Mayraah ta mike tace "Ni ai Allah ya san ba iskancin nake ba, kuma ban ce bazan koma gida ba, amma sai idan ta hadani da family din matar da na gani a hoto" Dr Khalil yace "Ai ko kina gida za a iya hakan, beside iyayenki na samun labarin kin samu aiki permanently a asibitin nan i know they will support u ki ci gaba da aikin ki, cause kowa yasan asibitin nan a kasar nan, it's ba privilege working here...." Mayraah tace "I will think about that" Dr Khalil yace "Kinsan menene matsalarki Mayraah?" Mayraah tayi shiru tana kallonsa yace "Taurin kai" Zata yi magana aka bude office din duk suka juya, MD ne tsaye bakin kofar, Mayraah ta kauda kanta tana kallon Khalil tace "We will continue on phone" Daga haka ta dau pack din burger dinta da jakarta ta nufi kofa ganin babu hanyar da zata wuce tace "Excuse me pls" Dr Khalil ya koma kujeransa ya zauna yana kallonsu yana murmushi, MD na mata wani kallo yace "Zan ƙwada maki mari, ni kike ce ma excuse you pls? Or are you harebrained?" Bata ko kallesa ba ta raba ta gefensa almost touching him tayi ficewarta a ranta kuwa cewa tayi sai dai ya ci kansa. MD ya juya ya kalli Dr Khalil a fusace kafin yace komai Dr Khalil yace "Kasan me Dr Aliyu? Har nayi picturing ka mace ma yarinyar nan kun fara soyayya da zai yi leading to marriage, it will really make sense, dama naga kamar yanzu baka da budurwa ko?" Yana kai wa nan ya fashe da dariya not minding MD's weird facial expression a lokacin. Mayraah na isa Suleja bayan tayi share sharen gidan don ta kwan biyu bata zo ba ko ina yayi ƙura, tayi wanka sannan ta dafa Indomie ta ci, tun jiya da daddare ta kulle sim card din da ta kira Musharraf da shi saboda yanda ya dinga kiranta, dauko wayar tayi kamar zata bude sim din kuma kawai ta fasa ta ajiye wayar, tana ta zaune dakinta maganganun Zainab na mata yawo a kai, making her feel so hurt a zuciyarta, kawai sai tayi murmushi tana goge hawayen da ya cika idonta, hoton nan da ceo ta nuna mata ne kawai ya jinkirta abinda tayi niyya a ranta yau, she really want to know who the woman in the picture is, amma da ta tuna Ceo tace mata ta rasu sai jikinta yayi sanyi sosai, Ahmad ne ya fado mata, ita fa ta dade bata yi mamaki irin mamakin abinda Ahmad yayi mata ba, to gani yayi tayi kama da yan iska ne ko kuma ya taɓa ganin tayi wani action da yayi kama da na iskanci? Har cikin ranta taji tana appreciating Dr Khalil kuma tana jinsa kamar Ya Maheer because he was there for her always, kiran azahar ya sa ta tashi taje tayi alwala, sai da tayi sallah sannan ta kwanta tayi baccin da bata samu tayi ba jiya. Bayan la'asar Mayraah na wanke plate din da tayi amfani da shi a kitchen taji ana knocking gate din gidan, so tari idan Maman Hanan ta lura ta dawo suleja ta kan shigo mata su yi hira, wani lokacin kuma daya neigbor dinta Harira ma na shigowa duk sanda suka ga ta dawo, Hijab dinta ta saka ta fita, tana tsaye jikin gate din gidan tace "Waye?" taji muryar namiji yace "Assalamu alaikum" Mamaki ne ya cikata, tace "Waye?" Yace "Baƙi ne ki bude gate din ki fito" Sosai gabanta ya fadi tace "Baƙi kuma? Ni bana expecting baƙi daga ko ina" Mutumin yace "Eh mu ma dalili ne ya kawo mu, bamu yi tunanin za mu zo anguwan nan yau ba" Kasa cewa komai Mayraah tayi don gaba daya ta tsorata, mutumin yace "To cut everything short don naga kamar kin tsorata, mu jami'an tsaro ne... We are not here to harm u Madam, amma idan kika ki bude gate din, we are sorry there is nothing we can do about it za mu bude gate din by all means" Mayraah that was so afraid tace "But what did u want from me?" Yace "Open the gate" ƙin budewa tayi ta koma ciki ta dau wayarta ta fara dialing number Dr Khalil a tsorace. [7/29, 3:44 PM] Khaleesat Haiydar💖: Bayan wani ɗan lokaci Mayraah ta dawo bakin gate din, tayi gathering courage duk da yanda gabanta ke faduwa tace "Sorry... brother na yace i shouldn't open the gate till he comes" shiru duk ta ji sun yi bayan ta gaya masu haka, sai kuma taji mutumin yace "Ki bada number brother din naki" Mayraah tayi tsuru tsuru jin abinda yace, sake maimaita maganar yayi, cike da karfin hali tace "Aa ni bazan bada ba sai na tambayesa tukunna" Mutumin yace "Kirasa yanzu kice we are requesting for his number, call him immediately" Komawa cikin gidan Mayraah tayi ta sake kiran number Dr Khalil, yana fara ring ya daga yace "I am on my way now kar ki bude gate din" Kamar zata yi kuka tace "Wai sun ce in basu numberka kuma" Ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Number na?? ohk ok basu kawai, but do not open the gate, just call out the number for them" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace "Kin ji me nace?" A hankali tace "Toh" Komawa gate din tayi bayan ya katse wayar, cikin karfin hali tace "Yace in baku number din, zan kira maku digit din yanzu" Mutumin dake bata amsa yace "Ohk, do so now" Kiran numbers din khalil ta shiga yi har ta gama, mutumin yace "Good" Ji tayi kamar sun bar bakin gate din, ita dai sai zare ido take har taji tafiyar motarsu, duk da haka bata yarda ta bude gate din ba ta koma cikin gidan duk hankalinta a tashe, gaba daya ta rasa wani tunani ma zata yi, tana ta zaune cikin fargaba har wayarta ya fara ring wajen karfe biyar da wani abu taga Dr Khalil ne ke kiranta, dagawa tayi ta kai kunne da sauri, yace "Fito ki bude gate din" Tace "Ka zo ne?" Yace "Eh ina waje" mikewa tayi dama har sannan bata cire hijab din jikinta ba ta fita zuwa bakin gate din, bugun zuciyarta ya tsanata cike da karfin hali ta makale jikin gate din tace "Ka kadai ne?" Yace "Ni kadai ne mana Mayraah" a hankali ta bude gate din with throbbing heart, tsaye ta gansa bakin gate din, ta marairaice masa tace "Did they call u pls?" Yace "Yea they called, but it's not even something serious" Tace "Toh me suka zo yi? Me ya faru? Did commit any offense?" Yace "Za mu je station din yanzu, kawai tambayoyi za su maki...." Ta fashe da kuka sosai tace "Toh ba sai mutum yayi laifi ba ake kai sa station, ni me nayi? Don Allah kar ka boye min ka gaya min" Yace "Nace maki it's not something serious Mayraah, yanxu haka daga station din nake, kawai suna daukan statement dinki zan dawo da ke gida, kar ki wani daga hankalinki" Cikin kuka tace "Statement of what? What wrong have i committed?" Yace "Na fa ce ki kwantar da hankalinki, i am with you, yanzu ba daga Abuja nake ba saboda ke?" Share idonta tayi tana kallonsa, yace "Dauko wayarki mu tafi lokaci na wucewa" A hankali ta juya ta koma cikin gidan, wayarta ta dauko da handbag dinta ta fito, a cikin motarsa ta samesa yana jiranta, bayan ta kulle gidan ta tafi ta bude front seat ta shiga motar, kana ganinta kasan duk jikinta yayi sanyi sosai kuma a tsorace take, bayan sun bar layin ya kwantar da murya yace "Pls calm down Mayraah, kema kinsan bazan bari ayi harming dinki ba, beside i told u it's not something serious, u need not to worry kar ki je jininki yayi kasa" Ta fashe da kuka tace "But i want to know what i did, ina son sanin menene ya sa suka zo za su tafi da ni, wani laifin nayi? I know kasani tunda kaje station din, definitely u are aware, you are just hiding it from me, don girman Allah ka gaya min menene ko zan samu relieve" Dr Khalil ya ɗan kalleta, sai kuma yace "Ohk bazan boye maki ba, kinsan me ke faruwa?" Ta girgiza masa kai da sauri zuciyarta na bugawa, ya ɗan yi shiru sai yace "Kinsan ko wani society or rather community, da irin ka'idarsu ko kuma ince da irin way of life dinsu, da yanda suka ba al'adarsu da addinin su muhimmanci, right??" Shiru tayi tana kallonsa waiting for him to go straight to the point, ya sauke ajiyar zuciya yace "To kin dai ga garin nan da kike ciki yawanci majority dinsu musulmai ne, sannan akwai Hausawa babu laifi, so the community are against gidan da kika kama kina zaune ke kadai kina zaman kanki don suna da yara kuma suna duba tarbiyar yaransu suna tsoron kada yaransu suyi tunanin hakan abu ne me kyau mace ta kama babban gida irin wannan tayi zamanta, sannan sunce ke kince kina karatu amma sun gano ba karatu kike ma a garin Abujan ba, iyaka idan kinje kinyi abinda za ki yi a Abuja sai ki dawo nan ki bude gida ki shiga bayan kwana biyu ki sake komawa cikin Abuja, sannan a complain dinsu sun ce akwai saurayin da ma yake zuwa ya sameki a nan din" Sake baki Mayraah tayi tana kallonsa har zuwa sanda ya dasa aya, she was so shock and speechless, yace "To ban san ko bayan zuwan da nayi last week ko akwai wani wanda ke zuwa wajenki ba" Mayraah bata san sanda ta fashe da kuka ba tace "Allah ya saka min, wallahi bazan yafe masu ba, tunda na dawo nan babu wanda ya taɓa zuwa wajena sai kai, bazan taɓa yafe wannan kazafin da suka min ba" Dr Khalil ya langwabar da kansa yace "Kinga abinda nake gaya maki ai ko, mutuncin ya mace gaban iyayenta, in ko ba gaban iyayenta ba to gidan mijinta, in dai a arewa ne duk inda za ki je to wallahi kallon da za a maki kenan baza ki taɓa canza su daga maki kallon nan ba, a takaice gani suke sharholiyarki kike shigowa kiyi a Abuja sai ki dawo nan Suleja ki fakee, let me tell u something.... kiwon mutane ake yanzu ba fa dabba ba, duk footstep dinki a kan idon mutane yake" Mayraah dai ta kasa cewa komai sai kukan bakin ciki da takaici take, har suka iso garin Abuja ta kasa daina kukan da take har ya ma daina lallashinta, wani station taga sun zo, bayan yayi parking a waje yana kallonta yace "Kiyi hakuri in sha Allah komai ya zo karshe daga yau, wipe off ur tears and trust me I will be by ur side" A hankali ta goge idonta tana kallonsa cikin rawan murya tace "Toh yanzu me zan ce masu idan mun shiga?" Yace "Kar ki damu, na riga na masu bayanin komai, iyaka Statement dinki za a dauka, shikenan" Daga haka ya sauka daga motar ita ma ta sauka har lkcn hawaye ya ki tsaya mata, she felt so hurt da irin kallon da mutane suke mata, ga Ahmad, Zainab, and now sulejan da take, calmly yace "Na fa ce ki daina wannan kukan" Ta gyada masa kai da kyar tana kara goge idonta, ya nufi cikin station din tana biye da shi a baya. Dr Khalil ya gaisa da yan sandan cikin station din yace "Za mu iya shiga office din Dpo din?" Police officern yace "Ehh suna ciki har yanzu, You can go in...." Ya kalli Mayraah dake tsaye gefensa kamar warce tayi ma sarki karya gaba daya a tsorace take don bata taɓa shigowa police station ba, calmly yace "Mu je" Bin bayansa tayi har xuwa office din Dpo din, ya bude kofar ya fara shiga da sallama sannan ita ma ta shiga gabanta na faduwa sosai, makalewa tayi jikin kofar tana kallon wanda ke zaune kan Sofa a office din babu ko kiftawa, can ta juya a hankali ta kalli Dr khalil kamar idanuwanta za su fito, Dpo ya daure fuska yace "Kee, shigo ki kulle ma mutane office" Ji tayi kamar ta zura a guje, ta dai kulle kofar da kyar ta sunkuyar da kai, amma ta kasa karasawa ciki don gaba daya tayi shock a wajen, tuni Dr Khalil ya tafi ya zauna kan kujera, Dpo ya bata thumbs up yana gyada kai cikin jinjina yace "The runaway girl!!" Kasa daga kai tayi, cikin daga murya yace "Ya sunanki?" Da kyar ta daga kai ta kallesa cikin karfin hali tace "Mayraah" Yace "Mayraah the runaway girl.... to nemi kujera ki zauna" Ta saci kallon wanda ke zaune kan sofa din, ai tana ganin irin kallon da yake mata tayi saurin dauke kai kamar munafuka ta tafi ta zauna kan kujera ta takure waje daya, shi dae Khalil murmushi kawai yake, Dpo yace "Kin san wannan da yake zaune?" Sunkuyar da kai tayi, ya mata tsawa yace "Ke..." Cikin rawan murya tace "Yayana ne" Yace "Ya sunansa?" saboda tsoron kar ya sake mata wani tsawan cikin rawan murya tace "Ya Usman" Dpo yace "Yau kwananki nawa da barin gida?" Ta fashe da kuka ta kasa cewa komai, yace "Ba kuka nace ki min ba malama, warce ta iya tsallakawa ta bar gida ai zuciyarta ya kekashe kenan babu wani batun kuka, kwananki nawa yau da barin gida?" Cikin rawan murya tace "Kamar 3 weeks" Yace "Kuma baki da intention din komawa anytime soon ko?" Daga kai tayi tana kallonsa hawaye na sauka idonta, Dpo din yayi shiru, sai kuma ya nuna mata kujeran dake gaban table dinsa yace "Dawo nan ki zauna" Mikewa tayi tana kuka ta tafi ta zauna kan kujeran, yace "Mayraah" Ta daga kai ta kallesa hawaye na sauka idonta, yace "Abinda kika yi kin kyauta kenan? Saboda wasu unforseen circumstances sun faru that doesn't mean it is the end of life my dear, what if hannun mutanen banza kika fada? Did you know the type of era we are in now? Kinsan irin munanan cases da muke dealing da kullum a wajen nan? me yasa za ki zabi kawai ki bar gida saboda an samu matsala? pls nan gaba ko wani kika ga zai yi abun nan da kika yi ki basa shawaran kar yayi ba shi da amfani, ita dama rayuwa kowa da ƙaddararsa taki a haka ta zo sai kiyi hakuri ki zama me imani ki amshesa hannu bibbiyu, ko da wasa karki sake tunanin wannan shine solution dinki ke macece, leaving home is never a solution, ke baki tunanin halin da iyayenki da yan uwanki za su shiga saboda abin nan da kika aikata? Ko ke ba musulma bace? Don duk musulmi an san sa da tawakalli ne" Ita dai kanta na kasa hawaye sai sauka idonta yake, yace "Yanzu kin san ta yanda aka bi ki har Suleja?" Ta girgiza masa kai, ya dauko wani kwali ya ajiye mata a gabanta, kallon kwalin ta dinga yi sai kuma ta saci kallon Usman dake kallonta tayi saurin dauke kai, Dpo yace "Ko da wasa next time do not try this nonsense again pls" Sai kuma ya kalli Dr Khalil yace "Kai kuma Allah ya saka maka da alkhairi for all ur effort, ni yanzu zan fita, za ku iya tafi Allah ya tsare gaba....." Har suka fito daga office din Dpo Mayraah bata yarda ta kalli Usman ba, sai makalewa kusa da Dr Khalil take, bayan sun fita daga police station din, Dr Khalil na kallon Usman yace "Ina kuka nufa yanzu, don naga it's almost magrib" Ita dai Mayraah na can gefe tsaye gabanta sai faduwa yake, ta saci kallon Usman yafi a kirga, Usman yace "Ba komai, na saba driving din dare, i will drive to kaduna in sha Allah" Dr Khalil yace "Toh ba damuwa, idan ka isa kadunan sai mu yi waya" Usman yace "To in sha Allah, thank you so much Dr" Dr Khalil yayi murmushi yace "You are welcome" Daga haka Dr Khalil ya koma gun Mayraah yace "Ki je ku tafi..." Ko rufe baki bai yi ba Mayraah ta fashe da kuka tace "Wallahi ni dai tsoronsa nake ji, na shiga uku" Dr Khalil ya buda ido yace "Saboda me?" Cikin kuka tace "Zai iya marina na sani, dama yaya Maheer ne" Dr Khalil yayi murmushi yace "Haba dai, ba abinda zai maki" Cikin kuka tace "Wallahi zai iya, me yasa ba Yaya Maheer bane ya zo" Juyawa Dr Khalil yayi ya kalli Usman da ya rungume hannu yana tsaye jikin mota fuskarsa babu yabo babu fallasa, komawa yayi wajensa yana ɗan murmushi yace "Barrister don Allah ayi mata hakuri, tace tsoro take ji zaka bugeta" Usman ya girgiza kai yace "Not at all.... Ka tambayeta ko na taɓa dukanta, she is waisting our time, muna da tafiya a gaba" Dr Khalil yace "To plss ayi hakuri barrister" Sai da Dr Khalil yayi da gaske da Mayraah sannan ta tafi ta shiga motar Usman, amma tana shiga sai ta wani tsuke fuska tana makale da handbag dinta, Usman ya kara yi ma Dr Khalil sallama sannan ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, Dr Khalil ma ya nufi motarsa, har suka hau kan hanya bai ce mata ba ita ma bata ce masa ba. [7/30, 8:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na ganin sun kusa Suleja ta kallesa a karo na farko tana fidgeting fingers dinta a hankali tace "Don Allah yaya zan iya dauko jakana?" Ganin bai ce mata komai ba driving dinsa kawai yake, ta kauda kai bata sake cewa komai ba. A hankali Mayraah ta bude idonta daga baccin da ya dauketa ta gansu a cikin garin kaduna, gyara zama tayi da sauru ta tana kallonsa don ya maida mata kujeran baya yanda zata zama comfortable sanda take baccin, shi dai driving dinsa kawai yake pretending kamar bai ma san ta tashi ba, tun daga Abuja har zuwa yanzu da suke kaduna yaki ce mata komai, duk da almost half of the journey ma bacci take, wani hotel taga sun shiga bayan yayi parking ya bude motar ya sauka, babu bata lokaci ita ma ta sauko tana kallonsa ya kulle motarsa ya nufi cikin hotel din, ta wani tura baki ta bi bayansa, executive room ya biya masu, bayan ya amshi makullin dakin suka bar reception din, ita dai bin sa kawai take a baya har zuwa dakin, har cikin ranta take wishing dama Maheer ne, babban parlor ne da bedroom suka yi lodge in... Bayan ya ajiye wayoyinsa da car key ya cire agogonsa ya ajiye kan kujeran parlon Mayraah dai sai bin sa take da kallo tana turo baki, sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta sunkuyar da kai da sauri kamar munafuka, sai kuma ta ga ya nufi kofa har ya fita ya kulle kofar, a hankali ta karasa ta bude kofar bedroom din ta shiga ciki, bayan ta ajiye handbag dinta da wayarta ta koma parlon, sabulun da hotel din suka basu ta dauka ta shiga bandaki tayi wanka sannan dauro alwala ta fito ta koma daki, bayan ta idar da sallah ta rage Ac din dakin ta kwanta duk da yunwan da take ji don ko abincin rana bata ci ba, tana ta kwance taji an bude kofar dakin, kin juyowa tayi sai ma kulle ido da tayi da sauri don bata san me zai ce mata ba, sai taji yace "Fito ki dauki abinci" tana jin haka ta bude ido ta turo baki duk da ba ganinta yake ba sai kuma ta mike zaune tana murza ido tana kallonsa, juyawa yayi ya bar bakin kofar, ta sauka daga kan gado ta bi bayansa, Kallon ledan abincin dake kan table din gabansa tayi, sae taki karasawa ta dauka don ita fa bata yarda da wannan shirun da yayi mata ba, can ganin bai ce mata komai ba a hankali tace "Toh ni don Allah ka ajiye min kasa in dauka" Sae a sannan ya daga kai ya kalleta, tayi narai narai da ido ita ma tana kallonsa, gani take kawai planning din yanda zai wanka mata mari yake, tashi taga yayi ya bar wajen ya koma 3 seater ya zauna, tana tafiya a hankali ta tafi ta dau ledan ta koma daki tana satan kallonsa, shi kuma ya bi ta da kallo. Washegari da asuba Mayraah ta idar da sallah bayan ta gama azkar dinta har ta koma ta kwanta taji yayi knocking kofar dakin, ta mike zauna tana kallon kofar har ya bude, zamowa kasa tayi daga kan gadon murya can kasa tace "Ina kwana yaya" yace "Ban sani ba... dauko stuffs dinki mu tafi" Ta ɗan buda ido tace "Bazan yi wanka ba" Kallon da taga ya mata ya sa ta tashi da sauri ta dau handbag dinta da waya, ya juya ya bar bakin kofar ta bi bayansa tana duba wayarta dake nuna karfe shidda da rabi, check out suka yi daga hotel din bayan ya basu makullin dakin, ta bude front seat din motarsa ta shiga, bayan some minutes of warming up the car suka fita daga hotel din ya kama hanyar kano. Karfe tara suka shigo garin kano, Mayraah na ganin sun kusa gida haka kawai jikinta yayi sanyi, lokaci daya taji ta rasa sukuni, she don't know how everybody will accept her back, bata san ko Ammi will still welcome her back home ba, tunanin hakan yasa hawaye ya cika idonta ba tare da ta sani ba don kawai ji tayi yana sauka fuskarta, rufe fuskarta tayi da hijab dinta tana shessheka, Usman ya kalleta yana ci gaba da tukinsa yace "Ohk in maida ki Abujan kenan?" Cikin kuka tace "Aa" Yace "To me ya faru?" Ta fashe da wani sabon kukan tace "Ban san ko Ammi..." Kasa ci gaba tayi saboda kuka, Usman yayi kasa da murya yace "Ammi missed you, since you left she is not fine" Mayraah ta daga kai ta kallesa hawaye na sauka idonta, bai sake ce mata komai ba har suka shigo anguwan, yana horn bakin gate mai gadi ya bude gate din da sauri, ya shiga ciki yayi parking a garage, Bayan ya kashe motar ya juya ya kalli Mayraah da ta fada duniyar tunani, yace "I hope u will never repeat such mistake again" Ta juya a hankali ta kallesa sai kuma ta gyada kai, a hankali yace "Abba was there for you, i was there for u, so was Doctor but u decided to follow ur heart that lead you astray" Cikin rawan murya tace "I am sorry" bude motar yayi ya sauka, amma ta kasa bude motar ta fito duk jikinta yayi sanyi wasu sabbin hawayen na zuba idonta, zagayowa yayi ya bude mata kofar yana kallonta, sunkuyar da kai tayi ta sauka ya nuna mata entrance din gidan yace "Mu je" Babu musu ta fara tafiya tana share hawayenta gabanta na faduwa, tsoro take kada Ammi taki ce mata komai, she don't think zuciyarta zai iya daukan hakan, yana biye da ita a baya har suka iso entrance din shiga parlor, ta kasa bude kofar ta juya ta kallesa har sai da ya karasa gabanta ya bude kofar bai shiga ba ya juya yana kallonta, muryarta na rawa tace "I am afraid" Yace "U need not to be, everyone misses u badly" Ta gyada masa kai tana goge idonta, yace "Shiga..." Ba musu ta wucesa ta shiga parlon ya bi ta da kallo, Mayraah na shiga parlon tayi ido hudu da Haseenah dake tsaye kofar kitchen tana jiran sabon mai aikin Ammi ta bata irish din da taji tana soyawa wai ita bazata iya girki ba, Sake baki Haseenah tayi tana kallonta, Mayraah ta dauke idonta ta kalli direction din stairs jin kamar ana saukowa, Maheer ne ke saukowa tare da Ammi yana ce mata "Gaskiya Ammi i am only doing this because of you, but it's stressful for me, menene yasa baza a sa ta a mota ita ma ta tafi kadunan ba...." Ido hudu yayi da Mayraah dake kallonsa babu ko kiftawa, ai bata san sanda ta nufesa da gudu ta rungumesa ba ta fashe da kuka, murya can kasa as if bai yarda ita bace yace "Mimi??" Haseenah tayi saurin dauke kai bayan ta saki wayarta dake hannunta ba tare da tasan ma tayi hakan ba, juyawa Usman yayi bayan ya dauke kai ya fita daga parlon, Ammi ta kasa motsawa daga stairs din da take tsaye, hawaye na zuba idon Mayraah ta rufe fuska a kirjinsa tayi karfin halin cewa "I missed you so much yaya" as if whispering yace "Why did u leave just like that Mimi?" Ido hudu tayi da Ammi dake tsaye hawaye a fuskarta ta kasa saukowa downstairs din, Mayraah ta sauke idonta kasa... Zame jikinta tayi daga na Maheer ta daga kai tana kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta babu ko kiftawa, he is just hoping this is not one of his everyday dreams, har sannan hawaye bai daina sauka idon Mayraah ba, kawai tayi gathering courage ta tafi wajen Ammi, Ammi na ganin haka ta fashe da kuka sosai, Mayraah ta rungumeta cikin rawan murya tace "Don Allah kiyi hakuri Ammi, ban san yanda zan yi ba ne..." Haseenah bata san sanda ta fita daga Parlon ba tare da ta amshi irish din da take jira ba ta koma Chalet. Mama Ladi da ta fito daga bangaren Ammi cike da masifa tana cewa "Haka kawai ba dangin iya ba na baba wannan wahala haka, o'o wallahi bazan iya ba don nayi ma kaina fada na daina shiga abinda bai shafeni, ga daki can an bar mata ban san me yasa take biyo mu nan tayi ta mana kazanta tana cutata ba...." Komawa baya Mama Ladi tayi da sauri tana gwalo ido bayan ta hango Mayraah tace "Wacece wannan kuma?" Sai a sannan Mayraah ta sake Ammi ita ma tana kallonta, Mama Ladi ta rike haɓa tana gyada kai tace "Ba shakka!! to ina iyayen naki da suka jefa ki a kwata kina jaririya? Inji dai tare ku ka dawo da su?" Mayraah ta sunkuyar da kanta, Mama Ladi tace "Amma wallahi ke kam da ba don kada Ammi ta kullaceni ba sai ince butulu ce ke me manta alkhairi, haka kawai kika kama hanya kika shiga duniya kika bar mata da hawan jini mu kuma kika bar mu da rashin isasshen bacci kullum cikin tunaninki da alhinin bacewarki, Sannan yanzu ba kunya ba tsoron Allah galau galau kin kwashi kafafuwa kin dawo ke kadai, ni fa duk tunanina tare ai za ku dawo da iyayen naki tunda baki da mutunci kiri kiri kin nuna ai babu abinda kika hada damu, duk abinda muke maki kika rufa ido kika ci mana mutunci, haka nayi kwana biyu a asibiti wajenki ko runtsawa ban yi ba ga yunwa, amma baki gani ba sai da kika zalunce mu kika daga mana hankali, Mamuda ya dawo kamar wani zautattce wani lokacin takalmi wari wari yake sa wa ya fita, duk caji opis din kano babu wanda bai tafi ya kai cigiyarki ba, mu dai Allah ya isa rashin cin abinci da wadatattcen bacci da kika janyo mana" Tuni Ammi ta kama hannun Mayraah suka bar wajen, Mama Ladi ta bi bayansu still. Tun da Mayraah ta shigo parlon Ammi take kallon Badiyyah dake kwance kasa tayi wani bakikirin kamar bata taɓa haske a rayuwarta ba ga wasu uban kuraje da suka cika mata fuska, Mayraah ta zauna kan kujera don Ammi da take son tambaya ko Badiyyar bata da lafiya ne tuni ta fita daga parlon, kasa daurewa Mayraah tayi tana kallon Mama Ladi tace "Mama bata da lafiya ne?" Mama Ladi tace "Wa? Wai Badiyyah? Ai Badiyyah cikin shege tayi in baki labari Mera, cikin shege dai da kika sani" Tsabar shock Mayraah bata san sanda ta mike tsaye ba, Mama Ladi tace "Aa koma ki zauna ba wani batun rikicewa don kema bamu san daga inda kike ba yanzu haka" Mayraah ta dinga kallon Mama Ladi babu ko kiftawa, Mama Ladi na kakkabe kujeran da taga Badiyyah ta zauna dazu tace "Hajja dai in gaya maki ta sallama ma duniya Badiyyah tace ko sunanta aka kira mata bata yafe ba, ta mata Allah ya isa yafi cikin kwando, ko ido suka hada sai ki ga Hajjan ta fara tari kamar zata shide yanzu haka zancen da nake maki Hajja tana can gidan Yahanasu a kaduna, sai kin ga gidan ko kiwon kare baza ayi a gidan nan ba don sai cuta ta kama karen ya mutu a banza, ni dai tun da na rakata ko minti sha biyar banyi cikin ɗan kuturun gidan ba na gudu gidan Mariya tunda dai abinda ya faru ba wai ya shafeni bane kawai zumunci nake dubawa, banda ma na kai zuciya nesa ai da sai dai ki dawo ki ga na canza wani pamilyn, don wannan pamilyn namu dai ba pamilyn nuna ma duniya bane, pamilyn mu ya zama barbadadden pamilyn, Badiyyah ta lalata mana Pamily kawai sai dai muce Allah ya isa, gidan Mariya da na gudu in samu sauki can kuma yanda kika san kasuwar kurmi tunda babban gida ne uwar mijin da uban mijin duk suna ciki da bataliyarsu, wannan karen ya shigo, wancan dokin ya fita haka dai abun ba tsari, ke in takaice maki washegari da asuba nasa aka kaini tasha na hau mota na dawo kano inda na fi wayo, to shine sabida rashin tsoron Allah aka makala ma baiwar Allah Ammi Badiyyar take ta fama yanzu haka, banda ma Mamudan mutumin kirki ne ina zai yarda wannan annobar ta zauna masa gida ta lalata masa tarbiyyar yaransa maza, ai da muna da yan uwa a kauye kyan Badiyyah kawai a turata can har sai ta haihu ta zauna tayi renon shegen a can, to bamu da kowa a kauye, Mamudan ma fa da farko kin amincewa yayi yace a fitar masa da ita daga gidansa, to kin dai san Abban naku da shegen tausayi ga kuma tausayin matarsa da yake, a haka dai daga karshe yace a kyaleta ta zauna amma ko nan da gate baya son ta je kada yan anguwa su sa shi a bakin duniya suce ga me cikin shege a gidansa, kiri kiri Mariya taki tafiya da ita aka bar Ammi da wahala, Allah dai ya isa kawai" Mayraah sai kallon Badiyyah da hawaye ke sauka idonta kawai take, kullum sai tayi kuka kamar ranta zai fita a gidan saboda Mama Ladi, da kyar ma in Mama Ladi bata daura mata depression ba saboda bad mouth dinta, Mama Ladi tace "Don haka kike baya baya da ita, mu ma duk baya baya muke da ita gaskiya, mu a zamaninmu idan mutum yayi cikin shege ma rataye kansa kawai yake ya mutu, ko kuma ya gudu ya bar garin sai bayan shekara hamsin, to ita kinga ai taki yin ko daya" Bude kofar parlon aka yi Ammi ta shigo da breakfast ta kawo ma Mayraah, ko bata bude baki tace komai ba kasan tana cikin farin ciki mara misaltuwa, she looks so happy wanda duk wanda yasanta yasan rabonta da wannan farin cikin an kwana biyu, Usman really took she and Maheer unaware don duk abinda yake yi bai gaya masu ba, Mama Ladi ta bi ta da kallo har ta ajiye tray din hannunta tana kallon Mayraah tace "Taho ki karya daughter" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Yanzu tun safe in tashi ko ruwan shayi da ke da shegiyar sabuwar me aikinki baku bani ba sai wannan mata da bamu san daga inda take ba zaki kawo ma tray guda na kumallo jikinki na ɓari? Ni da na kwana gidan baki ban komai ba sai warce bata kwana ba?" Ko kallon Mama Ladi Ammi bata yi ba sai ma daukan tray din da tayi ta wuce dakinta da shi tace "Taho Mimi" Mayraah da duk jikinta yayi sanyi da halin da Badiyyah ke ciki ta share hawayen idonta ta bi bayan Ammi tana tafiya a hankali zuwa bedroom dinta. Ammi da kanta ta hada mata shayin ta debar mata komai sannan ta koma ta zauna tana kallonta, Mayraah ta daga kai tace "Ammi Abba fa?" A hankali Ammi tace "Na kirasa yana hanya" Mayraah ta dau shayin da Ammi ta hada mata ta fara sha, Ammi ta mike ta fita daga dakin zata je kai ma Mama Ladi nata breakfast din, Ammi na fita babu dadewa Maheer ya shigo dakin, Mayraah ta daga kai tana kallonsa har ya iso inda take ya duka yana kallonta, ta sauke idonta tace "In hada maka shayin kai ma?" Ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Ki rage min kawai" Tace "Sai mu sha tare..." Zaunawa yayi saman darduman yana facing dinta, bayan ta kurbi shayin hannunta ta mika masa, ya amsa ya kai baki, ita kuma ta fara cin irish din da Ammi ta zuba mata da ketchup da kwai, Ya ajiye cup din shayin bayan ya sha a hankali yace "Me yasa kika tafi Mimi?" Bata yarda ta dago kai ta kallesa ba cikin sanyin murya tace "That's bygone yayana" Ya gyada mata kai kawai still looking at her, bayan few seconds tace "Baza ka ci irish din ba?" Dauka yayi ya fara ci, ta dau cup din shayin ta sha kadan ta ajiye, daga kai tayi suka hada ido, yace "I missed you Mimi" Ta ɗan yi murmushi tace "I missed you more" A haka Ammi ta shigo dakin ta samesu, Ammi na kallonsa tace "Ba ga can naku an kai maku ba?" Mayraah ta kalleta tace "Ammi ni ce nace ya ci" Shi dai murmushi kawai yayi, Ammi ta zauna gefen gado still looking at them. [7/31, 7:19 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na gama yin breakfast ta shiga yin wanka bandakin Ammi, Maheer kuma ya fita da tray din da suka yi breakfast din downstairs zuwa kitchen, ko da ta fito wanka ta tarar Ammi ta dauko mata kaya daga dakinta ta ajiye mata gefen gado, bayan ta shafa mai ta shirya ta fito parlor, har a sannan Badiyyah na parlon Ammi a kwance ita kadai, Mayraah na tafiya a hankali ta karasa kusa da ita ta durkusa tana kallonta tace "Ya jikin?" Kai kawai Badiyyah ta gyada mata, Mayraah tayi shiru tana kallonta hawaye na taruwa idonta, abubuwan da suka faru a baya ne da dalilin faruwansu kawai ke yawo mata a zuciya, da sauri ta goge idonta trying to shun away the thoughts off her mind, cikin sanyin murya tace "Kin yi breakfast ai ko?" Nan ma Badiyyah ta gyada mata kai tana kallonta, wani tausayinta Mayraah ta dinga ji har cikin ranta, she can't just imagine Badiyyah da ta sani ce wannan, a whole Badiyyah, Ammi ce ta shigo parlon, Mayraah ta juya tana kallonta, tana tsaye bakin kofar tace "Fito ki je wajen Abbanki Mimi, he is around" Mayraah ta mike tana goge wasu hawayen dake taruwa idonta ta nufi Ammi, a tare suka sauka downstairs, Mayraah na hada ido da Abba dake zaune kan kujera ya mike tsaye yana kallonta, sosai jikinta yayi sanyi ta sunkuyar da kanta and for the first time she felt guilty akan abinda ta aikata, for the first time ta ji bata kyauta abinda tayi ba, nan da nan hawaye ya cika idonta ta nufesa da sauri ta rungumesa sosai ta fashe da kuka tace "I am sorry Abba, don Allah kayi hakuri, i don't know what came over me, i was...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai, Abba yayi patting din bayanta a hankali bai ce komai, tayi kukanta me isarta sannan ta durkusa nan gabansa cikin rawan murya tace "Don Allah ka yafe min Abba" Har a sannan ta kasa hada ido da shi, Abba ya zauna kan kujera a karo na farko yayi magana yace "It's okay Daughter.... I am glad you are back home hale and hearty, that was our prayer and hope, Alhamdulillah" Ganin yanda take kuka ya shafa kanta yace "Nace ya isa haka my dear" Ta gyada masa kai tana goge hawayen dake sauko mata, gefensa ya nuna mata ta dawo ta zauna ta daura kanta a jikinsa, sai a sannan ta lura da mutanen dake zaune parlon, Mama Ladi ce dake ta taɓe baki tana hararanta sai Hajiya Amina dake ta kallon Mayraah tana murmushi, matar looks so happy da dawowar Mayraah, Mayraah ta kalli Abba ya gyada mata kai yace "Go and greet her" Mikewa tayi ta ɗan kalli direction din dining da ta hango Usman a zaune shi ma yana kallonta, ta karasa har gaban Hajiya Amina ta durkusa gabanta ta gaisheta, Hajiya Amina ta dago ta sitting her down by her side ta jawota jikinta tana amsa gaisuwar ta da fara'a, Ammi dai na tsaye stairs taki karasowa cikin parlon all her attention na kan Mayraah, Mama Ladi da take ganin abinda ake bai shafeta ba ta mike tana kallon Ammi tace "Ke har yanzu fa shegiyar me aikinki bata kawo ma bakuwar nan abinci ba, ko kafura ce mai aikin da bata san ance baƙon ka annabinka ba" Ammi bata tanka Mama Ladi ba, don dauke kai ma tayi, Hajiya Amina na murmushi tana kallon Mama Ladi tace "Ayya Mama nace mun yi breakfast kafin mu fito" Mama Ladi tace "Aa ko farfesun ne bari inje in debo maki da burodi mu bamu gaji rowa ba a pamilyn mu" Daga haka ta wuce kitchen da sauri, Ammi ta juya ta wuce sama Abba ya bi ta da kallo, Mayraah na son tashi daga kusa da Hajiya Amina ta bi Ammi amma sai ta kasa, gaba daya she is not comfortable sitting down with her, mikewa Abba yayi ya wuce sama. Sai kusan karfe sha biyu Hajiya Amina da Abba suka bar gidan har sannan kuma Ammi bata sauko kasa ba, sai upstairs Hajiya Amina ta tafi tayi mata sallama a part dinta, Mama Ladi kuwa babu wanda zai ce ba wajenta Hajiya Amina ta zo ba don babu labarin karaye da bata ba Hajiya Amina ba, saboda ita ne ma har Hajiya Aminar ta iya kai wa karfe sha biyu a gidan, tunda ita kadai ce downstairs sai Usman dake aiki da laptop dinsa a dining area. Mayraah ta shiga dakin Ammi bayan tafiyar Hajiya Amina ganinta kwance har a sannan ta zauna gefenta tana kallonta tace "Ammi ko dai baki da lafiya ne?" Ammi ta sakar mata murmushi tace "Aa kawai hutawa nake Daughter" Mayraah tace "Toh ba abinda za a kawo maki?" Ammi tace "Aa... i am okay" Shiru Mayraah tayi, tun dazu take zaune dakin da Badiyyah take kwance bayan Ammi tace ma Badiyyar ta koma can za a gyara mata part dinta, ita dai ta rasa wani irin tausayin Badiyyah take har cikin ranta, sai Mama Ladi ce ta zo ta kirata taje suyi sallama da Hajiya Amina tana mata mitar meye hadinta da Badiyyar zata ne ta makale mata kowa na baya baya da ita salon ta shafa mata wani cutar, ita dai Mayraah bata ce mata komai ba, bayan tafiyar Hajiya Amina ne ta hauro sama ta shigo part din Ammi, mikewa Mayraah tayi after some minutes, Ammi na kallonta a hankali tace "Anjima idan na tashi ki zo in gyara maki gashin ki" Mayraah tace "Toh Ammi" Fita tayi daga dakin ta koma dakin da Badiyyah take, Badiyyah na kallonta da kyar tace "Baƙin sun tafi? Ina son in je parlor na gaji da nan din" Mayraah tace "Eh sun tafi" Ita kanta Badiyyah yau ta ɗan samu sukuni tunda ba ayi neglecting dinta as always ba, yau gashi har ruwan wanka sai da Mayraah ta tara mata ta samu tayi wanka, hatta Ammi bata bi ta kanta a gidan iyaka ta ajiye mata abinci in ta ga dama ta ci, wanka ma idan ta ga dama taje ta tara ruwa tayi, sai kuma Maheer da ta saka yake bata medication shi ma yana ajiye mata magani yake fita, Mama Ladi kuwa sai dai bata kyallara ido ta ganta ba, munanan kalamu sai wanda ta manta ne bata sakar mata, hakan kuma ke sa Badiyyar kuka sosai taji kamar ta mutu ta huta kawai, yau kuwa tun da Mayraah ta dawo take by her side even if she is not saying anything to her, Mayraah tace "Sun tafi, za ki iya saukowa, ba kowa a parlon" Da kyar ta lallaba suka koma downstairs ta kwanta nan tsakar carpet, sabuwar mai aikin gidan ce ta kira Mayraah da ladabi tace "Hajiya ta hanata saukowa ta kwanta nan saboda baƙi masu shigowa fa" a hankali Mayraah tace "Ba jimawa zata yi a nan ba" Suna cikin magana Haseenah ta leko Parlon don tabbatar da Mama Ladi bata ciki kafin ta shigo, tana ganin bata parlon ta shigo zata kitchen ta debi abincin rana, dama yanzu ko gas bata kunnawa sai an girka a nan ta faki idon mama Ladi ta shigo ta diba tunda ba wai kanta ya gama healing bane ita ma har yanzu jinya take, tana kyallara ido taga Badiyyah ta fara wakar habaici tana taunar cingam wai wata tayi cikin shege don ta ci ragon suna.... Can kuma ta hango Mayraah wani matsiyacin kallo ta mata ta shige kitchen bata fasa wakar da take ma Badiyyah ba, Mayraah dai ta bi ta da kallo, ita dai Badiyyah dama ko kallon direction dinta bata yi ba don duk haduwar da za su yi da Haseenah a gidan wakar da take mata kenan, to tana fama da kanta ina taga ta kulata. Washegari wajen karfe goma na safe Mayraah ta tashi daga baccin da take, har ta mance rabon da tayi bacci peacefully kuma me tsayi haka, wanka tayi ta shirya sannan ta gyara ma Ammi dakinta ta fito parlor, Maheer ta gani zaune parlon shi kadai, ta karasa kusa da shi ta zauna kasa tace "Yaya ina kwana?" Yana kallonta yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kan ya daina ciwo?" Ta ɗan buda ido sannan ta cire dankwalin kanta don gashinta suka zubo kasa tace "Ya daina" Tun jiya da Ammi tayi mata kitson kalaba take complain din ciwon kai don ta dade bata yi kitso ba, hakan ma yasa ta kwanta da wuri jiya da daddare, yanzu kuma da ta tashi taji babu ciwon, yana kallon kitson nata yace "Yayi kyau" Murmushi tayi tace "Thank you, yaya result dinmu fa?" Sai bayan da tayi tambayar gabanta ya fadi sosai she can't imagine her spilling, ya ɗan yi shiru yana kallonta, nan da nan hawaye ya cika idonta, yanzu gaba daya hawaye baya mata wahala nan da nan take hawaye, cikin rawan murya tace "I had issues ko?" Yace "Nasan tsohon saurayinki ya gaya maki ai" Har sannan gabanta na faduwa tace "Wallahi yaya A'a, babu ta inda zai yi accessing dina ya gaya min" Yace "Ai na zata kin ga result din naki tuntuni" Ta girgiza masa kai tayi narai narai da ido, yace "To bari in nuna maki, but...." Hankali tashe tace "But what yaya??" Yace "Promise me u will be calm ko me zaki gani, kuma ki gode Allah" Wasu hawayen ne suka taru idonta, yace "Toh shikenan" Da sauri ta goge idonta tace "I will be calm plss" Yace "Good, dawo nan" Mikewa tayi ta koma gefensa da ya nuna mata ta zauna sai tsuru tsuru take da ido, ya shiga WhatsApp dinsa ya nemo chat dinsa da Hamidah da ta turo masa result din, Mayraah da duk jikinta ke bari don bata san me zata gani ba ta rufe fuskarta da kujera, ya dubo result din da Hamidah ta turo masa sannan yace "Here...." Ƙin dagowa tayi tace "Kawai ka gaya min plss" Yace "Toh shikenan bari in ajiye wayar" Dagowa tayi da sauri ta amshi wayar cikin dakiya tana kallon screen din, wani kara tayi ganin pass, ta maida dubanta da sauri gun CGPA dinta kawai taga da first class dinta ta fita, ai bata san sanda ta rungumesa ba cike da farin ciki, ya ɗan buda ido yace "Ke... baki da hankali ne" She was soo happy ta zamo kasa tace "Alhamdulillah" Sai kuma tayi sujud shukr, yace "To abinda ya kamata kiyi kenan kike shirme" Mayraah ta dade bata yi farin cikin da tayi a moment din nan ba, amma fa can kasar zuciyarta tunanin ta yanda za ace ta fita da first class take, ita fa tasan abinda tayi a exams din, how comes Kuma ta fito da first class dinta still, but all the same she is soo Happy, mikewa tayi ta dawo gefen Maheer ta zauna tace "Yaya how about sis Badiyyah's result?" Yace "She was expelled" Jikin Mayraah yayi sanyi tayi shiru tana kallon sa, shi ma kallonta yake, can ta sunkuyar da kanta, yayi kasa da murya yace "Je ki amso breakfast dinki" Mikewa tayi ta fita daga parlon ya bi ta da kallo. Bayan 4 days da dawowan Mayraah tana kwance dakin Ammi da rana wayarta ya fara vibrate, dubawa tayi taga Dr Khalil ne ke kiranta tunda ta dawo sau daya ya kirata sai yanzu kuma, dagawa tayi ta kai kunne tayi masa sallama, bayan ya amsa ta gaishesa, yace "Ya kike ya gida?" Tace "Alhamdulillah, ya Ashnaah da Ashfah" Yace "They are fine, kin koma gida kin mance mutane ko" Murmushi tayi tace "Aa ni ban manta ka ba...." Yace "Gashi nan ko hello babu" Tace "Ai bana son in kiraka ne saboda mom twins" Yace "I understand Mayraah, ya Umminki?" Tace "She is fine Alhamdulillah" Yace "Ranan ai Barrister ya hadani da ita mun gaisa" Tace "Da gaske??" Shiru Dr Khalil yayi saboda bude office dinsa da aka yi, ganin wanda ya shigo yace "I will call u back" Daga haka ya katse wayar ya ajiye, Files din hannunsa yayi dropping masa kan table yace "I will be flying to Adamawa later, attend to this files and submit them to me before evening" Dr Khalil yace "Ohk sir, zaka je wajensu Mama kenan" Bai ce masa komai ba yana duba wani textbook dake kan table dinsa, Shi dai Dr Khalil kallonsa kawai yake, after checking the textbook ya daga kai ya kalli Dr Khalil yace "At last ka hakura ka samar mata aikin a wani asibitin kenan, but i was surprise da naga baka yi resigning ka bi ta can ba" Dr Khalil yayi kamar bai gane maganar da yake ba yace "Wa kenan?" MD na kallonsa yace "Ka fi ni sani" Dr Khalil ya fashe da dariya yace "Wait!!! Are you trying to ask for her whereabout in disguise?" MD ya hade rai kafin yace komai Dr Khalil yayi saurin cewa "She is being sick, very sick, ko picking call bata yi.... Kuma as our boss ya kamata kai da any other Dr or Nurse including me mu je mu dubata, she is seriously sick, an tafi da ita kano gun iyayenta...." Juyawa MD yayi ya fita daga office din, Dr Khalil ya bi sa da kallo yana murmushi. Bayan magrib Mayraah ta sauko downstairs ta shiga kitchen don dafa ma Ammi shayin da ta saba yi mata, bayan ta daura tea din ta zuba duk kayan kamshin da zata saka aka bude kofar kitchen din ta juya da sauri, ya shigo kitchen din suna hada ido tace "Ina yini" Bai sake kallonta ba yace "Lafiya lau" Rabonta da ganinsa tun jiya da safe, plate ya dauka zai debi abinci ta bi sa da kallo jin yanda yake wani kamshi tace "Yaya Maleeha fa?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Wacece haka?" Ta wara ido tace "Ita Maleehar ce baka sani ba?" Yace "Tuna min dai" Dariya ta fara yi sosai, ya juya yana kallonta tayi dariyar me isarta tayi shiru, still shi dai kallonta yake, tace "Kilan ma daga wajenta kake yanzu haka yanda naji kana kamshi shine kake min pretending" Yace "Haba" Ta kara kyalkyala dariya tace "I am sure" Yace "Aa sai dai ki rakani mu je yanzu" Da sauri tace "To don Allah mu je, bari inyi sauri in gama yi ma Ammi shayi sai in kai mata kafin nan ka gama cin abincin sai mu tafi" Yana kallonta ya mayar da abincin da ya fara diba a warmer yace "Sai mun dawo zan ci" Ta ɗan buda ido tace "Toh kaci ko kadan ne mana" Girgiza mata kai yayi without saying anything, tace "Toh bari in baka shayin Ammi kadan ka sha" Daga haka ta maida hankalinta kan shayin da take, shi dai yana tsaye yana kallonta, cikin few minutes ta gama dafa shayin ta dauko karamin tea cup da saucer dinsa ta fara zuba masa, sannan ta nufesa tana kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta, mika masa tayi a hankali tace "Here" taga bai amsa ba kuma kallonta yake, tace "Yaya" Sai da ta sake kiransa yayi saurin mika hannu ya karba, tace "Why are u absentminded? Tunanin me kake yi" Bai sake kallonta ba yace "Nothing, idan kin gama ina jiranki" Daga haka ya fita daga kitchen din ta bi sa da kallo, wani mug ta dauka ta zuba ma Ammi shayin bayan ta kashe gas din ta goge wajen ta fita daga kitchen din, tana ajiye ma Ammi shayin tace "Ammi gashi na gama" a hankali Ammi tace "Allah maki albarka" Mayraah tayi murmushi ta mike tace "Ammi zan raka ya Usman wajen wata frnd dinsa yanzu" Ammi ta kalli agogo tace "Frnd kuma?" Dariya tayi tace "Eh" Ammi tace "Toh sai kun dawo amma plss kar ku jima dare yayi" Hijab Mayraah ta shiga dakin Ammi ta dauka, sai da ta fara shafa turare a jikinta, har ta mance rabon da tayi amfani da wannan special turaren nata tun kafin a fasa aurenta ta daina amfani da turaren sai yau kuma da ta daukosa cikin kayanta, bayan ta gama shafa turaren ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta fita tayi ma Ammi sallama, sai da ta fara shiga dakin da Badiyyah take ta sameta tana bacci, abincin da ta kawo mata ma kadan ta samu ta ci, Mayraah ta rufe sauran sannan ta fita downstairs, zaune ta tadda Usman a parlon yana jiranta ga tea cup din da ta zuba masa shayi ya sha rabi ya ajiye sauran, tana kallon sauran shayin a hankali tace "Yaya bai maka dadi bane?" Yana kallonta yace "Yayi" Tace "To naga baka shanye ba" Yace "Ya isa" Karasawa tayi ta duka gabansa ta dau sauran shayin ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, Mayraah na shiga kitchen din ta shanye sauran shayin ta wanke cup din da sauce ta ajiye inda sauran suke sannan ta fito, tana kallonsa tace "Yaya mu je" Mikewa yayi ya nufi kofa ta bi bayansa. Suna fita compound din bayan sun bar anguwan taji yace "Kar ki sake saka turaren da kika saka yanzu" Mayraah ta juya tana kallonsa da mamaki, can tace "Saboda me yaya?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Kar ki sake kawai nace" shiru tayi bata ce komai ba, bata ce masa komai ba, ita dai tana ta zuba ido ta ga ta inda za su billo gidansu Maleeha tunda ta san gidan kuma taga sun wuce hanyar gidan, bayan sun yi nisa sosai da anguwan ta kasa daurewa ta juya tana kallonsa tace "Yaya sun tashi ne daga gidansu?" Yace "Ehh" Tace "Ayya, i was wondering naga mun wuce unguwan tun dazu" Ya juya ya kalleta yace "Kin taɓa zuwa ne?" Ta zaro ido tace "Gaya min fa tayi" Yace "Ohk" after almost 30mins ride ta gansu a wani anguwa na masu shegen kudi, ta dinga bin manyan gidajen da kallo har taga yayi horn bakin wani gate mai gadi na lekowa ya gansa ya buda gate din ya shiga yayi parking yana kashe motar ya sauka, Mayraah ma ta sauka ya kulle motarsa, ganin ya nufi entrance din gidan da sauri tace "Yaya ba kiranta zaka yi ba tukun" Yace "Na kirata ai" Bin bayansa tayi har suka iso kofar shiga cikin gidan, Mayraah was shock ganin Hajiya Amina ta bude masu kofa, da fara'a take masu sannu da zuwa, Mayraah dai ta sunkuyar da kanta, da tasan nan Ya Usman zai kawota da babu abinda zai sa ta biyo sa, haka nan dai ta zauna kan kujera ta gaisheta, Hajiya Amina ta amsa da murmushi tana tambayarta Ammi Mayraah bata dago kanta ba tace "Tana nan lafiya" Hajiya Amina ta kalli Usman tace "Kwana biyu shiru baka billo ba Barrister" Sai kuma da sauri tace "Au na tuna Yallabai yace min kaje kaduna, to ya aikin?" Yace "Alhamdulillah" mikewa yayi yace "Zan shiga masallaci inyi sallah" Tace "Toh shkkn" Daga haka ya fita parlor zai tafi masallacin dake jikin gidan daga gefe wanda Abba ya gina, Hajiya Amina na kallon Mayraah tace "Mu je Abban naki na sama a parlor ki gaishesa" Mayraah ta mike har a sannan fuskarta babu wani walwala ta bi bayanta zuwa upstairs, Abba yayi farin cikin kawo Mayraah da Usman yayi, dama yana ta son ce ma Ammi a kawota gidan ko yini ne tayi amma ya bar ma zuciyarsa don bai san yanda Ammi zata dau batun ba, liyafar abincin da Hajiya Amina ta ajiye masa ya zuba masu tare da Mayraah, Hajiya Amina tace "Je ki ga ko yayan naki ya dawo masallaci ya zo ya ci abinci" Mikewa Mayraah tayi ta fita daga dakin ta sauka downstairs, Zaunawa tayi kan kujera ganin Usman bai shigo ba, bayan some minutes sai ga shi ya shigo parlon, ta tashi tana kallonsa tace "Yaya wai kaje sama inji Abba, pls yaya kana gama cin abincin ka maida ni gida plsss don Allah" Sosai ta marairaice masa don har ga Allah gida kawai take son ta ganta, Yace "Nan din ba gida bane?" Ta wani hade rai tace "Ni dai pls mu tafi gida" Sama ya wuce ta bi bayansa har zuwa parlon Abba, kusan duk bayan kwana biyu sai Usman ya zo gidan sai in baya gari, Maheer ne dai tun ranan da Abba ya kirasa ya zo bai sake bin hanyar gidan ba har yau, Da kyar Mayraah ke cin abincin da Abba ya zuba masu, Hajiya Amina na zaune parlon tana kallon TV, har daga karshe Mayraah ta mike tace ta koshi, Hajiya Amina tace "To mu je kiyi sallan isha" Babu yanda Mayraah ta iya haka ta mike ta bi bayanta suka fita parlon zuwa part dinta, bayan tafiyarsu with few minutes Usman ya ajiye spoon din hannunsa, Abba yace "Are you satisfied" Usman bai yarda ya kallesa ba, kansa na kasa yace "Sure... dama Abba akwai maganar da nake son zan yi maka" Abba na kallonsa yace "Ohk, i am all ears barrister" Ganin yayi shiru kamar me tunanin ta inda zai fara maganar Abba yace "Ina jin ka Usman, tell me what is it" Usman ya daga kai a hankali ya kalli Abba..... [8/1, 7:00 PM] Khaleesat Haiydar💖: Shiru Abba yayi yana ta kallon Usman, can ya ɗan yi murmushi yace "Did you say this to anybody? I mean did u discuss it to anyone?" Usman ya girgiza masa kai without looking at him, Abba ya sauke ajiyar zuciya, bayan few seconds yace "Not even her?" Usman yace "Eh" Abba na gyada kai yace "Gaskiya nayi farin ciki da wannan batun Usman, i am so happy about it, and this is what i wished for few months back, but...." Usman ya daga kai ya kalli Abba, calmly Abba yace "I want u to let ur intentions be known to her before anything...." Usman ya girgiza kai da sauri yace "Abba kawai ba sae nayi hakan ba, kawai dai..." Sai kuma yayi shiru, Abba yace "You have to Usman, kwanaki i wasn't willing to give her an alternative cause tunanina hakan kadae ne mafita gare mu da ita baki daya, and i understand you too then da kayi declining... But yanzu i don't think i will do anything without her consent, say ur mind to her, go on a courtship with her...." Kallon Abba kawai yake baya ko kifta ido, Abba jinjina masa kai giving him assurance yace "Ko nan da sati daya ne in dai da consent dinta you gat my back son" Usman bai iya yace komai ba ya sauke kansa, Abba dai sae kallonsa yake, bude kofar parlon aka yi Mayraah ta shigo da sallama, Abba ne kawai ke kallonta, Usman kam bai daga kai ba, har ta karaso ta zauna gefensa tana kallonsa tace "Yaya na gama mu tafi gida" Abba yace "Nan din ba gida bane?" Ta kallesa ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Abba ae ban ce ma Ammi zamu kwana ba shi yasa" Abba ya gyada kai yace "Toh in kin ce mata sai ki zo kiyi weekend a nan din" Mayraah dai bata ce komai ba ta mike tana kallon Usman tace "Yaya Ammi fa tace kar dare yayi sosai" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta yace "To ba yanzu zan tafi ba" Ta marairaice tana kallonsa, mikewa Abba yayi yace "Naga ko karfe tara bai karasa ba ai Mimi, so there is still time, bari inje inyi sallah" Fita yayi daga parlon, Mayraah ta zauna kusa da shi kamar zata yi kuka tace "Yaya pls kaga dai Ammi bata san za mu zo nan ba ko, kuma ce min kayi wajen Maleeha fa za mu je, ni dai ka tashi mu tafi gida don Allah" jin yayi shiru ta ɓata fuska tace "Ka ji mana yaya" Sai a sannan ya juya ya kalleta yace "Nan din daji ne?" Ta turo baki ta koma ta jingina jikin kujera tana kallonsa fuskarta a daure, har bayan minti sha biyar bai ce mata ba, ita ma bata ce masa ba a parlon, lkci lkci take turo baki duk yana lura da ita, can ya mike tsaye, tana ganin haka ita ma ta tashi, ya kalleta yace "Ke a nan fa za ki kwana" Ko rufe baki bai yi ba tace "Wallahi bazan kwana ba" Tana fadin haka ta nufi kofa yace "Kar ki fita" Dawowa tayi tana kallonsa kiris ya rage ta fashe da kuka, ya koma ya zauna kan kujera, a hankali yace "Now tell me, me yasa baza ki kwana nan ba?" Ta zauna kasa daga gefensa tace "Kawai wajen Ammi zan tafi" Jin bai ce komai ba ta daga kai suka hada ido, tace "Pls mu tafi yaya" Hajiya Amina ce ta shigo parlon tana kallon sauran abincin da ba a taɓa ba tace "Ka ci abincin kuwa barrister?" Yace "Eh na ci, za mu tafi ne" Hajiya Amina tace "Ina ce ai a nan Mayraah zata kwana" Usman yace "Bata zo da shirin kwana ba" Hajiya Amina tace "Toh shikenan, ko weekend ne sai ta zo" Mayraah ta sauke wani ajiyar zuciyar relieve sanda taga sun bar gidan. Sai da suka yi nisa sosai ta kallesa tace "Yaya baza mu siya ma Ammi Apples da watermelon ba?" Yace "Ok za ki siya mata?" Tayi er dariya tace "I am not together with my Atm?" Ya ɗan kalleta yace "Nawa za a ara maki?" Ta langwabar da kai tace "Like 10k" Yace "Ohk" gun da ake siyar da fruits yayi parking ta juya ta kallesa tana jiran ya bata kudin taje ta siyo, bude motar yayi ya sauka ta bi sa da kallo, bayan wasu mintuna ya dawo ya ajiye mata ledan kan kafarta yace "15k, sai ki biya yaushe?" Dariya tayi tace "Muna isa gida" Yace "Alright" Suna isa gida bayan yayi parking ta bude motar ta sauka ta jira shi ma ya sauka, bayan ya rufe motar ya jingina jiki folding his arms yace "Mun iso gida" Bata san sanda ta fashe da dariya ba tace "Yaya ko ciki fa bamu shiga ba" Yace "Toh" Daga haka ya nufi cikin gidan, ta bi bayansa tana murmushi, suna shiga parlor Maheer kadai ne zaune yana danna wayarsa, sau daya Usman ya kallesa ya wuce sama, Mayraah na ganin Maheer ta nufi kujeran da yake ta zauna kasa ta ajiye ledan hannunta tana kallonsa tace "Ina yini yaya" Yace "Ina ku ka je?" Ta buda ido tace "Yaya ce min fa yayi wajen budurwarsa zai je shine ya kai ni Miller road, ashe wajen Abba zai je" Maheer ya maida dubansa kan waya yace "Ohk" Tace "Yaya ka ara min 15k cash pls" ya kalleta yace "Me za ki yi da 15k?" Tana murmushi tace "Just borrow me pls" Yace "Sai ki maida yaushe" Dariya ne ya taho mata tace "Gobe da safe" Yace "Ohk, mu je in baki" yana fadin haka ya mike, tashi tayi ita ma ganin ya nufi kofar fita tace "Aa yaya zan jira a nan ka kawo min pls" Ya juya yana kallonta yace "Why?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya karasa kusa da ita, still looking at her yace "Why?" Ta sauke ajiyar zuciya tace "I am not going there because of ur wife" Yace "Do not call her my wife again Mimi, Haseenah is not my wife" Ita dai bata ce komai ba, yace "Mu je" a hankali ta fara tafiya tana biye da shi a baya, sai da suka iso chalet din tace "Amma bazan shiga ba, i will wait outside Yaya" Tana fadin haka ta tsaya dai dai stairs din chalet din, shi ma bai yi forcing dinta ta shiga ba, yana bude kofa Haseenah dake zaune kan kujera tana waya ta katse wayar tana goge hawayen idonta tana kallonsa, ko kallonta bai yi ba ya bar kofar a bude ya wuce daki, kamshin turaren da ta dinga ji na shigowa parlon ya sa ta mike ta taho bakin kofa don jikinta ya bata da mutum a wajen, tana ganin Mayraah bata bari sun hada ido ba ta koma inda take ta zauna, ba a dau lokaci ba Maheer ya fito da cash din a hannu, ya mika ma Mayraah ta amsa tace "Thank you Yaya" Shi dai bai ce mata komai ba yana kallonta, ta juya ta sauka daga chalet din ta koma main building din gidan da sauri, ledan fruits din ta dauko sai da ta fara zuwa dakin Usman tayi knocking ya bude kofar ganinta ya koma ciki ya zauna, ta bi bayansa tana murmushi tace "Ga kudin" Amsa yayi ya ajiye gefensa, ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Washegari Mayraah na idar da sallan asuba bayan ta gama azkar ta shiga dakin da Badiyyah take, zaune ta sameta kasa, Mayraah ta zauna tana kallonta tace "Ya jikin?" Badiyyah ta gyada mata kai, Mayraah tace "In kawo maki kunun ko shayi" Badiyyah tace "Ko wanne" Mikewa Mayraah tayi ta fita, Bangaren Ammi ta fara tafiya don ta gaisheta, tana shiga ta tadda Mama Ladi na minshari kan darduman da tayi sallah, dakin Ammi ta karasa tayi sallama, Ammi ta amsa mata, ta shiga dakin... Maheer na zaune gefen Ammi, ita kuma tana zaune kan darduma, Mayraah ta duka kusa da Ammi ta gaisheta, Ammi tace "Kin tashi lafiya" Mayraah tace "Alhmdlh" Kallon Maheer dake kallonta tayi tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau" Mikewa tayi tace "Zan dawo Ammi" Daga haka ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo har ta fita, sai kuma ta kalli Maheer a hankali tace "We will continue later Maheer" Bai bari sun hada ido ba yace "Ohk" daga haka ya mike ya fita daga dakin. The next day friday Mayraah na dakin Badiyyah da yamma Mama Ladi ta shigo, Mama Ladi tayi tagumi daga tsayen da take tace "Naga abinda ya isheni ni Ladiyo, Wato ke dai Mera baza ki ji shawaran da nake baki ba ko? Baki da aiki sai makale ma wannan mata kamar almajira, nace ki fita hanyarta kiyi ta kanki kin ki, me yasa kike cusa kanki a abinda bai shafeki bane? yarinyar da kowa yasan ba sonki take ba tun asali, yarinyar da saboda ita kiri kiri aka fasa aurenki da ɗan matsiyatan can, ko ke baki lura alhakinki ke bin ta ba? Ko wani me ciki za ki ganta fes fes gwanin sha'awa amma Badiyyah kamar sabuwar almajirar kana rod dake garin kaduna, ke ko don kar kije ki shaƙi wata cutar baza ki kama kanki daga zuwa inda Badiyyah take ba? To ni dai ba ruwana Mamuda na kiranki, yana can parlon Ammi yace ki je" Daga haka Mama Ladi ta fice daga dakin tana toshe hanci, Mayraah ta kalli Badiyyah da hawaye ya cika idonta, kasa ce mata komai tayi amma har cikin ranta bata son abinda Mama Ladi ke yi ma Badiyyah a gidan, abun yayi yawa, mikewa tayi ta fita daga dakin ta tafi bangaren Ammi, Abba na zaune parlorn Ammi, Ammi kuma na ta harkan gabanta, Mayraah ta zauna ta gaida Abba, Abba ya amsa yace "Anjima Usman zai kai ki can gidan Hajiya Amina kiyi weekend, mai aikinta bata nan" Sai a sannan Ammi ta juya ta kalli Abba, Mayraah dai ta kasa cewa komai tana kallon Abba, Abba yace "Sai ki dau kayan da za ki tafi da su" Ammi na kallon Abba cikin karfin hali tace "Mamuda kawai fitowa za kayi kace min kana son ta koma gidan matarka, ba sai ka yi wani corner corner ba, just go straight to the point" Mayraah ta sunkuyar da kanta lokaci daya har hawaye ya kawo idonta, Abba na kallon Mayraah yace "Tashi ki tafi kiyi abinda nace maki" Mayraah ta mike ta juya ta nufi kowa hawayen dake makale idonta ya zubo fuskarta ta fita daga parlon, sai a sannan Ammi ta fashe da kuka ta nufi dakinta, Abba ya bi ta da kallo, sai kuma ya tashi ya bi bayanta, kuka sosai ya sameta tana yi, ya zauna gefen gado yace "Kin ga, babu ta yanda za ayi kice zan raba ki da Mayraah, Mayraah is staying there for just 2 days ta dawo nan..." Cikin kuka Ammi ta katse sa tace "To ban amince ba Mamuda, kuma bazan taɓa amincewa ba, babu inda Mayraah za ta je ai ba wani ɗan iskan ya rainan min ita har zuwa yau ba, ba wani ya sha min wahalanta ba, ba wani ya...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai zuciyarta na mata zafi tace "Mamuda kar ka sa inji ina dana sanin aurenka, abinda ban taɓa yi ba sai yanzu da aurenmu ya doshi shekaru arba'in, wahalan da na ci a gidanka da irin sadaukarwa ta da abinda zaka biya ni kenan? Is this what i deserve Mamuda? Is this how to pay me? Ko me zan maka na cancanci haka? Me yasa zaka yi saurin mance halacci na gareka? After all my sacrifice yanzu wata from no where zata zo ta fi ni ƙima da mutunci a idonka, wata ce zata zo tayi reaping where she never sowed, ban taɓa zaton haka daga gareka ba Mamuda, kuma a duk zaman mu in dai na cuceka...." Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai ta mike ta bar masa dakin kawai, ya sake tashi ya bi ta parlor. Mayraah na dakinta bayan ta ci kukanta Abba ya kwankwasa kofar ya bude, mikewa tayi daga zaunen da take tana kallonsa, Abba yace "Dauko kayanki" Yana fadin haka ya bar bakin kofar, jikin Mayraah yayi sanyi sosai, fitowa tayi daga dakin ta tafi bangaren Ammi, a bedroom dinta ta sameta, Mayraah ta karasa kusa da ita ta zauna ta ma rasa abinda zata ce, Ammi tayi karfin halin cewa "Ki je kiyi yanda Abbanki yace Mayraah" Mayraah ta fashe da kuka tace "Ammi ni bana son in je gidan" Ammi tace "Ran sunday za ki dawo in sha Allah, in ma ba a dawo dake ba zan sa Maheer yaje ya dauko ki, be a good girl kije ki dau kayanki kala biyu" Kuka kawai Mayraah take, Ammi tace "Tashi ki je my dear" Mikewa tayi tana goge hawayen idonta ta tafi ta dau kayan nata kala biyu a karamin jakanta, tana dawowa bangaren Ammi ta tadda Abba a parlon, hakan ya sa ta juya ta fita ta sauka downstairs kawai, bayan kusan minti sha biyar Abba ya sauko yace "Je ki mata sallama ki zo mu tafi, i don't want go miss my flight" A hankali Mayraah ta mike ta wuce sama zuwa part din Ammi, a parlor ta sameta still a zaune, Mayraah ta zauna kasa tana kallonta cikin sanyin murya tace "Ammi don Allah kiyi hakuri..." Sai kuma ta fashe da kuka, Ammi ta dafa kanta tace "Kar ki damu daughter, u are not to be blame, ba komai, ranan lahadi Maheer zai je ya dauko ki" Mayraah ta gyada mata kai hawaye na sauka idonta, Ammi tace "Tashi ki je, idan yayi dropping dinki airport zai wuce" Mayraah ta mike tana goge hawayenta ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo tana kokarin ganin hawayen da ya taru idonta bai zubo mata ba, Sai da Mayraah ta fara shiga dakin da Badiyyah take, ta duka gabanta tace "Zan je Miller road" Da sauri Badiyyah ta mike zaune ganin jakar hannunta cike da karfin hali tace "Yaushe za ki dawo?" Tana fadin haka hawaye ya cika idonta, Mayraah ta kwantar da murya tace "On Sunday in sha Allah, ba dadewa zan yi ba" Kai kawai Badiyyah ta gyada mata hawaye na sauka idonta, Mayraah ta mike ta fita daga dakin duk jikinta yayi sanyi. Suna isa gidan a waje Abba yayi parking suka shiga ciki, Hajiya Amina tayi farin cikin ganin Mayraah sosai, ganin yanda ta makale bakin kofa tace karaso ciki mana, sai a sannan ta karasa ciki ta xauna, sallama kawai Abba yayi ma Hajiya Amina, tayi amsa addu'an Allah ya tsare ta rakasa har compound ita dai Mayraah na zaune kan kujera makale da jakarta, sabon drivern da Abba ya dauka a gidan shi yayi driving dinsa zuwa airport, Hajiya Amina ta dawo parlor tana kallon Mayraah tace "Tashi mu je ki ga dakin ki" Mikewa Mayraah tayi ta bi bayanta suka tafi sama, Hajiya Amina ta bude mata dakin tace "This is ur room" Mayraah ta dinga kallon dakin ganin tsadaddun furnitures din ciki kamar dakin amarya, sauke kanta tayi kasa ta karasa cikin dakin. Bayan isha Mayraah na daki tana kokarin dialing number Dr Khalil saboda miss calls dinsa da ta gani Hajiya Amina ta shigo, hakan yasa ta fasa kiran, zaunawa gefen gadon Hajiya Amina tayi tana kallonta tace "Abincin ya isheki?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Na koshi" Hajiya Amina tace "To maa sha Allah, ya kika baro su Amminku?" Mayraah tace "Lafiya lau, tana gaisheki" Hajiya Amina tace "Ina amsawa, chatting kike ne" Mayraah ta girgiza mata kai tace "Aa" Hajiya Amina tayi murmushi tace "To yanzu waye surkin namu ne?" Mayraah ta ɗan kalleta sai kuma ta sunkuyar da kai, Hajiya Amina na murmushi tace "Feel free to talk to me dear, i am also ur mother" Mayraah ta ɗan kirkiri murmushi da kyar tace "Aa ba kowa" Hajiya Amina tace "Are you sure?" Mayraah ta gyada mata kai, Hajiya Amina tayi shiru tana kallonta, can a hankali tace "Ni kuma kin san wa nake maki sha'awa Mayraah?" Mayraah ta daga kai ta kalleta ba tare da ta shirya yin hakan ba, Hajiya Amina tayi kasa da murya tace "Yayanki" Mayraah dai ta dinga kallonta tana imagining wani yayan take nufi har ranta bata kawo su Maheer ba fa tunda ita dai tasan ba aure tsakaninsu a mentality dinta, Hajiya Amina tace "Kin ga ya san halinki, ya san wacece ke, kema kuma kin san halinsa kilan har littafi sai ki iya rubutawa akan halayyarsa, you 2 will make a perfect couple Mayraah, beside he is a calm and gentleman" Mayraah ta sunkuyar da kai feeling uncomfortable with the conversation, har cikin ranta bata san wani yayan take nufi ba fa ita, Hajiya Amina tace "Kin dai ga abinda ya faru akan aurenki kwanaki, so hakan kadai shine rufin asirinmu gaba daya" Hajiya Amina ta kalli wayar hannunta dake ring ta mike tace "Bari in amsa waya" Daga haka ta nufi kofar Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita. [8/1, 10:45 PM] Khaleesat Haiydar💖: Wajen karfe goma Mayraah na kwance sai juye juye take, har a lokacin maganganun Hajiya Amina sun kasa fita daga ranta, tayi kokarin gano wani yayan nata take nufi amma taki bari zuciyarta ya kai tunanin ta kan brothers dinta she just believe ba su bane and she is sure of that, wayarta ne ya fara vibrate, ta jawo a hankali tana kallon me kiran, Dr Khalil ta gani da kamar bazata daga ba sai kuma tayi picking ta kai kunne, gaisawa suka yi yace "Ina kika shiga yau baki picking call?" A hankali tace "Bana jin dadi ne" Yace "Subhanallah, what's wrong with you?" Tace "Kawai kamar zazzabi ne" Yace "Allah ya sauke" Tace "Ameen thank you" Yace "Dama za mu shigo kano gobe, kinga if it's okay we can come over mu duba ki kafin mu koma Abuja" Mayraah tayi shiru, can tace "Kai da wa?" Yace "Dr Balogun da Hamid, mun shigo wani program ne" Mayraah tace "Toh shikenan Allah ya kai mu" Yace "Ameen, Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen Nagode sosai" Yace "Kinsan Ceo din ma ta koma tun last week but nan da few days zata shigo saboda workshop da za ayi" Mayraah tace "Ohk, Allah ya kai mu" Yace "Ameen, till tomorrow, in mun shigo kafin zan kira ki in sha Allah" Tace "To a gaida min twins" Yace "Za su ji" Daga haka ya katse wayar, mikewa zaune tayi tana tunanin yanda zata samu gobe ta koma gida wajen Ammi in ma Dr Khalil za su zo gwara suje can din su sameta a gidansu, don ita dai tasan nan ba gidansu bane, wayarta ta sake daukowa tayi dialing number Maheer, yana fara ringing ya daga a hankali tace "Yaya" Yace "Mimi" tace "Good evening" Yace "So u still have my digit" Tayi murmushi kamar yana ganinta, yace "To ya aka yi?" Tace "Yaya plss i want to come back home tomorrow" Yace "Da gobe da jibi duk daya ne Mimi, just be patient, or is there any problem?" Ta girgiza kai tace "I am not comfortable" shiru yayi, sae kuma yace "Kiyi hakuri ki bari har jibin sae ki dawo gida kar Abba yayi fushi" Bata sake cewa komai ba, yace "Are you there?" Cikin sanyin murya tace "Na ji" yace "Good gal" Tace "Zan kwanta" Yace "Ohk sleep tight, kin ci abinci?" Ta gyada masa kai yace "To sai da safe" katse wayar tayi ta ajiye ta rufe ido. Washegari da yamma Mayraah na kitchen tana girkin da Hajiya Amina ta sa tayi masu, tuwo ne da vegetable soup tace tayi, Mayraah har ta mance rabon da tayi girki, bata fito kitchen din ba sae kusan karfe biyar bayan ta gama komai, zaune taga Usman parlor, ta ɗan buda ido tace "Lah yaya yaushe ka zo?" Ya kalleta sannan ya ci gaba da danna wayarsa yace "Now" tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" Tace "Ya Ammi fa?" Yace "She's fine" tace "In kawo maka tuwon na gama" Yace "Na ci abinci a gida" tace "Ohk" karasowa cikin parlon tayi tana kallonsa ta zauna gefensa tayi murmushi tace "You look cute" ya daga kai ya kalleta yace "Really" ta gyada masa kai still looking at him, yace "Ke ma" ta zaro ido tace "Nima me?" Yace "Abinda kika ce min" ta kyalkyale da dariya tace "Ae ka fi ni kyau, shi yasa Maleeha take ji da kai" shi dai kallonta kawai yake, sai kuma ya kamo hannunta calmly yace "Ke kuma kin fi Maleehar kyau ai" Mayraah tayi shiru jin abinda yace, lkci daya ya saketa ya ciro wayarsa zai fara dannawa, tayi kasa da murya tace "Yaya don Allah in zaka tafi zan iya bin ka?" Yace "Abba yace sai gobe" Hajiya Amina ce ta sakko downstairs ganin Usman tace "Yaushe ka shigo barrister?" Yace "Yanzu" mikewa Mayraah tayi Hajiya Amina tace "Har kin gama girkin kenan?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Na gama" Hajiya Amina tace "To Sannu da aiki" Mayraah ta ɗan yi murmushi ta wuce sama Usman ya bi ta da ido, Hajiya Amina ta karaso ta zauna tana kallonsa tace "Ya gidan?" Yace "Alhamdulillah" Mayraah na shiga daki ta dau wayarta taga kiran Dr Khalil har uku an hour ago, zaro ido tayi don ta mance yace mata za su zo yau, kiransa ta fara yi, yana fara ring ya daga yace "Bacci kike ne?" Tace "Aa ina ƙasa ne, ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya jiki?" Tace "Alhmdlh naji sauki" yace "Ba don an ɗaga flight dinmu ba ae kilan da yanxu muna Abuja, sae 8pm Flight din, so now.... ina ne anguwan naku?" Ta ɗan yi shiru sae kuma tace "I will call you back in few minutes time" yace "Ohk then" katse wayar tayi ta sauka downstairs, gun Usman ta nufa don Hajiya Amina ta shiga kitchen, ta zauna kasa daga gefensa tana kallonsa tace "Yaya wannan Dr din nan ne za su zo su nan wai sun shigo kano wani program, can they?" Usman yace "It's okay... Mun yi waya da shi ae daxu na tambayesa ko zai karaso yace min babu time saboda flight dinsu 3pm ne" Mayraah tace "Eh yace min an ɗaga flight din sai dare, i just saw his call" Usman yace "Ohk send him the address" Tace "Ai ban sani ba to, gashi kayi masa sending...." Tana fadin haka ta mika masa wayarta, Amsan wayar yayi ya rubuta address din gidan ya bata tayi sending ma Dr Khalil, sai ga kiransa ya shigo wayarta ta daga yace "Ohk expect us in 30mins time" Tace "To Allah ya kai mu" katse wayar tayi ta ajiye tana kallon Usman dake kallonta yace "Kije ki gaya mata za ki yi baƙi" Mayraah tayi shiru, sai ga Hajiya Amina ta shigo parlon da abinci ta debo masa, ya kalleta yace "Na fa ci abinci a gida" Tace "Ko kadan ne ka ci" Mayraah dai ta mike zata wuce sama don taje tayi wanka Hajiya Amina tace "Kema naga ba ki wani son cin abinci, dawo sai ku ci tare" Mayraah ta kalli Usman da ya kalleta shi ma, Hajiya Amina ta ajiye masu tuwo da vegetable soup tace "Taho ku ci Hajiya" Mayraah tayi murmushin karfin hali kawai ta koma ta zauna, Hajiya Amina tayi wucewar ta sama, tuwon Mayraah ta fara ci ba tare da ta jira sa ba, bayan few minutes ya sakko kasa shi ma ya dau spoon ya fara cin tuwon, tana kallonsa tace "Is it sweet?" Yace "Wa yayi?" Ta langwabar da kai tace "Ni mana" Yace "Bari in gama tukun sae inji ko yayi" Dariya tayi ta ci gaba da cin tuwon ta, bata wani ci da yawa ba ta tashi ta bar masa ta wuce sama, sai da ta fara zuwa dakin Hajiya Amina ta sanar mata da zuwansu Dr Khalil sannan ta koma dakinta tayi wanka ta shirya, jikin windown dakin ta tsaya tana viewing din unguwan that's beautiful, sai abun yake mata kamar ta taɓa zuwa anguwan nan, ko ma dai ba shi ba ita dai tasan ta zo area kamar haka, Lkci daya Musharraf ya fado mata, ta zaro ido gabanta na faduwa, kamar unguwan da ta taɓa zuwa ta samesa fa, tana cikin wannan tunanin wayarta dake kan gado yayi vibrate ta juya ta dauko wayar ta daga ganin Dr Khalil ne, yayi mata sallama yace "To, ga mu a house number din" A hankali tace "Ohk" Katse wayar tayi ta dau veil dinta ta fita, bata tadda Usman a parlor ba, hakan ya bata mamaki, sai ta koma sama ta gaya ma Hajiya Amina baƙin sun iso, Hajiya Amina tace "Ba sai kin fita ba bari zan kira mai gadi ya bude masu gate din kawai" Mayraah tace "To, yaya ya tafi ne?" Hajiya Amina tace "Eh dama Daura zai tafi, kuma ya wuce" Mayraah tayi shiru, sai kuma tace "Bai ce min zai tafi ba" Hajiya Amina tace "Ai na zata kun yi sallama" Mayraah bata sake cewa komai ba Hajiya Amina ta kira mai gadi tace ya bude ma baƙi gate, Mayraah ta juya ta fita daga dakin. Bayan some mintues ta sauka Downstairs don bude masu kofa, tana buɗe kofar taga Dr Khalil, murmushi tayi masa tace "Sannu da zuwa Baban twins" har cikin parlon tayi masa iso bayan sun gaisa ta kawo masa ruwa da lemo, yace "Ya jikin?" Tace "Naji sauki, kace har da su Dr Hamid" yace "Ohh su mota za su bi zuwa kd sannan su dau train, sun wuce tun dazu, nima hakan na so yi but it's not possible" Mayraah tace "Allah sarki" Hajiya Amina ta shigo parlon suka gaisa da khalil da fara'a sannan ta koma sama, Dr Khalil yace "Ita ce Ammin?" Murmushi kawai Mayraah tayi, yace "I spoke to ur brother, the Barrister, about ur work.... he said he will get back to me idan yayi magana da Abbanku, that was today in the morning so ban san ya za su yi ba, ina dae jiran kiransa" Mayraah tayi shiru tana kallonsa, yace "So duk yanda Abbanku yace haka za ayi, i hope za su bar ki kiyi aikin, in future za ki ji dadin hakan, no matter how wealthy ur parents are yana da kyau ace kai ma kana da source of naka income din" Mayraah tayi murmushin karfin hali bayan ta tuna she is just an abandoned orphan warce ko gadon wa enda take ma kallon iyayenta bata da shi, tunanin hakan ba karamin distablizing dinta yayi ba a lokacin, Dr Khalil yace "I think zan zo in tafi airport kar in yi missing flight...." A hankali tace "Baka sha ruwan ba ai" yace "I am okay, i just ate" tace "Toh shikenan" ya mike yace "Kiyi ma Ammi sallama pls" tace "In sha Allah" rakasa tayi bakin kofar parlon, yace "Baza ki rakani har waje ba kenan" tayi murmushi tace "Zan raka ka" A tare suka nufi gate din gidan suka fita har kofar gida, ya kalli Mayraah yace "Mu je ku gaisa da wani Dr, kin dai san sa...." tace "Ohk" karasawa gun motar tayi Dr Khalil ya bude kujera me zaman banza, turus Mayraah tayi tana kallon wanda ke zaune, shi ma tunda ya kalleta sau daya ya dauke idonsa yana ci gaba da kallon abinda yake yi a waya ya wani keeping serious face, ta kalli Dr Khalil da yayi mata alama da she should greet him, hakan yasa a takaice tace "Good day" ko jira ya amsa bata yi ba ta bar wajen, bata san shi ma bayi da niyyar amsawa ba, tana kallon Dr khalil tace "To Dr Allah ya tsare, a gaida min twins" Dr Khalil ya girgiza kai yana kara jinjina halinta, ta sakar masa murmushi tayi wucewarta cikin gida, Ta madubi MD ya bi ta da kallo har ta shige gidan, sae kuma ya kalli Dr Khalil yace "Wannan fitsararriyar yarinyar kake dagewa in shiga cikin gidan in duba ko? Does she even look like someone that is sick at all? Wallahi idan na maka Allah ya isa ɓata min lokaci da kayi sai Allah ya kama ka, what nonsense, yanzu meye amfanin nan din da ka kawo mu?" Dr Khalil ya kasa rike dariyarsa don daga Mayraahn har MD din ba karamin dariya suka basa ba, Dr Khalil ya zagaya ya shiga driver seat, MD yace "Allah bazan yafe maka ba, haka kawai kayi forcing dina mun zo nan yarinya ta fito ta min rashin kunya? Do you have any grudges against me Khalil?" Dr Khalil na danne dariyarsa yace "Oga boss i never forced u, kai da kace zaka Yola meye na biyo mu kano program din da kafi karfin attending, da ba sae ka tafi yolan ba kawai, sai dai in sharri zaka min sir, kuma fa ta ce maka good day" a fusace MD yace "Da na buge mata baki zata san good day, ni sa'anta ne da zata ce min good day, do i look like her mate ko an gaya mata ina harka da yara, wannan fa bata wuce 16 years ba idan aka duba real date of birth dinta" Dr Khalil ya tada motar suka bar layin, MD ya gyara zama yace "Nonsense, saboda suna common Miller road shine take tunanin kowa sa'anta ne?" Dr Khalil yace "Yanzu dai ba Ghetto ka ganta ba balle ka samu abun fade" MD yace "Muna komawa Abuja zan yi erazing data din da ka bani, she should come for interview....." Dr Khalil dai murmushi kawai yake yana driving dinsa, can dai yace "Kai fa Dr ko manyan likitoci ba harkansu kake shiga ba, sabgar gabanka kawai kake baka da lokacin su balle wannan yarinyar da kace shekaranta 16, naga ita dai ta samu time dinka sosai" [8/2, 7:27 PM] Khaleesat Haiydar💖: Ranan Lahadi karfe sha daya Mayraah ta gama shiryawa ta rufe karamin jakarta, sannan ta dau wayarta ta kira Maheer, yana fara ring ya daga, yace "Mimi" Tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau, how was ur night" Tace "Alhmdlh, dama ce maka zan yi na shirya" Yace "But ai sai da yamma Mimi" Ta ɓata fuska tace "Don Allah yaya ka zo ka tafi da ni gida, yau fa Abba yace, it doesn't matter ko da safe ne ko da yamma" Yace "Toh kin ga ina wajen aiki yanzu, after work sai in biyo in dauke ki, be patient please" Ji tayi kamar ta fashe da kuka, yace "Are you there?" da kyar tace "Na ji" Daga haka ta katse wayarta tana turo baki, bude kofar aka yi ta juya, Hajiya Amina ta shigo tace "Mu je ki rakani gidan makotanmu in masu gaisuwa, they lost their daughter 4 days ago" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi ta ciro Hijab dinta ta saka sannan ta bi Hajiya Amina suka fita, gidan dake kusa da na Abba suka shiga, Bayan Hajiya Amina tayi masu gaisuwa ta gabatar masu da kanta a matsayin neighbor dinsu don tun zuwanta anguwan ba gidan wanda ta shiga, godiya suka mata sosai, Ita dai Mayraah na zaune, bayan ɗan lokaci Hajiya Amina tace "Toh bari mu koma, Allah ya gafarta mata, ya bada hakurin rashi" Suka mata godiya sosai sannan ta fita parlon da Mayraah, suna fita gate din gidan Mayraah ta dinga kallon motar dake tafiya duk da ya wuce gidan da suka fito, Hajiya Amina tace "Kinsan wanda ke cikin motar ne irin wannan kallo haka" Mayraah ta girgiza kai da sauri tace "Aa" Daga haka ta bi ta suka shiga cikin gida, tana komawa dakinta ta dau wayarta, dialing number dinsa tayi da ainahin sim da take using yanzu, har ya katse bai daga ba, ta sake kira sai ya daga, shiru tayi, yana jin haka yace "Mayraah" Ta sauke idonta kasa a hankali tace "Good morning Sir" Yace "Me yasa kika daina kunna line din da kika kirani da shi kwanaki, pls me yasa kike min haka Mayraah, is it because i care? Is it because i love you" Nan da nan jikin Mayraah yayi sanyi jin yanda yake maganar, a hankali yace "Mayraah" Cike da karfin hali tace "Ina ji... naga ka fito gida yanzu, ina za ka?" Musharraf ya kalli inda yayi parking a anguwan, everywhere was so silent balle ace ta ji hayaniyar mota or so, yace "Did u just guess?" Tayi murmushi tace "I saw you.... But in my dream" cikin sanyin murya yace "Mayraah my life isn't the same again ever since you left me, ban san haka so yake ba i wouldn't have started wllh, ni ban gujeki ba duk situation din da ya faru ke kika gujeni, da na sani da na ci gaba da zamana ban fara relationship ba, i had no luck in relationship kuma tsakanina da Allah na so ki ba da wani nufi ba, i resigned lecturing few weeks back, lecturing caused me all what i am going through now, i regret it, assuming a asibiti nake aiki may be sau daya zan ganki ki tafi shikenan ba lallai ki sake dawowa in ganki ba, amma as a lecturer, seeing you everyday made me fell in love with you without me realizing that, i never bargained for all this Mayraah, i am still yet to recover fully from the death of my father and only sister, then all of a sudden you...." Kasa ci gaba yayi, nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah jikinta yayi sanyi sosai ta kasa ce masa komai, ya katse wayar kawai, ta fashe da kuka, har ranta tasan she still loves Musharraf but su Abba baza su bari ta auresa ba, likewise his parent baza su bari ya aureta ba, kwanciya tayi tana kukan tausayin kanta. Wajen karfe hudu Maheer ya kirata, ta daga wayar tayi shiru, yace "Can i come over now?" A hankali tace "Yaya can i leave it tomorrow pls" Da mamaki yace "Why tomorrow?" Ta mike zaune tana dafe kanta dake mata ciwo tace "Kawai naji ina son in bari sai gobe da safe, ban san me yasa ba" Maheer yace "But are you okay?" Ta gyada masa kai tace "Ehh but deep down i want to leave tomorrow instead of today" Yace "Ohk then, zan gaya ma Ammi" Da sauri tace "How will you tell her?" Yace "Don't worry Mimi, zan ce mata ban baro asibiti da wuri ba" Tace "Yauwa yaya" Yace "Bacci kika yi ne?" Tace "Yanzu na tashi" Yace "Ohk, to bari in yi sallah it's almost time" Tace "Toh sai Anjima" Daga haka ya katse wayar ita ma ta mike ta shiga bandaki. Tana idar da sallah ta sake dialing number Musharraf, yana ta ring har ta fidda ran zai daga sai gashi ya daga, a hankali tace "When are you coming back?" Yace "To where?" Tace "Gidanka" Yace "I am home ae" tace "Naga ka fita dazu around 11:30" ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "How?" Tace "In ur white car, u were on either black or navy Blue polo" Musharraf that was very surprise yace "Wait! How did you know?" Tayi murmushi cikin sanyin murya tace "That shows i am with you now and always" Musharraf yayi shiru, can yace "I believe kin zo anguwan ne" Tace "Not at all" Yayi kasa murya yace "Pls Mayraah, for the sake of the love i have for you tell me where are you now? Ina kika tafi" Tace "Ina Miller road" Musharraf yace "Miller road? I don't understand" Tace "Yea" Yace "Wajen wa?" Tace "My aunt" Yace "But i am not too far from Miller, just few streets away" A hankali tace "I know" A bit confused yace "But which of ur aunt?" Tace "Baka san ta ba" Musharraf yace "Don Allah in da gaske kike send me the house address, don Allah ba don ni ba, don't play with my feelings Mayraah" Ta ɗan yi murmushi tace "I will send u the address" Daga haka ta katse wayar ta masa fowarding address da ta tura ma Dr Khalil jiya, tana tura masa ya kirata yace "Don girman Allah da gaske kike Mayraah" Tace "Toh shikenan" Yace "Ohk, ok i am on my way now, right away" Daga haka taji ya kashe wayar, nan gabanta ya fara faduwa, to wa zata ce ma Hajiya Amina zai zo, what if yana zuwa Maheer ko Usman suka zo fa, ko kuma Abba ya dawo, ya zata yi? wannan tunanin yasa taji hankalinta ya tashi sosai, tasan babu wani nisa daga gidansa zuwa nan, ta mike da sauri ta tafi ta samu Hajiya Amina, Hajiya Amina tace "What will u be making for dinner?" Mayraah tace "Akwai sauran abincin Aunty" Hajiya Amina tace "Toh shikenan" Sunkuyar da kai Mayraah tayi tace "Dama Aunty wani coursemate dina ne..." Sai kuma tayi shiru, Hajiya Amina tace "Feel free" Mayraah tace "Yana nan anguwan ne, zai zo mu gaisa" Hajiya Amina tace "It's okay, sai ki shigo da shi parlor ku gaisa ba komai" Mayraah ta girgiza kai da sauri tace "Aa za mu zauna a compound" Hajiya Amina tace "Toh shikenan" Mayraah har ta juya sai kuma ta sake dawowa tace "Aunty ai Abba bazai dawo ba yau ko?" Hajiya Amina tayi murmushi tace "Bazai dawo ba, kar ki damu" Mayraah ta juya ta fita daga parlon, tana komawa dakinta taga miss calls din Musharraf har 4, Hijab ta sa ta sauka downstairs, tana isa gate bayan mai gadi ya bude mata ta gansa tsaye jikin motarsa, kallonta yake babu ko kiftawa kamar yanda ita ma take kallonsa, she just can't explain how she felt seeing him at the same time sai taga ya rame, kana ganinsa kasan ba shi da rest of mind, tayi karfin halin cewa "Ka shigo" Ya nufota har sannan yana kallonta, ta juya ta koma cikin gidan, wajen shan iska ta tafi yana biye da ita ta zauna, shi ma ya zauna yana facing dinta, a sanyaye tace "Good evening sir" kasa amsawa yayi ya dafe kansa, ta sauke idonta tana goge hawayen da ya fara taruwa da yatsunta, cikin rawan murya tace "Kayi hakuri, this our destiny" Yace "What is our destiny Mayraah?" Ta daga kai ta kallesa tace "Allah bai rubuta za mu yi aure yanzu ba" Yace "Sai yaushe?" Tayi karfin halin cewa "May be years to come, in dai da rabon za mu yi aure babu wani abu da zai hana hakan amma a yanzu kam ban ga alaman za mu yi ba" Yana gyada kai yace "Sai yanzu na sake tabbatar da baki so na Mayraah, i now believe ni ne kawai nake son ki, ni ne kawai nake bata lokacina" Ta fashe da kuka tace "Saboda me zaka ce haka? Iyayenka baza su yarda ka aureni ba, nima iyayena baza su yarda in aureka ba bayan duk abubuwan nan da suka faru a dalilin wedding dinmu that never occurred, and ah baya da nake tunanin zan iya bin ka mu tafi mu yi aurenmu a wani waje may be ban zauna nayi tunani da kyau bane a kan hakan, i get to understand that it's the biggest mistake da ni da kai za mu yi making idan mun yi hakan, aure babu albarkan iyayenmu bazai mana lasting ba, daga karshe duk za mu zo muna da na sani ne, but keep in mind sir, you still remain my first love, a kanka na fara soyayya akan ka nasan menene so ina alfahari da hakan, sannan kayi min so na tsakani da Allah, kayi min so na aure, kuma har gobe bazan taɓa daina sonka ba sai ma sonka ya karu a zuciyata, kawai mu jira lokaci Sir, ina ji a jikina we are meant for each other kuma za mu yi aure amma ba yanzu ba, may be sai a gaba ta yanda bamu yi zato ba, but for now let act just like frnds mu ci gaba da zumuncinmu da communication don mu samu sauki a ranmu...." Ya ɗan yi murmushi ya mike, a hankali yana kallonta yace "Thank you Mayraah" kallonsa kawai take ganin yanda idonsa ya kada, ya juya ya nufi gate, mikewa tayi da sauri tace "Sir..." Ko waiwayowa bai yi ba har ya isa gate din ya bude ya fita, wasu hawaye ne suka dinga sauka idonta ta koma ta zauna ta hade kanta da table tana kuka a hankali..... Ammi na zaune parlon Abba tana xuba masa abinci bayan magrib, bayan ya kunna TV yace "Mayraan bata dawo ba yau ne?" Ammi tace "Maheer din yace bai baro asibiti da wuri ba sai gobe" Yace "Ohk..." Bayan ta gama zuba masa zata fita ya bi ta da kallo yace "Za mu yi magana ne idan na gama" Tace "Ka kirani in ka gama" Daga haka ta fita daga Parlon, duk kwanan nan ko zama part din nasa bata son yi unlike before, iyaka ta shigo ta basa abinci ta koma bangarenta, ko kwana ta daina yi a part din, yana gama cin abincin ya kirata, bayan ta dawo parlon ta zauna, yace "Duk kwanan nan ina lura kin maida bangaren nan baƙon ki" ta wani hade rai tace "Don Allah bana son wannan maganar... In wata magana ce ka min amma ba wannan ba" Ya ɗan yi murmushi yace "Ohk" Ajiye ruwan hannunsa yayi yana kallonta, bayan few seconds yace "Akan Usman ne...." Ammi ta maida hankali kansa tana sauraronsa, cikin few minutes Abba ya gaya mata maganar da Usman ya samesa da shi, Ammi sai kallon Abba take without blinking, can ta girgiza kai tace "I will prefer Maheer, don ya fi sa sanyin hali da sanin ya kamata, kuma nayi magana da shi akan hakan few days back, don haka ka bar maganar Usman" Abba dake ta kallonta da mamaki yace "But Usman showed interest first, saboda me za ki ce Maheer? Saboda me zan bar maganar Usman?" Ammi tace "Eh Maheer nace, saboda duk nasan halinsu ai, ita ma kuma nasan halinta da wanda zai iya hakuri da ita, ya kuma fi sanin ciwonta...." Abba yace "To tunda haka ne duk a bar zancen, daga Usman din har Maheer nayi cancelling maganar, tunda naga abun naki kamar son kai ne" Ammi tace "Babu batun son kai, future din yarinyata nake dubawa da inda zata samu kwanciyar hankali... Kuma duk yaran nan dai naga nawa ne babu wanda zai ce ya fini sanin halinsu gaba daya su ukun, kuma kayi hakuri zance dai baza a bar shi ba Yallabai, dama Maheer din ba wai yayi dacen mata bane, Mayraah kuma zata fi dacewa da shi don ina ga ko ni ban san halinta yanda Maheer ya sani ba" Mikewa Abba yayi ya bar mata parlon ya shige daki don baya son biye ta, ta kwashe warmer din abincin ta fita ita ma. Karfe tara na safe Mayraah ta sakko downstairs da jakarta, Hajiya Amina dake ta kallonta tace "Ko dai baki jin dadi ne, tun jiya naga you are not ur self, is anything wrong?" Mayraah tayi murmushin karfin hali tace "Ba komai Aunty, ciwon kai ne amma yayi sauki yau da safe" Hajiya Amina tace "Maheer din na waje ne" Mayraah ta gyada mata kai, Hajiya Amina ta dau ledan dake gefenta ta mika mata tace "Ga su nan turarruka ne, though they are not much" Mayraah ta risina ta amsa tace "Nagode Aunty" Hajiya Amina tayi mata murmushi tace "You are welcome, ki gaida Amminku da Mama" Mayraah tace "To za su ji in sha Allah" Daga haka ta nufi kofa ta fita, tana isowa kofar gida ta tadda Maheer a mota, ta karasa ta bude front seat ta zauna tana kallonsa tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau" A hankali tace "Yaya baza ka shiga ka gaisheta ba" Ya ɗan yi murmushi yace "Kin ga na makara, sai naje nayi dropping dinki sannan in tafi aiki" Mayraah tace "Just 2 minutes fa is enough yaya, kuma tasan kai ne ka zo daukata" Yace "Ohk i will do that next time in sha Allah" Bude motar tayi ta sauka tace "Ni dai sauko kaje ka gaisheta sai ka fito mu tafi" Shiru yayi yana kallonta, can ya kashe motar ya bude ya sauka ya zagayo, tana murmushi tace "Yauwa ko kai fa" Hancinta ya ja sannan ya shiga cikin gidan ta bi bayansa, har sannan Hajiya Amina tana zaune parlor tana kallo, Maheer ya karasa ciki bayan ta amsa sallamarsa, ya zauna sannan ya gaisheta ta amsa da fara'a tace "Ya aikin Dr" Yace "Alhmdlh" Tace "To maa sha Allah, ya su Ammi da Mama" Yace "Suna nan lafiya" Ta mike tace "Bari a hado maka breakfast" Yace "Aa i am okay, aiki zan tafi" Daga haka ya mike, Tace "Toh shikenan, Nagode kwarai, Allah ya tsare" Yace "Ameen" har balcony ta rakasa ya mata godiya ya sauka, Mayraah dake zaune inda ake shan iska ta mike ganin ya fito, ta jira har ya karaso inda take suka fita gate din a tare, suna barin anguwan tana kallonsa tace "Yaya" Ya juya ya kalleta sannan ya ci gaba da driving dinsa yace "Mimi" a hankali tace "You know what?" Yace "No Mimi" Tace "Kwanan nan naga u are somehow, is there anything wrong? You are not longer lively like before, baka magana sosai, you are always silent, why is that?" Maheer ya kalleta yace "Ba komai, i will be fine in sha Allah, stress din aiki ne" Mayraah tace "Ko har da na matarka?" Ya girgiza kai yace "Not at all, ai bana shiga harkanta, i have nothing to do with her, i am just waiting for time" Mayraah tace "To koma menene yasa kake zama silent kayi hakuri ka ji" Yayi murmushi yace "You are funny Mimi, ba komai kawai yanayin aiki ne" Murmushin tayi ita ma duk da nata damuwar da yayi mata yawa a zuciya ɗon ko baccin kirki bata yi ba jiya saboda tunanin Musharraf amma tun dawowarta gida bata jin dadin yanda ta lura Maheer bai cika son magana ba unlike before, she missed the old him, a haka har suka iso gida wanda in da ne ko bata basa labari ba shi zai dinga bata har su isa inda za su, bayan yayi parking kofar gida ta juya tana kallonsa tace "Take care of ur self" Yace "Toh Mimi" Bude motar tayi ta sauka ta dau jakarta a back seat sannan ta shiga cikin gidan, yayi reverse ya bar anguwan. Abba na zaune parlon Ammi tare da Usman da Maheer, sai Ammi da Mama Ladi dake parlon su ma, Mayraah ce ta shigo karshe bayan Mama Ladi taje ta kirata a wajen Badiyyah, Mayraah ta zauna kasa kusa da Ammi wondering why she saw everyone sitted kamar ana meeting, Mama Ladi tace "To kai yanzu Mamuda a ina ka taɓa jin an bar ya mace tayi aiki? Ni dai tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin haka ba gaskiya, kyan ya mace ai dakin mijinta, sannan kace Habuja kana nufin mu sake sakinta kamar akuya ta koma Habujan kenan, abinda fa hankali zai dauka shi ake yi Mamuda, ya mace take faa" Maheer dake ta kallon Mama Ladi yace "Wa yace maki mace bata aiki?" Mama Ladi tace "Aa ba ruwana, ba a pamilyn mu ba wallahi, yanzu duk abun magana ai kamata yayi mu gujesa, har yanzu fa bamu gama farfadowa daga bakin fentin da Badiyyah ta goga ma pamilyn mu ba, in ku kun farfado ni ban farfado ba wllhi, tunda gashi har yau bana iya fita sai ina boye fuska kar a danganta ni da Badiyyah" Shi dai Usman bai ce komai ba, Ammi ma tayi shiru amma kana ganin mood dinta kasan batun aikin bai mata dadi ba ko kadan duk da Maheer ya mata maganar jiya, Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Duk abinda kika fada gaskiya ne Mama, amma dama ai baza ta fara aiki haka kawai bata da kowa a garin Abuja ba, duk sai da na gama tsarina da Usman sannan na tara ku a nan...." Ammi ta daga kai tana kallon Abba, Abba ya ci gaba yace "Babban asibiti ne kuma sananne a Nigeria, ba kowa ake bama aiki a asibitin ba, na taɓa wani aboki likita yayi aiki a asibitin shi ma kafin ya koma kasar waje, shi yasa naji bazan bari damar nan ta subuce ma Mayraah ba...." Mama Ladi tace "Naga abinda ya isheni, to me zata yi da aiki? Ba ci ta rasa ba, ba sutura ba, ba komai ba" Abba yace "Aa zata yi aikinta in sha Allah...." Mama Ladi tace "Toh aure fa? Kana ta maganar aiki kamar wasu kafurai, haka za mu sa ta gaba sai ta tsofe a gida mu shiga uku Mamuda, aure fa shine martabar ya mace ina tunatar da kai" Abba yace "Aure ai lokaci ne Mama, wuyarta lokacin ya iso za ayi, aiki kuma baya hana aure, mutane da yawa na neman aikin basu samu ba" Mama Ladi ta kyabe baki tana girgiza kafa alamar ita fa batun aikin bai gamsar da ita ba, Abba yace "Saboda haka na yanke shawaran Amminta zata koma Abuja da zama gaba daya, don har na siya gida a can an zuba komai, tarewa kawai ya rage, tun da idan nace a fara ginin filina dake can din zai iya daukar lokaci kuma Mayraah zata yi resuming aiki next week" Mama Ladi dake gwalo ido tace "Ka siya sabon gida a Habuja Mamuda?" Kabbara Mama Ladi ta saki cike da farin ciki sannan tace "Alhamdulillahi, dama ance mahakurci mawadaci, shikenan Ammi zata koma er Habuja duk me son ganinta sai ya shirya nan kuwa ko wani kare da doki shigowa yake, dama Allah na tuba anguwan nan in ba dole ba me mutum zai yi da shi duk ɗoyin ƙwata, duk lungun da ka bi warin ƙwata, kai maa sha Allah amma nayi farin ciki da wannan labarin kuma ka kyauta Mamuda" Abba ya ciro wayarsa dake ringing yayi picking call din abokinsa, Mama Ladi da farin cikinta ya kasa boyuwa ta mike ta lallaba ta tafi kusa da Maheer tace "Mashir a ina zaka samo min wani akwatin wallahi na gaji da wannan dama" Maheer yayi murmushi yace "Usman ne yasan inda ake siyarwa" Zata koma gun Usman taga Abba ya gama wayar da yake ta koma da sauri ta zauna tana washe baki, Abba ya ajiye wayarsa yace "Amma magana ta gaskiya Mama baza ayi tafiyar nan da Badiyyah ba, tun da can kadunan ance Hajjan ba lafiya to ina ga in zaki koma Karaye zaki koma can tare da ita kawai, don zuwa jibi za su bi jirgi in sha Allah, kayan sawansu kawai za su dauka..." Sake baki Mama Ladi tayi tana kallon Abba bata ko kiftawa. [8/3, 8:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mama Ladi na gyara shimfidar da zata kwanta bayan ta ci kukanta ta gode Allah tace "Toh ma sai kace wata gantalalliyar tsohuwa mara makabuli ina ni ina bin ku wani Habuja, sai kace ban san me nake ba da zan kwashi kafa in bi ku kamar a garin gaɓa gaɓa, ai da wayo na kuma ni ba mahaukaciya bace nasan me nake, amma abinda yayi min ciwo har na zubda hawaye dalilin da zai sa Mamuda yace in dauki Badiyyah mu tafi karaye, a dubi girman Allah a gaya min me na hada da Badiyyah da Mamuda zai ce min haka? To wannan cin mutuncin da yayi min shi ya min ciwo har nake ta kuka amma ba wani abu ba" Ammi dai dake zaune parlon ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, Mama Ladi tace "Kuma a gaskiya ni ba a taɓa ci mun mutunci irin yau ba ma tunda uwata ta haifeni, wai in tafi da Badiyyah karaye ashe ma ni na mata cikin, to wallahi ki ja masa kunne ya fita harkata ya bar hada ni da Badiyyah, babu abinda na hada da ita haduwar bariki rabuwar bariki, kakarta ce fa yayata amma ko a lahira ni bazan ga Badiyyah ba, in zuciyata ta debeni sai in iya ja masu Allah ya isa daga Mamudan har shegiyar Badiyyan da yake hada ni da" Daga haka tayi kwanciyarta tana matsar wasu sababbin kwallan tace "Dama da asussuba Mashir ya zo ya kai ni tasha, maganina ma kenan da nayi ta zama nan kamar wata mara galihu" Ammi tace "Kiyi hakuri Mama Ladi duk bai kai...." A fusace Mama Ladi ta mike zaune tace "Rufe min baki, ke da kika ji yana cewa in koma karaye baki da bakin magana ne? Ni na cancanci Mamuda yayi watsi da ni? Da ba don ni ba ai gidansa fanko ya so komawa amma ɗan Adam me mance alkhairi, kullum fa sai an bugo min waya daga karaye ana tambayar Baaba ladi yaushe za ki dawo, da gata na kaca kaca a can, to kafin ku tattara ku koma Habujan ni gobe da Asuba zan bar gidan, kuma ki mayar masa da shegen kudinsa da ya bani bana bukata, ban rasa komai ba a karaye wallahi" Daga haka ta sake komawa ta kwanta tana matsar sabbin kwalla, Mikewa Ammi tayi ta shiga bedroom dinta don for almost an hour Mama Ladi ke ta mita da koke koke ita dai hakuri kawai take bata, wajen karfe sha daya da rabi ta sake fitowa parlon rike da wayarta ta ga Mama Ladi kwance ido biyu, Mama Ladi da bata wuce karfe tara da rabi da ta ci ta koshi take bacci, Ammi dai bata ce mata komai ba ta fita daga parlon ta sauka downstairs, Maheer ta ganin kwance kan 3 seater idonsa rufe, Ammi ta karasa kusa da shi ta taɓasa tace "Maheer" Bude ido yayi, ya mike zaune tace "Baka tafi ka kwanta ba kake bacci a nan" Ya kalli agogo sannan ya mike zaune, Ammi ta zauna daga side dinsa tana kallonsa tace "Ka ci abincin ma kuwa?" Yace "Na ci" Sai kuma ya mike yayi mata sai da safe ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita, Number Aunty Mariya ta fara dialing sanin mijinta baya gari, yana fara ring kuwa ta daga, tace "Baki yi bacci ba Ammi" Ammi tace "Ban yi ba" Aunty Mariya tace "To ya gidan? Ya su Mayraah?" Ammi tace "Alhamdulillahi" Shiru Aunty Mariya tayi tana sauraren dalilin kiran Ammi don tasan tunda ta kirata by this time akwai magana ne, Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta sanar ma Aunty Mariya abinda ake ciki, Aunty Mariya tayi farin ciki da samun aikin Mayraah da kuma garin Abuja da za su koma, she was so happy, tace "To yanzu Ammi ya za ayi da Mama Ladi?" Ammi tace "Mama Ladi? Badiyyah dai.... tambaya za kiyi ya za ayi da Badiyyah tunda ita Mama Ladi tana da inda za ta, Shi kuma yace babu inda za aje masa da Badiyyah, i am confuse ban san ya zan yi ba kuma" Aunty Mariya tayi shiru, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Amma dai Ammi shawaran da aka yanke tun farko shine a kai ta Bichi...." Ammi tace "To bari kiji tunda na kirasu na sanar masu abinda ke faruwa buden bakin shi yayan baban nata wai sun kwana biyu su basa Bichin sunyi tafiya, ita kuwa autarsu baban nata ita ma da na kirata bayan kwana biyu ce min tayi tana wajen mijinta a portharcourt yaranta ma na gun kakarsu, Kinga ai sun hada baki kenan, ni kuma gaskiya ban wani ga laifinsu ba, babu wanda zai karbi Badiyyah ko waye ma haka zai yi, ko don na bar zancen ban gaya maku ba? ita kanta Mama Ladi bata san yanda muka yi da yan Bichin ba ai har yau, to yanzu ga abinda Mai gidan yace i don't want to have any issues with him, don da farko cewa ma yayi Mama Ladi ta koma karaye da ita shine ta dinga rusa kuka wai an cuceta an hadata da Badiyyah" Aunty Mariya tace "Kinsan me zai faru Ammi, ai Hajjan yanzu jikinta da sauki don ko jiya naje gidan Baaba Yahanasun dubata don haka kawai ki tattara Badiyyar ki sa ta a mota ta koma can wajensu ai ta san gidan, kuma ba sai kin gaya ma kowa ba kawai su ganta, idan ya so ki kashe wayarki kawai, ni dai Hajja bazata fara cewa Badiyyah ta zo wajena ba tunda tasan yanda yanayin gidan nan yake, in kuma kince ba haka ba to ni kam ban san yanda za ayi ba kuma" Ammi tayi shiru tana nazari, Aunty Mariya tace "That is the only way out fa, infact don ma mun samu Abbansu Maheer din ne amma wallahi ba ko wani namiji ne zai yi tolerating haka ba, ko mai gidana nasan bazai fara yarda Badiyyah ta zauna gidana ba, dama Mama Ladin ce dai dai tafiya da ita karaye ni ko nasan ko daura ma Mama Ladi Badiyyah aka yi a kafa sai ta kunceta" a hankali Ammi tace "To shikenan, zan sa Maheer ya kai ta tasha gobe ya saka ta a motar Kadunan tunda babu wani mafita bayan wannan" Aunty Mariya tace "Shine kawai magana, yanzu yaushe za ku koma Abujan?" Ammi tace "Ya ce jibi..." Aunty Mariya tace "Kai maa sha Allah, wallahi nayi murna sosai Ammi Allah ya sanya alkhairi, dama duk mahakurci bazai taba taɓewa ba, sannan Ammi ina ta son zan maki magana akan matar Maheer, yanzu shikenan ana nufin haka zai ci gaba da zama da ita? Wato ta ci bulus duk abubuwan nan da suka faru uwa uba ga bin bokaye da malamai, asiri har a dakinki?" Ammi tace "Mariya, the girl is pregnant" Sai da Aunty Mariya ta mike zaune daga kwancen da take, tace "Pregnant kuma Ammi?" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Har wata uku kuwa, shi dai yace bai san da shi ba, shine Abban nasu yace a jira ta haihu ayi DNA, wannan dalilin yasa muka hanasa sakinta tukunna, yanzu ma nasan kawai suna zaune under same roof ne babu yanda zai yi tunda kinsan baya ketare maganata amma ba da son ransa suke waje daya ba, ai ko da ɗan sa ne ni bazan yi supporting ya ci gaba da zama da ita ba wallahi, for now dai we just have to be patient a jira ta haihu ayi DNA din, kinji dalilin da yasa take gidan nan har yanzu" Aunty Mariya jikinta yayi sanyi, a ranta kuwa har ta fara addu'a Allah sa Maheer have nothing to do with the baby, Allah ya rabasa hada zuri'a da irin Haseenah, can dai tace "Amma Ammi an tabbatar kuwa, anje anyi scan ko kawai da baki ta fadi? Yarinyar nan fa makira ce babu abinda bazata iya aikatawa ba wllhi, sai ta iya forging cikin ma ko a asibiti" Ammi tace "Kin manta shi likita ne Mariya? Anyi scan, ai shine nace maki har wata uku with few days" Aunty Mariya ta tabe baki tace "Ai shikenan, amma what if the DNA result comes out negative after still keeping her for 7 months Ammi?" Ammi tace "Ta cuci kanta ba mu ba" Aunty Mariya ta girgiza kai tace "Allah Ubangiji ya shirya mana zuri'a" Ammi tace "Ameen, sai da safe" Sallama suka yi Ammi ta katse wayar ta wuce sama zuwa part dinta, har a sannan Mama Ladi bata yi bacci ba, Ammi ta kalli agogo da mamaki tace "Baki yi bacci ba Mama Ladi?" Banza Mama Ladi ta mata, Ammi ta karasa cikin bedroom dinta. Washegari da sassafe Ammi ta kira Maheer ta sanar masa yanda suka yi da Aunty Mariya kan cewar ya dau Badiyyah ya kai ta tasha, shi dai yayi shiru yana kallonta, tace "Ko ya ka ga Maheer?" Maheer yace "To ya za ayi dama, tunda relatives din babanta na denying dinta and they are not to be blamed, kawai hakan shine mafita" Ammi tace "Dama nima ban yi blaming dinsu ba" Maheer bai sake cewa komai ba, Ammi tayi kasa da murya tace "Da zaka taimaka ma tunda yau Saturday da kayi dropping dinta a kadunan saboda situation dinta" Maheer yace "Ai yau din ma ina zuwa aiki Ammi, kawai dai ina dawowa da wuri ne" Ammi tayi shiru, sai kuma tace "Toh shikenan" Yace "In ba dai Barrister za ki ma magana ba tunda yana nan" Ammi ta rike haɓa tace "Wani Barrister din?" Maheer yace "Usman mana, shi da ya maida zuwa kaduna kamar zuwa cikin gari" Ammi ta taɓe baki tayi murmushi kawai bata ce komai ba, Maheer ya mike yace "Ko ni sai inje in masa magana yanzu" Ammi tace "Ka dai san dama ba Badiyyah bace, amma ko me zaka ce masa in dai Badiyyah ce bazai je ba" Usman ne ya sauko downstairs zai je kitchen ya hado shayi, Ammi ta bi sa da kallo, ya karaso ya gaisheta ta amsa, ya kalli Maheer yace "Bonjour" Maheer ya daga kai ya kallesa yace "Morning" Zai tafi kitchen Ammi tace "Usman zaka je kaduna ne yau?" Ya juyo ya kalleta yace "Eh" Tace "Kamar yaushe?" Yace "Zuwa karfe goma in sha Allah" Ammi tayi kasa da murya tace "Dama wai taimakawa zaka yi ka ajiye Badiyyah a gidan Baaba Yahanasu" Kallonta Usman ya tsaya yi, can yace "Duk da dai ban tabbatar da tafiyar ba tukunna" Ammi ta ɗan kalli Maheer da yayi murmushi kawai, Ammi tace "Toh shikenan" Juyawa Usman yayi ya shiga kitchen, Maheer yace "Zan dau excuse wajen aiki sai in ajiyeta in sha Allah" A hankali Ammi tace "Allah maka albarka, sai ku je da Mayraah to keep u company, kafin yamma kun dawo in sha Allah, amma sai kun fita da wuri" Karfe tara Maheer ya shirya ya yafi bangaren Ammi, tuni Ammi ta kira Mayraah ta sanar mata tafiyar da za su yi Kaduna, jikin Mayraah yayi sanyi don tausayin Badiyyah take har cikin ranta, Ammi ta sa taje ta hada mata kayanta duk a akwati, Mayraah na hada kayan Badiyyah dake ta bin ta da kallo tace "Me yasa kike hada kayan Mayraah?" Mayraah ta kasa kallonta, har sai da Badiyyah ta sake mata tambayar, ba tare da Mayraah ta kalleta ba tace "Za mu je kaduna ne?" Badiyyah ta mike zaune da kyar tace "Kaduna kuma? Wajen wa a kaduna?" Mayraah tace "Nima ban sani ba, Ya Maheer ne zai kai mu" Shiru Badiyyah tayi amma haka nan taji hankalinta ya tashi sosai, cikin karfin hali tace "Har da Ammi?" Mayraah ta girgiza kai tace "Aa" Daga haka ta mike ta fita daga dakin, tana share hawayen da ya makale idonta ta kulle kofar ta jingina jiki, Usman ne ya fito daga dakinsa ta juya ta kallesa sai kuma ta sunkuyar da kai, har ya karaso inda take tsaye bai daina kallonta ba, jin bai ce komai ba ta daga kai ta kallesa, a hankali tace "Ina kwana?" Yace "Why are you crying?" kamar jira take ta fashe da kuka, ya bi wajen da kallo sannan ya matso kusa da ita ya kamo hannunta da mamaki yace "What happened?" Cikin rawan murya tace "They are taking Badiyyah to kaduna, Yaya idan taje can babu wanda zai kula da ita and she needs care in this her condition, this is her destiny we are not suppose to neglect her..." Usman yace "Is that why u are crying?" Ta gyada masa kai, yace "Did anyone help u carry ur own destiny with you? I mean... did anyone partner with u in all what u went through this pass months?" Mayraah ta dinga kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "So she should carry her cross alone" Yana fadin haka ya kai fingers dinsa yana share mata hawayen fuskarta, Mayraah couldn't stop looking at him, she doesn't even understand if she is surprise or Shock at his action, kuma bai fasa kallon kwayar idonta ba while wiping away her tears. Ammi ce ta fito daga part dinta, tunda ta kallesu sau daya daga nesa bata sake kallon direction din ba, Mayraah ta matsa daga kusa da shi da sauri, har dai Ammi ta karaso tace "Kin gama hada kayan ne Mayraah?" Mayraah ta gyada kai tace "Na gama" Ammi ta kalli Usman da ya juya zai sauka downstairs tace "Kai kayi breakfast din ne?" Ba tare da ya juyo ba yace "Na yi" Ammi ta maida dubanta kan Mayraah tace "Shiga ki fito da akwatin ki kai motar yayanku, yana waje yana jiranku" Mayraah ta bude kofar dakin ta shiga, Ammi kuma ta koma part dinta, Mayraah na sauka downstairs da akwatin Usman yace "where are you taking it to?" Tace "Motar ya Maheer, Ammi tace shi zai kai mu" Usman ya gyada kai without saying anything, tana jan akwatin ta fita compound, Maheer na jingine jikin motarsa ya hango Mayraah, ya nufeta ya amshi akwatin, tace "Yaya ina kwana?" Yace "Lafiya lau, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah" tare suka karasa gun motarsa ya bude booth ya saka akwatin yace "Ina take?" A hankali Mayraah tace "She is inside" Daga haka ta juya ta koma cikin gidan, duk Haseenah na lekosu ta window with so many thoughts running her mind, can ta ɗan yi murmushi ta juya ta bar bakin windan. Ammi ta shiga dakin da Badiyyah take, ta sameta zaune kana ganinta kaga tashin hankali a fuskarta, a takaice Ammi tace "Maheer zai kai ki Kaduna, za muyi tafiya da Abba, kinga babu kowa gidan, Mama Ladi kuma zata tafi karaye, mai aikin zata tafi garinsu, Mayraah ta samu aiki a Abuja she will be traveling too" Badiyyah ta fashe da matsanancin kuka tace "Ammi ko ni kadai ce don Allah a bar ni zan zauna wallahi, don Allah ku rufa min asiri" Ammi tace "Kulle gidan za ayi, haka zaki hakura ki tafi kadunan sai sanda Allah yayi mana dawowa gaba daya" Tana kuka sosai tace "Ammi wajen wa a Kaduna?" Ammi tace "In an je za ki gani, ki dauko hijabinki ki fito lokaci na wucewa" Daga haka Ammi ta bar dakin, Badiyyah ta tashi tana kuka sosai ta dau hijab ta saka ta fito, dubu ashirin Ammi ta bata ta amsa tana kuka har suka sauko downstairs, har sannan Usman na zaune Ammi ta raka Badiyyah bakin kofar parlon, Mayraah ta dinga kallonta cike da tausayi har ta karaso parking space ta bude mata mota ta shiga ta kulle sannan ta tafi front seat don Maheer na cikin motar a zaune, babu bata lokaci suka bar gidan. Hira Mayraah take ta yi ma Maheer dake sauraronta bayan sun dau hanya, Badiyyah dake zaune a baya tayi nisa cikin tunanin da take gaba daya bata ma cikin hayyacinta bata san me suke cewa ba duniya ta mata zafi, after an hour drive Mayraah ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Maheer tace "Ni kadai nake ta labarina" Yace "No, ina jin ki mana Mimi, what were you even saying?" Ƙin cewa komai tayi ta hade rai tana kallon titin gabansu, ya ɗan yi murmushi yace "So now sai monday zaki amshi statement of result dinki kafin ku tafi Abuja? Since u will be going for interview on Tuesday...." Mayraah ta gyada masa kai kawai, yana murmushi yace "C'mon Mimi, i am sorry" Ta ɗan turo baki, yace "Baxa ki hakura ba" Tace "Na hakura but yaya ni tsoron interview din nake, MD din bashi da mutunci kwata kwata wallahi, yana da anger issues, sannan he is rude and arrogant, infact he is so loud for my liking komai masifa da jaraba" Maheer na gyada kai yace "Duk shi kadai?" Mayraah tace "Wallahi, just my few days in that hospital the experience was horrible, har bana son tunawa, wllh he is rude Yaya" Maheer na gyada kai yace "I trust you idan ya maki interview din ma you will only leave him with mouth agape, did u know that ur intelligence is extra ordinary lil sis? I am always amazed with ur intelligence, you graduated with first class, nursing science, ai shima sai yayi mamakin result dinki wallahi, shi kansa ba lallai yayi graduating da first class ba idan nursing science yayi...." Mayraah dai sai murmushi take saboda ƙodatan da yayan nata yake, kafin su isa kaduna Badiyya tayi amai yafi a kirga, suna isa kofar gidan Yahanasu Badiyyah ta fashe da kuka a galabaice, Maheer dai ya sauka ya fiddo mata akwatinta ya kira almajiri, jikin Mayraah yayi sanyi ta kasa sauka daga cikin motar, nan da nan hawaye ya cika idonta, Maheer ya bude ma Badiyyah bayan motar yana kallonta yace "Sauko" Saukowa tayi tana kuka sosai tace "Yaya don girman Allah ku taimakeni ku rufa min asiri, bani da kowa...." Maheer ya katseta yace "Ba Ammi tace maki tafiya za su yi ba, in kin shiga ciki sai ki gaya masu, duk sanda ta dawo sai ki koma kanon ai" Daga haka ya kulle motarsa ya zaga ya shiga driver seat, hawaye kawai Mayraah take tana kallon Badiyyah dake kuka kamar ranta zai fita, Maheer ya ja motarsa ya bar kofar gidan. [8/4, 8:39 PM] Khaleesat Haiydar💖: Sai kusan karfe hudu Mayraah suka iso kano daga kaduna, Mayraah ta kalli Maheer tace "Alhamdulillah for journey mercies" Kai kawai ya gyada mata, tace "What should I cook for u idan muka isa gida, kaga kai baka ci abinci ba, ni kuma ka siya min a Zaria" Ya ɗan kalleta yace "Baki gaji ba?" Er dariya tayi tace "Bayan ba ni ce ke driving din ba, i slept all through fa" Ba don yayi missing girkinta ba da bazai bari tayi girkin ba but he is craving her cooking, jin yayi shiru yana driving dinsa tace "Ko baka so?" Yace "Gani nake za kiyi stressing kanki after this long journey, kamata yayi muna komawa gida yanzu kiyi wanka kiyi sallan Asr ki kwanta ki huta" Mayraah ta ɗan yi murmushi bata ce masa komai ba, ya juya ya kalleta jin tayi shiru, sai kuma ya maida dubansa kan titi yace "Ko ba haka ba Mimi?" Tayi wani murmushin tace "Naga kamar u are avoiding me this days, baka son muna magana da yawa, i don't know! u are just being unusual, we weren't like this before" Maheer ya buda ido sosai, babu abinda ya fado masa rai sai lokacin da ita ma ta dinga kokarin avoiding dinsa 3 months back after finding out they are not blood, yasan she is talking about kafin su san matsayinsu ne, yana murmushi yace "Avoiding my lil sis? Kema kin san hakan bazai yiwu ba..." Tace "Then if u are not avoiding me kana da damuwa ne da baka son ka gaya min?" Ya ɗan kalleta yayi murmushi yace "You caught me" Tace "I definitely know there is something, yaya na fa san ka nasan halin ka, i know there is something bothering you, amma shine kake boye min whereas before baka boye min komai" A hankali yace "I will tell u Lil sis, but yanzu ina bukatar in huta na gaji" Tace "Tohm shikenan, and again yaya me yasa baza ka dau transfer ba kai ma ka koma Abuja, naga kuna da Branch a can ai" Maheer yace "Kin manta daga Abujan na nemi transfer na dawo kano, it will be a bit hard to get another transfer back to Abuja" A hankali tace "Try yaya, we will miss u idan muka tafi ba tare da kai ba, kaga shi Ya Usman dama yafi aiki a Abuja and kaduna, nasan he is going back to Abuja too" Maheer yayi murmushi yace "I will try" The rest of the journey was silent har suka iso gida, bayan yayi parking tace "Idan nayi sallah zan maka girkin" Yace "Toh Nagode Mimi" Tayi murmushi ta bude motar ta sauka ta nufi cikin gidan. Mayraah na shiga parlon Ammi ta tadda Mama Ladi kwance ta lullube da bargo, Mayraah ta karasa kusa da ita ta duka tana kallonta da mamaki tace "Baki da lafiya ne Mama?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Ae tun asuba da na tashi naji kafafuwana sun kasa daukata nasan da matsala, to ilai kuwa gashi" Mayraah tace "Ayya, to Allah ya sauwake, kin sha magani?" Mama Ladi tace "Wa zai bani er nan? Ai yanda kika gan ni a nan tun dazu a haka nake" Mayraah tace "To zuwa anjima sai in fita in amso maki maganin idan nayi sallah" Daga haka Mayraah ta mike ta karasa dakin Ammi, kaya ta sameta tana ta hadawa a akwatuna, Ammi tace "Ya hanya Mimi?" Mayraah tace "Alhamdulillah, ina yini Ammi" Ammi tace "Lafiya lau, ina yayan naki?" Mayraah tace "Kamar ya shiga gida" Ammi tace "Toh kiyi sallah ga abinci can na maku ki duba kitchen" Mayraah tace "Toh Ammi" Ta juya ta nufi kofa Ammi tace "Ki fito da kayanki gaba daya daga press din dakin ki ajiye kan gado, zan jera maki a akwati, amma sai kin ci abinci in kinyi sallah" Mayraah tace "Toh Ammi" Daga haka ta fita daga dakin, tana komawa dakinta tayi wanka sannan ta dauro alwala, bayan ta idar da sallah ta sauka downstairs ta shiga kitchen, duba abinda Ammi ta girka masu tayi, sai kuma ta fita ta koma ta dauko wayarta ta dawo parlon ta zauna tayi dialing number Maheer, yana fara ring Maheer dake kwance ya mike zaune ya daga yace "Mimi" Tace "Yaya me kake son ka ci?" Yace "Koma me kika girka zan ci" Tace "Ohk" Daga haka ta katse wayar, Haseenah dake kitchen din dake Chalet zata zubo masa abinci duk da tasan ba ci zai yi ba, tana jin wayar da yayi da Mayraah ta ɗan yi wani murmushi ta mayar da abincinta cikin warmer ta fito daga kitchen din ta wuce daki, dama girkin da Ammin tayi ne taje kitchen ta debo ba wai ita ta girka ba, Mayraah na kitchen tana ma Maheer girkin da tasan ya fi so wajen karfe biyar da wani abu aka bude kofar kitchen din ta juya, suna hada ido tace "Ina yini Yaya" Yace "Lafiya lau" Karasawa cikin kitchen din yayi yace "Babu abincin ne?" Tace "Aa akwai, Ya Maheer nake ma girki" Ya gyada kai ya dau plate zai debi abinci tace "Ko zaka ci wannan da nake yi" Yace "Aa akwai me shi ae" Tayi dariya tace "Ai zan iya tsam maka kaɗan a ciki" Bai sake kallonta ba ya debi abincin da zai diba ya fita daga kitchen, Ammi na shigowa kitchen zata hada ma Mama Ladi shayi tace "Mimi baki son abincin ne?" Mayraah ta kalleta tace "Aa Ammi yaya nake girka ma favorite dinsa" Ammi tace "Tohh ai shikenan nawa bai yi dadi ba kenan" Dariya Mayraah tayi tace "Aa ko ɗanɗanawa bai yi ba fa Ammi, kawai favorite dinsa nake masa saboda nasan ya gaji" Murmushi kawai Ammi tayi, ta hada shayin da ya shigo da ita ta fita daga kitchen din, Mayraah na gamawa ta fito parlor ta dau wayarta tana kallon Usman dake zaune kan kujera yana kallo a laptop, Maheer ta kira ta sanar masa ta gama, a hankali yace "Ki kawo min nan Chalet Mimi" Ta ɗan buda ido tace "Chalet kuma? Aa yaya kawai ka daure ka zo ka amsa" Yace "Na gaji ne" Ta ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ki bar shi kitchen din idan na shigo zan dauka" Tace "Bari in kawo maka yaya" Daga haka ta ajiye wayar ta nufi kitchen, Usman ya bi ta da kallo, daukan abincin tayi ta dawo parlor tace "Yaya kace baza ka ci ba ko?" Yace "Eh" Kofa ta nufa ta fita zuwa Chalet, tana knocking kofar yace "Come in" Ta bude ta shiga sannan ta karasa inda yake kwance, tun da Haseenah ta ji yayi waya da Mayraah ta kawo masa abinci ta sake fitowa Parlon ta zauna, Mayraah bata yarda ta kalli direction dinta ba balle har hakan yasa sai ta gaisheta, she pretends bata ma san tana wajen ba a zaune, tana ajiye masa abincin tace "Ga abincin yaya" Yace "Thank you Mimi" Tayi murmushi ta mike ta nufi kofa ta fita, Haseenah ta bi ta da ido. Ko da Mayraah ta koma sama ta tarar Ammi na ta hada mata kayanta cikin set din akwatunanta, Mayraah tace "Ammi ki bari in karasa" Ammi tace "Aa bar shi ai na kusa gamawa kije kiyi alwala kawai, it's almost Magrib" Bandaki Mayraah ta shiga don yin alwala.... Da daddare Ammi na dakinta tare da Mayraah, Mama Ladi kuma na kwance har sannan cikin bargo Maheer ya shigo parlon, ya zauna ya gaida Mama Ladi ta gyada masa kai kawai, yace "Mama ba lafiya ne?" Mama Ladi tace "Ai tunda na tashi da asuba na ji jikina na rawa nasan da magana, to ilai ga ni nan rai a hannun Allah" Maheer yace "Subhanallah, to kin sha magani?" Mama Ladi tace "Mera ta samo min wani gantalalle na hadiya dazu, amma ba sauki" Maheer yace "Zuwa karfe sha daya kafin kiyi bacci sai ki kara sha, in sha Allah za ki ji sauki" Daga haka ya mike ya karasa Bedroom din Ammi yayi sallama, sai da ta amsa ya shiga, Ammi tace "Ya gajiyan hanya?" Ya zauna yace "Alhamdulillah, ina wuni" tace "Lafiya lau" Wayarsa ya mika mata yace "Aunty Mariya zata maki magana" Sai da gaban Ammi ya fadi, tun barin su kano da safe ta kashe wayarta har yanzu ta ki kunnawa, dazu ma sai wayar Usman ta amsa ta kira Abba, Ammi ta amshi wayar, yace "Ki kirata" Daga haka ya mike ya fita daga dakin, Ammi tayi dialing number Aunty Mariya yana fara ring Aunty Mariya ta daga, Ammi tayi mata sallama, Aunty Mariya ta amsa ta gaisheta sai kuma ta ja wani dogon numfashi tace "Ammi Hajja fa tana gidana yanzu haka" shiru Ammi tayi don tasan kwanan zancen dama, Aunty Mariya tace "Yanzu fisabilillahi ina take son Badiyyah ta tafi? Ta dai san ba zaman kanmu muke ba balle ace lallai mu rike Badiyyah a wannan halin da take ciki, wata dayan da tayi gidanki ma abun a jinjina ma Alhaji ne wllhi, Sanda muke kokarin saita Badiyyah ba duk ita ke tabarbara komai ba take goyon bayanta akan duk wasu mugayen halayyan da take, saboda me kuma yanzu har da ita a gudun Badiyyah? Ai in kowa ya guji Badiyyah to banda Hajja tunda ita ce root din duk abinda ya samu Badiyyah" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Ban san me zance ba Mariya, bana son magana shi yasa ma kika ji wayata a kashe, i am tired wllhi" Aunty Mariya tace "To kuwa wallahi Baaba Yahanasu bazata yarda a makala mata Badiyyah ba tana fama da kanta tunda ga Hajjan har ta bar gidan ta dawo nan, ina me tabbatar maki in dai Baaba Yahanasu ce gobe zata kamo hannun Badiyyah ta kawo ta gidan nan ba wai karamin aikinta bane, kuma Ammi kece babba ke ya kamata ki gaya ma Hajja bata da wani Hujjan gudun Badiyyah don ita ce silar duk abinda ya sameta, wallahi ita ce sila, da ta bar mu mun mata tarbiyan da ya kamata da duk haka bai faru ba amma tayi kane kane kan lamarin Badiyyah tana ga kamar ba sonta muke ba, ta dauki kalman maraici ta hure kunnen yarinyar da shi yarinya tayi ta iskancin da ta ga dama babu me ce mata don me, kuma yanzu tace bata da makiyiya sama da Badiyyah, ai bazai yiwu bane, a gabanta ya kamata Badiyyah tayi jinya ba a wani waje ba" Ammi tace "Rufa min asiri, kema zaki iya gaya mata hakan Mariya ba kince tana gidanki ba, sai ki buda mata komai babu boye boye" Aunty Mariya tace "Wai kin ma ji maganganun da ta dinga yi ne ma kuwa, cewa tayi fa mun tura Badiyyah gidan Yahanasu ta karasa ta, idan bamu yi hankali ba wallahi Nijar zata shiga gun er uwarta, wai Bilkisu ce er uwarta yau, ni gaskiya ina ga zan kira kawu Rabi'u in sanar masa duk abinda ke faruwa, kawai Hajja tayi hakuri ta rungumi kaddararsu ita da Badiyyah ta dauketa su koma kaduna su ci gaba da zamansu har Allah ya sauketa" Ammi tace "Kirasa ki sanar masa...." Aunty Mariya tayi mata sallama ta katse wayarta. Washegari Mayraah ta shirya da wuri zata shiga school ta amso statement of result dinta, flight din nasu na karfe hudun yamma ne, so bata san how long zata gama clearance before collecting the result statement ba shi yasa ma ta shirya da wuri, tana shiga parlon Ammi ta tadda Usman zaune yana kallon Mama Ladi dake hadiyan paracetamol, ta karasa ta duka gaban Mama Ladi tace "Ina kwana Mama?" Mama Ladi tace "Ke ban cika son magana ba fa" Mayraah tace "To Allah ya sauwake" Kallon Usman dake kallonta tayi tace "Ina kwana?" Yace "Ina za ki je?" Tace "Zan shiga School inyi clearance ne sai in amshi statement of result, ko zaka yi dropping dina yaya?" Ya mike yace "Mu je" Tace "Toh bari in gaya ma Ammi" Daga haka ta shiga dakin Ammi shi kuma ya fita daga parlon, Usman na dropping dinta a school din yace "Ki kirani idan kin gama" Tace "Toh" Daga haka ya bar school din, sai kusan karfe sha biyu Mayraah ta amshi result din nata sannan ta kirasa, bai wani bata lokaci ba ya shigo school din ya dauketa suka koma gida. Maheer na zaune parlor wajen karfe biyu yana jiran Ammi da ta kirasa sai ga ta ta sauko downstairs, ta zauna tana kallonsa tace "Maheer ya zan yi da wancan tsohuwar?" Maheer ya ɗan yi dariya yace "Wai har yanzu tana kwancen ne?" Ammi tace "Wallahi sai kara lullubewa take fa" Maheer yace "Kar ki damu ku dai ku shirya nan da karfe uku sai in kai ku airport din nasan yanda zan yi da ita" Ammi tace "Toh shikenan" Daga haka ta mike ta wuce sama, karfe biyu da rabi Maheer ya shigo bangaren Ammi, har sannan Mama Ladi na kwance cikin bargo, Maheer na kallonta yace "Sannu Mama" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ko za mu koma can bangaren ne Kinga za su tafi airport ne yanzu" Mama Ladi ta ki kulasa, yace "In kuma kin fi son nan din to...." A mugun fusace tace "Kai dalla rabu da ni inji da cutar dake damuna, ko don ba kai ne ke jin jiki ba?" Maheer yace "Shine nace ma Ammi da naga ta dage a tafi Abuja dake nace mata baxa ki iya ba kina jin jiki, zaman jirgi sai me lafiya..." Mama Ladi na kallonsa tace "Ni muka yi haka da kai Mashir?" Maheer yace "Toh ai basa barin mara lafiya ya hau jirgi shine dama matsalar" Mama Ladi ta mike zaune tace "Ciwon kan ne ma kawai ya saka ni gaba amma ni kaina nasan jikina da sauki bana jin komai wallahi" Maheer yace "Sai dai in zan tafi mu je tare, tun da kin ga sati daya ake dauka kafin mutum ya samu kujeran jirgi don ba kullum jirgin ke tashi ba, wannan ma sai da Abba yayi sati biyu yana bi sannan ya samar masu kujeran" Mama Ladi ta koma ta kwanta, Mikewa yayi ya shiga dakin Ammi dake sauraronsu, yayi murmushi yana kallon Ammi yace "Bari in fita da akwatunan" Ammi dai bata ce komai ba tana mamakin Mama Ladi yanzu kawai sai ta kara kwasan jiki ta bi su Abuja, ina laifin ma ta bari sai bayan kwana biyu haka da komawarsu in ma zuwa zata yi, ai sai abun ya zama rashin hankali kuma, tun bikin Maheer fa take gidan, har Maheer ya kai akwatunan mota Mama Ladi na kwance ta maida bargon gefe daya, Ammi ta fito daga dakinta don karfe ukun ya kusa ta zauna tana kallon Mama Ladi tace "Toh Mama za mu tafi, idan ya so in Maheer zai je sai ku taho tare tunda kujera biyu kawai Abbansu ya samu...." Mama Ladi tace "Ai shikenan, banda ma jikina ya matsa min ai tun a shekaranjiyar nayi niyyar tafiya karaye, to kana naka ne Allah na nasa, ban yi zaton zan kai har yau a gidan nan ba" Ammi tace "Haka ne kam, sai kun zo din dai, bari in je kar mu rasa jirgin" Mama Ladi bata kara tankata ba har ta fita daga Parlon, Maheer ya kai su airport din tare da Mayraah, bayan sun shiga departure ya koma gida.... Karfe biyar suka sauka airport din Abuja, sabon Driver da Abba ya dauka ne yaje airport din daukosu. Ammi bata taɓa zaton irin gidan da Abba ya siya ba kenan a Abuja, she never expect it, mansion ne na gani na fada a anguwa me kyau, kai kana ganin gidan kasan account yayi bala'in girgiza, ga masu gadi biyu da ya saka a gidan da driver daya, har da me watering flowers da sharan babban compound din, abu daya ne babu a gidan wato swimming pool cause it won't be of any use to them, tsabar farin ciki sai da Ammi tayi hawaye bayan ta shiga part dinta it was something she never saw coming, Bedroom din Mayraah yayi biyun wanda ta bari a kano, bandakin ma was very big, dakuna sun wadata sosai a gidan, tun daga sama har downstairs, wajen karfe shidda Abba ya shigo gidan don yana Abujan, Ammi na zaune Bedroom dinta ta ma kasa yin komai sai kallon Mayraah dake jera mata kayanta a press take, Abba na shigowa dakin yana kallon Ammi yace "Me ya samu wayarki ne" cikin sanyin murya Ammi tace "Ban cire a flight mode ba" Mayraah ta gaida Abba, Abba yace "Kema na kira baki daga ba" Mayraah tace "Yana cikin handbag dina" Abba yace "Ohk" Mayraah na murmushi tace "Abba the house is so beautiful Allah ya sanya alkhairi, Allah ya kara maka budi da daukaka, Allah ya sa kafi haka" Abba ya dafa kanta yana murmushi yace "Ameen my Baby gal, hope u are prepared for ur interview tomorrow?" A hankali Mayraah ta gyada masa kai, yace "To maa sha Allah, i know u can do it, congratulations in advance daughter" Tana murmushi ta fita ta bar masu dakin, nan da nan hawaye ya cika idonta, tana komawa nata dakin ta fashe da kuka sosai, she knows she can never pay them in anyway, bata ta taɓa iya biyan duk abinda suka mata a rayuwar nan ba, even if she will how is she going to repay all this? with what will she repay? because of the genuine love they have for her they still have to relocate back to Abuja for the sake of her new work, Bayan Mayraah ta fita dakin Abba ya kalli Ammi da ta kasa dago kanta yace "Gidan ya maki ko a canza yan mata?" [8/5, 9:15 PM] Khaleesat Haiydar💖: Washegari karfe bakwai na safe Mayraah ta tashi ta sauka downstairs zuwa kitchen don girka masu Breakfast, babu abinda babu a kitchen din na foodstuff, bayan ta gama girkin ta kai dinning table ta jera kan table din, Ammi ce ta sauko downstairs Mayraah ta karasa ta gaisheta da ladabi, Ammi tace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah, Ammi ga breakfast na gama...." Ammi tayi murmushi tace "To sannu da aiki daughter, shiryawa za ki je kiyi yanzu ko? naga karfe takwas ya wuce kar ki makara" Mayraah ta gyada mata kai tace "Eh yanzu zan je in shirya" Ammi tace "To kiyi maza" Mayraah ta wuce sama don yin wanka, sai karfe tara ta sake saukowa downstairs sanye cikin black Abaya da handbag dinta sai envelope me dauke da credentials dinta, har ta mance rabon da ta sa Abaya sai Hijab, she look so cute and stunning kuma Abayan ya haska farin fatarta ta dawo kamar wata balarabiya duk da bata yi make up ba sai eye pencil da ta sa a ido, da lip gloss da ta goga a lips dinta, Ammi da Abba na dinning area ta samesu, Ammi na ganinta dama ta fara hada mata tea, Mayraah ta durkusa ta gaida Abba ya amsa da murmushi yace "Kin tashi lafiya?" Tace "Alhamdulillah" Yace "You look cute my dear" Mayraah tayi murmushi tace "Thank you Abba" Ammi ta nuna mata kujera tace "Zauna kiyi breakfast, u are already late" Mayraah ta mike ta zauna sannan ta dau shayin da Ammi ta hada mata, Ammi ta ajiye mata plate din irish a gabanta, tace "Amma after the interview za ki dawo ai, nasan ba yau za ki yi resuming aikin ba dai" Mayraah ta gyada mata kai, Ammi tace "Sai dai a samu food warmer ki dinga tafiya da abinci saboda lunch" Mayraah ta zaro ido ta turo baki tace "Food warmer kuma Ammi kamar er yarinya" Ammi tace "To da yunwa zaki je kina aikin, don nasan ba siyan abinci zaki dinga yi ba" Mayraah tace "To ai har na gama school bana zuwa da abinci fa" Abba dai yayi murmushi yace "In bazata dinga zuwa da shi ba sai drivern ya dinga kai mata abincin da rana kawai" Mayraah dai bata sake ce masu komai ba a ranta kuwa har ta gama deciding in dai drivern za a ce ya dinga kai mata abinci kawai ce masa zata yi yana fitowa ya cinye a hanya ya koma gida da warmer din don babu abinda zata yi da abinci a wajen aiki kamar wata baby, Tana gama breakfast din ta mike zata kai plate da cup din kitchen Ammi tace "Aa bar shi, lokaci ya wuce" Abba yace "Driver zai yi dropping dinki a asibitin, jiya a airport ai wayarki ya kira yaje ya dauko ku so i assume you have his number idan kin gama abinda kike yi sai ki kirasa yaje ya dauko ki, he is ur driver from henceforth" Mayraah tayi murmushi a hankali tace "Nagode Abba" Abba yace "You are welcome dear" Sallama tayi masu ta dau jakanta da Envelope, Ammi ta mike tace "Kiyi addu'a kafin ki fita" Mayraah ta gyada mata kai, har bakin kofar Ammi ta rakata tace "Allah ya bada sa'a daughter, stay safe pls" Mayraah ta ciro black glasses dinta ta saka tace "Ameen Ammi, in sha Allah" Murmushi Ammi tayi tace "Yau dai gayu kike ji daughter" Er dariya tayi ta fita compound din taga driver zaune yana jiran ta, ya sauko da sauri ya gaisheta da ladabi, maimakon ta amsa sai ta gaishesa ita ma sannan ta bude front seat ta shiga don bazata zama comfortable tana baya yana driving dinta ba, bayan sun bar gidan ganin ya kama hanya bai tambayeta inda zai kai ta ba sai kawai ta gaya masa, yayi kasa da kai yace "Ranki shi dade ai Alhaji ya sanar min tun a jiya, nasan asibitin ma, da yake na taɓa yin aikin Uber" Mayraah tace "Ohk" Agogon wrist dinta ta duba taga karfe tara da rabi, tafiyar minti talatin suka yi zuwa asibitin, Mayraah na fara hango babban building din hospital din ta ji gabanta ya fadi, yanzu zata je ta hadu da wancan jarababben mutumin ita wallahi ko irin farin cikin ta samu aiki a asibitin ma bata yi, she is not even excited don gaba daya ya sa taji bata son asibitin a ranta but bata son tayi shunning effort din Dr Khalil ga kuma Abbanta dake ta farin cikin ta samu aiki da ma brothers dinta, wnn ne kawai ya hanata cewa bata son aikin tun a kano, bayan drivern yayi parking ɗan gaba da gate din asibitin don kar yayi hindering masu shiga da mota, Mayraah ta bude motar ta sauka tace "Nagode, idan na gama zan kira ka" Yace "Toh Hajiya Allah ya bada sa'a" Tace "Ameen" Tana juyawa ta ga wani lafiyayyen mota ya taho zai shiga asibitin, tuni masu gadi suka bude gate din suka ɗaga karfen gaban gate din inda motar zata wuce, bata ga wanda ke cikin motar ba don tinted glass ne, bayan motar ya shiga ta bi ta inda ake bi a shiga cikin asibitin da kafa, tana tafiya a hankali, Tana shiga reception din ta gaida nurse din dake wajen sannan ta tafi sama not minding yanda aka bi ta da kallo, ko basu ganeta bane oho, office din Dr Khalil ta nufa duk da bata ga motarsa ba a parking space, knocking tayi to be sure if he is around ya mata izinin shigowa ta bude kofar, yana ganinta ya mike tsaye cause da farko bai gane ta ba yace "Mayraah...." Ta ɗan yi murmushi ta karasa tace "Ina kwana" Yana gyada kai yace "Lafiya lau, ashe haka kika iya gayu, ai ni ban gane ki ba wallahi" Murmushi kawai tayi ta zauna, yace "Maa sha Allah, you look cute, jiyan ku ka shigo kenan?" Mayraah ta gyada masa kai, yace "That's good, Jiya Ceo ma ta shigo kasar, i think she will be around today kinsan gobe za mu je workshop din lagos" Mayraah tace "Oh ok, ya twins?" Yace "They are fine Alhamdulillah, are you together with the credentials?" Ta gyada masa kai yace "Ohk let me have a look first" Mika masa Envelope din tayi, ya amsa yana ciro takardun ciki yace "MD din ma yana nan ai, tare muka shigo dazu, sai da naje na daukosa a motar sa, shi yasa ban ma zo da tawa motar ba...." Statement of result dinta ya fara dubawa, ya dinga kallon result din babu ko kiftawa, can ya nemi kujera ya zauna ya kalleta ya buda ido sosai da mamaki yace "Really?" Ita dai Mayraah tayi shiru bata ce komai ba, buda baki yayi yace "First class?" Still ta ki ce masa komai, Yace "Ikon Allah.. this rare, are you this intelligent Mayraah? I am really surprise wallahi" Mayraah ta ɗan masa murmushi kawai, ya gyada kai yace "Maa sha Allah, i am really impressed, ai duk nan ina ga banda MD we don't have any staff with first class na degree..." Sai kuma ya fara dariya kamar wanda ya tuna abu, Mayraah dai taki ce masa komai har da ɗan daure fuska, Dr Khalil ya duba other credential din nata sannan ya maida su cikin Envelope yana murmushi yace "Za mu shiga theatre nan da minti talatin, bari in samesa if u can go for the interview now, don banda shi za mu shiga theatre din" Mayraah ta gyada masa kai tace "Ohk" Ajiye envelope din yayi ya fita office din zuwa office din MD, a long pavement din saman ya samesa ya fito daga office din CEO walking towards his office, Dr Khalil ya jirasa har ya iso MD yace "3 nurses, 5 Dr's for tomorrow's workshop, zaka yi booking flight din yau, 10 ticket in all" Dr Khalil dai na biye da shi har suka shiga office dinsa, MD ya zauna letting out a sigh yace "Yanzu zaka ga ta sake biyo ni nan" Dr Khalil yayi dariya yace "Amma ana gama workshop din zata koma ne?" MD bai ce masa komai ba ya mike ya dau tea cup dinsa ya tafi ya wanke ya dawo ya zauna yace "Nan da sati biyu ne Conference din da tace a England ai, or is it even US, na dai manta" Har ya bude flask din sai kuma ya sake kallon cup din ya mike ya tafi ya kara wankewa ya dawo, Dr Khalil yace "Ohk ku biyu za ku yi attending Conference din kenan?" MD yace "No pls... Dr Balogun should go" Dr Khalil yace "Kai ma kasan she can't do without u in anything ai" MD ya kalli wayarsa dake ring ya dauka yayi picking call din ya kai kunne, cikin minti biyu ya gama wayar ya ajiye, ya kalli Dr Khalil yace "What were u saying?" Dr Khalil ya kalli agogon office din saboda theatre da za su shiga he is cautious of time, MD ya sake tashi ya tafi ya wanke tea cup din hannunsa ya dawo, kiran Ceo ne ya shigo wayarsa ya zauna ya daga yana sauraronta, sai kuma yace "Ohk ma, i will bring them in 30 mins time" Bayan ya katse wayar ya tashi ya sake wanko cup din ya dawo, Dr Khalil ya taɓe baki ya mike yace "Are you ready? Za ta shigo interview din yanzu, cause she is around" MD ya daga kai ya kallesa, sai kuma ya hade rai yace "Waye haka?" Dr Khalil yace "You insisted she should come for the interview last week, so she is around today" MD yace "Ohh shine yasa CEO ke tambayana ita da naje office dinta yanzu kenan, ashe ta ganta ne, ita dai ta dage lallai sai tayi aiki a asibitin nan, ko dai mayya ce yarinyar nan?" Dr Khalil yace "Ga dai ta nan with her credentials kamar yanda ka bukata, so i will send her right away, don ni zan shiga theatre" Ko tankasa MD bai yi ba ya sake tafiya ya dauraye cup da zai sha coffee, kafin ya dawo har Dr Khalil ya fita daga office din, yana komawa nasa office din ya kalli Mayraah yace "You can go to his office, but plss Mayraah be a good girl, kiyi abinda ya kamata he is our boss, and he is employing you, speak to him with respect and calmness, kalmominki kar su wuce Yes sir, Ok sir, sorry sir, thank you sir" Murmushi Mayraah tayi tana kallonsa ta rasa dalilin da zai dinga cewa she should be a good gal in zata je gun jarababben mutumin can, to tayi kama da bad girl ne? Ta sunkuyar da kai tace "Toh Dr" Yace "You can go now, yana jira" Mikewa tayi ta dau jakarta da Envelope din takardunta, ga cire glasses dinta zata saka a jaka, Dr Khalil yace "Me yasa kika cire, ki maida abun ki" Mayraah ta kallesa yace "Ki sa mana, ai ya maki kyau" Ɗan murmushi tayi ta maida glasses din sannan ta nufi kofa, har ta rike handle din sai kuma ta juyo tana kallonsa a hankali tace "But do u have any idea akan abinda zai tambayeni" Dr Khalil yace "Ki kwantar da hankalinki and be calm, ba wani tambayar da zai maki na sani, kawai zai duba takardunki sai kuma ya tambayeki informations dinki to be imputed, yana ganin result din ki ma nasan sai ya rasa tambayar da zai maki don mamaki.... So just go" da murmushi ya kare maganarsa, Mayraah ta sauke idonta kasa ta juya ta fita daga office din, last floor ta tafi zuwa office din MD, gently tayi knocking kofar har sai da ya amsa sannan ta bude ta shiga, Coffee dinsa yake sha bai kuma daga kai ba balle ya kalleta, ta karasa har gaban table dinsa ta tsaya calmly tace "Good morning sir" Dago kai yayi, kiris ya rage ya saki cup din coffee din hannunsa don har sai da ya ɗan zube masa a white shirt dinsa, mikewa yayi da sauri ya ajiye cup din yace "Kee, why will u just badge into my office are you okay? Ance maki kasuwa ne nan?" Bai jira me zata ce ba ya shige Bedroom dinsa dake office din, Mayraah ta bi sa da kallo, can ta taɓe baki a ranta tace kilan dai Dementia garesa, cause sai da tayi knocking ya bata permission din shigowa kafin ta shigo, tana ta tsaye har ya fito bayan minti biyar with another white shirt, ya wani daure fuska kamar bai taɓa ko murmushi ba, ita dai bata yarda ta kallesa ba har ya karaso table dinsa ya dau cup din coffee din ya tafi ya zubar ya dawo, still yaki kallonta yace "Me kike jira har yanzu?" Calmly tace "I came for the interview u ask me to come for, here are my credentials" Bata jira me zai ce ba ta ajiye envelope din kan table dinsa sannan ta koma gefe ta tsaya, yace "Ohk shi Khalil din ne yace maki kina zuwa ki ajiye CV din kan table dina?" Mayraah bata ce komai ba, ta dau envelope din ta nufesa ta tsaya a gabansa tana mika masa while looking at him, ƙin yarda ya kalleta yayi may be he wasn't expecting that, kawai taga ya bar wajen ya koma seat dinsa ya zauna, ta juya tana kallonsa still ya ki kallonta, kwankwasa office din aka yi, ya mike da sauri duk tunaninsa Ceo ce, Dr Balogun ya bude office din ya shigo da wani file, yana ganin Mayraah yace "Ohh Madam, where have u been all this while?" Mayraah ta gaishesa da ladabi, ya amsa da hausansa irin na yoruba yace "Kwana biyu baki zo aiki ba, ina kika tafi?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Ya ce in zo interview ne tukunna kafin in ci gaba" Dr Balogun ya kalli MD that was unnecessary clearing stuffs off his table, Dr Balogun yace "Ohk MD in je in dawo kenan after the interview, dama akan aikin da za mu yi da daddare ne..." Sai a sannan MD ya daga kai a takaice yace "You can interview her Balogun, i am a bit busy...." Dr Balogun ya kalli Mayraah yace "Are you with ur CV?" Ta gyada masa kai ta mika masa Envelope din hannunta, zaunawa yayi kan kujera ya nuna mata kujeran dake kallon wanda ya zauna yace "Sit..." MD yace "Why should she sit? She should take off those glasses we are not doing fashion here" Dr Balogun ya kalli Mayraah da ta cire glasses din idonta, sai kuma ya fara fiddo da takardun, Mayraah ta wani harari MD dake kallonta ta gefen ido, Statement of result dinta Dr Balogun ya fara dubawa, sai kuma ya kalleta da sauri yace "Waow, first class from this prestigious university? It's my alma mater also, nasan lecturers dinku sosai" Mika ma MD yayi, MD dake kallonsa yace "First class in Botany or what?" Dr Balogun ya zaro ido yace "Nursing Science Malam, ina jin fa department din nan rabon da a fita da first class zai kai shekara sha biyar ko ma ya fi, and she just graduated" MD dake ta kallonsa yace "Nursing Science?" Dr Balogun yace "Gashi ka duba" MD ya girgiza kai yace "Wani makaranta ne?" Dr Balogun ya gaya masa, MD yace "That's a lie" Da mamaki Dr Balogun yace "Ka taɓa ganin anyi forging result a makarantar nan?" MD ya dau wayarsa yace "I have a frnd that is a Lecturer in the department, i will confirm it now" Shiru Dr Balogun yayi yana kallon MD da ya amshi result din yana dubawa sannan ya dau wayarsa ya fara dannawa, Ita dai Mayraah ko kallon inda yake bata sake yi ba, har cikin ranta bata taɓa jin ta tsani mutum irin yanda take jin tsanar mutumin nan ba, she detest him with passion, ji take kamar ta fice daga office din amma bazata yi haka ba sbda Dr Khalil, tana ta jiran taji ya kira wayar sai kuma bai yi ba, ya maida wayar ya ajiye yace "I will confirm that later, Dr Balogun you can leave, we will discuss the issue at hand later" Mikewa Dr Balogun yayi, har sannan kallon Mayraah yake don ko kadan bai ji shakkan result dinta ba, bayan fitar Dr Balogun ya jawo laptop dinsa after some minutes ba tare da ya kalleta ba yace "Ur name?" Sai a sannan Mayraah ta kallesa, a takaice tace "Mayraah Mahmud" Ya hade rai ya kalleta yace "Kee sunanki zaki gaya min ba sunan gayunki ba, ko an gaya maki wajen wasa ne nan?" Tace "U can check the name in my result for ur self" ita kanta bata san sanda ta gaya masa haka ba, ya dinga kallonta, kawai ya rufe laptop dinsa yace "Get out" Bude office din aka yi Ceo ta shigo, ya mike da sauri yace "U need something Ma?" Karasowa ciki tayi tana kallon Mayraah cikin sanyayyen muryarta tace "Hello, how are you, i just asked of u not long ago" Mayraah ta gaisheta da ladabi, MD dai kallonsu kawai yake, Ceo tayi mata side hug, sosai gaban Mayraah ya fadi, Ceo na kallonta with calmness tace "Why are you not on scrub?" Mayraah ta kasa kallonta tace "I..." Sai kuma ta rasa me zata ce, Ceo ta kalli MD tace "Is there anything?" Da sauri yace "No, not really, just adjusting some mistakes in her data.... She is not on duty today" Ceo tayi murmushi tana kallon Mayraah a hankali tace "If he is done, Come make me coffee in my office Mary Ann" Mayraah ta gyada mata kai tace "Ok Ma" Daga haka ta ajiye takardun hannunta ta juya ta nufi kofa, Mayraah ta bi ta da kallo babu ko kiftawa, juyawa tayi suka hada ido da shi, lkci daya ya mike ya dau wasu textbook zai kai Library dinsa na office din, tace "Can i take my leave?" Wani shegen kallo ya jefa mata, hakan yasa ta fara kokarin tattara takardunta yace "Hey get out" Juyawa tayi ta bar takardun ta fita daga office din..... [8/6, 7:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na fitowa office din MD ta nufi office din Dr Khalil, zai fita suka hadu da shi a bakin kofa, yana kallonta yace "Har kun gama?" Mayraah ta taɓe baki tace "Ni dai in kaje office din ka dauko min credentials dina pls" Dr Khalil na jin haka yasan an samu matsala, yace "Tell me, ya ku ka yi da shi?" Tace "Ni yanzu na fara masa uzuri gaskiya, kamar fa ba shi da lafiya ne, but seriously bai kamata ana bari yana fitowa gida a wannan yanayin ba, his parent are not doing him good" Dariya Dr Khalil yayi ba tare da ya shirya ba, Mayraah ta sauke ajiyar zuciya ta koma gefe ta tsaya, har a zuciyarta ta fara tunanin da gaske MD na da problem may be in his brain or so, to ko dai karatu ne ya fara taɓa masa ƙwaƙwalwa, Dr Khalil that was just laughing ya dake yace "Amma dai ya maki tambayoyin da zai maki?" Mayraah ta daga kai ta kallesa tace "He was just talking gibberish and finding fault where there is no fault...." Dr Khalil na murmushi yace "Za ki jira har mu fito theatre?" Mayraah tace "Zan je office din Ceo ne yanzu, i am dropping my handbag in ur office" Dr Khalil yace "Kun hadu da ita ne?" Ta gyada masa kai tace "Ta shigo ne ta gan ni" Dr Khalil na murmushi yace "I love this bond that is forming gradually between u and Ceo, i like it, kuma fa bata da yarda matar, ke kuma gashi kamar taku ta zo daya, ko office dinta in ba MD din ba sai kilan Dr Ajay babu me zuwa, out of bound muke kiran wajen, you know she is so confidential...." Mayraah dai bata ce komai ba, ya mika mata makullin hannunsa yace "Idan kin ajiye jakan sai ki kulle min office" ta amsa tace "Ohk" Yana barin wajen ta shiga office dinsa ta ajiye jakarta sannan ta fito, ta kulle kofar ta tafi sama zuwa office din Ceo, Dr Elliana Alfred... Haka Mayraah ta fada a zuciyarta bayan ta ga sunan manne jikin kofar office din, ta kai hannu zata yi knocking kofar kenan taga an bude, ido hudu suka yi da MD, ita ta fara sauke idonta ta bi ta gefensa ta shiga cikin office din ta bar sa nan tsaye, kasa fita daga office din yayi, did he just open the door for this brat to come in? Kawai ya fice daga office din ya kulle kofar. Mayraah ta karasa har kusa da couch din da Ceo ke zaune da magazine a hannunta, har ta karaso kuma kallonta matar take, matar ta nuna mata inda zata tafi don making mata coffee din da coffee maker dake office din tace "The coffee maker is over there" Mayraah ta karasa wajen sai taga ba coffee powder a nan, dawowa tayi ta gaya mata, Ceo ta ajiye magazine din hannunta tace "Ki je office din Dr Aliyu ki amso, i took it home the last time i was here...." Mayraah tace "Ohk Ma" Daga haka ta juya ta fita, office din Dr Khalil ta tafi duk da tasan bazata gansa ba amma she wish he was there yaje ya dauko coffee din da kansa a wajen MD, ita dai bata son encounter da mutumin nan kwata kwata, avoiding dinsa ma ya kamata ta dinga yi don ta fara masa kallon mahaukaci, ganin babu wani alternative ta sake komawa sama zuwa office din MD din tunda babu yanda zata yi, tsaye tayi bakin kofar tayi knocking, taji yace "Who is there?" kawai ta bude office din a hankali ta shiga, tsaye ta samesa gaban table dinsa yana duba statement of result dinta, wasu takardu yayi saurin dauka a kan table din ya daura kan result din nata cikin few seconds, and she saw that, ta dai karasa cikin office din ba tare da ta bari ta kallesa ba tace "Ta ce wai ka bada coffee powder..." Shi ma without looking at her yace "Naga kamar kina nema ki dinga kawo min reni, don me za ki shigo min office kai tsaye kamar dakin ki? Are you okay?" calmly tace "I knocked first" ya kalleta a karo na farko fuska a daure yace "And who gave u the permission to come in?" Ita ma kallonsa take taki cewa komai, sai kuma ta hango coffee powder din da ya hada dazu a kan table dinsa, zagayawa tayi ta tafi zata dauka, ya bi ta da kallon mamaki, bayan ta dauka zata bar wajen bata lura da laptop dinsa da ke caji ba kawai kafarta yayi tangling wayar chargern, force din ya jawo tsadadden laptop din tun daga kan table din har kasa, komawa baya tayi ta dinga kallon laptop din a tsorace, lokaci daya gabanta ya wani fadi, ta durkusa da sauri ta daga laptop din tana duddubawa, bayan few seconds ta mike tana kallonsa cike da karfin hali tace "I am.. am sorry...." Sai kuma ta ajiye laptop din tare da makullin hannunta ba tare da tasan tayi hakan ba kawai ta dau coffee powder din ta nufi kofa ya bi ta da kallo, tana fita ta kulle office din ta sauke wani ajiyar zuciya har sannan gabanta na faduwa, ko dai bai ga abinda tayi ma laptop din bane, da sauri ta bar wajen ta koma office din Ceo, cikin minti kadan ta gama making mata coffee din, duk inda ta bi sai Ceo ta bi ta da kallo ta ma daina karatun magazine din da take, daga karshe Mayraah ta kai mata coffee din a Tea cup da saucer dinsa, Ceo ta nuna mata table din gabanta, Mayraah ta duka ta ajiye a hankali, Calmly Ceo tace "Thank you dear" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "You are welcome Ma" Ceo tace "Are your parent here in Abuja?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Yes Ma" Ceo tace "Mary Ann every movement of urs reminds me of my late friend, it's been long i felt heartbroken this way, har na koma England kina raina ban san me yasa ba, i think i asked Aliyu about you twice or so" Mayraah ta sauke kanta kasa, wani bugawa zuciyarta yake da ita kanta bata gane dalilin sa ba, Ceo ta dauki cup din shayin tace "You can take your leave, thank you dear" Mayraah ta kasa barin wajen, har sai da Ceo ta daga kai ta kalleta, sunkuyar da kanta tayi tace "But ma, kin ce za ki hada ni da relatives din friend din taki" Ceo ta ɗan yi murmushi tace "Sure i will, i am kinda busy now, gobe za mu je workshop Lagos, in 2 days time zan koma England ina da aiki a can" Mayraah ta gyada mata kai tace "Toh Nagode" Ceo tace "You are welcome" Daga haka Mayraah ta juya tana tafiya a hankali ta nufi kofa, matar ta bi ta da kallo babu ko kiftawa. Gaba daya Mayraah ta mance da batun makullin Dr Khalil har sai da ta sauko second floor ta lura she is not holding the key, nan hankalinta ya tashi don bata san inda ta bar makullin ba, ko a office din MD ko na Ceo, hango kofar office din tayi kamar a bude, hakan ya bata mamaki sosai ta dai karasa tana kallon kofar that was slightly opened, tura kofar tayi taga MD tsaye gaban table din Dr Khalil with her handbag in his hands, yana ganinta ya ajiye jakar keeping a straight face, ya kwashi wasu files kan table din Khalil, Mayraah ta kasa cewa komai don tsabar mamaki, to me yake nema a jakanta? Kofa taga ya nufo ta koma gefe tana kallonsa da mamaki tace "Meye kake nema a jakana?" Yace "Ohh jakarki ne ashe, ai na zata na Khalil din ne" Daga haka ya fice daga office din ta bi sa da ido, da sauri ta tafi gun jakar nata ta bude tana duba ciki, wayarta ne a ciki sai Atm card da glasses dinta, with oil perfumes, to me yake nema, is he even okay? Zaunawa tayi still tana searching jakan har sannan mamaki ya kasa barin ta, kenan a office dinsa ta bar key din. Sai kusan karfe daya Dr Khalil ya shigo office dinsa, Mayraah ta mike tana kallonsa tace "Uhnn I've waited all day" Dr Khalil yace "Wallahi muna fitowa kuma MD ya kirani office dinsa, kin samu kin ci abinci ma kuwa?" Mayraah ta dau jakarta tace "Dama kai kawai nake jira driver har ya zo yana jirana a waje, idan naje gida zan ci" Yace "Ohk, ina jin yayi imputing data dinki, so u are going to write me down ur account details, ur shift is from 8am to 6pm For now, resume work next week Monday" Mayraah na kallonsa tace "Ohk, thank you" Yace "Scrubs dinki kamar suna can gidan Ummi, so zan dauko maki a office din MD yanzu tunda kin ce driver yana jiranki...." Daga haka ya fita daga office din zuwa na MD, yana shiga MD dake tattara laptop dinsa da wasu textbooks yace "We are leaving together with Ceo now, idan an ajiyeta bazan dawo nan ba, sai after the workshop, na kai mata list din da muka yi creating na Dr's da 3 nurses da za aje Lagos din gobe, pls ka taho min da motata gida anjima...." Dr Khalil yace "Kana gida ai da daddare?" MD ya kallesa yace "Ka manta za mu fita tare da daddaren zuwa hotel din da frnds dina turawa suka sauka, kasan ban cika son driving at night ba, sorry for always inconveniencing you pls" Dr Khalil yayi murmushi yace "Su abokan naka turawa me yasa basu sauka gidanka ba?" MD zai yi magana Ceo ta shigo da list din da ya kai mata tana mika masa ya taho ya amsa da ladabi, tace "I saw just 3 nurses in the list, why is that?" Ya sunkuyar da kai yace "We chose just them Ma'am" Tace "Why not make them 4, include Mary Ann to the list pls" Ya daga kai yana kallonta da sauri, sai kuma ya ɗan shafa kai yace "But Ma'am, babu ticket for that same flight... Sai dai wani jirgin, wannan da muka yi booking jirgin ya cika, sai ma da muka yi contacting dinsu suka soke wasu ticket din aka samar mana 10 din da muke bukata...." Dr Khalil ya saki baki yana kallon MD don ko booking ticket din basu kai ga yi ba tukunna, Ceo tace "Ohk, that's fine" Daga haka ta juya ta fita daga office din, Dr Khalil na girgiza kai yace "Ka ji tsoron Allah Dr Aliyu, what's there idan anje workshop din da ita, ai ire irensu ma ya kamata...." Dakatar da shi MD yayi yace "Baza ta je ba, yaushe ma aka bata cikakken aiki a nan din da zata je workshop din manyan likitoci a Lagos, wa enda suka yi shekara da shekaru a nan ma basu je ba sai ita mara kunya da ko fara aikin bata yi ba" Dr Khalil yace "Toh dai Ceo da kanta ai tace aje da ita kuma ta san sabuwa ce" MD yace "To ni kuma as the MD of this hospital nace banda ita, baxata je ba, kuma abinda baka sani ba ni ba full employment na bata a asibitin nan ba, she will just work as an Intern in here, not a staff, beside ko service fa bata yi ba daga amsan statement of result kawai sai aiki?" Dr Khalil yace "Thank God dai ba government hospital bane nan din balle kace, kuma wannan kamar bakin ciki kake mata...." MD yace "Shi din ne ma" Juyawa Dr Khalil yayi zai fita, MD yace "Book the flight immediately pls... 10 seats" Dr Khalil yace "Ohk" Daga haka ya fita ya kulle masa kofa. Yana komawa office dinsa yace "Mayraah if it's okay anjima idan na amso su daga gida Ummi ko da daddare ne sai in kai maki gida, cause kamar babu scrubs din available yanzu" Mayraah ta mike tace "Ohk nagode" Yace "You are welcome, ki gaida su Ammi" Tace "Za su ji" Daga haka ta fita daga office din don tun dazu Drivernta ke waje. Wajen karfe biyu Mayraah ta isa gida, tana bude kofar parlon ta ga Usman a zaune shi kadai, sau biyu yana daga kai yana kallonta wanting to be sure ita din ce, ta karaso parlon ta ɗan yi murmushi tace "Yaya yaushe ka zo?" Ya hade rai yace "Yaushe kika fara wannan dressing din in zaki fita?" Tayi kasake tana kallonsa, can ta zagaya inda yake zaune, ya dinga kallonta daga sama har kasa, tace "Yaya me ya faru da dressing din?" Yace "Tambayata kike? Ok barin hijabs din naki kika yi a kano kenan?" Ta ɗan turo baki tace "Yaya Abaya ce fa ba wani abu ba, beside....." Calmly yayi shutting dinta yace "Keep quiet" Ammi ce ta fito daga kitchen ta tsaya tana kallonsu, A nutse yace "Kar ki sake wannan dressing din a gidan nan, were you trying to get someone impressed a hospital din?" Ammi tace "Ban gane kar ta sake wannan dressing din ba, meye da shigar tata da bazata sake ba?" Ya ɗan daga kai ya kalli Ammi don bai ma san ta fito daga kitchen din ba, Mayraah dai sai turo baki take, can dai yace "To gidan biki za ta Ammi, haka ake zuwa interview dama?" Ammi tace "Aa ba ruwanka, let her dress the way she wants as far as ba wando ta saka ta fita ba, meye laifin Abaya?" Mikewa yayi ya bar parlon ya shige daki, Mayraah ta bi sa da kallo, Ammi tace "Rabu da shi ki tafi kije ki yi wanka ki sauko ga abinci na gama" Mayraah ta gaisheta a hankali sannan ta wuce sama, wajen karfe uku ta sake saukowa downstairs bayan tayi wanka tayi sallah sannan ta canza kayanta, dinning area ta tafi ta debi abincin da Ammi ta ajiye a nan, spoon daya ta ci, sai kuma kawai ta mike ta nufi dakin da taga Usman ya shiga dazu, a hankali tayi knocking kofar dakin, tana ta tsaye taji ya bude kofar ta daga kai tana kallonsa, sai kuma ta bi ta gefensa ta shiga cikin dakin ta juya tana kallonsa ta marairaice tace "Yaya did i dress indecent?" Kulle kofar yayi ya koma ya zauna, ta bi bayansa tana kallonsa, yace "Amminki ta ce ba indecent bane... She gat your back" Murmushi tayi ta durkusa gabansa tace "Toh kayi hakuri yaya bazan sake ba, kuma ma ai uniform zan dinga sa wa ba kayan gida ba daga yau" shi dai kallonta kawai yake, ta mike tace "Have you eaten?" yace "Yeah" Tace "Toh zan je in ci abinci" Daga haka ta juya zata fita yace "Mayraah" Juyawa tayi ta kallesa, ba haka nan duk brothers dinta ke kiran sunanta kai tsaye ba, yace "In kin gama abinda kike yi da daddare ki shigo za mu yi magana" Da mamaki take kallonsa wondering maganar me za su yi, sai kawai tace "Toh in sha Allah" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Bayan magrib Mayraah na zaune kan darduma wayarta ya fara vibrate ta dauko a zaton ta Maheer ne don tayi masa kira har biyu bai yi responding ba, Dr Khalil ne ke kiranta, ta daga kiran bayan sun gaisa yace "Na dauko maki Scrubs din a gidan Ummi, can i come over yanzu in kawo maki, kin san za mu je lagos gobe da safe and probably monday za mu dawo" Mayraah tace "Ohk to Nagode" Yace "Address din fa?" Tace "Bari in tura maka" Katse wayar tayi ta tura masa address din, bayan minti sha biyar ya sake kiranta yace gashi a kofar gida, mikewa tayi sai da ta fara zuwa ta gaya ma Ammi sannan ta fito daga gidan sanye da hijab dinta har kasa, tana ta kallon motar wondering ko ya canza mota ne, ta dai karasa ya sauke glass din yana kallonta da murmushi yace "Good evening" MD ta gani zaune front seat ya wani hakikance, Dr Khalil ya sauko daga motar ya zagayo back seat ya dauko mata uniform din ya mika mata yace "Sai fa da yan sanda suka tsayar da mu kafin mu shigo nan, wai wajen wa za mu" Mayraah tayi murmushi tace "Sai kace masu wajena mana" Dariya yayi yace "Eh lallai kam wajenki" can yayi kasa da murya yace "Baki gaida boss dinki ba Hajiya" Mayraah ta sake kallon MD da yayi kasa da kai yana kallonta ta Mirror, don unguwan haske tarrr kamar da rana ko ina fitilu ne, yana ganin ta juyo ya dauke kai yana danna waya with a serious face, a takaice tace "Ina yini" jin bai amsa ba Khalil ya karasa har kusa da door din motar yayi knocking yace "Ana gaisuwa Oga" MD yace "Dalla ka zo mu tafi kana bata min lokaci kasan ana jirana" Mayraah na kallon Dr Khalil tace "Nagode Dr sai da safe" Ya mata murmushi yace "Ki gaida su Ammi" Tace "In sha Allah" Daga haka ta shige cikin gida, Dr Khalil ya zagaya ya shiga driver seat, MD ya kallesa yace "Burin ka kawai ka dinga ja mana raini wajen yarinyar nan, yanzu sai ta ga kamar biyoka nayi fa in her stupid mentality, ji wani iyayi da take, to meye da Unguwan nan?" Dr Khalil yace "Aa bawan Allah, sai da nace in ajiye ka eatry ka jirani in zo in kawo mata sakon kafin in koma in daukeka muje inda za mu kace no way sai ka biyo ni" MD yace "To ni ɗan iska ne zan yarda ka ajiyeni eatry ba abinci nake ci a eatry ba?" Dariya Dr Khalil yayi yace "To nan dai ne gidansu incase....." MD ya kallesa yace "Incase what?" Dr Khalil na murmushi yace "Incase Watarana mana" Mayraah na komawa dakinta ta dau wayarta taga miss calls din Maheer, murmushi tayi har zata kirasa sai kuma ta tuna za su yi magana da Ya Usman kamar yanda yace mata dazu, ta ajiye wayar with the intention of calling him back idan ta dawo, sannan ta sauka downstairs ko hijab dinta bata cire ba ta nufi dakin da ta gansa ciki daxu. [8/7, 8:39 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na isa kofar dakin tayi knocking, after a while ya bude kofar, shi in dai aka masa knocking baya bada izinin shigowa sai dai ya tafi da kansa ya bude kofar don bai fiye son ana shigo masa daki ba, she is already used to that, tana ganin ya bude kofar ta bi gefensa ta shiga ciki ya bi ta da kallo sai kuma ya kulle kofar ya karasa ciki yace "But i said later in the night" Mayraah ta zaro ido tace "To yanzu yaushe ne yaya? Everywhere is dark already" Zaunawa yayi yana ci gaba da abinda yake yi a laptop yace "Ai ba ayi isha ba" Ta turo baki tace "Yaya ni dai i am eager in ji maganar me zaka min, is it about my dressing dazu?" Ya kalleta yace "Ai Ammi tace dressing din ya maki kyau" Murmushi tayi tace "In dai shine ni dai kayi hakuri, nace maka bazan kara ba" Yace "Ba shi bane" Tayi shiru tana kallonsa, ya kashe laptop din ya ajiye yace "I just want to know what ur next plan is.... 2 years back kinyi saukan Al-qur'ani, this year kin yu graduating from university, immediately after graduation kin samu aiki, so what do u have in mind next?" Ta ɗan yi murmushi ta sunkuyar da kai tace "Kamar me fa yaya?" Yace "Ko iyakar burinki kenan a rayuwa?" Ta daga kai a hankali ta kallesa, she wish zai gane yanda ta zama desperate ta hadu da nata relatives din ko da guda daya ne, bata son ta zama an ingrate shi yasa take kauda tunanin nan ko da yaushe a ranta bata basa mafaka ba balle ya dameta, amma God knows in this few months har cikin zuciyarta tana son sanin ko da mutum daya ne a jininta, sauke idonta tayi bata ce masa komai ba, a hankali yace "Kinyi shiru" Tayi gathering courage tace "Duk wani abun Alkhairi will always be among my wish everyday Yaya, ba ni kadai ba kowa ma ina masa fatan abun alkhairi ya same sa kullum" Yace "Mayraah" Ta daga kai ta kallesa yace "So in ur wish there is nothing like marriage?" Ta ɗan buda ido, sai kuma tayi murmushi ta sunkuyar da kanta tace "Ai lokaci ne yaya, idan Allah ya kawo lokacin za ayi" Yace "Tell me the truth, is there anything between u and that Dr? I mean Dr Khalil" Mayraah ta zaro ido tace "Not at all wallahi, shi da yake da mata da yaransa biyu" Usman yace "Ohk ba a auren me mata?" Tayi dariya tace "Aa nima ban sani ba" Yace "Baza ki iya auren mai mata ba kenan?" Ta sunkuyar da kai tace "Ni dai ba ruwana" Yace "Abokina me mata ya ga hotonki yace yana so yanzu baza ki iya aurensa ba kenan?" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta turo baki bata ce komai ba, yace "Am serious" Shiru tayi tana kallon sa, ya sauke idonsa yace "Wasa nake bai da mata, he is single, a Barrister too, are u interested? maganar da za mu yi kenan dama" Nan da nan jikinta yayi sanyi don Musharraf ne ya fado mata, Shi dai Usman kallonta kawai yake examining her reaction at the same time, bayan few seconds tace "Yaya i don't think i will love again...." Hawaye ya cika idonta ta fara gogewa da sauri, shi dai yayi shiru yana kallonta, can yace "Mayraah" ta daga kai ta kallesa tana share idonta, yace "Why won't u love again" Ta fashe da kuka tace "I don't want to remember the pass, ko ma waye zai aureni yanzu dole sae ya fara sanin ko ni wacece, after that no parent will want their blood to marry me" Yana kallonta a hankali yace "Har Ammi da Abba?" Daga kai tayi ta kallesa as if trying to apprehend what he meant by so saying, Bai bata wannan space din ba yayi saurin cewa "Forget that pass u are talking about and concentrate on the future Mayraah" Ita dai bata ce komai ba sae kallonsa take, yace "So i will want you to give this guy a chance" Nan ma dai bata ce komai ba, yace "Banda kula kowa kuma" Tayi murmushin karfin hali bata dai ce komai ba, yace "Promise me that" Ta kallesa kamar yasan abinda ke running a mind dinta yace "Kin dai san bazan yi abinda zai cuceki ba ko?" Ta sauke idonta, yace "So now make that promise baza ki kula wasu ba" Ta gyada masa kai tace "In sha Allah" Yace "You can leave" Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita wasu hawayen na taruwa idonta ta koma dakinta. Wajen karfe tara bayan tayi wanka ta kira Maheer, Haseenah dake parlon ta mike jin wayarsa dake ajiye kan kujera na ring, shi kuma yana kitchen yana hada shayi, kallon screen din wayar ta dinga yi taga an sa Mimi with love emoji, ta dinga kallon wayar babu kyaftawa har ya fito daga kitchen, ta juya ta shige daki, ko kallon inda ta bi bai yi ba ya dau wayarsa bayan yayi picking Mayraah ta gaishesa, ya zauna yace "Ina kika shiga?" Tace "Kai dai zan tambaya, bayan tun dazu nake ta kiran wayarka" Yayi murmushi yace "Wayar na silent kika kira dazu, ya kike?" Tace "Alhamdulillah, ya aiki" Yace "Cool, kin je interview din yau?" Tace "Na je" Yace "No issues?" Kai ta gyada masa kamar yana ganinta, sai kuma tace "Ka fara processing transfer din naka yaya?" Yace "Not yet" ta ɗan hade rai tace "Do it soon pls, ko baka missing dinmu" Yace "I will try Mimi, ina missing dinku mana, ina Ammi?" Tace "She is in her room, Mama Ladi ta tafi ne?" Er dariya yayi yace "Jiya na kai ta har karayen wai bazata iya zaman motar haya ba" Mayraah tayi murmushi tace "Ayya, yanzu yaya idan ina son magana da sis Badiyyah ta ina zan sameta?" Maheer yace "I don't really know" Tace "I tried calling her lines severally amma duk a kashe" Yace "May be ta kashe wayar ne" Mayraah tayi shiru, shi ma haka, bayan few seconds tace "Pls try and request for the transfer kaji yaya" Yace "I will do so starting from tomorrow in sha Allah Mimi" Tana murmushi tace "Yauwa yayana, i want to go to bed now" a hankali yace "Alright Dear, sleep tight" Tace "Bye" Daga haka ya katse wayar, ya ajiye ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, tun da suka koma Abuja sai dai ya sha tea ko coffee, idan ya fita kuma ya biya restaurant ya ci abinci, kana ganinsa kasan he is not himself, a da yayi niyyar ko zai nemi transfer din sai zuwa nan da wata biyu ko uku, amma yanzu kam yaji bazai iya ba, damuwa yayi masa yawa, ganin daga shi sai Haseenah na kara saka masa damuwar nan, don haka dole ma ya nemi transfer din nan ko ta yaya ne ya koma wajen family dinsa soon. Ranan Sunday da yamma Mayraah ta gama shiryawa ta fito daga dakinta zuwa parlon Ammi, Ammi dake zaune tana kallon TV ta kalleta tace "Ko dai mu bari zuwa gobe ko da daddare ne in kin dawo aiki mu je daughter?" Mayraah ta zauna gefenta tace "Aa Ammi mu je yau pls kin ga fa na riga nayi girkin, nasan goben a gajiye zan dawo" Ammi tace "Toh shikenan, mu je kawai..." Mikewa tayi ta shiga daki ta dauko gyalenta da jaka, sannan suka sauko downstairs, sai da Mayraah ta fara shiga kitchen ta dau warmer din tuwo da miyar ganyen da tayi ta kai mota, driver na compound yana jiran fitowarsu, Mayraah ta sanar masa inda zai kai su sannan ta bude ma Ammi back seat ta jira har ta karaso ta shiga ta kulle motar sannan ta tafi front seat ta zauna, tafiyar kusan minti talatin da biyar suka yi suka iso gidan, Drivern yayi parking bakin gate, Mayraah ta sauka ta dauko warmers din biyu, Ammi ma ta sauko daga motar ta sanar masa jiransu zai yi sannan suka shiga cikin gidan, Karime ce ta bude masu kofar parlon tana ganin Mayraah ta rungumeta cike da farin cikin ganinta tace "Sannunku da zuwa... Ku shigo" Mayraah na murmushi suka shiga parlon da Ammi, ta ajiye warmers din hannunta, bayan Karime sun gaisa da Ammi ta mike tace "Bari in yi ma Hajiyar magana tana daki" Ba a dau lokaci ba sai ga ta tare da Ummi, shigowa parlon Ummi tayi da fara'arta tana masu sannu da zuwa, Mayraah ta koma kusa da inda Ummi ta zauna ta gaisheta, Ummi ta amsa da fara'a tace "Kwana biyu ko leko mu kin ki yi Ilham, shine ranan Khalil ke ce min ai mamanki sun dawo Abujan ma gaba daya, ina jin ko kwana biyar ba ayi ba da ya gaya min haka" Mayraah na murmushi tace "Ai naje kano nayi sati biyu ne shi yasa Ummi" Ummi tace "Maa sha Allah, Maman taki ce wannan ko" Ammi dai murmushi kawai take, Mayraah ta gyada kai tace "Ita ce" Suka kara gaisawa da Ammi, Ammi ta mata godiyan rikon Mayraah da tayi, Ummi tace "Kai haba babu komai, ai yi ma kai ne" Mayraah tace "Inna na daki?" Ummi tace "Tana ciki, ku shiga ku gaisa" Mayraah tace "Nayi mata girki ne" Ummi tace "Ai ko kin kyauta wallahi, Allah maki albarka" Mayraah ta mike tana kallon Ammi tace "Ammi mu je ku gaisa da Inna" Mikewa Ammi tayi ta bi bayan Mayraah zuwa dakin inna, karime ta dau warmers din ta bi su a baya zata kai dakin, Sosai inna tayi farin cikin ganin Mayraah bayan sun gaisa da Ammi tace "Kai amma wannan er taki er albarka ce warce bata mance alkhairi, na dade ban ga yarinya me hankali kamar ta ba, ki ji fa har da girki ta min abun sha'awa, yaushe ma na samu haka a gidan nan, doya ce fa yanka hudu suka hadani da shi dazu kamar a fursin wallahi" Ammi dai murmushi kawai take tana kallon Inna, su da suka yi niyyar barin gidan da wuri sai da inna ta ja Ammi da zance, su ne har kusan karfe shidda a gidan, Ummi ma tuni ta shigo dakin Inna ta zauna suna hiran gaba daya, magana daya biyu sai innan ta Gwale Ummi, Ummi dai ko bin ta kanta bata yi, a haka dai Ammi ta samu suka lallaba suka bar gidan inna na cewa tana nan zuwa zata sa Khalil ya kai ta, bayan sun kama hanya Mayraah na kallon Ammi tace "Kamar Mama Ladi ko Ammi" Dariya Ammi tayi tace "Wannan ai ta so ta fi mama Ladi, gaskiya Ummin na hakuri da ita..." Mayraah tace "Ai kam Ummi ba ruwanta bata biyeta" Washegari ko da Mayraah taje aiki su Khalil basu dawo Lagos ba wai sai Tuesday, hankalinta kwance tayi aikinta a asibitin babu wanda ya takura ta, a ranta ta dinga fatan da ma kar su dawo da MD din nan, a rikesa a branch dinsu na can Lagos din ace an masa transfer. Da daddare Mayraah na shirin kwanciya kiran Maheer ya shigo wayarta, dauka tayi ta zauna gefen gado sannan ta daga, bayan sun gaisa, a hankali tace "Was it successful yaya?" Yace "Nop Mimi, wai sai nan da wata uku" Lokaci daya jikin Mayraah yayi sanyi, for kusan 4 days yake ta kokarin ganin ya samu transfer din zuwa Abuja, har Abba sai da yayi intervening a issue din, duk hope dinta yau idan ya kirata zai ce an maidosa Abuja, jin bata ce komai ba yayi kasa da murya yace "Kin yi shiru" a hankali tace "To me zan ce?" Yayi murmushi yace "Ki ce min congratulations" Ta buda ido tace "Wai anyi Transferring dinka?" Yace "Yes Mimi" Ba karamin farin ciki Mayraah tayi ba, har sallan dare sai da tayi a yan kwanakin nan duk don ya samu transfer din sai gashi kuma ya samu, yace "But Abba ne fa yasan yanda ya bi aka yi Transferring dina, it won't have been possible idan ba don shi ba" Mayraah tace "Maa sha Allah, congratulations yayana i am so happy with this news, yanzu yaushe zaka yi resuming aiki a nan?" Yace "Sai monday next week, but in sha Allah zuwa friday zan dawo Abujan" Tace "Toh Allah ya kai mu yayana" Tana son tambayarsa ko da Haseenahn za su taho amma dai tayi shiru bata yi tambayar ba, yace "Bari in kira Ammi in gaya mata, i told u first before her" Mayraah na murmushi tace "To yaya, bye" Maheer na kiran Ammi bayan ita ma tayi farin ciki tace "To yanzu ya za kayi da yarinyar nan?" Yace "Kawai ta tafi gidansu" Ammi tace "Aa babu wannan zancen Maheer, babu yanda muka iya haka zaka taho da ita nan, the chalet here is almost 2 times bigger than the one u are inside now, hakuri za kayi ku taho tare" Maheer yayi shiru don bai yi expecting Ammi zata ce haka ba, Cikin kwantar da murya tace "I understand you dear, amma kayi hakuri na ɗan lokaci ne, bazan taɓa goyon bayan ka ci gaba da zama da Haseenah ba yanzun ma kai ma kasan akwai dalili ne" Shi dai bai ce komai ba, don gaba daya mood dinsa har ya baci. Ranan Wednesday Mayraah na shiga asibiti da safe bayan ta dubo wata patient a wani ward tana dawowa reception sai ga Dr Khalil ya shigo, tana hango wanda suka shigo tare kawai tayi saurin juya masu baya pretending bata gansu ba, da haka ta nufi wani ward da sauri ta shige ciki kamar zata je dubo wani patient, duk MD na kallonta, nurse din wajen ta gaishesu da ladabi, har MD din ya fara tafiya toward step sai kuma ya dawo ya cire glasses dinsa yana kallon nurse din da kyau yace "Anyi cleaning office dina yau?" Nurse din ta mike da ladabi tace "Yes sir, ai kullum sai cleaner din ya yi cleaning office din sannan ya maida ma secretary spare key... He does that every day ko baka nan" Yace "Fine, i need my library shelf carefully dusted and cleaned to my satisfaction today, Da muka shigo ai kamar ba ke kadai bace a nan" Ta gyada kai da sauri tace "Eh ni da nurse Ilham ce, amma ta shiga ward 3 zata dubo patient" Yace "Good, look for her ki gaya mata abinda nace don ita zata yi aikin ba wani ba, or you just tell her to meet me in my office immediately" Nurse din tace "Okay sir" shi dai Dr Khalil na tsaye yana kallon MD da mamaki, Nurse din ta tafi da sauri inda Mayraah ta shiga don kai mata sakon MD, Dr Khalil ya bi bayan MD da ya nufi step yace "Dama nurse ta taɓa maka gyaran office Dr? We have more than enough cleaners in here" MD yace "Za a fara yau, kai baka ga duk ka sa yarinyar nan ta gama raina mu ba, wato tafi karfin ta tsaya ta gaishemu shine zata shige ward, to zata yi gyaran every nook and cranny na office dina yau kuwa, next time ma idan tayi repeating haka abinda zan yi mata kenan, silly girl" murmushi kawai Dr Khalil yake yana biye da shi a baya. Mayraah ta dinga kallon nurse din da ta kawo mata sakon MD tace "In same sa a office kuma? Allura fa zan ma patient din nan idan ta gama cin abinci" Nurse din tace "I will handle that, kawai ki tafi ya ce yana jiran ki" Mayraah ta fita daga ward din ta taɓe baki ta wuce sama, jiya da baya nan asibitin so conducive wallahi. Knocking din office din nasa tayi tana hade rai, har sai da ta kwankwasa sau uku sannan taji yace a shigo, ta bude kofar ta shiga, gaban table dinsa ta tafi ta tsaya bata bari ta kallesa ba tace "Good morning sir" Bai amsa gaisuwar ba ya nuna mata direction da shelf din Libraryn nasa yake yace "Take out all those textbooks and articles, dust and clean, finish with that first...." Mayraah ta dinga kallonsa taki cewa komai, ya daga kai ya kalleta yace "What are you still waiting for?" Juyawa tayi ta nufi shelf din da ya nuna mata fuskarta a daure, ya bi ta da ido, tana isa nan ta fara sauke textbooks din daya bayan daya tana ajiyesu kasa, sai da ta sauke many of the textbooks ta fara jin kamar dust a hancinta, still dai ta ci gaba da fiddo su, tana ajiye na hannunta taji tari ya taho mata, da sauri ta rufe hancinta da hannunta, kamar tayi triggering tarin sbda ƙuran dake hannun nata, ta durkusa nan kasa da sauri within few seconds she began gasping for breath, bai san sanda ya karasa inda take ba ya duka gabanta ya dago kanta da sauri yana kallonta yace "Are you Asthmatic?" Sai kuma ya janyeta daga wajen textbooks din ya zaunar da ita kan office chair dinsa trying to help her with first aid, amma numfashinta sai kokarin daukewa yake, lkci daya duk ya daburce a wajen kamar bai taɓa zama likita ba a rayuwarsa, gashi dai bayan pills da injections har inhaler akwai a show glass din magunguna dake office din but he was just lost ya kasa yi mata komai, dai dai nan Dr Balogun ya shigo office din, da sauri ya nufosu lkci daya kuma yake tambayar me ya sameta, yana fahimtar Asthma ne ya fara mata abinda ya kamata a wajen, cikin kankanin lokaci ya dauko pills a show glass ya bude ya dau bottle water dake kan table ya bata, with his help ta hadiyi pill din, they were there for almost 15 mins yana kokarin calming dinta har ta fara sauke numfashi a hankali, MD was just standing like a quack Dr a wajen with no help, Dr Balogun ya dinga mata sannu, bayan some minutes yace "Are you okay now?" Ta daga idanuwanta da suka kada, duk da azaban da kirjinta ke mata ta gyada masa kai, yace "Ok now duk ward din da kika ga babu kowa a nan sama kije ki kwanta, get some rest" Tayi karfin halin mikewa tsaye Dr Balogun ya bata hanya yana mata sannu, tana fara tafiya ta ji kanta na juya mata tayi baya zata fadi, kafin ta kai kasa MD yayi saurin riketa, Dr Balogun yace "Her Bp is low" kwantar da ita MD yayi kan examination bed dake office din nasa, Dr Balogun na kallonsa yace "Akwai coffee powder ayi making mata coffee ta sha?" MD ya dauko Tea cup dinsa yana wankewa sau daya ya kalli cikin cup din keenly, kafin yayi attempting sake komawa ya wanke Dr Balogun ya amshi cup din yace "I will do it..." Cikin mintuna kadan yayi making coffee a cup din ya mika masa yace "I have a patient in my office... I will be back idan na sallamesa yanzu" MD ya amshi Coffee din ya juya yana kallon Mayraah da idonta ke a rufe, Dr Balogun ya fita daga office din da sauri don dama tambaya ya shigo yayi masa.... [8/8, 8:54 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na sauka second floor ta hadu da Dr Khalil ya fito office dinsa da wasu files, yana ganinta ya nufo ta da sauri yace "How are you feeling now?" Ta gyada masa kai a hankali tace "Alhamdulillah, i am better now" yace "Ina za ki je?" Tace "Driver yana jirana a waje" Yace "Did he ask you to go home?" Ta gyada masa kai, yace "Alright, Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen, Nagode" Downstairs suka sauka a tare, ta tafi ta dauka handbag dinta tayi ma Nurse Hafsat sallama sannan ta bar asibitin, tana isa gida Ammi dake parlonta suna waya da Aunty Mariya ta kalli agogo sannan tayi ma Aunty Mariya sallama ta mike tana kallonta da mamaki tace "Naga kin dawo da wuri" Mayraah ta kalli agogo dake nuna karfe biyu tace "Bana jin dadi ne" Ammi ta nufeta da sauri tana taɓa jikinta tace "Subhanallah, me ya sameki? Since when?" Mayraah tace "I had an attack daxu da safe" Ammi ta zaunar da ita kan kujera da damuwa tace "Garin yaya?" Mayraah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ina jin wajen kamar akwai ƙura ne, ni kuma ban sani ba, amma ai naji sauki yanzu, an bani magani na sha after sometime na dawo normal shi ne har nayi bacci" Ammi tace "Toh Allah ya sauwake, but duk in kika ga wajen da zai iya accommodating dust ki dinga saka nose mask Mimi, ki daina fita babu shi kin ji?" Mayraah tace "In sha Allah Ammi" Ammi tace "Bari in kawo maki abinci, kin yi sallah?" Ta gyada kai tace "Nayi" Ammi ta mike ta fita daga parlon zata je kawo mata abinci, Mayraah ta jinginar da kanta da kujera, bayan wani lokaci wayar Ammi ya fara ring, Mayraah ta mike tana kallon wayar ganin wanda ke kiranta ta karasa inda wayar yake ta dauka sannan tayi picking ta kai kunne, sallama yayi ta amsa, a hankali tace "Good afternoon" Daga daya bangaren yace "Are you okay?" Murmushi tayi tace "Me yasa ka tambaya?" Yace "I sense that from ur voice, baki da lafiya ne?" Tace "Asthma dina ne ya tashi a asibiti" Yace "Subhanallah, how did that happen?" Tace "I am very fine now, naji sauki sosai, yaya hope dai ka gama shiryawa? Kasan friday din ya kusa fa" Yace "Sure, Allah ya kai mu lafiya" Tace "Ameen" Yace "Kin sha magani amma?" Tace "Eh an ban a asibiti" Yace "Toh Allah ya sauke, be careful plss Mimi always go around with ur nose mask to avoid such issues" Tace "To yaya" Yace "Ammi fa?" Tace "Taje kitchen" Yace "Ohk, i will call her back later, go and get some rest Mimi" a hankali tace "Bye" Washegari Wednesday Dr Khalil na office dinsa bayan fitar wata patient MD ya shigo, Dr Khalil ya daga kai yana kallonsa har ya karaso ya zauna yace "I just finish speaking with Ceo, tana son zata yi magana da yarinyar nan, kaga daga common Asthmatic attack jiya shine tayi taking advantage taki zuwa aikin yau, who does that pls, idan nayi magana kace i am not being considerate..." Dr Khalil yace "Sai kace mata bata da lafiya mana..." MD yace "To dama idan ba haka ba me kake son in ce mata, imagine ceo fa, yarinyar da common workshop a lagos bata kai a fara zuwa da ita ba shine take tambayar ko tana da international passport, for what? ni ban ma san yanda zan mata bayani cewar ba a bisa ka'ida aka dauketa aiki a asibitin nan ba, idan ba ayi hankali ba fa sai ceo tace da ita za aje conference din nan" Dr Khalil yace "Nan din ba bakin ciki zaka mata sir? Tun da kaga haka ceo din is gradually becoming fond of her, jininta ya hadu da ita ne, kai ne har yanzu ka ki kwantar da hankali ka lura how lovely the pretty girl is ba" MD yace "And how will dat add any impact to my life? That is not my problem Khalil, yanzu cewa tayi a kira ta a tambayeta ko tana da international passport, and i should feed her back immediately" Kallonsa kawai Dr Khalil yake, MD yace "So now after some minutes i will call and tell her tace bata da international passport..." Dr Khalil ya jawo wayarsa yayi dialing number yana fara ring ya sa a handsfree, ba a dau lokaci ba aka daga, murya can kasa tayi sallama, her voice was so cool and calm, MD ya masa wani kallo ya mike amma sai bai fita ba, Dr Khalil ya amsa gaisuwar da tayi masa yace "Ya jikin?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Me yasa baki zo aikin yau ba" Ta ɗan yi shiru, sai kuma a hankali tace "I am still recovering, kuma ni bana son a dinga min masifa anyhow" Dariya ta ba Dr Khalil, MD ko ya gyada kai bayan ya ji me tace, Dr Khalil yace "To wa ke maki masifa Mayraah?" Tace "MDn ku mana, he is always finding fault where there is none, ko gajiya baya yi da fada, energy da yake sakawa a fada da ma a field dinsa yake sakawa da ya fi, kuma gwara ni ranan allura ne kawai na ɗan zama confuse da zan ma yarinya, shi kuwa a whole asthmatic patient a gabansa babu abinda ya iya yi, just going up and down like a student, i nearly thought him to be quack wallahi, ko ni da nake nurse bazan yi haka ba...." Dr Khalil ya cire wayar a handsfree da sauri laughing out loud, kallon wayar MD ya dinga yi babu ko kiftawa, yana ganin Dr Khalil ya cire a handsfree ya fizge ya mayar handsfree din, Mayraah tace "It's not funny fa, na dade ina mamaki da na dawo gida jiya, ko level 4 student a medicine bazai yi abinda yayi ba" Dr Khalil yace "To ai shikenan, a takaice dai kin fi sa sanin aikin likitanci kike nufi kenan?" Without thinking twice tace "Na fi sa composure a aikin, may be because i don't shout and Nag" Dr Khalil na dariya yace "To sai anjima, zan kira ki" Tace "Ohk" MD ya dinga kallon wayar hannunsa, ita kuwa ganin Dr Khalil bai katse ba sai ta katse kiran, MD ya ajiye masa wayar kan Table a takaice yace "Call her back tayi providing International passport dinta gobe" Dr Khalil yace "Aa kai da kace...." MD ya katse sa yace "Instruction din da Ceo ta bani kenan, don haka kayi abinda nace maka" Yana kai wa nan ya fita daga office din, dariya kawai khalil yake don har cikin ransa yaji dadin maganganun da Mayraah tayi a kan kunnensa, shi kansa jiya da Dr Balogun ke basa labari yayi mamaki, MD da ko shure shuren mutuwa mutum yake calmly yake masa abinda ya kamata as a medical Dr amma just common Asthmatic attack da ya sameta jiya ya kasa taɓuka komai ya dawo kamar learner, to in ba rami me ya kawo rami, daukar wayar yayi ya sake kiran Mayraah bayan ta daga yace "Kina da international passport?" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Eh" Yace "In za ki shigo gobe sai ki taho da shi" Da mamaki tace "Why?" Yace "Ceo ce ta ce a sanar maki haka" Mayraah was a bit confused, ta ma rasa tunanin da zata yi, to me za ayi da passport din nata, sallama Dr Khalil yayi ya katse wayar. Washegari da taje asibiti har rana MD bai shigo ba, tun da safe ta kai ma Dr Khalil passport din nata, wajen karfe biyu suka shiga theatre za su yi wani aiki da Dr Balogun da Dr Khalil, tana kokarin saka nose mask before putting on her sterilized hand gloves kamar ance ta juya suka yi ido hudu da MD, dauke kai tayi don bata ma san ya shigo ba and she felt unhappy after realizing tare da shi za ayi aikin, yawanci aikinta a Operation theatre bai wuce ta dinga mika Sterilized Instruments ba sai kuma suture, MD zata dinga mika ma Instruments din kamar wancan ranan, tana mika masa abinda ya bukata na farko suka hada ido sai kawai ya fadi daga hannunsa, wata nurse ta dauko wani Sterilized Instrument din da sauri ta kawo masa, sau hudu suna haka da shi, it is either idan zai maido mata sai ya fadi a hannunsa, ko kuma idan ta mika masa zai amsa sai a samu matsala, ita dai she is calm, Dr Khalil ya dawo inda Mayraah take yayi kasa da murya yace "May be u are tired, just go, nurse Sadeeya will continue...." Ta dan kallesa a ranta tace ko dai MD dinku is tired, duk fa sun ga shi ke contaminating Instruments din not her, daga hannunsa suke faduwa ba nata ba, juyawa tayi ta bar wajen, karfe shidda saura driver dinta ya zo ya mayar da ita gida. Ranan friday da yamma Maheer ya iso daga kano via flight, Mayraah was so happy seeing him don ita da driver ne ma suka je airport tarbo su, yana gama gaisawa da Ammi ta kai sa wani daki dake parlor da damuwa tace "Yaya naga ka rame, what's happening?" Yace "Aiki mana, kema nan da kwana kadan zaki ga kin rame ba dai kin fara aikin ba" Mayraah bata yarda ba, ta dinga insisting ya gaya mata what the problem is, Haseenah dai tafi minti ashirin zaune ita kadai a parlorn, Ammi da ke kitchen tana karasa girkin da take ta fito Parlon ganinta ita kadai ta nufi dakin da Mayraah ta kai Maheer, Ammi kanta wasn't happy with how she saw Maheer, tana kallonsu tace "Ka tashi ga chalet din can a bude yake, kun bar ta ita kadai parlor, ya kamata taje ta huta ita ma, Mimi zata kai maku abincin yanzu" Shi gaba daya ya ma mance da wata Haseenah, bayan some minutes ya mike ya fita a dakin. Bayan minti sha biyar Mayraah ta kai masu abincin Chalet, Yana bedroom Haseenah kuma na zaune parlon ta bi ta da ido har ta ajiye abincin sannan ta fita... Ammi na zaune parlonta da Maheer sai Usman dake danna wayarsa, da damuwa tace "Gaskiya ni dai hankalina bai kwanta ba kwata kwata, yaushe ma ta fara aikin ta samu full experience har matar zata ce xa aje conference da ita England? Ina manyan likitoci da Nurses din asibitin, aa gaskiya bazata ba" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Kai ya ka gani Barrister?" Sai a sannan Usman ya daga kai ya kallesu yace "It's weird gaskiya, daga fara aiki ko sati biyu bata yi ba a kawo maganar fita waje, irin wannan tafiyar ai da experienced staffs ake zuwa" Maheer yace "Haka ne, nima kuma nayi mamaki" Ammi da hankalinta ya tashi tace "Ni gaskiya aikin ma sai a bari, kuma fa matar ba musulma bace, gwara a samar mata a wani waje kawai ta hakura da wannan" Murmushi kawai Maheer yayi, Ammi tace "Abbanku da na dawowa yau zan gaya masa, aikin ya fita kai na gaba daya wallahi" Mikewa Usman yayi ya fita daga parlon, Ammi ma ta mike tace "Kasan zan yi bakuwa bari in je in ga ko me aikin ta gama abinda na sa ta" Yace "Ohk" Ammi na fita parlon Maheer ya mike ya tafi dakin Mayraah. Kusan karfe uku Hajiya Maimuna mahaifiyar Haseenah ta iso gidan, tun da ta shigo hankalin Haseenah ya ki kwanciya, kawai dai tana zaune parlorn ne tana yaken karfin hali, Ammi ta tarbeta sosai suka gaisa da fara'a, Mayraah ta kawo mata abincin da aka mata, Hajiya Maimuna tace "Kawai na ce ko a gurguje ne in zo in ga gida kafin in koma kano, gida kam Alhamdulillah yayi kyau Allah ya sanya alkhairi, Allah ya sa rai aka yi ma" Ammi tace "Ni da na zata kwana za ki yi Hajiya?" Hajiya Maimuna tace "Ai daga gidan nan airport zan tafi, biki muka shigo tun ran juma'a wallahi, to nayi niyyar zuwa jiya asabar sai Allah bai yi ba sai yanzu" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh amma ai za ki ci abinci Hajiya" Hajiya Maimuna tace "Wallahi na ci abinci kafin in fito, Alhamdulillah" Ammi tace "Da kika kirani dazu da safe har nake tunanin in kin zo akwai maganganun da za mu yi Hajiya" Sosai gaban Haseenah yayi mugun faduwa jin abinda Ammi tace, Mayraah dai na zaune parlon ita ma, Hajiya Maimuna tace "Flight din na dare ne Hajiya, ko yanzu za mu iya maganar, Allah dai ya sa lafiya" Ammi ta ɗan yi murmushi, sai kuma tace "To gaskiya ba lafiya ba Hajiya" Hajiya Maimuna tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ina ji Hajiya" Haseenah ta mike zata bar parlon, Ammi tace "Aa ki dawo ki zauna Haseenah" Sunkuyar da kai tayi ta koma ta zauna, Nan Ammi ta fara yi ma Hajiya Maimuna bayanin duk abinda ke faruwa bata boye mata komai ba, Daga karshe Ammi tace "Nasan kin san wasu maganganun nan wasu kuma ba lallai ki sani ba... To kin ji abinda ake ciki Hajiya" Hajiya Maimuna da ta kasa dago kanta sai zufa take bayan few seconds, tace "Amma baki kyauta min ba Hajiya, wallahi baki kyauta min ba, yanzu duk abubuwan nan su faru babu wanda ya sanar min, na kwanaki ma da tayi dambe da kawarta Badiyyah banda ta kira kannena suka je suka yi rashin mutuncin da suka yi babu yawuna wallahi ban sani ba Hajiya, ban san komai ba, yanzu ni Haseenah zata tona ma asiri ta kunyata ni a idon duniya duk zatona tana zaune lafiya gidan mijinta?" Sai kuma ta fashe da kuka ta mike tace "To wallahi Allah ya isa tsakanina dake Haseenah, kin cuceni don sai ace tarbiyar da na maki kenan, bayan Allah na gani nayi iya bakin kokarina ganin na maki tarbiyyar da ya kamata dai dai gwargwado" a fusace ta rufeta da mari ta ko ina tana zaginta, Ammi ta rikota da sauri tace "Aa Hajiya ba sai kin doketa ba, don Allah kiyi hakuri...." Hajiya Maimuna na huci tace "Wallahi dama in ta kashe auren ta nemi gidan wata uwar ba ni ba, kar ta kuskura ta nufo inda nake, da dadi ba dadi haka nayi hakuri a gidan ubanta har mutuwa ta rabamu ban taɓa yaji ba wallahi komin tsanani kuwa, shi kuma Maheer saboda me zai zauna yana hadiye wannan takaicin ya kasa sama ma kansa mafita ya kara aure tunda Allah ya rufa masa asiri, Kishiya kawai zai mata ya tattara ya koma wajen amaryar, kai ni ko yanzu ya saki Haseenah bazan ce masa don me ba don naga kokarinsa ya kuma nuna shi cikakken namiji ne, ina kuma me bashi shawara ya kara aure cikin gaggawa don huce wannan takaicin" Ammi tace "Yanzun ka akan maganar auren ake, don bazan boye maki ba aure xai kara nan ba da jimawa" Hajiya Amina tace "Toh maa sha Allah, Allah Ubangiji ya masa albarka wallahi" Kuka kawai Haseenah take kamar ranta zai fita bayan ta gudu bayan kujera, Hajiya Maimuna ta dau jakarta tana kallon Ammi tace "Duk hukuncin da ku ka ga ya dace ku yanke a kanta ni babu abinda ya sha min kai, ko me ku ka yi dai dai ne wallahi, kuma nayi da na sanin haihuwar Haseenah" Kofa ta nufa tana huci, Ammi ta bi bayanta tana kokarin dakatar da ita Hajiya Maimuna tace Airport zata kawai, a haka ta bar gidan ko minti daya bata kara ba, babu abinda ya tsaya ma Haseenah a rai take kukan da take sai auren da Mumynta tace Maheer ya kara har Ammi na cewa nan ba da dadewa ba zai yi auren, wato nan ba da dadewa ba zai auri Mayraah don karshenta kenan, kuma tayi mafarkin aurensa da Mayraah yafi a kirga a yan kwanakin nan, goge hawayenta tayi ta fita daga Parlon ta ɗan yi murmushi ta nufi chalet. Da daddare Maheer na parlon Ammi bayan ya gama sauraronta yace "Amma dai don Allah Ammi me yasa za ki ma mahaifiyarta wannan maganar, sulhu ma nake nema da ita kenan? Ni fa Ammi na gama zama da Haseenah wllh tllh, duk wannan maganganun da kika yi ma mahaifiyarta ba shi da amfani don ni dai bazan zauna da ita ba" Ammi tace "Aa gwara dai da na gaya mata Maheer, kaga ko da sakin Haseenah kayi we owe them no explanation afterward, nima ai ban ce za ka ci gaba da zama da Haseenah ba kawai hakkin uwar na fita na gaya mata abinda ke faruwa, saboda kar su mana kallon kananun mutane in suka ji ka saki er su" [8/9, 9:00 PM] Khaleesat Haiydar💖: Abba dake zaune parlon Ammi ya ajiye drink din hannunsa yana kallonta yace "Saboda ance za aje kasar waje da ita sai kice ta ajiye aiki Madam? Ai kamar this is a privilege for her, i see nothing wrong don asibiti ya zabe ta cikin wa enda za su je England conference...." A hankali Ammi tace "Gaskiya ni dai hankalina bai kwanta ba, of all the staffs in the hospital why her? Yaushe ta fara aikin har za a zabeta?" Abba ya kalli Maheer dake parlon yana kallonsu yace "Can you hear ur mother?" Murmushi yayi yace "Kuma conference din nasan bazai wuce kwana biyu zuwa uku ba fa Ammi" Ammi tace "Ko ma kwana daya ne ni dai kawai hankalina bai kwanta ba" Abba yace "Toh tunda haka ne sai Usman ya bi su England din, hope yanzu hankalinki ya kwanta?" Maheer ya juya yana kallon Abba, Ammi ma dai tayi shiru tana kallonsa, mikewa Abba yayi yace "Let me get some rest" Daga haka ya fita daga Parlon zuwa part dinsa, Ammi na kallon Maheer tace "Is there anyway da za a sanar ma asibitin a cire sunanta daga masu tafiyar pls? Wani Usman ne zai bi ta kanta in ma yaje England din, harkan gabansa kawai zai yi ya juyo ranan da yaji ance za su dawo" Maheer yace "Kawai ki bari ta je Ammi, kamar yanda Abba ya fada it's a privilege, don ba kowa ne zai samu hakan ba, may be ita me asibitin ta yaba da nutsuwarta ne sannan taga yanda take aiki, ko kin manta daughter din taki da first class ta fita? Did you know what that means? Kar ki ji komai ana samun haka sosai, beside ba da ita kadai bane ai za aje dole da akwai staffs da aka zaɓa, it's something we should be happy about" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh shikenan tunda ka ce haka" Mayraah na dakinta da daddare bayan tayi shirin bacci Ammi ta shigo da sallama, zaunawa Ammi tayi gefen gadon tana kallonta tace "Ya ciwon kan?" Mayraah tace "Yayi sauki tun dazu Ammi" Sai kuma ta marairaice tace "Stress din aikin nan ne fa Ammi, kullum da sassafe mutum zai fita bazai dawo ba sai 6:30, and every day the hospital is always busy with patients, ko lokacin hutu fa mutum bashi da" Ammi tace "A haka nan zaki saba daughter" Mayraah ta girgiza kai tace "Gashi kusan 5 weeks har yanzu ban saba ba, meaning bazan iya sabawa ba" Ammi tayi murmushi don kusan kullum sai tayi complain din zuwa aikin nan, Ammi tace "Toh yanxu yaushe ne tafiyar ta ku? You said ur Visa is ready" Mayraah tace "Nima ban sani ba, but naji kamar Dr Khalil yace next week" Ammi tace "To Allah ya kai mu, abincin da kika girka ma yayan naki ya kare ne?" Mayraah tace "Za ki ci ne Ammi?" Ammi tace "In zan samu ba" Murmushi Mayraah tayi tace "Akwai sauran kadan, bari in debo maki" Sauka tayi daga kan gadon ta fita daga dakin Ammi ta bi ta da ido, magana take son mata amma ta rasa ta inda zata fara, can ta sauke ajiyar zuciya still thinking of where to start from, Mayraah na sauka kasa taga Maheer parlon yana kallo, tun da ya dawo Abuja daga kano yau kusan 4 weeks kenan bacci ne kawai ke kai sa chalet shi ma wajen karfe dayan dare wani lokacin, yana dawowa aiki main building yake nufowa, komai a dakinsa da ke nan main building din yake yi, duk aka yi girki mai aikin Ammi ke kai ma Haseenah Chalet, wani lkcn ta kan shigo babba parlon gidan wataran ma kwata kwata bata shigowa tana can chalet ita kadai, Mayraah na kallonsa tace "Yaya ka sha shayin?" Yace "Na sha" Kitchen ta nufa ta zubo ma Ammi sauran abincin da ta dafa ma Maheer dazu sannan ta dawo parlon, yace "Yaushe kika fara cin abinci haka Mimi?" Dariya tayi tace "Ammi fa zan kai ma" Yace "Better" Murmushi tayi ta koma sama ta kai ma Ammi abincin, Ammi na amsa kawai ta mike don ta rasa ta inda zata fara mata maganar da ya kawo ta dakin, ta sa a rai zata bari in sun dawo daga England kawai. Yau tun da Mayraah ta tashi take dakinta a kwance bata fito ba, breakfast ma har Bedroom Ammi ta sa me aiki ta kai mata, it was a Friday kuma yau ne ranan tafiyar tasu zuwa Uk amma evening Flight, jin ana knocking kofarta ta kalli agogo dake nuna karfe uku na rana ta sauka daga kan gadon ta bude kofar, Maheer ne tsaye bakin kofar yana sanye da farin Gezna, daga sama har kasa take kallonsa, sai kuma tayi murmushi ta jingina da kofar a hankali tace "Good afternoon" Yace "Afternoon Mimi" Ta langwabar da kai tace "Kayi kyau kamar wani sabon ango, nasan yau mata suna ta kallon ka a hanya ko" Ya ɗan buda ido yace "Ango kuma" Tana murmushi tace "I am serious u look gorgeous" Bai kulata ba yace "Duk efizyn zaki je England ne yau ya sa kika ki fitowa parlor mu ganki?" Tayi dariya tace "Yaya wallahi kamar a fasa tafiyar da ni, i wish kawai za ace banda ni, i am so tense" Yace "Why?" kamar zata yi kuka tace "Kawai haka nan, i don't understand why i am tense" Ya sauke idonsa kasa yace "Sauko mu yi Lunch" a hankali tace "Ohk" Daga haka ya juya ya sauka kasa, ita kuma ta juya ta koma dakin zata dauko hular ta, suna zaune parlon su biyu kadai, eating from the same plate Haseenah ta shigo parlon, kamar hadin baki suka mata kallo daya suka dauke kai a tare, kitchen ta nufa ta je ajiye warmer din da za a sa mata abincin dare, tana fitowa bata ko kallesu ba ta fita daga parlon, Mayraah na gama cin abincin ta dinga ma Maheer hira a parlon tana basa labarin irin cases da take gani a asibiti, wanda kawai sauraronta yake a ransa kuma yana tunanin may be ta mance shi ma likita ne, a haka Ammi ta sauka downstairs ta samesu, ta kalli agogo tace "Ke ba karfe biyar bane Flight dinku kike nan zaune?" Sai da gaban Mayraah ya fadi don ita ko son a tuna mata da tafiyar nan bata yi, Maheer yace "Mimi that's true ki je ki shirya da wuri, gwara ki jirasu da ace sun jiraki" A hankali ta mike ta wuce sama, bandaki ta shiga tayi wanka ta dauro alwala ta fito, bayan ta idar da sallahn asr Ammi ta shigo dakin, tana kallonta tace "Kin sa kayan naki cikin akwati ne?" Girgiza kai tayi, Ammi tace "Ke dai komai kin fi son sai kinyi cikin kurarren lokaci, ance maki flight karfe biyar ya kamata ace kuna airport ma yanzu" Usman ne yayi knocking kofar dakin sannan ya bude, yana kallon Mayraah yace "Ina kika ajiye wayarki ake ta kiranki?" Ta ɗan buda ido da sauri ta nufi karkashin pillow da ta ajiye wayar dazu, miss calls din Dr Khalil ta gani har uku, ta kalli Usman dake mata wani kallo, Ammi ta fiddo mata wani abaya ta ajiye gefen gado tace "Gashi nan ki saka" Usman yace "Kin bar su tun dazu a waje suna jiranki" Daga haka ya juya ya bar bakin kofar, Ammi ta bude baki tana kallon Mayraah da ta kasa tabuka komai, da kanta ta fara hada mata few clothes dinta da duk wani abu da zata bukata a akwati, bayan barin Usman wajen sai ga Maheer, a bakin kofa shi ma ya tsaya yace "Mimi they are waiting for u outside kiyi sauri...." Kayanta ta dauka ta fara sa wa, Ammi ta gama hada mata komanta a akwati, Maheer na kallon Ammi yace "Akwai sanyi sosai Uk, she shouldn't forget her jacket" Ammi ta kalli Mayraah tace "Rigunan sanyinki suna dakina kije ki dubo da sauri" Mayraah na fita daga dakin Maheer ya bi bayanta yace "Do not forget ur sanitary stuffs, hopefully har ki dawo kila...." Mayraah ta buda ido don har ta manta, sai bayan kusan minti goma Maheer ya sauka downstairs da akwatinta tana biye da shi a baya, Ammi ta rakasu har compound tana mata Allah ya tsare hanya, kana ganin Ammi kasan babu yanda ta iya ne da tafiyar Mayraah, suna fita kofar gida Mayraah ta ga mota anyi parking, Dr Khalil ya bude masu booth Maheer ya ajiye akwatin, tana kallon Maheer tace "Yaya gobe Ya Usman din zai je can?" Maheer ya gyada mata kai yace "In sha Allah" A hankali ta bude back seat ta shiga don ko ba a gaya mata ba taga alamar da mutum a front seat din, Dr Khalil suka yi sallama da Maheer sannan ya koma cikin motar, Mayraah ta daga ma yayan nata hannu kamar zata yi kuka, Dr Khalil yayi reverse suka bar anguwan. Tana daga kai suka hada ido da MD ta madubi, sauke idonta tayi murya can kasa tace "Good evening" ya ji ko bai ji ba oho, don bata ji ya amsa mata ba, Dr Khalil yace "Ina kika ajiye wayarki, kin kuma san karfe nawa ne flight din naku" Tace "Shiryawa nake ne" Dr Khalil ya girgiza kai yace "Ku dai mata komai sai kun saka African time a ciki...." Mayraah dai ta ci gaba da danna wayarta bata ce masa komai ba, MD na kallon Khalil yace "Plss ka bi route din da za mu yi sauri, it's easy to miss a flight...." Dr Khalil yace "In sha Allah baza ayi missing Flight din ba we will get there in time" Suna isa airport MD ya sauka, Dr Khalil ma ya sauka daga motar ya fiddo hand luggage din MD wanda jacket dinsa ne kadai a ciki sai textbooks, sannan ya ciro akwatin Mayraah ma, tuni MD ya shiga airport din don baya son ace sun yi missing jirgin, Mayraah dai sai zare ido take tana neman sauran da za su je Uk din tare, Kasa hakuri tayi bayan sun nufi cikin airport tare da Dr Khalil tace "To ina sauran sir?" Yace "Doctors biyu ne kuma suna lagos, daga can za su tafi" Mayraah ta zaro ido tace "Babu nurse ko daya??" Yace "Babu" Mayraah ta marairaice tana kallonsa, dariya ta basa amma ya dake yace "It's fine Mayraah" Ta girgiza kai kamar xata yi kuka tace "Yanzu ni da shi kadai za mu hau jirgin?" Dr Khalil yace "Eh mana, in kun je can za ku hadu da sauran" Ji tayi hankalinta ya tashi tace "Ni dai wallahi i don't want to go with him" Dr Khalil yayi dariya yace "But he is not a monster Mayraah, look kin ga kun yi latti let's be fast pls" Bin sa kawai take a baya with different thought a zuciyarta, duk traveling document dinta suna wajen MD din, bata kara shiga tashin hankali ba sai da taga sun gama check in, Dr Khalil na masu sallama bayan za su shiga departure lounge, dauke kanta tayi don yanzun nan sai ta iya fashewa da kuka. Sun shiga departure lounge din immediately aka fara boarding plane din nasu, ita dai bin sa kawai take gashi ya ki juyowa ma ya ga ko tana biye da shi a baya ko akasin haka, a haka har suka shiga plane din, yana isa seat dinsa ya ajiye hand luggage dinsa a sama sannan ya zauna, tana ganin haka kawai tayi assuming seat din ta ne gefen nasa, ita ma ta zauna tana satan kallonsa. 2 hours into the flight ta fara jin bacci amma tayi ta kokarin ganin bata yi ba, abincin da aka yi serving dinsu ma bata taɓa komai ba, a haka har baccin ya dauketa bata sani ba, she can't tell for how long tayi baccin kawai ita dai kamshin turaren da ya cikata ne ya farkar da ita daga baccin bayan tayi isasshe, zaro ido tayi ganin inda tayi resting kanta, sai kuma ta daga kai da sauri ta kallesa, idonsa na kan wani littafi dake hannunsa, matsawa tayi tana gyara zamanta kamar munafuka, shi dai ko kallonta bai yi ba yana karatun book din hannunsa, ko gyangyadi Mayraah bata sake barin tayi ba har suka sauka UK, bayan ya cire seat belt dinsa ya mike ya dau hand luggage dinsa, ita dai kallonsa kawai take, ya bude karamar jakar tasa ya ciro jacket dinsa ya saka, tana ganin ya fara tafiya ta wani bi sa da harara sai kuma ta mike ko ruwa bata dauka a abincin da aka ajiye mata ba ta bi bayansa, suna sauka jirgin Mayraah taji ta kamar a freezer, nan da nan hankalinta ya tashi, ko wani mutum ta gani a wajen da thick Jacket dinsa, wani mugun sanyi ta dinga ji amma a haka ta dinga bin sa a baya, ko kadan bata shiri da sanyi, yanzu nan sai yayi distablizing dinta nan da nan kuma zata fara mura da tari, har suka shiga airport din tana jiran akwatinta MD yaki kallon inda take don waje ma ya nema ya zauna yake danna wayarsa, after many minutes of waiting akwatinta ya iso ta dauka ta kalli inda yake, kawai gani tayi ya mike ya fara tafiya, ta bi bayansa tana tafiya a hankali har suka fito daga wajen, she was just shivering daga inda take tsaye rike da akwatinta, shi kuma yana tsaye ɗan nesa da ita yana kiran Ceo don yaji hotel din da ta kama ma staffs din nata, tana dagawa tace zata kirasa sannan ta katse wayar, yasan yanzu sai su kai minti goma suna jiranta a haka, ya ɗan juya ya kalli direction din da Mayraah take ta wani takure saboda mugun sanyi, kasa ci gaba da jure sanyin tayi ga shi hankalinta bai je ta bude akwatinta ta ciro rigar sanyinta ba, she was shivering seriously, juyawa tayi da sauri jin mutum a kusa da ita ta kusa cin karo da shi, not minding that ya daura mata jacket dinsa a shoulders dinta sannan ya koma inda yake tsaye, ta kasa dago kanta, after few seconds ta daga kai a hankali ta kallesa, wrapping din jacket din tayi jikinta ba tare da ta saka ba, bayan kusan minti biyar Ceo ta kirasa tace kawai ya taho da ita gidanta, he was so surprise, don banda shi a duk staffs dinta infact har colleagues dinta na nan UK babu wanda yasan gidanta sai shi kadai, sai da ya sake tambayarta to be sure of what she said, ta kuma maimaita masa abinda tace, a hankali yace "Ok Ma'am" Daga haka ya katse wayar ya samu Cab din da zai kai su gidan nata, it's almost 11pm na dare, Mayraah na ganin Cab din ta ja akwatinta duk da jacket din da ya sa mata bata daina jin sanyin ba don ya riga ya fara shigarta sanyin, ya dau akwatin ya sa a booth sannan ya bude back seat ya shiga, ita ma ta shiga, har suka isa gidan Ceo Mayraah was shivering a gefensa, wannan dalilin yasa shi daukan akwatinta daga booth din motar tana biye da shi, Ceo na bude kofar mansion dinta ta kallesa da mamaki tace "Why are you not on Jacket Aliyu?" Sai kuma taga Mayraah, bude kofar tayi da sauri tace "Come in my dear" Mayraah ta shiga parlon that was soo warm and smelling nice, shi ma ya shiga parlon with her box da hand luggage dinsa, Ganin yanda take rawan sanyi Ceo kawai ta wuce wani daki dake parlon da ita giving her a huge duvet to cover her self, sannan ta dawo parlor tana kallon MD tace "Go make ur self a cup of coffee Aliyu" Yace "Ma'am Idan naje gida zan sha...." Tace "Ohk then, akwatinta ne wannan?" Yace "Yes Ma'am nata ne" daukan akwatin tayi ta kai dakin da ta kai Mayraah, ya jira har ta fito sannan yayi mata sallama, tace "Let me get u my car key, gobe da safe sai ka dawo da shi" Ya sunkuyar da kansa yace "Ok Ma'am" Makullin motarta ta dauko masa hade da sabon jacket, ya amsa jacket din da makullin sannan ya saka jacket din yayi mata godiya ya bar gidan ya nufi garage dinta, kitchen ta tafi zata hado ma Mayraah hot chocolate, Mayraah dai ta takure cikin farin duvet din da ta bata ga kamshin turaren jacket dinsa da ya cikata. [8/12, 3:41 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah ta daga kai a hankali jin an bude kofar dakin, Ceo ta karaso da cup din hot chocolate ta zauna gefenta tace "Here dear" Mikewa zaune tayi ta amshi cup din hade da sauce dinsa tace "Thank you Ma" Murmushi ta mata tana kallonta calmly tace "You are welcome" Mayraah ta fara shan chocolate din a hankali, Ceo ta mike ta fita, ba a dau lokaci ba ta dawo dakin da few pizza slices a plate ta ajiye mata tace "Will you be okay with this?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Thank you Ma" daga haka ta dau slice daya ta fara ci, after some minutes ceo ta mike ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita ta jawo mata kofar ta rufe, Mayraah ta sauke idonta tana ci gaba da cin pizza din, bayan ta gama ta dau handbag dinta ta ciro wayarta dake ciki, cikin minti kadan tayi activating international roaming sannan ta fara dialing number Maheer, yana fara ring ya daga, a hankali tace "Yaya" Yace "Mimi" Tace "Ka fara bacci ne?" Yace "No Mimi, was waiting for ur call, i couldn't reach you... ya hanya?" Kamar zata yi kuka tace yaya it's soo cold here, i am so cold" Murmushi yayi yace "Yeah i know, akwai sanyi sosai, hope you are on ur jacket?" Kallon jacket din MD dake jikinta tayi, ta kara lullube jikinta da shi murya can kasa tace "Yeah" Yace "kina ina yanzu?" Ta kalli babban dakin tace "Gidan Ceo din mu" Da mamaki Maheer yace "Ceo dinku kuma? Why? Where are ur colleagues?" Mayraah tace "Ni kadai ce dai a nan, su ba a nan suka sauka ba, may be they lodge in hotel, kasan duk maza ne" Maheer ya ɗan yi shiru, can kuma yace "But that's weird, why will she keep u in her home? Any way it's fine..." Mayraah tayi shiru, yace "Hope you are comfortable?" Mayraah ta gyada masa kai a hankali tace "Yeah" Yace "To abinci fa?" Tace "Ta bani har na ci" Da damuwa Maheer yace "Gashi har muryarki ya fara nuna alamar sanyi ya kamaki" Tayi murmushi tace "Yaya kasan fa bana son sanyi" Yace "I know Mimi, shi yasa nake tausayinki" Tace "But ta ban heavy duvet" Yace "To better" Tace "Yanzu Yaya tambayar ta inda zan kalla inyi sallah zan je in yi?" Maheer yace "But she is a Christian how will she know? Ke baza ki gane qibla ba?" a hankali tace "Bazan gane ba, i am confuse" Yace "Ohk try asking her... Meye ta baki kika ci?" Mayraah tace "Ta bani hot chocolate da pizza" Yace "Ohk to ki samu kiyi sallan, idan kin idar sai ki kirani" Tace "Toh" Daga haka ta katse wayar, tana sauka daga saman gadon duk da dumin dakin she was still feeling cold, a hankali ta saka hannunta a sleeve din jacket din MD sannan ta nufi kofa walking slowly ta bude kofar, tana shiga babban parlon gidan ta dinga bin ko ina da kallo sai kuma ta kalli sama, Muryar ceo ta ji ta juya da sauri ta ganta a study room dinta with heap of textbooks a gabanta, tasowa tayi ta shigo parlon calmly tace "You need anything Mary Ann?" Ta gyada kai da sauri tace "I want to pray Ma...." Ceo tace "Ohh kina tambayar gabas kenan ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Yes Ma" Kalle kallen Parlon ceo din ta shiga yi, can tace "I can't really tell where Aliyu faces and pray whenever he is around, let me call him on the phone sai ya gaya maki inda zaki kalla" Mayraah tace "Okay Ma" Ta koma ta dauko cellphone dinta ta fara kiran MD, yana dagawa tace "Aliyu zaka gaya mata inda zata kalla tayi sallah" Daga haka ta mika ma Mayraah wayar, Mayraah ta amsa da ladabi ta kai kunne tayi shiru, jin shi ma yayi shiru tace "Ina ji" Sai a sannan yace "Baki da Google a wayarki ne?" Taki ce masa komai saboda ceo dake tsaye, yace "In rashin kunya ne ai ba sai kin jira wani ya gaya maki yanda za ki yi ba, ba ni kika ce ma Quack Doctor ba, za ki sani" Mayraah dai taki cewa komai, Yace "Install Qibla finder on ur phone and stop being a nuisance" Mayraah bata sake tsayawa ta sauraresa ba ta katse wayar ta mika ma Ceo, Ceo tace "Ya gaya maki ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Eh ya gaya min" Ceo tace "Ae kina da darduma?" Mayraah tace "Ina da shi" Ceo tace "Toh sai kiyi using warm water kiyi performing ablution din so u won't catch cold" Yanda Ceo tace mata haka tayi da ta koma dakin tayi alwala da ruwan dumi bayan ta fito daga bandakin ta bude akwatinta ta ciro darduman da Ammi ta sa mata sannan ta tada sallan, tana idarwa ta kwanta ta kashe fitilar dakin sannan ta lullube da duvet nan da nan bacci ya dauketa ko Maheer din bata kira ba, cikin dare taji zazzabi ya rufeta ga tari da ta dinga yi, wajen karfe uku ceo ta bude kofar dakin ta shigo ta kunna wutan sannan ta karasa ta zauna gefen gadon ta cire duvet din jikinta tana feeling temperature dinta tace "Are you okay?" Mayraah ta mike zaune tana rawan sanyi, Ceo tace "You are running temperature dear" mikewa tayi ta fita, ba a dau lokaci ba ta dawo da magunguna da ruwan gora, bude maganin tayi ta ba Mayraah ta amsa ta hadiye da ruwan sannan ta koma ta kwanta ta takure waje daya, ceo ta lullubeta da duvet tace "Sannu kin ji...." Kafin gari ya waye ceo ta shigo dakin ya fi a kirga, da asuba haka Mayraah ta daure ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta koma ta kwanta…. duvet din da taji an cire jikinta ya sa ta bude ido a hankali, MD ta gani tsaye kanta, ta mike da sauri ta ja duvet din ta wani daure fuska tana kallonsa, sae kuma ta ga CEO tsaye a bayansa, sunkuyar da kai tayi, Calmly yace "How are you feeling?" Ta gyada kai a takaice tace "Fine" Ceo tace "Will u take noodles for breakfast?" Mayraah ta gyada mata kai, ceo ta juya ta fita daga dakin sai da yaji ta kulle kofa sannan yace "Cire min jacket dina" Wani kallo ta jefa masa ta sauka daga kan gadon ta bude akwatinta ta ciro towel din wankan ta da shower gel with sponge sai toothpaste and toothbrush tayi wucewarta bandaki ta bar sa wajen tsaye, ya bi ta da ido har ta kulle kofar ta sa makulli, Bayan kusan minti daya ya gyada kai ya juya ya fita daga dakin, Mayraah na fitowa wanka taji kamar zazzabin ya sake dawo mata, ta ajiye jacket din hannunta ta kwanta ta dukunkune cikin duvet ta fi minti goma a haka daga karshe ta daure ta mike ta shirya, ta dau jacket din tana kokarin sa wa Ceo ta shigo dakin tace "In kin gama ki fito kiyi breakfast" Tana fita Mayraah ta saka jacket din sannan ta fito parlor, dinning area ta nufa ta zauna kujeran dake facing na MD dake kallonta ganin she is still wearing his jacket, garnished noodles with chicken Ceo din tayi mash, MD dai na rike da spoon yana kallon plate din abincin, lokaci lokaci yake satan kallon Mayraah, Mayraah ta fara cin abincin haka ma ceo, bayan some seconds ceo ta kallesa amma bata ce komai ba, mikewa yayi ya wanke fork din da knife din hannunsa a washing hand basin dake dining area din ya dawo ya zauna, Ceo tace "Ya maganar Therapy da nayi maka kwanaki?" Karo na farko da Mayraah ta fara ganin murmushin sa, yace "Soon Ma'am" Ceo ta ci gaba da cin abincin ta a nutse, Mayraah sai kallonsa take kasa kasa without letting him notice, gaba daya he doesn't look comfortable a wajen, kawai ta ga ya jawo wani clean plate din ya goge da tissue ya juye abincin a ciki, Ceo ta kallesa ta ci gaba da cin abincinta, sae a sannan ya fara cin abincin, Mayraah bata ci abincin da yawa ba duk da ɗan manna masu ceo tayi a plate kamar wasu turawa, cikin minti kadan ya gama cin abincin ya mike ya bar dinning area din, duk suka bi sa da kallo, dakin da Mayraah take ya shiga, Mayraah dae sai kallon ikon Allah take, ba a dau lokaci ba sai ga shi ya fito, kallonsa Mayraah ta dinga yi da mamaki ganin Jacket dinta a hannunsa, yana kallon Ceo da ladabi yace "I will take my leave now ma'am” CEO tace “Ohk" Daga haka ya juya ya nufi kofa ya fita daga Parlon yana rike da jacket din, Mayraah ta mike zata kwashe plates din Ceo tace "Ki bar shi, yanzu mai aikin zata shigo" Mayraah tace "Toh" barin dinning area din tayi ta tafi daki, bayan ta kulle kofar ta dinga kallon akwatinta dake bude, ta wani hade rai, saboda me zai bude mata akwati, is he even okay?? tsaki ta ja ta karasa ta kulle box din, kwanciya tayi ta dau wayarta tayi dialing number Maheer har ya katse bai daga ba, ta ajiye wayar ta rufe jikinta da duvet. Har ta fara bacci Ceo ta shigo dakin cikin sparkling suit da skirt din da iyakarsa gwiwa, sosai tayi kyau kamar wata baturiya, tana kallon Mayraah tace "You just stay back and rest Mary Ann, za mu je conference din yanxu, it's only for today and tomorrow.... if u need anything feel at home ki shiga kitchen" Mayraah tace "Ohk Ma, nagode" Ceo ta mata murmushi sannan ta juya ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da ido har ta fita ta kullo kofar, a hankali ta jawo wayarta tayi dialing number Amminta.... Karfe sha biyu saura kiran Usman ya shigo wayarta, ta mike zaune daga kwancen da take da kyar saboda mugun ciwon da kanta yake mata, picking call din tayi ta gaishesa ya amsa yace "Mura kike ne?" A hankali tace "Eh" yace "Kin sha magani?" Tace "Na sha daxu" yace "Where is ur location?" Tace "Nima ban sani ba yaya" Yace "Ask around you" tace "Ni kadae ce a gida, sun tafi conference, i am not too fine saboda muran da nake...." yace "Hotel ne?" Tace "Aa gidan ceo, idan sun dawo i will ask for the address" ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Gidan Ceo? How comes?" Bai jira tace komai ba ya kara da cewa "Ok then, I will be waiting for the address" a hankali tace "Ohk" katse wayar yayi ta ajiye, gaba daya mura ya sa ta gaba and it's making her feel sick, tana ganin lkcn sllh yayi ta tashi taje tayi alwala, tana idar da slln ta kwanta, cikin bacci ta ji an bude kofar dakin ta bude ido taga Ceo, mikewa zaune tayi, Ceo tace "Baki yi lunch ba Mary Ann" Ta murza ido tace "I slept off" Ceo tace "This is pass 3, ki fito ki ci abinci" Daga haka ta juya ta fita, Mayraah ta sauka daga kan gadon ta tafi parlor. Karfe biyar saura Mayraah ta fito daga dakinta tana kallon Ceo dake parlor tace "Ma ya iso, yana waje" Ceo tace "Ohk, ba kince Yayanki bane?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Yayana ne" Ceo tace "Let him in, it's cold outside" Mayraah tace "Ohk Ma" Fita tayi daga parlon, inda ta hangosa tsaye ta karasa, idonsa na kanta har ta karaso ta kara gaishesa tana murmushi tace "Yaya kai ma ashe kana jin sanyi naga ka sa Jacket?" Yace "Kema kika ji sanyi balle ni" Er dariya tayi tace "To ai ni dama kowa yasan bana son sanyi, kai kuma baka bacci sai da AC" Yana kallon rigar jikinta yace "I see, where did u get this designer jacket u are putting on?" Mayraah ta kalli Jacket din MD dake jikinta da sauri, sai kuma ta kirkiri murmushi ta dawo gefensa tace "Ceo ce ta bani" Ya daga kafada yace "Ok, but ai na maza ne, yana da tsada sosai" Mayraah dai sai murmushin karfin hali take, Ya rungume hannunsa yace "But why did she decide to lodge u in her home? Na zata hotel zata biya maku...." Mayraah tace "Eh sauran maza ne duk suna hotel, ni ce kawai a nan, yaya tace fa mu shiga ciki akwai sanyi... She said u are welcome" Ko rufe baki bata yi ba, Ta yi ido hudu da MD da yayi parking ya sauka daga mota wanda da alama tasa ce, Usman ma kallonsa yake ganin he is walking toward them, shi ko bai sake kallonsu ba har ya wucesu, Usman ya bi sa da kallo ganin gidan da Mayraah ta fito zai shiga, sai kuma ya kalleta da sauri yace "Who is he?" Ta ɗan buda ido tace "MD dinta ne, he is the MD of the hospital" Usman yace "MD?" Mayraah ta gyada masa kai, yace "Shi ma a gidan nata ya sauka kenan??" Da sauri ta girgiza kai tace "Aa fa yaya, kilan ta kirasa ne ta aikesa amma ba nan ya kwana ba wallahi" Usman dai yayi shiru yana kallonta, can yace "Why did u do as if baki san sa ba, shi ma haka?" Da mamaki ta zaro ido tace "Yaya ai ni ban wani san sa ba fa, ka manta ni new staff ce a asibitin? We are not use to each other" Yace "You are never meant to get use to ur boss ai dama, do u know who a boss is? but i am surprise yanda zaki ga boss dinki and not greet him just like that in dai ba akwai wani abu ba, ga dukkan alamu ya sake maki fuska da yawa ko kuma akwai wani abu between u two...." Mayraah ta turo baki tace "Wani abu kuma yaya? To yaushe ma na fara aiki a asibitin, abinda ma zan iya kirga sau nawa na gansa a asibitin, office dinsa ma fa ba kowa ke zuwa ba, and his office is at the last floor of the hospital building, kawai dai ya fiye takura ne da masifa shi sa nake avoiding dinsa, baka ga dauke kai nayi ba kar ma ya gan ni" Usman ya jingina da brick wall din wajen yana kallonta as if not convince, ita dai ta sunkuyar da kanta, bayan few seconds yace "Yaushe tace zaku koma Nigeria?" Mayraah tace "She said gobe ko jibi" Yace "An gama conference din ai?" Tace "Aa gobe ne last day" Yace "Shi kuma da ya zo yanzu sai yaushe zai bar gidan?" Mayraah ta zaro ido tace "Yaya ai nima ban sani ba, kilan aiki zata sa shi.... And na manta tace mu shiga ciki saboda sanyi" A takaice yace "Bazan shiga ba, do u need anything?" Ta girgiza masa kai tace "Aa" Yace "I will be on my way" A hankali tace "Da wuri haka yaya?" Yace "In kina bukatan wani abu ki kirani" Ta gyada masa kai, Juyawa yayi har ya fara tafiya ya sake dawowa yace "Why don't u tell her u prefer hotel?" Ta zaro ido tana kallonsa, yace "Ohk kin fi son zama under same roof da katti ko? U are comfortable" A hankali tace "Yaya ni da ita kadai ne a gidan wallahi, kuma ai it's a privilege ajiyeni da tayi a gidanta a matsayina na karamar staff" Bai sake ce mata komai ba ya juya ya bar wajen ta bi sa da ido, sai kuma ita ma ta juya tana tafiya a hankali ta nufi cikin gidan, tana shiga parlor ta kulle kofa, MD kadai ne zaune parlon zata wuce dakin da ta sauka yace "Hey come back here" Juyawa tayi ta kallesa, ko damuwa da hade ran da yayi bata yi ba, ta dawo parlon tana kallonsa, ya mike yace "Halan an gaya maki wasa ya kawo ki UK? Idan kina son haduwa da wani namiji me yasa baki biya kudin jirgi kin biyosa ba? Wato ga opportunity kin samu? ko kin zata yawon bude ido kika zo nan? Saboda kin ga Ceo na lallabaki ta kawo ki gidanta ta ajiye ki ko conference din ma baki je ba shine bari ki kira saurayinki, to let me give u this last warning har mu bar kasar nan bana son in sake ganinki da wani namiji don ba abinda ya kawo ki ba kenan, any body that wants to meet with u should follow u to Nigeria" A takaice ta juya ido tace "Har yayana? Kuma ai dai ban fita ba sai da na nemi permission daga wajenta kuma ta bani izini, why didn't u ask her before waiting for me?" Shiru tayi jin ana saukowa downstairs, Ceo tace "Ya tafi yayan naki ne?" Mayraah ta juya ta kalleta tace "Eh ya tafi" Ceo ta shigo parlon ta karaso ta mike ma MD takardun hannunta tace "Here" Juyawa Mayraah tayi ta nufi hanyar daki, magana ceo take masa amma hankalinsa na kan Mayraah har ta shiga daki. Da daddare Mayraah na kwance wajen karfe sha daya Maheer ya kirata, tana daga wayar ya ji muryarta yace "Me ya faru?" Ta mike zaune da kyar tace "Cikina" Maheer ya mike zaune daga kwancen da yake yace "When did it start?" Kamar zata yi kuka tace "Not long ago?" Yace "Did u take any drug?" Ta girgiza masa kai tace "Since 8 na bar parlon, ita ma kuma tace she will be going to bed early.... " Yace "Ko za ki je ki mata knocking, if not nasan baza kiyi bacci ba" Tace "Ni bazan iya tashinta ba, though it's not as if the pain is that much for now, kilan sai zuwa gobe da safe, i will try and sleep now" Yace "Are you sure" Tace "Yeah, yanzu ma ai na fara bacci ka kirani" Yace "Toh kiyi baccin Mimi, Allah ya sauwake, i pray bazai matsa maki ba anjima...." Ta ɗan yi murmushi tace "Bye" ta katse wayar ta koma ta kwanta, ba a wani dau lokaci ba bacci ya dauke ta, can cikin dare axaba ya tasheta ta sauko daga saman gadon duk da mugun sanyin da ake sai taji kamar zufa ma take, ta jawo wayarta da kyar ta duba agogo taga karfe biyu saura, ajiye wayar tayi, tun tana kokarin ganin ta jure kawai daga karshe ta mike zumbur ba tare da tasan ma tayi haka ba, ta murda makullin kofar ta bude da sauri ta fita, hasken reading lamp da ta gani study room dake parlon ya sa ta karasa can da sauri, tana isa ta durkushe wajen ta fashe da kuka ta ma kasa cewa komai, matsar da littafin gabansa yayi ya mike da sauri yana kallonta yace "Menene?" Cikin kuka tace "Wallahi cikina ciwo yake min ka taimaka min" Ya kunna wutan wajen ya durkusa gabanta da sauri yace "Ya yake maki?" Ta kasa ce masa komai, keenly yake kallonta seeing how she is reacting to the pain yace "Dysmenorrhea?" Gyada masa kai tayi da sauri, ya mike ya bar wajen, magani ya yafi ya dauko mata da ruwa a glass cup, hannunta na rawa ta amsa ta sha, shi dai yana duke gabanta yana kallonta, don bata daina kukan da take ba, bayan kusan minti goma yace "Tashi ki koma daki..." Ko rufe baki bai yi ba cikin rawan murya tace "Aa wallahi bai daina ba, kilan allura zaka min, dama allura ake min" Daga sama har kasa ya kalleta seeing how confident she still is in between pains, Bai yi niyyar mata alluran ba saboda ta riga da ta sha drugs, but ganin she is still in pain har karfe uku kawai ya hada alluran ya mata, nan parlon ta fara bacci ya tasheta ta wuce daki. Washegari har karfe takwas bata tashi ba, har sai da ceo ta shigo ta tashe ta, bayan ta fito daga wanka ta shirya sannan ta dau wani jacket dinta dake akwati ta sa sannan ta fita parlor, Ceo na kallonta tace "Breakfast yana dinning table" Mayraah ta nufi dinning din ta zauna. Wajen karfe goma na safiyar Mayraah na waje tare da Usman da zuwan sa kenan, yana kallonta yace "Hope you are better now?" Ta gyada masa kai tace "Na ji sauki" yace "Me yasa baki kirani jiyan ba, though the ceo might not gree to that since...." Shiru Usman yayi bayan ya hango MD da ya fito daga cikin gidan, tunda Mayraah ta kallesa sau daya ta dauke kai gabanta na faduwa yake, kallonsa kawai Usman yake kamar yanda shi ma MD ke masa kallon cikin ido, har ya zo ya wucesu leaving his designer perfume scent behind, Usman ya dinga kallon jacket din da ya daura shoulders dinsa, can ya kalli Mayraah da ta juya kai taki kallonsu, a kan gado fa ta ajiye jacket din nasa ashe ya shiga ya dauka, Usman yace "Mayraah" Da sauri ta juya ta kallesa, yace "Wannan ba Jacket din da kika ce min Ceo ta baki bane?" Ta hadiye wani abu da kyar tace "Yaya shi ne, amma ai kilan shi ma ta basa ne ya sa...." Kana jin yanda take maganar kasan karya take, Calmly yace "Mayraah" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Whose jacket is that?" Ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Na shi ne, a airport ya bani saboda ni ban ciro nawa a akwati ba don ban san haka sanyin yake ba, shine sai ya bani nasa in saka" Kallonta kawai Usman yake, ta daga kai ta kallesa jin yayi shiru, after some seconds yace "To kin yi kokari" Tana ganin ya juya zai bar wajen ta marairaice tace "Yaya don Allah kayi hakuri, wallahi ina tsoron kar ka min fada ne shi yasa nayi maka karya" Yace "Infact karya kike still kice min babu komai tsakaninki da wannan mutumin, saurayin ki ne" Mayraah ta buda baki tana kallonsa da mamaki, juyawa yayi ya bar wajen ta bi sa da kallo, tafi minti uku tsaye wajen daga karshe ta juya a hankali ta fara tafiya zuwa cikin gidan.....