[12/1, 3:22 PM] +2348037420816: https://chat.whatsapp.com/IpsParMb6dOBXLpns86N2u °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-1/2* Wata tsohuwa ce zaune akan kujera 'yar tsugunno tana tankad'e garin masara, a cikin wata 'katuwar 'kwarya. "Oh! Ni Indo, ko ina Ameenatu ta tsaya ne? A ce tun almuru mutum ya fita har yanzu shiru." Shiru ta yi kamar wacce ake fad'awa amsa, wani gutun tsaki ta ja ta ce, "Ni ma na cika mantuwa halin Ameenatu sai dai wanda ba da shi Ibro da Hansai suka haifeta ba, yarinya sai ka ce rainon kaka." Tankad'enta ta ci gaba hankali kwance, ba tare da damuwar komai ba har ta gama, ta mi'ke ta shiga madafa. Kamar wacce aka jefo ta shigo a guje ta bi ta kan 'kwaryan ta yi d'aki, baki bud'e tsohuwar ke kallon garin da ke zube a 'kasa, sannan ta bi sahun 'kafafunta da kallo, tana shirin magana ta ji sallama daga zaure, tana tsaye a inda take ta bada umarnin a shigo, ta hau 'ko'karin tattara garinta da ke 'kasa. Ganin mutanen da suka shigo yasa ta d'agowa tare da mai da fuskarta alamun ba wasa, mutune biyar ne sai 'kananan yara 'yan ganin 'kwaf, Tumba mai awara da 'yarta, sai Halliru Mai Kaji, sai wata yarinya da namiji, jikin yarinyar sai zuba yake da manja, sama-sama suka gaisa, d'ayan namijin ne ya ce, "Mun zo ne domin Ameenatu." "Uhm ina sauraronku." "Uwar yarinyar ta aiketa ta kai man ja gidan Sahura doguwa, ta had'u da Ameenatu a hanya, ba laifin zaune tsaye ko kwance ta juye mata shi a jiki bayan ta d'ura mata shi a baki." Kallon yarinyar ta yi wacce a jiki da tsayi ta linka Ameenatu, nuna ta yi daga sama zuwa 'kasa ta ce, "Ke kina shirgegeyiya haka kamar buhun siminti ta ya jikata zata yi miki wannan aika-aikar? Kin kwaso wasu 'kafufuwanki kamar fatanya da wannan jemamman tsohon naki kun zo sharrin dai da kuka saba yi ko? Toh ahir d'inku kurwar jikata ko harararta maye bazai yi ba ballantana ci, kai kuma Halliru fad'i naka." "Zuwa ta yi kamar mutuniyar kirki tana taya Ni aiki da fira, ashe ta sa 'kawayenta su d'ebarmin 'kwayaye, sai da ja'irar yarinyar ta tafi na ga 'barnar da ta yimin." Halliru Mai Kaji ya kai 'karshen zancen yana haki kamar ya zai sha'ko wuyar Tsohuwar, kallon Tumba da ke cika tana batsewa ta yi ta ce, " ke ma fad'i kar ta kasheki." "Ni ai sai na ga fitinanniyar jikar taki ta fito tukunnan." Ta fad'a tana kallon yarinyarta, wacce goshinta ya kumbura ya yi lemon tsami, ba ta iya bud'e idonta saboda yashin da aka watsawa idon, ga bakinta na jini, fuskar kanta ta canza kammani, kakka'be hannnuwa Tsohuwar ta yi ta ce, "Ameenatu dai bata nan, sai ki fad'i abin da ke ranki ko ki had'eye abarki." Dukansu kallon shatin 'kafafuwan da ke zane a 'kasa da gari suka yi, ba sa tantamar Ameenatu tana ciki tana jinsu. Baki bud'e suka maida dubansu ga Tsohuwar, wacce ta 'kara tamke fuskarta. "Uhm ke fa nake jira, ina da abin yi fa, in ke baki da aikin yi to Ni ina da shi." Ta fad'a tana kallon Tumba, sannan ta waiwaya ga Halliru ta nunasa da yatsa ta ce, " Ban ta'ba ganin mutumin banza ba irinka, tsabar rashin mutuncin ka kalli tsabar idanuna ka kira jikata da ja'ira, to babu ja'ira a zuri'ata sai dai ka gani a kanka, da kake maganar sun daukar maka 'kwai, dad'ina da bad'i saurin zuwa, zakkar da baka fitarwa ita suka fitar, ka godewa Allah da ba kazar suka d'auka ba, da kuka kwaso jiki kuka zo so kuke na biyaku, ko kuma na kama marainiyar Allah na jiba kamar jaka, to ba da Indo ba, na daina zubin adashin da babu d'auka ballantana riba, da a ce iya gaskiya kuka fad'a da na biya, amma sai kuka yi rashin sa'a harda sharri a maganarku, dan haka ko gaban Hashimu Mai Gari zaku je ba Baballe Mai Unguwa ba ku je, ku ce Ni Indo Saleh 'kawar wasan 'kasar uwarsa Lantana Sabi'u nace ba zan ba ku ko sisi ba, ku wuce ko fitarmin a gida gayyar tsiya tun kafin nayi muku rashin mutunci, kun ci sa'a yau bana jin rashin mutunci da surutu da kun ga tsiye da ta uwayenku ja'irai." "Wallahi Inna ki ji tsoron Allah, wannan ba gata kike yiwa Ameenatu ba, a ce yarinya ta yi laifi ba za ki hukuntata ba sai dai ki goyi bayanta, wannan ba gata bane." "Na daketa saboda gani tsinanniya ko? Na ce na daketa saboda gani tsinanniya ko?" Gaba d'aya zaro idano waje suka yi ciki mamaki, bud'e baki Halliru ya yi da nufin kare kansu ya ce, "Inna ba haka muke nufi ba fa, tunatarwa ne dai muke miki." Wani kuka Tsohuwar ta saki,sai kace wacce aka ce wani nata ya mutu, cikin kukan ta ce, "Bayan kun kirani da tsinanniya sannan kuma kuka ce min ma'karyaciya, ko iyayenku ba su isa su kira Ni da wad'annan sunayen ba ballantana ku 'kananan 'kwari, bari na nuna muku cewa ku din kananan kwari ne." Ta'baryar da ke aje a gefen turmi ta d'auko, sanin halin Inna ya sa kafin ta jiyo sai dai ta ga takalma. "Ai da kun tsaya kun ga 'karshen rashin mutunci marasa mutunci kawai, ke kuma ja'irar sai ki fito ai." Lekowa tayi a hankali sai da ta tabbatar sun tafi kan ta fito tana kyalkyala dariya. Taɓe baki Kaka tayi kan ta ce, "Kin ganki nan da wuya kamar mariƙin lema da ma na bari sun jajjaga mun ke ai na huta." "Yoo su jajjagan mana wa aka ma asara? Kece za ki yi kuka wallahi bani ba,na ga ranar ma ban da lafiya kuka kike ehee sai in mutu ma kowa ya huta tunda kin gaji da ganina kuma ma." Zaro ido kaka tai kan ta tallafo kan Ameenatou , "Kin ga rufamun asiri bar maganar mutuwar nan, yanzu je kiyi wanka kin ga rabonki da wanka tun shekaran jiya." "Aradun Allah ba zan ba sai kace wata 'Yar ruwa,ni kifi ma na ke sha'awar ci bara in kira Furera da Lantana muje gun tumbiɗa mai kifi." Daura hannu akai Kaka tayi. "Oh ni Indo Allah Na Gode ma da ka bani Ameenatou yanzu duk abun da ki kai yau bai isheki ba sai kin karo wani?" Ameenatou ta fara tafiya tana tsalle-tsallenta , "ki aje mun ruwan wankan inna dawo zan yi,bara muje gun Alhaji tumbiɗa mu dawo aheee kifi dadi wallahi zan rago miki kar ki damu Babar Maman Ameenatou Indo." Har ta fita ta dawo aguje. Sai da Kaka ta firgita. "Ke lafiya? Me yafaru kuma?" Buta ta dauka tana nishi, "Wallahi kashi nake ji, kashi zanyi wayyo kashina kar ka fito." Tsaki Kaka ta yi, "yo ni na zata ma karshen duniyarce tazo ai irin wannan gudu." Ta ci gaba da shararta tana yan wake-wakensu na da. Ameenatou kuwa kamar an shuka dawa a bandaki tunda ta shiga kusan minti talatin ba ta fito ba. "Ke Ameenatou na ce ko Barci kika soma a bayinne?" "Eheeem, eheeem kaka yasin kwan nake kasayarwa." Sai da Ta kusa Awa daya a bandaki kan ta fito tana nishi. "Tab wallahi naci kwannan da yawa ni kaina warin yadameni,gidansu Furera mu ka je muka dafe kwayayenmu mu ka cinye su tas." Ta karasa maganar tana kyalkyala dariya. Kaka ta ce, "kyaji da shi dai." Ameenatou sai da tazo gaban kaka sannan ta sake mata tusa mai bala'in wari ta fice aguje tana dariya, "Kaka kema ga rabon ki." Rike hanci ka ke tayi tana masifa, "zaki dawo gidannan ki sameni wallahi sai na rama, har ni za afadawa tusa? Mu da muke adashenta ina jiran ki ba kaffara sai na rama tusar nan zaki sha mamaki." Ameenatou na fita....... A ci gaba ko a tsaya? In ga ruwan sharhi jama'a🤸‍♀️ 22/10/2021 _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 3:22 PM] +2348037420816: https://chat.whatsapp.com/IpsParMb6dOBXLpns86N2u °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-3* _*XAYYEESHERTHUO FANS CLUB ARADU SHARHINKU NA TAHIYA DANI🤣🥰💃💃INA YINKU IRIN SOSAI DINNAN* Taci karo da mai tallen alewa. Tsayawa tai kamar kamila. "Ina kwana Baba mai alewa?" Washe baki ya yi,yana "lafiya yar nan,na nawa za abaki?" "Ni fa da yawa ina so daman kakace ta ce in siyo za ta yi sadaka." Mai alewa son kudi anji banza. Tuni ya sauke alewa kasa yana washe baki, "ma sha Allah ki ce yau bani ba wahala anyi an gama duka zan bar miki jaka biyu." Ameenatou ta washe baki. "Tab ni dai sai dai in zaka bari jaka daya ai sari zan yi ma." "Haba yar nan alewar fa ba wani riba duka kudinta kenan." Ameenatou ta ce, "Shikenan, Shikenan to wallahi na fasa siya." Ta karasa maganar tana kokarin tafiya. "Haba 'yata ayi haka kuwa? To zo na bar miki jaka daya da rabi,bara ajuye miki aleda." (Alewar da dukanta ba ta kai na jaka dayan ba ma amman dan son zuciya za a saida jaka daya da rabi,hhhh Alhaji baba anga bati adole za ama 'ya wayo) "Yawwa to zubamun aleda nikam sauri ina yi kar kakata tamun fada." "Yi hakuri yar nan yanzu ma kuwa zan sa miki." Mai alewa harda yar wakarsa yana murna yau ya ci ganima ya zuba aleda tare da mika mata. "Yawwa yammata bani kudin to." Kallon cikin ledar tayi kan ta ce, "to rufe idonka ni karka kallemun kudina da yawa kaka tace kar inna ciro kudi gaban mutune." Rufe idon ya yi yana , "Yo ai da gaskiyar kakarki duniyar nan ce yanzu sam ba yarda." Kallon tai ta tintsire da dariya. "Aradu alewar nan taka kwai zaki." "Bari kawai 'yar nan ai kadan ma kikaji sai kin sha farar can Aradu har wani gardi take." Yana cikin maganar nan ta zame jikinta ahankali tana dariya. "wai baki gama ciro kudin bane? Ha'ah wannan kaka taki kwai wayo Aradu zan fa bude idona ni kam." Shiru dai ba alamar motsi bare maganar Ameenatou. Bude idon da zai yi ba alewa ba Ameenatou ba kudi. Suman tsaye ya yi yana. "Ina ki ke ne? Wai ina ki ke ne? Ince yau gamo nayi da aljana,na shiga uku kudina ." Zama ya yi awajen kawai ya fara kuka wiwiwi. Majina na bin hawaye. Lekosa ta yi tana dariya. "Wayyo cikina,ji tsoho na kuka, wayyo Allahna." Kara lekasa tai tana shan alewa tana dariya. Alhaji Baba mai alewa kuwa kukansa yake yana, "Allah ya isana wallahi,muguwa ja'irar yarinya,Ba zan yafe ba,wallahi ba zan yafe ba koma Aljannarce." Ganin yaki tashi yasa Ameenatou fara ihu tana. "Kai Malam,Kai Malam na ce kai Malam." Cikin murya mai tsoratarwa. Waige-waige ya fara ko zai ga inda ake kiran na shi ammman ina sautin magana kawai yake ji batare da alamun mutum ba. Ci gaba da magana tayi, "ka bar mana gida,na ce ka bar mana gida in ba haka ba ina daf da shigewa jikinka na fadama zan shiga zan shiga." Nan da nan cikin tsoho duri ruwa kan kace miye ya fara fitsari a zaune. Da ta kuma wata kara bai san lokacin da ya zura da wani mugun gudu ba. AMEENATOU na fitowa dan dariya har da rike ciki tana kwantawa, mussamman inta kalli gun da ya yi fitsari. Gidan su Furera ta shige tana shan alewarta da yar wake tana dariya. Innar Furare gwanar kwadayi ta ce, "Ah Ameenatou me aka samo mana ne?" Murguɗa mata baki ta yi kan ta ce, "Alawar Aljanuce na tsinta a hanya in kuma za ki sha to." Zaro ido Innar Furare tai , "tab yi hakuri Ameenatou wallahi na koshi ni tsoron Aljanu nake." Ta kalli Furera , "Ke Zo muje gun tumbiɗa dan wallahi kifi na ke son ci." Furera ta ce, "Haba Ameenatou dazu fa kina gani da kyar muka sha yanzu in aka kama mu fa." "Ke dallah bana son iskanci in an samo ma wa yafi ci ina kece da shegen baki kamar sabuwar akuya zauna kar kije ita ma lantanar bani zuwa gidansu Amma ku sani bani ba ku agarinnan kowa ya kama hanyar gabansa,banziya mai idon agwagwi." Furera ta ji Maganar rabuwa Da Ameenatou tuni ta yi karamar murya, "Goggo Ameenatou dan Allah kiyi hakuri kinji,kar azo tafiya binni ace bani." Washe baki Ameenatou tayi domin ba abun da ke faranta mata rai fiye da ace Goggo uwa uba kuma ayi maganar birni. "Kin ci sa'a wallahi yarinya, Allah raya min ke mu sha biki a birni yasin,hhh jeki kiramun Lantus tun yanzu zan mai da ku yan gayu kan Kawu Audu yazo kai mu binni ke Fures ita Lantus." Lantana zata fita Ameenatou ta ce, "Dalla dawo wawiya ba ki ce mun kin gode ba." "Na gode Goggo Ameenatou." "Yawwa yi sauri kuje ku dawo aradu yau tumbiɗa zai sha yasa." Bai fi minti biyu ba kuwa sai ga Fures da Lantus an shigo. Ameenatou ta ce, "yawwa wallahi ku goyani mutafi tunda Jiddah matar police ma kawayenta goyata suke." Ba yadda suka iya haka suka saba Ameenatou abaya tana shan alewarta suna gani ta hana. "Fures wallahi kibar hadiye yawo ma dan ba sammiki zan ba,ke kam kinyi gadon kwadayi wallahi innarki kamar kuda yaga suga haka take." Ba abun su tanka ba ta ce asauketa ba ita ba su. Suna isa gun tumbiɗa Ameenatou ta sauko tana , "Yaya Tumbiɗa wallahi kaf garinnan ka fi kowa iya suyan kifi,har mafarki na yi jiya fa inaci." Washe baki tumbiɗa ya yi kan ya ce, "Yoo ai na jima da sani kin ga fa har yan binni zuwa suke saye." Jansa da hira ta fara tana ɗiba Lantana na karɓa. Duk atunaninsu tumbiɗa bai san me suke ba. Tumbiɗa irin lutayen mazannanne karfafa masu kirar samudawa. Sai da ya bari suka diba son ransu suna kokarin fita ya janyo kofar shagon. Ameenatou ta ce, "Yaya Tumbiɗa zamu tafi ne fa." Dariyar mugunta ya fara. "In kinga kun fita agidannan to na maidaku kifaye ne na gasa na siyar." Jikin Ameenatou ya duri ruwa. Su Lantana kuwa hawayene kawai ke kwarara. Tumbiɗa ya ce, "dake Zan fara Ameenatou ina tunaninki duk ban san me kuke mun bane,gani banza ko? Maza zo nan inna maidaki kifin na ga yadda za ki ci ai." Ameenatou ta gama tsorata baba mai alewaa kawai ta tuna sai ga fitsari ita ma ya fara kwararowa, can kuma ta ce, "Yaya tumbiɗa ba ka ce kana sona ba rannan? Wallahi zan aureka kaji." "Dagaske zaki aureni?." Ehmna na fada jiki na rawa. Washe baki ya yi,"yawwa to ku tafi da kifin da kuka diba duka ga kari ma sai na zo mu zanta ko Amaryar." Ita ma ta washe baki , "eh sai kazo." Tana amshewa suka fice adari . Dan neman Jaraba ta dawo tana, "tumbiɗa mai tumbin giwa wallahi karya nake ma ba zan aureka ba,tab ji ka fa kazami kullum wari wallahi bana sonka wayo na ma ysin." Tana gani ya taso ta zura aguje tana mai gwalo. Biyota ya yi tana gudu yana yi gashi shi jiki ba kadan ba har tsayawa kallonsa take tana dariya. Gajiya ya yi ya tsaya yana haki, "zaki sani wallahi ba abun da zai hanani aurenki agarinnan nan da sati daya." Turo masa baya tai tana. "Fada ma Duwaisatu ba dai ni ba." Furera da lantana kuwa sun jima da isa gidan kaka. Tana shiga suka fara dariya. Kaka ta ce, "Ya naji zarni wake zarni acikinku kuma?" Ameenatou ta kalli su Lantana, "wallahi in baku bar mun dariya ba kwalelanku kifinnan,Kaka nice na yi fitsari kuma wallahi ba zan cire kayannan ba jiya fa nasa tab, Tumbiɗa ne ya turfamu ban san sanda na sake masa fitsari ba." Sallamar da akayine ya katse ma su magana. "Kaka ga shi kawu Audu ne ya kirawo waya akawo miki." Amsa tai tana , "to fa Malam Audu da yammacinnan Allah sa dai lafiya." "Shallo,shallo na ce kana ji na ko?" "Ina Jinki Inna,ina wuni ina gajiya ya aiki." "Yoo ni ka daga murya wannan abu naku ba wani nake ba,ehhh fa muna lafiya ya iyalan gidan fatan duk lahiya?" Ameenatou ta ce, "Kaka kice abawa Okul Al-ameen zan ji muryarsa." "Toh toh Audu abawa Al-ameen Yar uwarsa na son jin muryarsa." Dadyne ya mikawa Al-ameen wayar yana "ga shi Ameenatou za ta ma magana." Rai bace ya karba dan yasan in yaki karba yanzu zai jawa kan shi jidali Yar da bai taba gani ba ta nanike masa. "Shallo Okul ka mun magana kaji." Al-ameen ya ce, "kina lafiya?" Bai jira ta amsa ba ya datse wayar tare da mikawa Dady yana ba network,jin tsanar yarinyar yake ji har ransa mara dalili duk da cewa bai taba ganin ta ba. Ameenatou kuwa ta dage sai magana take taji shiru Kuka ta fara, "Kaka ni wallahi ban gama jin muryarsa ba abun ya dauke ni akiranmu shi ni wallahi ban yarda ba." Birgima ta fara yi akasa tana akira mata Al-ameen 23/10/2021 _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 3:23 PM] +2348037420816: https://chat.whatsapp.com/GeuRcMbmDGuHPBZu4928K8 *IN KINA NA FARKON KAR KI SHIGA WANNAN PLS🙏* °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-4* Kaka ta karbi salular tare da mikawa Halliru, "ka ga karba abun ka." "Haba Ameenatoun Kaka kiyi shiru kin ji zaki kara waya da shi anjima na tabbata Audu zai ƙara kira, kin ga jarumar jikata ba ta kuka sai dai tasa ayi ko?" Ameenatou ta girgiza kai, "Amman sai har in Zaki goyani inyi barci ni." Kaka ta wage baki, "ina ni ina daukan buhun sumunti?" Nan da nan Ameenatou ta kara bajewa akasa , "To ni wallahi mutuwa zan yi in baki goyani ba." Kan kace me Kaka ta dauko zani ta saba gardiyar jikarta abaya. Tamkar wata jinjira tai lum abaya. Su Lantana kuwa sun zama yan kallo ba abun suyi magana ba cibi ya zama kari. Daga karshe ma Ameenatou cewa ta yi , "Kuma tafi gida wallahi dan ba cin kifinnan za kuyi ba kwalelanku ehee naga ai Tumbiɗan cewa na yi ina son shi, munafukai ku bar mana gida." Dukkannunsu sai da sukai wani hamshakin hadiyan yawo domin ransu ya gama biyaws Amman ba yadda suka iya. "Munafukai ku fice mana wallahi." Haka Ameenatou ta korasu ba dan sun so ba Suna tafiya kuwa ta dirka abayan kaka ta fara damkar kifi. "Oh ni Indo Sale Ameenatou anji kunya da rowa ni da uwarki kam ba haka muke, yanzu dai sammun ladan goyo nima." "Ysn,ysn,ysn dan dai ina sonki ne amman da bazan sammiki ba ." Dan ficil kamar kuda ta gutsiro ta mikawa kaka, "ga shi dai amaida mugun yawo." "Yoo ina zan sa wannan? Aiko hanjin wuyana ba zai shige ba." Ameenatou ta ma kaka wani kallo kan ta ce, "bani,bani abuna nace tunda kin rena." Tuni Kaka ta zurma abaki tana mamula dan ta san halin Ameenatou sarai zata iya kwace abunta. WASHE GARI kamar kullum da asussuba Ameenatou ke tashi dibo ruwa saboda tafiya makaranta. Duk yan garin Ana idar sa salla suke fita diban ruwa. Lantana da Furera ne suka biyo mata yadda aka saba. Furera ta ce, "Goggo kiyi sauri mu tafi kin ga mu ka tsaya ba zamu samu da wuri ba." Ameenatou ta ce, "Wallahi tallahi na rantse sai na yi kashina baku isa ku hanani kashi ba,kuma na kama layi ai tun dare dan haka wallahi sai mun diba ba wanda ya isa ya hana." Ta karasa maganar tana shigewa bandaki (Wannan kashin gado kenan,dan kullum goggo in ba tai kashin nan da asuba ba to ba kwanciyar hankali) Tana shiga ji kake bututu bututu ga shegen bala'in wari da ya kaure gidan. Ban da toshe hanci ba abun da su lantana ke yi. Can sai gata ta fito tana nishi. "Dilla can ku bude hanci ai gwanda nawa kashin ma akan na innoninku mai warin jaba." Bakoti ta dauka suka bita abaya kawai. Suna zuwa wajem diban ruwa Ameenatou tai kane-kane ta matsar da botikan mutane tasa nasu.. Adamu ya ce, "haba Ameenatoun ba ki ga layi ake bi ba ne?" Kan ya karasa magana Washa ta ce, "kam bala'i wallahi ba ki isa ba aradun Allah in kinga su suna tsoron ki da masifar kakarki to wallahi ni na keresu." Ameenatou ta kallesu sama da kasa ta ce, "in kuna son zaman lafiya ku bar ni na diban ruwannan ko kuwa ayi ruwan bala'i da masifa a karkarar." Ta karasa maganar tana daura dammara da dan kwalinta. Ganin Washa bata ma san tana yi bane yasa Ameenatou kama hanya domin tasan tana kara magana zata iya domkota. Kofar gida taje tana kwallawa kaka kira, kaka na fitowa Ameenatou ta fara kuka "Kaka kin ga wani Washa za ta ce ma munafuka jikar munafuka?" Ta kara fashewa da kuka "Dan kawai na.... Kan ta karasa kaka ta ce, "Jar uba! Kara cino cinin bakin nan nata tai alamar za ayi masifar karshen zamani "Muje na ce muje sai ta fadamun yadda akai ta mai da mu munafukan." Suna zuwa Kaka ta bokatan kowa ta sanya na Ameenatou kan rike kugu tana, "Yawwaa gareki Washa kike ko washo? In ma masai kike to aradu ahir dinki da jikata kije ki tambayi kakar uwar kakarki da Ni Indo Sale da Ubanta mai fitsarin kwance nai munafurci ba da ku ba,yo ke har ma kuna da bakin magana daga kakannin naku har iyayen naku daga mai fitsarim kwance sai kashi awando,uwar uwarki ma yaushe yaushe ta gama cin tasono a karkarar nan?" Ameenatou da sauran yaran wajen ban da dariya ba abun da suke. Adam ya katse kaka da fadin, "Haba Kaka ba ki san meke faruwa ba kawai zaki fara magana haka?" Kaka ta zaro ido can kuma ta fara shekan majina, "Adamu ni ka ke ma tsawa a karkarar nan? Ni ka ke ma tsawa to wallahi kaje ka tambaya ko uwar ubanka ba ta isa ta mun kallon banza ba bare ta fadamun magana, kaf kauyenan an sani kune kamfanin faso,kakanin kakanku ma duk fason kafa ne ya kashe su tsabar tsiro. Adamu na jin kaka ta fara jero jawabai ya kama hanya domin inya tsaya zata iya ba da Labarin danginsu kaf. Tana face majina da zaninta tana, "Yoo ai sa ka tsaya dan gwanda ni ban gudu ran daren aurena ba yo uwar kakanka sai da aka kwana ana nemanta dan ragwanci." Malam Hashimu ne yazo wucewa ya durkusa yana, "lafiya kaka? Fashewa da kuka tai tana daura hannu aka "Wai har ni..... . Comments din ku shine karfin gwiwata🙏 *ALƘAWARI NA NA NAN BEST 3 COMMENTERS ZA SU KARANTA FREE IN SHA ALLAH,DUK WADDA TA SAI AMEENATOU KUMA ZATA KARANTA WANI LITTAFINA NA KUDI GUDA DAYA* 24/10/2021 _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 3:24 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-5* _*KADA KUCE YA YI KADAN KUCE YA YI YAWA KUNJI🥺MAI YAWA ZAI ZO GOBE IN SHA ALLAH*_ _*Kalaman Soyayya*_ _Zan so ace ko da na rana dayane kaji kwatankwacin irin son da nake yi maka azuciya,ina sonka,ina kaunar,ina fatan kasancewa da kai har karshen Numfashi na_🤍💫 "Adamu zai kalla yacewa mayya? Abun ba ma ga Jikata kadai ya tsaya ba har da ni?" Wiwiwi Kaka ta hwara zubda hawaye kai kace da gaske ne. Malam Hashimu ya ce, "kai Adamu dawo nan lallai ka cika mara kunya, kasan wace Kaka kuwa agarinnan? Maza ka bata hakuri." Adamu ya ce, "Baba Wallahi ban ce mata Mayya ba,cewa na yi fa.... Kan ya karasa Kaka ta katse da " Na yi karya ko? Na ce na yi karya ko? Dazu ka ce mun Mayya yanzu kuma ka karyatani,to wallahi ko tsohuwar kakar,kakarka ba ta isa ta karyatani ba dangin masu faso,na ga ubanka yana yaro har satan goruba suke zuwa gonar malam mudi, Amman yau ni za ka ci ma mutunci." Ta karasa maganar tana kars fashewa da kuka ana shekan majina. Malam Hashimu ya ce "Kaka Dan Allah kiyi hakuri yarone bai san ke wacece ba, Adamu maza bawa kaka hakuri." Adamu ya ce, "Dan Allah kiyi hakuri Kaka." Fara share hawayen tai tana "Aradu yau ka ci sa'ar Hashimu ne,shi ma dan dai mun sha tsallaka katangar gonar mai gari da Da Kakarsa Jummala Auduwa satan mangoro ne,amman Aradu yau da kaji ajikin ka dan kuwa tamola zan da kai, maza in kaje gida ka cewa uwarka ya akaji da hakurin Kandala mai tambotse? Ko da yake ma dakyar in ta Santa dan ko mahaifiyarta bana jin tasanta, dake Kakar, kakar ta ce." Malam Hashimu dai ya dau hanya batare da ya ce komai ba, gudun kar acigaba da tone-tone. Ba yadda suka iya haka suka bar Ameenatou da kawayenta suka gama diban ruwa kaf har suka gama Kaka na tsaye tana surfa uban bala'i. Karfe takwas Sun kammala shirin tafiya boko. Ameenatou, Lantana,tare da Furera. Ameenatou anci gazal daga gira har kunne,jan baki kuwa saman ido da baki kamar manja ita adole yar gayu, andaga wando zuwa iya gwiwa an dago safa fara saboda Aga safarta ta yan binni,kaf kauyen ita kadaice mai safar angayu da aka kawo mata daga binni. Tafiya take tana wani juyi da rangwada. Kai ku dakata ma aradu fures,lantus ku bini abaya ba zai yu inyi shigar yan binni ina jerawa da ku ba,sai kusa arainani ai." Haka suka bi bayanta tamkar boodyguard dinta. Can kuma ta kara tsayawa tana "ni fa wallahi sai na sha mangoro kan muje bokonnan danni bana so muje da wuri yanzu wannan malamin me *wata mie si niem* (what is your name) ne a ajin ya cika iya yi ya ce sai munyi yaren turawa." Furera ta ce, "Aiko na ga bishiyar gonar Baba Datti ta tsiro harda wa inda suka nuka fa." "Nima na gani wallahi, kuma manyane." "Munahikai shine baku fadamun da wuri ba? To aradu yanzu ko can zamu kuma kadan zan sammaku." Nan suka kama hanyar tafiya gona. Sunci sa'a kuwa Malam Datti ba ya nan. Tuni Ameenatou ta dane kamar tsuntsu. Cinkowa take tana jefamasu. "Yawwa wannan ne na biyar kenan, Aradu sai mun tsinke goma ko ashirin." Lantana ta ce, "Ameenatou wallahi ga Malam Datti nan Shikenan mun shiga uku inya kama mu wallahi mugune." Furera kuwa ido ya yi rudu-ruɗu an rasa abun fadi ma. Ameenatou ta masu tsawa, "Matsoratan banza da wofi to wallahi ba zan sauko ba sai na dibi rabona yo abun da in ya nuku ba zakka ake mana ba,ai gwanda mu diba rabonmu." Ameenatou na zuba zance su fures kuwa anga ba yi an tsere. Ji ta yi ana, "Kambala'i aradu yau Sai kinci Kuntsin Uwarki A karkarar nan." _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 3:25 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-6* _*INA MATUKAR BUKATAR ADDU'O'I DA GA BAKU NAN KU MA SU ALBARKA MASOYA🥰🙏KOMIN KANKATA KO GAJARTA KUMIN DAN ALLAH*_ _*KALAMAN SOYAYYA🤍💫*_ _"Ina ji ajikina cewa duk randa na daina sonka to numfashi na ne yazo karshe,ka sani ka kara sani in har zanyi numfashi to sonka na cikin raina ko ince rayuwata ma gabadaya, indai ana so bayan rai, tabbas zan ci gaba da sonka har bayan raina,tare da yi mana fatan kasancewar mu atare,shin ka san mahimmacin murmishinka gareni kuwa? tamkar yiwa makaho addu'ar budewar ido ne, misalta irin Farinciki da yanayin da zai shiga,to wannan kwatane a Farincikin da nake shiga aduk sanda na ga kana murmushi,bance ni kadai za ka so ba,amman ina da tabbacin zanyi kokarin cike duk wani gurbi da ke zuciyarka ta hanyar da ba za ka taba so ko tunanin kulla alaka da wata 'ya mace ba,Ina Sonka tamkar Raina! Ko ba yanzu ba kuma ba yau ba koda kuwa bana duniya ina fatan ka so ni kwatankwacin son da nake ma hakan zai matukar kara faranta mun rai Habeebiy Da'eeman ba iya suna bane ina fatan hakan akullum in sha Allah."_ _*Fisabillah🥰duk wanda yaji dadin kalaman ya kara mun àddua*_ A firgice ta jiyo tsabar firgita saura kad'an ta fad'o, duk da yanayin tsoro da ta shiga hakan bai ta yi laushi ba. "Kai dai Malam Dattin nan ka fiye jaraba da rashin ha'kuri, daga kawai ka ga mutum saman bishiya sai ka fara zage-zage, kamata ya yi ka samo tsafga ka ce keee uban me kike yimin a saman bishiyata, Ni kuma sai in ce bishiya ba ta uban wani ba ce tashen Allah ce sai dai mutum ya zama sanadi, na zo d'ibar zakka ce da ka gagara fitarwa, in kana iyawa sauko da Ni ka zane, sai ka kamo ni ka sauko ka fara duka, amma ka wani zo kana ta hayayaga ba." Kamar yadda ta kawo shawara haka Malam Datti ya yi, domin kusa da shi ya samu tsafgar, yana shaud'a mata d'aya a duwawunta ,ban da ihu da tsalle, ba abun da take, sai da ya yi mata shida masu shiga jiki a na bakwan ne yana shaud'a mata ta shige cikin malun-malun dinsa, cakulkulu ta fara yi masa mai kama da yakushi, da ya kai bulalar da niyyar duka sai ta zille, kuka take wujiga-wujiga har da majina, hakan bai ya sa ta nutsu ba ta daina, ganin tana neman haukatar da shi ne yasa ya fara 'ko'karin cirota, sai da 'kyar ya cirota yana haki, ganin ta ku'buta da 'kyar yasa ta bawa wandonta iska, har ta yi nisa ta dawo ta kwashe magwonron da ke 'kasa ta kara gaba fitttttt. Haka ta kama hanya tana tafe tana kuka harda majina tana kuma shan mangworonta kamar dole. Lokacin da ta iso bokon an fara tarar 'yan makara, firifect d'in da suke tsarewar tsabar dariya ko tsaida ita ba su yi ba, ita d'in ma bata yi niyyar tsayawa ba, amma ta 'kuduri aniyar duk wad'anda suka yi mata dariya tun daga hanya har makaranta sai ta d'au mataki a kansu. Tun daga nesa ta hango Malamin da ke cikin ajinsu, Malamin *wata mie is niem* ne a ciki. Tana zuwa ta shige aguje kamar zaburarriya. Tsawa ya mata yana, "You ba? You ba? U ar just coming now? Eheen I will deel with you in and out." Kallon shi tai tana daura hannu aka , "Onkul Aradu I Noyin Going to bishiyar Dirimi, going to Bishiyar Mangoron Baba Datti kadai,kuma shi ma Kaka ta ce dan uwanmune Kakan kakanshi abokin makocin Kakanmune wallahi Onkul." Uncle Ibrahim bai san lokacin da ya tintsire da dariya ba. Can kuma ya make, kan ya ci gaba da cewa, "Oya Go Out, i said Go Out." Ya karasa maganar yana nuna mata hanyat fita da hannu. Gatsinan Mangoron ta tai kan ta ce, "Sholly Onkul I noyin Karawa wallahi Na ce ma mangoro ne ba dirimi ba,kuma in zaka sha ma ga shi sai inje gida in karbo ma gishiri gun Kakata." Ba yadda ya iya haka ya bar Ameenatou a ajin nan ta zauna dan inya biye mata ba za suyi karatu ba sai dai cikinsa ya kulle dan dariya da takaici. Zama tai agefe su Furare na kallonta sai ta galla masu harara "Onkul wallahi i no lyk botin yara,ni ka ce masu stopi kallo mie, ehee in baka haka ba na kama yara wallahi botin (bitin) din su zan kuma sai na haifosu ehee dan ina da cikinsu." Ta nuna su Lanata da hannu. Kallon su ya yi ya ce, "Ku daina kallon mana sarauniyar turanci in ba so kuke ta kashemu da turancinnan ba." Wani dadi Ameenatou taji adole ance mata ta iya turanci kara washe bakinnan tai tana damkar mangoro. "Oyaa Class Wanene zai fadamun me za ace in Mutum bai da lafiya da turanci? Kun ga yanzu dai mu ka gama kuma duk wanda ya fada dai,dai zan mi shi kyauta." Cewar uncle . Ban da zaro ido ba abun da suke suna kallon juna domin duk basu san me zasu ce ba. Tuni Ameenatou ta daga hannu. Uncle ya ce, "Oya Meena." Ta tashi ta ce, "Onkul wallahi inna fada me kadai zaka ba wa kyautan ko?" Ya ce, "Eh Go On." Ta washa baki "Ita Noyin Lafiya Wal." Kallonta kawai ya tsaya yi. "Onkul ba ka ce su tafa mun ba fa kuma na fada ai." Dariya ya yi kan ya ce za su tafa miki amman Hausa da turanci kika hada ai..... Kan ya yi magana aka biga bell din fita break. Tuni suka fice suka bar sa tsaye mussamman Ameenatou da tayi wani irin tsalle. Tsayawa ya yi kawai yana tunani duk da rigimar yarinyar shi kam birgeshi take sosai. Ameenatou zama tai ta cigaba da shan danyen Mangoron ta kamar dole. Furera da Lantana suka zo. "Ameenatou dan Allah kiyi hakuri ba za mu kara guduwa miki ba." Harara ta dalla masu kan ta ce, "e da kuka tafi kuka bari ya tsalamun duka a Duwaisatu na ba." Furera ta ce, "Dan Allah kiyi hakuri Googo Ameenatou." Ameenatou ta yi tsaki kan ta ce, "Banzaye jikokin masu sai da daddawa sai kuzo ku zauna ai." Jiki na rawa suka zauna kamar iyayensu sun basu umarni. Lantana ta ce, "Ni kam wancenn Onkul din na mun kyau yasin dama ya aureni ya kai Ni birni." Ameenatou ta tabe baki, "tab wallahi bai kai onkul Al-ameen dinmu kyau ba Kaka ta ce fari ne sol kamar bature,ke tsaya ko son shi kike? Aradu in kina son shi mu tura mai sakon soyayya yadda na ga ni Film dinnan." Lanatana ta rufe fuska "ni ysn ina son shi tom." Ameenatou ta ce, "Fures dauko mana takarda da biro Aradu mun zama an binni ,zanna fada ku rubuta me za asa." Furera ta dauko ta karda da biro. Ameenatou ta gyara zama. Yawwa rubuta" Salamu alaikom,dilla ma bani in rubuta ai nima na iya burutun ehee." Nan ta fara. _"Onkul aradu tonda nigganka nafaddarijiyar sonkkaninakefa danAllah ka sonnnikarka kacebakasona,inkakisonimituwa, zanyi,dagamasoyiyarka *lantus* kowar,fures,da,goghoameenatou,inajira,kajojjmuyi,aure,mutaibbinni._ Akayi zannen wata markadaddiyar HEART mai kama da ayaba agefe. "Yesh wallahi ni yar binni ce yara na iya kalaman soyayya fa yanzu fures ki tashi muje mu kai,ke kuma Lantus ki tsaya amaryar onkul Ibrahim." Suna zuwa Ameenatou ta ce.... _*BANA GANIN SHARHI FA😟KO A TSAYA NE?*_ _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 3:25 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-7* _*KALAMAN SOYAYYA*_ _Kowasu Masoya Basa Da Burin Da Ya Wuce Kasancewar Su A Tare,Amman Ni Burina Ya Bambanta Da Na Su, Domin Kuwa,So Na ke Na Kasance A Zuciyarka Dukkan Bugun Numfashi, Ka Tuna Da Ni, Tare Da Sakin Murmushi A Fuskar Ka,Ina So Na Rayu Da Kai *RUHIY*_ _*SHARARRUN NOVEL GROUP,INA FARINCIKI TARE DA TAYAKU MURNA CIKE DA ALBISHIR CEWA ADMIN DIN KU TA SAI MAKU AMEENATOU DAGA FARKO HAR KARSHE ZA KU KARANCE KYAUTA🥰YO BAN MA SAN SUNAN ADMIN DIN TAKU BA FA (African Black Cofee)KUJI DADINKU KAMAR YADDA TA BUKATA*_ _______ Suna zuwa Uncle ya tsaya yana kallonsu kawai ganin Ameenatou na ta washe baki kuma ta kasa magana. "Ah Meena Me ya faru? Ina fatan lafiya ko?" "Uhumm uhumm Onkule dama Lantus ce ta aiko mu kawo ma wannan." Ta mika masa. Karba ya yi,ya bude. Ya rasa ma ta ina zai fara karatun domin shi dama ba wata cikakkiyar hausa ya iya ba,bare kuma ta wa innan hamshakan. Mika mata ya yi, "Karanta wannan yaren na ku ban iya ba ni kam." Kara washe baki ta yi tana, "Wai cewa ta yi fa sonka take." Cike da mamaki ya tsaya kallon Ameenatou kan ya kalli inda Lantana take. Hada ido su ka yi ta yi wani fari da ido tana rufe fuska da Hannunta. Murmushi ya yi, "owk to ki kirata kuzo office ku sameni." Ameenatou harda tsalle ita mai hadin aure. "Ke Lantus ta shi muje wallah yana sonki murna ma fa yake,wai kuma muje ofish ina ga ma maganar aurenku za ayi aradu." Tuni Lantus aka tashi adole za aje gun masoyi. Ameenatou ta ce, "Dilla mara kunya ba haka ana yi ba,tsaya ki ga nice agaba sai ke,sannan Fures a baya ,yanzu ai kin zama amarya, kuma tafiyar yan gayu za mu na yi har muje ofish din." Tafiya suke suna karairaya kamar zasu balle,idon kowa a kansu masu dariya na yi. Suna shiga ya kara sake masu wani hamshakin Murmushi. "Yawwa maza ku shigo." Cewar Uncle Ya kalli Lantana, "Ke ce ko?" Washe baki tai tana kallon shi,ana murza ido. Bulala ya janyo ta bayansa nan take ya bata rai. "Maza kuyi nildon anan wajen." Nan fa ciki ya fara durin ruwa. Wani irin hadiyan yawo Ameenatou tai ganin zabgegiyar dorinar sai da hanjin cikin ya yi sufa.. "Onkul Wallahi Noyin Me,Lantana ce." Lantana na kuka ta fara, "Onkul Kayi Hakuri wallahi ba ruwana, Ameenatou ce ta ce haka." "Onkul wallahi ban da ni su biyune ka yi hakuri dan Allah." Cewan Furera. Fara zabga masu bulalan ya yi yana, "ina ku bakwa da kunya? Wato kina sona ko? In zo muyi aure? Ke kuma meena ke ce mai hadin aure ko?" "Onkul ka yi hakuri wallahi,na rantse ba ruwana ka yi hakuri,wayyo kwakwallar jikina zata fada, onkul kashi na ke ji wallahi zai fito,bulalar da zafi,wayyo duwawuna,wayyo jikina,kwakwalwata za ta fashe, kashina zai fito." Ban da Sambatu ba abun da Ameenatou take tana ihu da kuka,tuni dalibai suka hadu suna kallo ban da sautin dariya ba abun da kake ji a makarantar. Ameenatou na samun hanya a guje ta bar makarantar tana kuka,Lantana da Furera suka bi baya. Gida ta shige ta baje a tsakar gida tana ihu. "Wayyo Allah na Kakata na shiga uku, wallahi Onkul ya kashe ni,wayyo cikina kashin zai fito na shiga uku." Kaka ta zaro ido tana, "wani ja'irin ya taba mun ke a karkarar nan? Tabbas yaro bai san zafin wuta ba sai ya taka yi shiru ka fadamun." Tashi tai aguje ta nufi bayan gida sai da ta zubda kashin cikinta kaf sannan ta fito tana. "Kaka Onkul Wata Mie si Niem ne ya dinga jibgarmu kaman sanayi taga dusar wake, wai kawai fa dan mun rubuta masa takardar soyayya Lantana na son shi.". Kaka ta kyalkyale da dariya, "Yoo har ma kin sa na ji sanyi araina,ai ba haka ake nuna soyayya ba,zamaninmu lokacin da na ke son kakanki kin san ya nayi har ya fara sona?" Ameenatou ta washe baki, "Aa fadamun Kaka." Kaka ta gyara zama "tunda na gan shi na ji cewa na fada a kogin son shi, Alokacin ina jin kunyarsa,sosai fa in fada miki,amman kawai sai Kakata ta bani shawara ta ce kullum in dinga wanka da kwalliya ina tafiyar yan mata ina rangwada aduk lokacin da muka hada ido kin san me nake masa?" Ameenatou ta ce, "Aa yi sauri ki fada mun kaka." "Hmm wani irin fari da ido na ke masa sai ya yi suman tsaye akwai ranar da tun da ya tsaya kallona ya kame har na tafi kwannan sa daya a haka sai da washe gari naje wucewa ya motsa,daga nan fa ya kasa hakuri sai ga Malam Mudi mahaifinsa agidanmu yana ataimaki dansa Aba shi ni in ba haka ba zai mutu,hmm Kakanki ya soni fa kamar zai mutu." Ameenatou ta fashe da dariya. "Kambala'iiiiiiiiiiiiiii ashe su kaka ansha soyayyar yan gayu yasin kaka yasha kallo dan yi mun inga." Da Kaka tayi wani fari da ido sai da Ameenatou ta fadi kasa dan dariya. Kaka ta ce, "ai wannan ma kadan na miki da na miki dayan suma zaki yi ina ga yarinya. Ameenatou ta ce, "Aradu kaka kin iya soyayya, haka zamu na ma onkul amman wallahi yanzu sai. Mun rama tsafgennan da ya mana ba ci bulus ba." Kaka ta ce, "Yoo ai kaf garinnan ni nake koya masu soyayya da duk wanda zaije zance sai yazo na fada masa abun da zai ce fa,bakiji wasu na ce mun Innar Soyayya ba,hhhh yarinya ni da SOYAYYA ai tamkar shan ruwa a modane,kin ga kakan me gari? Shi da babansa har dambe sukai zigidir akaina kowa sai ni,yoo ina zan iya niko nace Haliluna dan Amana kadai na ke so,ranar aurena kuwa ansha kuka gun samarin karkararnan da kam ta yi dadi arayuwa,chaaii inna tuna Halliru masoyi na kamar inyi kuka ana can." Ameenatou ta ce, "Kaka Masoyiyar Halliru kenan." Kaka ta galla mata harara , "Ja'ira bar ni ina kewar Halliru Masoyi Mussamman inna tuna yadda muke zuwa diban ruwa tare." Ameenatou ta ce, "nikam na ji,yunwa nake ji kuma wallahi hum humm gobe sai Onkul ya yi bayani da larabci." """""""""""""" Washegari Tare suke zasu tafi makarantar kamar kullum. "Aradun Allah onkul bai ci banza ba,yau dinnan zaku ga me zan masa,kuma kaka ta fadamun yadda xa ayi ya soki wallahi sai ya aureki ehee." Su dai su ka yi tsit suna binta da mamakinsu yau sune a makaranta tun karfe bakwai sun ruga kowa zuwa . AMEENATOU ta shiga ajin ta kulle kanta tana, "kar ku shigo fa abu zanyi ehee ban ce ku shigo ba." Sai da ta gama abun da take sannan ta bude suka shigo. Ban da dariya ba abun da Ameenatou take,kuma taki fadin me ke faruwa kawai dariya take tana, "Walahi anjima akwai kallo." Uncle Ibrahim ne ya shigo nan take ta bata rai ya kalleta yana masu dariyar kyeta. "Ah yau kune da Safe haka? Kuma ba rigima? Lallai jiya bulala ta yi aiki." Hararsa tai azuciyarta kuma tana fadin, 'aiki ma ai sai ka zauna zaka tabbatar ysin." Da ƙasaitarsa ya zauna akujerar zamansa nan take ya yi wata irin kara sai da ya fado akasa. "Wayyo Allah duwa....... _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 4:28 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-9* _*KALAMAN SOYAYYA🌹*_ _Ina Sonka! Ina Sonka!! Ina Sonka!!! Duk da kawancer a zahiri sau uku kawai na furta amman a zuciya ta ban san adadinsa,kasa aranka ina sonka kuma zan ci gaba da sonka har Karsshen Numfashi na_ .........Haka kuwa yan fadar mai gari suka dawo ajigace domin ba damar kama Ameenatou. Tana nishi ta ce, "Furera ku tsaya muje gidan Hajiya Jummala mai dan wake." Nan kuwa suka dau hanya. "Assalamualaikum Baba Jummala mun zo sallama." Cewar Ameenatou. Lekowa Matar tai tana, "Toh! Ameenatou 'Yar Kaka yau kuma nan aka nufo?." Ameenatou ta washe baki, "Eh Wallahi Baba Jummala Binni zamu koma da Kaka Gobe shine na zo ki sallameni." Kallon su ta tsaya yi sama da kasa da alamun tana kitsa wani abu aranta. Can kuma ta ce, "To shikenan ai dole in sallameki Ameenatoun Kaka jirani." Nan Ameenatou ta kara washe baki "Yawwa Baba Hajiya Jummala Dan Allah ki zabomun raken mai zaki dan Allah addu'ar ma mai zaki da kuma magaryar ma,Allah miki albarka Goggo Baba Jummala mai kusunbin kudi." Fitowar da jummala za ta yi sai gata dauke da tabarya . "Ki zo zan sallameki, tabbas zan sallameki har da rake mai zaki ma da su magaryar." Ameenatou na lura Baba Jummala da gaske take nan kafa mai naci ban baka ba gudu take su Furera na bin baya. Baba Jummala kuwa ce take, "Yoo wai ba za ki tsaya in sallamekin bane? Ku tsaya mana ja'irar yarinya kin manta satan rake da magaryar da kike mun har zaki zo kice in sallameki ai gwada ma ku bar kauyennan ko ma huta da jarabarku ke da kakarki duk kun bi kun addabi mutane." Sai da suka isa gidan kaka tukun suka tsagaita da gudun. "Yawwa Yasin Na gaji gobe kuma kuzo da sassafe muyi sallama in ba haka ba baruwana da ku,kuma inna tafi binni ba zan dawo in dauke ku."cewar Ameenatou. Lantana ta ce, "Tab Goggo ysn ko diban ruwa ba zan je ba sai nazo munyi sallama." Furera ma ta ce, "Nima tun wuri zan fita ai." Da haka sukai sallama Ameenatou ta shige gida. """""Washegari kuwa da sassafe sai ga Lantana anzo yiwa Goggo Ameenatou sallama. Karfe Bakwai daidai Baba Audu da drive sun iso. Ameenatou sai washe baki tana, "Baba Audu ina Onkul? Kaka ta ce da Onkul za ku zo mu ta fi ko shine mai tuka motar? Tab wannan ma mummuna ba onkul dina bane." Baba Audu ya ce, "Oh Allah Ameenatou kya tsaya kina numfasawa kan ci gaba da magana ko? To Uncle dinku ya yi tafiya amman na san cewa kan mu isa shima ya dawo dan jirgi zai biyo." Tabune fuska tai kamar za ta yi kuka, "Baba Aradun Allah na fasa zuwa binin indai Onkul ba zai zo ya daukeni ba,ni wallahi Onkul ne zai kaini binni amotar shi zani." Ta karasa maganar tana fashewa da kuka. Sai ga kaka ma na hawaye ana jan majina. "Yanzu Audu dan Allah Ba za ka zo da Al-ameen domin farincikin Ameenatou ba? Haba Audu,to nima na fasa tafiya binin mun hakura."ta karasa tana goge hawaye da majina da zaninta. Sannan halin kaka sarai zata iya komai dan Ameenatou Yasa Baba Audu dafa kai yana sallallami Baba Audu ya ce, "Subhannallah Iya ki rufamun asiri, Ameenatou Kiyi hakuri kinji Uncle dinki na nan dawowa shi zai kai ki Skul ma in sha Allah." Ameenatou ta ce, "Ka rantse Baba ka san bakyau karya." Murmushi ya yi kan ya ce, "To Ameenatoun Iya Na rantse." Kallon Kaka Ameenatou tayi kan ta ce, "Kaka kin ga yaronki ya rantse kuma in karya ya yi wuta zata ci shi ba ruwanmu kijo mu tafi binin kawai." Nan Kaka ta bi Ameenatou suka shige Mota tana yiwa su Lanatana byebyer. Suna hawaye tana yi masu dariya. """""Tafiya ta yi nisa domin kuwa har Su Ameenatou sun isa garin Abuja. Motarsu na shiga get din ta Al-ameen ma na shiga atare. Baba Audu ya kalli Ameenatou , "Alhamdulillah Menon Kaka ga yayanki taren kuwa muka iso." Tuni Ameenatou ta washe baki tana kokarin ture kofar motar ta fita. Da sauri driven ya fita ya bude mata. Aguje ta zura gaban motar Al-ameen tana, "Onkul Al-ameen.... Saura kiris ya bigeta ya ci birki.... Tsaki ya yi cikin zafin Rai ya fito.......... Waiwaye kan mu fara asalin dramar ya kamata ace masu karatu su san. *Wace ce kaka?* *Wace ce Ameenatou?* Kuma *Wanene Al-ameen?* Kaka Matace Ga Marigayi Malam Tare da 'Ya'yansu biyu tilo aduniya Abdullahi (audu) mahaifin Al-ameen tare Hafsatu (Hansai) mahaifiyar Ameenatou. Allah ya yiwa mahaifin Ameenatou rasuwa tun kan ta zo duniya, ya yin da kuma mahaifiyartama ta bishi aranar da ta haifeta. Kaka ta yi kuka matuka na rashin yarta ya mace daya tilo amman ba yadda ta iya sai mika dangana tare da karban diyar da ta bari kawancer mahaifinta Dan chiranine bai da iyaye a kauyen bare ko da akwai su Ba za ta taba barin Ameenatou gun su ba, tun haihuwar Ameenatou Audu ya so kaka ta koma binni amman ina sam taki ta ce, sai Ameenatou ta taso a kauyen da mahaifiyarta ta taso. Hakan yasa Ameenatou ta taso a sangarce kuma ashagwabe ban da fitina da tsokana ba abun da ta iya saboda ko me zata taro kaka zatayi kane-kane ta tsaya mata komin girman laifinnan kuwa. A suffar kyau Ameenatou kyakkyace har makura, chocolate color doguwa kuma mai madaidaicin jiki domin da shekarunta take tafiya a yanzu tana da shekara goma sha uku cif aduniya. *Al-ameen* shine babban 'Da ga Alhaji Abdullahi attajirin dan kasuwa daga zuwanshi cirani Allah ya bud'a masa,Matan sa biyu yaransa biyar . Hajiya Maryam ita ce babba mahaifiyar Al-ameen,Nauwara sannan kuma Nusaiba. Sannan Hajiya karama Zulaiha Mahaifiyar Hassana da Husaina. Al-ameen kyakkywane Ajin Farko gabadaya karatunsa a kasar waje ya yi, bai da fara'a ko kadan duk randa akaga murmushi a fuskarsa kuwa abu ya kai makura,tun yana kasar waje yan mata ke binsa amman ko ajikinsa baya tasu ma,hasali kullum cikin wulakantasu yake,acewarsa bai ga abun sa wajen 'ya mace ba,a yanzu ya kammala karatunsa ya dawo Nigeria ya bude asibiti na shi na kan shi yana da shekara Ashirin da tara aduniya. Ci gaban labarin. Dankota ya yi sai da ta saki wani wawan ihu Yana wa.......... *Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments* _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 4:28 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-8* _*KALAMAN SOYAYYA💫*_ _Zan so ace idanunka zai daina kallon duk wata mace sai ni kadai,zan ji dadi in akace ba ka taba sauraren muryar wata bayannk,hakan zai farantamun in ya kasance ni kaɗai ke iya sanya murmushi a fuskarka,ina kishinka,ina kaunar *abin sona*_ _ka sani cewa aduk sanda na furta kalmar ka rayu dani,hakan na nufin rayuwace ta har abada zan yi farinciki indai zai kasance da kai *Annier*_ _______*Afwan masoya kwana biyu banda lafiyane* Duwawuna,na shiga uku zasu kasheni sun tarwatsa mun duwawuna." Uncle ya karasa maganar yana rike mazauninsa. Mai yan aji zasu yi ban da dariya. Ameenatou kuwa kallon shi kawai take ta fuske ba alamar dariya illa kura masa ido da ta yi tamkar ta samu T.V. Ya ci gaba da magana, "Shikenan ina ga Shikenan sun ballamun duwawun bani ba zama." Afirgice ya bar cikin ajin yana Sambatu. Yana fita Ameenatou ta kwashe da dariya, "Yoo ni wasa ce? Wallahi ko Aljanu ban bari su tabani su sha lafiya bare bil Adam,hhhhhhhh ai aradu in dai muguntace yanzu aka fara indai za a taba ni a makarantar nan, Allah sa duwawun ma ya rufe ya kasa zama da gasken." Zama tai akasa ta dinga jibga uban dariya tana Sambatu tamkar zautacciya. Shi ko Uncle na can ana fama,ko da yaje staffroom aka tambaye shi miye cewa yake, "Zasu kashe mun duwawuna wallahi alluraine akan kujerar can." Hakan ya sa Wani Malami zuwa ajin domin duba meke faruwa Aikuwa ana duba kujerar nan da kyau ƙayoyine jeri ba adadi yadda duk mutum ya zauna sai ya ji ajikinsa. "Ku fadamin waye acikin ku ya yi wannan aikin ko kuwa dukkaninku laifi ya hau kan ku." Ameenatou ce tai karaf ta ce, "Onkul Aradun Allah Aljanune duba ka gani yadda suka zuba kayoyin fa kuma onkul bai gani ba sanda zai zauna saida suka tarwatsa masa duwawu,tab ni dai wallahi ba ruwana fita zan yi a ajin nan ma in zakuyi binciken domin aljanun na fitowa mutuwa zamuyi duka,kakata ta ce mun duk randa mutum ya ga aljani to wallahi mutuwa zai yi,ni dai ba ruwana na tafi wallahi." Kasancewar Ameenatou ta san Uncle Kabiru da tsoron Aljanu ya sa ta yin wannan shawarar. Nan da nan kuwa ya zaro ido. "Subhanallah nima ko kaman fa tabajin labarinan to kun ga afita da kujerar waje kawai." Ya karasa maganar yana sakawa bujensa iska. Ameenatou ta zo gaban aji tana, "Aradun Allah ba wani Aljanu nice nan kuma duk wanda ya ce nice sai na masa addu'ar mutuwa,kun san dai Kakata ta iyeee eheee,yara ku fada ku ga aradu kun sanni ai." Ta karasa maganar tana kyalkyalewa da dariya. _____A kwana a tashi Ameenatou za su zana jarabawar kammala primary daman kamar yadda Baba Audu ya tsara a binni za ta yi karatun secondary kasancewar kaka ta ce sai Ameenatou ta kammala makaranta zasu koma binni. Ameenatou ce ta fito da sassafe tana, "Kaka Aradun Allah ki cewa baba Audu gobe su zo da Onkul Al-ameen dina yanzu zamu tafi zana jarabawa kuma yasin ko mun kammala ba zan dawo da wuri ba,dan sai na yiwa kowa sallama a agarinnan Hatta mai garin ma kowa sai ya sallameni yasin eheee." Ba tare da ta jira amsar Kaka ba ta baiwa bujenta iska. Yau da kanta tabiyawa su Furera da Lantana. "Ku wallahi yau dinnan sallama za mu yiwa yan gari har fada zamuje kun ga muje mu zana jarabawar karshennan da sauri yasin yau mun girma mun huta da Onkul Wasi mie si niem. Haka kuwa akayi abun mamaki Ranar Farko da Ameenatou ta shiga makaranta ta zana jarabawa ba tare da rigimar komai ba. Suna fitowa daga jarabawa ta cire jibinta ta daura a kugu, wandon nan kuwa aka kara jan shi sama aka janyo safarnan ku san cinya. "Yawwa kuzo yasin ta gidan mai gari zamu fara." Nan kuma suka dau hanyar Fadar mai gari. Suna zuwa Ameenatou ta ce, "Baba Mai Gari Sallama na zo ma gobe zamu koma binni." "Ah To Alhamdu Lillah Ma sha Allah ɗiyar kaka mun gode Allah,Allah tsare hanya yar albarka."cewar Mai gari da har cikin ransa yake hamdalar barin Ameenatou a karkarar domin ita da kakarta sun addabi kowa shi kan shi basu bare ba bare yan garinsa. Ameenatou ta ce, "Amin din wato ma dadi kake ji ko? To wallahi sai in fasa tafiyan ma ehee ai naga kaka ta ce asalin garin nan dinma namune ehee." Mai gari ya zaro ido, "Subhannallah kar ki fasa,ai ni so nake kije binni ki zama yar binni kixo ki dauke mu muma ki kai mu can." Ameenatou ta ce, "To sallameni mu tafi." "Yoo Ameenatou wace sallama ce kuma bayan wadda mu ka yi?" Ameenatou ta ce, "Kambalaasss lallai ma mai garinnan ka cika son duniya,kudi fa za ka ciro ka ce ungo nan Ameenatou yar albarka Asiya magarya asha amota,in da hali ma ka siyamun harda alewar malam tanko,ni ko sai in ce na gode baba mai gari, Allah ya ma albarka, Allah ya shirya ka kadaina sa ana satan abincin gona,kuma Allah sa amutu ana kashi a bayi." Mai gari ya san tsaf Ameenatou zata iya kunce masa zani a kasuwa domin ita da kakarta in suka fara zuba tamkar wa inda suka kone aka suke. Da sauri ya ce,"Ungo nan jakka biyune asha magarya a hanya , Allah tsare hanya." Ta karba tana, "Yawwa mai gari mai kumatun cincin wallahi kumatun ka sak irin na cincin din da kaka ke soya mana, yanzu saura alawar." "Oh Allah na gode ma ku dakata in shiga gida ina ganin da kwai alawa."cewar mai gari yana ba yan fadarsa hakuri. Yana shiga gida Ameenatou ta ce, "kin ga furera rike mun kudinnan ha in zaga fitsari ina ji." Ta zaga bayan gidan mai gari ta tsinko karkashin sai da ta jajjaga shi tas agun kan ta dibo. Sai da ta bari kowa baya kallonta kan ta fara shafa leda gun zaman mai gari da karkashi. Tana gamawa kuwa sai ga mai gari ya fito da alawa. Da sauri Ameenatou ta karasa ta karba tana, "Ina Godiya Mai garinmu zan Turo adaukeka a gyarama kumatunnan ysn ya dawo na mutane." Shi dai mai gari bai ce komai ba ya nufi gun zamansa domin damuwarsa kawai Ameenatou ta bar wajen kan ta gama tona masa asiri. Lanatana ta ce, "Yawwa to Goggo ki zo mu tafi." Ameenatou ta ce, "dalla tsaya mu sha dariya na masa na bankwanane so inke in ga kukan mai gari yau Aradu." Tana gama magana kuwa sai ga mai gari dam akasa. Mai Ameenatou za ta yi ban da dariya. "Wayyo Allah kunkumina na shiga uku ya balle ku dagani waziri ku dagani." Cewar mai gari. Ameenatou ta ce, "Hhh wayaga mai gari akasa,kato da gemu a kasa." "Daman na sani sharrin ja'irar yarinyar cen ce ai gwanda ku koma binni ko ma huta." Yan fada suka bisu tuni su Ameenatou suka tsere. Ihu mai gari yake yana, "ku dawo ba iya kamosu zakuyi ba sai dai su kara targada ku a zo adumamamun kuguna wayyo ni zai balle." Ameenatou kuwa Kafa mai naci ban baka ba *Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments* _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 4:28 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-10* 🤍🤍🤍 *KALAMAN SOYAYYA* _Wani Hamshakin Murmushi ya sake mata tare da gyara zama yana kallon cikin idanunta, " *Hayatiy* ki sani duk da cewa na san kin sani amman ki kara sani cewa aduk sanda zan furta kalmar *INA SONKI* ba abu daya nake nufi ba,tamkar na ce Ina so in rayu da ke ne,kuma da ke zan rayu haka kuma kece Farincikin Rayuwata, aduk sanda kuwa zan ce *KE CE RAYUWATA* ba wai ina nufin ba zan rayu in babu ke bane aa,amman zan iya ba da rayuwata gareki aduk sanda bukatar hakan ya taso, ba wai so na soyayya kadai nake miki ba,kauna ta rayuwa tare nake miki,kuma zan ci gaba da hakan har karshen numfashi na, kin san meyasa?"_ _*Hayatiy* da ta durkusar da kanta kasa ba tare da ta dago ba ta girgiza masa kai ya yin da take wasa da yatsun hannunta._ _"Ke din tauraruwatace kuma haske ga rayuwata, ana yawan fadin kalaman soyayya karyane,amman aguna sam ba karya domin abun da ke cikin raina kawai nake fiddawa, Ina son farincikinki tamkar yadda kowace shuka ke bukatar ruwa domin tsirowa,ina sonki,zan ci gaba da sonki kuma bana fatan dainawa,kasancewar rayuwarmu atare ita ce burina akullum."_ _A hankali ta dago da fuskarta ya yin da ta sake masa murmushi,cikin sanyayyar murta ta ce, " *Ruhiy*." Shiru ta yi kan ta ci gaba da magana , "Nima ina sonka kuma ina so inyi rayuwa da kai,ka mun alƙawari cewa ba zaka barni ba kaji,ina so in rayu da kai kaji,kar ka barni kai din Farincikin rainane,ka tausayawa zuciyata,ko da zanma laifi na zabi da cewa ka mun fada komin zafinsa bana son kalmar rabuwa,domin tamkar rabuwa da bangaren rayuwata ne."_ _"ba zan bar ki ba *Hayatiy* na miki alƙawari in sha Allah,indai ina raye ba zan taba barinki ba."_ _"Na gode *Ruhiy* ka da ka manta da abu biyu Kasancewar ka cikin murmushi a kullum shine Farinciki da burina ,haka kuma kasancewar ka cikin kamshi shine walwalar ruhina,zan kasance mai alfahari da kai akullum."_ ______ "Wai Wannan Wace Irin Mahaukaciyace a gidannan?" Fisge Hanunta ta yi ta kalle shi kan ta murguda baki, "Aradun Allah ni ba Mahaukaciyace ba sai dai kai eheee." Kaka Da Baba suka karaso Tana, "Kai Al'ameen kanwar taka ce Mahaukaciyace? To ahir dinka wallahi." Ameenatou ta ce, "Yooo ni bama dani yake ba wallahi eheee ni ba Mahaukaciyace ce ba." Baba ya ce, "Ameenatou ba kyau rashin kunya bai san ke ce, Al-ameen wannan yar gidan Goggonkuce Ameenatou." Kau da kai Al-ameen ya yi yana cizon yatsa aransa yana tunanin yadda zai seta yarinyar nan can kuma ya ce, "Barka da zuwa Kaka." Daga nan bai Kara cewa komai ba ya wuce cikin gida. Tsaki Kaka tayi kan ta ce, "Kai Audu wai har yanzu 'Dannan naka bai bar wannan shegen nunkufarcin ba? Ko da yake ba laifin ka bane na uwarsa ne da ta hana abani shi mu zauna a kauye da tuni na seta shi,wai yana gaidani kamar ya ga kashi?" Ameenatou kuwa ina ko kula su kaka ba tai ba tabi bayan Al-ameen duk inda ya yi nan take shiga. Ba tare da ya san tana binsa ba. Baba ya ce, "Iya ina Ameenatoun kuma?" Tabe baki tai kan ta ce, "yoo waya sani muje ciki nikam hanjin cikina sun fara bayani." Al-ameen ba inda ya nufa sai toilet yana kyankyamin rike hannun Ameenatou da ya yi gabadaya ya tsargu da kayan tubewa ya yi ya fara wanka kawai. Ita kuwa zama tai kan kujerar dressing mirror tana kalle kalle, man shafawansa cream ta gani fari sol atunaninta abun sha ne budewa tai tana ta lasha abun ta hankali kwance. "Tab gaskiya Abunnan da dadi su Onkul aradu an iya shan kayan dadi,ysin ko kadan ba zan rage ba shanye kayana zan yi nikam." Ya Gama wankansa tsaf ya tuna towel dinsa na falo, da sauri ya fito domin dauka ya goge jikinsa kan ya duba wani kayan. Wata irin kara da Ameenatou ta sake sai da ya karade dukkanin bangaren gidan. Azabure Al-ameen ya juyo ya kalleta. Ganin jikinsa take kallo tana ihu yasa shi yin tsaki tare da janyo towel dinsa ya sanya ajikinsa. "You! Meya kawo ki dakinnan?" Kan tai magana sai ga su Kaka,Baba,Hajiya,karama da Babba. Ameenatou ta fara, "Kaka Aradu Onkul Dan iska ne tsirare yake yawo fa." Kaka ta kalle Al-ameen kan ta ce, "Yoo Daman ban da tambada da rashin kunya yaushe mutum zai zauna daga shi sai wani guntun zani mai kamar famfas ajiki,da shegen kai kamar kwallon mangoro." Tsabar takaici Al-ameen janye kayansa ya yi ya fice adakin batare da ya ce komai ba. Kaka ta ce, "Maza muje ciki ku kuma iyayen Kwainane da iyayi aba Ameenatou abinci daga zuwa har mun fara gamo oh ni Indo tabbas sai na gyara maku zama daga ku har 'Ya'yan naku." Hajiya Babba ta ce, "Ayi Hakuri Iya In sha Allah hakan ba zai kara faruwa ba." Hajiya karama kuwa ficewa tai ba tare da ta ce komai ba. "Ban waje yo duk ba ke kika koyawa dan naki futsara ba,oh kin ga wancer tsigen mai kama da farantin Dan malale wato hakurin ma ban isa ta bani ba?" Cewar Kaka. Ameenatou ce ta katse ta da maganar, "Kaka Aradu ina jin yunwa kuma ni da Yaya Al-ameen zan.......... *Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments* _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 4:28 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-11* _*KALAMAN SOYAYYA🤍*_ _Aduk in da zaka kasance ina so ka tuna da cewa Ina sonka, Kuma bana fatan bari, kasan dalili? Kai ne hasken rayuwata zan kasance da farinciki ne kawai in har ina tare da kai, ina kaunar ka_ _________ "Zan ci yana bani abaki ai haka yayu suke ma kanne ko?"ta karasa maganar tana goge hawayen fuskarta. Kaka ta ce, "Muje Ciki dai." Suna zuwa falo kuwa suka tarar da Al-ameen zaune yana aiki a system. Aminatou ce taje ta zauna kusa da shi tana, "Onkul Ka zo mu ci abinci ka bani abaki kaji Allah yaso ma nikam dazu fa ban ganka ba rufe idanuna na yi nikam bab ga komai ba kaji ko." Hajiya ce ta shigo da sallama tana, "To Ameenatou ga abincinki in bai isheki ba sai akaro. Ihu tasa tana , "Kaka? Kaka? Kaka kin gani dan abincinnan mai na ci bare in ba hanjin ciki da hantar kwakwalwata Kaka Ni da Onkul kuma zamu ci fa tab wallahi ni akaro Mana." Karaf Kaka ta ce, "Yoo daman ban da jarabbabiyar rowa wannan dan abinci wa zai ci? Kar ki manta fa ina sane da yadda aka auroki kamar tsinken gazari amman yanzu anzo anci ba iyaka sai hawa kamar fulawa, a tarihin danginku kaf tun daga yayan kakan kakanki ba wadda ta shiga gidan arziki sai ke ko ince ma ku da aka barwa gadon tusa? To ahir wallahi dibo mata abinci iya son ranta ta fiki gadara da gidan." Ameenatou ta kyalkyale da dariya, "Laaa Kaka daman ana gadon tusane?" Kaka ta murza ido kan ta ce, "Yoo ba ga shi kinji ba,ban da tusa ba abun da gidansu suka iya yanzu ma Allah rabamu da wannan tusa dan in tayita ina ga sai mun suma sau tamanin batare da sanin inda muke ba." Tsaki Al-ameen ya yi,yana kokarin tashi. Kaka ta ce, "Kai Ja'iri ni kake yi yiwa tsaki dan gyatumarka, kana sunkuyar da kai kamar munafikin kwarto har ni za'a kawowa raini a cikin gidan d'ana ni da idan na so zan iya hana kowa zama a cikin gidan nan. Ace daga zuwar yarinya har anfara yi mata hassada da ba'kin ciki abincin ma ba za'a saka mata wanda za taci ta 'koshi ba. Shi kuma wannan me zubin aljanun yana min tsaki saboda ya raina ni" Dariya Ameenatou tayi sai kuma lokaci guda ta d'aure fuska ganin Al-ameen ya bud'e 'kofa ya fita ta fashe da wani irin kuka tare da kwanciya a 'kasa tana birgima kamar wacce taji wani mummunan labari, lokaci guda hankalin Kaka ya tashi dan a tunanin wani abu ya faru da Ameenatoun. Hajiya Babba dake tsaye a gefe ma ta matsu kusa tana 'kokarin ta'ba Ameenatou, da sauri Kaka ta karasa kusa ta bige hannun Hajiya Babban ta fara magana cikin kuka tana fadin "Ba ga irinta nan ba anyiwa yarinya mugunta, yanzu haka ma mayu suka kamata dama tunda muka shigo gidannan na ga ana nuna alamun ba'ayi murna da zuwarmu ba, wayyo ni Indo na shiga uku ya zanyi da ha'k'kin marainiya" Gefen zani ta saka ta fyace majina ta cigaba da cewa''Kin tsaya kina kallona ne ba zaki wuce ki kiramin d'ana ba yazo asan wacce za'ayi dan ni ba zan lamunce haka ba." Jiki a sanyaye Hajiya Babba ta mi'ke za ta fita sai dai kafin ta 'karasa ta jiyo murya Ameenatou tana magana cikin shesshe'ka ta ce" Ni fa Kaka ba abinda aka yi kawai yunwa ce inaji yasin kamar hanjin cikina zasu tsinke na mutu haka nakeji." Kaka ce ta mi'kar da ita zauna ta ce" Bayani zakiyi ai 'yar lelena ga abinci maza kici a 'karo miki dan wannan ba isarki zaiyi ba nasani." Kuka Ameenatou ta fashe da shi tana fad'in" Ni wallahi ba zanci ba tare da Onkul Al-ameen za mu ci ya dinga bani a baki." Shiru Kaka tayi kafin ta ce'' Yo ai wannan ba wata matsala bace bari a kirashi ya baki ai kema 'kanwarsa ce" Kallon Hajiya Babba tayi wacce ke tsaye tana kallon sangarta irin na Ameenatou, Kaka tace"Ke Mero maza je ki kiramin yaron nan Ameenu ya zo ya baiwa 'yar uwarsa abinci a baki." Cike da ladabi Hajiya Babba ta ce" Mama yanzu kamar Ameenatou ace sai Al-ameen ya bata abinci a baki saboda sangarta ina gani hakan kamar bai dace bawai dan wani abu ba sai dan saboda girmanta yanzu ai abun kunya ne wani ba'ko ya shigo ya tarar ana bata a abinci a baki ba ciwo ba komai kawai dan shagwaba." Aikuwa me neman kuka an jefe shi da kashin awakai, nan Kaka ta fara surfa bala'i tana fad'in Hajiya Babba ta raina ta daga zuwa gidan d'anta zata fara zaginta, hakuri Hajiyar ke bata amma Kaka ta runtse ido sai masifa take yi. "Yoo zan ga yau ni da ke wayafi wani mahimmaci awajen Audu in kuma ke kika bani Nonon da na shayar da shi sai ki fadamun." Ameenatou dake gefe ganin fad'an Kaka ba tsayawa zaiyi ba ya sa ta isa ga plate din abinci ta fara ci hannu baka hannu kwarya dan abincin ya mata dad'i sosai farar shinkaface da miya wacce taji had'i ga nama, hakan yasa bata ko 'kara kallon inda Kaka ke tsaye ba bare tasan me take fad'a. Hayaniyar da Kaka ke yi ne ya fito da Hajiya 'Karama, ta taho tana rangaji kamar wata matashiyar budurwa dan ita irin matan nan ne ta suke wayayyu, batare da ta kula Kaka ba take tambayar abinda ya faru ko da Hajiya Babba ta fad'a mata yadda akayi sai ta ta'be baki ta fara magana cikin isa ta ce" Banda abinki Mama ta ina Al-ameen zai fara bawa wannan 'kazamar abinci a baki ai hakanma ba zai yiwu ba gaskiya dan idan ya taba wannan kazantar kila kwana zaiyi a asibiti dan kwalera ce zata kama shi." Ameenatou ta kwalara ihu da sai da ya karade ilahirin gidan. Kaka ta................... *Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments* _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 4:28 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-12* _*KALAMAN SOYAYYA🤍*_ _Ba kyau ko dukiya zan so ba zan sokana saboda ka daukeni tamkar sarauniya, hakan na bani tabbacin cewa babu wata da zata iya kasancewa acikin zuciyarka bayan ni, ina sonka ina kaunar aduk inda kake ka tuna cewa kai ne farincikina_ _*Oyoyo Harbeebbty Zeey Er Mutan Zazzau🥰🥰🥰💃💃💃 Tabbas ina cikin farincikin dawowarki*_ _*🎂🎂🎂Appy bornday Anty Zee (African Black Coffe) admins din Shahararrun Novel Allah ya karawa rayuwa albarka)*_ ___________ Tuni Ameenatou ta hau birgima ta jefar da plate ɗin abinci, ta fara kakkafe ido tamkar wata mai aljanu tana faɗin, "Wayyo Allah Kaka wallahi yasin wannan Ƙaraman Hajiya ce ko wace suke kiranta Mayya ce ta kamani, Wayyo zata kashe ni." Ameeenatou ta kwallara wani gigitaccen ƙara dai dai lokacin da Daddy ya shigo gate ɗin gidan, domin ya fita ya ɗan siyo musu yan kayayyakin da zasu bukata kafin gobe in Allah ya kaimu, ko gama gyara parking baiyi ba ya fito daga motar yayi cikin gida da gudu. Dai dai lokacin da Kaka ke saka na ta ihun ta nufi Ameenatou tana faɗin, "Wallahi Zulai kike ko waye sai kin sakamun kurwan jikata, dama ai na ji tarihin dangin ku an ce kaf Mayu ne saboda Maitanku ma kuka ƙi Auruwa shine aka laƙaba ma Ɗa na, to wallahi jikata ta fi ƙarfin ki kurwan ta kur, ki zo kawai ki tsallaka ta tashi." Daddy ne da Al'ameeen suka shigo a ruɗe suna tanbayar lafiya. "Yauwa gara da Allah ya kawo ka Audu." Kaka ta faɗa ta kakalo wasu hawayen, tana face majina. Gaba ɗaya Daddy ya ruɗe ya isa gurin kaka da Ameenatou yana tambayar kaka lafiya. "Ina fa lafiya Audu garin jajibe-jajibe irin naka kaje ka Auro mana Mayya, gashinan ta kama Ameenatou." Kaka ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka tana cigaba da jijjiga Ameenatou. Ita ko Hajiya ƙarama bata taɓa zaton sharin su kaka da wannan figigiyar yarinyar ya kai haka ba, Tabbas sai ta yi maganin su kuwa. Gaba ɗaya Hajiya Babba ta kasa motsi saboda da ganin sharri irin na Ameeenatou ƙiri-ƙiri domun ganin idon ta ta ga Ameeenatou na ma Hajiya Ƙarama gwalo da dariyar mugunta. "Wai Audu tsayawa kayi kana kallon ta ba zaka ɗauki mataki ba har sai jikata marainiyar Allah ta mutu ne." Kaka ta ƙarra saka kuka tana sallallami wai matan Audu sun asire mata yaro dole ta zo ta neman mai taimako tun wuri tun kafin su rabata da shi. "Ba dan na tuba ba tabbas yau da kunga asirin asali mu da muke mai da mutane kashi ma, to wallahi ahir dinku." Gaba ɗaya sun ishi Al'ameen ji yake kamar ya kwashe su ya mai da ƙauye, don shi irin mutanen nan ne da bai son hayaniya ya dawo ko hutawa bai yi ba ya haɗu da jaraban su kaka, tsaki ya yi ya juya zai fita, Kaka ta wuf ta sha gabanshi. "Ka ga wanda kayi ma tsaki nan gasunan tsaye da Audu da Mero, saboda baƙin hali an tsotsa a Nonon Uwa kana ganin ƴar uwar ka rai a hannun Allah Matar Uban ka ta kama mata kurwa Amma kake tsaki zaka fita to ba in da zaka sai Ameeenatou ta tashi eheee." Kaka ta ƙarisa maganar tana fiki-fiki da ido. "Audu in har na isa da kai ka sa Zulai ta tsallake Ameenatou, bayan ta tsallake ta kuma ta tashi sai ka rubuta mata takardar saki ta ƙara gaba don ba zamu zauna sa zuri'ar mayu ba, in kuma kaki ni yau a matsayina na uwar ka sai na ɗaga ma Nono kabi duniya eheee." Gaba ɗaya yan falon sai da suka razana da batun kaka, ban da Ameenatou da ita matuƙar murna tayi, maganar kaka kuma yayi dai dai da shigowar Hassana da Hussaina ƴaƴan Hajiya ƙarama sun dawo daga makaranta, sosai suka razana suma da maganar kaka. ************************* *ƘAUYE* "Wallahi Furera ina ta kewar guggo Ameenatou, ita ko tana can Binni tana cin daɗin ta." "Ke dai bari kawai Lantana ai ji nake kamar nima nayi tsuntsuwa in ganni a Binni ɗin nan." "Waya ga Fure a Binnni, Tab." Lantana ta faɗa tana kwashewa da dariya. "Ki ce dai waya ganmu a Binni ni da ke, kin ji ta shi mu shiga gari muga ina muka nufa ni duk zaman ma ya isheni fa." "Uhmmm ki bari kawai ai Ameenatou ta fara bamu kewa tun yanzu, na san da tana nan da tuni mun shiga gari. ************************* "Audu baka ji mai na ce ba ne wai."? "Naji Inna Amma don Allah ki soke maganar sakin nan zata tsallaka Ameeenatou, insha Allah zata tashi." Daddy ya ƙarasa maganar ya na mai durkusawa a gaban Inna. Gaba ɗaya yaran gidan sai suka ji sun tsani Ameeenatou don duk ita ce silar komai. "Kai Auduuuu Alllah............! *in ga ruwan comment sai ku ga ruwan typing*. *TEAM ƊIN AMEEENATOU GAFA AMEEENATOU TA ISO BINNI DAGA ZUWA TA FARA DA MATAN GIDA.*🤣🤣🤣 LITTAFINA NA KUƊI NE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MAGANA TA WHATSAAP TA NUMBER, KO KUMA A TURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abbdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU ALL, SHARE&COMMENT FISABILILLAH🥰 *Urs Xayyeesherthuo*💜 [12/1, 4:28 PM] +2348037420816: https://chat.whatsapp.com/IpsParMb6dOBXLpns86N2u °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-13* _*KALAMAN SOYAYYA🤍*_ _Zan So mukasance tare ne kawai da son ranka inko baka bukata na zabi bawa zuciyata hakuri duk radadin ko kunar da za ta ji,amman ina so ka sani,kar ka manta ina kaunarka har cikin raina._ _*TEAM AMEENATOU AYI KARO-KARO ASIYA MATA ABUNNAN FA🤭KO CIKO NE SAI AYI*_ _*MY GROUP MEMBERS ANTIES MASU SHARHI BARKA 😁SU GOGGOS MASU ƊUMAMA GROUP DAN ALLAH ABAMU WAJE MU SARARA😒✋*_ "Aradun Allah ko da Malam ne zai dawo yau ba Zan Yarda Zulai ta ci gaba da zama agidannan ba." Cewar Kaka tana fiki-fiki da ido kamar jinjirar munafika. Dady ya rasa abun fadi kawai yana kallon ikon Allah duk anyi shiru a falon. Kaka ta numfasa kan ta ce, "Ince so kake sai ta gama tsotse mata jinin bata tsallaketa ba? To maza ki tsallake mun jika komai ma ya biyo daga baya." Dady ya kalli Hajiya Karama kan ta ce, "ki tsallaketa dan Allah." Kamar ba za ta yi ba can kuma ta tuna abun da bata zato ma kaka zata iya abu mafiyin tunanin kowa. Hakan yasa ta tsallake Ameenatou. Tana tsallake ta kuwa ta ta shi tana attishawa tana, "Kaka, Kaka ki zo ta sakeni,Wallahi ta sake ni, Wayo kwakwalwar wuyana zafi anan ta shakeni kaka mutuwa zan yi shikenan wuyane ina jin ta kwashe hanjin wuyan." Riketa Kaka tayi tana hawaye da shekan majina, "Yi Hakuri Ameenatou na kin warke ba za ta kara kamaki ba kin san bana son maganar mutuwannan na fada miki ban so wallahi Ba za ki mutu ki barni ba aradu da ki mutu gwanda mun Audu ya mutu ma." Ta juya tana kallon Dady "Ka na gani kana kallo Matarka zata cinye mun jika? 'Yar 'Yar Uwarka amman ko ajikinka an riga an shanyeka ko? To ahir na ce rubuta mata takarda saki Hamsin dan uku ya yi kadan ina kallo." Dady ya kalli Kaka araunace yake fadin, "Inna Dan Allah kiyi hakuri bana so kiyi fushi ki bata dama zata gyara kuskurenta." "Iyeeee, na ce Iyeee Ashe ma ban isa da kai ba,yoo ko Malam Mahaifinka kafin ya bar duniya bana fada ya ja bare kai na ce ka saketa tun kafin in tarwatsa gidannan." Ameenatou ce ta ce, "Umm Kaka Kin san miye? Kin ga ita ta girka abincin can kuma ya yi dadi abarta tana mana girki irin wannan in ta kuma kamani sai mu korata ko?" Kaka ta ce, "kun ga 'Yar Albarka an cuceta kuma ta yafe dake batai gadon bakin hali ba, tabbas yau kun ci sa'ar Ameenatou ne amman da yau sai Dai ka zaɓa ko zulai ko ni Indo." Ficewa Al-ameen ya yi, ya yin da Hassana da Hussaina su ma suka nufi dakinsu. Kowa ya watse afalon anbar daga Ameenatou sai kaka. Kaka ta ce, "Yoo ni naga gyatumar fitina wato duk kowa ya yi daki anbarmu afalo gamu filajin ko? To ba a isa ba, ina kike Mero,mero,mero na ce ki fito nan." Hajiya Babba ta fito tana, "Inna Gani." Ta karasa maganar tana durkusawa gabanta. Kaka ta ce, "Ince mu anan kukeso mu dawwama Bama da dakin zamane?" "Aa Inna ga daki can angyara har kayan ku ma ankai can." Kaka ta ce, "To maza amun iso ga dakin nima inje in kwanta a kushin kamar kowa." Sai da Hajiya ta kaisu kan ta dawo dakinta. Ameenatou tsalle ta fara kan gadon tana waƙa, "Tab Kaka Ai bani ba kauye yasin kin ga gadon nan da di inaga irinsu ne a aljanna." Kaka ta latsa katifar , "Ba Shakka wannan abu kwai dadin zama kana lumewa kamar ka samu naman dawisu." A dakin suka hini har dare sai kai masu abinci aka yi, ban da tabe-tabe ba abun da Ameenatou take yi. Washegari. Ameenatou ta fita tana zagawa wani daki ta hango. Dakin Nauwara da Nusaiba, dake Nusaiba na bording bata gidan ita ko Nauwara tana aiki sai dare take dawowa in ta fita tun safe. Nauwara ta shiga wanka ta ciro kayan da zata sa harda su bra da pant Ameenatou ta shige dakin ba abun da idonta ya fara kaiwa sai kan bra din. Dauka tayi tana dariya sannan ta daura kan kirjinta , "Aradun Allah zan nunawa Onkul Al-ameen ya siyamun wannan abun saka Nonon ai nima na girma jibeshi ba laushi harda kushin aciki." Nauwara na fitowa da Mamakinta ta tsaya kallon Ameenatou tana, "Lafiya? meya kawoki dakinnan?" Washe baki tayi tana, "Ni ce Ameenatou da Kaka mu ka zo kuma." Murmushi Nauwara tai kam ta ce, "Welcome Ameenatou ta ajiyamun kayan in sa ko?" Ameenatou ta ce, "Aa ina Zuwa bara inje inunawa Onkul nima ya siya mun ina sa Nono ciki." Kallonta tai sama da kasa bata ga kirjin da za asawa bra ba kawai ta kyalkyale da dariya. Ita ko Ameenatou ko ajikinta yafawa tai a kirjinta tana tafiya tana kallo har ta isa bangaren Al-ameen. Kwance yake yana sharbam barci hankalinsa kwance. Dukansa ta fara yi tana, "Onkul tashi ka siyamun wannan ka tashi ka siyamun." Yana bude ido..... *Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments* _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 4:28 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-13* *MY GROUP XAYYEESHERTHOU FANS CLUB TABBAS INA YINKU OVER🥰🔥TEAM AMEENATOU ANTIES MASU SHARHI BAN DA GOGGOS YAN ƊUMAMA GROUP* ______ Mai zai gani? Bra ce sanye a kirjin Ameenatou tana nuna masa. "Onkul ka siyamun nima wannan ka ji, ka ga ya mun kyau ina so nima in fara sawa." Wani irin hamshakin Tsaki Al-ameen ya yi bai san lokacin da ya figi Ameenatou ya jafa waje tare da kulle kofarsa ba. Dafa kan sa ya yi, "Oh My God, Na tsani yarinyar nan amman tana neman takurawa rayuwata." Ameenatou kuwa bajewa tai tana bori da ihu, "Onkul wallahi ka fita sai ka siyamun aradun Allah ba inda zanje in baka siyamun ba, Kaka ki zo ki ce Onkul ya siyamun abun saka Nono nima zan sa nawa." Tuni kurarin Ameenatou ya baza gidan aka firfito. Kaka ce ta fara karasawa tana, "Meya Faru kuma Ameenatou kar dai waccen Zulai Mayyar ba ta barki ba har yanzu?" Kuka ta fara tana, "Kaka Onkul wai naje ina nuna masa ya siyamun wannan abun saka nonon shine ya koroni waje kuma ya kulle kofa, Kaka ki ce ya bude kuma ya siyamun ni." Kaka ta tashi tsaye da rike kugu kai ka ce Budurwa ƙauye, "Iyeee ai lallai Ameenu ka isa lallai ne tashen balagar tsuntsayen naka har ya kai haka da zaka jefomin Jika waje ba gaira ba dalili to ni da kai ne maza ka bude kofar nan kuma ka ɗauke ta kuje ku siyo in ba haka ba sai na tsinewa shegen goshinnan naka mai kama da albasar turawa." Nauwara ce ta karaso ta dafa Ameenatou tana, "Ameenatou ina wannan kikeso? To na bar miki kuma Uncle zai fito ya siyo miki wasu ma akasuwa amman yanzu ki fara sa wannan tashi ki daina kukan kinji." Share hawayen "tau Antu Naura kuma ki ce ya siyamun masu kyau." Hajiya Karama ta kallesu ta ce, "Oh Allah Gidadanci da ƙauyenci dai bai yi ba Arayuwa, ina brest din da za asawa bran ma kirji kamar kan giginya." Ta na karasa maganar ta juya ta tafi abun ta. Kaka ta ce, "Nace kinyi da Uwar gyatumarki mai kashin kwance da mijin ta mai ruɓaɓɓiyar kaciya kinji ko." Ameenatou ta ce, ,"Kaka ki barta na san haushi tana ji Antu Naura bata, ba ta irin nawa bane kuma yasin zan yi maganinta ai a agidannan haa haa." Ameenatou ta tashi tana tsalle ta shige daki. Ɗauko tsimmokaran dankwalinta ta yi tasa acikin brar kan ta sa ajikinta ta maida riga . In ka ganta kai kace wata falfela kirji ya tsaya jak kamar tumatur. Fitowan da zata yi suka ci karo da Al-ameen. "Onkul ka ga Antu Naura ta ban nata kafin ka siyomun ya mun kyau ko?" Wani bakin ciki ne ya kara turnike zuciyar Al-ameen da sauri zai wuce sai ga Kaka tayi charaf. "Kai Amenu maza ka dau Yar Uwarka kuje kasuwa ka siya mata rigar Mama kana ji na ko?" Ba tare da ya yi magana ba kawai ya fice Kaka na ganin Dady ta fara kuka, "Wai ni zan ma Ameenu magana ya harareni ya mun tsaki sannan kuma ya fice ya barni." Ta face majina da gefen zanin ana kuka wiwi. Da sauri Dady ya karaso, "Subhannallah Inna meya faru?" Kara fashewa tai da kuka. "Fisabillahi dan anga Malam baya duniya sai anemi wulakanta mu ni da Ameenatou a gidannan,yoo wai ni Al-ameen ni zai zaga ya ce mun Bakina kamar duwawun bera? Har ni zai kalla ya harara." Ta kara fashewa da kuka. "Dan kawai na ce ya dau yar uwarsa suje kasuwa asiyo mata rigar Mama kenan ni ban isa da shi ba ko? Ban isa ba ko." Face majinar ta kara kan ta kuma fashewa da kuka. "Shikenan, na ce shikenan daman na san ni ba kowa ba ce koma ban isa ince ayi komai agidannan ba." Dady ya ce, "kiyi hakuri Inna zai zo ya dauke ta suje kiyi hakuri dan Allah bana so kina kukannan haka kin riga kin tsufa yanzu ciwo zai iya rufeki dan Allah kiyi hakuri." Hajiya Babba ya kwalawa kira kan cewa ta kirawo Al-ameen nan take kuwa sai gashi. Da gudu Ameenatou taje ta dane cinyarsa ba yadda ya iya ba abun ya motsa ba Kaka ta fara suffar masifa. Ita ko Ameenatou sai lilo take mai ajiki minti ƙadan sai mintsini tun yana yi kamar bai ji ba har ya fara motsi. Ita ko ban da dariya ba abun da take masa takaici kamar ya haɗiye kansa. Dady ya ce, "Ka dau Ameenatou kuje kasuwa duk abun da take so asiyo mata komai da komai na bukata, maganar skul din ta ma zakuje ranar Monday in Allah ya kai mu." Al-ameen ya ce, "Dady Office zan tafi mai zai hana driver ya Kaita." Karaf Kaka ta ce, "Ka ci gidanku na ce ka ci gidanku ungo nan ba drevon da zai kaita da kai zaku eher mutum da yar uwarsa amman yana gudunta dan bakin hali, ansha a nonon gyatuma." Dady ya ce, "Hakuri za ka yi ka dau excuse in kun dawo kaje yanzu kam tun da anyi break kuje kawai i think yanzu 10:pm ma ta wuce." Ba yadda Al-ameen ya iya haka ya tashi babban tashin hankalin sa shine maganar siyo bra a kasuwa bai ma san ta yadda xai kwatanta ba ga kuma wannan aljanar yarinyar abun da kunya anganshi yaje siyan bra kuma da ita. "Onkul jirani insa takalmi na , "ta fada tana washe baki. Kaka ta ce, "Yawwa ka kulamun da ita kuma axaɓo mata bra mai Bala'in kyau ehee." Tun da ta shiga motsr nan ban tabe tabe da tambayoyi ba abun da take yiwa Al-ameen bai kulata ba ita ko ko ajikinta ta ci gaba kamar ana zugata, "Onkul yaushe za ka yi aure? Ka haihu kana daukan jinjiraye zannsma yaranka wanka da kaina aradu na iya har kai ma zan iya ma fa ko kashi kayi zan ma tsarki." Daidai da isowarsu kasuwar kenan ya yi paking tuni ta fito kamar an jefota....... *Me kuke tunanin zai faru?* *Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments* _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 4:28 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-15* _nayi mistake fejin baya maimakon 14 nasa 13 so take note wannan 15 ne dayan 13 din 14_ _*Afwan Ameenatou fans bana da lafiya ne kuka ji shiru🙏*_ _*Wannan fejin naku ne Harbeebbty da Aminiyata Ada kuji dadinku kadan domin namijin jajircewata yasa na baku fejinnan mai kama da ku😁*_ Free Page na daf da karewa wa inda suka biya sun huta😆 _____ Dai dai isowan wani mai mashine gashi ya shigo da gudu, Al'ameen bai san lokacin da ya dira a motar ba ko rufewa baiyi ba ya janyo Ameeenatou suka tafi tamkar zasu faɗi gaba ɗayan su yayi sauri ya dafe Motar ta tashi. Wiki-wiki Ameenatou tayi da ido ta lafe a jikin shi, tuni har Mutane sun fara taruwa kowa na tofa albarkacin bakin shi, finciko ta yayi ya jefa a Mota yana huce ya shige Motar bai saurari Mutanen da ke gurin ba ya figi Motar ya harba kan Titi, Sai da sukayi tafiya mai Nisa ba wanda yayi magana a cikin su gaba ɗaya Ameenatou a tsorace ta ke don ta sadaƙar da mashine ɗin nan ya bige ta sai tayi rugu-rugu, kawai Hausi ta tuna maƙociyar su da Mashine ya bige sai dai a ka cire mata ƙafa, tana gama wannan tunani sai kawai ta fashe da kuka. Parking Al'ameen ya yi dai dai wani guri da ba Mutane, ya fito a fusace ya jawo ta ya wanke ta da Mari, yana faɗin, "ke wacce irin mahaukaciya ce yanzu da Mashine ɗin ca ya bigeki fa,! banza wawiya ƴar ƙauye kawai,! kuma wallahi ko ki mun shiru ko in tafi in barki a gurin nan masu satan mutane su harbeki kowa ya huta da jaraba, kawai Daddy ya tashi ya jawo mana Annoba a gida.! "Onkle ya fa isheka don ba tsoron ka nake ji ba da zaka tasani kana mun masifa, kuma Yasin muka koma gida sai na faɗa ka da kaka ba dai ni ka mara ba, wallahi sai na ce ka mun shegen duka, ka turani titi kuma wai Mota ya kasheni saboda ba ka ƙauna ta." Ameenatou ta ƙarasa maganar tana juyawa ta shige mota ta cigaba da kukan ta. Takaici gaba ɗaya ya gama cika Al'ameen ya rasa mai zai ma yarinyar nan ya huce ne, ji yayi har kan shi ya fara ciwo don shi har ga Allah bai son dogon magana balle hayaniya amma wannan mayyar yarinyar ta sa shi yana ta buɗe murya a titi. Komawa motar yayi ya ja ya kama hanyar komawa gida da ita yace sai dai duk abun da zai faru ya faru, Muryan ta yaji tana cewa. "Onkle ya zaka maidani gida baka siyamun rigar Nonon ba.? Banza yayi da ita, da ta fasa wani uban ihu ta tuma akan kujerar Motaar bai san lokacin da ya taka wani wawan birki ba, kaɗan ya rage ya bigi na bayan shi. "Wayyo Allah na ni Al'ameen yau Allah ya haɗani da jaraba.! wani tunani ne ya zo mishi a rai sai ya juya Motar ya nufi Asibitin shi da ita, ita kuma ta cigaba da birgima da bige-bige a motar kamar mahaukaciya. Suna isa ya fito ya buɗe gurin da take ya jawo ta yayi hanyar Office ɗin shi da ita, Sister Surayya ce ta hangoshi da sauri ta taɓo wacce take kusa da ita ta ce, "Sister Rukky ga mutumin ki can ya shigo da wata ƴar ƙauyen yarinya, yanzu ya shige Office ɗin shi." "Uhmm ni wallahi na haƙura da Doctor Ameeen kullum ina bin shi yana wulaƙanta ni." Wayar ta ce tayi ƙara da take ajiye a tebur ɗin gaban ta, jawo wayar ta yi, zaro ido tayi ganin mai kiran na ta. "kinga wai yau ni Doctor Ameeen ke kira da ma yana da Number ta ne.? Ta faɗa fuskar ta ɗauke da mamaki. " To ki ɗauka mana kar ta yanke kin san bai kira biyu shi." Da sauri Rukky ta ɗauka ta kara a kunnen ta. Amsa sallamar da tai mai yayi ya ce mata, "ki zo Office ɗina ina son ganin ki." Yana gama faɗa mata haka ya katse kiran. "Kin ji wai yana son gani na bari inje in ji." "Ok sai kin dawo." "Ke Meena ki mun shiru wallahi ko yanzun nan in miki Allura." Ai bai gama rufe baki ba Ameenatou ta ɗauke wuta, don duk rashin jin ta Allah ya saka mata tsoron Allura. "Alhamdulillah yarinya tun da na gano lagon ki kin shiga uku kuwa, mara kunyar ƙarya." Duk a zuciyar shi Al'ameen yake wannan maganar, bai gama tunani ba sai ga Rukky ta shigo tana wani karairaya kamar zata karye dama gata ita ta tafi kaman one sai fuska ta ci bleching ga kafar ta da hannun ta baƙinƙirin. Tun da ta shigo Ameenatou ke kallon ta, can da ta tuntsire da dariya har ta na faɗuwa ƙasa daga kujera, gaba ɗaya suka bita da kallo suna mamakin mai ya bata dariya haka. Ita ko in ta ɗago ta ƙara kallon Ruƙayya sai ta ƙara kwashewa da dariya. "Meeenah! will u shut up! ya zaki ta samu gaba kina mana dariya kamar kin ga mahaukata.! Al'ameen ya ƙara sa maganar cikin fushi. "To Onkle ba dole in dariya ba naga abun dariya, dama a mutane ma akwai Muchiya da zani ban sani ba, gani nayi wannan Matar tayi kama da muchiyar kaka da take tuka mana tuwo, kuma wai ƙonewa tayi naga fuskarta fari kafan ta da hannun ta baƙi."? Ameenatou ta ƙarasa maganar tana kara kwashewa da dariya. Gaba daya kunya ya lulluɓe Al'ameen saboda irin tijarar da Ameenatou take ma Rukky ya rasa ma mai zai ce mata. Ita ko Rukky ji take a duniya ba'a taɓa mata cin mutunci irin wannan ba, gashi yarinya ƙarama tana muzanta ta a gaban wanda ta fi so duk duniya, a yau taji tana da ta sanin yin bleaching, da sauri ta juya zata fita Al'ameen ya miƙe da sauri ya bita yana kiran ta, "Rukky please ki tsaya kiji don Allah." Ko waigowa ba tayi ba, riƙe kanshi yayi da yaji yana sara mai ya koma Office ɗin, samun ta yayi tana ɗaɗɗaga takardun da ke kan tebur ɗin office ɗin. "Meeeeeenah! wai ke baki san darajar ɗan adam ba ne, baki da hankali wannan ba ta girmeki ba." "To ni ina ruwa na, ni na ce ta zo tana ma fari da ido tana wani girgiza jiki kamman sandar suluka shine naji ta ban haushi kuma naga kana kallon ta meyasa ni bazaka kalleni ba, ban fita kyau ba ma ni ƴar duma duman Kaka Nono ne kawai ta fini kuma ni ma ya fara fitowa kuma bari ka ganshi." Ta miƙe tana ƙoƙarin ɗaga mai riga. "Ke baki da hankali ne na ce miki ina son gani ne.? "Wallahi ni sai na nuna ma." Dafa kai Al'ameen yayi saboda tsananin sara mai da kan na shi ke yi..........✍️✍️✍️ TEAM AMEEENATOU HOW MARKET🤣🤣🤣 ni dai na fece Ameeenatouo tabbas tafi ƙarfi na nan fa kishi Ameenatou kaka keyi ikon Allah🤣🤣🤔🤔🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️ IN GA RUWAN COMMENT KU GA RUWAN TYPING YASIN🙄🙄 _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeeshert[12/2, 10:01 AM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-16* _*MAH GROUP MEMBERS MA SU SHARHINNAN ANTIES BA GOGGOS DIN BA FA😹👋IN SHA ALLAH ZA KU KARANTA AMEENATOU ABAGAS AMMAN MUTANE UKU KACAL🤸‍♀️💃*_ Ita kuwa Ameenatou da gaske ban da kokarin tuɓe riga ba abun da take yi. Ganin abun nata ba wasa ya sa Al-ameen saurin riƙe mata hannu yana, "Please Meena duk na miye wannan ki bari kinji." "Onkul,Onkle Wallahi ni ka sake mun hannu sai na nunama ai nima na ce ina da shi,Yasin ina da shi kuma in na girma ma sai sun fi nata kyau." Wata gigitacciyar tsawa ya yi da Ameenatou ba ta san lokacin da fitsari ya fara zubo mata a jiki ba. "I said You should stop it , ki mun shiru awajen ko in miki allurar nan." Kallon jikinta ta yi ta ga fitsari na zuba cikin rawar murya ta ce, "Onkul ni bana son rigar Nonon ka kai ni gida gun kaka." Wani irin kallo ya bita da shi cike da tsaki, a zuciyaarsa tunanin yadda za ta shigan masa mota da wannan kazantar yake wata irin tsanar yarinyar ne ya kara shiga zuciyarsa. Wayarsa ya dauko ya kira waya cikin minti biyu kuwa sai ga wani ya shigo . "Yawwa Ibrahim taimako Please ka kai mun wannan yarinyar gidan mu ku shiga keke nafef in ka kaita sai ka dawo." "Ok Sir An gama ." Ameenatou ta bisu da kallo. Al-ameen ya ce, "Oyaa follow him." Tsayawa tai tana kallonsa Dafa kai ya yi ganin bata ma fahimci me yake faɗi ba ya ce, "I said ki bi sa ku tafi zai kai ki gida." Ta shi tai kamar sabuwar bazawara tana wiƙi-wiƙi da ido ta bi bayan Ibrahim sai da su ka je bakin kofa tuyo tana, "Onkle ka tawo mun da rigar Nonon kar ka manta." Wani takaici ne tsantsa da kunya ya damƙe Al-ameen. Ita ko Ameenatou tsayawa tai tana, "Onkle ka ce to ba ka amsa ba fa kuma wallahi mai kau ina so in ba ta mun kyau ba aradun Allah Sai an maida an samo mai kyau." A fusace Al-ameen ya ce, "Oh My God Ibrahim take her out please." Rike hannunta Ibrahim ya yi suka fita tana mita, "Nima ai kuma na iya turancin irin na onkul wasi mi si niem in ka zo gida zan rama kuma." Suna komawa gida kuwa Aguje Ameenatou ta shige kaka ta fara, "Ina rigar Maman kuma ina Ameenun na ganki ke ɗaya." Taɓe fuska ta yi kamar za ta yi kuka, "Kaka fa munje kawai wani mai mashin ya jo zai bige mu, onkul ya riƙe ni kin san wani irin riƙo ya mun? Hmm yasin irin yadda muka kalla a tabijin dinnan jiya na masoya." Ta sheƙe da dariya tana miƙawa kaka hannu. Miƙa mata Kaka ta yi tana, "Ban baɗo ga dukkan Alamu Ameenu son ki yake munafurci ne da iya shege irin nasa kawai." Ameenatou ta ce, "Eh mana Kaka kuma wata mai bleaching fa ta zo tana ta wani kanne masa ido Kaka yasin inna kama ta ko? Sai na mata targaɗe a kumatu aradu." _______A gogon hanunsa ya kalla da mamaki ya ga saura 30minut atashi a office da sauri ya tashi da kan sa ya nufi office din Rukayya. Tana ganinsa ta sunkuyar da kai. "Excuse me Please,Ruky ki yi Hakuri kanwata ce daga kauye so kin san yanayin su."cewar Al-ameen. Rukayya ta ce, "Ba komai Sir na fahimta." Ta karasa maganar tana sakin wani murmushi da ita kadai ta san ma'anarsa. Ya ci gaba da magana, "I need your Help please Ruky." Da mamaki Wai yau Al-ameen ke mata magana asanyaye kuma har yana neman alfarma agareta ashe akwai ranar da za ta yi amfani wa Al-ameen. Murmushi ta kara sakewa tana, "Ba komai Sir ka fada duk abun da ka ke so As you wish za a yi." Al-ameen ya ce, "Thank you,so nake kije kasuwa ki siyo mun........ Sai kuma ya kasa fada ya rasa ma ta inda zai fara. Ya ci gaba, "Um wannan Abun what ma...." Ya dafa kan shi a zuciyar sa yana fadin wannan yarinya ta haɗani da aiki yanzu in koma gida babu ya zama matsala amman tabbas ba abun da zai hanani hukuntata. Ruky ce ta katse shi da fadin, "Am waiting Sir lafiya dai ko?" "Am totally Confuse Ruky." Ya fada yana kara dafa kansa. Can kuma tunani ne ya zo masa takardda ya dauko ya rubuta breziya ya mika mata. Tana karantawa cike da mamaki ta dago tana kallonsa asaninta dai Al-ameen ba ya da aure kuma ba ya shirin yi. Kau da kansa ya yi,ya ciro kudi dim akalla in bai kai dubu hamsin ba ya yi arba'in. Ya ce, "Ki siyo ko guda biyar ne." Washe baki tayi ace brar da bata wuce 1k 2k shine za abata dumin kudinnan ta siyo guda biyar? Aranta take fadin , "Oho dai koma wa zai siyawa ni gaba ta kai ni gobara titi a jos." Fita tai da rawar jiki ta nufi kasuwa. Bra guda 12 ta siyo yan 800 kuwa hankalinta kwance ta sanya sauran kudin a ajaka, tana zuwa Office ta miƙa masa. Karba ya yi yana fadin, "Thank you." Kan ya ciro bandir din dubu goma ya miƙa mata, RUKAYYA idon naira baki har wuya ana washewa an samu duniya. Ledar ya dauka cike da takaici ya fita a office din da niyar tafiya gida. ****# Kaka ce zaune tana surfa uban masifa wa Hajiya Karama. "Na faɗa miki Aradu in Ameenu bai shigowa da Yar Uwarsa rigar Mama ba gidannan za ku sha mamaki sai na ɗaga gidan na juyashi ta yadda kowa zai zazzage Mussamman waccer ta ɗakin mara kunya sai na mai da tsinke kamar yadda aka aurota." Daidai lokacin Hajiya karama ta fito tana tauna cingam da tafiyar kasaita, "Yoo mu kam kuma ai mun shige sai yadda Allah ya yi da mu, gida gabadaya ya sauya ban da wari ba abun da ke tashi,ke jummala fito ki sanya mana turaren wuta ko ma ɗan ji sanyi arai." Kaka ce ta dakatar da ita, "ke ƙaniyarki na ce ƙaniyarki kinji ko wa ya sanya maku gidan bashi? Yoo ke waya kai gyatumar uwarki bashi Matar da in ta zabga kashi tun ada sai an kira kamfanin iska da turare sai waje ya shekara ba a shiga amman yanzu har kina da bakin magana da shegen goshi awajen kamar jirgin sama,ni na rasa ma me Audu ya gani ajikinki Aradu, sai shegen faɗi amman ko irin lankwasar kwankwason nan ma mai fidda kyau baki da ke da slifas ba maraba ana tallan kugu ke kina tallen faranti bani waje agun." Ɓata rai Hajiya Karama tai ta nufi daƙi. Kaka ta ci gaba da magana, "Ji yadda ta kumbara kamar audugar sawa yara aɗuwawu taji fitsari in ce ai dukana za ai." Ameenatou ko ban da dariya ba abun da take. Sallamar Al-ameen ne ya katse su duka Ameenatou ta tashi aguje.... _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/7, 2:16 PM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-17* Ameenatou ta nufesa tana, "Oyoyo Onkle ka siyo mun rigar Nonon ko?" Kau da kansa ya yi cike da ɓata rai ya miƙa mata ledar batare da ya jira ta ƙara fadin uffan ba ya shige ɓangaren shi. Ameenatou kuwa tsalle tasa tana ihu, "Kaka Kin gani Onkle Al-ameen ya siyomun rigar Nonona irin na Antu Naura." Washe baki Kaka tayi tana faɗin, "to ko kaifa ɗan albarka, in da haka kake kula da ƴar uwar ta ka marainiyar Allah yaushe zan damu, Amma da yake an biyo baƙin halin Uwa shiyasa, tashi muje ɗaki ki gwada muga yanda ya yi na san ma dai zai miki kyau, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu." Kaka ta ƙarasa maganar tana hararar Hajiya ƙarama da ta fito daga kicin. "Oh yanzu Al'ameeen saboda rashin aikin yi ne da taya ɓera ɓari ka siyo ma wannan beran yarinyar bereziya har kala goma, tabdijam to ina Nonon da za'a saka abu kaman allon mayu, Allah ya kyauta ƙauyanci irin na ƴan ƙauye kuwa." Hajiya ƙarama ta ƙarasa maganar tana hayewa sama da sauri, don ta san in har ta tsaya sai kaka tayi mata zagin ƙare dangi. "Eh lallai wuyar ki ya isa yanka, tabbas za ki ga tijara don kin samu na haƙura ranar ban sa an kaɗaki gidan mai dattin hula ba ko, shiyasa har ni kike zagi bari Audun ya shigo zaki san kin zageni." Kaka ta ƙarisa maganar ta mai fashewa da kuka. "Kaka kiyi shiru ki barni kawai ni da ita zan miki maganin ta a gidan nan, zata san waye Ameeenatou kaka tabbass." "Yauwa ƴar albarka, shiyasa nake alfahari da ke ai, navsan kevɗin jinina ce ban ce ki ragawa kowa ba gidan nan ehe kowa yayi miki ki mishi." "Angama Kakan Ameeenatou ikon Allah, tashi muje in gwada rigar nono na kinji." ASIBITI "Sister Surayya ni abun ya ɗauremun kai, ko dai Dr Al'ameen aure zaiyi,? to in ba aure ba mai zaiyi da breziya, saboda tsaban cin fuska ma ni zai aika in siyo mai bresziyar kayan aure, ni kaina gaba ɗaya ya kulle a lokacin da na ƙarɓi kuɗin saƙon shi." "Hhhhh sister Rukayya kenan, ke dai kawai ki ce kin ga kuɗi ya ruɗaki kin mance da kishi sai yanzu hankalin ki ya dawo jikin ki, kika sani ko wannan yarinyar da suka zo tare ya siyan ma." "Yarinyar da ko ƙirgan dangi bata fara ba balle nonuwa." Cewar Rukayya. Surayya ta ce, "Ko ma yane dai tunda kin samu rabonki ai shikenan yanzu abani rabona." Harara Rukayya ta bi ta da shi kan ta tashi tana, "Wannan kudi kam ai ya shiga kuma ba fita Allah sa gobe yazo ya ce asiyo masa pant ma,kuma in sha Allah indai na cika Sunana Rukayya kamar Anyi an gama na Auri Al-ameen." Ta shige tana rangwaɗa. Dariya Surayya tai tana, "To ai shikenan Allah ya tabbatar da alkairi." ******Kaf sai da Ameenatou ta gwada breziyoyinnan suna shewa da kaka kai kace sabin kamu ne. Tana cikin sa kaya taji alamar maganar Hajiya Karama na fitowa. Ko bari ta karasa sa rigar ba tai ba ta ce, "Kaka ina zuwa." Da gudu ta nufi kitchen, robar yaji ta ɗauka,ta nufi ɗakin Hajiya Karama sidif sidif ta shige toilet. Buta ta dauka saida ta ciketa da ruwa dam kan ta juye yajinnan aciki. Ta fito tana dariya. Adaidai kofa ta ci karo da Hajiya karama . "Ke bagidajiya mai kikazo mun aɗaki?" Ameenatou ta murguɗa baki kan ta ce, "Hassana da Hussaina na zo nema muyi wasa ko da gaba ne?" "Iyeee Ni kike fadawa hakan da shegen ido kamar na bera." Cewar Hajiya Karama. Ameenatou ta sheƙe da dariya, "oho dai ni ban da duwawun akuya." Ta zura aguje. Hajiya karama na shiga ɗaki tana, "Wannan yarinya dole in dau mataki akanta wallahi cikinama ya murɗa bara in shiga toilet in fito kan dai in tafi anguwar nan." Aiko Hajiya karama ta shiga toilet cikin nishaɗi ta zabga uban kashinta tana nishi. Tana gamawa ta janyo buta domin tsarki. **Ameenatou kuwa na can na zabga uban dariya. Kaka ta ce, "ke wai lafiyanki kuwa?" "Hhhh Kaka ba za ki gane bane bari bomb din ya fashe ka...... Kan ta karasa suka jiyo karar Hajiya Karama tana. "Na shiga uku jamaa...... _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthu[12/8, 1:06 PM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-18* _*Anata tambayata wai ba kalamai ne?😹to tabbas akwai su yaku fans dina masu kwamushemun kalaman love ku saurara:*_ _*KALAMAN SOYAYYA🤍💫*_ _Ban yi karyar cewa ba zan rayuwa in babu kai,amman ina so kasani cewa rayuwata ba za ta taba samun walwala ba har sai da kai cikinta, ka rayu dani Ruhiy! Domin inganta mun rayuwata,ina sonka_ "Zan Mutu,Na shiga uku,ku kawo agaji." Nan da nan Kaka,Hajiya Babba da Ameenatou aka nufo ɗakin Hajiya Karama domin dubawa ko lafiya. Suna shiga suka tarar da ita kan gado tayi goho tana ihu, "na shiga uku ya shige mun ciki, can ciki wallahi ina jin macijini acikin ruwannan wayyo Allahna shikenan ya shige,ko yaushe zai fito oho."sai hawaye. Hajiya Babba ta karasa tana dafa ta, "Momyn Husaina lafiya kuwa?" Ƙaraf Ameenatou ta ce, "Wallahi ni ce nan nasanya mata yaji acikin buta tayi tsaki duwawun ya soye, waya ce ta na rainamun Kaka." Ta kyalkyale da dariya har tana rike ciki. Kaka ta ce, "Au to Ma sha Allah Ameenatou na shiyasa nake sonki maganin mara kunya ai kenan gwanda da akayi maganin takashin maga yadda za ayi rashin kunyar." Ta yi tsaki kan ta fice. Ameenatou ta bita tana dariya. Hajiya karama ta ce, "Wallahi ba zan yafe ba, Allah ya isa,Allah saka mun shegiyar yarinya mai kama da aljanu." Hajiya Babba ta zauna gefen gado ta dafa Hajiya ƙarama ta ce, "Momyn Hussaina na faɗa miki ki daina shigar harkar Inna da yarinyar nan, kwata-kwata inna bata da daɗi kina dai gani ka mata biyayya ma ya aka cika balle, don Allah duk abun da zasuyi a gidan nan ki daina kulasu sai a zauna lafiya." "Amma Momyn Al'ameen kina gani haka zamu zura ido matar nan ta zo har gida ta dunga mana tijara jikar ta ma tanayi, ni ba abun da ke ƙonamun rai irin wannan shegiyar ƴarinyar mai kama da zubin buzaye, duk ita take ƙara in giza kakar take ma mutane wulaƙanci." "To ni dai na baki shawara ki kiyaye musu, kina ganin gashinan yarinya tana neman naƙasaki ta illataki." Hajiya babba ta ƙarasa maganar tana mai fita daga ɗakin, tana kuma dariya ƙasa-ƙasa ganin in da Hajiya ƙarama ta yaye zani tai ɗai-ɗai a kan gado tana jin iskar fanka na shigan ta, duk ta fita hayyacin ta duk wannan gayun ya gudu a lokaci guda, ga hawaye shaɓe-shaɓe da majinu. Duk abun da ke faruwa Al'ameen naji kasancewar yana ɗakin momynsu suna magana da ita jin ihun hajiya ne yasa ta fita da gudu don ganin meke faruwa ta bar Al'ameen a ɗaki, bayan ta dawo ne take faɗa ma Al'ameen abun da ya faru shi kanshi sai da yayi dariya. "Wallahi momy yarinyar nan bata da hankali, zanyi maganin ta kuwa a gidan nan." "Kar ka kuskura ka jawomin bala'i gurin kakan ku, karka taɓa ta domin ka taɓata kasan a kaina tsohuwar nan zata huce saboda haka naka ido." "Shikenan sai a bar yarinya ta dunga hauka da rashin kunya baza'a tsawatar mata ba, shikenan Momy na rabu da ita,amman tabbas ta kuma shiga gaba gonata ba zan mata da sauki ba." Ya ƙarasa maganar yana mai tashi ya shiga kicin yasa abinci ya wuce ɗakin shi. ********** Suna Shiga ɗaki Kaka ta ce, "Allah miki albarka Diyar kwarai ai kin birgeni wallahi maganinta kenan." Ameenatou ta kyalkyale da dariya "Ai yasin ka dan ma ta gani ba ita yar gayu ba za ta ga gaye ai, Yauwa kaka tun da na gama gwadawa bari in ɗauka in je ɗakin Onkle in gwadamai shima yaga in da yamun kyau ko Kaka.? "Sosai ma kuwa Ameeenatoun kaka yi sauri kije ki gwada mai na san zai ce kinyi kyau Watakil ma ya kyasa." Ameenatou ta washe baki, "Kaka Miye Kyasa?" "Ina nufin watakil ma ya fada ramin soyayyarki?" Cewar Kaka Ameeenatou ta ce, "Iyee kuma fa wallahi nima ina son shi Kaka ki cewa Baba Audu ya Auramun shi kinji." Kaka ta ce, "Yar baɗo ba kunya, tabbas haka za ayi,bari audun ya dawo,yanzu dai jeki nuna masa ki dawo." Ameenatou ta kwashi bereziyon ta fita da gudu zuwa ɗakin Al'ameen don ta gwada ma Al-ameen. Zaune yake yana cin abinci kamar daga sama ta hankaɗo kofa. "Onkul ka ga yadda ya mun kyau ko? Ai kaka ta ce za ka kyasa ni." Wani irin takaici ne ya kama Al-ameen bai san lokacin da ya zaro belt ya fara jibgarta ba. Ihu take tana, "Kaka zai kashe ni, na mutu nikam wayyo cikina,wayyo maxaunina ya balle......... _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/9, 3:35 PM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *FREE PAGE-19* _*KALAMAN SOYAYYA🤍💫*_ _Ina Sonka! Kalmar sam bata mun wuyar furtawa gareka,kasan dalili? Ina rayuwa ne da soyayyar ka araina,amman duk da hakan xan so ace ana so bayan numfashi domin kuwa zan ci gaba da sonka a ko ina,a ko yaushe Noorry_ *_SAURA FEJI ƊAYA FREE PAGE YA ƘARE WA INDA BASU BIYA BA SU HANZARTA BIYA TABBAS DOMIN YANZU AKA FARA AMEENATOU KO INCE YANZU ZA A FARA😹😹💔💔_* ************ Kaka ta fito da gudu ta fincike Ameenatou tana, "Ƙaniyarka Ameenu na ce ƙaniyarka ka ci gidanku, a hakan zan aura ma ita? Lallai ma wato ka samu jakar duka to ahir dinka wallahi, kaf danginmu ba wa inda sukai wannan mummunan Hali na duka sam." Ficewa ya yi yana tsaki ba tare da ya ce komai ba. Hajiya Babba kuwa tana jin su taƙi fitowa domin ta san tana fitowa abun zai koma kanta ne. Ameenatou ta kalli Kaka. "Ni wallahi Kaka kar afasa auren ina son shi fa ni kar ki ce zaina dukana aradu son unkle ina yi kumq in ba a aura mun shi ba mutuwa zan yi fa." Kaka ta buɗe baki, "Iyee bar batunnan in ce yau Audu zai dawo daga tafiya? In sha Allah adaren yau za ayita ta kare za ki aureshi amman tabbas Sai nayi mai sharadi da kashedi kan dukanki yana fama da kai kamar na bazawarar agwagwa." Ameenatou ta share hawaye, "Yawwa Kaka kuma wallahi sai na rama abun da ya mun nima kuma sai na rama Ai." Kaka ta ce, "Yo nasani ai ba acin bashin mu a zauna lahiya ko da ta tusa ce." _____Dare Zaune suke Afalo duka nin su Dady ya dawo daga tafiya. "Yawwwa Al-ameen gobe Monday ya kamata Ameenatou ta fara zuwa makaranta."cewar Dady. Al-ameen ya ce, "To in sha Allah Dady,Amman da Nawwarata ta kaita in zata wuce Office." Karaf kaka ta ce, "To anƙi Nuauran ta kai ta, ka ci gidan ku na ce, kai zaka kai tan, Audu kai kuma daman ina da magana da kai." Dady ya dago kan ya ce, "To Inna ina saurarenki." Kaka ta yi gyaran murya kan ta gyara zama, "So nake A aurawa Al-ameen Ameenatou! Wani irin jin kaf yan falon sukai Mussamman Al-ameen da ya ji wani hatsabibin sauti na ratsa masa zuciya. Hajiya karama ce kawai ta iya furta, "Wonder Shall Never End!!" Kaka ta ci gaba da magana, "Tun da naga alamun suna son junansu kuma yarinyar nan dai ta isa Aure shi ko kokarin tsufa ma yake ina laifi dan ta taimaka masa ta aureshi." Ameenatou ban da washe baki ba abun da take. Al-ameen bai san lokacin da ya fara magana ba, "Haba Kaka arasa da wa za a haɗani sai wannan mahaukaciyar kazamar yarinya, Never wallahi ban ma da ra ayin aure bare ma ko da ace ina da wallahi ba zan auri wannan mahaukaciyar ba." Ya fada yana nuna Ameenatou kan ya fice afusace. Wani irin ihu Ameenatou ta sake, "Kaka ni wallahi onklu ina so,Kaka shi ina So ni Wallahi shi ina so." Nan take Kaka ta fashe da kuka, "Yanzu Audu kana gani? Na ce kana gani 'Ɗanka yake zagina? Yo zagina mana tunda ya zagi Ameenatou ai dani ya yi nice mahaukaciyar Kuma kazamiya? Kuma Wallahi in baka Aura masa Ameenatou ba,ba abun da zai hanani tsine ma." Ta fada tana face majina. Hajiya Babba na ganin haka ta tashi da Nusaiba,Naurawa ma ta bita,Hajiya Karama ta ce, "Hassana,Husaina maza Oya kuje ku kwanta wannan lamarin yafi karfin kunnuwanku muje daki maza." A hankali Dady ya ce, "Inna Dan Allah kiyi hakuri in sha Allah ba abun da zai hana a hada Ameenatou da Ɗan Uwanta kiyi hakuri Dan Allah." Gyara zama ta yi ta ce, "Audu,Audu,Audu sau nawa na kiraka?" "Sau uku." Cewar Daddy. "To ina so a ɗaura Auren Ameenatou da Al-ameen a gobe......... _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/12, 9:15 AM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_ _SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_ _*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_ _NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_ _*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_ *LAST FREE PAGE-20* _*Wannan shine fejin kyauta na karshe duk mai son ci gaba da karanta AMEENATOU zai biya 300 kacal tsarin yadda za a biya na kasa😹💔Masoya a hito ahadamun kudin tafiya dubai, ku nuna mun soyayyar ku ta hanyar siyan littafinnan eheeen masu sata😰🙏🏼 kuyi hakuri in kinsan zaki siyane dan ki fitar mun dan Allah kar ki siya*_ Dady ya zaro ido "Inna Gobe fa ki ka ce? Gobe kuma? Ina laifin Ki bari a hada dana Nauwara karshen watannan?" "Audu na ce adaura Auren Ameenatou da Ameenu gobe in dai ni ce uwar da na haifeka." Cikin firgici Dady ya ce, "Inna ki mun wannan alfarmar Dan Allah." Kara fashewa da Sabon kuka kaka tai tana yi Ameenatou na tayata. "Yanzu ni ban isa da kai ba kenan ko Audu? Matan ka sun shanyeka sun baka Nono ka sha ince bani ba? Ta janyo zani tare da face majina. "To na rantse sau saba'in da bakwai harda digo biyar in baka Aurawa Ameenatoun dan uwanta ba,bani ba kai ." Dady ya ce, "Abun bai kai ga haka ba Inna,In Sha Allah za a yi yadda ki ka ce." Ba tare da ya jira maganar Kaka ba ya tashi kawai cikin sarkakiya ya nufi ɗakin Hajiya Babba. Dafa kansa ya yi tare da zama agefen gado . Karasowa Hajiya Karama tai ta dafasa tare da fadin, "Alhaji lafiya kuwa? Ka san dai ba cikakkiyar lafiya gareka ba,kada ka daurawa kan ka damuwa dan Allah,komai ya yi zafi maganinsa Allah." "Maryam ya Inna take so inyi da rayuwata Don Allah? Ina zan sa kaina, yanzu Al-ameen ya zai yi da Ameenatou wai cewa take fa Gobe adaurawa Al-ameen Aure da Ameenatou." Duk da kasancewar abun ya taɓa ta har cikin ranta amman sam bata nuna ba. Zama tai daf da shi tare da sake masa murmushi, "Wannan sam ba abun damuwa bane Dadyn Al-ameen ni duk tunanina ma wani abune, Ameenatou da Al-ameen duk ɗayane awajen mu,miye laifi dan Inna ta ce a haɗasu aure? Jifan tsuntsu biyu zamu yi da dutse daya,mu taimaketa na maraici sannan mu zaba mata miji wanda ba zai cutar da ita ba,ko ma ya Ameenatou take dole haka Al-ameen zai yi hakuri Yar uwar shi ce ba yadda zai yi." Dady ya gyara zama "Hmm Maryam! Al-ameen bai kula matan nan bama sai Ameenatou? Kuma wai aure a gobe? Ni na ce ma ta bari zuwa karshen wata a hada dana Nauwara amman sam taki na rasa ina zan sa kaina zuciyata zafi take mun." Hannunsa ta rike tana, "ka nutsu dadyn Al-ameen akwai lokacin da komai zai sauya,yanzu ba duk wannan ba biyayya ga Inna shine farko,ka kirawo Alhaji Adam anjima ka sanar da shi komai, gobe a daura auren, Al-ameen kuma in sha Allah zan kirasa cikin darennan mu tattauna ,ni dai kawai ayiwa Inna biyayya duk sauran abubuwan masu sauki ne, kuma dama ga gidan cen naka an kammala komai ina jin har kaya ansa so ba ma da wata matsala mu mu zauna anan ba sai mun koma ba shi Al-ameen da Ameenatou su koma,ina fatan watarana muyi alfahari da biyayyar da mukai wa Inna." Ɗagowan da Dady ya yi ya sake wa Hajiya Karama Murmushi, "Maddala da samun mace ta gari mai son farinciki da inganta rayuwar Ahalinta,yanzu bara naje na dubo Alhaji Adam mu tattauna in sha Allah hakan za ayi." Yana fita Hajiya ta kira Al-ameen a waya nan take kuwa ya xo. "Al-ameen na san ka fiye da kowa na san wanene kai da kuma kudirin ranka amman ka da ka manta farincikin iyayenka a kullum shine gaba domin inganta rayuwarka cikin aminci, ka da ka bijire mana,kuma ka da ka ce mun zalinceka kamar yadda Inna ta bukata gobe in sha Allah za adaura ma Aure da Ameenatou." Wani irin faduwar gaba Al-ameen ya ji wanda sai da hanjin cikin sa suka haɗe waje guda. "Momy! Me ki ke fada? Aure ni? Aure ni fa? Kuma Ameenatou Momy wallahi bana da buƙatar auren kowacce mace a duniyar nan bare Ameenatou, Momy me na maku kuke son hukunta ni da auren yarinyar nan." Karasa maganar ya yi hawaye na zubowa daga idanunsa. "Al-ameen ban san ka da bijirewa umarni na ko na Dadyn ku ba, ina so kasa aranka wannan kaddara ce da muke fatan kasancewar ta mai kyau,dole sai kayi hakuri ka yi hakuri Al-ameen." Share hawayen ya yi kan ya ƙaƙulo murmushin dole wanda azuciyarsa yana tuna yadda zai ladaftar da Ameenatou ne kawai,"In sha Allah da kanta zata gudu ta barni." A zahiri kuma ya ce, "Bakomai Momy." Murmushin ita ma ta bisa da shi, "Allah ya yi maka albarka." Da Ameen ya amsa kan ya tashi ya fice ba tare da ya ce komai ba. Yana fita ya nufi ɗakinsa kwanciya ya yi kawai ban da saƙe-saƙe ba abun da yake,babban tashin hankalinsa yadda ya ga da gaske safiyar nan fa yi take kuma wai aure za a daura masa da yar ƙauyen cen. Washegari Da sassafe Kaka ta fito tana kwaleleto , "Audu na ce za ka fito Aɗaura Auren Ameenu da Yar Uwarsa ko kuwa ?" Dady ne ya fito yana, "Inna Gani za adaura in sha Allah,jiran Alhaji Adam nake zai tawo da goro." Kan Kaka tai magana kuwa sai ga sallamar Alhaji Adam. Amsawa sukai a tare Kaka ta ce, "Yawwa Dan albarka in ce kaine Waliyin Ameenu ko?" Murmushi ya yi, "Eh in sha Allah Inna." Kaka ta washe baki, "Yawwa to maza adaura zam zam." Dadyne yasa Al-ameen ya kirawo masa wasu daga cikin makotansu domin sheda daurin Auren. Haka Al-ameen ya kasance sam ba kumahari da ka gansa za ka san takaici fal cikin ransa amman abun mamaki wani lokacin sai ya sake murmushin da shi kadai ya san ma'anarsa. Ameenatou kuwa na ɗaki ban da tsalle tsalle da murna ba abun da take taso fitowa Kaka ta hanata wai ai ita Amaryace kuma boye amare ake hakan ya bata damar tiƙan rawa tana murna aɗaki yau tayi aure. A gaban Kaka aka daura auren Al-ameen da Ameenatou abisa sadaki Dubu ɗari da Alhaji Adam abokin Dady ya bada. Ana daurawa wata irin guɗa da Kaka ta yi saida ya zagaye illahirin gidan. "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah an daura Auren Ameenatou da Al-ameen yan bakin ciki sai dai su mutu." Nan take Dady suka fice da abokansa. Ita kuwa Ameeenatou ta fito da gudu ta rungumi Kaka tana, "Kaka da gaske wai yanzu ni matar aure ce kuma Matar Unkle Al-ameen?" Kaka ta ce, "Eh mana yan bakin ciki kam sai dai su mutu." Hajiya karama ce ta fito tana, "Cab Lallai Al-ameen ya shiga kaddarar rayuwa wayaga kwaila wannan kam fanko aka aura masa." Kaka ta ce, "me kika ce? Na ce kin ci gidanku da shegen baki kamar an taune gafiya bani waje ni." ***** Ranar ko zuwa breakfast Al-ameen bai yi ba. Bayan an gama kowa na hutawa Kaka ta ce, "Audu ince yaushe za a kai Ameenatou gidanta dana Al-ameen ne?" Dady ya ce, "Inna na ce ko za abari ayi mata siyayya kafin lokacin bikin Nauwara sai akaisu duka." "Aa aa na ce maka Audu haka kawai yara da aurensu kuma suna zumudin juna ace za arabasu? Sam ban lamunci daukan hakki haka ba,in ma za ka sani ka sani daren yau za akai Ameenatou gidan Al-ameen eheee." Dady zai yi magana Hajiya Babba tayi saurin fadin, "Bakomai Inna Yanzu zan bincika mata sabin kayan Nusaiba a hada mata kawai su tafi zuwa lokacin bikin in aka hada wasu sai akai mata." Kaka ta ce, "To Uwar azagwaigwai yau kam kinyi hankali ba shakka har kin fi mijin naki, hakan zai fi daren yau akai yara gidansu na sunnah." Hajiya karama ta ce, "Hmm akwai kallo,wayaga zumuɗin juna." Dady ya ce, "Nauwara ki kira mun Al-ameen awaya ya zo ɗaki ya sameni." Yana fada ya tashi awajen. ***** Jiki sam ba kwari Al-ameen ya nufi ɗakin Dady. Da sallamarsa Dady ya amsa. "Yawwwa Ameenu ga Keyn gidan cen nan domin a ciki zaku tare zuwa dare in sha Allah na san baku da bukatar komai hatta kayan abinci akwai sai dai inyi maku fatan alkairi,kayi hakuri da halin Yar Uwarka ka yi hakuri ka danne zuciya Al-ameen watarana sai labari, sannan maganar skul dinta kuma kaje ka karbo mata uniform din ta fara zuwa ranar Monday in sha Allah, Allah ya yi maka albarka." Al-ameen ya amsa da Ameen kawai kan ya fice batare da fadin komai ba. Dare na yi Ameenatou ta tsalla kwalliya,jan baki har kasan labba,girar kuwa har kunne,kamar dodonniya, ta zauna gefen gadon Kaka ana jira atafi. Aiko Dadyne ya yi sallama yana , "Inna in kun shirya ku fito,ga su Hajiya ma,mu rakata sai mu dawo ko?" Kaka ta ce, "To, to to gamu nan yanzun nan ma kuwa kasan amare sai da rarrashi ga mu nan tafe." A motar Dady suka je aka kai Ameenatou har gidanta ban da kalle-kalle da tabe-tabe ba abun da take,domin a kyau da komai wannan gidan ya ninka na Dady kai ka ce Aljanar duniya. Ba ka ce Amarya aka kawo ba domin tuni ta ware tana zagaye gidan. Hajiya Babba ta nuna mata wasu ɗakuna biyu masu kallon juna. "Yawwa Ameenatou wannan shine ɗakinki,wancen kuma na Al-ameen." Kaka tai karaf ta ce, "Au har raba masu ɗaki ake? To ahir irin haka ke janyo kishiya a banza baku iya tattalin miji ba, Ameenatou kar ki kuskura ki kwana ɗaki daban maza kuna kwana ɗaki daya,haka kawai acuceku to ban lamunta ba." Hajiya karama ban da ummm ba abun da ta iya furtawa. Dady ya ce, "to mun rakota,Inna ku zo mu tafi gida." Ameenatou ta washe baki "to Kaka da Hajiya, Baba Audu sai da safenku ban da waccer hajiya karamar kuma karta kara zuwamun gida ma." Kaka ta ce, "kar ki ji komai maza nemi waje ki zauna, Yanzu Ameenu zai shigo kin san dai me na fada ko? To a kiyaye sai mun zo zaman jego kuma." Ameenatou ta sheƙe da dariya. Kaka ta fita tana, "yanzu nan da wata tara za amun kawa Ah Alhamdulillah yo ai wannan aure ni akawa." Dady ne ya kira Al-ameen ya sanar da shi sun kai Ameenatou ya je gidan kar abarta ita ɗaya. Ita ko tanan ta ɗane kan kujera ban da tsalle-tsalle ba abun da take yi. Al-ameen na sallama taje da gudu oyoyo uncle ta rungumesa. Tsaki ya yi kan ya finciketa gefe. Dakinsa ya nufa kawai. Da gudu ta bisa ɗakin ya kara cillota waje. "Unkle Wallahi Kaka ta ce tare zamuna kwana ta ce kar in barka." Ko kulata bai yi ba ya share. Can ya shiga har ya fara barci Kasancewar ya gaji Ameenatou ta lallaɓa taje ta kwanta kusa da shi ji ya yi kawai ana taba masa baki. "Ji bikin unkle dinnan mai kyau kamar irin na yan tv da muke kallo gidan Baba Audu,bari in masa yadda suke." Ta kai bakinta za tai kissing na shi kenan kawai........ *😹💔 Ameenatou za tai kissing unkle ya kuke ganin rayuwar Auren Al-ameen da Ameenatou xai kasance? Maza ku hanzarta biya domin karanta naku cikin sauki yanzu aka fara ko ince har yanzu ma da sauki akan na gaba* Littafaina na kudi ga duk mai bukata Matar Police 200 Ashe haka so yake 300 Jameel 200 Ameenatou 300 Duk mai son duka hudun 800 maimakon 10000 _LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_ _*Urs Xayyeesherthuo🤍*_o🤍*_huo🤍*_