Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GJCgZzbBrsV8mesM7Zwyzf *KAZAR KWANCI...* ©Rufaida Umar *Free pages* *PAID BOOK* _*Haɗakar fiƙrah littattafai uku ne na marubuta👇🏽*_ Rufaida Umar 👉🏽KAZAR KWANCI. Fareeda Abdallah 👉🏽RANAR NAKA. Jeeddah Lawals 👉🏽NADIA _Labarai ne guda uku da marubutan suka yi haɗakar Fiƙrah domin daɗaɗa zukatan masu karatu😍 Domin samun damar karanta labaran duka uku za a biya N1500 ta wannan asusun bankin👉🏽_ 5407827015 FCMB Farida Abdullahi _Idan kuma guda ɗaya ake so a karanta daga cikin ukun za a biya N700, guda biyu kuma N1200, sai a tura screenshort na shaidar an biya ta ɗaya daga cikin waɗannan lambobi_ +2349034973645 +2347039080978 +2349030312094 *Masu buƙatar a tallata musu hajojinsu a ɗaya ko biyu ko duka littattafan sai su tuntuɓi wannan lambar 👉🏽 +2347039080978, Sai kun zo😍* *1)* " Mairamu! Mairamu!!" Matar dake zaune saman kujera ƴar tsugunno dafe da kumatu yayinda ɗaya hannun ke riƙe da buta ta yi firgigit ta farka daga kogin tunanin da ta lula har ba ta san da wanzuwar mutum ba sai jin kiran da ta yi a can cikin kanta. Ta dube shi sai kuma ta yi saurin ajiye butar ta miƙe tana ɗan ɗingisa ƙafarta da ta yi tsami dalilin jimawar da ta yi a zaune ta miƙa hannu domin karɓar ledar da ya shigo da ita tana fadin. "Sannu da zuwa Malam, yanzu ka ke tafe?" Wanda ta kira da Malam cike da damuwa ya girgiza kai, madadin ya miƙa mata ledar sai ya riƙe ya soma magana a tausashe. "Tun yaushe na shigo nake ta sallama ba ki amsamin ba, anya kuwa Mairamu rayuwa za ta tafi a haka? Ki rufamin asiri naji da damuwa ɗaya kar ki haifarmana da wata ki kwanta ciwo." Kanta a ƙasa ta share kwallar da ya zubo mata. "Toh Malam. In sha Allahu zan kiyaye." Daga haka ta sa hannu ta karɓi ledar ta kai masa ɗaki sannan ta koma ta zubo ruwa a kwanon tasa ta ajiye mishi a saman ɗan teburin dake falonsa. Shi kuwa koda ya shigo falon kai tsaye ɗakinsa ya shiga ya faɗa banɗaki, kafin ya fito ta koma tsakar gidan ta yi alwala don tuni an soma kiraye-kirayen sallar Magriba. Shi din ma yana fitowa daga dakin ya nufi hanyar fita zuwa masallaci sai ya dakata ta hanyar juyowa ya kalle ta. "Ki kira Hafsatu ki ce maza ta sa a maido yaran nan gida." Ta dube shi tamkar za ta yi magana sai kuma ta hadiye ta amsa da toh. Koda ya fita sai da ta gabatar da sallah ta ɗan yi addu'o'inta da ta saba kafin ta dauki waya ta yiwa Hafsatu flashing. Ko mintuna uku ba su cika ba ta biyo bayan kiran. Sai da suka gaisa ta ce. "Babanku yace ki sa a kawo yaran nan gida." Daga can Hafsatu ta amsa. "Inna ba za'a bari zuwa gobe ba sai na kawo su da kaina? Yanayin Hajara fa har yanzu babu sauki sai ta wuni ba ci ba sha sai aikin kuka." Inna Mairamu ta numfasa, ta sani dole Hajara ta shiga damuwa tsantsa ta yadda zai wahala lokaci guda ace komai ya wuce a wajenta. Ace har sau hudu ana neman aurenka a fasa? Sati biyu kenan da yi amma har lokacin ba a bar gulma da kuma zunɗensu a unguwa ba. Wasu su ce asiri ne kishiyar uwarta (Inna Mairamu) ta yi mata shi ne dalilin da yasa hakan ke faruwa don ba ita ta haife ta ba. Yayinda wasu ke Allah wadai da masu halin munana zato ga Inna Mairamu da suka yiwa shaidar arziki. "Hello, Inna kina jina?" Sai a lokacin ta dawo hayyacinta. "Ina jinki Hafsatu, hakanan za ta dawo gidan tunda Babanku ya yi umarnin. Zan dai roƙi alfamar ya bari zuwa goben ki taho da su." "Shikenan Inna, Allah ya nuna mana." Inna ta amsa da amin kafin su yi sallama, kaf yaran Malam a mata babu wata da ta ɗauke ta tamkar uwa irin Hafsatu. Ita ce babbar ɗiyarsa a mata idan ka cire manyan samarin yaransa su huɗu wadanda su ma a gidan ta tarar da su. Gaba daya yaran Malam su tara ne cif, biyu ne kaɗai yaranta. Hashimu, Sadik (wanda suke kira da Baba Habu), Mustafa, Zakari, Hafsatu, Safiyya da Hajara gaba ɗaya mahaifiyarsu ɗaya sannan mahaifiyarsu ta kasance yar uwar Malam, wannan yasa dangin Malam da dangin mahaifiyartasu a dunkule suke wuri guda, sai bayan rasuwarta ne Malam ya auri Inna Mairamu, dangin Malam kaɗan a cikinsu ne ke sonta, hakanan yaran Malam din, Hafsatu ce kusan tasu ta zo ɗaya sai ko Zakari ɗan baruwansa, amma sauran komai Inna Mairamu ta yi ba ta taɓa wanke kanta a wajensu. Haka ta dinga hakurin zama har ta haifi yaranta biyu duka mata. https://chat.whatsapp.com/GJCgZzbBrsV8mesM7Zwyzf *PAID BOOK* *KAZAR KWANCI* *Free pages* _*Haɗakar fiƙrah littattafai uku ne na marubuta👇🏽*_ Rufaida Umar 👉🏽KAZAR KWANCI. Fareeda Abdallah 👉🏽RANAR NAKA. Jeeddah Lawals 👉🏽NADIA _Labarai ne guda uku da marubutan suka yi haɗakar Fiƙrah domin daɗaɗa zukatan masu karatu😍 Domin samun damar karanta labaran duka uku za a biya N1500 ta wannan asusun bankin👉🏽_ 5407827015 FCMB Farida Abdullahi _Idan kuma guda ɗaya ake so a karanta daga cikin ukun za a biya N700, guda biyu kuma N1200, sai a tura screenshort na shaidar an biya ta ɗaya daga cikin waɗannan lambobi_ +2349034973645 +2347039080978 +2349030312094 *Masu buƙatar a tallata musu hajojinsu a ɗaya ko biyu ko duka littattafan sai su tuntuɓi wannan lambar 👉🏽 +2347039080978, Sai kun zo😍* 02 Malam ba shi da ra'ayin hana yara karatu, shi ɗinma tsohon Malamin makarantar gwamnati ne da a yanzu ya yi ritaya ya buɗa shago babba na siyar da litattafan makaranta iri-iri a kasuwar sabon gari. A yaransa mata Hafsatu da Safiyya duka koyarwa suke yi sai ko Hajara da ta fi su basira da son karatun wacce tun tana ƙanƙanuwa take da ra'ayin zama Likita. Lokacin da mahaifiyarsu ta rasu tana aji na uku a ƙaramar sakandire. Bayan auren Malam da Inna Mairamu kuwa, fitsara iri-iri ta ke yi mata. A wasu lokutan Malam bai fiye tsawatarwa Hajara ba saboda a cewarsa tausayi take ba shi don ba karamin shagwabar da ita Mahaifiyarta ta yi ba sai gashinan lokaci ɗaya mutuwa ta yi mata yankan kauna. Komai take so yana kokarin yi mata, Inna Mairamu ma duk iyaka kokarin da take na kyautata mata Hajara ba ta gani, asalima komai ta yi mata sai tace ai dama dukiyar mahaifinta ne ita ba ta da kudin da za ta kyautata mata da shi tunda ba ta aikin komai kuma ko boko ba ta je ba asalima tun a can Nanny ce a makarantar da Malam ya koyar a baya kafin ya yi ritaya kuma ya zo ya aure ta. Abin yakan yiwa Inna Mairamu ciwo matuƙa amma hakanan take dannewa. Mace ce marar son hayaniya ko kadan, dama can an santa da hakuri, rasuwar mijinta na farko ne ya sanya ta zawarci da kananan shekaru saboda auren wuri aka yi mata. Ba ta taɓa haihuwa da tsohon mijinta ba sai bayan da ta auri Malam. Tashin farko ta haifi ɗiya mace, ta kuma roƙi alfamar Malam akan ya sanya sunan mahaifiyarta wacce ta ke tsananin so kuma ta rasu ta bar ta tun tana ƴar shekaru goma. Malam ya yi mata wannan karar ya sanyawa ɗiyar suna Sadiya. Ta ji dadi kwarai, wanda hakan ba ƙaramin baƙanta ran su Hajara ya yi ba don sun ci burin ace sunan mahaifiyarsu ya mayar, ta tsani Sadiya tsana ba kaɗan ba. Inna ta shanye abubuwa da yawa akan Sadiya. Sai ya kasance masu so da kaunar Sadiya a yaran Malam, Zakari ne kawai sai ko Hafsatu. Su Mustafa dama babu abin da ya yi musu zafi da Innar don sai ta dau dogon lokaci ba ta sanya su a idanu ba. Idan sun so ganin mahaifinsu, kodai su shiga dakinsa ta kofar waje, ko kuma su bishi can kasuwa. Safiyya kuwa duk radda ta zo gidan sai ta yadawa Inna baƙaƙen maganganu ita da Hajara sannan take tafiya. Sadiya tana da shekara uku a duniya, Inna ta ƙara haihuwar ɗiya mace wacce ta ci sunan mahaifiyar su Hajara, Asma'u suke kiranta da Husna. Darajar wannan sunan yasa yaran suke ɗan tattalin Husnar ba sa nuna mata ƙyama. Hakanan Hajara, duk iskancin da take yi ga Inna Mairamu da Sadiya ba ta yinsa ga Husna, sai ya kasance ita da ɗiyarta ko tsawatar mata ta yi akan wata ɓarnar da ta aikata sai Hajara ta ji haushi har ma ta sanar da Malam wai saboda an saka sunan mahaifiyarta ne yasa Inna Mairamu ta tsani Husna take cin zalinta. Akan Husna, Inna Mairamu ta sha yin faɗa da Malam domin shima irin kaunar da yake yiwa tsohuwar matarsa sai ya tattara shi ya ɗora akan Husna, komai take so haka yake yi mata ga yayyunta wadanda su ma suka shagwaɓa ta amma fa ba sa ga maciji da uwarta. https://chat.whatsapp.com/GJCgZzbBrsV8mesM7Zwyzf *KAZAR KWANCI...* *PAID BOOK* 03 *Free pages* _*Haɗakar fiƙrah littattafai uku ne na marubuta👇🏽*_ Rufaida Umar 👉🏽KAZAR KWANCI. Fareeda Abdallah 👉🏽RANAR NAKA. Jeeddah Lawals 👉🏽NADIA _Labarai ne guda uku da marubutan suka yi haɗakar Fiƙrah domin daɗaɗa zukatan masu karatu😍 Domin samun damar karanta labaran duka uku za a biya N1500 ta wannan asusun bankin👉🏽_ 5407827015 FCMB Farida Abdullahi _Idan kuma guda ɗaya ake so a karanta daga cikin ukun za a biya N700, guda biyu kuma N1200, sai a tura screenshort na shaidar an biya ta ɗaya daga cikin waɗannan lambobi_ +2349034973645 +2347039080978 +2349030312094 *Masu buƙatar a tallata musu hajojinsu a ɗaya ko biyu ko duka littattafan sai su tuntuɓi wannan lambar 👉🏽 +2347039080978, Sai kun zo😍* *** Inda dai ta gode Allah, dalilin kaunar da Husna ke nunawa ga yayarta a wasu lokutan yasa Sadiya sai ta ci albarkacinta a wajen Hajara ta ke ɗan ragwanta mata. Ta ce duk abinda Mominta (sunan da take kiran Husna da shi) take so, toh fa nan duniya itama tana sonsa. Amma ganin irin farin jini da Sadiya ke da shi wajen jama'a ya sanya ta ji tana ba ta haushi. Mazan kuwa gaba dayansu sun yi aure kowanne na zaune da iyalinsa a unguwanni daban-daban. Asirinsu a rufe, babu dai wani mai arzikin a zo a gani sai dai ta ko'ina sai sam barka. Safiyya da Hafsatu ne dai suke auren masu kudin, mijin Safiyya, Barrister ne mai zaman kansa hakanan Hafsatu wanda mijinta ya kasance ɗan siyasa kuma Chairman na ƙaramar hukuma. Bai hana ta koyarwa ba amma daga baya sai ya gina mata makaranta mai kyau da tsari inda da safe ake boko, da yamma kuma ake Arabi. Sadda Hajara ta kammala karatunta ta soma aiki a wani ƙaramin asibiti, Sadiya duka-duka shekarunta takwas a duniya ita kuwa Husna shekararta biyar. Hajara takan yi shigar da take so na matsastsun kaya ta yafa siririn gyale ta fita babu dama Inna Mairamu ta yi magana sai ta taso mata da hayaniya. Wani lokacin kuma idan ta soma yi mata fitsarar tana ganin Husna ta soma hawaye sai ta yi kwafa ta daina ta ce wai ta ci albarkacin Mommynta. A karshe Hajara sai ta soma hurewa Husna kunne tana nuna mata ai Inna Mairamu ta tsane su ne saboda uwarta ta mutu ba ita ce ta haifesu ba. A hankali yarinyar ta soma jin haushin takurar da Inna Mairamu ke nunawa Hajara, yayarta mai sonta, duk abinda ta ce tana so shi take siya ta kawo mata. Koda ta soma aiki albashinta na farko akan Husna ya ƙare, ba ta damu da Sadiya ba sai idan ta ga Husna ta nuna rashin jin dadin ba ta yiwa Sadiyar tsaraba ba sannan take yi mata, tana yi tana wurga mata kallon tsana. Babu abin da yasa ta ƙara tsanar Sadiya sai ganin da ta yi ta fi Husna kyau nesa ba kusa ba. Fara ce tas mai hanci da manyan idanu, har da dimple. Takan cewa Husna, "Ke ba ki da wayo, Sadiya ta fiki kyau ki daina wasa da ita. Irinsu ne za kiga kowa ya fi so ya fi kauna, ke kuma sai ki ga mutane ba sa sonki." Husna takan yi watsi da zancen abinka da yarinta, ita ba ta fahimtar ma komai, amma ta sani Sadiya ta fi ta farin jini a wajen jama'a, ba ta da wayon gane komai. Ita baƙa ce don mahaifinsu ta biyo kuma ba ta da hanci kamar na Sadiya, kusan kamanninsu daya da Husna da suka biyo mahaifinsu. Dangi ne da ba su da kyawun fuska na a zo a gani sai ko ilimi da suke tunƙaho da shi. Hakanan halittar sura daidai misali. Inna Mairamu kuwa mace ce mai kyawun halitta kasancewarta ruwa biyu, mahaifinta asalinsa ɗan Nijar ne haifaffen Diffa kuma bafulani yayinda mahaifiyarta ta kasance bahaushiya ƴar Kano. Dangin Malam har watsa mata habaici suke yi wai idan dai kyawu na siyan zuciyar ɗa namiji toh bai siye na Malam ba, domin har gobe ba ta maye gurbin Asma'u a zuciyarsa ba. Don Asma'u ta rayu da Malam tun ba shi da aikin yi, soyayya ce tun ta ƙuruciya. Takan yi murmushi ba ta cewa uffan, zai wahala su ce wani abin ta maida musu martani face murmushi. A zuciyarta kuwa ta yi ta kiran sunayen Allah don samun sassauci daga bacin rai da suka ɗarsa mata. A haka rayuwar ta dinga tafiya, samarin sai su yi zuwa nawa gidan ba ta sani ba, wani lokacin daga can waje suke shiga ɗakin baƙi na Malam su gaisa da shi su fice, idan sun shigo toh fa Husna suke son gani babu mai bi ta Sadiya. Zakari kuwa babu abin da ya yi masa zafi, haka zai shiga ya sha hira da Inna Mairamu har da dariya. Kudaden da Hajara ke samu kusan kaso hamsin a ciki, akan Husna yake ƙarewa, ita a lallai sai yarinyar ta zama ƴar gayun da za ta ketare Sadiya a komai koda nan gaba. Kayan Husna kuwa kusan rabinsu Hajara ce ta yi mata, Sadiya takan ci albarkacinta. Amma da ta lura yarinyar tana fin Husna kyau a kayan sai ta koma siya mata wanda bai kai na Husnar daraja ba. Inna Mairamu tana shiga damuwa sosai ganin irin bambancin da Hajara ke haddasawa tsakanin yaranta, har ta kai Husna soma jin tsanar Sadiyar itama, wannan dalili yasa ta zaunar da yarannata su biyu ta ja musu kunne da nunamusu duk abu daya ne su. Ashe Hajara na ji, ta kuwa saka kuka da Malam ya zo ta sanar da shi wai Inna Mairamu ta kama su Husna tana musu iyaka da ita da sauran yayyunta, tana zuga su akan su din ita ce ta haife su, su kuna ƴan uba ne a wajensu. Abin mamaki koda Malam ya nemi ba'asi a bakin Husna sai ta ce eh hakane. Sadiya kuma ta ce ba haka Innar ta ce ba, Malam sosai ransa ya ɓaci, ya yiwa Inna tas, ya ce babu wanda ya isa ya raba masa kan yara. Har da cewa shi yasan da ace Asma'u na raye ba za ta taɓa bambanta yaranta da na Innar ba. https://chat.whatsapp.com/GJCgZzbBrsV8mesM7Zwyzf *KAZAR KWANCI...* *PAID BOOK* *Free pages* *04* _*Haɗakar fiƙrah littattafai uku ne na marubuta👇🏽*_ Rufaida Umar 👉🏽KAZAR KWANCI. Fareeda Abdallah 👉🏽RANAR NAKA. Jeeddah Lawals 👉🏽NADIA _Labarai ne guda uku da marubutan suka yi haɗakar Fiƙrah domin daɗaɗa zukatan masu karatu😍 Domin samun damar karanta labaran duka uku za a biya N1500 ta wannan asusun bankin👉🏽_ 5407827015 FCMB Farida Abdullahi _Idan kuma guda ɗaya ake so a karanta daga cikin ukun za a biya N700, guda biyu kuma N1200, sai a tura screenshort na shaidar an biya ta ɗaya daga cikin waɗannan lambobi_ +2349034973645 +2347039080978 +2349030312094 *Masu buƙatar a tallata musu hajojinsu a ɗaya ko biyu ko duka littattafan sai su tuntuɓi wannan lambar 👉🏽 +2347039080978, Sai kun zo😍* *** Ranar Inna ta zubda hawayen bakin ciki, ta kuma ba shi hakuri. Daga nan ta zuba idanu kawai sai ta koma kai wa Allah kukanta. Sanadin fasa auren Hajara da ake yi ya janyowa Inna baƙin jini a wurin yaran mijinnata da ma danginsu da makwafta. Wannan shi ne ainahin damuwar da Inna Mairamu ke ciki, jikinta ya yi sanyi, ta sani Allah kaɗai zai fidda ta daga zargin jama'a. Tana nan zaune tana ɗan jan carbi tana tunane-tunane har Malam ya dawo daga masallaci. Ta sanar da shi alfarmar da Hafsatu ta roƙa ya amsa da toh. Washegari da safe bayan Malam ya kammala kari ya fita babu jimawa wurin ƙarfe sha ɗaya Inna Mairamu na maida kayan wanke-wanken da ta yi kicin sai ga sallamar su. Sadiya ce a gaba, ta karasa da sauri ta rungume uwarta gami da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, ita kaɗai ta san a kwanakin nan irin musgunawar da Hajara ta yiwa rayuwarta a gidan Anti Hafsatu kai kace ita ce silar da aka fasa auren nan. Ba don ma Anti Hafsatun na kwaɓar Hajara ba da ba ta san ina abin zai tsaya ba. Koda za su taho daga ta taka ƙafar Husna ba tare da ta kula ba Hajara ta kwashe ta da wani wawan mari a fuska har sai da suka kusan faɗa da Anti Hafsatu. Haka suka shiga motar kowanne ransa babu dadi har suka ƙaraso gidan. Inna Mairamu ta ɗago Sadiya daga jikinta tana ɗan murmushin yaƙe duk kuwa da shatin yatsun da ta gani kwance gefen fuskarta. Abinka da farar fata har wurin ya yi ja ga idanunta su ma kana yin kallo ɗaya za ka fahimci ta ci kuka. "Ke kuma sai ka ce wacce ta shekara ba ta nan? Ni matsa can ki bani wuri." Kafin ta yi magana sai ga Husna ta shigo babu ko sallama tana turo baki, hannunta riƙe da jakar kayanta. "Ke Sadiya wa kika mayar ƴar aikinki? Wallahi ki koma ki shigo da jakar ki don ni ba baiwarki bace." Sadiya itama ta juyo ranta a ɓace, wannan raini da Husna ta yi mata yana baƙanta ranta ainun. Ta sani dai ba laifin kowa ba ne face Hajara, ita ce ta jaza mata. Ta dubi Inna, Inna ta yi mata alamar kar ta ce komai wannan yasa ta yin ƙwafa kawai, sanadin Husnar ta sha mari wajen Hajara. Matar da take tsananin shakka tun tana ƙarama sai dai zuwa yanzu ta rage jin tsoron ba kamar a baya ba. Kawai dai ba ta iya maida mata martanin zantukan da take yi musamman ga mahaifiyarta. Tana wannan tunanin sai ga Hajara ta shigo wannan ya sa ta haɗiye abin da ta yi niyyar faɗi. "Momina, wuce ki ajiye jakar mana. Ke karɓi ki miƙa mata ciki." Ta furta tana maida duba ga Sadiya dake tsaye gefen Innarta, kamar ba za ta yi ba sai kuma ta tuno marin da ta sha ta ƙarasa ta karɓi jakar hannun Husna ta shige dakinsu idanunta cike taf da kwalla, ban da gidansu, ina ne gidan da ƙarami ya raina babba ya mayar da shi tamkar bawansa. Ɗaki ne wanda ba ta da makwanci sai ƙasa a katifa yayinda Hajara ta maida gadon nata ita da Husna. A farko ma a ƙasa Sadiyar ke kwana sai da Inna ta yi magana ne sannan Malam ya siyo katifa maidaidaiciya ya ce Sadiyar ta dinga kwanciya a ƙasa acewarsa ai gaskiya Hajarar ta faɗi, gadon ya yi musu kaɗan su uku duk kuwa da girmansa. A tsakar gidan kuwa Hajara ba ta ko gaida Inna ba ta yi ɗakin, Sadiya ta fito da sauri gudun kada ta yi mata wani laifin. Inna ta bi ta da kallo sannan ta maida ga Anti Hafsatu dake sallama riƙe da jaka ganin haka Sadiya ta karɓa ta kai ɗakin ta ajiye. Falon Inna suka shiga gaba daya aka zauna ana gaisawa. Husna da har lokacin ba ta bar yiwa Inna kallon mai laifi ba da ta tauye rayuwar Yayarta ta hana ta aure saboda ba ita ta haife ta ba, zama kawai ta yi amma fuskarta gaba ɗaya babu wani annuri. "Ku ɗan bamu wuri toh, zamu yi magana." Cewar Anti Hafsatu tana dubansu, Husna ɗan taɓe baki tayi sannan ta miƙe, Inna ta bi shigar ta da kallo. Wani leshi ne wanda ko ba a faɗa ba a ido an san mai tsada ne an mata ɗinkin riga da siket da ya kama jikinta don ma dai babu wani abin a zo a gani a surar domin duka duka shekarunta goma sha biyu a sannan amma sai ka dauka ta gurmi Sadiya saboda girman jiki. Wannan leshi yana ɗaya daga cikin irin ɗinkunan da Hajara ke mata. Ko kusa Inna ba ta kaunarta da ire-iren ɗinkunan masu kama jiki sai dai ba ta isa ta yi magana ba Malam zai hayayyako mata ya goyi bayan ƴar gaban goshinsa Hajara. Bayan ficewarsu Anti Hafsatu ta soma magana fuska dauke da damuwa. "Inna na sani dole za ki fuskanci matsaloli game da fasa auren nan na Hajara da ake yi. Amma don Allah ina roƙon ki ƙara hakuri kuma ki toshe kunnuwanki daga dukkan wani abu da zai je ya zo ko a ɓangaren ƴan uwana ko danginmu. Mutane ne a yanzu sam ba su da tawakkali, gutsiri tsoma ya yi musu yawa. Ki yi hakuri da dukkan abin da su Gwaggo suka ce maki." Inna Mairamu ta ɗan yi murmushi, hankali da nutsuwa irin ta Hafsatu da Zakari yana matuƙar burgeta ainun. Tun faruwar al'amarin idan ka cire ɗaiɗaiku daga danginsu, babu wani ko wata acikin yaran mijinta da ya tare ta da irin wannan kalaman masu sanya nutsuwa da kwantar da hankali sai Zakari sai kuwa Hafsatun don ita Safiyya ma har iskokan ƙarya ta tayi ta zage ta tas. https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a *Kazar Kwanci free pages 1-5 sun sauka a arewabooks, kuna iya bin link ku sha karatu.* *** *Kazar Kwanci...* *Free page* *05* "Kar ki damu Hafsatu, da ace zan dinga damuwa da abin da mutane ke faɗi a kaina game da lamarin nan ai da yanzu na ƙare a kwance. Allah shi ne shaida ina zaune da ku da zuciya daya, kaf dinku ina muku kallo tamkar na yaran da na raina da hannuna. Komai zai wuce da yardar Allah. Itama Hajara in sha Allahu mijinta zai zo, Allah ya bata ikon yarda da ƙaddara." Anti Hafsatu ta share kwalla na tausayin Inna Mairamu, mace mai nunamusu kauna da zuciya ɗaya, ga hakuri da kawar da kai da kuma maida lamarinta gaba ɗaya ga Ubangiji. Kafin Anti Hafsatu ta kai ga cewa wani abu sai ga Hajara ta shigo ta musu tsaye a kai. Wani kallo take watsawa Inna kamar ta ga kashi fuskarnan jage-jage da ruwan hawaye tun bayan Husna ta fesa mata cewa Anti Hafsatu ta fito da su wai za ta yi magana da Innar ta yi saurin fitowa ta laɓe. Komai a cikin kunnenta suka faɗi. "Ke Hajara wane irin rashin ladabi ne wannan? Mu kika tsayawa a kai haka tamkar wasu sa'anninki?" Hajara ba ta ko bi ta kan Anti Hafsatu mai wadannan zantukan ba ta ɗora nata zancen. "Duk abin da ka yiwa ɗan wani a rubuce yake sai an yiwa ɗiyarka. Abin da kike fatan ya kasance a kaina, Mairamu (kamar yanda take kiranta tun farko wanda har ta koyawa Husna) ki sa a ranki har abada ba zai tabbata ba sai dai ki gani akan Sadiya. Zama ba aure, karuwanci, cikin shege duk za ki gani a jikin wannan ɗiyar taki mai kama da zabiya. Aure kuma ko ana ha maza ha mata zan yi shi, ki zuba idanu ki ga ikon Allah. Ƙaryar mutum wallahi!" "Ke Hajara!" Anti Hafsatu ta mike lokaci guda tana kiranta murya a ɗage, hannu ta ɗaga da niyyar marinta ko me ta tuna sai ta dunƙule ta fasa ta ɓige da nuna ta da yatsa idanunta na fitar da hawayen baƙin ciki. Ita ko Inna Mairamu kanta a ƙasa ta runtse idanu tana ambaton sunan Allah, zafin kalaman da Hajara a yau ke jifan ɗiyarta da shi da mummunan bakin da take yi gareta ya sanya ta kasa jure yin shiru wannan karon ta ɗago kai tana kallonta. "Hajara kar ki bari Allah ya kama ki da laifin ƙazafi da kuma ƙage. Sadiyar dai da kike aibatawa kin fi ni kusanci da ita don ko yau rabuwar aure zai iya zama dalilin da zan nisanta da ku gaba ɗaya, ita ɗin kuwa babu yanda za ki yi da ita saboda dolenki ce kuna tsatsonki." "Hajara ba ki da hankali, kin manta wace ce ita kike a wajen mahaifinki? Wallahi ki kiyaye harshenki domin nan gaba zai iya haifarmaki da dana sani marar iyaka. Yau ace Mama na raye an fadamaki za ta ji dadin irin wannan abu da kike aikatawa? Ko kuwa an faɗamaki Husna za ta so ki dinga yiwa Mahaifiyarta irin wannan cin kashin?" Idanun Hajara har ƙanƙancewa ya yi tsabar bala'i ta dubi yayarta murya a sama ta ce. "Ki bar kiran Mamana a wannan sha'anin, tana can kwance cikin kabarinta. Alhamdulillah ta rabu da mutane lafiya, uwa uba ta rabu da mijinta lafiya yana mai addu'a da nema mata gafarar Ubangiji. Sannan Alhamdulillah uwata ba ta cutar da rayuwar kowa ba. Husna kuma ita kanta ta fahimci wace ce Babarta Mairamu, ta soma gane ita ke haddasa rashin yiwuwar aurena. A hankali za ta gane komai." Inna Mairamu zuwa lokacin ma ta kasa ƙara uffan, Anti Hafsatu kuwa zagin Hajara take yi kawai tsabar takaici, abin da ya hana ta kai mata duka bai bwuce dokar da Malam ya sanya musu akan Hajara ba, har Allah ya isa ya yi ga duk wanda ya sa hannu ya taɓa masa ita. Koda dai ba akan Hajara ba kawai, shi tun fil'azal mutum ne da babu wanda ya isa ya dokar masa yara. "Lallai yau na ƙara yarda ba za ki taɓa sauya hali ba. Wannan rashin hankalin da kike yiwa Inna wallahi muddin ba ki bar yinsa ba sai kin ga sakamakonki a rayuwa. Shashashar banza da wofi wacce ba ta san girma da mutunci Dan Adam ba." Ita dai Hajara guntun tsaki ta ja ta fice tana banko labulen, Sadiya dake kicin tana ganin ta shige ɗakinsu ta fito a guje ta yi wajen Innarta tana kuka sosai a duniya ta tsani Hajara ba don komai ba sai saboda cin zarafin Innarta wanda nata ya ninka na sauran yan uwan, sukan ma nuna halin ko in kula irin na ƴan boko ga Inna, amma ita kuwa idanunta take murjewa ta ci mutuncinta son rai.  Itama Innar nata hawayen ba su bar zuba ba. Anti Hafsatu kuwa hakuri take ta ba Inna kamar harshenta zai tsinke. Har sai da Innar ta dakatar da ita da nuna nata kar ta damu babu wani abu.   A can ɗakin kuwa, Husna ta ji komai da ya wakana zuciyarta ta ɗan yi babu dadi, babu wanda zai so a dinga cin zarafin mahaifiyarsa haka, amma kuma ai a ganinta gaskiya Antinta ta faɗi, duk abin da ka yiwa wani za'a yi wa naka. Har Hajara ta shigo ba ta motsa daga inda take zaune rike da babbar wayarta ƙirar Infinix da Antin ta siyamata wai ta dinga kallo. Akan wayar ma sai da Malam da Inna suka yi faɗa, ba ta ga dalilin da za'a ba Husna waya ba, duka-duka a ganinta yarinyar shekarunta nawa a duniya? Karshe dai da Malam ya yi mata kaca-kaca dole ta zuba idanu, takan yiwa Husna nasiha da nunamata irin hakan da ake mata sam ba gata bane, amma yarinyar sai take ganin kawai Innar ta takura mata ne. "Anti Hajara." Cewar Husna fuskarta dauke da tsantsar damuwa, ita har ta rasa ma bayan wa za ta bi, takan ji ciwo idan aka yiwa Inna, kuma takan ji zafin asirin hana aure da aka ce Inna ta yiwa Antinta. Hajara ta dube ta sai ta ƙara fashewa da kuka ta janyo hannunta cikin nata. "Momina, meyasa Mairamu ba ta kaunar ta ga nayi aure? Me nayi mata da take fatan na dauwama a gida? Shikenan don uwata ta mutu sai na zama marar gata? Kinga don nace abinda ta yimin za ta gani a kan Sadiya shi ne Anti Hafsatu har kusan dauke ni da mari ta yi. Wato ba ta son a yiwa Sadiya amma idan da ace ke nace a yiwa babu abin da zai dame ta ko? Na fadamaki, saboda kina kaunata shiyasa Mairamu ta fi nunawa Sadiya so sama da ke, hum, ai shikenan. Ki yi addu'a na samu miji na yi aure, wallahi gidana za ki koma." Husna itama kukan take yi, bilhakki tausayin Antinta take ji, tana kuma jin zafi idan ta tuna wai Mairamu ta fi kaunar Sadiya saboda ita. Ta kuma soma yarda da hakan, kuma Hajara ta ce ba don komai ba ne sai ganin Sadiya kyakkyawa ce za ta yi amfani da ita domin ta zame mata tamkar jari, ita kuwa tunda ba ta da kyawun fuskar Sadiyar, kuma wai Sadiyar sunan mahaifiyar Innar ta ci, ita kuma saboda sunan maman su Hajara ce kuma matar da Babansu ya fi kauna shi ne dalilin da yasa komai ta aikata sai ta ce bai yi ba ta daina. "Kiyi hakuri Anti, kinji? Nima na fi so kiyi aure na bi ki gidanki. Na gaji da zama tare da Mairamu tunda ba ta kaunata." Hajara ta murmusa ba tare da ta ce komai ba sai aikin kallon lallen da aka zana mata a hannu don bikin aurenta har ma ya soma gogewa. ©Rufaida Umar. https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a *Kazar Kwanci free pages 1-5 sun sauka a arewabooks, kuna iya bin link ku sha karatu.* *** *Kazar Kwanci...* *Free page* 06 Anti Hafsatu ba ta kuma bi ta kan Hajara ba, abin da ya faru kuma bai sa ta iya zaman jira har Malam ya dawo su gaisa ba, tana yin sallar azahar ta ci abinci ta tattara ta bar gidan. Sadiya kuwa kamar yanda ta saba haka ta zauna tana taya Inna da wanke-wanken kwanukan da suka ɓata na abincin rana, Hajara da Husna ko ta kan abincin ba su bi ba, tana nan tana gyara wurin da ta kammala aikin Husna ta fito yafe da siririn gyale ta shuri takalmanta ta fice daga gidan. Da idanu kawai Sadiya ta bita, can kuma sai ta dawo hannunta riƙe da leda babba sai ɗaya dauke da lemo da ruwa ta shige ɗakin. Ita kuwa Sadiya tana kammalawa ta nufi dakin Innarta, kamar yanda ta bar ta haka ta tarar da ita. Ta zauna fuska dauke da damuwa. "Haba Inna, don Allah ki bar damun kanki da tunanin abin da ba za ki iya gyara shi ba." Inna ta sauke ajiyar zuciya ta dube ta. "Kar ki damu Mamana, ba wannan ke damuna ba, rayuwar Husna nake tausayawa, an ɗauki turbar lalata min tarbiyyarta amma ina ji ina gani ban isa na yi magana ba. Wannan shi ne damuwata." Sadiya ta sauke ajiyar zuciya. "Ki cigaba da addu'a Inna. In sha Allahu komai zai yi daidai." Ta gyadamata kai. "Allah ya dafamana." "Amin inna." *** WAIWAYE... Malam Sa'ad Shagari ya dubi Mairamu cike da nutsuwa. Ita kuwa kanta na ƙasa tana ɗan murmushi. Shima sai ya tsinci kansa da murmusawar kafin ya soma magana. "Sai kika yi mamakin gani na ko Mairamu? Ban ji kin tambayi abin da ya kawo ni ba?" Ba tare da ta dube shi ba ta amsa. "Ba komai, nasan ko da me ka zo alheri ne ai Malam, ya gida ya kuma ƙarin hakuri? Naji a wurin Malama Fauziyya cewa uwar gidanka Allah ya yi mata rasuwa, Allah ya gafarta mata na so shiga da na dawo na yi maka gaisuwa duk da ya dauki lokaci amma Allah bai nufa, kuma sadda aka yi rasuwar sai nima abin ya zo kan gaɓa, an yi min wata rasuwar a can gida na tafi, yayata da muke uwa daya uba daya, shi ne ma dalilin jimawata ban dawo ba." "Allahu Akbar, Allah ya gafarta mata." Mairamu ta amsa da amin, shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ɗora. "Mairamu, koda ban faɗa ba, nasan Malama Fauziyya ba za ta rasa sanar da ke kaɗan daga dalilin da yasa na zo wajenki ba. Amma zuwa da kai ya fi saƙo. Kamar yanda kika sani, Marigayiya matata Hajiya Asma'u, da mahaifina da mahaifinta uwa daya uba daya, hakanan iyayenmu mata su ma auren dangi na zumunci ne ya faru tsakaninsu har suka haife mu. Wanda cikin iko na Allah soyayya ta ƙullu tsakanina da Asma'u tun tana matsayin ɗalibata har Allah ya nufa ita za ta zamo uwa ga ƴaƴana bakwai. Ba zan ɓoyemaki ba, ta kasance mace mafi soyuwa a gareni, bana jin a duniyata na taɓa son wata ɗiya mace irin son da na yiwa Asma'u. Mace mai hakuri da kuma kauda kai, a tsawon shekarun da muka rayu da juna da ita, saɓanin da za ki ga ya haɗa mu sai dai ko irin na harshe da haƙori, kinsan ɗan adam ajizi ne. Lokaci ɗaya cutar annobar amai da gudawa ya zo da ajalinta, ta rasu." Ya ɗan numfasa, Mairamu ta ɗan dube shi cike da tausayawa, ko daga yanayin fuskarsa da yanda yake magana za ka fahimci cewa har a lokacin yana jin zafin rashinta, ta samu bakinta da furta addu'ar neman rahma gareta. Ya amsa da amin sannan ya ɗora. "Shekara guda kenan da rasuwarnan, manya sun matsa akan zamana a haka babu aure, nima kuma ban ga amfaninsa ba ko don kare mutuncin kaina da na iyalina. Wannan ta sa na nemi zaɓin Allah kuma cikin ikonSa muka haɗu da Malama Fauziyya ta zo shagona neman wani littafi, anan Allah ya kawo zancenki na ji har a raina zan iya zaman aure da ke, wannan shi ne dalilin da yasa na nemi ta nema min izninki kafin na zo gareki. Ba zan yi maki dole ba Mairamu, zan ba ki lokaci nan da kwanaki uku kiyi tunani zan dawo, idan har kin amince sai na samu magabatanki tunda dai mu yanzu ba yara bane ko? Koda dai na fiki tsufa." Ya ƙarashe da ƴar dariya itama sai ya ba ta dariyar, ta ɗan murmusa. A haka suka tsaida maganar cewa zai dawo ya ji amsa nan da kwanaki uku. Bayan kwanaki uku kuwa ya dawo, ya samu kyakkyawar amsa inda a take ta amince da yin fatan alheri a lamarin. Malam Sa'ad bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya ja amininsa Alhaji Abubakar wanda ya kasance shahararren ɗan kasuwa a kwari, suka rankaya wajen ƙanin mahaifin Mairamu wanda ta ke zaune gidansa tun bayan rasuwar iyayenta. A sati biyu aka kammala komai, aka tsaida ranar daurin aure. Sai a wannan lokacin ne kuma Malam Sa'ad ya tara yaransa kaf domin sanar da su. Ya dube su, su din ma shi suke kallo, sun riga sun ji labari a wajen ƴan uwa sai dai su na fatan ji daga bakinsa. Ai kuwa yana faɗi, Hajara ta shiga kuka. "Wayyo Mama, shikenan mutuwa ta raba mu da ke. Yanzu Malam zai ƙara aure. Na tabbata marainiya." Malam ya bita da kallon tausayawa, Safiyya ma sai da zuciyarta ta karye. Anti Hafsatu kuwa ba ta ce komai ba sai fatan Allah yasa ko wace ce ta maye musu gurbin Mamarsu. Caraf kuwa Mustafa ya karɓe. "Aa Hafsat, bar wannan magana. Ai babu wata da za ta iya maye gurbin Mama a zuƙatanmu. Malam dai ya yi aurensa kawai, muna mishi fatan zaman lafiya." "Wannan hakane. Ai babu kamar uwa. Malam Allah ya sanya alheri." Cewar Baba Habu. Hashimu kuwa babu abin da ya dame shi, kusan shi ya ma fi su halin ko'in kula da irin wadannan al'amuran, a ganinsa mene ne don Abban ya yi aure? Matar dai ai ba zama za su yi da ita ba tunda duka suna da gidajensu sun yi aure. Safiyya ma an saka ranar aurenta an kusa sai ko Hajara auta ƴar sakandire. Haka dai Malam ya kammala maganarsa ya tashi ya bar su don kukan Safiyya da Hajara na neman karya masa zuciya. Sai da Hashimu ya tsawatar kafin su nutsu su bari. "Murna kake yi kenan da auren Yaya Hashimu?" Baba Habu ya tambaya. Hashimu ya ja tsaki. "Ina ruwana don Malam zai yi aure? A kanmu za ta zauna? Ku mene ne naku ciki? Kuna fa gidajenku, idan ma ba ku so ba, ba za ta taba sanya ku a idanu ba ballantana wani mu'amalar ta haɗa ku da ita? Ni fa da dai ya auri wata cikin dangi gwara wata can bare da ba mu san ta ba." "Wallahi kuwa, nima haka na gani Yaya, da dai Malam ya kwashi wata a ƴan uwa da suka yi zumunci da Mama, gwara ya yi aurensa daga can waje." Zakari ya furta don shi dagaske ya ma ji dadin auren mahaifin nasu, zamansa haka tausayi yake ba shi koyaushe idan ya dawo gida sai dai ya yi zaman jugum da tunani. Anti Hafsatu ma ta nuna goyon bayanta, karshe mazan suka mike zasu wuce, cikin zolaya Baba Habu ya dubi Safiyya da Hajara. "Toh, Safiyya gwara ke kin ma kusa barin gidan abinki, ke kuwa Hajara sai ki shirya tarbar sabuwar Mommy. A kuma yi mata biyayya ba ƙaƙƙautawa." Aikuwa ta ƙara tunzura ta fashe da wani sabon kuka tana fadin ita wallahi ba ta isa ta kirata da sunan Mommy ba. Haka yana dariya ya fice ya bi bayan ƴan uwansa. Anti Hafsatu kuwa ta dubi Hajara wacce kukanta ya soma kai ta bango. "Malama ki yiwa mutane shiru haka. Wannan ai hauka ne da rashin hankali, shikenan haka zai zauna babu aure? Idan kin ga dama ki yiwa kanki faɗa ki rungumi ƙaddara don auren Malam babu fashi, idan kuwa kin ƙi sai ki zauna ki yi ta fama da ciwon zuciya tunda ba ki isa ki dawo da abin da yake dama can aronsa Allah ya bamu ba." Wannan ne dalilin shirun Hajara ta miƙe tana kunkuni ta shige ɗakinsu. Safiyya kuwa ta dubi Anti Hafsatu da mamaki. "Wai Anti Hafsatu ba kya jin zafin da muke ji a zuƙatanmu dangane da wannan lamari?" Harara Anti Hafsatu ta doka mata tana mai kunce goyon ɗanta Daddy dake bayanta wanda ya ishe ta da kuka. "Zafin me zan ji? Ku yanzu kun fi kaunar Malam ya dauwama a haka babu aure? Ba kwa la'akari da cewa kuma aure za ku yi ku bar gidan? Ai idan ita Hajara ta yi wannan wautar ke bai kamata ace har da ke ciki ba. Yaya Mustafa ma sun ba ni mamaki don na tabbatar su kansu ba wani murna suke da hakan ba. Amma kar ku manta, muddin kuna kaunar Malam dagaske, toh taya shi son abin da yake so shi ne mafi dacewa a garemu baki daya." "Tabɗijam! Shikenan ai, ya yi auren amma wallahi nidai babu abin da zai taɓa haɗa ni da matarsa. Har gobe ba da za ta taɓa maye mana babban gurbin da muka rasa ba a rayuwarmu." "Ku kuka sani. Aure dai babu fashi da yardar Allah." Daga haka ba ta ƙara tankawa ba, karshe ma Safiyya sai ta mike ta nufi dakinsu don su kara jajantawa juna ita da Hajara. *** Ranar juma'a aka ɗaura auren Mairamu da Malam Sa'ad bayan saukowa daga sallah. Aka bar tariyarta nan da sati daya bisa alfarmar da Malam ya roƙa don ya ƙarasa gyaran gida saboda a satin da ya wuce bai samu aikata komai ba dalilin tashin hankalin da hakan ya haifar a gidan. Inda Hajara da Safiyya suka yi ta faman kuka su Hajara har da kwanciya ciwo yayinda Safiyya ta tayar da iskokai su fa a dole Malam ba zai ƙara aure ba. Sai da babban yayan Malam ya tsawatar kafin su nutsu, dama abin nasu har da zuga inda facalolin Mama da kuma yan uwa suka dinga tada jijiyoyin wuyar ba haka ba. Musamman ma zawarawan da suka saka rai Malam din zai auri daya a cikinsu. Sai lokacin ya samu sararin fenti. Gidan dakuna biyar ne, daya mai ciki da falo na Malam ne sai ko falle biyu wanda a baya Asma'u ta maida daya daki dayan kuwa falo, sai ko daki daya na yanmatan yaran. Sai shago a waje na samarin gidan. Babu laifi akwai wadataccen tsakar gida har da ɗan shuke-shuke a gefe daya zagaye bangon tsakar wajen da kuma famfo da aka zagaye wajen da tayil inda ake wanke wanke. Gidan ma dai duka tayil ne a ƙasan. Ranar da Mairamu za ta tare, daga ita sai yan uwanta hudu, matar dan uwan maihaifinta da suke kira Dada sai kuwa yaran Dada mata uku, sai makwaftansu mutum biyu. Kwanansu uku suna kwasar amarcinsu, sai da ta yi sati ko ƙeyar ɗansa ko ɗaya ba ta gani ba, lokacin Zakari ya tafi bautar ƙasa a Yobe. Hajara da Safiyya kuwa sun koma sun tattare can babban gida wurin dangi tsabar baƙin ciki da takaici. Sai da suka yi sati biyu cif kafin su waiwayi gidan. Gani suka yi ma ai dama suka bayar da Mairamu za ta ci karenta ba babbaka a gidan Mahaifinsu, gwara su zo a yi komai a gabansu. *** Mairamu na zaune ta kammala suyar kifin da Malam ya kawo na miya, sai kawai ganin mutane ta yi sun faɗo kamar an koro su babu ko sallama har sai da ta ɗan razana. Suka yi tsaye cak su na ƙare mata kallo da kuma bin kifin da ke cikin mai yana soyuwa da idanu, sai kuma suka saki dariya gami da cafkewa. "Wasssh! Babu a house! An samu na bati!" Fadin Safiyya, suka ƙara tuntsirewa da dariya. Ita dai Mairamu kallonsu kawai take, ko ba a faɗa ba ta san wadannan yaran Malam ne don ta ga tangameman hoton family da suka dauka wanda ke manne a falon Malam. Ta yi kamar ba ta ji furucinsu ba, da ɗan murmushi saman fuskarta ta ce. "Ah Safiya ku ne tafe? Sannunku da zuwa. Ku shiga ciki." Suka watsa mata harara, cike da tsiwa Safiya ta ce. "Ai ba sai kin ce mu shiga daga ciki ba Mairamu tunda gidan ba na uban wani ba ne." "Atoh." Hajara ta karɓe. Inna Mairamu ta tauna maganar a ranta, ba ta ji zafi sosai da kiranta da sunanta na ainahi da budurwar ta yi ba kamar zagin ubanta da ta yi. Daga haka ta ɗan yi murmushin yaƙe ba ta ƙara cewa uffan ba ta cigaba da aikin dake gabanta. Tana kallo suka faɗa ɗakin da dama mallakinsu ne, a gyare yake tas don Inna Mairamu mace ce da ba ta son ƙazanta da ƙura, hakan yasa duk bayan kwanaki biyu take shiga ta gyara shi, Malam kan ce ta bari tunda babu mai kwana a dakin amma ta nuna masa babu komai ta san watarana za su zo. Ba kuma ta son su tarar da wurin kaca-kaca. Yakan yi murmushi cike da jin dadi, wato dai ta nunawa nasa kulawa. Shinkafa da miyar kifi ta yi sai kuwa ruwan shayi na Malam wanda ya zame masa jiki sai ya wuni yana sha idan yana gidan. Ganin haka yasa har ƙaton filas dinta na shayi take cikamasa ta sanya masa a mota ya wuce da shi kasuwa. Ta kai babban farantin da ta shiryawa mijinta abinci zuwa falonsa ta ajiye sannan ta fito da zummar daukar filas na shayi, turus ta tsaya ganin Hajara ta dauki faranti ta zuba shinkafa tili guda ga miya da kifi nasha-nasha a sama. Suna hada ido Hajara ta watsa mata kallon tara saura tana turo baki gami da fadin. "Ai dai tunda Ubanmu ne ya yi cefanen babu wata da ta isa ta hana mu ci." Ɗan murmushin da bai kai zuci ba Inna ta yi. "Hajara kenan, ko ba ki yi haka ba dama ku din nake niyyar ɗibarwa. Sannan eh Babanku ne ya yi cefane, amma kinga tunda ni na girka ina da iko akan tukunyata ko?" Hajara ta ɗaga kafaɗa. "Oho dai, ko me za ki ce ba zan fasa abin da nayi niyya a gidan nan. Kema din arzikin ubanmu kike ci, ban da haka ko ƙayar kifi sai ki shekara ma ba ki gani a kwanonki ba!" Tana kai wa nan ta kaɗa kai ta yi ciki, can kuma ta dawo daidai sadda Inna Mairamu ke kokarin juye ragowar miyar a wani karamin filas dinta, hannu ta kai da zummar ɗaukar ruwan zafin dake cikin filas, caraf Inna ta riƙe hannun gami da ɗauke filas din. "Wannan dai na mahaifinku ne. Idan sha kike son yi, ki bari idan ya dawo ya yi amfani da shi sauran ki ɗiba." Hajara na huci take bin Inna da kallo kamar ta tofa sai kawai ta yi ƙwafa ta koma ɗaki. Sai da aka soma kiraye-kirayen sallar Magriba sannan Malam ya shigo gidan. Inna na bandaki tana alwala, Hajara suka tarbe shi da oyoyo kai kace wasu yara ne ƴan shekaru goma shima ya yi farin ciki da ganinsu duk da daman sai da ya je can babban gida kai musu tsarabar kasuwa ya ƙara lallashinsu akan su dawo gidan ya iske sun ma taho. Da wannan murnar suka karɓi ledojin hannunsa zuwa cikin falonsa. Koda Inna ta fito sai kawai ta yi dakinta sanin da ta yi shima Malam din masallaci zai nufa. Sai bayan ta idar da sallah ne ta dan yi lazimi, ba ta kai ga idarwa ba ta ji Malam na faman kwalamata kira har kafin ta fita ya banko labulen ɗakin nata ya shigo. Suka yi kiciɓus bayan ta shafa addu'ar da ba ta kai ƙarshensa ba kirjinta har dukan tara-tara ya shiga yi domin dagaske dai ta tsorata da wannan kiran. "Lafiya? Sannu da dawowa." Shi ne abin da ta tsinci bakinta da furtawa lokaci guda. Bai ko amsa ba cikin ɗaure fuska ya hau fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kamar wanda aka jonawa batiri. "Ni bana son haka, daga dawowar yara har kin fara hana su abinda Ubansu ne ya kawo? Ba ki ba su abinci ba, don kuma sun nuna su na da buƙatar shan ruwan shayina kika ce ai ba su kika dafawa ba? Mairamu duk abin da nake kawowa gidan nan ba nawa ne ni kadai ba, na iyalina ne, bana son haka. Kin jefa zuƙatunsu cikin kewar mahaifiyarsu, wato kin soma nuna gazawarki a taya ni rikon amanarsu tun a yau da kika soma sanya su a idanunki. Kar ki bani kunya mana!" Daga haka ya sa kai ya fice a gidan. Inna Mairamu ta kasa motsa koda yatsa balle ta bi bayansa. Wasu ruwan hawaye masu ɗumi suka zubo saman fuskarta, ta shiga ambaton sunayen Ubangiji a cikin ranta. Lallai ta su da wadannan yanmatan ba za ta zo ɗaya ba. Tun yanzu? Tun ba a wuni tare ba sun soma ƙulla mata zarurrukan sharri? Ta sauke ajiyar zuciya, ta daurewa zuciyarta har aka yi sallar isha'i sannan ta fito zuwa falon Malam din. Yana zaune su Hajara na gefensa suna hira da dariya. Sallamarta ya sanya suka haɗe rai gami da amsawa ciki-ciki saboda ganin idanun Malam. Shi kuwa wani irin mutum ne marar riƙo, yanzun zai yi faɗa amma zuwa wani lokacin sai ya manta bar shi dai da daukar magana. Ransa ya dan yi sanyi musamman ganinta cikin ado kamar koyaushe. Murmushi ya yi itama ta mayar masa da martani. Ta nemi wuri ta zauna. Safiya ce ta soma mikewa ta bar falon ranta a jagule ganin haka itama Hajara ta bi bayanta. Malam ya bisu da kallo hakanan Inna Mairamu wacce ta ke musu kallon mamaki na yanda har babu kunya ba tsoron Allah suka haɗa ta da mijinta akan laifin da ba ta aikata ba. "Don na maki magana wato shi ne ko ki zo ki ba ni abinci ko?" Ya furta, kai ka ce ba shi ya gama sababin an taɓa yaransa ɗazu ba. "Ba haka bane, sallah na tsaya nayi. Akan abin da ya faru kuma ina mai ba ka hakuri. Nidai har ga Allah na sani ba zan iya cutar wata halitta ba balle kuma jininka, yaranka ai nawa ne. Ina mai ba ka hakuri bisa abin da suka ce na aikata, sai dai don Allah idan ranka ya ɓaci ka bar saurin yanke hukunci akan magana har sai ka ji daga bakin mutum. Mai yiwuwa kuskuren fahimta ne." Ya numfasa. "Shikenan, dama na sani za ki riƙemin amanar ƴaƴa, kawai dai yanayin da na gansu ciki ne ban ji dadi ba. Kin san ba ƙaramin shaƙuwa suka yi da mahaifiyarsu ba, wannan ne dalilin da ya sanya sai a hankali za su saba da ke. Kema kuma ki dinga kokarin jansu a jiki, in sha Allahu za ku ji dadin zama da juna domin yaran ba su da matsala." "Uhum." Shi ne iyakar abin da ta ce haɗi da ɗan murmushi ba don ta gamsu ba, tun a yanzu ta hango matsalarsu, ta kuma san ba ƙaramin abu za ta fuskanta a zamanta da su ba. Ya shiga jan ta da hira karshe ta watsar da zancensu itama ta sakarwa mijinta tamkar wani abu bai faru ba. *** Kamar dai yanda Innar ta yi zato hakan ne ya kasance, fitsara da rashin kunya iri-iri haka ta dinga cin karo da su a wurin Safiyya da Hajara. Ko tsinke ba sa kawar wa a gidan sai dai idan ta gyara su ɓata. Sai sun tabbatar ta yi shara sannan za su share nasu ɗakin madadin a kai kwando a zubar sai dai a watso tsakar gidan, ranta kan ɓaci sai dai kawai ta kai zuciya nesa. Abinci kuwa sai a faki idonta su ƙara uban gishiri a cikin nasu kason, idan Malam ya dawo su hau kukan munafurci su ce wai kashe su Inna ke son yi. Ganin haƙansu na cimma ruwa, Malam din na yarda da su ɗari bisa ɗari idan sun faɗi laifin Inna, ya sa duniyar ta ke gara musu sosai yadda suke so. A haka watarana Safiyya ta kimtsawa Hajara sharrin da ya dace su yi ga Inna wanda take da yaƙinin idan haƙansu ya cimma ruwa to zai wahala auren Inna da Malam bai zo ƙarshe ba. "Amma kina ganin zai sake ta? Nifa sai naga kamar yana sonta." Cewar Hajara bayan gama sauraron ƙullin da Safiyya ta ke son su aiwatar akan Inna. Safiyya ta ja tsaki. "Wane so? Ke kike ganin hakan. Malama ba wani sonta da yake yi kawai dai yana maneji ne. So ai ya ƙare a kan Uwarmu. Duk wacce za ta biyo baya kuwa, sai dai wani sunan amma ba so ba. Ke dai kawai ki yi abin da nace, ni na tabbata yau kwanan Mairamu ya ƙare a gidannan." Suka yi dariya har da shewa. *©Rufaida Umar* https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a *** *Kazar Kwanci...* *Ƙarshen free page* 07 A ranar wata Asabar abin ya faru, hadari ya haɗu sosai a garin, cikin gaggawa Inna Mairamu ta kammala girkinta a gawayi ta kashe ta gyara wajen ta tattara gidan tas, abin rufewa ta rufe, na killacewa ma haka. Sai da ta kai komai ɓangaren Malam kamar yanda ta saba tunda hatta su Hajara sun koma ci tare da shi idan ya dawo hakan yasa ba ta ware musu. Malam din ma ya ce ai ya saba al'adarsu ce tun Asma'u na raye sukan haɗu da yaransa su ci abinci wannan ne dalilin da ba ta karambanin zuba musu daban. Na almajirinta  Lurwanu ma sai da ta ajiye mishi a kicin duk da ba ta zaton zai samu ɓullowa sakamakon yayyafin da aka fara kaɗan-kaɗan. Ban da kiɗa babu abin da ke tashi a ɗakin su Hajara, ita ba ta nan ma ta je makaranta sai Safiyya a gidan amma ko leƙe da sunan taya Innar aiki. Ita dai ɗakinta ta shige bayan ta ɗaura alwala ta ja ƙofa ta rufe da zummar ɗan kimtsawa kafin Malam ya shigo gidan. Tunaninta gaba ɗaya yana kan Hajara, ko ya ya za ta yi da ruwa? Sosai take jin damuwa akan haka tamkar ƴar cikinta. Ta kasa jurewa ta fito ba ta damu da ruwan da ya soma ɗan ƙarfi ba ta shiga ɗakinsu. Safiyya tana ta danne-dannenta a wayarta tana faman hira a 2go ba ta ma ji sallamar Innar ba sakamakon kiɗan da ya cika dakin. Inna ta ƙarasa ta ɗan bubbuga ƙafarta ta kuwa yi zumbur ta miƙe tana huci, ganinta ya sanya ta jan tsaki gami da kashe rediyon. "Mene ne haka za ki tsorata ni?" Inda sabo ya ci ace ta saba don haka ta shanye tambayar ta shiga magana. "Ki kira Hajara ki ji tana ina? Ni ba kati a wayana. Ga ruwa nan ya fara ƙarfi kar ya yi mata illa a waje." Safiyya ta harare ta. "Ji? Sai ka ce damuwar ki ka yi dagaske. Uhum, ta ciki dai na ciki na sani. Toh Hajara ta cemin gidan Anti Hafsatu za ta kwana kuma ta sanar da Malam ma." Inna ta ɗan yi shiru, sai kuma ta amsa da shikenan daga haka ta fice ta bar ɗakin. Safiya ta bi ta da wani murmushi na zallar mugunta. Ba ƙaramin daɗi ta ji ba da abin ya zo musu a daidai, wato sun shiryawa Inna tuggu, sai kuma ga ruwa Allah ya kawo. Shakka babu abin zai ba da citta sosai. Ta dannawa Hajara kira, bai yi ko ƙara uku ba ta ɗaga. Ƙasa-ƙasa ta soma magana. "Ke ya ake ciki? Kin ga Allah ya na sonmu, ga ruwa ya sauka yanda komai zai fi tafiya daidai ko?" Tana jin sautin dariyar Hajara ita ɗin ma taya ta tayi. "Ke dai bari ƴar uwa. Ni kaina ina ganin yanda hadari ya haɗo na ji wani sanyi a raina. Faɗuwa ta zo daidai da zama." Suka yi dariya. Safiyya ta ƙara da cewa. "To ina Yusuf din? Ku na tare ko? Kin ƙara masa bayanin komai?" "Yes, ba mu da matsala da shi. Ya san abin da zai yi. Ina fatan wayar tana hannunki?" Safiyya ta gyaɗa kai. "Ai dole. Shashashar ba ta ko yi cigiya ba kin san fa babu dangin da za su neme ta." Daga haka suka ƙara darawa sannan suka yi sallama. Safiyya ta yi wata ƙwafa kafin a fili ta ce. "Yau Mairamu za ki kwanan gidanku." Ana cikin sallar isha'i Malam ya shigo gidan da sauri-sauri ya faɗa ɗakinsa. Kayansa har sun ɗan jiƙa. Inna ta ji shigowarsa amma kasancewar ta tayar da sallah ya sanya sai da ta idar kafin ta nufi falonsa da sallama ɗauke a bakinta, ta tabbata ruwan ne ya tsaida shi har isha'i. Lokacin ruwan ma ya tsagaita sai iska mai karfi da yayyafi, sai ko rugugi da ke nuni da har lokacin akwai sauran  ruwa wanda idan Allah ya nufa zai iya zuba a kowane lokaci.   Ganinsa a tsaye da waya a kunne ga Safiyya durƙushe a gabansa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya ya sanya kirjin Inna bugawa da ƙarfi, a fili ta kira sunan Allah kafin ta dubi Safiya karo na biyu san nan ta maida duba ga Malam. "Lafiya? Meyafaru?" Ta furta hannunta a saman ƙirji don sosai ta tsorata. Tunaninta ya fi karkata kan ko wata mutuwar ce aka yi. Malam bai ko kalleta ba fuskarnan a matuƙar ɗaure ya cigaba da magana a wayar. Da ta nutsu sai ta gane kwatance yake yi wa wani na gidan, karshe ta ga ya kasa nutsuwa yana fadin bari ya fito ya tarbo shi, daga haka ya zura takalminsa ya bi ta ƙofar waje ya fice. Inna wacce daga kallon da Malam ya bi ta da shi ta sha jinin jikinta a sanyaye ta ƙara jefawa Safiyya tambayar da ba ta da tabbacin samun amsa gareta sai don ƙarfin hali. "Safiyya, wani abu ya faru ne a gidan?" Ga mamakin Inna sai gani ta yi Safiyya ta miƙe tsaye tana wani murmushi haɗi da dariya kafin ta amsa a sheƙeƙe. "Ba za ki gane abin da ke faruwa ba sai yau kin yi kwanan gidan Jibo Ladan. Dama ai mun faɗamaki akwai ranar ƙin dillanci." Tana kai wa nan ta saka kai ta bi hanyar da Malam ya bi ta bar Inna da sakin baki gami da bin bayanta da kallo. 'Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!' Inna ta shiga maimaitawa a zuciyarta a sadda ta ga Malam ya dawo falon ɗauke da Hajara a hannunsa gami da kwantar da ita saman doguwar kujera. Gaba ɗaya ya ruɗe, a rikice ya ke faɗin. "Kar ki yi min haka Ƴar Malam, ki buɗe idanunki ko hankalina zai kwanta. Ya Allahu!" "Kar ka damu Baba, in sha Allahu fa yanzu komai ya daidaita, kawai allurar ce ba ta gama sakinta ba. Amma za ta farka a kowane lokaci a yanzu." Saurayin da ba ta san ko waye ba ne ya faɗi hakan, dalilin kenan da Inna ta maida hankali ga dubansa, sannan ta dubi Hajara wacce fararen kayanta duka sun ɓaci da ƙasa. Kanta babu ko ɗankwali sai farin bandeji da aka zagaye kan ga alamun jini da ya tsassafo ta cikin bandejin daga gaban goshin, babu inda ke motsi a jikinta idan ka cire hawa da saukar da kirjinta ke yi shaidar tana numfashi. Can kuma sai ta soma ɗan motsa kanta kamar irin a firgice, tarr ta buɗe idanunta ta miƙe zaune a gigice take faɗin. "Wayyo Allahna! Ga shi nan! Ga motar za ta taka min kai! Wayyo!" Malam sosai ya rirriƙe Hajara, Safiyya ma ta shiga taya shi ta hanyar riƙe ƙafafunta tana kiran sunanta da karfi. Sai da Malam ya haɗa da addu'a sai kuma ta nutsu. Ta dubi Malam kawai ta fashe da kuka tana ruƙunƙume hannunsa. "Babana kai ne? Dama akwai rabon mu kara ganin juna? Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!" Malam wanda idanunsa suka kaɗa sosai, yana jin kirjinsa ya mishi wani irin nauyi daƙyar ya haɗiyi miyau ya soma magana. "Ni ne ƴar Malam, Alhamdulillah. Babu abin da zai raba ki da Malam kin ji ko? In sha Allahu ko mutuwa za ki yi, ba ta wannan hanyar na tashin hankali ba." Hajara ta jinjina kai hawaye ya jiƙa fuskarta. "Mamana Allah ya gafarta maki. Yau na ga tashin hankali Malam, ni dai na san na fito daga makaranta ana ta iska tun wajen biyar na yamma, na dinga kiran wayar Inna yana ta ƙara ba ta ɗagawa. Anti Safiyya kuma nata a kashe dama tun kafin na fita ba ta da chaji. To ni dai ban ji ƙarar babur ba sai ji nayi wani ƙarfe kamar ya buge ni na faɗi na buge kaina. Daga nan ban san fa meke faruwa ba." Saurayin anan ya yi gyaran murya ya ɗora zancensa. "Wanda ya yi mata wannan lahanin guduwa ya yi bai tsaya ba, ni na kai ta chemist mafi kusa tare da wasu mutum biyu, komai ya zo da sauki ma babu karaya babu komai. Bayan an tabbatar da lafiyarta ƙalau ne shi ne na yi amfani da wayarta na fara kiran lambar da na gani a karshe wanda ta rubuta Inna Mairamu yana ta kara amma ba ta kusa, shi ne na kira lambar da ta saka Sis Safiyya." Malam ransa idan ya yi dubu to ya ƙara zafafa dangane da lamarin Inna, ya kara yiwa saurayin da ya ce sunansa Yusuf godiya ganin ya na bankwana zai tafi gida saboda dare, har waje ya taka masa inda yana fita Hajara da Safiyya suka tafa gami da yiwa Inna gwalo. Inna dai ta yi mutuwar tsaye tana kallon irin wannan zargen da aka ƙulla mata mai wuyar kwancewa. To ta ina ma za ta fara fidda kanta a wurin Malam? Wayarta ta faɗomata a rai, sai a sannan ta tuna ita tun da ta ajiye wayar saman kujera ba ta kara bi ta kanta ba don lamarin waya sam bai dame ta ba matukar ba labaran safe za ta ji ba. Tun sadda Zakari ya ba ta kyautarsa sai dai ko shi ko Hafsatu su kira ta sai kuwa jifa-jifa idan Kawunta Jibo ya kira ko kuwa yaransa a gaisa. Ba ta kai ga gama tunanin ba ta ji muryar Malam a tsakar kanta. "Mairamu!" Ta ɗago tana dubansa ba tare da ta iya cewa uffan ba. "Kin ba ni mamaki kodayake bai ma kamata na yi mamakin komai ba! Tunda Hajara ba ɗiyarki ba ce ba! Ba ki san ciwon haihuwa ba wannan na tabbata shi ne babban dalilinki na yin watsi da lamarin budurwar da ta wuce ƙa'idarta na dawowa gida ba ki ko tuntuɓa ki ji lafiyarta ba! Ni na san da ace ke ki ka haifi Hajara, ba za ki kasa nemanta a waya ba, ba kuma za ki ƙi amsa wayarta da gangan ba! Ok, Mairamu kin nuna min kin gaji da zama da yarana ko? To ai wanda ba ya son ɗanka ba ya sonka kai ma! Don haka yanda ki ka kusa ajalin ɗiyata, na rantse a yau a yanzu ba za ki ƙara ko mintuna ashirin a gidana ba. Ki fice ki bar min gida a yanzu tun kafin na ɗauki mummunan matakin da ya zarce wannan!" Ya ƙarashe a tsawance, Inna Mairamu da tun fara maganarsa ta ke kallonsa ta maida duba ga Hajara da Safiyya waɗanda duniyar ta yi musu mugun daɗi har wani murmushi suke yi a sace. Ta juya don ta fice a ɗakin sanin da ta yi babu wani bayani da zai wanke ta a zuciyar Malam a wannan dare. Tana hawaye ta ɗauki abin da duk ta san za ta buƙata, tana shirin zura hijabinta ta ji an bugo mata abu mai kama da ƙarfe ko dutse a goshi, Safiyya ce. "Ga wayarki. Ke da gidan nan kuma har abada muna mai tabbatar maki. Sakin da ba a yi a gabanmu ba na tabbatar zai biyo ki har gidan tsohonki." Tana kai wa nan ta fice tana ƴar dariya gudun kar Malam ya ji. Inna ta kai duba ga wayar da haskenta ya sa ta fahimci me Safiyya ta wurgo mata. Hannu ta saka ta ɗauka gami da duba kiraye-kirayen da suka shigo, eh tabbas an kikkira wayar sai dai ta sani koma mene ne shirinsu ne. Murmushi mai kama da yaƙe ta yi sannan ta share hawayen da ya zubo mata. Ɗakin ta rufo ta koma ta rufe na falonta sannan ta fice daga gidan ko hanyar wajen Malam ba ta kalla ba. *** Kawunta Jibo da matarsa Dada sun shiga tashin hankalin ganinta a daren, ga wani zazzaɓi da ya rufe ta har haƙoranta na haɗewa wuri guda. Ransu ya yi mugun ɓaci don dama suna da labarin irin haƙurin da Inna Mairamu ke yi a gidan. Kawu Jibo ya rantse ba zai nemi Malam ba har sai sadda ya kawo kansa gareshi duk da cewa Inna Mairamu ba ta basu labarin komai ba kawai dai ta ce Malam yace ta taho. Shi babban ɓacin ransa bai wuce na yanda babu ko tausayi ba ya koro masa ɗiyarsa a dare ga kuma ruwa da ake yi wanda har ya soma ƙarfi. Daga yanayinta kaɗai sun fahimci ma a ƙafa ta tako. Nan da nan Dada ta ba Inna kaya ta sauya, ta sha magani amma a wannan dare bacci bai iya ya ɗauke ta ba saboda damuwar abin da Malam ya yi. Sai da Inna ta shafe watanni biyu a gida babu ko ƙeyar Malam, Hafsatu da Zakari wanda ya zo ganin gida har sau biyu, sun yi zarya a gidan Kawu Jibo har sun gaji kan ya yi haƙuri ya kira Mahaifinsu a sulhunta Inna ta koma ɗakinta musamman ma da suka ji daga bakin ɗiyar Dada ta biyu mai suna Hajjo cewa Innar na dauke da juna biyu. Ƙarshe Kawu Jibo cewa ya yi matuƙar ba za su bar batun komen Inna ba to kar su ƙara tako ƙafafunsu gidan. Haka suka ja bakinsu suka yi shiru. A bakin Hafsatun ne Inna ke jin auren Safiyya ya taho ana ta shirin biki don har an kawo lefe. Ta taya murna har ranta gami da sanyawa lamarin albarka. Har aka yi bikin Safiyya, Inna ba ta gidan Malam. Zuwa lokacin gaba daya Malam din ya yi sanyi, kewa da kuma damuwa akan rashin Innar ya ci ya cinye shi. Amininsa Alhaji Abubakar babu yanda bai yi da shi akan ya je su sulhunta ba ya yafemata amma ya ƙi. Hakanan manya a danginsu. Ya sha faɗa sosai sai dai kuma yana jin dagaske ya kusa rasa ɗiyarsa sanadiyyar Inna Mairamu, to akan me zai je ya maido ta gidansa? Koda bikin Safiyya ma, a can gidansu na gado aka yi komai har tariya. Sai lokacin bikin ne yake jin labarin cikin dake jikin Inna daga bakin Hafsatu wacce ta cire kunya da ma tsoro ta sanar da shi duk a kokarinta na lallaɓa mahaifin nata kan ya yi haƙuri ya maido Inna ɗakinta. Wannan ne ya sanyaya jikinsa sosai musamman da ya tuna gorin haihuwar da ya yi mata kafin ta bar gidan, da ya tsaya lissafi sai ya ga kenan cikin zai yi watanni huɗu a lokacin. Wannan ya sa da taimakon Alhaji Abubakar suka ɗunguma zuwa ga Kawu Jibo don dama shi Alhaji Abubakar ya je yi wa abokinsa biko har sau biyu ba tare da ya aika shi ba amma Kawu Jibo yace ya fidda hannunsa don wannan ba huruminsa ba ne ya bar su da shi kawai. Ranar farko da ya gansu bai ko ba su damar magana ba face takardar Inna Mairamu da ya ce lallai Malam ya rubuta ya ba shi. Malam ya ga duk inda yake hasko rashin saukin lamarin abin ya shallake tunaninsa. Ga shi a ɗan ganin da ya yiwa Inna Mairamu ta gifta a tsakar gida ya ji nan duniya babu abin da yake so sai ya ganta a kusa da shi. Ta ƙara kyau da haske abinta, kana ganin yanayinta ka san tana ɗauke da juna biyu. Sam bai sanya ta muni ba. A ɓangaren Inna kuwa, ta riga da ta cirewa ranta damuwar Malam da lissafin yaushe zai zo bikonta, hankalinta kacokam ya koma ga rainon cikinta. Ko babu komai ita ma za ta ga gudan jininta a doron ƙasa da yardar Allahu. Ita a lokacin duk abin da Allah ya hukunta a aurenta da Malam tana ji a ranta lallai za ta karɓa da hannu bibbiyu. Ba za ta ce tana ƙin Malam ba, amma tana jin cewa duk auren da babu yarda da aminci a ciki, to fa za'a yi ta samun matsaloli barkatai fiye da misali. To dai idan zama bai ƙare ba, kome ya zama dole koda kuwa zuƙata ba su kai ga gama hucewa ba. Cikin hukuncin Allah Kawu Jibo ya sauko ya haƙura Inna ta koma ɗakinta da zama. Sadda ta je babu kowa a gidan don Hajara ma tun bikin Safiyya take can gidansu Malam ba ta dawo ba. Amma tana jin labarin Inna Mairamu ta dawo kuma wai tana ɗauke da juna biyu, ta tattaro ta dawo gidan a lokacin Innar tana da sati uku a gidan. Ganin tsinin ciki a jikin Inna Mairamu ya sanya wani abu mai ɗaci ya tsaya a maƙogwaron Hajara. Dama kafin ta zo gidan ta ci kuka sosai saboda tsananin baƙin cikin wai Malam zai samu wasu yaran kuma ba daga Mahaifiyarta ba. Inna kamar babu abin da ya faru haka ta tarbe t da murmushi saman fuska gami da yi mata sannu da zuwa. Hajara ta ja dogon tsaki a fili ta ce. "Aikin banza, Allah ta wadaran wacce ba ta da zuciya." Tana faɗin haka ta shige ɗakin da yake mallakinta ita kaɗai a yanzu ta banko ƙofa garam! Inna ta girgiza kai, dama ta san ai mai hali ba zai fasa ba. Sam ba ta ji zafi ba ta cigaba da cin kwaɗon zogalen da makwafciyarta Habiba ta aikomata. Kusan za ta ce duk a makwaftansu Habiba ce kaɗai sai kuwa Mama Iyabo wacce ba bahaushiya bace, suka taka har gidansu domin jajanta mata abin da ya faru. Saura kuwa kasancewar tsofaffin makwaftan Marigayiya Asma'u ne, sai suke shakkar shiga sabgarta saboda ganin yaran ba sa jituwa da ita. A wajen ma mutane da dama a layin gani suke yi dagaske Inna Mairamu mugunta take yiwa yaran don ba ita ta haife su ba. Suna kuma amfani da hirarrakin da suke ji daga wajen Safiyya da Hajara ne. Don a cewarsu har rowar abinci take musu, babban burinta ma ta raba su da mahaifinsu baki daya. Wannan ya janyowa Inna Mairamu baƙin jini a wajen mutane da dama idan ka cire Habiba da ba ta wani jima da tarewa a unguwar ba sai ko Mama Iyabo wacce ta san Marigayiya Asma'u amma hakan bai hana ta shiga sabgar Inna Mairamu ba, hakan kuwa ya ja mata zagi da baƙin jini a wurin su Hajara. Idan ma ta zo gidan kallo ba ta ishe su ballantana a kai ga gaisuwa. Ɗinkin da suke kai wa shagonta ta yiwa musu kasancewarta tela, sai gaba ɗaya suka gwammace su haƙura su nemi wani wurin. Zaman Hajara da Inna Mairamu sam ba ya yiwa kowannensu daɗi. Koda dai nace ma Innar tunda ita Hajara sai dai ta haɗa mata wani sharrin ta bar ta da fushin Malam. A haka a daddafe Inna Mairamu ta shiga watan haihuwarta, komai na buƙata kuwa sai da Malam ya siyo. Hajara kasa ma zama ta yi a gidan tsabar baƙin ciki ta tattara ta koma gidan Hafsatu ta cigaba da zuwa makarantarta ta can bayan ta fake da cewa Malam karatun jarrabawa take son yi a nutse ba ta son duk wata hayaniya. Bai matsa mata ba kuwa ya biye mata. Inna da aka yi zancen a gabanta ba ta ce musu uffan ba. A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah, Inna Mairamu ta haihu ta samu ɗiyarta mace mai matuƙar kama da ita kamar an tsaga kara an karya. Soyayyar yarinyar ta cika ko'ina a zuciyarta. Sanadiyyar wannan haihuwa da dama a makwaftan sun shigo barka, wasu don kawai su yi gulma ne su ganewa idanunsu irin kyawun da ake faɗi na yarinyar don a cewar masu kai musu tsegumin, kaf gidan Malam ba'a taɓa yi masa haihuwar fara mai kyau irin Halimatus-Sadiya ba. A ɓangaren su Baba Habu yaran Malam kuwa, babu wanda ya tako ya zo. Kunyar ma shigowa unguwar suke yi balle a tarbe su da yi musu barkar haihuwar matar ubansu. Shi kuwa Malam ko a jikinsa, fuskarsa a washe duk sadda ya ɗauki jaririyar yakan ji tamkar kada ya ajiye ta. Yana jin kaunarta a zuciyarsa. Ya so ace Asma'u ya raɗamata amma kuma ganin Inna Mairamu ta cire kunyarnan ta fulani ga yaran fari ta nemi alfarma akan ya raɗamata sunan mahaifiyarta ya sanya shi haƙuri da nasa ƙudirin don ya faranta mata ganin ta sha wuya sosai don sai da ta yi sati tana naƙuda. Inna Mairamu ta ji daɗin wannan karramawar da ya yi gareta. Ya nemi ko a ɓoye sunan ita kuwa ta ce aa, sai dai ko a kira ta da Sadiya tunda an fi sanin mahaifiyarta da suna Haleema. Haihuwar Halima da watanni biyu ne Hajara ta dawo gidan. Ko ganin jaririyar ba ta taɓa yi ba ita da Safiyya. Koda ta dawo ba ta bi ta kan Inna ba ballantana ta yi mata barka. Inna tuni ta wartsake mai tayata wanka ta tafi, ita ke yin komai na gidanta da kula da Sadiya. Ranar da Hajara ta fara sanya Sadiya a idanunta, a ranar ta soma jin tsanarta mai yawa a zuciyarta. Tabbas Allah ya yi halitta a fuskar yarinyar, duk kuma kushen mai kushe, ya yi kaɗan ya kalli Sadiya ya kushe ta. Dalilin kyau da kuma haushin Malam bai saka sunan Mahaifiyarta ba yanda za ta samu damar ƙara ƙuntatawa Inna Mairamu ba, su ne suka haɗu suka haifar da tsanar Sadiya a wajen Hajara. Wahala kuwa da Sadiya ta sha a wurin Hajara mai yawa ne, don hatfa da ruwan zafi Sadiya ta taɓa ƙonewa a cinya da shi sakamakon barinta da Inna ta yi a tsakar gida ta shiga wanka. Sai fitowa ta yi ta ga yarinya na ihun kuka da azaba ga ruwa ya zuba a cinyarta. Ba ta ga kowa ba, ta kuma sani Sadiya ba ta fara rarrafe ko jan ciki ba sai zama balle ta kawo  ko ita ta zubawa kanta. Wani lokacin idan ƙiriniya irin na yara ya tashi, ta faɗa ɗakin Hajara, Inna Mairamu sai dai ta ga yarinya ta fito tana kuka. Wani lokacin ma har da fasasshen baki za ta fito duk sadda Hajara ta siyo wani abin kwalam din, sai ta fake da cewa wai ta fiye kwaɗayi ne shiyasa ta buge bakin. Azaba dai iri-iri babu wanda Sadiya ba ta gani ba a wajen Hajara har ta shekara uku, lokacin Inna ta kara samun ciki har ya fito sosai. Wannan kuwa har waƙar mai ciki Hajara ke rerawa a tsakar gida tana habaice-habaice har da fadin wai duk dai maita irin na wata, ba za ta taɓa haihuwar bakwai cif kamar Asma'u ba. Kuma ba za ta haifi abin da zai ƙwace soyayyar da Ubansu ke musu ba. Inna dai ba ta ko kallonta. A lokacin ne ta dauki Sadiya ta kai ta can gidansu hannun Dada. Tana shiga watan haihuwarta ta sauka lafiya ta samu ɗiya mace wacce daga kallo za ka san jinin Malam Sa'ad ce saboda kamanninsa da ta ɗauka gaba ɗaya. Baƙa ce amma baƙinta bai kai na su Hajara ba sai ita ta kasance mai ɗan haske sakamakon nonon farar mace da take sha. Hajara tun sadda Malam ya raɗawa jaririyar sunan mahaifiyarta Asma'u ta ce a dinga kiranta da Husna. Abin da yake bai wa Inna Mairamu mamaki bai wuce ganin yanda Hajara kan tsallako ta shigo har ƙuryarta ba ta sa hannu ta dauki Husna ta fita da ita tana bata kulawa. Ta yarda lallai dagaske ba karamin so da kaunar Mahaifiyarta take yi ba. Ba ma ita kaɗai ba, hatta Safiyya sai da ta zo gidan ganin Husna har da kayan jarirai ta kawomata. Mustafa da Hashimu da Baba Habu su kansu wannan karon sun zo sun ga Husna. Inna Mairamu da ɗiyarta, amma Hajara babu irin tuggun da ba ta shirya mata ba sanadiyyar Husna. ©Rufaida Umar https://arewabooks.com/book?id=663894ac767a55b1dd421f6a *Akwai pages na gaba har guda biyu a manhajar arewabooks. Kuna iya bibiya a can*😃🥰 *** *Kazar Kwanci...* A kwana a tashi yau fari gobe baƙi, har lokacin da Hajara ta yi candy. Sun zana jarrabawarsu ta ƙarshe sannan suka haɗa ƴar ƙwarya ƙwarya da abokan karatunta don taya juna murna. Ranar walimar makarantar na graduation, kaf yayyunta da dangi sun je. Inna Mairamu haka ta kai zuciya nesa duk kuwa da furucin Hajara na cewa ba ta gayyatarta da zabiyar ƴarta, hakan bai hana ta shirya ta bi Malam ba. Husna dake gidan Safiyya kwananta biyu a can. Sadiya kuwa tana aji biyu a firamare yayinda Husna take na farko a nursery. Malam na iyakar kokarinsa wajen ganin yaransa sun yi makaranta mai kyau kuma cikin rufin asiri, kaf a yaransa babu wanda ya taɓa yin ta gwamnati sai Hashimu babban ɗansa wanda ya yi karatun tun duniya na kwance, makarantun gwamnatin ba su lalace da rashin karatu yanda ya kamata ba. Daga kan Baba Habu kuwa dukkansu ta kuɗi ce. Sai dai kuma irin ta kuɗin da na baya suka samu, su Sadiya ba irinta suka samu ba sakamakon chanjin yanayin samun na Malam. Amma kuma daidai gwargwado a na karatu. An yi bikin walimar yaye ɗalibai an kammala, Hajara kasancewar tana cikin farin ciki ko kallo Inna Mairamu ba ta ishe ta ba. Sam ba ta san da zuwanta ba ma sai da ta ji wata ƙawarta a murya ƙasa-ƙasa tana faɗin. "Kai Hajjo, dama kuna da fara a gidanku? Baby girl ɗin nan ta yi min kyau." Furucin ne ya sa ta ankara da Sadiya wacce Inna Mairamu ta sanya mata kayan sallarta da ya wuce, rigar shadda ruwan bula mai haske wanda ya ɗan ɗage mata, an yi aiki a wuyan sai ko ɗankwalin da aka yi mata ɗauri daidai da zamani. Ta yi kyau yarinyar kamar irin wacce ta fito daga gidan masu hannu da shuni. Wani abu ya zo wa Hajara wuya, sai ta ja tsaki ta maida dubanta ga ƙawarta. "Malama wannan kinga sun yi kama da ƴan gidanmu? Toh makwaftanmu ne suka zo gayyar soɗi. Dallah muje." Ta faɗi tana sa hannu ta ɗauki Husna wacce a farko take riƙe da hannunta. Inna Mairamu ta ji amsar da Hajara ta ba ƙawarta sai dai ba ta ji furucin ƙawar ba, girgiza kai kawai ta yi gami da yi wa Hajarar fatan shiriya a zuciya. Hotuna sun yi shi sosai kafin kuma su tattara su tafi gida aka bar Hajara a nan. Gaba ɗaya gidan Malam suka nufa, anan aka ci girkin da Inna Mairamu ta dafa musamman domin wannan ranar. Safiyya na ci tana korafi wai kamar maggi ya so ya yi yawa. Harararta da Hafsatu ta yi ne ya sanya ta taɓe baki ba tare da ta tanka ba.   "Allah ya gafartawa Mama, nasan da ace tana duniya wannan ranar ta zo, ba ƙaramin farin ciki za ta yi ba. Na so ace points dinta ya kai na samun medicine dinnan da Mama ke buri." Cewar Mustafa kenan bayan an kammala cin abinci an yi zaman hira. Malam ya yi murmushi. "Ai akwai wata shekarar, tunda har ranta itama ya fi son ɓangaren likitan, sai ta ƙara hakurin zama ta maimaita jamb, idan Allah ya nufa sai a dace a wannan karon." "Ni kuwa sai na ga da zaman jiran ba gwara ta haƙura ta yi nursing ba?" Faɗin Yayansu Hashimu. Baba Habu ya cafe zancen. "Kayya, Auta za ta yarda da wannan shawarar taka? Ta fa ƙwallafa rai." "Gaskiya dai ni ma ina bayan Baba Habu, ina ma ta hakura. Ai dai duka fannin asibitin ne ko? Zaman jiran ba shi da amfani." Faɗin Hafsatu. Malam ya girgiza kai. "Ku bar ta ta kara gwada wa. Na yarda da ita, na san za ta iya." Ganin haka kowa ya riƙe na shi ra'ayin, aka bi lamarin da addu'a. Kamar koyaushe Malam ya shiga tuntuɓar kowannensu idan akwai mai wata matsala koda a ɓangaren iyalinsa ne, kowa ciki yace babu. Daidai gwargwado asirin kowannensu a rufe. Mazan suna kuma zaune da matansu lafiya, idan ma akwai mai matsala a matan ba ta wuce matar Hashimu ba wacce kwana biyun ta tada hankali akan ginin da ya ke yi mai ɓangaren mace biyu, ita ta sani aure zai yi a cewarta bai isa ba. Amma ganin wannan ba matsala ba ce yasa bai kawo ta gaban Malam ba. Ko babu komai ai shi namiji ne, yana buƙatar sirri a rayuwarsa. Hafsatu ce ta miƙe tare da Safiyya suka bar falon zuwa tsakar gidan inda Inna Mairamu take zaune tana kiciniyar sauyawa Sadiya kaya ganin duk ta ɓata rigar shaddar da maiƙon abinci. Dama tun kammala cin abincinsu ta miƙe ta basu wuri don su tattauna da mahaifinsu. Safiyya ta ja gujera ƴar tsuguno ta zauna tana faman taunar cingam wanda ba ta rabo da shi saboda gudun tashin zuciya.  Nan Inna Mairamu suka yi ta hira da Hafsatu ban da Safiyya wacce a ƙarshe ma miƙewa ta yi ta nufi ɗakin Hajara ta kwanta ganin Husna ma sharar bacci babu abokin hira. A bakin Hafsatu ma Inna Mairamu ke ƙara jin cewa Safiyya na da juna biyu. Murmushi ta yi da fatan rabuwarsu lafiya da cikin, dama ai ta ga alamomin da ke nuni da hakan sai dai tunda ba huruminta ba ne ya sa ta ja baki ta yi shiru abin ta. *** A haka rayuwar ta cigaba da tafiya a gidan Malam Sa'ad, Hajara ba ta fiye zaman gidan ba, mafi yawan lokuta idan babu makaranta alhamis da juma'a, jan Husna take yi su je gidan Safiyya ko kuma can dangi su kwana. Farko har a lokutan islamiyya fita take yi da ita, sai da Inna Mairamu ta nunawa Malam ba ta son hakan sannan ya yi magana don shi ma sam ba ya son wasa da karatu ya san darajar ilimi tunda malamin makaranta yake. Hajarar ma ya so ta koma bayan saukar Alkur'ani da ta yi don cigaba da samun karatukan litattafai na hadisi da fiqhu amma abu ya gagara dole ya rabu da ita. Da dai boko ne, tana da matukar kokarin dagiya wajen karatu da ganin ma Husna ta yi don ita ke koyar da ita aikin makaranta har wani lesson na musamman take mata a gida. Takan cewa Sadiya, "Ki je Nanny ta koyamaki, kodayake me ma ta sani ban da wankin kashi da fitsarin yara da sharar aji. Sai dai ki yi ta daukar ta ƙarshen aji yarinya idan dai ni zan koyar da ke karatu." Inna kuwa sai dai ta yi murmushi, don tana matsayin Nanny a makaranta ba yana nufin ko yaya ba ta da ilimin ba, a baya ta soma na yaƙi da jahilci sadda mijinta ya rasu, kuma ilimi na addini sai dai ta godewa Allah don Kawunta Jibo ya tsaya tsayin daka wajen ganin sun yi. Sau da yawa kuma ita koyar da Sadiya aikin makaranta da aka basu, yarinyar ba ta taɓa zuwa ta karshen aji ba tunda ita ma da ɗan kokarinta. Daga baya ne kuma ma Abba ya cewa Malam ya dinga turo su ana musu lesson da yaransa a gida, Malam ya yi godiya don shi a yanzu bai cika samun lokacin koyar da su ba ganin Hajara na yi don tace masa har Sadiya tana mata. Gidan Alhaji Abubakar babban gida ne don ya fi Malam rufin asiri sosai, dan kasuwa ne wanda har yakan fita ƙasashen duniya sarin kaya, wani lokacin kuma ya tura babban yaronsa a kasuwa. Allah ya sanyawa kasuwancinsa albarka sosai. Matansu biyu kuma suna zaune lafiya kowacce da ɓangarenta. Ba su zauna sun dogara da abin hannun mijinsu ba, Hajiya Mariya uwargidansa kuma aminiya ga Marigayiya Asma'u mahaifiyar su Hajara, haifaffiyar garin Kano ce kamar mijin nata shi ma. Sun yi aure cike da so da kaunar juna. Yaransu tara cif. Babban ɗansu Hamza ya girmi Hashimu babban ɗan Malam, saboda Alhaji Abubakar ya riga Malam aure. Sai da ya shekara sannan aka yi bikin Malam da Asma'u. Sai da Haj Mariya ta yi haihuwa biyar kafin Abba ya ƙara aure. Duk yanda aka kai ga zigata sam ba ta tayar da hankali ba don dama tsakaninta da shi bai taɓa yi mata alƙawarin cewa da ita kaɗai zai rayu ba. Kuma ya sha faɗa idan har Allah ya ƙaddaro masa aure zai yi fa, shi ba mai ra'ayin zama da mace ɗaya ba ne. Tun tana kallon abin a wasa har ta soma jin haushi da kishi, karshe ma sai ta saduda. Wannan ne dalilin da yasa auren bai ɗaga hankalinta sosai ba sai dai abin da ba a rasa ba tunda kishi ya zama dole idan da so da kauna. Marigayiya Asma'u tana daga cikin masu kwantar mata da hankali da nuna mata muhimmancin hakuri, ta sani sarai Asma'u ba fa da kishi irin na jahilai. Matar ta san me take yi sosai. Kuma tana ji a ranta koda ace ma Malam ya dauko aure, Asma'u ba za ta tashi hankalinta ba, sai dai soyayyar da kowa ya shaida Malam na yi wa Asma'un ne yasa babu wanda ya taba kawo mata zama da kishiyar. Ga shi kuwa sai bayan rasuwarta ne ya yi auren. Lokacin da aka yi auren Abba da Amaryarsa Zulfa'u ne, Malam ya yi rashin matarsa Asma'u. Abba ya yi angwancinsa cike da jimamin mutuwar matar aminin nasa. Kar Haj Mariya ta ji labari, don zafin mutuwar Asma'u da tashin hankalin da take ciki ya kara mantar da ita wani abu wai kishin Zulfa'u. Girkin ma gaba daya sakarmata ta yi har tsawon sati biyu saboda ba ta cikin nutsuwarta. Hamza, Radeeya, Lubna, Huzaifa, Amir da Amira, Husna, Khalid da Affan. Su ne yaran Haj Mariya. Amarya Zulfa'u wacce aka auro daga Maiduguri kuwa yaranta uku. Musaddik, Amina (Meenat) da autarta Zainab (Zee Mama). Hamza ya yi aure yana zaune da iyalinsa a Kaduna inda yake a barikin soja, Radeeya da Lubna su na zaune a nan Kano da mazajensu. Sai ko Huzaifa da ke ƙasar India inda yake karantar fannin medicine. Amir da Amira suna dab da yin candy, Husna da Musaddik kuwa suna aji na farko a babban sakandire, yayinda Meenat ke aji na biyu a firamare, tare suke tafiya da Sadiya. Sai ko Zee Mama da suke tafiya aji guda da Husna. Wadannan su ne zuri'ar Alhaji Abubakar B Sharaɗa. Tun daga sadda ya yi magana kuma, Sadiya da Husna suka koma lesson a gidansa a daki na musamman wanda ya ci sunan Study Room don babu komai a ciki sai litattafai da sauran kayan karatu, nan inyamurar malamarsu ke koyar da su tare da Meenat da Zee Mama sai ko Husna da  Musaddiƙ. *** A lokacin ne samari suka dinga ɓullowa suna son Hajara, aikuwa duk wanda ya kawo kyauta to fa ita da Husna ke sanyawa a gaba su karar, idan na amfani ne na manya ta yi abin ta, idan kuwa kudi ne siyayyar akan Husna yake ƙarewa. Sadiya ko oho, sai ko idan Husna ta turje akan lallai sai an yiwa Sadiya ne saboda tana kaunarta sannan Hajarar ke yi tana kiranta da mayya kwadayayya. Shekara na zagayowa ta sake maimaita jarrabawar Jamb. Sai dai wannan karon ma sakamakon bai kai yanda ake buƙata na medicine ba, ta sha kuka a karshe don kanta tace ta hakura za ta nemi nursing. Shi kuma cikin ikon Allah ta hannun Alhaji Abubakar wanda tsabar aminta ne yasa Malam sanyawa dansa sunan suke ce masa Baba Habu, ya nema mata gurbin nursing din. Sadda aka yi jarrabawa ta yi nasarar tsallakewa. Murna kamar ta yi me. Shi kansa Alhaji Abubakar wanda suke kira da Abba ya yi farin ciki kwarai da Hajara ba ta watsa mishi ƙasa a ido ba. Aikuwa ana soma karatu ta maida hankali sosai, hakan ya sa ma ta rage shiga harkar Inna Mairamu, ita ma ta samu salama. Sadiya ta taso yarinya marar son hayaniya a wasu lokutan kamar dai Innarta, amma fa ko a kafa ba ta kama Inna a bangaren hakuri ba, Inna takan ji za ta iya yafewa mutum, ita kuwa Sadiya abu daya ta rike a ranta, Hajara da Safiyya da ma sauran yayyunta idan an cire Yaya Zakari da Anti Hafsatu, babu wanda ke son su ita da Innarsu. Shiyasa ita ma ba ta son su, koda dai tana mugun tsoron Anti Hajara don ko muryarta ta ji sai gaba daya ta ruɗe, ko wasa take yi a ɗaki za ta hankaɗe kayan wasan nata wani lokacin har tana bugewa haka za ta shige har bayan gadon Inna ta ɓuya tana rawar jiki. Sai da Inna ta haɗa da roƙon Allah da yawaita addu'a kafin wannan tsoron ya ragu da kashi talatin. Ko inda Malam yake Sadiya ba ta zuwa idan Hajara na wurin, wani lokacin abinci kasa ci take yi idan an yi zaman ci sai dai daga baya ne Inna ke zuwa ta kai mata ɗaki ta ci. A hankali kuma tana girma tana ƙara wayo tsoron na ɗan raguwa ba kamar a baya ba. ***   Tafiya ta yi nisa, Sadiya na ajin farko a sakandire, Hajara ta kammala karatunta na Nursing. Lokacin shekarunta goma sha biyu a duniya, yayinda Husna ke da shekaru tara. Ita kuwa tana firamare aji huɗu . A wannan shekarar dai Hajara ta fara aikinta a karamin asibitin dake kusa da su kafin a cewar Malam, ta samu aiki a babban asibitin gwamnati. Tun fara aikinta kuwa sai idanunta ya kara buɗuwa. Ita dai ba ta da kyau na a zo a gani, sai dai akwai dirin jiki ga uwa uba iya daukar kwalliya. Da wannan take jan hankalin maza. Kanta yana ƙara rawa da yanda suke ruɗewa su na sonta. Haduwarta da wata abokiyar aikinta mai suna Nusaiba, ya kara jefa rayuwarta cikin ruɗin shaiɗan. Sanadiyyar Nusaiba ta koyi sakin jiki ga duk wani likita ko abokin aikinsu da ya nemi ya latsa ta, farko takan biye musu ne kawai don son zuciya da kuma jin dadin abin, sai daga baya ta fara karɓar kuɗi. Sai ya kasance ba ruwanta, hatta club takan bi Nusaiba su je ta dinga fakewa da tana da night duty, sau daya Malam ke kawo ta a motarsa da magriba asibitin ya yi tafiyarsa, yana barin wajen za ta hau abin hawa ta nufi gidansu Nusaiba idan a ranakun ita ma ba ta da aikin kwana. Manyan mutane sosai Hajara ta sansu, inda ba ta taɓa tunanin takawa ba ta taka, sai ta ji a duniya ba ta da burin da ya wuce ta auri wani shahararren mai kuɗin. Don a yanda take ɗanɗana rayuwar kwana ko wuni a cikin  AC ba ta jin za ta iya auren talaka. Sanadin wannan yawace yawacen nata ne ta ja Malam da Inna suka yi fada kawai don Innar ta ce Malam din ya sanya idanu a kan Hajarar don tana tunanin da matsala. Aikuwa ya hau ta da fada sosai kan cewa tana zargin ɗiyarsa. A karshe har yajin kwana a shimfida daya ya yi da ita. Ya bar cin abincinta, sai dakyar Inna Mairamu ta samu suka dawo daidai. Tun daga lokacin ta dauke idanu akan Hajara, ba dai ta cire ta cikin addu'o'inta ba da yi mata fatan shiriya. Ta sanadiyyar wani babban Alhajin da take mu'amala da shi kuma mai faɗa a ji a gwamnatance, ta samu gurbin aikin jinya a asibitin gwamnati na Malam Aminu Kano. Ta rufe Malam da cewa neman aurenta yake yi shi ne dalilin da yasa ya nemar mata. Malam sosai bakinsa ya ƙi rufuwa musamman da ya ga babban mutum irin Alhaji Habibu Tofa ya tako har gidansa ya zo sun gaisa ya kuma yi masa bayanin cewa shi ya nema mata aikin saboda yana sonta da aure. Har da ba da hakurin rashin soma gabatar da kai kafin yin wannan karambanin, Malam ya nuna babu komai ya yi godiya sosai. Koda suka fito daga wurin Malam sai da suka yi wata dariya da cafkewa ganin an shirga mahaifin mata. Har a ran Hajara za ta so ya kasance mamemin aurenta dagaske amma ya nunamata shi gaskiya ba zai iya ƙara aure yanzu ba tunda bai jima da yin ta uku ba. A motarsa ma da sunan suna hira sai dai ya ɗan yi wasa da ita sosai kafin su yi sallama. ***   Zakari wanda ya samu aiki a wani kamfani kuma daidai gwargwado ana biyan kirki, nan da nan ya gingimo aure, tarin lefensa sai ya kasance a wurin Inna Mairamu yake yi. Hajara na kyallara idanu ta gani ai sai ta sanar da Safiyya da ma wasu a danginsu. Nan da nan abu ya nemi zama rigima wai don me sai a wurin Inna Zakarin zai yi tarin lefe. Malam bai dauki maganar wani abu mai zafi ba, ganin ma abin kamar zai tashi hankalin gidansa ya tsawatar ya kuma hana kowace mace a dangi zuwa don yin maganar. Anan kam Inna Mairamu ta samu sa'ida, amma fa zagi takanas Safiyya ke zuwa ta yi mata har da su Allah ya isa. Ga kuma na Hajara. Mustafa da su Hashimu dai Zakari suka yi wa caa wai don me ba zai yi shawara da su ba kafin ya kai mata. Har da cewa ba zasu ba shi komai na gudunmuwa ba. Haka har biki ya zo aka yi shi cikin rufin asiri, Inna Mairamu wasu abubuwan ita ta yi mishi da kudin ɗaya cikin tumakanta da ta siyar wanda take kiwo a wajen Kawu Jibo na gadonta. Ya ji dadi sosai da abinda ta yi hakanan Malam har godiya ya yi mata. A Daura ya auro matarsa yar fulani da ita, har fulatanci tana ji hakan ya sa ta shiga ran Inna Mairamu sosai, sunanta Hameeda. Iyakarta sakandire. Yarinyar na matukar girmama Inna, kuma tana kaunar Sadiya da Husna. Su kuwa su Hajara sai ta yi bakin jini a gurinsu tunda ita kadai ce a matan yayyun ke shiga lamarin Innar. Sauran duk basu wani damu da lamarinta ba. *** Daga wannan lokacin kuma sai tashin hankalin da ya biyo baya na fasa auren Hajara. Mutum na farko sun haɗu ne sanadin mahaifiyarsa da ya kai asibiti ba lafiya, yanda Hajara ta tsaya wajen nuna kulawa sosai gareta ne ya sa ya ji nan duniya ta burge shi kuma zai iya aurenta, haka ma a ɓangaren mahaifiyartasa ta yi na'am da Hajarar matsayin matar ɗan nata. Saboda har suka bar asibitin Hajara kan je har gida ta gaishe ta. Ita kuwa Hajara ganin irin kudin da suke facaka da shi a asibitin da ma yanayin wayoyin da yake amsawa yana batun ƙasashen waje, inda ya je da kuma dawowar da ya yi daga London saboda jikin Mahaifiyarsa da ya motsa duk su suka ruɗa ta, ta maida kanta wata salihar gaske a gabansu. Ranar da Sunusi ya fara zuwa gidansu ya nemi iznin zance wurin Malam kuwa, ai kwanan farin ciki ta yi. Har tana cewa Malam ita fa ta gaji ta gani shi take son aure. A gaban Inna Mairamu ta cewa Malam kuma duk sadda ta yi aure da Husnarta za ta tafi. Malam dariya kawai ya yi, ya sani babu kunya ko kadan tsakaninsu da yaransa don yakan yi hira da su sosai. Ya sakar musu fuska hakan yasa wasu lokutan yake gane damuwarsu da ma wasu abubuwan. Sai dai duk irin ganiyarsa, yarda da ya yi da Hajara ya sanya bai taɓa hasaso wai tana bibiyar maza a waje ba da sunan soyayyar shan minti. Ba dai ta taɓa bari a kusanceta kusanta irin ta mata da miji, amma ban da hakan, komai ta aminta namiji ya yi da ita. Watansu hudu tare da Sunusi, bayan sallah ƙarama ya turo aka sanya ranar aurensu har da kuɗi dubu dari mai matukar daraja a wancan lokacin. Kawayenta suka cika gida da yan uwa aka yi ta murna da farin ciki, Inna Mairamu ta sha habaici a wajen dangi inda wasu ke fadin ai fa Hajara ta yi goshi, kaf a yaran Malam ma babu wanda aka kawo kudin aurensa kamar nata, kuma an yi an gama ba za'a ƙara ba. Abba ne ya dauki nauyin yi mata komai na kayan daki, Malam ya rasa kalmar da zai yi amfani da shi wajen godiya gareshi, ga kuma kayan abincin da za'a girka na gida yan uwansa maza sun ce basu yarda ya siya ko gishiri ba, su zasu yi. A cewarsu Hajiya Asma'u mutuniyar kirki ce ta mutane wacce ba ta da rowa sam, don haka burin da ta ci na bikin Hajara idan babu idanunta, to su za su bugi kirji su cikamata shi. Ga kuma uwa uba shi Malam din mai kokarin zumunci ne da kyautatawa yan uwa daidai gwargwado. Watan tafiyar Alhazai na shiga aka kawo lefe na gani na faɗa a lokacin, wanda sai ɗan wane da wance. Hajara kanta ya kara fasuwa, gyaran jiki na musamman ta je can makwafciyar Hafsatu ƴar Maiduguri take mata. Ga kayan haɗe-haɗen da ta samu na wata daga Sokoto. Abin har daurewa Hafsatu kai ya yita kasa shiru tace. "Wai Hajara ina kika san duk wadannan magungunan? Dama kin san ana yin su?" Hajara dariya kawai ta yi ta basar yayinda mai mata gyaran jiki ke tarewa da fadin "Ai ba za ta kasa sani ba Malama, kar fa ki manta zamanin kullum sauyawa yake ƙara yi.  Ba irin namu lokacin ba ne." Da wannan Hafsatu ta ji mamakinta ya ragu. *** Tashin hankalin da ya riski Inna Mairamu ana gobe daurin auren Hajara ne ya sa dole ta nemi iznin Malam a daren ta fita zuwa asibiti don duba Kawunta Jibo da aka ce an kai shi bai san ma wanda ke kansa ba. Haka ta tsallake ta bar yan uwan Malam din da na maman Hajara sai ko yan bikin zuwa asibitin tare da Sadiya da ta dinga magiyar ta tafi da ita. Ita ma ba ta musa ba ta ja ɗiyarta suka bar gidan gudun zagi ko cin mutunci daga yan bikin. Har hawaye ta yi ganin halin da Kawu Jibo ke ciki, wai hawan jini ne ya yi sanadiyar zubewarsa a dakinsa, Allah ya taimaka Dada da kusa. Da taimakon makwafta da ɗansa wanda bai fi sa'an Safiyyar Malam ba, Sharu, suka kai shi asibiti. Sharu ne ya kira a waya ya sanar da ita. Jikin da sauki don likitan ya ce zai tashi da yardar Allah. Ta jima anan sai daga baya Dada ta saka Sharu ya tare mata abin hawa ta tafi gida da zummar gobe za ta yi sammakon dawowa kafin a fara hidimar biki. Washegari kuwa da sassafe ta je asibitin da abin kari, Malam bai samu shiga na sai saƙon gaisuwa da ya bayar yace a yi ga Kawun zai shiga ya duba shi bayan daurin aure, ganin har Kawu na magana hankalinta ya kwanta. Shi ya ba ta umarnin komawa ga hidimar bikin idan yaso daga baya ta dawo tare da mijinta. Da wannan Inna Mairamu ta koma gidan hankalinta kwance, sai dai na mutanen biki a tashe. Ta yi saroro a tsakar gidan ganin Hajara da Safiyya sun haɗa kai suna runtuma ihun kuka, wasu a manyan ma sharce hawaye suke yi. A bakin Hafsatu take ji wai Sunusi ya fasa auren Hajara kuma ma wai ya bar mata komai na kayan da ya kawo. Salati Inna Mairamu ta saki don ba karamin razana abin ya sanya ta shiga ba. Jin lamarin ta yi tamkar ga ƴar cikinta ya faru. Hawaye ta shiga matsewa. Ta karasa da zummar rarrashin Hajara aikuwa ta yo kanta. "Munafuka algunguma! Ni dama na sani! Tun ganin da na yi maki ki na safa da marwar shige da fice a daren jiya da safiyar yau jikina ya ba ni wata baƙar muguntar ki ke shirya min. Me na yi maki Mairamu da za ki datse min igiyar farin cikina tun ban kai ga ɗanɗana ba? Allah ya isa tsakanina da ke! Ni dama na san tun da aka kawo kudina ki ke bakin ciki da hakan! Don ba Sadiyarki ce ta samu miji kamar nawa ba! Wayyo Allahna, mutuwa mai yankan kauna ta raba ni da uwata abar sona!" "Ke Hajara yi min shiru haka, bana son hauka." Cewar Haj Mariya a tsawance kafin ta ja ta su yi daki tare da wasu a yan uwa. Wasu kuwa suka yi wa Inna Mairamu caa wacce ta yi tsaye tana ɗigar da hawaye ta ma rasa kalma ɗaya da za ta yi amfani da ita wajen kare kanta. Kai ka ce ba ta sanar da su  halin da ɗan uwan mahaifinta ke ciki ba har ma suka bi ta da addu'ar nema masa lafiya. Kowa ya shiga zaginta daidai gwargwado sai kuwa su Mama Iyabo da wasu a yan uwa masu kare mata. Ranar tashin hankalin da Inna Mairamu ta shiga Allah kaɗai ya sani. Da zazzabi sosai ta kwana ban da kuka da ta ci ga Sadiya da Hafsatu masu taya ta da kuma ba ta hakuri. Zakari ma shiga da fita ya dinga yi yana ba ta hakuri. Haj Mariya duk da ba wani shiga harkar Innar take yi ba, amma ba ta wani tsane ta, sai da ta shiga ta ba ta hakuri dangane da abin da Hajarar ta yi gami da nunamata ba ta cikin nutsuwarta ne. Karshe ma gidan Abban ta wuce tare da ita bisa umarnin Abban da ya cewa Malam ya dace Hajara ta dan bar layin na ɗan lokaci. *** A ka yi wannan ta wuce, tsana mai tsanani na Inna Mairamu ya ninki a zuciyar Hajara. Ko watanni biyar ba a yi da faruwar lamarin ba ta ƙara samun wani mutumin. Shi yana da mata amma yace ita Hajarar Lagos zai kai ta inda yake aiki. Shi ma sosai yake sakarmata bakin aljihu, gaba daya ya rude nan duniya ita yake so. Tun tana ɗar ɗar har ta saki jiki ta kai shi wajen Malam, nan fa magana ta yi karfi har aka tsaida rana. Sai dai shi ma ranar da aka ce za'a kawo lefe, a ranar saƙon fasa aurenta ya riskesu ta hanyar sako na waya da ya yo mata. Wannan karon har kwanciya asibiti Hajara ta yi. Koda ta dawo hayyacinta bayan tsawon lokaci, sai kuma ta tattara lamarin auren ta watsar. Yayar mahaifiyarsu mai suna Saratu, har gidan ta zo ta yi wa Inna Mairamu kashedi mai kyau akan ta fita a harkar ɗiyar yar uwarta ta bar ta ta yi aure idan ba haka ba za ta maka ta a kotu. "Abin da na sani Allah kaɗai ke da ikon hanawa da zartarwa ba ni Mairamu ba. Allah shaida ba zan iya cutar da Hajara ba koda kuwa kuma ganin ba ni na haife ta ba. Amma idan ku na tunanin ni nake hana ta aure, ai ina da yara matan, su ma hakan zai faru a kansu tunda ban isa na zalunci ƴar wata ba, ni kuma Allah ya bar nawa." Iyakar abin da tace kenan daga haka ba ta kara tofa uffan ba sai Gwaggo Saratu da ke faman sababi da jifan yaran Innar da mugun baki da kalami har ta gaji ta fice a gidan ta bar Inna Mairamu da zubar hawaye da kiran sunayen Allah da ma duk wata addu'ar da za ta haifarmata da nutsuwa a zuciya. Babban jin dadinta bai wuce yanda Malam ya yarda ita da ba, har nasiha da jan kunne ya yiwa Hajara da yan uwanta kan su maida lamarin ga Allah, mutum bai isa ya yi musu komai ba amma Hajara ba ta jin za ta bar zarginta har abada. Hajara ta cigaba da cin karenta babu babbaka a waje tana ba da fuska ga manyan mutane tana musu wayo tana karɓe chanjinsu, an sha ɗana mata tarko don kawai a keta haddinta amma Allah na tseratar da ita sai dai hakan bai sa ta hankalta ta bari ba. Rabuwarsu da Nusaiba ta samu kawayen da suka fi Nusaibar gogewa a harkar a nan asibitin da take aiki. Har ɓata gari a likitocin bibiyarsu suke yi. Sai da ta shekara ba ta ko kara kallon wani namiji da sunan aure ba, wani mai suna Yusuf ya dinga nacin yana son ya turo gidansu. Ma'aikacin banki ne, babu laifi yana da rufin asiri daidai gwargwado amma bai kama ƙafar wadanda suka tafi a baya ba, ta ƙi ba shi dama saboda tana tsoro amma kuma tana son abin. Sai dai koda ta tuntuɓi Gwaggo Saratu ta ja ta suka je wajen wani Malami ya ba su magani akan Hajara ta dinga amfani da shi babu wanda ya isa ya hana aurenta a wannan karon. Hajara sam ba ta yarda da wadannan abubuwan ba saboda ita ta sani ƙarya ne, sam a tsarin rayuwarta babu bin bokaye da malaman tsibbu tunda ta sani ba a haka a gidansu. Ta sha mamakin ma da ta ga Gwaggo ta yi amanna da su har haka. Don dai kar Gwaggon ta ga kamar ba ta yabawa kokarinta ba, ta yi amfani da shi sannan Yusuf ya turo gidan neman aurenta. "Wannan karon ko uban kuturu ya yi kaɗan ya hana min aure. Kuma mutum ya gwada ya gani." Haka shi ne furucin da Hajara ta bi Inna Mairamu da shi ranar da aka tsaida lokacin bikinta da Yusuf. Inna ban da murmushi ba abin da ta yi. "Hakurinki yana yawa a gidan Sa'adu, Mairamu sam ba na son wannan shirun naki, ni na san suna cutar da ke yawa." Abin da Dada ta taɓa furta Inna kenan a wata ziyara da ta kawo mata sa'ilin da Sadiya ta yi fama da rashin lafiya. Ganin yanda Hajara ke habaice-habaice ba ta ko girmama Inna a gaban mutane ya sa Dada yin maganar. "Babu komai Dada, komai mai wucewa ne. Rayuwar duniyar ma duka nawa take? Har yanzu yara ne, zafin rabuwa da mahaifiyarsu bai sake su ba. Ke ma ki yi musu uzuri. Watarana sai labari." Dada ta kalleta sosai a wancan lokacin ta jinjina kai. "Uhum! Kazar kwanci kirjinki ya saba da danna! Ki cigaba da hakuri, mai hakuri kan dafa dutse har ya sha romonsa Mairamu. Watarana za ki yi dariya sosai." Murmushi Inna Mairamu ta yi tana hasko wannan ranar a idanunta, tana da yaƙini lallai idan da rai da lafiya zai zo watarana. Ai babu abin da ya fi karfin iko na Allahu. *** Zaman taron zuri'a aka gudanar wannan karon a can gidan gado na Malam duka kuma akan fasa auren Hajara da aka ƙara yi karo na uku don wannan ma taron bai watse ba sai a ranar daurin aure duka an taru amma Ango Yusuf ya miƙe ya ce ya fasa. Hakan har faɗa da cece kuce ya jawo inda Mustafa da Baba Habu suka kusan yi doki in doka da dangin Yusuf din. Rabuwa dai aka yi babu dadi kuma dangin Ango suka ce lallai duk abin da suka kashe sai an biya su abinsu. Wannan lamari ya girmama inda Gwaggo Saratu ta daukowa Inna Mairamu ƴan sanda. Dakyar aka kashe zancen bayan Abba da wasu a makwafta sun je sun yo belinta. Dole aka yi zaman sulhu a gidan su Malam din. Nan fa wasu suka dage akan lallai sai Inna Mairamu ta yi rantsuwa cewa ba ita ke yin kullin da ake fasa auren Hajara ba. Wannan karon ƙirjin Inna Mairamu har zafi yake yi ga wani jiri dake kwasarta a zaune. Ban da innalillahi babu abin da take bita a zuciyarta. Ta lashi busassun lebbanta tana jin wani raɗaɗi a maƙogwaronta. A hankali ta dubi Malam wanda ba shi da ta cewa kansa yana sunkuye ya zabga tagumi. Sai ta kauda kanta ta kasa magana, ta maida duba ga Alkur'ani mai tsarki da aka ajiye a gabanta kan cewa ta rantse ba ita ce ke korarwa Hajara maza ba. Hawayenta suka zubo har suna ɗiga a saman alkur'anin ta goge su. "Ba zan iya rantsuwa da Alkur'ani mai girma ba. Amma ina muku rantsuwa da girman Allahu mahaliccin dare da rana, duhu da haske, fari da baƙi. Maƙagin kowa da komai, ba zan iya cutar da yaran Malam ko ɗaya ba koda kuwa yaran riƙo ya kawo. Me Hajara ta yi min da zan hana mata aure? Mece ce riba ta?" "Ƙarya kike yi algunguma marar tsoron Allah." Faɗin Gwaggo Atine ƙanwar Gwaggo Saratu, nan fa Kawu Haruna wanda kusan a maza tsoffi da suka rage a zuri'ar shi ne babba ya tsawatar mata. Nan ya ba Inna Mairamu hakuri ya kuma nusar da zuriar akan su tsoraci Allah saboda shi ne mai yi da hani. Kuma a cewarsa ya dace ma a tuntuɓi mazan a san ko akwai wani abu da suke ji da yake sanya su fasa auren. Shi ne ya yi dogon wa'azi daga bisani ya kara ba Inna Mairamu haƙuri ya kuma rantse akan duk wanda ya ƙara tayar da zancen zai gamu da fushinsa, dole aka bar maganar anan. Sai dai kuma gutsuri tsoma irin ta mata da bai taɓa yankewa. Don ko haihuwa aka yi ko wani abin idan an haɗu sai an yada wa Inna Mairamu habaici sai dai ta toshe kunnenta. *** Rayuwar na cigaba da gudu, har aka wayi gari Sadiya ta zama budurwa son kowa kin wanda ya rasa. Dama ga ta nan yarinya ce mai farin jini tun tana ƙarama, a yanzu da take aji na biyu na babbar sakandire sai take ƙara shiga ran mutane musamman yanayin kamewarta da nutsuwa. Sam ba ta da kwaramniya. Husna a lokacin ita kuwa tana aji biyu na ƙaramar sakandire (Jss 2). Yanayin girman jikinta sai ka ɗauka ta girmi Sadiya. Ita Sadiya ƙirarta na fulani ne. Tana da tsayi sai kuma ƙira mai kyau don idan ka kalli cikinta sai ka rantse ba ta cin abinci sau uku a rana. Akwai dai halittar ƙirji da kuma mazauna. Wannan ya sa ƙirarta ya yi kama da wanda ake cewa cocacola shape. Hajara ta tsani ta ga Sadiya a gabanta saboda wani takaici da take ji. Takan yawaita jan tsaki ta ce. "Aikin banza, duk wannan kyawun dai na ɗan maciji ne. Yanda ban auru ba haka har abada yarinya za ta ƙare a yawon bariki." Inna idan ta ji takan nemawa ɗiyarta a tsari a zuciya. Sadiya kuwa kallonta ma ba ta yi tunda ta kula abin na Antin nasu ba na ƙare ba ne. Lokacin Hajara na da shekaru ashirin da tara cif a duniya. A sannan manema auren ma sun ɗan ja baya sai dai kamar daga sama wani ya fito a karo na huɗu dagaske aurenta zai yi. Murna da daɗi suka kusan kasheta ganin babban Alhaji ne kuma mazaunin Abuja sai dai iyayensa a garin Kano suke, a hanya ya ganta ya biyo ta har gida. Nan fa aka shiga shirye-shiryen  biki. Shi ɗin ma dai bai je ko'ina ba don ana saura kwanaki uku a fara bikin ya ce ya fasa gaba daya. Wannan karon hauka ne kawai Hajara ba ta yi ba. Shi ne a ƙarshe Malama Hafsatu ta ja su zuwa gidanta don Hajarar ta samu nutsuwa ta kuma fita a bakin mutane. Sai dai gaba daya lamarin wannan karon ma kan Inna Mairamu ya dawo, ga kuam baƙaken addu'o'in da ake fa yi wa yaran Inna Mairamun musamman Sadiya. Da yawa sun ce sai Inna Mairamu ta ga sakayya a kanta. Hakan ba karamin damuwa ya haifarwa Inna ba dannewa kawai take yi. Sun kwana biyu a gidan Hafsatu sai yanzun da Malam ya nemi su dawo zaman ya isa hakanan. Wannan Kenan! *** *Kazar Kwanci...* Misalin ƙarfe biyar da mintuna na yammacin ranar Malam ya shigo gidan.   Sadiya da ke wanke kwanukan da Inna ta kammala aiki da su ta amsa sallamarsa fuskarta dauke da murmushi. Shi ma kallonta ya yi da murmushin yana amsa gaisuwar da ta yi masa bayan sannu da zuwa. Daga nan sai ga Husna ta fito da ɗan gudunta ta ɗan riƙo hannunsa tana oyoyo. Ya dafa kanta yana dariya. "Autar Malam an dawo?" Sunan da yake kiranta da shi kenan bayan Hajara a baya. Kasancewar Husnar ƴar gaban goshinta ce, sam ba ta jin zafin hakan. Ta ƙara narkar da fuska. "Eh. Ba kai ne ka ce mu dawo ba." Ya yi murmushi a daidai sadda ya ke miƙawa Sadiya ƴar jakar hannunsa mai ɗauke da na'urar laptop sakamakon hakan da ta buƙata. Kai tsaye falon nasa ta shige ta bar su da Husna dake faman zuba ruwan shagwaɓa. Inna ta mishi sannu da zuwa kafin ya tambayi Hajara. "Ta sha magani ta kwanta, kanta ke ciwo." Faɗin Husna cike da jimami da tausayawa Antin nata. "Ya Salam, Allah yasa kaffara. Amma dai ta daure ta tashi yamma ta yi. Kar hakan ya haifar mata da wani ciwon kuma na daban." Husna ta turo baki, don me Malam zai ce a tashi Antin alhalin bai san irin baƙaƙen maganganun da Anti Hafsatu ta yarfa mata ba. Inna da Malam suka yi gaba zuwa falonsa wanda tuni Sadiya ta fito ta ja tunga a gefen shiga falon don ta ba su hanyar wucewa ta ƙarasa aikinta. Tana ji Malam na tambayar Anti Hafsatu, Innar na ba sa amsa da cewa dalilin ta bar yara a gida ne ya sanya ta saurin tafiya.  Ɗan murmushi ta yi, Allah Sarki Inna, wato ita dai koyaushe kokarinta ɓoyewa Malam rikicin cikin gida wanda kuma babu ɗaya da ba shi da masaniya a ciki. "Assalamu alaikum." Sallamar da aka ƙara yi ce ta sanya Sadiya wacce ita kaɗai ta yi saura a tsakar gidan, don Husna ta koma ɗaki amsawa. Faɗaɗa fara'arta ta yi ganin  ƙawa kuma aminiyarta kaf layin nasu, Zahra. Ɗiya ce ga Habiba makwafciyarsu wacce ba ta taɓa ko kallon banza ga Inna ba a tun baya ma da makwaftan ba sa shiga harkarsu. Sai yanzu ne ma sauran makwaftan ke kula Inna wasu kuwa har gobe ba sa wani gayyatarta koda sabga kuwa. Dama Habiba da Mama Iyabo su ne da'iman ake zaune tare a na zumunci.   Zahra ɗan durƙuso ta yi a gefe ta harareta. "Ke dai ba ki da kirki, shi ne ko ki ce min tafiyar kwana ta kama ku. Sai biyo maki na dinga yi don mu tafi makaranta Inna na cewa ba ki dawo ba. Yau ɗin ma Musan gidanmu ne ya ganku kun fito daga motar Anti Hafsatu shi ne fa ya ruga ya sanar da ni." Kafin Sadiya ta ba ta amsa sai ga Inna ta fito. Zahra ta gaida ta, ta amsa ita ma fuska a sake. "Yau dai ga ki ga mutuniyarki taki hankali ya kwanta ko?" Sadiya da Zahra suka yi ƴar dariya. "Ya Umman taki?" Inna ta wuce don kai wa Malam ƙaramin cokali da zai saka zuma cikin shayi.  Ita kuwa Zahra ta shiga taya ta. Koda suka kammala suka shara wajen sai suka faɗa falon Inna. "Wai ni an ƙara karatu kuwa? Malam Nura fa ba kirki, kar ya yi min bulalan fashi." Faɗin Sadiya tana ɗan fito da idanu. "Ni daina zaro min idanun nan naki kar ki tsorata ni cikin dare. Ke wai an fadamaki za su yi zaman jiranki dama? Tab, wallahi dai an ɗora karatu an shiga Suratul Najm." Ta ɗan sauke ajiyar zuciya cike da jin babu dadi. "Ai shikenan. In sha Allahu zan kai haddar na baya gobe." "Ke, kuɗin aure fa za'a kawo, za'a sanya rana shekara da zarar mun yi candy." Wata ƴar zabura Sadiya ta yi ta dafe cinyarta. "Ki ce wasa ki ke? Shu'aibu turo wa zai yi? Hum, wannan mutum, ai shikenan. Ke kika ja wa kanki, kin san yanayinsa da kishin bala'i amma ki ka tsaya da wani har ya ganki. Gwara ma ya yi maki hakan. Amma kuma batun karatu, wai dagaske ba za ki ɗora daga sakandire ba? Rayuwar fa sai da ilimi Zahra." "Wajenku ba, ƴan gidan boko. Ni kuwa wa zai bar ni na ɗora wata jami'a a gidanmu? Hum, to zuwa sakandiren ma da ya ya? Kullum ina cewa ki godewa Allah don kin samu damarmaki da yawa a rayuwa waɗanda wasu ke nema, iyayenki su na da halin tsayamaki ki yi karatu, ni kuwa nawa yayyun ma ba su kai ga ƙarasa sakandiren ba aka yi musu aure. Ke a gidanmu fa na fita zarra ma da aka bar ni na kai har yanzu ina karatun. Nan ma na sani don dai Babanmu samunsa ya ragu ba kamar a baya ba, dalilin kenan da ya hana ya tashi zancen aurena da wuri. Ya haƙura har na kammala wannan din. Kuma Shu'aibu bai min alƙawarin boko ba. Ke ma kin san ba zai bari ba tunda bai ga wata a cikin Sajida da Zinnira ba suna yi. Balle kuma yayanmu Nura da yake namiji ma iyakarsa sakandire sai ko kasuwanci da ya faɗa." Ajiyar zuciya Sadiya ta saki kawai tana kallonta, kallo irin na tausayawa.  Yanzu idan ace ita ce za'a hana karatu ya za ta yi? Ita da kullum ba ta da mafarki face na zama likitar mata. Babban burinta ta taimaki mata masu ciki da ma masu larurori da dama wanda ta sha jin kokensu ana kawo wa gidan rediyo neman taimako. Sai ko wanda ta ji ko gani a makwafta ko asibiti idan sun je dubiya da sauransu. Zahra gaskiya ta fada, mahaifinta ba wani mai ƙarfi ba ne. A baya dai suna da ɗan rufin asiri don kasuwarsa ta gara sosai amma yanzu kam komai sai a hankali. Sanin ba za ta samu ma karatun ba ne ya sanya ba ta ma ɗorawa ranta kwaɗayinsa ba. "Allah ya sa hakan shi ne mafi alheri a rayuwarki. Amma dai za ki cigaba da sana'ar ƙunshinki ko?" Sadiya ta furta har lokacin ba ta ɗauke idanu a kan Zahrar ba. Ta yi ƴar dariya. "Eh bai hana ba, amma fa kinsan komai akwai ƙa'idarsa, ya ce babu ranakun juma'a, asabar da lahadi saboda duka yakan jima a gida kafin ya leƙa kasuwa. Kuma ni ma wai ina buƙatar hutu na kwakwalwa da jiki." Suka yi dariya. Sadiya ta kara yin addu'a da fatan Allah yasa su ga lokacin. Nan kuma Zahra ta sako tambayar ko yaya Anti Hajara yanzun? Sadiya ta ce da sauki dai. Ta ɗora da faɗin. "Ni kaf batun nan ma ba sonsa nake yi ba, eh ina jin ciwon abin da ke faruwa a rayuwarta, sai dai meyasa sai Innata? Meyasa ita mafi yawa ke zargi da wannan ɗanyen aiki? Ashe ba su yarda cewa Allah ya isa ya gudanar da mulkinsa yanda ya so ba? Allah da kansa ya ce zai jarraba waɗanda suka yi imani, ta ya ya idanun jama'a ke rufewa ba sa ganin gaskiya? Son zuciya ko kuwa dai tsantsar rashin tawakkali ne?" "Son zuciyar ce Sadiya, sai kuma tsanar Inna da ya riga ya dasu a ransu har ta yi girma kuma ta yi rassai. Ki ma bar tunanin nan, babu abin da za ka yi ka burge wasu mutanen, maida hankali kawai ga rayuwarku, shiyasa Inna ke burge ni. Tana iyakar kokarinta wajen kulawa da su da zuciya daya, abin da ta ga ya fi ƙarfinta kuma ba ta matsawa kanta, sai ta maida komai ga Allah." Sadiya ta share hawayen da ba ta san sun fara zubo mata ba. Girgiza kai ta ɗan yi. "Inna tana da karfin zuciya ba irin tawa ba. Ni na san yanda nake ji a kirjina duk lokacin da Anti Hajara ko Anti Safiyya suka yaɓa wa Inna magana a cikin gidan nan. Ba zan iya maida musu martani ba na sani Zahra, amma kuma hakan ba ya hana zuciyata jin wani irin zafi." "Ki yi hakuri Sadiya, ki ƙara hakuri da addu'a. Komai zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba." Ta yi wata ƴar dariya marar sauti ko hayaniya. "Ki ka ce kamar ba'a yi ba? An yi da yawa, abubuwa sun faru ba kaɗan ba wanda koda ace sun manta, ba zan iya mancewa ba." Zahra ta share hawayenta, tana da saurin kuka da raunin zuciya musamman akan abin da ya shafi rayuwar Inna da Sadiya. Ba ta son ta ƙara mata damuwa sai kawai ta wayance da miƙewa tsaye. "Ni zo ki raka ni, mu bar wannan maganar. Ba zamu iya gyaran komai da baki ba, duk abin da ya fi ƙarfinmu bai fi ƙarfin Allahu ba. Don haka mu cigaba da addu'a. Haba ta Isma'il, ɗan murmusa mu gani. Yace yana son fara ko mayya ce, da ya tashi sai ya haɗu da ke." Ta ƙarashe da dariya. Sadiya ta ja tsaki tana kai mata duka ta goce. "Allah ya yi min tsari, ai ko maza sun ƙare ba zan auri wannan mayen matan ba. Gwara ma ya tattara komatsansa ya koma ƙauyensu ya cigaba da noma." Ta ƙarashe tana kokarin warware hijabinta da ke ninke a hannun kujera, sadda ta idar da sallar la'asar ne ta bar shi a nan. Zahra wacce har a sannan dariya take yi ta amsa. "Ke fa ƴar rainin wayo ce, Jigawar ce ƙauye?" Taɓe baki Sadiya ta ɗan yi tana mai kokarin fita daga falon ta ce. "Ni dai muje ki gaida Malam sai ki tafi. Kar ya ga na fita da yamman nan." Suka ƙarasa kuwa da sallama falon Malam din, yana zaune har ya watsa ruwa ya sanya ƴar tshirt mai gajeran hannu da dogon wando marar nauyi, Zahra a ranta tace gidan ƴan boko kenan. Ita a gidansu babansu ai ba ta jin ta taɓa ganinsa da kananan kaya da girmanta dai. Shi kuwa Malam babu ruwansa, sam ba ya son abin da zai takura jikinsa. Wasu lokutan ma idan bokon ya motsa, shigar riga da wando irin na ma'aikata banki yake yi ya wuce kasuwa abin sa musamman a yanayin sanyi. Malam ya amsa gaisuwarta fuska a sake yana tambayar baban nata. Ta amsa da lafiyarsa kalau. Nan ta yi sallama da Inna suka fice tare da Sadiya. A hanya ma hirar makarantarsu suka dinga yi da sauran ƴan ajinsu har sai da Sadiya ta saki ranta sosai. Ba su yi wani nisa ba suka rabu don ta rantse ba yau za ta shiga gidan su Zahrar ba. Sun saba dama irin wannan rakiyar tunda layinsu daya amma akwai tazarar sosai a tsakanin gidajensu. Su na farkon shigowa layi, ita kuwa Zahra suna can ƙasa kaɗan. Idan Sadiya ta je gidansu ana hira a hanya har sai ta rako ta ƙofar gida zasu ankara, hakanan ita ma idan ta tashi yi wa Zahrar rakiya. Wannan karon ba ta bari sun yi hakan ba ta ja tunga jin an fara kiraye-kirayen sallar Magriba, haka suka rabu da zummar sai goben idan an haɗu a islamiyya don ba bokonsu ɗaya ba kuma ana cikin hutu ma sauyin aji za'a yi idan sun koma. Ita Zahra ta gwamnati ma take yi yayinda Sadiya ta kuɗi ce. ***   Da sallama Haj Mariya ta shiga falon Abba wanda ke amsa waya, ta ƙarasa ta nemi wuri ta zauna ganin yanda yake ta fara'a ta ji kamar ta canki da wanda yake wayar. Ba ta tabbatar da zatonta ba sai da ta ji ya ce. "Toh ni dai wannan maganar ba ni ya dace na yiwa Mamin taka ba, kai ya kyautu ka sanar da ita. Ga ta nan." Nan da nan fuskarta ta cika da annuri, ta karɓi wayar tana mai duba sunan. "Huzaif Abubakar." Haka dama Abban ke adana lambobin yaran nasa a waya. Cike da zumuɗi ta amsa wayar da sallama. Bayan gaisuwa ta tsinci muryarsa mai taushi yana fadin. "Mamina, na yi kewarki sosai." Murmushi ta yi mai sautin da ta san zai shiga kunnuwansa. "Kai fa daɗina da kai kenan, idan ka yi abu sai ka ce Affan ko Zee Mama. Ina ce jiya ma mun gaisa da kai." Ta na jin sautin nasa murmushin kafin ya ce. "Na fi shekaru uku rabona da gida kinga kuwa ai ba ni da maraba da su, sun ma fi ni gata tunda koyaushe kuma tare da su. Ni ma toh albishir zan maki cewa ina dab da zuwa na ganku na koma. Amma fa ba zan ce ga lokaci ba, sai dai kawai ku gan ni. Watakila nan da kwanaki, ko sati, ko watanni." Ta ɗan ɓata rai. "A'a Huzaifa, faɗamin rana ɗaya don a shirya maka tarbar da ta dace." "No Mamina, ke dai ku zama cikin shiri. Watakila ke ma jikinki ya ba ki isowata ƙasar irin yanda ya faru a film din Kabhi Kushi Kabhi Gam." Ta yi dariya. "Sannu ba'indiye, zama cikinsu ya sa ka fara daukar ɗabi'unsu ko? Toh ni ban koyar da kai wannan hali ba. Allah ya kaimu, ya dawo da kai lafiya." Ya na dariya ya amsa da amin. Nan ta miƙawa Abban nasa suka yi sallama kafin kuma ta dube shi. "Wai dagaske yake yi? Kuma bai tsayar da ranar zuwa ba?" Abban ya yi dariyar zancenta. Ya na taunar dabinon da ya siyo mai taushi irin na Saudiya ya ce. "Huzaif ne fa, ko kusa bai ba ni rana ba. Ya dai ce a yi maki albishir ya kusa zuwa gareki, shigowarki ta sanya na ba ki wayar. Kin san shi ya maida mu kamar kakanni a wasu lokutan." Ta ɗan ɗaure fuska don ita dagaske ta matsu yaron nata ya dawo kusa ta gan shi duk kuwa da cewa sukan yi video call wasu lokutan. "Shikenan ai, Allah ya kawo shi lafiya." Abba ya amsa da amin ba tare da ya ce komai bisa sauyin fuskarta ba. Idan da sabo dama ta saba mitar rashin dawowar Huzaif din, balle kuma yau din da ya yi mata ɗanɗani haukaci, gaba ɗaya za ta dinga zuba idanu ne ta ga ta inda zai ɓullo kuma yaushe. Dakyar ya samu ta saki fuska ta mance da batun Huzaif a ɗan taƙin. ***   "Wai Hajara dagaske fitar za ki yi? Ba za ki yiwa kanki faɗa da biyewa su Waleeda ba a wannan asibitin?" Nudrat ke zancen tana dubanta cike da mamakin ganin yanda ta yi shiri tsaf cikin wani arnen leshinta ruwan madara wanda ta samu tun a lefen da Sunusi ya yi mata. Gaba daya kirjinta a buɗe sai ko ƙugunta wanda tsabar matsa da siket ɗin ya yi mata kamar zai yage. Mamakin Nudrat bai wuce yanda Hajara ta ƙi karatun ta nutsu a rayuwarta ba, ta ya ya za'a ce neman aurenki na tarwatsewa amma har ki kasa barin munanan ayyukan da ki ke aikatawa? Kuma babban abin da ya tsorata ta bai wuce ganin yau har allurar hana ɗaukar ciki ta yi ba, kenan hakan na nufin za ta soma bada kai bori ya hau? "Please Sister Nudrat ki fita a rayuwata! Wai mene ne dalilinki na yi min kutse haka? Duk cikinmu ni kaɗai ki ka takurawa! Sauran da suke fitar me ya hana ki sanyamusu idanu haka?" Murmushin takaici Nudrat ta yi sa'ilin da Hajara ta dauki zundumeman hijabinta har yana sharar ƙasa ta zura. "Allah ya baki haƙuri, ina yawan yi maki maganar ne saboda na damu da ke ne. Ina tausayin yanda ake fasa aurenki. Kuma ina maki kallo kamar wata ƙanwata ku..." "Ya ishe ki, kar ki fama min tabon da har gobe ina jin raɗaɗinsa. Ki bar yi min kallon ƙanwartaki tunda dai babu abin da ya haɗa mu sai aiki. Ba na son sa ido da shiga sharo ba shanu. Mtsw." Wayarta dake ƙara ta cire a chaji don tsabar ɓacin ran da Nudrat ta jefa ta ciki har tana kokarin mantawa da ita. Ganin sunan Dakta Sani na yawo saman wayar ya sanya ta ƙin ɗagawa tana mai jan guntun tsaki. Ita fa ba ta son takura, mutum ba wani abin kyautar arziki ya ke yi wa mace ba amma sai jarabar tsiya. Gaba daya ta saka wayar da chajar a cikin jaka ta zuge zif kafin ta fice ta yiwa sauran ma'aikatan sallama da zummar ta tafi gida alhalin wasu a ciki sun san dawan garin. Wasu kuwa har gobe sun kasa yarda da abin da ake faɗi a kanta, suna yi wa hakan kallon ƙarya da kuma ƙage. Sai da ta fice daga asibitin gaba daya kafin ta tari abin hawa zuwa Zoo road inda anan me su Waleeda ke jiranta domin ziyartar gidan wani babba kuma hamshaƙin ɗan siyasa dake gidan hutunsa tare da wasu abokan ashararancinsa suna jiransu.   Saurin da take yi don ta je bai wuce jin cewa wannan karon akwai wani babban aiki da zasu ba su ba wanda hakan zai ba su damar mallakar kuɗaɗe masu nauyin gaske da ba su taɓa zato ba. Ana sauke ta daidai gaban wani katafaren Mall  dake wajen ta dubi Waleeda, Blessing da Azeema abokan aikinta da halinsu ya yi mugun zuwa ɗaya don wata ƙazantar ma da suke shukawa ita ba ta ko rabinsa ta ce. "Sorry, na ɓata maku lokaci." Blessing wacce ta ji hausa kamar jakar Kano ta ce. "Ai mun dauka wancan mayen Daktan ne ya tsaida ki." Ta yamutse fuska, ba wanda bai san nacin da Dakta Sani yake yi ga nurses mata ba a asibitin babu ma kamar sabbin zuwa. Wacce halinsu ya zo daya su daidaita, wadanda kuwa ba halinsu kenan ba su nemi tona musu asiri sai ya ja jikinsa. "Rabu da dan duniya, na ga yana ta kirana har a hanya da nake tafe, banza na yi na rabu da shi. Ana harka da manyan ƙwari wa yake ta shi? Ai yau da shirina na fito ko me zai faru ya faru." Suka yi dariya gami da shewa. Daidai lokacin da Waleeda ta shiga amsa waya tana yiwa direba kwatancen inda suke. Ba jimawa sai ga wata lafiyayyar mota baƙa wuluk mai bakaken gilasai ta faka a gabansu, suka buɗe suka shiga. Anan ne Hajara ta cire hijabinta ta shiga kwalliya a fuskarta. Ko mayafi ba ta yafa ba. Koda ta kammala shirinta, shiru ta yi tana duban waje, tana ji ƙirjinta na faduwa don yau ta rantse koda ace budurcinta zai tafi, to fa ta shiryawa hakan, a ganinta tunda aure ya gagare ta, ai komai ma yanzun za ta iya aikata shi. Tsanar Inna na ƙara ninkuwa a zuciyarta, ta sani ita ce silar jefa ta wannan mummunan tafarkin, da ace ta bar ta ta yi aure da hakan duk bai faru ba. Watakila da yaranta biyu. Mace da namijin da zasu ci sunan iyayenta mafi soyuwa a ranta. Ta tuno da Sadiya, ƙwafa ta yi. Ta rantse sai ta tarwatsa rayuwar Sadiya ko ta wace hanya ce yanda Innarta ta tarwatsa nata. Sai da Azeema ta taɓa ta tana magana kafin ta yi firgigit ta dawo hayyacinta. Ita da Blessing da Waleeda kadai ne masu aikin jinya a asibiti, Azeema kawar Waleeda ce mai zaman kanta. Asalinta ma ƴar Kaduna ce ta zo ta kama haya a Kano saboda iyayenta sun yafe ta adalilin barikin da take yi na gaske iyakar karfinta da jiki. Wannan ta sanya suka hade kawunansu suna cin karensu babu babbaka. Nusaiba kuwa wacce ta samu aiki a babban asibitin gwamnatin da ke can wajen garin Kano ya yi sanadin ja baya da alaƙarsu sai ko ta waya. Kusan koyaushe sai Nusaiba ta kira ko ta taɓo ta a chat su yi hirar rayuwa. Ita ma har lokacin ba ta yi aure ba, abin da ta ga dama take yi. Dama kullum huɗubarsu ga Hajara bai wuce ta saki jiki ta bada kai bori ya hau ba. Ita da ta san dukkan wata hanya ta tsarin iyali ai ba za ta taɓa daukar ciki ba. Kuma koda aure ne ya tashi sun ci alwashin yi mata ɗinkin da babu wani ɗa namiji da zai gane ta taɓa bariki. Ba ta taba ji a ranta za ta dauki huɗubarsu ba sai a yanzun da ta ke jin haushin auren ma tunda ba a yarda ta yi sa ba. Har suka isa jefi-jefi take tsoma musu bakinta a hirarsu. ***   "Ba wani aiki ne mai wahala ba a wajenku ma'aikatan abin, muna buƙatar mabiyar jariri, wato mahaifar da ke tahowa tare da jarirai har guda biyar. Idan har ku ka yi mana wannan ƙoƙarin muka samu, muka kuma yi nasara kwalliya ta biya kuɗin sabulu har muka hau wannan kujerar mulkin, toh muna rantse muku sai kun zaɓi nawa ku ke da buƙata a wajenmu." Gaba ɗaya kusan a gigice suke kallon kallo tsakaninsu, babu kamar Hajara wacce ta ji kamar ta saki fitsari a wando. Aikin tsafi da asiri? Kuma wai ita ake buƙatar saka hannunta ciki? Ta dubi Alhazan su uku, Alhaji Nasiru,  Garzali da Nuhu. Miƙewa ta yi tana girgiza kanta da ja baya har tana tuntuɓe da ɗan kamfen Waleedah da ke yashe a tsakar falon. "A'a, a'a, babu ni a cikin wannan tafiyar. Ba zan yi ba. Zan sadaukar muku da jikina ku cigaba da yanda ku ka so, ba kuma zan tona asirinku ba. Sai dai na rantse ba za'a yi wannan harkar tsafin da ni Hajara ba!" Daga haka ta shiga tattara kayayyakinta ta shirya tsaf, kallonta kawai suke yi babu kamar Alh Nuhu wamda ya ji hankalinsa ya yi mugun tashi, shi ne ya fara saninta a ɗiya mace, kuma shi yanda yake ji ma a ƙoƙon ransa aurenta zai yi ba zai bari ta kuɓuce masa ba don ta yi masa ɗari bisa ɗari. Miƙewa ya yi ya riko hannunta dake faman rawa, kai duka jikinta ma rawar yake yi, ta tsaya tana dubansa. "Kar ki yi mana haka Hajara. Mun ji, mun ji ba za ki tsoma hannunki a cikin harkar nan ba. Amma ina za ki je yanzu a daren nan? Don Allah ki yi hakuri ki zauna mu kwana a nan, gobe sai ki tafi." Hankali a tashe ta dinga girgiza kai, gaba daya ta ruɗe ta fisge hannunta, daƙyar ta yarda da batun Alh Nuhun wanda ya tsawatarwa su Alh Nasiru masu yi mata bambamin cewa ba ta isa ta fita ba tare da ta aminta da batunsu ba ko kuma su dauki mataki a kanta. Ɗaki ya ja ta ya rufe daga shi sai ita, nan ya dinga yi mata alƙawarin ba zai bari a cutar da ita ta ko'ina ba. Ita kuwa ban da uban kuma babu abin da take yi. Anan ne fa ya rantse mata shi da aure ma yake sonta. Ta dakatar da shi ta ce sam ba ta son batu na aure. Ya dai ji ta, ya kuma yi shiru amma ba don ya kyale batun auren ba. Haka ya lallaɓa har ya maimaita abin da ya yi ɗin a farkon zuwansu masaukin nasu, a karshe ya cikamata asusun banki da zunzurutun kudade har miliyan biyu, wannan ba karamin gigita Hajara suka yi ba. "Wallahi aurenki nake son yi Hajjo. Ki yi tunani ki ban damar da zan gabatar da kaina. Na rantse maki za ki ji dadi fiye da tunaninki a zamantakewarmu. Sai kin zama cikin mata abin kwatance. Na ji labarin yanda ake fasa aurenki a bakin Waleeda, kuma hakan bai karyan zuciya ba. Ni zan aureki mu sha sha'aninmu son rai. Wancan maganar kuma da aka yi, ki bar ta a inda ki ka ji ta. Ni zan yi maganinta. Ba za'a kara sanyaki ciki ba." A sanyaye ta gyaɗa kai alamar ta ji ta amince amma kuma ba wai don ta yi na'am da batu na auren ba.  Sai dai tunda uwarta ta haife ta ba ta taɓa ganin zunzurutun kudade haka a bankinta ba. Gaba daya ya gama kashe mata jiki, wannan rayuwa ta daula da take kwadayi ta soma hasko ta cikinsa a gidan Alh Nuhu. Sai dai tana tsoron kar shi ma sai magana ta kankama a fasa. Karshe ta ce ya bata lokaci za ta yi tunani. Yace ya bada. *** A can kuwa bayan sun keɓe su uku, Alh Nasiru rai a ɓace ya ce. "Ka san kuwa barin yarinyar nan ba zai yiwu ba ko? Wai Nuhu mai kake so ka ce? Wato a kyale ta bayan ta san wannan sirrin namu? Yan uwanta ba su yi mana taurin kai ba saboda sun san me ke musu ciwo sai ita?" Alh Nuhu ya yi dariya. "Kar fa ku samu damuwa, ni zan yi wa abin tufka. Aurenta zan yi. Hakan ne za mu samu damar toshe bakinta. Wai mu da muke da Boka Gagare? Har za ku yi tunanin tonuwar asirinmu? Idan har aka rufe mata baki ta ina za ta fesar? Kuma magana ta gaskiya ni dai ta yimin, aurenta kuma zan yi." Suka kyakyace da dariya gami da cafkewa. Sai a lokacin hankulansu ya kwanta. "Ya za ka yi da Haj Nuriyya?" Tambayar da Alh Garzali ya jefamasa kenan. Alh Nuhu ya shafi sanƙon dake tsakiyar kansa. "Ai ba kanta farau ba, wannan baƙin kishin dole ta yakice shi tunda a gidan ubanta ma huɗu na gani kafin na auro ta. Kuma ni ba ni da ra'ayin haɗa mata biyu a gida ɗaya. Ita dai ta cigaba da zamanta a Lagos, wannan Amaryar ta Abuja ce." Suka kara darawa. Ba wai nufinsa a Abuja zasu zauna ba, sai dai wata sara da maza ke yi na kiran gidan Uwargida da Lagos, na Amarya kuwa Abuja. Da wannan suka karƙare magana bayan Alh Nuhu sun ba shi tabbacin amincewar su Blessing saboda gaba ɗaya sun ruɗar da su da kyautar dubu ɗari biyar da aka yiwa kowaccensu da sunan somin taɓi. Azeema kuwa da ba a asibiti take aiki ba ta ce ita za ta shiga wajensu a asibitin ta karɓa ta fito da su ta ajiye a hannunta. *** ©Rufaida Umar https://chat.whatsapp.com/FQc8pWPPMQe2IE1dUoteD1 *Hajjaju kindade kina Neman inda Zaki dinga sarin kayayyaki domin kisiyar kisamu riba?😄😃... Sha kurumin ki yar uwa Maza kishiga wannan group din Mai albarka domin samun kaya masu inganci d kuma rahusa*💃💃💃 *Muna kawo kaya daga china, Lagos d kuma sauran wurare. Muna saida bags, shoes, jewery, kayan yara, sleeping dress da kuma sauransu. Kayayya kinmu a gida suke d kinsiya xa'a Miki delivery sharp sharp*🥰💃 SANNNAN GA MASU SON FARA BUSINESS BASUDA JARI ZAKU IYA REPOSTING KAYANMU KU DORA RIBARKU AKAI WATO DROPSHIPPING😍 muyi ma customers dinku delivery cikin sauki acikin Leda gari yayi zafi*🤣 *Muna aika kaya ko'ina cikin aminci d Amana* *** *** *** *Kazar Kwanci...* Sadiya ke duba sakamakon jarrabawar Husna cike da takaici ganin wannan karon ma ba abin kirki ta yi ba a makaranta. Ta rasa son wasa irin na Husna, koda dai, tun sadda ta samu waya ba ta da aiki sai buga wasanni sai ko kallace-kallacen fina-finan India fassarar Hausa. Da dai sauransu. Hannu aka saka aka fisge takardar har tana ɗan ɓantarewa. Hakan ya sanya Sadiya ɗaga kai ta dubi mai shi. Husna ce  ta yi mata tsaye a kai cikin shigar riga wacce ta ɗan kamata mai tsawo har gwuiwa sai ko dogon wandon da ake wa laƙabi da fensir. Sai faman huci take yi da jefa mata wani kallo na rashin mutunci kafin ta ce. "Kin ga ba na son irin wannan halin Sadiya! Ina ruwanki da kayana da za ki taɓa min? Aikin banza kawai, don kin ga kin ɗara kowa a ajinku da maki mai kyau shi ne ni kuma za ki buɗe min nawa sakamakon? Mtsw." Ta karashe da jan dogon tsaki, idanunta har kumbura suka yi tsabar kukan da ta ci na wannan rashin hazaƙa da ta nuna don hatta da Antinta Hajara sai da ta ce ba ta kyauta mata ba ganin yanda take tsaye wajen koyar da ita karatu amma ta watsa mata ƙasa a ido. "So ki ke yi ƴan uba su yi mana dariya Momina, gaskiya idan wata shekarar ba ki yi abin da ya dace ba zamu yi baram-baram da ke. Idan ba kya so a ji kanmu toh ki maida hankali." Abin da ta ce mata kenan, Malam kansa ya yi faɗa kuma yace muddin ba ta maida hankali ba to fa zai haramta mata riƙe waya. Duka wadannan batutuwa ne suka taru suka baƙanta ranta har ta sha kuka mai isarta. Dama daga Inna har Sadiya babu wacce ta kalleta hakan yasa ta zuciya ta fice a gidan ta shiga makwafta tunda uwarta Hajara ba ta gidan. Sadiya kuwa da aka hana ta ganin sakamakon Husnar, ta shigo dakin ta hange shi saman gado inda ta yi jifa da shi ta ɗauka tana karantawa, haka ta shigo ta iske ta. Sadiya ba ta ce mata uffan ba ta miƙe ta fice a ɗakin, idan da sabo zuwa yanzu ta fara sabawa da wannan rainin na Husna gareta. Ita kuwa Husna bin ta da harara ta yi kawai tana turo baki ta nemi gefen gadon ta zauna. Wayar ta dauka ta cigaba da dannawa, a ganinta ma sai me idan ta maimaita ajin? Ai ba kanta farau ba a makarantar. Da wannan ta yi watsi da dukkan wani tunani, sai kuma take jin babu dadi ga yadda ta yiwa Sadiyar, hakan duk sai ya hana ta sukuni. Amma da  ta tuno maganganin da Anti Hajara ta fadamata sai ta ja tsaki ta watsar. "Yanzu za ki ga hatta da Malam kowa zai maida hankali ga Sadiya, ji dai yanda yake ta yaba kokarin da ta yi har yana misalta hakan da shi a lokacin da yake sakandire. Hum, Momina idan Sadiya ta fi ki kyau a fuska da sura, kar ki sake ta fi ki a kwakwalwa, ki dage sosai. Ni na san yanzu murna take da farin ciki jin babu ya ita a gidannan." Abin da ta ce mata kenan wanda yasa babu damar ta ga Sadiya ta yi ko murmushi sai ta tsargu ranta ya baci ta ji kawai da ita take. ***   BAYAN WATANNI BIYU... Hajara ta gama tabbatarwa ba ta dauke da juna biyu, hakan na nufin tsarin iyalin da ta yi kafin wata mu'amala ta haɗa su da Alh Nuhu ya karɓe ta. Zuciyarta kuwa zuwa lokacin babu wani sauran fili da soyayyar Alh Nuhu bai ginu ba. Ko a cikin labari ta kasa labartawa wani ko wata mummunan aikin da ƴan siyasan nan suka sanya su. Ta kuma ga tabbacin cewa Waleeda sun yi aikin saboda yanda suke facaka da kuɗaɗe. Babu kamar Waleeda wacce har gida ta siya na kanta. Tana cikin manyan celebrities da suke tashe a duniyar soshal midiya a sannan. "Kar ki yarda ki yi wasa da damar da ki ka samu Hajjaju, ki ba da kai kawai bori ya hau. Na rantse maki ba ke kaɗai ba, mu kanmu da muka raɓe ki sai mun lashi wannan zumar da za ki tsunduma a cikin ƙoƙonta. Ni na san ba za ki watsar da mu ba duk sadda duniyarki ta yi faɗi." Abin da Waleeda ta ce mata kenan a farko farko sadda ta ƙi sakin jiki ta amshi tayin auren da Alh Nuhu ya yi mata. Yanzun kuwa ta yi amanna da shi. Alh Nuhu ya je ya ga Malam da Kawun su Hajara a can babban gida tare da magabatansa har da dukkyar aure. Abinka ma da manya, a ranar waliyyansa suka bukaci a daura aure biki ya biyo baya. Malam da Abba farko ba su yi na'am ba, amma koda aka tuntuɓi Hajara ta amince da hakan, nan take Abba ya yi wa Hajara walicci aka ɗaura aure sannan aka tsaida sati uku a zummar za'a yi biki da kai Amarya. Duk wannan buduri da ake yi Inna ko a neman auren ba ta da masaniyar komai. Tun a na saura sati da zuwan dangin Alh Nuhu, Malam da ma yayyun Hajara maza duka sun sani idan ka ɗauke Zakari wanda ya je Daura a ranar tare da matarsa Hadiyya, bikin Yayan Hadiyyar ake. Anti Hafsatu kuwa koda wasa Hajara ba ta sanar da ita ba, ta ma roƙi sauran yayyunta maza akan kar su faɗamata saboda tabbas idan ta ji to kamar Innar ta ji ne. Jin Innar tana nufin rushewar auren nata. A cewarta, Malam bai ji dadin zancen ba, koda ya nuna ba haka ba Hajara ta shiga kuka da sheshsheƙa tana zantukan da tasan dole su karya zuciyarsa musamman tunda suka shafi Asma'u. Wannan dalili yasa ya karɓi roƙonta ya kuma yi alfarmar yin shiru da bakin nasa sai bayan an ɗaure kamar yanda ta buƙata kafin a sanar da Inna. "Ba hakan na nufin na yarda da zaton da ki ke yi a kan Mairamu ba ne Autar Mama, sai dai saboda kin roƙi hakan, na kuma karɓa zan rufe yanda ki ka bukata. Ina so dai ki san cewa babu mai yi sai Allahn da ya ƙage mu. Komai na faruwa bisa yanda ya tsara shi. Ku kyautata zato ga Mairamu, mutuniyar kirki ce mai sonku da zuciya ɗaya." Kalaman na Malam sun shiga ta dama sun fice ta hagu don ba su yi tasiri a zuciyar Hajara ba, su Hashim da Baba Habu da Mustafa kuwa, kowa da yanda ya kalli zancen. A bangaren Hashim, kawai daɗin zama ne ya sanya Malam din goyon bayan matarsa, Baba Habu kuwa ko oho, Mairamu ko tana sonsu ko ba ta yi a ganinsa damuwarta ce. Shi kuwa Mustafa dama can ba ya kaunarta, to don me zantukan Malam za su karya zuciyarsa alhalin bai ga shaida a ƙas ba? Kusan dai dukkansu maganganun Hajara sun fi tasiri a zuƙatansu, sun fi yarda da cewa mai yiwuwa mugun hali irin na kishiyar Uwa ce ya yi tasiri a kan Inna Mairamu ta ke hana uwarsu aure. Amma fa babu wanda ya damu akan ta kaunace su ko a'a. Ba su ne suka ƙara gasƙata cewa fasa auren Hajarar daga Innar ba ce ba, sai da suka ga an daura auren ƙanwartasu lami lafiya ba tare da sanin Innar ba kuma hakan ya yiwu. "Biri ya yi kama da mutum, shiyasa ni fa sam hankalina bai kwanta da shiru-shirun matar can ba. Ashe dai zagon ƙasa ta ke yi." Faɗin Baba Habu yana girgiza kai cike da takaici da jin ɓacin rai game da lamarin Inna Mairamu. "Ai dama da walakin goro a miya, ba zai yiwu ace hakanan ba tare da wani kwakkwaran dalili ba a na fasa auren Hajara. Na yi shiru ne dai ban furta ba. Amma ai na jima ina zarginta." Faɗin Mustafa kenan.  Hashim ya yi murmushi. "Sai dai kuma ai Dukan Ruwa ba zai hana gwarje amo ba. Duk dai abin da Inna ta ƙi afkuwarsa yanzu ya riga ya faru. Hajara da rai da lafiyarta za ta shiga ɗakin aurenta da yardar Allah. Kar a ce mata komai please, akwai ranar ƙin dillanci tunda dai ita ma ta haifa." Gaba daya suka jinjina kai suna gasƙata zancen Hashim, tabbas ta haifa kuma za ta gani a kan nata. *** Idanu waje ta ke duban status din da Hajara ta ɗora. Dagaske an ɗaura  aurenta? To yaushe? Ya aka yi aka ɓoye neman ba ta da labari? "Kut! Ni Hajara za ta ci amana! Duk yanda nake bibiyarta da kyawawan kalamai, har ta yi aure ba ta shaida min ba?"  Faɗin Nusaiba a fili ƙarara, tana jin wani zugi da tsananin baƙin ciki mai kama da hassada a ranta. "Me kike so ki ce? Ba aminiyarki ba ce?" Faɗin Maman Boy cike da mamaki bayan ta ajiye biron hannunta saman tebur bayan ta kammala rubutawa wata mata kwanan wata da ya dace ta dawo don yin wata allurar na tsarin iyali, ko takardar ba ta kai ga miƙawa matar ba tsabar abin na Nusaiba ya ɗaure mata kai. Matar dai na tsaye tana kallonsu. Nusaiba kuwa wacce sai a lokacin ta ankara da suɓul da bakan da ta yi sai ta wayance da cizon yatsa tana duban Matar dake tsaye. "Ki sallami mata tana jiranki." Abin da kawai ta iya cewa kenan kafin ta dauki wayarta da ta suɓuce ta faɗi a dandaryar tayils din ɗakin nurses din nasu ta fice waje. Wuri ta samu ta zauna tana cika da batsewa, har wani gumi ke karyo mata tsabar tashin hankalin wannan aure na Hajara da aka ɗora. Ta yi ƙwafa gami da girgiza kai. A ranta take faɗin, 'Lokaci ya yi, lokacin da zan fasa ƙwai a gidan su Hajara ya zo. Kowa sai ya shaƙi warinsa.' Daga haka ta yi wata shu'umar dariya. Ta rantse yanda ta kasa aure a duniya dalilin munanan ɗabi'unta da ake bankaɗawa manema auren a unguwarsu, haka ma Hajara ba za ta yi zaman aure da daɗi ba. Wataƙila ma rufa-rufa ta yi wa wanda ta aura ɗin, amma tana da tabbacin idan ta tona asiri, to fa komai zai faru.  Ba ta da lambar kowa a dangin Hajara idan ka cire ta Safiyya da kuma Malam. Ta Malam ta samu ne sanadiyyar wani lokaci da Hajara ba ta da wayar hannu kuma aka yi sa'a ba ta koma gida lokacin da ya dace ba, hankalin Malam ya tashi. Dalili kenan da ya tako har asibitin, inda Allah ya taimaki Hajara sannan ko fita ba ta fara ba, iskancin nata bai yi ƙarfi ba a sannan. Hankalinsa ya kwanta jin cewa mai karɓar mata na dare wato Nusaiba ita ce ba ta shigo da wuri ba, a dole ta jira kuma kasancewar za ta kawo mata wani saƙo. Sanadin kenan da Malam suka yi musanyar lamba da Nusaibar da zummar duk sadda hakan ya ƙara faruwa zai neme ta. Wani murmushi ta yi, ta miƙe hankalinta kwance ta ƙarasa aikinta na ranar, lokacin tashinta yana yi ta fice ba ta ƙara yarda ta amsa tarin tambayoyin da Maman Boy ke jifanta da su ba don ita zancen Hajarar ta yi aure ma ba sonsa take ba. Ji take wani malolon abu na tokare mata ƙirji duk sadda aka shiga batun. ***   Inna ta yi shiru ta kasa magana, Malam da shirunta ya nemi tarwatsa kirjinsa ya kasa haƙuri ya ce. "Mairamu, kin ji abin da na faɗa?" Murmushi ta yi, murmushin dake ɓoye da maganganu masu yawa da cin rai a ƙirjinta. "Na ji Malam, Allah ya sanya alheri ya zaunar da su lafiya." Ya amsa da amin cike da jin nauyin rashin kyautatawar da ya yi na ƙin sanar da ita. Amma ya zai yi da alƙawarin da ya riga ya ɗaukarwa Hajarar? "Ki yi hakuri Mairamu, ki na da haƙuri. Ki ƙara kan wanda na sanki da shi, ba don na goyi bayan yara ne ya sanya ni shiru ba. A'a, da auren da..." "Haba Malam, na yi maka ƙorafi ne? Ai ban ce maka komai ba. Har a raina na ji ma Hajara daɗin wannan auren. Kuma dama ai ba komai ke buƙatar bayyana shi ba. Duk abin da ya faru, hakan ne daidai. Kar ka damu. Burinmi ta yi aure, kuma Allah ya karɓi addu'armu. To sai mu yi fata da addu'ar nema musu zaman lafiya." Malam ya numfasa, ya sani dole ranta zai sosu, ba shi da abin ƙarawa a kai tunda ya san wace ce Mairamu. Daga wannan ɗin da ta furta, to fa ba lallai ta ƙara koda kalma guda ba. A haka suka yi sallama bayan ya sanar da ita batun kawo lefe a goben. Nan ma da toh ta bi sa, ba ta buƙatar tanadin komai ga masu kawowar tunda tana da tabbacin yanda aka yi auren ba ta sani ba, shi ma kai lefen babban gidan ne za su yi ruwa da tsakin karɓa. "An ɗaura auren Anti Hajara kuma? Ko dai yana nufin za'a ɗaura?" Sadiya ta tambayi Innarta fuskarta dauke da maɗaukakin mamaki. "Ki bar mamaki Mamana. Hajara an ɗaura aure. Yar uwarki ce, ki yi mata fatan alheri." Daga haka Inna ta fice zuwa ɗakinta ta bar Sadiya tsaye baki kuma a buɗe. Dawowarta daga makaranta kenan ko jakarta dake rataye a kafaɗarta guda ba ta sauke ba ballantana a kai ga cire ƙaramin hijabin makaranta da ma takalmi.  Au dama shiyasa Husna ta tattare a babban gida? Dama ƙusƙus din da Husna ke yi a waya kenan idan ta shigo ta waske ta katse kiran? Husna ta yi girman da za ta san abu ta kasa sanar da mahaifiyarta? Anya akwai daidai a tafiyar nan ta rayuwar ƙanwarta? Anya Malam da yayyunta sun kyautawa Innarta? Hawaye take fitarwa masu zafi, jikinta tsabar ɓacin rai har rawa yake yi, daƙyar ta iya jan ƙafafunta da suke neman kasa ɗaukarta ta faɗa ɗakinsu. Nan ma sai da ta yi kuka mai yawa ba don komai ba sai na tausayin Innarta kafin ta miƙe jin Inna na kiran sunanta da tambayar ko ta yi sallah ne ya sa a dole ta share fuskarta ta na amsa murua a dusashe "A'a." Shi ne kawai abin da ta iya furtawa. Ta kula ko a muryar Innar babu alamar abin ya dame ta. Sallamar Anti Hafsatu ne ya katse tunaninta, sai ta ji kamar ma a masu laifin har da Anti Hafsatun idan ka cire Mahaifinsu da ta ji hatta da shi ɗin haushinsu take ji. Kasa fita ta yi bayan ta sauya kaya, duk yanda ta so ta watsa ruwa saboda ƙaiƙayin da jikinta ke yi idan ta cire kayan makaranta amma ɓacin rai bai bar ta ba. Ƙarshe ma tana jin shigar Inna da Anti Hafsatu ɗaki ta zura hijabinta ta fice a gidan zuwa na su Zahra. Ta san dai faɗa ne za ta sha a wurin Innar ta yanda ta fita a gidan ba da izninta ba.  Amma da dai ta zauna ta bi Anti Hafsatu da kallon ba ta kyauta musu ba, gwara ta fice a gidan. Ita kuwa Anti Hafsatu kuka sosai take yi a gaban Inna, ta rantse ta kuma kan cewa ba ta san da batun auren ba. Inna ta yi murmushi, ko Zakari ma ya kira ta daga Daura, ya kuma ba ta hakurin abin da Malam suka aikata mata. Inna ta girgiza mata kai. "Haba Hafsatu, mene ne na kukan? Ni fa tunda har Hajara ta yi aure, wannan farin cikin ya tafiyar da kaso mai yawa da damuwar ɓoyon da aka yimin ya haifa min a zuciya. Babban burinmu bai wuce mu ga ta yi aure ba, kuma sai ga shi nan Allah ya karɓi roƙonmu. Don Allah ki daina kukan nan. Ba su kyauta maki ba tabbas matsayinki na babbar yayarsu mace, amma kar ki duba hakan. Ko me suka yi ai da sanin Malam suka aikata shi, don haka ki yi haƙuri, kuma ki saka a rai ba komai ba ne hakan. Kar na kuma ji kin ce ba za ki saka hannu a hidimar bikin ba, yar uwarki ce. Kuma kin fada ta je har gidanki bayan an daura ta sanar da ke da kuma dalilin ƙin faɗamaki a farko, to ki yi hakuri, ta ci albarkacin cewa ita din yar uwarki ce da ku ka fito ciki ɗaya. Ke ce matsayin Uwa a wajenta, don Allah ki shiga a yi komai da ke. Idan har na isa da ke." Anti Hafsatu dake jan majina wanda ya taru sanadiyyar kukan da ta ci tun ma kafin ta ƙaraso gidan, daƙyar ma ta iya tuƙo kanta a motar. "Kin isa da ni Inna, wallahi kin kai maƙura wajen isa. Duk umarnin da ki ka ba ni matsayinki ta Uwa a gare ni ba zan watsa maki ƙasa a ido ba. Ina ƙara neman gafararki bisa abin da ya riga ya afku." Inna ta share ƙwallarta, wannan ƙauna da Hafsatu ke nuna mata ba ta jin za ta mance da ita har abada. "Na gode Hafsatu. Allah ya ƙara wa rayuwarki albarka. Ni dama ban riƙe su a raina ba. Komai ya wuce. Allah ya sa a yi lafiya a kammala." Anti Hafsatu ta amsa da amin. "Sadiya! Ko ba ta dawo ba?"  Cewar Hafsatu tana maido idanunta kan Inna. Ita kaɗai ta tambaya don dama Husna ta tare Hajara ta je da ita can gidanta. Inna ta girgiza kai. "Ta dawo, amma kuma na ga sadda ta fice a gidan ta tagar ɗaki. Ina kyautata zaton gidan su Zahra'u ta tafi." Ajiyar zuciya Hafsatu ta saki, ta kula Sadiya fushi take da ita kenan. A baya matukar ta zo gidan to fa duk abin da take yi tana sakinsa ne ta tarbe ta da fara'a. Aikuwa miƙewa ta yi tace sai ta shiga ta kira ta. Duk yanda Sadiya ta kai ga kaucewa haɗuwarsu sai da Hafsatun ta jawo ta suka komo gidan, ita ma nan ta jaddada mata rashin saninta kan batun daga ita har Zakari, sosai Sadiya ta fahimce ta har ta ji kunyar yanda Antin ke faman ba ta haƙuri. Zuciyarta ta yi wasai. *** Washegari aka kawo lefen Hajara akwati har saiti uku, nan fa babban gida ya ruɗe. Kowa ya na faɗin dama ai jinkirin alheri ne. Lokacin Hajara da Husna suna can wani katafaren shago na gyaran Amare ana mata gyara jiki, a waya Safiyya ta yi musu bidiyon kayan duk suka ruɗe, Hajara kanta ya ƙara fasuwa sosai. Husna kuwa kwadayi da burinta a kan auren mai kuɗi na ƙaruwa don ta kula komai sai da kuɗi yake samuwa cikin sauƙi a rayuwa. Gwaggo Saratu ta rasa ina ta saka ina ta ajiye tsabar farin ciki da daɗi. Inna Mairamu ta je karɓar lefe wanda sam Sadiya ba ta so hakan ba don har kuka ta saka na takaici. "Mamana ina yi wa Hajara kallon da nake maki, na ɗauke ta tamkar ɗiyar da na haifa a cikina. Wannan abu da ya faru, haka dama tsarin yake, zai farun babu yanda muka iya. Babu komai, watarana sai labari, zan je, zan shiga na haɗa idanu da Saratu na taya su murna da addu'a." Wannan ne amsar da Innar ta ba Sadiya. Aikuwa dai ta sha habaici da baƙaƙen maganganu wanda duk iyakar dauriyarta sai da zuciyarta ta karye. Da wannan ƙaton raunin da aka haifar a zuciyarta ta bar gidan ta koma nata. *** Sati na zagayowa aka fara biki, an yi kamu a nan cikin babban gida kafin a tattara a koma gidan Malam inda ta nan Hajara ke so a miƙa ta ɗakin aurenta. Ranar ne kuma masu kai kaya suka je aka dawo ana zuba uban santi na girma da tsaruwar gidan don a cewarsu har da wajen wanka. Wato swimming pool. Hajara na ta faman dariyar tsokanar da wata abokiyar wasansu  Baba Suwaiba ke mata wai ita ce ya dace ta auri Alh Nuhu ba ita ba, a gefe kuma wata babarbariya da ta zo gidan takanas tana reramata kitso don ba ta son zama babu kitson tunda tana da gashi mai tsawo da cika, wanda gadon gidansu ne. Kusan kaf dinsu sai kalilan, su na da gashi mai yawa da kuma laushi. A ranar ne kuma za'a fita yinin bikin da aka kamawa ƙaton hall kuma mai tsada. Ƙarar wayarta ce ta sa Husna da suke tare a ɗakin ta miƙa mata tana ambaton sunan mai kiran, 'Nussy'. Hajara ta karɓa da sauri ta ɗaga gami da karawa a kunne tana dariya. "Mutuniyar, ke ma na maki surprise ko?" A bangaren Nusaiba ita ma dariyar ta yi ta amsa da fadin. "Hajjo kenan. Na kuwa ga surprise da ki ka ba ni. Amma kuma ni ma na aikomaki da wani surprise din. Ki na iya duba whatsapp dinki." Daga haka ta katse kiran. Jin haka ya sa Hajara fiddo idanu kaɗan. Tuni mai mata kitso ta saki kanta ganin ta ƙi tsayawa gudun kar ya ƙi yin kyau.  A fili ta ce. "To Nussy ko ke ma auren ne ya zo?" Duk a zatonta ko katin gayyatar biki za ta gani, sai dai ganin hoto ɗaya da ya buɗe ya sa ta saurin miƙewa ba tare da ta kula kowa ba ta fito ta faɗa falon Malam don babu kowa a ciki. Ita ce dai, ita ke tsaye da wani saurayi wanda ke riƙe da ƙugunta, yayinda ita kuma ta zuro harshe shi kuma ya kama da nashi bakin aka ɗau hoton. Ba ma wannan kaɗai ba, wani tana tsaye a club cikin shigar rashin mutunci, wani kuwa bidiyo ne mai kyau tana rangaji bayan ta kwantar da dukkannin jikinta a saman kirjin wani matashin saurayi. Akwai wanda ma suna zaune a dakin saukar baƙi na Zuma Hotel. Jin muryar Husna ya sa a gigice ta saka wayar a key. "Anti meyafaru?" Ba ita kadai ta shigo ba, har da Safiyya wacce ta biyo ta. Ta yi kokarin saita fuskarta da murmushin yaƙe ta amsa. "Babu komai. Ina zuwa." Daga haka ta koma ɗakin zaure wanda yake mallakin samarin gidan kafin su yi aure. Ta ci sa'a sai yara kawai suna ta wasa da fararen kujerun da aka yi amfani da su a jiya ranar kamu. Wayarta dake ƙara ta ɗaga, kafin ta ce komai Nusaiba ta soma magana. "Na tabbata surprise dina ya fi naki girma ko? Kar ki damu, wannan ba ke kaɗai na turawa ba, yanzu haka Malam yana can hankalinsa a tashe. Kayya, ina fatan ma kar damuwa ta sanya shi faɗuwa." Cikin muryar kuka da tashin hankali Hajara ta zube warwas a ƙasa har yaran da suke cike a falon Anti Kubra suna kallon maimaicin shirin Dadin Kowa suka dube ta. Wannan karon ba ta ko damu da wanzuwar kowa a wurin ba ta ce. "Allah ya isa tsakanina da ke Nusaiba! Ashe dama ba ki da mutunci? Cin amanar da za ki yi min kenan?" Dariya sosai Nusaiba ta saki. "Ba ki da lokaci Hajjo, ko kaɗan ba ki da lokacin kuka yanzu. Ki tseratar da mutuncinki daga jin kunyar duniya ki nemi Malam kafin ya kai ga buɗe saƙona. Idan kunne ya ji..." Ai ba ta bari ta ƙarasa ba ta fito a guje ta koma ɗaki har tana tunkuɗe matar ɗan uwan Malam mai suna Anti Kubra dake shirin tafiya kwalliya. "Lafiya?" Haka kowa ke faɗi, tana shirin fita a ɗakin ba tare da ta amsawa kowa ba sai ga Malam ya leƙo ta falonsa yana tambayar wata da ta fi kusa da ƙofar falonsa Inna Mairamu. Hajara na ganinsa ta nufe shi, koda ta ƙarasa ya dube ta ganin duk ta ruɗe. "Autar Mama, lafiya? Meyafaru?" "Shi ne tambayar da muke ta yi mata, ta shiga ta fita tana gudu tamkar wacce aka jefa." Faɗin wata daga cikin facalolin Inna Mairamu kenan. Hajara kuwa ganin yanayin Malam ya tabbatar mata da cewa bai buɗo saƙon Nusaiba ba, ta yi wa kanta faɗa ta saita fuskarta sai kuma ta wayance da fashewa da kuka. Ganin haka Malam ya kama hannunta ya ja zuwa falonsa, babu wanda ya bi bayansa. Nan aka hau taraddadi da tsoron meke afkuwa. Gwaggo Saratu faɗi take. "Na rantse idan har Mairamu ce ta yi wani ƙullin na zautar min da ɗiya sai na ga bayanta! Ba zan ƙyale ba idan Hajara ba ta shiga gidan aurenta ba wannan karon!" Karaf a kunnen Sadiya wacce shigowarta kenan daga gidan su Zahra'u. Baƙin lalle aka zizara mata a hannu ba don ta so ba sai saboda Inna da ta ce ta je a yi ɗin kar a ce wani abu. Gudun ɓacin ran Innar ta yi iyaka baƙin. Ta dubi Gwaggo Saratu dakyau sai kuma ta haɗiye zafafan kalaman da ta yi niyyar yi don ba tarbiyyar da Inna ta ba ta kenan ba. Ba ta kula kowa ba ta nufi ɗakin Inna. Nan ta tarar da Dada tana faman yi wa yaranta mata faɗa don Rukayya ta dage sai ta fita ta rama wa Inna. Innar ma cewa ta yi babu ruwanta. "Haka za'a cigaba da faɗamaki ki na kyale su Adda Mairamu? To na rantse duk sadda waccan banzar dumɓarun ta ƙara faɗamaki baƙar magana a gabana sai na gwabje bakin ƴar banza!" Cewar Ruƙayya kenan wacce ta fi Fatima da Murjanatu ɗaukar zafi. Ita Fatima kawai hawaye take fitarwa don rauni ne da ita sosai. Dada ta taushe su sosai ta ce a bar zancen. Daƙyar Rukayya ta nemi wuri ta zauna. Sadiya dama jikinta duka ya yi la'asar hawayen ma sun ƙi fita. "Ita kuma waccan shashashar bari ta zo ta same ni tunda ba ta san zafin Uwa ba." Ruƙayyar ce dai ta ƙara faɗi, tana nufin Husna don gaba ɗaya haushi take ba ta. *** Duk iyakar binciken Hajara a wayar Malam ba ta ci karo da saƙon Nusaiba ba, hankalinta ya yi mugun kwanciya sai dai ba duka ba, ta sani tunda Nusaiba ta furta za ta yi, to fa akwai alamun aikatawar. Ta samu ta toshe tashin hankalinta da cewa Malam ai ji take kamar za'a ce Alh Nuhu ya sake ta shi ne take jin firgici ta ruɗe. Haka ya dinga yi mata wa'azi don dagaske ya yarda da abin da tace ɗin. Sai da ya shiga ɗakinsa ne ta yi nasarar ɗaukar wayarsa. "Me kike so?" Saƙon da ta tsinci kanta da turawa Nusaiba kenan. "Miliyan ɗaya." Ta maido mata martani. Hajara ta numfasa, har lokacin dai Malam bai kai ga fitowa a ɗaki ba. Dama karshen sati irin yau Asabar, ba ya zuwa kasuwa wani lokacin yakan huta a gida, ko kuma ya je can babban gida. A take Nusaiba ta turo lambar akawun, ga mamakinta kuwa a take Hajara ta aikamata kudin. Ta bi ta da saƙo. "Kar ki kara Nusaiba, kar ki ƙara yi min barazana tunda na sallameki." Daga haka ta samu nutsuwar zuciya sosai, ta kashe wayarta ta kuma dauki wayar Malam ta lalubo lambar Nusaiba ta rufe daga kira da ma kan whatsapp yanda ba za ta same shi. Sai dai kuma ba anan gizo ke saƙar ba!! ©Rufaida Umar https://chat.whatsapp.com/FQc8pWPPMQe2IE1dUoteD1 *Hajjaju kindade kina Neman inda Zaki dinga sarin kayayyaki domin kisiyar kisamu riba?😄😃... Sha kurumin ki yar uwa Maza kishiga wannan group din Mai albarka domin samun kaya masu inganci d kuma rahusa*💃💃💃 *Muna kawo kaya daga china, Lagos d kuma sauran wurare. Muna saida bags, shoes, jewery, kayan yara, sleeping dress da kuma sauransu. Kayayya kinmu a gida suke d kinsiya xa'a Miki delivery sharp sharp*🥰💃 SANNNAN GA MASU SON FARA BUSINESS BASUDA JARI ZAKU IYA REPOSTING KAYANMU KU DORA RIBARKU AKAI WATO DROPSHIPPING😍 muyi ma customers dinku delivery cikin sauki acikin Leda gari yayi zafi*🤣 *Muna aika kaya ko'ina cikin aminci d Amana* *** *Kazar Kwanci...* Duk irin yadda Sadiya ta so ƙin bin su zuwa liyafar hakan bai samu ba tunda Zahra da su Meenat ɗiya ga Anti Amarya (Zulfa'u, matar aminin Malam, Alh Abubakar da suke kira da Abba) sun matsa akan ta shirya su wuce, a dole bayan Inna ta sanya baki ta miƙe ta shirya cikin ankon da kowa ya saka. Ba ta shafa komai a fuskarta ba amma ɗinkin ya zauna ƙwarai a jikinta, ya fiddo da ainahin surarta mai kama da na cocacola. A can kuwa biki ya yi biki, duk irin nishaɗin da ke saman fuskokin jama'ar wurin babu wannan farin cikin a ɓangaren Hajara don har a sannan da take zaune saman wuri na musamman da aka tanada dominta kaɗai a wannan rana, ta kasa mance barazanar da Nusaiba ta yi mata. Saƙe-saƙe take yi na yadda za ta ɗau mataki a kai.   Hankalinta bini-bini yana kan wayarta, kula da rashin nutsuwarta ne ya sa Safiyya da kanta ƙarasawa ta yi mata raɗa a kunne. "Wai meke faruwa? Don Allah ki saki jikinki hankalin kowa fa yana kanki. Wasu sai su ɗauka ko akwai matsala ne." Hajara da ta ji abin ya haɗe mata da kewar Mamanta, kawai sai ta marairaice fuska. "Mama nake tunowa." Safiyya ta ji hakan a ranta ita ma, dama kuma ta yi wannan hasashen. Kwalla suka cika idanunta, ta yi saurin dauke su da yatsu. "Addu'a da haƙuri zamu cigaba da yi Autar Mama." Daga haka ta bar wajen. Ba jimawa Ango ya iso da tawagarsa, ranar dai an yi ruwan kuɗaɗe na liƙi. Abin da ya baƙanta ran ire-iren su Sadiya bai wuce zagewar da ya yi yana tiƙa uban rawa ba. Ta kula ita Anti Hajarar ma rangaji kawai take yi don dama gaskiya can ita ɗin ba ta kasance mazari ba. Don haushi ko tashi ba'a yi ba suka bar wurin ita da Zahra'u. Bayan tashi daga taron, a daren kowa ya watse sai na jiki sosai kuma na nesa da suka kwana a gidan Malam da zummar rakiyar Amarya ɗakinta a washegari. *** Kowa ya yi zaman kari, kofuna ɗauke da kunu da fanke kawai kake gani yana gilmawa ana yi ana hira.   Shigowar Malam tsakar gidan daga shi sai doguwar jallabiyarsa ya sanya aka hau gaishe shi. Babu wacce ya amsawa, anan suka kula ransa a tsananin ɓace yake don jikinsa har rawa yake yi sosai. "Hajara! Hajara!! Kina ina!" Sunan Hajara da ya ambata sai da ya sa dukkansu miƙewa a ɗan firgice, kowa na neman ba'asin. Hajara wacce kamar a mafarki ta ke jin kiran na Mahaifinta ga kuma muryar Husna na kiran sunanta da jijjiga ta, kusan a razane ta buɗe idanun. Ta miƙe zaune, ba tare da ta ƙarasa sauraron Husnar mai shaida mata Malam na kiranta ba tunda babu buƙatar ƙarin bayani. "Na'am." Ta amsa sadda ta fito daga ita sai doguwar rigar bacci iyaka gwuiwa mai kauri. Malam wanda a lokacin har Inna na tsaye tana tambayarsa ko lafiya amma bai kalli kowannensu ba. Ransa ya yi ɓacin da idanunsa suka makance, kunnuwansa suka toshe, ba ya tuna su waye a wurin. Hajara kirjinta ya faɗi sadda ta ke duban Malam wanda idanunsa suka kaɗa jawur, wayar hannunsa ya buɗo bidiyo ya ɗaga da hannunsa zuwa saitin fuskarta yanda za ta gani dakyau. "Ke ce wannan? Dagaske ke ce?" Ya tambaya murya a dusashe. Ji ta yi jiri ma neman kayar da ita, kowa a gurin kuwa ya hau salati, waɗanda ba su gani ba suna zuro kai, yayinda Gwaggo Atine hannu ta saka ta karɓi wayar a hannun Malam. "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Na shiga uku ni uwar Gambo, wallahi Hajara ce." Sai kawai ta fashe da kuka tana kai wa nan, Inna wacce ta ga bidiyon don a gefenta Hajara ke tsaye ba a hayyaci ba. Safiyya ita ma kukan ta saka ga wani irin tsantsar mamaki da ya rufe ta. Malam ya shaƙo wuyan Hajara. "Don ubanki abin da kike yi kenan idan kin fice a gidana da zummar aiki?  Kin cuce ni Hajara! Kin kuma cutar da kanki! Allah wadaran wannan halin naki!" Daga haka ya hankaɗe ta ya fice zuwa falonsa. Hankalin kowa ya tashi, Inna ce ta karɓe wayar ta bi bayan mijinta ranta babu dadi ga hawayen da take fitarwa. A tsakar gidan kuwa aka yi wa Hajara caa kowa na faɗa. Kowa faɗi yake ta ɓata wayonta. "To kodai dama wannan ne dalilin da yasa ake fasa auren nata a baya?"  Maganar ta fito daga bakin wata matar ƙanin Malam da suka hada Uba wacce bakinta ba ya shiru. "Uhum, ai zai ma iya kasancewa hakan ne. Baiwar Allah Mairamu an ɗauki haƙƙinta babu gaira ba dalili, ana zaton wuta a maƙera..." "Sai aka gan ta a masaƙa." Wata ta ƙarashe zancen da wata da suke kira Iya Sarai ta ɗauko. Nan da nan hayaniya da cece-kuce ya shiga tashi kowa na faɗin albarkacin bakinsa, ita kuwa Hajara sai Safiyya ta ja hannunta suka shige ɗaki ta rufo. *** "Haba Malam, ya kyautu ace ka fallasa wannan zance a bainar jama'a? Yanzu..." "Mairamu ki bar ni da zancen nan don Allah. Ki bar ni na ji da abin kunyar da yarinyarnan ta jima tana jaza min." Faɗin Malam ɗin har sannan fidda huci yake kawai na zallar ɓacin rai. "Assalamu alaikum." Inna da Malam suka dubi mai sallamar, Hashimu ne wanda Malam din ya yi wa kiran gaggawa, ba ma shi ɗaya ba, gaba ɗayansu ya yi wa wannan kiran. Ya ƙaraso kana kallonsa ka san cewa a gigice ya ke don ko wanka bai yi ba, riga ce tshirt a jikinsa sai wandon shadda da ya zura a saman gajeran wando na ciki. Allah ya taimaka ma a mashin yake. Ya gaida Inna ta amsa gami da miƙewa ta ba su wuri. Malam ya fiddo wayarsa, jikinsa duk ya mutu a sannan saboda damuwar da ke cin zuciyarsa da tsananin baƙin ciki. Abin da ya fi masa ciwo ma bai wuce na samun irin wannan banzan halin daga wacce bai taɓa zato ba a yaran. Hashim ya sanya hannu ya karɓi wayar, nan ya shiga kallon bidiyon ƙanwarsu Hajara tana ta shafa jikin wani namiji ita ma ana shafa ta ɗin. Ba a nan abin ya tsaya ba, sauran abubuwan ma da suke biyo wa baya babu kyan gani. "Innalillahi..." Hashim ya furta har ƙarshe yana mai miƙawa Mustafa wayar wanda tuni ya gama gani tun wayar tana hannun ɗan uwansa. Yana tsaka da kallon ne ya shigo falon, ganin yanayinsu bai ko iya kwakkwarar sallama ba ya zauna gefen Hashim yana kai idanunsa kan abin da yake kalla. Gaba ɗaya zuƙatansu suka ɗauki zafi. Hajara ce dai? Har a lokacin Mustafa tantama yake yi dalili kenan da ya ƙara buɗo bidiyon yana kallo sai ya yi maza ya kife wayar. Miƙewa ya yi jikinsa har wani rawa yake. "Koma ka zauna." Umarnin da Malam ya ba shi kenan. Ba da son ransa ba ya koma ya zauna, Hashim tsabar ɓacin rai ma kalma ɗaya ya gagara furtawa. Ko mintuna goma ba a cika ba suka haɗu gaba ɗaya mazan har Zakari da Anti Hafsatu wacce dama ta gama shirin tahowa gidan, kiran Malam ya tashi hankalinta ba kaɗan ba. A sannan har Hajara ɗin da Safiyya sun shigo har da Inna da Malam ya sa a ka kira ta. "Faɗa min Hajara, faɗa min da bakinki cewa ke ce a wannan faifan ki ke cuɗanya da wani namijin da ba muharraminki ba." Malam ya ƙara furtawa da wani irin sanyi na murya wanda za ka fahimci tsananin ɓacin rai ne ya haifar. Hajara da ta ci kukanta ta ƙoshi ta rarrafa gaban Malam. "Don Allah ku yafe min. Na yi kuskure, sharrin shaiɗan ne na tuba ba zan ƙara ba." Wannan ya ƙara wankewa yayyunta tantamarsu, dagaske ita ce, ba wai gizo idanunsu ke musu. Kuma ba wai kamanni ba ne ko kuwa a ce haɗawa aka yi. Ta amsa laifinta tabbas, wannan ya na nuni da cewa ita ɗin ce. Anti Hafsatu ta furta kalmar La'ilaha illal lahu har ƙarshe, Inna kuwa lamarin ya gama sanyaya jikinta. Ta tuna sadda ta ke jin rashin nutsuwa a yanayin irin yadda Hajara ke tafiyar da rayuwarta, har Malam ɗin ta yi wa ƙorafi amma ya hau ta da faɗa sosai tamkar zai ari baki wai don me ta ke zargin ɗiyarsa. Shi ɗin ya yarda da tarbiyyar da ya yi wa yaransa ba za su taɓa aikata mummuna ba. "Mairamu ki gafarce ni, ki yafe min. Haƙiƙa ke ce kika ankara kamar da sauyi a yanayin da Hajara ke gudanar da rayuwarta har ki ka sanar da ni sai dai ni kuma makahon yardar da na yi wa yaran ya rufe min idanu na kasa yarda, na kasa ganin cewa akwai kaddarar da za ta rigayi fata." Malam ke zancen kamar ya shiga zuciyar Inna ya ji tunanin da ta ke. Hajara wannan abu ya yi mata zafi ainun, wai yau a kanta ne ake wani ba matar nan haƙuri. Wato munafukar ta gano wasu abubuwan shi ne don munafunci ita ba ta ce mata komai ba amma har ta kai wa Malam ƙararta. "Bakomai Malam, yanzu duk maganar nan ya dace a yafe wa yarinyar nan tunda dai ta yi aure kuma gidan mijinta za ta shiga. Don Allah kar ka zafafa a kanta har ka kasa sanya mata albarka a aure." Faɗin Inna cikin kwantar da murya. Safiyya dai wannan karon ba ta Inna take yi ba, ita kunya ma take ji na yanda duk ta dinga zagi da zargin Inna kan hana ƙanwarta aure ga shi nan gaskiya ta yi halinta. Malam faɗa sosai ya yi wa Hajara ya kuma ƙarashe da faɗin. "Na rantse maki kuma, babu inda za ki je da Husna kamar yanda a farko kika roƙi wannan alfarmar a wurina na amince. Kuma kaf cikinku idan an miƙa ta ɗakinta ban yarda waninku ya koma ba idan kuwa ku ka tsallake umarnina ban yafe ba. Sannan ki gaggauta neman gafarar Mairama game da zargi da mugun ƙazafin da ki ka dinga jifanta da shi cewar ita ke yin surƙullen da ake fasa aurenki. Hajara, ki ka taka ki ka bar gidan nan kar ki sake ki dawo sai idan ni da kaina na neme ki. Maza tashi ki gurfana gaban Mairama ki nemi gafararta!" Ya ƙarashe a tsawance.  Inna ta girgiza kai. Za ta yi magana Malam ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu dole ta yi shiru. Hajara da ke kuka kamar ranta zai fita babu abin da ya fi baƙanta mata irin wai da Malam yace ba za ta tafi da Husna gidanta ba. Sannan ta durkusa ta ba Inna haƙuri. Ganin idon Malam ya sa ta mike ta je har gaban Inna ta durƙusa gami da furucin. "Ki yi hakuri." Iyakar abin da ta ce kenan amma ƙasan ranta zagin Innar kawai take yi. Inna ta ce babu komai. Abin da ya ba Hajara mamaki bai wuce ganin da ta yi wa Safiyya ta ƙarasa har gaban Inna ta durƙushe ba tare da an nemi ta yi hakan ba ta ce. "Don Allah Innar Husna ki yafe min, na yi maki munanan kalamai akan ƴar uwata. Na tuba ki gafarta min. Zan gyara zamana da ke daga yau." Inna jin abin ta yi kamar a mafarki, na Hajara bai shige ta kamar maganganun Safiyya ba. Kalmar nan ta zan gyara zamana da ke ya yi mata daɗi ya kuma zo mata a bazatan da ya sanya hawayenta fita. Ta kama hannun Safiyya. "Ya wuce Safiyya, komai ya wuce." Mazan ma (idan an cire Zakari wanda dama shi ba shi da matsala da Inna), koda ba su furta wani abu ba, amma fuskokinsu sun nuna tsantsar nadamarsu bisa zargi da cin fuskar da suke yi ga Inna wacce ko gaishe ta sai sun ga dama suke yi idan sun zo wurin Malam. Tsakar gidan ma sai su jima ba su leƙa ba duk don kar su haɗu da ita kawai. A yau kam dagaske suke jin nadamar komai. Komai da ya faru tun mafarin aurenta da Malam. *** Har aka yi shirin kai Hajara zuƙata gaba ɗaya a cunkushe suke, kan kace me kuma magana har ta yaɗu makwafta sun sami labari. Wai sai ga shi a na zuwa taya Inna murnar fita da zargi har da masu neman gafatarta. Husna jin hukuncin Malam ta yi bai mata wani zafi ba don ita ma tana cike da mamaki da jin zafin abin da Antinta ta aikata ga kuma tausayin Innarta don a cewarta Antin ta yaudare ta sosai. Koyaushe cikin nuna mata take yi ai Innar ce dalilin da ya sa ake fasa aurenta, ita kuma idanu rufe take jin haushin Innarta. Sai ga Husna ta rungume Innar tana kuka sosai tana kiran ta yafe mata. Abin da ya fi yiwa Inna daɗi kenan, Sadiya kanta sai da ta yi hawayen farin ciki. Ta kuma ji duk wani ƙunci da aka cusa mata a zuciya lokutan auren nan duka sun wanku tas. Allah ne dama mai wanke bayinsa daga zargi, yau kam ya karɓi addu'arta ya wanke Innarta.    Haj Mariya da aka yi komai a gabanta kuma har da ita cikin masu kai Hajara a hanya faɗi take. "Shiyasa munana zato ga ɗan uwa musulmi ba shi da daɗi. Ke kuma Hajara matsayina na Uwa a gareki, ina ƙara jaddada maki cewa ki ji tsoron Allah a zamantakewar aurenki. Abin da ya faru ya riga ya wuce, kar ki ƙara yarda shaiɗan ya yi maki famfo wajen saɓon Allah. Allah ya kyauta ya tsare gaba." Shi ne abin da kawai ta ce sauran jama'ar da suke motar suka amsa da amin idan ka cire Gwaggo Atine da ko magana ma kasa yi take tsabar kunya da nauyi. Har a sannan ta rasa da wane ido za ta dubi Inna Mairamu ta nemi gafararta don ta yi mata wulakanci fiye da zato akan abin da ba ta da haƙƙi. ***   HUZAIF ABUBAKAR SHARAƊA... ©Rufaida Umar Huzaif Abubakar Sharaɗa "Ga Yaya Huzaif! Ga Yaya Huzaif!!" Abin da ya dinga shiga kunnuwan Haj Mariya kenan tun tana kicin tana duba miyar da take yiwa Abba kasancewar ba ta taɓa barin ƴar aiki ta girkawa mijin nata abinci. Abban ma ba ya so, daga ita har Zulfa'u bai aminta su sakarwa ƴan aiki girkinsa ba. Rage wutar miyar ta yi ta fito falon fara'arta ta kasa ɓuya. Ƙarfe biyar da mintuna na yammacin ranar Talata, ta kasa tsayuwa iyakar falon ta nufo ƙofa za ta ƙarasa tsakar gidan don ji take kamar zolayar yaran ce kawai amma kuma da kanta ta ƙaryata tunaninta sadda ta yi arba da Amir ya shigo falon ɗauke da babban akwatin kaya na matafiya, kafin ta kai ga cewa wani abu sai ga su Amira da Meenat da ta rataya jakar makaranta mai adon ja da baƙi ƙatuwa. Sallamar Huzaif ya biyo baya, yana riƙe da hannun Auta Zee Mama da kuma na Affan. Fuskarsa gaba ɗaya yanayinsu ɗaya da na mahaifinsa, ba shi da hasken fata, baƙi ne kuma dogo kakkaura. Yana sanye da dogon wandon jeans baƙi da jan tshirt sai farin madubin idanunsa dake ƙara masa ƙarfin gani (medicated). Wani sassanyan murmushi ya ke kashe Mamin tasa da shi kafin ya saki hannayen yaran ya ƙarasa da sassarfa ya ɗan rungumo ta gefensa. "Mamina." Ta runtse idanu hawayen farin ciki suka zubo mata. Sai ta share su, yaran gaba ɗaya suka ji sun burge su matuƙa. Ya saki Mamin ya riƙe hannunta yana ta kallo da murmushinsa wanda har kana iya hango fararen haƙoransa reras. "Sannu da zuwa Huzaifa, barka da sauka. Ashe shiyasa na kasa samunka a waya? To lale marhabin." Ya yi ƴar dariya. Nan da nan Mamin ta sa Amir ɗauko muƙullin ɗakin Yayan nasu, ta saka su Meenat da Amira zuwa gyara. Ta rasa ma me za ta ba shi, Husna tuni ta yi kicin ta kawo mishi ruwan sanyi da lemon roba da kofi a faranti mai ɗan tsawo ta ajiye a gabansa. Shi kuwa mamakin girman yaran yake yi don gani ya yi kamar waɗanda ake jan su da igiya. Sai ya ga ashe hotunansu da yake gani ma rage musu girman suka yi. Ba kamar a fili ba. Nan da nan Mami ta ɗauki waya ta kira su Radeeya ta sanar da su dawowar ƙanin nasu. Babu damar zuwa ga kowaccensu don ba su sanar da mazajensu ba, dole ta wayar suka gaisa da zummar za su iso gidan washegari. Mami kuwa hira ce ta ɓarke tsakaninsu har sai da Husna ta yi mata tuni da tukunyarta da ta ɗan fara kamawa, haka ta tashi shi kuwa ya wuce sashinsa don watsa ruwa. Babu sallah a kansa, mutum ne mai kokarin sauke farillah wannan ya sa tun a Airport ya rama sallar dake kansa. Abba ma sai dawowa gidan ya yi ya ga ɗan nasa, sosai ya yi murna. Mami har kunya ta ji don ita shaf ta mance ma ta sanar da Abban ta waya. Nan da nan aka hau shiryawa Huzaif abinci. Ya je har sashin Anti Zulfa'u sun gaisa duk kuwa da cewa tana cikin ƴar tarbarsa a tsakar gidan da ya shigo. Ranar dai ga shi ga iyayen nasa mafi soyuwa a rai, kusan raba dare suka yi hira, a karshe Abba ya ce ya je ya huta tunda ba yau ɗin ce kaɗai ta rage musu ba. *** Kwanaki uku kenan da tarewar Hajara, sai dai har a sannan tabon da ta bar wa mutan gidan bai gama warkewa ba. Koda dai a ɓangaren Sadiya, ba ta taɓa hasko cewa Anti Hajara za ta aikata mummuna kamar wannan ba. Abin da ya yi mata daɗi a gefe shi ne irin yanda jama'a suka bar zargin Innarta da hana ruwa gudu ba. Damuwarta bai wuce alwashin da Malam ya ci ba na cewar babu wata ɗiyarsa da za ta ɗara sakandire ba tare da ta kasancewar tana ƙarƙashin inuwar aure ba. A cewarsa daga ita har Husna babu mai ɗara karatun sakandire. Haƙiƙa an rusa farin ciki da burinta na zama ƙwararriyar likita a fannin mata. Wannan abu yana nukurkusarta kwarai. Husna kuwa ta yi sanyi sosai kwanakin har kunyar Innarta take ji na irin maganganun da ta yi ta yada mata duk a dalilin Antinta wacce komai ya bayyana ita ce marar gaskiya. Gaba ɗaya ta dawo wata shiru-shiru, hatta da tsiwa ta rage yi ga Sadiya. Dama can wasu abubuwan sun faru ne a dalilin Hajara. Amma don ƙauna tana ƙaunar ƴar uwarta ta, duk da hakan akwai abin da ya riga ya ginu a zuciyarta na cewa Inna ta fi son Sadiya a kanta. Sai ya kasance komai aka yi takan auna shi da rashin kaunarta ne ya sa Inna ta yi mata. *** A ɓangaren Amarya Hajara kuwa, ta watsar da damuwar kowa ban da na mahaifinta da ya yi mata tsaye a ƙoƙon rai tana cin amarcinta. Satinta ɗaya a gidan auren kamar yanda Alh Nuhu ya yi mata alƙawarin ziyartar ɗakin Allah, haka kuwa ta kasance. Nan da nan aka shiga cuku-cukun yi mata passport na tafiya. Ta kira wayar Safiyya ya fi a ƙirga amma don haushinta da take ji ba ta ko ɗaga ba. Hafsatu ce mai sauƙin ciki muddin za ka haɗa Allah da Annabi s.a.w ka roƙe ta abu da niyyar ba za ka ƙara aikatawa ba to nan take zuciyarta za ta yi sanyi. Babu ma kamar da Hajarar ta sanya mata kuka a waya tana faɗin idan ba Hafsatun ba wace ce madadin Mama a gareta, meyasa zs ta hukunta ta kan abin da ya wuce ta ƙi waiwayonta a ɗakin aure. Dole Hafsatu a cikin satin ta je gidan Hajarar ta ziyarce ta. Ita ce ta lallaɓo mata Safiyya suka shirya. Safiyya kuwa ta ce har a ranta ta tuba ba za ta ƙara yi wa Inna wani wulaƙancin ba koda wasa kuwa. Idan da abin da ya ƙara baƙantawa Hajara to fa wannan kalamin ne na Safiyya. Tsanar Inna ya ƙara ginuwa a zuciyarta, ta kuma ci alwashin rusa dukkan farin cikinta, ai ta san yanzun Inna kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha haka ta ke ji saboda duniyar ta mata daɗi tunda asirinta yana waje.   *** Cike da fara'a Malam ya sauke wayar dake a kunnensa yana duban Inna da ita ma ke murmushi don ta fahimci da Amininsa yake wayar kuma ga dukkan alamu baƙi za'a yi a gidan. "Kin ji fa, anjima da yamma yaran Alh Abubakar suna tafe. Me ya kamata a shirya musu ne? Kin san har da baƙon Indiya, Huzaifa. Ya same ni a can babban gida tun wancan satin an gaisa da kowa, ai na faɗamaki kamar?" Inna ta gyaɗa kai tana murmushi. "Ka faɗa min Malam. Nan ne dai bai zo an gaisa ba." Malam ya yi ƴar dariya. "Shi ne ai yanzun zai zo da ƙannensa. Bari na wuce kasuwa da Sadiya sai ki lissafa mata duk abin buƙata ta taho da shi." Inna ta amsa da toh. Kasancewar ranar Asabar ce kuma aka yi sa'a yau ɗin basu da makarantar islamiyya sakamakon rasuwar da aka yi wa mai makarantar. Tana zaune ta kammala gugar kayanta da ta wanke, zuciyarta fara sol take jin ta a yau ɗin adalilin wai yau Baba Habu ne ya shigo har cikin gida ya gaida Innarta, shi ne har da zama a falon Innar, hakan kawai ta san nasara ce, kuma addu'a ba ta faɗi a ƙasa. A sannu-sannu komai zai wuce tunda kusan duka yayyunta sun sassauta wa ransu tsanar da suka yi ga Innarta. "Kin gama? Tashi ki sanya hijabi za ki bi Malam kasuwa, cefane za ki yo muna da baƙi." Nan Inna ta zayyana mata dukkan abin buƙata ita kuwa ta kwafe a ƙaramar wayar Innar wanda kusan rabin amfani ita ke yi da shi. "Inna su waye zasu zo?" Faɗin Husna dake kwance saman katifa tana buga game a wayarta. "Yaran gidan Abbanku ne." Husna ta yamutsa fuska ta yi shiru ba tare da ce uffan ba. Ai su Meenat ɗin ba baƙin gidan ba ne, ita ba ta ga dalilin da yasa duk sadda wani a ahalin Abba idan ya tashi zuwa Malam ke sanya a yi musu hidima babba. Sadiya kuwa suna kammala lissafinsu da Inna ta kai kayanta cikin sif ta ɗauko gogaggen hijabinta ta zura. Jin hon ɗin Malam a waje ya sanya ba shiri ta fice. Malam bai wuce shagonsa ba sai da ya kai ta ƴan kura sabon gari ya tabbatar ta siya komai na buƙata sannan ya ɗora ta a ɗan sahu ya biya a kai ta har ƙofar gida tukunna ya wuce shago. Ba kasafai ya ke zuwa a irin ranakun nan ba, sai idan yana da abu mai muhimmanci da zai yi a kasuwar. *** Sadiya da Inna suka shirya koma, dambun shinkafa da ya ji kayan lambu da hanta wanda aka yanka ƙanana a ciki. Sai ko chicken pepper da aka yi daban. A gefe kuma kunun aya ne mai sanyi da garɗi a baka. Har suka kammala Sadiya ta gyara tsakar gidan tas baƙin ba su iso ba. Ganin haka tana idar da sallar la'asar ta faɗa wanka saboda wani irin gumi da take haɗawa. Koda ta fito ɗakinsu ta shige, lokacin ƙamshin turaren wutar da Inna ta saka ya baɗaɗe tsakar gida tamkar a nan aka saka ba ɗakuna ba. Takaicin wannan bacci na Husna da yammaci ya kama ta. Ba ta da aikin da ya wuce ta gama danna wayarta ta kwanta bacci. Ta sa hannu ta ɗan bubbuga ƙafarta. Husna a ɗan firgice ta buɗe idanunta. "Malama ki tashi kin san dai Inna ta shigo ta ga ki na baccin yamma ba za ki ji ta daɗi ba ko?" Husna ta hau turo baki, kafin ta kai ga cewa wani abu suka tsinci sallamar mutane a tsakar gidan. Suna hango su ta labulen ɗakin mai shara-shara wanda kai na ciki za ka iya ganin na waje, amma na waje ba zai ganka ba idan da haske. Meenat ce kan gaba sai ko su Amir da Amira, Zee Mama, Affan. Kai duka dai yaran gidan Abban ne kamar yanda Malam ya ce idan ka ɗauke su Radeeya dake gidajen aurensu. Inna ce ta tarbe su hannu bibbiyu, ta kai su zuwa falon Malam wanda ya ce anan za'a sauke su idan sun zo. Meenat kuwa kai tsaye ta shigo wajen su Sadiya. Ganin Sadiya na shafa mai ta saki baki galala. "Kar ki ce min sai yanzu ki ke wankan safe?" Harara kaɗan Sadiya ta jefe ta da shi. "Sai aka ce maki ni ke ce ko? To zafi ne ya ishe ni Malama." Meenat ta yi dariya. Tana maida duba ga Husna wacce ba su wani fiye ɗasawa ba, yanzun ka ji kansu tamkar wasu sa'annin juna. "Sannu kaasa uwar bacci, ke dai aikinki kenan." Husna ta ja guntun tsaki. "Oho dai, ai baccin ma lafiya ce wasu su yi ma mana. Aikin ɓurr." "Ku, dallah tare fa muke da Yaya Huzaif, ya dawo daga Indiya." Dukkansu sun san shi, amma a can ɗin ma babu wani sabo tsakaninsu don ba zuwa gidansu yake ba. Su ɗin ma idan sun je lesson, ba kasafai suka fiye haɗuwa da shi ba. Amma duk da haka sun taya Meenat wacce ba ta da hira sai ta sa idan suna tare murna. Ai sai Husna ta miƙe. "Ke bari na gyara fuskata na je na ga Yaya Huzaif." Dariya Meenat ta yi. Ita ko Sadiya juyamusu baya ta yi ta cigaba da shirinta tana murmushin wautar Husna. Doguwar rigarta na shan iska kalar baƙi da ruwan toka ta saka. Irin rigunan nan masu zuwa haɗe da mayafi. Ƙarshen mayafin an yi adon fararen zarurruka mai gashi gashi. Ta saka hula a kanta. Daidai lokacin Inna ta shiga kwala musu kira daga tsakar gida akan su je can a gaisa. Meenat ta mike ta koma cikin ƴan uwanta, Husna kuwa daga bandaki ta fito bayan ta gama wanke fuskarta da sabulunta mai ƙamshi irin wanda Hajara ke kawo mata sadda suna tare. Sadiya ko tuni ta fita zuwa kicin don taya Inna hidima. Faranti babba da aka ɗora kayan ruwa da kofuna ta ɗauka. "Idan kin ke ko Meenat ki kira ta zo ta taimaka maki." Faɗin Inna, Sadiya ta amsa da toh. Ta sani sam ba ta saba da sanya Husna aiki ba, a baya ma ba ta isa ta sanya ta ba hakan ya sa wasu lokutan har mancewa ta ke yi da ita. Sai idan ko Husnar ta ce za ta yi wani abin sannan ta sakar mata. Yanzun ma hakan ce ta kasance, kamar an jefo ta ta shigo kicin ɗin, ba don Sadiya ta kauce ba ƙiris ya rage ta sanya ta yi ɓari. "Inna me za'a kai? Kawo na tafi da shi." Inna ta dube ta. Riga da siket ne a jikinta ƴan kanti, ganin ba su kama jikinta ba kuma ta yane kan da mayafi ya sa ba ta yi magana ba ta nuna mata ƙaton dispenser irin ta zamani mai mariƙi da ake zuba lemu ko ruwan sanyi a ciki, ita ma yana daga cikin siyayyar da Hafsatu ta yi mata da azumi kuma ya samu kulawa sosai don ba ta fiye amfani da shi ba. Da sauri Husna ta ɗauka ta bi bayan Sadiya. Sadiya tun kafin ta kai ga shiga falon Malam ɗin ta soma jin tashin muryoyi, dukkansu ba baƙinta ba ne ba idan ka ɗauke mutum ɗaya da ta jima ba ta sanya a idanunta ba, wato Huzaif. Sallamarta ya sanya su maido hankula gare ta har Malam da ke shan dariyar labarin da Huzaif ke ba su na bambancin al'adarsu da na Indiya, har ma da irin ƙauyancin da wani ɗan Nijeriya ya tafka a can. Ya amsa sallamar tabbas, ya kuma bi hannun da kallo sa'ilin da ƙaton farantin ya riga gangar jikinta bayyana. Ya maida duba ga wayarsa wacce sam bai kula da sadda aka kira shi ba sai missedcall da ya tarar har sau uku kasancewar tana silent. "Ina yini, fatan ka iso lafiya?" Zazzaƙar muryarta ya sanya shi ɗagowa kansa yan dube ta. Kanta yana ƙasa tana kallon ƙafafunsa waɗanda sai ka rantse ba su taɓa taka ƙasa ba don har wani sheƙi ta ga suna yi. Sai a sannan ta ɗago kai ta ɗan dube shi. "Lafiya ƙalau sister..." Sai ya rasa sunan da zai ambata don har ga Allah ya ga ta fita daban da ƴan gidan. Tana da kyau mai haifar wa da mutum faɗuwar gaba, ga wani irin duka da ya ji ƙirjinsa na yi kamar zai fito. Ya kasa kauda kai daga kallonta kamar yanda ya shiga tunanin ko wace ce a ahalin gidan. "Sadiya ce fa Yaya. Ba ka gane ta ba ko?" Cewar Amira wacce ta yi caraf da zancen. Tabbas sai yanzun ya tuno akwai Sadiya a gidan. Ya shafi sumarsa yana murmushi. "Oh, na gane ta yanzu." "Ina wuni." Ya ƙara jin wata gaisuwar daga Husna da ke durkushe ita ma tana kokarin ajiye abin hannunta. Sai lokacin ya dubi kannensa yana murmushi. "To kun ga wannan ko a hanya na gan ta zan san ƙanwata ce. Wannan kuwa idan muka jeru fa za'a yi tsammanin sato ta na yi." Aka yi dariya har Malam idan ka cire Sadiya da ta tsuke baki. Huzaif ya kauda kai yana wani murmushi, ba ya son ya cigaba da kallonta, ba zai ce ga abin da kallon ke haifar masa ba. Amma ko mene ne, ya sa ni ba yau ne zai zama ƙarshensa ba. Ƙila akwai tarin abubuwa da yawa da za su iya biyo wa baya. An ɗan taba hira da Malam kafin ya shige zuwa ɗakinsa, Husna kuwa ji ta yi nan duniya ta samu mijin aure. Wani irin son Huzaif ta ji ya mata dirar mikiya ba tare da ta shirya wa hakan ba. Ita kuwa Sadiya tuni ta fice don kwaso sauran kayan, ganin Husna ba ta da niyyar miƙewa ya sa ta duban Meenat, cikin rashin sa'a kafin ta kai ga duban Meenat din idanunta suka sauka kansa. Wani murmushi ya yi mata da ya jefa ta cikin jin nauyinsa don haka ta fasa kiran Meenat ɗin ta fice daga falon kirjinta na lugude.  *Kazar Kwanci...* "Lafiya?" Tambayar da Inna ta yi wa Sadiya kenan ganin yanda gaba ɗaya jikinta ya yi la'asar kamar wacce ta rasa sukuni. Sadiya ta yi yaƙe gudun kar Inna ta fahimci komai ta ce. "Babu komai Inna." Nan ta soma ɗaukar kulolin abincin guda biyu manya ta yi gaba. Kirjinta sai bugu yake don ta sani ko ba ta kalle shi ba, jikinta ya ba ta cewar idanunsa na yawo a kanta. "Meenat, zo mu taya Sadiya mana." Faɗin Amira kenan tana duban Meenat da ta shiririce a dole sai ta tabbatarwa Yayansu ta fi kowa ƙokari da maida hankali a gidan. Sai a sannan ita ma Husna ta bi bayan su, Sadiya tuni ta yi gaba har da su tuntuɓe tsabar saurin ta fita. Kamar ta cewa Meenat wannan yayan naku ya fiye kallon tsiya amma sai ta yi tunanin ba lallai hakan ya yi mata daɗi ba wannan ya sa ta bar wa ranta. Amma fa ba karamin takura yake mata da kallo ba. Har suka kammala kawo komai suka shiga zubawa Huzaif rabin hankalinsa na ga Sadiya yayinda rabin kuwa ya ke latsa wayarsa. Da uhum da uhm uhm kawai ya ke bin su Affan da Zee Mama don bai taɓa jin hirarsu ta gundure shi ba sai a lokacin. Husna ce ta ajiye mishi komai da aka yi wanda Sadiya ta zuba. Su kuwa matan suka haɗu wuri guda, mazan ma haka. Ya dubi na sa kafin ya ɗan haɗe gira da shagwaɓe murya yana duban Sadiya ya ce. "Wai meyasa ni za'a ware ni daban? Ni fa ba na cin abinci sosai idan ni kaɗai ne." Sadiya ta ɗago kai ta dube shi kaɗan, ganin ita ɗin yake kallo sai ta tsuke baki hakan ya sa shi murmusawa. Sau biyu ta yi hakan, kuma shi a wurinsa kyau sosai take masa. "To Yaya kuma a can ya ka ke yi?" Faɗin Amira kenan. "Ai ba ni ɗaya ba ne. Akwai abokan karatuna da muke ɗaki guda su biyu, tare muke ci." "To na zo mu ci tare?" Husna ta furta ba tare da ta shiryawa hakan ba, ganin kowa ya kalle ta ne ya sanya ta saurin gyara kalamanta. "Oh, ina nufin ku ci tare da su Yaya Amir?" Huzaif ya girgiza kai gami da ɗan murmushi. Bai ƙara kula kowa ba ya yi bismillah ya kai lomar farko na dambun bakinsa. Wani daɗi ya ratsa shi, sai ga shi ya zage sosai ya ci abincin, Sadiya rabin hankalinta na kansa, shi kuwa na sa yana kan abincin da ya ji daɗinsa sosai. Haka nan ma kazar ya ci ba laifi, kunun aya kuwa tana kallo sai da ya tsiyaya kusan sau uku yana kurɓewa. Haka nan ta ke yaba tsarinsa, a nutse yake komai, su ma tuni sun kammala sun miƙe. Ita kaɗan ma ta ci saboda rashin sakewa da Huzaif a wurin. Amma don ta su Amira da Meenat, tsaf suke cin abinci tare duk sadda suka haɗu. "Kai wallahi girkin nan ya yi daɗi sosai. Ni nasan Inna ce ta yi abin ta." Faɗin Meenat tana duban Inna da Malam waɗanda a sannan sun shigo falon. Dariya suka yi, Inna ta amsa. "Rabin girkin dai ƴar uwarki ce ta yi. Abin da na taimaka mata da shi kaɗan ne." "Wai Sadiya?" Ta ƙara tambaya tana fiddo ido waje, Sadiya da ke ƙoƙarin kwashe sharar da ta tattare ta fice ta ɗan dubi Meenat ƙasa-ƙasa tana harararta.  Meenat kuwa dariya ta yi don dama tsokana ce, ita ta san Sadiya ta iya girki sosai, yawanci idan sun je lesson Antinsu Zulfa'u ba ta nan, ita ke musu girki a ɓangaren kuma su kwashi gara don baiwa kam ta girki Allah ya ba ta shi. Sadiya ta fice ɗauke da tsintsiya da makwashin shara a hannu tana jin sadda Amira ke ba Meenat amsa da fadin. "Allah ya shiryeki Meenat, ni dai na san ko iyakar dahuwar indomie ne, ba za ki yi mai daɗin na Sadiya ba. Amma ba wacce ki ka raina sama da ita. Ki yi kamun ƙafa ta koya maki girki Malama." Ta dai ji wannan amma ba ta ji amsar da Meenat ta ba ta ba. Ta fice tana murmushi. Koda ta koma Huzaif ba ya nan, ta dai hango shi ta tagar falon yana tsaye yana waya ya ba su baya. Kauda kai ta yi. Can ba jimawa ya shigo, nan kuma ya ce su shirya zasu wuce. "Ba za ku bari a yi Magriba ba? Kar ta risƙe ku a hanya." Faɗin Malam bayan ya kai duba ga agogon dake maƙale a bangon falon. Huzaif ya amsa da toh, so ya ke ne ya bar gidan, ya kasa tantance me yake ji a kan Sadiya. Ya na ƙaryata wani sashi na zuciyarsa mai tabbatar masa cewa wannan shi ake kira Love At First Sight. Bai yarda ba, bai kuma aminta ba. Yana son ya ɗan ƙauracewa ganinta ko zai samu nutsuwar tunani.   Ana ta hira amma shi kuwa jifa-jifa yake sa musu baki. Sadiya gaba ɗaya ta kasa sukuni duk kuwa da cewa ta ɗago kai fiye da sau biyu amma ba ta ƙara kama shi yana kallonta ba. Ta ɗan samu nutsuwa kaɗan, sai ita ma ta sako fuskarta har ake hirar bikin Amira wanda bai fi sauran sati huɗu ba.   Kiraye-kirayen sallar Magriba ce ta katse musu hirar, matan gaba daya suka shige cikin gida. Amira da ke fashin sallah sai ta yi zamanta tana danna waya, su kuwa kowannensu ya ɗora alwala. Mazan ma daga can suka wuce masallaci. Nan kuma suka yi shirin tafiya, Husna sai rawar kai take yi ta kasa sukuni, babba burinta ta mallaki lambar Huzaif ɗin hakan ya sa koda ake ta sallama bayan an taka musu ta miƙa masa wayarta. Ya kai duba ga wayar kafin ya dube ta da alamar tambaya. "Lambarka za ka saka min Yaya. Zamu dinga gaisawa." Babu musu ya karɓa ya saka lambarsa ya miƙa mata. Sai ya kai duba ga Sadiya dake gefe jikin ƙofa ta ɓuya, kanta kawai da hannun da ta dafe ƙofar ake gani. "Ita ba ta da waya?" Ya tambaya yana duban Sadiya har lokacin, ta ji tambayar amma sai ta kauda kai daga gare su. Husna ta ɗan juya, ganin da Sadiya yake ta ji wani haushi ya turnuƙe ta amma kuma a yau sai ta ji daɗi na rashin mallakar wayar Sadiya. "Tab, ai wannan yanda ka san wata kifin rijiya haka take. Ba ta fiye fita ba sai Inna ta matsa mata sai kuma dole, wayar ma ba za ta riƙe a yi hira da ita ba. Idan a na son gaisawa da ita sai dai ko ta wayar Husnar ko Inna." Meenat ta ba shi amsa. "Ya fiye mata ai, tunda babu ruwanta da haukan da ku ke yi a tiktok." Faɗin Amir. Meenat ta turo baki, sau ɗaya ne ta taɓa kuskuren ɗora wani bidiyonta da ƙawayenta a Tiktok, shikenan abin ya zagaya inda ba ta yi zato ba, sanadin haka har wayarta Abba ya ƙwace, daga baya kuma ya ba ta bayan ya gargaɗe ta sosai. Tun daga wannan lokacin Amir ke kiranta da ƴar tiktok. Shi dai Huzaif murmushi ya yi. "Ku shiga mu tafi, dare na yi. Gaba ɗaya suka shige motar bayan sun yi sallama da su Sadiya karo na biyu, su Malam dama ba su fito ba daga gida. Har zai shige ya juyo ya ƙara duban Sadiya, ido huɗu suka yi wannan karon don ta fito sosai daga bayan ƙofa suna sallama da su Amira da Meenat. Idan dukkansu suka ce ba su ji wani lamari sabo na gewaye su ba da ba su da fassararsa to sun yaudara kansu da gangar jikinsu. Daƙyar ta janye idanunta ta juya ta koma ciki, sai a sannan ya sauke ajiyar zuciya mai karfi ya ya dubi Husna da murmushin ƙarfin hali. "Sai wani jiƙon sister. Mu kwana lafiya." Daga nan ya shiga motar, Amir ya ja suka tafi. Husna jiki a matuƙar sanyaye ta juya ta shige cikin gidan. *** Takan tsinci muryar Husna cikin dariya da kuma hira suna yi, tana jin abu ya yi mata tsaye a ƙoƙon rai, to ko dai ita kaɗai ke jin yanayin da ta ke ciki a kansa? Ko dama yaudarar kanta take yi da har ta fassara kallon da ya dinga bibiyarta da shi da wani abu na daban? Anya akwai hakan shi a ransa? Kwanaki bakwai da zuwansu gidan, amma gaba ɗaya ta rasa abin da ke mata daɗi. Za ta ji Husna na kyakyata dariya idan suna hira, ko kuma ta yi masa saƙon muryarta, amma shi ba ta taɓa ji ko sau ɗaya ya mata nasa ba. Sannan ba ta ji ko sau ɗaya Husna ta ce ya tambayi inda take ba. Hatta da Inna sun gaisa har sau wajen uku ta waya, nan ma ba ta ji ya tambaye ta ba. Sai gaba daya ya ba ta haushi, watakila ita kaɗai ce ta ji bambancin yanayi a kallon, zai yiwuwa ita kaɗai ke muradin ƙara sanya shi a idanunta da ma jin sautin muryarsa. Ganin suna ta shirye-shiryen zana jarrabawarsu ta mock (jarrabawar sharar fage da makarantun kuɗi ke yi kafin fara ssce exams) wanda daga shi babu jimawa za su yi soma Waec ya sanya ta maida hankali ga karatunta gami da watsi da al'amarin da take da tabbacin gaibu ne. Ba zai taɓa faruwa ba. *** A ɓangaren Huzaif kuwa, zuwa lokacin ya gama fahimtar me yake ji game da Sadiya. Ƙaryata kansa da zuciyarsa ya ke yi kawai don a tunaninsa, bayan tsohuwar budurwar da ya yi a Indiya, Ummu-Aimana, ba ya jin akwai gurbin son kowa a zuciyarsa. A lokacin ya yi wa Aimana so mai yawa, sai dai kuma yana ji yana gani aka aura mata wani ɗan uwanta. Allah kaɗai ya san da ya ya mance lamarinta a rai. Tun kuma daga kanta ne ya yi watsi da tarkacen so.   Murmushinta, yanayin yanda take tsuke baki idan abu bai mata daɗi ba, har ma da yanayin kallonta gaba ɗaya sun gewaye nasa tunanin sun hana shi sakat ta yadda ko idanu ya rufe to Sadiya ke mishi gizo a cikinsu. Ba ya so ya shiga rayuwarta kai tsaye gudun kar ya yi mata katsalandan a je ko akwai wanda ta ke so, komai a sannu ya fi. Dalili kenan da ya maida Husna abokiyar hirarsa a waya, ya kula tana da wauta iri-iri da kuma iya ba da labaran da mutum zai dara sosai. Hakan ba ƙaramin kewa ya ɗebe masa na Sadiya ba. Koda wasa bai taɓa tambayarta ina Sadiya ba, ko kiran Husna ya yi babban fatansa bai wuce a samu akasi wayar ta kasance a hannunta ba, amma kuma muryar Husna ce ko yaushe ke karaɗe dodon kunnensa, haka ma idan Inna ya kira. Ya ji dagaske ba zai jure ba, wannan ba irin wacce zai gani ya kauda kai ya haƙura ba ne ko kuma ya yi sanyi. A yadda ya wayi gari daƙyar a wannan ranar na Alhamis, ba ya jin zai jure wucewarsa matuƙar da ransa da lafiya bai sanya Sadiya a ido ba. Don haka ƙarfe uku da mintoci ya yi shirinsa tsaf cikin ƙananan kaya jeans da ruwan madarar tshirt, kamar koyaushe dama tun zuwansa yanayin shigarsa kenan zai wahala ka gan shi da manyan kaya. Turarukansa masu tsada da ƙamshi ya fesa kafin ya fito riƙe da wayoyinsa. Cikin gidansu ya soma shiga kai tsaye ɓangaren Maminsa ya faɗa da sallama. Mami dake zaune suna lissafi ita da Lubna da Radeeya waɗanda dawowarsu kenan daga kasuwa duka kayan an buɗe su ana kuma ƙirgen waɗanda suka yi saura a dangin kayan kicin da ba su siya ba.     "A'a, manya gatan wasa. Wannan wankan kuma sai ina?" Faɗin Lubna fuskarta a sake tana kallon ƙanin nasu. Huzaif da ya maida hankali ga yin cilli da Noor ƴar gidan Radeeya da ba ta fi watanni huɗu a duniya ba, ya zauna yana murmushi gami da shafar sumarsa. Mami da ke bin sa da kallo ita ma murmushin kawai ta yi, da ace ma zancen zai je ai za ta so hakan. Ta san akwai sauran watanni kusan shida da zai ƙara a Indiya kafin ya dawo nan baki ɗaya, amma kuma za ta so ya kasance akwai maganar aure a kansa sai dai ba ta da matsawa yaro, tana cigaba da nema musu zaɓin Allah. "Sis Deeya, ki shiga tsakanina da yayarmu, na faɗamata har yanzu yaron Mami ne amma ta ƙi rabuwa da ni da zancen auren nan." Radeeya ta yi dariya. "Ai shikenan, sai ka yi ta zama haka Huzaif tunda ba ka so mu zo gidanka mu ɗauki ɗanka. Ni na bar ɓata bakina ma, idan ta yi wari ai dole za mu ji." Lubna ta faɗi tana taɓe baki. "Yauwa, za ku ji tabbas idan ta yi warin. Mami." Ya ƙarashe da maida akalar zancen ga Mamin tasu. "Zan ɗan fita, ba nisa zan yi ba." Mami ta gyaɗa kai tana kokarin maida wasu tukwane gidansu. "Allah ya tsare ya maido ka lafiya. Ya haɗa ka da dukkan alkhairai, ya tsare ka dukkan sharri." Wani murmushi ya yi har ka na hango fararen haƙoransa. A duniya yana son Mami ta yi mishi addu'a. Ya amsa da amin yana mai miƙewa. "Af, amma sai dai ka ɗauki motar Abbanku, Malam Bukar ya kai Antinku Zulfa'u unguwa da Honda." Ya ɗan jan ya tsaya. "Ok, muƙulli fa?" "Za ka iya tuƙin garin nan?" Radeeya ta tambaya da alamar gargaɗi a fuskarta. Ya yi dariya daidai sadda Mami ke miƙewa ta shiga ɗaki don ɗauko masa muƙulli ya na amsawa Radeeya zancenta. "Har wannan ƙauyen unguwar taku sai na kai ki." "Huzaif da karambani, ko sadda suka zo gidana ai shi ya tuƙo." Cewar Lubna. Shi dai bai kara tanka musu ba sai kallo, a tunaninsu saboda sauyin da titunan suka samu zai iya rasa nutsuwarsa yayin tuƙi. Yana karɓar muƙullin ya yi musu sallama ya fice. *** Tun daga nesa ta hango kamar mota a gaban gidan nasu.   "Yau kuma wa muka samu?" Ta faɗi tana ƙara duban ƙofar, Zahra'u wacce suke tare ita ma kallon motar ta yi. "Ko dai Amarya ce ta kawo ziyara?" Taɓe baki Sadiya ta ɗan yi. "Anya? Zai wahala ta zo gidan nan. Na ji ma fa Yaya Zakari ya ce wai za ta je Makkah. To ko ita ta..." Sauran maganar ta maƙale a fatar bakinta sa'ilin da ta hango shi ya fito daga motar yana amsa waya bai ko lura da su ba. Ta ji miyan bakinta ya ƙafe. Zahra kuwa ido ta ɗan zaro gami da cewa. "Wow, masha Allah! Ke wannan waye haka? Ko shi ne yayan su Meenat ɗin da kike faɗa ya dawo? Wannan blackbeauty haka?" Ita dai Sadiya ba baka sai kunni, ita kaɗai ta san yanda kirjinta ke faman lugude. Ba ta iya ta amsawa Zahra ba har sai da ta ƙara magana. Da ƴan rawar murya ta amsa mata. "Yes, shi ne." Iyakar abin da ta ce kenan ta sunkuyar da kai da sauri ganin suna dab da ƙarasawa kusa da inda yake tsaye kuma ta tabbata zuwa lokacin ya lura da su. "Ina wuni." Sai da Zahra ta gaida shi sannan ita ma ta gaishe shi. Ya amsa yana kokari ya ga sun haɗa idanu. "Kin san kuwa zuwan domin ki na yi Sadiya. Ina fatan za ki ban aran lokacinki?" Sadiya suka dubi juna da Zahra wacce ke maƙale dariyarta. Kafin ta ce wani abu ta riga ta lokacin da ta sa hannu ta karɓi ledar dake wurin Sadiya. "Bari na shiga na kai wa Inna saƙonta, zan sanar da ita ki na waje." Ido a buɗe Sadiya ke duban Zahra gami da riƙo hijabinta ganin dagaske tafiyar za ta yi. "Ina za ki je? Don Allah jira ni. Ka yi hakuri Yaya Huzaif, ka shigo cikin gidan. Idan Inna ta ji mun tsaya a waje faɗa za ta yi, kuma ma za'a yi tunanin wani abin." Ya haɗe hannayensa a ƙirji yana bin fuskarta da kallo. "To amma kuma ni gurinki na zo. Ki na tunanin idan mun tattauna a cikin gidan babu matsala?" Ta gyaɗa masa kai da saurinta kamar ma a firgice ta ke. Ya yi murmushi. "Ok, mu je." Daga haka suka yi gaba yana biye da su. Sai da ya jira suka shiga suka sanar da Inna zuwansa kafin ta ce Sadiyar ta ce ya ƙaraso. "Haba Huzaifa, gidan nan ai ba baƙonka ba ne. Ka na da ƴancin shigowa kanka tsaye. Bismillah, shigo falon." Huzaif wanda har a sannan murmushi bai ƙaura a saman fuskarsa ba, ya bi umarnin Inna zuwa falon nata. Ita kuwa Sadiya ɗakinsu ta faɗa da saurinta, Husna ba ta gidan ta je gidan Safiyya dubo ta, ba ta jin daɗin jikin. "Ke, wai ko dai akwai wani abu tsakaninku? Ni kam gaskiya kun dace sosai. Don Allah kar ki wulaƙanta shi Sadiya. Na sanki sarai ba kya sakarwa samari fuska. Amma wannan na gida ne kuma ya fita daban ma a halitta da ma yanayi." Faɗin Zahra kenan cike da zumuɗi. Sadiya ta yi shiru tana kallonta, wani irin sanyi take ji a ƙasan ranta ga kuma murmushin da ba ta san ta na yin sa ba. Ko babu komai yau ta ba idanunta abincin da suka jima su na marmari. Ko iyakar ganin aka tsaya ta ji daɗi. "Ah, ƙawata ta harbu. Sai fatan Allah ya sa kar ta zurma da yawa, kai ni ina tunanin ma gaba ɗayanki ki ka dulmiya." Zahra ta ƙarashe da dariya. Sai kunya ta kama Sadiyar ta kuwa shiga maka mata hararar borin kunya. Kiran da Inna ta ƙwala wa Sadiya ya sa dole ta miƙe ta fito har Zahra na dakatar da ita wai ta cire hijabin ta saka mayafi amma ko kallo ba ta ishe ta ba. A tsakar gidan ta ci karo da Inna. Cikin ɗan haɗe rai Inna ke faɗin. "Ku yanzu idan mutum ya zo har sai an ce ku kai masa ruwa?" Kai Sadiya ta girgiza mata gami da ba ta hakuri ta nufi kicin ɗin. Ruwa da lemu mai sanyi na zoɓo wanda Inna ke siyarwa tun sadda ta yi firij su ta haɗo masa. A jug ta tsiyaye zoɓon dake ɗaure a ledoji har guda biyar sannan ta rufe ta ɗora komai saman ƙaton faranti ta nufi falon Inna ƙirjinta na bugu ta shiga ambaton sunayen Allah. Da sallamarta ta shiga ta ajiye ba tare da ta dube shi ba ta tsiyaya mishi ruwan roba a kofi ta miƙa, ya karɓa. Daga haka ta miƙe da zummar bar mishi falon ya yi saurin katse hanzarinta. "Kin ce za ki saurare ni." Dole ta tsaya cak gami da juyowa ta dube shi. Ya ɗan karkata kai cikin alamun roƙo ya ce. "Please." Sai ta tsinci kanta da jin kunya da murmusawa duka lokaci guda. A dole ta koma ta zauna. Sallamar Zahra ce ya hana shi furta komai, suka amsa mata. Ita ma wani babban tray ne ɗauke da flask na abinci. Allah ya taimaka ma shinkafa ce dafaduka da ya ji busasshen kifi Innar ta yi. "Thank you. Mene sunanki ke kam? Ke ma a nan gidan ki ke?" Huzaif ya watsawa Zahra tambaya yana dubanta fuska a sake. Ita ma da fara'arta ta amsa. "A'a, ni makwafciyarsu ce kuma aminiyar Sadiya." Ya jinjina kai. "Na yarda yanzu ke aminiyarta ce, amma kuma nan gaba kaɗan zan ƙwace maki wannan matsayin. Ni zan zama amininta har ƙarshen rayuwarmu. Right?" Yanda ya rufe zancen da tambaya ya na maida akalarta ga Sadiya lokaci guda kuma ya na marairaice muryar ya sa ta ji wani masifaffiyar kunya ta rufe ta. Zahra kuwa dariya kawai ta yi gami da fadin. "To, abin babba ne. Allah ya tabbatar mana da alheri. Zan jira na ga wannan ranar in sha Allahu." "Ina fatan ba a riga ni ba?" Huzaif ya ƙara faɗi ya na duban Zahra a wannan karon. Ta dubi Sadiya wacce duk ta rasa sukuni ta kuma fahimci dagaske dai wannan Huzaif ɗin a na yin sa tunda kunya ta gama rufe ta sai ta ba shi amsa. "Idan magana ta gaskiya zan faɗamaka, Sadiya tana da masoya da yawa. Ka san masu sunanta akwai farin jini masha Allah, amma kuma ina maka albishir da cewa, babu wanda ta ba shi damar zuwa inda ta ke. Mai yiwuwa kai za'a buɗewa ƙofar zuciyar." Ta ƙarashe da ƴar dariya ba ta jira amsarsa ba ta fice ta bar musu falon. Shi kuwa Huzaif sai ya rasa me zai yi don jin daɗin wannan farin albishir ɗin daga bakin wacce ya tabbatar Sadiya ba ta mata rufa-rufa tunda ta kira kanta da sunan Aminiya. Ita ko Sadiya ji ta je kamar ta miƙe ta bar falon, sai wasa ta ke da yatsun hannunta ta kasa kataɓus. "A taimaka a kalle ni ko ya ya ne." A hankali ta saci kallonsa, caraf suka haɗa ido, da sauri ta janye nata ƙwayoyin idanuwan. Ta ji sadda ya sauke ajiyar zuciya. "Ko ban ƙara wani dogon bayani ba Sadiya, na sani kin fahimci manufata a kanki. Daga kallo ɗaya idan aka yi min a gabanki, an san ni Huzaif na gama kamuwa da sonki. Soyayya mai tsafta nake son mu yi wanda zai ƙarfafa zumuntar iyayenmu da mu kanmu. Irin wacce na ke fatan ta kai mu ga aure. Sai dai duka waɗannan fata da burin daga ɓangarena ne, ban sani ba ko ba na cikin tsarinki." Shiru ya ƙara biyo baya, Sadiya jin kalamansa take yi kamar a na mata yayyafin ruwa. Ta kasa magana, ta kuma rasa dalilin shirunsa na tsawon daƙiƙa, kamar yanda ta rasa dalilin da ya hana Innarta shigowa alhalin idan dai ta yi baƙo, bini-bini koda aiki ta ke yi takan shigo su taɓa hira kaɗan. Ba ta yi aune ba sai ganin Huzaif ta yi ya yi wani durƙuso a gabanta, wuya a ɗan karye ya ke leƙa fuskarta. Duk yanda ta so kaucewa kallon fuskar a wannan karon hakan ya faskara, dubansa ta ke yi kamar yanda shi ɗin ma ita ya zubawa idanu yana ji tamkar idan ya rabu da kallonta, wani abin zai faru ga rayuwarsa. "Kin amince da ni Sadiya? Kin san Allah idan har ba ki yi min magana ba yau ba zan iya runtsawa ba. Ba kuma na jin koda na koma Indiya, zan maida hankali kamar a baya na ƙarasa abin da ya yi min saura. Tun ganin farko da na yi maki a zuwana gidan nan, na ji a jikina ba ranar ce za fa zamo mana ƙarshen haɗuwa ba. Jikina ya ba ni cewar akwai alaƙa mai karfi da zai iya giftawa tsakaninmu. Ban taɓa jin yanayin da nake ji a kanki a kan wata ɗiya mace ba, ban ware maki duk ƴanmatan da suka kawo min hari ko kuma waɗanda muka ɗan yi soyayya da su ba a baya. Sadiya dagaske nake, dagaske na zo wajenki. Nan ba gidan da Huzaif zai zo da wasa ba ne. Ina son jin ra'ayinki a kaina." Ta ɗan ciji ƙasan leɓɓanta kafin ta sauke ajiyar zuciya, wannan kusancin ya yi mata yawa, ga ƙamshin turarukansa da suka buɗaɗe ƙofofin hancinta. Ta yi narai-narai da fuska ta na dubansa karo na biyu da yake a gabanta. "Na ji, zan ba ka amsa, amma don Allah ka koma kujerarka." Ya yi wani murmushi kafin ya ce "Ooookay." Ya na mai jan harafin farkon kalmar sannan ya miƙe ya koma inda ya ke. Madadin ya ga ta ce wani abu, sai ya ga akasin haka. Zamowa ta yi ta ja filet ta shiga zuba mishi abinci ta ajiye masa saman madaidaicin teburin da ke a tsakiyar falon kusa da farantin lemu da ruwa. Kallonta kawai yake yi ya ma rasa me zai ce sai ƙirjinsa da ke faman bugu da sauri-sauri. Idanunsa har wani kaɗawa suka ɗan yi, idan Sadiya ba ta karɓi tayin soyayyarsa ba, ya zai yi? Ina zai saka kansa ya ji daɗi? Tana daga tsaye tana wasa da zoben dake cikin ɗaya a yatsanta na hagu ta ce. "Ina fatan Allah ya shiga lamarin, ya yi mana zaɓi mafi alheri." Tana kai wa nan da sauri ta juya ta a murmushi ta fice a falon. Ta bar Huzaif da sakin nannauyar ajiyar zuciya a lokaci guda yana zuba uban murmushin da ya fito tun daga ƙarƙarshin zuciyarsa. "Alhamdulillah." Ya tsinci kansa da furtawa a fili. *Kazar Kwanci...* Gaba ɗaya sai ta tsargu ganin uffan Inna ba ta ce mata ba akan jimawarta tare da Huzaif.  Zahra ma tare da Inna suna hira, sai ta kasa zama a wurinsu ta nufi ɗaki. Duk sai ta ji kamar ma turaren Huzaif ne ke yawo a hijabinta da sauri ta cire ta yi jifa da shi saman katifa. Ganin hakan ma zai ƙara sanya wa Inna ayar tambaya sai kawai ta yi shahada ta fito tsakar gidan. Zahra sai waƙe-waƙen soyayya na tsokanar ƙawarta ta ke yi, ita kuwa ta fakaici idanun Inna ta watsa mata harara. Ita dai Inna Mairama murmushi kawai ta yi ba ta ce uffan ba. Can ba jimawa sai ga Huzaif ya fito. "Ah wai har tafiya? Na yi zaton ma za ka jira Malam ya shigo ku gaisa." Cike da girmamawa ya shafi kansa yana murmushi. "Na fito Innarmu. Abincinki duk sadda na ci sai na yi santi. Allah ya ƙaro zaƙin hannu." Dariya Inna ta yi. Ɗakinta ta shiga bayan ta ce ya jira tana zuwa. Shi kuwa sai ya hau waige ta inda zai ga Sadiya wacce tun fitowarsa ta bar tsakar gidan ta faɗa ɗakinsu. Ya kalli Zahra wacce ke dariya. "Ki ta ya ni yaƙin nan kin ji?" Ta zaro ido. "Har ka soma karaya?" Ya girgiza kai yana murmushi. "Aa, amma ina buƙatar wannan taimakon." "Zan maka iyakar ƙoƙarina kuwa." Kafin ya ba ta amsa Inna ta fito hannunta riƙe da leda ta miƙa masa. "Ga wannan ka kai wa yaran gidan. An gode sosai da ziyara." Ya karɓa cikin ladabi ya ƙara godiya shi ma sannan ya fice bayan ya amsa sallamar da Zahra ke mishi. Ranar ko daga yanayin annashuwarsa za ka gane ba ƙaramin farin ciki ya ke ciki ba. Koda ya ƙarasa gida, Allah ya taimake shi ya ci karo da yaran a farfajiyar gidan suna wasa da kekunansu. Kai tsaye ya miƙa musu ledar. "Ga tsaraba daga Inna Mairama." Zee Mama ce ta karɓe nan suka sauka saman keke aka shiga buɗe ledar da Inna ta cika da kayan ƙwalam. *** "Na fahimci yaron nan ke ya ke son magana da ita ta waya, idan har saboda ni ki ke kasa amsa wayarsa, to ki sani, ba zan hana ki kula shi ba. Amma kuma kar ki zurfafa soyayya Sadiya. Ba komai muke so ya ke zame mana alkhairi ba. Ki yawaita addu'ar nema maku zaɓin Allah. Idan ku ɗin rabon juna ne, komai zai zo muku da sauƙi. Addu'a koyaushe ina maki ita, ke ma kar ki fasa yi." Inna na kai wa nan ta fice a ɗakin ta bar Sadiya riƙe da wayarta wacce har ta gaji da ƙara ta yanke. A sanyaye kuma cike da jin nauyi ta kai duba ga wayar karo na biyu sa'ilin da Huzaif ya ƙara danno kira karo na biyu. Ɗagawa ta yi ta amsa da sallama. Ta ji sadda ya sauke ajiyar kafin ya amsa mata. "Sai yaushe ne? Zuwa yaushe za ki saurare ni ma ji muryarki ki bar wahalar da zuciyata? Sati ɗaya ya rage min a garin nan zan tattara na koma bakin karatuna. Anya kuwa zan jure rashin waya a hannunki? Zan iya jure rashin ƙwakkwarar magana tsakaninmu?" Ta ɗan runtse idanu kaɗan, sati ɗayan da ya ce ya yi mishi saura a ƙasar Nijeriya, sai ta ji kamar kwana ɗaya yake nufi. "Ka yi haƙuri. Ina jin nauyin karɓar wayar Inna shiyasa. Amma komai ya wuce." "Shiyasa zan zo mu yi magana mai muhimmanci, dalili kenan da nake son mallaka maki waya har ma da kaina kafin na bar garin nan. Ma'ana, na kai zancenmu gaban iyayenmu. Idan sun san cewa muna son junanmu, komai zai zo mana da sauƙi." Idanu ta ɗan fiddo kamar ya na ganinta. "Bai yi wuri ba Yaya Huzaif? Don Allah ba yanzu ba, ka jira zuwa wani lokacin. Ba na son su Abba su san komai yanzu. Idan dai waya ce, Allah kuwa zan dinga amsa maka. Ka ji?" Ta ji sadda ya ɗan yi shiru kafin ya ce. "Zan iya zuwa gobe mu yi magana? Wajenki zan zo, ko gidan ba zan shigo ba." Ta na wasa da gefen ɗankwalin atamfarta da ya biyo ta wuyanta tana murmushi ta gyaɗa kai tamkar tana kallonsa gami da faɗin "Uhm." Ita ma ta yi kewarsa, kwanaki uku da zuwansa gidan, da ma kafa gwamnatin soyayyarsa a zuciyarta, amma ta na ji kamar sun fi watanni suna tare da juna. Musamman ma da ya kasance yau ɗin ne suka ji muryoyin junansu karo na farko a waya. Duk irin kiran da zai yi ba ta yarda ta ɗaga sai dai ta miƙawa Inna. Shi kuma yana jin nauyin ya ce da Innar ta ba ta. Dole sai ɓige da gaishe gaishe. Sai yau ta ƙara yarda da zancen Zahra da ta ce Inna fa ta san son juna suke yi don ta fesa mata tun ma ranar da Huzaif din ya zo gidan. Dalili kenan da ya sa ta kasa ce mata komai kan maganar. "Magana za ki yi." "Na yi ai. Na ce ka na iya zuwa. Amma zan je boko, idan na dawo muna zuwa islamiyya ba ma tashi sai ƙarfe shida na yamma." "Ok, kenan na shigo bayan Magrib?" "In sha Allah." "Nagode." Bai ja ta da hira ba suka yi sallama. Sai a lokacin ta kula da Husna da ta shigo ta yi mata tsaye a bakin ƙofar ɗaki. Tun soma wayar kusan tana ji, amma ta kasa gane da waye Sadiya ke waya. Gaba ɗaya ta sha jinin jikinta. Fargabarta ya ƙaru da ta yi tunanin ko dai da Huzaif ne? "Ke kuma da wa ki ke waya?" Ta tsinci harshenta da furtawa tana bin Sadiya da ke faman doka murmushi da kallo. "Ina ruwanki?" Shi ne amsar da ta ba ta kafin ta fice ta bar ta da bin bayanta da kallo. Gaba ɗaya jikin Husna ya yi mugun sanyi. Ta ji ba za ta iya sukuni idan ba ta ga wanda Sadiya suke wayar ba hakan ya sa ta bi bayan Sadiya wacce ta shiga ƙuryar ɗakin Inna ta ajiye mata wayar a saman dirowar gefen gado. Har karo suka kusan yi yayin da Sadiya ta zo fitowa, ba ta kawo ma ga abin da zai kai Husnar ɗakin ba ta fice ta bar ta. Da rawar jiki ta ɗauki wayar ta buɗe logs. Sunan 'Huzaifa' kamar yanda Inna ta yi saving ya fito ƙarara a saman screen. Ta kasa gasƙatawa har sai da ta buɗo lambar sosai ta karanta. Yanda ta haddace lambar Huzaif din ya sa ta tabbatar shi ɗin ne ba waninsa ba. Ba ta san sadda ta sulale ta zaune gefen gadon ba gami da ajiye wayar jiki a saluɓe. Hawaye masu zafi suka kwaranyo mata. Ashe Inna da Sadiya yaƙin da suke yi kenan? Dama raba ta aka yi da Huzaif ta bayan fage? Shikenan ta rasa farin cikinta? Mutumin da tun sadda ta ɗora idanu a kansa take mutuwar ƙaunarsa? Wani ƙunci da raɗaɗi suka yi wa duniyarta dabaibaiyi, ta rasa ina za ta tsoma rayuwarta ta ji daɗi. Kawai sai ta share hawayenta saboda ta rasa mafita ban da haƙura da Huzaif ɗin. Me za ta iya bayan son maso wani ta ke yi wanda hausawa ke kira da ƙoshin wahala. Ranar Sadiya ta yi kwanan farin ciki da walwala a gefe guda Husna ta kwana cike da damuwa mai ɗumbin yawa. A yau ta ji wata irin kewar Antinta Hajara a rai, duk da dama ba gaba ɗaya ta watsar da ita ba, takan amsa maganarta jifa-jifa a whatsapp. Ba su shirya sosai ba sai da buƙatar kuɗi ya taso mata za su haɗa wata fita a ɓoye da kawayenta daga makaranta, a nan ne ta tuna da Hajarar, lokacin ko sati biyu ba ta cika a gidan aurenta ba. Hajara har dariya ta yi har da cewa ita ta san koda kowa zai yi fushin duniya da ita, to fa babu Husnar a ciki. Har ce mata ta yi ta zo gidanta amma ta yi fuska don ba ta gama hucewa da ita ba. Sai dai a halin da ta shiga na yau babu wacce ta ke kewa sama da ita. Abin da kwakwalwarta ke ba ta game da lamarin Sadiya da Huzaif bai wuce cewa haɗin bakin Innar da Sadiya ba ne. Watakila ma yabawa da hankalinsa Inna ta yi hakan ya sa ta jona shi da ɗiyar da ta fi ƙauna a yaranta. Cikin bacci Sadiya ta ji sheshsheƙar kukan Husna, zumbur ta miƙe tana salati gami da ɗan mirgino da ita. Husna ta share fuskarta ganin Sadiya ta yi amfani da wayar Inna da ke hannunta ta haska mata fuska. "Innalillahi... Husna, lafiya? Mene ne ya same ki?" Sai ta ɗauki tambayar a matsayin na rainin wayo tunda ai ido ba mudu ba ya san kima, ko makaho ya laluba zai gane tana son Huzaifa amma tsabar mugunta irin nasu sun rufe ido sun kasa ganewa daga yanda take ta zancensa da ma yawan hira da take yi da shi ta waya. "Ki rabu da ni, kaina ke ciwo. Amma na sha magani." Sadiya ta numfasa, ta sani a irin sangartar da Anti Hajara ta yi wa Husna, hatta idan tana ciwo takan ɓata dare wurin lallaminta koda ciwon bai taka kara ya karya ba ita kuwa ta yi ta shagwaɓe mata. "Sannu, Allah ya sa kaffara. Ki daina kukan, ba zai ƙara maki komai ba face zafin ciwo. Ki yi addu'a ki kwanta." Haka kawai Sadiya ta ce mata sai ta juya ta gyara kwanciyarta bayan ta kashe fitilar wayar Inna, dama mafi yawan lokuta a wajenta take kwana, musamman yau ɗin kuma da suka ɗau lokaci a daren su na waya da Huzaif wanda silar hakan ne ya sa hankalin Husna ƙara tashi, ta kasa jurewa a daren sai da ta yi kukan ta samu sassauci. Dakyar bacci ɓarawo ya sace Husna a wannan daren. A ranta ta zagi Sadiya ya fi sau cikin carbi, har da su Allah ya isa akan ta raba ta da abin da ta ke so. *** Washegarin ranar da safe Inna ta kasa haƙuri musamman jin cewa Huzaif zai zo hira wajen Sadiya, ta ga dacewar ta sanar da Malam gudun abin da zai je ya zo. Dalili kenan da bayan Malam ɗin ya kammala karin safe ta sanar da shi batun zuwan Huzaif wajen Sadiya a ranar. Malam cike da rashin fahimtar inda zancen ya dosa ya ce. "Ban fahimta ba Mairama, wajen Sadiya? Son ta yake yi?" Inna ta yi murmushi. "Ni ma ban sani ba Malam. Amma ina tunanin haka." Ai sai ya faɗaɗa fara'arsa. "Kai Alhamdulillah. Idan kuwa hakan ya tabbata zan fi kowa farin ciki. Kin san kuwa Alh Abubakar da kansa sai da muka yi zancen nan kwanaki? Ya ce ba don yaran zamani da ba a yi musu dole ba, ai da ya nemawa Huzaifa auren ɗaya a cikin ƴanmatan nan. Muka yi dariya, har na ce to ko hakan za'a yi. Ya girgiza min kai ya ce ba zai so a aikata hakan ba, zai zama kamar dole muke son yi wa yara, mu bari dai Allah ya yi ikonsa. Idan da rabo sai mu ga ya kasance. Ashe kin ga rabon kan Sadiya zai faɗa." Inna da har lokacin murmushi ta ke yi ta jinjina kai. "Ai shikenan, Allah ya tabbatar da alheri." Malam ya amsa da amin bar yana cewa shi zai fara yi wa Amininsa albishir. Misalin ƙarfe takwas sai ga wayar Huzaif, Sadiya na ɗagawa ya ce mata ya zo yana ƙofar gidan. Husna na kallonta ta hau shiri cikin doguwar rigar abayarta baƙa mai adon ruwan madara a tsakiya. Ta zagaye fuskarta da mayafin abayar, hoda kawai ta shafa da man leɓe. Ta yi tsai tana kallon yayarta, ta sani dole ne dama Huzaif ya zaɓi Sadiya sama da ita. Ta saka a ranta hakan ya faru ne saboda kyawun da Sadiya ta fi ta. Ita kanta ta ga kyan balle kuma a kai ga maza masu cikakken lafiya waɗanda don su aka halicci matan. Ta kauda kai tana ji zuciyarta na tururi. Kamshin humrar da Sadiya ta shafa ya buɗaɗe ƙofofin hancin Husna, kawai sai ta maida kai ga wayarta tana cigaba da dannawa amma fa idanunta cike suke taf da ruwan ƙwalla don ko ganin abin da ke saman screen ɗin ba ta yi. Sadiya ta dube ta, kamar ta yi magana saboda ta kula da yadda Husnar ke faman basar da ita tun wayewar gari tana cin magani. Ba ma ga ita kaɗai ba har ga Inna. Babu dai wanda ya ce mata uffan. Ta ɗauka Husna za ta ce wani abu ko kuma ta tambayi wajen wanda za ta fita amma ganin ba ta ce uffan ba ta basar sai ita ɗin ma ta ɗauke kai ta zura takalmi ta fice. A wannan daren Huzaif da Sadiya suka ƙara ƙulla soyayyarsu mai tsafta. Har Malam ya gan su ya kuma ce daga ranar ko Huzaif din ya zo su dinga shiga falonsa wanda anan ya ke saukar baƙi. A cewarsa shi ɗin ba baƙo ba ne. Har addu'a ya yi musu kan Allah ya tabbatar da alkhairi. Babu abin da ya ruɗa Sadiya irin da ta ji Malam din ya ce zai samu Abba su yi magana. Ta kasa ɓoye tsoronta har sai da Huzaif ya lura, sai ta ba shi dariya ma. "Kina tsoron me? Har yanzu ki na kokwanto a kan son da nake maki ko kuwa wanda ki ke min?" Tambayar da ya watso mata kenan, ta girgiza kai kamar ta yi kuka ta ce. "Ya yi wuri fa. Likita nake son zama." Dariya ta ba shi sosai. Aikuwa ya hau darawa har sai da ta ɗan yi turus don a ganinta ba ta abin dariya ba, iyakar gaskiyarta ta faɗa masa. Girgiza kai ta yi. "Yaya Huzaif ko Waec ban yi ba." "Yaya Sadiya ko kammala karatuna ban yi ba. Ki na zaton Abba da Malam za su ɗauke ki su ba ni? Kin fi ni gata ga a wajensu." Yanayin kwaikwayon muryarta da ya yi sai ya ba ta dariya. Gaba ɗaya suka dara a tare. "Ki saka ranki a inuwa please, babu wanda zai min wannan gatan na aura maki Huzaif a yanzu a shiga haƙƙinki. Kin ji ko?" Murmushi kawai ta ke ba tare da ta ce uffan ba don sai daga baya ne ma ta ji kunya. "Oya mu yi magana, karatun likita kike son yi?" An sosa mata inda ke ƙaiƙaiyi. "Eh." Ya jinjina kai. "Field ɗaya muke da ke. Ni ma da zarar na koma zan haɗa degree ɗina na MBBS. Zan tattara na dawo gida in sha Allah. Nan da watanni ƙalilan." Ta murmusa. A nan ya gane inda aka fi samun bakin Sadiya, a hirar da ya shafi karatu. Sosai ta zage ta na ba sa labarin karatu da yanda ta ke burin zama likitar mata. Shi kuwa ya maida hankali ya ba ta nutsuwarsa gaba ɗaya yana ƙaremata kallo yana murmushi. Har a ƙarshe ta ji kunya ta yi shiru. Ta ji sadda ya sauke ajiyar zuciya. "Ina ƙaunarki sosai, zan yi kewarki idan na tafi." Ta kasa amsa mishi sai ta ji duk babu daɗi, ita kanta ya shiga ranta ta yanda ta ke jin za ta yi kewar tasa har fiye da yanda zai yi nata. Sun jima tare kamar kar su rabu. Haka ta shiga gida ranta fari ƙal tamkar an mata albishir da sauke farali. *** ©Rufaida Umar *Kazar Kwanci...* Mamin Huzaif ta yi mamaki ƙwarai hakanan ta yi farin ciki marar misaltuwa jin cewa Huzaif na son Sadiya. Ita tun daga yanayin haƙuri na Inna da ma abubuwan da ta ganewa idanunta sun faru lokacin bikin Hajara, ta ji har a ranta tana kwaɗayin haɗa zuri'a da mai halin haƙuri da kauda kai irin nata. Ta jima tana jinjina lamarin da ya faru a gidan don ta sani da ace a kanta ya faru to ba lallai ta cigaba da rayuwa a gidan ba. Hatta Hajara ta sha faɗa sosai don har fushi ta yi da ita daga baya kuma ta sauko ganin yadda ta dinga nacin kiran waya da ban haƙuri. "Kin yi shiru Mamin yara, ba ki ce komai ba." Maganar Abba cikin fara'a ya katse mata tunani. Shi kansa a jiya da yake jin zancen daga Malam, kuma ya ƙara samun tabbaci a bakin Huzaif ɗin, ba ƙaramin farin ciki ya shiga ba. Allah ya sani amintarsu da Malam ta kai inda wani ma ba ya tunani, don haka ba ya shakkar haɗa zuri'a da shi. Ya ɗauki abin da Hajara ta yi matsayin kuskure da ruɗin shaiɗan. Kamar yanda shi ne ya duba roƙon Hajarar ya yi tattaki har wurin Malam a babban gida aka hadu da manya aka naushe shi, aka kuma nemi ya yafe mata ya cire takunkumin hana ta zuwa gidansa. "Allah ya tabbatar da alheri. Abin ya yi min daɗi ƙwarai." Abba ya sauke ajiyar zuciya gami da hamdala a fili. Ya amsa da amin. Su Radeeya da Lubna koda suka ji su kansu sun yi murna da kuma fatan alkhairi. A cewarsu Sadiya yarinyar kirki ce ga uwa uba tana da nutsuwa. Huzaif ya rasa ina zai saka ransa don farin ciki. *** Amarya Hajara koda ta sauka a Nijeriya bayan dawowarsu daga Umarah, gidan Safiyya ta fara yi wa tsinke. Safiyya hangame baki ta yi kawai tana kallon yanda kuɗi suka zauna a jikin ƙanwarta. Ta ƙara ƙiba, fatarta kuwa sai ƙyalli ta ke yi. Ga haƙorin Makkah da ta sanya. "Wai ni wannan kallon na mene ne?" Faɗin Hajara tana dariya. Safiyya sai lokacin ta sauke ajiyar zuciya gami da murmushi. "Ai dole na kalle ki Autar Mama, kin ga yanda ki ka zama ne? Ni dai don Allah kar ki bari ƙibar taki ta fi haka. Masha Allah dai kin yi kyau kowa ya ganki ya san kina cikin jin dadi." Ta yi wani fari da idanu. "Ki ce idan na je gidanmu zan firgita Mairamu. Za ta ƙara fahimtar cewa na samu mijin kerewa sa'a da har abada Sadiya ba za ta samu irinsa ba. Momina kuwa miji sai wanda ta zaɓa." "Mamaki kike ban Autar Mama, koda dai bai kamata na yi mamaki ba, a baya ni ma rashin fahimta ya sa na yi wa Inna..." Wata dariyar da Hajara ta kwashe da ita ta yi sanadin katsewa Safiyya magana, Hajara ta ɗan yi tafi cikin dariya ta ce. "Yau Anti Safiyya ke da bakinki ki ke kiran Mairamu da sunan Inna? Ah lallai Mairamu sai ta ƙara wa Bokanta kuɗi, ku dai na san ta gama da ku, ni kuwa ba na jin za ta yi nasara a kaina domin kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, kuma ni Hajara ba duk kai ba, na fi ƙarfinta." Safiyya ta fusata sosai. "To aikuwa kin yi baƙar asara, tunda dai ke babu wani sauran abu a duniyarnan da zai sa zuciyarki ta yi laushi akan matarnan, sai dai nace maki Allah ya ganar da ke. A bayan ma da na dinga biye maki muna cutar da ita, rigakafi ne kafin ta cutar da mu irin na matan uba, mu nuna mata da wayonmu. Sai ko kishin da muke yi ta aure mijin Mamarmu. Sai dai kuma daga baya na gane tsantsar wautarmu. Koda dai an ce aure ma kaɗai kan koyar da ɗan adam darussan rayuwa, wayasani ma ko shi ne dalilin da ƙannen Mujahid suke takuramin a gidan nan. Kuma wayasani dalilin kenan da har yanzu ban samu ciki ba." Safiyya ta ƙarasa zancen cike da raunin zuciyar da har ya yi sanadin ciccikowar hawayenta. Wannan duk bai taɓa zuciyar Hajara ba sai ma haushi da ta bata. "To ke  ki ka ga za ki iya ɗora wa kanki wahala. Aure idan babu daɗi dole ne zama a cikinsa? Lallai ma Safiyya. Allah ba don Mujahid yana da kambun susa ba da sai na ce ki kashe auren kawai. Ke ki kashe ma cikin abokan Mijina ba sai ki samu wanda ya fi shi ba. Kuma kar ki kara haɗa ƙaddararki da alhakin waccan matar, wane haƙƙinta aka ɗauka? Dama gida ai na ubanmu ne ina ce? Toh mene ne laifinmu don mun nuna ba ma ra'ayinta? Wallahi uban kuturu ya yi kaɗan ace wai wani haƙƙin Mairamu ne ya shafe ki. Kuma kannen Mujahid su Munawwara ko? To zan shiga gidan nasu yanzu na ci ubansu sai na wuce. Ga tsarabarki nan." Hajara na kai wa nan ta shiga tattare komatsanta za ta fice. Hankalin Safiyya ya tashi ba don komai ba sai ji da ta yi wai za ta shiga gidan surukanta wanda yake a bayan layinsu. Nan da nan ta riƙe hannunta tana zaro mata ido. "Ke bana son hauka, dangin mijinki ko nawa? Wallahi ban ba ki iznin shiga ba, ki ka matsa sai kin shiga yanzu zan kira Malam na faɗamasa. Ki rufa min asiri kar ki kashe min aure." Hajara jin za ta faɗawa Malam ya sa kawai ta yi ƙwafa. Wannan ne kawai zai hana ta zuwa, ta samu daƙyar Abba ya sulhunta su da Malam ɗin, ana kukan targaɗe ga karaya kenan. Sai ta fasa niyyarta. Ta ja guntun tsaki "Na ji, babu inda zan je. Na fasa. Amma tafiya zan yi, gidan Anti Hafsatu zan wuce daga can zan je gidanmu." Tana kallon yanda Safiyya ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, ita Hajara ma sai mamakin wannan tsoron na Safiyya ya kama ta. Tab, ita wa ya isa ya sanya ta tsoraci wasu dangin miji? Ai ko miji ya  yi kaɗan ya taka ta balle wata kishiya ko dangin miji. "Ke, ni ban ma yi maki zancen Sadiya ba. Huzaif ɗan gidan Mami ne ke son ta, batun da nake maki sati mai zuwa zai turo magabata a tsaida magana." Ta ji zancen kamar an ƙwala mata guduma a tsakar kai. Sadiya? Aure da wuri? Tsabar baƙin cikin da ta shiga da ruɗu ta ma mance su waye waɗanda Safiyyar ta lissafo. Don haka daƙyar ta motsa leɓɓanta da suka yi nauyi ta ce. "Wane Huzaif? Wace Mami kuma?" Ita kuwa Safiyya wacce ta ji haushin kanta da yin suɓul da bakan sanar da Hajara wannan batu alhali ta san ba daɗinsa za ta ji ba, ta ji inama ba ta ce mata uffan ba. Daƙyar ta amsa tunda zai ai magana zarar bunu ce, idan ta fito ba ta komawa ciki. Sabon da suka yi irin wanda idan ɗaya ya ji magana a dangi sai ya fesawa ɗaya, ya mantar da ita komai. "Huzaif ɗan Haj Mariya ɗan gidan Abba fa, mai karatu a ƙasar Indiya." Sai a lokacin ta tuno waye hakan. Wata uwar ashariya ta lailayo har da fiddo idanu waje. "Wai dagaske ki ke wannan maganar? Huzaif fa?" "Toh meye?" Safiyya ta nemi sani. Girgiza kai Hajara ta shiga yi ranta a matuƙar fusace. "Aa, na rantse Sadiya ba za ta auru yanzu ba. Har abada Sadiya ba za ta yi auren ba, baƙin cikin da Uwarta ta ɗanɗana min, na rantse ita ma sai ta ɗanɗana shi akan Sadiya. Mu zuba ni da su." Tana kai wa nan ta yi gaba ba ta ko saurari salatin da Safiyya ta saka ba da kwala mata kiran da ta ke. Safiyya ta girgiza kai. Ta sani babu abinda Hajarar za ta iya tunda dai kowa da kalar ƙaddararsa a rayuwa. In sha Allahu rayuwar Sadiya zai inganta ba dai ta tagayyar ba. Ita yanzun suna ɗasawa da Sadiya don ma ta kula yarinyar ba ta gama mance abin da ya wuce ba, ba kasafai ta ke zuwa gidanta ba sam. Hajara kuwa da ta fito da zummar ziyartar har can gidansu ko don ta ga Husna da Malam, sai ta ji kamar ta fasa, gidan Anti Hafsatun ma a tsaitsaye ta shiga ta ba ta tsarabar da ta yi mata da yaranta sannan ta wuce. Haka ta daure ta nufi gidan nasu, har wani ƙwalla ta ji sun cicciko mata na jin wani zazzafan ɗaci a kirjinta, hasko Sadiya kawai ta ke yi cikin jirgi ta lula Indiya. Wato kenan ma su haɗa kafaɗa da kafaɗa a auren mai arziki? Aikuwa ta ci alwashin hakan ba zai taɓa samuwa ba. *** Sadiya na zaune tana tilawar Alkur'ani inda za ta kai hadda a gobe Asabar, kokarinta ta ga ya zauna a kanta yanda ya kamata. Inna ta fita zuwa wurin Kawunta Jibo. Husna kuwa na ɗaki tana baccin yamma wanda ya riga ya zamar mata jiki. Tashin duniya Sadiya ta yi mata amma tana ji ta yi banza da ita. Ita kuwa ganin rashin kunyar Husna gare ta ya dawo har ya ninka na baya sai abin ke ɗaure mata kai, ƙarshe ma ta tattara ta watsar da ita a gefe. Ta ƙara takatsantsan da duk abin da zai sa ta yi mata rashin kunya, waya ce dama wani lokacin idan ta Inna ba ta kusa Huzaif ke kira a na Husnar, daga baya ma sai ta ƙi sanar da Sadiya ya kira sai ko idan ya neme ta ta wayar Inna take sanin ya kira Husna amma ta ce mishi ba ta gida. Yanzu kuwa ta mallaki nata wayar, sabuwa dal a kwali Huzaif ya kawo mata ƙirar Samsung. Ko ɗaukar wayar Husna ba ta yi ba ballantana ta gwada murnarta. Jikin Sadiya yana sanyi sosai da lamarin ƙanwarta, Inna ta ce ta yi shiru kawai ta zuba mata idanu. Sallamar Hajara da ta yi a can ƙasan maƙoshi, ya dakatar da ita daga ɗora karatun da za ta yi bayan ta kai aya. Sai da ta ji ƙirjinta ya buga ta shiga ambaton Allah. A duniya ba ta san sadda za ta bar shakkar Hajara ba gaba ɗaya, duk sadda ta ji murya ko ta ga ta shigo wuri, to fa irin wannan faɗuwar gaban sai ya same ta. Tana gaba, wasu yara su biyu na biye da ita dauke da wasu manyan ledoji masu rubutun larabci a jiki. Hajara kuwa sai idanunta ya gane mata Sadiya kamar wani mugun kyau ma ta ke ƙarawa, tana cikin hijabinta ruwan ƙasa take zaune, wato idan har Sadiya ta faɗa gidan jin daɗi ai sai ta ce Hajara kauce ba ki iya gayu ba, don ta sani komai zai fi karɓarta fiye da ita, idanuwanta suka kai ga wayar dake gefen Sadiyar mai ɗaukar ido sosai. Ba ta ko amsa gaisuwar da Sadiya ke mata ba ta ja tsaki na zallar takaici ta wuce zuwa ɗakin da ya ke nasu a baya. Husna wacce ke bacci ta hau miƙa jin ana ta tashinta, muryar Antinta ta soma ji kamar a cikin mafarki, can ta wartsake ta gan ta zaune a gefenta. Nan ta kurma wani ihun murna suka rungume juna suna dariya. Sadiya daga tsakar gidan tana jin su, zuciyarta sai ta yi wani iri. Ita da ƴar uwarta, amma babu damar ta nuna kowane irin murna da ganinta. Ta ji karatun ma ya daina shiga don haka ta miƙe bayan ta yi addu'a ta kai Alkur'anin ɗakin Inna, ba ta ko shiga ɗakinsu ba ta dauki wayarta sannan ta zura silifas ɗinta ta fita zuwa gidan su Zahra. Ta sani Inna ba za ta ce mata don me ba idan har ta ji saboda zuwan Hajara ne. Husna kuwa ai sai ta nemi bacci ta rasa, fita ta yi da sauri ta wanko fuskarta da baki ta dawo. "Antina na yi kewarki sosai wallahi." Ta faɗi a shagwaɓe kamar wacce ke gaban mahaifiyarta. Hajara wacce ganin Husnar ya ɗan lafar da ɓacin ran dake cin ta dangane da Sadiya sai ta yi dariya. "Ni ma ai haka Momin Anti. Ga tsarabarki dai ko fara gani." Hajara ta ƙarashe tana janyo ɗaya daga cikin manyan ledojin nan ta ɗora saman cinyar Husna. Bakinta kuwa gaba ɗaya ya ƙi rufuwa. Ta zazzage duka a saman gado, dogayen riguna ta gani har kala uku tsula-tsula. Abaya guda biyu, ɗaya kalar ruwan madara sai ko baƙa. Ɗayar kuwa doguwar riga ce mai mayafinta. Sai turaruka har kala uku da kuma wani tsalelan agogo a gidansa. Husna ta rasa ina za ta saka kanta don farin ciki, yanda ta ke ta faman tsalle da murna ya sa Hajara ta dinga dariya. Haka ta dinga gwajin kayan nan, kuma aka ci sa'a dayake ta san tsayinta, duk wanda Husna ta saka daidai ita cif. "Inye, kin ganki kuwa, kamar matar wani Alhajin." Faɗin haka da Hajara ta yi ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙaiyi. Sai kawai ta dawo ta zauna jikinta babu kwari tana ɗan yamutse fuska. Nan da nan idanunta suka cicciko da ruwan ƙwalla. Sai ta kasa cewa komai ma. Hankali tashe Hajara ta ɗan tura kafaɗarta ta yi baya suka dubi juna. "Ke lafiya? Ni sai yanzu ma da na ƙaremaki kallo na lura kin rame. Momi me suke maki?" Sai ta ƙarasa fashewa da kukan gaba ɗaya tana ɗora kanta saman cinyar Hajara. Ita ma Hajara da ba ta kai ga jin meke faruwa ba sai ta ji ƙwalla sun cicciko mata. Ɓacin ran Sadiya za ta auri miji ɗan gidan manya da kuma na Husnarta da ke cikin damuwa duka suka turniƙe zuciyarta, wani irin ƙauna take yi ga Husna har zuciyarta. Takan ji kamar Mahaifiyarsu ɗaya. Koda za ta cutar da zuri'ar Inna a duniya, alƙawarina ta ɗaukarwa kanta, har abada Husna ta kuɓuta daga wannan cutarwar. Ba ta katse ta ba saboda ba ta san tun sadda ta ke riƙe da shi ba. Sai da Husna ta yi mai isarta sannan kowaccensu ta share fuskarta, ruwan da ta shigo da shi na roba ɗauke a hannunta ta ɗauka a gefen gadon ta miƙa mata. "Karɓi ki sha." Ba musu Husna ta kwankwaɗa kafin ta kwantar da hankali ta hau labartawa Hajara yadda ta kamu da son Huzaif tun farkon ganin da ta yi masa har ma da shigar saurin da Inna ta yi har sai da ta haɗa Sadiya soyayya da shi sannan hankalinta ya kwanta. Don a cewar Husna, dukkan komai sanadin Inna ya faru, ta ƙara da faɗin. "Wannan bai isa ba, ita da kanta ta soma sanar da Malam wai akwai soyayya tsakanin Yaya Huzaif da Sadiya. Malam kuwa ya sami Abba da maganar, batun da nake maki har Mami ta amince don har kiran Inna ta yi a waya ta yi fatan alheri." "Jar Uban can!" Shi ne abin da Hajara ta furta jikinta har wani mazari yake yi. ©Rufaida Umar *Kazar Kwanci...* Yadda ta ga Hajara ta yi mugun ɗaukar zafi abin har tsoro ya ba Husna, ta ji kamar ta faɗi da yawa amma kuma idanunta a rufe suke gam! So ya makantar mata su, ta yi nisan da ba ta jin kira. Hajara ta girgiza kai. "Na rantse maki tunda har haka zancen yake, toh ki saka a rai Huzaif ba shi da mata a gidan nan sai ke Momina. Ki saka a ranki cewa zan yi duk faɗi tashin da zan yi na ga ke ki ka aure shi ba Sadiya ba. Amma kar mu yi gaggawa, ki ba ni lokaci zan yi tunani mai kyau don mu san matakin ɗauka. Wato shiyasa har fiffiƙa yarinyar ke yi ta samu gidan danshi. Ai nasan zuwa yanzun kin ƙara fahimtar irin son kai na Inna, sam ba ke ce a gabanta ba, ki lura da duka takunta za ki fahimci ta fi kaunar mai sunan uwarta, ke kuwa ai sunan kishiya ki ka ci, ko mene ne ba za ta so ki samu ba ko din ta ƙuntatawa mu ƴaƴan Mama. Ki saka ranki a inuwa, ai tunda na dawo shikenan. Ba zan bari a yi miki irin wannan cin kashin ba. Zamu bi komai a sannu ta yadda idan bom ɗin ya tashi fashewa, zai girgiza su ba kaɗan ba." Hajara ta ƙarashe da wani irin murmushi na zallar mugunta tunawa da wani abun da ta yi. Tabbas tana ji a jikinta lokacin fara ramuwa ya zo. Daga Sadiya har Innar kashinsu zai bushe tunda abin ma ya shafi har rabin jikinta wato Husna. Wani sanyi ya shiga ratsa zuciyar Husna, ta ji nan duniya dagasken dai babu mai mata so da ƙauna kamar Antinta. Sai ga shi ta dawo da fara'arta. "Anti ni dai ki tambayar min Malam ya yarda na biki na yi weekend a gidanki." "Rufan asiri, ki bari a kwana biyu kin ji? Na fi ki son ki zo, amma ki bari mu ɗan ƙara samun daidaito da Malam. Kin ga tun faruwar abin can yau ne zuwana na farko gida, amma ai an kusa hutun zango na biyu (second term)  ko?" Husna ta gyaɗa kai. "Yauwa, toh ki sa ranki a inuwa, na tabbatar zuwa lokacin komai ya kara zama daidai, zai bar ki ki zo. Shi ma kuma batun Huzaif ki daurewa zuciyarki ki bar nuna musu wata damuwa a zahiri. Ki kuma sakarwa Sadiya fuska ki cigaba da mu'amala da ita yanda kike yi a baya. Ina da hujjata na faɗin haka. Kar ki bada ƙofar da za su fahimci komai, kin ji Momina?" Cike da shagwaɓa ta amsa. "To ni fa Anti ban san dalilin da yasa kallonta ma ba na son yi ba. Inna kuwa na gama fahimtar ni ba ta sona, ta fi son mai sunan Mamarta." Wannan furuci na ƙarshe da Husna ta yi, wato 'Inna kuwa na gama fahimtar ni ba ta sona, ta fi son mai sunan Mamarta.' Shi ya yi dirar mikiya a kunnen Inna wacce ta shigo har ta yi sallama ba su kai ga ji ba. Kirjinta ya buga da ɗan karfi, sai ta shiga ambaton Allah kamar koyaushe idan ta ji abin da ya firgita ta ko ma dai a wane irin yanayi. Jikinta ke ba ta cewa Hajara ce a gidan, aikuwa ba ta kai ga gama tantancewa ba sai ta ji muryarta tana wata dariya ga dukkan alamu furucin na Husna ya jefa ta cikin nishaɗi. Sallamar Sadiya ce ta sa ta juyowa ta dube ta. "Inna sannu da dawowa." Madadin Innar ta amsa sai ta ce cikin rashin walwala. "Ko wace ce a gidan, hakan hujja ce ta tsallakewa ki fita? Anya hakan da ki ka yi daidai ne?" Sadiya jikinta ya yi sanyi. "Ki yi haƙuri." Hakan ta furta, sauke ajiyar zuciya Inna ta yi kai tsaye ɗakinta ta shige. Hajara da Husna sai bayan sallama da maganar Sadiya ne ya sa suka fahimci Inna ta dawo. Hajara ta ja guntun tsaki. "Sai ki kula sosai, ki bar nuna kishinta a zahiri. Komai za ki yi, ki yi shi da takatsantsan." Husna ta amsa da toh. Nan fa suka yi ta hirarsu, Sadiya kuwa miyar da ta yi ne ta tuwo ta ƙara ɗorawa a wuta don ya yi zafi. Sai dab da Magriba tukunna Malam ya iso gidan. A lokacin ne kuma Hajara ta fito tsakar gidan. Inna ta dube ta, kamar ta share ta sai kuma ta ji ita ai Uwa ce bai kyautu ta yi hakan ba ko don darajar yan uwan Hajara ɗin da suke mata kallon Uwa a yanzu. Murmushi a fuskarta ta ce. "Hajara, ashe kin shigo gidan. Sannunki da zuwa." Hajara kamar ba za ta ce komai ba sai ta daure ta ce. "Yauwa Mairamu, sannunki ke ma." Cak! Sadiya ta tsaida ɗaurayar murfin filas ɗin da take yi, wannan sunan da Hajara ta kira da ma yanayin amsawa mahaifiyarta ta ji ɗaci sosai. Amma kuma ta sani, ba za ta iya cewa Hajara komai ba, a ranta ta ƙara ji ta tsani koda ganinta ne. Tunda har ta je gaban ka'aba ta dawo ba ta sauya hali ba, to ba ta jin nan duniya akwai abin da zai russunar da zuciyarta. Hajara kuwa gaba ta yi zuwa falon Malam. Ta iske ba ya falon ya shiga ɗaki don haka ta mike ta fito don ta san koda ta tsaya ba zai saurare ta ba saboda lokacin sallah ya yi. Bayan an idar ta ƙara dawowa, sannan ya shigo daga masallaci. Babu laifi ya sakarmata fuska, Hajara da kanta ta fahimci bai gama hucewa ba, a karshe har kuka ta saka sosai tana ƙara neman afuwarsa har da cewa yanzu tana da aure kuma ta san darajar auren, ba za ta sake ta ƙara yin kuskuren baya ba. Jikin Malam ya yi sanyi, anan komai ya wuce har ya karɓi tulin ledojin da ta yo masa tsaraba. Ƙatuwar darduma sai turaruka masu tsada da ƙamshi, sai ko jallabiyoyi har biyar. "Hajara, wannan sai ka ce don ni ki ka yi tafiyar? Duk a Saudiyar ki ka jido kayan nan? Kin ko tsaya ibada ko yawon kasuwa ki ka yi?" Ya ƙarashe da ƴar dariyar mamaki yana ɗaga wani kwalbar turare mai matuƙar kyau da ɗaukar idanu wacce ya fiddo a ɗan gidansa. Ita ma Hajara dariya ta yi. "Malam ibada na yi mana. Ai daga can Dubai muka yada zango, sai da muka yi sati kafin mu taho. A Abuja ma mun yi kwanaki biyu." Ya jinjina kai yana murmushi. "Allah ya yi albarka to, nagode. Ina na Innarki?" Ya furta yana dubanta, shiru ta yi ba ta ce uffan ba. Ya kula har lokacin Hajara ba ta karɓi Inna a matsayin Uwa ba. "Autar Mama ki yaƙi zuciyarki, koda babu yawa, ki ɗan buɗewa Mairamu ita, ina da yaƙinin za ki ji daɗin mu'amala da ita irin ta Uwa da ƴaƴanta. Mairamu tana kaunarki, da ace kin san yadda ta dinga bibiyata da roƙo da lallami kan na yafe maki, haƙiƙa na sani da zuciyarki ta sanyaya. Rayuwar duka nawa take Autar Mama? Ki tambayi kanki, me Mairamu ta taɓa yi maki marar daɗi a rayuwa? Ko don ta auri mahaifinki? Toh kin fi kaunar gida ya mutu babu mace a cikinsa? Kin fi so na dinga yawon shigowa da abincin siye? Ko kuwa kin fi kaunar ganin na ƙare rayuwata babu aure? Ki zama mai tawakkali da yarda da kaddara Autar Mama." Hajara hawaye ta ke fitarwa, kai ka rantse tsabar nadama ce ta sanya su zuba, sai dai kuma a nata ɓangaren ba na komai ba ne da ya wuce tunanin zaƙin soyayya har ya mantar da Malam da Mahaifiyarta. Wato dai Mairamu ta datse igiyar farin cikinta ta ko'ina, a wajen kuma kowa cikin zuri'arsu. Malam ɗin da take ganin koyaushe yana goyamata baya, yanzu wannan ɗin ma ta kau. Hum! Lallai Mairamu ta ɗauko ruwan dafa kanta, ita kuma za ta bi kowa da yadda ya so, idan sun sakankance da cewa ta ɗauki Mairamun tamkar uwa, sai ta nuna mata ba ta da wayo. Wannan tunani ya sa ta lanƙwasar da murya. "Ka yi hakuri Malam, zan yi iyakar bakin ƙoƙarina na ga komai ya wuce a zuciyata. Allah ya gafartawa Mamana, ya sa aljanna makoma." Ya yi murmushi sosai. "Amin amin. Allah ya maki albarka. Haka ake son musulmin kirki ya kasance." Ta yi murmushin da bai kai zuci ba tana wasa da zoben gwal ɗinta. "Amin Malam." Daga nan sai ta ga ya ƙara sakarmata fuska sosai ba kamar a farko ba. Ta ƙara fahimtar lallai ya ɗau sha'anin Mairamu da girma. A ranta ta yi ƙwafa kawai, tana tunanin kalar ƙuncin da za ta jefa ta ciki ta hanyar Sadiya. Sai bayan sallar isha'i tukunna ta yi musu sallama don har abinci aka ci tare da ita. Inna ta yi mamakin yanda Hajara ta sakar mata fuska har da yi mata fatan alheri na kawo kuɗin auren Sadiya da za'a yi, ba dai ta nuna mamakin a fili ba, ta bar shi a matsayin wataƙila Malam ne ya yi mata nasiha. A ranta tana fatan Allah yasa ta sauya ɗin dagaske. Sadiya kuwa ba ta ji ko ɗarr ba don wai Hajara ta yi tsaraba ga Husna ta ware ta. Dama ai ba ta sa a ka ba, ita ma ba ta kwaɗayin komai da zai fito daga hannunta. A wayar da Husna ta yi da Aminiyarta Shema'u ne ta ji ashe daga Saudiya har Dubai suka je, dalilin jimawarta kenan. ***   Hajara ce ke safa da marwa a tsakar falonta, maganganun Safiyya da ma Malam da ya tabbatar mata da kawo kuɗin Sadiya suka yi mata tsaye a rai. Ta dunƙule hannunta na dama ta kai wa na hagu duka.  Huci ta furzar gami da girgiza kai, a fili ta ce. "Na rantse Sadiya ba za ta yi aure ba. Ba asiri ba, ko tsafi ne sai na yi don ganin hakan bai kasance ba. Tabbas zan rama!" Ta ƙarashe tana duban kanta a madubi, gaba ɗaya idanunta sun kaɗa tsabar ɓacin rai. Bacci kuwa ya ƙaurace mata a idanu, har ga shi nan ƙarfe ɗaya ta buga da mintuna na dare amma babu ko alamun hakan. Duk kuwa da cewar mijinta bai kai da shigowa gidan ba, hakan bai wani dame ta ba a yau ɗaya saboda a ganinta damuwar Sadiya ta yi auren wuri ya fi yi mata karan tsaye fiye da kai wa daren mijinta a waje. "Kar ki kusa ki saka min idanu akan abin da ya ke sanya ni jimawa a waje. Idan ma wajen ƙadangarun barikin nake zuwa, ke ma ai a can muka haɗu. Don haka ki fidda idanunki harkokina, ni kuma zan sakarmaki bakin aljihuna, yadda ki ka dama haka za ki sha." Wannan ne kalaman mijin nata Alh Nuhu a ranar farko da ta hau borin kishi don ya kai ƙarfe uku a waje bai  shigo gidan ba. Tunani ta shiga yi, wa za ta yi haɗin gwuiwa da shi don zuwa wajen ƴan tsibbu? Wacce ta faɗo mata a rai ne ya sanya ta ƙyaƙyacewa da dariya na samun mafita. ©Rufaida Umar Tun sallamarta ya ɗauke kansa a fuskar wayar dake hannunsa ya na amsawa, kallonta yake yi sosai. Ta yi mishi kyau cikin doguwar riga na material kore mai ratsin fari. Ta yane kanta da farin mayafi. Suna haɗa idanu ta ɗan kauda nata kan tana murmushi a kunyace. Ƙarasawa ta yi ta zauna a can ƙarshen kujerar da yake kai sannan ta ce. "Yaya Huzaif ina wuni. Ya su Abba da Mami da Anti, fatan duk suna nan kalau?" Sauke ajiyar zuciya ya yi. "Lafiya lau Bebi, dukkansu lafiya lau suke. Abba yana can yana ƙoƙarin ya ga komai ya tafi daidai a goben." Ta yi murmushi ba ta ce uffan ba, a goben ne za'a tsaida lokacin bikinsu. Ta san zancen kenan. "Bebi idan na tuna sati na sama zan koma sai na ji kamar na cewa Abba a ɗaura auren kawai mu tafi, ƙafarki ƙafata." Ta ɗan tsuke baki. "Don Allah ni dai a'a. Ai idan ka tafin za ka dawo ka same ni lafiya kalau." "Dagaske? Ba za ki kula kowa ba?" Ta ɗan dube shi yanda ta ji ya marairaice murya, fuskar ma gaba ɗaya ta koma kalar tausayi, sai ta ji ya ba ta tausayin ta kawar da kai. "Bebi, please don Allah, roƙonki fa nake yi. Kar ki kula kowa idan ba na nan." "To ni dama ai ba wanda nake kulawa kafin kai, ban ga dalilin da zai sa na kula wani bayan na same..." Sai ta yi daurin jan mayafi ta ɗan rufe gefen fuskarta tana ƴar dariya. Shi ma dariyar ya ɗan yi cike da shauƙi, kalamanta sosai suka yi mishi daɗi. Ya sani sarai me take son faɗi, ya kuma san idan ya dage akan sai ta ƙarasa to fa za su wuni su kwana idan har Sadiya ce. Wannan dalili ne ya sa bai ja ba ya amsa zancenta. "Na gode ƙwarai Bebina. Allah ya sa mu zamewa junanmu abin alfahari kuma mafi alheri." Ta amsa da amin. Daidai sadda suka tsinkayi sallamar Husna, suka dubi ƙofar, ita ɗin a su take kallo da ƴar dariyar da ba za ka iya tantancewa ba ta ƙaraso tana ajiye tray dake hannunta. Sai fa a sannan Sadiya ta tuna ashe Inna ta ce ta tafar masa da ruwa da lemo mai sanyi, shaf ta mance. Husna kuwa ta haɗiye zazzafan kishin da ta ji yana bijiro mata, ta shiga jan magana ta sigar zolaya tana duban Huzaif wanda ke ɗan mamakin ganinta don tun ƙulluwar alaƙa tsakaninsa da ƴar uwarta bai ƙara sanya ta a ido ba, hirar ma da suke ɗan yi a kafafen sadarwa ta janye mishi don ko wayarta ya kira don magana da Sadiya a baya, sai dai kawai ta miƙawa Sadiya wayar ba tare da ta yarda sun gaisa ba. Yana so ya fassara hakan da abubuwa da dama, amma kuma ya sani babu ma amfanin hakan, gwara komai ya cigaba da tafiya a ninke, buɗawar ba zai amfane ta da komai ba tunda ita ke kiɗa da rawarta. "Yaya Huzaifa ina wuni, an zo lafiya?" "Lafiya Alhamdulillah ƙanwarmu, kwana da yawa kin ɓuya." Ba tare da ta kalle shi ko ta amsa zancensa ba ta yi murmushin yaƙe tana maida duba ga Sadiya. "Ke kam soyayya ta yi daɗi ba ki kawo wa masoyin naki koda ruwan sha ba. To ai shikenan, ga shi nan Inna ta ce a kawo. Ki karasa ladanki." Tana kai wa nan ta miƙe da zummar tafiya. Huzaif mamaki ya kusan kashe shi, duk a kalamanta bai ga inda ta tauna harshenta ba, ya yi mishi kama da kamar rashin kunya haka ko kuma wata manufa. Amma sai ya yi tunanin ƙila don saƙo da saƙo suke shi ya haddasa hakan. "Ni da kaina zan zuba, ke za ki fara sha tunda ko babu komai dama nan gaba ci da shayarwarki ƙarƙashina za su dawo." Karaf zancen na Huzaif ya dira a kunnen Husna da bai fi taki ɗaya ta bar falon ba, ta juyo ta dube su. Sadiya na kallonsa kaɗan, yayinda shi kuwa ya sauko gami da ɗan durƙuso ya buɗe jug na kunun aya ya shiga tsiyayawa a kofi. Babu wanda ya ƙara lura da wata halitta mai sunanta a wajen don haka a gaggauce ta karasa ficewa ta nufi ɗakinsu. Inda Allah ya taimaka ma Inna na ɗakinta. Kuka ta fara ta jawo wayarta ta shiga neman layin Hajara. Tana ɗagawa a ruɗe ta shiga tambayarta abin da ke faruwa. Murya a shaƙe ta amsa. "Anti anya zan iya cigaba da jurewa? Wani abin kamar da gayya ake yi don zuciyata ta sosu." Ta ji sadda Hajara ta sauke ajiyar zuciya. "Za ki iya Momina. Ai jinin da ke yawo a jikina shi ke yawo a jikinki. Ina da tabbacin ba za ki ɓatan shirina ba. Ke dai ki cigaba da haƙuri kina nuna komai ba komai ba. Gudun ma wani abin ya faru a yi wani zargi can. Kinga ki kwantar da hankalinki, na san gobe ma ba za ki iya yinin gidan ba, zan tambayar maki Malam ki shigo gidana kin ji ko?" "Toh Anti." "Yauwa Momina. Ki ƙara daurewa, ke za ki dara a gaba. Ke za ki zama Amaryar Huzaif kawai ki kwantar da hankalinki." Duk da tana ji kawai Antinta ta faɗi don ta rarrashe ta ne, amma sai ta ji murmushi ya suɓuce mata. Ba su jima tare ba suka yi sallama don Hajara ta ce ta maida hankali ga karatu tunda ta sanar da ita sun fara gwajin aji a makaranta (Test). *** Washegari da safe Sadiya ta tashi zuciyarta wasai idan ta tuna yau iyaye za su shiga maganarta da Yaya Huzaif. Haka suka yi shirin makaranta ita da Husna bayan sun gama kari. Falon Malam suka fara shiga kamar yanda suka saba suka gaishe shi, ya amsa lokaci guda yana karɓar kofin kunun gyaɗar da Inna ke miƙo mishi. "Ke Autar Mama ta ce za ki je gidanta ko?" Husna ta gyaɗa kai tana ɗan murmushin yaƙe tun bayan wayar soyayya da ta ji Sadiya sun yi da Huzaif a yau ta ji ranta ya sosu. "Shikenan, idan kin dawo sai ko shirya ki wuce. Ta nemi alfarmar ki kwana biyu zuwa lahadi kya dawo don ba ta jin daɗi ne." Cikin jin daɗi ta amsa da toh. Ita dai Sadiya kamar ya da Inna ba ta ce uffan ba, ita ma ba ta ce komai ba. Suka yi musu sallama suka fice bayan Malam ya ba su kuɗin mota da na kashewa. "Ina fatan babu matsala? Na yanke hukunci ban sanar da ke ba." Malam ya furta yana kallon Inna. Ta numfasa. "Ko kaɗan, ai kana da ikon zartar da kowane irin hukunci kan yaranka, kai ne fa Babansu. Sai dai Hajara ba lafiya  amma ba ka sanar da ni ba? Ai ko ban je dubiya ba zan kira a waya na ji ya jikinta." Girgiza kai Malam ya yi, sanyin zuciya irin na Inna na ba sa mamaki. "Ita ya dace ta kiraki matsayinki na Uwa gareta ta sanar da ke. Na yi mata faɗan hakan, sai na yi zaton ko ta kira ne. Amma ina mai baki hakuri." Murmushi Inna ta yi. "Shikenan, Allah ta ba ta lafiya ya sa kaffara." "Amin. Anjima can babban gida za'a karɓi baƙin da misalin ƙarfe uku na rana da yardar Allah." "Toh, Allah ya nuna mana. Ya sa albarka." Amsar da ta ba shi kenan. Shi ma ya bi da amin. *** Sadiya na zaune a ɗakinsu da yammaci sai ga Zahra ta shigo tana mata guɗa a kai. Harararta ta yi da murmushi ɗauke saman fuskarta. "Ka ga Amaryar Huzaif. Allah ya sanya alheri. Ai Mama ta cemin wai an saka nan da watanni goma. Kafin lokacin kuwa mun yi Candy abinmu. Toh ko auren wa za'a riga yi tsakanin ni da ke?" Zahra ta ƙarashe da dariyar mugunta, Sadiya ta kai mata duka don ta san dalilin dariyar, wato dai ta gama cin alwashin karatu da tutiyar babu namijin da za ta kula sai ta zama likita, amma kuma ga shi so ya yi mata tarko ta faɗa. Zahra idan tsokanar ta tashi haka za ta yi ta jan ta. "Ina ɗiyar tawa take?" Faɗin Maman Zahra dake shigowa kafin kuma ta yi sallama. Sadiya ta yi ƙasa da kanta tana gaishe ta a kunyace. Ƴar guɗa Maman Zahra ta yi wanda ya sa gaba ɗaya ta ɓoye kanta a kafaɗar Zahra tana murmushi. Fatan alheri ta yi mata ta fice. Haka ma wasu a cikin ƴan uwan Malam da suka zo yiwa Inna fatan alheri suka shigo dakin. Ranar kam Sadiya ta sha zolaya sosai. *** Hajara ta fito daga ɗakinta cikin shiri, Husna dake saman teburin cin abinci tana ba ƴar aikinta mai suna Atine umarni ya sa ta murmushi. Ba ta ce komai na ta tsaya ta na kallon diramar da suke yi. Wai Atine ta dafa mata Indomie da gwangwanin kifi alhalin da sauran farfesun kayan cikin da ta gani ta ce a dafamata. Atine kuwa sai haƙuri take ba ta. Husna ta ja tsaki. "Ni ba zan ci ba, ki ɗauke ki yi min yadda nake so." Ta yi jifa da cokalin ta miƙe ta taho falon. Anan ne kuma ta ga Hajara, Atine da sauri ta yi kicin da farantin Indomie tana tsoron faɗan Uwar ɗakinta Hajara. Kamo hannun Husna ta yi tana murmushi. "Momina, ina fata da burin na ga kin samu rayuwar jin daɗi ta daula irin wannan ko fiye da hakan. Allah ya sa ki zama matar Huzaif." Husna ta yi dariyar farin ciki gami a yin farr da idanu. "Amin Antina. Fita za ki yi?" "Eh, zan je wani wuri ba jimawa zan yi ba." Ta gyaɗa mata kai da fatan dawowa lafiya. Husna ta bi gidan da kallo sadda Antinta ta shiga mota direbanta ya ja. Hasko ta take yi a irin wannan daular ita da Huzaif ɗinta. *** Hajara da ƙawarta Waleeda ce zaune a gaban wani ƙasurgumin boka. "Yanzu me kike so a yi?" Tambayar kenan da ya watso mata. Ta sauke ajiyar zuciya. "Ina son komai a bi shi daki-daki, ba na so a yi ƙwaf ɗaya ne. So nake a fara haddasa rashin jituwa a tsakaninsu, ta yadda wasu lokutan zasu yi ta faɗa da juna, soyayyar dai ta dinga tafiyar hawainiya. A ƙarshe kuma idan lokacin da za'a raba tsakaninsu gaba ɗaya ya zo, zan yi magana." Boka ya yi dariya. "Ai wannan ba abin tashin hankali ba ne. Aiki ne ƙarami, aljani kawai za'a tura musu, kowanne ya dinga jin haushin ɗan uwansa.." "A'a, so nake shi ya dinga jin haushinta, ba na son ita ɗin komai ya sauya a tare da ita dangane da mu'amalarsu " "Na fahimta, a kan shi yaron zamu yi aiki kenan." Hajara ta jinjina kai tana murmushi. "Akan sa ne. Huzaif sunansa." "An gama. Kar ki samu damuwa. Ku ba ni nan da sati komai za'a yi shi a ƙare." Hajara ta dubi Waleeda suka yi murmushi kafin ta ɓalle bakin jakarta ta fiddo maƙudan kuɗaɗen da ba ta san adadinsu ba ta ajiye a gabansa. Daga haka suka tashi suka fice. *** Shirye-shiryen soma jarrabawa kawai Sadiya ke yi, sai ya kasance ƙarfe huɗu take dawowa gidan domin koda an tashi sukan tsaya bitar da ake musu a makarantar. Kamar koyaushe, yau ɗin ma tana falon Innarta tana karatun jarrabawa, wani al'amari ya faru tsakaninta da Huzaif da ya ɗaure mata kai. Layinta ya kira a yammacin daidai lokacin da ta ba Inna waya suna magana mai muhimmanci da Adda Ruƙayya wacce take kusan sa'ar Innar amma kuma sunan na Adda Ruƙayya ya bi ta tun suna yara. Sun ɗauki lokaci mai ɗan tsawo suna tattaunawa duk dai akan abin da ya shafi zuwa Gombe da zasu yi biki a zuri'arsu. Sun shafe kusan mintuna goma sha biyar kafin daga bisani su yi sallama, Sadiya da ke a falon Inna ta baza litattafai tana karatu ta ji shigowar Inna da kuma wayar da ta ajiye mata ta fita. Ba ta ma ko dubi wayar ba don ita a yadda ta saka karatun a rai, gani take idan fa ba ta mayar da hankali ba toh ba za ta samu ta haye darussan da za su taimaka mata kai wa ga gaci ba, abin nufi, watarana a wayi gari ta soma karantar fannin Likita da ta ke muradi. Daidai da Jamb da aka zana kwanakin baya, Malam sam bai bari ta zana ba don yana kan ra'ayinsa na cewa matuƙar ba ta shiga ɗakin aurenta ba to fa ba za ta soma karatu ba. Idan ta tuna sanadin Anti Hajara ne mahaifin nata ya sauya ra'ayi takan ji ƙarin tsanarta a zuciya, yanzun ma da tunanin ya faɗomata sai ta tsinci kanta da jan guntun tsaki. Wayarta da ta hau ƙara ya sa ta kai idanunta saman screen ɗin, sunan Yaya Huzaif ne muraran ya bayyana, murmushi ta yi kafin ta kai hannunta jawo ta. Ta ɗaga sannan ta soma magana. "As..." "Da wa ki ke waya Bebi?" "Inna ce ke waya da Adda Ruƙayya, wayarta batir ya ƙone shi ne na..." "Ya isa please Bebi, ba na son ƙaryar banza da wofi. Na san wani ƙaton ki ka ba lambarki, idan ba haka ba ki rantse da Allah cewa Inna ke amfani da wayar sannan ki yi min screenshot lambar ki turo min ta whatsapp na gani." Sai ta rasa me za ta ce, gaba ɗaya kanta ya ƙulle tamau. Ganin komai take tamkar a mafarki, daƙyar ta haɗiyi miyau cikin sanyin murya ta ce. "Na rantse? Rantsuwa fa ka ce Yaya Huzaif? Meyasa zan ba wani lambata alhalin na san da sanya rana a kaina?" Tsaki ta ji ya ja. "An faɗamaki ni mahaukaci ne kenan Bebi, zan yarda ni kaɗai ki ke kulawa ne alhalin ina da labarin duk sadda ki ka fita sai an samu mazan da suke biyo ki gida da sunan suna sonki? Ke na rantse ban yarda Inna ke amfani da wayarki ba. Ƙarya ki ke yi Bebi tunda har kin kasa rantse min. Ni za ki ci amana?" Tana jin alamar ɓacin rai a muryarsa, sai ta ji ƙwalla sun cicciko mata. "Wai Yaya Huzaif lafiya? Wane ya ɓata maka rai?" "Haka ki ka ce ko? Laifi ne don na nuna kishi a kanki? To ki je ko da waye ki ke magana Allah ya isa ban yafe ba. Da na san hakane wallahi ba zan siyamaki wayar ba idan ya so sai na ga ta hanyar da za ki ci amanar soyayyata. Amma bakomai, nagode." Yana kai wa nan ta ji kit, ya kashe wayar. Ta fiddo wayar a kunne tana ƙura idanunta. Hawayenta tuni sun zubo saman kuncinta. Yaya Huzaif dai? Ƙaryatawa? Zargi? Ja mata Allah ya isa? 'Meke faruwa ne?' Ta tambayi zuciyarta, ba ta sani ba. Ta ji ranta ya ɓaci sosai, ba ta kai ga tunanin komai ba ta ji ƙarar shigowar saƙo a wayar, da hanzari ta duba. Shi ne ya rubuto. "Dama an ce ka kiyayi mai kyau, babu abin da kuka iya sai yaudara. Za ku yi amfani da mutum ne don samun wani cikar burinku, a ƙarshe ku watsar da shi a kwandon shara. Babu yadda za'a yi Inna ta karɓi wayarki ta yi wanda ya zarta mintuna biyar tunda ba cinikin fili za ta ƙulla ba ai. Ni ki ka maida ɗan iska da bai san me yake ba. Shikenan, kar ki ƙara nemana a waya, ki rufe lambata kamar yadda ni ma zan rufe naki. Sai anjima." 'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Kalmar da Sadiya ta ambata kenan, hawayenta ya ƙaru, ya cigaba da zuba tamkar ruwan famfo. Sosai kalamansa sun yi mata zafi, ta ƙara karantawa, ta ji wani abu na taso mata na jin haushinsa don haka ta kashe wayar gaba ɗaya. Ranar karatun da ta kasa ƙarasawa kenan. Inna ta bi ta da kallo sadda ta fito a falon rataye da jakar karatunta za ta shige zuwa ɗakinsu. "Ke, lafiya na ga fuskarki ta sauya?" Ta ɗan rike kanta. "Bakomai, kaina ke ciwo sosai." Ta faɗa ne don kare damuwarta, amma kuma dagasken kukan da ta ci a dalilin wannan kalaman marasa daɗin ji da Huzaif ya fesa mata, su ne babban dalilin da ya haɗu da rashin cin abincin da ba ta yi ba na rana ya haifar mata da azababben ciwon kan. "To ai dole kanki ya yi ciwo Mamana, kin zauna za ki kashe kanki da boko alhalin ko abinci ba ki ci ba. Je ki ki ajiye jakar ki zo ki ɗebi abinci." Kamar ta ce ta ƙoshi, amma kuma ta san idan har ba ta bi umarnin Innar ba, to hakan zai sa ta fahimci ba lafiya ba don haka sai kawai ta amsa da toh ta shige ɗakin. Husna dake amsa waya ganin ta shigo ta koma amsa wayar da uhm da kuma uhm uhm. Ita sam hankalinta ma ba a kanta yake ba, abin da ke cin ranta ya ishe ta wannan ya sa koda ta ajiye jakar ta fita don ɗebo abinci. Husna ta ɗan leƙa ganin ta shiga kicin ne yasa cikin raɗa-raɗa ta ce. "Antina, na rantse fuskarta gaba ɗaya ta yi ja kamar kuka ta yi ma. Kinsan ita haka fuskar ke komawa idan ta ci kuka." "Eh Anti, ai ni ya kira sadda Inna ke wayar sai nace masa ni ina ɗakina, wataƙila Sadiyar ita ke yin waya." Husna ta yi dariya ta ƙara da faɗin. "To shikenan Anti, zan ƙara takatsantsan. Sai mun yi magana." Daga haka suka yi sallama ta katse kiran tana ƴar dariya. Tana kallon Sadiya ta shige falon Innar, kwanciyarta ta yi iskar fankar da ke kaɗawa yana mata daɗi. Zuciyarta kuwa wani irin sanyi ta ji yana yi. Huɗubar da Antinta Hajara ta yi mata ne ya shiga dawomata. "Zan taimaka maki, amma ke ma sai kin haɗa da irin namu makircin na mata. Kin ga dai na ce maki ki kula da duk wani taku naki da zai sa a zarge ki ta kowace fuska, yauwa, to kuma ina son duk sadda wani abun ya tashi wanda ki ka san zai iya haddasa hayaniya ko rikici tsakanin Sadiya da Huzaif, ki yi iyakar yin ki don ganin kin ƙara kunna wutar rikicin madadin ki kashe shi. Kuma ki dinga bi ta sigar da ba wanda zai maki kallon zargi. Idan har aka tafi a haka ina mai tabbatar maki komai zai zo mana da sauƙi. Za mu yi nasara kan ƙudurinmu." Tana kai wa nan a tunaninta ta buɗe idanun da ta lumshe su a farko, ajiyar zuciya ta saki. Kaunar Yayarta da ba ta da kamarta wato Hajara yana ratsa ta. Ta tabbata daga yanayin fuskar Sadiya akwai magana sosai. Wani tunani ne ya faɗomata a rai don haka ta yi saurin jawo wayar Sadiya da ta ajiye a gefen gadon ta duba, ganin a kashe sai ta mayar, murmushi sosai ta shiga yi, wayarta ta ɗauka gami da shiga cikin whatsapp. Kai tsaye saman lambar Huzaif ta tafi, ta ci sa'ar ganinsa a online kuwa. Don haka ta shiga rubutu. "Hi, Yayana akwai wata damuwar ne?" Kamar jira yake yi ta ga ya soma rubutu, can sai ga saƙon ya shigo. "Hum, babu komai ƙanwata, kawai yayarki ke neman ɓatan rai ne. Amma shikenan." Husna ta riƙe dariyar dake cin zuciyarta ta ba aikamasa da ɗan dodon da ya zaro ido na waya. Ta ɗora da faɗin. "Ya Salam, meke faruwa? Na ga Sadiya ta na ta cika da batsewa ta kashe wayarta. Wa ya ɓata wa wani tsakanin kai da ita." Ta ga sadda ya buɗe amma kuma an ɗauki mintuna kusan uku kafin ya tura mata martanin zancen. "Ƙila da ni ne ba ta son magana. Zan tambayeki ki faɗamin iyakar gaskiyarki please." Husna ta miƙe zaune sosai ta dubi ƙofar shigowa, har sannan babu alamun Sadiya sai ta cigaba da hirarta. "Zan faɗamaka, na yi alƙawari." "Bayan ni, akwai mazan da Sadiya ke kulawa?" Ta yi wata dariya kamar yana ganinta, ba komai ba ne face na nishaɗi. Wato dai tarkon da ta ɗana a ɗazun har ya harbu, a wautarta gani take yi shi ne ummul aba'isin na soma faɗansu, ba ta da masaniyar wancan aikin da Antinta ta ƙullo. "Gaskiya Yaya Huzaif idan nace maka hakane to na yi ƙarya, ba kuma zan ce ba haka ba tunda ni dai ba ma taɓa wayar juna da Sadiya tun sadda ka siyo mata nata. Amma ni dai don Allah koma hakan ne ka yi hakuri ka share. Me zai dameka tunda dai ka sani taka ce kai ɗaya, ka kwantar da hankalinka" Ta aika saƙon tana jin haushin kanta da fatan da ta yi mishi a ƙarshen rubutun hakan yasa da sauri ta ba kanta amsa a zuciya da cewa ba amin ba. "Jibi zan bar ƙasar nan Husna, a haka ki ke cewa na kwantar da hankalina? Kai ni ƙaryar da ta yi min ce ta rainin wayo ta tsaya min a zuciya, wato ta maida ni wani baho, tana waya da ƙato ta cemin Inna ke waya da Adda Ruƙayya. Hum. Anyways, shi kenan sai anjima." Tana gani ya sauka ya bar online ɗin, dariya sosai Husna ta yi, ta aika masa da fuskar dodo mai nuni da kuka, ita ba ta ce Sadiya na da gaskiya ba kuma ba ta ƙaryata shi ba. Nan take ta yi hoton hirar tasu ta aikawa Antinta Hajara. Ganin ba ta kan layin sai ta bar mata da zummar idan ta hau ta gani. Zuciyarta fari fes ta shiga kalle-kallenta a tiktok, har Sadiya ta shigo ɗakin ta ɗauki wayar tana kallonta ta gefen ido. Ta gani kamar za ta kunna sai ta fasa ta maida ta cikin sif ta adana can ƙasan kayanta. 'Allah yasa kun fara samun saɓani kenan.' Cewar Husna a ƙasan ranta. *** Abin ɗaure kai ga Sadiya, har ranar tafiyar Huzaif ya zo bai neme ta ba koda ta wayar Husna, hatta wayarta da ta kunna saboda kasa jurewar rashin kiranta da bai yi ba, nan ma ko saƙon whatsapp bai turomata ba. Abin kum sai ya ƙara ɓata mata, a gefe ga soyayyarsa dake nukurkusarta, sai dai ta rantse ba za ta kira shi ba muddin bai tuna da ita ba don kansa. Tana sane da cewa daren ranar zai tafi kuma zai zo gidan sallama da Inna hakan yasa tun dawowarta daga boko ta maƙale a gidan su Zahra wacce ta san komai. Ita kanta abin bai mata daɗi ba. "Amma hakan da kika yi za ki cutar da zuciyarki ne Sadiya, don Allah ki shiga gidan watakila idan ya zo ki ga kun shirya. Yau fa zai koma karatunsa." Faɗin Zahra kenan bayan sun kammala cin ɗan waken da Umman Zahra ta zuba musu. Daƙyar ma ta cusa abincin gudun kar Zahra ta fahimci ta damu amma ita kaɗai ta san me take dannewa, zumuɗin ta ga Huzaif ne yasa hatta da lesson ɗin da suke yi a tashi karfe huɗu ta kasa zama. Cike da son basarwa ta ja guntun tsaki. "Toh ya yi ta komawar mana Zahra, dama can da shi nake rayuwa ne? Ai ban san da zamansa ba. Duk abin da Allah ya zaɓa min zan karɓa da hannu bibbiyu." Ta karashe murya a raunane, kawai sai hawayenta suka zubo. Tana son Huzaif sosai, ta san da hakan. Amma fa ba za ta ɗauki cin fuska a tarayyarsu ba. Sam ba za ta yarda ya wulaƙanta iyayenta ko ma ita da kanta ba. Zargi tun kafin su kai ga zama a ƙarƙashin inuwar aure? Ta yi ƙwafa kawai. Kafin Zahra ta samu bakin magana suka ji muryar Meenat na gaida Umma, da sauri Sadiya ta share hawayenta. Ta tabbata tunda Meenat ta zo gidansu, to tare suke da Huzaif. Ƙila Inna ce za ta aikota ta duba ko tana nan ɗin. Meenat ta ƙaraso ta zauna gefenta tana leƙen fukar kafin ta yi dariya. "Kai jama'a, yau na ga sabbin shiga. Shi Yaya Huzaif gaba ɗaya jikinsa ya mutu kamar wanda aka watsawa ruwan sanyi, ke kuwa kallo ɗaya za'a yi maki a gane kin sha kuka." Ta kauda kai gami da jan guntun tsaki tana murmushin da bai kai zuci ba. "To ai wannan dole ne Meenat, rabuwar masoya ko kaɗan babu daɗi sai don ba yadda aka iya." Faɗin Zahra tana dariya. Ita Meenat dariyar ta yi sannan ta miƙe tana kamo hannun Sadiya. "Ki taso muje kar ya ƙara balbale ni saboda na jima. Shi ya ce lallai ƙafata ƙafarki wai na taimaka masa ki fito." Mamaki ya sa Sadiya da Zahra kallon juna, Huzaif da kansa yake zumuɗin ganinta? Sai ta kasa gasƙatawa don haka ta miƙe saboda magiyar da Meenat ke mata ba don komai ba. Hijabinta ta zura suka fito har Zahra. Ƙananun kaya ne a jikinsa gaba daya sai ta ga kamar ya ɗan yi rama. Shi ɗin ma kallonta yake yi kafin ya maida hankali ga amsa gaisuwar Zahra. "Tafiya kuma ta zo, to Allah ya tsare ya ba da sa'ar abin da za'a je nema." Huzaif da ɗan murmushi yana satar kallon Sadiya dake faman wasa da gefen hijabinta ya amsa da amin. Daga haka Meenat da Zahra suka bar falon Malam zuwa can tsakar gida wurin Inna suka bar su. Shiru ne ya biyo baya, sai ta ga abin da ta yi babu dacewa ciki don haka ta gaishe shi a sanyaye. Ya amsa da saurinsa kuwa kafin ya ɗora da faɗin. "Bebi mu yafewa junanmu, mu manta da gabar nan mai haifar da rashin nutsuwa da walwala a rayukanmu. Na kasa samun nutsuwa, ni ban san wane irin kishi ne ya motsa min ba ranar amma ke ma ba ki kyauta min ba. Kin san dai ba zan faɗi marar daɗi akan Innarmu ba. Ba zan taɓa haka ba." "Ka yi haƙuri." Shi ne abin da kawai ta furta, so take yi komai ya wuce, babban burinta su dawo da kyakkyawar mu'amalarsu. Ba ta son wata damuwa musamman a wannan ranar da ya kasance zai tafi ya bar ta, ba ta san sadda kuma zai dawo ba. Tana ji ya sauke ajiyar zuciya. "Shikenan Bebi, ya wuce. Amma fa ki shirya tare zamu je Airport, sai kin min rakiya." Ta ɗan dube shi, suka yi wa juna murmushi, wannan ƙaunar ta dawo mata sabuwa fil. Nan ya shiga jan ta da hira mai nuni da tsantsar kewarta. Malam da kansa ya yi wa Sadiya da Husna iznin bin su domin rakiya. Sadiya ta yi ado da ruwan tokar abayarta mai kyau da Anti Hafsatu ta kawo mata da jimawa, ya karɓe ta kwarai. Ita ma Husna abayar wajen Anti Hajara ta saka sai dai kuma ganin yadda Sadiya ta fito fes ya sosa ranta ba kaɗan ba. Ta daure dai ta shanye suka kama hanya. Sai da suka koma gidan Abba, Huzaif ya ƙara sallama da Mami da Anti Amarya sannan suka wuce. A hanya sai jan Sadiya yake da hira ita kuwa nauyi take ji sosai, daga yadda yake ta kallon Sadiyar yana magana ƙasa-ƙasa ya sa Husna samun tabbacin sun shirya, AC ne a motar ta ko'ina amma Husna gumi ke tsastsafo mata. Sam ba haka ta so ba, ba ta shirya ganin hakan ba ma kwata-kwata. Ta ji inama ta yi zamanta a gida. "Na yarda da ke ɗari bisa ɗari, ba na zarginki. Wancan abin ma da ya faru, kishi ne ya haifar da shi. Amma ina ba ki haƙuri, ina jaddada maki cewa ina sonki. Ki riƙe min amana Bebi, ki kula min da kanki." Waɗannan su ne zantukan da Huzaif ya yi mata sadda ya juya bayan ya buɗe tafin hannunta na dama ya sanya mata wani ɗan gida ƙarami na zobe a ciki. Ta janye hannun a hankali. Hawaye a saman fuskarta ta bi shi da kallo, shi kansa sai da ya ji idanunsa sun kada kamar ya fitar da hawayen. Haka suka rabu zuƙata babu daɗi. A hanya duk zolayar da Meenat ke jan ta da shi ba ta kulata ba, lumshe idanu kawai ta yi, a ranta tana jaddada cewa babu abin da zai sa ta ci amanar Huzaif. Kuma da yardar Allah ba ta da miji sai shi. Har abada babu wanda za ta kula da zummar soyayya. Mutum ɗaya take so, kuma Huzaif ne, dama ai tsakanin harshe da haƙori akan saɓa. Balle ma faɗa na masoya. Sai dai kuma ga rashin sanin Sadiya, wannan ne mafarin da Huzaif zai nisanta gare ta, irin nisan da dawowarsa zai zama jan aiki. *** Lamura suka daidaita tsakanin Sadiya da Huzaif, yakan kira ta ta whatsapp duk sadda ya samu sukuni, haka kuma suna taɓa hira. Soma jarrabawar Waec da suka yi ya sa hirar ta ragu tsakaninsu. Karatu sosai take yi, a gefe kuma ga Husna ƙanwarta da suke ɗasawa sosai don yanzu abin tun yana ba ta mamaki har ya daina. Za ta zauna su yi hira da dariya, hakanan tsakaninta da Inna. Inna ta ji daɗi sosai, kullum buri da addu'arta bai wuce na ganin yaran nata sun zama tsintsiya maɗauri ɗaya ba. Malam kansa ya kula da yanayin sauyi na jituwa tsakaninsu. A haka Sadiya ta kammala zana jarrabawar Waec sai kuma Neco da ke tahowa. A wannan ɗan taƙi na hutun da ta samu ne, Inna da su Dada da Adda Ruƙayya suka yi tafiya Gombe. Ganin haka Sadiya ta soma shiri kamar yanda aka tsara za su koma gidan Yaya Hashim. Husna na zaune tana kallonta sai ta yi ɗan gyaran murya hakan yasa ta dubanta. "Wai ke ba za ki je gidan Anti Hajara ba? Ba ki taɓa zuwa ba fa. Ko dai mu je can mu.." "Aa Husna, ke dai ki je. Amma kar ki ƙara sanya ni ciki ba na so." Husna ta yi murmushi, dama ta san ai hakan ce za ta faru. Ta ɗaga kafaɗa. "Ai shikenan." Sai dai ga Husna zancen bai tsaya a nan ba, Malam na dawowa gidan ta same shi da batun kamar yanda Antin nata ta tsara mata. "Malam me zai hana muje gidan Anti Hajara? Ka ga har yanzu Anti Sadiya ba ta kula ta sosai, sai na ke ga idan ta je gidanta komai zai wuce tsakaninsu." Malam da ɗan mamaki yake kallon Husna. "Toh amma rashin jituwar daga Sadiya ce yanzu ko? Ɗazu Autar Mamar ta kira tana magiya ku je gidanta hutu, ba ta ware min ke ko Sadiya ba. Akwai wani abu dake faruwa tsakaninsu ne?" Husna ta girgiza kai. Dama ai ta san Antin ta kira. "Aa, kawai dai babu wani sabo tsakaninsu shiyasa na ce ko zamu je can." "Shikenan hakan za'a yi Auta. Ku kammala shiri sai na sauke ku." Cike da zumuɗi kuwa Husna ta miƙe. Ba ta ce wa Sadiya komai ba. Ita ma Sadiya kasancewar hankalinta na ga waya tana duba saƙon da ta tura ga Huzaif tun a jiya amma bai buɗe ba gaba ɗaya ba ta cikin nutsuwarta sosai hakan ya sa ba ta kula ba. Sai da suka kammala komai Malam ya kama hanya suna tafe yana jan su da hira, ita dai Sadiya ganin ba hanyar gidan Yayansu Hashim aka ɗauka ya sa ta kasa shiru ta ce. "Malam an fasa zuwa gidan Yaya Hashim ne? Ko wani wurin zamu biya?" "Aa Sadiya, gidan Yayarki Hajara za ku je nan da sati kafin Innarki ta dawo." "Innalillahi..." Ta kasa ƙarasa saboda ba ta ma san cewa a fili ta furta ba, ƙirjinta sai da ya bada dam, wani baƙin ciki da tsoro ne suka dirar mata lokaci guda. Shi kuwa Malam da tsananin mamaki ya ɗan waigo kujerar bayan ya dubi Sadiya kafin ya maida duba ga kallon titi. "Innalillahi fa ki ka ce? Akan zuwa gidan ƴar uwarki? Sadiya?" Haba ai sai Malam ya shiga faɗa, yi yake kamar ya ari baki wai bai san haka Mairama ta yi nisa a ginamata tsanar Hajara ba sai yanzun! Ya kuma rantse ba don ba ta kammala gaba ɗaya jarrabawarta ba da sai ya ce ta koma gidan da rayuwa ya ga ta tsiya. Ita dai Sadiya hawaye kawai take fitarwa tana ba shi haƙuri. Husna ma ta shiga taya ta lallaɓa Malam ɗin da ban hakuri amma a can ƙasan ranta kamar ta kwashe da dariya ta ke ji. Koda suka isa ajiye su kawai ya yi sannan ya juya, a farfajiyar gidan Husna ta dube ta fuskarta itama duk ya jike da ruwan hawayen da ta ƙaƙalo tun kafin su sauka a motar ta riƙo hannunta tace. "Don Allah ƴar uwa ki yi haƙuri, na rantse ba ni nace mu je ba. Ashe wai Anti Hajara ce ta kira ta roƙi Malam ɗin mu zo gidanta." Sadiya ko kallonta ba ta yi ba ta janye hannunta ta goge fuskarta da tuni ya yi jazur saboda kukan da ta ci. Husna ta yi gaba tana share nata hawayen da murmushi ɗauke saman fuskarta. Hajara dake tsaye a ƴar barandar sama tana hangensu, wani murmushi ta yi na zallar tsana ga Sadiya. A fili ta ce. "Barkanki da zuwa gidana Sadiya, barkanki da shigowa inda zan tarwatsa dukkan wata alaƙar da ke tsakaninki da Huzaif. A sati ɗaya kacal! A sati kawai komai zai faru ya ƙare. Dukkan abin da zai biyo baya a rayuwarki, ba zai taɓa daidaituwa ba." Daga haka ta juya da nufin sauka ƙasa don tarbar shalelarta Husna. Sadiya na tsaye a gefe tana karewa gidan kallo, tabbas babu ƙarya an zuba uban dukiya a gidan kamar yanda ta ji labari. Tun da take a duniyarta ba ta taɓa kawowa ma akwai rana irin ta yau da za ta zo wai ita da kanta, da rai da lafiyarta ta taka gidan Anti Hajara ba. Tana kallon yanda Husna ta ruga a guje kamar wata ƙaramar yarinya suka rungume juna da ita, da ace da hurumin dariya a lokacin da tana da tabbaci zai suɓuce mata sakamakon riga da wandon da Hajara ta tsuke a ciki ita a dole ƴar gayu ta ƙarshe. Fatarta dai ba ƙarya ta ƙara gogewa sosai, kana kallonta ka san tana cikin ni'imar daula. Ko kallonta ba ta yi ba, ta ja hannun Husna suka haye sama. Dama ai ta san ta gayyace ta ne don ta wulaƙanta ta, sai da ta ji ƙafafunta na neman sagewa saboda tsayuwa ta nemi gefe guda a kasan kafet ta yi zamanta gami da fidda wayarta, har a lokacin Huzaif bai ce mata uffan ba kuma yana online, har status ta ga ya ɗora na bidiyon wasu kifaye a ruwa. Sai ta ji jikinta ya yi sanyi, amma kuma ta tsinci kanta da yi mishi uzuri, wasu lokutan mutum zai ga sako har ya buɗe sai wani abin ya ɗauke hankalinsa ya manta da saƙon. Wasu lokutan kuma saƙonnin ke yawa don haka ta sauke ajiyar zuciya ta yi mishi sallama. Akan idanunta ya buɗe har ta ji wani sanyi, shiyasa yi wa mutum uzuri ke da daɗi, wataƙila ma jira yake ta yi mishi magana. "Anti Sadiya, ki taso muje ɗaki." Muryar Husna ta ɗauke hankalinta. Sam ba ta ji dawowarta falon ba daga benen da suka bi suka haye sama a ɗazun, Sadiya wacce har lokacin take jin zafin Husna don ta kasa yarda ba ita ta cewa Malam ya kawo su nan ba saboda a iyakar tunaninta babu wani dalili da zai sa Hajara ta neme ta a gidanta. Mikewa kawai ta yi ba tare da ta ce mata uffan ba tana jan akwatin kayansu. Hannunta Husna ta riko gani da marairaicewa. Rantsuwa ta shiga yi akan ba ta da masaniyar ya hakan ta faru, Sadiya ta ɗauke kai. "Ya wuce ai. Muje." Daga haka ta ɗan yi gaba, Husna ta harareta ta baya kafin ta bi bayanta su jera suna hawa matattakalar. Sai a nan Sadiya ta ga wata sabuwar duniyar, ashe dai ɗazun ba ta ga komai ba. Tafkeken falo ta gani wanda ya sha kayan alatu, sai ƙofofi har biyar da ba ta san meke cikinsu ba. Babu ɗaya da suka shiga ta ga sun nufi wani ɗan ƙaramin lungu, wata ƙofa Husna ta buɗe mata suka shiga. Sanyin ac ne ya soma ratsa Sadiya kafin ƙamshin Airfreshner ya mamaye ƙofofin hancinta. Gadon da komai kwalliyar fari da ruwan hoda aka yi. Cike da walwala Husna ta dube ta. "Wannan ɗakina ne a gidannan. Komai da ki ka gani a ciki, da sunana aka sanya shi." Sadiya ta yamutse fuska. "Wannan bai dameni ba Husna. Sallah nake son yi." Husna ta yi dariya tana ɗan riƙo hannun Sadiya. "Haba mana ƴar uwata, please ki saki jikinki da gidannan. Na rantse Anti ba ta da matsalar komai. Za ki ji dadin rayuwa a gidannan. Kamar a turai haka za ki ji, babu wanda zai takura maki, sai abin da kike so za ki..." "Ya ishe ni haka Husna. Kar ki ƙara sanya ni tunzura. Na ce maki sallah zan yi ko?" Husna ta ɗan turo baki kaɗan ita a dole ba ta ji dadi ba. Da muryar shagwaɓa ta nuna ƙofar banɗaki da yatsa. "Ga fa toilet ɗin can." Girgiza kai Sadiya ta yi, Husna ba za ta taɓa sauyawa ba. Ta shige banɗakin, abin duniya duk ya ishe ta don ita kam har ga Allah komai na Hajara bai burge ta, ciki kuwa har da wannan daular. Wane jin daɗi za ta samu ta ɓangaren matar da ba ta girmama mahaifiyarta? A jikinta take ji ma yadda Hajarar ke yi wa Innar ladabi a yanzun na ƙarya ne. Husna ganin ta shige da sauri ta ɗauki wayar Sadiy, dama ba ta saka lock a wayar. Kai tsaye saƙon Huzaif ta shiga a whatsapp. Ganin ya aiko da saƙo ta buɗe da sauri. Sallama ce ya amsa kawai, cikin hanzari ta goge ta bar iyakar maganar Sadiya. A yadda ta san ƴar uwarta sam ba ta da naci akan komai, idan har ta ga bai amsa ba zai wahala ta ƙara magana duk kuwa da ta lura tana son Huzaif ɗin sosai. Kai tsaye ta fice daga ɗakin ta koma wurin Antinta don soma aiwatar da abin da ya kawo dalilinsu na matsawa da zuwan Sadiya gidan. A tsorace kuma ido a waje take duban Antinta Hajara, girgiza kai ta shiga yi tana mai ja baya. Riƙo hannunta Hajara ta yi ta maido ta gami da jan ta su zauna gefen gadon. "Anti asiri fa? Wannan ai asiri ne." Jinjina kai Hajara ta yi. "Yes Husna, asiri. Idan har kina son ki cimma manufarki a kan Huzaif, to ina mai tabbatar maki wannan kaɗai ne hanyar da za ki yi nasara. Ni kaina a sanadinki na soma yarda da ire-iren waɗannan abubuwa, a baya sam ganinsu nake yi shirme sa ɓata lokaci amma fa ban da yanzu. Ko kin san wannan rashin jituwar da ke yawan afkuwa tsakanin Huzaif da Sadiya sanadin asiri ne? Ban faɗamaki komai zai tafi daidai ba? Ko kuwa a zatonki ƴar dabararki ce ta yi sanadiyyar faɗansu ya yi ƙarfi sadda zai tafi? To ki saurare ni dakyau, aljani ke tasiri a jikin Huzaif. Shi ne musabbabin komai dake gudana tsakaninsu, Huzaif a yanzu koda yana son Sadiya, lokuta da dama ba ya jin komai sai haushinta a dalilin wancan shaiɗanin da ke jikinsa. A nan gaba kuma hatta da sunan Sadiya ba zai so ya ji ba. Zai kasance hirar da ya kamata ya dinga yi da ita, da ke ya ke yi, a lokacin da zai dawo garin nan, soyayyarki ce za ta maye gurbin ta Sadiya a ransa. Don kawai maganin da za ki tabbatar kina mata barbaɗensa a abinci shi ne zai sa ki tashi hankalinki? Kin san ba zan cutar da ita ba, ƙanwata ce fa ko na ƙi ko na so, maganin ba na komai ba ne sai na mantar da ita zancen Huzaif gaba ɗaya. Ta yadda za ta rufe babinsa a rayuwarta." Hajara na kai wa nan ta tsaya tana nazartar yadda maganganunta suka yi tasiri a wurin Husna daga ma yanayi na fuskarta da ya sauya ba kamar a farko ba. A haƙikanin gaskiya kuma maganin ba na komai ba ne face na baƙin jini. Babban burin Hajara ko bayan kawar da Huzaif daga rayuwar Sadiya, to ta yi baƙin jini wurin samari, Bokanta ya tabbatar mata aikin a hankali zai ci, akwai aiki mai kyau da zai mata na turen baƙar aljana ga Sadiya wanda ba zai sa wani namiji ya kalle ta da sunan so ba duk kuwa da kyanta. "Shikenan Anti, idan dai ba zai mata komai ba, aikin kuma zai sa na samu Yaya Huzaif. Zan bi umarninki." Sauke nannauyar ajiyar zuciya Hajara ta yi gami da murmushi, a hankali kuma ta shafi gefen fuskar Husna. "Haba Momina, babu cutarwa tsakanina da Sadiya, koda ace ba na kaunarta, hakan ba zai ban damar na cutar da ita ta kowane ɓangare ba. Ƴar uwata ce fa, jinin dake yawo a jikina yana yawo a nata." Murmushi Husna ta yi ta jinjina kanta cikin gamsuwa da bayanan Hajara. Nan ta karɓi maganin ta kuma ci alwashin za ta fara aiki da shi daga yau. Sai dai kash, duk yadda ta so Sadiya ta ci abinci a ranar cewa ta yi ta ƙoshi. Gudun kada ta zargi komai sai ta basar ta maida abincin kicin ta zubar a bola tana jan guntun tsaki. *** Washegari gaba ɗaya Sadiya ta tashi zuciyarta a jagule, haka zasu yi rayuwa da Huzaif? Babu kira babu amsa saƙo? Ko dai wani abin ne ya ɗauke hankalinsa ne? Sai dai kuma ta ƙaryata tunaninta a take ganin har Status yana ɗorawa abinsa a whatsapp. Ita ce dai ba zai kula ba. Wannan ya yi mata zafi ainun, ta saka a ranta ba za ta ƙara kula shi ba don ba za ta iya rantsuwar da zai janyo mata kaffara ba. So ne tana yi mishi, a kansa ta san ma'anar wannan kalmar, kuma ta sani, bai mata kamun wasa ba. Don haka batun ma ta yi rantsuwa akan ba za ta ƙara gwada yi mishi magana ba sam bai taso ba. Sai da ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfarta sannan ta bi Husna dake nacin ta fito su sauka ƙasa su yi karin safe. A ƙasan suka iske Hajara da maigidanta Alh Nuhu suna kari suna taɓa hira. Zuwansu ya sa gaba ɗaya suka ɗago kai. Sauke idanun da Alh Nuhu zai yi kan Sadiya ya ji wani irin maganaɗisu na fisgarsa. Ita kuwa Sadiya sai da ta fito ne ta ga ashe Antin nasu Hajara da mijinta na falon, ta ji kamar ta juya don ba ta iya sakin jiki gaban kowane namiji balle kuma Antin da mijinta da ganinsa sai dai daga nesa. Za ta iya cewa bai san ta ba kuma ita ma ba ta san shi ba a fili sai ko a hotunan biki. Hajara da ke jin kamar ta shaƙe mijin nata dake duban Sadiya, har ita ma Sadiyar da ta fito mata sakaka babu hijabi. Wani irin mahaukacin kishi take ji na taso mata ba ta san sadda hakurinta ya kare ta dakawa Sadiya tsawar da ta yi mugun razanata ba. "Ke!" Husna ita kanta sai da ta firgita, Alh Nuhu da ya shagala wajen kallon halitta mai jini a jika a lokacin ne ya dawo cikin hayyacinsa ya ɗan soma kame-kamen ɗaukar cokali ya hau shan farfesun dake gabansa har yana kona harshe. "Ba ki da hankali ne za ki fito min babu mayafi balle hijab? Haka Inna ta koyamaki? Maza ɓace min daga nan!" Sadiya da idanunta tuni suka cicciko da ƙwalla ta juya da sauri ta fice har tana haura matattakala bibbiyu. Husna sam abin bai mata daɗi ba musamman la'akari da nata shigar na riga da siket ƴan kanti ga babu ko hula a kanta balle ma a kai ga wani mayafi ko hijab. "To ni bari na wuce kar na makara, muna da meeting da..." "Ban tambaye ka ba don Allah. Jeka kawai." Hajara ta dakatar da shi da faɗin hakan bayan ta ɗaga masa hannu. Ya san halinta sarai, tana shakkarsa, amma kuma akan kishi idan ya yi wasu abubuwan a gaban idanunta ko kuma ta ganewa kanta a wayarsa to fa babu zaman lafiya. Inda Uwargidansa ke burge shi kenan, ita dai idan zai ba ta kuɗi to fa babu ruwanta da sanya mishi idanu akan komai nasa. Rayuwa suke yi na ba ruwan wani da wani, yaransu uku waɗanda gaba ɗaya suna ƙasar waje karatu. Hajara ta bi shi da harara da tsaki sadda ya sa kai ya bar falon gaba ɗaya. A fili ta ce. "Namamajon banza kawai." "Kai Anti. Me ya yi zafi haka? Laifi ne don Anti Sadiya ta fi..." "Husna kar ki ce komai a abin da ba ki sani ba kin ji ko? Don me za ta fito haka alhalin gidan nan akwai mijin da ba muharraminta ba? Shi kuwa kamar wani tsohon kwarto ya gwalalo idanunsu yana kare mata kallo. Uhum." Ta ƙarashe da ƙwafa. "To Anti ni kuma da nake yin kowace shiga a gabansa fa?" Hajara ta dube ta dakyau, ta kula yarinyar kamar ranta a jagule yake don fuskar babu ko alamun fara'a don haka ta ɗan numfasa da murmushin yaƙe. "Ke yarinya ce Husna, eh kina da sura daidai gwargwado amma fa kar ki manta Sadiya gaba take da ke. Kuma ke ɗin ai yana maki kallon ɗiyar cikinsa ba ma a matsayin ƙanwa ya ɗauke ki ba. Sadiya kuwa ta girme ki kuma ta fiki cikar halitta ta ko'ina, sannan gyara ai a na fara wa ne daga kan babba. Yanzu dai na gane ban kyauta mata ba, toh ki ba ta haƙuri, ɗauki abincin ki bi ta da shi ɗaki ki lallaɓa ta." Husna ta gyaɗa kai cike da gamsuwa, zuciyarta ta dan saki amma ba duka ba. Ta ɗauki babban tray dake saman tebur ta haɗa komai da zasu buƙata na karin safe sannan ta shiga ƙwalawa Atine kira, dattijuwar ta fito da sauri tana amsa wa cikin ladabi. Husna ta yi mata nuni da shi, "Ɗauki ki kai min ɗakina ba zan iya ɗaukar kayan nauyi ba." Ba musu kuwa Atine ta ɗauka ta yi gaba. Ita kuwa wayarta ta dauka da ruwan filas ta yi gaba. "Momina." Ta juyo jin Hajara ta dakatar da ita. Da murmushi saman fuskarta ta ce. "I am sorry, sannan ki yi bakin kokarinki wajen ganin komai ya tafi daidai." Sai lokacin Husna ta yi murmushin da ta ji komai ya wuce. Ta amsa da Ok sannan ta fice. Duk yadda ta yi ƙoƙari wajen ganin haƙanta ya cimma ruwa abin ya faskara don Sadiya kuka take yi sosai, dama ga damuwar Huzaif a gefe, wannan ya sa kukan ya zama biyu. A lokacin dai Husna ba ta iya ta shawo kanta ba sai da tace za ta kira Malam ta sanar mishi idan ya so su tattara su koma gida a ranar. Wannan ne dalilin da yasa Sadiya tsagaitawa, ta kuma karɓi roƙon Husna ta haɗa shayi. Amma ta kasa cin wainar ƙwai da ma farfesu waɗanda duk ta bi ta barbaɗe su da garin magani. Sai a abincin daren ne ta samu yadda take so domin Sadiya sosai ta ci abinci sakamakon cin da ba ta yi da rana ba gaba ɗaya. *** Kwanansu biyar a gidan, ba ta kara gangancin bari ta fita ko falon sama ba balle a kai ga na ƙasa, duk don gudun kar su haɗu da Mijin Antin nata don ta san a kansa ne ake mata tsawa mai kaɗa ƴan hanji. Shi kuwa Alh Nuhu kasancewar gangar siyasa na dokawa a lokacin hankalinsa gaba ɗaya yana kan taimakawa abokinsa kuma ɗan jamiyyarsu don ganin ya yi nasarar samun kujerar Sanata karo na biyu. Ba su da aiki sai ziyartar Bokaye da Malaman Tsibbu iri-iri kuma Jaha daban-daban, hakan ya sa ya ɗan mance da Sadiya da shirginta. Har suka kammala satinsu ɗaya cif suka bar gidan bai dawo daga tafiyar da suka yi zuwa can kudu ba wurin wani Boka. Ita kanta Hajara karɓar kuɗaɗe sosai take a hannunsa da sunan akwai waɗanda take sanya wa su yi musu aiki kuma sun tabbatar mata za'a dace sosai. A farko sai da ya ɗan yi mamaki daga baya kuma ya watsar da mamakin, mace mai bin maza a baya, ai babu lokon da ba ta faɗawa duk don samun kan abokin hulɗa. "Duk da haka wannan ya zama sirri, ba na so ko ƙawayenki su ji." Shi ne kaɗai abin da ya ce mata. Ita kuwa Hajara fantamawarta kawai ta ke yi, a gefe kuma aiki tuƙuru take gudanarwa don ganin ta gogawa Sadiya baƙin jini sosai ta yadda za ta fice a ran kowane namiji ciki kuwa har da nata Maigidan. Husna ta yi iyakar yin ta, an kuma yi nasara Sadiya ta ci abinci da garin magani har sau biyar a zaman kwanaki bakwai a gidan. Hajara ta ce kar ta sake ta damu tunda ba a iyakar wannan kawai suka dogara ba. Kudaɗe ta zuba a asusun banki na Husna ta saka direba kai su wani katafaren shago don su yi siyayyar tafiya gida. Sadiya ta danne komai ta bi Husna amma fa ba da niyyar taɓa ko kwandala a kuɗin Hajara ba. Komai na Hajara ya ƙara sire mata a rai, gaba ɗaya ta tsane ta. Tsanar da ba ta san adadinsa ba. Ta kula ba ƙaramin cutar da rayuwar ƙanwarta take ba ta hanyar sangarta ta da komai na jin daɗin rayuwa wanda gaba daya na lokaci ƙalilan ne tunda ba ta san gidan da za ta faɗa ba. Ga wani raini da Husna ke yi ga ƴan aikin gidan, daga Maigadi har mai wanki da ma Atine ba ta ragawa kowa, ba ta duba yawan shekarunsu haka take gasa musu magana ko ta ja musu tsaki. Hakan ba ƙaramin ƙonawa Sadiya rai yake ba. Ta kuma yi magana amma ta ga alamar ta yi nisa ba ta jin kira, ta sani ba za ta iya sanar da Innarsu ba, ba ta son tayar da hankalinta. Sai dai kawai ta yanke za ta cigaba da bin ta da addu'a. Wannan kaɗai ne mafita a yanzun. Tana tsaye jikin mota tana jiran Husna ta fito daga shagon don ƙin shiga ta yi, ita kuwa Husna ta ce sai ta faɗawa Malam, dole ya sa Sadiyar ta ce ta yi gaba tana nan tafe. A zahiri ba ta da niyyar shiga, ta ja tsaki ya fi a ƙirga amma kuma a ƙarshe dole ta sauya shawara ta shiga. Babban shago ne sosai, ta gama zagayenta a ƙasan babu Husna don haka ta kama hanyar bene ta soma takawa. Sai da ta kai hawa na uku inda kayayyakin sutura na mata yake sannan ta hango ta. Ta dage sai siyayyarta take jibga hankali kwance. "Wai ba ki gama ba?" Ta juyo ta dube ta. "Yanzu ma na fara, ke nake zaɓarwa English Wears." Ta ɗaure fuska tamau. "Bana so Husna, koda kin siya za ki yi asararsu ne." Husna ta saki baki kawai tans kallonta. Sadiya kuwa ta gyaɗa mata kai shaidar dagaske take. Dole ta haƙura ta cigaba da siyayyarta, ta yarda dagaske Sadiya ba ta don komai don har suka koma ƙasa wurin kayan maƙulashe nan ma ko tsinke ba ta nuna tana ra'ayi ba. Anan ne ma dole ta ɗaukar mata wasu kayayyakin tanɗe-tanɗen. Aka kammala ta ba da Atm card dinta ta biya suka fito Sadiya na ƙara jinjina wayewar kai irin na Husna. Don akawun na banki ita ma ta mallake shi, amma kuma ba ta taɓa wani amfanin da shi ba. Ba ta mancewa Yayansu Baba Habu ne ya kawo form din suka ciccike kuma suka je aka yi komai suka buɗe akawun a Ja'iz bank. Hatta da shagon da ta shigo ita duk a ɗarare ta ke komai ban da Husna wacce ta saba sosai kanta tsaye take gudanar da sha'aninta. Daga nan kuwa babu inda suka nufa sai gidansu, sun sani Inna sai washegari za ta dawo don haka gidan gaba ɗaya ya yi ƙura. Sadiya ce ƙarfin gyara ko'ina da wankewa. Falon Malam gaba ɗaya a hargitse, ita ce ta gyara komai ta shige ɗakinsa nan ma ta gyara ta wanke bayinsa. Kafin Malam ya dawo gidan ta yi musu girkin dare. Ya kuwa ji dadi sosai ya dinga sanya musu albarka don shi a nasa zaton har Husna aka yi aikin. Washegari kuwa sai ga Inna da tsakar rana sun dawo, sosai Sadiya ta shiga murna, ko babu komai kaɗaicin da ya yi wa zuciyarta yawa dangane da Huzaif zai ragu. "Me ya ramar da ke haka?" Tambayar da Inna ta soma jifanta da shi kenan. Ta yi dariyar yaƙe. "Inna rama dai? To sai dai yanayin jarrabawa." Inna ta bi ta da hakane kawai, ta sani wataƙila gidan Hajarar ce ta yi rayuwa a ƙuntace tunda babu shaƙuwa ko na sakanni tsakaninsu. *** Tun tana ƙirgen kwanaki, har suka soma zana jarrabawarsu ta Neco babu wani yunƙurin kira ko magana daga Huzaif. Zuwa sannan duk dauriyarts ta kasa, ta yi mishi magana har da kiran whatsapp amma bai ko bi ta kai ba. "Kin takura min Sadiya, don Allah ki bar ni ina fama da karatu ne. Ke ba ki san ki nemi mutum a gaisa ba sai kin gama wulaƙanta shi ko? To ni ma ai ina da abin yi. Ba a kanki zan zauna na ƙare rayuwata ba. Ki taimaka ki ba ni lokaci kar ki yi sanadin da zan ɗauki matakin da ba zai mana daɗi ba Hajjaju." Wannan shi ne amsar da ta samu sadda ta takura mishi da magana a whatsapp. Kalmar Hajjaju ta yi mugun baƙanta ranta, ta ji ciwon kalamansa. Ta sha kuka sosai. Haka ta daurewa zuciyarta ta kashe wayar gaba ɗaya ta cilla cikin sif ta cigaba da harkokinta da karfin hali. Zahra ke zaune tana kwaɓin lalle za ta yiwa wata Amarya, ita kuwa Sadiya ta yi shiru kawai ta zubawa lallen idanu amma sam hankalinta na ga tunanin Huzaif. Duk yadda ta so tattara komai ta watsat hakan ya faskara, sau da dama murmushinsa, daɗaɗan kalamansa kai har ma da yanayi na ɗaukar gayunsa sukan hana ta sakat, ta sani tana kaunarsa ba na wasa ba. Sauyin da ya ke zuwar mata da shi, sauyi ne irin wanda ba za ta iya jurewa ba. Satinsu ɗaya da soma jarrabawar Neco amma gaba ɗaya ta kasa saita kanta ta maido walwalarta yadda ya kamata. A gaban Inna kawai dauriya take yi duk da ta sani daga yanayin kulawar da Inna ke ƙara ba ta, ta fahimci tana da wata damuwar da ba ta fito ta bayyana mata shi ba. "Sadiya! Ke!" Muryar Zahra ta tsinta kamar daga sama ta yi firgigit ta dawo hayyacinta. Ajiyar zuciya ta sauke tana gyara zaman hijabinta gami da kauda kai daga kallon Zahrar da take sakamakon hawayen da suka cicciko mata sai ta waske da faɗin. "Ke bari na koma gida kafin Inna ta ji shirun ya yi yawa." Zahra ta riƙo gefen hijabinta wanda ya sa dole ta fasa miƙewar amma kuma hawayen sun zubo. "Meyasa Sadiya? Meyasa za ki takurawa rayuwarki ki hana kanki sukuni a dalilin ɗa namiji? Wallahi na tsani na ga kina zubar da hawayenki akan Huzaif. Ban ce bai cancanta ba, amma kuma duk wanda ya nuna kai ba ka da muhimmanci a rayuwarsa, kai ma ka fita hanyarsa gaba ɗaya ka hutarwa ranka. Don Allah Sadiya, ina haɗa ki da girman Allah ki yi ƙoƙarin rage damuwarnan. Kuma na yi alƙawarin zan ji ta bakin Huzaif, zan mishi magana. Da yardar Allah komai zai wuce." Sadiya ta share fuskarta tana murmushin da bai kai zuci ba. "Kin san ban taɓa son wani ɗa namiji ba Zahra, ban iya soyayyar ba, akan Yaya Huzaif na koya. Amma kuma yanzu ya ke wulaƙanta ni. Hum. Kar ma ki ɓata bakinki wajen yi mishi magana. To me za'a ce masa?" "Mu ke da abin cewa kuwa Sadiya. Bari na gama yi wa yarinyarnan ƙunshi zan shigo gidan ki ban lambarsa. In sha Allahu yau ba za ki kwana da damuwarsa ba." "Uhum." Shi ne kawai furucin da Sadiya ta yi sannan ta miƙe tana mata sallama. Ta gifta ƴanmatan biyu dake zaman jiran a yi musu ƙunshi ta fice. Tana shiga gidansu ta tarar Inna na sallar Azahar sai kawai ta faɗa ɗakinsu da sallama. Husna ta iske riƙe da waya tana ƙyaƙyata dariya ga dukkan alamu chatting take yi. Tana ganinta ta miƙe zaune fuskarta ɗauke da ƴar damuwa har Sadiya ta cire hijabinta tana ƙoƙarin ninkewa. "Sis, anya kuwa? Wai kodai na ƙara yi wa Yaya Huzaif magana ne? Ni na tsani ganinki cikin damuwarnan." Sadiya ta dube ta, tuni Husna ta fara hawaye. Sai ta ji haushin kanta ya kama ta ma. Don me za ta dinga sanya masoyanta kuka har haka? "Ba fa damuwarsa ba ne, kawai raina ne babu daɗi yau." Husna ta share hawayenta ta sauke ajiyar zuciya. "Har na ji sanyi. Dama za ki ban dama ai da na sami Abba na mishi..." "A'a, bana so. Mu bar zancen kafin ma Inna ta tsinkaya." Daga haka ta mike ta fice a ɗakin, Husna kuwa ta bi ta da kallo tana mata gwalo kafin ta toshe bakinta sakamakon dariyar da ta kama ta. Hauka take yi za ta bari sulhu ya shiga tsakanin Huzaif da Sadiya? Ko na farkon ma da ta ce mata ta yi masa zancen yace baya son maganar ƙarya ce kawai ta mata don kada ta yi tunanin ba ta yi ba. Yanzun ma da shi suke hira, koyaushe cikin ba ta labarin ƙasar Indiya yake yi. Ita ma haka za ta yi ta labarin gida da abin da ke faruwa amma koda wasa ba ta taɓa sanyo mishi batun Sadiya ba, shi ma kuma haka. Wannan ne yake ƙara yi mata daɗi. *** Bayan Watanni Biyar... Abubuwa da yawa sun fara masu daɗi da akasinsa, marasa daɗin kusan gaba ɗaya kan Sadiya ya ƙare a gidan, kamar dai abin arziƙi, Huzaif ya dawo da kula ta bayan sulhun da Anti Hafsatu ta yi musu. Ita ɗin ma a zuwan da Sadiya ta yi ne gidanta hutu bayan ta yi Candy ya sa ta fahimci akwai matsala tsakaninsu. Da kanta ta yi kiransa a waya ta whatsapp suka yi doguwar magana. Ta kula dai kamar kame-kame ne zantukansa marasa dalili, ƙarshe ta saka Sadiya ba shi haƙuri, shi ma ya ba ta. Rayuwar ta ɗan koma musu daidai amma fa ba ta bar fuskantar matsala daga wurinsa ba. Sai ta yi magana ya ƙi kula ta, kuma a gefe sai ta ji Husna na faɗin ai ba su jima da yin magana da shi ba. Wannan kan yi mata ciwo matuƙar gaske. Ba don tana ji a jikinta cewa Husna ba za ta taɓa ba da fuskar su yi soyayya da Huzaif ba da ta ce kodai soyayyar suke yi. A haka har suka ci waɗannan watannin, lokacin yaye Huzaif ya yi, Abba da Mami suka shirya suka tafi. A bakin Meenat take ji ai tuni Yayyunsa mata Radeeya da Lubna sun soma haɗa lefe don a lokacin da aka saka na biki ya kasance Huzaif na dawowa za'a ɗaura aure. Sosai Anti Hafsatu ke zuwa gidan tana kawo wa Sadiya kayayyaki na gyara hakanan Safiyya ita ma tana nata kokarin. Inna dai kallonsu kawai take yi abin na burge ta yadda yan uwan ke ji da Sadiya a yanzun. Husna gaba ɗaya zaman gidan ya fice mata a rai, damuwa sosai take shiga. Ranar da Yaya Lubna da Radeeya suka zo gidan har suka dauki awon undies ɗin Sadiya wuni ta yi kuka wannan ne dalilin da ya jawo ta tattara ta koma gidan Hajara bayan Hajarar ta kira Malam ta yi ƙaryar rashin lafiya. "Anti don Allah kada ki bari na rasa Yaya Huzaif. Na rantse mutuwa zan yi. Yanzu fa sosai muka shaƙu da shi, ya ce min ba ya kaunar Yaya Sadiya, ya dauke ni abokiyar shawararsa." Husna ke zancen a mugun firgice sa'ilin da ta ke zaune gefen Hajara tana kuka tamkar ranta zai fice. Hajara ta shiga rarrashinta gami kafin ta ce. "Kar ki sake ki sanya damuwa a ranki. Na faɗa maki Huzaif ba zai taɓa auren Sadiya ba. Ke ce matarsa. Yanzu dai ki zuba idanu ki bari ya dawo. Komai da zai faru za ki ganewa kanki. Za kuma ki sha mamaki kin ji ko? Ke ko biki kika ga an soma kar ki sake ki tashi hankalinki. Ni na san me na taka." Husna dai ta ji ne kawai ba don ta gasƙata ta ba, ta yaya za ta fasa damuwa alhalin ga shi nan komai na ta tafiya cikin tsari? Ita kuwa Hajara hankalinta kwance kasancewar ta yi imani kwarai da abin da Bokanta ya ce. Aiki ne ba na wasa ba zai soma tasiri a kan Huzaif duk ranar da ya sa ƙafafunsa a ƙasar nan. Komai zai juye masa ya ji nan duniya babu wacce yake so da aure kamar Husnarta. Wannan ne ya sa ta ji nutsuwa sosai. *** Ana gobe za'a kawo lefe su Abba suka dawo amma babu Huzaif wanda ya tsaya ƙarasa wasu abubuwa da ya shafi makarantarsu. A bakin Malam ne Sadiya ta ji cikin satin bikin nasu ne zai iso wato ana gobe ɗaurin aure. Ita dai gabanta kawai faduwa yake yi, Abba na dawowa gari da kwana uku aka kawo lefe na gani na faɗa can babban gida kamar yanda Malam ya tsara. Jerin akwatuna har saiti biyu ɗauke da tsadaddun kayayyaki. Husna kasa zuwa wurin ta yi, Hajara kuwa duk da ta san da shirinta sai da ta ji kamar ta yi hauka ganin tarin dukiyar da aka zuba da sunan mallakin Sadiya. Ta ƙara cin alwashi a rai ko za ta yi yawo tsirara auren Sadiya ba zai taɓa faruwa ba a duniyar nan dai. Sadiya kuwa duk da ramar da ta yi amma fa ta yi kyau sosai irin na gyaran Amare. Fatarta har wani sheƙi yake yi. Ɓangaren su Inna ma haka suke ta yi mata shirin da ya dace. Zahra wacce tuni ta riga Sadiya aure amma komai ake yi da ita don Mijinta ya san irin shaƙuwarta da Sadiya wannan ne dalilin da bai hana ta taka nata rawar ba. Babbar damuwar Sadiya lokacin bai wuce na shafe sati uku da ta yi babu wata magana tsakaninta da Huzaif ba, koda ta yi ba ya amsawa. A baya yakan amsa da ok, yes, no da sauransu, amma ban da yanzu. Tunaninta wane irin aure za ta yi babu kulawar miji? Ranar Litinin ma ƙunshi Zahra ke rangaɗa mata na bikin da za'a fara ran Laraba amma kuma hawaye take fitarwa. Faɗi take yi "Ta ya ya Zahra? Ta ya ya za'a ce zamu yi aure haka kamar irin na dolen nan? Meyasa Yaya Huzaif zai aure ni idan ya bar sona? Meke faruwa ne wai?" Zahra ta dakata da ƙulle ledar da ta saka a ƙafar da ta zanawa lalle ta yi tana jin ita ma nata idanuwan na ciccikowa da hawaye, don haka a raunane ta ce. "Ya zan maki Sadiya? Ya ki ke so a yi? Na ce maki mu sanar da manya don su san halin da ake ciki kin ce kina gudun faɗan Malam kar ya ga kamar ke ce bakya so. To don Allah idan ba su ji ba ta yaya za'a magance wannan matsala?" Sadiya ta haɗiyi miyau tana sanya bayan hannunta ta share hawayen dake saman fuskarta dalilin tafukan hannun rufe suke da leda wanda Zahra ta ɗaure bayan ta kammala zanen ƙunshi. "Ba zan iya ba, dagaske laifina za'a gani tunda shi bai fito ya nuna ba ya son auren ba, zan ɓata zumunci. Shirun ya fi alheri." Zahra ita ma ta share nata hawayen. "Ba ki fasa addu'ar da na ba ki ba ko?" Sadiya jinjina kai tana jan majina. Zahra ta ce. "To ki sa a ranki da yardar Allah komai zai daidaita. Allah zai maki zaɓi. Sadiya ba za ki taɓa auren wanda zai wulaƙantaki ba. In sha Allahu komai zai wuce ya daidaita tsakaninku. Kin ji? Ki bar kukan nan kada Husna ta dawo ta ganki itama ta rikice." Sadiya ta ƙara gyaɗa kai tana share fuskarta sosai. Husna dake laɓe a zauren gidan Zahra tana jin su ta yi murmushi da ƙwafa. 'Ai ba za ki taɓa auren Yaya Huzaif ba Anti Sadiya. Za kuma ki gani.' Ta furta a ƙasan ranta tana gyara zaman ledar lemo mai sanyi da ta karɓo musu a shago. Daga nan ta yi sallama ta shiga ciki. Ba ta nuna musu ta ji komai ba. Ana kammala yi wa Sadiya ƙunshi ita ma ta miƙa nata hannun. "Ni dai a yi min irin na Anti don Allah." Abin da ta ce kenan. Zahra ta harare ta. "Ba ki da wayo amma, ta ya ya za'a yi maki ƙunshi irin na Amarya? Sannu kin ji ko." Husna ta ɗaure fuska ta dubi Sadiya. "Sis don Allah a yi min irin naki. Mene ne a ciki?" Sadiya ta yi murmushi. Ita ta taya Husna roƙon Zahra akan ta yi mata babu komai. Zahra ta rantse ba za ta yi ba, wannan ya sa Husna ɗaukar zafi ta ce ta fasa ƙunshin za ta je a yi mata a wani wurin. Zahra kuwa tace sai dai a yi hakan. Ƙarshe ma tana gama cin abincinta ta fice a gidan ta bar su da zummar za ta neman gidan ƙunshi. "Ai kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan kwano." Shi ne abin da ta ce a ƙarshe sannan ta sa kai ta tafi. Sadiya cikin takaici ta dubi Zahra. "Ke dai akwai rigima wani zubin, mene ne ciki don ta yi irin ƙunshina?" Zahra ta ja tsaki. "Bana son hauka fa, kin taɓa ganin inda aka yi wa wata irin ƙunshin Amarya kuma ƴan gida ɗaya? To na rantse ba zai yiwu ba. Idan har ni zan yi mata ta jima ba ta yi fushin ba. Mahaukaciya kawai, sai ta je can ta ƙarata." Ita dai Sadiya girgiza kai ta yi kawai, Zahra da Husna ai sun saba tamkar wasu saƙo da saƙo. Kamar dai jininsu ne bai haɗu ba sam. Sai Magriba ta bar gidan Zahra don har baƙin ƙunshi ta zana mata mai ɗan karen kyau. Ita kaɗai ta koma gida madadin farko da suka fita tare da Husna. Har aka yi isha'i Husna ba ta dawo ba sai wuraren takwas na dare. Lallen da ta yi har ya fi na Sadiya kyau, kowa ya gani sai ya yaba kuma ace inama a ƙafar Sadiya yake tunda ita ce Amaryar. Ita kuwa Sadiya ko a jikinta don ba wannan ne matsalarta ba. Lamarin Huzaif ya shafe komai. Ranar kamu take jin batun dawowar Huzaif a daren. Meenat da ta zo gidan kwana ta yi ta zolayarta wai sai ta bar ƙunci tunda dai Angon ya iso gari. Madadin ma hakan ya yi mata daɗi, ba ta ji komai ba face faɗuwar gaba. "Ki tashi ki je falon Abba wai Yaya Huzaif ke son ganinki." Abin da Husna ta ce kenan kafin ta juya ta fice a ɗakin ta bar ƴanmatan dake ciki da yin guɗa a kunnuwan Sadiya. Ita kuwa sai ta ji ƙirjinta na cigaba da lugude tamkar an ce ta je ga ajalinta. Daƙyar ta mike bayan Zahra ta yi mata ido, har lokacin atamfar da ta sanya na kamu ne a jikinta, fuskarta fayau don ta ce ita sam ba za ta yi kwalliya ba. Ta yafa gyalenta ta fito. Ba ta kula zolayar su Adda Ruƙayya da wasu a ƴan uwan Malam dake soye-soye da yanke-yanke duk na shirin yinin gobe ba, ta yi hanyar falon Malam da sallama ɗauke a saman harshenta sannan ta sa kai ta shiga. Tana kuma ji a ranta ta shirya karɓar dukkan wani abu da zai zo da shi a wannan dare. "Wannan ma ai zancen banza da wofi ne. Shi wani abu yake sha a can Indiyan da zai kawo mana wannan wasan kwaikwayon? Ina aka taɓa haka? Daga kan Yaya ka koma kan ƙanwarta? Ba zai yiwu ba, bari na je na sami shi Alhajin, sai na dawo." Malam ke maganar cike da tsantsar ɓacin rai da mamaki don abin akwai ɗaure kai kafin ya sa kai ya fice daga falon. Inna dake zaune ta kasa ce mishi uffan har ya fita balle kuma wata Yayar Malam ɗin Inna Asabe da Ƙanwarsa da suke zaune a falon cike da jimami. Husna dake gefe kuka take yi kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa. Sadiya kuwa kallo kawai take bin kowannensu da shi. Babu baka sai kunni, ji take idan ta dage akan sai ta ce wani abu, wannan karon kukan ba zai yiwu ba wataƙila ta shiga kwarara amai tsabar yanda zuciyarta ke tashi sanadin kukan da ta sha. Idanun sun kumbura fuskarnan ta yi jawur da ita. A hankali ta lashi busassun leɓɓanta tana ji kanta na mugun sarawa da ƙarfi, bakinta gaba ɗaya babu ɗanɗano. Tun a daren ta ke kuka har wayewar garin yau da ya kama na yinin bikinta. Ta kai duba ga kujerar da Huzaif ɗin ya zauna a jiya, komai ya shiga dawowa a kwakwalwarta. Sadda ta shiga falon bayan an sanar da ita zuwan Angon nata, sallama ne ɗauke a saman leɓɓanta. Ya amsa bai amsa ba, ba za ta iya fahimta ba tunda ba ta ji ba, kuma ba kallonsa tayi ba balle ta yanke hukunci a kallon lebbansa. Har ta zauna ba ta ji ya yi magana ba, sai ta ɗago kanta kaɗan ta dube shi, kallon inda take ma ba ya yi, ya wani haɗe girar sama da ta ƙasa yana dunƙule yatsunsa. "Ina wuni, an zo lafiya?" Ta tsinci kanta da furtawa. Dama kuma hakan ya kamata ita ta fara gaida shi. "Lafiya." Shi ne amsar da ya ba ta a taƙaice, shiru ya ƙara samun matsuguni tsakaninsu na ƴan daƙiƙa kafin ta ji muryarsa ya soma magana a kaushashe. "Sadiya, zan fara da ba ki haƙuri, da kuma roƙonki wata alfarma." Duk da faɗuwar gaban da ta ji sai ta daure ta haɗiyi miyau tana dubansa, har a lokacin nasa idanun ba sa kanta. Wannan ya ba ta dalilin kallonsa sosai, ya ƙara kyau ya murje abinsa tamkar ba wanda ya je karatu ba. Ba ta ga alamun yana tattare da wata damuwar ba. "A farkon ganin da na yi maki, na yaudari kaina da sunan sonki nake yi. I am sorry to say, ban san soyayya ba, wataƙila shi ne dalilin da ya sa na ji kamar a raina sonki nake yi. Amma kuma a hankali na soma fahimtar babu wannan son a tsakanina da ke, ba na jinki a raina. Kuma..." Ya kasa ƙarasawa ya yi ɗan shiru yana furzar da huci. Ita kuma ga mamaki sai ta shiga wani murmushin da ko ba a faɗi ba za ka fahimci zallar yaƙe ne. Don kansa kuma ya ɗora zancensa. "Ba ke nake so ba, ban taɓa sonki ba Sadiya. Husna nake so da aure, da ita na zaɓi ƙarasa sauran rayuwata ta duniya a matsayin matata." Anan ne ta ji kamar an buga mata ƙaton guduma a tsakar kai, so take ta tuna wace ce ma Husna? Ji ta yi kamar a ranar ta soma sanin sunan, zuwa yanzu har wani bibbiyu take ganinsa don haka ta riƙe kanta sakamakon jirin da ya soma kwasarta daga zaune. Wannan ba shi ne damuwarta ba, babban burinta ya ba ta haske, ya fahimtar da ita wace Husnar yake so? "Ina nufin Husna ƙanwarki. Ita nake son aure. Ina neman alfamarki don Allah Sadiya ki taya ni roƙon su Malam su bar ni da abin da nake so. Na rantse maki ji nake idan ban auri Husna ba zan iya rasa raina." Ya ƙarashe yana mai zamewa daga saman kujerar, sai a lokacin ne kuma ya dube ta dakyau, ita ma ta maida dubanta gare shi. Magiya da roƙo har da hawaye a saman fuskar Huzaif yana mai tabbatar mata idan ya rasa Husna to shi ma mutuwa zai yi. Kawai sai ta ji kuka ya tahomata, ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta ta shiga rerawa. Shi ma gaba ɗaya ya ƙara fita hayyacinsa, wannan magiya da roƙon bai fasa ba kuma ba ta sauya zani ba. Ta gaji da sauraronsa don haka kawai ta share fuskarta ta miƙe, a hankali ta saka hannunta ta zare zoben da ya taɓa yi mata kyautarsa ta ajiye a gefen kujerar. Harafi ɗaya ta kasa furtawa wannan ya sa ta ficewa a falon amma kuma tana jin sautin muryarsa yana bin bayanta yana kiran sunanta. Ga mamakinta har ta zo tsakar gidan yana biye da ita, waɗanda suka soma zolayarsa da kirarin Ango suka yi shiru jin magiyar da yake zubawa Sadiya cewa ta yafe masa Husna yake son aure har wai yana yi wa Inna magana dake gefe akan ta sanya baki. Salati da salallami matan suka ɗauka. Huzaif gaba ɗaya ba ya cikin nutsuwarsa. Meenat idanu waje take bin Yayan nata da kallon mamaki da tsoro. Anya kuwa lafiyarsa ƙalau? Husna yake so? Wannan wane irin abu ne? Husna dake kallonsa a can ƙasan ranta ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta gan ta a gaban Antinta ta rungume ta su yi rawa da juyi, a fili kuwa gaba daya ta marairaice har da kuka. Adda Ruƙayya ce ta yiwa Huzaif tas ta ce ya tashi ya fice a gidan tun ba ta ɗauke shi da mari ba, haka gwuiwa a sake ya fice. Nan fa aka shiga tattaunawa, Inna Asabe ce mai kiran Malam a waya ta fesa mishi. Wasu fadi suke kodai ƙwaya yake sha. Sadiya kuwa ɗakin Innarta ta shiga ta dinga kuka kamar babu gobe. Inna dai sunayen Allah kawai take jerowa a ƙasan ranta jikinta har rawa yake don mamaki. Meenat a guje ta bi bayan Yayanta sai dai ya bar gidan wannan yasa ta komowa ta ɗauki jakarta da waya ta bi sahunsa. Tun ma a hanya ta kira gidan ta labartawa Maminsu komai. "Ki yi haƙuri Sadiya. In sha Allahu ko baki auri wannan munafukin ba, to rayuwarki ba za ta tagayyara ba." Muryar Gwaggo ce ta maido ta hayyacinta, ta sauke ajiyar zuciya gami da janye idanu daga kallon mazaunin Huzaif a daren jiya da ma tuna diramar da ya yi musu a gidan. Ba ta ce musu komai ba ta miƙe ta fice a falon Malam, ta san dai koda Malam da Abba sun tsaida magana kan lallai sai Huzaif ya aure ta, ba za ta taɓa bari ta aure shi ba. Koda an mata dole tana ji a jikinta za ta iya bar musu gidan a neme ta a rasa. Idan da abin da ya fi ficewa a rai, to Huzaif ya yi a ranta. *** Marin da Abba ya ɗauke shi da shi ne ya katse sauran kalaman da yake zuba musu duk domin su fahimci nisan da ya yi a ƙaunar Husna. Da yatsa yake nuna shi cike da ɓacin rai mai yawa. "Ƙarya kake yi Huzaifa! Ƙarya ka ke yi ka maida mu ƙananan mutane a wannan rana da na gayyaci dubban mutane domin su shaida ɗaurin aurenka. Mu za ka kawo wa zancen banza da wofi?!" Huzaif hawayensa kawai suke fita, bakinsa kuwa ya ƙi mutuwa. "Wallahi Abba ina sonta. Ina ƙaunar Husna. Don girman Allah..." Ya zube gwuiwoyinsa a ƙasa yana mai cigaba da roƙo. "Ku aura min Husna. Ni fa ban taɓa son Sadiya ba, kuskuren fahimta aka samu. Ita ma Husna a tambaye ta, tana sona mun jima muna son junanmu." Kalaman da suka dira a kunnuwan Malam kenan sadda ya sanyo kai falon saukar baƙi na Aminin nasa da sallama ɗauke a bakinsa. Mami ta kara gyara zaman mayafinta, ita gaba ɗaya tausayin ɗanta ta ji. To mene ne bambancin Sadiya da Husnar? Ita a nata ganin kawai a maida auren kan Husna. Abba zai yi magana Malam ya dakatar da shi. Sai a lokacin ma ya kula da shigowar Malam falon. Babu ko kunya Huzaif ya koma gare shi da magiya ya yi hakuri ya yafe masa ya ba shi auren Husna domin suna son junansu sosai. "Ya isa haka, Husna da Sadiya dukkansu abu guda ne. Amma kuma ba zamu yanke hukunci kai tsaye ba sai an haɗu gaba ɗaya." Ya ƙarashe yana jin ciwon abin a ransa, sai dai kuma ya sani, iyalan Alh Abubakar sun fi ƙarfin komai a wurinsa. "Wannan zance ne kawai kake yi Sa'ad, kai ma sanin kanka ne ba..." "Zai yiwu Abubakar, zai yiwu. Amma bari na yi musu magana kowa ya hallara anan, mu ji ta bakin dukkansu." Daga haka ya fiddo waya, Inna ya kira ya ba ta umarnin taso Husna da Sadiya gaba su zo sannan ya yi kiran babban ɗansa akan su zo gidan Abba. Kowa ya hallara har Hafsatu da Hajara da Safiyya waɗanda duk suke can gidan sun shigo biki. Hajara zyciyarta wasai, ta sani kuma komai zai tafi daidai kamar yanda Bokanta ya ce hakan yasa hankalinta a nutse babu wata fargaba ko damuwa. *** Tarin mutanen da ke zaune a babban falon saukar baƙi na gidan Abba, bai hana ta kuka har da sheshsheƙa ba. Yin sa ta ke iyakar ƙarfinta. "Ya isa haka Husna, ya isa. Share hawayenki. Ai yanzun komai ya zo ƙarshe da yardar Allah." Faɗin Abba kenan yana maida duba ga Huzaif dake zaune tanƙwashe da ƙafafu yana satar kallon Husna yayinda ya ke jin sautin kukan nata har tsakiyar kwanyarsa. Ji ya ke inama yana da damar ƙarasawa kusa da ita ya rarrashe ta. Hajara ce ta ja ta a jiki ta kwantar da kanta saman cinyarta tana shafawa a hankali wannan ne ya haifar da shiru na lokaci ya ratsa a falon. Malam zai yi magana amma Abba ya hana shi. Inna kanta na ƙasa, a gefenta Sadiya ce da ke fitar da na ta hawayen masu ɗumi, kanta har sarawa yake yi don rabonta da abincin kirki tun jiya, uwa uba baccin da ba ta iya ta yi sa ba. "Huzaif, yanzu ba anjima ba, ina so ka faɗamana gaskiyar wa ka ke so tsakanin Sadiya da Husna? Ka fitar da mu cikin duhu don mu san abin yi a gaba. Ka daina haifar mana da wannan ruɗanin, mu ba yara ba amma kana wasa da kwanyarmu." Huzaif da ke jin ƙirjinsa na bugu da ƙarfi, ya ɗan dubi gefen da Sadiya ta ke, aka yi sa'a suka haɗa idanu. Ta kasa dauke su a kansa, so take ta gano kodai dukkan abin da ke afkuwa a mafarki ne, yanzun furucin bakinsa zai sauya. Kokwanton da wani sashi na zuciyarta ke yi ne take son kawar da shi, ina makomar waɗannan zafafan gwala-gwalan kalamin da ya dinga yi mata a baya suke? Me ya ke nufi da kiran waya ya hana ta bacci ta hanyar sauraron daɗaɗan zantukansa masu ƙara narkar da zuciyarta a kaunarsa? A hankali kuma ta sauke idanunta ƙasa yayinda tsikar jikinta ke tashi yarr. Hawayenta suka ɗiga saman lallen da ta sha na bikin aurensu wanda yau da ya kasance ranar ɗaurin aure amma kuma reshe na nema ya juye da mujiya. Kamar daga sama ta tsinci muryar Huzaif na magana. "Abba ni Husna ce zaɓina, ita zuciyata ta aminta kuma nake so. Ban taɓa son Sadiya ba. Mun jima muna soyayya da Husna a ɓoye, mun kasa fitowa fili mu bayyana ne, dalilin kenan da ya sa na rage shiga harkar Sadiya. Na rasa ta yaya zan bayyana mata ba ita nake so ba, Husna ce zaɓina tun farko, akasi aka samu da rashin fahinta." Akasi? Rashin fahimta? Waɗannan ke yawo a kwakwalwarta. Hannun Inna ta ji a saman nata, wannan hannun da ke yawan ƙarfafa mata gwuiwa da jin cewa ba fa ita kaɗai ce ba a duniyarta, a yanzun ma jin wani ƙarfin gwuiwar ta yi sai ta tsinci kanta da ambaton Allah da ma dukkan addu'ar da ta zo bakinta. Tana ji Malam da Abba na faman buɗewa Huzaif wuta a dalilin wasan kwaikwayon da ya yi da ita, can kuma ta tsinkayi muryar  Hajara na fadin. "Abba laifi fa na Sadiya ne ba Huzaif ba, dama tun farko bai ce yana sonta ba. Ita ce dai ta dinga shigewa lamarinsa amma ko gidan ya je babu wacce ya fi maida hankali kanta face Momina." Haka dai maganganun suka yi ta tashi, Abba ya dage kan lallai Huzaif bai isa ya maida shi ƙaramin mutum ba, shi kuwa Malam ya ma kasa cewa uffan a wannan karon sai kallon ɗiyarsa Sadiya da yake yi. "Abba." Sassanyar muryar Sadiya ta shiga dodon kunnuwansu, sai falon ya yi tsit aka maida hankali ga abin da take son cewa. Ga hawaye a fuskarta amma wani murmushi ta ke yi mai tarin ma'anoni. Ta ɗan dubi Huzaif shi kuma ya kauda kai sannan ta kalli Abba. "Na haƙura da Huzaif. Ina roƙon Allah ya musanya min da wanda ya fi shi. Don Allah kuma ku bar shi ya auri ƴar uwata. Husna jinina ce, da ni da ita duka ɗaya ne. Wallahi na haƙura." Tana kai wa nan ta sadda kanta. Nan Abba ya yi shiru, a karshe ya dinga yiwa Sadiya addu'a da kuma fatan alheri. "Na rantse maki Sadiya da ace ina da wani ɗan da ya kai shekarun Huzaif, da babu abin da zai sa na sharemaki hawayenki. Amma ina maki fatan Allah ya ba ki wanda ya fi Huzaif komai na rayuwa. Allah ya albarkaci rayuwarki." "Ba amin ba." Wannan furucin da Hajara ta yi ƙasa-ƙasa ya shiga kunnenta, ta yi murmushi karo na biyu. Wai kuwa akwai ranar da Hajara za ta ƙaunace ta? Ta ba kanta amsa da a'a. Ita dai daga wannan ta miƙe ta bar musu falon ta kama hanyar fita. Anti Hafsatu ce ta biyo ta da sauri tare da su Radeeya da Lubna yayyun Huzaif. Haƙuri da ban baki suka shiga ba ta, ta nuna ita fa komai ya wuce. Anti Hafsatu wacce har su din ma haushinsu take ji kawai ta janye Sadiya suka fice daga gidan. Ba ta ma koma gidansu da ita ba kai tsaye gidanta suka wuce a motarta. A can ne Sadiya ta ci wani sabon kukan, Anti Hafsatu na rarrashinta har Safiyya wacce ita ma ta biyo su. Ƙarfe ɗayan da aka tsara za'a ɗaura aurenta da Huzaif, yana bugawa labari ya sauya, aka ɗaure auren Huzaif da Husna. Sabo turken wawa, wannan karin magana ta Malam Bahaushe shi ya taka rawa a rayuwar Sadiya, wannan ƙwallafa ran da ta yi akan Huzaif da kuma cin amanar da ya biyo baya sai da ya yi sanadiyyar kwanciyarta a gadon asibiti. Ta fi ƙarfin sati uku kafin komai ya soma wucewa rayuwarta ta fara daidaita. Sama-sama ta ji a wani yammaci, Inna da Anti Hafsatu da Baba Habu suna zancen karatun Husna da ba ta kammala ba don a lokacin ne za ta je SS1, Inna ke faɗamusu hukuncin Malam inda ya yi rantsuwar Husna ta gama karatu ta yi zaman aure kawai. Hirar Husnar ma ba son ji take ba dalili kenan da ta ɗauko wani tsohon littafi na Hausa mai suna Darasi Ne ta shiga maimaicin karatu, ita ɗin ba gwanar karance-karance ba ce, amma kuma tun sadda wata ƴar ajinsu Nabila Muneeb ta ba su labarin littafin ta ji nan duniya tana kaunarsa. Har ta kasa hakuri sai da ta tara kudi ta ba ta ta siyomata. Ta karanta ya fi a ƙirga amma duk sadda ta ɗauka sabo fil take jin sa. Tafiya na tafiya har aka ci watanni biyu da auren Huzaif da Husna. Lokacin bai fi saura kwanaki ya rage a fara azumi ba. Sadiya ta rage walwala amma kuma ta soma dawowa nutsuwarta. Gaba ɗaya ta tattara soyayya ta yi watsi da ita. Babu ko burɓushin kaunar Huzaif ko tunaninsa a zuciyarta. Ta maida hankali ƙwarai wajen neman ilimin addininta, zuwa lokacin tana ji babu sauran dama a wurinta na yin karatun boko. Malam sosai yake jan ta a jiki yana lallaɓa ta. Haka ma yayyunta maza da wasu a cikin matansu don har a sannan ba kowaccensu suke ɗasawa ba. Babban labari na farin cikin da ya same su a lokacin bai wuce na samun cikin Safiyya ba bayan dogon lokacin nan. Murna sosai Inna da Sadiya suka taya ta. Yanzun babu komai tsakaninsu face zumunci da kyautatawa. Sadiya kusan rabin azuminta a gidan Safiyya ta yi sa. Sosai ta ɗauke mata dukkan wasu ɗawainiya, Safiyya ke faɗi mata wai Hajara da mijinta sun tafi Umara. Ba ta ma ƙara bi ta kan zancen ba, ai ta ji Inna na faɗawa wata yar uwarsu wai Husna ta kira ta tana neman gafara za su wuce Umarah mijin Anti Hajara ya biyamusu ita da Huzaif. Kenan tare suka wuce gaba ɗaya. Ta san gudun jefa ta damuwa ya hana Safiyya yin maganar Husna, abin da kuma ba ta sani ba, ita har a zuciyarta yanzun babu ko ɗigon ƙaunar Huzaif, ta ma mance da komai tana kuma ji a ranta ta yafe wa ƙanwarta. Sai da ana saura sati ɗaya bikin ƙaramar sallah sannan ta tattara ta koma gidansu. Mijin Safiyya ne ya kai ta da kansa har da sha tara na arziki, atamfarta har da leshi duka ɗinkakku don tun sadda aka kawo suka je kai ɗinki da Safiyya. Kasancewar yanzun komai ya ƙara daidai tsakanin Safiyya da mijinta tun samun juna biyunta ya sa yake lallaɓata. Auren da mahaifiyarsa ke kokarin tilasta shi yi, yanzu ita ma ta fasa amma burinta bai wuce Safiyya ta haifi ɗa namiji ba. Wannan yasa suka san akwai sauran rina a kaba muddin ta haifo ɗiya mace. Wataƙila uzzurawar da aka yi mata a baya zai dawo sabo fil. Inna da Malam sun ji dadi sun kuma yaba. Zakari dake zaune a tsakar gidan inda suka sha ruwa sakamakon zafin da ake a gari, ya dubi Sadiya. "Ke na ga kayayyakin ma sun maki yawa. Ga Baba Habu ya aikomaki, ga Abba ma har kala uku, ga Yaya Mustafa. Toh ni dai sai dai na siyamaki jaka da takalmi kenan." "Yaya har da jalbab za ka ɗinko min." Ta faɗi tana murmushi. Ya jinjina kai. "Dakyau, in sha Allahu kuwa za ki same su duka. Allah ya nuna mana sallar lafiya." Gaba ɗaya suka amsa da amin har Hadiyya matar Zakari da ta biyo mijin nata yi musu barka da shan ruwa. A ƙarshe Malam da Zakari suka fice masallaci. *** Ranar sallah kuwa zuciyoyin kowa cike da farin ciki da murnar sallah ciki har Sadiya. Ta yi shirinta tsaf cikin adon farin jalbab da Yayanta Zakari ya kawo mata ta sanya baƙin takalmi, ta yi kyau tsaf, Inna ma ta sa sabon hijabinta suka ɗunguma zuwa masallaci har Malam. Ranar wuni suka yi ana kawo musu ziyara daga makwafta, dangin Malam har da yaran su Adda Ruƙayya. Washegari ta yi shirinta tsaf cikin leshinta baƙi mai kwalliyar ruwan madara a jiki, ya sha stones ɗinkin doguwar riga sai walwali take cikin rana, ta yafa mayafinta ruwan madara, tsayawa fasalta irin kyawun da ta yi ma ɓata lokaci ne. Gidan Zahra za ta je kai mata ziyara daga nan ta wuce gidan Yaya Mustafa wanda ba shi da nisa da Zahra. A jikinta ta ji ana bin ta a baya amma kuma sai ba ta juya ba har ta ƙarasa ƙofar gidan Zahra ta shiga bubbugawa. "Assalamu alaiki." Ta tsinci murya a gefenta, ta ɗago ta dube shi fuskarta a ɗaure, dogo ne marar jiki kamarta, fari ne tas. Ba shi da wani kyau na a zo a gani sai kwarjini ga shigar kamala. Duk yadda ta so yin tsiwa sai ta kasa ta daure ta amsa sallamar, daidai sadda Zahra ta bude mata ƙofar ta washe hakora za ta yi magana ta hango mutum da sauri ta koma bayan kyauren kasancewar ba ta da gyale a jikinta. "Au ashe ba ke kaɗai ba ce." Daga nan ta yi saurin komawa ciki, ita kuwa Sadiya da Allah da Annabi s.a.w ya shiga haɗa ta dole ta dakata ta fasa shiga amma ta ƙudurta a rai duk maganganunsa zasu shiga ne ta dama su fice ta hagu. Ta dai ji yace sunansa Suraj, yana kuma zaune ne a unguwar da ta shigo, wato Ɗorayi. Har ga Allah kuma bai zo mata da wasa ba, ƙaunarta yake yi da aure. Sai a lokacin ta katse shi. "Ka yi hakuri. Ni yanzu karatu nake yi ba ni da lokacin kula kowane ɗa namiji ma." Daga haka ba ta ƙara jin me zai ce ba ta shige ciki ta rufe ƙofar. "Waye shi? Ni kamar kallon sani ma nayi masa duk da a fisge ne." Tambayar Zahra kenan, Sadiya dake ƙokarin zame mayafin da ta saka ta ja guntun tsaki. "Ke kika ma kula da shi. Malama na kwaso rana ki ba ni abu mai sanyi." Murmushi Zahra ta yi tana ƙaremata kallo. "Kin kuma ja magana ba. Ke kin ga kyan da kika yi ne masha Allah? Kinga fa yadda ƙunshin nan ya kama a yatsunki. Kin rikita ɗan mutane kuma ki.... Ke! Na ma tuna waye, wallahi na gane shi. Amma don Allah me yace sunansa? Suraj ko?" Sadiya da ke kokarin buɗe firij ta zaro ruwan sanyi na roba tana kokarin buɗewa ta dube ta. "Haka yace sunansa." Ai sai Zahra ta hau murna. "Na rantse maki kin yi sa'a Sadiya, kin san kuwa waye babansa a unguwar nan? Taɓ, ai babban ɗan Alƙali ne. Gidan ƴan boko ne na ƙarshe kuma fa kar ki ce iyakar nan suka tsaya, a'a, akwai ilimin addini da girmama ɗan adam. Sannan akwai rufin asiri daidai gwargwado, shi wannan Suraj ɗin da kike gani kasuwanci yake yi bai dogara da..." "Zahra, wai zuwa na yi mu yi hirar zumuncinmu ko kuwa dai wancan sillan karan ya biyaki ki yi masa kamfen idan na zo? To kodai bakinku ɗaya?" Zahra ta yi dariya. "Ai shikenan, idan ma rabo ne zai tabbata ba sai na ɓata bakina wurin koɗa shi ba. Allah ya yi maki zaɓi." Yamutse fuska Sadiya ta yi, ta sanyo mata wata hirar daban, haka suka yi watsi da batun Suraj suka yi ta hirarsu. Yan uwan mijin Zahra suka zo nan aka haɗu don dama an ɗan saba suka yi ta hirarsu. Kwanaki biyar tsakani a yammacin ranar wata Juma'a, Sadiya na zaune tana tattare inda ta kammala yankan farcenta yaro ya yi sallama ya shigo. "Wai a na sallama da Sadiya." Daga jin sunanta da aka kira ta tabbata ƴan layi ne, koda ace ma ba su ba ne ba ita ba ta fita sai Inna ta tsawatar. Yanzun ma godewa Allah ta yi saboda Inna ta ɗan shiga duba Iyabo da ke ciwon ƙafa. "Kai, jeka ka ce ba ta nan." Ya juya kuwa ya je ya isar da saƙonta. Shiru har Inna ta dawo ba'a ƙara aike ba, sai bayan sallar Magriba ta ƙara jin sallamar yaro ya shigo kiranta. Kafin ma ta amsa Inna ta ce ya je yace tana zuwa. Bayan fitar yaron ta dube ta. "Mene ne dalilinki na korar duk wani da ya zo wurinki? A tunaninki ba za'a fassara hakan da cewa har yanzu soyayyar yaron can ke ranki ba? Ko a ganinki rashin sauraron kowa ne zai sa a gane an baƙanta maki? To ai ba ki rama ba muddin dai ba za ki ba wani damar fitowa ya aureki ba. Zamanki a hakan ba zai haifar da komai ba gareki sai kananun magana. Idan kin ga dama ki je ki saurari wanda ke tafe, idan kuwa ba za ki ba, ki na iya yanda kika so." Inna na kai wa nan ta miƙe ta tada kabbarar nafilarta. Jiki a sanyaye Sadiya ta miƙe, ba ta taɓa ganin Inna ta ɓata rai sosai kamar na yau ba wannan dalili ya sanya ta bin umarninta amma daga ita sai hijab din sallar dake jikinta, takalmi kawai ta zura ta fita. Ta sha mamakin ganin wanda ke tsaye, da ta tuno da yadda Zahra ke kiran waya tana zuba mata naci akan ta saurare shi kuma sai ta shanye mamakin. Ta sani ita ce za ta yi masa kwatancen gidan. Ya yi mata maganganu irin na wanda ya san me yake yi, babu ƙarya sai iyakar gaskiyarsa. Ya kuma nuna mata daidai da gini ya kammala aure ne ya kawo shi ba wasa ba. Idan ma ta yi izni zai gabatar da kansa ga Mahaifinta don a san da zamansa. Sadiya ta yaba sosai da kamala da mutsuwarsa, ta amince dai su dinga waya amma ta ce kar ya ƙara zuwa har sai ta yanke shawarar kula shi. Abin sai ya ba shi murmushi, ai a ganinsa tunda dai ta ba sa damar waya, shi kuwa ba zai hana ya shawo kanta ba ta amince da aurensa idan Allah ya nufa. *** Bayan Watanni Biyu... Ɓangaren Amarya Husna da Angonta komai na tafiyarmata yadda take so, gaba ɗaya soyayyar Huzaif ta ƙara ninkuwa a zuciyarta. Ta rasa ƙarfin sihirin da Antinta ta yi, amma tabbas ko wanne ne, mai azabar ƙarfi ne. Huzaif ta kula har rawar jiki yake yi idan ta nuna tana buƙatar wani abun. Har suka gama cin duniyarsu a ƙasashe uku da Alh Nuhu ya ɗaukar musu nauyin zuwa da sunan Honeymoon idan an cire zuwansu Umarah, sun je Dubai, London sai Misra kafin kuma suka dawo Nijeriya, babu abin da ya sauya daga soyayya da kulawar da yake gwada mata. Ta yi wani irin ƙiba da kyau. Fatarnan ta murje. Shi kansa ya yi kyau abin sa tsaf sai ramar babu dalili da ya yi. Ranar da suka ziyarci iyayensa, bai samu tarbar kirki a wurin Abba ba bayan gaisuwar da ya amsa mishi. Husna ce ma Abban ya ɗan ja da hira sannan ya fice daga gidan zuwa kasuwa. Mami kuwa ta rasa ina ta saka ina ta ajiye surukarta domin ita fa duk abin da Huzaif ke so, ba ta jin ƙinsa. Ta dai nuna damuwa da yanayin ramarsa. Meenat ko kallo ba su ishe ta ba asalima tana ganinsu ta shirya ta fice zuwa gidan Amira don dama can za ta je da yammacin, amma ganin su Husna a gidan ta fice a tsakar rana. Sai yamma suka nufi gidan su Husna. Zuwa lokacin Husna ta samu nutsuwa tunda dai suna waya da Innarta da Malam ɗin. Kuma tsabar kissa tana yawan tambayarsu Sadiya har takan nuna damuwar rashin samunta a waya. A lokacin Sadiya ba ta da waya don duk wani abin Huzaif ya bar burge ta, koda Malam ya siyamata wayar ba ta ko buɗe whatsapp ba iyakarta amsa kira kawai. Zuwa sannan ma ita ma ta share tambayarta hankalinta ya kwanta ganin iyayen sun ɗan saki jiki da ita musamman da Hajara ke sanar musu cewa tana ɗauke da juna biyu, sun saka a ransu dama wani ba ya haifar ɗan wani. Inna sakin baki ta yi da mamakin ganin uban ƙibar da Husna ta ƙara narkawa. Sai kuma ta yi ɗan murmushi tana amsa gaisuwarta, shi Huzaif kasa shigowa ya yi cikin gidan, iyakarsa can falon Malam suna gaisawa. "Inna na yi kewarku sosai, don Allah ina ƙara neman gafara idan na." "Ya isa Husna, komai nufi ne na Allah, ita kanta Sadiya a yanzu zancen da nake maki ta samu mijin aure. Ai matar mutum kabarinsa." Husna ta ji wani farin ciki sosai a ranta, dama ai tana son ƴar uwarta kawai dai soyayyarta da Huzaif ne ya sa ta fice a ranta. Yanzu kuwa tunda ita ke aurensa, to Sadiya ta auri duk mijin da ta so babu abin da ya yi mata zafi. "Kai amma na yi murna, Allah ya sanya alheri. Amma Inna shi ne kika aike ta gidan Kawu alhalin kinsan da zuwana?" Ta ƙarashe murya a shagwaɓe, Inna ta yi murmushi karo na biyu. Sadiya tun da ta ji daga gareta cewa Husna zasu zo gidan ta ji gaba daya ba ta da sukuni. Dole ta ƙirƙiro fita zuwa gidan Yayanta Zakari wajen Hadiyya. Inna ta fahimci yanayinta wannan yasa sam ba ta hana ta barin gidan ba. Ai sam ba ta fatan a maimaita irin wahalar da aka ci a baya kafin Sadiya ta mance Huzaif don sai da aka haɗa da roƙon Allah. Ta faɗawa Husna cewa ita ta aike ta wurin Kawunsu Jibo ne gudun kada ta ce za ta bi sahu tunda gidan Zakari babu nisa sosai da nan ɗin. Sun sha hira har bayan sallar Magriba sannan suka tafi. Malam ma bai nuna musu komai ba har Huzaif ɗin. A iyakar tunaninsa ai ba zai yiwu gaba daya su tarar masa ba ya kasa samun walwalar kowanne a cikinsu shi da Abban. Dalili kenan ya saki fuska kamar komai bai faru ba. Tsaraba leda guda suka dire musu har da na Sadiya. Sai da suka bar gidan tukunna Sadiya ta dawo. Ko kallon tsarabar ba ta yi ba don ba sa gabanta. Zuciyarta yanda gaba ɗaya ta tafi ga Suraj mai tsantsar nuna soyayya da kulawa gareta. *** "Aure? Sadiyar ce ta samu miji?" Shi ne tambayar da Hajara ta watsawa Husna ta waya. "Eh Anti, Inna ta ce komai ya wuce na bar damun kaina." Husna ta ƙara faɗi cike da wauta. Ita duk murna ta ishe ta yanzun za ta dawo alaƙar zumunci da ƴar uwarta tunda dai ta samu wani da take so. Kuma ita ma ta auri zaɓin ranta Huzaif. Ko kaɗan ba ta so ta tuna cewa ƙwace ne ta yi wa Sadiya, ta saka a rai dama can mijinta ne. "Yaushe za su turo neman auren?" Hajara ta ƙara neman haske. "Oho, ni ban ma tsaya bincikawa ba. Kawai dai Inna ta ce min ta samu miji aure za ta yi nan kusa." Hajara ta danne abin da ke taso mata ta ce. "Hakan ma ya yi daidai, Allah ya nuna mana. Na mata murna." Ta faɗi ne kawai gudun zargi daga Husna don ta fahimci lamarin ya yi mata daɗi. Bayan sun yi sallama ta kife wayar gami da zama a bakin gadonta tana maida numfashi. Kirjinta har wani ciwo ta ji yana mata duk a dalilin baƙin albishir da Husna ta yi mata wai Sadiya ta samu mijin aure. Girgiza ƙafafu ta shiga yi a fili ta ce. "Ba zai yiwu ba! Mairama sai kin ɗanɗani baƙin ciki fiye da yadda na ɗanɗana kafin na samu mijin aure. Na rantse ko zan yi yawo tsirara, Sadiya ba za ta yi aure a duniya ba da ƙuruciyarta." Tana cikin wannan yanayin aka shiga kwankwasa mata ƙofa. Kusan a fusace ta ce. "Waye?!" "Gwaggo ce ta zo" Ta tsinci muryar ƙanwar mijinta da ba ta wuce sa'arta ba, Zuhura. Da sauri ta miƙe tsaye, duk abinta tana girmama Uwar mijin nata Gwaggo don ba ƙaramin fada ta samu a wajenta ba. Domin a wauta irin na Uwargidanta Haj Nuriyya, ba ta ko damu da kowa a zuri'ar mijin nata ba musamman da ya kasance mafi yawansu ƴan ƙauyen Rano ne. Ita kuwa Hajara da kissa da kisisina ta ja mahaifiyarsa a jiki, kyaututtuka iri-iri take aika mata. Wasu lokutan ma girki na musamman za ta sanya a yi a kai mata. A nan ta ciri tuta sosai fiye da Haj Nuriyya. Duk rashin mutunci irin na Hajara ba ta taɓa yin sa ga Gwaggo ko yaranta. "Ke ki na girmama taki uwar mijin ni kuwa a baya kin so ki tunzura ni na yi wa tawa Uwar mijin rashin ta ido." Abin da Safiyya ta taɓa ce mata kenan sadda ta zo gidan ta ga yanda ta sa aka shirya garar abinci aka kai gidan uwar mijin nata. Gyara zaman ɗankwalinta ta yi ta yafa mayafi saman doguwar rigar atamfar dake jikinta ta fito. Zuhura tuni ta juya ta koma falon ƙasa. Ita ma sai ta bi bayanta. Gwaggo ce sai Zuhura, Atine ta kawo musu ruwa da lemo kamar yadda ta sanya mata doka duk sadda Gwaggon ta zo a yi mata tarba mai kyau. Fuska ɗauke da fara'a ta gaishe da Gwaggo, ita ma Gwaggon amsawa ta yi fuskarta a sake kafin Zuhura ta gaishe ta. "Kin gan mu hanya ta biyo da mu daga gidan barka na haihuwa nace bari na shigo na ga ɗiyata kafin mu wuce." 'Taki ce dai ta kawo ki.' Abin da ta ayyana a rai kenan, aikuwa can ba jimawa ta hau kawo mata ƙorafin ba ta da kudi ga bikin jikan aminiyarta ya tashi, faɗi take. "Ni ma Allah ya sa watarana na ɗauki jikana da hannuwan nan nawa." Hajara kamar mai jin kunya dagaske ta sunne kai tana murmushi, Zuhura kuwa na amsawa da ameen. Miƙewa Hajara ta yi zuwa ɗakinta a ranta faɗi take 'Idan haihuwa kike so na yi to kina yaudarar kanki Gwaggo. Ban ga ranar haihuwa da wannan ɗan naki mai shan jinin jarirai ba.' Ta faɗi ne sanin dukkan wani munanan ɗabi'u na Alh Nuhu, babu abin da ba ta sani dangane da tsaface-tsafacen da suke fita yi tare da abokansa su Alh Garzali ba. Ai ko farkon haɗuwarta da shi, aikin da suka ba su kenan. Ta dai rasa dalilin da ko a hira ba su ƙara tayar da zance tsakaninta da su Waleedah ba waɗanda har gobe ta sani suna tare ba ta da ƙarfin hana su mu'amala. Anan ta sani ta gaza. Kuma son abin duniya da ya rufe mata idanu, ta ma ɗanɗana riƙe maƙudan kuɗaɗe hakan ya haifar mata da jin cewa ko sata Alh Nuhu ke yi yana kawo wa za ta ci na cin ta. Dubu hamsin ta ba Gwaggo, Zuhura jiki da rawa ita ma ta karɓe dubu goman da ta ba ta. Gwaggo saura ƙiris ta zube ƙasa don godiya ga Hajara. Haka suka tattara suka bar gidan bayan sun ci sun yi nak da shinkafa da miyar kaji. Koda suka tashi tafiya direba ta saka ya kai su har gida ya sauke. Tana dawowa falon ta ja dogon tsaki tana toshe hanci. Can ta buɗe ta kwala wa Atine kira ta zo. "Ki tattara falon nan ki goge min a saka turaren wuta." Atine ta amsa cike da girmamawa. Ita kuwa Hajara dama babban burinta su fice ta samu damar yin dogon tunani akan hukuncin da ya dace ta ɗauka kan Sadiya da Innarta waɗanda suka zame mata ƙahon zuƙa. *** Ta kasa kallon ƙwayar idanunsa, sai wasa ta ke yi da gefen mayafi tana zuba murmushi. Shi kuwa ya samu damar ƙarewa kyakkyawan fuskarta kallo. "Ina son wannan kunyar taki. Yana ƙara fisgar zuciyata zuwa gareki." Suraj ya furta yana ɗan matsa yatsunsa wuri guda su bada sautin ƙas. Har sannan Sadiya ba ta ce uffan ba tun da ya soma batun ya matsu a yi komai ta zama mallakinsa. "Jibi war haka ai an gama tsaida ranar aurenmu nan da babbar sallah ko?" Ta ɗan turo baki. "Don Allah ni dai ka bari." Ya yi dariya. "Ok ba kya son batun? Shikenan na bari Honeyna." Ta lumshe idanu kadan tana murmushi, a duniyarta wannan sunan yana mata daɗi. Akan Suraj ta yarda ba duka maza aka taru aka zama ɗaya ba. Tana kuma ji a ranta halinsu ya bambanta da na Huzaif. Ta ma gane ƙaddararta ce a haka, shi Huzaif mijin ƙanwarta ce. Sun jima sosai suna hira kafin su yi sallama tamkar kar su rabu ya tafi. Ita ɗin ma zuciyarta wasai ta shiga gida tana jin farin ciki idan ta tuno a jibin za'a zo kawo kuɗi da kuma tsaida bayan babbar sallah matsayin lokacin bikin nasu. Malam ne ya ce ba ya son a ja lokaci, shi kansa Abba koda ya ji, hakan ya yi mishi daɗi sosai. Ya ce a karo na biyu ma ya ɗaukewa Malam nauyin kayan ɗakinta. Cikin hukuncin Allah ranar da ta kama Laraba aka kawo kuɗin Sadiya har dubu ɗari da hamsin kuma aka tsaida aure bayan babbar sallah da kwanaki. Mutane da yawa sun taya ta murna. Anti Hafsatu da Safiyya har gida suka zo da wasu cikin matan yayyunsu. Hajara kuwa washegari ta iso gidan. Fuska a sake ta taya Inna murna, Sadiya ta gaishe ta. Ta amsa a ciki-ciki tana jin wani irin tsanarta na mata yawo. Yarinya kamar aljana kullum ba ta sauyawa sai ma kyawun da ta ke ƙara zubawa. Kirarin da wata a danginsu ta taɓa yi wa Sadiya har gobe yana yawo a kanta kuma yana mata zafi, ita ta ma rasa dalilin da yasa ta kasa mantawa. 'Ka ganta kamar wata ɗawisu. Ke dai kin fita zakkah a yaran Malam Sa'adu. Matar manya, farar mace alkyabbar mata.' Wannan abu ya yi mata tsaye a rai kuma abin haushin duk sadda ta gan ta sai kirarin can ya faɗo nata. Daƙyar ta saita fuskarta ta tattara ta bar gidan don ba za ta iya wuni har Malam ya zo ba. Ta dai yi ƙarfin halin haɗa Husna da Sadiya a waya ta mata fatan alkhairi. Hajara ta ƙara nunawa Sadiya ta yi hakuri ta dawo zumunci da ƴar uwarta, dama matar mutun ai kabarinsa. Ita dai Sadiya ta amsa da toh, a duniyarta ba ta ji har abada za ta amince wai Anti Hajara da zuciya ɗaya take ƙaunarta. Ta sani zallar makirci ne. Bayan tafiyarta ne Inna ta ke yiwa Sadiya faɗa kan rashin sakin jiki da ta kasa yi ga Hajara. "Ƴar uwarki ce, tunda yanzun tana kokari wajen nuna tana so a yi zumuncin, ke ma ki manta da komai ku zauna lafiya." Sadiya da mamaki ta dubi Innarta. "Wannan saurin yarda haka Inna? Anya ba ki yi gaggawa ba? Anti Hajara fa, matar da ta dube ni gaba da gaba ta furta min kalmar tsana tun yarinta. Matar da akan kunnena ta furta ba amin ba sadda Abba ya yi kyakkyawar addu'a ga rayuwata. Inna don Allah kar ki gasƙata matar nan." Inna murmushi ta ɗan yi. "Kyakkyawan zato yana da kyau a addininmu. Babu amfanin zargi kan abin da bawa ba shi da haƙiƙanin masaniya a kai. Allah ne kaɗai masanin abin da ke cikin zuƙatanmu. Koda yanzun da biyu take yi mu yi mata fatan ya juye ya zama na gaskiya." Sadiya dai ta ja bakinta ta yi shiru, ta sani zuciyar Inna ba irin nata ba ne. Irin zuƙatan salihan bayin Allah ne da suke da saurin yarda da kuma saurin yafiya da haƙuri. Wannan yasa ta dawo da magiyar da ta fara yi ga Inna tun kafin zuwan Hajara akan ta ziyarci Gombe kafin aurensu. Inna ta miƙe ta kama hanyar shiga ɗakinta tana ba ta amsa. "Mun gama wannan batun ai Mamana, na ce ki tambayi mahaifinki. Idan ya amince sai ki bi Dada ku je tunda za ta je bayan sallar, sai ku dawo kafin auren." Sadiya ta ɗan tura baki, ta sani sarai Malam ba zai yarda ba cewa zai yi a bari har a kammala biki. Ita kuwa tana son ta je garin ta ga danginsu da ba ta sani ba don ko wancan lokacin aurenta su ma can Gomben suna biki bai fi mutum biyu ne suka zo ba cikin tsoffin sai ko maza ƴaƴan ƙanne. Haka suka juya da jimamin sauyin Amaryar da aka samu. Ba ta da tabbacin kuma Inna ta gayyace su wannan na biyun. Kiran wayarta ne ya sa ta watsar da batun zuwa Gombe ganin Suraj ne. Ɗaki ta shige suka sha hirarsu kafin daga bisani su yi sallama. Tana ajiye wayar ta ga saƙo ya shigo, ba ta da masaniyar lambar ko na waye, amma kuma tana karantawa ta fahimci Husna ce. 'Hello yar uwata. Wannan ne lambar wayata. Don Allah ki adana a wayarki. Love you. Husna Sa'ad.' Ta yi murmushi, ai ita dagaske ta maida komai ba komi ba, da haka ba ta kasance ba ai ba za ta san da Suraj ba. Kai tsaye ta adana lambar ta aikamata da amsar "Ok. *** "Zai yiwu a tsaida auren ta hanya ɗaya." Hajara ta zuba wa ƙasurgumin bokan idanu. Jira take kawai ya faɗi hanyar ita kuma a shirye take ta bi. Ba ta ji kuma ko ɗarr ba da buƙatarta da ya nuna. Ta yarda ta kuma amince ta haɗa jiki da shi duk ƙazantarsa kuwa matuƙar komai zai tafi daidai. Sai da Hajara ta shafe awanni uku a gidan Boka sannan ta fito ta tuƙa mota zuwa gidanta. A hanya ta tsaya kusan sau biyu yana kwara amai a gefen titi sannan ta tayar ta wuce. Tana ƙarasawa a gaggauce ta shige ɗakinta ta faɗa wanka. Ba ita ta fito ba sai da ta ji daidai, zama ta yi da ɗaure ƙirji tana maida numfashi sannan ta tunano zancen da Boka ya yi na ba ta tabbacin fasa auren Sadiya da Suraj a ranar da zai kasance na shafa fatiha. Dariya sosai ta shiga ƙyaƙyatawa gami da yin ƙwafa. Idanun Inna kawai take haskowa a ranar. "Baƙar munafuka, sai kin yi kukan jini akan Sadiya. Yanzu aka fara wasan. A ranar aurenku wannan ɗin ma zai fasa mu ga ta tsiya." Ta furta a fili cike da annashuwa kafin ta miƙe don sanya sutura a jikinta ran nan fari sol. *** A kwana a tashi ba wuya cikin hukuncin Allah, babbar sallah ta zo. Ana gobe sallah gaba ɗaya gidan kowannensu ɗauke da azumin arfah. Ita kuwa Sadiya jikinta gaba ɗaya a ranar wani irin sanyi ta ji ya yi ta kuma rasa dalili. Tun wayewar garin ranar take jin kasala da faɗuwar gaba. Ta kuma saka a rai ƙila ciwon cikin da Suraj yace mata ke damunsa ne sila. Inna ce ƙarfin ayyukan gidan a ranar, ba ta san meke damun ɗiyarta ba amma sanin da ta yi sam ba ta da ƙi wuyar aiki ya sanya ta yi mata uzuri. Dab da shan ruwa tana zaune tana karatun Alkur'ani ta ji shigowar Malam. Inna da ke zaune gefe ta miƙe ta shiga falonsa. Ta tsaida karatun ta ɗaga hannu ta yi addu'o'i masu tarin yawa ta shafa. Daidai sadda ta ji muryar Malam yana faɗin "Inna lillahi wa inna ilaihir raaji'un! Ya rasu? Yanzun nan?" Sai da ta ji ƙirjinta ya bada dam! Ta yi saurin dafewa, waye ya rasu? Tunaninta ya ba ta kodai ɗan yayan Malam ɗin ne da aka ce yana asibiti kwanaki biyu yana jinyar ciwon hanta ne ya rasu. Sai da wayarta ta yi ƙara ta duba ta ga sunan Zahra na yawo ta ɗaga a gaggauce amma kuma ta kasa cewa uffan. Cikin muryar kuka Zahra ke faɗin. "Sadiya kin ji rasuwar Suraj ɗinki ko? Wai tun yamma ya rasu a ɗakinsa ba a sani ba sai ..." Ba ta bari ta ƙarasa jin ta ba ta yi wurgi da wayar ta miƙe tana salati cikin ɗaga murya. Kai da ka ji ka san a gigice take. "Ciwon cikin ne ashe dai shi ne ajalin Suraj, ya azumci dukkan azumin ranakun nan, na Arfah dai Allah bai nufa zai yi shi ba. Babu abin da zan ce sai Allah ya ba shi aljanna maɗaukakiya don iyakar biyayya Surajo ya yi min." Kalamin da suka fito daga bakin mahaifiyar Suraj su ne suka ƙara raunana zuƙatan mutanen dake zaune a tsakar gidan ciki kuwa har da Sadiya wacce ta kwantar da kai jikin Safiyya tana kuka. Ranar sallah ta zo musu a hagunce. Gaba ɗaya ahalin gidansu idan ka ɗauke Hajara da Husna babu wanda bai shigo gidan su Suraj gaisuwa ba. Malam da Abba da ma wasu cikin dattawan iyayensu tare aka yi jana'iza da su. Sai yamma suka bar gidan kowa na jajantawa Sadiya gami da yi mata addu'ar samun madadin Suraj. Ta nemi ɗokin sallar da take yi ta rasa, tsoron Allah na ƙara ratsa ta. Wato ɗan adam ba a bakin komai yake ba, kwanakin biyu da suka wuce hatta da wayewar garin ranar suna maƙale da juna a waya. Tana tunano maganarsu ta ƙarshe inda yake ce mata. 'Ina sonki Sadiya, inama zan iya buɗe maki ƙirjina ki ga yadda ƙaunarki ta cika min shi. Amma ba komai, ke dai ki taya ni addu'a, Allah ya tashi kafaɗuna. Ya nuna mana auren nan.' Kafin ta yi magana ya ƙara faɗin. 'Honeyna zan kira ki idan an sha ruwa, daƙyar nake wayar nan. Na bar ki lafiya. Allah ya karɓi ibadunmu.' Wannan ita ce ƙarshen kalaman da suka shiga tsakaninsu, ko saƙo na addu'a da magiyar ya koma asibiti da ta aikamasa tana da tabbacin bai karanta ba. Hawaye masu zafi suka kwaranyo mata, ta sa hannu ta ɗauke su. Da ido kawai take bin yaran yayyunta da suka zo musu barka da sallah. Wasanninsu suke sha bayan kammala cin abinci. Ji take inama ta dawo su, ba su san wata aba soyayya ko ɗacinta ba. Rayuwar ma ba su gama tantance meke cikinta ba. Ajiyar zuciya ta sauke ta mike riƙe da kayayyakinsu da Inna ta saka su cirewa saboda zafin gari kuma kar su ɓata. Tana shiga ɗaki babu jimawa ta ji ihun yaran na yi wa Husna da Hajara oyoyo. Hajara faɗi take. "Kai ku bi min Momina a hankali mana kar ku kayar da ita." Sadiya ta yi juyi saman gado ta ɗauke sabbin hawayenta. Ta ji sadda Inna ke musu maraba har da gaisawar da suka yi. Husna ce ta soma tambayarta, ko sakanni ba ta ƙara ba ta faɗo ɗakin. Tun faruwar wancan al'amarin, sai yanzun ne suka yi ido huɗu da juna. Sadiya ta yi mata ƙuri da idanu, cikin da aka ce tana da shi bai kai ga nunawa amma kuma ta yi ƙiba, fatarnan ta murje ta yi fes da ita. 'Duk abin da ba rabonka ba ne, ba ka taɓa samunsa. Ba ki faɗa min ba, amma kin sani, ba a rasa masu tsegumi a sha'ani na aure. Ki saka a ranki dama rabon ƙanwarki ne wancan ɗin. Ni Suraj ni ne nan mijinki da yardar Allah.' Ta tuno wasu shuɗaɗɗun kalaman Suraj, sai ta tsinci kanta da murmushi lokaci guda kuma hawayenta ya zubo. Husna ta rungumeta ta saka kuka zuciyarta ɗaya, dagaske ta ji mutuwar saurayin ƴar uwarta. Tana ƙaunar Sadiya, sanadin Huzaif ne ya sa ta juyamata baya. Amma kuma ta yi murna jin cewa ita ma ta mance da Huzaif ɗin ta samu Suraj. Mutuwar Suraj ɗin ta jefa Husna cikin hali na tausayin ƴar uwarta. "To kuma ke haka ake yi? Maimakon ki taushe ta, sai ki zube ku yi ta kuka? Ya isa haka don Allah." Suka maida duba ga mai maganar, Hajara ce tsaye, ta sha adonta na wani arnen leshi da zai haura dubu sittin. Fuskarta ta sha kwalliya kai kace ba gaisuwar mutuwa ne ya kawo ta gidan ba. Sadda labarin rasuwar ya same ta ta hanyar Yaya Hashimu sai da ta kusan sakin dariya. Labari ne na bazata don ba ta tsammaci hakan ba. Ta gama tsara aikin rabuwarsu, sai ga mai gaba ɗaya ya afku, wato mutuwa. Ta tsinewa Bokanta a ranar ya fi a ƙirga saboda haɗa jiki da ta yi da shi ga aikin a sauƙaƙe Allah ya ɗauki ran bawansa. Sadiya ta kauda kai ga barin kallon Antinta tana goge fuskarta. Gaishe ta ma a yau ta kasa, ko ba a faɗa ba ta san Anti Hajara ba wani jin mutuwar Suraj za ta yi ba. Dama ba ta sa a kai ba. Kullum fatanta Allah ya tsallakar da Husna daga makirci irin na Antin tasu. "Sannu Sadiya. Allah ya ji kan Suraj. Har ina cewa Alhaji zan ɗauki nauyin kai ku Umarah? Ashe ma mutuwa zai yi." Sadiya ta dube ta dakyau, kalaman ƙarshe sun mata zafi. Sai kawai ta sauke kanta tana wasa da yatsunta. Ai mutuwa tana kan kowane bawa, lokaci kowa ke jira. Inda Suraj ɗinta ya je, dole dukkansu a wayi gari watarana sun je. Husna ta dinga tambayarta ko dama can yana ciwon cikin ko kuwa na lokaci ne, ta amsa mata kawai zuwa ya yi. Hajara kuwa chatting ɗinta take yi tana sheƙa dariya ƙarshe ma ta bar gidan wai tana sauri ana jiranta suna da walima na tsoffin ɗalibai na makarantar koyon jinya da ta yi. Husna kuwa sai wuraren ƙarfe takwas Huzaif ya zo suka tafi. A lokacin ne Sadiya suka hadu ta gaishe shi ba yabo ba fallasa shi kuwa da rawar murya ya yi mata gaisuwa ta amsa ta yi godiya duk don idanun Malam da mutanen dake gidan don har a sannan wasu cikin yaran ba su tafi ba, kwana zasu yi. Hatta da su Meenat su Radeeya da Lubna da Anti Amarya sai da suka zo mata gaisuwa. Mamin Huzaif ita ma daga baya ta zo. Zahra kuwa tun a ran farko dama da ita aka je gidan su Suraj. Ta kara dawowa har gida daga baya suka ƙara jajantawa junansu. *** An ɗauki tsawon lokaci kafin Sadiya ta cire damuwar rashin Suraj, ta sani koda ace za ta manta ba komai ba, wasu abubuwan sai a hankali. Watanni biyu da yin sallah kiran Malam ya risƙi daga Sadiya dake zaune a ɗakinta tana gugar kayanta a dalilin wutar da aka kawo. Ta kashe dutsen gugar ta bi bayan Inna ƙirjinta na ɗan bugu da sauri-sauri. Ba ta san dalilin wannan kira ba, amma tana ji a jikinta mai muhimmanci ne. Sallama ɗauke a leɓɓanta ta shiga cikin falon bayan Malam ya amsa. Durƙusawa ta yi gefe guda shi kuwa kallonta yake ɗauke da murmushi yana ƙara yaba nutsuwar ɗiyartasa, ya kuma gasƙata amininsa da ya ce ta bambanta da ƴan uwanta a fagen hankali da nutsuwa. "Yau na zo maki da albishir mai daɗi, kuma ina fatan za ki yi murna da ji." Sadiya ta ɗago kai tana duban Malam da har a sannan murmushi ne saman fuskarsa. Sai ta ji hankalinta ya kwanta. Kafin ta ce wani abu ya ɗora. "Ni da Abbanki mun yi magana, ko kuma ince ya nema maki alfarmar a kyale ki ki cigaba da karatunki. Ya ce da zarar an soma shirin zana Jamb za ki yi in sha Allahu. Sai ki shiga shiri." Ta ji kamar a mafarki, lallai wannan albishir ne mai girma da ta jima tana fatan ya kasance. Kawai sai ta faɗaɗa fara'arta, a gefe kuma hawayen farin ciki. "To mene abin kuka? Ai abin murna ne. Allah ya yi maki albarka, ya sa ki fara a sa'a." Malam ya furta ta amsa da amin. Inna ma murmushin take yi don hakan ya mata daɗi. Aure lokaci ne, za ta iya zaman shekaru ma idan Allah bai nufe ta da yin sa ba, to fa sai haƙuri. Babu abin da Sadiya ke hangowa sai cikar burinta na zama likita. Babban fatanta hakan ya kasance. Wunin ranar da ka kalli fuskarta ka san tana cikin farin ciki. *** Kwanaki suka yi ta shuɗewa zuwa satittika, watanni, har aka ci wata biyar da rasuwar Suraj. Sadiya ta yayyafawa zuciyarta ruwan sanyi, ta duƙufa karatun jarrabawar Jamb da za ta zana. A sannan sun yi walimar haddar Alkur'ani mai girma. Ya kasance makarantar islamiyyar ya koma mata iyakar Asabar da Lahadi kawai inda take zuwa karatun litattafan addini. Hakan ya sa ta kara samun lokaci sosai ta tattara hankalinta wuri guda. Ranar da zasu zana Malam ne da kansa ya kaita a sabuwar Honda da ya sauya. Da kansa kuma ya ɗauko ta suka dawo gida. Ta san dai ta yi iyakar ƙokarinta, sauran za ta bi da addu'a. Allah ma ji roƙon bawansa, sai ga sakamakon Sadiya ya yi kyau har ta wuce cutoff marks da B.u.k suka buƙata na karantar medicine. Daɗi da murnar da ta yi ba a cewa komai, Abba har kyautar sabuwar laptop ya aikomata, shi kuma Malam ya yi mata alƙawarin sauya mata waya idan ta ci jarrabawar shiga B.u.k. Duka wannan budurin da ake yi yayyunta mata dayake sun kwana biyu ba su leƙo gidan ba babu wacce ke da labari. Har lokacin zana post utme ya yi Sadiya ta je ta zana ba su sani ba. *** Kwanan watan da ya yi daidai da na fitowar sakamakonsu kuwa, ranar ta kasance na kwanaki biyar da haihuwar Anti Safiyya. Gida ta dawo wanka, Inna ke ba ta kulawa kamar ɗiyar ta haifa a cikinta. Ranar ce kuma Hajara ta zo ganin jariri da sha tara na arziƙi. Aka yi sa'a ita ma Anti Hafsatu ta zo gidan. Sadiya ta gaishe su amma fa hankali da nutsuwarta yana ga Yayanta Zakari, so take yi ya shigo ta ji ko sunanta ya fito ko a'a. "Wai Sadiya lafiya kuwa? Na ganki duk a firgice." Fadin Anti Hafsatu tana kallonta. Hakan ya sa Hajara da Safiyya su ma suka kalle ta. Murmushin yaƙe ta yi. "Lah Anti babu komai fa." Safiyya ta na dariya ta ce. "Matsoraciya, wai fa duk fargabar result ne ya sa ta yi shiru." "Result kuma? Wane irin result?" Muryar Hajara ya karaɗe ɗakin. Sam ba ta da masaniyar komai. Kafin wani ya ba ta amsa sai ga Zakari ya yi sallama, suka amsa ya ƙaraso. Sadiya ta miƙe don dama wayar tana hannunsa ya fita ne ya dawo. Farko fuskarsa ta nuna jimami, ya dube ta, gaba ɗaya sai ta ji ta karaya ƙafafunta ma suna neman kasa ɗaukarta. Sai ta ji ya fashe da dariya gami da faɗin. "Congratulations Dr Sadiya! Sun ba ki gurbin da ki ke so na Medicine." Ai sai ta gigice don murna amma fa cikin gigitar ba ta fasa hamdala ba har ta mance da wata halitta da a baya take mugun shakka a wajen, wato Hajara. Daidai sadda Inna ta shigo aikuwa ta ƙarasa da gudu ta rungume ta tana kukan farin ciki. "Lafiya?" Inna ta nemi ba'asi, nan Zakari ke shaida mata sadda Anti Hafsatu ke tambayar ko yaushe duk aka yi haka basu sani ba. A bakin Safiyya da ta ɗan yi kwanaki uku a gidan suke jin labarin wai Abba ne ya yi wa Malam maganar a bar ta ta cigaba da karatu shi ne ta ƙara zana jarrabawa. Hajara ta rasa me ke mata daɗi, ta kuma kasa ɓoye hassada da baƙin cikinta a zuci har sai da ta fiddo shi waje. "Medicine? Daɗaɗɗan burina da bai cika ba shi ne Sadiya ta samu?" Hakan da ta furta a hankali wanda ya shiga kunnuwan dukkansu ya sa suka dube ta. Sai ta share hawayen da ya zubomata wanda a zahiri ta sauya masa manufa, a baɗini kuwa na zallar baƙik ciki ne. "Sadiya na maki murna, na so zama likita a rayuwata amma Allah bai nufa ba. Don Allah kar ki yi wasa da damarki. Ki maida hankali kin ji?" Yanda ta yi maganar a sanyaye ya sa Inna jin ta ba ta tausayi, ta san irin nacin son karantar fannin Likita da Hajara ta yi amma kuma ba ta samu ba. Ta tuna duk da cewa tana takun-saƙa da ita a lokacin sai da watarana da ta ga tana lazimi za ta shige ɗaki ta tsaya ta dube ta a sheƙeƙe. 'Ke Mairamu ki sanya ni a addu'a na tsallake wannan banzan Jamb ɗin. Na ga ba laifi akwai ki da sallar dare da ibada. Ni dai ko bai kai zuci ba ki roƙa min.' Daga haka ta shige ɗakinsu. Aikuwa duk abin da zai sa a lokacin Hajara ta karya bille ta nemi alfarma a wurinta, to ba ƙarami ba ne. Kuma ba ta ƙi taya ta addu'ar ba amma komai na Allah ne. Wataƙila ba alherinta ba ne. "To ai sai ki ji daɗi tunda yar uwarki ta samu. Ƙila ita ki ke yi wa mafarkin. Kowa da ƙaddararsa. Ki yi hakuri." Anti Hafsatu ce ta ba Hajara amsa. Ta jinjina kai tana ɗan matse yatsun hannu damarta, ji take yi kamar ta yi tsalle ta shaƙi wuyan Sadiya har lahira, abubuwa da yawa suna mata raɗa na huɗubar shaiɗan, daƙyar ta haɗiye komai ta ƙara mintuna goma sha biyar a gidan sannan ta yi musu sallama ta fice. A hanya ma tuƙin kawai take yi amma fa rabin hankalinta na ga tunanin wai Sadiya ta sami gurbin karantar likitanci a B.u.k. Ba ta kula da cewa an tsaida hannunta ba a junction sai da ta yi dab da motar dake gabanta, kafin ta yi kokarin taka burki har ta kai mata wawan bugu, ita kuwa kanta ya bugi sitiyar har gilashin gaban motarta sai da ya tarwatse ta ji rauni ba kaɗan ba ƙarshe ma ta suma. Gaba ɗaya hankalinsu a tashe suka ɗunguma zuwa asibitin malam (akth) da aka sanar da su an miƙa Hajara. Sun iske ta farfaɗo an mata ɗinki a goshi. Tana kwance don har sannan kanta yana sarawa. "Hajara, sannu. Oh Allah, rai ba a bakin komai yake. Allah ya ƙara kiyayewa." Inna ce ta furta cike da jimami, sosai ta ji tausayin Hajara. Hafsatu dake waya da Safiyya da aka bari a gida tana kwantar mata da hankali gami da nuna mata da sauki sosai. Suna ajiye wayar ta matso ita ma tana yi wa Hajara sannu. Idanunta a runtse don ji ta yi kamar zantukan Inna baƙar magana ce kawai a ciki. Ta ɗan buɗe idanun karo na biyu daƙyar ta dubi Sadiya dake tsaye a gefe sai shaiɗaniyar zuciyarta ta dinga kissima mata wai murmushi ta ke yi. Sallama da shigowar Likita ya sa aka nemi gaba ɗaya su fita, har faɗa ya yi wai don me za'a bar mutum sama da ɗaya ma su shigo. Su dai suka janye jiki suka fice. "Allah ya nuna mana ki kammala karatunki ki fito a ƙwararriyar likita, hum! Ai asibiti guda zan gina maki idan na yi kudi in sha Allahu." Faɗin Zakari kenan ga Sadiya bayan sun fito waje, Sadiya ta yi murmushi kawai lokacin da take bin wasu ɗalibai da idanu, sun sha uniform din asibiti suna biye da wani babban mutum kuma ga dukkan alama likita ne babba, har suka bi wata baranda miƙaƙƙa suka wuce su ba ta bar waigensu ba. Sun yi matuƙar burgeta. Sai a sannan ma ta tsinci hirar da su Anti Hafsatu ke yi, tambayar Zakari ta yi ko Huzaif ya soma aiki. Tana ji Zakari ke fadin ai yanzun yana karɓar training na wata shida kafin ya zana jarrabawa Mdcn daga nan kuma idan ya ci zai soma aiki (Housejob) na shekara guda sai a yi ma batun service da sauransu. Ta yi kamar ba ta ji su ba, dama kusan ta ɗan san wasu bayanan na daki-daki na tsarin abin a bakin Huzaifa. Inna ce ta ba ta umarnin tafiya don ɗora girkin yamma. Sun ma ji a wurin Nurse cewa a yau za'a sallami Hajara. "Ki je ki kimtsa idan kin kammala, sai ki bi ta gidanta ki kwana biyu kafin ta warware." Sadiya ba ta san sadda ta juyo dubi Inna kamar za ta yi kuka, sai ta haɗiye maganarta don ba ta taɓa yin musu gareta, haka kuma idanun Anti Hafsatu da Yayanta Zakari ya sa ta amsa da toh. "Aa Inna, ai ba sai Sadiya ta je ba fa. Mun yi waya da mijinta wai zai ɗauke ta ne su je babban asibitin da yake ganin likita a auna masa ita sosai. Kuma a can akwai masu jinya ba sa ma buƙatar wani ko wata." Ajiyar zuciya Sadiya ta sauke don ji ta yi kamar an mata albishir da shiga aljanna. Inna ta amsa da shikenan, ta juya ita dai ta bar su a asibitin don jin ta take kamar a kan ƙaya. Tana ji sadda Yaya Zakari ke ta mita wai ya za'a yi duk ƙwarewar likitocin asibitin nan ace Alh Nuhu ya yi waɗannan kalaman. Ba ta ma ji amsar da Anti Hafsatu ta ba shi ba ta yi gaba. A hanya tana tafe ne tana ɗan murmushi idan ta tuna cewa watarana za ta wayi gari cikin asibitin nan da sunan ɗaliba. Motar Malam ta ga ta shigo, ta ɗaga mishi hannu, ya gan ta don haka ya ɗan tsaya daidai wajenta, ta gaishe shi. Ya tambayi jikin Hajara da kuma inda suke. Nan ta ce mishi Emergency daga haka ya yi gaba ita kuma ta fice titi ta samu abin hawa ta koma gida. Anti Safiyya ganin yanayi na fuskar Sadiya ya sa ta samun tabbacin jikin da sauki, ta iske ma wasu a dangin mijin Anti Safiyyar sun zo barka. Ta gaishe su sannan ta shiga hidimar ɗora girkin dare. Sai Magriba Inna da Malam suka shigo gidan bayan an sallami Hajara mijinta ya tafi da ita. *** Bayan Sati Biyu... Hajara sai safa da marwa take yi a falon Waleedah ƙawa kuma aminiyarta a yanzu, ta shafi goshinta da ya sha ɗinki har ya warke amma kuma tabon ta sani har abada ba zai ɓace ba. Ita mai tsantsar kula da jikinta, ta tsani ganin ko ɗigon tabo ya fito mata. Ba fara ba ce amma kuma koyaushe fatarnan sumul da ita tsabar kuɗaɗen da ta ke kashe wa a kansa. An wayi gari sanadin Sadiya ta samu mugun rauni. "Wai First Lady (kamar yanda suke kiranta tun aurenta da Alh Nuhu) , za ki taho mu je a ci maki uwar yarinyar can ko kuwa za ki tsaya nan ki na cizon yatsa da ba zai sa ki huce ba?" Waleedah ta yi furucin bayan ta zuƙo hayaƙin shisha ta fesar a sama. Hajara kuwa tsaki ta ja ta nemi wuri ta zauna. "Duk abin da zan mata ji nake ban rama ba Waleedah, ji nake kamar bai kai hukuncin baƙin cikin da aka ɗanɗana min ba. Ni fa ba iyakar tabon nan ne matsalata ba, a'a, kin san kuwa yarinyar nan ta samu gurbin karantar MBBS a B.u.k? Daɗaɗɗan burina Waleedah, a kan ban samu ba ƙawayena na sakandire sun min dariya sun ce dama cika baki ne. Na sha raba dare ina kuka duk sanadin rashin cikar burina. Ke bari na faɗamaki, rashin samun gurbin da nake son karanta shi ya soma sanadin biyewa Nusaiba tsohuwar abokiyar aikina na fara kula ƴan banzan samari irin nata. Yau an wayi gari wai ɗiyar Mairama ta samu abin da ni na rasa. Ki faɗa min ta ina zan samu nutsuwa da kwanciyar hankali?" "Tirƙashi! Ah dole ki ji kamar ki hadiyi zuciya ki mutu! Toh ki saka a kashe maki ƴar banza mana! Mene ne amfanin irinsu a doron ƙasa?" Hajara ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo tana share hawayen da suka zubo mata, kwanaki goma sha biyar da samun wannan mummunan labarin kuma daga bakin ɗan uwanta uwa ɗaya uba ɗaya Zakari, bai ko ji shakkar faɗin maganar a gabanta ba, bai ji nauyi ba. Bai tuna yadda ta dinga fafutukar nema ba ta samu ba, haka ya zo da kyakkyawar albishirin ga maƙiyarta. "Kin san shekarun da na kwashe ina jin tsanar matar nan a raina wai? Ai idan na kashe Sadiya na so ta huta kenan Waleedah, a'a, da ranta na fi kaunar na gasa wa Mairamu aya a hannu. Aure dai da matar nan ta so hana ni yin sa, har ta mutu ba za ta ga auren Sadiya ba. Babu abin da na fi buri a yanzu da ya wuce na ga karatunta ya ƙi yiwuwa kuma ta yi baƙin jini a idanun maza." Waleedah tayi murmushi sannan ta zuƙo shisha ta fesar. Hannu ta sa ta gyara jelar kitsonta na attach gami da cewa. "Shegiya tawan! Kin san ta kan mugunta. Yanzu dai wajen shi kike so a koma ko wani wuri ki ke da buƙata?" Hajara ta numfasa. "Wani, wanda ya fi shi hatsabibanci, wanda zai yi mana aiki ba tare da haɗa fata da ƙazamin jikinsa ba." Dariya sosai Waleedah ta kwashe da ita gami da zuba uban ashariya. "Ki ce ke ma ya maki irin nawa, ni fa daga kai masa sunan wani shu'umin bayarabe mai kuɗi nace ya shawo min kansa shikenan ya neme ni da lalata, aikuwa na kira shi na mishi tas a waya saboda aikin bai yiwu ba. Ƙarshe ma baram-baram muka yi da Bayaraben." Hajara ta yi ƙwafa. "Dama ai na so na gane yaudara ce, tunda wancan karon ai ya yi min na baƙin jinin Sadiyar, amma me ya faru? Sai ga shi ta haɗu da wancan mataccen Suraj din. Kin ga kenan na shi babu wani abu." Waleedah ta jinjina kai. Kafin ta yi magana Hajara ta ɗora. "Shiyasa tun farko na tsani aikin asirce-asircen nan, ni fa duk abin da ba zai zama dauwamamme ba sai ka na tisa aiki ba zan jura ba. Na fi gane na zuba salon makirci da kisisina, ƙazafi da mugunta iri-iri muddin haƙana zai cimma ruwa. Haka fa Gwaggo Atine ta taɓa yi min tayin wani bo...Yes! Gwaggo Atine!" Ta katse zancenta tana mai tunanowa da Gwaggon wacce har gobe ta tsani Inna da Sadiya musamman da ta kunyata a sanadinsu. "Ban gane Gwaggo Atine ba? Ke bayan ni har akwai wani na danginki da za ki iya fallasawa sirrinki?" Waleedah ta nemi sani tana bin Hajara da kallon wawiya. Hajara ta yi dariya. "Da ace kin san wace ce Atinen Mamman da ba ki ce wani abu ba. Ni na mance da ita ne gaba ɗaya tsabar ƙullewar kai. Yo matar da ke juya mijinta? Tsabar mulki da baƙar azabar da ta ganawa kishiya da mijinsu ya sa da ƙarfin tuwo iyayensa suka sa ya sake ta. Ƙarshe ma har sauya gari suka sa ya yi duk domin ita. Kuma duk bala'in nan ba ta taɓa haihuwa ba, yanzu aikin dillanci take yi har Aljeriya tana kai kayayyaki. Gwaggo fa baƙar muguwa ce ina faɗamaki, ta fi ki hatsabibanci nesa ba kusa ba." "Toh yanzu ni ma ya za'a yi ina so na je." Guntun tsaki Hajara ta ja gami da miƙewa. "Kya bari na fara magana da ita ko?" Waleedah ta yi dariya. Ta miƙe tana faɗin. "Ai shikenan." Har sun kai ƙofa Hajara ta tsaya gami da juyowa. "Akwai wancan abin naki?" Waleedah cikin rashin fahimta take kallonta, can kuma ta yi dariya. "Au, yau kuma? Ko ke fa, da ace ma tun farko ki na ɗan gwadawa da wasu damuwoyin naki sun kau. Bari na ɗauko maki da sanyinsu kuwa." Daga haka ta juya ta koma firij ɗinta ta kwaso kwalaben maganin maye har uku ta kawo mata, daidai sadda ita kuma ta buɗe jakarta aka saka mata a ciki. Motarta sabuwa ɗaya daga cikin na mijinta da yake da su wanda a yanzu ya zama mallakinta, har nan Waleedah ta yi mata rakiya.  Sai da ta ga ficewarta sannan ta koma cikin gidan da sauri ta ɗauki waya ta hau danna kira, ba jimawa a ka ɗauka. "Ta tafi, anjima zan shigo zan maki bayanin duk yadda muka yi." Daga haka ta cire wayar daga kunnenta, ta yi wurgi da ita saman kujera. *** Kasa bacci ta yi, juyi kawai take ga uban gumi da ta haɗa sakamakon mafarkin da ta yi marar daɗi, ita ba ta ma san ya za ta fasalta mafarkin ba, ta dai gan ta a wani yanayi marar dadi, ta buɗe idanunta da salati ɗauke a saman lebɓanta. Ta kai duba ga Malam, munshari kawai ke tashi shaidar baccinsa yake yi haiƙan. Inna ta share zufarta sannan ta miƙe ta shige banɗaki, ruwa ta kama ta ɗora alwala, falon Malam ta dawo, hankalinta ya kai ga agogo, lokacin ƙarfe uku da mintoci na dare. Darduma ta shimfaɗa ta yi sallah raka'a biyu sannan ta yi wa Annabi s.a.w salati. Ta karanta surorin Alkur'ani masu girma da ta rike a kanta sannan ta ɗaga tafukan hannayenta sama ta soma addu'a. Sosai ta ke roƙon Allah ya ba yaranta kariya daga dukkan mai nufarsu da sharri kowane iri ne. Ta roƙawa Husnarta shiriya kamar koyaushe kafin ta roƙarwa Sadiya fara karatu cikin sa'a da kuma nema mata tsari daga dukkan sharri. Ta jerawa Allah kirari iri daban-daban har hawayenta na ɗiga kafin ta kai ga shafawa. Haka ta zauna saman dardumar tana jan istigfari gyangyaɗi na kwasarta. Ƙarshe dai ba ta san ya aka yi bacci ya ɗauke ta ba sai jin Malam ta yi yana tashinta ta yi sallar Asuba. Haka ta mike ta ƙara ɗora sabon alwala tukunna. Washegari da safe ta aika almajirinta ya siyo mata ƙosai ta yi sadaka. Sadiya na ta shirin tafiya makaranta, a sannan Safiyya ta koma gidanta don dama wankan satittika ne za ta yi a nan kasancewar haihuwar fari ce. "Ki dage da azkar safe da yamma Mamana, ina yawan faɗamaki ki rage baccin dare. Duniyar nan sai mutum ya tashi tsaye wajen nemawa kansa kariya daga sharrin masu sharri. Ban ce wani ko wata na nufarki da sharri ba, amma kuma babu wani da ba shi da magauta komai ƙankantarsu. Ki dage da addu'a, ko babu komai ƙarin kusanci za ki samu tsakaninki da Mahaliccinki. Za kuma ki fi ƙarfin mai jin yana da ƙarfin ya zalunceki ko ta yaya." Inna ta tsaya domin ta  numfasa, Sadiya kuwa gaba ɗaya ta ji jikinta ya yi sanyi, gaskiya Innarta ke faɗi, tana da sakaci a nafilfilu da ma azkar. Ba ta manta akwai group din da take a whatsapp, wata baiwar Allah safe da maraice ba ta gajiyawa da turo musu azkar gami da tunasar da su su yi. Haka take tsallakewa ta tafi wani sha'anin na daban. Muryar Inna karo na biyu ya maido ta cikin hayyacinta. "Ki ji tsoron Allah Sadiya, duk abin da za ki aikata idan kin fita ko a gida, ki ji tsoron Allah a ciki. Idan kin kama mutuncinki, ba ki ba kowane ɗa namiji fuska ba, ire-irensu ba za su raɓe ki ba ballantana su kawo maki zancen banza. Ke dai karatu ya kai ki, domin Allah ki yi iyakarsa kar ki jawo mana abin magana Mamana. Na yarda da ke na kuma yarda da tarbiyyar da muka ba ki, ni na san in sha Allahu ba za ki ba mu kunya ba. Allah ya yi maku albarka, Allah ya shiga lamuranku. Ya shirya mini ku. Allah ya ba da sa'ar karatu." Inna na kai wa ƙarshe ta miƙe ta fito daga ɗakin tana kauda ƙwallar da ba ta san dalilin cicciko mata ba. Sadiya ita ma hawayen ta share ta miƙe tana mai ji har cikin zuciyarta da yardar Allah nasihar Innarta ba za ta tafi a banza ba. Za ta yi iyakar yin ta wajen aiki da shi. Malam ma da suke tafe a motarsa zai kai ta makarantar zuwan farko, nasiha iri-iri kusan hannunka mai sanda ya dinga yi mata akan abin da Hajara ta aikata a nata lokacin yana haska mata illolin biye wa son zuciya. Sadiya sosai take adana dukkan nasihohin iyayen nata, ta sani su na ƙaunarta matuƙa, ba kuma za ta watsa musu ƙasa a ido ba. *** Hajara a gaggauce ta ajiye wayar da ta amsa na mijinta dake sanar da ita tafiyarsa zuwa Abuja don halartar taro na jam'iyyarsu. Jira take yi kawai ya kammala maganarsa na batun atamfofi da ma kekunan ɗinki da za ta rarrabawa mutane duk don taya abokinsa kamfen wanda Uwargidansa Haj Nuriyya tuni ta yi nisa a harkar siyasarsu don ita sosai ake damawa da ita. Hajara duk ba wannan ne a gabanta ba jin Gwaggonta ta so gidan ya sa ta koge zuci-zucin ajiye wayarsa ta yi abin da ke gabanta.  Tun zuwanta gidansu ta tarar Sadiya ba ta gidan ta je makaranta kamar yanda Inna ta faɗamata ta ji hankalinta ya yi mugun tashi. Shagala ta yi a shaye-shayen da ta tsunduma a ciki yake ɗebemata kewa ta ke bacci son rai don gusar da damuwa, koda dai Gwaggon ce ma sai daren jiya Laraba ta dawo daga Nijar ta kai kayayyakin siyarwa irin waɗanda take sara. A falon sama ta iske ta zaune, ƴar aikinta Atine ta kawo mata kayayyakin motsa baki ta dage sai ci take. Ganin Hajara ya sa ta shiga gaisuwa cike da girmamawa tsabar son abin duniya ba ta ko jira ita a matsayinta na ɗiya ta gaishe ta ba. "Gwaggo kenan, sannu da zuwa." "Yauwa Autar Mama. Ki na ta nemana, nace Allah yasa samuwa ce. Ai da yake na je Ni..." "Yes Gwaggo na sani, an faɗa min. Ki hanzarta ki gama magana ce mai matuƙar muhimmanci nake son mu yi." Gwaggo Atine ta kai ƙarashen samosar hannunta zuwa baka ta cinye ta ƙara kai hannu ta ɗau wani. Hajara dai kallo kawai ta ke bin ta da shi, a duniya ba ta jin ta san wata mai hali irin nata. Matar da ke da kuɗaɗe da kadarori daidai gwargwado ita ke hannu baka hannau ƙwarya haka. Koda dai idan har a kan abin duniya ne, Gwaggo tana masifar sonsu ga shegen maƙon tsiya. Na wani na banza ne, amma fa kuɗinta kuɗinta ne. Gwaggo sai da ta ƙarashe cinye na hannunta ta kora da lemo kafin ta dubi Hajara. "Mu fara da abin da ya sa ki ke nema na Autar Mama. Daga ji kiran na san samu ne, ko mene ne dai, abu ne da ya girmi kaka. Ina jin ki." Hajara ta ɗaure fuskarta tamau shaidar babu wasa a abin da take shirin faɗi. "Na sani, kuma ke ma kin sani, mun haɗu ne akan turbar tsanar mutum ɗaya. Ko ban kama suna ba kin san ina nufin Mairamu." Fadin sunan Mairamu ya sa Gwaggo Atine ji kamar ta watsa mata garwashin wuta a ƙirji. Cikin ɗacin rai ta ce. "Hakane, a duniya idan da matar da na tsana to Mairamu ce. Kuma kin fi kowa sanin dalili." Ɗan murmushi Hajara ta yi tana ɗan matsa yatsunta da suka sha zobunan gwal suna ba da sautin ƙaƙaƙas. "Dakyau, kina da labarin Sadiya ta soma zuwa jami'a? Kuma abin da take karanta fannin da na so samu ne amma Mairamu ta yi min baƙin asirin da na kasa cin jarrabawa duk ƙoƙari da nacin karatuna sai ƴarta ce ta haye?" Ai sai Gwaggo Atine ta wani buɗe idanu a hargitse da kuma ɗan ɗaga sauti ta ce. "Me? Kambala'i! Sadiyar? Kenan Likita take karanta?! Na shiga uku! Kin ga abin da nake nusar da ku ke an akan matar nan amma kuna ganin kamar ƙage na ke mata ko? Idan akwai wacce ba ta ƙaunarku a duniya to Mairamu ce. Makirar ƙarshe ce, son kanta da nata ya yi wa zuciyarta ƙatutu. Ba za ta taɓa bari ku cigaba ba, ke ɗin ma don kin fi ƙarfinta ne amma saura duk ta bi ta shanye su. Toh wai an taɓa matar Uba mai zama da yaransa da zuciya ɗaya?" Hajara ta jinjina kai cike da gasƙatawa. Ta furzar da huci. "Hakane. Ba kuma za'a taɓa yin su ba har abada. Shiyasa nake son a wannan karon na karɓi tayinki na kai Mairamu gaban mutanenki a san me za'a yi masu ita da ƴarta. Yadda ban yi karatun abin da nake muradi ba, haka ma nake buri da son ganin Sadiya ba ta yi ba." Wani murmushi Gwaggo ta yi, a ranta faɗi take an zo wurin. Za ta mallaki kadarori ashe tunda har Hajara ta shigo tafiyarta. "Ba zan fasalta maki daɗin da na ji ba Autar Mama. Ai dama yanzu fa ba a zama, miƙewa tsayen da ake cewa ba na wani wurin ba ne sai gaban Bokaye. Ah, mun san komai." Ta ƙarashe tana kora ruwan lemo mai sanyi a maƙoshinta kafin ta dire kofin ta yi gyatsar da ta sa Hajara jan tsaki. Ta soma fusata, ita ba ta son wasa da lokaci, musamman yanzun da suke shirya kalar makircin da za su aiwatar a kan waɗancan biyun. Lura da hakan Gwaggo Atine da ta yi sai ta saita kanta. "Gobe ki ke so mu je ko kuwa yau?" Hajara ta numfasa ta ɗan saki fuska. "Ai ba a sanya, mu je a yau ɗin nan." Gwaggo ta yi dariya. "Shiryo mu je." Hajara ta miƙe ta yi hanyar ɗakinta, Gwaggo kuwa ƙwalawa ƴar aikin kira ta yi, bayan ta zo ta dube ta. "Takwara, haɗe min waɗannan a leda da su zan tafi. Idan da wasu ma a ƙara min." Atine ta amsa cike da ladabi ta ɗauka ta juya. Suna saukowa Atine ta fito a kicin ta miƙa mata leda ta karɓa. Gwaggo dai ƙara kalle gidan take yi, ji take a ranta inama ita ce mamallakiyarsa. Kai da ace tana da ɗiya ai babu abin da zai hana ta aurawa mai kuɗi irin Alh Nuhu koda kuwa Hajara ce a ciki. A cewarta ai so so ne, amma kuma son kai ya fi. *** Hajara wani irin gumi ne ke yanko mata, kawai jira take ta ji ne zai fito a bakin ƙasurgumin ƙaton da ya sha babbar riga da rawani ya yi zaune saman buzu. So take yi ko mene ne ma ya yi daidai da burinta, fatanta. Ya ba ta tabbacin yiwuwar rushe karatun Sadiya. Sai dai kuma daga lokacin da ya soma magana har ya kai aya, ba ta san sadda ta miƙe tsaye tana ɗura uban ashariya ba kafin a tsawance ta ce. "Ƙarya kake yi! Na rantse sai na ga bayan karatun Sadiya! Waye kai da za ka ce min hakan ba mai yiwuwa ba ne?!" Gwaggo a ruɗe ta ke dubanta kafin ta maida duba ga mutumin da ya gama shaƙar wannan hargagi na Hajara,shi tun da yake aikinsa ba a taɓa raina wayonsa irin yau ba. A ƙundumo masa ashariya sannan a ƙaryata bincikensa? Kafin ya ba ta amsa ta juya ta fice, Gwaggo hankali a tashe ta shiga ba shi haƙuri. A matuƙar fusace ya dubi Gwaggo. "Ki tashi ki bi bayanta! Ku je duk inda za ku je! Ba ta san ni ba! Amma ki mata albishir cewa mu zuba ni da ita! Hajara ko? Toh kuwa duk inda za ku je za ku dawo nan ku durƙusa ku nemi yafiyata! Ina nan ina jiranta!" Yana kai wa nan ya miƙe bai ko saurari magiyar Gwaggo ba ya bi wata hanya zuwa cikin gidansa. Gwaggo ke ta ban baki a mota yayin da Hajara ke tuƙi ranta a mugun ɓace, babu abin da take so yanzu da ya wuce ta ganta tana shan maganinta na gusar da tunani. "Haj Hajara, ina mai tabbatar maki da cewa yarinyar nan akwai wani haske da ke mamaye da rayuwarta a yanzu wanda ya yi mata katanga daga dukkan sharri. Zan iya rantse maki ko za ki yi yawo tsirara, sai dai ki yi nasara a wasu ababen a kanta amma ban ce maki su din ma cikin sauƙi ba. Yarinyar akwai wata ɗaukaka da ke bibiyarta, kuma..." Iyakarnan ta iya ji, daga nan ne ta ƙaryata shi. Ɓaɓatun Gwaggo ya ishe ta don haka ta daka mata tsawa gami da buga sitiyarin da ya razana ta. "Ya ishe ki haka Gwaggo! Ya isa! Ki bar ni na ji da guda ɗaya! Ki bar ni da damuwar da ke cin zuciyata! For God sake ki bar yi min wannan banzayen kalaman naki! Shi ɗin banza ne! Shi kaɗai ne malamin tsibbu da har kike tsoron kar ya cutar da ni! Ƙaryarsa don ubansa! Kuma na rantse da ace na san inda za ki kawo ni kenan da ban ɓatawa kaina lokaci ba. Aikin banza kawai! Mts!" Tana kai wa nan ta yi wani wawan U turn ta juya ta faka motarta. "Sauka maza ki bar ni! Sauka na daina ganinki a motarnan." Gwaggo da jikinta ke tsuma ta kasa cewa uffan sai rawar baki, duk gogewarta a duniya ba ta yi tsammanin za ta ji shakkar wani ba sai ga shi ɗiyar cikinta ta nawa ma amma tana tsoronta. Ta sani yanzu ko me za ta ce Hajara a fusace take ba sauraronta za ta yi ba don haka ta nemawa kanta lafiya ta fito a motar daƙyar ta ce. "Don Allah kudin mota." Hajara sai da ta watsa mata harara da idanunta da suka kaɗa tsabar baƙin cikin jiyo labarin ɗaukakar Sadiya kafin ta ja tsaki ta buɗe jaka ta fiddo dubu uku ta wurga mata. Da sauri Gwaggo ta tsince su, ta na kokarin sanyo kai ta gilashi don ta taushe ta ba shiri ta yi baya da gudu ganin yadda ta figi motar. Haɓa Gwaggo ta riƙe. "Oh ni wannan shegiyar za ta kai ni ga rami ban shirya ba. Da ni kike zancen, na rantse tunda na saka rai sai na ci kuɗinki to fa babu abin da za'a fasa. Gobe ma ina tafe zuwa gidan naki." Ita kaɗai ke zuba zantukanta kafin ta tari abin hawa ta koma inda ta fito. *** Da murmushi ɗauke saman fuskar Sadiya ta amsa sallamar ɗalibar da sati guda kenan suna haɗuwa da juna, sunanta Nudrat Mustafa. Ba ta son sakin jiki da ita don tana tsoron faɗawa hannun gurɓatattun ƙawaye amma ta kula kamar yarinyar na da nutsuwa kuma ga dukkan alamu za su yi sa'annin juna. Fara ce tas itama amma tana da ƴar ƙiba ba kamar Sadiya da take ƴar firit ba sai surar gaba da baya. Wuyanta babu rama dai. "Wash! Za ki ce na fiye naci da takura ko? Na kula kamar ba ki gama sakin jiki da ni ba. Ni kuma fisabilillah na ke ƙaunarki, ganinki nake kamar Yayata da ta rasu sanadiyyar cutar sankarar mama, Yaya Maryam. Ita ma ƴar siririya ce tubarakAllah, yaranta biyu kafin ta rasu. Daga nesa fa idan na hangoki har faɗuwar gaba nake ji wallahi don a zatona ita ce. Ki yarda mu yi rayuwar makaranta tare cikin aminci da tsoron Allah. In sha Allahu ba za ki yi nadamar haɗuwa da ni ba." Sadiya ta ji ta samu nutsuwa, ta kuma tausaya mata rashin Yaya Maryam. A fili ta ce. "Allah Sarki, Allah ya ji ƙan ta, sunan Mamana gareta." "Wow, wataƙila ma shiyasa na ji Allah y sanya min ƙaunarki. To Allah ya bamu sa'ar abin da muka zo nema." Da murmushi Sadiya ta amsa wa Nudrat da amin. Daga haka suka shiga duba abin da aka koya musu a ɗazun, ga mamakin Sadiya ita ma Nudrat akwai ƙoƙari sosai, ta kuma kula yanayin ma turancinta kamar ba na ƙasarnan ba ne. Kamar ta tambaye ta daga ƙasar da ta fito ko kuma ta yi karatu a baya sai kuma ta share kar shishshigin ya yi yawa daga farawa, ta bari da zummar ai za ta sani watarana. *** Tun sadda ta ji labarin komawa karatun Sadiya ta dawo cikin hayyacinta, ta farka daga baccin da take yi a baya. Dagaske ta taya ta farin ciki har a ranta, amma kuma ta soma gane ba ta da wayo. Makahon son da ta ke yi wa Huzaif na ko a mutu ko a yi rai sai ta aure shi, shi ya zama babban dalilin da ta sa ƙafafunta ta ture batun karatu a rayuwarta. "Mijinki ɗan boko na ƙarshe Husna, amma ki yi wasa da damarki ki ƙi maida hankali ga karatu. Ko sakandire fa ba ki kai ga kammalawa ba. Ina jiye maki halin maza a can gaba. Ai ko ba don ki yi aiki ba, ace ki na da takardunki. Amma tunda haka kike ganin ya fiye maki shikenan, Allah ya ba da sa'a." Ta tuna kaɗan daga cikin maganganun da Anti Hafsatu ta yi mata farkon zuwanta gidan tana Amarya kafin ma su kai ga tafiya Umrah. Kawai sai ta ji hawaye, ta shafi cikinta da ya ɗan soma girma, watanninsa huɗu. Ta ina za ta fara karatu yanzu? Wayarta dake gefe ta sa hannu ta ɗauka ta lalubo lambar Antinta ta danna kira. Ƙara uku a na huɗun ta ɗaga. "Hello, Momina ya ne? Ba dai jikin ba ne ko?" Furucin da Hajara ta soma kenan ganin ɗazun da safe sun yi waya. "Antina, ina son komawa skul ni ma." Tana jin ajiyar zuciyar da Hajara ta saki kafin cikin sanyin murya ta ce. "Saboda Sadiya ta koma ko Momina? Dama ban faɗamaki ba tun a baya ki cigaba da karatunki ki ka nuna min bakya so. Ni kuma a duniya kin fi kowa sanin ba na son abin da zai takura rayuwarki." "Anti sai da ta koma ne na ji ni ma ina son komawa. Na gama tunanina, nan gaba kar Yaya Huzaif ya guje ni saboda rashin ilimi mai zurfi." "Shi ya ma isa? Ke tun aurenki da shi kin ga daidai da daƙiƙa ya nuna maki yatsa ko ya bi ki da kallon banza? Faɗa min na ji ko akwai sadda hakan ya taɓa faruwa?" Husna ta yi shiru cikin nazarin zantukan Antinta Hajara, da gaskiyarta, tun aurenta da Huzaif bai taɓa ko ɗaga murya sama da nata ba, ita abin har kunya da tsoro yake ba ta idan sun shiga cikin jama'a. Rawar jiki ya ke yi gun hidimta mata, ta sani ko batun karatun nan ba ta ma shakkar tunkararsa da shi saboda tana da yaƙinin ba ma zai ce a'a ba. Ba ta taɓa zuwa da zance ya ce ba zai yiwu ba. Har wataran tana so ta ga sun yi faɗa irin na mata da miji ya yi mata ɗan fushi amma duk yadda za ta buga sai dai fa ta ga yana ba ta hakuri da magiya. Jikinta ya yi mugun sanyi. "Anti bai taɓa ba, kuma ni abin ma yana ban mamaki. Anti don Allah dagaske sona ne ya yiwa Yaya Huzaif yawa da har ya ke kasa hukunta ni akan komai? Komai fa zan aikata daidai ne a wurinsa." "Toh mene ne son idan ba hakan ba Husnata? Hakan da yake maki shi ne son ai. Ke ki bar min wannan magana kin ji ko? Ni dai na sani aikin da ke kan Huzaif ina rantse maki har abada kin fi ƙarfin wulaƙanci a wurinsa. A kanki zai iya fito-na-fito da kowa a duniya ciki kuwa har iyayensa. Don haka ki saki jiki ki ci karenki babu babbaka kin ji ko?" Husna ta ji ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta kasa magana. Ta sani dagaske kam Anti har wasu magunguna ta ba ta ta sha da ma wasu layu da ce ta bar su da'iman a tsakanin katifarta da falankin gado. Duka ta aikata hakan amma a mugun tsoroce, sai dai ta nuna mata duka wadannan fa ba wani abu bane sai na kore shaiɗan a shimfiɗarsu. Ƙarshe da ta matsa da tambaya ta dube ta tsakar ido ta ce muddin dagaske tana son Huzaif ya ƙaunace ta su yi zama na lumana toh har abada ya kasance ita ke gyaran ɗakin kwanciyarsa kuma kar ta sake ta cire layar da ta ba ta. Har ce mata ta yi ba wannan ne kaɗai aikin ba, an mata wasu zafafa amma kuma wannan ɗin shi ne sirrin shimfiɗarsu. Duk ranar da ta cire shi, to ta tabbata zai tsane ta a shimfiɗa koda bai fasa rawar jikin yi mata sauran abubuwa ba. "Momina kin ga ki cire komai a ranki, batu kuma na karatunki za ki yi koda a bangon duniya ne. Ke dai yanzu ki bari ki haihu lafiya kin ji ko? Ni da kaina zan yi wa Huzaif din zancen. Yanzu ina hidima da jama'a ne kin san gangar siyasa ta buga ba zama muna aikin taya Alh Garzali kamfen, zan kira anjima idan na sallami matan nan." Tana kai wa nan ba ta jira Husna ta ƙara uffan ba ta katse kiran, Husna kuwa kasa motsi ta yi. Kirjinta kuma ya ƙi barin bugu, ta fa tuna har yanzu akwai layu a ƙarƙashin shimfiɗarta da Huzaif. Sai ta ƙara tsorata, to kodai idan ma babu su sakinta zai yi? Mene ne kuma makomar wannan aikin da ta yi? Ba ta manta akwai sadda suka je gidan su Huzaif din, Maminsa da kannensa suka ga yadda yake ta rawar jiki da ita. Tun Mami na kawaici har ta ɓata rai ta ce ya tashi ya wuce idan a wuni sai ya dawo ya ɗauke ta. Abin kunya sai da ya dubeta saboda ya ji ita mene ne ra'ayinta, ta gyaɗa masa kai kafin ya yi musu sallama ya tafi. Tana ji tun lokacin ne Mami ta sauya mata, duk wani rawar ƙafa da take yi da ita idan ta je gidan ta daina, wajen Anti Zulfa'u ne take samun tarba mai kyau. Amma dama Meenat ko gidanta ba ta taɓa takowa ba. Sau ɗaya ta taɓa kawo mata dambun nama daga Mami, shi ma a waje ta tsaya ta ba Maigadi ya shigo da shi. Abba kuwa koda ace bai so auren ba, ba ya nuna mata komai, har tambayarta yake yi ko akwai wata matsalar, amma tana gani bai ƙarasa sakin jiki da Huzaif ba. Husna abubuwan suka yi mata yawa a kwakwalwa, ga nauyi da ƙirjinta ya yi sai kawai ta shiga zubar da hawayenta fiye da wanda ta soma a farko. Tana so ta fidda layu da suke ƙasan katifarta amma kuma tana ji a jikinta dagaske Huzaif zai juyamata baya a shimfiɗa. Idan kuwa namiji bai ƙaunar haɗa shimfiɗa da kai, ai duk sauran abubuwan da zai biyo baya a banza. "Zan yi ta istigfari, amma ba zan iya cire wa ba. Allah ka sani ina son Yaya Huzaif, Allah ka sanya masa soyayyata ninkin wanda nake yi masa a zuciya." Ta furta hakan a fili kafin ta share fuskarta ta miƙe ganin yamma na ƙara yi ba ta kuma ba ƴar aikinta umarnin abin da za ta girka na dare ba. Son jiki da sangarta irin na Husna ya sa ko ruwan zafi ba ta dafawa sai dai ƴar aikinta ta yi. Sai dai har gobe bisa umarnin Hajara, ba ta taɓa bari ta shigar mata turakar miji ba, ita ke gyarawa duk domin kar a hango binnin da suka yi a ƙasan katifarta. *** Yau tun sha biyu Sadiya suka fito daga aji, ba kuma za su ƙara shiga ba sai misalin ƙarfe huɗu na yamma. Magiya Nudrat ke mata akan kar ta yi zaman yini a makaranta ta bi ta zuwa gidansu dake unguwar Kuntau ta gaida Nenenta. Faɗi take. "Allah kuwa tana ta so ta ganki, kuma ni na tabbata Inna ba za ta yi faɗa ba. Don Allah yau ki zo mu je tare." Sadiya ta yi shiru jikinta a sanyaye, ita fa ba ta son shishshigewa Nudrat Yaqoob don a iya sati ukun da suka jera su na karatu tare, ta fahimci duk inda yarinyar ta fito, to fa gida ne na masu hannu da shuni da suka fi nasu nesa ba kusa ba. Ko daga irin hotunan da ta ke ɗorawa a whatsapp status na yan uwanta, wasu ma ta ga suna tsantsar kama ya ci ta gane daga inda ta fito. Ta zo gidansu sau ɗaya an kawo ta a mota, Malam da Inna duk sun gan ta, kuma sun yaba da hankalin yarinyar, ita ce dai har a yau din da suke zancen ba ta ziyartarsu ba. "Na sa ki dogon tunani don na ce ki bi ni gidanmu yau ɗaya Triple S?" Faɗin Nudrat kenan. Dama sunan da take kiran Sadiya da shi ne tun sadda ta ji duka sunanta ya fara da harafin S, wato Sadiya Sa'ad Shagari. Sadiya ta girgiza kai tana ɗan yaƙe kafin ta yi magana Nudrat ta miƙe tana gyara zaman jakarta fuska ɗaure. "Shikenan, na gane. Alaƙarmu alaƙar ɓangare guda ce, ni kaɗai ke ƙaunarki da zumunci fisabilillah. Na gode. Sai na shigo anjima." Daga haka ta soma tafiya cikin sauri Sadiya ta bi ta suka jera ko kallonta Nudrat ba ta yi ba don haka ta ce. "Ke kin fiye ɗaukar zafi, to ki yi hakuri." Ƴar harararta ta yi kafin su yi wa junansu murmushi daga haka suka ƙarasa waje don direban dake kawo Nudrat ya yi nisa tunda ya sani sai shida na yamma yake dawowa ɗaukarta. Napep suka hau har suka kai Kuntau suna ta hira, bai sauke su ba sai da Nudrat ta yi mishi kwatance har gaban wani tafkeken gida wanda iyakar tsari ya tsaru. Tun ma daga waje ya burge Sadiya fiye da gidan Anti Hajara, tunaninta kuma ya za'a ga ciki. Nudrat ta sallami mai napep suka nufi ciki bayan sun gaisar da Maigadin. Sadiya dai tana ta bin Nudrat har suka ƙarasa wata ƙofa ta danna ƙararrawar dake jiki ba jimawa aka buɗe. Wani matashi ne wanda da kaɗan zai girme su, Sadiya ta taɓa ganinsa hotonsa wajen Nudrat wai yayanta da take bi ma ne, sunansa Muneeb. Ƙin matsawa ya yi ya ba su hanya sai ma buɗe baki da ya yi cike da mamaki yake kallon Sadiya. "Whoo, yau wace rana ga Triple S ɗin Jerry a gidan nan." Nudrat jin ya kira ta da Jerry ya sa ta kai mai duka ya kauce yana dariya, ita Sadiya murmushi kawai ta yi tana fadin. "Ina wuni." Muneeb ya yi murmushin shi ma gami da nuna Nudrat da yatsa. "Kin ji yanda ake yi ko? Gaisuwa, Triple ki koyawa ƙawarki." "Wai Muneeb a rufe ƙofar nan haka mana, ko sai ƙudaje sun shigo min?" Sadiya ta ga fuskarta karo na babu adadi a wayar Nudrat, ta kuma taɓa gaishe ta ta waya. Gani dai na ido da ido sai a yanzun ta ga Nenen Nudrat. Sai ta ga a fili ma ta fi tsantsar kama da Fulanin, daga rashin girman jikinsu har ma da hasken fata da siririn hanci har baka masha Allah. Tana zaune a falon ciki doguwar riga marar nauyi ta rufe kai da hular rigar. Nene na ganinta ta saki fuskarta sosai. "Yau ashe ɗiyata ce a gidan. Sannu da zuwa Triple ɗin Nudrat." Sadiya cike da jin nauyi ta ƙarasa ta russuna ta gaishe ta. Nene ta amsa tana tambayar su Inna da Malam abin mamaki har Husna da su Anti Hafsatu sai da ta tambaya. Mamaki ya sa Sadiya kallon Nudrat baki sake, Nudrat ta yi dariya sai ta kauda kai ta amsawa Nene. "Ya na gan ku ko har an tafi yajin aikin?" Sai a sannan ma Sadiya ta tuna ashe wai ana raɗe-raɗen Malamai za su tafi yajin aiki, maganar ma ɓata mata rai take. Nudrat ce ta ba Nene amsa da cewa suna da tazarar lakca ne sai ƙarfe huɗu za su shiga, dalilin kenan da ya sa suka taho. "Kun kuwa yi dabara, toh ku shiga ku yi sallah sai ku fito ku ci abinci." "Ni fa Nene shiyasa ba zan iya makarantun ƙasarnan ba, daga farawa har sun soma tunanin tafiya yajin aiki? Mts. Gaskiya akwai cutarwa a lamarin. Shiyasa ban so karatun Jerry a garin nan ba don dai Baffa ba zai bar ta ta koma ba ne." Muneeb ke zancen yana yarfe yatsu. "Ni dai Nene ki ce ya daina kirana da Jerry kamar wata namiji! Allah kuwa ba na so!" Nudrat ta furta a zafafe tana turo bakinta, Muneeb ya harareta. "Idan ba sunanki kenan ba me za'a yi kiranki? Ke da ba ki da aiki sai faɗa da Imam kamar masu ganin hanjin juna." Za ta ƙara magana Nene ta ɗaga musu hannu. "Ya ishe ni haka. Nudrat tashi ku je ku yi sallah, a gaban Sadiyar ma sai kun raba hali. Kai da Imam din ai baku da bambanci tunda ba ragawa juna kuke yi da ita ba. Allah ya shiryeku." Sadiya ta amsa da amin ƙasa-ƙasa tana murmushi, Nudrat ta ja ta suka nufi wani ɗan corridor, ɗakin da suka shiga komai na cikinsa fari da green ne wannan ya ba Sadiya tabbacin ɗakin Nudrat ne, a iyakar zamansu tare ta kula tana ƙaunar tufafi da ma komai da ya danganci kalar kore. Ɗakin ya tsaru tsaf sai ƙamshi ke tashi. Nudrat ta nuna mata hanyar banɗaki ta shiga ta ɗauro alwala kafin ta fito ta mata shimfiɗar darduma hakan yasa tana zura hijabinta ta tayar da sallah. Ita kuwa dalilin ba ta da sallah ya sa ta rage kayan jikinta ta shige wanka. Can ta fito lokacin ma Sadiya har ta ninke abin sallah. Doguwar riga marar nauyi ta saka ta rufe kanta da hula, duk yadda ta so Sadiya ta watsa ruwa ko don rage zafin ranar da ake yi ta nuna sam ba za ta yi ba. Haka ta rabu da ita. Suka fito suka iske Nene ta sanya an zuba musu abinci, lokacin Muneeb ya bar falon sai Nene dake wayarta cikin harshen fulatanci wanda daga Nudrat har Sadiya suna ji sai dai ba su mayar da hankali ga tattaunawarta ba. Sadiya duk jin ta take a takure don haka ma kaɗan ta ci lafiyayyar shinkafar da ta ji kaji da haɗi duk kuwa da daɗin da ta yi mata a baki. Tana ajiye cokalin Nudrat ta harare ta. "Me kike son cewa? Ba dai kin ƙoshi ba?" Kafin ta kai ga ba ta amsa wani sassanyan ƙamshi ya mamaye falon, sai ƙarar taku ƙwas ƙwas ƙwas da ya soma sauka a kunnuwansu, kafin wata murya mai surkin harshen Hausa ne, fillanci ko kuwa turanci, ba ma Sadiya ta tantance ba, ya yi dirar mikiya a kunnuwanta. Waya yake amsawa amma sai da ya fidda wayar a kunne ya yi musu sallama suka amsa ya ƙaraso, har lokacin kanta yana ƙasa ba ta juya ba. Shi kuwa zama ya yi a saman kujera ta ba shi baya. Nudrat ke kallonsa, har Sadiya ta soma ƙoƙarin miƙewa da zummar ta ƙoshi Nene ta dakatar da ita. "A'a Sadiya me kika ci? Ba fa na son baƙuntar nan, ai an zama ɗaya duk gida ne nan ɗin. Zauna don Allah ki ci, ko kuma Nudrat tashi ku shige ɗaki za ta fi sakewa a can." Sadiya ta buɗe baki za ta yi musu Nene ta hana ta, dole suka bi umarninta, ta kula Nudrat so take ta yi wa yayan nasu magana amma wannan doguwar wayar tasa ta sanya dole ta kwashi farantin ita kuwa Sadiya ta ɗauki ruwa da lemukan suka nufi ɗakinsu Nene na fadin Nudrat ta dawo ta tattara inda ta zubar tunda ita ba ta iya ci ba tare da ta yi ɓari ba. Sadiya ko kallon wanda ke zaune ba ta yi ba, ta dai ji a jikinta wataƙila shi ne Yayan Nudrat da ta ke yawan zuzuta shi da koɗa shi idan ta ɗora hotonsa a whatsapp status, wato Hamma. Sunan kawai da ta san tana rubutawa a ƙasan hoton kenan, wataran ta ce My Hamma, wataran Hammanmu da dai sauransu. "Na so kun gaisa da Hammana, amma bari mu gama sai mu je. Ina yawan ba sa labarinki, har tambayata yake ina Triple ɗita. Kusan fa duk sadda ya zo sai na ba shi labarinki." Sadiya ta yi dariya. "Na shiga uku, ke kowa sai ya san ni wai? Ni har kin sa na ji kunya ma." Nudrat ta dara ita ma. "Toh ai zumuncin kenan. Nawa su sanki, naki su san ni. Ni ma da na je gidanku ai tashi guda Inna ta faɗi sunana. Zahra ma ga shi kullum sai mun gaisa da ita ta whatsapp." "To ban da gulmata dai." Nudrat ta dara sannan ta kurɓi ruwan lemo a cikinta, mikewa ta yi ta shige bandaki ta wanko hannu ta fita tana fadin. "Bari na je na tsaida shi kafin ma ya fice." Sadiya dai da ido ta bi ta, ita ma ji ta yi ta ƙoshi hakan ya sa ta shiga tattara wajen da Nudrat ta ɓata, da gaskiyar Nene, ta kuka Nudrat idan ta ci abinci sai ta yi ɓarinsa, abu daya ne dai, matuƙar da yatsunta take ci ba cokali ba ta ga ba ta zubarwa a ƙasa. Kowa da irinsa dai. Tsincewa ta yi ta zari tissue dake ajiye a saman dirowar gado ta zuba a ciki. Ita ma hannun ta wanko, ta fito ta gyara zaman ɗaurinta da ya kunce tana kai duba ga agogon dake rataye a bangon ɗakin. Ƙarfe biyu da mintuna arba'in. Suna da sauran awa ɗaya da mintoci kenan. Ruwa ta dauka ta sha tana shirin ajiyewa sai ga Nudrat ta faɗo ɗakin da gudu-gudunta. "Triple, taso muje ku gaisa da Hamma. Ya ce shi ma yau sai ya gan ki." Sadiya ta ɗan fiddo idanu amma ba ta ce uffan ba dalilin magiyar Nudrat, a dole ta miƙe ta yafa mayafin da ta zo da shi saman doguwar rigar atamfar jikinta suka fito. Yana magana da Nene amma shigowarsu ya sanya shi maida hankali gare su. Da ido ya bi matashiyar da aka kira da Sadiya wato Triple S ɗin Nudrat. Ba laifi akwai dai kyau ga kuma alamu na nutsuwa tattare da ita. Ta gaishe shi cikin girmamawa ya amsa fuska a sake. Ita ma sai ta ga a fili ya fi kyau sosai fiye da hotuna, don kamar ma rage kyawunsa wayar ta yi. "Kin ƙwace min Nudrat, ba ta da aiki sai hirarki. Yadda ta damu da ke ma yanzu ba ta wani damu da ni ba." Sadiya ta yi murmushi. "Ba haka ba ne." Shi ma murmusawar ya yi, yana jin hatta da murmushinsa na ɗan burge shi. "Ai shikenan. Ya karatu? Allah ya baku sa'a. Sai a ƙara mayar da hankali." "In sha Allah. Amin. Mun gode Hamma." Fadin Sadiya cikin girmamawa. Ya ƙara dubanta sai kuma ya kauda kai. Ɗakin suka koma suka bar shi da Mahaifiyarsa. Tun shigar su ɗakin Nudrat ke ba ta labarin Hamma, wai shi ne na biyu a ɗakinsu bayan babbar yayarsu da ta rasu wato Yaya Maryam. Bai yi aure ba amma a cewarta a na dab da kai kuɗin aurensa. Sadiya ta yi masa fatan alheri. Nudrat tace sosai ya shaƙu da Yaya Maryam don ya fi su kusanci da ita sosaima, kuma akwai tazarar haihuwa tsakaninsu don sai da Nene ta haihu har sau biyu suna rasuwa sannan ta haifi Qassim, Muneeb, Nudrat sai Jafar. Yanzun Nudrat kaɗai ce mace a cikinsu wannan yasa suke ji da ita sosai. Ƙarfe uku da rabi suka yi shirin komawa makaranta bayan sun duba karatunsu, Nene ta dakatar da su ta ce su fita tare da Hamma wanda zai yi Zoo road sai ya sauke su kafin ya wuce. Nudrat hakan ya yi mata dadi idan ka cire Sadiya wacce har ƙirjinta ke bugu. Na farko ta biyo Nudrat ba da sanin Innarta ba, ga laifi na biyu kuma za ta shiga motar Yayanta. Tsoronta kar a je wani a gidansu ya gan ta, abinka da wacce irin hakan ba ta taɓa aikata shi ba. Idanunta ya yi ƙwal, ta ji kamar ta cewa Nene ta bar su su tafi amma kuma ba za ta iya ba. Haka ta zauna jiki a sanyaye har Hamma ya shigo Nene ta ce ya sauke su. Ya amsa da ok ya yi gaba ya ce su taho. Ledar da Nene ta ba ta wanda ta karɓa daƙyar don har sai da Nene ta nuna ranta ya ɓaci sannan, ita take riƙe da shi a saman cinyarta sai ko jakarta na zuwa makaranta, tana son buɗewa ta sanya a cikin jakar amma kuma kunya take ji daga karɓar abu da zama a mota a ga tana cusa shi a jaka kamar me jira. Tana ji Hamma da Nudrat dake zaune a gefensa a mazaunin gaba suna ta kwasar hirarsu tana mitar ita ba ta so ya tafi Gombe saboda jimawar da yake yi a can. Ta ƙara da faɗin. "Haka kawai don yana wani taƙama shi wai Prince ne sai ya dinga wani wahalarmin da Hammana. To ai mu ɗin ma Prince ka ke a wajenmu." Ta ƙarashe tana ɗan turo baki. Hamma ya yi ƴar dariya. "Ke daɗina da ke sai yawan rigima. Kamar ba ki san yadda muke da Maina ba. Kodayake zan ɗauke ki mu je wataran. Triple, ba kya magana kin yi shiru." Ya ƙarashe yana kallon Sadiya ta madubi kasancewar daga bayan kujerarsa take a zaune. Ita ma aka ci sa'a ta ɗago ta kalle shi. Kauda kai ta yi tana ɗan murmushi. Nudrat ita ma ta juyo ta kalle ta. "Nan fa da kake ganinta kamar a ce mata arr ta gudu haka take ji. Hamma za ka yi mamaki idan na ce maka a ruɗe take." Sadiya ta ɗan fiddo idanu ta kalli Nudrat, irin kallon ya aka yi ki ka gane? Nudrat ta ɗan murguɗa mata baki. "Eh mana, ki ce min ba haka ba." "Ruɗewa kuma? Na me toh?" Ya ƙara faɗi da Hausarsa wacce ba ta nuna ba sosai. "Faɗan Inna take tsoro tunda ta je gidan Dodanni mun cinye mata nama. Kuma Allah na sani sharrinta ne kawai, Inna ba za ta taɓa cewa wani abu idan ta san gidanmu ta je ba. Ita ce dai farar kura kawai." Sadiya ta haɗe fuska tana hararar Nudrat dake dariya, a gefe guda kuma kunyar Hamma ta ji ya mamaye ta. "A'a Jerryn Muneeb, Triple fa ta fi ki gaskiya. Duk wata ɗiya ta gari tana shakkar iyayenta, da kuma aikata abin da ta san zai zame musu abin magana. Wasu za ki ga daga irin wannan suke faɗawa wata hanyar ta daban. Wani bin a karɓi tayin saurayi zuwa shan ice-cream, ko kuma a raka ƙawaye, kinga mafarin ɓarna ya samu. So ban ga laifinta ba, hakan ma yana da kyau. Daga yanzu ma kar a ƙara biye-biye wani wuri ba tare da an sani a gida ba. Har ke nake nufi." Ya furta yana duban Nudrat, ta amsa da toh sai dai a ganinta mene ne ciki don ita ko Sadiya sun je gidan ɗayansu? Ita ba ta ga wani abu ba. Sadiya kuwa sosai ta ji Hamma ya burge ta yadda ya fahimce ta. Har cikin makarantar ya shigar da su ya nemi wuri ya tsaya. "Toh yaran Nene, a maida hankali ga karatu. Iyakar karatun please, ban da shirme da shiririta." "In sha Allah. Mun gode." Sadiya ta amshe, Nudrat ma ta bi sahu. Ya bi Sadiya da kallo har ta fice a motar kafin ya kauda kai gami da sauke ajiyar zuciya. Ba ya son gasƙata abin da zuciyarsa ke raya mishi game da ita. A iyakar saninsa so guda ɗaya ne, kuma Najma yake yi wa shi. 'Ita tana maka son da ka ke mata?' Wani ɓangare na zuciyarsa ya watsa mishi tambaya. Ya kawar da wannan tunanin ta hanyar jan guntun tsaki gami da dakatar da Nudrat, a aljihu ya fiddo dubu uku yace ta ba Sadiya. Ta kuwa washe haƙora tana godiya kafin ya ja mota ya yi gaba. Sadiya baki sake ta ke kallon sabbin dubu ukun da Nudrat ta saka a tafin hannunta, ta yi saurin kai hannu za ta jawo ta don ta mayar amma Nudrat ta matsa da sauri. "Aa Nudrat, ba zan karɓa ba." Haka ta dinga magiya amma Nudrat ba ta ko kalleta ba. Ganin za ta ɓata mata lokaci kuma tana son gabatar da sallar la'asar kafin su shiga aji sai kawai ta zura a aljihun doguwar rigar atamfarta da zummar idan sun fito lakca za ta mayar mata. Amma har suka rabu Nudrat ba ta karɓa ba. Inda Sadiya ta ji dadi yadda Inna ba ta mata faɗa ba sai dai cewa da ta yi ta dinga kula kuma ta riƙe kanta, ba ta son zaƙalƙalewa mutane musamman masu hannu da shuni haka. Malam ma ya abin da Nene ta bayar, ya kuma ji dadin yadda Sadiya da Innarta ba sa ɓoyewa mishi komai, ko babu komai zai ƙara sanin ɗiyarsa da mutanen da take mu'amalanta. *** A kishingiɗe take a falonta, su uku ne zaune a cikinsa. Waleedah, Azeema sai ko ita Hajara cikon ta ukun. Gasassun kaji suke ci suna korawa da lemo ita kuwa tana aikin latsa wayarta. Sallamar ƴar aikinta wato Atine ce ya sa ta ɗago kai, Azeema suka amsa. "Lafiya?" Hajara ta faɗi a zafafe tana kallonta don ba ta ga dalilin da za ta zo ba a neme ta ba. Matar ta zube jiki na rawa ta ce. "Ki yi hakuri ranki ya daɗe. Dama Gwaggo Atine ce ta zo ta nemi alfarmar na ce tana so ku yi magana mai muhimmanci. Ta ce don Allah ki ba ta damar nan." Hajara ta ja dogon tsaki. A fili ta ce. "Wato matar nan na rufe ta daga kirana na kuma jaddada mata matuƙar ta sake sauya lambar wani ta kira ni sai na manta wace ce ita a wurina na zagi uwa da ubanta, shi ne ba ta daddara ba ta zo gidana?" Ta yi ƙwafa mai ƙarfi sannan ta dubi Atine. "Je ki ki ce ta ƙaraso. Yau zan mata wankin babban bargo!" 'A zumuntarku.' Cewar Atine a kasan ranta, a fili kuwa toh kawai ta amsa kafin ta miƙe tana ficewa zuwa falon ƙasa. Ta iske Gwaggo Atine a zaune ta sha wani uban leshinta mai shegen nauyi kalar na inyamurai, fuskarnan sai maiƙo take yi amma kuma bakin an shafe shi da jan jambaki. Dariya ce ma ta kusan suɓucewa Atine sai ta danne ta ce. "Yauwa ta ce ki hau." "Ok." Gwaggo Atine ta furta don ita a wasu lokutan jin ta take kamar wata baturiya. Ta dai yi karatunta har sakandire, tsalle-tsallen da iyayen suka kula tana yi ne yasa aka yi mata aure don kanta ya fiye rawa a lokacin. Da rawar jiki ta haye saman ta shiga falon da sallama. Waleedah da Azeema suka dube ta kafin su dubi junansu su fashe da dariya har da cafkewa. Gwaggo Atine kuwa ta kalle su a sheƙeƙe, ta san dai duk kusancinsu da Hajara ba su kai ya ita ba. Hajara dake ƙare mata kallo cikin takaici ta ja tsaki. Miƙewa ta yi ta na fadin. "Biyo ni." Daga haka ta nufi hanyar ɗakinta, Gwaggo Atine ta bi su Waleedah da harara sannan ta bi bayan Hajara. Waleedah duk sai ta kasa sukuni, hankalinta gaba ɗaya ya tafi a kansu, to me za su yi? Babu damar sani don haka kawai ta fiddo waya ta yi dogon rubutu ta tura saƙo ta ajiye. A ɗakin kuwa suna shiga Hajara ta rufe cike da masifa ta ce. "Wai ke ba na yi maki katanga da shigo min gida ba? Ko don ba ni da karnuka? Ko kuwa don kin ga ban nuna fuskarki ga Maigadina ba ta yadda ko kin tunkaro ƙyauren zai dakatar da ke?" Ta ƙarashe tana huci da jijjiga jiki tana watsawa Gwaggo Atine banzan kallo. Sai Gwaggo Atine ta zube gwuiwa a ƙasa. "Na tuba Autar Mama, ki yafe ni. Na rantse maki wannan mutumin hatsabibin gaske ne, ya san aikinsa akasi kawai aka samu. Amma ai ba a rasa nono a ruga, ga su nan da yawa kuma waɗanda su ma sun san ta kan aiki? Ki ba ni wata damar na rantse maki ko so ki ke yi a haukata maki yarinyar can da uwarta sai an yi. Ai mantawa na yi da Zakanyar Daji." Hajara ta yi shiru tana nanata sunan ƙarshe da Gwaggonta ta fadi. Zama ta yi gefen gadonta. Gwaggo kuwa sanyin na'urar yana ta ratsa ta amma fa ba ta bar gumi ba, ita babban burinta kar wannan garaɓasar na samun kuɗaɗe daga Hajara ya wuce ta. "Wace ce ita kuma?" Wannan tambayar ta sa Gwaggo jan numfashi ta furzar cike da samun nutsuwar zuciya, ko babu komai ai an zo wajen don haka ta gyara zamanta har da tanƙwashe ƙafafu ta soma magana. "Wata hatsabibiyar bokanya ce, matar da idan ta yi maki aiki zai wahala ki isa gida aikin bai riga ki kai wa ba. Ina tabbatar maki Autar Mama za ki sha mamakin yadda za ta kassara maki rayuwarsu. Ke ni ina ji a jikina ma kukanki ne ya zo ƙarshe. Ai da ma can na so kai ki tun farko, toh matsalar gaskiya ita ba nan take ba." "A bangon duniyar ina zan je na same ta?" Kai tsaye Hajara ta furta tana kallon Gwaggo, ji take dagaske ko a ina matar take za ta je gareta matukar kwalliya za ta biya kuɗin sabulu toh me zai dame ta? Ai buƙatar ma je Hajji sallah ne. "A Mubi take." Hajara kanta ya ƙulle ta ma rasa ina ne Mubin? Kafin ta nemi ƙarin bayani Gwaggon ta ɗora. "Can Adamawa." "Kin kuma tabbatar da ba zan yi zuwan banza ba?" Dariya Gwaggo Atine ta yi. "Autar Mama kenan. Ai ba zan kawo maki gaibu ba. Saboda na ga zahiri lokacin da na yi tashen rayuwa a gidan..." "Ya isa, ban nemi ki ɗauko min tsohon tarihinki ba marar cikakken tushe. Ki shirya, a goben nan zamu wuce." Da girmamawa Gwaggo ta amsa tana washe baki. "Yauwa yanzu na ji batu, ai da zafi-zafi daman ake bugun ƙarfe. Bari na koma gida na dauki abin da zai min amfani sai na dawo nan na kwana. Zai fi kyau ace sammako muka yi." A wulaƙance Hajara ta dube ta. "A wane gidan za ki kwana ki ke nufi?" Jikinta ya yi sanyi. "Wai da a nan, kin ga zai fi mana sauƙi ko?" "Babu wajen kwananki a nan ai Gwaggo, ki tashi ki kama hanya. Ke yanzu babu kunya goɗai-goɗai da ke ki wani zo ki tattare a gidan ƴarki? Auren ki ke son kashe min mu haɗu mu durƙushe?" Gwaggo ta kama baki, abin kuma ya fi ƙarfin ta mayar da martani don haka ta miƙe kawai, ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan doka. Tana son ta nemi na mota amma tana shakkar a yaɓa mata wata baƙar sai dai kuma ta sani ba za ta iya jurar tafiya daga gidan nan ba tare da ta tatsi Hajara ba ko yaya. Don haka ta juyo tana ɗan gyara zaman ɗaurin da ta yiwa zanin leshinta a saman riga ganin zai kunce. "Toh, Allah ya huci zuciyarki dai. Amma a taimake ni da na mota. Kinga goben ma durof zan ɗauko gudun kar su tsaya neman fasinja da Asubar fari mu je mu makara." Tsaki Hajara ta ja. A fili ta ce. "Dama idan ba ki tambayi kudi ba ai ba kya ji dadi ba." Gwaggo dai mamakin yadda raini ya gifta haka tsakaninta da ɗiyar ƙanwarta take. Koda dai, ba a fushi da masu kuɗi wannan ne dalilinta na danne ɗan zafi-zafin da ta ji zuciyarta ta fara ta saka hannu ta kwashe ƴan ɗari biyar sabbi da Hajara ta wurga mata saman ɗan teburin da ke haɗe da gadonta. Godiya ta yi ta fito bayan ta musu wuri a jakarta. Ko kallon su Waleedah ba ta yi ba ta fice, ita kuwa Waleedah da kallo ta bi ta don ta karanci yanayinta, ta gane kamar ma sun shirya komai ya wuce. Hakan ba ta gasƙata ba sai bayan da Hajara ta fito fuskarta dauke da walwala irin wanda tun zuwansu ba su gan shi a tattare da ita ba. *** Tunani iri-iri babu wanda bai zo mata ba a kwakwalwa. Idan ka ture wahalar doguwar tafiyar da ta biyewa Gwaggo Atine ta yi, da kuma taka tudu da gangare da ta dinga yi har ba don ma Allah ya kiyaye ba ta kusa faɗawa wani tafkeken rami. Ga raunin da ta ji a ƙafarta dalilin faɗuwar da ta yi dab da ramin. Duka waɗannan ba su ne ke sanya Hajara ji kamar ta shaƙe wuyan Gwaggo Atine a tsakar daji ta kashe ta har lahira ba face saboda rashin nasarar da zuwanta ya haifar. Koda dai Bokanyar ta yi mata ɗan albishir na cewa za ta yi komai don ta ga ta karya mugun sihirin da wancan la'anannen Bokan ya yi mata don ta tabbatarwa Hajara duk inda za ta shiga, aikinta zai matuƙar wahala ya cimma ruwa saboda da baƙaƙen aljanu ya yi wani haukataccen tsafi a kanta. Duk da haka ta dire wa matar kudade da ta ba ta tabbacin shafawa Sadiya baƙin jini a wurin kowane ɗa namiji. Hajara ta ƙara furzar da huci tana mai duban saitin da Gwaggo Atine ta ke, baccinta take shara tamkar babu wani abu da ya faru. Ta ja dogon tsaki ta kauda kai ta maida ga kallon dajin da suke ratsawa da ko sunan wurin ba ta sani ba. Ranta a jagule haka ta shigo gidanta don dama ana shigowa cikin garin Kano ta sallami direban da ta ɗauka haya da kuma Gwaggo Atine ta tuƙo motar da kanta. Motar mijin nata da ta gani a farfajiyar ya ba ta tabbacin ya dawo. Duk da cewa ta san bai ko damu da ina ta je ko za ta je ba, amma sai da ta ji kirjinta ya ba da dam saboda kwananta ɗaya a Adamawa. A zatonta ma yana can Abuja suna harkar kamfen dinsu. Kai tsaye ta nufi ɓangarenta ta soma da ajiye komatsanta kafin ta fito ta wuce zuwa ɗakin Maigidan. A falonsa ta iske shi zaune yana waya, yadda yake ba da umarnin a yi musu aiki da gaggawa don ganin komai na zaɓensu ya tafi daidai ya sa ta nemi wuri ta zauna ta yi shiru. Har a sannan ba ta gama huce zafin doguwar tafiyar da ta sha zuwa wajen da bai haifa mata ɗa mai ido ba. "Kin je Adamawa ba ki sanar da ni ba? Tafiyar ta mece ce?" Da wani irin mamaki ta kalle shi. Tunanin ya aka yi ya sani take? Don ko direbobin gidan ba ta yi amfani da ko guda ba, ita ce ta fice a motarta, suka hadu da wani direban daban da ta dauki hayarsa ta kuma biya shi maƙudai kawai don ya kai ta ya dawo da su saboda ta dauki aikin na sirri ne da ya shafe ta. Ƴar dariya Alh Nuhu ya yi. "Oh, kallon sakarai ki ke min ne Hajara? Ko a zatonki ina zaune da ke ba tare da ina gadinki ba? Ai ke ma kin san ba zai yiwu ba. Kin ga nan?" Ya yi mata nuni da tafin hannunsa. "Ko me kike yi yana nan ɗina. Babu abin da za ki iya ɓoye min. Ba zan matsa akan lallai sai na san abin da ya kai ki ba. Amma ko sani, ko me za ki yi, ki dinga aikata shi a sirri hakan na da kyau. Ni dai kar ki jawo a ɓatan sunana. Duk abin da ki ke aikatawa ina saka idanu ne don kar ki ƙetara iyakata, ma'ana ki shiga sabgar da ta shafe ni da abokan hulɗata. Shi ne kawai. Sai magana ta gaba, haihuwa nake so. Idan ma kin san akwai wani abin da ki ke sha to tun wuri ki dakatar. Idan kuwa ba ki shirya ba ki faɗa min, zan auro wacce za ta haifar min." Yana kai wa nan ya miƙe ya kwashi wayoyinsa ya nufi hanyar ɗaki. Hajara ta bi shi da idanu kirjinta na duka fiye da sadda za ta shigo, ba wai fargabarta akan meyasa yake bibiyarta ba ne, wannan ya kau a ranta. Maganar ta haihu ko kuma ya ƙara aure ita ta fi kaɗa mata ƴan hanji. Aure? Dama zai iya tunanin ya auri wata mace bayan ita? Duk irin zantuka da romon bakan da ya dinga zuba mata sadda zai auro ta? Meyasa wai idan ta kalle shi ba ta iya gaggasa mishi maganganu koda ta so hakan? Meyasa wasu lokutan take ɗan jin shakkarsa duk kuwa da cikakken ƴancin da ya ba ta na aikata yadda ta so a rayuwa? Ita ce ma ta ke kaucewa abubuwa da dama, to ai don kudi ta biyewa ruɗin shaiɗan ta ke bin maza a baya, yanzun kuwa ta auri mashahurin mai kudi irinsa na mene ne wani zai burge ta a waje? Dama komai tana yin sa ne don ta samu duniya, ga duniyar a tafin hannunta ai kuma zance ya ƙare. Ranta ta ji yana tafarfasa, ta ji ƙwalla ta cicciko mata, idanun nan sun kaɗa jawur. Ta miƙe har jiri na son ɗibarta, madadin ta shiga ɗakinsa sai kawai ta juya zuwa nata ɓangaren. Kai tsaye firij ɗinta ƙarami dake cikin ɗaki ta buɗe ta fiddo kwalbar abin mayenta da ya yi sanyi rau ta bude a take ta kwankwaɗe. Zama ta yi dirshan babu batun yin sallar Magriba da Isha'i da da ta rasa su a hanya, tana yin sallolinta sai dai dama a kurarren lokaci kuma ma ba a nutse ba. Tana salla ne kamar za ta tashi sama. Wani bin kuwa idan har ta kwanta a gado da zummar bacci, ta tuna ba ta yi sallar isha'i ba, shikenan ta wuce ba za ta tashi ta yi ba. Tun tana iya lissafo abubuwan da suka ɓata ranta a waɗannan kwanakin, har saboda ƙarfin mayen da ta ke bacci ya yi awon gaba da ita a wurin bayan gama sumbatu iri-iri da tsinewa Sadiya kai ka ce ita ce ummul-aba'isin komai. *** Mami ta yi shiru tana kallon ɗanta wanda ya ke amsa wayar Husna. Ta dai kula wani abin ta ke son ya taho mata da shi gaba ɗaya ya ba da hankalinsa ga wayar, ya nutsu, irin nutsuwar da za ta iya rantsewa ita da mahaifinsa ne kaɗai suka cancanci irinsa a halitta. "Mami ni dai jikina yana ba ni Yaya Huzaif ba ƙalau yake ba. Mami ki ga fa yadda ya ke rawar jiki idan suna tare, kalli irin yadda daga ta yi magana ya ke cafewa. Anya kuwa Mami?" Ta tuno da zancen Meenat a wata rana da Husna da Huzaif din suka zo gaishe su. A lokacin karyata zancen ta yi ta rufe ta da faɗa don a ganinta ta ya ya ma za'a ce wani asiri ne zai ci ɗanta? Kawai dai Meenat din ta faɗa ne saboda ba ta jituwa da Husna tun bayan ƙwacen da ta yi wa Sadiya. A yanzu kuma ta fara dawowa hayyacinta, tabbas ta soma yarda, wata zuciyar na raya mata ko saboda juna biyu ne, amma wani sashin na ankarar da ita akwai gyara a lamarin. "Mami shikenan zan iya tafiya ko?" Abin da Huzaif ya furta kenan bayan ajiye wayarsa da Husna. Mami ta girgiza kai cike da tsantsar takaici. "Huzaif, shikenan fa ka ce? Ina maka zance mai muhimmanci dangane da mai zuwa wurin Meenat saboda Uwarka ta kira a waya ka ke ce min shikenan? Anya ka na cikin hayyacinka? Ko dagaske Husna ta shanye min kai?" Ya hau kame-kame yana murmushin yaƙe. "Kai haba Mamina, duk duniya ai babu mai raba ni da ke. Ke ce fa mahaifiyata. To ki yi hakuri. Yanzu me ya rage? Yaron yana da wata matsala ne ko kuwa?" Yadda ya ƙarasa zancen yana duban agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ƙara wa Mamin nasa takaicinsa. "Huzaif kana Azkar safe da yammaci? Ka na sallolin dare da karatun Alkur'ani? Anya kuwa ka na tsayawa ka yi addu'ar kirki idan ka idar da sallolinka?" Tambayar da ta watsa mishi kenan idanunta a kansa har a sannan cike da tsantsar mamaki. Ba ya yi, ya sani ya mance rabonsa da buɗe littafin Allah ya karanta, ya kuma ma mance rabon da ya tsaya ya yi addu'a wa iyayensa da shi kansa bayan sallar farillah balle kuma ga ayyukan nafilfilu da ba su zame mishi dole ba. Sunkuyar da kai ya yi ya rasa me zai ce. "Anya Huzaifa? Maganar matarka yanzu har ta fiye maka tawa? Ina magana da kai, ka kasa ba ni nutsuwarka? Soyayyar Husna ta fiye maka tawa?" Nan ma babu bakin magana, shi bai ce ba, amma ya san yana jin wata muguwar soyayya da shakka ta Husna. Yana ji komai zai iya sadaukarwa dominta. Yana ji har a kasan ransa da ace Husna ce ya hangi ɓacin rai haka a saman fuskarta, sai inda ƙarfinsa ya kare. Amma kuma sai ya ji na Mamin bai wani dame shi ba, bai ɗaɗa shi da ƙasa ba don haka ya shafi sumarsa ya ce. "Ki yi hakuri." Ita ce kawai kalmar da ya furta. "Tashi ka tafi kawai, tashi ka wuce kafin matarka ta ƙara kira. Je ka." Jikinsa ya yi sanyi, ya ji babu dadi amma kuma bai san dalili bai ji zafin sosai ba, yana so ya zauna ya cigaba da ban hakuri da rarrashi, amma ankarar da shi da ta ƙara yi da jiran da Husna ke mishi ya taho mata da gasasshen kifi da take muradin ci, ya sanya shi miƙewa yana fadin. "Sai da safe Mami.". Daga haka ya fice bayan ya zura takalmansa, baki buɗe ta bishi da kallo, can kuma ta hau salallami ta ji kwalla sun cicciko mata. Tabbas dole su tashi tsaye da addu'a akan ɗansu, za ta sami Abba da zancen. Kuma ita ma daga rana irin ta yau za ta duƙufa kai wa Allah kokenta. Ji ta yi tsanar Husna na dira a ƙoƙon ranta, da ace ta san haka halayyarta suke, da babu abin da zai sa ta biyewa makauniyar soyayyar da take yi ga Huzaif ta ba shi goyon bayan aurenta madadin Sadiya. *** Ta tsaya masa a rai, ya kuma rasa dalilin wannan nacin da kwakwalwarsa ke masa da tunaninta alhalin kaf tarihin soyayyarsa babu wacce aka sani a ciki irin Fareeda. Shi kaɗai yake kiɗa da rawarsa, soyayya ce tun suna jami'ar Oxford dake Ingila. Idan ana neman kyau, wayewa da ma ilimi, ka samu Fareeda an gama. Ja mishi aji take yi ba ƙarami ba. Ya kuma yadda ya ji cewa ta kai ta isa a jira ta har ta gama yangar a jajirce a same ta matsayin matar aure. Ya sani ba ta yaudare shi ba, tun a sannan ta faɗamasa akwai wanda take so, ya kuma ji ya amince zai gwada sa'arsa, shi da kansa ya ji ba zai iya haƙura da ita ba. Kusan a kan Fareeda ma ya san soyayya, bai iya ta ba sam. Haka suka kammala karatunsu, ya dawo ya bar ta a can saboda akwai tazarar aji biyu tsakaninsu a makaranta, tsawin shekaru biyun nan kuwa ita yake jira, zuwa yanzu tana sauraronsa sosai. Ta kuma ba shi tabbacin ta yarda ta aminta da tsayar da shi matsayin mijin aure. Ta haƙura da wancan tunda har ya kasa jiranta ya yi aurensa. Wannan albishirin shi ne ya yi wa AbdulMajid da suke kira da Hamma daɗi fiye da komai a duniya. Dalili kenan da ya sanya shi yi wa Baffansu magana kan ya samu matar aure kuma nan kusa za'a kai kuɗi a tsaida rana. Iyayensa sun ji daɗi ƙwarai, ko babu komi aurensa suke matuƙar so su gani sai ga shi bayan Nene ta gama tallata masa yaran dangi, don kansa ya zo musu da magana a kan Fareeda. A yanzun kuwa bayan Fareeda, ya samu Sadiya. A jikinsa ya ke ji zai iya aurenta koda ace ya rasa zaɓinsa na farko. Bai ma taɓa ganin halittar da bayan Fareeda ya ji ta masa kuma zai iya aure ba irin ta. Ajiyar zuciya ya saki ya ja guntun tsaki gami da miƙewa daga kwanciyar da ya yi saman doguwar kujerar da ke falon. Daidai lokacin wayar sa ta ɗauki ƙara. Ya kai hannu ya ɗauko ta don har tana kokarin shigewa cikin kujerar dalilin danneta da ya yi wurin kwanciya. Ganin Nene ya sa shi miƙewa don ya san shirun da ta ji bai fito ya yi karin safe ne ba dalili, koda ya amsa kuwa hakan ne, cigiyarsa ta ke. Ya ba ta uzurin bacci ne ya ɗan mishi nauyi amma yana tafe. Da haka ya katse kiran. Koda ya fito falon Nene ya iske Nudrat na sauri-sauri za ta fice makaranta, kamar ya ce ta jira su fita tare ya sauke ta amma kuma yana kwaɓar zuciyarsa da ta ke ta kokarin manna mishi wacce bai san komai dangane da ita ba. 'Idan da amana, har akwai wacce za ka kalla da sunan So bayan Fareedarka?' Wannan tunasarwar ya fito daga wani sashi na zuciyarsa, haushin kansa ya kama shi har da jan istigfari kai ka ce wani saɓon ya tafka. *** Ranar Litinin da ya kasance na zuwa makaranta ga Sadiya, sai ta wayi gari da zazzaɓi da matsanancin ciwon kai. Ga test zazzafa da suke da shi, tun a wajen karin safe take ta dauriya gudun kada Inna ta ce ba za ta fita ba sai dai tana kammala shan shayi da wainar ƙwai ta maido su gaba ɗaya. Malam da kansa ya kai ta asibiti sai daga baya da ya kasance har da su ƙarin ruwa ne ya ce Inna ta shirya ta zo. Nudrat kuwa tun tana kiran layin Sadiya yana ringing ba a ɗaga ba har ta haƙura ganin Malami ya shigo. Koda ta fito ma duk ta yi wuri-wuri da idanu, ita tana ji a jikinta cewa ba fa lafiya ce ta hana Sadiya zuwa ba. Abokan karatunsu ma na ta tambayar ina Triple S kamar yadda sunan ya bi ta sakamakon yawan kiranta da shi da Nudrat ke yi. Ranar ce ta yi takaicin rashin amsar lambar Inna, duk gaishe ta da take yi sai dai su gaisa a wayar Sadiyar. Bayan ta fito a lakca ta biyu cikin ikon Allah tana ƙara kiran Sadiya ta ji an ɗaga a wannan karon, muryar Inna ta ji, bayan sun gaisa ta ke shaida mata an kwantar da Sadiya. Sosai Nudrat ta ji zancen ya buge ta. Dama tun rabuwarsu ran juma'a ta ce kanta na sarawa, duk kuma a zatonta na ɗan lokaci ƙanƙani ne da zarar ta sha magani shikenan. Ashe da sauran rina a kaba. Suna ajiye waya sai ga kiran Hammanta ya shigo. Da sauri ta ɗaga gami da amsa sallamarsa. "Ki na makaranta ko kin tafi? Gani nan dab da wurinku. Ko Sule ya zo?" Girgiza kai ta yi kamar yana gabanta, murya irin ta mai shirin ɓarkewa da kuka ta ce. "Hamma ni ko ban gama ba tafiya zan yi. Triple ba lafiya tana kwance a asibiti." Ta ji ƙarar jan burkin motarsa har sai da ta razana. "Hamma! Mene ne!" Ta faɗi a hargitse, can kuma ta ji ya amsa. "No, babu komai. Ki fito bakin gate ina jiranki na kai ki dubiya." Daga haka ta ji ya katse kiran, ba ta tsaya wani dogon tunani ba ta yi wa wasu ƴan ajinsu biyu dake gefenta sallama ta miƙe da sauri ta kama hanya. Kusan a tare suka iso kofar makarantar, yana tsayawa tana ƙarasowa waje, gaban motar kawai ta bude ta shiga. Shi ma sunan asibitin ya tambaye ta kai tsaye, sai a sannan ta tuna ba ta ma tsaya tambayar Inna ba don haka ta ƙara kiranta. Daga haka ya fisgi mota, Nudrat duk ta damu tana ta ba shi labarin ai dama tun ran Juma'a ta ce mata tana ciwon kai. "Ayya, Allah ya ba ta lafiya." Shi ne abin da ya faɗi kawai amma kuma a ƙasan ransa gaba ɗaya ji yake ya damu ainun. Tun ganin da ya yi mata a yanzun sati kenan tunaninta bai bar shi ba musamman da kwanakin nan ya ke cike da damuwar Fareeda da ta sauya masa kaɗan. Ba ta ɗaga wayarsa a sadda zai kira hakanan ba kasafai ta ke amsa mishi a chat ba. Sai yake jin kamar ta fi ƙarfinsa, kamar dagaske ne sadda wani abokinsa ya taɓa ce mishi Fareeda ba za ta tanƙwaru ba idan sun yi aure saboda wayewarta ta yi yawa amma sonta da ya rufe mishi idanu ya sa bai taɓa gasƙatawa ba sai yanzun da ya ke jin cewa Sadiya za ta iya yi mishi biyayya da ma soyayyar da bai samu ba a ɓangaren Fareeda. Haka ya dinga saƙe-saƙensa a zuci, bai ko kula surutan Nudrat ba, yana ji har waya ta yi da Nene ta sanar da ita ba sai Sule ya koma ɗaukarta ba, tana tare da Hamma. Ita kanta Nenen ta jajanta da ta ji batun rashin lafiyar. *** A raunane ta ke duban Nos din da ke riƙe da sirinji da ta zuƙo ruwan allura za ta yi mata a jijiyar hannu. Turo bakinta ta yi duk ta firgice har kwalla ta gama cicciko mata ta dubi Anti Hafsatu da Inna. "Don Allah Anti ki ce kar a yi min. Allah kuwa na ji ƙwarin jikina." Salallami Anti Hafsatu ta yi, wannan ne karo na biyu da Nos din ta yi yunƙurin yi mata allurar, na farko na kuka ta saki tana mammatse jiki ita wai ba za'a yi mata ba. "Yau na ga abin da ya fi ƙarfina ni Hafsa, ke yanzu ki na matsayin ɗalibar medicine amma ki na tsoron allura? Wato sai dai ki koyi yadda za ki yi wa wasu ke ba za'a yi maki ba ko? Eh shakka babu da aiki a gabanki. Sadiya tun muna shaidar juna ki nutsu a yi maki idan kuwa ba haka ba na sa mazan da ke wajen nan su rirriƙe ki." Inna da takaici ma ya ishe ta ta kasa magana, Nos din kuwa tun abin na Sadiya na ba ta dariya har ta soma ba ta haushi. Wayar Sadiyar ce ta yi ƙara, ganin Nudrat ce Inna ta ɗaga, lambar ɗakin ta tambaya don haka sai kawai Inna ta fita ta leƙa don ta taho da ita dama takaicin Sadiyar ya gama kai ta bango ji take kamar ta kai mata bugu. Ganin Nudrat da wani matashin bafulatani ya sa ta ɗan saki fuska, Hamma ya russuna ya gaishe ta ta amsa tana tambayar mutan gida. Nudrat kuwa tuni ta nufi ɗakin da ƙawarta ke ciki. Inna ce ta yi wa Hamma iso zuwa ciki. Ganinsu ya sa Sadiya shiga taitayinta babu ma kamar Hamma ɗin da koyaushe ke mata yawo a zuciya da gangar jiki. Kwarjini da kunya suka addabe ta, daƙyar ta iya buɗe baki ta gaida shi don har a sannan akwai zazzabi jikinta da ciwon kai da ya ƙi saurara mata. Anti Hafsatu ke ba Nudrat labarin wai allurar jijiya za'a yi amma ta ƙi tsayuwa ita kuwa me za ta yi ba dariya ba. "Our doctor to be, ke ce mai tsoron Injection?" Sadiya ƙasa-ƙasa ta wurga mata harara saboda kunyar da ta ba ta a gaban Hamma. "Wa ya faɗamaki tsoro nake ji? Yi min." Ta faɗi cikin dakiya tana miƙawa Nos ɗin hannunta. Kamar kuwa da wasa ta daure har a ka kammala, ita kuwa ta sani kwarjinin Hamma da ke wurin ne ya jawo haka. Haka kawai ta ji ba ta son bayar da kanta a gabansa. A na kammalawa kuwa ta kwanta ta ja ɗankwali ta rufe fuskarta. Nudrat ta janye. "Malama ki buɗe ki shaƙi iska. Wai, jikin nata zafi fa." Ta ƙarashe da hakan sanadin hannunta da ta kai goshin Sadiya, zafi rau. "Yanzu da sauƙi ai ba kamar ɗazu ba ma." Cewar Inna. Hamma ya ɗan dubi Sadiya, idanunta a lumshe, fuskar nan ta ƙara ɗanyancewa ta yi fes, kauna da tausayinta suka ƙara mamayarsa, ya ji gwara ya tafi, barin asibitin zai fi zame mishi alkhairi a kan ya zauna zuciyarsa na mishi saƙe-saƙe a kanta. Sallama ya yi musu bayan ya yi mata addu'ar samun lafiya. Nudrat ita ma haka ta bar asibitin kamar ta zauna ta taya su jinyarta ba dai don ranta ya so ba. Ita kuwa Sadiya tana jin fitarsu wasu ruwan hawaye suka zubo mata, ga zafin ciwo, ga zafin ƙaunar Hamma da ke nuƙurƙusarta. Za ta rantse ba ta da masaniyar sadda son ya yi mata dirar mikiya. Abu kamar almara, a kwanaki bakwai kacal? Soyayyar abin da ba za ta taɓa samu ba na neman gallabar rayuwarta haka nan? Ta tuna, kwakwalwarta ta yi mata tuni ya fi a ƙirga kan batu na kuɗin auren Hamma da za'a kai nan kusa. Toh kuma ai zance ya ƙare, ita har a lissafinta ma gani take yau, gobe ko jibi mai afkuwa zai iya afkuwa. 'Fareeda.' Ta tuno sunan matashiyar da ta gani a hoto a wayar Nudrat da ta nuna mata yau kwanaki huɗu kenan, kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa ƴar gayu ga gogewa, ita ce wacce Hamma zai aura a faɗin Nudrat. Ta ji haushin Nudrat karo na farko a lokacin, to mene ne nata a ciki? Meyasa za ta nuna mata hotonta? Ina ruwan biri da gada? A sannan ne ta ƙara fahimtar cewa lallai dagaske ta faɗa tarkon son maso wani wanda Hausawa suka ce ƙoshin wahala ne. A nata tunani da tsinkayen ma ta ji fargabar a binciken Likita ya sanar da iyayenta cewa tana dauke da hawan jini, sai kuma akasin haka, ashe Malaria ce ta taso mata lokaci guda. "Ai ta samu bacci ma. Inna ki je gida mana ni sai na zauna da ita kafin ki dawo ko?" Muryar Anti Hafsatu sama-sama ya shiga dodon kunnuwan Sadiya. A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta ƙara runtse idanunta, kanta sarawa ya ke yi ga bakinta kamar ta sha maɗaci. Tana jin sadda Inna ta fice, a haka har bacci mai ƙarfi ya ɗauke ta. *** Baccin AbdulMajid ragagge ne a wannan dare, son sanin halin da Sadiya ke ciki ya fi komai tsayawa a ransa. Ranar ce kuna ta farko da bai nemi ko yi wa Fareeda magana a chat ba har wayewar gari. Koda ya ga Nene ta yi shirin zuwa dubiyar Sadiya har da girkin da Nudrat ta yi mata ya ji dadi don ya sani shi ne ke kai Nene unguwa muddin dai ba wani babban uzurin ne ya taso ba. Baffa na gida sai saƙon gaisuwa da ya ce Nudrat ta miƙa masa ga Triple ɗinta don hatta shi ma ya na shan labarai kala-kala kan Triple. Sun iske Inna da Malam sai ko Safiyya da su Yaya Hashim da suka zo dubiya. Ranar ce ta kasance ta farko da Inna ta saka Nene a idanu, suka gaisa fuskokin kowannensu a sake. Sadiya a sannan ita ma ta ji kwarin jikinta don tun asuba ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa sai ko hula da ta rufe gashinta da shi. Malam cike da zolaya yake duban Nudrat ya ce. "Ɗiyata amma dai ba za ki yi fashin makaranta ba saboda ƙawarki babu lafiya ko?" Nudrat ta yi dariya. "Aa, dama yau babu lectures fa.  Koda na shiga sai dai mu yi group discussion saboda Lecturer din mu ba zai shigo ba." "Toh Allah ya kara taimakawa." Aka amsa da amin. Nene ta ɗan zauna don ita ce ma ta taimakawa Inna ta sanya Sadiya cin abinci sosai wai bakinta babu dadi. Hamma dama tun fitar da su Yaya Hashim zasu yi shi ma ya fita ya koma wurin mota, hankalinsa ya kwanta da ganin jikin da sauki. Zuwan Abba dubiyar Sadiya ne ya sa Nene miƙewa don dama tana dab da tashi, sallama ta yi wa Inna da Safiyya da suke faman hira kamar an saba tun can. Babu ma kamar ita da Innar da suka gane su duka biyun daga gari ɗaya suka fito, wato Gombe. Har waje Inna da Safiyya suka yi mata rakiya aka bar Nudrat zaune gefen Sadiya tana ba ta labarin sun yi test. "Kai kin fa rame." Nudrat ta furta, ita kuwa ta yi murmushin yaƙe idanunta suka ɗan cicciko da ruwan ƙwalla. Duk sadda za ta ga Hamman Nudrat din sai ta ji kamar ya fama mata gyambon ciwon sonsa da ba ta shiryawa ba, hakanan ta ji ta tsinci kanta a ciki dumu-dumu. A can farfajiyar asibitin kuwa, Hajara da Husna ce suka iso dubiyar Sadiya. A dole Hajara ta zo gudun kar ta ɓatawa Husna rai tunda ita ta kira tana mata magiyar ta biyo su je tare Huzaif ba ya kusa. Ta ja tsaki ya fi cikin kwando, ta kuma yi wa Sadiya fatan mutuwa ya fi sau a ƙirga daga wayewar garin ranar Talata din zuwa yanzun. "Ai ba ma sai na kira waya ba, ga Anti Safiyya can da Inna." Hajara ta kai duba ga inda Husna ke nuna mata, tsaye suke kusa da wata yar dattijuwa da ta yi tsaf cikin kyakkyawar sutura. A gefenta kuma wani matashi ne fari ƙal kamarta yana riƙe da murfin mota yana jira matar ta shiga shaidar tafiya za su yi ne sun fito. Tunanin Hajara da Husna bai wuce su waye su din ba musamman ita Hajara da ta yi musu ƙuri da idanu. Suka ƙarasa daidai sadda Nene ta shige motar Hamma ya rufe murfin. Inna da Safiyya suka ɗan ja baya don su ba su wuri motar ta fita sa'ilin da Hamma ya shiga mazauninsa ya tayar da mota. "Ah, Husna, Hajara yanzu ku ke tafe? Sannunku." Maganar Inna ta sa Hajara dauke kai ga kallon su Nene ta maido hankaki ga Inna. Nan ta gaishe ta a cikin ranta tana ji kamar ta ɗauke ta da mari don ita fa muddin za ta ga Inna fes da ita a kullum to ranta na susa ne. Ga shi dai ba wasu suturu masu tsada ne da Innar ba, amma akwai tsafta da yawan ƙunshi. Koyaushe za ka gan ta tsaf da ita. Inna ta amsa gaisuwarta da ta Husna, nan ma aka gaisa da Safiyya daga nan suka ɗunguma zuwa ciki. "Mahaifiyar ƙawar Sadiya ce ta makaranta, Nudrat Mustafa. Tana ma ciki za ki gan ta." Amsar da Hajara ta ji Safiyya na ba Husna me tambayar ko su waye suka fita yanzun kenan. Ta tuna Nos Nudrat abokiyar aikinta a baya, wato dai duk inda mai sunan nan za ta ɓullo, ba mai kaunarta ba ce. A can din ma ai Nos Nudrat ba abinda ta ke yi gare ta face takura da saka mata idanu a sha'aninta sadda ta ke yawon shanawarta. Yanzun ma ga wata Nudrat din ta fito a ɓangaren wacce ta tsana. Ita kaɗai ta ke so ta fi kowa mu'amalantar masu hannu da shuni cikin yan uwanta, ita kaɗai ta ke son ta yi zarra duk inda za ta shiga a dinga batunta. Amma Sadiya ta ko'ina ta na shigar mata hanci da ƙudundune. Har suka ƙarasa ɗakin ban da tsinuwa ga Sadiya babu abin da ta ke yi a zuciya. Duk yadda ta kai ga hasaso yanda za ta ga Nudrat din, sai ta ga ashe ta fi haka wayewa da ma tsari. Ga shi dai abaya ce a jikinta, amma hatta da zoben da ke yatsarta na gwal ne. Tashin ƙamshi ta ke yi mai sanyi, sadda suka shiga ma waya take yi tana ta yarfa turanci kai ka ce jikar sarauniyar Ingila ce. Hajara ta ja guntun tsaki a ranta tana hura hanci don a ganinta tsabar son a sani ne da iyayi. Daƙyar ta cije ta ƙaƙalo yaƙe a saman fuskarta sadda ta amsa gaisuwar da Sadiya ke jifanta da shi. "Ya jikin? Sannu." Haka ta furta don har zuciyarta ba za ta iya addu'ar Allah ya ba ta lafiya ba koda wasa. Sadiya ita ma kauda kai ta yi ta mayar kan Husna wacce cikinta ke ƙara fitowa ga hancinta da suka ƙara buɗewa. Duk da yanayin da ta ke ciki bai hana ta darawa kaɗan ba. "Wai haka ki ka koma? Allah Sarki. Allah ya raba lafiya." Husna ta ɗan turo baki sadda Safiyya ita ma ke taya Sadiya darawa. "Kin riga ni furtawa a fili Sadiya. Ki ga yarinya gaba ɗaya ta fashe kamar mai shan yis. Kai ciki masu gari, Allah dai ya sauke ki lafiya Auta." A shagwaɓe Husna ta dubi Hajara. "Antina ki na jin su ko? Muni na yi ne?" "Ko ɗaya, ko kin yi ma sanadin ciki ne da zarar kin haihu za ki dawo daidai." Nudrat da ta gama amsa wayar fuskarta a sake ta gaishe su. Ta kara da fadin. "Kun shigo ina waya ne. Amm wannan ce Sis Husna ko?" Ta nuna Husna lokaci guda tana kallon Sadiya. Murmushi saman fuskar Sadiya ta gyaɗa mata kai. Ita ma Husna murmushin ta yi mata, Hajara kuwa wani kallon banza ta ke jifan Nudrat din da shi kafin ta kauda kai. Ita sai ta ji zaman ma asibitin duk ya gundure ta, gwara ta wuce gida don ita ma bayan Magriba tana da ganin likitan mata (Gynea Doctor). Sallama ta yi musu ta miƙe, Husna kuwa cewa ta yi ba yanzun za ta tafi ba, Hajara ko a jikinta don a yau ita ma Husnar haushinta take ji don ba ta ga dalilin da za ta saki jiki da Nudrat su yi ta kwasar hira ba. Sai yamma lis Huzaif ya zo daukarta. Ya shigo yana sunne kai ya gaisa da Inna don Safiyya tuni ta bi Hajara ta rage mata hanya. Sadiya ta gaishe shi kamar babu wani abu da ya taɓa gitta wa tsakaninsu don har ga Allah ba ta jin komai a kansa ya amsa ya yi mata ya jiki. Bai jima ba suka wuce. Nudrat ma daidai lokacin Hammanta ya kira a waya cewa yana harabar asibitin. Ta ɗan ji mamaki don ba ta dauka kuma shi zai dawo ɗaukarta ba, amma da ta yi la'akari cewa lokacin tashinsa daga aiki ya yi sai ta ba kanta amsa ƙila shiyasa ya biyo tafiya da ita gida. Ta yi wa su Inna sallama da Sadiya sannan ta fice da kwanukansu bisa umarnin Inna don tun da rana ta wanke su a can wani loko na asibitin inda ake wanki da ma alwala. *** Kwana biyu Sadiya ta ƙara a ka sallame ta. Gangar jikinta dai ya warke amma wannan ciwo na kaunar mutumin da ya yi mata nisa tana nan daram a ƙoƙon ranta. Duk runtsi kuma ba za ta fallasa shi ga kowa ba sai nemawa kanta yayewa daga Allah. Satin dai gaba ɗaya ba ta shiga makaranta ba amma kuma ta maida hankali sosai ga karatu a gida don ba ta yarda soyayya ta hana ta yin karatun da ta ci ma buri ba. Ran litinin kuwa da wuri ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa sakamakon zafin da aka kwana kuma aka wayi gari cikinsa don har a sannan damina ba ta shigo sosai ba. Inna ta dube ta, duk ta rame sai hasken da ta ƙara. "Har kin yi shiri? Ga Malam motarsa ta ɗan sami matsala ballantana ya fidda ki ko zuwa babban titi ne." Sadiya ta yi murmushi. Iyaye dai duk inda suke akwai tausasawa ga yaransu. Wato tana hango mata ƴar tazarar lungun nasu zuwa titi, ita kuwa ai har ta saba ba ta ma ganinsa. Ta san Innar ta san da hakan, kawai dai ƙila ganin ba ta jima da farfaɗowa daga cuta ba ne. "Babu komai Inna, zan iya zuwa." Jinjina kai ta yi. "Shikenan, Allah ya tsare ya ba da sa'a. Kin dai yi Azkar ko?" Sadiya ta amsa da amin kafin ta ba ta amsar ta yi Azkar din. Daga haka suka kara sallama ta fice don Malam bai ko tashi a bacci ba. *** Abba ya yi kamar bai ji batun da Mami ke yi dangane da ɗan nasu ba. Mami kuwa ta kai wuya amma ta danne shirun da ya yi mata. Ta sani tun farkon fara batun Husna da Huzaif ya yi mata wani kalami akan yanda ta dinga zazzaga faɗa wai a rabu da ɗanta ya auri wacce ya ke so. "Zan bar shi, idan har Sadiya ta janye ita ma ta fasa auren ɗan naki, zan bar shi ya auri wacce ya so din. Sai dai ki sani, ko kusa kar ki kuskura ki zo min da wata magana daga baya. Ba na ƙin Husna saboda abin da ya yi Sadiya shi ya yi ta, amma ba na goyon bayan yaudara da cin amana." Tana kawo wa nan ta sauke ajiyar zuciya har sai da Abba ya ɗan ɗago daga duban wayarsa da yake yi ya dube ta sai kuma ya yi ɗan murmushi ya girgiza kai. "Ki rage wa zuciyarki damuwa Mariya, ki maida lamuranki ga Allah. Abin da ki ka zo min da shi zargi ki ke yi kuma matsayinmu na musulmai zato zunubi ne. Kin yarda kin yi imani kenan yarinya ƙarama kamar Husna za ta iya bibiyar Bokaye har ta cutar da ɗanki? Babu fa wanda ya isa ya yi wa mutum abin da Allahnsa bai mishi ba." Mami ta ɗan haɗiyi miyau. "Na sani, amma kuma asiri gaskiya ne yana ci, tunda tarihi ya nuna ya ci Annabinmu s.a.w, kenan zai iya kasancewa ta yi aiki..." "Ya isa haka Mariya, ya isa. Ba na son zancenku na mata. Idan dai dagaske kin yi imani Allah ke yi, to ki maida komai gare shi, ki cire zargi ki kuma bar munana zato ga surukarki. Hakan babu abin da zai ɗarsa maki a zuciya face tsanarta. Ba na son wannan magana don Allah, ya isa haka. Ta tsaya iyakar nan." Yana kai wa nan ya mike, dama fita zai yi ya tsaya jiran direbansa da bai ƙaraso ba, tun kuma yana maganar ya ga kiransa ya shigo hakan ya ba shi tabbacin isowarsa. Daidai lokacin ma sai ga Amir ya shigo da sallama, bayan ya gaishe su ya ɗauki jakar Abban dake saman teburin tsakiyar falon yana shaida wa Abban isowar Isuhu Direba. Mami ta bi shi da addu'ar Allah ya kiyaye, nan ta yi zaune cikin tunanin mafita. Toh za ta tunkari Inna ta yi mata babban gargaɗi a kan ɗiyarta ne? Ko kuwa ita Husnar za ta kira ta ja wa kunne? Girgiza kai ta yi. Duka waɗannan ba masu yiwuwa ba ne, kamar dai yadda Abban ya ce ne, addu'a za ta dage da yi wa Huzaif ɗin. Wannan ne kaɗai mafitarta. *** Bayan Sati Biyu... Cikin yanayi mai nuni da tsantsar baƙin ciki ta fito daga banɗakin bayan ta gyara jikinta. Bayyanar al'adarta ya rushe dukkan burikan da ta ci. A farko ba ta damu da haihuwar ba, amma kuma a yanzu da tarin mafarkanta ya koma ga son ganin gudan jininta, da ma sauran abubuwa da ba ta ko tunaninsu a baya wanda ba za ta samu ba face sai ta haihu musamman ɗa namiji a wannan gida na Alh Nuhu. A gefen gado ta zauna gami da riƙe kai. Ta ja tsaki ya fi a ƙirga, zuciyarta na tunzurata a kan ta je kawai ta buɗe firij ta ɗauko kayan aiki ta afa a bakinta ko za ta sami nutsuwa idan ta yi mankas, amma kuma wata zuciyar na kwaɓarta gami da yi mata tuni a kan burinta na samun haihuwa wanda ko ba a faɗamata illar shaye-shaye ga ɗiya mace ba, matsayinta na wacce ta karanta a makaranta, tana da masaniya dangane da hakan. Ta ƙara jan tsaki. 'Kishiyar nan dai da ki ka tsana ita ce za ta zo idan ba ki nutsu ba.' Ta faɗawa kanta, sai ta miƙe ta fice zuwa falo don zamanta a ɗakin zai iya haifar mata da dana sani marar iyaka. A wannan gaɓar ba ta Sadiya ta ke ba, babban tashin hankalinta Alh Nuhu ya ƙaro aure bayan ita, sanannen mutum ne kuma fitacce, aurensa ba ɓuya zai yi ba. Balle ma yanzu da suke kan ganiyar zaɓe kuma jam'iyyarsu ce a kan gaba ko'ina maganarsu ake yi. Ta sani idan har ya tashi aure to fa duniya sai ta shaida kuma wannan zai zama babban abin kunya a wajenta. Ƙawayenta su yi mata dariya hakanan ma waɗanda ta gama yi wa gani-gani a rayuwa da cika baki. Ta tuno ko sadda Likita ta auna ta tabbatar matsalar ba mai yawa ba ce muddin za ta maida hankali wajen shan magungunan da za'a ɗora ta a kai, ta sha har tsawon kwanakin nan, ta kuma saka rai cewa ba za ta fa hailarta ba kwatsam komai ya rushe a yau. Da kuma ta tsaya ta yi tunani, ta ga ba ta da dabara ko wayo a yanzun face kawai ta kira Atine su koma wajen Malaminta, ita tana ganin ma shi ne ya yi mata aikin da komai ba ya tafiya daidai a rayuwarta. Wayarta ta jawo, ganin lokacin karfe bakwai na dare ta san cewa ta makara sai dai ko goben. Gwaggo Atine ta dannawa kira amma abin takaici a kashe, koda ta kira ɗaya a cikin mutanen da ke zama a Babban gida, aka ce mata Gwaggon ta haura Nijar kai kayan da ta sara. Ta ja tsaki ta kashe wayar, za ta je ita kaɗai tunda za ta gane wajen. Da wannan ƙudurin ta ji ta ɗan sami nutsuwa. *** Nudrat ta dubi Nene fuskarta da alamar tambaya ganin yanayin Hamma AbdulMajid kamar marar lafiya. Daga gaisuwa ma ko kallonsu bai ƙara ba ya nufi ɓangarensa. Nene ta yamutsa fuska tana kai ludayin furarta a baka. Nudrat ta gaji ta yi gefe da littafin da take dubawa na makaranta ta ce. "Nene meke samun Hamma ne? Kwanakin nan gaba daya ya sauya. Ina ta son na tambaya amma karatun jarrabawa ke mantar da ni." "Me zai dame shi bayan soyayyar da ya sa a gaba? Baffanku ne ya ce ba zai mayar shi ƙaramin mutum ba, ya ce a je a nema masa auren ita Fareeda, kuma an je iyayen yarinyar sun tambaye ta tace ba ta san da zuwansu ba. Shi ne dalilin wannan ƙuncin na sa." Nudrat ta ji zuciyarta har wani tafarfasa ta ke yi, ita fa ba ta yin wannan Fareedar tun da sadda ta fahimci ba ta damu da sha'anin Yayan nata ba, ta gane shi ke kiɗa da rawarsa. Aikuwa ga zahiri nan ya tabbata. Ta yi ƙwafa. "Shi ma Hamma kamar babu sauran mata a duniya sai ita? Ni wallahi har na ji ta fice min a kai gaba ɗaya na tsane ta. Mts. Allah ya raka taki gona. Ya kawo masa wacce ta fi ta komai ma." Ta ƙarashe cike da ƙuncin rai, Nene ta yi murmushi. "Ke kuma ɗaukar wa kan ki dala ba gammo. To shi kuma bai ga laifinta ba, ya ce shi ne bai tunasar da ita batun zuwan ba. Ai shi ba zai yi fushi da ita ba tunda yana mata makahon so. Uzuri ya yi mata." Takaici ya ƙara turnuƙe Nudrat, ta ji zancen ma ya ishe ta. Hamman kansa haushi ya ke ba ta. Sai kawai ta ce Allah ya kyauta daga haka ta tattare kayan karatunta ta nufi ɗakin karatunsu (Study Room). Daƙyar ma ta samu yin karatun bayan ta gama kukan tausayawa Hammanta da ta fi so kaf cikin yan uwanta bayan Yayarsu Maryam da ta rasu. *** A makaranta Nudrat suna fitowa ɗakin jarrabawa labarin damuwarta ta soma ba Sadiya don gaba daya ranar ba ta da walwala. Ba Sadiya ba, hatta sauran ɗalibai sai da suka gane ba ta cikin walwalarta don ita din akwai tsokana da wasa da dariya. Kawai dai ta san wanda ta ke yi wa da kuma sadda ya dace a yi. Da wannan da ma kokarinta a aji, Malamai da daliban suka san ta, ita kuwa Sadiya da fara'ar ba ta cika yi ba sosai, an san ta ne sanadin kaifin kwakwalwarta a karatu sai ko sanadin Nudrat ɗin. "Allah Sarki, Allah ya yi masa sauyi mafi alheri. Idan kuwa matarsa ce, Allah ya daidaita lamura." Ta furta cikin dakiya bayan gama sauraron Nudrat. "Ba amin ba ma, in sha Allahu ba zai aure ta ba. Can ga su gada." Nudrat ta faɗi a gaggauce tana mai tarar numfashin Sadiyar. Ita kuwa murmushin yaƙe ta yi. Ba ta da abin cewa, ba ta sani ba farin ciki za ta yi ko akasin haka. Sai ta ji ma tausayi ya ba ta, ta san zafin son maso wani, da alama shi ya ke yi. Ta ji ina ma za ta iya kawar masa da damuwar Fareeda, amma kuma a take ta ƙaryata kanta sanin da ta yi ba zai taɓa yiwuwa ba. "Ni wallahi ina ma ya samu mai nutsuwa da hankali irin ki Triple." Maganar Nudrat ya sa ta kallonta da sauri kuma a firgice, ita ma Nudrat din ita ta ke duba fuskarta cike da rauni tana kuma so Sadiya ta yarda dagaske ta ke yi a kalaman ta. "Ke ni fa na jima da hango dacewarki da Hammana wallahi." Nudrat ta ƙara furtawa ganin Sadiya ba ta da ko niyyar tankawa zancenta na farko, asalima kauda kai ta yi. Wannan karon kuma guntun tsaki ta ja kafin ta miƙe. "Na kula yau dai damuwa ta so ta maki yawa. Ni kin ga tafiyata yamma na yi. Sai Allah ya kaimu goben." Daga haka ta soma tafiya, Nudrat ta biyo bayanta da sauri ta dafa kafaɗarta. "Allah kuwa ba damuwa ce ta yi min yawa ba. I am serious Triple. Idan akwai wadanda nake ganin dacewarsu tare a zamantakewar aure to ke da Hammana..." "Please Nudrat, mu bar zancen nan. Please, na haɗa ki da Allah. Ki bari ma ya ji da damuwar da ke cin ransa a yanzu. Kuma ni na ce maki ina sonsa?" Nudrat ta sauke ajiyar zuciya. "Shi ke nan, na bar zancen. Kin ji dadi?" Harararta Sadiya ta ɗan yi kafin ta ce. "Ni na wuce, sai goben." Daga nan suka yi sallama. Nudrat ta bi ta da kallo, haka kawai ta ji ba za ta haƙura ba. Haɗin ya yi mata, za ta so hakan ya kasance. Haka ta dinga wassafo wai har ga Sadiya sun shigo gidansu gaida Nene da Baffa ita da Hamma da yaransu uku. *** AbdulMajid ba ƙaramin raɗaɗi ya ji da wannan sauyin da Fareeda ta masa ba, duk a kan ya yi gaggawar tura iyayensa gidansu alhalin bai sanar da ita ba. Ya je gidan nasu, ya yi ban bakin a waya amma kuma ba ta sauya zani ba. "Ba fa ta sonka, ya dace a zo gaɓar da za ka yi wa kanka faɗa ka haƙura da ita Abdul." Ya tunano kalaman da Maina ya yi mishi a ɗazun da suka yi waya, gaskiya ce mai daci ya sani, ya kuma dace zuwa yanzu ya fita sabgarta dagaske. Ya rungumi ƙaddara ya kuma nemi soyayyar wacce ya ke ji a rai za ta iya maye masa gurbin Fareeda tunda ko babu komai yanayin kamalarta da ma abubuwa da dama na surarta masu fisgar hankalin ɗa namiji suna masa zubi da na Fareeda. Ya sani sanadin soyayyar Fareeda ce ta sanya Sadiya ke burge shi ita ma. *** Hajara ta kai sama da mintuna ashirin a cikin motarta yayinda karo na farko a rayuwarta ta ji zuciyarta na bugu da ƙarfi saboda tsoron wata halitta, halittar ma Boka. Babban tunaninta da wane idanun za ta dube shi karo na biyu bayan ta gasa masa baƙaƙen maganganu ga kuma uwa uba dariyar da ta ke da yaƙinin zai yi mata. Sai kuma ta ja tsaki a fili ta ce. "Kunyar mara kunya ma asara ce. Bari na shiga na ga me zai ce min." Daga haka ta dauki jakarta bayan ta kashe motar ta fita ta rufe. Sai da ya kammala da mutum biyar sannan layi ya zo kanta ta shiga falonsa na biyu. Yana ganinta ya yi wani murmushin mugunta gami da kauda kai ya na gyara zaman alkyabbarsa. "Ke ce yau tafe Hajara?" Ba ta sha mamakin yanda bai mance sunanta ba balle kuma fuskarta, ƙila ma har zuwanta zai iya sani tunda hatsabibin kansa ne. Zama ta yi gwuiwa a sake ta gaida shi. Gaisuwar da ko Mijinta ba ya samun irinsa daga wurinta, ta fara da ba sa haƙuri bisa tozarcin da ta yi mishi a baya. "Riƙe ban haƙurinki Hajara. Yanzu ki faɗa min meke tafe da ke? Har yanzu matsalarki da Sadiyar ce ko kuwa har ta ɓangaren aurenki?" Ya ƙarashe yana ƴar dariyar da ta yiwa kallon tsantsar rainin wayau amma ta shanye tunda mai nema ba ya fushi kuma tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. "Duka biyun ne ya kawo ni Yallaɓai. Na farko dai ina son a yi wa Sadiya aikin da zai sa har abada ta ƙi auruwa sannan a aika mata shashatau ta yanda za ta shiririce ta daina karatu sai wasa da bin maza. Na biyu kuma mijina ne ya tashi haiƙan ya na so ya ga na samu juna biyu idan ko ba haka ba zai yi min kishiya. Ni kuma a duniya na tsani kishiya, shi ne nake son na haihu ko ta wane hali ne don na tserewa wancan bala'in." Ya yi dariya sannan ya hau tsaface-tsafacensa. Tabbas ya gani, ya kuma shaida ba ya ganin dukkan wani abu da ya shafi Sadiya, ya ƙara yin wani tsafin, nan ma sai ya kula yarinyar gewaye take da kariyar Mahalicci, bai ga ta inda zai iya cutar da ita ba. Irinsu ma yadda suka dage da ibada cutar da su abu ne mai matuƙar wahala. Ƙila ya iya rasa rayuwarsa idan ya dage, ko kuma aikin kacokam ya dawo kansa. Ya ɗago kai ya a duban Hajara wacce ita ɗin ma idanu ta zuba mishi cike da fargaba, tsoro ta ke a maimaita abin da ya faru a wancan zuwan nasu. Ba ta son jin dukkan abin da ya ci karo da burinta da fatanta, ba ta son ya faɗa mata idan har hakan zai zame shiga tarkon nadama karo na ba adadi. Ta kauda kai daga kallonsa, ta dai kula a komai kamar ba ta da sa'a a rayuwa, komai ba ya tafiyar mata yadda ta so. Tun daga lokacin ƙuruciya har kawo yanzu da ta yi aure, komai kan zo mata a baibai. "Ki sha kuruminki, har abada Sadiya ba za ta auru ba. Zan yi maki aikin kwanaki ɗari a kanta. Ina ba ki tabbacin burinki zai cika a kanta. Sai kuma bari na gane maki kan mijinki." Yana kai wa nan shi kansa sai da ya sauke ajiyar zuciya yana muzurai, ya kula matar ta gama imanin cewa wannan karon ma haƙanta ba zai cimma ruwa ba. Ko babu komai tunda har ta yarda da shi haka ta kuma dawowa izuwa garesa to fa zai yi duk abin da zai yi don ganin ya kwashi rabonsa a asusunta yadda ya kamata. Gwara ya ci banza ya bar wa banza. Hajara kuwa wannan albishirin ne ya sanya ta sakin doguwar ajiyar zuciya don cikinta har wani ɗurar ruwa ya yi dab take da sakin fitsari, sai kuma sakamakon ya zo mata a bazata, kawai sai ta yi dariya mai cike da zallar farin ciki. Shi ko Boka har mamakin wannan irin ƙiyayya da ta ke yi ga yarinyar da ta kira Sadiya ya ke. "Batu na gaskiya za ki haihu, haihuwa nan kusa ma. Sai dai ta hanya ɗaya za ki iya haihuwa a yanzu." Nan da nan murmushin saman fuskarta ya ɓace ya koma firgici da tsoro ninkin na baya. Kallonsa take amma ta kasa cewa uffan. Ya cigaba da zancensa. "Sai dai ki nemi matashin saurayi a waje ki yi mu'amala da shi bayan kin ba ni haɗin kai. Zai zama shi ne na biyu, mijinki na uku. Muddin hakan ta kasance, toh babu mai hana ki samun ciki." (Wa'iyazubillah) Ta jinjina kai, a ganinta wannan ba wata babbar matsala ce a gare ta ba muddin kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, matashin saurayi kuwa ai ko ta hannun su Waleeda za ta iya samu. Ba ita ce ta bar gidan Boka ba sai bayan sallar Magriba. Shi jin sa ya ke yi kamar yau kyautar duniya aka ba sa a tafin hannu, ga asusunsa cike fal ga kuma aiki babba da ya yi da Hajara. Shakka babu ta yi masa fiye da tsammani kuma ya ci alwashin mai raba su sai dai mutuwa. Ita kuwa ta bar gidan zuciyarta wasai, ko babu komai yau ce ranar farko da ta samu kyakkyawan albishir dangane da al'amarin Sadiya. Wannan ya fi komai faranta mata. *** Bayan Wata Ɗaya... Ta shafa addu'arta bayan kammala Azkar ɗin safe da ta yi zaman yi, miƙewa ta yi ta ninke dardumar ta kuma cire hijab. A gaggauce ta shiga wanka ta fito zuciyarta fes, wannan yawan damuwar da ta ke yi a kan Hamman Nudrat ya ragu da kaso mai yawa sakamakon yawan addu'ar da ta ke yi ga kuma yanzun da suke da lambar wayar juna suna gaisawa ta whatsapp don babu ranar da ba za ta ga saƙonsa ba. Idan kuwa ba ya kusa har jin ta take yi kamar marar lafiya, ita koda yanda ya ke jan ta da hira ma hakan na faranta ranta. Koda ta fito zama ta yi gefen gadon tana shafa mai murmushi dauke saman fuskarta, tunanowa ta yi da yadda aka yi suka sami lambobin juna. A wani zuwa da ya yi makarantar tafiya da Nudrat ne bayan sun gaisa kawai kamar daga sama ta ga ya miƙo mata wayarsa yana duban cikin ƙwayar idanunta ya ce. "Babu ko daɗin ji ace ba ni da lambarki alhalin ke ɗin ma ƙanwata ki ke. A taimaka a sanya min." Ta tuno murmushin da ya yi a sannan ita ma ta ƙara murmusawa. "Yes!!" Furucin Nudrat ya faɗo mata a rai kamar a sannan ta furta. Har suka kalle ta, ta sa hannu a lokacin ta rufe bakinta tana dariya. Ta tuno sadda ta miƙa mishi wayar ya ce. "Thank you. Zan yi saving da sunan Our Triple S." Sadiya ta lumshe idanunta don ta yi zurfi cikin tunani har ba ta san ta lafci mai da yawa ba sai da ta goga a tafin hannun hagunta kafin ta zaro idanu ta maida shi tana yi wa kanta dariya ita ɗaya a ɗaki. A gaggauce ta yi shiri cikin kayan gida, murna take yi za su soma zuwa asibitin koyarwa na Akth, burinta na dab da cika kenan. Ta kammala shiri ba ta kai ga fita a dakin ba ta ji wayarta ta ɗauki ƙara. Ta sani Nudrat ce don haka ta ƙarasa ta cire ta a chaji , saura ƙiris wayar ta zame daga hannunta ganin kiran daga Our Hamma ne kamar yadda ita ma ta adana lambarsa. Sai kuma ta ji kirjinta na dukan tara-tara, kada fa ace ko Nudrat ce ba lafiya saboda bai taɓa kiranta a waya ba wannan ne karon farko. Ta daure ta yi sallama bayan ya amsa ya ce. "Triple kewarki ce ta yi min yawa. Tun jiya ba kya online ina fatan ba laifi na maki ba?" Da sauri ta kalli madubin ɗakin tana murza idanunta har da bubbuga fuskarta wai ta ji ko mafarki take yi ko kuwa idanu biyu, wani tsalle ta buga sai kuma ta toshe bakinta da sauri tana kallon hanyar waje, duk da ba ihu ta yi ba amma tana tsoro kada murnar ta janyo haka. Sai ta kori shaiɗan ta yi hamdala ga Allah. "Kin ji zancen wani iri ko? To ki bar mamaki, dagaske na yi missing dinki, kasa hakuri kuma na yi na kira. Please say something na ji ko zan ji sanyi kin ji?" Ta runtse idanu da kuma tafin hannun hagunta lokaci guda don kunya ta ji kamar yana ganinta. "Uhum. Karatu na yi kuma ban samu chaji ba sai dare. Ka yi haƙuri." Ta na jin sadda ya sauke ajiyar zuciya. "Kima da time zuwa bayan Magrib? Akwai maganganu dauke a harshena, ba guda ɗaya ko biyu ba. An ban damar zuwa?" Ta zaro idanu tana kallon kanta ta madubi, sai ta yi murmushi mai bayyana haƙora. Kwalla suka cicciko mata, wai Hamma dai da ta ke so da mafarki? Ya Allah, ta ƙara gasƙata cewa addu'a ce kaɗai takobin mumini, idan ka yarda ka yi imani da Allah, to zai maka komai. Yau dai Hamma da ta gama sakawa a rai rabon Fareeda ne, shi ke batun kewa, har ma da zuwa wurinta? 'Ke kuwa daga ganin hadari sai ki fara wanka da kashi? Ai duk gaggawar mai jego ta jira a ba ta ɗan.' Wani ɓangare na zuciyarta ta kwaɓe ta, ta yi ƴar dariya ciki-ciki yadda ta ke da tabbacin ba zai ji ba. "Shirunki yana razana ni, ina ji kamar yana nufin No. Ki daure ki ce min eh ko a'a. Ni ma zan daure na karɓa a duk yadda ya zo." Sai ta tuna fa ba ta amsa ba, da sauri ta ce. "Eh, ba komai Hamma, sai ka zo din." Ta ji saukar ajiyar zuciya karo na biyu. "Nagode. Sai anjima. Ki kula." Daga nan ya katse kiran bai jira cewarta ba, ita kuwa wani tsallen murna ta yi tana dauke hawayen da suka riga suka zubo. Ji ta ke kamar ta yi tsuntsuwa ta tashi ta yi yawo a sararin samaniya saboda tsabar murna. Ranar dai kowa ya gan ta ya shaida tana cike da farin ciki, koda suka shiga asibiti ma ba ta samu damar yin zancen ga Nudrat ba duk kuwa yadda ta so yi. Ganin ita ma ba ta yi mata zancen ba ya sa ta fahimci ƙila ba ma ta sani ba shiyasa ta bar wa cikinta sai Hamma ya zo din ta ji abin dabya kawo shi. *** "Na rasa Fareeda, na kuma sani rashi ne da ko na ƙi ko na so dole na yarda da hakan. Don Allah kar ki saka a rai cewa sai da na rasa ta ne sannan na zo gareki, ki saka a rai ƙaddararmu ce a hakan. Ina so ki maye min gurbin ta ne. Abin nufi, mu ƙulla alaƙar da za ta kai mu har ga aure." Ta rasa me za ta ce, kanta yana ƙasa tana wasa da zoben azurfanta, kirjinta kamar ya yi tsalle ya fito. Ga dai ranar da ta ke yawan mafarkin gani amma kuma kamar an saka allura da zare an ɗinke leɓɓanta, sun ma kasa motsi balle su ce wani abu. Daƙyar ta samu ta fara kunce zaren ta hanyar murmusawa. "Oh Triple ki yi magana mana. Shirunki na tsorata ni. Ko dai na maki tsufa?" Ta girgiza kai tana ƴar dariya shi ma ya taya ta, batu dai na gaskiya zai yi talatin da biyar haka, ya ma girmi Huzaif. Amma kuma ka na ganinsa ba ka ce ya kai ba. Yana da cika ido dai. Ga uwa uba kyawu da nutsuwa. "Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alheri." Ta furta a sanyaye, ya amsa da amin. Nan kuma ya hau ba ta labarin cewa tun farko ya ji tana burge shi, yana sonta amma kuma ya yi shiru ne bai furta ba kar ya shiga jerin mayaudara tunda ya sani za ta iya jin labarin sanya ranar aurensa. A wannan rana dai sun fahimci juna sosai, kowannensu ya yi na'am da ɗan uwansa kafin su yi sallama ya tafi. Koda ta shiga gida ba ta ɓoyewa Inna komai ba, Inna ma fatan alheri ta yi wa lamarin. Tun daga lokacin sai soyayyar AbdulMajid ta yi wa Sadiya ƙatutu a zuciya, kullum ko bai mata magana a waya ba za ta yi mishi. Ta nemi wani ajinta ta rasa, ta rasa kuma irin son da ta ke masa don za ta rantse ko Huzaif ba ta yi wa ba. Ita abin har tsoro ya ke ba ta. Sanda Nudrat ta gane sun haɗe kansu kuwa ruƙunƙume ta ta yi tana ihu da murna, ita sai ta ba ta dariya ma. Ko sanda ta je gidan Zahra wacce tsohon ciki ke hana ta fita ta ba ta labarin soyayyarta da Hamma ita kan ta ta ji dadi. Sadiya tana murmushi ta ce. "Wai meyasa duk wanda ya ga Hamma sai ya ce mun dace? Sai an ce in sha Allahu shi ne mijina?" "Saboda kun dace din ne, kun ba da kala tare. Kuma ai juma'ar da za ta yi kyau tun daga laraba ake gane ta. Ki duba kirki irin na Nudrat da Nene, sanadinki na san Nudrat amma sau uku tana takowa gidan nan bayan zuwanki da ita, takanas don mu gaisa mu sha hira. Toh wa zai ƙi zuri'a irin tasu da abin hannunsu bai rufe musu idanu ba?" Sadiya ta yi murmushi. "Kin san kuwa har Nenen sai da ta kira ni wai na bar zuwa gidanta ita fa ba kallon suruka take yi min ba. Na daina mata haka ko mu yi faɗa, wai ni ƴarta ce." Zahra ta yi dariya. "Allah Sarki, kin yi dace sosai wallahi yar uwa. Ke dai Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa." Sadiya ta amsa da amin tana mai jin wani sanyi a zuciya. Sai ta ji ta tuno da Suraj, ta mishi addu'a a fili, Zahra ta amsa da amin. *** Bayan Wata Biyu... Tana kwance a tsakar gidansu saman tabarma, Inna ba ta nan ta je gidan Baba Habu wacce ake sunan matarsa da ta haihu. Ita ba wani ɗasawa ta ke yi da ita ba ta dai je mata barka ta kai mata abincin da Inna ta girka a ranar da ta haihu. Wanki ta sha yau duk a gajiye ta ke jin ta ga kuma takaicin yanda suka shafe wata ɗaya zaune a gida dalilin yajin aikin da ake yi ga kewar Hamma wanda kwana biyun nan kawai ya ɗauke mata wuta, kamar yana cikin wata damuwar. Kiran ƙarshe ma da ta masa haƙuri ya ba ta ya ce zai neme ta da kansa. Ko Nudrat ba ta sanarwa ba da suka yi waya. Fargabarta kar dai soyayyarsa da Fareeda ce ta dawo sabuwa shi ne dalilin wannan sauyi. Amma kuma idan ta tuna ya ce mata ko waya ba sa yi sai hankalinta ya kwanta. Kamar kuwa ya san tunaninsa take yi, sai ga kiran waya ya shigo mata, ta kai hannu ta ɗaga wayar ta duba tana ganin sunansa na yawo saman screen ta miƙe zaune ba shiri ta amsa da sallama. Bayan sun gaisa ya ce. "Na yi kewarki, ki yi haƙuri da halina kin ji? Tafiya ce ta kama ni, ina Gombe ne. Shekaranjiya kuma ban jin dadin jikina ne, ni idan ina ciwo ko magana ba na son yi ne. Amma yanzu Alhamdulillah." Ta sauke ajiyar zuciya, ita wannan ma kiran ya wadatar da ita. Zuciyarta ta sanyaya. "Babu komai, Allah ya ƙara lafiya. Ya Gomben?" "Gombe ga ta nan lafiya. Ina tare da Maina, bari na ba shi ku gaisa." Ta ɗan yi jim, ta san Maina a bakinsa, ta kuma san shi tun ma farkon ganinta da Hamma din, sun yi hirarsa da Nudrat a gabanta. Haka nan Nudrat ta ƙara yi mata bayanin waye shi, ɗa ne ga ɗan uwa ga mahaifinsu, wato Mai Martaban Gombe ne, sun haɗu ne ta ɓangaren iyayensu mata, kuma amininsa ne suna girmama lamarin juna, sai dai Nudrat na jin haushin Maina ne saboda ta ce yana da izza da ji da kai. Ga kuma kaunarsa da Hammanta ke yi kusan ma fiye da yadda yake ƙaunarta. A nata cewar. Ba ta kai ga magana ba, sannan ba ta yi zato ba ta tsinkayi muryarsa a cikin dodon kunnenta. "Assalamu alaiki." Sadiya ta ji murya kamar an busa sarewa, ta tsinci nata muryar da ƙara ƙanƙancewa cike da girman da ba ta yi shirin ba sa ba ta ce. "Wa'alaikumussalam. Barka da yamma. Fatan ka na lafiya?" Ta ji shiru na sakanni kamar ba za a ce komai ba sai ta ji ya amsa. "Barka dai, a gaida su Mama." Kafin ma ta amsa ta ji muryar Hamma ta wayar yana fadin. "Ok My Triple, zan kira ki anjima. Take care." Ta kasa magana har ya katse kiran, ta harari wayar ta ja tsaki guntu. Ta kula dagaske dai Nudrat ta ke a kan wanda aka kira da Maina. Ai shi abokin saurayinta ne, toh kuma babu wani fara'a a muryarsa haka yake? Ta dauka a na gaisawa sosai kamar an san juna ne da abokin wanda za'a aura? Sai kuma ta taɓe baki, ƙila sarautar ce ta motsa mishi zai sauke a kanta. "Yo sarauta ai a garinmu ta ƙare. Har zai nuna mana mulki da ƙasaita?" Ta yi zancen a fili, sai kuma ta yi wa kanta dariya na wannan ƙarfin halin nata, miƙewa ta yi ta shiga hidimar ɗora musu girkin dare zuciyarta fari ƙal, jin muryar Hamma ya fiye mata komai daɗi. Da daddare ta whatsapp suka sha hirarsu, zancensa na ƙarshe ce mata ya yi. "Ki shirya fa, da zarar na dawo su Baffa za su zo nema min aure. Karatun nan na faɗamaki dama sai dai ki ƙarasa shi a gidana." Ta karanta ya fi a ƙirga, daɗi ya yi mata, emoji kawai na kunya ta aikamasa ba tare da ta ce uffan ba. Idan har shi za ta aura to fa ta shirya su yi auren ta je makarantar daga gidansa. *** Sun tashi da labarin haihuwar Aminiyarta, ta rasa ina za ta tsoma ranta ta ji dadi sadda Maman Zahra ta shigo ta sanar da su. Lokacin ma ta yi shirin tafiya asibitin ne wajenta. Ta samu ɗiyarta mace. Sadiya ce ta shirya ta bi ta yayinda Inna ta ce daga baya za ta zo. Ranar suna yarinyar Zahra ta ci suna Fatima ake kiranta da Batool. Nudrat ta jibgo siyayya kuwa ta kawo, Sadiya tana jin dadin yadda kowa nata Nudrat tana mutuntawa. Wannan ya ƙara musu shaƙuwa su uku tamkar dama har ita suka taso a unguwa. Husna ma da nata tsohon cikin ta zo, gaba ɗaya duk ta ƙara kumbura. "Anya wannan kumburin na lafiya ne Husna? Ki na zuwa awo dai ko?" Matar Yaya Hashim ta furta tana dubanta. Husna ta gyaɗa kai. "Ina zuwa Anti Rashida, sun ce wai hawan jini ne sun ban magani. Kuma na bar cin gishiri." Nan kowa ya tausaya mata, Inna na wurin ba ta ce komai ba sai tausayinta da ta ji ita ma. Koda suka tashi tare da ita suka wuce gida don dama tare aka wuce gidan sunan ta dawo gida sai ta haihu. Ita ma ta fi kaunar hakan, kwanakin nan ta rasa kan Huzaif, ba ta san dalili ba amma kamar ya ɗan sauya, kusan ma magana ba ya so ta cika yi mishi. Idan an ce shi ne ma silar hauhawar jinin nata ba za ta yi musu ba. Fargabarta kada ace aikin ne ya soma lalacewa. Tana son yi wa Anti Hajara bayani amma kuma tana jin tsoron kar shirkar ta yi yawa, kar ta wuce gona da iri. Ƙila ma wani abun ne ya ɓata masa rai ba wai dalilinta ba ne. Hakan ta saka a rai. Ta ga dai ko musu bai mata na da tace gida za ta je wanka. Tun tana ganin kamar shirye-shiryen bikin Meenat da ake yi ne ya dauke hankalinsa har dai ta gane dagasken haushinta ya ke ji kuma ya rage wani rawar ƙafa a kanta. *** Zaman Husna a gida ne ya sa ake ganin Hajara lokaci zuwa lokaci sai dai ba ta taɓa katari da AbdulMajid yazo wurin Sadiya ba. Kuma sam ba ta da labarin komai ƴar hirar ba ta zo wa Husna ba. Ita kuwa ɓangaren Sadiya sai zamanta da Husna karo na biyu ya ƙara musu shaƙuwa, sun koma makaranta a lokacin. Idan ta dawo haka za ta zauna su yi ta hirar karatunsu da ma yanda wasu lokutan suke fuskantar ƙalubale a ciki musamman idan sun je asibiti. Abin kan burge Husna gaba ɗaya sai ta ji damuwar rashin zuwan Huzaif ko kuma kiransa ya ragu a ranta idan suka yi irin zaman nan da Sadiya. Ita kuwa Sadiya ta fuskanci ƙanwarta na cikin damuwa ko ba ta fito ta furta ba, Inna ma kwanaki ke cewa ba ta ga gilmawar Huzaif a gidan ko wani a danginsa da sunan an zo ganin Husna ba. Amma ba su yi zancen a gabanta ba gudun ƙara jefa ta cikin damuwa. Sadiya ta sha ji tana waya tana kuka tana ƙorafi ga Huzaif a kan yanzu ba ya sonta amma kuma ba ta taɓa nunawa ta jin ba tunda ba ta son su sani. Meenat ce ma ta shigo gidan, ita ma kawo cingam da katin biki ne ya kawo ta. Sama sama ta yi wa Husna magana suka gaisa da tambayarta jikinta. Sadiya sai ba ta ji dadi ba, ita ta sakarmata fuska sosai amma kuma ai jini ɗaya ba ƙarya, abin da ya shafi Husna ya shafe ta. Koda ta taka mata zuwa waje bayan sun yi sallama ta ce. "Don Allah Meenat ki yi hakuri ki ba Husna ko wuri kaɗan ne a zuciyarki. Ni komai ya wuce a wurina amma meyasa ke har yanzu ba za ki hakura ki rungume ta matsayin yar uwa ba. Kar ki manta, ko aure bai shiga tsakaninta da Yayanki ba, mu da ku an zama ɗaya." Meenat ta yi murmushi mai ciwo. Don Sadiya ba ta san me ke faruwa ba ne. Ita da kanta ta je gidan Yayanta Huzaif don yin gyara saboda kwana biyu gidan ya yi ƙura tunda ba mace a ciki, bincike haramun ne amma kuma ta kasa haƙuri sai da ta dinga yi a gidan sai dai ba ta ga komai da za ta kama Husna da laifin aikata asiri ko tsafi ba. Ba da nufin bincike ta ɗaga gado ba sai don shara, manyan layun da ta gani dunƙule wuri guda ya mugun razanata. Hotonsu ta yi a waya amma ta kasa kiran Mami balle su Yaya Radeeya da Lubna, gani take yi kamar idan ta fadi za ta yi sanadin auren Husna. Da bismilla ta ciro su ta zagaya bayan gidan ta ƙone ƙurmus. Ko Mami ba ta faɗawa ba, amma kuma hakan ya ƙara rura wutar tsanar Husnar a zuciyarta. Ta kuma ƙara dagewa da addu'o'i ga ɗan uwanta bayan shi ma ta roƙe shi akan ya dage. Bai kuma musa ba sai ma godiya da ya yi mata duk da ba ta ce mishi ga dalili ba. Kuka kam ta sha a ranar. "Ke, duk a kan na nemawa ƴar uwata wannan alfarmar ne ki ka tsunduma kogin tunani haka?" Sadiya da ta jijjiga ta da ma maganar da ta yi ya maido ta hayyacinta, ta sauke ajiyar zuciya tana kauda kanta don tuni ƙwalla sun cicciko mata. Ta waske da fadin. "Toh ba ga shi nan yanzun har zuwa duba jikinta na yi ba? A sannu komai zai zama tarihi fa. Bari na je akwai sauran wuraren da zamu je. Sai mun haɗu." Sadiya ta gyaɗa mata kai tana murmushin da bai kai zuci ba. Jikinta kuma ya yi sanyi, tausayin Husna ta ke ji sosai. Ta dai bi Meenat da fatan alheri ta koma cikin gida zuciyarta ta yi mata wani nauyi. *** Ranar da Husna ta fara ganin Hamman Sadiya suka gaisa kusan kwana ta yi tana yi wa Sadiyar santi. Fadi take. "Kai sis, na rantse kun haɗu. Kamar fa na ɗauke ku na gudu tsabar kyau da matching da na ga kun min. Allah ya sanya alheri ya nuna mana auren nan." Sadiya ta yi dariya kawai. Satin Husna biyu a gidan ta soma naƙuda kuwa, an ci sa'a dai kafin haihuwar Huzaif ya zo har sau biyu, hankalinta ita ma ya kwanta. Lokacin da naƙudar ta taso ita Sadiya ma ta a makaranta sai Inna a gidan da Mama Iyabo makwafciyarsu da ta shigo. Ita ce ma ta fahimci Husna naƙuda ta ke. Nan suka nufi asibiti, cikin iko na Allah kuma bai zo da gardama ba, ba ta ɗauki dogon lokaci ba ta sauka lafiya ta haifi ɗanta namiji mai kama da babansa kamar an yi kaki sai dai kalar fatarta ce. Huzaif tun sadda Malam ya kira shi ya shaida masa suna asibiti ya zo. Haka ma Mami tana nan sai cika da batsewa ta ke, sama-sama suka gaisa da Inna da ba ta san dawar garin ba. Sosai ɗan ya shiga ran Mami sai ta ga kamar Huzaif dinta yana yaro, bayan ya mishi addua a karɓe shi ta riƙe. Inna ta kula Mami ta ɗan kawai ta ke yi don sau daya da ta kalli Husna ta yi mata sannu ba ta ƙara bi ta kanta ba. To haka ma Huzaif din. Mama Iyabo ce ta taimaka wajen gyara Husna, can ba jimawa Mamin ta wuce, Huzaif kuwa sai da ya tambaya ko akwai abin da ake buƙata. Inna ta ce a'a, ya karasa wurin ma'aikatan asibitin ya biya dukkan abin da ya dace sannan ya wuce da zummar sai anjima. Tafiyarsa ba jimawa Hajara ta dira a asibitin. Bakinta ya ƙi rufuwa, sai waya take tana sanar da mutanenta haihuwar ƙanwarta Husna. Sosai ake taya ta murna sanin yadda suke da Husnar. Husna ba ta jima ba aka sallame su tunda komai lafiya lau. Haka aka dinga zuwa barka kusan kullum sai sun karɓi baƙi. Dangin Huzaif da ma ƙawayen Hajara don ta rantse a abokanta duk wacce ba ta zo mata barka da sunan ɗan Husna ba to fa babu ita babu shi. Haka su Sadiya suka dinga ganin manyan masu hannu da shuni da ta ke mu'amala da su suna zuwa da sha tara na arziki. Nudrat ma sadda ta zo duk kallon da Hajara ke mata sai da ta ji ta burge ta saboda kayayyakin da ta jibgowa jariri ta kawo. Wai sai ga Hajara da Nudrat na hira da dariya. Abin ya ɗaurewa Sadiya kai. Amma kuma da ta tuna girman so da kaunar da ta ke yi wa Husna wanda ya shafi jaririn da ta haifa yanzu, sai ta bar mamakin. Ita ce dai ko ɗaukarsa ta yi Hajara sai ta ci gyaranta wai ba ta san ya ake riƙe yaro ba ta bar wuyansa na tangal-tangal. Abin kan mata ciwo har ta gaji ta bar ɗaukar yaron sai idan Hajara ba ta kusa. Ba ta ma da masaniyar zuwan da iyayen Hamma za su yi batun neman aure ya kama ranar sunan Husna wacce Hajara takanas ta kama Hall za'a yi shagali a can, sai a na gobe sunan Hamma ke sanar da ita. Ta so a bari bayan suna amma kuma ba ta ga hujjar da za ta musa ba tunda suna ai sabga ce ta mata. *** "Ayyiririi! Kai masha Allah Alhamdulillah. Ku ce min ɗiyata ta yi goshi. Allah ya kaimu da rai da lafiya. Watanni uku ai kamar yau ne." Abin da ya shiga kunnuwan Hajara da Husna kenan waɗanda sanyo ƙafarsu gidan ko tsakar gida ba su kai ga ƙarasowa ba suka tsinci muryar wata a dangin Malam da suke kira Umman Rabe tana wannan kalami. Dama fita suka yi kwalliya aikuwa Husna ba karamin kyau ta yi ba ta fito sharr dama an mata ƙunshi da gyara gashi. Hajara ke riƙe da yaron da ya ci sunan mahaifin Huzaif wato Abubakar ake kiransa Sadik. "Wai har an kawo kuɗin?" Tambayar Husna ta sa Hajara saurin kallonta, kenan ita ma ta san sha'anin da ake yi? Ita kadai ce ba ta sani ba? "An kawo Amaryar ƙarni, Sadiya ta yi goshi har dubu dari uku cas kudin aurenta. Nan da wata uku za ta zama rabon AbdulMajid." Hajara ji ta yi kamar an buga mata guduma a tsakar kai, auren Sadiya? AbdulMajid? Waye kuma AbdulMajid? Yaushe duk hakan ta faru ba ta da labari? 'Ki daure, ki danne ki ɓoye abin da ke ranki kar a ankara da ke.' Wani ɓangare na zuciyarta ya yi mata tuni. Don haka daƙyar ta iya yin murmushin yaƙe. "Masha Allah, na taya ta murna. Mu je Husna ki sauya kaya mu tafi lokaci na ƙurewa." Ta fadi ne tana sauri ta shigewa ɗaka, ita ta mance ma Husna tun a wurin kwalliyar ta saka kayanta. Da ace mutanen wurin sun kula da furucinta ma da kuma yanayinta za a gane a firgice ta ke. Gwaggo Atine tsaf ta karanci abar ta, ita ma baƙin cikin ne ya sa ta kasa kataɓus don jin labarin ta yi bagatatan. Ta tsome hannunta daga kwanon dambun da suke ci ta miƙe. Kamar ta bi bayan Hajara amma kuma ta fasa gudun zargi da ƴan tsurku. Dama sunan kashi biyu ne, da wanda Inna suka yi a gida sai ko wanda Hajara ta hada za a fita wanda tun kafin lokacin ta sanar ba kowa zai je ba sai wanda aka ba kati. Sadiya dai ba ta saka a ka ba amma kuma katinta da na Nudrat yana wajenta Husna ta ba ta. Dolenta kuma ta je tunda ba ta da hujjar cewa a'a. Taron ranar duka bai yiwa Hajara daɗi ba. Ko fara'a ta ke yi sai ta ji muryar Umman Rabe na amsa-kuwwa a kunnuwanta tana shelar kawo kudin auren Sadiya da aka yi. Hakan na nufin aikin da aka yi bai ci Sadiya ba ko kuwa ya ya? Tana da buƙatar komawa Bokanta don jin inda aka haihu a ragaya. Ta ya ya tufkarta ke warwarewa? Amsar na wurinsa. A ɓangaren Sadiya kuwa farin cikinta ba ya misaltuwa, mamakinta yadda har Mamin Huzaif sai da ta taya ta murna. Matar da tun auren Husna da Huzaif din ta bar shiga sabgarta kamar dama can ba ƙaunarta ta ke yi ba. Ita dai ta san Mamin ba ta da alƙibla sam. Ba ta ɓoye son abin da yaranta ke so, haka ma ƙiyayyar abin da suka nuna ba sa so. Komai ta ya su take yi. *** Ya kauda kai yana wani murmushi na yaƙe. A ransa faɗi ya ke. 'Wannan hatsabibiyar ba dai za ta haƙura ta bar yarinya haka ba.' A fili kuwa sai ya haɗiyi miyau kafin ya ce. "To ban da abin ki Hajara, hangen dala ai ba shiga birni ne ba. Kawo kuɗi ba ya nufin auren ai, na fa san dama za'a yi haka. Kuma abin ba zai je ko'ina ba. Ke dai ba na ba ki tabbacin har abada ba za ta yi aure ba? Toh ki kwantar da hankalinki ki saki ranki. Ko a fuska ki dinga dauriya kar ki nuna musu baƙin cikinki, ki shiga ko me za'a yi a yi shi tare da ke. Ke dai ki dinga ban haɗin kai, komai zai zama sai yadda ki ka ce. Hatta da uwarta sai kin juya ta kamar waina a tanda." Hajara jin haka ta sauke ajiyar zuciya, ji ta yi har hankalinta ya kwanta. Nan kuma ya nemi su je ɗaki karo na biyu, ba ta yi musu ba don ba ta san ma meke jan ta gare sa ba. Haka suka sheƙe ayarsu son rai kafin ta kimtsa ta bar gidan. Ya bi ta da kallo yana dariyar mugunta, a fili ya ce. "Aure kam sai yarinyar nan ta yi shi, ko mutuwa za ki yi sai dai ki mutu. Shashasha, ni da ke mutu-ka-raba kuma takalmin kaza." *** Kwanaki biyu ya yi saura a fita daga watan da suke ciki, Hajara ta gama tabbatarwa wannan karon dagaske tana dauke da juna biyu saboda ta ga alamomi da yawa matsayinta na Nos ta kuma fahimta. Farin ciki kamar ta yi me, wannan ne ma ya mantar da ita wasu damuwoyin, kasa hakuri ta yi sai da ta sanar da Alh Nuhu ta waya. Wata dariya ya kyakyata na jin dadi da farin ciki. Ya tabbatar mata zai sauya mata mota da waya saboda kyakkyawan albishirin da ta yi masa. Kanta ya fasu sosai. Ba ta damu da sanin ko cikin waye ba, ta dai sani ga Yusha'u saurayin da ta kwana da shi, ga kuma Bokanta ga kuma shi mijin nata. Ita ko ma na waye muddin dai za ta haihu ai shikenan kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Ai an yi mai wuyar. Ko me zai biyo baya dai ba zai sauyawa tuwo suna ba tunda kowa ya sani ba a shege a gidan miji. Ba ta san haka Alh Nuhu ke son haihuwa ba sai yanzu don har Gwaggo mahaifiyarsa da kannensa sai da aka zo wai duba jikinta ya ce ba ta jin dadi. Ita kuwa sai kara tanƙwashe murya ta ke, a dole tana jin jikin laulayi. Gwaggo ta so bar mata bazawarar ɗiyarta ta zauna amma ta nuna babu komai ai ta ji sauƙi don ba ta buƙatar wata takura. Can ɓangaren su Hafsatu ba kowa ya taya ta murna da fatan sauka lafiya. *** Sadiya ce tafe a barandar da zai sada ta da ɗakunan jinya na mata dake asibitin Malam bayan ta amsa wayar Nudrat ta sanar da ita suna can. Tafiya ta ke cikin nutsuwa tana shaƙar iskar da ke kaɗawa na hadari da ya haɗu a garin. Murmushi ɗauke saman fuskarta tana hasko ta tare da Hamma a zaune gaban tafkeken ruwa suna shan iska da hirar masoya. "Sadiya." Ta tsinci muryar kamar a mafarki a gefenta, ta juyo ta dube shi. Yana sanye cikin riga da wando ya dora farin coat na likitoci a sama. Ya rame amma kuma fatarsa ba ta wani sauya ba. Ta kauda kai kamar babu wani abu da ya taɓa giftawa tsakaninsu wai soyayya ta ce. "Lah Yaya Huzaif ina kwana. Dama a nan ka ke?" Huzaif wanda ya ji bakinsa ya ɗan mishi nauyi, jikinsa kuma gaba daya ya mutu. Sadiyar ce ta ƙara kyau ta kuma cicciko amma ba ta yi ƙiba ba, sai dai hatta da tafiyarta ta isa fisgar hankali. Idan ka gan ta sai ka ɗauka ɗiyar wani ko wata ce a ƙasar nan tsabar aji da ma kyawun fata. Har gobe yana sonta yana kaunarta, har goben kuma ya rasa dalilinsa na karkata aƙalar so da ƙaunar zuwa ga Husna. Wacce bai dauke ta komai a baya ba face ƙanwarsa. Ajiyar zuciya ya sauke ganin har ta soma shirin cigaba da tafiya ya katse hanzarinta da sauri. "A nan nake, kwanaki ai na ganki a can wurin Emergency, kafin kuma na yi maki magana na neme ki na rasa. Ya karatun? Fatan komai na tafiya daidai?" Sadiya ta murmusa. "Ayya, ban kula ba ai da na maka magana. Alhamdulillah." "Allah ya taimaka." Ta kauda kai tana duban agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta lokaci guda tana amsawa da amin. Ya kula ta ƙagu su rabu don haka ya yi mata sallama aikuwa ba ta jira komai ba ta cigaba da tafiyarta. Huzaif ya ɗan bi ta da kallo, ta mishi kyau ainun cikin doguwar rigar leshinta ruwan madara sai Lab coat da ta dora a sama, ta zagaye kanta da mayafi madaidaici, sai ko ƴar jakar da ke rataye a kafaɗarta. Sassanyan ƙamshi ta ke yi mai haifar da nutsuwa. Ya juya ya cigaba da tafiya gwuiwarsa a sake. Wallahi ya yi rashi, rashin da har abada ba zai bar jin ciwonsa ba. Ya kara jin tsana da haushin Husna sosai, amma kuma yanzun tana cin darajar Sadik, yaron ya ɗora wa son duniya.  Ya ji ina ma a na maido hannun agogo baya.  Da ya gyara ɓarnar da ya tafka, amma kuma ina! Bakin alƙalami ya riga da ya bushe. Ji ya yi idanunsa sun kaɗa, kwalla suka cicciko masa, dalili kenan da ya fiddo baƙin gilashinsa ya manna fuskarnan kamar bakin hadari saboda yadda take a murtuke. *** A hankali rayuwar tana gangarawa, lamura a ɓangaren Sadiya da Hamma sai abin da ya ƙaru. Soyayya ce mai tsafta ke gudana, tun ba a je ko'ina ba ta fahimci nata son ya fi na sa yawa amma kuma iyakar yin ta da kokarinta ta na yi wajen dannewa da ƙin nuna masa natan a fili. Idan a wuni bai kira ba ya ba ta uzuri, takan danne maitarta na son jin muryarsa ta yi ta harkokinta kamar babu komai. Haka har Husna ta yi kwanaki talatin da takwas cif, a sannan an yi bikin Meenat har ta tare a gidanta. Gyara sosai Inna ta yi wa Husna, ga Hajara da ke kawo mata wasu tsadaddun kayayyakin gyara na mata. Amma duka wannan buduri da ake a ɓangaren Husna ba ta wani rawar ƙafa face ma fargaba tsantsa. Ba ta san kalar zaman da za su yi da Huzaif ba wanda ya gama chanza mata. Ana gobe za ta tafi haka ta zauna tana kuka, Sadiya da ke jin ta ta gaji, ta ji ba kuma za ta iya shanye damuwar Husnar ba ba tare da ta yi mata magana ba don haka ta mike zaune, a gaggauce Husna ta hau share fuska don dama akwai hasken wayar da ta kunna, Sadik ke  kuka ta tashi shayar da shi har ma ya koma bacci sai uta a zaune. "Husna wai me ke damunki ne?" Husna ta dubi Sadiyar wacce ita ma idanunta ke kanta fuskarnan cike da matsanancin damuwa, ajiyar zuciya ta sauke. Ba za ta iya fitowa ta faɗa mata komai da komai ba, amma za ta gutsuro mata kaɗan daga cikin matsalarta da Huzaif. "Ban san me na mishi ba Sis, ya sauya min gaba ɗaya. Kira da zuwa inda na ke sai ya ga dama. Haka ma Maminsa, yanzu duk sadda za mu haɗu daure fuska ta ke yi, ba ma hira kamar a baya. Na rasa ina zan saka kaina na ji dadi. Damuwar ta yi min yawa. Tsoro da fargabar da na ke ciki yanzu bai wuce rayuwar da zamu yi da shi ba idan na koma. Na tambaye shi ko akwai abin da na masa ya ce min babu. To ina zan saka raina?" Ta ƙarashe da muryar kuka. Tausayinta sosai ya ƙara ninka na farko a zuciyar Sadiya. Ta kamo hannunta gami da girgiza mata kai. "Ki daina kuka, wa ya faɗa maki kukan ne zai magance maki matsalolinki? Kin tabbata kuma babu wani abu da ki ka yi mishi ko Maminsa?" "Na rantse maki babu shi Sis. Mami kullum burina na kyautata mata, yabona ta ke sosai a baya kafin wannan sabon sauyin. Dama Meenat ce ba ma shiri amma kaf sauran yan uwansa su na shiga sabgata ina shiga na su. Sis dole na shiga tashin hankali, na rantse maki ina son Yaya Huzaif sosai." Ta sauke ajiyar zuciya. "To sai ki miƙa dukkan lamuranki ga Allah. Babu fa wanda zai maka maganin komai a duniyarnan Husna sai Allahn da ya halicce mu. Duk wani mai imani da shi ya dogara. Sallolin nafila musamman na dare, karatun Alkur'ani mai girma, azkar safe da yamma, yawan addu'a. Na rantse da Allah sun isa su yi maki maganin matsalar nan. Kuma ki dage da kwantar da kai da biyayya da kiyaye ɓacin ransa. Babu matakin da ba za ki iya kai wa ba muddin ki ka yi hakuri. Ki fawwalawa Allah komai, Husna babu wani mai tsibbun da zai iya magance maki kowace matsala face Allahn da ya halicce ki. Kin ji ko?" A ɓangaren Sadiya ta yi amfani da zancen da ta ji Hajara na mata da yammaci da ta zo gidan, tana dab da shigowa ɗakin ta ji Hajara na ɗura ashar tana cewa ta kwantar da hankalinta za ta kai wa wani hatsabibin malaminta kuɗi ya ƙara yi mata sabon aiki a kan Huzaif din. Hankalinta sosai ya tashi da jin haka, har Inna ta faɗawa saboda tsoro, Inna ita ma kanta ta tsorata amma ta ce kar ta damu da yardar Allah za ta yi wa Husnar nasiha a faƙaice, ita ma kuma ta dage da taya ƴar uwarta a addu'a. Ita kuwa Husna, sai da cikinta ya ɗuri ruwa jin abin da Sadiya ta ce, ko dai ta ji hirarsu da Anti Hajara? Ta ƙara tsinkayar muryar Sadiya karo na ba uku. "Wallahi kin ji na maki rantsuwa da Allah ɗaya, dukkan wani aiki da za ka haɗa da wanin Allah don ya biyamaka buƙata ɓata ce zallarta. Kuma biyan buƙatar zai kasance na ɗan lokaci, da zarar alkadarin ya karye, komai kan iya sauyawa. Idan na ce komai to fa ina nufin ko mene ne da ma zurfin da aka yi don cimma manufa. Lokaci bai ƙure maki ba, Allah mai ƙarbar tuba ne, ki roƙe shi yafiya ki kuma miƙa lamuranki gare sa. Za ki yi mamaki wataran idan kin wayi gari soyayyarki mai tsafta ta wanzu a zuciyar mijinki. Amma fa sai kin yi hakuri kin kuma daurewa dukkanin ƙalubalen da za ki fuskanta tunda ki na kaunarsa. Kin ji ko?" Cike da tsananin kunya Husna ta gyaɗa kai, ta ma kasa haɗa idanu da Sadiya, kirjinta ko ban da harbawa ba abin da ya ke yi, tun yaushe Sadiya ta sani? Tun yaushe ta fahimci asiri ne ya ci Huzaif? Ko kuma dai sanadin hirar ce duk ta ji komai? Ta kasa kwakkwarar magana, sai ita ma Sadiya ba ta ce mata uffan ba ta juya ta kwanta. A hankali ta kwanta ringingine bayan ta kashe hasken fitilar wayarta, hawaye ta shiga fitarwa mai cike da nadama da tsantsar dana sani. Tabbas son zuciya ɓacinta, wataƙila ma da ta yi haƙuri tunda dai akwai rabo tsakani ƙila a ruwan sanyi za ta samu soyayyar Huzaif har ta kai su ga aure. Yanzu ga shi nan sanadinsa ta yi shirka, abin kuma ya zo ya saki Huzaif ya dawo daga rakiyarta. Wannan daren haka ta yi ta juyi sai wuraren Asubahi bacci mai ƙarfi ya yi awon gaba da ita. Daƙyar ta iya miƙewa ta yi sallar ta koma, tana gani Sadiya ta yi zaman yin addu'o'i amma ta sani baccin da ke idanunta ba zai bar ta zama ba. *** Nudrat ke duban wani bidiyo a wayarta tana kyalkyale dariya, Sadiya kuwa waya ta kammala yi da Hamma sai faman zabga murmushi ta ke. Can ta dubi Nudrat. "Wai ke ba kya gajiya da shiga shafin wannan Joker ɗin a tiktok?" Nudrat wacce daƙyar ta saita kanta daga dariyar da take yi ta dube ta. "Ke kanki ai idan ki ka kalli comedies dinsa ba kya iya riƙe taki dariyar." Ɗan guntun tsaki Sadiya ta ja har a sannan murmushi ne saman fuskarta ta ce. "Madam just fall in love, wannan duk shirme ne. A soyayya ce za ka yi kuka, za ka yi dariya, za kuma ka koyi darussan rayuwa." Nudrat ta saki baki tana kallonta kafin ta tsaida bidiyon da ta ke kallo. "Allah ko Mrs Abdul? Ah lallai, yarinyar ta kamu da yawa. Yau huɗubar ma ba na maida hankali ga karatu ba ne, a kan so ya faɗa." Dariya Sadiya ta yi tana ɗan runtse idanunta. "Gaskiya dai na faɗa maki." "Na ji, amma ke ma ki bi a hankali. Na kula ki na da zurfafawa a so, ki rage. Don Allah ki rage. Zurfafa abu ba shi da daɗi, ya na haifar da damuwa." Sadiya ta jinjina kai, dagaske Nudrat ta ke, komai idan ya yi yawa ba shi da kyau. Damuwa ce kamar yadda ta faɗa ɗin. To amma ya za ta yi? Zuciyarta ce a haka, ba ta iya son abu ba. Idan ta na so ba ta iya saita kanta, amma ya ci ace ta koyi darasi a kan na baya. Ko babu rabuwa, akwai mutuwa. Ita ganau ce ba jiyau ba. Duk da haka ta ji tana son sanin dalilin Nudrat na faɗin haka. "Amma meyasa ki ka ce haka?" Taɓe baki Nudrat ta yi tana girgiza kai. Har ga Allah ba ta hango irin wannan soyayyar da Sadiya ke yi ga Hammanta ba a ɓangaren yayan nata. Ta san eh yana son Sadiya amma kuma bai gama mance Fareeda ba. Ta taɓa kama sa ma yana waya da ita yana cewa ita ta jefa shi a condition din da yake, ba ta bar sa da kowane option ba face na ya nemi wata kawai. Wannan abu ya yi wa Nudrat zafi, sai ta ji kamar ma ba son Sadiya yake ba kawai dai don babu yadda zai yi ne ya dauke ta matsayin second choice dinsa tunda bai samu ta farko ba. "No ba fa wani abu bane. Kawai duba da labaran soyayyarki na baya da ki ka ban. Na karance ki, kina da zurfafawa a so." Sauke ajiyar zuciya Sadiya ta yi. "Hakane. Zan rage." Murmushi Nudrat ta yi. Ba jimawa kuma lokacin ɗaukar lakcarsu ya yi suka miƙe zuwa aji. *** Da wani irin mugun firgici Husna ke ƙara haska ƙasan gadonta. "Na shiga uku!" Ta ce a fili ganin dagaske babu layun da suke wurin. Dama ai da niyyar ta cire su ta zo, amma kuma suka ce ɗauke mu idan kin gani. Ta rasa wa za ta kira? Sadiya da suka zo tare da Habiba ƙanwar Zahra suka yi mata gyaran gidan, ko kuwa Huzaif da ta bari a gidan? Girgiza kai ta yi kirjinta na dukan tara-tara ga kuma Sadik da ke faman tsala ihun kuka yana son abincinsa. Ƙarar tsayuwar motar Huzaif da ta ji a farfajiyar gidan ne ya sa ta yi saurin gyara shimfiɗar da ta bankaɗa sannan ta nufi ɗan gadon jariran da Anti Hajara ta siya musu ta sa hannu ta dauki Sadik ta fito falon tana jijjiga shi. Daidai lokacin Huzaif ya murɗa ƙofar ya shigo da sallama ɗauke a leɓɓansa. Ta amsa gami da mishi sannu da zuwa. "Kukan me ya ke yi? Ki ba shi mama ya sha." Bai kula sannu da zuwanta ba, hankalinsa ya tafi ga ɗansa. Husna ta haɗiyi miyau, irin wannan kallon tsanar da ya ke jifanta da shi ne ta tsana. Ba ta ga ko alama yana wani rawar ƙafa ko marmarinta ba, alhalin a baya ko unguwa ta fita ta dawo ya dinga rawar ƙafa da jiki kenan yana sumbatun ya yi kewarta. Haka ta zauna ta shiga shayar da Sadik, shi kuwa ɗakinsa ya nufa bayan ya ajiye mata leda saman teburin dake tsakar falon, ya yi ciki da wata ledar a hannunsa ba tare da ya ƙara uffan ba. Ta dawo da dubanta ga ledar da ke ajiye, irin nasa ne mai tambarin Alheri Suya a jiki. Tun tana zuba idanun ganin ya fito har dai ta yanke shawarar bin bayansa. Aka ce cikin jego, damuwar da take ciki bai hana ta jin yunwa ba, ta kuwa juye suyar a faranti, ta ɗauko lemun roba mai sanyi da kofuna biyu sai ruwa ta dawo tsakiyar falon ta ajiye saman teburin. Duk da ta gan shi da wata ledar ba za ta ƙi yi masa tayin wannan ba, don ba haka suka saba ba. Sun saba da ci da sha tare. Duk da kirjinta da ke dukan tara-tara sakamakon shakkarsa da ta ke yi a yanzu, hakan bai sa ta yi karambanin ƙarasawa ga ƙofar ɗakin ta murɗa ba, ji ta yi gam a rufe. Ta hau ƙwanƙwasawa a hankali. Kamar ba za'a buɗe ba can kuma ta ji ana cire muƙullin a hankali sannan aka buɗe ƙofar. Kallon juna suka yi tsakar idanu, ta sunkuyar da kai sakamakon hararar da ya ke watsa mata. "Wani abu aka yi?" "Um um, dama abinci ne nace ka fito mu ci." "Naki ne, ga nawa nan zan ci a ɗaki." Nan da nan ta dube shi tuni hawaye sun wanke fuskarta. Kauda kai daga dubanta ya yi yana wani ƙara tamke fuska. Shi wallahi ta takura masa, ba ya buƙatar ko haɗa idanu da ita. Ga mamakinsa gani ya yi ta kai gwuiwoyinta ƙasa ta durƙusa cikin muryar kuka har da shessheƙa ta ce. "Don Allah ka yafe min idan wani laifin na maka Dear. Na gaji, zuciyata na shirin bugawa, na kasa sabo da fushinka. Ka taimaka ka faɗa min laifina zan gyara na maka alƙawari." Huzaif ya sauke ajiyar zuciya, jikinsa ya ɗan yi sanyi. Ko babu alaƙa ta aure tsakaninsu, ita ɗin jinin Malam Sa'ad ce, ta kuma fi ƙarfin wulaƙanci koda kuwa giyar wake ya sha. Ballantana a hayyacinsa ya ke. Bai san me zai yi ba ne, ya kasa controlling kansa da ma damuwar dake cin zuciyarsa. Har yanzu tunani yake akan dalilin da ya kai shi ga cin mutuncin Sadiya a baya har ya tsallake ta ya auri Husna. "Ki tashi, ba ki yi min komai ba. Tashi don Allah." Ya faɗi a tausashe, ba musu ta miƙe kuwa. "Ki je ki ci abinci, ni ma zan watsa ruwa ne zan fito na ci a falon." Ta amsa da toh. Ko babu komai ta ɗan ji sanyi a ranta. Huzaif ya bi ta da kallo, ya rasa ita zai tausayawa ko kuwa dai shi ɗin da ya wayi gari ba ya jin ko ɗigon zarra na sonta, so irin na aure. Husna murnarta ya koma ciki sa'ilin da a wajen kwanciya ya yi mata kai da ƙafa, bai kuma nuna alamar koda wasa ya na wani son kasancewa da ita a daren ba. Haka ta dinga sharar hawaye, ƙarshe bacci ya yi awon gaba da ita. *** Bayan Watanni Biyu.. Hajara wacce laulayi mai zafi ya sako a gaba irin wanda ko ruwa ta sha sai ya dawo, shi ya hana ta maida hankali sosai dangane da al'amarin Sadiya, koda dai ma a yanzun tun daga samun cikinta ta ƙara gasƙata zancen Bokan nata, ta yi amanna ba ya ƙarya, duk abin da ya ce zai faru to shi ke gudana a rayuwarta (Wa'iyazubillah). Tana ji a jikinta kamar yanda ya ce hangen dala ba shiga birni ba, to hakan ce za ta faru ga Sadiya. Wannan ne ya sa ta ƙara nutsuwa musamman ma da duniya sabuwa ta ƙara buɗewa mijinta bayan jam'iyyarsu sun haye matakin nasara a zaɓe. A gefe guda ga tarairaya da kulawa da yake ba ta, amma ba ta lokacinsa ba sai ta asusunsa. Duk abin da za ta ce tana so, komai tsadarsa to fa za ta ga ya mallaka mata. Ta kuma kula yanzu saboda cikinta sun fara ƴar tsama da Haj Nuriyya uwargidansa. Har baƙaƙen magana ta yarfa mata da ta zo duba jikinta wai Allah dai ya sa ɗan Alhajin ne saboda kamar shi ɗin juya ne, tunda da yana haihuwar a fara gani a kanta mana. Hajara ta firgita amma ta yi na ƴan duniya ta dake ba ta nuna mata razanarta a fili ba. Ita ma ta yi mata na ƴan duniya ta maida mata amsa daidai da ita wanda ya so zame musu faɗa, sai da ƙawar Haj Nuriyya da suka zo tare ta shiga tsakani ganin Hajarar ta fama laluben waya za ta sanar da Mijinsu wai za'a sheganta masa ɗa. *** Ɓangaren Sadiya ko, ban da shirye-shiryen biki a yanzun babu abin da suke yi. A sannan ma sun yi hudun satika uku na kammala semester. Biki bai fi sati uku ya yi saura ba. Hafsatu da Safiyya sai ko Adda Ruƙayya da Baba Habu sun je sun ga gidan Sadiya. Haka suka dawo suna ta santi da koɗawa. A waya suka shiga nunawa Inna tana kauda kai saboda jin nauyi.  Anti Hafsatu ta dara "Oh, Inna an fa bar yayin wannan kunyar." "Ai Mairama har yanzu fillanci bai sake ta ba. Amma kuma ban ga laifinta ba." Cewar Adda Ruƙayya kenan kasancewar kusan sa'anni suke ita da Inna ko ma ta girme ta da kaɗan. Shigowar Sadiya gidan daga shagon ɗinki ya sa suka dube ta. Safiyya ta riƙe hanci ta hau guɗa, ita dai ta fiddo idanu waje ma ta soma tunani a ƙasan rai ko yau aka kawo lefen madadin jibin da suka ce?  Sai da ta ji wai duk na taya ta murnar samun muhalli tsararre ne ta ji kunya ta rufe ta. Dama Nudrat ta fesa mata wai gidan ya yi kyau, ta kula sosai suke kashe kuɗi a bikin nan don hatta lefenta ta samu labari a bakin Nudrat  din wai a Dubai a ka haɗo da yawa a cikin wasu kayayyakin. Sauran kuwa a nan wata yar uwarsu ke haɗawa. An tambayi dai awon undies dinta ta aikawa Nudrat. "Ke waɗannan ba su ɗauki auren nan naki da wasa ba. Wannan ba uwar miji ba ce Sadiya, Uwa ce. Tana kaunarki." Abin da Safiyya ta ce da Sadiya kenan sadda Anti Hafsatu  ta ce wai Nene za ta turo mai gyara ta musamman daga Gombe, ƴar Sudan ce amma kuma mazauniyar Gomben,  da za ta zo takanas don Sadiyar ta yi mata gyararrakin aure.  Murmushi Sadiya kawai ta yi ba ta ce uffan ba sai Adda Ruƙayya ce ta cafe. "Ke dai bari, don ma fa wai a Kano ne, wani abin na san ba za su gudanar da shi irin yanda suke yi ga al'adarsu ba na aure a Gombe. Su kin ga buɗar kai ma na musamman ne, biki sosai akwai gudanarwa bayan an kai Amarya. Abin sai wanda ya gani." Ita dai Sadiya ba ta ce uffan ba. Abu ɗaya ta sani, dagaske Nene tana kaunarta, tana kuma murna da farin cikin kasancewarta wacce Hamma zai aura. Fatanta dai komai ya tafi lafiya, ita ma ta nuna wa Nene ƙaunar irin ta ƴa da uwa bayan aurensu da Hamma. Saƙo ne ya shigo wayarta, ta ɗauka tana dubawa. Hamma ke samar da ita zai shigo anjima da dare. Har wata ajiyar zuciya ta sauke na jin dadin hakan. Zuwa yanzu ta gama fahimtar cewa Hamma har yanzu bai gama mance tsohuwar budurwarsa gaba daya ba, ta gane dole sai tana hakuri da wasu halayyar nasa tunda tana sonsa. Tana ji a jikinta idan sun yi auren za ta iya sauya shi a hankali.  Damuwarta ɗaya, ita din tana son ta ga a na ba ta muhimmanci, ta saba ko Huzaif da Suraj a baya, kusan kullum sai sun gaisa an sha hira. Amma shi Hamma ba ta sani ba ko ita kaɗai yake yi wa hakan ko kuwa ɗabi'arsa ce. Bai cika kira ba, za su shafe tsawon kwana guda bai kira ta ko sun yi magana ba. Idan ta taɓa shi daga baya zai ba ta uzurin abubuwa ne suke mishi yawa amma tana ransa. Ko yanzu da ya ce mata zai zo da ta lissafa rabon da ya zo gidansu an fi sati biyu. Shi dai ba irin na baya ba ne, amma kuma komai ya yi ta rasa dalili ba ta ganin laifinsa sosai. Ita har haushin kanta take ji da irin wannan makahon so da ta ke masa. Amma hakan bai makantar da ita wajen addu'ar zaɓin Allah ba. Idan alherinta ne Allah ya tabbatar da shi matsayin mijinta. "Ke wai tunanin me ki ke yi haka kin bar mu da canki-canka?" Maganar Adda Ruƙayya ce ta katse ta. Sai a sannan ta gane zurfin da ta yi a duniyar tunani. Dubansu take cike da rashin fahimta don har ga Allah ba ta ma san me aka ce ba ake ta canki-cankar a kai. "Kin tabbatar dagaske mazan ne za su kawo lefen ba mata ba dai ko?" Sadiya ta gyaɗa kanta kawai a kunyace ba tare da ta dubi fuskokinsu ba. "To ai shikenan, Allah ya kaimu, abin kun ga zai zo da sauƙi." Cewar Adda Ruƙayya karo na biyu. Nan kuma aka shiga hira inda Adda ke ba su labarin yadda ake gudanar da al'adun biki a Gombe, ita a ƙarshe ma miƙewa ta yi ta nufi ɗaki cike da zumudi ta buɗe sif din kayanta tana son gano wanda Hamma bai taɓa gani a jikinta ba. *** Misalin ƙarfe bakwai da mintoci kuwa sai ga shi ya iso. Sai da ta jira suka gaisa da Malam sannan ta shiga falon bayan fitarsa. Sallama ce ɗauke a bakinta, Hamma ya amsa yana dubanta. Shigar ta mishi kyau, riga da siket ne na wani yadi ruwan makuba sai mayafi da ta ɗora fari. Idan ya ce Sadiya ba mai kyau ba ce to ya yaudara zuciyarsa, amma kuma Fareeda fa? Ba iyakar kyawunta yake so ba ya sani, ba kuma surarta ke fisgarsa kawai ba. A'a, wani irin so ne da ba zai misalta shi ba, irin son da duk abin da ki ka yi ba kya laifi a wurina, irin son da komai nata ado ne a wurinsa. "Barka da dare. Fatan ka wuni lafiya?" Muryar Sadiya ta maido shi hayyacinsa, ya sauke ajiyar zuciya. Ita kuwa a ɓangarenta kunya sosai ta ji na irin yanda ya ke bin ta da kallo tun shigowarta falon har ta kai ga neman wuri ta zauna. Zuciyarta kamar ta yi tsalle ta fito don jin daɗi, daga yanayin murmushin da ke saman fuskarsa yayin da ya ƙura mata na mujiya, ta fahimci kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Wato dai ta yi kyau ne fiye ma da yadda ta ke zato, a cewarta. "Barka dai My Triple. Fatan kina lafiya. Ya hutu? Ya kuma shirin biki?" "Uhum, lafiya." "Masha Allah. Ki..." Bai kai ga ƙarasawa ba wayarsa ta shiga ƙara, ya ciro ta a aljihun gaban rigarsa ya na mai duba sunan kafin ya kalli Sadiya. "Ina zuwa please. Bari na amsa wannan wayar." Ta amsa da toh, tana kallo ya miƙe ya fita, can kuma ya dawo. Sai ta kula kamar fara'arsa ta fi ta baya. "Sorry na zaunar da ke." "Bakomai." Hirarsu ma ta zama kamar dai ya rasa me zai ce. Sai ya shiga tambayar ko akwai abin da bai yi ba a gidan a gyara? Ta amsa da a'a, ba ma su yi zancen gidan da kowa ba. Nan ya ƙara sanar mata da batun kawo lefe a gobe. A ƙarshe kuma ya yi mata sallama ya tafi. Sadiya jikinta a sanyaye ta koma cikin gidan. Tunanin da ta ke yi shikenan? Mintuna goma kacal, har ya tafi? A jimawar da suka yi ba su haɗu ba har ya ƙoshi da hirar? Haka ta dinga tunani ƙarshe kuma duk ta ture ta yi masa uzurin wataƙila shirye-shirye ne ya ke hana shi kataɓus. *** Hajara tun tsayuwarta a gaban gidan nasu take cike da zullumi, lefen Sadiya za'a kawo yau? Kuma shi ta zo kallo? Abin kamar a mafarki. To wai ya yake? Wane irin suturu aka zuba? Zai doke na ta a haɗuwa da tsari ko kuwa dai a'a? Mairama za ta zuba ruwa a ƙasa ta sha da wurwuri haka kenan? Ashe ba za ta ƙunshi baƙin cikin ganin Sadiya ta tsofe a gabanta babu aure kamar yadda ta ke muradi ba? 'Na ce maki komai da ki ke gani gaibu ne, wannan yarinya har abada ba za ta auru yanzu ba. Ke mu zuba ni da ke, idan ta auri yaron nan ki zo na maida maki dukkan abin da ki ke mallaka min. Ni ma kuma ki maido min nawa.' Abin da Boka ya ce mata kenan a jiya da ta shiga wurinsa bagatatan hankali a tashe bayan ta amsa wayar Anti Hafsatu mai shaida mata kawo lefen Sadiya da za'a yi a babban gida. Ba ta san me yake nufi da ta maida mishi nasa ba, amma ta gama sanin bai wuce layu da magungunan da ya damƙa mata ba na sabon aikin da ta karɓowa Husna. Da ma dai dukkan wasu taimakon da ya taɓa bayarwa. Sauke ajiyar zuciya ta yi jin an ƙwanƙwasa gilashin motar kasancewar a rufe suke kuma na waje ba ya ganin na ciki. (Tinted glass). Ɗago kai ta yi ta kalla, Yayansu Mustafa ne tsaye. Baƙin gilashinta ta ciro a jaka ta rufe ƙwayoyin idanunta waɗanda tuni sun kaɗa jawur kamar wacce ta ci kuka. Fitowa ta yi ta rufe motar tana gaida shi bayan ta ƙaƙalo murmushin yaƙe. Ya amsa fuskarsa a sake. "Lafiya kalau Autar Mama. Waya ki ke ne? Tun ɗazu kin kasa fitowa." "Eh waya na amsa. Bari na shiga ciki." "To ba laifi. Ki je ai har an kawo kayan ma, mata sun soma kallo." Ya furta yana komawa can inda Yayansu Hashim da kuma babban wan su Huzaif suke tsaye suna hira. Ita kuwa tafiya ta ke yi tana jin amsa-kuwwar maganar Mustafa a kwanyarta, a zuciyar kuwa tamkar an soka mata mashi take ji. Yawun bakin Hajara sai da ya kafe na ɗan wucin gadi, duk da bai kai yawan akwatunanta ba, na Sadiya saiti biyu ne sai ko wani akwatin madaidaici da aka yi na Uwa da Uba. A gefe kuma ƙaton make-up kit ne kalar ruwan hoda. Manyan suturunta kuwa babu ƙasa da dubu goma, sai ko bangaren kananan kaya da sauran tarkace. Komai nata ka ɗaga an san na daban ne. Guɗa kuwa da mata ke yi a wurin ya sa Hajara ji kamar su na mata ihu a tsakar kanta. Ta daure iyakar dauriya ta na yaƙe, ƙarshe ta ɓige da karɓar Sadik a hannun Husna wanda ke tsala ihun kuka ta fita tsakar gidan da shi. Gwaggo Atine tana ganinta ta bi bayanta ta fito. Koda ta karaso ta fara da yamutsa fuska da tsaki. "Aikin ɓurr, ai wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, yo me..." "Za ki bar nan ko sai na buge bakinki?" Abin da Hajara ta faɗi kenan murya a kausashe tana watsawa Gwaggo Atine wani banzar harara. Gwaggo Atine ta saki baki sai kuma ta riƙe bakin ta bar wajen, girma ne ya riga da ya gama zubewa. Ta rantse rainin da Hajara ta mata ya haura na baya. A bayan ma ta fi ɗan ganin ƙimarta tunda gaisuwa kan gifta tsakaninsu, yanzu kuwa ai sauran mutuncin ya zube ƙasa warwas. Ta yi gaba tana jin uban tsakin da Hajara ta ja mata, sai da zuciyarta ta yi babu dadi amma kuma ya za ta yi da abin da ya fi ƙarfin wuta? Hajara kuwa ga kukan Sadik ga kuma shewar da ta ƙi ƙarewa, abu goma da ashirin dai. "Husna! Husna!!" Yanayin yadda ta ke ƙwala kiran Husnar ka san a zafafe ta ke. Jin Husna ba ta ma san ana yi ba ya sa a matuƙar fusace ta ƙarasa cikin falon. "Husna! Wai wane irin iskanci ne yaronki na faman ihu ba za ki dauke shi ki rarrashe shi ba?! Lefen baƙonki ne da za ki dinga rawar ƙafa wajen gani?" Ba ta kula ma da shirun wucin gadi da ya falon ya yi ba, idanunta sun rufe. Mamaki ne tsantsa a saman fuskokin jama'ar da ke falon ciki kuwa har da Husna don ita baki sake ma ta ke duban Hajara kafin a tsorace ta kai hannu ta karɓi Sadik ta fice daga falon idanunta cike taf da ruwan hawaye. Abin sabo ya zame mata, tun tasowarta, tsawon shekarun da suka rayu tare, ba ta san wannan ɓangare na Hajarar ba a kanta sai yanzu, ta dai  sha ganin tana gwadawa Sadiya amma kuma ita bayan shagwaɓawa da rarrashi babu abin da ta sani a wajenta. "Hajara, lafiyarki? Yau kuma abin kan ƴar lelenki ya faɗa?" Anti Hafsatu ta furta. Ganin manyan an fara ca akan abin da ta yi ne ya sa ta fice daga falon, tana jin wata na ƙusƙus wai baƙin ciki ne ƙila tunda ba ƴar ɗakinta ba aka kawowa. Ta so ta juya ta ga mai shi amma kuma ta fasa ga wani uban guɗa da wata ta saki har da faɗin. "Sadiya ta yi goshi! Amarya a gidan Audullahi, Allah dai ya kaimu a shafa fatiha!" Aka ɗauka da amin gaba ɗaya. Ta iske Husna zaune a saman kujera tana shayar da Sadik tana zubar hawaye, nan ta shiga rarrashi da fadin ba da niyya ta yi ba. "Wani magana marar dadi ne Alhaji ke  ya fada min ta waya, shi ne ki ka ga duk na ruɗe. Amma ki yi hakuri kin san ba halina ba ne ba ko? Na taɓa yi maki?" Ta girgiza kai tana share fuskarta. "Toh ki yi min uzuri. Kin ji?" Ta yi murmushi tana gyaɗa kai. Can kuma ta gano kuskuren da ta tafka a falon, hakan ya sa ta koma ta ware kamar ba ita ba. Waɗanda farko ma suka yi mata fassara duk suka ɗan ware gami da yi mata uzuri, wasu kuwa kallonta kawai suke amma gani suke har yanzu kamar da ƙiyayyar Inna a ranta. *** Biki na ƙaratowa, ana ci gaba da shirye-shirye. Ta ɓangaren gidan su Hamma. Tuni baƙi ƴan uwan Nene da na Baffa sun soma zuwa daga Gombe ciki har da wasu a ƴan gidan Mai Martaba. Nene sosai suka yi musu tarba. Baffa har ma'aikata ya ƙaro waɗanda za su dinga girki saboda baƙi. An yi fentin gidan gaba ɗaya, Nene har sauya mata kayan falo da ɗakuna ya yi. Nudrat gaba ɗaya ba ta zama, ita ce wajen Sadiya, ita ce karɓo ɗinkuna, can kuma a tsince ta a kasuwa. Haka ta ke faman zagaye. Idan ta tuno auren wa da waye sai ta ji zuciyarta na ƙara sanyi, tana alfahari da wannan auren sosai. Hamma AbdulMajid kuwa, gaba ɗaya ya koma wani shiru-shiru fiye da baya. Abokan wasa ma idan suka sako shi gaba sai dai ya yi murmushi. Ko a ranar yau da ya dawo gidan don ƙara kimtsawa sakamakon Airport da zai je tarbar Maina da wasu a cikin ƴan uwansu da suka taho daga Gombe. Nene ta kula har wata rama ya yi da ya durƙusa yana gaishe da Gwaggonninsa don haka ta miƙe ta bi shi a baya. "Wai lafiyarka kuwa? Meke damunka kwanakin nan. Hatta da abincin kirki ba ka ci, duk sadda ka shigo gidan a ƙoshe ka ke. Da safe kuwa kana gaggawa ka ke ficewa. Akwai wata matsalar ne?" Ya hau susar ƙeya yana murmushin yaƙe. "Babu komai Nene. Kawai dai yanayin zirga-zirgar kula da komai ne." Ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa sosai. Jikinta yana ba ta akwai wata a ƙasa, sauyin ya yi yawa. Ba haka nan ba. Amma kuma sai ta bi shi da toh. Shi ko lura da ya yi kamar zancen bai shige ta ba ya sa shi saurin ɗauko batun zuwan Maina. Nan da nan kuma ta saki fuskarta. "Wato haka ka yi niyyar wucewa ba ka faɗi ba balle a soma shirin tarbarsu? Tare da Mai Martaban ne?" Girgiza kai Hamma ya yi har sannan ya na ta kokarin sakin fuska yadda ya dace. "Aa, tare da su Lamiɗo ne. Mai Martaba sai safiyar ɗaurin aure zai shigo." "Allah ya kawo su lafiya. Sai ka hanzarta toh.  Bari na yi magana a fara shirin abinci." Kamar ya ce babu buƙatar hakan tunda ya sani Maina a Hotel za su sauka amma kuma ya amsa da toh ya wuce bayan Nene ta bar wurin. *** Fuskarsa cike da walwala a sa'ilin da ya fara hangen Maina, a gefensa Lamiɗo ɗa ga ƙanin Baffa. Sai Giɗaɗo ɗan wajen Fulani Amaryar Mai Martaba. Sai ko mafi kusa da Maina wanda bayan shi AbdulMajid din, Maina ba shi da amini sama da shi, wato Umar da suke kira Sadauki. Ga su nan dai su huɗu ne suke tafe, amma kuma yanayin shiga da tafiyar ƙasaitar kaɗai sun isa su bambance maka waye shi. Babu gajere a cikinsu amma kuma kaf ya fi su tsayi da jiki ƙira ta maza ababen so a wajen mata. Fari ne tas har wani ja ja yake yi, idan ko magana ake na baiwar kyawun fuska, to fa Allah zubawa Maina shi. Hamma da ke tsaye gaban motarsa fuskar ɗauke da murmushi ya ke dubansu su din ma shi suke kallo idan ka ɗauke Maina da ya maida hankali ga abin da ya ke tun kallon farko da ya mishi bai kara ba.  Shi ma AbdulMajid bai yi karambanin cewa uffan ba saboda sanin Maina ɗin waya yake yi. Suka janye zuwa gefe suka bar shi inda ya kama murfin motar ya buɗe ya shiga ya zauna yana ci gaba da zuba ruwan turanci kamar ɗan mango park. Ƙa'idarsa ce waya a handsfree, wani irin mugun sabo ya yi da hakan wanda duk masu rayuwa da shi sun sani. Sabo ne da Mai Martaba sam ba ya son shi da ita, har daina amsar kowace waya ya yi idan yana tare da shi. Can kuwa Hamma da su Giɗaɗo aka hau caccafkewa. "Ango! Ango!! Shegen kaya! Fargabar auren ce ta ramar da kai? Tun ba ka fara awo ba?" Faɗin Ishaq da suke kira Lamiɗo yana ƙarewa AbdulMajid ɗin kallo. Shi kuwa ƴar harararsa ya yi aka yi dariya. "Kai ma ashe ka kula, ni ma na ga ya yi wani haske kamar shi ma ya fara shafa lallen Amaren, amma ka rame. Sai dai tun da mun iso kafin nan zuwa ɗaurin aure za mu san yadda zamu yi ka murmure." Khamees ya ƙarashe cike da zolaya. Suka kwashe da dariya. "Kwa yi kwa gama ƴan iska. Ni har akwai auren da zai jefa ni firgici?" "Eh ai fa mun gani sadda ka maƙalewa waccan aljanar, yanzu da yake ka ƙwace daga bakin kura komai ma ka faɗi." Ya ji zancen sosai ya shige shi, bai dubi Giɗaɗo bai maganar ba ya yi wa ma'aikacin da ke tsaye kusa da su jaye da ƙaton keken da aka ɗora akwatunansu nuni da motar. "Ƙarasa a saka, boot ɗin a buɗe yake." A ladabce ya yi gaba. "Mu ma fa ba nan zamu kwana ba, don Allah ku dinga yi wa Maina faɗa. Ni fa na tsani a cika mana kunnuwa da hayaniyar da babu mu a ciki. Why on earth ace sai mutum ya saka waya a handsfree idan zai yi ta?" Dawud (Giɗaɗo) ya furta yana ɗan shan mur. "Ai kai ma ka na da baki, sai ka faɗa masa ko zai ji." Khamees ya furta da ƴar dariyarsa. Hon ɗin da suka ji ne ya ba su tabbacin su yake jira. Nan suka taka bayan AbdulMajid ya sallami ma'aikacin ya rufe boot dinsa, yana zaune gefen direba. "Manyan ƙasa, barka da isowa." Maina ba tare da ya kalle shi ba hankalinsa na ga kallon gaban motar ya ɗan murmusa. "Abdul Ango, fatan mun same ku lafiya?" Hamma ya jinjina kai. "Alhamdulillah." Khamees ya ce, "Ba ka kula da ramar da mutumin ya yi ba?" Ya ɗago lumsassun idanunsa ya ɗan dubi Hamma wanda hasken fitilun titin fita daga tashar jirgin sama ya haska fuskarsa, sai ya kauda kai yana ɗan ɗaga kafaɗa. "Wani abu ne? Bai wuce na rashin hutu." "Hakane." Khamees ya amsa a taƙaice su Lamiɗo na mishi dariya. Shi kuwa Hamma wata ƴar guntuwar ajiyar zuciya ya sauke. Shi kaɗai ya san meke cin ransa. Yana jin wayarsa na faman ruri a gefen aljihun rigarsa amma bai ko yi yunƙurin fiddowa ba sanin da ya yi tatsuniyar gizo ba ta wuce na ƙoƙi. *** A kwanakin da aka kwashe a na yi wa Sadiya gyara, idan ka gan ta kai ka rantse wata ɗiyar shahararren mai arziƙin ce. Fatarta ta goge ta yi tas tamkar ka taɓa jini ya fito, har wani sheƙi take yi ga santsi da laushi da fatar ta yi. Sosai matar da ke mata gyaran ta ba da himma a aikinta. A gefe ma ga su Adda Ruƙayya na mata nasu irin kalar gyaran na jiki. Kamar wancan karon, wannan karon ma Abba ne ya rantse shi zai yi komai na kayan ɗakin Sadiya. Kusan ma waɗanda ya yi a yanzun sun ninka na farko a tsada har sai da Malam ya so ya bari ko wani abin ya yi amma Abba ya ce sam. Ƙarshe ma har faɗa Abban ya yi akan don me zai yi kokarin taka masa burki a abin da zai yi ga ɗiyarsa. Duka waɗannan sha'anin da kowa ke yi, a ɓangaren Sadiya ita kaɗai ta san meke cin zuciyarta. Damuwa ce tsantsa da rashin sukuni na irin bagararwar da Hamma ke mata. Babu waya balle saƙon rubutu. Idan ma ta kira ko ya ɗaga bada haƙuri ne zai biyo baya da fadin zai kira ta yana wani abun. Ƙirjinta koyaushe cikin bugun tara-tara yake yi. Hankalinta kuwa idan ya yi dubu to fa a matuƙar tashe yake. A na gobe za'a sanya ta a lalle ta kasa haƙuri sadda Nudrat ta zo gidan kawo mata kayan fulanin da za ta saka ran kamu har da komai na kwalliyarsu. Ta dube ta bayan ɗakin ya yi saura su biyu kawai a ciki ta ce. "Ni kam Hammanki abubuwa ne suka yi mishi yawa haka? Ko ba shi da lafiya ne? Na ga mun jima ba waya ba chatting. Allah ya sa lafiya ya ke." Ta ƙarashe tana jin hawaye na cicciko mata amma ta haɗiye su gudun nuna rauninta a gaban Nudrat. Nudrat ta ji Sadiyar ta mata fami da abin da ke mata ƙaiƙaiyi a zuciya, amma kuma ba ta son ƙarasa karya mata nata zuciyar don haka ta yi ɗan yaƙe. "Kai lafiyarsa kalau sai dai ko hidimar. Kin san Maina sun zo, ko ban faɗi ba kin san yadda ya ɗaukake shi. Ni na san abin da ya hana ki jin sa kenan." Nudrat ta faɗi ba don tana da tabbacin Sadiya ta yarda da kalamanta ba ko a'a, ta faɗi ne don rasa abin da za ta ce ba kuma wai saboda kare ɗan uwanta ba, a'a, kawai don Sadiya ta ji sanyi a ranta. Ta kuma ji ƙarfin ci gaba da shirin bikinta. A gefen Sadiya murmushi da gyaɗa kai ta yi lokaci guda. Ta ji, amma ba ji irin na yarda ba, ji irin na a tafi a hakan kawai don ƙarfafawa Nudrat gwuiwar ta gasƙata kalamanta ɗin. Amma tana ji a jikinta ko mene ne ƙila ya sauya ra'ayi ne, ƙila ya gane ba ita ta cancanci zama matarsa ba. Ta san irin hakan, amma kuma ba ta so ta ci gaba da gasƙata gaskiyar. Inama wannan karon gaskiyar ta ƙaryata tunaninta, sai dai zai wahala kasantuwar hakan. Riƙo hannunta da Nudrat ta yi ne ya sa ta kalle ta. "Kar ki saka komai a ranki. In sha Allah jibi war haka mun miƙa ki ɗakin aurenki da Hamma." Murmushin ta yi karo na biyu wannan karon har fararen haƙoranta na bayyana. "Allah ya nuna mana toh." Nudrat ta amsa da amin. Daga bisani ta yi mata sallama ta fice. Sadiya ta ji zubowar hawayen da ta ke riƙewa. 'Ya Allah, ka tabbatar min da alkhairi.' Ta furta a zuciya kafin ta sa hannu ta ɗauke ruwan hawayen. *** Washegari aka sanya Amarya a lalle. Suƙa yi shi a zamanance a farfajiyar gidan Abba da ya sha ado. Ga mai hotuna nan. Sadiya ta sha atamfarta cote d'voire babbar. Ta yi kyau shar abin ta. Ga mai hoto da aka kira ya dinga ɗaukarsu. Mami sai nan nan take da Amarya don ji take inama tun farko ita Huzaif ya aura. Nadama tsantsa take yi. Ga Hajara kuwa kallon kowa ɗai-ɗai take sai dai a matuƙar firgice take. Ko yau Asubancin zuwa gidan Boka ta yi don jin yadda aka haihu a ragaya. Yo akan wane dalili a na gafara Sa kuma ba ta ga ƙaho ba? Har yaushe? Abu na ƙara tafiya, amma kuma babu wata alama ta nasara. Har aka kammala taron ba ta shiga hoto ko ɗaya ba. Koda aka tashi ta kula da Zahra wacce ta ja hannun Amarya Sadiya suka zagaya can wurin garden na gidan Abba suna ƙusƙus. Gaba ɗaya sai hankalinta kacokam ya koma garesu don haka a gaggauce ta miƙe daga inda suke zaune ita da su Waleedah ƙawayenta ta bi sahu. Ta ja burki daga nesa da su tana jin murya Zahra na rarrashin Sadiya da faɗin. "Don Allah ki saki ranki, hawayen ne bana so Sadiya. Me kike so jama'ar gidan nan su hankalta da shi? Kar ki manta fa gidan tsohon saurayinki ne ko me za'a ce ba zai sauya wa tuwo zani ba. Ki saka a rai ba wai fasa auren ne ya sa Hamma ba ya nemanki ba, da hakan ne ai ko yan uwansa ba za'a ga ƙyallinsu ba a yau. Kalli yadda suke kaunarki, ni ina ji a jikina ko mene ne bayan auren za ku magance shi. Please ki rage damuwarnan. Ni bana son ganinki haka. Kin ji?" Iyakar nan ta ji, sai ta juya ta tafi tana jin zuciyarta kamar ta yi tsalle ta fito tsabar farin ciki da jin daɗi. Har wata dariya ta yi na murna. 'Shege Boka.' Ta yi furucin a zuciyarta gami da ƙara ƙyaƙyacewa da dariya. Da ta ƙarasa ga su Waleedah har sai da suka kasa haƙuri suka tambayi ko wani albishirin aka yi mata. Ta yi farr da idanu tana doka uban murmushi. "Albishirin da aka yi min ai ya wuce zatonku. Ku dai a yi sha'ani kawai." Daga haka ta share su ta maida duba ga Sadiya da Zahra da suka taho wurin jama'ar da wani murmushin da ta riga ta gane na dole ne a saman fuskar Sadiyar sai ta ji kamar ta yi tsalle da juyi. Har wata ajiyar zuciya ta sauke tana kissima irin kyautar bajintar da za ta yi ga Boka idan haƙanta ya cimma ruwa. *** Hamma AbdulMajid kuwa babban abin da ya ke cin zuciyarsa a yanzun bai wuce samu da rashin da yake gani ƙiri-ƙiri na shirin afkar masa ba. Kullum soyayyar Fareeda ke ƙara ninkuwa fiye da baya a ransa. Musamman yanzun da take hana shi sukuni da rikici da koke-koke tana mishi rantsuwar tana sonsa. Tana roƙon kar ya auri Sadiya ya zo su yi aure. Wannan ke ƙara tada tsumin sonta. Ya ji ma waya da Sadiya ba ya buƙata balle zuwa wajenta. Sai ya shafe mintoci suna waya da Fareeda suna jifan juna da kalamai masu sanyaya rai. A gefe guda kuwa ganin yadda kowa ya duƙufa a shirye-shiryen bikinsa yana ƙara hana shi sakat. Ya yanke ya samu Baffa da batun Fareeda amma kuma yana shakkar hakan. Ba sa kawo wa Baffa wargi, sai dai yana ji a jikinsa ba zai iya zaman aure da wata bayan Fareedarsa ba. Ai da tsohuwar zuma ake magani. Dama a rashin ta ne ya koma kan Sadiya. Toh buƙatar maje hajji sallah, tunda yanzun ya samu tsuntsu daga sama gasashshe, aikuwa komai ta fanjama-fanjam! Ya shirya wa dukkanin ƙalubalen da zai fuskanta muddin haƙansa zai cimma ruwa. Yanzun ma yana tsaye a farfajiyar gidan ya yi zurfi a tunanin abin da zuciyarsa ta riga ta yanke mishi, akwai wani Kawunsu wanda kaf duniya ya sani shi kaɗai ne zai iya shige mishi gaba ko ba da sanin kowa ba ya kai ga nasara a auren Fareeda. Ya ji ya gani, idan har kuɗi su ne matsalar Kawun, zai cika mishi asusunsa muddin dai komai zai tafi yadda ya ke so. Bai ji zuwansa ba, sai ƙamshin turarukansa masu tsada ne hancinsa ya soma shaƙo mishi. Ya juya kai ya kalle shi. Maina ya kauda kansa ya na mai zura hannunsa cikin aljihun wandon shaddarsa ruwan toka da ta sha aiki. Kansa babu hula sai kwantaccen sumarsa mai cika da laushi. "Duka wannan a kanta ne? Ta cancanci wannan girman sadaukarwar?" Kan Hamma ya ƙulle, wai meyasa Maina ya karance shi fiye da kowa ne? Kwanakin da Maina suka yi, ya lura duka tarin tambayoyin da su Giaɗo ke yawan jifansa da su, shi ko sau ɗaya bai ce mishi uffan ba sai dai ya san shirun Maina na nufin abubuwa da dama. Kaifin idanunsa a kansa koyaushe ya sa ba ya ma son suna haɗa idanu don sai ya ga kamar a kallon ya gane komi da yake lulluɓe a duniyarsa. Yanzun ma ya ƙara ɗimuwa da jin yanayin tambayoyin nan. "Iyaye, yan uwa, abokai, duka kana tare da su. No Abdul, kar ka yi gangancin saɓawa umarninsu. Fareeda.." Ya furta a ƙarshe, ai gaba ɗaya kuma Hamma sai ya yi saranda kirjinsa na bugu da sauri-sauri. Shi ko Maina ba tare da ya ƙara kallonsa ba ya ci gaba da zancensa bayan wasu daƙiƙu. "Ba ta cancanci dukkan waɗannan sadaukarwa ba. Cikinsu kuwa har da kai, ba ta cancanci zama wata ɓangare a rayuwarka ba. Think!" Yana kai wa nan ya juya ya bar wurin. Wayar da AbdulMajid ke yi da Fareeda a daren jiyan, babu wanda bai shiga kunnuwansa ba. Ya ji yunƙurin da yake yi, ya ji abin da zuciyar Abdul din ke raya masa. Yana girmama soyayya, amma ya tsani yaudara da cin amana. Bai kuma fiye yi wa mutane kutse a lamuransu ba, amma wannan ba zai iya shiru ba. Shi kuwa Hamma ya fahimci komai, ko yaya Maina ya san wani abun. Girgiza kai ya yi. Yana girmama shi, girmamawa irin ta yadda ya ke jin nauyin ja da maganarsa, sai dai a wannan karon ya tsinci kansa a kokwanton yin ko bari. *** Hajara ke ɗirkar dariya yayin da ta yi zaman dirshan a gaban Bokanta wanda shi ɗin ma ke taya ta. Ya katse ta da fadin. "Ai na faɗamaki komai fa zai tafi daidai da yadda ake buƙatarsa. Ranar ɗaurin auren a nan za ki sha mamaki domin yarinyar nan har abada ba za ta auru ba ni na faɗamaki." Ta jinjina kai zuciyarta wasai. "Na yarda yanzu kam. A farko na tsorata ainun, amma yanzu na ƙara yarda da lamarinka ɗari bisa ɗari. Ka cigaba da aikinka, komai yana tafiya daidai." Ya yi wata shaƙiyyar dariya. Nan kuma da kanta ta nemi su ga juna duk don ta faranta masa. Aikuwa ya shiga washe baki kamar gonar auduga ganin abin nema ya samu. Sun kuwa jima suna sheƙe ayarsu don cikin dake tattare da Hajara ba abin da ya ƙara mata sai kwaɗayi, ba na kowa ba kuwa sai shi din. Ta rasa wannan jaraba amma kuma idan abin ya taso kamar ta yi hauka matuƙar ba ta zo wurinsa ba. *** Ta danne zuciyarta a daren da aka dawo daga shagalin yinin da aka fita can ɗakin taro na musamman a ka gudanar, ta kira Hamma a waya ganin shi da kansa kamar ya rufe babinta a rayuwa. Ringing ya dinga yi kamar zai katse kafin a ɗaga amma ya yi shiru bai ce komai ba. Ta haɗiyi miyau tana mai danne abin da ke taso mata na ɓacin rai ta yi sallama. Ya amsa mata ciki-ciki. "Barka da dare Hamma. Ya hidima?" "Lafiya." Ya amsa a daƙile. Hawayen da take riƙewa suka zubo a kuncinta. "Dama..dama.." Sai ta kasa cewa komai ta sa hannu ta toshe bakinta gudun kar ya ji muryarta tana kuka. "Zan kira ki gobe kin ji? Yanzu ko mene ne ki yi hakuri ki kwanta ki samu bacci don nasan a gajiye ki ke. Sai da safe." Bai jira amsarta ba ya kashe kiran. Ta kuwa shiga rera kuka tana mai ji a ranta har abada zai wahala aurenta da Hamma ya yiwu. "Sadiya, kuka ki ke? Mene ne?" Ta tsinci muryar Anti Hafsatu a kanta, da sauri ta shiga share fuska. Ta yi zaton kowa ya yi bacci don haka ta fito zauren gidan nasu domin amsa wayar, sai dai tun fitowarta Anti Hafsatu wacce motsi ko ya ya yake idan ta ji sai ta farka, ta hange ta za ta fita. A zatonta ma fitsari za ta je yi kasancewar bandakin dake cikin ɗakin yana da matsala don haka ita ma ta miƙe jin fitsarin ya taho mata. Farko kwankwasa bandakin ta yi, jin shiru kawai sai ta ji kamar muryar Sadiya a zauren, dalili kenan da ta ƙaraso jin kuka take yi. Sadiya tana jin an zo gaɓar da ba za ta iya ɓoye damuwarta ba, ta shige jikin Anti Hafsatun ta na kuka sosai. Hankalin Antin idan ya yi dubu to fa ya tashi. A gigice ta ɗago kanta. "Innalillahi...ki daure ki nutsu kar ki tashi mutanen gidan. Ki faɗa min mene ne. Wani abu ne ya faru?" Ta haɗiye kukanta gudun kar ta tashe su kamar yadda Anti Hafsatu ta tunasar da ita. "Anti, Hamma ne." Idanu waje Anti Hafsatu ta riƙe ƙirjinta. "Me ya faru?" Nan ta zayyane mata irin shariyar da ya ke mata kai ka ce dole aka yi mishi sai ya aure ta. Hatta da labarin soyayyarsa da Fareeda sai da ta sanar da ita har ma da silar fasa aurensu wanda Hamman bai ga laifinta ba. Sadiya ta ƙara da cewa. "Anti a haka goben za'a ɗaura aurenmu? Kalli yadda yake min. Tsoro nake kar ya ce ba zai aure ni ba. " Salati Anti Hafsatu ta ja, abin take ji kamar almara. Daga labarin da Sadiya ta ba ta, ta kula a rashin Fareedar ce, ya sanya shi dawowa gareta. "Tirƙashi!" Ta faɗi a fili zuciyarta na mata zafi. Hakan ya sa Sadiya yunƙurin fashewa da wani sabon kukan. Nan Anti Hafsatu ta shiga rarrashi kafin ta ja ta su koma ɗaki. Ita ta sanya ta yin alwala ta gabatar da sallar nafila. Addu'a sosai ta yi na nemawa kanta zaɓin Allah. Sai kuma ta ji zuciyarta ta rage nauyin da ta yi a farko. Har ta ji salamar da ta samu bacci ya yi awon gaba da ita. Washegari da safe Anti Hafsatu ta ɗauke ta zuwa gidanta sakamakon gyara na musamman kuma na ƙarshe a ranar da mai gyaran jikin wurin Nene za ta yi mata. Kusan abubuwan da ta sha ya fi na koyaushe hakanan gyaran ya kasance na daban da sauran kwanakin baya. Ana kammalawa ta yi wanka, dama tuni an yi magana da mai kwalliya za ta zo har gidan ta yi mata. Hakan kuwa ya faru, aka yi mata kwalliya ta fito fess da ita. Farin leshin mai adon zaiba dake jikinta ya zauna ɗas ya fiddo kyakkyawar surarta. Ta ko'ina ta ƙara cika ta yi kumari. Kirjin nan kamar ya fashe tsabar cika hakanan mazaunanta. Ta yafe kanta da babban mayafi. Duka wannan sha'anin da ake Anti Hafsatu suna zuzuta kyawun da ta yi,  hankalinta kusan ya soma rabuwa da jikinta. Kirjinta kuwa na dukan tara-tara. Da zarar ta duba agogo ta ga  ƙarfe biyun rana na ƙara gabatowa, sai ta ji kamar a na ƙara mata bugun zuciya ne haɗe da fargaba da tsoron makomarta a yau. Har aka kammala komai suka kama hanyar tafiya can gidan lokacin ƙarfe sha biyu ta wuce ba ta dawo nutsuwarta ba. *** A ɓangaren Hamma kuwa, tun wayewar garin ranar ya gama yanke shirin da ya ƙulla. Bai nunawa kowa komai ba kamar yanda suka tsara, asalima ya ɗan saki fuskarsa ba kamar kwanaki ba. Maina kallonsa yake amma bai ce mishi uffan ba sai dai a jikinsa ya ke jin wannan sauyi na farat ɗaya a wajen AbdulMajid akwai babbar alamar tambaya a tattare da shi. Su Baffa kuwa sun wuce ne tarbo Mai Martaba daga Airport. Koda ya zo sai da ya fara isa fadar Sarkin Kano bayan sun gaisa ne ya wuce kai tsaye wurin ɗaurin auren, lokacin ƙarfe biyu saura ƴan mintoci. Hankalin su Maina da ma sauran jama'a duka ya tafi can. Ba su ko kula da ɓacewar AbdulMajid a tawaga ba suna faman nan da nan da abokansu, wasu ma duk daga ƙasar waje suka zo. Mai Martaba na isowa kuwa aka fara shirin ɗaura aure. Wuri ya cika ba matsaka tsinke. A sannan ne Baffa ya shiga laluben Hamma a cikin matasan, nan Maina da su Giɗaɗo suka tabbatar ba ya tare da su. Koda aka kikkira wayar a kashe. Kawu Surajo wanda shi ne matsayin waliyyin Hamma, ya ji shigowar saƙo wayarsa. Kansa ya ɗauki zafi bai ko duba ba, an yanke ɗaura auren kawai idan ya so daga baya a yi batun inda Hamma ya ɓoye. Amma kuma kiran da aka dinga jera mishi ya sa tunanin duba wayar ya zo mishi. Cirowar da ya yi ya duba, sai ya ga missedcalls din AbdulMajid ne. Can ya buɗe saƙon ya karanta. "Kawu don Allah kar a ɗaura auren nan. Ko mene ne a jira zan zo. Zan muku bayani." Kawu Surajo ya yi kasaƙe, idan ya kalli Baffa da ke zaune ƙasan kujerar Mai Martaba, sai ya maida hankali ga su Liman da manyan mutanen da wurin ya tara. "Waliyyin Ango ya matso." Liman ya ƙara fadi a sifika. Maina dake gefe zaune kallo ɗaya za ka yi masa ka gane ransa ya ɓaci, yana tsoron abin da tunaninsa ke ba shi AbdulMajid ya aikata. Hankalinsa ya yi nisa a tunani ya ji muryar Baffa dake gab da shi na faɗin. "Wane irin wasan yara ne haka? Me AbdulMajid yake nufi da a tsayar da ɗaurin auren?" Maina ya ɗago kai ya dube su. Nan kuma aka fara ƙus ƙus wanda har ya je kunnuwan Abba da ke wajen matsayin waliyyin Amarya. Hankalinsa ya tashi ainun haka ma Malam da ya shiga salati a ƙasan ransa. Nan Mai Martaba wanda tuni aka sanar da shi, ya ba da umarni ga Maina ya kira AbdulMajid. Maina ya fiddo waya, da wannan mugun sabon na sa ya danna kiran wayar Hamma bayan ya sanya a handsfree. Kallo ɗaya Mai Martaba ya masa ya kauda kai ransa na zafi har muryar AbdulMajid ta cika wajen. Aikuwa na kusa da wurin suka yi shiru ana son jin ta bakinsa. "AbdulMajid, kana ina? Duk inda ka ke ka zo ana buƙatarka a nan." "No Maina, ba zan iya ba. Wallahi ba na son Sadiya. Na rasa ta yanda zan ɓullo wa Baffa da zancen. Yanzu haka zancen da nake maka muna tare da Kawu Ali an ɗaura aurena da Fareeda. Don..." Kitt Maina ya katse kiran har wani gumi ya ji ya tsastsafo a goshinsa. Wuri ya ɗauki salati. Mai Martaba wanda ransa ya gama kai wa bango da wannan ɗanyen aikin na ɗan nasa wanda a duniya bai iya waya ta sirri ba ya yi wa dogarinsa magana ƙasa-ƙasa. Malam da su Abba kuwa kansu ya yi mugun ɗaukar zafi, ransu idan ya yi dubu to ya yi ƙololuwar ɓaci. Baffa ya rasa ina zai saka kamsa tsabar kunyar da ta lulluɓe shi, ganinsa har wani dusashewa ya yi haka nan jinsa. Wato ka haifi ɗa ba ka haifi halinsa ba, yau a bainar jama'a AbdulMajid ya zaɓi ya tozarta shi? Nan da nan masu jiran ƙiris har sun fice sun fara yaɗa abin da kunnuwansu suka tsinta. Nan da nan aka ja Abba da Malam gefe suka tattauna da Jarmai babu wanda ya san me ake shiryawa. Su Maina da Lamiɗo sai gani suka yi an cigaba da daurin aure. Kamar a mafarki, kamar kuma almara ya ji muryar mai sanarwa yana shela a lasifika yana fadin. "An ɗaura auren Ibraheem Tafida ɗa ga Mai Martaba Sarkin Gombe da Sadiya Sa'ad Shagari akan sadaki naira na gugan naira har dubu ɗari biyar." Sai wuri ya ɗauki kabbara. Malam ya share hawayen tsantsar farin ciki da dadi. Mutane aka hau kallon kallo, Maina kuwa ya yi ɗif! Ya ji duniyarsa na juyawa, da gaggawa ya kai duba ga Mai Martaba sai dai tuni ya sadda kansa sakamakon haɗa idanun da suka wanda kwarjinin ya yi mishi yawa. Ƙirjinsa ke bugu da ƙarfi, shi kuma? Shi dai Maina ko kuwa akwai wani Ibraheem Tafida bayan shi? 'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Ya furta a ƙasan ransa. Sadiya gaba ɗaya ta yi wuri-wuri da ita. Tana zaune ne kawai a ɗakin nasu tare da su Zahra da Nudrat wacce tun safe ta taho nan don ta ce ita ɓangaren aminiyarta take, sai faman kai kawo na ajiyewa ƙawayen Sadiya abinci suke yi. A farko ma yaƙe take bin su da shi daga baya fuskarta kadai ka kalla za ka shaida cike take da tarin damuwa. Ta ƙara duban agogon wayarta, ƙarfe uku saura mintuna. Hayaniyar da ke falon na ƴanmatan da shewarsu bai sa hankalinta kasa kai wa ga babban dan Anti Hafsatu mai shekaru goma sha uku ba, Ameer. Yanayin yadda ya shigo falon kamar wanda aka jefo ka san cewa da magana a bakinsa haka kuma ya juya da sauri ya fita, kamar ta miƙe ta ji me zai ce tunda ta san ya bi su Abba ɗaurin aure amma kuma bakinta da ƙirji suka yi nauyi lokaci guda. Har ji ta yi fitsari ya cika mararta. Tuni ta ajiye ƴar ƙaramar fankar dake hannunta wanda ke taimakawa gurin sama mata wadatacciyar iskar da zai hana kwalliyarta lalacewa. "Kai Ameer! Ameer!! An ɗaura auren?!" Ta ɗaga kai ta kalli Zahra a gaggauce kafin ta bi hanya da kallo cike da fatan Ameer din ya dawo a ji amsarsa. "Haba ke ma dai kin san ta zama ta Hammana yanzu. Uku fa ina ji ya kusa. Bari na leƙa ma." Cewae Nudrat tana dariya daidai lokacin da take ficewa zuwa cikin gidan. Nan Zahra ta mara mata baya saboda ta gama karantar Sadiya, ta san kuma tsoron da ta ke yi. Ita ma kuma ta ji nata hankalin ya ƙi kwanciya, so take ta samu labarin ɗaura auren yadda za ta kawo wa Sadiya albishir mai daɗi. Hayaniyar da ke tashi a tsakar gidan ya sa wasu dake zaune suna cin abinci har ma ita kanta Sadiya miƙewa zuwa can. Mutane sun yi yawan da ba ta iya hangen fuskokin su Anti Hafsatu da ma Husna da sauran dangi dake maganganu. Sai dai kunnuwanta tsaf suke zuƙo mata muryoyinsu suna buga salati. Can kuma ta ji muryar Antinta Safiyya a hautsine tana faɗin. "Kai Ameer dagaske ka ke yi? Ango ya gudu? Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!" Ita ma sai ta ji bakinta ya hau ambaton Innalillahi da ta ji Anti Safiyya na faɗi. Ta ɗan yi taga-taga, wata ƴar makarantarsu ta yi saurin rungumota ta gefen kafaɗa. "Kai! Maza ɓace min daga nan! Yara sai ɗauko zance!" Gaba ɗaya suka maida hankali ga duban mai maganar, su Baba Habu ne. Nan ya dubi kowa. "Ku kwantar da hankalinku, aure har ma an gama ɗaura shi. Ba wani tashin hankali ba ne." Nan kuma ya ja hannun Sadiya wacce ta rasa wane yanayi take ciki, ciwon kai, zazzaɓi da ma faduwar gaba fiye da na baya sosai suka tarar mata. Ganin haka su Anti Hafsatu da Hajara wacce ta ga sama ta ga rashi suka mara mishi baya har kuwa cikin wasu a dangin Malam din da ma Inna. Ta zauna kawai tana duban yayan nata. Falon dai babu wani bare. Kafin Baba Habu ya kai ga cewa wani abu sai ga Abba da Malam sun shigo gidan daga can gidan Baffa inda Mai Martaba ya buƙaci ganinsu aka yi magana sosai. Hajara gumi ta ji ya fara tsastsafo mata musamman ganin fuskar Abba a sake. "Habubakar, meke faruwa ne? An saka mu a duhu." Wata dattijuwa a dangin su Malam wacce ke matsayin Uwa a wurinsa ta fadi tana duban Abba. Ya na murmushi ta ce. "Babu abin da ya faru sai alheri. Aure kuma an riga da an ɗora shi. Ku zauna a yi magana ta nutsuwa." Nan kowa ya zauna. Hajara wacce dama tun kafin ya kai aya ta zube ƙasa sharaf babu ma wanda ya kula da ita. Gaba ɗaya jikinta ya gama mutuwa ta yadda ƙafafunta suka kasa ɗaukarta, ɗazun tana tsakar gida ne ta ci uban ado tana tauna cingam a zaune saman kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ƙarewa masu shige da fice kallo zuciyarta wasai, ko a mafarki ba ta yi tunanin wannan baƙin cikin za ta riska a gaba ba don har wata shewa take bugawa ita ce har da gayyatar jiga-jigan ƙawayenta kawai don a zo a taya ta dariyar rincaɓewa da auren Sadiya zai yi. Sai dai me? Jin zantukan da Abba ya shiga yi ya sa ta ji ashe dai firgicin da ta shiga da zancen farko na Abba mai sauƙi ne kan labarin da ya soma ba su bayan bude taro da addu'a da ma yin doguwar nasiha ga Sadiya har da nunawa kowa na falon muhimmancin yarda da ƙaddara. Kamar daga sama kuma ta ji yana fadin. "To a ƙarshe da haka ta faru, auren a take bisa umarnin Mai Martaba Sarkin Gombe, aka ɗaura shi da ɗansa Ibraheem da suke kira Maina." Nan falon ya ɗauki kabbara sai kuma wata guɗa da wata Gwaggonsu ta ɓangaren Malam ta rangaɗa duk da hawayen da suka yi wa fuskarta kaca-kaca saboda ruɗanin da zuƙatansu suka shiga da farko. Su Anti Hafsatu da Safiyya su kansu sai kukan ya koma dariya. Inna dama ba ta falon tana can ɗakinta amma kuma cike take da fargabar me ke gudana a falon Malam. Sadiya har a lokacin kanta tana ƙasa, rawar sanyi sosai take yi. Hawaye kuwa wani na bin wani, wai Hamma ne ya ce ba ya sonta? An ɗaura masa aure da Fareeda? Meyasa duk wanda ta ƙaunata yake gudunta ne? Ko soyayyar ce ba ta karɓe ta ba? 'Maina? Mai..." Cikin daƙiƙa biyar ta tuno shi, shi ne tabbas. Ɗan uwa kuma aboki ga Hamma ɗan Sarki. Kawai sai ta ji ƙarfin kukanta ya ƙaru. Mutumin da ko ganin juna ba su taɓa yi ba? Za ta iya rantsewa tun wayarsu ta farko kuma ta ƙarshe ta ji bai mata ba, ta tsane shi. "SubhanAllah, ai zazzaɓi ne a jikinta." Ba ta ji ma sadda Husna ta kai hannu saman goshinta ba, sai furucin da ta ji ya dakar mata kunne. "Ki yi hakuri Sadiya, bari a karɓo maki magani. Amma lallai ki sani gobe idan Allah ya kaimu jirgin safe za ku bi zuwa Gombe tare da mijinki." Abin da Abba ya furta kenan. Nan kuma ya ba wa kowa umarnin tafiya yace a bar Sadiya a falon ta huta bayan ya ba Baba Habu umarnin siyo mata maganin zazzaɓin. Bayan kowa ya watse a falon daga shi sai Malam sai Sadiya dake dunƙule a gefe tana kuka murya a shaƙe. Abba ya ƙara yi mata doguwar nasiha ya kuma roƙe ta kar ta ba su kunya, kamar yadda shi AbdulMajid ya so su kunyata amma Allah ya rufamusu asiri, toh ta daure ta yi hakurin zama da mijin da Allah ya zaɓar mata. Ta jinjina kai tana share majina da hankicif dake hannunta. Sai da ya kammala sannan Malam shi ma ya sanya mata albarka ya ƙara da ƴar guntuwar nasiha kafin su ce ta kwanta ta huta za su koma sallamar baƙin da suka zo daga nesa waɗanda ke can babban gida. Bayan fitarsu ta haye saman doguwar kujerar mai cin mutum uku ta kwanta, ba jimawa sai ga Zahra ta shigo. Ganinta yasa Sadiya miƙewa ta fada jikinta ta buɗe sabon shafin kuka. Ita ma Zahra hawayen ta ji sun zubo mata, ta yi mata murna da wannan sauyi, sai dai kuma hakan bai hana jin tausayinta ba. Ta riga ta san irin zafafa so da ƙawarta ke yi idan ta tashi, komai na son ba ta iya shi ba. Ba ta tafiyar da kanta a duniyarsa a hankali, tana zurfafawa ne gaba ɗayanta ta shige. Toh irin wannan ranar ake tsoro. Can kuma ta share nata hawayen don bai kamata ita da za ta lallaɓa ba, ta sanya ta wani kukan.  Sadiya ta ɗago kai ta na dubanta. "Ki na ganin hakan daidai ne? Ya rayuwata za ta kasance a Gombe? Zahra na taɓa baki labarin Maina, ba kalana ba ne. Ya fi ni aji da ma dukkan wani abu da zan ɗaga na yi tutiya da shi. Babu wanda ya hango shi ma kamar dole aka masa a kaina? Ta ya ya zai so macen da bai santa ba bai san halinta ba? Ni fa? An tabbatar idan muka rayu tare zan so shi?  Kuma da suke batun tura ni Gombe shikenan na bar karatuna?" Zahra ta yi murmushi a kokarin danne nata damuwar. "Sadiya godiya ya kamata ki yi wa Allah. Kar ki yi baƙin ciki bisa dukkan zaɓin da ya yi maki. Ki duba iyayenki da ma manyan mutanen da suka hallara a taron ɗaurin aurenki, idan har AbdulMajid bai ko duba su ba ya tsallake ya je aka aura mishi Fareeda, toh ki sani girman sonta da yake yi ya wuce misalin da zan kwatanta maki. Idanunsa sun rufe ya zaɓi ya kunyata iyayensa da namu da ke kanki a idanun jama'a ya bi son zuciyarsa. Dayake Allah ba azzalumin bawansa ba, sai ya yi maki sakayya nan take. Ya ba ki wanda ya fi Abdul kyan nasaba da komai na rayuwa. Don Allah kada ki yi baƙin ciki, addu'a ki ke ta yi na nemawa kanki zaɓin Allah ko? To ki saka a ranki Ibraheem Tafida shi ya zaɓa maki. Kukanki kamar butulci ne ga ni'imar da Allah ya maki. Ke ba za ki gane akwai masu jiran faruwar hakan ba sai idan kin ga yadda Anti Hajara ta fice daga gidan nan kamar kububuwa ta cika ta yi fam! A kan kunnena cikin harshen turanci na ji cikin ƙawayenta na fadin ta gama cika musu bakin yau ba za a ɗaura aurenki ba har tanadin liyafa ta yi a gidanta zasu je can ƙarfe huɗu a yi shagali. Toh Sadiya wannan kaɗai ba..." Maganganun Zahra suka katse saboda sallamar da Anti Hafsatu ta yi ta shigo hannunta ɗauke da leda mai tambarin wani babban kemis dake kusa da su. Sadiya wacce nasihar Zahra ya shige ta sosai gaba ɗaya ta ji zuciyarta ta sanyaya, abu ɗaya kuma da ta sani har ga Allah ba ta san ta ya za ta fara rayuwa da wanda ba ta ma san shi ba balle ta ji sonsa a zuciya. Ga kuma mamaki da tsoron Hajara da ya ƙara ɗarsuwa a ranta. "Sannu Sadiya, amma da sauƙi yanzu ko?" Faɗin Anti Hafsatu tana zana a gefenta. Zahra ta mike ta ɗauko ruwan roba dake ajiye a gefe guda kusa da firij ɗin Malam sai kofi. Nan ma Anti Hafsatu lallaɓa Sadiyar ta dinga yi har tana faɗamusu wai Maina zai shigo da daddare ya gaisa da iyaye. Ita dai ba ta ce uffan ba. "Tsaya kin ci abinci?" Anti Hafsatu ta faɗi tana dakatawa daga ɓallo maganin da take shiri. Girgiza kai ta yi. "Bari na ɗebo mata." Faɗin Zahra tana miƙewa ta fita. Can kuma ta dawo, sai a sannan Sadiya ta dube ta. "Ina Nudrat?" Ta furta a sanyaye. Ajiyar zuciya Zahra ta sauke. "Tun bayan da Ameer ya ce an fasa daurin aurenki ta ɗauki gyalenta da mayafi ta fice tana hawaye. Na tabbata gidansu ta nufa." Jinjina kai kawai Sadiya ta yi ba ta ce uffan ba. Ta sani dole Nudrat ta ji ciwon abin da yayan nata ya aikata. Hawaye ta ji sun cicciko sai ta share su da sauri. Ba ta son jefa zuƙatan da suka damu da al'amarinta cikin damuwa da rashin sukuni. *** A gidan su Nudrat kuwa, hankalinsu gaba ɗaya ya tashi bayan labarin abinda ya faru da ya iso musu. Nudrat ma a hargitse ta shigo gidan sakamakon wayar da ta yi da ƴar Yafendonta, Khalisat wacce ta ba ta labarin ai Hamma dagaske ya gudu ya auri Fareeda, kuma wai Mai Martaba sun iso gidan ana ta yi wa Maina busar sarewa da kirarin ya zama Ango wurin Sadiya. . Kuka wurjanjan haka Nudrat ta shiga yi, ba ta taɓa hasko ƙaddara za ta musu wannan juyin ba. Hamma ne ya yi musu wannan cin kashin? Sadiya da Maina an musu aure? Haka ta dinga tunane-tunane har ta ƙarasa gidan, wuri a cike daƙyar ta samu ta rufe fuskarta da mayafi ta wuce zuwa ciki kunnuwanta na dauko mata muryar Hasken Fadar Sarki yana ta zuba uban kirari ga Ibraheem Tafida Ango. Tana ƙarasawa ta ga wuri a hargitse ana yi wa Nene firfita, da gudu ta ƙarasa. Ashe suma ta yi da ta ji tsiyar da ɗanta ya shuka. Nudrat ta rungume Nene ta cigaba da rera kukanta. Tausayin Nenen ta ji, a karan kanta kunyar Sadiya da ma danginta take ji, da wane ido za ta ƙara kallonta? Ƙila ma Sadiyar ta yi zaton ta sani shiru kawai ta yi. Daƙyar dai ƙura ta lafa a gidan su Nudrat. Bayan tafiyar Sarki da tawagarsa da ma baƙin da aka gayyato na cikin garin da suka zo biki, Baffa ya keɓe da Nene ya taushe ta. Ya kuma ƙara da faɗin. "AbdulMajid kansa ya yiwa. Ki taushi zuciyarki kar ta kai ki ga yi masa mummunan baki. Zuru ma kaɗai ya ishe shi. Ya zaɓi duniya a kan mu iyayensa. Ya tozarta mu a bainar jama'a, toh ina mai tabbatar maki ko ba ki ce komai ba, zai ga ishara a rayuwarsa. Ki shirya idan an yi Isha'i ku je ku ƙara ba iyayen yarinyar nan haƙuri." Nene daƙyar ta haɗiyi miyau mai ɗaci tana gyaɗa kanta. *** IBRAHEEM TAFIDA (MAINA) Tun shigarsu falon ya yi zaune saman kujera gami da kwantar da kai ba tare da ko cire alƙyabbar da ke sanya a jikinsa ba. Na'urar sanyin da ke kaɗawa a falon bai tafiyar masa da gumin da ke tsastsafowa a goshi da ma cikin gargarsar dake kwance luf a hannunsa ba. Lamiɗo ya dubi Giɗaɗo kafin su maida duba ga Khamees wanda shi kansa ya yi shiru. Cikin su huɗun aka rasa wanda zai fara furta koda harafi ne. Can Khamees ya dube su, daga yanayin da ya musu inkiya ya sa su miƙewa su ba su wuri. Ya sani kaf ɗinsu babu mai iya tunkarar Maina da kowane irin zance bayan sa. "Maina." Ya furta bayan ya yi ƴar gyaran murya. Ya ɗago idanunsa da suka yi mugun kaɗawa ya sauke a kansa ba tare da ya ce kanzil ba. Sai dai kallo ɗaya Khamees ya fahimci ran maza ya ɓaci. Khamees ya ɗan kauda kai yana ƙara shiga taitayinsa kafin ya ce. "Komai ya faru, ka ɗauke shi matsayin ƙaddara." "Na ji." Khamees bai ƙara magana ba sanin hali, har ya fidda ran ma zai ji ta bakin Maina ɗin sai ya ji ya ce. "Hukuncin nan na Mai Martaba bai yi tsauri a kaina ba? Laifina bai yi girman da za'a hukunta da aure ba. Aure irin wannan ma na huce haushin Abdul. Why me? Yes na yi laifi wurin amsa kira a fili har ya yi sanadin da Abdul ya yi zafafan kalamai ga ɗiyarsu, toh a ba ni hukuncin da zuciyata za ta iya ɗauka. But Khamees aka aura min ita? Sa..Sadiya right? Yarinyar da ban taɓa gani ba, ba ma ni ne a ranta ba. Ni ma kuma ka sani auren ma ba ya cikin abubuwan da na saka a gaba yanzu." Ya na kai wa nan ya furzar da huci mai zafi kafin ya ƙara kwantar da kai jikin kujera ya lumshe idanu yana jin raɗaɗi a ƙirjinsa. "Ko mene ne, yanzu bakin alƙalami ya riga da ya bushe. Dama kuma Allah ya tsara matarka ce ba ta AbdulMajid ba. Ka yi hakuri, don Allah kar ka jawo abin da Mai Martaba ransa zai ɓaci fiye da wanda ka jefa shi ciki a wajen ɗaurin auren. Ko meke a ranka, ka bi umarni anjiman mu je can gidan nasu a gaisa da iyayenta. A bi umarni zuwa safen a wuce. Na sa a mana booking na jirgin safe goben." Maina bai ce uffan ba. Sanin ma ba zai ce ɗin ba ya sa Khamees miƙewa ya fice wajen su Lamiɗo. Shi kuwa har a sannan jin lamarin yake kamar a mafarki wai an ɗaura masa aure da budurwar AbdulMajid. Da ace ba ya wurin abin ya faru zai kira hakan da wasan yara, sai dai gani ya kori ji ai. Shi dai Maina jinin sarauta gaba da baya? Ya auri yarinyar da bai san ta ko a hoto ba? Don ba ya mantawa sadda suke tare da Hamma a Gombe, da ya gaisa da ita ta waya Hamman ya nemi gwada mishi hoto ya nuna don me? Ashe ma auren da shi za'a yi. Guntun tsaki ya ja kafin ya miƙe ya shige ɗaki don wanke jikinsa sai dai kuma ji ya ke daidai da ruwan ma ba ya buƙatar haɗawa da kansa. Sai ya ji inama ya bi shawarar Fulani da ta ce ya ɗauki Baharu (amintaccen bawansa) sun taho tare idan ya so a kama masa ɗaki a hotel din da suke. A dole haka ya rage kayansa ya faɗa banɗakin bayan gabatar da addu'ar da ta ce kafin shiga. ***   A ɓangaren Hajara kuwa, daƙyar ta iya tuƙa kanta cike da wani mahaukacin gudu ta ƙarasa gidan Bokanta. Sadda ma ta sulale babu wanda ya kula sai munafukan ƙawayenta da suka dinga doko mata kira. Da kuka kashirɓan ta shiga falon nasa ba ta ko jira yaronsa mai cewa ta jira ya sallami matar da ke ciki ba. Ganinta a wannan yanayin ya tashi hankalinsa, nan ya ba matar haƙuri ya ce ta jira a waje. Miƙewa tsaye ya yi yana ƙoƙarin riƙo ta gami da faɗin. "Hajjaju tawa lafiya?" "Ba lafya ba! Maci amana kawai! Don me da ka hango fasa ɗaurin auren Sadiya da AbdulMajid ba ka hango aurenta da ɗan Sarkin Gombe ba?! Ashe kai macuci ne! Dama cutata ka yi ka yaudare ni! Yanzu ga shi can an ɗaura aurenta da wanda ya ci uban mutumin da ka yi aiki a kansa! Na shiga uku ni Hajara!" Ta zube ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita, kusan tun zuwanta duniya idan ka ɗauke mutuwar Mahaifiyarta, ba za ta tuna sadda hawayenta ya zuba irin na yanzun ba.  Boka ya sauke ajiyar zuciya ya nemi wuri ya zauna, shi dama wane aikin ya yi? Duk hangensa ma bai hango komai na sha'anin rayuwar yarinyar ba.  Inama aikinsa ke da ƙarfin yin tasiri a kan wannan Sadiyar mai babban tsari a jiki? Ya rasa ma me zai ce ga Hajara sai kuma wata dabarar ta faɗo masa. "Ki kwantar da hankalinki don Allah, to so kike na faɗi abin da zai tayar da hankalinki? Eh dama na san hakan za ta faru, amma kuma da yake na san auren babu inda zai je shiyasa na ce maki ba ita ba au..." "Dallah can rufe min baki! Aikin banza da wofi! Ka riƙe ƙaryarka! Ta bar tasiri a wurina! Cuta dai ka riga ka yi min shi! Kuma tsakanina da kai Allah ya isa!" Tana kai wa nan ta miƙe za ta tafi, ya yi wani irin yunƙura da sauri ya zagayo gabanta ya riƙo hannayen. Zuwa lokacin zai ce ma son Hajara yake ji a ƙoƙon ransa. Ya rantse ta yi masa ɗari bisa ɗari a shimfiɗa don haka ko giyar wake ya sha ba zai yarda ta suɓuce masa ba tare da ya gama cin moriyar ganga ba. Ta yi kokarin fisge hannunta tana kuka da kunduma ashar sai ya saki hannun ta fice amma ko gezau sai ban haƙuri da rarrashi. Ƙarshe ma ya yi nufin kai mata sumba anan ne ta ci nasarar fisge hannun ta sharara masa mari a kunci. A gigice ba tare da ya taɓa tsammani ba ya dafe kuncin yana kallonta da tsananin mamaki. Idanu a waje ta ke binsa da kallon banza kafin ta ja dogon tsaki ta fice har tana bangaje kafaɗarsa. Ya shafi kuncin da ta mara ya jinjina kai gami da yin ƙwafa. Can kuwa ya yi wata dariya. "Kin yi babban kuskure Hajara! Mari? Toh kuwa zan nunamaki ƙarfin tsafina!" Ya furta a fili yana mai cin dogon alwashi a kanta. *** Sadiya na kwance jikin Innarta wacce ta ture ta ya fi a ƙirga amma a ƙarshe Dada ta hau ta da faɗa wai ta ƙyale ta na bankwana ta ke mata tunda nesa za su yi. Ita kuwa ganin abin kunya ne matsayinta na bafulatana babban ɗiya ta maƙalƙale mata har haka ya sa duk ta kasa sukuni. Su Hafsatu da Safiyya sai shige da fice suke yi wajen ganin an haɗa mata kayanta ba tare sun taɓa ko tsinke a lefenta ba. Dama kuma su a al'adar gidan babu wani abu da ake taɓawa a lefen yarinya har sai ta shiga ɗakin mijinta ta yi amfani da abin ta. Doka ce ta mahaifinsu. Ƙirjinta kawai ke bugu, hawayenta suka zubo daidai sadda ta ji kiran sallar magriba a kunnenta. 'Zai zo bayan sallar isha'i, za ku gaisa.' Ta tuna maganar da Malam ya faɗi ga Innarta. Maina zai zo gidansu? Wace tarbar zai mata? Ita kanta me za ta ce ga mijin da ba su san komai da ya shafi junansu ba? Ta ji hawayenta sun zubo sa'ilin da Inna ke ture ta don ta fita yin alwala. Ta janye jikinta ta jingina da bango. Har sai da Inna ta dawo, ganin dai kowa na fita zuwa yin alwala ita ma ta mike zuwa ɗakinsu, wata ƴar uwarsu na fitowa daga banɗakin ta shiga ta ɗauro. Koda ta fito sallarta ta yi a nutse, tuni ta goge kwalliyar da ta yi mata caɓa-caɓa a fuska ta kuma sauya sutura zuwa doguwar rigar atamfa da ya sha stones. Ana idar da sallar Isha'i sai ga Anti Hafsatu ta shigo inda take zaune tare da su Zahra suna hirar abin da ya ƙi wucewa a zuƙatan kowa ma. Ta kula dai har wasu a ƙawayenta da suka ƙi barin gidan burin kowa ya yi ido huɗu da wannan Ango. "Sadiya taso muje." Gabanta ya faɗi. "Ke ba wani abu ba ne dallah. Gidan su Zahra zamu shiga. Zahra ke ma taho." Jin haka sai ta miƙe gwuiwa a sake, ita ma Zahra ta mara musu baya riƙe da wayarta da na Sadiyar da tun da ta kashe ba ta kunna ba. Dakin Maman Zahra suka shiga, ganin wani arnen leshi fari ƙal wanda a farko shi aka yi za ta saka idan za'a miƙa ta ɗakin Hamma, yanzun kuwa wai an kawo ta ne don ta shirya saboda zuwan da Maina zai yi su gaisa. Hawayen ma kasa zuba suka yi sai zafi da raɗaɗi da idanunta ke yi duk sun ɗan kumbura sun ƙanƙance, fuskarnan ta yi jazur. Haka ta bi umarninsu ta yi wanka kamar wacce za'a kai ta gidan aure a lokacin, ta shirya bayan an turare mata kayan da turaruka kala-kala masu kyau da aka siya a wurin mai gyaran jiki. Hoda kawai Zahra ta shafa mata sai kwalli. A hakan ma sai ta yi kyau saboda ɗinkin riga da siket ne da aka yi shi ya zauna sosai. Mayafi ta yafe kanta da shi bayan Zahra ta yi mata ɗauri. Maman Zahra dake gefe riƙe da Imam ɗa ga Zahrar sai nasiha ta ke mata da nuna mata dama can Ibraheem ne mijinta ba AbdulMajid ba. Ta yi hakuri ta kuma yi biyayya. Dauriya kawai ta ke na dole don ta sani ko ta yi niyyar kukan ma ba iyawa za ta yi ba, ji take kamar ma hawayen nata sun ƙare. Ana kammalawa suka koma cikin gidan. Kamar jira ake su shiga, motar su Maina ta tsaya da ƙofar gidan. Dama Malam ya ce yaransa maza su tsaya don a tarbe su. Ciki har da babban ɗan Abba a maza, wanda shi ma sunansa Hashim ake kiransa Baba Karami. Giɗaɗo ne ya fara fitowa ya buɗe wa Maina ƙofar ɓangarensa, sai dai har su Khamees suka fito ba shi da niyyar saukowa. Sanyin Ac na motar har yana bugun na kusa da wurin. Sai da ya gama ƙarewa gidan kallo kafin ya sa ƙafarsa ɗaya a wacce ke rufe cikin takalmi mai rabi sahu ciki (half cover shoe) sannan ya fiddo dayar. "Nan ma mulkin zai gwada kenan." Yaya Mustafa ya faɗi kamar mai raɗa a kunnen Zakari dake kusa da shi, hakan ya sa Zakari ɗan murmusawa kaɗan duk da har a sannan bai huce daga abin da ya so afkuwa ba a ɗazun wajen ɗaurin aure. Wato laifin AbdulMajid. Suka dube shi sadda Hashim yayansu ke musu sannu da zuwa. Maina ya ɗan russuna kai bai ce komai ba sai ɗan murmushi kaɗan wanda ga na kusa da shi sun fi kowa sanin na yaƙe ne. Haka suka yi mishi jagora har falon Malam wanda ya sha gyara don dama matar gidan gwanar tsafta ce wato Inna. Ƙamshin turaren wuta ma sai tashi ya ke, amma fa duka wannan bai hana ƙamshin turarukan Maina karaɗe falon ba, koda dai ga su Baba Habu ba za su iya tantance waye mai ainahin ƙamshin ba a tawagar ta Maina, sai dai jikinsu ya ba su cewa babban goro fa sai magogin ƙarfe. A karo na uku, Maina ya ƙara sanya Malam mahaifi ga Sadiya a idanu. A ladabce ya gaishe shi, Malam ya amsa shi ma yana kokarin girmama shi ta hanyar ɗan yin ƙasa da idanu. Bayan gaisuwar ce kuma kowa ya fice ciki har da abokan Maina aka bar shi tare da surukinsa wanda ya zo mishi bagatatan. Shi fa ba mai raina arziƙin mutane ba ne don ba haka a ka tarbiyyantar da shi ba, sai dai bai hango wa Hamma zaɓen mace a gida irin wannan ba wanda ya sani a arziki irin na Baffan, ko kyauta aka tashi zai bayar da fin wannan. "Ɗana Ibraheem." Jin haka Maina ya ɗan dube shi kaɗan cikin wadataccen hasken da ya haskaka falon wanda ya sha sabon farin fenti, kafin ya sadda idanunsa yana nanata sunan a zuci. Bai jin ko mahaifinsa ya taɓa jingina sunansa da kalmar Ɗana. Malam ya cigaba da zancensa. "Zan fara da ba ka haƙuri, ka yi haƙuri idan har an maka ba daidai ba a auren nan. Mu kanmu mun sani wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. A kuɗi, ilimi, kyakkyawar nasaba, da komai ma na rayuwa na sani kai ɗin ba sa'an auren Sadiya ba ne. Amma kuma kaf ɗin mu babu wanda ke da ƙarfin ikon da Allahnku ke da shi a kanku da mu ma. Kamar yadda ba ka yi zaton aure a lokacin ba, haka mu ma ba mu taɓa hasko faruwar abin da ya faru a yau ba. Ina roƙon Allah da ya ba ku ikon riƙe junanku bisa amana, ya kuma ba ka ikon sauke dukkan haƙƙoƙin da suka rataya a wuyanka." Malam haka ya yi ta kwararo nasiha da ban baki da rarrashi kafin ya ƙara rufewa da addu'a. Maina da ya yi shiru kawai yana sauraronsa, ko a fuska ba za ka ce ga kalar tunanin da ya ke ba. Jin shirun na Malam ya sa shi motsa leɓɓansa ya soma magana. "Nagode Baba, zan kuma yi amfani da nasiharku." Malam ya ji daɗi ainun, ya ƙara godiya a fili kafin ya leƙa ya yi wa su Giɗaɗo magana kan su shigo. Ba jimawa kuwa su Anti Hafsatu da sauran ƴan uwa aka shigo falon har da waɗanda ma ba a kira ba. Sai dai duk wacce ta ga Maina sai ta raina kanta musamman cikin ƙawayen da suka tsaya ganin ƙwaf. Kusan ma su Lamiɗo ne bakinsa, shi fuskar ba murmushi kuma ba za ka ce yana cikin fushi ba. Hatta da wacce ta shigo da zummar guɗa fasawa ta yi saboda yanayin kwarjinsa sai ta ga kamar idan ta yi to fa laifi ne gagarumi. Kusan samarin dai akwai cika idanu. Bayan fitarsu kuma bisa jagorancin Baba Haba suka shiga har tsakar gidan zuwa falon Inna aka gaishe ta tana sunne kai. Maina ya ji duk ya gama gajiya, babu abin da ya ke buƙata kamar ya gan shi kwance saman gado yana hutawa. Karo na uku kuma da ya yi zaton gaisuwar ta isa tafiya za su yi bayan shigarsu falon Malam, aka dakatar da shi wai Amarya za ta shigo su gaisa. Jin haka ya ɗan matse tafin hannunsa na dama gami da ɗan cije pink lips ɗinsa kaɗan, bai ce uffan ba. Wata yar uwar su Sadiya ce a gaba riƙe da hannunta ta shigo da sallama sai ko Sadiyar da fuskarta ke buɗe, ta yane mayafi ta yi lulluɓi irin na matar aure. Ƙirjinta duka kawai yake yi, ta firgita da irin ƙamshin da ke tashi tun daga tsakar gidansu har shigowa falon Abban. Giɗaɗo, Lamiɗo da Khamees da ke kallon Sadiya, suka kalli junansu kowanne fuska ɗauke da maɗaukakin murmushi. Khamees har da wani irin hamdala a zuciya kai ka ce shi aka aurawa ita. A hankali ta zauna nesa kaɗan da inda suke zaune. Ta zame jikinta ta ɗan durƙusa ta ce. "Barkanku da dare." Daga yanayin rawar muryar za ka fahimci kamar kuka ta ke yi ko kuma ta ke shirin yi. "Barka dai Ranki ya daɗe." Kusan lokaci guda suka amsa. Maina bai kalli inda take ba, ba shi kuma da niyya. Muryar dai ya so ya ɗauka tunda yana sane da cewar sun taɓa gaisawa. Sai dai wannan karon cike take da rauni sosai, ƙila ma kuka ta sha don an aura mata shi. A ransa ya ja tsaki, to wa ya kama ta ya yi kukan tsakaninsu? "Bari mu ɗan ba ku wuri." Faɗin Giɗaɗo a tausashe yana kallon Maina. Bai ce musu uffan ba, shirunsa na nufin eh koda kuwa ba haka ran nashi ya so ba. Tunanin ma da ya faɗa, a bar su tare ya ce mata me? Bayan zuciyarta ba shi take so ba yaudararta aka yi. Falon ya yi tsit daga shi sai Sadiya da ita ma ta kasa kallon Mainan, tsoron ma haɗa idanu ta ke da shi har ga Allah. Shirun ya yi mata yawa don haushinsa ma ta ji ta soma ji, ita tun farko dama bai mata ba, ballantana yanzun da laifin Hamma ya shafe shi. "Goben da misalin ƙarfe bakwai ne." Ta tsinci muryarsa na fita tamkar an busa sarewa, ta gyaɗa kai a hankali lokacin da hawayenta suka ɗiga saman ƙunshin bayan hannun. "Toh." Ta faɗi da rawar murya fiye da farko. 'Kuka take.' Ya furta a zuciyarsa. A hankali ya ɗaga kai ya dubi awarwaron da ya cika kunnuwansa da ƙara wanda tun zamanta take wasa da su. 'Fara ce.' Ya ƙara furtawa a ƙasan ransa. 'Ƙila kuma farin mai ne.' Ya nanata duka shi kaɗai. Sai kuma ya ji haushin kansa. Duka me ya kawo wannan. Sai ta ga ya miƙe tsaye. Ta share fuskarta har a sannan ba ta kalle shi sai ko ƙafafunsa da ta bi da kallo waɗanda suke tamkar ba sa taka ƙasa. "Asuba ta gari." Ya furta karo na biyu yayin da shiru ya ratsa. Ta rasa dalilin rashin tafiyar ta sa don haka ta miƙe. "Allah ya tashe mu lafiya." Ba ta jira amsarsa ba ta juya, ya juyo kai ya bi bayanta da kallo kaɗan sai kuma ya kauda nasa kan ya nufi hanyar ficewa a falon. Daren ranar Sadiya raba shi ta yi da yayyunta da Inna ana ta mata nasiha. Tare da Anti Hafsatu da wata Gwaggo Jummai wacce take matsayin Yaya a wurin Malam. Su Adda Ruƙayya da Safiyya kuwa za su biyo su ta mota ne da sauran kayayyakin Sadiya. Tunani babu irin wanda Sadiya ba ta yi a kan Maina ba. Magana sau biyu kacal ya yi mata, wannan ya sa ta ƙara fahimtar bai karɓe ta ba shi ma kamar yanda yake a wurinta. Madadin hakan ya ƙuntata mata, sai ta ji sanyi kaɗan tunda itama ba ta sonsa. Kuma yanda ba ta tunanin ya kalle ta, ta ji dadi da ba ta ko kalli fuskarsa ba. Har abada ma ta saka a rai ba za ta so shi ba tunda shi ma ba ya sonta. Za dai ta yi masa biyayyar da ake ta nanatawa, duk zaman da ya zaɓar musu ita a wurinta daidai ne. Babbar matsalarta, karatunta. Sun ce ta kwantar da hankali tunda an san tana karatun ƙila a samar mata mafita. Ta bi yayyun da toh kawai. *** Washegari... GOMBE Cike da tsantsar mamaki Fulani Kausar ta ke duban Mai Martaba wanda ya gama magana. Sai kuma ta kauda kai gar wasu kwalla na tsantsar baƙin ciki da takaici na tarar mata. Ta ƙara maimaita abin da ya ce a ƙwanyarta. "Mun karɓawa Maina auren da suka so tozarta mu a bainar jama'a, sai a taya shi da addu'a, kuma a ce kiyaye wulaƙanta ɗiyar mutane don gujewa faɗawa fushinmu." Ta gyara leɓɓanta ya fi a ƙirga tana son magana amma zallar takaici bai sa ta iya firzarwa ba. Ƙarshe ta yi mishi sallama ta fito da saurinta, bayi na mara mata baya. Ba ta nufi ko'ina ba sai ɓangaren Mai Babban Ɗaki. Ta iske ta kishingiɗe tana magana da wata amintacciyar baiwarta Hindu. Ta sani duk abin da zai sa Fulani Kausar takowa zuwa sashenta to ba ƙarami ba ne, kusan ma za ta iya cewa ba alkhairi ba. Hindu ta kwashi gaisuwa kafin uwar ɗakinta ta ba ta umarnin fita. Fulani kamar jira ta ke a zafafe ta ke duban ta. "Kin san da batun auren Maina?" Wani murmushi Hajiya Saratu wacce suke kira da Mai Babban Daki ta yi. "Bismillah ga wuri ki zauna." Wani banzan kallo Fulani ta watsa mata. "Ke kanki ba ki ishe ni kallo ba balle shirginki. Yanzun ma saboda ya shafi ɗana ne. Ashe shiyasa ki ka ba da umarnin a fara shirin tarba? Burinki ya cika an ci zarafina an aura wa Maina ƙasƙantacciya wacce ba jinin sarauta ba?" Murmushin da har yanzu bai gushe ba a fuskar Haj Saratu, da shi ta dube ta a kokarinta na son hadiye radadin da maganganun Fulani suka haifar mata. "Na sani Fulani, ban kuma saba tsallake umarnin Mai Martaba ba ke kin sani. Dukkan abin da ya ce, shi za'a yi. Auren da aka riga a ka ɗaura, ai ko a ɗaya daga cikin bayi ne, sai ki rungumi ƙaddara." "Shikenan, mu zuba ni da ku! Daidai nake da ke da shegiyar da aka aurawa ɗana!" Tana kai wa nan ta juya a zafafe ta fice, Haj Saratu ta girgiza kai tana fadin Allah ya kyauta don a cewarta, ba ta ga ranar da Fulani za ta yi hankali ba. *** KANO "Wannan mutumin ya tashi daga wani da baki sani ba, ya tashi daga sunan aboki ga wanda ki ka sani a farko, ya amsa sunan mijinki a yanzu. Girman haƙƙoƙinsa a kanki, sai dai a ƙara jaddada maki. Idan ki ka yi mishi biyayya ki ka saka tsoron Allah a lamuranki, toh ba ki da kaico. Duk runtsi ki zama mai bin umarninsa, aljannarki ki ke nema. Kuma ki saka a ranki bautar Allah ya kai ki. Ba ruwanki da ɗaukar magana, ki kaunaci yan uwansa. Ki zama mai sirri, ban amince ki zama mai tona dukkan abinda zai faru tsakaninki da shi ga kowa ba. Aure yana buƙatar sirri. Sannan abu na ƙarshe da zan faɗamaki, ki riƙe addu'a. Babu maganin da ba za ta yi maki ba. Mu da muke zaune a gidanmu, ita ce ta zaunar da mu. Ƙarfin addu'a, Allah ya albarkaci aurenku ke da yar uwarki. Ya shige maku gaba. Ameen." A hankali ta sa hannu ta goge fuskarta tana duban titi. Tafe suke a hanya na zuwa Airport a motar gidan Abba. Ita da Anti Hafsatu sai ko Husna da Zahra'u da Adda Ruƙayya da suka biyo su rakiya. Tunanin maganganun da Inna ta yi mata da asuba take yi, ga Malam shi ma ya yi mata doguwar nasiha sosai. Ya kuma ce koda karatunta iyakar abin da ta samu yi kenan, toh ta godewa Allah kada ta yi baƙin ciki ballantana yana addu'a da kyautata zaton cewa za su bari ta yi koda kuwa a Gomben ne, koda hakan na nufin dawowa daga farko ne a jami'arsu ta can. Ita ma tana fatan Allah ya sa hakan ne, idan har za'a bari ta yi za ta ji sauƙin wani abin. A ɓangare ɗaya kuwa ta rasa me ya sa Nudrat ba ta yi mata ko waya ba, ga Nene ma wacce ba ta zo ba kuma ba ta yi waya ba. Duk da Dada ta ce a yi musu uzuri ƙila kunyar abin da ɗansu ya aikata ne, amma sai ta ga kamar ya dace ace sun zo ko sun mata magana. *** Ga Maina haka Baffa ya dinga ba shi haƙurin da kuma yi mishi kyakkyawan addu'ar zaman lafiya da Sadiya sadda suka je yin sallama da su. "Yarinya ce mai nutsuwa da kirki, in sha Allahu ba za ku samu matsala ba. Yadda ka nuna kai ɗin ɗa nagari ne, ba ka kuma bijirewa umarnin mahaifinka ba, in sha Allahu rayuwarka za ta yi kyau. Ba kuma za ka taɓa dana sanin auren nan ba. Ba iyayen Sadiya kaɗai ka rufawa asiri ba, hatta da ni wanda ɗan uwanka ya nemi ya jawo min zagi da zubewar mutunci ka cece ni. Nagode Ibraheem, Allah ya karawa rayuwa albarka." Abin da Baffan ya ce kenan, haka ma Nene wacce har hawaye ta zubar sadda ta ke mishi addu'a, ita ma sosai ta yabi zaɓin da Allah ya masa na auren Sadiya. Shi dai ya ji su kuma ya amsa da amin amma kuma sanin taƙamaiman wace ce Sadiya, wannan sai zama ya yi zama. Ya dai gane ba ƙaramin kauna suke yi ga Sadiya ba. Hatta da yarinyar (Nudrat) da zai ce magana ba ta haɗa su da shi bai mance sadda ya zo giftawa zai fice daga falon Nene ba ta dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa a hankali. Ya tsaya cak ya na dubanta bai ce uffan ba ganin har da hawaye kwance saman fuskarta, ta yi ƙasa da nata idanun, da wani irin raunin murya ta ce. "Ina roƙawa yar uwata Sadiya alfarma, don Allah ka kula da ita. Ba ta da matsala, in sha Allahu nasan za ta shiga ranka ɗari bisa ɗari. Koda ba ka so ta ba, ka yi mata gurbi ko ba yawa a wani sashi na zuciyarka. Nagode. Allah ya tsare hanya." Daga haka ta bar shi tsaye kafin bayan tafiyarta shi ma ya wuce. "Ai ina jin ga motarsu." Ya tsinci muryar Lamiɗo na faɗi, Khamees ya amsa da fadin. "Yes su ne, ga kiran Baba Habu." Daga haka ya fito a motar yana amsa wayar gami da ɗaga wa Baba Habu hannu. Maina na fitowa ya yi gaba zuwa ciki, akwatunansu dama Giɗaɗo da ma'aikacin wurin sun yi gaba da su. *** Su Sadiya na fitowa aka gaisa da Khamees. Ta kula kamar a hanzarce suke yanayin yanda Khamees din ke tambayar kayayyakinsu. Nan aka sanya akwatunan kayanta da na Anti Hafsatu guda daya a keke aka yi ciki da su. Suka yi sallama cike da kewar juna da su Zahra da Husna da Adda kafin su bi bayan Khamees da Baba Habu wanda shi ma iyakarsa Airport din zuwa ciki. Kirjinta na yi ta bugu don ta sani yau dai dole za ta ga Angon nata. Koda aka kammala komai suka yi sallama da Baba Habu ya tafi ya bar su, bayan Khamees suka bi har zuwa ɗan falon da matafiya ke zama don jiran jirginsu. Takunta cike da nutsuwa, sanye take da doguwar rigar abaya baƙa mai adon duwatsu, ta yane kanta da mayafin abayar sai ko ƴar jakarta, takalminta mai ɗan tudu wanda ya ƙarawa tafiyarta salo na daban. Fuskarta duk da hoda kadai da man leɓe ta shafa sai kwalli, ta fito fes da ita. Lamiɗo da suke zaune ya ɗan taɓo Giɗaɗo dake latsa wayarsa. Giɗaɗo dake gefen Maina ya kalle shi cike da alamar tambaya. Lamiɗo da hankalinsa ke kan Sadiya a hankali cikin raɗa ya ce. "His princess." Hakan ya sa Giɗaɗo shi ma ya dube ta. Kauda kai ya yi yana jan istigfari, har ga Allah wanda zai kalli Sadiya bai yaba tsarin halittarta ba to fa kalle shi kawai. "Masha Allah. Dama ai babban goro sai magogin ƙarfe." Wannan furucin na Lamiɗo karaf a kunnen Maina da ya gama amsa wayar abokin aikinsa da ke can babban kamfaninsu na motoci dake London. A hankali ya ɗaga lumsassun idanunsa ya kai duba gare ta. A kallo ɗaya ya gane kyakkyawa ce, farinta mai kyau ne, sai a ɗauka ta haɗa dangi da ƴan Somalia a yanayin halittar fuska. Takunta ma irin wanda ke fisgar hankalin maza ne. Ya kauda kansa ya maida hankali ga wayarsa. Ƙila da gayya ta ke takun ma, to wa za ta burge a bainar jama'a haka? Ya yi wa kansa tambayar da babu amsa. Dagaske dai ya rasa me zai kushe a abin da ya kalla, jikinsa kuma ya ba shi ita ce Sadiya Sa'ad Shagari. "Barkanku da asuba. An tashi lafiya?" Muryar Anti Hafsatu kenan, nan su Lamiɗo suka gaishe ta. Maina ma ya ɗan dube ta kafin a tausashe ya ce. "Barka da asuba." Anti Hafsatu dake murmushi tana dubansa ta amsa, ita sai yanzu ta ƙara hango tsananin dacewar da ma'auratan suka yi. Ita kyau shi kyau, tana fata yadda halayen Sadiya suke da kyau, ya kasance shi ma haka. Tabbas da Sadiya ta gama dacewa duniya sai kuma lahira idan ta yi rayuwar aure mai kyau. Sai ta shiga addu'a a ranta akan Allah ya haɗa kawunansu. Sadiya ta zaune gefen Antin bayan ta gaishe su kanta har a sannan a ƙasa, su Lamiɗo suka amsa, Maina babu wanda ya kula da ya amsa din ko a'a don ba jimawa da zaman aka kira su zasu wuce. Gaba ɗaya suka miƙe suka ɗunguma ciki, ita dai ta riƙe hannun Antinta gam! Ita kuwa Anti Hafsatu kasancewar ba yau ne farkon hawanta ba tun da sun taɓa sauke farali tare da Maigidanta, a nutse take tsaf. Allah ya karɓi addu'arta mazauninta guda da na Antinta. Hakan ya ɗan kwantar da hankalinta. Ƙasa da awa ɗaya suka sauka a tashar jirgin sama na garin Gombe. Sai da suka fito daga jirgi ta gan shi, ta ga fuskarsa. Ta ga kuma yanayin shigar da ke jikinsa irin na gidajen sarakai. Riga da wando ne ruwan makuba sun sha surfani. Sumarsa kwance luf, kyakkyawa na bugawa a jarida. Ga tsayi ga kuma faɗaɗɗan ƙirji, giant da shi masha Allah. Sai ta ji gabanta ya faɗi, za ta rantse shi ne Maina. Ta raina kanta, ta ga kamar ba ajinta ba ne ta ko'ina. Sai ma da ta ga yanda ma'aikatan wurin ke ta gaishe shi a ladabce. Suna fita farfajiya wurin parking na motoci, ta ga uban dogarai sun nufo shi ana zubewa da kwasar gaisuwa. Kallon da ta yi mishi wannan karon sai ta ga ya yi mata mugun kwarjini ita kanta, ta kauda kai tana damƙe hannun Anti Hafsatu wacce ba za ta kirga adadin damƙar da Sadiya ta kai mata ba. Nan da nan ta ga wasu manyan motoci baƙaƙe wuluk masu kuma baƙaƙen gilasai sun ci burki a gabansu. Na tsakiyar aka buɗewa Maina ya shiga, su ma a ka buɗe musu na baya suka faɗa, daga yanayin kirarin ma ta san labarin aurensu ya isa ga masarautar. "Anti tsoro nake ji, ƙirjina sai bugu yake." Ta faɗi a hankali kamar mai raɗa, Anti Hafsatu ta ce. "Addu'a, ki yi addu'a Sadiya." Nan kuwa ta shiga karantowa a zuciyarta har suka shiga ginin Masarautar. Tsayuwar motocin, ta ga bayi maza da mata an wani jeru an cika har da ma mutanen gidan maza da mata da jikoki domin tarbarsu. Koda dai mafi yawansu so suke su ga wace ce Amaryar Maina. Ciki kuwa har da cousin sisters waɗanda ke mutuwar so da ƙaunarsa kai ka ce dama a gidan wasunsu suka kwana. Ba Sadiya ba, hatta da Anti Hafsatu sai da jikinta ya yi sanyi musamman da Maina ya fita bayin suka shiga zubewa suna kwasar gaisuwa. Bai kuma jira ba ya yi gaba ba tare da kula masu bushe-bushe da zuba kirari ba. A gefe ga mata na faman guɗa. Haka ta kama hannun Sadiya suka fito bayan dogari ya buɗe musu murfin motar. Nan fa aka zubo musu idanu kamar a cinye su. Duk dai kushen masu kushe sun kasa hangen ta inda za su raina Sadiya, asalima Abayar dake jikinta mai tsadar gaske ce tsarabar Abba da ya je Saudiya ya kawo mata duk don a sanyaya ranta bayan auren Huzaif da Husna. Ita ma haka bayin nan suka hau gaisuwa da ladabi, suka bi bayan Hindu da ke musu jagora. "Wai! An ji mai." Karaf maganar ya shiga kunnen Sadiya da ta zo gifta wata, ba ta ɗaga idanu ta kalle su ba amma ta ji wata na ba da amsa da "Ƙaryarki Najma, wannan ya fi karfin mai." Har sai da ta ji tana tuntuɓe ga uban kirarin da ake zuba mata ita mamaki ma take yadda har sunanta da na mahaifi da kakanta ya iso gare su, wato Sadiya Sa'ad Shagari. Murmushi ne kwance saman fuskar Haj Saratu tun shigowar Hindu tare da su Sadiya sai ko mutanen gida da suka mara musu baya. Ba don bauɗaɗɗen halayya da kafiya irin na Fulani Kausar ba, acewarta ita ba ta ga abin tada hankali a auren mace kamar wannan ba da Maina. Yarinya son kowa. Sadiya da Anti Hafsatu suka russuna a ladabce kamar yanda suka ga Hindu ta yi suka gaishe ta. "Barka da zuwa masarautar Gombe, Gimbiya Sadiya. Muna maki maraba, Allah ya sanya albarka a zamantakewarku." "Ameen Mai Babban Ɗaki. Bangon sukari kowa ya jingina da ke sai ya lasa, Uwa ga Babban Yarima. Baya goya marayu, giwar Mai Martaba!" Wannan kirarin na fitowa daga wata baiwa dattijuwa da ke tsaye, sai kuma ta rangaɗa guɗa. Wasu a wurin na taɓe baki wasu na harararta a faƙaice yayin da wasu ke murmushi cikin jin daɗin wannan kirari don masu jin dadin ma sun fi akasinsa yawa. Domin duk wanda ke tare da Haj Saratu, ya sani ba ta da baƙin ciki, ga kyauta. Hakanan ta dauki duka yaran Mai Martaba tamkar nata sai ko waɗanda suka kasa biyayya gareta, waɗanda iyayensu ke hure musu kunne. Ta kuma ja girmanta yadda ta kamata dalili kenan da ba kowa ke iya kawo mata wargi ba sai ko su Fulani Kausar wacce ke tunƙahon ita ma jinin sarautar ce gaba da baya kamarta, ba ta isa ta juya ta ba. Don ma shakkar Mai Martaba ya sa wani abin takan bar wa cikinta. "A kai su masauki su huta su ci abinci." Iznin da ta ba Hindu kenan, nan bisa cika umarni ta miƙe, su ma suka bi bayanta. A nan dai sashen Haj Saratun ne aka kai su wani ƙaton ɗaki mai ciki da falo. An gyara shi tas, ba ka jin komai sai ƙamshin turarukan wuta. Sun iske hatta da kayayyakinsu an kawo. Nan Hindu ta musu sallama ta ba su wuri su ɗan huta. Bayan fitarta Sadiya ta zube saman kujera tana sauke ajiyar zuciya, sai a yanzu ta shaƙi iskar ƴanci. Anti Hafsatu da jikinta ya gama la'asar da mutanen gidan duk da haka yadda Sadiyar ta yi wani zuru-zuru ya sanya ta darawa. "Sadiya, mene haka? Faɗuwar gaba fa ba naki ba ne. Aiki ne ja ki ke da shi nan gaba. Ki daure ki yakice wannan tsoron da ke saman fuskarki, sai kin zama jarumar gaske ina faɗamaki." Sadiya ta gyaɗa kai. Ƙuryar ɗakin ma wani tafkeke ne ba kamar nata da ta saba rayuwa a ciki ba, can ƙarshe ka ke ganin gadon. Wanka ta faɗa bisa umarnin Anti Hafsatu don gaskiya da ace na ita ce to kwanciya za ta yi ta huta ko za ta nutsu gaɓɓanta su bar rawar da suke yi. Tana fitowa ta tarar har Antinta ta fiddo mata wata sabuwar atamfarta glitters irin manyan ƴan dubu talatin da ɗoriya wanda Malam a aljihunsa ya dauka ya  bayar aka siya mata don fitar biki sai dai kuskuren da tela ya yi yasa ba ta sanya ba sai yanzun. "Su Safiyya sun taho fa. Husna wai Hajara ta ce ta bari su taho gobe ta jirgi." Ambaton Hajara da Antin ta yi sai da Sadiya ta ji ƙirjinta ya ɗan faɗi, ta tuna maganar da Zahra ta faɗamata da sunan ƙawayen Hajara ke faɗi. A fili kuma ta yi musu fatan isowa lafiya daga nan ta hau shiri. Ita ma Anti Hafsatu wankan ta faɗa ta yi. Cakarewa ta yi cikin nata Voyel din mai tsada don kaf kayanta ba ta ɗauko wanda ta ke da tabbaci za'a raina ajinsu ba. Hakan yasa da kanta ta yi wa Sadiya zaɓin kayayyakin da ya kamata ta ɗauko. "Kin ga abin da na kula wannan ita ce Uwargidan Mai Martaba daga yanayin kirarin da ake mata da ma sunan da ake kiranta da shi, Mai Babban Ɗaki. Kuma kamar dai ba ta da matsala.  Sadiya dole sai kin nutsu kin karanci dabi'ar kowa a gidan nan kafin ki saki jikinki da su. Wasu zasu raɓe ki ba don Allah ba, wasu kuwa zuciya ɗaya za su so su mu'amalance ki. Ke dai ki girmama duk wand ya girmeki musamman idan ya riƙe girmansa. Dama ban sanki da rashin kunya ba, in sha Allahu ki ka riƙi addu'a komai zai zo maki da sauƙi. Don Allah Sadiya ki rufe idanu ki ba masu jiran ƙiris a auren nan kunya. Ki wanke zuciyarki ki rungumi zaɓin da Allah ya yi maki. Baiwa ce ba kaɗan ba a daidai sadda wani bai aureki ba, Allah ya kawo maki madadi da ya fi wancan komai na rayuwa. Gina sonki a zuciyarsa ba abu ne mai wahala ba a gurinki mace. Ke dai ki zama mai biyayya da kyautata tsakaninku. Wataran za ki ɗaga hannu ki godewa Allah da ni'imar da ya yi maki na auren Maina. Ina jin wannan a jikina." Anti Hafsatu ta ƙarashe tana mai murmushi, ita ma Sadiyar ta ɗan murmusa. Ba ta san irin adadin ƙaunarta da Antin ba, mace mai sonta da Innarta. Takan mance ma ba Uba suka haɗa ba, ji ta ke kamar ciki guda suka fito da ita. "Nagode Anti. Allah ya bar mu tare." Ta amsa da amin. Daga haka suka fito falon kamar kuwa jiran fitowarsu ake sai ga sallama bayan an kwankwasa ƙofar. Amsawa suka yi, Hindu ce tare da wasu bayi ɗauke da manyan fulas na abinci, haka aka dinga jera musu, bayan sun kwashi gaisuwa. Hatta da lemuka da ruwa sai da aka ajiye. Bayan fitarsu ne kuma suka ci kaɗan a cikin wanda za su iya don wani ma ko taɓawa ba su yi ba. Ba jimawa kuwa sai ga Hindu da ɗaya a cikinsu riƙe da wani ƙaton bowl da aka yayyanka kayan marmari. Ganin sun kammala ya sa ta ba da umarnin a fara kwashe kayan, sai da aka kammala ita ma ta musu sallama ta fita Anti Hafsatu na ƙara furta godiya. Can kuma suna nan aka ƙara sallama, wannan karon ba muryar Hindu ba ce, suka amsa, wata mace ce da za ta girmi Anti Hafsatu tare da wata baiwa wacce kalar kayan da ke jikinta ne irin na bayin da suka zo ɗazun ya sa su fahintar ɗaya ce a cikinsu, ita kuma riƙe take da ƴar jaka. Matar doguwa ce mai jiki kaɗan. Ta ci ado kamar mai zuwa gidan biki. Fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙaraso ta zaune tana kallon Sadiya. Ganin haka Sadiya ta yi gaggawar saukowa tana kokarin russunaws ta gaishe ta duk da ba ta san ta ba amma suna tsantsar kamanni da Maina. Da sauri ta riƙo ta miƙar gami da zaunar da ita gefenta a lokacin da ta ke amsa gaisuwar Anti Hafsatu tana ƙara wa da tambayar ya gajiyar hanya. "Alhamdulillah, gajiya ta bi lafiya." "Masha Allah. Suna na Saudatu, ɗaya daga cikin Yayyun Maina." Dama ko ba ta faɗa ba sun ɗauki haske, kamannin sak kawai dai ita ɗin  tana da ɗan duhun fata.  Daga haka Gimbiya ta waiga ta dubi Baiwar da ke durƙushe kanta a ƙasa ta ce. "Fauziyya." Sunanta kawai ta kira yarinyar ta fahimta don haka a ladabce cike da ladabi ta matso ta buɗe jakar ta fiddo gidan wata sarƙa ta ajiye, ta ƙara fiddo wata alkyabba fara ƙal mai adon zare kalar golden ita ma. Gidan sarƙar ta fara miƙawa Gimbiya Saudatu. Ita kuwa ta taimakawa Sadiya da cire fashion mai tsada da ta sanya sannan ta taimaka mata da saka wani arnen gwal mai daukar idanu. Anti Hafsatu sai ta rasa ma me za ta ce, ƙasan ranta wani irin farin ciki da hamdala kawai take ga Allah na wannan sauyin da Sadiya ta samu. Daga zuwansu ko awa ɗaya ba su kai ga cikewa a garin ba har rayuwar Sadiya ya fara sauyawa? Gimbiya Saudatu kuwa ta ƙara kallon Sadiya wacce har a ƙasan ranta ta ji dadi da ta gan ta a haka, tabbas idan an cire nasabar da mahaifiyarsu ke ta faɗan wai ba a duba jinin sarauta an aura wa autan nata ba sai bare, toh kuwa ba ta ga makusa a tattare da ita ba. Ita kam ta yi mata kuma tana fatan halayyarta ma ya kasance irin fuskarta. Wato mai kyau. Sosai ta ga sarƙar ta karɓe ta sannan ta miƙe tsaye riƙe da hannun Sadiyar, da sauri Fauziyya ta ɗauki alkyabbar ta da ke wani irin ƙamshi mai daɗi ta miƙa mata. Nan ma mayafin da ta yi Sadiya ta lulluɓa ta cire ta ajiye ta sanya mata alkyabbar. 'Allahu Akbar! Masha Allahu la kuwwata illa billah.' Faɗin Anti Hafsatu a zuciya har da wasu ƙwalla ta ji sun cicciko mata a idanu ganin wani irin kwarjini da haiba a fuskar Sadiya wacce ita kanta jikinta ya yi sanyi ga kuma nauyin da bakinta ya yi ta ma rasa me za ta ce. "Kin yi kyau sosai ƙanwata. Allah ya sa kin shigo gidan nan a sa'a. Ki saki jikinki, a hankali za ki san mu don ba laifi yawa ne da mu. Komai a sannu za ki fahimta kin ji ko?" Ta gyaɗa kai a ɗan kunyace, Anti Hafsatu ta amsa addu'ar da amin. "Ku na iya biyo ni muje, Mai babban ɗaki tana jira." Suka amsa da toh suna masu bin bayanta. Ita kuwa Sadiya ta ji duk ta takura, daga zuwa an ƙaƙaba mata alƙyabba? Allah dai ya sa ba haka za ta dinga yawo a gidan ba. Ƙila ma iyakar na yau ne. Haka ta dinga saƙe-saƙenta, can wani ɓangare na zuciyarta na tunanin ko ina Angon nata ya shige? Amma kuma tana ta kokarin basarwa don a ganinta me ma zai dame ta da tunaninsa? Haj Saratu ta amsa gaisuwar Sadiya ita ma ta yaba yanda ta yi kyau. Nan kuma ta umarci Gimbiya Saudatu da yi musu jagora zuwa sassan Fulani Kausar da ma sauran matan Sarki Abdallah Tafida don ta gaishe su. Falon na Haj Saratu a cike da mata, haka aka dinga bin Sadiya da kallo ga gefe ta ɗazun ba cigaba da zuba mata kirari. Ita dai tana rungume jikin Gimbiya Saudatu jefa ƙafafunta kawai ta ke. Haka har suka iso wani ɓangare jama'a na biye da su a baya. Falon shi ma yana da girma kamar na Haj Saratu, ga kuma ɗakuna a can ciki. Iya tsari ya tsaru don ba ma za ka iya tantance wanda ya fi kayan alatu da na Fulani Kausar da na Haj Saratu ba. Tana hakimce a saman kujera ta yi wani irin zama na ƙasaita. A gefenta zaune can ɓari na daban wasu ƴanmata ne su biyu sai ko wata babbar mace ita ma dake bin su da kallo. Anti Hafsatu ta kalle Fulani Kausar dakyau, ko kaɗan ba ta ga kamarta da Maina ba, ta dai gane uta ce mahaifiyarsa a kirarin mai zuba kirari dake ta yi babu ko gajiyawa. Fuskarta kawai ya fallasa sirrin zuciyarta don babu ko ɗigon walwala a samansa. Gimbiya Saudatu duk ba ta ji dadin yanayin dake saman fuskar Umman tasu ba, ai ko don masu ɗaukar bidiyo ta daure ta yi murmushi koda kuwa bai kai zuci ba amma ta kasa. A wulaƙance ta amsa gaisuwar Sadiya tana cin magani. Daƙyar ta iya faɗin. "Allah ya yi albarka." Mutane aka hau amsawa da amin. Haka aka zagaya da Sadiya har sauran ɗakuna biyu na matan Mai Martaba. Daga nan kuma bisa jagorancin Jakadiya da aka kai ta wajen Mai Martaba. Babu wanda ya shiga, hatta da Gimbiya Saudatu duka tsayawa suka yi. Ita ɗin yake son yin magana da ita sai ko Maina da ke zaune tun ma kafin ta shigo. A ladabce Sadiya ta miƙa gaisuwa, ya amsa mata. "Alhamdulillah. Muna maki murna da shigowa wannan masarauta mai albarka. Ba ma yi maki kallon suruka, ke ɗiya ce a wurinmu. Za kuma mu riƙe amanarki, dukkan wani abu da kile buƙata, ki sanar da mu za mu yi ƙoƙarin ganin an maki matuƙar bai saɓawa addini da al'adunmu ba." Mai Martaba ya shiga yi musu nasiha da kuma yin alƙawari ga Sadiya zai ɗauki mataki mai tsauri a kan ɗansa muddin ya kama shi da zaluntarta ko yaya. Haka nan ya jaddadawa Maina ya ji tsoron Allah, ya kuma kiyaye yin abin da zai ɓata ransu. A ƙarshe ya sanya musu albarka ya kuma yi musu addu'a. Nan ta miƙe fuskarta da hawaye ta fito ta bar shi da Maina. Ji take kamar ba ita ba, wai ita ce da wannan matsayin da muƙami. Ita ake ta girmamawa, ta shiga roƙon Allah a rai kada hakan ya haifar mata da girman kai, ya sa ta zama mai tausayin na ƙasa da ita kamar yadda ta ke tun farko. *** "Za ki zauna a nan ne har zuwa nan da kwanaki uku da za'a kammala gyaran sashenki a kuma yi bikin miƙa ki zuwa can." Ta tuno kalaman Haj Saratu sadda ta ke ninke alƙyabbar, ita kuwa Anti Hafsatu na faman kallon sarƙar da take mayarwa cikin gidansa. "Anti." Sadiya ta furta, ta ɗago ta kalle ta tana murmushi. "Na'am Gimbiyar Maina." Sadiya ta nanata sunan a ƙasan rai, wai Gimbiyar Maina. Sai ta girgiza jai ta zauna gefen gadon. "Anti zan iya rayuwa a gidan nan?" 'Yar dariya Anti Hafsatu ta yi. "Za ki iya, babu abin da zai cinye ki. Kar fa ki manta kina da Allah, toh akwai wani abu da ya gagare sa?" "A'a. Amma ba ki kula kamar wacce aka ce mahaifiyarsa ba ce..nufina kallon da na ga ta yi min. Ban sani ba ko don a fakaice na kalle ta, ko ban gani da kyau ba ne." Ajiyar zuciya Anti Hafsatu ta yi. "Wannan kar ya dame ki, ki kyautata mata zato. Ba za ki samu matsala da ita ba. Yanzu duk ba mu isa yankewa kowa hukunci ba sai zama ya yi zama. Ki fidda komai a ranki." Sadiya ta yi ɗan murmushi sannan ta jinjina kai ba ta ƙara cewa komai ba, amma tabbas jikinta na ba ta cewa ba ta samu karɓuwa a wurin surukarta ba yadda ta samu a wajen sauran matan Mai Martaba musamman Haj Saratu da suke ɗakinta. Su Safiyya ba su ne suka iso ba sai dab da sallar Magriba. Su ma nan suka sauka amma ɗakinsu daban shi ma babba, su kansu sun jinjina irin tarbar arziƙi da aka yi musu. Zahra kamar ta shiɗe don farin cikin wannan daular da Allah ya jefo ƙawarta a ciki. Ranar dai kusan raba dare aka yi hira ya yin da tuni Zahra ta shiga IG tana kallon bidiyon da tuni ya yaɗu na Sadiya a cikin alkyabba. Wannan ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba. Kamar jira ake yi har an ɗora ta? Kuma ma har da fuskarta a waje? Toh amma ya za ta yi tunda ba ta ma san ko aikin waye ba, kuma koda ta sani ina ta ga ƙarfin cewa wani abu? *** Misalin ƙarfe tara da mintuna na washegari Litinin, Hajara da Husna suka iso. Anti Hafsatu wacce suka yi waya da Khamees ta sanar mishi da zuwan nasu, tuni ya aika mota can a yi jiransu. Suna kuma zuwa, aka shaidawa direban, ta hanyar waya ya gane su ya ɗauko su. Tun daga motar Hajara ta san an zo wajen. Sadiya ta samu duniya yadda ya kamata. Husna kuwa bakinta ya ƙi rufuwa tana rungume da Sadik da ke bacci tana bin hanya da kallo kamar ta yi fiffike ta gan ta cikin masarautar a gefen yar uwarta. A fakaice Hajara ta watsa mata harara gami da jan tsaki a zuciya. 'Banza marar zuciya. Maimakon ta yi bakin ciki ba ita ce a wannan matsayin ba, sai faman rawar jiki ta ke yi.' Ta ayyana a ranta. Babban dalilinta na zuwa bai wuce abu biyu ba. Ta wanke kanta a wurin dangi daga zargin tana yi wa Sadiya hassadar da aka fara mata saboda lura da yanayin ficewarta a gidan ba a hayyaci ba ranar da aka ɗaura auren. Sai ko ganewa kanta muhallin Sadiya, har yanzu ganin komai take kamar a mafarki, za kuma ta so ta ganewa idanunta. Ta san Inna na can ta a farin cikin ta aurar da duka yaranta da ƙuruciyarsu. Ta kuma sani Sadiya ta taka sa'ar da Husna ba ta kama ko ƙafarsa ba. Wannan baƙin ciki da shi za ta mutu. Sai dai ta yi rantsuwar gallazawa Inna, ta ci alwashin sai ta zama abar tausayi. Gwara su biyun duka ta yi maganinsu ta haɗa musu zafi ta ko'ina. Zai fi kyau da ta zo Gomben da kanta don gane ta inda za ta fara ƙulla zaren makircinta. Wani irin gumi ne ya shiga tsastsafowa Hajara tun daga irin yadda bayi suka shiga zubewa a sashen Haj Saratu su na gaishe su. Ga uwa uba daular da aka narka a falon. "A yi musu jagora zuwa Gimbiya  Sadiya." Wannan laƙabi na girma da aka jingina sunan Sadiya da shi ya ƙara tayar da hankalinta. Dama ta san a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. To amma ai ta gama ayyana dukkan hakan a rai bai kyautu ace ya mata zafi kamar haka ba. Abu ne da ta kwana da sanin jin fiye da shi idan sun zo. Haka ta daure da yaƙe saman fuskarta suka bi bayan baiwar don dama akwatinsu na kaya ya riga su yin gaba. Su Anti Hafsatu duka suna falon, Sadiya na zaune cikin wani leshi ɗan ubansu kalar purple an bi patterns dinsa da adon stones har ƙasa daga gaba. Ta yi ɗaurinta tsaf haka ma fuskarta ta sha kwalliyar da Zahra ta tursasa mata yi acewarta ko don masu shige da fice suna zuwa ganinta, su gan ta tsaf. Baiwar nan ta zube ta fara da yi wa Sadiya gaisuwar ban girma. Sadiya ta amsa hankalinta na ga Husna suna yiwa juna murmushi. Hajara kafafunta daƙyar suka ƙarasa da ita ga kujera ta zauna tana yaƙen dole. Nan kuma hira ta ƙara ɓarkewa har sadda aka kawo wa Husna da Hajara abin kari. Nan ma kayyakin abinci ne iri iri. Daƙyar Hajara ta iya cusawa a cikinta, ƙarshe ma ta ce amai take ji tana buƙatar kuma ta huta. Zahra ce ta yi mata rakiya ɗakin da babu wanda ya sauka a ciki wanda a nan aka ajiye kayanta ita da Husna. Tana shiga ta rufe kofar ta zauna gefen gadon ta shiga fidda hawayen baƙin ciki. "Wannan gidan bai dace da Sadiya ba!  Na rantse ko zan yi yawo tsirara sai na fisge Sadiya daga gidan nan don uwarta!" Ta firta a fili tana share fuskarta. Ta rasa meyasa take shakkar Boka ta yadda ta kasa fushi da shi. Wuyarta ya ɗauki waya ya kira ta akan ta zo, ban hankalinta ke tashi ta rasa nutsuwa jiki na rawa take amsa mishi za ta zo din. Idan ta zauna kamar irin na yanzu, sai ta dinga mamakin abin, amma kuma a karshe dole take watsarwa tunda ta rasa mafita, wuyarta dai ya kira. Ga kuma alƙawarin da ya ƙara yi mata da ta tsinci kanta da amsa mishi da toh, wai zai yi iyakar yin sa ya raba Sadiya da gidan. Ita kam dama a inda ya fadi a nan ta bar shi, ta sani ba zai iya ba. Abu ne da ba zai faru ba sai dai faɗi a baka. *** Maina bai samu sukunin zama tare da Mahaifiyarsa ba sai a safiyar ranar dalilin umarnin da Mai Martaba ya bayar na ya tsaya ya tabbatar da kammaluwar komai na ɓangarensa saboda Sadiya ta shiga ɗakinta. Ba don yana so ba sai don bin umarnin da ya zama dole, bai kuma isa ya kauce masa ba koda giyar wake ya sha. "Ibraheem." Sunansa da Fulani Kausar ta kira a kausashe kuma kai tsaye madadin Kakan da take kiransa da shi ya sanya Maina ɗago idanunsa a hankali ya dubeta kafin ya mayar. "Na'am." "Ban amince da auren nan ba." Ya rasa me zai ce, bai kuma sauya daga yanayinsa na farko ba. Ya sani duk abin da kowa zai ce, to fa sai dai gareshi ɗin, amma babu wani a cikinsu da zai ja da Mai Martaba. Wannan a rubuce ya ke. "Ni Kausar da Mahaifina ya kasance Ɗan Sarki jika na Sarki, sarauta mai girma irin ta Daura, na auri jinin sarauta, babu kuma wani a gidanmu da ke auren maƙasƙanciya ko maƙasƙanci, don me zan zuba idanu ka yi zaman aure da talaka? Ita ba wai iyayenta wasu ba ne. Meyasa Mai Martaba zai min haka? Saboda ya ƙara nuna min fifikon yaran Saratu a kan nawa ko?" Maina ya lumshe idanu ya furzar da huci kaɗan, buɗe su ya yi ransa gaba ɗaya babu dadi da maganganun Fulani. "Shirunka na nufin kai kana sonta? Ka yarda ka yi zaman aure da ita? Hakan na nufin..." "Hakan ba ya nufin duk abin da ku ke tunani Ummi. Sai dai shirun na nufin ba ni da zaɓin da ya wuce bin umarnin Maihaifina." Fulani Kausar ranta ya ɓaci, ta kuwa ɗaure fuska tamau tana harararsa. Ita ta haife shi kuma ta fi kowa sanin halinsa, mutum ne da ba ta taɓa ganin ya wulaƙanta wani ko wata ba, yana da halayya irin ta mahaifinsa. Ko bai son abu, ba zai nuna ba. Hakanan son ma ba kasafai ake gane yana yin sa ba, yana da wuyar fahimta wasu lokutan. Ta sani ko giyar wake ta sha auren nan ba zai mutu ba don al'adar gidan ce ba sa sakin aure sai da dalilai masu ƙarfin gaske sai ko kaddarar da babu yadda aka iya. Yaranta goma cif, dukka guda taran mata ne, Maina shi kadai Allah ya ba ta namiji. Yayyunsa biyar duk suna gidajen aurensu sai ko ƙannensa uku, su ma an yi auren autarta Ummulkhair ce kaɗai a gabanta sai ko Najma da Hidaya yaran yan uwanta da suke jini ɗaya da take riƙonsu. Burin duniya ta ɗora a kan Maina ɗa ɗaya tamkar da dubu a gareta saboda Allah ya ba shi farin jinin jama'a. A na ji da shi matuƙar a gidan, duk da ba shi da hira da sakin fuska sosai amma kuma maza da mata kaunarsa suke. Tana kuma ji a jikinta ko bai yi sarauta yanzun ba, watarana zai yi ɗin. Gudun sarautar yake ita kuwa ta sha alwashin sai ya riƙa. "Ina iya tafiya? Mai Martaba ya..." "Saboda ni ban isa da kai ba shi ne kadai ya isa da kai ko? Muna magana ka na kawo min uzuri?" Ɗan lasar leɓɓansa ya yi. "Allah ya huci zuciyarki." Ta yi ƙwafa tana murza yatsunta da suka sha adon gwal. Maina ya yi shiru, shi fa bai ga abin tayar da hankali ba don wai ya auri Sadiya. Umarni ne kuma ya ji ya gani zai bi, zai kuma kula da ita wato sauke haƙƙoƙin da ya san zai iya, shi hakan ma da ya yi tunani kamar wani katanga zai zame mishi daga harin da ƴanmatan zuri'a da na waje suke kawo mishi. "Goben za ta tare?" Tambayar Fulani ta ƙara katse shi. "Hakane." Ya ba da amsa. "Uhum. Ka na iya tafiya." Maina ya yi godiya ya miƙe, har zai fice sai kuma ta ce. "Kakana." Ya juyo ya dawo yana ɗan yamutse fuska ga dukkan alamu ba ya son magana. "Ka na sonta?" Ta tambaya tana dubansa. Bai san sadda ya yi murmushin da ya ƙara bayyana tsantsar kyawunsa ba. Wani bin idan Fulani na ririta shi kamar ƙwai, ji take da shi sosai. Wasu lokutan kuma idan ta birkice har mamaki yake. "Wannan ya ba ni tabbacin ka na so. To dama tun kuna tare da ɗan uwan naka ka na son ta Ibraheem?" "Please Ummi, ki min iznin tafiya." Ta kara harararsa, shi kuwa ya ɗan ƙara murmusawa. "Je ka." Ya kuwa fice. Ta bishi da kallo ta sauke ajiyar zuciya. Tunanin mafita take yi, toh idan kuma dukkan wannan abin da take yi shi yana sonta fa? 'Ibraheem ba zai taɓa son yarinyar nan ba. Ni na san waye ɗana.' Ta ba kanta amsa a zuciya. *** Washegari gidan ya ɗauki haramar shiri na biki da za su gudanar wato buɗar kai wanda daga shi kuma Amarya za ta shiga ɗakinta. Hajara ta firgita da irin tsadadden suturar da ta ga an kawo wai Sadiya ta yi amfani da su. Komai na babban kamfani, har da wani sarƙa ƙarami na diamond. Sai da ta kai zuciya nesa matuƙa kafin ta iya danne baƙin cikinta ba tare da ta bari ya bayyana a fili ba. Ta kula kamar haba-haba ake yi da Sadiyar. Fuskar Gimbiya Saudatu da ma Gimbiya Bilkisu (diya ga Haj Saratu) da suka shigo kawo kayan wannan karon su ma fuskokinsu a sake har aka yi wasa da dariya tare. Ta kula dai lokacin ne Gimbiya Bilkisu ta sanya Sadiya a idanu sai tasbihi take yi wai Sadiyar ta dace da Maina. Aka gudanar da buɗar kai bisa al'adar masarautar tasu. Kyaututtuka kam Sadiya ta sha su masu firgitarwa. A karshe aka ƙara kai ta dakunan matan gidan kafin a sanya ta a mota zuwa ɓangarenta dake ginin masarautar wanda ya ke da ƴar tafiya tsakani. Tun kafin a kai ga shiga ciki daga waje kawai ka ga gidan sai ya burgeka. Gini ne babba mai zaman kansa, bai raɓu da jikin wani ba, don wurin ma daga gefe garden ne lafiyayye sai can idan an yi tafiya kadan a iske ginin ɗan Mai Babban Ɗaki, Yarima Zubair. Farin fenti ne gaba ɗaya daga waje, sai ko baƙaƙen gates hakanan rufin kwanon ma baƙi. Jikin Hajara tun a lokacin ya fara rawa, Sadik dake hannunta ta tabbata ba za ta iya cigaba da riƙonsa ba don haka ta miƙa shi ga Gwaggo Atine wadanda suka iso da yammacin da sha tara arziki da Malam da Abba suka haɗa su kawo matsayin gara don a cewarsu ba za su zuba idanu a ɗauki ɗiya sukutum, a kuma hana su zubamata kayan ɗaki su zauna ba su yi komai ba. Daidai gwargwado sun yi kokarinsu kuma koda wasu ba su yaba ba wasu kam sun ga kokarin. "Hajiya ki daure, kar ki fallasa zuciyarki. Fuskarki gaba ɗaya ta sauya." Cewar Gwaggo Atine cikin raɗa-raɗa dab da kunnen Hajara yanda za ta ji sosai, don ma dai ana ta bushe-bushe da guɗa da zuba kirari ya sa babu wanda ya lura. Hajara ta ɗan dube ta sai kuma ta kauda kai tana ƙaƙalo murmushin yaƙe. Da aka shiga gidan kuwa, sai da numfashinta ya tsaya cak na wasu daƙiƙu kafin ta jawo shi da ƙarfin gaske. Tsayawa fasalta ma tsaruwar falon ɓata baki ne. Falukan biyu ne, na farko bai kai na biyun tsaruwa da kayan more rayuwa ba. A na biyun ne kuma akwai hanyar matattakala, daga gefe, sai ko ɗakuna har huɗu a cikinsa. A nan aka shigar da Sadiya ɗaya daga cikin ɗakunan. Ba Hajara ba, hatta su Zahra da Husna sai da jikinsu ya yi la'asar da dukiyar da aka narka. Kuma tunanin da suke yi duka a kwana biyu aka zuba ko dama can ya shirya gidansa sai ƙarashe? Anti Hafsatu kuwa wacce ta ji daga bakin Gimbiya Saudatu cewar dama ginin Maina an jima da kammalawa haka ma ɓangarensa a shirya yake, na Sadiya ne aka zuba kayayyakin da ya dace da mace aka kuma yi komai yadda ya dace bisa umarnin Mai Martaba. Sai dai ita kanta ba ta yi zaton tsaruwar gidan ya kai haka ba. Sai da kowa ya watse a cikin yan uwan Maina da ma iyaye dangin Sadiya da suka zo na ɓangaren Inna dake Gomben da ma kuma su Dada su Gwaggo Atine waɗanda suka koma masauki cike da santi, Hajara ma bin su ta yi don ta rantse idan ta cigaba da tsayuwa a gidan da aka kira wai na Sadiya ba. Yarinyar da ta ke yiwa kallon ƙasƙantacciya irin uwarta a duniya, wacce ko suturar arziƙi ba ta da su kamar nata da Husna, yau ita ce a wannan daular da har wata ƙanwar Malam mai shegen surutu ke cewa ai haƙurin Sadiya ne ya sa ta dafa dutse har ta sha romo. Har ita za'a faɗawa haƙuri? Ita da ake fasa aurenta a ranar da ya dace a yi shi? Aikin banza kawai. *** Idanu waje cike da alamar tsoro ta ke bin ɗakin da kallo. Sai ta inda ma wardrobe dinta yake ya yi nisan taku ya kai ashirin daga gadonta da ya zo da wani irin labule. Kayan ɗakin gaba ɗaya adon baƙi da ruwan golden ne. Ga fitilun da suka ƙawata shi mai zuwa kala uku, ja, fari da kuma blue. Duk sadda ka kashe ka kunna to fa zai sauya kala. "Anti wannan gidan zan zauna na rayu ni kaɗai?" Ta faɗi idanunta suka yi rau rau. Su Zahra suka dara. "Sadiya wannan gidan, shi Allah ya baki. Gidanki ne. Don ma ba ki ga falukanki da kicin ɗinki ba. Komai na gidanki an ƙawata shi, sai dai mu yi addu'ar Allah ya zaunar da ku lafiya ya baki aljanna fin haka. Amma fa Sadiya samun aljannarki to yana ga bin mijinki. Don Allah Sadiya kar ki ba mu kunya, ki bi Maina sau da ƙafa. Ki zauna lafiya ku yi rayuwar mutunta juna. A hankali za ki fahimci waye mijinki, shi ma kuma na san zai fahimceki ya so ki in sha Allahu. Mun samu kyakkyawar tarbiyya daga iyayenmu, mun gani yanda suke girmama miji da lamuransa, Sadiya ki kauda komai a zuciyarki ki rungumi aurenki da hannu bibbiyu. Mijinki shi ne komai naki a yanzun, ki yi hakuri da dukkan abin da za ki gani ko ki ji wanda zai zo maki a hagunce, watarana a hankali za ki fahimci kowa kuma ki ci maganin zama da su. Allah ya sanya albarka a aurenku, yadda ki ka yi biyayya ga su Inna da mu kanmu yayyunki in sha Allahu rayuwarki ba za ta tagayyara ba. In sha Allahu wataran za ki yi alfahari da aurenki da Ibraheem Tafeeda." Su Zahra suka amsa addu'ar Anti Hafsatu da amin. Sadiya wacce jikinta ya ƙara sanyi ta share hawayenta ta na mai yin godiya ga Antinta. Jikinta ya ƙara sanyi sadda aka watse aka bar ta ita ɗaya ƙwallin ƙwal a gidan. Ta yi wuri-wuri da idanu tana zagaye idanunta cikin ɗakin kafin ta sauke ajiyar zuciya. A jikinta take jin ba zai shigo inda take ba. Dalilin kenan da ya sa ta miƙewa ta cire alƙyabbar da aka ɗoramata a saman wani tsadadden voyel sku blue mai adon dark. An yi mata beadwork a wuyan da ma bakin hannayen. Tana shirin kai hannu saman ɗankwalin ta tuje shi ne ta ji shigowar mota, sai da ƙirjinta ya buga don ta san babu mai zuwa a wannan lokacin face Maigidan. *** Ya fito daga motar, Baharu na riƙe da ledoji yana bin sa a baya har suka shigo falon, iyakar Baharu falon farko, nan ya ajiye ledojin ya rufe musu ƙofar. Maina ya ƙarasa ya sanya muƙulli sannan ya nufi falo na biyu ba tare da ko kallon ledojin ba. Har ya soma taka matattakalar da za ta sada shi da na sa ɗakunan ya tsaya cak. Rashin kyautuwar duba kiwon da Allah ya damƙa mishi ya ji, ga Mai Martaba a gefe da ya ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa da nasihohi, a gefe ga wasu a yayyunsa da kuma Haj Saratu. Duka sai ya ji ba zai iya shigewa alhalin bai leƙa ta ɗin ba, ya tabbata kamar yadda auren ya zo mishi a bazata to ita ɗin ma hakan ne, toh a wane dalili zai ƙuntata mata tunda dai ba wai shi take so ba? Dawowa ya yi da baya ya koma falo na farkon ya ɗauki ledojin da bai ma san me da me Khamees ya siya ba ya ƙarasa. Kallon ɗakunan ya tsaya yi, zai rantse bai san wanda take a ciki ba tunda kowanne babu inda ba a zuba kaya ba. Can dai ya zaɓi wanda ya ke tunanin zai iya kasancewa nan ne ya murɗa ya shiga da sallamarsa ƙasa-ƙasa. Sadiya da ke zaune gefen gado ta yi shiru ta ɗan zabura ta kalle shi, idanunsu ya sarƙe wuri guda. Kusan kuma lokaci guda suka janye daga kallon juna. Ya ƙaraso a hankali ya ajiye ledojin saman teburin dake gaban gadonta. A hankali ita kuwa ta ɗan zame daga saman gadon kafin murya a tausashe ta ce. "Barka da dare." Maina wanda bai motsa daga inda yake ba, ya zura dukkan hannayensa a cikin aljihun wando yana kallonta son rai har jelolin kitsonta da suka zubo a kafaɗa. "Barka dai. Akwai abin da ki ke buƙata?" Ta girgiza kai. "A'a. Ba na buƙatar komai. Nagode." Godiyar ya ji daɗinta hakanan, hancinsa ya saba da jin ƙamshin turaruka iri daban-daban, sai ya ji wanda ke tashi a ɗakin ya bambanta da waɗanda ya san, ya kuma yi mishi. Sadiya jin shirun ne ya sa ta ɗago kai ta dube shi, idanunsu suka sarƙe wuri guda karo na biyu. Bai kauda na shi ba sai ita ce da sauri ta yi ƙasa da nata kan. "Ki na iya amfani da abin da ke cikin ledar. Allah ya tashe mu lafiya." Ta san dama hakan ce za ta faru, ba ta kuma kawo zai kwana ɗakinta ba. Ita ma kuma kwanan zai haifar mata da rashin sakewa da ɗari-ɗari. Kafin ma ta kai ga amsawa har ya juya ya soma tafiya. Bayan fitarsa ta sauke ajiyar zuciya na samun cikakken 'yanci a lokacin don tsayuwarsa a ɗakin ya sa ta kasa nutsuwa sosai. Yana da qualities na suffa wanda kowace mace za ta yi kwaɗayin ya kasance mijinta sai dai hali ne ba ta sani ba sai zama ya yi zama. Ya dai shayar da ita mamaki don ba ta zaci ko hanyar inda ta ke ma zai kalla ba balle ya nuna kulawa. Miƙewa ta yi ta rufe ɗakin da muƙulli, ba ta kalli inda ledojin suke ba duk da tarin yunwar da ta ƙunsa don tun rana kasa nutsuwa ta yi ta ci abinci tsabar fargaba da ta shiga jin wai za ta tare a ɗakinta. Sai da ta rage kayan jikinta ta zuwa doguwar riga mai taushi wanda tsawonsa da kaɗan ya wuce ƙaurinta, ta rufe gashinta da hula. Ta tattare kayan wuri guda ta ajiye su inda ya dace sannan ta zauna ta kara bin ɗakin da kallo. Murmushi ta ji ya suɓuce mata da ta tuna wai gidanta ne, kuma ita ɗin mata ce ga matashi kamar Ibraheem Tafida. Ta ɗan lumshe idanu tana tunano shigar da ya yi na kufta ruwan madara. Ya karɓe shi sosai. Ga maganarsa da ke fita a nutse kuma muryar ba a sama ba, ƙasa-ƙasa wanda sai ka nutsu za ka ji. Ta lura haka yake magana tunda ba wannan ne karon farko da ta ji ya yi ba. Ta yi saurin buɗe idanunta tana mai jin haushin kanta, ko mene ne toh na tsayawa wassafa Maina har haka? Ta ɗan cije leɓbanta cike da takaicin kanta, idanunta suka sauka a kan ledojin da ya ajiye, nan kuma ta tuna da yunwar da ke cin ta, ta miƙe ta ƙarasa ta janyo ta buɗe ta farko. Soft drinks ne sai ko ɗayan ledar da ta buɗe, gashin kaji ne har guda biyu. Na ukun kuwa tarkacen su brush da toothpaste, mouth wash da sauransu. Ta miƙe ta buɗe ƙofar gami da murɗawa a hankali ta fito, falon shiru an kashe fitilun amma kuma akwai hasken waje da ma ɗan hasken dake gefen hawa bene da ya ratso cikin falon. Ta koma ta ɗauko wayarta, da taimakon hasken ta gane inda makunnan suke ta kunna ɗaya, ya ba da kalar blue, an zuba kayan ƙawa a cikinsa. Ta ƙarasa ga ƙofar da ke jikin dining table, aikuwa kicin ɗin ne kamar yadda ta yi tsammani. A zatonta ƙarami ne sai ta gan shi da girma wanda a wata duniyar zai iya zama madaidaicin falon wata. Ta ƙara godiya ga Allah da wannan ni'imar da ya yi mata, ta kuma yi fatan Allah ya sa aurenta ya zame mata haske da zai haskaka duniya da lahirarta. Ta shiga ciki, a jerin farantai dake jere a plates rack irin wanda ke manne jikin bango, guda daya ta ɗauka sai kofi ta ɗauraye su ta kashe fitilun ko'ina ta koma dakin. Ta yi tunani ya fi a ƙirga ko ta zuba ta miƙawa Maina, amma kuma tana jin fargabar kar ya ji haushin ganinta a ɓangarensa. Ita dai ta san ya mata yawa don ko rabi ba za ta iya ci ba balle a kai ga kaza biyu. Haka ta ɗiba ta ci ta kora da ruwa ko lemun ba ta sha ba ta tattara a dole ta buɗe ƙofa karo na biyu ta koma kicin. A firij ta saka kazar da sauran lemukan wanda ta tarar ma akwai lemun a ciki, ta rufe komai ta koma ta yi alwala sannan ta kunna karatun kur'ani a wayarta. Tun tana bin karatun a hankali har dai bacci ya yi awon gaba da ita cikin lallausan gado da abin rufarta. Ƙarar alarm ɗin dake wayarta ne ya farkar da ita ta kuma gane asuba ce ta yi. Fitowarta daga banɗaki ba jimawa ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofar, ba ta yi dogon tunani ba don ta sani rai biyu ne a cikin gidan idan ka cire ma'aikatan waje. Hijabi ta zura a gaggauce ta ƙarasa ta buɗe ƙofar. Sanye yake cikin doguwar rigar jallabiya fara ƙal, ko ba a faɗa ba shirin sallah ya yi. "Oh kin tashi ashe." Hakan kawai ya faɗi bai kuma saurari cewarta ba ya yi gaba zuwa masallaci. Sadiya ta bi shi da kallo sannan ta rufe ƙofar ta koma tana tunani kenan tashinta ya zo ya yi. Murmushi ta ɗan yi don har a zuci ta ji daɗin haka. Ɗan ƙaramin wuri ko kuma ace masallaci da aka ɗan kewaye mata, an saka darduma sai ɗan gini da aka yi aka ajiye kur'ani har uku kowanne da wajensa ga kuma wani abin ƙamshi mai daɗi da aka ajiye a gefe. Duk a wajen babu inda ya fi burgeta kamar nan ɗin, ba buƙatar ta nemi gabas a gidan, yanayin da aka shimfiɗa dardumar ma ya sa ta fahimta. Bayan ta idar ta yi karatun kur'ani kafin ta shiga azkar na safe. Koda rana ta fito ji ta yi baccin ma ya fice mata a idanu don haka ta gyara gadonta ta faɗa wanka. Zama ta yi ta murje jikinta da zazzafan turaren da Antinta ta bayar takanas aka kawo mata daga Kaduna wanda Safiyya Jibril ke haɗawa. Ba ta shafa mai a jiki ba sai tafin ƙafafu da hannunta. Ta shirya cikin atamfarta super holland ruwan masara sai ko kalolin da aka ƙawata zanensa da ita. Ɗinkin riga da siket ne, ya zauna ɗabas a jikinta ya kuma fiddo surarta ainun. Hoda kawai ta shafa da man leɓe. Baƙin mayafinta ta yafa a kafaɗarta ta zura takalmi flat ta fito zuwa falon. Kamar jira ake ta fito aka shiga kwankwasa ƙofa don sai da ta saurara sosai ta iya ji. Ta ƙarasa har falon farko sannan ta buɗe. Wata baiwar gidan ta gani ɗaya daga cikin masu yi musu hidima tun zuwansu a sassan Haj Saratu. Su uku ne, suka ɗan russuna suka gaishe ta. Ta amsa har lokacin ta kasa sabo da wannan girmamawar da ake mata, son samunta ne ma su daina a dinga gaisawa kamar 'yan uwa. Hanya ta ba su suka shiga har falonta na biyu bayan neman iznin hakan a wurinta, nan suka ajiye kwandunan da suka shigo da su da aka shaƙe da kayan kari. "Saƙo ne daga Mai babban ɗaki." Abin da suka ce kenan. Ta yi godiya, bayan tafiyarsu ta fiddo. Ta jera komai saman tebur, ta shiga kicin ta ɗauko farantai da cokula har ma da kofin tangaraye guda bibbiyu ta ɗauraye ta goge su ta ajiye. Ta haɗa shayi ta sha da soyayyar agada da ƙwai don ko farfesun ma ba ta sha ba ita. Ta tattare ta kai kicin ta wanke su tas ta goge ta maida inda ta ɗauko har a sannan Maina bai fito ba balle ta zuba masa abin kari. Ta gaji da zaman ta koma ɗakinta ta fiddo waya ta kira Anti Hafsatu amma wayarta ba ta shiga, hakan ya sa ta kira Zahra. Jin su kamar a hanya yasa da sauri ta tari numfashin Zahra mai tsokanarta da cewa Amarya. "Wai ban gane ba, kun wuce ne? Ina Anti Hafsatu?" "Muna hanya har mun fara nisa, Anti Hafsatu kin san ta jirgi ta koma, dama zuwa da komawa aka biya mata." Ran Sadiya ya ɓaci, kwalla har sun tarar mata ta ce. "Shi ne ba ku zo mun yi sallama ba Zahra? Har da ke? Haka za ku yi min don kun daina sona?" Kawai sai ta fashe da kukan gaba ɗaya ma. Ta dai ji Zahra na faɗawa sauran wai kuka take, sai kuma ta ji muryar Dada. "Sadiya, yi shiru bana son kukan nan. Toh ai kin ji, wannan kukan naki ne yasa muka watse gaba ɗaya ba tare da mun maki sallama ba. Ki nutsu ki yi saurare ni kin ji ko?" Ta kuwa bi umarninta, nan Dada ta yi mata ƴar gajeriyar nasiha ta kuma ƙarashe da addu'a da faɗamata irin karamcin da aka yi musu na haɗa su da sha tara na arziki don kowannensu sai da aka ba shi manyan atamfofi guda biyu ga kyautar turaruka da kuma kuɗi da Maina da kansa ya yi musu. Wai a daren jiyan ya shiga sun gaisa ya kuma yi sallama da su. "Ke dai ki dage da addu'a sosai Jikata." Wannan shi ne kalaman ƙarshe a safiyar da Dada ta furta gareta. Ya kuma shige ta sosai, ta yi musu fatan isa lafiya daga nan suka yi sallama bayan Zahra ta tabbatar za ta kira ta idan sun isa. Miƙewa ta yi ta koma falon don gani take kamar babban laifi ne ta bar Mijinta ya fita ba tare da ya karya ba. Ba ta wani jima ba sai ga ƙarar takunsa yana saukowa daga bene sai ko muryarsa da ta ɗan tsinkaya yana magana dab da zai ƙarasa saukowa. Ya zuge gilashin da ya raba benen da falon ya fito, nan da nan ƙamshi ya gauraye falon. Zai iya rantsewa bai ankara ma da ita ba har ya zauna hankalinsa na ga wayar da yake amsawa mai muhimmanci da ya shafi kamfaninsu. Ita kuwa duk ta takure a wurin, sai kuma a lokacin ne ta tuna da mayafin da ta laluba da idanunta ta ga ba ya nan, wato a ɗakin ta bar shi. Maina yana kammala wayar ya ɗago kai yana duba kiran Fulani da ya shigo sa'ilin da yake kan wani layin. A lokacin ne kuma hankalin ya kai gare ta. 'Masha Allah.' Ya yi furucin a zuci, a gaggauce ya kauda kansa ya hau danna wayar da zummar bin bayan kiran Fulani sai dai hakan ya gagara. "Barka da asuba fatan an tashi lafiya?" Ya tsinci muryarta, dole ya ƙara kai dubansa kanta, ba wai wani sashi ne ya bayyana a tare da ita ba, ko kaɗan, amma fa kayan sun yi wani irin zama a jikinta. Amma kuma tunani yake haka surar take ko kuwa dai irin abin nan ne da ya ji ana kira da acuci maza? Sai da ta ɗan kai hannunta da ya sha lalle ta sosa goshinta kaɗan sannan ya tuna bai amsa gaisuwarta ba. Ɗauke idanun ya yi. "Barka dai, lafiya. Kin tashi lafiya?" Tambayar ta mata daɗi, ba ta zaci zai damu da sanin ya ta tashi ba. "Lafiya Alhamdulillah." Shiru ya ɗan biyo baya. "Ga abin kari, nan za'a kawo ko kuma a can za'a zuba?" Ya ɗan kalleta, ya kula kamar kallo ma bai ishe ta ba. Toh ba ta ga abin kallo a tattare da shi ba ne ko me? Ya yi wa kansa tambayar da ba shi da amsa. "No, can ɗin ma is ok." Ta miƙe ta juya ta fara tafiya ba tare da ta jira shi ba. Runtse idanu ta yi gaba daya kunya take ji, tafiyar ma yin ta kawai take duk da ta san ba ta wani ishe shi kallo ba amma sai ta ke ji kamar idanunsa na kanta. Kamar kuwa ta san haka ɗin ne. Ya bi bayanta da kallo a hankali tun daga kan jelolin kitsonta da suka bayyana ta saman ɗankwalin da bai kammala rufuwa ba har zuwa yadda ta ke tafe bayanta na wani juyi kamar da gayya. Ya kauda kai ya shafi goshinsa. 'It's all fake.' Ya faɗi a ƙasan ransa kafin kuma ya ja istigfari da sauri na yanke hukuncin abin da bai sani ba, kuma ma ya ga mene ne amfanin sa mata ido har haka? Ya miƙe ya soma takawa har ya ƙarasa inda Sadiya ke tsaye ta dai ɗauki kofi amma kuma ta rasa ya za ta yi tunda ba ta san me da me yake ci ba. Zama ya yi saman kujera daidai inda ta ke a tsaye, ta kuwa ja baya kadan. Daga yanayinta ya karanci duk ta diririce ƙila ta rasa me za ta yi ne. Don haka ya ce, "Haɗa min tea ba madara." "Toh." Ta amsa, ta zuba sugar na ɗaya, na biyu ya ɗan dakatar da ita daga ɗiban na uku ta hanyar ɗan ɗaga hannunsa. Ta rufe ta ajiye, ita jikinta har wani rawa yake ma tsabar rashin sabo da kuma tsoron kar ta yi ba daidai ba. Ta janyo faranti ta zuba mishi suyar da aka yi haɗe da sauce ɗin hanta a gefe sai ta ga bai ce uffan ba, ta sanya fork a gefe ta ajiye. Farfesun ma da ta zuba a bowl ba ta ji ya ce wani abu ba. Tana kammalawa ta ji ya yi magana. "Nagode." Sai da ta ɗan yi murmushi, ashe bai da girman kan da ta ke yawan kallonsa da shi. Falo ta ƙarasa ta zauna a kujerar da ta ba dinning area din baya. Wayarta ta shiga latsawa kawai tana kallon hotunan status, anan ne ta ga Husna ta mata magana ta saƙon whatsapp. Ta buɗe, tun ma asuba ne. "My sis, i am so sorry nikam na so na shigo mu yi sallama amma hakan ba zai samu ba. Antinmu ta hana wai za mu saka ki kuka. Flight ɗaya zamu hau da Antin da Antina, zan kira ki idan mun isa lafiya. Allah ya albarkaci rayuwar aurenki. Ameen. " Ta yi murmushi, nan ta shiga ba ta amsa kafin ta fito. Kamar daga sama ta ga saƙon Nudrat wanda bai kai ko mintuna uku da shigowa ba. Ta kuwa buɗe da sauri don babu ranar da tunaninta ba ya faɗo mata a rai. "Hi my besty, ya kike? Koda dai nasan ki na lafiya, kin ji ni shiru ko? Kunya Sadiya, kunyar abin da Hammana ya maki na ke ji, na kasa zuwa inda kike, na kuma kasa taɓo ki a waya. Sai na ke jin kamar kowa zai min kallon munafuka, za'a ga kamar na san komai saboda irin kusancinmu da shi. Sadiya na rantse babu abin da na sani a abin da ya faru. Abin da ya sa ma Nene kasa zuwa gidanku kenan sai a jiya suka je da yan uwa aka ba da haƙuri. Nene ta shiga damuwa ƙwarai don har kwanciya rashin lafiya ta ɗan yi. Amma Alhamdulillah, sai kika ga kunya da tozarcin da Hamma ya so ya yi mana gaba daya, Allah bai nufe shi da aikatawa ba. Sai ki ka samu wanda ya fi shi." Sadiya ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ɗan juya kai ta dubi Maina, idanunsa ba ya kanta yana amsa waya kamar kuma da Fulani inda yake kawai ambaton Allah ya huci zuciyarta, ba ta ma son jin me suke tattaunawa don haka ta maida kai ta tafi saƙo na biyu da Nudrat ta aiko cikin guda uku. "Ibraheem Tafida, kar ki ga ina cewa na tsani halayyarsa, wallahi Triple kin yi dace. Ni kin fi kowa sanin na fi son mutum mai sakewa da shiga lamurana, idan muna da kusanci da kai amma kana nuna seniority a komai to fa haushinka ya zame min dole. Haka ɗabi'ata take. Amma a ture wannan, zan ba ki kyakkyawar shaida akan Maina wanda kowa ke yabonsa a zuri'armu. Kyauta, kyautatawa da girmama ɗan adam, ba ya raina su, ban kuma taɓa jin ya wulaƙanta wani ba. Shi dai haka halayyarsa ta ke, ba ya shiga sabgar mutane. Ya fi ganewa wasu lokutan ya yi rayuwa da waɗanda suke shiga sabgarsa kuma ya aminta da su ɗari bisa ɗari. Na san da haka saboda amintarsu da Hamma. Ɓata baki ne idan na ce maki ya haɗa dukkan abin da mace ke son mijinta da shi tunda kin shaida wasu, ya fi Hamma kyau, aji, ilimi, kuɗi, nasaba mai kyau, uwa uba kuma gudun ɓacin ran iyaye." Sadiya ta numfasa, meyasa kowa ke son nuna mata Mainan nan mai kyau ne wai? Ita fa koda zai shiga ranta ba ta fatan ta so shi saboda kyawun nasa, fatanta Allah yasa yana da halaye masu kyau. Koda dai ko a yanzun da yake lallaɓa Fulaninsa ai ya ci ace ta gane yana bin iyayen. Ta ƙarasa zuwa saƙo na ƙarshe da Nudrat ta turo. "Humm, ba ina zuzuta Maina don ki ji a ranki ya fi Hamma saboda son kawar da laifinsa a zuciyarki ba, a'a Triple. Ina mai ba ki tabbacin za ki ga zahirin abin da nake faɗamaki idan ku na tare. Ina maki addu'a da fatan alheri, ina roƙon Allah ya haɗa kawunanku. Ya sanya wa Maina so da kaunarki a zuciya, ke ma kuma ya sa ki ƙaunace shi fiye da dukkan wani ɗa namiji da ki ka taɓa so a rayuwarki. Ameen. A ƙarshe ina ƙara neman gafararki." Ta numfasa tana dannawa saƙon sitika na Love. Kafin ta ɗan juya kaɗan ta kai duba ga Maina, wannan karon karaf suka haɗa idanu yana shirin kai kofin ruwa bakinsa, da sauri ta juya kanta tana ɗan runtse idanu irin na ta kwafsa. Sai ta kasa ma bai wa Nudrat amsa a lokacin, hakan ya sa ta fita gaba ɗaya a whatsapp din ta ma ajiye wayar a gefen kujera. Tana nan zaune ta ji takunsa zuwa tsakar falon. Wannan karon ba ta yi karambani ɗago kai ba balle su haɗa idanu. Shi kuwa ya ɗan dakata ya dube ta sosai ya ce. "Ki na buƙatar wani abu?" Kai ta girgiza kafin a hankali ta amsa. "A'a." Shiru ya ɗan biyo baya, can kuma ta ji ya ce. "Ok, sai na dawo." "Allah ya tsare ya kiyaye hanya." Leɓɓansa suka motsa a hankali ya ce ameen sannan ya soma tafiya. Ta bi bayansa da kallo tana ɗan murmushi har ya fice. Ita ba ta ɗauka za ta same shi da sauƙin kai har haka ba, ta fi zaton yana da mugun girman kai da wulaƙanci. Amma abin mamaki shi ke amsa gaisuwa, addu'a da ma maganarta. Tana roƙon Allah ya sanya mata soyayyarsa a zuciya kamar yadda masoyanta ke taya ta roƙo, ita ma kuma ta ƙaunace shi su zauna lafiya tunda shi ne zaɓin da Allah ya yi mata. Ta tattara komai ta kai kicin, ta wanke waɗanda aka ɓata, sauran abincin ta bar su da zummar idan an zo tafiya da kwanukan sai su ɗauka. Ba ta jima da komawa falon ba aka shiga ƙwanƙwasawa. Koda ta buɗe ta yi arba da wasu ƴanmata su biyar. Wacce ta fara tozali da ita, kallon sama da ƙasa ta shiga bin ta da shi ta a taunar cingam. Sadiya ta ba su wuri suka shigo fuskarta ɗauke da ɗan murmushi. "Sannunku da zuwa." Ta furta. Ta san dai wasu sun amsa amma ba ta tunanin dukkansu. Suka ƙarasa shigowa suka zauna a falon. Wacce ta fi sauran gaba ɗaya sakin fuska ta cikinsu ce ta fara magana. "Barka da safiya Anti Sadiya." Da haka sauran ma suka gaishe ta, ta kula wannan mai taunar cingam din sai da mai maganar ta farko ta ɗan zungure ta sannan ba tare da ta dube ta ba ita ma ta gaida ta. Ta amsa musu kuwa ta mike ta kawo musu ruwa da lemu a saman tray. "Anti da kin bar shi ma, daga gida muka fito. Amma mun gode." "Babu komai." Ta ƙara ba ta amsa. "Ni suna na Hindatu, sai wannan (ta nuna wata ƴar baƙa mai ɗan ƙaramin jiki) sunanta Mabruka, sai wannan (ta nuna baƙar cikinsu gaba ɗaya don dukkansu farare ne ƙal) sunanta Nasiba. Wannan kuwa Ummulkhair autarmu. Wannan kuma (ta yi nuni da mai taunar cingam da harare-harare) ita ce Najma. Dukkanmu ƙannen Maina ne." Sadiya ta ƙara yi musu kallon tsaf tana ƙara faɗaɗa murmushinta. Dama daga ganin Hindatun ka san cewa yar uwa ce ga Maina don za ta iya cewa ma kaf cikinsu babu wanda ta ga sun yi kama da shi kamarta. Ƙila kuma kammanin Mai Martaba ne ba lallai sun haɗa ɗaki ba don ta ji Anti Hafsatu ta ce mahaifiyar Maina mace ɗaya ce a gabanta ba ta aurar ba. "Masha Allah, nice to meet you all sisters." Ta faɗi suka amsa da godiya da maida martani, Najma ta ja guntun tsaki kafin ta ce. "Wai ku ba za ku tashi mu wuce ba? Oh, ashe ba mu ga gida sosai ba jiya, bari mu shiga." Daga haka ta miƙe, Sadiya na kallonta ta soma shiga ɗakuna, ba ta ce uffan ba. "Kai Najma wai mene ne haka?" Cewar Hindatu tana harararta bayan ta fito daga ƙuryar ɗakin Sadiya cike da jin haushin babu wani abin ƙazantar da Sadiya ta bari don so ta yi ta ga wani abu na ba daidai ba ta dara. "To mene ne laifi? Dama gidan Amarya ba ko'ina ake shiga ba?" Ummulkhair ta amsawa Hindatu cike da tsiwa. "Za ki rufe mana baki ko sai na gurje shi yanzu? Ku tashi ma tafiya zamu yi ai Mai babban ɗaki ma ta ce kar mu daɗe." Faɗin Mabruka wacce suke sa'anni da Najma, duka sun girme musu. Ita dai ba ta ce musu komai ba, idanunta ya kai ga Najma da ke ƙoƙarin zuge gilashin bene wai za ta hau. Anan ne kuma ta miƙe ta ƙarasa. "Ki yi hakuri, za ki iya shiga ko'ina na gidan nan ki kalli abin da ba ki gani ba, amma ban da nan." Mamaki tsantsa ya bayyana saman fuskar Najma. Ranta kuma ya ɓaci har wani huci ta shiga yi. Sadiya ta kauda kai daga dubanta gami da jan gilashin ya rufe ruf sannan ta koma mazauninta. "To ni kuma sai na shiga na ga me za ki yi." "Najma wallahi ke da Maina, kuma sai na faɗawa Mai babban ɗaki muddin ki ka buɗe. Ba tun jiya an faɗamana ɓangaren Maina ba ne?" Faɗin Hindatu a zafafe. Najma ta fasa ta yi ƙwafa, haushin Sadiya ta ji ya ninka na farko a ranta. Tana mata kallon kamar wata wawiya ashe da wayonta. "Sai ki je ki yi ta faɗa uwar sharri. Mts." Daga haka ta yi gaba ta zura takalmanta ta fice har tana ƙoƙarin buge Hindu da isowarsu kenan bakin ƙofar tare da bayi har huɗu suna shirin ƙwanƙwasawa. "To ita kuwa lafiyarta?" Hindu ta faɗi tana bin ta da kallo kafin ta girgiza kai kawai ta yi sallama zuwa ciki bayan an amsa. Nan da nan su Mabruka suka yi wa Sadiya sallama. Ita ko ta gaisa da Hindu, bayin su ma suka gaida ta. "Ranki ya daɗe, waɗannan hadimai ne daga Mai babban ɗaki. Ga Zuwaira, Karima, Bintu da Jamila. Bintu aikinta shi ne girki, Karima kuwa kula da ɓangarenki, Zuwaira za ta dinga taimaka maki da gyaran ɓangaren Maina. Ita kuwa Jamila an ba ki ita ne saboda kula da dukkan abin da zasu yi, sai ko taya ki hira." Ta ji abin sam bai mata ba, toh ita zaman me take? Kawai ta ci ta miƙe ƙafafu? 'Duk gatan da za su nuna maki, kar ki sake kwanon mijinki ya fita a hannunki, haka nan ɓangarensa. Ki zama ke za ki dinga ba shi dukkan wasu kulawa. Komai nasa ya kasance ke ce za ki yi da kanki ba wata baiwar ba. Hakan zai ƙara maki ƙima da kankaro mutuncinki a wajensa.' Maganganun Anti Hafsatu suka faɗo mata a rai. Shirunta ya sa Hindu dubanta dakyau. "Gimbiya Sadiya ko ba su yi maki ba ne a sauya maki da wasu?" Ta girgiza kai da sauri. "A'a Baba Hindu, ba haka ba ne. A taya ni miƙa godiya ga Mai babban ɗaki, a ce kuma na yaba da kyautarta gare ni. Sai dai ina neman alfarma su zama mutum biyu kawai madadin huɗu idan har babu damuwa." 'Baba Hindu', wannan sunan da Sadiya ta kira ta da shi ya faranta mata rai sosai, girma ne da za ta iya rantsuwa bayan Maina da Saudatu babu masu ba ta shi a gidan. Maina kan kira ta da Inna ko kuma Innar Jibril, yayinda Gimbiya Saudatu ita ma ke kiranta Inna. Sai ko yanzun da Sadiya ta raɗa mata suna duka don darajta tsufanta. Murmushi ta yi, ta yaba sosai da hankalinta, dama a yadda ta ke kallon yarinyar, ba ta da matsala sam. Ta fahimci ga dukkan alamu ba ta son wasu bayi su yi ta mata hidima, kuma ya dace a ba ta wuri su shaƙu da mijinta kafin duka wannan. "Shikenan zan isar da saƙonki Gimbiya. Suna iya kwashe kwanukan safe?" Sadiya ta gyaɗa kai tana murmushin ita ma. "Eh. Nagode." Su kansu bayin sun ji dadi, yarinya ƙarama amma akwai alamun tana da hankali. Bintu da Karima suka shige kicin ɗin bisa umarnin Hindu suka fara fiddo kwanukan suna ɗorawa a kwandon da aka kawo ɗazu. Tunawa da kajin dake a firij yasa ta miƙewa, ta fiddo ta miƙa musu ta ce su yi amfani da shi. Nan suka shiga godiya. Bayan tafiyarsu tunanin gyara ɓangaren Maina ya zo kanta amma kuma tana jin fargabar kar ta yi mishi ba daidai ba, kar ya zo ya kushe. Ƙarshe dai ta bi shawarar zuciyarta a kan ta hau ta gyara masa. Nan ta zuge gilashin tana tuna diramarsu da yarinyar da ta aka kira da Najma, ba ta san matsayin yarinyar ba a wajen Maina, amma ta karanci tsanarta a fuskarta. Koda dai har wacce ta ji sun kira da auta wato Ummulkhair alamu sun nuna itama ba ta wani marhaba da ita. Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon gefen bangon, wani ƙaton madubi ne mai adon silver a gefensa har da wata fulawa ta ado. Ta cigaba da takawa har ta ƙarasa falon farko da ke saman. "Ya Allah." Ta yi furucin a fili, ashe ita ba komai ta gani a wajenta ba. Nan ɗin ƙamshin ma na daban ne. Madadin faluka guda biyu, shi nasa guda ɗaya ne mai girma sosai. Ta sani ba za ta iya ƙiyasta kuɗaɗen da aka narka a falon ba, don ko ba a faɗa ba an san komai na ciki zai yi tsada. Shi komai fari da baƙi ne a falon, hatta da tayils ɗin farare ne tas. Labulayen ma adon fari da baƙi ne. Wurin tsaf ta iske shi. Ta buɗe wata ƙofa, babu komai a ciki sai kayayyakin motsa jiki, ta ja ta rufe. Ta can gaba kuwa study room ne. Nan ma komai a tsaftace. Rufewa ta yi. Sai da ta bi wani ɗan ƙaramin corridor, nan ne ta ga ƙofa na kallonta, ta murɗa a sannu ta buɗe. Daga yanayin ɗakin ta gane nan ne ɗakin baccinsa. Gadon duk a hargitse, hatta da kayansa da ya cire a saman wata ƴar kujera ya bar su. Ɗakinsa shi ma yana da girma irin nata, shi gadonsa wani mai zagaye ne a dunƙule. Ta soma tunani anya mutum biyu za su iya rayuwa a kansa? "Bari dai na gwada." Aikuwa ta faɗa gadon ta kwanta a gefe, sai ta ga akwai fili sosai da mutum biyu ma zasu iya kwanciya ba tare da sun matsu ba. Daddaɗan ƙamshin turarensa ta shaƙa a jikin filon da ma bargon, da sauri ta miƙe tana tsoron kar ƙamshin ya mamaye jikinta har a ƙarshe ya gane ta shigar masa ɗaki. Nan ta watsar da komai ta hau aikin da ta shigo dominsa. Hatta banɗakin ya burgeta, nan ma ta wanke shi tas ta sanya turare. Ta fito ta dawo falon, duk da bai yi wani datti ba sai da ta goge. Ta ga har wata baranda yake da ita har da kujeru ya saka sai a gefe shukoki ƙanana guda biyu a tukunyar ƙasa. Idan kana tsaye kana iya hango har hasumiyar masallacin Mai Martaba wanda ya ɗan yi nesa kaɗan da gidan nasu. Hatta da filin gidan da ma mai shigowa ko fita kana iya gani. Wurin ya burge ta sosai, ganin bai yi ƙura ba sai ta tattara ta dawo falon. Nan ma ta jona burner ɗin da ta gani ta zuba turaren wuta. Benen ma sai da Sadiya ta bi ta goge tas sannan ta rufe masa. *** Ina labarin Hajara?   KANO Fuska a turɓune Alh Nuhu ke bin Hajara da kallo, ita kuwa idanunta ta shiga wulƙawa a ɗakin kafin ta gane a asibiti take. Da wani sauri ta yi yunƙurin miƙewa ta ji an riƙe ta gam. Ta dube shi, kallon da yake watsa mata ya sa ta jin shakkarsa na shigar ta, ƙirjinta sai da ya buga da ƙarfi. "Me za ki yi idan kin miƙe? Umarnin likita ne ki kwanta ki sami hutu." Ta koma ta kwanta tana ɗan satar kallon mijin nata. Ya ɗan yi taku zuwa ƙofar ɗakin sannan ya juyo ya nuna ta da yatsa murya a kausashe ya ce. "Kar ki ƙara yin gangancin da ki ka yi a yau, wai shaye-shaye har ki yi overdose? Har ki rasa sadda za ki afa kayan mayenki saboda wata banzar damuwar da ki ka saka a ranki na auren ƙanwarki ki dinga sumbatun banza da wofi sai yanzu? Sai yanzun da kike ɗauke da gudan jinina? Toh na rantse maki ki ka yi kuskuren da cikin nan ya bi rariya ki saka a ranki a ranar zan sake ki. Ranar aurenmu zai ƙare! Ke ko mutuwa za ki yi a wurin haihuwa ni dai Nuhu ina buƙatar abin da za ki haifa min ya zo da rai! Don haka ki sani ina maki gargaɗi da babban murya kar ki ƙara gangancin wasa da lafiyarki muddin akwai ajiyata a jikinki! Idan kuwa kin ƙi ji toh ki shiryawa abin da zai biyo baya! Shashashar banza kawai! Mts!" Yana kai wa nan ya sa kai yana baza babbar riga ya fice daga ɗakin har da banko ƙofar. Hajara ta runtse idanunta don har a lokacin kanta bai bar sarawa ba. Ta tuna dai bayan shigowarta gidan a hankali tashe ta yi kuka ta kuma yi ihu, a ƙarshe ta fiddo ajiyarta na kayayyakin maye da Waleedah ta siyo mata ta shiga sha babu ƙaƙƙautawa har sai da ta daina gane me ake yi a duniyar. Sai yanzun da ta farka, ba ta san hawa da sauka ba amma kuma ta dai tsinci wani ɓangare na katoɓarar da ta yi ba a hayyaci ba daga maganganun mijin nata. Ajiyar zuciya kafin ta buɗe idanun, hawayenta suka kwaranyo saman fuska. Ta kai hannu saman mararta ta shafa. A dalilin Sadiya ta ke shirin yi wa kanta illah? Ina! Ba za ta ƙara gangancin shan wani abu da zai jaza mata fushin mijinta ba. Yanzu idan ya sake ta wa za ta kama? Ina take da ikon yin yadda ta so a gidan Malam? Za ta tattara lamarin Sadiya ta ajiye gefe guda tukunna amma fa ba don ta haƙura ba, sai don cikinta ya ɗan yi ƙwari. Ta dai kula da wulakantaccen kallon da wacce ake kira Fulani Kausar kuma mahaifiya ga Maina ke musu, ga dukkan alamu daga su har wacce suka kawo ba su samu karɓuwa ba a wajenta. Wani murmushi ne ya suɓuce mata duk kuwa da yanayin da take ciki. Fatanta Sadiya ta ɗanɗana baƙin ciki a hannun uwar miji. Shigowar Inna da wasu yan uwan Malam su huɗu da Baba Habu da su Yaya Hashimu ne ya katse tunaninta. Ta rantse har ba ta kaunar ganin Inna don sai ta ke ga kamar ma murmushi ne shimfiɗe a saman fuskarta. "Sannu Hajara, Allah ya ba ki lafiya. Ashe kuma tsautsayin da ya afku gareki kenan? Faɗuwa daga bene? To Allah ya tsare ya kiyaye. Sai ki dinga kula." Abin da ya fito daga bakin Baba Asabe kenan. Ta gane ya ɓoye musu ainahin abin da ta aikata, hakan ya mata dadi. Nan kowa ya shiga jajanta mata, a ƙarshe dai wata ma'aikaciyar asibitin ta ce su taimaka su tafi saboda ba a son ta da hayaniya. Haka suka bar ta don asibitin akwai masu jinya ita ma ta fi buƙatar hakan. Daƙyar ta iya cusa abinci  kafin daga bisani bacci ya ƙara awon gaba da ita cike da mafarkin Sadiya da irin matsayin da ta taka a yanzun. *** Nene ce zaune ta zuba uban tagumi ta yi shiru gaba ɗaya zuciyarta a jagule. Ta share hawayen dake saman fuskarta ya fi sau a ƙirga sai dai ba su rabu da zuba ba. "Haj Aziza." Ta ji muryar Baffa a kusa da ita, ko kusa ba ta ji sadda ya shigo falon ba don haka ta ɗan razana kafin ta numfasa. "Sannu da zuwa. Yanzu ka shigo?" Madadin ya ba ta amsa sai ya girgiza kai cike da takaici ya ce. "Haba Azizat, ki raba kanki da wannan koke-koken da ba zai maido hannun agogo baya ba, abin da fa ya faru ya riga ya afku. Da ace yaron nan ya damu da lamarinki kamar yanda ki ka damu da shi, toh da bai tsallake umarninmu ba har ma ya zaɓi wasu iyayen da suka fi mu ba. To muddin ki na son mu zauna lafiya da ke sai kin bi umarnin likita kin ragewa kanki damuwa a kan wanda bai san mutunci da ƙimarmu ba. Mun rasa Maryama yarinya mai tsananin biyayya ma mun haƙura balle wani AbdulMajid?" Nene ta ɗauke hawayenta. "Ka yi haƙuri. Duk yadda na so na kawar da tunaninsa na kasa ne. Ka yi min alfarmar kai zuciyarka nesa ka ƙara tuntuɓar iyayen yarinyar nan inda ɗanmu ya tafi da ɗiyarsu. Mu yi hakuri mu manta da abin da ya faru, ƙila dama ba matarsa ba ce Sadiya. Ƙila..." "Azizat mene ne haka ki ke yi? Idan kin rasa AbdulMajid ba ki da Muneeb da sauran yara?" Nene kawai sai ta fashe da kuka sosai, kwanakin nan gaba ɗaya kewar AbdulMajid take yi, duk da ta yi fushin amma tana ji har ta huce. Ita dai burinta ya dawo su dinga ganinsa.  Allah ne shaidarta, ta so Sadiya ta kuma ji zafin rashin aurenta da ɗan nata, sai dai tana gudun ta yi masa baki ya zo ya lalace ko kuma ya haɗu da bala'i iri-iri a rayuwa. A yanzu ba ta da addu'a sai nema masa gafarar Allah kan kada ya hukunta shi a kan ɓacin ran da ya haifar a zuƙatansu na fifita son zuciyarsa da watsi da haƙƙoƙinsu da ke rataye a wuyansa. Baffa ya yi ta lallaɓa ta da kuma yi mata alƙawarin zai bincika ya ji inda yake. Hakan ya ɗan nutsar da zuciyarta. *** GOMBE Fuskarta ɗaure ta ke bin sa da kallo kamar mai son karantar zuciyarsa. Ba ta iya gane komai ba don haka ta soma magana murya a kausashe. "Sai yanzu ka ga damar shigowa wurina Kakana? Me suka ba ka ka ci da yau ɗaya ka manta da kwanonka na wajena? Har akwai girkin da Saratu za ta sanya a naka da nawa hadiman ba su iya ba? Kuma ka rasa ina za ka yi zaman ci sai wajen matarka? Ni na rasa gane wannan lamari, auren na dole aka maka ko kuwa na so ne?" Maina da ke sauraron Fulani bai katse ta ba har ta kai aya, duk da ya ji babu daɗi a yawan munana zaton da ta ke yi ga abokan zamanta musamman Mai babban ɗaki amma kuma jin abin da ta ce a ƙarshe ya sa ya ɗan murmusa. Mamaki yake yi idan Fulanin na faɗin yana son Sadiya, kuma duk da ya sani babu hakan a ransa, amma kuma idan ta faɗi yana jin daɗin abin. Ba kuma don ya san dalili ba. "Allah ya huci zuciyarki." Ya ƙara furtawa bayan duka waɗanda ya yi ta faɗi sadda suka yi waya. Ta ja guntun tsaki. A hankali kuma ta sanya hannu ta ɗauko wata rufaffen kwanon sha na silba ta miƙa masa. "Maza shanye ka ba ni. Tsari ne na jiki don ban yarda da dangin matarnan taka ba. Ba kuma na son na ji komai. Umarni ne nake ba ka." Jikinsa duk a sanyaye ya sa hannu ya karɓa ya sha da bismillah. Yana kammalawa ya ajiye ya dube ta. "Zan shiga na gaishe da Mai Martaba." "Daga nan idan ka so ka shige ɗakunansu ma. Kuma ka saka a rai ba za ka dauwama da yarinyarsu ba muddin ni Kausar ina raye sai ka auri zaɓina ni ma." Ya ji kalaman kamar sukar kibiya, duk yadda ya ke kauda kai ba ya son yi wa Mahaifiyarsa zancen da zai sosa ranta sai da ya yi magana. "A tun farko kun sani ba ni da ra'ayin aure yanzu amma kuma don na samar maku da farin ciki, na baku zaɓin ku nemo min matar aure idan na ga tana da ɗabi'un da zan iya zaman aure da ita, zan amince. Ko sati bamu yi da maganar ba kuma wannan abu ya faru. Ummi ku saka a rai ita ce zaɓin da Allah ya yi min. Please kar ku ƙaƙaba min wani auren da ina ji  jikina ba zan tsinci komai a rayuwa da mace sama guda ɗaya ba face tarin zunubai." Nan da nan Fulani ta hau buga salati kafin kuma ta shiga girgiza kai tana huci. "Shikenan, ta faru ta ƙare. Tun ba a je ko'ina ba ka soma ji a jikinka za ka iya rayuwa da Sadiya kaɗai a duniyarka. Yaushe ne aka yi daren Ibraheem da har garinku ya waye? Ashe wayewar garin har ya ci ace an juyar min da kanka har haka? Toh na rantse maka sai ka ƙara aure ko ba nan kusa ba. Mu zuba ni da kai!" "Ki yi haƙuri." Maina ya ƙara nanatawa karo na ba adadi. Wani irin mutum ne da ba ya gajiya da ba wanda ya yi wa laifi haƙuri balle kuma wacce ta haife shi. Ya yi mata sallama ya miƙe ya fice ta bi bayansa da kallo. Wani ƙwafa ta yi. Wayarta ta ɗauka ta danna kira ba jimawa ya soma ƙara. "Fulanin Gombe, ranki ya daɗe. Fatan kina lafiya?" Abin da aka faɗi kenan. Fulani ta yamutse fuska. "Ina fa na ga lafiya Haj Falmata. Kwana ɗaya yaron nan ya yi da wannan ƴar talakawan amma har wuyansa ya yi kaurin da ina faɗa yana ba wa aurensa kariya?" "Uhum, ai ni na san irin waɗannan ba sa shigowa haka kawai. Ke ce tun farko ki ka tsaya jin ta bakinsa akan Zainab. Da tuni ba an wuce wajen ba. Da ace na taɓa haihuwa a duniyarnan babu abin da zai hana ni ɗaukar abin da na haifa mu aura masa. Ya fiye mana sau dubu akan auren nan da Mai Martaba ya yi masa." Jikin Fulani ya yi sanyi. Ta tuna kukan da Zainab ta kira ta na rusa mata a jiyan akan wanda bai san tana hauka a kansa ba don Maina ko kallo ba ta ishe shi ba. Asalima a wurinta take samun sukunin hira, amma shakkar Maina ya hana ta ma neme shi da zancen so. Ita ɗin ƙanwa ce ga Haj Falmata, dukkansu yaran Galadiman Katsina ne kuma Haj Falmata ta kasance aminiya ga Fulani tun zamanin ƙuruciya, ita Fulani ɗiya ce ga Sarkin Katsina. Ba ta da abokiyar shawarar da ta wuce Falmata, wasu gani suke yi ma kamar shakkarta take yi domin komai za ta yi sai ta jira ta ji ta bakinta. "Fulani ko kin sauka a kan layin ne? Na ji ki shiru. Yanzu me kika tsayar za ki yi a kai?" Maganar Falmata ya maido ta nutsuwarta, ta sauke ajiyar zuciya. "Ke zan yi wa tambayar Haj Falmata. Sai na ga kamar ma ya fara son yarinyar nan." Wata dariya Falmata ta sheƙe da ita kafin ta ce. "To asiri ai ba ƙarya ba ne, ke a tunaninki za su shigo gida irin wannan ba tare da babban shiri ba? Hum! Ai kalle su kawai. Idan ma kin ga ya so ta to fa ki shaida ba a cikin hayyacinsa yake ba. Yanzu dai ki kwantar da hankalinki, kar ki ƙara matsa mishi da batun aure. Idan ma matsi da takurar ce, ki dinga yi ga ita yarinyar. Shi kuwa ki bari sai nan gaba zamu ɓullo masa da zancen auren Zainab ta yadda ba zai ƙi bin umarninmu ba." Fulani ta jinjina kai. "Hakan ma shawara ce. To amma ta ya ya zan addabi rayuwarta? Ta wace hanya?" Tsaki Haj Falmata ta ja. "Ke fa daɗina da ke wani bin kamar 'yar fari, ki yi tunani sosai, ba za ki rasa wata hanyar ba. Kuma duk sadda ta zo wajenki, ki tabbata kin mata wulaƙancin da sai ta ji ta tsani rayuwar gidan." Fulani ta jinjina kai. "Hakan ya yi. Zan gwada ko zamu dace." Daga nan suka yi sallama. A gefen Haj Falmata dake zaune saman kujerar tangameman falonta ta yi wata dariyar mugunta kafin ta yi ƙwafa, a fili ta ke faɗin. "Ai Kausar sai na lalata maki dukkan wani nishaɗinki ke da yaranki, yadda na haddasa ƙiyayyar abokan zamanki a zuciyarki, haka zan saka ki tsani surukarki tsanar da har ɗanki sai ya fara bijirewa umarninki. Muje zuwa!" Zainab dake zaune a gefe cikin shiga ta riga da wando ta yarfo da gashinta saman kafaɗa ta dubi Haj Falmata idanunta cike taf da ƙwalla ta ce. "Amma Anti bakya tunanin cutar da Maina kamar cutar da ni ce? Na rantse maki dagaske nake sonsa, a ture ma ƙudurin da ki ke da shi na wai na mallake shi ta yadda zai gagari Fulani. Ina kaunarsa ne ba na jin zan iya..." "Ke! Rufe min baki ko na tashi na ɗauke fuskarki da mari! Shashasha! Wa yake ta wata soyayya? Ni wannan ƙudurina ne tun da jimawa sai na ga bayan dukkan wani abu da zai yi wa Fulani daɗi a duniya. Tana murnar ta haihu ta huta ko? Toh kuwa ba ta huta ba. Tun muna yara rayuwarta ta fifitu akan tawa, ubanta Sarki, nawa uban da yake matsayin yaya a wurin ubanta ya kasance a ƙarƙashin ikon ubanta. Kausar ta fi ni kyau da farin jinin jama'a! Ta zo ta fi ni dace da auren ɗan Sarki wanda a yanzu yake riƙe da kambun sarautar gaba ɗaya, na ƙare a auren wannan soloɓiyon Tafidan Bauchi wanda bai san komai ba sai boko ba kuma ya sha'awar mulkin sai wanda a ka ƙaƙaba masa a dole. Ta haihu, ta san daɗin haihuwa, ni kuwa ban san ko guda ba. Komai na rayuwarta tamkar ita ta tsarawa kanta, ki faɗa min toh Zainab, ta ya ya zan samu nutsuwar zuci?" Haj Falmata na kai wa nan ta hau share hawaye, ita ma Zainab na ta hawayen ta share, ba wai na tausayin 'yar uwarta kawai ba, a'a sai na ƙara hango bambancin da ke tsakanin nata manufar ta son auren Maina da kuma na 'yar uwarta. Ta rantse ba za ta cutar da shi ba muddin ya aure ta sai dai duk abin da Falmata za ta yi mata to ta ji ta gani ta kuma shirya mata. *** Misalin ƙarfe takwas da mintuna na dare motar Maina ta shigo gidansa. A lokacin Sadiya ta yi sabon wanka ta baɗaɗe gidan da turaren wuta yayin da ita kuwa ta yi wa kayanta turare na musamman da ma jikinta, ba ta yini ita kaɗai ba don Mai babban ɗaki ta karɓi roƙonta ta bar mata mata biyu, Karima za ta ɗan girme mata wacce aka ba ta domin girke-girke, sai ko Bintu da ba ta fi shekarunta ba, ita za ta dinga taimaka mata da gyaran sashenta. Ta saki jiki da su kwarai, girki kuwa abin da ya sa ba ta hana ba saboda bisa shawarar Anti Hafsatu ta jira ta koyi duk wani abu da ba ta sani ba, ta san me Maina ke ci da wanda ba ya ci. Sai dai yinin ranar kawai hira suka ɗan taɓa da su an riga da an kawo abinci daga can gidan. Bayan haka ma wasu a cikin ƴan uwan Maina sun shishshigo an gaisa da masu bin ta da kallo mai kama da harara, da kuma masu sakar mata fuska. Ita dai dukkansu ta karɓe su da shimfiɗar fuska. Ta ji sadda ya murɗa ƙofar falon na farko ya shigo, ta tsinci muryar wani bayan shi a nan ta fahimci ba shi kaɗai ba ne, sai ta ji kamar ta miƙe ta zura a guje. Kunya ta ke ji kada ya ce ta zaƙe da yawa tunda ga shi har ado ta ke masa. Ita kuwa a yanzu sosai ta kwantar da hankalinta ta haƙura da komai. Aka buɗe falon da take ciki aka shigo. Sallamarsa ce ta fara dira a dodon kunnuwanta kafin ta ɗaga idanu ta dube shi tana amsa sallamar. Ta sunkuyar da kai sadda suka haɗa idanu. Bayan ya ƙaraso ciki, ya rasa dalilin da ya tsayar da shi a falon har da neman wurin zama. Farko dai zai iya cewa ƙamshi, wani irin ƙamshi ke tashi mai daɗin gaske, sai ko kwalliyar da ya ga ta yi na doguwar rigar atamfa ya sha adon stones daga wuya. Niyyarsa kawai ya wuce ɓangarensa, idan an mishi tayin abinci ya ci, idan ko ba ta yi ba ya share. "Barka da zuwa." Muryarta ya katse shi. "Barka dai. Ya ki ka wuni?" Ta ɗan ɗago kai ta wulƙa gefensa kaɗan na tare da ta kalle shi ba, sai abin ya zo da wani salo kai ka ce da gayya ta yi. "Lafiya lau, na gode Allah." Ya gyaɗa kai. Sai kuma ya rasa me zai ce don haka ya miƙe ya nufi hanyar tafiya ɓangarensa. "Ko kana buƙatar abinci yanzu?" Ya ɗan dakata ba tare da ya juyo ba ya ba ta amsa. "Kina iya kawo min ɓangarena?" Sai da kirjinta ya ɗan ba da ras, sai kuma ta amsa da toh. Daga haka ta ga ya yi gaba abin sa. Ta miƙe ta ɗan zauna da nufin jinkirtawa kaɗan kafin kuma ta ƙarasa wajen teburin. Kicin ta shiga ta ɗauki ƙaton kwanduna biyu da aka sanyo fulasan abinci a ciki ta maida su ciki ta kama hanyar saman. Ba ta gan shi a falon ba, ta ajiye ta komo ƙasa ta tattaro farantao da duk abin buƙata. Haka ta dinga hawa da sauka tana nishi har ta kammala bai fito daga ɗaki ba. Jikinta ya ba ta wanka yake yi sai kawai ta zauna ta shiga danna wayarta. Status din wata ƙawarsu ta makaranta ta gani da ke murnar test din ranar ta yi mata daɗi. Zuciyarta ta ji tana neman tsinkewa sai kawai ta ajiye wayar, ita kam a ta sani ta yi bankwana da karatu. Babu wani ko wata da ya yi mata zancen, hakan ya ba ta tabbacin ba za'a bari ta yi ba. Ƙamshin turarukansa ne suka fara sauka a kofofin hancinta kafin ta kalle shi ta kuma sauke kai lokaci guda. Riga da wando ne na pyajamas a jikinsa baƙi da maroon colour sun karɓe shi ƙwarai. Waya yake amsawa yana zuba turanci kamar wani rainon Ingila. Ita ba ta taɓa ganin wanda turancinsa ke burgeta ba irin Maina duk da wannan ne karo na biyu da ta tsince shi yana wayar. Na farko sadda suke a Airport zasu taho garin, sai ko yau ɗin. A wayar ta gane kamar tafiya ma zai yi nan da sati biyu kamar yadda ya sanar da abokin wayar tasa da ya kira da suna Mr John. Ganin ya zauna ta buɗe flask din farko, cous-cous ne da ya aka dafa sai ƙaramin filas din na miyar kayan lambu da kaza. Ta shiga zuba wa a faranti, ta yi zubi huɗu za ta yi na biyar ya dakatar da ita lokacin ya kammala waya. "No kar ki ƙara, ya isa haka." Ta kuwa maida wanda ta ɗebo sannan ta zuba miyar ta saka cokali ta ajiye a saman centretable din dake gabansa. Hatta da ruwa da kunun ayar da aka kawo sai da ta ajiye masa. Gefe ta samu ta zauna cikinta na ƙugi amma tana jin nauyin cin abinci a kusa da shi ta gwammace idan ya kammala ta sauka ƙasan ta ci. "Kin ci abinci ne?" Tambayar ta zo mata a bazata, sai ta kasa cewa eh tunda ƙarya ba ya daga cikin ɗabi'unta, ba ta ma iya ba. "A'a." Ya ɗan ƙara kai idanunsa kanta, sai ya ji duk ta ba shi tausayi. Ita ma fa ba wai da son ranta aka yi auren nan ba, ya sani kuma har yanzun ba ta gama warkewa daga tabon da AbdulMajid ya bar mata a zuciya ba. Shi sai ya ji ma ba ta ba shi haushi, ya ƙudurta a rai zai kyautata zamantakewarsu koda kuwa wata mu'amalar aure ba zai gifta tsakaninsu ba. Zan ba ta kulawa kamar yadda zai yi ga ƙannensa. "Ɗauko plate ki ɗiba ki ci. Ki na wasa da lafiyarki ashe?" Sadiya ta ɗan ji abin banbarakwai, wannan kulawa har haka? Sai ta ɗan yi murmushin rashin sabo da hakan. Ba ta yi musu ba ta zuba a wani farantin ta soma ci a nan saman kafet ɗin tana kaffa-kaffa kada ta ɓata wurin. Shi kuwa bai ƙara kula maida hankali gareta ba, ya ci abincinsa sosai. Dama kaɗan ta zuba wa kanta don haka kusan a lokaci guda suka kammala. Tana cikin tattara kwanukan ne ta tsinci muryarsa. "Kin shigo nan ne bayan fita ta?" "Eh. Na shigo na gyara." Ta ga ya yi wani murmushin gefen kumatu da ya yi matuƙar yi mishi kyau. Ita ba ta taɓa ganinsa yana murmushi ba sai yanzu. A ɓangarensa kuwa tunani yake wai wannan ƴar yarinyar har ta san gyara ɓangaren miji, ya tuna a gabansa Hindu ke faɗawa Mai babban ɗaki saƙonta na ba ta buƙatar masu hidima da yawa, ciki kuwa wato har da na ɓangarensa kenan. Sai ya ji ta burge shi, yana son girmamawa, ko babu komai ta girmama abin da ya shafe shi. Amma kuma duk da haka so ya ke ya ji ta bakinta don haka ya ce. "Akwai masu hidimar da za su yi. Ki daina wahalar da kanki " Sadiya ta russuna kanta a ladabce kuma cikin sanyin murya ta ba shi amsa. "Ban ɗauki aikin lada ba matsayin wahalar da kai. Ni da kaina na nuna ba na son wata ta sanya min hannu a aikin da ya rataya a wuyana. In sha Allahu ba zai gagare ni ba a koyaushe muddin da lafiyata." Ya ƙara kallonta sosai yana nazarin kaifin kwakwalwa da tunani irin nata. 'Sadiya Sa'ad Shagari sunanta. Iyayenta asalinsu garin Kano, mahaifiyarta ƴar nan Gombe ce gidan marigayi Muhammadu Liman. An mata shaida mai kyau a unguwa, haka nan kowa ya shaida ba silarta ne aurenta ake fasawa ba. Kaddara ce. Tana karatu a jami'ar bayero a shekararta ta farko tana karantar Medicine.' Ya tuna kaɗan a cikin bayanan da Khamees ya ba sa nata, bayan binciken da ya sa a yi a mishi a kanta. "Dama ki na da niyyar barin makaranta bayan aure ne ko kuwa sanadin wannan ƙaddarar ce?" Tambayar ta zo mata a bazata hakan yasa da wani irin zumuɗi ta ɗago kai ta dube shi fuskarta ɗauke da murmushi sosai. Shi ma ya lula cikin tunanin dama ta fi kyau idan ta yi murmushi? Ita kuwa ta ma mance da komai a lokacin face hango tabbatuwar mafarkanta. "A'a dama akwai niyyar karatun. Amma saboda..." Sai ta kasa ƙarasawa ta sadda kai ƙasa tana wasa da siraran awarwaron da ke hannunta. Maina ya murmusa. "That means idan kin samu damar karatun za ki yi?" Sadiya ta ƙara kallonsa lokacin har wasu hawaye sun zubo mata na tsantsar farin ciki ta shiga gyaɗa mishi kai don ta ma rasa me za ta ce. Maina ya ji ta ƙara ba shi tausayi don haka ya tausasa murya. "Kar ki yi kuka. Ba na son kuka." Ta kuwa share hawayenta. "Toh." Ta furta kamar a shagwaɓe har sai da ya bi ta da wani kallo kaɗan. "Za ki yi karatu, sai dai ki yi haƙuri ba yanzu ba. Amma na miki alƙawarin za ki yi in sha Allah." Koda yace ba yanzu ba, ba ta ji zafi ba. Ko babu komai ai ya gama magana tunda ya saka Allah a lamarin. Kuma ya shayar da ita tsantsar mamaki. Dama ba a fidda rai da rahamar Allah. A sadda ta ke ganin kamar shikenan ta bar karatu, sai ga dama ta ƙara zuwar mata. "Nagode. Allah ya saka da alheri, ya ba da ikon cika alƙawari." Murmushi ya yi yana kai kofin kunun aya bakinsa. Sai da ya yi kurɓa uku sannan ya sauke kofin. "Bayan karatu ki na da wani burin?" Kai ita fa Sadiya sai mamaki Maina ya ke ba ta a daren. To ko dai dagaske su Nudrat suke da suke ta yabawa da ɗabi'unsa? Dama yana da magana? Sauƙin kai? Kulawa? Sai ta kasa cewa komai. "Na yi alƙawarin kula da ke, rashin sanayyar juna da bamu yi ba, ba zai sauya komai ba. Idan kin saka a ranki zaman ibada za ki yi da ni, ni kuma me zai sa na kasa ba ki kulawa? Ki ɗauke ni matsayin wani abokin shawara kuma ɗan uwa, ni ma zan riƙe ki tamkar yar uwa." Shi ne kuma ƙarshen maganar da ya yi mata a daren. Ta yi mishi godiya da addu'a, ganin ma ya shiga amsa waya ne ya sa ta miƙewa fuskarta a sake ta tattara kwanukan da komai cikin kwandon. A gefen Maina kuwa, wayar yake yi amma kuma hankalinsa na gare ta, shi kansa sai ya ji zuciyarsa ta sanyaya. Ko babu komai ya saka rai cikin farin ciki. Duk sadda zai kalle ta, ko tana ɗaure fuska ko kuwa yanayinta ya yi kama da mai ɗauke da tsantsar damuwa. Wannan ne karon farko da ya ga walwalarta, duk kuma akan ya yi mata zancen makaranta. Har ta fice ta kuma dawowa bai ajiye wayar da yake kai ba, ita kuwa tana son ta ce masa sai da safe gudun kar ta yi laifi ya ce an fasa karatun, amma kuma ganin wayar ba ta ƙare ba ce kawai sai ta fice. Koda ta shige ɗakinta bayan rufe ko'ina da kashe kayan wuta, wani juyi ta shiga yi tana ƙara hamdala ƙafin ƙarshe ta zauna saman ɗan kujera mai kamar gado dake gefe guda a ɗakin tana murmusawa. Ba don dare ya yi ba ai da ta kira Innarta da Anti Hafsatu ta ba su wannan albishir ɗin. Ta soma yarda Maina na da kirki, kamar dai ba yadda ta zace shi ba a farko. Ta kula kuma kamar shan ƙamshi da magana ƙasa-ƙasa ɗabi'arsa ce. Yana yi ne tamkar ba ya son yi. Wannan daren dai haka ta kwana zuciyarta wasai sai tunani da begen maganganun Maina, musamman da ya ce zai zauna da ita matsayin 'yar uwa. Ita ba ta ga wani aibu a hakan ba. *** Washegari kamar koyaushe a ka kawo musu abin kari. Har ta yi wankanta ta yi shiri cikin wani material mai baƙi da adon light green ɗin fulawoyi Maina bai sauko ba. Ƙarshe ma sai da ta gaji da jira ga yunwa da ke nuƙurƙusarta har ta yi zaman haɗawa kanta shayi don lokacin sha ɗaya saura. Zamanta kuwa ba jimawa sai ta ji motsin saukowarsa, kallonsa kawai ta ke ya yi wani irin kyau cikin shigar ƙananan kaya marasa nauyi. Ya ƙaraso ya ja kujera ya zauna. Sadiya ta ɗan russuna ta gaida shi. Ya amsa kafin da mamaki ya ce. "Me kike ba ki yi breakfast ba har yanzu?" Ta ɗan tsuke baki cike da ɗan jin kunya, haka kawai to sai ta ce shi ta ke jira alhalin babu dalilin jiran nasa? "Ban ji yunwa ba ne sai yanzun." "Ok." Abin da ya furta kenan. Kamar jiya ta haɗa masa komai sannan ita ma ta yi nata haɗin ta zauna a ɗarare ta shiga karyawa. Jifa-jifa sukan haɗa idanu ba ta gayya ba kuma lokaci guda su ɗauke kai. Ya riga ta tashi a wannan karon saboda yana da aikin da zai yi, meeting za su yi ta Zoom da wasu ƴan ƙasar waje duk a kan kamfaninsu na can. Har ya soma tafiya ya tsaya ya ɗan juyo. "Idan da hali ki jinkirta gyaran ɓangarena zuwa nan da ƙarfe ɗaya. Akwai aikin da zan yi mai muhimmanci ne." "Toh. Allah ya ba da nasara." Addu'arta ya sa ya juyo gaba ɗayansa har gangar jikin yana murmushi ya lumshe idanu kadan ya bude a kanta ya ce. "Ke ba kya rowar addu'a?" Ta yi murmushin ita ma da ɗan mamaki ta ce. "Rowar addu'a? Dama akwai masu yi?" Sai ya ɗan taɓe baki gami da ɗaga kafaɗa kaɗan amma kuma ya rasa amsar bayarwa don haka ya ce. "Ƙila." Daga nan kuma ya juya ya koma saman, ta bi shi da kallo tana dariya kaɗan. Ban da Maina to wa yake rowar addu'a, ita kam ba ta taɓa ji ba. Ta dai lura cewa kenan yana jin daɗin addu'arta kuma sai ta ji za ta ƙara daɗa ƙaimi wajen yi mishi a fili da ɓoye. "Ɗan ƙauye ya yi agogo." Furucin da ya fito daga bakin babbar baiwar Fulani kenan wato Sailuba sa'ilin da ta shigo falon Sadiya ta iske ta zaune tana shan haɗin fruitsalad a gefenta Bintu ce zaune ta maida hankali ga kallon shirin daɗin kowa a talabijin, sai ko Karima da ta buɗe musu ƙofar.  Sau ɗaya Sailuba ta taɓa shigowa sadda Gimbiya Saudatu ta zo amma hakan bai sa Sadiya ta gane ta ba, koda dai bai wuce na mamakin irin kallon banza da haɗe-haɗe ran da ta dinga yi mata ba a wancan shigowar kai ka ce ta fi ta matsayi a gidan. Wannan karon Sailuba tafe take da wata budurwa mai sanye da kayan da ta zuwa yanzun ta gane uniform din bayin gidan ne. Kamar ba su da sukunin sanya suturar da suka so sai ranakun juma'a. A yadda ta ji daga bakin su Karima da Bintu, har ranakun bukukuwa a gidan da kuma shagalin sallah suna iya sanya suturarsu kamar kowa.  "Sannu da zuwa." Cewar Sadiya tana mayar da cokali mai yatsun da ke a hannunta cikin bowl din da yake ajiye saman teburin gabanta.  Sailuba sai da ta ɗan yamutse fuska kafin ta gaishe da Sadiya kamar ba ta so.  "Barkanki da rana, an wuni lafiya? Dama mai girma Fulani ce ta turo ni." Abin da ta furta kai tsaye kenan ba ta ko ba da dama ga Sadiya ta amsa gaisuwar ba. Bintu da Karima suka ɗan kalli juna da mamakin Sailuba, koda dai ba yau suka san ita ɗin ba ta da kirki ba, su kansu a farkon zuwansu masarautar daga wadda aka ba da kyautarsu sun sha wahala a hannunta matsayinta na manyan bayi da suka jima a gidan kuma iyayensu da ma yara da jikoki duka suna nan.  Sadiya jin an ambaci surukarta sai ta ƙara maida hankali sosai ga Sailubar bayan ta dubi ƴar budurwar da ba ta fi shekarun Husnarsu ba. "Kyautar baiwa ta baki, tana da tabbacin ba za ki ƙi kyautarta ba. Sunanta Jidda. Idan ma babu gurbin wani abu da za ta yi maki, to bisa umarnin Fulani ta ce a maida ɗaya da cikin Karima da Bintu can ita kuma ta maye gurbin ɗaya." Abin ya yi wa Sadiya wani irin girma a kai, ta ji gaba ɗaya ranta babu daɗi. Wannan ai sai dai kai tsaye ya zama umarnin ba wai kyauta ba. Ta ɗan dubi Bintu da Karima waɗanda kansu ke ƙasa, jikinta ya yi sanyi. Ta fara sabo da su, suna da daɗin zama. Ga kuma ilimin da suka fara  ba ta na yadda lamuran masarautar ke gudana. Ta ji za ta karɓi Jidda saboda kiran da Sailuba ta yi mata da umarnin Fulani, amma ba don ta san taƙamaiman abin da za ta dinga yi ba. Ɓangaren mijinta ne dai har abada idan da rai da lafiya ba ta ga abin da zai sa ta ba da fuskar wata ta gyara ba.  "A cewa Fulani na karɓi kyautarta da girmamawa. Na kuma ji daɗi. Allah ya ƙara girma." Ta faɗi tana ɗan murmushi. Sailuba da har a sannan ranta a haɗe yake ta amsa.  "Zan isar da godiyarki. Na bar ku lafiya." Daga haka ta miƙe daga zaune da ta yi a saman kafet ta fice tana barin Jidda a nan zaune. Ita kuwa Sadiya ta kai duba ga  tafkeken agogon dake bangon ɗakin. Saura mintuna kaɗan ɗaya ta buga, wato dai Maina ya kusa kammala meeting ɗin da ya ke yi. Ta dubi Jidda, baƙa ce ga wasu billaye a gefen kuncinta duka biyun.  "Jidda." Ba tare da ta kalle ta ba ta ɗan ƙara ranƙwafa kai. "Na'am ranki ya daɗe." Girgiza kai Sadiya ta yi.  "Anti za ki dinga ce min kin ji ko? Ɗago ki kalle ni." Ta ɗago kai ta dube ta. "Ina fatan zamu yi zaman amana da ke?" Ta yi saurin maida kanta ƙasa ƙirjinta na lugude tana tuna babban maƙasudin kawo ta aiki a gidan. Amma a fili ta daure ta gyaɗa kai ta ce.  "Da yardar Allah ba za ki same ni me cin amanarki ba Anti. Zan zauna da ke zuciya ɗaya." Tana murmushi ta amsa da Allahu ya sa. Nan kuma ta gabatar mata da Karima da Bintu matsayin masu taimaka mata da wasu aikace-aikacen. Ta ce dai ta dinga taimaka musu da wasu ayyukan. Daga haka kuma ta miƙe a ɗan gaggauce ganin har ƙarfe ɗaya ta buga da mintuna, kamar jiya, haka ta yau ma ta ɗauki kayan abincinsa niƙi-niƙi har Karima na taimaka mata da zuge kofar gilashin hawa benen. Jidda ta bi ta da kallo. Ba ya falon amma kuma ga takardu a saman kujeru da tebur da tarkacen wayoyinsa da ma laptop. Ga dukkan alamu ma bai jima da shiga ɗakin ba. Ta ajiye tray ɗin a gefe, tana so ta tattara amma kuma sai take tunanin ko dai bai kammala da su ba, kawai sai ta nemi wuri ta zauna tana jira ya fito ta ji ko yanzu zai ci abinci.  Ba ta jima zaune ba sai ga shi. A farko kasancewar bai san da mutum ba sai da ya ɗan firgita amma kuma iyaka zuci ne bai nuna a fuskarsa ba.  "Barka da rana." Ta yi furucin cike da girmamawa. Bai amsa ba sai da ya shigo falon ya nemi wuri ya zauna yana ɗan kwantar da kai jikin kujera don ji ya yi duk ya gaji ga yunwa. "Barkanki dai. Me na samu?" Ya ƙarashe yana kai duba ga inda ta ajiye kayan abincin ɗin da ya hango. Daga yanayinsa ka san yunwa ya ke ji. Ta kuwa miƙe tana dubansa.  "Ina iya tattara takardun nan?" Kansa kawai ya gyaɗa yana ƙare mata kallo. Anya kuwa za'a kira surarta da ciko? Kai wannan ya bar yi masa kama da acuci. Ya kauda kai yana lumshe idanunsa cike da ɗan jin haushin kansa, to wai mene ne dalilin da zai dinga yi wa 'yar mutane kallon ƙurilla? Alhalin so ya ke kawai su saba su ɗan shaƙu ya zame mata kamar abokin shawara? Ya tuna wayar da AbdulMajid ya yi mishi a jiya bayan fitarsa, ƙin ɗagawa ya yi saboda bai ma san me zai ce masa ba. To kiran na mene ne bayan da ya gama aikata abin da ransa ke so? Idan ya ce ba ya kewar dan uwan nasa ma ya yi ƙarya, amma kuma har yanzu yana fushi da shi sosai kan wannan zalunci da ya yi ga 'yar mutane da ma watsawa iyayensu ƙasa a idanu.  Ya buɗe lumsassun idanunsa waɗanda gajiya da ma yunwa da bacci ke ɗawainiya da su ya na duban Sadiya ta nutsu wajen zuba masa shinƙafa da miyar kayan ciki.  Toh wai shi ya san Fareeda amma kuma idan har zatonsa akan Sadiya na ciko ya kasance ba haka ba ne, ya rantse bai ga abin da Fareeda za ta nuna mata ba. Ƙuruciya, hasken fata, dogon hanci, dara-daran idanu, leɓɓanta kamar da reza aka yanka 'yan... "Bismillah."  Muryarta ta katse shi daga tunanin da ya cilla, gaba ɗaya sai ya kauda kai yana ɗan shafa sumarsa cike da jin kunyar kamun da ta yi mishi kafin ya waske ya zauna sosai.  Ita kuwa Sadiya da rawar hannu ta kammala zuba masa abincin saboda ta saci kallonsa ya fi a ƙirga tana ganin idanunsa da ke mata matuƙar kwarjini a kanta, ƙirjinta ya cigaba da lugude. Ta kasa gane dalilin wannan kallon ƙurillar. Daƙyar ma ta iya samun damar mishi magana, ganin ya gyara zama ne ya sa ta ɗan miƙewa ta buɗe firij ɗin dake falon, gorar ruwa da lemu ta fiddo ta ajiye gami da ɗaukar kofi ta tsiyaya masa ruwan. Kasancewar hailarta ya zo ya sa ba ta yi yunƙurin tafiya gabatar da sallah ba sai ta soma kokarin shiga ɗakinsa da zumar gyara.    "Abinci fa?" Maina ya furta ba tare da ya dube ta ba wannan karon.  "Na sha fruitsalad ba na jin yunwa sai zuwa anjima." Bai ce komai ba ya yi bismillah ya fara cin abincin, ita ma ta yi wuf ta faɗa ɗakinsa, sai a lokacin ta sauke nannauyan ajiyar zuciya na samun nutsuwa. A hankali ta taka ta fara da kwashe kayan da ya cire ta saka a kwandon dake can gefe na kayan wanki. Undies ɗinsa kuwa ta tattare, tana tunanin ko ta wanke su ko kuma ta bar su? Duk da a huɗubar da yayyunta suka yi mata har da na wanke su tas. Amma kuma gudun wata fassarar daga Maina ya sa ta tattare su wuri guda ta ajiye bayan ta ninke. Ta fito ta ɗauki tsintsiyar laushi da makwashin shara ta koma har a sannan bai kammala ba, duk da ba ta ƙara kallonsa ba ta ji a jikinta dai kamar ya bi ta da kallo.  Sai da ta kammala gyaran ɗakin kafin ta faɗa wankin banɗaki bayan ta cire abin hannu da agogonta ta ajiye a gefen gado. Ta saba ko a gida idan za ta yi muddin siket ne a jikinta to fa sai ta ɗage shi sama har zuwa ya wuce gwuiwarta ko kuma ta cire shi ta ɗora zani idan ko ba haka ta yi ba to ba ta yi cikin daɗin rai. Don haka ta tattare siket din har ya haye gwuiwarta, tunaninta ai ba zai shigo ba tunda dai ya san tana ɗakin don haka hankalinta kwance ta shiga aiki. Cikin Jacuzzi ɗin ta shige ta hau wankewa da ruwan omo mai ƙamshi da ya sha hypo.  "Ba ki kamma..." Muryarsa ya sa ta razana garin ta juyo ta santsi ya kusa kwasarta da sauri ta kama makunnin shower ba ta ankara ba kuwa ruwan ya soma jiƙa ta tsabar ma tsoro ya sa ta kasa kashewa. Ba ta yi aune ba ta ji hannun Maina a saman ƙugunta, ya jawo ta da sauri kafin ya sanya hannu ya kashe shower ɗin. Inda ma Allah ya taƙaita mata na ruwan sanyi ne.  Idanunta a runtse ta kasa buɗewa sai da ta ji ya ɗaga ta cak ya fiddo ta daga cikin wajen kafin ta zaro duka idanunta tana kallonsa, shi kuwa bai ko dube ta ba har sai da ya dire ta a ƙofar banɗakin. Matsananciyar kunya ta saka ta sadda kanta a ƙasa tana gyara zaman siket dinta. Shi kuwa kauda kansa ya yi daga kallon ƙurillar da yake bin surarta da shi tun daga sama wanda ruwa ya jiƙa mata saman rigar ya yi kwanci luf a fatarta har zuwa santala-santalan ƙafafunta farare ƙal don har sun ma fi fuskarta hasken ya koma banɗakin ya ɗauko farin tawul wankakke a jikin towel hanger ya miƙa mata yana satar kallon zilin kitsonta da ya yi kwance luf a gadon bayanta sakamakon ɗankwalinta da ya zame ya fice sadda zai ɗauko ta.  "Ki na iya amfani da shi. Take care please." Ta sa hannu ta karɓa don godiyar ma ta kasa sai ƙirjinta da ke lugude. Ba ta ƙara sauraron komai ba ta shige banɗakin karo na biyu har da ɗan gudunta. Maina da ya ƙarasa wajen kayansa da nufin sauya tshirt ya juyo yana murmushi ya dubi hanyar da ta bi, wannan karon ma har da rufo banɗakin. Ɗan taɓe baki ya yi yana son kawar da abin da idanunsa suka gani na daga ƙirarta amma kuma ya kasa. Har ya sauya riga ya fice zuwa banɗakin falon don kama ruwa da ɗora alwala ba ta fito ba. Wayoyinsa ya ɗauka da muƙullin mota ya fice har a sannan murmurshi ke zuwar masa da zarar ya tuna Sadiya.  Ita kuwa sai da ta ji ficewarsa a ɗakin kafin ta ƙarasa da sauri gaban madubin dake a bangon banɗakin tana kallon jikinta, ƙirjinta daga sama a bayyane ga kuma ruwan da ya jiƙa mata rigar daga sama ta kwanta a jikinta. Haushin kanta ya kama ta, ta cije leɓɓanta, yanzun da wane idon za ta ƙara duban Maina? Ta ɗan dunguri kanta da yatsa kafin ta ja guntun tsaki, har ta juya ta kuma juyowa a hankali ta kai hannu ƙugunta, wai nan fa ya riƙe mata ko? 'Na shiga uku.' Ta furta a zuci, kamar lokacin ya faru, ta tuna ai har ɗaga ta ya yi cak ta kuwa yi saurin rufe fuskarta da tafukan hannayenta. Ranar dai haka ta ƙarasa gyarawa Maina wurare cikin tunanin ta yadda za ta yarda su haɗa idanu da shi kuma.  ***  Khamees ke zuba zance amma gogan kusan rabin hankalinsa ba ya gare su, da zarar ya tuna yanayin da a yau ya gani a Sadiya sai ya hau murmushi. Tun Khamees bai ankara ba har dai ya fahimci Maina ba ya tare da shi don haka ya ajiye laptop ɗin ya zuba mishi idanu. Ganin haka Maina ya kalle shi.  "An yi wani abu?"  Shi ma Khamees wannan karon murmushin ya yi.  "Kai zan tambaya ranka ya daɗe don na kula kamar an fito ne daga gida kawai amma zuciyar tana can." Nan da nan Maina ya ɗan sha mur yana waskewa da ɗan jan hanci kai ka ce mura ya ke yi.  "Shirme lokacin aiki?"  Khamees ya yi dariya.  "Kuma kamar ba daga gare ni hakan ya ɓullo ba ko?"  Ɗan guntun tsaki Maina ya ja yana ɗaukar wayarsa ya shiga dannawa.  "Ya batun tafiyar?" "Tana nan. Sai dai ni bana jin zan je saboda motocin da za su iso daga Lagos, zan jira. Dama an fi buƙatarka a can ɗin. Zai fi kyau ku tafi tare." Cikin rashin fahimta Maina ya dube shi dakyau ba tare da ya ce komai ba, Khamees kuma ya riga da ya fahimci ƙarin bayani yake nema.  "I mean tare da Madam ɗinka." Shiru ne ya biyo baya, toh akan me zai je da ita? Me za ta yi a can shi da aiki ne zai kai shi? Sai ya haɗe rai don kar Khamees ya cigaba da zancen.  "Ba wasa zai kai ni ba. Ka fi kowa sanin ba na haɗa aikina da komai." Jinjina kai Khamees ya yi yana murmushi, kamar kuma ba zai ce komai ba sai ya ce.  "Hakane, ba lallai kuma tana da passport ba, nan ma zai iya janyo a ɓata lokaci." Ya ƙarashe yana danne dariyar da ke cin sa, ya san tayin ya yi wa Maina kwarai, amma kuma bai gama yarda kamar ya fara son Sadiya ba alhalin alamu sun fara nunawa musamman ga shi da ya san waye Mainan tun ƙuruciya.  Shi kuwa Maina ya kasa cewa uffan ma sai danna wayar dole, bai taɓa tunanin kodai ya je da ita ba sai yanzun. Ƙila ma su saba da ita sosai. Kawai so yake ya ga suna tare ta sake da shi tana masa hira sosai.  ***  Fulani ke duban Jidda fuskarta ɗauke da zallar takaici.  "Ki ka ce ita ke gyara ɓangarensa da kanta?"  Jidda ta ƙara ƙasa da kanta a ladabce ta ce.  "Hakane ranki ya daɗe." "Makira! Wato ita bariki za ta gwada mana. Hum!" Shiru ya mamaye ɗakin, ita dai Jidda ƙirjinta sai lugude ya ke yi, ta san duk ranar da ba ta yi wa Fulani ba daidai ba kashinta ya bushe don ta rantse idan ta same ta da cin amanarta sai ta kashe ta kuma ta kashe banza tunda ita dai marainiya ce gaba da baya.  "Shikenan, ki cigaba da aikinki, ki kula da duk wani motsinta. Na tabbata sai mun kama ta da wani laifin mai muni." "An gama ranki ya daɗe. Zan bi umarninki zan kuma yi yadda ki ka ce." Fulani fuskarta a ɗaure ta mata alama da ta tashi ta bar wajen. Sailuba dake gefe ta dubi Jidda.  "Tashi ki je an sallame ki."  Jiki na rawa Jidda ta miƙe bayan ta zuba uban godiya kai ka ce kyautar wani zinaren aka yi mata.  "Sailuba." "Na'am Fulanin Mai Martaba." Ta faɗi sunan da Fulani ta fi kaunar a kira ta da shi. "A cigaba da lura da takun yarinyar nan, kar ta kusa ta raɓi wasu bayin." "Ina kan yi zan kuma ƙara zage damtse. Ba za'a samu wata matsala ba." Fulani ta jinjina kai tana ɗan murmushi. Tana ji a jikinta Sadiya ba matar arziƙi ba ce musamman da ba ta kasance jinin sarauta ba. Jikinta yana ba ta ma za ta yi kokarin mallake Maina don haka za ta zuba idanu ta ga gudun ruwanta zuwa lokacin da zai auri zaɓinta.  *** Duk yadda ta so ta yi wa Maina ɓoyo saboda kunyar da ta ke ji idan ta tuna yadda ta kasance tsakaninsu hakan ya faskara saboda dole a daren ta kai masa abinci. Inda dai ta ji daɗi bai nuna wani abu ko a fuska ba sai dai yawan satar kallonta da yake ɗan yi jifa-jifa. Daƙyar ta iya cin lomar tuwo biyar saboda jin ta da take a takure. "Ki ƙara." Abin da ya furta kenan daga haka ya maida hankali ga cin nashi tuwon semovita miyar kuka da ya ji manshanu da nama. Ba ta yi musu ba ta ɗan ƙara sannan ta ƙara yunƙurin bari. "Ƙara." Ya ƙara nanatawa, ta yi narai-narai da fuska, cikin muryar shagwaɓar da ya zo mata ba da niyya ba ta ce. "Allah kuwa na ƙoshi." Sai da ya ɗan kalle ta, sai ta ji kunya ta sunkuyar da kai tana tunasar da kanta ba a gaban Innarta take ba. Ita ke matsawa sai ta ci abinci sosai wai kullum cikin a shafe kamar ba a sanya abinci a ciki. Shi kuwa sai da ya ji kamar ba ita ba, muryar ta ƙara yi mishi zaƙi a kunne. Yau kawai ya ji so yake su yi hira su ƙara fahimtar junansu, don haka koda shi ma ya kammala ya ga ta soma tattara wurin da zummar sauka ƙasa sai ya ce. "Idan kin kai ki zo, zamu yi magana." Ta ɗan kalle shi kafin ta amsa da toh. Tana saukowa ta ji shiru dama kuma ta san hakan ne zai kasance tunda sun yi sallama da su Bintu. Sai dai ganin Jidda zaune ya yi masifar ɗaure mata kai. Ita ma tana ganinta ta ɗan firgita, gaba ɗaya sai ta ji ta rasa na cewa saboda ba ta da hujjar zama alhalin dama ana yin sallar isha'i Sadiyar ke cewa su tafi. "Jidda, lafiya ba ki tafi ba?" Ta tambaya tana ɗan kula da yanayin yarinyar, dama kusan kullum idan ka gan ta kamar a firgice ma ta ke. Tun sadda ta zo kawai ba ta kwanta mata ba, babu ma kamar idan ta tuna labarin da su Dada da Anti Safiyya suka dinga yi kan tsaface-tsafacen wasu a gidan sarauta, kuma an gargaɗe ta a kan saurin yarda da mutane, su Bintu ma ta san irin hirar da take yi da su idan sun zauna balle kuma wacce ta fito daga ɓangaren surukarta da aka shaida ba ta yi marhaba da ita ba. Jidda ganin kwandon da ke riƙe a hannun Sadiya ta yi saurin sunkuyar da kai a ladabce ta ce. "Dama na ɗauka za'a wanke kwanukan ne Anti. Shi ne na dakata." Girgiza kai Sadiya ta yi kafin ta ce. "A'a ki bar shi ba buƙatar ki yi hakan, zan yi da kaina. Ki je kawai sai da safe. Nagode." Jidda har gumi ya tsastsafo a goshinta kamar ba fanka a falon. Ta yi mata sallama ta fice ta ja ƙofar. Tsaye ta yi a bakin barandar shiga wurin tana ta tunani, haka za ta tafi ba tare da ta kai wa waccan muguwar Sailubar gamsasshiyar amsa na inda Sadiya ke kwana? An ce ta saka idanu ko idan ta kammala ba Maina abinci shikenan ba ta komawa saman, amma kuma babu damar hakan tunda ba ta da hujjar zama alhalin matar gidan ta sallame ta. Ta fasa tafiyar don haka ta juya bayan ta kula babu idanun maza masu aikace-aikace a gidan, kai tsaye baya ta zagaya daidai wata barandar da aka ajiye shukoki a cikin tukwane guda biyu hagu da dama, sai ko dogon window da ke a rufe wanda akan iya buɗe shi a sha iska, Allah ya taimaketa labulen dake wurin shara-shara ne, duk da hanyar hawa benen ya yi lungu, amma kuma ƙofar kicin da ma na ɗakin Sadiya tarr ta ke iya hango su. *** Sadiya kuwa ƙarasawa ta yi kicin ta ajiye kayayyakin, a gaggauce ta juye abincin a kwanukan plastics ta sanya a firij sannan ta wanke komai ta kife su ta rufe. Har ta kashe fitilar kicin ta rufo ta nufi bene, sai ta dawo ta koma falon farko ta rufe ta kashe fitilun haka nan ƙofa ta biyu. A kan idanun Jidda ta yi hanyar da zai sada ta da benen ɓangaren Maina, ganin har fitilun falon ta kashe su kafin ta hau ya sa kawai Jidda ta kawo a can ɗin za ta kwana. Don haka ta sulale ta fice, ko babu komai tana ɗauke da labari duk da ba mai daɗi ne a wurin waɗanda za ta kai wa ba, amma ita me ruwanta tunda ta cika umarninsu na ranar. *** Ita kuwa Sadiya ta iske ba ya falon don haka ta nemi wuri ta zauna tana bin wayarsa da saƙo ya shigo da ido. Saman screen ɗin hotonsa ne sanye da kayansu na sarakai a saman doki, ya sanya baƙin gilashi da ya fiddo hasken fatarsa da kuma kyawunsa tsantsa. Ta kasa kauda idanu daga kallon hoton don sai ta ga kamar wani ado da ya shafi gidan sarauta bai taɓa yi wa wani kyau kamar Maina ba. Can kuma hasken ya ɗauke, ta sauke ajiyar zuciya ta na mai ɗan waigawa ta ga ko ya fito ma ya kama tana kalle shi, ganin babu kowa ya sa ta gyara zama ta nutsu. Can ya fito, ƙamshin turarukansa ta soma shaƙa kafin ya ƙaraso ya zauna, jallabiya ce fara ƙal a jikinsa irin mai santsin nan, hakan ya sa ta kwanta ta fiddo ainahin cikar halittar ƙirjinsa da ma tsawonsa mai tafiyar da hankulan mata da dama musamman ma'abota kallon haramun wato na ƙurilla. Sadda kanta ƙasa ta yi da sauri tana wasa da yatsun hannunta. "Afuwan, na bar ki ki na jira." Ya ƙarashe da kai hannu ya ɗau wayarsa, sai da ya duba saƙonnin da suka faɗo kafin ya sanya ta a silent mode ya zauna fuskanci Sadiya sosai, cikin muryarsa ƙasa-ƙasa ya soma magana. "Ba wani dogon zance ba ne, tafiya zan yi end of this week, on Sunday kenan in sha Allah. Zan iya yin wata guda kafin na dawo. Kar ki ga kamar na sanar da ke a ƙurarren lokaci, matso da tafiyar na yi dalilin ayyukan da nake da su masu muhimmanci a can." Shiru ya ɗan biyo baya yana dubanta amma bai iya ganin yanayin fuskar sosai ba kasancewar ta yi ƙasa da kanta. A ɓangaren Sadiya kuwa, ta lissafa ƙarshen satin ta ga ai jibi kenan ma zai wuce, ba ta san dalili ba sai hakan bai mata daɗi ba. Kuma har tsawon sati huɗu? Ita wa ta sani a duniyar masarautarnan ta su bayan shi ɗin? Maganarsa ta katse tunaninta. "Dalilin sanar da ke, idan an cire haƙƙoƙinki da ke rataye a wuyana, sai don na ɗan nusar da ke wani abu. Zan iya kiranki da baƙuwa a masarautarnan saboda ba ki san komai dangane da ita ba. Don haka please ba na son kowa ki ja shi a jiki, ina so ki kiyaye duk wanda za ki mu'amalanta. Sannan ba na son fita, komai da ki ke buƙata ki yi list ki ban zan sa a kawo maki. Fitarki koda za ki yi kar ya wuce idan an kwana biyu ki na iya shiga ki gaida su Mai babban ɗaki da mutan gida. Sai kuma..." Ya ɗan yi shiru yana sauke numfashi gami da shafa sumar kansa lokaci guda yana ɗan lumshe idanunsa kafin ya ce. "Surutu, ba na son surutu. Ba ki yi kama da mai buɗe sirrin mijinta ba, so please ki kiyaye. Na shiga ɗakinki ko ban shiga ba, wannan ya kasance tsakaninmu kin ji?" Ya ƙarashe da wata murya mai nuni da kewa da ma abubuwa marass ƙidayuwa da suka girmi fassarar kwakwalwarsa. Sadiya wacce ta kauda kai daga duban da ta ɗan ɗago a farko tana mishi, ta gyaɗa kai cike da jin nauyi. Bakinta da ya yi nauyi daƙyar ta yi ɗan gyaran murya yadda zai fita sosai maganarta ta ce. "Zan kiyaye dukkan abin da ka ce. Ina roƙon Allah ya ba da nasarar abin da za'a je nema, ya kuma tsare ya dawo da kai lafiya." Maina da ke dubanta, ya amsa da amin. Shirun da ta ji ya sa ta gane ya gama magana don haka a sanyaye ta ce. "Zan je na kwanta, Allah ya tashe mu lafiya." Daga nan ta miƙe. "Ɗakin Maina fa? Ba wuri ne da za ki iya miƙe ƙafa ki kwanta ba?" Ta juyo da sauri ta dube shi, shi ma lumsassun idanunsa suna kanta don haka da saurin ta ƙara kauda kai, sai gaba ɗaya ta daburce, wai Maina? Shi dsi ya ke so ta dawo nan da kwana? Ta ma rasa me za ta ce. "Idan har babu matsala, daga yanzu ba na son kwananki ke ɗaya a ƙasa kamar aljana. Gidan akwai faɗi, kuma ke amanar Mai Martaba ce." Ya ƙarashe da murmushin da ko ba ta kalle shi ba ta ji ɗan sautinsa. "Toh, zan je na dawo." Ta furta a hankali. Ta dai ji kamar ya amsa ko bai amsa ba, ita dai gaba ta yi. Ba ta samu damar jan numfashi mai kyau da furzarwa ba sai da ta sauka daga benen. A ɗakinta kuwa gefen gadon ta nemi wuri ta zauna tana cigaba da sauke ajiyar zuciya a kai a kai, ta dafe ƙirjinta da ke lugude. Tunani take yi ta je ko kuwa ta basar da shi ta yi kwanciyarta a nan? Daƙyar dai ta miƙe ta faɗa wanka ba don da yamma ba ta yi ba sai don tana gudun duk da ƙamshin da ke fita a jikinta kar kwanciya a gadon Maina ya sa ya ji wani wuri na tashi a jikinta. Ta san dai ba ya sonta don haka tana ji ba zai taɓa ta ba. Koda ta fito bayan shafe jikinta da turaruka iri-iri masu daɗi da sanyin ƙamshi, ta ɗauki rigarta mai kauri na bacci doguwa ta zura. Ta rufe kanta da hula. Sai kuma ta kasa fita a ɗakin tana tunani, kada fa ta bayar da kanta, daga kira kawai ace har ta tafi kamar jira take? 'Mijinki ne, ba ke kika nemi zuwa makwancinsa ba, shi ya nemi wannan alfamar, duk kuma abin da za ki yi ki tuna cewa sama yake da ke.' Wani sashi na zuciyarta ya tunasar da ita. Ta kuwa miƙe ta ɗauki wayarta ta kashe fitilu ta rufe ɗakin sannan ta koma saman. Yana falon zaune, ga dukkan alamu ita yake jira don haka tana zuwa ta ga ya miƙe ya nufi inda fitilun suke ya rage ya bar guda ɗaya marar haske sosai. "Bismillah." Ya furta a hankali, ba musu ta bi hanyar ɗakin da ya nuna ta yi gaba, ta kai duba da gadon, wani mulmulalle da shi wanda duk sadda ta zo gyarawa burge ta yake yi. Ta tuna sadda ta gwada kwanciya a kai, yau ga shi nan za ta yi kwanan ƴanci, irin wanda nema aka yi da ka zo. Haka suka kwanta kuma suka wayi gari ba tare da wani abu ya gifta tsakani ba, sai dai ga dukkansu, bacci ɓarawo ne ya sace su kawai. Kowannensu na jin baƙon lamari a jikinsa, sun saba kwana su ɗaya, yau kuma abin ya zame musu banbarakwai babu ma kamar Sadiya da gaba ɗaya ta takure jikinta. Da asubahi dai ta farka ne ta ga kanta a ƙirjin Maina, inda ta godewa Allah kuma ta riga shi miƙewa gaba ɗaya sai ta ji nauyin hakan. Ita fa dagaske takura mata zai yi ma idan ya matsa ta dawo kwana wajensa don jiyan ma daƙyar baccin ya ɗauke ta. Ƙarar alarm ɗin wayoyinsu lokaci guda ne ya farkar da Maina, ita kuma ta yi saurin kai hannu ta waske da ɗaukar wayarta tana kashewa. Maina da bacci ke cin idanunsa daƙyar ya riga ta miƙewa ya nufi banɗaki don kama ruwa da ɗauro alwala. A irin lokutan nan idan ya ji ya kasa tashi saboda bacci, yakan ji wani ɓangare na zuciyarsa na nusar da shi, mene ne ribar baccin da ba za'a tashi a bautawa Mahalicci ba? Wannan ke zaburar da shi koyaushe har ya yakice baccin ya miƙe. Ita kuwa fita ta yi zuwa ɗayan ɗakin nasa ta shiga banɗakin, koda ta dawo tuni ya fice zuwa masallaci don haka itama ta yi nafila kafin ta gabatar da sallah. Niyyarta ta zauna kamar koyaushe yin Azkar har sai rana ta fito, amma a zaunen ma ji ta yi gyangyaɗi na kama ta har tana mance me take karantawa dole ta sallame da zummar ta yi anjima ta koma bacci. *** Washegari ya ce ta shirya su shiga ta gaida su Fulani. Ta shirya kuwa tsaf cikin leshinta swiss light pink colour mai ratsin silver ya sha adon stones wanda da shi ya zo. Ta yafa mayafinta silver sai ko takalminta flat. Ta yi tsaf da ita, sadda ta fito ya dube ta sai da ya kasa ɗauke idanu kafin can kuma ya janye. Ɓangaren Mai babban ɗaki suka fara zuwa, duk wanda ya gan su sai ya zube ya hau gaisuwa, jama'ar gidan kowa ya cika da mamaki. To ko dama suna son juna ne tun a baya? Yanayinsu dai ba su yi kama da waɗanda aka wa dole ba. Haj Saratu fuskarta a sake ta ke dubansu har suka ƙaraso inda take zaune saman kujera, kusan a tare Maina da Sadiya suka zube suna gaida ta. Ta amsa musu tana tambayar Sadiya lafiyarta. "Alhamdulillah." Amsar da ta ba ta kenan. Sun zauna nan sun ɗan jima har wasu maza biyu suka shigo yayyun Maina yara ga Haj Saratu. Nan ma gaishe su Sadiya ta yi. Ba su wani jima ba suka shiga sauran sashe biyun na matan Mai Martaba kafin a ƙarshe su je na Fulani Kausar. Ba su iske ta a falo ba sai su Najma da Ummullhair, har da Hindatu da ba ta iske a ɓangaren Fulani Amarya ba wacce a yanzu Sadiya ta fahimci ita ce mahaifiyarta daga bakin su Karima da Bintu masu taya ta aiki. Ganinsu tare da Maina sai 'yanmatan da sun kai su biyar da wasu samarin su huɗu suna ta hira suka shiga taitayinsu. Nan kowa ya hau gaishe su. Maina da fuskarsa kamar ba ya wani abu wai dariya, ya ce. "Ban hana ku irin wannan cakuɗewar a dinga hirar shirme ba?" Kowa ya yi shiru an rasa mai bakin magana. Ya nemi wuri ya zauna, ita ma Sadiya ta zauna wani gefen daga saman kafet. Maina ya dai dube ta amma bai ce komai ba ya juya ya dubi Ummulkhairi bayan fitar samarin da ma su Hindatu da Nasiba. "Fulani fa?" Kafin Ummulkhairi ta amsa sai ga ta ta fito cikin shigarta na alfarma. Ta yi kyau sosai kai ka ce wani wurin za ta je sai dai ga duk wanda ya san Fulani Kausar an san mace ce mai gayu ga ta ba ta rabo da lalle. Duk sadda za ka ga yatsun nan akwai lalle a jikinsu. Fuskarta a sake hango ɗan nata mafi soyuwa a rai, ɗa namiji tilo da Allah ya mallaka mata, ko kusa ba ta kula da Sadiya ba sai bayan ta zauna, nan da nan ta haɗe rai. Sadiya ita ma ta yi ƙasa da kanta kirjinta na dukan tara-tara, daga yanayin kallon da ta ga Fulanin ta watsa mata ya sa ta ƙara fahimtar har a lokacin ba ta sami karɓuwa ba a wurinta. "Barka da safiya My Fulani. Fatan kun tashi lafiya?" Maina ya faɗi a ladabce yana murmushi kamar bai ga yanayin fuskar mahaifiyartasa ba. Duk a kan Sadiya da ba ta yi mata laifin komai ba sai na auren ɗanta. Fulani ta amsa ba kamar yadda ta saba ba da annuri da komai a samna fuska. Wannan karon laifin Sadiya ya shafe shi. "Barka da safiya." Faɗin Sadiya da sanyin muryarta. Wani banzan kallo Fulanin ta bi ta da shi duk da a banza saboda idanun Sadiya na bisa ƙafafun Fulanin, sai dai kawai kallo take amma hankalinta  da kunnuwanta su na ga Fulanin ta ji ko za ta amsa gaisuwar. Sai ma ta ji muryar Fulanin na faɗin. "Ban ce maka ba na buƙatar matarka a sashena ba?" Maina ya ji babu dadi, don haka a nutse ya dubi Ummulkhair da ke kokarin ajiye masa tray ɗauke da ruwa da lemu sai ko kofi guda biyu wanda a farko ɗaya ta bada umarni a saka amma tsoron faɗan Maina ya sa ta sa aka ɗauraye na biyun aka saka. "Ki kai Antinki ɗakinki." Ummulkhairi ta ji kamar ya watsa mata garwashi a zuciya, wai Antinta, ta ina ɗin? Ita fa tunda ta fahimci Anti Najma na sonsa ta ji inama ita ya aura ba wannan 'yar talakawar bayinsu ba. "Sadiya." Ta ɗago idanunta da suka ɗan cicciko da ƙwalla ta dube shi kafin ta sadda kai gudun kar ta ƙara janyowa kanta tsana a wurin Fulani  ace tana kallon mijinta. Murya na rawa ta amsa kiran da Maina ya yi mata. "Tashi ku je ɗakin Ummulkhairi." Ta amsa da toh sannan ta miƙe ba tare da ta ƙara gangancin kallon Fulani ba don tsoron kuma me za ta tsinta a saman fuskar karo na biyu. Ummulkhairi ta yi gaba tana turo baki, ita kuwa Sadiya tafiyar take yi amma a ɗar-ɗar, gani take yi kamar Fulanin tsawa za ta daka mata sai dai har suka shige ba ta ji ta ce uffan ba. Rai a ɓace Fulani ta dube shi, kafin ta yi magana ya riga ta da taushin murya ya ce. "Ki yi hakuri, don Allah kar ku dinga irin haka a gabanta. Ba girmanku ba ne. Ya dace ku girmama zaɓin Mai Martaba, ku ba ta dama ko yaya ne kafin ku yanke hukuncin tsanarta. Ina jin ciwon akwai wani abu da a rayuwata da na aikata wanda bai muku daɗi ba. Kar fa ku manta, ni ma bin umarnin Mai Martaba nake saboda ban isa kaucewa ba. Kuma ba na jin zan iya. Kamar yadda ku ka isa da ni, toh don Allah ku taya ni addu'ar sauke nauyin da Allah ya ɗora min." Jikin Fulani ya ɗan yi sanyi, duk abin da Maina ya ce ta sani iyakar abin da ke ransa ya faɗi, yana tsananin gudun ɓacin ranta, ba ya ƙaunar abin da zai sosa ranta. Ta sani dagasken yana cikin damuwar hakan. Toh ya za ta yi? Haj Falmata ta ƙara jaddada mata kar ta yarda ta ba da ƙofar da Sadiya za ta sake a gidan. Ba ma girmanta ba ne haɗa surukata da dangin matsiyata da ba su gaji sarauta ba. Duk sadda ta ji kamar ta bi shawarwarin manyan yaranta mata waɗanda ba su ɗauki auren Maina da wani muhimmanci ba, akan hakan ba wani abu ba ne tunda dai an yi wa iyayenta kyakkyawar shaida, da zarar ta yi magana da Haj Falmata sai ta ji zuciyarta ta ƙara tunzura da tsanar Sadiya. A gefe kuwa ɗiyarta ta biyu, Gimbiya Juwairiyya ce dake zama a Abuja mai auren wani ɗan majalisa ita ko garin ba ta shigo ba duk a sanadin tsanar labarin auren da ta yi don a cewarta Mai Martaba ya nuna ƙarara ya fi fifita farin cikin yaran Haj Saratu a kan nasu. "Amma dai ba tare da ita za ka tafi ba ko?" Maina ya girgiza kai. "A'a. Kun ce ba da yawunku ba." Ta sauke ajiyar zuciya. Wani tunani ne ya faɗo ranta, me zai hana ta saka Sadiya dawowa ɓangarenta da zama? A nan ne za ta ƙara gane take-taken yarinyar da ma inda ta dosa. Wata ɗaya dai ai duk wasu munanan ɗabi'unta za su fito fili. Hakan ya sa ta dubansa. "Ina so matarka ta dawo ɓangarena da zama har ka dawo." Ya kalle ta da sauri, har ransa ya sani ba haka kawai ta nemi hakan ba. Ya ji a jikinsa ƙuntatawa Sadiyar kawai za'a yi, toh amma kuma me zai ce? "Umarni fa na ba ka, ba shawara ba." "Toh." Abin da ya furta kenan kawai, ita kuwa ta ji ɗan sanyi a rai, ta ƙudurta a wata ɗayan da Sadiya za ta yi a gabanta sai ta gwammace inama ba ta yarda ta tako Gombe ba, balle a yi maganar shigowa masarautar da sunan matar ɗanta. A ɗakin kuwa, wata kujerar da ke gefe kawai Sadiya ta nemi ta zauna. Komai na ɗakin fari da pink ne har da wasu ɗirka ɗirkan teddies a saman gadon, ita kuwa Ummulkhair kai tsaye ta wuce gadon ta kishingiɗe ta na danna wayarta. A haka Najma ita ma ta shigo. Ganin Sadiya a gefe ya sa ta ɗaure fuska ta ma fasa gulmar da ta shigo yi natan, haushi ne ya cika ta sakamakon laɓen da ta yi wa Fulani da Maina ta ji a na batun zaman Sadiya a wajensu kafin dawowarsa daga tafiya. "Matar Yayana me ya ɓata min ranki?" Sadiya sai ta ɗago kai ta dubi Ummulkhairi duk kuwa da tana mamakin ya kasance wai da ita take. Sai kuma ta ga Najma saboda ba ta san ma ta sadda ta shigo ba ita ma ta shagala can a bai wa Zahra amsar saƙon da ta turo mata tana tambayar meye labari. Najmar sai da ta kalle ta suka haɗa idanu kafin tana wani murmushi ta kauda kai cike da jikin daɗin wannan suna da Ummulkhairi ke yawan kiranta da shi ta yi farr da idanu ta ce. "Ke ma dai Auta da zolaya ki ke, ni ce matar Yayan? Toh wanne ki ka ban a cikin yayyun naki?" Ummulkhairi ta yi dariya. "Ai ke ɗin babban goro ce don haka kuwa sai magogin ƙarfe. Ki saka a rai Maina na dawowa kamar an yi aurenku an gama ne. To wa muke da shi da ta fi ki?! Ai gado sai ɗan gado, kuma jinin sarauta ya fi ƙarfin zama da rayuwa da wata baiwa can ƙazama. Ke ce daidai Yayana. Allah dai ya kai mu lokacin." Suka yi dariya da cafkewa lokaci guda gami da shewa. Ta nuna kamar ba ta san suna yi ba amma kuma a ƙasan ranta maganar ta ɗan shige ta. Baiwa kuma ƙazama? To waye ba bawan ba? Ita kalmar ƙazamar ma ya fi baƙanta ranta. Da me mutanen nan suke taƙama ne haka? Kusan dai yinin da ta yi a wajen Fulani ba mai daɗi ba ne don ko kallo ba ta ishe ta ba, asalima bayan tafiyar Maina sanya ta aka yi fitowa daga ɗakin Ummulkhairi ta komo falon ta raɓe a gefe. Haka dai ba ta ishi mutanen falon kallo ba sai ma habaici da akan jefa mata kaɗan kaɗan, abinci ma Sadiya ba ta iya sakin jiki ta ci ba. Sai bayan sallar isha'i ne ma Fulani ta dube ta sadda suna zaune su biyu sai ko Sailuba da ke gefe. Su Najma waɗanda suka fita unguwa wai bikin wata ƙawarta a sannan ne suka dawo. A lokacin ne kuma Maina ya zo ta yi wa Fulani sallama suka fice gaida Mai Martaba. Sun iske shi zaune, bayan sun gaisa ya ke ƙara tambayar Sadiya lafiyarta yana murmushin ganinsu tare haka. Ta amsa a sanyaye. Sallama ta yi ta miƙe ta fita don ba su wuri. Koda Maina ya ƙara yi wa Mai Martaba batun tafiyarsa a washegari, sai da ya ɗan yi shiru sannan ya ce. "Sati huɗu bai yi yawan da ya kamata ka ɗauki matarka ba?" Ya kasa cewa uffan, ya ji har ransa inama hakan zai iya kasantuwa amma kuma ba ya son Fulani ta yi fushi da shi don haka a ladabce ya ba da uzurin ayyukan da yawa kuma ba lallai ne ya cika watan ba. "Allah ya sa albarka. Ita kuma zan yi wa Hajiyarku magana a samar mata wanda zai taya ta zama." "Allah ya taimake ku, wai da Mami ce ta nemi ta zauna a ɓangarenta har zuwa lokacin da zan dawo." Shiru ya yi bai ce uffan ba, ko a jiya sai da Fulani Kausar ɗin ta zo mishi da batun wai Maina ya ƙara aure ya nuna bai amince ba, anya babu ƙuntatawa a faɗin da ta yi cewa Sadiyar ta zauna a wajenta? Da kuma ya yi wani tunani sai ya yi ɗan murmushi da girgiza kai. "Hakan ma ya yi." Maina bai so ba, ya so ace Mahaifin nasa ya nuna ƙin amincewa da batun Maminsa, ya san shi kaɗai ne zai iya takawa Mamin burki akan Sadiya. Amma kuma jikinsa sai ya yi sanyi jin abin da ya fito daga bakin Mai Martaba. Haka ya yi mishi sallama ya fito ya iske Sadiya zaune a ɗan barandar shiga falon tana jiransa. Har suka je gida yana kula kamar ranta babu daɗi amma tana ta ƙoƙarin duk abin da ya ce ta amsa da murmushin yaƙe. A ɓangarenta kuwa, suna isowa ta faɗa ɗakinta ta zauna gefen gado tana fitar da hawaye. Karshe ma kwanciya ta yi saboda gaɓoɓinta da ke ciwo na zama a wuri guda da takura. Tunani take wai kuwa wannan tsanar da Fulani da su Ummulkhairi suka yi mata akwai ranar da za su ƙaunace ta? Me ta tare musu? Kawai saboda ita ba 'yar kowa ba? Ta jima a haka kafin ta iya miƙewa ta rage kayan jikinta ta faɗa wanka. *** KANO