01 *DABI'AR ZUCIYA*❤‍🩹❤‍🩹 _FREE PAGE_ *JANUARY!* *JANUARY!!* *JANUARY!!!* *_A SABON WATAN JANUARY 2022_* *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar *DABI'AR ZUCIYA* _FREE PAGE_ 01 Rana ce sosai wadda ta qwalle daga kowanne sashe na sararin subhana zuwa fadin filin duniya iyakar hangen dan adam,wadda take bada tsananin haske da kuma zafi,irin zafin dake sanyawa kowanne mai rai wala mutum ko dabba neman mafaka da zai samu inuwa da zata hutashshehi ta kuma dauke zafi da radadin da ranar ta haifar tun daga gangar jiki izuwa qwaqwalwa. A irin wannan lokacinne ummukulsum ke tafiya cike da bacin rai da wani irin fushi,yarinya matashiya,wadda gaba daya shekarunta ba zasu haura sha biyar kacal a duniya ba. Baqa ce ita,ba irin wuluk din nan ba,saidai tafi chocolate colour duhun fata,tana da yalwar gashin kai dana gira,madaidaicin baki da matsakaitan idanuwa,tana da baiwar fararen idanuwa,haqoran bakinta milk colour ne masu qyalli,madaidaicin baki da matsakaiciyar haba wadda ta qawata shape din fuskarta,a taqaice ummukulsum na cikin mata masu matsakaicin kyau. Zafin da take ji a zuciyarta yafi wanda takeji a tsakar kanta sanda ranar ke kwadarta,idanunta cika yake da hawaye tana ta qoqarin maidashi,saboda sam batason tayi kukan,mutum ce ita mai jumuri da dakakkiyar zuciya,wanda wasu suka fassara hakan da tsananin taurin kai da kuma baqin hali. Tana tafe tana hadiye abinda ya dunqule mata a wuyan,tana kuma duban yadda hanyoyin layukansu ya dade qwal babu jama'a,da alama kowa ya nufi gona,wadanda kuma basu da gonakin zuwa ko basu da abinda xasuyi cikin gonar sun tafi sabgogin gabansu. Hannun hagunta ta kalla sanda take gab da gota wani siririn lungu,saita yanke shawarar tabi tanan din,don zaifi mata saurin isa gida,duk da ba kasafai ta fiya son bin lungun ba saidai dole,hatta da mahaifiyarta wani lokaci takan ce su haqura da bin hanyar,saidai a yanzun tana son isa gida da wuri ne,don ta baro mahaifiyar tata tana dakon dawowarta. Ko tsakiyar lungun batayi ba ta soma hangota,asiya,'yar uwarta ta jini,wadda suke 'ya'yan maza zar ita da ita,da mahaifinta da nata mahaifin uwa daya uba daya suke. Ci gaba tayi da nufosu yayin data kafesu da idanuwa tana kallonsu. Ita da ayuba,daya daga cikin matsan qauyen wadanda suke ji da tashen samartaka,ta gefe guda kuma sukeji da tashen rashin kunya,rashin ganin girman kowa,iskanci rashin tarbiyya da badala iri iri,saidai duk da wannan halayya tasa kusan babu wanda yake iya bugar qirji ya qalubalanceshi,shi din ko kuma daya daga cikin abokansa,sakamakon mahaifinsa ya kasance mai abun hannunsa cikin fadin qauyen,ta daya gefan kuma,mahaifiyarsa qanwa ce ga mai garin garin nasu,hakan ya sanya yake iya aikata dukkan abinda yaso,ya kuma taka dukkan wanda yaga dama,cike da gadara da kuma ganin karensa yakai tsaiko. Asiyan na sanye da uniform na makarantar boko,makarantar da suka sha gori baqar magana gami da habaici kala kala a kanta,makarantar da ake mata wani kallo na musamman,aka dora dukkan buri na ci gaba kyautatuwa da gyaruwar rayuwar asiyan ita da duk wanda ya jibanceta a kanta. Gefe daya ayuba ne tsaye gab da ita,kamar zasu shige jikin juna,magana suke da juna,saidai ba zata iya jin abinda suke fada ba,sakamakon 'yar tazarar dake tsakaninsu,sosai ranta ya sake baci fiye da dazun lokacin da ta hanhi ayuban ya kama hannun asiyan ya riqe cikin nasa,wannan ba shine karon farko da taga asiyan cikin wani yanayi da yayi kama da wannan ba,saidai babu wanda ta taba furtawa bayaga mahaifiyarta,kuma har yau har kwanan gobe itace mutum daya tak data taba shaidawa abinda idanun nata ya gani,wanda daga bisani data fuskanci mahaifiyar tata batason dukka wata magana daya danganci wannan sai ta daina gaya matan,saidai a kullum kwanan duniya,duk sanda zata ga asiyan a yanayi irin wannan,tana jin ciwo sosai cikin ranta,tana jin baqinciki,amma ita din babu yadda zatayi da ita,saboda bata da wani iko ko qarfi wajen yanke hukunci cikin al'amuranta,haka taci gaba da takawa harta iskesu,ta kuma rabasu ta wuce ba tare data ce da kowa cikinsu komai ba,yayin da asiya da ayuban suka bita da kallo,har sai data kusa bace musu sannan suka dauke dubansu daga kanta lokaci guda "Yar gidanku ta ganmu asy,kina ganin ba zata kai maganar gida ba?" Baki ta tabe tana gyara tsaiwarta sannan ta dubeshi "To saime don ta ganmu?,zancan kai magana gida bata taba ba,don ba yau farau ba" wani duba yayi mata,a zahiri yayi kama dana burgewa dana qauna,saidai can qasan ransa yana taɗinta shi daya "Ashema fanko ce,ballagaza,bani kadai ma kenan na saba latsawa ba,bari na saki jiki kawai na kwashi rabona,indai kudi ne matsalarta ta samu", da wannan zancan zucin ya jefeta da murmushi,wanda ya sanyata itama ta maida masa martani. Tana gamutsa wadan nan abubuwa guda biyu cikin kwanyarta ta fuskanci gidansu,gidan da kullum tsanarsa ke qara darsuwa cikin ranta,ana cewa da uba ake ado,itakam anan ta qalubalanci wannan karin maganar,a nan a bigiren da take....tana ado ne da mahaifiyarta ba wai mahaifinta ba,hausawa na cewa gida mai dadi...banda nasu gidan,bata hangi wani dadi nutsuwa ko kwanciyar hankali dai dai da qwayar zarra cikin nasu gidan ba,batasan yaushe ne zasu kalli gidansu suji farinciki kwanciyar hankali ko alfahari dashi ba. Duk da cewa babu lallai a iya jiyota amma bakan bai hanata yin sallama ba sanda take shiga gidan,saidai kamar yadda ta zata ne ba'a jiyota din ba,har sai data qaraso babbar harabar gidan nasu mai yalwa sosai,kamar yadda mukasan gine ginen gidaje na 'yan uwanmu 'yan karkara,sashen dake hannun damanta,wanda aka gewayeshi da dangar kara saboda a rabashi daga kasancewa wani yanki na babbar harabar gidan ta nufa,tana iya jiyo tashin sautin qarar redio daga daya sashen dake hannun hagunta,yake kuma kallon nasu sashen,wanda shikam yafi nasu,don ko babu komai ya samu ariziqin katangar bulo na jar qasa kamar yadda ilahirin ginin gidan yake. Sallama ta sakeyi karo na biyu,kusan a tare suka amsa mata,mata guda biyu qarqashin rumfar buni dake a tsakar gidan nasu,zaune suke saman tabarmar kaba,matashiyar da batafi shekara sha hudu ba,da kuma mahaifiyarsu wadda nata shekarun zasu kai arba'in,saidai idan bakayi mata mallo na tsanaki ba,zaka tsammaci tafi hakan,sakamakon hudowae furfura saman baqar sumar kanta,wanda hakan yake da nasaba da yanayi da hali na rayuwa. Tana dosu su amma hankalinta yana ga 'yar qaramar rumfa da suka tayar suke girki a cikinta,qamas take,ba'a hura wutar kara da sukanyi amfani da shi ba,hasali ma tukwanen a kife suke gaba daya a wanke qal kamar yadda ta barsu a dazun,alamu na nuna mahaifin nasu tunda ya fita bai waiwayosu ba kenan?,saita dauke kanta ta qarasa saman tabarmar da suke kai ta zauna,zuciyarta na qara dagulewa da baqin ciki. "Har kin dawo?" Mahaifiyar tata ta jeho mata tambayar,idanunta ta soma saukewa saman ciwon dake saman qafarta,wanda a kullum yake dada rami,qafar tata tana sake kumbura,kowanne dare zuwa wayewar gari na duniya da wannan ciwon take kwana cikin zuciyarta tana tashi,tana jinsa tamkar a jikinta yake "Ta yaya umma zaki tsammaci dadewata dama a wannan gidan?" Ta fada sautin muryarta yana nuna alamu na fushi. Tsam mahaifiyar tata ta daga idanunta tana dubanta,ta wani fannin tana nazartar yanayin fuskarta na wasu sakanni,saita sauke boyayyar ajiyar zuciya,sannan ta kira sunanta a hankali "Kaltume.....wannan gidan dai da kike magana a kanshi mahaifiyata a cikinsa ba wani ba kin manta ne?" Saita dauke idanunta daga kan ciwon karon farko tun daxun data zuba mishi idon,kamar wanda hakan zai taimaka mata wajen janye ciwon daga qafar mahaifiyar tata "Na sani umma,na sani,amma saidai kiyi haquri umma,saboda bakina bazai daina fadar maganganu makamancin wadan nan ba,saboda shine gaskiya kuma ainihin abinda yake cikin zuciyata,matuqar ba zata daina ba itama....matuqar ba zata canza ba,nima banajin zan canza umma" sosai ta sake kafeta da ido,sannan ta buda baki a hankali tace "Kaltum......" "Kiyi haquri umma" tayi hanzarin fada ba tare data bari umman ta sake cewa komai ba,ajiyar zuciya umman tata ta sauke,sannan ta janye idanunta daga fuskar diyar tata,ta sani cewa kaltum yarinya ce mai fushi idan aka tabata,tana da zafi,tana da fushi idan aka tabata,saidai tana da tausayi da kuma sauqin hali a wasu lokutan. Shuru ne yaci gaba da ratsawa tsahon wasu mintuna,sannan ta bude baki a sanyaye tace "Ya kukayi da ita?" "Kamar kullum kuma kamar ko yaushe,yau ma abinda ta saba tayimin,na samu kawu labaran....yaji maganar da mukeyi da ita,ya dauko kudi zai bani amma ta saka hannu ta karbe,tace ba zai bayar ba,idan ma an baki a gindinmu da babanmu kike qarewa.....wai umma me yasa ayi bata sonki?,anya kuwa mahaifiyarki ce da gaske....?" Wani kallo ta jefawa kaltum,wanda ya hanata qarasa fadar abinda tayi niyyar fada din,saidai duk da haka labarin abinda ya farun data shaida mata ba abinda ya hanashi tasiri saman fuskarta,duk da cewa wannan ba shine farau ba,ta saba da dade da sanin wannan dabi'a ta mahaifiyar tata,har kusan ya zame mata jiki,amma ta kasa sabawa,duk sanda wani abu mai kama da wannan ya faru sai taji zafin hakan har cikin zuciyarta. "K'nnnnn" habiba qanwarta wadda ke xaune tun dazun gefan mahaifiyarsu ta fada,ita din mutum ce mai tarin haquri fiye da kaltum,bata da yawan magana,tana da sanyin hali tamkar na mahaifiyarsu,saidai duk da haka ita din ma abun na damunta matuqa da gaske,yana ci mata tuwo a qwarya,saidai bata fiya tankawa ba,amma idan hira ta tashi tsakaninta da 'yar uwarta wani lokaci takan fada. Kallonta kaltum tayi,iya saman fuskarta kawai tasan itama ranta ya baci,ci gaba da maganar tata kuwa tasan bashi da wani alfanu,hakanan bazai haifar da da mai ido ba,don haka ta sauya akalar zancanta zuwa neman mafita "Yanzu umma ya za'ayi kenan?" Shuru nadan sakanni tayi kafin ta amsa mata "Babu komai,zanci gaba da nema kawai har Allah yasa a samu,idan ban samu din ba....zanci gaba da amfani da wannan maganin muga abinda Allah zaiyi" shuru kaltumen tayi tana hadiye wani yawu mai tauri,saita kalli sashen da suke girki wanda yake a bushe ba girki babu alamarsa,ta maida dubanta ga umman "Baba bai dawo bane har yanzu?,naga baku dora komai ba" kamar ba wata tambaya tayi mai muhimmanci ba haka umman tata ta bata amsa "Bai dawo ba,amma nasan yana kan hanya in sha Allahu" miqewa kaltum tayi,saboda ba abinda ranta ke sakeyi sai baci,tasan umman ta fada ne kawai,umman ta fada ne saboda ta bashi kariya a idanunsu,bayan babu wata kariya data rage masa da zai samu a idanuwansu,ya gama wargaza komai,ya kuma gama kwancewa kansa zani a kasuwa,don ba zata iya tuna sau nawa ta fita tayi kitso ta dawo ta kawo kudin sukaci abinci dashi ba,to kuma me yayi saura?. Buta kawai ta dauka,har zata wuce bayan gida ta juyo ta dubi umman tasu "Umma ina bilal ya shiga ne?" "Bai jima da fita ba kika shigo,yacemin zaije wajen dan bala,yace kamar akwai aikin da zasuje yau" kai kawai ta gyada,bacin ranta yana sake ninkuwa,bilal da gaba daya bai cika shekara sha biyar ba amma yasan dukkan wata wahala ta duniya,yaro ne da gaba daya kamar baisan ciwo ko dadin jikinsa ba,Allah ya zuba masa tausayin mahaifiyarsa da son 'yan uwansa,dukkan wani aiki da za'a kirashi na wahala bilal ya iyashi,kama daga kwabin bulon qasa,aikin gini,kwasar qasa,haqar masai ko rijiya,kai hatta da kiwon dabbobi idan mutum nada buqata zaije ya karba yayi masa,burinsa kawai a biyashi kudin,burinsa kawai su samu abinci suci,tun yana aikin wahala ya dawo gida yayi jiyya har ya saba. *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar Duk wannan aikin da yake baisan tari ko adani ba,burinsa daya samu kudin ya siya abu mai dadi yaci,ya kuma kawowa mahaifiyarsa a boye,baya taba bari mahaifinsa ya gani,don yana da tabbacin indai ya gani ba rabonsa bane kudi ko abinci,koda na nawa ne kuwa,zai karba ya kalmashe a aljihunsa,rashin kawo musu baisa yaji kunya yaqi amsar nasu idan sun samu. Sosai abun ke cima kaltum tuwo a qwarya,tana qaunar bilal sosai,yana da sauqin kai,bashi da rashin ji ko hayaniya irin ta yara,wahalar da yakeyi tana ganin tayi yawa,saidai kusan ta zame masa jiki ma,ya zama tamkar bawa,don baya iya zama wuni guda a gida ba tare da yayi aikin komai ba,saidai idan bashi da lafiya. Shi dinma da kaltum taso yayi karatu koda su din basuyi ba,tunda shine da namiji guda daya tilo da mahaifiyarsu keda shi,amma sam yaqi,ya nuna aikin neman kudinsa ya fiye masa,koda ta zauna tayi tunani,sai taga idan ta takura dinma sai yayi karatun dame zaiyi?,su din da kullum sai sunyi fafutukar abinda zasu ci?,saidai taci alwashin dagewa tuquru ta tara kudin da bilal din zai koma makaranta,koda baya so,saboda tana kallon shi ne tamkar shine madubin rayuwarsu,kuma wani tsani da zai kai rayuwarsu izuwa tudun mun tsira anan gaba. Har azahar suna zaune zaman jiran gawon shanu,babu baban nasu ba alamarsa,dukka sun ukun idan ka kalli fuskokinsu babu tantama yunwa suke ji,daga nan sashensu suna iya jiyo qamshin man ja,wanda da alama ana soyashi ne daga sashen baba iliya,wato sashen dake fuskantosu,amma ba qamshin manja ba,ko qamshin me zasuji babu lallai a miqo musu koda babu yawa saboda haqqin maqotaka dana zumunci,saidai idan Allah ya tsaga da rabonsu. Tana idar da sallar azahar ta miqe tana karkade baqin hijabinta daya kwashi qasa,ta dubi ummansu "Ummanmu.....na tuna ina bin ladingo kudin kitson da nayi mata tun rannan ita da 'yarta,bari naje ko zan samo,saina siyo mana ko gari ne" cike da tausayi ta dubi diyar tata,wannan rayuwar da suke sam bata qaunarta,to amma ya zatayi da ranta,ita ba sana'a gareta ba,hasalima bata da jarin kuma bata dame bata,bata da wata kadara da zata saida ta zame mata jari,kai koda ta fara sana'arma mai gidan shike amshewa da wayo har sai ya durqusar da ita,dolen dole ta zuba idanu komai ma ke faruwa. Saidai ko kadan bata bari ba,bata sanya idanu ba,hakanan batayi sanyi ba kan tarbiyya 'ya'yanta,bata da sauqi ko sanya wajen kula da tarbiyyarsu,kuma kowa yasan da hakan "Karki dade,idan baki samu ba ki maza ki dawo gida" "In sha Allahu....habiba zo muje" tace da qanwar tata,itama bata dade da idar da sallar ba,don haka ta miqe suka fice a tare. Suna tafe a hanya saidai babu wanda ke magana a cikinsu,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,basuyi nisa ba suka hangi asiya tana tahowa,dauke da jakar makaranta kamar gaske,wato yanzun yayi dai dai da lokacin tasowarsu kenan,shine ta dawo gida. Suna hada ido da kaltum tayi kicin kicin da rai,ta kuma dauke kanta bayan ta gasa mata harara,wanda kaltumen batasan daga inda ta faro kota samo asali ba,saidai hausawa sunce....tabarmar kunya da hauka ake nadeta,wala'alla abinda tayi shirin yi kenan. Sai da suka giftata sannan habiba tace "Wai yaya bakiga kallon da asiya tayi miki ba?" Kai ta jinjina "Na gani habiba,tana son nannade tabarmar kunya ne da hauka" cikin alamun son qarin bayani habiban tace "Me ya faru?" Kamar ba zata gaya mata ba,sai kuma taga cewa barin kashi a ciki baya maganin yunwa,hasalima duk duniya bata da kamae habiban,hakanan tafi kowa sanin halin habiba,bata da yawan surutu ko yarin qawaye,hakanan nutstsiya ce bare tace zata yi zancan da wani,abinda yayi habiba shi yayita. Ta yadda zata fahimta ta gaya mata komai,ga mamakinta sai habiban ta tabe baki "Na saba ganin asiya a wannan yanayin yaaya,saidai fatan Allah ya shirya" cike da mamaki da kuma baqinciki ta ware idanu tana dubanta "Amma habiba kin sani baki taba yin wani abu da zai daqile 'yar uwarki daga fadawa halaka ba?,kinsan cewa kema kina da kamasho duk abinda ya faru tunda baki taimaka mata kin tunkudeta daga cutarwar da takeson jefa rayuwarta ba?" A sanyaye tace "To ya zanyi yaaya?,na gayawa umma,tace mu tayata da addu'a kawai,kada nayi magana,saboda ita batason tashin hankali,don babu lallai baaba lami ta fahimci abinda zan gaya matan,kinfi kuma kowa sanin halin jarabarta,da yadda ta tsangwamemu hakanan babu gaira babu dalili" shuru kaltum tayi,ta kasa furta komai,hankalinta na wani irin tashi,jininta ce keson fadawa wannan hanyar?,me yafi wannan tashin hankali?,sam bata jin zata iya shuru koda baba lami zata tsireta,duk da ma basu da tabbacin zataqi amsar maganar,don babu wata uwa ta gari da zataso ganin lalacewar diyarta,itace mutum na farko da zataso ta gyaru,don haka taci alwashi cikin ranta ba tare data furtawa habiba ba. Basu sake magana ba har suka iso gidansu ladingo,shima dai babban gidane irin na karkara,mai dauke da sassa sassa,ta gaida mutanen data taras a harabar gidan ta wuce sashen ladingo. Zaune ta sameta daure da zani da riga mabanbanta,yaronta na saman cinyarta yana shan nono,ita kuma tana irgen kudi,fanteka ce a gabanta wadda take duqun duqun,ba'a jima da dawo mata da ita daga tallar awarar da take bayarwa tana biya ana yi mata ba,kitson da kaltum tayi mata har ya fara soshewa,amma har yau ta kasa biyan kudinsa,kamar yadda wasu daga cikin matan qauyen keyi mata,takanyi kitson ne kawai saboda ko banza yana toshe mata wata kafar,duk da cewa su din talakawa ne tilis....basu mallaki komai ba,amma mutane ne masu tsananin tsafta,kamar yadda suka gada daga mahaifiyarsu,ita dinma haka take,ta washi qazanta gaba daya,tana da tsafta qwarai,ta yadda duk kodewar kayanta da rashin kyansu ba zata ga datti kowani abu mai kama da qazanta ba,dalilin da yasa da qyar take iya kama kan wasu ta kitse saboda tsabar rashin gyara da tsafta,da yawansu suna ganin cewa zallar wulaqancine kawai da girman kai,saidai ba haka take ba,qazantarsu ce kawai ke damunta,tana mamakin yadda basu damu da jikinsu da kawunansu ba,mace saita wuni a tsaye tana aikin neman kudi,amma gyaran jikinta saiya gagareta,ba zata iya siyan man shafawa dangwali yaba ko turaren abulbula ta siya ba saboda kauda wari da qarni,duk da talaucinsu wanda da yawansu wasu sun fisu,bata taba ganin qazanta jikin mahaifiyarsu ba. Tana jin sallamarsu ta soma qoqarin boye kudin ta hanyar cusasu cikin zaninta,sarai kaltum ta gani,amma saita dauke kai kamar bata gani ba,ta soma washe musu bakin qarfi da yaji. Da qyar habiba ta samu wajen da yayi mata ta zauna,kaltum kuwa kasa zaman tayi,saita jingina da bango kawai tana gaida ladingo,yarinyar macace mai haihuwa daya tak,amma qazanta da zafin nema sun qara mata yawan shekaru a fuska da jiki gaba daya. "Don Allah kudin kitson nan nazo ki bani ladingo,na matsu ne zanyi amfani dashi" kicin kicin tayi da fuska "Kai kaltume.....ke kam baki da kara wallahi,kudin kitson nan har yanzu baki manta dashi ba fisabilillahi?,kwana wajen nawa?,ki rage son abun duniya gaskiya" sosai kalaman nata suka bata haushi da mamaki,uba uba yanayin yadda tayi zancan a wani gadarance,kamar ita ta tsuguna ta haifeta "To ai da nazo cemin kikayi nayi miki kitso zaki biyani kudin,baki gaya min cewa kyauta kikeso nayi miki ba,kinga kenan ko kwana dubu sukayi ai haqqina ne ko?" "Kinga kada kimin rashin kunya....ungo kudinki" saita zaro naira darin daga cikin kudin da take ta boyonsu cikin zani ta miqa mata,sauke qafafunta tayi ta soma zura takalmanta,a yanayin data nuna yasa habiba ta gane tsaf zata wuce bata amsa ba,saboda cin fuska daya shigo ciki,don haka ita ta miqa hannu ta karba,ta miqe tabi bayan kaltum suka fice daga gidan,suka bar ladingo tana mita. *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar *DABI'AR ZUCIYA* _FREE PAGE_ 02 *Zafafa biyar books 2022*🔥🔥🔥🔥🔥 *SO DA ZUCIYA* _miss xoxo_ *DEEN MARSHALL* _Mamuhghee_ *HALIM GIRMA* _Hafsat rano_ *TAKUN SAƘA* _Billyn abdul_ *DABI'AR ZUCIYA* _Huguma_ *KU TUNTUBI WADAN NAN NUMBERS DIN* 08184017082 KO KUMA 09134848107 Saida habiba ta qara hanzari sannan ta cimmata "Ga kudin yaaya" waiwayowa tayi ta dubi kudin sannan ta kalleta tana ci gaba da tafia "Saura kadan na daina yiwa mutane da yawa kitso cikin qauyen nan" kai habiba ta kada tana sake matsowa sosai kusa da ita "Kada kiyi fushi yaaya,indai kana sana'a dole ka sanya haquri" "Na fara gajiya da wulaqancinsu da cin fuskarsu,ta yaya za'ayi ace kaida haqqinka sai an wulaqantaka sannan a baka,sai kace bara kayi ko roqo?" "Kiyi haquri,komai mai wucewa ne,watarana sai labari" shuru tayi bata amsata ba,haka suka ci gaba da tafiya tana hadiyar bacin ranta,tana son ta cinye abinda ke ranta kafin su isa gida,don bataso ta koma wa ummansu a haka bare ta damu da sanin abinda ya faru. Kanti lawandi suka nufa da niyyar siyan garin kwaki da suger su isa gida dashi,saidai sun taras kantin nasa a rufe yake,saboda rana ta tasa,wala'alla sai wajejen la'asar kuma zaya sake budewa,tsaki kaltum taja "Kinga,zo mubi ta gidansu wasila,baabarsu tana siyarwa saimu siya a can" da haka suka karkata suka bi wata hanya dake hannun hagunsu. Wasila itace qawa daya tilo wadda kaltum keda ita kaf fadin qauyen,kusan kowa ya sansu tare,kasancewar bata da tarin qawaye bare ta sanyasu a jikinta,shi yasa wasilan ce kawai za'a iya kiranta qawa ta sosai ga kaltume,akwai sauran 'yammata da take hulda dasu,saidai mu'amalarsu ta tsaya ne kawai iya gaisuwar mutunci,koma bayan wasilan da takanyi shawara da ita,kuma sukanyi musayar sirri a wadansu lokuttan. Kusan tare sukayi sallama ita da habiba a tsakar gidansu wasilan,gidan nasu su sassa uku ne,daya hada da nata sassan dana qannen babanta su biyu,babar wasila da daya matar qanin baban nata ta samu qarqashin rumfar da suke girki,an sauke tukunya ana kwashe abincin rana,a ladabce kamar yadda halayya da dabi'arsu take suka duqa suka gaidasu,suka amsa suna tambayar ummansu "Hala kin biyo qawartaki ne,yau baki ganta ba ko?" Babar wasila ta fada tana dariya,murmushi kaltum tayi,sannan ta amsata "Dama munyi magana da ita jiya,tace zata shiga talla yau har ɓaure,bata dawo ba kenan?" "Wallahi,inata dai zuba ido,nasan tana kan hanya" kaltum din bata amsa ba saita miqa mata kudin hannunta "Kwaki zaki bamu baaba na hamsin sukari na hamsin" "To...to" ta fada tana karbar kudin,sannan ta miqe tana dosar sassanta. Tana shiga babu jimawa wasila ta kwada sallama farfajiyar gidan,kanta dauke da babbar kwalla wadda akw cika mata ita da awara kusan kullum kwanan duniya,abu guda daya tak da basu taba yiba tsahon rayuwarsu shine talla,ko kusa ko alama ummansu tace bata da sha'awar dora musu tallan koda tana da jarin yin abun sana'a,ta gwammace tayi koma meye a gidan,idan da rabo za'a shigo har inda take a siya,abinda mutane da dama sukewa kallon ba komai bane illa zallar girman kai da ganin tafi wani,ganin cewa kusan mafi yawa mafi akasari 'yammatan qauyen suna talla,kuma dashi suka dogara,don yawancinsu dashi sukewa kansu kayan daki kaf harda sauran canji da za'ayi shagalin biki dashi. Da sauri kaltum ta qarasa tana tayata sauke kwallar daga kanta,ta duqa suka ajjiyeta a qasa a tare,saita dago tana kallon wasilan cikin murmushi "Sannu...yanzu muke zancanki da baba" gammon dake kanta ta sauke ta riqe a hannunta tana gantsarewa,alamun bayanta ya riqe,fuskarta a yatsine tace "Wallahi wahalar abun hawa,sai da muka sha wahala yau kafin mu samu abun hawan daya qaraso damu cikin qauyen nan". Kafin kaltum tace wani abu baabar wasila ta fito da baqar leda a hannunta,ta miqawa habiba da tafi kusa da ita tana kallon diyar tata "Yar halak kinqi ambato,yanzun nan muke maganarki nida qawar taki" bata amsa mata ba sai data isa saman wani turmi dake girke a wajen ta zauna sannan tace "Ni yau babarmu ba abinda nasha sai baqar wahala,saboda kaf masu abun hawa kin qarasowa sukayi wallahi" ganin sun shiga wata magana daban yasa kaltume motsawa,don itama saurin take,kaf hankalinta ya tafi gida inda suka baro ummansu,fatanta su isa su samu su jiqa garin susha ko zasu toshe wata kafar "Baabar wasila sai anjima,wasila munyi gida" saita dan zabura "A ah ki tsaya mana mucu abinci,gashi babarmu ta gama?,kuma ma inaso muyi zance dake wallahi" kaita girgiza,duk da cewa yadda kayan cikinta ke qugi,suna kuma haduwa su cure waje daya,kana su saki bayan wani lokaci,ba abinda suka fi buqata kamar abinci me zafi irin wannan,amma saidai duk da yadda suka kai ga buqatar abu,zaiyi wuya su amsa hannun wani,ummarsu ta riga ta horesu,ta kuma tarbiyyancesu da gudun abun hannun mutane,da gujewa dabi'ar kwadayi,tasha gaya musu sau tarin da babu adadi "Indai kanaso kayi qima da mutunci a idanun al'umma,to ka guji abun hannunsu,saboda shi kwadayi shine mabudin dukkan wani sharri",wannan yana daya daga cikin karatun data riqe ram a kanta "Ki barshi kawai suwaiba,ummanmu nacan na jiranmu,nace mata ba zamu dade ba....kada ki damu,idan mun hadu mayi maganar" ta qarasa fadin maganar tana kama hannun habiba dake tsaye kusa da ita "Shikenan,an jima a dandali mayi maganar....don Allah yau kada kice ba zaki fita ba kamar yadda kika saba" qaramin murmushi tayi wanda ya fitar da lobawar kumatunta data mallaka a daya daga cikin kumatunta "Idan dai banyi bacci da wuri ba ba" taja hannun habiba suka wuce,tana jiyo suwaiba naci gaba da yi mata magiyar fitowar tata. Layi daya ne a tsakaninsu,don haka babu jimawa suka qarasa gida,a bakin inda suke tara ruwa ta hangi bilal durqushe yana wanke qafafunsa,wadanda sukayi futu futu suka kuma yi jazur da kwababbiyar qasa,da gani babu tambaya yauma wuni sukayi suna aikin kwaba laka tayin bulon qasa,yayin da umman tasu ke zaune a wajen da yawanci suke kashe wuninsu a nan,qafafunta miqe har mai ciwon,idanunta akan bilal,wanda kallo daya zaka mata ka canki cewa akwai wani dan tunani dake kai komo cikin ranta dai dai wannan lokacin. Sallamarsu ta sanya bilal dagowa yana dubansu,kusan lokaci daya suka amsa sallamar da ummansu wadda ta bisu da kallo bayan sun shigo din,fargaba tana cika qirjinta kan cewa Allah ya sanya ta samo biyan bashin,idan har ba'a samun ba kuwa ta tabbata zasu wuni sur ba tare da qwayar gero ta ratsa cikinsu ba. Ledar hannun habiba ta sanyata sakin boyayyar ajiyar zuciya,dai dai sanda ta jiyo muryar kaltum tana yiwa bilal fadan data saba lokaci zuwa lokaci "Shikenan kai ba zaka dinga zama kana hutawa ranka ba,ba dare ba rana kullum cikin bautar aikin al'umma kake,duk da suna biyanka amma aikin yana yin yawa a matakin shekarunka,idan an ganka zaune haka kawai baka komai saidai idan dare yayi ko kuma baka da lafiya" dai dai sanda ya gama wanke jikin nasa,ya soma tube rigarsa ya cilla saman igiyar da suke shanya idan sunyi wanki "Saina zauna yaaya zuciyata ta mutu tun yanzu?,nifa a ganina amfanin lafiyar da Allah yayimin kenan" "Eh haka fa.....shi yasa baka iya tattali ba,komai ka raruma ka kai cikinka?" Ta masa tambayar sanda habiba ke qoqarin juye garin cikin wata madaidaiciyar roba yadda zasu jiqashi da kyau ta yadda zaifi musu auki,maimakon ya amsa tambayar kaltume sai yace "Kai kai.....habi,Allah karki jiqa dani,haka kawai,ace kullum aikinmu kenan sai kace awaki,gaskiya bazanci garin nan ba na gaji dashi" "Kajimin dan rainin wayo,idan baka ci ba saika gayamin me kake dashi da zakaci?" Habiba ta fada tana jifansa da harara,yayin da umma da umma ta zuba masa ido,kaltum kam kota kansa bata biba,don ta saba da halayyar bilal din,matuqar taji ya fadi haka to la shakka an biyashi kudin aikinsa ne. "Hakanan zakayi haquri bilal kaci,idan yaso ko zuwa anjima idan babanku ya shigo sai a sarrafa wani abun" "Ai wallahi kawai ku rufe garin nan,umma bari naje na samo mana shinkafa....an biyani kudin aikina na shekaran jiya jiya da yau" "Bilal" umman ta kira sunansa "Amma shine zaka barnatar da kudin a wunin yau kawai?" Fuska ya narke yana kallon umman "To umma dama ba don aci ba ake neman?" Sai a sannan kaltum data dauko kofuna ta kalleshi,koda yaushe tunanin bilal din daban yake,abinda ya dameku sau tari shi bashi ya dameshi ba,babbar damuwar bilal din yaji yunwa cikin cikinsa,koda ace bashi da kudi....matuqar zai qoshi to yayi maganin dukkan matsalarsa,abu daya takejin dadi,kamar yadda suke zuwa makarantar allo da sassafe haka shima ke zuwa,duk da karatun nasa baya sauri kamar nasu,amma yana bakin qoqarinsa wajen zuwan da bibiyar karatun. "Ba saboda ciki ba kawai ake nema....bilal baka sha'awar karatun boko?,kamar yadda yaran kowa keyi?,tunda su 'yan uwanka duka mata ne,kuma su basu samu damar yi ba?" Kai ya rausayar yana nufar qofa "Wanne karatun boko umma......kawai....kawai....." Bai qarasa furta abinda ke zuciyar tasa ba ya fice daga sashen nasu,kai kawai ta girgiza tana dauke idanunta daga kanshi bayan ya fice,ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana sauke idanunta qasa,tsahon wasu sakanni tana saqar zuci,kafin ta tsinto muryar habiba na fadin "Umma...an gama" muryarta na nuna ba kiran farko kenan data yi mata ba,kanta ta daga da sauri,da kaltume suka fara hada idanu,tun dazun da tabar musu gangar jikinta,ta dauki zuciyarta ta lula duniyar tunani kaltume ke nazartarta,kullum kwanan duniya cikin damuwa zuciyar mahaifiyar tasu take,damuwa ta zama daya daga cikin abubuwan dake damfare da rayuwarta,takan jima cikin rauni tausayi da wani irin narkewar zuciya a duk sanda ta daga idanu ta kalli mahaifiyarta,macace mai tarin haquri nutsuwa ibada da hangen nesa,saidai matsaloli sun taru sun dabaibaye mata rayuwa,suka kuma hada harda tasu rayuwar sukayi tafiyar ruwa da su. Duk da nata kofin na riqe a hannunta amma ta kasa shan garin,sai juya cokalin ciki kawai da takeyi,kamar yadda ta karanci ba wani ci sosai umman tasu takeyi ba itama,ita kadai tasan tarin abubuwan dake cunkushe cikin qirjinta,wanda girma da nauyinsu yake sanyata wani lokaci kamar ba zata iya dauka ba. Bai jima ba bilal din ya dawo da shinkafar hausa gwangwani uku,dai mai da barkono da dunqulen maggi,sai kuma ya zauna ya amshi garin shima ya soma sha,yana yi yana basu labarai wadanda duka kusan abubuwan da suka faru ne a wajen aikin da yakeyi. Kaltum ce ta karbi shinkafar ta juye saman faranti ta soma tsince dattin dake ciki,tana yi tana sauraren hirarrakin bilal din,wanda a ciki take nazartar abubuwa da dama da suke da alaqa da rayuwar bilal din,wanda wala'alla shi din qarancin shekaru ya sanya hankali da tunaninsa baika ga hango hakan ba. Kakkaurar muryar data karade filin tsakar gidan nasu zuwa sassan nasu cikin furucin sallama ya sanya kowanne cikinsu ya tsaya cak,yanayin kowannensu ya soma sauyawa daga ainihin yadda yake a dazun zuwa wani nau'i na daban. Ga kaltum dai sake duqar da kanta tayi sosai ga farantin da tak tsintar shinkafar bayan ta sake riqeshi da hannu daya,habiba wadda ke a kashingide saita tashi ta zauna sosai,ta jingina bayanta da katangar dakinsu,yayin da bilal wanda ke riqe da kofin garinsa,wanda surutu ya hanashi gama sha da wuri ya soma kai garin bakinsa sannu a hankali kamar me tsoron tauna wani abu,ummansu kuwa saita janye qafafunta dake a miqe a dazun,duk da cewar akwai mai ciwo a ciki,amma bata kula da wannan ba. Dattijo ne wanda a qalla shekarunsa zasukai hamsin da bakwai zuwa da takwas,yana sanye da wani farin yadi da kana masa kallo daya na tsanaki zakasan ba farin Allah da annabi bane,ko ince ba farinsa kenan na ainihi ba,hadda farin dadewa da kuma yadda yake shan wanki,qafarsa slippers ne da ake kira dan madina,wanda wa'adin rayuwarsa yakai tsakiya,ba wani tsufa yayi na azo a gani ba,amma ya dauko hanyar tsufan. Tun daga yanayin fuskarsa zakasan cewa ba ma'abocin wasa ko sakin fuska bane,wala'alla haka yanayinsa yake?,ko kuma shine ya maida kan nasa hakan?. Kusan a tare kamar hadin baki suka amsa sallamar daya sake kwadawa,a qoqarin da kowa yake na ganin cewa ya kaucema zama mai laifi na farko a wajensa daga isowarshi cikinsu. "Sannu da xuwa baaba" habiba da bilal suka hada baki wajen fada "Yauwa" ya amsa yana sauke kallonsa mai kama da harara kan bilal "Kai....." Da sauri bilal din ya daga kai yana dubansa hadi da aje kofin hannunsa,don ko bai gama cin garin ba hakanan yakejin ya qoshi "Uban waye ya daure maka gindin daukar min takalmi ka saka?" Ya fada cikin fada,dukkansu suka kai dubansu ga takalmin dake qafar bilal din,takalmi ne da dadde wanda mahaifin nasu ya jima yana cin duniyarsa dashi,ya kuma kakkatse saboda gajiya da yayi da yadda ake morarsa fiye da kima,dalilin da ya sanya baban nasu ya jefashi cikin tarin shirginsa dake aje dafa'an gefan qofar dakinsa,baiko sake bi ta kansa ba,har sai dazu da bilal din zai fita aiki,bashi kuma da takalmin da zai sanya din,ya dauki takalmin ya fita dashi aka diddinke masa,ko kudin bai samu sukunin biya ba,sai daya dawo daga aikin aka biyashi,sannan ya biya ta rumfar shu'aibun ya biyashi kudin gyaran,amma shine a yanzun daga shigowarsa,ko kyakkyawar iskar gidan bai gama shaqa ba,idanunsa suka sauka kan takalmin,ya kuma dira masifarsa akai. "Wato kana jina ma ina magana kayimin shuru ko?,ga dan iska yana baloqoqo....koda yake....ba laifinka bane,laifin uwarku ne,ita ta sanya kuka rainani,saboda bani da komai ban mallaki komai ba,to duk tsiya dai nine ubanku,bata isa ta canza muku wani uban ba". A hankali umman ta saukar da idanunta qasa,tana jin yadda idanunta keson tara ruwan hawaye su fito zuwa saman fuskart don rage radadin da take ji cikin zuciyarta amma ta hana hakan faruwa,kome amadu zaiyi mata,koda yankar naman jikinta zaiyi zata iya jurewa ta shanye,abu daya ne da bataso,takejin tarin tozarci,rashin daraja da qimarta na ratsa har cikin qashinta shine ya tashi wannan tijarar gaban yaransu,yaran da ako da yaushe take tattalin tarbiyyarsu,take yaqi da fadin tashi tsaida martabar ubansu daram cikin idanunsu,koda basu so hakan ba,saidai a kullum shi dinne mutum na farko dake fara hawa kan kyakkyawan gini da tubalin data azasu ya rusa komai da komai,ba gaban yaran ba....hatta da faccalarta kusan haka ne,daya daga cikin abinda ya zamo tushe na zallar raini qanqanci da kyara da take mata ita da yaranta ba dare ba rana,kuma babban makamin gori da tayi riqo dashi,take gallazawa da gasa zuciyarta dashi "Ahaf....aiki cika mace har a wajen miji shine kika ci sunan mace" wadan nan qayyadaddun kalmomi ta dade tana amfani dasu wasu cutar da zuciya da tunaninta,batakai ga fita daga wannan ba ta sake jin muryarsa yana fadin "Saboda tsabar iskanci da ganin dama keda 'yarki ban isa kuyimin sannu da zuwa ba ko?,gaku riqaqqu tatattu.....ke dama sababbiya ce cikin yarana kaf kin fita zakka...." Bai sauke numfashi ba bare ya basu damar furta komai ya dora kan gaba ta biyu ta zancansa "Wannan shinkafar kuma a ina aka samota?,ko yauma anje an saidamun mutunci ne aka baku sadakarta?" Yayi tambayr idanunsa akan kaltume,kamar wanda ke jiran qiris yakai mata bugu,itace mutum ta biyu data fi kowa karbar bahagon halayyarsa baya ga mahaifiyarta,sau tari idan yana wasu halayen a kanta sai taji shakka da tantamar kasancewarsa mahaifinta yana shigarta,cikin sanyin jiki data murya tace "Bilal ne ya kawo.....,sannu da zuwa" ta hada harda gaisuwar da yake mita a kanta,duk da cewa dama ce bai basu ba da zasu marabceshin,maimakon ya amsa duk da ya nuna muradinsa na yi masa maraban....a'ah....saiya waiwaya ya sake duban bilal wanda ta miqe tun dazu yana jiran ya gama fadan ya shige daki,shi kuma ya samu ya fice,don ya tabbatar ya kuskura ya fitan yana tsaka da fada,ya sake jawa kansa wani sabon al'amarin "Wato kai na fuskanceka,mugu ne kai wani lokacin,ni ina can ina fafutukar sama muku abinda zakuci,kai kuma kana nan kana kashewa uwarka da 'yan uwanka duniya,tunda kake nemanka qwandala baka taba kawomin na sanya albarka ba,saboda tsabar baqin hali irin naka,shegen yaro dan iskan banza da wofi,fitarmin daga gidana kafin na sanya itace na sauke maka gwiwoyi"idanu umma ta rintse sosai,tana jin wani zafi yana ratsa qirjinta,koda zaiyi sala sala da namansu 'ya'yansa ne,bata data cewa,bata kuma da wani iko saman nasa,saidai bata qaunar kalaman da yake yawan furtawa akan bilal da kaltume,kalamaine da duk yadda takai ga jurewa dauke kai da alkunya amma sai sun taba can cikin zuciyarta,tana tsoro....tana tsoron wani abu.....wani abun da bame kyau bane da zai iya faruwa watan watarana,ko ba komai shi din mahaifi ne,daya kamata ace shi ya zama garkuwa ta farko a garesu. Bin bilal yayi da kallo.harya fice sannan ya dauke idanunsa,ya taka ya nufi dakinsa dake a kulle da muqulli,dakin da dukkansu haka suka taso suka ganshi,koda yaushe a rufe,baya barin kowa ya gitta ta qofar dakin bare akai ga batun shiga ciki,koda mahaifiyarsu kuwa tana da geji a dakin,baresu karan kada miya da basusan komai ba,banda kalar labulen dakin babu abinda zasu iya dorarwa a cikinsa. Suna jin sanda ya wulla taliya qwaya biyu daya shigo da ita a baqar leda cikin dakin,wadda dama bai taba basu sama da hakan ba yana mitar "Tunda kunyi gaban kanku kun samowa kanku abunci aini gaba ta kaini" sannan ya dauko butarsa daga cikin dakin ya wuce bayi. Shuru ne yaci gaba da wanzuwa a tsakaninsu,kowanne da irin tunanin dake kai kawo tsakanin qwaqwalwa da zuciyarsa. Sosai wani irin bacin rai yake ratsata,har bata qaunar koda motsawa ne ma tayi bare tayi tozali da fuskar mahaifiyarta,fuskar data tabbatar babu abunda ke yawo a samanta illa bacin rai wanda ke cike maqil a zuciyarta,duk da kasancewarta jaruma,mai qarfin hali juriya da jumurin cinye duk wani bacin rai,saidai kasancewarta cikin 'yan adam da aka halitta da ajizanci....qoqarinta wani lokaci yakan gaza kaiwa ga gaci. Duk da irin cin zarafin da yabita dashi ita yaran nata,hakan bai sanya farar zuciyarta ta daina girmamashi ko sauke dukkan wani haqqi daya rataya saman wuyanta ba,matsayinsa yana nan babu abinda ya canza.....kamar dai yanzun,data yunqura ta miqe bayan fitowarsa daga bandaki,duk da ciwon dake qafarta,duk da bata da abun bashi kamar yadda bai basu komai ba,face bacin rai cin fuska da rashin tabbas. Cike da sanyi da nutsuwa tayi sallama tana yaye labulen dakin,dai dai lokacin da yayi hanzarin cusa kudin daya fiddosu cikin aljihunsa yana zare idanu gami da sake hade rai,dai dai kuma lokacin da kaltume ta dauke idanunta daga kan mahaifiyarta data yi mata rakiya dasu har zuwa sanda ta daga labulen dakin mahaifinsu,saita sauke idanun nata kan habiba,suka hada idanu,wanda hakan ke bayyana mata yadda abunda ke faruwan yake sukar zuciyarta haka yake sukar zuciyar habiban,banbancin kawai ita din ta iya hadiyewa da kuma cinyewa. A tare suka janye idanun nasu daga na junansu,da alama kowanne abun ya masa nauyi tun daga baki zuwa zuciya,cin zarafin mahaifiyarsu a gaban idanuwansu,abune da har yau zukatansu suka kasa sabawa dashi........... "Ya zaki fadomin daki haka kai tsaye ba tare da neman izini ba,wannan wanne irin halin banza ne amina?" Wadan nan sune kalaman daya taryeta dasu sanda take samun waje tana tsugunnawa saman qafafunta,kanta a qasa ta furta "Sannu da zuwa.....kayi haquri" shuru yayi yana maida numfashi,tare da tunanin abu na gaba da zai janyo,wanda zai janye tunaninta daga kudin da taga yana turawa yanzu yanzu a aljihunsa,ya nema abun laifi sama da qasa ya rasa,kuma har ga Allah so yake ta fita ya samu ya sake ya lissafa kudadensa ya musu ma'ajiya,don haka ya yunqura ya janyo ledar taliyar daya wurgar ya jefa mata saman cinya "Idan don taliyar dana adana muku ce keda 'ya'yanki saboda gobe kika kasa haquri kika biyota...gatanan,tashi ki bani waje" cikin matuqar karaya ta girgixa kanta "Ba ita na biyo ba yaaya,ko kadan kada ka kawo haka cikin ranka" "To meye na biyonin zungui zungui na shigo xan huta" mamaki ya rarrafo a guje ya rufeta,me yasa shi kullum a hagunce yake?,koda yaushe ba'ayi masa dai dai?,me tayi masa ne haka ya maisheta wata babbar abokiyar adawarta?. Bata manta ba ajiya akan haka ya sauke mata dukkan wani sababi iya son ransa,sanda ya shigo tana can tana fama da qafarta,duk da irin zogi da radadin da take mata haka tayi qoqari ta yunqura ta iskeshi,maimakon ya yabata mata....a'ah.....sai yahau masifa da tashin hankali,dan jinkirin kawai da tayi bata qaraso wajensa da wuri ba,amma sai gashi yau awannin da basu haura ashirin ba yana kuma qalubalantarta akan hakan,kawai saita miqe tsam,hannunta dauke da ledar taliyar,saboda ta tabbata barinta a wajen kamar ta sake jawa kanta wani sabon tashin hankalinne........ *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar *DABI'AR ZUCIYA* 03 *Free page* *_GARABASA DAGA ZAFAFA BIYAR_*🔥🔥🔥🔥🔥 *_Bononza kashi na hudu !!!_* *Mun saurara koken masoya,mun kuma amsa,domin farincikinku shine namu!!!* *Daga yau zuwa TALATA zuwa gobe LARABA,zaki iya samun litattafan zafafa biyar bisa farashin ragi wato 700 kacal* *MAZA GARZAYA KAFIN RAHUSAR TA QARE,KI TURA 700 DINKI ZUWA WANNAN LAMBAR ACCOUNT DIN* 6019473875 MUSAA SAFIYA ABDULLAHI keystone Bank *Saiki tura shaidar biya ta nan*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 08184017082 *Ga masu tura katin waya ko kuma VTU,saiku tura ta nan,kudi da shaidar biya*👇🏾👇🏾👇🏾 09134848107 *_ALLAH YA BAWA ME RABO SA'A_* Dai dai sanda take kalmashe jela ta qarshe daga kitson data yiwa ummansu yaran sukayi sallama,umman tasu ta janye kanta daga tsakanin qafafun kaltum din tana amsa sallamar kana ta qarashe mitar ta data fara dazu "Daga yau ba zaki sakemin kitson dare ba" ta fada tana janyo dankwalinta me santsi ta daure kanta dashi. Hannun kowanne cikin yaran uku riqe yake da littafi exercise da kuma pencil,idanunta a kansu,tana binsu da kallon mamaki,mamakin yadda akayi suka sake dawowa gurinta bayan tataburzar da aka gama yi wancan satin,wanda ya tilast ummanta tayi magana akai,duk da kasancewarta mai matuqar kara da kawaici,ba kasafai akejin bakinta ba kan al'amura da dama ba,wannan yana daya daga cikin dalilin da ya sanya azzaluman mutanen dake tare da ita suke amfani da wannan damar suna cin karensu babu babbaka a kanta,daya daga cikin tarin abubuwan dake ciwa kaltum tuwo a qwarya. Dukkansu suka haye saman tabarmar suna rige rigen miqa mata littafin hannunsu suna fadin "Ni zaki fara yiwa,dabbobin dake cikin gidansu kowa akace kowa ya zana,yasa kala" a hankali ta maida dubanta ga ummanta dake zaune daga gefan tabarmar,wanda ta matsa ne ta basu waje ta yadda sararin wajen zai ishesu,a duniya babu abinda take qauna kamar zane,duk da cewar batayi karatun boko ba,amma Allah yayi mata baiwa ta iya zane,wanda dukkaninsu basu isa suce ga daga inda ta samota ba,idan ta zana maka abu zaka rantse da Allah an zanashi ne bisa ilimi da kuma qwarewa,wannan dalilin ya sanya duk sanda aka baiwa yaran zane a makarantar boko basu da wanda suke kawowa sai ita,kusan mafi yawan yaran maqotansu ita ke musu,kota kwatanta musu yadda zasuyi. Kallon da ta yiwa umman tasu a yanzu ta yishi ne cike da kwadayin ta bata umarni kan tayi musun,saidai ko kallo inda take umman batayi ba,hakan ya sanyayar mata da jiki,ya kuma bata amsar hukuncin daya kamata ta yanke,don haka murya a sanyaye ta dubesu "Kuje ku kaiwa asiya,ta iya zata zana muku" sak dukkansu sukayi,sai daya daga cikin yaran ne yayi qarfin halin yin magana "Nidai ki zana min don Allah,Allah wancan karon data zana mana babu wanda yaci,malamin ma sai daya zanemu" ajiyar zuciya ta sauke,cikin sigae lallama tace "Habibu....kuje,wannan ba mai wuy....." Kafin ta qarasa taji muryar umman nata sanda take miqewa tana barin tabarmar tana fadin "Zana musu" wani dadi taji ya sauka har qasan ranta,ba bata lokaci ta miqa hannu don amsar littafin daya daga cikinsu nan fa rigima ta kaure,da qyar ta sasanta su akayi quri a,wanda yaci ta karba nasa,ta qwalawa habiba kira ta basu aron wata fitilar aci bal bal din,ta ajjiyeta a tsakiyarsu,sannan ta duqufa ya fara zanen cike da nishadi. Boyayyar ajiyar zuciya umma ta saki,daga nan inda take zaune tana iya hango komai yadda yake faruwa,tana iya hangen zallar nishadi a fuskar kaltume din da yadda take zanen cike da karsashi suna hira da yaran,batasan me takeji ba,batasan meye a zane ba har haka da take qaunarsa,saita kuma sakin wata ajiyar zuciyar karo na biyu,zuciyar tata na cika da fata na alheri ga iyalan nata. Suna tsaka da zanen sallamar wasila ta cika sassan nasu,kaltume da umman tasu suka daga kai suna amsa sallamar,sanye take da atamfa riga da zani sai wani yalolon mayafi saman kanta daya dan soma tattarewa,saboda rashin damuwa da guga,sai data fara gaida umman tasu sannannta durfafo inda kaltume ke zaune,bakinta a washe tana kallonta "Sarkin zane zane,an fara aikin kenan,ho kaltume kina son zane alqur'an,kamar wata mai iska" ta fada tana cire silifas dinta bayan ta zauna gefan tabarmae da suke zaune a kai,murmushi kaltum tayi mata tana sake saita ruler din dake hannunta tana jan layi saman takardar sannan tace "Inason zane wasila,dadi nakeji idan inayi,idan na gama kuma nima sai nayita mamakin nice nayi wannan" baki ta tabe "Aiko....wanda kika yiwa habu rannan ma yana nan ya maqaleshi a dakin babarmu,kowa yazo sai yace waye yayi?,kina da basira sosai kaltume" murmushi tayi kacokam tana sake tattare hankalinta akan zanenta,yayin da wasila taci gaba da yi mata hira ita kuma tana aikinta,tsahon wasu mintuna sannan tace "Wai ba zaki dandali bane?,yau fa akwai gada me kyau wallahi,nima suwaiba ce ta biyomin,nace su wuce saina biyo mun tafi tare,kada ayi babu ke,don sababbin waqe yau za'ayi" kai ta daga ta dubeta sannan ta mayar ga zanen "Dama kinyi tafiyarki kawai,kin san ba wani fiya son zuwa nake ba,kuma ko naje ma zuwan nawa bashi da amfani,tunda ba rawa nake ba,kema kin sani" fuska wasila ta bata "Amma dai duk da haka ko tsaiwa kikayi a wajen kinga mutane suma sun ganki ko?....Allah sai kinje" kai ta kada "Daina saurin rantsewa mana wasila" bata ankara ba taji wasilan na qwalawa ummansu kira tana kai qararta "Idan kinkai wannan ki tashi kuje,ai babu dadi tazo takanas don ke amma kice ba zakije ba,amma kada ki jima,ki dawo da wuri" ta gama magana tunda ta hadata da ummansu,itama tasan hakan,dalilin da ya sanya kenan tana kaiwa din ta tattarawa yaran takardunsu ta basu,tana jinsu sunata ihun murna da shewa saboda yadda dukka zanen nasu yayi kyau,ta shiga dakinsu ta dauko dan yalolon hijabinta,wanda ya soma rage kauri saboda yawan wanki da ake masa akai akai,sabili da rashin wadatarsu,dole ya zamana kusan kullum shine dai ɗan ɗaya ɗaya. Kafin su fice saita tasa qeyar auwalu da sani suka fita tare,don kada babarsu ta fahinci suna sashen nasu qilu ta jawo bau,sai data tabbatar sun shiga sannan suka durfafi zauren gidan dake a bude fayau kamar tsakar gida don ficewa zuwa dandalin. Zasu fita zai shigo,sai sukayi kacibus dashi,yaya ashiru ne,yayanta ne wanda suke uba daya,shine ɗa na farko a wajen mahaifinsu da matarsa ta farko,wanda tana haifar yara uku zaman aurensu da shi ya qare,saboda wasu tarin dalilai wanda sai a yanzun suke fuskantar wasu daga ciki,dalilan da ita ba zata iya jure musu ba,a yanzun kume sune suka zame musu suda mahaifiyarsu qarfen qafa cikin rayuwarsu. Baya taja ta gaidashi fuskarta kadaran kadaham,saboda babu wani cikakken shaquwa tsakaninsu,ba wata mu'amala bace can mai zurfi take hadasu ba,iyakarsu dama gaisuwar,shi ashirun baya gidan,yayi aure shida matarsa,gidansa yana can bayan gari,lokaci lokaci yake zuwa gidan,ya gaida mahifinsu ya bashi ihsanin daya kawo masa,zuwan nasan ma kusan asha ruwan tsuntsaye ne,yakan dan dauki wasu kwanaki bai zo ba,hakama me bi masa zubairu,shima kusan kalar tashi rayuwar kenan,qaninsu ne yakubu bai kai gayin aure ba,saidai yana nema har ma ankai kudin na gani ina so,shima dai duk da baiyi auren ba ba kasafai yake zaman gidan ba,wani lokaci yazo yayi kwanaki sannan yayi tafiyarsa,saboda kusan ya fisu rashin kirki ma duk cikin su ukun,duk da suma bawai kirkin suka cika ba,don sau daya basu taba kallon umma a matsayin mahaifiyarsu ba,abinda yasa kaltum ta shata musu layi gaba dayansu,daga gaisuwa ba abinda ke shiga tsakaninsu,saidai idan sunso su din sun qara daga saman hakan. Basu fiya jure halaye da dabi'un mahaifinsu kamar yadda su kaltume ke dauka ba,hakan ya sanya suke nesa nesa dashi,sai lokaci zuwa lokaci yake ganinsu. Kadaran kadaham shima ya amsa,suka wuce bayan wasila itama ta gaisheshi,suka jera zuwa dandalin,jefi jefi suna hira da suwaiban,har suka soma gamuwa da wasu daga cikin 'yammatan qauyen da suma suka makara basu fito da wuri ba,don haka suka rankaya gaba daya da duk wadda suka hadun suka nufi filin. Sanda suka isa wajen ya cika,samari na hannun hagu a tsaitsaye,yammata na hannun dama,gada ake sosai,kowacce na baje basirarta,yayin da daga bayan fage kuma masu saida rake ne,gyada,balangu da sauran kayan maqulashe,wajen akwai haske sosai,duk da babu wutar nepa,amma sun haskaka wajen da wuta ta kara da kuma fitilun aci bal bal dama fitilun qwayaye na masu siye da siyarwar dake filin,sun riga dasun saba dama,wutar nepa wahala take musu,sukan jima kafin suga wulgawarta,ba kasafai suke damuwa ba,tunda ba wani amfani da ita sosai dama sukeyi ba. Suna isa kaltume taja ta toge "Ki shigo don Allah,kin dade bakiyi mana waqarki bafa" magiyar da wasu qwayensu guda biyu nana da basira suka fara yi mata,wanda taja hankalin wasu yammatan suma suka fara roqarta,saboda basira da baiwar murya da Allah ya bata ya sanya kusan kowa keson waqenta,duk da tana tsaiwa ne kawai a filin,bata rawa sam,zata basu wajen su kuma suna juyawa "Dalla ku qyaleta....don taga tana da murya shine take jawa mutane rai" kubra daya daga cikin qawayen nasu ta fada cikin jin haushi tana komawa cikin filin. Ko kallonta kaltume bata yi ba tace dasu "Yau ban shirya yin waqa ba,amma kuyi haquri,duk randa na sake zuwa a shirye,zanzo da wuri nizan fara yi ma" dole suka qyaleta,saboda sunsan halinta,tunda tace ba zata din ba to ba zata ba,saita zauna saman wani kututturen dabino da aka sareshi qasansa yayi saura,tana kallon yadda suke gudanar da al'amuransu. Kiran sunanta da taji anyi daga gefanta ya sanyata daga kanta da sauri,nasiru ne,saurayi guda daya tilo a garin daya samu damar zuwa jami'a,saurayin da 'yammatan garin ke rububi qwarai da burin ganin sun mallakeshi,saboda ruwan karatun boko daya fara wankeshi,ya kuma fara sauya masa yanayi da kamanni da 'yan garin. Basarwa tayi kamar bata ganshi ba,tana boye murmushin fuskarta,saboda ita din gwanace dama a wannan gefan,tana tuna yadda ya cimmata sanda take samowa inna ruwa a rafi,ya gabatar mata da soyayyarsa,yace a yanzun zai koma makaranta ne zaiyi jarabawa,amma idan ya dawo zai dakaci amsarta. Saidai zuciyarta ta rabu biyu gami da kokwanto da kuma shakka,saboda wasila data shaida mata cewa kowa na masa kallon kafiri dan wuta kuma dan iska,idonsa ya bude da yawa wai a yadda takejin labari,saboda sudai babu wata makaranta da akeyi me dadewa haka har shekaru masu yawa irin nasa,anfi kyautata zaton kawai sheqe ayarsa da iskancinsa yake tafiya yi birni,amma haka kawai taji jikinta bai bata abinda wasilan ke fada haka bane,saboda tasan jama'ar qauyensu,gwanaye ne kuma qwararru wajen yada jita jita da kuma qadar da abinda basu sani ba,basu da tabbas ma akan hakan. Kiran sunanta daya sakeyi ya katse mata tunaninta,saita sake waiwayawa ta kalleshi,murmushi ya sakar mata,wanda ya tilastata sassauta fuskarta itama "Ko zaki daure ki taso mu koma daga can,saboda muryoyin wadan nan basa bari aji maganar mutun sosai,don Allah ba jimawa zakiyi ba,gaisawa kawai zamuyi" shuru tayi tana nazari,tun daxu dama takeson tafiyar,inda ace ma da habiba suka zo da tuni tayi tafiyarta,to habiban ciwon kai takeyi,dalilin da yasa ta barota kenan,ta yiwa wasila magana tun daxu yfi sau uku sai tace mata bari tayi waqar qarshe saisu tafi amma shuru,tana ganin wannan ce damarta kawai da zata koma gida,saboda dare na sakeyi,don haka ta miqe,cike da farincikin yadda ta amsa masa ya motsa yabi bayanta,wani gefe na zuciyarsa yana hango masa banbanci qarara tsakaninta da yammatan garin. Tana jingine da wani teburin me rake tana sauraren yadda yaketa qoqarin tsara mata kalamai,ba laifi ya burgeta fiye da sauran samarin qauyen,wadanda a cikinsu har yanzu babu wanda ta taba tsaiwa dashi a matsayin saurayinta,duk wanda ta kalla sai taga nutsuwa da hankalinsa baikai mata yadda takeso ba,wani irin fata ne mai girma ya ginu cikin zuciyarta,tun daga lokacin data budi idanu ta fahimci sarai rayuwar gidansu,ta karanci wanne irin miji mahaifiyarsu ke aure,saita samu kanta da gayawa kanta da kanta,lallai ya zama tamkar wajibi a garesu ita da 'yar uwarta....yin dogon tsinkaye da nazari,sanya hankulansu cikin jikinsu kafin fidda mijin aure. Abu daya zuciya da qwaqwalwarta ke gaya mata shine....namiji mai ilimi shine haske kuma mafitarsu,duk da ita din ba wata me karatu bace,bata tsira da komai ba banda karatun muhammadiyya da take nema a kullum,amma wata iriyar qwaqwalwa mai zurfi da nauyin tunani....gamida quality na auna dai dai da kuma akasinsa Allah ya bata,a tsahon nazarin data debe lokutta masu tsaho da batasan adadinsu tana yi ba,zuciyarta ta gaya mata jahilci na taja rawa wajen kauda danne haqqin mata,da kuma zaluntarsu. Idan akace ilimi bawai ana nufin karatun boko ba,a'ah,ana magana ne kan karatun addini,wanda shine tsanu na farko dake saita rayuwar namiji,ya karbi iyalinsa ya kula dasu ta hanyar data dace,tunda shine na farko daya fara koya mana yadda zamu mu'amalanci junanmu tsakanin mutum da mutum hary zuwa gidan aure,ta hanyar haska mana madubin rayuwar gidan ma'aiki S A W(yake 'yar uwata,indai kinason kubuta daga sharrin kurkukun gidan aure,da baqincikin namiji,a farkon zabin abokin rayuwarki,kiyi qoqari ki zabi namiji me ilimin addini me kuma aiki dashi sama da kowanne irin miji daya mallaki koma wanne irin qyalqyali na duniya,haqiqa idan kikayi hakan kin samawa kanki kyakkyawar mafita da makoma ke da yaran da zaki samarwa al'umma). Ya dade yana tsara mata kalaman da taji ta gamsu dashi,ya kuma kwanta a ranta,yace ta jirashi minti kadan,bata ankara ba sai gashi ya dawo gareta da tarin siyayya fal leda "Muje na rakaki,kinga hanyoyin sun soma duhu" ya fada yana murmushi,batace komai ba tayi gaba,ya biyota riqe da ledar da baikai ga miqa mata ita ba. Basuyi nisa ba idanuwanta suka hango mata asiya cikin wata duhuwa,sosai ta zubawa wajen idanu da kyau,abinda ta gani ya sanyata dauke idanunta babu shiri tana kiran sunan Allah,abu daya da zai hanata riskar asiyan shine nasiru,ba zataso ya gani koya fuskanci wani abu ba,tunda baqo yake ga rayuwarsu,zuciyarta tayi mata baqiqqirin,har bata iya fahimtar abinda nasirun kece mata sosai,a haka suka qarasa qofar gidansu,saiya miqa mata ledar yana murmushi,bay taja kawai ba tare data amsa ba tana kada kai "Ka barshi na gode" "Don Allah ki karba,haba kattum,duka saboda na siya fa,indai bawai baki amsa tayina bane" ganin ya damu ya sanyata ta saka hannu ta karba,bata fiya son amsar abu daga hannun samari ba,sabida tasan halin ummansu sarai,ta musu iyaka,hakanan ta shata musu layi daga amsar abun hannun wani,sa'annan tana tsoron karbar abun hannun wani ya zamana aurensu baiyuwu ba,kamar yadda ta faffaru a baya. Tun a sannana akwai ragowar zumunci tsakaninta da asiya,ita ke feqewa tana zaqalqalewa "Wallahi karbi abunki,ai bake kika roqa ba,baki sukayi" to koda bata karba din ba asiyan zata karbar mata ita,ta kuma fita ci ma. Godiya ta yi masa sukayi sallama sannan ta nufi cikin gidan,tun kafin ta isa sassansu ta jiyo muryar kawu iliya shida matarsa,tambaya yake ina asiya,tana kuma shaida masa cewa ita ta aiketa gidan kuluwa,bata dade ai da fita ba,kuma yanzu zata dawo. Wani abu mai kama da tausayin kawu iliyan ya ratsa kaltum,duk da kasancewar shi dinma babu wata qauna da kulawa da yake nuna musu,shida uwar dakin nasa xamuje ta tadda mujemu,wanda su kansu har yanzu basusan meye ainihin wannan tsana kyara da tsangwama da suke nuna musu ba,amma duk da hakan....abun tausayi ne mace ta rufi uba game da yaransa,rufewar kuma da zata iya zame musu cutarwa me girma cikin rayuwarsu....dama rayuwar wadanda ke kusa dasu. Sallamar da takeyi ne ta maqale a fatar bakinta sanda ta cusa kai sassan nasu,sakamakon ganin mahaifinsu zaune saman tabarma daga gefan dakinsa,ummanta na duqe daga gefan nasa,idanunsa ya zube fes bisa fuskarta yana mata wani kallo mai nauyi da ban tsoro. "Kin dawo daga yawon karuwancin naki?" Taji kalmar mai azabar nauyi ta sauka a kunnuwanta,da sauri ummanta ta cira kanta tana kallonshi,habiba dake kwance cikin dakinsu ta miqe ta zauna sosai ba tare data shirya ba,yayin da itama kaltume take kallonsa a matuqar tsorace,kafin ta duqa a wajen a hankali jikinta yana rawa. Kalaman nashi na yau sunyi tsauri fiye da kullum,a baya yakance kin dawo daga yawon naki!,amma a yau abin nasa yaci gaba,har ya iya dangantata diyar cikinsa da yawon karuwanci?,wannan wanne irin alkaba'i ne?,ledar hannunta ta zame daga hannun nata,saita fadi a wajen ta tarwatse,kayan da suke ciki wanda itama batasan meye da meye a ciki ba suka sukayi dai dai a wajen,ita umman tasu da baban nasu sukabi kayan da kallo. Tsam baban nasu ya miqe,yana sake cika yana duban ummansu "Oho....kin gani ko?,kin gani da idanunki,to wallahi bazan yarda,baku isa ba daga ku har uwarku,wallahi zuwaira baki isa ba,gaba daya kin lalatamin yara,banda yawon karuwanci take ina ta samo wadan nan kayan,nidai Allah ya isa tsakanina dake zuwaira,kin cuceni,kinyi amfani da talaucina kin lalatamin yar,yanzu ina bilalu....ace har yanzu yaro bai shigo gidan ubanshi ba?,to idan yazo ki gaya masa ya fita yabarmin gidana,yaje ya kwana a duk inda zai kwana" daga haka ya banka dakinsa ya shige,a guje itama ta miqe tayi dakinsu,tanajin nauyin kalaman mahaifin nasu a kanta da kan mahaifiyarta yana mata yawo tsakiyar kai,kamar ana yamutsa qwaqwalwarta. Zubewa tayi saman yaloluwar katifarsu data fi kama da tabarma saboda sudewa ta saki kuka mai nauyi,ita kuka habiban kuka,kowa yanajin zafi da radadin kalaman baban nasu har cikin zuciyarsa. Wani irin kuka take mai cin zuciya,wanda batasan adadin lokacin data kwashe tana yinsa ba,har sai da habiba ta gama nata kukan ta dawo lallashinta,a tsakiyar hakanne sukaji shigowa da kuma fitar bilal daga gidan,da alama umman nasu ta shaida masa cewa kada ya kwana gidan kamar yadda me gidan ya bada umarni,sai kukan kaltumen ya tsagaita,bilal takeji a yanzun ba kanta ba,ta kalli habiba sabbin qwalla na fito mata "Idan bilal be kwana a gida ba a ina zai wana habiba?,fisabilillahi yana da gidan wani uban ne bayan nan?,a filin gidan nan zai kwana ko a maqota?,ko a jejin Allah ko a gona?" Kafin habiba tace komai ummansu ta daga labulen dakin ta shigo,dukka sai suka bita da kallo har kaltume. Gefansu ta samu ta zauna,ta kuma ajjiye ledar hannunta a tsakiyarsu,sai data bude sannan kaltume ta gane ledar data saka ce dazun,umman ta maida idanunta kan fuskar kaltum ta kafeta dasu "Nidai nasan ban baki kudin da zakiyi irin wannan siyayyar ba a dandali,hasalima bamu da arziqin da zaki iya irin wannan siyayyar....kaltum,kada halin matsi da talaucin da muke ciki ya jaki ki aikata abinda zai janyo miki fushin ubangiji da namu gaba daya....kaltum ina kika samu wadan nan kayan?" Ta fada tana kaurara muryarta alamun da gaske take,muryarta cike da tuhuma,abinda ya sanya kaltume sake sakin kuka kenan "Ba kuka nace kimin ba,ki amsa min tambayarki" ta fada kamar a dan tsawace,muryarta cike taf da kuka ta soma magana "Ummanmu.....wallahi wallahi wallahi tunda nake ban taba koda sha'awar aikata wani abu makamancin abinda kike tunani ba,idan qarya nake na mutu yanzu a nan,nasiru ne ya siyomin,sai dana ce bazan karba ba yayita yimin magiya,idan kuma har qarya nake Allah....." Hannu ta daga mata,tana jin tsoronta da firgici daya cika zuciyarta yana kwaranyewa yana sauka daga zuciyarta,duk da cewa tana da qarfin gwiwa da kuma yaqini cikin zuciyarta kan yaranta,yaqinin da kusan rabin qauyen basu dashi akan nasu yaran kamar nata,saidai ta sanyawa ranta ba'a shaidar dan yau,kuma ba zata taba shaidar nata ba,duk sanda wani abu da taji zuciyarta bata gamsu dashi akan yaran nata ba,taci alwashin bin diddigi har sai ta gano gaskiyar lamarin (Yake uwa!!!,ki xama me yiwa kanki adalci....ki guji shaidar yaranki a duk sanda akacemiki sunyi abu,ki amsa laifin da akace miki sunyi koda zuciyarki bata gamsu da sun aikata ba,ki tsaya kiyi amfani da shekaru da kuma hankalin da Allah ya baki,kibi diddigin wannan maganar har saikin gano gaskiya,idan har abinda aka fada din haka ne,saiki miqe tsaye ba dare ba rana kiga kin gyara,ki hada da addu'a da neman agajin ubangiji,idan kuma kika taras ba hakan bane,saiki godewa Allah,kici gaba da nema musu tsari da kuma addu'ar neman shiriya,Allah ya dafa mana bisa tarbiyyar yaranmu,ubangiji ya iya mana🤲🏽🤲🏽) "Ya isa,daga yau ban amince ki sake karbar komai daga hannun kowa ba,sannan ki sake kiyayewa,ku tsare kanku,ku tsare mutuncinku,idan ni bana ganinku kuma bana tare daku,Allahn da yayini yayi ku,ya kuma wajabta mana biyayya a gareshi yana tare da kowanne bawa,kudin 'ya'ya mata ne,sau daya tak aka taba rayuwarku an cuceku,cuta ta har abada,wadda ba zata kankaru ba,wallahi wallahi wallahi duk wadda a cikinku taje ta aikata abinda Allah da manzansa basaso Allah ya isa tsakanina da ita ban yafe mata ba" daga wannan ta miqe,tana jin zuciyarta na samun nutsuwa,ta yarda da tarbiyyar data bawa yaranta,saidai hausawa suna cewa,ana tauna tsakuwa ne don aya taji tsoro,sannan Allah yana cewa:ku tunatar,domin tunatarwa tana amfanar da mumini. *_GARABASA DAGA ZAFAFA BIYAR_*🔥🔥🔥🔥🔥 *_Bononza kashi na hudu !!!_* *Mun saurara koken masoya,mun kuma amsa,domin farincikinku shine namu!!!* *Daga yau zuwa TALATA zuwa gobe LARABA,zaki iya samun litattafan zafafa biyar bisa farashin ragi wato 700 kacal* *MAZA GARZAYA KAFIN RAHUSAR TA QARE,KI TURA 700 DINKI ZUWA WANNAN LAMBAR ACCOUNT DIN* 6019473875 MUSAA SAFIYA ABDULLAHI keystone Bank *Saiki tura shaidar biya ta nan*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 08184017082 *Ga masu tura katin waya ko kuma VTU,saiku tura ta nan,kudi da shaidar biya*👇🏾👇🏾👇🏾 09134848107 *_ALLAH YA BAWA ME RABO SA'A_* *ƊABI'AR ZUCIYA* *Free page* 04 *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar A daren ranar idan tace tayi isashen bacci to tayi qarya,haka ta dinga baccin rabi da rabi,abunda ya faru ne kawai yake dawo mata daya bayan daya,ta fuskanci kaf rayuwarsu qalubale ne a cikinta kala kala,tako wacce fuska akwai kalar jarrabawar dake fuskantosu,ko sai yaushe al'amura zasu daidaitan musu kamar kowanne mutum?,amsar data kasa lalubowa kenan,har xuwa wayewar gari,sanda ta tsinci muryar ummansun saman kanta tana kiran sunanta. A kasalance ta miqe,cikin yanayin barcin da bai ishi mutum ba,ta zauna sosai tana murza idanu,tana kuma duban umman nasu,ganinta sanye da hijabin da takan sanya idan zata je wata unguwar "Ki tashi hakanan.....matar malam ta aiko kije kiyi mata kitso,nizan fita,zanje dubo inna" "Inna kuma ummanmu?" Ta tambaya cikin mamaki tana duban fuskarta,don ta sani cewa ita dinma aiba isashshiyar lafita gareta ba,ciwo ne a qafarta wanda kullum yake ci gaba,take kuma neman kudin maganin da zatayi,saboda lokitocin cikin gari da suka ja kunnenta kan ta gaggauta yin maganinsa,yin jinkiri ko wasa dashi zai iya haifar mata da komai,ciki harda rasa qafar tata ma gaba daya,to amma ko a mafarki,koda wasa basu taba ganin gilmawar inna cikin gidan da sunan tazo dubata ba,hasalima a kafatanin rayuwarsu xasu iya lissafa sau nawa suka taba ganinta tazo gidan nasu,kallonta umman tayi sosai tana karantar yanayin fuskarta "Eh ita,ashe kwana biyu bata jin dadi,sai dazu Allah ya kawo yaron nan salisu na kusa dasu yake gayamin" sosai ran kaltum din ya baci,wato kwata kwata mahaifiyar tasu ma bata da darajar da za'a aiko a shaida mata bata da lafiya,sabida bata da abun duniyar da zata bata,tana da yaqinin inda rahama ko zaliha ce koda babu aike innar zata je da jan gindi da kanta ta sanar musu,qoqarin miqewa kawai kaltum tasoma yi,don ba zata bar umman tasu ta tafi ita kadai ba,gwara suje tare,duk da wanzuwarsu a wajen babu abinda xai hana na daga abinda inna tayi niyyar aikatawa akan umman tasu,amma dai biyu tafi daya "Umma don Allah jirani ja watsa ruwa kawai muje tare" "A'ah....to kitson fa da ake jiranki kiyi?" Umman ta fada tana binta da kallo,a lokacin har takai bakin qofa "Zan aika habiba ta basu haquri,idan muka dawo naje nayi musu" saita qara wuta ta fita da sauri don ma kada umman ta sake tsaidata. Nannauyar ajiyar zuciya ta saukar,tasan abinda yasa kaltum ta nace saita bita sun tafi tare,saboda tafi kowa sanin yadda dangantaka keda tsami tsakaninta da innar,duka sabili da ita,abinda kuma take gudarwar kuma babu abinda xai hana faruwarsa sai wani ikon na Allah,ta sani duk cikin yaranta babu me kishin uwa da qawa zucinta irin kaltumen,bata iya bari ko qyale abinda xai tabata koda za'a yankata ne kuwa,mutum guda take iya daukewa kai,tayi masa wannan alfarmar shine mahaifinsu. Cikin mintina qalilan ta shirya,duk da yadda take da nauyi wajen yin wanka da sauransu,ta iske umman tasu na barwa habiba sallahu "Ba dadewa zamuyi ba,yanzu zamu dawo". Ta baya sukabi suka yanka,don a qafa zasuje,duk da cewa akwai tazara yar kadan tsakaninsu,to amma babu abun hawan dake zirga zirga daga nan zuwa can,duk da cewa koda akwai dinma babu kudin da zasu hau. Umman tasu ce tayi mata dole saida suka biya ta qofar gidan matar malam,ta shiga ta shaida mata zata raka ummansu anguwa,amma idan suka dawo ta nan zata biyo tayi mata kitson,sannan ta fito ta samu umma dake tsaye tana jiranta suka ci gaba da tafiya,gefan zuciyarta wani rauni na ratsata,duk sanda zata daga idanu ta kalli umman tasu sai taji wani madaukakin tausayinta yana ratsata,tako ta ina ita din abar tausayi ce,har gwara su suna da uwa irinta. Sun danyi nisa kadan sukaji ana fada cikin qanqan da murya "Barka da warhaka umma" a mamakance suka juya dukansu,yusufa ne,daya daga cikin matasan qauyen,wanda yana daga cikin matasan da aka yiwa shaidar nutsuwa da hankali cikin qauyen,ya qaraso kana ya duqa har qasa yana gaida umman,ta amsa cikin fara'a da sakin fuska,saita danyi gaba kadan yadda zata iya hangosu,xuciyarta tana bata sahunsu ya biyo ita da kaltume. Ba'a rufa minti uku ba taga sunyi sallama ya juya ya nufi cikin gari,ita kuma kaltume ta nufo inda umman ke tsimayenta "Waye wannan ne?" Umman ta jefawa kaltume tambayar sanda suke ci gaba da tafiyar,murmushi kaltume tayi "Umma baki ganeshi ba?,yusufa ne fa dan gidan huwailan malam baffa" "Af...af,saikuma da kika fada naga kamarshi da mahaifinsa....ai ban shaida shi ba,na kwana biyu ban ganshi ba" "Eh....legas yake zuwa ya dawo,bai fiya zama garin na ba" "Ma sha Allah,Allah ya taimaka....." Ta fada tana son jin qarin haske game da tsaida kaltume da yayi,kamar tasan meke kai kawo a zuciyar ummantata saita ce "Nifa nan babbar yaya ce,bakiga yadda yake gaidani ba cikin girmamawa" ta fada tana dariya,har hasken haqoranta na bayyana,wanda hasken rana suka qara masu sheqi,dan murmushi umman tayi "Babbar yaya kamar yaya?"saida tadanyi dariya mai sauti sannan tace "Habiba fa yakeso,wai don Allah na masa hanya ya sameta" shuru umman tayi tana dan qaramin nazari,a nata lissafin kaltume ce gaba,ita zata fara aurarwa kafin habiba,ko kum duka ta hada ta aurar dasu gaba daya,wala'alla walwalar da suka rasa cikin rayuwarsu su sameta a gidajen mazajensu,don bataga alfanun zamansu ba,dukkansu sun tasa,a karkarar sun isa aure,don an aurar ma da wadanda basu kaisu ba,to amma ita kaltume sam maganar aurenma kamar bai gabanta,har gwara jiya da abun nan ya faru taji tayi zancan nasiru. "Ummanmu.....bakice komai ba,ko baiyi miki bane?" Kaltume ta fada da alamun sanyin jiki,sai umman ta sauke ajiyar zuciya "Ba wanda bansan iyalan gidan malam baffa ba,yarane nutsatstsu duk da kuwa kusan duka yaransa maza ne,abu daya zuwa biyu kawai nakeso......banason ya fara neman habiba kansa tsaye,ya fara neman izini daga wajen mahaifinku sannan su gana,abu na biyu,kema inason ki shaidawa nasiru.....indai da gaske yake karya qara tsaiwa dake saiya nema izini wajen mahaifinku,saboda gujewa sake faruwar abinda ya faru a jiya" maganar umman tasu tana hanya,amma jin zafin abinda mahaifin nasu keyi ya sanyata ta zunbura baki "Ni ummanmu baba mamaki yake bani,irin abubuwan da yakeyi umma kamar ba shine ubanmu ba,jarrabar yau daban ta gobe daban,anya kuwa shine ya haif....." Faf! Taji an doke mata baki,wanda ba kowa bane illa umman tasu,cikin bacin rai take kallonta bayan ta dakata da tafiyar "Kina cikin hankalin ku kuwa kaltume?.....sau nawa nake ja miki kunne akan irin wannan maganganun ne?,to bari kiji...." Ta fada tana nunata da yatsa "Yau ya zamana itace rana ta qarshe da zan sake jin magana makamanciyar wannan ta fito daga bakinki,idan ba haka ba ranki zaiyi bacin da baki taba tsammani ba" saita juya zata ci gaba da tafiya tana qoqarin maida qwallar dake taso mata,da sauri kaltum ta cafki hannunta ta zagayo gabanta,itakam tunu qwallar ta soma zuba "Kiyi haquri ummanmu,in sha Allahu hakan bazai sake faruwa ba,na miki alqawari" ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,bata iya dogon fushi dasu,musamman kaltum din,dukkansu suna bakin qoqarinsu wajwn yi mata biyayya da kyautata mata,ta sani cewa a irin halin rayuwar da suka tsinci kansu dole akwai tarin bacin rai fushi da saqe saqe marasa ma'ana da zasuyi ta dawafi a qwaqwalwarsu,hakanan tarin damuwa zata yi musu yawa,idan tace zatayi fushi dasu me tsayi dukan saiya musu yawa su rasa na tarewa,amma hakan ba yana nufin zata sanya musu idanu tana gani su kauce hanya ba "Ya wuce amma kada ki qara,saboda ke din kece babba a cikinsu,dukkan abinda kikayi zaya zame musu mudubi ne kuma abun koyi,dukkan wani tsanani yana tare da sauqi,hakanan kowanne yanayi bawa ya tsinci kansa me wuce wane,kuyita addu'a kuyita jurewa,Allah yayi miki albarka keda sauran 'yan uwanki. ******** Tafiyar mintina talatin a qasa suka qaraso gidan tsohuwar wato inna,tun kafin sukai ga shiga zauren gidan ran kaltum ya gama baci,idan tana qaunar mutuwarta to tabbas tana son shiga cikin gidan,a duniya babu abinda ta tsana irin zuwanta gidan,saidai don bata da yadda zatayi ne,ba yadda ta iya,haka tabi bayan ummanmu suka sanya kai cikin gidan. Filin tsakar gida ne babba kamar nasu,saidai su nasu wannan malale yake da sumunti,a share yake fes saboda badai tsafta ba tsohuwar,daga hagunka madafa ce wadda da bandaki daga kusa da ita,wanda akillace suke a gyare ba kamar na sauran al'ummar karkara ba,da yawancinsu a bude suke,hakanan zaka samu tarin turbaya,daga daya gefan hannun damanka dakuna ne a jere,ginin bulo,wanda aka yi musu rumfa gaba daya gaban dakunan,saboda kare rana da kuma zama saboda shan iska,da kuma zama yayin saukar ruwan sama da sauransu. A qasan rumfar kuwa tabarma ce babba a malale,sai filo daga bayan tsohuwar wadda ke zaune riqe da mafici tana firfita,daga gabanta danta ne zaune wato qani ga mahaifiyar kaltum wanda suke kira da kawu ado,kusa dashi yaransa ne maza guda biyu,bisa dukkan alamu zuwa sukayi dubata,sai jikokinta guda biyu yaran kawu sama'ila suma,kusan sa'anni suke da kaltum,duk da cewa tadan girme musu da watannin da basu wuce hudu ba. Sallamarsu ce dukka taja hankalinsu,suka amsa musu kafin su gama fahimtar su waye,tashin farko fuskar innar ta sauya sanda suke qarasowa saman tabarmar don yiwa kansu masauki,cikin qanqanin lokaci walwalarta ta ragu,sai kawu ado ne ke maraba da zuwan umman,fuskarsa a sake yana matsar da yaransa gefe don ta samu wajen zama "Yanzu nake shirin yin maganarki yaaya,tunda nake zuwa ban taba samunki ba,duk sanda nazo kuma inason qarasawa wajenki,sai hira tayi hira nida inna lokaci saiya quracemin,hakanan nake juyawa na koma" fuskar umman a washe,cike da jin dadi yadda har kwanan gobe ado na daya daga cikin jama'ar dake girmamata,gami da ganin mutunci martaba da qimarta,kafin ta bashi amsa innar ta magantu,cikin sautin dake nuna zafinta "Yo me zakaje kayi mata?,me xaka ce mata ma?,yau gashi tunda akwai rabo kun hadu" duka sai suka kalleta,hatta da jikokin nata fatsima da kubra sai da suka waiwaya suka dubeta,amma ba wanda yace komai,tunda halin innar bawai sabon abu bane a wajensu,hakanan wannan ba baquwar dabi'a bace,don haka umma ta maida hankalinta kan innar tana matsawa kusa da ita,muryarta cike da ladabi ta ambaci "Ina yini inna?" "Lafiya" ta amsa a gajarce "Ya qarfin jikin naki kuma?" "Mun godewa Allah" ta sake fada a dake,maficinta yana hannu tana kadashi a hankali,ta lanqwasa qafarta ta dama ta dorata saman gwiwar qafar hagu,idanunta kuwa ko sashen da umman ke zaune bata duba ba,duk da haka umman saita dora "Ban sani ba inna,sai da salisu yazo maqwafta sannan ya shigo ya gayamin,kusan sati inna amma ba'a aiko an gayamin ba?" Wani banzan kallo ta watsa mata "Idan an aiko mikin me zaki tsinanawa mutane,zuwanki da rashinsa duk daya fa zuwaira" sunkui da kanta kawai umman tayi,tana ji ranta yana mata suya,yayin da kaltume ke gefe tana qoqarin tausar zuciyarta,kada ta furta wa inna maganar da tasan umman ba zataji dadinta ba,shuru ne ya dan wanzu kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa,muryar kaltum tana gaida kawu ado ita ta katse shurun,fuska a sake ya amsa mata ya dora da cewa "Ku dinma kaltume ba'a ganinku?,kuda umman naku duk kunqi zumunci,idan ita batazo ba aiki kwazo ko?" "A'ah ado.....dakata,banason kwashe kwashe,na meye sai sunzo gidanka sun matsanta maka kaida iyalinka sun dora maka nauyi,ni banason irin haka" "Inna naga...." "Kaga me?,kar na sake jin bakinka,mara kunyar yarinyar,data shigo ma kaga ta gaisheni ne?" Tasan da wannan zata fake dama,don haka tayi wuf ta gaisheta,sai data gama sheqar iska sannan ta amsa mata,daga daya itama kaltum din bata qara ba,saita waiwaya suka soma magana dasu fatsime,inna kuma sukaci gaba da hirarsu da ado,duk da jefi jefi yana sanyo umman,saidai bata fiya tankawa ba,sau tari saidai tayi murmushi kawai,daga bisani saita ja daya daga cikin yaran adon ta soma hira dasu. Tun hirar batayi nisa ba fatsime tace da kaltum "Don Allah ranar saukata kuje da wuri keda habiba,sai kuyita dari dari ku kam,kamar bakuson shiga mutane?" Duban fatsime tayi da mamaki saman fuskarta,don su kam sam basusan da wani batun sauka ba,kafin tace wani abu innar ta rigata "A'ahhhhhhh....fatsima?,suje da wuri suyi miki me?,wai ni don Allah don annabi sai yaushe zakuyi hankali?,kuyita kalan dangi kuna jajibowa kanku nauyi?,wai meye alaqarku dasu kattume ne?,mantawa kukeyi iyayenku uwa kawai suka hada dasu basu hada uba ba?,kunga wannan...." Saita nuna kawu ado da yatsa "Shine shida yaransa dolenku,sune suka hada uwa da uba da uwarku,sune abokan yin zumuncinku...." "Haba inna....haba inna,don Allah ki daina irin wannan abun,baifa kamata ba,ina cewa dukkanmu 'ya'yanki ne,daga cikinki muka fito?,su kuma duka jikokinki ne tunda ke kika haifa iyayensu,kowanne mutum a rayuwa da kalar rayuwar da Allah ya nufata xaiyi,hakanan kowanne da irin arziqinsa,don Allah don annabi inna ki daina,abun bayamin dadi" "To ubana,idan ka gama wa'azin saika gayamin" tace tana tsareshi da ido,ransa ya baci don haka kawai ya miqe tsaye yana laluba aljihunsa tare da umartar yaran nasa dasu tashi,kudi ya ciro masu yawa ya duqa ya ajjiyewa innar a saman filon dake ajjiye a gefanta "Gashi,a qarasa siyan abinda babu" caraf ta dafe kudin,bakinta har kunne,kai kace ba itace ke zabga bala'i ba yanzu,tahau godiya da sanya masa albarka kamar zata maidashi cikinta,saita soma cewa yaran su wuce susa takalmansu,shima ya shige ya tafi sanda taga yana maida hannunsa aljihunsa,da alama wasu kudin yake lalubowa. Ilai ashe kuwa ta fahimci abinda yakeson yi,su fatsima ya miqawa kudin yana cewa "Gashi kwayi kudin mota" sai tabi kudin kawai da kallo ba tare da tace komai ba,saboda ta sani cewa suma tana morar uwarsu,ya sake dauko wasu ya miqa saitin inda umma da kaltum ke zaune yana cewa "Yaaya,gashi wannan ba yawa....." Kafin ya qarasa inna ta yunquro zata cafkesu,tuni kaltum ta fuskanci nufin innar,don haka kafin ta kai ga qarasawa ita nata hannun yakai,ta amshe tana fadin "An gode kawu ado" yayin da inna ta cafki iska,shima ya fahimta abinda yaso faruwar,kuma hakan da kaltum tayi yayi masa dadi,don haka yayi gaba yana sanya takalmansa,yayin da innar ta tsiri mitar babu gaira babu dalili "Yanzu kai ado saboda rashin sanin ciwon kai,wannan uban kudin haka ka dauka ka baiwa zuwaira?,yarinyar da zuciyarya ta riga ta mutu?" Baice komai ba illa "Inna Allah ya baki haquri,sai anjima,Allah ya qara lafiya" ya juya ya fice abinsa. Kamar jira take ya fita kuwa ta dasa bala'i da masifa kan umma da kaltum,kai bakace ita ke jinya ba,koda yake bahaushe yace sabo dayi......wai gawa da gatsine,kusan masifa da bala'i a jinin inna take,kaf jama'ar unguwarsu babu wanda bai sara mata ba,macace mafadaciya da kowa yasan da zamanta,uwa uba mutum ce ita maison abun duniya,wanda duk girma ko qanqantarka matuqar kana da abun hannunka to kaine mutum kuma abokin huldarta. Cikin sanyin jiki umma ta waiwaya ta dubi kaltum,ganin mitar innar taqi qarewa,muryarya can qasa tace da ita sanda inna ta miqe ta shiga bandaki,daga nan ma suna jiyo qananun mitocinta kamar ba'a makewayi take ba "Kaltume.....baiwa inna kudin nan" "Kiyi haquri ummanmu.....wallahi bazan iya bata ba" ta fada cikin qwarin gwiwar dasu fatsima suka bata "Ashe ban isa dake ba?" Umman ta sake fada,wannan karon kubra ce data cika tayi fam tayi magana "Umma,kiyi haquri,amma maganar gaskiya kaltume ta fi inna gaskiya,itafa inna maganar gaskiya hadamammiya ce kawai,umma saidai kiyi haquri,amma banda haka mu kanmu mama nawa ta bayar mu kawo mata?,amma da muka kawo ma gani take kamar mun rage wani abu ne a ciki,maimakon ma ta gode mana,maganar kaltum gaskiya ce,kada ta bada komai wallahi" shuru kawai umman tayi tana dubansu,ganin yadda suka hade kai suka daurewa kaltum qarqashi,a haka innar ta dawo daga bayan gidan,saita zauna tana duban umma "Tashi ki shiga madafi,akwai tukunya,ki zubomin naman dake ciki" duk da cewa akwai yara a wajen,amma bata sanya kowa ba sai ita,amma ita umman sam bata damu ba,hakanan bata kawo komai a kanta ko a ranta ba,kasancewar inna uwa ce,ta isa da kowa,ta kuma isa ta sanyasu kowanne irin nau'in aiki ne. Harta isa bakin madafar ta qwala mata kira "Kinga daukomin tukunyar gaba daya,don ban yarda dake ba,an dade ba'a gamu ba,kada aje yimin dauki ɗai ɗai,a qulle a gefan zani,a tafi dashi gida" sosai maganar ta daki kaltum,ta waiwaya ta duba ta tabbatar umman tasu ta shige madafar,saita kalli innar "Kinsan ai dama ana gadon hali fa",innar ba qaramar yarinya bace,hakanan da hankalinta ras,shekaru kuma ba qarya bane,ta fuskanci me kaltum takeson fada a fakaice,don haka cikin mamaki take kallonta "Kattume?,ni kike cewa barauniya?" Abun sai yaso bata dariya baya ga mamakin daya lullubeta,ashe dai abinda taso kiran tata mahaifiyar a gabanta kenan?,ashe dai abun babu dadi "Yaushe kika ji na fada haka?,ni?" Ta fada tana nuna kanta. Tun ba yau ba tasan halin kaltum sarai,cikin yaran zuwairan ita daya ce idan ka nunawa uwarta yatsa kokai waye saita lanqwasashi,don haka bata da mafita saita soma kwararawa umma dake qoqarin dauko tukunya kira "Zuwaira.....zuwaira,fito fito" tunda taji kiran ta tabbatar wani mummunan abunne ya sake afkuwa,banda Allah ya taimaketa saura kadan tukunyar ta subuce saman ciwon dake qafarta,ta daukota ta fito da ita ta dire gaban innar,sannan tace "Gani"ciki haki tsabar bala'i da masifar dake cinta ta soma nuna kaltum "Dama takanas kika dauko diyarki kuxo ta cimun mutunci saboda baki daukeni uwarki ba ko?" Cikin tashin hankali take duban innar "Inn...." Bata barta ta qarasa ba ta dora "Ni yarki zata kalla ta cewa barauniya?" A birkice umma ta maida dubanta ga kaltume,batayi wata wata ba ta shimfide yatsunta guda biyar saman fuskarta "Wallahi ummanmu bi ban fada ba,ga fatsima da kubra nan ki tamb....." Tsawa ta daka mata ba tare data barta ta qarasa magana ba "Tsugunna ki roqi gafararta,inna uwata ce da nake neman albarkarta" tabbas innar babu darajar wanda taci saita ummanta,ba zata taba iya musu da ita ba,don haka ta matsa kusa da ita ta bata haqurin,sai data maimaita sau uku sannan ta sauke kumburin da tayi tace ta haqura,tana direwa taja tukunyar naman gabanta ta budeta,sai umman ta juya da sauri tabar wajen ta nufi dakin innar,tana jin wani rauni da tausayi yana ratsata,tasan cewa tabbas akwai wani abu da ba haka yake ba,saidai bata isa ta tanka ba,a tsarin tarbiyyarta ma ba zata taba tankawar ba. Kayan sawar innae ta fara fitowa dasu masu datti,wanda ta saba kusan sunnarta ce,duk lokacin data xo gaida innar koda bata da cikakkiyar lafiya saita hada kayanta ta wanke mata,duk da cewa ita din bata wanki sam sam,kaltum ta dauke nauyin wankin kayanta,data wanke kuma bilal xai hada wuta ya goge mata,duk da cewa ba wani yawa garesu ba,ba kuma wasu tsada bane,a nata ganin tunda bata mallaki abinda innar keso ba,bata kuma da abin bata,ko yaushe bata farinciki da ita,wannan wala'alla shine abu guda da zata dinga yi wanda zai faranta mata. Tasha shan mita da qorafi a wajensu kaltum harma da bilal,bilal da kansa yace xai dinga zuwa a madadinta yana yiwa innar wankin harna da guga,amma tace sam,ai uwa batafi uwa ba,hakanan itama tana neman albarka,bugu da qari ba zata turasu suje su batawa uwarta rai a madadin wanki ba. Duk da cewa ko sau daya bata taba yaba mata ba amma bata fasa ba,idan taso ma wani lokaci tayita bin zannuwan tana cewa basu fita ba idan 'yan tsiyar a kusa suke,koda a gaban qannenta ne,idan basa kusa kuma ta tafas ba zata ce mata ba,har tayi ta gama,tayi mata sallama ta tafi,koda kuwa a gaban qannenta ne,a matsayinta na babba,wadda ita ta zamto diya ta farko a wajen innar,amma duk hakan bai taba sawa ta daina ba. Laifinta guda daya ne saboda bata da abun duniya,laifinta guda daya bata da komai bata mallaki komai ba,laifinta shine tana auren miji talaka ba mai abun hannunsa ba,hakan bai taba damun ummanmu ba,ta sani ta kuma yi imani Allah shike zartar da komai,shike azurta bayinsa aduk sanda yaso hakan. *ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,ZASU FARA ZUWAR MUKU CIKIN YARDAR ALLAH DAYA GA WATAN JANUARY 2022,GARZAYA MAZA KI BIYA NAKI KUDIN,DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA DUKA LITATTAFAN,KO KUMA WASU DAHA CIKINSU,ZAKI IYA TURA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA *SAIKI TURA SHAIDAR BIYANKI GA WANNAN NUMBER* 08184017082 *KATIN WAYA TRANSFER KO VTU KUWA,ZAKI TURA TA NAN NE* 09134848107 *DABI'AR ZUCIYA* *LAST FREE PAGES* 05 *ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,zaki iya biyan naki kudin ta hanyar tuntubar wadan nan numbers din guda biyu* 08184017082 Ko 09134848107 ______________________________ Jiki a sanyaye tabi tabayan umman nata sanda taga ta jibge himilin wankin innar ta soma jan ruwa,ta karbi gugan don taja mata,har ta qiya sai da kaltum din tayita mata magiya sannan ta sakar mata,tana ja mata ruwan tana tara mata zuciyarta na mata wani irin nauyi saboda tausayin umman nata,da dabara da wayo ta kama mata wankin suka dinga yi tare,saboda su samu su gama da wuri,tana jin innar nata jansu fatsima da hira bayan ta hanasu zuwa inda suke,suma basu sake wani jimawa ba suka yiwa innar sallama sukayi tafiyarsu gida,don duk cikin 'ya'yan qannen umman tasu sunfi shiri dasu kaltum din akan kowa. Bayan fitarsu saiya zaman gidan sai su yasu,innar bata sake kula kowa cikin umman da kaltum ba,sai qananun mitoci da taketa faman yi lokaci zuwa lokaci,wanda kusan fiye da rabi gugar zana ce baqar magana da habaici take yada musu,dukkansu sun fahimta,saidai babu mai ikon tankawa ko nunawa a cikinsu,duk da kaltum ta cika ta tumbatsa,amma dole ta lanqwasa zuciyarta saboda farincikin ummanta. Basu kammala ba sai da akayi sallar la'asar,don daga nan ma alwala suka daura,suka bada faralin saman shimfidar innar,wanda zuwa sannan ta tashi. Waiwayowa umma tayi tana duban kaltum "Ki tafi gida hakanan kije ki samu ki yiwa matar malam kitson,don nasan yanzu haka tana can tana jiranki" sam ko kusa ko alama batason ta motsa tabar umman tata a wannan gidan,saboda haka tace da ita "Ke kuma fa umma?"sai data shafa addu'a sannan ta bata amsa "Zan dan qara dakatawa saboda qila inna zata buqaci a dafa mata abinci" "Umma ma tafi tare,tunda ga kudin kawu ado a hannuna xamu iya amfani dashi koda baba bai kawo komai ba" kai umman ta girgixa "A'ah kaltum,ita sana'a aiba sai sanda ake da matsala ake nemanta ba,ba'a wasa da sana'a kaltum,tashi kije,saina taho" batason ta koyi yin musu da mahaifiyartata,don haka kawai ta miqe,ta karkade dankwalinta data shinfida ta daura saman kanta,ta maida hijabinta jikinta,sannan ta zira takalminta,duk yadda batason ta tafi tabar umman hakan dole xata tafin. Bata wani tsaya yiwa inna sallama ba tayi wuf ta fice don kada ma umman ta tsaidata,tana tafe ita daya iskar la'asar tana busata,tunani ne fal kwanyarta,fuskar ummanta kawai take hangowa,yadda suka wuni suna wanki amma koda wasa.....ko sau daya inna batayi musu tayin abincinta ba,duk da kalolin cimar da taketa fama da ita,kallo daya ta yiwa ummanta ta fuskanci tana jin yunwa,fade ne ba zatayi ba,saidai ita tana iya karantar haka a saman fuskarta. Bata isa gidan matar malam ba sukayi kacibus da nasiru,ya baibayeta da murmushinsa yana kallonta "Daga ina haka sarauniya?" Murmushi kawai itama tayi ta rausayar da kanta gefe "Naje duba inna ne?" Fuskarsa ta nuna alhini sannan yace "Ayyah,bata da lafiya?" "Eh wallahi.....amma dai da sauqi" "To Allah ya qara mata lpy....zanje na dubata idan na samu lokaci" tana son ce masa a'ah,to amma batasan da yaren da zata gaya masa ba wanda zai fahimta,bugu da qari ma batason xancan nasu yayi nisa,don tana son cika umarnin ummanta "Har zaki wuce da sauri haka?,bari na taka miki" ya soma motsawa da niyyar binta,saita dakata tana kuma tsaidashi "Da ka barshi ma,na gode....kawai inason shaida maka saqon umma ne" cike da bawa maganar tata muhimmanci ya fuskanceta "To...Allah yasa lafiya,me umman tace?" "Tace idan harda gaske kake,ka soma neman izinin baba kafin kaci gaba da tsaiwa dani" shuru ya danyi,kana ya gyada kai "Umma tayi gaskiya,in sha Allah kuma zanyi maganar,hakan shine dai dai dama" a nan sukayi sallama dashi,ta wuce,ya bita da kallo,tana sake burgeshi tare da shiga ransa,bugu da qari kuma zuciyarsa da ruhinsa cike fal da buri da fatan mallakarta. ********** Shuru gidan yake sakamakon dare daya shigo,bayan sallar isha'i ne,bilal baya nan ya fita,wanda dama yawanci bai shigowa gida da wuri,barci ne kawai yake maidoshi,kamar ma bayajin dadin gidan sam,fadi ne kawai da baiyi ba,habiba kuwa na zaure ita da yusufa,wanda tuni ya aiko aka nema masa izinin zuwa wajenta,cikin ikon Allah kuma sai Allah ya hada kansu da hankalinsu gaba daya,yusufa da iyayen nasa ma gaba daya ba wasu baqi ko boyayyu bane,kowa yasan gidansu halayyar mahaifansa dama na yaran gidan,dalilin da yasa baaban baiyi wani musu ko goce goce ba ya bashi izini kai tsaye,don dama shi din kamar yana neman hanyar da zai rabu dasu ne. Tsakar gidan daga ita sai umman nata,ita ta dasa farantin dake dauke da ragowar wata guntuwar shinkafa tasu tana tsinceta,don ita ce kadai abinda ta rage musu cikin gidan,itama cikin kudin da kawu ado ya basu ce suka siyota suketa ci da kadan kadan,sam abincin da mahaifinsu yake basu baya daga cikin abinda suke lissafa ko sanya rai,saboda babu tabbas din samuwar abincin,idan yaga dama ne ya kawo,idan baiga dama ba kuma ya barsu haka,sa nema suci. Hira suke jifa jifa da umman,tana magana ne kan bikinsu idan ya taso,ta sani bata da komai,kuma bata bawa kowa ajiya ba,juyayin da take nunawa kenan,kaltum dake tsintar shinkafa kanta a qasa tace "Babu komai umma,kiyi addu'a,Allah zai kawo da ikonsa" tana rufe baki suka hangi inuwa daga bakin qofar shigowa sassan nasu,hakan ya sanya kowa yaja bakinsa ya tsuke suna duban inuwar,ba'a cika minti daya ba wanda ke laben ya fado,mahaifinsu ne,duk da tsakar gidan babu wadatar haske amma suna iya ganin yanayin fuskarsa "Munafukai....zancan wa kuke?,munafurcina ko?" Waike zuwaira me yasa kullum ta Allah baki da qoqarin da ya wuce ki barar min da mutuncina a idanun yarana?....ke kuma annamimiya muna fuka,tashi ki koma daki!"ya dakawa katum tsawa,wadda batasan hawa ba batasan sauka,saita sauke farantin kawai ta miqe zuwa dakinsu kamar yadda ya buqata,batasan me yasa ya tsani yazo ya ganta tare da mahaifiyartata a zaune su biyu suna hira ba,koda yaushe yana ganin kamar idan suka zauna kamar hakan hirarsa sukeyi,abinda bai sani ba shine,umman tasu bata taba tattauna kuskurensa ko sakacinsa dasu ba,bata daga cikin irin wadan nan matan,hasalima kosu basu iya suyi qorafi a kansa ba,duk yadda suka kai ga shaqar baqiciki ko bacin ransa,tana horarsu da suci gaba da kyautata masa,ubansu ne,mahaifinsu ne,kamar jiya,datayi kitso ta samu kudi,ta siyo sabulu,ta dawo gida tana tattara kayan umman tasu da sukayi datti,amma ba'a samu damar wankewa ba saboda babu kudin sabulu,amma sai umman ta dakatar da ita "Kibar nawan,a wanke a gaba,ki debo na babanku,naga wankakkun nasa sun kusa su qare" bata isa ta musa ba,haka taje ta debo kayan nasa,duk da cewa dama can itace mai wanke masa kayan nasa,saidai ko idan wani dalili yasa bata yin ba,bilal zai dauka ya wanke masa,haka ta debo nashin,ta kuma qarar da sabulun kaf a kansu,saidai taci alwashin da zarar tayi wani kitson koda nata ba'a wanke suke,zata fara wanke na umman nata. Daga cikin dakin tana iya jiyo sababin da baban nasu yakeyi,wanda ita batasan dalilinsa ba,idanunta ta rufe gaba daya ta kwanta rigingine,tana jin yadda kullum kwanan duniya rayuwa ke sake musu nauyi da kuma tsanani,a zuciyarta....bilal da habiba su tafi tausayawa fiye da kan kanta,sai kuma mahaifiyarsu,tana jin da tana da iko da su zata fara tsamewa daga wannan rayuwar da suke ciki,ta kowanne fanni babu dadi,babu wata walwala babu farinciki,batasan iya tsahon lokacin daya kwashe yana sababinsa ba,sai shigowar habiba taji,hannunta riqe da baqar leda,ta aje gefan kaltum tana dubanta "Yaaya,kada dai ace har kinyi bacci" bata amsa ba sai miqewa da tayi ta zauna kawai tana duban habiban "Idona biyu,baba yana nan?" "Eh.....kamar yana dakinsa" "Umma fa?" "Tana bakin rijiya,ruwa take ja masa" ajiyar zuciya ta sauke,bakinta ya kasa furtawa habiba dake kallonta komai,har sai da ita habiban ta magantu "Baba ne ko?" Bata iya amsa mata ba,sai kai kawai data gyada mata,bakinta ta tabe "Ni ai gwara mutum kawai yayi aurensa ya huta da wannan rayuwar,yaaya gwara kawai muyi aurenmu,ko itama umma ta samu sauqin wasu abubuwan,tunda kinga ko banza zamu dinga taimaka mata da wasu abubuwan,sannan yusufa ma ni yace babu matsala,koshi xaya yimun kayan daki,don shi a nan kurkusa yakeso ayi komai" daga haka ta janyo.ledar ta bude,awara ce mai zafi mai uban yawa,sai qunshin tsire,sai rake wanda aka gyarashi fes,aka yankashi qananu "Kinga abinda ya kawomin" ta fada tana turawa kaltum ledar,kalla kawai tayi,saita saki murmushi tace "An gode" yusufa yana da qoqari,yana kuma da hannun kyauta,hakanan yana da kirki kamar yadda ake cewa mamansa ma haka take,sosai kaltume ke yiwa habiba sha'awar aurensa,a yadda kowa ke yabon halayyarsa,tana sanya mata ran cewa zata dace da gidan aure in sha Allahu. Matsantawa kaltum tayi,har sai data raba abun kashi hudu,nata dana umma dana kaltum din saina bilal,basuyi tunanin su raba da baban ba sam,saboda sun riga sunsan halayyarsa,yanzu akan wannan sai qilu ta jawo bau. ******* Karfe biyu da minti talatin da uku na azahar ta dage labulen dakin ummansu,wadda suke ciki ita da habiba sunata sauke kayan kwalla na mahaifiyar tasu,da tayi shawarar gwara ta saukesu ta saidasu tun yanzu saboda bikinsu,tunda ba wani abu suke tsinana mata ba "Umma na gama zan tafi" "To Allah ya kiyaye,kina gama mata ki dawo gida,kada babanku ya rigaki dawowa" "In sha Allahu umma bazan zauna ba" "Saikin dawo yaya" habiba ta fada,ta amsa mata tana sauke labulen kana ta doshi qofar fita daga gidan. A farfajiyar data hada sassan nasu ta samu baabar asiya da suke kira da baaba laure,a zaune saman tabarma,qaqashin inuwar bishiyar data baza rassanta a filin tsakar gidan,da alama sassan nata ya dauki zafi,da yake shi rana yake kallo,hatta da rumfar dake sashen idan rana ta take zafi take dauka,a nan kawai suke xama su samu iska da inuwa mai kyau,sabanin nasu sashen,da ya bawa rana baya,saidai dakunansu kawai su dauki zafin,amma banda tsakar gidansu,duk da cewar tun asali kowa a muhallinsa yake a zaune,amma baba laure sai data qalubalanci hakan,tace anyi ne da gayya ana sane aka bata nan din,saboda rana tayi mata lahani ita da yaranta. "Yar baqa mayya" taji baba lauren ta ambata,ta sani sarai da ita take,ta tsani sunan iyaka,kuma ita ta sanya mata shi,duk sanda ta tashi taji 'yan wulaqancinta a kusa haka take kiranta,tasha ce mata "Baba laure,ba suna bane me kyau,malam na makarantar asuba yace babu kyau mu dinga kiran junanmu da laqabi mummuna fa" saita rafka salati,tace tana son kiranta da jahila,ita zata yiwa kiɗifiri da iyayin banza da wofi,suna ne tun tana tatsitsiyarta ba xata fasa kiranta dashi ba,takan qara da cewa "Wannan inda kinyi karatun boko Allah ne kadai masanin abinda zaki dinga yi,to sai Allah yasa wadanda ba'a so din su sukayi bokon,kuma sha maka Allahu su zasu zama madubin gidan nan,ehe" baba laure wata irin macace mai.matuqar son kanta,da son 'ya'ya,son 'ya'yan ma har yayi mata yawa,itafa duk duniya yaranta sune kawai 'ya'ya,na kowa ma ya mutu,nata ya rayu,tunda ta taba zuwa cikin gari,taga yadda ake karatun boko,gidan da taje gidan qanwar qawarta ne data haihu,taga yadda suke karatun boko,taga manyan yaran gidan yadda suke,akace mata kowanne ma'aikacine,kuma boko sukayi,shikenan tunda ta dawo ta tasa baba iliya a gaba,ta dinga shirya masa zance,tare da nusar dashi romo da amfanin karatun boko,babu jinkiri ya gamsu,ya kuma yarda,suka ganganda dukkanin kudadensu suka tasamma sanya yaransu a makarantar boko ta cikin gari. Tun ba'aje ko ina ba suka ga ba zasu iya ba,basu da sauran zabi illa su dawo dasu makarantar boko ta cikin qauyen,wadda a qalla shekara ashirin da wani abu da ginata,fiye da rabin ginin makarantar ya zube,a qarqashin biyu suke karatun,nan fa manyan yaranta maza guda biyu,munzali da muxammilu suka ce sufa ba zasuyi ba,a barsu kawai suje kudu neman kudi,juyin duniya sukaqi fafur,dole ta haqura,saita karkatar da akalar burin nata zuwa kan babbar diyarta mace wato asiya,burinta shine asiyan ta zama wata tauraruwa kuma ta musamman abar kwatance akaf fadin karkarar tasu,a lokacin da suna qananunsu,idan kowa yana fadin abinda yake sha'awar yi ko xama tsakaninsu kaltum da asiyan,idan kaltum tace zane takeso,kuma fannin zane zane takeson karanta,baba laure kan karkace tayita ɓaɓɓaka dariya,babu ma sanda taji ummansu na cewa "To Allah yasa,Allah yasa ya zame miki alkhairi", takan ce " ban taba ganin mutane marasa sa'a a rayuwa ba irin zuwaira da yaranta,komai.naku ku a cabe yake zuwa?,banda tohewar basira me za'ayi da wani zane?,zanen 'yan aljanu fa?tabdi,da alama a haka zaku qare ko,ni ai asiyata babu abinda ya dace da ita sai karatun aikin banki gidan kudi,ko karatun inda za'a dinga haqo man fetur,tunda ance shima abune mai daraja"umman bata taba daga kanta dai dai da rana daya ta dubeta kota dubin maganganunta ba,ko sau daya ita wannan baya a lissafinta,addu'arta.....burinta dare da rana shine su samu mazajen aure na gari,shine tabbas!.....shine dahir!....dahir din da babu gaibu a cikinsa. Saidai abu daya da baba laure ta kasa fahimta,ta kuma kasa yiwa tufkar hanci,asiya tun tana qaramarta yarinyace maras kunya,bata da kunya ko qanqani,fadace fadace kullum yinsa akeyi da ita,dambe da maza ba sabon abu bane a wajenta,babu wanda take kunya ko tsoro,manyance a wajenta abun ba'a magana,maganganu kuwa idan tayisu saika dauka.macen aurenta ne,a sannan ana ganin a bakin mahaifiyarta da bata da kintsi take jinsu,musamman idan tayi baqi suna hirarsu,tun ana kallon abun a matsayin quruciya da tunanin zata daina,harya zame mata jiki,ta girma ta tashi a haka,sannu sannu kuma sai dabi'ar kwadayi ta shigi asiyan,wanda buri da son rayuwar jin dadi....da kuma son ganin ta kerewa duk wata sa'arta cikin qauyen suka haifar mata da hakan,dalilin kenan da ya sanya ta duqufa karatunta,duk da cewa bata da wata basira ko qwaqwalwa,idan kaga yadda take sakewa da malamanta,har wani lokaci suna wasan jakai kamar qananun yara xakayi.mamaki,wannan sake musun da takeyi ya sanya ko yaushe ita ce ke zuwa ta daya a ajinsu,don haka ma,saiya zamana bata wani damu da karatun ba,tunda zata zo ta daya,zata nunawa babarta,ita kuwa tayita tiqar rawa tana murna tare da yada habaici,shikenan tana ganin babu wani sauran damuwa,takanje makarantar sanda ta gama yawonta da xuwa duk inda zata,wanda kusan rabi amsar kudi ne daga hannun samari,wadanda saisun gama wasan banxa kamar wani miji da mata sannan su bata. Ko sau daya baba laure bata taba damuwa da ganin gilmawar kudi a hannun asiya ba,bayan ta sani cewa....ba ita ta bata ba,ba mahaifinta ne ya bata ba,tunda dukkaninsu basu dashi,ba wata sanaa suke ko takeyi ba,amma sam hakan ba damuwarta bane,musamman idan ta tashi buqatar kudi,asiyan zata ranta mata,kota bata kyauta. A hankali baba lauren ta fahimta samari ne ke yiwa 'yarta hidima,a maimakon shiga tashin hankali a matsayinta na uwa,tsaurara bincike da yanke duk wata alaqa,saita hau murna,ranar kamar zata taka kan shege,ta yiwa yarta kirari a filin tsakar gidan nasu "Kaga diyar da ba'a haifi kamarta ba kaf fadin qauyen ƊINYA,yarinya mai farinjini tamkar daren sallah,ah....ashe nidai na haifi mai sharen min hawayena ban sani ba,daa na qwallafa raina akan wadancan sakarkarun su muxammilu,wadanda saisunga dama zasu waiwayo gida su bani abinda sukaga dama,Allah ya karemin ke,ya tsole idanun maqiya" dukka wadan nan maganganun ta yisu ne sanda asiyan ta miqa mata danƙwaleliyar gasashshiyar kaza sukutum da guda,da sassanyar fanta,dukkan maganganunta kuma da umma take,wadda ta fito tana kwashe shanyar kayansu da habiba ta manta bata kwashe ba. Bata ce komai ba sai data gama ta kaisu sassansu sannan ta dawo inda baba laure take,ta yanke gaya mata gaskiya ne saboda girman zumunci da zaman tare,sannan ko banza JININ YARANSU DAYA,ko banza basu isa su cire jinin su asiya daga nasu bilal ba,har abada duniya ba zata daina kiransu da sunan 'YAN UWA BA!,ba tun yau ba,tasha jin gulmammaki akan asiyan da irin abubuwan da takeyi,sai Allah ya nuna mata sau biyu itama,amma bata taba tunkarar baba lauren ba,a tunaninta na kada ta daga mata hankali,tana shawarar kiran asiyan tayi.mata fada sai kuma akayi haka. Fara nade ledarta tayi ganin tahowar umman,duk da ta sani cewa ita din sam ba makwadaiciya bace,hasalima tana cika da mamakin yadda take da haquri da kuma wadatar zuci,duk da bata da komai,hakanan mijinta baya kula da ita,amma hakan bai sauya dabi'a ko halayyarta ba "Laure,ni a nawa tunanin,wannan abun da kikayi bashi ya kamata kiyi ba,ke uwace mace,wanda tasan ciwon yaranta,ya kamata ki fara sanin dawa dawa asiya ke tare dasu?,meye alaqar dake tsakaninsu?,idan aurenta suke da niyyar yi....." "Dakata zuwaira" baba lauren ta tsaidata "Babu alaqar dake tsakaninsu saita alkhairi,yarinyata kintsatsiya ce,kuma na yarda da tarbiyyarta,don haka kada.kizo min da wani qabli da ba'adi,farinjinin samari ne dai kawai da Allah ya bata,kuma koni ban isa na dakushe ba" saita kwashe kayanta tayi sassanta tana mita,zucuyarta baqiqqirin,kawai gani take babu wani babu wata,baqinciki zuwaira take tsagoransa,tunda ita kaltum kusan duk wanda yazo tafiya yake,habiba kuma a sannan bata tsaiwa da kowa,don tana ganin tayi quruciya,duk da cewa a qauye suke,amma ita tarbiyya idan za'a bada ita,babu alfanun duba yanayin muhalli,a bada ita kawai yadda ya dace,wannan shine abinda ke wakana a tsakaninsu da kalar halayyar asiya da.mahaifiyarta,wanda sannu a hankali abunda asiyan takeyi yake bunqasa ba tare da sanin lauren ba,tunda tun a karon farko taga goyon baya qarara daga mahaifiyartata,babu bincike ko.matsantawa cikin lamuranta,kudi takeso.....kuma tana kawo mata su,shikenan an wuce wajen 👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽. "Ke 'yar baqa dake nake" baba lauren ta sake fada cikin daga murya,sai kaltum ta dakata,ta waiwayo tana duban baban,ko kafin lauren ta sake samun sukunun yin magana saita jiyo sautin bilal tun daga zaurensu,hakan yaja hankalinta zuwa zauren da hanzari ba tare data sake sauraren lauren ba. Tabbas bilal ne,ya shigo futu futu dashi kamar wanda aka turbuda a qasa,yana dingisawa yayin da hawaye ke wanke masa fuska. A rude ta nufeshi ta kama kafadunsa tana kallonsa "Kai bilal?,meye haka?,lafiya me ya sameka?" Muryarsa a dakushe ya soma magana da qyar "Su musbahu ne,mun gama aiki an biyamu kudinmu,shine suka ce wai ba zasu raba dani ba,ni kuma nace saboda me,wallahi saisun bani kudina tunda haqqina ne,shine suka taru suka yimin duka,kuma don nace zan tona musu asiri ne,muna kwabin qasa suka kwashe kayan aikin suka boye,wai idan muka gama aikin zasu je su siyar su qara samun yawan kudin aikin" sosai ran kaltum ya baci,ba wanannan ne karon farko da suka fara dukan bilal ba,bama su ba,wasu mutanen da yawa cikin qauyen,saboda suna ganin kamar bashi da wani gata ko galihu,bata iya tanka masa da komai ba ta kamashi suka koma cikin gidan,tana jin baba laure tana dariya "Oh...aikin qwadago badai wuya ba,toh...mudai namu rabon yana jikin biro da takarda in sha Allahu,daga me yawon qwadago sai me gawon kitse sumar jama'a,suma dake cike da datti da annakiya,kai....itadai zuwaira bata iya haihuwa ba....hhhhhh" ta qarashe da dariyar dake nuna cikar nishadi da farinciki. Har tasa qafa sashensu saita tsaya cak saboda kalaman da kunnenta suka dauko mata,uwa uba dariya ta biyo baya daga bakin lauren da baquwarta abu,wadda kusan kome ke wanzuwa na samun goyon baya da asiya tayi da shawarar zainabun ce,wadda a kullum ita ke nunwa baba laure 'yarta me sa'a ce,ta barta,kada ta toshe musu kafar samu,duk maganar da mutane zasuyi zallar baqinciki ne,abun ke dorasu akan komai. Kaltum din zata iya jurewa komai amma banda taba qima da mutuncin mahaifiyarta,taba qimar mahaifiyarta shine abu na qarshe da mutum zai mata,koda kuwa shi waye,don haka saita saki bilal,ta dawo da baya,yayin da laure ta zuba mata idanu zuciyarta cike fal da taraddadin kada kaltum din ta yarfata,tunda tafi kowa sanin halinta kan mahaifiyarta. Bata tsaya ba kuwa sai data isa gabansu,idanunta cikin na baba lauren ta maida mata amsar data tashi hankalin baba laure "Ummata itace kuwa ta iya haihuwa,tunda ta haifi tsaftatattun 'ya'ya,babu me yawon bin maza.....babu kuma wanda ta bazama duniyar qabilu da arna neman abun duniya,yaranta na killace gabanta tana qoqarin basu tarbiyya da kulawa,duk da tsananun babunta,don haka babu haihuwar datafi wannan sa'a" saita juya abinta,tana sake dannar zuciyarta,saboda tana jin amsar data bayar dinma kamar bata isa ba,kamar bata isa ta wanke mata hucin da zuciyarta ke fitarwa ba. 06 *Kiji tsoron Allah☝🏽,karka/karki taba haqqin wasu,saboda akwai ranar biya,randa baka da abun biyan🤌🏾* *KI TUNTUBA WADAN NAN NUMBERS DIN DON SAMUN DAMAR KARANTA NAKI HANKALI KWANCE* 08184017082 KO KUMA 09134848107 ____________________________ _ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR FAMILY💯💯🙌🏽❤️_ _MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR ZUMUNCI_ _KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR YOUTUBE CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN ALKUR’ANI MA GIRMA_ _WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA KARARRWA DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE KWARAI💯🙌🏽❤️_ _GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN👇🏾_ https://youtube.com/c/sudaiskura _Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur'an at a very young age._ _Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairan🙏🏻_ ______________________________ "Kambu" ta furta da qarfi,wani irin zabura baba laure tayi ta durfafi kaltum dake niyyar shigewa sashensu,kafin ta ankara harta shaqo wuyanta ta fisgota baya "Ni kike zagi don u****rki kaltume?" Ta fada cikin hargowa da daga murya "Kibar zagarmin uwa baba" "An zagetan....ko zaki rama mata ne 'ya'yan kuka?" Ta sake fadi hannunta riqe da bayan hijabin kaltum,wanda tuni ya feke sanadiyyar fisgotan da tayi,dubanta take ranta na sake baci,yana kuma raya mata abubuwa da yawa akan baba lauren,batason tayi rashin kunya,kota aikata abinda zai sanya ran ummanta ya baci....kafin tayi tunani na gaba ruwan ashar ya fara fitowa daga bakin lauren,wanda ya sanya umma fitowa daga daki kusan a tare ita da habiba bayan sun saki aikin da sukeyi. Abinda ta gani din ya bata mamaki,laure riqe da hijabin kaltum tana dura mata ashariya,abu na tsaye abinta tana kallonsu hankalinta kwance. Cikin sanyin nan nata ta qaraso tana duban laure,bayan ta dauke kanta daga irin ruqon da lauren ta yiwa diyarta "Lafiya laure?,me ya faru?" "Bani zaki tambaya ba,tunda kin fini sanin komai,qila ma ke kika aikota tazo ta zageni"cikin mamaki umman tace "Zagi kuma?,kaltum?,ban baku irin wannan tarbiyyar ba" ta fada cikin takaici tana girgiza kai,ran kaltum ya baci,qiri qiri zata mata sharri ta bata ran mahaifiyarta,bayan itace silar faruwar komai?,saita fincike hijabinta daga hannun lauren,wanda hakan yasanya yagewar da yayi ya dadu,ranta a bace tace da umman "Don Allah umma kada ranki ya baci,ki koma ciki kawai ki zauna,ni ban zageta ba na rantse da Allah,magana ta gaya miki ni kuma na gaya mata zahirin abinda ke faruwa,wanda ita batasan dashi ba" anzo wajen umman ta fada a ranta,har kullum idan kaji fadan kaltum dama ko waye to an taba tane,bata fiya fada akan karan kanta ba,ta rasa yadda zatayi ta rabata da wannan dabi'ar,saidai wasu daga cikin mutanenta na yawan gaya mata,kaltum din haka take,haka Allah ya halicci wasu bayinsa,me kishin uwace,ba yadda zatayi da ita "Yimin shuru!,ni nafi kowacce halitta ne a duniya da ba za'a zageni ba?,annabin Allah ma aka zageshi wanda akayi duniya da lahira saboda shi,bare ni da ba kowan kowa ba?" "Don Allah ummanmu kizo mu wuce mu qarasa aikinmu" habiba ta fada cikin yanayin bacin rai,duk da rashin son maganarta sai data tanka,saboda ranta baqaramin baci yake ba idan har taga ana yiwa kaltum din fada alhalin ita keda gaskiya,mawuyacine kaga tana fada da wani a sanadinta,saidai a sanadin uwa ko 'yan uwanta,ko kazo mata da rainin hankalin da ba zata iya dauka ba. Maganar habiban saita harzuqa laure tahau zage zagen umman ta haifa marasa albarkar yara,ana fara haka habiba taja hannun kaltum don kada a sake batacciya zuwa ciki,babu jimawa umman ta biyo bayansu,bayan tayi tayi da lauren tayi haquri amma ta qiya,wanda sai data kwashi tijararta iyakar yadda ranta yayi mata sannan abu ta janyeta zuwa sashenta ta dora a can. Kaltum din na zaune gefe tana qoqarin saisaita kanta tana kallon yadda umman ta hadawa bilal ruwan zafi yake gasa jikinsa,sannan ta sanyashi ya shiga wanka,sai daya shiga wankan sannan ta waiwayo ya dubeta "Allah ya shirya min ke,ya kuma sawwaqe miki,shidai haquri maganin zaman duniya ne,kuma riba gareshi,ki tashi ki wuce inda zaki,bance kuma ki sake kula kowa ba,koda su musbahu kika gamu dasu bance ki musu zancan bilal ba" daga haka ta sanya kanta cikin dakin,sai kaltum din ta miqe,don itama zaman gidan ji tayi ya soma yi mata zafi,ta taka ta fice,har a sannan tanajin tashin maganganu daga sashen baba iliya,duk da baka gane ainihin me ake cewa. Harta xarta gidansu wasila saita yanke ta biya tacan ta rakata gidan kitson,da yake wani lokaci tana rakata,kuma wasilan na yawan qorafin yadda kullum itace a tafe gidansu kaltum din,amma ita ko kara batayi ta zo mata saida dalili. Taje kuwa a sa'a,donta isketa fes da kwalliyarta,da yake suna da yan uwa a cikin gari da suke bata kwancen kaya,ita kuma tayita gayunta da qwalisa dasu,tasha yiwa kaltum tayin wasu ma kan ta bata kyauta,amma sai tace aah,nata sun isheta,duk da cewa a kode suke,amma bata taba sha'awar karba ba,ta samo wannan qwarin gwiwar da wadatar zucin daga wajen mahaifiyarta "Qawata irin wannan shan kyau haka?" Kaltum ta fada wasilan na bata sha'awa,irin yadda ta samu kulawa daga wajen mahaifinta,duk da cewa tana talla amma ba talauci ne yasa take tallan ba,kawai sabo ne da kuma yanayin al'adarsu ta shegen neman kudi,ji take inama itace wasilar,wadda bata da wata matsala a rayuwarta. Murmushi wasila tayi "Kwalliyar bakarabe ce,yanzun nan ya tafi,Allah ne yayi ba zaku gamu ba" murmushi tayi tana dosana da wani dutse da mutan gidan ke zama kansa idan zasuyi alwala,sannan ta saki murmushi "Kullum.zancanki kenan,idan kinaso mu hadu ai takanas zaki aiko kirana duk randa yazo" wannan ba shine karon farko ba,don tunda wasila ta hadu da balaraben take baiwa kaltum labari,bata taba hadasu ba,saidai idan yazo ya tafi ta bata labari dariya wasila tayi "To kiyi haquri,zuwa na gaba in sha maka Allahu zan aika kizo kafin ma ya qaraso" "To Allah yasa"ta fadi cikin rashin baiwa zancan muhimmanci "Rakani kitso zakiyi dorawa don Allah" "To bari na gayawa babarmu" ta fada wasilan tana wucewa ciki da ledar hannunta,da alama balaraben ne y kawo mata wani abun. Bata fi minti uku ba ta fito tana ware mayafinta ta yafa saman kanta "Muje" tayi gaba kaltum na biye da ita a baya. Duk da yake ranta na abace ne amma tayi qoqarin sakin fuskarta,suna tafe suna hira da wasilan,wanda hakan yadan rage damuwar dake ranta,duk da komai yana nan daram cikin zuciyarta. Basuyi nisa ba ta hango nasiru tun daga nesa,shi dinma ya ganta,hakan ya sanya ya saki fuskarsa sosai yana jifanta da fara'a tun kafin ya riskosu. "Kinga wancan....dan bokon garin nan,sai murmushi yake mana" wasila ta fada tana washe baki,idanunta akan kaltum,shuru kaltum din tayi ba tare data ce komai ba,don nasirun yana gab dasu. Bai wuce minti daya ba kuwa ya riskesu,idanunsa akan kaltum din,har yanzu murmushi yake "Gimbiyata.....sai ina haka da ranar nan,anya kuwa kina jin zafin rana?" Murmushi itama ta saki,ba laifi nasurun ya iya magana ta nutsuwa kuma a tsare "Dole ce ta sanya hakan....,ina yini" "Lafiya lau gimbiyata....ina fatan kin wuni lafiya" "Lafiya qalau....." Saita waiwaya ta dubi wasila wadda ta zuba musu idanu tana kallonsu cikin mamaki "Ga wasila nan,qawata ce,kuma aminiyata,ku gaisa" da murmushi ya dubi wasila "Barka da warhaka hajiya wasila" qoqari tayi ta saita yanayin fuskarta sannan ta sake muryarta sosai "Yauwa....barka kadai,nasuru ko?" Kaiya gyada "Haka ne,ashe kinsan sunana" murmushi ta saki "Na sani mana,ai kusan yammatan qauyen nan dai dai kune wadanda basusan sunanka ba,saboda banbamta da kayi dasu ta fannin ilimi" fuskarsa yadan motsa a mamakance "Amma kuma cikin yammatan banda kaltum..." Saiya waiwaya yana dubanta,kafin ya dawo da kansa ga wasila "Sanda na santa ita bata sanni ba,har sai dana gabatar da kaina dakuma sunana" dan tabe baki wasila tayi "Idan ana magana ba'a sanyawa da kaltume,saboda kifin rijiya ce ita,daga daki sai tsakar gida,babu inda ta sani,ba wanda ta sani" murmushin farinciki ya saki "Ma sha Allah,haka akeson mace ta zama ai" kafin wani cikinsu ya sake cewa wani abu kaltum din ta magantu "Inaga zamu wuce,sauri nakeyi,nabar mutane suna jirana" saiya waiwaya ya maida hankalinsa gareta "To shikenan....amma yau zan samu ganinki?" Kaita kada "Gaskiya bana jin...." "To gobe fa?" "Allah ya kaimu" ta fada tana fara yin gaba,wanda hakan ya sanya wasila biyota suna sallama da nasiru. Shuru ne ya ratsa tafiyar tasu ya maye gurbin hirar da suka dinga yi a daxun,zuwa wani lokaci kaltum ta ankara,ta waiwaya ta dubi wasila,sai taga kamar yanayi fuskarta akwai damuwa,dama kuma ita ke qoqarin sanyo hirar tun daxu,kaltum din tayata kawai takeyi "Lafiya dai ko wasila?" Da sauri ta dubi kaltum din,sai tayi murmushi tana kada kai "Lafiya qalau...." "Naga kamar damuwa a fuskarki,wadda babu ita a dazun" shuru ta danyi kafin ta sauke ajiyar zuciya,sannan ta fara magana a hankali "Gaskiya bazan boye miki ba kaltume,banji dadin yadda kika boyemin soyayyarki da nasuru ba,a matsayina na aminiyarki,ace kun fara soyayya da nasuru amma ni ban sani ba,badon idanuna sun gani ba da sai yaushe kenan zan sani?" Hannun wasila ta kama tana murmushi "Haba qawata,ba'a wani dade bafa sosai" hannun nata tadan zame da qarfi "Ni ba abunda zaki gayamin,tunda ko na kwana daya ne aiya kamata na sani ko?" Dan jimm kaltum tayi tana mamaki,saita sake cewa "Kiyi haquri wasila,bansan zakiji babu dadi ba,amma hakan ba zata sake faruwa ba" "Shikenan,ya wuce" ta fada muryarta can qasa sosai,daga haka sukaci gaba da tafiya,saidai har a yanzun ma tafiyar kurame ce ba kamae dazun ba,hakan yasa kaltum take ganin kamar hucewa ne wasilan har yanxu batayi ba,don haka ta dinga qoqarin sanyo hira a tsakaninsu,da haka suka qaraso gidan. Jan tunga wasila tayi tana duban kaltum "Kaltume...kamowa zanyi gida fa" cike da mamaki kaltum ke kallonta "Gida kamar yaya?,lafiya?" Fuskarta tadan yamutsa kadan "Banajin dadin jikina ne" "To.....baya bata da kadan" kaltum ta fada tana dan yin jim sannan ta dora "Shikenan,Allah ya sawwaqe,ki koma din ki samu ki kwanta ki huta,idan na dawo zan biyo ta gidan na ganki,Allah ya sawwaqe" tana nan a tsaye har sai da wasila ta bace sannan ta saka kai gidan,zuciyarta duk babu dadi,musamman yadda suka taho tare kuma lokaci daya irin haka ta faru. Data gama kitson sai data biya ta gidansu wasilan kamar yadda tayi alqawari,Saidai ance mata bacci take,don haka ta yiwa babarsu sallama ta wuce zuwa gida. *_BAYAN WANNI BIYU_* A inda suka saba zama koda yaushe cikin tsakar gidan nasu suke zaune bayan sun idar da sallar magariba,ummansu na saman tabarma ita da habiba,kowanne lazumi yake,yayin da kaltum ta shimfida sallaya tayi tata sallar,kuma tuni ta idar,rashin wani abu da zatayi ya sanyata dauko pencil ruler da farar fefa da usaina 'yar maqotansu ta bata kyauta,ta zauna sosai saman daddumar yadda zataji dadi,saita zubawa takardar idanu tana tunani,xane takeso tayi,saidai ya rasa me zata zana,murmushi ta saki samda zuciyarta ta bata shawarar zana duk abu na farko da yazo kanta,sai ta sake sakin murmushi karo.na biyu,ta duqa a hankali ta ware takardar ta soma zanen cike da nishadi,tana kuma rayawa a ranta,daga wannan karon duk abinda ta zana din zata dinga ajjiyewa ne,tana gani itama tana tunawa,bata mantawa,cikin irin hirarrakin da sukeyi da nasuru,sanda ya taba ganin wani qaramin gida irin nasu na karkara data zanawa 'yar maqocinsu,ya shaida mata cewa shi kansa zanen wani babban ilimi ne me zaman kansa da ake karatu a kansa,sai tayita mamaki tana jinjina abun,hakanan saita samu kanta da kwadayin inama ace zata samu wannan damar,ba shakka tana qaunar zane,kuma idan har zata samu dama,ko kuma a bata zabi,shi zata karanta kamar yadda nasuru ya shaida mata "Inda ace ni wani ne,da bayan munyi aure,saina kaiki wannan matakin da zaki karanxi zanen" duk da ba cewa yayi ya dauki nauyi da alqawarin sanyata tayi karatun ba,to amma iya lafuzansa kawai sunyi mata dadi,harta kasa haquri sai data tanka "A hakanma na gode qwarai da gaske,tunda ka bani labarin wani abu da bansan da wanzuwarsa ba a duniya,idan da rai da rabo,matuqar ina da rabon sai kaga wataran nayi" wannan ce amsar da ta bashi. A hankali suka fara jiyo sautin murya,kamar fada fada kamar zage zage,dukkansu sukayi sak,kowa ya tsaya da abinda yakeyi,jin cewa muryar asiya ce,kuma sassansu take dosowa. Ba wani jimawa ta bayyana a qofar shigowa sassan nasu,ta tsaya ta kama qugu,tana iya hangen duk wanda yake tsakar gidan,maganganu take fada na rashin kunya da rashin mutunci akan kaltum,wanda duka kan abinda ya faru ne dazu "Munafuka algunguma,ina bacci anamin munshari,jahila kawai,wadda bata taba shiga aji ba,to wallahi duk munafurcin mutum saidai yayi ya bari,don ni na tserewa sa'a,na kuna wuce ajin mutum,hakanan aibantawar mutum b zata mana komai ba ehe,mun sha tabara mun sha yasin,mun kuma sha rigakafin Allah Ala tsine". Duk da kalaman asiyan sun mata zafi,duk da ranta ya baci amma bata daga kanta ta kalleta ba,sai kawai taci gaba da zanenta,hakan ya sanya taci gaba da zage zage cike da rashin mutunci. Wannan karon habiba ce ta gaza daurewa,ta miqe tsaye tana duban asiyan daga inda take tsaye "Ke asiya dalla ki shiga hankalinki,saboda kinga an miki shuru shi yasa zakici gaba da rashin mutunci?,ki tako har cikin gida kice zaki mana rashin mutunci,kema kinsan wallahi baki isa ba,banda darajar wasu da kike ci" "A hayye,ai so nake na daina cin darajar wasun,idan an gaji a dauki mataki a kaina kawai,tunda tsohuwa na zaune ko?,to bari kiji,wallahi bana tsoron ta mutu balle tayi rai,ko ita ta shiga hurumina bazan raga mata ba,ni babu datajar wanda zataci a wajena....yo ina ma masu darajar suke da zataci ta?...." Ai kaltume batasan sanda ta zubda abun rubutun dake hannunta ba,tayi fatali tabi ta kansu,cikin wani irin gaggawa da sauri wanda babu wanda ya kula dashi ta isa gaban asiya,sai jin saukar wani lafiyayyen mari taji saman fuskarta,wanda ya sanyata ganin wulqawar wasu taurari gami da daukewar ji da ganinta na wani lokaci,kafin daga bisani komai ya dawo dai dao,sai sannan ta tsinci muryar kaltum cikin tsananin fushi tana bata gargadi a kausashe "Nan gaba idan tashen iskancinki ya tashi,qwaqwalwarki ta sake gaya miki kizo ki tabamin mahaifiyata!"kiran sunan yayi dai dai da sanda umman ta qwalla ma kaltum kira,hankalinta a tashe,don ita din babu abinda tafi tsana irin tashin hankali,cikin tsawa umman tace "bar wajen nan kafin na qaraso nayita dukanki a wajen" ta idar da abinda ta niyyata,don haka ta juya da niyar komawa mazauninta,saidai ina,tuni asiya tayi wani kukan kura takai mata cafka,cikin qaraji tana fadin "Wallahi baki isa ba,ba zaki daki banza ba" ta danqaro ashar ta makawa umman da kaltum,wanda hakan ya sake harzuqa kaltum din,ta waiwayo ta dumfari asiya,take kokawa ta barke a tsakaninsu,soma qoqarin miqewa umma tayi cikin dabara saboda ciwon dake qafarta,tana umartar habiba kan ta rabasu,saidai habiban gefe ma taja abinta tana shan kallo,don tana da tabbacin yau dai za'a dan fiddawa asiya raini,wanda kafin umman ta samu zarafin miqewa takai dauki kaltum din ta daki asiya sosai kuwa. Dai dai sanda take rabasun baba laure ta fito,saita soma ihu itama tana son rabasu,wanda fiye da rabin rabiyar taimakawa asiya take wajen dukan kaltum,cikin ikon Allah Allah ya jefo malam amadu mahaifinsu kaltum,wanda yana shigowa ya daka musu tsawa,take kowa ya tsaya cak,sannan ya fara neman ba'asi. Take asiya ta sake rakwarkwabewa fiye da dukan da akayi mata,ta saki kuka mai qarfi ta fara rattabo bayanan qarya,take malam amadu ya gasgata hakan,don ko sanda ya shigo din kaltum na riqe da asiyan ne. Baiyi wata wata ba ya kaiwa kaltum dake tsugunne a gabansa mari,ya kuma sameta sai tau a fuskarta,take shatar yatsunsa suka samu muhalli a kumatunta,inda ace fara ce ma babu abinda xai hana a gani a haske farin watan daya dallare ilahirin tsakar gidan "Wacce irin 'yar Allah bani ce ke na haifa?" Kalmar data fara fita a bakinsa kenan,wadda ta sanya umma rintse ido,saita juya a hankali don komawa cikin sassan,don dambe ya fito dasu ne har filin tsakar gidan nasu. Ta zabi komawa ciki ne,don kunnuwanta ba zasu iya jure mata jin kalaman da ya fara furtawa ba,wanda tana da tabbacin cewa,tunda ya fara da haka,Allah ne kadai masanin sauran kalaman da zasu biyo baya. "Ni na gaji dake,na kuma gaji da halayanki,nayi na Allah nayi na ma'aiki,shekarunki sunkai ki tafi gidan mijinki dama kije can ki qarata....ko.kasheki ma zasuyi ke kika so,yau din nan na bada 'yar uwarki habiba ga yusufun malam baffa..... Saboda haka na baki nan da kwana uku rak!...ki gayawa duk wanda yake zuwa wajenki,koda bai shirya ba ya fito,ya tanadi sadaki kawai,idan ba haka ba kuwa,zan bawa duk wanda naga dama" daga haka ya juya yana baiwa asiya haquri,wadda ta saki baki taketa sharbar kuka fiye da dukan da akayi mata,itadai kaltum tunda ta dafa qasa ta miqe zuwa ciki,ta samu takai kanta dakinsu,bata sake bi takan komai ba. *HALIN GIRMA*             7 *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*  I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb *** Kukan ta ne yake karuwa Mama na tsaye a kanta, ta ja tsaki tace "Bana son shirman banza kina ji na? Akan namiji zaki zauna kina rafka wannan kukan kamar uwarki ce ta mutu ko ubanki?" "Mafita nake so mu samawa kanmu, saboda anga zaki huta shine aka shiga aka fita ake so ayi mana bakin ciki, idan ba haka ba, me ya kawo wadannan zantukan?" Cikin kuka tace "Wallahi Mama nasan Iman ce taje ta samu Gaji da maganar tunda dama ita yace yana so ai, shine dan taga wanda yazo wajen nata talaka ne shine zata min bakin ciki, toh wallahi babu wanda ya isa ya hanani auren Bashir, naji na gani kowanne hali ne dashi." Shiru Maman tayi tana kallon yar ta ta, idan har ta bari maganar ta sha ruwa akwai matsala, sanin cewa Zeenat din ba wani farin jini bane da ita, dama dai jamaar Iman din ne tun farko take sanin yadda zatayi, dole ta san abinda ya kamata amma duk da haka ba zata nunawa Zeenat din komai ba " Kina jina? Ki tashi ki tafi dakin ku, ki daina wannan kukan tunda ba ubanki bane ya mutu, zan san yadda zanyi komai ya daidaita." Da bayan hannun ta ta goge kukan, ta fice tana rangaji, tana sake kudurewa a ranta babu gudu babu ja da baya a auren ta da Bashir din.   Tana isa daki ta tarar da missed calls din sa, ta bi kiran da sauri tana sake daidai ta kanta. " Gani a waje." Yace tana dagawa. " Mu hadu a bayan layi akwai matsala karka zo gida." " Me ya faru?" Yace a kidime. " Babu komai gani nan zuwa." Kashe wayar ta, tasan zai ta tambayar ta menene gwara kawai taje suyi magana su sama wa kansu mafita dan ba zata iya hakura dashi ba.   Ficewa tayi ta kofar kitchen bayan ta gyara fuskar ta, ta bar gidan cikin sauri tana tsoron haduwa da Ya Habib ko wani.   A chan bayan layin ta hange shi jikin motar sa, a tsaye yake yana ta jijjiga jikin sa daga gani baya cikin nutsuwar sa, tana isa ya juyo da sauri. " Lafiya baby?" Yace yana riko hannun ta. Kuka ta saka da sauri yace " Na shiga uku, me ya faru?" " Abba ne yace wai na rabu da kai, wai yayi bin..." " Shisshsh..." Yace da sauri yana dora hannun sa a saman bakin ta " Kinsan dai hakan ba gaskiya bane ko? Sharri akayi min ko menene akace domin a hana mu aure, duk wanda ya yi min wannan sharrin na bar shi da Allah kawai." Yace yana girgiza kansa " Shikenan yanzu rabuwa zaki dani? Nasan rayuwata shikenan ta kare, idan har zaki iya yarda mahassada su shiga tsakanin mu, bakya so na baby, rayuwata shikenan ni." " Ni ban yarda da duk abinda akace ba ai, kawai sharri ne na sani, amma ya zanyi da Abba? Bayan shi din kaifi daya ne akan maganar sa." " Dan Allah Zeenat karki yarda a raba mu, wallahi Ina sonki , bansan ya zanyi da rayuwa ta ba idan har baki aure ni ba." Hawaye ya fara yi tayi saurin sa hannu ta goge masa "Zanyi duk yadda zanyi, ba zan bari a raba mu ba..." " Da gaske? Kinyi alkawari?" " Nayi maka alkawari." " Dan Allah karki saba alkawari dan Allah, ki taimaka wa rayuwa ta, kinji?" " Karka damu." Tace tana jin wani karfin zuciya, " Ba zan taba yarda su yi min abinda bana so ba, Kai nake so kuma duk yadda kake ina son ka a haka.* "Nagode nagode baby, in sha Allah ba zakiyi dana sanin amincewa dani ba." Zatayi magana wayar sa tayi kara " Sorry." Yace mata kafin ya daga yana rage volume din wayar sosai " Malam tun dazu nake jiran ka, ka dawo min da mota zan fita, wai ina ka tsaya ne?" " Gani nan yanzu in sha Allah." Ya kashe kiran ya ce " Baby bari naje, urgent call daga Baba, zamuyi waya kinji?" " Tam shikenan." Tace a sanyaye " Yawwa ga sakon ki..." Ya bud'e murfin motar ya fiddo da ledoji, hannu tasa ta karba tayi godiya, ta juya ta soma tafiya shi kuma ya shiga motar ya tada ita da sauri ya bar wajen, yasan ba zasu kare kalou ba da ita, amma kuma hakan shine kadai zai kankaro masa mutuncin sa. ***Daki ta koma ta ajiye ledar bayan ta bud'e taga ice cream ne da Pizza, sai charger waya da yake ta lalace ta ta, sai wasu tarkachen alawoyi. Bata taba komai ba sai charger din ta jona wayarta a jiki sannan ta fice zuwa bangaren Gaji dan ta samu Iman a yi wacce za'a yi.    Iman din ce kuwa kadai a falon tana karanta hisnul muslim. Sai ganin mutum tayi a kanta, bata tanka mata ba ta sauke kanta ta cigaba da karatun ta kawai. "Saboda kina bakin ciki kin samu fakiri talaka shine zaki kai munafurci kice Bashir bashi da hali ko?" "Wacce irin magana ce wannan Zeenat?" " Malama karki pretending kaman baki sani ba, idan bake kika fad'a ma Gaji wata magana akan Bashir ba waye ya samu Abba ya fad'a masa Bashir bashi da hali me kyau?" Tashi tayi zaune tana kallon ta, ta girgiza kanta kawai kafin tace " Kinsan bani da lokacin batawa akan irin wadannan maganganun, dan haka please bana son maganar." " Zaki ce bakya so mana kina min bakin ciki, toh wallahi sai dai ki mutu da bakin ciki amma aure na dashi babu fashi, kije chan kiji da wanda zaki aura, mutum kamar shi ya kawo talauci duniya." Tashi kawai tayi ta bar falon zuwa bedroom din Gaji dan ba zata iya irin wannan shirmen na Zeenat ba, sai dai da gaske maganar ta taba ta, har taji ta rasa gaba daya walwala da farin cikin ta, kwanciya kawai tayi ta rufe idon ta tana hasaso rayuwar ta nan gaba! ***Cikin shigar Khaki pants da wata jibgegiyar rigar sanyi da ya saka a saman armless rigar sa ya fito, kansa da yake a kwance yasha gyara ya tsaya yana sake dubawa a katon mudubin da yake ajiye a falon, yasan Takawa zai saurare shi ya kuma bi abinda yake so sai dai baya son ko kad'an karya ko wasa ya shigo a cikin maganar auren sa. Kallon kafar sa yayi, sai ya koma ya sauya takalmin zuwa wani daban sannan ya fice yana tura hannun sa cikin aljihun dogon wandon nasa.    Suna tsaye k'yam suna jiran fitowar sa, kowanne su cikin shigar da take nuna shi din waye, bud'e masa motar akayi da sauri ya fad'a yana makala bakin glass din sa yasan yau zai same shi a wajen hutawar sa, in da ya dace da maganar da zasu tattauna, shiyasa ma yayi shigar sa da yasan Takawan bazai masa surutu ba, dan ya riga ya san shi, ko yace kowa ya san shi da tsanar manyan kaya musamman a lokacin zafi sai yace wai takura masa suke.    Da yake sun san in da zasu, kai tsaye suka wuce dashi Family house din, in da Takawan ke hutawa a duk ranaku irin wannan ba tare da shigowar wani shaani na mulki ba. Iyakar abinda ya shafi kansa da iyalin sa kawai yake tattaunawa a rana cikin saukakakkiyat shiga da ba zaka taba cewa sarki bane duba da ko yaushe yana nannade cikin rawani da manyan kaya.    A kofar wajen motocin nasa suka tsaya, ya balle murfin tare da me bud'e masa ya fito yana kallon ko ina na harabar gidan. Kansa sanye da hular sanyi ya cire glass din idon sa ya shiga takawa zuwa ciki. Gaisuwar da ya tsana ya dinga kokarin kaucewa har ya dangana da inda takawan yake ya hange shi a zaune a cikin wajen yayi matashi da pillow yana kallon yadda yan yaran da suka kasance jikokin sa ke wasa a wajen.    Sarkin dogarai ne ya fara ganin shi,ya washe cikin farin cikin ganin shi yace "Maraba da Yarima!" "Sarkin dogarai..." Muryar sa ta saka takawa d'agowa, ya gyara daga gishingid'ar da yayi, ya fad'ad'a fara'ar fuskar sa da tayi ma Moh iso har gaban kakan nasa. Russunawa yayi cikin girmamawa ya kai gaisuwa, hannu ya mik'a masa ya matso kusa dashi sosai, ya shafi saman kansa " Sai yau kaga damar leko ni ko Muhammadu?" " Tuba nake Takawa, ayyukan ne suka yi min yawa." " Toh madallah, naji kace kana son gani na, toh gani ya akayi?" " Dama magana ce akan abinda Bubu yayi maka magana." " Auren ka? Jairi toh sai akayi yaya?" Dariya ya saka sosai " Toh kunce sai nayi aure yanzu kuma nazo da maganar kuma, sai na fasa auren ma gaba daya." " Fasa mana, waya yayi asara? Kaji dan nema." Dariya suka saka a tare, kafin Takawa yace " Toh sai ka fadi a inda yarinyar take ko? Idan yaso sai a nemi iyayenta." " A ah ni dai Takawa, ayi min aikin gafara a bari a samu wasu suje su nema min auren ta." " Wasu?" Yace yana kallon sa " Eh a dangi haka ba, ba manya sosai ba, Ina nufin ba cikin manyan masarauta ba, yan chan kasa kasan dai." " A wanne dalili?" " Kawai ni bana so suji tsoro su ga kamar mun fi karfin su." Girgiza kai Takawa yayi " A neman aure babu boye boye Muhammadu, a sak dinka zaka je, kai ne fa jika na farko a gidan nan, sannan a wajen mahaifin ka, wanne irin tunani ne haka ya shiga kanka?" Sosa kai Moh yayi yana marairaice fuska "Ni dai dan Allah takawa, a bar wasu suje." "Sam sam kaima kasan hakan ba mai yiwuwa bane, dole ne su san kai din daga gidan da ka fito." Shiru yayi yana jin kamar ya daure kansa da ya budewa Takawa zuciyar sa, yasan shi sarai da tsayawa akan ra'ayin farko, amma yayi tunani zai fuskance shi duba da irin son da yake masa, dama Musaddik ya gaya masa, babu me yarda da shirmen sa kamar yadda yake jaddada masa a kullum, babu me biye masa ko bashi goyon baya. Tun daga lokacin yasan sarai babu me tsayawa ya saurare shi, balle ya yarda da tsarin sa. Ammin sa ce kadai itama bata ja da maganar Takawa, ballantana Bubu da baya iya aiwatar da komai sai abinda Takawa din yace.    "Kana jina Muhammadu, maganar da kazo da ita bata kamawa bace. A tsari na gidan nan ma zamu iya aika musu suzo nan din domin muna da damar bada diyar tasu, sai dai ba zamuyi haka ba, zamu basu girman su da darajar su in Sha Allah, za kuma musu duk abinda Muhammad yake so amma banda shiririta." Ya karashe yana murmushi, murnushin shima yayi kawai ba tare da yace komai ba. Suka cigaba da hira irin wadda suka saba har be san iya adadin awoyin da ya bata ba, sai da suka ci abinci da Takawar sannan ya lallaba ya shiga gidan ya gaida matan gidan ya kare a dakin kakarsa ya tarar da yan matan family din sunzo suna da wani get-together da suka shirya sannan suyi maganar tsari bikin Abidah guda daga cikin jikokin gidan.    A kaidar sa baya sakar musu fuska ko kad'an domin suna da rainin hankali sosai, duk da shi basa yi masa neman ma ya kula su suke amma shi sam baya tsayawa shirmen su, da gaske suka shakkar shiga shirgin sa hakan yasa yana shigowa shashen suka dinga yayewa da d'aya d'aya.   Dan tsiririn tsaki yaja sanda suka gama ficewa ya zauna yana muzurai a dole baya son raini shi. Mutane da yawa na fad'a masa yadda yake abubuwan sa kadai ya tabbatar da shi din jini ne na sarauta amma shi sam be san ma yana yi ba ma.    Ya dan jima a wajen nata kafin ya tafi yana jin zai dan dade kafin ya sake waiwayo su duba da tafiyar dake gaban sa akan aikin sa. ***Yana zaune a gate din gidan yana dakon shigowar Abba Babban, a kan idon sa ya dawo ya tashi da sauri ya tare shi ya bud'e masa kofar mota. "Sannu da zuwa Abba." "Yawwa Ibrahim, kaine yau a gate din kenan." " Wallahi kuwa Abba, sannu da dawowa, ya aiki?" " Alhamdulillah mun gode Allah, ya naka aikin?" " Alhamdulillah." Yace yana tuna abinda ya faru dashi. " Allah ya taimaka ya bada sa'a." " Amin Abba." Yace yana bin sa rik'e da jakar sa a baya. " Mika jakar ciki bari na fara gano Gaji." Yace yana bin hanyar da zata kaishi bangaren Gajin, da sauri Khalil din ya kai masa jakar ya dawo ya zauna yana jiran ya fito. Ya dan jima a wajen Gajin kafin ya fito sai dai ganin Khalil ya saka shi mamaki, abunka da Babba nan da nan ya gane akwai wani abu. " Ya akayi Khalil? Kana son gani na ne?" " Eh Abba." Yace yana sosa kansa " Haba ko da naji, toh zan turo a kiraka kaji?" " Toh Abba Nagode." Girgiza kai Abban yayi ya wuce bangaren sa. Maimakon ya koma gida sai yayi zaman sa anan yana jiran kiran Abban. Yana zaune kuwa yaga fitowar Sadik ya tashi da sauri ya tare shi "Yawwa wai kazo in ji Abba." Rik'e hannun sa yayi suka koma yana jin wani iri a ransa, bakin sa dauke da addu'a ya shiga falon ya tarar Abban ya chanja kaya yana zaune da alama abinci ya gama ci. A chan gefe ya zauna yana jin kunya. "Yawwa ina jin ka Ibrahim, ya akayi?" Shiru yayi yana tsara yadda ya kamata ya ce, sai da ya dau sakanni yana hado maganar kafin yace "Dama Abba akan maganar Fatima ne." "Uhum ina jinka. Ya akayi?" "Dama... Dama so nake dama a bani dama kamar yadda tsarin gidan nan yake." Murmushi Abba yayi cikin jin dadi yace "Masha ALLAH naji dadin wannan abu matuka, Allah ya tabbatar mana da alkhairi kaji? Allah yayi muku albarka." " Amin Abba." Yace a ciki-ciki farin ciki na kamashi, " Kaje ku daidaita idan Allah yayi mu haka muke so, an riga an zama daya ai in sha Allah babu wata matsala." " Nagode Sosai Abba, Allah ya kara girma." " Amin." Yace yana chanja tasha a tv, shiru Khalil din yayi kafin ya mike " A huta lafiya Abba." " Yawwa Ibrahim." Yana fita ya daka tsalle a wajen yace "Yes!!" Da sauri ya bar wajen yana jin kamar ya same ta ya gama ne, zai nuna wa fakirin saurayin ta cewa dan gida yafi bare. ***Sabon yadi ne me saukin kudi sosai, dinkin ma irin dan 1500 din nan ne, a rayuwar sa be taba hasashen saka ire-iren kayan da yake sakawa a yanzu ba, wani kallo Musaddik yake masa yana jin kamar ya kamashi yayi ta bugu. "Yanzu Moh irin kayan da zaka saka kenan zaka ganin sirikin ka?" "Wait and see." Yace yana kawo wata leda a kusa dashi, ya wurga masa yana cigaba da kallon kansa a mudubi "Ka chanja mu tafi idan yaso muyi sallar magriba a hanya sai mu karasa." "Na saka me?" Musaddik yace da sauri yana bud'e ledar. "Wait what! Kana nufin ni zan saka wannan kayan." "Mu nawa ne a dakin nan?" "You must be kidding me, haba haba an fad'a ma kowa ma irin ka ne." "Allah su zaka saka mu tafi, kayi sauri karka batan lokaci I'm dying to see my love." "Aiko sai dai ka tafi kai kadai wannan karyar ba dani ba." "Da wa toh? Wa nake dashi bayan kai? Kasan da ace ban samu kanta ba dole kaima ka tattaro ka dawo sabon shagon nan dana zauna mu zauna tare. Allah dai ya taimake ka wallahi." " Ai wallahi babu yarinyar da ta isa nayi mata irin wannan son, the whole you, Captain Muhammad Ahmad Santuraki, dan ga sarki jikin sarki sannan kuma babban soja, ko da yake fa dama ance ku sojoji baku iya soyayya ba, musamman idan allurar ku ta motsa." Daina abinda yake yayi ya matso kusa dashi " Idan bansa an saka min kai frog jump ba, kace ba suna na Muhammad ba." Dariya maganar ta bawa Musaddik, " Ni zaka saka frog jump?" " Sosai, ka cigaba da batan lokaci kaga." Tashi Musaddik yayi ya sake daga kayan, kafin ya fara sawa yana cigaba da mita. " Kanka akeji wallahi." Moh yace yana cire agogon hannun sa. " Ka cire watch dinka please, anything da zai sa ta zama suspicious, I don't care idan kowa na gidan su yasan ni waye, amma ita? Da marikiyarta will be the last da zasu sani, surprise ne me kyau nake son basu dukka, sai dai kowanne da yadda surprise din zai zo masa." " Wicked soul." Musaddik yace yana jefar ta watch dinsa akan mirrow " What ever!" Yace yana yin gaba yabi bayan sa yana jin dadin kayan jikin sa, babu nauyi shawai shawai amma kuma ba zai yarda Moh din yasan ya ji dadin kayan ba. A daidai shagon aka daajiye su, yace su je chan in da suka saba jiran sa su jirashi zai kirasu. Duk da basu so ba amma haka suka tafi suka barsu, Musaddik ya dinga jan tsaki suna tafiya a k'asa har suka isa kofar gidan. Wayar sa ya ciro ya kira ta, tayi ta ringing bata daga ba, " Bata daga ba." " Da ka kirata tun kafin muzo ai." " Wannan ba matsala bace, bari kaga." Ya kwankwasa gate din kafin ya dan tura shi suka shiga, dai-dai lokacin Khalil ya taho zai fita sukayi kichibis, wani kallo ya bisu dashi irin na sama da k'asan nan, kafin ya tuntsure da dariya sosai, hakan yayi bala'in bata ran Musaddik da dama chan baya daukar nonsense. " Malam lafiya zaka kalle mu kayi dariya?" " Lafiyar kenan, sai dai kun makara, dan gida ya shiga ya fita ya gama tabbatar da komai akansa, sai abi wani sarkin dan an riga an gama magana kuma su din ba kananan mutane bane da zasu sauya maganar su." " Kana nufin?" Musaddik yace a zafafe " Ina nufin kamar yadda na fada mishi ne a baya, Iman matata ce an riga an gama magana rana kawai ake jira a saka mana." Wani kallo Moh yayi masa da ya saka Khalil shan jinin jikin sa, amma sai ya dake ya cigaba da gaggayawa musu magana. Muhammad be ce komai ba har ya gama, ya juya ya fice ya barsu a tsaye kamar mutum mutumi. " I have no option than to show him my real identify, idan yaso duk abinda ya biyo baya yayi kuka da kansa ba da kowa ba, karfe nawa ne appointment dinsa?" " Da safe ne, goma kamar." " Owk Allah ya kaimu." " Amin." Musaddik ya amsa ransa na sake baci akan abinda Khalil din yayi musu HALIN GIRMA Hafsat Rano WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 _*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar . ___________ 08 *zafafa biyar na kudine,tuntubi wadan nan numbers din don samun naki copy din ki karanta cikin aminci* 08184017082 Ko 09134848107 *_follow us @ instagram_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1h9y2qgfg67x5&utm_content=nj79azb Or facebook https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share ___________________________ Dan kwantar da kujarar yayi kana ya miqe sosai Samanta yana jin yadda gajiya take bin jikinsa,don gaba daya wunin yau bai shirya fita ba,ya shirya zama ya huta sosai a gida,saboda satin gaba daya cikin aiki ya yisu,babu dare babu raba,har inda ma a tsarinsa babu schedule na zuwansa sai daya ratso masa a sannan din. hannayensa saman kansa yayin da idanuwansa suke a rufe,yayi nisa a tunaninsa sosai,busy busy ne dashi irin wanda mutane da yawa ke mamakinsa,sam bai bawa kansa hutu ba. a qalla ya kusa minti ashirin a zaune a haka,wanda hakanan yaji zaman yayi masa dadi,ko ba komai ya dan samu break na wasu mintuna. Dan waiwayawa yayi gefansa,a sannan ya hango tahowar professor shi da wasu mutane hudu,saiya miqe ya gyara zamansa,ya kuma kunna motar yana jiran qarasowarsa. yana jin sanda ya shiga yana sallama da mutanen,suka maida murfin motar suka rufe masa,don haka saiya tashi motar,dai dai sanda professor ya furta "alhamdulillah"yana sauke ajiyar numfashi. A nutse yake tuqin har suka fita daga airport din,a hankali professor rashid yace "lawan....ko ka sake koyon sabon salon tuqi ne?"raba idanu samir yayi hagunsa da damansa,saiya lanqwashe murya yace "eh alhaji"dan jim professor yayi sannan yace "to yayi kyau"daga haka bai sake cewa komai ba,zaman shuru yaci gaba da ratsawa a tsakaninsu. "Daka sani ai baka wahalar da kanka ba samir....."yaji abban nashi ya fada bayan tsahon wani lokaci,ya ganeshi kenan,qyaleshi yayi kamar bai gane ba,qaramin murmushi ya subuce a kuncinsa,jerarrun fararen haqoransa suka bayyan,har yayi kamar bazaice komai ba sai kuma ya tanka "yau daya dai abba....ai nima na samu ladan yau din"wayar hannunsa professor ya ajjiye,ya tsurawa gaban motar idanu,kamar anan fuskar samir din take,baisan me yasa a kullum shi da tilon dan nasa komai nasu yasha banban ba,komai nasu ba iri daya bane,abinda yake sam ba cikin tsari da burinsa ba,ya jima da sanin cewa ba haka yakeso ya kasance ba,ba haka tsarinsa yaso ya zama ba,to amma duk ta inda yake tunanin zai gyarota babu wani sauran dama data rage masa,don haka a maimakon yayi magana,saiya buge da hade yatsunsa waje daya,yana maida tunaninsa wani waje daban. Duk sanda yayi tafiya irin wannan ya dawo iyalansa dama ma'aikatan gidan kan cika da murna,kamar yanzun,da samir ke biye dashi dauke da wata qawatacciyar qaramar jaka mai zubin akwati,yana biye da professor har zuwa cikin qawataccen falon gidan,mai yalwa da kuma burgewa,wanda ya wadata da dukkan wani nau'in kayan alatun rayuwa. mutum uku ne ke dakonsa zaune cikin falon,biyu daga cikinsun matasan yammata ne,daya tafi daya tsaho da haske,kamar yadda daya tafi daya shekaru da basu wani taka kara sun karya ba,don dukkansu ba zasu gaza shekara sha tara da ashirin ba. Daga wata kujera kuma mai mazaunin mutum biyu,macace xaune itama wadda ta mallaki shekaru ɗai ɗai har shekara hamsin,saidai idan har kai mai kallo xa'a qyaleka kayi mata ƙiyasin shekaru,to ba shakka zaka ce dauka cewa bata wuce shekara talatin da biyar ba. Tun a kallon farko xaka bata sunan HAMSHAQIYA saboda ta cancanci sunan,fara ce sol,shekarunta sam basu boye hasken fatarta ba,tana da matsakaicin kyau wanda ya cakuda da tarin ado da qawar da take qawata kanta dashi kullum kwanan duniya,kallon farko zai gaya maka ta saba da ado ya zame mata jiki,salon irin abun nan da hausawa suke cewa WANKA YABI JIKI,tun daba hannayenta zuwa wuyanta kayan ado ne na mata,fuskarta wadace take da murmushi kamar bakinta zai yage,idanunta qur bisa saman fuskar wadan nan halittu guda biyu,wato samir da professor,tana dubansu da wani irin kallo me nauyi da zurfi. Dukkaninsu suka miqe kowanne fuskarsa na nuna tsantsar farinciki,daya daga cikin matasan yammatan nan wadda da alama batakai shekarun daya ba ita ta tako da sauri zuwa inda professor yake "Abba.....sannu da dawowa"ta fada da 'yar siga ta shagwaba,da alama kuma hakan habit dinta ne,tana dora kanta saman kafadarsa,kamar marayan daya samu tallafi,murmushi ya saka yadan dora kansa saman kanta "barka kadai auta....na sameku lafiya?" "lafiya qalau abba,saidai munyi missing dinka"murmushin yakuma saki "gani na dawo ai jauhar,duk wata kewa ta qare ko?"kai ta gyada,sai dayar itama ta matso,tasa hannu kadan tana gyara eye glasses dinta,fuskarta itama murmushinne kwance "barka da zuwa abba" "barka kadai lelen abba.....na sameku lafiya?" "lafiya lau abba ya hanya?" "alhmdlh,ya karatu?"saida ta saki wani ni'imtacce murmushi,tana jin wani dadi na ratsata,ta daga idanun a hankali ta maida gashi,samir.......wanda har yanzu yake tsaye a bayan abban nasu tamkar wani dogari,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa yana kallon dukkan abinda ke faruwa, inside him yana jin tsaiwarsa a wajen cikin abubuwan da suke gundurarsa nan da nan,ya qagu duka a gama wadan nan gaishe gaishen. dauke idanunta tayi ta maida kan abban,a duniya tana jin dadi tana alfahari abban nasu ya tambayeta karatunta,tana jin wani qwarin gwiwa yana shigarta aduk sanda ya tambayeta wani abu daya danganci karatunta,takanji burinta kwadayinta da qwarim gwiwarta yana daduwa "alhmdlh abba....komai lafiya" "ma sha Allah"ya fada yana maida dubansa xuwa gareta,har yanzu bata matsa daga inda take tsaye ba,amma hankalinta idanuwanta da hankalinta dukka yana kansu "sarautar mata.......yada tsaiwa a nan?"murmushi ta saki "to ai naga hankalinka duka yana kan yaranka,kaga gwara na barku ku gama tukunna.....barka da dawowa" "barka kadai.....na sameku lafiya?" "alhmdlh"ta fada taba jifansa da wani murmushin,saita tako a hankali ta raba ta gefansa,idanunta saman fuskar samir,suna hada idanu ya kauda kansa ya miqa mata jakar professor dake riqe a hannunsa,hannu ta miqa zata amsa tana cewa "ka kyauta samir"ya fahimci abinda take nufi,saiya saki qaramin murmushi yana juyawa kadan zai fita "ya da haka son...ka bari daddy ya kintsa muci abincin rana tare mana"ta furta cikin nuna zallar kulawa,kansa ya girgiza yana sosa kan mashi da tsinin key din mota,shida yakeson tsallakewa fadan professor,yayi imanin idan ya zauna suci abin tare zai tono laifin da shi yaketa qoqarin bunnewa ne "akwai abubuwa da yawa dana bari,zanje na rage wasu,bazan jima yau a waje ba zan dawo gida" sanda yake maganar shima professor ya nufi hanyar da zata sadashi da sassansa da suka qunshi bedrooms manya guda biyu,da.katafaren falo guda daya "da zaki daina wahalar da kanki wajen tsaidashi,ki barshi ya tafi kawai, saboda haka yakeso,hakan ya tsarawa kansa kamar ko yaushe" sarai samir yasan magana ce mai harshen damo yayi masa,sai data waiwayo ya kalli samir "ohk....saika dawo,Allah ya tsare" kansa ya gyada sannan ya juya zai fice,itama ta rufawa professor baya. "ya saraki"kiran da aka masa shine abu na biyu daya shiga kunnensa daga hirar professor da matarshi,sai yaja tunga ya tsaya sannan ya waiwayo a hankali sanda take tasowa a shagwabe ta riskeshi. Idanuwan najwa tar bisa fuskar jawahir sanda take nufar yayan nasu,saita sanya hannunta ta cire airpiece guda daya cikin biyun dake maqale a kunneta,tana jin wani abu na tokare zuciyarta,ta tsani taga tana magana dashi sam,tana son taji yanzun me zatace da shi ne. "ya saraki.....please,alqawarinmu fa" ajiyar zuciya yayi hade da lumshe idanu,lokaci guda kuma ya furzar da iska daga bakinsa,baice komai ba saiya cusa hannunsa cikin aljihunsa ya fiddo sabbin 'yan dari biyar biyar masu dama ya miqa mata,wani dan tsalle ta saki bayan ta amshu kudin "thank you so much,am proud of you my yaya"murmushi kawai ya bita dashi sannan ya taka ya fice. kudin na hannunta tana juyasu,fuskarta a wadace da murmushi ta koma kujerar data tashi akai ta zauna,duk abun nan da ake idanun najwa a kanta,tana binta da wani kallo da zai nuna maka zallar tkaici da haushinta daya cika mata zuciya,sam jawahir batasa me take ba tana irga kudinta hankali kwance,ganin cewa da gaske jawahir batasan tana yi ba,lissafin kudinta kawai take,saita miqa hannu ta fusge kudin a tare tana furta "banza"da qarfi,hakan yaja mata hankalin jawahir din yadda takeso,dubanta take baki bude "me na miki ya najwa" "banza"ta sake maimaitawa tana hararta,idanuwanta kamar zasu fado akan jawahir din "wai me na miki?" "ke wai.me yasa baki da zuciya,kuma baki da kishin kanki?,na meye zaki tambayesa kudi,momi ba zata baki bane da ba zaki tambayeta ba?"sosai jawahir ta bata fuska tana kallon najwan,ranta a dan bace "amma shi da momyn ai duk daya ne ko?,kuma ko ita ai taga ina tambayarsa,kuma bata ce komai ba"baki najwa ta tabe 'bakya ganewa,kuma ba zaki taba ganewa ba....." "nidai koma meye bani kudina"ta furta tana miqa mata hannu "naqi na bayar din"najwa ta fada tana cusa kudin a gefan cinyarta,sai jawahir din ta sake gimtse fuska sosai "kinga ki bani kudina ya najwa,ko momy tace ki daina shiga harkata ko?" "idan kina da qarfi ki danne ni ki qwata,sarai dai kinsan babu abinda zanyi da kudin nan.....". A hankali ta buda qofa ta dawo ta cikin falon,idauwanta ya sauka a kansu sanda jawahir ke sake maimaita wa najwan ta bata kudinta "lafiyanku?"momyn ta jefa musu tambayarsu,wanda banda tayi magana babu wanda yaga fitowarta cikinsu "momy....ya saraki na tambaya kudin ankon yasmin tun rannan,to ya bani shine ya najwa ta karba ta hanani,tana masifar wai don me zan tambaya ya saraki"jawahir tayi caraf ta gaya mata,sai data tabbatar ta aikawa jawahir saqon harara sannan ta maida dubanta ga mony da nufun yin nata bayanin "momy wai ba....."wani kallo momyn ta aika mata,sannan ta daga hannunta kawai ba tare da tabi takan qorafin da takeso. sako.mata ba tace "bata kudinta"fuska ta bata "momy...." "nace ki bata kudinta ha'an...?"ta fada da dan zafi zafi yanzun a muryarta,fuskar najwa a cunkuse,ta zaro kudin ta jefawa jawahir,ya fada saman cinyarta,bata damu ba ta dauki kudinta taci gaba da irgawa,momyn ta kalleta "ajjiye kudin nan kizo kitchen ki hadama daddynku drink" "to momy"ta amsa mata tana miqewa da kudinta a hannu tabi bayanta,yayin da najwa ta bita da harara,tana jin kamar ta shaqeta,saita gyara glass din fuskarta,ta kuma gyara zaman qaton littafin dake ken cinyarta taci gaba da dubawa,can qasan ranta abubuwa da yawa na mata yawo,inda tana da qarfin iko da sai ta canza abubuwa da dama cikin gidan nasu,abubuwa masu tarin yawa da basuyi rayuwarta yadda takeso ba,basu zauna kuma a gurbi da muhallin da takeson ganinsu ba. *_9:30 am_* *_DARMANAWA HOUSING ESTATE_* *_PROFESSOR RASHID USMAN AZARE RESIDENT_* Daya ne daga cikin jerin qawatattun gidaje dake gine cikin unguwar,,wanda suka qawatu aka kuma ginasu bisa basira da kuma kyakkyawan tsari. Gini ne na alfarma mai cike da qayatarwa da ban sha'awa,kamar yadda akasan ire iren gidajen masu sukuni suke da kuma unguwaninsu. A hankali momy ta daga kanta,fuskarta na fidda wani irin murmushi mai haske tunda ta jiyo sautin muryarsa,tun gabanin ma ya iso inda suke din,yayin da ta tsaida dukkan abinda takeyi,ciki harda cin abincinta,da kuma hira da take da 'yammatan dake gefanta su uku,najwa jawahir da kuma ramla da take 'yar ruqo a wajenta. Dukkaninsu sunsan meye ta baiwa hankalinta haka gaba daya,ba wacce bata saba da ganin tarin kulawa da qauna daga gareta ba zuwa ga samir,wadda ta banbamta da ta kowanne da dake cikin gidan. Kallo daya professor yayi mata yaci gaba da cin abincinsa a nutse,don shi din ma hakan ba baqon al'amari bane a wajensa,illa dai ya kada kansa sannan ya maida hankalinsa ga farantin gabansa. Cikin sakanni da basu kai goma ba ya bayyana cikin falon dab dasu,matashin saurayi muhammad samir me laqabin saraki,ma'abocin tsaho,wanda murjewar jikinsa ta hana bayyanuwar tsayin da Allah yayi masa yadda za'a fahimta,ya mallaki kalar fatar da hausawa suke kira da wankan tarwada amma irin wankan tarwadan nan dake da haske,taqi kadan zai dada ka kirayeshi da farar fata,matsakaicin kyau gareshi,saidai abubuwa guda biyu sun taru sun qarawa siffarsa kyau da cikar haiba KWARJINI da yake dashi,da kuma wasu lumsassun idanuwa masu kama da na me jin bacci. Yana da sanyin murya,irin sanyin da bai hana bayyanar cikar mazantakarsa gami da jarumtarsa ba,sam ba miskili bane,kamar yadda wasu mutane da yawa suke masa kallon haka,abubuwa ne guda biyu suka sanya suke masa wannan kallon,baya shiga sabgar da bata shafeshi ba,bashi da shishshigi sam,hakanan bai fiya magana kan abinda yasan yana da qarancin muhimmanci,koma kwata kwata bashi da muhimmancin,yana da kamewa da wata irin nutsuwa mai jan hankali,yana da zurfin ciki a yawancin lokuta,komai nasa bisa tsari da dacewa yake tafiya,shi yasa wasu ke ganin abune mai wuyar gaske iya zama dashi,abunda basu sani ba shine,zama dashi din wani abune mai dadi ga duk wanda ya soma mu'amala dashi. Akwai boyayyun halayyensa da ba kowanne ya sanshi dasu ba,ciki kuwa harda makusantansa,yana da tausayi yana da taimako,a wasu abubuwan ba zaka taba tsammanin cewa ya fito daga gidan girma da arziqi irin wannan ba,rayuwa sassauqa da yakan gudanar....saidai,matuqar kazo lokacin da yake kan tsininsa,zaka dauka baida kirki ko kadan. Muhammad samir,da namiji guda daya tilo da Allah ya mallakawa professor rashid usman azare,wanda tarin banbamce babancen halaye da zabi na rayuwa yaso ya zama babban shinge tsakaninsa da mahaifinsa da samun dukkan wata yarda da qauna tashi. "welcome son.....na tsammaci yau ba zaka fita ba?,naji shurun yayi yawa,duk da na kira wayarka taqi shiga....saina zabi na barka ba tare dana aika ba,wala'alla kana bacci ne kada a katse maka shi" hajiya jidda wadda auke kira da mommy ta fada,dukkan kulawarta tana tare da samir din,fuskarta na fidda wani kalar murmushi dake nuna farincikin dake tattare da ita na ganin fitowar samir din,kamar yaune lokaci na farko data fara ganinsa,ko kuma wani gari yayi tafiya mai nisan zango ya dawo a yau din. Washewa fuskarsa tayi da wani murmushi mai aji,ya soma qoqarin jan kujera daya don yiwa kansa mazauni sannan ya amsa mata "A'ah anna....bani da wani abu da zan aiwatar ne da safen....shi yasa na zabi na huta kafin na fita yau,don jiya ban samu zama yadda naso ba" ya qarashe maganar yana duqawa zuwa qasa gefan mahaifinsa,muryarsa cike da tsantsar ladabi ya furta "Barka da asuba daddy" kallo daya yayi masa ya maida kansa ga abincinsa yana amsa masa da "Ka tashi lafiya?" "Lafiya alhmdlh" sai ya maida dubansa ga mommy wato hajiya jidda "Barka da asuba mommy" "Barka kadai yarona....da fatan ka tashi lafiya" "lafiya qalau alhdmdlh" "To ma sha Allah" ta amsa masa fuskarta na nuna jin dadin samunsa lafiya da tayi kamar kullum,saita miqe da kanta ta fara bude dukkan wani kwano dake saman teburin sanda qannensa ke gaisheshi daya bayan daya yana amsa musu,kamar yadda ta saba tanayi kullum kwanan duniya matuqar ya halarci wajen cin abinci,zata bude masa dukka ya zaba abinda yakeson ci,don wani lokaci ma abinda ya zaba yana so shi za'a dafa kowa da kowa,koda ba zabinka kenan ba,tun suna yiwa mommy mita da qorafi har ya zame musu jiki. "Me zakaci a ciki samir?,Allah yasa akwai wanda ya dace da ra'ayinka" mommy ta fada tana murmushi kamar kullum,wanda baka rabata dashi saman fuskarta,sai a sannan alhj mukhtar yayi magana tun fitowar samir din,idanuwansa saman fuskar mommy,wani abu na yawo saman zuciyarsa,wani abu mai nauyin daya wuce a aunashi a mizani "Ki kalleshi mana da kyau,ba yau ko jiya ko shekaran jiya aka haifeshi ba,amma kullum kina kallonshi ne kamar ranar nan da aka miqo miki shi cikin tsumman goyo,a qa'ida ya isa aure,a kuma qa'idance kamata yayi ace a gaban matarsa yake" kanta ta langabe tana duban professor "Haba daddy.....kai kake ma samir kallon yayi girma har haka,ni kam a wajena har yanzu kamar yaron goye nake kallonsa.....bugu da qari ma daddy idan ba'a kula da samir ba...wa zamu kula dashi?,karka manta shi kadai Allah ya bamu...." "Abbaaaa"sautin muryar jawahir tayi kutse cikin maganar mummy,sautin daya fito a narke,kamar me shirin sakin kuka,waiwayawa suka dukka suna kallonta,sai daddyn ya daga hannayensa duka biyun kafin yace "You see.....su kuma daughters dina ki kaisu ina?" Murmushi ya saki,wani abu na lilo can qasan ranta da zuciyarta "Dole dukkaninsu subi bayan samir a wajena" a nutse tsaf daddyn ya waiwaya ya dubi samir din sosai kuma kai tsaye,duk da idanun samir din na kai kawo ne tsakanin yan uwansa,fuskarsa tana fitar da wani murmushi me sanyi mai kuma cike da nutsuwa "Gwara da kika ce a wajenki,ta ina yaronkin zai kama qafar yarana?,yaron naki da ba jin magana yake ba,wanda ya sarayar da alqiblarsa,babu wanda ya gane har yau inda yasa gaba" samir ya gama fahimtar qorafinsa na jiya da yaketa gujewa shi yakeson sokowa a yau din,saiya dan sunkui da kansa,kana ya daga kan nasa,yana muradun rushe wannan maganar,don baida sha'awar ci gaba da yinta,don haka cikin girmamawa yace da ita "Kome akayi yau din zanci mommy,ki zauna ki huta....zan zuba da kaina,ina sauri ne ma,jiya akwai taron da zanyi da ma'aikata,ban samu zama ba nasa aka maidashi yau"ya fada yana miqa hannu zai hada tea. jawahir ce ta miqe da hanzari ya dauka cup din ta soma hada masa,mummy tadan kalleta saita dauke kanta "yi a hankali sarkin rawar kai,kada ki zuba masa a jiki"mummyn ta fadi sanda jawahir ke aje masa tea din,murmushi yayi ya dauka yana.kaiwa bakinsa,shi yasa yakeson autar tasu,sosai take nuna kumawa kan dukkan wani abu daya shefeshi,ba kamar 'yar uwarta ba,wadda har yanzu bai fuskanci inda ta sanya gaba ba,shegen sin jiki gayunbanza,izgili da yiwa.mutane kallon banza hadi da rashi iya magana dukka najwa ta hadasu,abu daya da yasa bata iya wani kyakkyawan abu a gabansa ko a kansa shine,baya daukar raini,kamar yadda baya raina kowa,tafi kowa sanin ainihin wayeshi,wannan shine ya ke mata waigi a kansa. miqewa prof yayi yana yagar tissue "idan ka dawo yau din bayan sallar isha'i,ka sameni zamuyi magana dakai" "ok daddy"ya fada da muryarsa mai dadi,sannan yaci gaba da kurbar tea din a nutse. cup din ya ajjiye bayan ya gama amsa wata waya,mummy ta dubeshi "bakaci komai bafa samir?" "mommy,am late" "a maka packaging ka tafi dashi mana,ya zaka fita aiki babu cikakken abinci a cikinka" "ba komai mommy,zan nemi wani abun naci idan na samu break" "a'ah..,.najwa......maza,shiga kitchen ki cewa baraka ta baki warmers qanana"fuska tadan bata "Mommy.....yace a barshi fa"idanu ta fitar mata gaba daya "ni kuma nace ki dauko....."tuni ta miqe ma kafin mummyn ta qarasa bayani,saboda wani kallo da samir din ya jefeta dashi,harta soma takawa tajishi yana fadin "dawo ki zauna,jawahir.....jeki dauko,guda daya ma is ok"taf tsoro ya cika cikinta,saboda ba kasafai yake bi takanta ba,tana tsoron irin wannan kallon nasa,saita ci gaba da tafiya ta miqe zuwa kitchen din,wata tsawa ya watsa.mata wadda ta sanyata tsaiwa,ta kuma kasa juyowa,har jawahir tazo ta wuceta da saurinta kuwa kamar yadda ya umarceta bata motsa ba har sai dataji fitarsa yana cewa idan an zuba jawahir din ta miqa masa yana cikin mota. koda ta koma harara Mommy ta bita da ita,sannan ta rufeta da fada,tana kallon fuskar jawahir,da alama taji dadin yadda mummyn ta balbaleta da fadan,sai tayi sakato,mamaki fal ranta,me yasa mummy ke mata fada da zafi har haka?,bata tanka ba har jawahir ta fice daga parlour din,saita dauki jakarta dake gefe wanda dama shirin makaranta tayi,kawai ta fice a falon. yana daga zaune a driver seat ta buda gidan baya ta sanya warmer din sannan ta rufe,saita zagayo inda yake zaune din,fuskarta da murmushi "a dawo lafya yaya" "Allah yasa"ya amsa yana shirin rufe murfin motar,saidai jawahir din bata matsa ba tana tsaye still a wajen,kansa ya daga bayan ya sauke glass din motar yana dubanta "ya akayi auta?"murmushi ta sakeyi "kayi haquri yaya da abinda ya najwa keyi....ni kaina bansan meya canza ba"qawataccen murmushin gefan baki ya saki "karki damu, she's still my sister.....ina tunanin tana da damuwa,but we will talk later"kaita gyada kawai kana taja baya,ya tada motar a nutse,ya qarasa bakin gate ya danna horn,idanunsa saman fuskar mai gadinsu da yaketa marmashe gyada yana zubawa cikin jiqaqqen garin kwaki,ya taso da hanzari ya durfafi qofar zai budeta,sai samir ya yafitoshi da hannu,don haka yabar bude qofar ya iskoshi da sauri ya iso bakin window inda samir ke zaune "Allah ya taimaki saraki" "an tashi lpy baba" "lafiya qalau dana" "abinda aka dafa ne yau baba bai maka ba,na ganka da garinka harda gyada?"samir ya tambayeshi yana dan murmushi,murmushin shima yayi,a ladabce yace "ko daya mai gida,yau dai bamu samu abun karin bane"fuskarsa cike taf da mamaki bayan yadan yamutsata yace "kamar yaya?,kune baku da sha'awar ci?"da sauri ya girgiza kai "ko daya,Allah ya taimakeka wazaiqi abinci irin na gidan professor?,inajin dai yau da gobe ne irin ta bahaushe,wani lokaci ku samu,wani lokacin kuma saidai kowa ya siya abinda yake dashi"baice komai ba saiya duba agogon hannunsa,bashi da lokaci da cikin gidan zai koma,bai zaci wasu cikin gida dake rayuwa tare dasu ba'a basu abinci ba,saiya bude aljihun gaban motarsa ya aciro yan dubu dubu guda biyu ya miqa masa "gashi,ka ajjiye wancan ka siya wani abun me dumi kaci"hannu bibbiyu yasa ya amsa kudin yana zabga masa godiya,sannan ya tafi qofar ya dage masa gate din,yaja motar da dan hanzari ya fice. 09 *zafafa biyar na kudine,tuntubi wadan nan numbers din don samun naki copy din ki karanta cikin aminci* 08184017082 Ko 09134848107 *_follow us @ instagram_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1h9y2qgfg67x5&utm_content=nj79azb Or facebook https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share ___________________________ cikin nutsuwar data zame masa jiki,kuma dabi'a yake tuqi,hankalinsa da kunnensa yana kan redion jikin motar daya kunna yana sauraren labaran safiya dake fita tar kamar yana wajen,yayin da wani sashe na hankalinsa ke jefo masa tunani iri daban daban kadan kadan,ciki harda sauyawar dabi'un qanwarsa,duk da cewa dama can halinta daban dana jawahir,ba zakayi tunanin ciki daya suka fito ba. tafiyar minti kusan arba'in babu wani abu ta sadashi da inda kamfanin nashi yake,wato rukunin ma'aikatun dake sharada industrial area,ya sake rage gudun motar sosai,yana gangarawa sannu a hankali kan kwaltar dake shimfide tsakiyar hanyar,wanda hagunta da damanta dukka gine ginen masna'antu ne. sa da yakai qarshe sannan ya karya wata kwana ya sake shiga wani titin,titine mai kyau,hakanan babu tarin gine gine barkatai kamae wanda ya baro,a hankali ya tsaya bakin wani babban katafaren gini,wanda yake dauke da bene hawa uku,iya ganinka gini ne daya amsa sunansa gini,wanda da gani ba tambaya kamfanine babba,wanda zaici jimillar ma'aikata masu dama,tako ina hasken gilasai da aka qawata benen me hawa biyu ne yake daukan hankali da idanun me kallo,yayin da manyan rubutun da akayi da manyan baqi can saman qololuwar ginin yake bada wani irin haske da kala me kyau,wannan shine M.S CONSTRUCTION COMPANY,kamfanin da ya shara yayi shuhura wajen karbar kwangilar gine ginen tituna,makarantu asibitoci ma'aikatu dama gidaje da suka amsa sunayensu,daga hannun mutane daban daban,kamfanine da ba'a taba samun kamarshi da yaro matashi ya mallakeshi ba,sannan kuma kamfanine da yayi suna ya danne sunan kowanne kamfani dake jin ya isa,hakan ya sanya yake da tarin abokan adawa da abokan takara bila adadin,saidai akwai wasu turaku dake riqe da kamfanin,wanda su wadancan sam basu san da wannan sirrin ba. tsaiwar motarsa ba tare da ya dannan horn ba daya daga cikin securities dake tsare da katafariyar qofar shiga da fita ta kamfanin ya taso cikin gaggawa ya bude masa,yana rusunawa cikin girmamawa ya miqa gaisuwarsa,cike da kulawa ya amsa masa,sannan ya dage motar zuwa ciki. kamar kowanne ma'aikaci,inda kowa yake aje abun hawansa nan shima ya aje tasa,ya kashe motar yana zare muqullin daga jiki,sannan ya waiwaya ya diba wayoyinsa tare da briefcase dinsa,ya dannan lock ya bude motar da niyyar zura qafarsa ya fita,saidai wata mota daga sako kai ta kuma faka da da tashi ya hanashi aiwatar da hakan,sai daya jira tsaiwar motar ta daidaita sannan ya bude ya fito,ba tare daya tsaya shaida waye a dayan motar ba. saidai yana cikin rufe motar tasa yaji magana daga bayansa "barka da warhaka yallabai,kaima yauka makara"duk da bai juya ba amma yasan wacece,saidai hakan ba hanashi juyawar ba,ya dubeta fuskarsa ba yabo ba fallasa "Allah ko?,nima yau na dana,naji abinda kuke ji"saita fara rufe tata motar itama tana murmushi "saboda mu sababbu ne ko?"kafadarsa ya daga yana watsa hannayensa "eh kusan haka ne" "shikenan,i surrender" "good"ya furta yana dan qaramin murmushi,sannan cikin hanzari yayi gaba yana amsa gaisuwar datake miqa masa,saita rufa masa baya da sauri itama tana qoqarin dai daita tafiyarsun don kada ya kubce mata koya mata nisa,ta kuma fuskanci idan batayi da gasken gaske ba tsaf zai wuceta ne ya barta. yana tafe yana amsa gaisuwar ma'aikatan cikin kamfanin cikin kulawa,gefe guda yana qoqarin handling surutunta daya soma damunsa,saidai ita bata kula da cewa ta fara damun nasa ba. Suna gaban elevator,yana shirin sanys qafarsa wayarsa tayi qara,sai ya dakata yana zaro wayarsa,daya duba me kiran sai yaga PA dinsa ne, rejecting yayi kawai ya riqe wayar a hannunsa,don yasan wala'alla yace masa suna jiransa ne,don haka a gaggauce ya shige. a ginin tsakiya babban dakin taron yake,wanda dukkan wani ma'aikaci daya kamata ace ya halacci wajen yana ciki. tsaiwa yayi daga bakin qofar dakin taron,ya dubeta yana mata nuni data shiga,saita noqe tana kallonsa "me yasa baka son jerawa dani ne saraki?"wayarsa yadan juya kadan a hannunsa,ba kasafai ya fiya son doguwar magana ba,amma saiya amsa mata "tsarina ne hakan"ya amsa mata a taqaice,sannan ya daga kai ya dubeta,sosai idanuwansa suka yi mata nauyi,sarakin wani mutum ne na daban a zuciyarta da idanuwanta,shi kadai ne mutumin da zai dubeta da idanu tajinta rusuna,ta kuma sauka daga kan tsarinta cikin lokaci kadan "ki wuce,saboda kinsan indai na rigaki shiga ba zaki shiga din ba,kin rasa zaman"wannan tsarinsa ne,shi yasa da wuya a sanya lokacin taro ya saba,yakanyi qoqari ya shiga kafin lokacin da aka sanya za'ayi din,ba yadda ta iya saitayi gaban cikin mutuwar jiki ta shige dakin taron. kamar yadda ta zata a cike yake,kowa ya kama mazauninsa,a hankali ta shiga wulga idanuwanta,sai suka sauka akanta,FAUZA tana zaune kan kujerar dake daura data samir,saboda a tsarinsu iya matsayinka iya kusancin kujerarka da tashi. Sam fauzan ma batasan me take ba,don ta tattara dukka hankalinta kacokam kan wayar dake hannunta,rubutu take da sauri da sauri,hasken wayar na bayyana qyallin faratan hannunta data qara dana kanti,ta matse sosai tayi kyau cikin suit na mata,siririn mayafi ne kadai ya nannade kanta zuwa wuyanta dashi,fuskarta tasha lite makeup,yayin data dora qafarta daya kan daya,hakan ya bayyana tsabar tsinin da takalmin qafarta keda shi,fauzan fara ce qal,saida bata da hanci bare idanuwa,amma haskenta ya santa duka wannan bai fiya bayyana ba,don tana da daukar ido,farar fatarta na haskata,tana kuma qara mata kyau duk kalar kayan data sanya. fauza na daya daga cikin yaran abokan siyasar Prof,ta zabi aiki da kamfanin MS construction ne batare da kowa yasa dalilinta na hakan ba,shi kansa Prof din yayi mamaki sanda mahaifinta ke shigar da credentials dinta gareshi don a bata aiki,saboda kwata kwata ba abinda ta karanta kenan ba,ba fanninta bane,amma saboda girma da qimar da Prof yake ganinsa dashi ba 'yar haka tsakaninsu,ya umarci samir ya bata vacancy. qaramin tsaki taja,sannan ta lalubi kujera ta zauna,ta soma magana da mutanenta da suke wajen,batayi cikakken minti biyu ba samir ya bayyana wajen. Idanuwanta na hango mata sanda fauza ta maida wayar jakarta,fuskarta ta wadata da murmushi,sannan ta miqe tsaye don girmamawa kamar yadda sauran mutanen dake dakin taron suka miqe gaba daya. Sai daya tsaya gaban kujerarsa sannan ya baiwa kowa umarnin xama ba tare dashi ya zauna din ba,kusan tare suka zauna da sauran ma'aikatan,yana amsa gaisuwar da suke miqawa gareshi,saiya maida hankali yana duban kowa dake wajen,yana laluben wanda bai shigo ba cikin wadanda ya cancanci ace suna wajen,saidai kowa ya hallara,daga qarshe yana niyyar janye idanunsa suka fada kan fauza. Murmushi tadan masa,saiya dan saki fuskarsa kadan yana janye idanunsa,mutum na hudu dake zaune daga hannun damansa ya duba "salisu.....a bude mana da addu'a"ya fadi yana dora wayoyinsa saman teburin bayan ya kashesu,kamar yadda yake a dokarsa,ya hada tafukan hannayensa waje daya yana bin addu'ar da salisun ke kwararowa................ *BAYAN AWA UKU* Zaune yake a qawataccen gidan abincin dake daura da kamfanin nasa,waje nw dake da wadatar iska mai kyau da kuma tsafta,uwa uba babu cinkuso a wajen,bayan samun hutun awa daya sanda ya kammala da taro kashi na farko,sai kuma ma'aikata kashi na biyu da zai zauna dasu,wanda kusan shine mafi muhimmanci ma a wajensa,already yasa an fitar da abincin da yazo dasi daga gida an bayar,a yanzun kuma yana buqatar wani abu da zai saka a cikinsa,idan suka kuma shiga a qalla yasan akwai kusa awa biyu kafin su kammala ganawar. Gasashen kifi da chips yayi order yake kuma ci,a hankali cike da tarin nutsuwa yake kaiwa bakinsa da fork,gefe daya kuma fauza ce,wadda ganinsa zai fita ya sanya tace su fita tare mana,itama abincin zata je taci,baice mata uffan ba illa buda mata motar da yayi,ta kuwa bude gidan gaba ta shige,saidai tunda suka taho din har suka zo babu wanda ya cewa sa dan uwansa komai. sanda aka bashi menu ya zaba abunda yake da buqatar ci saiya tura mata gabanta itama,baisan meta zaba ba,amma da aka kawo din,lemuka kawai yaga an aje mata da ruwa,duk da ya gani bai tanka ba,yaci gaba da cin nashi abincin,yana cin yana duba lokaci kada lokacin sallar ya qwace. Ture farantin yayi yana goge bakinsa da tissue inda yakejin kamae ya baci,daya hannun nasa kuma yana yafito waiter din,ya saki abinda yake ya matso da hanzari zuwa wajen. "gani yallabai"ya fada cikin girmamawa,hannu samir din ya sanya cikin aljihun wandonsa bayan ya tashi tsaye. kudade ya ciro sannan ya miqa masa,ya saka hannu biyu kuwa ya karba ya soma lissafawa,zuwa sannan samir ya kwashe maqullin motarsa da wayoyinsa dake zube saman tebur din ya soma yin gaba "yallabai,kuna da canji" "ka riqe nabar maka" ya fada sounding seriusly yana sake dosar qofar fita "hajiya a tayani godiya,Allah ya qara arziqi"ya fada yana duban fauza,wadda ta miqe tana rataya jakarta ganin zai wuce ba tare da yace da ita komai ba,bakin ma'aikacin kamar zai yage sabosa murna,don kusan albashinsa na watanni biyu ne suke cure dunqule a hannunsa a mazaunin kyauta. sanda ta isa gaban motar har ya tadata,ta bude ta shiga ta gyara zamanta sosai,ya kunna motar sannan ya tasheta suka fice. yanzunma kamar sanda suka zo,babu wanda ya tankwa dan uwansa komai,cike da qosawa fauza tadan muskuta kadan,tana jin wani bacin rai yana dan taba zuciyarta,bata taba kawo haka sarakin yake a ranta ba,duba da yadda ta sanshi da nuna kulawa ga duk mutumin da yake tare dashi,yanayinsa data karanta yasa zuciyarta ta bata tabbacin sauqi da saurin samun kansa,a yadda take da aji da kuma kyau kamar yadda ta saba ji daga bakunan mutane da dama wadanda batasan adadinsu ba,bata jin wannan tafiyar zata dore,tunaninsa daban nata daban,duk inda take tunanin mafita ce ko bullewa ce a tattare dashi,idan ta isa wajen saita taras a rufe yake ruf,samir din bashi da sauqi,karantarsa ta fahimci abune mai wahala,inda kake zatonsa daban,inda kuma zaka sameshi daban,batason taci gaba da aiwatar da abubuwan da zasu janyo mata zubewar ajinta,bata shiryawa hakan ba. Batasan tayi tsaki a fili ba,har sai da sautinsa ya fito,ta waiwaya da sauri ta dubi sashen da samir yake,dai dai sanda shima ya waiwaya yana dubanta da lumsassun idanuwansa masu daukar hankali "ar you okay?"ya fada kafin ya dauke idanuwansa daga kanta "yeah"ta amsa murya qasa qasa tana jinjina kanta,daga hakan bai sake cewa da ita komai ba,yaci gaba da tuqinsa a nutse,har suka qaraso qofar company din. A bakin gate taga ya ja burki,tadan dubeshi suka hada idanu,ta fahimta abinda yakeson nuna mata,da alamu yana son ta sauka ne,a hankali ta sanya hannnta ga mabudin qofar ta bude ta zira qafafunta ta fita,ta soma takawa a hankali tana shugewa ciki haushinyana cikata,tana jin sanda aka dage masa gate yabi ta gefanta ya wuce zuwa ciki. qarfe biyu saura mintuna goma aka idar da sallar cikin masallacin dake cikin kamfanin,masallaci ne me yalwa da aka ginashi bisa tsari mai kyau saboda gudanar da ibada ga ma'aikata,aka sanya liman wanda ke jagorantar sallolin nann biyu wani lokaci har uku ma da suke ruskar ma'aikatan cikin ma'aikatar. kamar yadda yakeyi wani lokaci,yakan badda kama,ya zauna daga can wani saqo na cikin masallacin,musamman idan yana sin yin addu'o'i bayason tashi da wuri,yauma hakkane,yana zaune sosai cikin nutsuwa,kansa a qasa yana azkar da yakanyi duk lokacin daya idar da salla,kusan masallacin babu kowa,sai wani lebura guda daya dake zaune daga bayansa,baisan me ya zaunar dashi ba,ya tabbatar daya fuskanci shine zaune a wajwn bazai zauna ba haka kusa da bayansa sosai ba,wannan na daya daga cikin dalilan da yasanya idan zai zauna din baya gani a gane fuskarsa ko a gane waye. yana tsaka da addu'o'in ya duba lokaci,akwai sauran mintuna biyar da suka rage,ya sauke hannunsa yana ci gaba da irga tasbihinsa da yatsun hannunsa,dai dai sannan daya daga cikin leburorin dake aiki a kamfanin ya shigo,jikinsa da lema,da alama alwala yayi xaiyi tasa sallar,bai samu jam'i ba. "malam labaran.....ashe har kun idar?"leburan daya shigo ya fada,muryar wancan din da alamun laushi da sanyi yace "wallahi,nima ka ganni nan,tunanin duniya ya hanani tashi,damuwa ce fal raina,dama ina cewa zan sameka mun zanta" "subhanallahi,to Allah yasa lafiya"ya fadi yana zama gefansa. Tagumin ya cire,yana sauke nannuyar ajiyar zuciya,kafin ya soma magana "wato malam tanimu takaka ya shiga uku a wannan zamanin......ka ganni nan na rasa inda zan dora raina,bikin yarinyata ne ake ta saka rana amma abu ya gagara,sau uku ana saka rana ana dagawa saboda babu kudin da zan mata kayan daki,yanzu mijin yace idan aka qara dagawa ana hudu to ya fasa,abu na biyu yarona bashir da na sanya raina da burina akan zai taimaka min idan ya qare karatunsa......shima yanzu saura kwana uku a rufe registration amma ban masa ba,saboda bani da kudin yi masan,munje neman taimako gidanjen 'ya siyasan nan har mutum biyu amma saidai suce za'a kiramu har yanzu shiru,mutanen nan malam tanimu nasa tsoron Allah,sun gina manyan gidaje,suna hawa manyan motoci,sutura ta alfarma amma sun kasa taimakawa talaka dake nemam tsira da rayuwarsa koda da iya abincin da zai sanya a bakin salatinsa ne,kudin da bai gagaresu ba amma suna qyashi da baqincikin su dauka su taimaka maka,bayan duk wata qafafa tasu da suke da ita kudinka ne,da bazarka suke rawa,sai daka zabesu sannan suka zama abinda suka zama,sai da ka zabesu sannan suka je inda suke a yau,naje na yiwa murtala magana,ya taimaka min cikin albashina ya bani,ko katifa na samu da asiya mata da labulaye amma yace sam,ai wata sai yanzu yayi rabi ma,baza bani ba,na haqura waina jira har watan ya qare a soma albashi,ya ilahi ina mutum xai tsoma rayuwarsa ne?" . wani abu ne yaja hankalinsa kan hirar da sukeyi din,saidai kafin yayi tunanin komai wayarsa ta shaida masa cikar sauran lokacin da ya rage masa,dole ya miqe ya dauki rigarsa ta sama daya cire ya cukuikuyeta ya taka a hankali ba tare da sun lura da shi ba ya fice. ajiyar zuciya ya sauke,yana tsara abubuwa masu yawa cikin ransa,ran nashi yaji ya dan baci game da murtala,tun ba yau ba yana dan ji da samun qorafe qorafe a kansa game da ma'aikatan, akwai abubuwan da suka sanya yake daga masa qafa ne,banda haka da tuni ya dade da yanke masa hukunci,saboda shi din bai da wasa ka irin wadan nan al'amuran,dalilin da yasa kamfaninsa ya zama daban da sauran. sai da ya zauna sosai kan mazauninsa sannan aka sake sabuwar gaisuwa,dakin ya dauki shuru,kowa ya nutsu yana jiran yaji daga bakin shugaban nasu. fawwaz ya hanga cikin jerin ma'aikatan,ya masa kallon da bai wuce na sakanni uku ba saiya dauke kansa,cikin muryarsa Mai cike da kwarjini da wani nauyi dake cika kunnuwa,wanda ke nuna nutsuwa da confidence ya soma magana cikin harshen nasara,duk da yana jefa hausa lokaci zuwa lokaci a ciki "abu na farko da zan soma bude taronnan dashi albishir ne....."take fuskar duk wani ma'aikaci dake wajen ta washe da fara'a da kuma farinciki,tun basu ji ke zaya ce ba,sunsanshi tun ba yau ba,duk sanda yazo da albishir to kowa saiya dara "akwai qarin albashi ga ma'aikata"take wajen ya hautsine da farinciki,duk da cewa m.s construction company yana daya daga cikin kamfanunuwan dake bada albashin da babu kamarsa a gadin Nigeria "amma ga wadanda suja dace....akwai tantancewa da zamu aiwatar kafin faruwar hakan"farincikin sai ya dan ja baya daga fuskokin wasu,yayin da kowa ya cika da fata da burin ya zamana cikin wadanda suka cancanta. sauyawar tasu bai hanashi kiran sunan murtala ba "murtala" "yes sir"ya fada yana miqewa tsaye, hannunsa dauke da wani littafi mai manyan shafuka,da rubutu birjik a cikinsa,yadan rusuna masa sannan ya miqe "daga yau....."ya dakata yana kallonsa,yayin da dakin ya dauki amsa amon na muryarsa "daga yau......duk wani ma'aikaci,kama daga babba zuwa qarami,duk wanda yazo maka da buqatar albashinsa kafin lokacin bada salary yayi,a dauka a bashi"kallon kallo suka soma yi a junansu,kalamansa na yiwa wasu daga cikinsu dadi,yau kam zaman na musamman ne a wajensu,yazo musu da abubuwa masu dadi. Duban fuskar murtalan yake yana jiran yaji abinda zai fada,muryar fawwaz ta maue gurbin muryar murtala da samir yake kira yaji yace wani abu akai "amma samir.....hakan sai nakega baiyi tsari ba,ya ace tun ba'a ga performance na mutum ba a cikin watan sai a dauka salary dinsa kawai a bashi,bugu da qari kuma ma.....kowa ya sani cewa,akan iya samun asara a kamfani ko riba,duka ba zakayi duba da wannan ba zaka zaka yanke wannan hukuncin,idan asara ta samu kuma kenan kamfani shi kadai zai dauka bazai shafi ma'aikata da albashinsu ba"kallo.ya zubawa fawwaz na wasu sakanni,yana mamakin yadda fawwaz ke masa shishshigi haka cikin lamuransa,yana sane dashi,ya dage masa qafa ne saboda albarkacin wasu mutane guda biyu,saiya janye idonsa daga kan fawwaz din ba tare da yace masa komai ba,ya maida dubansa ga murtala "this is an order"ya fada kai tsaye cikin salo na bada umarni,kai murtala ya gyada "in sha Allah sir"ci gaba yayi da kallonsa yana jefa masa tambaya ta biyu, analysis ne na wasu abubuwa da suka shafi kudin dake shiga da fita a kamfani,murtalan da team dinsa suka soma bayani,tsahon wani lokaci da samir ya tabbatar komai yayi dai dai, bayani kuma ya kammala yadda ya kamata,murtala ya miqa masa takardun ya karba,da zummar idan yaje gida zai sake dubawa,ya kuma sanya hannu,saiya miqawa umar dake zaune daga gefansa,sannan ya sallami wasu daga cikin ma'aikatan,yabar wadanda suke cikin gaba ta biyu da zasuyi magana akanta. "umar....ina da ina aka binciko bayan qauyen dan sarari?"samir ya fada yana shafa kansa da hannunsa,saboda gajiya da ya farayi da zaman,uwa uba kansa ya dauki chargy sosai,miqewa umar yayi a nutse shima da wasu takardun a hannunsa "sir....akwai qauyuka guda biyu,qauyen ɗinya da kuma qaunyen me saje,dukkaninsu suna buqatar makaranta da masallaci,koda na kamsus salawati ne"kai ya jinjina idanunsa qur kan file din dake gefansa "cikin biyun wanne qauye ne sukafi buqatar hakan"bubbuda shafukan takardun hannunsa umar yayi sannan ya dago ya dubi samir "qauyen dinya,don makarantar dake kaf qauyen guda daya ce,an ginata shekara talatin da suka gabata,kuma tun wancan lokacin ba'a ake sabuntata ko bi ta kanta ba,sannan qauyen basu da masallacin kamsus salawatin ma,suna salla ne qarqashin bishiya"kansa yake qara jinjinawa,ransa na baci,idan ya tuna shuwagabanninmu,me sukeyi?,meye amfaninsu?, duk wani abu da aka zabesu don su yiwa talaka shi bashi suke yi ba,yanzu wadan nan mutanen abinda sukafi buqatar ayi musu ba'a musun ba,kuma baya raba dayan biyun,suna iya shiga har can neman quri'unsu idan lokacin zabe yazo,amma a yanzun tamkar basusan akwai wata al'umma dake rayuwa a wajen ba "i hate it"ya furta can qasan ransa,kamar yadda yake dukkan wannan tunanin cikin ransa. Kwayar idanunsa ya daga yana katse shurun ta hanyar cewa "murtala....a dubamin putting smile account aga nawa muke dashi,idan kudin baikai ba a sanya dukka albashina a ciki,a soma shirin zuwa yi musu aiki,idan ina free zani wannan karon,idan kuma akwai aikin dake da buqatata cikin kamfani zan turaku ku aiwatar kamar yadda aka saba" "an gama sir"ya fada cikin girmamawa. Kafeshi da idau fawwaz yayi,yana jin wani abu na taso masa cikin ransa,sam samir baima ga kallon da yake masa ba,har sai daya tashi daga kashingiae da yayi yana soke yatsunsa cikin na juna yana kallonsu daya bayan daya "akwa mai wata magana qorafi ko qarin haske?"haka yake,duk sanda akayi taro irin wannan yana baiwa kowa dama ya tofa albarkacin bakinsa,yakan gayawa kansa dakansa cewa "kowa ma mutum ne kamar shi,nawai saboda Allah ya bashi jagorancinsu ba kuma ya zamana shi kadai yake da abun cewa,kowa ma baida abun fada". Fawwaz ne yayi gyaran murya sannan ya zauna sosai yana duban samir "akwai qorafin da zanyi"dubansa yayi na wasu sakanni sannan ya gyada kai alamun ya bashi dama "amma ni a ganina mr samir kai ba gwamnati bane da zaka ce saika farantawa kowa,koda gwamanti bata iya aiwatar da komai da komai,kowanne lokaci kama kwashe kudaden kamfani kana zuwa kana wahaltawa wasu mutane da basu gama sanin dadin rayuwa ba bare susan ciwon kansu,ko wata biyu ba'ayi akaje wasu qauyukan aka musu aiki,kafin su ka yiwa wasu da dama da bansan iyakacinsu ba,hakan bai isa ba?",cike da mamakinuake duban fawwaz,yasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,naisan aninda ke damun fawwaz din ba,amma ya soma gajiya a wasu baqin halayensa,kusan maganar fawwaz din taja hankalin yawa yawan wadanda ke wajen,murmushin gefan baki samir din yayi sannan yace "kana da matsala da hakkanne?,ko kamfani na tauyeka da wani abun?" kai ya girgiza "ko kadan....amma...."hannunsa ya daga masa "bana son amma....matsalarka nakeson naji idan akwaita,idan kuma babu fine,zamuyi addu'a mu tashi"shurun da ya biyo baya shiya tabbatar masa da cewa.....dukka qorafin da zaiyin ba mai ma'ana bane,ba kuma muhallinsa bane...... 10 *Zafafa biyar na kudine,siya ki karanta cikin aminci* 08184017082 Ko 09134848107 tun daga safiyar jiya zuwa yau din nan babu abinda ke yawo a ranta illa zallar farinciki da jin dadi,duk inda ta kalla cikin sassan nasu farinciki ne yake mamayeta,farincikin da take ciki ya sake ninkuwa a safiyar yau,bayan sunje gidan habiba sun mata dukkan jeren daya dace. Jere ne da ya yiwa kaltum ba zata,don bata taba zaton habiban zata tsira da abinda ta tsira a yanzun dashi ba. Sun isa gidan sun samu.mahaifiyar yusufa mai tarin kirki da karamci kamar yadda aka dinga gaya musu habiban ta dace da surukai,bangarenta na cikin gidansu yusufa ne,wanda babu kowa daga ita sai bangaren surukar tasu,sai sashen qanin yusufan da yake gini shima yana saka ran aure nan kusa,su biyu ne yara maza da babarsu ta haifa,sai hudu mata wadanda duka an aurar dasu,sai kuma wasu matan su biyu da babarsu ta rasu kafin a auro babar yusufa,babar yusufan ce ta riqesu harta aurar dasu. Sassan habiba an kewaye mata shi da gajeriyar katanga,ba wata mai tsaho ba can,akwai dakuna guda biyu falle ɗai ɗai,sai bandaki,sai langa langa da ya saka ya kewaye mata wani guri daga yankin faɗin tsakar gidan da langa langa,ya zamana a mazaunin kitchenaka jera mata kayan aikin girki,wanda ummansu ta samu ta ganganda ta hada mata su cikin rufin asirin Allah,ɗaya ɗakin aka sanya mata kayan gado,ɗayan kuma kujerun iron ne guda hudu wadanda kawu ado ne ya mata su,gida dai ma sha Allah,ya baiwa mutane da yawa sha'awa babu laifi,yakumbo indo ce tayi mata labule, labulaye masu kyau kuwa,umma altine da suke uwa daya uba daya da ummansu,itama mai qaramin qarfi ce kamar umman tasu,saboda.mahaifinsu da inna ta aura dama talaka ne mai rufin asirin Allah,ita ta siyawa habiban kayan amfanin tsakar gida,kamar botikan wanka da rabobi,kujerar tsugonno,tsintsiya mafitai abun kwashe shara dama kwandon adana sharar da sauransu,cikin agaji na ubangiji,sai gashi umman tasu bataji kunya ba,yadda suketa fargaba ita da kaltum,kusan kullum rana da wannan fargabar suke kwana suke tashi. Yamma lis suka dawo dauke da kular abinci qatuwa da babar yusufa da yan uwansa suka dafa musu,kowa ya buda baki sambarka yakeyi,baba laure na daga bangarenta,tunda aka soma abun babu wanda yaga idanuwanta,ko dangin babansun ma da suka zo sai su suka isketa sassanta aka gaisa. Duka wannan bai damesu ba,tunda tako ina Allah ya rufa asiri saidai su gode masa,shi kansa baban nasu tunda yaji su muzammilu sun bada kudin gado da sif saiya tsame hannunsa yana fadin alhamdlh,daman shine dolensa,tunda ya samu masu dauke masa kuma falillahil hamdi,haihuwar yara maza mai rana. idan umma ta tanka masa wayar dake hannunka ta tanka masa,ya gama maganarsa ya fice ta tafas bata ce masa ba,kaltum dake tsaye a gefe wadda itama saida ya gama zageta kan cewa munafuka ce,Allah ne kadai yasan me uwar tasu take samu suke hada kai tana xugata tana boyewa,taja hijabinta ya sanya ta fice daga gidan,amma sai komai ya wanke a ranta washegari dataje tana mazaunin 'yar uwar tata. Yamma lis suka dawo daga wajen jeren,suna tafe ana hira,da yake ba wata tazara mai nisan gaske bace tsakaninsu,dududu bai wuce tafiyar minti ashirin ko da biyar ba. Daga nesa suka hangi tahowar wata mata,gefanta yaron ne da bazai wuce shekara goma ba,tun daga inda suke suna jiyo muryarta,duk da basa iya fahimtar me dame take cewa,saidai da alama fada take,fada kuwa irin sosai din nan "tofa......ga lanti nan,jarabar duniya,ko waye ya tabota kuma oho?,ke kaltume gyara ga sirikarki nan"rakiya maqociyarsu wadda da ita akaje jeran ta fada,maganar tata ta danja hankalin mutanen da suke taren, yakumbo indo ta magantu dab da lanti din zata qaraso inda suke "oho....wannan ce babar nasurun kenan?"kai rakiya ta gyada "ita ta haifeshi,danta na fari kenan......lanti daga ina haka?"rakiya wadda bata dire daga basu amsa ba ta jefawa lanti data qaraso inda suke tambaya. Har wani huci lanti take "ni za'a yiwa iskanci rakiya,bashi nake bi sati biyu kenan an hanani?,to wallahi yau ko kudina ko kaya kudina"da sauri rakiya ta dakatar da ita ganin tare suke da surukanta,kada taga kamar bata gaya mata ba nan gaba taji haushinta,don kusan kowa yasan halin lantin bai dai masifa da jaraba ba "kinganmu,tare muke da surukanki ai,iyayen yarinyar da nasurunki ya aika aka tambaya masa"saita koma kallonsu daya bayan daya,da wani irin duba da kaltum ta shiga nazarin matar,tana tsaye daga bayan yakumbo indo itama tana qarewa matar da aka kira da surukarta ta gobe kallo "aiho...Allah sarki"abinda ta iya fada kenan,saita dubi rakiyan "nikam rakiya minti daya mana". Gefe guda ta koma rakiyan ta bita,dai dai lokacin fatsima ta daukewa kaltum hankali da hirar abinda aka manta ba'a siya ba cikin kayan habiba,saidai yakumbo indo hankalinta na wajen dasu rakiya suke tsaye,yana iya juyo sanda lanti ta soma magana "kinga rakiya karki sake ganina kiyimin irin haka,don zancan auren nasuru babu tabbas,don mi har yau bannkarbi maganar ba,zaqalqawar dangin ubansa ne,amma a rasa yarinyar da za'a hadashi da ita sai mara gata da galihu,wadda kaf qauyen nan sunsan wahalar da suke ciki?,me za'a jera musu ma a dakin da yake ginawar?,me na sama yaci ballantana na qasa?" rakiya tasan halin lanti sarai,batanda sauqi,gwana ce wajen fada da masifa,bata gajiya da bala'i,kamar ma wani gardi yake mata,ita kuwa ba zata iya biye mata ba,don haka tace "Allah ya baki haquri"wucewarta tayi ta barta a nan,yayin da rakiyar ta koma cikin abokan tafiyarta,suka dunguma suka wuce,saidai hirar da sukayi din ya tsayawa yakumbo indo a rai,tana ta juya zancan,saidai batason ta shaidawa zuwaira,don ta tabbatar zata sanya mata tunane tunane ne kan lamarin. washegari aka fara da wankan amarya,wanda a al'adarsu ake sanya yarinya tayi daurin qirji ta zauna saman turmi a tsakar gidansu,maqota 'ya uwa da qawayen amarya zasu hallara,za'a mulketa da lalle wanda aka yiwa hade hade,sannan daga bisani a wanketa fes,anayi ana waqoqin aure kala kala,ana tafa hannu,a qa'idarsu su kakar yarinya ce keyi, saidai idan babu kakar ta bangaren uwa ko uba sannan za'a je ga qanwar kaka ko 'yar uwarta ko yayar uba ko qanwarsa. Tun kusan yammaci gidan ya fara cika da mutane,babban abun alfahari, duk da cewa ummansu miskiniya ce,duk da cewa ummansu bata da komai,bata mallaki komai ba,talaka ce ita tilis,amma kuma tana da kyawun mu'amala,tana da.matuqar kirki da kuma iya mu'amalantar jama'a,hakan shi ya gadar mata samun tarin al'umma,kowa so yake yazo ya nuna mata kara kan bikin farko da zata fara,kowa so yake ya miqo mata alkhairi,duk da ita bata da wadatar da take iya samun yiwa mutum biki bare ta sanya ran za'a rama mata,saidai hakan bai hana mutane miqa mata ihsani ba,saboda kirki da karamcinta,hakan ya sanya ta samu alkhairi sosai,wanda taji a jikinta bata da matsala na dukka abincin da za'aci cikin bikin,wanda a wancan satin wannan shine babban tashin hankalinta,sanda babansu kaltum ya gabatar mata da shinkafa kwano uku man gyada kwalba daya,yace iya abinda yake dashi kenan. Wannan karon mamakinta ya gaza boyuwa,ta dinga kallonsa,dama yasan bashi dashi,bai shirya komai ba amma ya tashi bikin,ya aza dukkan wani nauyi nasa ya koma saman wuyanta?,cikinsu muzammilu da munzali kuwa babu wanda ta gani bare qwandalarsu ta shiga hannunta,bata sani ba sun baiwa baban nasu kamar yadda suka saba,ko kuwa a'ah,basu bashi bane gaba daya?,saita tattara lamarin ta watsar,tunda dama ko can ita ba dabi'arta bace sanya rai da abun hannun wani,shi yasa take zaune lafiya abunta. Shima baban bata sake tunkararsa da komai ba,taci gaba da sallar darenta kamar yadda ta saba tana gayawa ubangiji,sai gashi cikin hikima da ikonsa,ya share mata hawayenta kamar yadda yayi alqawarin zai amsa addu'ar dukkan bawan daya roqeshi. To a daren tun ana sanya idanun ganin zuwan inna ta wanke jikanyarta har aka fidda rai,wasu daga cikin 'yan uwan umman da sukan halin da take ciki dangane da innar tata suka dinga jinjina abun suna mamaki,mamakin da basu taba kamarsa ba,baya ga rashin zuwan innar,babu ko silin tsintsiya data bayar da sunan gudunmawar bikin jikarta na farko a wajen zuwaira. duk da bataso ba abun ya qayatar,kuma aka gama lafiyar Allah,kaltum nacan tana taya umman tasu hidimar mutane akace ana sallama da ita inji nasuru,sai umman ta sanyata aje komai ta fita wajensa. Dab da zata fita zauren nasu ta kusa cin karo da wata,taja baya da sauri tana duban me shigowar,asiya ce ta taho abunta gaba gadi,kai kace saboda ita qwallin qwal aka gina qofar,hasken farin wata ya haskewa kaltum ita,tana sanye da wasu matsatstsun riga da skert na lace,ta yane kanta da qaramin mayafi,kwatankwacin shiga abar Allah wadarai a qauyen nasu,saidai a yanzu wannan itace shigar asiya,da sutturu kala kala wadanda ta tabbatar inna laure bata da kudin siya mata su,bare kuma kawu iliya. hannunta dauke da wata babbar baqar leda,bisa alamu wani waje suka je da wani yayi mata wannan siyayyar. Binta da kallo kaltum tayi har sai data gotata,tunda aka fara hidimar bikin babu wani abu guda daya da asiyan ta sanya kanta a ciki,kai kace ma ba bikin vidansu akeyi ba,ba ruwanta da kowa ba ruwanta da komai, iyakacin idan ta dawo daga yawon gantalin makarantar taci gayu ta fice idan tana da wajen zuwa,odan babu kuma ta wuni a daka kwance,baba kaire na fama da ayyukan gida,duk dai ita dinma babu abinda ta sanya bakinkota tanka na bikin,kai kace ita asiyan habiba ba 'yar uwarta bace,qanwa ma tace a gareta. Saida ta wuce sannan kaltum ta tafu zuwa qofar gidan,ranta yana mata quna,me yasa idanun mutanen gidan nasu kamar sun rufe ne?,kamar ma basa ganin aibun abinda asiyan takeyi,kamar ba wani abu takeyi mai muni ba. A jikin dangar gidan ta sameshi tsaye ya jingina da ita,hannunsa riqe da leda,saita qarasa tana mas asallama,ya amsa idanuwansa bisa kanta yana dan murmushi. Gaidashi ta soma yi,ya amsa yana tambayarta ya taro,ta amsa mas ada alhmdlh sannan ta dora "muna ciki muna aiki saiga aiken kira" "wai kaya na kawo miki na fitar biki"ya fada cikin murmushi yana miqa mata ledar hannunsa,ja baya tayi kadan kana ta noqe kafada kamar wanda ya bata wani abun tsoro,tun daga wancan ranar da abun ya faru umman ta hanata amsar komai daga hannunsa bata qara din ba kuwa,duk da ya turo anyi tambaya,amma ta kasa ci gaba da amsar komai nasa,sai data girgiza kanta sannan tayi magana "Bazan karba ba nasuru,ka barshi na gode"fara'ar fuskarsa ce tadan ragu,yana dubanta "kamar yaya kaltume?,yar atamfa ce fa na kawo miki kiyi fitar biki"duk da taji abinda ya kawo din,kuma tana da buqatar sabbin kayan,don kala daya ta samu daga ummanta,bilal ya siya mata sabon mayafi da takalmi da madina cikin kudin aikinsa daya siya yadin daurin aure shima yayi ragowa,amma bata jin zata amsa din. Ganin ya dage ne yasa ta gaya masa dalili umma ce ta hana "ki karba kice nine na baki ba tare da kin tambaya ba,idan har ta qiya bata yarda ba to zan karba abina"da wannan ya samu ta karba,tana shiga cikin gida kuwa ta direwa umma ledar,suna zaune tare da yakumbo indo suna hira,wadda bata wuce tattaunawa kan sha'anin bikin. "meye a ciki?"umman ta tambayeta "nima ban buda ba,nasuru ne ya bani"rai umman tata ta bata "amma ban hanaki karbar komai daga hannunsa ba?"barin abinda takeyi tayi ta langabe kanta "amma ummanmu....saida nace bazan karba bafa,ya dage,yace idan baki amince ba zai dawo ya karbi abinsa" "wai wanne nusurun?,ba wanda ya aiko aka tambayar masa neman aurenta ba?" "eh shifa"umman ta fada ranta a hade,sai yakumbo indo ta janyo ledar ta buda,ta ciro kayan da suke ciki. Atamfa leda ce guda biyu da aka yiwa dinkin riga da xani, yakumbo ta janyo ledar tana maidasu ciki tana cewa "haba yaaya,ke kuwa ki barta mana ta amsa,ai ba'a hana amsar kyauta irin wannan,samarin yanzun ma da ba kowane mai kyautar ba,ki barta ta sanya abunta,tunda ba aikin banza ake ba,ansan da zamansa,akwai maganar manya a ciki.....ke kaltume,dauki abunki ki adana"sosa taji dadi cikin ranta,saita karba din sannan ta wuce dakinta,tana juyo uammansun tana cewa "ni tsorona daya....gaba kada aje abun nan bai yuwu bafa azo ana zancan maida duk abinda ya bata" "in sha Alla hakan ba zata faru ba,kuma don dai yau daya ta karba ma aiba wani abun bane"yakumbo indo ta bata amsa,saidai gefe daya na zuciyarta yana tuna mata maganganun lanti na dazu. habiba ta samu wadda ta fito daga wanka bayan wanda aka yi mata,tana goge jikinta da turaren da umma altine ta bata,kayan ta zazzage tana nuna mata,ga tunaninta sai taga habiban ta kyabe baki "wato yaya kin gwammace ki amshi kayan wani kina farinciki,amma ni na kada dake na raya ki dauki wasu daga cikin na lefe na kema ki dinka....amma daga ke har umma kowa yaqi,bansan ko wani abun nayi muku ba"murmushi kaltum tayi,tsakaninta da 'yan uwanta qauna ce sosai,suna son junansu, kowa kuma buri yake ya faranta ran dan uwansa,wannan shine kadai abun farinciki guda daya da suka tsira da shi "habiba,kinfi kowa sanin yanayin qauyen nan,bawai minqi dauka bane,amma kinason mutuncinmu ya zube ne?,kaf kayan lefenki a qirge suke a idanun jama'a kin sani,ya sa ido sun riga da sun gama gane meye da meye a ciki,kiyi haquri karki bata ranki,wataranma fa ke zaki dinga dinkawa umma kayan sawar nan,idan ta nice kuma,ni dinma ai kinga ba wai jimawa nasuru zaiyi ba zai aiko da saka rana,daga nan nima zan samu nawa lefen ko?"da kalamai.na hikima masu kyau ta cirewa habiba haushin da taji nasu,sai suka shiga wata hirar ta daban. ************* washegari ne za'ayi kamun amarya da yamma,don haka tunda safe da kaltum ta gama duk aikin da tasan ya kamata tayi,ta cimma umman tasu ita da yakumbo indo da kuma inna altine,tace zata gidansu suwaiba,don jiya bata ganta ba waje wankan amarya,tace mata saita dawo,sannan ta bata saqo gidan wata mata dake saida kabewa can wajen hayin makaranta,tace takai mata kudin,ta gobe ce da za'ayi amfani da ita,ta karba tayi mata sallama ta nufi qofa. Har ta kusa fita umman ta kirata "ki biya ta wajen umman asiya,naji dazu tana neman wanda zata aika wajajen,ki karba aiken ki hada gaba daya". dan jim kaltum tayi,saboda har ga Allah ita batason hada sabga da inna laure,amma hakanan ta amsawa umman sannan ta fice. Sau uku tana sallama amma shuru ba'a amsa ba,ga magana qasa qasa tana jiyowa daga dakin inna lauren,da alama akwai mutane a rumfar tata,don haka saita qara matsawa ko zasu jiyo sallamarta. "ke wallahi zamanin nan kowa a waye yake,duk yarinyar da kika gani tana dan taba tabe taben nan fa,duk ƙarya cr suce basayi" "kai asiya....nidai gaskiya kamar bazan iya ba,haka kawai duk abi a sassaka maka hannu lungu da saqonka" "to ai saikije kita zama,yo Allah na tuba taɓawa dai da shiga ba,wallahi indai xaka cemin ungo sakar maka zanyi,to sai me tunda ba nunawa zaiyi a jikina ba?". Kadan ya rage numfashin kaltum yayi qaura daga jikinta sabida hirar da taji tana tashi da muryar asiya da muryar kuma wata da batasan wacece ba,kamar ta juya sai kuma ta kasa,ta qarasa da hanzari tana bankade labulen dakin,sai sukayi ido hudu,ita da wata yarinya ce 'yar gidan malam qaura,sak sukayi da ganinta,ranta a matuqar bace,zuciyarta na tafarfasa ta dubi asiyan "kiji tsoron Allah,wallahi kiji tsoron ranar da zaki mutu,kin gwammaci saida mutuncinki saboda wani abun duniya?me zasu baki?,zasu baki yanke talauci ne?kome zasu baki dama rabonki ne,da kinyi haquri kinbi ta hanya mai kyau zaki sami koma meye har inda kike din,kome xasu baki idan kudine zasu qare,idam sutura ce wataran tsumma ce,idan kuma abun ciye ciye na kwadayine masai xaki tsugunna ki kasayarwa dasu,zunubinki kuma yana rubuce nan cikin littafinki,yana jiran randa zaki tsaya gaban zatin Allah ki kare kanki....... Cikin salon na me kama da nade tabarmar kunya asiyan ta miqe "kinga malamar munafunci,wadda ta damun da sanya ido a rayuwar wasu,ashe haka kika koma yiwa mutane labe?"hannu kaltum ta daga mata cikin fushi "kada ki sake bakinki ya sake furta wata mummunar kalma a kaina,idan ba haka ba zan miki hauka wallahi"ta fahimci ran kaltum din a bace yake sosai,ta kuma san halinta sarai,kuma bata manta bugun da tasha kwanaki a hannunta ba,don haka ta koma magana ciki ciki "hauka ai kowa ma ya iyashi" "banza shashasha wadda batasan ciwon kanta dana rayuwarta ba,ki guji randa duniya zata miki hukunci ta kuma baki darasi"daga haka ta juya tabar bangaren ba tare data karbi aiken ba,hasalima ta manta abinda ya kawota sashen. Tana tafe ita daya tana tariyar komai,sunanta taji an kira,ta gane muryar waye,saita waiwaya tana qoqarin sakin fuskarta,nasuru ne,ta gaidashi kamar ko yaushe,ya tambayeta inda zata,tace gidansu suwaiba,sai yace suje ya taka mata,ba don taso ba tayi gaba ya bi bayanta,don ba dabi'arta bace jerawa da wani namiji,idan ka cire dan uwanta bilal. Suna tafe cikin ransa yana yabawa da tsaftarta,uwa uba iya magana da kamewa,komai nata a nutse yake,ya dade da sanin cewa ta banbamta da sauran matan karkarar,abinda yaja hankalinsa sosai kenan a kanta,har yaji sha'awar mallakarta. A qofar gidan ya tsaya yace zai jirata,ita kuma ta shige ciki. A tsakar gidansu ta samesu ita da babarta,babar tana gyara waken awara,suwaiban na zaune daga gefe,sanye da rigar atamfa waddabta banbanta da zanin jikinta,hira suke a sake da babartata,saidai kaltum nayin sallama fara'ar fuskar tata ta janye sosai,ta koma kadaran kadaham,kamar ma dai bataji dadin ganinta ba. Duk da hakan kaltum bata kawowa ranta komai ba,ta tsugunna ta gaida babar suwaiba din,sannan ta dubi suwaiban tana jifanta da harara,duk da fuskarta akwai wadatar murmushi "aini wallahi nayi fushi,ace bikin habiba guda?,na zaci ko babu ni a bikin habiba sai inda qarfinki ya qare?" "Bana jin dadi ne?"ta fada cikin halin ko in kula,tana kawar da fuskarta gefa guda "Ayyah,Allah ya sawwaqe,ai da nazo ne da niyyar inyi miki tas,amma rashin lafiya aita kori komai,Allah ya sawwaqe,amma dai yau zaki zo ko?" "wataqila"ta sake amsa mata cikin shakulaton bangaro,wanda a wannan karon mamakinua fara kama zuciyar kaltum,batasan me yasa suwaiban ta sauya ba,gaba daya ta canza kamar ba ita ba,amma ita kam iya tsahon canzawarta batasan wanne irin laifi tayi mata ba,bare ta nemi sulhu ko ta bata haquri ba,jikinta a sanyaye ta miqe "shikena zan wuce...idan kinji dadin jikin naki ki daure ki leqo.....nabar nasuru a waje yana jirana"juyowa tayi daga inda ta maida fuskarta tana duban kaltum,wannan karon fuskarta tada washe ba kamar dazu ba "au tare kuke?" "eh,mun hadu hanya ne yace bari ya rakoni"miqewa tayi tana gyara daurin xaninta "muje na rakaki.....babarmu aramin mayafinki"tace da babar tasu sanda take futowa daga sashen nasu, saita zare mayafin daga wuyanta ta miqa mata,ta daura saman kanta tabi bayan kaltum. Bakinta a washe da fara'a ta qarasa gaban nasiru "ranka ya dade,dama ana ganinku?,tunda ita qawar tawa bata da kirki taqi ta hadamu,ai aikai yaci ace kayi zumunci da babbar qawa"murmushi yayi sannan yace "Alla ne dai bai nufa nazo ba,amma yanzu daya nufa gashi munzo tare da itama gaba daya",gaidashi ta soma yi ya amsa yana tambayarta wasu abubuwan da ba'a rasa tambayar mutum haduwar farko. Koda suka gama kaltum tayi tunanin shikenan zasu wuce ne,saiga suwaiba ta zauna sosai tana ta sokowa nasiru hirararki,labarai kala kala,tun kaltum na tsaye har ta gaji ta nemi wajen zama. Ganin har rana tana qara zafi,suwaiba kuma taqi barin hirar haka,saita dubi nasiru "inajin zan wuce.....saboda ummanmu na jirana,daga nan akwai inda zanje,suwaiba saina ganki"ta fada tana miqewa, sai nasirun yayi zumbur "a'ah bari muje,nima zan leqa gona zamuyi magana da baba" tuni kaltum din ta soma yin gaba abunta,sakato suwaiba tayi tana dubansu sanda yake mata sallama,tana tsaye a wajen har suka wuceta. 11 A mararrabar hanya suka rabu da nasirun,shi yabi hanyar da zata sadashi da gonakinsu,ita kuma tabi hanyar da zata kaita gidan matar da zata kaiwa kudin kabewa. Tun daga nesa ta hangi sashen da tsohuwar makarantarsu take da al'umma a tsaitsaye,wasu manyan lafiyayyun kyawawan motoci guda uku fake a gefe,saita dauke kanta ta wuce zuwa gidan mari mai Saida kayan miya,ta shiga suka gama magana ta bata kudin ta fito. Idanunta sake sauka yayi ta gefan makarantar,har yanzun mutane ne a tsaye a wajen suna zagaya makarantar,zuwa yanzu jama'ar dake cika wajen sun dadu,don an samu dadin 'yan kallo,wadanda kallon motocin dake wajen da kuma aikin da taga kamar ana danyi ya kawo,cikin masu kallon kuwa harda manya. Baki ta tabe tana dannjan tsaki,mutane suna bata mamaki,komai qanqantar abu abun kallo ne a wajensu "yaya"taji kamar muryar bilal tana qwalla mata kira,saita dakata da tafiyar sannan ya waiwaya. Bilal dinne kuwa,ta zuba masa idanu tana jiran qarasowarshi,kamar ko yaushe fututu dashi,da wahala kaga bila din tsatsaf dashi,idan ba ranaku irin na juma'a ba ko kuma ranakun idi, saboda koda yaushe cikin aikin wahala da neman kudi yake. "kai kuma me kakeyi a nan?,Allah dai yasa ba fada ake ba"dariya ya danyi "ni bana tsokana ai yaya saidai a tsokaneni....ba fada ake ba,wasu ne wai suka turo a sake ginin makarantar me tafasa,sannan a gina mata masallaci babba nayin sallah,shine na maqale a wajen ko Alla zaisa a sakani cikin masu aikin ginin"tsaiwa tayi tana kallonsa sosai,kamar kowanne lokaci shi.bilal din tunaninsa daban,ba kasafai yake hango wani abu ba,saidai shi a hango masa "kai wato samun aiki ne ya dameka,bama ka tunanin shiga sahun daliban da za'a dauka ida an gama gyaran makarantar ko?"dariya ya danyi "karatu fa yaya?....tabdi ba yanzu ba" "au bazakayi ba kenan"sai yayi murmushi "zanyi amma ba yanzu ba" "Allah ya shiryeka"ta fada tana yin gaba,ya biyota a baya yana ci gaba da bata labarin irin mutanen da sukazo wajen,'yan birni sosai 'yan gayu,kowa sai kallonsu yake,harda cewa "yaya motarsu kamar madubi,idan ka tsaya a gabanta Allah har kanka kana iya gani,da guduwa fa aka dinga yi,kowa yana tsoron kada ya bace"murmushi ta saki kawai "naji,kaidai ka kula,ba ruwanka da kowa,ka kiyaye" "ni dama yaya meye nawa?,kawai aiki nake nema"shiya rakata har gida suna hira,sannan ya zauna yaci abinci ya sake ficewa. Da yammacin ranar aka kama habiba,kuma shima abun ya qayatar kamar dai jiyan,komai a tsare akayi lafiya aka gama lafiya,saidai rashin ganin mutum biyu ya baiwa kaltum mamaki qwarai da gaske inna da kuma suwaiba,babu su babau labarinsu har akayi aka gama. Washegari akayi wuni da daurin aure,wata washegaein kuma aka dauki habiba zuwa gidanta,ranar sun sha kuka dukkaninsu,sai kaltum ta dinga jin kadaici sosai,ta dinga jinta wani iri tun a ranar,ta tabbatar wani sabon zaman ke sake fuskantota,wanda batasan da wacce fuska zaizo mata ba,ta dawo gida jiki a sanyaye bayan sun baro habiba da tsohuwar da zata zauna mata kafin gobe suje ayi mata budar kai. Washegari da safe suna tsakar gida suna karyawa saiga sallamar inna,abinda ya bawa dukkaninsu mamaki, tare da tambayar kansu dalilin zuwan innar,tunda dai har akaci aka cinye innar bata koda rabo dangar gidan ba,hakanan sisinta da sunan gudunmawa ga bikin jikarta bai ratsa hannun umman ba,sai yau a rana ta qarshe da za'a gama komai kuma sai innar tazo?. Daga umma altine,yakumbo indo kowa fuskarsa cike da mamaki take,hakanan babu watq cikakkiyar fara'a jin dadi ko walwala suka tarbeta,saimw umman ce daya yunqura cikinnzallae farinciki ta shimfida mata sabuwar tabarma wadda ta habiban ce da aka manta ba'a tafi da ita ba,yau za'a tafi da ita,jikin umma na rawa tasa aka zuba mata kunu da qosai da sukayi aka aje ma innar,sannan ta tsugunna gefanta tana gaidata,bayan umma altine da yakumbo indo sun gaidata,sai kaltum wadda ke zaune gefe,ta zubawa sarautar Allah idanu,ta kasa ta tsare taqi tashi,don itama tana son taji dame innar taxo. Badai tace komai ba har aka gama gaisawar,hakanan bataqi jan kwanon kunu da qosai ba ta fara kaiwa baka,har zuwa lokacin da masu tafiya suka fara da taruwa. Tsaf kaltum itama ta shirya cikin daya daga cikin atamfofin da nasuru ya siya mata,wadda ta saka shekaran jiya,yau din sai tayi maimaice,zata shiha dakinsu ta debo ragowar kayan sawar habiba taji innar na cewa "Wannan saqar tabarmar tayi kyau....irinta naketa nema zan siya ba'a samomin ba"tasan halin innar sarai,don haka saota fasa shiga dakin,ta waiwayo tana cewa "Kuma gata na ko ina a kasuwar darimi,idan kina so ajjiye kudinki jibi naje da kaina na siyo miki" harara ta balla mata "Naqi na bayar din,wannan din da kika dawo dominta ita zan dauke dan uwaki,shegiya manna'il lil khairi"baki kaltum ta tabe,sannan tayi gaba,dama tasan abinda innar keso kenan,ita akuwa bataga dalioin da zaia bata kawo komai ba sannan ta dauki wani abu sabo na amarya ta tafi dashi ba,Allah ba zata bar mata ba,saida duk yadda za'ayi ayi. Tana tsaye bakin window tana fakon innar,har Allah yasa ta tashi zata shiga bayi,da sauri kaltum ta fito,taja tabarmar ta nade tsaf tayi dakinsu da ita,ta daga shimfidarta ta fara shimfida tabarmar daga qasa,sannan ta maida kayan kai,ta yadda babu yadda zaka gani kace tabarmar tana qasan,sannan ta fito tsakar gidan,tana ci gaba da hada abinda take da buqata. Tana jin sanda innar ta fito tana neman shimfidar tata,neman duniya anata juyayi amma kaltum tayi fir da ita,umma ta kirata taja mata kunnen indai ita ta dauka ta fito da ita amma tace batasan zance ba,daga qarshe ma da innar ta soma zarginta tana antayo mata zagi saita dauka mayafinta ta fice "Shegiya mai baqin hali,gadon tsiya da talauci,shi yasa gashinan ubanku har yau jiya iyau"haka ta dinga gayaqa kaltum din,darajar ummansu kawai taci ta fita bata tanka mata ba. Bata dawo cikin gidan ba sai data daidaici lokacin tafiya yayi,ta dawo kuwa a dai dai,don an gama haduwa,an fito da sauran kayan da za'a tafin dasu. Dai dai sanda ta shigo ta ji inna na fadin "To zuwaira.....ina kayan garar ne?"muryar umman a tausashe tace "Babu inna,ba'a samu yi mata ba" haba innar ta kama "La'ilaha illallahu,yanzu zuwaira garar ma saita gagari yarinya?,haba wannan wanne irin abun kunya ne?,ace kun kasa yiwa yarinya gara fisabilillahi?,yo ko bashi bakwaci kuyi mata ita ba ku fidda ita kunya?,wallahi ba don na riga nazo ba,kuma banason surutu kada ace banzo ba da babu inda zani,haba" tsit wajen yayi,aka koma kallon kallo na mamaki,yayin da umma ta samu waje ta zauna jin yadda mahaifiyarta ke shirin kwance mata zani a kasuwa,yakumbo indo ce ta karba "Haba inna wannan aikinki ne ai dama a matsayinki na kakar yarinya,ke ya kamata kiyi,basu da suka gama hidimar biki qarfinsu ya qare ba" shalele ce tayi magana,shi yasa innar yin shuru bata sake cewa komai ba baya ga "To naji uwar iyawa"da haka aka tattaru aka dunguma gidan amarya habiba. Ba shakka habiban tayi sa'a,don kwana daya tal a gidan yusufa amma sun sameta tare da tarin alkhairansu,ita kanta 'yar tayin zaman yabonsu take,anan akayi budar kai cikin karamci,aka sake tattarawa kuma biki ya qare akabar amarya ita da angonta,daga nan kowa ya wuce gida,na nesa ma suka je suka kintsa kayansu suka yiwa umma sallama suka wuce,umman nata godiya a garesu saboda tarin karamci zumunci da kuma karar da suka nuna mata. *_MABUDIN RAYUWA_* Tun bayan tafiyar habiban sai gidan gaba daya ya rage yi mata dadi,sauqin abun ma dama can ita da umman abokan hira ne,bata mata irin alkunyar nan da akewa dan fari,suna hita sosai,hakanan suna shawara sosai da ita,saidai wani lokacin ba komai zata yi magana da umman a kansa ba,dole akwai buqatar abokin shawara,ada suwaba ce,amma a yanzun suwaiban gaba daya ta yada ita,ta kuma janye jikinta,sosai da kaltum din,kai kace basu taba wata mu'amala ba,tun kaltum din na bibiyarta har itama ta gajibta qyaleta,sai bilal,wanda shi ba mace bane bare,asalima bilal din ba mazauni bane,bama kamar yanzu daya samu aka sanyashi cikin masu aikin ginin sabuwar makarantar da akewa qauyen,sam baya wuni a gida,daya karya da safe ya fice wani lokaci sai dare,ko abincin rana baya waiwaya,kullum ya zauna hirar da yakewa ummansu shine,zasu samu kudi sosai idan suka gama aikin,idan aka bashi kudin umman tashi za siyawa kayan sawa,ya gyara sashen nasu,sannan ya bata jari,itama yaya kaltume zai siya mata kaya ya bata jari,sam babu sunan babansu cikin lissafinsa,koda umma tace babanku fa bilalu?,ka manta dashine?,budar bakinsa sai yace "Banda shi umma,ba yanzu ba tukunna, Shima idan ya samu baya tunawa damu"kai umman ta kada,har cikin ranta tana jin takaicin wannan abu,Allah ya sani iyakar iyawarta tayi domin ganin sun qaunaci mahaifinsu yadda ya kamata,amma shida hannunsa yake rushe duk wani gini da tayi,saboda a gabansu yake iya cin zarafinta,a gabansu yakeniya barinsu da yunwa,su kansu basu tsira ba,don basa samun dukkan wata kulawa da sauke haqqi irin na uba daga gareshi "Nima kuwa bazan karbi komai ba kenan bilalu"ta fada umman tana tsareshi da idanu,idon nashi ya zaro "Saboda me umma?,na miki laifi ne?"saita daga kanta alamun eh sannan tace "Bilalu indai ba zaka yiwa mahaifinka abu ba nima ba zaka min ba watarana,mahaifinka mahaifinka ne,kome yayi maka,kome ya zama kuwa,don shine silar samuwarka,baka da abinda zaka saka masa dashi,kome zaka bashi,kyautata masa kuwa wajibinka ne bilalu,bakai ba dukkaninku"ta fada tana dubansa shida kaltum,wadda tunda suka fara zancan bata ce komai ba,tana ta cinn tuwonta,wanda dawar ma bilal dinne ya kawota,don ita a wajenta hukuncin bilal yayi mata dai dai,bataga laifin yaron ba ko qanqani,kai kawai ta gyadawa umman tasu tana miqewa da kwanon hannunta,ta isa gaban tukunyar tuwon da aka jiqa da ruwa,wadda ita kadai ce tayi saura ba'a wanke ba,saboda umman bata bari su kwana da wanke wanke,tana jin sanda bilal din yake cewa "Kiyi haquri umma,indai na bashi zaki karba to zan bashi" zuciyarta cike fal da tausayin bilal din tace "Allah yayi muku albarka gaba dayanku,ya rabaku da sharrin zamani" ya amsa da amin. Daga saman dan wani dutse da suke zama suyi wanke wanke kaltum ta zauna kawai tana qarewa umman tasu kallo ita da bilal,wai abu me nauyi yana reto a zuciyarta,tana jin yadda hawaye ke kwaranya daga can cikin zuciyarta,tana qaunarsu,tana sonsu,saidai batasan yadda zata inganta rayuwarsu da tata rayuwar ba,tana fatan idan tayi aure nasuru ya cika mata burinta,wanda dashi take fatan ya zama mabudin yayewar dukkan wata damuwa tata a rayuwa. Ta jima zaune a wajen tana kallosu yadda suke hira,bilal yana kwasar umman kamar kakarsa,da yake ya saba haka yake mata,har sai da umman ta dubi sashen da take,ta yafitota da hannu tana cewa "Taso ummukulsum daga nan wajen,magangara ce,kuma dare ne"ta fada cikin nuna qauna da kulawa,saita miqe a hankali tana dawowa inda suke din ta nemi waje ta zauna. Dubanta bilal yayi "Yaaya....tun dazu nakeson baki wani albishir amma saina mata"ya fada cikin excitement yana miqewa tare da kakkabe rigarsa daya kwashi qasa,harara kaltum ta watsa masa "Allah yasa da gaske kake kake wani cika baki ba albishir din shirme bane" baki ya bude yana kallonta,sannan yace "To wallahi yaya qatoton albishir ne,kuma kin yarda indai hakanne idan na baki zaki bani goron albishir din?" "Na yadda"ta fada tana qaramar dariya,saiya wuce zuwa dakinsa da sauri yana fadin "Zan baki mamaki kuwa". Bai jima ba ya dawo hannunsa dauke da maka makan takardu guda uku masu tsaho da fadi,ruler da abun rubutu,sai marker da colour da drowing ya zube a gabanta. Ido ta fitar tana duban kayan sannan ta dubeshi kusan lokaci daya ita da umma "Bilalu,ina ka samo wadan nan?"sai daya zauna sannan ya amsa mata "Wadan nan takardun na jikin bangon ajujuwan da aka rushe ne,aka ce mu dauka idan muna so,su kuma saura kudin abincin aikina ne,na raka bashir kasuwar lahadi na gansu acan na siya miki". Fuskarta ta cika da murmushi da wani irin qaunar dan uwanta,farinciki sosai ya kamata na abinda yayi matan "Kai....kai bilalun umma,da gaske kake kuwa?" "Gasu gabanki yaya?" "Ashe dama kana sona haka?"ta fada tana dariya idanunta a kanshi,sai yayi murmushi kawai ba tare daya amsa mata ba "Umma.....kinga abinda Bilal ya siyomin dan Allah" "An gode maka Allah ya qara zumunci ya hadamin kanku" "Amin umma wallahi" ta amsa tana jujjuya takardun tare da sake qare musu kallo,tana tunanin abinda zata zana a cikinsu. Sai data gama murnar sannan kuma ta dubi bilal din "To a ina kake cin abinci?,kai daba gida kake dawowa kaci ba?,kuma gashi ka tattara kudin haka kawai ka siyomin kayan zane?" "Ana kawo mana abinci lokaci lokaci,ko a kira masu talla a siya mana,ko mantawa suke sun bamu kudin?" Kai ta jinjina,taga qoqarinsa,shi da bai iya tara kudi,daya samu aci cikin ciki kawai,idanunta ta dauke daga saman kayan ta mayar kan fuskarsa "Amma dai zanfi so ace ka tara kudadenka bilal,idan aka gama ginin nan,koda ni ban samu shiga ba....kai ka shiga bilal,kayi karatu don Allah" "Tare dake fa muke zuwa makaranta duk bayan sallar asuba yaya kin manta?"kaita kada tana ci gaba da kallonsa "Na sani,karatun zamani bilalu,karatun boko.kamar kowa,ni ina sha'awarsa sosai,amma tunda bani da wani isashen lokaci babu kuma dama zanso ace kai kayi,ko don ka taimaki kanka,ka kuma taimaki ummanmu" shuru yayi na wasu sakanni,sannan daga bisani ya amsa "Me zai hana yaya ke na tara miki kudin ki shiga?"kanta dai ta kuma kadawa "Kai yafi cancanta kayi bilal,kainw namiji,ni dana fara za'a fara batun aurena,azo a cireni kaga anyi asarar kudin da aka kashe" "Zanyi yaya"ya bata amsa yadda ya saba bata,da alamun baison zancen ma gaba daya. Murmushi ummansu tayi,ta jima da fahimtar bilalun baya son makaranta sam,musamman karatun boko,shi yasa duk yadda kaltumen tayi dashi yake zillewa,itama kaltum din dole tayi shuru ganin ya miqe,saiya qarasa ya dauki wata tsohuwar hularsa daya wanke ya sanya a kansa yana cewa "Umma zani dandali......yaya gaba daya kin rabu da zuwa" "Hmmmm"kawai tace,don ita kanta tana son zuwan,amma hakanan zuwan ya fita a kanta,tun wancan ranar da babansu ya fadi mummunar kalma a kanta "Zanje,sai wani lokacin saimu tafi tare" kansa ya gyada ya fice abinsa ta bishi da.kallo. Bilal kenan,shi sam a rayuwarsa bashi da tension,duk da tarin qalubale iri iri dake bibiyar rayuwarsa,amma kamar baisan dasu ba,duk da cewa akwai quruciya a sha'aninsa,tunda har yanxu shekara sha hudu yake,sai tsahon qafa da zai sanya mutum yayi tunanin yakai shekara sha bakwai. 12 D/Z *Zafafa biyar na kudi ne,ki biya ki karanta ciki aminci,yadashi wato sharing tamkar xalunci ne,Allah kuma baya barin zalunci* Ku tuntubemu ta nan 08184017082 Ko 09134848107 Sanye yake da jallabiyya fara qal mai sulbi,wadda ta saukar masa har daidai idanun sahunsa,bata qarasa masa har qasa ba saboda yanayin tsahonsa,tattausan farin slippers ne a qafarsa,idanunsa saye da farin glasses,sai jarida dake riqe a hannunsa wadda suke buga bayanan kasuwanci da kamfanunuwa,tattausan qamshin turaren tuscany ne ke fita a jikinsa,kamar yadda sumarsa ke sheqi,duk kuwa da cewa dare ne. Yana tsaka da dubawa ne kiran prof ya shigo wayarsa,don haka ya miqe ya tattara dukkan abinda yake ya fito don amsa kiran nasa. Qasa qasa yayi sallama cikin falon nasu,wanda yake shuru sai qarar na'urar sanyaya daki hade da qamshin turaren daki. Mutum uku ne xaune a falon,wanda kusan koda yaushe haka zaka samesu,kowa yana abinda yafi qwarewa akai. Jawahir wadda ke kwance rub da ciki tana game a tab,sai najwa sata tasa litattafai a gaba masu tulin yawa tana dubawa,yayin da humaida ke gyaran faratanta,a yadda suke zaunen saika dauka kowa a cikinsu baisan da zaman dan uwansa ba. Sallama yayi muryarsa can qasa,idanunsa saman tvn wadda babu wanda yake ta kanta a cikinsu,hasalima volume dinta can qasa yake,kuma suna wani program ne mai muhimmacin daba lallai su ya burgesu ba,saboda basu san muhimmancinsa ba. Dukkaninsu kowacce cikinsu tadan gyara yanayin yadda take saboda nuna sunsan da shigowarsa,jawahir ta miqe zaune daga rub da cikin data yi,najwa ta gyara glass din fuskarta bayan ta kalleshi,humaida ta lanqwashe qafafunta,duk da bata gama yankan farcen ba. Kusan kamar a tare humaida da jawahir suka gaidashi,ya amsa cikim yanayin kulawa yana dubansu,sannan idanunsa suia sauka kan najwa,saita sake sanya hannunta ta gyara glass din fuskarta sannan cikin wani yanayi kai kama da jin isa isa tace dashi "Barka da dare" "Barka"ya amsa a taqaice yana duban hanya,inda hajiya jidda ke fitowa,kamar kullum kamar kuma kowanne lokaci daya kasance prof yana gida ta fito cikin shiga ta alfarma,wani dandatsetsen lace ne da duwatsun jikinsa keta bada qyalli da walqiya,isan ka ganta a sannan zakayi tsammanin zata wata dinner ce,bawai kwalliyar me gida a cikin gida ba. Fuskarta dauke da madaukakin murmushi take dubansa,cike da kulawa da tsantsar qauna data bayyana cikin qwayar idanunta "Son....kada dai ace ka gaji da jiran abincinka ka biyo sahu?,yau ba favourite dinka akayi ba,sai nasa hasana ta sake girka maka wani abun,don banson ka fita waje neman wani abun,ko ka kwana da yunwa" dan murmushi ya saki,wanda yafi kama da washewar fuska,koda yaushe kulawa take bashi ta musamman,a kullum soyayyar da take nuna masa tafi ta kowanne mutum dake cikin gidan,idan ua debe mahaifinsa kawai,koda yaushe kuma kowanne lokaci komai nasa yakan kasance na daban kuma na musamman a wajenta,saidai kuma.....baisan dalilin da yasa zuciyarsa ta zama wata irin zuciya mai tarin butulci da saka alkhairi da sharri ba,ko sau daya ta kasa jin farinciki da wadan nan shekaru data kwashe tana bashi dukkan kulawa goyon baya da qauna,ta kasa jin nutsuwa akan kanta na dinga alkhairi da hidima da takeyi dashi,idanunsa sun kasa manta ta,itace dai a wannan matsayin daya santa,itace dai wannan din daya sani,ta kasa gogewa daga yanayinta na baya,duk da tarun shekaru da kuma sauyawar rayuwa da kuma yanayi,wanda dukkan dan adam yake samun kansa a ciki. "Yau din ban shigo da yunwa ba mommy,da kin qyaleta,abba nazo gani,yace min yana son ganina,ina tsoro kada naje bacci ya debeni ban samu zama dashi ba,kada ya tsammaci ina gudu ne kamar ko yaushe"murmushi tayi "My son....dan abbansa,nikam naga sanda wannan dramer taku kaida abbanka zata qare,shi har yau ya gaza fuskantarka,ya sallama...,kai kuma kana kam bakanka.....ka gaza sakar masa...." "Wacce gulmar tawa akeyi?"suka tsintsi muryar prof daga bayansu,yana fitowa daga qofar data sada wannan sashen da nasa sashen,cikin doguwar rigar jallabiyya,shi dinma kamar dai samir din,sai jini yayi aikinsa,daka kalli samir ta yanayin qirar jiki....sak prof din,saidai kuma kamanni a fuska bashi bane,kana iya daukan wanna ka baiwa jawahir dake zaune,itace Prof din zammm,don najwa ma mommynta ta biyo. Dukkansu suka waiwaya suna dubansa sanda yake fitowar,jawahir da mommy murmushi sukeyi,yayin da najwa ta dake kamar bata a wajen,duk sanda irin haka zata faru takan yi dif kamar bata wajen,tana matuqar kishin samir,sau da dama tana jin inama ace itace shi,inama ace itace babbar diya namiji kuma ga professor din ba samir ba. Inda suke tsayen ya qaraso,fuskarsa kadaram kadaham,cikin girmamawa kowa ke gaidashi,sannan daga bisani ya waiwayo yana duban samir din "Ba don nayi kiranka ba da ba zaka nemi ni ba kenan?"ya fada da wata murya mai nauyi,idanuwansa saman fuskar samir din,wadda take fayau,bata dauke da kowanne irin emotion,a ladabce yace "Afwan daddy....."yayi maganar ne yana dan ranqwafawa alamun girmamawa,shuru yayi bai sake cewa komai ba,saiya juya yana neman wajan zama nan cikin falon,duk da cewa ba dabi'arsa bace yin hakan,da wuya ka sameshi zaune a nan,indai ba abinci zasu ci su dukka gaba dayansu ba,ganin haka ya sanya humaida miqewa,don ba kasafai take zama cikinsu ba idan tagansu dukka tare waje daya kamar haka,kuma tasan ba wani kira ko zama daddyn ya umarxi kowa da kowa ba. Qasan carfet din samir ya samu ya zauna sosai daura da daddyn,don taqin dake tsakaninsu kadanne,a sannan jawahir tuni harta miqe,ta shiga kitchen ta hado musu abunsha mai sanyi,irin sanyin nan baina baina mai saukar da nutsuwa,wanda bazai cutar da haqora ko bakinka ba,ta hadashi ne da kanta,saboda sanin da tayi,daga daddyn har samir din suna son natural juice. Sai data zubawa kowa cikin cup sannan ta turashi gabansu,ta miqe tabar falon,saiya zamana daga mommy najwa sai samir din da daddyn. Lemon daddyn ya soma kurba mai dan yawa sannan ya ajjiye yana harde qafarsa daya cikin daya,idanunsa saman fuskar samir din "Kamar dai kowanne lokaci,duk da cewa dukkan alamu sunata nuna kansu akan cewa ban isa da kai ba......" Da sauri kalmar daddy ta sanya samir daga kanshi cikin yanayi na rashin jin dadi ya dubi daddyn sannan ya sunkui da kai,baisan me yasa har kwanan gobe daddyn ya gaza fahimtarsa ba ballantana yayi masa uzuri,koda yaushe tunanin daddyn a kansa daban yake,sai yayi kama zai fahimceshi sai kuma komai ya sake damalmalewa"akwai wani taro na musamman da xamu gabatar,wanda ya danganci dukkan wani babban mutum mai fada aji cikin jam'iyya.....shima dai zan miqa goron gayyatata zuwa gareka,bazan fasa ba bazan gaji ba,saboda bani da magajin daya wuceka,inason in sake nuna fuskarka a wajen,kamar yadda kullum kowa ke qoqarin jan nasa,yana sake nunashi,da qulla kyakkyawar alaqa tsakaninsa da manyan mutane"shuru yayi sanda yakai aya yana duban samir,wanda qwaqwalwarsa ta tafi tunani,zayaso ace addyn nasa ya gane,ya kuma fahimci tsantsar rashin sha'warsa kan dukkan wata harka data shafi siyasa,zayaso ace ya fahimci abun babushi sam a jininsa,amma yanzu dukkan wata magana da zaiyi daddyn zai fassarata ne ta wata fuska daban,ma duk da haka bai fasa ba,saboda yasani cewa abinda zaiyin gaba yake da abinda daddy yakeso yayi,don haka cikin kwantar da murya dake cike da zallar girmamawa yace "In sha Allah zan halarta daddy.....saidai kuma a jibi nakeson zuwa wani qauye zan gabatar da wani aiki,zanyi qoqari na katse wani abun na halarci inda kakeso din"ya fada ba don wai har cikin zuciyarsa yana jin farinciki da abinda ya fada din ba. Da sauri najwa ta daga kai ta dubi samir don bata tsammaci jin haka daga bakinsa ba,wannan wata babbar dama ce da take dako,wadda zata fara gwada sa'arta,sai kuma gashi samir din ya wargaza mata budget "Shikenan......babu damuwa,nidai fatana kaje din" "In sha Allah daddy"ya amsa masa a ladabce "Allah yasa...."ya amsa yana kuma dorawa da fadin "Fawwaz ya kawo qararka" daga kai ya sakeyi a take,kai tsaye yana duban daddyn,maganar saita dakeshi ta kuma bashi mamaki,qararsa tame?,me yayi masa?,idan da akwai mutumin daya kamata ace an kawo qararsa din fawwaz dinne,saidai kafin ya furta komai mommy ta rigashi magantuwa ta hanyar fadin "Qarar son?,me yarona kuma yayi?ta yaya za'a kawo qararsa?"tayi maganar ne cike da tarin mamaki,fuskarta kuma babu alamun fara'a ko kadan,waiwaya prof ya soma yi ya dubeta,kana ya bata amsa "Shi yaron naki kenan har abada baya laifi,baya kuma aikata ba dai dai ba?......"kai ya girgiza ranta a hade "Bance haka ba daddy,amma.ina da tabbaci ko meye samir zai aikata yana da dalilinsa,ka soma jin ta bakinsa kafin yanke kowanne irin hukunci" duake idanuna prof yayi daga kanta ya tattara kan samir sannan ya fara magana "Fawwaz ya gaya min hanyar da kakebi wajen sarrafa duk wata riba da alkhairin da kamfani ya samu,har zuwa yau dun nan da kayi qarin albashi kanka tsaye,ba tare daka tsaya kayi la'akari da irin abubuwan da shi ya hango maka su ba,wansa ni duk cikin lissafinsa ina ganin maganarsa da ra'ayinsa suna tafiya kan dai dai,kuma bisa mizanin da ya kamata,sannan a wajena hasashensa yafi zama dai dai fiye da.naka kai hasashen da tunanin".sosai abinda fawwaz din yayi ya daurema samir kai,tun ba yau ba yake lura da tarin abubuwa masu yawa tattare da fawwaz din,baisan me yasa ya sanya idanu da hankalinsa kacokam kan rayuwarsa da yadda yake gudanar da ita ba "Kai nake sauraro" prof ya fada har yanzu yana kallon samir,kamar yadda mommy ma idanunta suke a kanshi. Zama yayi sosai ya tanqwashw qafafunsa,sannan shima ya aza idanunsa kan fuskar mahaifin nasa "Daddy,dukkan abinda nake aiwatarwa bai saba doka tsari ko yarjejemiyar da muka dora tsarin kamfanin akanshi ba,duk wani aiki da nake aiwatarwa ina yinsa ne bisa tsarin daya dace,daddy....yau koda ace ba bisa tsari nake komai ba,kudin da nake fiddawa ina gabatar da wadan nan abubuwan dani dakai dukka munfi qarfinsu.....wani tallafi da nuna tausayi ne tsagwaronsa zuwa ga wasu gungun mutane da suke neman ayi musu wani abu guda daya biyu zuwa uku cin rayuwarsu,ruwan sha ilimi da wajen ibadarsu" sosai mommy ta ritsashi da idanu tana nazarin wani abu,yana da fasahar harshe da iya magana,wadanda akullum sune abubuwa guda biyun da take jinsu saman wani mizani mai girma,saita sauke ajiyar zuciya mai nauyi,kafin wani daga cikinsu yace komai ta fara magana "Ni nasan yarona bazai.aikata wani abu da bai dace har irin haka ba,hasashe ne da tunani mara tushe kawai fawwaz din yakeyi,maimakon yayi qoqarin kula da kwaikwayo da ayyukansa.....bari fawwaz din yazo,saina bata masa ransa wallahi"ta fada tana qara tim kicin kicin matuqa da fuskarta. Hannu prof ya daga mata kawai sannan ya magantu "Ni bance ba,ban aiki kowa ba,kome fawwaz yakeyi yana yine saboda qaqarin ganin daidaituwar lamuran dan uwanshin nan mara tartibiyar alqibla"ya qarashe maganar yana tsagaitawa kamar me buqatar hutu,kafin daga bisani ya dora "Shikenan,wannan naji bayaninka....amma wanne irin zuwa qauyenw haka wannan,babu ji babu gani,da wannan tafiye tafiyen naka,har yaushe ka maida hankalinka kan aikinka yadda ya dace?" Tamkar ita prof din yakewa wannan 'yar titsiyen haka ta marairaice fuska "Daddyy....don Allah ka barshi haka nan,ya zuwa yanzu fa samir.ba qaramin yaro bane,kai da kanka ka fada fa...." "Kada ayi masa fada kenan?"ya furta yana duban doguwar fuskarta,wadda duk yadda tsufa yakai ga son haike mata taqi bari hakan ta faru,cikin ranshi yana sake jinjina mata da yaba qoqarinta,zallar qauna da kulawa da take nuna ma samir din tana bashi mamaki kullum kwanan duniya,zata yarda kowa a gidan yayi kuskure ko laifi ciki harda autarta amma banda samir,koda yaushe ita daidansa take gani,dai dansa take nuna masa,duk da tarin tulin wannan sabanin da suke yawan samu,kan banbance na tsari da ra'ayin rayuwa da suke samu "Ba haka bane.....ba kuma haka nake nufi ba....."ta soma fadi a tausashe,saidai kuma qarar wayar samir din ta katse dukkan abinda zata fada,ya fara qoqarin cirota ya maidata silent,baisan yaya akayi ayau din ya manta bai sata silent din ba,kamar yadda yakeyi duk sanda zashi gaban daddy prof din. Mummy jidda ce ta katse masa yunqurin nasa ta hanyar fadin "Jeka amsa wayarka.....zan turo maka da sauran abinda kake buqata" Tsam ya miqe,don dama abinda yake nema da buqatar ji kenan tun dazu daga mahaifin nasa amma ya qiyi masa,yaqi jinin ranaku irin wadan nan,da daddyn nasa zai zaunar dashi yana sake tuna masa qadamin da suke kai dukka su biyun. Gefanta ta ajiye littafinta tana cire gilashin fuskarta shima ta dorashi saman littafin,fuskarta ta yamutse sosai tun kafin ma ta furta komai "Daddyyy" ta kirayeshi,wanda kiran yaja hankalinsu dukka su biyun shida hajiya jidda,saidai ita mommy kanta ta dauke tana sake tsiyayawa prof lemon da tuni ya shanye cup din farko "Daddy.....wai me yasa ba zaka haqura hakanan da ya samir ba,gani daddy,na dauki damarar share maka hawayen daya kasa share maka,duk don saboda kai daddy nake wannan karatun fa,saboda kai na zabi wannan course din da nakeyi don na faranta maka,beside ni ma ga jawahir....duk da na fita sha'awa da qarfin zuciyar son zama maka hasken idaniya....daddy what man can do woman can do even better mafa daddy....ka barshi kawai ya rayu yadda yaso,mu biyun nan mun isheka makwafinsa". Wata hadaddiyar tsawa mommy ta dakawa najwan tana dubanta,fuskarta murtuke tsaf,wanda babu mamaki da najwa din tana kusa da ita babu abinda zai hanata zazzabga mata mari,amma tunda ta danyi nisa da muhallin da take zaune saita fara zuba fada kamar xata ari baki "Ashe ke din baki da hankali najwa?,kin manta waye samir ne a wajenku?,yayan naki kike fadin wannan maganar a kansa?,mahaukaciyar ina ce ke?,tashi maza ki bani waje kafin na taso nabi ta kanki keda tarin litattafanki,shashashar banza kawai mara azanci"ta fada tana huci. Cikin mamaki najwa ta janye idanunta daga fuskar mahaifiyar tata,saita soma debe litattafan nata bayan ta miqe tsaye "Xo nan najwa" Daddy ya fada a hankali,wanda hakan yasa ta dakata da abinda takeyi,ta qataso inda yake ta zauna daga gefansa "Kullum kuma koda yaushe ina alfahari da ku,musamman ke din nan,koda baki fada ba na sani kuma ina hankalce,kuma ina yabawa da qwarin zuciya da kike dashi akan kaina,da son cika min burina da kuma mafarkina,amma abu daya nakeso ki dinga tunawa,samir inda ace shi din wani ne shi yafi cancanta yahau bigiren da kika fara hawa,saboda wataran ya zame muku babban bango majingina kuma garkuwa a gareku,koda bayan babu raina,inaso kici gaba da kallon sakir a matsayin babban wa uba a gareku kinji,hakan bazai hana rayuwarki ci gaba da tafiya kamar yadda take ba a yanzu,kiyi koyi da jawahir ta wannan bangaren,bani da burin daya wuce koda yaushe na ganku tamkae tsintsiya madauri guda,wannan ne kada zai hana maqiya da mahassada suci galaba akanku.....kin fahimta?"ya fada yana dubanta,kanta kawai ta daga a sanyaye,amma a zahirin gasiiya babu wani abu da kalamansa suka qara mata illa dafi da guba a cikin zuciyarta,sai take gamin a fakaice kamar yana gaya mata cewa......mace fa ba kamar namiji take ba,mace ba zata taba zama kamar namiji ba "Allan yayi muku albarka,ya albarkaci rayuwarku....." "Amin" ta amsa ciki ciki tana miqewa,dukkansu suka bita da kallo,shi da mommy din,tana jiyo sanda daddyn yake cewa "ke kuma hajjaju banason fada irin wannan......najwa jaruma ce,zuciyarta kuma a dake take,karki kassaramin qwarin gwiwar diyata,nasan ta fada ne kawai saboda tana hangen dan uwanta zai bawa mahaifinta kunya kamar yadda ya saba,ita kuma kunyar ce bata son naji ta,ke kuma matsalarki anytime when it come to samir baki ji baki gani,kowa ma baida gaskiya saishi" wannan kalaman su suka janye kas mafi rinjaye daga abinda najwa taji da farko ya tokare mata qirji,yayin da hajiya jidda ta saki wata ajiyar zuciya,wani yanki na farinciki ya ratsa zuciyarta,wanda batasan na meye ba,daga kuma ina yake,saidai duk da hakan bata fasa amsa masa ba "Am sorry Prof,amma samir yayansu ne,dole su bishi,haka kuma bazan gaji da nuna musu su girmamashi ba"..….... Wayar na riqe a hannunsa yana qoqarin maida kiran da aka masa ganin cewa umar ne me kiran,wanda tuni kiran umar din ya riga daya zama miscal. Bugu biyu umar din ya daga,saiya tsaida tafiyarsa,ya jingina da qarafunan barander da yake tsaye akai,sannan ya goya hannunsa guda daya a qirjinsa,daya kuma yana riqe da wayar yana amsa wayar. Cikin nutsuwa irin tashi yayi sallama,cike da matuqar girmamawa umar ya amsa,sannan ya gaidashi,ya dora da bayanin dalilin kiran "Na bincika yallabai,kuma dukkan abinda kaji suna tattaunawa gaskiya ne,yanzu haka ma a gobe yake tunanin maida musu kudin qurensu,hakanan gobe ne rana ta qarshe ta biyan kudin registration din kamar yadda kaji ya fada" Sauke hannun nasa dake harde a qirjinsa yayi bayan yaji bayanan umar na qarshe,kansa a qasa yana ci gana da sauraren sauran bayanan da Umar din yake masa,yasa qafarsa guda daya yana tona fararen duwatsun da aka yiwa qasan harabar varender ado dashi,yana jin zuciyarsa na masa wani nauyi kadan kadan. Har saida umar din ya kammala bayanansa tsaf sannan ya sauke ajiyae zuciya,cikin sanyi yace "Ka duba account dinka,zan turo maka da saqo,ayi dukkan abinda ya dace,inason ka gama da matsalarsa a gobe....." "In sha Allahu sir" "Yauwa"ya fada sannan ya sauke wayar daga kunnensa. Muryar jawahir da yaji daga bayansa ya sanyashi tsaiwa daga latsa wayar da yakeyi,ya waiwaya ya dubeta,tana takowa inda yake tsayen,hannunta dauke da wani kyakkyawan kwando,daya daga cikin abinda yake iya hangowa a ciki flask na tea,wanda yake da yaqinin favourite tea dinsa ne a ciki. D/Z 13 *Zafafa biyar na kudi ne,ki siya ki karanta naki cikin aminci ba tare da kin shiga haqqin kowa ba* Ku tuntubi wadan nan numbers din 08184017082 Ko kuma 09134848107 "Yaya....abincinka ya xama ready"jawahir ta fada da yanayin shagwabar nan tata,kai kace har yanzu bata rufa shekaru goma bama,da qaramin murmushi ya saki,akwai abinda yakeson sani amma ta hanyarta,don haka yace "Thank you autar momy...muje ki hadamin,saiki koma cikin gida" "An gama yaya"ta fada tana dariya,ya jinjina kai ya soma takawa tabi bayansa. Baiyi taku biyar cikakke ba wayar tasa ta sakeyin qara,saiya dagata yana duban waye kuma ke sake kira,Hajiya hafsatu ce wadda suke kira da hajiya qarama,qanwa ga Professor rashid azare,qanwa 'yar gaban goshi wadda yakeji da ita qwarai da gaske,kasancewarta diya mace qwaya daya kaf a fadin dakinsu da mahaifiyarsu ta haifa,har ta koma ga mahaliccinta,sai qanwarta mahaifiyarsu me suna karimatu da suke kira ya dikko da a yanzu suke kalla a madadin mahaifiyar tasu,wadda ke zaune a azare cikin ainihin gidan gadonsu da ayanzu professor ya qawata mata shi,babu yadda baiyi ta zauna kusa dasu ba amma sam taqi,tace tafison qasarta,tafison ta rasu a inda aka haifeta,amma halan baisa sunyi watsi da ita ba,lokaci zuwa lokaci suna ziyartarta,hakanan dukka yaransu suna daukarta kamar kakarsu ce wadda ta haifa iyayensu. Hakan na mata dadi ba kadan ba,yadda yaran yayarta suka maisheta uwa,saboda dama yaro daya tal Allah ya bata,ya rasu yabar nashi yaron guda daya shima,wanda a yanzu suke tare dashi cikin gidanta,ita dinma tunda can macace mai kirki qwarai,ta hadasu ta rungume duka,saika rantse da Allah yaranta ne. "Hajiya qarama?"ya fada qasa qasa murmushi na fita saman fuskarsa,babu abinda ya fado masa sai drama dinta,mutum ce mai rigimar tsiya,idan ta gaddame kan abu babu mai saukar da ita,idan bashi ba da Allah ya hada jininsu qwarai,ya kuma sanya mata qaunarsa saiko daddynsu,don ko yaranta idan ta hutsance musu saidai su nemi agaji a wajensu. Sallama ya soma yi mata sannan ya dora da cewa "Mamana..,maganin kuka na" "Eh....kace haka mana,tunda ko ranar da zan dawo ma baka riqe ba?"murmushi mai dan sauti ya saka "Kiyimin afuwa don girman Allah,wallahi abubuwa ne masu yawa suka sha kaina" "Nayi maka,ka shigo gobe inason ganinka" saida fargaba tadan kamashi,saboda sanin halinta,ba kasafai take masa irin wannan kiran na gaggawa su qarketa ta dadin rai ba,dama ko kafij ta tafin akwai tsumammiya a tsakaninsu,amma don duka ya wanke kansa sai yace "Ina nan zuwa in sha Allah hajiya" "Allah ya kawoka lafiya,kafin ka tafi,kaje wajen babanka ka karbarmin man zafin nan a wajensa,don da ciwon qafa na dawo" "To hajiya,babu damuwa"daga haka dukka suka gimtse layin,ya sauke wayar yana sauk ajiyar zuciya,sai suka hada idanu da najwa dai dai sanda take ajjiye kwandon hannunta a qasan makeken lallausa carpet din dake shimfide a falon,wanda kusan kaf gidan nan ne kawai babu tiles,dariya take tana fadin "Ho hajiya qarama,don Allah yaya idan xaka goben na shirya na rakaka". Girarsa ya dage sama yana neman wajen zama,sannan ya girgiza kansa alamar a'ah "Ba zaki bina ki kwabamin al'amura ba"dariya ta saki sosai ta samu waje ta zauna ta fara zuba masa abincin,sannan kuma tana bashi labarin wasu dramomi da suka sha da hajiya qaraman,yanata murmushi yana saurarenta. Bai katseta ba,haka baice da ita komai ba,yana cin abincin tana ci gaba da yiasa hira,wanda ta dauke masa kewa sosai. Kusan dukka cikin gidan yafi kowa fahmtar jawahir,zahiri tana da surutu sosai,saidai kuma akwai hankali nutsuwa da sanin ya kamata,fiye dana 'yar uwarta,tana da sauqin kai da tausayi fiye dana najwa,ta wannan fannin kam ta mata fintinkau,sabanin najwan dake da shegen daukan kai da fadin rai,da kuma miskilanci idan taso,harda na banza da wofi ma. Sai daya tabbatar labarinta ya qare sannan ya dubeta "Akwai wani abune da bansanshi ba?"ya mata tambayar data je mata a baibai,don bata gane abinda yake nufi ba,duk da dama tasan halayyar yayan nasu,gwanine wajen magana da kalmomi masu harshen damo "Me kenan yaya?"ta tambaya kai tsaye,sai daya gyara zamansa sosai sannan yace "Meya kawo sauyawar najwa fiye da yadda take a baya ne?" Take alhini ya bayyana sama fuskar jawahir,ita kanta abun yana damunta,sannan yana bata mamaki,duk da dama najwam ba kirki ta cika ba,amma a ya zu abun nata yana qara gaba ne,tamkar wani tunzuri,tsahom wasu sakanni tana tadi da zuciyarta da tunanun amsar da zata bashi,shi kuma tsahon wannan lokacin yana karantar fuskarta,yana kuma karanto amsar tambayarta ba tare data furta ba "Ban sani ba yaya,nima abin yana ta banu.mamaki" ta bashi exactly irin amsar da yake sanya ran dama ita zata bashi,saiya dauke idonsa daga kanta yana jinjina kai gami da sauke numfashi "Ohkey...ohkey....shikenan to" "Amma yaya kona tambayeta,ko kumw na bincika?"ta fada har yanzu yanayin alhini baibar saman fuskarta ba,hannu ya daga mata yana fadin "No auta....barshi,zan aiwatar da komai da kaina"saita sauke ajiyar zuciya mai nauyi,da alama itama abun na ci mata rai "Shikenan yaya".... *******. ******. ******** Idan banda qamshin daddadan turare babu abinda jikinsa yake fitarwa a yammacin,wanda dukkan wanda ke kusa dashi idan ua shaqi qamshinsa gamida sassanyar iska mai dadi dake kadawa,babu abinda xai haifarwa zuciyarsa sai wani yanayi na farincikin da baisan daga wace nahiya ya taho ba. Sosai yayi kyau cikin shadda ruwan makuba,wadda koda ba'a gaya maka ba kasan cewa sabuwa ce,hakanan bata qananun kudi bace,saidai duk da tsadarta hakan bai hana ayi mata dinkin zamani ba wanda ya dace sosai da mamallakim shaddar,ya bayyanar da sunan na nasa na THE GIANT SARAKI wanda mafi yawan abokai ke kiransa tun ba yau ba. Ainihin ginin gidan ya nufa,yana tafe yana daura gogo tare da amsa waya da zakayi tsammanin surutansa kawai yake shi kadai,saboda baka hangi ta inda wayar da yake magana da ita take ba,saika lura da kyau sannan zakaga abinda ya maqala cikin ramin kunnensa. Koda yayi sallama cin falon ma ya kusa kashe minti uku yana wayar,da alama bayanin sa ake masa ta cikin wayar mai tsaho ne,amma ganin fitowar mommy saiya ginmtse wayar ta hanyar cewa zai kira,ya daga kai yana dubanta sanda take isowa,fuskarta kamar kowanne lokaci dauke da murmushin dake bayyanawa duk wanda ya mu'amalanceta koda na minti biyu ne bare wanda ya zauna tare da ita tsananin kirkinta "Daka qarasa wayar son ai" kai ya girgiza yana sakin qaramin murmushi "Umar ne,zan kirashi later....za fita ne nace bari na shigo na gaya miki.....zanje gurin hajiya qarama,ta dawo jiya" yayi maganar ne sanda yake sanya links din hannunsa guda daya da bai qarasa sanyawa ba,baima kula ba sai yanzu. Da sauri ta gimtse abinda ke tasowa saman fuskarta ta maye gurbinsa da murmushi,muryarta a tsananin washe tace "Ma sha Allah,amma hafsatu ta dawo babu wanda ta shaidawa cikin gidan nan saikai?,bana jin ko daddynku ma yasan da dawowarta,don inda ya sani zai shaida min" "Ayyah...bansani ba,da nasan bai sani ba dana gaya masan" murmushi ta kuma yi "Wala'alla har yanzun fushi dai take ci gaba dayi dashi.....idanma hakanne mu ba zamuyi fushi da ita ba ai,bari na baka saqo ka kai mata,duk da babu yawa,bansan da dawowarta ba"tayi zancan a lokacin da take gab da shiga kitchen. Daga baki bakin qofa ta tsaya,ta riqe dukka hannayenta a qugunta,idanunta na yaw cikin kitchen din,ta zuqo iska daga hunhunta ta fesar,sannan ta sauke hannayenta ta taka zuwa ciki,sai a sannan kuma mutanen ciki suka ankara da shogowarta. Katafaren kitchen ne wanda ya hada dukkan wani abu na buqata da kitchen ke da buqatarsa,masu aiki ne har mutum uku a ciki,kowa da abinda yakeyi. Cikin nuna tsantsar girmamawa ta matakin farko kowa ke mata barka da shigowa,bayan kowa ya dakata da abinda yakeyi don jiran me zatace "Zuwaira..." "Hajjaju"ta amsa a ladabce "Hada abinci maza ki miqawa samir yana falo zaici fita zaiyi,ki tabbatq kome kin zuba masa a tsaftataccen mazubi" "Angama" ta fada da hanzari tana ajjiye abunda ke hannunta ta nufi aikin da aka sanyata "Lami" ta sake kiran daya daga ciki "Gani hajiya" tana matsowa dab da mommyn,duk da ta bada 'yar rata a tsakaninsu "Ina kilishin nan da aka kawomin jiya?" "Yana inda kikaje na ajjiyeshi" saita jinjina kai "Deboshi ki kawomin shi nan" "Duka hajiya?" Ta tambaya a mamakance,saboda bata manta yadda tayita jaddda mata tayi masa ajiyar mutunci ba,don ma'abociyar son kilishi ce "Gaba dayansa"ta fada mata yadda zatafi fahimta,da sauri itama ta wuce,minti daya bata rufa ba ta dawo dauke da leda,wanda ko a ido idan ka kalla zakasan yana da yawa basai ka duba ba,hannu tasa ta karba,sannan ta juya ta fice daga kitchen din,su kuma suka ci gaba da abinda sukeyi. Duk da mamakin ganinsa a tsaye bai taba kwanukan ba,amma murmushi bai bar fuskarta ba "Ya haka samir?,kai da zaka fita,ka zauna kaci mana" "Babu komai mommy,zanci wajen hajiya,duk a yakema ba wata yunwa nake ji ba",saita dan tsuke fuska kadan "Samir,kanason ka jawomin hajiy qarama tayi tunanin baka samun kulawa kenan?" Murmushin daya bayyanar da haqoransa yayi "Haba mommy,nidin kamar qaramin yaro,karki damu" bata amsa masa ba,ta miqa masa ledar hannunta "Gashi ka kai mata,kace ina gaidata da kyau kafin na shigo" sai daya kalli ledar kafin ya amsa,idan ba mantawa yayi ba jiya aka kawo mata abinda ke ciki,kuma juyin duniya auta jawahir tayi ta diban mata amma tace sam,idan tanaso su niqi gari ta basu address sukai namansu suma yi musu,amma gashi kacokam ta kyautar ga hajiya qarama,duk da rugurgujajjiyar alaqa sa dangantakar dake tsakaninsu "Xataji" ya amsa yana juyawa "Saika dawo"ta furta tana juyawa itama don barin falon. Gefansa ya ajiye ledar a seat mai zaman banza,ya saka muqulli yana yunqurin tada motar wayarsa ta katseshi. Wani qawataccen murmushi wanda yake jimawa kafin ya fita daga fuskarsa ya bayyana bayan an karanto masa sunan wanda yake kiran nasa,amsa kiran yayi, bai kuma bari anyi magana daga wancan sashen ba shi ya fara cewa "Kai....kada kacemin kun dawo" dariya aka saki "Mun dawo,minti hamsin kenan" fuska yadan bata "Amma baka kyauta ba, at least ai ka gayamin ko nazo na tarbi abba a airport" "Idan kana free a sannan ba,nafa sanka?"saiya lumshe idanunsa sannan ya bude "Jokes apart don Allah,abba ne fa?" "I know,wasa nake maka nima" "Ok ka tsammaci zuwa na,am on my way" bai jira amsarsa ba ya katse kiran,ya tada motar da hanzari,da alamu uzurinsa da saurinsa ya qaru akan nada. Har ya gota supermarket din saiya rage gudu kuma,yayi reverse ya dawo a hankali,ya samu waje ya tsaida motar sannan ya kasheta ya fito. Baya taba iya shiga wajen hajiya qaraman hannunsa haka,yana ganin girma da qimarta,yana girmama qaunar da take nuna masa,duk da yawan fadanta,saiya taka cikin nutsuwa zuwa cikin supermarket din. A hankali yake duba abubuwan da yasan tafiso yana zabarsu daya bayan daya,har sai daya kammala gaba daya,sannan ya nufi inda suke ajjiye Madara don ya siya mata,yasan qaunarta da madara tun ba yau ba,musamman ta gari. Yana shan wata kwana yarinyar na bullowa itama cikin gudu irin na yaran da basu rufa shekara uku a duniya ba,taqin dake tsakaninsu kadan ne,da alama akwai wanda ya biyota,saiya tsaya ya mata lamfo,tana qarasowa ya dauketa cak zuwa sama,suka hada idanu,saita qara sakin dariya sosai tana cewa "Anty mubina ce...."ko kafin ta rufe bakinta daga maganar anty mubinan kuwa ta bayyana,siririya farar budurwa,wadda shekarunta basufi ashirin ba,sanye da abaya ruwan jinin kare,ta yafa mayafinta saman kanta ba tare da tayi rolling ba,wanda hakan ya bayyana wani daga sashen gashinta da yake a tsefe. Tsaiwa tayi tana duban yarinyar tana kuma duban samir dake dauke da ita,tana kuma sake maqaleshi tunda ta hangi mubina din,rada yayi ma yarinyar a kunne,sai taga ta sakeshi,maimakon ya miqa mata ita,saiya dauki kwandonsa ya juya yabar wajen,ya nufi wajen biya,tilas badon taso ba ta soma binsu a baya,qirjinta na dukan uku uki,ganin yayi gaba da yarinyar mutane. A saman canter ya dora yarinyar yana tambayarta sunanta "Afra" ta bashi amsa,saiya ciro atm dinsa ya miqa musu ya sanya musu pin bayan sun buqaci hakan sannan ya maida hankalinsa kan afra yana tambayarta meya sakata gudu "Wai don na cewa anty mubina.....mu bari sai dan anjima saimu tafi,ta barni na gama kallo shine tace a'ah" dariya sosai yarinyar ta bashi,yasaki faffadan murmushi yana dubanta "Waye yace miki ana zama cikin shago?,ba anan ake kallo ba kinji?,idan kinason yin kallo akaiki wajen wasa" yanayin fuskar yarinyar yaga ya canza,saita narke fuska "Aida abbana ke kaini" "Yanzu fa?"ya tambayeta shima yana rage fara'ar fuskarsa "Anty mubina tacemin ya rasu,kuma idan aka mutu ai ba'a dawowa ko?" Juyawa yayi ya dubi sashen da mubinan ke tsaye tana kallonsu,sosai ranshi ya baci,tausayin yarinyar ya kamashi,ta yaya yarinya qarama kamar wannan zata dinga gaya mata babanta ya mutu kuma bazai dawo ba,ba mamaki she's mad. Kafin ya sake cewa komai ya miqo masa katin yana shaida masa an gama cirewa "Hold it.....ina zuwa"ya fada yana sake saba yarinyar a kafadarsa ya koma cikin shagon. Siyayya ya dinga mata sosai,duk abinda ta nuna tana so saiya daukar mata,har sai data ce babu saura sannan suka dawo wajen biya,ya sauketa yana sake miqa musu,suka lissafa suka zari kudinsu suka zuba masa a leda,saiya riqe hannunta,suka qarasa inda mubina ke tsaye,wanda zuwa yanzu ta sake tsurewa sosai,ga tsoro ka fargaba,kamar ta dora hannu saman ka tayita ihu,tana qiyasta dukan da zata yiwa afra ne kawai da irin wannan giggiwar tata yau da takeson janyo musu tashin hankali. Tura afra yayi gabanta,ya hangi hararar da take zabga mata,cikin husky voice dinsa yace "Wawanci ne gayawa yaro wani nasa mai muhimmanci ya rasu,it hurts alot koda agun babba ne bare yaro da kanshi bazai iya dauka ko jurewa ba"saiya zame hannunsa daga cikin na afra,ya ajjiye ledar "Don't do it again....." Ya fada sounding seriously Yana kaiwa haka ya juya ya soma takawa,sai kuma ya tsaya,ba tare daya waiwayo ba yace "Karki sake ki taba lafiyarta koda wasa" saiya qara gaba,ya dauki ledarsa yabar shagon. Bata dauke idanunta daga kanshi ba sai daya fice,taja iska sosai har cikin hunhunta tana jin sauran qamshin daya tafi ya bari a wajen,hakanan taji ta kasa dukan afran,tana shirin jan hannunta taji an dafa kafadarta,ta waiwaya a hankali,basma ce "Waye wancan,wani mai zafin kika samo hala?"ta fada tana murmushi murmushi dariya dariya,sai datasa hannunta ta zame hannun basman daga kafadarta sannan tace "Wannan me sanyi ne tako ina" "Wannan uban kayan da kika debo fa mubina?kinsan dai maama tace kada mu diba kaya da yawa ko?" Basman ta tambayeta tana duban ledar gabanta "Daga mai sanyi ne,shi ya siyawa afra"sai tayi hanyar barin shagon itama,yayin da basma ta biyota cikin mamaki tana jera mata tambayar ta sanshi ne "Ko sau daya"ta amsa mata a taqaice sanda suke isa bakin motarsu,don a yanayin da take ciki bata buqatar dogon surutu da doguwar magana irin ta basman. A farfajiyar harabar gidan yayi parking,kallo daya zaka fahimci gidan akwai wadatar rayuwa da kuma sukuni,yana kashe motar ma'aikatan dake farfajiyar gidan suka qaraso inda yake,dukkaninsu cikin sakin fuska,saiya fito ya maida murfin motar ya rufe,yana basu hannu daya bayan daya suna gaisawa,suna ganin girma da mutuncinsa,saboda yadda yake baiwa duk wanda ya cancanta irin girman daya dace dashi,kusan yasan darajar kowa,yana kuma mutunta kowa,kamar ba ma'aikatan gidan ba,ihsani yayi musu kamar yadda ya saba duk sanda Allah ya kawoshi gidan kana ya wuce zuwa cikin ainihin gidan. ,daya daga cikin ma'aikatan yana riqe da ledar daya mata siyayyar a ciki. Da sallama ya shiga falon bayan ya karba ledarsa,ta amsa masa sanda take zaune gaban zainaba me mata kitso,tana lallabe mata kan nata da manyan kitso dan hannu biyu,duk da girma amma sumaeta tana nan,saboda sunyi gadon gashi sosai,duba da irin asalin jinsin yaren da suka fito. Ana qarshe dama suke,don haka bai jima da zama ba zainaba ta gama tayi mata sallama ta tafi bayan ta sallameta,saiya zamo daga saman kujeran ya zauna qasam carfet sosai shima yana duban hajiya qarama tare da sake gaidata,gami da yi mata barka da dawowa,cikin kulawa da kuma jin dadi ta amsa,saita daga murya tana kiran 'yar aikinta. Ba jimawa ta qaraso,ta rage tsaho sosai tana gaida samir,duk kuwa da cewa ta girmeshi,ya kuma dade yana hanasu duqa masa wajen gaidashi amma sun kasa,saboda girma da qimarsa sosai da suke gani "Ki kawowa samir abinci"ta umarceta,saita amaa tana juyawa da sauri zuwa ciki. Ledojin gabansa ya ajye gaban hajiya qarama wadda ke qoqarin daure kanta da dankwalin atamfar jikinta "Ga wannan hajiya,babu yawa,wannan ledar kuma.... mummy ce tace a kawo miki" yana kallon yadda ta tabe baki,sannan ta saka hannu taja iya ledar daya kawo mata tana cewa "Ni nace ta kawomin wani abu ne?,saboda irin haka fa yas ako yayan bai gayawa na dawo ba,don karta cikani da kayayyakin da ba domin Allah aka shiryasu ba,sai don shegiyar riya da son iyawa" shuru samir kawai yayi baice komai ba,don dama bashi daya cewar,yana ganin tunda aka kai wadan nan tsayin shekarun babu jituwa tsakanin hajiar da mummy,baya tunanin nan gaba za'a samu,yana daya daha cikin abubuwan dake sanyashi a tunani,wadanda har yau ya gaza samun amsoshinsu,meye tsakanin hajiyar da mummy da har yanzu ta kasa qaunarta,duk da tarin kyautatawar mummyn a gareta,hakanan shidai da idanunsa bai taba ganin mummy ta damu game da abinda hajiya qarama take mata ba,bata taba nuna fushi gazawa ko qpsawa ba,amma hakan baisa hajiya qarama yin haquri ya zubda makamanta ba. Abinda ba kasafai yake yinsa ba,tunda yana ganin sha'ani ne daya shafesu,hakanan na sama dashi ma sunyi sun gaji sun bari,amma a yau din saiya murmusa sannan yace "Kiyi haquri hajiyata..... nummy kan da murna da kirkin nan nata ta bada saqon a baki,duk da kuwa har autarta ta hana,amma keta zabeki ta baki" baki ta sake tabewa tana dan jifansa da harara "Yoni ina ruwana?,nina sanyata?,ai bani nace tayi kyautar ba,data sani ma auta din ta baiwa taci ta more,tunda na tabbata kudin uba nata ne,kirki kuma da kake maganarsa,ai ba zata gayawa aminatu kirki ba" ambatar sunan saiya hado da faduwar gabansa,wadda ta tilasta masa lumshe idanu yana furta "La'ilaha illallah" zuciyarsa,tsahon wasu sakanni sanna ya bude idanun nasa,sai suka fada cikin na hajiya qarama,da yaga kamar tsareshi tayi da idanu tun dazun tanw kallonshi "Ai wallahi Allah ya kyauta.....kuma duk nisan jifa qasa zai fado,kuma qauna nidai jidda ta samu soyayyata har abada,saidai ta wadanda ta rufewa idanu da wani hali wanda ni nasa shiga akayi kasuwa aka samoshi" daga haka ta miqe qafarta wadda da alama itace meyi mata ciwon,har tana shure ledar da mummyn ta batan,saika dauka da gayya tayi hakan. Dai dai nan mai aikin ta dawo da abinci a shirye ta ajjiye gabansa,hajiya qarama tace "Dauki wannan ledar ki shiga da ita ciki,idan abun kaiwa baka ne ki rabe muku keda jummai"godiya ta shiga jerawa hajiyan,sannan ta duqa ta dauka zata wuce da ita,a lokacin affan yayi sallama,dan hajiya qarama na qarshe wato autanta. "Wannan ledar fa?"ya fada cikin salo na raha kamar yadda yanayinsa yake,yana amsar ledar daga hannun mai aikin saboda son ganin qwaqwaf,yana bude ledar ya bude idanu "Hajjaju.....wannan lafiyayyen kilishin fa?" Fuska ta tsuke sosai,bata ko waiwaya ta dubeshi ba tace "Daga inda ka aikeni,su sukace na kawo maka babana" ya fahimci kamar adan hasale take,saiya saki murmushi "Allah ya huci zuciyar hajjwju" ya sanya hannu yana gutsirar kilishin ya jefa a bakinsa sannan ya bata ledar ta wuce shima ya qaraso inda suke zaune. "The giant ya saraki" affan ya fada cikin salo na barkwanci,wanda ya sanya samir murmusawa,saiya miqa masa hannu,shima affan ya bashi hannun suka gaisa,sa'annan ya soma laluben wajen zama yana fadin "Barka da warhaka yaya" "Yauwa affan.....ya karatu?" "Hmmmm....gashinan alhmdlh,yanata gasamu"ya amsa masa yana shafa qeyarsa zuwa wuyansa "Ni yau ka ganni yaya ko cikakken abinci wallahi ban samu na zauna naci ba,yanzunma takaddun kawai na ajjiye na shigo nan" gyara zamanshi samir yayi sosai yana fadin "Saika matso muci tare"ya bude murfin kwanim abincin yana ajiyeshi a gabansa,hakan ya baiwa affan damae matsowa yana cewa "Kai amma fa na gode yaya daka bani damar cin abinci dakai" maganar affan ta sanya murmushi ya subucewa samir,idan ya biyewa affan abincinma bazai bari suci sosai ba,ya cika surutu kamar jawahir,shi yasa tasu tazo daya,wani lokaci har yakan tsokanesu da cewa zai musu baiko shida ita,zasu dace sosai,saboda yanayin surutunsu daya,saidai suyita dariya shi da ita,saboda su sam basa ganin surutun nasu da yake fada din,kawai dai qilan sabodashi bai bawa hira muhimmanci mai yawa cikin rayuwa da lokuttansa ba,yana selecting lokutan hira da abubuwan da sukafi muhimmanci ya ambata ne. D/Z 14 *Zafafa biyar na kudi ne,ki siya ki karanta naki cikin aminci ba tare da kin shiga haqqin kowa ba* Ku tuntubi wadan nan numbers din 08184017082 Ko kuma 09134848107 Suna cin abincin suna hira,affan din yana bawa samir labarin makaranta,yanayin karatun nasu irin wahalarshi da sauransu,lokaci lokaci hajiya qarama na sanya musu baki,har suka gama,affan ya kira jummai ta debe kwanukan,saiya miqe tsaye yana miqa ya dubi hajiya qarama "Hajjaju zanje nadan kwanta,baccin jiya da banyi ba duk ya cikamin idanu" "Ala kiyaye"ta amsa shi,saiya waiwaya ya dubi samir daketa faman goge hannu duk da cewa ya wanke,da yake shi mutum ne da ba kasafai yake cin abinci da cokali ba "Yaa saraki.....zanje nadan watsa ruwa,idan na sameka to,idan ban sameka ba a gaidamin twin sister na" dan qaramin murmushi ya saki,kana yace "zata ji" saboda yasan wa yake,da haka yabar musu falon su biyu kadai. Shuru ne ya ratsa na wadansu sakanni sannan hajiya qarama ta gyara qafarta dake miqe daya kan daya "Muhammadu" ta kirashi da sunan da ba kasafai ake kiransa dashi ba,samir ko saraki yaso ya shafe na ainihin,saiya daga kai ya dubeta yana amsawa "Ina waccar maganar da uwarka data taso da ita?,ina fatan dai ta mutu kamar yadda ka gayamin?" Kai ya jinjina a nutse yana duban hajiyan,saita gyada kan nata itama "Kun kyautawa kanku......abinda yasa nayi kiranka shine,kaga daga ni har mahaifinka kowanne so yake ka fitar da macen aure,bama mu kadai ba,duk wani masoyinka,hatta da yadikko dake azare,kayi qoqari ka zabi yarinya cikin dangi ko wajen dangi,bana so luma bana qaunar na sake jin labarin wai jidda ce zata zaba maka ko ta zabar maka wadda zaka aura,saboda halan bazai haifar mana da daa mai ido ba a tsakanina da ita,idan kuma baka maida kai ka zabi mace ba,to tabbas ni zan zabar maka,don suna nan sun kua guda goma wadanda nasa abincika minsu,kuma kowacce ta isa macen aure" murmushi ne zai subuce masa,amma sai ya sanya tafi hannunsa saman bakinsa,kamar mai shafa kwantaccen gashin daya zagaye habar tasa zuwa qasan hancinsa,a hankali yana duban hajiya har takai qarshe,cikin girmamawa yace "In sha Allah ba za'a kai haka ba,nan kusa zan kawo miki ita ta gaidaki" wanda shi kansa yasan ya fada ne kawai,saboda a yanzun koda bindiga aka ritsashi ba zaice ga wadda yaji ta kwanta masa ko yake soyayya da ita ba,duk da tarin masoyan da yake dasu,wasu sun bayyana,wasu suna dakon kayansu,hakanan kullum wayewar garin Allah baya rasa samun saqonni daga wajen mata kala daban daban,wasunsu ma baisan su waye ba. ****************** Karfe tara da ashirin na safiya yana tsaye cikin falon,wanda babu kowa,daga shi sai mai aiki dake hada masa breakfast da xaici ya fita,kasancewar yau jawahir bata nan,ta fita tun takwas tana da lactures,haka ma daddy tun bakwai ya fita,suna da wata tafiya shida mai girma gwamna,najwa na ciki tana bacci,mommy ma tana nata dakin,saidai ta leqo tace a hada masa abun karyawar,zata shiga wanka ta fito. Sai data gama hadawa sannan tadan russuna sanda yake danne danne a wayarsa,yayi kyau cikin wani yadin maza da aka yiwa dinkin zamani,wanda ya dace sosai da jikinsa,fuskarsa kawai zaka kalla kasan yan tafiya da zamani,komai nasa dai dai a muhallinsa "An gama yallabai" dauke idanunsa yayi daga saman wayar,ya dubeta "Yauwa......sannu" kai ya gyada taja baya ta soma barin wajen,sai taji yace "Zo mana" ba tare data jinkirta ba ta dawo inda ta tsaya daxun,yana hada tea din yana motsashi da cokali saboda ya rage zafi ya dubeta "Me ya faru su baba mai gadi basa samun abinci kullum sau uku a rana?" Shuru tayi kanta a qas,tana nazarin abinda zata fada,bai katse ta ba amma yaci gaba da sauraren amsarta ba tare da ya sake cewa komai ba,sai daya kurba tea din sannan ya sake maimaita tambayar,dai dai sannan mommy ke fitowa,taji tambayar da yake yi din,don haka tace da ita "Jeki zuwaira" ta fada tana jan kujera daya ta zauna tana dubanshi. Second kusan uku sannan tace dashi "Bansan ya zan musu fada su gane ba,nasha gaya musu babban abuj kunya ne ace mun kasa ciyar da ma'aikatanmu.....amma in sha Allah daga yau hakan ba zata sake faruwa va,zanwa tufkar hanci" kansa ya jinjina sannan ya aje cup din hannunsa "Bai kamata mu dinga qoshi suna kwana da yunwa ba,alhalin mu sujewa aiki,sun sadaukar da lafiyarsu da qarfinsu duk saboda mu.....ki musu magana mommy a gyara please,idan mangyaran bai yuwu ba ni da kaina zanyi maganin abun,i sure daddy bai san da haka ba" kai ta daga tana dubansa "Tunda nace an gama daga yau, trust me an gama din son" ta fadi da murmushi kan fuskarta,shima saiya saki murmushin. Sama sama ya qara abincin kana ya miqe,saboda kiran da umar da murtala sukayi masa kan sun iso,ya dubi mummyn "Zamu wuce mummy......ni suke jira"idanunta saman fuskarsa ta jinjina kai "Allah ya tsare,sai kun dawo" "Koda daddy zaiyi qorafin nan......" "Baka da damuwa da wannan,jeka abinka" ta tareshi tun kafin yakai qarshen maganar,hakan ya masa dadi,tako wanne bangare ya tsaya tana tare dashi,tana kuma bashi goyon baya dari bisa dari akan duk abinda ya yanke,don haka cikin karsashi da jin dadi ya juya ya nufi qofar fita,yayin data rakashi da idanuwanta harya gama ficewar. Nannauyar ajiyar zuciya ta saki,sannan ta maida idanunta gurbin daya tashi yanzu a kai na wasu sakanni,sannan ta janye idanun nata,taja sauran kayan breakfast din daya gama ta fara hadawa,don itama tana son ta fita taje ta dawo kafin azahar. **********Daga gefe daya na tsakar gidan nasu dake a share fes take zaune,saman kujera 'yar tsuguno,tana yiwa wata matashiya da bata wuce sa'arta ba kitso,da qyar take kama kan,don babu yadda zata yine,da lashakka ma bazata mata kitson ba,duba da yadda kanta yayi datti,har wani toka toka yakeyi,saidai a wannan karon ta tayar da neman kudi sosai,kitso take babu ji babu gani,dalilim ciwon qafar mahaifiyarta da a yanzu ya fara daga mata hankali,saboda kullum qara gaba yakeyi,burinta kawai a hada kudin magani da zata kai asibiti,ko yaya ta samu relief na ciwon dake jin jikinta. Bilal ne daga gefe zaune yake daura qwabja qwabjan takalmansa da yake fita aiki kullum dasu,surutu yaketa mata saidai hankalinta bai wajen gaba daya,nata can tana lissafa adadin abinda ta tara ne,duk da kitson data kama babu dare babu rana tanayi. "Inama zan samu wanda zai dinga sayen zanena" ta fada cikin zuciyarta,saboda yawan zanan data tara da kayan da bilal ya kawo mata,saidai duk wanda tayi ma maganar dariya yakeyi cikin karkarar,yana ganin zallar haukarta,waye zai wani sayi zane?,yayi me dashi?,mutum daya ne take ganin kamar zai mata hanya ko yasan inda za'a siya din,wani abokin nasuru ne da yace mata ya taba zuwa kano,ya wuce ya wani waje yaga an maqala zanw cikin glass ana siyarwa,tunda ya bata labarin bata manta ba,saita yanke ta tanbayeshi ko za'a dace,saidai kash nasurun yace mata baya nan,amma tana sanya ran dawowarshi cikin satin. Sai daya gama daura takalman sannan ya miqe yana kakkabe jikinsa "Na tafi yaya,inajin ma yau zan dan dawo da wuri,zan samowa umma wani abun da zata ci,don yau za'a fara biyanmu kudin aikinmu inji oganmu,mun kusa gama rushe ko ina da ina,aikin ginin kawai za'a fara" "Toh Allah yasa" "Amin" ya amsa yana yin gaba da dan hanzari,yana tafe yana dan buga duwatsun da yaci karo dasu,yana ji da takalmin sosai,ji yake babu kamarshi. Tana gamawa wadda takewa kitson kitso ta kakkabe jikinta,ta wanke hannunta sosai sannan ta sake tattara wajen,gidan habiba takeson zuwa,don tun shekaran jiya take aike kan tazo din amma.bata je ba,don Allah ya sani tun asali ita dama ba maison yawo bace,koda cikin qawayensu duk wadda akayi biki da wahala ka ganta ta koma gidan a kusa. Sai data leqa dakin umman ta tabbatar bacci takeyi,sannan ta shiga nata dakin,ta dauki hijabinta ta maqala sannan ta fito tana dan jan qofar kara da aka sakayawa sashen nasu sannan tayi gaba. Tana shirin fita asiya na shigowa da uniform jikinta,duk me hankalin daya kalleta yasa ba daga makaranta ta dawo ba,don fes take a nutse,babu wasu alamu dake nuna gajiya da tarin yunwa irin tadan makaranta tattare da ita,kallon banza data saba yiwa kaltum shi ta watsa mata,ita kam bata ma isheta duba ba,don haka kota gefan da take bata kalla ba tayi gaba abinta,abu dayane data sani shine,ba zata dauki ranini ba,sannan a dake asiyan ba zata dauki komai a jikinta ba. Ta qofar gidan me gari ta ratsa saboda sai tafi mata sauri,tun daga nesa take hangen wasu maka makam motoci da suke zamewa 'yan karkara irinsu da basu taba leqa birni ba abun tsoro,saboda haske da walqiyar da suke cikin hasken rana,yara da manya ne tsaitsaye gaban motocin guda uku,da alama suna morewa idanuwansu kallon abunda basu taba gani bane,ta haka ta ratsa ta tsakiyarsu ta wuce,tana tafen itama tana waigen motocin,tare da mamakin wai wadan nan abun hawa ne,kuma sunansu mota kamar sauran motocin da suke gani suke safararsu zuwa qauyensu,bata taba zaton ma akwai samfurin wata aba wai mota irin wannan qirar ba,kwata kwata babu hadi da iein nasu motocin,don idan aka kwatanta wadan nan da nasu,toba shakka sunayen nasu motocin gwangwani ko kuma kace fanko kai tsaye,Allah daya gari banbam,da irin wannan tunanin ta qarasa gidan habiba. Bata sameta a sassanta ba,a sashen surukarta ta sameta,suna zaune qasan rumfarta mai sanyi suna barar gyada abinsu suna hira,fuskarta wasai take fadin "Maraba da kaltume,kaltume kinyi tsada kamar kudi?,idan za'a leqomu dinma sai munyita roqo?" Tafadi tana miqa hannunta tana warewa kaltum gefan tabarmar da suke kai,tana murmushi ta zauna,cikin kamewa da kunya ta gaida babar yusufa din,ta amsa mata cikin kulawa da dattako,tana tambayarta ummansu da kuma jikinta,ta amsa mata da sauqi,saita miqa hannu ta debo gyadar da zummar tayasu ɓarar. Dakatar da ita baban tayi tana fadin "A'ah,ajjiye kada ki bata jikinki,ke habi dauketa maza ku wuce bangarenki,idan na gama dambun zan aiko muku dashi,ba sai kin fito ba" cikin ladabi habiba ta miqe tana cewa "To baba" dole kaltum ta miqe itama tabi bayan habiban suka wuce sashenta. Daga tsaye kaltum ta qarewa rumfa zuwa dan tsakar gidan habiban kallo,ko ina fes qal kamae yadda suka gada daga mahaifiyarsu,hakan ya yiwa kaltum dadi qwarai "Gani,lafiya kike nemana?"ta fadi tana duban habiba wadda tayi qiba abinta,koda ba'a gaya maka ba kasan tana cikin kwanciyar hankali da nutsuwa,duk kuma sanda suka daga idanu suka kalleta ita da ummansu,suna samun wani sukuni da farinciki na dacen gidan aure da habiban tayi. Kama baki tayi tana kallon kaltum "Kai yaya?,kamar akan qaya kike?,Allah da yau yaya yusufa cewa yayi indai bakizo ba da kansa zaije ya tahomin dake,shikenan saiki yanke zumunci dani?,watanni nawa da aurena amma har yanzu bakizo min sau uku ba?,bilal kawai fa ke leqoni lokaci zuwa lokaci,ko ummanmu taqi zuwa har yanzu,dama ni bana zancan baba,anya kuwa baku daina sona bq?" Tayi maganar kamar zata saki kuka,hakan ya sanya kaltum nema waje ta zauna tana cewa "Idan ma mun daina sonki aikin samu wasu sabbin masoyan da suka fimu iya kula da habi ta" maganar ta sanya habiba dariya,da alama kaltum din ta sauko kenan daga niyyar komawa cikin gaggawa datayi aniya,habiba bata zauna ba,saita dinga rakitowa kaltum din duk wata cima da take da ita ciki da wajen dakin,gyada ce,rake ne,ragowar tsirenta na jiya,harda kiifi ma da kantu. Dukkansu kaltum tana sha'awar ci,saboda an jima ba'a hadu ba,saidai ta kasq cin komai a ciki idan ta tuna ummanta,ba zata iya ci ita kadai ba,duk da cewa habiban na yawan yi musu aike irin wannan na kayan taba ka lashe. Ganin taqi ci habiban tasan halin yar uwar tata sarai,don haka saita samu leda ta juye mata komai,sannu sannu kaltum ta saki jikinta,suka dinga hira sosai da habi,har babar yusufa ta kammala dambun,ta aikowa da habiba nata cikin qatuwar kula da kaltume ta tabbatar tafi qarfinta,sannan kuma ta ciko wata babbar samira tace ta kaltume ce,miqewa kuwa tayi tace gida zata tafi,ita baci zatayi ba,habiba ta kada ta raya taqiya,har sai data hadota da babar yusufa "Ke kaltume,karbi maza,keda gidan 'yar uwarki?,banda ma shirme irin naki a mu yanzu 'yan uwa ne,babu abinda zance da habiba ni sai godiya,don tq zamarmin diyar cikina ba suruka ba,Allah ua bani 'ya daga sama,babu abinda zan masa sai godiya,na kuma godewa mahaifanku da suka tarbiyyanceta da kyawawan dabi'u" wannan kalaman suka qarawa kaltum qaunar matar,suka kuma sanyaya mata zuciya saboda yabo da ummanta ta samu. Ko da tazo dawowa a yanzun babu motocin data gani dazu,hakanan babu taron mutanen nan,sai dai daiku da suke zuwa gidan,wasu matsala ce ta kawosu wasu gaisuwa,haka ta wuce zuwa nasu gidan. Tun kafin ta isa sassan nasu ta jiyo muryar inna,gabanta ya fadi,me kuma ya kawo inna yau gidan nasu?,ta sani da wuya alkhairi ya kawota,ku kumq tazo a qarke qalau da ita,saita fara jan "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kamar yadda aka koyar dasu a makarantar asuba ga wanda bala'i y asameshi,don ita a wajenta inna bala'i ce cikin rayuwarsu,domin bata kawo musu kowanne alkhairi face sharri,da tana da iko,da tana kuma da hali data shafeta cikin babin zuri'arsu,ta kuma canzawa ummansu mahaifiya da wata ba innar ba. Sosai ta tamkae fuskarta,ya aro duk wani bacin ran duniya ta azawa fuskar tata sanda take sallama a tsakar gidan nasu,innar ce kuwa,tana zauna akan kujera 'yar tsuguno,yayin da ummansu ke saman tabarma,da alama ma zuwan innar ne ya tasheta daga baccin data tafi ta barta tana yi. "Har kin dawo kenan?"umman ta tambaya tana duban fuskarta,kai kawai ta gyada mata,ta isa gefan umman ta ajjiye kwano da ledar hannunta,sannan cikin cushewa ta soma gaida inna "Lafiya lau"ta amsa mata,amma idanunta kacokam na kan kayan da kaltume din ta ajjiye "Nazo akace kina gidan habiba,itama shegiyar da bata neman kowa sai uwarta da yan uwanta.....wannan din meye kikq shigo dashi?,me aka same acan din?,Allah yasa ana qulla abun arziqi itama bata fada irin gidan da uwarta ke ciki ba"innar ta fada wuyanta kamar zai tsinke ya isa ga kwanon,tuni kaltum tasa hannunta ya dafe kayan,don bata jin innar ko mayyace zata bata kayan nan,saidai kallo daya umman tayi mata ta janye hannunta daga kai,don babu yadda zatayi "Dauka kikai mata"unma ta umarceta,kamar zata sanya hannu aka ta zunduma ihu haka taji,ta jefi innar da harara,saidai ina batasan tanayi ba,zuba surutu take idanuwanta kan kwanon dai,haka ta miqe ta dangware mata komai tayi wucewarta daki abinta,inda tasan zata zo ta taras da ita wallahi ta gwammace tabar abincin bata karbo ba. Rub da ciki tayi saman shimfidarta,tana jiyo yadda innar keta zuba surutu taga dambu,ga nama harda kifi,tana jin sanda ta saki guda "Kai lallai ba shakka,habiba Allah ya tseratar dake,ai nima na leqa mu gaisa" maganar tata tadan cunkushe daga qarshe,wala'alla dambun ta cika bakinta dashi. Tsaki kaltum taja kamar zata tsinke harshenta,ta juyar da fuskarta ta daina kallon qofar dakin wai ko zata rage jin kalaman zalama da tsantsar kwadayi daga bakin innar "Kema kiyi kiyi ki tattara ki qara gaba,har yanzu shuru,shi yaron da yace adaga masa qafa gashi wata nawa basu sake magana ba,sai kace wadda ta ɓincino baqin jinin ubanta,don dai wannan baqin jinin bana uwa bane,saboda ni kaf yarana babu wanda ke wuce shekara goma babu baiko,itama donta biyewa son raine tazo tq haifeku a wanna qangin" kalaman da suka sanya kaltum miqewa sa sauri ta tura qofar dakin nata ta rufe abinta,sannan ta dawo ta kwanta. Bata qara miqewa ba sai da taji ummansu na kiranta,ta miqe a hankali taja dankwalinta ta daura,sannan ta fito,ta samu innar ta gama kasafta komai ta dauki nata,dubanta umman tayi "Ki dauka abincin kici" fuskarta a hade tsaf tace "Na qoshi,ki qara mata kawai" sarai umman ta fahimci magana ta fada a fakaice,amma batason cewa komai kada innar ta samu wata mafakar,tana son su rabu lafiya,ko banza yau dai ga innar tata a gidanta. Washe baki innar tayi "Aina qoshi 'yar nan,kedai Allah yasa kema ki dace kamar habi" batace mata ci kanki ba bare ta amsa mata,saita gyara zama,sanda ummansu ta miqe ta dauki buta don zuwa bandaki "Nace ba......zuwa nayi ki bani aron dubu da dari biyar,wallahi jiya jiya ado da indo suka aikomin da kudi,zan siya kiwo,to saura cikon dubu da dari biyar,babarki tace min kina tara kudin magani,ko su zaki aramin,koma dai ki bani kyauta,tunda kukan jima baku yiwa kowa alkhairi ba,na tambaya babarki ko akwai sauran na gudunmawar bikin habiba ta bani,to ashe babu duk kun qurmushe" mamaki ya cika zuciyar kaltum,ta soma bin innar da wani kallo.na mamaki,tana ji har cikin zuciyarta,data dauki abunta ta baiwa innar ta mora,gwara su fadi "Ina zuwa" kaltum din tace da ita tana miqewa,saita sake washe baki,murna sosai ta cikata "Allah dai yayi miki albarka,kare ma yana da ranarsa gaskiyar bahaushe" ta fada innae tana gyara zama. Inda take ajjiye kudin ta soma bankadawa ta debe kudin,ta dauresu sosai bakin habar zaninta,sannan taja hijabinta daya cire dazu ta mayar jikinta,ta saka slipper dinta ta fito. "Yauwa miqosu nan,sauri nake nayi na koma,na baro gidan babu kowa" tsaiwa tayi saman kanta ya dubeta,saita kwance kudin ta dagasu sama "Kin gansu nan?,to wallahi sisi a ciki ba zakici ba,saboda gumina ne bana wani ba,aimu marasa amfanine a wajenki,to a tafi a hakan har duniya ta nade,kuma gidan habiba indai kika sake kika je,yasin saina sakar miki karnukan gidan mati dake hanyar" saita sura da mugun sauri tayi waje,saboda taji ummansu daketa doka mata gyaran murya tana gaggawar fitowa,da alamu taji komai a kunnenta. Hanya kawai ta miqa ta dinga shawagi abinta,ta dade bakin rafinsu zaune,abinda bata taba yi ba,saidai wajen yayi mata sosai,batasan haka wajen yake da dadi ba sai ranar,saitaga zai dace da wajen zamanta idan zatayi zane,taga abubuwa da yawa da zata iya zanawa tana zaune daga wajen. Anan ta shimfida dankwalinta tayi sallar azahar,batason komawa gida a yanzun,saboda wata nutsuwa da wajen ya saukar mata,sai data qara awa guda sannan ta miqe,ta yanke tabi ta wata hanya,duk da batasan ainihin inda zata maidata ba,amma tana da tabbacin xata kaita gida. Ga mamakinta saita bulla da ita layin gidan yaya muzammilu,gidan da aqalla ta kusa shekara uku rabonta da zuwansa,ta laluba kudinta taji suna jikinta,zuciyarta ta bata shawarar ta kaiwa matarsa lariya ajiya,don haka ta kutsa kai gidan da sallama. Kadaran kadaham ta karbeta,suka gaisa,bata zauna ba ta kwance kudin tace "Babar haruna,ajiyemin zakiyi,zan dawo na karba nan da kwana uku" jikinta na rawa ta karba,kudin sunzo mata akan gaba,dama su take nema "To kaltume,Allah ya kaimu" daga haka sukayi sallama ta juya gida. Koda ta shiga bata samu inna ba,sai ummansu dake zaune,suna hada idanu umman ta kauda kanta taci gaba da abinda take,tasan ummanta sarai,ta santa ciki da bai,tasan yadda zata saukar da ita,don haka saita zame takalmanta ta isa gabanta ta duqa "Don girman Allah,don manzan Allah ummanmu kiyi haquri idan kinji haushi,wallahi ummanmu bazan iya bata bane" shuru ne ya ratsa kamar umman ba zatayi magana ba,sai kuma tace "Idan ba zaki iya bata ba kuma saiki gaya mata maganganu kamar sa'arki?,idam farincikina kike nema to bai samu ba,tunda daga qarshe akaina koma meye ya qare" "Kiyi haquri ummanmu,kinyafemin" shuru ta sakeyi,kafin daga bisani ta fidda wata ajiyar zuciya "Allah ya shiryamin ke kulsum" don ta fahimci kaltum din ba zata taba sauyawa ba,saidai addu'ar "Amin" ta amsa murmush na subuce mata na ganin nasarar data samu ta sauke umman nasu. D/Z 15 *Littafin kudi ne,guji daukan nauyin haqqin wasu,ki biya ki karanta cikin aminci* Ku tuntubemu ta wannan numbers din 08184017082 Ko kuma 09134848107 *_ka/ki gujeta!!!_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 *_Dabi'ar da zata iya sanya ubangiji yayi maka kaca kaca!,RIQO QULLACI KO KWANA DA WANI DAN ADAM_* *_Me yiwuwa wanna bawan da kake kwana dashi cikin ranka koka qullata,ubangiji na sonshi fiye dakai,ya fika matsayi a wajen ubangijinka,kaga qullatarshi ko gaba/ko kwana dashi a rai daidai yake da SHIRYA YIN YAQI DA UBANGIJI NE_* *_Allah ya haskaka mana zukatanmu_*🤲🏽🤲🏽🤲🏽 ******Rana ce sosai akeyi a ranar ta lahadi,wadda tun safiya dama ta qwalle sosai da zafinta,kusan indai ba lalura ba da wadanda ta kama dole,kowa ya samu mafaka yana shan iska,tare da jiran ranar ta danyi sanyi kafin ya wuce yaci gaba da aikinsa. Ita daya ce qwal a tsakar gidan nasu,tsit gidan yake,babu motsin kowa,sai waqe waqen baba laure dake tashi tsakanin babban tsakar gidan nasu zuwa sassanta,tana aikace aikacenta,da alama duniya tayi mata dadi. A duqe kaltum take tana wanki kayan ummansu da nata dana bilal,ranar ce ke dukan gadon bayanta,duk da zafin da ranar keda ita hakan bai wani dadata da qasa ba,qunci ne fal zuciyarta,wadda babu abinda take mata sai zafi da quna,musamman idan ta tuna da irin tijarar da mahaifinta ya tsiyaye musu tas ita da mahaifiyarta a dazun kafin ya fita,a kullum idan yana irin wadan nan halayen mamaki kamata yakeyi,kai bazaka ce shine ya haifesu ba,ba zaka taba dauka mahaifinsu ne da suka fita ta tsatsonsa ba. Ta gama matse wasu tana shanya ta soma jiyo dan qaramin kuka da nishi,saita dora sauran kayan dake hannunta saman igiyar tana waiwayawa bayanta da sauri,bilal ne ke shigowa yana dingishi,yayi futu futu dashi da qasa sai kace wanda yayi wanka da gari. Sakin abinda takeyi din tayi,ta nufoshi da sauri tana kallonshi,fuskarsa daga gefe ta kuje,hancinsa kuma da alamun jini daa hade da qasa,dafashi tayi tana kallon fuskarsa cikin tashin hankali "Kai....lafiya bilal...meye haka?,waye yayi maka haka?" Cikin haki dake nuna zallar kukan da yasha yake magana "Su musbahu ne...."sosai ranta ya baci fiye da tunaji,batasan me yasa suke masa haka ba,sun maidashi kamar wani jakinsu,ko yaya yayi musu abu saisu kamashi suyita duka,bayan duka duka ba wani girme masa sukayi ba,kusan sa'anninsa ne "Me kayi musu?"ta fara da tambayarsa duk da fushin da take ji yana cinta "Ban musu komai ba wallahi,wai don kawai am bamu kudin aikinmu yace na ranta masa zai siya sabuwar waya,saina hanashi,saboda wancan karanma da suka ranta basu biya ni ba" wani fushi taji ya taso mata,wannan ba shine karon farko da suka fara dukansa ba,kuma a yau din bata jin zata qyalesu,rashin gatan nasu da galihu baikai har haka ba,don haka tace dashi "Ina zuwa"saita shige daki. Ko zanin jikinta bata sauya ba,ta zaro hijabinta dake cikin kayan datti ta saqala,ta tabbatar ummansu bacci take,ba zataji fitar ta ko dawowarta ba,hakan kuma yayi mata,don haka ta warci hannun bilal suka fice daga gidan,tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta isa wajen. Sauri take falfalawa kamar zata tashi samq,cikin mintina qalilan suka isa wajen,ko ina ma'aikata ne birjik,sai tarin was ada duwatsu na aikin ginin makarantar,iya kayan aikin da aka zube kawai ya isa kasan cewa aikine za'ayo tuquru babu wasa,sai taja ta tsaya tana wulga idanunta inda zataga su musbahu. Daga can ta hangosu,sunata daukan kwababben sumunti cikin kwanon sarki zuwa cikin sabon foundation din makarantar da aka fitar aka kuma soma sanya bulo. Tsaiwa tayi ganin isyaku na dosowa inda suke,shine abokin bilal da tasu tafi zuwa daya,ci gaba tayo da dakonsa har yazo gab dasu "Isiyaku"ta kirasa ganin bai gansu ba,ya waiwayo sannan ya taho inda suke "Isyaku.....me ya faru tsakanin bilal dasu musbahu?" Sak yadda bilal din ya gaya masa hala shima isyaku,sannan ya dora da cewa "Saida nace ya daina bawa kowa bashi amma yaqi ji,ni ya gani aiba wanda nake bawa,shima kuma dukkansu babu wanda yake iya ranta masa naira biyar,amma shi duk wanda yace bilalu aramin kaza,ko ragowar kudinsa duka saiya dauka ya basu,kuma yawansu ba biyansa suke ba,idan sukaci sunci kenan" Duban bilal tayi,kamar ta mangareshi haka takeji,saidai yanayin yadda yaji jiki a hannunsu musbahu yasa ta daga masa qafa,kuma tunda Allah yasa taji zata yiwa tufakr hanci,maida dubanta tayi ga isyaku "Yanzu dawa dawa yake bin bashi a wajen nan" Dukansu isyaku ya lissafa mata,daga inda take tana iya hangosu da idanu,sai daya gama sannan tace "Muje wajen nasu" tayi gana cike da qarfin hali da qwarin gwiwa,duk da cewa musbahu ya girmesu bama su ba har ita,amma batajin koda tazarar shekara nawa ya bata zata qyaleshi. Tun kafin su qarasa musbahun yaga tahowarsu,saiya tsaya da abinda yakeyi ya riqe qugu yana jiran isowarsu. A gabansa ta tsaya tana kallonsa ido cikin ido "Kudin bilalu nazo karba" "Na qarfi ne,idan kina dashi saiki amsar masa" "Bana qarfi bane,kuma nwzan qwata ba,kuma dole ka bashi" "Bazan bayar ba,duk wanda zaki kira ya karbar masa ki kira" sosai ranta ya baci,hakan ya tunzurata ta fara magana cikin daga murya,cikin masifa da tada jijiyar wuya tana nuna musbahun tare da jaddada masa ba zata bar wajen ba sai ya bada wannan kudin. Daga can gefe daya dukka cikin sansanin da ake gabatar da ginin makarantar,qarqashin wata qaramar rumfa da akayi da ciyawar bunu,zaune yake saman wata kujera mahadi da teburin dake gabansa,saman teburin lemo ne da cup sai ruwan roba,gefe daya kuma kwamfutar tafi da gidanka ce ta laptop,duk da haka jarida ce a hannunsa yake dubawa shafi bayan shafi,jikinsa na sanye da jeans da shirt wadanda sukayi qura saboda qasar dake wajen,sai rigar ma'aikatan kamfaninsu mai kama da apron daya dora saman kayan nashi. Hutun minti talatin ya tafi a yanzu yanzu daga filin da ma'aikata suke,wanda kusan duk wani aiki da ale gabatarwa a kowanne qauye indai yana nan yalan shiga yaga yadda yanayin aikin nasu yake,daga irin nashi experience din ya musu gyara a inda yake ganin yana da buqatar gyaran,ya dauki jaridar kasuwanci ne yana duba yanayin hawa da saukan hannuwan jari dollar da sauransu. Kadan kadan hayaniya daga can gefansa ta soma shiga kunnuwansa,tana kuma rarraba masa tunani,saiya cira kansa a hankali ya waiwaya gefan nasa. Tana tsaye tsakiyar ma'aikatan maza,sanye da duqunqunen nan hijabi wanda habarda ta koma gefen kuncinta,tsingilallen zani wanda ya tsaya iya qaurinta,da wasu sudaddun silifas,fuskarta sai shining take cikin hasken rana,sakamakon baqar fatarta da kuma gumin da take saboda zafin rana. Sosai ya zuba mata idanu yana kallon yadda take wulwulga hannu,gamida motsa bakinta da sauri da sauri,duk da baya iya jin muryarta sosai amma ya tabbatar rashin kunya take,dubda da yadda na bayanta keta mata magana,amma batajin me suke fada ma bare tabar abinda takeyi din. Ranshi yadam baci,donshi mutum ne da baison rashin kunya ko qanqan,shi yasa yake respecting duk mutumin dake sama dashi a shekaru,koda kuwa qasa yake dashi a muqami,daya daga cikin abinda yasa ya tsani SIYASA kenan,saboda yadda dan qanqanin yaro zai iya tsaiwa gaban sa'an kakanshi bama babansa ba,ya danna masa zagi,rashin mutunci ko cin fuska yadda zuciyarsa ta raya masa,saboda kawai ya fishi wani abun duniya,muqami ko matsayi ko kuma kudi ko fada aji. Ajjiye jaridar hannunsa yayi,saiya kiqe tsaye yana sanya hannayensa cikin aljihun wandonsa,kana ya taka zuwa bakin rumfar ya tsaya yana ci gaba da kallon abinda ke faruwa. Tsahon wasu mintuna ya hangi umar na nufo rumfar da yake tsaye din,sai yasa hannu ya fitoshi,ya qaraso wajen cikin girmamawa "Me yake faruwa a can wajen?" Yayi masa nuni da idanuwansa,saida umar din ya kalla wajen sannan ya dawo da kansa wajen samir din "Nima dai naxo na tadda abun na faruwa....dana tambaya sai yaron yacemin,kudin aikin da aka basu ne babu canji ba'a bawa yaron nashi ba,shine yaje yacewa yayar tasa an hanashi,shine tazo karbar masa,tanata zaginsa yana qoqarin yi mata bayani amma taqi saurarsa" Tsaki yaja yaa ci gaba da sauraren umar "To nidai ban mata magana ba,saboda kasan halin wasu yaran qauyen nan ba tarbiyya garesu ba,yanzu 'yar cikinka saita qunduma maka ashar" komawa yayi da baya ya zauna kujerar daya tashi din,ya zura hannunsa aljihun wandonsa ya fiddo kudi,'yan dari biyar biyar ne sababbi guda shida,ya miqawa umar "Ka kai mata,tayi qoqari tabar wajen nan yanzun nan,banason hayaniya" karbar kudin umar yayi,har yayi gaba samir dake murza goshinsa yace "Ka gaya mata,indai taci gaba da zuwa wajen nan,to qaninta zaibar aikin da yakeyi a wajen,saboda ba wajen zuwansu bane" "Ok sir" umar ya fada yanayin gaba. "Kinga madam,kiyi haquri,karbi kudin aikinku da Allah" umar ya fada yana shan gabanta,saida ta yima umar din wani irin kallo sannan ta saka hannu ta karbi kudin,ta kallesu sosai ganinsu sababbi a miqe,idanun musbahu qur akan kudin,ji yake a ransa dama shi aka baiwasu,saboda yana ganin yawansu yasan sun wuce adadin da aka basu din na ainihi,daya sani ma ya biyashi kudinsa,da bai samu wannan garabasar ba,ga mamakinsa saita maidawa umar kudin "Da irin kudin da aka biya kowanne ma'aikaci za'a biyashi haqqinsa,bama huqatar sabon kudi ko wani abu daban" duban mamaki umar yayi mata,ganin kamar tazo da sabuwar tsirfa,amma kuma daya tuna nau'in muhallin da take rayuwa,sai mamakin nasa ya ragu,ya kuma danganta hakan da qila zallar qaunyanci ne ya sanyata aikata hakan,akwai wasu kudaden a aljihunsa,don haka ya laluba ya irgo 'yan dari biyar biyar guda shida kamar yadda suke a sababbin. Karba tayi ta irga,saita dubi bilal "Nawane kudin aikin naku?' "Dubu biyu ne" ya bata amsa,ta sake waiwayawa ga kudin,ta irga dunu biyun,ta linke dubu daya ta miqawa umar "Mun dauka iya kudinsa,ga canjinku" "Ku riqe gaba daya"kaita kada "Bamaso,haka aka biya sauran abokan aikinsa,shima haka za'a biyashi" sosai umar ya cika da mamakinta,ya tsammaci tun a karon farko zata karbi kudin cikin murna da farinciki,ba tare data tsaya neman musaya da tsaffin kudi ba,bare ta tsaya ta irga iya haqqinsu. Kafin ya ankara tuni ta juya taja hannun bilal sun fara barin wajen "Oga yace a gaya muku....idan kika ci gaba da zuwa nan wajen,to qaninkin xai rasa aikinsa" cak ta tsaya sannan ta waiwayo,sai data watsa masa wani kallo sannan tace "Ko da baka fada bama bilal bazai sake aiki a nan wajen ba,tunda babu amfani yin aiki qarqashin mutanen da basa da adalci" daga haka taci gaba da jan hannun bilal suka bar wajen,yayin da tabar umar yana binta da kallo,cike taf da mamakin daya cika masa zuciya. "Ka gani ko mai gida,dama bata da kunya,duka 'yan gidansu ma,ana xargin qanin nata ma barawo ne" musbahu ya fadi haka,cike da fatan bilal din ya sake nisa gaba daya da wajen aikin,ta yadda shi zai samu ya dinga aikin mutum biyu yana karbar kudin,kallonsa kawai umar yayi,saboda ya shiga shakku ga zaton da suke mata,saiya jiya ba tare da yace komai ba ya koma wajen da saraki ke zaune. Dakatar da umar din yayi yayi kafin ya gama bashi labarin abinda ya faru,yace yaje kawa yaci gaba da duba abinda za'a qara saman kayan aikin dake wajen. Suna isa gida ta tattara sauran kararen dake ajjiye kusa da bayan gidansu ta kunna wuta ta dora ruwan zafi,tas ta gasawa bilal jikinsa,tana yi tana baqin rai ita kadai tana mita harta gama sannan ta dubeshi "Idan na sake ganinka wajen daga yau nida kaine wallahi,tunda kai bakasan dadin jikinka ba bare ciwon kanka,kuma zan koma,duk wanda kake vi bashi a cikinsu saisun hada maka kudinka" hada masa sauran ruwan ya shiga bayan gida yin wanka,daidai sanda umma ta fito daga dakinta,tashinta kenan a bacci,tana dabarun yadda zata miqe saboda yanayin qafarta ta jiyo mitar kaltum din "Wai lafiyarki kuwa....ke kaltum keda waye?,ga wankin ma har yanzu baki gamashi ba,garin yaya?" Tas ta gayawa umman komai,shuru tayi umman ta sanya buta a gabanta zata daura alwala,shurun na umman ya tabbatarwa kaltum akwai inda tayi kuskure kenan,duk da ita bataga wajen da tayi ba dai dai ba "Yanzun kin kyauta kenan kaltume?,ki tafi cikin maza kina fada kina babatu?,tarbiyyar dana baki kenan?ina kunyar dana sanki da ita?,shine har kike cewa zaki koma?,to idan kece da kanki ki koma din" daga haka umman taja butar da kaltum din ta xuba mata ruwa taha daura alwala. Sosai jikinta yayi sanyi,sai a sanna ta gane rashin kyautawarta,saidai ranta ne ya riga daya baci a sannan din,takai maqura kan abinda akewa bilal din,tunda ba yaune na farko ba da hakan take faruwa ba. A sanyaye taci gaba da aikinta,da zummar idan umman tasu ta huce zata je ta lallabata ta bata haquri. Bayan sallar isha'i sanda tasan umman nata na zama su danyi hira,tayi amfani da wannan damar ta bata haquri,kamar kowanne lokaci umman na yawan mata uzuri,wannan karonma uzurin tayi mata,tayi mata nasiha "Kiyi koyi da haquri kaltum,babu abinda yafi haquri riba,duk wanda kikaga yayi haquri baici ribarsa ba,to ba shakka ba ainihin haqurin yayi ba" kai ta jinjinawa umman tasu,saidai cikin ranta tana juya kalmar umman ta haquri,wa shin wanne haqurin umman takeso tayi baya ga wanda sukeyi a yanxu?,ko so take a daga hannu a dagesu,a zagesu,a dalla musu mari su tsugunna su baiwa mutum haquri harda tukuici ma?,to idan ba irin wannan haqurin ba batasan wanne umman takeso suyi ba. Suna nan zaune umman tana basu labarqi na rayuwa da zai amfanesu,ya kuma zame musu izina saiga sallamar suwaiba,sosai kaltum tayi mamakin hakan,saboda ta manta rabon da suwaiban tazo gidansu,harda bikin habiba,wanda har akaci aka cinye babu ita babu dalilinta,duk kuwa da takawar da tayi taje gidansu,ta kuma sake roqarta tazo din,tun daga wannan lokacin itama kaltum din taji haushin hakan,ta kuma janye jikinta daga suwaiban,dama ita ba gwanar tara qawaye bace,gaisuwa dai ta mutunci tana yi da sauran sa'anninta,an kuma san junq,amma ba qawance irin nata da suwaiba ba. Wannan dalilin bai sanya kaltum sakar mata fuska ba,ta kuma bata wajen zama. Daga gefan tabarmar ta zauna kamar wadda take a darare,ta gaida umman,sai umma ta tashi ta basu waje,sai bayan barin umman sannan suwaiba ta kalli kaltum "Kwana da yawa" murmushi kadan kaltum din tayi "Ke za'a cewa haka,harna zaci ma ko batan kai kikayi,ba gidan nan kikayi niyyar shigowa ba" murmusawa ta danyi kadan sannan ta tabe baki "Nikam ai ana ganina,kece dai,daga ke jar nasuru kunyi batan dabo" "To me zan fita nayi a waje suwaiba" kaita jinjina "Nasiru fa?"sai data kalli suwaiban sannan tace "Baya nan,yana cikin gari,yacemin jarrabawa sukeyi a makaranta,sai kuma sun gama zai dawo" yanayin fuskar suwaiban ne ya canza,sai tace "Allah sarki,Allah ya bada sa'a....."tayi furucin tana miqewa tsaye "Bari na wuce" "Da wuri haka?"kaltum ta fada tana dubanta,baki ta sake tabewa "Eh....dandali zani,kuma nasan ke ba zuwa zakiyi ba" "Gaskiya kam"ta amsa a gajarce,cikin nuna halin ko in kula tace "Su lantana ma sun bani saqo,sunce suna jiran sabuwar waqar dandali da kika musu alqawari....naga sai wani kulawa take da lamarin,ban sani ba ko sabom qawance kuka qulla ba" Murmushi kaltum tayi,lantana tana da kirki,hakanan duk wani abu daya shafeta tana shiga ciki,saidai ita qawance bata daukeshi wani abu ba,ummanta a yanzu itace babbar qawarta "Koda yake idama hakanne ba laifi,sai anjima" Cewar suwaiba tanayin gaba,sai kaltum din ta bita da kallo kawai,kullum mamaki ke qara kamata kan silar canzawar halaye da dabi'un suwaiban,wanda batasan daga inda ya samo tushe ko kuma asali ba. Tana tsaka da wannan tunanin ummansu ta fito daga daki "Harta tafi kenan suwaiban" tana gyara zama ta bata amsa "Eh umma,tace wai dandali zata" kan kujera 'yar tsuguno ta zauna tana miqe qafarta yadda zatafi jin dadin zaman "Bansan me yasa sam yanzu bakison fita kiga mata 'yan uwanki ba,ba hanaki fita nayi ba kaltume,kawai dare ne banaso kinayi sosai a can" dan murmusawa tayi "Inason zuwa ummanmu,zan leqa wani lokaci". Umman bata sake bi takan wancan zancan ba ta sako mata wani "Kinga daxu fatsima tazo,lokacin bacci ya daukeki bata tasheki ba,inna bata jin dadi,ni kuma ga yanayin qafata data matsamin,gobe idan kin gama abinda kikeyi ki shirya kije ki dubomin ita" "Toh" ta amsa qasa qasa alamun batason zuwa dai,sai umman ta share bata bi takan sauyawar yanayinta ba. D/Z 16 *MIERAH'S DUKKAH is ur plug!!!* *_Muna siyarda kaya kala kala kamar_* *jaka da takalmi kamfanin* *lamis,Dior,vellabela da dkny da sneakers 'yan yayi dominku da yaranku* *Muna order kaya daga kasashe daban-daban na duniya* *Muna siyarda da kayan decors,plated gold,da turaruka kala-kala Hadi dna tasa (oil perfume) dga kamfanin naseem hr suratti* *Muna da room fresh da turarukan wuta Dan gangaria* *Muna adashe na yargata(kaya) Dana kudi* *_ku tuntube mu awannan number kamar haka_* 07039773001 *Muna turawa ko Ina a fadin Nigeria da wasu kasashen ketare* _LOCATION_= Kano ND gusau *NAGARTA DA INGANCI SHINE TAKENMU* *MIERAH'A DUKKHAN farincikin customers dinmu shine namu*🤞🏽🤞🏽🤞🏽 ________________________________ Karfe biyu na rana ra gama duk abinda tasan umman nasu na buqata ayi mata,ta shirya tsaf cikin atamfarta wadda tasha wanki,fes da ita,ta sanya hijabinta wanda bata da kamarshi,tunda a qalla kala biyu gareta kwata kwata hijaban data mallaka kenan,duk da cewa su fatsima da yaran kawu ado suna basu suttura ita da habiba,amma nasa samun isowa garesu,inna tana amshewa ne ta saida,kota bada kyauta ga wadansu bayan su gasu a zaune,cikin lefan habiba kuma babu yadda batayi da ita ta dauki guda daya cikin kala biyar din da akayi mata ba amma sam taqiya. A idanu fes take,saidai kayan sun nuna kodewarsu matuqa,wanda ga duk mai kallo yana gani yasan cewa anajin rayuwa yadda ya kamata. Gaban ummansu ta tsugunna tayi mata sallama "Saikin dawo,don Allah idan kin tadda aiki,kada kice ba zakiyi mata ba saboda bana wajen..,kinji ko?"umman tafada,saboda tasan halin kaltum din sarai,kaita jinjina "In sha Allah" ta furta tana kallon qafar umman,da alama yau din tana mata radadi sosai fiye da kullum,tsabar haquri irin nata ya sanya bata furta ba bare ma ayi mata sannu,da wannan tunanin ta fice daga gidan,ta yanki hanyar unguwarsu inna. Tana kashingide baya fitar kaltum din da minti goma malam amadu ya shigo,riqe da jakar buhu da muke kira da bacco,miqewa tayi da hanzari ta zauna tana masa sannu da zuwa,gabanta na faduwa,saboda yanayin data ga fuskarsa,ba shakka akwai wani abu,daga sanda tayi masa maraba kuma bai amsa ba ta tabbatar da zarginta. Sa daya jingine jakarsa can qofar dakinsa sannan ya dawo inda take zaune,ya riqe qugunsa da hannayensa biyu yana dubanta,kai kace ya tsaya ne don ya tausayawa qafarta dake dauke da mikin ciwo,wanda kullum kwanan duniya azabtar da ita yakeyi,hakan kuma bai hanata yi masa dukkan wata hidima ba,qas tayi da kanta,tana jiran taji da wacce yazo,ciwonta ko akasinsa baisa amadu ya taba sassauta mata ba,wanda kaf iyakar lalube da bincikenta da tayi ta gaza gano wani qwaqwqwaran laifi guda data yi masa wanda harta cancanci irin wannan tarayyar tashi,bata sauke wannan tunanin ba kuwa amsa kuwwar muryarsa ta cika mata kunnuwa "Can na hango kaltume hanyar bayan gari.....ta tafi yawan ta zubar dinne?,kin aikata kenan yauma ko?" Idaunta ta rumtse sosai,tana jin saukar furucin nasa har tsakiyar zuciyarta,ta tsani wannan kalma da yake yawan jifan diyar cikin nasa da ita,tana tsoron watan watarana ya fada gaban wasu,wasu dun da bazasu iya rufawa kaltum asiri ba,koda ba gaskiya bane maganar,tana tsoron yadda za'a lanqwasa zancan a sauya masa fuska da ma'ana,ya zama wani zance abun tattaunawa da yiwa juna albishir cikin qauyen "Ba wani waje ta tafi ba,inna ce babu lafiya,ni kuma qafata tana ciwo,shine nace taje ta dubata,ta rage mata wasu ayyukan" tsaki yaja yana sauke hannayensa,sannan ya juya yana barin wajen,saidai fa baiyi shuru ba,bambamin masifa ya soma yi "Koma ina taje dai wannan ya rage naku,ana fakewa da suna kitso,yau kuma da sunan inna aka fake,to wallahi ta dawo ki shaida mata,na gaji da ganinta haka,ta gayawa nasirun,ya fito kawai da iya abinda Allah ya hore masa ayi auren a huta,idan kuma bai shirya ba ta fitar da wani,kai koda bata fitar da wani ba,to zan aurar da ita ga duk wanda naga dama" daga haka ya bude qofar dakinsa ya dauki jakarsa ya shige ciki abinsa. Hannunta daya tasa ta dafe kanta dashi,tana jin yadda zuciyarta ke wani ciwo kamar ana matsata,hasbunallahu ta dinga ambata babu qaqqautawa,har zuwa sannan tana jin yadda yake mita yana daga cikin daki,tsahon wani lokaci kafin ta samu relief,a haka ta rarrafa ta dauki kwanon abincinsa,wanda dama tazarce akayi mai kama da cin lokaci guda,saboda duka duka abincin sun kusa cinyeshi a iya rana kawai,saboda qanqantarsa da rashin wadatarsa,tana ajjiye masa kwanukan ta fito,ta tattare abin zamanta ta wuce dakinta,don ba zata iya jurar ci gaba da zama a wajen ba. *********** Tana iya hango yadda taja murfin kwanon ta rufe da qarfi sanda taji tayi sallama,fuskarta kicin kicin ta amsa sallamar tana miqe qafafunta bayan ta hardesu waje guda. Takalmanta ta cire sannan ta qaraso cikin rumfar tsohuwar,wadda kana ganinta,duk da cewa a qauye take 'yar gatar tsohuwa ce,don 'ya'yanta suna mata hidima babu laifi,duk da cewa ta ware wasu daban ta bari duniya ta musu radin suna da shafaffu da mai,inda Allah ya taqaita,dukkaninsu ubangiji ya kula da halayya da kuma tarbiyyarsu,basu tabarbare ba sakamakon abinda ta aikata din. "Ina yini inna,ya jikin?" Sheqeqe ta kalleta sannan tace "Da sauqi" "Ummanmu tace ayi miki sannu,ciwon qafarta ne ya matsanta mata shi yasa ba zata iya zuwa ba" "Madalla" ta fada a banzace,sai xaman nasu ya zama zaman kurame,kamar basusan juna ba,innar nata muzurai,saboda so take kawai kaltum din ta matsa ta bata space da zataci namanta,don ba zata iya san mata ba. "Mara mutunci,kin gama min gorin kudin da basukai komai ba a cikin arziqin da Allah ya yiwa 'ya'yana,shine yanzu babu kunya ba tsoron Allah kika kwaso qafafu kikq min gida ko?,xuwaira ta daure miki gindi" dubar innar tayi sosai,sai taji dadi da umman bata kusa,yau xata sauke magana yadda ranta yakeso,babu mai taka mata burki "Ai yanzun ma dana zo badon wani abu naki nazo ba,saboda ni nasan hannun 'yan dambe ne dake,baya bayarwa saidai ya karba,indan ta abun hannunki ne kinsan ba zamu rabeki ba,kuma haushina da kikaji kan kudi Allah inna yanzu kika fara ji,don inda arziqi nane karki saka aka ma kan cewa zaki cishi" hasala sosai innar tayi,don kafin ma ta fara magana sai data janyo wani sandan mariqin maficinta daya cire ta wurga mata "Dan uwarki don ubanki kada naci arziqin naki,basaima kinyi arziqin ba?,shegiya me baqar aniya,nida ubanki ai aga wanda yafi wani hannun 'yan dambe,kuma idan zuwaira ce ta daure miki qarqashin kimin diban albarka bari na warware,daga ke har ita sai naga uban daya tsaya muku,nice fa nusaibatu,wallahi dai dai nake da kowanne dan iska da shegen gari" baki kaltum ta tabe,ko banza burinta ya cika ta kunnota,saita miqe tana cewa "Oho dai,shi wanda kike zagin ko banza baya rufa sati baice mana ungo ba,ke kuwa fa?,ni idan kina da wanki tattaro min na miki,idan kuma babu na qara mai" "Anqi a baki wankin don ubanki,ba zakiyimin ba" "Allah sai nayi,gwara ma kiyi haquri tunda bake kika sani ba" daga haka ta sanya kai uwar dakan innar,saita fara yunqurin tashi tana cewa "Kada ki kuskura fa ki tabamin kayana kattume,zanci ubanki fa" ta qarasa maganar sanda take komawa ala tilas ta zauna,saboda amsawa da gwiwarta tayi,tana daga zaune ta babbakun masifa kaltume na hado kayan wanki,batabi ta kanta ba ta hada kayan kaf ta fita dasu,sai daya fara share mata farfajiyar gidan sannan ta zauna ta fara wankin,har a sannan tana iya jiyo yadda innar keta surfa bala'i,ko gajiya bakinta ya kasa yi,tabe baki kaltum tayi "Ba banza ba ake ce miki 'yar azaba" kaltum ta fada cikin ranta,don sunan da kaf unguwarsu suke kiranta dashi kenam,sanoda yadda tayi shuhura wajen masifa,ba'a tabata ta qyale,shi yasa wasu ke mamakin yadda ta haifi mutum mai haquri irin ummansu,umma altine ce kawai tadan dauko fada da masifar inna,duk da cewa dama kadanne daga aikin ubangiji,don yana fitar da rayayye daga matacce. Ana tsaka da haka kawu ado yayi sallama ya shigo gidan,yaransa mata biyu suna biye dashi,sahura da karimatu wadanda sa'anni ne ga kaltum,kuma sune manyan 'ya'yanshi,sam babu haduwar jini ko jituwa tsakaninsu da kaltum,su din suna da rashin kunya da ganin sunfi kowa,musamman daya kasance inna tana ji dasu fiye da kowa cikin jikokinta,hakan yasa suka bala'in raina su kaltum din,su da suke ƴaƴan bora,duk da cewa ba haka mahaifinsu yake ba,wannan dalilin yasa kwata kwata kaltum bata sabgarsu,bama kasafai suka fiya magana ba. Cikin matuqar girmamawa ta gaida kawu ado,ya amsa mata yana mata sannu ganin aikin da takewa innar,wanda kaf cikin jikokinta dama yaranta su kadai suke mata irin wannan hidimar,ganin har zasu wuce daga kubra har sahura babu wanda ya kula kaltum din,sai kawu ado ya kallesu "Bakuga 'ya uwarku bane xaku wuce baku gaisheta ba?"kasancewar tadan girmewa sahura da watanni,karimatu kuma kaltum din ta bata shekara dindi,sama sama suka gaidata,ta amsa musu da yanayin da suka gaidatan itama,ta debesu ta watsar. Tana jiyo yadda kawu ado ya dinga mata mita kan fadan da taketa faman yiwa kaltum din,bata ko duba da aikin da take mata,da qyar ya sanyata tayi shuru,a halan ma don shalelenta ne shi din,da bai isa ba. Sanda ta gama wankin ta shanya ta gyara waien,saita daura alwalar sallar la'asar data dan kubce mata,ta shimfida dankwalinta anan tsakar gidan daga gefe tayi sallarta,ganin har a sannan suna cikin dakin basu fito ba. Sanda ta idar tana saman dankwalinta tana addu'o'in data koya daga makarantar darensu su sahura suka fito suka fice,da alama tafiya gida sukayi duba innar ne dama ya kawosu,ko da can su dama basu fiya zama wajenta ba ida sunzo,ita din ce ke qalatarsu. Itama tashi tayi ta maida dankwalinta ta daura sannan ta rufa hijabinta,saita matsa daga qofar dakin innar ba tare data shiga ciki ba tace da ita "Zan tafi gida,Allah ya bamu alkhairi" "Har zaki tafi kattume?"kawu ado ya fada yana karkacewa,da alama wani abu xai zaro ga aljihun wandonsa "Eh kawu....zan koma ne saboda umman namu itama bata jin dadi sosai" "Ke banason qaryar banza da wofi,ita kullum cikin ciwo take?,ko kuma salon maular ne ya koma haka?" Ba wanda yace mata komai,sai zaro kudi da kawu ado yayi ya miqawa kaltum din "Allah ya sawwaqwe,zanje in sha Allahu na dubata,na jima aima rabona da gidan" "Kar ka bada wanna kudin ado,na gaya maka" da mamaki ya waiwaya ya dubi innar "Kamar yaya inna?,kattume ce fa?,yar gidan yaya zuwaira" "Ka fini sanin hakan kenan?,ina sane,kuma nace kada ka bayar,indai albarka kake nema ai wajena zaka sameta,miqo min nan"ta fada tana kaiwa kudin warta,sai gasu a hannunta,kota kanta kaltum bata biba ta juya tana sake musu sallama ta fice daga gidan,batasan ya suka qarke ba,saidai tana tafe mamaki na dada kamata,wanne irin shegen son abun duniya innar ta dorawa kanta?,don ba za'a ce Allah ya dora mata ba,wanne irin gagarumar qiyayya kuma take musu saboda kawai basu da abun duniya? "Ba komai,akwai Allah" kaltum ta fada tana qoqarin hadiye bacin ranta. Ta kusa da gida taga tabiyo ta hanyar gidan yaya muxammilu,saita yanke shawarar ta shiga ta karbo kudinta data bawa matarsa ajiya,idan yaso ko chemist din dake maqotaka da unguwarsu taje ta samowa ummansu maganin rahe radadin qafar,tunda kudin sunqi haduwa yadda takeso. Da sallama ta shiga gidan,saita samu fiddau matar muxamillun xaune a tsakar gida,daga ita sai daurin qirji,don ko dankwali babu saman dagargajajjen kanta,dif fara'ar fuskarta ta dauke,amma hakan bai damu kaltum ba,saboda sam bata kawo zuwanta ne yasa fara'ar fuskarta daukewar ba,hasalima daurewa zuciyarta tayi,ta duqa ta dauki qaramin danta zakari dake rarrafe,kai kace an qwatoshi ne daga ire iren garuruwan da akaci da yaqi,futu futu dashi,ga zarni yana zubawa,bayaga majina da tasono data cika masa hanci. Da qyar ta amsa gaisuwar kaltum din "Kudin nan nazo karba"kaltum tace da ita,tana qoqarin ragewa zakari majinar hancinsa da wani tsummansu mai da ubansun dauda. "Aiko kudin nan dai kattume saidai ince Allah ya baki haquri,don wallahi matsuwa ta sameni nayi gararin gabana dasu" ta fadi maganar kanta tsaye,saboda tasan cewa babu wani abu da zai biyo baya,inda asiya ce tafi kowa sanin bata isa ta karba koda tsinken sakacenta ta cinye ta kuma gaya mata hakan ba. Sauke zakari kaltume tayi a qasa tana duban fiddau "Ban gane bafa" "Inaji cewa da hausa nayi miki bayani ko?,meye a ciki baki gane ba?" "Kudina fa dana ce ki ajjiyemin,shi naji kina cewa matsuwa ta sameki kinyi amfani dashi,to aro kikayi,ko kuwa?" Wani kallon banza tayi mata,kana ta gatsina fuska "Aro kamar yaya?,kinyi sadaka dai kawai,don babu ranar biya" danqari!,kaltum ta fada cikin ranta,ta dade da sanin fiddau bata da kunya ko kadan,tana da labarinta,amma tasu bata taba hadosu ba,tadai taba hadosu da asiya,itama kan ajiya data bata,amma salin alin ta biya asiyan abinta,sabida sanin ta fita iya tijara,batajin koda kyauta zata barwa fiddau din bai kamata ta biyo ta wannan fuskar ba,tunda ba'a kyauta dole,tana mamakin yadda mutane basa kunya ko tsoron Allah,hakanan basa shayin danne haqqin wani,amma tunda ta biyo mata ta hakan,ita kuwa zata nuna mata ainihin kalarta,zata ajjiye matsayinta na matar wanta "Wallahi wallahi banyi niyya ba,saboda haka bazan bayar ba,ki nemo kin kudina tunda wuri wallahi,na baki kwana uku" daga haka ta miqe ta nufi hanyar fita. Saidai kuma hausawa sunce tabarmar kunya da hauka ake nadeta,ba kunya ba tsoron Allah fiddau ta biyo bayan kaltume ta soma zuba mata masifa da bala'i,kai kace itace ta cinye mata kudin,daga bisani ma sanda suka kai qofar gidan,taga tana shirin tafiyarta ne ba tare da anyi uwar watsi ba,saita soma zunduma mata ashar,cikin rashin sanin halin kaltum ta kirayi sunan umma tace ko ita bata isa ba. Cak kaltum ta tsaya,sannan tayi wani reverse cikin wani irin zafin nama tayi niyyar komawa gaban fiddau din don ta banbance mata aya da tsakuwa,sai mutanen da suka fara tsaiwa saboda hargowar fiddau din suka rirriqeta "Wallahi wallahi zaki gane kinyi kuskure,kuma karki wuce kwana uku baki dawomin da kudina ba"saita qwace hannunta daga wajen mutanen tayi gaba tana fidda numfashin bacin rai "Ke zaki gane kinyi kuskure,zakisan dani fiddau kwalba kike magana" cewar fiddau din tana dukan qirjinta da hannunta. Dogon tsaki yaja yana sauke hannayensa daya nade a qirjinsa,saiya juya zuwa hanyar da suka baro din,wanda hakan ya baiwa umar dake tare dashi mamaki sosai "Ya naga ka juya sir" "Na fasa fitar" samir ya bashi amsa,saroro umar yayi,a iya saninsa baisan meya bata ran sarakin lokaci guda ba,saiya dubi wajen da aka gama rabiyar fada da yarinyar ranar nan,ya dauke idanunsa ya maida kan samir da har ya soma bada tazara da inda shi yake tsayen,ya cira qafarsa da sauri yabi bayansa,babu jimawa ya tarad dashi,a lokacin yana qoqarin cusa earpiece a kunnensa "Am sorry,ya fahimci abunda ya bata ransa,mutum ne shi da yaqi jinin rashin baiwa na gaba girmansa master......kasan duk inda akace akwai rashin ilimi da rashin wayewa sai ana ma mutum uzuri" baice masa komai ba,illa kunna abinda yafi yawan saurara lokaci bayan lokaci saboda debe kewa,bai taba zama a wani qauye ba idan za'ayi aiki irin wannan ba sai a wannan qauyen,shima zaman nasa yana da nasaba da wani tarko daya dana,wanda yake saka ran kama abinda ya danawar kafin komawarsa gida.......... D/Z 17 *_littafin kudi ne,ki biya ki karanta cikin salama ba tare da kin debi haqqin wani ba_* Ku tuntubemu ta nan 08184017082 Ko kuma 09134848107 *_manzan Allah S A W ya kasance...bai taba aibata abinci ba ko sau daya a rayuwarsa,idan an kawo masa ya qayatar dashi yakan ci,idan baiyi masa ba saiya barshi ba tare daya ci ba,ba kuma tare daya aibatashi ba(don haka mu kula,mu kuma hana yaranmu aibata abinci saboda bai dace da ra'ayinsu ba)_* _____________________________ "Alhamdulillah" kaltum ta fada tana rufe kwafin qur'ani bugun qira'ar warsh dake gabanta,tare da janye fitilar aci bal bal din da tayi amfani da ita gefe,ummanta dake zaune a gefanta tana gyara saitin gidan redion da takeson jin ta daga kai ta dubeta "Kunkai izifi nawa ne a yanzu?" Murmushi kaltum tayi,tana jingija bayanta da bango bayan ta miqe qafarta "Ummanmu.....idan na gama haddar nan zakiyimin walima amma?" Murmushi umman tayi itama,tana jin in sha Allahu zatayi iya bakin qoqarinta ta tabukawa kaltum din wani abu,duk iya tsahon zamansu tare bata taba tambayar wani abu wajenta makamancin wannan ba,a wannan karon itama tana son ta mata wani abu koda guda daya ne da zata dinga tunawa dashi,kaltum din yarinyace da tayi imani cewa samun irinta sai dai daiku,duk da fushi da zafin zuciya a wadansu lokutan,amma kuma ta wani fannin tana da zurfin hankali haquri juriya gami da kawaici mai yawa,da sannu kake fahimtar hakan idan zamanku da ita yayi nisa,fatanta kawai Allah yasa nasiru ya fahimceta yadda ita din ta fahimci diyarta "Me zai hana kaltume?,in sha Allahu" "Allah yasa ummanmu,yanzu shine kadai burina....naga haddata ta hadu" ta fadi tana fidda murmushi saman fuskarta,da alamu da gaske take har qasan zuciyarta burin nata kenan. Kafin wani daga cikinsu ya sake cewa komai lantana tayi sallama,daya daga cikin yammatan qauyen da aka sanyama rana,kuma za'a sha shagalin bikinsu bada dadewa ba,kasancewar qauyen nasu bashi da wani girma mai yawa,saiya zamana kusan kowa yasan kowa,sa'annan idan aka tashi bikin yammatan da suka kai aure,sukan yishi ranaku a jejejjere koda ba ranaku daya ba,akan lwashi sati daya koma biyu ana aurar dasu kafin a tsagaita,sai kuma zuwa wani lokaci idan an sake samun wadanda suka tasa. Kamar yadda ta sabawa duk wanda suke mu'amala dashi,fuskarta da fara'a ta matsawa lantana gefanta,ta zauna tana gaida umma,sannan ta maida dubanta ga kaltum "Kattume wajenki nazo" "Ni?,Allah yasa ba wani abu nayi ba" dariya lantana ta saka,sannan tace "Ba wani laifi,tashi dai zakiyi mu tafi dandali,haba kattume....kullum sai naga wasila,idan na tambayeta sai tace batasan meya hanaki zuwa ba" "Wallahi har kin tsoratani,saboda ummanmu ne lantana nabar zuwa,ciwon qafar nan da take fama dashi,kinga mikin wajen kullum qara......." "Tashi abinki kije,nima kwanciya zanyi,amma kada ki jima" cewar umman tana duban diyar tata cike da qauna da tausayi,duk da cewa kaltum din ba gwanar zuwa dandali bace tun a baya,amma a sati takan leqa sau biyu sau uku,saidai a yanzu gaba daya ta tauye kanta saboda ita,ta rufe babin abubuwa da yawa a rayuwarta saboda kula da ita. Bata musa ba ta miqe,ta shiga dakinta neman hijabinta na gado,saidai ta sameshi ya jiqe da ruwan da tasha dazu a moɗa ta barshi,tsaki taja,taji haushi sosai,don batason yafa gyale,amma ya kamata dole ta janyo wani yamutsatstsen baqin mayafi,tadan budashi kadan saboda nannadewar da yayi ta yafashi saman dankwalin kanta dake daure tamau. A tsakar gida ta samu lantana,suka yiwa umma sallama suka rankaya suka fice,lantana ta kalli sassan su asiya sanda suke kan ficewa "Oh,su asiya manya,itakam rannan cemin tayi wuce nan,ta girmi zuwa dandali yanzu,saimu da bamu waye ba,bama zuwa makarantar boko" "Uhmmmm" shine abinda kaltum ta fada kawai,don a yanzun lamarin asiya ya daina bata haushi,sai mamaki da tsoro,yadda kullum likkafarta ke qara gaba,bata jin kunyar kowa,harkarta take gaba gadi,kuma a hakan idanun baba laure kamar suna a makance ne ita da kawu iliya,sam basa ganin wannan aibun da yanzu yawan jama'ar karkarar idanunsu ya fara kaiwa kai. Itama lantana ba gwanar surutu bace sosai,don haka hirar tasu jifa jifa sukeyi,lantanar na bata wasu labarai da suka shafi qauyen nasu,wanda ita kaltum din batasan dasu ba,wasu kuma tasan dasu,har zuwa sanda tace da ita "Wai nikam kaltume ba munafunci ba,wai meye gaminki da wasila?" Cikin mamaki kaltum tace "Wasila kuma?,qawance" dakatawa da tafiyar da sukeyi lantana tayi "Ba wannan ba,ai kowa ya sani,kuma shine abinda yake bawa mutane mamaki,yadda wasilan ke nunawa idan akayi zancanki,ko aka tambayeta ina kike,duk maganar da aka kawota indai a kanki ne saita kusheta,abun yana matuqar bamu mamaki,sannan yanzu ko a dandali ita kadai take zuwa ta koma ita kadai,idan ance ma kina ina cewa take,oho,bata sanmana ba" shuru kaltum tayi cike da mamakin wasilan,wasilar data gaya mata cewa itama ba zuwa dandalin take ba sanda tayi.mata qorafin ko biyo mata ta daina yi?,itakam har yau ta gaza gano dalilin da ya sanya wasilan ta canza haka ba "Saiki kula kawai,saboda dan adam mugun icce ne" cewar lantana,bayan ya duqa ta dauki daya daga cikin karan dake zube a qasa,da alama wadanda sukayi sharar gona suka deboshi ne ya dunga zuba kafin sukai ga ma'ajiyarsa,bata iya cewa lantanar komai ba sai binta da tayi a baya tana juya zancan cikin ranta,tasan halin lantana sarai,bata da gulma ko jada gurmi,inda wata ce ma ba zata fsaya sauraran abinda take fada ba,to amma har yanzu tana mamakin sauyawar wasila,kamar basu taba wani abu waishi aminci ba,da wannan tunanin suka qarasa babban filin dake shaqe da yara da yammata da kuma samari,sai masu siye da kuma siyarwa da suka qarawa wajen haske da armashi da hasken fitilu dana cinikayyarsu. Kusan 'yammatan da yawa sunyi murnar ganinta,saboda kusan kowa tana zaune dashi lafiya ne,wadanda nasa jituwar dasu qalilan ne,su dinma kuma ba'a karon banza ne hakan ta faru ba,akwai dalili,tana iya hangen wasila daga inda take tsaye tanata sharfinta da sabbin qawayenta,saidai ta nuna bataga kaltum a wajen ba,hakan ya sanya kaltum din sanya mata idanu taga iya gudun ruwanta,sam bata sha'awa waqa yau,dama can bata rawa koda zata bada waqa saidai tadan rausaya,don haka sai ta samu gefe guda ta tsaya,ta kuma jingina da wani kututturen dabino da aka jima da yankeshi sai saura,ta harde hannayenta tana kallon abinda ke gudana cikin filin,yayin da samari masu tarin yawa dake da muradi a kanta da kuma sha'awar qulla alaqa da ita hankalinsu ya dunga yawo a kanta,duk da cewa wasunsu suna mata kallon mai girman kai,mai wulaqanta samari,amma tana burgesu,saboda yadda dabi'arta da halayyarta ta banbamta data 'yammatan qauyen,da dama da basusan alaqarta da nasuru ba suna qulla yadda zasu tunkareta,don shima ba kasafai yake zuwa dandalin ba bare kowa da kowa ya fahimci alaqar dake tsakaninsu. Batasan cewa tayi kewar wajen ba sai data zo shi,ta dinga tuna abubuwa da suka wuce,baya kadan sanda take ziyartar wajen,komai akayi saiya tuna mata da jiyan ta,jiyan tata data sauya izuwa yau,batasan kume me zata haifar mata a gobe ba,har wata cikin qawayensu mai suna lube ta shiga ta fara rero wata tsohuwar waqarsu. Sosai waqar ta tuna mata lokacin daya shude,ta tuna mata da qanwarta habi da takan riqo hannunta su taho nan din,hakan yasa ta tashi daga jinginar da tayi daga jikin yankakken dabinon,ta fara tafa hannayenta a hankali itama tana murmushi,kamar yadda saura 'yammatan ke tafa hannuwansu. Shadda ce a jikinsa wadda ta dace da yanayin yawancin jama'ar qauyen,a yanayin shigar da yayin ba zaka kalleshi kace ya mallaki dubu hamsin ta kanshi ba,jikin shaddar ya koma kamar atamfa saboda tadan kwana biyu,babu qyalli ko maiqon sabunta ko kadan. A nutse yake kewaye filin yana nazari da duban sana'o'in da jama'ar waje ke gudanarwa,wanda da alama itace rayuwarsu,sun kuma ta'allaqa jin dadinsu kacokam a wannan wajen,hannafi wanda ya zama shine idonsu cikin garin yana biye dashi a baya,gefansa kuma umar ne da yasha jeans da shirt,ya zuba kyau shi kam,kuma yaci gaba da tafiya cikin dandalin yana daukar hankalin yammata da yawa,hanafin shike musu jangora a duk wani abu da suka shiga duhu game dashi,tun bayan saukar saraki a wani kebantaccen gida na musamman da aka bashi ya sauka,bayan ya nuna sha'awar zamansa a wajen,ya gudanar da hutun daya rubutawa kansa da kansa zaiyi na sati uku,wanda hakanan ya tsiri hutun saboda target dinsa. Duk inda ya kewaya yana lura da abinda ke faruwa,wani abun ya bashi mamaki,wani ya bashi sha'awa,wani ya bashi mamaki,bazaice basu da qauye ba,suna dashi,amma ba irin wannan ba,ba irin wadan nan jama'ar bane kuma a ciki ba,wannan qauyen yasha banban da nasu nesa ba kusa ba,akwai abubuwa da yawa da yake gani masu tarin ban mamaki da al'ajabi,basusan duk wani abu najin dadi ko more rayuwa ba,yana mamakin yadda mutum xai rayu kamar haka. "Ga tacan haka,ko zaka leqa kaga fasahar 'yammatan qauyen ɗinya?"murmushin gefan baki ya saki,cikin nutsuwar nan tasa yace "Me zai hana,muje mana,ka sani kona samo mata a ciki ma" dariya sosai hannafi ya saki,don gani yake yadda aljanna ta haramta ga kafiri,haka yallabai saraki ya haramta ga duk wata mace wadda ba 'yar gayu irinsa ba,inda ace da gaske sarakin zaiyi muradin hakan,da babu shakka sai inda qarfinsa ya qare wajen bashi qanwarsa 'yar uwarsa ramatu,da wannan tunanin nasa suka qarasa inda samarin qauyen ke zaune,sun yiwa filin qawanya daga bangare daya,daya bangaren kuma.mata ne matasansu da yaransu,saiya kutsa a hankali ya isa daga gaba,inda idanunsa zasu fi ganin komai. A hankali yake zagayawa da idanunsa wajen yana ganin abinda ke faruwa,tsayin wasu mintuna kafin ya janye idanun nasa ya lumshesu,kana ya budesu gami da sakin numfashi,yaga abubuwan burgewa da yawa,yaga kuma gyarararraki daya kamata ace an gyara din,saiya sake bude idanun nasa don maidasu cikin filin. Wannan karon a kanta suka fada,tana tsaye daga gefe daya tana tafa hannuwanta,karon farko daya soma ganinta bata fada,bata kuma rashin kunya "Ka ganta can dan dali,har yanzu bata tafi ba,don Allah ka gayamin yadda zan tunkareta,kwarjininta yayi yawa wallahi,ta hadu kaf yammatan karkarar nan Allah ta tsere musu,ta musamman ce" kalaman da yaji wasu samari dake gefansa suna fadi kenan,hakan yaja hankakinsa,yadan waiwaya don ganin su waye. Samarine guda biyu,daya yana riqe da kafadar dayan,da alama shike maganar,gaba daya hankalinsu kacokam sun azashi kan kaltum daketa tafi batasan ma wainar da ake toyawa ba,hakanan saiya samu kansa da maida hankalinsa kan fuskarta,yaci sa'a kuwa wutar wajen ta hasketa sosai,baqar fuskarta sai shining take da maiqo da baisan na meye ba a hasken wutar,mayafinta a nade yake har yanzu yayi spring spring saboda rashin guga,alhali wanda ya qerashi yayi rayuwarsa ta tabbta bisa kyaune tare da taimakon gugar,rashin samun hakanne ya sanyashi nannadewa,kanta a daure yake tamau,kwamae wadda ta boye quli quli a ciki,ya sauko ga kayan jikinta,tsingilallen zani wanda bai qarasa ko idanun sawunta ba,wanda ta daurashi saman rigar jikinta,hakan ya taimaka wajen fitowar shafaffen qugunta da bashi da wani shape,sai zallar sirantaka data cikata tako ina,don hatta qirjinta shikam bai hango komai ba,duk da cewa ta cukuikuye mayafinta sosai ta wajen,da alama sirranta wajen takeyi wanda hakan yaso bashi dariya,don baiga abun boyewar ba,daga qasa kuma qafafunta na sanye da wasu sidaddun silifas,wanda idan ka kallesu a tsanake zakaga ba kala daya bane,da alama wari da wari ne,uwa uba kuma sunwa siririyar qafarta yawa,dukka wannan nazarin ya qarashe shi ne cikin wasu taqaitattun daqiqu,sai kalaman saurayin ya fado masa "Ta hadu ne......kwarjininta yayi yawa" dariya ce taso subuce masa,saiya dan dake tare da qoqarin maidata,ya furta "Astagfirullah" qasan ransa,indai har tafi duka yammatan karkarar haduwa toba shakka baisan wanne irin gari bane wannan,yana tunanin dai kawai soyayya ce ta rufe masa idanu,amma gashi wanda baqar mace sam bata burgeshi,ya hangi 'yammatan da suka fita dama dama da yawa tsakiyar dandalin. Mutum ne shi maison barkwanci wani lokacin,don haka sai yadan matsa gefan samarin,ko banza daren yau zai samu abunda zai sanyashi nishadi yadda ya kamata,gyaran muryar da yaja hankalin samarin guda biyu yaja,haqarsa ta cimma ruwa kuwa,don waiwayowa sukayi suna dubansa "Ammm,abokina salamu alaikum"ya fada yana miqa musu tattausan hannunsa,duk da ya hangi nasu hannun daqal daqal da raken da suka gama danqa,cikin yanayi na rashin sani da baqunta suke kallonsa,kafin suyi qarfin hali bashi nasu hannun sukayi musabaha sannan ya dora da cewa "Kuna bayana naji duk abinda kuke tattaunawa,yawa ne abokina ka dinga tsoron tunkarar mace,haba kamar ba namiji ba?,be a man mana" tsaiwa sosai haladu yayi saman qafafunsa jin an samu mai bashi qwarin gwiwar daya dade yana nema,duk da bai gane jimlar samir ta qarshe ba,ya washe haqoransa talatin da biyu yana duban samir,duk da baisan wayeshi ba "Alqur'an abinda naketa gayawa kaina kenan,amma yarinyar ce abokina ba sauqi fa...."maganar data sake sanyawa samir ya kuma maida idanunsa kan kaltume,wanda zuwa yanzu ya tsayar da tafin,ta goye hannuwanta a qirji kamar maijin sanyi,still amma tana tsaye tana ci gaba da kallon masu gadar,haladu yaci gaba ".......bata kula kowa,bata sakarwa kowa fuska,qawance ma bada kowa takeyi ba,bata taba saurayi ba sai yanxu,na dade ina sonta na kasa furta mata" "Wannan din?" Samir ya samu kansa da furtawa cikin subutar baki idanunsa har yanzu saman fuskar kaltum "Ita din fa"haladu ya fada yana qura masa ido,sai sannan ya fahimci yayi subutar baki,don haka ya waske da sakin murmushi "Aita hadu" hakan yasa haladu sake washe bakinsa sosai "Allah ko abokina,shi yasa na dage fa,amma kayi a hankali karka fada tarkon sonta,don ina kishinta sosai" kamar samir ya bushe da dariya amma saiya dake yana fadin "Ai taka ce,kada ka damu,idan kana so zan tsara maka ita yau din nan" dubansa haladu yake sama da qasa cikin kokwanto 18 D/z *_manzan Allah S A W yana cewa:musulmi dan uwan musulmi ne,kada ya ha'inceshi,kada yayi masa qarya,kada ya tabar dashi ko wulaqantashi,kowanne musulmi akan dan uwansa musulmi an haramta masa yaci MUTUNCINSA DA DUKIYARSA(ba tare da yardarsa ba) KO JININSA,YA ISHI MUTUM SHARRI YA TOZARTAR DA DAN UWANSA MUSULMI_* _sadaqa rasulul kareem_ ________________________________ *_Littafin kudi ne,sharing mana ko karantawa ba tare da kin biya ba tamkar zalinci ne,ki tuntubi wadan nan numbers ki biya naki ki karanta cikin aminci_* 08184017082 Ko kuma 09134848107 _____________________________ Ya lura da kyau ya fishi kyan fata da kuma kyan fuska,duk da cewa sutura jikinsan ba wata ta az a gani bane,amma sai yaji shakka da kokwanto,kada fa yabar wannan baqon yaje labari yasha bamban,saboda yana da labarai da dama kan irin hakan data faru akan wasu samarin,wasu ma rakiya suke zuwa,amma daga qarshe suke yin wufff da 'yan matan. Jin cewa har zuciyarsa bata gamsu ba saiya girgiza kai "Kai anya kuwa?,aradun Alla tsoro nake,bansan irin zaqin baqinka ba,kada ka janyomin asara" Dariyar dake cin samir ji yake kamar ya saketa,musamman idan ya hango kaltume a tsaye a yadda take,ana zancan wai kada ya qwacewa wani ita,yarinyar da ko 'yan aikin gidansu sunfita kyan gani. Abokinsa dan ladi ne ya daki kafadarsa "Dalla malam wannan baiyi kama da masu cin amana ba,tunda yace zai maka naji na amince dashi,kuma ma ai kai kankarowa kanka girma zakayi ma,ka bashi dama,mu tsaya muga ikon Allah" Dan jimmm haladu ya sakeyi,alamun har yanxu yana kokwanto,daga bisani saiya gyada kai "Naji na amince,Allah ya bamu sa'a" "Amin" samir ya fada,a halin yanzu babu abinda yakeso irin ya samu sarari ya kwashi dariya,yadda haladun duka ya rude ya tsure kai kace mai tallan yalone zai shiga fadar shugaban qasa neman aurenta,amma dai yana son ganin qwaqwaf ne,saboda haka yace su biyoshi sanda yaga tana neman hanya tana barin filin,da alamu gida tayi. Saida suka gota wajen hayaniyar yace su tsaya daga wani waje daura da inda kaltumen take tafe a hankali,suka tsaya suna binsa da kallo,tare da dakon abinda zai biyo baya. Sai daya dan tsaya yana qoqarin controlling kansa saboda dariyar dake cinsa,wai yau shine lokaci na farko a rayuwarsa zai tsaida budurwa,budurwar ma ta qauye,inama ace Aamirunshi yana kusa suci wannan dariyar tare?,kai yama zama dole ya tattagoshi daga inda yaken ya dawo gida,zaman ya isa haka. Kamar gaske ya matsa daura da ita ya rangada sallama,da fari ta tsorata,don a firgice ta waigo,sai taja burki ta tsaya gami da matsawa gefe kana ta tsura masa idanu,tana kallon baquwar fuskar da bata taba ganinta ba tsahon rayuwarta "Yammata....an yini lpy?" Muryarta can qasan maqoshinta ta amsa masa tana sake matsawa nesa dashi,wai koda abun gudu zai taso. Tsaf ya soma tsaratan cikin mintunan da basu gaza biyar ba sannan ya dora da cewa "Ni aikoni akayi,dubi can" waiwayawa tayi a mamakance tana duban inda yake nuna matan,inda su haladu ke tsaye,ta gansu sarai,ta kuma dama fahimta take takensa,saita janye idanunta,ta maido kan mutumin da batasan waye ba. Tsaki takeso taja,amma hakanan sai harshenta yayi mata nauyi ta kasa,haka kawai taji mutumin ya cika mizani da ma'auninta na ganin girman mutane,cikin jerarrun kalamanta wanda bai zaci jinsu a haka ba,duba da yanayinta tace "Ka shaida masa ni an riga an aiko gidanmu,an kuma bada ni,kada ya sake tsayar dani ko ya aiko wani" abinda bai taba kawowa ba sai yaga ta juya tayi tafiyarta abunta. "Ya....ya ake ciki?,ba'a dace ba ko?" Haladu ya fada cikin damuwa yana taba kafadar samir,sai ya kada masa kai "Abokina ai an bada aurenta ashe?",hayaniya suke da alama musu suke a tsakaninsu,zuwa can hayaniyar ta qara yawa "Kai kai bashari....qaniyarku" Hannafi daya baro wajen gini ya fada yana nufar yaran da suka fara shirin dambacewa cikin hanzari,sai samir din ya taka a hankali zuwa wajen shima yana dubansu,wani abun sai cikin karkarata. uniform din makarantar a qa'ida fari ne na yara maza,matan blue da farin hijabi,amma idan ka dubesu a nutse da kyau zakaga kowanne kalar kayan jikinsa ya banbamta dana dan uwansa,wani ma wandon goda ko rigar gida ce a jikinsa,kamar yadda wasu daga cikinsu hijabin gida ne a jikinsu. Hannafi ya tambaya rigimar m suke,yayin da yaran gaba daya suka zuba mishi idanu,har kwanan gobe basa gajiya da kallonsa,ganinsa suke wani baqon halitta a cikinsu,baisan me yasa ba,duk da cewa shima irin kayan ma'aikata yake sanyawa ba wasu kaya bane na daban,don baya burin su gane koshi din waye. Saidai kafin hannafi yakai ga bashi amsa wani zaqaquri cikin yaran ya soma magana "Zane aka bamu a makaranta akace mu kawo.....shine nace kattume za kaiwa wadda ta yimin wannan zanen,saboda itace takeyi mana,sai alasan yace shima ita zai kaiwa,duka wadan nan ma sukace itace xata yi musu,nace to ni za'a fara yiwa tunda ni na fara fada,shine labaran yace saidai mu kaiwa yayarsu,kuma kattume tafi iyawa". Sosai sunan ya bashi dariya cikin ransa,ya maimaita sunan wajen sau biyu,hakanan sai yaji yana sha'awar ganin zanen nata da ake kodawa ana cewa tafi kowa iyawq "Mu gani" ya fada yana sakin guntun murmushi,saidai kafin bashari ya bashi har mutum uku dake tsaye cikin yaran sun miqa masa takardun hannunsu,ya samu nasarar karbar ta mutum daya daya daga ciki. A hankali yake kallon zanen yana nazartarsa,ko da wasa tunaninsa bai taba hango masa zaiga kyakkyawan zane haka ba,yayi tunanin zaiga shirme ne kawai duk yadda yaran ke masa bayani,mage ce aka zanata sosai a zaune tana cin abinci,tako inq zanen ya cancanci a bashi maki,abubuwan da ake buqata don qawata zanen da kuma fiddq ainihin taswirarsa kadanne,saiya jinjina kai ya daga kan nashi yana miqa musu zanen yana duban hannafi "Wace kattumen ne,wace makaranta tayi?" Hannafin na gyara zaman hular dake kansa,wadda ta cimmasa har kunne ya amsa masa da "Yar gidan amadu ce,ko furamare batayi ba" Da mamaki ya kalli hannafi,har zaice wani abun sai kuma ya fasa,kasancewarshi bamai yawan shiga sharo ba shanu bane,don ua raba gardamar yaran saiya fidda ragiwar sabin kudi dake jikinsa 'yan ashirin ashirin ya baiwa hannafi ya rarraba musu,yana tsaye daga gefe yana kallon yadda sukeya murna,suna tambayar hannafi inda ya samu kudi sababbi "Ban sani ba,dan mai da tambaya"haka yake fada idan ka dameshi,har sai daya kammala sannan ya dawo wajensa "Yallabai....nace ko xamu qarasa kaga filin?" Kai ya gyada masa kawai yana amsar gorar ruwa me sanyi da umar ya iso da ita ya miqa masa. *********Abu na farko da yazo kanta ta zana shine gida,gidan da take sanya ran zata siyawa ummanta,gidan data ci buri watan watarana zata dauke ummanta ta kaita can,ta zauna ita kadai ta huta da masifar babansu,a shekarunta da basu wuce sha biyar ba,ta koya abubuwa masu tarin yawa a rayuwa saboda yanayin yadda rayuwar tazo ta risketa,duk da abinda wasila tayi mata ya tsaye mata a rai,ta kuma rasa yadda zata fassarashi,amma tayi masa waje can aljihun baya ta ajjiye damuwar maganganunta,tunda dai tasan iya tsahon zamansu ta zauna a wasilan da zuciya daya,bata taba yunquri ko sha'awar cutar da ita ba. "Yallabai nan ne wajen,idan ka duba da kyau yana kusa da magudanar ruwa" cewar hannafi bayan sun gama zagaya wajen,kai samir yake jinjinawa,wajen ya masa kam,zai kuma dace da gidan gonar da yake da burin yi cikin qauyen,don haka ba tare da yace komai ba ya soma tattaki zuwa saman dan gajeran dutsen dake gabansa,bai tsaya ba sai daya kai qarshensa sannan ya tsaya akai,yana sake qarewa wajen kallo. Ƙarqashin wata bishiya take,dake tsakankanin duwatsun dake kusa da ruwan,ta duqufa sosai kan abinda takeyi,wanda lokaci bayan lokaci takan dakata kadan sannan taci gaba. Tsai yayi yana kallonta,daga inda yake yana iya hango abinda takeyi cikin takardar,zane ne,zanen kuma na gida,cikin mamaki yake bin hannuwanta da kallo,yadda take sarrafa alqalamin a hannunta saika dauka taje makaranta ne,kowanne lokaci ita daya yake ganinta,bai taba ganinta tare da wata qawa ba "Kattume!" Yaji an ambata,ya dauke idanunsa ya maida nahiyar da yaji ana kiran sunan,sunan da baisan ko na waye ba,saiya tuna a dazu yaji sunan a bakin yaran,take qwaqwalwarsa ta dawo masa da abinda yaga tanayi din "Itace kattumen?,eh kamar sunan da yaji saurayin jiya dan ladi ya ambata kenan. Lantana ce,riqe da abun diban ruwa a hannunta,fuskarta cike da fara'a ta qaraso inda kaltum ke zaune "Ke kadai kattume anan?" Takardar hannun nata ya aje a qasa sosai,wanda hakan ya sake bashi damar ganin zanen fes. "Na hadu dasu wasila ai suna fita,tace kina ciki kina aikin banzan da kika saba" duban lantana tayi tana qoqarin zama gefan kattumen,idanuwanta kan zanen kaltum din "Kai.....wannan gida yayi kyau,wannan aiki naki kattume dama ana iya yin kudi dashi" maganar ta sanya kaltum murmushin daya bayyanar da jerarrun haqoranta masu sheqi "Anayin kudi inji nasuru,ya bani labari,yace idan mukayi aure,zai kaini inyi karatu akansa" Dariya lantana ta saki harda tafa hannu "Kai kattume,anya ba raha yake miki ba,ko kuka tsokana?,banda haka ina ake karatun zane zane?,a rasa wanne karatu za'ayi saina zane?" Cewar lantana,qaramar dariya kaltum ta saki tana dauke zanenta daga qasa,gami da lanqwasa takardarta "Haka yacemin dai" "To Allah ya tabbatar da alheri"ta fada tana tashi tsaye "Bari na qarasa na diba ruwan nan,bayye tana can tana jirana" "Debo saimu koma ciki tare,nima na dade anan din" can cikin ranta haka kawai taji batason komawa gidan,kamar tayita zamanta anan waien. "Yayi wajen yallabai?" Hannafi daya biyo bayansa ya fada,saiya sauke ajiyar zuciya yana waiwayawa bayansa,gami da soma sauka daga sakan dutsen,ya cimma umar a hanya "Kuje ayi ciniki ka biyasu,ayi musu biya mai kyau tunda marayu ne" cewar samir yana barin wajen "Yes sir" umar din ya amsa masa. A hankali take takowa cikin gidan nasu,tana kuma kasa kunne ko zata ji wani motsi da yayi kama dana babansu. Abu taji ta bangaza,ta bugu sosai kamar tayi karo da bishiya,sai taja baya da sauri "Kaiiiiiii" taji an ambata cikin wata murya mai kama da sautin mutumin da bacci me nauyi yake dibansa,abinda ya sanyata hanzarin daga kanta cikin matsananciyar faduwar gaba,tana fata ba abinda zuciyarta ke gaya mata ba haka bane,hasashe nw kawai. Auwalu ne,yaron kawu iliya,dan inna laure na farko,yayan asiya,cikin tsoro tsoro take qare masa kallo sanda yaja baya shima yana kallonta tun daga yatsan qafa zuwa fuskarta,yatsunsa biyu saman lebbansa da suka rine zuwa kalar baqi yana zagayasu dasu. Saman kansa idanunta suka fara kaiwa,yana dauke da wani irin aski da bata taba ganin kalarsa ba kaf fadin karkararsu,duk da cewa a hakan kansa akwai aski,saidai sam ba za'a kira askin da sunan aski ba,don gefe da gefan kan nasa ne kawai a saisaye,daga tsakiya kuwa uwar suma ce,wadda tafi kama da tudun kabari,tayi wani cibiri cibiri da ita,kai kace kamawa akayi aka murmurdeta. Idan ka sauko ga idanuwansa kuwa gaba daya sun qara qanqancewa sun canza kala,kamar yadda yatsun hannunsa zuwa haqoransa da labbansa suka canza ainihin kalarsu zuwa wasu kaloli na daban,ko ba'a gaya maka ba,kana masa kallon farko kasan bleaching yakeyi,kamar yadda shaye shaye ya hudashi a ganin farko,duk da cewa dama can auwalun kafin barinsa qauyen yana taba shan taba sigari,boyewar da inna lauren da kawu keta qoqarin yi duka a banza,saboda yanzun kiwon mutum ake bana dabba ba,kome kayi idanun jama'a yana kai,kana tunanin cewa ka boye musu ne,yayin da su din suke kallonka tamkar tsirara,wannan shi ake kira da baya babu zani. Wani kallon qurilla yake mata,kallon data dinga jin kamar ana bugun zuciyarta da dutse ne,tana tuna wani abu daya taba faruwa tsakaninta dashi shekarun baya kafin barinsa garin zuwa kudu neman kudi,abinda ya sanya ta cure jikinta waje guda,ta kuma yi taku uku baya da sauri,dai dai sanda taji ya saki wata dariya da tayi kama data 'yan daba,cikin muryar 'yan shaye shaye ya sake cewa "Kaiiiiiiiiii......haka yarinyar nan ta girma?,lallai na dawo a dai dai" maganar data sanyata juyawa da hanzari,ta kuma nufi sashensu cikin gudu gudu sauri sauri cikin wani irin fargaba da faduwar gaba,so take ta isa ga ummansu taji shin da gaske auwalu dawowa yayi gida ko kuwa?.......... D/Z 19 *_Littafin kudi ne,kiji tsoron Allah kada ki mana sharing dinsa din gudun shiga haqqin mutane,ki biya naki ta nan ki karanta cikin aminci_* 08184017082 Ko kuma 09134848107 Follow us on Wattpad @ *ZAFAFABIYAR* *INSTAGRAM* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb *FACEBOOK* https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *TELEGRAM* https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw _______________________________ Ƙarfe hudu saura minti uku a unguwarsu tayi masa,dai da lokacin da masallacin layinsu suke haramar tada sallar la'asar,don haka sai ya sanya umar ya faka motar daga gefan masallacin,suka sauka suka bi ta famfunan masallacin dake jere reras suna bada ruwa suka daura alwala,wanda aikinsa ne,shi ya sanya akayisu tare da borehole ba tare da mutane da dama sunsan shi ya sanya ayi din ba. Bai lura a gefan daddyn nashi ya tada salla ba sai da aka idar,daddyn baice dashi komai ba,bayan ya gama addu'o'insa sai ya miqe,don haka samir ya miqe da hanzari yabi bayansa suka jero a tare,ya yiwa umar inkiyar ya shiga motar ya qaraso gida da ita. Tun daga gaisuwa ba maganar data kuma shiga tsakaninsu,takatsantsan samir din yake,yana tauna abinda zaice din,baiso daga isowarshi ya fadi wani abu da zaisa daddyn ya qalubalanceshi kamar ko yaushe,don haka shuru yaci gaba da yi musu rakiya har suka isa gidan. Falon nasu masu aiki ne suketa shige da fice a cikinsa,mommy na tsaye tsakiyar falon tana bada umarni tare da nuna yadda takeson komai ya kasance daman dining table din dake shaqe da nau'in girke girke kala kala,wanda da alamu an tanadi komai ne saboda baqin da aka kirashi saboda su. Dandatsetsen lace ne a jikin mommyn,wanda aka yiwa dinkin buba,akabi bakin hannun zuwa wuya da wasan rigar akasa bakin lace din aka masa wani ado me azabar kyau. Suna hada ido da samir din ta saki murmushi cikin nuna zallar farinciki "Sannu da zuwa son" gefanta ya qaraso "Yauwa mommy,na sameku lafiya?" "Lafiya qalau alhmdlh,ya hanya?" "Alhmdlh mommy" fitowar jawahir dauke da wani babban tray ya dakatar da gaisuwar da sukeyi,tuntuni daddy ya wuce sashensa "Yayaaaaa" ta fada a shagwabe cikin farinciki,sannan da hanzari ta dora farantin saman dining ta dawo inda yake tsaye "Yaya sannu da zuwa,i missed you yaya" murmushi yayi yana duban jawahir din,she cares so much,tana masa qauna ta 'yan uwantaka na haqiqa,shi yasa shima yake ji da ita "Me too our auta,ya makarantar?" Sai data dan sosa kanta kadan tana tabe fuska,don ita sam ba wani son makaranta take sosai ba,tun daga yarinta izuwa girma,abun mamaki wani irin so da sha'awar sana'a da kuma kasuwanci Allah ya sanya mata,ba kamar najwa ba,abinda ke hadasu fada kenan ko yaushe da mummyn,saboda ita tafi son suyi karatu,tace koma meye daga baya ayishi idan an gama karatun "Makaranta ba dadi yaya?" Qaramin murmushi ya saki yana girgiza kai "Ba zaki canza ba auta" saita saki dariya shima ya tayata da murmushi "Gafara.....kin cikashi da surutu,kuma ke baki kawo masa komai ba" cewar mommy tana dan jefa mata harara "No mummy,ta manta ne,amma banda haka saina ce ya isa haka,i need to take bath ma before I eat something" "Ba damuwa,hakan yayi,daddynku ma yace na shaida maka tare za'aci abinci" "Ohkey" ya amsa yana duba lokaci a agogon hannunsa,ya daga kansa dai dai sanda jawahir ke cewa "Mommy,i have finished....nima wanka zanje nayi" "Good,hakan yayi......idan kin shiga ki turomin waccar uwar bokon tazo" dariya jawahir tayi kamar kowanne lokaci kafin ta juya zuwa ciki. Tun daga dan medium falonsa ya soma rage agogon hannunsa zuwa suit din jikinsa,ko ina neat kamar yadda yakeso,bai taba dawowa daga tafiya ya sami bangaren nasa ba dai dai ba,wanda wannan kusan dukka aikin mommy ne,ta kula da duk wani buqatu nashi tun kafin yakai ga furtawa. Kai tsaue toilet dinsa dake bedroom dinsa ya shiga ya hada ruwa me zafi yayi wanka,sannan ya dawo dakin don ya shirya,a sannan ya lura da wayarsa tana haske,koda ya duba screen din missed call din Aamir ya samu,ba tare da bata lokaci ba yabi bayan kiran. "the giant saraki" shine abinda Aamirun ya fara fadi,wanda yasa murmushi subucewa daga fuskar sarakin,indai yaji amirun ya fadi hakan yanason shafe laifinsa daga wajensa "Zaka fara kamun qafar ne?,malami idan zaka yanki ticket ka dawo tun ban biyoka ba gwara ka dawo" "I almost done guy, don't worry,am on my way very soon.....meye labari?" Murmushi ya kubce masa daya tuna waccan qauyen da irin abubuwan da suka faru "Labarai zaka ce....but babu ko daya da zan baka a yanzu,idan na samu chance may be zan kiraka,but not now" dariya Aamiru yayi,yasan samir din duk yayi haka ne saboda yana jin haushin rashin dawowar tashi,kafin ya ankara ma ya kashe wayarsa abunsa,sai yabi wayar da kallo yana jinjina kai kawai. Gaban yalwatacciyar ma'ajiyar kayan sawarsa ya nufa,yafi ta'ammali da qananun kaya fiye da manya,saiya fidda wata shirt light ash da baqin jeans. Yana tsaka da shiryawar ya soma jin shigowar baqin motoci cikin gidan nasu,yaja dan qaramin tsaki,saiya koma shiryawa slowly,koda ya kammala shirin ma zama yayi ya buda safe dinsa yana ajjiye wasu muhimman takardu. Kira ne a jejjere ya dinga shigowa wayarsa,wanda ya tilasta masa barin abinda yake din,ya nufi wayar ya daga yana duba me kiran. Da fari daddy ne,sai kuma ya koma number mommy, lastly kuma jawahir,sai ya zabi ya fara da kiran number jawahir din "Yaaya,ka fito inji daddy,baqin suna gab da shigowa" yaji jawahir din ta fada,muryarta qasa qasa, "Ok" ya amsa can qasan maqoshinsa,fuskarsa da alamun gazawa da rashin walwala ya janyo wani tattausan baqin takalminsa da yafi zubi da slippers ya sanya,kana ya miqe ya sale feshe jikinsa da turare,hannunsa riqe sa wayarsa ya fice zuwa ainihin cikin gidan nasu. Da sallama ya shiga falon nasu,saiya samesu dukka a zaune saman kujera,banda daddy dake tsaye hannunsa daya riqe da wayarsa,daya hannun nasa kuma na a cikin aljihun rigar shaddar jikinsa dinkin tazarce. Da daddyn suka fara hada idanu,ya jefa masa wani kallo me kama da harara,wanda ya sanya samir din yin qas da nasa idanuwan,kafin ya tako a hankali ya giftashi "Duk wani qoqari da nake mafi yawancin lokuta saboda kai nake yinsa,amma kuma kowanne lokaci baka da wani qoqari kuma babban farincikin da ya wuce ka bula min qasa a idanuna......" Ya fadi cike da kamalar dake muna tsahon lokuttan daya shafe a duniya,daga haka ya juya a hankali ya nufi qofar barin falon,najwa ta miqe da hanzari ta rufa masa baya. Shima hannunsa na cikin aljihun wandonsa,ya dunqule su waje guda cike da zuzzurfan tunanin abinda ya aikatawa daddyn daya cancanci qorafi,amma tunaninsa kaf ya gaza gano hakan,saiya maoda idanuwansa kan mommy cike da fatan ta warware masa abinda yayin?,saidai kamar kowanne lokaci taqi basi damar karantar komai,hakanan batace dashi komai din ba,saiya sauke ajiyar zuciya yana yiwa damuwar tasa mazauni na daban,ya maida idanunsa kan teburin dake shaqe da kaya sannan daga bisani ya dubi jawahir daketa buga game "Hope kowa ya samu abinci a gidan nan?" Earpiece din kunnenta ta zame guda daga ciki sannan ta dubeshi "A'ah yaya,abincin baqi ne gaba daya,zuwa anjima zasu dora nasu ya nasu" shuru yayi na sakannin da basu wuce biyar ba,still idanuwansa akanta,saiya fara takawa zuwa gaban tebur din,ya ciro hannunsa daya daga aljihu ya dafe teburin yana irga adadin yawan nau'ikam abincin da aka tara,wanda yana da yaqinin ko baqo ashirin ne zasu zo a yau din ya musu yawa "Taso ki duba wasu daga cikin wadan nan ki zuba musu suci" ya furta kansa tsaye yana duban jawahir daga inda take zaune,idanuwansa da jikinsa na nuna zallar zararrasa da kuma cikar kwarjini. Daga kai mummy tayi cikin murmushi "Yanzu zansa zuwaira ta dora musu wani abun,wannan na baqim daddynka ne,ai ba'a taba ba son" kai ya girgiza alamun a'ah "Indai zamu farantawa wasu daga waje.....na cikin gida da suke tare damu koda yaushe suke qoqarin hidimta mana,su yafi cancanta su fara cin gajiyarmu.....taso ki dauke waccar golden warmer din" ya sake baiwa jawahir umarni.kai tsaye,idanuwan mummy saman fuskarsa tana dubansa,tana son nuna masa tata zararra amma wani abu daga fitowa daga gareshi ya taso ya danneta,ta tsani wannan raunin nata daya jima yana cutarta,duk kuwa da yadda take yaqi dashi babu dare babu rana,rauni ne wanda ada batasan dashi cikin halittarta ba sai yanzu. Kamar yadda yace haka jawahir ta aiwatar yana tsaye har komai ya kammala,saiya samu daya daga cikin kujerun falon shima ya zauna bayan ya fidda wayarsa yana duba wasu sabbin tractors da aka tura masa da zasu qara cikin kamfaninsu, bulldozer ce da sauran wasu kayan aikin. Miryoyine a cakude cike da hirarraki dake nuna farinciki da walwala suka doso qofar falon,cikin sakannin da basu wuce biyar ba suka bayyana daga qofar falon zuwa cikinsa. Mahaifinsa ne,gefansa wani dattijo ne kamarsa,wanda a qalla zasuyi shekaru kusan daya,baikai hasken mahaifinsa ba,saidai kusan tsahonsu daya,duk da cewa daddyn ya dan dara masa,daga bayansu wani matashin saurayine mai kama da mutumin dake gefan daddy,sanye da wani yadi na maza mai tsada da aka yiwa dinkin zamani dai dai jiki,duka duka bisa qiyasi bai wuce shekara sha bakwai ko sha shida ba. Daga can bayansu kuma matane su biyu,matashiyar budurwa da wadda ta data,kana gani kasan mahaifiyarta ce,cikin wani lace dake nuna alfarmar wadda ke sanye dashi,hakanan diyarta dake gefanta,itama lace dinne,saidai nata straight gown ce,tayiwa kanta wani irin dauri daya zauna das a goshinta,sai.mayafin da kwata kwata tsahonsa iyakacin wuyanta zuwa saman kanta ta nade dashi,hannayenta sunsha fixing na faratan kanti,wanda aka yiwa ado da nail polish kalar lace din dake jikinta. Mommy najwa da jawahir dukkaninsu suka miqe tsaye don nuna farincikin ganinsu,yayin da budurwa tadan taho da sassarfa zuwa inda momy ke tsaye ta rungume kafadarta,itama mummy ta tarbeta fuskarta qunshe da fara'a madaukakiya,ta sanya hannunta a gadon bayanta tana bubbugawa tare da fadin "Oyoyo daughter jauhar" "Oyoyo mommy" wadda aka kira da jauhar din itama ta fada fuskarta dauke da fara'a. Duk wannan abun da ake samir na zaune,hankalinsa saman wayarsa,qasa qasa yaji kamar an kirayi sunansa,daya daga kai kuwa sai yaga daddy ne,wani kallo yake masa da yafi kama da harara,tsam ya miqe tsaye,dai dai sanda baqon me suna honorable bukari mustapha yake duban samir din "Ah....yarona kana nan ashe" qoqarin sakin fuskarsa yayi kana ya qara taku uku zuwa gabansu,ya miqa masa hannu gami da cewa "Ina nan abba" qwaqwalwarsa tana tuna masa mutumin,duk da cewa ya dauki wasu shekaru rabon da ya ganshi,hannun ya miqa masa shima sukayi musabaha,yana jaddada yadda yaga samir din ya sake zama babban mutum,cikakken mai hankali fiye da shekarun baya,qaramin murmushi samir din ya saka yana dan ja baya. Tunda ya miqe yaja dukkan wani hankali nata,ko na minti daya saita kasa janye idanun nata daga kanshi,abinda tunda aka fara zancan tahowarsu wasu kwanaki da suka shude bata taba kawowa zaya faru ba,dui tsahon lokacin da maama ta dauka tana mata bayani bata tsammaci haka ba,cikin dan qaramin taqin lokaci irin wannan. "Hi"ta fada da zazzaqar muryarta ganin bai lura ma da wanzuwarta a bigiren ba,waiwayawa yayi a hankali,suka hada idanu,ta sakar masa murmushi,shima saiya maida mata martanin murmushinta,yadan daga hannunsa kadan ya maida mata amsa da "Hi" "Son......ga hajiya murjana" mummy ta fadi,ya sake juyawa zuwa sashe da take tsaye,cikin girmamawa ya gaidata,ta amsa fuskarta dauke da fara'a farinciki,gami da gamsuwa kan lamari da kusan shi yayi silar takowarsu zuwa cikin gidan,yayi jagoranci kan tafiyarsun,muryar jawahir ta ratsa falon sanda take fadin "Daddy....... food is ready" "Da kyau auta... honorable bismillah,mu fara da cin abinci kada lokacin sallar magariba ya shigo" "To....to babu laifi"sune a gaba,suna takawa zuwa wajen yana jan samir dake gefansa da hirarraki,wanda hakan ya faranta ran daddy qwarai,yayin da mummy maama jauhar najwa da jawahir suka rufa musu baya. Da kansa samir din ya jawa daddynsa kujera,sai ya bawa honorable damar zama,don haka ya sake ja masa wata,sannan shima yaja tasa ya zauna,su mummy suka qaraso suma kowa ya yiwa kansa wajen zama,duk da hira dake tashi tsakanin mummy da maama,sai kuma jauhar da najwa. Jawahir itace ta soma serving din kowa, mummy ta dubi najwa "Tayata mana saboda kufi sauri" hakanan taji kawai kaman mummy ta rage mata qima wajen jauhar,tasan yarinyar sarai,yar hutu ce kuma 'yar gata ta qarshe,komai yi mata ake,cewa tayi serving nasu kamar wani ragin qima ne a wajenta,haka dai ta miqe saboda babu damar musu saboda idanu ta soma zuzzuba abincin a yangance,tanayi kamar ba zata kai ba,yayin a jawahir ke komai bisa karasashi da walwala. Cikin mintuna qalilan kowa abincinsa ya isa gabansa,kowa ya soma qoqarin kaiwa cikinsa,banda samir da yaji sam zaman wajen bai wani yi masa ba,karo kusan na uku kenan suna hada idanu da yarinyar,saita sake masa murmushi,yana qoqarin maida mata koda shi nashi murmushin baikai zuci ba,yana ganin kawai idan ya maida matan kamar ya girmama baqin daddyn ne. Game dinsa daya saba yi lokaci bayan lokaci idan kansa ya dauki zafi musamman wajen aiki ita yake bugawa,duk abinda ke faruwa hankalin mutum biyu na tare dasu,daddy shi da mummy,duk suna ankare da samir din,tsayin mintuna kusan goma "Am son" muryar mummy ta ratsa kunnensa,saiya cira kansa a hankali "Ko zaku koma cikin parlour kaida jauhar.......kaman sai tafi sakewa a can taci abincin sosai ko?" Maganar mommyn ita ta sanyashi maida qwayar idanunsa kan yarinyar da suke kira da jauhar din,tana cin abincinta yadda ya kamata,duk da batayi nisa a cin ba,so baiga wani abu da zaisa su kebe ba kuma,saidai kuma bazai iya musawa mummyn ba,don haka muryarsa can qasan maqoshi ya furta "Ok" dai dai sanda murmushi ya kubcewa jauhar din,da idanu tace da mummyn "Thank you" saita gyada kai kawainta dubi jawahir "Jawahir saukar musu da abincin qasa" da murmushi ta miqe tana dan boye dariyarta "Ok mummy" idonta kan yayan nata,suna hada idanu saita waske,hakan ya gaya masa da wata a qasa,shima basarwa yayi yana miqewa,cikin takunsa mai cike da wata nutsuwa data cakuda da qasaitar data gadar masa da sunan saraki ya sauka daga wajen. Kujera daya mai cin mutum biyu ya zaba ya zauna,dai dai sanda itama ta qaraso tiqe da cups guda biyu data cika da lemon inibi,gabansa ta qaraso idanuwanta a kansa tana yana kamewarsa da ginshira irin tashi ta miqa masa cup din,sai daya kalleta ta jefeshi da murmushi,yasa hannu ya karba,qasa qasa ya furta "Thanks" saiya aje cup din gefansa hannun kujerar da yake kai,ita kuma ta koma a hankali ta zauna kam kujerar dake fuskantar tasa,har yanzu idanuwanta a kansa,tana qoqarin karantarsa. Komai najwa ta jere musu,daga qarshe ta tsiyaya coffee mai zafi data dafa saboda yayan,kuma taga baisha ba ta miqa masa tana murmushin dai,harara ya jefe mata data sanyata kintsa bakinta,ya miqa hannu ya amsa cup din,ta juya tabar wajen,sanda shi kuma ya gyara zansa sosai saman kujerar ya aje wayarsa gefe ya fara surbar coffee din a hankali. "Hi"ya kuma ji ta ambata,saiya dora idanuwansa saman fuskarta,hakan ya sanyata sauke nannauyar ajiyar zuciya a boye sannan tace "Am jauhar,daughter of honorable bukhari mustapha...... Muhammad samir isn't it?" Kansa yadan kada yana dubanta,saita saki murmushi,sannan ta kurbi lemon hannunta "Nice meeting you" "Me too" yayi qoqarin fada,kai ta sake jinjinawa,shuru ya sake ratsa tsani,kafin daga bisani ta gyara zamanta,ta dora qafarta daya saman daya "Kasan dalilin da yasa mummy tace mu sauko nan.......?" Kafadunshi ya dage kafin ya girgiza kai,duk da cewa ya jima da fuskantar komai,saita sake gyara zamanta sosai tana fuskantarsa,bayannta hade tafukan hannayenta waje daya "Dukkaninmu iyayenmu manyan mutane ne,munyi ilimu me zurfi.....mun samu gata da kulawa daga garesu,kasantuwar mu yaran farko a wajensu nida kai gaba daya....inaga abun zaiyi kyau idan muka fuskanci juna,muka kuma qulla alaqar auratayya,kamar yadda yake buri da mafarkin iyayenmu" D/Z 20 *_littafin kudi ne,kiji tsoron Allah kada ki mana sharing dinsa,ki guji cin haqqin wani,yadda bamu cutar da ke ba kada ki cutar damu,ki biya naki ta wadan nan numbers din ki karanta cikin aminci_* 08184017082 Ko kuma 09134848107 *SHIGA LINK DINMU NA WATPAD KIYI FOLLOWING DINMU DOMIN SUMUN TSOFAFFIN LITATTAFAN ZAFAFA* @ *ZAFAFABIYAR* _______________________________ ........tako ina mun dace da juna" takai qarshen maganar tasa ne hadi da fitar bugun zuciyarta,kaf tsayin rayuwarta wannan shine karo na farko data taba magana irin wannan da wani da namiji,kowanne lokaci suke qoqarin kawo kansu zuwa gareta,da furta kalaman da zasu sanya ta aminta dasu,sai gashi a wannan karon reshe ya juye da mujiya,dan mutan azare ya wargatsa mata record. Murmushin gefen baki ya fitar,tako ina ta kuma kowacce fuska baiga dacewar da take magana a kanta ba,tana da wasu siffofi daya zuwa biyu da yake ra'ayin matar da zai aura ta mallaka,amma akwai kuma tarin abubuwa da nauyinsu ya haura muradin siffofin da suke tare da itan "Bamu dace da juna ba" yayi maganar kanshi tsaye yana ajjiye mug din hannunsa idanuwansa a kanta "Like how?"ta fada cike da mamakin yadda ya iya kallonta kanshi tsaye ya gaya mata hakan,babu wani kwane kwane ko kara "Babu ta inda na hangi dacewarmu dake,alaqarmu ba zata taba bada wani abu me armashi ko kuma sakamako mai kyau ba.....dan taqadirin misali da nake ganin zaki fi fahimta dashi shine....ni dake din tamkar wasu halittu ne dake rayuwa bisa duniyoyi mababanta....."saiya miqe tsaye yana duban agogonsa,akwai sauran mintunda suka kusa ashirin kafin akirayi sallar magariba "Wannan itace tattaciyar gaskiya mara algus.....am sorry if i hurt you" daga haka ya soma takawa ya nufaci qafa fita,saita bishi da kallo ba tare da tasan meye abu na gaba daya dace ta aiwatar ba. Cikin qididdigaggun sakannni ya bacewa ganinta,ta sauke jiyar zuciya tana janye idanunta,duk da cewa martani ta samu mara dadi daga gareshi,amma sai taji zuciyarta bataji haushinsa ba,saima burgeta da yayi,saita maida bayanta tana mai jingina da kujerar tana fitar da iska daga bakinta. Koda ya fito din bai tsaya cikin gidan ba sai daya isa waje,hakanan ya samu kansa da yin tattaki cikin layukan unguwar tasu,iskar dake tafe da duhun magariba tana kadashi,duk shaqa daya da zai mata sai yaki ta fita ne da sauram guntuwar damuwa ko matsewar zuciya daya samu kansa a ciki,ya fahimci wannan duka plan din daddy ne,saidai babban abun tambayar,kamar mummy ma wannan karon tana goya masa baya. Bukar mustapha,idan ya tuna dai dai,kamar shine mutumin da daddy ya shaida masa zaya bawa kamfaninsa babbar kwangilar da kamfanoni da dama suke farautar samunta,hakan na nufin zaiyine saboda diyarsa?,ko daddy nason ya amshi diyarsa a matsayin tukuici na kwangilar da zai sama masa?,wannan tunanin ya sanyashi ciro wayarsa da sauri,ya fara laluben number ezikwe. Tun daga nesa idanuwanta da zuciyarta ke gaya mata shine,bata samu yaqinin haka ba sai da suka sake matsowa kusa dashi,samun kanta tayi da jan mayafin basma,wanda saura kadan ya zame daga kanta,tayi hanzarin dafeshi,ta kuma juyo a fusace cikin fada tace "Bakya gani ne hala mubina zaki ciremin mayafi tsakiyar hanya" "Sorry..... sorry don Allah,duba can da Allah,kamar me sanyi nake hangowa,mutumin afra" dubanta ta mayar wajen,ta koma ta kalli mubina "Shine mana" "Oh god" mubina ta fadi,duk yabi ta rude "Meye kike haka mubina,kinyi hauka ne?"ta fada ganin yadda mubinan ke mazari,ta kuma tafi kanta tsaye,dakatawa tayi sanda taji abinda basma ta fada "Sorry,wallahi rudewa nayi,kinsan tun ranar zuciyata bata huta da tunaninsa ba,duk sanda na fita kuma zuba ido nake ko zan dace" "Hakane,amma kuma saiki sanya nutsuwa ko?" "Yes" mubina ta fada tana daidaita numfashinta "Muje to" ta fadi cikin dakiya da qwarin gwiwa,fatanta idan sunje wucewa ta gabansa ya ganta,har yayi qoqarin mata magana ma. "A shirya dukka takaddun da suka dace,gobe zan shigo da sassafe,banason kowa yasan da shigowata,zan zauna mu rubuta takardar nema kwangilar nan" "Amma sir.....ina cewa kana da hanya mai kyau da aka tabbatar maka da samun contract din.....akwai kamfanoni da yawa da suke a buqata,ko dazu munyi hirar da daniel,babbar kwangila ce,hakan yasa masu so sukayi yawa fiye da yadda ake buqata" ya fada da gurbataccen turancinsa,iska samir ya furzar "Na sani,kawai kayi yadda nace din" yakai qarshen jimlar idanunsa na sauka akanta,bugun zuciyarta taji ya qaru fiye da dazu,sai tayi qoqarin aika masa da murmushi,saidai bisa rashin sa'a kansa taga ya dauke,babu wata alama data nuna ya taba sanin fuskarta a rayuwarsa,duk kuwa da cewa sun hada idanu dashi,har kuma suka gota bai waiwayi sashen da suke ba,bare ta sanya ran ya ganeta. Kamar zata saki kuka sanda suka giftashin saita dakata tana duban basma "Wannan wanne irin bad luck ne basma,kinga fa,kamar bai taba ganinmu ba" "Komawa zakiyi kenan kiyi masa bayanin kanki?"kai ta kada alamun a'ah,tayi gaba zuciyarta na gaya mata abinda ya dace tayi,tunda dai har ta ganshi cikin unguwar,zuciyarta dama gangar jikinta na bata lallai tabbas nan ne unguwarsu,indai ko hakane to ta kwana gidan sauqi. Bai dawo gidan ba sai wajen tara na dare,zuwa sannan baiga kiran kowa ba,wala'alla saboda kashe wayarshi da yayi ne,koda ya dawo sashensa ya wuce kai tsaye ba tare da ya nemi kowa ba,yayi relax saman sofa yana maida numfashi yaji an tura qofar dakin an shigo,yana daga kwancen ya wulga idanunsa bakin qofa,wanda yaga yana shogowar ciki ne yasa ya miqe sosai ya zauna,shigowar daddy bangarensa wani baqon al'amari ne,wanda baifi a qirge adadin lokutan daya taba shigowar ba. "Barka da warhaka daddy" hannu ya daga masa,fuskarsa a dinke tsaf tamkar bai taba dariya ba "Kai za'a yiwa barka da kuma sannu gaba daya,samir.....kayi qoqari kaga ka watsa min qasa a idanu,ka kuma nuna rashin muhimmancina kaji" daga haka bai qara ba ya juya abinsa ya fice,maganar data sanya samir din cikin tunani,ko meye dole yayi qoqari yabi dukka abinda daddyn yace har baqin su gama zamansu a rabu lafiya,indai har abinda jauhar ta fada daxun haka yake......to shine abu guda daya da baiga hanyar bullewarsa ko dai daituwarsa ba. Hutawar da yayi niyyar yi ya fasa,saiya fidda kayan jikinsa ya shige toilet don ya watsa ruwa,ya wuce zuwa cikin gidan daddyn yaga gilmawarsa ko hakan zai sassauta zuciyarsa. **********Sake riqe gyada me gishirin data siyo tayi da kyau sanda take tunkaro saronsu gabanta na dan faduwa,daga sanda auwalu ya dawo gifansu gaba daya ya zamana bata da wani sauran nutsuwa,duk sanda zata fita da dare koda yammaci cike da fargaba zata shiga,hakanan cikin fargaba zata fita. Sai da tayi bismillah sannan ta saka qafarta soron,a hankali take tafiya cikin sanda kamar wadda ke taoron fadawa wani wawakeken rami,gabanta yayi wani mugun faduwa sanda taxo tsakiyar soron,hancinta ya fara jiyo qamshin wani abu me kama da ganyan taba. Wani wawan ihu ta saki sanda taji an cafki hijabinta ta baya,ba tare da wani jinkiri ba ta fara kokawar qwace kanta,jin motsin tahowar mutane ya saketa ya koma lokon daya lafe,hakan ya bata damar fellawa da mugun gudu zuwa cikin gidan. Karo sukayi da ummanta data fito da sassarfa,inna haule dake sashensa itama ta fito saboda ihun dataji din,jikin umman nata ta fada jikinta na wani irin rawa,hannu biyu umman tasa ta riqeta tana tambayarta lafiya?,muryarta na rawa kamar wadda aka watsawa ruwan qanqara ta hada kalmar "Au....walu ne" "Wanne auwalun?" Inna laure ta fada bayan ta gama daura zaninta wanda tayi daurin qirji dashi,wanda kusan aikinta kenam,a haka take kwana ta kuma wuni,shi yasa dukka zannuwanta suka kode suka nar rigunanta,ta kuma koma tana gyara daurin dankwalinta dake barazanar suncewa ya bayyana diddigeggen gashinta da kaltum ce dama marufar asirinsa,tunda kowa ta dauki gana dasu bayan karan tsanar data jima da dora musu tabar barin kaltum din tayi mata kitso. "Auwalu nawa kika sani a gidan nan?"umma ta amsa mata cikin wani irin fushi dakr tashi saman fuskarta,ita kanta inna kauren sai data kalli inna sanda taji ta tofa tata,abinda batasanta dashi ba,duk da kuwa irun cin kashin da take mata cikin gidan "Ke zuwaira,banason sharri,haka kawai 'yarki taga wani abun daban za'a laqawa auwalu na,koma wanne dan jakar uban ta rakito bari na leqa na ganshi don ubashi zai jawa yarona bacin suna ba gaira babu dalili,baya duk sanya idanun da jama'ar qauyen nan suka masa" daga haka tayi hanyar soron bakadan bakadan,bata ko damu da yanayin suturar jikinta ba. Umman na tsaye anan tabi laure da kallo,tana zuwa dai dai sanda auwalun ke zuqe sauran abun mayen dake hannunsa,salati tahau rafkawa "Yanzu dama auwalu baka daina zuqe zuqen nan ba?,to don ubanka zoka wuce ka fice daga gidan nan,ba zaka jawomin magana ba bakin magauta,tattarawa zakayi ka koma inda ka fito,matuqar ba zaka daina abinda kakeyi ba" "Habba....laure....yawa kike,nifa inason yarinyar nan,tayimin wallahi.....tun....ba yau ba,kuma keda iliya......duka kun sani" "La'ilaha ilallahu....muhammadu ya rasaulullahi,to wallahi haihata haihata,maza ka fita"ta fada tana tankadashi zuwa waje da hannu bibbiyu har sai data tabbatar ya fice sannan ta dawo ciki. Babu kunya babu tsoron Allah data dawo ta iskesu a wajen sai tayi mursisi,cikin muxuran borin kunya ta fara magana "Ajawa yarinya kunya ehe.....banason aikin banza da wofi,shi yana qoqarin yakiceta amma ita tana liqe masa ina dalili?,to wallahi auwalu na dan gata kuma dan asali gaba da baya yafi qarfinta,babu abinda zaiyi da ita" "Ke laure" inna ta kirata cikin kakkausar murya,cak ta tsaya tana mamakin yadda umman ta kirata "Idan har ke kin manta abinda ya faru a baya ni din ban manta ba,duk wannan soki burutsun da tabarmar kunyar ba abinda ya shafeni dashi,abu daya nakeso shine,ki jawa danki kune,ki jawa danki kunne,ki jawa danki kunne,bazan dauki duk wani ganganci nasa tsageranci ko rashin kunya akan diyata ba,maganar gata da asali indai kaltume bata dashi to ita da auwalu duka sammakal suke,gata kuma babu gatan daya wuce na ubangiji,duk wani dan adam da zai baka gata to koma bayan gatan ubangiji ne,ki tilastashi yayi qoqarin kiyaye shiga hurumin diyata" ta dakata a nan,sannan ta kama hannun kaltum zuwa ciki ba tare da tabi takan inna laure kota damu da gyadar da tuni kaltum din ta watsar da ita ba cikin qasar dake wajen. Iya fushin da kaltum yau ta gani a idanun ummanta abune da bata taba ganun makamancinsa ba ko sau daya,tabbas rayuwar auwalu cikin gidan kar barazana ce ga tata rayuwar,sai da umman ta danganeta da dakinta,sun jima zaune shuru babu wanda yace wani abu,a qalla kusa awa guda sanda sukaji muryar babansu yana doka sallama da wannan fusatacciyar muryar tasa,wanda babu abinda yake sawa ta rusuna bare kalaman cikinta su fita da taushi "Kici gaba da kulawa da kuma takatsantsan,ki yawaita addu'a,daga yau kuma kada ki sake kwanciya baki kulle qofar dakinki ba" saita juya ta fice a hankali jikinta cikin matuqar sanyi....... *********Jikinta take kakkabewa bayan ta gama yiwa wasu mata su biyu kitso,ta sanya tsintsiyar laushi ta share wajen tas,duk da cewa dan sumunti ne daya fara farfashewa,wanda dama iyakacinsa qofar dakunanasu,inda sukanyi shimfida su zauna,sauran duka qasa ne da yashi. 'yar rumfar da suke dora abinci ta isa,ta shirya itace cikim qwarewa da gwanancewa ta kunna wuta,sannan ta cika tukunya da ruwa ta dora,kafin ta wuce ta daura alwalar sallar la'asar,yau cikin farinciki suke,saboda zuwan yakumbo indo,wadda ta taho musu da buhun shinkafa 'yar hausa,harda kwalin taliya sukutum da guda,taliyar da idan sukaga babansu ya basu ita to babu yadda zaiyi ne,a haka ma baifi cikin wata biyu suci sau daya ba,saidai 'yar murji ta hausa,itama idan ta samu. Ta hada musu da manja da man quli kowanne kwalba bibbiyu,haka take musu,lokaci baya lokaci takan yi musu irin wannan kyautar,ko ita ko kawu ado,ammafa saida su boye,su dinga diba da kadan da kadan suna dafawa,saboda matuqar babansu ya fahimci an kawo tofa babu sauran xaman lafiya a gidan,hakanan su da abincinsa sai bayan wani lokaci mai tsaho,koda wanda ta kawo.ya qare din,amma a yanxun da bai sani ba bakinsu alaikum,zai dauka buga bugar da suka saba sukayi suka dafa,idan yaga dama ya basu saisu tara zuwa lokacin da wanda suke dashi ya qare. Sanda ta idar umman itama ta fito ta daura alwalar ta bada faralin sallah,lokacin kaltum na gaban tukunya tana sake iza wutar data hura,suna hira jifa jifa da umman,saidai ita umma har yau ranta babu dadi,tun daga lokacin da wancan abun ya faru,har yanzu ba'a sake take ba,tun daga ranar kullum tunaninta shine ta yaya zata baiwa diyarta tsaro da kariya har Allah ya kawo sanda zata bar gidan,tabbas da tana da inda zata kai kaltum din da zai zameta mata garkuwa daga barazanar gidan babu ko tantama zata haqura da zamanta a gabanta ta miqa ta can din. Sallamar qaramar yarinyar da bata wuce shekara tara ba shi ya tsaida hirar tasu,daga umman har kaltum fuskarsu da fara'a suke kallon yarinyar,kaltum ce ta fara magana "Hali dubu 'yar gidan gwaggo habiba,yau an tuna damu?,ko gwaggon taki ce ta aikoki?" Dariya yarinyar ta saki tana gaida kaltum,sannan ta qarasa tabarmar umman tana gaisheta "Cewa tayi nazo na gaya muku batajin dadi,wai ida n yaya kaltume bata komai tazo dan Allah ko yau ko gobe" girgixa kai kaltum tayi "Dake za'a hada baki ko dubu?,to kwa gama qage qage ciwonku ku haqura" murmushi kawai ummansu tayi,tasa dama za'a rina,saboda tun zuwan habiba gidan na qarshe taga wasu canje canje daga gareta,tasan babu jimawa dama ciwo zai bayyana,kusan kwanaki bakwai kenan tana kasa kunnen jin hakan. Ga mamakin kaltum sai taji ummansu da kanta tana cewa "Kice mata zata zo in sha Allahu kinji ko?" "To ummanmu" dubu ta fada kamar yadda taji habiban tana fada,yarinyar nata dariyar jin dadi ta fice yiwa uwar dakinta albishir. "Ummanmu....kinsan fa banason zuwa wallahi,ni kunya nakeji,gidan qanwata ne fa" dubanta umman take,tausayinta yana ratsata,banda haka Allah ya shirya ai da yanzun itace adakinta ba habiba ba,saidai tsarin Allah kuma shine dai dai,tasan cewa kaltum din na kunyar zuwa,kodon surutu irin na jama'ar qauyen,duk da cewa ahalin yusufa basu da matsala,mutane ne masu karamci da dattako,har cigiyar babar yusufa take idan taji shurun kaltumen yayi yawa "Na sani,amma ni kikeso naje naji matsalarta banda abinki kaltume?,kece fa 'yar uwarta,ke kadai take da" shuru kaltum tayi tana gamsuwa da zancan umman,saboda hala bata sake cewa komai ba. Bilal ne yayi sallama yana shigowa gidan,yayi futu futu da qasa kamar kullum,qoqari kawai yake ya cire gwabza gwabzan takalman qafarsa tare da neman wajen zama,kaltum ta dago taga firfita wutar da takeyi,idanunta ya kada yayi ja saboda hayaqi tana dubansa "Sarkin nema,a ina ka sake samun wajen aiki kuma?" Sai daya kalli umma sannan ya sosa kansa "Wajen aikin nan dai nawane?" Idanu kaltum ta zuba masa "Wanne wajen aiki?,inda na hanaka zuwa?,bilalu bakajin magana?,baka tsoron mutanen nan su illataka?baka son lafiyarka ko?" Fuskarsa cike da alamun damuwa yace "Ummanmu ce wallahi,ita tace na koma,ki tambayi xunnu,mutumin ne yayi cigiyata akace masa na daina zuwa,da kansa yazo Allah ranar bakya nan kin tafi tsangayar sarki yin kitso,yace na koma,yana da kirki mutumin,ya tambayeni amma nima dalibin makarantar ne ko?,da nace masa bana zuwa bakiga fadan daya ringa yimin ba,yace lallai idan aka gama gini dani za'a koma,zai siya min komai har uniform da litattafai,kuma nima daya yimin fadan sai naji yaya inason na koma,kullum saiya bani ragowar abincinsa,baki gani ba harda nama a ciki" idanu kaltum ta zuba masa,zuwa wani lokaci ta dauke idanunta ta maida kan ummansu,kallon data yi mata yasa ta gane umman tasan komai,kai ta jinjina mata,sannan ta soma magana "Duk wani abu daka zama a duniya haquri shine jigo da yake maka jagora izuwa wannan matsayin,saurin fushi baya haifar da komai illa dana sani,sa'annan duk sanda wani yayi maka kuskure daga bisani ya dawo ya nuna maka cewa ya gane abinda ya aikata din ba dai dai bane,cikar dan adamtakar mutum shine ya yafe masa,gajen haquri....saurin fushi da saurin yanke hukunci basu da wani amfani arayuwarmu,ina fatan zaki dauki darasi" a hankali kaltum ta gyada kai,dukka maganganun ummansu tasan kan hanya suke,koda yaushe umman tasu burinta shine taga sun zama wasu nagartattun mutane. Tana gaban murhun tana tunanin maganganun ummansu,har zuwa lokacin data kusa gama dahuwar shinkafar,bilal din ya qaraso wajen da take zaune yana roqarta ta kara masa ruwan zafi a wata silver idan ta gama girkin,saita yafitoshi da hannu,ya qaraso ya zauna dab da ita "Don Allah kada kice na firfita miki wutar nan,Allah yunwa ta gama cinyeni abinci kawai nake buqata" harara ta jefeshi da ita,bilal din qwallo ne wajen ci,baya qoshi sam,dalilin da yasa ya shiga nema haiqa kenan,tun daga sanda ya budi idanu ya fuskanci gidan nasu ba wajene na ciyar da yaro ya qoshi ba,inda take godema Allah bai taba daukar kayan wani ba,saidai ya sadaukar da dukka qarfinsa ya nemi abinda zaici "Kace mutumin zai siya maka komai?,wanne irin kudi ne dashi haka?" Dariya bilal yayi "Babu wani kudi,shima kullum tare damu yake aiki,amma kamar abinda ake biyansa yafi namu yawa" kai ta jinjina tana mamaki,dama akwai ragowar mutane masu kyawun zuciya haka?.... 21 D/z *_littafin kudi ne, sharing dinsa tamkar xalinci ne a garemu,ki tuntubi wadan nan numbers din ki biya naki ki karanta cikin aminci_* 08184017082 Ko kuma 09134848107 _______________________________ *_INNA KAFAINAKAL MUSTAHZI'EEN_*👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽 ________________________________ A daren ranar suna zaune a tsakar gida saboda yanayin zafi,ummansu na qofar dakinta,haka babansu na nashi qofar dakin qarqashun rumafarsa ta bunu,yaci ya qoshi da abincin da bashi ya nemo ba,yana zaune kuma ya kunna radio gamida kasa idanunsa a tsakaninsu,yana neman wani dan qaramin dalilin da zai sanyashi ya bude faifan bala'insa,dole ce ta sanya kaltum itama zama qofar nata dakin,dukkaninsu ba'a sake suke ba,saboda zamansa a tsakaninsu babu abinda yake haifarwa sai da mara idanu,da zarar ya gansu a zaune tare zaice sun hada kai suna munafuncinsa ita da 'yarsa,don haka matuqar yana nan din sun gwammace su raba wajen zama. Addu'a kaltum take cikin ranta kada Allah ya shigo da bilalu,ta tabbatar idan har ya shigo din sai baban nasu ya samu abun fada. Sallamar munzali ce ta ratso tsakar gidan,ya shigo hannunsa dauke da buhu,ummansu ta amsa masa tana miqewa ta zauna sosai daga jingina bayanta da tayi. Fuska babu fara'a ya gaidata ta amsa masa cikin kulawa,idan da sabo ta saba da wannan halayya da dabi'a tasu,kai bakace itace ta rainesu ba a sanda mahaifiyarsu ta fita tabar gidan ba,sam babu wani halacci kara ko kunya a tsakaninsu,duk da cewa da wayonsu ta samesu,amma duk sauran hidima da yaro ke buqata kafin zamowarsa cikakken mutum ita ta dauki gabarar yi musu ita har zuwa sanda sukayi aure. Ta gaban kaltum ya wuce,wadda take ta gaidashi yayi watsin tsiya da gaisuwarta,saima harara daya balla mata,ya qarasa gaban baban nasu,yaja kujerar mata ta tsuguno ya zauna akai ya soma gaidashi "Ya akayi munxali?" Baice komai ba sai zazzage kayan dake cikin buhun da yayi,ya soma ware wasu gefe wasu kuma yana miqawa baban. Sai daya ware jallabiya kala hudu,takalmi da agogo,da hular tashi ka fiya naci da kudi 'yan dubu dubu guda hudu ya miqawa baban "Gashinan inji innarmu tace a baka" "Allahu akbar kabiran,hajjaju mutan saudiyya,ta dawo ne?" Ya fadi cikin wata madaukakiyar fara'a data baiwa kaltum mamaki,ta kuma sanyata kallon ummansu,saboda ita dai bata saba ganin hakan ba,saidai suna hada idanu ta dauke kanta,saima ta janyo wani dan abun hannu na duwatsu me kyau nata daya katse dazu taci gaba da gyarashi,kanta yana kallon qasa "Bata dawo ba,ta dai yo aikene,ni da muzammilu da sani da muka ce mata muna son jari" ya fada yana jin haushin baban nasu can qasan ransa,saboda har yanzu bai manta yadda babar tasu tasha wahala hannunsa ba kafin ya saketa ta tsallake zuwa saudiyya neman kudi "Ma sha Allahu,kai Allah ya saka da alheri" "Wata shekarar take saka ran zuwa,zata tafi damu muyo umara" "To madalla alhaji munzali,ince dai baku manta dani ba?" Sai daya miqe tsaye sannan ya bashi amsa,saboda ya soma gajiya da yadda yake fidda son zuciyarsa quru quru,baya ma tuna abinda shi ya aikata a baya "Idan Allah ya kiraka kaima sai kaga ta biya maka ai" "To Allah amin" ya fada yana jujjuya kayan hannunsa,wanda ba'a taba masa kyauta irin haka ba tunda yake. Har munzalin ya gota kaltum saiya dawo da baya "Ke kattume" ya kirayeta sa qarfi "Na'am yaya" ta amsa tana daga kai da hanzari "Rannan nazo nemanki ban sameki ba,bansan me kika yiwa fiddau ba,nayi nayi ta gayamin taqi,wallahi ki kuka da kanki duk randa ta shaidan naji rashin mutunci kikayi mata" "Kaga yaya fa ba....." "Rufemin baki!" Ya dakata mata tsawa,sannan ya shura takalmansa yayi gaba abinsa,saita bishi da kallo,a lokacinne kuma baban nasu ya dira nasa "Wani diban albarkar hala kika yi musu?,ke wai me yasa kike da daukar magana kamar 'yar Allah ya bani?,to wallahi indai kuwa taba munzali ko ahalinsu kikayi nima ba qyaleki zanyi ba,shashasha mara lissafi,shi yasa qanwarki ta tafi dakin miji ta barki ke gododo a zaune" shuru tayi harya kammala jafa'insa ya koma kan murnar kayansa,yanata yada magana da habaici,kanzail ummansu batace masa ba,sai kaltum ta fara tattare shimfidarta jin ya koma kan umman tasu daya fuskanci bata da niyyar kulashi "Wato saboda tsabaragen baqin hali da kishin banza,kin kasa yiwa uwar yaron nan godiya....a gabanki ya kawo kayan nan,kuma koda ya tafi ma kin gaza daga kai ki tayani murna" a hankali ta daga kanta ta dubeshi sau daya "Allah ya sanya alheri,a kashe lafiya" daga haka ta maida haka ta maida kanta taci gaba da abinda takeyi,saidai duk da haka shi hakan baiyi masa ba,haka yaci gaba da qananun mitocinsa kafin ya tattara ya shige daki yana yiwa kayan boyo na musamman,tare da qiyasta sanda zai sanyasu. *********Jawahir najwa da jauhar ne tsaye a farfajiyar gidan,sai saraki dake tsaye gefe guda sanye da wasu qananun kaya da sukayi masifar fitar da kyau da kuma kwarjininsa,hannunayensa gaba daya zube cikin aljihun wandonsa,ya zubawa motarsa a aka gama wankewa ana gogeta idanu. Fita zasuyi zuwa gidan hajiya qarama,wanda mummy ce ta shirya fitar,da sunan yaje ya kaisu su gaidata,a gaban idanun daddy ne,don haka bashi data cewa,bama wannan ce damuwarsa ba,yadda yaji suna tsiro da zancan zuwa azare,abinda sam sam yakejin bada shi xa'ayi ba,zuwansa azare tare da jauhar kamar ya bada lasisin dake nuna amincewarsa da aurenta,saboda tafiyar zata zamana tamkar tattakine na nuna jauhar ga dangin mahaifinsa. Horn ake saki a bakin gate din,wanda hakan yaja hankalin samir,saboda yadda ake danne horn din babu qaqqautawa,hannuwansa ya sauke yana duban gate din sanda malam salahu ke rawar jikin budewa,kauda kansa yayi sanda motar ta shigo,ba kowa bane sai fawwaz,don haka ya taka zuwa gaba,ya bude motar kafin ya qarasa gabanta,ta bada wata 'yar qata ta security,hakan yaja hankalinsu jawahir suka matso suma sannan ya saka key ya bude. Dakatawa yayi daga qoqarin shigar da yakeyi saboda jiyo muryar fawwaz cikin fada yana yiwa malam salahu fada,wanda a qalla ya kusa haifarshi idanma bai haifeshin ba,qafarsa daya zura cikin motar ya cire,yaja rigarsa qasa ya gyara ta sanna ya fara takawa zuwa inda suke tsayen "........dukka alamu sun nuna bakasan aikinka ba" kalmar qarshe da samir din yaji daga bakin fawwaz kenan,wanda ke tsaye gab da malam salahu,kamar me shirin gabza masa mari "Baba" samir ya kira malam salahu cikin nutsuwa,waiwayowa yayi cike da girmamawa "Na'am dana" "Lafiya....meya faru?" Fuskar cike da alhini da alamun rashin jin dadin cin fuskar da fawwaz din ke yawan yi musu matuqar zai tako qafarsa cikin gidan ya shaida masa cewa,yana bayan gida yana fitsari ne sanda ya iso,kuma yana fitowa yazo ya bude masa,ya masa bayanin dalilin jinkirin nasa amma yace bai yarda ba. Idanunsa samir ya dauke daga kan malam salahu zuwa kan fawwaz,wanda duba daya zaka masa ka hangi yanda ransa ya sosu dajin abinda fawwaz din yakeyi,idan bai manta ba shi akaran kansa wannan ba shine karon farko da fawwaz din ya aikata haka a gabansa ba,amma a yau din yakai maqurar da bazai iya qyaleshi ba "Kayi haquri baba don Allah kaji?" Cewar samir da sassanyar muryarsa bayan ya maida.ganinsa ga malam salahu "Babu komai dana,ba komai" ya amsa masa cikin nuna girmamawa yana cakude tafukan hannayensa waje daya,sannan ya motsa ya bar wajen,samir ya bishi da kallo cike da tausasawa. "Ji mana" samir ya fadi sanda fawwaz ya gyara kwalar rigarsa yana shirin barin wajen zuwa cikin gida,dakatawa yayi fuskarsa a daure ya waiwayo yana duban samir din "Kayi qoqari wannan ya zama karo na qarshe da irin haka zata sake faruwa takaninka da duk wani ma'aikaci na gidan nan,don mu muna girmamasu.....saboda daraja ta fifiko da tazarar shekaru da Allah ya bamu tsakaninmu dasu,banason na sake ji ko na sake gani,nan gidan akwai ɗa'a" ya qarashe maganar yana gyada kanshi,sannan ya taka zuwa wajen motarsa ya barshi a nan,cikin zuciyarsa yana jin zafi,saboda ya fuskanci maganarsa ta qarshe tamkar baqar magana yake gaya masa,gugar xana yake masa kenan?,qwafa yaja cikin ranshi yana fadin "Idan kere na yawo,zabo na yawo....." Yasa kai zuwa cikin gidan da sassarfa,samir dake qoqarin tada motar ya bishi da kallo,abubuwa masu tarin yawa suna kaiwa da kawowa cikin qwaqwalwarsa. Tunda ya shiga motar ya zama tamakar kurma,duk yadda jauhar taso jansa da hira bata samu damar hakan ba,gwanine idan yaso miskilanci,duk da cewa bawai halayyarsa bace,hasalima mutum ne shi mai son ababen nishadi da abinda zai sanyashi dariya,saidai a wannan karon ya ari wata halayyar ta daban. Jawahir da dama kusan tafi kowa sanin halayyarsa,tunda ta fahimta hakan bata sakoshi cikin zancansu ba ko sau daya,kusan magana daya biyu sai jauhar ta tambaya jawahir wani abu game da samir din,duk da yaqi bata hadin kai suyi hira yadda taso har suka kawo gidan hajiya qarama. Da fara'a ta tarbesu,kamar yadda take da karrama baqo,duk da cewa mafadaciya ce,amma tayi gadon karamci da kuma dattako gami da halin qwarai. Sosai jauhar ta sake cikin gidan,duk da cewa hajiya qarama bata ganeta ba,amma ta karbeta kamar yadda ta karbi su najwa,saida suka kebe da samir sannan ta samu sararin tambayarsa "Saraki wannan fa?" Ajiyar zuciya ya sauke yana shafa fuskarsa har zuwa tsakiyar kansa,yama rasa makama da kuma ta yadda zai yiwa hajiya qaraman bayani "Kayi magana mana,sai wani faman shafa gemu kake,ko labarinsa na tambayeka?" Ta fada tana hada fuska,saiya saki murmushi yana gyara zamansa "Yadda kika ganta nima haka naganta hajiya,saidai ita yarinyar da bakinta ta gayamin manufar zuwansu shine a hada aurena nida ita...." Shuru hajiya qarama tayi tana nazari,a yau idan samir ya tashi aure tanajin babu wanda zai kaita farinciki,koda kuwa mahaifiyar data haifeshi ne,saidai tana tsoron daga inda aka qullo masa matara auren akeso a cusa masa ita,don ko sau daya bataji zancen daga bakin yayanta ba,to amma ba zata yanke hukunci da kai ba,don haka ta gyara zama tace dashi "Waye gwanin hadin?" Hannunsa yadan jujjuya alamun shiga rudani "To abundai gashinan hajiya,abinda na lura daddy da mommy dukka suna son abun" faduwa gabanta yayi,haka nan a take zuciyarta taji abun bai mata ba,ta yaya za'a kawo wa samir din matar aure,kuma wai da hadin gwiwar mommy a cikin lamarin,sannnan ta zauna tana ji tana gani?,ba zata lamunta ba "Yanzu kai wannan mai zubin ruwan askin tayi maka kenan?" Dariya ce sosai ta qwace masa,ko banza idan yazo gidan hajiyan yana samun nishadi ko na minti kadan ne,hajiyar zuma ce,ga zaqi ga harbi,saidai tana da wani baban gurbi a zuciya da kuma rayuwarsa,qoqarin daidaita kansa yayi saboda harara da yaga tana jefa masa,sannan ya tattara kalaman da zai gaya mata "To hajiya ni ya zanyi.....,gaba kura baya sayaki,kinsan sarai yadda muke ciki da Daddy,duk abinda zan aiwatar komai kyansa kawai gani yakeyi ina yine saboda na qalubalanci ra'ayinsa,tunda naqi siyasa sai yake ganin komai ma da zanyi bashi da wani muhimmanci ko fa'ida" tsaki hajiya qarama taja ta tabe baki "Wanna duk makircin jidda ne bana wani ba.....to idanma kana so ka fiddata daga zuciyarka tuntuni,idan kuma bata ma shiga zuciyar ba to ka hutawa ranka" tana fadar maganar ta kama kanta hadi da shan mur,batajin har abada zata sake bawa jidda wata qofa komai qanqantarta,ta yadda koma a ina samir ya samo matar aure,amma zabin kansa da kansa,bawai zabin hadin gwiwa ba,koma ya zamana zabi daga bangarenta ita daya. Wani sanyi yaji ya ratsa zuciyarsa,ya tabbatar mafita tazo masa,tunda hajiya qarama ta qyamaci abun to yana sanya rai babu shakka komai zai warware cikin sauqi,kuma koda laifinsa zaizo a cikin lamarin a wajen daddy,to zayazo ne da kaso mafi qanqanta. A nan gidan ya barsu ya wuce green garden abinsa inda yayi zasu hadu da Ezekiel saboda hada takardun neman kwangila daga qarshe ma saiya turama jawahir tex kan idan sun gama abinda zasuyi su wuce gida ba yanzu zaya dawo ba. Sannu a hankali take takawa cikin duhun magaribar,wanda ya mamaye ilahirin duniya gaba daya,ya kuma cakuda da sassanyar iskar dake nuna gabatowar lokacin sanyi kowanne lokaci. Za'a iya cewa yawaitar duhu tafi a qauyen fiye da haske,saboda rashin wutar lantarki da basu da ita. Iskar ke kadata daga hagunta zuwa damanta,a gajiye take tubus,ga wata bahaguwar yunwa data kwaso,kan hanyarta kenan ta komawa gida daga gidan inna,wanda matar qaninta ta haihu,ta kuma umarce taje ta yiwa mai jego kitson suna. Da fari taqi zuwa,saida ummanta ta mata da gaske sannan ta shirya taje,saboda ranta ya baci sosai da yadda akaja baki akayi shuru,babu wanda ya shaidawa umman tasu haihuwar,saida tasu ta taso nason ayi musu kitso sannan aka nemeta,duk da kadaram kadaham suka karbeta,babu yabo babu fallasa,saidai bata yarda ko ruwan gidan ya shiga cikinta ba,bayan an gama abinci an dire mata,tace ta qoshi,daga haka inna tasa aka dauke ba'a qara mata tayi ko bi ta kanta kan taci din ba,haka ta nado yunwarta ta wuni guda tayo gida da ita. Tana gab da isa gidansu ta hangi mutum jingine a qofar gidan nasu,ya harde hannunsa a qijri ya zubawa hanya idanu,da fari tayi tsammanin nasuru ne,saboda jiya ya dawo bayan kammala jarabawarsa,a yau kuma yace ta tsimayi zuwansa,saidai data matso kusa sosai sai taga bashi bane,don haka bata wani maida hankali kan ganin wanene ba ta tasamma wucewa zuwa soronsu. "Ke kattume.....ke!" Ta jiyo kiran kamar daga wata duniya ta daban,wanda hakan yadan razanata,ta waiwaya baya da sauri,sai taga yaya munzali ne,yana dosota tamkar zai tashi sama,sai qura yake tadawa kamar wanda ala bugawa kugen yaqi. Cak ta tsaya tana dakonsa har ya qaraso,abu na farko data fara ji shine saukar wani lafiyayyen mari a kuncinta na hagu da dama,wanda hakan yasanya duk wata wuta ta jikinta daukewa,ta daina ganewa tsayin wasu sakanni kafin sadarwa jikinta zuwa kwanyarta ta dai daita,qara takeson saki amma kamar an riqe mata murya saboda tsananin zafi,kalamansa suka fara shiga kunnuwanta kamar saukar kibiya,wanda sai daya fara da manya manyan ashar sannan ya dora "ashe 'yar iska ce ke tantariya?,shegiya mara mutunci kawai,yau kuma ta kaina iskanci da fitsarar taki zata biyo?,to wallahi baki isa ba,don ni ba sa'anki bane" wani irin ciwo kalamansa suka saukar mata a zuciya,batasan sanda hawaye ya sulmiyo mata ba,tafin hannunta biyu dafe da kuncinta,a sanyaye tace "Me nayi maka yaya?" Shuri yakai mata da qafarsa,wanda badon tayi hanzarin ja da baya ba tabbas da taji jiki "Ni kike ma tambaya?,ashe iskancinki yakai kije har gidana ki ciwa matata mutunci ki qala mata sharrin sata?,banda ita din mai hankali ce dakai zuciya nesa kikasan me hakan zai haifar muku?,don u*****rki ni baso nayi ta kamaki tayi miki mugun duka ba inga uban daya tsaya miki ba?" Kalmar uwarta daya fada ita tafi komai bata mata rai,zuciyarta ta fara motsawa,bakinta ya gaza dannewa "Uwata yaya?" Ta tambayeshi tana dubansa kai tsaye "Eh uwarki an fada,ke mai uwa ko?,dama ance idan aka zageta bakya qyalewa,to a fada don u****rki don u***rki" "Badai uwata ba wallahi,badai uwata ba". Gadan gadan ya yiwo kanta yana fadin "Saidai tawa,sai tawa kike nufi?". Kafin tayi kowanne motsai har ya iso gareta,bata ankara ba yasa qafa ya kwasheta,sai gata warwas a qasa,qugunta ya bugu da qasa,wanda ya tilasta mata qwalla qara ba tare data shirya ba saboda tsananin azaba,bai jira komai ba ya soma kai mata wani irin duka tako ina,tamkar wani mahaukacin kare,abinda ya fara jan hankalin mutane dake nesa kadan dasu suka fara tasowa. Dukanta yake kai kace Allah ne ya aikoshi,yayin data dinga kuka mai qarfi da ihun neman dauki saboda azabar irin dukan da yake mata kamar ya samu qato dan uwanshi,mutanen farko da suka soma isowa sukayi sukayi ya bari amma ya qiya idanunsa sun rufe,har sai da hijabin dake jikinta yayi nasa wuri,data miqe ya maidata ta hanyar duka,saida wasu suka qaru,Allah yasa akwai maqocinsu malam sule,wanda yana zuwa ya hankade munzalin "Ashe baka da hankali munzali?" Malam sule ya fada cikin fushi,yayin da munxali ke haki yana kallon kaltum dake duqe a wajen tana rusa kuka,jikinta na kakkarwa. "Shin wai mema tayi maka kake mata irin wannan dukan kamar Allah ya aikoka?" "Ni zata nunawa iskanci da bariki?,ka barni na qara mata" "Idan ka kuma kai hannunka a kanta sai ranka ya baci kaji na gaya maka" cewar malam sule yana nunashi da yatsa. Dai dai nan bilal ya qaraso wajen,saboda labarin abinda ya faru da aka kai masa can inda suke kankarar rake,tutture mutane ya shiga yi har ya isa inda kaltum ke duqe "Yaaya"ya fada yana dagota,saiya miqa hannu ya fara da dai daita mata hijabinta sannan ya kamata suka miqe tsaye. Idanunsa cike fal da fushi ya dubi munzali "Indai ka zalunceta Allah ya saka mata" maganar data sanya munzalin nufoshi cikin fusata,saidai tuni aka riqeshi aka hanashi tabashi,sanda yake riqe da kaltum dake takawa da qyar yace dashi "Ni zaka yiwa rashin kunya?,zaka gane kuskurenka kaima" shidai bilalu baiko waiwayo ba bare ya saurareshi,hankalinsa naga 'yar uwarsa dake takawa sannu sannu da qyar,hawayen ciwo da baqinciki na sauka kan fuskarta. 22 Wucewarsu bai sanya taron jama'ar da suka taru a wajen barin wajen ba,ciki kuwa harda wasila da labarin dukan yakai mata,ta kuma garzaya don ta ganewa idanuwanta,kowa gulma tana cinsa,yana son yaji ainihin abinda ya faru don su samu abun qadarwa,sai qananun maganganu sa qus qus ke tashi a tsakaninsu,gashi munzali ya wuce fuuu cikin fushi bare su nemi jin qarin bayani daga bakinsa. Dai dai qofar shiga da fita daga gidan suka samu ummanmu a tsaye,ga duk mai hankali duba daya zai mata ya karanci tashin hankali saman fuskarta idanuwa harma da zuciyarta,macace mai tsananin biyayya wa aurenta,bata nemi izini ba,wannan ne babban dalilinta daya sanya ta kasa fita ceton diyarta,duk da yadda takejin gunjin kukanta cikin matuqar neman taimako,inna laure da zata mata kara kuwa birki taci ta koma ta zauna tana 'yan maganganu ciki ciki,wanda ta tabbatar idan ta saurara da kyau,bana kome bane saina jin dadin irin jibgar da munzali yakewa kaltum din,ko a yanzun ma shewa take qasa qasa me cike da nishadi,saidai lauren ba itace a gaban ummanmu ba,hannun diyarta ta kamo ta taimaka mata zuwa cikin sashensu. A hankali ta zaunar da ita,saita wuce kawa kanta tsaye zuwa rumfar da suka maida madafi tahau qoqarin kunna wuta,wannan yasa bilalu yabar abinda yake yazo ya karbi umman tasu,ya fara hada wutar da kanshi,qwalla na cika masa idanu,yau zaiwa yaya abinda itace kusan ba'a rufa sati sai tayi masa,bazai yafewa ya munzalin abinda ya yiwa yayar tasa ba,saboda baiga girman laifin data aikata wanda ya cancanci ayi mata wannan hukuncin ba,koda sata tayi bare ma ba ita tayi ba. Umman bata iya dawowa ta zauna ba,sai taci gaba da tsaiwa a bayan bilal,ta rungume hannayenta a qirji,duk sanda tayi irin wannan tsaiwar ba shakka ranta a bace yake,koda ba zata furta kota nuna ba,har ruwa ya tafasa tana tsayen,ta juye a babban baho ta surka shi da zafinsa,tasa bilal ya kaimata gaban kaltum da har yanzu kuke take,jikinta ko ina yana mata ciwo,bilal tasa ya fita ya basu guri,sannan ta sanya kaltum din ta fitar da kayan jikinta tayi daurin qirji. Sai data gasa mata duk inda tasan zai zame mata miki ko yayi mata zafi,kuka kam ta yishi matuqa kafin a gama gashin,sannan tasa tayi wanka da sauran. Kafin tafito bilalu ya siyo mata man zafi kaman yadda yaga tana mulka masa,ummansu ta ajjiye mata abinci,tasa ta shafe dukka jikinta dashi sannan ta zauna ta sanyata a gaba taci abincin. Duk wannan abun da ake batace da ita komai ba sai data gama cin abincin,muryarta cike da wani nauyi dake nuna ya taso ne tun daga qasan zuciyarta take tambayarta "Me kika yiwa munxali,kaltume ban haneki shiga sabgarsa shida matarsa ba tun randa yaxo nemanki afujajan?" Kuka ne ya qwacewa kaltum din,cikin muryar kuka ta amsa mata "Wallahi ummanmu tun ranar ban qara ba,ban qara bi kota hanyar gidansa ba" Kwashe yadda abun ya faru tayi ta gaya mata,shuru umman tayi,ranta yana suya,tanajin kamar haqurinta yana gab da gazawa,da wanne zataji?,duka tako ina wanne zata kare?,wanne hannuwanta zasu iya dauka,ida amadu yayi masu mijinta ne,mahaifinsu ne,idan inna tayi musu mahaifiyarta ce....jikokinta ne,to amma munzali fa?,saboda kawai yana a matsayin yayansu saiya kamata cikin bainar jama'a saboda tozarci da wulaqanci yayi mata irin wannan dukan?,kamar wanda ya kamata tana zina ko sata?. Lokaci mai tsaho tana tausar kanta kafin ta samu zuciyarta ta fara sanyi,saidai bata gama direwa ba sababi masifa da tashin hankalin babansu ya biyo baya. Ko sallama bai samu zarafin yi musu ba sai qwala kiran sunan kaltume!....kaltume!!!!.. Tana daga zaune ta amsa masa don ba zata iya miqewa cikin hanzari ba,kafin wasu sakanni ya bayyana cikin gidan "Ni na banu na lalace,wannan wacce irin diyar jaraba Allah ya jarabceni da ita?,don ubanki munzali sa'an wasanki ne?,ba sbine madadina ba randa bani?,kin dauki baqar hudubar uwarki kin fara muna musu 'yan ubanci ko?,wallahi wallahi kaltume ki fita daga idanuna,kiyi qoqarin da hannuna bazai kai jikinki ba,kinsan Allah?,duk sanda kika bari hannuna yakai jikinki saina qarar miki da numfashi". Sosai furucin ya sauka zuciyar ummanmu,a wannan karon ta gaza shuru "Malam....ka daina fadar haka,idan ka fada da bakin mala'iku fa?" "Da zan fada da bakin nasu ai da nafi kowa murna,me za'ayi da yarinya irinta?,to na soma gajiya,kuma wallahi aka kaini bango ran kowa saiya baci a gidan nan,kowa bazaiji da dadi ba,kin taramin jama'a qofar gida saboda dai ni a tozartani?,kamar ni kadai ne me 'ya'ya a duk garin nan?,to idan xaku shiga hankalinku ku shiga,in ba haka ba zanbi takan kowa a cikinku,ai ba gagarata kukayi ba" daga haka yayi gaba kamar zaiyi ball da qafar umma dake miqe. Shuru ne ya ratsa wajen na wasu sakanni 'yan kadan,kafin kaltum takasa jure abinda take ji ta saki kuka me sauti,sai umman ta kasa hanata,ta miqe tayi daki,tabar bilalu da rarrashi. ********Washegari wani abun mamaki sai 'yan dubiya suka dinga shigowa gida nasu,wannan na fita wannan na shiga,kowa ya shigo abinda zaice shine "Allah ya kiyaye gaba,ya sawwaqe". Da amin umma ke amsawa,tun tana irga wadanda suka shigo har ta daina,saidai tana jiyo inna laure daga can babbar farfajiyar gidan tana 'yan waqe waqenta cikin madaukakin sauti,da alama ma abun shinfida ta zauna kamar me karbar gaisuwa,duk kuma wanda ya fita daga wajen ummanmu sai yaja birki wajen inna laure,mafi qaranci mutum ya kwashe minti talatin kafin suji fitarsa yana yiwa inna laure sallama,ranar haka suka wuni har dare,abun ya yita basu mamaki,saida cikinsu babu wanda yayi maganar da dan uwansa. *********A wata washegarin misalin qarfe shida na safe tana kwance kan shimfidarta tana jiyo motsin umma a tsakar gidan nasu,duk kuwa da yadda iska ke kadawa. Lokaci lokaci takanyi juyi a hankali saboda yadda har a sannan wasu sassa na jikinta ke ciwo,musamman qugunta daya bugu,a duniya ya washi ta tashi cikin lalurar da zata hanata taimakawa ummanta,kota kama mata wasu ayyuka,a rayuwarta tana bala'in tausayin uammansu,tunda ta taso ta sameta ne cikin haquri da rayuwa,haquri da halin duniya,haquri da mutanen da take mu'amala dasu,mutanen da take jin dadinsu dai dai kune,wata irin bahaguwar rayuwa mara dadi,wadda babu wata walwala ko nishadi a cikinta ko kadan. Sama sama take jiyo sallama daga tsakar gidan nasu,tana jin ummansu dake duqe can bakin magangara tana wanke kwanukan abinci tana amsa gaisuwar da akeyi mata,saidai kaltum din bata dauki muryar ko wacece ba,sai taja tsaki,ta gayara kwanciyarta,tana fatan ba 'yan dubiya bane. Ita ko daya dubiyar da aka dinga zuwa din nafa burgeta ba,saboda magi akasarin mutanen da suka shigo din babu wani abu dake hadasu da ita,wasu ko gaisuwa bata shiga tsakaninsu,wasunsu ma bata gama wayewa da fuskarsu ba,saboda tun asali ita din bame shige shige bace,koda yaushe tana maqale jikin ummanta,tana da ƙawa zuci da kuma ƙulafucin uwa,kuma kusan duka haka yaran umman tasu take,saboda itadin macace mai tausasawa ga yaranta,ta iya bi da damuwar kowannensu. Tsaiwa taji anyi daga bakin qofar dakin ana cire takalmi kafin daha bisani ayi sallama a shigo ciki,sai a sannan ta daga kanta tana duban me shigowar,lantana ce,mamaki yadan kama kaltum,saboda lantanar bata tana shigowa gidansu a irin wannan lokaci ba,dole ta miqe daga lullubar da tayi da wani tsohon xaninta data maida abun rufa tana amsa sallamar lantana. Gefan kaltum din ta qaraso,tana zama tana furta kalmar "Sannu kattume" dan murmusawa tayi cikin qarfin hali,saboda sam batajin murmushin a zuciyarta "Yauwa lantana" "Yaya jikin naki?" Lantana ta tambayeta "Alhamdulillahi,da sauqi" "To Allah ya rufa asiri" "Amin lantana,na gode" kaltum ta amsa mata. Shuru ne ya biyo baya,cikinsu babu wanda yace wani abu,daga bisani lantanar ta sauke ajiyar zuciya "Waime ya hadaki da munzali yayi miki irin wannan dukan kaltume?" Lantana ta fada fuskarta qunshe da alhini da damuwa. Ajiyar zuciya kaltum ta saki,tana jin zafin irin yadda ya munzalin yayi mata bainar jama'a,inda cikin gidansu ne gaban mahaifiyarta ya daketa irin hakan da da sauqi,bata boyewa lantana komai ba ta labarta mata,sai taga lantanar tayi qasa da kai bayan ya dafe kuncinta da hannu daya. Zuciyar kaltum cike da tamabaya take dubanta,bakinta ya gaza shuru "Lafiya lantana?" A hankali ta dago ta dubi kaltum "Don Allah wai me kika yiwa wasila ne a rayuwa me zafi haka data zabi ta saka miki ta wannan hanyar?" Kasa gane kan maganar tayi,saita zabi taci gaba da kallon lantana ko zatayi mata bayani,ganin hakan ya sanya ta gyara zamanta,ta dora dukka idanunta da hakalinta kan kaltum "A iya sanina a abinda ya faru....na riga wasila zuwa wajen ma,saidai babu yadda zanyi na qwaceki daga hannun munzali,saboda idanunsa sun rufe,kuma wadanda suka fini shekaru ma sunyi sunyi ya bari yaqi.....amma kuma bayan komai ya lafa muna shirin barin wajen......kawai sai wasila ta fara wasu maganganu da suka jawo hankalin mutane kanta,wai ai dama ta gaya miki,ki daina duka abubuwan da kike,saboda ta sani cewa idan wasu sunyi sunci riba,ke din duka zakici hannun 'yan gidanku,yanzu wa gari ya waya?' "kowa dai bai gane abinda take magana a kansa ba,don haka wasu suka takura da tambayarta meke faruwa?,ta fara cewa ita ba za'aji mutuwar sarki a bakinta ba,wasu suka tafi,wasu suka matsantsa saboda sunsan baki da makusanciyar qawa irinta,budar bakin wasila......" Sai kalaman lantana suka tsaya a wajen,tana jin nauyin qarasa gayawa kaltumen abinda ya faru,tana jin nauyi,don ita kanta ba qaramin razana tayi ba dajin labarin da wasilar ta qirqiro cikin qaramin lokaci ba,don har ga Alla sam bata yarda ba,hankalinta bai dauka cewa hakan zata faru ba "Me tace lantana?" Kaltum ta tambayeta a sanyaye,haka nan tun kafin taji komai taji gabanta yana faduwa. Daga ido lantana tayi ta dubi kaltum "Kiyi haquri,ya zama dole ne na gaya miki,tun jiya naso zuwa,amma naga gidan nan ya cika da 'yan gulma,masu zuwa dubiyar qarya......wai cewa tayi cikin shege kikayi,labari yakai kunnen ya munzali,ita kika fara gayawa tace ba ruwanta....babban abun baqincikin shine,duk wanda yazo dubiyar ya biya ta wajen inna laure don tabbatar da gaskiyar lamarin saita bashi tabbaci,ta kuma dora da nata bayanin qanzon kuregen". Wani irin abu taji yana yamutsawa saman kanta,wani sanyi ya saukar mata tun daga saman kanta har qafafunta,tana daga zaune amma ji take kamar ana dawafi da ita,saita lumshe idanuwanta tana kiran ya Allahu,ya Allahu,tausayinta ya kama lantana,cikin salo na rarrashi tace "Kada ki damu katume da abinda kikasan baki aikata ba,baki isa ki iyawa mutum ko ki burgeshi ba" sannu a hankali ta bude idanuwanta tana duban lantana "Tabbas haka yake,na gode lantana da qaunar da kike min saboda Allah,su kuma.....amma babu komai,akwai Allah.....ya ubangiji kana kallo.....Allah kaine shaida" daga haka bata sake cewa komai ba. Cikin hikima lantana take bata baki har na wasu lokuta kafin tayi mata sallama,bayan ta bata shawarar duk wanda yazo dubiya kada ta sake fita,su qaraci gulmarsu su koma. Ita kadai cikin dakin,tana jinta kamar wadda aka haqa rami aka zurata iya wuya,labarin da lantana tazo mata dashi ke yawo a kanta,sai data fada din sannan ta tuna irin yadda duk wanda ya shigo yake mata wani kallo da bata fahimci dalilin yinsa ba sai yanzu,qwalla ce ta silalo mata duk da yadda take qoqarin riqeta,ta kuma sanya hannunta da sauri tana ta qoqarin shareta sanda taji ummansu na shigowa dakin tana tambayarta bata tashi bane? "Na tashi ummanmu" dai dai sanda ya daga labulen,dan tsaiwa tayi na sakanni tana kallonta,sai kuma tace "Ki tashi ki saka ruwan zafi a jikinki,kizo ki sanyawa cikinki wani abun" "To ummanmu" ta amsa tana qas da kanta tare da yunqurin miqewa. Rana batayi nisa ba 'yan dubiya suka fara shigowa,a hankali cikin hikima da nutsuwa take karantar duk matar data shigo,saita fara tabbatara da zancan lantana,duk da cewa tayi yunqurin yin zamanta cikin daki taqi fitowa koda anzo,sai kuma wata zuciyar ta gaya mata,yin hakan tamkar tana tabbatar da zargin dake cikin zukatan mutanen,don idan wani ya fahimta.....wani cewa zaiyi da gaske cikin shegen tayi take buya bata son a ganta. Yadda jama'a ke kallonta yayi bala'in kadata,bata taba tsammanin akwai wani qunci a duniya sama da wanda suka ciki ba sai a wannan karon,dama aminta da qawance yana juyewa ya zama sharri mai girma da nauyi haka?,dama qauna da soyayya tana jirkita ta koma mummunar sakayya irin wannan?,babu wata daqiqa da zata kubce mata ba tare da abun yana mata yawo cikin qwaqwalwarta ba,wai wasilanta?,wasilan da suke kuka tare suyi dariya tare,wasilan da take gayawa sirrinta,wasilan da suke shawara tare,su kashe su kuma bunne tare,to wai shin meta aikata mata data cancanci sakayya mafi muni irin wanna?,tambayar data dinga yiwa kanta da kanta kenan,saidai ta gaza gano amsar tambayar tata. Sati gida cur tayi tana jinyar jikinta kafin ta warware,a tsahon satin bata ga koda gilmawar mai kama da wasila cikin gidan ba bare ita,sai tarin qawayenta da kullum ke kaw mata zancan abinda wasila keta yamadidi dashi. Dakatar dasu tayi,ta kuma shaida musu batason ji,saboda jin bashi da wani amfani,hakanan babu wani magani da zaiyi mata,face baqin wasila da zata dinga gani. Randa ta cika satin misalin sha daya na rana,tana tsakar gida tana tsince musu busashshen zogale da suke shirin yin miyar zogale ayau din,cikin shinkafar da yakumbo indo ta ajjiyr musu,har zuwa yau kuma suke amfanarta. Alamun sauti kamar na kuka datake jiyowa kamar daga nesa kadan da inda take yasa tayi sak,ta kuma dakata da abinda takeyi,tana jiran taji daga ina kukan ke tahowa. A hankali taji alamun sashensu yake yowa,kuma kamar muryar habibanta,abunda yasa babu shiri ta dangware farantin dake kan cinyarta ta miqe tsaye,gabanta da wani irin mugun faduwa,ta zubawa qofar shigowa sashen nasu idanu,tana jira tagani shin ita dince?,idan itace da wacce tazo?,me kuma ya faru,bugun zuciyarta na daduwa har batasan ummansu ta fito tana tsaye daga bayanta ba itama tana jiran shigowar habiba,dukkaninsu kowa ya kasa motsawa daga inda yake tsaye bare yaje ya tarota. D/Z 23 *_Littafin kudi ne,ki guji shiga haqqin wasu ta hanyar yadawa,ki tuntubi wadan nan numbers din don biyan naki ki karanta cikin aminci_* 08184017082 Ko kuma 09134848107 Ba'a dauki wani dogon lokaci ba habiba ta bayyana a tsakar gidan,zani daban riga daban,idanuwanta sunyi jazur dasu,da alama kuka tasha take kuma kanyi har yanzu. Sai a sannan kaltum ta samu qarfin halin tunkarar habiban,hankalinta a matuqar tashe duba da yanayin data shigo dashi,riqeta kaltum tayi tana jaddada tambayar "Lafiya?,habi lafiya?". Bata iya magana ba sai da suka isa gaban umma da tayi mutuwar tsaye,cikin qarfin hali itama ta sake tambayarta "Umma.....anacan ana yamadidi da yaaya a gari wai tayi cikin shege,dalilin kenan daya sanya wai ya munzali yayi mata dukan tsiya". "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda ummanmu ta ambata,a tunaninta cikin zuciyarta tayi,saidai tsabar rudanin data samu kanta a ciki baisa ta fahimci a fili tayi ba har sai da sautin ya fito,saita nema jikin katangar dakinta ta jingina tana kamo hannun habiba gami da zaunar da ita cike da qarfin hali,wanda kaltume ma da taji tana niyyar faduwa saita sulale ta zauna kusa da 'yar uwarta. Duk wani yawun bakin umma ya bushe,ta qaqalo wani da qyar sannan ta samu damar yiwa habiba bayanun yadda komai ya faru "Na sani ummanmu,yaaya ce fa,ni nasan ba zata taba aikata wani abu mara kyau ba,bansan iblishin da yaketa yada zancan ba,har gida aka sameni tun shekaran jiya ake gayamin,baaba ce take korarsu fata fata,tace batason gulma su tashi su bamu waje,to umma daga shekaran jiya zuwa yau karo na hudu kenan ana zuwarmin da zancan,wannan wanne irin bata suna ne umma?,me muka yiwa mutane?" Sai kuka ya sake kubce mata,wanda a wannan karon ita kanta umman bata data cewa,ta rasa dukka kalama bakinta. A daidai lokacin inna laure tayi sallama a tsakar gidan nasu cikin nuna hali na gigita,shigowarta yasa habiba saurin boye kuka ta tare da goge fuskarta,don ta sani ba alkhairi bane ya shigo da ita ba. Diri diri ta fara yi,kafin daga bisani tace "Zuwaira lafiya habiba ta shigo tana kuka?,ko daga gidan aurenta ne?" Idanu umma kawai ta zuba mata tana dubanta,tana kallon zallar rashin alkhairi daga laure,wadda a kullum bata fatan musu alkhairi sai sharri "Ba komai sai alkhairi" shine amsar da umman kawai ta bata,saita juya tana cewa "Au too.....to Allah yasa,koda yake idanma ba'a gaya mana ba idan tayi tsami zamuji,kamar yadda mukaji na dayar muna daga zaune" Wani mugun kallo kaltum ta bita dashi,duk da cewa a yanzun takanta take da mummunan baqin sharrin da aka laqaba mata,tabbas da zata samu dama da saita maidawa inna lauren martani dai dai da maganarta. "Saurareni habiba da kyau......" Umma ta fada tana yunqurin baiwa kata qearin gwiwa,saboda ta hangi rauni a idanun dukkaninsu,kuma ta tabbatar cewa qwarin gwiwar da zasu gani a idanunta itace zata motsa tasu jarumtar "Kowanne bawa da kalar qaddararsa,wani tasa tafi wanna muni,dukkaninmu mun sani hatta da annabawan Allah an jarrabesu,halitta mafi soyuwa ga wanda akayi duniya da lahira saboda shi annabi Muhammadu wato nana aisha an jefeta da qazafin zina,ko kin manta?,kina tunanin indai hakane akwai wanda zai tsallake?" Kai ta girgixa a hankali,daga ita har kaltum din suna jin nutsuwa ta fara saukar musu,hakan ya bata qwarin gwiwa naci gaba da maganar da takeyi,duk da ita kadai tasan abinda takeji a zuciyarta. "Duk wanda ya jefeku da sharri ko qazafi,ku barwa Allah komai,shi baya zalunci,kuma baya yarda a zalunci bawa,da sannu zai fitarwa da dukkan me haqqi haqqinsa komai daren dadewa" cikin hikimar iya zance,da qwarewa irin ta uwa ta gari ta sauke rudu da dimuwar da suka shiga,sannan daga qarshe ya dubi habiba "Yanzu yusufa yasan kin fito?" Kai ta jinjina "Ya sani ummanmu,shine ma ya rakoni,baaba tace ya rakoni saboda jikina babu dadi" sam sun mance da batun ma lalurarta saboda wannan yanayin da suka shiga "Alla ya sawwaqe,saiki tashi ki koma gida ai ko?"narkewa habiban tayi "Ummanmu ya barni fa,yace na zauna har dare,zaizo ya daukeni". Zaman nata ya yiwa kaltum dadi sosai,ya debe mata kewa fiye da kima,tayi rashin 'yar uwa a kusa,wanda bata sake gasgata hakan ba sai yau da suka wuni tare cur da habiban,tsoro da fargaba dake ranta kaso mafi yawa ya ragu a ranta. A nan babansu ya dawo ya taddata,ya fara zabga sababi kenan kan ta tashi ta tafi gidanta,shi ba mahaukaci bane da zatazo ta zaune masa.....saiga yusufa dan halak,harda tsabar kayan marmarinsa,lemo,kan kana da ayaba harda biredi. Ita dai umma ta sani cewa,ubangiji kawai ya dubi irin rayuwar dasu habiba ke ciki ya bata miji na kerewa sa'a,hakanan itama ya dubeta,ya duba darajar addu'ar da take musu ya hadata da surukai na gari,fatanta ubangiji yasa 'yar uwarta kaltum ta dace kamar yadda itama ta dace din. Suna kewar habiban itama tana kewarsu yusufa ya tasa kayarshi a gaba suka tafi gida,saidai ba wata damuwa bace mai yawa a ransu,saboda sunsan tana samun kulawar da bata taba samun irinta ba cikin gidan mahaifanta. *******WASHEGARI******** Ƙarfe goma na safiya tana duqe tana sake sharen wajen da bilalu ya gama dabdalarsa bayan sun gama karin safe,tana yi tana mitar sai tayi maganin bilal din,yayin da shi kuma yake shirin fita aiki abinsa yana dariya "Haba yaaya kattume ta wajena,kasa kisa a ganmu a rana mana ayi mana dariya" umma dake kwance cikin daki saboda zugin da qafarta takeyi mata ta tabe baki,saman fuskarta kwance da murmushi,dramer din kaltum da bilal sai su din,ka gansu nan ka qyale kayi wucewarka abinka. Kayan ummansu da babansu data jiqa ta nufa ta soma daurayewa,tun bayan ciwon da tayi sai yau zata fita,zata zagaya bayan katangarsu ta yiwa wata amarya da aka kawo daga qauyen kusa dasu kitso,shi yasa take aikin da hanzari hanzari,tayi ya gama taje,don tun jiya ta aiko amma bata samu zuwa ba. Sallamar da aka rangada ce ta sata waiwayawa bayanta inda qofa take,duk da bata dago daga abinda take ba,ta amsa tana ci gaba da wankin,saidai yadda aketa koda sallamar a jejjere yasa ta saki zanin ummansu dake hannunta,ta miqe sosai tana amsa sallamar,zuwa sannan har sun iso filin tsakar gidan dake sashen nasu. Mata ne su su uku,kowacce sanyi da hijabi,suna rarraba idanu gami da kallon kowanne lungu da saqo na gidan,hakan ya sanya kaltum sake amsa sallamar,ga zatonta ko basuji ba,ko kuma basu gan bilal ba,idanma haka ne gata ita dake tsaye tana kallonsu. Sake amsa sallamar saiya zamana kamar kiran jan hankali kuwa a garesu,gaba daya suka waiwayo suna kallonta. Idanunta suka haska mata fuskar daya daga cikin matan,kamar ta santa,kamar lantai babar nasuru,duk da cewa sai daya tabtaba ganinta,amma bata da saurin mance abu,tabbas ita dince,sai kunya da nauyi suka kamata,da sauri ta jawo hijabinta dake ka igiyar dake daura dasu ta zura tana fadin "Baaba sannunku da zuwa" kafin a hankali ta nufi gabanta,ta durqusa a saman gwiwarta tana gaidasu,yayin da bilal dake gefe shima yake tayata gaisuwar. Babu wanda suka amsa gaisuwarsa a cikinsu,sai daya daga cikinsu ce ma ta taushe gaisuwar da tambayar "Babanki yana nan?" Kai ta girgiza cikin mamakin lafiya? "Bai jima da fita ba" "Babarki fa" "Tana daki,tada kwanta ne batajin dadi" "Ba wannan muka tambayeki ba,kira mana ita maza maza,sauri mukeyi" mamaki sosai ya sake kamata,amma duk da haka bata fasa qarasawa ta dauko musu tabarmar kaba ta shimfida musu ba,dai dai lokacin da taji daya daga cikinsu na cewa "Lanti itace?" "Eyi.....itace". A kwancen ta tadda ummansun,bacci ya fara daukarta,motsin shigowarta ya farkar da ita "Yaya akayi?,bilalun ya tafi?" Kai ta kada,rabin hankalinta yana ga tsakar gida "Baqi kikayi" "Baqi.....ganinan" ta fada taba miqewa zaune,saita daura dankwalinta ta rufe gashinta da har yanzu yake da santsi sannan ta miqe cikin qarfin hali tabi bayan kaltum wadda bayan ta shaida musu gata nan,saita kasa zama tsakar gidan ta wuce dakinsu,su kuma suka rakata da kallo,kasa zama tayi,ta rakube bakin windownsu,tana jin gaba daya qafafunta sunyi sanyi da laushi,kamar ba zasu iya daukarta ba. "Sannunku da zuwa,ya kuke tsaye ga shimfida anyi,ku zauna mana" cewar umma cikin fara'a da faram faram "Ba zama mukazo yi ba,duk gidajenmu akwai wajen zama,hasalima saqon daga tsaye sai yafi tafiya" dan dumm umma tayi mamaki yana daureta,har ta gaza daurewa tace "Tooo,ikon Allah" "Ikon gaske......" Suka maida mata,sannan daya daga cikin ta matso gaba,ta yadda ta fita daga jerin matan "Gwara na matso sosai yadda zakifi ganeni.....sunana lanti,nice nan na haifi nasuru da kaina,ba doguwar magana ko jan zance ya kawo mu ba,don haka baro baro za'a yita.....mun samu labarin cikin shegan da 'yarku tayi,sahihin labari kuma daga majiya mai tushe,wato daga bakin mafiya kusanci da ita har mutum biyu,saboda haka mukazo mu shaida muku cewa.....mun yanke igiyar alaqar auratayya da akazo aka tambayawa dana,babu shi babu 'yarku,kudin aure da muka kawo kuma nan da anjima manyansa zasu zo su karba a mayar masa da abinsa....." Duk da rudanin da umma ta shiga,amma tayi namijin qoqarin dannewa "Shikenan saqon naki?,inason komawa daki?" "Eh shine saqona,ni dama can bason abun nake ba,wannan baqar yarinyar me kama......" Hannu umma ta daga mata,don ba zata lamunci cin fuska ba kuma,ga mari ga tsinka jaka? "Ya isa,tunda dai kin isar da saqonki kuje,Allah ya bamu alkhairinsa" borin kunya lanti ta soma ita da 'yan rakiyarta,suka hau qananun maganganu,saboda basu zaci zuwan abun haka ba,suna qananun haibaice habaice da yarda maganganu suka fita a sashen,umma ta bisu da idanu. Bisa mamakinta sai tajiyo muryar inna laure tana musu su gaida gida "Mukusantanta mutum biyu" maganar ta dawo kan umma,su waye suka bada shaidar zurr kan abinda basuji ba basu gani ba?,basu da tabbaci?,mutum biyu makusantanta su waye kenan?,tambayar data yi mata nauyi aka,saita juya kamar kazar da qwai ya fashe mata a ciki ta nufi dakinsu kaltum inda take jiyo sautin kukanta. Labule ta daga,tana tsaye daga vakin qofar dakin ta kalleta "Kul.....kada na sake jin kukanki a kan namiji,Allahn daya baki nasuru shi zai sake baki wanda ya fishi da izinin ubangiji" da wannan ummanmu ta saki labulen ta wuce zuwa nata dakin,tana ta qoqarin tausar kanta da kanta,wannan babban abune da muninsa baici ta gayawa kowa shi ba,irin damuwar daya kamata isu isu su hadiyeta ne,ko kuma su tona rami su binneta. Nan inda take ta sulale ta qoqarin tilastawa kanta ta hana kanta kuka kamar yadda ummanmu ta buqata,wani abu ya riqe mata wuya kamar zai tafi da numfashinta,da sauri da sauri tayi saurin kama "Ya hayyu ya qayyumu,ya zuljalalu wal ikram" ta dinga maimaitawa a fili,saidai can qasa ta yadda idan ba'a kusa kake ba babu kallai ka iya jiyota. Tsahon lokaci gidan ya dauki shuru,saika dauka babu umma bare kaltume a ciki,kowa yana kwance yana jinyar zuciyarsa,yayin da suka dinga jiyo karakainar inna laure da 'yan waqoqinta,tanata shige da fice daga qofar sashen zuwa nata sashen,wanda hakan duka baya wuce taji ya suke ciki ne,bayin Allahn kowanne na kwance yana tufka da warwara,salla ce kawai ta azahar ta tadasu,a haka la'asar ta riskesu. La'asar din data zo musu da wani babban tashin hankalin na daban,bayan kaltum ta idar da sallar la'asar,tana zaune saman abun sallarta tana karanta sunayen Allah. Kamar daga sama sukaji muryar mahaifinsu,babu sallama a bakinsa,sai faman qwalawa ummansu kira da yakeyi kamar tshon makahin da ya warke daga makanta,kira ne da kana jinsa zai kada hanjin cikinka,musamman idan kasan halayyarsa. Kaltum dake zaue batasan sanda ta miqe tsaye ta dafe qirjinta ba,tun kafin taji abinda mahaifin nata zai furta ta tabbatar tashin hankali ne ya samesu,idan ka ganta a sannan sai kayi tsammani ana cewa kyat zata zura aguje. Ko addu'ar da takeyi din bata samu damar kaiwa qarshe ba ta yanke tana ambatar "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" sannan ta fito daga dakin. Yana tsaye tsakiyar tsakar gidan,tamkar xaici babu,fushi da masifa sun bayyana muraran akan fuskarsa da kuma duk wani motsi nasa,zirga zirga yake yakai gauro yakai mari amma masifa ta hanashi shiga daki ya cimmata har sai data fito ta kawo kanta "Ina kattume?" Ya jefawa umman tambayar "Tana dakinsu" ta amsa tana kafeshi da idanu,gabantana faduwa,saboda batasan da wacce yazo ba "Ba shakka zuwaira....yadda auren kattume yayi rawa,har iyayen yaron nan sukazo suka amshi kudinsu haka naki auren yake rawa......ke zan baiwa wannan saqon,duk da na tabbatar tana jina.....iyayen nasuru sun zo har wajen sana'ata sun karbi kudin aurensu....to inason ki gayawa 'yarki.....ki gaya mata da babbar murya,ki jaddada mata cewa.....sanda tayi abun kunyarta ni ban sani ba,hakanan batayi shawara dani ba,to ki gaya mata,na bata wata daya kacal.....wata daya kacal ta fitar da mijin aure,ta kuma kawomin shi,idan kuma ba haka ba,billahillazi la'ilaha illa huwa saina bada ita sadaka ga duk meso,ga duk wanda Allah yayi rabonsa ya tsaga" daga haka ya juya fuuuu cike da fushi,iska tana cika babbar rigarsa tana qara kumbura surarsa ya fice waje abinsa. A hankali umma ta dafa katangar dake kusa da ita,sannan ta koma ta zauna a hankali tana furta "La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim" ta furta a hankali,tana son hana kanta kukan da taji yana son qwace mata,zuciyarta na kwabarta,idan ita tayi kuka ita kuma kaltum tace meye?,sai tayi fakare ko zataji sautin kukan kaltum din kamar yadda taso yi a daxun ta hanata,saidai shuruuuu....abinda ya dauki hankalinta kenan,ta miqe a hankali ta nufi dakin. Koda ta yaye labulen wayam dakin babu kowa,sakin labulen tayi zulumi yana cikata,ina tayi?,tasan dai kafin shigowar mahaifin nasu tana dakin,kuma baya ya fita ita din tana zaune a nan,amma bataga fitarta ba. Qwararawa kanta gwiwa tayi ta soma lalubenta daga bandaki zuwa qarama da babbar tsakar gidan gidan,saidai babu ita babu dalilinta,don haka ta koma ta zauna a hankali tana kiran sunan Allah,tare da addu'an ba wani abun na daban ke shirin faruwa ba bayaga wannan wanda suke ciki a yanzu....... ZAFAFA KARO NA FARKO SUNAYEN SU: 1_GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDULL 2_KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO 3_BURI DAYA NA MAMUH GEE 4_DAURIN BOYE NA SAFIYYAH HUGUMA 5_SAUYIN KADDARA NA HAFSAT RANO DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500 SAI ZAFAFA TAKU NA BIYU 1-DAURIN GORO NA HAFSAT RANO 2-ALKAWARIN ALLAH NA SAFIYYAH HUGUMA 3_QAUNAR MU NA MAMH GEE 4_IGIYAR ZATO NA MSS XOXO 5_WUTSIYAR RAKUMI NA BILLYN ABDULL. DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500. SAI ZAFAFA TAKU NA 3, 1_MIN QALB NA MAMUH GEE 2_SARAN BOYE NA BILLYN ABDULL 3_KIBIYAR AJALI. NA MISS XOXO 4_ABINDA KE CIKIN ZUCIYA NA HAFSAT RANO 5_SIRADIN RAYUWAR BILKISU NA SAFIYYAH HUGUMA DUKA DOCUMENTS DIN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500) SAI ZAFAFA TAKU NA HUDU. 1-ALKIBLA NA SAFIYYAH HUGUMA 2_DALAAL NA MISS XOXO 3_UBAYD MALEEK NA MAMUH GEE 4_MABUDIN ZUCIYA NA HAFSAT RANO 5_MAKAUNIYAR KADDARA NA BILLYN ABDULL DUKA LITTAFAN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500) SAI ZAFAFA KARO NA BIYAR DA AKE A HALIN YANZU, (ON GOING PAID NOVS) 1-SO DA ZUCIYA NA MSS XOXO 2-TAKUN SAAKA NA BILLYN ABDULL 3_HALIN GIRMA NA HAFSAT RANO 4_DAB'IZAR ZUCIYA NA SAFIYYAH HUGUMA 5-DEEN MALEEK NA MAMUH GEE DUKA BIYAR DIN NERA DUBU DAYA NE( 1K)IDAN AN KAMMALA SU KUMA 1500. YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN: ACCOUNT NAME: MUSAA ABDULLAHI SAFIYYAH.. BANK NAME: KEYSTONE BANK SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA: 08184017082 IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA: 09134848107 D/Z 24 *_MANZAN ALLAH S A W YACE: Duk wanda yaci abinci,bayan ya gama cin abincin yace:ALHAMDULILLAHIL LAZI AD'AMANI HAAZA,WA RA ZAQANEHI MIN GHAIRI HAULIN MINNI WALA QUWWA Allah zai gafarta masa abinda ya gabata na zunubinsa"_* _______________________________ *ZUWA GA MAKARANTA DABI'AR ZUCIYA❤‍🩹❤‍🩹* *_kuyi haquri,muci gaba da bin komai a hankali,kuci gaba da haquri da duk abinda zaku ga ya afku,kar muyi gaggawa,kowanne labari da irin salonsa,hakanan sau tari idan kace zakabi salon da masu karatu keso tabbas zaka shiga sahun marubutan dake tafka shirme da rubuta labarin da bashi da ma'ana sam,babu kuma manufa,labarin daya gaza isar da saqonshi,wanda su kansu masu karatun basa gane hakan sai an gama littafi😁😁,saboda a sanda suka qagu aje wani bigire suna tsaka da shauqi ne,basa gane idan an musu hakan ba dai dai bane sai bayan kammaluwar littafi,muna godiya a gareku da bakwa gajiya da kasancewa da ZAFAFABIYAR,Allah yayi mana jagoranci cikin dukka lamuranmu🤲🏽🤲🏽🤲🏽,muje zuwa_* Jefa qafarta kawai take ba tare da tana kallon gabanta ba,wani zafi qirjinta yake mata,kamar yadda taji idanuwanta na suya,saboda radadin hawayen dake taruwa cikinsu,wanda sukeson zubda kansu amma ta hanasu sauka. Tunda ta samu nasarar fitowa daga cikin gidansu saboda sanda mahaifinta ke zazzagar masifa,cikin tashin hankali,saboda batason kunnuwanta su sake ji.mata wasu kalaman na daban bayan wadanda taji,A hankali ta yiwa kanta hanya zuwa bakin rafi,cikin ikon Allah kuma bata hadu da kowa a hanya ba,bare ya tsareta da tambaya ko ya kawo mata cikas. Dab da ruwan ta zauna,yayin data rungume gwiwoyinta dukka a qirjinta,ta kuma zubawa ruwan idanu,babu abinda ke yawo a kanta sai kalaman mahaifinta,tana jin yadda suke yawo a saman kanta,kamar ana mata tsawa cikin kunnuwa. Wani rauni ne ya mamaye zuciyarta,wanda ya sanyata ballewa da kuka,kukan da ya taho da nauyi da kuma qarfinsa,saboda yawa da girman damuwar da take ciki,kuka take sosai,irin kuka daka rasa matallafi ko wanda zaka dora kanka a kafadarsa da zummar samun lallashi ko kuma qwarim gwiwa. A hankali yake tattaki a kewayen gurin,yana sake nazarin filin,tako ina filin yayi,kuma zai dace da gidan gona qwarai da gaske,yana buqatar wasu shawarwari daha wajen wani mutum babba mai hankali,kamar dai mahaifinsa,saidai shi yasan bashi da wannan gurbin ko kuma damar,saboda ya riga daya sani,abune mawuyaci mahaifin nasa ya fahimceshi,baisan meyasa ba kasafai yake fahimtar dumuwarsa ba?,baisan me yasa bai auna damuwarsa da ra'ayinsa da kuma abinda yakeso akan mizanin ababen da yake buqatar a kula shi domin su?,wani aikin sai uwa.......wani sashe na zuciyarsa ya gaya masa,maganar data sanyashi lumshe idanu yanajin wata faduwar gaba da wani suka a qirjinsa "La'ilaha illallah" ya furta a hankali,baikai kuma ga hade labbansa ba sautin kukan ya shiga kunnuwansa. Da sauri ya bude idanuwan nasa,sannan ya fara waige waige a nutse yana neman daga inda kukan ke fitowa. Taku ya soma yi zuwa gaba kadan ganin bai samu nasarar ganin mai kukan ba,sai sautin kukan dake ci gaba da tashi,takun nasa da bai haura goma ba ya hangeta. A durqushe take kamar me neman gafara,saidai kuma kuka take haiqan mai cike da nuna rauni da kuma gazawa. Idanu sosai ya zuba mata,yana iya hangenta tar daga inda yake tsayen,hannayensa soke a aljihun wandonsa "Kuka?" Ya fada cikin zuciyarsa kama me tambayar kansa da kansa,a ganin da ya mata tun karon farko,zarrar da yake ganin tana da ita,baiyi tsammanin ganinta cikin hali na kuka irin haka ba,saiya soma takawa a hankali yana nufarta. Saidai tun baiyi nisa ba yaja ya tsaya,gami da takawa kansa da kansa burki,sam ba halinshi bane,ba kuma dabi'arsa bace shiga shirgin daba nashi bane,yana ganin kuma bai kamata ace a yanzu ya fara ba,kan mutanen da yake hangen baqin dabi'u wanda jahilci rashin ilimi da rashin wayewa ya haifar musu da su. "Kattume.....kattume" kiran sunanta ya mamaye wajen,shi da ita dukka suka maida idanuwansu ga inda kiran ke fitowa. Lantana ce afujajan,tana tafe kamar zata tashi sama,sai kaltum din ta zuba mata idanu tana kallonta da dan sauran hawaye da suka fuskarta kwalliya. Gab da kaltum ta zube,fuskarta kamar zata fasa kuka tace "Wai me yake faruwa kaltume?,me yake faruwa a cikin gari?,yanxun nan wasila ta fito ita da qawayenta suna shewa.....wai an kawo kudin aurenta da nasuru gidansu yanzu yanzu.....har tana cewa da zafinsu suka iso,saboda fitowar kudin kenan daga gidanku?,me yake faruwa?,da gaske hakane?" Sai data lumshe idanunta tana jin yadda labarin ke barazanar danne fitar numfashinta,kafin tayi jarumtar baiwa kanta qwarim gwiwa,ta gyada ma lantana kai tana dubanta kai tsaye "An karbi kudin auren nasuru daga gidanmu lantana haka ne,amma bani da masaniyar an kaiwa wasila,tunda ba'a fi awa da karbar kudin ba". Tsaiwarsa sosai samir dake tsaye daga can baya inda ba lallai su iya hangoshi ba ya gyara,yana sake cusa hannayensa cikin aljihun wandonsa,idan bai manta ba.....kamar wanda take maganar a kana saboda shine taqi saurarar abokinsa haladu....to amma how comes aka amsa kudin?" Ya samu kansa yana yiwa kansa wannan tambayar,saiya sake tsaiwa yana sauraren amsar da lantana take bawa kaltum "Kai jama'a......haka wasila take?,wacce iriya annmimiya ce ita?,ta yada qarya da sharri gareki,ta rabaki da masoyinki,sannan kuma ita ta mallakeshi?.....". Lumshe idanu samir dake tsaye yayi,bayanan lantana da suka fito a jejjere ya daki zuciyarsa,qarya,ha'inci,cin amana,qazafi.....yara qananu da duka duka rayuwarsu a yanzun take tasawa,amma har su iya shirya irin wannan aiki?,banda ma rayuwa ce irin ta qauye,kafataninsu suna qarqashin kulawar karatu ne data iyaye,babu wadda a cikinsu yake ganin takai girma da zata dauki irin wadan nan abubuwan,saiya tuna qanwarsa kuma autarsu jawahir.....duk cikinsu babu sa'arta,amma har yanzu kallon qaramar yarinyar da bata gama mallakar hankalin kanta suke mata ba. Baiji sauran tattaunawar da suka biyo baya ba,sai jin magana yayi cikin daga murya da fushi. Matashin saurayine tsaye gaban kaltum din,tashin hankali sun bayyana qarara saman fuskarsa,yayin da kaltum ke fada cikin fushi "Baka da sauran abinda zaka gayamin nasuru,kaje kawai yayi biyayya wa iyayenka" "Don Allah ki saurareni kaltum,ki fahimceni mana,lantana ki ganar da ita,duk abubuwan da suka faru babu wanda nake da masaniya a ciki,wallahi Allah nima sai yanzu baaba take gayamin komai,koda naje gida nemanki umma tace batasan inda kikayi ba,itama nemanki take,bansan komai ba". Wani kallo ta watsa masa,muryarta na rawa tace mishi "Nasuru" saiya amsa da sauri,yana fatan jin kalaman fahimta da kuma goyon baya daga gareta "Kana tunanin inda nice ummanmu tayimin abinda baba tayi maka....zan bijire mata ne?,zan sake kallonka da sunan aure?" Saita girgiza kai "Har abada na haqura,iyaye su na dabanne.....ka koma kabi zabinsu". Babu wanda maganarta bata burge ta kuma dakeshi ba a wajen,hatta samir dake tsaye da basusan da tsaiwarsa ba dariya nason subuce masa,shikam salon soyayyarsu dariya take bashi,wani lokaci abun kamar wasan 'yar tsana,duk da cewa a wannan karon sai yaji yanayin da suke ciki ya dan tabashi,amma ta wani fannin idan ya kalla kaltum din,dukanta bata wuce ace rainonta ake ba,amma ake maganar soyayya da aure......saida kuma,maganarta da tayi a yanzun sosai ta tabashi,ta kuma sanyashi cikin wani yanayi daya jefa tunaninsa izuwa wani bigire mai nisan da baisan iya adadin lokacin da zaikai kafin ya kamoshi ba,ya tuna masa wani babban jigo na rayuwarsa,majinginarsa kuma wani gwaggwaban sashe dake da kaso mafi girma cikin rayuwarsa,sai jikinsa yayi sanyi shima kamar yadda jikin sauran yayi,su duka ukun hardashi dake a bayan fage,suka zuba mata idanu sanda take bin hanyar barin rafin zuwa gida. Batayi cikakken taku goma ba sukayi kacibus da bilal "Yaaya,ina kika shiga umma nata faman nemanki?" "Muje bilalu" ta furta da sauri tana yin gaba,saboda batason nasir ya cimmata,tana fatan yanke alaqa ta har abada tsakaninta dashi,tana son zuciya ruhi da gangar jikinta ta manta dashi,ya kuma bace bat daga cikin rayuwarta gaba daya,bacewa ta har abada. Daga inda yake tsaye yaga zuwan bilal da juyawarsu a tare,ci gaba yayi da kallonsu suna yiwa ganinsa nisa,bilal......ya ganeshi,a hard worker,yana mamakin qwazon yaron wajen aiki,baya fushi,baya gajiya,yakan hada aikinsa dana wasunsa duka yayi ba tare daya damu ko ganin ido ba,a tashi biyansu kuma a biyasu kai daya,kullum sh yake riga kowa zuwa,ya gama karantarsa....yana aikine da zuciya da kuma jikinsa gaba daya,babu alamun ha'inci ko gajiyawa cikin aikinsa,dalilin da yasa aka nemoshi bayan tafiyarsa da daina zuwansa aiki,dalili da yasa yaji cikin zuciyarsa yaron zai zama wani abu,yana da wasu nagartattun boyayyun halaye da yaji sha'awar sanyashi yayi karatu me zurfi,yakan dan dauki wasu mintuna lokaci bayan lokaci su danyi hira dashi,yana magana cikin nutsuwa da girmamawa. Cikin zuciyarsa yake jin tabbas akwai wata rayuwa,akwai wata rayuwa cikin rayuwarsu,akwai wani abu,duk da ba kasafai yake damuwa da abinda ba'a sanyashi ciki ba,bai daukar al'amuran da basu shafeshi ko ba'a nemi jin ta tashi ba,matuqar ba cikin nemon taimako ko halin hau'ula'i kake ba,to amma,shima mutum ne kamar kowa,wani lokaci akwai ƊABI'AR ZUCIYA,nason jin wani abu da son sanin ainihin abinda ke faruwa. Ajiyar zuciya ya sauke yana juyawa don barin wajen,zuciyarsa na qoqarin yakice masa wancan abun da yaji ya gani,tana tuna masa tarin nasa matsalolin,amma ba shakka,cikin maganganunta akwai abubuwa da yawa data fada,wanda suka tsame masa kamar wani tuntuntuni cikin rayuwarsa. ********kwanaki biyu kenan tana jin wani ciwo a ranta,duk sanda ta tuna wasila sai taji babu dadi har cikn ranta,duk da tasamu gudunmawar qarfafawar gwiwa da maganganu masu ma'ana daga mahaifiyarta,to amma totally gaba daya batajin dadin komai,tana jin gidan nasu kamar wata maqabarta,duk wani sauran walwala da suke qoqarin ganin cewa sun samar a gidan babu ita ta gudu,wani shafi na masifa bala'i mita da cin fuska mahaifinsu ya bude,babu wata rana da zata fito ta kuma fadi basu ji babu dadi ba dangane dashi. Dukkansu sun fawwalawa Allah,suna qoqarin kai zuciyarsu nesa,dannewa da kuma dabi'antar da zuciyar tasu bisa doro da bigire na haquri. A dan tsakanin rayuwa ta koya mata abubuwa masu tarin yawa,wani dimbin ilimi ta samu,ilimin daya tasamma sauya wasu daga cikin halayenta,ta koyi taushi da laushi,ta koyi cinye da danne matsi da qunci. *********A nutse taja murfin langar data cikata da dambu,wanda sukayi da ragowar shinkafar data rage musu cikin gidan,daga ita kuma basu da wani sauran tartibin abunda zasuci sai abinda baban yaga dama ya basu. Tun daxu aka gama dambun,ana kuma jiran shigowar bilal ya kaiwa habiba dambun,saidai har yanzun shuru babu shi babu dalilinsa,ummansu dake fitowa daga bayan gida ta dubi kaltum din "Kinga kaltum,dauki mayafinki ki xagaya ki miqa mata kinji,dawowae bilalu ba yanzu ba,tunda aka kusa gama ginin nan yanzu ba kasafai yake shigowa da wuri ba" tunda abun ya faru batason fita ko ina,zata iya cewa bata qara fita koda babban tsakar gidansu ba bare waje,amma yanzun ba zata iya musu da umman ba,saidai gidan habiban ne ma batason zuwa,saboda ta layinsu wasila zata wuce,rashin son bi ta layinsu wasila kuma bai isa hujjar da zata wofantar da aiken umman ba,don haka ta amsa mata da to,ta miqe ta shiga daki. Da hijabinta a hannu ta fito,sai taja ruwa ta zuba a buta,ta wanke qafafuwanta da fuskarta ta shafa mai,sannan ta saka hijabin ta dauki kwanon ta fito. A farfajiyar gidan nasu taga inna laure da siya a tsaye,asiyan taci ubansu ado,sai tashin qamshi take,riqe da wata qaramar jaka da tafi kama data matafiya,idaunta ta dauke,sai su duka suka tabe baki,kafin asiya ta sheqe da dariya sannan tace "Nidai inna zamu tafi,sai Allah ya dawo damu,kuyi amfani da wadan nan kudaden,banason naga kuna cikin garau garau" Sosai inna lauren ta wage baki,kamar wadda aka danqarawa kyautar kujerar makka "Yar halak,'yar arziqi irin albarka,yarinyar dana haifa da bismillah,kedai kin shigo duniya a sa'a,Allah ya tsaremin ke,ya qara nesanta tsakaninmu da talauci" "Ameen baabata" ta fada cikin farinciki. Tuni kaltum ta qara sauri ta fice abinta,bata bari kunnuwanta sun jiye mata sauran maganganunsu ba,bare ranta ya ida baci,zuciyarta cike fal da mamaki. Mamakin nata yana da nasaba da asiya,da jiya ta shiga bayan gidansu tana wanka,taji asiyan na shaidawa babanta suna da tafiya a gobe,daga makaranta kuma aka shirya tafiyar,zasu cikin gari kwana daya zasuyi,su 'yan babban aji. D/Z 25 Lantanar tana sake jin tausayin kaltum cikin ranta,saboda gaba daya ta rame,ta kuma sauya,ba kamar yadda fa santa ba "Dauki ruwa kisha kattume" lantana ta fada a tausashe,bata musa mata ba,saboda tuni maqogoronta ya bushe,saboda tsoro da firgici tare da tunanin kalar amsar tambayar da tayi daga bakin lantana,saita dauka din,ta kurba sau uku ta ajjiye,dai dai sanda lantana ke tambayarta "Amma dai lafiya kattume?" Kai kaltum ta girgiza,sannan ta fara magana cikin sanyi da rauni "Wai lafiya lantana?,me yake faruwa dani?" "Me kika gani?", Lantana ta maida mata tambayar tana kallonta Kai kaltum ta juya sannan tace "Duk inda nabi ko nayi.....sai naga kaso mafi yawa na mutane suna bina da kallo" shury lantana tayi,wanda hakan ya qara yawan fargabar kaltum,ta kuma kasa sake tambayar lantanar,har sai data magantu da kanta "Da kaina dama na yanke inje har gida na sameki koda baki zo ba.....kaltume,lallai mutum abun tsoro ne,bayan abinda wasila tayi miki bai isheta ba,tana ci gaba da yadaki,tana gayawa mutane cikin shege kikayo shi yasa aka gasa aurenki,nasuru wai da kansa ya buqaci aurenta saboda ya rama cin amanar da kika yi masa,wannan shine babban dalilin da yasa kikaga mutane na miki irin wannan kallon". Batasan hawaye take ba sai da taji duminsu saman fuskarta,wai dama haka mutum yake?,kodai tasu jama'ar ne haka?. Tunaninta ya yanke sanda lantana take cewa "Wasila ta bawa mutane masu irin tunanina mamaki,ta barki mana da tabon data yi miki?,yanzu ta ina zaka fara wanke kanka daga wannan batancin?" Sak irin tambayar data zo kan kaltum kenan,ta yaya zata sauya tunanin mutane daga kanta,duk da cewa ba'a bari a kwashe duka,duk da cewa koda ta wanke kan nata ba kowa bane zai yarda?,amma a qalla ta rage wani abun. Zumbur ta miqe tana goge damshin lemar hawayen fuskarta "Idan zaki dandali anjima,ki biyomin" ta qarashe maganar tana yin gaba,sai lantana ta bita da kallon mamaki,tare da tambayar kanta me xata je yi a dandali,matar da duk randa aka ganta a dandali lallai ba qaramar sa'a aka ci ba,saidai kafin ta tambayeta harta fice daga gidan ta quracewa ganinta,ta barta da tambayar kanta tambayar da bata da amsarta. *8:00 pm* Sanye yake da wata qawatacciyar tattausar riga hoodie zip mai hade da hula,tana da dogon hannu,hakanan tana da dan kauri ba laifi,kalarta ruwan hanta ce mai asalin kyan,trousern jikinsa ya dace sosai da kayan daya sanya din,sai wata hula daya sanya a saman kansa,wadda take shige data sanyi,sakamakon sauyin yanayi na busawar iska da aka samu,sakamakon sanyi dake sallamawa mutane. Har ya janyo takalman daya saba sanyawa duk yayin da yayi irin wannan shigar,sai kuma ya fasa,sakamakon tunawa da yayi cewa,yazo garin ne a sunan lebura kamar kowa,saiya watsar dasu,ya miqe zuwa qofar dakin,yana fidda zazzafar iska daga bakinsa,zafin da zuciyarsa tayi tun dazu har yanzu batayi sanyi ba,dalili kenan daya daga waya ya kira hannafi,yacewa umar ya shirya suje dandali ya rage dare. Duk da cewa akwai abubuwa masu tarin yawa cikin qauyen da yake kallonsu cike da kusakurai,to amma yanayin yadda wajen ke cike da masu neman na kai,da kuma qoqarin nishadantar da kansu da sukeyi yana burgeshi. Sama da qasa umar ya kalleshi sanda ya fito,ganin har yau dai wata shiga yake a hargitse,kamar ba sarakin daya sani ba,wanda baya saka kaya sai designers,wadanda suka amsa sunansu kaya "Muje ko?" Saraki ya fada yana tsare umar da ido,saboda yadda yaga yana kallonsa,saiya dan sosa kansa kana yabi sarakin a baya. Su biyu suke tafe zuwa dandalin,lantana da kuma kaltum,wadda tunda suka taho take riqe da kara a hannunta tana dan kadashi,zuciyarta cike fal da tunani,lantana dake gefanta itama tana nata nazarin,ganin har yanzu kaltum batace ga abinda zataje dandali yi ba "Amma dai kaltume ba fada zakije kuyi dasu wasila ba ko?" Wani busashen murmushi ta saki,ba tare data kalli lantana ba tace "Fada?,Allah ya kiyaye,zanje ne kawai na isarwa da jama'ar qauyen saqon daya kamata ace sunsani,tunda sun kasa tunkarata,wanda ya yarda ya kyautatawa kansa,wanda kuma ya riqi akasin hakan shi yaga zai iya" kai kawai lantana ke gyadawa,tasha jin ana fadin kaltumen gwanar iya magana ce da tsari,duk cikinsu babu wanda ya kamota,bata tana sake gasgatawa ba irin yau,haka shuru yaci gaba da wanzuwa a tsakaninsu,har zuwa sanda suka qarasa dandalin. Abun tamkar wani afi,dandalin yau ya cika sosai da jama'a,har hakan yaso basu mamaki gaba dayansu daga ita har kaltum,saboda ba kasafai aka fiya samun irin wannan cikar ba,saidai hakan bai hanasu kutsawa zuwa muhallin da suke tsaiwa ba,kutsowar tasu dataja hankalin mutane,suka fara kawo idanuwansu kansu. "Alqur'an gata can,gata ca yauma tazo,gaskiya nazo wajen nan a sa'a" cewar haladu yana washe baki,kamar wanda aka yiwa bushara. Maganar data sanya samir dake zaune saman wani dan teburi,da alama wata sana'a akeyi a kanta yau mai teburin bai samu zarafin yinta ba. ,tunda yazo ya samu su haladun a wajen,suna ganinsa suka sake masa,kamar sun jima da sanin juna,tun yana biyewa hirar da suke masa har ya qosa,kasancewar bai saba ba ya koma yaqe,daga bisani da yaga abun bana qare bane,sai yace musu ciwon kai yake,abinda yasa suka janyo masa tebur din kenan ya zauna "Amma haladu baka da hankali.....wai kana nufin har yanzu son yarinyar nan kakeyi?" Abokinsa da samir ya sansu tare tun a ganin farko ya fada yana duban haladu cike da mamaki fal sama fuskarsa. Tsaki haladu yaja yana daidaita tsaiwarsa,ta yadda zata bashi damar ganin kaltum da kyau "Tome za'a fasa?,mutuwa ko hisabi?,ni ai fasawar wancan gajan gaba ta kaini,wai gobarar titi a jos" "Amma haladu bansan baka da hankalo ba sai yau.....yarinyar da tayi cikin shege.....,qawarta ta shaida haka,matar qanin babanta ma ta bada shaidat faruwar abun,wanda xai aureta ya karbi kudinsa.....shine kai zata sanya kanka a cikin irin wannan hadarin?". Lafuxxan bakin labaran su suka dauki hankalin samir,ya cira kansa a hankali dake duqe a dazu yakai shi zuwa sashen da kaltum ke tsaye ita da lantana,tazarar dake tsakaninsu da ita ba wata mai nisa bace can,hakan ya bashi damar kallon fuskarta sosai. Very young girl,wadda baiga komai tattare da itaba face qananun shekarunta,siririn jiki da kuma baqar fuskarta da babu koma a samanta sai karan hanci,ko cikakken qirji bai hango ba bare su zame mata ado,har a yaushe tasan wani abu da zata bata rayuwarta irin haka?,bama wannan ba,shi wanda suka aikata abun tare,indai har hakanne....indai har da gaske ne,meye abunda yaja ra'ayinsa a kanta?,baya bata da duk wani abu da zaija ra'ayin namiji akanta?,bata mallaki komai ba face baqar fata,mai duhun da bashi da kyan gani. Idanunsa suka sauka kan qafafunta dake saye cikin takalmin roba da yaji ana kira da BURIN ALMAJIRAI,sai ua sauke idanun nasa,yana jin qirjinsa yana nauyi,ba shakka tafiya mabudin ilimi ce,yaga abubuwa masu tarin yawa da suka sha bamban da abubuwan dake faruwa a duniyarsa. Kallon banxa haladu yayi masa,yana sake jan tsaki "To saime?,ita soyayya bata duba wadan nan,bakasan yadda nake sonta bane da ba zaka ce haka ba" kai abokin nasa ya kada,da alama maganganun haladu sun kaɗashi "Amma dai kasan duk yadda kakai ga sonta su gamandi ba zasu barka ka aureta ba ko?,tunda babu wanda baiji labarin abinda ta aikata ba" a fusace haladu ya fuska ci labaran "Wai tsaya labaran,kai da kaketa wannan hanqilon,a gabanka akayi ne?,ko zaka iya rantsuwa sa alqur'ani izifi sittin cewa lallai ne ta aikata abinda ake zargin?,zargine fa..." "Eh zarginne,amma bisa qwaqwwarar shaida da hujja daga makusantanta........" Sauran maganar da labaran yayi niyyar fada ta maqale,saboda yadda sukaji filin ya gaba daya ya dauki wani irin shuru,sai dukka suka maida hankalinsu ga filin,don ganin abinda yake faruwa,ciki harda samir,kamar wadanda akaja hankalinsu zuwa can Kaltum ce take takowa zuwa tsakiyar filin,sanye da fingilalliyar rigar atamfa wadda taci duniya dai dai gwargwado,zanin jikinta yasha bamban da rigar jikinta,sai maqalallen hijabinta daya zama kamar na gado. Kowa idanu ya zuba mata yana kallonta,saboda sun manta rabon dasu ganta cikin fili irin haka,baka filin ba,dandalin ma zuwansa ya zame mata wani tsohom tarihin da sai sanda taso waiwayarsa take zuwa,koda tazo ta watsar da waqenta mai dan karen dadi da takeyi,duk kuwa da nacin da ake mata,dama can kuma ba rawa take ba,yana waqen ne hade da rausayar da har yau 'yammatan suka kasa kwaikwayar irinta. Abu na biyu kuma kusan labari yaje kunnen kowa na cewa wai tayi ciki,ga tunaninsu tabar fita koda nan da qofar gida,wala'alla ma a gaba kadan ta tattara tabar qauyen,saboda matan da irin hakan ta faru dasu cikin qauyen basa qara wasu kwanaki masu yawa suke barin qauyen,saboda gudun kada abunda suka aikata ya bullo kowa ya gani xahiri,da wadanda suka yarda dama masu shakka. Kamar saukar ruwan sama saman kwano a lokacin da ba'a shirya ba muryar kaltum ta fara fita,cikin wani irin amo da sauti daya ja hankalin na kusa dama na nesa. A hankali take rausayawa,cikin wata irin tarin nutsuwa data tafi hade da sautin amon waqarta,wani irin karin waqa dake sanya zuciya ta rusuna,ya kuma ja hankalin mutum daga farko yaji abinda ke faruwa a tsakiya da kuma qarshen waqar,shurun da wajen kawai yayi ya isa ya shaida maka cewa waqar na daukar hankalin jama'a tana kuma ratsasu yadda ya kamata. Tsahon minti uku waqar ta dauka kafin takai qarshenta,wanda zuwa sannanZukatan mutane da dama sun shiga shakka da kuma kokwanto,aka shiga cece kuce da qananun maganganu a wajen,kowa da abinda yake zantawa da 'yan uwansa,kawunan mutane ya rarrabu,mafi rinjaye daga cikinsu sun yarda da abinda ta fadi din,musamman wadanda sukasan yanayin rayuwar gidansu,da yadda ta rayu,take kan rayuwar ma,yayin da wasu kuma suka ce sam,kawai tabarmar kunya takeson nadewa da hauka cikin waqe,daga cikinsu akwai wasila da jama'arta,wasilan ta cika tayi fam saboda irin magangnun da kaltum din ta yaba mata a habaice,ta kirata da sunan wadda bata ramin kanta,saidai ayi mata ta shige,ta kirata da matar cushe wadda bata daraja,maicin amanar masu amana,itakam kaltum ta gama da ita. Fit aka nemeta a waien aka rasa,ciki harda lantanar da suka xo tare,ji tayi bata da wani sauran dalili da xai zaunar da ita a wajen,uwa uba batason babansu ya dawo gida bai cimmata ba,batasan me zai afku ba. Tafiya take a hankali,tana jin yadda jikinta yake a sanyaye,duk da cewa ta furxar da abinda yake cikin zuciyarta,aqalla ta samu wani relief ko yaya yake,saida qafafunta a sanyaye suke,gabanta na yawaita faduwa,tana jin kamar akwai sauran qura a gaba,qurar data sani ta fiddo mijin aure,dama wadda bata sani ba wadda ubangiji kadai ya barwa kansa sani. Ta gama lalubenta kaf bata san wanda xata tsayar din a matsayin miji nan da wata guda ba,indai kuwa hakan ta faru,bata da wani xabi illa ta saurari haladu,duk kuwa da yadda ranta da zuciyarta basu kwanta dashi ba. Yana daya daga cikin mutanen da waqenta ya jefa nazari cikin zuciyarsu,daga nan inda yake zaune yana jin yadda tabar baya da qura,yadda jama'a keta cecekuce akan maganganun data fada,masu fashin baqi nayi,masu qarawa abun gishiri suna yi,kowa da inda yasa gaba. Tsaki yaja yana watsa matsalar gefe guda,baiga amfanin shima ya tsaya yabi sahunsu ba,ta hanyar baiwa kansa aikin tantance abinda kalamanta ke nuni akai,shima fa yana da abubuwan daya kamata yaui concentrating akansu. Har ya buda baki zaiwa umar magana akan ya taho su tafi saiya fasa,ya saki wani qaramin murmushi sanda ya hangeshi ya tsaida wata budurwa yana tsarata,ko hankalinsa baya kaiwa bayansa. Ya sani kawai salon abun nan ne da hausawa ke cewa rage dare,saboda already umar din akwai wadda ya tsayar jalila,har momy yasa taje ta gaisar,ba tare daya nuna ya ganshi ba ya juya ya kama hanya shi kadai,bai nemi umar ba bare hannafi. Ci gaba take da tafiya hankalinta naga tunanin da tayi zurfi a kai,kamar daga sama taji mutum yif ya cake a gabanta,razana tayi sosai,ihu taso qwalawa Allah ya taimaketa bakinta ya furta "A'uzubillahi minashshaidanir rajim!" Da qarfi tana fidda idanunta sosai,tana son bambance waye ta hasken farin watan da ya haske sararin samaniya... 26 D/Z *_MANZAN ALLAH S A W YACE:idan dayanku ya tashi daga guri,sai ya sake dawowa gurin(da niyyar sake xama) to shine yafi cancanta da wajen"_* *_A wani hadisin kuma yana cewa"bai halatta ka shiga tsakiyar mutane biyu dake zaune ba(da sunan zaka zauna) saida izininsu_* ________________________________ *LITTAFIN KUDI NE,KI BIYA KI KARANTA NAKI CIKIN AMINCI TA WADAN NAN NUMBERS DIN* 08184017082 KO KUMA 09134848107 "Kaiiiiiii.....nine ma shaidan din da kike korata?" Auwalu wanda yake tsaye gabanta cikin duhun daren da hasken farin wata ya ratsa,kuma cikin yanayin dake nuna a dan buge yake yayi maganar,take hantar cikinta ta kada,bata maganar da ya fada ba take,tana lalubar hanyar da zata gudu ne kawai,don ta dade da sanin tarayyarsu irin wannan ita da auwalun babu alkhairi a cikinta. Duk da ta kadun,amma hakan bai hanata aro juriya da qarfin hali ba,ta durfafeshi zata wuce,saidai tuni ya sake shan gabanta,yana tangal tangal kamar zai fada kanta,hakan ya sanyata ja baya da sauri,cikin tangadi yace "Waikeeee......bakisan irin son da nake miki ba?,Allah saina aureki,ko duk garin basa so,ni babu ruwana da wata laure.....ita take haukanta ita kadai" yafada yana watsa hannaye,haushi ya cika kaltum,ta baro wani takaicin taci karo da wani,don haka saita watsa masa harara "Allah ya kiyaye na aureka,me zanyi da kai?,kaga ni ka matsamin hanya na wuce gida,dare yana dada yi" tayi maganar tana neman hanyar wucewa cike da jarumta. Bata ankara ba yasa hannu ya fincikota baya ta hanyar riqe hijabinta,kafin ta daidaita nutsuwarta taji yana cewa "To ai shikenan,kin ragemin wahala,tunda bakya sona bari kawai ayi shortcut a wuce wajen" yana kaiwa nan ya fara yunqurin jawota zuwa gareshi,tare da turata wani sakaye dake daura dasu. Matuqar tashin hankali taji ya rufto mata,don bata manta wancan ranar da makamancin irim hakan ya kusa faruwa ba,saita fara turjewa tare da neman mafita da matsera,saidai babu kowa wajen,duk wasu suna gida,samarin da 'yammatan kuma mafi yawansu suna dandali. Gigicewa tayi sanda yaja hajibinta,qarar yagewarsa ta ratsa kunnuwanta,saiga hijabin ya dawo kafada,sassalkan gashinta data manta rabon data kitseshi ya bayyana,saboda rashin dankwali da bata daura ba,saita cukuikuye hijabin tana sakin tsumammen kuka. "Saki hijabin mana masoyiyata.....nifa aurenki zanyi Allah....ko babu goro da alawa....." Ya fada yana niyyar kai hannunsa jikinta ya zarw yagaggen hijabin data cukuikuye cikin jikinta,saidai kuma bai samu damar aikata hakan ba,saboda hambarar dashi da yaji anyi,yayi taga taga ya koma da baya ya fadi dabas a qasa,ya daga kai don ganin wanda yayi masa wannan aika aikar. Samir ne tsaye yana hadiye yawu,Adams Apple dinsa daya bayyana sosai saman maqogoronsa yana ta sama da qasa,abu guda dake saurin nuna cikin fushi yake "Kaiiiiii....... wallahi kaci sa'a bacci nakeji,da yau na nuna maka kurenka,amma dai......idan mukayi aure ko?,ba zakaci taliyar gidana ba" daga haka saiya koma ya maida kansa qas ya kwantar hankalinsa kwance,kamar wanda ya samu katifar cikin dakinsa. Tun isowarsa wajen dama ya fuskanci a buge yake,banda haka garjejen qato kamar wannan yadda ya hangi abinda ke faruwa daga nesa,inda ace cikin hayyacinsa yake,mawuyacine ta iya daqileshi daga abinda yayi niyyar aikata mata. Tsaye cak yayi yana jin yadda take kuka bayan ta dunqule a qasa da barkakken hijabinta,kallonta ya danyi sannan ya dauke kai,kwanaki qalilan da fara ganinsa da ita,amma yaga abubuwa da yawa kanannade da rayuwarta,'yar qanqanuwar rayuwar tata da bata kammala ginuwa ba,abun sai yaketa bashi mamaki,tare da ganinsa wani bambarakwai. "Ki tashi ki nunan hanya na rakaki" yayi maganar yana dan qara taku kadan zuwa gaba,ba musu zumbur ta miqe,saboda gaba daya tsoro ya gama kassarata,rakiyar dama tafi buqata fiye da komai. Waiwayowa yayi kadan kana ya dauke kansa yana dakatawa da tafiyae daya fara "Kina iya tafiya ke kadai idan ba zaki iya shuru ba,bazamu tafi a haka ba a dauka nina miki wani abu" yayi maganar da dakakkiyar muryarsa dake nuna zallar abinda ake nufi da nutsuwa wanda ke tattare dashi. Dole ya dinga cinye kukanta,har ta samu yatsagaita,a sannu a sannu suke tafe,tana dai biye dashi,har zuwa sanda suka kusa da qofar gidansu,sai taga yaja ya tsaya daga baya yana goye hannayensa "Ki qarasa,ina hangoki daga nan" saita gyada kanta,cikin dasashshiyar muryar kuka tace "Na gode" kansa yadan daga kadan,kana ya bita da kallo sanda take nufar qofar gidansu. A rayuwa bai tsammaci yarinya mai shekaru kamarta zata iya fuskanta da daukar nauyin matsalolin rayuwa ba,sai gashi a yau ya gani zahiri. Kiran wayarsa da akayi yasa ya dauke idanunsa daga kallonta,sanda take takawa da wani irin tattaki kamar na bawa farin shiga,wa da ke tsoron shiga qangin bautat da baisan zafa bulle masa ko akasin hakan,matsasttsen kuma siririn qugunta na sake bayyana muraran. Idanunsa ya mayar kan wayar bayan ya zarota,Aamiru ne,fushi yake dashi,saboda haka ya katse kiran ya jefata aljihunsa,yana maida dubansa gareta,dai dai sanda take shigewa gidan gaba daya. A qalla ta kusa minti biyar tsaye a soron tana qoqarin dai daita yanayinta da nutsuwarta,saboda batasan shiga da yanayi da zai sanya hankalin ummansu ya tashi,don ta tabbata ko yaya yanayinta ya sauya,tana da saurin gane hakan. Sallama tayi cikin qoqarin son dai daita muryarta,ummansu ta amsa sannan taci gaba da shafa man da takeyi a jikinta,saboda iskar sanyi dake saurin busar mata da jiki,bilalu na zaune saman kujera 'yar tsugono da kwano a gabansa yana cin abinci,danqararriyar dafa duka da sukayita tun kusan azahar,shinkafa mai tarin tsakuwa,wadda saida kaltum tayi tsaiwar gwamin jaki sannan ta samu nasarar gyarata,duk da haka baka kubuta ba,daga sanda ka fara cin abincin zuwa kowanne lokaci kana iya cin karo da tsakuwar da zata kashe maka haqora su kasa moruwa. Bilal ne ya daga kai yana yiwa kaltum magana,saidai batajin zata iya tsaiwa ta biyewa shirmensa,hakan dai dai yake da ummansun ta gane yanayin data shigo cikin gidan dashi "Kaina ke ciwo bilalu,kwanciya nakeson nayi" ta fada,sai umman ta bita da kallo,duk da ta shinshino damuwa cikin muryarta,amma ayau din bata matsa ba,saita bita da addu'ar "Allah ya sawwaqe,ya bada lafiya" Ta jima cure waje daya cikin shimfidarta tana fitar da qwalla,wai me yasa mutuncinsu da darajarsu ba komai bane wajen 'yan uwansu,kowa da irin salon tozarcin da zaya zo dashi cikin rayuwarsu. Ta dade a haka,tun tana jin motsin su umma sama sama harta dena ji sanda babansu ya shigo gidan,da alama kowa ya kama gabansa an bar masa filin tsakar gidan,kamar yadda ya zame musu jiki tsahon rayuwarsu,saboda koda shigowa yayi ya gansu zaune a tare waje guda,tofa bashi da aiki sai muzurai,da kuma fadin maganganu marasa dadi,yakance gulmarsa suka zauna sunayi ba wani abu ba,su da munafukar uwarsu. ********Yana tsaye daga a qofar gidan daya kasance masaukinsa ne cikin qauyen,sanye yanke da riga mai dogon hannu da wandonta,wanda suka fi kama da jessy,duk da ba jessy din bane,amma sun masa kyau sosai. Hannunsa daya riqe da mug wanda ke cike da hot black tea,duk da cewa yafi sha'awar shan coffee amma baya tunanin xai sameshi a dan qauyen nan,dalilin da yasanya dole ya haqura yayi amfani da abinda ya samun. Zamansa a qauyen yana masa dadi ta fuskoki daban daban,yana ganin yanayin rayuwa da dabi'u iri iri,a yanxun haka yadan saba da wasu daga cikinsu,yakan xauna da yammaci suyi hira dasu wani lokaci can qarshen layin da yake ciki. "Barka da safiya sir" yaji am furta daga gefansa,koda bai waiwayo ba yasan waye,hakan yasa bai juya ba illa amsa masa da yayi yana ci gaba da kurbar tea dinsa "Barka kadai,ka tashi lpy umar?" "Lafiya lau og,jiya kuma saika tafi ka barni ba tare da nasan ka taho ba?". Dan qasa yayi da cup din yana sakin murmushin gefan baki "Ina fatan ka fara irgen ranakun aurenku da yarinyar daka tsaida jiya" Idanu umar ya fitar waje yana duban samir daya bashi baya "Aure kuma sir?,ai ba aure zamuyi ba" Murmusawa ya sake yi,da alama yau da 'ya miskilanci ya tashi "Koma yaya ne ka shirya,kaga gaba ka sake tsaidama wani yarinyarsa" Cikin alamu na nuna damuwa yace "Am sorry sir,kawai nima na dan gwada ne....." Kadan samir ya waiwayo ya kalleshi,dariya na motsa masa kadan kadan cikin ransa,ya gane sarai abinda umar din yake nufi,kawai ya fada masa ne saboda kada shi ya zarme da yawa ya kuma zarma wata azo ana dogon turanci "Kayi a hankali....kada daga zuwa aiki ka koma gida da mata" kansa yadan sosa,yana qiyasta yadda hakan zata faru yana murmushi "Allah ya kiyaye sir.....za'a kula in sha Allah" Baice dashi komai ba,saiya waiwayo yana miqa masa mug din hannunsa,yasa hannu ya karba ya juya zuwa cikin gida dashi. Yana dab da shiga samir dake biye dashi yace "Ka kiramin hannafi,kace mishi ina son ganinsa" "Yes sir" umar din ya amsa suna shigewa gidan gaba dayansu. Kamar jiran shigarsa ciki akeyi wayarsa ta dauki qara,ya soma lalube zuwa inda ya ajjiyeta,kafin yakai ga dagawa ta zama miscal,saiya shiga duba kiran daya rarrasa da safen,saboda barin wayarsa da yayi cikin gida. Missed call ne guda tara,biyu daya na fauza,uku na salimat duka abokan aikinsa,wadanda suke son sanya kansu cikin rayuwarsa,rayuwarsa kuma baiga gurbin da zai basu ba komai qanqantarsa. Kiran mummy da auta su suka biyo baya,sai jauhar wadda yakan manta da babinta ma gava daya,yayi dan qaramin murmushi ganin miscal din jawahir yana ci gaba da duba kiraye kirayen,yasan duk yadda akayi akwai abinda takeso ta gaya masa. Miscal din salisu yaja hankalinsa daya gani barkatai sama dana sauran,kuma dukka kiransa yafi na kowa muhimmanci a wannan lokacin,don haka ya fasa kiran duk wanda yayi niyya,ya maida akalar kiran zuwa ga kiran salisu. Saidai ko shiga batayi ba yunqurin kiran ya yanke,kiran jawahir ya danno kai,dole ya daga,saboda yasanta sarai yanzu saita masa mita,hakan nan ya daga yana kara wayar a kunnensa,bayan ya samu gefan katifa ya zauna yana miqe dogayen qafafuwansa. "Yaayaa...kama manta damu ko?" Ta shigar da qorafinta cikin shagwabar data zame mata jiki "Auta rigimar gangan,shekaran jiya mafa ina jin munyi waya ko?" "Amma yaaya kace zaka kirani baka kuma kirani ba,nikam wannan karon inajin zan biyoka naga aikin daya riqe ka yaya a qauyen nan" murmushi ya qwace masa,har sai data jiyo sautinsa kadan,ya jujjuya idanunsa yana kallon irin dakin da yake ciki,shi kansa yayi mamakin yadda ya zauna a qauyen bai wani damu ba "Wannan qauyen....ba zaki iya zama a cikinsa ba auta" "Why yaya?,me yasa kai ka zauna,nima zan iya" fuskarsa a fadade da murmushi yace "Akwai alot of funny here, amazing abubuwa da suka bambanta da gida,i assure you will enjoy it.....but,ba zaki iya zama ba,daddy ma bazai barki ba,baki gani nima yadda yake qalubalantata ba?" "Amma yaaya....." "Ke mayya,ki haqura" ya tsinto muryar najwa ta cikij wayar tana fada cikin tsawa,da alamu da jawahir take,taji abinda suke tattaunawa ne Shuru suka danyi dukansu,shi yana jin yadda tsawar ta ratso har cikin wayar da sukeyi "Yaaya" jawahir ta fada a shagwabe,ranta kuma a dan bace "Bata wayar" yace da ita kai tsaye,yanajin sanda ta miqa mata wayar ta amsa "Yaya....barka da asuba" baibi takan gaisuwarta ba,don bayau ta fara irin wannan dabi'ar ba idan suna waya,yana iya jin yadda takan hantari jawahir din "Kiyi dukka iya tunanin da zakiyi,ki samu abun fada min randa na qaraso gida kan dalilin da yasa kikewa auta haka…...bata wayar" cikin tsorata da sanyin jiki ta bude baki da niyyar baiwa kanta kariya,cikin tsawa tsawa yace "Shut your mouth.....ki bata waya nace" hakanan badon taso ba ta miqawa jawahir wayar tana jifanta da harara,qasa qasa yadda bazaiji ba tace "Munafukar Allah" batabi ta kanta ba ta amsa wayar tana maidawa kunnenta,daga can inda yake ya daga wayar daga kunnensa yana kallon screen din jin alamun kira yana shigowa,sai yaga salisu ne still,don haka yace da ita "Auta....i will call you in the evening in sha Allan" "Ok yaya" ta fadi tana katse kiran,yayin dashi kuma ya daga kiran salisun. "Banza kawai asararriya,wallahi duk abinda kika sanya yayimin a kanki zan huceshi,kuma aishi din ba Allah bane,sai yazo din,idan yaso ya kulleni a kurkukun bayan duniya ya jefa maqullin teku,ko kuma ya zaremin raina" ta fadi zancan cikin son nuna bata damu ba,duk kuwa da yadda ranta ke cike da fargaba,don sunfi kowa sanin waye saraki idan ransa ya baci,jawahir bata ce komai da ita ba sai data miqe tsaye ta saita hanyar daki "Oho dai,ke kika jiyo kuma,ni ba matsalata bace" da hanzari najwa ta yunqura zatabi bayan jawahir data qara wuta ta shige dakinta tana shirin kulle qofa,saidai kaifafan idanuwan mummy suka maidata suka zaunar,mummyn ta qaraso wajen,ba tare data zauna ba ta dubeta "Ki dinga yawan tunawa da cewa,'yar uwarki ce da baki da kamarta kaf fadin duniya" Ran najwa a bace tace "Momy kina gani fa,yasa ta soma rainani" saida mommyn ta fara tafiya ta bata amsa "Ke kika ja,tunda kika kasa riqe sandata domin ta yimiki jagorancin da bazaki fada kwata ba bare rami" shuru najwa tayi tana jujjuya zancan momy a ranta,saita miqe zumbur tabi bayanta,dai dai sanda daya daga cikin ma'aikatan gidan ta fito dauke da farantin data shiryo kayan ciye ciye a kai "Ranki ya dade gashi an kawo" "Koma dasu kitchen" najwan ta bata umarni tana ci gaba da tafiya sauri sauri zuwa dakin mommyn ba tare da tako juyo ya kalleta ba,saifa girgiza kai tana juyawa da uban farantin zuwa inda tasha wahalar shiryo kayan da sai da iyayenta suka zagu kamin ta gama lissafa mata dame dame takeso. Cike da girmamawa ya gaidashi,sannan ya fara shigar masa da dalilin kiran,baqi gareshi,'yan qasar china dakeson zama dashi,an masa saqo ta email dinsa saidai basu samu respond ba,sai a sannan ya tuna cewa yabar system dinsa a gida wancan zuwan da yayi "Am on my way jibi in sha Allah,ku shirya dukkan abinda ya dace,daga wannan karon ina saka ran zuwa daya xanyi na gama zuwa,zan bar ragowar aikin a hannun mutanen da aka amince dasu na dawo muci gaba da aiki,but....kada ka shaidawa kowa ranar dawowata" "Yes sir,in sha Allah" daga haka sukayi sallama,dai dai lokacin daya ji muryar hannafi daga bakin qofa yana neman izinin shigowa. Izinin yayi masa,hannafin ya shigo ya samu waje ya zauna yana gaidashi cikin girmamawa,ya amsa masa,suka dan tattauna kan batun gini,da abubuwan da za'a qara siyowa na kayan aiki,kusan komai akwai,langa langa kawai za'a dado bandir daya,suka lissafa abinda zai isa,ya bashi harda dori,saboda kusan da wuya yayi aike ya baiwa mutum kudin kai da kai. Har hannafin ya miqe saiya tuna "Nace a garin nan akwai teloli?" Murmushi hannafi yayi "Yallabai akwaisu,amma kamar ba zasu dace da tsarinka ba" baibi takan zancansa ba yace "Hijabai nakeso guda uku,daga nan zuwa anjima,zan samu?" Kai hannafi ya gyada "Zaka samu sosai,yau kasuwar mafara take ci,ko a can saina gangara na siyo maka" Baice komai ba,ya zaro wasu kudin ya miqa masa,hannafi yasa hannu biyu ya dafe sanna ya fice yana masa sallama. A iya qaramin karatunta da tayi,da kuma dan wayewar data samu game da yanayin yadda karatu yake daga bakin nasuru,da kuma sanin data yiwa makarantar garin nasu,bata taba jin inda suka diba daliban J.s 3 aka tafi kaisu wani waje ba,koda na wuni daya bama bare akai ga kwana,sai gashi ita asiyan ta qirqiro qaryarta tayi mata fenti,iyayenta sun sanya hannu bibbiyu sun amsa. "Allah ya kyauta" ta furta cikin zuciyarta,tare da tattare duk wani abu daya shafesu ya watsar gefe,abinda ta sani kawai shine,wanda baiji bari ba zaiji hoho. Abu na farko data lura dashi kallo da wani lokaci akr binta dashi,idan ta hadu da wasu mutanen "Akwai wata kenan" ta gayawa kanta,tasan dabi'a da halayen mutan qauyensu kaf,mutanene da basu raina abun magana,sun iya gila gutsiri tsoma da yanyana magana,don haka saita qara kama kanta,har ta isa gidan habiba. Ta samu habiban jikinnnata da sauqi,laulayin nata ba wani mai zafi bane,kamar ta dauki kaltum ta goya,saboda ba qaramar sa'a bace zuwan kaltum gidanta,ta karba dambun tana murna,ta dibawa surukarta takai mata,baban ta amsa kuwa tana ta godiya,surukar arziqi kenan,wadda ta dauka habiba kamar 'yar cikinta. Sanda kaltum din tayi yunqurin tafiya hanata habiba tayi,ta tareta da hira,duk a yunqurinta na qata ragewa kaltum damuwa da debe kewa,don ganin farko tayi mata taga ta rame,hakanan babu zafin nan data santa dashi. Duk da haka saida kaltum din ta yakice tace gida zata,ba hala habiba taso ba,amma bata sake matsa mata ba sukayi sallama,baya ta dauki hijabi guda biyu ta bata,hijabin da sai da akasha dambarwa kafin ta karba,har sai da babar yusufa tasaka baki,ta fita babar yusufan tana binta da kallo,cike da tausayinta,lallai inda ace tana da wani yaron bayan yusufanta,da sai ta sanyashi auren kaltum din,tana bata tausayi qwarai. Kan hanyarta ta komawa gida ta yake shawarar leqawa gidansu lantana,a jikinta takejin akwai wata matsalar kuma,bata kuma fatan wata matsalar ta sake tunkarota a yadda take,tasan ba zata rasa jin abinda ke faruwa daga bakin lantana ba. Ta tarar lantanar bata nan,innarta ta aiketa gidan yayarta,tace amma ta jima,don haka tana gab da dawowa,tayi tayi kaltum din ta jira amma tace a'ah zata gida,idan tazo a gaya mata. Saidai tana fita qofar gida sukayi kacibus da lantana tana dawowa,fuskarta cike da fara'a da kuma ganin kaltum din agidansu tace da ita "Wai....batan kai kikayi ko umma ce ta aikoki?"murmushi kaltum tayi da busashshiyar fuskarta "Wajenki nazo kuma ban sameki ba" lantana tana qarasowa waje tace "To ai gani na dawo,da tafiya zakiyi kenan ba zaki jira na dawo ba?" Ta fadi tana kama hannun kaltum zuwa cikin gidan "Sauri nake wallahi,ban cewa ummanmu zan biyo ba" "Idan kika ce mata nan kika biyo ba zata ce komai ba,ummanku da innata qawayene,inna laure ce tasa babanku yayi silar daina zuwansu gidajen juna da shegen kitsa gulma da munafuncinta.....inna na dawo" ta hade maganar tata da shaidawa innar tata dawowarta,tana jawa kaltum abun zama "Yauwa....ashema kun hadu,yanzu nake shirin shaida miki ai tazo" inna data leqo daga daki ta fada "Eh wallahi inna,a qofar gida mukayi karo" lantana ta amsa mata tana daukar kofin silba,ta ciko ruwa a randa tasha,sannan ta sake debo wani ta ajjiye gaban kaltum din sannan ta zauna tana dubanta *_Assalamu alaikum masoya 'yan cikin gidanmu na zafafa,fatan alkhairi a gareku tare da fatan dimbin nasara a rayuwarku,ina mai shaida muku cewa in sha Allahu nawa hutun xai kasance juma'a da asabar,saboda nawa jadawalin rayuwar nafi buqatar hutun juma'ar saboda shine nake da issue da ita😁😁,nasan in sha Allah hakan ba matsala bane,kunga zai kasance ranar washegarin randa 'yan uwana zasu je hutu xaku samu guda daya da zai tayaku zama,ina fatan muna cikin wadanda xami rabauta da juma'ar,MUN GODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR_* #TEAM ZAFAFABIYAR ANA TARE✌🏾✌🏾✌🏾 27 D/Z https://youtu.be/tymhRI5zfbQ 👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽 *Kada dai ku gaji,ga tashar dan uwanku,danku kuma qaninku SUDAIS tana buqatar gudunmawarku,shiga kawai zakuyi,ku dannan maballin SUBSCRIBE,ku kuma kunnawa yara 'yan uwansa dake gida su dinga saurara don zaburar dasu suma* *Jazakumullah bi ahsanil jazaaa*👏🏽👏🏽👏🏽 Tana zaune a tsakar gidansu,yamma ne liqis tana bin gashinta layi layi tana shafa ruwan danyan karkashi data jiqa,hanya ce da take bi wajen gyaran gashinta,yana qarawa lallausan gashin nata baqi,da kuma hanashi zubewa. Tana aikin tana tuna abubuwan da suka faru kwanakin da suka shude cikin rayuwarta,har yanxu har kuma kwanan gobe walwala da sakewarta bata dawo ba,tana jin tamkar an bude sasari ko kuma mari an sanya hannu da qafafunta,ta tuna irin nacin aiken daya ringa yi mata a jiya kan ta fito ta saurareshi,saidai gana daya lokaci guda,tunda abun ya faru taji kamar am zareshi fit daga ranta baki daya. "Ka jirani,ina zuwa.....ai bance bazan baka ba,yanzu zan fito" ta tsinci muryar bilal yana fada,tun kafin ya qaraso sashen nasu muryarsa ta rigashi qarasowa,kasancewarsa mutum me murya. Idanunta kan qofar har ya shigo,hannunsa dauke da wata baqar leda da baka iya ganin abinda ke ciki "Kaida waye,me kuma zaka bashin kake fadin ya jiraka?" Tayi masa tambayar tana taje kanta da santsin karkashi ya sanya tsahonsa sake daduwa Dan qaramin turminsu da suke amfani dashi ya janyo kusa da ita ya zauna yana amsa mata "Dan ladi ne yake neman rancen kudi" wani kallo ta watsa masa mai kama da harara "Kai din har yaushe kayi kudin da zaka dinga bada bashi,bana hanaka basu bama?,nawa kake binsu amma shuru babu wanda yake da niyyar biyanka?kai sun taba baka aron kudi saboda kana da buqata?,idan fa ka tambayesu kowa cewa yake bashi dashi a cikinsu" "Kiyi haquri yaya a basu,meye a ciki?,ai na fisu lada har a wajen Allah ko?,yanxu baga irinta ba,saboda Allah yaga zuciyarmu,hijabi aka bani akace na kawo miki" ya fada yana ajjiye mata ledar,ta bita kuwa da kallo bayan ta tsaya da tazar kan da takeyi "Waye ya baka?,ince dai ba nasuru bane?" "Haba yaya,ni ko kallonsa yanxu banayi....mutumin nan da yace zai sakani a makaranta ne,bansan ma ya akayi yasan hijabinki ya yage ba" "Ina fatan na roqarsa kayi ba?" Da sauri ya girgiza kai "Haba yaya,kin manta ummanmu tace babu kyau roqo?" Hannu ta miqa ta janyo ledar bayan ta dauke idanunta daga kanshi,ta zazzage hijaban dake ciki. Guda ukune,blue,butter colour,da purple,yadinsu mai bala'in kyau da kauri,tsoro yadan darsu a ranta,wannan ubam hijaban ko cikin lefenta aka sanyo mata shi ta taki babbar sa'a,yo ina ita ina saka wannan hijabin?,saita soma tattarawa tana maidawa ledar "Kai maza ka maida masa,baka da hankali ne bilalu?,bakaga jikinsu yadda yake ba?" Dariya bilal ya saki har yana doka qafa "Wallahi yaya kin cika tsoro,mutumin nan yana da mugu mugun mutunci,Allah idan aka mayar masa baxaiji dadi ba" "Nidai nace ka mayar" "Toki ajjiye,bari ummanmu ta dawo,duka abinda tace shikenan" ta yarda da maganarsa,don haka bata sake ce masa komai ba sai gyaran gashin dataci gaba dayi,ya miqe tsaye yana ture kujerar daya zauna baya "A zuba maka abincin ne?" "Me kuka dafa?" Ya fada yana leqa tukunyar dake saman murhu "Ragowar tsaki ne akayi fate(gote)" baki ya tabe "Tabdi,ni yau abinci me dadi ya bani,harda nama,gaskiya mutumin nan yana da kirki Allah yaaya" baki ta tabe kawai tana jinsa ba tare data tanka masa ba. A hankali ta tuna da mutumin daya ceceta a jiya,kamar ta taba ganin fuskarsa kafin wannan lokacin,zuciyarta tana bata shine ya bada hijabin,saboda banda ita dashi bata tunanin akwai wanda yasan abinda ya faru,don ba'a zancan auwalu ma da baya cikun hayyacinsa,wanda tun lokacin bata sake jin koda motsinsa cikin gidan ba,saita yafito bilalu,ya qaraso yana goge ruwan daya gama sha daga bakinsa. Siffanta masa samir ta shiga yi,ya tabbatar mata shine,saboda duk qauyen kusan shi kadai ne mai irin wannan siffar,data tabbatar da hakan saita sallameshi. Ummansu ce tace ta karbi hijabin,bayan data tsare bilal da tambayoyi ta kira nasidi wada tare dashi aka basu hijabin,ta tabbatar da ingancin aiken,can qasan ranta ta dinga jin dadi da farincikin samuwar hijabin a tare da ita,duk sanda ta motsa saita juya ta daukosu ta bude ta sake gani ta maida,har ta gama tsara lokuttan da zata sanyasu,saboda yadda sukayi mata kyau suka burgeta. ********. ******. ******* Sannu a hankali lokaci ya soma murginawa,murginawar data ke murqushe al'amura iri daban daban,masu dadi da marasa dadi,wasu su bar maka tabonsu,wasu kuma lokaci ya shude dasu yayi tafyar ruwa. A irin hakanne kaltum ke ci gaba da lissafin kwanakin da suka rage mata cikin kwanakin da baban nata ya diba mata akan ta fidda miji,duk ranar da zata fito ya fadi saiya yada mata habaici....baqar magana da kuma munanan kalamai,ya tattara dukkan wani laifi ya aza mata,yace koma meye ya faru itace sila ba wani ba. Daya daga cikin irin wadan nan kwanakin ne,tana zaune a tsakar gidansu tana dinke wasu daga ckkin sutturunsu da suka yage,suke kuma lalabasu don suyi musu dogon zango,ummansu tana gefe zaune suna taba hira tana shafa magani a kan ciwonta. Bilal ne ya shigo afujajan,kai kace wani ne ya biyoshi,yayi futu futu da qasa kamar kullum,alamu sun nuna daga wajen aiki yake ya tsamo yayo gida,saika rantse da Allah jikinsa bai bata ganin ruwa ba. Sallama kawai yayi musu ya urfafi qofar dakin babansu,wanda keda rumfar da yake ajjiye ajjiyensa da basu kai kayan dake uwar dakansa muhimmanci ba,kaf cikinsu babu wanda ya isa ya doshi rumfar bare dakin,tsakaninsu da ita kallo daga nesa,to amma saiga bilal ua dufefeta sa qano irin kazar kazar "Kai bilalu....kai lafiya." Dakatawa yayi daga tafiyar da yakeyi yana duban ummansu "Ummanmu.....na samu me siyan langa langar baaba,yana siya da daraja,zan dauka nakai masa ya siya" "A'ah bilalu,na rabaka,kada ka taba masa kaya,kabar masa abinsa,da kansa idan ya samu me siyan yaga dama ya saida din" "Allah ummanmu idan ya tafi bazai samu me siya yadda yake siya ba.....ki bari kawai a siyar masa,ko yazo zai fara fada yaga kudin bazaice komai ba" sai yayi gaba da sauri zuwa inda langa langar take "Nidai da zaka bi ta tawa bilalu a haqura,kada aje garin neman gira......a rasa ido" "Bazaice komai ba ummanmu,bari kiga" ya fada yana lanqwasata bayan ya daukosu daga inda suke jingine,yana jin ummanmu na qananun mitoci har ya fice daga gidan. Bayan sallar isha'i baban ya shigo gidan,a sannan kaltum tana dakinsu tana gyara 'yan tsummokaran kayan data mallaka. Idanunsa ne suka qyalla masa wajen,saiya fasa bude qofar dakin nasa da ya sanyawa muqulli yake da niyyar yi,ya fara qwalawa umma kira. Tunda taji kiran nasa gabanta ya fadi,ta miqe da hanzari ta fito ta ruskeshi "Waye ya tabamin kaya?,wato rashin mutuncin gidan nan har yakai na ajjiye kaya wani ya saka hannu ya dauka zuwaira?". "Babansu ba taba maka kaya akayi ba,yaron nan ne ya samu me siya da daraja,shine yace bari ya saida maka yadda zaka fi samun riba" "To ni na sakashi?,koni nace masa?,ko kuma nidin makaho ne?,idan inason siyarwar bansan a inda zan siyar ba,to maza a nemoshi duk inda ya shiga yazo ya gayamin yadda yayimin da kayana". Tsam ta miqe daga tsugunnon da tayi,dama irin hakan ta guda ta cewa bilal ya ajjiye masa kayansa,saita qarasa qofar dakin kaltum,tana jinsa yana ci gaba da bambami da fada,ta yaye labulen dakin. Suna hada idanu,tun kafin ummanma tace wani abu ta miqe ta zura hijabinta ta janyo sudaddun slipper dinta ta soma doso qofar dakin,sai umman ta saki labulen ta juya,ita kuma ta biyo bayanta. Tana ta yi masa sannu da zuwa amma ko saurarenta baiyi ba bare ya amsa mata,itama saita qara wuta ta fice waje,lallai saita tattalli bilalu a duk inda ta soma ganinsa,ba yadda ummansu batayi dashi ya bari ba saboda gudun irin wannan amma yaqi yarda,shi ala dole sai yayi abun arziqi. Can ta samoshi gaban teburin abokinsu me saida rake,yasa an kankare masa guda uku,yana ganinta ya saki murmushi "Yauwa yaya,kamar kinsan zancanki nake,ungo riqe min wannan,na ummanmu ne" karba tayi fuskarta a murtuke "Muje ummanmu na kiranka" "Dama ai gidan zani" ya furta yana gabtarar raken da yake hannunsa,ya juya suka jera tare,yanata zuba mata surutu,shi baima damu ko ya kula da yanayinta ba har suka isa gida. Da fara'arshi ya shiga gidan,amma suna hada idanu da baban nasu yayi collapse "Zo nan don ubanka" cikin hargagi yayi maganar,saiya qarasa gabansa. Mari yakai masa yayi saurin duqawa kan qafafunsa,baban ya zaburo "Ina kakaimin kayana?" "Siyar maka nayi baba,sunce suna so ne,zasu siya da tsada" "Ina kudina?"ya tambayeshi cikin muzurai,kamar zai hadiyeshi,dan jim bilalu yayi,sannan yace "Na karbo,amma nakai kudin wajen mai magani,zan amsowa ummanmu maganin qafarta dashi. Wani irin zagi ya maka masa "Kayana zaka dauka ka saida kace zaka karbowa uwarka magani dashi?,nina dora mata ciwon?,a rasa da kudin da za'a nemo maganin sai nawa?,qarya ma kake munafuki,ni ban yarda sa wannan zancan ba,nafi gasgata sacemin ita kawai kayi,dama an gaya min ka fara dauke dauke,to wallahi tallahi,billahillazi la'ilaha illa huwa.....duk jaranar daka dauko kada ka tunkareni.....ka tunkari uwarka da kake samowa kana bata tana lamushewa.....kai in sha Allahu.....in sha Allahu ma saika dauko jarabar da zata sanya a daureka,naga ta tsiya,matsiyatan banza matsiyatan wofi,tashi ka bani waje dan iska shege...." Sai yakai masa shuri da qafa,yayi saurin gocewa. Ba wanda ya iya motsawa a wajen,saishi daya bude dakin nasa ya shige yana ci gaba da bambaminsa. A sanyaye umma ta kalli bilal "Me yasa kayi haka bilal?,kaga irin abinda nake gaya maka ko?,gobe duk inda kakai kudin kayan nan ka karbosu ka kawo masa abinsa" "Amma ummanmu....." "Dakata,banason jin komai daga bakinka,nidai na gaya maka" daga haka ta yunqura ta miqe,zuciyarta na mata wani irin ciwo,a duniya babu abinda ta tsana irin taji kalaman aibatawa daga bakin babansu akan yaran nata,ta sani cewa bakin uba shima yana da nashi dafin,tana tsoran kada yaje yayi musu illa da nashi bakin. Bayan shigar umman daki harara kaltum tabishi da ita "Meya kaika taba kayansa?,yanzun wa gari ya waya?,ran umma ne ya baci a banza a wofi,saika shige ka tafi,kaji dadi" ta juya zata shiga daki,saiya zabura ya bita da rake "Ki karba yaya don Allah,fadan baba ya riga ya saba,bazai daina ba,in sha Allahu ma na kusa yin kudi mu huta" murmushin da bata shiryawa ba ya subuce mata,ta amsa raken tana dungure masa hannu "A hakan,bayan kaqi karatu?" "Zanyi fa yaya,idan na fara ma bazan tsaya ba,ba abokina din nan yace zai dauki nauyina ba?" "Allah yasa"ta fada tana ji masa sha'awar yin karatun "Bari naje na kaiwa umma nata,tana can ta damu kanta" saiya miqe ya wuce dakin ummansu,kaltum ta bishi da kallo,sau tari idan yana wani abun kamar shine gaba dasu ita da habiba,yana da qarfin gwiwa,tare da jarumtar daukar nauye nauye koda wadanda sukafi qarfinsa ne. Bai jima ba kuwa ya fito yana dariya,da alama ya saukar da umman nasu. *Bayan kwana goma* Kusan qarfe takwas ne na dare,amma har a sannan tana bakin murhu tana fama da hayaqin itace,saboda dare da sukayi wajen dora abincin daren,sakamakon rashin kawo abincin da maigidan baiyi da wuri ba,don bai shigo musu da abinci ba sai magariba,sai 'yan kame kame da sukayi,da ragowar abincin da bilal ya kawo musu wanda samir yaci ya rage mai yawa ya bashi,ya taho kuwa dashi ya kawowa ummansa da kaltume,yana ta basu labarin kirkinsa,da yadda yake sanyasu salla daga zarar lokacin sallah ya shiga,duk kuwa irin aikin da akeyi. Daga can rumfar baban nasu kuwa yaya munzaline,wanda yaxo tun dazu suketa maganganunsu shida baban,babu kuma wanda yasan abinda suke cewa,saidai daga yadda fuskar baban take a washe zakasan cewa cikin farinciki yake. Wannan kuwa ba baqon abu bane a wajensu,don tunda mahaifiyarsu munzalin ta fara yi musu aike,ya kuma zamana da kasin baban a ciki ya sake dinkewa da yaran nasa. Ba jimawa saiga muzammilu ya shigo,shima yabi sahunsu ya samu waje ya zauna bayan ya gaida umma a tsaitsaye. Hayaniya ce tafara tashi a farfajiyar gidan nasu,tun tana tashi kadan kadan har tayi qarfi,wanda hakan ya tilasta baba sanya munzali yaje ya gano meke faruwa. Ba'a jima ba sai gashi ya shigo "Yaron nan yaushe ya fara dauke dauke?" Duk saida maganar taja hankalinsu,baban ne ya tambaya "Wanne yaron kenan?" "Bilalu mana" Ai yana kaiwa qarshe baba ya saita takalmansa yana fadin "Dan kuka,ya jawowa ubansa jifa kenan?,me yayi kuma?" "Wai kayan aikin makarantar mai tafasa ya sace wasu daga ciki" "Uhumm,ya kuma kenan,ai dama idan ka daurewa yaro gindi wahala ya sameka,nan ya daukarmin langa langa ya saida ya cinye kudin,uwar bata iya tabuka komai ba,to saiki taso kije kiga gingimemen aikin da danki ya janyo miki" yana kaiwa nan yayi gaba,munzali da muzammilu suka take masa baya. A rude kaltum dake tsaye ta dubi ummansu,har yanzu bata fasa aikin tsinke zogale da takeyi ba,kai bakace da ita ake ba,kamar kaltum zata saki kuka tace "Ummanmu....ki taso kije" bata daga kanta ba ta amsa mata "Na taso nayi me?" Jin hakan sai kaltum din ta kasa jumurin jira,cikin hanzari ta nufi qofa. Gidan nasu ya cika kamar wanda ake wani dan biki,bilal na tsakiya kamar an samu nama,tsakanin babansu da munzali,harma da muzammilu,suna sauraren jawaban qarya daga bakin musbahu,wanda yana kaiwa qarshe,ba tare da baban ya tsaya anji ta bakin bilalun ba yace "Ai nasan za'a rina,tunda ka faro daga gida dama na waje sune al'umma ta gaba.....kai musbahu,kuje,gobe da safe da kaina zan tasoshi har zuwa wajen aikin naku" saiya juya ya baiwa munzali umarni sukai bilal ciki,suka tankadashi sai sashen nasu "Don ubanka ina kayan mutane?" Baban dake tsaye bisa kansa kamar zai hadiyeshi ya fada,cikin qwalla bilal yace "Wallahi baba ban taba daukan kayan kowa ba...." "Qarya kake munafukin yaro.....ba daga kaina ka fara ba?,tunda ba zaka fada ba,munzali ku lallasamin dan banza" ya fada yana ja baya. Ai kuwa tamkar suna jiransa ne suka hau dukan bilal babu ji babu gani,irin duka na rashin hankali,dukan da babu tsari a cikinsa,duka tako ina,duk inda suka samu ko hannunsu yakai nausa suke,tun yana iya jurewa har ya fara zabga ihu yana neman taimako,kaltum ta kasa daurewa,ta durfafesu cikin qaraji tana neman su bari,amma ina,babu wanda ya saurareta a cikinsu,saima duka da munzali yakai mata,wanda dama tun wancan lokacin bai huce da ita ba "Tofa....qauna,saboda soyayya shine zaki hana a hukunta yaro,tunda ya fara dauke dauke kuma wa yasan me zai faru naj gaba?" Inna laure dake tsaye abinta daga bakin qofa tana shan kallo tavfada hankalinta kwance,kamar ba dukan daya wuce qa'ida sukema bilal ba. Kuka ta fashe dashi ganin yadda bilal din ya zube gaba daya ya daina yunqurin qwatar kansa sanda suka kaima cikinsa suka kusan a tare munzalin da muzammilun,a gigice tayi wajen ummansu "Ummanmu,don Allah ki hanasu.....zasu kasheshi wallahi,kinga ya fadi fa ummanmu,kice wani abu....... 28 D/z *wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa* 08184017082 Ko kuma 09134848107 Wani irin miqewa tayi da hanzari,har tana hankade kaltum dake duqe a gabanta tana son tace wani abu "Kada wanda ya sake tabamin yaro a cikinku" muryar ummanmu ta ratsa tsakanin ihun bilal da dukan da suke masa. Tsabar mamakin da sukaji ya sanyasu tsaiwa cak daga abinda sukeyi din,kowannensu ya waiwayo cike da mamaki,mamakin jin kalma daga bakinta dangane da danta a rana ta farko a lokaci na farko,tsahon zamansu da ita,tarin kawaici dauke kai gami da haquri dake cikin dabi'unta yau dukka ta kauda,basu taba jin kalma makamanciyar wannan daga bakinta ba,sai a yau din. Idanu dukkansu suka zuba mata sanda take takowa inda bilal ke kwance hajaran majaran,idanuwanta na tara ruwan qwallar da taketa bakin qoqarin hanata zubowa. Hannu ta sanya zata dago bilal din,muryar babansu tayi mata waigi "Sakeshi,kada ki kuskura ki tabashi" ya fada cikin fushi,bata fasa sanya hannu ta daga shin ba kamar yadda ya haneta,ta miqar dashi tsaye,tsaiwar daya kasa yinta da kyau,saida kaltum ta rugo ta tayata riqeshi. "Zuwaira!,ni nake bada umarnin a hukunta min dana,gaban 'ya'yana kike nuna musu ban isa ba?,bayan rainin da kika saka suka riga suka gama yimin shi?,ni zaki hana hukunta dana,nace kada kiyi ki aikata?" Yana fada cike da kunya da kuma mamakin yadda a yau ta saba umarninsa,abinda bazaice ga ranar data taba yinsa ba tsahon zamansu da ita "Tabdijan,to wallahi wallahi billahillazi ba'ayi matar da zan bada umarni a gidana ta bijire ba,ba'ayi matar da zan gyatta kara ta tsallake ba.....duk zuba miki idanun da nayi kika lalata min yaro bai isheki ba?,to ki tattara ya naki ya naki ki tafi gidanku.....kai munzali.....muje"ya fada yana saba babbar rigarsa yanayin gaba kamar zai tashi sama,sai suka mara masa baya suma ba tare da sun tsaya jiran komai ba. Kalmar ta tafi gidan nasu ta shigeta da wani irin qarfi da ba zata,kalmar da bata taba shiga tsakaninsu ba kenan tunda sukayi aure,sanoda haqurin datake hadiya a kulli yaumin,bata taba kawowa ranta amadun zai iya gaya mata haka ba,a tsayin shekarun da suka kwashe a tare,rauni ne sosai ya mamayeta,yayin da tausayin mahaifiyarta ya rufe kaltum,ta san tsoronta,tasan fargabarta,tasan dalilin daya sanya taji rauni akan kalmar taje gidansu. "Mu tafi ummanmu,mu tafi mubar masa gidan kamar yadda ya buqata" kaltum ta fada da wani irin emotion me taba zuciya,a lokacin da suka sanya bilal a gaba,wanda har yanzu dafe yake da cikinsa. Kai umman ta girgiza "Babu abinda zamu kaltume,bamu da inda ya wuce nan din,koda zan tafi ku baku da gidan daya wuce nan,nan ne gidanku,a nan zaku ci gaba da zama" sai muryarta ta fara rawa,da alama kuka keson cij qarfinta,kukan da tuni kaltum ta fashe da nata,ganin irin murqususun da bilal yakeyi. Basu gushe ba suna zaune a haka tsahon kusan awa guda suka sake jin tafiyar mahaifin nasu,kowanne yayi sak yana duban hanya. Turus yayi daga nesa yana qare musu kallo,cikin wata hargoqa da hargagi ya fara nunata da yatsa "Ba cewa nayi ki tattara kayanki ki tafi gida ba?,to ki hada ya naki ya naki,na baki minti goma,ki tabbatar kafin na fito daga daki babu ke a wajen nan,yau zaki gane idan ina da amfani" daga haka yayi fuuu ya wuce dakinsa ya bankada ya shige. Tsam ta miqe daga tsakiyarsu ta nufi dakinta,kaltume ta rufa mata baya cikin kuka kai taba zuciya,tana tsaye umman tasu ta zari kayanta guda uku ta zura hijabinta sannan ta juyo ta sake fitowa,kaltum ta biyota tana cewa "Ummanmu.....ki tsaya na dauko mana kayanmu kinji don Allah" waiwayowa tayi ta dubesu,cikin muryar dake nuna nauyin abinda take dannewa "Ba inda zaku kaltume,nan ne gidanku,baku da inda ya wuce nan...." "Ki tattara tsiyarki su biki,babu wanda zai zaunar min daga ita har shi,yara kamar yaran Allah bani,maza kubi uwarku" ya fada yana watsa hannu,kamar wanda ke kaɗa kaji dake son yi masa ɓarna. A sukwane ta shiga dakinta ta figi hijabinta,ta tazo ta taimakawa bilal suka rufa mata baya duk a cikin hanzari,ganin cewa tuni har ita din tayi gaba. Tsaiwa tayi da tafiyar da take sanda tajiyo takun sawunsu a bayanta,ta waiwayo tana kallonta tana riqe da bilal "Me yasa zaku biyoni kaltum,ko kuma gidan mahaifinku,can ne marufar asirinku" "Kiyi haquri ummanmu,ba zamu iya komawa ba,ba zamu iya barinki ba,koda zamu koma ma ummanmu ta yaya zamu barki a irin wannan daren ke daya ki tafi har gidan inna?,barema tunda ya koreki tare ya koremu". Tsaiwa tayi tana hadiye wani abu mai tauri daya riqe mata maqoshi,tana kallon yadda take riqe da bilal cikin ciwo,ko ina na jikinsa rawar sanyi yake saboda duka,da alama zazzabine ke shirin kada shi. Itama tanajin wani wawakeken rauni na shirin kama zuciyarta tun daga wannan lokacin na rabuwa dasu,bata ce su koma saboda fushi ko qyamata ba,ta fada ne saboda nuna musu muhimmancin mahaifinsu cikin rayuwarsu,an kai gabar da bazata iya sake cewa su koma ba,don haka ga juya taci gaba da tafiya suka mara mata baya. Kafin sukai gidan innar sun shafe lokaci mai da tsaho saboda yanayin jikin bilal,ga kuma tafiyar qasa,hakan ya qarawa dare tsaho kafin su isa,don har sunyi tsammanin ma zasu taras da gidan a garqame,saidai sun taki sa'a,gidan yana a bude ne,amma kuma an sayashi,da alama gab ake da rufeshi. Sallama kusan hudu umman tayi amma ba'a amsa ba,saita qarasa zuwa qofar dakin mahaifiyarta ta daga labulen tana sake maimaita sallamar. Saman gadonta na rufa ta hangeta a kashingide daga baki baki,da alama bacci ne ya kwaeheta ba tare data shirya hakan ba,saita saki labulen tana komawa da baya,ta dubi su kaltum "Muje,inna tayi bacci" ta fada tana yin gaba,tare da duba dakunan dake cikin dakin,ta bude musu daya daga ciki,wanda babu komai ciki sai sumunti da tabarmar kaba. Cikin kayantabta cire zani ya shimfidawa bilal saman tabarmar,kaltum ta taimaka masa ya kwanta,dukkansu idanuwansa a kansa yadda yake murqususu,zuciyar kaltum ta sake karyewa,cikin hawaye tace da ummansu "ummanmu.....ruwan zafi ya kamata a saka masa a jikinsa fa,idan ba haka ba bazai iya barci ba" ita kanta tasan da hakan,amma batason daga shigowarsu gidan su taba wani abun na innar ba tare da saninta ba. Saidai kafin ta qare tunaninta tuni har kaltum ta isa kitchen din innar,ta kuma fara hada wuta,babu jimawa ta dora ruwan,bai dauki lokaci ba ya tafasa,ta juyoshi ta nufo inda dakin da suke ta ajjiye a tsakaninsu,sannan ta taimaka masa ya tashi ya zauna da qyar yana nishi yana numfarfashi. Dankwalin ummansu ta karba ta fara gasa masa jiki,tuni ya fara nishi yana kiran wayyo Allah,duk inda tasa ruwan mai zafi zafi ta danna masa sai ya saki ihu cike da radadi yana murgina kai yana cije labba. Ihu ihun bilal din ya farkar da inna a firgice,saura kadan tayi adungure daga saman gadon nata zuwa qasa,sai data kaza kunne,ta tabbatar bil'adama me sannan ta zame ta sauko daga gadon dankwalinta a hannu tana sauri kamar zata ci da baka,tanason ganin wadanda suka shigo gidan. Ta tur qyauren dakin dai dai sanda kaltum ta gana gasa masa jikin,ta kuma maidashi ya kwanta "Me zan gani haka ni zainabu?,zuwaira?,meye haka?" Ta fada cikin hargagi da masifarta wadda ta riga data zame mata jinin jikinta "Wallahi mune innah" sosai ta shigo dakin tana qare musu kallo "Aina gani,naga kune din,yo meye haka za'amin irin wannan gangankon da tsakar dare a diro min gida ba tare da masaniyata ko izini na ba?,kamar masu fashi da makami?" Dan shuru umman tayi,tana fasalta da harshen da zata yiwa inna bayani "Ki bude baki kiyimin magana,keda 'ya'yanki kun yimin duru duru" tayi maganar tana rungume hannayenta a qirji,tana kuma sake zubawa inna ido "Inna,mun samu sabani ne da baban habi,shine yace na taho gida" wani dan zakudawa innar tayi kamae wadda ta taka wani abu,kana ta daidaita tsaiwarta "Shine sai kika tattaro qwanki da qwarqwatarki keda ahalinki kaffff kika taho gidan inna mai masaukin baqi ko?,wadan nan marasa kunyar 'ya'yan naki,gaskiya ba'a taba rainamin hankali ba irin yau....to banda ma zuwaira ta yaya kike tunanin zan amsheki a gidana?,koda ke daya ce bare keda bataliyar wannan yaran haka saket,wato nice me wuyan dauka ko?...." Sai innar ya ranqwafo dai dai saitin umman "To na rantse da aradu badai a gidana ba,babu masaukinki a gidana,saboda haka sahunki a likkafa kisan inda kika kama,badai nam ba,bare azo a dauramin nauyin babu gaira babu dalili".. "Ke kuma keda wa kike ta maganganu?" Muryar jafaru dake riqe da leda ta ratso dakin "Wacece idan ba zuwaira ba,haka kawai ta debomin bataliyar tara tayo yaji dasu,na riqeta na riqe mata 'ya'ya,uban daya haifesu ba yaqi su bare ni karan kada miya?" Qaraso shigowa dakin jafaru yayi,ya ajjiye ledar hannunsa a gefansa yana cewa "Wallahi na zaci ma wasune,ashe umma ce,yanzu inna banda abunki,umma zuwaira ai dolenki ce,ko 'ya'ya dari tazo dasu kuwa" "A'ah,bada ni ba sa lallen karya,'ya'yana ne suke dawainiya dani,banga dalilin da za'a doramin nauyi ba,saboda haka dole ta tattara yanzu yanzu ba anjima ba tasan inda dare yayi mata". Tun jafaru na daukar abun da wasa har ya haqiqance da gaske inna take,duk irin mamakin da yake kanta saida mamakinsa ya ninku,qarshe ma ya fahimci cewa qoqarin sata ta barsu su zauna da yakeyi qara damal mala al'amarin kawai yake,don haka saiya sauka daga wannan bigiren,ya soma yunqurin qyalesu zuwa safiya,idan Allah ya kaimu wayewar gari,da qyar yasha kanta,ta fice tana maganganu tare da kumfar baki "Saboda kinga akwa wadatar dakuna,to dakuna na bana zamanku bane,ba kuma gadon ubanki a ciki bare kice ban kyauta ba,ubanku bai barmin komai ba a gidansa sai wancan rugurgujajjen dakin,nan duka arziqin ubansu indo nake ci". Tunda ta fita dakin ya dauki shuru,tsakaninsu babu mai iya cewa komai,baka jin komai sai nishin bilal,wanda ko sau daya inna bata ma damu ta tambayi me ya sameshi ba,burinta kawai su fice mata daga gida shine abinda ya dameta. Cikin hijabi kaltum ta shige ta dinga ruzgar kuka,gani take kwata kwata basuzo duniya a sa'a ba,kota wanne bangare qyamata ce da baqinjini yake bibiyarsu,tana iya jin yadda ummans keta sauke ajiyar zuciya akai akai,kamar qaramin yaron da aka yiwa shegen duka. Tun bilal na nishi lokaci lokaci yana cewa "Wayyo Allaj cikina" har wani wahalallen bacci mata dadi yayi awon gaba dashi. Duk yadda kaltume kejin wannan daren bacci yayi kadan ya dauketa amma sai daya gwada mata qarfa qarfarsa,can tsakiyar dare sanda suke zaune ita da ummanta,kowa tunaninsa yayi nisa kan meye makomars a gobe da safe idan inna ta tsaya kan ra'ayinta na su bar mata gida?,da wannan tambaya mai nauyi da firgici baccin ya sureta. Ƙaqqarfar bugun qofar da aka yiwa dakin ta samu nasarar ratsawa har cikin tsakiyar baccinsu,ya haifar musu da farkawa gaba dayansu a firgice daga dan gajeran barcin da ya wafci idanuwansu,duka kowanne ya miqe ya zauna daram saman mazaunansa suna duban qofar,yayin carar zakaru ke tashi daga wancan gida zuwa wannan gida,da alama a yanzu ne assalatu tayi. Inna ce tsaye a kansu tana dubansu,kai kace daren jiya batayi barci ba,kamar ta zauna gadin daren ne tana jiran asuba tayi "Saiku tashi ko?,kusan inda dare yayi muku" ta fada kanta tsaye,tana sake matse fuska. Mamaki maganarta ta basu,kaltum takai dubanta ga tsakar gidan,dudum yake,duhunsa bashi da maraba da tsakiyar dare,hakan kuwa ba abun mamaki bane,saboda ko salla ba'a shiga ba a qananun masallatan dake qauyukan "Wai da gaske kike inna?,to ina zamuje?" "Ki tambayi uwarki!" Innan ta fada tana zazzaro idanuwa,tare da nuna ummanmu da yatsa,waiwayawa tayi kuwa ta kalli ummansu,wadda ta sad da kai "Duk yanayin data samu kanta ita ta jama kanta,babu yadda banyi da ita kada ta haifeku a gidan nan ba,ta fito ta samu wani mai damshin arziqin ta aura amma taqi,sai data tara ku kuma sannan yanzu haka kawai saita debomin wallahi,to ba dani ba sam,duniya da girma da fadi,ai maye baya ci kansa ba" ta fada tama riqe da qugunta kamar qaramar yarinya "Kiyi haquri inna zuwa gobe,ko anjima gari ya sake wayewa....zamu tafi" cewar umma cikin sanyin murya,a karon farko kenan tsakanin jiya da yau a aka fara dambarwar "Me? Inji akuya?,idan kin isa shegiya nake,billahillazi kinyi kadan,ko sakan bazan qara muku ba,ku tashi ku fita?,idan kunqi kuwa saina tijara ku" ta fada cikin bambami da daga murya "Qofar gida zan tsaya ma naga fitarku,wallahi bame qara yimin minti guda a guda" ta sanya kai tana shirin ficewa daga dakin sukayi karo da jafaru "Wai inna maganar ce ne da farar safiya ko ince tsakar dare?,haba inna,ko gari ai kya bari ya gama wayewa ko?" Ya fada cikin jin takaicin halin innar "Kai jafaru,kai jafaru,kai jafaru,sau nawa na kira sunanka?,ba sau uku ba?,to wallahi wallahi ka fita daga idanuna,idan ka qara magana a nan saina tsintstsinka maka mari" tafada tana huci gami da zare masa ido,ala dole yaja bakinsa yayi shuru yana kallo tana ci gaba da tijararta har zuwa qofar gida,fadi take "Ki fito ku barmin gidana,wallahi sai kun tafi,ku fita ko nasa a fitarmin daku" cikin daga murya,wanda sautinta ya karade dukka maqotan take gefe da gefe gaba da bayan gidansu,ya kuma fara jan hankalin jama'a wadanda suka tattashi domin bada farali na sallar asuba,masu fita zuwa masallaci maza,dama mata masuyin sallar a cikin gidajensu. Kafin kace meye mutane sun dan fara tattaruwa,dai dai sanda ummanmu dasu kaltum ke fitowa a gidan,kaltum na riqe da bilal da har yanzu jikinsa baiyi qwari ba,ummansu na riqe da 'yan kayanta data debo. Fitowarsu tasa jama'a suka koma kallon kallo,kowa ka kalla fuskarsa cike da alhini da kuma mamaki,anya kuwa innar kanta qalau?,wasu daga cikin jama'ar suka soma yiwa kansu tambaya,wasu kuwa sun riga da sunsan lafiya ras take,saboda sanin hali yafi sanin kama,kowa Yasan innar yasan abinda zata aikata da wanda ba zata aikata ba,a tsahon shekarun da take zaunen a nan,duk mutumin daya zauna da ita ya santa da halaye gusa biyu datayi shura dasu,zallar masifa da kuma son abun duniya,ba shakka iya wadan nan dabi'u kawai sun isa suyi mata jagora ga abinda ta aikata din a yanzu. Suna sake nisa da ita kunnuwansu na sake kasa kama maganganu da hargowar data ke musu,idanuwan ummanmu a wannan karon sun gaza riqe ruwan hawaye da suka danno cikin idanuwanta,irin abinda innar tayi mata a yanzu yana cikin lissafin irin abubuwan da take zato tunani ko mafarkin innar zata iyayi mata a rayuwa,ta shiga matuqar rudani da mamakinta,ta zaci koda bare ne wanda innar bata sanshi ba bawai gudan jininta ba bazata aikata masa haka ba,wai dama haka qin jininta yayi nisa cikin ran inna?,laifinta kawai don babansu bashi da komai,bai mallaki abun duniya ba har ya mutu?,laifinta don taqi kashe aurenta sanda arziqi da dukiyar amadu ta durqushe?,ta gaza tantance wanne ne laifi cikin abinda ke faruwa,dabi'ar da inna ke nuna mata lailan wa naharan?,ko kuma ita abinda ta aikata da kuma yanayin rayuwa a mahaifinsu ya sami kanshi kafin rasuwarsa?. "Ummanmu......ina zamuje yanzu?" Muryar bilal dake cike da gajiya da kuma ciwo ta fargar da ita cewa a hanya suke,sai a sanna ta daga kanta,sunyi nisa da gidan inna,zuwa sannan an shishshiga masallatai sallar asubahi "Muje gidan umma altine" kaltum ta amsa masa maimakon umman tasu "Ko umma?'" ta maida tambayar gareta don ta samu tabbacin abinda ta yanke din ya yiwa umman tasu. Har cikin ranta taji bai dace sujewa altine ba,saboda ita kanta neman dauki da taimako takeyi,nauyin dake kanta itama tallafi take buqata,zuwanta wajenta a irin wannan lokacin tamkar rashin sanin abinda ya kamata ne,uwa uba ma ita din qanwarta ce bawai yaya ba,don haka saita girgizawa kaltum kai "A'ah,ba gidanta zamu je ba,itama tana da wasu wahalhalu da dawainiya a kanta....." "To gidan yakumbo indo?" Bilal yayi saurin sake fada,da alama a jigace yake,so yake kawai su samu muhalli ko wanne iri ne da zai bashi damar hutu. Nan ma kai umman ta girgiza "Itama macace,a qarqashin wani take,ba zamuje mu dora mata jigilar mu ba har mu uku" "To gidan kawu ado" wannan karon kaltum ce ta fadi haka,shuru umma tayi,yayin da suma dukka sukayi shurun suna dubanta,daga kai tayi,sai taga dukkaninsu ita suka zubawa ido suna jiran suji amsa "Shikenan,muje can din" ta gada tana riqe hannun bilal da kyau,don kaltum ta samu ta huta itama,don tafiyace miqaqqiya a qafa daga nan zuwa gian kawu ado,tunda babu wani abun hawa sa zasu hau da zai rage musu wahalar tafiyar,a qalla zasu iya shafe awanni biyu kafin sukai. 29 D/Z *wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa* 08184017082 Ko kuma 09134848107 Kafin su iso gidan kawu ado gari yayi haske tarwai,don har wasu daga cikin mutane sun fara fita zuwa sabgogin gabansu na rayuwa. Area din da gidan kawu ado yake,area ce mai dan kyau,saboda akwai gidajen dake da ginin bulo ma,kamar yadda gidan kawu adon yake ginin bulo,da malalen siminti a tsakar gidansu,wanda hakan yasa gidan ya bambanta da sauran gidaje wansa jar qasa tayi musu qawanya har cikin tsakae gidajensu. Da sallama suka shiga gidan,matarsa dake cikin dakin girki ta amsa tana leqo da kanta daya dan rage girma saboda hayaqin icce da take amfani dashi. Suna hada ido da umma saita miqe tana fitowa daga dakin girkin "Lale maraba,kune a tafe?" Ta fada fuskarta a washe tana qoqarin goge fuskarta,gefe daya qasan zuciyarta tana mamaki "Wallahi mune tsaiba,kin ganmu da sassafe ko?" Murmushi tayi tana qoqarin karbar kayan hannun umman,don tsaiban badai kirki da daraja dangin mijinta ba "Ah haba dai yaya?,wacce safiya?,bayan yara ma duka sun wuce makaranta?,ku shigo daga ciki mana" ta fada tana yin gaba,umma bilal da kaltum bita a baya,tana sake musu barka da zuwa. Faffadar rumfarta dake malale da leda da kujeru 'yan duƙui duƙui suka shiga,ta ajjiye kayan itama tana zama idanuwanta kan bilal "Bilalu,zauna a hankali,amma dai bilalu babu lafiya ko?" Murmushin da yafi kama da yaqe umma tayi "Baya jin dadi" "Haba ai na gani,Allah ya sawwaqe.....ina kwana yaaya zuwaira" taqarashe zancan nata tana hadewa da gaisuwa zuwa ga yayar mijinta "Lafiya lau tsaiba alhmdlh,ya gida ya yaran?" "Lafiya qalau yaaya" "Adon baya nan ko?" "Wallahi ya fita ta'aziyya yaaya,amma ba nisa yayi ba,nan unguwar dake kusa damu ne,bazai jima na,natabbatar yana hanyar kusa da dawowa" "To shikenan"umman ta fada,sai tsaiba ta miqe "Kaltum,zoki karbqr muku abun kari" cewar tsaiban tana ficewa,ba tare da jinkiri ko bata lokaci na kaltum ta rufa mata baya. Kunu ne mai zafi ta zuba musu cikin kwanon sha,sai 'yar tsala data ji mai da quli mai dan yawa itama da duminta. Bilal da bai wasa da cikinsa tuni ya miqe ya zauna ya fara kaiwa cikinsa,duk sai suka zuba masa ido cikin yanayin tausayawa suna kallonsa,kaltum ta janyo kofi guda biyu ta zuba kunun,ta miqawa ummansu daya,saifa girgiza kai "Kusha kaltum,bazanci komai ba yanzu" narkewa kaltum tayi kamar zata saki kuka "Don Allah ummanmu kisha,yana da yawa fa bare kice bazai ishemu ba" ganin yadda kaltum din tayi yasa ta miqa hannu ta karba,saidai iya kunun kawai ta iya sha,tana sha shi dinma tana ji yana tsaya mata a wuya. Koda suka gama kaltum saita tattare kwanukan ta fice dasu,ta hada cikin wanke wanken da tsaiban bata samu yi ba ta ja ruwa mai yawa ta fara wanke mata su,tana mamakin meye amfanin su sahura da karimatu da bazasuyi mata shi ba kafin tafiyarsu koma ina ne,tanayi tsaiban na janta da hira har ta kusa gamawa,dai dai lokacin da kawu ado yayi sallama ya shigo gidan. "A'ah'ah....batan kai kikayi ne kattume?" Kawu ado ya fada yana murmushin mamakin ganin kaltum din a gidan,saboda yasan halinta na rashin son zuwa gidan mutane,tana murmushin maganar daya fada din ta gaidashi "Aiba ita kadai bace,ita da yaya zuwaira ne,tana ciki" tsaiba ta fada ganin yana shirin zama "Au to....ma sha Allah,bari na samesu" saiya qara gaba zuwa dakin,ya cire takalmansa ya shiga,ganin haka yasa kaltum data gama wanke wajen ta kife mata kwanukan,sai tayi zamanta a nan tsakar gida ba tare data koma cikin dakin ba. Kusan awa guda ya kusa shafewa a dakin,batasan me suke tattaunawa ba,taga dai daga bisani kawun ya fito ranshi a bace,ya kuma baiwa tsaiba umarnin a sake share musu dakin,zai aiko da ledar tsakar daki a shimfida musu,ta samu labule ta saka musu window da qofa ta amsa masa da to. Ba'a kai dare ba kuwa aka shimfida musu sabuwar leda,sai labule da tsaiba ta kafa musu,ta kuma basu babban zanin gadonta saboda kwanciya. Su zasu dinga kwana na cikin dakin,bilal kuma za dinga kwana tare da yaran kawu ado maza. Kwanakin da sukayi cikin gidan hankalinsu a kwance yake,babu rashin ci babu rashin sha,babu kyara,babu tsangwama,tsaiba nada kirki sosai,hakanan yaranta basu da matsala,idan ka dake karima da sahura,wadanda suke jin kansu da nisa,hatta tsaiba da take a mazaunin uwarsu ba wani mutuncinta suke gani sosai ba,kowa yasan halin kaltum,bata daukan raini,don haka tunda tazo gidan taja jiki dasu,babu abinda ke hadasu,ko dakinsu ba shiga suke ba,sai idan zasu gaida ummansu. Komai na tafiyarmusu lafiya,saidai ta lura umman nasu na cikin damuwa,ga yarinta da quruciya irinta kaltume,bataga wani abu da zai sanya umman nasu damuwa ba,bayan Allah ya musu sauyin wajen zama,zasu ci susha su qoshi ba tare da sun sha wahala ba,babu mai gaya musu baqar magana ko ya bata musu rai,ita kam bata ga wajen daya fi nan ba,addu'arta ma su dawwama a nan,suyi zamansu kawai. *******Bayan sallar magariba ne suna cin tuwon dare ita da ummanta a kwano daya bilal ya shigo,tunda ya futa sallar magariba sai yanzu a dawo,mutum ne shi mai saurin sabo,gashi na jama'a,don kwata kwata bashi da qyuya ko son jikinsa,hakanne yasa duk inda ya shiga zaka ga nan da nan ya saba da jama'a. Zubewa yayi saman tabarma yana yamutsa fuska,umman ta kalleshi "Kai kuma fa?" "Ahto,tambayeshi umma,tun shekaran jiya ya dauki wannan sarar ta yamutsa fuska da riqe ciki,a yanzu dai babu yunwa ko qishirwa bare kayi mata sharri" "Ni tunda muka zo gidan na ban taba jin yunwa ba,kawa dai cikina ne yakemin ciwo" tsaiwa da cin abincin ummansu tayi "Tun yaushe kenan?" Dan jim yayi kafin ya amsata "Gaskiya tun washegarin ranar dasu yaya munxali suka dakeni" tsame hannunta umman tayi daga kwanon abincin,sai kaltum tace "Ai dole kayi ciwon ciki,har cikinka suka nausa fa,saidai Allah ya saka maka,azzalumai....." Kallon da umman dake qoqarin kwance habar xaninta ta watsa mata yasa ta tsuke bakinta,ta ciro naira dari biyu,cikin irin kudaden da kawu ado yake bata duk idan zai fita "Habibu ya rakaka dan case dincan da ake baka magani,ka siya maganin ciwon cikin" sai yasa hannu ya karba yana miqewa "Tsaya na rakaka,kada kaje ka musu shirme" kaltum ta dakatar dashi tana miqewa,saita fita waje ta wanko hannunta,sanna ta fara lalubem hijabinta. Kallon hijabin tayi sanda take zurawa a jikinta,wanda ya bata kyautar hijabin ya fado mata arai,ba qaramin jin dadin hijabin take ba,don yana rufa asirin kodaddun suturar da take dasu,kamar bilal yasan tunanin a takeyi kuwa yace "Oganmu na wajen aiki zaita cigiyata,sai ya jini shuru" ya fada cikin yanayin dake nuna kewa da alhini "Nima ina saka hijabin na shi na tuna" kamar kuwa an wa bilal susa a inda yake masa qaiqayi ya shiga bada labarinsa,irin yadda yake kyautata musu,har suka fice daga gidan labarin da yake bawa kaltum kenan. A dawowa suka samu sahura qofar gida tana zance,tana ganin dasowar kaltum din ta hade rai tayi kicin kicin,ganin haka sai kaltum din itama ta dauke kai suka shige da bilal da qwayoyin magungunan da aka bashi. Duk da maganin daya soma sha dai ciwon sai a hankali,idan yasha maganin yana samun relief na murdawar ciwon,saidai bayan wani lokaci sai kaga yadawo,ganin haka yasa kawu ado ya daukeshi da kansa ya kaishi wani asibiti na sha katafi dake gaban qauyensu aka hada masa magunguna,kusan wuni sukayi a can din saboda babu wadatar ma'aikata,ga ubam himilin masu son a rubuta musu magani,hakan ya sanya a gaggauce suke komai,daka gaya musu abina yake damunka,babu wani dogon jira ko bincike zasu rubuta maka ganin da suke ganin shine ya dace da ciwonka ka qaro gaba. Satinsu daya a gidan saiga habiba,tazo ta dinga kuka,wai don me zasu tafi basu gaya mata ba,sai dataje gida ta taras basa nan,yanzu haka daga gidan inna take,tace batasan inda suka nufa,sai da Allah ya kawo mata jafaru ya gaya mata,yace amma ita kanta innar batasan suna gidan ba. A nan ta wunu ummansu tana lallabata don kada taqi komawa gida,ta cika tayi fam dasu munzali da babansu,tace inda tasan abinda ya faru kenan,ko barkar matar muzammilu ba zata je ba,suka hadu sukayita tattaunawa ita da kaltume,shidai bilalu da ciwon cikinsa ya motsa yana kwance yana jinsu,kafin daga baya bacci ma yayi awon gaba dashi. Washe gari saiga inna ta duro,basusan a inda taji labarin suna gidan ba,ta dira da masifarta da bala'inta,da kuma maganganu masu tsauri marasa dadin ji "Wato ke zuwaira kin zama kaska raɓi me jini?.....to nan dinma ba gurin zama kika gani ba,tunda dai ado bake kika haifamin shi ba,ki tattara kayanki ki sake sabon lale" Maganar tayi mugun daga hankalin ummanmu,ashe dai da gaske bata da wani gata sama da gidan amadu?,duk da irin abinda yake mata?,ashe idan ta baro gidansa da gaske wajen xama ma saiya gagareta?,ashe gwara data dinga hadiye abubuwan data hadiye din shekaru masu dama?. "Kiyi haquri inna,nan din dai gidana ne,mallakina ne,kuma dana bar yaaya zuwaira ta zauna ban sabawa Allah ba,tunda bata da wani wajen daya wuce nan,taje gidanki kin korota,kuma sannan nima kice na koreta?,bazan iya ba,a nan zata ci gaba da zama har zuwa sanda Allah zaiyi ikonsa" amsar da kawu ado ya bata kenan alokacin data umarceshi ya fatattaki umma daga gidan cikin bacin rai da takaicin halayyar innar tasu,daga haka ma saiya fice daga gidam gaba daya yadda ba zata samu damar ganinsa ba bare ta turasashi aikata abunda bazai iya ba. Ai kuwa ta baje faifan masifa da bala'i da kuma cin mutuncinta,har tsaiba ranar ta amshi rabonta,duk da tarin kirkinta ranar ta fada komar inna. Itadai umma tana daki tana kuka kaltume da bilal na tayata,basu samu sauqi ba har sai data taɓo ƴan rashin kunya sahura da karime shka wanketa fes,suna jinta tayi qus bata iya ce musu komai ba,saita fara tattara ya nata ya nata ta lalubi hanyar gidanta. Kawu ado bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i,koda ya dawo sai daya fara shiga wajen umma ya ganta,haƙuri ya dinga bata yana kwantar mata da hankali kan babu inda zata in sha Allahu indai shine me gidan. Murmushi tayi wanda yafi kama da yaqe,yaqen kuma da yafi kuka ciwo "Babu komai ado,ni nasan komai me wucewa ne banda ikon Allah,amma abinda bake ganin yafi kamar yadda inna tace.....ka nema babansu habi muji ta bakinsa,idan da damar sasanci ma ayi mana" da mamaki kawu ado ya kalleta "Amma yaya zuwaira hakan kuwa zaiyiwu?,kiga fa abinda mutumin nan yayi muku?,amma mu zamu nemeshi bama ni ba?" Sake murmusawa tayi wanda yake nuna zurfin haqurinta "Shi aure ibada ne kamar yadda mai fura(kakarta) tasha gayamin,kuma kome zakiyi cikinsa,kisa a ranki saboda Allah zakiyi da cika umarninsa,babu gidan daya wuce gidan auren mace a wajenta,haquri kuma baya yawa,sannan duk sanda wani ya cuceka kasa a ranka sakayya na nan tahowa a kusa ko a nesa" Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke,kaf yaran innarsu babu wanda Allah ya yiwa baiwar haquri irin zuwairan,ya amince da haka dari bisa dari,inda ason ransa ne babu abinda zaisa su nemi amadu,zai riqe yaaya zuwairan ne har lokacin da zai gane kuskurensa,ya gane amfaninta ya biyo sahunta,iya tsahin shekarun zaman aurensu da amadun,kowa da kowa yasan akwai cutarwa,amma bata taba kai qararsa ba koda ga yan uwansa kuwa,har zuwa yanzu a shekaru fara turawa,to amma shi dui baiga hakan ba,sai shine ma zaice taje gida?,amma a yanzu dole ya sauke nashi shirin yayi amfani da abinda tace,tunda hakan takeso,amma yayi imanin masu juriya haquri da jajircewa,da daukar aure ibada dari bisa dari irin yayar tasa a wannan zamanin qalilanne,badan badan bama da sai yace babu su. Kwana biyu a tsakani da yammaci,suna tsakar gida,kaltum tana yiwa inna tsaiba kitso,umma na saman tabarma sanye da hijabinta,da carbinta a hannu tana jan lazumi suna hira jifa jifa,kawu ado da bai jima da fita ba yayi sallama ya shigo "Amadu ne shida iliya,ke karimatu" ya qwalawa diyarsa kira,wadda ke daki zaune,saita fito "Dauko tabarma ki kawo dakin soro" ta amsa masa ta juya,ta fito da tabarmar takai musu ta dawo,sanna tace da umma taje inji kawun,bismillah tayi ta yunqura ta miqe ta fice soron. Kaltum na yiwa inna tsaiba kitson tana saqe saqe cikin ranta,rabi da rabin hankalinta yana ga soron,saidai ba huruminta bane zuwa idan ba kiranta akayi ba. Suna gama kitson kuwa kawu ado ya leqo ya kirayeta,ta saka nata hijabin tabi sahun ummansu. Shida kawu iliya dinne kamar yadda kawu ado yace,sai cika yake yana batsewa,ummansu na daga gefe ita da kawu ado. A sanyaye ta tsugunna ta gaidasu,ita dai bata kula ba baban nasu ya amsa ko bai amsa ba,ta samu waje kusa da mahaifiyarta ta rabe,sanda kawu ado yace "To gata nan" gyara zama baban nasu yayi yana gyara zaman babbar rigarsa dake saman kafadarsa tare da cewa "Yauwa.....to gata nan,tana daya daga cikin matsalolina na rayuwa,ta samu miji ta koreshi,kwanaki duk inda nabi sai naga ana nuna ni da baki,ana cewa diyata tayi cikin shege shi yasa aka fasa aurenta,kuma babu dama yayyensu din nan su muzammulu su saka hannu da zummar hukuntasu,sai ta haike musu tace bataso.....to yanzu dai duka ba wannan ba,na yarda zata koma dakinta,amma bisa wasu sharudda,idan ta amince falillahil.hamdi,idan bata amince ba taci gaba da zama,don ni bansan da wanne zanji ba,magana ta gaskiya ehe" ya qarashe maganar yana daga hannayensa sama. Gyara zama kawu ado yayi yana qoqarin tausar zuciyarsa "Sharudda kamar wanne da wanne kenan?" Ya tambayeshi yana zuba masa idanu "Yauwa" ya ambata yana gyara zamanshi "Na farko....duk sanda yaron nan bilalu ya sake dauko wani abun maganar,zan wanke masa hannu aka,sannan zan sallameshi daga gidana" wani kallo kawu ado ya bishi dashi,ya yunqura zaiyi magana umma ta dakatar dashi da idanunta "Na biyu kuma....ita kattume,dama ma deba mata kwanakin fidda miji,to tun suna gidan nan kwanakinta sun cika.....zan mata adalci daya,zan qara mata sati biyu kacal ta kawo miji,idan ba haka ba,zan aura mata dan uwanta auwalu kowa ya huta" Ba kawu ado ba kawai,wannan karon gaba dayansu suka daga kai suna duban baban,wala'alla maganarce tayi musa nauyi,sai ya waiwaya yana kallon dan uwansa "Ko ba haka ba iliya?" Kai ya gyada "Wannan haka yake,banda ma lalacewar zamani ai gida bata qoshi ba ba'a kaiwa dawa,sannan duk lalacewar naka ai naka ne,da a zamanin kakannu ne da saidai aji sanarwar daurin aure ma kawai,daga uwa har 'yarta sai a sannan zasusan da batun" ya fadi kamar gaske yana wani tsume fuska. Wani abu ne yazo ya tsayawa umma a wuya,kaltume kuwa tuni ta fara ruwan hawayem baqinciki da takaici,don ji take kamar ma an daura auren da auwalun,tunda dai a zahirin gaskiya ta sani cewa a yanzun bata da wanda zata bugi qirji tace shine maneminta,kawai sun qulla bata shi,shine za'a ce an bata sati biyu ta kawo mijia,ummanmu na ganin sanda kawu ado ya buda baki zai magana kan wannan hukuncin,tuni ta rigashi,ta bude baki da sauri tana fadin............ 30 D/Z 30 "Mun amince indai wannan shine sharadin" da mamaki kawu ado ya kalleta,amma duban data yi masa ya sanya yayi shuru baice komai ba,ya tabbatar akwai sauran bayani a bakinta "Shikenan,wasalam wa kitabihi,kina iya komawa dakinki" baban ya fadi yana miqewa yana kade babbar rigarsa,kawu iliya shima ya miqe,suka bawa kawu ado hannu,baiqi ba ya basu hannu sukayi musabaha kana suka fice daga dakin. Shuru neya biyo baya,sai tashin kukan kaltum,wadda ta kasa haquri jin umman batace komai ba,kamar yadda kawu ado yayi shuru,cikin muryar kuka tace "Yanzu ummanmu,da bakinki zaki amince na auri auwalu?" "Abinda ya bani mamaki kenan,dukkan wata doka da sharudda da naso gindaya masa sun rushe,saima shi daya bada tasa dokar da qa'idar,bansan meye mahangarki ba zuwaira" kawu ado ya fada cike da mamaki kamar yadda kaltum itama ta cika da mamaki,dukkansu suka zuba mata idanu suna jiran jin abinda zata fada "Ba zaki auri auwalu ba kaltume,ba zaki auri auwalu ba da izinin ubangiji,ado......kasan gayawa jini na wuce?" Saiya gyada kanshi yana mamakin tambayar data yi masa. "Sallar dare nada tasiri mai ban mamaki,tasiri mai matuqar yawa,hakanne uasa kadanne daga cikin bayinsa ke ribantarta,take da wahalar da kuma wuyar jurewa,duk kuwa da cewa dukkanmu akwai buqatun da muke nema wajen ubangiji,wanda da zamu tsaya mata.....ba shakka dukka kuka da damuwarmu ta qare,saidai idan har qaddarar hakan bai qare ba cikin kundin qaddararmu,kamar dai qaddarar aurena da amadu.......zanta gayawa ubangiji,....zanta roqarsa,zanta masa magiya game da lamarim kaltume,ina ji a jikina ubangiji zai mata musaya mafi alkhairi,inaji a jikina ubangijina xai share min hawayena,inaji a jikina kukana na shekara da shekaru watan watarana zai zama dariyata,danme zan bata wannan lokaci mai tsaho?,don me zan yanke doguwar tafiyar da jikina ke bani na kawo qarshenta?" Sosai maganganunta suka shigi kawu ado,amma ga kaltum bata fahimci komai ba,bataga wata mahanga ko mafita dange da auren auwalu ba,wanda idan har ya tabbata batajin zata ci gaba da rayuwa a duniya gaba daya,bama iya cikin qauyen ba. Kawu ado ya shirya musu komawarsu gida,gidan da suke masa kallon wani kurkuku mai tarin qunci takura da kuma tsanani,saidai a hakan ummansu ta zabar musu su koma ciki,basu kuma da wani sauran zabi ko ta cewa. Sayayyar kayan abinci masu yawa kawu ado yayi mata,sannan ya damqa mata kudi "Wannan jari na baki,ki nemi abin sana'a don Allah yaya zuwaira,kada ki yarda wannan karon ya amshe miki jarinki ya karyaki bayan bai taba doraki ba" murmushi tayi,ta karba ta kuma yi godiya,tana godew mahaliccinta daya bata 'yan uwa dake qaunarta saboda Allah,ya kuma sanua hadin kai a tsakaninsu,duk da tushiyar bata so ba. Tun daga sanda suka koma kaltum ta lura da wani binbininta da auwalu yakeyi,bini bini saiya mata siyayya ya faki idanun laure ya aiko mata dash,abun yana bata mata rai da kuma ci mata tuwo a qwarya,da alama an fesa masa cewa shi za'a baiwa nan da sati biyu. Idan ya aiko da kayan bata ko kallonsu,saboda ummansu ta hanata ta dinga maida masa,saidai idan bilal ya dawo,ya dauka abinda yakeso a ciki ya qara gaba abinsa,don ya riga ya gayawa kaltume "Yaaya,ki dauka kici,wahalar banza yakeyi kawai,waye zai bashi ke?ni tun sanda ummanmu ma tace bazai aureki ba hankalina ya kwanta,don ummanmu bata magana biyu" a lokacin gani take ba zasu gane abinda takeji ba,kullum kwanan duniya tana kwana ne sa fargaba ta tashi da ita. ***********Zaune take saman kujera 'yar tsuguno daga can magangarar ruwansu tana musu wanki ciki harda kaya bilal,umma tana daga bakin qofar daki tana tsefe kanta,duk da tsaho da yalwar gashinta bata bari ya dade bata sabunta kitson kanta ba. Sharaf sharaf sukaji tafiya,duk sai suka maida hankalinsu bakin qofa. Bilal ne ke shigowa da takalman aikinsa a hannu,ya qaraso tsakar gidan ya sulale ya zauna "Acici mala'ikun tauna,yunwar ce?" Kaltum ta tsokaneshi,don yau koda safe ma baisa komai a cikinsa ba,data yi masa maganae karyawa ma sai yace zaici saiya dawo,baya jin dadin bakinsa ne. To a nan ma kansa ya girgiza "Bana jin yunwa,bakina da cikina ne babu dadi wallahi" ya fada yana yamutsa fuska,tare da qoqarin kashingida kan gwiwar hannunsa "Wannan neman kudin daka sanya a gaba ne,kullum babu hutu,awa a shirin da hudu amma kana bautar da jikinka?ya kamata dai ka dinga hutawa" umma ta fada tana ci gaba da tsifarta "Zan huta ne umma,nima sai naji inason na huta" ya fada yana zamewa,tare da kwanciya rigingine,amma ya miqe sambal,yayin da kaltume da umma sukaci gaba da hirarsu,har zuwa sanda kaltum ta gama wankin ta soma shanyawa a gurguje a gurguje,saboda koda kiran sallar la'asar da aka fara. Har umman ta miqe,saita ankara dashi "Kai bilalu?,meye haka?,kazo ka wani mimmiqe ka rufe fuska da riga kaman wata gawa,tashi kaje kayi sallar la'asar gashi can ana kira" miqewa yayi ya zauna yana dafe da cikinsa "Umma zanyi a gida,baza iya zuwa har masallaci ba,ciwo cikin yake min" "Wannan ciwon ciki Allah ya rangwanta,ya yaye shi,saika tashi ka watsa ruwa a jikinka ka daura alwala kayi sallar,sai kazo kasha sauran magungunanka" amsa mata yayi da to,sannan ya miqe cikin dauriya da dakiya,kaltum ta bishi da kallon tausayi irin na 'yan uwantaka. A iya kwanakin ta lura har dan fadawa yayi,tana yawan ganinsa da daddare idanu biyu,idan ta nema ba'asi sai yace tashinsa kenan. ********"jiya da yau duka banga hard working boy din nan ba....." Saraki ya fadi sanda yake takawa zuwa inda motarsa ke ajjiye tana jiran qarasowarsa,yana kuma cire lethier hand socks din dake hannunsa,wanda yayi amfani da ita yanzu wajen duba ingancin wani sumunti da za'a qarasa plaster ginin makarantar daya kawo qarshe a yanzun "Kamar bashi da lafiya fa,don shekaran jiya daga nan aka maidashi gida ma,ya fadi ciwon ciki" dakatawa da tafiyar samir yayi,ya waiwayo yana duban umar "Amma me kukayi akan hakan?" Dan sosa kansa yayi kadan,don yasan amsar da zaya bayar kuskurece a wajen samir "Babu komai,munyi magana da murtala yace tunda akaji shuru lafiya ce" kadan adams apple dinsa ya motsa,alamun abun ya masa ba dadi,yadan lumshe kyawawan idanuwansa da Allah yayi musu wani irin yanka mai daukar hankali da kwarjini,kamar zaice wani abu saiya fasa,yaci gaba da takawa zuwa inda motar tashi take umar na biye dashi cikin fargaba har suka qarasa. Budeta yasa akayi,saiya cire 'yar saman rigarshi ya jefa ciki,ya fidda takalmin qafarsa shima ya maida cikin motar,saiya zari slippers dinsa da yake sakawa idan zaiyi alwala a wajen ya sanya,yana nade hannun lon sleeve shirt din dake jikinsa yace "Kiramin hannafi" ba tare daya waiwaya umar ba,ajjiye litattafan hannunsa yayi ya juya zuwa sashen da makarantar take da hanzari,don suna daga bayan makarantar ne,inda ba wanda yake iya ganinsu,yawancin lokuta anan yake ajiyar motarsa,hakan yasa har yanzu da gini ke daf da kammala ba kowa ne yasan matsayinsa ko kuma waye shi ba. Minti uku sai gasu tare da hannafi,takawa ya fara yi sannan ya gayawa hannafin inda zasuje "Gidansu yaron nan.....bilal" "To mai gida" hannafi ya fada yana shigewa gaba da hanzari. Shuru ya ratsa tafiyar tasu,hakan yasa samir yin amfani da wannan damar "Ba abu bane me kyau ba mutum na aiki qarqashinka,ka jishi shuru ka kasa bincikar lafiyarsa,idan lafiya lau yake to alhmdlh,idan kuma bashi da lafiya....sai kayi tattaki kaje ka duba lafiyarsa,wannan shine halin ma'aiki S A W,yayi cigiyar matar dake share masallaci kullum bayan ya jita shuru,aka shaida masa ta rasu,yaje kan kabarinta yayi mata addu'ar samun rahama,yayi cigiyar mutumin da yake ba musulmi ba,wanda kullum sai yazo yayi wani abun cutarwa ga ma'aiki,aka shaida masa bashi da lafiya ne,yayi tattaki yaje dubashi,qarshe ya laqqana masa kalmar shahada,ya karba ya musulunta,ya mutu a musulmi" saiya tsagaita yana tuna daga inda ya samu wannan karatun,yana tuna sanda take karantar dasu,yana hango lokaci da yanayin tarrrr a idanunsa,amma me yasa komai ya goge?,me yasa komai ya shafe?,me yasa dukkan wani abu da zai tuna masa da ita babu shi?,tambayar da yakewa kansa kenan a wasu lukutan. "Allahu akhbar.....Allah ya bamu ikon yin koyi" hannafi ya fada "Ameen ameen" umar ya amsa masa,girma da qimar samir na qaruwa a idanuwansa,ba dan kasuwa bane kadai,badan babban dan siyasa bane kawai,ba jagora bane zalla,ba mai kudi bane tsantsa,a'ah....yana da wata nagarta,nagartar da sai a tara mutane dubu masu irin abinda Allah ya bashi a rayuwa basu da ita. Tafiyar minti biyar takawosu qofar gidansu bilal,shuru a yashe babu kowa "Tab,kada Allah ya kawo wannan mafadacin uban nata......" Hannafi ya fada yana leqe da kansa ko zai hangi wani "Kamar yaya?,daga ganinmu sai yahau fada?" "Bakasan amadu ba,tosu kansa matar da yaran ba dadinsa suke ji ba,bashi da kirki bashi da mutunci...." "Hannafi....."muyar saraki ta ratsa tattaunawarsu "Yallabai" ya waiwayo yana amsawa cikin girmamawa "Muyi abinda ya kawomu" "To...to yallabai,bismillah mu shiga mana" wani kallo samir yayi masa "A musulunce haramunne ka shiga gidan mutane ba tare da neman izini ba,Allah cewa yayi kada ku shiga gidajen daba naku ba,har sai kunyi sallama kun nemi izini daga masu gidan......koda kunyi sallamar ma idan suka ce ku koma to ku koma" "Afuwa ranka ya dade,bari ayi sallama" ya fada yana yaye muryarsa ya doka sallama,yayin da samir ya koma gefe ya goye hannayensa a qirji yana nazarin gidan,gajeriyar katanga wadda idan anso haurawa ba wani abu bane mai wahala,tako ina zagwanyewa take,da alama tafi samun wannan matsalar da damuna,ita kanta qofar gidan kyakkyawan bugu guda daya rak ya isa ya kaita qasa. Leqowar inna laure yasa hannafi ya dakata da doka sallamar,sunsan juna,sai suka fara gaisawa da ita su samir na tsaye a gefe,da fari cikin fara'a fuskarta take,amma sanda taji wajen wa sukazo sai fara'ar ta dauke dif daga fuskarta,ta koma qarewa su samir kallo. Ajiyar zuciya ta saki a boye sanda ta gama kallonsu,a haka dai fea suke,amma bataga alamun nera a tattare dasu ba,duk da hakan tanajin ba zata iya yi musu iso wajen zuwaira ba,sai tace "Ka jira" kawai ta juya zuwa ciki. Minti daya biyu shuru,dai dai sanda asiya ta keto cikin shigar wani lace,lace ne mai kyau amma an masa dinkin ganin dama,tana tafe tana tauna chewing gum,tana taku ɗai ɗai,tana jin kaf qauyen babu yarinyar data kama qafarta,sani da iya gayu,da kuma morewa rayuwarta,kallo itama ta bisu dashi,daga bisani ta sauke idanunta kan fuskar samir,ido ta zuba masa,can qasa kadan kadan tana hangar wani kyau da tsarin halittar da bata taba ganin irinta ba,wanda ba kowacce mace zata tantance hakan ba,sa irinsu da suka fara gogewa da duniya da sanin maza. Kwarjinin daya zuba mata da idanunsa su suka sanyata janye nata idon ba shiri,ajiyar zuciya na qwace mata ba tare data sani ba,sai tayi cikin gida,wanda shigarta yayi dai dai da budar bakin hannafi "Yar kusun uwa mara kunya,kin addabi 'yar uwarki da rashin mutunci,ke ko koyi da ita bakya yi......" Kallon da samir din ya sake watsa masa yasa yaja bakinsa ya tsuke,saiya waske ta hanyar qarawa gaba ya cusa wuyansa cikin soron yana sake kwarara sallama. Kaltum dake wankin kayan umma a magangarar ruwa,ta waiwaya ta dubi umma dake zaune saman kan bilal dake kwance,wanda ta gama bawa maganin data jiqa "Ummanmu kamar sallama ake a waje ko?" "Eh nima naji,sa hijabinki kije ku duba" dan jim tayi,sam ita yanzu bata son fita ko nan da can,saboda kada ta hadu da auwalu da take ganinsa kamar wani baqin kumurci "Ummanmu,idan kuma baqin asiya ne fa?" "Babu lallai,tunda kikaji basu amsa ba" saita tsame hannunta daga ruwan dattin,ta goge jikin tsohon zaninta,ta janyo hijabinta da bata rabo dashi ta zura sannan ta durfafi soron. Ganin baquwar fuska haf biyu saita ci gaba da takawa a hankali,haka kawai gabanta na faduwa,tana addu'ar ya rabbi ya kauda matsala,ubangiji yasa ba wata sabuwar wutar bace ta kunno kai. Shi ya fara hangota,tana tahowa a hankali,iska na kadata kamar zata fadi tsabar sirantaka,ba ita kadai iskar ke kadawa ba,harda tsumman zanin jikinta,da hijabinta da yake mannewa a jikinta saboda yadda ya fara tsufa,ga kuma yanayin sanyi da aka fara shiga. "Ina yininku?" Ta fada a tausashe tana dan rusunawa,muryarta cike da fargaba,karon farko da yaji muryarta dab dashi,karo na uku da mamakin yadda Allah ya bata murya ya mamayeshi,koda yake.....ya tabajin wata hira tasu auta cewar..... majority masu kyan fuska ba kasafai suke da murya mai dadi ba......wadanda kuma suke basu da wani kyau,Allah yakan basu baiwar murya "Lafiya lau" hannafi da umar suka amsa,sannan hannafin ya dora "Ya jikin bilalun?,munzo dubashi ne daga wajen aiki" kanta tada sosa sannan tace "Bari to na fara gayawa ummanmu,saiku shigo" "To babu laifi"cewar hannafin,saita juya da dan hanzari fiye dana dazu,da alama ta samu qwarin gwiwa ne. Hijabi ummansu ta saka,ta sanyata kuma ta sake shinfida musu wata tabarmar daban,tare da aje musu ruwa a kwanon sha,sannan ta koma tayi musu iso. Sosai bilal yayi mamaki,ya kuma ji dadin zuwansun,duk da yadda yake jin jiki. A nutse kuma cike da hikima samir yake karantar yanayin yaron,yanayin yadda yaga jikinsa a nasa ilimin ya kamaci a kaishi asibiti,saboda yadda yanayin launin idanunsa suka dan jirkita. Da gani koda ba'a gaya maka ba yasan suna cikin rayuwa ta buqata,saidai babban abinda ya burgeshi,yanayin yadda komai nasu yake a killace a kuma tsaftace,daga inda yake yana hangen yadda take zaune tana wanki da sili silin hannunta,wadanda suke juya kayan da qyar,da alama ba nata bane,tunda ta musu iso ta koma saman kujerar 'yar tsuguno taci gaba da wankinta. Yanajin ya kamata ya tallafi rayuwarsu da abinda zai iya,duk mutumin da kunnensa ko idanuwansa suka nuna masa shi a muhallin mabuqaci,kawai yana gayawa kansa Allah ne yayi nufin nuna masan domin ya taimakeshi da abinda ya hore masa na arziqinsa,bare bilal.....haka kawai yakejin yaron ya kwanta masa tun daga wancan lokacin da tazo amsar haqqin dan uwanta har wajen aikin,bai fahimci abinda tayin ba sai daga bisani,daya dinga shiga cikin ma'aikatan yana rayuwa dasu a matsayin ma'aiakaci,ya gane cewa wani zalunci akayi tazo ta dakusar dashi. Tunaninsa ya katse sanda malam amadu ya danno gidan da wata iriyar sallama,dukkansu su ukun sai yaga reaction dinsu ya canza,har kaltum dake wanki a zaune ta kasa ci gaba da zama,ta saki wankin tana masa sannu da zuwar daya amsa da qyar ta wuce quryar daki. Bai ankara dasu ba sai daya gama shigowa,saiya kuma saki fuska,kamar ba shine wanda ya shigowa iyalansa a wani yanayi ba. Suna gama gaisawa samir ya miqe daga tsugonnan da yayi a gaban bilal,don dama bai zauna ba,duk da cewa fes tabarmar take,umar ya kalla kana ya fice bayan ya sake yiwa bilal da umma fatan samun sauqin bilal anan kusa,ya fahimci abinda yake nufi,don haka yana fita ya soma qoqarin ciro kudi,sai hannafi ya qyara masa ya cusawa bilal din qasan filo,don yasan halin malam amadu,haka kuwa akayi,don har suka fice bai lura da kudin ba. "Bashi da tausayin iyalansa,shegiyar masifa da shegen son kudi kamar tsohon bazawari" maganar data bawa unar dariya kenan suka fito suna darawa,saidai suna iske saraki tsaye a qofa gidan kowa ya kama kanshi suka sake takawa zuwa inda suka fito. "Gida zamu wuce,inason nakai gida nan da minti talatin" saraki yafada bayan ya gama kallon agogon hannunsa,a mamakance umar ya kalleshi,har ya kasa boye abinda ke bakinsa "Yallabai kai da bakason gudun wuce qa'ida?" "Yau nace maka kayi?" Qaramin murmushi yana subuce masa,yau din babbar rana ce mai mihimmanci a wajensa,yau Aamirunsa zai dawo gida,bayan tsahon lokacin daya dauka basa tare,yana buqatar bawa amirun mamaki bayan ya kashe wayoyinsa gaba daya ya kasa samunshi,saidai kawai ya ganshi. Kamar yadda ya buqata haka kuwa umaf ya tsula gudu iya son ransa a yau din,duk da haka sanda suka iso mintunan ba zasu iseshi ya koma gida yayi wanka ya shirya ba sannan ya tafi tarar amirun ba,don haka yacewa umar su wuce kawai airport din da kayan jikinsa,duk da cewa sun diba qura ba laifi. Su uku ne a tafe dukkansu sanye da doguwa riga abaya,yammata uku sai qaramar yarinya daya,daya daga cikin 'yammatan tana riqe da hannun yarinyar daketa faman tsalle tsalle tana son qwacewa "Laaaa uncle?" Yarinyar ta fada tana qoqarin xame hannunta daga cikin hannun budurwar,abinda yaja hankalin mubina kenan daketa faman hira,ta waiwaya tana dakawa yarinyar tsawa "Meye hakane afra?" Kafin ta gama maganar ma tuni ta kubuce ta durfafi inda samir yake tsaye,wanda sam hankalinsa ma baya wajen bare yaga tahowar yarinyar,saiji yayi kawai an kama qafafunshi ana cewa "Uncle....ina ka tafi?" A hankali ya sauke kansa yana kallon fuskar yarinyar,ya tunata,murmushi ya wadaci fuskarsa,saiya tsugunna a gabanta ya kama hannayenta "Umm....ummm" ya fadi yana qoqarin tuna sunanta "Afra" ta amsa mishi tana dariya,sai dariya ta qwace masa,shegen wayo ne da yarinyar da alama,gashi harta fahimci abinda yakeson cewa,ta kuma tuna masa "Keda wa kukazo?" Waiwaya tayi inda mubina tayi mutuwar tsaye tun sanda ta ganshi,tana nuna mishi ita da hannunsa,suka hada idanu na sakanni,saiya janye qwayar idonshi daga kanta,kallonsa kawai ya sanya tayi suman tsaye,taja numfashinta da qyar,ta tattaro dauriyarta tana takawa zuwa inda suke tsugunne,mamaki yana cikata na irin yadda ya gwanance a iya shariya. Sau daya tak ya daga kai ya kalleta ya maida ga afra sukaci gaba da hirarsu kamar wadanda sukayi mugun sabo da juna,ganin da gaske kamar bai ganta ba saita dan gyara muryarta kadan sannan tace "Ina wuni" daga kansa yayi kadan ya amsa yana sake maida kansa ga afra,kusan minti uku tana tsaye daga gefe,a nutse take qare masa kallo,da alama yana da son yara,ya sakewa afran sosai,har sai data ji wayarta tana ringing a jaka,saita zaro ta duba,nan ta tarar da tarin missed calls din basma,tana shirin bi wani kiran ya shigo "Wai ina kuka shiga ne keda afra?" "Gani nan" ta fada tana maida wayar jakarta tare da cewa "Zamu tafi" a yangance,saiya miqe tsaye yana saka hannunsa a aljihunsa,yana fatan samun sauran alawar da ya siya daxun yasha,ya kuwa samu guda biyu, chocolate ne,da yake baya rabuwa da alawoyi masi Coco,ya miqa ma afran,hannu biyu ta amsa cikin murna,sai yayi waving hannayensa yana maida mata bye din da take masa har ta isa kusa da mubina. A sanyaye ta kama hannun afra,tana neman dalilin da zai sanya ta samu number dinsa. Tsugunnawa tayi gaban afra a tausashe "Ba zaki karbi number uncle ku dinga gaisawa ba?" Har ya juya zai fara takawa yaji abinda ta fada din,saiya tsaya cak sanda yarinyar ke cewa "Ehhh kuwa anty,uncleeee" saita diba da sauri tayi wajensa "Uncle, your phone number please" dauke idanunsa yayi ya maida kan mubina a karon farko,saiya janye idanunsa sanda suka hada ido,ya sakarwa afra murmushi. "Yes!" Mubina ta fada sanda taga ya ciro biro daga aljihunsa,ya zari qaramar paper ya fara rubutu akai,yana kaiwa qarshe ya miqa ma afra "Ga number wata antyn taki nan,gidanmu daya,ki dinga kiranta kuna gaisawa,idan kika kira nima zan kiraki, alright?" Kai ta gyada tana murmushi sannan ta sake daga masa hannu ta juya a guje. Fuska mubina ta bata sanda take kallon jerin gwanon numbers din da wani irin rubutunsa mai kyau,ba haka taso ba, number dinsa taso samu kai tsaye,to wai shin wacece ma antyn afran da yace gidansu daya?,kada dai ace matarsa cema?,saita girgiza kanta da sauri "No...no it can't be......" Tunaninta ya katse sanda taji su basma na kiranta,saita kama hannun afra da hanzari suka nufi inda suke tsaye suna faman yi mata mita. Qyam yake tsaye hannayensa saye cikin aljihun wandonsa,idanunsa gaba daya ya tattarasu ga ina fasinjoji ke fitowa. A hankali fuskarsa ta washe sanda ya hangi amirunsa,dan uwa kuma babban aminin da bashi da kamarsa,giant ne kamae sarakin,saidai yafi saraki qiba da duhun fata. Duk yadda yaso shawa amiru kunu saiya kasa,murmushi ya wadata a labbansa,abu guda yaqi masa shine ya taka ya isa inda yake su riski juna har amirun ya cimmashi. Hannu yasa ya daki kafadar samir "The giant saraki....wallahi da gaske....ka zama dan qauyen, you are looking qauyis.....kalli kayanka fa?" Dole ya sanya saraki sakin murmushin da yafi kama da dariya,sai ya bashi hannu suka tafa,sannan suka rungume juna. Suna riqe da hannun juna har suka isa bakin mota,sarakin ya bude musu da kanshi suka shiga,umar ya tashi motar suka bar airport din. Ko a hanya ma hira suke sosai da sosai,irin hirar dake nuna yadda sukayi kewar juna,kamar ma babu kowa cikin motar saisu,da haka har suka iso gidan professor rashid. Sanda suka danna horn sai malam datti ya dage musu qofar a maimakon malam salahu,saboda ranar ranar aikin malam salahu ce,suka gaisa a mutunce yana wa zaratan samarin barka da zuwa,fuskarsa cike da annashuwa,don sunyi kewar matasan suda tarin alkhairinsu. *******Tun kusan bayan qarfe goma na dare yake matagugu yana juye juye,tare da fadin sunan Allah "Cikina ummanmu,cikina....don Allah ku kaini asibiti,akwai matsala a cikin nan nawa" shine abinda bilal din yaketa fada,wanda hakan ya hana idanuwansu bacci,daga umman har kaltume,don tuni kaltume ta fara kuka tana riqe da bilal din tana jera masa sannu,hankalinta yayi matuqar tashi,saboda bata taba ganin bilal din cikin yanayi irin wannan ba na matuqar ciwo,duk da yadda wani lokaci yake da raki. Duk wani magani da ummanmu take ganin ya kamata ta bawa bilalun ta bashi a daren,amma abun yaci tura,don babu abinda ya sauya daga matagugun da yakeyi na ciwon dake addabarsa,bugu da qari ga wani kumburi da cikin nasa yayi. Tun babansu na sharewa harya bankada dakinsa ya fito,fada ya farayi,amma da yaga yadda bilal din yake saiya ja bakinsa ya tsuke. Ya dan zauna na mintuna kafin dare ya qara nisa,daga bisani ya tattara ya shige dakinsa ya barsu nan,lokaci lokaci yakan farka,ya leqo yaga bilal,wanda babu wani canji game da jikinsa na samun sauqi,face lafawa da ciwon yakeyi ya dawo. Hakan ta tilasta musu suna kammala sallar asuba ummanmu da kanta ta shiga maqota,gidan malam sale mai amalanke,ta roqi alfarmar ya fitar dasu can bakin titi,inda zasu samu motar da zata kaisu asibitin cikin birni. Babu komai malam sale yace,kasancewarsa mutum me matuqar kirki,uwa uba su kansu suna duba kirki irin na umma zuwaira,suna kuma tun alkhairinta a garesu. "Nidai bani da ko asi,idan zaku iya zuwa to,saidai nace Allah ya kiyaye hanya" cewar malam amadu yana muzurai "Allah zai rufa asiri" ummanmu ta fada tana duqawa gami da dago bilal,wanda gaba daya jikinsa yayi yaushi,hatta da mazagin wandonsa saida kaltum ta sake daure masa shi,sukayi masa kama kama ita da ummanmu,bayan ta tattaro 'yan kudadenta da kawu ado ya bata yace taja jari,batakai ga jan jarin ba,tana nazarin sana'ar da zatayi sa wannan lamarin ya ratso. Babu wanda suke dashi bare suyi masa sallama,malam sale ya daukesu a amalankensa,cikin matuqar nuna tausayawa,bai saukesu ba har sai da aka samu motar da zata kaisu har bakin asibitin sannan ya taimaka musu suka sanya bilal,yana musu fata alkhairi har suka daga,sannan ya juyo cike da tausayawa,yana tuna son aiki da kazar kazar irin na bilal,amma lokaci guda kamar bashi ba,ya tuna sanda sukayi masa aikin katangar gidansa,kusan shine jigon aikin,amma daga baya ma kason da sauran suka samu na kudi shi bai samu kamarsa ba,bai kuma damu da hakan ba. 31 D/Z *wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa* 08184017082 Ko kuma 09134848107 31 Daga ita har ummanmu shuru sukayi a dakin likitan,suna jiran suji bayanin da zaiyi musu,kowanne a cikinsu zuciyarsa dukan uku uku take,a haka har likitan ya dago ya dubesu. Wani irin kallo yayi musu,wanda yake nuni da raini raini irin da kuma qyama,irin wanda aka sabawa mutanenmu 'yan uwanmu al'ummarmu ta karkara "Baaba,yaya akayi kuka barshi haka a gida,har ciwonsa yayi tsanani haka?" Tashin hankali ne ya fito baro baro kan fuskar umman,cike da nuna damuwa ta zakuda zamanta kan kujerar tana cewa "Likita?,me ka gani?,me yake damunsa?" Sai saya jujjuya takardar hannunsa,cikin shan qamshi sannan yace "Eh to.....yanzu muna buqatar kuje ayi masa scanning tukunna....." "Me kenan likita?" Ummanmu ta tambaya a rude tana kallon yadda jikin bilal din ya saki gaba daya,ya daina juye juyen,sai kallo da sauraren abinda likitan yake fada. Goshinsa yadan sosa sannan yace "Oh,sorry,hoton cikinsa....sannan zamu gane ainihin inda matsalar take,ayi kuma abinda ya dace" ya fada yana sakeyin wani rubutun saman takardar ya miqa mata. Kaltum ce ta karba,sannan ta isa inda umma ke qoqarin sauko da bilal daga saman gadon,sukayi masa kama kama,ya dogara da kafadarsu suka fara tafiya don ficewa daga office din. Tun basuyi nisa a tafiyar ba ya zame "Bazan iya takawa ba" ya fada yana kallon ummanmu,hankalin kaltum ya sake tashi,dukkansu matane,bata tunanin zasu iya daukan bilal,har gwara ita akan ummanmu,saita dubu takardar hannunta, ayanzu burinta kawai shine sune wajen hoton a samu a gano abinda yake damunsa a cikinsa "Ka daure bilalu muje,kaga likitannyana jiranmu" kansa ya mirgina yana ajiyar numfashi "Bazan iya ba yaya,Allah bazan iya ba" ya fada a raunane,babu wata sauran mafita data rage musu,don haka kaltun ta miqawa ummansu takardar "Riqe ummanmu.na goyashi" "Anya ko zaki iya kaltum,ki barshi dai ya sake gwadawa" "Zan iya ummanmu in sha Allahu" ta fada tana juyawa bilal bayanta,da taga taga umman ta tareshi ya shau bayan kaltum,duk da nauyin da bilal din yake dashi amma sai data ar jarumtar data shanye wannan nauyin,saidai daqyar take iya taka qafarta,hakanan kafin sukai wajen scan din ta huta ya kusa sau biyar,a haka har suka isa wajen. Sun tadda layi,suka tambayi mutum na qarshe a wajen,suka zaunar da bilal suna tsaye a kansa "Ruwa" ya fada qasa qasa,idanuwansa na kan al'ummar dake kai kawo,ummanmu tace kaltum din taci gaba da tsaiwa dashi,bari ta samo masa ruwan,cikin hanzari ta miqi hanya. "Amai zanyi" bilal din ya sake fada,saita cafko wata baqar leda dake yawo a qasa kusa dasu,tana tara masa kuwa ya fara shara aman,yana aman tana kallonsa tana kuma kallon aman,hakana jama'ar dake kusa dasu,saboda wani irin baqin amai da yakeyi,harda gudaji gudaji kamar na nama ko fasashiyar mahaifa,a haka ya kammala tsaf,dai dai sanda ummamu ta dawo,ta balle pure water din data zo dasi guda uku,ya shanye biyu daga ciki. Tafi tafi layi yazo kansu sannan suka shiga,kaltum na daga waje ummansu ce ta shiga tare da bilal din,yadda taga ya natsu ya zubawa na'urar idanu sai taji jikinta ya sanyaya haka kawai,ya daga kai suka hada ido "Kece mamansa?" Kanta ta gyada a maimakon ta amsashi,saiya maida kansa yaci gaba da aikinsa da sauri sauri ba tare dayace da ita komai ba,yana gamawa ya linke takardar bayanan ya bata "Kuyi hanzarin kaiwa likita wannan" "To na gode" ta fada tana karba hannunta yana rawa,sannan ta kama bilal suka fito. Kai likitan yake jinjinawa sanda ya karbi bayanan yana dubawa,kansa ya daga ya dubi umma "Baiyi amai ko sau daya ba?" "Yayi likita yanzu babu jimawa" sai taga ya dafe goshi,ya ajjiye takardar ya dubi nurse din da a yanzu take tare dashi "Kuje dashi a bashi gado, a daura masa drip....baaba,kuje ku nema kudin aiki dubu takwas,za'ayi masa operation ne na gaggawa,kada ya dara awa daya" Gaba daya kamar an kwarawa jikinta ruwan sanyi haka ummanmu taji,kaltum kuwa mutuqar tsaye tayi,saboda sunfi kowa sanin cewa basu sa wannan kudi,basu kuma da hanyar samunsu,data laluba jakarta ma kudin da suka rage a ciki wanda suka taho dashi na jarin nata dubu daya ce,banda haka basu mallaki komai ba,don haka bayan an masa duk abinda likitan yace,sai ummanmu ta kalli kaltum "Bari na fita daga waje ko zan samu wajen buga waya,na kira ado ko indo,ko Allah zaisa a dace a samu koda wani abune daga wajensu" "To ummanmu" ta amsa mata idanunta nakan bilal,wanda nashi idanun suna kan umman "Don Allah ummanmu kada ki dade" Takowa tayi a hankali gabansa ta tsaya,ta kamo hannunsa da babu qarin ruwan ta riqe gam sannan tace "Yanzun nan zan dawo in sha Allahu" "Ayimin aikin nan ummanmu ko zanji dadin cikina" "Da yardar Allah yau ka rabu da ciwon nan" saiya gyada kai kawai yana lumshe idanu,umma ta zame hannunta ta fice da sauri. Kujerar roba da ake ajewa guda daya a gaban kowanne gado kaltum ta jawo ta zauna gaban bilal,duk a darare take,saboda wannan shine karon farko data taba shigowa waje irin wannan,sai take ganin kamar kowa kallonta yakeyi,duk kuwa da cewa ba haka bane,kowa ta mara lafiyansa yakeyi "Zanyi amai yaya" bilal ya sake fada,saita miqe da sauri ta sake samo masa leda,kamar aman dazu ya sakeyi,itadai kaltum ta zubawa aman ido cike da mamaki,ganin wani abu guda guda kamar hanta hanta a ciki da yake ta fita,gashi yayi wani baqi kamar ajiyayyen jini,haka ya gama ta rufe ledar taje ta yar. Tana dawowa ta taras da wani ma'aikacin lafiya a kanshi yana dubashi,ya kammala yayi rubuce rubuce ya bata takardar,yana barin wajen yana mata bayani "Magunguna ne,aje a siyasu yanzu" fakare tayi da takardar a hannunta tana juyata,ita da zuciyarta suna qiyasta adadin kudin maganin da babu su babu dalilinsu A hankali ta daga idanunta,sai suka hada ido da bilal din,hannu yasa ya yafitota,ta taka a hankali zuwa gab da gadon ta sunkuya sosai daidai kansa,saboda yadda muryarsa take fita yanzu a hankali,da alama dukkan wani qarfi da kuzaru nasa ya qare "Yaaya,inabin lawandi kudi,don Allah aje wajensa,ya bayar da kudin ayi mini aikin dasu,ni kadai nasan abinda nakeji,idan basu cika ba ko baba ne ya taimaka ya cikamin" wasu hawaye ne suka zarto mata,saita miqe tana gogesu daga fuskarta,tsananin tausayin dan uwan nata yana cika qirjinta,ta yadda har takejinnkamar ta fiddo zuciyarta waje. Roqo abune da bata taba yi ba tunda take,amma ayau zata yishi saboda ceto rayuwar dan uwanta,don gabas da yamma,kudu da arewa a yanzu batasan inda zata sama masa kudin magani ba idan bata wannan hanyar ba "Ki kiramin ummanmu,tazo ta zauna a kusa dani" ta sake jin muryar bilal,saita juya da sauri don yi masa abinda yace din,sai kuma ga umman ta dawo "Kin kirasu ummanmu?" Tayi tambayar tana duban yanayin umman "Ban samu ba,amma wani bawan Allah yace na jira ya karbo wayarsa daga wajen chargy,saina koma ya kiramin. Kai kaltum ta girgiza,tana ji lokaci yayi tsaho da yawa,tana ganin gwara ta fita su roqa,koda basu cika ba a ciki tayi kudin mota ta koma qauyensu ta amso kudin bilal din a hada a cire masa ciwon dake damunsa "Ina zuwa ummanmu" kaltum ta fada da sauri tana bin hanyar waje,sai umman ta saki ajiyar zuciya ta maida dubata ga bilal daketa binsu da ido "Me yasa kika tafi ummanmu?" Ya tambayeta a hankali,tana qoqari maye gurbin da kaltum ta tashi ta amsa masa "Kayi haquri bilalu,inacan wajen nema maka kudin aiki,amma gani na dawo" saiya gyada kai yana miqa mata hannunsa "Riqemin hannuna" "To bilalu" ta amsa masa tana saka hannunta cikin tafin hannunsa. Abunda baka saba ba,diri diri ta shiga yi a dan filin asibitin,ta rasa ta ina zata fara?,wa zata fara roqa?,saita fara takawa a hankali zuwa nahiyar da mutane ke zaune,wasu suna jinyar 'yan uwansu,wasu kuma dubiya suka zo. Duk wanda ta dosa katin take miqa masa tare dayi maaa taqaitaccen bayani. Bata taba sanin duniyarmu ta cika tab da marasa tausayi ba.....bata taba tunanin duniyarmu ta cika da nau'in jama'ar da basa jin qan junansu ba sai a ranar,mutane da yawa saidai suce Allah ya sawwaqe suma basu dashi,idan ma taci sa'a kenan an mutuntata,duk kuwa da cewa mafi yawa a cikin masu fadin hakan,ba za'a rasa kudi koda qanqani a jikinsu da zasu iya bata ba,wanda inda sunyi hakan....kadan kadan din su zasu hadu su bata yawan adadin abinda take buqatar. Wasu daga cikin mutanen ma saidai su dauke kai,ta gama bayaninta ba tare da wani daya cikinsu yace komai ba,a haka taci gaba da jarraba sa'arta. A hankali motar tasu ta ratso cikin asibitin,matasan zaratan samari,wadanda kudi da ilimi suka yiwa ginshiqi,samir tare da amini kuma dan uwanshi aamiru,dukkansu suna sanye da shadda,wadda aka yiwa wani nau'in dinki mai qayatarwa,wanda yayi musu kyau,ya kuma fidda sigarsu da zatin da Allah yayima kowannensu. "Wannan wanne irin asibiti ne haka?" Amiru ya fada yana bin asibitin sa kallo,sai a sannan samir ya aje wayarsa saman cinyarsa,kasancewar bashi ke tuqin ba amiru ne,shidai yana zaune kawai a gefansa. Ajiyar zuciya mai nauyi saraki ya sauke,tsahon wasu sakanni sannan ya magantu "Bakaga komai ba....wannan asibitin da kima da darajarsa akan saura,bansan me shugabanninmu keyi ba,totally basu san responsibility dinsu ba,yanzu wai a irin wannan muhallin ake neman lafiyar dan adam....Allah ya kyauta" ya fada tare da bin bayan maganar tasa da tsaki bacin rai yana cikashi,saiya buda murfin motar ya zura qafarsa waje yana sake qarewa harabar asibitin kallo. Cak ya tsaida idanunsa yana dubanta waje daya sanda take kai kawo a tsakiyar asibitin,da yadda take tsaida jama'a jefi jefi,sannu sannu har ta iso dab da motarsu,sai yaga ta zagaya daga baya inda amiru ke tsaye yana amsa waya,bai waiwaya ba amma yana iya hango black face dinta ta jikin mudubi,wadda ta qara duhu da shining. "Lafiya?" Yaji amiru ya fada,wanda bai gama wayar ba,ya dakata ne saboda tsaiwarta a wajen "Taimaka mana zakayi fisabilllahi da kudin magani,don Allah,bamu da kowa bamu da komai sai Allah....." "The giant,are you there?" Gyaran murya kawai samir yayi masa "Ok,miqo wani abu" ya fada yana dariya dariya,saboda tuna wani abu da yayi,baice komai ba ya bude aljihun motar,ya ciro kudi a ciki,cikin ransa yana tambayar waye nasu a asibiti babu lafiya?. Har zai miqawa amiru kudin saiya tuna yadda aka tabayi da ita akan sabon kudi,saiya maida,ya laluba ciki ya dace da samun wasu,sai ya miqawa amiru su gaba daya. Har zaiyi magana da yaga yawan kudin sai kuma ya fasa,ya miqa mata,tsayawa tayi turus tana duban yawan kudin "Ki karba mana" kanta ta girgiza "Sunyi yawa ai" ta fada adan tsorace tana ja da baya,dariya da mamaki suka tasowa amiru amma ya dannesu "Nawa kike so to?" Kamar ta taka da sauri tabar wajen,sai kuma ta tuna bilal yana da buqatar kudin,a hankali kamar wadda batason fadi tace "Duka har kudin magani da kudin aikin dubu goma da dari biyar ne,na samu dubu daya,saura dubu tara da dari biyar" da boyayyar dariyarshi ya irga kudin dake hannunsa,ya zare dubu goma a ciki ya bata "Ga dubu goma nan,dubu dayan kai sai ku sayi wani abu" hannu biyu tasa ta karba tana godiya har qasa,saita baiwa amiru tausayi,yana dariya bayan ta wuce yace sa samir "Kaida ka kawomu nan kuma kayi zamanka kaqi ka fito,gashi na fara haduwa da mutanenka,ka ganemin yarinya?,iya abinda takeso shi zata karba?" "Haka take" ya bashi amsa sanda yake fitowa daga cikin motar "Ka santa ne?" Da mamaki amiru yatambayeshi "Kusan hakanne" ya amsa masa yana gyara rigarsa data dan tattare ta baya "Kodai daya daga cikin 'yammatan daka yone daga qauye ka yaudaresu bayan ka gama aiki?,kai....no wonder mafa naga kaqi fitowa har sai data tafi" amirun ya fada yana dariya,tilas ya sashi murmusawa,daga baya qaramar dariya ya subuce masa,har haqoransa suka bayyana,babu abinda ya tuna sai fuskar kaltume,da qwailan jikinta "Kaci abinci amiru,amma babu laifi,zan rama ne" yana fadar haka ya danyi gaba da hanzari,amirun ya bi mashi a baya zuwa ciki,suka fara tambayar inda mai gadinsu malam salahu yace an kwantar sa dan nasa,don dama dan dama shi suka zo dubawa. Shan gabansu da wata mace mai dan wadatar shekaru tayi yasa suka tsaya cak "Yallabai,kune gwamnatun ta aiko da tallafi?" Ta tambayesu tana kallonsu,duban juna sukayi a tare,amiru ya dagewa samir gira kana yaja baya,alamun ba ruwansa,yaji da ita. Murmushi samir yayi mata sannan yace "Mune iya,me ya faru?" Zaro idanu amiru yayi jin abinda samir ya fada,ai kuwa matar ta kaikaice tana ta fadin matsalolinta,wanda kusan duka nakudi ne,sai data gama sannan ya zaro kudi masu dan dama daga aljihunsa ya bata,wayyo,zo kaga murna,kamar zata zuba ruwa a qasa tasha,tausayinta ya kama saraki,tausayin halin da takalan qasata yake ciki. Godiyar da take zabga musu yaja hankalin mutanen wajen saika marmatso,saita hau gaya musu gwamnati ta turosu,saifa aka fara tururuwar fadar matsaloli,tun yana raba kudin aljihunsa har suka qare ya karbi na amiru,shima suka qare,daga bisani dai wanda bai samu ba sai alqawarin kawo tallafi daga baya yayi musu. Amiru na biye dashi a baya yana kwasar dariya,shi kansa yanda sukayin ya bashi dariyar,saidai kuma tsantsar tausayinsu ya danne dariya,saiya dakata,suka jera da amiru,ya fara masa wasu bayanai da yanayi da halin da al'ummar karkara ke ciki,wanda duka ya karanci hakane a makarantar duniya,da dan shiga garuruwansu yi musu aikin da yakeyi,kafin su qarasa dakin da zasu saiga amiru yana gyada kai,sau tari shi kansa yana yaba halayya da dabi'un samir,yana kuma yaba kaifin tunani da hangen nesan da yake dashi. A gaggauce kaltum ta tsallaka can wani wajen saida magani dake da da tazara da asibitin ta karbo dukan abinda ke rubuce jikin takardar,cikin tsananin sauri ta dawo asibitin,saboda so take akaiwa likitan kudin da wuri ya yiwa bilalunsu aiki ya huta. Tun daga farkon qofar babban dakin ta hango ummansu zaune gaban gadon da bilalun yake kwance,ya canza yanayin kwanciyarsa ba kamae dazu ba da yayi kwanciyar hannu daya,kuma ma kamar a rufe yake yanzun,amma me yasa ummanmu ta rufeshi har saman kansa bayan tasan bashi da lafiya?,ta tambayi kanta,idanu da hankalinta a kansu har ta isa gaban gadon. Kafin tace komai ummanmu ya dubeta,wani abu kakkaifa data hanga daga idanun ummansu,yasa dukkan wani sassan na jikinta yayi sanyi qalau,hatta maganar data furta a sanyaye tace "Ummanmu ya samu bacci ko?" Kai ta gyada mata "Yayi bacci kaltum,babban baccin da babu wanda yasan ranar tashinsa sai Allah,yayi kwanciyar da zai huta,irin hutun da muka gaza samar masa" kasa fahimtar maganar ummansu tayi kwata kwata,kamar ma ba hausa take mata ba,muryarta na rawa tace "Kamar yaya ummanmu?" "Allah ya karbi ran bilal,ina fatan kuma ya huta kenan har aljanna" batasan ledar hannunta ta fadi ba,batasan ta zame ta fadi ba ita kanta,qafarta ta bugu da qarfen gadon,abunda ta iya sani shine wani kuka data saki wanda ya amsa kuwwa a dukka ilahirin lungu da saqo na dakin,kukan da yaja hankalin dukka mutanen dakin,har ma da wadanda basusan bilal din ya rasu ba,ya kuma ja hankalin su samir dake bakin gadon dan malam salahu suna dubashi,ya waiwaya yana tuna inda yasan wannan muryar da irin kukan,sai idanunsa suka hange masa ita. "Ya salam" ya fada yana jin qirjinsa yana bugawa,tabbas wani ne ya mutu,juyawa yayi a hankali zuwa inda take ummansu da wasu mata na qoqarin dagata tare da bata baki,bai tsaya ba sai daya isa gaban gadon,ya saka hannu ya bude rufin,saiga bilal,the hard work boy title din da yake masa. Sakin abun rufar yayi yayi baya yana fadin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" yana jin wani abu yana zaga kwanyarsa,bai taba tunani ko kawowa ransa haka ba,duka duka yaushe sukaje dubashi,ya daga kai ya sake kallon gawar,ko a haka cikinsa ya nuna kumburin da yayi harta saman mayafin da aka rufeshi 32 D/Z *wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa* 08184017082 Ko kuma 09134848107 32 Shi ya dinga kai kawo tsakanin biyan bill din kudin bilal dana dan malam salahu,duk da cewa shi bilal nashi kudin ma ba wani masu yawa bane,saboda bai jima ba,duk motsin da zaiyi fuskar yaron yake hanga,wani tausayi yana ratsashi. Tare da amiru suke komai,duk inda yasa qafa yana biye dashi,saidai bakinsa fal yake da tambayoyi ga sarakin game da su umman. Bai sake shiga mamaki ba sai daya ji samir din yana bada umarnin sanya gawar bilal cikin motarsu,ya kalleshi,duk da baice komai ba,umman da kaltum daketa rusa kuka cikin wani yanayi mai matuqar ban tausayi suna daga baya,shi da samir din suna gidan gaba,malam salahu na musu addu'ar sauka qalau da samu rahama ga mamacin,samir din ya tada motar suka fice daga asibitin. Kukanta kawai ke tashi cikin motar,ta kasa tsaida kukan ko dai dai da minti daya "Don Allah bilal ka tashi,ka tashi kace wasa kake mana" shine abinda take fada lokaci bayan lokaci tana girgizashi,. Sannu a hankali kukan yaci gaba da ratsa kunnuwansu,harda samir da sitiyarin motar ke hannunsa,lokaci bayan lokaci yakan ce "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" a sarari,daga bisani saiya sanya casset na karatun qur'anu,qira'ar khusari,wanda hakan ya rage kaifin kukan kaltum. Suna isa qauyen labarin rasuwar bilal ya ratsa ko ina,kafin kace meye wannan jama'a sun fara cika gidan,habiba na daya daga cikin wadanda suka fara zuwa,sun shigo tana riqe a hannun surukarta tana gunjin kuka,tana faduwa tana tashi,tana kiran bilal din tare da fatan abunda ke faruwan ya zama mafarki,xuwanta ya sake sanyawa kaltume dake ta son bawa kanta juriya sa qwarin gwiwa saita sare,suka taru suka dinga kuka baji ba gani,sai inna da bata jima da isowa ba,tana doje daga bakin qofa tahau musu fada,fadan da badan cikin yanayi yake ba duk sai sun tsaya kallonta,saboda mamakin dama innar tasan Allah?. Cikin abinda bai gaza awa biyu ba aka gama shirya bilal,a sannan kaltum ta sake aro juriya,ta taka tana rangaji kamar zata fadi,saboda yadda takejin iska tana yawo da ita ta fita harabar gidansun,inda abokan bilal suka cika,harda wadanda kaltum ma bata sansu ba,ba 'yan unguwar bane. Abokinsa na kusa kusa ta kira "Ka tambaya cikin abokanku,ko akwai wanda yake bin bilal bashi?" Kai ya kada cikin alhini "A iya sanina babu,saidai ma wadanda bilal yakebi....amma bari na tambaya" juyawa yayi ya koma cikinsu,amsoshin dake fita daga bakunansu duka irin wadda ya bata ne daxun kafin yakai ga tambayarsu Hawaye taji yana sauko mata,haka rayuwarsa ta qare gaba daya,ya nema da guminsa da qarfinsa,yaci iya cinsa,ya baiwa 'yan uwansa,ya bada bashi ga abokansa,koda zasu cinye bashin ba zasu biyashi ba. Rudewa gidan yayi da koke koke,yadda gidansu ke cike damqam da mata ashe a waje abun yafi haka,mamaki ya kusan kama kowa na jama'ar da bilal ya tara,idan bakasan waye ya rasu ba,zakayi tunanin cewa wani babban mutum ne ya rasu,saboda yawan al'ummar daya samu,suna ji suna gani bayan an gama sallar ama daukeshi akayi gaba dashi,ya barsu da kuka,ya barsu da kewa,ya barsu cikin gidan da ake yunqurin korarsa,sai gashi tun ba'a koreshi ba,shi ya tattara nasa ya nasa ya tafi inda ba dawo,inda kowanne me rai zaije. Cikin dare a ranar ta kasa bacci,ganin komai take kamar wani wasan kwaikwayo,kamar wani wasa ne bilal din yake musu,kamar yaje ne zai dawo musu,ta dinga juyi tana kuka,yayin da gefe guda kuma abinda ya faru a wunin duka ya dinga dawo mata,yadda su ya munzali da muzammilu suka dinga rawar qafa wajen hada gawar bilal,sune kawo turare sune kawo sabulu da likkafani,idan ka gani kai ba zakace sune sila ko muzajar mutuwarsa ba,Allah ya sani,ba zata iya gogewa ba,ba zata iya hana kanta kallonsu a matsayin wadanda sukayi sila ko sanadiyyar tafiyar bilalunsu zuwa qiyama ba. Sai kuma ta hango fuskar mahaifinsu,yadda yaye tsugunne gaban gawar bilal,gawar da sai da aka gama hada bilal din sannan ubangiji ya bashi ikon qarasowa,don bai samu labari da wuri ba,saboda a ranar yayi sammakon zuwa wani waje. Ganin juyin bana qare bane saita miqe don ta dauro alwala,sai sukaci karo da ummanta,da alama itama baccin ya gagareta ne,batasan sanda wani sabon kukan ya qwace mata ba "Da kika ce abar habiba ta zauna,da haka zaku zauna kenan ke da ita kuyita yi masa kuka?,kukan da bashi da wani amfani ko rana a wajensa?" Abinda umman tace kenan tana cika buta da ruwa don daura alwala. To cikin kwanakin zaman makokin abubuwa da yawa sun faru,sunga jama'a masu yawa,wadanda basu tsmmatarwa bilal din ba,jama'a masu kamala da mutunci,wadanda zaka zaci ba zasu zo gun jana'izar yaro ba,yaron ma mata gata irin bilal,amma sai gasu,kowa yazo kuma saiya koka kan rasuwar yaron,saboda yadda kusan kowa ke amfanar sa,bashi da qyuya ko san jiki ko kadan,baisan rashin kunya ko fitsara ba ko kadan,girmama kowa yake,hakanan bashi da abokin fada. Kudadensa da mutane suka kakkarba bashi masu tsoron Allah suka dinga kawowa ummanmu da kaltum sunyi mamaki,saboda wani ma basuyi tunanin bashi zai shiga tsakaninsu ba,yawan kudin da suka riqe sai yanzu suke biya,inda a zamanin da yake raye suka biyashin,babu shakka da sun isa ya kafa qaramar sana'a,da bai mutu cikin wahalar daya mutu ba,da bai mutu yana neman kudin da za'a masa aiki ba. Yawan mutanen da suke zuwa gaisuwa ba shakka banda taimakon Allah,da kuma taimakon kawu ado da gwaggo indo da basusan da abinda zasu ci dasu ba,saidai a taimakon wadan nan bayin Allahn aka dinga dafa abinci ana ci. Inna kuwa rabonta da gidan tun randa aka dauki gawar bilal,bayan an dawo daga binneshi,kawu ado yasa aka sauke buhun shinkafa babba dana wake,saita hau cewa a diba mata,wannan ai ya yiwa zuwaira da ahalinta yawa,ta dauko babbar qatuwar leda baqa ta buda bakinta. Ran wasu daga cikin 'yan uwa ya baci,amma saboda kowa yana shakkarta,saboda masifarta da bala'i yasa aka rasa mai tanka mata,sai wasu daga cikin jikokinta da suka fara qananun maganganu. Ganin da gaske take yasa yakumbo indo ta murje idanunta tayi mata magana "Inna,wannan kayan abincinfa ba dafawa akace a dinga yi ana ciyar da masu xaman makoki,kuma ko a hakanma yayi kadan,saina aika an sake siyo wani buhun" mita ta hau yi,har sai da taga ran yakumbo indon ya baci,kasancewarta 'yar gaban goshinta da batason tayi fushi,tilas ta haqura,daga bisani ma ana sallame sallar la'asar tace zata koma gida,ba wanda ya hanata ko ya tambayeta ba'asi,hasalima ma hakan yafi ma kowa kwanciyar hankali. ********Sanyi gami da lallausan qamshi ne kawai ke fita daga qawatacce kuma madaidaicin falon,wanda zai burge duk wani mutum ko da ina matsayinsa da arziqinsa yakai. Zaratan samarin ne su biyu kacal cikin falon,wato samir da Aamiru,samir din na sanye da wata riga short sleeve shirts da wando da iyakacinsa qaurinsa,dukkansu ruwan toka da adon baqi,wanda suka zauna jikinsa suka fitar da duk wata qira tasa tan murdewar jiki da murjewa, system ne a gabansa,yana duba wasu dokuna da akayi masa tallansu tun daga wata qasar,irin dokunansu ne na can,kasancewarsa mutum mai son dawakai,wanda a yanzu haka yana da guda uku nashi na qashin kansa,hakan duk sanda za'a gabatar da wasan tseren dokuna na polo to yana daga gaba gaba wajen zuwa,ba'a nigeria kawai ba,wani lokaci qafa da qafa yake fita wata qasar idan za'ayi,musamman idan akwai wanda yakeso a cikin wandanda xasuyi gasar tseren dawakan,wannan dabi'a tasa na daya daga cikin dalilan da yasa sunan saraki ya bishi. Amiru kuwa na kwance saman doguwar sofa yana amsa waya,yanayin yadda yake wayar ya isa ya gaya maka cewa wayace ta masoya,don kuwa iya murmushin da yake fita saman fuskarsa kadai zai gaya maka hira ce ta musamman. Kowa abinda yake gabansa yakeyi,kuma kowa najin dadin sabgarsa,har zuwa wani lokaci da aamirun ya gama wayar,sai ya miqe ya zauna kana ya zuro qafafunsa qasa,idanunsa akan samir,wanda ya gama zaben dawakan da yakeso cikin wadanda suka turo masa video dinsu "Yauwa,ina jinka,kace mene?" Inji amiru yana miqa hannu,ya janyo drink din da jawahir ta shigo musu dashi,musamman saboda yayan nata. Idanunsa masu kwarjini da kuma girma,wanda hasken system ya qarawa kyau ya daga ya watsawa aamiru yana murza tafun hannayensa waje daya,saboda sanyin ac din daya dan fara damunsa,duba da yanayin sanyi sanyi da aka fara a gari "Kaga malam,yi ta kanka kawai,zama zanyi nata yi maka bayani?,ko dan aikinka ne ni da zan zauna inta maimaita maka zance bayan ka gama gabatar da naka uzurin?" Dariya Aamir ya qyalqyale da ita yana jjiye cup din hannunsa "Sorry man,amma dai gaskiya ni bazan zauna na tasa aiki a gaba ba,kullum bani da abunyi saishi,tunda dai bashi zan aura ba ko?,bazan kuma biye maka ba,ya zamana daga ni har kai babu wani me qwaqwaran magana akansa,waima tsaya.....ina natun jauhar?" Yayi maganar yana zunkudawa gaba gami da tsare samir da ido. Dubansa yayi da manyan idanunsa da gasken computer ke sake shiga ciki,sannan ya kauda idon nasa,kamar bazai amsa ba sai kuma yace "Kaga malam,nifa bazan auri yarinyar nan ba" "Saboda me?,look saraki,wasu lokutan fa kai kake sake haifar da sabin fahimta tsakaninka da daddy,yarinyar nan she has everything da akeson mace dashi, she's beautiful...tana da gata tana da ilimi...then...me kake buqata sama da haka?" Fuskar computer din ya rufe ba tare daya kasheta bama,ya tsare amiru da ido don ya gane cewa kome zai fada da gaske yake "Duk abinda ka fada hakane,tana da komai,but....bazan aureta ba" daga haka yatsaya kawai,sai suka shiga kallon kallo shida amiru,wanda daga bisani amirun shiya dage kafadunsa kawai gami da tabe baki "Well,da alama you are ready to face the consequences,any way......dazu kamar kana maganar zuwa qauye gobe ko?, right?" "Dan rainin hankali,ashe ka jini" ya fada qasa qasa,kamar meyin mita,yana buda fuskar computer din da niyyar kasheta gaba daya,bai amsawa amiru ba har ya kashe,sannan ya dubeshi "Haka nace,saboda ginin makarantar ya kammala,ya kamata a budeta,saboda a samu dama a fara karatu,sannan....."sai yayi shuru yana jan iska hunhunsa,a duk sanda zai tuna da yaron sai yaji babu dadi "Akwai ragowar hakkin yaron nan,inason na kaiwa iyayensa" kai amiru ya jinjina,shi kansa daga yadda ya samir ya bashi labarin iya abinda ya sani game da rayuwarsu,da abinda yaji daga hannafi,da kuma abinda ya gani da idanunsa,sai ya tsinci kansa da tausayin yaron duk da ya tafi yayi nisan kiwo "Hakan yayi,kace na shirya,am in love with garin fa?,nima yanayin qauyen yamin.....sai naji nayi kewar azare,duk daba qauye bane" murmushi samir ya saki,shikam ya soma jin dadin tafiye tafiyensa zuwa qauyukan da yakeyi,saboda ya zame masa tamkar wata makaranta ce daya bude ta qashin kansa,yana ganin salo da nau'in rayuwa iri daban daban,harda wadda mafarkinsa bai taba kawo masa ba,saiya soma baiwa amiru labarin garuruwan da ya jajje,ciki harda qauyen dinya,wanda a cikinsa ne ya soma kwana. Wani abun yayi dariya wani abun yaja tsaki,amma dariyar da yakeyi din yafi yawa,bama kamar da yake bashi labarin yadda 'yammatan qauyen suke,da kuma yadda abokinsa haladu ya mato akan kaltum,daya fasaltawa amirun yadda kaltumen take harda fadowa qasa saboda dariya,don a ranar daya ganta ana cikin rudani da alhini ba wani kallonta yayi sosai ba "Dole muje,nima nayi koda 'yammata biyu ne na kafa tarihi" harara samir ya jefa masa sanda ya miqe da niyyar zuwa toilet "Kamar a kunnen khalisa" "Dama dai kuna shiri" ya amsa masa,sanin cewa ba wani shiri suke sosai da samir din ba,saboda kowa tsarin dan uwansan bai masa ba. ********Tafe take a hankali tana ratsa 'yan zaman makoki,iskar sanyi na kadata yadda taga dama,kasancewar ta sake wani ramewa da bushewa tun daga wancan ranar,hannunta dauke da geron data auno,wanda yakumbo indo ce tace a auna din,za'a kai ayi gumbar sadakar uku a gobe. "Yammataaaa" taji an fada,da muryar nan data tsani ji,har ta wuceshi yayu wuf yasha gabansa,ta daga kai ta dubeshi,itakam bataga amfanin rayuwa irin ta auwalu ba,koda yaushe ace mutum ba'a saitinsa yake ba,dai kaga yana gyangyadawa ko yana girgidi?. Wani busashen murmushi ya sakar mata "Yas......yaaa kuma wai qarun haqurinmu?,Allah ya jiqan bilale.....eh....ya kuma kyauta eh yane" tsaki taja tamkar xata tsinke harsheta,ta kuma maka masa harara sannan tayi gaba,tana jiyo lafazinsa na "Zaki bayani eh.....gobe zaki zama tawa" daukar zancan nasa tayi a matsayin shirme da molanka da wadanda suka bugu suka sabayi,don haka koda ta shiga ciki,ci gaba tayi da sabgarta,bata ma sake tuna maganarsa ba bare ta dameta,gaba daya su da uwarsu sun sake fice mata akai,laure tunda aka gama hada bilal aka fita dashi bata sake takowa bangarensu ba,dama ba zatace taga asiya bama sam,duk da yake ita kanta uwarta yanzu ganin nata sai sa'i,sa'i,saboda ta fantsama gari da sunan makaranta,makarantar da babu wanda yasan taqamaimai dinta,amma saboda tsabar ƁABI'AR ZUCIYA na son rai,duka sunbi sun rufe idanunsu daga kallon abinda yake faruwa,da kuma abinda zai biyo baya. Bayan sallar la'asar,suna zaune a dakin ummanmu ana hada 'yan tsummokaran bilal da za'a bada sadaka,idanun kaltum jiqe da hawaye,yayin da zuciyar ummanmu ke suya,jarumtar da tayi babu wanda ya zaceta,dai dai sannan babansu ya daga labule ya kirata ita da umman zuwa dakinsa. Dukkansu a darare suka shiga,bama kamar ya kaltum,wanda ta manta ma yadda fasalin dakin yake da abinda ke cikinsa "Ku qaraso ciki ku zauna" maganar data basu mamaki kenan,amma sanin cewa zukata a tausashe suke matuqa,cike da rauni saboda rashin da sukayi,sai mamakin nazu ya zama gajere,kowanne ya samu mazauni yana jiran ji daga bakinsa. "Yauwa,na kiraku nan ne don na tuna muku keda kattume cewa,wa'adin dana deba mata na fidda miji ya cika....tun ranar da bilalu ya rasu,to saboda wannan rashin ya sanya na daga mata qafa,na qara mata wadan nan kwanakin,koda na qara dinma abinda na fuskanta shine babu wani data tsayar,wannan dalilin yasa ni da iliyasu da laure.....muka yanke shawarar zamu baiwa auwalu aurenta kawai,kowa ya huta,tuwona maina". Wani irin kallo umman tayi masa,wani abu mai kama da bacin rai yana ratsata,laure?,iliyasu?,auwalu?,inda zata iya tambayarsa zatayi,shin laure ko iliya suka daukar mata cikin kattume har suka haife mata ita ko kuwa?,shin su ke da ahaqqu da ita da zasu dauki ragamar bada shawarar a hadata aure da lalataccen dansu?,wanda suma suka rasa yadda zasuyi dashi?,amma ba zata iya hakan ba gaban 'yarsu,zaidai bata jin zata iya shuru,saboda haka tace "Ka aura mata koma waye,matuqar mutuncinsa dabi'arsa da addininsa sun cika amma banda iliya". "Zuwaira me kike nufi?,wai ko abinda laure take fada naketa karewa ya tabbata gaskiya ne?" Kallon dake nuna ranta ya fara baci tayi masa,me yasa har kwanan gobe fifita laure yake a kanta?,kamar ma itace matarsa ba ita zuwaira ba?,kafin ta dire fadanta ya fara bambamin bala'i "Indai zuwara bakison jinin iliya nima baki sona,saboda abinda yayishi shi yayini,kin daurewa yarinya qarqashi taci gaba da zama gandandan a gabanki tana abinda taga dama ko?to wallahi ni nafi qarfin gidana,ba macen data isa ta takani kona mata biyayya,saidai a bini" Ranta yakai maqurar baci,saita kasa shuru "Yaushe Allah yayi daren bare gari ya waye?,kwanan kaltum nawa duka a duniya?,banda al'ada a yanzun kaltum bata isa aure a wasu guraren ba,ba abinda zaisa naqi jinin iliya,saboda jinin 'ya'yana ne,abu daya nace....ka aura mata koma waye,ko daga ina yake,ko wanne jinsi yare ko qabila ne matuqar ya cika sharuddan da za'a bashi aure amma banda auwalu,saboda banga wani garanti qarko ko kwaliti da yake dashi ba". Sai a sannan kaltum data kifa kai tana kuka ta daga kaibta dubi ummanta,karon farko kuma a kanta umman tasu ta maidawa babansu magana,abinda bata taba jin ko ganin ya faru ba tunda ta haifeta. Wannan abun shi ya qara harzuqa malam amadu "Ni kike maidawa magana zuwaira?,to wallahi wallahi ko ga waye saina aurar da kattume daga yau zuwa gobe,zabi guda uku,inma daga yanzu zuwa sallar magariba ta fitar da miji?,in bata kawo ba zanyi shelar bada sadakarta a sallar magariba ta anjima,idan ba'a samu me karba ba kuwa,babu uban daya isa ya hanani daura mata aure da auwalu a gobe wajen addu'ar uku koda sama da qasa zata hade.....ku tashi ku fitarmun daga daki zan kulle dakina" ya fada yana kadasu da hannu kamar wasu kaji. Duqawa ummanmu tai ta kama hannun kaltum ta miqar da ita,tana jin qirjinta yana suya,kamar takai gejin da ta fara gaza daukar abubuwan da suketa afkowa cikin rayuwarta ne,tana jin haka cikin ranta. Sannu a hankali suke takawa shi da amiru zuwa bakin masallacin da byan zuwan samir garin aka masa kwaskwarima aka gyarashi. Dukkansu suna daure da alwalar sallar magariba kowannensu,saboda mintuna kadan suka rage lokacinta yashiga. Suna tafe samir na nuna masa guraren da ya dan sani a zamansa a garin,abun sai yake qayatar da amiru,fuskokinsu kawai zaka kalla ka tabbatar da irin nishadin da suke ciki,duk da sunyi shiga ta baina baina,amma kana musu kallo daya zakasan cewa fatarsu da irin fresh da jikinsu yake dashi,basu saba rayuwa a irin wannan gurbin ba. A haka har suka iso bakin masallacin,sanda liman yake qwala kiran sallar,sai suka shige masallacin gaba daya. Sahu suka hada sannan suka zauna kafin lokacin da za'a tada iqama,yayin da hirarsu ta yanke,wannan dabi'a ce da suka samota tun asali daga wajen professor,tun suna qanana sanda suke zuwa masallaci salla. Daga bayansu kadan ya hangi hannafi ya shigo,ya samu waje shima ya zauna,da kadan kadan masallacin ya fara cika,aka tada iqama sannan aka kabbara salla. Minti biyar aka liman yayi sallama,masu azkar suka fara,masu gaggawar barin bigiren da sukayi sallah,ba tare da sunsan romon xama a inda mutum yayi sallah ba bayan ya idar suka fara gaggawar tashi "Ah jama'a assalamu alaikum,kowa ya dakata a inda yake,akwai muhimmiyar sanarwa" malam amadu ya fada bayan ya miqe tsaye daga sahun gaba da yake yana fuskantar masallaci,hakan yasa masu niyyar fita suka tsaya cak,na zaune kuma suka bada hankalinsa akanshi,ciki harda samir da amir da suka bishi da kallo. "Salamu alaikum jama'a a karo na biyu,kowa dai yasan sunana yasan waye ni,sanarwa nakeso na bayar na auren diyata kattume game buqata,inason aurar da ita a asubahin gobe idan Allah ya kaimu,ga duk wanda keso....na dauke masa nauyin komai,ya biya sadaki,shaidu su shaida a daura masa aure da ita" tsit masallacin yayi kafin daga bisaninya rude da hayaniya,kowa da abinda yake fada,wasu na fadin lallai ta tabbata yarinyar ta aikata abinda ta aikata shi yasa abinda ya faru ya faru din,yayin da wasu ke da sukasan ainihin rayuwar gidan malam amadu ke cike da mamakin abunda ya afku a yanzun,a iya saninsu wannan abun tsohuwar al'adace,wadda su kamsu qauyen duk da qarancin wayewa suka daina amfani da ita,cikin masu ganin baiken hakan harda hannafi,wanda yasan komai game da rayuwar gidan malam amadu. Ganin abun zai zama cece kuce sai liman ya karbi lasifiqa yayi magana "Jama'a batun nan ba'an kawoshi don a tattauna ba,duk me buqata,malam amadu na cikin masallacin nan sai ya nemeshi su tattauna,ko ya iskeshi a gidansa,kowa yana iya tafiya" "Nagodewa Allah da haladu baya nan" sukaji an fada daga bayansu,waiwayawa samir yayi,sai yaga abokin haladu ne,ya tuna abinda ya faru tsakaninsu a dandali,sannu sannu mutane suka fara yoyewa,wasu suka kafa sansani daga waje ana tattauna maganar,wasu na nuna sha'awarsu kan abun,amma sun gaza tunkarar malam amadu,sabida baqin fentin da aka yiwa kaltum din,yayin da wasu sukace zasu tsaya su kuwa suga tunqwal uwar daka. Dariya amiru yake sosai sanda suke komawa gida akan hanya "Gaskiya dole kaso zama a qauyen nan,abun dariya har gida,kaga yadda ake bada mace kyauta free babu ko sisin kwabonka?,anya kuwa master bani zan saka kaina ba?kasan Allah abun yayi min,kaga idan nadan more kona watanni ne,saina sallameta da abubuwan arziqi na qara gaba abina" Saraki wanda tunda suka taso baice komai ba ya juya ya dubi amiru,saiya sakar masa harara "U r very stupid amiru,baka da hankali hala?" Fuskarsa ya gyara sosai gami da muryarsa ya koma serious "Da gaske nake maka man.....wannan fa wata hanyace mai sauqi,aiba zina bace" qaqqarfan tsaki samir ya saki,sai kuma ya bushe da dariya "Babu abinda zakayi da wannan yarinyar malam, infact ma babu abinda zaka tsinta a jikinta,bata da komai din da kake kwadayi" dariyar amiru ya tayashi "Ka santa kenan?" Kafin yakai ga amsa masa saiga malam amadu kamar an jehoshi,cikin hanzari samir yayi gaba yana cewa "Salamu alaikum" dakatawa yayi ya waiwayo yana duban samir kafin ya amsa masa,samir din ya miqa masa hannu suka gaisa sannan yace "Sunana muhammadu,daya daga cikin masu ginin makarantar me tafasa" "Toto...eh...anyi haka" "Yauwa yaronka daya rasu bilal,akwai kudin sallama na aikinsa a wajenmu da zamu biyashi" wani farinciki ya saukarwa malam amadu,saiya fara matso hawaye "Allah sarki,Allah sarki bilalu,yaro mai qoqarin neman na kai,ai nayi rashi,nayi rashi ba qarami ba" duk da cewa ba komai samir ya sani ba game da abinda ke wakana,amma a yadda yaga kulawarsa kan rayuwar yaron,a ganinsa wannan kukan baikai ko ina ba,tun daga kaishi asibiti,rasuwarsa da kawoshi da sukayi gida.... Kansa ya gayawa wannan ba huruminsa bane,huruminsa ya sauke nauyin dake kansu,don haka ya share wannan daga ransa,ya irgo kudaden da gumin bilal ha samar dasu ya miqawa malam amadun,yasa hannu ya cafke yana zabga godiya ya wuce suma suka wuce. Ita kadai tana zaune amma cikin jikinta tana jin akwai abinda zai faru,tanajin tabbas babansu bai haqura ba,tunda ya fada din sai ya aikata,tunda ya quduri aniya sai yayi. Bata sake samun yaqini ba saida qawayenta,tawaga daga wasila sukazo mata wai da niyyar gaisuwar,abunda ya bata mamaki ya kuma daure mata kai,wasilar dako a hanya bata nuna alamun ta santa bare wani abu ya hadasu?. Bata nuna musu komai ba,tunda mutum ya nuna don kai yazo,sadai lantana dake tayata zama ko kallo basu isheta ba,har sai daga bisani sanda suka niyyaci tafiya sannan wasilar tace "Lantana abunma harda 'yar shariya?,saboda zaku zama amaren gobe da asuba?,muna muku murna,shi auren sadaka ai falala gareshi,Allah ya sanya alkhairi yasa a daura a sa'a,idan auwalunne ta kwana gidan sauqi,idan bashi bane kuma sai munxo ganin wanda aka canka". Idanunta ta daga tabi wasila da kallo,wadda ta kusa barin sassan nasu,wani birkicewa kwanyarta taji tana shirin yi,zancan ya fita kenan?,idan kuwa ya fita ba shakka babansu yakai maganar masallaci,idan taje masallaci da gaske auren zai mata a gobe da asuba?,ranar sadakar ukun dan uwanta?,lallai ummansu batasan da za can ba,saita daga idanu ta azasu akan ummanta. Tana zaune cikin 'yan uwanta,tanata qoqarin yaqi da damuwoyin dake ranta,indai hakane ya kyautu takai mata wannan zancan ta qara mata damuwa?,baya tasan babu abinda ya isa ya canza qaddararta?,sai kawai ta lumshe idanunta,tana qoqarin ganin ta saisaita tunaninta. Tabatan da akayi yasa ta bude dukka idanunta,lantana ce,fuskarta da idanunta cike fal da damuwa "Don Allah kada ki dorawa kanki damuwa saboda zancansu,wani abunma zasu qireshi ne saboda su bata ranki" wani busashen murmushi ta sakarwa lantana,don ta gusar mata da tata damuwar itama "Ban damu ba lantana,kawai ina tuna bilalu ne" "In sha Allahu hutu ya samu" "Muna fata" ta amsa mata,wani girma da qimar lantana take gani,ko meye zai faru da ita tana tsaiwa a gefanta,bata taba lissafa lantana cikin masoyanta ba saida wadan nan abubuwan suka faru,dama baka sanin masoyinka ko maqiyinka sai abu mara dadi ko mai dadi ya sameka,Allah kaci gaba da hadamu da masoyanmu na gaskiya,masu sonmu bilhaqqi amin. *********Ƙarfe biyar saura na asubahi,amiru na daga tsaye yana dora lallausar sweeter dinsa saman jallabiyar jikinsa bayan ya gama alwala,ya dubi samir dake zaune saman abun salla bayan ya idar da raka'atanil fajr yana qarasa tasbihinsa da yatsun hannunsa "Don Allah ka tashi haka mu tafi,kada mu rasa sahun gaba fa" sai da yakai sannan ya daga kai ya harareshi "Wai yaushe ka zama magulmaci ne?,koda kaje da wuri fa baka da ladan zuwa da wurin,don ba manufarka kenan ba" dariya ya saki yana dora hular tashi ka fiya naci saman kansa da yake aje suma "Allah so nake naga wannan dramer din ya zata kaya,sabon salon aurar da 'ya'ya mata,sai kace game?" Tsaki samir ya saki,ya dauko salati adadin yadda zaiyi ya qarasa sannan ya miqe yana nade dardumar da yayi sallah akai,zuwa sannan har amiru yayi waje,ya zura slippers yabi bayan amirun wanda yaketa faman kiran ya fito su wuce don Allah. *Duniya a yanzu ta cika da abubuwan da kake tunanin babu su,amma har wadanda baka taba kawowa akwai ba akwaisu* Labarin rayuwar da umma ke ciki gaskiya ne,ya faru,ni ganauce ba jiyau ba,ranar da yarinyar ke bani labarin rayuwar da suke ciki na gaya mata cewa "Banda ke da kanki kika gayamin zan qaryata ne!" Ranar da naji labarin rayuwar auren wata mata cewa nayi "Inda a novel ne cewa za'ayi DAMA AI SAIDAI A NOVEL DIN" saboda bamu rubuta koda kwatar rintsi tsanani da tashin hankalin data fuskanta ba Yaron dana sauya sunanshi da bilal yayi mutuwa sak irin ta bilal Na tsaya gaban gawarshi nayi kuka da idona Tana zaune a gidan sabida bata da wani gata ko kuma tsayayye da zai tsaya mata Idan tace zata koma gidansu gaban mahaifiyarta bata da wannan gurbin Yaranta duka mata ne Duka basuyi aure ba Gwara umma anan ta aurar da habiba Me yasa ko yaushe mukafi karkata ga zaqin labari Soyayya Dukiya Kyau Da jin dadi? Me yasa bamason mutuwa ko jarrabawa cikin labaranmu? Me yasa muke gudunsu bayan rayuwarmu a daure take da qalubalensu? Irin wannan ke canza tunanin marubuta masuyin labarin da zai zama ilimi da izina zuwa rubuta baragada saboda faranta ran masu karatu! Allah madaukakin sarki yana cewa "Shin mutane suna tsammanin za'a barsu saboda sunce sunyi imani ba zamu jarabcesu?,haqiqa mun jarrabi wadanda suka gabacesu........" 33 D/Z _ki tuntubi wadan nan numbers din don biyan naki ki karanta cikin aminci_ 08184017082 Ko kuma 09134848107 Suna shiga masallacin ana shirin tada sallar,yau masallacin a cike yake saboda addu'ar ukun bilal,don haka basu samu sahun gaba ba,sai a can baya suka zauna. Kamar ko yaushe aka idar da sallah,saidai yau mafi yawan mutane basu motsa ba aka fara gabatar da addu'o'i wa bilal,wanda aka dauki kusan minti talatin anayi kafin a kammala. Niyyar tashi samir yayi,sai amiru ya danneshi,dubansa samir yayi "Ka zauna malam,ai ba'a gama ba" kamar zaiyi magana saiya fasa,ya koma ya zauna,dai dai sanda malam amadu ya miqe "Jama'a akwai wanda keda sha'awar auren diyata kaltume?,idan har babu zan bada ita yanzu ga dan uwanta auwalu" maganganu ne qasa qasa suka fara tashi,tsahon wani lokaci shuru sai qananun maganganu "Akwai wanda ya shirya?" Malam amadu ya sake jefa tambayar ga mutane "Akwai" babu zato bare tsammani muryar amiru ta sauka kunnen samir,da sauri ya waiwaya ya dubi amirun,suka hada ido,sai ya fuske masa,tsoron halin amiru daya sanshi dashi ya darsu a ransa,yasanshi sarai,komai yana daukarsa wasa ne koda gaske ne,hakanan yana iya fadar magana a cikin wasa ka ganta a zahiri a aikace "To alhmdlh,yaro kaine zaka karba ko?" Malam amadu ya fada yana murmushin samun wanda zai baiwa kaltume din,kai amiru ya gyada "Ni zan karba,nawa sadakin?" "Aiko nawa kake dashi yaro ka bayar" mai gari ya amsa wannan karon. Tun samir yana ganin abun a wasa,sai gashi ya tasamma zama gaske,mutane sun fara matsowa ana dai daita magana,har takai ana buqatar amiru ya miqo sadaki. Aljihunsa ya shafa,bai fito da komai ba,amma kamar yaga samir yana zuba kudi a aljihunsa,wanda yace zai qarasa biyan ma'aikatan kudin gininsu,saboda a gobe yake son a bude makarantar "Aramin dubu talatin mana" "Baka da hankali amiru?" Ya tambayeshi qasa qasa yana zuba masa idanu a rikice "Yaro miqo mana,ko ila ajalin za'ayi?" Mai gari ya tambaya amiru,bayan sun gama magana qasa qasa da malam amadu kan baqin fuska ne,shin ya aminta a daura auren diyarsu dasu yace ba komai,zai bincikesu daga baya. "Gashi....shi ya karba min ne,za'a daura auren da sunan muhammad samir,shine waliyyi na" samier ya fada yana miqa kudin daya irgo. Baki da hanci amiru ya sake,ya jima da sanin cewa samir ya fishi sanin takan tsiya,idan ya debo rigimarsa dama shi kadai ke iya solbata,wannan abun da samir yayi masa yasan da manufa a ciki,bai sake tabbatar da haka ba sai da suka hada idanu ya banka masa harara. Cikin lokaci qanqani aka daura auren muhammad samir da ummu_kulsum kaltume,wanda ana gamawa mutane suka fara watsewa kowa ya tafi da lamarin a bakinsa,ta yaya malam amadu zai dauki diyarsa ya baiw baqo?,duk da an dan sanshi sakamakon aikin makarantar da sukeyi?. Raguwar da jama'a sukayi ya basu damar ganawa da me gari,shi ya damu yadan yiwa su samir wasu tambayoyi,da suka shafi cikakken sunansa da kuma garinsu da sunan mahaifinsa,dukka ya gaya musu,saidai ta sigar da bazasu gane waye ba,me garin yadan masa nasiha kan ya riqe amana,shi kuma ya shaida masa an bashi umarnin gobe a bude aikin makarantar da aka gina daga mai gidansa,murnar wannan ya sanya zancan auren yadan lafa,har gari yayi haske suna tare da me gari,tuni samir yaji ya gaji,sai yace zashi gida akwai saqon da za'a kawo,a sannan ne malam amadu da shima ke shirin tafiya gida don ya shaida musu daurin auren kaltumen yace "Zaka leqa kaga amaryar ne ko kuwa?" Kansa daya fara ciwo ya girgiza "Zanzo baba daga baya" "To...to saika shigo" Baiko samu sararin amsa masa ba yayi gaba,amiru da bakinsa ke cike fal da tambayoyin da ya gaza samun amsarsu ya dafa masa baya... Tunda suka fito yake jefa masa jerin gwanon tambayoyinsa amma bai kulashi ba,har sukayi nisa,suna haramar tadda gida "Kace wani abu mana....waime ka shirya ne?" Ya sake tambayarsa wannan karon adan qage saboda yadda ya gaza samun amsar kowacce cikin tambayoyinsa. Ba zato yaja cak ya tsaya,sannan ya waiwayo ya zubawa amirun idanu na wasu lokutta,har sai dashi amirun ya gaza daukar kallon samir din,gwani ne shi wajen iya hukunci da idanu,ya san da wannan tun ba yau ba "Idan kai zaka dinga wasa da rayuwarka kana daukar hakan ba'a bakin komai ba....ni bazan dauki wannan ba,akanme zaka rakitowa kanka auren gangan amiru?,oh....da nufinka shine kayi yadda ka gayamin ko?,ka gama tsara hakan,me yasa?" "Kai me yasa ka tare auren?,me yasa ka bari ya fada kanka?" Ya maida masa tashi tambayar cikin damuwa,don har ga Allah ya shiga damuwa,yace zai karba auren ne ba don wai yana nufin hakan ba har cikin ransa,ya fadi hakanne saboda yana ganin ba zasu bashi ba,kasancewarsa baqo kuma baquwar fuska a garesu,zasu qalubalanceshi akan hakan. Ajiyar zuciya samir ya saki,shi dinma yace shi zai karba ne saboda shigen irin tunanun amiru,ta yaya zasu bawa mutumin da basusan waye ba auren diyarsu?,ashe wautarsu ta wuce duk inda yake tunani "Na karba saboda na shirya sakinta ne da zarar kwadayin ubanta na aurar da ita ya fada,kuma hakan zai faru daga yanzu zuwa anjima,zuwa safiyar gobe da zan gama aikin daya kawoni garin na tattara na koma duniyata.....amma ka sani,kada ka sake gigin sake aikata wani kuskuren makamancin hakan,saboda idan kayi yanzu ka tsira,gaba zaka iya rasa wani abu da baka tsammata ba" daga wannan ya saki hannayensa da ada ya rungumesu a qirji ya soma takawa. Sai amirun ya kasa cira qafarsa daga wajen,ya bishi da kallon mamaki,duka yayi wannan abun ne saboda shi,ya dauki wannaj risking ne saboda shi,saboda ya tunkudeshi daga fadawa wanan matsalar,shi yasa a rayuwa yayi amanna da qaunar da samir yake masa wadda babu na biyunta,baya ga qaunae mahaifiyarsa a gareshi,wannan tunaninnm ya bashi qwarin gwiwar cira qafarsa da hanzari yabi bayansa. Yauma gidan akwai jama'a dake ta shigowa gaisuwar sadakar uku suna fita,sai kuma wasu daga cikin 'yan uwa na kusa sosai da suke tare da ummanmu,kamar su yakumbo indo,da umma altine habi sa sauransu. A filin tsakar gidan suke zaune saman tabarmi,a yanxun sai iya su isu,habiba da kaltumee na saman tabarma daya su biyu suna hirarsu qasa qasa,wanda su kadai sukasan me suke tattaunawa. Sallama yayi ya shigo,suka amsa masa,masu masa sannu da zuwa sukayi masa,ya gaisa dana gaisawa,sannan ya dubi kaltume "Ki kiramin babarku,kuzo keda ita" sai ya qara gaba yana bude dakinsa. Jikinta a matuqar sanyayen da batasan musabbabinsa ba tun dazu ta miqe,ta shiga dakin ummanmu ta shaida mata. Tare suka fito da ita suka nufi dakin nasa,zuciyar kaltum na wani irin bugawa da saurin da bata taba jin irin hakan ba,har kamar ana dan matsa zuciyar tata ne. Gefan gadonsa suka cimmasa a zaune,ya baza babbar rigar jikinsa yana dakon isowarsu,gefe daya ummansu ta zauna,sai kaltun din ta bita ta zauna a jikinta tanajin jikinta yayi wani irin laushi. Gyaran murya yayi kamar me shirin fara karatu,sannan ya dubesu,kanshi tsaye yace dasu "Kamar yadda nace,na kuma alqawarta,to na bada auren kaltum" a tare maganar ta bugi kowannensu,kaltum da batayi shirin kallonsa ba,batasan sanda ta daga kai ta dubeshi ba. Ya fahimci irin kallon da suke binsa dashi,a karon farko kuma yaji yadan daburce "Eh,yau dai nima na sauke nauyin da yake kaina,na aurar da sauran 'yata data ragemin,zanyi bacci kamar kowanne uba" mamaki mai girma ya kama umma,taci gaba da kallonsa kamar wani sakarai "Waye ka aura mata?" Dubanta yayi yana matse fuska "To meye na gaggawa?,koma waye na aura matan ai zaku ganshi,tunda kunqi auwalu ba shikenan ba an muku abinda kuke so?" Yayi maganar cikin fada fada,saboda baiso taci gaba da tambayarsa waye mijin?,don idan hakan ta faru bashi da amsar bata,shi kansa baisan waye ya aurawa kaltum din ba,amma koma waye yasan babu abinda zai faru bazai cinyeta ba,a iya nasa dan qaramin sanin da ya yiwa duniya kenan. Can qasan ranta umman ta saki ajiyar zuciya,tana jin fiye da rabin tashin hankalinta na kwaranyewa,saidai kuma akwai sauran fargaba a tare da ita,don batasan waye ne ya dauko ya maqalawa kaltum din ba,taji ranta yana motsawa,tausayi da bacin rai suka cakude waje daya suna karafkiya cikin ranta,kamar ba zata tankashi ba saita kasa,duban fuskar kaltum kawai ya daga hankalinta "A wannan zamanin?,a irin wannan lokacin zaka yiwa diyarka irin wannan auren na rashin siyar daraja da mutunci?" Idanunsa ya bubbude sosai yana hura hanci,baya so kuma baya sha'awar tayi masa wata magana,kota kawo masa tarnaqi kan hukuncin daya yanke ko misqala zarratin,don baiga uban daya isa yasashi ya janye wannan hukuncin ba "Ke zuwaira ki fita daga ido na,ita din uban wace da bazan zaba mata miji ba?,ina cewa yarinya budurwa uba ne dama yake da haqqin zaba mata miji,shine zaki hurewa yarinya kunne ki sakata ta bijiremin?,to wallahi ta gwada,bismillah,ga fili ga me doki nan,nida ku uban wanda ya fasa" da alamu jama'a yakeson tara mata,saita miqe tana riqe da hannun kaltum zuciyarta na quna "Ko da wanne lokaci fa zan tattarata a miqa masa ita" ya bisu da kalmar sanda umman ta kama hannun kaltum da tuni hawaye ya jiqe mata fuska,tsantsar tashin hankali kuma ya cika zuciya har saman fuskarta. Mamaki ya kuma kama umman,wanne irin abu ne kuma haka,a daura ma yarinyar aure ba tare da tasan mijin ba,sanna ace ta shirya kowanne lokaci zata iya barin gidansu?,babu wani shiri tanadi ko sakawa rai?,mema suke dashi da zasu kaita dashi?. Kamar yasan tunanin da takeyi saiya fiddo sadakinta daga aljihunsa,wanda sai daga baya daya nutsu ya lissafa yaga dubu arba'in da daya harda dari biyar akai,yana da yaqinin zata yi ma yarinyar kayan daki,ya lissafa ya dauki dubu ashirin ya miqa mata "Nasan dai tunanin da kike,gashinan ayi mata wani abu dasu wanda zata tafi dasu,daga baya aje ayi mata jere" "Amma wannan wanne irin al'amarine fisabilillahi malam?,wannan abun fa kwata kwata baiyi dai dai ba,yadda kake da haqqi a wuyanta itama tana da nata haqqin....." Saiya zaburo ya fara maganganu,maganganun da suka sanyata dole ta janye kaltum,suka fice ranta a mugun bace. Kasa riqe kukanta kaltum tayi sanda suka koma daki,su yakumbo suna tambayar lafiya?,ganin yadda yanayin fuskarsu ya nuna zallar tashin hankali. A karon farko bayan dukka abindanya faru,qwalla ta subuce daga idanun umman sanda take gaya musu abinda ya faru,ran yakumbo a bace ta miqe "Haba,wannan abun yayi yawa,bari naje na sameshi,yarinyar yar tsana ce ita da za'a bada ita sadaka?,batasan miji ba miji bai santa ba?,sannan ace a shirya kowanne lokaci za'a kaita?" Harta sanya kai kawu ado ya shigo gidan,ta dubi qofar dakin amadu a kulle,da alama ya fice abinsa "Ke kuma lafiya kamar wadda aka koro" kawu ado ya fada yana kallon fuskar yakumbo indo data cika da bacin rai "Shigo daga ciki yaya" ta fadi tana juyawa dakin umma,saiya sanya kai shima,ya samu kujera yaja ya zauna. A taqaice yakumbo ta labarta masa komai,sai yayi shuru yana jinjina kai,tabbas lamarin ya bugeshi ya kuma bashi mamaki,hakanan tun a hanya daya taho aka bashi labarin,saidai bai gasgata ba,ganin labarin yayi kama dana qanzan kurege. "Da farko mu soma aiki da hankali tukunna,dukkaninmu nan amadu ya fimu iko da diyarsa kattume,hakanan a cikinmu babu wanda ya isa yaja da hukuncin daya yanke akan diyarsa koda gaban alqali akaje kuwa....saidai idan ita yarinyar taja da kanta,idan akwai abinda zamu iya cikin wannan lamarin bai wuce mu bashi shawara,mu kuma nusashe da shi ba,idan ya dauka haka mukafi so,idan bai dauka ba kuma,mataki daya zamu dauka,mu binciki halayyar yaron sana'a gami da nasabarsa,idan muka tabbatar da bashi da matsala a dukka wadan nan,sai muyi haquri,mu bi auren da addu'ar sanyawar albarkar ubangiji" a hankali zukata suka soma sauka daga bayanan da kawu ado yayi,ga duk me nisan hankali a cikinsu idan ya yiwa kalaman kallo na tsanaki,zai hango ya kuma shanshano gaskiyar zancan kawu ado,saidai ko daya zuciyar kaltum bata rusuna ba,saima tashin hankali data sake shiga dajin zancan kawu adon,yana nufin kenan a haqura a miqata ga duk wanda baban nata ya bata aurensa?,saita sake fashewa da kuka cikin tashin hankali. *******A nutse yake shiryawa duk da cewa yayi nisa a tunanin da yakeyi,har ya gama shirinsa tsaf,ya dawo a hankali ya zauna gefam katifa yana jan kayan breakfast dake saman wani babban tray da niyyar yin break aamiru na zaune saman wani stool yana dubanshi,hannayensa goye a qirijinsa. Hannayen nasa ya saki yana sauke ajiyar zuciya,fuskarsa da alamun damuwa yace "Am asking you since yesterday.....ya zakayi da auren nan,bakace min komai ba" kamar ko yaushe harara ya watsa masa yana hada tea din,sai daya kammala ya riqe kofin a hannunsa zaikai baki sannan yace cikin wani irin soft voice "Da zaka dameni duk ba kaine ka jawo komai ba?,dana sani ma na qyaleka,idan yaso in ka koma hajiya qarama tayi banda da namanka" duk da tasirin damuwar dake tattare dashi amma sai daya daara,kana ya koma ya daidata zamansa sosai,cikin seriousness yace "Am bother to ask you ne saboda hajiya qaraman da kuma boss professor,but u are feeling bossy,sai wani jamin aji kakeyi" "An ja makan,idan kaji haushi ka barni da matsalata" kafada amirun ya dage "Kome zakace zan dauka,saboda bamu saba hadiye damuwoyinmu mu kadai ba" qaramin murmushi ya subucewa saraki,saiya aje cup din a gabansa,ya hade yatsunsa waje guda yana kallon amirun "Wani abun mamaki,ban dauki wannan abun daya faru a bakin komai ba,but amma sai naketa jin nauyinsa a kaina tun jiyan?" Shuru ya ratsa tsakani,amiru ya saki ajiyar zuciya,muryarsa tayi sanyi fiye da dazu "Ni kaina gaba daya tunani na ya qare akan yadda wannan al'amarin zai warware....ni inaga.....me zai hana ka qara ko one week ne,ka more sadakinka kawai,daga nan ka rubuta masa takardarta kawai ka maidata gida?" Wanu banzan kallo ya jefa masa "Kana tunanin zan iya hada jiki da wannan yarinyar?,kai anaka tunanin yarinyar ma dukanta ta isa wani moro ne?" Kai ya kada "Ba haka nakeson matata ta kasance ba,baya ga haka ta yaya zan cutar musu yarinya?,na karbe mata darajarta kuma na rabu da ita alhalin bata yimin komai ba?" Gira amiru ya dage "Ok,kawai ka gama bude school din muyi tafiyarmu,dole idan suka gaji da nemanka su warware abinsu su ba wani" fuska saraki ya matse yana dubansa "Ya kakeson canzawa daga amirun dana sani ne?,ka manta who iam?" Shuru ya sake biyo baya,idanunsa ya janye ya dauki cup dinsa ya sake kurban tea sannan yace "Zanje kawai na basu haquri kan ban shirya ba na karbi aurenta,zan rubuta mata takardarta na bata kawai shikenan an wuce gurin,ba wani yaudara ko kwana kwana" kai amiru yake jinjinawa,yasan halin samir,dama ba zaya dauki shawararsa ba,yana tarar komai gaba da gaba ne,bai iya boye boye ko qumbiya qumbiya ba,idan kuwa har kaga yayi hakan,to ba qaramin abu bane. Sanin cewa koda ya sake cewa wani abun,hakan bazaisa samir ya sauka daga ra'ayinsa ba,saiya miqe yaci gaba da shiryawa,dai dai sannan umar yayi sallama ya shigo "Ka dauki kayanmu duka ka saka a booth,get ready....ana gama bukin bude makarantar gida zamu wuce direct,ya kamata nayi facing my agendas" "Ok sir" umar ya fada yana jan babbar jakarsa daya zuba komai nasa a ciki yayi waje da ita. Taro akayi sosai na bude babbar makarantar primary da secondary ta me tafasa,wadda aka canzawa suna,kamar yadda samir din yakeyi a duk sanda yayi wani aiki. Bangaren primary daban,na secondary daban,ga bandakuna da offices na malamai,abun dai masha Allah gwanin sha'awa,za'a iya gabatar da karatun boko da kuma islamiya duka a ciki. Duk wani motsinsa yaro daya ya tsaye masa a rai wato bilal,ya dinga kallon guraben dayafi yin aiki a guraren,a irin wannan ranar yayi masa tanadin abubuwa masu yawa da zasu inganta masa rayuwa,saboda yadda ya karanci yana da buri kan yayarsa da mahaifiyarsa,saidai tsarin ubangijinya danne,ya kuma shafe tsarun dukkan wani me tsari. Farincikin daya gani saman fuskar al'ummar mabuqata,talakawa bayin Allah shi ya dasa nasa farincikin da walwala kan tasa fuskar,har cikin zuciyarsa ya dinga jin farinciki da nishadi,he believes a rayuwa babu abinda yafi ka farantawa wanda yake da buqata ta hanyar biya masa tasa buqatar,yana jin abu daya ne a yanzu ya rageshi a duniya,RASHIN UWA MAHAIFIYA DAURA DASHI,KO TANA INA???,itace tambayar da yake yawan yiwa kansa,yana da tabbacin tana raye,saboda karo na barkatai da yasha yin mafarkinta tana gaya masa cewa tana raye,amma wani SHAMAKI data sanyawa zuciyarsa yasa ya kasa yunqurin komai wajen isa gareta. *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar 34 Kamar wadda ta tashi jinya haka take tafiya salalo salalo zuwa sashen kawu iliya,hannunta dauke da botikin qarfen inna laure da umma ta bata takai mata,yara suka kawo nan sashen ta suka ajjiye. Sau biyu tana sallama,saidai kallo daya asiya dake tsakar gida saman kujera 'yar tsuguno fesa kwalliya tayi mata ta baiwa banza ajiyarta taci gaba da kwalliyarta,tana sa ye da wani tsalelen lace,har sai da inna laure dake daki ta fito,tana sanya slippers dinta da asiyance ma ta siya mata "Au...au ashe amarya ce,amarya manya,amarsu kin sha qamshi,amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida" kamar hadin baki sai suka kwashe da dariya gaba dayansu,asiya ta fara tsaida tata dariyar "Ni wallahi Allah har mamaki nake ma yadda kattume ta fito tatsatsanmu,kaf yaran gidan nan babu wanda ya kaita baqi da muni,kiyi haquri fa gaskiyata nake fada,koda yake ma ke da kika kusan tafiyarmi gidan miji....au na manta ban miki Allah ya sanya alkhairi ba,kada ace kana baqinciki,duk da ma kafi qarfin ka yiwa mutum baqinciki,Allah ya sanya alheri,ya kawo tsala tsalan yara" dariya suka sake kecewa da ita "Ga munu ga talauci,ta ina tsala tsalan yara zasu samu?,don nasan duk wanda ya dauketa dai ajin rayuwarsu daya,tun daga suffa zuwa wadata,ai yara tsala tsala saiku a gidan alhaji uba" farrrr asiya tayi da idanu,kafin su sake cewa wani abu kaltum ta ajjiye botikin ta juya da hanzari,duk yadda taso maida amsa amma ta gagara,kalamansu sun mata muni sosai da bazata iya juresu ba. A qafa suka tako shida amirun,tun daga makarantar har zuwa qofar gidansu kaltum,amirun yanata mitar yasa takalmansu duk sunyi qura,me yasa bazai bari a qaraso dasu a mota,bai kulashi ba har suka qaraso qofar gidan. Qarqashin bishiyar dake basa iska a wajen ba kowa sai kawu ado da babban dan yakumbo indo,a nutse suka qarasa da sallamarsu,saiya miqe daga kashingidar da shi kawu adon yayi ya zauna sosai yana amsa sallamar,tare da basu damar zama. Takalmansu suka tube sannan suka zauna din,sukayi musabaha mai cakude da gaisuwa ya amsa musu,shuru ya ratsa na sakanni,sai amiru yace "Wajen mai gidan mukazo" "Wanne daga ciki?"kawu ado ya tambaya yana kallonsu sosai,sabida baqin fuska ne a wajensa "Baban kal.....kal" samir ya fadi yana kakarewa,saboda son tuna sunan da yake qoqarin yi "Baban kaltume?" Kawu ado ya qarasa masa,sai amiru ya gyada kansa yana cewa eh "Ko kaine mijin kaltumen?" Kawu ado ya tambaya yana duban amiru,sai yadan daririce,hakan yasa samir ya nuna kansa "Nine" kallonsa ya dauke daga kan amiru ya maida ga samir yana qare masa kallo,gami da fadin "Ma sha Allahu,sannunku dan samari,dama ina bidar ganinka kuwa" kawu ado ya fada yana gyara zamansa sosai. Kwarjini yadan yiwa samir din ganin yadda kamalarsa ta sake fitowa bayan ya zauna sosai yana fuskantarsu,sai shima ya gyara zamansa yana cewa "Ma sha Allah,nima magana ce ke tafe dani dama" "To bismillah mana" kawu ado ya bashi dama "A'ah baba,ba damuwa,ina saurarenka". "To alhmadlh,nasan dai baka sanni ba,bakuma kasan alaqata da kattume ba,kattume kamar diya take a wajena,diyar yayata ce,banu wani boye boye a tsakaninmu,tunda an riga da an zama daya,duk da dai kai din da alama baquwar fuska ne,to amma kattume marainiya ce duk da tana da uba,sannan ita da dan uwanta gaba daya rayuwarsu ta kawo yadda take akaine a yanzu aboda huwacewar ubangiji kawai,yarinya ce da gwara wani marayan da ita,don Allah,don son annabi,ka riqeta bisa gaskiya da amana,saboda tasha wahalar rayuwa,tun batakai haka ba take ci da kanta danuwarta dama qannenta,tana buqatar matallafi,tana buqatar bangon da zata jingina dashi,munso yi mata hakan,amma bamu samu hadin kai daga wajen ubanta ba,sai muka rakata da addu'a,saboda munsan cewa ita din diya macace,kuma komai daren dadewa zata samu miji ne tayi aure,wala'alla wannan shine silar hutawarta daga dukkan wani qunci da matsi,ka duba darajar fiyayyen halitta kayi mata ruqo na mutunci da adalci.....kai din asalin da inane?" Ya zarce da tambayar samir,bayan yakai qarshen kalamansa da suka sauke duk wani shiri na samir din ba tare daya shirya hakan ba,ya buda baki da niyyar magana hayaniyar yaran data tunkarosu ta mamaye wajen,hayaniyar taja hankalinsu,ya daga kai yana duban yaran da suka taso wani saurayi a gaba "Kaga da wanda akayi shirin bata nan,Allah ya dubu irin maraici da girman biyayyarta ga mahaifiyarta ya musanya mata,tunda kai din muna kyautata maka zaton alkhairi" A hankali ya daga idonsa yana dubansa,shine wannan saurayin daya kubutar da ita daga hannunsa "Meye alaqarsu?" Ya samu kansa da tambayar kawu ado sanda yaga auwalun ya shige cikin gidan,bayan badaru dan yakumbo indo ya kora gayyar yaran "Dan qanin babanta ne,kuma ba haka suka so ba,don ko a yau auren kattume ya mutu sai sunsan yadda sukayi suka liqa mata shi" ya fada cike da takaici,shuru yadan sake giftawa,saiya sake maimaita tambayarsa "Yaro dan inane kai?" Kansa yadan saddar qasa,yana tunanin yadda zai yiwa mutumin dake a karkara irin wannan bayanin mahaifinsa "Ni dan garin azaren jihar bauchi ce,amma kuma a kano nake zaune,anan na taso" "To...to ma sha Allah,to ta yaya yaro zamu iya samunka kenan?" Shuru ya sake biyo baya kafin ya samu abun fada "Unguwar makwarari,duk wanda ka tambaya gidan malam nura zai kaika,ka cewa malam nura kana neman samir ko saraki,zai kawoka inda nake" "Samir,saraki....to to....to shikenan,babu damuwa" ya fada yana jin gamsuwa a ransa,bayan ya hada wannan bayanan,da kuma bayanin da malam amadu yayi masa a tsaitsaye kan cewa su aka turo sukayi ginin makarantar da ake budewa yau,haka kawai yakejin wata gamsuwa da nutsuwa kan yaron,yasan unguwar daya fada din,yakan shiga cikin gari,kuma yana da abokima a anguwar,dake zuwa sari wajensa duk qarshen wata na kayan hatsi. "To malam samiru banji naka batun da kazo dashi ba". Shuru ya danyi,yana jin dukkan wani bayani da quduri nasa da yazo dashi yana saraya gami da bin iska,tamkar bayanin da kawu ado yayi masa ya warware komai daki daki ne,sai yaji nauyin mutumin,a yadda kamalarsa take,da irin roqon daya dinga masa da fatan alkhairi,yanzu shi kuma ya buda baki yace yazo sakin diyarsa ne?. Muryar malam amadu ta ratsa tsakiyar tunaninsa ta tsinka zaren "Tun yaushe kuka iso malam muhammadu?,kada dai ace daukar yarinyar nan kukazo yi aka barku a nan?" Kallon takaici kawu ado yake bin malam amadu dashi,shi sam.bai damu da sanin komai akan yaron ba?,sai qoqarin cusa masa yarinya yake kamar yar tsuntuwa ba diyar cikinsa ba "Amm....malam amadu,ni a ganina daukar yarinyar nan yana da buqatar nutsuwa ko kuwa?" Dubansa yayi "Wacce nutsuwa kuma?,bazai wuce kuce siyayyar kaya ba,yo ku basu kudin kayan mana,sayi siyayyarsu su siya abinda ransu keso,kabar yaro ya dauki matarsa,daga baya maje muga waje" . A sannan inda ya lura da kyau wani kallo samir ke binsa dashi,ya yadda ya amince ya kuma yi imanin lallai yarinyar batayi sa'a da kuma dacen uba ba,yasan tsaf zai bata ran kamilin mutumin da ya shaida musu suna kawu ado,don haka ya shiga maganar "Kawu,inaga a barta din kamar yadda kace,idan naje gida na dawo sainazo na dauketan" murmushin takaici kawu ado ya saki "Babu komai malam samir.....bari amusu magana,ku tafi din,Allah ya tsare hanya,ya baku zaman lafiya" kafin ya dire wannan kalaman ma tuni malam amadu yayi ciki,ransa a bace yana mitar ana shiga gonarsa,shida iyalansa amma ana musu shishshigi?. Yasan komai yana iya faruwa a cikin gidan,don haka da murmushi saman fuskarsa ya miqe "Ina zuwa,kuyi haquri don Allah bari a fito da ita,kunsan sha'anin mata,kada suje su bata muku lokaci" a hankali amiru ya gyada wuyansa da yakeji kamar an sauke masa guduma,yayi alamar to,yabi kawu amadu da kallo sanda ya shige cikin gidan yana saba babbar rigarsa. Sai daya shige ya maido dubansa ga samir,magana yakeson masa amma wanzuwar badaru a wajen ya hanashi magana,bashi kuma da tabbacin ko yaqinin baya jin turanci ko qanqani bare ya juya harshe,saboda ya ganshi fes dashi fiye da yanayin sauran samarin qauyen,yasan kuwa bazai rasa karatu a tattare dashi ba,sai shuru yaci gaba da sukwane musu lokacin,amiru cike da mamakin samir din daya ruguza duk wani abu da yace masa zai aiwatar,kuma ko sau daya bai kalleshi ba bare yayi masa nuni kan ya taso su kebe suyi magana kafin a kai ga fitowa da yarinyar. Tana daga dakinsu,amma sallama guda daya tak ta mahaifinsu ta haifar mata da wata mummunar faduwar gaba data hanata zama,saita miqe tsaye cak ta tsaya sanda taji yana maganarsa gaba gadi a tsakar gida "Ke zuwaira..…ku shirya yarinyar nan,mijinta yana waje yana jiranta zasu tafi,kuyi maza maza ku hanzarta" a hankali ta daga kai ta dubi mijin nata,tana jin yadda zallar rashina adalcinsa yakai mata ko ina ma rayuwarta,bazai sauya ba,babu abinda zai sauyashi,saidai ta sani cewa ta roqi Allah,koma meye zai shigo rayuwar kaltum din yazo mata da sauqin da babu wanda ya zata a cikinsu "Dake fa nake magana,ku hanzarta da Alla kada kubar mutane suna jiranku" daga haka ya juya hankalinsa kwance ya nufi cikin dakinsa. Tsam ta miqe daga durquson da tayo gaban murhu tana shirya itace,saboda girkin da takeson ta dora musu,sakamakon yadda kaltume din gaba daya ta koma bata iya tsinana komai,mayafinta dake kan igiya ta janyo ta sanya,sannan ta kutsa kai ta fito ainihin babban tsakar gidansu. Tana niyyar zarcewa zuwa waje tanimu dan maqotansu daya fito daga sashen inna laure ya fito "Yauwa tanimu,leqa daga waje qofar gida,idan kaga baqin fuska kace musu anason magana da mijin kaltume" tace da yaron "Nama sanhi ai,ogan ginin makarantar mai tafasa ne"ya amsa mata,saita dafa kansa "Yauwa,yi maza ka kiramin shi" ya cilla kuwa da gudunsa yayi waje,yayin daya barta da juya maganar tasa,indai hakane kenan yana nufin uban gidan su bilalu ne?,ya akayi har yaje ya karbi auren kaltume da hannunsa da kuma amincewarsa?,tambayar data tsaya mata kenan a rai. Dan jim samir yayi yana juya kiran da aka masa daga cikin gidan,yana kuma jinjina kalmar mijin kaltume da aka kirashi dashi,sai yaji kalmar shi kansa tayi masa nauyi qwarai,sai kuma ya miqe yana zura takalmansa,cikin tafiya ta nutsuwa ya kutsa kai cikin soron,yana kallon zaizayayyar katangar gidan,yana sake girmama ubangiji da yayo mu mabambanta,hakanan ya bambanta mu cikin rayuwa wadata da samu da kuma jin dadi. Tunda ya doso soron ta zuba mishi idanu a fakaice,tabbas shi dinne,duk da gani daya tak ta taba yi masa amma ta shaidashi,duk wani karatu irin na hankali nazari da kuma lissafi daya kamata kayi akan mutum tayi namijin qoqarin yi a kansa kafin ya cimmata. A zahiri bata ga wata siffa ta tawaya ko siffar da zata nuna maka cewa akwai wani matsala dangane da dabi'a da kuma halayyar mutum ba,duk da kuwa cewa bawai ta sanshi bane sani na dabi'a da halayya ba,to amma kuma....data dauko wanna nazarin ta hada da labarai da bilal je basu a lokacin da yake raye dangane da halayya da dabi'unsa,sai taji wani sashe na zuciyarta yana mata sanyi da haske,duk dadai ta hangi tarin tazara da kuma bambanci a tsakaninsu,ta kasa jin nutsuwar cewa shida kansa ya zabi diyarta kaltume,ba zata bari ta yaudari kanta ba,wannan sam baiyi zubi ko suffar irin mutanensu ba,akwai alamun tazara da bambancin duniyar rayuwa a tsakaninsu. Shuru ne ya ratsa tsakaninsu bayan gaisuwar data gilma,umman ta tattara dukkan kalaman bakinta sannan ta motsa cikin yanayi na nutsuwa irin na uwa "Duk da cewa babu wanda ya gayamin ko mukayi maganar dashi,amma zuciyata ta kasa yarda gasgatawa ko kuma gamsuwa akan cewa kaine da kanka ka zabi kaltume na amatsayin matar da zaka aura,banbamcin yanayi da kuma yadda aka bada tallanta ko ince sadakarta ya gayamin haka,zuciyata tafi gayamin cewa......ka karba auren kaltum ne saboda wala'alla tausayi taimako ko kuma wani abu daya shafi hakan,toh....koma meye,nidai zan roqeka,koda ka auri kaltum ne don ka nesantata da rayuwarmu zuwa wani lokaci,zan gode maka,aqalla zata samu wani sukuni na taqaitaccen lokaci da muka gasa samar mata....zan kuma roqi alfarmarka akan ka riqemin ita amana,ka kulamin da rayuwarta,nayi yaqini da kuma imani da Allah,tunda har na roqeshi,na kuma nemi zabinsa,toba shakka abinda ya aiwatar a yanzu akan kaltum dai dai ne,kuma ina saka ran alkhairi ne ga rayuwarta,ban damu ba,koma daga ina kake?,koma daga ina ka fito,nasan cewa ubangiji baiyi koma meye ba domin wofantar da addu'ata ba,ALQAWARIN ALLAH NE cewa,bawansa bazai taba daga hannunsa ya roqeshi ba,shi kuma ya dawo masa da hannunsa haka ba tare daya amsa masa ba,ko a kusa,ko a nesa,kaje da kaltum amma bisa ruqo na amana". Kowanne gefe idan ya juya sai yaji ya kasa amayar musu da dalilin xuwansa,baizo don ya tafi da diyarsu ba,yazo ne saboda ya warware igiyar data dauru a kanta dalilin amiru,amirun dashi kansa ya aiwatar da komai bisa wasa,wasan da yayi kama da ganganci sak!. A hankali umma ta yaye labulen dakin,zuwa sannan ta jima ta suman tsaye,fuskarta tayi sharkaf da hawaye,tamaqale jikin bango sai kace mai shirin tsagashi ta wuce ta ciki. Tun umman bata qaraso ba ita ta isa gareta a sukwane ta fada jikinta "Ummanmu...ummanmu" sai kuma ta kasa furta komai,cikin wata irin dakiya tace "Ya isa,a ko ina kike Allah yana tare dake,hakanan kina tare da addu'ata da izinin ubangiji" data daga kai ta kalli ummantata,sai dakiyar umman ta bata tsoro da mamaki,ta bita da kallo sanda take isa inda take tara kayan sawarta ta fara hada mata waje daya "Ummanmu,bamuyi sallama da habi ba" ta fada hawaye yana sulmiyo mata "Indai da rai da rabo,watarana zaku gana" kalaman umman da sukazo mata kenan,suka kuma fi yi mata kama da kalaman wanda ke sallamar bankwana izuwa qiyama idan anayi. Idanunta qyar bisa ga mahaifinta sanda yake sallamata izuwa ga hannun baquwar fuskar da bata taba koda magagin cewa wata alaqa zata hadasu ba,riqe da qullin kayanta da ummansu ta hada mata "Muje ko?" Ta tsinkayi baquwar murya tana bada umarni a gareta,saita daga jiqaqqun idanuwanta ta dubeshi,ta sauke a hakali ta maida ga bigiren da mahaifinta ya wanzu ashi dazu,wayam yake babu kowa,ta sake duban hanyar da ummanta ta rakota,itama babu kowa sai takun sawayenta,saita sake dubansa karo na biyu,karo nabiyun da zuciyarta ta buga mata da wani irin qarfi,saboda yadda taga fuskarsa a tsuke,cike da wani irin kwarjini da bata taba katarin ganinsa a fuskar wani ba. A hankali ta fara daga qafafunta tana jefasu zuwa gaba,tana fatan dagasun da takeyi yayi da dai da sunan tafiya,zasu turata zuwa gaba kamar yadda ya buqata,tana iya ji da ganin sanda suka zartata a tafiya,shida amirun da a sannan batasan ko waye ba,taga dai ya qara sauri ya kuma cimma wanda aka kira da sunan mijinta,taga ya kama hannunsa da alama magana yakeasa,saidai bata damu da jin me suke tattaunawa ba,idanuwanta sunfi hango mata zaizayayyen gidansu,da ummanta dake cikin dakinta tana kuka. 35 D/Z *Littafin kudi ne,don girman Allah idan kin gani karki mana sharing,biya naki ta wadan nan numbers din ki karanta cikin aminci* 08184017082 Ko kuma 09134848107 "Saraki....wai me kake shirin aikatawa ne?,are you in your sense?" Aamir daya riqo samir a rude ya furta yana duban qwayar idanun samir din. Hannunsa ya zame daga cikin ma Aamir yana dubansa shima "So kake nace bazan karbeta ba?,so kake nace musu na saketa?,so kake na gayawa wannan rarraunar uwar cewa na saki diyarta kwana daya tal da daura mata aure?,wannan uwar data karbi dukkan qaddarar auren diyarta ga wanda bata san ainihin koshi waye ba?,ko kuma so kake na gayawa wannan dattijon kawun cewa na saki 'yar 'yar uwarsa?,aurenta baya nufin komai...hakanan bazai sauya komai ba" "Duk da haka.....ta yaya zaia fuskanci daddy prof ka gaya masa ka daura aure ba tare da sani ko yardarsa ba?" Qaramin murmushin da iyakarsa lebe ya saki,don shi kansa yasan murmushin bai kai qasan zuciyarsa ba,shi da kansa yake gina tunanin abubuwan tashin hankalin da xasu biyo baya ya kuma yi musu fenti su fito radau kamar gaske,ciki kuwa harda sake tabarbarewar soyayya da fahimtar junan da yake tattali,wanda tayi qaranci tsakaninsa da mahaifinsa,sakamakon bambance banbamce na abubuwa masu yawa a tsakaninsu,wani sabanin ma baya sanin ainihin abinda ya haifar musu da shi,yakan zo ne haka siddan a wadansu lokutan "Kada ka damu a abinda zan gaya masa, just wait and see what will happen". Kanshi amiru ya dafe "Me yasa nayi coursing maka wannan matsalar?,why?" Gajeran murmushi ya sake fiddawa "Bawa baya wucewa qaddararsa,dama qaddarar tawa ce" itace amsar daya bashi,kafin amirun ya juya zuwa bigiren da kaltume ta wanzu akai tana biye dasu,har yanzu fuskarta shafe da hawaye da qananun majina "Tana bayanmu ne fa saraki" "Garinsu ne,ba zata bata ba" ya amsa masa a gajarce. Shuru ne ya zamar musu babban dan rakiya,har suka riski motocinsa guda biyu dake dakon jiran dawowarsa,tunda taga sun nufi motar ta fara takawa a hankali,cikin tsoro da fargaba,mamaki kuma ya maye gurbinsu gaba daya sanda taga amiru ya bude murfin motar ya shige,shima samir din ya bude daya bangaren da niyyar shiga,sai taga ya fasa,ya waiwayo yana dubanta,xuwa sannan ta tsaya cak maqale da kayanta tana qare musu kallo "Zoki shiga"yayi maganar yana bude murfin daya motar da tafi kusa dashi,sannan ya sake maida dubansa ga baqar fuskarta,wadda tsabar tashin hankali gami da kuka ya qara mata shining,ga kuma hasken rana dake dukan fuskar tata. Kanta ta girgiza alamun a'ah,don tanq jin cewa koda sama da qasa zasu hadu ba zata yarda ta shiga wannan abar da taji suna kira da sunan mota ba,hasalima wajen gudu take nema,mutanen da bata taba ganinsu suna yawo dako keke ba a karkarar tasu,amma su suka bude wannan abar mai suna motq zasu shiga?,to shin waima ina suka samota?. "Ki shiga mu tafi,lokaci yana qure mana" ya fada wannan karon yana dan dava murya. Da qarfi ta girgiza masa kanta,donta fuskanci kamar bai fahimci na daxu ba,amiru wanda yake kallon duk abinda ke faruwa ta mirror,yana kuma qoqarin boye dariyarsa,kasancewarsa ma'abocin dariya koda yaushe,ya leqo da kansa ta window sanda yaga ta fara takawa da baya da baya alamun barin wajen. "Saika mata dabara,da alama batasan irin wadan na motocin ba" dauke kansa yayi daga duban amiru,ya maida ga kaltume data fara ja baya sosai da inda suke,ya fara takawa a hankali zuwa wajenta,yana mata bayani ta yadda yake saka ran zata fahinceshi,saidai ko kusa ko alama babu alamun hakan,bisa dukkan alamu ma takowarsa zuwa inda take din qara tsoratata yakeyi,don sai qara hanzari kawai take wajen ja da bayan,daga bisani ma data lura ya fita hanzari,saita juya da sauri zata take,hakan yasa ya rufa mata baya cikin zafin nama. Taku biyar kyawawa ya cafkota,ya damqi hannunta sosai ya fara tafiya,saita turje tana zubar hawaye tare da roqarsa ya barta ta koma wajen ummanta,kada ya cutar da ita,saiya waiwayo ya kalleta,a yadda tayin,babu wani bayani da zata gane,bata masa lokaci kawai takeyi,ya kalli siriein hannunta,ko ba'a gaya masa ba bazatayi nauyi ba ko na sisin kwabo,saboda haka ya dagata cilak ita da qullin kayanta ya nufi bakin motar yana dauke kai gamida riqe numfashinsa,saboda fargabar kada ya shaqi wani abu da zai sanyashi amai ko ya yamutsa masa 'ya'yan hanjinsa. Ihu ta saki sanda ya sakata a motar,ya tabbatar idan ya canza mota ya barta a nan hauka kawai zata musu,don haka shima ya shiga bayan ya bada umarnin qara qarfin sanyin ACn dake aiki. Tsawa ya daka mata wadda ta sanyata curewa waje daya,ya fidda dukka idanunsa waje yana dora yatsansa saman lips dinsa alamun tayi masa shuru,ta kasa koda qwaqwqwaran motsi kuwa,sai kanta data cusa tsakanin cinyoyinta tana rawar dari na tsoro daya cakuda da kuka da kuma sanyin da aka balbalawa motar,tana jin a ranta tata ta qare,ita kuma ta wannan hanyar ce sanadin barinta duniya?,ashe babu nisan tazara tsakaninta da bilalunta. Wayarsa ya fidda ya kira amiru ya gaya masa su wuce gaba a wannan motar zai tafi,ya kashe wayar ya ajjiye ya fidda iska daga bakinsa "Inason mu isa gida da wuri" ya bawa drivern umarni "An gama yallabai" ya fada yana tayar da motar cikin sauri. Shuru ne ya ratsa cikin motar,babu abinda yake tashi sai sheshsheqar kukanta can qasa,tsahon wasu mintuna,yaja qaramin tsaki yana gyara zamanshi,saboda yana jin kukan a matsayin wani abu da zai sake takurashi. Tafiyar awa guda da wasu mintuna motarsu tayi parking a parking lot na gidan,ya sanya hannunsa zai bude qofar motar,saiya tuna da ita,ya waiwaya ya dubeta,har yanzu tana zaune a cure waje guda,saika dauka cewa a saman wuta aka azata "Fito" ya ambata sanda ya bude mata murfin motar,ta daga kai da sauri,idanuwanta suka kan ginin da idan a mafarki ne,banda a zahiri take sai tace gidanta ne na aljanna,aljannar da ake bata labari,to amma wannan kuwa babu ko tantama duniya ce,cikin gidan masu yanka kan mutane,saita fashe da kuka,ta san cewa kwananta ya riga ya qare "Don Allah kayi haquri karka yankemin kai,wallahi ba laifina bane" ta fada jikinta yana rawa,idanunsa ya lumshe ganin tana neman bashi wani ciwon kan,wannan wanne irin xallar qauyanci ne,saiya bude idanunsa bayan ya saki dogon tsaki "Kinga....ki fito nace miki,bakiga mutane ba gasunan suna wucewa?,ta yaya za'ayi yankan kai kamar haka?" Sam taqi yarda da zancansa,har sai da amiru ya qaraso wajen,cikin hikima da hilata irin tasa ya fiddota,tana qanqame da kayanta tabi bayan samir,yayin da amiru ya wuce sashensu kai tsaye. Duk tafiyar second daya ko biyu sai ya waiwayo ya jirayeta,da qyar take daga qafafunta tana saukesu,kai kace tana tafiya ne saman qaya,qafafunta babu takalmi,duk wani motsi tsoranta yake nunawa muraran. Kallo daya zakayi mata ka hangi zallar isa izza mulki da kuma iko a tattare da ita,dukkansu sun bayyana kansu ta yanayin shigarta,uwa uba kuma yanayin fuskarta dake a hade. A zahiri jarida take karantawa,yayin da kuma a badini tayi nisa cikin duniyar tunani da kuma lissafe lissafenta da bata so su kaucewa qa'idarta kosu subuce mata,tayi wannan zaman ne mintuna kadan bayan sun gama waya da mahaifiyar jauhar hajiya na'ima,gefanta najwa ce data nutse cikin luntsuma luntsuman kujerun falon,hannunta dake da wayarta tana latsawa,ba kamar sauran lokutan da zaka sameta dauke da tarin takardu ba,wadanda take jin sune tamkar makwafin rayuwarta. A nutse daya daya cikin ma'aikatan gidan ta shigo,hannunta dauke da babban tray da aka cika shi da kayan shaye shaye da ciye ciye na qwalam sa maqulashe,ta qaraso cike da wani irin nau'in ladabi gaban najwan,taja mata qaramin teburi gabanta ta dora farantin a kai,ta bude duka qananun farantan dake kai,sanna ta tsiyaya mata lemukan har kala biyu kowanne a kofi daban. "An gama ranki ya dade" ta fada tana ja baya gami a ranqwafawa,duk wannan hidimar da takeyi najwan bata daga kai ko sau daya ta dubeta ba sai da tayi magana. Teburin gabanta ta kalla kafin ta daga idanunta ta watsawa matar wani banzan kallo,saita miqe ta zauna sosai tana jifanta da kallon qasqanci "Wai wacce irin kidahuma ce ke zuwaira?,da baka gane komai a kanki,tunda muke dake a gidan nan....kin taba ganin an kawo min wannan lemon?" Idanunta ta runtse wadda aka kira da xuwaira din,tana jin ciwon cin mutunci da cin fuskar da jawahir din ke mata,duk da cewa ba wannan ne karon farko ba,cin fuskar da suke mata kusan asali ya samo,banda akwai dalilin dake ci gaba da xaunar da ita agidan,ba shakka da tuni ta aje musu aikinsu ta huta,ta dan dubi sashen da hajiya jidda take,tana da yaqinin cewa daman ba zata magantu ba,koda najwan tayi abinda yafi haka rashin kyautawa da muni Dannewa gami da daure zuciyarta tayi "Kiyi haquri,wacan da kike sha din,babu shi a fridge din gaba daya,har store na duba koda saura amma kuma babu". "Momy.....ya akayi lemona ya qare?,kuma ba'a kawo wani ba?" Ta fada ranta a bace,fuska a narke,rufe jaridar hajiya jidda tayi,sai idanunta suka shiga cikin na zuwaira,take ranta ya baci,ya murtuke fuska kafin ta janye idanun nata zuwa kan diyar tata,a duniya duk sanda zata kallo zuwaira sai taji wani abu game da ita,wanda har yanxu ta kasa tantance asalin meye shi?duk kuwa da cewa,ta san bata da sauran wani abu da zai zama tarnaqi ga duk al'amuranta,tarnaqin ma ta jima da zame masa shima tarnaqi "Tsarin yayanku ne,yace akwai lemuka da yawaba store,ana kawosu suna lalacewa,so daga yanzu saisun kai rabi ko fiye da haka sannan za'a kawo wasu" ta qarashe maganar tana daukar wayarta dake ajiye gefe,gefe guda tana jin wani abu yana motsa mata dangane da sabuwar dokar. Cikin yanayi na masifa da bala'i ta zauna sosai saman kujerar tana sauke qafarta wadda ada take daya saman daya "Wai wannan wanne irin abu ne momy?,ni da gidan ubana?,amma sai anmin gate kan abubuwan da suka shafeshi?sai kace wata agola ko kare re?,idan bani da gado a gidan a fito a gayamin mana fyn?"ta fadi tana huci,daga zuwaira dake duqe gefe daya kanta a qasa,har momy dake danne danne a waya babu wanda ya daga kai ya dubeta,sai da takai aya sannan momyn ta jefeta da wani irin kallo da yasa ba shiri ta maida wuqaqen data waso,ta maida kallonta ga zuwaira "Kwashe tarkacenki malama ki mayar,baza'a ci ba" sum sum ta miqe tana debe kayan,cikin qunan rai da baqincikin yadda yarinyar data haifa take mata wannan cin kashin. Saida zuwaira ta nutsa zuw cikin kitchen sannan mommyn ta ajjiye wayar hannunta,ta kuma gyara zamanta "Duk yadda kika so al'amuranki suyi kyau.....idan kikayi wasa ba zasuyi ba,koda yaushe ina qoqarin......" Bata kai qarshen zancanta ba sallamar saraki ta cika falon. Lumshe idanunta tayi saboda faduwar gaba data sameta wadda batasan ta mece ba,cikin sakannin da basu wuce uku ba ta saita fuskarta,sannan ta juyar da fuskar tata zuwa direction din da yake,ta miqe tsaye cak don nuna murna da girmamawarta "Oyoyo son.... welcome"ta fada tana gyara tsaiwarta sosai,wadda zata nuna maka irin alfaharin da take dashi,murmushi ya aika mata dashi kamar kowanne lokaci,saita dora da cewa "Hala ba zata kaso yi mana ko?,Allah yasa an gama dukkan ayyukan daka qudira zaka aiwatar din" maganartata ta sauka tare da saukar idanunta saman fuskar kaltume,wadda dukkan wata juriya tata ta qare,saboda tsintar kanta da tayi a makeken falon na alfarma,wanda ita a nata hasashen yafi kama da irin kwatancen da malamansu na makarantar asuba suke musu na yanayin yadda aljanna take "Komai yazo min ne a qurarren lokaci,inata qoqarin shaida miki tahowata kuma ya gagara saboda yawan ayyyuka"Yakai qarshen maganar yana yiwa kansa mazauni saman kujerar dake daura da qofar shiga falon,ya kuma dora idanuwansa akan kaltum dake shawara tsakanin shigowa ko fita "Qaraso ciki" ya bata umarni kai tsaye,yana kausasa muryarsa,hada idanun da sukayi bayan umarnin daya bata shiya hanata komawa a guje kamar yadda tayi niyya,ta qaraso daura dashi kadan,ta zame a hankali ta zauna saman lallausan carfet din dake gaban kujerun,tana jin kamar zata nutse saboda tsananin laushi,sai a sannan idanun jawahir yakai ga kaltume,ta zuba mata idanu sosai tana yamutse fuska,ita kuma wannan daga ina?,daga ina yayansu ya debota?,ta yiwa kanta tambayar,saidai babu ikon tambayarsa,saboda tasanshi sarai ba sanin shanu ba. A nutse momy ta koma ta zauna,saidai har yanzu hankalinta yana kan kaltume,duk da cewa idanunta ba'a kanta yake ba. Najwa ce ta gaisheshi bisa dole kamar yadda takeji a kullum har cikin zuciyarsa,ya amsa ba tare daya bawa yanayinta muhimmanci ba,ya maida hankalinsa ga momy,ya gaidata ta amsa tana bada umarnin a kawo masa abun tabawa cike da nuna tsantsar kulawa kamar yadda ta saba nuna masa a ko da yaushe,ya tsaida hakan ta hanyar cewa sai zuwa anjima. "Wannan fa son?" Ta tambaya tana nuna kaltum da baki 36 Hkan ya baiwa najwa damar juyawa zuwa sashen da kaltume ke zaune a rakube,kamar zakace kyat ta zura da mugun gudu "Mai aiki na qaro muku" ya fada kansa tsaye yana relaxing saman kujerar da yake zaune,yana jin yadda gaba daya ya gaji. "Me aiki yaya?"jawahir ta fada cikin wani salo me kama da gatsali "Jawahir......" Momy ta kira sunanta da qarfi "Na'am" ta amsa tana duban momyn,da idanu ta gaya mata kada ta sake magana,sai taja bakinta ta tsuke,haushi da takaici na cikata,ta taya zai dauko kucakar ya kawo musu gida da sunan mai aiki,gidan ma irin nasu,gidan professor rashid guda,wanda mutane da yawa ke kwadayin yin aiki qarqashinsu,koda an tashi daukar mai aiki momyn nasu saita zaba,ta kuma jarraba mutum ta aminta dashi take dauka,ma'aikatan daba ita ta daukesu ba cikin gidan batajin basu wuce uku ba,shine kawai zai wani kwaso musu kalar qyanqyami,saboda yana taqama da ikon da yake dashi a gidan,qwafa taja can qasan ranta,tana jin sauran qiris ta rushe komai,ta maye gurbinsa,wannan shine babban buri da muradinta,wanda dashi take kwana take kuma tashi. Da murmushi saman fuskar momyn,tana qoqarin dai daita komai ta dubi samir din "Banda abinka son....ai kasan tsarin daukan ma'aikata a gidan nan,ko baya ga haka ma professor kasan baya bari a dauki qananun yara kamar haka,banason wannan ya jawo wani sabuwar matsalar tsakaninku fa?". Numfashi ya fidda "Babu komai momy,a bata wajen zama,zanyi magana da dadyn" "Shikenan....."ta fada tana mutstsuka hannaye ta,tana jin wani abu nason kutsawa cikin zuciyarta amma tayi gefe dashi,ta dubi jawahir "Kuje da ita ki bata daki" "Kaman zuwaira ke kaisu boys quarters din" jawahir ta fada,sai momyn ta tsuke fuska sosai "Ba cikinsu zata zauna ba,a bata daki nata na daban" idanu jawahir din ta fiddo,kamar zatayi magana sai kuma ta fasa,mamakin abinda momy ke nufi ya kamata,kamar wata 'yar gida za'a bata daki guda?,miqewa tayi da hanzari ranta a bace ta soma yin gaba "Tashi ki bita.....meye sunanki ne?" A hankali samir ya bude baki zai amsawa mommyn,sassanyar qaramar muryarsa ta maye gurbin tata "Kaltume" ta fada da qaramin sauti mara amo. "Tashi kije ta baki masauki" kamar wadda ciwon paralyze ya kamawa qafafu haka ta dinga ji sanda ta miqe,tsoro baqunta rauni da kuma firgici sukayi mata qawanya gaba daya,tana riqe da qullin kayanta taci gana da bin gurbin da jawahir kebi har suka isa wani kebantaccen corridor me dauke da dakuna manya guda hudu. Muqullin jiki ta murza ya bude ta soma shiga,tayi tsaye sanda kaltume ke takowa sannu a hankali,kamar wanda ke shiga wuta "Dalla malama ki shigo,nan ba bukka bace ko rumbu" ta fada cikij tsawa,tsawar data razana kaltume din,saboda haduwa da tayi da tsoro da kuma ganin yanayin dakin da bata taba katarin ganinsa ba,hakan ya sanya qullin hannunta faduwa saman qafafunta,jawahir ta bisu da kalllo kana ta tabe baki "Ga daki nan,amma ki sani,ba qyaleki za'ayi ba,duk abinda kika barnatar saikin biya,don haka kibi a hankali" ta qarasa maganar tana galla mata harara,sannan ta kewayeta ta fice,ta bita da kallo har zuwa sanda taja mata qofar. Zafafan hawaye suka sauko mata,wannan rayuwar kuma itace yanzu zata fuskanta,su waye wadan nan da zata rayu cikinsu ne?,me zata tarar,shi kansa wanda aka kira da sunan mijinta wayeshi?,bata da tabbas a kansa bata da tartibin wata amsa guda daya gamsashshiya game dashi,ta juya ta kalli gabas da yamma kudu da arewa na dakin,ta yaya ma zata iya rayuwa a wannan wajen me kama da gidan aljanu?,ko ina glass,da wani abu mai santsi da qyalli,shiba daben sumunti ba,hakanan ba ledar tsakar daki ba,saita zame taja da baya a hankali ta zauna a qasan da batasan na meye ba,kuka na balle mata. A zafafe jawahir ta koma falon,ta tadda saraki ya fice sai mommyn "Mommy,ta yaya......" Bata kai ga qarasawa ba mommyn ta daga mata hannu "Babu abinda kika sani ko kima kika iya sai shirme,wadansu lokutan ina raina hankali da wayonki....." Daga wannan bata sake cewa sa ita komai ba, taci gaba da kankare farcenta data taras tana yi,saita juya ta kwashe wayarta da headphone dinta ta yi dakinta fuuu,mommyn ta bita da kallo,daga bisani ta dauke kanta tana girgiza kai,nan da wasu mintuna tasan zata dawo da kanta,don haka taci gaba da gyaran farcenta. Sai daya gama sharce kansa sannan ya lalubi undies ya feshesu da turare ya fara sakawa,sai daya gama sawa ya dubi Aamir "Zamu leqa wajen hajiya qarama,amma sai zuwa anjima,zan leqa company yanzu kafin lokacin tashi yayi,akwai abubuwan da zan dudduba" "Ba damuwa,inason na leqa mutuniyar" ya fada yana dan kashingida "Saika nema kuma abokin rakiya,badai muhammad samir ba" ya amsa masa yana qoqarin bude katafaren ma'adanar kayanshi. Qaramin murmushi kawai Aamir ya saki,yasan halin kayanshi dama,abu daya da bai yarda dashi ba yayi rakiyar zance,yace shiba yaron kowa bane,baiyi,kuma shima ba wanda zai nema yayi masa,kowa ya iya allonsa ya wanke,rakiyar zance ko gulma. Cikin kayansa ya dudduba,ya fitar da wani lallausan yadi butter color ya sanya,a nan yabar Aamir yayi ɗai ɗai,shi ala dole ya gaji,ba yadda samir din baiyi ya tashi su fita tare ba yaqiya. Tun tana kasa kunne ko zataji motsi ko gilmawar wani,harta saddaqar da cewa an kawota qare kukanka,inda babu wanda zata ji,babu kuma wanda zai jita. Duk sanda agogo ya kada saita daga kai ta kalleshi,duk da cewa batasan qarfe nawa yake bayarwa ba,yanayin shigowar hasken rana dakin kuwa bashi da banbanci daga shigowarta zuwa yanzun da take zaune a jikin bago kamar wata qadangaruwa,ya kamata ace taji yunwa,amma tunanuka dake cunkushe cunkushe cikin kanta ya hanata taji yunwar arziqi,sannu a hankali lokaci ya dunga motsawa zuwa gaba,cikin jikinta ta dinga jin yakamata ace tayi salla,koda lokacinta baiyi ba,bare tana ji a ranta ma lokacin yayi qila ma har ya gota,saidai batasan inane zata nufa don daura alwala ba. Zagaye ta dinga da idanunta harta hangi qofar toilet,ta miqe zuwa qofar sannu a hankali ba tare da tana da tabbacin wane waje bane nan,sai a sannan tasan lallai tana buqatar abinci,saboda jinta da tayi fayau iska na dibarta,ga sanyin wajen da taketa jin ya mata yawa. Tsaye tayi a bakin qofar,ta jima tana qiyasta ta yadda zata budeta,kafin daga bisani tayi shahada ta soma gwada budewar na wasu mintuna kafin ta samu nasarar turata ta bude. Bin bandakin tayi da kallo,wanda yafi mata kama da daki,don kaf karkararsu bata taba ganin mai kya makwanci kwatankwacin nan wajen ba,take ranta ya bata cewa wani dakinne mai zaman kansa,kenan babu wajen zub da ruwa bare ta daura alwala?,idan kuma tace zata fita ina ta nufa?,ba zata iya maida kanta inda ta baro dazu ba bare ta koma wajensu ta tambayesu. Sake qudundunewa tayi a yadda take zaunen,sanyin tiles dana ac na ratsata,wanda batasan sanyin meye ba,sai dan banzan takura matan da sukayi,zuwa wani lokaci cikinta ya sake buqatuwa qwarai zuwa ga abinda zai sarrafa ya bawa jikinta kuzari. Mamaki qwarai ya mamayeta,wadanne irin nau'in mutanene wadan nan?,masu qarancin karamci?,iya rayuwarta da yadda suka ga ummansu nayi akan baqi sam ba haka bane,duk da kasancewarta mai qaramin qarfi,wadda itama idan aka bata da farincikinta zata karba,amma duk sanda baqo ya shigo gidan,nata ko ba nata ba,saita zuba ta miqa mishi,koda bangaren kawu iliya yazo ba nasu ba,ta riga ta saba da ganin hakan,sai gashi yau ta fada hannun wasu mutane,an yasar da ita a wani daki dake mata kama da qiyama. Qarfe shida da mintina ashirin ta shigo gidan a gajiye daga makaranta,mintuna goma kenan a gaba suka rage a kirayi sallar magariba,duk da cewa kaita ake a daukota amma hakan bai hanata jin gajiya a jikinta ba,tayi mita tayi qorafi kan a bata mota,amma saraki yace ba yanzu ba,yasan yadda jawahir keda tarin qawaye,kasancewarta mai faran faran da son jama'a,ta haqura da tsarin yayan nata,saboda tasan cewa kome ya tsara a gareta baiyi don ya cutar da ita ba,sai don amfanin kanta,bata kuma damu da kalar motar da najwa ke hawa ba,ta tattara ta barwa lokacin da yayan nata ya zaba mata. A falo ta zube tana ajjiye takardunta,mommy dake shirin shigewa shiyyarta don shiga wakan tarbar mai gidan da bai mata tsufa ta dubeta "Yanzu nake shirin daga waya na kiraku,yau dadewar tayi yawa" "Wallahi momy,yunwa da gajiya,bamu zaci muma zamu kai hakan ba" "To barkanku tunda kun dawo,saiki shiga ki saka a kawo miki abinci" "Sai nayi sallah momy,saura 'yan mintuna a tayar,idan naci yanzu kasa tashi zanyi nayi sallar akan lokaci" ta amsa mata tana qoqarin miqewa saman doguwar kujera abinta. Ganin falon babu kowa saita dauka remote tana canza channel din dake aiki saman screen din tvn dake falon,tare da maida hankalinta ga channel din data sauya. Sosai program din da take kallo ya dauki hankalinta,har aka tayar da sallar aka idar bata sani ba,motsin shigowar samir da fitowar mommy cikin shigar alfarma ya sanyata miqewa ta zauna,kamar ko yaushe fuskarta qunshe da murmushi takewa samir din murnar dawowa "Yaya,bari naje nayi salla na dawo naji nasarar da aka samu wannan karon,bamuyi waya sosai ba tunda ka tafi" "Au,dama bakiyi sallar ba tun daxun?" Tana zura takalminta cikin sauri tace "Wallahi momy bansan an idar bama" ta hada da mayafinta tana yin bangaren dakunansu da hanzari. Kayanta duka ta aje sama madubi ta nufi bandaki,saidai ta taras da heater din bandakin nata babu ruwan zafi "Ya salam" ta fada tana fitowa daga bandakin,ta nufi daya daga cikin dakunan da tasan ko yaushe a gyare su,ba zata rasa ruwan zafi a cikin toilets dinsu ba. Kanta tsaye ta tura qofar dakin data lura shi daya ne a bude ba tare da wani zato ku tunanin ganin kowa ba,kacibus tayi da kaltum dake kwance a qasa a cure waje guda,tana fidda sautin kuka ta cikin hijabinta. A matuqar tsorace taja da baya tana shirin bada iska,amma sai tayi ta maza,ta tsaya tana kallon kaltumen gami da karantarta,saida zuciyarta tadan samu nutsuwa sannan ta soma takowa zuwa ciki,ta tsugunna a gabanta a hankali ta dan tabata. A firgice ta miqe,da alama itama a tsorace take,saita tsaya suna yiwa junansu kallon kallon,tsahon wasu sakanni kafin kaltume ta gyara zamanta ta lumshe idanunta hawayen da suka cika mata idanu suka sake gangarowa "Me kike a nan?,daga ina kike?" Jawahir ta tambayeta tana ci gaba da dubanta cike da mamaki,kasa bata amsa tayi,saboda mugun qullewa da cikinta yayi "Keda wa kuka zo?" Ta kuma tambayarta "Nida wanine,daga qauyenmu" maganar ta daurewa jawahir kai,amma sai tayi gajeran tunani daya sanyata miqewa ta koma zuwa falo. "Daddy ya saba lokacin shigowarsa yau,ko wani abun ya tsaidashi?" Samir ya tambayi momy. Fuskarta qunshe da fara'ar nan tako yaushe tace "Eh....yace min suna da taron jam'iyya,amma tunda na kirashi naji bai daga ba,basu gama bane" agogon hannunsa ya kalla "Ok"ya fada,yana shirin sauke idonsa daga kan agogon muryar jawahir ta bayyana "Momy....wace yarinyar ce acan dakin take kuka?,tacemin ita da wani sukazo daga qauyensu,shi ya kawota" maganar taja hankalin samir sosai,shaf ya manta da yarinya kwata kwata,saboda koda ya fita din ma baiyi zaton za dade haka ba "Kuka kuma?,ko bata qoshi bane?" Tayi tambayar tana kallon samir wanda baisan irin amsar da zai bata ba "Gaskiya banga ma alamun abinci a wajenta ba kwata kwata,don kamar ma yanayinta yafi kama da name jin yunwa" ta fada tana raba kallonta tsakanin mommy da saraki "Kada dai ace basu kai mata komai ba.....inasu tambaya.....jeki tattaro minsu" ta soma magana cikin fada kamar zata ari baki cikin matuqar bacin rai,har falon na amsa muryata saboda yadda take fadan cikin nuna fushinta. "Idan kin shiga ki samo abinci da ruwan Lipton me zafi,ki barsu basai kin kirasu ba" cewar samir bayan ya tsaida jawahir cikin wata iriyar murya me cike da nutsuwa,sannan ya fara takawa a hankali yana dosar dakin da yake tsammanin an ajjiyetan. A tsorace ta dago sanda taji an kuma bude qofar,suka hada idanu,yabi fuskarta da kallo,wadda ta qara muni saboda yadda idanuwanta suka kumbura da labbanta sakamakon kukan data shaqa,sai yayi sallama,wadda ta sanyata sakin ajiyar zuciya,ta kuma yi qoqarin amsawa,ya tako a hankali yana kallon dakin. A zahirin gaskiya shi kansa yasan ba lallai ta iya sakewa a dakin ba,saboda bambancin yanayi dana rayuwa dake tsakaninsu "Kinci abinci?" Abu na farko daya fara tambayarta kenan,qas tayi da kanta bayan ta zare idanuwanta daga cikin nashi,wasu sabbin hawaye suna sauko mata ta girgiza masa kai,sai ya qaraso ciki,ya murza qofar toilet ya budeta yana duban bandakin,yanzu haka fitsari da bayan gida,da duka sauran buqatunta na bayan gida riqesu kenan tayi tsahon wannan lokacin,Saiya saki qofar yana juyowa,dai dai lokacin da jawahir ta dawo dauke da babban plate,wanda aka cika da shinkafa da miya da nama,sai hadin coleslaw daga gefe,hannunta daya ruwan roba ne da lemo. Zuciyarsa na yabawa sanin ya kamata irin na jawahir yasa ta ajjiye abincin gaban kaltume,sannan ya baiwa kaltume din umarnin ta dauka taci,yace da jawahir data wuce toilet don daura alwala,bakinta cike da tambayoyi da bata furtasu ba,idan ta fito tayi masa kiran baba zuwaira,sunan daya ambata ya sanya kaltum daga kai,tana raba idanu cikin dakin,tamkar zataga tata mahaifiyar dake da wannan suna,saidai wayam,bazaiyiwu ta ganta bama,ta maida qwallar dake shirin xubo mata,taja plate din abincin kamar yadda taji yana umartarta,ta sanya cokali amma saita zubawa abincin idanu wani abu yana tsaye mata a maqoshi. Ummanta ta tuno,wadda a yanzu haka take can ita daya tana rayuwar kadaici,babu ita babu habi babu bilalu,kome taci yanzu?,ko waye yake tayata hira?,waye yayi mata shara?,wa zai dinga mata wanki?,wazai faranta mata bayan babansu ya bata mata ranta?,qwalla na qoqarin rufe mata idanunta ta soma ture hadin coleslaw din gefe,wanda take kallonsa a baqon abun da yafi mata kama da jagwalgwalon da ba zata iya ci ba,ta soma kai lomar abincin a bakinta a hankali,ba tare da tabi takan ruwan Lipton da aka ajjiye mata a cup ba. Idanunsa yana kanta harta fara cin abincin, dai dai lokacin baba zuwaira tayi sallama,fuskarsa ta sake fiye da daxun yana dubanta,tana da wani qima da daraja dukka cikin tarin ma'aikatan gidan,hakanan itama take dubansa da tata fara'ar "Biba(sunan da suke kiranta dashi can wani lokaci daya shude,har zuwa yanzun kuma shi bai fasa kiranta dashi ba) baquwa ce da Allah,pls ki dan zauna da ita,ki nuna mata bandaki da sauran abubuwa,duk abinda kika ga akwai damuwa ko motsala ki sanarmin kai tsaye,karki damu da momy" kanta ta kada cikin gamsuwa tana bashi tabbacin haka,saiya juya ya kalli kaltume sau daya sanda taketa faman qoqari sarrafa lomar datayi,saboda banbamcin taste da spices da seasonings na girki da bata saba jinsu ba,wanda a yanxun tana jin abincin na mata wani qamshi ne na daban wanda bai mata dadi sam a harshe da zuciya,saiya nufi qofa yana zaro wayarsa,tare da qoqarin kiran ahalan,wanda koda yaushe shike tiri tiri da professor,da shirya masa duk schedule dinsa,ya tabbatar xai samu cikakken kwatancen inda suke a yanzun. 37 D/Z ☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠 *_K'AMSHI,K'AMSHI RAHAMA NE MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA SU SUKA SAN MUHIMMANCIN DA K'AMSHI YAKE DASHI MUSAMMAN A WAJAN MAI GIDA ,_*💃🏻💃🏻 *_Zafafan turarruka masu zazzafan k'amshi hade da wasu irin manyan sirrika na mallaka cikin sauki ba boka ba malam hajiya , Zaki jefe tsuntsu biyu da dutse d'aya , domin zamowa star azuciyar mijinki_*🌟🌟🔥 *_nasan dai kunada labarin mashahuriyar Mai Saida kayan k'amshin Nan Wanda akafi sani da *HUMKAM GIDAN K'AMSHI* *_a wannan karon ma ta sake kawo maku da sabbin kayanta masu abun al'ajabi Wanda da kud'i k'alilan zaku more zafafan turarruka Kuma ki shiga jerin Mata masu aji_* *IDAN SARI KIKE BUKATA INA BADAWA SANNAN INAGYARAN JIKI CIKI DA WAJE SHIN KINA FAMA DA INFECTION INA HADA MAGANIN SA DA IZININ ALLAH KISHA KI WARKE* *Kadan daga cikin kayan da muke dasu*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *BLACK KAJII* shin kina bukatar turaren da Zaki turara gidanki ya dauke maki warin sanyi ya kwana biyu Yana k'amshi ,?ki saye black kajiji Zaki Gane banbancinsa da sauran wannan ba k'amshi kawai yake ba idan kina turara. Jiki dashi Yana maki maganin kala kala ciki kuwa har da na sanyi , nemi naki Kar ayi Babu ke☀️🟢☀️🟠🌟08132506044 HUMKAMINCENSE *ANA WA HABIBY* Wannan harkan na oza room ne special turare Dan matan aure kadai yana dauke da abubuwa Wanda bazan fadesu anan ba sannan bashi kadai bane akwai Crazy powder da na ke hadawa dashi zakisha garin sannan kishafa turaren hmm *SUDANESE HUMRA* Turare dake dauke da sirrika Mai DAUKAR hankali kamshin ya banbanta da sauran turare Hajiya babbar sirrine Wannan hadin manyan Mata 08132506044 HUMKAMINCENSE *GLOWING OIL* Wannan yasha bam bam da irin Wanda kuka Saba gani ,Yana kashe kuraje Yana cire tabo Yana maganin kezbi da duk wani matsalan fata ,stretch marks duk Yana ciresu .... *MOWAR MACE* turaren mowar mace turare ne da larabawa suke amfani dashi Wanda da yawa mutanenmu Basu San da wannan iccen ba Mai dauke da magani k'amshi da sauran abubuwan masu matukar amfani ga fata ba Shi wannan iccen yanasa hasken fata yanasa fata tayi laushi da santsi sannan d'an alk'awari ne matuk'ar kina amfani dashi zai tsirga maki cikin fata ta yadda ko Bakiyi amfani dashi ba zakiji k'amshin shi na fita ta cikin fatar ki ,ke amfanin iccen mowar mace yanada yawa jaraba ko don gyaran fatarki , 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Muna gyaran jiki na amarya da uwargida zakizo har gida ayi maki gyaran jiki irin na Mata masu aji zakiyi kyau kiyi fresh ga kamshin da zai Kama jikinki💃🏻💃🏻💃🏻 Munada 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *JAS OUD* (hatsabibin turare kenan ) *AL'AJAB* ( Mai abun mamaki kenan )AL'AJAB Turaren tsuguno mai abubuwan Al'ajabi Yana maganin sanyi (infection) Yana matse HQ (Tightening)sosai 08132506044 yasa HQ dumi yasa jikinki da hq kamshi lokacin da kike AMFANI dashi idan Yana shiga gabanki zakiji wani Dadi na ratsaki Yana k'ara Dadi da Yana ciko gaba ya rikita oga🙈 *FIRST LADY* na Mata masu aji turaren Kaya Dana daki HAWII KAJIJI HALUT 👸🏻 *_PRINCESS_* _Sabon turare Dana hada na shafawa ajiki da gashi *PRINCESS* Yana da Dadi cool kamshi gare shi babu hayaniya na fad'a muku sabbin turaruka na Nan tafe princess na daya daga ciki kisayi *PRINCESS* kiji sabon Hadi me sanyin kamshi babu kosarwa da ace zan iya zabi tabbas zan zabi princess a matsayin turaren gashina zan dauki princess ya zama shi zan farawa shafawa jikina idan zan kwanta zan dauki *PRINCESS* sbd yara na Dan kamshi bamai hayaniya bane musamman zan rika yi musu amfani dashi *PRINCESS* salon na daban kamshin daban dadin na daban *PRINCESS* Zabin ku ne Zabin Humkam shine farin cikin ku Masoya *PRINCESS* gidan kowa_ Duk wad'an Nan turarruka ne hatsabibai masu rikita mazaje masu wani irin k'amshi Mai shiga zuciyar masoya 💃🏻💃🏻💃🏻 *SHU'UMAR HUMRA* ke daga jin sunan kinsan ta dabance mashahuriyar humra ce ta tayi shuhura wajan birkita tunanin Yan maza , humra ce da indai namiji yajita a jikinki to komai muskilancinshi sai ya susuce maki tana tado da sha'awa shauk'i sirrin mallaka, cikin kankanin lokaci ki rikita maigidanki da daddadan k'amshin ki😍😍😍🥰 *HUMKAM GIDAN K'AMSHI INA NAN ZAUNE A KANO GA MASU BUK'ATAR ZAFAFAN KAYANA INA AIKAWA KOWANE GARI DAKE NIGERIA HAR MA DA K'ASASHEN K'ETARE* *Zaku iya tuntubata kai tsaye ta wannan number wayar* 08132506044 *KO KU DUBANI A SHAFINA NA INSTAGRAM* _humkam_turare wuta_ *KARKU MANTA A DADE ANAYI SAI GASKIYA,KUMA SAI AN GWADA AKAN SAN NA QWARAI*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke sanda ya tsaida motar a harabar wajen bayan ya gama dai daitata,ya dinga bin wajen dake cike da 'yan jagaliya da kallo,dukkaninsu matasa ne masu jini a jika,wanda ya kamata a ce a dai dai wannan lokacin tunaninsu fresh yake,yana kuma gudana ne kan yadda zasu gina rayuwarsu data al'ummarsu dama qasarsu gaba days,sai gasu sun qare a wani waje zaune zube a wulaqance,mutum sama da ashirin na jiran mutum guda da sunan yi masa hidima ko bashi kariya,wanda basu da wani alfanu da zasu samu wanda ya wuce rugujewar rayuwarsu,da dan kudin dako cikakken abincin wuni guda babu lallai ya samar musu. Idonsa ya lumshe yana jin ciwon hakan cikin ransa,yana daya daga cikin abinda yasa har kwanan gobe,ko sau daya siyasa bata taba burgeshi ba,yana ganin duk yadda kakai ga son tsaftace kanka ko zamewa hakan ba zai yiwu ba,wata qurar saita taddaka,inama ace mahaifinsa zai fuskanceshi yadda shi yakeso?. A yadda ahalan ya gaya masa,mintuna biyar kenan suka rage su fito daga hall din,saboda haka saiya fito daga motar baya ya kasheta,ya tsaya a jikinta ya jingina yana ci gaba da nazarin wajen,har zuwa sanda aka fara fitowar,hakan yasa ya janyo hular kansa ya rufe fiye da rabin fuskarsa,don baisan yin magana da kowa,mahaifin nasa kawai yazo dauka. Sannu a hankali ya tunkareshi sanda yake fitowa shida jama'arsa "Barka da fitowa daddy" ya fada cikin girmamawa,saiya maida hankalinsa gareshi,yana masa wani duba na sama da qasa,gaisawar da suka fara yi da jama'ar dake tare dashi ta hana maganar da yaso yi din,saidai duk motsin da samir din zaiyi sai yaga idanunsa a kanshi,har zuwa sanda ya take masa baya zuwa bakin motarsa ya bude masa ya shiga,shima ya shiga mazaunin driver ya tayar da motar suka fara tafiya. "Idan har kazo wajen nan ne don ka burgeni,babu abinda kayi illa ma bata min rai da kayi,ka duba tarin jama'a masu girma da mutunci a wajen nan,ka rasa dame zakazo min sai da qananun kaya?"professor ya fada cikin nuna zallar bacin rai,kafin samir yace wani abu ya sake magana "Sai yau kaga damar dawowa kenan?,me yasa a kullum kai maqiyin burina ne da muradina?" Sosai furucin ya daki samir har zuciyarsa,ko yaushe yana aiki don ganin ya dai doita komai,amma idan komai yayi kamar zai gyaru saiya sake tabarbarewa da zarar ya danyi nesa da mahaifin nasa na wani lokaci "Nakanji a raina wani lokaci inama ace kaine najwa....najwa ce kai,da nasan hakan ba zata faru ba" hannunsa ya dora kawai saman kansa yana shafan kan nashi tare da son hadiye abinda ya riqe masa wuya,ire iren wadan nan lokutan yafi qyamata cikin rayuwarsa,shi yasa koda zuciyarsa ta bashi shawarar kusantar mahaifin nasa,sai wata zuciyar ta haneshi,ya gwammace nesanta dashi saboda kubuta daga kalamansa masu ciwo irin wannan. "Kayi haquri daddy" itace kalma guda daya daya iya furta masa,ya kuma maimaita masa ita kusan sau biyar kafin isarsu gida,wanda yana saukeshi ya wuce sashensa kai tsaye. Kasa zama yayi ya dinga kai kawo a tsakiyar dakin yanason lissafa abubuwan da yawa da suke zuwa kanshi,kaushin daddyn agareshi kullum abune da bashi da sauqi ko rangwame,bayaga sabanin ra'ayoyi da zabe zabe na rayuwa babu wani mai muni tsakaninsu,amma a yadda yake mu'amalantarsa saika fassara abun da wani lamari mai girma wanda bashi da kyau. Ya tafi da baya saboda samawa kansa mazaynu gefan gadonsa ki zuciyarsa zata samu nutsuwa,qafarsa ta daki locker gefan gadonsa,yakai kallonsa ga wajen,saiya fasa zama gefan gadon ya zamo ya zauna gabanta,ya zura hannunsa wani saqo dake jikinta ya fiddo muqulli ya zura ya budeta,ya sanya hannu ya fara fitar da abubuwan dake ciki yana binsu da kallo daya bayan daya. Tarin hotuna ne mabanbanta,duk da cewa kowanne hoto mutanen jiki daya ne,amma yanayin sutura da kuma wajen da aka daukesu ya banbanta,a hankali wani abu ya fara taso masa mai kama da bege kewa da kuma qauna,saidai tashi daya wani abu mai qarfi ya taso ya dannesu,wanda hakan har yasashi miqewa daga tsugunnon da yayi,har zai bar wajen a haka ya tuna akwai Aamir a dakin,dalilin daya sanyashi dawowa ya tattara komai ya mayar muhallinsa kenan,saidai wannan feelings din daya taso masa yana jinsa yana motsawa a qasan zuciyarsa yana ci gaba da kaiwa sassan zuciyar nasa. *********Zaune yake a gabansa da sanyin safiyar,zaman daya kusa kaiwa na mintuna talatin bayannya gama masa dukkan bayanin daya jima yana tsarawa zai gaya masan dangane da zaman kaltume a gidan,zai iya cewa tunda yayi hankali,kusan wannan shine kari na farko daya taba gaya ma daddyn abinda ba haka yake ba ma'ana qarya,komai tsanani ko kuma rintsi baya boye masa gaskiyar abu,kome gaskiyar kuwa zata haifar masa,har sai daya gama jiransa ya qarashe kallon labaransa,sannan ya maida kansa gareshi da wani irin duba,sanda mommy ke ajjiye masa zazzafan ruwan baqin shayi don ya dumama jikinsa da hanjinsa kafin lokacin cin abincin safensa yayi "Kafin ka sanarmin komai.....mommynka ta riga data shaidamin" ya fada muryarsa a nutse,a hankali samir din ya daga kai suka hada idanu da mommyn,don basuyi haka ba,ya shaida mata da kansa zai gaya masa,to amma kamar yadda zuciyarsa ta gaya masa tayi hakanne don bashi kariya kamar yadda ta saba,hakan ce ta faru,don alamun kada ya damu tayi masa da idanu,dai dai sannan kunnuwansa sukaci gaba da dauko masa maganganun daddyn "Abun mamaki,koda yaushe jidda qoqarin baiwa samir kariya kikeyi akan duk abinda yakeso,kina sanya qafa kina fatali da nawa muradin,basan me yasa kike daure masa qarqashin yin duk abinda ya tsarama kansa ba" cikin salo da kwantar da murya tace "Banda abinka daddy,meye ne da son yakeyi wanda ba dai dai bane ba?,shi daya fa Allah ya bamu,yanzu idan ban bashi qwarin gwiwa da kariya ba?,waye zan bawa?" "Ok,hakan shi ya baki qarfin gwiwar tayashi ya dinga karya min tsaruka da dokokina ko?" Da sauri ta girgiza kai "Ba haka bane.....daddy yaran yanzu bada qarfi ake binsu ba,ba'a son a dinga tilastasu saboda gudun abinda zaije yazo" shuru ya ratsa falon,wani abu ya sauka zuciyar samir,hakanan yaji kamar wannan amsar batayi masa ba,shi ba yana yin komai sabida bijirewa ba,ba yanayin komai saboda yana tunanin shine dai dai ba,a'ah,yana yin komai ne saboda yana da tabbacin haka komai din ya kamata ya kasance,maganar momy ta gaba ta tsaida tunaninsa "koda raheena bata a nan,ina kallonshi a matsayin amanar....." "Dakata....kada ki sake min magana makamanciyar wannan" daddy prof ya katseta yana dubanta,saita kafeshi itama da nata idanun tana karantarsa,akwai wani abu data jima tana qoqarin karantarsa tattare dashi,wanda har yanzu hangen ta da tsinkayenta ya kasi canko mata ainihin meye shi,saidai ta karanci akwai fushi daya cakuda da wani abu,abunda shi dinne takeson ganowa. Sauke idanunsa samir yayi daga yake rarrabawa a tsakaninsu,ambatar sunan kadai ya daki zuciyarsa,baikai ga rarrabe tunaninsa ba muryar daddy ta sake ratsa kunnensa "Bana daukan masu aiki underage,ka sani dokata ce,don hakan kamar kashe musu rayuwa ne,kuma koda zan dauka mutual person sai nasan daga ina mutum yake.....saboda haka ka dauka yarinyar mutane ka maidata inda ka daukota tun muna shaidar juna dani da kai" sosai gaban samir din ya fadi,in har daddyn ya kafe akan haka ba shakka akwai matsala,saboda ba yanxu ya shirya fuskantar wannan damuwar ba,ya bada lokacine zuwa sanda qura zata lafa "Daddy.....amma da zaka saurareni da ka fahi......" "Samir......na gama magana,gobe idan Allah ya kaimu akwai tafiyar dake gaba na,kada na dawo na sameta a gidan nan,bijirewa hakan xai iya zama ggarumar matsala tsakanina da kai" daga hakan ya dauki cup din dake gabansa ya fara shan tea dinsa,sai kawai samir din ya miqe,yana jin sanda mummy ke qoqarin sanya baki a cikin matsalar amma daddyn ya dakatar da ita. Tunda tayi alwala da taimakon biba ta bada faralin salla take xaune a inda ta idar da sallar,har zuwa lokacin da biba zuwaira ta turo qofar a karo na biyu tun bayan fitarta "Har yanzu kina zaune?,inaga ya kamata kiyi wanka ko?,tunda na nuna miki yadda zaki kunna shayar" dan gyara zamanta kadan kaltume tayi,tana qoqarin sake fuskarta,ganin yadda duk abinda biban zatayi,tana yi mata shine fuskarta cikin fara'a "Da cewa nayi sai zuwa anjima"ta bata amsa tana wasa da qasan hijabinta daya dan bule. Kai biba ta girgiza "A'ah fa,gidan nan dabam yake,kamar yadda mutanen ciki suke na daban,kiyi wanka,saiki fita ku gaisa,sannan ki samu abu kici karki zauna da yunwa irin ta jiya" kai ta daga mata a sanyaye tana duban agogon dake maqale a bango,duk da bata gane qarfe nawa yake bayarwa,amma a jikinta tasan safiya ce sosai yanzu,wanda bazai wuce tara na safe ba,duk da ko a gida bata kaiwa rana sosai ba tare tayi wanka ba,irin na 'yammatan garinsu da suke kaiwa yamma lis,sai an dawo daga tallah,la'asar sakaliya,sannan ayi wanka,a hade harda kwalliyar zuwa dandali. Kalle kallen data tsaya yi a bandakin ya sanya ta bata lokaci sosai,ta tsaya gaban babban madubin dake bandakin tana kallon fuskarta,kallo na sosai a karon farko. Koda ake cewa tafi habi duhu bata taba zata duhun nata yakai haka ba,a gurguje ta cuccuda abinda ya samu sanda taji muryar biba ta sake dawowa,ta maida kayan jikinta ta fito. Dubanta biban take cikin mamaki "Bakizo da wasu kayan bane?" Sai data kalleta kafin ta bata amsa,tun sanda wancan da batasan sunansa ba ya kirata take kula da damuwa da al'amarinta,tana ganin hakan muraran cikin idanunta "Nazo dasu" "Yauwa,dauko ki canza wasu,ki ajjiye wadan nan" qarasawa tayi inda ta sakaya qullin kayan nata,ta bude ta soma dubawa,biba na tsaye tana bin kayan da kallo "Sune kayan naki wai?"ta sake tambayarta,dauke idanu kaltum tayi daga kan kayan ta mayar ga biban,tana mamakin yadda ta tambayeta "Eh" ta amsa mata a gajarce "Shikenan ba laifi,dauki daya a ciki ki saka" ta qarashe maganar tana ajjiye mopper da abin shara don kintsa dakin. Da hanzari kaltume din ta karba "Ki barshi zan share" da tace ta barshi,don batasan matsayinta cikin gidan ba,kada ta aikata ba dai dai ba ta jawa kanta wani abun na daban,ganin ta dage sai ta sake mata,ta koma bandaki ita ta fara gyarashi. Tana tsaka da sharar tana cike da mamakin yadda wajen yake sharuwa subul subul,babu qasa,babu qura,ga sauqin shara. A dan zabure ta dago jin an turo qofar dakin,har jawahir data shigo cikin shirinta tsaf na tafiya makaranta ta ankara da hakan,saita sake mata murmushi "Yi haquri,na tsorataki ko?,sauri nake,ina biba zuwaira?" Qofar bandaki dake budewa ta kalla,dai dai sanda biba ke fitowa "Diyata an fito?" "Eh wallahi....don Allah biba zoki zubamin.....zan makara Allah,ya saraki na samu zai saukeni" da kallon mamaki kaltume ki binta,da alamu tana da kirki sosai a fuska,saidai kuma yadda take magana a shagwabe ya bata mamaki,ita bata taba ganin inda babba kamarta ke shagwaba ba,wanda inda a karkararsu ne tana da yara uku ma. Nauyi taji ya kamata sanda suka hada idanu da jawahir,ta kamata tana kallonta,ga mamakin kaltume saita sakar mata murmushi "Baquwa ya sunanki ne?" "Kaltume ce" biba ta amsawa jawahir sanda jawahir din tayi gaba,biban na biye da ita a baya suna surutu. Tana hakimce saman dining din tana breakfast cikin salon da zai nuna izza mulki da kuma iko da take dashi,falon baby daya cikin yaran gidan,sai masu aiki daketa kai komo suna gudanar da hidimar gidan ta yau da kullum wadda ta zame musu jiki. A irin haka kaltume suka fito tana biye da biba,a mugun darare tana raba idanu tana kallon yadda Allah ya zuba ruwan kyau cikin falon da batasan wanne suna zata bashi ba. Sai data kusan gama cin dankalin gabanta sanda suke duqe suna gaidata sannan ta ture farantin "Lafiya lau....ita zaman me takeyi da baki shiga da ita cikin ma'aikata an bata aikin daya dace da ita ba?" Mommyn ta jefawa biba tambayar,kasancewar itace shugabar duka ma'aikata mata na gidan,saboda dadewar da tayi cikin gidan "Ai dama bansan wanne aiki ya kamata a bata bane,nace ne bari na fara tambayarki tukunna" shuru ne ya biyo baya tana nazari,akwai abinda takeson aiwatarwa,saidai batason wanzar dashi da kanta lallai saita hannun professor,duk da tana hangen lokaci xai mata tsaho kafin komai ya mata yadda takeso,amma zatabi lokaci bisa takatsatsan da rashin gaggawa kamar yadda ta saba "Kije ki bata duk aikin daya kamaceta.....amma tayi qazanta da yawa,banason a bata aikin daya dangancin abincinmu" ta fada fana dan qarewa kaltume kallo "To hajiya" biba ta fada tana miqewa. A hankali kaltume dake duqe itama ta miqe kanta a qasa,ita sam bata gane abubuwan da suke faruwa da ita,tun daga sanda aka daura mata aure zuwa yanzu,ita ba haka tasan ana zaman aure ba,shi wanda yake a sunan mijinta har yanzu jikinta da zuciyarta sunq amsar kalmar,a kallon ma datayi masa a jiya gaba daya sai taga wani irin bahagon dacewa tsakaninta dashi,tunda ya kawota gidan ya ajjiye bata ganshi sau biyu ba,na biyu an kawota wajen wannan matar dake tsareta da wani irin kallo dake sanyata fargaba da tsoro,kuma taji ana maganar a bata aiki,har tana qyamarta,bayan ko kafin ta fito ma sai da tayi wanka,to meye abun qyama a jikinta,to ko su a tasu duniyar haka ake zaman aure?,ta kasa warware wannan zaren,amma dai....koma meye zata zuba ido taga iya gudun nasu ruwan. Babban kitchen ne,wanda duk girmansa an yishi bisa tsari na zamani,tsari me qawatarwa,kowa dake cikin kitchen din aikinsa yake gabatarwa,sai biba ta dinga bi da ita gurin kowa tana nunata suna gaisawa,kana daga bisani ta nuna mata waje tace ta zauna. Bata musa ba ta zauna din,tsahon lokaci idanuwanta suna biye dasu,duk da rabi da rabin hankalinta naga gidan wajen ummanta,tare da tunanin a wanne hali take ciki,amma ta cika da mamakin yadda za'a ce wai wannan qawataccen wajen wurin an tanadeshi ne kawai saboda dafa abinci,tabdi,lallai wani aikin sai binni,ashe duk labarin maraya da sukeyi basusan ma komai game da ita ba,tunda hasashensu bai taba hasko musu irin hakan ba,to waishi mijin nata wayeshi ne,kuma me suke a wannan gidan?,a nan zasu dawwama ko zasu tafi?. Ganin zaman ya soma tsaho ba tare da biba ta waiwayeta ba saitace da ita ta bata aikin da zatayin "Ki zauna abunki,babu wani aiki me yawa yau,sai gobe idan Allah ya kaimu,idan kin gaji zaki iya komawa dakinki ki zauna" zata iya gane hanyan komawar amma bata da sha'awar ta koma din,don haka taci gaba da zama a wajen,har zuwa lokacin da najwa ta fito yin breakfast,ta kuma aiko cewa biba takai mata kayan karinta dakinta. Kaltume ta baiwa wasu qananun kofunan qarau masu kyau da wani plate tace ta tayata dashi,tana biye da ita,suka wuce wani qayataccen falon kafin su dangana da dakin najwa din. Tana zaune saman sofa ta miqe qafafunta da alama wayarta dake saman cinyarta take amsawa,kanta babu dankwali,tana sanye da wasu kayan bacci masu kauri da zasu iya tare mata dan sanyin da aka fara busawa,sai gashinta da bai wuce tsayin dan yatsa ba,saidai kuma a kwance yake yasha gyara. Suna shigowa ta katse wayar,fuskarta a murtuke ta sauke qafafunta qasa tana bin kaltume da kallo sanda ta qaraso tana dire kofunan kamar yadda taga biba tayi "Move dalla malama,matsa nace!" Ta fada cikin tsawa kamar zata sanya qafa ta buge kaltume,tsoratar datayi yasa taja baya da sauri,saura kadan kofunan da bata gama ajjiyewa ba su daki qasa su fashe "Zuwaira meye haka din?,zaki kwaso min yarinya tana wari ki shigomin da ita?,tana tabawa mutane kayan abinci?" Kan biba a qasa tace "Kiyi haquri" "Fita ki bani waje,kin tsaya kina dumamawa mutane waje....idan ta fita ki dauka freshner ki fesa min". Da sauri kaltume taja da baya sannan ta juya tana hada hanya saboda sauri ta nufi qofa,tana jiyo sanda biba ke fasa freshener din,saita lumshe ido tana sakin ajiyar zuciya,tana jin yadda bugun zuciyarta ke qaruwa saboda tsoratar da tayi,su wadanne irin mutane ne wadan nan?,wacce iriyar rayuwa suke?. "Kiyi haquri kinji?,haka take bata da kirki,nan muma kowa haquri yakeyi da halayenta" biba ta gaya mata bayan fitowarta daga dakin,kai ta kada,ta motsa labbanta a hankali "Ba komai" saidai tana ji a zuciyarta,tunda har ya tabbata haka halayyarta take,ya zame mata dole ta nisanceta,duk da cewa ta girmemata,haka nan yanayin sukuni da muwalati na rayuwa sun bayyana banbancin dake tsakaninsu,to amma fa zuciyar nan tata har yanzu itace a qirjinta,ba zata juri cin mutunci da wulaqanci ba,bayan ba wani abu ta aikata mata naba dai dai ba. *********Cikin takun dake qara nuna qasaitarsa,hannyensu biyu duka soke a aljihun Blazer din dake jikinsa ya isa bakin babban gilashin daya mamaye bangon yamma na office dinsa,wanda hakan yake bashi damar hangen ilahirin makekiyar harabar kamfanin dama wasu sassanni na unguwar,hannu yasa ya yaye dan wani abu da aka zuba daga gaban glass din me madadin labule yana furzar da iskar bakinsa,idanunsa ya sauka parking lot dake cike da motocin ma'aikata,can ya hangi fawwaza gaban tata motar,ta sanya muqulli tana bude motar,duk da ka gane yanayin fuskarta sosai,to amma daga nam yana iya karantar yanayinta. Daga bakin office dinsa take,ya tabbatar ranta a bace yake,saboda hanawa da yayi a barta ta shigo wajensa,gaba daya yau ita da ire irenta babu wanda ya bari ya shigar masa office,shi yasa ya zaunar da umar daga waje,saboda yana da tabbacin shi din zai iya yadda yace masan. Bai bar wajen ba har sanda ta shiga tabtada motar ta fice daga kamfanin,ya sani cewa ba lokacin tashi bane,kuma fitar tata tamkar ta karya dokar kamfani ne,saidai yana sane da komai,zai kuma yi maganin matsalarta. Sauke labulen yayi,ya juyo a hankali yana duban saman table dinsa dake cike da files wadanda dukkansu shi suje jira,ga alamun gajiya da kasala sun bayyana qarara cikin kyawawan qwayar idanunsa. Gaban teburinsa ya qarasa,ya dauki wayar landline yayi magana ta sakanni da basu wuce takwas ba sannan ya sauke wayar,ya koma ga files din yana buda wasu daga ciki,har zuwa sanda qofarsa tayi 'yar qara alamun ana neman izinin shigawa,sau daya ya danna wani abu dake gefansa,qofar ta bude aka shigo 38 Dauke da babban faranti mutumin dake sanye da uniform irin na ma'aikatan cikin kamfanin ya shigo,ya qaraso cikin girmamawa ya ajjiye zazzafan coffe din,ya juya ya fita dai dai sanda saraki ya fara kai cup din coffee din bakinsa,yana sake kiran waya da wayar landline din dake gabansa "What are you waiting for?...... file na office dinsa kawai nake jira fa,u r wasting my time" ya fada cikin fushi,dan jim yayi,da alama yana sauraren abinda ake fada daga daya bangaren ne,ba tare da yace komai ba ya sauke wayar "Kai da waye?" Ya tsinci muryar amiru dake shigowa office din kansa tsaye,wanda kusan shi kadai keda wannan ikon,sai ya waiwayo yana riqe da cup din yana dubansa "Fawwaz.....already na gaya masa ya tattara dukkan wasu bayanai dake offices din dakw qarqashinsa na qarshen shekara,kusan na karbi ko wasu bayanai amma nashi ya gagara zuwa?". Baice komai ba,sai daya ajjiye file din daya shigo dashi kan sauran dake wajen,yaja kujera ya zauna sannan yace "Not surprisingly" cira kai samir yayi ya dubeshi,yana nazarin fuskar amirun na wasu sakanni,shima amirun shi yake kalla,kafin daga bisani ya dage masa gira,sannan ya tashi ya zauna sosai yana fadin "Aje wannan a gefe......ya kukayi da daddy?" Kujerarsa ya koma ya zauna,ya hade hannayensa duka waye daya,sannan ya fara gayama amirun yadda ake ciki. Shuru ne ya biyo baya na wasu sakanni kafin amiru yace "Yanzu....what next?.....tunda kaqi yarda da shawarar mayar da ita?" Bayansa ya mayar ya jingina da fuskar kujerar "Ko wajen hajiya qarama zata koma?" Amiru ya sake fada kafin yaji amsar samir. Kansa ya kada "A nan din dai zata zauna tare damu,duk da sabanin ra'ayi da muke yawan samu.....kusan nafi kowa karanta da sanin waye daddy,so i wil do my best naga nayi duk abinda nasan cewa zai hanashi sauya komai" kai amir ya kada,shi kansa tsayin shekaru har yau ya kasa sabawa da wasu abubuwan dake gudana a tsakanin samir din da daddy,hajiya qarama tasha gaya masa cewa, professor rashid nason samir fiye da duk wata halitta dake doron qasa,saidai kuma ayyukansa sun qaryata hakan,wannan abun ya sanya shakku a zuciyar shi kansa amir kan sahihancin maganar. Neman izini da kuma shigowar fawwaz ita taja hankulansu dukka su biyun,babu wanda ya cewa komai a cikinsu,ya qarasa gaban table din saraki ya sakar maaa file din yana daga tsaye,sannan ya juya yana gyara suit dinsa zai fice,amiru yayi motsi da niyyar maida martani,samir ya masa nuni da hannu kan kada ya tanka "Why....me yasa kake qyale gayen nan ne saraki?,wayeshi?,meye taqamarsa?,mommy jidda ko kuwa?" Wani qaramin murmushi samir ya saki yadan daki kafadar amiru "Cool down....." Ya fada alamun ranshi bai baci ba,hakanan hankalinsa a kwance yake "Ba dole bane saiya nuna akwai sanayya tsakaninmu,aikine ya kawoshi shi kuma ya hadamu,hakanan shi xaiyi,abu daya na sani,bai isa ya taka koya karyamin dokar aikina ba....yafi kowa sanin me zai biyo baya idan hakan ta faru.....so please karka damu da wannan" ya fada yana tura masa coffee gabansa "Mu tattauna abinda ya kawoka" *********Kyawawan fararen dawakai ne guda uku a daure,sai wani mai ratsin fari da baqi,sunci sun qoshi sai harbin iska kawai da sukeyi,duk wanda ya kallesu saiya kuma kallonsu,saboda cika qoshi da alamun cikikakkiyar lafiya da tsafta dake tattare dasu. A hankali samir ke zagayawa cikinsu shi da wanda ya ware musamman saboda kula dasu,ya gama duba lafiyarsu,suka danyi magana da mutumin da yake kira da wakili,sannan ya soma takawa yana barin sashen da dawakan suke,yana zaro wayarsa da aljihun wandonshi,karo na farko tun wayewar garin yau,wanda gaba daya wunin yau ya yishi a gida ne. Number jawahir ya nema,bugu daya ta daga tana gaidashi "Ki kawomin abun sha bamai sanyi sosai ba,ina ta wajen barga" "To yaya" "Wait.....ki tahomin da baquwar nan" "Kaltume yaya?" Ta tambayeshi "Yes" ya amsa mata yana mamakin yadda tayi caraf da sunan cikin kwanakin da basufi bakwai ba. Qarasawa yayi a hankali inda yasa aka zuba masa kujeru,yana daura da inda dawakan suke,ta yadda duk wanda ke zaune zai iya hangosu,a wadansu lokutan suna daya daga cikin abinda ke debe masa kewa. Da sauri ta dago daga durqushen da tayi daga can bayan kitchen din tana wanke 'yan tsumman kayanta,tuntuni takeson wankewar,amma ta rasa a inama zatayi wanki cikin gidan,don ta fuskanci komai nasu a tsare yake,hakan ya sanya ta samu roba ta tari ruwa ta cikin famfon kitchen take fita ta baya take wankewa. Murmushi jawahir ta sakar mata,ta lura kusan koda yaushe a tsorace take,har yanzun taqi sakin jikinta kwata kwata "Wanki kike ne?,inata nemanki ai ban ganki ba" murmushin itama ta maida mata tana gyada kai "Akwai washing machine ai,da baki wahalar da kanki ba" ta bata amsa tana qarasowa ciki,idanunta kan kayan da take wankewar,wanda ita a wajenta basu da maraba da tsumma,duk sanda zata ganta cikin kayan binta take da kallo,tanataso ta bata wasu kayan,saidai kwata kwata cikin satin bata samu sukunin zama ba bare ta fidda mata "Muje yaya yana kiranki" fararen idanuwata da suka haska baqar fuskarta ta daga ta dubi jawahir,don bata gane wa take nufi ba,amma saita saki zanin hannunta ya koma cikin ruwan,ta janyo sudaddun takalmanta tana sanyawa,jawahir ta bisu da kallo kana ta juya,kaltumen ta soma binta a baya "Wai bakya magana ne kaltume?" Murmushi tadan saki "Kinga ki saki jikinki,mu gidan nan kowa yana da 'yancinsa,matuqar kawai zaka bi dokar mummy to ita ba ruwanta da kai,ki saki jiki kiyi walwalarki kamar kowa" da kadan da kadan take janta da hira har suka isa inda samir ke zaune. "Gata yaya" jawahir ta fada tana ajjiye masa abinda ya buqaci ta kawo masan "Good auta,kije zan kiraki" ya fada yana murmushi,saita dan tsaya tana murmushi "Amma yaya...." Murmushin shima ya saki,kaltume ta dan bishi da kallo "I will call you when I'm done" "Tom"ta fada tana juyawa ta soma barin wajen,kaltume ta bita da kallo tana jin kamar tabi bayanta,ita kadai a cikin gidan baya ga biba da take dan jin sukuni da 'yar nutsuwa idan suna tare,barinta datayi a wajen sai takejinta wani iri gaba daya,gabanta na wani irin faduwa "Bismillah....zauna" tattausar muryarsa ta ratsa kunnenta,saita waiwayo a hankali ta dubeshi da farare qal din idanunta,ta samu ya kafeta da ido yana duban black face dinta,sauke idanunta tayi a hankali,kana ta sulale zuwa qasa tana gaidashi "Lafiya lau,tashi ki zauna" ya sake maimaita mata,duban kujerar tayi ta dauke kai,ba zata iya zama saman kujera ba yana kai,bata taba ganin ummanta ta yiwa babanta hakan ba,don haka ta girgiza kanta alamun a'ah "Ta yaya kenan zamuyi magana a haka?,tashi ki zauna"ya furta yana gyara kujerar,tasan musu kusan haramunne,don shine abu na qarshe da bazata iya tuna sau nawa taga ya faru a gidansu ba,don haka ta miqe a darare ta nufi kujerar tana damqe da nannadadde mayafinta data yafa,tunda ta wanke hijabinta. Idanunsa ya dauke zuwa wani sashe na daban yana boye murmushin daya taso masa,shi kadai yaji cikin ransa abun ya bashi dariya idan zuciyarsa ta raya masa cewa matarsa ce kenan. Gyaran murya yayi kadan yana kwatanta ya yadda zai mata maganar da zafa fahimta dai dai da hankalinta,don yana ganin kamar tayi qanqanta da duk abinda zaya gaya mata "Kinsan matsayina a wajenki?" Sai data dubeshi sannan tace "Eh,miji....." Kalmar tayi mata nauyi,ta kasa qarasawa,qaramin murmushi ya saki "Haka" gyara zamanshi yayi sosai "Inason daga yau ki dinga kallona a matsayin yaya ba miji ba kin fahimta?" Maganar tasa ta bata mamaki,ta sake dubansa ta dauke kai "Eh,ki daukeni a matsayin yayanki,kinga yadda yanayin abun yazo,babu wanda yasan matatace ke,akwai lokacin da zan gaya musu da kaina,so karki damu da sai kin gayawa kowa,kinsan sunana?" Ya tambayeta,saita kada kai "Muhammad samir,nan gidanmu ne gidan mahaifina,nasan kinga mahaifiyata,wadda ta rakoki qanwata ce,akwai yayarta nasan itama kin santa,kin fahimta?" Kai ta sake gyadawa tana saurarenshi "Zaki ci gaba da zama tare damu har zuwa wani lokaci,yanzu ajinki nawa a makaranta?,kin gama junior secondary school ne?" "Banyi karatu ba" shuru yayi cike da mamaki,ya dauka da bilal baiyi karatu ba ita din tayi,kasancewar ta girmeshi,amma kuma daya tuna yanayin society din data fito daga ciki sai mamakin nasa ha ragu,saidai kuma tabbas akwai aiki kenan a gaba?. Sauya akalarshi yayi zuwa ga fannin addini,anan din alhamdulillah saiya samu babu laifi tana da sani sosai ta wannan fannin,hakan yasa yaji sauqin fargabarshi akan ta ina zai fara. "Kina sha'awar karatun boko?" Ya jefa mata tambayar data sanya take fuskarta fadada da fara'a,da sauri ta gyada masa kanta,babban burinta kuma mafarkinta kenan a rayuwa "Is ok,but ki saki jiki,ki daukeni tamkar yayanki kinji ko?" Kai ta kuma gyadawa "Bakya magana?" Ya tambayeta yana murmushi,sanda ya tuna masoyanta da qauye irinsu haladu,qanqantar shekarunta na fita muraran,amma a hakan ake fada a kanta kamar wata cikakkiyar mace?. "Inayi" ta amsa da siririyar muryarta wadda alamun farinciki ya bayyana ta cikinta "Ku nawa ne a gidanku?" Ya jefa mata tambayar,sai yaga annurin daya bayyana dazu a fuskarta yana raguwa,sannu a hankali yanayin fuskarta ya sauya,da alama akwai abinda ya taba ranta yanzun "Ni habiba......sai bilalu" ta qarashe fada muryarta na rawa,kansa ya gyada "Allah ya gafarta masa" "Amin"ta amsa tana duban tafin hannunta,tunanin ummanta da kullum take kwana dashi take tashi dashi ya bijiro mata "Wa zai kula da ummanmu?" Tambayar ta subuto ta fito daga bakinta,har yanzu idanunta na cikin tafin hannunta. Idanu ya zuba mata,sai yaji wani abu ya taba ransa "Uwa" kalmar data sauka tsakiyar zuciyarsa kenan har sai daya lumshe idanunsa,ta wannan fannin rayuwarsa a hagunce take,ina tashi uwar?,tana da rai ko babu?,ida tana da rai wake kula da ita?,sune tambayar da suka hadu suka tsaye masa a rai "Akwai wani abu da zai iya?" Tambayar daya yiwa kansan kenan,saidai tunanin nasa ya katse sanda ya fara jiyo alamun kukanta,haka kawai tausayinta ya saukar masa "Habiba zata kula da ita,haka ne?" Ya samu kansa da fada,saita ji wani sassauci na saukar mata,qaramar ajiyar zuciya ta subuce ta fito daga bakinta,ta kuma daga fararen idanuwanta tana gyada masa kai alamun eh "Good" ya fada yana bata qwarin gwiwa,yasan cewa akwai cakwakiya sosai cikin rayuwarsu,kusan shi ganau ne ba jiyau ba,amma akwai abubuwa da yawa da yasan cewa baisan dasu ba,bayason kuma shiga rayuwar data shafeta. Shuru ya ratsa wajen sanda yake ciro wayarsa ya kira jawahir,ba'a jima ba sai gata,taja kujera daya ta zauna tana cewa "Yaya da baquwarsa,ina fatan ba zata qwacemin fadata ba" qawataccen murmushin nan nasa ya sake ba tare daya bata amsa ba,saiya tashi sosai ya zauna yana dubanta "Zaki iya squeezing time dinki ki dinga yima qanwarki lesson?" Ya tambaya jawahir din,tana murmushi ta daga gira "Me zai hana yaya?,ka manta koyarwa yana daga cikin favorite dina,har ya najwa na ganin sakarcina?" "Yes....i remember that,so daga yau ta zama dalibarki,zaku fara from the beginning ne,ayimin list na komai da komai da ake buqata zan siya" "Tom yaya,amma yaya.....she need some items haka" ta fada tana jujjuya hannunta,ya fahimci bayani takeson masa,don hakaya bata hankalinsa "Like?" "Clothes" "Ok,ba matsala" "Thank you" "You are welcome" ya amsa mata,sannan ya basu umarnin tafiya. ☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠 *_K'AMSHI,K'AMSHI RAHAMA NE MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA SU SUKA SAN MUHIMMANCIN DA K'AMSHI YAKE DASHI MUSAMMAN A WAJAN MAI GIDA ,_*💃🏻💃🏻 *_Zafafan turarruka masu zazzafan k'amshi hade da wasu irin manyan sirrika na mallaka cikin sauki ba boka ba malam hajiya , Zaki jefe tsuntsu biyu da dutse d'aya , domin zamowa star azuciyar mijinki_*🌟🌟🔥 *_nasan dai kunada labarin mashahuriyar Mai Saida kayan k'amshin Nan Wanda akafi sani da *HUMKAM GIDAN K'AMSHI* *_a wannan karon ma ta sake kawo maku da sabbin kayanta masu abun al'ajabi Wanda da kud'i k'alilan zaku more zafafan turarruka Kuma ki shiga jerin Mata masu aji_* *IDAN SARI KIKE BUKATA INA BADAWA SANNAN INAGYARAN JIKI CIKI DA WAJE SHIN KINA FAMA DA INFECTION INA HADA MAGANIN SA DA IZININ ALLAH KISHA KI WARKE* *Kadan daga cikin kayan da muke dasu*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *BLACK KAJII* shin kina bukatar turaren da Zaki turara gidanki ya dauke maki warin sanyi ya kwana biyu Yana k'amshi ,?ki saye black kajiji Zaki Gane banbancinsa da sauran wannan ba k'amshi kawai yake ba idan kina turara. Jiki dashi Yana maki maganin kala kala ciki kuwa har da na sanyi , nemi naki Kar ayi Babu ke☀️🟢☀️🟠🌟08132506044 HUMKAMINCENSE *ANA WA HABIBY* Wannan harkan na oza room ne special turare Dan matan aure kadai yana dauke da abubuwa Wanda bazan fadesu anan ba sannan bashi kadai bane akwai Crazy powder da na ke hadawa dashi zakisha garin sannan kishafa turaren hmm *SUDANESE HUMRA* Turare dake dauke da sirrika Mai DAUKAR hankali kamshin ya banbanta da sauran turare Hajiya babbar sirrine Wannan hadin manyan Mata 08132506044 HUMKAMINCENSE *GLOWING OIL* Wannan yasha bam bam da irin Wanda kuka Saba gani ,Yana kashe kuraje Yana cire tabo Yana maganin kezbi da duk wani matsalan fata ,stretch marks duk Yana ciresu .... *MOWAR MACE* turaren mowar mace turare ne da larabawa suke amfani dashi Wanda da yawa mutanenmu Basu San da wannan iccen ba Mai dauke da magani k'amshi da sauran abubuwan masu matukar amfani ga fata ba Shi wannan iccen yanasa hasken fata yanasa fata tayi laushi da santsi sannan d'an alk'awari ne matuk'ar kina amfani dashi zai tsirga maki cikin fata ta yadda ko Bakiyi amfani dashi ba zakiji k'amshin shi na fita ta cikin fatar ki ,ke amfanin iccen mowar mace yanada yawa jaraba ko don gyaran fatarki , 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Muna gyaran jiki na amarya da uwargida zakizo har gida ayi maki gyaran jiki irin na Mata masu aji zakiyi kyau kiyi fresh ga kamshin da zai Kama jikinki💃🏻💃🏻💃🏻 Munada 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *JAS OUD* (hatsabibin turare kenan ) *AL'AJAB* ( Mai abun mamaki kenan )AL'AJAB Turaren tsuguno mai abubuwan Al'ajabi Yana maganin sanyi (infection) Yana matse HQ (Tightening)sosai 08132506044 yasa HQ dumi yasa jikinki da hq kamshi lokacin da kike AMFANI dashi idan Yana shiga gabanki zakiji wani Dadi na ratsaki Yana k'ara Dadi da Yana ciko gaba ya rikita oga🙈 *FIRST LADY* na Mata masu aji turaren Kaya Dana daki HAWII KAJIJI HALUT 👸🏻 *_PRINCESS_* _Sabon turare Dana hada na shafawa ajiki da gashi *PRINCESS* Yana da Dadi cool kamshi gare shi babu hayaniya na fad'a muku sabbin turaruka na Nan tafe princess na daya daga ciki kisayi *PRINCESS* kiji sabon Hadi me sanyin kamshi babu kosarwa da ace zan iya zabi tabbas zan zabi princess a matsayin turaren gashina zan dauki princess ya zama shi zan farawa shafawa jikina idan zan kwanta zan dauki *PRINCESS* sbd yara na Dan kamshi bamai hayaniya bane musamman zan rika yi musu amfani dashi *PRINCESS* salon na daban kamshin daban dadin na daban *PRINCESS* Zabin ku ne Zabin Humkam shine farin cikin ku Masoya *PRINCESS* gidan kowa_ Duk wad'an Nan turarruka ne hatsabibai masu rikita mazaje masu wani irin k'amshi Mai shiga zuciyar masoya 💃🏻💃🏻💃🏻 *SHU'UMAR HUMRA* ke daga jin sunan kinsan ta dabance mashahuriyar humra ce ta tayi shuhura wajan birkita tunanin Yan maza , humra ce da indai namiji yajita a jikinki to komai muskilancinshi sai ya susuce maki tana tado da sha'awa shauk'i sirrin mallaka, cikin kankanin lokaci ki rikita maigidanki da daddadan k'amshin ki😍😍😍🥰 *HUMKAM GIDAN K'AMSHI INA NAN ZAUNE A KANO GA MASU BUK'ATAR ZAFAFAN KAYANA INA AIKAWA KOWANE GARI DAKE NIGERIA HAR MA DA K'ASASHEN K'ETARE , KARKU MANTA A DADE ANAYI SAI GASKIYA* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 39 D/Z _Ki tuntubi wadan nan numbers din ki biya kudi naki ki karanta cikin aminci_ 08184017082 Ko kuma 09134848107 *_Bayan wani lokaci_* Sannu a hankali kwanaki suka fara shudawa kaltume a gidan fiye da yadda ta zata ko ta tsammata,bata taba kawowa kanta cewa zata zauna cikin irin wannan gidan ta rayu cikinsa ba,saidai lokaci da kuma qaddarar rayuwa sun tabbatar mata da hakan,saita fara tilastawa kanta zama ta fuskanci rayuwar a duk yadda tazo mata. Jawahir da kanta ta zauna tayi list da total na dukkan abinda ya kamata ace an siyawa kaltumen,haka kawai cikin ranta takejin yarinyar tayi mata,duk kuwa da cewa a qalla zata bata shekara biyu ko uku,amma yanayin halayya da dabi'un kaltume,wadanda suka kusa zuwa iri daya da nata tana jin dadin hakan. Ba tare da bata lokaci ba da aikawa da saraki amount din da take da buqata,bai tambaya ba ya tura mata,don a sannan kansa ya dauki zafi,anata lissafe lissafe na qarshen shekara cikin kamfanin,bai wani samun zama sosai,kullum da sassafe yake fita,ya kuma dawo bayan duhu yayi. Randa zata siyayyar ta sanya kaltume a gaba kan sai sunje tare tunda kayanta za'a siyo,da fari ta doje,tace ba inda zata,amma daga bisani da taga jawahir din ta matsa saita amsa mata. A tamfa ta fidda riga da zani cikin kayanta ta baiwa kaltumen kan ta saka,ta kada kanta "Zani da kayan jikina" ta fada with confidence,bata jin saka kayan,kasancewarta mutum me gudun abun hannun wasu, fuska jawahir ta hada "Shikenan,na gode" tayi furucin ne a sanda take tattare kayan zata fita dasu daga dakin kaltume din,dukkan alamu sun nuna taji haushi,sai kaltumen taji bataji dadi ba,ko ba komai jawahir da biba,sune mutanen da kaf cikin gidan bata da kamarsu,sun damu da ita da kuma rayuwarta,tamkar wata halitta ce ita din me muhimmanci. Ruqo hannunta tayi kana ta karba kayan,ta shiga bandaki a take ta sauyasu,sannan ta fito tana jin yadda kayan suka sake ta,ma'ana sun danyi mata yawa,duk da siranta jawahir,saidai ita tafi jawahir din sirantaka. Murmushi jawahir keyi,atamfar ta karbeta sosai da sosai,dama kalar da zata haska kowanne mutum ce "Kinga ko kyau bata yimin ba,tayimin yawa ma,gashi kin bata kayanki" murmushi ta sakar mata "Fada dai kawai kike,yadda tayi miki kyau ma ni bata yimin ba,yawa tayi miki dan kadan shima,qarasa shiryawa muje mu dawo don Allah" ta fada tana ficewa don dauko mayafinta. Sanda zasu fice najwa na makaranta,mummy kuma tana bacci,don haka babu wanda yasan da fitarsu. Babban store ta kaisu,inda suke da dukkan wani abu na buqatar rayuwa,baki kawai kaltume ta saki tana bin komai da kallo,tunda ta baro garin dinya take kallon komai kamar a majigin film,kamar wadda tayi hijira daga wata duniyar zuwa wata,komai da take gani a yanzu babu hasashensa ko sau daya cikin hasashe na duniyar mafarkinta,sai gashi yanzu komai yana zuwa mata a zahiri. Tana biye ne kawai da jawahir sanda take diban mata kaya,lokaci lokaci takan waiwayo ta tambayeta wannan yayi?,saidai kawai ta gyada mata kai,don ba wani ganewa lamarin sosai take ba bare ta tantance,har suka gama siyayyar suka taho mamaki na nan cike fal kanta. Ko a mota ma jawahir nata mata bayanin amfanin wasu abubuwan data siya mata,ji kawai take ba ganewa ba,tunaninta ya koma baya can ya lulaqa gida. Dauko rayuwarsu take tana hadata da wannan,tako ina babu misali,babu kamanceceniya,ta rakito rayuwar asiya da a sannan ake ganin tayi fice,sai taga tazarar dake tsakanin tamkar kwatankwacin misalin tazarar sama da qasa ne,da wannan tunanin suka isa gida,jawahir ta diba wasu ledojin kaltum ta diba wasu. Da sallama suka shiga falon,fuskar jawahir dauke da dariyan kaltumen data kewa bayani tace mata itafa bata ganewa. Mommy na zaune qasan carfet,sanye da wata doguwar riga mai taushi mara hannu,kana mata kallo daya zakasan cewa rigar ta lashi kudi,duk kuwa da cewa an mata zubin riga mara nauyi wadda ba zata takuraka ba,hannunta dauke da cup na tangaran da aka cikashi da lemo,mawuyaci ne ka sameta a zaune hakanan qalau babu kayan qwalama a gabanta,sai najwa da aka ajjiyewa dan tebur gabanta aka cika mata shi da abinci tana ci,da alama yanzu ta dawo itama daga inda taje. Fara'ar fuskar kaltum ce tayi qasa sosai,gabanta ya tsananta faduwa sanda suka hada ido da mommy,haka kawai take jin wani abu game da matar,ita dai tasan ba tsoro bane,amma yafi kama da shakka,uwa uba kuma ga dodon tata najwa dake zaune a gefe,dukkaninsu suka bisu da kallo har suka is tsakiyar falon,jawahir ta zube kayan gefan mommy gami da zama tana cewa "Wash Allah na" "Daga ina kuke haka?' mummy ta jefa mata tambayar,wani abu yana fita daga tsakiyar sautin muryarta "Siyayya naje muka yiwa kaltum......" Sauke idanunta tayi akan kaltum din,saita sadda kai,ita daya ta hangi wani abu tsakiyar kallon data jefeta dashi "Yayi kyau.....ku kwashe kayan daga nan kun cikamin waje" ta furta tana ci gaba da shan lemon hannunta. Miqewa sukayi su dukka,jawahir ta dauka wasu kayan kaltum ta dauki wasu suka nufi dakin kaltume din. Suna shiga tun daga bakin qofa kaltum din tace "Yaya jawahir kibar kayan nan,zan qarasa dasu,kije wajen mommy" dubanta tayi da alamun tambaya kan fuskarta "Naje nayi mata me?,yanzu fa muka gama magana da ita" "Kije kamar tanason yin magana dake ne,don Allah kije" dariya ta saki "Shikenan,ki fito da dukka kayan kafin na dawo,zanzo na miki bayanin amfanin wasu a ciki" kaita gyada mata ta soma jan ledojin,yayin da jawahir din ta juya zuwa falon,tana mamakin yadda akayi kaltum din ta fahimci tanason mata magana,amma ba'a qin ta mutum,bari taje ta gani. Mugun kallo daga wajen najwa ne ya fara mata sallama,amma sai ta dauke kanta,ba wani baqon abu bane,sun riga sun saba,mommy ta bita da kallo har ta zauna kusa da ita tana daukar remote dake gefan mommy tana sauya tasha "Yaushe kuka fara yanke hukunci keda saraki a gidan nan ba tare dana sani ba?" Ta tsinci muryar mommy tana jefa mata tambayar,saita sauke remote din tana duban mommy "Mommy.....me mukayi?" "Wannan siyayyar da akayi da izinin waye akayita?,wa kika shaidawa?" Shuru kadan jawahir tayi,ita a iya nata lissafin bata ga wani abun ba dai dai ba a cikin lamarin gaba daya,fadan da mommyn ta fara ya sanyata shuru bata bata amsa ba,ta kuma rufe da cewa "Zan sameshi shima,zan ja masa kunne" "Banza kawai wadda bata kishin kanta,kwata kwata kudi daraja arziqi da kuma mulki basu dace dake ba,ta yaya kina jinin professor rashid zaki dinga zubar da kanki cikin 'yan aiki,ke baki da wasu abokan hulda sai 'yan aikin gidanku?,common wasu fitattaun qawaye 'ya'yan manya baki dasu?,zaki gane kuskurenki ne sai randa bikinki ya tashi,baki da masu fiddaki kunya, mommy saiki daura damarar yiwa 'yan aiki anko a matsayin bridesmaids" cike da jin haushi ta jefawa najwa harara kana ta murguda mata baki. Abinda ya fusata najwa kenan,kasancewarta mutum me bala'in dagawa da son girma,bata qaunar raini ko kadan,sai tayo kan jawahir din da sunan kai mata duka amma mommy ta tareta "Banason wannan sakarcin naku fa,wai ku mene yake damunku ne?" "Mommy baki gani abinda ta yimin,ni zata harara?" "Ya isa,ke tashi ki bawa mutane waje" mommyn ta fada saboda raba rigimar,abun yana damunta arai sosai,ta rasa yadda zata hade kansu yadda takeso,so take su qaunaci juna fiye da yadda take imagining cikin ranta,amma abun yaci tura,jawahir ta kalli gabas najwa ta kalli yamma,kowa tsarinsa halayyarsa da dabi'arsa tasha bamban data dan uwansa,kai bakace ciki daya suka fito ba. Sai data ga bacewar jawahir sannan ta soma magana da najwa "Kullum ina gaya miki kibar biye mata,dukka wadannan halayen nata zata barsu,akwai lokaci,kuma lokacin na bata" "Amma mommy ta yaya kina xaune,kina cikin gidan nan har wani lokaci yazo da wani daya zai fara yanke hukunci kan wani ba tare da tuntubarki ba?" Murmushi ta sake kawai tana gyada kai "Yaro man kaza" shine amsar data baiwa najwa,taci gaba da surbar lemonta a hankali,yayin data xubawa waje daya idanu kamar me nazarin nau'in qasar da aka gina wajen da ita. Ringing wayar mommy shi ya ratsa shurun daya sanya kowannensu cikin nazari. A hankali ta ajjiye kofin hannunta,ta miqa hannu ta dauki wayar tata tana duba sunan me kiran. Da hanzari ta miqe ganin wanda yake kiran nata,ta daga kai ta dubi najwa "Kyauro ne" ambatar sunan ya sanya najwa duban mommyn sosai,kafin tace komai mommyn tayi gaba da hanzari xuwa dakinta tana cewa "Ina zuwa,Allah dai yasa lafiya" bata tanka ba tabi mummyn da kallo kawai,daga nan inda take tana jin sanda take murza key tana rufe qofar dakin. Numfashi ta fidda tana kyabe baki,ita a nata ganin mommyn nata tana wahalar da kanta ne kawai,duka wadan nan hanyoyin sun mata tsaho da nisa. Mintuna kusan goma sha biyar cikakku mommyn ta fito tana riqe da wayar a hannunta,yanayinta ya sauya kadan ba kamar sanda ta shige ba,xuba mata idanu najwa tayi tana jiran taji wani abun daga bakinta "Dole naje ma'ajiya,kyauro yace kwanakin nan kamar suna hangen akwai matsala" wayarta ta aje gefanta sannan ta dubi mommyn "Bazan iya bun turbar da ko da yaushe kike bi ba mommy,bani da wannan juriyar,me yasa ba zaki me gaba daya ba ki huta?,me kike jira?" Ta tambaya uwar tana kafeta da idanu. Kai mommy ta girgiza "Banason haqqin rai bisa wuyana,a yadda nake kallon abubuwan komai ya kusa kawo kansa da kansa qarshe ba tare da ina da wani jibi ko tuhuma akan abun ba" shuru ya sake biyo baya,kafin mommyn ta sake magana "Ki shirya zamuje nan da kwanaki biyar" "Ranar lahadi kenan?" "Eh....hakane,kamar dai yadda muka saba" "Ranar zan shiga makaranta clearance.......saidai ki zaba wani dan rakiyan,don already ma na soma qosawa da xuwan" harara mummyn ta watsa mata "Kyaci qaniyarki,ko meye nake ba dominku nake ba" dariya najwan ta saka,cikin ranta tana jin koma meye mommyn take domin su,ya zame mata dama dole tayin,idan ma batayin ba,bata jin ita zata zauna bata yiwa kanta wani gata ba. ********** Dukka idanunta ta zuba tana kallon kaltumen sanda take maimaita karatun data gama yi mata shi yanzun nan kamar ta shekara da iyashi,sau tari takan cika da mamaki tare da shakkar anya kuwa kaltumen ba boye musu tayi ba ta iya wasu abubuwan?,wani lokaci kuma mamakin nata yakan ragu idan ta tuna cikin hirarrakin da sukeyi da biba,ta taba shaida mata,su yaran qauye mafi yawancin lokaci sunfi na birni fikira basira da kuma azanci,saboda yanayin cima da kuma muhallin da suka girma,mai wadatar korran tsirrai,wanda ke cike da wadatacciyar kuma tsaftatacciyar iska mai kyau. Sannu a hankali yake takowa zuwa inda suke zaunen,kebantaccen waje ne da yake malale da tattausan koren grass carpet. A nutse yake tafiya cike da ginshira,kai idan baka sanshi ba sai ka dauka wani jinin sarauta ne,komai nashi me kyau a tsare a killace cike da tsafta da kuma aji. Qananun kaya ne a jikinsa da sukayi matuqar karbarsa,suka kuma fitar da siffar da Allah ya bashi,ta tsaho wanda ke tafe da murjewar jiki daya bayyana surar qarfi a tattare dashi sakamakon daga qarfe da yake yawan yi,iska ce ke raba turarensa mai tattausan qamshi zuwa kowacce kusurwa dake daura dashi,hakan yasa yana dab dasu jawahir ta shaqi turaren ta kuma daga kanta don tabbatarwa da kanta shi dinne. Murmushi ta saki saiya maida mata sanda yake dab da su "Yaya,u are welcome..."ta fada tana gyara zamanta. Kiran sunan yaya da tayi yasa kaltume dake faman son fara hada sentence da kanta duk da karatun baiyi nisa ba ta daga kanta,idanunta ya sauka a kanshi. Suna hada ido saita sauke nata idanun a hankali tana gyara zamanta,ba wai don zaman nata baiyi ba,hakanan kawai taji tana buqatar ta gyara din. Yana murmushin dake qarawa fuskarsa kyau da kwarjini yaja kujeran guda daya dake wajen,wadda da alama wani ne ya kawota ya zauna a kai "Auta,an fara karatun kenan?" Ya fada sanda yake zama saman kujerar,qamshinsa yana mamaye wajen "Allah yaya ka zama kudi,wahalan gani kake?" Murmushin ya sake saki,yana duqawa ya diba litattafan kaltume dake zube a wajen "Ina wuni" ta gaidashi da siririyar muryarta,ya daga kansa daga litattafan daya fara budewa ya amsa "Kina lafiya?" "Lafiya qalau" ta amsa masa "Babu wata matsala ko?" Ya kuma tambayarta a karo na biyu sanda ya buda shafin farko,itakam anan bata ga wata matsala ba,bata da rashin ci,babu rashin sha,babu rashin muhalli me kyau,matsalarta daya ce zuwa biyu,tunanin ummanta da habi dinta,sai kuma najwa da bata qaunar taga koda giftawarta,a iyaka saninta babu wani abu data taba aikata mata na kuskure ko ba dai dai ba,matsalar mummy kuma bata jinta da wani girma can,tunda a qalla tunda suke bata taba buda baki ta gaya mata wata kalma mara dadi ba,saidai kallon da take yawan yi mata yana sanyata jin tsarguwa aranta da kuma rashin sakewa,sai taji kamar an dabaibayeta. "Babu" ta amsa masa a taqaice,tana jin wani nauyinsa da kwarjini,itakam yafi mata kama da baiwa da uban gidanta,gaba daya ta zame kalmar miji daga kansa,kallon uban gida tafi yi masa "Ma sha Allah" ya amsa tana ci gaba da duba litatafan,wanda tun baiyi nisa ba ya soma mamaki,don bai tsammaci komai zaizo haka da sauqi ba. Tsahon wasu mintuna sannan ya kammala dubawar,ya daga kai yana kallom jawahir "Auta ya dalibar taki?" Murmushi ta saki tana miqawa kaltume wani littafi data gama duba mata wani dan qaramin aiki data gama duba mata "Yaya,wannan dalibar tawa ta kusan zama malama, to my surprise duk abinda aka karanta sau daya ta gama daukeshi,abun yana bani mamaki sosai" kansa ya jinjina,alamun qarfi yana ga me qiba,tun kan yayi tambaya idanuwansa suka gane masa komai "It means zata iya zana common entrance kenan?" Murmushi me kama da dariya tayi "Yaya saidai placement gaskiya,wata uku na gaba fa?,karatun namu yana sauri ne fiye da tunanin me tunani" "Good,am happy to hear that" kafin su kuma cewa wani abu daya daga cikin masu aikin gidan ta shigo. A ladabce ta gaida samir,sannan ta dubi kaltume "Hajiya najwa tana kiranki" shuru wajen ya dauka,yayin da qirjin kaltum ya soma bugawa cikin tsoron kiran nata "Muje na rakaki" jawahir ta fada tana miqewa "Barta taje ta dawo,zamuyi magana dake" da baya ta dawo ta zauna badon taso ba,tafi kowa sanin halin najwan,babu lallai saboda Allah tayi kiranta,saita dubi kaltume sanda take saka wani lallausan slipper,yana cikin siyayar da jawahir tayi mata "Jeki kaltum,amma ki dawo mu qarashe karatun yau,tunda kin iya wanda akayi" kanta ta gyada ta soma takawa a hankali tana biye da jamila data zo kiranta. Ajiyar zuciya jawahir ta sauke sanda kaltume ta bacewa ganinta,tana juyowa suka hada ido da saraki "Ya akayi auta?" "Tausayinta nakeji yaya,da mahaifinka da mahaifiyarka amma a kawoka wata uwa duniya da sunan aiki,ka daina ganinsu kwata kwata,tana da hankali sosai yaya,tana da sanin ya kamata,shi yasa ko yaushe take shiga raina take burgeni" hanyar yabi da kallo kafin ya dawo da hankalinsa ga jawahir,shi kansa yana jin she needs more attention daga wajensa,har ransa yana jin zai kula rayuwarta a madadin rayuwar bilal da yayi niyyar taimaka,tunda ita dashi duka abu guda ya yisu........ "Ranki ya dade gata" jamila ta fada a ladabce tana matsawa gefe. Waiwayowa tayi tana duba kaltume ita da sauran mutanen dake wajen,fuska a murtuke tace "Ke,cikin dakina xaki shiga,qadangare ne ya shigomin ta window din baya ki ciremin shi,nasan ku qauyawa ba tsoronsa kuke ba mazanku da matanku" tayi maganar tana riqe da qugunta idanunta qir a kan kaltume. Lokaci guda tsoro ya saukarwa kaltume,a duniya qadangare na daya daga cikin abinda bala'in tsoratar da ita,tund a gida basa hada hanya dashi,tun wani lokaci data yiwa inna laure laifi ta sanya mata shi a jikinta,sai dibanta akayi a sume. Kai ta girgiza cikin rawar murya "Wallahi ban iya cirewa ba,nima tsoronsa nake" Zare idanu najwan tayi cikin salon masifa "Ke ni zakiwa qarya,ku jimin yarinya da samun waje.....har a gayawa baqauye kama dabbobi,to wallahi yau saikin cireshi ko me zakiyi saidai kiyi" jin haka yasa kaltume dan ja da baya zuciyarta na bugawa tana girgixa kai "Allah nima tsoronsa nake,da na iya dana cire miki" kafin ta ankara ta sanya hannu ta fincikota,ta kuma turata dakin ta maida qofa ta rufe. Tsoro ne ya kamata,ta soma raba idanu,cikin rawar murya ta fara roqon najwa kan ta budeta bata iya cirewa ba,saidai tana jinta tana kuma tsaye bakin qofar dakin tana masifa tare da cin alwashin ba zata fito ba harsai ta cireshi,idan ba haka ba ta zauna a dakin,tsahon wasu mintuna amma najwan ta kafe kai da fata. Razananniyar qara kaltum ta saki sanda qadangaren dake maqale jikin labulen ya fito yabi takan qafarta,gaba daya ta fita hayyacinta,sai kuka data saki mai qarfi. Qarar ita taja hankalin samir da jawahir dake tattaunawa "Yaya muryar kaltum ce fa?" Jawahir ta fada tana miqewa idanunta akan samir din,saiya miqe yace "Muje". Dukkaninsu darewa sukayi da ganin shigowarsa,banda najwa da tayi ta maza ta maze,sam batayi zaton yana kusa ba. Bai kalleta ba ya isa bakin qofar dakin sanda jawahir ke tambayar najwa ba'asin abinda ke faruwa,ya murxa muqullin a nutse ya tura qofar ta bude. Tana ganin haske bata tsaya banbamce abinda ke faruwa ba tayi hanyar da gudu,babu bata lokaci sukayi clashing,tayi kyakkyawan masauki a jikinsa. Hannu yasa ya zareta a hankali yana jin yadd zuciyarta ke mugun bugu,saiya kama hannunta ya fiddota bakin qofar dakin ya tura qofar ya rufe,don ya fuskanci akwai abinda take tsoro cikin dakin. A hankali ya saki hannun nata ganin yadda suke bin hannunshi dake riqe da siririn tsintsiyar hannunta da kallo,fuskarsa a matuqar dinke ya dubi najwa "Me kika mata?" Cikin son nuna dakiya tace "Qadangare nace ta ciremin fa kawai" "Ce miki tayi ta iya?" "A'ah" "Amma meya saki turata dakin harda rufe qofa?" "Yaya bakaga daga inda ta fito bane,har tace bata iya cire qadangare ba saboda sanabe?" "Meye nasabar inda ta fito da iya cire qadangare?" Ya jefa mata tambayar wannan karon cikin matuqar fushi "To ai......" "Mtsw common keep quiet!" "Yaya kowa fa....." "Will you shut up ko sai na saki a dakin kema kinji yadda akeji?" Ya fada yana tura qofar dakin,wanda hakan ke nuna mata da gaske yake "Am sorry" ta fada ba tare data shirya ba,don taga bacin ransa qarara. Wani mugun tsaki yaja kamar xai cire harshensa,ya waiwaya ga jawahir da itama haushi da takaici ya cikata "Ki tafi da ita dakinki" "To yaya...." Ta amsa mishi tana kama hannun kaltume sukayi gaba,ya taka a hankali yabi bayansu ba tare da yabi takan matsalar najwan ba. Bin bayansa tayi da kallo zuciyarta na quna,lallai ya tabbata mutumin nan bai qaunarta shima,tunda har zai barta da abinda take tsoro.yayi tafiyarsa,bayan yasan ko mommy bata a gida,saita juya fuuu tayi hanyar fita zuwa farfajiyar gidan,zata juyewa security nasu rabon. D/Z 40 A hankali kowannensu yake kaiwa cikinsa a bincin,yayin da kowanne hannunsa yake dauke da wayarsa,table din yau fayau yake,saboda babu kowa a kai,daga mummyn sai najwa. Wayar hannunta mummy ta ajjiye a gefanta,ta dora idanunta a kan najwa "Ina jawahir ne?" "Tana daki" ta amsa mata tana ci gaba da danna waya "Me yake damun yarinyar nan ne?,kwanakin nan duka ta daina zaman cin abinci?" Fuska najwa ta yamutse ta ajiye wayar itma a gefan plate dinta "Ina gaya miki mummy yarinyar nan bata da hankali,duk sanda zanyi mata magana saiki hanani,kinsan abinda yasa ta daina cin abinci damu?,saboda waccar banzar 'yar qauyen mai aikin,tare suke cin abinci cikin daki,kuma kina zaune an maida miki yarinyar baiwa,ita kewa yarinyar can karatu,ni wallahi badan badan ba da sai nace jawahir ba jinina bace" "Ke!....kul!..." Mummyn ta fada cikin hanzari da muryar tsawa tana duban najwa "Kada na kuma jin irin wannan furucin daga bakinki,jawahir jininki ce halak malak" baki najwa ta sake tana bin mummy da kallo "Bakiji abinda nace miki ba?,nace kada na qara jin wannan kalmar daga bakinki" "Naji" ta amsa,fuskarta ta fara nuna fushin nan nata da bata iya boyeshi duk sa'adda aka bata mata rai,tana daukar cokali taci gaba da cin abincinta,yayin da mummy ta sake daukar wayarta tana laluben number jawahir. A daidai lokacin suna zaune saman carpet din dakin jawahir din,wanda tun ranar da saraki yace suje dakinta bata bar kaltumen ta koma dakinta ba,anan suke kwana,saidai jawahir din tana boyewa bata bari mummy ta fuskanta ba. Mayukan data siyawa kaltum take daddagawa,sai data gama ta waiwayo tana dubanta,cikin yanayin jin haushi tace "Ai wallahi tunda na kalli fatarki naga bata fara komai ba nasan baki amfani dasu,kinsan tsada da kyan mayukan na kaltum?" Kai ta girgixa "Ni wallahi tsoron koilin nake,banason bilicin,masu yima qyanqyaminsu nake,asiyata tana yi,amma ko hanya banason mu hada,tasha yimin ba'a da tsokanata,wai ni baqa ce,amma ni bana damuwa kwata kwata,saboda nasan haka Allah yakeson ganina,kuma tunda ya bani baiwar ji da gani,ya bani hankali,ya bani idanu da qafafuwa to nafi mutum miliyan dasu wannan ma suke nema" murmushi jawahir tayi,sau tari tana tsintar kyawawan dabi'u daga kaltum din "Maganarki haka take, black is beauty ni a wajena,ke kyakkyawa ce kaltum" ta fada tana kallonta,zaro idanu kaltum tayi itama tana duban jawahir,fuskarta da zuciyarta cike fal da mamakin kalamanta,saboda ita din ce mutum ta farko data fara gaya mata wannan kalmar,ko da yaushe saidai ace habiba ko asiya sune masu kyau a gidansu,saboda sun fita hasken fata,amma itakam bata taba jin wanda ya gaya mta hakan ba sai yau. Ta lura da tarin mamakin dake qunshe a fuskar kaltume,saita sanya dariya kafin ta tsaya "Wai mamaki kike?,da gaske nake ke kyakkyawa ce" "Ki daina fada don Allah,sai naga kamar kinamin ba'a ne" ta fada tana shafa 'yar kewayayyar fuskarta,tare da shafo zara zaran gashin idanunta masu tsaho,da a wadansu lokuta take jin suke rage kyan fuskarta "Kaltum,irinku ne masu boyayyen kyan da ba kasafai aka fiya ganinsa ta farat daya ba,sai sanda suka sake girma,suka kula da kansu,a sannan kyau mai ban mamaki yake bayyana daga jikinsu,fari tsaho ko sirantaka ba shine kyau ba,kowacce mace kyakkyawa ce ta irin hanyar da Allah S W T ya halicceta,amma ina me tabbatar miki ke.din kina daga sahun kyawawan mata,ina kuma da yaqinin nan gaba maza sai sunyi gware a kanki" Idanu kaltum din ta sake fiddowa,wadanne mazan?,badai mazan irin wannan garin da take gani ba,saidai mazan qauyensu. Jawahir ta sake katse mata tunaninta ta hanyar cewa "Wannan man dana siyo,bana komai bane,baya saka hasken fata,bazan ma yarda ki shafa ba idan muna tare,saboda ya saraki ya taba gayamin shafa man da zai sanya mutum hasken fata haramunne haramunne haramun ne......,kuma duk wadda takeyi ta shirya gamuwa da fushin ubangiji matuqar bata tuba ta daina ba,kuma dabi'a ce da shaidan yayi alqawarin dama sai ya sanya mata sun yita ita da qarin gashi" saita miqe ta soma bare ledar jikin mayukan tana dorawa saman mudubi "Daga yau sune man shafawarki.....gana gyaran gashi ma.....wait...." Ta fada tana waiwayowa "Ni ban taba ganin kanki bama fa kaltum,ya kike iya wuni ki kwana da dan kwali?" Murmushi tayi tana sake janyo dankwalinta tana rufe kanta,batason kowa yaga kan nata,saboda tsufa da kitsonta yayi,ranar da taso tsefewa a ranar suka tashi da kai bilalu asibiti,abinda ya hana tsifar kenan har yau,sai taji qwalla ta cika mata idanu "Allah sarki bilalu,yana can qarqashin qasa a kwance" wannan tunanin ya qara yawan qwallarta,sai tayi qasa da idanuwanta,wanda kiran wayar mummy ya hana jawahir ganin hawayen "Gani nan" ta fada tana katse wayar,saita duba sashen da kaltum ke zaune "Zanje na dawo mummy na kirana,shima man wankin kan nan yana sake gyara gashi,idan ya karbeki ma har tsahon gashi yake qarawa,Allah kafin lokacin shigarki makaranta dole ki fara amfani dasu don kada su rainaki,nasan ya samir private zai kaiki,ba kasafai yakesaka mutum a government school ba" daga haka ta fice daga dakin. "Ni dinma ba kowa bace,yadda kika daukeni jawa(haka take kiranta) ba haka bane,ban samu dukka wannan darajar a gidan uban daya haifeni ba,saidai na gaji,na gaji" ta fada tana kifa kanta saman cinyarta,hawayen da take riqewa suka fara zuba,jinta take a wani irin takure,ta gaji da zaman gidan,ta gaji da kewar ummanta da takeyi da habibanta,tana kewar dakin kwananta duk da nan ya ninka shi sau babu iyaka,amma tana kewarsa,tana kewar qauyensu qwarai. Yadda mummy ta zuba mata idanu har ta qaraso ya tabbatar mata akwai damuwa,tun kafin takai ga zama ta balbaleta da fada,abinda ta jima bataji tayi mata ba "Izinin waye kika nema da xaki fara koyawa yarinya karatu haka siddan,daga zuwanta gidan,ba'asan wacece ba ita?,ko yau ta cutar dake ta gudu babu inda zamu sameta,saboda bamu da tabbacin asalinta?da zaki dauketa ki kaita dakin kwananki ku dinga kwana tare,dakin kwananki fa jawahir?,anya kuwa kina tunawa da waye ubanki da kike hada matsayinki dana wasu?" Fuskar mommy take kallo tana mamakin yau kalaman dake fita daga bakinta,baya koda yaushe ita mai son taimako ce da jan mutane a jiki gami da faran faran dasu,gwiwa a sanyaye tace "Mommy kece kuwa?" Idanunta ta lumshe tana qoqarin cooling down kanta,tare da controlling fushinta,batasan ta fidda maganganu haka ba "Tunzurani kike son yi jawahir na soma aikata halin da ba nawa ba" ajiyar zuciya jawahir din ta sauke,ta gyara tsaiwarta "Mummy,ya samir ne yace na koya mata karatu,kuma shine yace na kaita dakina,kuma mummy itama ta fara koyamin karatun islamiya,tana da karatun addini,zaki mamaki sosai idan kikaga yadda ta iya....." "Ya isa,jeki" mummyn ta katseta sanda samir yake takowa cikij falon "Thank you mummy" ta fada tana jin dadin yadda bata ja abun da yawa ba,tafi zargin ma najwa ce ta zugata,don haka ta wuce najwan tana yar waqarta. Yana isowa wajen kwarjininsa ya mamaye gurin,fuskarta da mayalwaciyar fara'a kamar kullum tace "Barka da fitowa son" tana gyara masa kujerar dake daura da ita,yana gyarawa kansa wata kujerar tare da shirin zama ya amsa "Yauwa mummy" saiya soma gaidata bayan ya zauna,najwa ta gaidashi tana sauri ta kammala tabar wajen,abu guda dayan da take mtuqar jin haushinsa shine yadda kwarjininsa yake bugar da ita,sau tari shike mata burki kan abubuwa da yawa da take da burin aiwatarwa. Umarni mommy ta bata tayi saving dinsa,ta miqe ta hada masa komai,sannan ta kwashe wayoyinta tabar wajen "Samir,me yasa ne kwanakin nan kamar kana aiwatar da abubuwanka gaba gadi ba tare da sanina ko izini na ba?" Ta jefa masa tambayar data sanyashi daga kai ya dubeta,idanuwansa daya zuba mata ya sanyata gyara maganar "Duka masu aikin gidan nan qarqashina suke,nice ahaqqu da cinsu shansu da suturarsu,to amma ita wannan yarinyar ka dauki kudinka da kanka kayi mata abinda nice zanyishi,why son?" Ta qarashe tana fidda boyayyen numfashi,yau batasan mene yahau kanta take sakin magana haka anyhow ba. Ci gaba da cin abincinsa yayi kafin yace "Ita na daukota ne daga gaban iyayenta da sunan amana,so dole kinga nima na kula da wasu abubuwan,amana ba abune qarami ba" "Qwarai kuwa son,kayi gaskiya,dole ne kowanne mutum ya dinga kula da amana,kuma tunda haka ne nima zan tayaka in sha Allah" ta fada tana murmushi sosai kan fuskarta,saidai can qasan zuciyarta tana kallon haka kamar ragin matsayine a gareta,amma koma meye zatayi amfani da fikirarta kamar kullum,komai yaci gaba da gudana a qarqashinta. "I called daddy several times amma bana samunshi,akwai wani specific line daya kiraki dashi?" Wayarta tadan kalla sannan tace "Oh god.....tunda yaje bakuyi waya ba son?" Kansa ya gyada,fuskarta cike da damuwa tana jawo wayarta gabanta tace "Bai kamata ba, that's why ko yaushe yake kallonka a matsayin wanda bai damu da al'amuransa ba,pls put the digits ka kirashi yanzun nan" ta fada tana buda wasu shiryayyun numbers ta fara gaya masa yana rubutawa. Sai daya gama jerasu tsaf ya sake kallonsu,kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fara gwada kiran,a take na'ura ta gaya masa cewa a kashe wayar take "Maybe he is busy shi yasa ya kashe wayar,but please try to call him again" "Ok"ya amsa yana yunqurin aje wayar,dai dai sanda amiru ya shigo,a shirye tsaf dashi,kamar yadda ta lura shima samir din yayi ado ne cikin wata shadda da suke iri daya sak data amiru,dinkin matasan yanzu qaramin hannu,haka tsahon rigar bai wuce cinyarsa ba. Da fara'ar shima ta amsa gaisuwarshi tana masa tayin zama yaci abincin,saidai shi ya kada kansa "Sauri muke mummy,man,mu suke jira fa" "Sai ina haka 'yan samari?hala surukan nawa zaku ganomin" Ta tambayesu tana murmushi "Zamu daukarwa abokinmu amarya ne" samir daya miqe daga kan abincin ya bata amsa yana goge hannunsa da tissue "Allah ya bada sa'a,saikun dawo" ta rakasu da addu'a sanda suke ficewa,idanunta na kan amiru,saita koma ta zauna,taja wayarta tana neman wata number,tana jin a yau ya kamata ta tada zancan,bai kamata tayi sake akansa har haka ba,kamar yadda hajiya kulu ta shawarceta. "Pls kayi tuqi da kyau mu isa on time,wai me yasa kake hakanne,baka kyautawa IB bafa,tunda aka fara bikin nan babu abinda kaje masa,yau dinma kuma kana wani yanga akan titi kamar ba zamuje ba" "Nayi maka kama da mara aikinyi da zan yita zaryan bikin abokai?" Ya fada tana dan jefawa amir harara,duka amiru yakai masa a kafadarsa yana dariya "Allah ya sakamin,nine mai kama da marasa aikinyin kenan ko?,na gode" "Wa yasani,abu a duhu" ya fada yana qaramar dariya,sannan ya qarawa motar wuta kamar yadda aboki kuma dan uwan nasa ke so. Kamar kowanne qofar gidan amare sanda ake shirin daukar amarya,shima wannan a cike yake da motocin dake jere bisa tsari,yammata kowacce na nufar motar datafi kusa da ita. Amiru ya sanya hannu zai bude motar saraki ya tsaidashi "Me zaka fita kuma kayi,just ka bari ma hadu dasu a can" "No,kasan yanzu an canza tsari saboda rashin tsoro,sai anyi marking motarmu a cikin masu kai amarya" "Ok.....but pls" yayi maganar idanunsa nakan gungun wasu 'yammata dake tsaye,da alama suna laluben motocin dq zasu hau ne "Kada ka kwasomin yaran can masu rawar kan tsiya,a bani dattawan mutane" harara amiru ya jefa masa "To baba na" saiya saka qafa zai fice "Am telling you ne....duk wadda tayimin rawar kai saita fice" daga haka amiru ya rufe masa qofar yayi gaba. Mintuna kusan goma yaji ana knocking Glass din motar,ya daga kansa a hankali ya sauke glass din "Saraki...... best friend din amarya zata dauka pls,bata jin dadi ne sosai" qaramin tsaki yaja yana mita qasan ransa,me yafi lafiya dadi ne wai?,amma su mata akan kai amarya basa ji basa gani sai sunje,kafin ya gama mitarsa ma amiru ya buda gaban motar,ta shigo a hankali,dai dai sannan ya buda murfin motar shi kuma ya fice ta side dinsa. Sai data zauna sosai qamshin daya cika motar ya soma shiga hancinta,da alama na turaren mamallakin motar ne,wani qamshi mai taushi da dadi,sai ta waiwaya ta dubi drivern,take ta lumshe idanu,ta dora kanta saman qafafunta tana jiyo hayaniyar yammatan daga waje. Minti kusan goma taji wasu mata an bude musu murfin baya sun shigo,daga muryoyinsu tasan cewa dattijaine,ci gaba tayi da kwanciya har sanda taji an sake bude mazaunun driver an shigo "Bismillah" ya furta,muryar data ja hankalinta,har ta dago da kanta tana dubansa,suka hada ido,ya janye nashi idanun yana tayar da motar,yayin data lumshe ido tana jin kanta ya sake wani sarawa. Ta nemeshi har ta gaji,layin data taba ganinsa tayi bulayin nemansa a fakaice amma bata sake ganinsa ba,number daya bata idan ta shiga ba'a dagawa,abinda bata sani ba shine ba kasafai jawahir ke daga baquwar number ba,yau sai gashi dab da ita,amma yadda taji ciwon kanta yana qaruwa ya hanata yin komai ko cewa komai,sai komawa da tayi luf ta sake kwantar da kanta saman cinyarta tana shaqar daddan qamshi,wanda zata iya cewa hancinta bai taba shaqar mata turare mai dadin wannan ba. *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar 41 Tunda suka tafi hankalinsa naga titi,tuqinsa kawai a hankali cike da nutsuwa har suka kawo gidan amaren,jama'ar daya debo suka fita,saidai mubina ta kasa koda motsawa,saboda yadda kan mata ciwo ainun,ya kuma qaru ke ciwon saboda saraki,wanda baisan meke faruwa ba,don suna zuwa bayan ya kashe motar ya fice daga ciki shima. Baisan tana ciki ba sai sanda zasu koma,da yake wadanda ya debo din ba komawa zasuyi ba,amiru ya bude gaban da niyyar shiga ya ganta,ya shaidata don haka ya tambaya,da qyar ta iya amsa mishi "Please saraki ka daure mu ajeta koda pharmacy ne ta amshi magani,daga nan ta kira wani ko daga gida ne ya maidata gida" yace da samir sanda yake tada motar,shuru ya masa bai amsa masa ba,ya fara tuqinsa abinsa. A bakin wani madaidaicin private hospital ya tsaida motar,yayi horn sau biyu mai gadi ya taso ya bude masa ya saka motar ciki "Ho samir" amiru ya fada a ranshi,bai tsammaci ma yana da niyyar yin abinda ya sakashi ba,duk da yasanshi sarai,yana da matuqar tausayi da kulawa,mutum ne kuma shi mai tausayin mace qwarai. Nurse ce ta fito ta kamata zuwa ciki saboda yadda take tafiya da qyar saboda ciwon da kan nata yake mata. Mintina qalilan ta gama ganin likita,amiru na zaune yana waya yaga shigowarta,ba jimawa samir din ya shigo shima ya tada motar suka wuce. Bakin wani pharmacy ya tsaya,ya wurgawa amiru dake zaune a baya takardar hannunsa ba tare da yace masa komai ba,ya dauka ya duba saiya saki qaramar dariya,ya fuskanci kamar bisa dole yake duk wannan hidimar,kuma yasan dama baiso zuwa kai amaryar ba,shi ya tattagoshi,don haka baice komai ba shima ya fita,ba jimawa ya shigo da ledar magungunan,samir din ya kuma tada motar suka wuce. "A wacce unguwa zamu saukeki,zamu wuce gia dare na dada yi" lallausar muryarsa ta sauka a kunnenta ta sake haifar mata da kasala,saita lumshe idanu,murya can qasa ta gaya mishi sunan unguwar,tana kallonshi ta gefan ido. Nutsuwarsa da jan ajinsa sunyi yawa,komai nashi bisa salo me qayatarwa,abinda ya fara fusgarta akanshi kenan tun karon farko. Dai dai sanda zasu wuce ta wani waje taji amiru ya sako masa hira kan wajen,wanda dukka maganar tasu kan kasuwanci ne,sai tayi fakare tana sauraren yadda muryarsa ke fita da haruffa a jere masu cike da nutsuwa da kamun kai,hakan ya sake dulmiyata cikin wata duniya,har batasan sun shigo unguwar tasu ba,tadai ji amiru na tambayar number gidansunta gaya masa. "Na gode sosai,Allah ya saka da alkhairi,na gode" ta fada cikin raunanniyar murya,tana wassafa yadda zata samu number dinsa cikin sauqi. Sai a sannan ya kalleta,ya gyada kai kawai yana kauda fuskarsa,tadan leqa baya kadan tana yiwa Aamiru godiya sannan tayi hanyar gida. Shigowar kira wayarsa ya sanyashi waiwayawa ya dubi Aamiru "Pls karbi driving din nan" sai ya fito suna qoqarin musayar sit,yana shiga wani yaro ya fito da hanzari daga cikin gidan,dai dai sanda amiru ke fitowa shima don shiga gidan driver,yana amsa wayar,baiji abinda yaron ke cewa ba,har sai daya gama wayar,dai dai sanda suka dauki hanyar barin unguwar "Ta aiko a bata phone number din ka zata maka godiya idan ta samu sauqi" "Kai kuma saika dauka ka bata kenan?" Samir ya tambayi amiru ba tare daya waiwayo ya dubeshi ba,yana qunshe dariya ya amsa masa "Tunin ma,mukasan inda rana zata fadi,tunda kaine a kasuwa ai gwara a bata,mu mun riga da mun sayar" harara ya balla masa "Idan ban girgide maka auren ba kace bani bane" "Tuba nake the giant saraki" ya fada yana daga hannayensa sama alamar surrender,saiyayi qwafa kawai,bai sake ce masa komai ba. ***********Gefanta ta ajiye wayar kana ta miqe tsaye,goye da hannayenta a baya ta soma kai kawo da alamun zuzzurfan tunani. Wayar landline dake dakinta ta daga kai ta kalla,kana ta isa wajen da hanzari ta zauna daga gefan gadon,ta fara kiran sashen masu aiki. Bugu biyu aka daga "Turomin saratu" ta bada umarni sannan ta kife wayar,taci gaba da xama a bakin wayar,har zuwa sanda taji ana knocking qofar bedroom din nata. Zamanta ta gyara sannan ta bada izinin shigowar,cikin daqiqu kadan matar ta bayyana,kakkaura ce baqa,bata da tsaho sosai,saidai da alamu shekaru sun fara zuwar mata,duk da ba wani masu yawa bane amma tayi qaura daga gurbin quruciya zuwa na manyance. "Zauna saratu" mummy ta bata umarni tana bin saratun da kallo,saidai abinda ta kirata dominshi har a sannan bataji nutsuwar hakan cikin zuciyarta ba. Bata saba saka kowa cikin sabgar ba tsahon shekarun data dauka tana gudanar da al'amuranta a sirrance,to a yanzun ma batason ta soma sanya kowa gudun cabewar lamura,duk da cewa saratu amintacciyarta ce,saidai bata sakar mata ragamar komai ba,ta barta ne tasan iyakar abunda taso ita saratun ta sani Dan tsakin da batasan ya fito ba ta saki,saita dubi saratun "Jeki abinki" har ta isa qofa tunaninta yakai mata ga yarinyar "Ki kiramin wannan baquwar me aikin" "Kaltume?"kai ta gyada "Eh ita" "To hajiya" ta amsa mata tana ficewa daga dakin. Karamar ajiyar zuciya ta saki,bata kaisu shekaru ko wayewa ba,bare aje ga batun wayo ko gogewa da sanin rayuwa ba,hakanan tafiya da itan zai sake zama mata tamkar wani tsani izuwa wani bigire. Kanta ta sake gyadawa tana sake tabbatarwa da kanta hakan yayi. Daga karatu kaltum din ta shiga bawa jawahir labarin qauyensu,bada labarin a wajen kaltume dai dai yake shawagin ruhinta cikin qauyen,tana jin nishadi har tsakiyar zuciyarta duk sanda zata bawa jawahir labarin,kamar yadda jawahir din labarin ke burgeta,tana jin kalar wata rayuwa ta daban da batasan da wanxuwarta ba. Dai dai nan saratu ta shiga dakin,ta kuma shaidawa kaltum kiran mummy,gabanta ya fadi,suka hada ido da jawahir,sai jawahir din ta miqe "Muje na rakaki" kanta ta girgiza "A'ah....tunda batace kizo ba tabbas ni kadai takeson nazo din,ki zauna kada mummy tayi fushi,yanzu zan dawo" jawahir din batace komai ba har suka fice daga dakin zuwa katafaren sassan mummy,bisa jagorancin saratu. Tun daga yanayin dakin kaltum ta tabbatar da cewa lallai akwai qatoton bambanci,akwai kuma izza da jin isa bisa ga komai na lamarin hajiya jiddan. Binta take da kallo tare da qoqarin sake karantarta sanda take tunkaro inda take,duk wani motsi nata da yanayin dabi'unta ta gama karanceshi,tun a farkon xuwanta ta gama gane cewa,bata da rawar kai,yawan surutu ko kuma shishshigi "Kaltume" mummy ta kirata sanda ta zauna a cure waje daya "Na'am momi" ta amsa mata a nutse "Inaso zaki rakani anguwa gobe,ki shirya kamar gobe na safe,banason ki wuce haka,hakanan banason ki gayawa kowa batun zuwa unguwar,ni mutum ce mai son sirri,banason mutum mara sirri kin fahimta ai" kai ta gyada mata,sannan ta bata umarnin tafiya. Har takai bakin qofa ta kirayi sunanta "Hatta jawahir banason taji,don ba inda zanje da ita" kai ta gyada tare da ce mata "To" *********Goma na safiyar washegari har da mintuna goma sha biyar ne,daya daga cikin motocin dake farfajiyar gidan,wadda take mallakin hajiya jidda aketa zubawa kaya a booth tari guda. Hamshaqiyar mota ce wadda ta lashi kudade masu yawa kafin ta mallaketa,amma duk wanda zai kalleta koda baisa kudin abun hawa ba yasan motar taci kudinta. Cikin shiga ta qasaita dake nuna ainihin zallar alfarma da cikar arziqi da dukiyar mutumin da take aura ta fito,tana taku ɗai ɗai tare da qarewa farfajiyar kallo sanda ta tsaya tana jira a bude mata mazauninta. Daga can wata shiyya dake mahada da sassanshi na gidan shima yake takowa,cikin shigar suit na alfarma ,hannunsa riqe da wani file dake cike da takardu yana budawa daya bayan daya,yana takowa ne cike da sassarfa,gefansa umar ne yake masa wasu bayanai,wanda da alama sun shafi takardun hannunta. Ita ta fara hangoshi,saita dan gyara tsaiwarta,sam idan zatayi irin wannan tafiyar bata qaunar su hadu kafin fitarta daga gidan,duk kuwa da cewa yawa yawan siyayyar da take fita daga gidan zuwa wancan wajen tana fitowa ne daga aljihunsa. Rufe file din yayi ya miqawa umar kana ya masa magana kadan,sai umar din ya juya zuwa mota,shi kuma ya qaraso inda take tsaye "Barka da safiya" kamar ko yaushe,cikin kallon dake nuna qauna da kulawa tace "Barka kadai my son....za'a fita kenan" "In sha Allah" ya amsa mata yana kallon kayan da ake zubawa a booth din motar,kayane masu yawan gaske na amfanin yau da kullum,tun kafin ya gama mallakar hankalinsa take zuba irin wadan nan kayan take fita dasu zuwa duba gidan marayu,wannan tshohuwar dabi'arta ce da kaf gidan sunsan da ita. Yana tsaye harta shiga motar,shi da kansa ya rufe mata murfin motar,yana jin kyautatawarta data shaida masa zata fita ne da kaltume,hakan yana shaida masa cewa ta soma sakewa dasu cikin gidan kamar yadda yakeso. Duka duka tafiyar bata wuce ta minti arba'in ba suka isa wata unguwa,akwai gine gine wanda suke a tsare,saida akwai qarancin zirga zirgar jama'a qwarai da gaske. Qofar wata babbar katanga mai tsaho motar tasu ta tsaya,sai a sannan kaltume dake zaune gaban motar ta daga kanta tana bin katangar da kallo,tun shigarta motar bata motsa ba,saboda tsoro rashin sabo da kuma hada muhalli da mommyn karo na farko,duk da cewa tunda suka shiga motar mummyn ke waya,wadda ko abu guda daya kaltumen bata fahimta ba cikin hirar da takeyi din. Babu wanda ya tanka ko ya motsa,har zuwa sanda mummyn ta daga wayar,ta kuma shaida isowarta,ba'a rufa mintuna biyu ba wani kakkauran mutum dogo baqi ya fito ta qaramar qofar gate din,fuskarta dauke da madaukakiyar fara'a ya qaraso dab da motar,sannan ya fara bawa dirvern mummyn wucewa zuwa qofar da zuwa yanzu aka wangale mata ita. A hankali ta zuro qofafunta da suka fara rawa. ,kallon farko ta yiwa asibitin ta tabbatar asibitin masu rangwamen hankaline,duba da yadda suke ko ina bajaja a farfajiyar asibitin,kowa yana sharafin gabansa. Tunda take bata taba tsintar kanta a muhalli makamancin wannan ba,hasalima ita din mugun tsoron mahaukaci gareta,jakar mummy dake hannunta da qyar take ruquwa,ji take kamar ta kama mummyn ta ruqunqumeta amma tasan batayi wannan isar ba,ta dubu drivern mummyn da matashin da suka taho tare,wanda sai da aka jirayi zuwansa daga wani waje da batasan ina bane sannan suka taho,saita fuskanci hankalinsu kwance yake,babu wani tsoro ko fargaba irin nata tattare dasu. Cikin mintuna qalilan wasu mutane maza biyu mace daya suka iskosu,sunfi kama da likitoci dake kula da marasa lafiyan saboda yanayin suturar jikinsu,cikin wani irin girmamawa suka tarbi mummyn. Sakin ajiyar zuciya kaltume tayi sanda taga sun durfafi wata qofa da babu yawan jama'a sosai,tsoron dake cike fal a zuciyarta ya ragu,don tayi tsammanin zasu kewaye marasa lafiyan ne kamar yadda tasan anayi idan mutum yakaiwa marasa lafiya ziyara. Babban office ne me kyau ba laifi,su suka jawa mummy kujera daya don ta zauna,saita girgiza kanta "Ai banga ta zama ba,muje na ganta tukunna,inga in akwai matsala sai a san matakin dauka tunda wuri" "To ba laifi,amma yau da wannan zaku shiga?" Ma'aikacin daya tarosu ya fada yana nuna kaltume dake tsaye riqe da jakar mummyn da hannu,sai a sannan ta waiwayo ta dubu kaltume,batasan tana biye da ita ba da alama "Ki koma can wajensu alasan ki zauna" ta bata umarni,saita gyada kai tana hade yawun tsoro,ta juya zuwa wajen motar tasu tana addu'ar ta isa lpy. Qofar motar ta bude ta shiga saboda tsoro,tana bin harabar asibitin da kallo cikin nazari,wato ta karanci wani abu a rayuwa,shi mai lafiya duk inda yake dan gata ne,duk wanda Allah ya bawa kyautar lafiya ya gode masa,babu wata ni'ima data kai ta lpy dadi,gasu dai wadan nan bayin Allah,Allah ya amshe ni'imar hankali daga garesu qila badon sun masa wani laifi ba,sai don haka nan yaga damar ganinsu...... Tunaninta ya yanke da sautin qarar wayar mummy data bari cikin motar,kafin tayi wani motsi alasan ya zuro da kansa yana duban wayar "Ko zaki dauki wayar ki miqawa hajiya?, professor ne yake kira,kuma fada take a irin haka idan ya kira ba'a kai mata ba,shima kuma bayaso ya kira ba'a dauka din ba" tabbas tsoro takeji sosai,amma babu yadda ta iya tunda ya buqaci hakan,saita ajjiye jakar hannunta,tasa hannu biyu ya dauka wayar tana kallon irin kyan da wayar ke dashi,duk da hankalinta ba'a nan yake ba,ta buda murfin motar ta zura qafafunta ta fito. Tana tafe tana waige hara ta dawo office din,saidai wayam babu kowa,sai wani mutum guda dake tsaye yana rubuce rubuce cikin wani file. Muryarta nadan rawa alamun tsoro da rashin sabo take tambayarsa mommyn. "Tare kuke?" Ya tambayeta bayan ya kafeta da idanu,kai ta gyada,kamar bazaiyi magana ba,sai kuma ya nuna mata wata siriryar qofa hanya "Ki shiga ta nan,daki na can qarshe hannun hagunki" kai ta gyada masa sannan ta nufi qofar. Tsoro ne sosai ya kamata saboda yanayin duhun wajen daya bambanta dana waje,duk da haka bata fasa saka kai ba,saboda yadda wayar dake hannunta kiran yaketa shigowa yana yankewa,a haka harta isa dakin daya ce mata,saidai kuma qofar kamar a kulle take,sai qaramar taga dake bude,ta yanke shawarar ta leqa ta nan ko wani ta bawa ya miqawa mommyn wayar....... *_KO KUNSAN DA YAWANMU LAIFUKAN DA MUKA YIWA 'YAN UWANMU KE HANKADAMU WUTAR JAHANNAMA?_* *_ZAGIN MUSULMI,CIN ZARAFIN MUSULMI,WULAQANTA MUSU,CIN HAQQIN MUSULMI,TOZARTA MUSULMI,YI DA MUTUM,RASHIN BASHI HAQQINSA NA KARE HAQQINSA DAKE KANKA,WATO KARE MUTUNCINSA DA ADDININSA,DA YAWA ABINDA MUKE RAINAWA MUKE GANIN BAIKAI YA KAWO BA,YA KUMA ZAMA JININ JIKINMU SHIKE KAIMU WUTA,Allah ka bamu dacewa_* 👏🏽👏🏽👏🏽👏🏽 *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar 42 Window din yadan kerewa tsahonta,don haka ta danyi dage don takai ga bakin window din. Dakine fetal dake malale da siminti,babu komai cikin dakin da zaka iya hanga,sai wani gado guda daya mara kyan fasali,daga gefan gado kuma saman daben simintin dakin kana iya hangen wata mace zaune jingine da bango,fuskarta ta nuna tarin shekaru sosai,tana sanye da wasu tufafi da ba lallai ka gane ainihin kalarsu ba saboda tsufa da rashin wadatar haske,kanta na lullube da mayafi da yayi kalar kayan,fuskarta na fuskantar window din,saidai bashi take kalla ba, mommy dake tsugunne gabanta ta zubawa idanu "Me zaki gayamin?" Mommy ta furta tana ci gaba da kallonta,kamar yadda itama matar ta zuba ma mummyn idanu,kallon dake ratsa jiki da jijiyar mommy,kallon da zata iya cewa bata taba ganinsa a idanuwanta ba irin yau. Shuru ne ya biyo baya,sai kallo dai da take binta dashi,irin kallon da zaka iya kiranshi da kallon qurilla. Sake tashin ringing din wayar mummy dake hannun kaltume ya tsoratar da mutum hudu,mummy da mutane uku da suka shigo dakin tare,wanda suka juyo zuwa window da hanzari,sai kuma kaltume datayi saurin xamewa daga dagen datayi,ta sake daga wayar tana duba me kiran,tare da qoqarin hada alphabet ta karanta sunan me kiran dadan guntun karatun data fara samu. Kafin takai ga aikata haka dukka sun fito "Me kike a nan?" Mummy ta dakawa kaltum tsawa tana dubanta cikin fushi,kafin kaltum din ta bata amsa ta sake jefa mata wata tambayar "Wa ya baki izinin biyoni?,bakiga yanayin wajen ba?,ko su kike su miki illa?" "Mommy,ki haquri,alasa ne yace wai furofesa yana kira,shine yace na kawo miki kada kiyi fada" da hanzari ta tako,ta fusge wayar daga hannunta ta soma duba kiran,kafin takai ga kiran kuma wani ya sake shigowa,saita daga da hanzari tana kaiwa kunnenta,gami da yin gaba ta soma barin wajen,bayan ta yiwa kaltume nuni da idanu kan tayi gaba. Professor ne ke shaida mata cewar yana hanyar dawowa daga yanzu zuwa yammaci "Naje duba marasa lafiya,amma ina hanyar komawa gida yanzu in sha Allah" ta fada cikin salo na kwantar da kai,basu jima ba a wayar sukayi sallama,ta katse wayar,ta juyo tana duban mutanen da take tare dasu. "Miqomin jakata" ta bawa kaltume umarni tana jifanta da harara,a ladabce ta miqa mata jakar,sannan ta wuce ta koma bakin motar inda su alasan ke jiranta suma. Fuskarta cike da yanayu na bacin rai tace "abunda mukayi magana dakai a kanshi ni ba ganshi ba,ban sani ba ko kunnenka ne yayi maka gizo,amma abinda nakeso guda daya shine,aci gaba da sanya kula ta ninka ta baya,gaf zuwa sanda hali zaiyi,saidai abu daya zan sake maimaitawa,banason matsala,na tsaneta,hakanan bansan kalmar sakaci ko kuskure ba,nafi yarda da ganganci" kai kawai yake gyada mata namijin,da alama maganar tata na shigarsa sosai "Yadda matsala bata gifta ba tsayin shekarun da suka shude,bana jin a yanzu da komai ya riga da yayi nisa matsalar zata faru" macen ta maida amsa. "Haka nake fata" ta amsa musu cikin yanayin izza da isa,sannan ta sanya hannu cikin jakarta bayan ta zugeta. Kudi ta irgo kudi masu yawa ta miqa musu "Duk sanda kuka karanci wani abu da bai muku ba komai qanqantarsa,bana buqatar jinkiri a shaida min" "In sha Allah.....sai batun kaya" "Nakune kamar ko yaushe,amma kuna iya cirar wani abu a ciki da zai iya amfanarta ku san mata" da wannaj furucin ta soma takawa zuwa waje,suka rufa mata bata,haka ta keta tarin marasa lafiyan har zuwa bakin motarta. Sai data shiga sannan suka rufe mata motar,sukayi sallama suka juya, driver yaja motar suka bar gidan. Waya taci gaba dayi,kafin ta isa tana bada umarnin cewa a tsaida komai dake gudana cikin gidan,a shiga aikin tarbar professor da dukka abinda ya dace,gata nan a kan hanya. Kaltum na daga zaune,ko qwaqwwaran motsi ta gaza yi,hakanan takejin jikinta a mugun mace,ba abinda ke kai kawo a idanunta sai bayin Allan nan dake fama da lalurar tabin hankali,lokaci lokaci kuma fuskar waccar matar na dawo mata a kwanyarta,shin da wannan tsufar lalurar ta sameta?,ko kuma tun quruciya ne?,me yasa take tsare a nan?,ta fara samun sauqi shi yasa ba'a hadata da sauran ba ko kuwa?,duka ko daya cikin tarin tambayoyin nan bata da amsar kowacce. "Dakata" muryar mummy ta sauka a kunnen kaltume,baya driver ya tsaida motar ya kasheta,harma shi ya fice daga motar. A sanyaye ta tsaya daga qoqarin daukar mata jakar da takeyi "Kamar yadda na gaya miki,karki sake kada kuma ki yarda naji wata magana data danganci inda mukaje daga bakinki,kome kika ji ko kika gan,kiyi kamar baki ji ko bakiga komai ba,wannan ni shine doka da qa'idar xamana cikin gidan nan,kowa da kika ganshi akwai tashi dokar,toke taki kalar dokar kenan,kin fahimta?" Tun tasowarta tasan cewa biyayya ga uwar miji a tasu karkarar dolene,tunda itace mahaifiya ga mijinta,to binta ya zamar mata dole,kamar yadda zata bi wanda ya kawota gidan,don haka ta gyada mata kai gami da cewa "Eh in sha Allahu" saidai ta shiga cikin gida cike da saqe saqe,da kuma tuna tunane masu tarin yawa,tunani da hasashe masu toshe basira da qwaqwalwar mutum,duka kanta ya kwance,duka iya yanda taso ta dora lamarin bisa wani mizani da zatayi masa duba na tsanaki abun ya gagareta. A iya sani da ganinta,kai bama ita kadai ba,ganin dukka mai hankali,tattakin da mommy tayi aikine na alkhairi,wanda tasan mutane masu halin qwarai gami da dattako ke yin aiki irinsa,to amma me yasa batasan 'yar cikinta ma tasan taje wajen?,ko kuma wani zuhudu ne da gujewa riya?,wadda ke rusa aikin bawa?,tayi kuma tafiyar ruwa da dukka wani lada daya cancanci bawa ya samu?,ko ita take gudu?. Ta samu gidan kuwa ya dauki harama kamar yadda mummy ta bada umarni tun kafin isowarta,itama tana ji da daukar kanta a matsayin me aikine kamar yadda taji uwar mijinta na kiranta da wannan sunan da batasan daga ina ta samoshi ba,don haka ta shiga cikinsu,ta karba aikin biba,matar da take jinta tamkar mahaifiyarta,saboda sunan ummanta da take dashi,uwa uba kuma yadda ta damu da al'amuranta,take kuma kulawa da dukkan komai nata. Tana bala'inson ta shiga cikinsu ana aikin girki,tana matuqar qaruwa da abubuwa masu tarin yawa,wadanda batasan dasu ba a duniyarta sai a yanzu,duk da cewa wasu abubuwan da yawa idan aka dafa din bata iya ci,wani abun ma ko kwata ci ma batayi,sabida tana ganin bazai ciwu din ba,duk da yadda jawahir ke mata dariya gami da ciwon baki. *_7:00 pm_* Zaune yake cikin qawataccen falonsa,sanye da da jallabiyya ruwan makuba me santsi. Kallo daya zaka masa kasan cikakken dan boko ne kuma dan siyasa,wanda ya wadatu da ilimi da kuma gogayya ta sanin duniya. Daga gefansa najwa ce zaune,ya bata dukkan hankalinsa,da alama wata magana take dashi mai matuqar muhimmanci,saboda kana iya ganin yadda fuskarsa ta wadatu da murmushi. Dai dai sannan hajiya jidda ke shigowa falon,cikin kwalliyar wani dandaqeqen lace maroon,kai baka ce safiya bace,bayanta jawahir ce ita da kaltum,wadda jawahir din ta tada tun safiya kan zasu shiryawa daddyn abun kari,kasancewar jiya bai shigo gidan da wuri ba,so kusan dukkan abinda aka tanada masa ma bai sami ci ba ya kwanta saboda gajiya. Sallamarsu kawai ya amsa yana ci gaba da kallon su sanda suke shigowa,har fuskarsa ta fada kan baquwar fuskar kaltume. Saida jawahir ta aje farantinta ta gaida daddyn ta koma gefansa ta zaunsa sannan kaltume ta qaraso. Cikin nutsuwa da tsantsar ladabi,saboda duban da take masa na uba a idanunta ta duqa ta ajjiye kayan nata hannun,sannan ta zube har qasa tana gaidashi,saiya amsa yana dorawa da tambayar wacece?. Najwa daketa hararar kaltum kamar ta hadiyeta tayi saurin bashi amsa "Me aikin da ya samir ya kawo kace ya maidata kafin ka dawo" Gyara zamansa yayi sosai sanna ya dubi kaltum "Tashi kije" a sanyaye a kuma salube ta miqe ta fice daga falon,sai a sannan ya maida dubansa ga mummy,cikin yanayi na bacin rai yace "Ban gayawa samir ya maida yarinyar mutane ba kafin na dawo?,rainin dake tsakanina dashi har yakai na bashi umarni yaqi bi?" Cikin taushi bisa salo na kissa mummy tace "Kayi haquri professor,don Allah kada ka bari qaramin abu irin wannan ya bata ranka,abunda ka riga ka sanshi ne ka kuma saba dashi,meye baqo a halin samir a wajenka?" Banbarakwai maganar ta yiwa jawahir aka saita maida dubanta ga daddyn sanda yake cewa "Duk wani iskancin samir da daurin gindinki yake yinsa,rashin uwarsa a gidan nan ba hauka bane da zan dinga shinfida doka yana takewa,har ya zamana cewa qanwar bayansa ta zama kusan itace makwafinsa,tanayin fiye da abunda ya kamata ace shine yayishi,sannan kice naci gaba da qyaleshi jidda....to ya fara isata". Idanu mummyn ta lumshe kana ta bude cikin sakannin da basu wuce biyu ba,yayin da najwa ta saki wani boyayyen murmushi sannan tace "Kayi haquri daddy don Allah ka qyaleshi,amfanin haifar yara da yawa kenan,idan wannan bai share maka hawaye ba wancan sai ya share maka,pls ka manta dashi daddy,haka ya zabawa rayuwarsa" "Ke banson shirmen banza,waya sako bakinki a nan?,wa shin bama fita zakiyi ba?,tashi ki bama mutane waje" mummy ta fada cikin hade rai,don sam har yanzu najwa bata hau saiti yadda takeso ba,batason ta soko wani zancan daban "Bamu gama da daddy bafa" "Naji abinda kikace,anjima idan kin dawo zamu qarasa maganar,kafin lokacin nayi magana dashi" "To daddy" ta fada tana miqewa,fuskarta na nuna zallar annuri da farincikin data samu. "Daddy....don Allah kayi haquri ka fuskanci ya saraki,kome yayi saraki yayi idan ka tsaya ka duba sosai....yanayin abinda ya dace ne,kawai don dai baka fuskantarsa ne,amma yaya samir yana da zuciya me kyau......" "Wa yasa dake kema?,me yasa kuka son shiga maganar manya ne?,tashi ki bamu waje kema ko na sabar miki" mummy ta fada cikin hade rai tana duban jawahir,wadda ta tattabe fuska kamar zata saki kuka. Har ga Allah ta saba da kaltume adan taqin,tana fuskantarta irin fuskantar da 'yar uwarta ma bata taba yi mata irinta ba,tana fahimtarta sosai,tana zama ta saurari hirarrakinta wanda ko mummy bata samu wannan sakewar da ita ba,tana son zamanta tare dasu,saboda ta hangi tarin baiwa masu yawa tattare da ita "Um...um,qyaleta ta qarasa" professor ya samu kansa da fadin haka,najwa tafi kowa bin tsari da ra'ayinsa cikin gidan,amma kuma sau tari yakanji nutsuwa a zantukan jawahir,da kuma dadin saurare "Daddy kaltum bata da gata,yaya ya daukota ne don ta samu gata,ba shi ya gayamin ba,na fuskanci hakanne a hirarrakin da mukeyi da ita,da labaran da take bani,sunashan wahalar rayuwa abba,idan ka riqe kaltum lada zaka samu,ya samir bai bijirewa umarni da ra'ayinka ba,yasan tsarinka,bisa hakanne ma ya sanyani nake koya mata karatu,yanxu haka cikin satin nan zata zana placement zata tafi ss one" shuru yayi yana farfasa zantukan jawahir,shurun daya jefa hajiya jidda wani tunani na daban,ya akayi jawahir tasan dukka wannan ita tana zaune?,yayin da jawahir din kuma ya bata qwarin gwiwar bawa daddyn labarin yadda kaltumen ta iya zane abun mamaki,hakan yasa ma ta bata shawarar ta zabi fannin zane tun daga nan har zuwa gaba idan Allah yayi zata din. Nan ta zage tana bawa daddy labarin zanen datayi wanda ya bata mamaki sosai "Idan ka biyewa shirmen jawahir ba zaka ci komai ba prof,tashi ki tafi hirar ya isa haka,Allah ya bada lada" mummy ta fadi tana miqewa zuwa gaban kwanukan da suka ajjiye tun dazu. Kallon da mummy ke aike mata yasa ta miqe tana yiwa daddyn sai anjima zata kawo masa zanen. Murmushi ya saki "Duk da jawahir auta ce,amma tana da hangen nesa da nutsuwar da batayi kama data autoci ba" baki mummy ta tabe sanda take maida murfin tea flask din data zubawa daddyn zazzafan shayi. Cikin nutsuwa yake takowa zuwa cikin gidan,sanye da wasu blazers ruwan sararin samaniya,sunyi matuqar haskashi da qara masa kwarjini,jikinsa na fidda qamshin turarensa da koda yaushe,zatinsa na tsaho da murjajjen jiki ya fito sosai,hannunsa daya dauke da wasu takardu dake qunshe cikin files dinsu. Cikin lallausar muryarsa yayi sallama cikin falon,daga can inda take tsaye gaban katafaren teburin cin abincinsu da taje dinan kofunan da biban tace ta kawo ta jiyo kamar muryarsa,duk da bata tantanceta sosai ba,saita waiwaya a hankali tana amsawa. Amsawarta yaja hankalinsa yakai duba inda take,saita tako a hankali riqe da kofunan,ta iso gabansa ta durqusa qasa tana gaidashi,cikin yanayin kulawa yace "Lpy alhmdlh,ya karatun?" Dan murmusawa tayi kadan,karon farko da yaga fara'arta tunda yake ganinta "Alhamdulillahi" ta amsa masa "Ina jawahir" sai data kalla sashen dakinsu sannan tace "Tana ciki" "Kiramin ita" ya fada yana dan zama hannun kujera,tace to tana miqewa da hanzari. Da sallama ta tura qofar dakin,tsaye ta samu jawahir gaban tarin kayan shafarta,hannunta riqe da wata zungureriyar roba,ta amsa tana ajjiye robar. Tun kafin tace wani abu jawahir din ta soma magana "Fada kawai kikeso muyi dake kaltum,kayan nan har yanzu banga kina amfani dasu bafa,yanzu man wanke kan nan banga alamar kin taba amfani dashi ba" dan murmushi tayi,batasan me yasa ta damu da lamuranta da yawa haka ba "Kiyi haquri jawa,ki fara zuwa wajen....."sai kuma tayi shuru,don batasan da wanne suna zata kirashi ba,daga bisani ta yanke tayi kiransa da yaya kawai "Ok,ina zuwa" ta fada tana juyawa ta nufi qofa da sauri. Sai data fice itama tabi bayanta don kaiwa biba kofunan. Kamar ko yaushe ta gaida samir din cikin girmamawa,ya amsa mata shima cikin kulawa "Idan baki komai ki shiga ki gyaramin sashe na" "To yaya" ta amsa tana masar muqullin bangaren nasa,shi kuma ya wuce zuwa sassan daddy. Kitchen ta duba bata samu biba ba,saita wuce zuwa dakinta don ta gaya mata takai. A nutse ta daga labulen dakin,idanuwanta suka fara sauka kan biba dake tsaye riqe da wani dan qaramin hoto a hannunta,wanda bata iya hango wanda ke ciki saboda da kadan ya wuce girman passport. Sallamar kaltum yasa ta soma qoqarin boye hoton,a hankali ta qarasan gaban biban tana cewa "Nakai kofunan kitchen,amma saina taras bakya nan,nama wanke na mayar dasu inda suke" kai ta gyada mata ba tare da tace komai ba,sai kaltum ta lura da hawayen dake idanun biban da take qoqarin gogesu,cikin mutuwar jiki tace "Baki da lafiya ne?"kai ta gyada mata "Kaina ne yake dan ciwo kadan,shi yasa na taho na huta" duka sai kaltum taji babu dadi "Ayyah,sannu,Allah ya sawwaqe,gwara ki huta kam,Allah yasa kaffara" "Amin"ta amsa tana sake goge idanunta da kyau,tayi kamar zata zauna tare da ita,amma biban tace babu komai taje,itama yanzu zata fito,tunda ciwon ba sosai bane,bai matsa mata ba. *_SHIN KINSAN CEWA AKWAI RAMUWAR SALLA A KANKI ME JININ AL'ADA?_* ________________________________ *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar 43 Tsahon wasu mintuna yana duqe gaban daddyn bayan ya gaidashi ba tare daya maido masa amsar gaisuwarsa ba,kamar bazai amsa din ba,har sai daya gama kurbe baqin ruwan shayinsa sannan ya dubeshi "Sai yanzu ka damu dani daka ganni?,sai yanzu ka damu kasan lafiyata?" Ƙas yayi da kansa,don baisan da wanne yare zai wanke kansa ba,iya yinsa dukka yayi ya sameshi a waya amma abun yaci tura,baisan me yasa hakan ba "Duk dai tsiya baka da mahaifi sama dani,kuma ba'a cazawa tuwo suna ko?" "Tuba nake" ya fada cikin ladabtacciyar murya,yana zaune har daddyn ya qarashi fadansa yadda ransa yayi masa,duk da qoqarin dakatar dashi da mummy keta yi,saiya hada harda itama cikin fadan. Sai daya tabbatar ya gama sannan ya sake gaidashin,ya amsa sama sama,sai ya miqe ya lalubi kujera ya zauna bayan ya aje masa file din hannunsa a gabansa "Wannan file din dukka lissafinmu na qarshen shekara ne da dukka bayanan komai da komai,zaka sanya hannu ne asanya cikin documents na kamfani". Baiko daga kai ya duba file din ba,yana zuba wani ruwan tea din a kofi yace "Ka dauka ka baiwa fawwaz ya duba ya sanya hannu" Banbarakwai yaji lamarin,ta yaya fawwaz zai shiga cikin lamari irin wannan?,ta yaya babban sirri irin wannan zaice a baiwa fawwaz din ya saka hannu?,bayan abune daya shafi daddyn?,share dinsu ne shi dashi,me ya shafi fawwaz banda yayi aiki a biyasa kowanne wata kamar kowanne ma'aikaci,ya zaci zaiji mummy tace wani abu,amma baiji tace komai ba,saiya dauke idanunsa daga kan file din zuwa fuskar daddyn "Amma kamar ba hurumin fawwaz bane,wannan abune daya shafi masu share a kamfani" "Kudin waye?" Daddyn ya fada kansa tsaye yana duban qwayar idanun samir "Naka ne,Allah ya huci zuciyarka" saiya miqe ya qarasa inda ya ajjiye file din ya dauke "A huta lafiya" ya fada yana nufar qofa "Son,yau da wuri haka?,abincin fa?" "Zanci a waje mummy" "Jirani,ko wani abun sassauqa a hada maka ka tafi dashi" ta fada tana miqewa da hanzari. Hannu tasa ta amshi packaging da tasa aka yiwa samir din tana miqa masa "Kaga bance komai ba kan batun bawa fawwaz file ya saka hannu ba ko?" Tayi tambayar tana miqa masa,yasa hannu ya karba ba tare da yace komai ba,tasan kuma zaiyi wuya yace din,don ta karanci fushinsa da bacin ransa fiye da kowa "Kayi haquri son,daddynka ya fara zargar goya maka baya akan komai,banason wannan rashin jituwar dake tsakaninku taci gaba da dorewa,gudun kada takai har kan 'ya'yanka,shi yasa na yanke shawarar yin shuru kan wasu abubuwan,badon inason hakan ba,sai don babu yadda zanyi" kai kawai ya gyada mata yana lumshe ido,tare da qoqarin hadiye bacin ransa,saiya juya zai soma barin wajen,tayi hanzarin sake tsaidashi,tana ganin wannan wata dama ce gareta daya kamata tayi amfani da ita. "Son" ta sake kiransa,saiya dakata ya kuma waiwayo,takawa tayi zuwa inda yake tsayen da kanta,fuskarta na nuna russuna da kuma alhini. Dukka nutsuwarta ta tattaro tana dubansa,irin duban da zai gaya masa cewa dukka zancan da zata furta na gaske ne,shima ita yake kallo,da alamu kuma ya tattara mata dukkan hankalinsa ita yake sauraro "Akwai abu guda daya da mahaifinka yake ra'ayi da kuma buri,wanda aikatashi zai zama silar warwarewa,dama dawowar dukkan wata fahimta da jituwa a tsakaninku" shuru ta danyi kafin taci gaba "Mahaifinka bashi da burin daya wuce ka auri jauhar 'yar abokinsa,me zai hana ka sadaukar da wannan farincikin zuwa gareshi?,ina da tabbacin hakan zai sake kawo qauna da jituwa tsakaninku.....amma kaje kayi tunani,burin kowanne da ya samu qauna da kulawa ta mahaifinsa,kana da wannan damar" Zaman irin na dirshan tayi gaban professor,irin xaman da idan tayi shi yasan tabbas akwai babbar magana da takeson yi dashi,idanunta cikin nasa,cikin wani laushi ta soma magana dashi "Ko kusa ko alama bana jin dadin irin wannan mu'amalar dake gudana tsakaninka da samir,raina baya min dadi sam,ko babu komai kusan nice a tsakaninku,kuma samir tamkar dan dana haifa nake jinsa,kaga kuwa ko meye zaya sameshi hakan bazai taba yimin dadi ba" Sosai yake kallonta,yake kuma yaba kyan hali dana zuciya irin nata,tsahon shekarun ko sau daya bai taba ganin ra kwarewa samir baya ba,komai wuya kome dadi tana a gefansa,saiya zauna sosai ya gyara zamansa "Babu abinda yake hadani da danki illa taurin kai da kafiya,da kuma ganin ko meye ta yankema rayuwarshi nashi shine dai dai,kome na yanke a rayuwarsa yana kallons a matsayin opposition na ra'ayinsa,ni kuma bazan zauna yana yankamin da gindayamin dukka sharudda da yaso ya kuma ga dama ba,don bashi ya haifeni ba,nine na haifeshi" shuru tayi bayan ta sauke ajiyar zuciya ta dago ta kalli professor "Babu abinda yake zama cikasa hankali da kamalar dan adam irin aure,koda kuwa nutsuwarsa ake da buqata,tofa la shakka aure shike gyara mutum....inajin option daya kuma hope daya muke dashi akan samir....shine aure,aure ya kamata kayi masa" Hannuwansa ya wara kafin ya maida bayansa ya jinginar a jikin kujera "Ya isa ya yiwa kansa aure ai,ni meye nawa a ciki?" Kai ta jinjina wani abu na taso mata tana danneshi,tana tuna wani abu daua faru shekarun baya da suka shude,wata magana shigen wannan data taba faruwa,ba shakka duk inda take tunanin nasararta bata kai ba tama shallake nan,saidai a yanzu kuma ba irin wannan amsar take buqata daga bakin daddyn ba,tana so ne ya shiga lamarin tsundum fiye da kowa. Kanta take kada masa kafin ta sake cewa "A'ah,daddy wannan sam ba kalmar data dace ta fito daga bakinka bace,kanason ka sake jawomin sabuwar tsana daga mutane ire iren hajiya qarama?,wannan aikinka ne,dole ka sanya hannu,koda kuwa shine abu na qarshe da zaka yiwa danka,ba'a sakarwa yaro garma" saita dakata tana karantar yanayin fuskarsa na wasu sakanni kafin yace "Kin fiya damuwa da lamuran samir da yawa....." "Wa nake dashi sama dashi?" Ta tari numfashinsa fuskarta dauke da murmushi,sai yayi shuru ya zuba mata idanu,tana sake burgeshi,tare da sake jinjina mata,yana ji a ransa lallai ta cika macen qwarai,duk da har yanzu yana jin wani emptiness can qasan zuciyarsa,wanda har yau wannan gurbin ya gaza cikuwa. "Daddy,duk da samir ya haura shekara talatin....amma ni har yanzu kallon yaro.nake masa,kamar yadda kowa ya sani,yaro baya taba girma a wajen iyayensa koda kuwa furfura gareshi,matuqar suna raye,har abada kallon yaro suke masa.....yaronmu Allah ya masa baiwar arziqi da daukaka,ba za'a rasa tarin 'yammatan dake son shiga rayuwarsa ba,wanda da yawansu wala'alla ba don Allah suke sonsa ba,so abinda na hango anan shine......ka zaba masa mata ka aurar dashi,matar da kasan ta dace dashi,yar asali kamarsa,yar gidan arixiqi,ga misali jauhar......har yanzu ita da iyayenta suna nan akan bakan son bawa diyarsu samir din" kai daddy yake jinjinawa,ba shakka tayi zurfin tunani da kuma hange,kuma maganarta na bisa turba,mahaifin jauhar kusan abokinsa ne na kusa,tare suke gudanar da duk wata harka ta siyasarsu,hakanan mahaifiyarta akwai qawance mai qarfi kuma dadadde tsakaninta ta da mummyn?,to me yayi saura? "Na yarda dake,nasan zaki iya komai,na baki wuqa da nama akan lamarin" qasaitaccen murmushi ya subucema mummyn,tuni ta soma hango nasara ruwa ruwa,saita gyada kai cikin salo tace "Na gode qwarai da gaske mijina da wannan babban matsayi daka bani"murmushi kawai ya mata yana ji a ransa inama inama?........ Wadan nan kalaman na mommy sune sukayi ma samir qawanya,suka dinga kai kawo a kwanyarsa,har zuwa sanda yakai office. Ringing din da wayarsa keta faman yi sai yakejin kamar ana yamutsa kwanyarsa ne,bashi da mafita illa ya daga wayar,saiya miqa hannu ya dauka ya kuma kara a kunnensa. Sallama yayi cikin muryarsa da tayi sanyi,daga can daya bangaren aka saki ajiyar zuciya sannan aka amsa. Cikin nutsuwa aka fara gaidashi,ya amsa yana Allah Allah yaji saqo ko dalilin da yasa aka kirashin "Mubina ce,kira nayi dama nayi maka godiya kan dawainiyar da kuka yimin" sam bai gane wace ba,a yanzu kuma qwaqwalwarsa babu wani space da xai iya tuna wace ita "Ok yayi kyau" kawai ya amsa,yana qoqarin ajjiye wayar,kamar ta karanci hakan saitayi hanzarin cewa "Kamar baka gane wace ba,mubina da kuka kai clinic kai da abokinka da daddare" "Oh....ok,sannu,ya kike?" wannan tambayar da yayi mata ji tayi kamar ya mata wata babbar kyauta,saita gyara kwanciyarta dadi na ratsata "Alhmdlh,nama samu sauqi" "Ma sha Allah,haka akeso" ya fada yana fitiwa daga motar,sannan ya dora da cewa "A gaida mutanen gidan" ya katse wayar yana sanyata a aljihunsa. Sama sama ya gaisa da ma'aikatan yakai kanshi office dinsa,iska me zafi ya furzar sanda yake zama saman kujerarsa,tsahon wasu sakanni yana qoqarin saisaita tunanukan da suka cuse masa kwanya,kafin ya dauki wayar tafi da gidanka yayi kira daga can reception kan shaidawa fawwaz yana nemansa,yaci gaba da juyawa saman kujerarsa a hankali a hankali. Minti goma aka shaida masa isowar fawwaz,aka bashi izinin shigowa. Kan idanunsa qofar ta bude,fawwaz din ya shigo,yana takawa dai dai idanunsa saman fuskar samir,kamar yadda Shima Samir din shi yake kallo,da wani irin kallo dake nuna zallar kwarjini qasaita da kuma isarsa. Tsaye yayi gaban table din samir din,a hankali saraki ya janyo file din gabansa ya turashi gaban fawwaz,idanuwansa tsakiyar na fawwaz din yace masa "Ka saka hannu on behalf of daddy,but.....karka fita dashi out of company,kayi singing a nan ka dawo dashi" daga haka ya tura kujerarsa baya yamiqe a hankali ya murda qofar toilet ya shiga,saboda lokacin sallar walha yayi,yana kuma saka ran zuwan amiru,akwai abubuwa da yawa da yakeso su tattauna. *_SANNU SANNU KWANA NESA_* Ta farat daya kamar a mafarki ta soma tsintar sauye sauye kala daban daban daga rayuwarta,sauyin da iyaka kaifin tunani da basirarta basu taba kawo mata su ba. Cikin watanni qalilan saiga kaltume ta soma sauyawa,tun daga suna daya koma kulsum ahmad zuwa yanayin fatarta,murjewar jikinta da kuma gashinta da ayanzu take kallonsa kamar ba nata ba,kamar na kanti ne aka aro aka dora mata,tun daga ranar da jawahir ta turketa ta sakata ta tsefeshi,ta wanke mata shi tas,sannan ta kwasheta zuwa wanki da gyaran gashi,saiga tsahon cukurkudadden gashinta yana neman ninka tsahonsa na asali,abinda ya sanyata ita kanta a zallar mamaki. Tsaye najwa tayi a kanta kan duk wani amfani data siyo saboda ita,tace sam ba zata yarda ta fito daga gidan professor rashid ba a dinga ganinta a haka ana rainata ba,hakan kamar ci baya ne da koma baya ga sunan gidansu,saboda sunan ba boyayyen suna bane,duk kuwa da cewa da sunan mahaifinta take amfani,amma dole wataran a gane daga inda ta fito. Sannu a hankali zama da gogayya tasa ta soma sauya abubuwa da yawa,rayuwarta ta fara sauyawa zuwa daga kattume zuwa wata kulsum,'yar makaranta,mai ilimi,ba kaltumen qauyen dinya ba. Daga gefe guda kuma hazaqarta tsafa da rashin quiya saiya sanya ta zama kusan kome na gidan ana sanyata ciki,ko kadan bata taba kawowa ranta komai ba,hakan ma dadi yake mata,a qalla ta zama busy sosai,tunda ta fuskanci babu xancan zuwa ko komawarta gida,saita watsar da komai ta fuskanci gobenta,ta fara kwasar gardin ilimi,takan mata kwata kwata da cewa wai aure ne tsakaninta da samir,don ba wani haduwa sukeyi dashi ba sosai,mutum ne me yawan aiki da sabgogi,wanda mafi yawanci yana fita ne da safe,dawowarsa kuwa sai bayan sallar magarib. Ta fannin daddy kuwa yana daukarta ne kamar jawahir,musamman saboda shaquwar dake tsakaninta da jawahir din,saiya sanya kome zatayi tana sanyo kaltum din a ciki,duk kuwa da irin kallon banza kyara da kuma hantara da take samu daga najwa,hakan baisa ta sare ba,dole take dauke kai daga dukkan wasu halayya da dabi'u na najwan,wanda ta sani,inda ta sameta a matsayin kattume ne a qauye,bata isa tayi mata irin wadan nan abubuwan ba,koma meye tana daukarsa da sauqi,saboda bata taba sanya iyayenta a ciki ba. Sannu a hankali rayuwar taci gaba da jujjuyawa,cikin watanni ta gama ss one ta tafi ss two,babu jimawa kuma aka fara batun zana qualifying. Batasan yadda abun yake ba,don haka hankalinta ya dugunzuma,tayita fargaba,tana tsoron kada ta fadi ta jawa samir din daya tsaya da aljihunsa yana biya mata kudin makaranta da dukka sauran buqatunta,zataji kunya matuqa idan hakan ta faru,ba kuma zata yafewa kanta ba. Sanda take gayawa jawahir haka dariya ta dingayi mata "Babu fa komai kaltum,ba wata jarabawa bace ta tashin hankali ba, infact ma idan bakici ba za'a biya miki ne shikenan an wuce wajen" kai ta kada "A'ah,nifa nafison na ciyo da kaina,hakan nasan dole zaifi faranta masa akan abiyamin,xaifi kuma yarda da cewa ba asarar kudinsa yake yi ba" "Kaltum....wannan idan kika tafi University sai kuma yaya kenan?" Murmushi ne ya subuce mata,ta riqe matashin kujerar da suke kai sosai "Wayyo Allah na,ranar bazan iya bacci ba" "A gidan ubanwa zata University din?,badai a gidan nan ba,taimakon ma da akayi mata aka fiddata daga duhun jahilci da kantar qauyanci ai ya isa,amma muje University itama taje?,babu wannan maganar,gwara ma ki shiga hankalinki ki daina kwadaita mata abinda bazai yiwu ba,ko ta fidda miji dai dai ita tayi aure,ko kuma ungulu ta koma gidanta na tsamiya" najwa dake nutse cikin daya daga cikin lausasan kujerun falon riqe da remote na tv ta fada,tana gyara zaman gilashin fuskarta. Sosai bacin rai ya bayyana kan fuskar jawahir,yayin da kaltum tayi qas da kanta,dadin hira da jawahir yasa ta manta gaban waye take magana,ta kuma so manta ita din wace,wanda kullum takewa kanta tilawar daga inda ta fito,kada ta sauya hanya kota manta asalin nata,abunda ba zata taba iya yafewa kanta ba kenan idan ta bari hakan ta faru. Miqewa kawai jawahir tayi ta kama hannun kaltum tana cewa "Muje ciki saimu qarasa hirarmu" "Cikinki xaki maidata ba daki ba,banza local kawai" najwa ta fada,ko waiwayowa ta dubeta jawahir batayi ba suka shige ta gabanta. "Karki damu da maganar ya najwa pls katum" murmushin qarfin hali tayi,duk don ta kauda bacin ran data gani saman fuskar jawahir "Kin manta hali da dabi'arta ba baqona bane?, don't bother,babu komai fa" murmushin turancin da kaltum din ta jefo ta saki,tana ganin qoqarinta matuqa da gaske, gifted ce irin wadda ta jima bataga kamarta ba,bata taba tunanin zatayi catching up har haka ba,duk da cewa sanda ta gayawa ya saraki tana da hope sosai a kanta,sai gashi ta tabbatar mata da hakan "Bari na duba ko bibi ta gama tuwon nan na karbo" "Baza dai ki manta ba" tasan me take magana a kai,sai tayi murmushi "Gado ai sai dan gado,kowa yabar gida gida ya barshi" kai ta jinjina ta bita da murmushi harta fice,saita zauna gefan gado tana wani nazari,itakam ba zata iya tuna lokaci na qarshe da mummy ta kaisu sukaga nata dangin ba,duk wannan tarin alkhairin nata bata ce ga wani nata na kusa da yake amfana ba,tana tsananin mamakin hakan,tayi mata magana tayi qorafi da mita har kamar bakinta yayi ciwo,takan ce musu garinne yayi nisa,tanason kuma ta shirya sosai kafin suje,sanda suna qanana wai basa daukan dogon lokaci basu je ba,najwa tace ita takan tuna sanda suke zuwa din,amma ba sosai ba sabida abun ya danyi nisa,yanzu ne dai da abubuwa sukayi yawa a cewar mummyn zuwan ya gagara,ta rasa gane wane irin shiri ne wannan,amma takan baiwa faruwar hakan uzurin cewa don dai mahaifi da mahaifiyarta sun rasu ne. Da sallama ta shiga dakin biban,saita amsa mata tana qoqarin boye takardar dake hannunta,a lokaci guda kuma tana yunqurin goge hawayen daya jiqa mata fuska. Sosai jikin kaltume yayi sanyi fiye da ko yaushe,wannan kusan shine karo na uku data taba riskar bibi a irin wannan yanayin,saidai kullum amsa daya take bata "Yar uwarta data rasu take tunawa" "Kin biyo sahun tuwonki ko?" Bibin ta fada tana dora murmushi kan fuskarta,kai ta daga mata a sanyaye "Muje na baki,nima jira nakeyi nayi sallar magariba tukunna kafin naci" ta fada tana sake goge fuskarta da habar zaninta tana yin gaba. Har ta kusa fita saita dakata,ta waiwayo tana duban kaltume "Kada ki sake ki shaidawa kowa yanayin da kike shigowa kina samuna a ciki har karo na uku,yin hakan zai iya zamewa rayuwarki hadari" bibi ta fada muryarta nayin rauni,tana kuma girgixawa kaltum kai alamun tabbatarwa 44 *_Daure ki biya ki karanta cikin aminci ba tare da kinci haqqin da ba naki ba,ki tuntubemu ta wadan nan numbers din_* 08184017082 Ko kuma 09134848107 ________________________________ Gudun zuciyarta ne ya qaru sosai,ta zubawa biba idanu tana kallonta tare da son gano abinda take fada,kawai don ta fadi cewa ta ganta tana kuka hakan saiya zama barazana ga rayuwarta,ta buda baki a hankali da niyyar yin magana biban ta rigata "Kada kice zaki tambayeni komai,domin yin hakan shima qarin hadarine ga rayuwar dukkaninmu,kiyi haquri kattume,ba daga ni bane,na daga gareni bane" daga haka ta saka kanta waje da sauri,da alama wani abun ya sake taba zuciyarta ya kuma raunatata. Kusan a kidime ta shiga daki,amma saita taras da jawahir tana rolling mayafinta a ka gaban mudubi,bata juyo ta dubeta ba tace "Ki shirya zamu raka ya saraki gidan hajiya qarama,dama baki taba zuwa ba" a salube ta isa bakin gado ta zauna idanuwanta akan jawahir,saidai tunaninta yayi nisa da nan "Anya ko jawa?,kice dai ina gaisheta idan kunje,wataran saiki rakani naje na gaisheta" barin abinda tayi ta juyo tana duban kaltum "Hajiya qarama fa?,maman ya Aamiru?,qanwar daddy,bashi da 'yar uwa a duniya sama da ita" yanayin yadda ta mata bayanin ya nuna tana son nuna mata muhimmancin hajiyan a wajensu ne,saboda haka saita miqe kawai ta jaqo hijabinta ta zura "Dakata,wallahi kaltum kina da maida bara bana" fa fada tana zaro mata kaya cikin kayan sawarta,ta feshe da turare da kyau sannan ta miqa mata su "Saka wadan nan,ni bakiga sai dana canza ba" kanta a cake yake,don haka bata ce mata komai ba ta saka din. A tamface mai manyan zane da kaloli masu kyau a jiki,wanda suka haska baqar fatarta,wadda a hankali ta soma rikidewa zuwa kalar wankan tarwada,kala mai bala'in kyau da daukan hankali,batasan kalae fatar nata na canzawa ba saida taji daga bakin jawahir,don ita din ba kallon mudubi ta cikayi ba,takance me zata kalla a fuskar tata?. Dukka idanunta mummy ta zuba mata sanda take shaida mata zasu gidan hajiya qarama,ta jinjina kanta a hankali "Saikun dawo,kice ina gaisheta da kyau" ta fada tana miqa mata wani kwalin turare mai guda uku a ciki,mai tsadar gaske ne sosai,zuwanta dubai ta siyoshi,ta karba tana juyawa ta fice da sauri,da alama tafiyar tana mata dadi. "Kin tsani zaman front seat,yau kam a nan zaki zauna" jawahir ta fada tana mata dariya bayan ta bude mata gidan gaban,kwanyarta cike take da kalamai da tunanin maganganun biba,don haka komai akace kawai yi take,saita shige a hankali ba tare data cewa jawahir komai ba,ta kwashe qafafunta zuwa cikin motar tana shirin jan qofar,qamshin lalausan turarensa tare da sanyin ac yana shige mata hanci. A hankali ta waiwaya ta dubeshi sanda yake qoqarin aje wayar hannunsa da sauran tarkacensa a tsakiyarsu,wani irin takura da nauyinsa takeji,kusancin dake tsakaninsu takejin kamar yayi yawa,tana jinsu very close da juna "Ina yini?" Ta gaidashi tana dan rusunar da kanta saboda nuna girmamawa,sabida yau gaba daya basu hadu ba. Kansa ya dago da niyyar amsa gaisuwar,sai idanunsa suka fada fada cikin nata,ya janye qwayar idon nasa a hakali,fuskaraa kadaram kadaham kamar yadda suka saba ya amsa mata tare da dora fadin "Kina lpy?" Sanda yake yunqurin daura seat belt dinsa "Alhamdulillah" ta amsa masa itama kamar kullum,tana jin lallausan muryarsa mai dauke da wani heaviness irin na mazantaka can cikin kunnenta sanda ya furta bismillah ya kuma tayar da motar. Lafewa tayi sosai cikin kujera sanda suke tafiyar,rabin hankalinta naga tunani,yayin da lokaci lokaci kuma hankalinta ke kaiwa ga hirarsu,musamman idan jawahir din ta sanyota a ciki. Sun danyi nisa ya faka a store din daya saba yiwa hajiyan siyayya,ya dubi jawahir "Muje ki rakani" ta amsa masa tana bude murfin motar,tare da cewa kaltum itama ta fito "Zan zauna a nan kuje ku dawo" ta fada da wani irin sanyi da take jinsa har qashinta "Ya kayi mata magana,ai tare zamu shiga ko?" Kai ya gyada yana duban kaltume din kadan kafin kuma ya soma yin gaba,dole ta zuro qafafunta ta fito tunda ta sakashi cikin maganar. Waje ta samu ta jira jawahir ta gama daukan komai,don dama samir din daga can wajen biyan kudi yayi tsaye yana jiranta yana duba wasu roll on da deodorant. Kwandon hannunta shaqe da kaya tace "Muje kaltum" bayanta tabi,ta kuma yi tsaye dai a bayanta wajen biyan kudin,ba kowa saman seat din masu karbar kudin,sai sun dan jira kadan,saboda zagayawa da yayi bayan ya nema afuwarsu. "Me zakiyi da wannan haka?" Tambayar da samir yayiwa jawahir,murya qasa qasa saidai ta yadda zaiji tace "Kaltum na siyawa,waifa bata fara sawa ba yaya har yanzu" a hankali ya juya inda kaltume ke tsaye yana dubanta,ya tuna watannin baya,ganin da yai mata tsaye cikin dandali,tabbas bata isa fara sakawar ba,saiya sauke idanuwansa tun daga qasan qafafunta har zuwa muhallin da aka siyawa abar,zuwa yanzu bambancin kadanne da yadda ya gani a baya "Kuma wallahi yaya ashe qarya takemin,nina gani kunyar sawa kawai take" maganar data dawo da kaltum hayyacinta kenan,takai dubanta kan kwandon da jawahir ta zuba siyayyar a ciki,me zata gani?. Brassier ce kusan dozen guda,idanuwanta a warwaje taso maidasu ga jawahir sai suka hada ido da samir,kamar zata nutse a qasa haka taji sanda ta fuskanci kallonta yake saita jingina da kantar kusa da ita da sauri sanda shi kuma ya dauke idanunsa,yayi ma kamar babu abinda ya faru ya maida hankalinsa ga me karbar kudi sanda yake dawowa wajen. Harara ta jefi jawahir dashi sanda take mata dariya qasa qasa,ita babu abinda ya shalleta da alama,mamakin jawahir din take,ta yadda batajin nauyi da kunyarsa take gaya masa wannan maganar,duk da tasan halinta dama faranse ce ita,amma ta sanyata jin wata iriyar kunya,wadda ta hanata sakewa har suka isa gidan hajiya qarama. A falo suka taddata tana zaune tana kallon tafsirin sheik Dr Bashir Usman,gefanta lemo ne da cake a ajjiye,da alama ta fara ci ta ajene. Da hanzari jawahir ta isa gareta ta zube a cinyoyinta,itama tana dariya ta dora tafin hannunta a gadon bayan jawahir din tana murmushi da murnar ganinta. A nutse kaltum dake dauke da ledar siyayyar hajiyan tayi sallama a falon,sallamar data ja hankalin hajiyan,ta dago tana amsawa tare da zubawa kaltum idanu harta qaraso,ta zube ledojin a hankali sannan ta zauna ta soma gaida hajiyan. A nutse cikin yanayi na karantar dan adam ta amsa,sannan ta sake maida kanta ga jawahir kafin samir ya shigo. Yadda shima ta amsa sallamarsa zuwa gaisuwarsa zai tabbatar maka da cewa ba qaramar qauna bace tsakaninsu shida ita da jawahir din "Ina waccar mai baqin halin?" Hajiyan ta fada sanda take miqewa zata kawo musu wani abun su taba,saidai da qyar ta miqe din saboda ciwon dake qafarta,kusan kuma shine silar zuwansu gidan su dubata. "Tana gida hajiya,kema kinsan bazata zo ba" "Nima bana gayyarta,randa duk taga dama tazo,bari na kawo muku abun sha" sai tayi hanyar kitchen,kaltum ta bita da kallo,wani abu na taba ranta,tana tuna mata da ummanta da nata ciwon dake qafarta,saita lumshe idanunta,tana sauke qaramae ajiyar zuciya. Batafi minti daya ba ta dawo "Yau ni nake ganin rayuwa a gidan nan,masu aiki biyu amma babu ko daya a ciki?,dambu fa nace ayi an hada komai amma ya gagara gasucan zube a kitchen?,ke jawahir duba store ki debo muku ruwa da lemo,na fridge dinma ya qare an rasa me zubawa,nikam qafa ta matsamin,bazan iya ba,inajin masu aikin da naqi dai su za'a qaromin din" ta fada tana zama,sai jawahir ta miqe tana cewa kaltum tazo suje,suka miqe dai dai sanda samir ke gyara zamansa yana tambayar hajiyan ina duka 'yan aikin,ya za'ayi a barta haka ita kadai a irin wannan yanayin. "Baraka dama ta tafi gida tun sheran jiya,ita kuma hansai zata dora girkin kenan akayi kiranta surukarta nakan gwiwa" Kitchen ne me kyau da tsari sosai,kai baka ce kitchen din babbar mace bane kamar hajiya qaraman. Tsaye tayi daga kitchen din tana dan kallonsa kallo irin na baqunta,jawahir kuma ta shiga ciki tana debo lemukan "Zo mu wuce,wadan nan ai sun isa" tace da kaltume "Jeki kai musu mu dawo nan mu zauna,wala'alla magana zasuyi da ita mu basu waje" "A nan kuma?,ai akwai wani parlour din,saimu koma ciki" kai ta kada "Kije dai ki dawo" tunda ta fadi haka tasan da dalili,saboda haka bata sake musa mata ba ta fice,babu jimawa ta dawo "Tana da couse couse?" Kaltum ta tambayi jawahir "Eh ba za'a rasa ba" saita gyada kai "Dauko ko guda dayane na gwada wani ganganci mu gani,naga yana kama da barjajjiyar shinkafa da kuma tsakin masara,ko zaiyi mata dambun" "Yes,correct.....dama anyin dambun couse couse din ai" jawahir ta fada tana murmushi,sannan ta ake shiga store din hajiyan ta soma laluboshu,babu jimawa ta fito dauke dashi guda biyun ta miqawa kaltum,ta karba ra durfafi inda taga an ajjiye duka kayan hadin ta janyo roba ta fara aikin. A hankali ta dinga aiki da hankalinta da kuma hasashe na yadda take musu dambu a gida,tanayi tana fagabar kada yaqiyi tunda wannan din ba tsakin masara bane,bayan ta hada komai sukayi tsaye a kitchen din jawahir na mata hira,saidai ita hankalinta duka nakan girkin,da kuma kasadar da tayi daga zuwanta baqon waje,yanzu idan ya lalace baiyi bafa me zatace?. A hankali ya soma fidda qamshi sosai,qamshin daya cika kitchen din gaba daya,mintunan data bashi kuwa na cika ta duba,saita kira jawahir tazo ta dandana. Lomar farko ta fiddo idanunta waje "Wow...wow, you make it kaltum....."sai data sake kai hannu ta debo takai bakinta sannan ta sake cewa "Kinji dan ubansun dadin da yayi kaltum,ya akayi kika iya har haka?" Murmushi kawai tayi mata tana zaro plate guda biyu,ta cikasu dashi,jawahir ta riqe hannunta "Haba malama,ya zaki kwashe?,mu kuma fa?" "Hajiya iya da saura ai,ba duka na debe ba" kaltum ta fada tana mata dariya "Kikai musu saiki dawo kici" ta fada tana tura mata farantan. "Wai nikam qamshin girki fa nakeji,ko hancina ne saboda yunwar da nakeji?" Hajiya qarama ra fada bayan ta dakata daga maganar da sukeyi "Qamshin abinci ne,amma ina zaton iskar kitchen ke kadowa ko,bari na fita nan kusa daku akwai eatery na samo miki wani abun da zakici,kafin a san wadda za'a kawo miki ta zauna miki kafin masu aikin naki su dawo" yana fadin hakanne dai dai sanda jawahir ta fito da plates din a hannunta fuskarta fal fara'a. Da kallo suka bita har ta iso gabansu,ta ajjiyewa kowa plate din sannan ta bude masa ta sanya masa spoon "Kuci kuji don Allah" ta fada tana dubansu,duban plate din sukayi hajiya tace "Meye wannan ne kamar dambu" "Kici don Allah hajiya.... please yaya kada kace ka qoshi" ta fada tana marairaice masa,basu sake cewa komai ba kowa ya dauki nasa cokalin. "La'ilaha illallahu....wai dambu kukayi haka a dan wannan lokacin me shegen dadi?" Dariya ta qwacewa jawahir,kafin ta dakata "Hajiya dambun couse couse ne fa?" Idanu hajiyan ta fitar "Couse couse dai da nake kallonshi a abun banza shine haka?" Dariya ta basu harda samir daya dan murmusa,dadin abincin shima yana ratsashi,duk da dama shi cimarsa ce couse couse,musamman da vegetable soup liver or kidney soups "Wallahi hajiya aikin kaltum ne,ni kaina abun ya bani mamaki" "Ikon Allah,wannan yarinyar dai da kuka shigo tare?" Hajiyan ta fada tana fara kai lomomi bakinta,gardin gyada dana zogale gami da wadatacciyar albasa da kayan dandano na hadewa a bakinta "Ita" "Ina kuka samota ne?" "Na daukota ne daga garinsu" samir ya bawa hajiyan amsa sanda jawahir ke niyyar bude baki tace 'yar aiki ce,kai hajiyan ta kada tana ci gaba da kaiwa cikinta abincin. Ganin hajiyan ta nutsu da abincin,saita juya ta koma kitchen wajen kaltum don bata labarin yadda ta kaya tana dariyar yadda taga hajiyan na cafkar dambun babu qaqqautawa. Tana mamakin ta yadda aka sarrafa couse couse haka aka baddan masa da kama. Tana dab da cinyewa suka fito daga kitchen din,hajiyan ta daga kai tana kallon "Sannu 'yar nan,sannu da aiki kinji?" Murmushi kawai ta saka,ta qarasa tana daukowa hajiyan ruwan da take yunqurin daukowa hannunta baikai ba,ta bude mata ta miqa mata "Aini mamaki ne ya kamani,kin samu ladana ba kadan ba" murmushi ta sakeyi tana samun gefe kusa da jawahir ta zauna "Allah yayi albarka" "Amin" ta amsa da muryarta qasa qasa,yayin data maida hankalinta ga jawahir dake nuna mata wata drama da ake nunawa. "Yauwa....yanzu sai nafi fuskantarka,me kake cewa?" Tafin hannunsa yasa ya shafi sumar kansa "Ba wani magana bane dama,yarinyar da xan aura ne muka daidaita kanmu,so inason shaidawa daddy,nayi magana da mummy sai tace na gaya miki,saiki gaya masa" bakinta ta tabe,kana ta dubi inda su jawahir take,sam hankalinsu baya wajen "Waini za'a yiwa bariki,da ta zartar kawai ai yadda ta saba....wacece ita ya sunanta?" "Jauhar ce"ya amsata a nutse bayan yin shuru na 'ya sakanni,tsareshi tayi sosai da idanu "Jauhar dai,yar wajen murjana?" Ta tambayeshi tana tattara hankalinta a kansa Kansa ya jinjina mata yana kallonta,saita hade ranta tsaf "Eh lallai....jidda taci alwashin daga qarshen rauwarka ma kenan itace zata zaba maka mata,to ba zata sabu ba,tunda shi yayan ya zama sai yadda aka juyashi,wannan wacce irin masifa ce ke bibiyar rayuwar raihana har yanzu bata huta ba?" Idanunsa ya lumshe yana jin sunan har tsakiyar zuciyarsa,yana kuma jin wani abu me daci yana motsa masa,cikin muryarsan nan me cike da nutsuwa yace "A'ah hajiya...,.ki fahimta mana,babu ruwan mummy a wannan maganar,amma idan baki gamsu ba kina iya tuntubar daddy da kanki" shuru hajiya qaramar tayi tana kuma karantar fuskar samir dake kallonta shima,tsahon wasu sakanni kafin ta gyada kai "Shikenan tunda har kace haka....idan akwai alkhairi cikin lamarin Allah ya tabbatar,idan kuma babu alkhairi....ina roqon Allah ya watsa abun,ammafa ka sani,wannan ba yana nufin na gamsu duka bane na miqa wuya,daga yanzu zuwa ko yaushe ma,idan na gani ko.naji abinda baiyimin ba,to tabbas babu abinda zai hana a fasa ko a dakatar da komai" kansa kawai ya gyadawa hajiyan,har yanzu baisan me yasa ta kasa so ko jituwa da mummy jidda ba. Sun dan jima a gidan,don har bayan sallar isha'i,sai da suka jira hajiyan ta kira wadda zata tayata zama,saidai har suka zo tafiya bata qaraso ba. A sace kaltum take kallon hajiyan,itadai duk yadda jawahir ke cewa mafadaciya ce bata gani ba,hasalima saboda ciwon qafarta sai take jin kamar ummanta,duk wadda ta gani da ciwon qafa saita dinga ganin kamar ummanta "Don Allah kice ya barni na zauna tunda me zaman bata zo ba" ta radawa jawahir,ta dubi samir ta gaya masa,saiya waiwayo yana dubanta "Makaranta fa?" Ya tambayeta kanshi tsaye,sai sannan ta tuna "Kwa dawo gobe" hajiya qarama na murmushi,cikin jin dadin yadda take ta nuna kulawarta a kanta tunda tazo tace "Allah sarki yarinyar kirki,kada ki damu kinji,mubina na hanya,ba jimawa zaki ganta" da wannan sukayi sallama,bayan ta baiwa jawahir wani abu a leda tace su raba ita ba amfani dashi zatayi ba. Saida suka shiga motar,samir yana qoqarin tada motar jawahir ta bude ledar "unbelievable...." Saita saki dariya "Wlh hajiya nada abun dariya,ta rasa yau kuma me zata bamu sai pad?,to ai wanna ni ta yiwa wannan kyautar,don kaltum ma yaa har yanzu bata fara period ba bare mu raba tare" tayi maganar tana ajjiye ledar gefanta Kamar motar ta tsage ta fita ta qasanta haka kaltum taji,wai yau me ya samu bakin jawahir ne take ta bare magana haka? "What?" Samir dake qoqarin tada motar ya fada bayan ya tsaida abinda yake qoqarin yi din "Me kace yaya?" Jawahir ta tambaya,bai amsa ba,saiya waiwaya gefansa a nutse,ya dora idanunsa kan kaltum "Shekararki nawa?" Ya tambayeta kai tsaye,tambayar data bata kunya "Sha biyar" ta amsa masa a hankali,saiya janye idanun nasa daga kanta "Akwai matsala" ya fada yana tada motar tashi,sannan ya fiddata daga jerin motocin gidan inda ya ajjiyeta,yana qissima lallai akwai wani matsalan,amma bata tadda za'ayi tana da 15yrs ta kasa period. A komawan ma shuru tayi,saboda kunyar da jawahir ta gama bata,don damuwar maganar biba ma ta fita a ranta ba kamar dazu ba,bayan ta yankewa ranta yin shurun kamar yadda biban tace da ita. Washegari ita da jawahir suka sake shiryawa zuwa duba hajiyan,bayan sunyi waya da saraki yace shima zaya biyo daga gurin aiki saisu wuce tare. A falo suka tadda hajiyan,taji dadin ganinsu sosai,ta amsa gaisuwarsu cikin kulawa da tambayar yadda sukaje gida. Suna tsaka da gaisawa yar matashiyar budurwar da kadanne bata qarasa sa'ar jawahir ba ta fito daga kitchen,hannunta jiqe da ruwa da alama aiki takeyi. Qarasowa tayi tana dubansu,da alama sunsan juna ita da jawahir,saidai ba wani sanin can can ba,ta zauna kan daya daga cikin kujerun suna gaisawa da jawahir sannan ta dubi hajiyan "Me za'a dafa?" "Idan na gaya miki ma me nakeso quiya irin ta 'ya'yan yau ba lallai ta barki ki iya dafamin ba" duban hajiyan tayi,tadan maida bayanta ga kujera ta jingina bayan tayi luu da idanunta "Kamar kuwa kinsan na gaji,ga baqi mun sake qaruwa,kawai ayi spaghetti jallope" idanu ta fidda "Wa?,Allah ya sawwaqe,bama ta shinkafa ba saita taliya,nikam ba dani ba,ni ason raina ma na sami lafiyayyen tuwon dawa da miyar kuka" daga jawahir har mubina dariya suka fashe da ita "Allah ya sawwaqe,haba hajiya me kika rasa da zakici wani dawa?" Cewar jawahir,mubina ta dora da "Tayani gani dai,wai makaho yaso gulma" baki hajiyan ta sake,kamar yadda kaltum ke binsu da kallo kawai,tana dan qaramin murmushin da bai bayyana a saman fuskarta ba,tausayinsu take da suka jahilci amfanin dawa da har suke ganin baikenta,gayu da gata suka sanya su hasarar alfanu me yawa,tabbas da sunsan amfani da Allah ya zuba a cikinta wawasonta za'a dinga yi,amma abunda ta fuskanta a rayuwar maraya shine,kawai duk gidan da akaga suna cin tuwon masara ko na dawa,to talauci ne yake damunsu,idan kuma masu wadata ne,tofa la shakka za'a lasafta mai gidan cikin sahun mutane masu rowa qanqamo da dan hannu. Bayanin amfaninta hajiya qarama ta fara musu,amma saita fuskanci basa ganewa,jawahir na dariya tace "Hajiya,abincin dokuna ce fa?,ita naga ana yamutsawa da wani abu ana bawa dokunan ya samir" "Me yasa dokunan suka fimu qarfi da lafiya?" Kaltum ta jefa musu tambayar ba tare da tasan ta fito a bakinta ba,dukka sai hankulansu sukayo kanta,saboda funda aka fara maganar batace komai ba kallo ne nata,sai taji wani nauyi,amma kuma haka ta daure taci gaba da magana "Dabbobinmu wani lokacin sun fimu lafiya qoshi da kuma kitse ajikinsu,saboda muna daukan dusar kayan amfaninmu dama tsabar muna basu,da sunan shine abincin daya dace dasu,mu kuma muqi ci saboda muna neman dadi,bamu damu da kyau ko ingancin abinda zamu ci ba,dadi kawai muke yiwa" sai sukayi shuru suna nazari,zuwa can jawahir tace "Kuma fa hakaneeee kulsum na yadda dake wallahi" yayin da hajiya qarama ta zuba mata ido,tana mamakin fasaharta da kaifin hankalinta a shekraun da take dasu,duk kuwa da cewa.ba wami abun mamaki bane ga duk mutumin daya rayu cikin karkara,wata baiwar basira hikima da fasaha Allah ke musu,wala'alla kyan nature irin nasu da bata baci da hayaqin kamfanoni da ababen hawa bane,da kuma cimar ganyayyaki da zallar abinci masu gina jiki damu muke musu kallon banza da suke ta'ammali dasu "To kundai ji" hajiyan ta dora da fada musu,ita dai mubina sam bata gama yarda ba,daga qarshe dai kaltum tace suje ta tayata ta dora girkin,sai gashi sun buge da barwa kaltum din girkin,wanda ita kuma ta sauya akalar abinda sukayi niyyar dafawa ta maida tuwan dawar da hajiya qarama keso,dawarta me kyau kuwa,jar dawa wadda tafi kowacce amfani,niqanta kuma yayi laushi yadda ya kamata. Sanda ta jerewa hajiyan komai bayan sun gama sallar magariba,hajiyan don dadi kamar tayi me,albarka kawai take sawa kaltum din "Hajiya mu ba zaki gode mana ba" jawahir daketa kai lomomi bakinta ta fada,don ita ba zata iya tuna when last data ci tuwon dawa ba,don haka ta manta dadinsa ma kwata kwata,saidai babban abun mamakin shine,ashe haka kaltum din ta iya girki?,eh tabbas don girki ummansu ta horesu dashi,tun tana da shekara goma take dora sanwa,shekararta biyar tana girki,girki kuma kowanne irin irin dai wanda suke tu'ammali dashi zata yishi fes aci ayita santi,abu daya ne zuw biyu dama bata iya shi ba,girke girken da tazo ta tarar suna yi na zamani,sai kuma kayan dandano dana qamshi kala kala dasu basa amfani dashi,amma zama da take yawan yi a kitchen yasa ta gane amfanin da yawa daga cikinsu,ta kuma iya sarrafasu,amma yanzun data tashi yiwa hajiya qarama girkin ma,dukka ajjiyesu tayi,tayi amfani ne kawai da komai a gargajiyace,nan ta barsu suna santi,tayi dakin da mubina ta sauka don daura alwalar magariba. *SAƘONE MAI NAUYI,BUDE IDANUNKI DA KYAU KI KARANTA!!* *_RAMUWAR SALLAH GAME JININ AL'ADA!!_* *_Shin kinsan cewa,duk sanda jini ya dauke miki,minti biyar kafin rana ta fadi saikin RAMA SALLAR AZAHAR DA LA'ASAR?_* *_Idan ya dauke miki minti biyar kafin alfijir ya keto,saikin rama sallar magariba da isha'i ta jiya?_* *_idan ya rage saura minti uku alfijir ya keto ko biyu ko daya,ba zaki RAMA MAGRIBA BA AMMA ZAKI RAMA ISHA'I tana nan a kanki_* *_idan ya rage saura minti daya rana ta hudo to SALLAR ASUBA TANA KANKI SAI KIN RAMA TA_* _wadan nan wajibi ne ki riqe ki kuma ramasu,idan ba haka ba zaki tashi a littafin ayyukanki baabu su_ *_YAYA KIKE QARA KWANAKIN AL'ADA IDAN KIKA LURA DA QARIN KWANAKIN DA JINI YAKE MIKI KAFIN DAUKEWARSA???_* 👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 45 *_KIJI TSORON ALLAH,ki biya ki karanta cikin aminci,ba tare da kin taba haqqin kowa ba_* 08184017082 Ko 09134848107 _______________________________ Ana gama sallar magaribar daga masallacin layin gidan hajiya qaramar gidan yayo,a qasa yake tattakowa cikin nutsuwarsa har ya kawo gidan. Sanda yayi sallama falon dukkaninsu ke qoqarin amsa mishi sallamar,amma banda mubina da tayi suman xaune,tana jin jinin jikinta kamar ya daskare ne waje daya ya dauna zagayawa yadda ya kamata. Babu wanda ya fahimta halin da take ciki,shima duba daya yayi mata ya ganeta,amma bataga alamar haka ba,saiya samu waje ya zauna yana duba hajiya qarama da jiki,yayin da jawahir ke masa sannu da xuwa,gami da yunqurin miqewa da gaggawa tayi ciki itama don tayi sauri tayi sallar kafin yace su fito su tafi,don tasan bayason jira. Da wata shaqaqqiyar murya mubinan ta gaidashi,tana jin wani iri babu dadi da ganinsa qalau da tayi,don ta gwada kiran wayarsa yafi a qirga amma baya dagawa,ta rasa wacce irin rashin sa'a ce irin wannan,ta mallaki number dinsa cike da fata da burin samun soyayarsa,sai kuma ya datse hanyar da take fata da burin tabbatuwar hakan. Ganin babu kowa a falon sai ita ya sanya dole itama ta miqe tabi bayansu,saidai dukka wanda ya kalleta yasan jikinta a matuqar sanyaye yake "Kicewa kalsum tazo ta bawa yayansu abinci....yauma dai ita ta ciyar damu,wadan nan iyayen qyuyar ba abinda suka iya sai abincin bature mara inganci bare qara lafiya" hajiya qarama tace da mubina tana kuma yiwa samir bayani,gami da yunqurin miqewa itama don taje tayi salla. Sanda take gayawa kaltum din taje takai abincin sai jawahir ta bi mubinan da kallo ganin yadda lokaci daya tayi laushi sosai,yanayinta ya canza. Miqewa kaltum tayi daga saman abun sallar data kafu a kai tana addu'o'i,kwanakin nan kawai daurewa takeyi tana mazewa,amma ranta damuwa ce fal,tayi kewar gida kamar hauka amma babu wanda ta nunawa,bata kuma da yadda zatayi,kullum da tunaninsu take kwana take kuma tashi,uwa uba kuma ita din asalan da wuya kaga bata kwana gida kusa da ummansu ba,bako ina take zuwa ta tarda ta kwana ba,sai gashi yau wani qaddara ta kawo silar rugujewar zamansi,ta nesantata da gida zuwa wani waje me nisan da tunaninta bai taba dauko mata wannan ba. Daga nan dakin kitchen din kawai ta wuce ta hado kayan abincin dai da yadda ya dace,don tasan qila samir dinne ya iso. Tun kafin ta qarasa ta hangeshi yana amsa waya,sai tayi qas da kanta tana takawa a hankali zuwa inda yake zaunen. "Barka da yamma" ta fada cikin wani yanayi fa batasan yadda akayi tayi magana a hakan ba,wala'alla kodon idanunsa daya zuba mata ne da sukayi mata nauyi?. Zare idanun nasa yayi daga kanta,don baima san yana kallon nata ba,saiya amsa mata daka yana ci gaba da amsa wayarsa,shida jauhar ne,a yanzun tana jinta kamar tafi kowacce mace sa'a a duniya,ta fara sarewa daga samun samir din kwata kwata,duk kuwa da yadda yayi mata,saiga albishir kwatsam na dukkan dama ta samun mallakar tasa,wannan dalili yasa ta buse wutar mallakar zuciyarsa babu qaqqautawa. Yadda taga jawahir na masa,saita duqa tayi serving dinsa,bayan ta gama ta yunqura zata miqe sai ya dakatar da ita da hannu yana ci gaba da amsa wayarsa,hakanan ta koma gefe ta zauna tana,ta takure waje daya tana wasa da yatsun hannunta,jinta take wani iri,saboda babu kowa a falon daga ita saishi,sai take ganin kamar ya cika falon shi kadai. Batasan me yasa a duk sanda zasu kebe daga ita saishi ba saita dinga jin wani nauyinsa,tana auna hakan a ma'aunin girma da nauyin alkhairin da yake shigowa dashi a rayuwarta. A hankali kunnuwanta ke dauko mata wasu daga cikin wayar da yakeyi,ta fuskanci da mace ne,haka kawai sai takejin wani abu mara dadi a qirjinta,amma tafi ta'allaqa hakan da ajjiyeta da yayi tana suraran sirrinsa,saita qara tsumewa a waje daya,tana ta faman murza yatsunta kamar wadda aka baiwa wannan aikin. Shi da kansa ya gimtse hirar ta hanyar daukar excuse din zaici abinci,saboda bayajin wani dandano nata ko armashi,ya sauke wayar idanuwansa na sauka kan zara zaran yatsunta wanda ke nuna dukkan alamu na laushin da fatarta keda ita. Sai da yayi bismilla alamun fara cin abincin sannan ta farga ya gama,a hankali ta gyara zamanta ba tare data iya kallonshi ba. Hankali kwance yake cin abincinsa,tare da mamakin yadda girkin yayi dadi,dama can ta iya girki ne ko zuwanta ta koya,tunda tazo basu taba wata doguwar hira tsakaninsa da ita ba,saiya jefa mata tambayar "Ya akayi kika iya girki?" Ka ta jinjina masa sannan ta bude baki da 'yar qamar muryarta ta amsa masa da eh "Waya koya miki?" "Ummana ce" ta amsa masa "Madalla da umma,tayi qoqari sosai" maganarshi ta sanyata daga kai ta dubeshi,sannan murmushi ya qwace saman fuskarta. Karo na farko da yaga wadataccen murmushinta irin haka,fuskarta ta qawatu matuqa,ta sadda kai murmushin taci gaba da wanzuwa kan fuskarta "Na gode" ta fada tana jin dadin yadda ya yabi ummanta,sama sama yake kallonta,yana kuma karantar farincikin dake zuciyarsa dangane da yabon mahaifiyarta da akayi,sa yaji wani abu yana taba ransa sosai akan hakan,harma yaji ya qoshi,duk da dadin da abincin yayi masa,don bazai iya tuna yaushe yaci irin wannan tuwon ba,gidan hajiya qaraman yake samu dama,to ita kanta kwana biyu daya zamana yau lafiya gobe babu sai ta sakarwa masu aikin girkin duka,su kuma bason tuwo suke ba,kamar yadda ya fuskanci mummy bata sonsa,hakan ya sanya ba'ayinsa sam a gidan. "Tunda kike baki taba period ba dama?" Ya tambayeta kansa tsaye,tadan daga ido ta kalleshi,sai tayi saurin sakewa,nauyi da kunya suka cikata,saita cure waje daya kamar mejin sanyi,ta kasa amsa masa tambayar,murmushin gefan baki ya saki,sabida ganin yadda tayi daga yi mata tambayar,saiya tuna sanda take bala'i lokacin da zata amsa haqqin dan uwanta,duk yadda suke hasashen bata da kunya ashe ba haka bane,abu daya ne zuwa biyu kawai,ita din bata bari a danne haqqinta indai tana da ikon karba,sai kuma zamantowar mutum me qaunar mahaifiyarta da yan uwanta. "Ki dauko takalminki muje,yanzu zamu dawo,ki gayawa jawahir ta zauna" bata iya tambayarsa ba,sai kawai ta miqe kamar zata harde ta nufi daki,binta yayi da kallo kafin ya janye idanuwansa,yana tuna ganin da yayi mata a dandali ne,a sannan halayyarta ce ta gaskiya kenan?,kansa ya shafa yana ture tunanin gefe guda tare da duban hajiya qarama dake dawowa falon. "bazan boye miki ba,sonsa nake kuma yayimin.......zaki iya taimakamin?" Wadannan ne kalaman da suka shiga kunne kaltum sanda take shiga dakin,duka sai suka juyo suka kalleta,kanta ta dauke tana nufar inda ta ajjiye takalmanta,ba tare data sak dubansu ba tace "Yaya yace ki jirashi,zamuje mu dawo"ta fadi mata tana nufar qofa "Ok,saikun dawo" ta amsa mata tare da maida hankalinta ga mubina,wadda gaba daya ta koma kalar tausayi,bisa kuma dukkan alamu zuciyarta a karye take sosai. Ta cikin hasken gidan yake hangota yana zaune daga cikin motarsa sanda take fitowa,ya fuskanci bata da wani zafi ko kadan,komai nata tana yinsa ne cikin sanyi,saiya buda gida gaba kafin ta qaraso,ya kuma janye idanunsa ya maida ga wayarsa da tayi qara alamun shigowar saqo. Sai data zauna sosai sannan ta rufe qofar,ya ajjiye wayar gefansa ya tayar da motar sannu a hankali suka fice daga gidan. Tafiyar mintuna ashirin suka iso wani guri da tun daga waje yafi mata kama da asibiti,da suka shiga ciki ta daga kanta tana duba rubutun dake maqale a qololuwar ginin wajen,a nan ta tabbatarwa kanta a sibiti ne,tana jin sanda yayi waya da alama da wanda sukazo wajensa yake,kana ya bata umarni suka fito,yana gaba tana biye dashi har cikin asibitin. Kai tsaye reception suka tsaya,wanda ke dauke da files na marasa lpy a tsare cikin wata kanta,sai tarin computers da suke amfani dasu wajen karbar kudi da bada receipt. Da mutane a wajen don haka suka dan tsaya daga baya,hankalin samir na ga wayarshi yana qarasa duba saqon da ya samu dazun,daya hannun nasa kuma riqe da key na mota yana dan kadashi. Tunda suka shigo wajen hankalinta ya dauko a kansa,ta juyo ta kalleshi yafi sau shurin masaki,saidai shi baisan abinda ke faruwa bama. Kaltum kuwa duk abinda ke faruwa tana kallo,har zuwa sanda tadan matsa kusa dashi,da wata maqalalliyar muryarta dake nuna gayunta tace "Hi" sai a sannan ya daga kanshi ya dubeta "Hi" ya mayar mata yana qoqarin maida kansa ga wayarsa,ta yunqura zata sake magana muryar receptionist din ta katsesu "Sir.....kaine muhammad samir?" Kai ya gyada mata "Sorry sir.....Dr labaran yace ka shiga office dinsa ka zauna,zaka ha sama ne,daga hannun damanka daki na qarshe a nan zaka samu office dinsa" "Thanks" yafada yana yin gaba,kaltum tabi bayansa,saidai koda bayan sun gota ta din sai data waiwaya ta kalleta,itama su take kallo,ta sakarwa kaltum murmushi tare da daga mata hannu,saita dayke kanta tana tabe baki,itakam koda a karkararsu tana ganin baiken irin wannan zub da kan,ashe har a nan ma da ake ganin matansu sun waye suma suna irin wannan dabi'ar?. Tana biye dashi tana mamakin me ya kawosu asibiti?,waye baida lafiya?,kuma.taji ana zancan dr,koshi za'a duba?,duka bata da amsa,saita haqura taci gaba da binsa tana zubawa sarautar Allah ido. Har suka shiga suka zauna yana duba wayar hannunsa,shuru yaci gaba da ratsa office din,lokaci lokaci tana satar kallonsa,abinda ke fado mata a rai kawai shine....maganar mubina data tabbatar tana da alaqa da shi,sai kuma yarinyar yanzu,mamaki ke kai kawo a ranta,me yasa kowa sonshi yakeyi?,idan bata manta ba mata kusan uku tana gidan sunzo ne kawai saboda shi,wasu su wuni su tafi,tana nazartarsa tsaf,tun asali mutum ne mai girmama kowa musamman mace,bashi da wulaqanci saidai ya iya jan aji da kuma mutunta kai,hakanan sauqinsa baisa ya zama me daukar raini ba. Bata tsammata ba ya dago kai sai suka hada ido,da sauri ta janye idanunta ta mayar kan wani dan qaramin frame dake dauke da certificate of honor da aka baiwa asibitin. Karamin murmushi ya saka,ya gane cewa ta iya basarwa itama,saiya maida wayarsa aljihu a hankali,yaji yana son qureta,don haka ya kafeta da idanu,so yake ya kamata red handed,ya kuma tabbatar mata da kallonshi takeyi,abinda ya fuskanci tana avoiding kenan,don tun dazu da idanunsa ke kan wayarsa jikinsa ya tabbatar masa da kallonsa ake. Wasu mintuna ta diba da take da tabbacin ya koma sabgar da yakeyi,zuciyarta naci gaba da raya mata ta sake juyawa ta kalleshi ko zata gane abinda yasa mata ke sonshi. A hankali take juyar da kanta kamar me ciwon wuya,caraf ya sake kamata,ta kuma dauke kanta da sauri tana jin kunya fiye da dazu,wannan karon murmushi yayi mai dan sauti,sannan ya hade hannayensa a tsakiyar qafafunsa,cikin lallausan muryarsa yace "Me yasa kuka gwanance wajen iya satar kallon mutum,sai kuma an kamaku kuji kunya.....amma ke me yasa bakya son na kamaki kina kallona?" Daburcewa tayi sosai,nauyi da kunya suna cikata,karon farko da taji wasu kalamai da suka samu matsugunni a ranta har suka rudata,itama batasan tsautsayin da yasa ta nace saita kalleshin ba,kame kame ta fara yi,tahau gyara fuskar hijabinta,gyaran da bashi da tushe bare makama,hakan yasa ya sake kafeta da ido. Sosai ya lura baqin fuskarta dukka a yanxu babushi,sai wata kala da fatarta ke fitarwa ta daban. Sauko da idanunsa yayi saitin qirjinta,har yau bai gasgata jawahir data ce wai ta isa saka breezier ba,cikin wani mugun sauri ya kauda da idanunsa sanda ya rage qiris ta ganshi,ya sauke boyayar ajiyar zuciya yana godewa Allah da bata ganshi ba,da girmansa ya zube. Kafin wani a cikinsu ya sake wani motsi an turo qofar dakin anshigo. Dogon likita baqi,mara jiki sosai,saidai akwai alamun nutsuwa sosai a tattare dashi. Hannu ya bawa samir sukayi musabaha,sannan yaja kujerarsa ya zauna yana amsa gaisuwar kaltum. File din dake gabansa wanda da alama sabone ya bude,ya fara yiwa kaltum din tambayoyi. Da qyar take iya amsawa saboda nauyin da takeji,kusan tunda ta girma ba'a taba sakata gaba ana mata tambaya irin makamanciyar wannan ba,samir na zaune kam kujerar yana monitoring nata har likitan ya gama. "CT scan za'ayi mata,shine zaifi nuna dukka abinda nake buqatar gani,saidai akwai 'yar tsada" ya fada yana qarasa rubutunsa jikin file din. Tunda suka shiga dakin scan din gaba daya tsoro ya kamata,musamman data kalli machine na scan din,har batasan sanda ta tara qwalla a idanunta ba,ta waiwayo tana duban samir dake tsaye a bayanta,hannunsa daya cikin aljihun wandonsa,yayin da daya hannun nasa yake dan saman kanshi yana shafawa a hankali gami da karanta wani rubutu dake manne a farar takarda jikin bangon dakin. A hankali wata nurse ta tura qofar dakin tashigo,hannunta dauke da wata riga da tafi kama data marasa lafiya,ta ajjiye rigar saman wani dan abu,sannan ta isa wajen machine din tana goge gadon dake maqale dashi,gami da gyara shimfidar kai. Sai data gama tsaf kaltum na tsaye tana kallonta,ji take kamar ta zura da gudu tabar dakin saboda tsoro,gefansu nurse din ta tsaya tana ajjiye wasu allurai,sannan ta fara hadesu waje daya a syringe "Idan na gama miki wannan allurar,zaki cire abinda kikasan akwai qarfe a jikinsa da yake jikinki,kamar bra da rigarki da kuma skert tunda akwai zip a jiki,saiki sauya da wannan rigar" ta fada tana nuna rigar da yatsantsa. "Bismillah qaraso" ta fada tana duban kaltum sanda ta gama hada ruwan allurar waje daya. Kanta ya daga sai suka hada idanu da samir wanda ya kafeta da ido,tuni ya hangi tsoro muraran cikin idanunta,saiya taka a hankali,ya isa wajen,yaja wata kujera dake gefan nurse din zuwa gabanta,sannan ya yiwa kaltum din nuni kan tazo ta zauna. Narai narai ta sakeyi da idanu ba tare data ko motsa ba,wani qaramin murmushi ne ya subucewa fuskarsa,ya gane tsoron allura takeyi,abunda ya bashi mamaki,saboda ya tuna tsiwarta,baiyi tunanin zatayi tsoron allura ba "Hala madam din taka tsoron allura take,anya basa an riqe mana ita ba?' matar ta fada tana murmushi hadi da miqewa riqe da allurar tata. "Bari na taimaka miki" yace da matar Hannunsa ya cire daga aljihun nasa,ya qara taku biyar zuwa inda take tsayen,ya tsaya daga bayanta,,dab da ita sosai,har tana jin hucin lallausan turarenta "unhummm......remove it" ya fada a hankali kamar me rada,abinda yasa taji gaba daya ta diririce kenan,kusancin dake tsakaninsu tana jin yayi yawa,saita sanya hannu a hankali ta dage hijabin nata,ta kuma miqawa nurse din hannunta,gami da rintse idanunta sosai saboda tsoron tsinin allurar. Wani qaramar qara ta saki sanda aka saka allurar,ta yamutse fuska sosai tana jin wani iri har zuwa sanda ta zare syringe din tana cewa "Muna gab da tashi,da sauri madam ki canza kaya sai kuyimin magana"tana kaiwa qarshen maganar ne sanda take bude qofa ta fice. Kanta a qasa tana mulmula wajen da aka yi mata allurar,tana tsammatar jin ya fita amma bataji ya motsa ba,harta gama ta cire audugar "Be hurry" ya fada muryarsa qasan maqoshi yana kallonta,batasan ya zata ce masa ba,amma hannunta ya qage,batasan da yadda zata cire kayan ba. Kamar ya karanci matsalarta ganin bata da niyyar motsawa saiya sake takowa zuwa inda take,ya saka hannu a hankali ya zare hijabin jikinta,wanda ya hado da dankwalin dake kanta gaba daya ba tare da yasani ba. Sassalkan gashinta data matse da dan qaramin band ya ware gaba daya ya bazu daga baya zuwa fuskarta. Idanunsa ya dauke da sauri yana lumshe idanunsa,saiya bude ya sake maidawa kan sumartata dake qyalli a hasken fararen qawayayen dake dakin,jiya jiya jawahir ta tirketa aka tsefe ta sake wankeshi,ta kuma sanya streacher ta ja mata shi,ita tana mitar bai tsufa ba kuma baiyi datti ba,jawahir din kuma tana mitar dama masu gashi basason kitso ko kuma a taba musu kansu,inama itace keda suma kamar tata da anyi kallo. Hannunsa biyu ya sanya ya tattaro gashin dake qamshin man da akayi oiling dinsa dashi dake dukan fuskarsa,daure mata shi yayi,sannan ya sake qara taku biyu yana rage tazarar dake tsakaninsu,ya sanya hannuwansa duka biyu ya juyo da ita tana fuskantarsa. Hannunsa ya dora saman zip din rigarta ya zuge mata tun daga sama zuwa qasa,idanunsa na kallon wani waje na daban,saboda qamshin turarenta da yake shaqa sosai,wanda baisan me yasa yake sauya bugun zuciyarsa ba. Sai da yakai zip din qarshe sannan ya saketa a hankali,yayi taku biyu baya sannan ya juya yana takawa a hankali cikin wani mutuwar jiki zuwa bakin window din dakin,bayan ya maida hannuwansa cikin aljihun wandonsa,daya hannun kuma yana duba agogon hannunsa yana cewa "Ki canza da sauri karmu bata musu lokaci" ya dage labulen yana kallon farfajiyar asibitin. Bude qofar akayi,amma duk da haka bai waiwaya ba,har zuwa sanda ya sake jin muryar nurse din "Sir,she need your assistance,allurar tana dan riqr hannu" gaban kaltum yayi mugun faduwa,wannan matar zata jiqa mata aiki,riga a bude tana kokawar cire bra,ta samu ya kalli wani wajen kuma tayi calling attention dinsa,a hankali ya waiwayo,idanunsa suka sauka a kanta sanda ta tsaya cak da abinda takeyi din,zuciyarta na harbawa a jajjere,bata iya sake daga kanta ba harya sake iskota,wanda taji kamar ya bace bat daga dakin,zuciyarta ta qara nauyi sanda dumin hannunsa ya ratsa fatar bayanta,ya saka yatsuntsa guda biyu ya balle damammiyar bra din jikinta,wanda hakan ya baiwa abinda ta takura din damar sakewa. Ajiyar zuciyar data kusa fita ita ya subuce mata sanda yake sabule rigar daga jikinta,yanayin komai ne yana tsaye daga bayanta,ya dauki rigar ya zura mata yana cewa "Hurry up" Da saurinta ta saka rigar wadda take ta yadice,a tsaye kamar ta masu aikin shara a asibiti. "Ya salam!!" Ya fada qasan ransa har sai da labbansa suka motsa,da wani irin amo mai nauyi sanda kaltum ta juyo ta soma takowa zuwa wajen machine din kamar yadda nurse din ta bata umarni,tana jin kamar zata fadi da saboda nauyi,tana iya jin yadda rigar ta lafe a jikinta,ta kuma bayyana surarta dukiyar fulanin da Allah ya mata baiwarsu,take kuma boyesu tun daga sanda suka fara bayyana kansu,saboda kunyar hakan da takeji,har da yawa suke mata kallon qwaila. Wani irin laushi da yaji qafafunsa sunyi suna shirin gaza ci gaba da daukan nauyin tsaiwarsa sai yaja kujerar dake dakin ya zauna,yana kallonta har zuwa sanda ta kwanta saman gadon kwanciyar rigingine kamar yadda nurse din tace mata,hakan saiya zamana kamar dama ce suka samu ta bayyana kansu sosai ta cikin rigar,gaza ci gaba yayi da kallonta ya zare idanunsa ya maida ga machine din sanda gadon ya dagata sama ya kuma turata tsakiyar machine din. Shuru ne ya ratsa dakin,babu komai sai qarar machine din daketa wasu bayanai,ko sau daya bai qara daga idanu ya dubeta ba,yayin da kaltum tsoron machine din da kuma abinda ya farun ya karya duk wani kuzari nata,tanajin wani nauyi na ratsata,tunda take wannan shine karon farko da wani ya taba ganin ainihin surar jikinta,saita lumshe ido tana tuna yadda taji hannunsa saman jikinta,zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri da sauri. Duba takaddun likitan yayi ya ajjiye CD plate din da suka hado dashi,tsahon wasu mintuna sannan ya dubi samir "Gwajin da nayi mata a nan,da kuma wannan scan din ya nuna komai,akwai qarancin sinadarai a jikinta wanda zasu taimakawa zuwan period a jikinta,kuma hakan zai zamana yana da alaqa da matsalar haihuwa,so amma ba wani damuwa in sha Allah,akwai magunguna da zata fara sha daga yau zuwa sati biyu,suna da kyau magungunan sosai,zasu taimaka wajen samuwar sinadaran isassu da zasu kawo mata al'adar a kusa,kuma ina saka ran insha Allah tana kammala shansu period dinta na farko zaizo" Kai samir ya jinjina,likitan yayi rubuce rubucensa ya bashi takaddun,ya miqe ya bashi hannu suka sake musabaha,yayi masa godiya suka fice. Shuru ne ya zame musu jagora cikin motar,kowa da abinda yake saqawa,abinda idanunsa suka gani sune kawai ke kai kawo a qwaqwalwar samir din,wanda yaketa kokawar ajjiyeshi a gefe,saboda muhimma ayyukan dake tunkaroshi daga office,amma ya kasa tunkude tunanin daga kwanyarsa,hakan yasa yadan juya a hankali ya kalli gefan da take zaune,sai yaga har yanzu tana mulmula inda akayi mata allurar ne,saidai a badini itama tayi nisan kiwo wajen tunani ne,tunanin yadda zataci gaba da hada idanuwa dashi bayan duka wannan abun kunyar daya faru tsakaninsu wunin yau gaba daya. Sai daya tsaya a wani waje na wasu mintuna sannan ya dawo cikin motar ya tayar suka qarasa gidan hajiya qamar. *_ASHA HUTUN WEEKEND LAFIYA_* *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar 46 "Ki kira jawahir mu wuce,saiki zauna da hajiyan" shine abinda yace da ita sanda ta bude motar xata fita,yayin da yake zaune a nan wajen ba tare daya motsa ba "To" ta amsashi dashi,sannan ta wuce zuwa cikin gidan. Ta taras jawahir harta kwanta abinta,sai mubina dake zaune,idanunta sun dan canza kala,bata sani ba kuka tayi kome tayi oho. Hajiya qaramar ta nuna jin dadi sosai da taji kaltum din zata zauna da ita,saidai tace dama yabar jawahir din ta kwana kawai "Gwara naje gidan hajiya,gobe da makaranta,kuma ban debo komai na zuwa makarantar ba,amma kafin ki warware zan dawo na kwana idan kaltum ta kusa komawa,saimu koma tare.....hajiya kindai daukemin qawartawa da take debemin kewa" jawahir ta fada tana ɓata fuska "Yo basai ki hanata zama ba?" "Ni na'isa hajjaju,Allah ya huci zuciyarki,aro amma na baki ita" tayi maganar tana roller mayafinta,dai dai nan kira ya shigo wayarta,ta duba da sauri ta suri jakarta "Ya saraki,babu jira" "Dakata,zaku sauke mubina gida,jikin hajara ya motsa zata kula da ita" hajiya qarama ta fada,dai dai sanda mubina ta fito dauke da qaramae jakarta,idanunta har yanzu a jirkice suke "Khairan in sha Allah,ki daina wannan damuwar,haka zakije kina daga mata hankali maimakon ki kwantar mata da hankali ki bata qwarin gwiwa,haba....banason irin wannan sakarcin" kai mubinan ta daga tana dan goge fuskarta,ita kadai ce tasan irin tashin hankalin da takeji cikin qirjinta tun sanda taji daga bakin jawahir cewa an kusa kai kudin aure da sanya rana na samir din da wata wai ita jauhar,duk da umminta bata da lpy amma batakai ta koma gida ba,ta yanke ta shawarar gwara ta koma gidan qila tafi samun nutsuwar tunanin da zaya kawo mata mafita,kafin ta waiwayo ta dawo gidan,don tunda ta fuskanci alaqarshi da gidan taci alwashin sai inda qarfinta ya qare. *********Washegari da wuri ta tashi ta kammalawa hajiya qarama komai daya kamata ayi cikin gidan,hatta da abincin da zataci,sannan tayi shirin makaranta,wanda already tun kafin su kwanta hajiyan ta gaya mata wanda zai dinga kaita din,don haka ta fice zuwa farfajiyar gidan inda yake jiranta. Harta shiga ta manta batasha maganinta ba ta dawo ta dauko,ta ballosu tana kallonsu a tafin hannunta,murmushi ya qwace mata saboda tuna abinda ya faru a jiyan da tayi. Can wani bari na zuciyarta taji yana burgeta,a caring person,sunan ya dace dashi qwarai,da alama ya damu da damuwar wasu,ba iya kanshi ya sani ba,she never expected akwai mutum irinsa a yanzu,a rich and handsome man,amma bai dauki rayuwarshi da wani zurfi ba,saita afa qwayoyin da sauri ta bisu da ruwa a gurguje ta fito saboda tunawa da tayi tabar mai kaitan yana jiranta. A lokaci irin wannan ba kasafai malamai ke shigowa aji ba,saboda shirye shiryen fara exam na qualifying da sukeyi,koda sun shigo din ma revision ne kawai akeyi. Yauma kusan ajin ba malami,masu hira nayi,masu wayo kamarta sun kama litattafansu suna dubawa. Duka wadanda seat dinsu ke kusa da nata wadanda suke komai tare idan ya kama ta bawa hannu suka gaisa,suka dan taba hira da bata wuce ta minti biyar ba,sannan ta karbi note book din saliha ahmad da zata kwafi wani note,ta koma seat dinta ta zauna bayan ta ciro nata littafin ta fara kwafa. Tana aikin tana sauraren hirarrakinsu,wanda dama idan suka hadu basa gajiya,kusan dukka hirar tasu kan samarinsu ne da kuma aure,kowacce burinta data gama nan tayi aure,wani abun ta girgiza kai,wani tayi murmushi,tsahon lokaci har suka cika mata ciki,saita rufe note din da takeyi ta dubesu tana murmushi "Wai nikam....duk cikinku babu wanda yake sha'awar yin karatu ne sai aure aure kawai?" Dukka suka waiwayo suka kalleta,sai suka sanya dariya,saliha ahmad ce ta amsa "Wa yake ta wani karatu?,ai idan ka dace da gidan mijin qwarai karatu duk wahala ce,wanda akayi ma Allah ya amfana,tunda duk tsiya da secondary School certificate ba wanda ya isa ya kalleka ya kiraka da sunan jahili" "Kulsum fa batasan dadin aure ba" madina ta fada tana dariya,sai kaltum din ta jefeta da harara "Sannu uwar masu gida,keda kikayi ai kin sani" dariya suka sake yi "Ba haka nake nufi ba,ko hirar akefa shuru kike ki zuba mana ido,iyaka naki sauraro,baki bada naki gudun mawar" littafinta taci gaba da budawa da sunan ci gaba da rubutunta sannan ta bata amsa "To me na sani bare na samu ta cewa a kai,kudai da kuketa naci Allah ya bada sa'a,nikam karatu zanyi" "Aure ai baya hana karatu,malama ki tsaya ki saurari ni'imar aure,da kanki zaki canza ra'ayi,kinsan dadin soyayya kuwa da auren masoyi?" Bakinta ta tabe bata kuma tanka musu ba,saidai kunnenta yana tare dasu sanda take rubutun. Abubuwa da yawa da suke fadi yatsaya mata a rai game da soyayya,itadai ta sani taso nasuru kuma sunyi soyayya,amma abubuwan da suke fada din sai take ganin kamar qarya ce kawai,don duka bata ji wannan akan nasurun ba. Sun jima suna hirar tana dauke wasu abubuwa daga ciki,har zuwa sanda malaminsu na maths ya shigo,kowa kuma ya koma hankalinsa ya bashi hankalinsa. Sanda ta koma ta samu hajiya qarama parlor,ita da baqi da alama masu dubiya ne. A ladabce ta gaidasu sannan ta sake duba jikin hajiya qarama "Da sauqi kaltum,kinsha hidima,na tashi na tarar har kin gama komai,Allah yayi albarka" murmushi ta sake kana ta amsa da amin,amma itakam bataji wata wahala ko wani abu ba,dadin jikinta ma taji sosai a yau din,saboda tayi irin ayyukan data saba sanda tana gida,sai takeji jikinta yayi dadi. Dakin da hajiya qarama ta bata ta shiga,dakine dabam ba wanda mubina ke zaune ba,shima wannan din akwai komai a ciki,tana mamakin yadda suke ajiyar dakuna haka da komai a ciki amma kuma babu wanda yake zaune a ciki. Uniform dinta ta cire ta duba kayanta data tarar an kawo mata,duk da basu wuce kala biyu ba ta sanya wata atamfa riga da zani,saita daura alwala tayi sallar azahar,sannan ta dawo parlor ta tambayi hajiya qarama abinda za'a dafa "Na bar miki zabi kaltum,nasan ba zakiyi zabin banza ba" murmushi tayi ta juya zuwa kitchen din. A nutse kasancewar babu kowa cikin kitchen din ta fara duba abubuwan da suke ciki,kafin daga bisani ta yanke abinda zata dafa din. Koda ta kammala la'asar liqis,har yanzu baqin hajiya qarama basu tafi ba,saita koma daki ra jirayi sallar magariba,wadda bayan ta idar dinma taji sabuwar hayaniya,da alama wasu baqin tayi,saitayi xamanta a dakin,har tayi sallar isha'i tanajin motsin 'yan dubiyar,tasan babu abinda hajiyan zata buqata,don ta riga data hada mata komai,kuma itama bata jin yunwa,don haka saita bude school bag dinta,ta ciro wani novel da saliha ta bata ta fara karantawa. Tun batayi nisa ba taji karatun ya fara gundurarta,saboda wannan shine lokaci na farko data fara karanta novel a rayuwarta,yadda suketa maganar yasa ta dinga kushe abun,saidai yadda suka raja'a kan don bata karantawa ne yasa abun bai burgeta,amma ta gwada ta gani,akwai qaruwa sosai a ciki,duk wanda kuma yayi winning su ko shi to akwai wani abu da za'a sashi yayi,kuma dole yayi accepting koma mene,ta yarda ta kuma karba din. Tun batajin armashin abun har labarin ya fara daukar hankalinta,jarumar ciki me bala'in aji da gayu. A hankali a hankali sai gata tana gyara kwanciya gami da sakin murmushi,labarin yana sake shiga jikinta tare kuma da ratsata,soyayyar ciki me sanyi da sanyaya zukata. Kife littafin hannun nata tana murmushi,saita fara imagining kanta a matsayin star din cikin littafin. Turo qofar da akayi yaja hankalinta,ta miqe da hanzari ta zauna,hajiya qarama ce ke dingisawa,miqewa tsaye tayi da sauri "Hajiya....aida kin kirani,wani abu kike buqata?" Murmushi tayi,yarinyar ta kwanta mata a rai hakanan,saboda ta jima bataga yarinya mai qananun shekaru me hankalinta ba,adai 'yammatan yanzu "A'ah yi zamanki ki huta,dama najiki shuru shuru ne,shine na leqo naga lafiya?" Murmushi tadan saki "Lafiya qalau Hajiya,naji kina da baqi ne" "Ahaf,yo baqi duka 'yan uwana ne,yan uwan kuma saraki,ki daina qunshe kanki a daki don sunzo,ki dinga fitowa ana gaisawa,ai da haka za'a saba,gashi kowa yaci abinci yana sambarka da kuma santi" "Bari nazo na gyara wajen" ta fada tana qoqarin miqewa,saita maidata "Zauna nasa sun gyara komai,ki kwanta ki huta,naji jawahir na cewa jarabawa zaku fara,kuma naga kamar karatu kike,nima na gaji,zan dan kwanta idan nasha magani,saida safe" "Allah ya bamu alkhairi,Allah ya qara lafiya" ta fada tana binta da kallo,tsakanin ita da jawahir batasan waye yafi wani sonta ba,saita girgiza kai,tana sake daukan littafi,duk da karatun jarrabawa takeso tayi,amma labarin ya soma daukan hankalinta,tanason sake qarawa kadan kafin ta ajjiye. Tsahon wasu mintunan suka shude,wasa wasa sai gashi ta kwashi lokaci mai tsaho tana karatun bata sani ba,sai data duba agogo taga lokaci yaja,sannan ta rufe,ta nufi bandaki da zummar yin fitsari tazo ta kwanta. Kanta ta kalla sosai a mudubi bayan shigarta bandakin,tuna jarumar littafin kawai take tana fidda murmushi,saita samu kanta da tube kayanta tana tara ruwan zafi,rayawa take a ranta bari ta gwada wanka yadda ta karanta jarumar nayi. Wanka tayi sosai tayi brush,saita dinga jinta wasai,bacci na sake kama idanunta,ta daura alwala ta fito daga bandakin. A dakin nata ta janyo kayan shafarta,dan murmushi ta saki,jawahir kenan,ta sako mata kayan sawa kala biyu don kada ta jima,amma kuma ta hado mata dukka kaya shafarta data siya mata,wanda har yanzu da yawansu,sabida bata basu muhimmanci sosai ba,saidai duk da haka ita a karan kanta take ganun canji gyaruwa da kwanciyar fatarta,sai ta samu kanta da duba sunan man shafawar nata,abunda bata taba yi ba,iyakarta da man ta lakata ta shafa. Ido ta fiddo da taga yayi daidai da sunan man data gani cikin littafin,sai kuma ta maida idon tana sakin murmushi,mamaki na kamata,ta matshi a hannu ya fara shafe ilahirin jikinta dashi. Tana gamawa ta feshe jikinta da turarenta,karon farko data fara amfani dashi,da iya body spray din kawai da roll-on take sakawa. Ita kadai take sakin murmushi sanda tayi rub da ciki saman gadon tana qanqame pillow,ashe dai da gaske ne,wani sirri ne a cikin wankan dare a duk sanda zaka kwanta,taso ta sake duba ci gaban labarin,amma hakanan fa haqura,ta dauki daya daga cikin litattafan karatunta ta fara dubawa,saidai duk da haka lokaci lokaci labarin yana fado mata tare da jin shauqin ci gaba da karatun,a haka bacci ya dauketa da litattafai tule a gabanta. Washegarima sai data gama komai sannan ta tafi makarantar,saidai a yau din sunyi sallama da hajiya qarama,harda bata kudin makaranta wanda batasan me zatayi dasu ba,ko nata da samir ya ware mata ma yana wajen jawahir bata karba,ganin hakan sai jawahir din ta qyaleta,tare da cewa zata yita ajjiyemata har ranar da zata buqacesu. Sannu sannu sai gata ta kwashe kwana hudu gidan hajiya qarama zata shiga na biyar,a kwanakin ta saki jiki da hajiyan kamar yadda ta shiga ran hajiya qarama sosai,sai takejin kamar daya daga cikin yaranta data aurar aka dawo mata da,don duk wani abu da 'ya zata yiwa uwa shi kaltum ke mata. Ita kanta kaltum din tana jin sakewa a gidan fiye da can gidan professor,har mamakin yadda ta sake din takeyi,amma takance qila a nan din saboda babu idanun mummy,qila saboda babu kowa daga ita sai hajiya qaraman,sai kuma baqon da Allah ya kawowa hajiyan,ta sakar mata ragamar komai,ta bata yarda sosai kamar diyarta. Cikin kwanaki biyar din kacal ta gama littafi uku,wanda ta dauki abubuwa masu yawa na darasi a ciki,ta kuma tsinta wasu ta fara aiki dasu,banda jarabawa dake gabanta ma batason labarin ya dauke mata hankali ya hanata karatun da batasan guda nawa zata dinga gamawa a rana ba,don tana kaiwa dare can batayi bacci ba. Koda jawahir ma tazo gidan sai data tambayi kaltum me ya canzata haka?,wanda ita babu irin qoqarin da batayi ba ma ta wofantar,sai dan abinda ba'a rasa ba?. Dariya tabi jawahir dashi,saita dafe baki "Ni sai nakega dariyarma kamar ta canza taki,amma gaskiya kinso jamin asara da baki amfani da mayuka da sabulan nan ba,kaltum,kinga yadda kika soma zama fresh?,ashe da gaske keba baqa bace,hasahena ya tabbata cewa kalar fatarki chocolate ne?. Maganar data sanya kaltum kallon fuskarta a mudubi,tabbas itama fa hangi abinda jawahir ke fada,bata taba zaton fatarta me kyau bace sai yanzu,bata taba sha'awar kalar fatarta ba kamar wannan lokacin. Sanda ta raka jawahir bakin motar da taxo maidata gida ta kalleta "Na debo miki wasu kayan suna nan saman gadon dakin,amma sababbi ne, mummy ce ta siyamin na daukar miki guda uku,karfa kiga na kawo miki kaya ki shantake,Allah hajiya qarama najin qwarin jikinta zamu koma gida,bakiji ba gaba daya gidan babu wani dadi" yar dariya kaltum tayi "Amma baga yaya najwa ba?" Baki jawahir ta tabe tana shigar da qafafunta cikin motar "Wannan an gaya miki ana abun arziqi da ita?,ya jauhar cema naketa lissafin sanda tace min zata zo,to itace ma idan tazo mukan taba hira....itama tata matsalar ta bawa waya lokacin da muhimmanci mai yawa,ba kasafai take iya daurewa zama babu waya ba" rufe mata qofar kaltum tayi tana dan murmushi gami da cewa "Allah ya kyauta to" don ita batasan ma wacw jauhar ba,ko matsayinta a gidan. Sai da taga fitarsu sannan ta dawo cikin gidan da dan sassarfarta,saboda tana son jiqa shinkafar tuwo,don gobe tashin asuba takeson yi ta yiwa hajiya qarama wainar shinkafa,don yau din da sha'awar cinta taga ta tashi,kuma tayita aikawa duk inda tasan za'a samu ba'a samo ba,shi yasa ta qudirta yi mata kafin ta wuce makaranta. *******washegari******** Karfe bakwai da rabi na safiyar washegari ta kammala komai,tana tsaye a falon gidan sanye da uniform dinta da sukasha guga,fes gwanin kyau,riga ce wadda ta fitar da qugunta sosai,saboda daga sama cas jikinta take,yayin data bude daga qasa,tsahonta gaba daya iya qaurinta ne,sai farar safa data kai mata har gwiwa,wanda ita ta taimaka wajen rufe qaurin nata. Hijabin makarantar tasu qarami ne sosai,don iyakarsa saman qirjinta,wannan dalili yasa take amfani da abaya,wadda bata cireta sai zata shiga aji,hakanan koda waje zata fita siyan abu sai ta sanyata take fita din. Ta gama komai,doguwar rigarta ce kawai bata dauko ba,jakar makarantarta na gefe a ajjiye,hannunta daya riqe da littafin makaranta tana dubawa,lokaci lokaci tana daga kai ta kalla agogo,saboda ganin yadda lokaci keta quracewa amma har yanzun me kaita baizo ba. Qarar bude gate din gidan da taji ya sanyata sakin ajiyar zuciya,ta miqe da hanzari ta nufi window din da tasan zata iya hangen wanda ya shigo,ta yaye window din tana leqawa,saidai bata iya hangen wanda ya shigo din,hakan ya qara mata qaimi,ta dinga dage tana leqawa,a tunaninta driver dinne. Sannu a hankali yake takowa zuwa qofar falon,cikin wani sanyi nasa daya wayi garin safiyar yau dashi,safiyar data yakejin kansa fresh,babu komai a cikinsa sai abubuwan da zai iya fuskanta a yau din. Sanye yake cikin wasu sexy slim fit one button blazzer Baqaqe,da ratsin ash,kamar yadda takalmin qafarsa yake baqi,wanda ba abinda yake sai daukar idanu saboda yanda yake fes dashi,ya saka ash socks,agogon kamfanin D&G me asalin tsada ne daure a tsintsiyar hannunsa,yau din idanunsa sanye suke da wani sun glasses mai kyau,wanda ya dace da zagayayyar fuskarsa mai dan tsaho kadan. Tun kana daga nesa kana iya jiyo qamshin lallausan turarensa mai saukar da nutsuwa. A hankali ya dora hannunsa ga handle din qofar ya budeta kana ya tura yana sako kanshi falon a hankali,saboda ya qudurce idan bai samu hajiya qaraman ta tashi ba zai wuce ne kawai office,idan ya tashi ya samu dama ya dawo ya dubatan. Ko kusa ko alama bata ji alamun shigowar mutum ba,saboda yadda ta bada himmar leqen isowar habibu driver,uwa uba ma qofar falon sam bata da qara ko qanqani bare kayi noticing shigowar wani. Yana sako kai falon a kanta idanuwansa suka fara sauka,tana ta dage don ta hango waje sosai,saiya sakaya qofar,yatsaya daga bakin qofar yana harde hannuwansa a qirji,tare da binta da idanu tare da mamakin meya hanata wucewa makaranta a irin wannan lokacin. From head to toe ya bita da kallo,bai tana sanin haka uniform din makarantar tasu yake ba, infact ma ko color dinsa bai sani ba sai yau,ya tsaya cak da idanunsa daidai qugunta,wanda shape din da aka fitarwa rigar makarantar ya taimaka wajen fitar da qugun nata. Dai dai lokacin data saki labulen tana juyowa a sanyaye,saboda ta fuskanci lallai yau din da qyar idan bata makara ba. Bata taba kawowa ranta ganinsa ba,sai gashi tana juyawa itama shi ta fara gani unexpected,a tsaye cak yana binta da kallo. Zuciyarta tayi wani irin bugawa,tayi qas da kanta da sauri bayan ta qare masa kallo cikin sakannin da basu wuce biyar ba,ba abinda ya fado a ranta irin jarumin littafinta na jiya,a yanzun da take ganin samir din sai taga kamar jarumin ne ya fito a zahiri "Ina kwana" ta fada tana jin kamar wadda akayiwa dabaibayi,saboda tunda take ba wanda yataba ganinta da uniform din nan a haka a tsaye,daga jawahir sai biba A hankali yanjanye idanunsa da yakejin kamar zasu lumshe,ya mayar dasu kan agogon dake hannunsa yana duba time,kana ya sauke hannun yana hadawa da amsa mata gaisuwar,ya jefa mata tambaya kuma a jere "Meya hanaki tafiya makaranta har iwar haka?" Yayi mata tambayar sanda yake bin fuskarta da kallo,fuskar da tayi wani smooth,ainihin kalarta tana fita,wanda hutu zama waje daya,sauyin muhalli da kuma ingantattun sabulai da mayuka suka taimaka wajen fitarta,to me ya haddasa wannan baqin?. "Bai qaraso ba wanda yake kainin,nima shi nake jira" maganarta ta katse masa tunanin da baisan daga inda ya ratso ba,kai yadan kada yana dan cije lebansa na qasa "Hajiya fa?" "Ta tashi,tana daki" "Ok, call her" ya bata umarni yana saukowa daga steps din dake bakin qofar falon zuwa ainihin cikin falon yana dan bin bayanta da kallo,haka kawai yaji wani abu ya tsaye masa. Duk taku daya da zatayi zuwa wajen hajiya qaraman sai taji wani mugun nauyi ya saukar mata,saita waiwaya kadan inda jakarta take da niyyar dauka ta goya ko zata rufe mata wani abu. Hada idanu sukayi,ya zare idanunsa daga kanta yana zama hannun kujera "I hope ba haka kike fita makarantar ba?" Kai ta gyada masa tana saurin rataya jakarta,sannan ta amsa masa da "Eh" tana qara sauri zuwa ciki. Ajjiye carbin hannunta hajiya tana murmushi "Kada dai kicemin duka aikin nan kin gamashi?,indai kuwa hakane dole ki makara kultum" Murmushi ta sake "Tun dazu,donma bai iso ba da tuni na tafi...." "Subhanalla,garin yaya?,kuma maimakon ki shigo ki gayamin.....miqomin wayarcan na kirayeshi" tana nuna mata saman bedside drawer,ta qarasa tana dauko wayar gami da miqa mata sannan ta shaida mata zuwan samir din "Dan halak yaqi ambato,sune a raina shida dan uwansa amiru,muje saiya saukeki ma a makarantar" tayi maganar sanda kiran data yiwa habibu ya shiga,ta yunqura tabi qofa kaltum na biye da ita. Zamewa ta fara yi taje ta sanua doguwar rigar tata saman kayanta sannan ta biyo hajiyan,zuwa sannan har ta isa parlor din sun gama gaisawa da samir din,da alama a tsaitsaye yake shima wucewa yakeson yi,saita tsinta maganar hajiyan ta qarshe "........wannan halin nasaran babu inda zai kaiku,kaltum zuba masa abinci maza yaci kuyi hanzarin wucewa kada ku makara" Sumar kansa data samu wadataccen gyara tana sheqi ya shafa "Saidai fa tayimin packaging dinsa cikin wani abun,naci acan idan naje" tun kafin ya qarasa ma tayi hanyar kitchen,ta hada komai ta zuba ga wani dan kwando ta dauko ta fito,dai dai sannan yake tambayar me suka dafa ne ma "Mutuniyarka ce wainar shinkafa,shi yasa nayi maka tayi" kai ya jinjina "Kinyi qoqari,da safen nan?" Saita nuna kaltum "Kaganta nan,aikinta ne,ni inama zaku barmin ita aida ba haka ba,tafimin duka taron masu aikin nan,shi yasa rashin dawowarsu ma bai dameni ba" idanunsa ya sauke saukewa akanta,har yanzu baisan wanne makoma ce tata a wajensa ba,wannan tunanin yasa ya gaza bauwa hajiya amsa sai gaba da yayi yana mata sallama,kaltum na biye dashi da basket dinsa a hannunta hajiya qarama na mata a dawo lafiya. Har zuciyarta tana jin tausayin kaltum,yarinya me hankali,ya akayi iyayenta suka yarda suka bada ita zuwa wani gari ba tare da suna da yaqinin hannun da zata fada ba?,ita dinma dai kamar professor ce,bata daukan me aiki underage,duka sai masu hankali,don tana adawa da aikatau din yara mata qananu. 47 D/Z A gaba ta zauna kamar yadda tsarinsa yake,suna shiga motar jauhar na kiransa a waya,saiya hada wayar da speaker din motar yana amsa wayar. Duk yadda taso dauke hankalinta daga hirar tasu hakan ya gagareta,saita samu kanta da bibiyar duk wata hira da jauhar din ke masa,shi kuma yana qoqarin amsata,wanda kana jin yadda yake amsawar dauriya kawai yakeyi da qoqarin tursasawa kansa,don hirarma batayi tsaho ba yace mata "Am on my way to office,i will call you when I'm back" "Ok honey,byeeee" ta fada da wani baby voice da take amfani dashi wajen ganin taja hankalinsa. Shuru ne yaci gaba da wanzuwa,wanda mintunan da suka qara basu wuce biyar ba ya tsaida motar bakin makaranta,ta dauki jakarta ta fita tana cewa "Na gode" ta maida murfin ta rufe bayan tabar masa sauran qamshin turaren data durfafa a yanzu. Yana motsa motar zuwa gaba yana hangen sanda ta shige makarantar ta madubi,saiya dauke idonsa ya maida hankalinsa sosai ga tuqinsa,yana qoqarin daga wayar amiru data shigo. Shaida masa yayi yana nan dawowa da yammacin yau,amma zai dan zauna gidan hajiya qaraman kafin ya qaraso nan gida,yaji dadin dawowar tasa wannan karon da wuri,sabida amirun shi daya ne amini ga samir,wanda yake iya tattauna matsala ko damuwarsa dashi,hakanan yakan samu courage na aiki a duk sanda amirun ke cikin kamfani,saidai dole wani lokaci akan rashi a kusa,sabida shike kula da dukiyar da mahaifinsa ya rasu ya barmusu shida 'yan uwansa mata biyu dake aure a wata qasar. Yau din tana aiki tana duba novel din,don da qagu taga qarshensa,sosai labarin yake dibanta gami da tafiya da ita,batasan sam haka soyayya take ba sai yanzu,batasan haka rayuwar auren masoya take ba sai data karanta littafin,saita tsinci kanta tana hasaso kanta da gina rayuwar soyayya irin ta cikin littafin,amma kuma dawa?,a yiwa kanta tambayar data katse dukka zaran tunaninta. Idan ta dauko soyayyar da tayi a qauye sai taga ashe badan badamarsu kawai sukeyi,basusan meye ma ainihin soyayyar ba,kawai wani abu suke mai kama da wasan kwaikwayo. Zamantakewar aure a karkararsu kuwa dama ta jima da sanin cewa ana yinta ne illegally ,abubuwan dake faruwa kwata kwata basuyi kama da zaman aure ba. Ita kadai a kitchen tana aikin abinci tana sakin murmushi a duk sanda ta tuna da labaran novel din,sun sanyata nishadi ba kadan ba,abinda kuma ya jawo mata delay kenan,tayi nawar gama girkin da takeyi,har akayi kiran sallar magariba. Ajjiyewa tayi taje tayi sallar sannan ta dawo tana duba abinda ya rage din,a hankali tanayi tana duba sabon novel din data karbo din. Bakwai na dare motar tayi parking a parking lot na gidan,zaratan samarin guda biyu suka fito daga cikin motar,fuskokinsu wasai,suna taba hira har suka qaraso qawataccen parlour din hajja. Tana daga zaune taji sallamarsu,murmushi ya wadata a fuskarta,farincki ya cika zuciyarta,ta bisu da kallo tana musu fatan dacewa da samun mataye na gari,a yanzu babban burinta shine taga dukkaninsu sunyi aure,sabida tsakanin ita da yayan nata yara maza biyune rak dasu,sai mata,ita uku shi biyu,tana fatan wadan nan da Allah ya basu yaci gaba da albarkacesu,su kuma tara musu zuri'a me dumbin yawa. Waje suka samu suka zauna cikin nuna mata kulawa,amiru ya zamo ya gaidata yana mata sannu da jiki,yayin da samir shima ke sake mata sannu kamar ba daxu yabar gidan ba. Hira suka fara tabawa kadan kadan,wadda ta shafu tafiyar tasa,da kuma abubuwan da suka faru bayan bashi nan. Karo na kusan hudu wayar samir tayi tsuwwa yasa hannu yayi rejecting kamar yadda yakeyi tun dazu,hajiya qarama ta dubeshi "Ka daga mana ba kiranka akeyi ba?" Saiya jinjina kai "Barsu hajiya,idan na gama komai zan kira" maganar amiru ta katse zancan "Nifa tunda na shigo nakejin qamshin girki hajiya,kuma anmin fuska,a amatsayina na baqo yaci ace an tarbeni da wani kyakkyawan girki nan" kallonsa tayi ta tabe baki "Idan abun bai maka dadi ba kayi zuciya ka kawomin mata qarshen watan nan,ni dama na gaji da ganinku wallahi a gabana,shi wannan kamae bashi da idanu saida aka zaba masa mata,wadda har yanzu nikam ban gama yarda da ingancinta ba,kai kuma har yanzu shuru,to gwanda gwanda shi da kai ma" gyara zamansa yayi sosai yana duban hajiyan "Wato hajiya kada ki damu,tana qarasa NYSC zan gabatar miki da ita in sha Allah" baki ta sake tabewa "Zuwa yaushe kenan?" "Nan da wasu 'yan watanni ne,tana dawowa" kai ta dauke haushi yana cikata,badon sanin halin yaran zamani ba,da tuni kowanne ta zaba masa mata sun aurar dashi an huta,to amma ita kanta tana adawa da auren dole "Data gama abincin da tuni ta kawo,amma yanzu ma nasan tana dab da gamawa" ta amsa musu,sai samir ya miqe,don da gasken shikam yunwa yakeji,wunin yau banda baqin coffee babu abinda ke cikinsa,sai cake guda biyu "Bari na samo wani abun" "Yauwa mutumina,ka hado dani please" hara rarsa yayi "Idan ka matsu kaje ka dauka da kanka,yaron gidanka ne ni?" Dariya ya saki "Ban isa ba,ataimaka min" bai sake ce masa komai ba ya wuce cikin kitchen din. Bai lura da ita ba sai daya isa cikin kitchen din daga bakin qofa,saiya dakata a hankali da tafiyar da yakeyi din,tana tsaye riqe da littafin tana karantawa,fuskarta na fitar da wani murmushi dake nuna nishadin da zuciyarta ke ciki. Sanye take da daya daga cikin kayan da jawahir ta bata,high tummy skert me wata belt a jikinsa me fadi wadda gabanta ke dauke da tambarin kamfanin DG daya bayyana asirin shafaffen cikinta,daga baya kuma mazaunai da qugunta da suka fara bajewa suka bayyana,sai long sleeves t.shirt turtle neck wadda ta dace da kalar peach din skert din me adon green,dan kwalin kanta shima peach ne me santsi sosai,wanda ya hadu da santsin gashinta ya hana dankwalin zama yadda ya kamata,hakan yasa ya zame daga kanta ba tare data sani ba. Fuskarta yabi da kallo,fatarta data koma chocolate colour ta haska sosai cikin peach color kayan data sanya,daga gaban goshinta gashin kanta ya kwanta sosai ya sauka zuwa kafadunta. Wani motsi yaji zuciyarsa nayi,yabita da kallo sanda ta furta "Yes,anzo wajen" qasa qasa bada wani qarfi ba,saboda laushi da zaqin murya da Allah ya bata daya dade da sani tun a qauyen dinya,saita kife littafin,ta tafi ta juya miyarta ta kuma dan dana. Fararen idanunta da suka qara girma da gaske ta dinga rarrabawa bayan ta gama dandanar miyar taji da sauran tsami,saita ajjiye ludayin,ta matsa gaba kadan gaban wata locker ta jikin bango dake sama,inda hajiya ta nuna mata nan suke ajjiye kanwa koda akwai buqatar amfani da ita,tasa hannunta ta bude locker tana fatan Allah yasa tsahonta yakai,saboda ta kere mata sosai. Hannunta ta sanya ta laluba sosai,saidai bataju komai ba,saboda gwangwanayen sun shige can ciki,don haka ta duba hagu da damanta ko akwai abinda zata taka takai saidai babu,abinda yasa ta fara yin dage kenan tana tana ta zura hannu amma a banza. Murmushi ya qwace masa saboda yadda yaga tana yin dagen,gami da tsalle duka,ya sauke hannayensa daya rungume a qirji,ya fara takawa a hankali zuwa inda take tsayen. Ko kusa ko alama bataji wani alama na shigowa mutum ba ko qarasowarsa inda take,sabida socks ne kawai a qafarsa,sai dumin tsaiwar mutum da kuma jinginarsa data ji a bayanta,kamar anyi huggin nata ta baya kenan,saidai babu hannunsa guda daya daya tabata illa ya miqa hannunsa cikin locker yana qoqarin dauko mata abinda ta kasa daukowar. Da fari ta tsorata,harma ta juyo da sauri,bugun zuciyarta na sake qaruwa gabanta na faduwa,saidai suna hada idanu sai komai kwance mata,tsoron yayi nasa waje,sai kunya nauyi da gudun zuciyarta wadda taci gaba da harbawa cikin qirjinta da sauri da sauri. Sosai idanunsa suka mata wani irin tasiri,kamar yadda yaji dumin jikinta da tudun bayanta a lokaci guda suna wani ratsashi tare da saukar da wani yanayi a jikinsa,kusan lokaci daya suka sauke idanuwansu,ita ya sauk su qasa tana kallon tiles din kitchen din,shi kuma ya mayar cikin locker din ya fara sauke mata gwangwanayen ciki da daya da daya,kamar wanda cutar kasala ta kama,lokaci guda qamshin man datayi oiling kanta dashi ya cakuda da turaren jikinta yana shige masa hanci. Sai daya sauke mata dukka gwangwanayen sannan yaja baya a hankali yana jingina bayansa da kantar kitchen din "Zabi saina mayar,ko kuma nabar miki su duka?" Ba zata iya amsawa ba saboda yadda jikinta ke dan rawa rawa,ita kadai tasan feeling din daya haifarwa jikinta,irin abinda bata taba jin ya motsa cikin jikinta ba. Da idanunsa ya kafeta sanda take budawa tana duba wanne ne kanwa ke a ciki,yabi hannayenta da kallo wanda ada basu da wani kaurin kirki,amma a yanzu sun ciko sosai,idanunsa suka sauka kan wani abun hannu guda uku dake daure a tsintsiyar hannunta,na dutsune irin dutsen shirin nan shigen na fulani,saidai wadan nan wasu irin masu garai garai da sheqi ne,butter colour ne masu dan girma circle shape. Rubutune a dutsen tsakiya daya kaso hangowa,ya zuba idanu sosai amma bai gane me aka rubuta ba,har zuwa sanda tace "Na gama" da siririyar muryarta,ya qarasa a hankali,saiya kama tsintsiyar hannunta,wanda hakan ya sanyata daga idanu ta dubeshi da sauri,sai taga dutsen yake kallo wanda aka rubuta i'm in love da qananun baqaqen rubutu. Dazu dazu ta siya abun hannun a makaranta,an jima ana saidashi,duk da yadda kuma 'yan ajinsu keta siya bata taba marmarin siya ba,saboda akwai mai sunan samari a jiki da yawa,kowa yana siyan me sunan saurayinsa ne,sai dazu da aka kawo wadan nam design din sukayi mata saita dauka. Yana gama karantawa ya dago suka hada idanu,tayi saurin dauke idonta tana jin bugun zuciyarta na sake ninkuwa fiye da da,wani irin maganadisu idanunsa ke dashi,ta dade da ganin haka,tun ranar daya tsaidata zai shigar da haladu wajenta,abinda ya janyo a sannan ta kasa maida masa maganganun da tayi niyya kenan. Ya lura wanu nauyinsa da kuma kawaici take masa,sai yaqi sakin hannun nata,yaci gaba da kallon abun hannun,a hankali ya sakar mata hannun sannan ya fara diban containers din yana maidawa,hakan ya bata damar yin gaba da sauri ta jiqa kanwar,ta matsa gaban tukunyar ta bude ta zuba,ta juya miyar ta tattabatar komai yayi,saita kasa juyowa sanoda tana da tabbacin yana cikin kitchen din,baisan shi mugun nauyinsa takeji bane?,tanason ta qarasa aikinta ne tabar kitchen din,amma wanzuwarsa a nan ya hanata ci gaba da yin komai. Littafinta na saman freezer din da zai dauki abu,bai kula ba ya bude sai littafin ya fado qasa,ya sunkuya a hankali ya dagashi,zai gyara mata alamar data saka na shaidar inda ta tsaya,saiya buda shafin,idanunsa ya sauka a inda ta saka alamar. Layi hudu ne,amma suna dauke da wasu zafafan kalaman soyayya,da alama sun jima suna dakon soyayyar junansu,sai ranar jarumin ciki yake bayyanawa jarumar soyayar da yake mata. Alamarta ya maida mata,ya rufe littafin ya dora mata a gefanta,sannan ya bude freezer din ya dauko fresh milk da basuyi sanyi sosai ba,yana da buqatar daukan cups,saidai kuma tana tsaye a wajen,hakan ya sakashi takawa,ya sake tsaiwa dab da bayanta,dyk da kusancun baikai na daxun ba amma saida numfashinta ya dauke na wucin gadi. Dai dai sanda ya miqa hannu ta gefan wuyanta zai dauka cup din ya jefa mata tambayar data sanyata diriricewa "Waya koya miki karanta litattafan soyayya?,bakisan koya maka soyayya suke ba?,ko kin shirya yinta a yanzun?" Kalmomin daya gaya mata kenan da suka shige deep inside her da wani irin sound me nauyin amo. Tambayar tayi mata tsauri da yawa,hakanan batasan kalar amsar da zata bashi ba,saita zabi yin shuru "Yaka dade ne,am starving fa,fuska kawai nayi" suka tsinci murya amiru tsakiyar kitchen din,abinda yasa samir ya janye baya a hankali hannayensa dauke da kofunan,ya dubi amiru wanda idanunsa suka hango masa kaltum dake tsaye bakin tukunya,taqi kuma juyowa "Gasunan acici,ka fado waje babu sallama" "Don zan shigo kitchen sai nayi sallama?,wanne sabon salo ne kuma hakan?" Ya amsa masa tana matsawa gaba tare da gocewa gefen saraki daya tsaya a gabansa ya kare masa abinda yakeson ganin "Ashe mana,dole mu zauna da yunwa ashe jawahir ke girki" ya fada da salon tsokana irin wadda sukewa juna lokaci zuwa lokaci shi da jawahir din. Dole ta juyo saboda batason yacu gaba da dauka jawahir din ce "Ina yini" ta fada tana sake takurewa waje daya,tare da Allah wadan rashin fitowa da mayafinta da batayi ba "Oh, sorry.......ashe ba ita bace,kamar kaltum ko?" Ya fada yana nunata da yatsa,saita daga kanta kawai "Ma sha Allah,lafiya lau" ya amsa yana juyawa,saiya hangi samir tuni yayi gaba yama kusa ficewa daga kitchen din,don haka ya juya yabi bayansa,bakinsa fal da maganganu. Tunda ya fito samir din ya karanci maganganu ne fal bakin amirun,don haka yaqi bashi damar cewa komai ma,ya maida hankalinsa ga hajiya qarama dake masa bayanin tanason suje azare qarshen watan nan,fada take musu sosai shi da amiru "Dukkanku zuba muku idanu ai nayi,naji wanda zai fara maganar zuwa a cikinku amma ba'a samu ba,wasa wasa so kuke gaba daya a watsar da zuwa azare,bayan kunfi kowa sannin ammi tana da rai,kai koda bata da rai hakan bame yuwuwa bane,to ku shiga taitayinku da kyau na gaya muku,tunda shi yayan yana kallonku ya qyaleku,saboda haka ku shirya.....bikin salis za'ayi da farida,kuma dukkaninsu 'yan uwanku ne auren zumunci ne,saboda haka zuwa ya kamaku,kowanne ya kammala uzurinsa kafin sannan,ashirin da biyar ga wata nakeso mu wuce dukka harda su jawahir da najwa,uwarsu kuma idan taga zataje taje,wannan ba matsalata bace" can qasan rashi samir ke sakin murmushi yana kurbar fresh milk dinsa,har kwanan gobe dai hajiya qarama ba zata sauya ba,bai taba ganin wani abu data riqa ta kuma qi jininsa irin mummy jidda ba,taqi gaya masa dalili,kuma shima ya kasa ganowa,abu daya ya fahimta,tanayin komai ne akansa da mahaifiyarsa,mahaifiyar data gudu ta barshi,ta zabi ta shiga duniya ta barshi. Jin zuciyarsa ta fara quntata da wannan tunanin yasa ya janyowa hajiyan wata hirar,tunani ne dake sanyashi yanzu yanzu ya burkice,shi yasa ba kasafai yake barin kansa yinsa ba. Babu jimawa kaltum ta fito ya shirya komai,saidai wannan karon gaba daya jikinta lullube yake da wani cotton mayafi mai kyau baqi,ta gama shirya komai ta matso wajen hajiya qarama tana rusunawa "Hajiya an gama" addu'a tayi mata sosai cikin kulawa da yabawa,har zuwa sanda kaltum din ta wuce daki bakin hajiya qarama baiyi shuru ba yaba mata take,mutum ce ita da bata raina ko manta alkhairi komai qanqantarsa "Saraki.....wannan yarinyar....wankan engine akayi mata ne?,kasan rabona da ganinta kwana uku bayan zuwanta garin nan?" "Wa ya sani ne?" Ya bashi amsa yana miqewa zuwa dining inda hajiya qarama ke kiran suzo ga abincin suci "Anya kuwa kana kallonta da kyau samir?,kaga yadda ta canza? black skin din nan ta koma wani beautiful chocolate color?,ba sirantaka,komai nata moderate,baka gani ba wai?" "Ban sani ba!,ba aikina bane wannan observation din, shut up your mouth kaci abinci malam" ya fada masa yana tsareshi da ido Kai ya dauke ya fara zuba abincin,saidai bai iya yin shurun ba "Saifa na fada malam,anya ba akwai abinda ka gano ba a sannan kayimin wuff ka amsha aurenta ba?" Haushi ya cika samir,ya rasa me zaiwa amiru ya huce,dama tun asali ya sanshi,mutum ne da yasa ainihin diri da halittar mace,aka haka yake da zabe zabe da ruwan idanu,a nan halinsu ya saba,kuma akan wannan suke fada,saiya dauka wani qaton saving spoon ya jefi amirun dashi,Allah yasa ua goce,don ba shakka daya sameshi saiyaji babu dadi Kallonsu hajiya qarama data qaraso wajen kawai tayi ta tabe baki "Har yau ku bakusan kun girma ba kenan" zuwanta ya yanke maganar,saidai duk sanda suka hada idanu da amiru saiya karanci maganar bata isheshi ba kenan. Har suka gama cin abincin suka gama hirarsu bata sake fitowa ba,daga qarshe dai yadda amiru yaso kwana gidan bai yiwu ba,saboda daddy daya kira yanason ganinsu,dole tare suka tafi. 48 D/Z Kwanakin da suka biyo baya ta maida hankalinta ne sosai ga jarrabawar da take gabanta,cikin ikon Allah kuma sai ta dinga zuwa mata da sauqi sosai kamar yadda jawahir ta gaya mata,sai abun yayi mata dadi qwarai a ranta. Tafiya azare ta kama,kuma dukka kowa yayi amannar zuwa,har mummy da hajiya qarama bata damu da taje ko kar taje ba,sai gashi kamar ma tafi kowa damuwa da tafiyar,tun kafin ta isa garin kuma ta aika da tata gudummawar mai tsokar gaske ga bangaren gidansu amarya data ango,kamar dai yadda ta saba hidima kan jiki kan qarfi duk sanda wani sha'ani ya tashi daga dangin professor. A satin da za'a tafi a zaren professor ya tako gidan da kansa wajen hajiya qarama,da alama kuma zuwan yana da alaqa da maganar auren samir da kuma bikin azaren. Kaltum kusan itake kula da duk wani baqo da hajiya qaraman zatayi,tunda taji tace yaya rashid zaizo kaltum tayi abinci da abun sha na musamman saboda professor din,hatta hajiya qaraman bata sani ba,sai da yazo sannan taga kaltum din nata shirya masa kalolin abinci "Kina wajen hajiya kenan?" Professor ya fada bayan ya gama amsa kasuwar kaltum dake duqe,hajiya ce ta karbi xancan ma tun kafin kaltum din tace komai "Wallahi yaya,nace ina kuka samo haziqar yarinya haka,bason jiki ba ganda babu qyuya,na dade banji mutumin da naji dadin xama dashi ba kamar yarinyar nan" kada kai professor yayi,shi kansa yana yaba yadda yarinyar ke hidima da kowa cikin,duk da ba zama yake sosai ba amma yana lura da hakan,karon farko da zuciyarsa tayi sanyi da wuri kan wani abu da samir yayi gaban kansa ya aiwatar dashi ba tare da yarjewarsa ba "Ki koma daki ki huta hakanan kinji,kya samu damar duba karatunki,zasu qarasa aikin"cewar hajiya qarama,tunda daya daga cikin masu aikinta ta dawo,dayar kuma ta kawo wadda zata riqe mata aikin kafin ta dawo. Kai ta gyada tana shigewa ciki. Hira sukayi sosa irin ta zumunci ita da dan uwan nata,wanda dama duk sanda irin hakan ta faru yakan jima a gidanta,akwai shaquwa da qauna sosai tsakaninsa da hajiya qamar,daga qarshe ta fadi abinda take ganin ya kamata ya bayar kan hidimar bikin,ta kuma shaida masa ranar da ita zata tafi "Ke kuma sai yaushe zaki tura taki gudunmawar hajjaju,naga jidda wannan karon ta rigaki bayarwa" ya fada yana saka hannunsa a aljihun babbar rigarsa yana ciro kudi. Baki ta tabe tana duban wani barin "Dama haka takeso ace,tayi qoqari,amma ni bana abu don a fada ko kuma saboda gasa,Allah sarki raihana.......har batason ace tayi wani aikin alkhairi,takan ce tayine saboda Allah,kuma shi take bida ya mata sakayya" Wani kallo ya yiwa hajiya qaraman,tayi zaton abunda ya saba shi zaiyi a yanzun ma,saidai ga sabanin tunaninta sai taga ya dauke kai ba tare da yace komai ba,yaci gaba da irga kudaden daya debo din. Miqewa yayi yana ajjiye mata kudin "Wannan ki riqe a hannunki,nasun kuma zan saka a tura musu su cire ta banki" baki ta sake tabewa "An gode,Allah ya qara arziqi ya rabaka da sharrin maqiya da munafukai" ya saba da jin wannan addu'ar daga bakinta,itama kuma tasan cewa an kawo qarshen hirar shi yasa daya miqe ma yana mata sallama ma bata damu ba. Da kaltum hajiya qarama taso tafiya azaren,saidai kuma abun yazo da akasi,don randa xasu tafin ita da yaranta guda uku da jikokinta shida ranar kaltum din tana da sauran jarabawa guda uku,hakan yasa dole hajiyan ta barta suka wuce ita da yaran,da kuma jawahir banda najwa da ita tace sai ana ya jibi daurin aure zata je,ba zata iya zuwa azare ayi sati ba tana da schedules da yawa. Jin cewa samir bazai samu tafiya ba sai ana ya gobe daurin aure tace ta zauna nan gidanta tunda masu aikinta suna nan,ya taho mata da kaltum din itama taga jama'a. Hakan ya yiwa kaltum din,saidai jawahir bataso hakan ba "Don Allah idan kin gama exams kafin ranar ki gayamin,Allah zan yankar miki ticket da kudina ki taho bauchi a ranar" murmushi kawai tayi mata,itakam banda ma hajiya nason taje da babu abinda zata,zatafi farinciki ace qauyen dinya akace taje,taje ta gano ummanta,don a yanzu bata da burin daya wuce haka. Su amiru kuwa washegarin randa su hajiya suka tafi shima yabi bayansu,saboda akwai abota sosai tsakaninsa da angon fiye da samir,don yafi samir ma zuwa azare,hakan yasa professor ya sakashi ya tattaro ya dawo gidan hajiyan,saboda yace kada a bar mata gidan babu wani babba namiji sai masu aiki,dama kuma yana da niyyar hakan,saboda gyara daya bayar ayima sassansa,har mummy na tsokanarsa gyaran me?,shi daya kusa tafiya yabar gidan gaba daya?. Ko daya kaltum batasan yana gidan ba,don ba shigowa ciki yake ba,iyakarsa sassan da suke zama yawancin lokuta shi da amiru idan suna gidan,hakanan da safe yake ficewa sai dare yake shigowa bayan ya gama sabgoginsa. Yau tunda ta tashi takejin mararta babu dadi sosai,duk kuwa da cewa tun sanda ta gama shanye magungunanta dama takejin wani iri a mararta,amma na yau yafi na kullum,a haka ta samu ta rarrafa taje makaranta ta dawo,sai tayi lamo tun la'asar a bargo tana karatun novel tare da daukan darusa masu yawa,saboda jarrabawa biyu suka rage musu,kuma dukkansu masu sauqi ne,bata da wata matsala ko fargaba akansu,hankalinta kuma na rabuwa kashi biyu,saboda yadda mararta ke sake daurewa. Bata tashi ba saida akayi sallar magariba,tayi alwala tayi salla,ta zauna saman abun salla kamar yadda ta saba kullum tsakanin magariba da ishaa,saboda lokacine na amsa addu'a,lazumi take a lokacin,idan ta gama kuma ta duqufa da addu'o'i kan ingantar rayuwarta data iyayenta. Bata tashi ba saida tayi sallar isha'i,daga nan tayi bandaki tayi wanka da brush,kamar yadda yanzu ta sabarwa kanta ya zame mata jiki,ta tsane jikinta tayi oiling gashinta ta hadeshi waje guda tayi masa tufka daya sannan ta dauki wasu riga da wando milk colour masu taushi da kauri da hajiya qarama ra bata su,cikin wasu ragowar tsarabarta zuwanta saudiyya da professor ya kaita shekara biyu baya ranar ta dauko jakar ta gansu a ciki. Tsaiwa tayi tana kallon kanta yadda kayan suka karbeta,ita kanta a yanzu takan jima tana kallon kanta yadda ta sauya lokaci daya,tasan mutane da yawa idan akace musu wanna kattumen da suka sani ce saisun qaryata kafin su yarda ita dince,abu daya ne yake daqila mata farincikinta,idan ta tuna ummanta da kuma habi,ko a wanne hali suke ciki?,ko habi ta haife abinda yake cikinta?,ko ummanta ta warke?,uwa uba kuma idan ta tuna ko zata karade duniya ba zataga dan uwa rabin jiki bilalunta ba,ita dashi sai a lahira,sai taji hawaye sun sauko mata,dukkan wata walwala tata da jin dadinta sun kau. Yau a sanyaye ta koma ta zauna,ta jima a haka tana nazari,kafin ta sanya hannu ta shafi mararta dake sake qulle mata,wunin yau bataci wani abun azo a gani ba,abincinta na rana dana dare tasan duk suna kitchen din a ajjiye,kuma ko yanzu bata jin cin komai,bata da matsalar dafa ko cin abinda takeso,kamar yadda kowanne cikin masu aikin gidan hajiyan batayi masa shamaki da cin abinda ranshi keso ba ta hanyar data dace,babu almubazzaranci babu barna ko ha'inci,tana da kyauta da kyautatawa dukkan wanda ya zauna tare da ita,itakam.kaltum ba zata iya lissafa adadin kyautatawar hajiyan gareta ba,ko diyar data haifa a cikinta iyakar abinda zatayi mata kenan. Komawa tayi ta sake kwanciya tana jawo littafin tana cije labba,wala'alla ko zuwa anjima zata iya jin yunwa ta tashi ta nemi abincin. Yau da wuri ya dawo,don a nan unguwar ma yayi sallar magariba kana ya shigo gida bayan yadan tsaya wajen masu gadi sun dan taba hirar da bata fi minti biyar ba,duj da cewa ba jimawa yake wajensu ba,amma hakan yana musu mugun dadi,ta yadda baya qyamatarsu,ko kuma nuna banbamci ko fifikon dake tsakaninsu. Yana fidda kayan jikinsa yana kiran wayar jawahir,yana sone yaji ina yarinyar take,saboda akwai siyayyar da yakeson mata,ya dade yana son mata wasu 'yan siye siye,saboda ko babu komai tunda har agiyarsa ta hau kanta to dukka sharuddan kulawa yahau kansa a musulunce,to amma baisani ba ko tare suka tafi dasu jawahir din,don baisan taqamaimen ranar da xasu gama jarrabawar ba. Bugu biyu jawahir din ta daga,da qorafi ta fara kamar kullum "Yaya,ban tabajin azare ba dadi ba irin wannan karon,don Allah yaya kaida kaltum ko taho sooner" murmushin daya qawata fuskarshi ya qara mata kyau ya saki sanda yake zare tie din wuyansa "Mr qorafi,babu gaisuwa,babu jin ya nake sai qorafi" "Am sorry yaya"saita fara gaidashi ya amsa mata,yana tambayarta azaren tana bashi amsa,tare da bashi labarin yadda aketa tsara bikin,saboda an dade ba'ayi biki ba a familyn sai yanzu,sannan kuma ma auren zumunci ne tsakanin angon da amaryar. Yana da jumurin sarare,abinda yasa alaqarsu da jawahir keda tsaho da kuma nisa,yasan cewa tana da sauqin kai kamar yadda take da surutu,amma banda daddynsu duk cikin gidan babu mai iya bata attention dinsa yadda takeso,shi yasa yake jumurin biye mata. A handsfree ya saka wayar,har ya gama shanye yoghurt din daya tsiyayo,zuwa sannan ya soma cire socks dinsa saboda wanka da yakeson yi,ya gama jin cewa kaltum din na cikin gidan,saboda haka yayiwa jawahir bayanin zai shiga wanka,ya katse wayar,ya dauki qaramin towel ya shige bathroom din. A hankali ta ajjiye littafin hannun nata,ta miqe ta zauna sosai kafin ta janyo dankwalinta me santsi ta daura akanta. Tunani tayi ta fara samun ruwan dumi sosai tasha ko ruwan lipton ko xata samu sauqin cramping din da mararta keyi,don taga walida qawarta idan tana ciwon mara shi take sha,kuma cikin ikon Allah tana samun relief. Kitchen ta isa kai tsaye,ta samu daya daga cikin masu aikin ta kammala komai,tana daukar cooler din tata abincin,wanda indai ta dauki cooler din ta shiga dakinta kuma saida safe,saboda tana da saurin bacci ne. Dukkansu tsakanin kaltum dasu girmamawa ce ga junansu,da dan murmushin qarfin hali kaltum tace "Har kwanciya baba?" Dariya ta danyi "Tome zan zauna yi,gida babu kowa hajiyarmu bata nan,ai saida safe kawai kaltume....am.....amma ga abincinki nan tun na rana fa banga kinci ba" fuska tadan motsa kadan "Yau banajin dadin jikina ne baba shi yasa" cikin fuskar alhini tace "Ashsha....Allah ya sawwaqe,to ko za'a sanya hasanu(yaron gidan) ya yiwa yallabai samir magana ko dan qaramin dakin shan magani kije?" Kai ta kada tana mamakin dama yana gidan,rabonta da ganinsa tun ranar nan,ranar data tsaye mata a rai,take kuma yawan tuna abubuwan da suka faru a ranar "Ruwan dumi xansha yanzu,ina kuma saka ran zanji dadin jikina" "To....to Allah ya qara afuwa" da haka sukayi sallama,baba ta fice da flask din abincinta. Tana tsaye ruwan ya tafasa,ta dauko cup ta juye ta dawo falo. Tana daga tsaye take surbarsa saboda tana ganin kamar zaifi tsarga mata,tana gab da shanyewa taji motsi kamar an buda qofar falon,saita waiwaya a hankali tana dan jin tsoro ya kamata,duk da tasan cewa gidan cike yake da tsaro,babu wani abu da zai gifto su har nan. A hankali yake takowa cikin parlour din,idanuwansa zube kam wayar hannunsa da yake amsa kiran dake shigowa,wanda handsfree ya sanya mata. Yayi wani sassanyan kyau cikin wasu yellow din Kaya da sukayi matuqar fitar da sigar kyans da kwarjininsa. Idanu suka hada shida ita,nauyin daya zuba ciki nata idanun ta hanyar nutsa nashi idanun cikin nata ya sanya ta janye kallonta,yayin da shi kuma yaci gaba da kallon nata yana ci gaba da amsa wayar. Kamar kowane lokaci da zai dora idonsa akanta,zuciyarsa ta soma masa lissafe lissafe a kanta,baisan yana mata kallon from head to toe ba sam,koda wani ya fada zai iya qaryatawa,maganar amiru ta soma dawo mishi akan canzawarta,tabbas hakane,shima ya gani,ya hango abubuwa masu tarin yawa,kayan jikinta sunyi matuqar amsarta da haskata,baisan yaushe chocolate colour skin ta fara masa kyau a idanuwansa ba,murya can qasa yace "Bye" yana katse wayar tare da sokata a aljihunsa,har yanzun kaltum dake tsaye yake kallo,wanda taci gaba da tsaiwar ne saboda a ganinta sam bai kyautu ta ganshi ba ta kuma wuce,duk da yadda takejinta a takure saboda kayan jikinta,wanda suka bayyana albarkatun qirjinta qwarai,don ta dauka daya daga cikin brasier din da jawahir ta sako mata cikin kayan. "Ina yini" ta fada da zazzaqar muryarta ba tare data juyo ba,sautin ya tafi a hankali cikin kunnensa,yadan rage girman idanuwansa kadan "Kina lafiya?" "Alhamdulillah" ta amsa shi still ba tare data juyo ba,hakan ya bashi mamaki,tsaiwar me take ta bashi baya haka?,idanunsa saman hips dinta na wasu sakanni,saiya dauke kai,yana sake matsawa zuwa inda take tsayen,yana jin a ransa kamar akwai wani abu da take boyewa batason ya gani ne. Koda ya qarasa din sai da yayi dana sanin zuwan,tsigar jikinsa ne ta dinga zubawa,ya dauke idanunsa ta hanyar daukan remote yana lalubar tashar da akace masa yau zasu sanya wasan polo live daga Amsterdam lokaci daya kuma yana bata umarnin "Ki dauko hijabinki kizo muje" babu musu a tsakaninsu,ko wanne ciwo takeji a jikinta ba zata iya masa jayayya ba,don haka ta ajjiye cup din hannun nata da sauri ta juya ta nufi daki,duk da haka sai daya dan bita da kallo kafin ya sake janye idanun nasa yana sakin ajiyar zuciya. Bata jima ba ta fito ta hijabin sallarta har qasa,ta sameshi ya bawa tv attention,da alamu yana jin dadin kallon,saita saci kallon tvn don ganin me yake kallo haka,a iya dan zamanta dasu ta karanci yana son doki da wasan dokin ma gaba daya,duk da haka haka ya ajjiye remote din ya miqe ta bishi a baya. Kamar kowanne lokaci shuru ne ya musu rakiya har zuwa makeken kantin zamani,wanda yake maqare da dukka nau'in kayan amfani. Yadda suke haba haba dashi ya tabbatar mata ba qaramin customer bane,kuma ba qaramin jin dadin zuwansa suke ba da alama,kujera ya samu nan ya zauna,yace ta shiga ta zabi dukkan abinda taga tana so,sai tayi saroro,saboda sam bata taba zuwa ita daya ba,yawanci da jawahir suke zuwa,daga bisani ta fara takawa a hankali a tana duddubawa har tayi nesa da wajen da yake zaunen. Tayi nisa sosai cikin babban kantin amma haka taketa shawagi,ta kasa zaben wani abun azo a gani,saboda kome tayi niyyar dauka sai tayi tunanin me tsada ne,ta qyale kada taje a lafta masa kudi,saboda nan din ta fuskanci komai nasu kudi ne tsububu a cikinsa. "Hey baby" taji an fada daga bayanta,saita waiwaya da hanzari,suka hada idanu dashi yana jifanta da murmushi,matashin saurayine wanda a qiyasce bazai wuce shekara ashirin da biyar ba,sanye da qananun kaya,hannunsa riqe da wayarsa,yana da kyau dai dai misali,hakanan kana kallonsa kasan dan gayu ne "Bari na tayaki zaben,na fuskanci tun dazu kike yawo kin kasa daukan komai" kafin tace wani abu ya karbi dan kwandon hannunta,ya fara duba kayan mata na amfani yana jefawa a kwandon,yana kuma dan janta da hira ta yadda zata saki jikinta dashi. Sannu a hankali ya fara cika kwandon da kayyakin amfanin mata,saita ci gaba da binsa a baya,duk da cewa amsar kowacce tambaya tasa daga eh sai a'ah. Sun kusa qarshen layin da suke ciki,kamar ance ta daga idanu ta hangi samir a tsaye daga qarshen line din kayan turaruka,dukka hannayensa zube a aljihun wandonsa,ya kum tsaya qyam ya raba qafafunsa kamar wani soja,babu digon annuri a saman fuskar tasa,sai idanuwa daya kafesu dashi ita da saurayin........ D/Z 49 Wani mummunar faduwa gabanta yayi,saita dakata da bin saurayin,wanda sam shi baima kula da abinda akeyi ba,saboda ci gaba yayi da tafiya yana zuba kayan,har yakai gab da samir daya soma takowa shi kuma inda take yana ci gaba da kallonta. Gab da ita ya tsaya,taku kadan zai qara su hade da juna,numfashinta kamar zai dauke tayi qas da idanunta,ta kuma qame waje daya tana runtse idanuwanta sanda taga ya daga hannunsa zuwa gareta,daga bisani ta budesu a hankali lokacin dataji motsin daukar cart din dake ajjiye gefanta. Kusan lokaci guda kowannensu ya sauke boyayar ajiyar zuciya sanda ya kama tsintsiyar hannunta ya riqe,ya fara takawa a hankali riqe da ita suka fara daga farkon layin. Mamaki ne ya cikata sanda taga irin kayan da yake zaba,kusan duk abinda ya taba ya daukoshi yayi mata choice dinta ne,kaya yake zubawa kamar baisan mutuncin kudinsa ba,tsoro ya kamata,amma daga bisani saita dan sake data tuna maganar da suka tabayi da jawahir sanda ya taba siya mata wani set na man shafawa "Allah dai ya biya ya saraki,Allah yaci sunansa,ba don yayana bane da tuni nayi wufff da abina,harso nake mu fita shopping dashi,bayajin komai ko meye zaki zaba,ba kamar mummy ba da zata yita mitan zamu qarar mata da lalitarta,yana da kyauta kaman ba gobe,babu ruwanshi" Nauyinsa ya cikata sanda ya sakar mata hannu,ya bata damar ci gaba da zabar ra'ayinta,shi kuma yana tura cart din kamar wani me aikinta,ya ilahi,ta kasa gano ainihin halinsa,wani lokaci kamar zazzafan mutum,wani lokaci kuma sai taga sauqinsa da sanyinsa yayi yawa,har yayi kamarma ba kowa bane shi. Sun gama da inda suke suka shiga bangaren undies,kamar ta nutse a waje taji sanda suke ratsawa ta sakanin panties da braziers,sai ta dinga tafiya da sauri da sauri don sunyi su fice a gun. Danqo hannunta taji anyi daga baya,ta tsaya cak kana ta waiwayo,idanunsa akanta,ya mata nuni da wani abu,saita maida ganinta zuwa abinda yayi mata nunin dashi. Brazier ce a hannunsa,daburcewa tayi tana dauke idonta,bakinta na dan rawa tace "Ni...bana sawa" baisan sanda qaramin murmushi ya qwace masa ba,ya yadda da abunda jawahir ta fada,da gaske pretending takeyi,shi yasa zakayi tunanin bata da komai din. "Wanne size kike sawa?" Dagowa tayi a dan diririce,saiya lumshe idonsa cikin second daya ya bude,saboda wani kyau da yaga sunyi masa a karon farko,sunyi haske sosai,dama can kuma suna da hasken yasan da wannan,amma a wannan karon sun sake kyau saboda girma da suka dan qara yi. Kai ta sake girgiza masa "Bana sa......" Bata ankara ba taji ya fusgota a tausashe,sai gata dan dashi,wanda motsi kadan zatayi ta hade da jikinsa "Idan na auna da hannuna zan gane ai" ya fada yana daga hannayensa,hijabinta taga ya fara tattarawa tare da qoqarin zura hannayensa ciki,batasan sanda ta cafki hannun nasa ba ta riqe,a rude kuma ta gaya masa number din tana jin yadda mararta tayi wani mugun murdawa,da alamu kuma tsoratar da tayi ya kawo hakan. Murmushi ya saki ganin yadda gaba daya ta wani rude,sai ya janye hannayen nasa ,amma duk da haka baija baya ba,saiya qara ma matsowa,hakan yasa ya hade gap din dake tsakaninsu,jikinsa na gogar nata,baisan sanda ajiyar zuciya ta kubce masa ba "Na zaci kinmin qaryar size ne......but ki daina takurewa haka,suna iya lalacewa ko su zube tunda wuri.... brazier is necessary for you tunda kinkai shekarun" Ji tayi inama qasa zata tsage ta shige ciki ta huta,jikinta ya dauka rawa ta rigashi ja da baya tana dafe mararta data sake murdawa kamar ta tsage,har sai data dan sunkuya "Are you okay?" Ya tambayeta muryarsa na shaking kadan,dagowa tayi yana gyada masa kai,saiya juya yana duba size din data gaya masan,ya saka iya yanda ya kamata,tana kallonsa ya hada harda pad. Da qyar take takawa zuwa motar,ta bude seat dinta ta zauna,tana jin sanda ya qaraso shima ya bude ya shiga,baya an saka musu kayan a booth ya tada motar suka fara tafiya,saita cure waje daya,tare da dora fuskarta saman cinyoyinta,tana jin yadda pain ke tasowa daga mararta har zuwa qafafuwanta,wanda dauriyarta ta fara qarewa,harta fara motsi kadan kadan wai ko zataji sauqin radadin. "Are you okay?"ya sake tambaya karo na biyu,bayan ya fuskanci yadda taketa motsawa,saita gyada masa kai,saidai suna gab da isa gida juriyarta ta qare ta soma fidda qaramin sautin kuka. "Marata" ta amsa masa "Ya salam" ya fada yana tsaida motar "Kin gama shan magungunanki?" Kai ta gyada masa "Ok...." Ya amsa yana dauko wayarsa,number din dr labaran ya laluba ya kirashi,cikin sa'a kuma ya sameshi,ya masa bayani "Babu komai,dama hakan na iya faruwa saboda motsawar mahaifa,zata fitar da jinin dake cikinta ne,zan tura maka pain reliever tasha,zata samu sassauci,sai kuma hot or cold water therapy,amma fa,zata iya samun kamar bleeding haka,so she needs somebody else close to her" "Okay dr, thank you for your help" "Ba komai" suka kashe wayar,ya maida dubansa ga kaltum wadda batasan ma bayanin da akeyi ba,saiya tada motar yasa kafin su isa bakin pharmacy din ya turo da maganin. A gaggauce ya karbo magungunan ya dawo ya sake tada motar suka wuce gida,kokaci lokaci yana juyawa yayi mata sannu. Da kansa ya zagaya ya bude mata murfin motar,yadan matsa gefe don ya bata damar fitowa. Kasa motsawa tayi,sabida a jikinta take jin danshi,wanda batasan na meye ba,data duba kadan sai taga kamar jini,don haka ta sauke idanunta qasa,ta kuma kasa motsawa. "Taso" taji ya fada,sai taga hannunshi yake bata,rau rau tayi kamar zata saki kuka,sai kuma ta hadiye ta miqa masa hannun nata a hankali ya dagota,qin motsawa tayi,don tana ji a jikinta ta bata masa seat,tana kuma kunyar ya gani,amma ba yadda zatayi haka ta motsa. Karon farko ya hangi inda ta bacin,saiya sake mata hannu,ya zagaya ya bude booth din ya zaro ledar siyayyar ya sake dawowa inda take tsaye. Tafin hannunta ya sanya cikin nashi ya hade yatsunsu waje guda,abinda yasa wani shock a jikin kowannensu kamar haduwar wutan nefa da ruwa,sai yaci gaba da takawa zuwa cikin gidan sannu a hankali tana biye dashi. *BAYAN AWANNI* A hankali ta bude idanunta daga nannauyan baccin da yayi awon gaba da ita,wanda batasan yaushe ya dauketa ba. Ci gaba tayi da bude idanuwan,har sukayi tarwai,saita dan dakata tana duban dakin,take abinda ya faru awanni uku da suka shude suka dawo mata,ashe komai a gaske ne ya faru ba mafarki ba yadda ta tsammata A hankali ta juyar da fuskarta muhallin daya zauna a dazun kafin bacci yayi awon gaba da ita,wayam yake wajen babu kowa,da alama ya fice ne daga dakin,saita dora hannunta saman shafaffen cikinta zuwa mararta,tana iya jin yadda hannunsa ke yawo har yanzu a wajen,tsigar jikinta ta zuba,saita runtse ido tana girgiza kai,abinda bata taba kawowar faruwarsa ba,wai wani namijin da taba jikinta ba tare data iya hasala komai ba. A hankali idanunta suka doru kan agogon dake dakin,qarfe shida na safe saura minti daya,da sauri ta miqe,saboda yau din suna da jarabawa,kuma qarfe takwas invigilator din zaizo,sai kuma ta tsaya cak tana wara idanu,saboda canjin da taji a jikinta,sai a sannan ta tuna cewa itama yanzu ta fara period kenan kamar yadda sauran mata keyi,hakan yasa ta fara takawa a hankali ta nufi bandaki. Tana gab da qarasawa taji an tura qofar dakin,batakai ga waiwayawa ba,hakanan baikai ga magana ba ta gane cewa shine ta hanyar sassanyan qamshinsa,baice komai ba ya koma da baya,a hankali ya mayar mata da qofar ya rufe mata. Ajiyar zuciya ta saki da taji ya koma din,don nauyinsa ma bazai bari ta iya hada ido dashi ba "Yanzu bakan kalar pant dina da brazier din da nake boye masa duka ya gani,innalillahi" ta fada tana dafe qirji,bayan tayi tsaye a gaban mudubi,saita kauda tunanin,ta fara cire kayan jikinta. Wanka tayo gaba daya,sosai taji dadin jikinta,tana shiryawa tana tuna yadda ya dinga treating nata jiya with care,saidai kuma ya haifar mata da feelings da wasu abubuwa masu wuyar mantawa cikin zuciya,saboda wannan shine karon farko da suka taba zama kusa da juna very close irin haka,wannamn shine karo na farko data taba kallon fuskarsa sosai,fuskar da take cike da kwantaccen saje mai duhu sosai,wanda ya qawata ta ya kuma qawara labbansa masu tudu da suka yiwa fuskarsa kyau. Tsaf ta gama shirinta kamar ba ita tayii fama da ciwo jiya ba,tayi cas cikin uniform din da akullum suke mata kyau kamar kayan gida,tsai tayi gaban madubi tana kallon fuskarta,sai ta sanya hannu tana shafar gefan fuskarta tana jiya yadda yayi.mata jiya,idanunta ta lumshe murmushi yana qwace mata,sai kuma ta bude idanun da hanzari sanda taji alarm na agogon ya buga qarfe bakwai. A kitchen ta samu su baba,suka gaisa a gurguje,ta karbi wani daga cikin breakfast din daya zama ready ta soma karyawa dashi,baban na tambayarta ya jiki tace mata aita samu sauqi,don babu wanda yasan ma ciwon da tayin a jiyam cikin gidan daga ita saishi. Tea din data kurba ya tsaya mata a wuya sanda taji tattausan muryarsa na magana cikin kitchen din,cikin girmamawa baba ke bashi haqurin rashin kammaluwar abincin da wuri "No,no need to worry.....zanyi break a waje" ya furta maganar yana sauke idanuwansa akanta,duk da baya ganin fuskarta yasan cewa itace. Ajjiye cup din tayi,ta juyo a hankali,kallo daya tayi masa tayi qas da idanunta,yau shigar ta fari ce,suit ce wadda ta amsa sunanta three in one,saidai komai nata fari ne kamar yadda shima duk abinda ya saka a jikinsa yake fari,wataqa hakan yana da nasaba da kasancewar ranar juma'a ce,ba qaramin zama shigar tayi a jikinsa ba,itakam ba zata iya cewa ga wasu kaya da ya saka basuyi masa kyau ba,ba tare data bari sun hada ido ba tace "Ina kwana"cikin rusunawa "Lafiya lau" ya amsa mata yana juyawa tare da fadin "Muje na saukeki,ya kirani ya gayamin bazai samu zuwa yau ba" da sauri ta bi bayansa bayan ya fice tana yiwa baba sallama. Cikin motar saukar numfashinsu gami da qamshin turarukan jikinsu,jinta take gaba daya a takure,wani kwarjini yake mata matuqa "Ya jikin naki?" Sai data dan qwato numfashinta sannan ta amsa "Na samu sauqi" shuru na second biyu ya sake cewa "Ma sha Allah,but idan kikaji ko kikaga wani abun daban kiyi magana,yace a gaya masa zai duba" "In sha Allah,na gode" ta furta qasa qasa,kansa kawai ya gyada yana ci gaba da tuqin,amma kuma wani abu yana dawo masa a kansa shima,wanda daga jiya zuwa yau mutuwar jikin da yakeji bata sakeshi ba,har i yanzu babu wani qwaqwwaran kuxari tattare da shi,har ya sauketa makarantar,ta jawo jakarta ta rataya,sai kuma tace dashi "Don Allah inason inje gidan mummy....." Dubanta yayi "Kiyi me?,suma daxu sun tafi azare,su biba kawai suka rage" "Abubuwana na manta nakeso na dauko" kamar ya tambayeta wanne abu sai kuma ya fasa,ya gyada kai yana cewa "Is okay" hannu ya zura aljihun gaban motar ya ciro kudi ya miqa mata,kudin ta kalla ta kalleshi,ta girgiza kai alamun a'ah,yadan matse fuska kadan yana dubanta "Jawahir ta gaya min bakya karbar wani abu cikin kudinki na wajenta....me yasa?" Kai ta kada,tana jin zuciyata na karyewa,duk sanda tatuna da cewa ummanta nacan cikin tsananin buqatarsu,sai taji tamkar taci amanarta idan ta karba tayi amfani dasu taji dadi alhali umman nata nacan a wani hali da batasan wanne iri bane "Ohhhh....na manta fa,bakyason sababbin kudi kudi ko?,to amma fa.....wannan mijinki ne ya baki su ko?" Furucin nasa ya sanyata daga kai da hanzari zuwa gareshi,cikin sa'a suka hada idanu,kunya ta sanyata sadda kai tare da kubucewar murmushin da bata shirya masa ba,sai yaji dadi a ransa,yayi hakanne don yaga murmushinta kuma haqansa ya cimma ruwa,a taqaice yace "Take it" hannu biyu ta saka ta karba "Na gode,Allah ya biya" tayi maganar sanda ya sake kunna motar yana gyada mata kai,ta juya ta nufi ajujuwansu. "Mijinki" kalmar data dinga yi mata amsa kuwwa kenan cikin kunnuwanta,da qyar ta samu ta kori sautin muryar sanda aka gama raba musu question paper ta fara amsa tata. Tana daga dalibai na farko da suka gama amsa tambayoyinsu suka kuma yi submitting,saita zauna daga bishiyar dake gefan ajinsu tana jiran fitowar saliha. "Anya ba umara ko hajji aka biya miki ba?" Ta tsinci muryar saliha daga saman kanta,saita daga kai "Me kika gani?" Kaltum ta tambayeta tana matsa mata wajen xama "Tunda kika shigo aji kike murmushi,yanzun kuma tunda na fito nake daga miki hannu amma baki ganni ba" husna dake tsaye tana maida question paper Jakarta tace "Indai ko hakane wannan sign ne na falling in love wallahi,irin farin shigar nan,kin manta alamunsu ne?,yawan tunanin da yawan murmushi kai kadai?" Dubanta sosa kaltum tayi,maganar husna kusan tafi jan hankalinta,me husna takeso tace?,indai ko ta fahimta wani abu,lallai husna dince tafi cancanta tayi mata tambayar da take damun ranta. 50 DZ Wani littafin ta sake karba wajen salaha,tanaji suna mata tsiya amma batabi ta kansu ba,ita kadai tasan yadda take qaruwa da karatun da takeyi din,wanda ya haska mata abubuwa da dama "Husna muje tare mu taru napep,nima yau mai daukan nawa baya kusa" kaltum tace da husna,saida husnan ta tsaya ta siya agwaluma daga bakin makarantar sannan suka soma takawa zuwa bakin titin "Nikam husna.....wata tambaya nakeson yi miki" "Duk yadda kike ja kaltum?,kece fa kike daukan 1st position a ajinmu duk term" kafadarta kaltum ta daka tana murmushi me kama da dariya "Ke dalla,ba akan karatu bane,wannan karatun kun fini ilimi ta fanninsa" murmushi tayi mata itama tana gyara saqalen jakarta "To ina jinki,ai wai don karki qureni ne" sukayi dariya gaba daya,sannan shuru ya biyo baya,kaltum din cikin ranta tana juya yadda zata gabatar mata da tambayar,tsahon wasu mintuna sannan tace "Asa misali kece kika tashi cikin rayuwar rashin wadata,baki da ilimi kyau ko arziqi,kwatsam sai Allah ya kawo wani kyakkyawan matashi,wanda ya fiki kyau kudi ilimi dama wayewa nesa ba kusa ba,irin nesan nan can can can,kawai tausayinki yasa ya aureki,yazo ya ajjiyeki a gida,ba abinda ke hadaku,kuna zaune kamar yaya da qanwa......" "Wai,wanann shi ake kira da tsintar dami a kala" husna ta katse kaltum na tare data bari kaltum din takai qarshen maganar ba,tana ta murmushi tare da sake bawa kaltum hankalinta. ,ganin yadda husnan ta bawa zancan muhimmanci hakan ya bata nutsuwar ci gaba da magana "A hankali kuna zaune kika fahimci yadda mata ke rububin sonshi,da kika lura da kyau,sai kika gane bayan dukka wadancan siffofi.....yana da kyawawan dabi'u kuma" Hannayenta sama husna ta daga "Wallahi ta fadi gasassa.....wannan mata idan nice sai inda qarfina ya qare wajen janyo hankalinsa ta dukkan wata hanya data dace,duk namijin da ya hada wadan nan siffofin tabbas babu shakka ya isa,ya kuma cancanci a soshi,rasashi kuma babbar hasara ce" maganganun da suka sanya kaltum nazari kenan,tayi shuru tana sauraren yadda husna keta wassafa kanta cikin lamarin har suka qaraso titi. Tsaki yaja a hankali yana rufe file din gaban nasa,tare da dora bironsa akai,ya maida bayansa ya jingina da kujerar yana relaxing a jikinta,kana ga furzar da iska me dumi daga bakinsa,a hankali kuma ya soma juya kujerar daga hagu zuwa dama,daga dama zuwa hagu. Tun daga lokacin har kawo yanzu ya kasa jin qwarin jikinsa kwata kwata,yanajin kowacce jijiya ta jikinsa ta zama weak,ya dunqule hannunsa waje daya kamar wanda ya boye wani abun yana kallon hannun,jijiyoyin dake tsintsiyar hannun sun tashi rada rada,har yanzu yana iya tuno laushi da dumin fatar cikinta,tun a lokacin jikinsa ke shaida masa da matsala,amma burinsa na ta samu relief na pain din yasa yaci gaba da abinda yakeyi. Idanunsa ya lumshe,saiya dinga gano fuskarta wadda bayan ta gama jigata bacci ya dauketa har sai da kanta ya karkace,shi ya gyara mata kwanciya amma har ya gama yabar dakin batasan anyi ba. A hankali aka tura qofar, secretary dinsa ya bayyana yana shaida masa neman izinin shigowa da fawwaza keyi,shuru ya danyi,sam baison hayaniya yau din,a niyyarsa yace ya shaida mata yana da ayyukan da yake dubawa,kuma suna da muhimmanci da kuma buqatar nutsuwarsa,saidai kafin yakai ga furtawa har ya hangi fawwazan tsaye daga bayan secretary din,da alama a shirye take ta shigo koda bai bata dama ba,don haka yace "Ok, let her" ya fada yana tura kujerarsa baya,sannan ya miqe tsaye yana zuba hannayensa a aljihun wandonsa kafin daga bisani ya fara takawa cikin nutsuwa zuwa sashen da fridge dinsa yake. Tunda ta shigo ta kasa zama,ya bata baya amma kallo take qare masa,tako ina samir din yakai namiji,tana jin sonsa yakai mata ko ina cikin rai da rayuwarta,amma ta fuskanci har yau ya kasa gane hakan. A duk sanda zata dauko maganar saiya sako wani abun da zai kauda gaskiya da kuma qarfin maganar a ranta,ta rasa me zata masa ya tabbatar masa da dukkan abinda take fada da nunawa a kansa gaskiya ne?,tun tana ja masa aji da kuma shan qamshi,har ta daina ta sauko,da a tunaninta baiwar kyan da Allah yayi mata da iya gayunta kawai sun isa suja mata ra'ayin saraki,saidai kuma a hankali ta gane cewa tayi bahagon tunani ta kuma canki kuskure. "Have a set" ya furta bayan ya juyo dauke da kwalin lemo da kuma cup yana nuna mata empty kujerar dake gaban table dinsa,saita dauke kanta a hankali ta qarasa ta zauna. Gaban kujerarsa ya tsaya ba tare daya zauna ba yace "Allah yasa lafiya" yana dan kurbar lemon kamar wanda aka yiwa dole,fuskarta fal da damuwa ta girgiza kai "Ba lafiya ba samir,kuma babu lafiyar sam a tattare dani?" Dukka girarsa ya dage bayan ya dakata da shan lemon,abinda yayi masa kyau sosai "Me ya faru kuma?" Kai take kadawa tana hadiye wani abu "Hakafa....haka kullum kake pretending kan cewa bakasan komai ba,baka gane komai ba,bayan na maka bayani basau daya ba basau biyu ba,to yau zan gaya maka baro baro, Muhammad samir sonka nake,ni fawwaza ina sonka" a hankali ya sauke cup din hannunsa saman table din,tabbas yana daga cikin tsarinsa mace tace tana sonshi,irin hakan idan ta faru yasan cewa zai samu dukkan wata kulawa fiye da yadda yake da buqata,gidansa kuma zai sarrafu fiye da yadda yake tunani ko hange,saidai kuma bata wannan sigar da fawwaza tazo da ita ba,abu na farko totally fawwaza batayi masa ba tako ina,sannan yasan waye mahaifinta sarai,bashi da sha'awar hada zuri'a dashi. "Da farko dai nan wajen aiki ne,ba muhalli bane na irin wadan nan maganganun,amma inaso na fara da gode miki kan qaunata da kikeyi,naji dadi na kuma yaba miki,amma ina me baki haquri.....am sorry to say.....na fitar da matar aure,yanzu haka kwanaki kadan suka rage a saka ranar aurenmu,ina mai baki haquri akan hakan,tare da miki addu'ar samun miji na gari" sam batasan sadda ta barke masa da kuka ba "Ya salam.....mene haka?" Samir din ya fada,iyakar qoqarinsa don tayi shuru amma taqi,kuka take sosai tare da fadin dukka abinda yake zuciyarta,har sai daya zauna saman kujerarsa,ya tsiyaya sassanyar lemo ya tura gabanta "Sha wannan sai muyi magana" tana goge qwallarta ta dauka tasha kadan ta ajjiye Cikin siga ta lallashi ya soma magana "Banga abinda zaisa hankalinki ya tashi ba,bayan a cikin maza nidin ba kowa bane,akwai dubban maza da suka fini komai da komai,don na gaya miki hakan ba yana nufin yankewar rayuwarki ba,idan kikayi haquri kikabi komai a hankali sai Allah ya kawo miki wansa ya fini komai da komai....." "Ba ruwana da kowa,ni kai nakeso" ta fada zuciyarta na sake yin zafi . Sake birkicewa tayi gaba daya,daga qarshe ma tana kukan ta zari muqullin motarta ta ficw daga office din,kiranta yake amma taqi saurararsa gaba daya. Ya tabbatar tuqi zata je tayi a hakan,kuma idan tayin a yadda take din komai na iya faruwa,don haka ya koma da sauri,ya dauki wayarsa ya kira umar,ya bashi umarnin ya tabbatar yayi qoqarin settling komai,sannan ya kife wayar ya koma ya zauna yana fidda iska daga bakinsa,hannunsa saman kansa yana shafashi kadan kadan. Ya jima zaune a hakan,kafin yaja qaramin tsaki ya miqe a hankali,yana jin jina qaramar qwaqwalwa da kuma wauta irin ta wasu matan. Dukka abinda yake da buqatar wucewa dasu gida ya tattare ya fice daga office din. Duk da cewa hankalinsa a rabe yake,amma hakan bai hanashi ganin alamun wahalar abu hawa ba,saboda yawaitar jama'a tsaye a bakin tituna,baisan ya akayi ba,saiya tsinci kansa da sauya akalar motarsa zuwa hanyar makarantarsu kaltum,bayan ya duba lokaci. Tsaiwarsu basu rufa minti biyu ba ta hangi bullowar motar,da fari harta dauke kai saboda bata taba kawowa kanta shine din ba,amma sai taji zuciyarta nason tabbatarwa,hakan yasa tadan bi motar da kallo. Sai daya tsaya gabansu ya rage tsayin glass din sannan ta tabbatarwa kanta shine. Da idanunsa ya mata nunin ta shigo,kamo hannun husna tayi,tana sarrafa wanne suna zata bashi wajen husnan,har tayi ta maza duk da batason tafiya tabar husnan kada taga rashin kyautawarta,hakanan batason azarbabin cewa tazo suje tare "Husna,yaya na ne yazo" "Ayyah to sai ranar final kenan?" Kai ta gyada bayan ta mata sallama,ta bude gida gaba ta shiga. Yana zaune sosai kam seat dinsa,ya cire 'yar saman suit dinsa ta farkon da takalmin qafarsa,saidai har yanzu mayen qamshin nan nasa na manne da motar kamar wanda ya fesa turaren yanzu bawai tunda safe ba Taja murfin motar a hankali ta rufe,sannan ta fara gyara rigarta tana dan janta kadan don ta rufe mata cinyoyinta sosai yadda zataji dadin zaman. Dubanta yayi suka hada ido,kowa ya dauke kanshi,ya tayar da motar suka soma tafiya. Ya a faka motar ta fita zuwa cikin gidan,saidai kamar yadda yace dinne babu kowa cikin gidan sai ma'aikata,don haka tana ajjiye jakarta ta soma neman biban cikin gidan,bata ganta ba,saboda haka ta nufi dakinta. Kadan ta tura qofar,sai taji kamar ana kuka,don haka ta leqa da kanta ta yadda zata iya hango cikin dakin. Biba ce,zaune saman carfet,hannunta riqe da hoto,data duba sosai sai taga hoton nan ne dai data saba ganinta riqe dashi,hoton da har yau bata taba katarin ganin fuskar waye ba. A hankali taga ta ajjiye hoton,ta miqe ta nufi bandaki,ta tura qofar bandakin ta shige. Qarasa tura qofar dakin tayi,ta shiga a hankali har ta isa inda biban ta tashi,idanunta suka sauka kan hoton,ta miqa hannu a hankali ta dauka. Kyakkyawar macace wadda a qalla zatayi shekara talatin da takwas zuwa arba'in,wankan tarwada mai dogon hanci da manyan idanuwa,kanta babu dankwali sai qananun kitso da aka yiwa sassalkan gashinta,tana sanye da atamfa dinkin riga da zani,rigar mai kwala ce,irin dinkin mutanen da,fuskarta a wadace da murmushi,har wushiryarta tana fitowa,kana kallonta kasan macace 'yar kwalliya da son ado. Sosai ta zubawa hoton idanu,fuskar na mata yawo a qwaqwalwa,tana jin kamar tasan fuskar,kamar ta taba haduwa da me irin kamannin,amma ta gaza gano a ina?. Motsin fitowar biba ya sanyata saurin tura hoton aljihun rigarta cikin firgici da tsoron kada ta ganta,da murmushi tambayar kaltum din yaushe tazo,tace yanzun nan,tana takawa zuwa inda ta ajjiye hoton gaban kaltum na faduwa,cikin ikon Allah daya daga cikin ma'aikatan ta turo qofar,tace tazo maza mummy ta kira wayar gida tana nemanta,saita dubi kaltum "Muje ki tayani rubutawa,wasu abubuwa takeson a siya mata a baku ku tafi mata dashi" Da to ta amsawa biba,ta kuma bi bayanta gabanta nata faduwa. Sam ta mance da cewa ta taho da hoton,sai bayan ta koma gida,tana hada uniform din xata sanya cikin laundry basket ta zaro shi,komawa tayi ta zauna tana sake nazarin hoton "Tabbas tasan fuskar,ta taba ganinta,amma ba zata iya tunawa a ina ba,to amma ya meye alaqarta da matar da har zatasan fuskarta?,bayan idan bata manta ba,biban ta gaya mata cewa 'yar uwarta ce data rasu,wadan nan abubuwa biyu yasa ta saddaqar bata santa din ba,saita cusa hoton qasan pillow dinta,ta gama dukka shirin kwanciyarta,saita janyo ledar da saraki ya bata a dazu bayan ya sake dakkota daga gidan mummy sun dawo gida. Murmushi ta saki bayan ta gama kallon kazar,saita tuna sanda hannayensu suka hadu waje daya sanda yake miqa mata kazar,ita ta fara zare hannunta saboda wani yarrr dataji,saiya aje mata ledar daga gefanta. Gasashshiyar kaza ce da chips a ciki,kadan taci ta rufe,ta kwanta,tun tunani kala kala na bijiro mata har bacci ya saceta. _DUNIYAR MAFARKI_ Sannu a hankali take takawa cikin sanda tsakiyar hanyar dake dauke da dakuna hagu da dama,hanyace mai duhu sosai,sai wani dan siririn haske data hangowa daga can gabanta kadan. A hankali take dosar hasken,harta cimmasa,qofa ce yar siririya sosai,sai taga kamar jikinta bazai iya shiga ta qofar ba,don haka ta koma ta window,tayi dage ta leqa cikin dakin,fetal hake dauke da gado guda daya,sai wata mace dake zaune kanta a qasa,kamar matar tasan ta tsaiwarta a wajen ta daga kanta a hankali tana yaye rufin mayafin data lullube fuskarta dashi,sai suka hada ido. Tarwai taga fuskar matar,kamar matar rannan ce,ta sake duban dakin,kamar dakin rannan ne shima,saita maida kallonta ga matar,sai taga ta zuba mata idanuwa qurrrr,wanda daga bisani kuma hawaye ya fara fita daga idanuwan matar shar shar babu qaqqautawa,a hankali kuma sai hawayen suka fara canza kala kamar kalar jini,ta miqe a hankali matar ta tako zuwa inda take tsaye hawayen naci gaba da fita daga idanunta. A bakin window din ta tsaya,ta daga hannunta ta dorashi saman nata hannun,take kaltum taji wani irin sanyi yana shiga jikinta ta kowacce gaba dake jikinsa. Ci gaba da kallon juna sukayi ita da matar,ta bude baki tana magana amma kaltum din bata iya jin abinda take fada,gashi dai a haka bakinta yana motsawa sosai,magana takeyi amma bata iya jin koda harafi guda "Kaltum!!!" Taji an qwala kiran sunanta daga bayanta,sai tayi maza ra waiwaya,mummy ta gani tana nufota da sassarfa,sai taji ta zame daga dagen da takeyi,data daga kai kuma sai taga babu wannan matar daga gabanta,babu komai a gabanta sai wani mutum dake tsaye,shi kuma bata iya ganin fuskarsa sai bayansa "Samir!" Taji bakinta ya kira da mugun qarfi,wanda sautin kiran ya shiga kunnenta ya kuma farkar da ita daga nannauyan baccin da ya dauketa. A mugun firgice ta tashi,zuciyarta na bugawa da sauri kamar wadda tayi tsere,haki ra fara yi tana maida numfashi,qirjinta yana dagawa,ta fara bin dakin da kallo,babu abinda ya canza,yadda ta kwanta haka komai yake,hatta qwan fitilar da bata kashe ba yana nan a hakansa a kunne "La'ilaha illal lah,wahdahu la sharika lah,lahul mulku wa lahul hamd,yuhyi wa yumitu wa huwa ala kulli shai'in qadir" ta dinga maimaitawa qasa qasa a hankali. Sannu sannu taji nutsuwarta na dan dawowa,tasa hannunta a hankali ta zame dankwalin kanta saboda gumin da takeji,maqogoronta ya bushe sosai,don haka ta zame daga gadon da niyyar sauka,hakan yasa pillow din data tada kanta dashi ya biyota saboda santsin zanin gadon. Duqawa tayi ta daukw pillow din,idanuwanta suka fada kan hoton data cusa anan kafin ta kwanta,idanu ta zuba masa sosai,kamar yanzu ta fara ganinsa,take jikinta yayi sanyi ta koma dirshan ta zauna,saboda sak kamannin matar da tayi mafarkinta a yanzu su take ganin a wannan fuskar dake jikin hoton "WACECE ITA?" Tambayar data yiwa kanta kenan,wadda bata da amsarta,batasan ma inda zata samu amsar ba,tabbas!,akwai wata a qasa,wannan hoton shike saka biba kuka,kukan da biban tace matuqar ta gayawa wani tana yinsa to rayuwarsu na cikin barazana,barazana a wajen wa?,wa zata tambaya ya gaya mata wacece wannan matar?,meye hadin mommy da ita har da zata bayyana cikin mafarkinta?,me yasa suna sa siffar samir suka fito cikin mafarkin?,kukan me matar takeyi bayan biba tace mata ta mutu?. Miqewa tsaye tayi wani abu na dawo mata,dakin dataga matar shine dakin dataga wannan matar randa ta raka mommy gidan masu tabin hankali,saita sake kallon hoton da kyau,da matar data gani a asibitin mahaukata,da matar data gani a mafarki,da matar dake jikin wannan hoton kamarsu daya,tabbas kamarsu daya,saidai banbancin shekaru,amma suna tsananin kama,to me kenan?,meye wannan?,su wadan nan matan su waye su?. 51 D/Z Tana sake matsawa kanta da tambayar tana sake jin maqogoronta yana bushewa,wanda ya sake tabbatar mata da cewa ruwa take da buqatar sha,cusa hoton ta kuma yi qasan filon,ta miqe jikinta na rawa a hankali cikin sanda ta doshi falon. A hankali ya murda qofar falon ya turata kana ya shigo,jikinsa ko ina yana fidda zufa saboda mafarkin da yayi,babu abinda yake da buqatar sha illa ruwa,sanda ya niyyaci shan ruwan,saiya taras babu komai a fridge din sashen sai drinks,wadanda ba zasu kashe qishirwar da yakeji ba sam. Idanu ya zuba mata daga nesa cikin mamakin ganinta a dai dai wannan lokacin,duk da cewa babu wadatar haske sosai a falon amma ya ganeta sosai,baqin gashinta daya ware ya sauka a bayanta yanata qyalli,ci gaba yayi da takowa a hankali yana nannade hannayen rigarsa ko zaiji raguwar zufar dake sauka a jikinsa. Da hanzari take zuba ruwan cikin cup tana daga tsaye a bakin fridge din bayan ta budeshi,alamun takun sawayen da taji ya sanyata firgita sosai,hakan ya sabbaba mata tsoron daya tilasta ruwan da robar faduwa gaba daya a qasa ruwan ya soma malalala a qafafunta,sannan ta waiwayo tana duban bayanta. Fararen idanunta sun fito tarwai wadanda suka cika da tsoro,tsoron daya bashi mamaki,saiya qarasa gabanta a nutse,ya sunkuya ya dauke ruwan kana ya dago yana duban tsakiyar idanunta,fuskarta tayi wani fayau, fresh babu komai saman fatarta,gab suke da juna har suna iya musayar numfashi,still yana kallonta a tausashe muryarsa can qasa maqoshinsa yace "Wannan tsoron fa?" Qas tayi da kanta tana son dai daita kanta,tana kuma jin nauyin yadda yake tsaye gab da ita,ta fahimci kuma idanunsa na yawo ne a kanta,har zuwa qirjinta da maballan rigarta guda biyu na sama suke a bude,hakan ya bawa qirjin nata damar fitowa kadan ta saman Ganin ta kasa cewa komai saiya dauki wani cup din daga saman fridge din,a hankali taji ya kama hannayenta,ya sanya mata cup din a hannu days,daya hannun kuma robar ruwan bayan ya budeta,dora hannayenshi shima yayi saman nata hannayen,ya tayata riqe cup din da robar ruwan,suka fara tsiyaya ruwan a tare,kowannensu idanunshi na ka robar da cup din,saidai kowa da abinda zuciyarsa ke saqa masa. Sai daya cika shi da ruwan sannan ya tayata daga cup din zuwan bakinta ta hanyar ci gaba da dafe bayan hannunshi cikin tafi hannunta,a hankali take aika ruwan daga bakinta zuwa maqogoranta cikin wani yanayi,sanyin ruwan na kai mata ko ina,jikinta na mutuwa saboda wanzuwarsa a wajen. Rabi tasha tadan janye shi daga bakinta,ta tsammaci zai sake mata hannu ne amma sai taga ya sake sauke hannun nata tare da sake zuba ruwan ya kuma cika cup din,wannan karon bakinsa yakai ruwan,ya fara sha shima a hankali, Adams apple dinsa na sama da qasa,yayin da idanunsa masu haske da girma ke zube cikin nashi,qas tayi da kanta,tana ji ya gama shan ruwan,ya zare hannunsa cup din da kuma gorar ruwan gaba daya ya ajjiye. Bata ankara ba taji ya kama tsintsiyar hannunta,haka kawai.mafarkin ya birkita shi,yaji yana da buqatar wani abu da zai daidaira bugun numfashinsa,yana buqatar wanda zaiji yadda zuciyarsa take bugawa,sai ya sake taku sosai ya hade jikinsa da nata,hakan bai masa ba,sai daya dora qafafunta saman nashi,hakan ya qara mata tsaho,sai taji ya zagaya hannayensa zuwa bayanta ya rungumeta gaba daya cikin jikinsa. Qamshin turarensa laushin fatarsa da dumin dake fita daga jikinsa da kuma ba zatar da yayi mata yaso tafiya da numfashinta gaba daya,bugun zuciyarsu ya cakuda waje daya,kowanne a cikinsu yana iya jin yadda zuciyar dan uwansa ke bugawa da wani irin gudu. Numfashi mau nauyi ya dunga saukewa ajere,a hankali a hankali har zuwa wani lokaci,cikin jikinta ta karan kanta ta dinga jin wata nutsuwa,kamar yadda shima nutsuwar ta dinga ratsashi ta kowanne sassa na jikinsa,nutsuwar da bai taba jin kamarta ba duk sanda yayi irin wannan mafarkin "Me ya tsorataki?" Ya kuma jefa mata tambayar cikin wata murya dako a falon kake baka isa kaji abinda ya fada ba,saboda wani feelings dake tsarashi,yana iya jin tudun komai na jikinta a jikinsa "Mafarki nayi" "Na umma?,ko na bilal?" Tambayar data sosa mata wani tabkeken miki dake danqare a zuciyarta,wanda dare da rana taketa qoqarin ganin ta sayashi,kiran sunan da yayi ya shiga sosai cikin kunnenta,ya kuma motsa zuciyarta,duk da mafarkinta bashi da alaqa da umman,amma sai taji a take hankalinta ya karkata zuwa gareta,hakan ya bawa hawaye damar taruwa cikin idanunta,cikin qanqanin lokaci kuma suka fara sauka saman fuskarta. Batasan yadda akayi ya fahimci ta soma kuka ba,saidai hannunsa data ji saman fuskarta yana share mata,batasan cewa yaji sauyin fitar numfashinta da bugun zuciyarta ba,yana sharemata yana runtse idonsa,akwai wani abu daya sanyashi ya zama qwararre wajen gane fitar hawaye ba tare daya kalli fuska ba matuqar a jikin mutum yake,hawayen AMMAnsa,daya daga cikin abinda yasa ya tsani kukan mace,abu guda daya dake sanya rauninsa bayyana. Yana da burin kaita gida,a yadda aqarta take da yan uwanta da mahaifiyarta yasan cewa tayi namijin qoqarin zama har zuwa wannan lokacin bataga kowa nata ba,bayan an daukota a lokacin da take tsaka da jinyar rashin dan uwanta,to amma a wanne matsayi take?,wacce amsa ce gareshi na matsayinta a wajensa?,MATA KO QANWA?. **********Tunda drivern ya daukota takejin wani farinciki cikin ranta,kammaluwar jarabawarta cike da alamun sa'a da nasara,nan bada wani jimawa ba zata tsinci kanta a ajin qarshe na secondary,abinda bata taba mafarkin kasancewarsa kaf tsayin rayuwarta,tafi mafarkin gata can gidan nasuru,gatacan a matsayin matar nasurun,sai gata yau cikin wata mota da take hange a baya daga can qololuwar nesa,bata taba sha'awar hawanta bama saboda tasan ba zata hau ba. Abu daya ne a yazu yake dan motsa mata,daga sanda ta fara karatun litattafan nan ta gane meye aure?,meye ma'ana da manufar aure?,tun daga ranar daya fara rungumeta cikin jikinsa yabar mata wani abu,ya kuma dauki wani abu daga zuciyarta yayi gaba dashi,to amma ta ina zata fara yaqi da qoqarin karbarwa kanta matsayinta?,wannan shine matsalar da takeji lokaci zuwa lokaci tana motsi a zuciyarta. Yana tsaida motar ta fito zuwa cikin gida,tana da masaniyar gobe zasu wuce azare kamar yadda ya shaida mata cikin wancan daren data yi masa kyakkyawar ajiya a zuciyarta,don haka tana son hada komai nata aka tsari,ta ciri kayan da take da buqata cikin siyayyar da yayi mata wancar ranar. Ta saba duk sanda zata shiga waje tayi sallama koda babu kowa,yauma sallamar tayi,duk da tasan mawuyacine ta samu masu aikin cikin falon. Ga mamakinta sai taji an amsa mata,abinda ya daure mata kai kenan,ta maida dubanta ga wajen da taji an amsata din,sai suka hada ido da mubina tana sakar mata murmushi "Sonshi nake da gaske jawahir,ko zaki taimaka min?" Kalaman mubina a ganinta da ita na qarshe ya dawo mata,hakanan taji yawan farashin fara'ar da takeson maida mata ya ragu,yaqe taji tana mata,amma duk da haka saita dakata suka gaisa kamar yadda suka saba "Hajiyan suna azare gaba daya" kaltum ta gayawa mubina tana miqewa bayan ta dauki takardunta "Eh na sani,ai har mama itama tana can,tare suka tafi,kinsan mama aisha kishiyar yayata ce,ni kuma a hannun yayar tawa nake" dan dubanta kaltum tayi ta gyada kai kawai "Dama ba wajen hajiya nazo ba ai wannan karon....wajen ya saraki nazo,ancemin yana gidan nan ko?,na taras ana masa gyara ta can bangarenshi na gidan daddy professor" "Eh.....bari na qarasa ciki" kaltum ta amsa mata a gaggauce kawai,wanda sam mubinan bata kula ba,saita miqe "Tun dazu nake zaune ba abokin hira,tunda kin dawo muje tare,na samu abokiyar hira" bata hanata ba kamar yadda batace mata komai ba,ta bita a baya tana mata surutu,nata eh ko a'ah. Da suka shiga dakinma bayan ta aje jakarta bandaki ta wuce,sai tayi tsaye gaban mudubi tana kallon smoothy skin dinta cikin dan qaramin hijabin makaranta dake jikinta,fararen idanunta take kalla tana son gano ko akwai wani abu daya bayyana cikin idanunta?,wani abu take ji ya tokare mata wuya tunda taji me mubina ke fadi?,to me kenan hakan?,tana da tabbacin mubina batasan wace ba ita ba,batasan alaqarta dasu hajiya qarama ba,hakanan batasan matsayinta a wajen muhammad samir ba. Kayanta ta cire kawai gaba daya tayi wanka,ta fito,tana shiryawa mubina na janta da hirarraki,tana da zaton akwai dangantaka tsakanin kaltum ne dasu jawahir,dangantakar da zata iya taimaka mata ta samu waje a zuciyar samir. Koda ta gama shiryawa ma hada kayanta ta fara yi,har zuwa sannan mubina nata binta da hira,ita kuma tana qoqari qwarai wajen amsa mata ba tare data yarfa ta ba,duk da zuciyarta na mata wani iri babu dadi. "Wai tare zaku tafi?,ai kuwa inajin dani za'ayi tafiyar nan" mubina ta fada tana dariyar jin dadi,murmushi kawai kaltum tayi mata,saita miqe daga aikin tana dosar qofar fita tayi kitchen. Ba kowa a kitchen din,da alama sun gama aikinsu ne sunfice,tasan tazarce sukayi abincin,haka suke yawancin lokuta da hajiya qarama bata nan,sai taji sha'awar shirya masa abinci,don tunda yazo gidan bataga ya zauna yaci wani abincin kirki ba,hakan ma zai taimaka mata ta rage lokacinta sosai,ta kuma rage zangon hirarta da mubina. A nutse ta fiddo komai ta fara aikinta cikin nutsuwa,cikin wani yanayi me burgewa na tsafta da sanin makamar aiki. ,bata jima da farawa mubina ta biyota,ta sanyata a gaba da hirar da sam ita bata jin armashinta. Har ya gota sassan hajiyan qaraman sai ya dakata saboda jin qamshin favourite food dinsa,da baya ya koma a hankali yake takawa zuwa ciki,fuskarsa na ga fuskar wayarsa sanda jauhar ke kiransa,ya maidata silent ya sanyata a aljihunsa,kwata kwata baya qaunar wannan nacin kiran nata ko yaushe ba tare da wani specific time ba,baisan me take nema haka dashi ba. Sallamarsa qofar falon tayi dai dai da qaruwar bugun zuciyarta,ta daga kai daga yanka lettuce din da take tana taya mubina da tuni ta saki hirar ta maida hankalinta kanshi amsa sallamar da yayi "Ya saraki....sannu da zuwa" mubina ta fada taba murmushi gami da miqewa tsaye "Yauwa,ya kike?" Ya tambayeta a gajarce,idanuwansa nakan kaltum dake kallon qasa,dankwalinta ya zame kadan,kwantaccen gashin gaban kanta ya fito sosai saman chocolate colour skin dinta "Sannu da zuwa" ta fada tana qoqarin dai daita heart rate dinta ba tare data iya duban idanuwansa ba "Yauwa,sannu" ya fada yana duban kitchen din,alamu sun nuna masa cewa itace keyi girkin,agogon hannunsa ya kalla "Ana gama sallar magarib a kawomin abinci" ya fada yana lalubar qwayar idanunta da taqi bari ya gani "Tohm" ta amsa mishi a tausashe,saiya juya yana niyyar barin kitchen din,da sauri mubina takai hannu xata karbi brief case dinsa "Ya saraki....kawo na tayaka mana" Batasan ta daga kai ta dubi sashen da suke ba saida suka kusa hada ido da samir,saita sauke kanta,tana jin wani abu na matsar zuciyarta,kunnuwanta naga amsar da xaya bata "Nop,na gode" ya amsa mata yana yin gaba,binsa da kallo mubina tayi,saita koma da baya ta zauna jikinta na mata sanyi,kada fa ace sauqin kan da take hanga tattare dashi ba haka bane?. Tun sanda suka baro kitchen din kowanne a cikinsu kuzarinsa ragagge ne,ga kaltum bata da tabbacin abinda ya sanya yanayin jikinta sauyawa,saidai tana jin zuciyarta da gangar jikinta duka babu dadi,hakanan ta kasa sakewa da mubina. Mubina kuwa hasashenta daya ne,a yau din ta shirya ta kuma tattara dukkan wani qwarin gwiwarta na fuskantar samir din,a yau ta shirya shaida masa abinda yake cikin zuciyarta,durqusawa wada ba gajiyawa bace,matuqar zata samu samir a matsayin mijin aure zata iya aikata dukkan wani abu da bai taka kara ya karya ba irin wannan,bai kuma kasance kauce hanya mabayyaniya ba. Tana saman abun salla bayan ta idar amma tayi nisa a tunani,maganganun saliha ke dawo mata tar a kwanya tun daxu,idan itace da miji irin samir kenan sai taga abinda ya turewa buzu nadi?,ita din zata iya itama kamar yadda saliha tace?,wannan tamkar tunkarar wani babban yaqi ne wanda batasan ya tsakiyarsa zata kaya ba,qarshensa dama nasara ce ko akasinta,batasan wanne matsayi take dashi ko ta taka a zuciyarsa ba bare ta dora daga nan,tafi kowa sanin yawan 'yamnatan dake qaunarsa suke kuma farautar soyayyarsa,tun kafin ta soma jin cewa itama ya kamata ta tabbatarwa da kanta matsayinta a wajensa,tana ji da ganin komai daga wajen jawahir,wani lokaci ita kanta jawahir din takan qi daga wayar wasu da dama daga cikinsu,wadanda ke kamun qafa da ita,to amma idan ta saddaqar.....hakan na nufin zai auri wata a gabanta kenan kamar yadda ta soma jin qishin qishin?,haka na nufin warwarewar igiyar aurensu kenan?, Ta koma ta auri wani?,idan kuma qudurinta ya tabbata fa?,ta yayq zai kalli idanun family dinsa ya shaida musu cewa ita din matarsa ce daya aurota a wani qauye waishi dinya ba tare da sanin magabatansa ba?,idan maganar ta fito waye da waye zai amsheta?,waye kuma zai mata mummunan kallo da mummunan fassara?. Samun kanta tayi da runtse idanunta sanda sunan mommy da najwa ya darsu a ranta "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" labbanta suka motsa a hankali,kalmar ta kwarara cikin zuciyarta,sannu a hankali kuma hancinta ya cika da qamshin turaren data tabbatar a zahiri take iya jiyoshi,kafin kuma fa bude idanun nata muryar mubina ta cika kunnuwanta. "Kaltum da magariba fa yace akai masa,nidai a ready,ki debo kayan na tayaki kaiwa,dama inason muyi magana dashi" a nutse ta daga kanta ta sauke ga mubina dake gaban mudubi tana sake fesa turare baya wancan data fesa,wani abu ya matse zuciyar kaltume,amma saita aro jarumta ta miqe tana nannade abun sallarta ba tare data cewa mubina komai ba ta fice izuwa kitchen. Tana tsaka da harhada kayan abincin mubinan ta shigo,tayi shar cikin wani riga da skert da yadin material na mata me sulbi,sai baza qamshi take kamar tayi barin turare. Ita tayi uwa tayi makarbiya ta amshe kwandon kayan abincin,kaltum din najin wani abu me kama da haushi yana son sauka a zuciyarta ta sakar mata kwandon,ko banza ita din macace,ya kamata kuma ta mutunta tare da martaba darajarta da mutuncinta na diya mace,bata tanka mata surutanta ba ta dauki flask na tea data hada masa ruwan zafin da bata da tabbacin zaisha tunda batasan zabinsa ba ta bita dashi. Sanya yake da fara qal din long sleeves shirt,wandon jikinsa ash ne me turuwa,wanda iyakacinsa qauri,sun sameshi zaune da jibgin files a gabansa da alama aikin office ne ya deboshi zuwa gida,waya yake amsawa,amma idanunsa na kan qofar sanda suke shigowa. Amsa sallamar mubinan yayi yana mamakin shigowarta sashen,saidai kafin ya dauke idanunsa ya hangi kaltum daga bayanta,sanye da madaidaicin hijabi light blue,wanda ya haska zagaggayar fuskarta,ya kuma qara fito da hasken qwayar idanunta. Duk da amsa waya yake amma yana karantar sanyi cikin yanayinta,daga sanda yaji karatu akan girman amana gaba daya hankalinsa ya sake karkata a kanta,yana jin ashe wani babban nauyi ne akansa daya kamata ya bashi dukkan wata kulawa iyaka qarfinsa. Ya gama wayar ya katseta yana ajjiyeta gefe,yana daga kai suna hada ido da mubina,saita saki murmushi tana sunkui da kai ita dole taji kunya. Bai kula da wannan ba,ya fara janye hannun rigarshi zuwa baya tare da lanqwashe qafafunsa sanda take aje masa abincin a gabansa "Sannu" ya furta can qasa,yanayin da sautin maganar ya fito ya tilasta mata daga kai ta dubeshi,saboda yayi maganar ne tamkar me rada. Fridge ta nufa da niyyar dauko masa ruwa,sai yace "Dawo nan ki zauna....jeki cikin gidaki daukomin ruwa mara sanyi" yace da mubina. Dadi ne sosai ya rufeta,ta miqe da saurinta ta nufi qofar fita,saiya maida dubansa ga kaltum dake laluben wajen zama "Dawo nan" ya fada yana nuna mata gabanshi,a sanyaye ta dawo ta zauna din inda yace mata,duk da cewa zaman kusa dashi irin haka ya mata nauyi amma ba zata iya kaucewa umarninsa ba "Mene yake damunki?" Ya jefe mata tambayar yana bin fuskarta data dan cika ta murje da kallo kusan irin na qurilla,dan mitsitsin bakinta yana motsawa kadan kadan, Tambayar ta isketa a bazata,don bata zaci jin haka daga bakinsa ba,saita girgiza kanta "Babu komai" ta amsa mishi,baice mata komai ba sai yaja abincinsa ya fara ci,ba jimawa mubina ta shigo da ruwan,hakan yasa kaltum miqewa tana neman izinin tafiya,don bata jin zata iya zama mubinan tayi maganar da take da qudurin yin a gabanta. "Ki jirata ku wuce tare....uhmmm,ina jinki" samir ya fada duka lokaci daya. Bai fasa cin abincinsa ba sanda take koro bayanta cike da kunya da kuma ɗar ɗar,saidai ya kafeta da manyan idanunsa,zuciyarsa cike fal da mamaki,yana kuma qoqarin danne mamakin da kuma dariyar data bashi har ta kammala bayananta. Abincin ya aje gefe yana kallonta,ya karanci mata wani bin duka tunaninsu iri daya ne,basa kallon abubuwa a yadda suke,sau tari komai suna kallonsa a baibai a maimakon zahirin yadda yake "Shekarunki nawa?" Tambayar data jita banbarakwai,saita tsargu,ta saci kallon kaltum,wadda tunda ta sunkui da kanta bata dagashi ba "Sha....sha,ashirin" yadda ta bashi amsar ya tabbatar masa ta dan qara wani abu akan ainihin shekarunta,murmushin gefan baki ya saki "Karki bari matata ta san ainihin abinda kike nufi ko fada a kaina,if not kuma.....saita zaneki,ku tashi kuje ku kwanta,gobe akwai tafiya a gabanmu" daga haka ya balle murfin ruwa ya soma sha a nutse. Tuni kaltum takai qofa,saboda amsar daya bayar tamkar saqo ne zuwa ga mutum biyu kenan,wacece matarsa?,me kuma hake nufi da ita,mema maganarsa gaba daya ke nufi?,wadan nan sune ire iren tambayoyin data kwana tana yiwa kanta. Tana iya jiyo kukan mubina bayan ta gama gayama kaltum din cewa "Me yasa ya dauka abinda nake gaya masa bada wani muhimmanci ba?,bayan ni ina gaya masa saqo ne mai muhimmanci?" Ba zata iya cewa da ita komai ba,don itama ta kanta take,har ta gama maganganunta ta barke da kuka,tun tana jin kukan mubina har taji shuru,da alama tayi ta gaji,ko kuma bacci ya dauketa,saita sauka a hankali ta zura qafafunta qasa tayi bandaki. Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana ture ayyukan dake gabansa,duk yadda yaso ya tilastawa kansa yin aikin abun ya gagareshi,fuskar kaltum din yake hangowa sanda mubinan ke isar mishi da saqon,yana sane ya zaunar da ita,akwai abinda yakeson gani da kuma karanta daga gareta,saidai kuma iya zamanta da tashinta taqi bashi damar komai. Mirginawa yayi ya koma rub da ciki,yana tallafe fuskarsa da tafukan hannayensa,gami da lumshe idanunsa,yana jin yadda sukayi masa nauyi saboda baccin da ya cikasu,amma zuciya da qwaqwalwarsa sunqi bashi hadin kai. Saidai shi bacci ba'a ci masa bashi,kamar yadda ba'a qayyade masa lokacin yinsa,a hankali idanunsa suka dinga rufewa har sukayi nauyin da bazai iya budesu ba,ya lula duniyar bacci. *_DUNIYAR MAFARKI_* A firgice ya farka,saidai bakinsa dauke da addu'a,a hankali yake karanto addu'o'in da ma'aiki ya bayar ga duk wanda yayi mafarki mara dadi,saiya miqe ya nufi bandaki,idanuwansa na haska masa fuskar mahaifiyarsa da yake gani tsugune a gefansa,tana kuma masa nuni da mahaifinsa dake tafiya zuwa wani wawakeken rami wanda wuta ce fal keci a cikinsa. ******Babu wani cikakken kuzari a jikinta take qarasa hada jakar kayanta,banda hajiya qarama da jawahir da suka damu da zuwan nata da babu inda zata. "Ya na ganki a zaune?" Kaltum tayi qarfin halin yiwa mubina magana sanda ta dauki jakarta bayan samir ya aiko a shaida mata ta fito,kaita girgixa qwalla na sauko mata "Bani da nutsuwar da zan iya binku,saikun dawo" bata iya ce mata komai ba ta soma takawa tana ficewa,mafarkinta na jiya na sake tsaya mata sosai a rai,duk kuwa da cewa kusan maimaici tayi na abinda ya faru a mafarkinta na wancan karon,amma abun sai ya tsaye mata a rai fiye da wancan. Ga hoton matar har yanzu a wajenta,amma bata da wanda zai gaya mata wacece ita?,ta kasa fassara ma'anar yawan ganinta da takeyi cikin barcinta,saidai a yanzu zuciyarta ta karkata da zuwa gidan masu lalurar tabin hankali taje ta ziyarci matar data gani a gidan,wadda take mata kama da.matar dake zuwa mata a mafarki,duk da cewa waccar ta gida masu lalurar tabin hankalin shekarunta sunfi na wadda take cikin hoton da kuma wadda take gani a mafarkin tsufa........ 52 D/Z Tunda ta tunkaro wajen ya gaza dauke ganinsa daga kanta,karon farko daya soma ganinta cikin shiga irin wannan. Abaya ce a jikinta baby pink mai sulbi mai kuma hawa biyu,wadda ta wadata da adon baqaqen duwatsu masu wani irin walwali da sheqi,duk da cewa shiya siyo kayan,amma ba tsammaci zasu karbeta har haka ba. Yayi tayi rolling mayafin ya baiwa gaban gashinta mai santsi damar fitowa,idan ka kalleta zakayi tsammanin irin kyawawan Ethiopians din nan ne,saboda yadda kalar fatarta ya sake fes kamar bata shiga rana. Igiyar da akayi daga tsakiyar ciki don daure rigar ta zauna daidai jikin me ita,ta taimaka wajen fitar da surar albarkar qirjin da Allah ya bata,wanda sam batasan hakan ya faru ba,saboda ko madubi bata tsaya kalla ba,idanunta sun sake shanyewa saboda rashin wadataccen baccin da bata samu ba a daren jiya,babu koma a fuskarta banda wata powder da jawahir ta siya mata ta masu kalae fatarta, powder din kuwa ba qaramin kyau takewa fatarta ba,sai labbanta daketa qyallin man lebe daya qarawa leban nata taushi da kyau. Baisan ajiyar zuciya ya saki ba,saida ya tsinci zuciyarsa tana tuhumarsa da yadda ya qure kaltum din da kallo har ta kamashi yana kallon nata,abinda ya sanyata jin kunya,ta saka hannu a hankali ta bude gidan gaba ta zura jikinta kafin qafafunta da suka sha hill shoes su biyo baya,abinda ya qarawa adon nata kyau,budurcinta daya fara bayyana ya sake fitowa fili muraran. "Ina yini" ta gaidashi a ladabce tana dora purse dinta saman cinyarta "Lafiya lau" ya amsa mata yana kallon yadda garin ya fara hada hadari,ba kasafai yakeson tuqi da damina ba saboda ruwa,yaso tafiya ne a jirgi,so amma duka yau babu jirgin da zai tashi daga kano zuwa bauchi,don haka ya maida tafiyar kawai a mota,saboda lokaci ya riga ya qure,gobe ne daurin aure,a haka ma yayi missing events masu yawa,ya kuma sha mita da qorafi wajen amiru,amma duka ya shareshi,don dama shi ba kasafai ya fiya shiga irin wadan nan shagulgulan ba sai wadanda suka zama dole. Yana qoqarin tayar da motar qamshinta nason dagula masa lissafi,sai zai murza key din sai yaji kamar bazai iya ba,kamar wanda aka zarewa dukka lakar jikinsa,har taji shurun yayi yawa,ta daga kanta daga murza yatsun hannunta da take tare da wassafa yadda xasuyi tafiya tare dashi ta awanni masu tsaho daga ita saishi. Kallon datayi masa akayi katari shima ita yake kalla,a hankali ya motsa labbansa,idanunsa kan dan qaramin bakinta "Wannan rigar....." Sai kuma yayi shuru ba tare daya qarasa ba,ya cire hannunsa daga kan motar a hankali ya nufo inda take zaune,numfashinta ta dauke gaba daya ganin ya nufo da hannunsa qasan qirjinta. Yatsa daya ya saka ya kunce igiyar data daure tsakiyar rigar da ita,take rigar ta ware,ta batar da duk wani shape nata daya fito. Sake qamewa tayi tare da runtse idonta ganin ya matso da jikinsa gaba daya inda take,qwayar idanunsa cikin nata,cikin second biyu qamshin turarensa,da hucin numfashinsa da dumin jikinsa gaba daya suka mamayeta. Seat belt ya zaro a hankali ya zagayo da ita ta saman cikinta,wanda garin hakan yadan shafi qirjinta da bayan hannunsa,al'amarin daya sanyashi jin wani shock tun daga yatsun qafarsa zuwa kwanyarsa,ya sauke numfashi me nauyi sanda ya gama saka mata ya maida bayansa ya jigina da kujera yana qoqarin maintaining nutsuwarsa. Har zuwa sanda ya bude nashi idanun,ya murxa key din ya tashi motar yana karanta addu'ar matafiya a fili amma qasa qasa. Tata addu'ar itama ta fara karantawa sanda suka ficewa daga gidan,wanda basuyi wata doguwar tafiya ba ya sanya karatun daya daga cikin shahararrun malamai kuma bayin Allahn da ubangiji yayi mana kyautarsu wato mlm dr umar sani fage. Karatun kusan shine ya janye hankalin kowannensu,karatu ne cike da tarin hikima da kuma maganganu na fasaha,tare da tunkuda bawa zuwa kusanta kai da Allah matuqar kusantuwa,tun tana iya jin abinda malamin ke fada tana kokawa da bashin baccin data ci jiya,har yayi nasarar yin awon gaba da ita ta daina jin komai. Tafiyar awa uku da rabi suka shiga garin azare,kai tsaye suka nufa cikin garin,zuwa lokacin garin azare ya fara duhu saboa hadarin da ya yiwa sama rumfa,saidai mutane da yawa basu kawo zubarshi ba,saboda wannan kusan shine hadarin farko tun bayan sanya ran shigowar damina. Idanunta biyu a sannan,sabida sun tsaya sunyi salla,ya siya musu take away duk da itadin bata iya ci a gabansa ba. Ringing wayarsa tayi,yana tuqi a hankali da hannu daya,yasa daya hannun ya daga wayar ya sanyata a kunne idanunsa na bisa titi. Magana suke da amiru,ya shaida masa akwai dinner din mr and mrs da za'a gabatar takwas na dare,amma saboda ganin hadari yasa an maidota nan da awa biyu "This is none of my business.....meye amfanin gayamin?,kai kanka ba zaka samu shiga ba tunda tuzurun banza ne,har gwara gwara ni" dariya sosai amiru ya qyalqyale da ita,bazai biye masa suyi abinda suka saba ba,don so yake yallaboshi yazo kodon saboda kada angon ya fassara wani abu daban,saboda yarinyar da zai aura din tadan so samir "Wai tula ne zaiwa audi gori......gwara kai ame?,tuxurantaka?,meye marabar dambe da fada,ni dakai ai duk d same,amma dai afuwa master,na yadda da kai,yanzu abinda za'ayi,kada ka wuce gida,ka tsaya dai dai Round about din nan da zaka shiga titin gidan ya dikko,kafin ka shiga titin ka tsaya,am on my way" katse wayar kawai yayi ba tare daya amsawa amirun ba,sai ya koma tuqi a hankali yana duban hanya. Tun kafin su qarasa ya hangi samir din jingine da wata sabuwar baqar mota,dai dai sanda motar take fakawa,daidai lokacin yaga ya cusa kanshi ta window din motar,da alama magana yake da wasu,sai samir din ya kashe motar kawai yaci gaba da xama cikin motar ba tare daya fita ba,ganin haka amirun ya tunakarosu,kanshi tsaya ya tsaya side din kaltum,ya bude murfin motar yana cewa "Sannu da hanya madam,ga mota can shiga ta ciki" duban samir tayi suka hada idanu kana ta dauki jakarta ta fice daga motar,wanta tashinta ya sanya wani abu fadowa daga jikinta,hannu ya miqa yana qoqarin dauko takardar,saiya kula hotone,ya juya hoton a hankali,take idanunsa sukayi arba da fuskar dake jikin hoton,abinda ya sanyashi bin baya kaltum da amiru dake tafiya zuwa wancan motar da kallo,mamaki na mamayarsa na inda ta samo hoton,saiya bude locker din motar ya saka hoton ya rufe yana juya tambayar inda ta samo din cikin ransa. Ruqunqumeta jawahir tayi sanda suka shiga cikin motar,kamar xata koka cikin kaltum din,jtakam dariya kawai kaltume din ke mata,har zuwa sanda amiru da yaga basu da niyyar rufe motar ya rufe musu ya koma wajen samir. *********kayan da amirun ya miqe masa ya kalla "Am telling you fa,babu inda zanje,ina buqatar na huta malam" kicin kicin amiru ya masa,yasan idan baiyi da gasken ba ba zaya je ba "Wallahi koda wannan shine last thing da xakayi a azare sai kaje" gira ya dage ma amirun dukka biyun yana dubanshi "Really?" Harara ya watsa mana,saiya fincika kayan daga hannunsa ya watsa gado ya bisu ya kwanta kawai a kai,qyaleshi amiru yayi,tunda yayi hakan yasan zayaje din koda baiso ba. Kanta ta karkatar ta dubi jawahir "Don Allah ki shiga na jiraki anan mana" kaltum ta fada tana kwabe fuska,tun daga sanda akayi.mata kwalliyar dake fuskarta har zuwa yanzu duk a takure take,sanda taga fuskarta a madubi sai data tsorata,irin kyan da tayi bata taba zata ko tsammatar ganinsa a fuskarta ba,dukka jama'ar dake wajen sai da suka tsaya suna kallonta,saboda yadda kwalliyar tayi masifar bin lafiyayyar chocolate colour din fatarta ta kwanta sosai. Idanu jawahir ta fitar "Wa?,ai wallahi saikin shiga,nima setup mukayi da ya amiru a matsayin miji da mata zamu shiga,kema haka zaki haquri kizo mu shiga.....kinga ma yana kirana,hala ya iso" jawahir ta fada tana daga wayarta tana duban me kiran,sai kawai taga ta balle murfin motar ta fita tana duba ta inda suke. Ta bangaren da take ta leqo ta mata alamar ta fito,a hankali ta janyo jikinta ta zuro qafafunta daga motar. Yana tsaye ya basu baya kadan,hannayensa zube a aljihun wandonsa yana duban wajen,ranshi baiso zuwa wajen ba,kawai dai yayine saboda ya faranta ran amirun daya dage. "Oya....muje already ma an fara event din" amiru ya fada,abinda ya sanya samir juyowa kenan. A hankali idanunsa suka sauka kanta,tana tsaye dab dashi,sai yaji wuta ta dauke masa na wucin gadi,baisan sanda ya bita da kallo tun daga sama zuwa qasa ba,wani kyau na musamman da bai taba tsammatarsa ba tayi masa,komai ya fito perfect,duk wata baiwa tata ta fito,ta zama cikakkiyar budurwar me tashen shekaru da zata iya jan hankalin kowanne namiji da zai dora idanunsa a kanta. Wani abu da yaji ya tsaya masa a wuya ya hadiye,ya dauke idonsa daga kanta ya maida kan amiru,saiya miqa hannu ya fincikeshi gefe "How dare you zaka sata tayi irin wannan kwalliyar amiru?" Idanu amiru ya fitar "Mene aibu to?" "Ka manta matar aur......." Maganar ta maqale masa ba tare data gama fita gaba daya ba,saboda rashin sanin ma'anar yin maganar. Dariyar da amirun ke boyewa tadan fito kadan "Bari na qarasa maka tunda kunyar qarasawa kake,na manta matar samir ce?,ko?,karka damu,ni kadai na sani fa,amma yau kowa a hakan zai kalleta......muje please muna sake makara" amirun ya fada yana yin gaba da sauri,ya jera shida jawahir itama daketa boye dariyarta,duk da batasan alaqar dake tsakani ba amma cewa take "Wallahi ya Aamir sunyi kyau sosai,sun dace da juna Allah yadda kasan miji da mata,dama zaiso kaltum, she's cute wlh,duk da bayason baqar mace amma kaltum ta dace dashi,yau ka yima ya samir shigar sauri" murmushi shima yayi ya waiwaya yana satar dubansu sanda suke gab da shigewa hall din. Shuru ya biyo baya a wajen,tana tsaye a inda take kanta aqasa tana wasa da yatsun hannunta,saboda gaba daya jinta take a takure,yayin da yake tsaye,har yanzu hannayensa zube a aljihunsa yana ci gaba da qare mata kallo,a hankali ya tako zuwa inda take,ya zare hannunsa daya dake aljihunsa ya kama nata hannun,gaba dayansu wani abune yabi ta jijiyarsu ya aikama qwaqwalensu saqo,saiya fara takawa a nutse tana biye dashi,wanda kafin sukai ga shigewa ciki yayyafi mai qarfi ya fara sauka. Suna shigowa wajen idanun jawahir na kansu,baki ta bude tana mamaki,yau yayansu ne da kama hannun wata?,kasa daurewa tayi sai data tabo amiru. Daga can baya ya zabar musu sit,tunda suka shiga wajen bai motsa ba kamar yadda itama bai barta ta motsa ko nan da can ba,bayaga ango da yaje ya yiwa Allah ya sanya alkhairi,abinda ke bashi haushi da mamaki shine duk wanda zai wuce ta wajen saiya kallesu yakuma juyowa,wayarsa na hannunsa yana amsa saqonnin da baiyi niyyar dubawa bama,lokaci lokaci yakan saki tsaki ya kuma jewa amiru harara. Sanda aka fara rabon abubuwan motsa baki jawahir ta matso gurin ganin bata taso ba "Kaltum....bakwa sha'awar komai ne?" Ta fadi tana ajjiye wani paper plate dake hannunta "Get out malamarsu" samir din yadan fada a kausashe,da alama akwai abinda ya taba rashi,ba zata iya tuna yaushe ne na qarshe daya mata hakan ba,don haka ta dauke plate dinta tana boye fuskarta tabar wajen. Da kadan da kadan ake raguwa awajen,duk da ruwan saman daya fara sauka bai hana mutane tafiya ba,saboda kusan kowa da motarsa yazo shida iyalinsa,wajen ya qayatar sosai,babu hauka babu baragada,kowa da matarsa yake,masu setup irinsu jawahir kadanne,sai zuwa sannan ya daga kanshi yana maida wayarsa aljihu yana kuma dora kansa a kan kaltum. Kwalliyarta na nan kamar sannan aka yita,dan qaramin bakinta da yasha jambaki yana motsawa kadan kadan,baisan me take fada ba,daya tsura mata idanu sanda aka yi tsawa sai ya lura addu'ar tsawa take,ta dan rufe idanunta kadan,wanda hakan ya fito da zara zaran gashin idanunta da zaka tsammaci sa mata akayi,saidai mascaran da aka sanya musu ya sake fitar da kyau da tsahonsu,ya fuskanci tsoron tsawa take sosai,saiya miqe a hankali ya miqa mata hannunshi. Jin tsaiwarsa saman kanta yasa ta bude idanuwanta,suka sauka akan lallausan tafin hannunsa da yake miqa mata,karo na biyu kenan daya taba bata wannan damar,tana jin kunya tana kuma jin nauyi,yana kuma sanyata shiga wani yanayi,amma haka ta dora masa nata hannun a hankali ya rumtse cikin nasa ya kuma jirayi tashinta kana suka nufi hanyar fita. Dukka akan idanun jawahir,mamaki yana sake kamata,bata taba ganin haka daga yayan nata ba,hannunsa cikin na wata?,me aikin gidansu?,kuma ba muharramarsa ba,shida kullum maganarsa itace su kare mutuncin kansu,kada su yarda koda wasa su hada jiki da wani da namiji?,binsu tayi da idanu har suka fice daga hall din. Dakatawa yayi da tafiyar yana kallon ruwan,ya soma qarfi sosai,wanda mutane da yawa dake ciki basusan da hakan ba,waiwayawa yayi kadan ya dubeta,sai yaga ruwan ta zubawa idanu itama,da alama tana wasafta ta yadda zata shiga cikinsa. Yana riqe da hannunta a hankali suka fara taka cikin ruwan suna dosar motarsu,idanuwanta ta runtse sanda sanyin ruwan yake ratsa jikinta,saukarsa ta farko ji tayi kaman numfashinta zaya dauke,tunda can ita me tsoron ruwa ce,shi yasa kaf rayuwarta bata taba shiga rafi wanka ba,saidai tayi rakiya wa su wasila,tana tsaye kuma har suyi su gama. Qarfin ruwan ya sanya kafin su isa motar ta jiqe,duk da bame yawa ba amma tana jin sayin har cikin qashinta. Takurewa tayi sosai a sit dinta,tana kallon singalilin hannunsa da ruwa ya jiqa yana kashe ac ya maidata zuwa heater,sumar gargasarsa itama tayi luf,ta rufe idanunta sanda akayi wata walqiya,ta tabbatar tsawa ce zata biyo baya don haka ta sake curewa guri guda. Binta yayi da kallo,saiya saka hannunsa ga seat din baya,ya dauko hiramin daya siya dazun a store din da sukaje siyayya shida amiru,ya farke ledar ya wareshi ya soma rufa mata,abinda ya sakata bude ido,idanunsu ya shiga cikin na juna,eye lashes dinta sun jiqe sosai sunyi wara wara,sai tayi qas da kanta tana jin dadin rufetan da yayi "Na gode" ta samu kanta da fada,ya tada motar yana amsa mata da "You are welcome". Tun basuyi nisa ba ruwan yayi wani irin qarfi naban mamaki,tituna suka fara cika saboda rashin kyakkyawar magudanar ruwa,tsaki samir din yaja yana kallon yadda titi ya shafe da ruwa,ya rasa aikin me gwamnati keyi?,ruwa a saman titi kamar layukan unguwanni?" Baka bambace titi da kwata?,yana daya daga cikin abinda yasa ya tsani siyasa iyaka kenan,babu komai cikinta sai yaudara da daukan alqawuran dako kusa ko alama basa iya cika koda kaso daya cikin ukunsu. Ji yayi bazai iya ci gaba da tuqin ba,don baisan yadda zai tadda unguwarsu ya dikkon ba,bugu da qari ma ya tabbatar idan yaje zaiyi horn ne ya taso me gadin da a yanzu yake cikin dakinsa ya samawa kansa mafaka daga dukan ruwan saman,wannan tunanin yasa ya gangara a hankali hannun da yake tuqi qofar wani katafaren guest in,ba tare daya tuna inda zai ajjiye kaltum din ba. Umarnin fitowa yayi mata bayan ya bude mata murfin motar,ta fito a hankali tana sake hade jikinta waje guda,saiya saka hannunsa saman daya kafadartata ya janyota zuwa jikinsa,abinda ya rage mata dukan ruwan,saidai kuma hakan da yayi mata tamkar ya sake jefa abun fashewa ne cikin zuciyarta,ta dinga sauke qaramar ajiyar zuciya a hankali. Da tarba ta mutunci receptionist din ya karbeshi,ya buqaci daki biyu "Saidai kayi haquri yallabai idan babu damuwa kuyi squatting a daki daya,babu dakuna sai wannan da ka karba yanzu guda biyun da suke ba kowa a ciki gyara ake musu,babu damar iya zama a ciki" "Ba matsala" ya fada a hankali. Sai daya bude mata dakin ta shiga sannan taga ya sake fita ya dawo bada jimawa ba,hannunsa dauke da wani irin akwati dan qarami me dauke da tambarin wani store,wanda manyan customers dinsu da sukayi siyaya da yawa ko me manyan kudi suke zubawa kaya a ciki. Tana daga zaunen ya kunna heater din dakin,ya rage haske qwayayen,sannan kuma ya kunna water heater ta bandaki ya shige bayan ya tara ruwa me zafi sosai. Har sanda ya murda qofar toilet din ya fito tana zaune a wajen jikinta a hade,duk da dumi ya fara ratsata,saidai hankalinta ya rabu biyu,ta yaya zasu kwana a dakin nan daga ita saishi?,me zata cewa jawahir idan ta tambayeta ina sukaje?,zatace mata ne sun kwana tare bayan babu wanda yasan alaqarsu?. "Ki cire wadan nan kayan kafin sanyi ya kamaki,ki shiga toilet ki dumama jikinki da ruwan zafi" ya fada sanda yake fitowa daga toilet din sanye da sabuwar rigar wanka ta towel har qasa me budadden qirji,abinda ya bayyana tarin sumar dake kwance a qirjinsa baqa sosai mai kuma santsi. Numfashinta ta dauke gaba daya tana sake qanqame jikinta,ruwan da yayi wanka ya sanya kowacce suma ta jikinsa kwanciya,hatta da qawataccen sajen fuskarsa mai kama da qasumba,saidai baikai qasumba fadi da cika ba. Wani abu ta hadiye,cikin dakiya tace "Da zaka qarasa dani gida....saboda su jawahir....." Kasa qarasawa tayi saboda ji da tayi a jikinta ita ya zubawa ido,ilai kuwa haka ne,har baisan sanda murmushi ya subuce masa ba,yana da tabbacin batasan waye samir ba,wannan rayuwar ba irin waddanya fasaltawa kansa ko yake sha'awarta bace,inda tazo masa a matsayin matar aurensa da suka fahimci juna,duniya tasan da aurensu da ba wannan zancan ake ba a yanzu,kwata kwata wannan ba irin rayuwar auren daya tanadarwa kansa bace,saidai akwai wani qwaqqwaran bond da yakejin yana son gilmawa a tsakani,duk da haka aure duka aure ne,zai tunasar da ita abinda takeson mantawa,duk da cewa baison ya wuce gona da iri,saboda yanajin cewa gaba kadan xai bata dukkanin zabi ne. Batasan ya tsaya a gabanta ba sai da idanunta suka dauka kam xara zaran yatsun qafarsa da gashin ke kan kowanne dan yatsa ke akwance shima,kafin tayi wani motsi ya kama dukka kafadunta ya dagata,sai ya saka hannu ya zare hiraminsa ya aje gefe,jawota yayi jikinsa ya mata sasssuqar runguma,abinda ya kusa sanyata daukewar numfashinta kenan saboda jikinta daya gogi nashi,shi dinma yaji,amma ya dake,yanason ya mata tuni ne kan abinda ta manta,saiya kama zip din rigarta ya saukeshi qasa gaba daya,duk da cewa a iya nata qarfin fa cukuikuye rigar a jikinta amma hakan bai hanashi sabule mata ita ba ya hada harda bra dinta,adalci daya yayi mata tana jikinsa bazai iya kallonta ba saidai duk wata fata ta jikinta da hannunsa ya taba yana jin aiken saqo zuwa kowanne sashe na jikinsa,sai ya dauko hiramin ya rufa mata,ta kamashi kuwa tsam ta riqe tana sake lullube jikinta,ko ina na jikin nata yana rawa,qafafunta kamar ba zasu iya daukarta ba "Akwai ruwa me zafi kije kiyi wanka kixo ki kwanta,idan sun tambayeki gobe,kina iya gaya musu mijinki kika biyo,naki da zunubi ko dis a wajen Allah" ya fada yana juya mata baya yana takawa zuwa gaban madubin dake fuskantosu,saidai yana iya hangenta ta madubin sanda take takawa da sauri kamar zata fadi ta durfafi bandaki. Ta dade a tsaye tana haki tare da sauke numfashi,gaba daya ya aza mata wani irin nauyi da tsoro,bata taba kawo haka a tsakaninsu ba,duk da cewa tana jin abubuwa masu yawa dangane dashi cikin zuciyarta....... *_A WANNAN DAREN_* Su biyu ne rak zaune cikin dakin,duk da suna saka ran shigowar mutum na uku wato najwa. A hankali hajiya jidda ke qarewa dakin kallo,tana qiyasta yawan dukiyar da aka sake narkawa dakin,kafin maganar hajiya shuwa ta shiga kunnenta "Idan bakiyi wasa ba hajiya jidda kwabarki tana dab da tayi ruwa,dava tafiyata ace babu wani ci gaba da aka samu?,saima tarin koma baya dani na hango?,me yasa ba zaki kawo qarshen komai kowa ya huta ba kema ki huta?,tun kafin akai lokacin da zaki dora hannunki aka?" Murmushi mummy ta saki tana duban hajiya shuwa "Akwai abinda nake jira da dako,banason garin sauri naje na aikata kuskuren da kika kusa aikatawa" murmushi hajiya shuwa ta saki "Iya gidan nan kadai amma ya isheki amsa ko?" Maida mata murmushinta mummy tayi "Eh qwarai,saidai akwai banbanci,banajin zan iya qarasawa bigiren da kike kai a yanzu" dariya sosai hajiya shuwa ta saki "Kijimin mata.....da wanda yaci alade,da kuma wanda yaci mushe meye bambancinsu?"kai mummy ta girgiza "Banbanci me tarin yawa kuwa,tunda ko banza shi mushe ai yankan Allah ne......". A hankali najwa taja da baya hannunta riqe da cup din tea data hado da niyyar sha,ta taka kuma zuwa dakin da aka sauketa cikin gidan hajiya shuwa tun bayan zuwansu garin azare,wanda sukaqi zama gidan ya dikko. Katafaren dakin da sai ka zaci dakin wata hamshsqiyar ne,ranta a bace take duban tvn dake aiki a dakin,duk da cewa bata tvn take ba,hirarsu mummy ke dawo mata,ko daya bataji sun tattauna kan matsalarta ba. shedan ke dake zafafa mata zuciya,ta fuskanci mummy tana slow ne kan abubuwa da dama,to itakam a yanzu tanajin qarfinta ya kawo,zata shiga nata yaqin,zata aiwatar da abubuwan da mummy ta kasa aiwatarwa,bata jin xata yarda ta amince....tasha dukka wata wahalar karatu saboda cikar buri da muradinta,sannan a qarshe daddy yace taje tayi aiki da kamfanin saraki a qarqashin sarakin?ba zata iya ba,kuma da sake. Miqewa mummyn tayi tana tattaki gaban hajiya shuwa,maganganun da suka sakeyi suna mata yawo akai,hajiya shuwan kuma na binta da kallo. Tsayin wasu mintuna mummyn ta dawo gabanta ta tsaya "Na gamsu da dukka bayanai da hujjojinki,kuma a wannan karon ina ji a jikina zan aiwatar da tunaninki,muga kalar naki takun" kalaman da suka sanya fitar murmushi daga fuskarta hajiya shuwa,ta daga hannu tana jinjinawa mummy. . "Ya na ganki ke kadai?,Ina kaltum din?" Hajiya qarama ta tambayi jawahir wadda take fidda kayan jikinta da suka jiqe da ruwan sama. Tsaiwa tayi da cire kayan,ta ta waiwayo ta dubi hajiya qarama "Sun rigamu fitowa fa,basu iso ba kenan?" "Nidai babu wanda na gani a cikinsu" "Ok,bari na gama na kira ya sarakin" ta fadi tana dauko kayan da zata sauya din masu dan kauri saboda sanyin ruwan da ya ratsata,sai data gama shiryawa sannan ta zauna ta soma kiransa. Tana shiga amma ba'a dagawa,already ya sanyata a silent ne,kaltum dake duqunqune cikin bargo tana sheqar lallausan qamshin turarensa daya kama kayansa tana iya hango hasken wayar saboda a saman kanta take a ajjiiye,saidai batason yin magana kwata kwata,tafison ya dauka tayi baccin ne kamar yadda ga zata,tun sanda ya bata rigarsa ta sanya kunya da nauyi suka cikata,saboda barin nata kayan da yayi cikin mota. Shafa addu'arsa yayi a hankali,sannan yaja bargon daya dora saman dogayen qafafunsa ya dawo zuwa qugunsa,sannan ya zame a hankali ya kwanta a hannunsa na dama. A hankali ya lumshe idanunsa kana ya budesu,idanunsa suka sauka a bayanta,duk da cewa baya iya hango komai na jikinta sai bargon data duqunquna har kanta da shi. Wani numfashi mai nauyi ya sauke,yanayi irin wannan yana saukar masa da feelings sosai tun ba yanzu ba,qamshin qasa hade da sassanyar iskar damina ta dare,saiya sanya hannayensa tsakiyar gwiwoyinsa kamar maijin sanyi,haka kawai kasancewarta kusa dashi ke neman dagula lissafinsa,tsahon rayuwarsa wannan shine karo na farko daya taba hada makwanci da diya mace,yaso ya barta ta kwana a qasa kamar yadda ta zaba,saidai kuma yaga hakan bai dace ba,duba da sanyin ruwan dake sauka,ga kuma tiles da ya yiwa dakin qawanya. Hasken wayar ya hango,wanda ya bayyana bayan walqawar walqiya a sararin samaniya,walqiyar data sanya kaltum runtse ido sosai da kuma curewa waje guda tana addu'a qasan ranta,kan Allah yasa ba tsawa za'a saki ba. Hannu ya miqa ta saman kanta zai janyo wayar,dai dai sanda qarar tartsatsin walqiya mai qarfi ya baje a fadin duniya ya sauka zuwa kunnen kowanne abu me rai dake sararin subhana. "Alhamdulillahil lazi yusabbihur ra'adu bi hamdih,wal mala'ikatu min khifatihi" saraki ya fada a hankali yana dan runtse ido saboda qarar tsawar,sannan ya bude idanun nasa a hankali ya sauke a kanta. Baiyi tsammanin cewa batayi bacci ba saida aka saki tsawar yaji yanda ta firgita,har kuma bayan shudewr tsawar yana iya jin yadda ta sake tattarewa waje daya,bai fasa dauko wayar ba,ya budeta ya shiga app din karatun qur'ani,qira'ar shaik abdur rahmani assudais,ya kunna suratul baqra,ya sanya volume dinta saisa saisa (indai har zaki iya kwana da waya saman kanki bayan kin gama danne dannenki,to yana da kyau ki koyi sanya karatun qur'ani cikin dakinki sanda zaki kwanta bacci,cikin qaramin volume ba mai yawa ba,hakan yana taimakawa wajen yin bacci me dadi mai kuma cike da nutsuwa,uwa uba ga tsaro da zaya baki daga dukkan sharri,koda bunu chargy indai akwai wuta,jonata a socket,ki kunna qur'anin,yana playing tana chargy,zaki mamakin yadda wayarki zata cika da wuri,ga kuma qur'anin yana yi har safiya,koda chargynki ya kusa qarewa kika kunna,wani hukuncin Allah wayar bata mutuwa,tana kaiwa har safiya yanayi,Allah ya bamu albarkacin qur'ani mai girma,alfarmar shugaba S A W👏🏽👏🏽). Saman kansu ya sanya wayar,ya raba a hankali zuwa bayanta ya kwantar da jikinsa,idanunta ta lumshe gaba daya zuciyarta ta soma gudu yadda ta saba a duk sanda ya rabota....lokacin data jishi cikin bargon da take,hannunsa saman ruwan cikinta,muryarsa can qasa kamar meyin rada yana cewa "You are safe..... good night" cikin son yin aiki da maganarsa ta rufe idonta a hankali tana sauke numfashi,dumin kowanne na ratsa dan uwansa yana haifar masa da wani yanayi na daban......... _to sai ince asuba ta gari kalsam_ 53 DZ "Ina hanya,yanzu zamu iso,koma meye idan nazo ka tambaya" abunda ya fada kenan sanda yake jingine da motarsa a farfajiyar gidan saukar baqin,saiya latse wayar kawai sanda yaji amirun nason masa cari,ya soma sanya wayar a aljihun wandon shaddarsa,lokaci guda kuma yana daga kansa. A kanta idanunsa suka sauka,tana sanya da atamfa riga da zani,sai mayafi wanda yayi matuqar dacewa da kayan jikinta. Kyakkyawar kalar fatarta ta haska tarwai cikin kalolin kayan jkinta,kwantaccen gashinta me santsi ya fiti ta gefe da gefan kunnenta,da kuma qeyarta inda ta nadeshi kamar alkaki. Baisan sanda ajiyar zuciya ta kubce masa ba,yana tuna yadda hannunsa ya dinga yawo a jikinta daren jiya cikin mafarkinsa,wani abu ya tsarga masa sanda ta daga fararen idanunta suka sauka akansa,saiya sanya hannayensa duka cikin aljihun wandonsa yana qyara tsaiwarshi da kyau. Faduwar gaba taji sosai,karon farko data ganshi da shigar da bata taba ganinsa da ita ba,shigar shadda fara sol sai maiqo da walqiya takeyi,wadda akayi mata aikin zare baqi,takalmi sau ciki wanda shima yake nashi kalar qyallin,hannunsa sanye da Rolex me asalin tsadan,sumar kanshi wadda bata da wani yawa sai sheqi takeyi saboda hularshi dake aje saman motar bai sanya ba. Hardewa taji ta fara yi saboda takalman qafarta masu dan tsinin dunduniya da sukayi mata kyau suka kuma sake qawata kwalliyarta. Tana dab da isowa inda yake ya sanya hannunsa saman motar ya.janyo hularsa ya aza a kansa,har a sannan bai fasa kallonta ba. "Kinyi kyau" kalmar data subuce masa a bakinsa kamar fitar kibiya,hakan ya qara aza mata nauyinsa. A hankali ya kutsa da motar cikin layin gidan ya dikko,duk kuwa da saurin da ya dinga yi amma hakan baisa ya iso a sanda yaso ba,saboda wani laziness da yakeji a jikinsa gaba daya,a hankali ya dannan wani madanni dake gefansa ya dage dukka gilasan motar sama sanda yake yiwa motar gun tsaiwa,hannu tasa zata bude motar "Wait" taji ya fada,hakan yasa ta tsaya din kamar yadda ya buqata,ta qagauta ne su raba jaha,don ita kadai tasan wanne yanayi take riskar kanta a ciki duk sanda suka kadaice irin haka,wani mugun nauyi da kunyarsa takeji fiye da kowanne lokaci. Wayarsa ya ciro ya dannan numbers din jawahir, ringing biyu ta daga,zata barke masa da surutun nan nata ya dakatar da ita,yace ta fito ya sameshi a waje,sannan ya aje wayar . Daga nesa ya hangi fitowarta,tayi duru duru tana nemansu,saiya dan danna mata horn sannan ya bude motar ya fita,dai dai nan ta iso,saiya dan saka kansa kadan yace da kaltum din ta fito. "Wai a ina kuka kwana kaltum?" Ta tambayi kaltum din cikin mamaki da kokwanto,saidai kafin tace komai samir din ya tsaidata "Ba'a sani ba tambaya,ku wuce muje" bata qara tambayar ba,saidai tana mata susa a rai,tare da tambayar kanta inda sukaje suka kwana,kuma su biyu,ba muharraman juna ba,duk da cewa ta yarda da hali da dabi'ar yayan nata,dama ta kaltum din. Suna gaba yana biye dasu a baya,duk da jama'a na tsaidashi suna gaisawa,duk inda ya wulga sai ya dauki hankalin jama'a,farinji da kwarjini gareshi,uwa uba yadda yake kyautatawa al'umma ya siya masa soyayyar jama'a me yawan gaske,a haka suka isa babban falon yadikko,wanda yalwar gidan da wadatar guraren zama ya sanya babu yawaitar mutane,kusan suna dakuna...... "A ina kika samo wannan beb din......ban santa ba a cikin danginmu" daya daga cikin samarin dake xaune a falon ya fada,abinda kuma kunnuwan samir suka jiye masa sanda yake shigowa,idonsa ya sauka kan yaron wanda ake kira da muntasir. Sallamarsa yasa maganar da yake shirin yi ta yanke,duka suka waiwaya,sannan suka miqe cikin nuna girmamawa suna masa sannu da zuwa kafin su fara gaidashi. Fuskarsa a hade tsam ya kalli jawahir "Ina mummy?" "A gidan haj shuwa ta kwana,amma munyi waya tace min ta taho,duk yadda akayi ta kusan qarasowa" ido ya lumshe kana ya bude cikin sakannin da basu wuce biyu ba,haka kawai cikin zuciyarsa jininsa baya son matar,kuma bazai iya tuna wani laifi data taba yi masa ba,koda na kallon banza kuwa "Ki rakata wajen hajiya qarama" "To" ta amsa masa tana yin gaba,kaltum tabi bayanta,saiya tsinci kansa da rakasu da ido. Muntasir ya tabo dan uwansa "Kaga guy din nan,ashe shima ya iya kallon mata?" Boyayyar dariyar ciki ya sake "Waye baison mace dama?,aisu sunfi qarfin zuciya da qwaqwalwar kowa,saidai idan bai samu ba,bare wannan....ta wanku fa,kalar fatarta ta musammance wlh,ga wani kyau mai sanyi alaji,wanda saita matsoka kake ganinsa",dif sukayi sanda ya waiwayo ya dubesu,don kalamansu na qarshe sun shiga kunnensa,baisan me yake taba zuciyarsa ba duk sanda sukayi magana irin wanann,dukansu ba sa'ansa a cikinsu,don haka ya miqe ya nufi bangaren dakin ya dikko don su gaisa,tun kafin daddy ya qaraso yaji basu gaisa din ba. Fara'a fal fuskar hajiya qarama,farincikin ganin kaltum ya bayyana sosai "Lale maraba da diyata,ina nan inata kewarki,dama yanzu nake shirin kiran saraki naji can gidan abokin nasa zaku yita zama ne?,sai amirun yacemin matar abokince bata jin dadi sosai,kin dan tsaya kin taimaka mata ta kintsa gidan" itadai murmushi kawai take,kanta a qasa tana jinjina yadda amiru ya iya tsara irin wannan qaryar,duk da tayi mata dai dai,don bata da kowacce amsa da xata bata. "bari naje mu qarasa packaging abincin 'yan daurin aure.....ina zuwa kaltum" ta fada tana juyawa gami da ficewa daga dakin,zuciyarta dai na tantamar labarin da amiru ya bawa haj qaraman kan rashin kwanansu gida,tunda a gabanta ne yake neman shima inda suka shiga,ture batun tayi,sabida batason baiwa shaidan qofa akansu,ta yarda da kowa a cikinsu. Sai data zauna sosai sannan ta daga kai da niyyar gaida hajiya qarama,saidai gaisuwar taso.maqale mata a maqogaro,saboda sauka da idanunta sukayi kan wani hoto dake maqale a bangon dakin da yake tamkar na hajiya qaraman,saboda duk sanda tafiya ta kawosu azare a nan take sauka,idan zata tafi kuma ta rufe ta bawa ya dikko maqullin. Hoto ne dauke da taswirar fuskar matar dake a jikin hoton data taho dashi zuwa azare,wanda tayi masa duban duniya amma ta rasa inda ta yada shi,gabansa kadan wani hoton ne irinsa,tana sanye da atamfa da akayi mata riga da xani,ta yane jikinta da mayafin atamfar,wadda ta haskata ta kuma fidda kyanta sosai. Tattaro kalaman bakinta tayi tana gaida hajiya qarama,amsa mata tayi tana waiwaya bayanta don duba abindan ya dauki hankalin kaltum din haka,sai taga hotunan,hotunan da a kullum idan ta kallesu sai taji wani abu mai qarfi ya motsa mata,takan ji karyewa zuciya qwarai,har yau zuciyarta ta kasa gasgata abinda aka fada akan raihana,har yau ta kasa jin nutsuwa da kalaman da akayi a kanta,har yau zuciyarta tana gaya mata cewa tana raye. "Suna kama ne da samir?" Hajiya qarama tayi mata tambayar tana murmushi gami da duban fuskar kaltum,maganar hajiya qarama ya sanyata janye idanunta daga kan hoton,murmushi yana subucewa daga fuskarta ta girgiza kai gami da saukar da kan nata qasa. Shuru ne ya ratsa dakin na wasu sakanni kamar ba kowa a dakin,ajiyar zuciyar da haj qarama ta sauke yasa kaltum kallonta,suka hada ido,sai hajiya qaraman fa gyara zamanta "Shekara kusan ashirin da takwas,amma har yau zuciyata ta kasa gasgata bacewar raihana.....wadda ta bace rana tsaka,sama ko qasa,a lokacin samir nada shekara biyar a duniya,bayan ana tsaka da wata hatsaniya,ba'a gama kamo bakin zaren ba,a yadda jidda tace.....a gaban samir akayi,tace ne ta gaji da zama da rashid,dama kara take mishi,ita ba sa'ar aurensa bace,akwai maza da yawa dama dake dakon fitowarta,ta bashi wata wasiqa data tabbatar da dukka abinda ta fadi cewa raihana tace,kuma tabbas kowa yasan rubutun na raihana ne,hatta da 'yan uwanta sun tabbatar da hakan. Hatsaniyar da ake tsaka da yi da kuma wannan abun daya faru ya haifar da gagarumar tsanar raihana a zuciyar rashid,abinda yasa ya karkade hannunsa daga batun nemanta,wannan ne kuma ya hasala danginta,wadanda 'yan asalin qasar sudan ne,sukaga koba komai ai matarsa ce,kuma shine silar zuwanta qasar nan,bugu da qari su basu da ido a nigeria,shine zai shige musu gaba waje batun neman raihana,amma ya qeqasa qasa yaqi,yace dama can yana da hujjojin dake nuna cewa ita din bibiyar maza take,haquri yayi da ita,maimakon ya zauna a duba matsalar batanta,sai saki da ya rubuta mata ya baiwa 'yan uwanta takardar,yace idan sun ganta su wuce da ita qasarsu" shuru hajiya qarama tayi tana sauke numfashi,da alama har kwanan gobe abun yana tabata bai wanke daga zuciyarta ba,yayin data jefa kaltum cikin zuzzurfan tunani. "Tun kawo raihana qasar nan babu wanda ta shaqu dashi irina,hasalima a sannan tare muka qarasa karatu ni da ita,bani da aminiya kamarta saboda mu biyu mahaifiyarmu ta haifa,kamar yadda nima ta maidani 'yar uwarta,a sannan ina gidana,ni naso karbar baquncin dangin raihana da suka shiga nemanta babu ji babu gani,amma saboda fusatar da sukayi sukaqi sauka,suka kama hotel.....lamarin da yayi matuqar girgiza mu shine,iyakar nema me sunan nema mun yiwa raihana amma babu ita babu dalilinta,cigiya kafafen yada labarai babu inda ba'a kai ba shuru maqatau,yan uwanta sun share watanni suna nema amma babu nasara,har suka koma qasarsu suna zuwa lokaci bayan lokaci amma har yau da nake baki labarin nan babu labarinta,wannan daliline yasa muka saddaqar cewa an sace raihana ne an kuma kasheta,amma inda tana raye ko da bata kawo kanta ba yadda cigiyarta ta watsu a na qasar dama waje....ba shakka ba za'a rasa wanda zai kawo rahoton ganinta a wani waje ba...." Yan uwa raihana sun jima da sarewa,sunma tattara sun bar koda leqo qasar nan,lefin rashid ya sanya suka daina koda waiwayar samir,wanda shima bansan dalilin daya sanya tun tashinsa bai sha'awar yaje dangin mahaifiyarsa ba,tun ina masa maganar lokaci bayan lokaci nima harna haqura na qyale.....tabbas jikina har yau yana bani jidda tana da hannu kan bacewa da mutuwar raihana,har yanzu na kasa jin qaunarta a raina....kuma zuciyata ta kasa gamsuwa da soyayyar da take nunawa samir" maganar hajiya qaraman ta katse,da alama tana hadiyar dacin daya taso mata ne. Dubanta kaltum keyi,itama tana jin wani abu cikin zuciyarta,tana kuma sake kallom hoton dake maqale,ba shakka itace a jikin hoton biba data dauko,to meye alaqar biba da mahaifiyar samir din?,meye haka yayi tasiri a ran samir daya sanya ya nesanta da dangin mamarshi?,meye alaqar matar dake gidan masu lalurar hankali da wannan matar?,tabbas akwai kamanni a tsakaninsu,saidai akwai wasi banbamce banbamce kuma data kasa ganesu,meye alaqarta da mummy harta ziyarceta a wanacan lokacin?. "Na jima banyi wannan maganar da wani ba sai ke kaltum,bansan me yasa ba hakanan naji ina sha'awar baki wannan labarin,qila zaki tayamu da addu'a,addu'ar da har kullum mu masoya raihana mukeyi,kan koda kabarinta ne Allah ya nuna mana shi" qas tayi da kanta tana jin tunaninta na hautsinawa,yana son hada mata fuskokin nan uku waje daya "Allah ya shiga lamarin?" "Amin don nabiyyur rahmati" hajiya qarama ta amsa tana janyo wayarta,yayin da kaltum taci gaba da son daidaita makamar wadan nan zantukan da dukka hasashen zuciyarta a mizani guda,yadda zasu bata cikakken bayanin da take so. "To ya rashid kodai suna hanya har yanzu bai qaraso ba?,gashi an kusa fara daurin auren,kuma wayarshi a kashe" hajiya qarama tayi maganar tana sauke wayar daga kunnenta,saita tashi ta na nufar qofar fita daga dakin. A babban falon ya dikko sukaci karo da mummy,wadda ke keto falon cikin shigar alfarma ta wani baqin material daya haskata sosai,sai sheqin duwatsun da aka masa qawanya dasu yakeyi,tun daga wuyanta zuwa hannunta designers ne na jewelry daketa sheqi suma,bayanta kuma photocopy din tata ce wato najwa biye da ita,tana hura hanci tare da yiwa kowa kallon daya daya,kusan wannan din halayyarta ce,kada ma taga 'yan son zuciya da neman gindi zama....hadi da masu ganin kimar mummyn saboda yawan kyautarta na miqa gaisuwa da girmamawa. Cikin salon nan nata da koda yaushe take amfani da shi wato fara'a da sakin fuska take amsawa kowa,kafin ta maida hankalinta ga hajiya qarama ta soma gaidata,ba tare data damu da cewa ita dince matar yaya ba,ita ya kamata ta gaida. Kamar ko yaushe ta amsa mata babu yabo ba fallasa,tayi gaba zuwa dakin ya dikko,mummyn na biye da ita a baya. Tsohuwa ce sosai,don gaba daya kanta ya cika da furfura,saidai kuma yadda tayi quruciya me cike da nagarta da bin Alla sai tsufan nata yaxo mata da kyau,bata rasa baqora ba kamar yadda bata rasa hankalinta ba,hannu biyu ta karbi mummy kamar ko yaushe,saboda yadda mummyn ta maidata,kamar itace ta tsugunna ta haifi professor rashid. Hajiya qarama na daga gefe tana ta gwada wayar professor din amma still dai taqi shiga,saboda sun riga da sunyi magana da ita kan cewar,zai iso nan da awa biyu ne,akwai ganawar da zasuyi shi da ita da ya dikko kan auren samir. Tsaki ta danja sai duka suka kalleta "Ya dikko na kasa samun yaya rashid,bansan ko matsalar network bane irin na qasar nan" "Muna daya ashe,nima tunda na fito daga gidan hajiya shuwa nake gwada kiran nasa amma ban sameshi ba" mummy ta fada fuskarta na nuna damuwa,ajiyar zuciya hajiya qarama ta saki,ta duba agogo "Amma yaci ace ma ya qaraso,indai ba fasa zuwan yayi ba" "To Allah yasa lafiya" yadikko ta fada "Ameen" duka suka amsa a kusan tare. Ba kasafai ta fiya zama waje daya ita da mummy ba,amma wannan karon sai ta kasa tashi,taci gaba da zama a wajen. Turo qofar da akayi ya sanyasu daga kai,kowa ya bawa qofar hankalinsa. Samir ne ya bayyana,kana duban fuskarsa zakasan cewa cikin tsantsar tashin hankali yake,saidai yanata qoqarin dannewa da kuma boyewa,amma hakan bai boyu ba a idanun hajiya qarama,don haka sai ta miqe tsaye. Cikin dakiya da qarfin zuciya yace "Yanzu aka kirani a waya,su daddy sun samu hatsari a hanya,cikin bauchi" dukkansu suka miqe tsaye suna zabga salati,hajiya qarama hannu a ka a matuqar rude,mummy hannunta bisa qirjinta,idanunta a waje,hannu ya daga musu cikin son kwantar musu da hankali "Karku daga hankalinku,ba wani mummunan abu bane ya faru dashi din,ban gayawa kowa ba,kuyi addu:a,zanje na duba yanayin da yake ciki nida amiru"..... *_KOMAI NISAN JIFA....KUMA KOMAI NISAN DARE....SHARRI KARE NE.....ME SHI YAKE BI.... muje zuwa yanzu zaren zai soma warewa_*🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️ 54 A rude hajiya qarama taja mayafinta mummy ta biyo bayanta "Mu tafi tare samir,muje tare" hannu ya sake daga musu "A'ah hajiya,kuyi haquri ku zauna,zamuje mu duba,duk abinda ake ciki zakuji" da kalaman kwantar da hankali ya samu yasha kansu,duk da cewa shima a sare yake,hakanan zallar tashin hankali yakeji yana dawainiya da shi. *_ƘAUYEN ƊINYA_* Kowanne lokaci irin wannan tun bayan zamantowarta ita daya a sashen,lokacine da yake zame mata bata aikin komai,domin kuwa tana gama komai nata da wuri,sadai ta zauna tayi sana'arta,wadda kullum kwanan duniya take habaka,wanda ta samu kakkauran jari daga wani tallafi da wani bawan Allah ya bayar ga mata marasa galihu dake qauyen,kuma cikin ikon Allah sunanta ya fito a sahun farko,abinda bata taba zata ko tsammata ba,hakanan adadin kudin da aka batan ya bata mamaki qwarai,don kaf tsahon rayuwarta bata taba mallakar kudi makamancin haka ba. Sai data gama kallonta daga dan nesa,sannan ta kwado sallama sashen tana tabe baki,sai data daga kanta ta dubeta kana ta amsa mata. Qarasowa tayi tayi tsai a kanta,hannunta a qugunta,ta fara magana "Ni wallahi zuwaira kullum kwanan duniya mamaki kike bani,ke kamar ma baki damu da bacewar diyarki ba sama ko qasa?,kin kama sana'a baji ba gani?,ko tunanin mijin nata ya saidata ko ya batar da ita bakya yi?". Ajiye abinda take auna man qulin da aka kawo mata tayi,ta tada kai sosai ta kalli inna laure "Ke kin taba ganin wanda yake da Allah....ya kuma yi imani da wanzuwarsa,da kuma cewa shidin yana cikin lamuran bayinsa ya girgiza?,kin taba ganin wanda yake addu'a bisa yaqinin Allah na jinsa ya kasance cikin damuwa?" Baki inna laure ta tabe,don ita sam ba haka taso taga zuwaira ta kasan ce ba,so tayi bayan tafiyar kaltume ta lalace ya daidaice,tunda dama itace me tagazawar,sannan kuma ya zamana ita kanta kaltum din batakai wannan lokacin ba babu labarinta,so tayi cikin wata daya biyu ko uku ta dawo gida a wulaqance tunda taqi auren auwalu,duk da cewa yanzun ma tana qasa tana dabo,tunda ba'asan duniya ko nahiyar da take ba "Ai shikenan,zuwa nayi na gaya miki dama kada kice ba'a gaya miki ba,kinsan idan ana harkar arziqi kunya ake bawa tsiya,ajima kadan za'a kawo kayan lefe da na sa ranar asiyatu yarinya haihuwar la'asar" murmushi ummansu tayi "Kai ma sha Allah,'yata asiya lokaci yayi,to ubangiji ya bada sa'a,ya kauda dukka abunqi" ta fada tana daukar abun awonta taci gaba da aikinta,don bata da abun fadan daya wuce wannan,tunda take bata taba ganin neman aure irin na yaran gidansu ba,daga asiyan har kaltume kamar yaran tsintuwa?,har gwara kaltum siya mata akayi?,amma asiya fa?,su sukace sunji sun gani,kaf maganar aurenta da alhj dauda har kawo yau babu wani magabacinsa,abokansa ne suke aiwatar da komai,ko kayan auren da za'a kawo din abokansa ke tsaye akan komai,amma ko a gefan silifas din kawu iliya ko ita inna lauren,iya kudin da yake barar musu kawai ya ishesu,ba abinda ya shafesu da yanayin yadda komai yake tafiya. Kamar hadin baki,inna lauren bata jima da barin wajen ba ta jiyo gudar mutanen da xasu jeren wasila,wadda za'a daura aurenta a gobe da nasuru,nusurun da sai da umma tayi masa nasiha da gaske sannan ya haqura yabi abinda mahaifiyarsa lantai keso na auren wasila data wajabta masa,wanda ita tayi uwa tayi makarbiya ta gabatar da komai na auren. ******kallo daya zaka yi masa ka karanci zallar rudani gami da tashin hankali dake saman fuskarsa,gaba daya launin idanunsa sun canza,yana tsaye qyarrr a gaban gadon da daddy ke kwance sashe na musamman na intensive care unit,wadda na'urori ke faman aiki a kansa cikin cikakkiyar kulawa. Tun ranar da aka kawoshi asibitin washegari ake sanya ran farfadowarsa,sai gashi an kwashe kwanaki biyar amma babu batun farfadowar tasa,abinda yasa aka daukeshi daga dakin da yake aka dawo dashi nan din tsahon kwanaki hudu kenan,wamda hakan ya sabbaba tashin hankali da rudani a family professor rashid,ba family dinsa kawai ba,hatta abokan siyasarsa dama kasuwancinsa gaba daya. A hankali ya sauke hannyensa dake rungume a qirjinsa, yajuya a hankali saman qafafunsa ya fice daga dakin,yana jin wani nauyi na sake mamayarsa dangane da situation din da mahaifin nasa ke ciki,bai taba tsammatar soyayyar mahaifinsa na danqare a ruhinsa ba sai a wannan lokaci,bai tana tunanin akwai wani burbushin soyayya a tsakaninsu ba sai yanzu da yaga yana dab da rasashi. Yana fitar farfajiyar dake gaba da dakin dukkaninsu suka miqe,ya bisu da kallo daya bayan daya,gaba dayansu ahalin professor ne,kowa ya sashi gaba da idanunsa,wasu na tambayarsa,kowa so yakeji yaji labarin wani canji ko ci gaba game da ciwon nasa,tunda shi daya ne mutumin da suke bari ya shiga wajensa. Dauke idanunsa yayi daga fuskar hajiya qarama,wanda cikin kwanakin yanayinta kawai zai nuna maka tashin hankalin da take ciki,ya maida idanun nasa gefan hannun hagunsa inda sheshsheqar kukan jawahir ke tashi,ta dora kanta samam kafadar kaltum. Idanunsa ya maida fuskar kaltum din,itama kamar sauran ahalin gidan,ya rame har a fuska,yana sane da yadda take dawainiya da zirga zirga kullum sau babu adadi tsakanin gida da asibiti,kawo abinci da sauransu,duk da abincin ba wajen kowa yake ciyuwa ba. Yana ganin bai mata adalci ba idan ya barta tana ci gaba da ganin tashin hankalin da iyasu familyn professor rashid ya shafa ba,ya kamata ya kaita inda zatayi nisa dasu. "Jikinsa alhamdulillahi,saidai yana buqatar addu'arku dai" itace amsar daya iya basu. Cikin hikima da dabara ya kwantar musu da hankali,sannan ya waiwaya inda umar ke tsaye "An samo drivern alhajin,yanzu haka yana wancan dakin ana bashi kulawa" dakin yabi da kallo sannan ya dawo ya dubansa ga umar "Likita ya bada damar ganinsa ne?" "Eh,saboda shi nashi raunin da sauqi,an fara bashi treatment a wani asibiti kafin a samu damar ganoshi" kai ya gyada ga dubi umar din "Ka yiwa bashir magana,a tabbatar an maida kowa gida,saboda nan ba wajen xama bane,jiya likita yayi magana kan haka,zamansu anan xai sanya 'yan dubiya suyita zuwa,idan ka gama kaima ka wuce kawai" "Yes sir" ya amsa masa,sannan yayi gaba zuwa dakin da umar din ya nuna masa. A hankali ya tura qofar dakin bakinsa dauke da sallama,ya amsa masa da murya irin ta mash ciwo. Idanun samir a kansa ya janyo kujera ya aje gaban gadonsa,maimako n zama sai ya dogara da ita,sannu yayi masa ya amsa yana gaida samir din,hanunsa guda daya an saqalo masa shi ta wuyansa,kamar yadda qafarsa ke nade da bandage haka kansa ma. "Wallahi yallabai.....kaga tsautsayi ko?,shekara da shekaru ina tuqa alhaji,sai wannan shekarar tsautsayin yazo......muna tsaka da tafiya irin motocin nan masu yiwa mutane overtaking ta dakemu,ban ankara ba kan motar ta qwace min muka gangara.....ashe ni na fada wata gona,sai manoma ne suka tsintoni,alhaji kuma.yayi wannan mummunar buguwar" ya qarashe maganar yana matse hawaye. "Haka Allah ya qaddara,Allah ya rufa asiri" samir ya fada yana sauke qafarsa guda daya daya dora saman kujerar,dai dai sanda wayar dake aje gefan bala drivern professor ta dauki qara,abinda yaja hankalin samir din,ya waiga don taimaka masa wajen daga wayar,yana mamakin ma yadda akayi yake tare da wayar yana a irin wannan yanayin,saidai har bala ya daga wayar da daya hannun,ya tallafeta da hannunsa me ciwo wanda yake daure,yana kuma qoqarin dannan wajen amsa kiran. "Kayi a hankali karka fama ciwonka" samir ya fada,saiya daga kai da sauri ya dubi samir din "To yallabai"ya amsa masa yana dan sakin wayar,abinda yasa ta sulale kenan daga hannunsa. Da dan mamaki tattare da shi ya baro dakin,sai ya zaro wayarsa,ya bada umarni aje gidan bala,a tabbatar an ajjiyewa iyalinsa kudi da kayan abinci wadatattu saboda yanayin jiyya,sannan yaci gaba da takawa a hankali ya isa office din likitan sukayi magana dashi,daga nan ya wuce zuwa bangaren ajiyar motoci,saboda yana son nan da gobe matuqar daddyn bai farka ba,kada ya wuce jibi a qasar nan. Har ya sanya hannu zai bude murfin motar idanunsa suka sauka a kanta,tana tsaye riqe da kwando na kayan abinci,saidai kanta na kallon qasa,da alama ta shiga zurfin tunani ne ba tare da ita kanta tasan da hakan ba,saiya fasa bude motar,ya fara takawa zuwa inda take a hankali idanunsa bisa kanta. . Bataji isowarsa ba har sai daya tsaya a gabanta,tana daga kai suka hada idanuwa,ya kafeta da idanun nashi yana hango wani rauni cikin qwayar idanunta,raunin da baisan na meye ba,yayin da ita kuma take kallon yadda lokaci guda ya sauya kamar bashi ba,tana da tabbacin cewa duk mutum me uba irin professor dole ya shiga irin wannan dimuwa a duk sanda irin haka ta faru dashi,duk kuwa da cewa ta karanci akwai wata bahaguwar alaqa a tsakaninsu,DABI'AR ZUCIYA ne damuwa dame kyautata mata,da kuma qin me munana mata,a kwanakin tana jin zuciyarta a matuqar matse,saboda duk abinda ya shafi jawahir ya shafeta,bare kuma uwa uba shi din,da takeji a ranta yayi tafiya me nisa ya nutse ciki. Dumin hannunsa kawai taji saman nata yana qoqarin amsar kwandon,sai tasa daya hannun ta dafe "Ka barshi zan dauka,ya najwa ce tace na tsaya a nan" Ransa yaji ya dan baci,don yasan tana sane ta sakata tayita tsaiwa kenan?,tunda already babu kowa nasu a asibitin,duka sun wuce gida,duk da yanayin da zuciyarsa take ciki,yana jin cewa lokaci yayi da ya kamata yayi wani abu a kai,amma baisan yadda zai fuskanci daddy ba,bayason a irin wannan lokacin ya rasa daddyn ba tare da sun fuskanci juna ba,ba tare daya gaya masa komai ba,koda zai masa mummunan hukunci kuwa. Karban kwandon kawai yayi yayi gaba,hakan ya sanya dole ta biyoshi a baya. A hankali yake tuqa motar kamar wanda bashi da laka a jikinsa,motar ta dauki shuru,kowa da abinda ke kai kawo a zuciyarsa. Ta qofar gidan motarsu ya gara a hankali zata wuce,saita daga kai tana bin gidan da kallo,a duk sanda zasu wuce ta qofar gidan sai taji ya dauki hankalinta,sai taji matar ta fado mata a rai,sai taji tana sha'awar shiga gidan,sai taji kamar akwai wata babbar mantuwa da tayi cikin gidan wadda bata daukota ba tun ranar da suka je da mommy. Kallonta yazo yi saboda jin yadda ko motsinta baya ji,saiya dauke kansa yana duban inda take kalla,gida ne da yasha attempting ziyartarsa amma har yau ya kasa zuwa,ko a yanzu a kullum idan yayi yunqurin zuwa sai wani abu ya dauke hankalinsa,bai sani ba ko tana kallon gidanne saboda tana tuna rakiyar data taba yiwa mommy?. "Kina kewar gida ne?" Ya jefa mata tambayar cikin ba zata,abinda ya dauki hankalinta harta waiwayo ya dubeshi,suka hada idanu,saiya maida kansa ga tuqin da yakeyi. Shuru tayi ta kasa bashi amsa,sai qas da tayi da kanta,maganar ma ace tana kewar gida ai bata baki ne,taje gida taga ummanta da habibanta wannan shine babban burinta,to amma a irin wannan yanayin da take ciki,shin kyautawa ce ta nisanci jawahir daya kasance ita ke bata baki da kwantar mata da hankali?,ko kuma dai dai ne tayi nesa dashi din?,wanda bashi yake da buqatar ganinta ba,zuciyarta ce keda buqatar gani tare da sanin halin da yake ciki. "Ki shirya zansa gobe a kaiki" idanunta ta lumshe da sauri,wannan shine furucin data jima tana son ji daga bakinsa,saidai yazo a lokacin da ba zata iya tafiya gidan ba "Bazanje yanzu ba.....ba yanzu ba" ta furta da lallausar muryarta da har kwanan gobe yake mamakin zaqinta,maganar tata ta daure masa kai,baiyi shuru ba ya tambaya "Saboda me?" Sai data danyi jinkiri sannan ta amsa masa "Sai Allah ya bawa daddy lafiya" sosai maganar ta dokeshi ta kuma bashi mamaki,ya waiwaya yana duban sashen da take,kafin ya maida kansa zuwa titi,dai dai lokacin kuma ya fara qoqarin taka birki saboda matar dake gabansu,saidai abun mamakin,duk yadda yayi qoqari ya taka burkin abun yaci tura,hankalinsa yadan tashi,yayita yunqurin tsaida motar amma bai cimma nasara ba,har sai da tayi gab da motar sannan ya samu nasarar tsaidata. Gefen titi ya gangara ya kashe motar gaba daya yana sauke numfashi tare da godewa Allah daya sanya ba gudu yake ba,ba shakka da saidai aji mummunan labari. Tsahon minti daya idanunsa na a rufe yana fidda numfashi tare da sauke ajiyar zuciya,sai kuma ya buda dukka idanun nasa kamar wanda aka yiwa allura lokaci guda saboda shigar wani tunani qwaqwalwarsa. Wayarsa ya zaro da sauri kaltum na binsa da kallo,don kusan batasan me ya faru ba,ya dannan wasu numbers ya kira wani,ya masa kwatancen inda suke,yace yazo da mota akwai wanda zai dauka,sannan ya kashe ya sake kiran umar,ya bashi umarnin zuwa inda suke shima,amma ya taho masa da abdulganiy mechanic su taho tare. Wayar ya ajjye,ya bude motar ya fita zuwa waje,zuciyarsa na hasaso masa al'amura da dama,tabbas idan hasashensa gasky ne to akwai lauje cikin nadi,tabbas there is something he needs to know,ya gayawa kansa yana gyada kai. Motar daya fara kira ita ta fara isowa,saiya yiwa kaltum umarnin ta shiga,tana iya hangen fuskarsa koda bayan barinsu wajen,yanayin fuskarsa ya sake sauyawa fiye da yadda suka baro asibitin,wanda ita batasan silar afkuwar hakan ba. Dukka motar ya bude bayan isowar umar da bakaniken kamfaninsu "Ka duban min ita da kyau,ina cikin tafiya na laluba birki naji babu" cewar samir,wanda ke tsaye yaui folding hannayensa a qirji "Ok sir" abdulganiy ya amsa masa yana nufar motar. Daga shi har umar bin abdulganiy suke da kallo,har ya gama bincikensa ya dawo inda suke tsaye "Birkinka aka kwance maka sir" ya amsa masa da gurbatacciyar hausarsa. A mamakance suke kallonsa,umar ne ya motsa baki "Kamar yaya?" Ya tambaya yana tsareshi da idanu "Eh haka nima na gani,kusan awa daya kenan da tsinkeshi,alamu sun nuna bawai ya tsinke bana a kan kansa ba". Kai samir ya jinjina,sannan ya dakatar da abdulganiy "Shikenan....umar,ka kira hashim yazo ya dauki motar ya biyomu da ita garage din company.....muje can,ka duba min motar daddy dake aje wajenku,inason sanin abinda ya sameta itama". Cikin qananun mintuna suka isa company din,wanda kusan amiru ne yake gabatar da komai,don bashi da cikakkiyar nutsuwar zama cikin office dinsa. Ta qofar baya ya sanya suka shiga,saboda baya buqatar kowa yasan cewa ya shigo din,sannan suka wuce inda suke ajjiye tsofaffin tractors dinsu,inda aka ajjiye motar daddy bayan an daukota daga inda abun ya faru. Yana tsaye jikin wata mota still hannayensa goye a qirjinsa sanda abdulganiy ke yiwa motar binciken qwaf,tsahon awa kusan guda kenan kafin ya fito,ya hada gumi saboda aikin,yana share zufa ya masa bayani "Itama tsinkewar birki ne,saidai na kasa tantance tsinkawa akayi koda.kansa ya tsinke,duk da dai gaskiya duba da lafiyar motar,da kuma 'yan watannin da tayi bata jima ba,nake ganin kamar shima kwanceshi akayi,amma ba lallai ne hakan ya zama gaskiya ba" "Ya salam" ya furta yana yin qasa da kansa,tabbas.....babu ko shakka haka na nuni da cewa akwai wadanda ke farautar rayuwarsu,shi da daddyn kenan?,xai iya yiwuwa da duk wani wanda yake kusa dasu?,lallai ya zama dole yayi wani aiki,ya zama dole ya aiwatar da wasu abubuwa,don haka bai iya amsawa abdulganiy ba ya fara takawa yana ficewa daga warehouse din yana zaro wayarsa daga aljihunsa. 55 Dz A hankali cikin kasala da mutuwar jiki take takowa zuwa kitchen din gidan,kitchen din data jima rabonta dashi,saiko yau,tun bayan wayar da samir din yayi,ya umarci hajiya qarama ta baro gidanta su tattaro su dawo cikin gidan professor rashid din,bayan nan dinma ya sanya an qara securiy,wanda gaba dayansu babu wanda yasan abinda hakan yake nufi,don babu wanda ya yiwa bayani a cikinsu. Baccin daya yanke mata tun cikin dare ne cike a idanuwanta,tun daga sanda tayi mafarkin matar bata sake rintsawa ba,don haka ta yanke shawarar fitowa zuwa kitchen din ta kama wani aikin ko hakan xai debe mata kewa,ya kuma qwarara jikinta. Tun daga nesa ta hangi biba tsaye cikin kitchen din tana feraye dankali,sai tayi sallama,biban ta waiwayo fuskarta dauke da fara'a tana amsa mata. "Ina kwana" kaltum ta gaidata tana zaro wuqa a ma'ajiyarsu,ta fara tayata firar dankalin,amsa mata tayi kamar kullum cikin sakewa,sai suka fara taba hira sama sama,duka hirar tasu akan ciwon daddy ne da makamantansu,saidai can qasan ran kaltum maganar da takeson yi mata tana tsunkulinta,bata samu damar yi mata ba har sai sanda suka gama gyara komai suka dora kan wuta. "Ashe hotonki maman yaya saraki ce a jiki?,kuna da alaqa daman?" A birkice ta dago kanta ta dubi kaltum,razana da firgici suka bayyana baro baro saman fuskar biba,ta soma waige waige da hanzari,ta tabbatar babu kowa sai kawai ta wafci hannun kaltum ta tura qofar baya ta kitchen din ta jata ciki. Idanuwa ta tsare kaltum dasu,kafin hawaye ya soma wanke mata fuska,cikin muryar kuka,kans murya can qasa ta fara magana "Duk yadda nayi dake karki tona wannan maganar kaltume saida kika tono ta?,shin bakyason lafiyarki ne?,ko bakison ranki dana iyayenki?,to bari na buda miki komai ko hakan xaisa ki janye kika ki kuma yiwa kanki da yan uwanki gata.......tabbas mamar samir ce a jikin hoton,raihana......wadda ni ba kowa bace face 'yar aikinta shekaru masu dama,yar aikin data dauketa kamar 'ya uwa,ta yimin dukkan wani gata,ta bani kulawa da dan uwa zai baiwa dan uwansa,hakan yasa nima na dauketa kamar yar uwata,na kuma riqi samir kamar d'ana.....mutum ce iya mutum,wadda duk yadda za'a kwatanta miki kirkinta ba zaki fahimta ba sai zama ya hadaku da ita.....kwatsam dare daya hajiya jidda ta shigo rayuwar professor rashid.....ta zama matarsa,abinda babu wanda ya taba zato ko tsammanin zai faru,duk da cewa kusan auren cin amana ne jidda tayi da professor amma haka hajiya raihana ta karbi qaddararta....." Dubanta kaltum tayi tana mamakin kalmar auren cin amana,kamar biba zuwaira tasan me take rayawa saita gyada kai "Eh.....auren cin amana,domin kuwa jidda 'yar aikin hajiya raihana ce" idanuwa kaltum tadan bude kadan alamun mamaki,wannan wanne irin labarine haka a birkice? "Karki dauka gama garin me aiki" biba ta fada tana sake matsawa kusa da kaltum muryata a kwance "A'ah,irin masu aikin da basu da kowa,suke da matuqar buqatar taimako,ta daukota ta kawota cikin gidanta,ta nuna mata dukkan gata da rufin asiri,ta sanyata taci gaba da karatun jami'a,bayan ta kammala,tasa Daddy ya bata aiki a wani kamfani nasa da alokacin yake gudanar dashi,duk da hankalinsa a sannan ya fara karkata ga siyasa.....amma jidda ta aure mata miji,ta kuma janye hankalinsa gareta ita daya qwallin qwal,munyi imani bata asiri bata kuma aiki dashi,bamusan da wanne siddabaru take amfani ba,amma ta juya tunanin professor gaba daya,bashi da cewa sai tata,kullum kwanan duniya akwai fada ko tashin hankalin da zai saukewa hajiya raihana,tun bata damuwa harta shiga damuwa,kwata kwata ta zama kamar 'yar kallo cikin gidan,qalilanne cikin 'yan uwan professor suka koma suna ta tata,kamar irinsu hajiya qarama,jidda ta janye komai ta kuma janye kowa......,lokaci mai tsaho ana a haka,har zuwa sanda jidda haihu yara mata guda biyu,tazararsu shekara biyu kacal,ba jimawa hajiya raihana ta samu ciki itama,wanda tunda ta sameshi babu zaman lpy,cikin da ta fita dashi kenan,rana daya muka tashi cikin gidan nan da maganar bacewarta,qaura wambai babu ita babu dalilinta,sai samir data bar mana,duba na duniya ba'a samu hajiya raihana ba,a sannan jikina ya bani ba mutuwa tayi ba kamar yadda mutane keta fada,saboda ganin girman cigiyar da akayi amma babu labari ko motsinta. Zuciyata ta sake yarda da abinda take raya min ne na cewa ba bata tayi ba,akwai abinda ya faru da ita,saboda wasiqa dana samu saman gadonta,kuma bisa dukkan alamu tana tsaka da rubutata ne abinda ya sameta ya faru da itan,sirrine tsakanina da ita,bazan iya gaya miki ba.....a lokacin jidda ta shigo dakin kawomin samir daketa rigima akan na lallasheshi,taga wasiqar,ta karanta,a gabana ta duqunqune wasiqar ta kuma sakata a toilet tayi fuloshing dinta "Dukkan abinda ta rubuta ki daukeshi ki watsar dashi gefe.....bari na gaya miki,yau ba watan raihana uku ba bata nan?,to ki sanya a ranki watanta uku cikin kabarinta.....domin ba zaku sake ji ko ganinta ba,wannan maganar ina gaya miki itane tamkar kana tona sirrinka ga wanda yake kan gargarar mutuwa,kinga ba wanda zaiji saidai ko qasar kabarinsa.......fitar wannan maganar dai da take rasa ranki,hakanan dukkan wanda kika shaidawa shima kin sakashi cikin babban hadari,babbar soyayyar da zaki nunawa dukkan wanda ke tare dake shine,ki kiyaye kunnuwansa daga sauraren wannan batun" maganar data gaya min kenan cikin kakkausar murya da yanayi me ban tsoro. . "Na tsorata sosai,don haka a sannan na roqeta kan zan ajjiye aiki,zan koma gida" "Bismillah,kina iyawa indai kin shirya mutuwa keda duk wanda yake rayuwa tare dake" wannan maganar tasa nayi shuru ina tsuma saboda tsabar tsorata,ta jefeni da wani kallo,sannan ta matso gabana "Bari na gaya miki wani abu....keda duk wanda yasan qamshi qamshin abinda ya faru bashi ba fita daga gidan nan,aiki kuma yanzu kuka fara har zuwa .lokacin mutuwarku,bance ba zaku dinga zuwa gida ba,amma babu tabbaci har sai abinda na gani" da wannan maganar ta fita ta bani waje......haka na rayu dukka shekarun nan ina kuka a boye na rashin raihana,ina addu'ar Allah ya bayyanata idan tana raye,idan kuma da gasken ta rasu.....to ina mata fatan samun rahamar Allah da dacewarsa,ina kallo take nunawa samir soyayyar da nasan bata gaskiya bace amma bani da abinda zan iya aikatawa.....sai taso sangartashi da lalatashi amma haqarta bai cimma ruwa ba,ban sani ba ko qarfin addu'ar mahaifiyarsa ke bibiyarsa,da kuma alkharin da tayi a rayuwarta ne yayi masa tasiri?......da wannan bata yiwu ba saita canza salo,ta sanya samir yana sabawa dukkan muradi ko buri da abinda mahaifinsa keso,ta wannan hanyar ta kauda dukkan wata jituwa da qauna da yakewa samir din,ya koma kallonsa a matsayin bijirarren da mara biyayya,a fakaice takeson ture samir daga zuciyarsa ta cusa najwa ta qarfi da yaji,taso hadawa da jawahir....amma yarinyar sai Allah ya halicceta daban,kusan ta debo dabi'un samir din,wannan yasa sukafi jituwa qwarai da gaske......abu daya ne yasa naqi shiga wannan yaqin kan rayuwar samir...." Shuru ta danyi,murmushi kuma ya subuce daga fuskarta ta tsakiyar hawayenta "Duk abinda takeyi tana yine saboda ta raba samir da mahaifinsa.....tana qarfafa samir yayi abinda ya tsarawa ransa kar ya damu da abinda mahaifinsa yakeso......sai Allah ya bashi wata kariya,ya bashi wata zuciya ta alkhairi,wata zuciya ta hangen nesa,zuciya meson taimako......ya zamana dukkan abinda ya dage zaiyi din me kyau ne,tayi hakan don ta nisanta shi da ubansa,sai kuma hakan ya zame masa alkhairi ba tare data farga ba,samir.....bai manta ni ba,bai manta wacece ni a wajen mahaifiyarsa ba,duk sanda zai aiwatar da wani abu yana tambayata shawara koda aboye ne ba'a gaban idanun kowa ba,ina kuma bashi shawara dai dai gwargwado,duk da cewa....a wasu abubuwan hajiya jidda ta riga tayi tasiri a tunaninsa,misali,yabar zancan mahaifiyarsa sam ya daina daukoshi,ya daina yinsa,na rasa ta yadda zan dauko masa wannan tunanin na dawo dashi cikin kwanyarsa,na rasa yadda zan fahimtar dashi cewa hajiya jidda ba masoyiyarsa bace,hajiya jidda maqiyaya ce gashi da rayuwarsa........" tana kaiwa nan wani kuka me nauyi ya taso mata,kukan daya sanyata komawa ta qofar kitchen da sauri. Sulalewa kaltum tayi a hankali ta zauna sosai a qasa,yau tana ganin wata rayuwar bayan rayuwar ta data sani,ashe kowacce rayuwa da irin nata qalubalen?,tayi tunanin cewa matuqar kana cikin wadata baka da wani sauran qalubale,ashe karatun ba haka yake ba. Amma wacece a gidan masu tabin hankali?,wacece ita?,anya sunsan da zamanta?,meye dangantakarta da raihana maman samir?,mahaifiya?,qanwa ce ko 'yar uwa?,jikinta yana bata tabbas akwai wani abu a qasa,saidai kunnuwanta suna mata amsa kuwwa,tare da tuna mata maganar mummy a ranar da sukaje gidan,jan kunne da gargadi da kakkausar murya "Ko 'yar cikina ban yarda naxo da ita wajen nan ba,waje ne dake cike da sirri,waje ne kuma me hadari,kisa a ranki baki taba zuwa wajen ba,hakan shi xaisa ba zaki gayawa kowa kinxo din ba kinji kaltume?" Bata dauki komai ba a wannan lokacin,ta dai gyada mata kai a ladabce,ba tare data fahimci ko hasaso komai a kanta ba. ******Tun daga wannan ranar kaltum bata sake samun nutsuwa kan maganar ba,kullum maganar ke yawo cikin kwanyarta,gefe daya kuma hankalinta ya dauku ga mummy,haka kawai ta samu kanta da nazarin mummy,cikin nutsuwa da ankarewa ta dinga fuskantar wasu abubuwa da dacan hankalinta bai kai ba,yanayinta daban kam ciwon daddy a gaban samir da kuma sanda baya nan,yadda take mu'amala da masu aikin gidan daban da yadda take mu'amala da biba,mu'amalarta da qawayenta da sauransu. A kwanakin duk sanda ta kalli Samir wani tausayinsa yake lullubeta,gaba daya ya fada yadan rame,saidai hakan bai fiddashi daga nutsuwarsa ba,nutsuwar nan tana nan,amma akwai tarin damuwa saman fuskarsa da ta gaza bayyanuwa,hankalinsa gaba daya ya tattara kan shirye shiryen fitar da daddy waje. *******Karfe biyu na rana ta gama shirya abincin da zata tafi asibiti dashi,duk da cewa wadanda takeyi dominsu basa samun damar sanya koda loma guda a bakinsu,tanayin komai ne saboda jawahir samir hajiya qarama dama daddyn dake kwance,wanda zuwa yanzu am fitar dashi daga icu,saidai yana wani dakin daban na musamman. Tsaf ta shirya cikin atamfa maroon colour,me torches na blue black,da hijab tayi amfani,wanda ya dace da kayan jikinta,ya kuma haskata sosai. Fuskarta ta kalla a a mudubi sanda zafa gotashi,kullum kwanan duniya wani sake gogewa take gami da sajewa da al'ummar gidan,a yau sai taga abun har yafi na kwanakin baya,don tunda aka shiga wannan rudanin na ciwon daddyn rabon data tsaya cikin nutsuwarta haka,gefe daya ga tunanunnuka iri daban daban,fatarta sake fresh take tana bada color me masifar tafiya da hankali,a chocolate color din ma tasu skin din ba kowa ke samun irinta ba,saita qara gaba da sauri,saboda tuna inda zata je da tayi,ta kuma tabbatar driver na nan yana jiranta,hajiya qarama ma na can na xuba idon zuwanta,ko yaya taga batazo din ba saita damu,matsalar gabanta ta daddy baisa ta manta da ita ba,tana mamakin yadda take treating dinta kamar diyar cikinta. Suna tafe a motar zuciyarta da qwaqwalwarta na nutso a duniyar tunani,tunanin daya zame mata qa'ida,har zuwa sanda zasu gifta ta gaban gidan,ta bishi da kallo kamar yadda ta saba,a wannan ranar......sai taji zuciyarta na tsananin bugawa,kamar xafa fasa qirjinta,ta lumshe ido sanda suka gota gidan tana furta "La haula wala quwwata illa billah" saita maida idanun nata ta rufe,har zuwa sanda suka qarasa asibitin. Sai data gaida dukkan wanda ya kamata ta gaida,suka hada idanu da wata baquwar fuska,tana zaune dare dare saman kujera tana danna waya,saita zare idanun nata kaltum din tana miqewa,ta isa gaban hajiya wadda suke zaune tare da jawahir ta zauna ta fara fiddo abincin tana zuba mata. Sai data kammala zubawar hajiya tace "Kinga kaltum,dauki abincin nan ki xagaya ta bayan dakunan can,samir yana can ki miqa masa,na jima rabon da naga ya sanya wani abu a bakinsa,dole yaci abinci ko yaya ne ai" kai ta gyada kana ta miqe tana sake daukan wani plate din abincin "I wanna see him...muje na gani" jauhar ta fada tana sauke wayar dake hannunta,bata waiwayo ba hakanan bata tsaya ba,ta fara tafiya zuwa direction din da hajiya qaraman tace takai masan,haka kawai gaba daya yau takejin zuciyarta a rikice,bugun da take ya zarta qa'ida. Su biyune xaune kan kujeru gufa ukun dake wajen,tun bayan fitowarsa daga wajen likita suka hadu da amiru a wajen "Zuciyata tana gayamin akwai wata a qasa tabbas ba shakka,kuma zargina yafi karkata kan abokan siyasar daddy,kamar sun kutso cikin lamaransa da shirin kau dashi,sannan sun nema hadin kai da taimakon wasu nasa na jikinsa,saidai na rasa gano ko su waye?,amma ba shakka......tabbas bala suspect ne a wajena,duk da cewa bani da gamsassu da qwararan hujjoji.....amma inaji a jikina" ya fada yana kallon amiru da idanuwansa wadanda sukayi laushi,saboda qalubalen daya soma tunkaro rayuwarsu ba tare da shiri ba. Kai amiru ya jinjina cikin dogon nazari,mamaki fal zuciyarsa da kuma shakku,bai bar abun a ransa ba ya dubi samir shima "Dukka bayananka na gane na kuma gamsu,but samir.....bala fa tsohon drivern daddy ne,kuma amintaccensa,ka manta?" Miqewa samir yayi a hankali,ya sanya hannayensa duka a aljihun wandonsa,yayi taku hudu daga inda suke zaune,kana ya baiwa amiru baya "Koya yana iya zama suspect amiru.....idan nace kowa ina nufin harda mommy.....zan sanya idanu akan kowa,zargina kuma zaibi takan kowa" miqewa yayi a hankali,ya taka shima zuwa inda samir din yake,ya tsaya dab da bayansa,sannan ya dora hannunsa saman kafadrsa "Zaka samu dukkan wani gudunmawa da kake da buqata daga gareni,zamu fuskanci wannan challenge din tare kamar yadda muka saba,na maka alqawarin rufe sirri,da kuma dafawarka har sai mun cimma gaci" kai samir ke jinjinawa,baikai ga cewa komai ba ya hangi bullowarsu,tana gaba jauhar na bayanta. A hankali ya zubawa kaltum din idanu,fuskarta sam babu alamu na fara'a ko walwala,duk da cewa tunda daddy ya gamu da wannan tsautsayin yadda walwala da farinciki ya yiwa familyn qaranci ita dinma haka,abinda ya sake daga daraja da qimarta gami da martabarta cikin idanu da zuciyarsa,hidima take bilhaqqi,zaka rantse mahaifin daya haifeta ne. A hankali ya maida idanunsa ga jauhar,wadda take tafe tana latse latsen waya,baya ga earphone dake kunnenta,nazarinta itama yayi na wasu sakanni,yanason tantance wane interest ne dashi a kanta?,ya dauke idanunsa a hankali yana juyawa baya,sai suka kusa karo da amiru dake tsaye bayansa,da alama shima sashen da suka taho din yake kalla,hada idanu sukayi,kowa sai ya dauke idonsa,da alama akwai abinda ke zuciyar kowa,saidai kuma ba muhallin magana bane nan din. Sallamarta ta mamaye wajen a zazzaqar muryar nan tata,wadda ta cika da sanyi da taushi fiye da lokutan baya,amiru ne ya amsa,samir kuma ya sauke mata idanunsa,bata kalleshi ba har ta gaidashi bayan ta ajjiye kayan abincin a gabansa. "Sweet baby......kana ta nan ashe,hajiya tace ga abinci nan kaci.....ayi serving naka?" Jauhar ta fada sanda ta iso kujerar daya koma kai ya zauna,ta dafe bayan kujerar dab da bayansa tana kallonsa. Idanunsa ya maida ga kaltum,wadda tuni tayi nisa wajen zuba masa abincin ba tare da taji da bakinsa ba "Kadan.....hakama is ok" ya fada a tausashe ganin yadda kaltum din ke loda masa abincin bata ko kalleshi ba,daga isowarsu wajen kawo yanzu ta gane dawa suka taho,jauhar....sunan data riqeshi tsaf a kanta,tun wancan lokacin da jawahir ke yawan bata labarinta,a lokacin da batasan ciwon kanta ba,a lokacin da batajin komai don an ambaceta a gabanta. Tura masa gabansa tayi ta miqe "Ni ba za'a sanmin ba?,ko yayan naki kawai kika sani?" Amiru ya fada yana dan murmushi sanda ta miqe zata bar wajen,juyowa tayi,tadan saki murmushi,kana ta dawo a hankali shima ta soma zuba mishin. "Kaci mana please sweet baby,ko sai na baka da kaina,bakaga yadda ka zama bane?" Kaltum ta tsinci muryar jauhar tana fada a wani mugun shagwabe,kamar zata saki kuka,abinda ya sanya hannunta kakkarwa kenan ba tare data ankara ba,ta ajjiyema amiru abincin ta miqe da hanzari ta soma barin wajen. Haka kawai taji batason ma komawa wajensu hajiya qarama,saita nufi qofar fita daga asibitin,tana jin zuciyarta a matse,tare da wani irin nauyi,taci gaba da takawa a hankali tana barin harabar asibitin. Batasan tayi tafiya me nisa ba sai data ga tana hango asibitin masu rangwamen hankalin,haka nan kawai taji kamar ana mata umarnin tafiya zuwa wajen asibitin,sannu a hankali sai gata a bakin gate din asibitin. Idanun masu tsaron qofar a kanta "Hajiya ina zaki?" Murmushi tayi qoqarin qirqirowa "Akwai wanda nakeson gani cikin ma'aikatan?" "Wa kenan?" Daya daga cikinsu ya tambayeta,shuru tayi na sakannin da basu wuce uku ba,tana laluben qwaqwalwarta ko zata iya tuna sunan daya daga cikin ma'aikatan da taji mummy ta kira sanda suka shigo Idanunta suka sauka kan kyauron dake daure a hannun daya daga cikinau "Kyauro" tayi caraf ta ambata "Shiga,yana ciki" ya fada yana bude mata gidan,ta sanya qafarta a hankali,gabanta yana tsananta faduwa,zuciyarta nason raurawa,amma taci gaba da kutsawa zuwa ciki. Kai tsaye taci gaba da sanya kanta,bata tsaya ko ina ba sai office din da aka saukesu wancan karan. A hankali ta tura qofar ta shige zuciyarta na bugawa,babu kowa cikin office din,sai take ji a zuciyarta kamar wata dama aka bata,don haka cikin hanzari ta soma laluben qofar da aka bude musu suka shige wancan karon. Tana kusantar dakin bugun zuciyarta na qaruwa,duhu ne sosai a wajen,da alama duk dakin dake wajen dakuna ne na wadanda ciwonsu yayo worst,aka kuma fitar da ra da samun lafiyar wasunsu,waje ne tsit mai rashin wadatar haske,kai kace maqabarta ne,tana kutsa kai zuciyarta na gargadarta,amma ta wani sashen kamar ana qara mata qaimi da kuma qwarin gwiwa,da haka har ta isa qofar dakin,saidai a kulle yake da kwado,hakan yasa ta matsa kadan zuwa bakin window din,a bude yake,saidai tsaho daya danyi mata kamar wancan karon,ta waiga kadan,saita hango wani dan katako,ta tabbatar zai qara mata tsaho yadda takeso,don haka ra daukoshi cak,ta ajiyeshi saitin window din,ta taka a hankali tana sanya idanuwanta zuwa cikin dakin. Daga can take hangenta,xaune a daya daga cikij corners din dake dakin,a takure kamar wadda ke jin sanyi,habarta na saman gwiwoyinta,idanunta kuma alumshe suke,saidai tana hangen yadda take tattaba yatsun hannunta,kamar wadda ke irga tasbihi da su,hakan yasa kaltum din taji kamar ta sauka ta juya,saboda zuciyarta na tunasar da ita inda take,da kuma wajen wadda take tsaye. "Salamu alaikum" bakinta ya subuce ta furta da sautin da dukka wanda ke cikin dakin xai iya jin abinda tace "Subhanallah" taji ta furta tana daga kanta da sauri ta saukesu ga kaltum dake riqe da qarfe window din tana kallonta. Idanu ta zubawa kaltum din tana kallonta,karo na farko data ga wata baquwar fuska haka tsaye a gabanta,yayin da kaltum ke kallonta tana karantar tsantsar kamanni da suke sake bayyana kansu a yanzun da suke kallon juna kallo irin na qurilla,yayin da wani gefe na zuciyarta ke cike fal da mamakin ambaton subhanallah din da taji tayi. Zuciyarta ta sake raya mata ta aikata wani abu,cikin buguwar qirji ta buda bakinta a hankali "Samir yana gaisheki" zumbur taga ta miqe kamar wadda wani abu ya tsikara,lamarin da yayi matuqar razana kaltum,har ta dan ja da baya,saboda tana ganin kamar zata rugo da gudu ta cafketa,saidai bata qara wani motsi ba illa zuba mata idanun data sakeyi "Muhammad samir rashid azare?" Kunnuwanta suka tsinto kalaman da suke fitowa daga bakinta a sanda take ci gaba da tsaiwar. Ta riga da tasan cikakken sunan daddy,ta kuma tabbatar cikakken sunan samir kenan,saboda haka saita gyada kanta suna ci gaba da kallon juna. Jikinta yayi matuqar sanyi lokacin da taga hawaye yana saukowa daga fuskar matar daya bayan daya,wani busashen murmushi yana son mamaye fuskarta "Ke wace?" Ta sake jifanta da tambayar da batasan amsar da zata bata ba,saidai kafin ta amsa din taji takun tafiya,abinda ya sanyata waiwaya da hanxari cike da tsoro da fargaba tana duban hanya. 56 Sake maida kallonta tayi ga qofar dakin bayan ta dauke idanunta daga doguwar hanyar da har yau wanda ke tafiyar baikai ga bayyana zuwa inda take ba,ga mamakinta sai taga qofar na bude,sabanin daxu da ta ganta kamar a rufe,kafin ta kammala tunanin da zatayi taga anja qofar an bude mata,saita sauka da sauri ta sanya kai cikin dakin. Hannunta taji an fincika,data duba sai taga matar ce,kafin ta gama tantance komai ta isa da ita bakin dan duqurqushin gadonta ta dage mata,ta gane me take nufi,don haka ta shige,ta sauke xanin gadon da ya sauka ya lullube har qasan gadon,tana iya hangenta ta tsakanin labulen ta koma ta zauna kamar yadda take daxun,wanda da zamanta da qarasowar wanda taji takun nasa duka bai wuce second biyar ba. Yana mita ya shigo,kamar wanda yake magana da mutum me hankali "Lalle sabi'u yana wasa da aikin nan,baisan girman aikin dana bashi ba,baisan kuma wace hajiya jidda ba,banda guntun iskanci ya za'ayi ya barwa mutane daki a bude?,salon ki fita ya jawo mana jidali?,dole nayi masa jan kunne me qarfi,idan bazai iya ba ya ajiye a bawa wani". Abinci taga ya ajjiye mata,ya dan tsaya kadan a kanta na wasu daqiqu,ba jimawa wayarsa tayi qara,yayi hanzarin dagawa ya soma amsawa,saiya juya yana ficewa daga dakina da alama wayar da yakeyi ta shagaltar dashi bai rufe dakin ba yadda suka saba ya fice da sauri. Kaltum dake qasan gadon gaba daya jikinta ya jiqa da gumi,gaba kura baya sayaki,gata a cikin dakin me lalurar tabin hankali,wanda har sarqa aka tanada cikin dakin,da alama ana sanyata lokaci bayan lokaci idan buqatar hakan ta taso,na biyu ta ratso ta shigo wani shinge da aka jima ana mata gargadi kan furta koda kalma daya a kanshi,yau sai gashi,bama zancan muhallin ba,ta keta duk wani gurbi ta dangana da tsakiyar shingen tsundum "Fito,ba zasu dawo ba sai tsakiyar dare ko kuma gobe....." Taji ta furta da muryarta a sarqe kamar daxun bayan ta yaye xanin gadon. Mamaki ya sanya kaltum ta xuba mata idanu,ta yaya take magana sak irin ta masu hankali,muryarta ras a kuma nutse?,banda yanayinta babu abinda zai sanyaka kayi tunanin ba lafiyayya bace,kamar tasan tunani da mamakin da takeyi sai ta sake jin muryarta "Cikin hayyacina nake,kar kiji tsoron komai,fito....ina jin kece addu'ata dana jima inayi" wadannan kalaman nata su suka bata qwarin gwiwar fitowar kamar yadda ta buqata. Zama tayi dandaryar qasa kamar yadda take daxun,saita yiwa kaltum nuni da wajen xama da hannunta,ta qaraso a hankali har yanzu da ragowar fargaba cikin ranta,saidai kuma ta samu qwarin gwiwa,ta zauna tana fuskantar kaltum din,a hankali ta buda baki "Duk da bandan wacece ke ba,aiken jidda ce ke ko kuma ubangiji ne ya jeho min ke ki xame min haske kamar yadda na dauki tsayin shekaru ina roqa.......inason insan wacece ke" qas kaltum tayi da kanta,taga abubuwa masu tarin yawa suna kai kawo "Ni ba kowa bace,face wata mara gata da galihu da samir ya dauko daga qauyensu,ya dawo da ita cikin gidansu,ya bata gata da galihu da kuma dukkanin kulawa" "Samir dina?,ya zama mai tausayi da taimako kenan kamar yadda nake roqon ubangijina?" Ta fada muryarta na rawa,da alama zuciyarta fa tsinke,kuka na dab da zuwa mata kowanne lokaci. Kai kaltum ta gyada mata tana dubanta "Amma ya akayi kika sake dawo kanki cikin wannan hatsarin?,bayan na tabbatar zuwanki na farko qaddara tasa jidda zuwa dake?,kuma ina da yaqinin kin samu kyakkyawan jan kunne daga gareta?kinsan wacece ni ne?" Shuru tayi zuciyarta na raunana,batasan amsar da zata bata ba. "Zuciyata ce ta kasa nutsuwa,tana ta gayamin na dawo gareki,bayaga tarin mafarkan da suka cika barcina" kai ta gyada tana kallonta,cike da yabawa da jarumtar yarinyar,tunda har tasan jidda,amma ta yadda ta fuskanci kowanne qalubale ta dawo gareta,ba tare da tasan ainihin wacece ita ba. "Nice mahaifiyar samir.....samir dana ne" maganar data sanya kaltum ta kusa shidewa bayan ta dago da kanta,tabbas ta jima tana qiyasta haka,ta dade tana jin kamar hakane,ashe hakanne da gaske?. Dauke idanunsa yayi daga kanta sanda take bacew ganinsa,ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciya,idanunsa suka sauka kan amiru,sam baisan ya xuba masa ido yana kallonsa bane sai yanzu,wani qaramin murmushi amirun yayi ya dauke kansa,shima sai ya janye idanunsa,ya maida ga jauhar daketa fama da chart,amma rabin hankalinta na ga samir da takeja da hira,saiya miqe a hankali,a sannan ta daga idanunta daga kan waya tana dubansa "Bakaci ko spoon daya bafa" kai ya girgiza yana zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa,a daqiqun da suka dan shude lokaci kadan yana jin kamar akwai wani dan waje da zai iya koda loma biyar ne,to amma bayan barin kaltum wajen.....sai yaji kamar ta tafi da dukkan wani sauran waje daya rage da zai iya zuba abincin "Am coming"ya fada yana takawa a nutse yana barin wajen,gaba daya hankalinsa yaji ya dauku xuwa wajen daddy,mintunan da likitocin suka bashi zasu duba daddyn yana da tabbacin kafin qarasawarsa dakin sun cika. A nutse yake takawa zuwa cikin dakin,bayan likitoci sun kammala aikinsu,sun kuma gama masa dukkanin bayanai kan cewa akwai ci gaba a ciwon nasa,su qara haqurin fitar dashi a basu kwana uku,idan hakan yaci tura saisu daukeshin. Duk duniya baya jin akwai wanda yakejin abinda yakeji a qirjinsa,yana jin wata muguwar kewa tare da fargaba tana shigarsa,idan ya rasa daddyn ya tabbata bashi da kowa kenan,tunda har yau baisan duniyar da MAHAIFIYAR DATA GUDU TA BARSHI TAKE BA,abinda ya kasa goguwa cikin idanunsa,yana iya tuna sanda ta fice daga gidan ta gaban idanunsa,yana kuka yana daga mata hannu,amma ko sau daya bata waiwayo ta kalleshi ba. Runtse idanunsa yayi,a hankali ya taka zuwa gaban gadon,ya sake janyo kujerarsa da kusan kowanne lokaci take ajjiye a wajen ya zauna gaban daddyn yana ci gaba da kallonsa. Ya jima yana karanta addu'o'i yana tofa masa saman kansa,kafin ya sanya hannunsa cikin tafin hannun daddyn ya runtse a nasa,sannan a hankali ya saukar da kansa yana kallon hannuwan nasu dake sarqafe da juna. Motsawa kadan yaga sunyi,abinda yasashi sake qura musu idanu ba qaqqautawa,still ya sake ji da ganin sun motsa din,sai kuma ya damqe hannun nasa gaba daya,abinda ya saka samir daga kansa da hanzari kenan zuwa fuskar daddyn. Kamar numfashinsa zai dauke saboda farinciki sanda sukayi ido hudu da daddy yana kallonsa,bakinsa ya sarqafe,ya kasa furta kowacce kalma "Allah yayi maka albarka" yaji kalmar ta fita daga bakin daddyn,saiya sake qura masa ido yana mamakin furucin daga bakinsa,sake maimaitawa daddyn yayi,bakin samir yana rawa yace "Am....een.....ameen daddy,sannu"saiya gyada masa kai "Dagani na zauna" ya fada a hankali muryarsa na sarqewa "Bari a yiwa likita magana" ya fada da sauri yana miqewa "Fara daga nin tukunna,ba abinda zai faru da izinin Allah,akwai maganar da nakeson gaya maka kafin shigowar kowa" cikin hikima ya dagashin ya jinginar dashi,yana fatan basuyi kuskuren aikata hakan ba,saidai yana zama yadan fara haki "Daddy....ka bari a kirasun" qaramin murmushi ya saki yana dafa kafadar samir din,cikin hakin ya sake cewa "Nayita roqon Allah......ya bani aron......rai da lokacin da zanta ce maka......Allah.....yayi maka albarka.....na....godewa Allah da.... .ya aramin din.....,abu na biyu......banason kace komai akan ciwona.....koda kuwa akwai wani abu da kake zato......ina bala?" Cikin mamakin kalaman daddyn yace "Yana dakin da aka kwantar dashi,amma da gobe zasu sallameshi" sai daddyn ya gyada kai,yana son cewa wani abun amma hakin ya qara yawa,abinda ya tilastawa samir din fita da hanzari kenan,saidai wani sashe na zuciyarsa ya cika da farincikin da zai iya cewa tunda yake rayuwa a duniya bai taba jin irinsa ba. "Ni din mahaifiya ce ga samir,yaro daya tilo nawa dake raye a duniya....haifaffiyar qasar sudan ce,birnin Khartoum,munyi auren saurayi da budurwa da rashid a lokacin da yake University of Khartoum wato U of K,bayan ya kammala karatunsa muka tattaro muka dawo qasar nan da zama bisa amincewar dangina da kuma yarda da nagartar halaye da dabi'unsa. Muna zaune cikin lumana da rufin asiri,da amintattun masu aikina guda biyar,saidai biyu daga cikinsu sunfi shiga raina,kuma minfi shaquwa dasu,zuwaira da kuma harira. Muna zaune da kowa lafiya a dangin rashid,saidai bani da 'yar uwa qawa kuma aminiyar da nake jinta a raina kamar hafsat,ta daukeni kamar ciki daya muka fito da ita,kamar yadda nima na dauketa hakan. Mun samu zama na fahimtar juna da qauna,har zuwa lokacin da rashid ya shiga siyasa bayan na haifi samir da wasu 'yan watanni,siyasar data dauke hankalinsa matuqa fiye da yadda yake a da,duk da cewa dukkan wani haqqinmu babu abinda ya sauke ko ya fasa bamu,saidai mun rage samun lokacinsa kamar da,saboda harkokinsa na siyasar da kuma kasuwancinsa da Allah ya sawa albarka yaketa habaka. Kowacce rana a rayuwar dan adam tafe take da qaddararta,muna cikin wannan xaman namu na aminci,kwatsam jidda ta shigo rayuwarmu,shigar data sauya qaddarata izuwa bigiren da muke kai a yanzu. A wata rana bayan mun fito daga asibiti,nakai samir dake fama da zazzabi,nida zuwaira,zuwaira na gaban mota ita da driver ni ina baya muna hira kadan kadan sanda driver zai fito daga cikin asibitin,daga gefe a rakube na hangi wata yarinya,wadda a qalla zan bata shekara uku ko hudu,kuka take sosai tana kakkarwa,har zamu gota tausayinta ya tsargamin saboda irun kukan da take,na saka driver yayi parking,na fita na sameta. Ta dan tsorata da farko da ganina,amma daga baya saita saki jiki,na tambayeta ta gayamin labarinta kan cewa,su ba 'yan garin nan bane,bata da kowa a duniya,saida kakarta ta rage mata,ita ke riqonta,to itama kakar tata sai Allah yayi mata rasuwa,sai wata mata dake siyan quli da daddawa wajen matar ta dauki riqonta,ashe matar magajiyar karuwai,data kaita gidanta tayi tayi da ita kan ta shiga harkar neman maza amma taqi,dalilin da yasa ta dinga gana mata azaba kenan,data gaji shine ra gudo. Sanda na dauketa zuwa gidana banji komai a raina ba,hakanan ban kawo komai ba,kawai na saka a raina cewa,duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimakeshi. Amma tunda muka zo gidan muka tattauna da xuwaira naga rashin gamsuwarta da lamarin,abun ya dan bani mamaki,saboda nasan cewa ba halayyar zuwaira bace,tana da kirki tana da tausayi,abinda yasa muka jitu kenan tamu tazo daya,saidai duk da na karanci hakan ga fuskarta,bata fito fili ta gayamin ba,har sai dana tuntubeta da cewa "Naga kamar xaman hauwa dana yanke tare da mu baiyi miki ba ko?" Murmushi kawai tayi sannan tace "Ba haka bane,rayuwa ce yanxu ta canza,duniya ta zama abar tsoro,taimako ya zama shima abun tsoro,kawai dai inaga ya kamata kisan ainihin wacece ita kafin ki xauna da ita" a lokacin murmushi nayi "Banda abinki zuwaira.....ta yaya zansan wacece ita?,bayan bata da kowa?" Kai zuwaira ta kada "Bazaiyu mutum ace kaf danginsa babu mutum ko daya ba,ba'a rasa saura,idanma babun,can inda ta zauna ita da kakarta kafin rasuwarta ya kamata ki tambayi halayyarsu kiji" a lokacin gani nake kawai hasashe ne irin na zuwaira,amma kamannin jidda basuyimin kama dana wata mai mummunar dabi'a ko halayya ba,don haka nabi zuwaira da cewa zan bincika na share zancan kawai,jidda taci gaba da rayuwa damu. Abun kamar hadin baki haka hafsa tace min,da yake tana da zafi ma har sabani mukaso samu da ita,tace nikam bani da wayo ne ko bansan ciwon kaina ba,da zan dauka mutum rana tsaka na kawoshi rayuwata ban bincika ainihin wayeshi ba,nace mata babu komai,Allah na nufa,kuma ina fatan ya sanyawa nufina albarka,tun tana mita da qananun maganganu har ta haqura ta zuba idanu,saidai a yadda take kallon jidda da yadda take mu'amala da ita zakasan kwata kwata bata kwanta mata a rai ba,don ba haka take mu'amala da sauran masu aikin gidan ba. Ta bangaren rashid ban samu matsala ba,saboda a sannan din jiddan da girmanta,budurwa ce,ta haura shekara ashirin ma,saboda haka ta haura shekarun da baya daukar masu aiki a cikinsu,yace dai kawai idan ina ganin dai daine shikenan,ta zauna din tare damu. Maganganun zuwaira da hafsa suka sanya naqi sakin jiki lokaci daya da jidda,na dinga karantarta a nutse,amma banga wani aibu ko mummunan hali tattare da ita ba,sai hidima da soyayya da take nunawa samir,fiye d wadda ni uwarsa nake nuna masa,hakanan fiye da wadda su zuwaira ke nuna masa,idan tana gidan samir baya kuka,babu me tabashi,babu me masa fada,baya neman abu ya rasa,kai hasalima idan kaga samir a wajena tun a lokacin nono kawai zai sha ya koma wajenta,ko yaye dana tashi ita ta karbeshi ta yayeshi,a lokacin hafsa ta tada ballin bala'i kan ita tace zata yayeshi ai,zata hadashi da yaronta amiru,wanda suke sa'anni,tsiran kwana biyu ne haihuwarsu,jidda na kuka tana bata haquri ra tattara samir ta kai mata,don ko sau daya bata taba nuna ta gane hafsa bata qaunarta ba,hakanan bata taba nuna damuwa kan rashin qaunar dake idanun hafsa ba,kullum girmamata take da nuna mata qauna. Kowa sai daya tausaya mata sanda samir ya tafi yaye wajen hafsa,ta koma sukuku babu wani walwala,har rashid ya gane,a sanna magana ta soma hadasu,ya tsokaneta da maman samir,yace kuma zai lallaba hafsan ta dawo mata dashi. Wannan shine silar fara magana tsakaninsu,saboda mahaukacin son da rashid yake nunawa samir,kamar an gaya masa cewa shi kadaine abinda zai haifa a duniya. Na riqe jidda cikin martabawa da girmamawa,na bata suttura irin wadda nake sawa,na bata irin abincin da muke ci,na bata makwanci tamkar na matar gida,na kula da buqatunta fiye dana kowa,saboda a lokacin ina ganin tafi sauran ma'aikatana quruciya,inaso ta tsare kanta da mutuncinta har tayi aure. Cikin hakan na duba certificate na secondary dinta,banyi qasa a gwiwa ba na samar mata gurbin karatu cikin jami'ar da nake koyarwa,ba matsala ko wahala ta samu saboda muqamin da nake dashi a sannan, course me kyau na samar mata,saboda dukka ina duba gobenta. Tafi tafi jiddan ta soma sakewa damu,ba jimawa ta koma kamar 'yar gida,a hankali sai duk wata sabga ta gidan ta fara komawa wuyanta,bayan tsantsar kulawa da samir,wanda wani lokaci tare suke zuwa lactures su dawo,har wasu ma na tsammatar danta ne,wanda sukasan bata da aure kuma sun dauka qanwata ce,dukka ina ce musu eh,saboda nima inajin dadin zama da hauwa,tana da matuqar ladabi da biyayya,hakanan tana yabawa sosai da dukka hidimar da nake mata,saboda babu abinda zan siya ban siya mata ba,don a lokacin dan dai Allah ya hadani da mutane masu tsarkakakkiyar zuciya ne,daba shakka a sannan babu abinda zai hana hassada da qyashi shiga zukatan su zuwaira akan jidda,amma Allah baisa sun nuna komai ko sun damu ba. Cikin qanqanin lokaci ban farga ba na fara ganin wasa da dariya sun fara shiga tsanin rashid da jidda,na danju kishi kadan,amma abun ban wani bari yayi tasiri sosai a raina ba,saboda naga dukka akan samir ne,fiye da rabin hirar tasu ma duk kan samir ne da abinda zasuyi yaji dadi,rayuwarsa ta inganta,don haka sai na saki raina,da zuciyata daya naci gaba da sabgata. Kwatsam ban ankara ba sai sabo da shaquwa ya fara gittawa a tsakaninsu,hira raha da wasa da dariya,tun ban damuwa har na fara jin kishi sosai a raina,amma na rasa ta yadda zan yiwa rashid qorafi,saboda yadda jidda ke bani girma tana kuma sake bada himma wajen kula da samir da nuna masa soyayya da kulawa. Wasa wasa abu yaci tura,har takai ta kawo rashid zai dauki jidda da samir su fita shopping ni ina zaune,koda abu ne wani lokacin idan bana kusa saidai ya bawa jidda ta riqemin kota ajjiyemin,idan nayi magana sai yace,ai yaga na aminta da jiddan ne,kuma yarinyar nan tana da hazaqa da qoqari,komai.naki dana yaron nan ita ke muku shi,haushi ya cikani,na tsuke fuska nace "Ai ba gazawa taga nayi ba ko bare ka gayamin haka" dariya ya fashe da ita "Kai raihana,ban sanki da wannan ba,kishine kawai yake damunki hala,amma jidda ai hutu ce a wajenki,kaf masu aikin gidan nan babu wanda yake aikatuwa irinta" gaskiya ne abinda ya fada,amma abinda na gani shine,babu wata sabga data zama wajibina dana gaza,komai na kula da mijina ban fasa ba,aikina bai sanya na rageshi da komai ba,kuma shi dinma harkokinsa sun sanya ba mazaunin gida bane. Abu daya ne da ban ankara dashi ba sai sannan,jiddan tana da azarbabi,wasu abubuwan na rashid ko na samir duk sanda na tashi xanyi saina tarar tayi wuf tayishi,koda baqi nayi kafin nace ayi musu kaza tayi,duk wanda yazo gidan saiya tafi da kirkin jidda a bakinsa,duk sanda muka hadu ya dinga tambayar ina jidda?,yarinya me kirki,musamman dangin rashid,cewa suke nayi dace da yarinya me kirki,ranar da family na daga sudan sukazo kuwa,zaka ce wajenta suka zo,duk wata hidima tasu a wuyanta take har suka tafi,da na dan motsa zatace aa na zauna miyi hira da baqina. Randa na hada undies din rashid xan wanke a toilet dina,nayi baqi na fito muna gaisawa bayan ta saukesu a wannan lokacin na fara taka mata burki kan ta daina shiga hurumin daba nata ba,tana hawaye ta bani haquri,idan raina ga baci nayi haquri,ita batayi don wani abu ba,tayi ne saboda taga jiya iwar haka ina kwance bani da lpy ina fama da zazzabi,yadda naga tanata kuka tana bani haquri sai naji babu dadi,naga kamar ban kyauta mata ba,tunda kulawa ce tasa haka,amma komai kulawa bai kamata ta taba kayan da suke sirrin mijina ne,nace mata ya wuce amma ta kula. Kwana biyu haka ta dinga rayuwa sukuku a gidan,har samir sai daya koka saboda yadda ta koma ba kuzari,rashid ma ya fuskanci haka,ya kuma sameni da maganar. Fada sosai na dinga yi,ta inda nake shiga ba ta nan nake fita ba,saboda raina haka kawai naji yana quna,bugu da qari kima yaron cikin dake jikina,wanda ya qaramin zafi,baice komai ba harna gama,sannan ne ya amsa min da "Kada dai kije kishi ya rufe miki ido ki batawa wanda yake qoqarin kyautata miki" lafazin da ya sanya jikina yayi sanyi kenan,na rage daurewar dana fara yi mata. Yan kwanaki tsakani laulayi ya sakani a gaba,sai komai ya sake komawa hannun jidda,ni kaina a sannan na yaba mata,yadda take hidima damu kan jiki kan qarfi,bata xama ta huta kona minti daya,ga makaranta tata data samir wanda ya fara zuwa ba jimawa,ban samu kaina ba har sai da nayi barin cikin,taci gaba da hidima da ni har na warke na koma kan harkokina. Ban jima ba na sake samun wani,shima dai itace komai.namu,wannan ya qara kusanci me qarfi tsakaninta da samir dama rashid,shima dai cikin sai da ya fita na samu sauqi,bayan na warke saina sake ganin canji sosai tsakanin rashid da jidda,idan nayi magana yahau fada,yace duk kyautatawar da takemin bana gani?,sai shi don ya kyautata mata?. A wannan lokacinne rigima kusan taso barkewa tsakanin hafsat dashi,ta shiga maganar,ya hadamu duka yace bamu da kirki kuma bamu da halacci,kamar yadda na gaya miki,hafsat tana da zafi,saita qyaleshi kamar anbar maganar,tafiya tana kamashi tazo ta sanya jidda tattara kayanta tace lallai sai tabar gidan. Yadda jidda ke kuka tana roqon tayi haquri ya karyarmin da xuciya,ina qoqarin cewa ta barta,amma hafsa ta hada harda ni,haka nan tasa jidda ta tattara tabar gidan,ta gama kin bambamin fadan na zauna lusaranci,idan baiyi wasa ba zafa qwace rashid a hannuna,tayi ta gama ta fita. Tunda jidda ta fita duka sai tausayinta ya kamani,na kasa nutsuwa,musamman idan na tuna cewa bata da kowa,to ina zataje?,itace tambayar data dinga damuna,na tsaya gaban madubi na dubi kaina,sai naji bana ji sam bana tsoron zama da jidda,banjin zata iya qwacemin rashid,duba da irin halaccin da na yiwa rayuwarta,halaccin da nakejin ya isa yasa jidda taji kunya da nauyin aikata min ba dai dai ba,uwa uba bata ko kama qafata wajen kyau da diri ba?,to meye zanji tsoro?,wannan tunanin ya sanyani fita neman inda jiddan tayi. 57 "Tun ba'ayi nisa ba aka sameta rakube gefan gidana zaune ita da kayanta,taci kuka ta godewa Allah,nasa aka shigo da ita ciki,kafin ma ta qaraso ta soma roqata na rufa mata asiri na barta ta zauna,nace kada ta damu,taci gaba da zama damu,saidai na kafa mata wasu qa'idoji tace zata kiyaye in sha Allah,a baya ma duk abinda ya faru nayi haquri,nata dauka zan zaci wani abu ba. Da wannan mukaci gaba da zama da jidda lafiya qalau,wanda bayan 'yan watanni saita nemi na barta ta koma zama a hostel,ta dinga zuwa gida weekends,ban musa ba na barta,saboda ina ganin nima hankalina sai yafi kwanciya da hakan,data koma din kuwa sai naji tsarin ya yimin,har zuwa sanda na sake yin bari na uku,a sannan naci wuya,su zuwaira da samir ke kira bibi wato baba,bai iya fada ba a sannan saboda yarinta,har ya soma wayo kuma ya bita a haka,su suke komai,saidai na fuskanc sam rashid baya ganin qoqarinsu,bashi da aiki sai mita,bini bini yace da jidda tana nan kaza za'ayi,na zauna tsaf naga babu ta inda suka gaza,duk abinda jidda keyi sunayin ma fiye da hakan,ina fama da ciwo saina tattarashi na watsar kawai shida mitarsa. Ban tashi gane cewa komawar jidda hostel wani babban illa ta shirya yimin ba sai bayan wani lokaci da soyayya tayi nisa tsakaninta da rashid ba tare dana ankare ba,nayi kuka nayi kuka na godewa Allah randa na ganshi cikin school ya dauketa sun fita cikin shauqin soyayya,na dawo gida nasha kuka son raina,na zauna na yiwa kaina hisabi,na kuma binciki kaina tsafff...naga me na rasa?,me kuma na gaza dashi?,saboda gudun yanke masa hukunci kan kuskure,babu itace amsar dana lalubo,saboda ado da gayu da kuma tsafta dukka a wajena jidda ta koyeshi,kyau kuwa ko gefan takalmina nasan cewa jidda ba zata iya riqewa ba da suna karawa dani,iya kula da miji ta wannan fannin ni malama ce,mata da yawa na neman sani a wajena,wajen gyaran shimfidarmu kuwa.....sam bana yarda ma nayi amfani da kayan qasar nan,saina tantance masu kyau na qasarmu dana wasu qasashen da suke da qwarewa ta fannin. Ganin na gagara gano dalilin.....saina azawa raina cewa,kawai dabi'ar maza ce,a haka kuma Alla ya haliccesu,komai kyanki ko iya gayunki idanunsa basa kasa gane masa wata da zai dinga jin ta fiki,jidda halal dinsa ce,saidai hanyar da suka bi tana da ciwo,yarinyar dana riqa kamar qanwata saboda kyautatawa?,to amma kuma.....babban abun mamakin ma shine,ta yaya har ta iya janye hankalin rashid?,tambayar dana kasa baiwa kaina amsa,na kuma kasa hutawa har sai dana samo amsarta,saboda ina tsoron kada ya zaman tana bin malaman tsubbu ne,na zauna ta cimmani,gwara nasan a wanne mataki nake?. Jidda tayi amfani da zallar KISSA ce,wadda hausawa sukance TAFI MAGANI,ta shiga rayuwar rashid ne ta hanyar amfani da abinda yafiso duk duniya wato dansa samir,tayi amfani da duniyanci da gogewa,wadda bansan ina ta samota ba?,da ita na daukota na kawota gidana?,ko kuma.bayan shigarta makaranta ta hado harda karatunta?. A lokacin nayita qoqarin shanyewa,ban nuna masa na gane komai a tsakaninsu ba,saidai deep inside ina karantarsa,ina karantar duk wani motsi nasa,saina fahimci wasu abubuwa da ban fahimta ba a baya,kamar yawan yin adonsu ranar juma'a,suyi anko shi da samir yace zaya kaishi gidan hafsa,ba zasu dawo ba sai magariba,wani lokaci nakan gansu tare da jidda,sai yace min suna tahowa suka gamu da ita ya qaraso da ita,to amma ban taba kawo komai a raina,saboda bana zarginsu shida ita. Ranar data dawo gida duk qarshen sati kamar yadda takeyi itama ban nuna mata komai ba,saboda inason na gama karantarta,mamaki ya dinga cikani saboda yadda suke pretending wa junansu,saidai idan har kayi tsaiii da ranka zaka iya shinshino akwai wani abu a tsakaninsu,abun yayi masifar baqanta min rai,wato ni suka maida wawuya kenan tsahon lokaci?. Lamarin kishi abune da ba kowacce mace ke iya cinyeshi ba,musamman kishi da irinsu jidda masu yaqar mace da takobin kissa,naso na danne amma sai naketa ganin canje canje,kaf hankalin rashid yana kanta,lokaci daya ta canzashi kamar asiri,shine tashi cikin dare yaje falo suyi waya,shine fitar yammaci ko dare,shine zaman charting shi daya baya so kowa ya rabeshi. Ranar dana kasa jurewa.....randa ya tashi tsakar dare,ya shiga toilet yana waya,ga zatonsa bacci nakeyi,na tashi na zauna na jirayi fitowarsa har kimanin awa daya,yana ganina mamaki da 'yar razana ta nuna kan fuskarsa,amma da yake namiji ne saiya fuske,yana tambayata ya tsaremin bandaki ko?,shiga zanyi?,kaina girgiza masa "Jira nake ka gama wayan da jiddan,inason yin magana da kai" sosia fuskanshi ya nuna shock,sai ya zauna jikinsa a sanyaye,cikin nutsuwa na fara masa maganar mamakin da ya bani kan boyemin da cij amanata da suke shirin yi da jiddan,na fitittike masa,ya tabbatar min soyayya suke da jidda,kuma aurenta yakeson yi,abinda yasa ranar bamuyi kwanan dadi ba,don ya bani mamaki,abun kuma ya dagamin hankali duk da na sani,amma tabbacin da na samu daga bakinsa ya sake sani cikin qunci da baqinciki. Wasa wasa zamanmu ya hargitse,rigima har wajensu yadikko,hafsa ta shiga ta fita yadikko ma tace bata yarda da auren ba,saidai idan har ni na amince,abinda yasa rashid ya tattare ya dawo min,ya dinga roqona na barshi ya auri jiddan,da farko na kafe,amma bayan na dauki wayarsa rannan naga irin saqonnin da jidda ke tura masa,na tabbatar da cewa koda su yadikko sun tsaya min auren bai yiwu ba bani da wani sauran kwanciyan hankali a gidan,don haka na zubda makamaina nace masa na amince. Aranar naga zumudi da farinciki da soyayyar da zan iya cewa rabona da ita tun lokacin da muke zaman lafiya lumana ni da shi,hawaye ne kawai ya dinga sauka a idona,tun a sannan nasan cewa tawa jarrabar kenan,don haka na duqufa da addu'a,ina gayawa ubangiji na. Tabbas naga tasirin addu'a,saboda sai Allah ya ragemin damuwa sosai cikin raina,duk yadda na zaci abun sai ubangiji ua huwace min shi,har ya zaman Hafsa ta fini shiga damuwa da tashin hankali,daga qarshe ma take ganin nice na daurewa rashid baya,tsanar data yiwa jidda ta ninku. Tun daga lokacin jidda gaba daya ta daina dawowa gida na weekend,banace ga a inda take ba,amma dai tabar dawomin. Ba'a dauki wani dogon lokaci ba rashid ya hada lefe,wanda ya kusa fin nawa ma,saboda a sannan ya fara siyasa,wadda ta karbeshi sosai,saidai ta sake taka rawar gani wajen canza masa halaye da dabi'u,bamu da rashin ci ko sha ko suttura,hakanan bana rasa kudi a hannuna,amma abubuwa da yawa sun canza. A lokacinne hafsa ta dire tace sam batasan zance ba,yadda ya yiwa jidda kaya haka zaimin,bai musa ba,saboda ganin bana ce masa ko uffan kan dukka lamuransa,na kawo idanu na zuba masa. Abubuwa da yawa sun faru,akayi biki kai kace lokacinne zaiyi auren fari,saboda irin abubuwan da yakeyi,hafsa kamar zata zauce saboda baqin ciki,tace ita bata yarda ba,ba shakka jidda asiri tayiwa rashid,ni kuma nasan ba asiri bane,kirsa ce ta gwanaye,mummunar kissa da warwareta sai Allah da malaman gari. Fadin ma irin amarcin da akayi da rayuwar dana fuskanta bayan aurensu da jidda bata baki ne,saidai na tattarashi gaba daya na sallamashi,saboda komai nayi bana burgeshi,hankalinsa gaba daya baya kaina,wani abun ma idan yayi sai inga kamar wanda aka yiwa dole yake zaune da ni. Ta fannin dangi da 'yan uwa kuwa,dai daikune basa yi da jidda,duk da cewa bawai sun juyamin baya bane,nima ban canza dukkan halayyata da mu'amalata dasu ba,haka nan ban fasa yi musu alkhairin da aka sanni dashi ba,amma suna matuqar sonta dayi da ita. Tafi tafi rayuwa ta dinga garawa,na zama tamkar nice asalin 'yar aikin jidda,cikin ruwan sanyi da wani salo na kissa me kama da siddabaru ta qwace komai daga wajena,gidana mijina d'ana,kowa cewa yake jidda kamar kece kika haifi samir?,shi kansa yaron akwai shaquwa me girma tsakaninsu,saboda yadda take shagwabashi,saidai wani lokaci abun yana min ciwo,don abubuwa da yawa daya kamata ace ta kwaba masa bata kwaba masan,ina tsoron kada ya lalace,shi kuma mahaifinsa idanunsa ya rufe da soyayyar ta,baya ganin ba dai dai dinta ba,komai tayi dai tayi. A sannu a sannu jidda ta fara fiddomin da muna nan halayenta muraran a fili,bayan ta tabbatar da cewa ta qwace komai ya koma hannunta,saidai fa a bayan idanun kowa,daga ni sai ita kadai take gwadamin wanna fuskar. Ni kadai ni da mata irina ke kadai zasu fahimci irin jahannamar da nake ciki,don kowa yabonta yake,kowa cewa yake na dace da abokiyar zama,jidda batayi butulci irin na sauran mata ba,batayi butulcin da aka zatar mata zatayi ba,da yawa kan tambayeni....me yasa nake rama?,bayan ban rasa komai ba?,wasu kawai saidai na bisu da murmushi,saboda duk yadda naso yi musu bayani ba zasu gane ba,ba zasu taba fahimta ba,ba zasu gane quncin da zuciyata take ciki ba. Cikin wannan yanayin rayuwa ta dinga tafiya damu,yau fari gobe tsumma,tuni jidda tayi aminai,masu bata shawara,cikinsu babu kamar hajiya shuwa,wadda na jima da sanin cewa hatsabibiya ce,kusan da gudunmawarta komai yake sake wanzuwa yake dada tabarbarewa cikin gidan,itama yarinyar macace,kusan sa'ar jiddan,saidai a sannan ita yaronta guda daya fawwaz. A haka a irin wannan rayuwar har ta haifi najwa,tsirar shekaru uku ta sake haifan jawahir,a hakan nake haquri nake zaune,ina duba abubuwa masu yawa,ina duba cewa komai yayi farko zaiyi qarshe,ashe qaddarar tawa me tsaho ce,ashe banyi komai ba cikin tafiyar qaddarata...... Domin kuwa shekara daya tal da haihuwar jawahir.....na sake samun wani cikin,shima dai mai wahala kamar wancan,ni kadai nake wahalata nida zuwaira da harira,amma a gaban idanun mutane kuwa,ciki harda rashid.....tsinke jidda bata bari na daga,abun ya zame min jiki,ba baqona bane,don ta qware wajen iya wannan. Kwatsam rana tsaka ina zaune da wani yammaci saiga rashid ya fadomin afujajan,jidda na biye dashi a baya cikin tashin hankali tana qoqarin riqeshi,tare da neman ya tsaya,amma yana qwacewa yana sake yin gaba,ina zaune a inda nake ban motsa ba har ya iso gabana "Waye uban wannan cikin na jikinki?" Itace tambayar daya jeho min,tambayar data rudani har na miqe tsaye ba tare dana sani ba,saboda ban taba kawo fitar irin wannan tambayar daga bakin rashid ba,ko wanne irin xama kuwa muke,na maida masa da amsar cewa.....bashi da uba daya wuceshi,saiya jefomin takardar hannunsa,wadda ban iya dauka na duba ba,shima bai iya tsaiwa na duba din ba ya shiga bayanin "Tun bayan buguwar da nayi watannin baya da suka shude aka yimin gwaji,wanda bai fito ba sai cikin satin nan,suka kuma shaida min akwai jijiyoyina da suka tabu,wanda bazan sake samun haihuwa ba sanadiyyar hakan,a ina kika samo wannan cikin?" Maganar data sanya jiri ua debeni ya maidani kan kujerar dana tashi a kanta,innalillahi wa inna ilaihi raji'un na dinga maimaitawa,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba,ya kuma barmin gargadin cewa lallai ne na samo uban cikina. Wannan shine abunda ya kusan tarwatsa rayuwata,ya kuma kaini kabari tun jidda bata gama shirin kaini ba,cikin gidan ya zame min tamkar sansanin yaqi,duk wani sauran farinciki da walwalata da nake tattali gaba daya suka yi nasu waje,babu mai kusantata da zuwa inda nake,hatta dasu bibi,duk da cewa su din jidda ce ta kafa musu dokar,matuqar suna son ci gaba da aiki a gidan,amma bibi da harira basu yarda ba,don suna biyo dare suzo su ganni,su kuma kawomin abinci,don bana iya ci,jidda kuma bata damu a bani ba,a sannan nayi burin akwai isassun kudi a hannu na,da babu shakka saidai a wayi gari a ganni a sudan cikin mahaifata,wadanda basu san halin da nake ciki ba,sakamakin bacewar wayata lokaci guda sama ko qasa,ni kuma ba fita nake ba a sannan,ko lecturing din da nake ban iya zuwa saboda azabar ciwo daya hadu da gagarumin baqinciki. Duk wannan yanayin nida hafsa muke karbar takaicin,a haka ma ina boye mata wasu abubuwan bata sani ba,saboda banason na bata kyakkyawar alaqa da kuma dangantakar dake tsakaninta da dan uwanta,wadda dama tun aurensu da jidda yau shiri gobe fada,kuma duka a kaina ne,ya kuma koka da hakan shi kansa,kan cewa ina shiga tsakaninsa da 'yar uwarsa. A irin wannan yanayinne wata rana ina zaune,na gama rubuta kan wani mummunan furuci da jidda tayimin daren shekaran jiya,makomata,da kuma hasashen abinda zaizo ya sameni nan gaba muddin naci gaba da irin wannan rayuwar......gidan babu kowa,don ko dama samir yana nan,zanga yana yawan kallona,amma yaqi zuwa inda nake,abun yana daya daga cikin abubuwan da suka sake kassaramin ruhina,gani nan ni ba mutun ba niba mutum mutumi ba,na fice daga kamannina,ina tsaka da tunani na naga inuwar jidda saman kaina,gabana yayi wata mummunar faduwa da ban taba jin irinta ba akan jiddan sai ranar. "Tun ranar dana sanyo qafata cikin gidan nan zuciyata ke gayamin nazo inda zan huta,nazo inda zanyi kudi nima,nazo inda rayuwar talauci zata qaremin,daga randa nayi ido hudu da mijinki na sake tabbatarwa kaina na samu mijin aure,duk da cikin da nayi sau biyu aka ciremin,wanda baqincikinsa ya kashe kakata dake riqona,abun kunya da gudun talauci yasa na kasa komawa garinmu....cikin farar sa'a kika tsinceni,na gode da halaccin da kika yimin,karki dauka nayi amfani da sihiri ne zalla wajen zama dukkan abinda na zama cikin gidan.....a'ah,KISSA TAFI MAGANI AIKI,kina da kiyaye sallolinki da yawan ambatan sunan Allah koda zama zakiyi ko tashi,na tabbatar wannan kadai zai iya maidamin hannun agogo baya,hakanan sihiri bashi da tabbas,don haka na zabi tsarma shi kadan a guraren da na gaza juyawa, na dan wani lokaci,kafin na maye hikimata da basirata a gurbin wajen,ina me baki haquri da dukkan abinda zai biyo baya.....zan miki alqawari guda daya,ladan halaccin da kika yimin....zan bar danki ya rayu,amma ban miki alqawarin irin rayuwar da kika tsara masa ba......na gaji da ganinki cikin gidana raihana,nayi aiki tuquru na tsahon lokaci,nayi juriya na kuma yi haquri.......ya kamata ki matsa ki bani waje hakanan,albishir guda daya da zan miki shine.....bazan kasheki farat daya ba,amma zan miki daurin rai da rai,irin wanda alqali yakewa me laifi......" Daga wannan ta fesa min wani abu,wanda ya sanyani ficewa daga hayyacina,na kuma taka da qafafuna na lalubi hanyar ficewa daga gidan,ina iya ganin sanda aka sauke samir daga makaranta,cikin qaramar motar da babansa ya siya masa ya mallaka masa ake kaishi makaranta da ita,wanda da daurin bayan jidda aka siya masa motar,ina iya jin sanda yake qwalamin kira,ganin ban waiwayeshi ba,yasha gabana,naji banason duk wani shamaki da xai tareni daga fita waje,nasa hannu na yageshi na jefar gefe,duk da zuciyata batason aikatawa,amma kawai ji nayi inason na aikata din,babu me gadi babu duk wasu masu tsoron qofar gidan,hakan shi ya bani damar fita ba tare da wani tarnaqi ba. Ina fita naci karo da wata mota mai baqaqen glass tsaye qofar gidan,tamkar dama suna jiran fitowar tawa ne,suka kamani suka sanyani cikin motar,ban bude idona ba sai cikin wannan dakin da muke ciki a yanzu,wanda na gaza tantance inane?,sai bayan wani lokaci dana fara jiyo ifce ifce da maganganun zararru,sai kuma bayan wani lokaci da aka fara dirka min alluran da suka fara jirkita min kwanyata,da wasu alluran da suka matsantawa cikin jikina ficewa......... Cikin lokaci kadan gaba daya na daina fahimtar komai,na daina gane dai dai daba dai dai ba,da zarar allura da magungunan da suka dirkamin ya sakeni.....suna fuskantar haka sai su sake danna min wasu,na rasa waye silar kawoni gidan?,wanne laifi nayi?,duk sanda sukazo zasuyimin nakan dage da roqonsu akan su barni,ni lafiyata qalau,ni kadai nasan irin azabar da nakeji,to amma sai naga ko a jikinsu,burinsu su aiwatar da abinsu su fice. Tunda aka kawoni mutum uku ke shigowa inda nake,kuma har yanzu da nake wannan maganar sune dai babu canji,ban gane wanda ya kawoni ba sai bayan shekara guda sai ga jidda,ranar data zo sai naji sanyi a raina,nayi tsammanin cewa tazo ta fitar da nine daga inda nake din,amma maganganun da sukeyi ya tabbatar min da cewa wannan qaddarar data sameni itace sila,a gabanta aka hada alluran da sukafi qarfina aka danqaramin,tun ina iya ganinta da idanuna dishi dashi har duhu ya mamayeni,sai surutunta da take basu umarnin cewa,a qara yawa da qarfin alluran da ake mini,batason dukka wani hankali da yayi saura a jikina yaci gaba da aiki,daga haka muryarta ta soma cakude min na dinga jin kamar ana ihu saman kaina,alamar alluran sun fara min aiki. Tun daga randa ta bada umarnin suka matsa qaimi kamar yadda tace,sai na daina ganewa gaba days,tsahon wasu shekaru bansan wacece ni ba,amma iko da hikima ta ubangiji,duk randa tazo kawomin ziyara ina ganewa,duk da zan ganta ne kamar irin a mafarki,saboda rashin wadataccen tunani da aka hargitsa min shi. Tsahon shekaru masu yawa ina cikin wannaj uquba a wannan kurkukun da bana ganin kowa sai mutum uku,bansan ya akayi ba,cikin wani dare,cikin baccina me kama da mutuwa naji kamar an tasheni,kamar ance TASHI KIYI SALLAH! cikin sautin tsawa. Ina farkawa na ganni a nan,na soma bin dakin da kallo,ina tuna wasu abubuwa da suka faru dani,ina ganinsu kamar cikin dogon barci me cike da mafarkai,na dinga taba jikina,inason naji a kabari nake ko a duniya nake?,idan a duniya ne ta yaya na farka cikin hankalina?,ya akayi hankalina ya dawo jikina?,ruwan dana gani a gefe na jawo,wanda ba tantama shi nake sha,na daura alwala duk da bani da tabbacin tsarkin jikina dana ruwan,na fuskanci gabas,na dinga salloli,banji na gaji ba tsahon lokaci kafin na xauna ina hutawa,a nan gyangyadi ya fusgeni,a nan wajen na fara mafarkin qaramar yarinya tana jan hannuna zata fiddani daga wani rami,wanda wannan mafarkin shi ya zame min qa'ida kusan kullum. Na jima ina juya wanda xai xama silar fitata daga wajen,ina juyayin ta yaya yarinya zatayi silar fitata a nan?,amma daga baya nayi istigfari.....na tubarwa Allah,saboda shi din me yin yadda yaso ne a duk sanda yaso,shi ya bani kariya tsahon shekarun da akayi ana dibgamin Alluran da a qa'ida ya kamata ace na rasa hankalina gaba daya ko kuma na mutu......amma ya dawo dani cikin hayyacina,ya kuma dawomin da hankalina,lallai shike raya matacce. Ban yarda na nuna musu farfadowata ba,wani hikima ta ubangiji.....duk sanda sukazo sukamin alluran da suka saba,zanji babu dadi,zan fita hayyacina.....saidai bana wuce minti ashirin sai ta sakeni,bansan daga ina ubangiji ya saukarmin da wannaj ni'ima tasa ba,ban sani ba ko addu'ar da nakeyi ne?,ban sani ba ko a rayuwata ta baya ina da wani kyakkyawan aiki da Allah ya duba ya bani wannan kariyar?,wannan itace rayuwata tsahon shekaru ashirin da wani abu da nayi cikin wannan gidan....... Wani irin dummmm gaba daya kaltum taji kanta yayi,hawaye ne kwance shabe shabe saman fuskarta,kallon baiwar Allahn take tana mirgina kai hagu da dama,ta kasa fadin komai,ta kasa cewa komai,tausayinta dana samir ne fal cikin zuciyarta,yayin da tsanar mummy ta cika mata zuciya,ashe tata rayuwar ita da ummans a aljannar duniya suka yita?,ashe duk inda rayuwarka takai ga tsanani akwai wanda ya fika?,ashe wani maras imanin idan yaga wani saiya nemi tsari dashi saboda gawurtar wancan a zalunci? 58 Tamkar wata mashahuriyar barauniya haka ta dinga bibiyar bango cikin sanɗa sanda take baro dakin da momma raihana ke ciki,hikimar ubangiji ce ta sanya ranar gidan kamar anyi shara,duhun magrib yana shigowa zirga zirga ta ragu sosai,qwalla fal idanunta,zuciyarta na mata wani irin ciwo da quna take tafiya,babu abinda ke amsa kuwwa cikin kanta illa labarin momma. Fuskarta a lullube kanta a qasa ta giftasu,kyauro ne,ya wuce yana sababin bala'i da masifa kan barin qofar dakin da akayi a bude har kawo wannan lokaci,sai data fita wajen gate din gidan sannan ta saki qatuwar ajiyar zuciya,ta tabbatar tayi escape,saura next step kenan. Tun lokacin data baro gidan bata sake samun nutsuwa ba sai data hada dukkan hanyoyin da take ganin xasu xama sanadiyyar fitowar umma samir zuwa duniyar 'yanci,tana ji a jiki da zuciyarta cewa.....zata sadaukar da dukka ranta don aiwatar da wannan aikin,babu abinda ke yawo a ranya face zallar mamaki da kuma tsanar mummy jidda,tunda take a rayuwarta....bata taba katari da azzalumin mtum kuma butulu irin Mommy din ba....don haka ko bayan ta dawo gida,bata zauna ba,ta dauko dukka wani abu da take da tabbacin zai bata gudunmawar zane. Ana kiran assalatun farko tana kammala zanen surar fuskar raihana,ta dagashi sosai tana kallo,tunda take a rayuwarta bata taba zanen da ya kama qafar wannan a kyau ba,natasan meye dalili ba,amma ta danganta hakan da wala'alla samuwar ilimi a gareta,sabanin baya da take komai bisa radin kanta da kuma iya hasashenta. Ajjiye takardar tayi ta nufi bandaki kai tsaye ta daura alwala,ta fito ta fidda hijabi cikin kayanta,ta mulke jikinta da turare ta hada da hijabinta da abun sallar,kusan wannan al'adarta ce a duk sanda zatayi sallah,domin samun kusaci da mala'iku. Cikin nutsuwa ta tada sallarta,ta jima tana ganawa da ubangiji cike da tarin addu'o'i da neman dafawar ubangiji,a duk wani motsi da zatayi momma raihanan ce a idanu da xuciyarta,qila a yanzun itama tana can gaban ubangijinta,tabbas lamarinta cike yake da al'ajabi,zallar qudura ta ubangiji da buwayarsa,wanda ya nuna ikonsa da kuma qinsa ga zalunci. Gefe daya samir ya fado mata a rai,shi kansa abun tausayi ne,ya rayu tsakanin numfashi da kuma hannun azzaluma data cutar da halitta mafi muhimmanci da soyuwa a wajensa.....sai kuma taja qaramin tsaki can qasan ranta.....data tuna abinda ya faru a dazu tsakaninsa da jauhar.....sanda suke hanyar dawowa gida,duk da cewa cike suke da farincikin farkawar daddy,amma hakan bai hana jin wani abu mara dadi na yawo saman zuciyarta ba. Sake jan tsakin tayi,batasan me takeji cikin zuciya da ruhinta ba kan abinda ya farun,ta rasa sunan da zata bashi,bata yadda kishi bane....saboda ba haka taji ba akan wasila sanda take ganinta tare da nasiru ba,wannan din ya fita daban.....sai kuma tayi qoqarin watsa lamarin gefe ta miqe ta tada sallar asuba wadda tuni kiranta ya karade masallatan kusa dana nesa. Qarfe bakwai da wasu 'yan mintuna ta fita daga dakinta sanye da hijabin data idar da sallar,tana son ganin bibi a yau din nan,dole saita taimaka mata da shawara,batason tayi kwaba,bibi zata fita hangen abinda ya kamata. Ko data shiga kitchen din bata taras da kowa ba,tayi mamakin bibi da bata fito ba,amma jikinta ya bata koma yaya ne tana gab da fitowa,tunda dama tana riga duka sauran 'yan aikin fitowar,hakan ya sanya ta jawo abubuwan da take tunanin za'a iya buqata a girkin safiyar yau,ta fara gyarawa tana daga tsaye don tafi sauri. Yadda hijabinta ke saukowa yana hanata jin dadin aikin ya sanyata zareshi ta dora saman qofar kitchen din,hakan ya bata damar yin komai da sauri. A nutse yake takowa kai tsaye zuwa cikin kitchen din,duk da cewa safiya ce amma jikinsa wani lallausan qamshi yake fitarwa,yayi kyau cikin fararen qananun kaya da suka haskashi ainun,qal dasu kamar ba'a tabasu. Fita ce ta kamashi bayan kiran da daddy yayi masa direct daga Asibiti,dakinsa ne ba'a gyare ba,kuma sam bayajin dadin zama a cikinsa,samun zama da baya yi ne yasa bai tsaya gyaranshi ba. Dan qaramin tsaki yaja,yana jin kawo yanxu ya kamata kowa ma ya daina shiga masa daki,lokaci matsayi da kuma shekarunsa yaci ace akwai wata mace by his side. Dai dai sanda yakai qarshen tunanin idanunsa suka masa maraba da ita yana gab da qarasawa kitchen din,sai ya rage hanzarinsa ya soma takawa a hankali zuwa ciki. Ko baa gaya masa ba koda kuma bai kalli fuskarta ba yasan tayi nisa a tunani,duk kuwa da cewa aiki take sosai cikin kuzari,bin bayanta yayi da kallo,tana sanya da wasu silk sleeping dress riga da wando milk color,wanda suka kwanta a fatarta da jikinta,hakan ya bawa mazaunanta damar fitowa sosai,ta bayan qasan dankwalinta sassalkan gashinta ya leqo,ta motsa kadan zuwa gefanta tana zuba mai cikin frying pan,abinda ya bawa jikinta damar shaking. Tsigar jikinsa ce ta xuba,tun daga saman kansa fuskarsa har yatsan qafarsa,yadan matse idanunsa kadan,saidai kafin yakai ga budesu sautin qaramar qara ta fito daga bakin kaltum din hade da yin tsallen daya sanyata yin kyakkyawan masauki a jikinsa. Tsam ya riqeta cikin jikin nasa,kamar wanda ke sauraron faruwar hakan,abinda ya sanyata waiwayo da sauri cikin tsoro,sai suka hada idanu,sauke kanta qas tayi da sauri saboda wani bugawa da taji zuciyarta ta fara yi,a hankali tadan soma takawa da baya don xame jikinta daga tsakanin hannayensa,sai taji ya fincikota da sauri,abinda yasa ta qarasa fadawa jikinsa gaba daya,kanta yayi masauki a faffadan qirjinsa. Dukkansu wuta ce ta dauke musu na wasu sakanni,kafin taji heavy voice dinsa data ratsa kunnenta,ta shiga aika mata da saqo qwaqwalwarta "Kinyi gudun fallatsin mai,zakije kuma ki daki pan din ya dawo miki jikinki gaba daya...." Har yanxu bugun zuciyarta daduwa yake,musamman da taji hannunsa saman bayanta yana shafawa daga sama zuwa qasa "Wa yace miki ana shigowa gaban wuta da silk material?" Ya fada da wata sassanyan murya can qasa,ba zata iya amsa mishi ba,sai kanta data girgixa masa,tuni qafafunta suka fara shaking,bata sani ba ko abinda yaji kenan,saiya saketa a hankali ta zame ta koma gefe tana juyar da fuskarta daga sashen da yake tsaye. Second kusan biyar ba wanda ya iya cewa komai "Bani ruwa" muryarsa ta ratsa shurun,saita juya a hankali zuwa sashen da suka girke na'urar sanyaya abu,tana jin yadda qafafunta sukayi sanyi laqwas. Binta yayi da kallo,komai na jikinta na bayyana kanshi,sai yanzun ya gasgata zancan jawahir,tana boye komai ne don kada asan tana dashi,to amma dasu tazo ko kuma a nan ta samu?. Feeling din da yakeji ke qara yawa,gashi ita kuma tafiya take kamar ba zata kai ba,saboda ta sani a karan kanta duk sanda ta motsa din sai jikinta ya amsa,saboda yanayin kayan jikinta,don bata tsammaci xai ritsata haka ba,shi yasa ta fito haka,da babu abinda zaisa ma ta cire hijabinta. Binta yayi a baya,duk wani daukewa da saukewar qafarta yana binsa da kallo,yana noticing canje canje da dama tattare da ita,wanda rashin nutsuwarsa kan ciwon daddy da jinyarsa,kawo yau dan daukewar idanunsa daga kanta yaga abubuwa daban daban tattare da ita. Cikin rashin sani dukkansu suka kai hannunsu saman mabudin fridge din,hakan ya bawa hannuwansu daman haduwa waje daya,hannunta a qasa nasa saman nata,ya dan lumshe ido cikin mamakin yadda dumin hannun nata yake ratsashi,duk da sanyi sanyi safiya da yake kadawa,da kuma na hadarin daya hado a jiyan bai kai ga zub da ruwan ba ya baje ya bada iska har kawo safiyar yau din. Ita ta zare hannun nata,kana da sauri ta miqa hannunta ta zaro hijabinta da suka kawo gab dashi ta sanya,yayin da shi kuma ya buda ruwan ya kafa kansa yana sha cike da nutsuwar nan tasa,ka kace wani abu me maiqo yaci daga tashinsa,sai da yasha da yawa sannan ya ajjiye,yana amsa gaisuwarta,wanda tuni ta koma ga dankalinta da har ya fara ja,Allah yasa bai qone ba. Gefanta ya ajjiye keys din dakin nasa "Zan fita,ki shiga ki sharemin dakin,after kin gama komai" "To" ta amsa a sanyaye tana gyada kanta. Ya juya yana niyyar fita a kitchen din jauhar ta sako kai,fuskarta cike da murmushi cikin salo nason janye hankali tace dashi "Hi sweet baby,good morning" "Morning babe" ya amsa mata da muryar nan tasa dake sake narkar da zuciyar mata da yawa "Ina zaka haka da sassafen nan" agogonsa ya kalla,bayason ta tsaidashi,ita har yanzu ta kasa fahimtar cewa yana mata kara ne,amma gaba daya ita din ba tsarinsa bace,bayason mace irin jauhar kwata kwata,yaga yaran masu kudi bila adadin....yaga gidajensu na aure.....sam rayuwarsu batayi masa ba,qalilan ne a cikinsu suke iya kula da gidansu dama mijinsu,suie kuma iya sauke responsibilities dinsu "Wani waje me muhimmanci" sai ta dan bata rai "Har unguwa ta fini muhimmanci kenan?" Ta fada a shagwabe,sai kaltum ta ajjiye spoon din hannunta,a hankali kuma a nutse taxo ta kewayesu ta fice bayan ta kashe wutar suyar,haka kawai takejin qirjinta na mata nauyi,yanayin kuma kamar yafi qarfin zuciyar tata,ba zata iya dauka ba. Da kallo duka suka bita,kafin samir din ya fara takawa shima yana bin hanyar da kaltum din tabi a yanzun "Ina sauri ne.....idan na dawo ma tattauna" ya fada yana dan qara speed nashi. Haka kawai yaji hankalinsa ya dauko ga fitarta,har ya nufi motarsa ya bude sai ya mayar ya rufe,ya dawo zuwa cikin gidan a nutse,bayan ya jefa hannayensa duka a aljihun wandonsa. Tsaye ya hangeta gaban qaramar bishiyar ayaba dake gidan,baya ganin fuskarta amma yana iya hangen bayanta,baiyi magana ba yaci gaba da takawa,yasan ba zataji takunsa ba,saboda grass carpet ne lallausa shimfide a wajen. Dab da bayanta ya tsaya "Girkinki na can yana jiranki.....karki makara" ya fada cikin voice dinsa,ba shakka tayi mamakin zuwansa inda take,hakan yasa gabanta faduwa,a hankali cikin dabara ta fara qoqarin daidaita mood na fuskarta "Ok to" ta amsa masa,sannan ta tsaya na wasu mintuna da take qiyasta cewa ya tafi daga wajen,saita juyo da confidence dinta,abinda yasa goshinta ya daki qirjinsa kenan,sai taja baya da sauri tana furta "Otchhh....." Tana dan mulmula wajen,bawai don taji xafi ba,a'ah,ta fada ne kawai sabo batason yaga yanayin da fuskarta ke ciki. Maimakon yadda ta zata,zai mata sannu ne ya tafi,sai taga ya sake matsowa da dan hanzari,yana son kamo fuskarta don ganin inda ta buge din yana fadin "Oh....sorry" qememe taqi bashi dama,sai tayi saurin cewa "Ba wani xafi bane me yawa....." "Ok....let me see" kafin ta qara yunqurin yin wani abu harya dago fuskar tata,ta hanyar kamo habarta,cikin second guda qwayar idanunsu suka manne waje daya. Kamar wani magnet ke jansu haka kowannensu yakeji,cikinsu babu wanda ya iya janye idanunsa daga cikin na dan uwansa,wasu abubuwa yake karanta masu yawa tattare da ita,duk yadda kaltum taso tayi hakan kuwa amma abun ya gagareta,har sai daya sakar mata fuskar don kansa cikin sanyin jiki ya ja da baya yana cewa "Lokaci yana tafiya" bata iya motsawa a wajen ba har ya bacewa ganinta,saita samu kanta da murguda baki,abinda ba al'adarta bace,yadda ya kashe mata duk wata laka ta jikinta bata jin zata iya ci gaba da aikin,amma kuma ta gefe daya har yanzu idanuwanta na ganinsa tsaye tare da jauhar.....anya a yadda takeji a zuciyarta kuwa zata iya jurar ganinsu a hakan?,wai me ma yasa takejin wannan zafin ne?,bata sani ba itace amsar,sai tana matattun qafafunta ta nufi hanyar gidan. Tana shiga ta taras tuni bibi ta kusa kammala aikin,ta dubi kaltum din cikin fara'a "Tunda naga wannan aikin nasan ke kika fara shi" saita maida mata da murmushi,ta samu waje ta zauna suna gaisawa,don bata jin zata iya ci gaba da aikin. Duk inda bibi ta gifta binta kaltum take da idanu,tana wassafa ta tadda zata iya sanarwa da bibin cewa hajiya raihananta tana raye?,amma kuma wannan shine dai dai lokacin daya kamata ace ta sanar mata din,don haka ta miqe a hankali tabi bayan bibi,wadda ta bude backyard na kitchen din ta shiga tsinko lemon tsami. "Kinga lemun nan kwana biyu da ba's tabashi sun qara kyau da yawa" bibi ta fada bayan ta waiwayo tana taga kaltum a tsaye,saita qaraso kusa da bishiyar,kamar tana taya bibin duba wadanda zata cira din "Kinsan kuwa momin samir tana raye?" A bazata maganar ta zowa bibi,har sai da dan bowl din hannunta ya subuce daga hannun nata ya fadi qasa,sa'annan a razane ta juya tana duban kaltum "Ke 'yar nan?,anya kuwa hankalinki daya?,kinsan kuwa abinda kike fada?,mafarki kikayi ko kuwa?,to idanma mafarkinne kiwa Allah ki yiwa ma'aiki ki shuru da bakinki ba tare da kin gayawa kowa ba". Idanunta dake cike da qwarin gwiwa,tare da jin cewa zata iya tunkarar komai ta dubi bibi dasu "Kiyi magana a hankali bibi,tunda bakison kowa ya jimu,a haka duk wanda ya taho zai dauka muna tsinkan lemo ne,zan shaida miki dukkan abunda baki sani ba,amma tabbas momin ya samir tana raye" da qyar bibi ta tattaro nutsuwarta,ta durqusa ta dauko bowl din,ta riqeshi a hannunta kamar yadda yake a dazun. A nutse kaltum ta bayyana bibi dukkan wani abu da bata sani ba,saiga bibin taja da baya tayi zaman drishan a qasa tana ruwan hawaye,kafin ta zame bowl din daga cinyarta ta sulale goshinta zuwa qasa tayi sujjada,ta dago tana sake sakin kuka tare da kiran sunan Allah cikin girmamawa hamdala da kuma hailala,sai kuma ta taso ta rungume kaltum a jikinta gaba daya "Tabbas alheri ce ke,ba shakka Allah ne ya jefo dake rayuwarmu gaba daya,don ki fitar damu daga duhu izuwa haske,na fiki shekaru,na fiki sanin duniya da gogewa,amma an sakamin waigin da bazan taba iya tasiri ba,sai gashi ke da qananun shekarunki sha takwas kinyi aikin da babbar mace ta kasa,tabbas ba shakka dukkan wani tsoro ya qare,tunda har muna da tabbacin hajiya raihana na raye....lokaci yayi da jidda zata kwashi kashinta a hannu,zata kuma girbi abinda ta shuka" "Shine abinda nake tunani,ya kamata ta fito,ya kamata ta huta,ya kamata taga danta da aka rabata dashi tun bai mallaki hankalin kansa ba" kaltum ta fada cike da damuwa tana duban fuskar bibi,bibi data fada nazari........ Bakinsa dauke da sallama ya tura qofar dakin asibitin, professor rashid ya daga kansa yana amsa sallamar gudan dan nasa,fuskarsa ta wadata sosai da murmushi da ganin samir din,abinda daga shi har samir din suka manta yaushe rabonsu da ganin hakan. Ta wani gefan shima samir din zuciyarsa fes take,cike kuma da farincikin ganin daddyn nasa zaune sosai,mutumin da suka fara debe tsammani da samuwar rayuwarsa,sai gashi a zaune tangargar,saidai yanayi da zai nuna maka cewa lallai yayi jinya,da kuma saran ciwuka qananu dake qafarsa da hannunsa. Kai tsaye ya isa gaban daddyn,ya fara gaidashi yana tambayarsa jikin nasa,tare da dudduba ciwukan jikinsa "Da sauqi sosai samir.....Allah yayi maka albarka" daga kansa yayi ya dubi daddyn kafin ya amsa,tunda ya farfado yake sanya masa albarkar da baisan ainihin meye ya kawota ba,abar daya jima rabon da ya jita daga bakin mahaifin nasa "Kana mamaki ko samir?" Daddyn ya fada da wata karyayyar murya,wadda zata jefa tausayi a zuciyar duk mutumin da ya jita,kasa amsa masa shima yayi,sai tunani da lalube da zuciyar samir din ta tafi....laluben meye haka yaketa karya qwarin gwiwa da jarumatar mahaifin nasa?,kamar yasan tunanin da yakeyi sai yace dashi "Hadamin ruwan shayi ka kawomin,kazo ka zauna muyi magana" bai musa ba,ya qarasa inda aka kammale duk wani kayan breakfast,tamkar a gida,duk kuma aikin asibitin ne,asibiti ne babba me tsadar gaske,suna da me jinyar patient,sannan duk wani abu da mara lpy xai buqata naci da sha su suke hidimar yi,saidai duk cikin kudinka,hakan ya sanya duk wanda zaka gani cikin asibitin to ba shakka yaci ya sha ya tada kai ne. "Na gode" daddyn ya fada bayan ya karba cup din da ya tabbatarwa samir din zai iya sha da kansa,samir din na zaune har ya kammala,ya karba cup din ya bashi ruwa "Sai zuwa anjima,zauna Muhammad" yayi kiransa da sunan da bazai iya tuna when last da yaji ya kirashi dashi din ba " Da farko abunda zan fara cewa shine....ka yafemin abisa mummunar fahimta dana dinga yi maka tsahon rayuwata,bahagon kallo.....da kuma kallon da nake maka a matsayin da mara biyayya,wanda yake sabawa dukkan wata magana ko qudurina......" Hankalin samir din ne yaji ya tashi,jin mahaifin nasa wai yana neman gafararsa,saiya matso sosai yankama hannun professor din "Daddy... Meye ya kawo wannan maganar?" Wani busasen murmushi daddyn ya yayi "Samir....na dade ina jin haushi da takaicinka cikin raina,na dade ina tuhumar kaina ya akayi na haifeka,na dade ina maka kallon bijirarre,ban taba tsaiwa nayi dogon nazari akan hakan ba.....ashe duk abinda kake yi samir baka taba saukeni daga matsayin uba daka daukeni,ashe abubuwa masu yawa da kakeyi kana yine saboda ka gyara sunana ....rayuwata.....da kuma duniyata.....abinda ya faru shine.....lokacin da muke kan hanyar zuwa azare nida baka driver....sakamakon babu wani jirgi da zan samu da zai tashi a ranar,tun kafin mu nausa tafiya na siyi jaridun da suka fita a ranar donsu tayani debe kewa idan muka shiga inda babu service.......katsam ina tsaka da duba jaridun.....saina fara cikin karo da wasu ayyuka,masallatai,makarantu,asibitoci da hanyoyi da akayi a qauyuka masu tarin yawa.....wanda kowanne dauke yake da cikakken sunana, professor rashid azare,wanda kowa yasan duk wanda aka kira da wannan sunan wa ake nufi......nayi mamaki kamar yadda na shiga doubting din waye yake aiwatar da wannana ayyukan da sunana?,daga qarshe sai naga hotunanki a matsayin wanda yake zuwa dukka wadan nan qauyuka da kwangilar aikin.....ya kuma ce daga waje na aka aiko ayi aikin.....,mamaki ya kamani,ban tsaya sanya ba na daga waya,Allah ya taimaka da sauran network bai gama daukewa ba,na kira amiru,bai boyemin komai ba ya gayamin cewa kaine kake wannan ayyukan da sunana,dukka qauyen daka tafi kaje ne saboda kayi ire iren wannan aikin,da sunana bada sunanka ba.....a take abubuwa guda biyu suka sauko suka rufeni,har bansan sanda amiru ya gaji da dakona ba ya kashe wayar. Abu na farko shine.....kaico da nadamar irin abubuwan da suka dinga faruwa tsayin shekaru,yadda na dinga yi maka.......,kai samir ya daga yana kallon daddyn,wani farinciki yana lullubeshi. A hankali ta rufe katafariyar cupboard din tata ta alfarma,wadda take danqare da dukiya da kuma dukkan wani abu daya zama sirrin tane,ta waiwayo tana duban najwa dake shigowa "Ke me yasa har abada idan zaki shiga waje ba zaki koda 'yar sallamar nan ba,na sha gaya miki ki daina min irin wannan shigowar ko?" Dariya ta saki,ta jawo pillow din gadon xata zauna a kai,ta dora saman cinyarta sannan tace "Sorry" kai ta gyada tana takowa zuwa inda take,batasan me ya sauya najwa din ba gaba daya a 'yan kwanakin,ta lura akwai abinda take boye mata,take kuma nuqu nuqu akai,takardun hannunta ta aje sama madubi sannan tace "Dama takardun wajenki zaki bani,da sarqoqinki,haka kawai jikina bai bani zamansu a gida nan ba,zan kai bank a ajjiye muku,ga na jawair duka" wani kallo najwan ta yiwa mummyn "Haba mummy,mufa yanzu ba qananun yara bane da ba zamu iya kula da kayayyakinmu ba,mun mallaki hankalin kanmu,ya kamata a sakar mana mara muyi fitsari" galala tayi tana duban najwan,ta dade da sanin hutsuwa ce ta qarsge,wasu dabi'u da batasota dasu ba ta debo,ranta yadan baci da yadda ta gasa mata magana tana diyar cikinta,saboda haka ta fara magana cikin fada "Duk hankalin da zakuyi ai baiki na uwarki bako?,to banason shashancin banza,ki tashi kije ki kawomin,tun kafin ranki ya baci" zumbur ta miqe tana cika tana batsewa "Nifa mummy tsahon lokacin da na dauka ina biyayya tare da bin tsarinki....banga wata riba dana samu ba,a maimakon na zama magajiyar daddy....wadda duk inda yasa qafarsa ya cire zan maidata tawa kamar yadda kike kwadaita min....abun sai ya canza,na qare da komawa aiki a company qarqashi samir,kuma a gaban idahunki,sannan baki iya tabuka komai ba.....to na kwashe dukka takaddu suna wajen fawwaz,ya fara shirya min wasu plan,duk da basu tafi a yadda muka so ba amma na fara ganin alamun nasara" kallo mummy jidda tabi najwa dashi baki bude,gabanta yana faduwa,kada dai ace alaqar soyayyar data dade da guntuleta tsakanin najwan da fawwaz tana na ta sake dinkewa ba tare da saninta ba,ta yaya zata bar fawwaz dan hajiya shuwa ya shiga nasabarta?,kwata kwata basu kai tarin dukiya da arziqin da takewa diyoyinta fatan kasance familyn masu irin wannan dukiyar ba. Bugu da qari kar tasan kar ne,yaya za'ayi ta tura diyarta cikin mutanen da suka san sirrinta?,kai......ta yaya ma hajiya shuwa zata yarda tabar danta ya auri najwa indai ba akwai wata manufa a qasa ba?" Cikin qarfin hali da zallan bacin rai mummy tace "Ni mahaifiyarki kike gayawa haka?,wadda ba don naso ba da bakuzo duniyar ba,ba don naso ba kuma da baki cikin daular da kike magana akanta?,fawwaz?.....ban yanke alaqar dake tsakaninku ba?" "Mummy muna son juna,yana sona ina sonshi,banga aibunsa baiga nawa ba,mahaifiyarsa aminiyarki ce?,me yayi saura banda musha soyayarmu hankali kwance?,gaskiya mummy saidai kiyi haquri,a wancan karon kin rabani da fawwaz....amma a wannan karon.....bazan iya rabuwa dashi ba" daga haka tayi gaba abunta. Binta da kallo mummy tayi hankalinta a tashe,tabbas dole ta yiwa tufkar hanci,saboda matsawar tana raye ba zata taba bari fawwaz ya auri najwa ba,saita dauki wayarta da hanzari ta fara kiran wayar fawwaz din,saidai kuma cikin rashin sa'a aka gaya mata a kashe wayar take. Cikin matuqar gajiyar jiki data ruhi ya bude qofar dakin nasa,yana jin kansa bari daya yana masa wani azababben ciwo,wunin yau dukansa wani irin wuni ne me cakude da al'amura masu tsauri a gareshi,al'amura masu ban tsoro da ban mamaki,sauqinta daya akwai dafawar amini kuma dan uwa a tare dashi.....wato amiru. Idanunsa ya lumshe yana furzar da iska daga bakinsa gami da shaqar daddadan qamshin da sasahen nasa ke fitarwa,duk da cewa ba wani cikin nutsuwarsa yake ba,amma ya kula da gyaran da sashen nasa ya samu,kamar ka sanya baki ka lashe. Man shafawarsa ya jawo ya fara shafawa,har ya kammala ya feshe jikinsa da turare bayan deodorant da roll-on da yake amfani dasu duka saboda dare. Jallabiya ya xura saman gajeran wandon jikinsa,yana gaban mudubi yana sanya maballi idanunsa suka tsaya can saitin fuskar dake bayansa,zuciyarsa ta buga da kyau,ya waiwaya da sauri,zanen hoton mahaifiyarsa ya mamaye wajen. A hankali ya dinga takawa zuwa inda hoton yake,yana cike da mamakin ta ina ya shigo dakin,yakai hannu ya dauka yana qura mata idanu,saiya sanya hannu a hankali yana shafa fuskar,zuciyarsa na qara gudu,yana jin kamar kallonsa take,kamar itace tsaye a gabansa,wata kewa wadda bai taba jin irinta ba ta rugo a guje ta rufeshi,yaji cewa inda tana raye ko tana kusa da ayanz yana a zaune a gefanta yana kallonta,suna tattauna matsalolinsu da hanyoyin da zasu magancesu,yakai bakinsa a hankai yayi kissing da dai goshinta,yana dagowa takarda ta fado saman qafafunsa,saiya duqa a hankali yana riqe da hoton ya daukota,yadan juyata kadan sannan ya bude _su iyaye koda sun rasu akwai sauran haqqinsu a wuyanmu,yi musu addu'a,samar musu da sadaqatul jariya,kamar masallaci da sauransu,wanna kyauta ce daga UMMUKULSUM....zaka iya bamu lokacinka mu da bibi zuwa wani waje da zai sama maka farincikin da ya bace maka bat a rayuwa?.....,FATAN ALKHAIRI_ UMMUKULSUM ya maimaita sunan tare da motsawar labbansa,fuskarta ta fado masa tarwai cikin kwanya da idanu,saiya daga hoton da sauri yana kallonsa,unbelievable......ashe ta iya zane har haka?,ya manta gaba daya ya santa da zane tun fil azal.....amma.....ina ta sani da zata kaishi?,amma kuma tace ita da bibi....wanne farinciki ne da ya bace masa bat a rayuwarsa?,ya kasa fahimta,saiya koma saman sofa din dake dakin ya zauna,yana son bawa kwanyarsa hutu ko zata fahimci abinda maganganun ke nufi,saidai maimakon hutun wayarsa ce tayi qara,tsaki yaja kamar bazai daga ba,saidai tunawa da yayi ya bada muhimmin aiki yasa tilas ya miqa hannunsa da kyau har ya jawo wayar. Wanda rasa ke raya masa dinne kuwa,ya daga wayar ya kara a kunnensa bayan yayi sallama qasa qasa,sallamar dake alamta akwai gajia tattare dashi "Sorry sir.... Kayi haquri,sai zuwa gobe bincikenka zai kammalu,daya layin wayar akwai tsaro sosai tattare dashi,amma zuwa tsakiyar dare in sha Allah zamuyi accessing komai" "Alright" ya amsa a taqaice "Thank you sir" mutumin ya amsa dukansu suka ajjiye wayoyinsu. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana shafa kansa,maganganun da sukayi dazu da daddy na dawo masa,wayar da yaji bala nayi kafin faruwar hadarin bayan ya rufe fuskarsa da jaridar da yake karantawa saboda nauyi da zuciyarsa tayi saboda tausayin abubuwan daya dunga aikatawa dan nasa tsayin shekaru,yayi shuru kuma na wani lokaci wanda a wannan shurun komai ya afku "Indai abinda kunnuwana sukaji dai dai ne.....lallai ba shakka akwai gagarumar matsala,matsalar data wuce ta accident din da nayi,lallai akwai wani babban qulli a qasa da bana fatan tabbatuwarsa" "Allahumma la sahla illa ma ja'altuhu sahla,wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla" ya fada yana miqewa gami da zama sosai,dai dai sanda amiru ya shigo dauke da ledan da ya musu takeaway na irin abincin da yasan samir din yana son ci,saboda yace baya jin cin komai,bazai yiwu kuma ya barshi ya zauna a haka ba. Saida amiru yayi wanka sannan ya dawo ya zauna yana bude musu takeaway din,gefe daya suna dake tattauna matsalolin dake faruwa,wanda kaf duniya su uku sukasan da wannan,shi samir sa daddy. Amiru ya jima yana kallon takardar da kuma zanen hoton baya da samir ya gabatar masa dasu "Ba shirme bane kuwa wannan?"kai samir ya girgiza yana zama sosai tare da fuskantar amiru "Banajin hakan a jikina,akwai wani gagarumin abu,ta ambato bibi a ciki fa?"kai amiru ya jinjina "Of course.....bashi da amfani jan magana,inaga...gobe kawai ku shirya,sai kuje din kamar yadda ta buqata,idan kuma buqatar mijinta take ta kasa gaya maka kai tsaye ne to?" Amiru ya qarashe da zolayar samir,wani qaramin murmushi ka gefan baki samir din ya saki,wanda har ga Allah ya ratsa har ta qasan zuciyarsa,hakanan sai yaji wani kaso mai yawa na nauyin qirjinsa ya ragu,ya lumshe idanu a hankali,saiya dinga tuna lokuttan da suka kebe tare shida ita,zuwansu a zare da sauransu,tsahon lokaci yana tuna abubuwa masu yawa a kanta "Mutumina......ya daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaqi?" Yaji amiru daya taboshi yana fada,ya bude idanunsa da suka canza kala a hankali ya zubewa amirun su "Ina cikin wannan cakwakiyar kana min maganar soyayya?" Dariya amirun ya saki yana gyara zamansa,duk da shima ransa ba dadi,amma ya tabbatar samir ya fishi shiga cikin matsala da kuma damuwa "Bakasan cewa shi feelings ko a wanne irin mood kake ba yana iya motsawa?,baka ga idanunka bane a yanzu, beside ma ita mata kowanne irin jarrabawa ka shiga,suna da power din sama maka nutsuwa da daidaito na hankalinka,dukkan wani tashin hankali da zaka shiga......idan kana tsakiyar qirjinsu.....kana samun wani irin peace, they are blessing from God......shi yasa in sha Allah bazan kai qarshen shekarar nan ba aure ba,na gaji da rayuwar gaurantaka" maida idanunsa yayi kawai ya rufe yana maimaita kalaman amiru cikin kwanyarsa,tabbas dukka maganganunsa haka suke,shi din shaida ne,kwana daya tak....lokaci daya tak da sukayi da ita a wanca guests house din,yayi wani bacci da bai taba jin nutsatsen bacci irinsa ba. "Mr tunani.....jauhar na kiranka fa" "Please switch the phone,i need a rest" ya gayawa amirun ba tare daya bude idanuwan nasa ba,amirun yasan gaskiya ya fada,don haka ya kashe wayar kamar yadda ya buqata. *_COMMENTS DINKU NADA QAYATARWA,JAZAKUMULLAH 👏🏽👏🏽_* *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾100 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar 59 Yadda amirun yace zuwa washegarin bai samu ba,saboda ya wuni tare da daddyn,shi da hajiya qarama wadda tun wancan lokacin bata bar gidan ba,da kuma auta jawahir,kusan wuni sukayi kusa da daddyn. A zahiri jinya daddyn yake,saidai kuma a badani wani idanu da kwanya basira ce tazo masa,dukkan wani motsi na mummy yana ankare dashi. Daga sanda taji kalaman "Allah yayi maka albarka" da suka fito daga bakin daddyn bayan sun dawo daga toilet,inda samir ya taimaka masa yayi alwala wani abu ya daki zuciyarta,saida tana ta qoqarin boyeshi da fake murmushi da jin dadi a zahiri,abun da yasoma daga hankalin daddy,daurewa yake,cikin ransa yana maimaita "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" yana fatan idanunsa ne kadai suka ga hakan,zuciyarsa nata bijiro masa da tarin tunane tunane kala daban daban. Ba yadda mummy batayi da najwa taje ta zauna ba itama amma fafur taqi,sai kumbure kumbure take,da alama fushi take ko gaba ga dauka akanta saboda maganar takardun kadarorinsu?,abinda takejin ko zata fashe ba zata barwa fawwaz ajiyarsu ba,kaya ne masu tarin tsada da daraja. Kaltum kuwa daki ta koma,faduwa gaba dama qunci takeji sosai cikin ranta,duk sanda taga wulgawar jauhar da yadda take shigewa samir gaban kowa sai taji ranta ya baci,don haka ta kebe kanta a daki,ta dauki qur'ani dan qaramin,ta fara tilawar haddarta,wanda zuwa dare sai gashi ta kammala izifi ashirin cif. Zuwa magariba kowa ya watse daga dakin sun tafi sallar magariba,sai samir wanda ya daurawa daddyn Alwala,ya kuma sanya masa abun sallah,sannan ya dawo ya zauna bayan ya dauki wani littafin azkar . Yana shirin budawa wayarsa ta dauki tsuwwa,gaba daya ya manta da ita,tun daxu kuma yaji ana kiransa,alwalar da yake daurawa daddy ta hanashi dagawa. Mamaki sosai ya kamashi ganin sunan murtala da umar sai kuma amiru,amirun da tunda ya fita office bai dawo ba,don yanzun shine ke tafiyar da ayyukan office dinsa. Bai gama wannan nazarin ba kiran amiru ya sake shigowa,ba tare da jinkiri ba ya daga "Har yanzu bakasan abinda ke faruwa ba?" Amirun ya jefa masa tambayar "Me ya faru?" "Ya akayi aka fidda maquden kudade daga asusun company haka?,daga daren jiya kawai?,ko akwai abinda zakayi da kake buqatar kudade masu yawa haka saraki?" Mamaki sosai ya kamashi,gaba daya tunda lalurar daddy ta tashi hankalinsa baya kan company din sosai,koda muhimman takaddu da shi xai sanya hannu wani lokaci saidai a kawo masa su gida,ko shi ya shiga a tsaitsaye ya duba ya saka hannu,sauran ayyukan kuma amiru ya tafiyar dasu "Bansan abinda kake magana a kai ba, please amiru.....ka yimin bayani" "Kudade masu matuqar yawa da zasu iya jawo girgizar kamfanin nan aka fitar,kuma abun mamakin dana tsananta bincike.....akwai sanya hannunka dana daddy gaba daya,dukkan wata alama ko shaida suna nuna cewa akwai masaniyarka kai da daddy" "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin....turomin dukka bayanan ta email" "Ok" amiru ya amsa,dukka suka kashe wayoyin,cikin hanzari ya jawo computer dinsa dake ajjiyr gefe,wanda dama yau ya wuni duba wasu ayyuka,da contact da suka sassamu masu tsoka,wanda yake sanya ran nan da wasu 'yan kwanaki zai maida hankali kansu ya karbi aikinsa. Shuru ne ya ratsa dakin bayan sun gama duba komai shi da daddy,sai system din da suka sanya a gaba suna kalla "Inaji a raina dama akwai babban qalubalen daya tunkaromu......kabi komai a hankali.......mu qara kaifin addu'ar da mukeyi.....karka nuna maganar ta tada maka hankali,kaci gaba da rayuwarka kamar ko yaushe,bincike kuma ya gudana ta qarqashin qasa" ajiyar zuciya mai nauyi ya saukar,ya samu fiye da rabin nutsuwa cikin ruhinsa,lalllai kudi aka fitar musu maqudai,kusan fiye da rabin jarin kamfanin,amma shi wannan ba shine damuwarsa ba,tunda cikin abinda Allah yayi masa zai iya maida gurbin kudin cikin tashi lalitar,abinda yake tsoro.....irin fahimtar da daddy xaiyi masa,kada wannan ya jawo yarda da amincin da ya fara samu daga gareshi,saiya rufe idonsa kadan,qwaqwalwarsa na lissafa masa mutanen da xasu iya kasancewa suspect. A rikice mummy ta koma da baya,ta kuma fara laluben hayar dakinta,ba shakka ko tantama babu najwa nada masaniyar wannan al'amari,wacce irin yarinya ce wannan takeson xame mata 'yar fata?,sai data fara biyawa ta dakinsu,ta tabbatar mata ta sameta yanzu a dakinta sannan ta wuce can uwar dakanta. Kasa zama tayi,sai kai kawo da take daga can zuwa nan,har zuwa sanda najwa ta turo qofa ta shigo dakin,idanun mummy dake cike da zallar bacin rai da tashin hankali ta xuba mata har ta qaraso "Me kika sani dangane da fitar kudi daga azare company?" Yanayin reaction na najwan kadai ya isa gaya ma mutum gaskiyar abinda ke faruwa,tun asali najwa irin mutanen nan ne da basa iya boye abinda ke ransu da zuciyarsu,saita sauke headphone din kanta,ta jingina da mudubin mummy bayan ta ajjiye wayarta saman madubin ta goye hannuwanta a qirji "Ni da fawwaz muka fitar dasu,saboda ni gaskiya it's high time to get the money nima,na gina kaina na gina rayuwarta,saboda gaba daya ke na fuskanci ki fara sanyi,dukkan wasu plan naki sun daina aiki.....bazan zauna na qare a haka ba, Daddy ya mutu nida jawahir a bamu kason saraki ace mu raba ba,ke kuma a baki one over eight,kinga mu asara ta hau b......." Wani lafiyayyen mari ra zabgawa najwa,marin da yasa wuta ya dauke mata na wasu sakanni kafin ta dawo dai dai ta zubawa mummy idanu,zuciyarta tana tafarfasa,tunda aka haifeta ba'a taba marinta irin na yau ba,ko duka ba zata iya tuna sanda akayi mata shi ba,sai yau?,kamar ita da girmanta da shekarunta?,tana da matakin karatu mai zurfi,tana jin kamar ta maida hannu ta rama marin ne ko mummyn xataji irin yadda taji...... "Shashashar banza da wofi,wadda bata komai da hankali,fawwaz dai fawwaz dai?,qanin ubanki ne shi din?,da har zaki fara aiwatar da abubuwa bada shawarata ko masaniyata ba?,inda ta haka na tara duk abinda na tara da yanxu nakai warhaka ina al'amurana?,abun ba iya taku bane?,yanzu wannan kinsan matsalar da zata haifar?,kinsan dimbin masifun da xai tono?,to xanyi maganinku daga ke har fawwaz din" qarar wayar najwan dake gefe ya sanyasu maida hankalinsu,gaba daya suka kai hannunsu a tare,mummyn ta riga warcewa saboda ganin sunan fawwaz din,dama nemansa take ido rufe ya dawo da takardun nan,ga kuma wannan ta sake faruwa "Kana jina da kyau?,ka saurara kaji abinda xan gaya maka,bisa kakkausar murya da kuma gargadi,baka da gadon najwa koda mutuwa tayi.....bare gadon ubanta.....saboda haka.....na baka awa ashirin da hudu,duk wani abu nata data baka da wanda ka karba,ka tattaromin shi ka kawomin cikin girma da arziqi,duk wani abu namu dake hannunku kaida uwarka,don na tabbatar akwai masaniyarta cikin komai,ida ma kun shirya wani zagon qasa ne to haqarku bata cimma ruwa ba,amma na baku awa ashirin da hudu,daga yamzu zuwa gobe,tunda baku san abun arziqi ba" daga haka ta datse kiran,tama kashe wayar gaba daya "Ya haka mummy,tunda kin gama fada ai sai ki bani wayata kuma ko?" Najwa ta fada cikin fada da qunar rai "Idan kuma na hanaki fa?" Bata ankara ba najwan cikin fushi ta kaiwa wayar wafta,ta samu nasarar finciko abarta kuwa ta kuma qara gaba babu ko waiwaye,saidai kuma hakan yayi sanadiyyar faduwar mummyn,kwankwasonta ya bugu da gado. Wajen ta dafe tana ringse idanu,saidai kuma ta bangare guda tsoro ne da firgici fal zuciyarta,tsoron sauyawar najwan zuwa wasu halaye da dabi'u data jima da saninsu a wani muhalli na daban. ********Tsaye take a gaban madubin tana nada dankwalin rigar jikinta,gabanta ne keci gaba da faduwa,a ranar yau nasara ce ko kuma faduwa a garesu,tuni bibi ta fita zata samesu bakin titi,a yanzu ita da samir da amiru ne suka rage cikin gidan,cikin wata qatotuwar sa'a kuma......mummy ta fita tun sassafe,dama kuma basa son ta gane ko ta fahimci fitarsu zuwa dawowarsu. Tana fitowa daga daki taga giftawar hajiya qarama,sai ta lumshe idanunta tana qiyasta yadda Hajiya qarama zataji duk sanda labarin raihananta tana raye yakai kunnenta,zataso ace da ita za'ayi tafiyar nan.....saidai dole a dakata da xuwa da itan saboda wasu dalilai,komai zai kasa yiwuwa yadda sukeso matsawar ya zamana anje ne da hajiya qaraman. Tun kafin ta qaraso ta ya hangota ta madubin gaban motar,tsaida idanunsa cikin madubin yana binta da kallo,tana sake matsowa inda suke suffarta na sake bayyana,tayi kyau sosai cikin orange atamfa me adon dark brown,madaidaicin medium mayafi brown,fuskarta fayau,sai wani kwantaccen kyau da fuskarta ke fitarwa,qawatacciyar brown skin dinta ta sake kyau wadda laushinta da santsinta a idanu kawai ya bayyana,lips dinta babu komai akai,saidai yanayin yadda Allah ya tsara mata lips dinta gwanin sha'awa ne game kallo. Kamar walqiya yaga juyawar madubin da yake kallo zuwa robar dake bayan madubin,ya juya a nutse zuwa gefansa,sai yaga amiru na dubansa,da alama shine ya juyar da mudubin. Ido daya ya kashe masa "How far bro?" Kansa samir ya dauke sannan yace "Me ya hana bude gate din nan ne?" Yayi maganar dai dai sanda yake tada motar,dariya amiru ya bushe da ita "To ai driver din motar bai shirya ban....." Daidai lokacin kaltum ta bude murfin motar ta shigo. Cikin sassanyar muryarta ta gaidasu,suka amsa samir ya fara motsa motar suna ficewa daga cikin gidan,yana jin amiru nadan tsokanarta,bata amsa ba,saidan sautin murmushinta kawai,kafin daga bisani shuru ya ratsa motar,har suka cimma bibi suka dauketa sannan ya qara speed na motar. "Ina muka nufa bibi?" Amiru ya waiwaya kadan ya tambayeta "Kaltum ce jagorar tafiyar,zata dinga muku kwatance har mu kai" dukkansu sun danji mamakin furucinta,to amma ba wanda ya tanka,samir yaci gaba da sauraron kwatancen da take masa cikin sassanyar muryarta,har suka kawo qofar wajen. "Nan ne?" Samir ya nuna qofar gidan da yatsan hannunsa cikin kokwanto "Nan ne" bibi ta amsa masa a maimakon kaltum,kamar zaiyi magana kuma saiya fasa,ya gangara da motar a hankali xuwa ina aka tanada saboda ajiyar motoci ya tsaidata,sannan ya faka,kowa ya kama murfin motar suka fito. Tun daga farfajiyar wajen bibi ta soma sharar hawaye,babu abinda take tunawa illa tsahon shekarun da hajiya raihana ta share cikin wadan nan mutanen,tsahon shekarun data share tana rayuwa irin tasu,wahala data fuskanta tsauri da tsanani. Kai tsaye office din shugaban gidan aka kaisu,ya karbesu hannu bibbiyu,basu shaida masa ainihin su su waye ba,don kusan ma bibi ce tayi masa bayanin cewa,sunzo ziyartar marasa lafiyanne. Sosai ya nuna jin dadinsa,saboda yanayinsu kadai ya bayyana masa cewa lallai yau gidan akwai samuwa,don haka ya tashi da kansa suka fara zagayawa gurare gurare. Dukka gaba dayansu ba wanda jikinsa baiyi sanyi ba,lallai lafiya babbar ni'ima ce,duk wanda Allah ya bashi kyauta da baiwar lafiyar hankali ji da gami da gani ba qaramin abu bane. "Alhamdulillah" saraki yake furtawa a fili,saidai qasa qasa,kana duban qwayar idanunsa zaka gane cewa yanayin da ya bayin Allah ya taba zuciyarsa. Minti kusan arba'in suka diba,wani abun ya basu tausayi,wasu a cikinsu su basu dariya,sosai saraki yayi rabon kudi,kudi sosai ya raba musu,musamman wadanda hankali ya fara samuwa a garesu,sannan suka dinguma sukayo hanyar barin wajen. Sosai ta riqe hannun bibi sanda sukayi kusa da wajen,bibin najin hakan ta fahimci abu na gaba dake shirin faruwa,don haka kaltum na sauka daga hanyar tabi bayanta. Kyauro shine mutum na farko daya fara ankara dasu,tun shigowarsu wajen dama yaji sam hankalinsa bai kwanta ba,musamman lokacin da yayi idanu hudu da yarinyar,ya shaidata sarai,ya kira hajiya jidda kuma yafi sau hamsin daga shigowarsu kawo yanzu amma wayar taqi shiga,har ya fara murna sanda yaga sun kammala ziyarar lafiya,sai ya hangi kaltum na nufar wajen da yake tamkar rayuwarsu ne a wajen. "Ke.....ina kuma zakuyi?,baga hanya nan ba?" Ya fada da wata irin rudewa data gaza boyuwa "A'ah,akwai sauran baiwar Allah da ba'a dubata ba ita,kuma ta cancanci a dubata din" kaltum ta fada cikin wata dakiya tana duban qwayar idanun kyauro. "Ba kowa ta nan bangaren,dukkansu kun gansu a inda ake fito dasu ai hajiya" ya fada fuskarsa na fitar da wani busashen murmushi,bushewar data zarce har maqogwaronsa cikin sakanni 'yan kadan "Akwai saura,akwai wadda ni ban ganta ba,bayan wanacan karon na ganta" wani gumi ne ya zartowa kyauro,yaga alamar akwai wani gagarumin tashin hankali da yarinyar ke son ballo musu,don haka ya fara takawa zuwa inda suke tsayen yana kafe kaltum da ido "Hajiya kiyi haquri,kowa da kowa yana waccar farfajiyar da kuka baro,lokacin ziyara ma ya kusa fita". "Babu inda zani sai na ganta" ta amsa masa kanta tsaye babu wani tsoro ko dar,don ta riga ta shiryawa koma meye "Kaga sani.....qyaleta,aiba wani abu bane" yaji umarnin shugabansa daga bayansa,adan rude ya juyo ya dubeshi,sannan ya maida dubansa ga kaltum "Shikenan,ki shiga ki fito sab......" "Bani kadai ba.....gaba dayanmu muke da buqatar shiga" sosa samir dake tsaye daga baya yake karantar fuskarta,fuskar da bai taba ganin makamancin abinda yake gani a yanzu cikin qwayar idanunta ba,tabbas akwai wani abu,tun ba yau ba,ya jima da sanin halinta,bata kafiya akan rashin gaskiya.....taurin kanta akan gaskiyarta ne....tun ganinsa da ita na farko. Fusata yayi sosai daa datsar numfashinsa da tayi,abin yayi matuqar fusata shi,dama abunka da maras gaskiya cikin fada ya fara magana "Ke wacce irin matace?,to ba zaki shiga din ba,kece qarama amma kinfi kowa musu da taurin kai?" "Stop...ya isa.....matar aure ce,why all this?,minti nawa ne mun shiga mun fito?,i believe shigar nada muhimmanci shi yasa ta dage" amiru daya riga samir magantuwa ya fada,sak kyauro yayi yana binsu da kallo lokacin da sukayi jerin gwano zuwa cikin wajen,ba shakka yarinyar akwai abunda ta shirya....take gumi ya masa rumfa kamar wanda aka sheqawa ruwa daga saman kansa,qafafunsa suka fara kyarma,ba shakka jikinsa yana bashi yau din ranar tonuwar asirinsu ce,yau din itace ranar da bahaushe ke cewa rana dubu ya barawo.....rana daya tak tame kaya,saiya soma ja da baya sanda yaga sun qule,ya take da sauri zuwa wajen motarsa qirar 206 ya shige ya bata wuta yana neman hanyar ficewa daga wajen gaba daya. Duk taku daya sai faduwar gaban bibi da kaltum ya dadu,yayin da mamaki ya cika samir da amiru na yadda aka samar da waje irin wannan cikin gidan,kunnuwansu kuma na sauraren bayanin shugaban wajen,wanda ke shaida musu cewa,wajene da aka tanada shekarun baya can don ajjiye wadanda ciwonsu ya tsananta,aka kuma fidda rai da warkewarsu,saidai daga bisani da ilimi ya yawaita an daina amfani da wajen kwata kwata,yace yana tunanin cikin karance karancen kaltum din taci karo da labarin wajen,shi yasa take sha'awar shiga taga gurin. Dai dai qofar dakin kaltum ta tsaya,yayin da kowa cikinsu yaci burki a wajen "Ko za'a iya bude dakin nan?" Kaltum ta tambayi shugaban gidan "Ai a bude ma suk....."sai kuma maganar tasa ta tsaya sanda yayi idanu hudu da padlock jikin qofar "Ikon Allah" ya fada yana kama muqullin tare da juyashi a hannunsa "Wannan tsohon muqulli ne,bazaiyi wahalar buduwa ba" ya fada yana tattara qarfinsa tare da qoqarin budewa. Ganin ya kasa sai samir ya matso,tun tsaiwarsu a wajen yakejin wani bugun zuciya mara misaltuwa,ba tare da yace komai ba ya kama padlock din,ya murda sau biyu take ya bude,qofar ta fara yin yin baya a hankali,take ta bude sosai,dakin ya bayyana......... . Tana tsaye tsaf tana fuskantar qofar,cikin yanayin tsaiwar da zai nuna maka nutsuwarta,hannayenta goye a qirjinta tana kallon qofar. Duk da babu wadataccen haske amma kana iya gane mutum musamman idan ka sanshi "Hajiya....raihana" bibi ta fada muryarta na rawa kafin ta fashe da mugun kuka wanda ta kasa riqeshi,abinda ya hana shugaba barin wajen da gudu kenan,saboda tsorata da yayi da ganin bil'adama a wajen da iyakar saninsa babu kowa tsahon wasu shekaru. "Bibi zuwaira...." Hajiya raihana ta fada da wata dakusashshiyar murya,sannan itama cikin rawar jiki ta fara takawa zuwa bigiren da bibin ke nufota. "Momma?......." Saraki ya fusgi kalmar daga bakinsa bayan jiyo sautin muryarta,muryar da bai taba kwana sau biyu a jere ba ba tare da yaji sautinta tsakiyar kansa ba,tuj daga ranar data tafi ta barshi har kawo jiya,sautin muryar da yake kwana yake tashi da kwadayin sake jinta. Cikin wani irin kuzari da hanzari ya ratse ta tsakiyar amiru da shima yayi mutuwar tsaye,da kuma kaltum dake gefe hawaye na layi bisa kuncinta,kafin bibi takai gareta shi ya rigata isa......kallon second uku yayi mata,ya sake tabbatarwa itace,duk da wani irin kalar toka toka data zama,duk da wani irin nau'in tsufan dole daya keto mata,saiya ware hannayensa gaba daya ya rungumeta izuwa jikinsa,numfashinsa na wani irin fusga,kamar zai tsige daga gangar jikinsa. 60 A hankali bibi ta sulale a wajen saboda kasa qarasawa da tayi zuwa wajen momma raihanan,duk da burin hakan da takeyi,amma sam qafafunta sun kasa daukarta,ganin abun take kamar almara,kamar cikin irin mafarkan data saba yi,idanunta suna iya hango mata sanda samir da momman suma suka durqushe zuwa qasa,sai giftawa kaltum da amiru suna qoqarin dagata. *******. *****. *****. ***** Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke bayan dawowa da yayi daga dogon tunani,yau babu kowa a parlor din nasa,samir da amiru sun fita sun shaida masa zasu wani waje,jawahir dinsa ta shiga makaranta,mommy ta tafi asibiti a duba mata bayanta dake ciwo,najwa kuwa dama sau daya tal take shigowa dubashi......sau dayan da idan zai yiwu da ya hanata shigowa ma,saboda wasu tarin dalilai,da kuma rashin alfanun zuwa dubiyar tasa ma gaba daya. Ko sau daya yaga gilmawarta kota mahaifiyarta sai yaji wani abu yana motsa ranshi,abun da har yanzu yake masa zafi da ciwo a qirji,kullum addu'a yake dare da rana,tun daga wancan lokaci kam rabbus samawati ya warware dukkan wani qulli dake cikin rayuwarsa. Wannan zaman da yake a yanzu yana yinsa ne badon bai warke ba,a'ah,yana yinsa ne saboda jinyar zuciyarsa,a duk sanda ya tuna irin musgunawa da miyagun kalaman da yake jifan samir dasu a baya sai yaji zuciyarsa ta quntata,babban abun tambayar shine......a koda yaushe jidda bata hanashi jifan samir din da miyagun kalamai,saidai kawai fa nuna a fuskarta,bata taba tursasa samir dai dai da rana daya yayi abinda yakeso ba,koda kuwa shi baya so,inda raihana ce zata bar haka ta faru?...... Gabansa yayi wani muguj faduwa da tuna raihanan da yayi,a hankali tunaninsa ya koma baya,zuciyarsa ta shiga tuna masa wace raihana?,tun daga haduwarsu har zuwa rayuwarsu....... "Daddy......kayi baquwa" muryar najwa ta katse masa dogon tunanin da ya fada,ya daga kai yana duban yarinyar,duba me kama dana qurilla,sai ya buda bakinsa a hankali "Wacece?" "Hajiya shuwa,.....maman fawwaz,tace saqo tazo kawo maka" mamaki sosai ya kamashi,a iya tsahon saninsa da hajiya shuwan aminiyar matarsa ce,tun suna da jajayen sawayensu kawo yanzu,babu kuma abinda yake hadasu da ita illa gaisuwar mutunci,to amma,baisan wanne irin saqo bane wannan "Ki rakota ta shigo" ya fada yana gyara zamansa saman kujera,sai ta juya da saurinta ta fice,tana addu'ar Allah yasa maganar nemawa fawwaz aurenta ne,saboda tasan indai hakan ta faru tofa burinta ya cika,daddynta bashi da matsala,yana qaunarta,hakanan yafi mummyn sauqin kai. Daga kai yayi yana amsa sallamarsu ita da fawwaz sannan yayi musu izinin zama,suka gaisa sukayi masa sannu da jiki,sannan najwa ta juya tana cewa "Hajiya bari na kawo muku abun motsa baki" daga haka tayi gaba tana jin dadi cikin ranta,shuru ya ratsa wajen na wasu sakanni sannan hajiya shuwa ta fara magana "Nasan zakayi mamakin jin cewa gurinka nazo.....nazo kawo maka saqo ko?" Kai ya gyada yana dubanta "Qwarai kuwa" saita motsa jakar hannunta me dan fadi da yalwa "To ba abun mamaki bane,duba da cewa.....jidda ta buqaci duk wani abu nata dake hannunmu na dawo mata dashi.....to.....kasan mu da riqon amana da kuma cika alqawari,nazo na taras bata nan,to banason baiwa diyarta kayanta tunda da alama diyar halin mahaifinta tayo.....kayi haquri,bakai nake nufi ba,domin kai din ba mahaifinta ba,kai ubanta ne,uba kuma irin na riqo,wanda ya dauki nauyin dukkan wasu nauye nauyen na diyoyin daba nashi ba har zuwa sanda suka zama mutane......" Takai qarshen maganar tana ciro wasu takardu daga jakarta,sannan ta dora idanunta ga daddy wanda ya zuba mata ido sosai,yana son gaya alamun hauka ko tabin hankali tattare da haj shuwa da take furta wadan nan kalaman "Nasan ka shiga mamaki ko?,to ina tafe da hujjata ta gaya maka haka,ungo wadan na takardun guda biyu" ta fada tana miqawa fawwaz su,shi kuma ya miqawa daddyn sannan ta dora "Takardar farko takarda ce ta asibitin daka taba kwanciya jinya sanda ka samu hadari shakaru talatin baya,a lokacin da danka samir bai wuce shekara uku a duniya ba,baya nine na cewa wata jijiya cikin jikinka da zata iya bayuwa ga samun cikin matarka ta tabu,saidai daga shekara uku zuwa hudu zata iya komawa kan aikinta,matarka zata iya daukan ciki harma ta haihu.....,a wannan lokacin raihana cikin gidanka bata da wani amfani,saboda siddabaru da kissa da jidda tayi amfani dasu ta shiga tsakaninku.....don haka jidda ita ta karba takardar. Da ganin bayanan jiki hankalinta yayi matuqar tashi,tayimin bayanin cewa indai haka ta kasance shikenan bata da wani riba a aurenka,saboda raihana nada da namiji,ita kuwa bata da qwai ko guda daya,yaushe zata yita zama har sai ka warke?,warkewar da babu tabbas?ita data shigo da burin tayita haifa maka yara,dalilin da ya sanya duk cikin da raihana ta dinga samu bayan samir ta dinga lalata mata shi kenan ba tare da saninku ba gaba dayanku...." Daga kai daddy yayi da sauri ya dubeta,kai ta gyada masa alamun tabbatarwa sannan kuma taci gaba Da wannan dalilin jidda ta boye wannan takardar bata bari kowa ya gani ba,qarshe ma saboda gudun bacin rana ta bani ajiyarsu,tun daga ranar jidda ta shiga neman hanyar da zata samu ciki,dalilin da yasa ta komawa ainihin saurayinta daya fara yi mata ciki har sau biyu a duniya. DAGE cikakken dan sara suka,kuma tantiri,wanda ya taso a gidan da babu cin yau babu na gobe,bangar siyasa da daba sata da shaye shaye shine aikinsa,ba wani jimawa kuwa ta samu cikin NAJWA dashi,ta kuma haife maka,ka amsheta a matsayin 'yarka.......,bayan wannan tasan yadda ta hada masa TARKON da ya kashe mutum aka kaishi gidan kurkuku,daurin rai da rai,yanzu haka yana can. "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" daddy ya furta kansa a qasa,hawaye na qoqarin saukowa daga idanunsa "Bayan ta haifa najwa tun kafin takai dage gidan kurkuku dama tace ba zata koma masa ba,da alama yara mata iya baiwa mahaifar mace,don duk cikinta na baya guda biyu data zubda mata ne,saita koma kan lecturer dinta data qyalla idanu ta gani,ta kuma samu labarin 'ya'ya maza gareshu guda hudu rigis,burinta bai cika akanshi ba,sai satoshi tasa akayi,ta kuma bashi abun gusar da hankali yayi mata yadda takeso,tsahon wata biyu yana aje a wajenta tana yadda takeso dashi ba dare ba rana,bata sakeshi ba sai data tabbatar ta samu abinda take da buri,wanda bayan komai ya kammala ya shiga baqinciki da takaici,abinda kusan yayi ajalinsa kenan,ya hadu da hawan jini,wannan shine mahaifin jawahir" Kamar ta buga masa guduma aka da qahon zuciya haka yaji,saboda bai taba tsammatar hakan akan jawahir ba,yarinyar da tayi matuqar shiga ransa,yarinya mai hankali da nutsuwa....tausayi da kuma sanin ya kamata,har gwara najwa....tun daga ranar da yaji bala na waya da ita....tana bashi umarnin ya watsar da daddyn bisa titi bayan an tsinke musu burki yasha jinin jikinsa,jikinsa yake bashi tabbas ba diyarsa bace ta halak,saboda abune mai matuqar wuya ɗa na tsantsar halaliya,dan da aka auri mahaifiyarsa bisa tafarkin shari'a,aka haifeshi bisa tafarkin shari'a ya iya kashe mahaifansa "Sanda raihana ta sake samun ciki abun yayi matuqar daga hankalin jidda,kuma ya tabbatar mata da cewa lallai ka samu sauqi,tana tsoron kada raihana ta sake haihuwa ta samu da namiji ita tana zaune,abinda yasa ta yanke shawarar kau da ita,ta kuma yita qoqarin ta samu haihuwa da kai koda sau daya ne.....saidai inaa,bata samu wannan rabon ba har yau........ "Wadan nan takardun na qasa sune zasu baka tabbacin maganganuna na yanzu......raihana kuwa......" Gabansa yaji yayi wani mummunar faduwa data kira sunansa "Ya Allahu" ya furta a sarari,hakan baisa haj shuwa ta tsaya ba,don burinta kawai ta gama kwancewa mummyn zani a kasuwa "Bayan ta gaza kau da ita daga duniya.....Gidan mahaukata jidda ta kaita.....har yau kuma tana raye......saidai ni kaina bansan wanne gida bane,kuma a ina yake......ga wadan nan,duka takardun kadarorin raihana ne data sace ta rabawa yaranta,wadan nan kuma kudaden kamfanin saraki da 'yarka tasa dana ya debo mata,ta hanyar amfani da siddabarun na'ura........ Tunda ta fita daga gidan takejin gabanta yana faduwa,abinda ya hanata dogon tsaiwa kenan cikin asibitin,ta kasa tsaiwa ma taga likitan ta juyo gida. "Sannu da zuwa hajiya" saude mai aiki ta fada ga jidda,saidai bata amsa mata ba ta jefa mata tambayar dake cin ranta tunda ta shigo,saboda taga motar hajiya shuwa a farfajiyar gidan,batayi mamakin zuwanta ba,saboda a jiya sunyi waya,tayi mata cin mutuncin da dukka yazo bakinta,gami da kakkausan gargadin ta jawa fawwaz kunne ya maido komai dake.hannunsu,ta daukoshi zuwa daular gidanta ne saboda ya amfana shi da uwarsa darajar amintar dake tsakaninsu,hajiya shuwan batace mata ta tafas ba,wanda mummy ta dauka shakka ce tasa haka,har sai data gama sannan tace "Ki kwantar da hankalinki,gobe zan dawo miki da komai da kaina ba saqo ba" tayi zaton zata sameta a falo a zaune,sai kuma taga falon wayam "Su waye sukazo?" "Hajiya shuwa ce da fawwaz,amma suna wajen alhaji" saude ta amsa mata,gabanta yayi mummunar faduwa,me ya kaita wajen daddy kuma?,me taje yi?,a iya tsahon zamansu bata taba haka ba,amma sai zuciyarta ke qoqarin gamsar da ita cewa dubashi suka shiga yi,don haka ta sauya akalarta zuwa parlor din daddyn a sukwane tun kafin hajiya shuwan ta mata wata barnar,tasan halinta sarai,bata barin kota kwana,hakanan koda zatayi asarar wani abu nata muddin zata dauki fansa zata iya aikata komai. Najwa dauke da babban faranti data cika da fruit tabi bayan mummy,wadda batasan tana biye da ita ba,itama bata kirata ba saboda mugun haushinta takeji,saboda tana son kawowa soyayyarta dama plans dinta tarnaqi,don haka taci gaba da bin bayanta har suka shiga falon. Kallo daya ta yiwa daddy kamar yadda shima yayi mata ta fuskanci lallai akwai gagarumar matsala,hakanan kuma komai ya qare Dukka wanda yake cikin motar kuka yake riris,amiru ke driving kaltum na zaune daga gefansa gidan gaba,daga baya kuwa bibi ce riqe da hannun momma,sai samir daga daya side din ruqunqume da ita,zaka zaci cewa zata sake bace masa,kanta na boye cikin qirjinsa saboda haske da ya yiwa idanunta yawa,sakamakon dadewa da tayi bataga hasken rana ba. Hadiyar wani abu kawai yake daga maqoshinsa zuwa cikinsa,idaunsa tamkar garwashin wuta,zuciyarsa na ayyana masa wanne irin hukunci ya kamata ya dauka akan duk wanda keda hannu wajen qarara da rayuwar mahajfiyarsa cikin wannan wajen?,wajen da duk wanda ka ganshi a ciki to dole ce ta kaishi bawai son rai ba?,ya dauko mahaifiyarsa ne cak ya fito da ita daga wajen,ba tare daya tsaya yabi ta ba'asin komai ba,don a yanzu ta tata yake tukunna kafin zuwan komai. Wayarsa daya manta da ita gaba daya cikin motar ta dauki tsuwwa,tafi kusa da amiru saboda tana kusa gear "Sabi'u yana kiranka" baiyi niyyar amsawa ba,amma jin sunan me kiran nasa yasa ya karba wayar ya kara a kunnensa. "Najwa?,najwa kuma?" Shine abinda ya maimaita,bayan sabi'un ya bashi bayanan cewa itace waya ta qarshe da bala yayi da ita bayan ta sanya an tsinke birkinsa dana mahaifinsa,bisa taimakawar fawwaz. "Wuce gida damu" samir ya gayawa amiru a tsawace,kamar wanda ya fara fita a hayyacinsa,yana jin cewa tabbas akwai babban tashin hankali kenan,abinda da farko ba haka ya tsara ba,ya tsara ya wuce da momma din daya daga cikin gidajensa. Dadi ya saukarwa bibi,don dama haka takeso,tanaso taga yadda qaryar jidda zata qare,tana son taga tadda zata kalli momma raihana...... A rikice ta maida dubata ga hajiya shuwa,wadda take binta da kallo tare da murmushin mugunta a fakaice,ganin mummyn ta gaza cewa komai sai kallo da take rarrabawa a tsakaninsu tace "Yauwa.....gwara da Allah yasa ma muka hadu,ga saqonki nan dukka na damqa hannun mijinki" take qafafun mummy jidda suka dauki rawa,wato an samu sabani kenan?. Ta aika yara bayan fitarta su qaddamarwa hajiya shuwa su dauko mata dukkan wasu takardu nata da suka shafeta na sirrinta da take bata ta adana mata,sannan su karbo dukkan wasu kudi da takaddar kadara ta najwa dake hannun fawwaz,ashe ita nan ta nufo kenan?,ko kuma sun sameta tsallakewa tayi?,kamar tasan abinda take tunani sai tace "Ai yaran da kika tura ya karbo miki saqon munyi sabani dasu ne,muna fita daga layin suna shiga......" "DAGE da gaske shine mahaifin najwa?,lecturer mahaifin jawahir?" Daddy ya jefi mummy jidda da tambayar don tabbatarwa da kansa abinda hajiya shuwa ta fada. Yadda tayi wani mugun shock daya sanyata yin taga taga zata fadi saboda girma da nauyin tambayar ya sanya duk wanda ke wajen fahimtar gaskiyar maganar,ciki kuwa harda jawahir da maganar ta sanyata kurumta na wucin gadi,basu kuma fahimci tana wajen ba sai da plate din hannunta ya fadi ya tarwatse da dukkan abinda yake ciki "Qar.....qarya take min,so take taga bayana......qarya take" mummyn ta fada jikinta yana rawa "Da dukka wadan nan shaidun dake hannuna?.....duk da hakan qarya take?!" Daddyn ya qarashe tambayar cikin daka tsawa mai kada hantar mutum,ya wani jirkice zuwa mayunwacin zaki dake farautar dukkan dabbar data gifta ta gabansa. Ja da baya mummyn ta fara yi a tsorace sanda daddyn ya miqe yana tsuma yana nufota,idanunsa a birkice,tunda take bata taba ganinsa cikin siffa irin wannan mai ban tsoro ba,gaba daya ya sauya daga rashid din zuwa wani mutum da zuciyarsa da kuma fuskarsa ke cike taf da bala'i. Cak taga ya tsaya ya tsurawa bayanta idanu ,abinda ya sakata waiwaya itama da hanzari. Tashin hankalin da tayi arangama dashi sai taji yafi wanda ta shigo ta taras cikin dakin,tayi wata muguwar girgixa da razana kamar zuciyarta zata yanko daga qirjinta ta fado qasa. ,sai data gwammace dama bata waiwaya ba,ina ma suman qarya tayi kafin idanunta suga wannan babban bala'in da tashin hanakalin,yau din wacce irin baqar rana ce a gareta?,wanne abu ne yake shirin samunta haka?. Tuni daddy ya miqe tsaye,labbansa suna haduwa suna rabuwa,jikinsa ko ina rawa yake,idanunsa qyam saman fuskar momma,yana son magana amma kowanne furuci ya kasa fita daga labbansa. "Raihana.....ya akayi kika fito?" Kalaman da suka subuce kenan daga bakinta sanda momma raihana ta kafeta da idanu,a zatonta tana zanta hakanne a zuciyarta,batasan cewa maganar ya fito fili ba sai sanda taji bibi na maida mata amsa "Ubangijin da baya barci bare gyangyadi shi yayi ikonsa ya fiddata daga kurkukun da kika jefata ba tare data aikata laifin komai ba"...... Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai sai jin qarar mummy sukayi,dafe da gefan cikinta jini yana bin qafafunta,kafin hankali yakai ga abinda ga sameta cikin qiftawa da bismillah muryar najwa cikin wani mahaukacin sauti ta mamaye wajen "Gwara na kasheki na kuma kashe kaina,gwara na dawwama a gidan prison,da ace wani riqaqqen dan daba talaka shine mahaifina,Allah ya isa tsakanina dake......Allah ya isa,bazan taba yafe miki ba,kin cuceni daya zama ba daddy ne ubana,gwara na kasheki....." Ta fada tana daga wuqar hannunta,wadda ta daukota ne cikin fruits din data kawowa su hajiya shuwa. Babu wanda ya motsa saboda cetar mummy,sai zagaye da suka fara yi a parlor din,duk da jinin dake diban mummyn amma najwa yunqurin binta ta qara mata takeyi. Hajiya qarama ce wadda basusan sanda ta iso ba ta hankade najwan ta fadi gefe "Meye hakan?,kinyi hauka ne?ku dukanku kuna kallonta tana yunqurin kash......"maqalewa maganar tayi a maqoshinta sanda idanunta suka sauka fuskar momma,fuskar data jiqe da hawaye tana bin hafsanta da kallo. "W.....waw.....wa nake gani kamar raihana ta?" Kusan tafi momma kuxari,saboda haka kafin ta qaraso ita ta rigata,suka rungume juna kana suka fashe da wani nannauyan kuka mai ratsa zuciya. Hayaniyar da ta barke cikin falon yasa suka saki juna,najwa ce ta isa ga hajiya shuwa taci kwalarta da kyau,fawwaz na tsaye daga bayanta yana qoqarin rabata da wuyan mahaifiyarsa qarfi da yaji "Munafuka algunguma,ki gaya musu gaskiya,ki gaya musu gaskiya,dama ba qaunata kuke ba?,zuwa kikayi ki rabani da ubana ki manna min wani uban?" Murmushi hajiya shuwa ta saki "Sakeni 'yar nan,yanzu kuwa zan maimaita a gaban kowa saboda su xama shaida" Hankali kwance hajiya shuwa ta maimaita dukkan maganar data gayawa daddy,sulalewa hajiya qarama tayi qas kamar yadda momma ta sulale itama,yayin da samir ya dafe bango jiri na shirin kada shi,kaf cikin zancan ba wanda yake hangowa.....tausayinta keson wasa da numfashinsa irin jawahir, innocent girl......son zuciya yasa mahaifiyarta ta bata mata rayuwa.....ta jirkita mata asali,ya Allah.....yanzu jawahir ba jininsa bace?,ba daddy bane ya haifeta?. Amiru da idanunsa suka kada jazur ya dubi sashen da hajiya jidda take,jini take zubdawa sosai,kuma ci gaba da zamanta a haka dai dai yake da rasa ranta,sai ya hango fuskar jawahir.....mutuwar mummy da mummunan labarin professor rashid ba shine ainihin mahaifinta ba abun zaiyi mata yawa,abinda yasa yayi tattaki kenan ya fita ya kira driver ya taimaka suka kamata zuwa mota "Ko kwana daya baxan iya qarawa da igiyar aurena a kanki ba.....na sakeki saki daya,na sakeki saki biyu,na sakeki saki uku jidda.....daga can idan kin rayu kada ki dawomin gidana,ki jirayi kuma sammaci daga kotu" wadan nan kalaman sune suka yiwa mummy jidda rakiya sanda su amiru suke fita da ita,abinda yasa numfashinta ya qarasa tsaiwa cak daga qirjinta...... Kansa samir ya girgiza,ya zaro wayarsa ya kira jawahir,bayan yayi qoqarin dai daita muryarsa "Kina ina?" "Ya saraki....ina makaranta" "Idan kin fito ki wuce gidan hajiya qarama,gobe da safe da wuri xan turo driver ya kaiki azare wajen yadikko" "Azare kuma yaayaa?" Ta fada a shagwabe cikin mamaki "Eh azare, just say yes" "Yes yaya" ta fada tana dariya,saiya maza ya katse wayar,karon farko hawaye na sulmiyo masa,yasa yatsansa ya dauke,wannan wanne irin son zuciya ne da zaiyi nasarar cusa baqinciki a rayuwar wanda baiji ba bai gani ba?. 61 Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya gidan ya canza ya koma wani iri,tamkar gidan da ake zaman makoki,duk da wani ɓarayi na farinciki da ya samu cikin zukatansu,to amma mummy ta bar musu babban tabo a rayuwarsu. Mummy tana kwance a asibiti,ta samu mummuna yanka wanda ta illata qodarta,najwa na hannun 'yan sanda,saboda asibiti da suka qi amsar mummy lokacin da aka kaita,suka dage kai da fata sai an nemo 'yan sanda,drivern gidan professor da yaga zai shiga ciki bayan bashi yayi aika aika ba yayi musu bayanin komai,take suka garzaya,suka kuma damqe najwa sukayi ram da ita,baiwar Allah jawahir na azare tana ta tambayar kanta abinda ya faru amma bataji komai ba hakanan bata ga komai ba,don haka sai tadan kwantar da hankalinta,sukaci gaba da zama da tsohuwa yadikko tana kula da ita da ciwon suger dinta daya tashi,ta ta'allaqa zuwan nata ma da ciwon nata da ya motsa. Ta gefen dadday gaba daya tunda al'amarin ya faru yana dakinsa ya kulle kansa,babu wanda yake bari ya shiga kamar yadda shima baya fitowa,yayi kuka yayi kuka har baisan adadinsa,yayi nadamar da yace baiga amfaninta ba,yaji gaba daua siyasa ta fice masa fit a ka,ya tabbatar abinda ya sake kawo wannan matsalolin da gidansa ya fuskanta shine rashin samun wadataccen lokacin zama da iyalinsa da ya fara samu sanadin siyasa,ya tuna yadda rayuwar gidansa take a baya,ya tuna irin soyayya qauna da kulawa da yake samu daga raihana,yayi kukan da tunda mahaifiyarsa ta haifeshi bai taba irinsa ba,har sai da idanunsa suka soma rauni. yayin da saraki ya duqufa wajen ganin an duba lafiyar mommansa an tabbatar da ingancinta. Cikin hikima da isa irin ta ubangiji treatment kadam take da buqata,sai kuma idanunta da ya samu raunin gani saboda zama a duhu data jima tana yi,so ko yaya ta shiga haske sai yayita damunta,wannan dalilin ya sanya aka yi mata glass da zata dinga amfaji dashi sanda zafa fita ga haske har zuwa sanda ganinta zai dai daita. Sai da yaga yadda jikinta ya fara kyau,ta fara dawowa cikin hayyacinta sannan ya karkata zuwa ga gyaran dukkan abubuwan da suka wakana. Da farko bai sanya an kama bala ba,saboda bisa dukkan binciken da yayi ya tabbatar masa da cewa tursasashi akayi ya aikata abinda yayi din,saidai kuma ta yaya zaka yarda kaci amanar mutumin daka jima kana aiki qarqashinsa yana hidimta maka?,wannan shike nuna babu aminta ko kadan tattare dashi,wannan dalilin yasa ya sallami bala daga bakin aiki,abunda ya sanyashi cikin tashin hankali da baqinciki me yawa,haka nan ya kori fawwwaz shima,sa'an nan yana jiran samun lafiyar mummy ya hada ita da hajiya shuwa ya shigar da qara akansu,saboda lallai ba shakka akwai abinda yasa hajiya shuwa yin wannab tonon sililin,ya tabbatar ba banza ba,da ita kuma da mummy shi a wajensa dukka masu laifi ne,laifinsu daya. Abu na gaba ya sanya an tattarewa mummy dukka wasu kaya da suka shafeta an kai Warehouse na kamfaninsa an jibge,bayan ya samu Tex daga daddyn kan ya aiwatar da hakan,saidai abu daya ya kasa tabawa ya kuma kasa magana akai shine najwa,sosai jikinsa ke sanyi idan ya tuna waye mahaifinta?,meta aikata?,don jawahir ko sama da qasa zasu hadu baya jin zai bari sunanta ko rayuwarta su baci,kuma bayajin zai bari ta kufce daga hannunsa ko a cire mata sunan 'yar uwa kuma autarsu,saidai kuma ta yaya zai binne abun?,bayan idan ta dawo zata tambayi mahaifiyarta da 'yaruwarta?,ba shakka yaqi ne babba a gabansu. Baiyi qasa a gwiwa ba wajen sawa a cafko dukka ma'aikatan da mummy tayi amfani dasu wajen tsarewa da cutar da momma,daga nan aka miqa su kotu aka kuma fara shari'a dasu,bayan ya dora umar kan case din,cikin qaramin lokaci saiga batun ya yadu,cikin manyan shafukan jarida,labarai na gidan radio da television,kafofin sada zumunta,ko ina ka leqa zancan ake tattaunawa "MATAR BABBAN SIYASA KUMA DAN KASUWA PROFESSOR RASHID AZARE TA BAYYANA A GIDAN MASU TABIN HANKALI,BAYAN DA ABOKIYAR ZAMANTA KUMA 'YAR AIKINTA DATA AURE MATA MIJI TAYI MATA QULUMBOTO TA BADDA ITA TSAHON SHEKARU ASHIRIN DA DORIYA SABODA KISHI KAWAI" topic ne daya dauki hankula matuqa da gaske,aka dinga tattaunashi ana yamadidi dashi. Koda batun yakai kunnen samir sai yaji dadi da ya karbi wayar jawahir babbar ya hadata da keypad kan zai sauya mata wata,gidan yadikko kuwa ba wani kallo ta cikayi ba,yasan ba lallai labarin yakai kunneta ba,idan ba takanas wani zaiyi ya gaya mata ba. Cikin qanqanin lokaci al'umma da dangi makusanta suka fara tururuwar zuwa yiwa momma barka da fitowa da kuma jajen abinda ya faru,abinda ya sanya samir ya bada umarnin duk wanda yazo ace momma din bata gidan,badon komai ba,sai don yana buqatar ta samu hutun daya dace,ta sake komawa hayyacinta,don har a sannan tana samun kulawar lafiya daga wajen qwararren likita da samir din yayo haya takanas aka ware daki guda ya zuba duk abinda ya kamata kamar dakin asibiti yake kula da ita. Cikon sati na uku momma ta fara komawa nutsuwarta,da taimakon bibi da kuma kaltum da take qoqari wajen girka dukka kalar abincin da tasan zai maida ma momman lafiyarta cikin sauri,takan dafa mata dawa kamar shinkafa,tasa mata manja da gishiri,kuma momm din bata qi,tana amsa taci,hakan tasa qashinta ya fara samun qwari nan da nan,kuzarinta ya dawo,abinda zai baka mamaki,tamkar ba itace ta rayu tsahon wannan lokacin tana azabtuwa a rufe ba,saidai idan kayi duba da kasancewarta mace mai tsananun ruqo da ibada tun da can ba abun mamaki bane,to sai kuma zamanta a wancan wajen ya sake sawa ta kusanta kanta da Allah sosai,yawan ambaton Allahnta yafi na baya kafin wannan musibar ta sameta,lalllai ba shakka ambaton Allah kat ne!,dashi kadai kuma zukata suke samun nutsuwa. Amiru shine ya ankarar da samir rashin fitowar daddy kwata kwata,sanda yaje gareshi ba yadda baiyi ya fito din ba amma daddyn yace yayi tafiyarsa,ya shiga damuwa samir,saboda yasan abinda daddyn ke dubawa da abinda ke damunsa,saidai yadda ya roqeshin ya tafin hakanan ya tafin kamar yadda ya buqata. Wata sabuwa......sanda yake gayawa momma matakin da daddyn ya daukarwa kansa saita kauda kai "Ka rabu dashi,qila wannan shine abinda yafi dacewa da shi,saidai a gobe inason ka hadani dashi,ina buqatar takardar sakina,don inason nan da rana ita yau na wuce gaban dangina,wadanda basu da labarin fitowa ta" kai samir ya daga,fuskarsa cike fal da damuwa gami da tarin fargaba,da gaske momma take tafiya zata sakeyi a karo na biyu ta barsu?,idan ta tafin to ya zasuyi su rayu?,waye zai zauna dasu?,wacce rayuwa daddyn zai fuskanta a nan gaba?. "Momma....idan kika tafi kuma?....." Hannu ta daga masa "Bance kace komai ba" sai yayi shuru yana sadda kansa,kafin ya miqe a hankali,yana jin maqogoransa a bushe,don haka yayi hanyar kitchen don ya samu ruwan da xai sanya masa ko xai dawo dai dai. Tarin ganyayyaki ne gefe guda a kitchen din,wanda dukka tayi amfani dasu,wasu cikin girkin da a yanzu takewa momma din,wasu kuma ta zuba cikun kunun ganye data kammala ta sauke,tana ta kiciniyar bude flask don xubawa a ciki kada ya huce. Daga bakin qofar kitchen din ya dakata,duk kuwa da tarin qishirwar daya kwaso,ya zuba mata idanu yadda taketa bata fuska da yarfa hannu saboda yadda murfin flask din yayi mata tauri yaqi buduwa,sake gwadawa tayi still yaqi,sai ta sake yamutsa fuska taja ta zauna kan kujerar plastic din dake kitchen din tana tura baki,kamar wani ne yayi mata laifin. Idanunsa ya lumshe a hankali,murmushin da baiyi zato ba ya kufce masa,yana jin wata qauna da soyayyarta mai qarfi tana zarmewa gami da kwarara cikin zuciyarsa,tana hawa kuma wani mataki da matsayi mafi qololuwar daraja cikin ransa,matsayin da mahaifiyarsa kadai yakejin ta wuce nan. Bai taba zato ku tunanin yarinyar tana da dakiyar da zata aikata abinda ta aikata din ba,bai taba kawowa tsayayyar zuciyarta takai haka ba,abu mafi burgewa tattare da ita tausayi da imani irin nata,da son tsage gaskiya komai dacinta.....wanda dama wannan halayyarta ce tun dadewa. Sake dubanta yayi,ta dan fada ita kanta,tunda momma ta shigo gidan bata huta ba itama,bayan ta gama dawainiya da lalurar daddy,shikam a duniya me zaiyi mata ya saka mata?,bayan tsaftatacciyar soyayyarsa da yakejin kaf duniya babu matar data cancanci ta mallaketa irin ita?,UMMANTA ta fado masa a rai,dukka jiki da zuciyarsa sun masa amannar cewa za'a samar da mace kuma uwa ta gari a wajen,haqiqa ta canci dukkan wata soyayya da qauna gami da kulawa. Hannayensa ya sauke ya saka kai zuwa cikin kitchen din ahankali,idanunsa na akanta,cinyoyinta sun fito sosai ta cikin wandon rigar baccin jikinta,hakan ya bawa hips dinta damae fitowa sosai,sai ya maida hankalinsa ga qirjinta,wajen da akoda yaushe yake tsole masa ido . Sun fita sosai sun kuma tsaya car a jikinta,hakan ya sake baiwa structure na jikinta fita,yabi santala santala hannayenta da a baya suka cika sirantaka,wanda a yanzu sun cika sosai. Gab da zai isa gareta ta miqe,ta dan qara gaba kadan zuwa gaban famfo ta tara,ta kunna ta tara saman flask din,wai ko saukar ruwan zai sa flask din ya saki ta samu damar budeshi. Ba zato taji an kama dukka qugunta an riqe,amma sai qamshin turarensa ya bata amsar waye,take jikinta ya amsa gaba daya sanda yake sake matso da ita cikin jikinsa,rungumeta yayi sosai sannan ya miqa dogayen hannuwansa ya gefe da gefanta ya jawo flask din yaa bude mata shi,ya daurayeshi sosai sannan ya ajjiye a gabanta "Gashi nan,me aka dafa mana ne?,saboda rowa gaba daya mu ba'a taba yi mana tayi ba ko?" "Subhanallah" ta fada cikin zuciyarta tana qanqame jikinta waje daya,saboda yayi maganar cikin kunneta,hucin numfashinsa da na bakinsa wanda ke bada qamshin mint ya shige kunnenta,ya tada duk wata tsiga ta jikinta,yayin da shi kuma yaci gaba da sansanar wuyanta,sassanyan qamshin turaren data shafa daren jiya na shiga hancinsa,yana aikawa da wani rikitaccen saqo zuwa qwaqwalwarsa,a nutse ya shinfide tafukan hannayensa saman mararta,idanunsa a rufe yana ci gaba da sansanar wuyanta zuwa gashinta dake qamshin man kitson da tayi oiling dashi. Idanunta ta mayar ta lumshe itama,saboda yadda gaba daya kowacce gaba ta jikinta lakarta ke mutuwa,ta dora hannuwanta saman nashi hannun tana son zamesu daga mararta,saboda yadda ya tsayar qara gudun zuciyarta "Karki cire......baki qara wani period din ba?" Ya tambayeta muryarsa qasan maqoshi,kamar wanda ke mata rada,fitar furucin ya qara rudata,saita girgixa masa kai da sauri alamun a'ah "But....me yasa baki gaya min ba sanda ya dawo?,ko baki shirya karbata a matsayin mijinki ba?" Gaba daya ya sake rudata dajin abinda ya fada din,miji?,ita a yanzu har isarta takai yayi matar aure da ita?,kamar yasan me take tunani,saiya saketa,yaja baya kadan,sannan ya juyo da ita tana fuskantarshi,ya zuba mata idanu da birkitattun idanuwansa da suka sauya launu,tun tun tuntuni......baisan wane baiwa ne da ita haka ba,da yakan samu kansa cikin burkicewa duk sanda jikkunansu xasu hadu waje guda,ko don bai saba hakan ba sai a kanta?. Dukka tafukan hannayensa biyu ya saka a kuncinta na dama dana hagu,ya dago fuskarta sosai ta yadda zai iya kallon qwayar idanunta "Bansan ke alheri bace a rayuwata sai a yanzu,ban kuma sani ba.....ko zai iya karbar wannan samir din a matsayin mijinki?" Idanunta ta runtse,tambayar tayi mata tsauri sosai,yana kasheta ne da wannan tsaiwar tasa cikin jikinta ba tare daya sani ba,muryarsa kadai matuqar dab da ita take hautsina mata tunani take,tasa ta manta abinda takeyi "Bansan wanne irin tukuici kike da buqata daga wajena ba" "Ka kaini gida,inason naga ummata" ta samu kanta da fada,hawaye kuma ya biyo bayan maganar tata. Kai ya fara girgizawa "No....no, stop it please" ya fada yana sanya yatsansa yana dauke mata hawayen saman fuskar tata,ido ya tsura mata sosai yana kallon zanen fuskarta,komai yana zaune bisa muhallinsa bisa tsari da halitta me kyau,wannan shine kallo mafi kurkusa daya taba yiwa kaltum din,dan madaidaicin bakinta idanunsa yakai kai,ya zarto da hannunsa wajen zuwa daidai hancinta,ya dora yatsansa guda biyu ya soma zagaye tattausan lips dinta. Da hanzari ta qwace fuskarta ta hanyar ja da baya saboda jin wani shock da tayi kamar an jata,tun daga yatsun qafarta har zuwa qwaqwalwarta,sai ya harde hannayensa yana fidda murmushi yadda ta juya baya ta kasa hada ido dashi,idanunta na nuna zallar kunyarsa data kamata. Qarasawa yayi inda flask din yake ya dauko ya biyota dashi,ya ajiye kusa da ita yana cewa "Zan dauki lokaci me tsaho ina koya miki yadda zaki rayu dani,babu abinda kika sani dangane dani illa kamannin fuskata......a yau na shiryawa shaidawa dukkan wanda ya kamata cewa KE MATATA CE" Haka kawai taji gabanta yayi mugun bugawa,tsoro ya kamata,saita daga fararen idaunta ta kalleshi kafin ta janyesu,ta koma qoqarin sauke tukunyar kunu. Duk sanda ta kalleshi da fararen idanun nan nata yakanji wani abu ya tsarga masa,ba tun yau ba,ba tun wannan lokacin ba....yakejin hakan,kusan tun ganin farko da yayi mata,ya manta rabon da yaga mace mai fararen idanu kar haka irin nata,sai ya dauka wannan banbancin ne. "Bakya sona ne?,ko ban miki ba?" Ya fada yana ware hannayensa gaba daya bayan ya zagayo gabanta ya tsaya,a sace ta kalleshi ta dauke kai,cikin ranta tana fadin,komai kyau isa mulki dukiya ko nasabar mace,bata isa ta kalli samir yace baiyi mata ba.....indai ba irin mazan aljanna takeso a kawo mata duniya ba "Kalleni sosai....." Ya fada yana sake matsota,sai tayi saurin ja da baya,sannan ta take ta fice daga kitchen din da gaggawa,don tabbas ta bari yaci gaba da hada jikinsa da nata.....batasan iya yadda adadin sonsa zaikai cikin zuciyarta ba. ******Qarfe bakwai na dare ne,cikin shigar laffaya mai azabar kyau butter colour ta nannade jikinta,kamar yadda take kusan rabin shigarta kenan a shekarun baya tun duniya tana kwance. Samir ne ya sake knocking qofar,wanda cikim jagulewar rai da zuciya dama yayo rakiyar,don kawai bazai iya saba umarnin momman tasa ba. Karo na kusan biyar ya sake bugawa kafin ya iya jiyo maganar daddyn can qasa "Waye?" "Samir ne....momma keson magana da kai" daga nan inda yake tsaye,yana iya jiyo qarar saukowarsa da qarfi,da alama amsar da samir din ya bashi tayi masa ba zata,ba'a kuma cika minti daya ba qofar ta bude,karo na farko tun bayan satittikan da suka shude daya rufe da kansa. Kallo daya samir yayi masa tausayinsa ya sauko masa,gaba daya ya hada wata qasumba a fuskarsa da kansa,wadda ta cika da furfura,ramar da yayi ta bayyana har saman fuskarsa,wasu qashi dukka sun bayyanar masa. Idanunsa nakan momma din a sanda ya bude qofar,sannan ya matsa yana basu damar shigowa. Samir yana iya ganin yadda ya saka wani qyalle yana kadewa momma kujerar tare da gaya mata ta zauna,saidai a maimakon hakan saita koma can wani waje nesa kadan ta jingina,fuskarta kuma babu alamun annuri ko fara'a ta fara magana "Na riga dana hada kayana,inason komawa qasata cikin dangina,nazo ne domin karbar shaidar sakina.....saboda al'adarmu saikin nuna ta koda wani auren naki na gaba zai taso,ina fatan ba zamu tsawaita magana ko bata lokaci ba" sosai tashin hankali ya bayyana kan daddyn,sai samir ya kauda kansa,saboda tausayin daddyn nasa,ya dade da yi.masa uzuri,saboda yasan dukkan abinda ya faru MAKIRCI DA KISSA ne sukayi aikinsu,mummunar kissa abar qyamata. Muryar daddyn a dakushe ya fara magana "Raihana....kiyimin rai don Allah......karki ce zaki tafi ki barni,kunyar ki da kunyar yadda zan tunkareki ya sanya na kulle kaina tsahon wadan nan kwanakin,saboda bani da wani abu da zan gaya miki wanda zan wanke kaina,nasan cewa na rusa dukkan wata yarda da aminci dake tsakaninmu" "Kayi haquri na roqeka nima,komai da ka yimin na yafe maka albarkacin danka,amma a yanzu ina buqatar shaida ta,saboda inason na koma qasata cikin ahalina na qarasa rayuwata" "Har yanzu da aurena a kanki raihana......saboda bayan na rubuta saki guda daya......munyi rigima sosai da hafsa a sannan duk da ba'a ganki ba bakya nan,ganin yadda ran hafsa ya baci sai nace na maidaki,kuma daga ranar har kawo yau a yanzun ban janye ba......saidai in sake jadda miki cewa ke matata ce,hafsa itace shaidata" Wani nannauyan numfashi samir ya sauke,yanajin wani sanyi yana ratsa zuciyarsa,saidai cikin lokaci kadan momma ta kafe kan batasan wannan ba,don haka samir ya zare jikinsa daga dakin,bai kuma tsaya ako ina ba sai dakin hajiya qarama. Baiyi qasa a gwiwa ba ya gaya mata abinda ke faruwa a sashen daddyn,daquwa ta watsa masa "Don qaniyarka me yasa zaka rakatan?,me yasa baka zo ka sameni ba tukunna" kanshi ya shafa,yadda yaga hajiya qaraman ta miqe cikin gaggawa yasan komai zai dai daita,mayafinta taja kuwa ta fice,shi kuma ya koma ya zauna cikin kujerun dake dakin yana sauraron dawowarta. Kusa awa guda hajiya qaraman ta sake dawowa,da alama ansha fama ansha gwagwarmaya,saidai yanayin fuskarta kawai ya tabbatar masa komai ya dai daita "Kaje yaya yanason ganinka" tsam ya miqe yabi bayanta har zuwa sashen daddyn. Kallo daya yayi musu dariya taso kubce masa,fuskar daddyn wasai ,saidai momma da har yanzu a cunkushe take,fuskarta na nuna fushi,amma kuma idan kayi mata kallon tsanaki zakasan cewa fushi ne akeyi irin na masoya. Gaban daddyn ya qarasa ya duqa "Gani daddy" gyara zamansa yayi sosai yana kallonsa "Samir....inason in sake neman afuwarku ne gaba daya kan dukkan wani abu da ya faru" "Daddy.....kasa a ranka nidai a wajena.....kamar komai bai faru ba......saidai.....inason dukkaninku kuyimin afuwa,saboda na aikata wani babban kuskure watanni masu yawa da suka shude,kuma na kasa gayawa kowa a cikinku" dif sukayi,kowa yana dubansa,kowa kuma da abinda zucuyarsa take ayyana masa,aka rasa me magana,sai daddy "Na yadda dakai samir,kome zaka aikata ina da kyakkyawan fatan da zaton bazai zama mai munin da zai cutar da al'umma addini ko mutuncinka ba,kada kaji komai,sanar dani" zama yayi sosai,cikin nutsuwa ya shiga shaida musu dukkan abinda ya faru,tun daga lokacin da ya fara sanin bilal,rayuwar kaltum har zuwa yadda auren ya dauru. "Alhamdulillah" hajiya qarama ta furta tare da wata ajiyar zuciya mai qarfi "Mun godewa Allah da ya sanya iya haka ce ta faru.....hankalina har ya kwanta" to ga momma da daddy ma kusan abinda ya faru kenan,saboda ya sanya kowa a cikin taraddadi,saidai amsar daddy ta sake kwantar masa da hankali "koda kaltum bata zauna damu ba....koda ita ke da buqatar ta aureka tabbas zamu aura mata kai.....barema tun zuwanta.....babu wanda bai yaba da dabi'u da halayenta ba" "Banajin a duniya akwai yarinyar da zanso banda kai bayan ita" amsar da ta fito daga bakin momma kenan,sai ya runtse idanu yana tasbihi ga ubangijinsa,lallai duk wanda ya nufaci ubangiji wajen aikata wani aiki.....to babu makawa zai shige masa gaba,zai share masa hawayensa,hakanan duk wanda yaji tsoron Allah xai samar masa mafita......zai kuma azurtashi ta inda baya zato. 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *_DA ZAFINSU_* *_A TSARE SUKE_* *_SUN TANADESU_* *_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_* *_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_* *_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_* *_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_* _WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_ 08184017082 _MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_ 09134848107 *_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_* 62 *10:48* Yana tsaye gaba mudubi yana sharce ruwan kansa,yana kuma kallon kansa a madubin,sosai fuskarsa ta wadatu da murmushi,musamman idan ya tuna abubuwan da suka faru a wunin yau din,gaba daya dukkan wata matsala tasa ta warware cikin ikon Allah,abinda ya rage masa a yanzu kawai shine yadda zaiyi da jawahir ya badda mummunan labari a kanta,don ko shari'ar gidan masu tabin hankali a dazu da safe aka qareta,kyauro da sauran mutum uku da suka taimaka masa wajen ajiyar momma na wadan nan shekarun,an yanke musu hukuncin daurin rai da rai. Sake murmusawa yayi da ya tuna yadda hajiya qarama ta tubure haiqan da gaskiya aka baro momma sashen daddy,duk da kuwa itama tuburewar da taso yi,saidai rigimar hafsatun tata tafi tata girma. A yau komai ya kawo qarshe,ya tabbata kaltum ta zama tasa,wadanda ya kamata su sani sun riga da sun sani,sun karba su lamunce masa,iya wannan kadai idan ya tuna yana sanyashi nishadi. Da fari tausayin kaltum ya fara,bai sani ba so ashe yana farawa daga tausayi,ya fara sonta ne ba tare da yasan sonta yake ba,ya aza cewa tausayinta da tausayin rayuwar da suke ciki yake yi,da kuma sabo da sukayi da da uwanta bilal. Ja da baya yayi,hakanan yaji a daren nan gangar jikinsa tana buqatar jin duminta,sai ya bude ma'ajiyar kayansa,wadda taci cupboard guda,ya lalubo wasu pyjamas farare qal masu budadden qirji ya sanya,ya feshi jikinsa da lallausan turarensa na bacci,sanna ya zura wasu slippers na fata ya dauki wayarsa ya baro sashen. A hankali ya tura qofar dakin nata,babu haske kwata kwata sia qamshin dake tashi,da alama ta jima da kwanciya,don lokacin da ya kunna fitilar wayarshi ya hangeta ne duqunqune cikin bargo,kyakkyawar fuskarta ta haska tarwai cikin milk din duvet din da take ciki,sai ya maida qofar,ya taka har zuwa bakin gadon. Da qaramin haske yayi amfani ya kalli fuskarta son ranshi,murmushi kwance saman fuskar tasa,saboda tunawa da wasu abubuwa daya dinga yi a kanta,wamcan lokacin da ya fara ganinta,cikin qauyensu,a yanzun sai yake ganin kamar ba ita ba,komai dake tattare da ita ya canza. Jan bargon yayi a hankali ya sauko zuwa saman cikinta,ta sake bayyana sosai cikin kayan baccin da suka kwantawa fatarta,sai ya kasa daurewa,ya raba ta bayanta ya kwanta a jikinta tare da sake jawota cikin jikinsa sosai yana sauke numfashi,abinda ya farkar da ita kenan a tsorace "Shshshsh..... mijinki ne, keep calm sai tayi shuru tana sauraren bugun zuciyarss dake fita da sauri da sauri. A hankali ya zura hannunsa saman fatar cikinta ta qasan rigarta,ya fara yawo dashi,abinda yaso tafiya da numfashinta kenan,ya kuma qara bugun zuciyarta,saita riqe hannun nasa jin yana son zarcewa zuwa sama,bayan ta tabbatar babu bra a jikinta,da ya gota din kuwa tasan koma meye zayaji shi. Cikin kasala ya girgiza kansa "No....dan kadan please....nima na dana,karki hanani,nafa yi qoqari,ba wani abu bane me yawa.... please" ga tsoro ga kunya,saidai cikij wani salo dake nuna qwarewa a iya tafiyar da tattausar soyayya mai narkar da xukata,ya dinga karantar da ita wasu darussa masu wuyar mantawa,ya kaita duniyoyi da babu komai cikinsu face zallar farinciki da masoya ke tsinta a cikinsa,sunyi musayar kalamai,yadda ya fallasa a sirin zuciyarsa a gareta,hakanan bai qyaleta ba itama sai da ta fidda masa dukkan wani sirri dake ranta,ya jita a jiki da zuciyarsa sosai a ranar,da quar ya iya qyaleta bau zarme ba zuwa next level ba,saidai kuma ya qare da ciwon mara sosai,wanda bai sakeshi ba sai gab da asuba. Tunda ya fito daga wanka yake son su hada ido amma taqi,sbaoda wani nauyinsa da ya dora mata,ya kaita makarantar da bata taba leqawa ba,saidai ta samu tarin karatu da ilimi,ya kuma sake loda mata soyayyarsa ninkin baninkin. Allah Allah take kawai ya fice daga dakin,kada wani cikin jama'ar gidan ya ganshi ya gane a nan ya kwana,amma sai ta lura shi kam ko a jikinsa,sabgarsa yake hankalinsa kwance "Ki daura alwala muyi sallah" ya fada yana shimfida abun salla tare da cije dariyarsa,saboda yana son yaga qarshen pretending dinta. Baki tadan turo gaba,ta tsammaci xai fita ne ya barta,saboda maganar Allah tana kunya yaga tayi wanka a gabansa. Daga kai yayi yana dubanta,sai tayi maza ra runtse idanunta,ya saki lallausan murmushin nan nasa,sai ya miqe daga sunkuyon da yayi,ya soma takawa zuwa inda take zaune ta nade dukka jikinta da duvet,saboda yadda ya yamutsa gaba daya kayanta. Dan zabura tayi sanda ta jishi gab da ita,a dole ta juyo ta fuskanceshi,gashinta daya gama yamutsewa ya rufe fiye da rabin fuskarta "Don Allah.....zan tashi,amma kaje......momma fa?" Murmushi ya sake,tana qara yi masa kyau,sai yakai hannunsa a hankali yana janye gashin nata zuwa baya,hakan ya baiwa fuskarta damar bayyana sosai,yakai idanunsa kan lips dinta wadanda suka danyi ja,yasan kuma hakan xafa faru,saboda ya tsotsesu son ransa "Momma ma wajen daddy ta kwana,so kada ki wani damu.....ya kamata ki cire wannan kunyar kwata kwata idan kina tare dani,ni mijinki ne kamar yadda kike matata,halal muke ga juna,amma ban sani ba,ko sai ni da kaina na qarasa cire miki ita gaba daya a wuce wajen ne?" Yayi maganar yana sake matsota,abinda yasa taja baya da sauri,ba shire ta sauka daga gadon sai bandaki. Bin bayanta yayi da kallo kamar wani zautacce,sai kuma murmushi ya subuce masa,yasa hannu saman kansa yana shafa sumarsa,idanunsa a lumshe yana tuna daren jiya,yana kuma jin yadda alwalarsa ke karyewa,saiya daura sabuwa kenan. Tun bayan futarsa ya barta kwance cikin bargo bacci ya qauracewa idanunta,kamar yadda murmushi yaqi barin fuskarta,ashe haka soyayyar miji da mata take da dadi da kuma gardi?,duk inda ta juya a kaf fadin gadon qamshinsa ke tashi,ta rasa da wanne irin maye turare yake amfani,ya tafi ya bar mata qamshinsa,tasan kuma shine zai hanata sakewa. Ajiyan ya dasa abubuwa masu matuqar qarfi cikin zuciyarta,saidai wasu guraren a jikinta radadi suke mata,saboda saqonnin data karba masu zafin gaske daga wajen sarakin,ashe a baya yadda take jinsa a ranta wasa ne farin girki inji hausawa. Gyara kwanciyarta ta sakeyi a karo na barkatai,saidai saukar sautin kuka daga can waje ya sanyata tsaiwa cak,kafin ta samu kanta tana dirowa daga gadon ba tare data shirya ba,bata tsaya neman dankwali ko hijabi ba,daga ita sai doguwar rigar atamafar da sarakin ne ya zabo mata ita kafin ya fita tayo waje,saboda muryar jawahir takeji. Kafin ta isa har samir hajiya qarama da momma sun rigata isa wajen,sai securities su biyu dake tsaye a can bakin qofa,daga gefe kuma yadikko ce da amiru. Momma da hajiya qarama ke riqe jawahir din,wani irin kuka take mai ban tausayi,tana sulalewa qasa suna dagota,jiki da qafafuwan kaltum sukayi sanyi,hawaye ya balle mata,bisa dukkan alamu labari yaje kunnnesu,dama kuma zancan duniya baya buya,duk kuwa yadda kakai ga son boyeshi,sai ta kasa tsaiwa,ta nufi jawahir din da hanzari,tana ganinta itama ta nufota suka rungume juna,suka sake sakin sabon kuka. Samir ne ya qaraso wajen a hankali ya rabasu,sannan ya kama hannun kaltum,zai kama na jawahir ya tuna a yanzun haramunne aikata hakan,sa ya yiwa hajiya qarama alama da ido,ta kamo jawahir din suka nufi falon gidan gaba daya,banda securities da sukaci gaba da kula da gidan. Sun jima zaune cikin falon wanda yake shuru,bakajin sautin komai sai na kukan jawahir,babu wanda ya hanata kuka kamar yadda babu wanda ya hanata fadar dukkan abinda ke ranta,kalamai ne da suka sanya kowa kuka a wajen sosai,har da daddy da ya fito daga baya "Ashe ni din ba kowa bace face wulaqantacciya wadda ta fito ta qazamar hanya,ashe bani da wani cikakken asali?,ashe ni da najwa ba mahaifinmu daya ba?,ashe ya saraki bamu hada alaqar komai dashi ba?,me yasa mommy bata tsaya ta haifemu wajen nagartaccen mutum irin daddy ba?,me yasa ta yiwa Allah shishshigi?,bata tsaya mun fito ta tsatson daddy ba?,tayi gaggawa taje ta haifemu daga wani tsatson na daban?,yanzu ace har bushewar zuciyar ya najwa yakai ta cakawa mahaifiyarta wuqa?,wannan wanne irin bala'i ne?" Sosai tausayinta ya cika zuciyar momma,ta matsa kusa da ita ta rungumeta sosai cikin jikinta,tana bata kalamai na ban haquri da yarda da qaddara "Ni din ki daukeni tamkar mahaifiyarki,daddynku kuma har abada daddynku ne,babu me canza muku wannan" cike da mamaki ta daga ka daga jikin momma din ta dubeta "Yanzu bayan dukka abinda mummy tayi miki har zaku iya ci gaba da riqeni?" Murmushi momma tayi,tausayin yarinyar na sake ratsata,saboda ta tabbatar nagartacciya ce saboda yadda kowa ke yabonta,tare da kaffa kaffar kada taji al'amarin "Qwarai kuwa,ke din diyarmu ce halak malak" saita sake fashewa da kuka,wanda daga baya ta sassauta saboda kalaman ban baki data dinga samu daga wajen kowa,kukanta ya koma ajiyar zuciya. A sannan samir ya miqa hannunsa ya matsa hannuwan kaltum,tadan dubeshi kadan,qasa qasa yace da ita "Ya isa....kukan ya isa haka,ki adanashi,kada ki rasa na first night" kamar qasa ta tsage ta shige haka taji. Ido suka hada da amiru,sai ya sakar masa wani kallon tsokana,dauke kansa yayi bayan ya maida masa da harara "Idan kina fitowa irin haka,zuciyata zata iya bugawa" da sauri ta daga kai ta kalleshi,saiya wara mata idanunsa sosai yana gyada kai alamun tabbatar mata "U have no idea how much I love you.....but the time will reveal,jeki nemo hijabi" abinda ya sanyata miqewa a kunyace zuwa daki,sai ya dubi jawahir "Auta bita kuje,karki sake kuka,ki dauka kamar komai bai taba faruwa ba" "To" ta amsa a matuqar karye "Promise?" Ya sake cewa da ita,saita gyada kai tana qoqarin maida qwallarta,fuska yadan bata "No,ki bude baki ki amsa min" murmushi ne ya taho mata mai hade da hawaye,har yanzu da gaske yana nan a matsayin yaya sarakinta,babu abinda ya canza "Yes yaayaaa" ta amsa masa da yanayin da aca baya take amsa masa,abinda ya taba zukatansu gaba daya "Good girl" ya fada yana qoqarin boye rauninsa,suka bita da kallo gaba daya sanda take tafiya zuwa dakin kaltum. A nutse ya faka motarsa a harabar asibitin,wanda suka dauko jawahir da dukkansu sukayi amannar taje taga mahaifiyarta,shi da kaltum ne zaune a gaban,yayin da amiru da jawahir din suke baya. Sai da yakashe motar sannan ya waiwaya yada dubeta "Duk abinda ta aikata miki mahaifiyarki ce,she need your respect,sannan idan kika shiga kika zauna kina kuka?,ki tabbatar bazan sake barinki zuwa ba, understand?" Kai ta jinjina tana boye qwallarta "Ok" ya fada,abinda yasa amiru bude side dinshi ya fito,itama jawahir din haka. Caraf ya kama hannun kaltum itama dake qoqarin bude nata side ta fita,ya manne tafukan hannuwan nasu waje guda,dumin jikin kowannensu yana ratsa jikin dan uwansa "Ina zaki madam?" "Zan raka jawahir" wani narke mata yayi,tamkar dan yaye "Haba madam.....wannan wata dama ce fa,da mun koma gida shikenan za'a sanya mana ido,don naji hajiya qarama daxun ta fara wasu maganganu....." Qasa yayi da muryarsa "Please,abun jiya za'a dan sanmu na qara ɗanawa" idanu ta fitar waje gaba daya,amma ganin yadda ya tsareta da nasa idanun masu tsananin kaifi saita sauke nata qasa "A waje muke fa" tana rufe baki taga motar ta soma duhu,saita daga kai da sauri,ashe danne madagar gilasan motar yayi gaba daya,saidai bai juya ba still ya tsareta da idanuwa ne,gilasan kuma sunayin sama har suka gama rufewa ruffff. "Yanzu fa?" Ya jefe mata tambayar yana sake jifanta da wani tsumammen kallo,saidai kafin takai ga bashi amsa ma tuni ya hade tazarar dake tsakaninsu. Da zafi zafi yaji ana knocking glass din motar,ya zare jikinsa a galabaice yana duban wanda ke bugun glass din,amiru ne,bai sauke ba sai daya tabbatar ta gyara daurin da kwalinta,ya gyara xaman rigar jikinsa,sannan ya dauki ruwan dake ajjiye kusa dasu ya bude ya kafa kai ya fara kwankwada,zuwa sannan amirun harya qagauta,ya zagayo ta gaban glass din motar yana duban samir,wanda baiyo ko darr ba sai daya gama shan iya yadda zai iya ya miqawa kaltum sauran sannan ya sauke glass din "Kaima fa dan iska ne da alama inda ka samu waje....ka fito mummy nason ganinka urgently, she's in serious condition,da gaske nake,jawahir ta kasa riqe kukanta,ni kaina na kasa controlling nata please......" Da sauri ya buda murfin motar ya fito,sannan ya zagaya ya budewa kaltum,ya riqeta sosai cikin hannunsa suka fara takawa zuwa cikin asibitin,kome zaiyi zaiyi ne saboda jawahir badon mummy ba,don ko sau daya a rayuwarsa baya buqatar sake ganin fuskarta indan ta shine. Duk wanda yaga mummyn yasa a gargara take,banda gursheqen kuka babu abinda jawahir keyi,shigowar samir gaba daya hankalin mommy ya karkata a kansa,saidai duk yadda taso bude baki tayi masa magana abun ya gagara,'yan maganar sun tafi,kalamanta na duniya sun gama qarewa,sai jawahir ta hau girgizata "Mommy na yafe miki,ga ya sarakin,kice su yafe mikin.....ki fada musu" gaba daya jikinta ne ya saki cikin yan qananun daqiqu,taja wata qatuwar shaquwa me qarfi,abinda ke alamtawa duk wanda ke dakin cikawarta,bayan likitoci sun duddubata suka tabbatar masu da hakan. Kuka sosai kaltum itama ta saki,mutuwar bilalunta ta zamar mata sabuwa,mikin dake zuciyarta ya dawo sabo,kama hannun samir yayi ya maidata mota ya zaunar ita da jawahir,ya bar amiru ya kula dasu,ya koma cikin asibitin,ya biya dukka wani bill nata dana sauran jama'ar dake dakin,wanda dama ya saba hakan,kusan dabi'arsa ce,bawai yayi ne kawai don ita kadai ba,yayi ne saboda Allah,yayi ne kuma saboda ranar gobe. ********Cike da farinciki take hada kayanta cikin wani qawataccen akwati,duk da cewa tana qoqarin danne farincikin nata saboda ta yiwa jawahir dake zaune a gefanta kara,wadda a jiya akayi addu'ar bakwai na rasuwar mummy. Bayan shafe watanni masu tsaho da yawa,sai gashi a safiyar gobe zata sauka garinsu na dinya,zata yi tozali da ummanta,zataga habiban ta,yakumbo indo kawu ado umma suwaiba sai kuma lantana,wadan nan kusa sune mutanen da take muradin gani kaf fadin qauyen dinya,masoyan da bata da tamkarsu,ji take a goben kamar zata tafi saudiyya ne aikin hajji. "Nayi mamakin yadda kika iya jarumta da qarfin hali.....wadda keda miji kamar ya saraki.....amma kika zauna a wancan lokacin 'yammata na miki farautarsa?,bansan baki da wayo bafa sai da nasan cewa yaya saraki mijinki ne" ta tsinci dakusashshiyar muryar jawahir na fada sanda take zuge jakarta. sakin aikin tayi,ta juyi fuskarta dauke da fara'a tana kallon jawahir dake zaune saman abun sallah,sanye da hijabi,gefanta alqur'ani ne data gama karantawa,tayi matuqar jinjinawa gami da sarawa dauriyar da jawahir ta nuna,idan ka ganta a yanzu,zaka tsammaci ba itace wadda abubuwan nan suka faru da ita ba,saidai tayi imani da cewa QUR'ANI WARAKA NE kuma ambaton Allah shike sanyawa zukata nutsuwa,tun daga ranar kullum sai kaltum ta yiwa jawahir tofi a ruwa ta bata tasha,daga qarshe sai ya zama ma tofin ne ruwan shanta,bugu da qari da qur'ani take wuni a hannunta,tunda ta samu izifi me yawa a wajen kaltum din,sanda suke musayar karatu da ita,sannan idan xasu kwanta dashi suke kwana cikin wayar jawahir din. Gefan jawahir ta dawo ta zauna tana murmushi "Ban taba kawowa cewa akwai randa zatazo da zaya soni ba,ban taba hada kaina dashi ba,saboda nasan akwai tazara me tarin yawa a tsakaninmu,nafi kowa sanin cewa ceto ne yasa ya aureni bawai soyayya ba,amma a yanzu.....banajin akwai wadda zan iya barwa shi" murmushi jawahir ta saki "Koni bazan bari ki barwa kowacce mace shi ba,saboda ke kikafi cancanta....." Tsagaitawa kadan jawahir din tayi "Inaji a raina inama ace nice ke?,inama ace cikin tsanani irin naki na taso?,a yanzu rayuwa tayimin kyau kamar haka?" Qwalla ta cika idanunta sanda takai qarshen maganar. A tausashe kaltum ta dafa kafadarta "Ki godewa Allah da yayoki musulma,cikin al'ummar annabi muhammad.....ya kuma barki da imaninki.....sannan ya hadaki da mutane irinsu daddyn,da Allah yaso sai ya halicceki akuya ko tunkiya ko kuma zaki,ko ya halicceki kafura,kinga ko iya wannan ni'imace,duk wani yanayi da dan adam yake ciki mai gushewa ne watarana,a shekarun baya sanda nake cikin tsanani nida mahaifiyata da dan uwana,ban taba kawo cewa watarana komai zai wuce ba,to kamar hakane....kema wataran zakiga kamar komai bai faru ba" "In sha Allah" ta amsa tana dauke qwallarta,sannan ta miqe ta ciro wata jakarta,ta dawo ta zazzageta,kudadene suka fado masu yawa,kusan dukka sababbi ne,saita tura gaban kaltum "Kudaden break dinki ne da yaya saraki yake bani na baki,tun sanda kika fara zuwa makaranta wadanda baki taba amsa ba,dama ya gayamin gasunan na baki,amma bai sani ba.....ba lallai bane ki amsa,saboda bakison sababbin kudi bakya amsarsu....." Ta qarashe maganar qaramar dariya na kubce mata,tayata kaltum din tayi sannan tace "Bari na baki labarin abinda ya sanya yake tsokanata har yau" tiryan tiryan ta gaya mata,abun da ya sanya jawahir din dariya sosai,ganin labarin ya sanyata nishadi,sai taci gaba da bata wasu labarai na wautarta sanda take a matsayin kattume,har zuwa sanda wayar jawahir tayi qara ta daga tayi magana ta sakanni sannan ta sauke "Kije ya samir yana kiranki" miqewa tayi tana laluben hijabinta "Bari naje na dawo na qarasa baki labaran" harara jawahir ta jefa mata "A haka ake zuwa turakar mijin?" Saita miqe tana qwace mayafin,ta kama hannunta zuwa gaban madubi,duk da jikinta tashin qamshi yake,don bata jima da fitowa a wanka ba,amma sai da jawahir ta sakeyi mata wankan turare tun daga gashinta har qafafunta "Duk inda zai shanshana yaji qamshi.....kuma karki dawo min,kawai kice min sai da safe" ta fada tana jefa mata wani farin mayafi mara kauri instead of hijabin data saka dazu. Sakato tayi tana duban jawahir sanda take komawa saman abun sallarta tana zama "Amma qamshin nan yayi yawa,zan keta ta falo ne fa,yanzu idan na hadu da daddy ko momma fa nace meye?" "Haram ne?,wurin mijinki zaki fa,lada zaki samo...."kafin takai qarshe wayarta ta sake tsuwwa "Ki rufan asiri ki tafi,Allah shine yake sake kira" dariya ma jawahir din ta bata,yadda ta hade hannayenta waje daya tana roqarta,saita yi gaba a hankali ta fice,tausayin jawahir din na sake cikata,ta samu zuciyarta da yi.mata addu'ar samun miji nan kusa da zai zame mata sanyin idaniya itama. 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *_DA ZAFINSU_* *_A TSARE SUKE_* *_SUN TANADESU_* *_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_* *_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_* *_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_* *_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_* _WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_ 08184017082 _MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_ 09134848107 *_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_* 63 A bakin qofa ta taras dashi a tsaye kamar wanda aka bawa gadin qofar,cikin wasu Cotton kayan bacci na maza ash colour,qamshinsa ya budade ko ina,iskar damina na baza qamshin daga hagu zuwa dama,fuskarsa tayi wani fresh,duk da qarancin hasken dake sararin samaniya,sakamakon kwantaccen hadarin dake linqaya a saman,wanda yake bada iska me sanyi,me kuma cakude da qamshin qasa. Birki taja ta tsaya saboda yadda ya cinye qofar gaba daya babu hanyar da zata raba ta wuce,idan ta matsa kuma sai ta raba din to tabbas sai ta fara masauki a jikinsa kafin ta samu wucewar. Idanu ya zuba mata, Adams apple dinsa na sama da qasa kamar me hadiyar wani abu,daga nan inda yake tsayen yana iya shaqar daddadan qamshinta dake sake ta'azzara yanayin da yakeji dangane da ita a jikinsa. A tausashe ya cafkota ya kuma yi mata kyakkyawan masauki a qirjinsa,ya zagaye hannyensa gaba daya ta bayanta,da wata iriyar murya dake shaking yace "na gode da jan aji.....amma ki sani.....bazan iya jura ba,bazan iya jurar jan ajinki ba,rauni na a kanki yawa ne dashi" ya qarashe maganar yana cusa kansa tsakanin wuyanta zuwa qirjinta,da wani irin zafin nama,wanda cikin sakanni 'yan kadan ya birkice ya kuma birkitata itama,tsaiwa ta gagaresu gaba dayansu,saiya tallafeta ya wuce da ita kai tsaye zuwa bedroom dinsa. Kyakkyawa masauki yayi mata kan tattausar katifarsa,cike da wani irin shauqin so da qauna,wadda ta bayyana kanta muraran har cikin idanuwansu. Da zafi zafi ya shiga aika mata da saqonni,kamar zai cinyeta danya,zafafan kisses masu badda hankalin masoyi,daga dama ya maidata hagu,daga hagu ya maidata dama,tun yana yi da ragowar hankalinsa cikin jikinsa.....har ragamar hankalin ta qwace daga hannunsa gaba daya,yaji a ranar a wannan daren yanaso qetare shingen da yake tsayawa a baya. Ta bangaren kaltum tun tana iya karbar saqonnin da yake aikata mata har suka qetare saninta da hankalinta,jiki da zuciyarta suka fara gaya mata lallai muhimmin al'amari ne zai faru,kafatanin jikinta ya fara rawa sanda hannunsa ya tsallake boarder,tayi caraf ta riqeshi,hawaye ya soma ambaliya saman fuskarta. Cak ya tsaya,ya sanya hannayensa duka ya tallafo kanta,yana kallon fuskarta data cakude da hawaye,gashin kanta kuma ya barbazu saman fuskar,sai ya saka hannunsa guda daya ya yaye mata gashin gefe,abinda ya bashi damar ganin sukarta da kyau. Da wata iriyar kwantacciyar murya me cike da nauyi da kuma taushi,cikin kuma rawar muryar kamar wanda xai saki kuka yace mata "Dukka jiki da xuciyata sunyi amanna dake........cikin qanqanin lokaci kuma sun cika sun tumbatsa da soyayyarki,ban taba kawowa soyayya me zafi irin wannan tana yiwa mutum kamu kamar haka ba sai a kaina........" Sai yadan rage nauyin da ya aza mata,ya miqe a mugun kasalance ya zauna sosai bayan ya juya mata baya "Duk yadda nakai ga dokanta na kasance tare dake.....na maishemu abu daya,bazan iya aikata komai ba saida gamsuwarki......,zan baki lokaci ki nutsu har cikin zuciyarki dani" saiya fara jan jikinsa yana saukowa daga saman gadon yana layi ya nufi bandaki,ta bishi da kallo a sace,tana jin wata soyayyarsa na tsarga mata,dama haka yake?,saita cusa kanta cikin pillow cike da kunya. Duk da cewa haqarsa bai cimma ruwa ba,amma a ranar yayi yadda yaga dama,ta luguiguita sosai a hannunsa,wannan din ya rage masa zafi fiye da kima,saidai ita din ta rabauta da ciwon mara,wanda sai daga bisani ta samu relief,ta kuma gudu daki yana fita sallar asuba. A abun salla ta sake samun jawahir,suna hada idanu tayi turus,sabida bata zaci a dakin zata kwana ba,ga kayan jikinta gaba daya a yamutse,wanda duk wanda ya kalla ya tabbatar akwai ayar tambaya akai. Dauke kai jawahir din tayi,tayi kamar bata gani ba,sum sum sum ta shige bandaki,ta sakarwa kanta shower bayan ta daidaita duminsa. Ƙarfe biyu na rana dai dai motar da suke ciki ita da samir,da kuma spare wadda tayi musu rakiya ta tsaya cikin garin dinya,qofar gidan malam amadu. A nutse ta bude qofar ta tura,sai kuma ta tsaya turus tana kallon qofar gidan nasu,maida kallonta tayi ga gidajen dae hagunsu da damansu,duk sune dai gidajen data sani,duk da su din ma kamaninsu sun jirkice da shafen suminta da kuma fenti daya haska gidajen gaba daya. Waiwayowa tayi ga samir,sai taga ita ya zubawa idanu gaba daya,yana jingine da bayansa a owners corner,tun asubahin jiya ya zama wani me sanyi maras laka a jikinsa,duk motsin da xatayi idanuwansa na kanta "Anya su ummanmu basu tashi ba?" Tayi maganar cikin taraddadi,saboda batasan amsar da zata samu ba. Batasan ya iso inda take ba,sai maganarsa taji cikin kunnenta "Ummanmu tana ciki,tana dakon isowarki.....maza ki shiga ki sameta.....amma ina nan ina jiranki kizo muyi sallama,kada a manta dani" wani qawataccen murmushi ya subuce mata,ta ritsashi da idanu tana son karantar wani abu tattare dashi,zuciyarta na gaya mata yayi halin da ya saba duk yadda akayi,sai taji gaba daya zumudi ya cikata,don haka cikin wani irin hanzari.....ko duba da high hill din dake qafarta ba ta zuro qafafunta waje. Dai dai sanda ta doshi qofar gidan nasu wata mata dauke da qullin kaya saman kanta tazo zata gifta kaltum din,babu abinda yake tashi a jikinta illa tsami hade da wari,sai maganganu take kai kace wata zararriya ce,fuu ta wuce ta gefan kaltum din,bisa dukkan alamu bata gane wace ba. Daukin shiga gidan ya sanya bata tsaya wani dogon tunani akan wasilan ba tayi cikin gidan,daga ciki ta tsaya tana shawarar inda zata shiga,saboda gidan ya zama kala biyu,daya sashen gini ne na musamman akayi kai bazakace a qauyen bane,daya sashen kuma an masa kwaskwarima,babu laifi..... Yaran da suka fito daga ainihin sashensu riqe da robar man quli suka bita da kallo,ta ganesu dukansu,saidai suma da alama basu shaidata ba "Nan ne wajen umman bilalu?" Ta tambayesu "Eh nan ne" suka hada baki wajen bata amsa,kana suka bita da kallo sanda take wucewa sashen nasu a gaggauce. Tana tsaye ta bawa qofa baya,sanye da atamfa ABC ja me kwalliyar korayen ganye,idan ka duba wajen qafafunta da hannayenta da kake iya ganowa ta baya lalle ne ja shar,hakanan jelar gashinta ta nuna sabintar kitso dan hannu biyu dake kanta. Muryarta kawai taji ta tabbatar ummanta ce,magana take da wata dake daya daga cikin dakunan da aka qawata da window da qofofin zamani,batasan dawa take magana ba,amma muryarta kawai zata gaya maka cikin farinciki da walwala take. Da sauri ta matsa ta rungumeta ta baya sannan ta saki kuka tana dora kanta saman kafadarta,qawataccen murmushi ya subuce daga fuskar umman "Alhamdulillah" ta ambata tun kafin ta waiwayo ga diyar tata,kaltum dinta,wadda ta kwashe watanni da kwanaki masu tsaho bata bacci,ta kwashe lokaci me tsaho tana begen ganinta....tana taraddadin a wanne hali take ciki?,wacce rayuwa take?,a hannun wa ta fada?. Juyowa tayi ta rungumeta sosai cikin jikinta itama,muryarta na bayyana tsantsar farinciki da take ciki "Ahaf.....daga shigowa kuma sai kuka?" Tayi mata maganar itama tana qoqarin hana kanta kukan dakeson qwace mata "Ummanmu....ummanmu" ta tsinkayi muryar habiba daga cikin daki,da hanzari kaltum ta daga kafadar umman,saidai kuma tana riqe da hannayenta da qarfi ta qwalla sunan "Habi ta" kan kace kwabo saiga habiban tsaye a qofar daki,aka shiga kallon kallo,kafin dukkaninsu su barke da kuka suka nufi juna suka rungume. "Wai lafiya naketa jin koke koke?" Muryar inna laure ta ratsa kunnuwansu,wanda dama kusan yanzu aikinta kenan,bata iya zama,ko yaya taji wani motsi daga sashen,tun daga sanda ta bude idanu taga sauyin rayuwa ya fara saukarwa zuwairan,shikenan bata iya wani cikakken bacci da idanu biyu,kullum cikin fargaba take,musamman da asiya ta fara haduwa da gwagwarmayar rayuwa daga gidan alhajin data aura,yau fari gobe tsumma,kullum cikin nuqu nuqu da qoqarin boye halin da suke ciki take. "Ah....baquwa kukayi ne?......tofa....ikon Allah,wannan fuskar kamar na taba ganinta" inna lauren ta fada bayan ta zagayo saitin fuskar kaltum "Eh,'yarku ce kaltume,tazo ganin gida gaidamu" ummanmu ta fada,dai dai sanda yara suka fara shigowa da kaya suna jibgewa a tsakar gidan daga gefe daya "Kal wa?....kai haba zuwaira....ina kattume zata samu kyau da zatin wannan?,kigs fuska luwai luwai,jiki lukui lukui....jiki sai tahin qanhi yake.....ke bakiga kayan jikinta bama,anya kuwa zuwaira akwai Allah a ranki?" Inna laure ta fada tana kama baki,rabi da rabin hankalinta kuma akan kayan da yaran ke jibgewa,wanda sun fara cinye bakin qofar gaba daya. Murmushin yadda hassada ta fito sosai muraran saman fuskar inna lauren ummanmu tayi "Kayya,amma abu baiyi dadi ba da uwa ta kasa gane diyarta,matsa dai da kyau ki sake dubawa" koda inna lauren ta matsa ta tabbatar kaltum din ce,saita juya sumi sumi ta bace daga sashen,yayin da kaltum ta bita da kallon mamaki,gaba daya ta lalace,tsufa ya keto mata,idan suka jera da ummanmu sai ka dauka umma diyar inna laure ce. Falon da aka qawata kuma aka kira da falon ummanta take bi da kallo,sanda habiba ke feshe shi da freshener samir zai shigo,qamshin freshener din ya cakude da qamshin sabon gini da kuma sabon fenti,ita har yanzu gani take idanunta nayi mata gizo ne,idan ta kalli qawataccen gidan da sunan gidan mahaifanta,kamar ba'a karkarar ba,ko ina tiles da tiles,ga ruwan famfo ga wutar solar inverter,fankoki kota ina?,fakadeden tsakar gida da yasha tiles aka qawatashi da shuke shuke,ga yalwataccen kitchen irin na zamani,ga dan qaramin gas,abun kamar a mafarki?,bayan maka makan dakuna dake tsakar gidan,duk da bata bude ba batasan meye a ciki ba,kai koda a cikin garin ba kowa zai dace da irin wannan gidan ba. Har samir ya shigo suka gama gaisawa da ummansu tana cikin duniyar tunanin wanda ya yiwa rayuwar ummansu wannan baban aikin,umman tasu ta qara qiba tayi wani shar da ita,idan ta hada umman data bari lokacin aurenta data yanzu sai kace uwace da 'yarta,babu wani gami ko kadan. Bayan sun gama gaisawa umman ta qwalawa muntasir da shigowarsa gidan kenan kira,murna da mamakin ganin kaltum din ya cikashi,ta bashi key "Ka bude masa dakin can hanyar soro,yadan huta kafin su wuce,ai baya juyawa ba daga zuwansu" ummanmu ta fada bayan ta yiwa samir magana ya dakata da zancan tafiya tun yanzu,muntasir ya karbi muqullin cikin murna ya fice. Nannauyar ajiyar zuciya kaltum ta saki,tabi habi da kallo wadda ke ajjiye fulasan abinci masu kyau a gabanta da batasan inda suka samo fulasai masu kyau haka ba,habi din tata ta cika ta zama babbar mace,tayi qiba sosai,kamar ba 'yqr ficikar habi din data tafi ta bari ba,tayi adonta cikin wani lace mai kyau,da alama tana samun kulawa daga wajen mijinta yadda ya kamata. "Ina dana ko 'yata da ban sansu ba?" Kaltum ta jefawa habi tambayar,saita dago kai,suka hada idanu,suka sakarwa juna murmushin dake cike da qauna irin ta 'yan uwantaka "Yaya kaltume,ki fara sallamar dan aljannar mijinki din nan tukunna,yau kwanan hira zamuyi" saita dan dubeta "Ki baro yusufan a gida?" "Baya nan ma,ya tafi Lagos,kuma koda ya nan shi da kansa zaice nazo na kwana din" "Lallai yusufa,likkafa ce taci gaba haka?" "Duk ya sanadin mijinki ne ai,arziqinku muke ci" ta amsawa kaltum,duk da maganar ta daure mata kai amma haka ta duqa ta dauki kwandon,sannan ta fice tabar su ummanmu suna binta da kallo,kowa zuciyarsa fes qal,suna mamakin yadda kaltumen ta sauya gaba daya,kai baka ce ita bace. Zata fita taci karo da wata mata na shigowa,idanu jage jage da hawaye tana sharbar qwalla,sai taja da baya don bata hanya,saboda ganinta riqe da yaro ga kaya ga kuma tsohon ciki. Data sake dubawa sai taga ashe asiya ce,mamaki sosai ya kasheta,asiyan ce haka?,yarkace yarkace cikin tsumma?,itama asiyan idanu ta zuba mata,amma sam zuciyarta taqi yarda cewa kaltum din ce,don haka ta gwada kiran sunanta,jin ta amsa saita zabura,sannan da sauri ta qara gaba zuwa sashensu tana waigenta tare da qoqarin boye hawayenta. Mamaki ya cikata sanda take ajjiye kayan abincin data jiyo muryar samir a qofar gidan tare da muryoyin jama'a,ko data leqa,sai taga qofar gidan nasu cike yake da al'umma,samir na cikinsu,daga gefe daya kuma wasu kaya ne aka sauke,da alamu kuma wannan al'ummar za'a rabawa,don kowa ka kalli fuskarsa cike yake da farinciki. Idaunta ta maida kan samir,ta zuba mishi idanu tana masa kallon qurilla,irin kallon da bata iya masa matuqar yana tsaye a waje gata gashi,yadda yake ta haba haba da mutanen kawai zai alamta maka he's so simple man,bashi da qyamata,hakanan bai dauki duniya da fadi ba,kuma yadda suke gaisawan kadai xai gaya maka sabo sukayi,ba iya na yau ba kadai. Ci gaba tayi da morewa kallonsa,duk inda ya matsa idanunta suna biye dashi,daga bisani ma saita zauna saman wata 'yar kujera stool dab da window din tana bibiyar duka motsinsa da idanunta,murmushi na qwace mata lokaci zuwa lokaci,har zuwa sanda taga sun fara rabon kayan,yana miqa wani abu a envelope da tafi kyautata zaton kudi ne,ana dorawa kowa saman kayan. Komai da yakeyi yana yinsa ne cikin nutsuwa,cikar haiba da kamala,zuciyarta ta dinga qara gudu saboda yadda yake sake burgeta da shiga ranta,ganin bai qyamaci al'ummarta ba. Hayaniya ce ta tashi daga can baya,harta qaraso inda samir yake tsaye,da alama kuma duka akan rabon abincin ne,matar da suketa tarewa ta qaraso,data duba da kyau sai taga wasilarta ce data shige dazu,wasilar da ayanzu tafi kama da mahaukaciya tuburan. Idanu ta zuba mata daga inda take tsaye,mamakin abinda ya samu wasilan takeyi data sauya haka gaba daya,saika dauka kakar kaltum ce bawai sa'anni suke ba,banda ma tayi mata farin sani ba zata shaidata ba,tana tsaye taga samir din ya sanya an loda mata abincin me yawa ya bada umarnin a daukar mata,sannan ya fidda envelope din guda uku ya miqa mata,tana hangen sanda ta durqusa har qasa tana godiya,yayi mata alama da hannu ta tashi,yayi taku uku ya koma cikin mutanen yana ci gaba da kula da yadda ake gabatar da rabon. Kamar wanda aka gayawa ko kuma wanda jikinsa ya bashi,saiya waiwaya saitin window din sanda yake qoqarin jingina da itaciyar dake wajen,karaf idanunsu suka hadu,sai taja baya da wani mugun sauri cikin faduwar gaba. Sarai ya ganta,sai ya saki wani miskilin murmushi,ya kirayi umar daga inda yake,ya danyi magana dashi na wasu mintuna sannan ya juya ya fara takawa zuwa cikin gidan. Da sauri sauri tayi hanyar fita,saidai yana sako kai itama tana sanyo nata,abinda ya basu damar yin karo kenan da juna,sai yaci gaba da tafiya zuwa ciki,yana korata da baya a baya zuwa cikin dakin,kana ya sanya qafarsa daya ya maida qofar ta bame,bai barta ba har sai da suka dagana da bangon dakin,takai qarshe,sai ya sanya hannunsa daya ya dafe bangon dakin,idanunsa akan kyakkyawar fuskarta,bugun zuciyarta ya qaru saboda yadda take iya jin saukar numfashinsa saman fuskarta "Meye hukuncin mutumin daka kama yana satar kallonka?" Kunya da nauyinsa suka rugo suka dabaibayeta,ta kasa magana,ganin bata tanka ba sai ya qara matsarta sosai,tayi gefe zata goce,ya tarota ta hanyar sanya daya hannun nasa ya sake dafe bangon,ya sakata a tsakiya kenan "Babu inda zaki motsa daga nan,saikin bani amsa" a dan tsorace ta kalleshi,tana iya jiyo hayaniyar mutane har yanzu daga waje,kada wani ya shigo dakin ya samesu a haka "Ni ba kai nake kallo ba" ya saki da qaramin murmushin gefen baki,yana tuna wasu abubuwa da suka shude,kaltum me tsiwa,kaltum mara tsoro,gata yau gaba daya ta sukurkuce tsakanin hannayensa,tun baikai ga tabata bama "To wa kike kalla idan bani ba?" "Yan garinmu" tayi hanzarin bashi amsa,waiko hakan zaisa ya kubuta,fuska ya bata sosai "Wasu mazan kike kallo ma ba mijinki ba?.....lallai sai na hukuntaki" yana kaiwa nan ya tallafo kanta,ya kuma hade bakinsu waje guda. Wani salon tsotsa yakewa lips dinta,har sai da sukaso sakwarkwacewa gaba dayansu,dama ga sauran dafin jiya da bai gama barin jikinsu ba. Baya ya koma a hankali ya zauna dabas a qasa,banda cikin tahowar kaltum din akwai umarnin momma da baisan hikimarta na yin hakan ba,da babu shakka bazai iya tafiya ya barta ba,bazai iya nesa da itaba na wasu kwanaki. Sai da nutsuwarsu ta daidaita sannan ya karbi zuba abincin da kansa,yace ta zauna gabansa kawai yayita kallonta ya wadatar,ya fuskanci zallar soyayyarsa ke ci mata zuciya,amma batasan ya zata sake dashi ba,don haka bai barta ba a sannan sai daya samo kanta da kaso sittin cikin dari,yana cin abincin da bata tsammaci xaici ba yana janta da hira,har tazo ta iya maida masa. Sake kallon agogon hannunsa yayi,qarfe uku na rana,a qalla sun shafe kusan minti ashirin xaune cikin motar kawai yana kallonta,bayan ta fito ne kawai da sunan yi masa rakiya. Numfashi ya sake ja yana dubanta,sai ya kamo hannuwanta zuwa cikin nashi yana murxa tafin hannun nata,abinda yasa ta dunqule jikinta waje guda,kwanakin nan gaba daya wani dafi yake saukarwa jikinta,wanda mutum bai isa ya kauce masa ba. "Suna jiranka fa,kamar sun gaji" tayi jarumtar fada sanda take hango tsaiwarsu murtala ta baqin gilashin motar da suke ciki ita da sarakin "Zan tafi.....amma,sai kinyimun abu daya" wannan karon samun kanta tayi da sanya qwayar idanunta cikin nasa,har cikin jiki da jininta itama cikin wadan nan daqiqun takejin cewa zatayi kewarsa,kamar kada ta barshi ya tafi "Ya salam..... what a beautiful eyes..... kada ki zubamin dafin da zan kasa tafiya na barki mana" tattausan murmushi ma cakude da kunya ya sauka saman fuska da lebanta,sai ta sadda kanta,amma kafin ta gama saukarwar ya kama fuskarta ya dago zuwa gareshi "Nooo......ki barni na kalla na mitunan da suka ragemin na tafi" fararen idanun nata ta zaro "Mintuna kuma?" "Yes....so kike na tafi ko?" Kasa amsa masa tayi,saita maye gurbin amsar da murmushi "Is okay,nasan kinyi missing ummanmu.....but before na tafin, give me a kiss" ya fada yana miqa mata tausasan labbunansa sirara masu taushi da sanyi" sake fito da idanun nata tayi waje tana girgiza kai alamun a'ah,sai shima ya fitar mata da nasa idanun "Just do it....idan ba haka ba kuwa,zamuyita zama anan"kafin ya rufe bakinsa tayi saurin dora nata bakin ta manna masa kiss din mai tsaho kuwa,wani numfashi mai nauyi yaja,ya koma da baya ya zube cikin kujerar yana shafa qirjinsa,bata ankara ba yasa hannunsa daya ya fuzgota cikin jikin nasa,tsahon wasu mintuna har sai da nutsuwarsa ta daidaita. Hannunta ya kamo ya saka mata sabbin kudi masu kauri yana cewa "Wannan dai kyautace daga mijinki,don naga alama fada kike da sabbin kudi...... don't say no" dariya da kunya suka cikata,cike da girmamawa tayi masa godiya,ya fito da kansa ya bude mata qofar motar,yana tsaye yana binta da kallo har sai data shige gidan,sannan a sanyaye ya kada kai ya koma cikin motar,su umar dake tsaye gefe suna gulmar kallon da yake binta dashi,suna masa tsiya da dariyar ba sabon ba,suka shige motar "Ku kuka da kanku akan gulmata,ku kuma dauke idanunka daga kan matata,if not, I'll definitely deal with you" saraki ya fada fuskarsa a washe,saidai kuma akwai alamun da zai nuna maka shi dinne boss. "Sorry sir" suka fada cike da mamakin yadda akayi ya fahimci gulmarsa suke,sai kowa ya shiga taitayinsa,suka tada motocin. 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *_DA ZAFINSU_* *_A TSARE SUKE_* *_SUN TANADESU_* *_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_* *_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_* *_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_* *_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_* _WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_ 08184017082 _MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_ 09134848107 *_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_* 64 Farincikin data tsinci kanta a ranar bazai misaltu ba,gata ga ummanta,ga kuma habi dinta,bata manta da bilalu ba,sai data kokawa rashinsa a dai dai wannan lokacin. Hira iya hira,labarai rankatakaf na abubuwan da suka faru cikin gidan dana qauyen sanda bata nan sai da habiba ta sauke matashi,ko abinci saida ummansu tayi da gaske sannan ta tsaya taci. Habiba da umman sun fara mata ne da labarin abinda ya faru cikin gidan,bayan tafiyarta ummanta ta shiga damuwa qwarai,saboda rashin sanin taqamaimen inda aka kaita,sanda kawu as ya shaida mata ya karbi address na samir ta dan samu sauqi cikin ranta na wasu lokuta,daga bisani kuma kwanciyar hankalin ta wargaje,saboda jin an debi watanni shuru babu kaltum din babu labarinta,gefe guda kuma inna laure tana murza tsiyarta,tare da baza habaici akan auren kaltum,saidai cikin hikimar Allah,data durfafi tashin dare tana kaiwa Allah kukanta,sai ya sanya mata dangana,ya fidda mata damuwa,har ma tayi mafarkin kaltum din sau biyu cikin kyakkyawan yanayi a wasu darare guda biyu bayan ta gama sallar bacci ya dauketa,abinda ya sake sanya mata kwanciyar hankali kenan. Babu dadewa sai ga wata qungiya me suna professor rashid women aid forum,wadda tazo rabon jari ga matan karkarar,ummanmu bataje ba,amma sai gashi anzo har gida an kawo mata nata tallafin jarin me tsoka,wanda kusan yafi na kowacce mace yawa,suka dinga qara mata kudin da kadan da kadan,ta cika da mamaki da kuma tsoro,daga bisani zuwan qarshe da suka kawo.mata tace ba zata karba ba,saiga samir yazo da kanshi,ya bayyana mata kansa,bai boye mata komai ba,saboda yace yasan ita din uwace,tsayayya jajirtatta,kuma a soyayyar uwa da yarta tabbas hankalinta bazai taba kwanciya ba idan batasan inda diyarta take ba,saidai bai bayyana mata yadda zaman aurensu yake da kaltum ba. Sosai hankalin umman ya kwanta,ta kuma samu salama mai tarin yawa,taja bakinta ta rufe kuma,bata gayawa kowa waye samir din ba,saidai kuma tun daga wannan lokacin ya dauke musu nauyin ci da sha,gefe daya ga sana'ar ummanmu nata habaka,kasancewarta dama mace mai tarin kirki tun da can,tun mijinta malam amadu nada dukiya,kasancewarsa mutum me arziqi ada,bayan aurensu ya soma tsiyacewa,mutane suka fara cewa ya auri mai farar qafa. Tun baya dauka har ya soma yarda,abinda yasa ya tsaneta ya tsan gwameta kenan ita da yaran. Abun mamakin da ya faru a lokacin shine,yadda hankalin malam.amadu ya fara tashi,saboda jita jita da laure ke yadawa cewar anya ba kudin diyarsu sukeci ba kuwa?,sai a sannan ya fara tada hankalinsa nason sanin inda ya miqa kaltum din,ummansu tana kallonsa bata ce masa ta tafas ba,haka zai qaraci zirgillonsa kullum rana yana zuba idanun ganin samir ya kaishi inda diyarsa take,ko sau daya ummansu bata taba tanka masa ba. Ba jimawa kuma sai ya fara wani zabura,yana tsaka da barci sai aga ya farka a firgice ya fito da gudu yana kiran sunan bilalu,yana hirji kan bilalun ya yafe masa,gaba daya sai ya koma wani firgitacce,ko baccin rana baya samun yi bare na dare,daya fara gyangyadawa zai farka a firgice. Da farko ance masa wai fatalwa ce,umma ta kafe kai da fata kan cewa ba ita bace ba,danta bazai taba fatalwa ba,tunda ma ai saiya kwanta bacci yake ganinsa,daga bisani da suka samu wani malami masanin addini sosai,yayi masa bayanin komai,sai ya tabbatar masa haqqin bilalun ke bibiyarsa,ya bashi shawarar ya tuba ga Allah,ya kuma yawaita sadaqa wa bilalun,da ziyartarsa duk ranar juma'a idan hakan zata yiwu. Da taimakon wadan nan addu'o'in ya fara samun salama,sai ya jima baiyi mafarkin ba,saidai gaba daya yayi laushi ya kuma canza,bashi da buri da addu'a koda yaushe illa addu'ar Allah ya bayyana kaltum din. Ana tsaka da wannan samir din ya dawo da plan na canza musu ginin gidan gaba daya,saidai hassada da qyashi suka sanya laure d kawo iliya cewa basuso,yarsu asiya wadda tayi aure tace zaa canza musu suma. A sannan asiyan tayi irin auren da suke burin tayin,alhj dauda ya kashe mata kudi kamar baisan zafinsu ba,sunata murna da alfaharin sun kafa tarihi cikin qauyen,bayan ya musu romon bakan suna zuwa asiya zataci gaba da karatu,saita zama babbar likita,duk kuwa da cewa basusan kowa nasa ba,amma su murna suke yarsu tayi goshin da kaf fadin qauyen babu wanda yayi irinsa. Baibi ta kansu ba ya gyara sashensu kaltum din,saidai bai duba halayyarsu ba yayi musu kwaskwarima kamar yadda ya yiwa maqotan. Tun tafiya batayi nisa ba jikinsu yayi sanyi da lamarin asiya,saboda tunda taje gidan alhj dauda cikin wahala da wulaqanci take,bata da wani girma ko kima,saboda sun gama watsewarsu a waje kafin auren,don haka ko a gaban 'ya'yansa da matansa guda uku data taras goranta mata yakeyi. Ashe alhj dauda inuwar giginya ne shi,na nesa kasha dadinta,kowacce mace a gidansa ita kewa kanta komai,idan yaranki kuma sun tasa suyi miki,daga qarshe dai sai ya zamana laure ita ke ciyar da asiya dake aure wani gidan,sun dinke bakinsu saboda gudun dariyar jama'a,ta zauna duk da wannan wahalar da take ciki,saidai zancan duniya baya buya,kamar yadda dadi da wuya basa buya,tuni zance ya fantsama,saidai an kawo idanu an zuba musu,ana jiran ranar da zata fashe. Babu jimawa ciki ya bayyana a jikin asiya,nan alhj dauda yayi tsalle yace ba dashi ba,ba kuma a gidansa ba,don shi bai aurota don ta haihu ba,ya aurota ne don ya huta da ita,abinda ya dagawa inna laure hankali kenan,saboda sun kama shirya plan na asiyan tayita haihuwa,kodon kwadayin abinda alhj dauda ya tara,da qyar aka ciyo kansa,bayan yarjejeniyar cewa bazaiyiwa asiya komai ba,data haihun kuwa haka akayi,laure ce tayi komai kamar ita tayi cikin,aka rufa akaci gaba da zama a haka,ba dadewa kuwa wani cikin ya sake bayyana,sai fa aka koma 'yar gidan jiya,kullum asiyan na tafe a hanya,wadanda ake boyewa kar su san komai tuni komai ya gama bayyana,a haka ake,har zuwa jiya da hukumar NDLEA ta kawo samame gidan ta cafke alhj dauda,ashe tsohon dan safara da saida muggan qwayoyine,wannan ne abinda ya kawo asiya gida abirkice,gashi batasan wani dangi nasa ko daya ba,na kusa ko na nesa,matansa kuwa ba zaman lafiya sukayi ba bare ta tambayi wata arziqi ta gaya mata,ita sai taga ma sam cikinsu ba wanda ya damu,kowa sabgarsa yaci gaba dayi,aka tattarata aka watsar,don dama kusan kamar kowa ya tsaneta cikin gidan,kamar mujiya,babu me mu'amala da ita. Malam amadu da yusufa mijin habiba kuwa,rumfa guda biyu cikin babbar kasuwa samir ya siya musu,ya zuba musu jari me kauri a ciki suna juyawa,idan kayansu sun qare,yusufa zai tattaki har jahar Lagos yayi musu sari,rayuwa tayi albarka,saidai har yanzu tabon mutuwar bilalu na taba amadu,da mafarkinsa da yakanyi jefi jefi,sai kuma burin ganin kaltum,wanda kunyar abinda ya aikata ya hanashi tambayar samir kaltum din. Ita kuwa wasila,tun randa aka kaita gidan nasuru,sati daya kacal nasurun ya tsallake yabar garin nan ba'a sake jin labarinsa ba,tun lantai babarsa na ganin xai gaji ya dangana ya dawo har abun ya fara damunta,yayin da wasila kuma ta miqe qafa,tana cewa zama daram,duk inda yaje zai dawo ma,ita ba zatayi zuciya ba,hakanan ba zata gaji ba,sai ya zamana lantai ke ci da ita. A zaton lantai zata zauna da ita kamar uwarta,sai taga ba haka bane,cangal wasila bata iya mata,saidai taci tasha ta qoshi,ta tara qawaye susha hira da shewarsu,kamar ba itace wadda mijinta ya bace ba. Lantai bata da haquri,don haka ta yuwa wasila kaca kaca kan abinda take,nan fa wasilan ta tsiri fushu da maidawa lantai maganganu,daga bisani ma sai lantai taga ta tsira fita unguwa,tun safe sai dare,ta kuma dawo da abubuwan arziqinta taci tayi hani'an ta kwanta abinta,tama daina cin abincin lantai din,tace idan ma saboda shi take uzzura mata. Sai zaman gidan ya koma kamar na kishiya da kishiya,idan kaga lantai da wasila ana cashewa zaka dauka kishiya da kishiya ne,haka suke zaune. Sannu a hankali wasila ta fara mulka wata uwar qiba ta tashin hankali,tayi dimimi abinta,sai hankula suka fara dawowa kanta,zargin ciki ya tabbata akanta,koda lantai ta tuhumeta.....sai ta shaida mata eh tabbas ciki ne da ita,kuma cikin nasuru,abunda lantai ta musashi kenan,saboda tunda aka kawo wasila nasurun bai taba kwana a sashen bama,yana tsohon dakinsa,har zuwa sanda ya tsallake ya tafi ya barsu. Sanda lantai ta musa gagarumar rigima ta barke,ita tana ba cikin danta bane,wasila na cewa dole ta musa tunda ita ke tayasu kwana a daki,daga qarshe dai aka yanke zuwa cikin gari ayo scanning,wasila batasan meye ba,tace aje din ayi,saime?,ko shi akayi zai nuna ciki na nasuru ne,su kwano za'ayi ayi. Anayin scanning kuwa ya bayyana watannin ciki,tafiyar nasuru wata shida kenan,shi kuma ciki wata uku,tun daga nan jikin iyayen wasila yayi sanyi,ita kuma ta dage kan hakane,ana tsaka da wannan rigimar Allah ya jeho da nasuru,suka bayyana gaban mai gari,ya kafe wasila da idanu yana mamakin qarfin halinta,cikin bacin rai yake bayyana gaskiyarsa,sai wasila ta fashe da kuka tana fadin,tabbas ciki ba nasa bane,ciki na wani dan maqwafcin qauyensu ne,wata barratu cikin qawayenta ita ta bata shawarar cewa,taje kawai tasha sabgarta,tunda tana da aure yanzu babu me ganewa,koda ta samu ciki akwai na nasuru ne tunda shine mijinta,ta dnga samun 'yan kudaden da zata kashe sabgar gabanta,basai uwar miji ta bata ba,tunda miji ya ajjiye ta ya tafi,me zata zauna yi itama. Hankalin kowa ya tashi a wajen,iyayenta suka dinga kuka suna tsine mata,sai da me gari ya tsawata musu,a take anan nasuru ya rattaba mata saki uku,bayan wasu watanni tana gidansu da suka juya mata baya suma,nasuru ya aure lantana qawar kaltum,ya dauki matarsa suka wulla ibadan inda yake neman kudi. Cikin naquda wasila ta hadu da jijjiga eclampsia,wannan yadan taba mata qwaqwalwa,ta haifi danta namiji,amma yazo babu rai saboda wahalar da yasha a ciki,haka iyayen wasilan suka fara nema mata magani,saidai sunyi saunyi harsun gaji sun watsar,bata warke ba saidai ta samu sauqi,wannan tabban guda biyu yasa tarasa me aurenta,bayan rasuwar mahaifiyarta taci gaba da rayuwa ita kadai cikin gidansu,ita ke dawainiya da kanta da komai nata,tausayinta ya sanya ummanmu ta dauke mata abincin rana dana dare,hakanan kuma takan aika mata dan kudin batarwa,kullum tazo gidan cikin nadama da neman yafiyar kaltum take,takan ce jifa tayi,ya kuma dawo ya sameta tsakiyar kanta. Cikin matuqar sanyi da mutuwar jiki kaltum tace "Allah ya kyauta,ya rufa mana asiri,ya rabamu da sbarrin zukatanmu da kawunanmu" tabbas zalunci abun tsoro ne,kuma tun a nan gidan duniya Allah ke sakayyarsa,babu daga qafa,babu jinkiri,lallai Allah baya son zalunci,kuma baya jinkiri wajen ramawa wanda aka zalunta. A iya wunin ranar kadai kaltum ta tabbatarwa da kanta lallai sabuwar rayuwa ta zowa ummanta,mutane maqota wannan ta shiga waccar ta fita,kowa tazo ganin kaltum,tare da godiya kan kabakin arziqin da samir ya saukewa kowa,kafin kace meye wannan gida ya cika da abinci,kwano kala kala,kowacce da kalar abinda zata kawo. Ko can dama ummansun mutum ce ta mutane,tana da kirki da kuma hannun kyauta sun suna da shi,abun hannunta bai tsone mata idanu ba,don haka ko a yanzun ma abun bai zame mata sabo ba,tana da hidima da jama'q,duk sanda wani cikinsu ita ko habi wani ya miqe sai kaltum din ta bisu da kallo,farinciki na ratsata na yadda sukayi kyau suka murje,rayuwar tayi kyau fiye da yadda tayi hasashe,kowaccensu sanye da sutura ta rufin asiri gwanin sha'awa. Har magariba suna zaune ana abu daya,abinci kuwa har kaltum ta rasa wanne zataci a ciki,don har babar lantana sai data aiko da nata,bayan sun idar da magariba aka kawo yaron habi,sultan,yaron fes dashi sai qamshi yake,kyakkyawan bafulatanin yaro me kama da ubansa,bul bul dashi,da alama yana samun kulawa da soyayya daga mahaifinsa. Shida uwar mijin habi din sukazo,tunda dama yana wajenta,a wajenta ya wuni,kuma dama ko suna gida ma wajenta take wunin,yadda taqe qaunar yusufa da habi haka soyayyar ta koma kan yaron. Suka gaisa da kaltum cikin girmamawa,tayi mata godiyar abun alkhairin da samir yayi wa yaronta yusufa,kunyar baban ta kamata,macace ta gari,wadda bata qyamaci hada zuri'a dasu ba sanda kowa yake gudunsu,taso 'yar uwarta,ta mutuntata qwarai,ta nuna mata soyayya,sun kuma riqeta da girma da mutunci "Baba da kin bari nazo da kaina ma ai" ta fada tana murmushi,itama murmushin tayi "A'ah kaltume.....wannan abun alkhairin yafi qarfin sai ke kinxo za'a miki godiya". A ranar duk sanda ta rufe idanunta muryoyin jama'a daketa mata godiya ke yawo a kanta,wai yau itace dimbun mutane ke mata godiya tare da son rabarta?,kowa yana farincikin samun wani alkhairi ta qarqashinta?. Sultan dan habi yana jikinta,duk inda zata motsa dashi take motsawa,shidai kallonta kawai yake,saita zage tanata masa rawa sa waqa,tana cillashi tana cafewa,sai kuwa ya buda baki ya dinga bangala mata dariya,ta tsaya tana tayashi qaunar yaron na ratsata,tana jin kamar ita ta tsugunna ta haifeshi,habi na gefe tana musu tsiya. "Wai ni kam inna?,tana nan da halin nan nata?" Baki habi ta tabe kafin dariya ya subuce mata "Inna ai saura kadan a kaita gidan masu rangwamen hankali banda taimakon ummanmu......in gaya miki sata aka shiga akayi mata gagaruma,tun daga kudaden data mallaka har kadara,ke kaza wannan ba'a bar mata ba,hatta suturunta masu kyau sai da aka tsitsince,daga tafiyar sunan karime ta haihu,da inna ta dawo zaman 'yan bori ta dinga yi tana kururuwa,ke daga qarshe dai abu kamar tabi tabi,amma da yake yarinyar nan karime bata da mutunci,wallahi cewa tayi zakka ce Allah ya fitarwa innan,turmin zani wannan kasa dauka tayi ta bawa inna,bakiga kudin da umma ta dinga kashewa akanta ba,don jarinta ma sai daya tabu a sannan,amma da yake Allah ya sawa sana'ar tata albarka babu dadewa ta maida komai,ta sissiya mata kaya masu yawan gaske,sannan aka fara samo kan inna,waisai ga inna ba kunya ba tsoron Allah tana shiwa ummanmu albarka,wai dama ashe har yanzun ita irin arziqi ce?,yau gashi ta maganta mata damuwarta" baki kaltum ta tabe,son abun duniya a jinin innar yake,sam bataga amfanin soyayyar da zata nuna musu a yanzu ba. Ana gama sallar isha'i baba ya shigo gidan,fuskarsa kamar gonar auduga yana neman kaltum din,ta gaidashi cikin girmamawa a matsayinsa na ubanta,saida daga haka babu wani walwala ko sakewa ta taso daga dakin da akayi masa ciki da falo ta dawo dakin ummansu,tayi xaton umman zatayi mata fada,amma sai taga batace da ita komai ba. Cikin awannin da suka rage kafin su kwanta ta karanci yadda baban nasu yayi matuqar yin sanyi,babu wannan fadan babu masifa,tsakaninsa da ummansu sai kulawa da kyautatawa,don kafin su kwanta din haka ya danno musu uwar fura da tsire me kyau,yace a basu ita da habiba suci. Sai da dare ya raba sannan suka kwanta ita da habiban,sultan na gaban kaltum ba jimawa bacci ya daukesu. Saidai tun kiran sallar farko sukaji muryar babansu a can sama,dukkaninsu suka farka,da suka kasa kunne sai suka fahimci mafarkin bilal dai yayi yadda ya saba,don haka kowacce cikinsu ta maida kanta ta kwantar. Basu kai ga komawa baccin ba muryar muzammilu ta karade gidan da wani irin ihu da yake kwararawa,abinda ya sanyasu tashi dafa'an suka zauna,suna jin sanda ake bude qofar sashensu,don haka suma suka miqe suka tsaya daga tsakar gida,suna jin gunjin kukansa da tambayar da ummanmu da baba ke masa "Gobara ce,ta tashi muna bacci,ta kama gidan gaba daya ta qone,salisu da jamilu da shamsu duka an fito dasu basa motsi,asibiti xamu kaisu yanzu" Allah sarki ummanmu,duka saita rude,ta koma cikin gida ita da baba wanda ke laluben babbar rigarsa da kudade ya zuba a aljihu,ummanmu ta debo wasu ya qara musu,baban yace ta zauna suje su dawo. Daga habiba har kaltum kwanciya suka koma sukayi,duk da kowa cikinsu yaji susa cikin ransa,kodon saboda abinda ya samu yaran,saidai gaba dayansu ba abinda ke kai kawo a ransu face irin abubuwanda muzammilu ya aikatawa,wanda ya jawo mutuwar bilalunsu. Sunajin yadda ummansu ta kasa zama,sai zirya take,babu jimawa ana idar da sallar asuba,ko addu'a ba'a kammala ba saiga baban ya dawo cikin mutuwar jiki,gaba daya yara sun rasu,biyu na muzammilu,daya da munzali,wanda wani lokaci yakan kwana a gidan,sun shaqi hayaqun gobara ne,har ya musu illa,ya toshe musu hunhunsu,fiddau kuma matarsa na can asibitin sun bata kwanciya saboda qonewa da tayi gaba daya a fuskarta. Suna jin ummanmu na shiri tana salati,ba wadda ta bita ita da baban suka tafi,sukam sai da suka qarashe baccinsu,suka gyara mata gidan sukayi abun kari,suna aikinsu suna hira a tsakaninsu irin na 'yan uwantaka. Kaltum na mopping habi na kallon yadda wajen keta qyalli "Wannan abu da kyau yake,yusufa dai yace in sha Allahu muma ya kusa yi mana gyara,kamar haka zai.mayar mana da gidan,harda tiles din xai saka mana" sai kaltum tayi murmushi,habi na dakai na karatu,inama yusufa zai barta tayi karatu,ko ita da zata dauki nauyinta,koda iya matakin secondary ne,koda kaltum ta gaya mata abinda ke ranta sai tace "Haka baaba tace dashi,to baidai amsa ba bai kuma qi ba,kawai yace akwai nisa tsakanimu,amma idan da rabo wataran zanyi,shima yana sha'awar hakan". Wankansu sukayi tsaf suka shirya,sannan kaltum ta zabo flask mai kyau ta zubawa ummansu kayan breakfast din,sannan ta zuba musu ita da habiba da sultan,suka zauna a parlor suna karyawan,da nufin idan sun gama su wuce gidan mutuwar suyi musu gaisuwa. Suna cin abincin suna hira,kaltum na tambayar habiba wai ina auwalu kuwa "Hmmm,wa ya sanine?,ki cikin gidan sai suyi wata basusan ina yake ba,sai kuma ya kado sannan ake ganinsa" "Allah ya gyara" kaltum ta fada tana duba agogon hannunta,data dago kai sai suka hada idanu da habiba,habiban ta saki murmushi "Sai.nayita ganin kamar ba yaya kattume ta mai kitso ba,gaba daya kin canza,kin zama wata 'yar gayu sosai,kalar fatarki ta canza,hanci ido dama gashinki kamar ba naki ba,irin matan da muke gani a tv" dariya kaltum tayi "Lallai habi,ke bakiga yadda kika koma ba?,ni na zaci fa makaranta kika koma da kika waye haka?" "Rufin asiri ne da yusufa ya sake samu.....sannan kuma ya koyamin karatun hausa,ina iya karanta hausa da rubutawa,sai yake samomin litattafan hausar nan na soyayya nake karantawa,ashe makaranta ce guda?,kinga abubuwan dana qaru dasu wanda ada bansan dasu ba?,gaskiya da ka muke rayuwar aurenmu" cikin doki da jin dadi kaltum tace "Kai ashe kema kinbi sahu,amma naji dadi wallahi,saboda akwai qaruwa sosai a ciki,musamman zaka tsinci darussan rayuwa masu yawa,bama irin labaran da aka tsaftace alqalami,babu batsa sai soyayya mai tsuma rai,yadda zaki zauna da miji da al'umma lafiya ki samu tsira duniya da lahira.....gaskiya inajin dadin karatun novel sosai,saboda makaranta ce guda" Suna tsaka da wannan hirar muntasir daya zama dan gidan yanzu yayi sallama "Kaltum kizo kiyi baqo" harara habiba ta jefa masa "Malam kaltum take yanzu.....ka daina bata mata suna" sosai ya saki dariya yana tsokanarta,kasancewarsa mutum me barkwanci da kirki kamar mahaifinsa kawu ado,kaltum na jinsu ta miqe tana sanya hijab tare da tambayar waye "Kamar umar,yaron mijinki" jin haka ya sanya ta biya ta kitchen,ta hada kayan breakfast tace a fara kai masa,sai bayan wasu mintuna tabi bayansa,saita sameshi zaune saman motar anan ya karya din,yaji kuma dadin abincin,don ko breakfast din samir bai barshi yayi ba ya tasoshi. "Gashi inji mai gida,yace ina kawo miki kiyi qoqari ki kunna,zakuyi magana" ya fada bayan sun gaisa cikin girmamawa yana miqa mata wani kwali,tun bata bude ba ta fahimci waya ce,tayi masa sannu da qoqari tare dayi masa sallama ta juya zuwa ciki bayan ta aiko yara su kwashe kwanukan sukai mata cikin gidan. Yana qoqarin tayar da motar samir din ya kirashi "Na bata yanzu yanzu" "Ok" ya fada muryasa a qasa,sannan ya kashe wayar,umar ya saki murmushi "So,soyayya wato bata da kirki,oga an masa mugun kamu da alama" umar din ya fada yana sakin murmushi shi kadai. Tun a parlor din ta bude kwalin ta kunna wayar,tana gama daidaituwa kamar dama jiranta yakeyi kira ya shigo,Muhammad samir yayi saving sunanshi akan wayar,batasan murmushi ya subuce mata ba,ta saki kwalin ta shige dakin ummanmu,ta haye gadonta. Sai data daidaita numfashinta,gab da zata katse ta daga ta kara a kunneta. Wani nannauyan numfashi taji an saki kamar wanda ya tserewa abun tsoro "Alhamdulillah..." Ya fada cikin tattausar muryarsa,data qara zama wani cool "Da baki daga ba na rantse da Allah yau a garinku zanyi sallar azahar" dariya da mamaki ya kama kaltun,ta fidda idanu waje ba tare data iya cewa komai ba "Da qyar jiya na iya bacci,banyi tsammanin zan iya kaiwa safiyar yau ba babu ke a gefena.....,abu daya ne ya ragemin damuwa da nauyin da zuciyata tayi....na kwana a dakinki,naga tarin sirrikan da aka boye ba'aso samir ya sani,naga zane kala kala na fuskar samir......ashe haka kema kike sona amma kika iya cinyewa baki furta min ba" wayyo,duk da baya kusa da ita amma ji tayi kamar qasa ta tsage ta shige ciki,saita bude baki kawai bat iya cewa komai ba,kunya na dawainiya da ita,tana tuna meye da meye ma ta boye ne a ma'adanarta,ba shakka akwai tarin abubuwa masu yawa dake nuna zallar bege da soyayyar samir din "UMMUKULSUM" yayi kiranta da cikakken sunanta,abinda bata taba ji daga bakin kowa ba saishi,sautin da ya kashe mata duk wata gaba ta jikinta,saita sake lafewa saman gadon ummanmu,kamar zata nutse a ciki "Idan kikaci gaba da yin shurun nan....to ki tsammaci isowata nan da awa daya,kuma bazan koma ba sai da ke....." "Am sorry" tayi hanzari fada da wani irin sound daya sashi sakin ajiyar zuciya mai nauyi. Lokaci mai yawa suka bata kan waya,yana fallasa mata sirrin zuciyarsa,tare da narkar da ita cikin duniyar soyayyarsa,har ya sanyata itama ta dinga fallasa sirrikan zuciyarta ba tare data sani ba,batasan ta yiwa kanta barna ba sai da suka gam wayar ta fara tariyar kalaman data gaggaya masa,murmushi ta dunga yi tana juya wayar hannunta,wayace me shegen tsada,don irinta ce a hannunsa,saida habiba ta leao tayi mata magana sannan ta fito suka wuce. Sun tadda gidan makokin a cikea dagule,duk kallo sai ya koma kansu,kowa sai ya tambaya "Wai wannan kattume ce?" Habiba ke gyara musu "Kulsum dai ko kaltum" cikin lokaci kadan suka zama wasu taurari su da uwarsu,kowa son rabarsu yakeyi,daqyar kaltum ta janye umma taje ta karya,sai gashi ana jira da rububin abinda taci ta rage din,kowa yana neman saura. A waje suka ga munzali da muzammilu sunata share qwalla,muzammilu ma daya kasa jurewa kuka ya fashe dashi,baki habiba ta tabe "Ashe dai kowa nason nasa" maganar data ja hankalin kaltum kenan,saita kada kai kawai,ta tabbatar zaluncin da suka yiwa bilal ne Allah ya nuna musu ishara. Cikin kwanakin zaman makokin kusan umma ke dawainiyar abinci ita da baba,saboda muzammilun yanzu basu da komai,an daina jin duriyar mahaifiyarsu kwata kwata bare ta aiko musu da wani abu,wasu suce ta mutu,wasu suce an kamata tana sijin,to sanin gaibu dai sai Allah. 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *_DA ZAFINSU_* *_A TSARE SUKE_* *_SUN TANADESU_* *_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_* *_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_* *_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_* *_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_* _WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_ 08184017082 _MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_ 09134848107 *_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_* 65 Cike gidan yake da mutane,wasu suna shiga wasu suna fita,idan ka kalla zakayi tsammanin biki akeyi,eh....kusan bikinne saidai bashi bane,su momma ne suka yiwa garin tsinke,ita da hajiya qarama,da jawahir da biba,suka kuma kawo kayan lefen kaltum akwati dai dai har guda goma sha takwas,set shida shida different colors masu azabar kyau da tsada. Sunzo da duk wani kayan aure na al'ada da akasan ana neman auren diya mace dashi,nema kuma irin na masu wadata da rufin asiri. Saukar girma ummanmu tayi musu,don dama tasan da batun zuwan nasu,girki sosai akayi na alfarma,bayan lemuka da samir yasa aka kawo ruwa da sauran duka kayan buqata. Wannan kaya da aka kawo ya hautsina qauyen dinya cikin mintuna kadan,labari ya bazu ko.ina,sai ga jama'a anata tururuwar zuwa gani,sai ka rantse da Allah wani sha'anin biki akeyi. Kaltum kamar bata sansu ba tayi gidan habiba dauke da sultan dinta,ba kowa a gidan,don babar yusufa ma tana gidansu,da ita aka karba kayan,habiban ma tana can,sai sallamar jawahir taji. Cikin farinciki suka rungume junansu,kamar wadanda suka dade basuga juna ba,ta bawa jawahir ruwa tayi alwala sannan tayi sallah,sai kaltum din ta zuba musu abinci cikin wanda ummanmu ta aiko musu dashi. "Da alama bakinki fa akwai magana" "Akwai matar the giant saraki" jawahir ta amshe ba tantama ko kwana kwana "Bayan tafiyarki abubuwa da yawa sun faru,ciki kuwa harda yankewa najwa hukuncin daurin rai da rai da kotu tayi" tayi maganar idanunta na tara qwalla,jikin kaltum yayi sanyi itama,ta fara lallashin jawahir tare da bata baki,har ta samu tadan nutsu sannan ta dora "Lefen aurena yana gida irin naki kuma kamar naki,Amiru ya karbi soyayyata,ya kuma nemi yardata kan zai aureni....bisa goyon bayan hajiya qarama da momma harma da daddy,bayan sun lalubi dangin mahaifina.....da farko sun doje,amma da suka bincike sosai,sai suka samu dama akwai abinda ke damunsa kafin ya rasu,cikin rubuce rubucen wasiyyar da ya bari suka samu nice,sun karbe ni sun kuma mutuntani,musamman mahaifiyar abbana,qannensa dukka maza ne,don haka babu wani cece kuce me yawa suka girmamani ba wulaqanci,saidai ya samir ya roqesu kan su boye al'amarin,saboda sunaso duniya taci gaba da kallona a matsayin diyar professor rashid azare kamar yadda take kallo na a baya......saidai nidin kunyar kallonsu nakeyi....saboda hanyar da mummy tabi ta samar dani.....abun yana min ciwo kulsum,naga matuqar qoqarin ya amiru daya bugu qirji zai aureni....." Ta qarasa maganar qwalla na sauko mata. Cikin sigar lallashi da kwantar da hankali kulsum ke mata magana "Duk abinda ya faru ya riga ya wuce jawahir,kada jiyanki tasa ki rushe gobenki,yanzu babu abinda yafi kamata dake illa ki fuskanci gobenki,sannan shi a aure.....nagartar mace na iya shafe duk wani aibu dake tattare dashi...kedin nagartacciya ce jawahir,kina da dukkan DABI'A ta qwarai,baki bari ƊABI'AR ZUCIYA na son rai da son kanta ya rinjayeki ya gurbata miki halayya da ƊABI'A ba,kina da matuqar kirki da tausayi,na tabbatar wannan yaa amiru ya kalla,Allah kadai yasan manufarsa na fiddoki a haka da yayi,wala'alla ke wannan ce taki jarrabawar nan gidan duniya,kuma nayi imanin idan kika cinyeta....zata iya zame miki silar shigarki aljanna" kalamai masu taushi tayi amfani dasu wajen kwantarwa da jawahir hankali,ta kuma samu nasarar hakan,don ta sake sosai,suka dinga hira,jawahir na bata labarin abubuwan da suke faruwa da bata nan,gidan yayi dadi sosai,ya koma kamar da,yadda momma ke bata kulawa har yafi yanda mummy ke batan,saboda lokacin mummy tana fuskantar tsangwama saboda ra'ayinsu baizo daya da mummy da jawahir ba,amma a yanzu duka babu wannan. Ya samir kuwa tace yafara zama mara kunya ta fadi tana dariya,wallahi baya iya boye soyayyar da yake miki,kinsa momma ce taja masa kunne kan ahir dinsa yazo ya dameki?,ai inajin da ko kwana hudu vakiyi cikin qauyen nan,gaban kowa kuwa banda momma da daddy amsa waya yakeyi,shi da ya amiru kuwa yanzu baram baram jawahir ta fada tana tilliqa dariya "Me yasa?"kulsum ta tambayeta itama tana tata dariyar tare da jin wata kewa ta mijin nata na kwarara sassan jikinta "Yace wallahi ya samir din ya fara zaucewa,baya barinsu suyi barci,bashi da aiki sai waya" sai suka sanya dariya gaba daya. To sai yamma lis su momma suka tashi tafiya,ciki har da 'yan uwanta daga sudan mutum biyu,sai wasu daga azare 'yan uwan daddy mutum uku suma,saidai kulsum ta kasa zuwa bare ta hada idanu dasu, momma ta dinga mita "Shikenan samir ya shiga tsakaninmu kenan yayi mana farraqu?,to ban yarda ba,da sake" da kanta tayi tattaki har gidan habi ta ganta sannan sukayi sallama,saidai jawahir ta roqi momma ta barta,sa dawo tare da kulsum din. Hakan kuwa akayi,a nan qauyen suka barta,tare da ita suka dinga zagaya dangi,har gidan inna,wadda ta fashe da kuka sanda taga uban kabakin da su momma suka ajjiye mata a matsayinta na kakar kulsum,saboda momman tace duk wani daya danganci kulsum sai yaci arziqinta ya kuma ya qara,kulsum mutum ce,kulsum nagartacciyar mace ce mai kyakkyawar zuciya,wadda kudi ko dukiya ko wani qyale qyale na rayuwa bai dameta ba,sanda zata tafi saiga innar ta zube tana roqarta gafara "Basai kin nema gafarata ba inna,badai abun duniya kikeso ba,kuma gashi an baki,zaki iya ci gaba da tsinema muda ummanmu" sarai innar ra gane magana ta gaya mata a fakaice,to amma tasan yaran sunyi haquri,sun kuma yi kawaici,kome zata fada kuwa,ita a yanzu nadamarta hade da kunya take,ashe wanda ka raina watarana shine zaiji qanka ya rufa maka asiri?,ashe RABON BAWA DA ARZIQI MUTUWA ce?. "Allah ya yafemu gaba daya" itace kalmar qarshe da kulsum tayi mata suka baro gidan. "To haka kawu ado yakumbo indo da umma suwaiba,kaf dangi 'yan uwa abokan arxiqi babu wanda baice HAIHUWA TAYI RANA ba akan su kulsum din,abun sai son barka da godiya ga Allah S W T wanda yake azurta bawa a sanda yaso. Yakumbo indo ita ta dauke kulsum da jawahir ta ajjiye gidanta ta fara tsumasu,gyara na gaske take musu musamman kulsum da take ganin 'yar hannu ce,batasan komai bai gudana ba,har sai wani dare an hadu ana hira,kwanaki bakwai da suka rage su koma gida ayi walimar da za'a raka amare gidajensu,da ita da fatsima da karima wadda a yanzu itama ta sauko take kuma jin kunyar abinda suka yiwa kulsum din a baya,ashe arziqinta yaci uban nasu,gefe ga jawahir da habi dake baiwa danga nono,karime ke tsokanarta kada fa ta koma asake sabon gashi yawa sabuwar amaryar da aka kawo yau yau. Yatsina fuska tayi tana dubanta "To da mecece?,kar nake a leda,babu wani abu daya gudana" dariya suka sanya gaba daya,habi ta kama baki ta kasa magana,jawahir tace "Allah ya samir ya gama hure miki kunne,ya koya miki rashin kunya" "To meye laifinsa?,yama yi qoqari ai" shewar suka sake saki "Zaki bayani da babban baqi wallahi,don indai wannan mijin naki ne a yadda dai na ganshi ko.....hmmmm" dukkansu suka sake saka dariya,sai kuma tsoro ya dan tsarga mata,ta basar da zancan aka shiga wata hirar. Da magariba bayan sun bar gidan habi tayo wajen ummanta,sai umman ta kama hannunta zuwa qofar wani daki,ta tura ya bude,cike fal dakin yake da kayan jeren cikin gida da kayan qyale qyale,masu kyau masu tsada kuma na zamani "Ki duba da kanki kaltum,kar kiji kunya,idan akwai abinda babu kiyi magana za'a siyoshi kafin ku tafi" idanunta cike fal da qwallar qaunar da umman nata ke mata "Ummanmu....duka wadan nan kayan?" Kai ta gyada mata "Nakine kaltum,duka abunda na mallaka a duniya naku ne keda habi,saboda bani da kwafinku" rungume umman nata tayi a jikinta sosai,tayi kuka tayi kuka,tayiwa bilalu addu'a,sannan tana tsaye aka dinga fito da kayan tana gani. Komai yaji yayi daidai,babu wani abu da babu shi koda kuwa ina za'a kaita a aure,sun jima suna hira da ummansu har zuwa sanda babansu ya shigo,bakinsa dauke da sallama,kai bakace shi bane. Sannu da zuwa tayi masa ta miqe zata shige daka kamar yadda suka saba a baya "Kulsumu" taji yayi kiranta,saita tsaya cak "Zo nan" ya kirayeta,ta dawo da baya,tazo gabansa ta tsugunna "Fushi kike dani har yanzu ko?" Yayi maganar muryarsa na rawa,saiga hawaye na sauka,abinda ya daga hankalin kaltum kenan,ta girgiza kai da hanzari "A'ah baba" "Idan ma kinyi ai bakiyi laifi ba,amma ina roqonki don girman Allah ki yafeni,bana buqatar komai daga wajenki banda yafiyar,koda bazan tsira da komai ba a rayuwata ba damuwata bace indai na tsira da yafiyarku" "Ban riqeka ba baba,kai kayi silar kawoni duniya,na yafe maka,kuma kaima ka yafemin idan na taba bata maka" adaren su ukun suka zauna sukayi hirar da suka kafa tarihi,irin hirar da tun haihuwarta basu taba ba. Ana ya gobe zasu tafi saiga lantana Allah ya kawota ita da nasuru,da fari kunyar kulsum ta dunga ji tana buya,wai kada taga kamar taci amanarta,saida zasu fita da yammaci xasu karbo wasu kaya wajen yakumbo indo,tayi wa lantana ba zata ta fada gidanta,sun sameta tana ta ware tsarabar doya da manja da dankalin turawa da takanyo,ta saukesu da ruwan da lemon roba cikin mutantawa da kuma jin kunya,xata fice kulsum tayi caraf ta damqota "Na kamaki,waini lanatana kikejin kunya?,me kika yimin banda alheri?" Kanta ta sadda qasa,saidai yadda kulsum din keta dibanta da tuna mata da rayuwarsu ta baya ya tabbatar mata babu komai a ranta kulsum din,daga qarshe ta shaida mata ita dadi ma taji data auri nasurun,saboda sun dace matuqa,sukayi sallama ta hada mata doya da yawa tace ta kaiwa ummanmu,dama kuma ta saba kai mata duk sanda ta dawo,ba zata samu zuwa walimae tarewar kulsum din ba saboda tayi nauyi,amma ta karbi address dinta,ta tabbatar mata da cewa tana nan zuwa in sha Allah duk sanda suka shiga garin. Kudin da tazo dasu taga sam babu wata buqata da ummanta ko babanta ke dashi,saita rabasu gida hudu,kaso biyu ta bawa habi wadda keta tunanin irin san'ar daya kamata tayi,ta bata shawarar sarar atamfofi da hijabai,kaso daya ta aikawa da wasila,daya kashin kuma ta aikawa da asiya,duk da tana tunanin ba zata karba ba,saiga asiyan da kanta tazo godiya,inna laure ta rakota,saida suka gama godiyar asiya ta fashe da kuka,suna neman gafarar ta,bata wani tsaya batama kanta lokaci ba tace ta yafe mata,sabida ta riga ta wucen wajen ita. Bata jima da fita ba wasila tazo da nata kukan da neman gafara,itama cewa tayi ta yafe matan,saboda ubangiji ya ruga daya hukunta kowa dai dai da laifinsa,to me yayi saura?. ******** Cike da wata irin nutsuwa me ratsa zuciya gangar jiki da ruhi yake rufe kowanne sashe na gidan,har zuwa sanda yakai ga qofar qarshe wadda zata sadashi da ainihin falon gidan,saiya daga kansa a hankali yana kallon sama,wadda ta hada hadari me kyau daya fara feso yayyafi yas yas a jejjere me dan yawa. "Alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimmus salihat" shine abinda ya furta,bayan samun kansa da yayi tsakiyar falon gidansa da yake mallakinsa,wanda tako ina qamshi yake fitarwa mai taushi da dadi,komai kuma na falon kalar fari ne da light ash. Tafiya yaci gaba dayi yana sanya hannunsa yana fidda babbar rigar jikinsa ya riqeta a hannunsa,komai na jikinsa farine qal kamar hannu bai taba tabashi ba,tun daga samansa har qasa. A hankali ya tura qofar dakin da yake da tabbacin a ciki take a zaune,dakine wanda babanta yayi mata komai na ciki,bayan dakin da umman ta ta shirya mata,da kuma wanda shi karan kansa samir din yayi mata,amma sai ta zabi zama ana babanta,saboda tasan cewa da uba ake ado. Maida qofar yayi ya rufe,fuskarsa na fidda wani yalwataccen murmushi,sallama yayi da tattausan muryarsa data qara laushi,tun daga bakin qofar ya tsugunna ya zare takalminsa,safa kawai ta rage,sannan ya miqe a nutse,idanuwansa a kanta ya soma takawa zuwa inda take zaune,duqunqune cikin fararen tufafin lace mai taushi,da sassalkan mayafi mai ado irin na jikin lace din. Waiwaya yayi ya hangi wata dunqulalliyar kujera ta cusion,ya sanya hannu ya janyota zuwa gaban gadon inda take zaune,gab da ita,gwiwoyinsu na gogar na juna,hannunsa ya sanya ya lalubo hannayenta ya riqesu ga cikin nasa,sannan ya sake maimaita sallamar da yayi dazun. Da dasashiyar muryarta mai sanyi ta masa masa,ta sanya hannu a hankali ya zare mayafin data rufe kanta dashi "Look" ya fada yana ci gaba da tsura mata idanu,wani shegen dinki akayima lace din kamar qasar arna,saidai ya qayatar dashi matuqa,ya kuma ja hankalinsa "Karki fara karya alqawari tun yanzu..... please ummu kulsum" ta tuna dukkan wani alqawari data dauka masa a shekaran jiya,hanyarsu ta zuwa gidan qunshi,yabi ya dauketa,ya isa da ita wani guest house,sun dade acan yana karanta mata karatun yadda yakeson rayuwarsu ta kasance,da qyar ya maidata gidan qunshin. Daga kan nata tayi yadda ta buqata suka hada.idanu,babu kwalliyan komai kan fuskarta,sai qamshi na bala'i da jikinta ke fitarwa tako ta ina,saboda amfani da tayi da kayan kamfanin YERWA INCENSE AND MORE. Dukka hannayensa ya sanya yana goge mata fuskarta "Ya akayi kikayi kuka da yawa,ko zafi bakiji,babu ac dakin ba fanka" anutse ya tashi ya isa makunnar ac ya kunna kana ya daidaita,ya dauki remote na fanka itama ya saita ta kadan,har zuwa lokacin yayyafin na nan,saima qara qarfi da yayi. Inda ya tashi ya sake dawowa ya zauna,na wasu sakanni sannan ya bude baki cike da nutsuwa "ki rage kayan jikinki ki watsa rawa,sai samu sauqin gajiyar jikinki" ya fada yana dubanta,kallonsa tayi sai kuma ya dauke idanunta da sauri "A'ah....sai zuwa da safe" "Banason musu" ya fada yana miqewa "kafin na dawo ki shirya,minti goma kawai" sai ya dauki babbar rigarsa ya soma takawa zai fice daga dakin,ya fuskanci kamar a darare take dashi,shi yasa bai matsa mata ba,ya zabi bata space. Yana fita ta sauke ajiyar zuciya,ta ware mayafin kanta hade da dankwalin tana qarewa dakin kallo,sannan daga bisani ta miqe a hankali,ta tabbatar yaja mata qofar sannan ta nufi bandaki. Ruwa me zafi sosai ta hada tayi wanka,taji dadin jikinta kuwa sosai,harma taga baiken kanta da ada taqi yarda tayi wankan,ta fito a gurguje ta shirya cikin wata tattausar doguwar rigar barci ta dora madaidaicin hijabi saman kanta ta zauna gefe daya,tana sake qarewa dakin nata kallo. Da sanyin nan nasa dai yayi sallama yana turo qofar dakin,ta amsa mata itama a tausashe,tana satar kallon fuskarsa,qamshinsa ya baibaye dakin gaba daya,wani kyau taga ya qara mata,fuskarsa ta sake fresh,kamar wanda aka bawa kyautar wata. Babbar dardumar da ya shigo da ita ya shimfida,bayan ya ajjiye plates da cups daya shigo dasu,sannan yayi mata izinin ta taso,a nutse ta tashi,ta tsaya daga bayansa hannun damarsa,kamar yadda qa'idar sallar jam'in mace daya da namiji guda daya take. Matsakaitan raka'o'i guda biyu sukayi,suka sallame,bai juyo ba yana fuskantar alqibla ya fada jero addu'o'i,addu'o'i masu dauke da fa'idoji da kuma tarin ma'anoni masu yawa,ta lumshe idanu tasirin addu'ar na ratsata,ma'anoninta na mata amsa kuwwa cikin kanta,har zuwa sanda ya kammala,ya shafa,ya waiwayo yana dubanta. Idanunta ta sake rufewa zuciyarta na bugawa sanda ya dora hannunsa akanta,gaban goshinta,ya karanta addu'ar data dace kowanne ango yayi sanda aka kawo masa amaryarsa,ko kuma mutumin da ya siya sabon abun hawa. Da kansa ya miqe ya dauko ledar da ya shigo da ita,ya bude komai ya kuma zuba sannan ya kauda ledojin ya sanya farantin a tsakaninsu,idanunsa cikin nata yana son lalubo qwayar idanunta da suka cika taf da tsoro,tsoron dakan sanyashi yin murmushi,baisan su waye suka gaya mata labari me yawa haka kan daren farko ba data tsorace masa sosai,cikin hikima ya dinga hilatarta,har ta dan sake,ta sha sassanyar fresh mik din daya cika mata cup da ita,saidai daga ita din bata iya sake cin komai ba. Ya rigata tashi,ya barta tana ta laqai laqai dinta,saiya koma gefan gadon ya zauna yana duba wayarsa,duk da cewa fiye da rabin hankalinsa yana kanta,har zuwa sanda ta gama tana kammale wajen,shima sai yayi amfani da wannan damar ya gama shirya duk wani plan dinsa,bayan yayi rub da ciki kan gado yana hangenta daga kwancen. "Ummukulsum" yadda ya kira sunan nata da wani shaqaqqen sauti,sai da da haifar mata da faduwar gaba da wata irin kasala,Bai jirayi amsarta ba yace "Kizo ki kwanta,ruwa na sake qarfi,sanyi kuma garin yake dada yi" itakam har ga Allah a tsorace take,sai ta fara takawa a hankali xuwa bakin gadon,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki......saidai kafin ta qarasa wata walqiya ta haske sararin subhana,ta kuma ratso har dakin nasu ta window din da daddadar iska ke ratsowa,wadda tafi ta fanka da ac dadin shaqa da lafiya a jiki,ta runtse ido cike da tsoro,kafin kuma tayi tunanin meye abunyi na gaba,an kwararo tsawa,wadda ta korata da gudu,sai gata tsamo tsamo saman gadon,ruqunqume da saraki. Murmushi ya saki mai cike da jin dadi "Alhamdulillah" ya furta qasan ransa yana yiwa Allah godiya da ya kawo masa ita cikin sauqi,sai ya laluba makashi switch na fitilun dakin ya kashesu gaba daya,ya maida gurbinsu da wasu kalolin fitilu masu bada dim light,kalolin da suka maida dakin a idanu wata kala me kyau da qayatarwa. A hankali ya daidata kwanciyarsa,ya kuma sanyata da kyau cikin jikinsa,yana sauraren yadda zuciyarta ke bugawa,da gasken gaske take tsoron walqiya da tsawa har haka,sai yaci gaba da riqonta cikin jikinsa,yana shafa gashin kanta da ya bayyana,bayan dankwalibta yayi nasa wajen tuntuni. Sai data fara dawowa dai dai sannan ta tuna wautar data tafka,saita motsa tana yunqurin zame jikinta daga nasa,sake sakata yayi tsakanin qirjinsa,ya cusa kansa ta cikin wuyanta ya lalubu kunnenta ya rada mata "Amma dai ya kamata a bani tukucin aikin da nayi ko?" Bai jirayi amsarta ba ya fara aiwatar da abinda yake ganin shi kadai ne a yanzu abinda ya rage masa ya qarasa maidata tashi halak malak,tun yanayi a sannu har dukka jikinsa ya amsa,ya koma aike mata da saqonni masu zafi cikin kuma zafi. Cikin sakanni kadan jikinsa ko ina ya dauki rawa,sai kace wanda aka tsoma cikin ruwan qanqara,sai da ya tabbatar ya dorata a hanya itama sannan ya fara yunqurin zarcewa,ta sake masa kuka dai dai sanda ruwan saman ya kece da qarfin gaske. "No....no.....no ummukulsum, you promised me......ba zaki hana ni ba...... please ummu" kasa qarasawa yayi saboda yadda bakinsa ke rawa sosai,ya miqe ya zauna ya sake janta jikinsa. Da kalaman bakinsa ya sake aiki ta bashi dukkan yardarta,cikin tausayi da tausasawa diya mace,bisa bigire na girmamawa da sanin darajar halittar ya tafi da ita,wanda kusan a jininsa yake,girmama dan adam,musamma diya mace. Saidai duk yadda ya tafi da itan bisa lalama.....hakan bai hanasu dukkaninsu ji a jikinsu ba,kasancewarsu farin shiga,da basusan komai ba. Koda suka isar da sallar asuba kasa daga idanunta tayi ta kalleshi,kanta a qasa,shi kuma yaqi matsawa ya bata waje taji da abunda ke damunta,ya tsareta da idanun nan nasa da suka qara daraja da kima daren jiya zuwa yau. Ganin da gaske ba zata kalleshi ba sai ya qaraso ya kama hannayenta "Am sorry matata.....nasan na miki rauni da yawa.....amma bani da wani option daya ragemin,ina fatan zaki yafemin.....kuma wannan zai zama kamar harsashi ne da muka kafa ta gina ingantacciya kuma sabuwar rayuwa cikin duniyar soyayya" wata irin qauna da tausayi mai girma suka kamata,shi da abunsa?,shi da halalinsa amma yake bata haquri,lallai shi din lu'ulu'u ne,tsintarsa saimai dimbin sa'a "Kayi dukka yadda kaga dama dani,ba sai da amincewata ko yardata ba,ni halalinka ce ta har abada" kamar xai tsaga qirjinsa ya sanyata haka ya dinga ji,bai samu sasaucin azalzalarsa da zuciyarsa keyi ba,sai daya rungumeta tsam na tsahon wasu mintuna sannan yace "Ina da tabbacin kinji yadda zuciyata ke bugawa,kuma duka saboda ke ne.....don Allah....kimin alqawarin zaki rayu dani,komai wuya komai dadi,ba zaki taba barina ba,komai girman laifin da nayi miki,ki hukuntani yadda kikeso,amma bazan iya jurar rabuwa a tsakaninmu ba" ya fada yana sake matseta cikin jikinsa "Nayi maka" ta fada da zazzaqar muryarsa dake sake tsumoshi,sai da yayi yaqi da zuciyarsa sannan ya kaita nesa,ta hanyar daga mata qafa da yi mata alfarma ta koma bacci abinta,amma gashi,sai baccin ya gagareshi,don haka ya dauko qaramin qur'ani ya dawo gaban gadon daga qasa ya zauna,kamar me gadinta,yana karantawa qasa qasa,yadda sautin bazai damu kowa ba,duk bayan wasu ayoyi idan ya karanta sai ya daga kai ya kalleta,ta saman fuskarta zaka iya ganin yadda idanunta suka tasa,wanda hakan ke alamta maka taci kuka,ya saki murmushin gefan baki yana tuna daren jiyan,wani irin dare da bai taba zaton akwai irinsa ba akafatanin rayuwar dan adam,ya kasa jurewa,sai daya dan miqe kadan yayi kissing soft lips dinta zuwa goshinta sannan ya dawo ya zauna,ba ita kadai yake ganin kima ba,har umma da tayi qoqarin tsare mutuncin diyoyinta har sai da suka kaishi inda ya kamata ya kuma cancanta(qalubale gareku yammata,gurbin ido ba ido bane),talauci tsangwama da babu basu sanya umman tayi watsi da tarbiyyarsu ba,ta yarda su rasa komai amma banda mutunci(qalubale gareku iyaye mata). Lokacin data farka taji dadin jikinta sosai,ta taras da abinci yana jiranta,saqon gaisuwa daga momma,da kuma saqon bankwana daga 'yan qauyen dinya cewa sun wuce gida. Tun jiya suke gaya mata ba zasu dawo ba,ta dauka cewa fadi kawai suke,ashe da gaske suke,saita narke zata masa kuka,ya zauna dirshan ya lallashi abarsa,don shikam hakan yayi masa,ko banza zasu sake,zata kuma huta itama ta warke babu sa'idon kowa. Cikin kwanakin amarci ake bugawa iya amarci,amarcin da har takai tsakanin amiru da samir ko a waya,duk da cewa layi daya suke,amma akwai gidaje kusan shida a tsakaninsu,abinda tsahon rayuwarsu bai taba faruwa ba,matuqar suna gari daya. A kwana na bakwai ne ma amirun ya nemi samir,sun dan jima saman waya suna hira,sannan ya hada jawahir da kaltum. Hirar tasu kusan ta sabuwar rayuwar da suka tsinci kansu ne,saidai alhamdulillahi,kowacce al'amura na tafiyar mata dai dai. Batasan cewa samir ya biyota dakin ba,kunya ta sanyata take zata gudu,yayi caraf ya kamota yana cewa "Tunda kika iya hira haka rai rai yau kam akwai daukan magana,ki shirya" saiya fadar mata da gaba,ta marairaice masa,shima sai ya narke mata,hakanan ta bada kai bori ya hau,saidai salon qauna da tarairayar data gamu da ita ya shafe sauranb tsoron dake ranta. Wasa wasa daga samir har amiru sai aka daina ganinsu,qarshe dai daddy ne ya cire kunya ya wankesu fes,yace daga ranar litinin me zuwa yana neman kowa,saboda gyara da zasu fara yiwa company,da kuma bude sabon reshe wanda yafi wannnan girman,zai dauki ma'aikata kusan dubu da wani abu,don tuni daddy ya shaidawa duniya ya ajjiye siyasa,ya kama kasuwancinsa kadai ya isheshi,siyasa qaddararsa ce dama,kuma yana fatan ya cinye jarrabawarsa. Dole ran Monday din babu kunya suka shirya suka fitan,kowa na kewar matarsa,suka tadda daddy suna wani sussunkui da kai suka gaidashi,ya share kamar bai gane me sukewa ba,suka shiga maganar data tarasun,ganin haka suma sai suka sake,suka kuma shiga tsara abinda zai fishshesu. 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *_DA ZAFINSU_* *_A TSARE SUKE_* *_SUN TANADESU_* *_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_* *_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_* *_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_* *_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_* _WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_ 08184017082 _MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_ 09134848107 *_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_* 66 Kamar yadda ya zame mata al'ada,duk sanda ya fita aiki kafin ya dawo ta kammala komai da tasan zai iya buqata,kama daga tsaftar gidanta dama gwanace,zuwa kwalliya wanda shima wannan ba sabon abu bane a wajenta,har abinci da ruwan wankan da zai iya buqata. Yau dinma haka ta fito zuwa falon nata daya wadata da qamshi,tayi kyau cikin wata fitinanniyar mai zubin straight gown,saidai tsahonta iyakarsa qauri,ta daure kanta da band kalar kayan,sai qamshi da sheqi gashinta yake. Wayar jawahir take amsawa,suna magana ne kan wasu taruruka da sukayi order wadanda suka iso,suna hannun jawahir din,tace zuwa gobem idan ta samu ya samir din ya barta,zata leqo ta karba,idan kuma yaqi ta aiko koda yaron gidanta ne,don samir din wani mugun boyonta yake,kishinta yake kamar me,hatta da abokansa bai yarda ya shigo dasu gidan ba,musamman idan kaima ba da iyalinka kake ba,yafi ganewa su gama sabgarsu da kai a office,idan ta kama zakazo gida kuma ku tsaya daga daya daga cikin falukan da aka tanada daga can wajen saboda baqi,ki wajen shan iska dake cikin gidan. Wayarta ta jona charge sannan ta dawo ta zauna saman kujera,idanunta kan tv tana niyyar sauya tasha,saboda nan din news sukeyi. Kamar da wasa aka nuno wani mummunan hatsari daya faru daga kano zuwa kaduna,saiga fuskar hajiya shuwa ta bayyana,hannu da qafa sun fashe babu kyan gani,daga gefanta kuma fawwaz ne,wanda ko motsi ma baya iyayi. Maimaita sunan Allah take tana girmama girmansa isa da buwayarsa,duk da bata musu wani farin sani ba amma abun ya tabata,ta canza tasha tana rayawa a ranta,wala'alla sauran haqqin mutane dake bisa wuyansu ne ya musu haka. Tana jin tsaiwar motarsa ta daga kai ta kalli agogo,murmushi ya subuce saman fuskarta,baya saba lokaci,ta godewa Allah da ya bata mijin da bai iya yawon dare ba,bai kuma san zaman majalisa ba,daga gurin aikinsa sai masallaci sai gidan,idanma zaya fitan to tare zasu su dawo,idan kuma ya fita shi kadai,to momma ko daddy,ko hajiya qarama keson ganinsa,da ya gama kuma zai dawo gidansa,itace abokiyar hirarsa,itace abokiyar sirrinsa,da ita kadai yake hira yaji ya gamsu,a yanzu takarbe wani kason matsayi mafi girma na amirun,kamar yadda jawahir ta karbe na samir din a wajen amiru. Bata iya barinsa ya tsaya jiranta tazo bude masa qofa,don haka kamar ko yaushe yana zuwa yake shigowa,tana kuma tsaye tana jiran gama shigowarsa,saidai wannan karon kafin ta maida qofa ta rufe ya sureta yana juyi da ita,ta qanqameshi saboda yadda yake hajijiyar da ita,ya dakata ya sauketa yana qare mata kallo daga sama har qasa. Hakan yayi mata dadi sosai,bai taba ganin wani abu tattare da ita ba tare daya yaba ba,ita kuma abinda ke qara mata qaimi da zaburar da ita wajen ganin tayi dukkan abinda tasan zata burgeshi,don haka saita fara juyi a gabansa,yaga ko ina kenan gaba da baya "Wayyo haske na,zaki kasheni da raina....wannan kwalliyar na siyeta.....akwai biya mai daraja da zan miki.....saidai kafin sannan,na manta banyi sallama ba" da murmushi ta bishi,baya yadda ya shigo ya zauna baiyi sallama ba,saboda duk magidancin daya aikata hakan,a ranar shaidanun da suka biyoshi sun samu wajen kwana da kuma inda zasu ci abinci,amma matuqar ya yiwa iyalinsa sallama,to zasu dakata,su gayawa junansu cewa a yau dai cikin gidan basu da abinci basu da wajen kwana. "Amincin Alla ya tabbata a gareki 'yar aljanna" da wani qawataccen murmushi take takawa har inda yake tsaye,ta miqa hannu ta amshi jakar hannunsa,tabar masa envelop din kawai "Amincin Allah ya tabbata a gareka dan aljanna" saiya tako ya shigo falon,ya sake jawota gareshi,sannan ya miqa mata envelope din hannunsa,ya mata signer akan ta buda. Wani tsalle ta saki da qaramin ihu ta daneshi sosai bayan ta gama dubawa,sai kuma hawaye ya balle mata "Ashe da gaske mafarkina zai tabbata?,ashe zan iya zama qwararriyar artch?" "Definitely....." Ya amsa mata cikin bata qwarin gwiwa,saita rasa bakin magana,ta kifa kanta a qirjinsa ta sanya masa kuka. Wata makaranta ce ta musamman ya samar mata a wajen qasar nan,wadda babu ta biyunsu a universities da suke da qwararrun malaman dake koya course din,private uni ce,mai tsadar gaske,wadda bata taba kawota cikin kanta ba. Sulalewa tayi qasa saman gwiwoyinta zata fara gode masa,sai ya dakatar da ita,ya dagata yana cewa "Wannan godiyar marowata ce,ba kalar godiyar da nakeso ba kenan" Cikin murya me sautin kuka tace "Ka fadi kome kakeso,zan sadaukar maka dashi" matsawa yayi jikinta ya saka bakinsa a kunneta ya rada mata wani abu. Wani dan ihu ta saki na jin kunya,tana fidda idanunta waje,ta juya da sassarfa ta wuce zuwa dakinsu,yana dariya shima ya rufa mata baya,yana jinta can cikin bargonsa. *******Babban dakin taro ne wanda ya cika maqil da jama'a,saidai kuma duk da yawan jama'ar hakan bai hana wajen zama cikin tsari da doka ba,kowanne mutum na zaune a mazauninsa,hakanan kowa ya bada hankali kam stage din da ake gudanar da taron. Kallo daya zaka yiwa wajen ka fuskanci taron yafi kama da taron yaye dalibai,fararen fata sunfi yawa kamar yadda yake qasarsu ne,sai tsilli tsillin baqar fata,wadanda sukunin rayuwa da huwace ta ubangiji qaddararsu ta zartar da yin karatunsu cikin jami'ar. Taro ne da akayishi saboda miqawa daliban da suka kammala karatu a jami'ar wasu watanni da suka shude shaidar zama cikakkun artchecture,wadanda zasu iya aiki da kowanne kamfani a fadin duniya,sannan kuma an yarda da ingancinsu da kuma qwarewa da gwanancewarsu,bayan sun gabatar da jarabawa ta musamman. Cikin lanqwasashen harshensa baturen ya kira sunan "Ummu_kulsum ahmad" da wani irin sauti na rashin cikakkiyar hausa. Shuru wajen ya dauka,kowa na dakon fitowar dalibar data ciri tuta,ta kuma zo a sahun farko. Nima da kaina sai dana waiga sanda na fara jin takun takalmi cikin nutsuwa da aji,can na hangi wata mace chocolate color skin,sanye da lallausar atamfar England ruwan sararin samaniya da torches na ash a jiki da dark orange,dinkin riga me dogon hannu da plain zani,ta nannade jikinta da laffaya ta alfarma itama ruwan sararin samaniya. Daurin da tayi ya sake qawata fuskarta matuqa da gaske,saboda yaddda ta kawo daurin goshi,ta kuma nannade gashinta samfurin nannadewar doughnut ta baya daga qasan daurinta. Wuyanta sanye yake da wata siririyar sarqar gold me kama da chine na sarqa,saidai kuma akwai wasu qananun qulalai a jiki,iri daya da dan kunnen kunnenta abun hannu da kuma zoben dake yatsanta,kyawawan sexy eyes dinta saye cikin farin gilashi,wanda zaka iya ganin qwayar idanun nata tar,sosai Glass din ya qara qawata mata adon ya kuma qara mata kwarjini. Daga qafarta kuma highshoes ne,wanda yadan qara mata tsaho kadan,daga baya da bayansa ana daureshi da wasu irin igoyoyi masu kyau,wanda suka dace doguwar qafarta,jikinta na bada wani ni'imtaccen qamshin humrori na jiki dana gashi da kuma turaren kaya duka na kamfanin YERWA INCENSE AND MORE,qamshi me nutsar da zukata da sai ka kusantota sannan zakaji tashinsa. Daga gefanta kuwa the giant saraki ne saqale da hannayenta,murjajjen matashi,wanda ilimi hankali nutsuwa suka jiqashi,gefe kuma sassanyan kyau wanda baiyi yawan da zaka ganshi yana doso ka ba,saidai kuma baiwar kwarjini da Allah ya bashi,wanda ke firgita zukatan mata da sanyasu daka. Sanye yake cikin wasu suit da sukayi shige da color din kayan jikin rayuwarsa UMMUKULSUM,sun dace shima da jikinsa,kamar don shi aka samar dasu. Har yanzun yana nan da tsahon nan nasa,don kuwa....duk da takalma masu tsinin da kulsum ahmad ta sanya iyakacinta tsahonta har kanta kafadarsa. Sake maimaita kiran suna kulsum din akayi,dai dai lokacin da suke qarasowa wajen,yaci gaba da riqe hannunta har suka hau saman step din,ta qarasa ta karbi certificate din,saidai tana karba ta miqawa samir,sai mai gabatarwa ya bata abun magana. Cikin tsaftataccen turanci da sai ka dauka dashi aka haifeta a bakinta ta fara magana "Wannan shaidar tashi ce....domin kuwa shine yafi cancanta ya kuma fi dacewa da ita....." Sai ta daga kai tana dubansa cikin ido "Mijina....aljannata....rayuwata,kuma duniyata gaba daya,na gode karo na babu adadi cikin rayuwata" tana kaiwa nan ta miqa abun maganar ga mc,saidai kafin takai ga juyowa har tafi ya karade wajen,saboda yadda suka burge kowa,ya kama hannunta ya hade cikin nasa sannan suka fara saukowa cikin nutsuwar da zata bayyana maka yana matuqar ji da ita cikin rayuwarsa,kuma wani sashe ce me girma a tattare dashi. Ganin yadda dakin taron ke sake yamutsewa da mutane kala kala,da kuma manyan kamfanoni daketa kawo mata invitation letter suna gayyatarta zuwa kamfanoninsui,sai ya janye abarsa,sai daya bude mata side dinta ta shiga kamar yadda ya saba duk sanda zasu fita ko zasu dawo tare,sannan shima ya shiga ya tada motar. Ta gefan idanunta taketa satar kallonsa,a karo na qarshe ya kamata,sai yayi caraf ya kama hannunta da hannunsa guda daya,ya damqe cikin tafin hannunsa. Murmushi suka saki lokaci guda,sai ta kwantar da kanta a kafadarsa "Am proud of you the giant saraki" murmushi ya fitar me sauti,ya saki hannunta ya kama hancinta yadan matsa,ta saki qaramar qara "Zaka ciremin hancina.....salon ka sani na koma mummuna,kaje ka auro wata ni ina gefe?" Murmushi ya sake saki,cikin yanayin da zai nuna maka yana cikin zallar nishadi yace "Ko yaya ummukulsum dita take ina sonta a haka,zan kuma ci gaba da sonta,babu wani abu a duniya da zai tsaidani daga soyayyar da nake mata......ita din rayuwata ce,ta bani rayuwa ta kuma tabbatar da rayuwar tawa cikin farinciki.....mace ta biyu mafi daraja a wajena" idanunta ta lumshe tana jin farinciki na ratsata,wannan sunan na sanyata taji kanta ya fashe a duk sanda ya furta mata shi,mace ta biyu mafi daraja cikin rayuwarsa,sai ta qara lafewa a kafadarsa,tana ta sakin murmushi,farinciki na cika zuciyarta. Gidan da suke bashi da nisa da inda aka gudanar da taron,don haka cikin mituna biyar suka isa,ya bude mata qofa ta fito,sannan ya taka mata gar qofar gidan,ya sanya key ya bude mata ta shiga "Bakici komai ba na sani,saboda zumudin tafiya wajen taro,ki shiga,zanje yanzu na samo mana abinda zamu ci" sai yadan ranqwafo yayi kissing forehead dinta sannan yaja da baya ya rufe mata qofar. Idanunta ta lumshe tana sakin nannauyar ajiyar zuciya me hade da murmushi,ta koma da bata ta fada saman daya daga cikin kujerun dan madaidaicin falon,har yanzu bataga miji kamar nata ba,sam batayi kuskure ko daya ba idan tace mijinta yafi na kowa,tun daga aurensu da samir kawo yanzu shekaru bakwai kenan.....farinciki ne yake shigowa cikin rayuwarta daki daki gami da tarin alkhairai,kamar yadda yayi alqawari,tun gabanin ta gama karatunta ta kuma samu shaidar kammalawar ya bunqasa sunanta,tayi shuhura a duniyar zane,zane kama daga wanda idanu zasu iya gani,da kuma zane na ilimi,kama daga zanen na planning din gida ma'aikata kamfanunuwa makarantu xuwa gidaje,da designs da za'a yiwa atamfofi zuwa laces da sauransu,ba zata iya tuna irin alkhairin data samu a rayuwarta ba sanadin zane,wanda kome ta zama din samir shine jagoranta,wanda yayi ruqo da hannuwanta daga duhu izuwa haske. Zumbur ta miqe,a daren yau ta shirya faranta masa fiye da yadda yake hasashen zaya samu daga gareta,zata maida wannan daren na musamman,zai kuma shiga cikin jerin darare masu tsada daraja da kuma tarihi cikin rayuwarsu. Kayan jikinta ta fidda,baya ta duba agogo,gab ake da sallar isha'i,saboda dama taron daga yammaci aka farashi zuwa dare,ta daura farin towel yalwatacce,sannan ta daure kanta da wani,sabida batason ruwa ya taba gashin ba tare da samir ya mori gyaran da tayi masa a daxun da safe ba,idan hakan ta faru,sai take ganin tamkar tayi asarar kudinta ne,ko sau daya bata bari tayi wani ado ko kwalliya ba tare da samie ya zama mutum na farko da zai gani ba. Ta jima tana wanke jikinta kamar wadda ra jima dayin wankan,bayan ta cika ruwan wankan da turarukan wanka masu sumar da tunani da hankali sannan ta fito. Tana fitowar wayarta na tsuwwa,data duba sai taga jawahir ce,wadda tayi serving number din tata a yanzu da maman yara,saboda duk sanda samir ya kwasheta yawo wani waje ita suke barwa yaran ta hada da yaranta ta riqe har su dawo,shi din samir wani abu Allah yayi masa,tafiya koda ta sati daya ne bai iya tafiya ba tare da kulsum din tasa ba,momma tace ita abun ya isheta,ba za'a yita mata jele da yara ba,su din dai da sukaga zasu iya sai sun dawo,Allah raka taki gona,ummanmu kuma ta goyi bayan momma,wani lokaci shima amirun idan ya tashi nashi abun sai hajiya qarama momma ko ummanmu s karbesu,hakan ya sanya yaran suka shaqu sosai da kakanninsu. Murmushi tayi ta daga video call din da take mata,ta maqale wayar yadda zata ganta sosai,ta amsa wayar bayan ta janyo mai ta fara shafawa. Sai data fara da yiwa kulsum da samir tsiya kamar yadda suka saba koda yaushe sannan ta dora "Kozu ku karbi yaran nan,muma zamu tafi namu honey moon din" dariya sosai ta kulsum ta saki "Sharrin da zakiyi mana kenan?" "Eh mana,jiya har sun fara maganarku wallahi,jiya da mukayi magana da ummanmu bakiga fadan da tayi ba,wai takardar meye da itama sai an mata wannan takakkar an karbota" "Tayi haquri,an karbo certificate dazu,abinda ya rage mana tahowa,kuma ina tunanin a satin nan zamu taho" "Ya daifi gaskiya" ta fada tana hararta,dariya kulsum ta sakeyi "Lallabani yarinya,idan ba haka ba kamar a kunnen yayanki abinda kikamin" "An gaya miki yanzu ina tsoro?,nima fa ina da me taremin din nan,kawai kara muke muku ni da hubby na,amma tunda abu 'yar hakan....." Qarar bude qofar dakin da jawahir taji ya sanya ta saurin katse maganar da takeyi,don ta tabbatar saraki ne ya shigo,ta goce tana dariya,ta jonasu da yaransu. Kyawawan twins guda biyu,identical twins ma kuwa,masu kama da mahaifinsu sak,irin jinin professor rashid,wanda a idanu zaka basu shekara takwas,saidai shekararsu biyar biyar kacal,bayan auren iyayensu da shekara biyu Allah ya albarkacesu da samunsu. A hankali ya qaraso bayanta sanda take magana da yaran,tunda ya shigo tayi matuqar daukar hankalinsa,saboda wani qyalli da kyau da fatarta ta qarayi. Dab da bayanta ya tsaya,ya dora habarsa saman kanta,kasancewar ya fita tsaho,murna ta kama yaran kamar su shigo ta wayar. Taso zamewa ta qarasa shirinta,saboda tasan hirarsa da yaransa bame qarewa bace,amma ya hanata,ko yaya tayi gefe zata goce sai ya tarota,daga qarshe da qafafunta suka gaji da tsaiwa tilas ta sulale a jikinsa ta kwanta,tana ta murmushi tana sauraren hirarsu,har sai da wayar jawahir din ta saka low battery sannan aka haqura,ya dangwala yatsansa ya kashe kiran,saiya maida hankalinsa kanta. Dagota yayi gaba daya ya dorata saman madubin yana fuskantarta,itama idanunta saman fuskarsa,ido daya ta kashe masa tana murmushi,saiya kama kumatunta yaja "Yau akwai jan magana kenan" wannan shine salon furucin da sukewa juna a irin wannan lokacin,kai ta gyada sannan tace "Amma yaran nan fa....." "I know,nima nayi kewarsu,naso ki rakani kallon wasan polo,but na fasa,ina buqatar jin dumin yarana.....sai me kuma?" Kafadunta duka ta kada "Babu" "Ni kuma akwai" "Yes sir....ina saurarenka" "Me yasa kikayi rejecting duk wata gayyata ta daukarki aiki da manyan kamfanoni suka miqo gareki? Bayan kina da right nayin mu'amala da kowa ta fannin zanenki" Qawataccen murmushin daya sake narka masa zuciya ta saki,sannan tamiqa santala santalan hannayenta ta dorasu saman kafadarsa,ta sake matsowa dashi sosai dab da ita,har ya zamana suna musayar numfashi "Kaine baban kamfani na,kaine arziqi na,kaine kuma jarina......a yanzu bazan iya aiki qarqashin kowa ba sai kai,saboda babu wani abu da nake da buqatarsa a duniya da ban samu ba.....hakanan duk abinda zan buqata a gaba nasan da cewa zan sameshi IN SHA ALLAH,sabida ina tare da jarumin namiji,mijin da yafi na kowa" dire maganarta yayi daidai da daukarta caraf daga saman madubin yayi gado da ita,salon yadda take masa maganar salone da bazai iya kaucewa tarkonta ko haquri da ita ba. *_TO NIDAI DAGA NAN NA FICE NA BASU WAJE,KUMA ANAN LITTAFIN DABI'AR ZUCIYA YA DAKATA,KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MANA,YA BAMU LADAN DAKE CIKI_* *_DABI'AR ZUCIYA ce son rai_* *_DABI'AR ZUCIYA ce son kai_* *_duk kuma wanda ya biye ma wadan nan abubuwan yana tare da nadama da dana sani,kana da iko da damar da zaka iya DABI'ANTAR DA ZUCIYARKA KAN KYAKKYAWAN AIKI,qarfi bawai a jiki kawai yake ba,a'ah qarfi yana ga mutumin dake iya mallaka da kuma sarrafa zuciyarsa_* *_Annabi S A W yana cewa akwai wata tsoka jikin mutum,idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,idan ta baci kuma dukkan jiki ya baci,yace ku saurara itace ZUCIYA,ALLAH YA BAMU TSARKIN ZUCIYA_*🤲🏽🤲🏽 *_BAZAN RUFE BA SAI NA MIQA GODIYA GA 'YAN AMANAR ZAFAFA,WANDA BASA GAJIYA DA SIYAN LITTAFINMU,ALQAWARIN ALLAH YAKAI MUKU A KODA YAUSHE,ALLAH YA SADAMU DA ALKHAIRI,YA KUMA SAKE HADAMU A WANI SABON KAFCEN NA GABA IN SHA ALLAH_* *_DUK INDA AKAGA WANI KUSKURE,TO AJIZANCI NE IRIN NA DAM ADAM,WANDA YAKE TARA BAI CIKA GOMA BA_* *_FA SUBHANAKALLAHUMMA WA BI HAMDIKA,ASHAHADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'A TUBU ILAIKA_*🤲🏽🤲🏽🤲🏽🤲🏽🤲🏽