*BAK'AR TA'ADA* *NA* *Surayya Dahiru Gwaram* *(Mrs M.I. Nashe)* *Marubuciyar Halin yau da Sabo da kaza*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *Rok'on addu'arku*! *A irin wannan ranar ta 09 ga wata 09 shekarar 2000. Ubangiji ya karbi ran mahaifiyata. Dan haka ina baran addu'arku dan nema mata raham da gafarar Allah daga bakunanku masu albarka dan Allah*. *Haka nan ina mika sak'on ta'aziya ta ga dukkan musulmai bisa babban rashin da muka yi na bijimin malaminmu kuma uba*. *Sheikh Abubakar Giro Argugun* *Allah ya jikan magabatanmu gabad'aya kwata.* *JAN KUNNE* *KADA A TA'BA MINI LABARIN NAN, KO KARANTA SHI A KOWACCE IRIN KAFA TA SADARWA BA TARE DA IZININA A RUBUCE BA*. *IDAN KUMA AKA YI KARAMBANIN TABAWA, ZA'A FUSKANCI TUHUMA DAGA LAUYANA BAR MUSTAPHA ISA GWARAM*. *GARGADI*. *WANNAN LABARIN KIRKIRARREN LABARI NE* *BA SHI DA ALAKA DA KO WANNE MAHALUKI*. *IDAN KIN CI KARO DA RAYUWAR DA TA YI KAMANCECENIYA DA TA KI, KO WANINKI, TO ARASHI NE*. *DOMIN MANUFAR MARUBUCI ISAR DA SAKO DA HANNUNKA MAI SANDA A CIKIN ZAMANTAKEWARMU*. *LITTAFAN SURAYYA BASA NUFIN HABAICI KO SHAGUBE GA RAYUWAR WANI KO WATA.* *NA GODE*. *GODIYA GA* *SADIK ABUBAKAR* *NA GODE MADALLAH*. *GAISUWAR GIRMA GA IYAYENA KUMA MARUBUTA* *HAJ SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI ZARIA*. *HAJ HAFSAT C SODANGI*. *HAJ MARYAM KABIR MASHI*. *HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM*. *YABO GA* *K'AWATA JAMILA JANAFTY* *IDAN DA WANDA NA GAMSU DA TULIN SOYAYYARTA GA RUBUTUNA DA CIGABANSA TO KE CE* *DUK WATA KALMA TA YI KA'DAN TA FAYYACE GIRMAN SHA'ANINKI A WAJENA* *INA FATAN UBANGIJI YA SHIGA AL'AMARIN KI, YA BAKI MIJI NA GARI*. *GAISUWAR SADA ZUMUNCI GA MARUBUTA* *Sumayayyah Takori* *Binta Umar Abbale* *Fadilah lamido*. *Hassana D'anlarbawa* *Zainab MAZAWAJE* *Lubna Sufyan* *Nazifa Nashe* *Ayusha Muhd* *Nana Diso*. *Kulsum Baffah*. *Safiyya Um Abdul* *Umm Asghar*. *Aisha Dansabo* *Aisha jos* *Zee Kumurya* *Da dukkan y'an kungiyarmu ta lafazi*. *FATAN ALHERI GA IYAYEN D'AKINA*. *HAJ HALIMA D'ALHA SHEHU* *HAJ RABI SANI* *HAJIYA HALIMATUS SA'ADIYA* *HAJIYA HADIZA FARI*. *HAJIYA ZAINAB ABDULWAHAB* *ALLAH YA HA'DA Y'AY'ENKU DA MUTANAN DA ZASU MUSU KARAMCI FIYE DA YADDA KUKE MINI, INA MATU'KAR GODE MUKU*. *TUKUICIN LABARIN SUKUTUM GA* *AISHA MUHD LAME* *ALLAH KA SO AISHA, KA FARANTA MATA, KA BIYA MATA BU'KATUN TA NA DUNIYA, KA BATA BABBAN RABO A LAHIRA*. *IDAN AKWAI WANDA JINI BAI HA'DAMU BA, NA KE DAKACEN INA MA JINI YA RATSA TSAKANINMU TO AISHA LAME CE MAI KAYAN Y'AN GAYU TA ORIFLAME* *SURAYYA DEE TA GODE, TA YABA MIKI, UBANGIJI YA TAYA NI GODE MIKI*. *Doka mi lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha Babban laifine da yake dai-dai da satar Dukiya* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*. *1&2*. *SHIMFI'DA*. Sunana Asiya Sani Toro. Amma mafi yawa da Yabi ake kira na a dalilin mahaifiyata ta yi aikin Hajj da ni a cikinta. Mama ce kawai bata kira na da hakan sai Asiya saboda tana adawa da Yabi tunda ana nufin nima Hajiya ce. Gidanmu babban gida ne a garin na Toro domin ko yaro k'arami ka tambayi gidan Marina zai nuna maka. A dalilin asalin kakanmu da ya zo daga Kano ya fara kafa wannan sana'ar a garin. Fiye da shekaru saba'in kenan, amma har yau ba'a juya wa sana'ar baya ba, duk da dai an zamanantar da ita, ba kuma cikin gidan ake yin ta ba saboda warinta. Gidanmu babban gida ne k'warai da gaske. Idan na ce babban gida ina nufin mai d'auke da ahali daban daban masu yawa. Ko a k'ofar mahaifinmu Alh Sani (Baban Marina) da shi ne babba mata uku ne. Hajiya Habiba ita ce uwargidan mahaifinmu, mace mai k'ifadi da kutunguila. Duk wani rikicin da yake k'ofarmu, dama cikin gidan tana da sa hannu, ta tsani ta ga ko wanne irin cigaban d'an wata sai nata yaran kawai. Sannan komai cikin dabara da girma ta ke yinsa, ba kowa ne ya fahimci irin makircin da take k'ullawa ba. Sai mu da mu ke rayuwa da ita kullu yaumin. Ta kanka ne komai, ta yadda komai ta shimfi'da akan haka za'a tafi, sai dai ranar da ta samu bacin rana Baba ya bijire mata. Ya'yanta biyar. Yaya Musa, Yaya Hadiza, Yaya Salamatu, Yaya Indo sai autarta da ta haifa bayan ta shafe shekaru masu yawa Nazira, wacce ita ce sa'a ta ta girme ni da wata uku. Sai Mahaifiyata Hajiya Àsma'u wacce muke kira da Goggo. Ba dan tana mahaifiyata ba, amma mace ce mai sanyin hali da matsanancin ha'kuri. Idan na ce ha'kuri, ina nufin ha'kuri gangariya, irin ha'kurin nan da mai yinsa kan saka a alummar da suke kewaye da shi su halaka saboda hakkinsa da za suyi ta d'auka. Yaranta takwas cif. Yaya Salisu, Yaya Rabi'u, Yaya Ummi, Yaya Adnan, Yaya Ali, sai ni Yabi, duk dai bani nake bin Yaya Ali ba, akwai wani ya rasu ne, sai Anas da kuma autarmu Ikilima. Wannan yawan yara da mahaifiyata ta tara a d'akinta, kuma maza, ya sanya Mama ta tisa ta a gaba da masifa da tuggu, kusan kowa a gidan ya tsani mahaifiyarmu, ba kowa ne yake mua'amala da ita ba. Duk gidan bakinsu daya ne a kanta. Duk kuma Mama ce ta b'ata ta, take adawa da duk wanda zata ga ya mu'amalan ce ta Shi yasa hatta mu yaranta bamu da wani kwarjini har a wajen Dada kakarmu da ita ma tana cikin gidan bangarenta daban. Sai Hajiya Sahura muna k'iranta da Innah. Yaranta biyar Na farkon ma mun dan girme masa ka'dan Ubaid, Ubaida sai Abida, Hajara, Ismail da autarmu gaba'daya Saliha. Duk yadda Mama ta so wajen raba zumunta a tsakaninmu bai yi tasiri a tsanina da Nazira ba. Duk yadda bata kula ni, bata sakar mini fuska hakan bai hana ni yin dabdala a dakinta ba a dalilin Nazira. Bare ita kuma da dakin Goggonmu take kwana.. Sau dubu gara Inna akan Mama. Domin dai ba yadda za'a yi Inna ta ha'da wa Goggo sharri, ko ta tsokane ta da gangan, amma bata wani girmama ta a dalilin Mama ta dabarbarce ta, ta hana ta yin mu'amala da Goggo ta hanyar fa'da mata Goggo ce da gida, duk yaranta maza ne, idan Alhaji ya mutu duk su din y'an kallo ne. Da na fara mallakar hankalina sai nake tambayar kaina wai mene ne mahaifinmu ya mallaka da har ake fatan ya mutu? A da kam ya yi arziki k'warai da gaske, domin duk girman Gidanmu shi ya zaga ye ya gine shi, sannan mafi yawa na cikin zuri'arsu shine ya biya musu suka sauke farali. Amma tun shekarar da aka haife ni ya ha'du da y'an damfara suka yi masa sanadin karayar arziki, har yanzu da muke da shekaru goma sha biyar bai farfad'o ba. Yan'uwansa kuma kowa ya zuba masa ido ya zama abin tausayi. Amma a hakan Mama take fa'din Goggonmu ce zata ja komai. Wannan kenan. Sai k'ofar Alh Badamasi(Baban Tsakiya). Matansa biyu da yara sha biyu. Na uwargidan Hajiya guda bakwai . Babban d'anta Yaya Jabir, Zakiya, Jamila, Hauwa, Firdausi, Aisha sai k'aramarsu , Basira. Nan Firdausi ce warinmu. Sai amaryar Momi tana da yara biyar, Nasiru, Naziru, Sararu, Rumanatu da Kubrah. Anan ma Saratu ce sa'armu. Sai kofar k'arshe ta Alh Iliya (Baban kasuwa). Matarsa daya da yaransu shida. Amina, Aminu, Maijidda, Kaltume Abba andda Aliya. Maijidda ce sa'armu Sai wajen kakarmu Hajiya Binta! wadda Yaya Umminmu sunanta ta ci. Kowa Dada yake ce mata, wata irin tsohuwa mai wahalar sha'anin gaske. Tana daga zaune rikicin da take yi ba dan ka'dan bane, haka nan bata damu da ha'din kai a tsakanin ahalin gidan ba. Domin bayan su Babanmu akwai yan'uwansu mata biyu. Bangaren Dada ma hawa biyu ne, domin akwai wata k'ofar a can ciki bayan ka wuce k'ofarta ta farko, sannan ana iya fita waje ma ta wannan wajen Sai dai kofar a rufe take. Amma ba kowa ciki sai kayan ajiye ajiye da dangin kayan noma da tarkace. Babar Bulkachuwa(Hauwa) ita ta biyo Baban Tsakiya, tana aure a Bulkachuwa, mijinta Alh Yusufu babban d'an kasuwa ne a kasuwar kayan miya ta Muda lawal a Bauchi. Ita ce amarya amma sai a kanta ya samu haihuwa ta tsaya masa, uwargidan wabi take yi, ma'ana idan ta haihu sai su koma. Tijjani ne babba sai Aliyu, sai Nasir. Sai bayan haihuwar Nasir ne uwargidan ta haifi Maryam da kuma Hafsa. Daga nan sai Babah ta sake haifar Ihisan. Kenan yaranta hudu na uwargidan kuma biyu. Tijjani ya taso cikin wani irin gata a wajen mahaifinsa a dalilin tsawon lokacin da ya shafe babu haihuwa. Sai dai kash gatan ya zame masa d'an zani domin gaba'daya sai ya kangare, tun yana karaminsa ya ko yi fitina iri iri, shine kame kaji da awakin jama'a yana siyar wa, gaba'daya ya ki kar'bar tarbiyar da ake ba shi a sanadin duk abokansa lalattu ne. Duk yadda Baba ta Bulkachuwa da mahaifinsa suke son fige masa wannan dabi'ar abin ya ci tura. Akan dole suka raba shi da garin, suka dawo da shi wajen Mahaifinmu da Baban Tsakiya, tunda su din zafi ne da su ainun. A lokacin bai fi shekaru sha biyar ba. Sa'an Yaya Salisu ne, amma shiriritarsa ta mayar da shi cikin kannensa su Anwar, duk dai su din ma sun raina shi, sun ware shi ba wanda yake son a ganshi da Bulkachuwa saboda munanan TA'ADODIN sa. Yayin da mu muke k'ananu sosai Sai Baba Maryo ita ce autar Dada. A nan Toro take aure, yaranta biyar amma biyun farko na wajen Dada da ta haifa da mijinta na farko. Anwar da Nasiba. Yaya Jabir, Yaya Rabi'u, Yaya Abba da Yaya Anwar duk sa'annin juna ne tare suka taso, fikon junansu mafi girma watanni biyar ne. Kazalika muma y'anmatan tare muka taso. Duk da babu ha'din kai ko ka'dan a tsakanin iyayenmu mata, hakanan ni da Nazira an fi mayar da mu banza da wofi a dalilin mahaifinmu ba shi da shi, ga shi dai shine babba amma ya zama fanko, ya zama wofi dai dai da shawara ba a yi da shi. Duk yadda ba wani shakuwa a tsakaninmu irin na zumunci, in dai fita ne, to tare ake tafiya zuwa makarantar boko ko Islamiya. Haka za'a ganmu zaratan y'anmatan reras da mu. Kusan ba'a ta'ba yin y'anmata da muke sa'anni da yawa a gidanmu irin akan mu ba. Domin mun doshi bakwai Ni Yabi, Nazira, Basira, Firdausi, Maijidda, saratu, Nasiba. Dukkanmu kowa turbarakallah babu makusa, tunda asalin Kakarmu Dada Bafulatanar Lame ce asalin fulanin Mali. To kusan dukkanmu mun samu tsayi da gashinta. Duk da ni din bani da tsayi, yar shafal ce, matsakaicin kyau ne da ni amma fara ce sol, sannan kuguna a dan bude yake ka'dan, sai dai kirjina kam ko na kai shekarun budurci sosai baza su yi wani girma ba. Kowanne irin sutura na saka sai ta yi mini kyau. Duk da kayan nawa mafi yawansu masu sau'kin farashi ne a dalilin mahaifinmu baya samun sukunin yi mana sutura. Abinci ma da wahalar gaske muke cinsa, duk da ga yan'uwansa nan suna cin duk abin da suke so. Amma ba'a yi mana kara ni da Nazira idan zasu yiwa y'ay'ensu sutura su ha'da da mu. Ko da yake Nazira ta fini sutura a dalilin Mama tana sanya yayyenmu na d'aki suna yi mata. Yaya Salamatu tana d'an yin kara tana bada kuncen har da ni, da yake babu laifi mijinta yana da rufin asiri, amma Mama bata bari a bani, sai dai da Yayar ta fahimci hakan sai take bani a b'oye tana fa'din ba sai na fa'da ba. Ni kuma bana iya yin shiru sai na nuna wa mahaifiyarrmu, ita kuma sai tasan yadda ta yi ta yi mata godiya tana kuma jan hankalina na kula da ita. Sosai nake ganin kirkin Yaya Salamatu duk da dai sai ta zab'e mafi kyau ta bawa Nazira ni kuma ta bani saffa saffa, amma dai ta k'ok'arta a yadda mutanan yau suka dauki y'an uban ci. Yayata da muke d'aki d'aya ita ma tana cikin matsanancin babu, domin duk talaucin gidanmu a hakan Goggo take tara mata k'anzo dan ta ci ita da yaranta. Wani irin bahagon miji take aure, bai san hakkin komai ba sai hakkin auratayya tunda kusan duk shekara biyu suke haihuwa ita da uwargidanta tamkar masu gasa. Dan ma yanzu uwargidan ta daina yi. Hatsin da za'a yi tuwon dare kawai zai bayar, dai-dai da cefanen miya mace ce zata yi, da safe a yi dumame a ci yadda ya samu, ba dan an koshi ko dan da'di ba. Da rana kuwa ko wacce ita zata ciyar da kanta da y'ay'anta. Ba maganar sabulun wanki bare a je ga na wanka. Yaya Ummi kyakkawar mace amma wahalar da miji ya sakar mata da muguntar kishiya ta saka duk ta fita a hayyacinta. Domin ita ce mai k'ananun yara, ita d'ayar al'amura sun fara saisaita mata, tunda manyan ya'yanta sun kawo k'arfi, amma komai zasu kawo a boye ne, ita kawai zata amfana. Duk cikin yaran gidanmu tafi kowa shan wahala a gidan aure. Shi yasa take a ware, sai idan Yaya Rabi'u ya d'an figi wani abu ya kai mata a dalilin suma suna fama da rik'ewa Babanmu gidanmu. Rayuwar ta yi mana tsananin gaske, mahaifiyarmu ha'kuri take yi kan ha'kuri. Kuma wani abin mamaki da Mijin Yaya Ummi mai tarin dukiya ne amma fa baya iya ci, sai dai ya yi ta lissafin kadarorin da ya tara. Manyan yaransa sai fatan ya kauce su ci abin da bai bari sun ci ba suke. Gaba'daya tausayin Yaya Ummi nake ji, abubuwa sun yi mata yawa, ga tashin hankalin gidanta, ga azabar yan'ubancin da su Yaya Indo suke yi mata. Sun wareta, Yaya Salamatu ce mai sassauci kawai. Duk sadda ka je gidanta haka zaka ganta tamkar mahaukaciya. Wankau take yi, kamar me? yini take tana wanki. A hakan take samu ta wanke kayanta da na yaranta, ta kuma samu ku'din da zasu ci abinci da rana. Duk da dai bashi yafi yawa, sai ta yi wanki sau nawa ba a biya ba. Na kan yi mamakin yadda mutanen yau suka shagala da fa'din Annabi (S.A.W.) na cewa "Mafi adalcin mutum shine Wanda yake biyan hakkin Wanda ya yi masa aikin wahala kafin guminsa ya bushe. Amma a wannan zamanin sai mutum mai wadata ya bawa miskini aikin wahala amma biyansa hakkin wai sai ya zama bashi, abin kaicon ma idan an yi masa aikar a bayar da ku'din nan, sai ya zama laifi. Mace ma'aikaciya sai ta bari ku'din mai wanki, ko markade, ko kuma mai dakan hannu ya taru a kanta. Ba tare da yarjejeniyar sai k'arshen wata zata biya ba. Anya kuwa muna son ganin dai-dai jama'a? Wannan wahalar data taru ta yi mana k'awanya ya sanya na mayar kitsona na ku'di. Domin tun daga alhamis idan na fara k'itso har lahadi, amma ba wanda zai cire ko da sisi ya bani a cikin matan gidanmu da duk kusan sati nake yi musu kitson su da y'ay'ansu. Kuma na sani hakan baya hana su karbin ku'din kitson a wajen mazajensu, ko iyayensu. Bisa shawarar Nazira na daina yiwa kowa kitso sai ta biya. Iya y'an k'ofarmu kawai nake yiwa kitso kyauta. Mama kuwa bata yarda ta ba ni kanta dama. Amma ina yiwa Inna da Gwaggonmu. Da kuma yan'uwana na k'ofarmu. Ai wannan bijirewar da na yi akan sai an bani ku'din kitso ya sake jefa tsana a tsakaninmu, domin duk inda Mama ta zauna sai ta ce "Uwarta ce ta kitsa mata, me za'a yi da irin wannan haihuwar a ce ba zaka bari aci arzikinka ba?" Iyayenmu maza da suka san suna biya basu dauki al'amarin a wani abu ba. Domin suna k'yashin a ce mu d'in muna da mamorar da zamu yi musu alfarma. Domin fa'di suke yi "Idan ku'di ne ku bata kudinta daidai da yadda na waje zasu biya ta, ko kuma daidai da wanda idan kun je wajen bare zaku bayar. Ita ce bata gaji arziki ba". Yayin da muka k'udire a ranmu ni da Nazira ba wanda zai sa na yiwa yaransa ko matarsa kitso akan dole domin suma basu taimake mu ba, dai-dai da ku'din islamiya da bai taka kara ya karya ba, basu ta'ba ha'da mu da y'ay'ansu sun biya ba. An sha koro mu da sauran k'annenmu, akan ku'din islamiya. Yayin da sauran yaransu basu da wannan matsalar. Idan zamu yi wata a zaune, Mahaifinmu ko iyayenmu mata basu samu sukunin biya ba, ba wanda zai dube mu. Dada kuma ba zata ce wane biya wa yaran nan ba. Ita kanta ta manta irin da'din da Babanmu ya jiyar da ita. A yanzu kam ta mayar da shi da dukkan ahalinsa tamkar wasu barori a cikin ahalinta. Tarin Baban kasuwa ya fi maganar Babanmu sau dubu. Tunda shine yafi kowa rufin asiri, sai Baban tsakiya. A batun soyayya kuwa kowa shaida ne Dada bata ha'da lamarin Yaya Anwar, da Tijjani da kuma Nasiba da kowa. Sun fi kowa lasisi a gidan, gasu dai ba y'an gidan ba ne tunda iyayensu mata ta haifa. Amma sun fimu gata da gadara a gidan. Yanzun nan Dada zata hau ihu matu'kar aka ta'ba guda a cikinsu. Sai yaran Baban kasuwa, sai na Baban tsakiya. Hakan dai hawa hawa abin yake. Canjin da nake samu a kitso ba k'aramin taimakona yake yi ba. Haka Gwaggo tana yin kokon safe, muna samu mu sha a ciki, har watarana a aikawa Yaya Ummi. Asusu na siya nake tura dan wani abu, domin ina matu'kar jin haushin yadda mu da gwaggonmu muke koma baya a gidan. Yaranta maza an d'ora musu nauyi mai yawa. Yaya Salisu ne kawai ya yi aure, shima ba wai wadatar ne da shi ba, aikin gini yake yi duk da ya yi karatu amma aiki ya yi wuyar samuwa tunda babu hanya. Su Yaya Rabi'u kuwa koami na gidan sune, Mama fa'di take ai sune maza, sune zasu taimaki ubansu, ga karatunsu su suke daukar nauyin kansu. Dan haka Gwaggonmu bata samun komai, amma idan an nutsu za'a fahimci kowa a kofarmu yana cin arzikin yaranta. Duk yan dakinmu ni ce mai tsiwa, ban dauko sanyin halin uwarmu ba. A tsaye nake kan kafafuna cak, haka zuciyata bata daukar raini. Sai dai kuma bani da kullaci, ina da saurin afuwa. A duk sadda na kalli Gwaggonmu da Yaya Ummi sai na tsinci kaina da yiwa kaina da Iklima addu'a samun miji na gari mai wadata, ko muma ma shiga sahun masu mutunci. Tun kafin hakan kuma sai Ubangiji ya hore mini iya yarfa kitso. Duk wata matashiya yar kwalisa a yankin nan ni ce mai yi mata kitso. A hankali sai na fara gwada lalle. Nan da nan sai Ubangiji ya sake haska mini. Layi ake yi mini na kunshi da kitso duk satin duniya. Muka fara dan warware wa, domin muna samun yan kuda'den yin bu'katar yau da kullum. Hatta Yaya Ummi ta d'an samu sau'kin matsatsacin da take ciki. Domin duk sati sai na cire mata wani abu. Da ku'din asusuna ya yi auki na fasa na siya mana kayan kwalliya masu sau'kin ku'di ni da Ikilima da Nazira, har ma da Ubaidan Innah. Sai kuma na sake siyan wani na k'udire niyyar dinki zan yi mana idan kudi ya taru. Tsawon dauki lokaci ina zubi, kafin na samu na yi mana y'an suturu ni da Iki. Ai Mama tana ankara da y'ar nutsuwar da muka fara samun kanmu a ciki, sai ta tayar da ballin sai na bar kitso, domin gashi yana yawa a gidan, ba dama ta zubo abinci, zata yi ta ganin gashi. Ko ina gashi ne, ta gaji da wannan k'azantar. A wannan karon Babanmu ya yi jarumtar cewar ba zai hana ni yin sana'a ba, tunda shi da kansa ya sani ba k'aramin rufa masa asiri sana'ar take yi ba. Kusan kullum sai na ba shi naira dari hud'u. Maganar maganina kuwa idan ba ni da lafiya, na dauke wa kowa. Dan haka sai muka fara saje wa da su Maijida. Tunda muma yanzu muna samun yan suturu babu laifi, duk da bai kai nasu daraja ba. Idan akwai abin da ya yiwa Mama tarnaki rashin kintsuwar Yaya Musa ne. Gashi dai shi ne babba, amma gaba'daya ya lalace, ya zama d'an iska, hakan kuma yak'i ya zame mata izna, a kullum cikin aibata yaran da ba nata ba take. Ta kuma gasgata hannu aka sawa d'anta, da kuma bakin mahassada. Ta kasa fahimtar rayuwa har yanzu. Tsabar kyashinta ta hana ya'yanta mata su tallafawa Babanmu da d'an abin da zasu iya . Kullum fa'di take ai hidima ta y'ay'a maza ce. Dan haka komai yaranta mata zasu kawo gidan to nata ne, sai ko idan dafaffe ne sai ta samma wadanda take so, wadanda bata so kuwa ko ta yi babu. Sai nake mamakin idan tana habaicin ku'din kitson da nake kar'ba, wai Gwaggo ta kasa bari a mori haihuwarta, ko ita wa ta bari ya mori tata haihuwar? Ko Babanmu da ya yi mata hidimar yaran ba dai tasa su kawo masa wani abu na tallafin gida ba tunda yana da k'ananun yara. Idan ma sun yi hankalin kawo wa to fa ita ce a hakku a kan kayan, ta dinga gadara kenan duk ba wasu kaya masu yawa ba ne, tunda dai ba wai ku'din ne da su ba, rufin asiri ne kawai. Sai nake mamakin wai mene ne manufarta ne? Da na kasa gane wa sai na ha'kura, amma hakan ya ja hankalina har nake sha'awar yin bincike da nazari akan gidan yawa mai dauke da mabanbanta iyalai. *GIDANMU ne kawai kwamacala ta dabaibaye shi?* *A GIDANMU ne kawai ake yin kasafi irin na kashin dankali ma'ana na sama ya danne na kasa?* *A GIDANMU ne kawai ake mayar da babba k'arami saboda ba shi da wadata ko kuwa?* *A GIDANMU ne kawai ake ta'ba yan ubanci ko kuwa?* *Ba k'aramin caji kwakwalwata take yi ba dan neman sahihohin amsoshi wadannan tambayoyin*. *Ayi bitar da nutsuwa domin wannan karon gidan yawa zamu kutsa sosai* VIP 1K. REGULAR 500. 2384876855 SURAYYA IBRAHIM ZENITH BANK. *ASSALAMU ALAIKUM* *Masoyan rubutun Surayya Dee na gaishe ku, na kuma yaba muku* *Dafatan zaku yi hakuri, ku bi labarin sannu a hankali, har ku fahimci sakon da nake nufin isar wa.* *Ba zan ce muku komai ba. Abu d'aya nake da tabbaci ba zaku yi nadamar bibiyarsa ba.* *Kawai fatana kada ku kosa da yanayin rubutuna.* *Allah ya taimakemu, Allah ya zaunar mu lafiya da y'anuwanmu da abokan zamanmu*. *Allah ya bamu lafiya, ya bamu hakuri da k'addarar da muke fuskanta a rayuwar nan*. *Surayya Dee* ✍️. *BAK'AR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *MARUBUCIYAR HALIN YAU DA SABO DA KAZA* •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *GODIYA* *INA MATUKAR GODIYA BISA ADDU'AR DA KUKA YI WA MAMA*! *ALLAH YA KARBA, YA BADA LADA*. *HAKA NAN INA NEMAN UZZIRINKU BISA RASHIN AMSAWA. DOMIN NA KARBI SAKON MUTANE SAMA DA DARI BIYAR, TUN INA AMSAWA HAR AL'AMARIN YA GAGARI KUNDILA*. *DUK WACCE BAN AMSA BA, INA AMFANI DA WANNAN SHAFIN WAJEN GODIYA TARE DA YABAWA A GAREKU GABADAYA* *ALLAH YA JIK'AN DUKKAN MAGABATANMU*. *KUNSAN DAI YADDA AISHA LAME MAKEUP ARTIST DIN GUDUYO, TA KWARE WAJEN SANIN HAKIKANIN MAN DA ZAI DACE DA KOWACCE FATA, WALA DRY KO OILY*. *BABBAN ABIN BIRGE WA DA KAYANTA FARASHI MAI SAUKI NE DA YA ZARTA NA SAURA SALAMA* *HANZARTA KI TUNTUBE TA DAN KI GA JERIN KAYAYYAKIN ORIFLAME KALA DABAN DABAN* *SANNAN TANA DA HADADDEN GANYEN SHAYIN DA AKA YI SHI DA GANYAYYAKI MASU SAISAITA JINI DA KITSE A JIKIN DAN ADAM.* *LAME TEA YAFI SHAYI MAE MADARA*. *IDAN KUWA KIKA CI LAME POPCORN INA TABBATAR MIKI KIN YI ADABO DA SAKE CIN WANI GUGGURU MATUKAR BA LAME POPCORN BA NE*. *07036662633*. *3&4* K'aramar hukumar Toro tana cikin k'ananun hukumomin jahar Bauchi. Duk wani mai nazari yasan yadda Ubangiji ya wadata Toro da girman k'asa. Ita ce k'aramar hukuma mafi girma a dukkan fa'din tarayyar Nigeria dama Africa ta yamma gaba'daya. Garin Toro an kasa shi zuwa Gundumomi uku. Gundumar Toro, gundumar Jama'a da gundumar Lame. Sannan akwai kabilu daban daban bayan Hausawa da Fulani. A karkashin jahar Bauchi ta ke amma tafi makwbataka da jihar Filato. Shi yasa garin kewaye yake da ni'imomin kayan itatuwa da rashin zafin rana sosai. Ba dan ina y'ar garin ba, Ubangiji ya dabaibaye garin Toro da tarin faloli Alhamdulillah. Dare ne amma ba ainun ba, mafi yawa mun ha'du a kofar Kakarmu Dada ana ta hira da tatsuniya. Kannenmu kuma sai wasan d'an dunmi suke yi. Dukkanmu y'anmata mu bakwai da muke kai d'aya muna zaune akan tabarma, idan aka dauke shalele Nasiba da take kishingi'de a jikin Dada. Sannu a hankali Dada take taunar goron bakinta tana mulmulawa. Kyakkawar dattijuwa mai kyakkawan jiki. Asalin Bafulatanar Lame ce, kowa kuma yasan asalin mutanan wannan garin fulanin Mali ne da kiwo ya saka suka tsallako Nigeria suka yi sansani a yankin na Lame. Wani ikon Allah mafi yawa na ahalinta sun samu kyawun halittar fulanin Lame. Haka muke y'an gidanmu son kowa k'in wanda ya rasa. Wani irin kallo take mana na kurillah. Ta kasa ha'kuri ta ce "Na fa'da muku dukkanku ku zauna cikin shirin ko ta kwana. Domin kuwa ba zaku fi haka gandare wa a gabanmu ba. Dukkanku abubuwa sun cika muku k'irji. Ko wacce a cikin ku wanki take yi a gabanmu, ina kallon zamani ni Binta! Muna cikin alhini. Allah yasa intingifarin da muke nacin yi mun samu rabauta ana karban sallarmu". Dariya ta kama mafi yawanmu. Ni da nake da kaud'i na ce "Dada Ashe ba'a karban sallarku ne?" Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Ai matu'kar kana da yarinyar da ka yi saken da ta fa'di a gabanka, to kuwa babu makawa sallarka bata isa gaban zati, daga bakin k'ofa ake dakatar da ita!" Nasiba ta ce "Allah ya kawo mafita. Yanzu biya mana karatun na yau". Nan da nan ta furzar da goron bakinta dan girmama karatun da zata d'ora mana. Ta tsume ta ce "Mu karanto na jiya". Muka ha'da baki wurin rera karatu cikin sigar wake muka ce "Idan attishawa ta sauko mana, idan wani bawa a kusa da mu ya ce mana "Rai ya hadu da Gafarar Allah!" Sai mai attishawa ya ce "Ya-hadi kumalle. Idan kuwa zamu ci adda'ami. Zamu fara da ambaton Allah. Idan koshi ya zo mana sai mu ce "Sawaba ta sauka akan me nemo wa da mai dafa wa". Dada ta murmusa tabbacin ta gamsu mun ri'ke karatun nata da kyau. Ta ce "Madallah!". Cikin alfaharin muna da fikirar fahimtar karatun da take yi mana. Ta muskuta ta ce "yau karatun yiwa kai rigakafi daga shaidanu da makarai zan dora muku". Muka ha'da baki wajen fa'din "Mun gode Dadarmu, Allah ya kara miki nasibi. Annabi yasan da ke". Ta numfasa ta ce "Ameen, a kuma tsananta yi mini rokon dacewa da shiga cikin masoyan SHEHU". Na kasa jure wa na ce "Ashe Dada ba zaki bar zancen Shehu ba? Kowa ya bar Allah da ma'aiki ai ya bar hanyar tsira." Nan da Nan ta fusata ta ce "kaico da Yabi! Yabi ba zaki tsira ba, waya yake inkari da jikan Manzo? Tabbas sai gafalalle". Na ci je na sake ce wa, Annabi dai aka ce mu ri'ke ba waninsa ba Dada, iyalan gidansa suna da girma da hakkin mu so su mu kare mutuncinsu. Amma ba'a ce a kai su wani bigire da zai iya zama halaka ba. Da kansa ya ce "Zan bar muku kura'ani da sunnata wato (Hadisansa) idan kuka bisu kun tsira. Amma ku kun shure komai, kun dauko shehu kuna neman mayar da shi abin bauta?". Ai kuwa ta sake harzuka ta ce "Wahalar rayuwa akan ki Yabi! Mai gadon taurin rai da kafiya, kaicon ki, kaicon ki! Da yi mini izgilanci Asiya". Jikina ya sabe da rawa a dalilin ba irin jan kunnena da Gwaggo bata yi mini ba, akan kada na sake na janyo abin da Dada zata dinga yi mini mugun fata. Ga shi ban ji ba, na yi sanadin da take fatan na dauwama cikin wahalar rayuwa. Kafin na ce komai sai ga Tijjani wanda mafi yawa an fi k'iransa da sunan garinsu Bulkachuwa. Wani irin zabgegen saurayi. Dogon gaske har d'an rankwafa wa ya yi ka'dan. Fari ne tas, irin fulanin Bulkachuwa, a murde yake, shi ba siriri ba, kuma ko ka'dan baya cikin masu kiba. Ga dogon hanci da ya k'awata doguwar fuskarsa. Baya ga hakan manyan idanuwansa ka'dai sun isa abin burge wa. Ban ta'ba ganin namiji mai jajayen lebe ba sai Tijjani kyakkawan gaske. Wani irin mutum mai saurin fishi, da k'arfin zuciya. Amma mai saurin saukowa da mantuwa. Illarsa d'aya manemin mata ne, a yadda a ke fa'da. Na shaida kuma duk wata budurwa ballagaza a Toro to kuwa budurwarsa ce ko kuma suna d'asa wa, shiyasa kowa yake jan kunnen y'arsa a kansa, barin ma ni, kullum ne sai Gwaggo ta ce kada na sake na bashi fuskar da zamu dinga doguwar magana. Gaba'daya dabi'unsa na tantiran yan-iska ne, sannan k'azami ne, baya damuwa da yin wanki sai kayansa sun k'are. A hakan kuma shashan y'anmata suke sonsa, ko da yake baya yarda ya fita da dattin sosai, yana wanke wa ya jira su bushe, guga ce sai ya samu ku'di, sai ya bayar da kayan ma a wanko a gogo masa, amma da wahalar gaske ya yi guga da kansa. Duk yadda Dada take kulafacinsa, matu'kar ya shigo muna nan sai sun haura da shi, domin yafi kowa takalarmu da magana, yana yi yana lumshe ido ta yadda zai sure zuciyoyinmu. A hakan ya yi nasarar yin wuf da zuciyar Nasiba. Idan Dada ta ga yana sakin maganganu ko lumshe ido a gabanmu ta dinga bagarar da shi, ko ta tsiri aiken sa, ko kuma ta ce mu je ta sallame mu, duk yadda take sonsa to bata son doguwar magana a tsakaninmu, kazalika kuma bata son a k'i gaishe shi. Burgar da yake yiwa mata ya sanya har yanzu bai bar dauke dauke ba, komai ya gani zai dauka ya siyar ya kashe wa budurwa ku'di. Amma iya kayan Dada yake dauka. A duk sadda take yi masa fa'da kuma zai waske ya ce bashi ba ne, ko kuma sharri ta yi masa, haka kuma sai ya d'auke mata wuta, har sai ta nemo shi ta bashi ha'kuri. Bayan soyayyar da take yi masa, yana sake samun alfarma a wajenta saboda sunan SHEHU ne da shi. Kullum bakin ta akan ya nutsu ne, ya bar shiririta ya kawo matar aure, tunda ga Yaya Salisu nan da yake sa'an sa tuni ya yi aurensa har matar ta haihu, amma shi ko maganar aure baya yi saboda sharholiya da mutuwar zuciya. Duk da k'arancin shekaruna ina tambayar kaina ko waye zai iya d'aukar y'arsa ya bawa Bulkachuwa aurenta? Tabbas sai idan yarinyar ta kasance shasha ce irinsa. Na tabbatar mahaifiyar Nasiba ba zata ta'ba bari a bashi ita ba, domin kuwa kowa nasa yake so, bare idan maganar gaskiya za'a yi bai cancanci a bashi ba, domin bashi da sana'a, gashi manemin mata, shiyasa kowa yake masa kallon shasha. A duk sadda Dada take yi masa fa'dan shigar da yake yi ta gajerun wanduna yana yawo a gari babu kunya, ko tara suma ya gegareta daga gefe, ko kuma wani zubin ya sauya launinta bayan ya mayar da ita cibiri cibiri. "Akan kunnena na sha jin tana ce wa "Saboda bamu da mutunci a idonka shiyasa kake iya zuwa gabana a hakan ko kuma gaban kawunanka". Ba jin nauyi yake ce wa "Tunda nake yin sallah a hakan, ai kin ga bai zama aibu dan kun gan ni a hakan ba. Domin Ubangijina ma a hakan yake gani na, kin takura mini fa Tsohuwa" Nan da nan ta zabura ta ce "Imaninika ai a makogaro yake shi yasa kake hakan, amma da za'a jarrabe ka da son wata yarinyar ba zaka yarda ka je mata a hakan ba. Alfarmar Shehu sai ka samu wacce sonta zai hanaka yin wannan shakiyancin. Tunda ka ki daina wa saboda Allah da Ma'aikinsa." Dariyar iyashege yake yi ya ce "Ni da nake da y'anmata kamar jamfa a Jos suna bina dan na so su, shine har son wata zai canja ni? Lah! Ba dai Bulkachuwa ba". Da wani kuma a Cikinmu ko a cikin samarin gidan matu'kar ba Yaya Anwar ba ne zai saka musu baki, a take Dada zata nuna wa mutum shine bare a tsakaninsu. Tana kuma sake kambaba shi da kawar masa da kai saboda alfarmar mai sunansa ne, domin ko ta yi masa sababi, sai ta yi ta tuba tana kamun kafa da mai asalin sunan akan a saka mata jikanta cikin shirayayyu. Hatta shi kansa dariya take bashi akan yadda take tuba idan ta saki harshe a kansa. Amma wani ikon Allah jarumi ne na gaske. Idan na ce jarumi ina nufin zai tsaya ya fafata da kowa akan hakkinsa, matu'kar kuma ya sanya kansa zai yi abu, to duk tsananin wahalar abin sai ya ga abin da ya turewa buzu nad'i. Baya ga hakan kuma tausayi ne da shi, duk zafinsa inda zai ga kana kuka to zaka ga ya bar yi maka tijara. Sai dai kallon marowa ci nake yi masa na gaske, ni dai ban ta'ba ganin ya yi kyauta ba. Ko garinsu ya je ya dawo, duk abin da zai samo ba dai ya kawo gidanmu ba. Amma kullum a cikin karbe wa jama'a nasu yake, mussaman Dada da ko ta hana shi a k'arshe take kasa juriyar ganinsa cikin rashin sukuni, sai kawai ta bashi. Mazan gidan kuwa basa bashi duk irin yadda zai karyar da kai yana fa'din bashi da lafiya, tunda suka gane matu'kar ku'di ya shiga hannunsa y'anmata banza yake kashe wa, sai kowa ya kulle bakin aljihunsa dama kuma masu k'aramar niyya ne. Sai dai gara shi ma suna bashi, amma da a ce wani ne cikin y'an k'ofarmu baza su bayar ba, daman kuma bamu isa mu ce a bamu ba. Haziki ne na sosai, kwarai da gaske yake ja, amma lalacewar da ya yi ya sanya da k'yar ya iya kammala Diploma a kwalejin Tatari Ali data ke cikin Bauchi. Ya riga su Yaya Salisu samun gurbin karatu a jami'ar amma yak'i mayar da hankalinsa akan karatun har sai da aka kore shi. Hankalin mahaifinsa ya yi tashin gauron zabi, domin zaryar da ya dinga yi tsakanin Bulkachuwa zuwa Toro ba ka'dan ba ce. Haka ya sake samo masa yin diploma akan shaanin tsaro da tafiyar da gwamnati wanda da k'yar ya kammala dan ma shekaru biyu ne. A hakan kuma sakamakon ya yi kyau, domin ya wuce fallasa. Duk da hakan Babansu bai bar shi ba, sai da ya sake samo masa gurbin karatun digiri a jamiar jahar Bauchi ta garin Itas-gad'au. Inda zai karanci ilimin halayyar dan Adam. Wannan kam da taimkon Ubangiji ya kammala domin ba ya zuwa sai an kusa fara jarrabawa, sannan bai fasa al'amari da y'an mata ba. Shekaru biyu da rasuwar mahaifinsa kenan. A kuma wannan shekarar ya tafi bautar k'asa, da shekara ta dawo ya kammala. Yanzu zaman kashe wando kawai yake yi. Sai dai yana yar buga bugarsa domin kusan kullum sai ya je Bauchi. Haka ya dinga satar jiki yana siyar da kadarorin da ya mallaka. Abin kaico kuma ba komai ya yi da kudin ba sai sharholiya da burga a mata. Wani k'aton fili a Bauchi kawai ya tsira da shi, shima dan an zuba masa matakan tsaro ne. Yau da wata sana'a yake da ku'din ko kuma wani gini yake fa'da'da wa da an samu sau'kin bacin ran da ake ciki. Ya zauna kusa da Nazira da take kusa da karshen tabarmar. Murya ba amo ya ce "Madallah da Dada da y'anmatantanta". Duk suka hau rige rigen gaishe shi Amma ban da ni. Ya amsa hankalinsa na kaina. Ya kasa ha'kuri ya ce "Asiya Toro how far?". Na yi banza da shi. Domin dai na tsani yadda yake gatsa ainihin sunana, dan kuturun wula'kanci har sai ya ha'da da Toro. Kusan kowa Yaya Bulkachuwa yake ce masa, ni da bama shiri bana ce masa Yaya Bulkachuwa. Amma sai nake mutuntunta shi wajen kiransa da Yaya Tijjani amma bai yaba ba, bare ya gode. Yabin da zai ce ne yake ganin asara saboda an cika zuciyarsa da k'yashi. Shi yasa nima na janye yayan tuntuni nake gatsa Tijjani gatsal wanda na lura shi ko oho. Ina nan, ina kallon wadanda basa ce mini Yabi, duk ranar da Ubangiji ya sanya na je Saudi akan girma da hankalina ko tsarabar abin da ba'a so ba zan basu ba. Tijjani na cikin sahun farko. Yaya Ummi ce mutumiyarsa, baya zuwa gidan kowa amma yana zuwa gidanta, har idan da ku'di a tare da shi ya yi wa ya'yanta alheri. Sosai suke d'asawa, mutimiyarsa ce ta sosai. Dada ta fusata ta ce "Mugun nufi ya k'are miki Yabi! Ko wacce ta gaishe da dan-uwanku amma ban da ke, bai yi fishin wula'kanta shi da kika yi ba, ya sake bu'de baki ya yi miki magana amma kina ji sarai kin k'yale shi, saboda ke din kina gaji nunkufurci da ba'kin hali ko?" Raina ya baci domin a kullum kalaman Dada a kaina kenan, bansan me Goggo ta tsare mata da a kullum sai ta jingina mata munafurci da ba'kin hali ba, ko da yake na taba jin labarin cewar tun haihuwar Yaya Ummi da dangin Goggo suka zo suna daga garinsu na Kangire cikin k'aramar hukumar Birin Kudu suka fuskanci wulakanci daga wajen Mama. Shikenan duk haihuwar da take yi basu sake yin gayya sun zo ba. Sai dai a samu mutum biyu su zo su ganta washagari su juya sassafe. Wannan matakin da suka dauka shine ya zama laifin da yak'i wuce wa a wajen Dada da take ta musguna mata da gorin ba y'ar babbar haula ba ce, sannan yan'uwanta masu k'ullaci ne, duk kuma cikin matan gidan mahaifiyarmu ce kawai bata da kowa a garin Toro shi yasa ma wani abin ake yi mata da gan gan. Duk da ba jin dadin zaman take yi ba, ta jure dukkan kalubale dan kawai ta zauna da mu yaranta, amma bata tsira ba tunda Babanmu ma haka siddan sai ya dauke mata wuta na tsawon lokaci mai yawa. Mama kuwa bata fasa yi mata yankan baya a duk inda ta zauna ko ta samu damar yin hakan ba. Ko yaushe Gwaggo a cikin mutuntunta Dada take hatta wankin kayanta har yau bata daina yi mata ba, amma babu gwaninta bare yabawa. Nan da nan na tunzura na ce "Da yake shi kina jin tsoron kada ya keta ki shiyasa kike fa'din hakan. Amma ni kin bu'de baki kina niyyar tozarta ni. Tunda ban gaishe shi ba, ya yi mini magana ban amsa ba, ba sai ya rabu da ni ba? Bana son harka da shi ne, a duniya na tsani sunan da yake kirana da shi. Sannan idan zai mini magana sai ya lanjare murya, kuma kinsan dai ba sosai nake ji ba, bare na ji shi da kyau". K'wafa ta yi tare da cewa "Kowa ya yi na gari ai dan kansa Yabi". Basira ta ce "Yi ha'kuri Dada d'ora mana karatun kawai". Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Kayya Basira zuciyata ta jagula ainun karatun nan sai gobe kuma". Firdausi ta ce "Yaya Bulkachuwa saka baki Dada ta d'ora mana karatun, bata ha'kuri mana". Ya kalle ta ya ce "Dadarmu share kawai, nima na ha'kura ai. Kinsan hankalin Asiyan Toro a k'auri yake". Na sake hauro wa na ce "Tijjani ka bari, ka ga dai bana shiga harkarka akan me zaka nemi takure ni ne? Gaskiya bana son haka". Dada ta sake yin k'wafa tare da cewa "Yabi kin janyo muku, domin na lura tashen balaga kike ji, zan kuwa yi maganinki." Kafin wani ya yi magana sai ga Ikilima k'anwata da a yanzu take shekaru tara. Ta shigo cikin nutsuwa ta kalle ni ta ce "Adda Yabi ki zo". Da azama na mike domin nasan Yaya Jabir ne. Saurayin da yake gigita zuciyata da ruhina. Ban ce komai ba, na mike ina cewa "Sai da safenku". Dada ta bimu da ido tana cewa "Jabiru ne ko kuwa wani ne?" Ban kula ba, ba kuma wacce ta tanka. Domin dai na fi su farin jinin mane ma duk kuwa da ba finsu kyau na yi ba, asalima wasu sun fini kyau, sun kuma fini cikar mace. A bakin kofar Shashenmu ya jingina. Matashin saurayi mai cike da nutsuwa da kamala. Wankan tarwada ne, siriri mai matsakaicin tsayi, mai sanyi a halayya da kuma dabi'a. Bashi da kwaramniya tun tashinmu, mai hakuri ne na gaske, da wahalar gaske ka ga fa'dan Yaya Jabir. Sosai muke shiri da shi, duk kuwa da ni din mai tsiwa ce, mai kuma hayaniya ce. Amma jininmu ya ha'du sosai. Kusan tun soyayyar kuruciya ce ta rikide ta zama ta gaske. Dalibi ne a jami'ar tarayya ta Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Ajinsa uku sawess yake yi a cikin Jos. Sannan ya yi sa'a ma'aikaci ne a karamar hukuma da aka dauke shi aiki da sakandire a lokacin kawunsa kanin mahaifiyarsa kansila ne a yankin gundumar Toro. Na isa gare shi, yana sanye cikin farin yadi fari k'al. Wato duk samarin gidanmu babu mai tsabtar Yaya J. Ina jin da'din k'iransa da Yaya J. Na lura shima ba karamin son sunan yake yi ba. Ni ka'dai ce nake fa'da masa hakan kuma. Kusan halayyarmu daya ni da shi, domin nima tsabta ce da ni, har fa'di ake yi aljanun tsabta ne da ni. Baya ga haka muna da son y'anuwanmu, bama jin k'yashi wajen salwantar da duk abi da yake namu ne akan d'an-uwanmu, har rashin girman jikinmu iri d'aya ne. Shine d'a na farko a bangaren Baban Tsakiya. Mutane da yawa suna fa'din kama muke yi ni da shi, ni kuma bana ganin kamar kawia dai yanayinmu ne daya tunda shi din ba wani girma ne da shi ba, haka yake dan madaidaici avarage height ne. Haka nima duk cikin y'anmatan da muka taso ko wacce ta fini tsayi, bani da tsayi, nafi kusa da gajerta. Ina da gashi sosai, sannan ina da manyan idanuwa baya ga hakan fara ce sosai. Yadda nake yar cif cif sai nake matu'kar daukar hankalin mutane. Kullum idan zan fita sai Gwaggo ta ce ban da wulakanci Yabi, domin al'adar gidanmu ne yarinya bata kammala karatun sakandire. Shekaru sha biyar ake aurar wa, amma mu da alamu za'a bari mu kammala duk da dai Dada ta fara fa'din mu shirya dama kuma ita ce take matsa lambar sai an yi aure. Ya zuba mini ido babu walwala jikina ya yi sanyi na yi kasa da kaina ina fa'din "wannan kallon tuhumar fa Yaya J?" Ya saki gauron numfashi ya ce "kin kama kanki da kanki Yabi. Jiya ma fa sai da kuka tsaya da yaron nan dan gidan Sarkin k'ofa ko?". Na yi murmushi na ce "Ai dai baka ji me na ce masa ba". Na fa'da cikin shagwaba shagwaba. Ya sake yin kasa da murya ya ce "Ban ji ba, amma yanzu fa'da mini na ji". Na yi k'asa da kaina na ce "Na fa'da masa cewar ni bana sonsa akwai wani bawan Allan da ya riga shi yin wuf da zuciyar Yabin Marina". Ina kallonsa ya dan murmusa ya ce "Waye wannan bawan Allan?" Na dago amma ban kalle shi ba a dalilin hasken kwai na kanmu. Na juyar da fuska na ce "Yaya J mana". A wannan karon murmushi mai sauti ya yi. Ya nisa ya ce "Yauwa Yabin J, kin biya ni. Amma idan kina son ki burge ni, ki daina ma sauraronsa ba shi kawai ba, kowanne namiji ma. Sannan ki daina fa'da dazu ma sai da kika yi dambe da Saratu. Kin ta'ba gani na ina dambe?" Na girgiza kai tare da cewa "Ha'kuri ne ya yi maka yawa, ni kuwa bani da shi, domin duk wacce ta ta'ba ni ba zan k'yale ba" Ya girgiza kai ya ce "Ha'kuri fa falala ne da shi Yabi". Na girgiza kai na ce "To ka dinga yi mini addu'a na shiga sahun masu ha'kurin domin kuwa ni duk wanda ya ta'ba ni idan ban rama ba sai nake ganin na zama sullutu". Ya murmusa sosai domin ba mai dabi'ar k'yal-k'yala dariya ba ne. Ya zuba mini ido ya ce "Wai Goggo ce ta haife ki, al'amarin Ubangiji da girma yake. Waton idan kika rama baki zama sullutu ba?". Da hanzari na ce "Ras Yaya J domin dai kai din shaida ne na yadda ake kaffa kaffa da ni, da duk kayana". Ya zuba mini ido ya ce "Allah ka sanyawa Yabi ha'kuri da juriya, a mayar mini ita ta zama mai shanye dukkan kalubale da ha'kuri da kuma kawaici". Na ce "Gaskiya Yaya J kada mu yi haka da kai, roka mini na zama yar gwagwarmaya mana, sai kawai ka roka mini na zama mai ha'kuri komai aka yi mini sai dai na yi kuka, ko ya yi ta cina a zuciyata, watarana sai dai kawai a budi ido aga Yabi ta ha'du da jinya ko ta mace ma gaba'daya. To ni ba zan zama hakan ba". Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Kinsan darajar ha'kuri kuwa Asiya?" Na kalle shi domin bai cika fa'din zahirin sunana ba, tunda ya fahimci ina son inkiyata ta Yabi shi kenan ya wajabta ma kansa fa'da mini duk da dai yafi son Asiya. Domin an sha dakuwa da ni akan ce mini Asiya, ina ganin duk wanda ba zai ce mini Yabi ba, to hassada yake yi mini, tunda an yi dawafi da ni a ciki, an yi tsayuwar arfa da ni, an yi jifan shaidan da ni, an yi sa'ayi da ni to mene ne na tauye mini Hajjin?" Ban bashi amsa ba ya ce "W anda Ubangiji ya masa baiwar ha'kuri to ina tabbatar miki an ba shi arzikin duniya da lahira, ba kuma abin da ba zai cimma ba a rayuwarsa, daure ki zama jaruma amma ba jarumtar rashin ha'kuri ba". Na girgiza kai ina murmushi domin dai ban gamsu ba. Har yau da na fara mallakar hankalina ban ga ribar ha'kurin da mahaifiyata take yi ba. Ban ga ribar kawaici da ha'kurin da mahaifinmu yake yiwa zumunci ba. Ban ga ribar ha'kurin da Yaya Ummi take da mijinta da uwargidanta ba. Tunda har yau ita ce a wahale, kuskure ka'dan zata yi ya mata tijara a tsakar gida a gaban kowa tamkar ba ita ce mai k'uruciya ba. Dan haka na k'udire a raina ba wanda zai nemi ta'ba ni, na k'yale shi, zan yi komai dan na tabbatar ban bari na zama gajeriyar katanga mai da'din k'etara ba. Yanayina ya tabbatar masa ban yarda zan iya yin hakan ba. Ya girgiza kai ya ce "Ai shikenan sai dai zan cigaba da yi miki addu'ar dace wa da babban arzikin duniya wato Ha'kuri". Na yi dariya na ce "Dama addu'ar na zama hamshakiyar y'ar kasuwa kake yi mini, ta yadda kasuwacina zai d'auke mini hankali daga dukkan wani rashin ha'kurina da kake ga ni". Da sauri ya ce "Ina yi miki Yabina! Da ikon Ubangiji komai kika kasa sai kin sayar, kullum sai na roka miki Ubangiji ya baki dauwamammiyar sana'a da zaki tsufa kina cin gajiyarta". Da'di ya kama ni, domin Yaya J ne kawai ya fahimci irin yadda nake son na zama shahararrriyar y'ar kasuwa. Ya miko mini tsarabar Jos leda biyu da ya ajiye a bayan k'yauren shiga shashinmu. Na karb'a ina godiya sosai. Na tabbatar Atile ce da kuma turare, tunda sune abu mafi soyuwa a mini kyautarsu. Fahimtar hakan da ya yi, sai ya dimanci yi mini tsarabarsu. Shine ya fara koya mini amfani da turaren Far-away. Daga haka muka yi sallamah. Kai tsaye dakin uwata na nufa ban koma wajen Dada ba. *Akwai kayayyakin gyara mace sosai irin na kasar Chad.* *Akwai maganin sanyi sadidan* *Ku tuntube ni a wannan lambar* *08032773332.* ✍️ *BAK'AR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *(MRS M.I.NASHE)*. *Marubuciyar* *Halin Yau* *Sabo da kaza* •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYERS* https://www.wattpad.com/1381521145?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=SurayyaIbrahim1&wp_originator=2c15XL0D2bIzHhiZQM1Ufz9MWPlKieRkWxJuGH2P9gX0b9XHQk5Jym8fxiz%2BPI0TAhOUhwh2GWl2lunKDNI2ObmS%2B%2FfL1BUVY3%2Ft%2BNKg%2B0D0iEZNLOPdWH9AZxOaGd51 https://arewabooks.com/book?id=64e93a53984f91b3605ae432 *Ina makaranta labaran Books ɗin Ayshat Ɗansabo lemu, marubuciyar TAIMIYYAH DA NUFIN ALLAH kai har ma da sauran daɗaɗan littafanta? Marubuciyar na muku albishir da cewa sabon littafinta mai suna ƘADDARAR ZOYA ya fara sauka da zafinsa,labarin ƘADDARAR ZOYA labari ne da ya faru a gaske ba ƙageggen labari bane.Don haka kar ku bari ayi wannan tafiyar babu ku a cikinta,labarin zai zo muku akan 500 Whatsapp group sai VIP group on Telegram 1k.Ku tuntuɓi marubuciyar akan lambarta 08167768704 domin samun free pages na labarin kai tsaye, kafin ku kai ga yin payment.Kar ku manta it's a true life story,don haka ku hanzarta shiga cikin tafiyar da babu danasanin bin alƙaminsa....✍🏻* 5&6. A zaune na tarar da ita tana kullin siga, da yake tana auno rabin kwano tana k'ullawa, idan an zo siyan koko ana siya. Ikilima tana gefenta tana faman barci. Na ajiye ledar a gabanta. Ta kalle ni ta ce "Yabi na sha fa'da miki, jikina na bani sha'aninku da Jabiru ba mai yiwuwa ba ne, ba sa'an auren ki ba ne, gara ki tsaya akan Abdulrashid zai fi mana sau'ki da kwanciyar hankali". Na yi shiru, amma zuciyata sai tsalle take yi. Babban tashin hankalina a duniya shine Gwaggo ta ce mini aurena da Yaya J ba zai yiwu ba. Na yi k'asa da kaina a hankali na ce "Gwaggo fa'da mini dame ya fini da kike ganin yafi k'arfina?" Ta murmusa ka'dan ta ce "Saboda Babanki ba shi da arziki, sun tsere mana, sannan uwarsa tana da buri a kansa, bayan haka ga Mama k'ut take da uwarsa, dan haka zata yi dukkan mai yiwuwa ta sake b'ata lamarin tunda akwai haske a tare da shi, ba zata so wannan hasken a tare da ke ba. Sanin kanki ne kuma mutanen gidan nan baza su dauke ki su ba shi ba, tunda kuna da yawa, zasu yi kwarya tabi kwarya ne a tsakani. Da ace ke din diyar Baban kasuwa ce to, da ba fargabar da zan yi". Na numfasa k'irjina ya daure ainun. Na dinga tambayar kaina shin zan iya rabuwa da Yaya J? Da gaske har lalacewar zumunci ya kai za a iya hanamu aure ba tare da wani dalili gamshasshe ba? Ashe har za'a iya ture karfin jini saboda kawai dan-uwanka ba shi da wadatar abin duniya? Na sauke nannauyan numfashi na ce "Ki daina damuwa Gwaggo! Ban tsananta ba, ban kuma dage sai shi ba. Ki cigaba da yi mini addu'a". Ta sake kafe ni da ido ta ce " Ina yi miki addu'a sosai Yabi, amma zata yi tasiri ka'dai idan kin barwa Allah ya yi miki zabi, kin kuma yak'i zuciyarki akan Jabiru. Ina nufin ki rage zurfafa a al'amariinsa." A sanyaye na ce "To Gwaggo". Sai kuma na zauna ina taya ta k'ulla sigan ina bata labarin yadda ta kaya a tsakanina da Dada. Ta nisa ta ce "Ba kya jin magana ne, ban da hakan mene ne zaki dinga janyo wa tana yi miki mugun fata? Kinsan kuwa bakinta zai kama ki domin ita ma uwa ce a wajen ki". Jikina ya sake yin sanyi, na dinga yin addu'ar Allah yasa na daina tanka mata akan Shehu tunda mafi yawa saboda hakan take fusata. Ta ke tsanata mini, har take yi mini mummunar addu'a. Washagari takwas saura muka d'unguma zuwa makarantarmu ta jeka ka dawo ta gwamnatin jahar Bauchi. Ajin mu hudu wato ss1. Ko wacce tana cikin tsafta, duk inda muka wuce sai an kallemu wataran akan kunnenmu mu ke jiyo yadda ake fadin "y'an Marina ne, kasan yawa ne dasu tamkar tsaki." Ko muji an ce "kai wato gidan Marina akwai zuka zukan zaratan y'anmata fa." Muna tafe ina tambayar Basira da Nazira jiya Dada ta d'ora musu karatun kuwa bayan na tafi?. Nasiba ta ce "Bayan kin bata mata rai yaushe zata iya yin karatu? Kin san kullum sai ta ce haramun ne yin karatun addini a cikin fishi ko a cikin rashin tsarki". Muka k'yal-k'yalale da dariya gaba'daya. Muka isa makaranta hatta Malamai kwarjini muke yi musu saboda yawanmu da kuma yadda muke kama da juna baya ga hakan tare ake ganinmu tamkar kashin awaki alhalin a gidajenmu babu wannan soyayyar da jin kai da ake gani a tare da mu. Lokacin tashi yayi muka dawo a jiga ce a dalilin rana ake yi duk da zafin ranarmu da sau'ki akan ta Bauchi da Jigawa. Wajibi ne idan zamu tafi sai mun shiga mun gaida Dada, haka nan idan mun dawo. Tsabar saka ido da kwakkafin baiwar Allan nan duk wacce bata je ba sai ta ga ne, hakan kuma na iya zama sanadin rikici a gidan, domin bai zame mata komai ba, ta kira uwar yarinya ta yi mata tass, ta ce da sa hannunta y'arta ta raina ta. Kuma abin mamakin idan baka kama sunanta ba, to da kai da wacce bata je ba daidai kuke. Ina tsaye suka dinga shiga suna fitobwa ba abin da ake ji sai "Dada mun dawo, sannu da gida" . Yayin da ita kuma take kama sunan kowa tana cewa "Sannunku da dawowa, lale da y'anmata Dada". Sanin da na yi garina da tsakuwa da ita, ya sanya nake jingirta wa sai na je gabanta sosai ta yadda zata shaida ni da kyau. Tunda kullum sai na je, amma idan ta so ci mana mutunci ni da Gwaggo sai ta ce ban je ba, ko kuma na yi mata gaisuwar gadara da wulakanci daga bakin k'ofa Dan haka da na k'ara wayo sai nake isa gabanta mu hada ido sosai sannan na yi gaisuwar. A gajiye na k'arisa k'ofarmu na tarar da bacin rai domin tsagwaya na tarar an yi a matsayin abincin rana, wani irin nau'in abinci ne da ake sirfa dawa sai a dafa a ci da manja. Na tsani abincin ba dan babu da'di ba, sai dan kawai bana so. Na zauna a tsakar d'akin Gwaggo ina kunci sosai. Ta shigo ta kalle ni ta ce "ban ga kin cire inifom din naki, kin yi sallah kin zuba abinci ba?" Na tumbatsa da fishi ban tanka ba. Ta kafe ni da ido ta ce "Yabi kullum aka yi tsagwaya sai kin tayar mini da hankali? Sanin kan ki ne mahaifinku ya saka takunkunmin siyo abinci a waje ko a ro'ko a wani waje. Me yasa ba zaki rufe ido ki ci dan ta yi miki maganin yunwa ba? Idan kin yi ha'kuri ai wataran barin gidan zaki yi, ranar da Allah ya kai ki dakinki komai kike so sai ki yi wanda bai wuce wadatar mijinki ba". Cikin bacin rai na ce "Ki taimake ni ki bar ni na jika gari na sha, Allah ya sani yunwa nake ji kamar na mutu". A sanyaye ta ce "To ki jika amma nafi son ki dinga ci tunda idan kin ci din ba illah take miki ba." Haka na jika gari na bu'de jakar makaranta na dauko gyada maro na bushe na zuba, ina sha, ina fa'din "ba dan na k'osa ba, da Iklima ta siyo mini madara, to aikenta bana me sauri bane ko wanda yake a matse irina, domin shad'arta ta yi yawa". Gwaggo ta girgiza kai ta ce "Ke dai duk salon k'wadayi kin san shi, ki dinga bin duniya a sannu sannu Yabi". Na yi dariya na ce "Gwaggo tuni aka daina bin duniya a sannu. Saboda gaggawar mutanen cikinta ba zasu bar mai binta a sannu ya kai ga gaci ba, yanzu da nake yin kitso na ha'da da lalle ba gashi muna d'an samun taro da k'wabo ba, da sannu nake bi iya kitson kawai zan yi Gwaggo. Yanzun ma so nake na koyi wata sana'ar na sake ha'da wa domin ina da burin na samu ku'di masu nauyi na jiyar da ke da'di, na jiyar da su Iklima". Ta girgiza kai ta murmusa ta ce "Na gode sosai Yabina! Allah ya ida nufi, amma dai ki bi a sannu da ikon Ubangiji komai zai saukaka a gareki, kullum sai na rokar muku kada a jarrabe ku da rashin abincin a gidan aurenku kamar yadda aka jarrabi Yayarku, ita ma ina fatan da'di ya biyo bayan wannan wahalar da take ciki". A sanyaye na ce "Allah ya amsa bakinki Gwaggo". Ina kammala wa na yi haramar sallar azahar, sannan na shiga wanka dan shirin tafiya Islamiya. Dai-dai lokacin Babanmu ya dawo daga wajen sana'arsa. Gwaggo ce mai girki ta hau hidimar kai masa abinci, a raina sai kiyastawa nake yi ina ma ina da hali na dinga soya masa miya mai d'auke da naman kaji ko na shanu zuk'u zuk'u a ciki. Din ya dinga ci da abinci. Na fito na gan shi zaune a rumfa akan tabarma jikinsa duk ya yi futu futu, ga alamun gajiya mai yawa a tare da shi. Tausayinsa ya tsirga mini, cikin rauni na ce "Sannu Baba, sannu da kokari". Ya dan sassauta ya ce "Sannun ka dai Yabi Asiya". Na dan murmusa domin shi ka'dai ne yake ha'da mini sunan guda biyu. Tunda ya fahimci ina bacin rai idan ba'a ce mini Yabi ba, sai ya kankare kirana da gayan Asiya. Na wuce shi na fa'da d'akin Mama wajen Nazira. Na tarar itama shirya wa take yi. Tare muka fito muka risina muna cewa "mun tafi Baba". Ya amsa da cewa "A dawo lafiya, ku kula da kanku". Muka shiga sashin Baban Tsakiya muka fito da su Firdausi da Saratu. Amma wani irin abu ya tsirga mini mai nauyin gaske, ba dan komai ba illah ganin da na yi Baban Tsakiya yana cin dafadukan shinkafa gefe kuma kunshin balangu ne, ga pure water mai sanyi a gefensa cikin yar bak'ar leda da alamu shi ya shigo da su. A banzan ce ya amsa gaisuwarmu tamkar ma bai ganemu ba. Na tuna gabzar da muka baro Baban Marina yana ci zufa tana yanko masa. A hankali na ce "Àllah ga Yabi! Ka buda mata hanyoyin arziki ta jiyar da iyayenta da'din duniya". Kafin muje k'ofar Baban kasuwa muka yi kicibus da Maijidda, ta fito. Na ji da'din hakan domin shi kam ma tsiyatakunsa sun fi na Baban Tsakiya yawa. Gaba'daya muka d'unguma k'ofar Dada dan yi mata sallama da kuma biya wa Nasiba. D'aya bayan d'aya muke gaisuwar tamkar masu neman tabarraki, kuma dole sai an kama sunanta idan ba hakan ba sai ta dauke kai tabbacin bata karbi gaisuwar ba. Abin da zai biyo baya kuwa ba mai sau'ki ba ne. **** An idar da sallar isha dukkan mun hallara a k'ofar Dada. Sai jiranta muke ta kammala nafilfilinta ta d'ora mana karatu, domin karatun nata ba k'aramin nisha'di yake sanya mu ba. Ta idar ta dinga jan dogon carbinta wanda kafin ka kammala jan k'afa d'aya ma lokaci ne mai yawa. Amma haka muka jira ta kammala. A fili ta cika addu'arta da salatil fatih. Dada tsohuwa ce da bata samu ilimi sosai ba, amma Ubangiji ya cika zuciyarta da son addini, ta rabauta da yawan yin istigifari, matsalarta guda tana da son zuciya, matu'kar zaka bata abin duniya to zata juya gaskiya ta koma karya. Hakan kuma ya yi tasiri a zukatan ahalinta, domin kuwa a tsakaninmu ma mun k'ullaci yadda take fifita Nasiba akanmu, ta yadda ta fimu gata da iko a gidanmu. Kowa yasan Dada tafi son jikokinta da y'ay'anta mata suka haifa, mussaman su Nasiba sannan Bulkachuwa. Saratu ta ce "Dada muna dakon karatun ne, jiya kin ce addu'ar tsari da makarai da miyagu zaki d'ora mana." Ta dan yi tari ka'dan ta ce "Hakkun Saratu". Ta numfasa ta ce zan biya sau uku daga nan sai ku dinga fa'da bayan na fa'da." Muka amsa da cewa "To". Ta yi Basmalah, ta yi salati ga Annabi, sannan ta nemi tabarrakin SHEHU. Na yunkura zan yi magana sai kawai na yi maza na saka hannu na kame bakina. Da karsashi ta ce *"Wa makaru, wa makaru, Wallahu kairan makirina".* Na amsa karatun nata ina ganin kuskuren ciki ka'dan ne. Muna saurare har ta biya sau uku kamar yadda ta fa'da. Sannan muka koma tana yi, muna amsawa har kuma ta ce mu yi da kanmu. Muka dinga yi har muka rike dama kuma mun biya ayar a islamiyya. Ina son na yi mata gyara amma ina jin tsoron abin da zai biyo baya. Ganin mun ri'ke sai ta ce "To zan baku addu'ar farin jinin samari, ku yawaita yinta atafe kuke, ko a zaune ko kuma a kwance". Muka yi shiru dan nuna kunya. Ta numfasa ta ce *"Ya tifa risubuha ragadan".* Muka k'yal-k'yalale da dariya, na kasa daurewa na ce *"Min kulli.."* kafin na karasa ta ce "Lah! Ai iya inda na tsaya, zaku dakata, duk wacce ta yi karambanin cika ayar to ta kuka da kanta. Domin maza kala kala zasu yi ta bin ta har mazan dabbobi sai sun bi'de ta da sunan soyayya saboda karfin addu'ar, kunsan Annabi Isibu aka saukar wa ayar." Muka kasa cewa uffan domin kowa dariya ce a bakinsa yake gimtse wa". Ta kalli Nazira, Saratu, da Nasiba ta ce ku dimance ta babu kakkautawa kune masu nauyin jini, ke Yabi ba sai kin yi ba, ku kuma ragowan saffa saffa zaku dinga yi tunda kuna samun mane ma." Nasiba ta bata rai ta ce "wanne irin nauyin jini kike magana Dada? Duka duka fa shekarunmu sha shida ne wasu ma basu cika ba, ban da dai ana auren wuri a gidan nan ina ma muka isa a samu a sahun y'anmata a wannan zamanin?". Dada ta ce "A wajena kun wuce y'anmata ma kun zama iyayen mata, tunda ba wacce bata yin wanki duk watan duniya, ni kam kullum sai na yi tuba sama da sau dari uku, tare da addu'ar Allah ya cika mini burina wajen sallar layya ace ko wacce maneminta ya tsaya duk sai mu tattara mu rabu da ku salin alin. Amma a duk sadda na hango zugar ku gabana faduwa yake yi, inta shiga firgicin yadda sallolimmu suke goriya a madakata basa isa gaban Zati". Cikin dariya na ce "Wai a ina kike koyon wadannan karatun naki irin na makafi ne?". Haka kawai na fa'da ta rusa ihun da ya janyo hankalin ahalin gidanmu, mu kuwa gaba'daya muka zuba mata ido muna mamakinta, yayin da jikina ya yi mugun sanyi, zuciyata ta shiga kaiwa da komowa cikin fargaba mai yawa. Cikin kankanin lokaci dukkan iyayenmu maza sun bayyana, wasu daga cikin matan gidan suma sai iso wa suke yi cikin zullumi duk da dai ta kan yi irin haka sa'i, sa'i. Tana kukan tana fa'din "Yabi ce, Yabi ta zage ni, ta mini gorin mijina makaho ne". Mamaki ya sake kama mu, domin sai a ranar muka san kakanmu Alh Garba wai ashe ya makance a karshe karshen rayuwarsa, duk cikinmu ma ba wadda ta san shi bare har a yi mata gori, sannan dama ana gorin ciwo ne?" Haka Baban kasuwa da yake jin shine a saman kowa, ya hau cin mutuncina yana fa'din ba zai yiwu kullum sai na tozarta uwarsu ba. Zai dauki mummuna mataki a kaina ya ga take takena so nake na gagari kowa, to shi ba zai zame masa komai ba akan mahaifiyarsa ya kore ni daga gidan, ko kuma ya dauke Dada su bar mini gidan, idan ya so iyayena su shata jan layi da shi. Baban Marina kuwa cikin sanyi yake fa'din "Haba Iliya yaushe zan haifi y'ar da zata shiga tsakaninmu, komai zaka yi mata ai ka isa ne". Baban Tsakiya ya ce "A a ai yaran yanzu basu da kunya balle mutunci baka ganin yadda ta saka uwarmu kuka to mu kuma idan muka ce zamu shiga shirgin ya'yanka ai sai dai su rufe mu da duka tunda a cikin idonsu muke ganin bakincikin da suke yi da mu, tamkar dai mune muka hanaka ka sake tara arziki, ko muka hanasu yin zuciyar tallafa maka. Ban da lalace wa Musa ka'dai bai isa ya ri'ke kofarka ba? Ya'yanka wajen hudu ko biyar ne a daki amma duk wula'kantattu ne, basa taimaka maka da komai, amma abin kaico sun raina kokarinmu akan ka." Baban Marina ya sunkuyar da kai kasa gwanin tausayi yana fa'din sai ha'kuri da yaran yau, ni kuma har yau din nan basu fiye mini ku ba". Na kalli Nazira na ga hawaye na tsere akan fuskarta, na sake kallon ragowar, su Firdausi kowa idonta a bushe tabbacin basu da kaico akan cin mutuncin da iyayensu suke yiwa ubanmu. Na kasa hawaye a dalilin ba'kin cikin da yake cina yafi gaban hawaye. Ba abu mai ciwo irin wanda ba za'a barka ka keta shi ba, ya tisa iyayenka a gabanka da cin mutunci akan idonka. Na sake kai idona kan Dada da take matsar hawaye, na dinga mamakin yadda ta tara mini jama'a haka. Na gama yarda kafatalin jikokinta ba wacce take jiran kiris akanta iri na. Duk yadda Nasiba take zage wa suna yin sa in sa, hakanan kowa a cikinmu tana mayar mata da magana amma ba wanda take mayar da laifinta garma sai ni. Tausayin mahaifina ya yi matu'kar kama ni ta yadda kannensa suka tsaya a gabansa suke fa'da masa maganganun da komin sanyin halinsa sai sun mintsine shi. Kirjina ya sake nauyi akan wanda ya yi dazu da naga Baban Tsakiya yana cin da'di a kofarsu amma mu muna cin abinci irin na yan fursuna, kuma suna da halin tallafa wa. Amma sun runtse idonsu. Haka Baban Marina ya dinga bawa Dada da sauran y'ay'anta ha'kurin katobarar da na yi tamkar dai shi din ba uwarsa ba ce. Sai lokacin hawaye mai ciwo ya goce mini, ina jin tsanar mutanan da a baki Baffanina ne. Maganar gaskiya kuma na fi jin ciwon Baban kasuwa. Haka suka fice suna kumfar bakin na fitine su, na fitini y'ay'ensu, tunda ba'a sati ba a doku da ni ba a cikin gidan. Rainin da aka yi mana ne ya sanya dukkan mutanan gidan suke ganin zasu mayar da mu gidadawa, shiyasa ni kuma na lashi takobin duk wanda ya nemi ta'ba ni, ko taba wani cikin yan k'ofarmu la shakka ni ya ta'ba domin zan siyi fa'dan ne ya dawo kaina, duk yadda nake yar shafal amma Ubangiji ya hore mini wani irin karfi tamkar shari'a, ko dan da dukkan zuciyata nake yin fa'dan ne oho. Yadda nake tare wa kannena fa'da da muke daki d'aya haka nake tarewa na yaran Inna amaryar Babanmu babu banbanci. Hatta Nazira da take yayata ni nake tare mata fa'da domin duk wanda ya fa'da mata maganar banza zan yi ruwa na yi tsaki na shiga na dinga yarfa bak'ar magana har sai abin ya juye kaina. Duk yadda nake jin haushin Mama bai shafi son da nake yiwa Nazira ba. Domin yar-uwata ce da uba ya ha'damu, idan da abin da na tsana ban kuma yarda da shi ba shine yan'ubanci. Ina matu'kar takaicin yadda wai gidanku daya da mutum, cikinku daya, gadonku daya amma babu yarda da amana a tsakaninku. Duk wani alherinka baka son dan-uba ya ji, zaka iya fa'dawa bare matsalarka amma ban da dan-uwanka da uba daya ya hada ku. Kuma mafi yawa iyaye mata ne suke bari yaransu su shiga cikin rikicin da ba nasu ba. Da ace Nazira tana biye hudubar Mama da tuni ta gurbata mana zumunci da soyayyarmu, mun koma muna adawa da junanmu. Wai uwa ce zaka ji tana zayyane wa y'ay'anta laifin kishiyarta, ko kuma laifin y'a ko d'an da ba nata ba. Da ace iyaye mata zasu dinga ha'diye rikicin kishi a tsakaninsu, suna boye rashin jituwarsu a gaban yaransu, sannan idan matsala ta faru suna barinta a tsakaninsu da an samu sassauci wajen yan ubancin da ake yi a yau. Idan d'an kishiya ya yi miki laifi ko ta yi miki, daure ki ha'diye ba sai kin baza wa yaranki da basu sani ba, gudun haddasa gabar da baki san iyakacinta ba. Ko wanne d'a a duniya gaibu ne, ba wanda yasan me gobe zata zo da shi, ba lallai d'an da kika haifa ya samu daukaka ba, wata'kila sai d'an miji ya samu daukaka fiye da yaranki, adalcin ki ne zai sa Ubangiji ya sarrafa zuciyarsa ya ji k'anki, haka nan ke ma babu jin kunya ko nauyin kin yi abubuwa a baya marasa da'di. Na sani mutanan yau bamu cika gode wa da yaba kokarin abokan zamanmu ba, muhimmi dai mu yi adalci a tsakanin zaman kishi da yaranmu, ko ba a shiri ya zama akwai sassauci da ha'diye bacin rai, shi adalci yana haifar da farin-ciki da yalwar arziki da hadin kai a cikin gida. Addinin musulunci cewa ya yi ko wanne musulmi dan-uwan musulmi ne, bare kuma wanda jini mai k'arfi ya ratsa a tsakaninku. Daga shakiki sai li-Abbi a duniyar musulunci da zumunci amma mutanan yau mun dauki wata irin *Bak'ar Ta'ada* ta mayar da dan-uba abokin gaba kuma makiyi. Da kaina na jinjina wa kaina da duk wacce bata da wannan mummunar manufar a ranta. Madallah da mutanan da suka yarda Ubangiji ne yake zaba mana mutanan da zasu zama iyayenmu da yan'uwanmu. Alhamdulillah, Allah ka bamu ha'kuri da juriya wajen mua'amalantar mutanan da ka d'ora mana hakk'in zumunta da su. *Kafin lokacin zaku iya fara payment ta yadda idan an kammala free pages babu dogon jinkiri.* *Madallah da masoyan RUBUTUNMU*. *Madallah masu sauke hakki komin kankantar sa, madallah da masu k'arfafa guiwarmu*. *Fatan alheri ga masu kiyaye hakkin sana'ar y'anuwansu*. *500 for regular* *1k for VIP* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *ZENITH BANK* ✍️ *BAK'AR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *(MRS M.I.NASHE)*. *Marubuciyar* *Halin Yau* *Sabo da kaza*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KO DIYAR DA ZAKI AURAR. TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S ONLY* *Ina makaranta labaran Books ɗin Ayshat Ɗansabo lemu, marubuciyar TAIMIYYAH DA NUFIN ALLAH kai har ma da sauran daɗaɗan littafanta? Marubuciyar na muku albishir da cewa sabon littafinta mai suna ƘADDARAR ZOYA ya fara sauka da zafinsa,labarin ƘADDARAR ZOYA labari ne da ya faru a gaske ba ƙageggen labari bane.Don haka kar ku bari ayi wannan tafiyar babu ku a cikinta,labarin zai zo muku akan 500 Whatsapp group sai VIP group on Telegram 1k.Ku tuntuɓi marubuciyar akan lambarta 08167768704 domin samun free pages na labarin kai tsaye, kafin ku kai ga yin payment.Kar ku manta it's a true life story,don haka ku hanzarta shiga cikin tafiyar da babu danasanin bin alƙaminsa....✍🏻* *Shafin nan kyauta ne sukutum ga mamana* *Hajiya Hadiza Sodangi* *Na gode sosai Ubangiji ya shirya zuria* 7&8. Maganar Baban Marina ta dawo da ni tunanin da nake yi. Kamar a sama na ji ya ce "Na gode miki Asiya! Duk yadda nake jan kunnenki akan b'atawa Dada rai, da kuma dukan yaran gidan nan ba kya ji, saboda kin riga kin zama y'ar kuka. Uwarki kullum cikin yi miki kashedi akan shiga fa'dan yara da kuma tsokanar Dada, amma duk a iska ko? Na gode sosai da wannan bacin rai da kika sanya ni, Allah ya shirye ki". Ya tsugunna gaban Dada ya ce "Ki yi ha'kuri! Halin Asiya ni kaina ha'kuri nake yi da ita, amma zan dauki mataki akan ta'ba ki da take yi". Ta kyabe baki ta ce "To ka fara dan takidin aurensu. Jiya mun tattauna da kannenka sun ce su babu matsala ko yaushe auren ya zo a shirye suke, kai dai za'a fa'dawa ka fara tanadin tunda yaran ka har biyu ne". Ya yi gyara murya cikin k'arfin hali ya ce "Babu damuwa Dada ina saka rai Ubangiji zai kawo mini hanyar da zan samu na yi musu iya abin da zan iya." Ta murmusa tamkar ba ita ce mai kuka tana face majina ba. Ta ce "To babu laifi Allah ya basu na gari, masu kuma ha'kuri, domin mai yakana ne zai iya zama da Yabi dan wuyar zamanta ya kai inda ya kai, ba inda ta baro uwarta". Cikin sanyin jiki Baba ya mike yana cewa"Dada sai da safe mu kwana lafiya". Ta amsa masa da fa'din "Allah ya tashe mu lafiya". Na mike, Nazira ma ta biyo ni muka fice, ba tare da mun ce uffan ba. Domin na sake fusata da ta ce sun tattauna da kannensa amma shi ba'a saka shi cikin zaman ba. Muna jin ta tana fa'din "Wanda Allah ya bashi tsawon rai zai yi kallon tak'ama a wajen ki Yabi. Yarinya da ke amma kusan ke kike juya shashinku gaba'daya. Kina tashi Yayarki ta biki zungui zungui ko sallama ta kasa yi mini saboda tana rarrashin zuciyarki?". Ban juya ba, bare na tanka mata, balle kuma Nazira da take da sau'kin hali. Muna shiga shashinmu muka yi turus a dalilin halin da muka ga mahaifinmu a ciki, zaune yake akan tabarma a tsakargida. Sai fifita Gwaggo take yi masa, gumi na yanko masa babu kakkautawa. Muka isa gabansa, muka tsugunna, baki na rawa na ce "Sannu Babanmu! Abin mamaki sai ya daga mini hannu tabbacin ya amsa gaisuwar tawa. Nazira ma ta yi masa sannu ya amsa ta hanyar gyada mata kai. Mama ta fito daga bandaki ta kalle ni ta ce "Wannan ja'irar yarinyar sai kin zama sanadin mayar da kananun ya'yansa marayu, fitananniya tabtacciya. Ai duk gwanin na iya a rana ya ke" Ta ja tsaki mai tsanani ta wuce d'akinta. Bata jima da shiga ba ta k'walawa Nazira kira, ta mike a hanzarce ta nufi dakin nasu. Daidai lokacin Baba ya dan samu sau'kin zufar da take karyo masa. Ya yafito ni, jiki na rawa na isa gabansa. Ga mamakina sai ya mik'o mini hannunsa na dama. Hannu bibbiyu na ri'ke hannun nasa, cikin barin jiki gaba'daya. A sanyaye ya ce "Ina alfahari da ke Yabi! Kafatalin ya'yana ke nake da tabbaci akan ba zaki cigaba da yin mini *Bak'ar Ta'ada* ta y'an ubanci ba, na tabbatar da hakan. Ina saka rai ta dalilinki yarana zasu dawo tsintsiya. Na so ace da wuri na haife ki Yabi. Da al'amuran da suka dame ni basu yi mini tsananin da nake ciki ba. Amma Alhamdulillah! Ubangijinmu baya kuskure na gode masa, ina kuma tuba a gare shi." Hawaye tuni ya goce mini dukkan zuciyata a jagule take da tsananin tausayin Mahaifina da a yau nake ganin wani irin tashin hankali da raunin da ban ta'ba ganinsa a ciki ba. Gwaggo tana fifita, tana kuma share k'walla.y Ya numfasa ya ce "Idan na mutu Yabi, duk runtsi ku gaisa da yan'uwana, ko ba zasu taimakeku ba, to lallai ku dinga saka su a cikin al'muranku, idan kina yi, sannu a hankali zaki samu wanda zasu yi koyi da ke, tunda tun yanzu al'amura sun haska ke ce mai tsayayyen ra'ayi wanda yafi kusa da kyau da kuma dace wa." Murya na rawa na ce "Mu sasu a alamuranmu ko da ba zasu taimakemu ba, ko da idan mun fa'da musun ba zasu dauki al'amarin namu da girma ba?" Ya sake damk'e hannuna ya ce "Haka nake so Yabi". Da karfin zuciya na ce "Da Ikon Ubangiji zan yi yak'i da dukkan zuciyata na yi hakan. Amma ina ro'kon arziki ka mini afuwa, ka yafe mini muzancin da na janyo maka dazu". Ya girgiza kai ya ce "Baki yi laifi ba, na sani. Sannan su d'in ma bana son ki d'auki abin da suka yi mini a matsayin muzanci ko tozarci, na sani baki da sauki, kina da ru'ko, dan haka na umarce ki, ki manta komai". Na murmusa hawaye na kwaranyo wa na ce "Shi kenan Babanmu! Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, yadda a ke mini habaicin tunda aka haife ni ka tsiyace, ina ro'kon Ubangiji kullum, ya saka idan na girma na samu sanadin da arzikinka zai dawo ta dalilina fiye da wadda ka rasa a shekarar da na iso duniya". Ya ce "Rabu da maganar jahilai, ko iya hakan na ga ni ai na gode, sanadin sana'arki na daina fargabar a tambaye ni ku'din sabulu a gidana. Alherin da kika janyo mini mai yawa ne, mafi farin-ciki a ciki shine wanda kike yarda ya'yan da na haifa duka daya ne a wajenki ta fuskantar mua'amala ta zahiri." Da'di ya tsirga mini ban ta'ba zaton Baba ya fahimci yadda nake da ra'ayin rikau akan kannena ba, bansan ya fahimci ina tare musu fa'da ba, hakanan ban san hakan yana yi masa da'di ba, tunda kullum a cikin kirarin bani da hakuri yake. Sannan kuma baya ta'ba nuna mini ina abin a yaba, sai dai ya ce ai duka yan'uwane tunda ragowar ma y'ay'ansa ne da yan'uwansa suka haifa masa. Cikin son na sake k'arfafa nasa guiwa na ce "Duk d'an da ka haifa ina jin sonsa har cikin zuciyata Baba". Idonsa ya ciko da k'wallah cikin k'arfin hali ya ce "Allah ka shirya mini yarana, ka saukaka musu, ka basu lafiya, ka cika zuciyarsu da tsoronka, ka jefa soyayya da tausayin juna a tsakaninsu. Allah ya yi miki albarka Yabi". Daga ni har Gwaggo muka hau fa'din "Ameen ameen". Na kalli Gwaggo na ga hawaye ya goce mata, jikina ya sake yin sanyi, domin ita din wata irin mace ce mai k'arfin zuciya k'warai da gaske, abin da zai saka ta yi kuka to kuwa ya girgiza ta ba ka'dan ba, duk tsananin da take fuskanta a rayuwar gidanmu ban ta'ba ganin ta yi kuka ba. Na yi kasa da kaina cikin rauni mai yawa na ce "Ameen Baba! Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana mai albarka. Na gode sosai". Duk muka yi shiru kowa na cikin alhini. A hakan Nazira ta fito rai a bace da gani Mama sababin yadda ta like mini ta yi mata. Kusa da ni ta zauna, cikin sanyin murya ta ce "Sannu Baba". Murya ba amo ya ce "Sannu kadai Nazira, Allah ya kara miki ha'kuri kin ji. Ki cigaba da jajirce wa a kan gaskiya ko da hakan ya ci karo da ra'ayin kowa, ku so junanku, ku binne a tsakaninku, kin fi Yabi ha'kuri, a duk sadda kika ga zata yi aikin nadama yi amfani da fikon da kika yi mata ki dakatar da ita, komin runtsi kada ki bari ta dauki hukunci cikin fishi. Ke kuma Yabi kul kika ki jin shawararta, idan ta ce yi ha'kuri, to na roki ki bar abin nan komin girmansa. Ina jaddada muku ne dan ku ri'ke su da kyau, ko babu ni idan kuka ri'ke maganganuna ba zaku ta'be ba. Allah ya yi muku albarka ya ha'da ku da maza na gari, ya raba ku da sharrin shaidan a cikin zumunta". Muka amsa da Ameen amen cikin sanyin jiki. Nazira ta mika hannu ta karb'i Maficin hannun Gwaggo ta cigaba da yi masa fifita, duk da gumin ya yi sau'ki. Har lokacin kuma bai saki hannuna ba. Ya jima kafin ya saki hannuna yana sake cewa "Na hore ki da ha'kuri Yabi! Ku zauna da yan'uwana lafiya, ku mutunta su, ku gaishe su da girmama wa". Na gyada kai yayin da Nazira ta ce "Duk yadda kake so hakan zamu yi, amma ka taimake mu ka daina sanya damuwa a ranka Baba! Fatanamu mu ganka a tsaye akan kafafuwanka, idan muna ganinka cikin walwala ba abin da zai dame mu sosai." Haka muka kwanta ni da Nazira tana ta jan kunnena na kiyayi Dada, tunda zata iya yin ha'din kitifo har ya zama sanadin da za'a samu damar cin zarafin Babanmu akan idonmu. Tun daga wannan ranar na kame bakina a gaban Dada, duk karatun da zata yi bana tankawa, haka nan ban cika zama na yi doguwar magana da ita ba. Zanje gaishe ta babu fashi, kuma sai na tabbatar mun ha'da ido sannan zan kama sunanta na gaishe ta. Na daina jan magana a tsakaninmu ne kawai. Sannan na soke zuwa hirar dare, amma matu'kar zata d'ora karatu sai ta sa an kira ni. Janye war da na yi da ita kuma sai ya dame ta, amma ta kasa bu'de baki ta yi magana. Tunda Nazira ma ba wani sake wa take yi ba, balle ta yi mata korafi. *** Karshen wata Yaya J ya dawo. Mun taso daga Islamiya muka ganshi zaune akan dandamalin kofar gidanmu. Sanye yake cikin kananun Kaya da suka yi matu'kar kar'barsa, sai kamshin turaren Dagmar yake tashi sannu a hankali. Dukkan y'anmatan suka hau rige-rigen gaishe shi, yayin da ni na sunkuyar da kai kasa alamun kunya. Na zo wucewa ta gefensa na saci kallonsa ai kuwa karaf muka hada ido, wani irin abu ya tsikare ni, kwalliya da tsabtar Yaya J ko mace ce ta kai a sata a masu tsabta, sannan kankantarsa tana sawa na ji mun dace da juna. Domin da ka'dan ya zarta ni cika ido da tsayi. Babban abin burgewa mai nutsuwa ne, sannan mai ha'kuri ne, bashi da hayaniya ko ka'dan. Da sauri na janye idon nawa, murmushi yana subuce mini wanda ban shirya yinsa ba, na tsananin shauki ne. Na wuce ba tare da na yi gaisuwar ba. Cikin raha ya ce "Nasiba ki koya wa Asiyan Toro gaisuwa tunda ta zama bak'auya". Da dariya ta ce "Yaya Jabir kaine da fa'din Asiyan Toro yau? Babu ruwana a shirginka da Yabi". Ya k'yal-k'yale da dariya ya ce "Tsoron ta kike ji ne Nasiba? Kin fita tirinya fa, to kuma ya za'a yi ne tunda ku biyu zan ha'da na aure rana guda?". Ta yi maza ta ce "Lallai kuwa ka shiryawa darun Yabi domin har ka tafi ba zata saurare ka ba, ni kuma ba zan taya ka rarrashi ba". Ta wuce ni da sauri ta shige shashin Dada. Ni kuma na wuce shashinmu a dalilin yau Nazira ba ta samu damar zuwa ba, saboda tana fama da ciwon mara. Zuciyata har wani tukiki take yi na tsananin bacin ran kalaman Yaya J. Wai zai ha'da ni da Nasiba ya aura. Na yi tsuka na ce "Sai dai ya aureta ita ka'dai. Dama na san dunbula dunbulan kirjinta na iya tafiya da shi, ba'kin ciki ya sake turnike ni a dalilin ni ba mai cikar k'irji ba ce. Har yanzu bana saka breziya sai dai half best, domin a manne suke a kirjina yan kananu da kadan suka fi tsakuwa. Amma Nazira da Nasiba kam kirjinsu a cike yake sosai. Wataran har rayawa nake yi ko dai na fara shan ruwan baru ne ko zan yi sa'a su fito su cika mini kirji ni ma. Amma sai na kasa, mussaman da sai na ro'ko ruwan kuma sai nake ganin kamar za'a gane dalilin shan da zan yi. Da daddare ya dinga aiken na zo amma na yi mirsisi na ki fita. Washagari a zauren Dada na tarar da shi. Na sani sammakon tashi ya yi dan ya hadu da ni. Domin shi ba ma'abocin tashi sassafe bane, da zarar ya dawo daga sallar asubahi idan ya kwanta sai tara yake tashi. Nazira ta gaishe shi ta shige, yayin da na dauke kai fuska murtuk zan wuce shi. Ya yi maza ya sha gabana yana fa'din "Haba Yabin J baki san wasa ba ne? Na yi bakam tamkar dai ban fahimci da ni yake magana ba. Na yi kasa da kaina. Ya sassauta murya ya ce "Yanzu Ashe zaki iya mini irin wannan fishin Yabi?" Na dago na kalla shi na ce "Oh wai ka yi zaton ba zan iya ba? To kuwa ka dauka zan yi maka fiye da hakan domin zan iya shafe babinka gaba'daya." Ya jima yana kallona cikin ki'dima. Ya yi k'arfin halin cewa "Me ya yi zafi haka, daga wasa?" Na sake d'aure fuska na ce "Bansan wasa ba, ban iya shi ba, ban kuma ta'ba daukan al'amarinka a matsayin wasa ba, bare har na yi maka tsokanar da zaka ji ka tozarta". "Hakane, na kuma gasgata ki, yanzu ki yi ha'kuri ba zan sake miki irin hakan ba kin ji". Na jijjiga kaina tare da yin wata irin shakiyar dariya na ce "Ha'kurin ma ban iya shi ba. Ba kuma zan koyo shi a dalilin cin fuskar da aka yi mini ba. Na riga na barwa Nasiba kai, dan haka ka manta da wata Yabin Marina". Ya yi tsam cikin kaduwa wata'kila yana mamakin yadda kishi yake kutsowa tunda ga kasan zuciyata ne, kallon yarinya k'arama yake yi mini, sai dai bai san yar shekaru goma ma zata yi kishin abin da take so ba, bare ni da nake da shekaru sha sha biyar, na ke harun sha shida. Ya lankwashe murya cikin rarrashi ya ce "Ai na yi zaton ina da wata alfarma ta daban a wajen ki, ban ta'ba zaton zan yi miki laifin da zaki shafe ni a zuciyar ki ba. Yau dai daya tak da na sab'a miki, ki daure ki mini uzziri, ni kuma na yi al'kawarin ba zaki sake kama ni da laifi irin wannan ba". Na dauke kai na ce "To idan na yi ha'kuri na ce maka komai ya wuce, ya zan yi da tafasar da zuciyata take yi idan na ga Nasiba? Ya zan yi na goge amincin da zuciyata ta yi akan ita kake so bani ba, tunda ita din ta fini zama y'anmata?" Tsananin mamakin da na ba shi ya sanya ya kasa magana na tsawon lokaci. Sai da ya jima kafin ya numfasa ya ce "Ni fa ba wacce take burgeni nan duniya idan ba Yabin Marina ba. Kinsan dai ina tsokanar Nasiba tun fil'azal tunda abokiyar wasanmu ce, yar mace da dan namiji muke. A kaikaice na ce "Oh oh, ashe dama ana wasa har irin haka? To kuma wai ya matsayin wannan *Bak'ar Ta'adar* a shari'a tunda ba'a wasa da maganar aure?" Ya dan tunzura ka'dan ya ce "Ke Yabi". Nima na ce "Ke Yabi ko kuma ke gaskiyar magana?" Ya girgiza kai ya ce "Shi kenan na gode, na gode sosai da yadda kika ajiye ni". Ya fice ya bar ni, kafin na shiga wajen Dada Bulkachuwa ya fito daga dakinsa. Ya yi fitoh irin na tantiran yan-iska ya kalle ni ya ce "Asiya Toro rikakkiyar budurwa". Ya kwashe da dariyar iyashege ko me ya tuna kuma sai ya gintse dariyar tasa. A fili ya ce "Ban da ma shan koko d'aukar rai ne, ta yaya kamar Jabir da yake ganin Bigger babes zai tsaya wajen kwailaye irin Asiya Toro? Ya wuce yana sake fa'din " Soyayya da kananun yara menene a cikinsa ban da raini da ba'kinciki, yar yarinyar da bata gama iya wanka ba ma sai ta caccaba maka magana son ranta, abin ba'kinciki kuma dole ka rarrasheta ko ka hadu da gallazawar zuciya." *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* Na yi kwafa a dalilin yadda furucinsa suka sake sawa na washe shi. A dole na shiga ciki na gaida Dada. Ina kallon yadda Nasiba take rawar jikin zuba masa ruwa a buta, dan ya yi brush. A raina na ce wannan fa shine shan kokon. Sai da ta gama barebaren yi masa hidima sannan muka fito muka wuce makaranta. Gaba'daya wannan zuwan na Yaya J ban yarda mun shirya ba, haka ya koma Jos. Ni kuma ina k'arfafawa kaina gwara mini Abdulrashid kamar yadda Gwaggo take so, domin ni da kaina ban san waya fi sona a tsakaninsu ba. Sai dai me? Juma'a da maghariba muna tsakar gidanmu sai jin ihun yara muka yi suna "Oyoyo Yaya Jabir, oyoyo". Nazira ta ce "wannan dawowar taki ce Yabi. Na ro'ke ki huce hakanan ai ya garu". Na tabe baki na ce "Rabu da shi, nifa dama ina ta neman hanyar da zan yakice shi a raina, ki ga fa irin yadda Baban Tsakiya ya yi wa Baban Marina, akan idonmu". Ta fesar da iskar takaici ta ce "Amma Baban ya ce ba ruwanmu da kasafinsa da yan'uwansa, a gabanki ya tabbatar bamu fi yan'uwansa a gunsa ba. Aure ai kaddara da rabo ne Yabi. Ban da haka da wani namijin bai isa auren wacce yake aure ba, sai kaddara ta ba shi, haka nan wata macen bata isa mijinta ya kalle ta da nufin soyayya ba, amma saboda karfin kaddara da rabo sai kiga ta zame masa mata kuma uwar ya'yansa. Matu'kar Yaya Jabir mijinki ne, sai kaddara ta sanya aurenku ya yiwu komin k'in da iyayensa zasu yiwa al'amarin. Mu da muka yi sa'a ma dukkan iyayenmu suna da ransu, kullum kuma suna roka mana mu dace da maza na gari, na yi imanin Ubangiji ba zai juyar da addu'arsu ba, hakan kuma ba zai hana mu ga kalubale a cikin ko wanne zabi ba, domin sunnar rayuwa ce komai na da irin nasa cikas din, sai dai albarkacin addu'ar iyaye sai ki ga komai ya saukaka. Jikina ya yi sanyi, na kasa bu'de baki na ce komai. Ta ru'ko hannuna sosai ta ce "Ki yi ha'kuri kin ji Uktina". Na nisa na ce "Na yi ha'kuri saboda ke, amma ki fa'da masa bana son irin wannan wasan, bana so". Cikin jin da'din na yarda da maganarta ta ce "Madallah da K'anwata kuma kawata YABIN J". Na murmusa a raina kuma sai addu'a nake yi mata ita ma Ubangiji ya kawo mata saurayin da zan taya ta sonsa, domin hatta Abdulrashid da ba wani sonsa take yi ba, bata ta'ba kushe shi ba, illah iyaka tafi son Yaya J. Idan ina yi mata d'an bikin ita bakin ganga ce, domin a gabansa bata ta'ba nuna masa akwai wanda take supporting sama da shi. Sai ta murmusa ta ce "Tunda har zuciyar Yabina tana dan sonsa ai kuwa yafi karfin na wula'kanta shi, baya ga haka son ki yake yi, dan haka nake girmama shi. Amma ai bazan so shi na bar Yaya J ba domin yafi shi cancantar ya same ki". Bata ta'ba nuna k'yashi ko takaicin ina da samari ita bata da su ba, duk da ta fini zama cikakkiyar budurwa. Ni da kaina na sani Nazira tana cikin Yan ka'dan da Ubangiji ya wanke musu zuciya akan k'yashi. Allah kenan! Sarkin hikima sai ya bawa bak'ar uwa karimi ko karimar yarinyar da za'a yi ta yi mata alfarma saboda kunyarsu. Hakan ce ta kasance domin sau tari sai na yi yun'kurin yiwa Mama iyashege irin ta dan yau dan ta fahimci dan Babanmu da Gwaggo suna shayinta, tunda laya ce ita, ni kuma mai zamani ce dole kuwa ta kiyaye ni. Nauyin Nazira ka'dai yake sawa nake hadiyar dukkan matsatsin da take sanyamu. Domin na riga na ajiye alakar matar Babana ce tunda bata ta'ba yi mini karar ni din y'arta ce ko ta mijinta ba. Ana idar da sallar isha ya aiko na je. Yana jingine jikin katanga hannuwansa biyu a kirjinsa, sanye cikin shadda shud'iya kalar sararin samaniya. Sai kamshi yake yi. Na rakube gefe guda ba tare da na ce kanzil ba. Ya matso kusa da inda nake ya ce "Assalamu alaikum Yabi". Murya babu amo na ce "Wa'alaika Salam". Ya ce "ki yi ha'kuri, na yi kuskure, tunda na gane da gaske ba kya son irin wannan wasan bazan sake yi miki ba shi kenan?". Na yi kasa da kaina, ba tare da na ce komai ba. Ya numfasa ya ce "Kin yi shiru". Cikin yauki domin da k'yar na ce "Ya wuce". Ya murmusa ya ce "Yabina sarkin ginshira, da rikici". Na kawar da fuskata gefe ban ce uffan ba. Ya dan damu ya fara fa'din "Kin ce "Ya wuce amma kin k'i sakar mini fuska, saboda ke fa na dawo". Fuska ba walwala na ce "Ya wuce mana, mantawa ai sai a hankali, yo ban da ma dai ina ganin mutuncin ka ai da an rabu ke nan, ina ruwana da duk wanda zai nuna mini yana son wata dan ta fini tirinya". Ya kame baki alamun mamakina. Tsawon shudewar mintina sannan ya iya ce wa "Yabin Marina ho". Na sake tsuke fuska. Murya ba amo ya ce "Ba tone tone zamu yi ba, ai kin gama magana tunda na yi sa'a kina ganin mutuncina. Na gode miki da wannan karamcin, ina son ki fiye da komai". Ya lankwashe murya ya ce "Mutunci da soyayya idan suka hadu fa'din irin al'amuran da zasu haifar na nutsuwa ma bata lokaci ne Yabin J". *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* ✍️ *BAK'AR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *(MRS M.I.NASHE)*. *Marubuciyar* *Halin Yau* *Sabo da kaza*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S ONLY*. *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko kuma kina sha'awar yin register da su. Ki tuntubi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn mai kore dukkan kwadayi*. *07036662633* https://arewabooks.com/chapter?id=64ff47e14ba2e11c69ef3f2f 9&10. Na sunkuyar da kaina k'asa alamun kunya, gane hakan da ya yi, sai ya mayar da hankalinsa wajen kwarzanta ni, tare da maganganun masu taushi da nuna kurewar matsayin mutum. A hakan har ya samu na dawo masa Yabin J bata Marina marar ragayya idan an tabo ta ba. Domin sai da kunyarsa da nake ji ta dawo, walwalar da fuskata take yi idan ina gabansa ta dawo. Hakanan shaukin da zuciyata take yi ya bayyana. Sai goma saura ya tafi bayan ya bani ledar atile da kuma turare, wannan karon har da takalmi mai kyau. Ina shiga gidan na ci burki a dalilin maganganun da suka ja hankalina. Muryar Mama nake ji daga dakinta tana cewa "Da gangan kake zuba mata ido take yin yadda ta ga dama. Jiyan nan yarinyar nan ta muzanta gyatumarka, amma tana shigowa ka bita da addu'ar da ban ta'ba jin ka yiwa wata cikin manyan ya'yanka ba. Ba wacce ta samu lasisin tara samari a gidan nan sai Yabi, nan Indo ta yi farinjii fiye da nata, sai ka fititke akan sai dai ta zabi guda daya, amma wannan da yake y'ar tijara ce ka barta ta zamo wa uwarta haja, dan kuwa nasan baka samun abin da take roro musu. Saboda ba'kin cikin kada wasu su ci. Yau Jabir ya kawo musu, jibi Audurashid, gata malamin makarantarsu". A hankali na ji muryar Baba yana ce wa "D'a ai mallakin uwarsa ne Habiba, duk abin da uwa ta ci ko ta samu a sanadin y'ay'anta bai zama abin a yi magana a kansa ba domin ta cancanci dukkan sadaukarwa daga wajensu. Ban da Dada da take da ra'ayin auren wuri wai duka nawa ma suke ne? Inda za'a bar ni da ra'ayina kamar yadda ake barina da hidimarsu da ba wacce zan aurar sai ta kammala sakandire bare Yabi mai karamin jiki ce". Ta harzuka ta ce "Waton ba zaka dai dakatar da su, ka bar guda daya ba ko? Wai yaushe ka zama mai son zuciya ne haka? Jikina ya yi sanyi da irin amsar da ya bata. Ya ce "Kinsan talauci ba abin da baya sawa, bana haufin shine ya mayar da ni mai son zuciyar, kamar yadda kika mayar da ni banza ko wacce magana zaki fada mini babu fargaba. Kin ta'ba jin na yi magana akan yadda yaranki ke ka'dai suke nufa da tallafinsu, ai saboda nasan uwa mafi uba ce ko da kuwa uban sarki ne". Ban sake jin harshenta ba, na wuce a raina ina ta murnar Babanmu ya fara gwada k'arfin halin taka mata burki, duk da a yanzu ma babu garantin ba zai lallabata ba. Domin ta riga ta jarraba shi ainun. Washagari asabar da wuri na tashi na ha'da kayan wankin dakinmu gaba'daya. Na aiki Anas ya siyo mini sabulu da omo tun daren jiya dama. Na fara wanki, yayin da shi kuma yake janyo mini ruwa a rijiyar bayan shashinmu. Kafin karfe takwas din safe na kammala na shanya su reras. Tuni kuma Inna ta kammala abin karin kumallo. Na karbo mana namu dumamen tuwon da Nazira, ga kuma kokon a jug da kullum Gwaggo sai ta bawa duk wanda yake son sha a gidan. Kusan kullum sai na tambayi ko ribar nawa take samu? Yadda bana gajiya da tambayar itama bata gajiyawa wajen cemin "Wanda ake sha ne ribata". A duk sadda ta fa'di hakan ban cika fahimtar rufin asiri ba ne sai kawai na kalli ita din mace ce mai yin hidima a inda ba'a ganin darajarta. Kafin Nazira ta gama wanke baki na k'osa domin indai na yi wanki to bani da jarumtar ri'ke yunwa sai na ji tamkar an mini yasa a cikina. Ta tarar tuni na fara cin tuwon. Ta zauna tana fa'din "Yabi sark'a, yanzu da ni ce na fara ci ban jira ki ba, sai kowa ya ji kwakwazon ki" Na rausayar da kai tare da fa'din Ayyah Addah Nazi kinsan bana shiri da yunwa ko kadan. Muna karyawa ina bata labarin yadda ta kaya a tsakaninmu da Yaya J. Ta murmusa ta ce "Yabi duniya! Yanzu Yaya Jabir din ma ba zaki dinga raga masa ba? Na dan daure fuska na ce "Ai matu'kar zai tsokano ni tabbas zan ajiye komai na yamutsa shi inta kama a rabu ma shi kenan. Ba zan dauki wula'kanci ba ko ka'dan. Ta girgiza kai tare da cewa"Allah ka shirya mini Yabina". Dai dai lokacin Baba ya fito da nufin fita. Muka gaishe shi ya amsa yana cewa Nazira da Asiya albarka ta kewaye mini ku". Cikin farin-ciki mai yawa muke fa'din ameen Babanmu". Amma sai na sake cewa "Babanmu Asiya fah?" Ya murmusa ya ce " Ho Yabi! Da ikon Allah sai kun sauke farali daga ke har y'ar-uwarki. Sai kin zama Hajiyar ta sosai". Cikin karadi na ce "Ai kuwa dai Babanmu "Dawafi na mussaman zamu yi maka!" Ya fice yana dariya. Babanmu wani irin uba ne da yake wasa da raha a tsakaninsa da y'a'yansa, babbar matsalarsa kawai Mama ce, domin yanzun nan sai ta saka ya ci mutuncinka ko na uwarka akan idonka dan ma an yi sa'a abin ya dan fara sau'ki, na sani kuma karfin addu'ar da muke yi ne mu da Gwaggo". Kwanaki suna ta shude wa har muka yi jarabawar zangon karatu na uku. Muna tafe kowa da sakamakonsa a hannunsa, Nasiba da su Firdausi sai murna suke yi a dalilin sakamakonsu ya yi kyau. Nazira ma babu laifi domin ta sha biyu ta zo. Amma ni kam sakamakona ba zai nunu ba domin kuwa ta arba'in da takwas na zo a cikin mu hamsin da bakwai. Kowa ya nuna sakamakonsa a tsakaninmu. Amma ni na boye nawa kamar yadda na saba. Muna tafe Maijidda sai fa'di take "Akan me za ki dinga ganin results dinmu amma ke ba zaki yarda a ga na ki ba?" Na gallah mata harara na ce "Saboda mahaifina bai fara gani ba, ba kuwa wanda yafi cancantar ya fara gani sai shi". Ta tunzura ta ce "Kins an Allah yau sai na ga ni, ai na sani ta karshen aji kike yi. Ban da class master din ajin naku saurayinki ne ai demotion ne ya kamace ki Asiya". Na fusata kwarai da gaske na ce "Tabdi jam! Yabi kika je fa wa wannan maganar?" Ba shakka ta ce "An fa'da miki Asiya. Kin dauka ina jin tsoron ki ne? Idan ba jakar aji kika dauka ba to miko mini sakamakon ki kamar yadda na baki nawa kika ga ni". Na girgiza kai da tare da yin k'wafa mai tsananin gaske. Nazira kuwa sai fa'di take "ba ruwanki da al'amarin Yabi fa Maijidda". Ta ce "Na shiga komai zata yi, ta yi ina daidai da ita". Ban ce komai ba sai da muka isa zauren Gidanmu ba zato na shake Maijidda da dukkan k'arfina, ina kai mata duka ko ta ina. Kafin ta yi yun'kurin ramawa na jibge ta sosai, sannan kuma muka ci gaba da gwabza wa. Aka rasa mai rabamu domin duk wacce ta ta'ba ni kanta fa'dan zai koma sun san haka dabi'ata take. Nazira sau fa'di take Yabi sake ta, amma bata ri'ke ni ba, domin ta san ce wa zan yi bata taya ni fa'da, ta taimake ni ba tunda bata kishina, akan me zata ri'ke ni? Na turmushe ta ke nan na debo k'asa ina shirin cika mata bakin da ya yi mini izgilanci sai ga Bulkachuwa ya shigo. Ya hau fa'din ke Asiya Toro wanne irin abu kike yi haka ne?" Ganin na fara kokarin danna mata a baki ya sanya shi iso wa garemu, bai jira komai ba ya saka hannunwan sa ya cira ni cak kamar y'ar tsana ya yi wurgi da ni. Na yi sa'a na dire akan sayyadata. Da yake a hassale nake sai na durfafe shi ina cewa "To kai ma din ai ba tsoronka nake ji ba, ka zo ka zaune mana a gida ka uzzira mana haba.?" Na kalli yadda ya harzuka amma ko gezau ban yi ba, duk da ban fi iya cikinsa ba. Ya kalli Nazira ya ce "Me ya ha'da su?" Ta tsara masa yadda aka yi ba ragi babu kari. Ya juya ga Maijidda da take hawaye ga jini a hancinta tabbacin habo ne ya goce. Ya ce "Dube ki gansamemiya da ke amma wannan y'ar tsakon ta lallasaki haka, wanne irin mutuwar zuciya ce ta same ki?" Na galla masa harara tare da murguda baki na ce "To ni komin girman gardi ma ba zai hana na zubar masa da jini ba, bare kuma mace yar-uwata". Ya nuna kansa ya ce "Asiya Toro ni kike tunanin zaki buga?". Na ce "Ba dan ha'da jiki da kai sai ballagazaye ba, ba abin da zai hana na zage mu gwabza y'ar k'ashi Wallahi". Ya nuna ni da yatsa ya ce "Asiya Billahillazi zan sumar da ke, yar iska marar mutunci kawai.". Yana rufe baki na ce "Ga ka nan babban dan-iska mai shiga fa'dan mata, yabi bayan wacce take da abin da zai lallaba ya cuce ta." Ya yo kaina yana fa'din ashe "Izgilancinki mai girma ne haka?" Ga mamakinsa sai kawai na yi shirin kai masa naushi tamkar bacaniya. Wannan dunukule hannu da saitin da na yi, ya yi matu'kar bashi dariya da tu'ajjibin k'arfi halina. Ya tsaya ya ce dambe zaki yi da ni? Na ce "Allah suturu bu'kui na yi dambe da mai daudar zunubi irin ka, kuma ni ba ballagaza ba ce, kawai zan kare kaina ne daga cutarwar ka". Ya jima bai ce komai sai ya kalle ni ya ce "shahsa da bata iya komai ba, sai fa'da da rashin kunya a aji kuwa ita ce dalkiya". Ba'kin ciki ya mamaye ni, idona ya ciko da hawayen takaici na ce "Na gode wa Allah da na yarda ina zuwa makarantar, wani ma tsabar akuyanci korarsa aka yi daga karatun nasa. Me za'a yi da mai halin bunsuru?" Ya rasa yadda zai yi da ni sai kawai ya shammace ni ya dauke jakata yi wuf ya zaro takardar sakamakon da take a farko farko. Ya juya zuwa waje ya bu'de ya ga yadda jan biro suke mamaye sakamakon. A karshe ya ga ta yadda na zo sannan ya mayar ya shigo ya kalli yadda na tumbatsa ya ce "Anya Asiya ba dusa kike ci ba kuwa? Ace har kin doshi hamsin? Gaskiya ina taya Baba ba'kin cikin asarar ku'din taran da ya wanzu yana baki". Cikin rawar murya na ce "Bulkachuwa Yadda ka tozarta ni a gaban wanda suke son na tozarta in sha Allah sai an tozarta budurwarka fiye da yadda ka mini, da ikon Ubangiji sai ka ha'du da sharrin mace, sai ka muzanta a idon duniya". Ya make kafa'da alamun ko a jikinsa tare da cewa "Yabi yanga mai kwakwalwar kifi". Ganin hakan ya sanya Maijidda ta mike tana jin karfi yana shigar ta tunda ta ji abin da take son ji. Ta mini gwalo tare da cewa "Na ji dai, dama nasan baki tsinana komai ba". Ta shige wajen Dada da saurin ta. Yayin da ragowar suke fa'din "Yi ha'kuri Yabi, ai kin nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane. Ba gashi ta tsere ba". Na jijjiga kai na ce "Ai dan ta ga Bulkachuwa ya tsaya mata ne". Yayin da shi kuma ya ce "Ba dole na tsaya mata ba, tunda ke din karfinki na aljanu ne, na tabbatar ba ke ka'dai kike fa'da ba, kina samun tallafin aljani mai kilabo da gwaigwai". Duk wajen aka fashe da dariya illah ni dana sake fusata na daga murya "Ina ce wa "Allah ka dora wa matar Bulkachuwa aljanun da zata dinga daga shi sama tana danfara shi da k'asa". Ya wuce yana fa'din "Duk bala'in aljani ba zai shigo mini gida ba, domin hafiza zan aura mai hazakar gaske a ilimin boko da na addini. Safiya da marairaice ta yi ta tofe mini gidan da azkhar, idan kin ga aljanu sun yi tasiri, sai a gidan wanda basa mayar da kai a wajen bautar Allah irin ki". Na wuce shi zuwa shashin Dada. Na tarar da Maijidda tana ta kuka yayin da Dada take sakacen hakori da tsinken zabori hankalinta a kwance. Na bu'de baki na ce "Dada sannu da gida, mun dawo". Ta amsa ba alamun damuwa a tare da ita. Na juya na tafi sai na ji kukan Maijidda ya karu tana cewa "Kin bar ta tafi baki bi mini kadina ba?" Na yi tsam dan na jiyo amsar Dada. Kamar ba zata tanka ba sai kuma na ji tana ce wa "Na k'i na yi mata maganar. Yar kankanuwa a gabanki, sannan kin bata kwanaki arba'in cif amma kin kasa kwatar kanki a hannunta sannan dan asaranci ki ce na tare miki fa'da? Ai kinsan fa'dan ta baya mutuwa akan me zaki tsokano abin da yafi karfinki?" Maijidda da bata yi zaton haka Dada zata ce ba, domin mun saba yin fa'da da yan k'ofarsu ta basu gaskiya ko da kuwa ni ce mai gaskiya. Dada ta ja tsaki ta ce "Sadda nake cikin shekarun kuruciyata haka nake nima duk girman mace bata bani tsoro, haka nan duk wanda ya mini kan ice sai na yi masa na kara. Sai yanzu na fahimci wannan tijarar ta Yabi sawuna ta biyo domin komin sharrin mai sharri ba zai ce ubanta mafadaci ba ne ko kuma uwarta. Dukkan iyayenta sanyin kalau ne, dan kuwa inta sune kiyama ba zata tsaya ba." Kukan Maijidda ya tsananta ta dinga yi tana ce wa "Ai dai kinsan bata isa ta kai ni k'asa ba, dunbular mini kirji ta yi ta yakushe ni a wajen." Salati Dada ta dauka tana cewa "Ikon Rabbani, tarihi na maimaita kansa ni Fadimatu. Wallahi Maijidda sadda aka mini auren fari ina kankanuwa aka kai ni babban gida, matar wan miji ta saka ni a gaba, duka, kyara zagi. Har na fara girma a cikin fargabar wannan baiwar Allah na ke. Ai kuwa da tura ta kai bango na fara rama abin da take yi mini. Har muka kai jallin da muka fara dokuwa, sai dai kashi take bani da yake ta fini sosai, ai sai kawai nake fakar ido idan muna damben ina mintsinin nonuwanta ko na na cije su. Shi kenan na yi maganin gallazawarta, ta shiga kiyayata. Yau ga Magajiyata na samu a haulata". Ta fa'da tana tafa hannu tana sake jan salati. Na wuce ina son yin dariya amma ba'kin cikin Bulkachuwa ya dabaibaye ni. Na wuce shashinmu ina jaddada wa kaina ko a gaban Baban kasuwa ne Maijidda ta tsokano ni sai mun sake cire raini, bare Dada. Bamu jima da dawowa ba sai ga mahaifiyar Maijidda da kanta ta kawo togaciya. Fadi take "Tura ta kai bango kullum Yabi sai ta yi mini sanadin bacin rai jiyan nan ma sai da ta dakar mini Kaltume akan sun samu sabani da Ismail, akan me zata tisa mini yara a gaba irin haka?" Ha'kuri kawai Gwaggo take ta bata, Inna da ta rage tsananta gaba da ni a dalilin ina yiwa yaranta hidima tamkar yan dakinmu, sannan ba mai tab'asu a waje matu'kar ina wajen sai hakan yayi tasiri, ta rage daukar zugar Mama. Dan haka sai ta ce "Ban da ke ma Abu da shiga shirgin yara ina ce Maijidda ta girmi Yabi ne? Sannan idan kinsa ha'kuri anjima ka'dan zaki iya ganinsu tare". Nan da na ta harzuka ta ce "To Yabi ni kaina ai sai ta dake ni tunda fa'dan yan-iska take yi, ban da dai ta riga ta rik'a ta yaya zata dinga dumbular kirjin y'anmata, tabbas dayan biyu ne, ko dai niyyar kisa take yi ko kuma ta shiga sahun masu *Bak'ar Ta'adar* neman mata." *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko kuma kina sha'awar yin register da su. Ki tuntubi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn mai kore dukkan kwadayi*. *07036662633*. Gwaggo ta ce "Dutse a tsakaninmu da duk masu wannan al'amarin, muna neman tsarin Allah da su, muna kuma nema musu shiriyarsa." Ta ce "ASMA'U Wallahi kin siffatu da agwagwa, ace wai baki isa ki sarrafa y'ar cikinki ba, ta gallabi kowa a gidan amma ba k'ya yi mata fa'da, saboda tana samun ku'di shiyasa ta gagareku? Sai ayi ta fankamar ku'din kitso da na lalle ne, alhalin munsan samarin da suke mata layi ne suke bata. Wallahi idan ba sa'a kika yi ba sai Yabi ta hana ki shan ruwa kamar yadda ta fitine mu". Na fito na ce "Umma ya isa haka nan, ba zai yiwu fa kizo k'ofarmu ki zagi Gwaggo ba". Ta mini dakuwa ta ce gidanku tabbataciyar yarinya marar albarka". Tana rufe baki na ce "yarinya tana bayan uwarta Wallahi, albarka kuwa da ikon Ubangiji sai na yi ta". Gwaggo ta yo kaina na ki guduwa tasan kuma matu'kar ta kawo mini duka ban gudu ba, na riga na shiga yanayin da nake bu'katar a kashe ni kawai na huta. Inna ta yi maza ta karbe itacen hannun Gwaggo tana fa'din "Wannan ai sai ki sabauta ta". Yayin da Umma Abu ta juya tana fa'din "Zaman babban gida ko masifa, ba dama a ganka da haske sai an tisa ka a gaba da ba'kin ciki da hassada tamkar dai kai ofne ka tare wa mutum nasa arzikin". Tana fita Gwaggo ta kalli inda nake a tsaye kik'am tana fa'din "Kin ji da'di ai da wannan wula'kancin da kika janyo mana". Ban ce komai ba, sannan kuma ban ji a raina cewar zan koyi ha'kurin dole idan an ta'ba ni ba. Wannan rikicin yana cikin al'amura masu tsananin gaske da ya faru. Domin da daddare babu kunya bare kawaici Baban kasuwa ya gurfanar da mahaifina a gaban Dada yana ta sababin ya gaji da yadda na takura wa ya'yansa amma ubana ya kasa tsawatarwa. Da yake Dada bata iya tsallake umarninsa sai kuwa tabi bayansa. Ta dinga fa'din ai tsoron zuciyata yake yi. Cikin rishin kuka Baban kasuwa ya ce "Ki gafarce ni Dada! Wani satin zan koma gidana dana kammala gina wa tun bara, amma na kasa tashi saboda ke, to yanzu kam zan tashi na gaji da wannan masifar Wallahi". Dada ta ce "Wallahi ko ubanta ba zai tashe ka ba tunda matsayinku guda a cikin gidan bare kuma ita. Share hawayenka ita ce zata bar mini gidan". Na sake kasa kunne domin tunda aka aiko cewar Babanmu ya zo in ji Dada nasan karata za'a kai sai na bi bayansa ba tare da yasan ina binsa ba. Na makale a soron Dada ina addu'ar kada Allah ya kawo Bulkachuwa tunda dakinsa a cikin soron yake. Ta ce "ka fa'dawa Yabi ta tsayar da miji da dukkan yaran ma. Na umarce ku, ku aurar da su nan da watanni biyu". Baban kasuwa ya ce "Shi kenan" Ya fice ya barta da Babanmu." Ganin zai fito ya gan ni sai na yi maza na fice daga soron na tsaya a bakin k'ofar shashinmu. Ya zo wuce wa ya dallaro mini ido da sabuwar tocilayit dinsa da alamu suka nuna yau ya zuba mata sabbin batira saboda tsananin hasken ta. Na dauke kai tare da saka hannunwana na rufe fuskata dan rage wa kaina kaifin hasken da ya dauke mini ido. Takaicin rashin gaishe shi ya sanya ya ce "Asiya ce?" Na dauke kai a shak'e na ce "Yabi ce?" Ya kuwa bu'de murya ya ce "Ja'irar yarinya mai mugun y'anci dama nasan ke ce zaki gan ni ki mini irin wannan iyashegen. Na ce ba, zaki yiwa ubanki Sani hakan?" Na dauke kai ina kunkunin fa'din "Ai kai ma ba zaka yiwa su Maijidda irin hakan ba". "Me kika ce? Bude Baki sosai ki fa'di abin da kike ce wa shedaniya." Ganin Baban Tsakiya dawo ya nufo mu dan ya shiga wajensa ya sanya Baban kasuwa ya d'auki k'arfaffan salati. Ganinmu hakan ya sanya Baban Tsakiya ya dakata ya ce "ya ya ne Iliya?" Ai kuwa ya hau rattab'a masa bayanin da aka yi masa na karya akan fad'anmu da Maijidda. Wani abin mamaki a gabana ya lauya zance yana fa'din a gabansa ma, na zage shi yanzu nan. Da kunnensa ya ji ina zaginsa. Baban Tsakiya yana bu'de baki sai ce wa ya yi "Tuni fa na d'iga alamar tambaya akan yarinyar nan domin wacce ta saba cudanya da maza ne take irin wannan dibar albarka." Gabana ya yanke ya fa'di wacce irin magana ce mai muni ta fito a bakin kanin mahaifina kuma uban wanda nake burin aure?" Na yunkura da nufin mayar masa da zazzafar magana sai kuma na tuna girman aika aikar da zan janyo wa kaina da uwata. Na sani mahaifina ba zai d'auki al'amarin da sauki ba, domin kuwa zai ce tunda na iya zagin dan-uwansa shima zan zage shi, hukuncin da zai biyo baya kuwa na tabbatar zai zama mai tsananin gaske. Na ha'diye maganar na juya na tafi na barsu dan kada na yi subutul kalam. Sai na sake juyo muryar Baban kasuwa yana sake cewa "Na kagu a samu mai tsautsayin daukar kara da kiyashi ya zo ya kwashe ta, ko zamu sarara da musibarta domin ta riga ta zame mana tamkar annoba" . Baban Tsakiya ya ce "Lallai kuwa kara da kiyashi daukar marar sani, na tausaya wa ahalin gidan Sarkin gida q tunda ina ganin d'ansu a wajenta" "To namu d'an fa? In ji Baban kasuwa. Baban Tsakiya ya yi wata irin dariya ya ce "Ta yaro ai kyau take yi bata k'arko, yaushe kana ganin kashi a jikin mutum, za kuma ka yi kuskuren bari naka ya dauki abin nan?" Kai-tsaye dakin Gwaggo na fa'da na zauna akan tabarmar da take shinfide, yayin da take zaune gefe daya, yanayinta ya nuna a takure take ma'ana tana cikin zullumin kiran da aka yiwa Babanmu me zai haifar mata. Na sassauta murya na ce "Gwaggo ki yi ha'kuri dan Allah" Ta muskuta ta ce "Idan ban yi ha'kuri ba ya ya zan yi ne Yabi? Ai a gabanki aka tabbatar mini ni agwagwa ce akan ki. Kinsan me hakan yake nufi kuwa?" Manufa kina gaba ina bin ki a baya, saboda gudun zuciyarki da nake yi. Ace yanzu kullum a cikin d'aukar wa kanki baki kike, sai ka ce ke kad'ai ce a gidan? Ga yar'uwarki nan ban ta'ba jin an kawo togaciyar Nazira ba. Amma ke idan ba'a kawo k'ararki ba, sai idan baki fita ba, ko kuma kin ha'du da masu alkunya, anya Yabi kina ganin kin hau turba mai b'ille wa? Jikina ya yi sanyi sosai na ce "Duk fa'dan da nake yi kowanne takala ta ake yi, ba wanda nake yin sa na rashin gaskiya, amma ki yi ha'kuri zan yi kokarin koyo ha'kuri idan an nemi ganin rikicina". Ta kafe ni da ido tana cewa "koya ma zaki yi Yabi? To fa'da mini zuwa yaushe zaki fara bita?" Na yi kasa da kaina na ce "Addu'a zaki tsananta yi mini a sanya ni cikin bayi masu ha'kuri da kawaicin cutarwar mutane. Amma a zahiri saboda ke zan yarda na zama mai kawaicin tunda abin da kike so ke nan. Domin ni dai har yau ban ga ranar da ha'kurinki ya miki ba, ban ga kuma ranar da kawaicin Babanmu yayi masa ba, tunda yau an kai dan-uwansa ne mai kirana da lalatacciya mai bin maza". Na fa'da hawaye na kwace mini ba tare da na shirya zubarsu ba. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* *VIP 1k, regular 500.* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *Shaidar biya ta* *08032773332.* *BAK'AR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *(MRS M.I.NASHE)*. *Marubuciyar* *Halin Yau* *Sabo da kaza*. *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ──────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* 11&12. A ki'dime Gwaggo ta ce "Baban Kasuwa ne ya fada miki hakan Yabi?". Na girgiza kai na ce " A a Baban Tsakiya ne". "Tirk'ashi" Gwaggo ta fa'da a hautsine. Na sunkuyar da kaina k'asa ina jin wani irin al'amarin tashin hankali na ratsa ni. Da kaina nake jin shekaruna sun yi k'aranci na dinga fuskantar irin wannan rikita rikitar. Na rasa dalilin da ya sanya nake da ba'kin jini a cikin gidanmu. Hatta a k'ofarmu mak'iyan da nake da su sun wuce misali. Domin kafatalin y'an d'akin Mama Nazira ce take sona fisabidillahi, sai ko Yaya Salamatu ita ma kuma ba yadda za'a yi alheri ya samu ta doshe ni da shi, sai dai Nazira, tana dai bani kuncen kayanta da suka sha ruwa ainun. Ni kuma murna nake yi domin tafi sauran yi mini adalci da sassauci. Mama kuwa da tana da ikon da zata kore ni a gidan da tuni ta yi hakan tsabar yadda ta washi ta bude ido ta gan ni, mussaman yanzu da sana'ata take sake kafuwa. Y'an dakinmu ne bana fuskantar adawarsu sai dai muna yawan haura wa sama da su a dalilinsu na ce wa ina daga wa Gwaggo hankali tunda kusan kullum sai na janyo mata bacin rai. Inna kuwa tare wa yaranta fa'da da nake yi ne ya sanya na kubuta daga nata kaidin. A hankali ta ce "Ai kuwa ribar ha'kurina gashi nan a bayyane tunda ban yarda na tafi na barku kun yi rayuwar ni y'asu a dalilin rashin uwa ba. Kina gani ina nan din ma ya ya kuka kare ne, bare kuma na zubar da ku na tafi? Ashe yanzu yadda yayunki suke dawainyar rike gidan nan bai isa abin alfaharina ba? A bayyane yake kafatalin ya'yan gidan nan ba wanda Babanku yake mora irin yaran dakin nan. Ai kuwa ko iya hakan na ga ni ba abin da zan ce da Allah sai godiya. Domin wasu da yawa yaran nasu basu amfani kansu ba bare waninsu ya amfanesu. Ubangiji ba abin da bai yi mini ba, na gode masa, kema na hore ki ri'ke ha'kuri ba abin da hakuri ba zai baki ba. Ta ri'ke kaina ta ce "Àllah ya miki albarka, ya sassauta miki al'amuranki. Ina fatan Ubangijin da yake sarrafa zuciya, ya sarrafa taki ta zama mai sassauci da afuwa". Kuka ya k'wace mini sosai ina cewa "Ameen Gwaggo". Ba komai yake sanya ni d'imuwa ba irin maganar Baban Tsakiya. Maganarsa ishara ce akan aurena da Yaya J ba zai yiwu ba. Zuciyata ta yi nauyi ainun. Na shiga rud'ani mai yawa, na sani idan har zan yi aiki da lura kamata ya yi na nisanci d'ansa tunda har yake neman maraba da ni a cikin gidanmu, ina kuma ace na zama cikin ahalinsa? Mutumin da bakinsa yake ambaton jaje da alhini ga ahalin wanda d'ansu zai kwashe ni. Bansan yadda aka yi ba na tsinci kaina da fashe wa da matsanancin kuka. Saboda fishin Baban kasuwa ya sanya Baban Tsakiya tsayawa ya mini irin wannan tozarcin da zai yi wahalar gaske na sake ganin girmansa. Na samu kaina da tambayar anya kuwa Babanmu ba dan uba ba ne a tsakaninsu? Sai nake ayyana ai ko y'ay'an Baffanni suke (cousins) bai kamata su dinga yi masa irin wannan kaskancin ba, dan kawai sun fishi wadatar abin duniya. Balle kuma girman nasaba irin ta uba guda, sai dai kuma babu haufi cikinsu daya ma'ana Dada ce ta yi nakudarsa tun gabbannin a yi tasu. Babban farin cikina d'aya, bai rasa wadatar zuciya ba, tunda duk tsananin wahala ba zai bu'de baki ya ce su taimake shi ba. Idan sun yi niyya akan kansu sun yi masa kyauta to zai kar'ba, amma idan zamu kwana mu yini bamu ci ba, ba dai ya ce wane ga halin da nake ciki ba, sai dai idan ya'yan cikinsa ne. Har ya k'wammace ya fa'da wa aminisa Alhaji Tanimu tsananin da yake ciki, ya tsananta. Matu'kar kuma zai fa'da masa to kuwa zai sauke masa buhun masara, dawa, dana gero. Sau tari kallon wadatar da ake yiwa su Baban Kasuwa yake hana masu k'arfi tallafa wa Babanmu. Sannan mutanan yau suna da dabi'ar k'in taimaka wa matu'kar ba ro'konsu ka yi ba, yayin da mafi yawa aka fi taimako da azumi, shima fake wa ake yi da sunan neman lada alhali a ku'din zakkar da Allah ya wajaba a fitar ne suke siyan kayan abinci suna rarraba wa. Oh mutanan yau mun rungumi *Bakaken Ta'adodi* daban daban. Allah ya shirye mu kawai. Muryar Inna na ji cikin sigar umarni ta ce "Ki cire Jabiru a ranki, nasan zai yi matu'kar wahalar gaske wannan al'amarin bai zama sanadin yin shamaki a tsakaninki da shi ba. Ina son ki ninka jarumtar ki, tun kafin su miki 'kwalele da shi." Kafin na bu'de baki sai ganin Baban Marina muka yi ya shigo a fusace yana fa'din "Ina Asiya?" Da rawar murya na ce "Ga ni Babanmu". Ya ce "zo ki fice ki bar mini gida tunda har zaki iya tsaya wa gar da gar ki zagi Badamasi da Iliya akan idonsu. Ai bansan zaki iya irin wannan dib'ar albarkar ba. Na dauka abin naki akwai lissafi a ciki amma tunda kina ganin idan kin yi karo tsakanin kwai da dutse zai miki daidai sai ki je ki yi a wani gidan, amma ba a nan ba. Ban haifi d'an da zai zagi dan-uwana akan idonsa na bar shi ba. Na sha fa'da miki babu ruwan ki da shiga tsakanina da y'anuwana. Amma sam kin k'i ji" Cikin kuka na ce "Ka yi ha'kuri Babanmu! Ba yadda aka fa'da maka al'amarin ya kasance ba. Ban zage su ba, har abada kuma ba zan zage su ba, kada ka kore ni a gidanka, zai iya zama sanadin tabarbare war al'amura masu yawa, ka mini dukkan hukuncin da zaka gamsu. Ka taimaki kanka, ka kuma tserar da ni fa'da wa halaka akan wad'anda basa nufin ka da alheri". Ya jijjiga kai ya ce "Yabi ki yawaita hamdala da baki zo a cikin mutanan farko ba, lah shakka da irinku ne masu kafiya akan ra'ayinku ko da ya ci karo da gaskiya. Na ji ba zan kore ki ba, amma dole ki yi nisa da gidan nan tun ban fusata na miki baki ba, tunda ba'kin cikin da kika cusa mini a sanadin musayar yawun da kika yi da iyayenki ba mai sau'ki ba ne, akan kannena mahaifiyata take mini mugun baki. Yabi kibi a sannu fa." Na sake tsorata na ce "Àllah ya huci zuciyarka Baba, Allah ya shiga cikin al'muranka, ya iya maka da iyawarsa". Nan da nan ya sauka ya hau fa'din "ameen". Gobe ki shirya ki tafi gidan Salisu har sai na nemi ki, saura can din ma ki nemi gigita masa zaman lafiya a gidansa, dan nasan zaki gano masa laifukan da iyalinsa take yi wanda shi yake yin uzziri a cikinsu". Na yi kasa da kaina na kasa cewa komai. Washagari kuwa Gwaggo da kanta ta shirya mini kayana a ledar biba tana ta jaddada mini idan na kuskura na yi rikici da matarsa to ba tantama da ita na yi. A sanyaye na ce "Komai zan ga ni zan runtse idona babu ruwana, ko da kuwa zata tsokane ni." Wani irin salama ya shiga Gwaggo ta dinga fa'din "Yauwa Yabina Allah ya sassauta miki". Anas ne ya fara yi mini gaba da kayana. Yayin da zamu tafi da Nazira da Iki idan anjima. Nazira sai kuka take akan tafiyar da zan yi na barta. Na yi shirin zuwa gaida Dada wanda rashin zuwa wannan gaisuwar ba k'aramin abu take mayar da shi ba. Babu kuzari na ce "Nazira mu je mu gaida Dada". Ta girgiza kai tare da cewa "je ki kawai, bana jin dadi anjima na leka". Na ce "Tom na tafi, ina jin da'di tare da k'arfafa wa kaina guiwar ko na rasa soyayyar kowa a fuskar zumunci ina da yakinin ba zan rasa soyayyar Nazira ba. Tana sona fiye da zatona, haka nima nake sonta tamkar yadda nake son shakikiyata Yaya Ummi. Tun daga bayan katangar Dada nake jin tashin muryoyinta da na Ya'yanta Na karasa har cikin soron sosai na dinga jin kumfar bakin da Baba Maryo uwar Nasiba take yi akan ba zata ta'ba yarda a dauki Nasiba a bawa Tijjani ba. Kuka take yi wiwi. Tana cewa "sai dai a ga laifina a banza, amma wannan ha'din ba mai yiwu wa ba ne." Yayin da Babah ta Bulkachuwa take fa'din "Ai ban ga laifinki ba, gaskiyar magana kika fa'da. Kuma dama mutum shi yake mutunta kansa, da ya nutsu ya zama mutumin kirki ina ce a ko ina zai nemi aure a ba shi?. Yanzu kuwa da ya zama abin da ya zama a cikin danginsa ma gudunsa za'a yi bare a waje". Dada ta ce "Ya isa haka, ba cece-kuce zaku yi mini ba. Na rufe wannan maganar, na yi zaton auren nasa da ita zai kawo masa dai-daito tunda tana sonsa, idan aka yi sa'a sai ya shiryu, ruwan wankan aure ka'dai maganin wanda ko wacce suka fand'are ne. Amma tunda abin zai zama tashin hankali a bar maganar haka nan Nasiba ba matarsa ba ce." Kafin na yi wani motsi sai jin muryar Baban Tsakiya ya yi yana fa'din "Kazalika wannan yar iskar yarinyar ba matar Jabir ba ce, ko bayan raina idan aka bari ya aure ta Wallahi Allah ya isa, na fa'da a gabanku, kuma yanzu ma idan na tashi zan je na sami Yaya Sani na tabbatar masa babu maganar aure, mun gama magana da Iliya, Maijidda zai aura. Domin ba zan yadda ya dauko mini majuniniyar yarinyar nan ta zo ta tarwatsa mini zuri'a ba". Daidai lokacin na yi sallama na gaida Dada sannan na gaishe su a jamma'u. Babar Bulkachuwa ce ta amsa cikin karfin hali tana danne bacin ran da ya ke kutso mata. Nima na yi jarumtar cewa "Ashe kin zo Babah?" Ta ce " Na zo dazun nan kin san sammakon zuwa nake yi saboda motar Jos muke shigowa. Na yi yake na ce "Sannu da zuwa". Na mike da nufin tafiya sai kuwa Baban Tsakiya ya ce "Dawo ki zauna. Na zauna ina kallonsa k'ir domin ya riga ya wanke mini a zuciyata. Ya kausasa murya ya ce "ki hanzarta turo wanda kuka shirya domin kuwa watan jibi da saba'a zaku bar gidan nan". Cikin son nuna masa iyaka na ce "To ai Jabir naka muka daidaita da shi, wannan satin zai iso garin, wajenka zan turo shi, ko wajen Baban Kasuwa?" Ya zabura ya mini dakuwa ya ce "Marar kunya, marar mutunci ki zagi dan-uwana, ki mini tsaki a gabana ki yi zaton kuma zaki zama surukuta, ko dai bayan sharholiyar da kike yi har shayeshaye kike had'a wa da shi? To saurara ki ji! Jabir ba zai auri wanda zata zagi ubansa ba." Babu fargaba na ce "Na karbi wannan hukuncin da hannu biyu Baba, ban kuma saka ka cikin masu son rai ba, domin na yi laifin da na cancancin hakan. Alfarma d'aya nake ro'ko a wajenku tunda ni ce bani da tarbiya, to ku musanya wa Yaya Jabir ni da Nazira domin dukkanku nan ba wanda zai zargeta da rashin tarbiya ko sharholiyar da ni nake yi". Nan da nan Baban kasuwa ya ce "Anki a bashi ita din dan uwarki, makira, algunguma, Maijidda ce matarsa har a kiyama kuwa". Ga mamakina sai na mike na tsinci kaina da cewa "Gaskiya Baban Marina ne ba a so, shi kuma har yana kora ta saboda ku. Ba komai Ubangiji ya sanya alheri". Har na fice ba wanda ya iya bu'de baki ya ce mini kala tsabar kad'uwar da suka yi da furucina. Baban Tsakiya ne cikin fishi ya ce "Ba shakka dangin uwar yarinyar nan akwai majununai". Na so na tsaya na ce "ko wanne d'a yafi gadon dangin ubansa, dan ya gane sune majununai ba mutanan Kangire ba. Sai dai kuma duk iyashegena ai wata fuskar tafi gaban mari, kannen ubana ne, ta ko wacce fuska idan na yi musayar yawu da su ni ce bani da gaskiya. Sai kawai na had'iye. Ina fitowa na yi kicibus da Bulkachuwa yana tsaye da buta a hannunsa, tabbacin daga bayi ya fito. Na tabbatar kuma ya ji komai har maganganun da aka yi a kansa da Nasiba. Domin gaba'daya manyan idanuwansa sun kad'a, sun yi jajur. Na wuce shi ban sake kallonsa ba, kallonsa ka'dai ya sanya na ji tamkar na yi amai tsabar yadda na washe shi. Wannan abin da na yi ya sake ki'dima wadannan bayin Allah domin dukkansu ba wanda maganar bata shige shi ba. A ranar na koma gidan Yaya Salisu ban san wainar da ake toyawa a gidan Marina ba. Zama nake yi irin na taka tsantsan a gidan, ba dan komai ba sai togaciyar da aka yi ta yi mini a gida. Da safe zan yi wanke wanke da shara, na yiwa dansu wanka shi kenan sai na shige daki. Idan ta gama abinci zata mini zubin auki. Yadda nake gudun bata mata, hakan ita ma take kaffa kaffa dan kada na ga beken ta, ko idan na koma gida na bada ba'kin labari a kanta. Ranar da na yi kwanaki hudu sai ga Nazira da Iklima. Muka yi hira, sun kusa tafiya Nazira ta ce da Iklima ta fita ta jira ta a waje. Ba musu Iki ta fita. Ta sassauta murya tabbacin bata son a ji maganar ta ce "Kinsan me yake faruwa kuwa a gida?" Na girgiza kai ina fa'din a ina zan sani Adda Nazi?" Ta sake yin kasa da murya ta ce "wata yarinya ce ta yi cikin shege har ta kusa haihuwa fa, to ana ta shari'a, da ta lissafo wadanda suke mua'amalantar ta har da Yaya Bulkachuwa yanzu haka kullum sai sun je kotu". Zuciyata ta harba da tsananin gaske, na ce "Tijjani gaskiya baya kyauta mana, gaba'daya sai ya gama ruguza darajar gidanmu alhalin shi ba dan gidan ba ne". Nazira ta ce "Hmm abin sai ha'kuri ba ki ga yadda ya zama ba, ya kuma kafe akan ciki ba nasa ba ne ba zai kar'ba ba. Babah ta Bulkachuwa ita ma ta zama abin tausayi sosai tsabar ba'kin ciki." Hawaye ya balle mini wata irin damuwa ta shige ni, kishin zumunta ya murde ni, ko yaya ba zaka so ganin jininka a cikin tozarci ba. Mun jima a hakan kowa da k'wallarsa ta ce "Jiya Malam Yunus Econs ya aiko a bashi izinin neman aurena kinsan tunda matarsa ta rasu a wajen haihuwa har yanzu bai sake wani auren ba, ga yaron nan tuni ya shekara biyu." Na ru'ko ta ina fa'din "Kai na yi murna sosai Allah ya tabbatar da alheri mutumin kirki ne, na amince Adda Nazi ta so shi ta bashi dama, Allah sanya albarka a tafiyar". Muka fito ina musu rakiya tana ce wa "Abdul sau uku yana zuwa amma Baba bai bari an fa'da masa inda kike ba." *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*. Na ce zai bari ne, domin ko Yaya Jabir ne autan maza na bar shi Nazira". Ta ru'ko hannuna ta ce "Madallah da zuciyar Yabin Marina! Ni nasan zuciyarta ba zata cigaba da son wanda zata yi kuka a hannun ahalinsa ba, ba zata so wanda ubansa yake k'yamarmu ba, in sha Allah sai kin auri wanda ya fishi komai, aurensa da Maijidda kuma bama adawa. Sai kuma kuka ya goce mata, nima hawaye ya sake zubo mini, domin idan na ce bana sonsa ko abin bai dame ni ba na yi k'arya. Amma zan nuna wa su Baban Tsakiya ni din yar halak ce ina kishin ubana, ina kuma kishin kaina. Babban rufin asirin da Allah ya yi mini shine dama ina da Abdulrashid. Su biyun duk ina sonsu amma nafi son Yaya J. Yafi daukar hankalina matu'ka da gaske sai dai zan iya rayuwa da Abdul ba tare da na takura ba. Sai da muka yi kukanmu son ranmu sannan muka je gidan Yaya Salamatu, muka bata labarin halin da ake ciki. A sanyaye ta ce "Babanmu ne basa so fa, gara miki ma hakan, Allah ya kawo miki mafi alheri me za'a yi ma da auren dangi irin namu ne?" Mun jima sosai sannan muka tafi, bayan na bata labarin Malam Yunus da yake son Nazira. Ta yi murna, ta yi farin-ciki, ta bamu dari biyar mu hau mashin. Bayan ta bawa Nazira kaya a leda ta kaiwa Mamansu. Na koma gidan Yaya Salisu, su kuma suka wuce gida. Kwanana shida da barin gida sai ga Yaya J a gidan Yaya Salisu. A matu'kar birkice na ganshi. Ya kasa mini magana, tsawon lokaci kafin ya ce "Me yasa haka Yabi?" Ba walwala na ce "me yasa, me ke nan?" Ya ce "na dauka ko baki ha'da komai da su Baban Tsakiya ba zasu ci darajata bare kuma iyayenki ne da zasu daura miki aure". Na bata rai na ce "Bana ma bukatar su mini walittaka Jabir, domin komin kashin Babanmu da ake ga ni, Ubangiji ya azurta shi da yara mazan da zasu maye mana gurbin kowa. Kai ko ba ni da yan'uwa maza a cikin gidan Wallahi Ammar da Bulkachuwa zasu iya daura mini aure duk da kasancewarsu ya'yan mata ne, amma idan har ya kasance sai ku to lah shakka zan iya saka hula na wakilci kaina ko kuma na samu alkali ko liman". Jikinsa ya yi matu'kar yin laushi. A sanyaye ya ce "Ni yanzu mene ne laifina a nan Yabi?' Yana rufe baki na ce "Rashin biyayyar ka. Na tabbatar an fa'da maka ka kiyaye ni, domin ban cancanci ka aure ni ba, saboda mahaifina ba shi da daudar duniya". Ya yi kasa da kansa ya ce "Ni da ke muke magana ki daina sako mini manyanmu domin wannan ba dabi'a ce mai kyau ba. Na gallah masa harara na ce "Madallah" Na tsuke bakina na yi gum. Ya marairaice ya ce "Yabi kada ki bari a bada kofar da za'a yi mana farraku, ina son ki, ina kaunar kasance wa da ke, jikina na bani kamar ma na kusa barin duniyar nan, ki taushi zuciyarki kada ki zalunci wanda yake tsananin sonki Yabi. Ban miki komai ba, kada ki hukunta ni da laifin da bani na yi miki shi ba". Jikina ya yi sanyi. Na kasa magana domin gaba'daya ya d'aure ni da jijiyoyin jikina. Zufar da take karyo masa ta sanya na sake jin sonsa na taso mini. Kafin na yi magana sai kawai na tuno maganganun mahaifinsa a kaina, wai ni da nake matsayin y'arsa, yar dan-uwansa amma ya jefe ni da mafi munin kalma wai ina bin maza, ke nan karuwa ce? Bayan ga hakan kuma ya ci mutuncin mahaifina wanda wansa ne. Take na ji karshen jakanci ne na cigaba da mua'amalantar jininsa da sunan soyayya. Mussaman da ya ce yana tausayin zuri'ar da d'ansu zai kwaso musu ni. Na dago cikin karfin zuciya na ce "Jabir mu yi datse wannan soyayyar ka ji, na rantse maka tun jiya na shak'e ta, na kwashe mata karama. Babanka ya tabbatar mini Maijidda ya za'ba maka, domin ita ce arzikin ubanta yayi daidai da shi, ban yi ba'kin ciki ba, domin kullum zabin Allah muke nema. Alhamdulillah! Na karbi wannan kaddarar da hannu bibbyu, domin Ubangiji na bar wa al'amarin, ya yi mana za'bi da kansa. Amma zan roke ka Yaya Jabir ka yi iya kokarinka wajen taka burki a ta'ba mutuncin Baban Marina da ahalinsa. Ina jin tsoron kada wannan matsalar ta yi girman da ba zata gyaru ba. Ina jin tsoron kada a wayi gari a ga gidan Marina ya zama sansanin yaki a tsakanin jini guda". A matu'kar birkice ya ce "Allah kada ya kaddara mini ganin hakan Yabi! Ina fatan mutuwa ta riske ni kafin wannan lokacin" Na girgiza kai na ce Shi kenan". Ya marairaice ya ce "Na tsugunna miki Yabi Asiya? Ki taimake ni, ki fahimce ni, idan kin kwantar da hankalinki ai za'a a samu sulhu ta sanadin aurenmu. Sai mu kawo dai-daito, an yi abin da yafi haka muni, kuma an dawo an shirya, kada ki tsananta, ki yanke mini hukuncin da babu laifina. Allah da kansa baya kama mu da laifin iyayenmu ko na y'ay'anmu. Daure ki ji tausayina, na rantse idan kin bani ha'din kai ba abin da zai sa na bar ki komai za'a yi kuwa" . Na girgiza kai na ce "Idan na yi hakan ba sonka nake da gaske ba. A gaban iyayenmu Baban Tsakiya ya ce "Idan aka baka aurena Àllah ya isa. Baya ga hakan kuma ya tsane ni, tsanar da ya danganta ni da karuwa ce ni, kuma ya ce na zage su, hakan ya janyo ubana ya kore ni saboda shi kullum yana sonsu, yana musu kyakkawan zato". Daga haka kuma sai kuka ya subuce mini. Bai hana ni yi ba, shima kuma idonsa ya ciko jijiyar kansa ta yi rud'u rud'u tabbacin yana cikin rud'u mai girma. Da murya kuka na ce "Maijidda ta fini kyau, ta fini gata tunda Babanta mai ku'di ne, ta fini komai, ka karbi zabin iyayenka na tabbatar Ubangijin adalci zai juya maka al'amarint fiye da al'amarina, tunda ka yi biyayya. Zan fa'da maka gaskiya ko zan yaudari kowa bazan yaudare ka ba. Kana da muhimmanci a rayuwata, da gaske ina ganin mutuncin ka. Na roki arzikin ka rabu da ni, na riga na ha'kura da kai Wallahi, maganar soyayya kam ta kau". Ya numfasa ya ce "Oh! Haka kaddara ta za'ba mini? Na so ace kin saurare ni, na so ace kin bani dama mun ha'da hannu da k'arfe mun yaki wannan *BAK'AR TA'ADAR* da take neman zame wa alummarmu tamkar wutar jeji. Ina cikin zullumin yadda zumuncin yau ya koma tsakanin masu kumbar susa. Ina cikin takaicin yadda aka jahilci d'an-uba. Ina matu'kar so a ce kin zama matata ta yadda zamu kawo cigaba ta fuskar zumunci a cikin zuri'armu ta hanyar mua'amalantar kowa da girmama wa. Amma babu komai, mu ci gaba da addu'a Allah baya juyar da addu'ar masu kyakkawar manufa". Ya saka hannu ya zaro hankicif ya fara goge zufar tashin hankali da take yanko masa, kalaman sa ba k'aramin sukurkuta ni suka yi ba. Amma na yi jarumtar waske wa domin har cikin zuciyata nake jin ban cancanci na zama cikin ahalin Baban Tsakiya ba. Ya kasa cewa tsawon lokaci sannan ya yi karfin halin cewa "Fatan alheri mai yawa gare ki Yabin J". Sai ya dawo da sauri cikin rawar murya ya ce "Yanzu kin mini adalci idan kika jingina sunan ki da wani na? Yanzu kin manta komai, bani da wata alfarma a wajen ki?" Na yi kasa da kaina na ce "Alfarmomi masu yawa kuwa . "Kai na fara so, kai kawai nake yiwa uzziri da sassauci bayan iyayena, sannan idan akwai wanda na yarda da son da yake mini to kuwa kai ne. Sai dai ko kusa bazan yaudari kaina ba. Iyaye girmansu yawa ne da su, Annabi (S.A.W) ya yi ta jan hakankalinmu akan mubi su. Idan kuwa hakane zan gwada maka cikakkiyar soyayya ta hanyar dora ka akan turba sahihiya, iyayenka duka biyu basa son almarinka da ni. Dan haka ka bar son zuciyarka, ka musu biyayya, na yi imani Ubangiji ba zai barka haka ba". Daga haka na fashe da azababben kuka. Jikinsa ya dinga kyarma ya ce "Na sani kina sona. Na roki arzikin, ki mini uzziri, kar ki ce mu rabu, mu bar wa Allah ya yi mana za'bi, mu yi addu'a mu ga ni. Jikina bai bani akwai namijin da zai aure mini ke alhalin ina numfashi a wannan duniyar ba". *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633*. *BAKAR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *(MRS M.I.NASHE)* *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ──────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *ALBISHIRINKU* *MASOYAN LITTAFAN MARUBUCIYA HAFSAT C SODANGI*! *DUBA DA YADDA KUKE KEWAR RUBUTUNTA YA SANYA TA YI SHIRIN SAKE DAWOWA DAN TA SAKE MUKU WANI RUBUTUN SABO DAL* *AMMA KAFIN HAKAN TA DAWO MUKU DA TSOFAFFIN LITTAFAN TA ZUWA KAN WAYA, DAN KU SAKE BITA TARE DA NAZARIN KYAWAWAN SAKON DA TAKE NUFIN ISARWA GAREMU*. *A YANZU HAKA LITTAFAI HUDU NE RIGIS* *WAYYO DUNIYA 1-3* *KYAUTATA 1-3* *DAGA K'IN GASKIYA 1-3* *MATA MASU DUNIYA 1-3* *KO WANNE 1K NE AMMA AKWAI DISCOUNT IDAN ZA'A SIYA SAMA DA GUDA DAYA* *MISALI GUDA BIYU-1500* *GUDA UKU 2500* *GUDA HUDU 3500* *ZA'A TURA KUDIN TA ASUSUN MARUBUCIYAR KAMAR HAKA* *0082739293, ACCESS BANK HAFSAT YUNUS ABDULLAHI* *SAI A TURO MINI SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *SAI NA BADA LITTAFIN DA AKE SO* *MADALLAH DA KARFAFA GUIWARKU* *MADALLAH DA SOYAYYARKU GA RUBUTUNMU* *AKWAI LITTAFANTA SAMA DA GUDA GOMA DA A YANZU SUKE SOFT COPIES, KAWAI KI TAMBAYI DUK WANDA KIKE NEMA A WAJENA CIKIN LITTAFANTA NA BAYA*. *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* 13&14. Da azama na shige cikin gidan na bar shi domin na samu sau'kin halin da nake ciki. Kuka na dinga yi tamkar zuciyata zata fa'do k'asa, bansan son Yaya J ya tumbatsa a zuciyata irin hakan ba sai yau, domin sai na tsinci kaina da addu'ar na zama gawa kafin igiyar aure ta d'auresu da Maijidda. A wannan daren barci rabi rabi na yi shi. Washagari da hantsi sai ga shi ya dawo, kallo d'aya na yi masa na gane yana cikin zullumi mai yawa domin gaba'daya ya zube ya sake fige wa. Yaya Salisu da ba shi da matsala da kansa ya masa iso har cikin falon gidan da yake dakuna uku ne a jere falle falle. Na fito a sanyaye sanye da hijabi idanuwana a kumbure a dalilin kuka da rashin barci. Na zauna a kujerar da ta yi nesa da wacce yake zaune. Tsawon lokaci muna zaune jigum jigum, tamkar masu makoki, daga karshe dai ya k'osa cikin murya marar amo ya ce " Yabi babu gaisuwa ne?" Kaina a kasa na ce akwai gaisuwar da tafi nema maka amincin da na yi? Shin ka raina sallamar ne?" Ya girgiza kai ya ce "Hakkun Yabi. Kin fini kusa da daidai, kin yi barci kuwa?". Kaina a k'asa na ce "Me zai hana Yabin Marina barci a wannan duniyar? Sai mutuwa, ko ciwo". A matu'kar sanyaye ya ce "Idan kuwa hakane ki shirya kwanan zaune domin kullu nafsin za'ikatul maut. A kowanne lokaci muna iya rasa mutane mafiya daraja a rayuwarmu, ko kuma a jarrabemu da ciwo mai hana runtsawa. Fata dai Allah ya bamu ikon cinye dukkan jarabawowin da suke dunfaromu. Ban da dai dan-adam an jarrabe shi da tsoron mutuwa, mene ne abu mai da'di a cikin wannan duniyar da a kullum tsanani da bacin rai suke sake yiwa mumini k'awanya?" Ban tanka masa ba, domin kuwa gaba'daya zuciyata babu sukuni, kuma cike take da ba'kin ciki mai nauyi. Cikin alhini ya ce "Yabi ban yi zaton munin dambarwar da take faruwa ta kai lalacewar da ta yi ba! Na gamsu, na ha'kura da aurenki a yanzu, dan na tsaremu daga fa'dawa halaka. Amma na rantse miki babu wata macen da zan sota irin son da nake yi miki, zan kuma dauwama a cikinsa. Tsoron hakkkm iyaye ne kawai zai sanya na yarda na yi aure kuma na mua'amalaci matar cikin adalci. Amma ban ha'kura da ke ba, zan cigaba da kokarina har sai Ubangiji ya mini taimakon tabbatar da aurenmu. Hawaye ya balle masa tamkar ba namiji ba. Da rawar murya ya ce "Akwai bukatar mu tsananta addu'a a cikin zumuncin Gidanmu Yabi. Daga jiya zuwa yau na fahimci BAK'AR TA'ADAR wariyar launin fata, ta yi kane kane a cikin gidan". Na dago idona jage jage da hawaye na ce "Komai zai dai-daita idan arzikin Baban Marina ya dawo, ko idan ya'yansa suka kawo k'arfi." A kasalance ya ce "Ba wannan ce matsalar ba kawai. Shin menene ribar hana ni auren ki?" Na dago na ce "Saboda ana ganin zan samu cigaba, ana ganin ban cancanci na samu irin wannan darajar ba, bai kuma kyautu ayi wa Baban Marina irin wannan zumuncin ba tunda ba za'a amfana da shi ba, an kuma rufe ido an mance irin amfanar sa da aka yi a shekarun baya". Ya yi shiru ya ce "ban gamsu ba, idan kuma wannan ne hujjar da gaske? Menene dalilin da zai sa ba za'a bawa Bulkachuwa auren Nasiba ba? Ai duk lalacewarsa jininmu ne. Idan za'a hana shi mace a cikin danginsa to ina za'a bashi? kawai halin da ya jefa kansa ne ya sanya baya iya tanadi. Amma idan aka bashi mace na tabbatar indai yana samun nutsuwa da ita, zai nutsu ya zama mutum na sosai, sannan zai daina zalama da tsilla tsillar da yake yi tunda yana da tasa ta halal a dakinsa ." Duk da matsananciyar damuwar da nake ciki sai da maganganunsa suka jefa ni cikin kunya da takura. Na kasa magana. Ya sake cewa "To saboda Allah idan ba'a taimake shi a cikin danginsa an rufa masa asiri, an tsaya kai da fata wajen ganin al'amarinsa ya kintsu ba, me za'a yi masa? A wajene ake son ayi masa irin wannan sadaukarwar da kishin kai? Babban tashin hankalin ita Nasiban sonsa take yi kamar ta kai kanta dakinsa. Da ace bata sonsa na zan ga laifin kowa ba. Shin wanne irin zamani muke ciki ne mai cike da son zuciya?" Nan ma na kasa cewa uffan domin tunanina ya riga ya tsuke, ban sani ba ko dan har yanzu ban gama fahimtar al'amuran da shi ya fahimta a tsakanin yammacin jiya zuwa yau ba. Ko dan ya fini shekaru, ya kuma fini ilimi da hangen nesa ne oho. Gaba'daya a rikice yake, k'warai kwamacalar da take cikin gidanmu ta gigita shi. Nasan bai san haka abin ya tsananta ba, tunda ba kasafai yake zaman garin ba. Ya jima kafin ya sake cewa komai. Ya mike ya zura hannunsa a aljihunsa. Ya ce "Bansan me zan ce miki ba, amma nasan zan rayu da son ki a raina muddin rai. Zan kuma rayu tamkar wanda ya rasa bangare guda a jikinsa. Ina fatan Ubangijinmu Allahu ya sanya mu cikin masu soyayya dan Allah. Har kuma yanzu da nake miki wannan jawabin ban cire alkalamina a cikin tawada ba. Ban cire rai cewar kaddara tana iya bani damar mallakar ki a matsayin matata ba. Ina neman alfarma, komin kankantar damar da zamu samu ta cikar burinmu kada laifin da bani na yi ba, ya shafi hakan Yabi. Ina da burin idan mun yi aure na mayar da ke makaranta ki zurfafa a ilimummuka daban daban. Amma ko yanzu ma ban fitar da rai ba, lokaci zai zo da zaki tsaya ki yi karatu tuk'uru, ki cire shiriritar da kike yi. Mu tsananta addu'a, mu barwa Allah ya yi mana zabin da ba zamu koka ba. Kin fini gaskiya duk al'amarin da babu saka albarkar iyaye to tsinannen al'amari ne. Fatan alheri gareki Yabin J". Ya fice da sauri. Jikina ya yi matu'kar sanyi, domin na tabbatar akwai abin da Yaya J ya ga ni a cikin zumuncin Gidanmu da ya warware masa duk wani confidence dinsa. Na kagu na samu labarin irin wainar da ake toyawa a gidan Marina. Na rasa yadda zan yi, domin Yaya Salisu ba mai zama ya tattauna magana da mutane ba ne. Na matsu kwarai na ga Nazira domin a bakinta zan ji komai kuma babu k'arya ko karin gishiri a cikin kalamunta. Kwanaki suka yi ta shudewa, ban samu ganin Nazira ba, ban kuma ji labarin komai ba. Abin da yake damuna daya ne takunkunmin hana ni zuwa gida da aka sanya mini. A hakan har na shafe kwanaki ashirin da biyar a gidan Yaya Salisu. Na riga na kai k'ololuwar gajiya da son jin makoma ta. Gashi ba wanda ya zo daga gidanmu. Dan ma ina samun y'an kitso da k'unshi, suna biyo ni, haka na unguwar ma suke yi mini layi. Rannan da na gaji, sai kawai na zari jiki na doshi gida a sayyadata duk da tazarar gidan Yaya Salisu zuwa Gidanmu tafiya ce mai tsayi ainun. Tunda na kusa k'arisa wa na fara jin jikina na kakkarwa, ga kuma luguden da zuciyata take yi tamkar ta faso ta fito. Bakina na ambaton sunan Allah, duk da idan ance na fa'di me nake fa'di ba zan iya tantance wa ba. Na fa'da zauren na yi kicibus da Baban Tsakiya, zai fita, da alamun rashin sukuni a tare da shi. A farko kamar ba zan gaishe shi ba. Bansan ya aka yi ba, cikin rawar murya na ce "Baban Tsakiya ina yini?" Ina daga tsaye ban rusuna ba. Ya mini dak'uwar da ta zame masa dabi'a ya ce "Baban farko ba na Tsakiya ba. Wato ke tabbataciyar yarinya ko? Sai kin ha'da da inkiya saboda ba kya mini kallon arziki.l? Zan ga mai daura miki aure, sai dai Ubanki ya waklice ki da kansa. Kuma indai ina numfashi duk wanda ya zo neman auren ki sai na fa'da masa rashin d'aarki da hatsabibanci irin na ki, domin fadar gaskiya a neman aure jihadi ne kabiran". Na yi k'asa da kaina ba tare da na ce komai ba. Ya juya ya tafi yana ta yi mini sababi da kwashe albarka da fatan tsiya iri iri. Na jingine a jinkin garun ina tambayar kaina "Wai haka kowa yake fuskantar bacin rai da danginsa ko kuwa iya ni ce? *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH*. Take na tuno Nazira bata fuskantar tsanani irin nawa a wajen Baffannin namu. Amma kuma ko ka'dan bata samun sakin fuska da alherin da suke yiwa ya'yansu. Na sake tafiya dogon tunanin yadda Baban Marina yake mua'amalantar nasu yaran. Mua'amala ce ta sassauci da ja a jika. Domin duk talaucinsa, yana k'ok'arin siyan albasa ko su mangwaro ya ce mu mika kofofinsu. Hakanan indai zai yi aski sai ya ha'da da ya'yansu an musu ya biya. Bayan nan duk wani rikicin da ya'yansu zasu rakito shine zai yi ta zarya yana bada ha'kuri har sai komai ya daidaita. Amma su ba ruwansu damu, wani ikon Allah Yaya Musa da yake a lalace sun fi sonsa, sun fi yinsa, sun fi tattalin farin-cikinsa. Na jijjiga kai a fili kuma sai na ce "Allah haska kofar Baban Marina, Allah ka jibanci al'amarinsa da na ya'yansa. Na shige cikin gida ban doshi k'ofar Dada ba. Yanayin da na tarar da Babanmu da ahalinsa ya sake sanyaya mini jiki. Na shiga bakina da sallama na isa kan tabarmar da suke zaune na tsugunna ina gaishe shi cikin girmama wa. Ba walwala Baba ya ce "Asiya me kika zo yi? Ba na ce sai na neme ki ba?" Da rawar murya na ce "A mini afuwa Baba! Na kasa jure ji daga gareku ne." A sanyaye ya ce "Na miki afuwa Yabi zo ki zauna. Da rarrafe na karisa kusa da shi a dalilin rawar da jikina yake yi ya sake ta'azzara. "Na yi godiya Baba Allah ya k'ara maka lafiya, ya shirya maka zuri'a, Allah ya mayar da ahalinka wasu masu fa'da aji". Ya yi murmushin da babu nisha'di. A sanyaye ya ce "Ameen Yabi! Duk yadda zan yi ba zan iya cire miki wannan BAK'AR TA'ADAR k'ullaci da ta shiga ranki ba. Amma abin da zan fa'da muku duk taku, duk wanda bai mutunta y'anuwana ba, to nima kar ya mutunta ni". Jikina ya yi sanyi, na yi kasa da kaina, na kasa cewa komai. "Yabi". Ya k'ira ni murya babu amo. Na amsa a hanzarce "Na'am Babanmu". Ya yi gyaran murya ya ce "Nan da kwanaki goma sha biyu auren y'anuwan ki. A duk wanda kuka taso ke da Nasiba ne kawai babu ku a cikinsu. Da gobe zan je na sanar da ke maganar a nutse cikin kwanciyar hankali. Na tura wa iyayen Abdulrashid su turo ayi magana to bansan inda aka haihu a ragaya ba, sai suka aiko mini da sun yi wa d'ansu mata tuntuni, ba da yawunsu yake neman auren y'ata ba." Jikina ya sake daukar bari a dalilin idan na fahimci maganar Babanmu kenan zan rasa Yaya J da kuma Abdul tashi guda, wannan shine biyu babu, kamun gafiyar b'aidu. Na tattaro dukkan jarumta na yafa a dukkan sassan jikina da fuskata. Na ce "Babu damuwa! Allah ya sanya alheri. Amma Baba har da Adda Nazi kenan?" Na fa'da cike da karsashi irin na tsananin karfin hali. Ya ce "Da ita Yabi, sai dai bana jin za'a yi tariya da ita, domin ban mallaki komai na aurenta ba, tunda titsiye aka yi mini." Na kalli dukkan yaran gidanmu masu hankalin suna wajen hatta Yaya Musa kuwa. Hawaye ya b'alle mini na ce "A a Babanmu da ikon Ubangiji a ranar zata tare. Na kalli Yaya Salamatu na ce "Yaya" Sai kuma na fashe kuka sosai. Dukkansu matan sai suka taya ni kukan in ban da Yaya Ummi da take Jin zafin yadda nake damuwa da lamarinsu alhalin ita ma ba sonta suke yi ba in aka dauke Naziran. Da rauni Yaya Salamatu ta ce "su uku sun kawo dubu sha biyar biyar, yan dakinsu kenan. Sai ummi ta kawo dubu biyar, Ni kuma na bayar da ashirin maigidana kuma ya bada buhun masara da na shinkafa ayi hidimar biki da su". Su Salisu kuwa sun ha'da hamsin a tsakaninsu dan haka dari da ashirin ne a k'asa kacal". Nan da nan na zaro magana tamkar babbar mace na ce "Ai kuwa sun isa Yaya, kuje ku siyo mata katifa da labule da ledar tsakar daki. Na kunce hannun zanina na kunce na fito da kudi kimanin dubu sha bakwai da dari takwas. Na ce ga nawa a siya mata bargo da zanin gado. Su Mama ku fito da kwanuka da tukunya. A kai ta a hakan da ikon Ubangiji watarana sai ta yiwa wani kayan daki na alfarma, ai duniya ce mai rawar y'an mata na gaba ya koma baya". Hatta Mama a wannan ranar na ga kallon sassauci da adalci take yi mini, domin da ta ga na sake dauko bankina na mik'a wa Nazira na ce "Ki fasa ki yi dinkin fitar biki nasan zasu ishe ki tunda kinsan mu din masu k'aramin karfi ne, masu nema a wajen Àllah." A fili take fa'din "Yabi da Nazira sai Allah". Baba kuwa zuba mini ido ya yi, tsawon lokaci kafin hawaye ya goce masa. Duk muka ha'du aka yi ta kuka tamkar an ce ya mutu ne. Domin ita kanta Mama da take ha'da kai da matan su Baban Tsakiya suna sake tsananta mana, ta sha mamaki da ta ga suna yiwa ya'yansu hidimar aure basu yi kara sun saka da Nazira ba. Wata'kila a haukanta zasu yi ko saboda da ita. Da rawar murya Baba ya ke fa'din "Allah ka sake jefa soyayya da tausayi a tsakanin ya'yana, Ubangiji na gode maka". Yaya Indo ta kira Malam Yunus ta fa'da masa ku'din lefe ya bayar yadda zai iya ba sai ya yi ba , domin kuwa muma abin da zamu iya za'a yi. Da yake ba yaro bane ainun, sai ya gamsu ya ce zai yi mata lefen yadda ya sauwaka, sannan zai bawa Yaya Salisu ku'din da ya sauwaka shi mutunci ya gani dan haka komai zai yi. Ba wanda ya san me ake ciki domin kowa ya zuba ido yana jira aje ganin dakunan amare Yayin da ta bangarena nake ta danne damuwar auren da Yaya J zai yi da Maijidda. Ita ka'dai ce amaryar da bata da kuzari a dalilin babu ha'din kai ko zumudin ango, komai sai dai mahaifinta ko na angon su yi mata. Gefe guda kuma Nasiba ta susuce domin ba karamin son Bulkachuwa take yi ba, wanda aka ce ya fito kuma a dangin Babanta sun ce bai shirya ba sai bad'i. Bulkachuwa kuwa yarinyar da suke takaddama ta haihu an yi gwajin halittar dan Adam bashi da alaka da jaririn. Sai dai an yi masa hukuncin bulala tamanin tunda ya amsa da bakinsa ya ta'ba takarta. Wannan lamarin, da bulalar ya yi matu'kar sururuta shi. Ya zama abin tausayi, duk wani iyashegensa ya zubar da rabi. Kowa ya ganshi sai ya tausaya masa. Hatta ni da bama ga maciji sai da na yi masa jaje. cike da alhini, ya dinga fa'din na gode "Asiya Toro, ki yafe mini, a duk sadda na tuna addu'ar da kika yi mini cikin fishi da kika ce sai na hadu da sharrin mace, sai na ce ashe dai Asiya bayan samun tallafin dan aljani yayin fa'da, har baki idan kika yiwa banu adam sai sun taimake ki, ya zama wajabat. Shiyasa na k'udire zan roke ki, ki mini addu'a na zama yadda mutane na gari suke". Na girgiza kai na wuce shi "Ina cewa "Allah ya shirye ka Tijjani". Ya d'aga murya ya ce "Da biyu kika yi wannan addu'a domin da zuciyarki fes take da ni Yaya Tijjani zaki ce". Ban tsaya ba, bare na tanka shi, a zuciyata kuwa ina fa'din mashiririci, ba sauya wa zaka yi ba, borin kunya ne kawai, ka zubar da mutuncinka a idon kannenka da iyayenka, Allah ya shirye ka kawai. Shikenan sai na dawo gida, muna ta shirin bikin Nazira. Auren da ya zo tamkar dirar mikiya, ya yi matu'kar rage mini tashin hankalin da nake ciki. Kitso da lalle nake yi babu hutu, tun safe idan na zauna sai magariba, sallah kawai take tayar da ni. Haka nake mika ku'din ga Baba ina fa'din "A dinga siyan kayan cefanen biki Baba" Da farin-ciki yake fa'din "Madallah da Yabi Asiya". Kallo daya za'a mini a gane ina cikin tasku kawai boye wa nake yi, sannan son Babanmu ya fita kunya da tozarta da ake son ya yi, ya danne wanccan damuwar. Domin yadda nake kishin Babanmu da yan k'ofarmu bana jin anan kusa za'a samu mai yin hakan. Shiyasa na cire son jiki, da lalaci nake sana'a, Ubangiji kuma ya haska, ya saka mini hannu, domin a rana ina hada dubu shida zuwa bakwai, mussamna idan kwanakin da ake yin biki ne. Da ce a birnin Kano nake yarfa kunshin nan ai da ku'di masu nauyi zan dinga ha'da wa, amma hakan ma na gode sosai, tunda mafi yawa manyan mata idan sun zo basa bayar da iya ku'din sai sun mini k'ari. Bana kuma jin k'yashin na bayar da komai dan mu yi hidimar mu cikin rufin asiri. Duk yadda Yaya J yake son mu ha'du na rufe kofofin da zasu sa mu kebe. Ranar litinin dukkanmu muna wajen Dada. Ana ta hira, na yi lakwas a dalilin bani da kuzari, ba k'aramin cizona auren J da Maijidda yake yi ba, har addu'a nake yi kada a wayi gari aga zuciyata ta buga a dalilin ba'kin ciki. Kwana nake yi ina kuka, ina kalubalantar wannan hukuncin da aka zartar mini tare da tsanar Baban Tsakiya da Baban Kasuwa. Tabbas a idona su din ba kowa bane face mutane masu son kai kuma y'an jari hujja. Dada sai farin-ciki take zata aurar da jikokinta kusan goma. Ta kalle ni ta ce ",Ke da Nasiba ne aurenku ya yi gardama, ga shi kune fitanannu." Ban kula ta ba domin abin da yake zuciyata fadinsa da ciwonsa sai ni da mahaliccina. Balle Nasiba da ta bari halin da take ciki ya bayyana a komai na ta. Ni mamakin da take bani wai akan Bulkachuwa take wannan ba'kin cikin, sannan abin kaicon shi bai ce yana sonta ba, kawai ya lura da yadda take mararinsa sai yake amfani da hakan yana sata tana yi masa bauta. Misali komin dare zai kawo indomie ya ce ta dafa masa, ko kuma ya ce ta dafa masa ruwan wanka, ko shayi. Haka idan zai fita zai bata mukullin dakinsa ta je ta gyara masa. Bai zame masa komai ba, ya kawo mata kayansa matu'kar zai ga tana wanki, yana fa'din "Ga karo". Bata damuwa hakan zata karba, ta wanke, ta goge. Shi kenan sai yake sassauta mata ya daina yarfa ta. Ita kuma ta dauki son duniya ta d'ora masa bata ko lura da rashin nagartarsa, duk kuma wanda zai zo da nufin yana sonta bata sauararansa, sai Dada ta yi mata wuta wuta. Matu'kar kuwa yana gida ba zata yarda ta fita ba, duk tijarar Dada kuwa. Tunda mahaifiyarta ta ce bai cancanci a bashi aurenta ba, ya dauke mata wuta, ya daina kula ta, ya koma muzurai ne a tsakaninsu shi kenan sai ta k'aratanwa kanta walwala, tunda ba yadda bata yi ba, ya fahimce ta shi kuma ya taurare. Saura kwanaki biyu aure domin tuni gidan ya fara cika da jama'a ana ta hidima tuni an yi wa amare jere. Da ni aka je jeren Adda Nazi, na dinga k'walla a dalilin irin rufin asirin da Ubangiji ya yi mana. Komai ya yi, ba wanda ya zaci za'a samu hakan. Na dawo Yaya J ya rutsa ni a soro. Murya a dushe ya ce "Yabi mene ne ya yi zafi ne, shin gaba zamu yi?" Da sauri na ce "Eh mu yi gabar kawai, yafi mini sauki da na saurare ka." Ya numfasa ya ce "Oh no! Kada ki yi mini hakan, ya miko mini leda mai dan dama. Na dauke kai na ce "Bana bukatar komai na ka". Ya rausayar da kai ya ce "saboda zumunci na baki fah". Na ce "To kuwa bana so, domin na shafe alakar da ta ha'damu". Ya fusata, sai kuma ya ha'diye dukkan fishin ya ce "To karbi dan Allah, dan soyayyar da nake yi miki". Na mika hannu na kar'ba ba tare da na ce uffan ba. Ya sassauta ya ce "Wannan auren ba zabina ba ne Yabi, ba abin da zuciyata ta za'ba mini ba ne. Dan haka zan yiwa kaina auren da zuciyata take so take kuma muradi. Na rok'e ki, kada ki juya mini baya. Kada ki haramta mini farin ciki a zuciyata da rayuwata." Yana diga aya sai kawai na rushe masa da kuka mai tsananin gaske. Fadi nake "Lallai kuwa wato zan yi ta zaman jiran ka ko? To ko dai kallon Yabin mahaukata kake mini ba ta Marina ba?" Ya ki'dima ya ce "me ya kawo wannan maganar? To ai ni ko a turu nake kallon ki ra'ayil aini, zan cigaba da son ki babu gazawa, cikin kowanne hali son ki nake yi, zan kuma cigaba da son ki YABIN J". Na ha'diye kukan da nake yi. Na zuba masa ido na ce "Na gode da soyayyar ka, Allah ya bada lada". Kafin ya yi magana Bulkachuwa ya shigo, ya kalle mu kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya kasa ha'diye maganar ya ce "Poor baby haka kawai kin zuba ido an k'wace miki abin da yake na ki ne, ni fa akan abin da nake so sai dai ayi kare jini, biri jini da ni." Ya kalli J ya ce "Jabir ka daina tare yarinyar nan tunda dai an baka wata ka karba, bar ta ta ji da suyar da kirijinta yake yi mata kawai". Yaya J ya daure fuska ya ce "Menene hakan kuma Bulkachuwa?" Ai kuwa ya ce "Gaskiya ce mana Jabir, ni yanzu da aka hana ni Nasiba ka ga na damu ne? Ai saboda dama soyayyar ba mai karfi ainun ba ce. Da son ya zama so deep da komai zai faru, ba zan yarda na musanya ta da wata ba". *Dukkan littafan Saliha Abubakar Abdullah Zaria akwai su in soft copies a hannuna.* Takaicinsa ya shake Yaya J. Ya nuna shi da yatsa ya ce "Bana son irin haka Bulkachuwa". Ya make kafa'da alamun ko oho ya wuce yana sake fa'din "Ato ai gaskiyar magana kenan, ku barta ta ji da bacin ran da take ciki mana, ai kowa yasan tana sonka, akan idonta da na iyayenta aka dauki wata aka baka, ka karba da sunan biyayya, amma ka kasa gwada kwanjin ayi maka alfarmar ka ha'de su biyun ka yi wuf da su. Sai kuma ka dinga tare ta kana tayar mata da hankali a wofi. Ita ma k'uruciya ce ya sanya take zubar da hawaye akan ka. Ni yanzu da na fahimci inda aka ajiye ni, na sake yiwa Nasiba kallon soyayya ne? Duk nacin ta bana sauraron ta". Daga haka ya fice gaba'daya. Yayin da Ba'kin ciki mai tsananin gaske ya dabaibaye Yaya J. Ya ce "Ban da ma idon ka babu kunya Bulkachuwa har ka iya tsayawa ka ce zaka fa'da wa wani dai-dai? Ina ka santa, ai kanka zaka fara yiwa bitar gaskiyar kafin wani, wanda tsoron Allah baya iya hana shi aikata kaba'ira, shine zai yi kishin ana bata wa wata lokaci, kai kuma *BAK'AR TA'ADAR* lalata y'ay'an jama'ar da kake yi fa? Ko an ce maka daga sama suka fad'o babu mai kishinsu?" *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* ✍️ *BAKAR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *(MRS M.I.NASHE)* *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ──────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAYAN G.H.T.* *DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA*. *HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *07039269802* *Follow me @Arewa books* https://arewabooks.com/chapter?id=6504c04660ef31f52af5ad6c *VIP 1k* *Regular 500 via* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *08032773332*. *Free pages na daf da tsinke wa* *Ku zo ku shiga tafiyar Yabi. Sa'adan Mk da Guduyon Gudale tuni suna cikin paid group*. 15&16. Bulkachuwa ya juyo ya ce "Tir da masu gori, Albarkar Annabi ba zaka samu Asiya Toro ba, tunda kallon kitse nake yiwa rogo, marar mutunci kawai". Ya juya ya yi tafiyarsa a tunzure. Ya juyo da nufin yi mini magana sai kawai na d'aga masa hannu na ce "Kada ka ce mini komai Yaya J. Wannan maganar fa, gaskiya ce tsagwaro. Na roki arzikin ka bar ni na ji da damuwata". Na juya na tafi. Na bar shi yana fa'din "Kaicon Bulkachuwa, ko har yaushe yasan mutuncin gaskiyar da har yake wannan zugar?" Ina shiga d'akin Gwaggo na zube na fashe da kukan da ya ja hankalinta k'warai da gaske. Ta jani jikinta ta ce "To mene ne kuma? Kin yi k'ok'ari, kin yi ha'kuri, sake daure wa mana, komai zai wuce fa". Na saka hannuna na rike ta sosai, baki na rawa na ce "Yi mini addu'a Gwaggo, ki yafe mini bacin ran da na yi ta sanya ki. Ina jin mutuwa zan yi." "Ba zaki mutu ba Yabi. In sha Allah! Ubangiji ba zai bar ki hakan ba, ai yasan an zalunce ki, amma daure ki cigaba da nuna jarumta, ki cigaba da sha'aninki tamkar baki da wata damuwa." Na ce "Abin ne yake neman fin k'arfina". Na fa'da, kuka na sake kwace mini. Ta dinga bubbuga bayana tana fa'din "yadda aka yi din ne akwai tozarci a ciki, amma ni dama bana son wannan ha'din domin tsananin da zaki fuskanta mai girma ne. Allah ya sa haka ne mafi alheri. Share hawayenki ki d'oro alwallah ki yi ta nafila tunda hantsi ne yanzu." Na kuwa mike ina share idon nawa, na fita da zummar yin alwallah. Na dawo na tarar da ita, tana ganin kayan da suke cikin ledar. Leshi mai kyau, da mayafin da ya dace da shi, da doguwar riga abaya, da takalmi da jakarsa, sai tarkacen sark'a da abin hannu ga kayan kwalliya da turaruka. Da envelope mai dauke da wasika da kudin dinki. Gwaggo ta ce "Wannan kaya masu daraja haka? Ajiye wa za'a yi sai Babanku ya ga ni". Na tayar da sallah ban ce komai ba. Mama da zata dafawa Nazira kazar aure har da Maijidda ta hada ta dafawa. Ina kallo yadda ta samo tattabaru ta hada da saiwowi ta sake dafa musu. Haka Gwaggo ta maze kamar bata gane ba. *Mai bukatar saiwowin dahuwar kaza ko na tattabaru da sauran kaya na mussaman ta mini magana akan lambata 08032773332*. Ina ji, ina ga ni aka daura auren Yaya J d'ina, da Maijidda. A ranar kam buya na yi, a makwabta na yi kukan da ban ta'ba yin irinsa ba. Na dinga jin wani irin abu tamkar zai fasa mini zuciya gaba'daya. Fa'di nake "Ya Allah! Ya Allah". Idan na tuna nagarta da sanyin halinsa sai na ga ba karamar asara na tafka ba, wacce na saddakar ba zan mayar da irinta ba. Har dare ba wanda yasan inda nake, sai da na ji dirin isowar motar daukan amare sannan na fito. Dan ba zai yiwu ace ban raka Nazira d'akinta ba. Da na fahimci Nazira za'a fara kai wa domin motocin kai ta ne suka fara iso wa sai kawai na fa'da daya daga cikin motocin. Sai a dakinta muka ha'du. Duk yadda ta ke lullube a cikin mayafi said da ta riko hannuna ta ri'ke gam tana sake kankame shi tabbacin farin-cikin da take ciki bai sa ta manta tawa damuwar ba. Sai da kowa ya watse aka bar ni da ita, domin dai bamu da wasu kawayen da zasu kai mana dogon dare. Ta kalle ni ta ce "Mu yi ha'kuri Yabi, kara daure wa, idan muna ganin ki a hakan ba wanda zai samu sukuni. Kinga ma yunwa nake ji, tun jiya da muka ci abinci ban sake saka komai a bakina ba, ba wanda hankalinsa ya kai a bawa amarya abinci, na sani da kina kusa da ni da kin bani". Na ce "Afuwan Adda Nazi, amma ai yanzun nan Malam Yunus zai shayar da ke nama da madara". Ta galla mini harara tare da fa'din aku sarkin magana". Na mike domin na ji ana fa'din mai motar ya dawo. Da k'yar ta bar ni na tafi, tana kuka, ina yi. Kwanaki ukun da suka biyo bayan bikinsu Yaya J sun fi ko wanne tsauri a gare ni. Sa'ar da na yi ma ba a gidan aka yi masa gini ba, a can bayan gari ne da kansa ya gina abinsa sai dai da tallafin Baban Tsakiya. K'aramin gida mai fasali na ban sha'awa, ba burin da banci akan wannan gidan ba. Ko bandakin gidanmu da yake sani takaici, da zarar na tuno bandakina a cikin daki yake a gidan Yaya J sai komai ya wanke mini, na yi ta zumudin zuwan lokacin da zamu yi aure, ashe dai wasikar jaki nake tsara wa. Tayals a ko ina, ga furanni har da fasadabir ya shuka mini, ga bishiyar mangawaro da ni na bayar da kwallon ya shuka, ita ma ta kama sosai. Amma tashi guda aka ruguza mini komai, Maijidda na cikinsa an kuma sake kawata mata gidan da kayan alfarma domin takanas aka tafi Jos aka siyo mata furnitures, ko yaran Baban Tsakiya su Firdausi basu samu gatan ta ba. Haka na dinga rama tamkar ku'din guzuri. Ban samu sassauci ba sai da aka doshi kwanaki ashirin da auren a dalilin na koma zuwa makarantar boko mun shiga aji shida. Da k'yar Dada ta bari muka koma. Gaba'daya na zama shiru shiru, idan ba kure ni aka yi ba, na daina fa'da, ko yara na gani sai dai na rabasu na yi musu sulhu. Amma na daina rama wa wani duka, bare ni na doku da kaina. Duk da yadda na canja ba yaron da yake kuka sabo da ni, ban tsira a wajen mutan Gidanmu ba. Gaisuwata da kyar Baffanina suke amsa wa. Na rasa laifina, zamu gansu tare da Nasiba mu gaishe su, su amsa ta ta gaisuwar cikin walwala har suna ambaton sunan ta amma ban da ni. Na fa'dawa Gwaggo ta ce "Na cigaba da gaishe su kada na gaji suna da hakkin na mutuntatasu. A sanyaye na ce "Gwaggo ni bani da hakkin su sakar mini fuska su mua'amalance ni da mutunci tunda jininsu ce ba agola ba? Nasiba fa ba yar gidan nan ba ce, amma ace ta fini a wajensu?" A duk sadda na yi mata wannan k'orafin dauke kai take yi ta ce "To ai laifukan da kika yi musu ne, da yawa, sannan ita Nasiba ko ba y'ar gidan ba ce amma tana da wata alfarma tunda a ko ina ana son y'ay'an da yar'uwa mace ta haifa, ke ma ai har da halin ki ya sanya suke yi miki hakan". Idan ta fa'di hakan sai kawai na kalle ta na yi shiru, domin na sani ta fa'da ne dan kawai na fahimci girmansu. Ba dan suna yi mini adalci ba. Har sati uku sannan na warware na rungumi zuwa makaranta duk da karatun ma sai a hankali saboda kewar Nazira na damuna. Dada kuwa fa'di take na fito da miji domin wanda za'a bawa Nasiba ya ce "Kowanne lokaci zai iya gama gidansa ba sai bad'i ba, ita kuwa ranar auren Nasiba ita ce rana ta, ko na fito da miji, ko a bani Malam Nata'ala shine damo sarkin ha'kurin da zai jure wa dukkan iya shegena. Malam Nata'ala dattijo ne da yake zaune a unguwarmu mutumin kirki ne kwarai da gaske matansa biyu da yara da dama, tsanagaya ce da shi ma'ana Malami ne mai almajirai. Ban wani dauki maganarsa da Dada ta ambata da muhimmanci ba, illah k'anzon kurege. Kwanci tashi asarar mai rai har aka cinye kwanakin wata da auren su Nazira. Har lokacin kuma ban yarda na je gidanta ba duk nacin aikar da take akan tana nema na. Ikilima ce take zuwa akai akai duk sadda ta je kuma akwai abin da zata bata ta kawo mini na ci ko na sha. Ga wasiku birjik tunda bani da waya duk da an kawo mini har uku amma Baban Marina ya ce "Baya son mu ri'ke waya. Duk yadda Yaya J yake nacin mu hadu gaba'daya na tsike zuciyata, domin yanzu haushinsa nake ji ba ka'dan ba. Kan dole ya koma makaranta tunda ya kammala sawes din da yake yi a Jos. Ina cikin wannan yanayin da na cire komai a raina nake iyakacin bakin kokarina wajen mayar da hankali a karatuna, sai dai ba wani fahimta nake sosai ba. Na dai yi sa'a zan iya karatu da rubutu. Na gama fahimtar ni din basirata a wajen kirkirar abin ado ne, misali idan na samu kan mace mai gashi zan b'ata lokaci na yarfa mata kitson da kowa sai ya ce "wow". Haka kuma duk gunjin gashi sai na kitse shi, zana adon lalle kuwa tamkar wanda aka bu'de mini ido. To yanzu da nake sake koyon kwalliyar da ake ya yi, ban jima da fara koyo ba amma har hannuna ya fara fa'da wa. Dan haka na daina takura wa kaina sai dai ina ta kokari dan na samu na ci jarabawar kammala sakandire. Ranar asabar tun safe nake ta murnar zan je gidan Nazira, tunda muka zo duniya bamu ta'ba rabuwa na lokaci mai yawa haka ba. Mutum uku kawai na yarda zan yi wa kitso, duk masu zuwa lalle kuwa ha'kuri nake basu, sai d'aya da take unguwar Nazira, layinsu d'aya domin Naziran ce ta turo mini ita. Dan haka na saka mata lallen a gurguje na barta da nufin ta same ni gidan Naziran na yi mata kitso a can. Da murna nake komai domin Allah ya sani ina son Nazira, ina samun farin-ciki idan ina tare da ita. Har Malaminmu na tarar yana dakon iso wa ta, ga abinci an shirya mini tamkar wata babbar bak'uwa ta mussaman. Spaghetti ce da miyar kifi, saboda ita ce favorite dina. Ga kuma zobo ya sha ha'di an fasa masa k'ank'ara, gefe kuma babbar kula ce shake da pure water da aka jefa masa k'ank'ara yini guda aka yi mini tanadinsa. Da farin-ciki yake taya amaryarsa marabta ta. Ta rungume ni tana k'walla da mitar ashe zan iya yin watsi da ita na tsawon wannan lokacin? Da dariya na ce "Babanmu ne ya ce "Ba zan dinga yi miki sintiri a gida ba". Malam Yunus ya ce "Ba wani sintiri idan kin so ma ki tattaro kayanki ni bazan gaza ba". Na yi dariya ina fa'din "Na gode da karamci, Allah ya sanya alheri". Ya fice ya barmu tare da cewa "Ameen Asiya". Tunda muka zauna hira muke yi, ba a gama wani zancen ba za'a sake, a kama wani. Na bata labarin yadda muka yi da Dada akan Malam Nata'ala. Ta dinga dariya tana tintsira wa tamkar ta samu tab'i. K'wallar dariya a idonta ta ce "Lallai ma tsohuwar nan, ke ce za'a bawa wannan tsohon?" Na taya ta dariya tare da cewa "To ba namiji ba ne? Kuma ai ta ga ya dace da ni ne, tunda ana kore mini duk wanda ya zo da niyyar aure na". Ta yi shiru ta ce "Kawai lokacin yin auren ne da saura, amma ba dai Alaramma ba." Muka shiga hirar duniya, muka ci abinci, muna santi a fili na ce "Na ji da'din ganinki Addah Nazi, Allah ya kara miki kwanciyar hankali, ya kawo zuri'a dayyiba". Ta ce "Ameen Yabi! Yanzu addu'ata mafi yawa taki ce Àllah ya kawo miki miji na gari". Na yi shiru. Ta ce"Baki amsa ba?". Idona ya cika dam da ruwa na ce "Baban Tsakiya ya lashi takobin duk wanda ya zo sai ya b'ata ni, ya fa'di munanan dabi'una kin ga kuwa aure ai zai yi mini wuya tunda kanin mahaifina ne yake fa'din munanan kalami a kaina." Ta yi shiru sai kuma ta ce ",Ba abin da yafi k'arfin addu'a Yabi! Fa'da kawai yake yi ba zai yi hakan ba". Na hade fuska na ce "bana son haka, wanne irin zance kike yi? Kema kin san gaskiya, zai yi abin da yafi haka in dai Alle Badamasi ne" Dariya ta subuce wa Nazira ainun, tana yi tana nuna ni da yatsa tare da ce wa "Ho Yabi". Tsawon lokaci muna hira tana ta bani labarin aure. Na dube ta na ce "Ya ya maganar da ake fa'da na ha'duwar farko, ya take kaya wa?" Ta galla mini harara ta nuna kanta ta ce "Ni kika yi wa wannan tambayar?" Na k'yal-k'yale da dariya ina fa'din "Adda Nazi manya. Yo wa nake da ita da zan tambaya, kawai fa'da mini Malama". Ta leka ta ga ko Iki na jinmu, sai ta ga game take yi a wayarta a falo, mu kuma muna uwar daki. Ta ce "Kawo kunnenki ki ji". Da rawar jiki na mika mata, ai kuwa ta gantsara mini cizo. Na saki kara a ki'dime. Ita kuma ta ci magani tana fa'din "Maganin mai son jin almarin da bai shafe shi ba, maganin mai son jin abin da Allah ya sakaye shi, maganin mai son ya ji sirrin da Annabi ya tsine wa mai bayyana shi". Ai kuwa na fara hawaye ina shesshe ka. Nan da nan ta hau shafa kafa'data tana fa'din "Yi ha'kuri mana Yabina a hankali fa na yi miki, menene zaki zubar da hawayenki?" Na zum'bura baki ina fa'din "Mun bata gaskiya! Kuma dan kin zama babba ce ai dai kinsan fa'da na." Ta yi murmushi ta ce "Ni ban girma ba." Muka yi dariya gaba'daya. Sai lokacin wacce na bari a gida da k'unshi, ta biyo ni, akan na yi mata kitso. Muka fara, yayin da Ikilima ta hau wanke wanke ita kuma Nazira ta hau gyara wajen da muka yi dabdala. Da zan taho ta hado ni da kayan kwalliya masu yawa har Ina fa'din ta kwashe mini kayan ai. Da sabuwar doguwar riga da ko sata bata yi ba, da sabon takalmi. Na kalleta na ce "Ki rage kayan sun yi yawa Adda Nazi". Ta ce "Idan ina da fiye da hakan baki zan yi Yabi". Na jijjiga kai na kasa cewa komai na yi gaba na bar Iki tana dauko mini. Muna tafe ni da Iklima muna hirarmu na ce "Idan kin gaji dai, ki bani na karbi kayan." Ta ce "zan iya Adda Yabi". Muna tafe wani Alhaji sai binmu yake a hankali a cikin dankareriyar motarsa. Duk hon dinsa ban yarda mun tsaya ba. Har muka je gida, bai fasa ba. Muka shige gida, ya yi parking. Dai-dai lokacin Bulkachuwa ya danno kai. Na shige na bar Iki tana lekensa. Ba wani jima wa ta shigo da sauri tana fa'din "Adda Yabi wai ke ya biyo. Yaya Bulkachuwa ya fa'da masa babu maganar wani a kanki, ya bashi ku'di, ya kuma aiko shi wajen ki". Tana rufe baki sai ko ya shigo, daga tsaye ya gaida Gwaggo da Inna yana fa'din "Asiya Toro zo mana". Na yi kamar bazan kula shi ba, sai da Gwaggo ta ce "Yabi wai Yayanki ba magana yake yi miki ba ne? Ni fa bana son wannan wula'kancin na ki". Na mike ina fa'din "Shi ai Tijjani kayan haushinsa yawa ne da shi." Ya yi dariya ya ce "Ashe duk yadda na yi ba'kin jini a wajen Jabir akan ki ban wanke laifina na baya ba?" Muka dan fita wajen k'ofa. Ya sassauta ya ce "Kin ga Àllah ya dubi takaicin da aka cusa miki Asiya Toro! Kin zargo babban kifi. Wannan mutumin son ki yake yi da aure, kwamshinan harkokin addini ne na jahar nan, sannan babban dan kasuwa ne. Mutumin kirki ne, kin ga abin da ya ba ni". Ya nuna mini rafar dubu guda. Na zaro ido na ce "Billahillazi dan yankan kai ne Tijjani! Ban da hakan daga haduwa ya baka dubu dari?" Ya yi dariya ya ce "Kin san istigifari nawa na yi yau kuwa? Na yi yafi dubu goma, Ubangiji kuwa ya yi al'kawarin warware mana komai matu'kar muka dimanci istigifari har da bude kofofin arziki. Bana haufi Ubangiji ne ya turo mini arziki ta hannunsa. Ki yiwa kanki fa'da Asiya kin ga dai ba shiri muke yi da ke ba, amma na fi jin ciwon abin da aka yi miki sama da wanda aka yi mini. Ki saurare shi, ki yi addu'ar zabin Allah. Idan kin samu nutsuwa ki ba shi dama azo a yi auren ki ko kya samu sau'kin masifar gidan nan. Nima kin ga wannan ku'din ajiye wa zan yi wani satin zan bayar akai mini ku'din aure, ko wannan yar'uwar ta ki zata shafa mini lafiya". Na sauya fuska na ce "Nasiba fa bata da laifi Tijjani". Ya kwabe fuska ya ce "To ai ni kuma ko ita ce ka'dai ta rage a duniyar nan na haramta wa kaina ita. Bulkachuwa bai yi wannan arahar ba, ba za'a ci mutuncinsa, a tozarta shi kuma ya lik'e ba". Ya mik'o mini dalleliyar waya a kwalinta ya ce "Da caji da kuma layi a ciki ki kunna zai kira ki." Ya hade hannu alamun rarrashi ya ce pls ki saurare shi ko za'a dace". Na ce "Baba fa ya hana ni rike waya, yanzu haka akwai sabbin wayoyina a ajiye, da wacce Yaya J ya siyo mini, da ta wajen Abdulrashid har biyu. Wai sai na kammala makaranta, ko idan na yi aure na ri'ke". Ya ce "Wannan dai kin ga Babban mutum ne Yabi, ga shi kowa ya yi masa shaidar nagarta. Ki boye ta ba sai an ga ni ba, bana son ya kubuce miki. Bauchi zai kai ki, ba zai ajiye ki anan ba, ko ma Abuja. Babbar waya ce ki yiwa Allah kada ki bari ta salwanta". Ya juya na bi shi da ido ina raya ina ma yadda ake zuba masa kyakkawar sura kuma cikakkiya haka yake da kyakkawar dabi'a da nagarta. Inda a ce shine yake da dabiun Yaya J da ya zama komai an hada masa. Mafi yawan lokacin ina yawan ayyana da Yaya J ne yake ingarma kaman Bulkachuwa da an yi namiji tsayayye mai kyakkawar manufa. Amma halayyar Bulkachuwa shine nak'asunsa, mussaman na yadda yake iya keta alfarmar shari'a yana aikata kaba'ira, ga rashin ta ido, ga shigar iyashege, yau har barima na ga ni makale a kunnensa, gashin kai ya sha tiri (dying) gashinsa mai kyau ne irin na fulanin Bulkachuwa amma ya mayar da shi cibiri cibiri tsabar fitina da son yaudare y'anmatan da ba susan ciwon kansu ba, ga kafiya akan ra'ayinsa, ko k'uda ya shafa masa lafiya wajen naci. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* Amma akwai tausayi mussaman idan ya ga kina kuka, to kin karya masa lagonsa, sannan yanzu ya fara sanin kishin kansa har yana taya wani ciwon abin da aka yi masa. Ashe da ya fita wajen Baban Marina ya raka wannan mutumin da ko sunansa ban sani ba, ya nemi a bashi izinin fara magana da ni. Baba ya ce "Ya bashi damar neman yardata, amma idan ban amince ba, ba zai mini dole ba. Shi kenan sai Alhaji Mustapha Zaki yake zuwa, ni da kaina kunyar yadda nake yar mitsil a gabansa nake yi. Dogo ne sosai yana kuma da jiki, ga tumbi sai dai tumbin bai yi muni da yawa ba, ustazu ne sosai domin ya tsayar da gemun sunnah. Ku'di yake sakar mini da suturu na alfarma, ga kuma mutunta ahalin gidanmu. Dada kanta sonsa take yi a dalilin idan zai zo sai ya kawo mata rafar sabbin ku'di, y'an 100, da na 50, da na 20. Yana cewa gashi ta ajiye canji a hannunta, duk zuwa kuwa. Ga ledar tufa da kilishi. Nawa kuwa y'an 500 da 200 ne. Bulkachuwa ya zama magayak'insa. Kullum sai ya masa kamfen, fa'di yake "Gidan ki daban zai baki Asiya, idan kika yi sa'a ma Umrar bana da ke za'a yi, aikin hajji kuwa tabbas ne. Ba ruwanki da tsufansa, lallaba ki zai yi. Ni kaina alherin da nake samu a jikinsa ba ka'dan ba ne. Kin ga "Na kalli hannunsa da yake karkada wa. Mukulli na ga ni ya ce "Mashin ya ba ni sabo dal, gwamnatin jahar Bauchi take raba wa matasa, shine ya saka sunana. Dan Allah Asiya ki so mutumin nan, oh wani hanin ga Allah baiwa. Yarinya kin tako arziki, na tabbatar Gwaggo data haife ki da akwai wutar Nepa a time din Wallahi. Na miki murna ma da wannan dan tsurut din bai same ki ba. Ai ke babbar mace ce, sai manyan maza, amma yana tafiya tamkar iska ta hure, kirjinsa duk bai fi allona na makarantar tsangaya ba". Na b'ata rai na ce "Yaya J din kake yiwa haka akan bare? Sannan nima ai y'ar tsurut ce ta ina na zama babbar mace?" Ya murmusa ya ce "Ba sai na bu'de maganar ba, ke ma kinsan yadda ake miki layi ai akwai sirri na mussaman a tare da ke. Na'kasunki biyu ne tsayayyiyar zuciya, kuma taurarriya, da fitsara, dole handle dinki sai tsayyayen namiji k'arfaffa ba lusari irinsa ba". Na sake b'ata rai na ce "To yadda kake ganin zuciyata, tasa har tafi tawa tsayuwa da jarumta". "Ke tafi can, me kika sani? Wai har yau son Jabir kike yi? Tabdi jam lallai so ba k'arya ba ne. Jiya fa na gan shi goye da Maijidda a mashin ina ga d'an yawon shan iska suka fito". Nan da nan idona ya k'ada sosai hawaye ya cika su, ya mike yana fa'din "So sorry Asiya Toro. Ki gode Allah da ya kawo miki Honarable Zaki. Domin da ki yi kuka a inda kike so, gara ki yi a inda ake son ki, da ki yi kuka a gidan cin abinci gara ki yi kuka a gidan daula sosai, domin mu maza da kika ganmu so baya hanamu murza kanku". Na girgiza kai na ce "Zan amince ne idan kai ma ka yarda zaka shirya da Nasiba, ni shaida ce akan ba wanda take kula wa saboda kai". Ya bata fuska ya ce "Kin san Allah? Zan ci mutuncinki Asiya Toro! Kada ki saurare shi mana, shawara na baki saboda ina nufin ki da alheri, idan baki so ba, ki sallame shi, ki jira wanda zaki dinga kuka a gaban murhun gawayi, da kishiya. Ga kuma ba'kin cikin da zaki kunsa a wajen ahalinsa, shasha da bata san me ya dace ba". *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633*. ✍️ *BAKAR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *(MRS M.I.NASHE)* *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ──────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *ALBISHIRINKU* *MASOYAN LITTAFAN MARUBUCIYA HAFSAT C SODANGI*! *DUBA DA YADDA KUKE KEWAR RUBUTUNTA YA SANYA TA YI SHIRIN SAKE DAWOWA DAN TA SAKE MUKU WANI RUBUTUN SABO DAL* *AMMA KAFIN HAKAN TA DAWO MUKU DA TSOFAFFIN LITTAFAN TA ZUWA KAN WAYA, DAN KU SAKE BITA TARE DA NAZARIN KYAWAWAN SAKON DA TAKE NUFIN ISARWA GAREMU*. *A YANZU HAKA LITTAFAI HUDU NE RIGIS* *WAYYO DUNIYA 1-3* *KYAUTATA 1-3* *DAGA K'IN GASKIYA 1-3* *MATA MASU DUNIYA 1-3* *KO WANNE 1K NE AMMA AKWAI DISCOUNT IDAN ZA'A SIYA SAMA DA GUDA DAYA* *MISALI GUDA BIYU-1500* *GUDA UKU 2500* *GUDA HUDU 3500* *ZA'A TURA KUDIN TA ASUSUN MARUBUCIYAR KAMAR HAKA* *0082739293, ACCESS BANK HAFSAT YUNUS ABDULLAHI* *SAI A TURO MINI SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *SAI NA BADA LITTAFIN DA AKE SO* *MADALLAH DA KARFAFA GUIWARKU* *MADALLAH DA SOYAYYARKU GA RUBUTUNMU* *AKWAI LITTAFANTA SAMA DA GUDA GOMA DA A YANZU SUKE SOFT COPIES, KAWAI KI TAMBAYI DUK WANDA KIKE NEMA A WAJENA CIKIN LITTAFANTA NA BAYA*. *Saura kiris shaufakan kyauta su k'are* *Turka turkar da ke cikin labarin nan kabiran ne. Har yanzu shimfi'da kawai muke yi bamu kutsa labarin ba tukun*. *HANZARTA ki shiga tafiyar dan karfafa guiwarki ga marubuciya da karatun cikin SALAMA.* *Kudin karatun ki 500/1k* *Via 2384876855* *Surayya Ibrahim Dahiru* *Zenith Bank*. *Ko* *7061488065* *Surayya Dahiru Ibrahim* *Opay Bank*. 17&18. Na bishi da ido yana tafiya cikin gajeren wando tiri k'wata, da riga t shirt mai kama da singeleti. Ko kunya baya ji. Na girgiza kai ban ce komai ba dan nasan da dukkan zuciyarsa ya yi magana. Kwanaki suka yi ta shud'ewa har aka samu wata uku da auren ahalin gidanmu, dai-dai da wata biyu da haduwata da kwamishina. Zuwa lokacin alherin da ya same mu ba ka'dan ba ne. Domin ta hannun Yaya Salisu ya saka an gyara mana band'akin k'ofarmu an zamanantar da shi, an yiwa kofar kwaskwarima ta farfad'o sosai. Sannan ya karbi takardun Yaya Salisu da Yaya Rabi'u da alk'warin zai nema musu aikin yi. Hatta Yaya Musa sai da ya saka ya samu tallafin injin nik'a da na markade, kuma Alhamdulillah yana zama wajen sana'ar. Tun Babanmu yana fa'din hidimar ta yi yawa mussamna yadda ake sauke mana kayan abinci, wannan kam duka kofofin gidan ake sauke wa. Har ya koma yin shiru domin dai kwamshina bai fasa ba, sai dai ma ya ce "Tallafi ko samo aikin yi ga matasa ai hakkinsu ne domin y'an jahar Bauchi ne, hanya kawai na yi musu, ko ba ta sanadin Yabi ba, matu'kar ina da damar yin hakan ai nima hakki ne a kaina na yi hakan." Nan da nan na canja tunda cimar Gidanmu ta canja, ga kayan kwalliya da dangin shower gel masu kyau. Domin dukkan setin kayan Oriflame na siye su ta online. A hannun Aisha lame 07036662633 tunda na bude account saboda manyan mata masu yin transfer din kudin lalle. Sutura kuwa duk zuwa sai ya kawo mini su, manyan zannu wa da leshi. Na sake zama so cute, ga fata tana sheki ga kuma sutura ta d'aukar hankali. Hijabai har sun mini yawa duk da ina bawa Nazira da Yaya Ummi, bai ta'ba kawo mini mayafi ba, sai dai abayoyi kaloli daban daban, hakan ya tabbatar mini mai ra'ayin kiyaye ka'idojin shari'a ne. Su Gwaggo kuwa komai zai kawo uku ne tare yake musu babu banbanci, hakan ya sake daga darajarta domin kuwa duk y'ay'an d'akin Mama bata bari ko sabulu suna kawo uku. Sai dai ita ka'dai, idan yan arzikin suna kusa ta samm musu, idan basa kusa sai ta bawa Inna a boye, Gwaggo kuwa ko labari. Bakin Mama ya mutu murus sai dai dama tun abin da na yi a auren Nazira ta saukaka al'amura masu yawa. Ba sai kuma aka fara cece-kucen auren kwadayi za'a yi mini ba, ban da haka ta ina za'a dauki yar mitsitsiya kamata a bawa wannan mutum da idan na tsaya a gabansa sai a zaci yarsa ce bama ta fari ba. Su Baban Tsakiya suka fara raddi, domin ba karamin gyagije wa ahalin Baban Marina muka fara ba. Dada ta fara taka tsantsan da lamarina, tunda yanzu tana samun kayan ciye ciye da ku'di saboda ni, ga turare da atamfofi da ya kawo mata har sau uku. Ni da kaina na gamsu ku'di suna kan gaba wajen magance tozarcin d'an-adam, haka nan suna saka wa a ga girman ka aji tsoron zuciyar ka ko da baka da siffa mai kyau. A raina sai k'yamar wannan *BAK'AR TA'ADAR* nake yi. Domin na hakikance rashin wadata ya sanya aka mayar da ubanmu ya koma k'arami a cikin gidanmu, wai daga d'an zuwan Kwamshina har an fara raga masa, inda ace shine mai ku'din ko wani cikin y'ay'ansa fa? Sai dai Baban Tsakiya da na Kasuwa basu sanya wa lamarin albarka ba, asalima fadi suke a ina na hadu da shi? Ba d'an gari ba? A sharholiyarmu muka ha'du kawai. A raina bana sonsa, bana burin aurensa, amma ya zan yi? Tunda shi ka'dai ne ya tsaya ya na sona a yanzu, sannan gaskiya na gaji da zaman Gidanmu ba dan komai ba, sai dan yadda nake shan matsin lambar na fito da miji da kuma k'iyayya da aibantawa. Sannan tunda ake yin hassada a lamarin, sai na kudire zan sadaukar da komai na aure shi, ko dan ya zame mana garkuwa a k'ofarmu tunda mutumin kirki ne wanda ya siffantu da dabi'aun addini. Rannan kwatsam na fito daga inda nake koyon kwalliya sai ganin Yaya J na yi a zaune kan wani dutse da alamu suka nuna dakona yake yi. Na zo zan wuce ta gabansa tunda ba zai yiwu na koma na fasa tafiyar ba. Sanye nake da k'aton hijabina har kasa irin wadda ake ya yi mai hula ta baya. Ban ce masa k'ala kanzil ba, asalima ban nuna na ganshi ko na san shi ba. Da azama ya biyo ni a fusace ya ce "Yabi ashe zaki iya ganina ki mini irin wannan wula'kancin?" Ban ce komai ba, ban kuma fasa tafiya ta ba. Yana bina yana fa'din "Tun jiya ban runtsa ba, ba abin da nake so irin na ganki na tambaye ki abin da ya rikita mini al'amura". Na tsaya cak na ce "Tambaye ni Jabir, ina jin ka". Ya zuba mini ido, nima na zuba masa tsawon lokaci, ga mamakina sai kawai abin da na binne a kansa ya nemi taso mini da k'arfin gaske. Na yi maza na dauke kaina, tare da sake d'aure fuska. A sanyaye ya ce "Da gaske ne Mustapha Zaki yana son ki?" Ba ja in ja na ce "Da gaske ne". Ya kadu amma sai ya ce "Ke nan kin amince masa?" Na kalle shi cikin ido, na ce "ko ban amince dan ra'din kaina ba, idan kaddara ta amince masa ai shike nan kamar yadda kaddara ta amince maka zama da Maijidda". Na yi gaba na fara tafiya, ya biyo ni yana fa'din"me kike nufi Yabi?" Ban kula shi ba, domin gaba'daya wani irin abu ya cushe mini zuciya da mak'oshi. Sai fa'di yake "Kina nufin zaki aure shi ke nan?" A tunzure na juyo na ce "A a ba aurensa zan yi ba, debe mini kewa zai yi, kafin a sahale maka ka nemi aure na". Ya girgiza kai ya ce "Wacce irin magana ce haka Yabi?" Kai tsaye na ce "Mai da'di kuma ta gaskiya". Ya rasa yadda zai yi, hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi. Ya saki gauron numfashi ya ce "To ni kuma mene ne makomata ke nan? Na kadu na ce "Ban gane ba? Nusar da ni." Kai tsaye ya ce "Ina nufin ya maganar tawa soyayyar, ya batun aurenmu?" Na kafe shi da ido cikin tsananin kad'uwa. Kawai tambayar kaina nake yi "Ko dai ya samu mental disorder ne? Amma sai na shanye mamakina na ce "Jabir ke nan". Da sauri ya ce "ki ha'da ki ce Jabir Badamasi Toro, ba komai ba ne watarana In sha Allah zaki dawo da yayan domin ko kin yanke alakar da ta ha'damu ai baki isa ki wanke jinin da ya cakudamu ba" Na daure fuska ainun ban ce k'ala ba. Ya ce "Fa'da mini inda kika ajiye ni Yabi! Ina son ki, ina son na rayu da ke, ki yiwa Allah kada ki zalunci zuciyoyinmu, ki mini adalci ko da kina mini kallon azzalumi." Na murmusa na ce " Wanne irin adalci kake nufin na yi maka?" Ba nauyi ya ce "ki aure ni Yabi, ki bani damar da zan rayu da ke". Ido cikin ido na ce "To kuma ya zaka yi da Maijidda da aka baka dan ana ganin ta fini nagarta, kuma y'ar babbar k'ofa ce?" Ya ha'de rai ya ce "Ni da ke ne anan ba ruwanki da kowa, ni nake tsaye a gabanbki, kin sani kuma ina son ki, ina kaunar ki, idan kin bani dama ina da sauran dama uku a gaba da shari'a ta bani". Na jinjina k'arfin halinsa na murmusa na ce "zaka ha'da ni da Maijidda kishi? D'iyar attajiri irin Baban Kasuwa da ta fak'iri irin Baban Marina?" Ya naushi hanunsa ya ce "Kina da bak'ar magana Yabi! Ki yi kokarin kiyaye harshen ki, gubar harshe ta fi ta maciji dafi". Na yi gajeriyar dariya na ce ", Gaskiya na fa'da amma tunda ba'a sonta, to na janye" Nan da nan ya sace ya ce "To ki yafe mini, ina son ki, idan har kika ba ni dama zan tsaya miki, ba zaki yi kuka da ni ba. Zan fafata da duk wanda ya nemi shatale farin-cikinki da iznin Lillahi." Idona ya k'ada tsakanina da Allah ina matu'kar son Yaya J ba kowa zai fahimci hakan ba sai wanda suka yi soyayyar k'uruciya ta rikide ta zama ta gaske, irin wannan soyayyar tana matu'kar tasiri a cikin zuciyar banu adam. Amma na sani idan zan yaudari kowa, bazan yaudari kaina ba. Ba za'a ta'ba bari ya aure ni ba. Bayan k'iyayyar ubana to ni kaina wata irin kiyayya iyayensa suke mini wanda basu ki su gan ni da abin kunya ba. Dan haka hawaye ya b'alle mini, da rawar murya na ce "Yaya J ba kowanne Dan Adam ba ne yake nasarar rayuwa da wanda yake so. Mata da yawa ba wanda suke so k'addara ta aura musu ba, hakan nan mazan. Yarda da k'addara kuma sharadi ne na cikar imani. Ka sani, na sani ba za'a ta'ba barinka ka aure ni ba. Na tabbatar za'a bari ka auro ukun da kake kirari a ko'ina amma kuma ba za'a bari ka aure ni ka'dai ba, na gamsu kana sona, nima kuma har yau din nan ban so wani kamar ka ba, ba kuma zan so din ba. Mu yi addu'a Ubangiji ya sanyamu cikin masu soyayya dominsa wanda sakamakon hakan Aljannah ce". Idonsa ya k'ada ya ce "kin yi magana ta hankali Yabin J. Rabon da na samu aminci irin na yau, tun kafin ki juya mini baya. Abin da nake so da ke na yarda na gasgata ki, amma ki bani dama na sake jarraba wa ko za'a dace a wannan karon, zan yi iya kokarina dan na same ki, ai na yi biyayyar a farko". Na murmusa na ce "Shari'a bata hana hakan ba, amma zan ji nauyi mai yawa a ce ina kishi da Maijidda! Sai kuka ya subuce mini na gaske". A rikice ya ce "Wallahi zan iya rabuwa da ita matu'kar ita ce cikas din cikar burin ranmu. Sai dai ace na aikata *BAK'AR TA'ADAH* na saki aure akan wata macen da bata zo hannuna ba". Na girgiza kai na ce "Ba za'a kai ga hakan ba". A hanzarce ya ce "To ki huce da ni, ki bani damar auren ki". Hawaye na zuba na ce "Na baka Yaya J. Nan da sati biyu ka fito, idan har ya wuce baka bayyana a gaban Baban Tsakiya da Baban Kasuwa da nufin ka je neman aurena gabansu ba, ka tabbatar magana ta k'are a tsakaninmu ta soyayya har abada, na kuma baka dukkan damar da zan iya, sai dai ka sani ba zaka ha'da ni zama da ita a gida guda ba". Ga mamakina sai gani na yi ya zube a kasa yana sujjada. Ya dago ya ce "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah. Zaki ji sakona kuwa daga yanzu zuwa ko wanne lokaci. Sannan na miki al'kawarin a Bauchi zan nema miki inda zaki zauna kafin na samu halin gina miki naki gidan". Ya tako mini har titi ya tarar mini Napep ya biya, na tafi yana d'ago mini hannu cikin matsanancin farin-ciki. Ni kaina wani irin shauki ke fizgata mai danne dukkan bacin rai. Na manta k'iyayyar da Baban Tsakiya yake mini azima ce. Sannan Baban kasuwa ba yadda za a yi ya goyi bayan ayi wa diyarsa kishiya da ni. Amma dukkanmu hankalinmu ya gushe duk da ni din gatse na yi masa, amma TASIRIN soyayyar da nake yi masa ta taso mini haik'an ta saukar mini da farin-ciki mai tsananin gaske. Har nake fatan al'amarinmu ya kasance. Na isa gida na ci abinci na yi sallah na hau kitso tunda mutum uku na tarar suna jirana. Da yake a cikin nisha'di nake kafin ka ce kwabo duk na kitse musu. Hatta Gwaggo sai da ta fahimci irin walwalar da nake ciki, rabon da ta ganni hakan tun komai bai tabarbare mini ba. Ina idar da sallar isha na nufi wajen Dada. Na tarar ta idar da sallar ita ma tana jan dogon carbinta. Ni da Nasiba muke hirarmu, akan makaranta. Dada ta shafa addu'a. Muka gaishe ta ta amsa da walwala a dalilin yanzu shiri take yi da ni tunda tana samun alheri a dalilina. A sanyaye Nasiba ta ce "Kin daina d'ora mana karatu dai Dada". Ta murmusa ta ce "To kuwa yau zamu yi. Zan d'ora muku addu'ar da idan kuka lazumce ta babu ku babu yunwa ila yaumil k'iyamati, ina nufin duk tsanani, Ubangiji zai yassare muku abin da zaku ci". Nan da nan na nutsu domin idan na ji ingancinta na d'orawa Yaya Ummi domin ita kam tana wahala kafin ta k'oshi. Ta gyara zama ta ce " *ALLAHUMMA RABBANA ANZIR ALAINA MA'IDATUN MINAS SAMA'I TAKULU LAANA IDDAL LI AUWALI WAL AKIRI...*" Da sauri na ce "Ai mun haddace tuni, a cikin suratul ma'ida take Ashe haka take da falala Dada". Ta washe baki ta ce "Ai wani bajimin Malami ya tabbatar mana matu'kar zaka biya wannan addu'a to haularka ba dai su rasa abinci ba bare kuma kai da kake bitar ta". Na 'kyal-k'yale da dariya domin ni na dakatar da ita ne saboda kurakurai da na ji a ciki. Tunda ba yarda zata yi na gyara mata ba. Ta ce to "Kun ga ni, ni da ku ne anan zan d'ora muku wata muhimmiyar addu'a, sadakar da zaku bayar ku yiwa Annabi salati, ku nema wa Shehu karin karama". Cikin zakuwa muka ce "To". Ta yi kasa da murya ta ce " ku dimanci *Ya ladifu* Idan kun yi dari ba daya a cikon na dari ku rufe da fa'din *"Allahu ladifin bil ibadihi, yar-Razaku man ya shaa'u Wallahu Qawiyin Azim*". Karon farko da Dada ta biya karatun da babu kuskure, da haka na dage nake ta biya wa a zuwan koyo nake yi, ita kuma sai fa'di take, tana sake gyara mini". Muka kammala tana jaddada mu ri'ke adduoin nan falalarsu ta kai matu'kar shahara.Ya ladifu kundin sirri ne, gashi babu wahalar fa'da. Na maze domin tsokanar ta zan yi, dan na ga reactions d'inta. Na ce "Dada ki daina jan carbi fa, babu kyau Annabi ya ce mu yi da yatsun hannunmu domin su mana shaida ranar gobe". Ta b'ata fuska kamar ba zata yi magana ba, sai kuma ta kufula ta ce "Asiya tun kafin a haifi Ubanki nake jan jarbi, duk wani sabon addini da kuke son kawo wa na raini Wallahi ba zai yi tasiri a wajenmu ba". Nasiba ta fashe da dariya yayin da nake jira ta tara mini gayya irin wanda ta mini watannin baya, amma na ji muk'us. Na jijjiga kai a raina sai fa'di nake "Allah ka sake bawa Yabi tsaron da ba za'a dinga tozarta ta ba." Ta ja robar maganinta da Honarabil ya kawo mata na warwarewar gajiyar tsufa da kara kuzari. Sai kuma na daidaita siga da bugawar zuciya duka daga kamfanin G.H.T. Na murmusa ina tuna a wajen FASEELAT ba zai kai kudin da na ga ni a manne a jikinsu ba. Na Santa a littafin Guduyo. Nemi dukkan nau'in kayan ght daga gare ta cikin RANGWAME. *07039269802* Muna cikin haka sai ga Yaya J. Ya sha kwalliya da wani farin yadi, d'inkin ya zauna masa sosai. Ga kamshin turaren Dagmar ya baibayemu. Cikin farin-ciki Dada take fadin maraba da Jabiru angon Maijidda". Zuciyata ta buga da k'arfi, shi kuma ya dan diriri ce. Ya waske da ce wa "Angon Dada dai, ai ke ce ta karfen". Ta yi dariya ta ce "Yaudara ke nan." Ya gaishe ta ta amsa da walwala tana tambayar amaryarsa. Ya bata amsa da ce wa"Tana lafiya a gajar ce. Ya shige cikin dakinta yana cewa "Zo mu yi sirri Dada". Ta rarrafa ta bishi domin kuwa mutuminta ne baya rabuwa da kawo mata tsire da turare. Ita kuwa duk wanda zai mata ungo tana mutunta shi. Muka ci gaba da hirarmu wacce galibi Nasiba tana fa'da mini ciwon da take ji akan sharewar da Bulkachuwa ya yi mata. Fa'di take "Dan Allah laifina ne? Inda ya fahimce ni, da ya k'arfafa soyayyarmu ai komai za'a mini bazan kula kowa ba, amma daga maganar fatar baki ya d'ife, ya ce kada na kuma shiga sha'aninsa. Da yana sona ba zai yi irin wannan fishin ba." Ta fa'da k'walla na zubo mata. Jikina ya yi sanyi ainun domin kuwa Bulkachuwa ya riga ya yi rantsuwar ya yanke hulda da ita. Kamar daga sama na ji muryar Dada cikin karadi tana cewa "Ina! Jabiru ka zo da *BAK'AR TA'ADAH* Mai wahalar tabbatuwa, ta ya ya zaka ha'da mini jikoki kishi? Dama kuma ba jituwa suke yi ba. Ha'kuri zaka yi da Yabi domin tuni ta samu miji ita ma, dattijon arziki irin albarka." A sanyaye na ji yo shi yana ce wa "Idan ban samu goyon bayan ki ba akwai matsala Dada. Kin sani Yabi nake so tun fil'azal. Amma saboda na yi biyayya ya sanya na karbi auren Maijidda. Yanzu da nake son na cike wanccan burin nawa ba sai a taimake ni ba?". Ya dinga magiya, tamkar zai fashe da kuka. Cikin kad'uwa ta ce "Jabiru ka zo da babban al'amarin da yafi Dutsen dala nauyi. Bana jin iyayenku ma zasu amince maka, ka bar maganar nan tun baka tono wani bacin ran ba". Ba shakka ko nauyi ya ce "Ba zan barta ba Dada! Domin da zan iya barinta da ko ke baza ki ji ba. Idan ba zaki taimake ni ba, to ki mini adalci kada ki b'ata al'amarin a gaban iyayenmu". Ta ce "ita Yabi ta gamsu zata aure ka ka had'asu da Maijidda?" Da sauri ya ce "Ina da tabbacin soyayyarmu ba zata yi zangwayenwar da babu alfarma ko fahimta ba, ban tuntu'beta ba, amma ina da yakinin ba zata juya mini baya ba". Tsawon lokaci sun yi jigum jigum, muma da muka bar maganarmu muka kashe kunne muna jiyosu, jikinmu ya yi la'asar". Nasiba ta ce "Tabbas soyayyar da take ta gaskiya kuma k'arfaffa ce ake yin afuwa da sassauci a cikinta." Na kasa cewa komai domin hausa ta yi cikin hikima. Da Bulkachuwa take. Bansan ya aka yi ba, kawai sai ganinsa na yi ya fito ya fice a hanzarce. Sai ga Dada ma ta fito cikin rashin sukuni. Ta zauna jiki a sanyaye. Ta kasa jure wa ta kalle ni ta ce "Yabi Jabiru zai ballo wani irin tashin hankali, kada ki sake ki saurare shi. Ki rike Alhaji nan yafi miki, ina tsoron abin da zai biyo baya." Na yi k'uri ina kallonta a zahiri gaskiya ta fa'da tashin hankali zai iya biyo baya. Amma kuma a zuciyata sai nake ganin son zuciya ne kawai yasa ba zata goya masa baya ba. Dan kawai Maijidda d'iyar shalelenta ne, kuma mawadacin gidanmu. Dan sai yanzu na fahimci ba fa wai ku'di ne da Baban Kasuwa ba, kawai a gidanmu ne yafi kowa wadata, saboda talakawa ne mu na sosai. Me yasa a farko bata hana a bashi ita ba, tunda tasan ni yake so? Me yasa a wanccan lokacin ba ta yi zaton hakan zai zama tashin hankali a dalilin gaba da kullaci da zai shiga zukatan y'an gidan gaba'daya ba?. Duk yadda nake da ba'kin jinin a cikin ya'nuwana sai da suka yi kishin abin da aka yi mini, suka yarda ubanmu aka tozarta. Tashin hankali tuni an shige shi ai, kawai sa'ar da aka yi Baban Marina mai sassauci ne, shi yake ta tsawatarwa dan kada mu kullaci y'anuwansa ko muce zamu rainasu. Amma iyakacin wula'kanci da kaskanci an yi mana. Ba kuma wanda ya k'alubalanci hakan sai Baba ta Bulkachuwa ita ma kuma bata da power kamar Babanmu. Duk da a cikin rufin asiri take, dai-dai gwargwado tana dan tagazawa wajen yiwa Dada hidima. Haka nan ita ka'daice kafatalin yan'uwan Babanmu zata aiko da wani abu da sallah ta ce a bawa y'ay'ansa. Wani lokacin sark'a da yan kunne, ko hijabai, ko y'an takalma masu sau'ki haka. Dan ko sallar da ta wuce da hijabanta muka je sallar idi ni da Nazira. Amma Baba Maryo uwarsu Nasiba da bata iya tsinana komai har a Dadan ma ita take zuba mulki, haka nan komai aka yiwa Dada na dangin sutura ko wani abu mai k'yau karshe sai ya zama nata ko na y'ay'anta, ita kuma saboda auta ce da ta shiga rai. *BAK'AK'EN TA'ADODI* masu yawa na faruwa a gidanmu da dole duk kawaicinka sai zuciyarka ta motsa sa'i da lokaci. ✍️ *Ina tallata muku kayan gyara na mussaman na mutanan Sudan da chadi*. *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin Tsumi da Zaki dafa da kanki, ki ajiye ki sha sosai ya ratsa miki jiki* *Y'aya'n gadali na mussaman* *Hadadden daka emergency* *Tsumin kwakwa da zuma* *Turaren matsi na tsugunno* *Maganin sanyi sadidan na mara har ma da gabobi* *Gumba* *Goran tula syrup and fruits* *Tsumin Goran tula na asali* *Duk zaku same su da RANGWAME kuma na asali me ba karabiti ba.* *Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*. *Tuntube ni a wannan lambar* *08032773332* ✍️ *BAKAR TA'ADA* *NA* *SURAYYA DAHIRU GWARAM* *(MRS M.I.NASHE)* *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ──────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* *Last free page* *500regular page* *VIP 1k twice pages* *2384876855* *Surayya Ibrahim Dahiru* *Zenith Bank*. *Ko* *7061488065* *Surayya Dahiru Ibrahim.* *Opay Bank.* *08032773332*. 19&20. Jin na yi shiru tsawon lokaci a dalilin tunanin da nake ta yi. Ya sanya Dada ta ce "Yabi da alama zaki bawa Jabiru ha'din kai". Na yi murmushi na ce "A a sai dai na yi imani Ubangiji ne yake shirya komai, dan haka shi na barwa al'amurana ya yi mini zab'i. Dama kuma ban k'ullace shi ba domin ba shine ya mini laifi ba, sannan Dada idan har auren Maijidda da aka sanya ya yi ya bar ni, bai zama abin kaico da rikici ba, ashe kuwa nawa auren da yake hak'ilon yi a yanzu adalci ne da tsantsar gaskiya". Jikin Dada ya yi tub'us tabbacin tasan gaskiya na fad'a. Da k'yar ta ce "Ana barin halak dan kunya Yabi". Are yi murmushin da yake nuna ba wananan maganar. Ta sake ce wa "Kuma yanzu wannan dattijon arzikin sai ki bar shi, duk dawainyar da yake faman yi dake da dukkan dangin ki?" Na sake murmushi na ce "To ai aure gaibu ne, sannan Allah ne ya gadar wa maza su yi ta hidima da macen da suke so dan su ja ra'ayinta. Abin farin cikin ba rok'arsa nake yi ba, haka nan wani nawa bai ta'ba rok'arsa ba." Ta yi shiru ta rasa me zata ce kuma. Sai ta hau addu'a da kamun k'afa a wajen Shehu kada zuri'arta ta rikice a dalilin wannan al'amarin. Har k'asan raina da al'amarin zai yiwu ba wani nauyin da zan ji, domin nawa ne aka k'wace mini saboda kawai zuciyar ahalin gidanmu a cike take da gilli da ba'kin ciki mai yawa. Kwanaki biyu kullum sai na ga Yaya J ya zo gidanmu, kusan a nan yake yini, ba shi k'ofarsu ba shi a wajen Dada. Rashin sukunin da nake ga ni a tare da shi, ya tabbatar mini kasafin ya cud'e fiye da zatonsa. Bai kuma neme ni ba. Kwanaki suka yi ta shud'e wa har aka samu kwanaki bakwai babu tartibiyar maganar Yaya J. Dama na sani mawuyacin abu ne su amince, sai dai dan ya ce zai iya ha'diye gatari ne, shi yasa na sakar masa k'ota ko zai dace ya ha'diye, bayan ya sha kakarin tagwaitakar riskar ajali. Ina cikin wannan yanayin sai ga wani b'acin ran, gidan da Bulkachuwa ya tura su Baba akai masa ku'din aure suka shafa wa idonsu toka suka ce basu san wannan maganar ba, ba zasu dauki y'arsu su bawa wanda aka bulale a bainar nasi bisa k'azamin laifi irin wannan ba, kuma marar tartibiyar sana'a. A sanyaye su Baba suka dawo babu kuzari. Dukkan iyayenmu ukun nan sun ji ciwon abin da aka yi musu. Amma ba wanda ya hango irin wannan tozarcin mai ciwo suka yiwa Babanmu ta hanyar hana Yaya J aure na. Shi kuma Baban Kasuwa ya dauki tasa y'ar ya ba shi. A gabana Baban Marina yake yiwa Bulkachuwa bayanin halin da ake ciki, cikin alhini da bacin rai. Ba wata damuwa mai yawa ya ce "Babu damuwa Baba! Ban damu ba, domin an hana ni aure a cikin gidan nan ma. Dan haka dan waje sun hana ni ba zai zama abin kaico ko tashin hankali a gare ni ba. Ciwon da nake ji daya ne! Da na yarda da hukuncin Allah. Na amince aka mini bulala sai kuma na zama abin k'yama a idon al'umma. A wauta ta imani na yi, domin na yi biyayya ga abin da Allah ya zartar ba tare da bin ra'ayin turawa na yiwa hukuncin Ubangiji tawili ba. Na sani na yi laifin da ku kanku na zubar da darajar gidanku, amma ina yiwa Allah kyakkawan zato zai katange ni daga sake aikata wa tunda na yarda da hukuncinsa, na zabi tereren duniya akan na lahira. Matu'kar kuwa mutane zasu ci gaba da nuna irin wannan *BAK'AR TA'ADAR* Akan mai laifin da ya d'aura d'amarar taubatun nasuha ba shakka zasu dauwamar da mutum cikin b'ata, tunda idan ya dawo kan sahihiyar turba, ba zasu karbe shi ba, ba zai tsira daga yamididinsu ba." Baba ya kasa ce masa k'ala domin jikinsa ya yi sanyi da kalaman na Bulkachuwa. Ni kaina da nake gefensu ina wa Baban Marina wanki ba k'aramin sanyaya jikina kalamunsa suka yi ba. Na sani gaskiya ya fa'da, hana shi aure da ake yi kuma ba shine mafita ba, illah bashi lasisin sake dulmiya cikin zunubin da ake k'yamarsa. Baya ga hakan basu taimaki y'ay'ansu ba, tunda dukkan y'anmata nasa da aka hana shi auren su sonsa suke tamkar su bashi kyautar kansu, ashe kuwa idan ya so lalata rayuwar yaran nasu cikin ruwan sanyi zai yi hakan, tunda Ubangiji ya kyautata masa halittarsa k'warai da gaske . Dan haka zai iya amfani da son da suke masa ya lalatasu a banza, idan kuma hakan ta faru zai yi wahalar gaske ya karbi aurensu domin komin lalace war namiji baya son lalatacciya. Cigaba aka samu ko tabarbare wa? A wannan rana na fahimci ashe cikakken mutum ne mai nutsuwa, kawai sharholiyar ce ta yi masa k'awanya. Ya katse shirun da Baba ya yi ta hanyar ce wa "Baba na gode sosai, zan cigaba da istigifari, idan al'amura suka sake daidaita mini zan fara sana'a, zan je Bulkachuwa na nemi aure ina da tabbacin a dangin mahaifina ko nafi hakan lalace wa zan samu mai k'arfin halin da zai bani aure tare da fatan auren ya zame mini sanadin shiriya da bud'ewar arziki." Ya mike ya tafi yana sake godiya sosai. Ajiyar zuciya kawai Baban Marina yake yi, na lura ba k'aramin ki'dima ya shiga akan al'amarin ba. Murya babu amo ya ce "Yabi idan kina son Alhaji ki ce masa ya turo wakilansa, idan kuma ba kya sonsa to ki fa'da mini zan sallame shi". Na yi k'asa da kaina na kasa amsa masa, daga haka kuma sai ya fita, na bishi da ido amma tunanin a yadda jikin Baba ya mutu murus akan al'amarin Bulkachuwa da ace Adda Nazira ba ta yi aure ba, Babanmu na iya juya wa nak'asunsa baya, ya bashi auren ta. A fili na furta "Alhamdulillah da Allah ya sanya ta yi auren ta ta barranta da auren tantiri ma'abocin *BAKAKEN TA'ADODI*. Haka kawai sai zuciyata ta buga da tsananin gaske, a dalilin ayyana wa da na yi, wata'kila fa idan ban tsayar da miji ba, Baba yana iya cewa ya bashi ni. Nan da nan na tsirtar da yawu saboda kyankyaminsa da ya taso mini. Gashi dai zabgegen saurayi ne dogo cak mai murdadden jiki tamkar ya fito cikin Kyawawan Tirkawa(Turkish). Amma kwata kwata baya burge ni duk da farar fatarsa da bak'ar sumarsa, da suke rudar y'anmata. Asalima Y'ar tsama muke yi, sassaucin rikicinmu a dalilin kwamshina ne, domin sosai yake yi masa alheri. Ya karbi takardunsa, samun aikin ne dai shiru, amma ana saka rai tunda kwamshina baya wasa kuma mutuminsa ne. Tuni Yaya Salisu ya samu aiki a asibitin Toro a matsayin accountant na asibitin tunda dama bangaren ya karanta. Yaya Rabi'u da Bulkachuwa ne shiru amma akwai kyakkawan zaton suma zai samo musu. Wananan dalilin ne ya sanya ya daina tsokanata ta hanyar muzanta ni. *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* A fili na furta "dutse a tsakanina da Bulkachuwa ya Rabb". Ina wankin ina jaddada wa kaina matu'kar Yaya J bai yi yun'kuri mai k'arfi ba, to nan da lokaci kankani zan bawa kwamishina dama ya fito tun zuciyar Baba bata ayyana masa wani al'amarin da zai iya kassara ni, ya dauwamar da ni a cikin ba'kin ciki mai tsananin gaske ba. Na kammala wankina. Mama ta fito ta ce "Yabi anjima zan aike ki gidan Nazira". A ladafce cikin murna na ce "To" Domin kuwa ha'din baki muka yi da Naziran, saboda na yi ta tambayar Baba zani gidanta yana hana wa, basan me yasa yake hana ni zuwa ba, amma bai ta'ba yin k'orafin zuwa koyon sana'ar da nake fita ba kullum. Duk kuwa da ce wa ake yi shargalle nake yi da sunan koyon sana'a. Shiyasa Nazira ta ce wa Mama ta bani kwanuka na kai mata kar aba wa marar wayo ya yi b'arinsu su yi lamba. Tunda idan ita ce ta aike ni Baban ba zai hana ba, ba kuma zai tambayi aiken menene ba. Dan haka a gurguje na shirya na tafi. Muna zaune ina bata labarin yadda muka yi da J. Ta galla mini harara ta ce "um um uhum. Ashe dai Yabin bata san ciwon kanta ba. Har wane ne Jabir kuma? Idonta ya ciko ta ce "Allah ka sanya sai bayan raina zaki zama matarsa!. Jikina ya sabe da rawa na ce " Addda Nazi! Cikin gigita domin ban ta'ba ganin fishi mai yawa a tare da ita irin hakan ba, ita din mai ha'kuri ce, mai kuma sanyin hali ce tamkar dai ba daga tsatson Mama ta duro ba. Murya na rawa na ce "mene ne na wannan mugun fatan Nazira?" Idonta taf cike da hawaye ta ce "Da kin fahimci yadda na k'yamci al'amarin, da baki zo gabana da wannan maganar mai bak'i tamkar zunubi ba. Ban iya fishi ba, shi yasa nake kaffa kaffa da duk abin da zai ha'da ni rikici da jama'a, domin ni kaina ina tsoron fishina ina kuma yawaita neman tsarin Allah da shi. Amma zan fa'da miki, matu'kar kina son ganin fishina da barranta kaina daga al'amarinki to ki cigaba da yi mini wannan maganar da nake fatan ajalina ya riske ni kafin ta wanzu". Sai ta fashe da kuka sosai. Cikin kuma kukan take cewa "Yanzu duk ba'kin cikin da aka cusa wa ubanmu, duk yadda aka wula'kanta ki, dan ke ce asararriya har ki kalli dan Baban Tsakiya da sunan soyayya irin ta aure? Na rantse miki da Allah idan ace Jabir ne ka'dai namiji a duniya gara ki tabbata babu aure, ko ni na mutu ki maye wa mijina madadina da dai Yaya Jabir ya same ki. A haukanki Baban Tsakiya zai bar shi ne? Ko kuwa kwantaccen tunaninki ya fa'da miki Baban Kasuwa zai bashi aurenki alhalin tasa y'ar ce matarsa? Kaico da wannan maganar da kika nufo ni da ita. Nima cikin kuka na ce ",Takura mini ya yi shine na yi masa gatse dan ya shafa mini lafiya." Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da fa'din "Amma shine kike rawar jikin fa'da mini, idan ba kya so me ya sanya zaki yi mararin sanar mini?" Ta nisa ta zarce da fa'din "Idan zaki ha'kura da shi ki hakura Yabi. Domin Jabir ba mijinki bane, na tabbatar duk sanyayyar zuciyar Baban Marina ba zai ta'ba bawa Jabir aurenki ba, ban da dai ma mai k'arfin halin jure damuwa ne da kuma kawaici da tuni bai ha'du da ciwon shanyewar barin jiki ba a dalilin abin da yan'uwansa suka yi masa. Ashe duk zafin ranki, da kishinmu da kike yi a banza ne a kuma fatar baki ce? Wallahi matu'kar zaki nemi zama ahalin gidan Baban Tsakiya ki tabbatar kin fita daga namu ahalin Yabi" Ta tashi ta bar ni tana kuka sosai. Jikina ya mutu wato ba k'aramin gaba ba ce ta shiga dangimu ba kenan? Duk ha'kuri da kawaicin Nazira ita ce take fadin tsauraran kalmomi akan zumunta irin haka? To idan har Nazira mai sau'kin hali da k'ullaci zata yi hakan to ina ga Yaya Ummi shakikiyata kuma mai ra'ayin rikau?. Domin ita hatta zumuncina da Nazira adawa take yi da shi tana ganin ita ce tafi kusa da ni, ita ta cancanci mu yi irin wannan soyayyar, ta kasa fahimtar tazara mai yawa ce a tsakanina da ita, Nazira kuwa tare muka taso tamkar tagwaye, kuma Ubangiji ya jefa mana soyayyar juna duk da k'unbiya k'unbiya irin ta iyaye mata da kishi yake haifar wa. Bare kuma mazan Gidanmu. Yaya Rabi'u shine sa'an Yaya J tare suka taso, bayan jini da ya ha'dasu, abokanta suke yi sosai, amma Yaya Rabi'u da kansa bayan an yiwa J aure da Maijidda na ji yana fa'dar bai k'i wani a duniya har cikin zuciyarsa irin Baffanninmu ba, yana kuma fatan kada a k'addara auren zumunci a tsakanin y'an k'ofarmu da tasu ila yaumil k'iyamati. A sanyaye na bita uwar d'akinta na dinga rarrashinta da k'yar na shawo kanta ta ha'diye kukan nata tamkar yarinya y'ar k'arama haka ta koma mini. Wannan yinin bai yi wani armashi ba tunda zuciyarta ta riga ta baci. Har na dawo gidanmu a takure nake jin kaina, domin ban ji da'din yadda Nazira bata sake mini kamar yadda nake so ba. Na iso gida na tarar da Yaya J gurfane a gaban Baban Tsakiya kansa a k'asa da alamun kuka yake yana fa'din yayi masa alfarma ya bar shi ya yi abin da Allah ya hallata masa. Ba sassauci ko nauyin ganina ya ce "Na gama magana idan baka gamsu ba, ka je ka nemi wanda zai shige maka gaba, babu damuwa, amma fa babu albarkata a ciki". Na shige da sauri, ina ambaton "Innalillahi wa inna ilaihir Rajiun". Ina shiga gida sallar almuru kawai na gabatar na dauki waya na k'ira kwamishina na ce "Baba ya ce ka turo waliyyainka". Ya dinga murna yana sanya alheri da albarka, tare da addu'ar Allah ya sanya yadda na aminta da shi, kada ya kunya ta a idona. Na ajiye wayar ina mamakin ni kuwa a duniya me na tsare wa Baban Tsakiya ne? Na dinga Jin haushin kaina yadda na makance ina son Jabir! A yau na yarda na gamsu tazarar da take tsakaninmu tamkar tazarar sama da kasa ne . Ba zan ce bana son Yaya J ba, domin kuwa ikon zuciyata ba'a hannuna yake ba. Amma na yarda da maganar Nazira ko shi ka'dai ne namiji a duniya to haramun ne a gare ni. Bayan Baban Marina ya dawo gida bayan sallar isha a tsakar gida Inna ta shimfida masa tabarma a dalilin zafi da ake fama da shi. Ya kammala cin abincin da ta gabatar masa kenan. Ya kalli ni duk da muna da tazara ya ce "Yabi zo nan". Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Na matsa kusa da shi kamar yadda ya yi mini umarni. Babu sukuni ya ce "Ya ya maganar Alhaji?" Kaina a kasa na ce "Na isar da sakon na ka". Ina rufe baki ya ce "Madallah da Yabi! Ubangiji ya tsare ki, ya sanya albarka a dukkan sha'aninki". Farin-ciki ya mamaye ni, na amsa da ameen da karsashi. Ya sallame Ni. Na shiga dakinmu na tarar da Gwaggo tana ta kulla siganta hankali kwance. A zuciyata ina ta jinjina mata na yadda bata raina riba duk kanknatar ta. Domin sigan nan mafi yawa sai ta yi ciko duk sadda za'a auno mata. Idan na ce ta bari, sai ta ce da bata siyar wa, da ba zamu sha yadda muke so ba. A hankali na ce "Sannu da kokari Gwaggo! Allah dai ya nuna mini ranar da zan hutar da ke zaman kullin sigan nan dan kawai mu saka siga a koko ya ji". Ta yi murmushi tana fa'din Yabi da dogon buri kike, dama ana wuce yin sana'a ne? Na ce "Indai bata kawo ku'di ba. Ta yi murmushi ba tare da ta ce komai ba. Na bu'de baki zan yi maganar sai kawai muka ji sallamar Yaya Jabir a tsakar gidan. Baba ya amsa masa tare da cewa "iso mana Jabiru". Ya zauna a tabarmar ya gaishe shi cikin nutsuwa. Baba ya amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsa iyali da karatunsa. Tsawon lokaci Yaya J bai iya cewa Baban komai ba. Sai Baban ne ya ce "Akwai matsala ne Jabiru?". Cikin rauni sosai ya ce "Baba so nake ka bani Yabi na aura". Zuciyata ta buga, na yi matu'kar kasa kunne a kansu, ko kwakkwaran motsi bana son yi. Hatta Gwaggo tsaya wa ta yi tana saurare. Murya da walwala Baba ya ce "Jabiru ka zo inda za'a yi maka komai, ina tabbatar maka da a ce a wani wajen kake son auren da na je na nemo maka. Sai dai da yake y'ar tawa ce shiyasa bazan iya komai ba. Kana da siffar da za'a baka aure babu haufi. Amma akwai mishkiloli da baza su bari na baka Yabi ba. Farko matarka da take hannunka itama y'ata ce da kanina ya haifa. Kasan kuma matan yau basu dauki lamarin kishi da sassauci ba. Ha'dasu kishi zai iya ruguza komai ya mayar dasu abokan gaba, sannan zuri'armu zata dare ne, wasu na bawa Yabi kariya, wasu na bawa Maijidda. Da ace Yabi ka fara aura, ka zo kana son Maijidda daga baya to ina tabbatar maka da sai inda karfina ya kare, domin ina da tasirin da zan lank'awasa ta a zauna lafiya. Amma tunda ka riga ka auri Maijidda a farko, dole a ha'kura da maganar Yabi dan a samu a cigaba da lallaba zumuncin da ya dan yi saura." Tsawon lokaci ban ji Yaya J ya ce komai ba tabbacin ba haka ya so ji ba. Murya ba amo ya ce "Baba kai ne tsanin da nake ganin zan taka dan na samu cikar burina." Baba ya numfasa ya ce "Ai kuwa a wannan karon ba zan zame maka tsanin ba Jabiru. Domin ina sane da yadda Mahaifinka bai amince maka ba, ka yi kankanta da yawa ka jefa kanka a cikin manyan matsaloli, domin auren da kake son yi ba zaka samu nutsuwa da shi ba tunda babu albarkar iyaye, sannan su kansu matan naka ba gode wa kokarinka zasu yi ba, kullum zaka zauna ne cikin zullumin zarge zargensu." Yana dasa aya Yaya J ya ce "Zan jure Baba, zan iya, da sannu Ubangiji zai hore mini su gaba'daya. Sannan ina fatan sanadin wannan auren ya zama silar daidaita al'amura a gidan nan". Ga mamakina sai jin muryar Baban Marina na yi cikin kaushi ya ce "Jabiru ba zan baka ba, na rok'e ka, kar ka kuma dosa ta da wannan tatsuniyar domin ko mak'oshina bata je ba, bare ta shiga zuciyata. Bana son na yi maka abin da zaka mini kallon marar kirki, ko na rashin inganta zumunci, amma idan ka cigaba da dagewa to ba shakka zaka sha mamaki, domin kuwa na riga na haramta soyayyarku a zuciyata, dan haka kai ma ka shafe ta domin ba rayayya bace". Bamu gama fita da mamakin maganganun Baba ba, Yaya J ya sake shayar da mu wani sabon mamakin ta hanyar cewa "To Baba idan kuma Allah bai shafe ta ba, ya raya ta fa?" Takaicinsa ya k'ume Baba ya kasa ce masa komai domin bai ta'ba zaton Yaya J zai iya fada masa hakan ba tunda mutum ne mai biyayya, mai kuma gudun zuciya. A sanyaye ya ce "Kowa ya ki fahimtar halin da nake ciki, me yasa zaka biyesu wajen yin watsi da zumunci Baba? Annabi cewa ya yi mu yiwa wanda basu yi mana ba". A matu'kar zafafe Baban Marina ya ce "To dai ni ne uban Yabi! Ni kuma shari'a ta girmama ta mayar a hakku ya za'ba mata miji, idan kuwa hakane, ko mutuwa ce ta riske ni gabannin na aurar da ita da kaina. To waliyyinta baza su baka ita ba, bare kuma ina fatan a ara mini dama na aurar da ita da kaina. Ka je ka yiwa Mahaifinka biyayya, na gode sosai da soyayyarka. Mu cigaba da addu'a da sannu komai zai dai-daita mana. Amma Yabi kam ba matarka ba ce". Tsawon lokaci bai amsa ba. Ni dai daga sama na ji muryarsa yana cewa "Sai da safe Baba". Ajiyar zuciya mai nauyi na ji Gwaggo ta yi tare da cewa "Alhamdulillah! Ubangiji ka sake nisanta wannan al'amarin kamar yadda ka nisanta gabas da yamma." Na kasa magana, amma dai zuciyata ta yi nauyi, na kuma gamsu da gaske Yaya J yana sona da dukkan zuciyarsa. Gefe guda kuma ina gasgata tsinkayen Nazira da ta ce Baban Marina ma ba zai bashi aurena ba. Na k'udire bazan sake bari mu hadu ba, bare zuciyata ta dinga karaya a dalilin ta so mini da soyayyarsa da nake ta kokarin danne wa da dukkan iya wa ta. Washagari na tashi sukuku ba wanda ya tayar da maganar. Da yamma sai ga kwamshina ya zo, sai da ya fara zuwa wajen Baban Marina a wajen sana'arsa, ya sanar masa nan da kwanaki biyar zai zuro a yi maganar aure da saka rana gaba'daya. Shi yake fa'da mini hakan. A wannan ranar ma kayan da ya kawo mini ba k'aramin yawa ne da su ba. Tunda ga kan sutura, ga provisions tamkar wacce nake rike da kaina. Sai kuma dalleliyar waya da zoben gold wai a matsayin tukuicin amincewa da shi. Tuni Baba ya sallama ya bar ni ina rike waya. Wadanccan ma da ya rike tuni ya fito mini da abina. Dama k'ananu ne sai kawai na ce ya bawa iyayenmu mata tunda uku ne dama. Ni bansan me yake faruwa ba, ashe Yaya J bai fasa sintiri a wajen Mahaifinsa da Dada ba. Da ya kasa samun tallafinsu, sai kawai ya doshi Baban kasuwa mahaifin Maijidda. Nan ma fatattakarsa ya yi tare da alwashin idan mummunar k'addara ta afko aurenmu ya tabbata, to kuwa ya kwana da sanin sai dai ya sako masa Maijidda. Hankali ya fara tashi domin gaba'daya Yaya J ya susuce ya rasa nutsuwa har ta kai Maijidda ta dawo gida a dalilin zaman nasu babu da'di sam, ita kuma ta gaza ha'diye damuwa ta taho, da k'yar Dada ta mayar da ita. Baban Marina da kansa ya fa'da wa Dada da yan'uwansa cewar ranar asabar za'a zo neman auren Yabi, kada su yi nisa. Daga Baban Tsakiya har na Kasuwa suka gabatar da uzzirin suna da daurin aure muhimmi a wannan ranar. A wannan karon hankalin Baban Marina ba k'aramin tashi ya yi da wula'kancin da suke yi masa ba. Ya gabatar da korafinsa gaban Dada cikin kankan da kai ya ce "Ba zai yiwu na dauko wasu daga waje su marabci masu neman auren y'ata ba. Alhalin ga y'anuwana ban da ransu da lafiyarsu, har wanne daurin aure zasu je da yafi al'amarina muhimmanci Dada? Ki shiga cikin wannan maganar, ina jin tsoron kada na kasa jurewa fa." Ita da kanta ta sani ba'a kyautata masa ko ka'dan amma da yake bata iya tsawatar wa wadanccan shiyasa bata iya magana, har komai ya rincab'e. Da rashin walwala ta ce "Zamu zauna da daddare dukkanmu". Da daddare kuwa dukkansu uku suka hadu a gaban mahaifiyarsu, a sanyaye take gabatar da k'orafin da yayansu ya zo da shi. Babu kunya dukkansu suka ce suna kan matsayarsu ba yadda za'a yi suna cikin hankalinsu su jagoranci bawa mai saka d'agaggen wando aure, kema da za'a fito k'arara a fa'da miki ainihin yadda ak'idarsa take da kin k'yamace lamarin wannan mutumin. Mun yi shiru ne kawai dan kada ace hassada muke yi. Ko bamu da kirki, amma waye a jahar nan bai san yadda Mustapha Zaki ya yi k'aurin suna wajen yiwa masu akidar yin maulidi kafar ungulu ba. Duk wani masallaci indai ba na yan kungiyarsa bane sai ya durkushe shi, ke kan ki da yasan yadda kike son shehu da ya d'aure ki saboda zuciyarsa babu alheri." Dada ta kad'u kwarai da gaske. Domin babban b'acin ranta a nemi ta'ba mata mutuncin ra'ayinta. Ita din mai mai zazzafar akida ce akan hakan. Ta fara tafa hannu tana cewa "Ashe hakane? Allah na gode maka da ka kubutar da jinina fa'da wa hannun wanda zai yi mata sanadin rashin samun rabo ranar gobe". Sai ta hau kuka tana sake godiya ga Allah da Annabi. Jikin Baban Marina ya yi matu'kar yin sanyi ta yadda yan'uwansa suka shammace shi, suka gabatar da hujjar da ba mai kankareta a zuciyar Mahaifiyarsu. Ya tabbatar sun dade da kitsa maganar dan sun tabbatar auren ya rushe gaba'daya, kuma wannan hanya ita ce mafi sau'ki da zasu ja hankali gyatumarsu ta lalata komai. A zuciyarsa ya dinga ayyana shin wanne irin zamani muke ciki wanda dan-uwanka ma baya son ya ganka a inuwa? Me ya tare musu ne? Shi ka'dai ne yake fuskantar irin wannan tsananin ko kuwa a ko wacce zuria ce? "Allah kai ne mai zamani, a kawo mana mafita, da sassauci" ya fa'da a ransa. Ya sake kallonsu, yana ganin sun hade sun bar shi daban, sai dai a zahiri ne suke shiri a bad'ini kuwa ba wani taimakon juna a tsakaninsu, tunda kowa iya y'ay'an da ya haifa ne dolensa. Sannan kowannensu boye wa dan-uwansa wadatarsa yake yi. Ya sauke gauron numfashi kafin ya yi magana ya ji Dada tana fa'din "matu'kar ina da iko akan ka ba za'a bashi aure ba, idan kuwa ka kafe sai dai na barka da Ubangijin gizagizai ya bi mini kadina a wajenka". A ki'dime ya ce "Har abada maganar ta mutu, Allah ya yanke mata wahala ya fito mata da wani mafi alheri wanda za'a yi alfahari da shi". Dada ta goge idonta tana fa'din "Ameen". Baban Tsakiya kuwa ya ce "ai y'ar fariya ce , ba zata tsaya a matsayinta ba, dama ya ta kasance? bare yanzu da wannan tsohon banzan ya sake kambaba burinta. Ai idan ba tashi aka yi akan ta ba, sai ta tsofe tana gabanmu tana zuba d'ibar albarka, ko yanzu tana ganin sakamakon hatsabibanci, tunda duk kintsatsse ba zai zo wajenta ba. Har yau ta k'i barin Jabir ya fuskanci matarsa sosai, da sun fara zama lafiya idan har ya yi tozali da Yabi zai gigice. Gashi kuma Maijidda matarsa ce, tunda cikine da ita, idan ba'a bashi aurenta da ake ta munafurci ba, ta ya ya ake so wannan rabon ya bayyana?" Baban kasuwa ya ce " Ai ha'kuri Muna cikinsa, amma sai ace mune da laifi, ban da sha'anin jini tasirinsa yawa ne da shi ai wata shari'a sai a lahira kawai." Dada ta ce "To ni kam ba zaku bar gun nan ba sai an samo wanda za'a ba shi auren Yabi. Domin na fuskanci matsalar gidan nan tana 'damfare da ita." Baban Tsakiya ya sake cafe wa da cewa "Kinsan dai ni da Iliya bamu da mutuncin da zamu yi irin wannan ikon da ita, wannan maganarki ce da ubanta." Cikin rawar murya irin ta sare wa da lamari Baban Marina ya ce "Yau muna watan Safar ko Dada? To matu'kar rayuwata ta kai, watan jibi na gaban maulidi ke nan, zan aurar da ita. Domin ina da wadanda zan basu aurenta su kar'ba, sannan ita ma Ubangiji ya hore mini ita zata ta yi mini biyayya. Ubangiji kuma zai duba manufar kowa a nan ya cusa wa wanda zan ba shi auren ya kar'ba da dukkan zuciyarsa". Dada ta ce "Allah ya tabbatar ya nuna mana lokacin, amma ba za'a tashi ba sai ka fadi wanene, d'an wacce haular ce? Gudun kada a sake kitso da kwarkwata." Baban Tsakiya ya ce "yarinyar nan fa ta riga ta rik'a, idan aka kai ta wani wajen ma mutuncin gidanmu zata zubar, me zai hana a lallaba a bawa wannan yaron kawai, tunda shima yana da tambarin da aure zai yi masa wuyar samu wa?" Baban Kasuwa ya ce "Ni ma tuntuni nake son na fa'di hakan, to amma ina jin tsoron sharrin zuciyar da take raina alheri, yanzun nan sai a juya magana a ce da mugun nufi aka yi kaza". Dada ta ce"Ku yi magana sosai mana, ni duk kun saka ni a duhu ban gane wa kuke nufi ba?" Tirk'ashi Karshen littafi na d'aya. *Gaba'daya wadannan shafuka shimfida ne dan ku fahimci labarin da kyau, asalin labarin da turka turkarsa yana littafi na biyu da na uku* *Bisa soyayyar da kuke yiwa rubutuna ya sanya zan yi muku tsarin VIP. *In Sha Allah babu jira. *Babu posting ranar Lahadi* *Sau biyu za'a yi posting a rana*. *Ku zo mu yi tafiyar da babu nadama* *Zaku dara, zaku koka, jikinku zai tsumu, zuciyoyinku zasu motsu. Tunani kuma zai tafi cancanken me zai faru a gaba*. *Marubuciyar HALIN YAU da SABO DA KAZA* *Yanzu kuma alk'alaminta yana tafe da BAK'AR TA'ADAH* *500regular page* *VIP 1k twice pages* *2384876855* *Surayya Ibrahim Dahiru* *Zenith Bank*. *Ko* *7061488065* *Surayya Dahiru Ibrahim.* *Opay Bank.* *08032773332.* *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *07039269802 *Surayya Dee* *Yar mutanan Gwaram* ✍️ *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. Cikin kasala irin wacce b'acin zuciya ke sababa wa, Baban Marina ya ce "waye kuke ganin ba zai auru ba, tamkar Yabina! Wane ne shi?" Hatta Dada jikinta ya yi lubus da Baban Marina ya ce Yabinsa a akan idon ta da na y'anuwansa. Wanda hakan na alamta ce wa ya kai makura wajen kawaicin da yake yi amma ba'a yi masa kara. Daga Baban Tsakiya har na Kasuwa ba wanda ya iya cewa kanzil domin sun shiga yanayi na jin nauyi da borin kunya. Sun fahimci fishin da yake shinfid'e a fuskar yayan nasu ya tunbatsa. Sai suka yi dabarar kame wa daga jaye jayen maganar. Bai sake jiran komai ba, ya mike tare da yiwa Dada sallama ya fice. Yana fita Baban Tsakiya ya ce "Muna cikin wani irin kalubale a wannan duniyar. Ace ba dama ku tattauna da dan-uwanka ya fahimce ka, shike nan sai ya zama sanadin tabarbare war al'amura?" Ya yi k'wafa mai nuna takaicinsa muraran. Baban Kasuwa yana bu'de baki sai ce wa ya yi "To ai irin wannan al'amarin wuya ne da shi. Tuni Ubangiji yasan al'ummar Manzonsa zamu riski wannan zamanin shi yasa ya saukar mana suratul Yusuf dan ta zama izina ga masu hassada da k'yashi. Ta kuma zama gargadi ga masu hankali. Wani abin kaicon ma mu babu y'an uba a cikinmu, amma babu yadda za'a yi a ha'du a yi hira da walwala cikin farin-ciki saboda kawai ka fi mutum haske? Gaskiya zan fa'da miki Dada. Tunda ke kin isa da shi, ba wanda ya cancanci Yabi sai Tijjani, su rufa wa junansu asiri, shine kuma zai iya biyar da ita, ya yi maganin shak'iyancinta". Baban Tsakiya ya numfasa ya ce "Tunaninmu d'aya Iliya, sai dai ba lallai ne ya amince ba. Tunda duk iyashegenta bai yarda ja'irar yarinya ba ce. Zai yi wahalar gaske ya ba shi tunda shi lalacewarsa ta bayyana a gida da dawa. Ita kuwa mu na kusa ne muka fahimta kawai". Dada ta saki ajiyar zuciya ta ce "Idan haka ta faru kuwa ina da yakinin mai sunan manya zai nutsu domin komin ginshirarsa ba zai kushe ta ba. Ubangiji ya kyautata halittarta, gata yar shawalwala da zata da'de tana cin zamaninta". Suka gintse fuska suna fa'din "Kyaun hali da tarbiya ai sune kyaun mace Dada." Kawai dai ki sanya baki a ba shi ko ma sarara, domin idan shine mijinta zai karya dukkan lagonta." Basu tashi ba, sai da suka tabbatar ta gamsu bawa Bulkachuwa auren Yabi fa'ida ne mai yawa a garesu bakid'aya. Baban Tsakiya ya fi kambaba lamarin, a zuciyarsa kuwa so yake a yi a yi a auren ta tunda kusan kullum sai ya yi mafarkin Jabir ya bijire masa ya aure ta. Sun ki kwamishina ne dan kada haske ya shiga k'ofar dan-uwansu, tunda sun tabbatar nagartacce ne, basa son ya'yansa su yi k'arfi. Sun fi son a ce su da y'ay'ensu sune masu fa'da aji. Auren Bulkachuwa kuwa sun san ba wani fiffika da y'ar iskar yarinyar nan zata yi musu. Tunda a bayyane yake matu'kar mace bata samu miji na gari ba to rayuwarta ta na'kasa. Washagari da sassafe Baban Marina ya yi sallamah ya ce ya tafi Azare. *** Na fito sanye cikin uniform, na isa mashigar zauren Dada dan gaisuwa da kuma biya wa Nasiba. Sai na ji magana k'asa kasa daga dakin Bulkachuwa. Na kasa kunne dan na ji me yake fa'da. "Bazan sake turo kowa gidanku ba Bilki. Na yarda ki na sona, amma kuma ai ba zaki iya aurar da kanki ba, dole sai da wakilcin iyayen ki. Kema kin san ina sonki, amma tabbas bazan sake turo kowa da zummar a nema mini aurenki ba". Na yi fakare, jikina ya yi laushi akan abin da na ji. Waton ba karamin son Bulkachuwa y'anmata suke yi ba. Bansan me yasa shi kuma yake da jarumtar juya wa soyayya baya ba, matu'kar aka nemi muzanta shi. Na tsinci kaina da fa'din "Ina ma irin zuciyar Tijjani nake da ita?" Da tuni na yi watsi da tunanin Jabir da soyayyarsa. Amma ina! Har yanzu ina jin sonsa, kawai na danne ne dan babu yadda na iya. Na shiga cikin gidan na tarar da Nasiba ta shirya. Na gaida Dada kamar yadda na saba. Sai dai amsa mini da ta yi, ya banbanta da sauran watannin baya. Domin tunda kwamshina ya bayyana mini, da karsashi take amsa mini gaisuwa ta. Amma a yau cikin wani irin yanayi da na kasa tantace wa. Sai kuma ta zarce da fa'din "Wanda duk ya yiwa mahaifinsa biyayya ba zai tab'e ba. Ina da tabbacin ko wuta na rura na ce da tsohonku ya shiga zai fa'da ne kawai babu tambihi. Ina rokonku ku dinga yi masa biyayya, ku yarda ya isa da ku, mussaman ke Yabi da tun shekarar da kika iso duniya ya shiga cikin tala jaurar duniya". Ta fa'da kuka na subuce mata. Jikina ya mutu murus a dalilin kalamanta, tunanina ya shiga canke canken akwai al'amarin da zai biyo bayan wannan jirwayen na Dada. Muna tafe da Nasiba duk uban maganar da take yi mini akan Bulkachuwa na kasa ce mata uffan. A dalilin zuciyata ta riga ta baci da yadda Dada ta ce wai tunda na iso duniya ubana ya fa'da cikin ibtila'i. Na sani ba yau ake fa'da ba, Mama ta sha fa'da mini ni din tauraruwa mai wutsiya ce, haka ma ya'yanta su Yaya Indo. Tun ina damuwa har na zo abin ya daina damuna, domin Baban Marina bai ta'ba yi mini wannan izgilancin ba. Amma a yau sai na tsinci kaina da jin ciwon furucin Dada kwarai da aniya. Na dinga hasashen me ya janye mini alfarmar da na a samu y'an watannin nan a idonta? A daren ranar Babanmu ya zaunar da ni da matansa ya fa'da mana aurena da Alhaji ba zai yiwu ba, bisa wani dalili da bai bayyana mana shi ba. Ya je shi da Alhaji Tanimu sun bashi ha'kuri. Ya gamsu sun yi masalaha, duk da ya shiga rud'ani sosai. Ya kuma ce ya yafe duk hidimar da ya yi. Jikina ya mutu, zuciyata ta tsinke. Na kasa bu'de baki na yi magana. Ya sallami matansa suka bar ni da shi. *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S* Ya tausasa harshe har ya bani tausayi. Ya ce "Yabi kinsan Nura dan wajen Babanku Tanimu?" Na daga kai tabbacin eh. Ya numfasa ya ce "Madallah! To zai zo ku gaisa, shi na za'ba miki ya zame miki miji. Ubansa tuni yake ro'kon na ba shi ke ya bawa Nura, tunda ya samu labarin abin da y'anuwana suka yi mini, ina ta bagarar da maganar. Saboda ganin Alhaji ya shigo da k'arfinsa. Amma a yau din nan na amince masa. Ina ro'kon arziki Yabi, kada ki kunyata ni. Kinga shi namiji ma ubansa yana fa'da masa ya amince da farin-ciki da walwala. Ki kwantar da hankalinki irin k'alubalen da kike fuskanta da kananun shekarunki na alamta cewa zaki samu kyakkawar rayuwa a gaba". Hawaye taf a idona na ce "Na amince Baba! Allah ya sa hakan shine mafi alheri". Ya amsa da ameen ikin farin-ciki mai yawa, tare da sanya mini albarka. Ya sallame ni bakinsa dauke da addu'a a kaina da lamarina. Ina shiga d'akin Gwaggo na fashe da kuka. Ta ru'ko ni sosai ta dinga bani ha'kuri. Wannan rarrashi da Gwaggo ta yi mini ya sanyayya mini zugin da nake ji a zuciyata. Da na nutsu sai na fahimci ba kukan rabuwa da Kwamshina nake yi ba. Domin ba wani sonsa nake ba, dama na yarda zan aure shi ne, dan na gaji da zaman Gidanmu. Sannan Bulkachuwa ya kitsa mini cewar da na yi kukan takaici a gidan babu, gara na yi a gidan wadata. Amma sam babu soyayyar da zan yi ba'kin ciki irin haka. Kawai ina kukan yadda al'amarina ya banbanta da na kowacce y'a a gidanmu ne. Maganganun Gwaggo sun sake fahimtar da ni ita dama ba son aurena da Alhaji take yi ba, ta yi shiru ne dan gara aurensa akan na Jabir. Amma ta ce bata fasa addu'a ba, bata fasa nema mini zabin Allah ba. Dan hakan kuma ya kasance sai ta gamsu Ubangiji ne ya amsa mata. Kwanki biyu na warware tamkar komai bai faru ba, na cigaba da harkokina. A yammacin wannan rana ta litinin mun taso daga Islamiya sai ga aike wai ana sallamah da Yabi in ji Nuru Tanim. Na dan diririce na kasa magana a dalilin yadda ya zamanantar da sunan na shi. Na dinga canki canki wane ne Nura a y'ay'an, Baba Tanimu? Domin y'ay'an gidan yawa ne da su, matasa sun kai bakwai ko wanne ya isa aure. Na kasa cankar wane ne shi a cikin jerin matasan gidan. Inna da kanta ta cewa yaron ya je ya ce "ina zuwa". Hijabina har kasa na sanya, bayan Gwaggo ta matsa mini na shafa hoda. Na fita cikin zullumin yadda zan gan shi. Tunda bani da sauran za'bi akan lamarin. A babban zauren na hango shi sanye cikin shudiyar shadda sosai, kansa sanye da hular da ta dace da kwalliyarsa. Ko ka'dan ba shi da makusa, ya fi Yaya J cika, tsayi ne dai zasu yi taya. Batki ne sosai, amma ma'abocin tsabta ne daga ga ni. Take na ji abin da ya d'aure mini kirji ya fa'da mini domin ban ganshi a cikin mummunan yanayi ba. Baya aikin gwamnati, amma yana koyar wa a wata firame mai zaman kanta, boobies a sannan yana da shagon caji da turin wakoki ko finafinai a wayar hannu. Muka gaisa cikin yanayi na babu yabo, babu fallasa. Muka yi shiru. Tsawon lokaci kafin ya katse shirun ya ce "Asiya! Zuciyata ta harba domin har cikin raina nafi son a ha'da mini da Yabi. Na amsa a hankali da "Na'am". Ya tausasa murya ya ce "Na da'de ina son ki, na sha fa'da wa Babanmu ya taimake ni ya nema mini auren ki, sai ya bada hanzarin dan-uwanki ne yake son ki, ba zai yiwu ya gabatar da maganata ba, tunda akwai nauyi a tsakaninsa da Baban nan gidan. Dan haka ko da kika gan ni anan ba turo ni aka yi akan dole ko biyayya ba, dama ina son ki tun ina zuwa makarantarku". Na yi kasa da kaina ina sake samun nutsuwa mai yawa. Ya sake sassauta wa ya ce "Idan har kina da matsala ko kina ganin ban yi dai-dai da ra'ayinki ba, zan san yadda zan yi na zulle wa maganar ba tare da an ga laifinki ba, domin al'amarin aure ba k'aramar tafiya ba ce da za'a yi ha'kurin dole a cikinsa." Na tsinci kaina da cewa "Babu damuwa Allah ya tabbatar mana da alheri". Dadi ya kama shi, ya ce" kenan Asiya ta aminta da ni?" Murya babu amo na ce "Yabi bata da burin yin fatali da burin iyayenta ko da ya ci karo da nata ra'ayin." Farin ciki ya sake lullube shi. Ya dinga fa'din ma sha Allah! Madallah da Yabi". Na taya shi murmushi. Ya ce "da alama kina son Yabi, ni kuma sai nake ganin karamci ne na kira ki da Asiya." Na cuna baki na ce "Tunda na riga na sami wannan falalar ta zuwa gabas, kawai ka kira ni Yabi domin ina son sunan da dukkan zuciyata". Ya murmusa ya ce "An gama Yabin Nuru". Zuciyata ta tsinke yau ga abin da Yaya J ya guda, na jingina wa Yabinsa sunan wani ba nasa ba. Mun jima muna dan tattauna wa duk da shine yafi yin hirar sosai. Ya ciro ku'di ya bani, na ki karba. A sanyaye ya ce "Matu'kar baki karba ba, to alama ce ta ban samu karbu wa ba". Jin hakan ya sanya na mik'a hannuna duka biyu na karb'a. Daidai lokacin Bulkachuwa ya shigo a hargitse rigarsa daban haka ma wando daban duk a yamutse. Da alamu ba nisa ya yi ba. Inda a ce d'an wanka ne sosai bansan irin rubibinsa da za'a yi ba, tunda a hakan ma ba'a fasa sonsa ba. Nura ya mika masa hannu suka gaisa ya wuce babu walwala nasan kuma yana taya kwamshina kishi ne. A lokacin na sake tabbatar da tsayi da cikar Bulkachuwa ya kai k'ure wa domin sai na ga Nuru bai kai kafadarsa ba. Daga haka muka yi sallamah ya tafi. Na shiga gida ana kiran magariba. Bayan mun idar da salla na bawa Gwaggo ku'din da ya bani sababbin yan dari biyar guda goma cif. Ta yi shiru sai kuma ta ce "Allah ka sawa al'amarin albarka, ya sa karshen wahalarmu kenan". Na amsa da Amin a zuciyata domin ni kaina na gaji da yadda komai yake kwace mini. Gaba'daya shekaruna sha shida ne da ka'dan amma na gaji tunda al'adar auren wuri ne a gidanmu. Wai duk yadda nake da k'arancin shekarun nan, da yadda nake y'ar tsurut habaicin rashin aurena a ke yi mini, ko a jefi Gwaggo da bak'ar magana. Har ta kai bani da kalubalen da ya wuce zaman gidanmu a rayuwata. Rayuwar gidanmu da ta gidan Yaya Ummi ta sanya na k'yamaci zaman babban gida. Wani zaman idan an yi sa'a sai ya zama tsintsiya dan ha'din kai. Wani kuwa sai ya zama tamkar sansanin yaki dan fitina. Ta sake kallona ta ce "Nasan yaron dan wajen Sahura ne, yana da zuciyar neman na kansa ga shi mai jin maganar iyaye ne, duk cikin matan gidan dakinta yafi na ko wacce fasali da kayan jere mai kyau, kuma duk shi ne yake yi mata, shi ka'dai ne namiji a d'akinta, y'ay'anta duk mata ne, amma da ya ke mai zuciya ne sai tafi mai y'ay'a maza biyar gata da kyan ga ni, ta bar uwar maza je da fankamar ita ce da gida. Shikenan rabuwarmu da Kwamshina. Ya mini waya washagarin da Baba ya ce ya je Azare. Ya fa'da mini yadda Baba ya je ya ba shi hakuri. Ya fahimci Baba suka rabu cikin girma da arziki, tare da ro'kon idan auren ya zo a sanar masa zai halarci dauri aure. Nima ya mini maganganun masu taushi da nuna muhimmancin yiwa mahaifi biyayya. Duk da ba wani sonsa nake yi ba, sai da na yi kukan yadda kalamansa suka dagargaza ni. Kewarsa ta taso mini ba ka'dan ba. Ya dinga rarrashi tare da tambayar me zai siya mini na kayan aure dan na yarda ya gode da karamcin da na yi masa. Na kasa cewa komai sai shine ya ce "Zan aiko miki da sako zuwa satin sama in sha Allah" Ya k'are maganarsa da fa'din "Allah ya sa ki shiga gidan auren a sa'a, Allah ya zaunar da ke lafiya". Bulkachuwa a bakin kwamshina ya ji maganar aurenmu ta ruguje. Rannan da hantsi ya aiko yana kirana. Zuciyata d'aya na je na tarar da shi a tsakar gidan Dada yana zaune kan kujerar tsuguno. Na zauna akan turmin da yake fuskantarsa. Ya kalle ni da tarin kulawa ya ce "Asiya Toro me yake faruwa ne? Jiya na shiga Bauchi sai nake jin labarin da ya ki'dima ni a bakin Honarable. Nasan ba zai mini karya ba, me yasa kika canja? Me yasa dan Allah?" Na yi k'asa da kaina haka kawai na ji hawaye ya k'wace mini. Domin idan aka cire yan kofarmu ba wanda ya nuna damuwarsa ko alhini akan shiririce wa da maganar Kwamshina ta yi sai Tijjani. Na tabbatar bayan soyayyar da yake yiwa lamarin, to akwai kishin wula'kanta ni da aka yi a gidan, shi yasa yake son na yi auren ke ce raini. Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi ya ce "Ba kuka zaki yi ba, ya ce mini Baba ya gabatar masa da hujja mai k'arfi shi yasa ya ha'kura. Wacce irin hujja ce wannan dan Nabiyur Rahmati?" Ya fa'da a matu'kar zafafe. Kafin na ce komai sai Dada ta rarrafo ta ce "Ni ce nan! Na barranta lamarin, na kwashe masa albarka, ba zai yiwu na ha'da jini da mai kafirtamu ba. Ba zai yiwu ta auri wanda iyayenta suka tabbatar ba mutumin arziki ne ba". Da kakkausar murya ya ce "Dada me kika yi hakan? Su waye iyayenta?" Yana rufe baki ta ce "Su Badamasi mana". Maimakon na ga ya sake fusata sai kawai na ga ya kwashe da dariyar iyashege ya na fa'din "wannan shine abin dariya kunama ta ciji danwanke. Shi Baban Tsakiya idonsa da kwalli har ya ce wani bai cancanci Yabi ba? Sanin kowa ne Jabir da Yabi masoya ne tun suna yara k'ananu, amma shi da kansa ya datse soyayyar kuma yanzu Allah ya turo mata wani sai ya ce bai cancanci a ba shi aurenta ba. Wanne irin lamari ne mai kama da k'yashi da kuma hassada?" Dada ta rabka salati tana fa'din "Kawunka kake fa'din wannan kalaman a kansa? Mai sunan manya anya zaka yi hankali kuwa? Kusan ma fa saboda kai ya yi wannan al'amarin amma ka ke sakin maganganun da suka yi daidai da zaginsa kake yi." Ya sake fashe wa da dariya ya ce "a kaina, ni kuma? Lallai kuwa, zan ga ta yadda za'a yi, wannan bawan Allan ya nufo ni da wani alheri. Rannan ba abin da bai fa'da mini ba, akan sun je kai mini ku'din aure gidan kananun mutane ba'a karba ba. Ya dinga cin alwashin ba zai sake shige mini gaba a harkar aure ba. Ni kuma abin da bai sani ba, ai kawu ba uba ba ne, dama dangin uba ne a hakku su nemo mini aure, bare ya ce zan wani damu." Dada ta sake rangada salati tare da cewa "Mai sunan manya wanne irin dibar albarka kake yi ne haka tamkar ka sha k'waya?" A tunzure ya ce "Ras nake! Na gaji da fitinar mutanan ne, duk wata fitina su suke kitsa ta. A gabansu uwar Nasiba ta dinga sakin maganganu a kaina ta barranta y'arta da ni, ba wanda ya ce kala a cikinsu. Haka nan shima har yau ba wanda ya kalubalan ce shi akan hukuncin da ya yiwa Jabir na auren Maijidda saboda yana da cikakken iko a kansa. Akan me zai yiwa lamarin Asiya katsalandan alhalin ba kallon y'a yake yi mata ba? Akan me zai nemi ya dinga nuna ya isa da ni alhalin akan idon uwata suka kasa yi mini alfarma da kawaici." Ta ce "Allah ya shirye ka, albarkar mai sunanka shiriya zata sauko maka." Ya bata fuska ya ce "Tare zaki roka ta zo mana da ke, tunda akan idonki ake yin abubuwa na kura kurai amma ba kya iya tsawatar wa. Rannan na ji wani malami yana fa'din ainihin manufar ma'anar kuyanga ta haifi uwargijiyarta. Sak fatawar da ya bayar tamkar ke ya siffanta haka na dinga ji". Na zuba ido. Ina jiran ta rushe da kukan da zata tara masa jama'a tamkar yadda take yi mana. Amma sai ta share ta yi mirsisi ta fanshe da cewa "Shi ubanta ai ya yarda na isa da shi, shi yasa ya katse al'amarin babu tashin hankali. Allah ya shirye ka mai sunan Shehu.". Ya shareta ya kalle ni ya ce "Yanzu kina son wannan ba'kin yaron ko kuwa dole aka yi miki?" A hankali na ce "ko bana sonsa tunda Baban Marina ya amince ai maganar ta kare". Ya girgiza kai ya ce "Baban Marina mutum ne Wlh amma ban son ha'kurinsa, any way Allah ya sanya albarka all the best Asiya Toro". Daga haka ya mike ya fice yana fa'din da kin ce ba kya so. Wallahi da tsaya miki zan yi, komin sharrin mai sharri ba za'a baki wanda ba kya so ba, domin kema y'a ce ba baiwa ba. Kina da hakkin ki so a kuma so ki". Wannan abin da ya yi mini sai ya rage tsanar sa a raina. Dada ta dinga fa'din "Sha sha kamar ba saboda shi aka yi komai ba." Na rasa gane manufar wannan maganar ta Dada. Tsawon sati da kulla alakarmu da Nura wanda ya yi zuwa uku kenan. Mamakin kaina nake ta yadda ya shiga raina sosai. Ko dan sau'kin kansa da yadda ya iya kwalliya da shirya zan ce ne? Ga shi ma'abocin kyauta duk zuwa sai yasan me ya ru'ko mini wala na ci, ko na amfani, gwargwadon k'arfinsa. Mahaifiyarsa da ake kira Yaya itama ba karamin son al'amarin take yi ba. Domin da kanta ta zo da kuma ledarta mai shak'e da kayan kwalliya. Kusan yini ta yi lamarin da ya takura ni, kunyarta sosai na ji. Wanda ko kusan ban ta'ba jin irin hakan akan mahaifiyar Yaya J ba. Karba ta samu daga ahalin gidanmu, dan kuwa ko Mama bata yi abin kaico ba, har ta tafi. Dada ce dai bata wani karbe ta da fuska mai yakanah ba, hatta shi da kansa da ya je gaisheta bai ji da'din karbar da ta yi masa ba. Hankalina ya fara tashi domin kuwa ba hannu Rabbana ya je mata ba, sai da ya siyo mata lafiyyayun lemo da kankana da ayaba tika tika. Na dinga fargaba da tunanin wata'kila wannan d'in ma, ta yi mini sanadinsa tunda su Baban Tsakiya kullum cikin fadin Alh Tanimu munafiki ne wai yana nuna wa ya fisu kusanci a wajen Dan-uwansu". Kuma gaskiyar magana a yanzu da muka shafe satika kusan uku ba k'aramar shakuwa muka yi da shi ba. Ina matu'kar kad'uwa a duk sadda zuciyata ta ayyana mini muna iya rabuwa. Ban ta'ba kuma shiga irin wannan yanayin a baya ba. Duk kishin Yaya J a kaina ya ha'kura ya bar ni da Nuru domin da kansa ya ce ba zai hana ni kula shi ba, amma shima kada na ce na sallama shi, ya yarda ni din allura ce cikin ruwa mai rabo ka dauka. Dan haka zai cigaba da lalube cikin ruwa har Ubangiji ya taimake shi ya damk'e abin da yake nasa ne KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* ✍️ *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *08089965176* *07084653262* *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *MASU BUKATAR YON RIGISTA DA G.H.T. KAKARKU TA YANKUE SAKA DOMIN KUWA FASEELAT ZATA MUKU JAGORA HAR KU FAHIMCI KOMAI CIKIN KYAKKWAR MU'AMALA DA KYAUTATAWA*. *07039269802* Haka rayuwar ta cigaba da tafiya, kusancina da Nuru yana sake shahara. Har ta kai ya goge mini rad'ad'in rashin kwamshina a zuciyata. Rashin Yaya J ne bai bar ni gaba'daya ba, amma ya yi rauni matu'ka da gaske. Yayin da Bulkachuwa ya d'ora masa karan tsana haka siddan. Sau biyu yana ganinmu idan Nuru ya ba shi hannu sai kawai ya d'aga masa, amma ba zai yarda ya ba shi nasa ba. Na cigaba da zuwa makaranta hankalina ya fara kwanciya. A lissafi saura kwanaki talatin da tara na bar gidan. Tare za'a ha'da da na Nasiba domin tuni wanda za'a bata ya ce ya kammala gininsa dan haka ba za'a kai bad'in da suka ambata da farko ba. Lafiya lafiya yan uwan Alh Tanimu suka kawo komai na al'adar aure aka karba, cikin mutuntunta juna. Saboda Baban Marina ya gayyato yan'uwansu na Lame da Kano kan dole su Baban Tsakiya suka zauna aka karbi bak'i da su. Gidan Nuru da yake bayan gari k'arami mai kyau shigen na Yaya J. Irin murnar da nake ciki na barin gidanmu tamkar wacce na girma ba'a gaban uwa da uba ba. Domin na riga na kai makura wajen son na kauce na bar wa su Baban Tsakiya gidan su tabbata a cikinsa. Ubaida ce farkon wacce aka kai makaranta kwana a gidanmu. Idan mai karatun bai manta ba diyar Baban Marina ce itama diyar Inna ta biyu. Yau an yi hutun zangon karatu na biyu. Bulkachuwa ne ya taho da ita tunda shi kusan akai akai yake zuwa Bauchi. Tana GGC Bauchi ne ajinta uku, mutumiyar Ikilima ce haka suke tamkar ni da Nazira sai dai banbanci akwai tazara mai yawa tunda shekaru kusan uku ta bawa Iki. Amma amincin da yake tsakaninsu sai Allah. Saboda Ubaida, Iki ta nace boarding ita ma zata tafi, duk da dai ta fara day ajin ta d'aya a sakandire su d'in kamar karatunsu ba zai yi sauri irin namu ba. Tunda a yanzu haka har Dada ta fara maganar auren Ubaida, a dalilin tana da garin jiki, kuma tana shirin shiga shekaru sha biyar ne. Cikin farin-ciki muke hutunmu, na saje a tsakanin Ikilima da Ubaida tunda ni din ba ni da auki. Ba abin da yake damuna sai bibiya da nacin yaya J. Matu'kar kuma na yi saken da muka ha'du yini nake yi babu sukunin a dalilin fama da tsallen badake da zuciyata take yi. Da yake aurena ba kwatsam ya zo kamar na Nazira ba, Baba ya samu damar siyan dimemiyar katifa mai nagarta. Ya tanadi labulaye da kafet, da ledar tsakar daki da kuma bargo. Irin dai kayan da aka yiwa Nazira. Ya ce idan ya samu dama ko a ranar da za'a kai ni ne idan ku'din gado da kujeru sun samu sai a siya tunda gasu nan a bakin titi ko ina, idan kuma bai samu ba to a hakan zai kai ni arzikin gidan miji yafi na uba. Ban damu da rashin kayan katako ba, na sani in sha Allah yan'uwana zasu yi mini irin na Nazira. Sai dai bani da garanti akan manyanmu yan dakin Mama. Domin sun yi nisa a cikin *BAK'AR TA'ADAR* Y'an ubanci. Su Yaya Salisu ne kawai zasu tsaya mini tunda sun fara daukar albashi duk da dai ba mai wani nauyi ba ne amma dai sunfi da . Ranar asabar mun dawo daga Islamiya. Yammaci ne sosai muna tafe da yan ajinmu. Mun zo daidai wani gida da bai kammala ba, muka ga Bulkachuwa da wata yarinya wacce nafi zaton ita ce Bilkin da na ji yana fa'da a waya kwanaki, sun fito daga cikinsa. Gajeriya ce, amma fara ce sai dai ko kusa bata kai ni ba. Sannan ita din yar duma duma ce tamkar su Nasiba. Kirjinta a cike yake, jikinta irin rugu-rugu ne. Nan da nan shaidan ya kawo wa zuciyata caffa domin take sai na yi aiki da zato, na zarge su da al'amarin da shaidarsa yana da tsananin tsauri. Na kalli Nasiba na ga hankalinta na kansu, tausayinta ya kama ni, domin sai yanzu na gane ba son Nasiba yake yi ba, domin ko ka'dan bai yi mata uzziri irin wanda ya yiwa Bilki ba. Ko da yake maganganun da mahaifiyarta ta yi wa uwarsa ne suka yi masa ciwo ba ka'dan ba. A zuciyata na ce shi kuma Bulkachuwa yana son lukataye masu manyan nonuwa. Na sake kallonsu na gan shi kamar kullum ba wani wadatatcen wanka, yana cikin yanayin babu yabo babu fallasa. Amma ni kam duk saurayin da ya zo mini a haka ina da tabbacin ba zan saurare shi ba. Domin an sanya mini son namijin d'an wanka, haka nan na k'yamaci marar gyara irin Tijjani. Amma a hakan yake murza zuciyoyin yan mata kintsatssu da watsatssu. Na sani kuma kyaunsa da zubin k'arfin da yake da shi yake rudarsu. Gaba'daya a murde yake dukkan physiques dinsa sun bayyana alamun yana motsa jiki yadda ya kamata. Na ja tsaki muka wuce, yayin da ya yi kamar bai hango mu ba. Ba zato na ji Nasiba ta barke da kuka mai sauti. Wani har tsayar da mu ya yi yana tambayar ba'asin kukanta, domin dai ya dauka ta samu labarin rasuwar uwa ko ubanta ne. Kukan nan na Nasiba ya yi matu'kar dukan zuciyata, domin na san pain din da ake ji na kubuce war masoyi domim ni din katuwar victim ce. Muna tafe, tana kukan bata fasa ba, duk yadda nake bata ha'kuri da kalamai masu nutsar da zuciya. Kukan nata sai ya zama sanadin tabarbare war sassaucin da na yi akan al'amarin Bulkachuwa. Domin na dauke shi a mai son kansa, mai fifita bare akan jininsa. Sannan fitowar da suka yi daga kongon gidan da babu kowa a ciki ya sanya na sake k'yamarsa da dukkan zuciyata, domin kowa ya shaida shi din mai BAK'AR TA'ADAH ne. Da k'yar na shawo kanta ta yi shiru. Amma a k'asan raina haushin makauniyar soyayyar da take yi masa nake yi. Gaba'daya ta lalace, ta zube bata farin-ciki ko ka'dan da auren da za'a yi mata. Uwarta kuwa ta ja ta dake akan sai dai ta canja uwa matu'kar ta ce ba zata yi wa mahaifinta biyayya ta so d'an-uwanta da ya za'ba mata ba. Duk da k'arancin shekaruna na fahimci Tijjani ne kawai mahaifiyarta bata so, domin kuwa mahaifin su Nasiba bai cancanci ya yi irin wannan ikon ba, tunda gaba'daya fita ya yi daga hidimarsu, ba wanda ya taba ganin an kawo musu wani abu daga mahaifinsu, ko danginsa, duk wahalarsu uwarsu ce da danginta. Amma an zo batun aure ya nuna ikonsa na uba, ita kuma duk ba'kin cikin da ya k'unsa musu daga ita har Dada sun manta. Abin da nake tambayar kaina shine shi wanda Baba Maryon ta fifita akan dan yar'uwarta tana da tabbacin nagari ne? Ko dan kawai ma'aikacine, ya kuma gina gidansa? Na yi imani da ace Bulkachuwa yana da ku'di to ko yafi haka lalace wa za'a ba shi, duk wani na'kasunsa sai an yi masa kwaskwarima ya zama abin uzziri. Amma da yake bashi da ko sisi, sai take ta akilon y'arta ta nisan ce shi, ta so d'an-uwanta na dangin ubanta, na d'an yar'uwarta kuma ya tabbata a lalace. Muna isa gida Dada ta hau tambayar makusidin kukanta. Kai tsaye na shiga rattaba mata dalilin. Ta yi tsaki ta ce "Kare ya cinye miki zuciya Nasiba. Ina ce jiya a gabana ya tsaya yana miki kashedi akan ki sakar masa kurwarsa? Bakaken maganganun da ya cusa miki, ai masu cizo ne da kina da hankali. Domin bai ji kunyar idona ba ya ce miki komin k'wadayin ki shi yafi k'arfin ko dandana shi ki yi, bare kuma ki mallake shi a matsayin miji. Amma dan lalace wa har ki zauna kina kuka dan kin gan shi da wata? Bayan Allah ya baki mai son ki, nutsatssatse ba irinsa ba. Bayan hakan kuma mai abun hannune ta ko ina ya yiwa mai sunan manya fintikau. Ban da ma darajar jini me zai sa ki so shi haka? Ko an yi auren ma wahala zaki sha tunda ba sonki yake ba, ga kuma talauci da takaicinsa." Jikina ya sake mutuwa ina ayyana duk soyayyar da take tsakanin Dada da Bulkachuwa amma take iya fa'din hakan a kansa saboda Nasiba? To wai wa take so ke nan a tsakaninsu? Take na yanke hukuncin Nasiba take so. Na tsinci kaina da jin haushin yadda bai san ciwon kansa ba. Kullum a fa'din ya daina mugayen dabi'aunsa yake, ashe ba hakan ba ne. Ina tsaye tamkar gun ki aka fara kiraye kiraye sallar maghariba. Murya a dashe na ce "sai anjima Dada". Na tafi na barta tana ta kumfar baki da dan mulmulallen bakinta. Muna idar da sallar na kalli Gwaggo na hau rattaba mata bayani. Ina fa'din "Gwaggo ashe har yau Bulkachuwa yana yin iskanci? Dazun na gan shi da wata sun fito daga kongo". Ba zato na ji ta gwabe mini baki. Tare da cewa "A ina kika san iskancin? A ina kika ga yana iskancin? Kinsan girman al'amarin da kike fadi kuwa?. Dan sun fito daga kongo shike nan sai ki yi shaidar zurr? Annabi ya tsananta jan kunnenmu akan shaidar zurr. Kinsan matakan da sharia ta gindaya kafin a zartar da ce wa mutum ya yi zina? Sai an ga mutum turmi da tabarya, kuma daga bakin muminai da aka gasgatasu har guda hudu. Ba dan komai ba saboda kiyaye nasaba da mutunci. Amma mutanan yau sun manta wasiyyar ma'aiki a kan kazafi da shaidar zurr. Ki kiyayi yada sharri Yabi." Na kasa ce wa komai a dalilin ba k'aramin azaba na ji ba, domin da k'arfi ta bugi bakin nawa. Ta zarce da fa'din " Àllah ka shiryi duk wanda ya kauce hanya, Allah ka shirya zuri'ar al'ummar Annabinka. Allah ka shirya Tijjani, ka bashi sana'a, ka tsare shi, ka mayar da shi nagartacce". Na amsa ameen a zuciyata, ina alkalancin maganganun Dada da na Gwaggo akan Bulkachuwa. Shike nan sai na kame bakina ban yarda na sake fa'din wannan maganar ga wani ba. A hakan har aka shafe sati dai-dai lokacin saura sati biyu aurenmu. An kawo lefen Nasiba. Lefe kuwa mai kyau, komai sai son barka, domin komin kushen mai kushe na zai kushe kayan ba. Amma gare ta babu wata murna. Dan ko dazun nan sai da na ga tana wanke wa Bulkachuwa kayansa. Ba kuma sata ya yi ba. Ajiye wa ya yi a inda ake wankin ita kuma ta jika ta wanke tare da na Dada. Kwanaki biyu a tsakani aka kawo lefena. Sun yi kokari kwarai da gaske domin duk ha'duwar kayan Nasiba, nawa sun zarta nata da ka'dan. Amma abin mamaki ahalin gidanmu basu zuzuta kayana kamar yadda aka yi ta kuranta na Nasiba ba. A lokacin kuma Dada da y'ay'anta kullum sai sun zauna, Babanmu ne kawai ba'a sa shi a cikin zaman sai Baba ta Bulkachuwa ita kuwa ba a garin take ba. Saura kwanaki goma sha biyar auren Dada ta zaunar da Babanmu. Bamu san me ta ce masa ba, amma dai mun ga ya shiga cikin rashin sukuni har washagari. Ashe ce wa ta yi auren Yabi da Nuru ba zai yiwu ba matu'kar tana da iko akansa. Ya nemi sanin ba'asi ta ce ya saurare ta zuwa jibi. Bai sanar da kowa ba, har sai ranar da ta ambata. Dukkansu suna zaune a dakinta. Cikin rashin damuwar komai ta ce "Alhaji! Yanzu ya kyautu ace an bar mai sunan manya yana gararanbar neman aure ana hana shi, alhalin akwai yara a gabanku? Kullum da abin nake kwana, nake tashi, tare da zullumin kar'bar da zaka yiwa al'amarin. Sai kuma na tuna ikon da shari'a ta bawa uwa ". A sanyaye ya ce "Hakane". To maganar auren Yabi da wannan ba'kin yaron ba shirayayya ba ce daga Allah. Domin mai sunan manya za'a bawa ita." Wani irin zullumi ya shige shi. Murya a raunane ya ce "Dada ina ce Nasiba yake so?" Nan da nan ta ce "Nasiba ai ubanta ne ya yi iko a kanta ya ce dan k'aninsa zai bawa." Ya ce "Dada ina ro'kon arziki a ba shi wata cikin yaran Badamasi ko na Iliya tunda an riga an karbi komai na aurent a, akwai nauyi mai yawa a tsakaninmu da uban yaron nan ke ma shaida ce". Ta kai kallon ta ga Baban Tsakiya ta ga ya murtuke fuska. Nan da nan ta ce "Duk abin da yake tsakaninku da Tanimu ya kai da yar'uwar ka ne?" Da sauri ya ce "Ba kai ba Dada! Sai dai haramun ne neman aure a cikin aure." Baban kasuwa ya ce " Ai ba bisa son zuciya ba ne, biyayya ka yi, Allah kuma zai karrramaka tunda ka bi uwa. Idan ya so sai a bawa Nura Kaltume ba shike nan ba." Baban Marina ya kalli kaninsa da wani irin duba. Yana mamakin son zuciya irin tasa. Ya dauki y'arsa ya bawa Jabir yasan kuma saurayin Yabi ne. Yanzu kuma a kan idonsa yake fadin zai sake bawa Nura y'arsa tunda yasan akwai mamora a tare da yaron. A hankali ya ce "To ko zaka lamince na bawa Tijjani Kaltumen kawai?" Nan da nan ya ce "Ina! Ai ba ita Dada ta umarta ba, so ka ke na shiga fishin uwa?" "Shike nan Allah ya amsa addu'ar ka, Allah ya sanya albarka a cikin wannan ha'din , ya amintar da lamarin. Na bawa Tijjani Yabi, da dukkan zuciyata"! Baban Marina ya fa'da cikin wani irin yanayi mai ban tausayi. Dada ta ce "Allah ya yi albarka". Har ya yunkura zai tashi sai ya ce "Zan bawa shi Nuran kanwarta. Komai da suka kawo da sunan Yabi ya koma kan Ubaida". Ya fita yana ha'da hanya. A zaure suka yi kicibus da Bulkachuwa. Baban Marina ya kalle shi cikin wani irin yanayi. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Dubi gashin kanka, kamar ba bahaushe ba, ka dubi wando jikinka, tamkar babu iyayenka a gidan, yaushe zaka zama cikakken mai kamala ne?" Ya sunkuyar da kai ya ce "Za'a gyara Baba" Domin kuwa da dukkan zuciyarsa yake ganin kimar Baban Marina fiye da su Baban Tsakiya. A dakin Dada kuwa Baban Kasuwa ya dinga fa'din"Dada ai da kin ce a ba shi Kaltume kawai, ina ce ta fi Ubaidan a haife?" A dan tsorace ta ce "Ga ni na yi zan takura da yawa, sannan dole hankalin mutane zai dawo kanmu". Ba shakka ya ce "To ya dawo mana! Idan ka daka ta mutane ai ko sallah ba zaka yi ba, domin kana yi suna kallon ka, ba dan su gyara maka ba, sai dan su gano na'kasunka su yi zundenka Bare kuma akan wani al'amarin duniya da bai zame komai a juya maka manufarka kyakkawa zuwa mummuna ba." A sanyaye Dada ta ce "Hakane". Suka tashi ba tare da sun so a bawa Nura Ubaida ba. Washagari sassafe Baban Marina ya zaunar da matansa ya shaida musu juyin da aka sake yi, da kuma hukuncin da ya yanke akan yin madadi da Ubaida. Daga Inna har Gwaggo abin bai musu da'di ba. Mussaman Gwaggo da take gani ita ce zata fi shiga cikin tashin hankali, domin matu'kar Yabi bata samu dacen aure ba, to komai ma zai kwace mata ne. Ga Ummi ita ma fama take a nata gidan. Shike nan a hakan zasu kare ita da y'ay'anta?. Shirun da suka yi gaba'daya shi ya sake sanyaya masa guiwa. Ya ce "Kun yi mini zuru?" Mama cikin walwala ta ce "To me zasu ce Alhaji? Y'ay'anka ne fa ka yi iko da su, sannan ba shawara ka nema ba, tunda an riga da an zartar to wace ce zata yi inkarin hukuncin Dada matu'kar tana son ka rabauta?". Maganar Mama ita ta sanya wa Gwaggo k'warin guiwa domin ta sani so take ta ganta cikin rashin sukuni da tashin hankali. Nan da nan ta ha'diye damuwarta, ta murmusa tare da ce wa"Allah ya sanya alheri da albarka, ina fatan Allah ya sa ace gara da aka yi". Wata irin nutsuwa ta zo wa Baba domin dama uwar Yabi yake ji. Ya sani borin da Yabi zata yi ba zai yi tasiri ba tunda an yi sa'a ita din mai jin maganarsu ce mai kuma kishin kada su kunyata ne. Ya dinga yaba mata tare da sanya mata albarka. Ya juya ga amaryarsa Inna uwar Ubaida. Ya ce "Ke kuma fa?" Murya babu amo ta ce ", Allah ya sanya albarka". Ya sake numfasa wa tare da cewa"Yadda kuka kwantar mini da hankali a lokacin da aka jefa ni cikin matsanancin hali, ina rokon Ubangiji ya kewaye y'ay'anku da farin ciki da kwanciyar hankali a wannan aure. Allah ya sanya alheri mai yawa ya biyo baya. Allah ina rokon a azurtasu ta inda muka zata da ta inda bamu zata ba". Suka amsa da ameen cikin juriya. Amma Mama bata ce uffan ba. Ha'din kai da ya samu daga wajen matansa ya taimaka kwarai wajen kwantar da hankalinsa. Har dare muna namu yi, ban samu labarin komai ba. Sai dai na lura da rud'anin da Gwaggo take ciki, gaba'daya ta zama wata iri, ta yi zuruzuru. Na tambaye ta ta ce mini gudawa take yi. Take na gasgata na tura Anas ya siyo mata filagil. Da daddare bayan dare ya d'an fara tura wa Baba ya kiramu ni da Ubaida. Na cika da mamakin ha'damu da ya yi. Muna durkushe a gabansa, shi kuma yana kan kujerar ba'kin karfe irin ta da, da take dakinsa. Ya kalle ni ya ce "ku zauna sosai. Ina bu'katar hankalinku da nutsuwarku". "Muka nutsu kuwa, amma gaba'daya zuciyata ta shiga rud'ani sosai. "Shi da kansa ya jima bai iya yin maganar ba. Ya jima yana juya maganar yana tunanin ta yadda zai iya fa'dawa Yabi a karo na biyu za'a bawa wata saurayinta. Babban damuwarsa irin yadda ya ga ta sanya Nura a ranta. Ransa ya baci fiye da jiya. Ba'kin cikin y'anuwansa ya mamaye shi. Wai me ya tsare musu a wannan duniyar ne? Da k'yar ya yi k'arfin halin cewa "Yabi kinsan ce wa a duniya ba wanda zai so ki, ya so cigaban ki irin ni da gyatumarki ko?" Ba haufi na ce " "Eh Baba". Ya ce "Madallah! Sannan kuma ba wani abin kaico da zai dunfaro d'a mahaifi ya zuba ido ya cimmasa, sai idan abin ya gagare shi. Ina son ki fahimce ni, ki mini adalci, ki kuma ninka biyayyar da zaki mini a wannan karon.". Jikina ya fara tsuma, zuciyata ta shiga zullumi, idanuwa suka cika da ruwa. Na kasa bu'de baki na ce komai dan tsananin bugun da zuciyata take yi. Ya numfasa sosai ya ce "Ina son na fa'da miki auren ki da Nura ba zai yiwu ba, ba kuma na son ki kalli hakan a matsayin shirina ko shirin wani, ki yarda shirin Allah ne, shi kuwa idan Ubangiji ya jarrabe ka, ka yi ha'kuri a farkon al'amarin kana da lada da sakamako mai girma". Take ruwan da ya cika a gurbin idona ya tumbatsa ya fara zuba. Ina jin nauyin da zuciyata ta yi ba zai kwatantu ba. Wacce irin Bak'ar kaddara ce nake gudu take bina da gudu shigen na fanfalaki? Na kasa bu'de baki na ce uffan domin sai na fara hasashen mafarkin da nake yawan yi ne akan aurena da Nura zai iya ruguje wa. Jin shiruna ya sanya ya ce "Na sani kina sona, son da yake sanya ki son duk abin dana haifa, ko nake so. Ina ro'ko ki taimake ni, na yiwa mahaifiyata biyayya, ni kuma zan dauwama ina miki addu'ar wanye wa lafiya da kuma rufin asirin duniya." Cikin rishin kuka na ce "To Babanmu". Ganin irin rudin data shiga sai wata dabara ta zo masa. Sai ya ce "Babanku Iliya ya bu'kaci na bawa Nura Kaltume a madadinki". Na d'ago a matu'kar birkice na ce "Wai me na yi muku ne Baba? Yan'uwanka suna azabtar da ni, kai kuma ka zuba ido kana kallo, ka kasa kare mini darajata! Ko dai da gaske karayar arzikinka tana damfare da zuwana duniyar nan mai cike da ba'kin ciki mai tsanani?" Na fa'da ina kuka sosai. *Auzubillahi! Na yafe miki Yabi! Na sani kina cikin ki'dima ne, ni kaina da na haife ki kiris ya rage ban zautu ba a dalilin wannan al'amarin. Allah ka sassauta, Allah ka kawo mafita. Allah kada ka jarribi Yabi da jarrabawar da zata bijire mini. Bare ta haifi wanda zai bijire mata." Na yi kasa da kaina ina kuka kasa kasa. *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. Tsawon lokaci kafin na ce "Na ha'kura da shi Baba. Amma Wallahi indai aka ba shi Kaltume to zan roki Ubangiji ya matso mini da ajalina kusa, domin na sani bazan sake farin ciki ba. Indai kunyar Babansa kake ji, to ka bashi Ubaida tunda dama saboda kai ya turo d'ansa ya neme ni, ka bashi ita, zai fi mini sauki a maimakon ka rasa suruki nagari irinsa". Ina rufe baki kawai Babanmu ya fara hawayen da ya daskarar damu. Wanda na tabbatar na zallar ba'kin ciki da kuma farin cikin yadda nake tsananin son y'anuwana. Ai ko murya na rawa ya ce "Irin yadda kike son yan'uwanki haka nake son nawa, amma shaidan da son zuciya sun shiga cikin al'amarinmu sun yi kane kane." Ya daga kai ya ce "Allah kada ka jarrabi ya'yana da rugujewar zumunta". Jikinmu ya sake yin mugun sanyi ya ce "Ubaida kin ji me yayarki ta ce shin zaki bi bayanta wajen sadaukar da burinki, ki mini biyayyar da ke ma zan dauwama ina yi miki farar addu'a?" A sanyaye ta ce "Zan yi Baba! Na amince, da ikon Ubangiji ba zan kunyataku ba, komai zan zama kuma a duniya a sanadin auren nan, na sani arzikin Adda Yabi na ci, ba kuma zan juya wa al'amarinta baya ba". Zan yi zumunci da ita a cikin ko wanne hali da rayuwa zata wullamu". Daga hakan kuma ta fashe da kuka sosai. Wanda ita kanta bata san dalilinsa ba, amma dai tana jin na tausayin Yabi ne. Da ya rasa yadda zai fadi Tijjani ne mijin da aka zaba mata sai ya ce "Yabi ki tsananta addu'ar shiriya ga Tijjani! Ki kuma rage tsananta al'amarinsa ta yadda zaki fahimce shi da kyau, Annabi ya ce "Addu'ar miji akan matarsa karbabbiya ce, haka addu'ar mata akan mijinta karbabbiya ce. Dan haka ki tsananta yi masa addu'ar shiriya, da kuma a cika kirjjnsa da soyayyar ki da tausayin ki, sannan a buda masa kofofin arziki" A ki'dime na ce "Baba dan Allah warware mini wannan curarren bayanin, d'an yi mini gwari gwari". Da matu'kar rauni ya ce "Tijjani zan aura wa ke". Ai kuwa na dage na zunduma ihu ina birgima, ina fa'din "Wayyo Allah mutuwar tsaye ta samu Yabi! Wayyo Allah nakasa ta zo mini. Yabi zata zama iyalin mai *BAK'AR TA'ADAH* *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin *Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*. *08032773332* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *08089965176* *07084653262* *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* Ina alwallah ina kuka. Ba abin da ya sake karya mini zuciya irin yadda na jiyo Baban Marina yana cewa Baba "Ni fa ki daina ro'ko na Hauwa! Tuni na yafe mata, amma walwalata ce ba zata ga ni ba, har sai ta kwantar da hankalinta an yi hidimar nan lafiya lafiya. Sannan kuma ta zauna lafiya da mijinta kamar yadda y'anuwanta suke zaune lafiya. Ina ce Ummi gidan mai iyali aka kai ta? Ga kuma mijin ya d'orawa ransa masifar son abin duniya. Ba ya sauke hakkin da shari'a ta wajabta masa. Duk k'uncin da take ciki yau shekaru kusan takwas da aurenta, bata ta'ba zuwa gabana da nufin wata matsala ko da zummar na taimake ta ba. Na sani kuma tana bu'katar a taimake ta, amma da yake ta dauko ha'kurin uwarsu ta shanye komai tana zaune da y'ay'anta, sai kuma ta yi tabarar koyon sana'a cikin cire girman kai da buri. Shiyasa ni kuma ban ta'ba yin sallah ban roka mata sassauci a wajen Ubangiji ba. Duk kuma wanda Allah ya ba shi nisan kwana zai ga yadda Allah zai albarka ci zuri'arta. Allah sai ya yi mata tukuicin hakuri da biyayyar da ta yi da ikon Allah". Da k'yar na tokara na tashi zuwa daki na tarar da Gwaggo tana share hawaye. A sanyaye na ce "Gwaggo baki huce da ni ba ne?" Ta girgiza kai sai kuma ta ce "Ina mamakin duk alherin da mace zata yiwa namiji na ha'kuri da juriya akan al'amarinsa ko na ahalinsa. Amma idan d'anta ya yi laifin da ita kanta bata sani ba sai ya shafeta. Ko sai yaushe uwa zata kubuta daga irin wannan kalubalen a k'asar hausa? Duk lalacewar uwa ba zata so d'anta ya zama marar tarbiya ba. Na sani akwai uwayen da basa son laifin ya'yansu, amma me yasa aka fi yiwa masu hakuri da kawaici raddi? Yanzu duk laifinki a kaina ya k'are. Yana wahalar gaske Babanku ya yaba ha'kurin da nake yi a gabana sai dai a bayan idona. Shikenan ita mace ba za'a yabe ta a kurzanta ta ba? Ba za'a yayata alherinta ba, amma kuskuren da ba ita ta yi shi ba ma sai an yi mata tuya a kai". Ta fa'da hawaye na sake k'wace mata. Na taya ta kukan da take yi domin na sani sanadin tafiyar da na yi ne. Da rawar murya na ce "Ki k'ara hakuri Gwaggo! Idan kika yi sa'a Ubangiji ya yabi ha'kurinki shikenan kin gama dace wa." Ta zuba mini ido sosai ta ce "Kema na hore ki, ki yi hakuri, ki yi juriya, ko bana raye shine tsanin da zaki ri'ke, ki tsallake dukkan k'alubale a wannan duniyar". Jikina ya sake sanyi. Domin kalmar ko bata raye ta yi matu'kar dukana. Na ha'diye kukan na tayar da sallah. Sai dai hawaye bai yanke mini ba, na idar da sallar ina zaune ina lazimin Ya ladifu da fatan na samu sau'kin halin da nake ciki. Washagari sassafe Babah ta koma Bulkachuwa. Ala dole na ha'kura na zuba ido aka cigaba da shirin aure, wanda yake sake k'arantowa. Duk da na ha'kura amma wata irin rama nake yi mai tayar da hakankalin masu kallona. Na sake zama wata yar sumoli da ni. Ba annuri a fuskata. Na kasa yiwa jama'a kitso bare kuma lalle. Idan ba k'ure wa ta yi ba yana wahalar gaske na yi magana. Na zama very silent. Makarantar boko ma na daina zuwa duk da a shekarar k'arshe muke. Kwatsam sai ga Yaya J ya dawo daga Bauchi. Bai samu labarin aurena da Bulkachuwa ba sai a jiya. A ki'dime ya iso gidan Marina. Ya gurfana gabana Dada yana fa'din "Dada wanne irin abu ne haka? Ta ya ya za'a dauki Yabi a bawa Bulkachuwa! Saboda Allah Dada wannan daidai ne? Me yasa aka hana shi Nasiba baki tsawatar ba? Me yasa aka tirsasa ni na auri Maijidda? Akan me ita kuma za'a yi mata hakan? Ciwon abin ba shi ya yana sonta ba. Idan saboda kada na sameta ne kuka k'ulla wannan al'amarin, na sadaukar da soyayyar da nake yi mata, na janye, bazan sake furta sonta, ko a bani aurenta ba. Amma ki yiwa Àllah Dada kada ki kassara mata rayuwarta. Waye bai san BAK'AK'EN TA'ADODIN da yake yi ba? Ta ko ina basu dace da juna ba. Yabi mai son sana'a ce, yayin da Tijjani bai damu da ya gina kansa ba, irin mazan da suke barwa mace hidimar da shari'a bata dora musu ba ne. Tijjani manemin mata ne, yayin da Yabi ta kasance mai tsananin kishin gaske. Tijjani fari ne, Yabi bak'i take so. Tijjani mai zafi ne. Yabi mai tsiwa ce. Ta ina zasu ji da'din zama? Ta ina suka dace?" Kafin Dada ta ce wani abu Bulkachuwa da yake tsaye a bakin k'ofar Dada ya ce "Bamu dace da juna ba Jabir. Sai dai ka sani Ubangiji ne yake jujjuya al'amura, yake kuma k'addara afkuwar komai ko da bamu tsara faruwarsa ba. Maganganunka sun yi matu'kar ta'ba zuciyata. Tabbas gaskiya ka fa'da, duk da na ji na muzanta. Da a ce son Yabi bai yi mini kamun kazar kuku ba. Dana tirje wa aurenta. Sai dai an jarrabe ni akan ta cikin kankanin lokaci." Ya numfasa ya sake fa'din " Na gode da ka ankarar da ni, duk inda sana'ar da zan gina kaina take zan nemota zan kuma yi duk wahalar ta. Laifin da ka jingina mini kuma na neman mata wannan kai da Allah! Domin baka ta'ba ganina na yi ba. Allah ne shaidar na yi tuba, Allah ne shaidar tunda na yarda aka zartar da hukuncin da ya yi a kaina ban sake yi ba. Amma kun rike abu kuna ta faman jifana da shi." *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. Ya fa'da cikin wani irin yanayi na bacin rai mai tsananin gaske. Dada ta zuba masa ido cikin son ta nazarce shi. Ta k'asa ha'diye abin da ta fahimta akan sa cikin dak'ik'a. Ta nisa ta ce "Mai sunan manya, shin ka fa'da komar Yabi ne har haka?" Takaicin ta ya k'ume shi. Bata ce da Jabir komai ba, da yake faman sakin maganganun da suke nufin tozarci a gare shi. Amma tana neman shiriritar da maganar. Bai ce mata k'ala ba ya juya tamkar ya tafi, sai kuma ya toge a jikin bishiyar zogalen da take gefen dakunan ka'dan. Cikin bacin rai na sosai. Yayin da jikin Jabir ya yi sanyi domin ya fahimci ba k'aramin son Yabi Tijjani ya afka ba. Sannan ya ji kunyar maganganun da ya ji yana yi a kansa. Dada ta kalli Jabiru ta ce "gara ma da baka auri Yabi ba Jabir. Na fahimci irinsu ne matan jaraba. A kansu ba abin da namiji ba zai yi ba. Mafi yawa haka zaka gansu yan firit amma suna murza mazaje ingarmai. Yadda kake sanyi k'alau din nan ba zaka sarrafa ta ba. Ko mai sunan manyan da yake a tsaye, tun komai bai gitta a tsakaninsu ba, ga shi nan yanayinsa ya nuna ta riga da ta shiga ransa ta yi kane kane". Cikin jin nauyin maganarta Jabir ya ce "wacce irin magana ce haka Dada da girman ki?" Ta nisa ta ce "Gaskiya ne mana! Kawai murnar da nake yi masa d'aya ce. Ta iya sana'ar samun ku'di, dolenta ta fito da ku'di su ci abinci. Idan ku'din da suke saka ta yiwa iyayenta raini basa zama mata ai ta nutsu ta girmama manya". Tana rufe baki Jabir ya ce "Haka su Baban suka fa'da miki shiyasa kika tirsasa aka yi wannan bahagon hadin?" Ta yi dan tari kafin ta ce "Gaskiyarsu ne ai! Sannan shi mai sunan manya tunda ba shi da sana'a asirinsa zai rufu". Jabir ya ce "Gaskiya kun kassara rayuwarta, amma akwai Allah. Ina fatan alheri ya biyo baya, sai dai har yau din nan ban hakura ba. Na sani *Hannu daya* baya daukar jinga. Bazan ha'kura da ita ba har sai na ga ranar da aka shafa fatiharta da wanina. Daga ranar na zubar da makaman nemanta. Amma matu'kar ban mutu ba idan an kaddara mini cikar burina zai zama gaskiya. Idan da rabona zata dawo mini, ni kuwa zan aureta komin tsufanta, domin ita nake so ba wani abu a tare da ita ba". Dada ta kyabe baki ta ce "Idan k'asa ta rufe mini ido komai ma sai ku yi tunda ban ga ni ba". Tijjani da yake jinsu zuciyarsa ta dinga bugawa da k'arfin da ya zarce ka'ida. Yana son ya je ya fa'da wa Dada duk lalacewarsa bata kai mace ta ciyar da shi ba, bai yi mutuwar zuciyar da macen aurensa zata dauki nauyin kanta da nasa ba. Sannan ta fahimtar da y'ay'anta hakan. Amma sai ya daure ya ha'diye. Ya ja jikinsa ya fa'da dakinsa ya fa'da kan katifarsa. Wani irin yanayi na shigar sa na tsananin bacin rai da ya sababa masa k'arfin zuciya. Domin gaba'daya ji ya yi hatta dako na daukar buhun gero da na su wake zai iya yi, dan ya ciyar da Yabi da guminsa ba wai ta ciyar da su ba. Idonsa ya ciko da hawayen tausayinta domin ya gane k'iyayyar da ake yi mata ne ya sanya aka bashi aurenta. Ya yi shiru yana nazari wato saboda ana ganin shi din lalatacce ne. Ana ganin shi ba zai amfana wa kansa komai ba, bare ita ta amfana da shi. Ana kuma fatan ya dauwama cikin lalace wa da mutuwar zuciya. Sai ya tsinci kansa da tambayar shi da Yabi wa aka fi tsana ne a gidan Marina?" Take ya muskuta ya janyo wani kwali. *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* *Lame fa garin su Yabi ne* Ya dauko memo da biro, ya yi rubutun magananun Jabir, da wanda su Baban Tsakiya suka yi da ya ji a harshen Dada. Da irin manufar ba shi Yabi. Da yadda ake fatan ta tabbata cikin halin ni 'ya su. Sai kuma ya je shafi na gaba sosai ya rubuta "Zan yi komai na halal dan na sauke nauyin da yake kaina.! Allah ka sani ban sake aikata zina ba! Allah ka taimake ni ka cigaba da tsare ni. Allah ka fahimtar da ni sarrafa mace ta yadda Yabi zata rayu cikin farin-ciki a hannuna. Allah ka hore mini kofofin arziki ta yadda zan sauke nauyinta ba tare da tallafinta ba. Na sani al'kawarin ka baya tashi, da kanka ka yi al'kawarin taimakon wanda ya k'udire niyyar aure saboda kai. Ga ni bawanka, Ibnu bawanka cikin kankan da kai, ka taimake ni, ka kubutar da ni kunyata a idonta da na dangimu. Allah ka hore mini lafiya, ka sanya mini hakuri akan sha'anin ta, sannan a mallaka mini zuciyarta da tunaninta." Sannan ya rubuta kwanan wata. Ya rufe yana jin girman k'alubalen da yake gabansa. Wani irin son ta da tausayinta yana sake bin dukkan jikinsa yana kutsawa. Har yake jin anya akwai wanda ya so mace kamar yadda yake jin son Yabi ya sake shak'e shi a yanzu? Domin shi son ta yake yi babu wani dalili na sha'awa ko na burge wa. Na farko yafi son manyan mata masu manyan halittu. Yabi kuma yar mitsil mai k'ananun halittu, maimakon ya ga ba hakan yake so ta zo ba. Sai yake jin ko bata da komai na cikar mace yana sonta a hakan. Na biyu yafi son mace mai sanyin hali, mai kawaici. Amma daga ranar da aka jefa masa sonta shikenan ya ji da tsiwarta zai yi amfani wajen kutsawa dan ya sami kusanci a zuciyarta. Ya sani ba zai yarda da rashin kunyar da ta wuce ka'ida ba. Amma yana fatan a cikin rashin kunyarta ya dinga isar mata da sakwanni masu girma. Na uku akan abin da aka yi mata na tirsasa Jabir auren Maijidda, da kuma yadda uwar Nasiba ta ture komai na zumunci ta fadi maganganu marasa dad'i a gaban mahaifiyarsa! Shike nan ya k'yamaci auren zumunci. Amma a yanzu yadda yake jin Yabi zai iya yin komai dan ya same ta. Ya gamsu tausayi da sonta sun masa rubdugu. Ya rufe littafin ya mayar da shi ma'adaninsa. Ya jima a zaune yana ta tunanin sana'ar da zai fara. Ya saki gauron numfashi! A fili kuma sai ya ce "Allah ka hana Tijjani sanya Yabi kuka! Allah ka hana ni zaluntar ta. A hore mini ita ya Ubangiji". Ya zabura ya mik'e yana ganin lokaci ya yi da zai daina buga buga ya samu tartibiyar sana'ar da zai dogara da ita tunda nauyi mai yawa ne zai hau kansa, wata'kila ma badi war hakan yana shirin zama Abba. Murmushi da kunya suka subuce masa ya dinga sosa k'eyarsa tamkar yana gaban manya ne. A fili ya furta wa ya ga "Yabi as uwa?" Sai dariya ta sosai ta kama shi, har bacin ran da Jabir da Dada suka cusa masa ya yi sauki. Ya fito ya nufi wajen Alh Tsoho magini dan ya ji ko zai masa hanyar samun aikin ginin. Yana tafe sanye da yadi na wando da riga bata kai guiwar sa ba. Kamar kullum a wanke suke amma fa babu guga. Sannan ya saka hular sanyi ya rufe gashin kansa. Domin tunda aka furta za'a bashi auren Yabi. Bai sake yarda an ganshi da gashin kansa ba, duk da ya ki aske wa. Ba wanda yake jin kunyar ya ganshi da sumar irin Baban Marina. Domin ya sani baya so, ya sha tisa shi a gaba ya saka a masa askin akan dole. A yanzu kuwa wata irin kunyarsa yake ji ta sosai domin bayan kawunsa ne da yake yi masa adalci, yanzu shirin zama surukinsa yake yi. Bulkachuwa da kansa ya yi amannar ba dan zuciyar Baban Marina irin ta daddako ba ce da ba za'a yi masa wannan k'arfin akan diyarsa ba. Ba dan alherinsa mai yawa ba ne, da ba zai ba shi aure ba, komai za'a yi kuwa. Amma ya yi shahadar ba shi, babu dogon turanci. Yana tafe yana fa'din "Allah ka fitar da Tijjani kunyar Baban Marina". Ya sha kwanar shiga cikin wani kwararo sai kawai ya fara jin k'amshin turaren da yake ji a jikin Yabi da kuma wanda yake shaka a jikin Jabir. Ya shiga sai kuwa ya hangosu kowannensu jingine a garu. Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi. Kishi mai tsananin gaske ya dabaibaye shi. Tamkar ya juya sai kuma ya tsinci kansa da tunkararsu. Ya zuba musu ido. Yabi na kuka sosai yayin da Jabir idonsa ya kad'a ainun. Sau d'aya za'a kallesu a gane suna cikin tsananin soyayya da kuma halin cankacakare. Ya kalli Jabir da yake tsab da shi cikin shadda ruwan toka ta sha guga. Farin gilass ya mak'ala. Ga k'amshi mai da'di na tashi a jikinsa domin komin hassada baka isa ka ga wani abu na rashin tsabta ko gayu a tare da Jabir ba. Yayin da Yabi take sanye da hijabanta har k'asa sai dai duk ya b'aci da hawaye har da ba'kin kwalli. Kishi sosai ya turnike Bulkachuwa. Har ji ya yi zukar numfashi na neman yi masa turjiya. Amma a hakan ya motsa k'wanjinsa ta hanyar cewa "Jabir na tabbatar babu jahilci a tare da kai tunda ka yi zurfi a ilimummuka daban daban. Sai dai abin mamaki sanin naka bai amfana maka komai ba, tunda zaka iya tsayawa da wacce kwanaki kadan ya rage a daura mata aure a cikin lungu inda babu sawu. Ni ba zan yi maka rashin adalci na yi maka kazafi irin yadda ka yi mini ba. Sai dai na sha fa'da kai din azzalumi ne, ba masoyi ba. Ta ya ya an baka aure ka karba, dan kwadayin albarkar iyaye ita kuma ka dinga hure mata kunne da ga yiwa nata tsohon biyayya? Ban da ita din sakara ce har wanne kalami ne a bakinka da zaka tsara mata da yafi na ubanta da kannensa tasiri?". Jabir ya sandare ya zuba wa Bulkachuwa ido, yana jin wata irin fargaba from no where tana shigarsa. Yayin da ni kuma na dago ido jage jage da hawaye na watsa masa kallon kiyayya da raini na ce "Ba ruwan ka da ni Tijjani! Na saurare shi din, domin shi nake so, nake fatan kasance wa da shi". Ga mamakina sai kawai ya ja kakkuran tsaki tare da ce wa "Ai ke din shasha ce! Kuma kin ji na saka maganata da ke? Da shi na ke wanda na gamsu da hankalinsa da iliminsa, kawai adalcinsa ne bai gamshe ni ba. Amma ke da baki da hankali ina ruwana da ke? Jiyan nan na gan shi da matarsa a asibiti yana ri'ke da ita. Yana faman tattalinta. Wai matar da ya aure ta ba dan yana so ba yake yiwa irin wannan son da adalcin, amma ke kullum yana cikin dama miki lissafi. Da yake ya mayar da ke shargalle marar tunani." Ai kuwa yana rufe baki kuka ya k'wace mini sosai. Jabir ya kasa magana domin ya tabbatar Bulkachuwa ya gansu a asibiti ba k'arya ya yi masa ba. Bulkachuwa ya sake yin k'uta tare da nuna Jabir da yatsa ya ce "Neman aure cikin aure haram ne in ji ma'aiki (S.A.W). Da ku'din aurena akan ta, ko ba zaka yi mini kawaici irin na zumunci ba, to ka yiwa ka'idojin shari'a biyayya. Ka fita mini a harkar Asiya! Ubangiji ya baka Maijidda wacce ita ce mafi alheri a gare ka. Amma bar mini Asiya Toro domin ina da yakinin akwai babban al'amari a tsakanina da ita. Daga ranar da aka tabbatar mini an ba ni ita, na fara addu'ar na yi nisan kwana mai yawa dan na tabbatar ni kad'ai na mallake ta". Still Jabir ya kasa magana domin gaba'daya almarin ba k'aramin bugunsa yake yi ba. Kishin Bulkachuwa ya shak'e shi k'warai da gaske. Domin idan gaskiya zai fa'da ya ga son Yabi a idonsa irin wanda bai yi zaton Tijjani zai yi mata ba. Mussaman yadda bai dauki soyayya da muhimmanci ba. Mace tana bata masa rai zai juya mata baya duk yarda yake da ita kuwa. Ina kuka, ina kallon Yaya J. Na sani dan na yi ba'kin ciki ya sanya Bulkachuwa sako maganar Maijidda. Ban da haka mene ne dan ya nuna kulawa akan matarsa ta aure? Nan da nan zuciyata ta hassala cikin rawar murya na ce "Mene ne dan ya kula da lafiyar Iyalinsa? Tabbacin nima zai kula da ni ke nan tunda har ya yiwa wacce baya so adalci to ina kuma a ce ni ce da yake so? Kai sau nawa ana ganinka da tambadaddun matan banza?" Take jikin Yaya J ya yi k'wari domin yasan yadda nake da kishi na gaske, maganar Bulkachuwa na iya tunzura ni na yi masa fishi. Dan haka ya dan murmusa. Sannan ya ce "Ko yanzu na mutu a sanadin rashinki ba ni da kaico tunda kin mini kyakkawar shaida Yabin J". Da rawar murya na ce "Idan ka mutu, kuma ka bar ni da wa? Wanne irin ba'kin fata ne, akan me zaka mini fatan irin wannan asarar haka?" Tijjani ya harzuka ya ce "Ba zaka mutu ba ka ga yadda Asiya Toro zata manta da al'amarinka ba Jabiru. Ya sake sakin tsaki sannan ya ce "Idan kuwa har ka mutu ba wanda ya yi asara irin abin da yake cikin Maijidda, sai kuwa ita Maijiddan, da zata shiga takabar mijin da yake sonta yake gudun bacin ranta". Na sake fasa kuka ina fa'din "Allah ga Tijjani nan ya takura ni, ya fitine ni haka siddan, ka sani bana sonsa, ka gaggauta cire mini shi a duniya ta". Sai lokacin Yaya J ya ce "Yi hakuri kin ji Yabi! Ko zan mutu ba yanzu ba, da saura In sha Allah". Na wuce na fara tafiya a hankali. Bulkachuwa ya ja tsaki ya ce "k'aryar banza! Dan Allah ka mutu yanzu Jabir. Da an ga tsiya domin kuwa ana dawowa daga rufe ka zan lallaba na koma. Tamkar wanda zan yi maka addu'a. Nan kuwa fitsari zan tsula maka a kabarinka ta yadda sai ka shekara a kwance kafin addu'ar jama'a ta riskeka, mussaman ta Asiya Toro. Kai da addu'a ta riske ka sai damina ta zo. Idan na so k'eta ma, daminar na dauke wa na sake tsula maka wani. Kuma idan juninka tsiya ne Maijidda na haihuwa zan aure ta. Na ha'da su da Asiya Toro su yi ta faman buga competition a kaina". Na juya da nufin na yi masa raddi ya nuna mini yatsa ya ce "Idan kika kuma tozarta ni sai na fasa miki bakin ki domin ban yi da ke ba, marar kishin kai". Jabir ya yi hanzarin ce wa "Kar ki ce komai Yabi cikin yanayi na kad'uwa sosai. Ya kalli Bulkachuwa ya ce "Har zaka iya yi mini fitsari a kabarina Bulkachuwa? Sannan ka ce "zaka auri matata akan idona?" Wani irin murmushi Bulkachuwa ya yi mai dauke da nisha'di da ma'anoni. Ya ce "In dai son Asiya ya zama ajalinka zan tabbatar na hana adduarta riskar ka. Sannan dan na auri Maijidda ai rufa maka asiri na yi tunda tare da abin da ta haifa zan ha'da na rikesu. Idan kuwa kana kishinta kamar yadda yanayinka ya nuna har ka kasa ha'diye hakan a gaban wacce kake kirarin kana so. To kawai ka k'yale mini Asiyata.." *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman* *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. *Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*. *08032773332* ✍️ *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. "Shikenan idan ka yi haka ba zan maka fitsari idan ka riga ni mutuwa ba. Ba kuma zan aurar maka bebinka ba, tunda wani irin so kake yi mata wanda baka iya b'oye kishinta a gaban kowa" Ba'kin ciki mai tsanani ya lullub'e ni. Na kasa bu'de baki na ce komai domin na tabbatar yana iya fasa mini baki kamar yadda ya fa'da din tunda baya fa'dar magana da zummar wak'e. Na juya na tafi, ina tafe ina hawaye, ina kuma ha'da hanya. Domin idan akwai abin da yake ci mini zuciya bai wuce a mini zancen Maijidda ba. Na kuma fahimci Bulkachuwa yana son bani labarin irin tarairayar da J yake yi mata. Na tuna tun kafin zancen aurena da shi ya b'ullo, ya sha fa'da mini yana ganin Yaya J goye da Maijidda a mashin dinsa. Har na isa gida kukan sharbe nake yi. Na shiga dakinmu na zauna bakin gado ina kuka sosai. Domin abin ya ha'de mini, ga bacin ran auren dole da mutumin dana tsana ga kishin Maijidda da yake azalzalata tamkar zuciyata ta fa'do kasa. Gwaggo ta kalle ni ta yi k'wafa tare da fa'din "ki yi ta kuka har hawayen idonki su k'afe, aure kuwa kinsan babu fashi". Ta fice ta bar ni. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* *Dada* Bulkachuwa zaune a kusa da ita kan baranda sai faman bacin rai ya ke yi. A hankali ta ce "To menene zaka tisa ni a gaba kana ta faman k'unci kaki fa'da mini damuwar ka?" A hankali ya ce "Jabir ne mana ba dama Yabi ta fita sai yasan yadda ya yi ya tare ta. Gaskiya abin ya fara tayar mini da hankali, ki fa'da masa ya bari". "A sanyaye ta ce "zan fa'da masa kaima ka kara hakuri duka kwana nawa ya rage ne? Ai da zarar am shafa mata fatiharka dole kuma su kiyayi juna." Bai kai ga amsa mata ba, ya ga masu aikin gini da fenti sun shigo da kayan aiki sun shige k'ofar ciki". Ya kalli Dada ya ce "me suke yi a ciki ne?" Da walwala ta ce "Tun dazu suke fama, sallah suka je yi. Kawunanka suka saka a gyara maka wajen sun ce bai kyautu su barka da neman muhalli ba". Ransa ya baci ya ce "Shi Baban Tsakiya ne zai ce haka? Me yasa bai mini gini irin na Jabir ba? Idan kuwa Baban Kasuwa ne me yasa ya hana Salisu zama a lokacin da ya roki a bashi ya zauna kafin ya samu sararin yin nasa?" To bana so, na sani kuma Yabi ba zata so wajen ba, ya yi tsufa da yawa". Daga haka ya tashi ya barta tana faman buga salati tare da fa'din "Ni Binta ina kallon wuyar zama irin ta y'ay'an yau. Komai aka yi musu babu mutunci bare su yi godiya. Wannan zamani da wuyar sha'ani yake". Ta yi k'wafa sannan ta sake cewa "Allah na yi tuba, kai ne mamallakin zamani. Allah ka shirya". Har washagari bani da sukuni, a kuma wannan ranar aka kawo mini lefe daga Bulkachuwa. Sosai aka zuba kaya a lefen tamkar na masu wadata. Na sani kuma y'anuwan ubansa da Babah ta Bulkachuwa suka hada kayan, sisinsa bai yi ciwon kai ba. Maza ne suka kawo kayan dan haka ba ayi gayya ba. A k'ofar Dada aka taru aka ga ni, masu fatan alheri na yi, masu shagube na yi. Sai da ya kwana ya yini a wajen Dada sannan ta saka aka kawo kofarmu. Hatta Babanmu sai da Inna ta bu'de masa kayan ya ga ni, ya yi addu'ar alheri tare da fa'din "Oh haka suka yi wahala mai yawa?" Ni kuwa ko kallon kayan ban yi ba, bare na ga mene ne a ciki. Da yamma ina zaune ina k'ulla wa Gwaggo siga. Sai ga Anas ya shigo ya kalle ni ya ce "Dada ta ce ki je yanzu". Na bata rai na kasa amsawa domin na tsani na je kofarta saboda dalilai masu dama. Na farko haushinta nake ji. Sannan bana son ganin mawuyacin halin da nake ganin Nasiba a ciki. Domin sosai ta mak'ala wa zuciyarta son Bulkachuwa. Kishina sai ya galgalata yake yi, duk da bata bu'de baki ta mini maganar ba, sai ma murnar da ta yi mini na samun miji irinsa wacce na ji tamkar ta caka mini wuk'a ne. Wannan shine daidan wani, karkataccen wani. Sannan kuma ina sake k'in shiga wajen Dada ne saboda kada na ga Tijjani. Shi yasa ma bana zuwa gaishe ta sai hantsi ya yi sosai. Gwaggo ta ce "Je ka ce tana zuwa". Ya ce "To" ya tafi. Akan dole na dauki mayafi na nufi shashin Dada. Ina hasashen menene dalilin kiran? A zauren Dada na tarar da shi a tsaye. Zuciyata ta tsinke sosai. Na yi kamar ban gan shi ba. Na wuce da nufin shiga cikin gidan. Ya bu'de baki ya ce "Ni ne mai kiran na ki ai". Na tsaya cak. Ba tare da na iya ce wa kanzil ba. Ya saki gauron numfashi kafin ya ce "Ga ni na yi abu ya matso kusa sosai amma babu fahimta a tsakaninmu bare nasan abubuwan da kike bu'kata". Na ja tsaki na ce "auren so ake yiwa irin wannan tagomashin". Fuskarsa ta yamutse kadan. Ya ce "To na biyayya fa?" Nan da nan idona ya ciko da hawayen takaici. Na yi k'asa da kaina na kasa ce wa komai. Murya babu amo ya ce "Abokina da muka yi karatu a Gad'au gobe zai zo. Ya dame ni akan na ba shi lambar amarya ko na kawarta dan ya ji irin yadda ake sallamar amarya da kwayenta a nan, da kuma abubuwan da kike bu'kata". Na ja tsaki tare da ce wa "Komai zai fito ta hannun ka ko ta sanadin ka bana sonsa ba kuma zan kalle shi ba." Ya zuba mini ido sosai cikin damuwa mai yawa. Cikin wani irin yanayi ya ce "Asiya Toro alfarma d'aya nake so ki mini, ko da kuwa ita ka'dai ce alherin da zaki yi mini. Ki taimake ni kada ki tsinka ni, ki yi mini wannan arzikin dan Allah". Ban san ya aka yi ba, jikina ya yi sanyi, mussaman yadda na ga ya yi kalar tausayi tamkar ba Bulkachuwa ba. Na yi shiru amma fuskata a cukune sosai. Ya sake ce wa "ki bani lambar wacce zai yi magana da ita Asiya. Sannan idan sun zo mini ranar daurin aure kada ki wula'kanta ni a gabansu. Na yarda bayan sun tafi ko menene ki yi mini, zan jure". Na sake gallah masa harara tamkar idona zasu fa'do k'asa. Tare da ce wa ban iya Yaudara ba, ba kuma zan fara yanzu ba. Ai na sha jin kana fa'dawa abokan naka ba macen da zaka aureta alhalin kasan bata sonka. Ba ayi macen da zata ce baka yi mata ba, sannan ka nace sai ka aure ta, duk wanda ya sanka yasan wannan alwashin na ka. To me yasa yanzu ka yarda zaka aure ni alhalin kasan bana son ka, bana farin-ciki da al'amarinka gaba'daya?" Kuka ya k'wace mini sosai. Murya babu amo ya ce"Kaddara ta ce a hakan Asiya! Ni kaina na kasa gane kaina. Wata'kila cika bakin da na yi ta yi ne, ya sanya aka jarrabe ni da son auren wacce ta washe ni, wata'kila kuma Ubangiji ne zai mini wani alherin ta sanadin ki shiyasa ya jingina mini sonki mai yawa." Na sake jan tsaki na ce "Ba wani alheri domin da zan ga sadda zai tunkare ka zan karkatar da shi na bawa wanda suka fika mutunci da so na". Ya girgiza kai ya kasa magana domin ransa ya baci idanuwansa har canja wa suka yi. Tsawon sakwanni bai iya ce wa uffan ba. Ni kuma sai fama nake da kuncin zuciya. Sannan sai yanayinsa ya sanya na ji babu da'di, domin duk yadda na tsane shi. Sai na ji ya d'an ba ni tausayi ka'dan. Muna haka Baban Marina ya dawo, ya zo wuce wa ta babban zaure ya hango mu a zauren Dada. Ina kallon yadda yake murmushi yana amsa gaisuwar Bulkachuwa da walwala. Ni kaina a wannan lokacin ya sace da fishin da yake yi mini. Domin da murmushi a fuskarsa ya amsa barka da zuwan da na yi masa. Har yana fa'din "Sannunku Yabi" Kunya ta saka na yi nufin shige wa wajen Dada. Sai ce wa ya yi "Dawo ku cigaba da tattaunawarku. Allah ya yi muku albarka. Allah ya sa ku zamo abin alfahari, Allah ya shiga al'amarinku". A hankali Tijjani yake amsa wa yayin da ni kuma ban amsa ba ko da a zuci ne. Yana shige wa ya kalle ni a sanyaye ya ce "Asiya Toro Baban Marina bai dauki auren nan namu da wasa ba fa. Mu ha'da kanmu, kada mu ba shi kunya dan Allah". Na ja tsaki tare da ce wa "Ni Malam na gaji tafiya zan yi". A sanyaye ya mik'o mini wayarsa ya ce "Saka mini lambar" A tunzure na ce "Ba ni da k'awa". Da sigar lallashi ya ce "Yanzu duk ro'kon da na yi miki? Farin cikin da Baban Marina ya yi a dalilin ganinmu bai sa zuciyarki ta rusuna ba?" Na murguda baki na ce "To ai dai kasan ba ni da k'awaye, Adda Nazira ce kuma ta yi aure, sai kuwa Nasiba ita ma kuma ai auren ta za'a yi ko?" Ya girgiza kai ya ce "Hakane! To Ina wannan fara mai dan jikin nan da yanzu kuke dawowa daga boko tare? Sannan tare nake ganinku a wajen koyon kwalliya". Na zuba masa harara na ce "Tsabar sawa mata ido har ka gane halittar ta? Har abada ba zaka burge ni ba Tijjani. Ba kuma zan baka lambar ba, domin dai da bakin ka ka tabbatar mini nema cikin nema haramun ne. Bari na shaida maka tuni an kai ku'din aurenta. Dan nasan kana iya lallabawa wajen ta". Ya yi sororo sai kuma b'acin ran fuskarsa ya ragu. Ya ce "Bana ma son lambar, na fasa, zan ba shi lambarki sai ki fa'da masa ta yadda zai turo miki ku'din kunshi da na kitso, ya damu akan a sallame ki ke da kawayen ki ne". Na yi shiru ban ce komai ba. A hankali ya ce "ya yi miki hakan?" Na sake yi masa banza. Ya sassauta ya ce "please mana Asiya Toro". Na harzuka na ce "Gaskiyar magana baka yi mini adalci, idan ina kaunar yadda kake gatsa sunana ha'de da na garina Allah ya tsine mini!. Ya dan murmusa ya ce "Da sannnu idan kin kwantar da hankalinki zan daina fa'da, na samo miki sunaye masu da'di da tsuma zuciya". Ba'kin ciki ya sake turknike ni. Na ce zuciyar waye din zata tsumu?" Ya make kafa'da ya ce ta "Asiya Toro". Na yi kwafa na ce "Ai na gane zuciyarka babu alheri ne shi yasa kake k'yashin ce mini Yabi. Da'din abin ma dubun ka suna fa'da mini cikin girma da arziki". Ya ce"Nan da lokaci ka'dan komai zai zama tarihi. Kin ga dai na nemi arzikin ki, ban kuma mayar miki da martanin bakaken maganganun da kika yi ta yab'a mini ba. Ina sake ro'kon ki idan abokina ya kira ki, ki taimake ni kada ki bayar da ni." Ban amsa ba. Ya sake cewa dan Allah Asiya Toro". Cikin fishi na ce "Na ji". Da'di ya kama shi ya dinga fa'din "Na gode sosai. Ina fatan na ga ranar da zaki fahimci irin tarin alkhairorin da suke zuciyata mussaman akan lamarin ki". A hanzarce na ce "Ai kuwa dai ba zaka ga ranar ba". Ya girgiza kai tare da ce wa "Babu damuwa time will tell". Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ina son na tambaye ki, zaki iya zama a wanccan daya bangaren na Dada?" Maimakon na yi masa magana da baki, ai sai kawai na d'ora hannu aka na fashe da wani irin kuka na tashin hankali. Murya na rawa na ce "wato dai a cikin masifar gidan nan zan tabbata? Idan kuwa har a cikin gidan nan ake nufin na zauna da sunan zaman aure Allah ya dauki raina kafin hakan ya tabbata. Na shiga uku ni Yabi". Ya rikice ya hau fa'din yi shirun ki dama na fa'da mata wajen ya miki local da yawa, sannan baki samu sauyin muhalli ba. Yau din nan duk inda gida yake zan nemo kafin dare. Da ku'di a hannuna. Yi hakuri ki daina irin wannan kukan. Kin ga yadda kika koma kuwa Asiya?" Da k'yar ya lallaba ni, na yi shiru. Ya zura hannunsa a aljihu ya ciro cakulet manya masu da'di da tsada k'waya biyu ya mik'o mini. Bansan ya aka yi ba na fashe da dariya ga kuma hawayen ba'kin ciki na ziraro mini. Da yake d'an duniya ne sai kawai shima ya fashe da dariyar yana cewa "Ni nasan Ubangiji zai cusa miki soyayyata dan yasan yadda ya gina ki a tawa zuciyar. " Da k'yar na samu dariyar ta tsaya. Da hawaye a idona na ce "me zan yi da wannan abar?" Ya zuba mini ido yana wani lumshe su ya ce "Wai fa dan kada na zo hannu na dukan cinya ya sanya na taho miki da su" Na rasa me zance masa tsabar takaicinsa da ya d'ada makure ni. Na ce "To ajiye idan ka ga Yarinya k'arama ka bata amma ba ni ba". Ya waske ya ce "Asiya Toro maraina ka'dan fa barawo ne. Kowa ba iya karfinsa zai yi kyauta ba? Kin san wahalar da na sha kafin na samo miki wannan cakulet din a garin nan? Saboda nasan kina son ta ne. Amma ban burge ki ba? Idan kin yi hakuri wataran katon zan siyo na ajiye miki." Da sauri na ce "da dai ace ba hannun jinjirai ne da kai ba tsabar rowa." Ya nuna kansa da yatsansa ya ce "Ni ne mai hannun jarirai? Lallai kuwa zan baki mamaki Asiya Toro local government. Bauchi state of Nigeria". Ko kula shi ban yi ba na wuce shi na tafi na bar shi a tsaye. Tsabar takaicinsa da ya sake kular da ni. Ya d'aga murya ya ce "Sai gobe zan dawo, ko da anjima ma na dawo?" Da kansa ya bawa kansa amsa da ce wa "To zan dawo da daddaren ran ki ya da'de." Har na isa k'ofarmu mamakin Bulkachuwa kawai nake yi. Ban da dai ya riga ya same ni a araha ya rasa me zai kawo mini sai cakulet k'waya biyu. Shi ko kunya bai ji ba? Amma da na tuna halin rowarsa sai kawai na janye mamakinsa. Na shiga tambayar kaina wanne irin zama zamu yi ne da shi? Na tabbatar sassaucin da ya yi dan baya son na yarfa shi ne. Amma da tuni ya baje mini kalolin rashin mutuncinsa. Na zauna na fara kokarin cigaba da k'ullin sigan. Zuciyata ta shiga hakaito mini kayan jikinsa. Shadda ce a jikin sa kalar ganye wato kore sosai. Ya d'ora hular sanyi mai tambarin kungiyar Manchester United. Na sani kuma d'an ya boye wa Baba curarriyar sumarsa ne tunda zafi ake yi ba sanyi ba. Daga ni tun farar safiya ya sanya kayan a hakan kuma shi ya k'ure malejin kwalliya ne. Na ja tsaki tare da ce wa "Idona ya saba ganin samari ma'abota wanka da gayu. Irinsu Yaya J da Nuru Tanim. Ta ya ya Bulkachuwa zai burge ni?." Gwaggo ta shigo ta ce "me ya faru da kika je?" Na yi kasa da kai na ce "Ba Dada ba ce ashe". Ta ce "To waye?" Na bata rai duk da kan nawa yana kasa na ce "Tijjani ne". Daga hakan bata kara ce wa komai ba ta dauki abin da zata dauka ta fice tsakar gida. Washa gari da azahar ina kwance a tsakar daki sai ga Nazira ta zo. Karon farko da ta zo gida tunda aka yi mata aure. Duk rud'anin da nake ciki sai da na tashi da azama na rungume ta. Muka haye k'aramin gadon Gwaggo da muke kwana a kansa ni da ita tun fil'azal. Da murmushi a fukskata na ce "Yau Adda Nazira ce a gidanmu?" Ta d'aka mini duka tare da cewa"oh har kin cire ni a cikinsa, to kema kwana nawa ya rage miki mu yi kunnen doki?" Na bata fuska sosai. Ta ce "daga wajen Dada nake suna can, suna artabu da Yaya Bulkachuwa akan inda zaku zauna. Wai akan me zai je ya kama haya tamkar ba shi da kowa a Toro? Shi kuma ya kafe ba zai zauna a cikin gidan nan ba.". Na bata rai na ce "Ai Wallahi na fa'da masa indai ya yarda da tsarinsu to kuwa sai dai a tsine mini dan bazan zauna a gidan nan ba'kin ciki ya karasa ni tun ajalina bai zo ba" Adda Nazira ta ce "Haba ashe tirjiya ya samu daga gare ki, kin ga yadda ya fitittike akan ba zai zauna a wajen ba? Dada har da kukanta wai sai da ya bari su Baban Tsakiya sun gama gyara masa wajen sannan ya ce zai fita ya kama haya tamkar wanda bashi da galihu a Toro? Shi kuma kinsan shi ya ce "Salisu da yake hayar rashin galihu ne ke nan? Ashe ashe Gimbiya Yabi ce ta saka ya rikice ya turje. Ya kama miki gida mai kyau a bayan sakatariya. Ba ki ga gidan ba. Yanzu muka dawo a mashin dinsa ya goye ni muka je ya nuna mini gidan. Ni Wlh har na ji na daina k'insa. Kin ga rawar jikin da yake yi. Sai fa'di yake ya kika ga wajen Nazira? Nasan idan ya burge ki to zai burge kanwar ta ki ma. Gaskiya Yabi ke d'in mai sa'a ce. Gaba'daya kin rikita namiji irin Yaya Bulkachuwa. Murna nake yi, da dukkan zuciyata nake jin addu'armu ta karbu. Da ikon Ubangiji sai kowa ya yi mamakin alherin da zai biyo bayan wannan auren." Na tab'e baki na ce "Hmm ai ni dai an cuce ni kawai. D'azu muna maganar k'awayen amarya. Na ce masa ba ni da k'awaye, ke ce to kuma kin yi aure. Yana bu'de baki da yake shi d'in bunsuru ne sai ce wa ya yi wai ina k'awata fara mai dan jiki. Kin san wa yake nufi?" Kafin ta ce komai na zarce da ce wa "Shafa'atu yake nufi fa. Har ya k'yalla ya ga halittu a tare da ita shine zai silala me za'a yi da Tijjani ne. Na fa'da cikin kunan rai. Ga mamakina sai ganin Nazira na yi ta k'yal-k'yale da dariya sosai. Sannan ta ce da wuri haka Yabi?" Na bata rai na ce 'ban gane ba?" Ai kuwa cikin ido ta ce" tun yanzu kin fara kishin Yaya Bulkachuwa ina kuma idan kin shiga hannunsa?" Hawaye ya b'alle mini ina ce wa "Allah ya sauwake, ashe ba ki fahimce ni ba Adda Nazira?" *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBE TA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* "Tunda Kika kasa gane abin da yake zuciyata ba wanda zai fahimce ni dai-dai". Na fa'da cikin kuka sosai. Ta maze ta ce "Ai kuwa dai kinsan na sanki tamkar yunwar cikina. Wata'kila kuma y'an watannin da muka yi ba tare ba ya sanya na soma mance ki. Amma tunda kin ji bacin rai a dalilin maganar ki yi hakuri da wasa nake yi shikenan?" Da haka na fara goge hawayen idona. Sai yamma lis ta tafi. Na rakata hanya ta hau abin hawa. Ina kan hanyar dawowa sai ganin mutum na yi tamkar daga sama yana biye da ni. Bai yi magana ba, bare ni kuma. Har muka iso gida sannan ya ce "Asiya Toro manyan mata. Na wuce shi na yi shigewa ta. Ina ayyana shi bai san ya kintsa kansa idan za shi wajen budurwa ba. Ina shiga na tarar da Babanmu a zaune. Ko hijabi ban cire ba, sai ga yarinya cikin yaran Baban kasuwa ta shigo ta ce "Adda Yabi Yaya Bulkachuwa ya ce "sauri yake yi ki je yanzu sakon zai fa'da miki". Ba'kin ciki ya tokare ni, wai shi nan masharranci. Na fito babu b'ata lokaci na fita ba dan komai ba sai dan Baban Marina yana zaune ba dan haka ba sai dai ya bushe a wajen. Da fishi shinfide a fuskata na isa. Ya kalle ni ya ce "Me kuma ya faru dan Allah. Dazun nan fa na ganki kina ta murmushi har na yi zaton ko labarin gidanki da Nazira ta gano miki take baki ya saukar miki da farin ciki mai yawa." Na d'ago na kalle shi ina rasa ma ajin da zan ajiye Tijjani. Na lura kusan halin mahaifina ne da shi. Zaka yi musu abin takaici sai su waske su nuna basu gane ma me kake nufi ba, bare su nuna sun damu a karshe kuma sai su yi maka abin da kai ne zaka shaki takaici cikin salama. Na wuce shi na yi tafiyata. A hakan har kwanakin suka zo ya rage saura kwanaki biyu daurin aure. A wannan ranar kuma aka yi mini jere. Da yake Yaya Salisu ya na aiki bansan yadda aka yi ba an ce dai an yi mana gado da kujeru ni da Ubaida. Na tuna irin yanayin damuwa da Nura ya shiga a dalilin rashina. Da hawaye a idonsa yake fa'din "Na tafka asara Yabi! Tijjani ya zama mai sa'a. Na yarda da kaddara. Na kuma karbi auren kanwarki da hannu biyu in sha Allah kuma zan yi mata adalci. Allah ya sanya alheri. Allah ya sanyamu cikin masu biyayyar iyaye da ha'kuri saboda shi". Da alhini mai yawa muka rabu. Kimanin kwanakin sati kenan. Na nisa ina sake hakaito wa ban da y'an kofarmu ba wanda ya yaba lefe ko kyaun gidana na rasa irin wannan masifar. Har gara ma an dan yaba gidan Ubaida kadan duk da gidanta gida ne mai kyau sosai. Amma da yake da ahalinmu aka fi adawa ba a wani yaba an zuzuta kamar yadda aka kurzanta na su Maijida da Firdausi ba. Haka gidan Nasiba aka yaba aka kod'a lefenta tamkar me? Amma namu mukus kake ji. A hakan har asabar din da ta yi daidai da 20 ga watan 5 ta zo aka daura aurena da Bulkachuwa, sannan aka daura na Ubaida da Nura. Daga nan aka d'unguma gidansu Nasiba aka daura nata. Fa'din halin da nake ciki na damuwa ba sai na fa'da ba. Amma dai ji na yi tamkar na sheka barzaku. Ina takure a dakin Gwaggo Nazira sai kai komo take yi cikin kwalliya. Ga cikin jikinta da ya fara tasawa ya kara mata kyau sosai. Ihisan k'anwarsu Bulkachuwa ta shigo wai na je abokan ango na jirana. Akan dole na yarda na bita bayan na ce sai dai ta tsaya ni idan mun je. Haka na dinga yak'e ina gaisawa da su. Ala tilas na yarda aka yi hotuna. Shi kuma ganin ya samu dama har da sawa ayi mana daga ni sai shi. Cikin rufin asiri aka yi hidimar bikinmu. Ubaida aka fara rakawa da yake bamu da nisa. Ni kuwa Baban Marina hannuna ya kama ya damkawa Babah ta Bulkachuwa. Ya ce "Rakata dakinta Hauwa! Allah ya kawar da dukkan abin da muke tsoron faruwarsa a cikin aurensu. Ki kula da ita, ko bani ne na haifa miki ita ba, ta zama y'arki tunda surukuta ta mayar da ke uwa a gareta. Bare kuma ni din cikinmu guda. Ina ro'kon ki duk kuskuren da zata miki a zamantakewarku kada ki mata hukunci cikin zato. Kada kuma ki bari shaidan ya rinjayar da aibunta a zuciyarki. Yarinya ce ita din a gaban ki koda kuwa ta kai shekaru hamsin a duniya. Na damk'a miki ita, cikin gasgata cewar na bayar da ita a amintaccen hannun da ko bana raye za'a yi adalci da sassauci. Ina fatan wannan ya zama sanadin karin zumuncinmu ba wai sanadin tabarbarewarsa gaba'daya ba". Duk da fuskata a rufe take amma na lura da yadda jikin Babah ya yi lakwas. Domin ta kasa bu'de baki ta ce uffan. Na dai ga tana goge fuskarta da na tabbatar hawaye ne. Tsawon lokaci ba wanda ya yi magana a tsakaninsu. Sai Baban ne ya katse shirun ta hanyar fa'din "Ki saurare ni da kyau Yabi. Aurenki ya banbanta da na dukkan y'ay'an gidan nan. Ina fatan kuma ya zama mafi da'din misali a cikinku. Ki dauka ibada zaki yi. Kinsan kuwa ibada wajibi ce ba wai ra'ayi ba. Ina ro'kon ki zauna lafiya da mijinki. Ina alfahari da ke tabbas Asiya. Amma zan sake alfahari da ke ne idan har kika taka muhimmiyar rawa wajen mayar da Tijjani yadda muke son ganinsa. Na sani babban aiki ne mai nauyi. Amma tunda an yi sa'a yana sonki to matu'kar kin kwantar da hankalinki za'a samu dai-daito. Ina fatan na ganku da iyali masu yawa kuna cikin rufin asiri. Tashi ki je, Allah ya bada sa'a ya maki albarka". Ina kallo yadda Babah ta tashi da k'yar amma bata yarda ta saki hannuna ba tunda Baban Marina ya damka mata. Ta tayar da ni ta fita da ni har lokacin kuma bata iya cewa komai ba. Har muka shiga mota, muka isa gidan tana rike da ni. Da kanta ta shigar da ni dakina bayan ta jira ni na karanta falaki da nasi da attahiyatu har zuwa inda ake yin sallamah a bakin kofa. Ita ce ta bani umarnin yin hakan wanda sai lokacin na ji ta yi magana, rawar da muryarta take yi ya sanya na gane kuka take yi sosai. Duk yadda jama'a suke shiga da fita na ganin dakin amarya bai sanya Babah ta tafi ko ta saki hannuna ba. Matan gidanmu duk wacce ta shigo ta ga Babah sai ta yi turus. Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*. *08032773332* Hatta mamah da matan Baban Tsakiya da suka rakoni tare da ita sai da suka tsokane ta suna cewa "To ko dai ba zaki bar ta a dakinta bane kamar yadda aka yiwa kowa?" Duk da hakan kuma bai sa ta bar ni ba. Har sai da Aliyu ya dauko mata Bulkachuwa cikin abokansa da suke dakon a gama watsewa su rako shi. Yadda mahaifina ya damka mata ni a hannunta, bata saki hannuna ba duk tsawon lokacin nan. Ta kamo hannunsa ta ha'da da nawa ta damk'e cikin nata. Ta ce "gata nan ubanta ya bani amanarta na kawo maka ita da kaina saboda ya nuna mini ita ce tawa ba kai ba. Na karbi amanarta, ni kuma na baka amanarta. Ka dinga tuna dalilin ha'da wannan auren. Ka zama cikin mutane masu halarci da kuma sakanta alheri da alheri. Ban ta'ba farin ciki irin na yau ba. Ka sani na ha'diyi takaici da wahalolinka daban daban. Zan mance komai na yi alfahari da kai har ma na daga maka sawuna ka shiga aljannah idan Yabi ta kubuta daga tozarcinka da gangan. Ko bana raye idan ka kyautata mata tamkar ni ka yiwa. Albarka da farin-ciki zasu kewaye ka. Ka kula da tarbiyarta, kada ka bari ta bijire wa ka'idojin shari'a. Amma ka zama mai sasauci da kawaici domin dai yarinya ce y'ar k'arama. Ina fatan auren nan ya bud'a maka k'ofofin arziki da kuma fahimtar rayuwa daidai. Àllah ya shirye ka ya shirya maka iyali. Allah ya albarkaceku gaba'daya". Ta mik'e ta bar shi a durk'ushe yayin da nake kan gado, hannunmu kuma suna sark'e. Sai da na tabbatar ta yi nisa na fincike hannuna, na ja tsaki na koma gefe. Murya a dushe ya ce "Na yafe miki Asiyata! A gabanki Babah ta ce amanarki ta bani, na tausaya miki, na kuma yi miki sassauci." Na sake jan tsaki fiye da na farko. Ya mike ya fita bayan yan tsirarrun kawayena sun fara hayaniyar ba'a sayi baki ba dare na yi. D'aya ce ma k'awata a ciki ragowar hudun duk wanda suka zo daga Kangire ne wato cousin dina na dangin Gwaggo. Sai kuwa Ihisan k'anwarsa. Ita kuma a takure take a dalilin yayanta ne angon. Ba jima wa suka zo. Suka taba barkwancinsu, sannan aka yi nasiha da addu'a. Suka gwangwaje k'awaye da ku'din sallama mai auki. Sannan suka tafi da su. Ina ganin sun fita, shi kuma ya bisu da niyyar rakiya. Na tashi na rufe kofar dakina. Da ya dawo ba yadda bai yi dan na bu'de kofar ba na ki. Ta windo ya leko ya ce "Ga leda nan ki dauka ki ci nasan da yunwa a tare da ke". Washagari ina jin ya fita sallah na yi maza na fita na doro alwallah a bandaki, takaicina daya bandaki a tsakar gida yake ba a cikin daki kamar yadda na ci buri ba. A gurguje na kammala uzziri na koma na rufe dakina. Ina idar da sallah na yi kwanciya ta. Sai tara da kadan na bu'de k'ofar dakin, domin barci na yi mai nauyi. Ina bu'de wa kuwa ya shigo da sauri. Ya ce "Kin tashi? Sannu ya kwanan bakunta?" Uffan ban ce ba. Amma wani irin bakin ciki ne ya turnike ni. A dalilin rashin bandaki a cikin daki. Na hakaito kusan duk wadanda muka taso tare ko wacce band'akinta a dakinta ne. Na tuna gidan J da na Nura, hatta Nasiba band'akinta a dakinta ne sai ni ce na samu dakuna tamkar na Islamiya tunda na ga falon ma daban ne ba'a hade suke ba". Sai kawai na fashe da kuka mai sauti sosai. Ya diririce ya ce "Daga tashi sai kuka Asiya? Tun dazu fa nake zaman jiran ki tashi ki karya. Ina son na fita muyi sallama da abokaina zasu koma garuruwansu". Ban ce masa komai ba. Illah kukan da nake yi mai tsananin cin rai da nuna k'ololuwar ba'kin cikin da mai yinsa yake ciki. Ya dinga rarrashi yana Fa'din "Ki yi ha'kuri Asiya komai zai dai-daita, daure ki tashi ki yi wanka anjima ka'dan zaki fara yin baki, duk wadanda zasu tafi yau sai sun biyo sun gan ki. Ina ganin kafin Babah ta wuce Bulkachuwa ma sai ta zo, idan ta ganki a hakan kinsan ba zata ji da'di ba." Gaba'daya ya rikice ya ce wannan ya saki, ya ce wancan. Da kuka na ce "Ni ban ta'ba hasko zan shiga gida mai bandaki a waje ba. Gaskiya an cuce ni, an gama da ni. Na saka fashewa da kukan da yafi na farko tsanani. Hankalinsa ya tashi domin a ki'dime ya tattaro ni. Na zabura na k'wace ina sake jin taikacinsa tamkar na rufe shi da duka. Jikina har bari ya dauka domin lokacin ne karon na farko da jikin namiji ya rab'i jikina irin haka. Da muryar kuka na ce "kada ka kuma ta'ba ni. Bana son ka, bana ko son ganin ka". Ya rasa yadda zai yi da ni. Ya zauna a gefena cikin rashin abin yi. Tsawon lokaci ina shesshekar kuka. A hankali ya ce "Ko na samo miki katon baho sai ki yi wankan anan idan kin gama sai na dauke na gyara wajen". Yadda ya yi maganar sai na ji wani irin abu mai kama da tausayinsa yana neman kama ni. Na sassauta kukan nawa. Amma ban kula shi ba, bare na tanka masa. Ya sake lank'awasa harshe ya ce "Ki yi ha'kuri Asiya! A yanzu bani da halin irin gidan da kike mafarkin samu. Ban ta'ba jin takaicin ta'adin dukiyata da na dinga yi ba irin yau. Amma ina ro'kon arziki ki yi mini ha'kuri . Da ikon Allah zan yi aiki tukuru dan na cika miki burin ki. Na miki al'kawarin matu'kar rayuwata da taki ta kai lokacin da zan yi miki ginin da zai dace da ke, to ke zan bawa zabin yadda za'a fasalta ginin". Na ja tsaki na ce "Duk kana nufin ina nan tare da kai, ina kuma dakon ganin wasikar jaki irin taka?" Idonsa ya kad'a ya ce "Ni na sani Allah zai taimake ni, dan haka ba wasikar jaki nake yi ba". Na ja bakina na tsuke. Ya dinga magiya tamkar zai fashe da kuka akan na je na yi wanka. Da k'yar na yarda na tashi sai dai ban yarda na tube kayana akan idonsa ba. Sai da ya fita. Sannan na cire. Na dauko sabon zanina gyauto guda. Na daura na saka hijabi. Na bu'de akwatin da na shirya kayana a ciki. Na ciro soson wanka da sabulu da burush, hadi da makilin. Na ajiye tawul akan gadon. Na fito na tarar da shi zaune akan baranda duk jikinsa ya saki babu kuzari a tare da shi tamkar ba Bulkachuwa wanda baya barin ta kwana ba. Yana ganin na fito ya mik'e ya dauki botikin da yake gabansa cike da ruwa. Ya nufi band'akin. Na dakata ya fito, ya kalle ni ya ce "yanzu na janyo miki a rijiya da dumi tunda garin da zafi." Ta tafasa ban ce ba. Na shiga na turo kofar na sanya sakata. Ina wanka ina ayyana, ina ma a cikin daki bayin yake? Dan karami amma ko ina tayals ne. Na fahimci sabon gini ne mune muka fara zama a ciki. Sosai na yi wanka. Sai da na alwala da kuma brush sannan na fito. Na shiga daki na tarar da tsintsiya a hannunsa tabbacin shara ya yi mini. Ga gadon ya gyara tamkar gyaran mace. Daga kasa kuma kwanukan abinci ne. Ko kallonsa ban yi ba, bare na yaba masa ta hanyar cewa sannu ko na gode. Ya kalle ni ya ce "Bari na baki wuri ki shirya". Ya juya ya fice. A hankali nake shafa mai tamkar mai ciwo sannan na goga powder. Na shirya cikin sabuwar atamfa ta Buyers Batik. Doguwar riga ce amma dinkin ya yi kyau domin a Jos aka dinko mini. Gata shudiya ce sosai aka yi mata yarfen ja. Tsaya fa'din yadda farar fata ta haska atamfar bata lokaci ne. Na goga rol on din Nivea a raina sai tsaki nake yi ina fa'din da an bar ni da kwamishina ko Yaya Jabir da tuni roll on din oriflame zan dinga tu'amalli da shi dama sauran product dinsu gaba'daya. Tunda su zance a zubo mini a lefena. Na fesa turaren Far-away, na shafawa lebena jan baki mai jan duhu. Gefe na ajiye jan mayafi Wanda ya dace da atamafar. Da yake yanzu a hutar da mata bata lokaci wajen daura dankwali ana ta yin huluna. Nima hular aka yi mini. Ai kuwa na kafata a kaina na isa gaban madubi ina daidita zamanta. Ni da kaina na dinga fa'din "Fatabarakallahu ahsanul khalik'in. Sosai na yiwa kaina kyau. Maimakon na zauna sai na tsinci kaina da son yin walaha tunda na yi alwallah kafin na fito a band'akin. Na idar na tsaya ina kallon dakin. Madaidaici ne sannan kayan gadona suma matsakaita ne masu sau'kin ku'di. Amma sun yi kyau babu laifi. Labulayen sun fi komai dqukar hankalina, ledar tsakar dakin ma mai kyaun aka saka mini wacce za'a kwana biyu bata fatattake ba. Na bude akwatin na dauko wayata na kunna. Na koma bakin gadon na kishingida ina dakon ta gama daidaita. Ina cikin dube dube ya shigo shima tamkar alamara ya sanya shudiyar shadda irin shud'in atamfar jikina. Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Domin komin k'in da nake yi masa tun fil'azal nasan yana cikin yan ka'dan da Ubangiji ya yi masa kyaun fuska da kuma ciakken zati. Da walwala ya ce "Amarya kin sha kyau. Nan gaba fa idan zuciyoyinmu suka zama aminai ba karamin gidan farin ciki zamu gina ba. Tun yanzu zabin zuciyoyinmu ya zo d:aya. Mun sanya kaya iri daya ba tare da mun shawarci juna ba". Na zabura na cire hular na bu'de akwati ina laluben wasu kayan. Da sauri ya karaso kusa da ni. Ya ce "Dan Allah! Ba dan ni ba. Dan alfarmar Annabi ki bar kayan ki, sun miki kyau ainun. Ina ta fa'da miki baki zaki ta yi yau. Ni fita ma zan yi". Magiyar da ya yi ta sace mini guiwa na fasa canjawar. Ya bu'de flask din abinci ya ce "Wannan doya ce da kwai Salisu ne ya aiko mana. Ya bu'de d'ayan kuma masa ce itin tamu ta mutanan Bauchi da kuli kuli. Ya ce wannan kuma daga gida aka kawo ga kuma kunu". Yana nuna mini jug din. Ya sake cewa "Na tafasa miki shayi na dauko miki?" Ina kallonsa amma ko motsi ban yi ba bare na tanka shi. Bai yi fishi ba, ya mike ya dauko flask din shayi wanda nawa ne a cikin kaya ya dauko. Ya koma ya dauko kofina da kayan hada shayin a leda wanda alamu suka nuna siyowa ya yi. Ya zauna ya ce "Sauko to mu karya". Na sake sharewa. A hankali ya ce "Da ace kin ji nasihar da aka yi ta yi Miki, iya ta jiya kacal da kin raga mini, domin dai ko ya ya nake ni din Ubangiji ya za'ba miki ya zame miki miji. Shi kuwa miji komin kashinsa ai daraja ne da shi." Na yi kamar ban ji ba, na cigaba da danne danne wayata. Ya karya, ya kwashe kwanukan da ya yi amfani da su. Ya dawo ya ce "Zan fita Asiya. Zamu je yiwa iyayenmu ban gajiya. Nasan ba zaki yini da kewa ba yau". Ya sake cewa sai "Na dawo". Daga hakan ya juya ko uffan bai sake cewa ba. Sai tashin mashin dinsa na jiyo. Yana fita na sauko na karya. Na kai ragowar kicin. Na tsinci kaina da son karewa gidan kallo. D'akuna biyu ne a jere akan baranda. Sai kuwa guda daya daga can gefe kusa da bandaki. Sai kicin a dayan gefen. Gini ne ba laifi gashi ya sha fenti. Kan barandar ma tayals ne. Haka kicin dinma. A fili na ce "ko me ya hana a saka tayal a dakin? Na kalli yadda aka k'awata mini kicin din da kayayyaki. Na sani kuma mafi yawa dangin mahaifiyata ne suka zo da kayan. Da sauri na nufi d'akin da yake mak'wabtaka da dakina wanda na tabbatar shine falon. Ina shiga na ji sau'kin takaicin da nake ciki. Domin dai falon ya yi kyau daidai na masu karamin buri. Kujera ce irin mai L din nan. An saka ta a bango guda, da yake falon ma an saka tayals sai aka saka madaidaicim kafet a tsakiyar falon. Ga kuma TV an mak'ala a bango, sai fridges daga can gefe. Shikenan sai labulaye kalar kujeru da kafet din wanda suka kasance royal blue ne. Ga katon agogo mai kyau shima an kafa shi. Na zauna ina jin da'din yadda na ga wajen. Na sani da ace Yaya J ne mijin tabbas da na kasance cikin farin-ciki mai yawa. Na kunna fanka ganin da akwai wuta. Na fita na nufi daya dakin da ya fi kusa da band'aki. Na leka na ga bashi da girman wanda aka saka mini gado a ciki. Ba komai sai labule. Gefe kuma akwatin kayansa ne da tarkacensa sai takalmansa. Na janyo kofar kamar yadda na ganta a sakaye na fito. Na koma falo ina jin dau'kin tv na kama ni. Duk kokarina na kasa ha'da ta. Dole na hakura na kashe na jona wayata a caji. Na zauna iska.lr fanka tana kad'a ni. Ina haka sallamar babbar mace ta saka na zabura ina amsa wa. Na marabce ta da sakin fuska duk da dai ban gane fuskarta ba. Sannan a kallon farko na fahimci ba bahaushiya ba ce, tunda ga siffarta har tsagun da suka cika faffadar fuskarta Na gaishe ta da girmama wa tunda na ga zata haife wacce ta fini ma. Ta ce "Ni ce a waccar kofar. Suna na Gadatu. Ana kirana Maman Safiyanu. Mijina bara ya rasu, ina da yara maza da mata. Allah ya sanya alheri. Allah kuma ya zaunar da mu lafiya. Na yi k'asa da kaina. Na tashi na kawo mata cin cin da dubulan. Bata ci ba. Na juye mata a leda ta tafi da shi. Bata Jima da tafiya ba sai ga y'arta da alamu suka nuna zata girme mini. Gata da garin jiki. Doguwa ce sannan a koshe take ainun. Ta ce "wai Mamansu ta ce na bada kasko a kawo mini garwashi ko zan yi turare. Na dauko na bata, fuskata a sake. Ta kawo mini kuwa. Na tambayi sunanta ta amsa mini da cewa "Rafi'a" Na ce "To na gode miki". Na zuba turare nan da nan gida ya kaure, ya zama na amaryar sosai. Ba jima wa kuwa jama'ar Kangire suka zo motarsu guda, suka dinga addu'a da jan kunnena akan bawa marar d'a kunya na zauna lafiya da mijin da Allah ya za'ba mini. Daga haka suka tafi wanda kai tsaye Kangiren suka wuce. Haka kuwa aka dinga shigi da fice. Hatta Babah ma ta zo kafin ta tafi Bulkachuwa ta dinga yaba yadda ta gan ni. Tare da su Nasiru da Ihisan ta zo. Da kulawa mai yawa ta ce "Duk abin da zai miki kada ki biye shi waya kawai zaki dauka ki sanar da ni, ni kuwa zan miki maganin matsalar. Ki yi hakuri, ki yi biyayya, ki yawaita addu'a. Sannan ban da rashin kunya. Allah ya yi miki albarka." Kuka kawai nake yi. Kukan da bansan dalili ba, ban saniba ko dan na ga ita ma hawaye take yi. Bansan kukan da take ta faman yi ba, na farin-ciki ne ko na tausayina ko kuwa na yadda aka juya al'amarin ne oho. Ashe tare suke da shi ya coge a tsakar gida. Sai da suka fito sannan ya bi bayansu ya rakasu. *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *08089965176* *07084653262* ✍️ *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633*. 37&38. Da yamma lis sai ga Yaya Ummi da tarkacen su tsintsiya da sauran kayayyaki har da su kuloli masu kyau da zannuwan gado na sani wanda aka samu na gudunmawa ne aka karo zabo mini masu kyaun cikinsu. Ta sake gyara mini kicin din. Na bata tarkacen robobi da wani flask din roba irin mai biyun nan. Kayan lefena kuwa turamen atamfofi biyu na bata da hijabi hadi da kayayyakin kwalliya. Ta dinga yi mini addu'ar Allah ya zaunar da ni lafiya. Ta bu'de jakar hannunta ta dauko wata yar roba mai dauke da garin magani kore. Ta sassauta murya ta ce ko zaki dinga shan wannan a cikin madara ko yoghurt?" Na kar'ba na ce "Na menene?" Ta yi k'asa da kai ta ce "farin ciki da dokin juna zai sanya muku" Na yi maza na mayar mata cikin jakarta. Tare da cewa "Da dai ba irin wannan mutumin aka aura mini ba." Ta ce "shikenan da har da INGANTATUN SAIWOWIN DAHUWAR GIMBIYAR KAZA. Amma zan ajiye miki. Na sani wataran zaki nema da kan ki. Idan kuma na yi amfani da su, sai a kawo miki wani ta hannun kanwar kawata Aisha Lame mai siyar da kayan kwalliya masu daraja (oriflame). Tasan Surayya Dee da take kawo su daga chadi. Baki na tab'e baki, ina kallonta kawai, domin har abada ni Yabi bazan yi wani abu dan na sanya Tijjani farin ciki ba. Muna haka ya shigo, suka gaisa sosai cikin walwala da tsokanar juna. Bai jima da dawowa ba, ta yi haramar tafiya nata gidan. Da yake mutumiyarsa ce. Ya ce "Ta jira ya kai ta a mashin". Ta galla masa harara da cewa "Ni zaka goya Yaya Bulkachuwa?Wallahi ba zan sake biye wa tsokanar da kake yi mini ba, dan ka riga ka zama k'anina". Ya kwashe da dariya ya ce wannan kuwa shine tatsuniyar gizo da k'oki. Ke yanzun nuna mini kika yi Asiya Toro ta fini a wajen ki?" Ta mak'e kafa'da ta ce "Ato Wallahi ka kama k'afata dai". Ya tsugunna a gaban ta ya ce "Dai-dai ina zan kama Ummi?" Ta yi gaba ta bar shi tana fa'din "Hmm sai ka yi kai ka'dai". Ta goyi y'arta shi kuma ya d'aukar mata ledar kayanta. Ya yi gaba ya na jiranta. Da k'yar muka rabu. Cikin lallashi take ta nanata "Ki zauna lafiya, ki kwantar da hankalinki da na iyayenmu dan Allah. Kin ga dai an riga an yi auren nan. Allah ya taimake ki, ya hore miki shi. Nan da wata daya ki cigaba da sana'ar ki, domin mace mai neman na kanta ta huce takaicin babu". Ta bata rai ta ce "kinsan dai ba'kin cikin da na kwankwada a dalilin bani da yar'uwar da aka aurar da muke daki daya. Yanzu murna nake yi kema an aurar da ke na samu abokiyar ha'di. Komai ya taso miki ni ce a hakku saura ki ce zaki bayar da ni a wajensu ta hanyar nunawa duk daya muke ni da su a wajen ki. Gasu nan su hudu ne dakinsu daya." Nima na bata rai na ce "To idan hakane ita kuma Ubaida dawa zata hada kai kenan? Ko so kike ita ma ta fuskanci tsananin da kika fuskanta? Ni fa dukkan y'ay'an Babanmu ina sonsu da dukkan zuciyata". Ta zaburo mini ta ce "Ban ce kada ki so su ba, amma ai wata kusan tafi wata". Na yi dariya na ce "To kawai ki ha'da ni da Nazira da kuma Ubaida ki jamu a jikinki, ki dai-daita su da ni. Shikenan Kinga kin samu k'anne uku aurarru tashi guda. Da sannu suma manyan sai su dawo cikinmu mu zama madaurin tsintsiya". Ta yi gaba tana fa'din "To uwar Iyah! Ta ya ya zan ha'da shakikiyata da dan uba su zama duka daya ne?" Na k'yal-k'yale da dariya tare da fa'din "Yaushe zaki dawo?". Ta ce "sai an kwana biyu". Na zauna ina nazarin Yaya Ummi mutumiyar kirki ce, amma rashin adalcin da manyanmu suke yi mata da kuma yadda kishiyarta ta jefa yan'ubanci a tsakanin y'ay'ansu ya sanya ta k'yamaci dan uba. Na yi mata uzziri domin ita da yaranta suna fuskantar zazzafan yan'ubanci. Ina fatan watarana duka y'ay'an Babanmu mu zama abu guda, ina matu'kar son mu gane girman nasaba irin ta uba daya. *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* *** Bai dawo ba, sai da ya sallaci Isha. A falo ya tarar da ni, na yi wanka na zira doguwar riga cotton mai zuwa da mayafi babba. Na shafa turaren oudi(concentrate). Ya kalle ni ya ce "Ranki ya da'de Asiyata". Na galla masa harara na ce "Ba taka ba ce". Ya murmusa ya ce "Ta Ummi ce shikenan?" Na yi shiru domin so nake na fa'da masa abin da zai bak'anta masa rai. Amma tunda ya saki maganar bari na k'yale shi sai idan ya sake katobarar cewa ni tasa ce zan tabbatar masa ba tasa ba ce, ba kuma zan zama tasan ba. Ya ajiye ledar hannunsa ya fita. Sai gashi ya dawo da kananun bowls da kuma fork biyu. Ya zauna kusa da ni. Ya bude ledar kamshin hadadden balangu ta buge ni. Ya juyo mini dauri guda ya turo mini gabana. Tare da robar yogurt madaidaiciya mai sanyi, da kuma robar ruwa shima mai sanyi. Sannan ya juyo nasa daurin. A hankali ya ce "Bismillah Amarya". Ban kula shi ba. Na gama yaukina na dauka na fara ci. Sosai naman ya yi mini da'di, sannan kuma mai laushi ne. Na cinye tas na bu'de yogurt na fara sha. Rabona da abinci tun karyawar safe. Duk da an kawo mini daga gida amma ban iya ci ba. Ganin na cinye yasa ya turo mini nasa ya ce "Kara Asiya". Na yi kamar ban ji ba. A sanyaye ya ce "Ba kyau a yi magana mutum ya yi kamar bai ji ba". Nan ma tamkar ba na wajen. Ya yi k'wafa alamun ya k'ulu. Ganin hakan ya sanya na tashi na bar shi na yi dakina ko kwanon da na ci ban kawar ba, bare na kawar da nasa. Ina shiga kuma na sanyawa dakin sakata. Na cire mayafin rigar na haye gado na yi kwanciya ta. Tunda na kwanta ban farka ba, sai da asuba shima kwakwasa mini kofa ya yi. Kafin na fito tuni ya bu'de gida ya wuce masallaci. Yau kam har na gama barcina na tashi k'arfe goma. Da na bu'de kofa na fito a zaune na same shi akan barandar. Babu alamun gaggawa a tare da shi. Yana ganina ya mike da sauri yana fa'din "Bari na janyo miki, na roba da sanyi, na rijiyar kuwa dumi ne da shi. Ya bu'de bandaki ya dauko botiki ta nufi rijiyar. Na bishi da kallo. Mamaki nake yi dama Tijjani zai iya yin laushi haka? Duk wula'kancin da nake yi ba ya fasa yi mini hidima. Na sake bin kayan jikinsa da kallo. Alamu sun nuna ya yi wanka. Sabon yadi ne a jikinsa amma ba alamun karin guga. Na tabbatar yadda tela ya ba shi hakan ya saka su. Na ja tsaki sosai. Dai-dai lokacin kuma ya zo daf da ni. Ya ce "Asiya Toro wata rana za'a wayi gari a ga kin zama tsaka fa". Ban kula shi ba, bare na tanka ya samu sanadin da zai jani da surutu. Ya wuce ya kai mini bayin. Na shiga na yi wankana na fito. Yauma atamfa na dauko koriya Shar. Doguwar riga ce da ta manne a jikina. Na gyara sosai. Na gyara d'akin, na zauna. Ya yi sallamah na amsa a dole. Ya ce "Na shigo?" Na ja tsaki, na kame bakina na tsuke. Jim ka'dan ya shigo. Na daga kai na kalle shi. Fuska a daure na ce "Na baka izinin shigowa ne?" Da walwala ya ce "Tunda baki zabura kin ce kada ka shigo mini ba, ai nasan kin kammala adana yan kananun abubuwan da kike yi mini k'yashin ganinsu". Ba'kin ciki ya turnike ni. Na murguda baki na ce "A a kiyasai ne k'arewar kankantar". Ya zauna bakin gado ya ce "Ban da samun guri irin na ki Asiya. Ta ya ya zaki dinga rufe mini kofa, kina hayewa gadon da ba'a siya miki ba sai saboda ni, ni kuma ki bar ni da kwanan kasa. Kwana nake yi ina artabu da sauro. Amma ke babu ruwan ki, ba kya gudun maleriya ta yi mini illah?". Na ki kula shi, bansan me yasa yake bani haushi ba, baya burge ni ko ka'dan. Ya sake yin k'asa da murya ya ce "Ki yi kokarin kyautata lahirarki Asiya. Babu ruwan alkalami da cewar ba kya sona. Matu'kar ina kwana da ba'kin ciki ki sani kina cikin fishin Ubangiji". Na rasa me zance masa domin dai ya sako wanda ban isa na fa'di bak'ar magana a kansa ba. Kan tilas na share ban ce komai ba. Ya tashi tsaye ya ce ki taso ki karya ga abin kari can a falo. Bauchi zan je. In sha Allah ba zan wuce la'asar ba. Za'a kawo miki abinci da rana. Ki shirya gobe zaki fara yin girki". Sai lokacin na fashe takaicinsa da cewa "Ba zan yi ba. Har abada ba zan dora tukunya saboda kai ba". Babu damuwa a tare da shi ya ce "Babu laifi. Lokaci zai fayyace komai ai". Ya juya ya tafi bai sake cewa komai ba. Har shad'aya ina daki ban fita falon ba. Sai da cikina ya tsananta yi mini kartan yunwa. A dole na fita. Na tarar da waina a karamin flask. Sai kunu a jug. Daga dukkan alamu siyowa ya yi. Kan dole na zauna na karya. Ina zaune har aka fara kiran sallar azahar. Na idar kenan sai ga almajiri yana kwankwaso kofar shigowa wajena. Da yake ni ce a farko su kuma su Mama na can ciki. Bamu ha'da komai ba, sai kofar shigowa gidan. Da sauri na fita na bu'de masa. Ya mik'o mini flask din abinci babba mai kyau. Wai wani ne ya bashi ya kawo wannan kofar. Na kar'ba ba tare da na ce komai ba. Na sani abincin da ya ce za'a kawo mini ne. Sai da na zauna a falo na bude na ga alalan gwangwani ya ji manja. Da alamun kifi a ciki. Na ji wani iri a dalilin yunwa nake ji ba ka'dan ba. Ni kuma bana iya cin alala na koshi. Tabbas an gyara shi ne dan a burge ni. Na rufe, ina sake jin yunwa na taso mini gadan gadan. Na yi shiru ina nazari. Sai na ji wayata na k'ara. Ina dubawa na ga Tijjani ne domin ina da lambarsa tun lokacin kwamshina da muka fara dan gaisawa. Na ki amsawa har ta katse. Ya sake kira ban dauka ba. Bai fasa ba, sai a karo na hudu na dauka a fusace na kan ga a kunnena, bayan na danna alamar amsa wa. "Yaro ya kawo miki abinci?" "Eh". Na fa'da a gajarce. Ya ce "kin ci na safen kuwa?" "Wai ni kam jinjira ce ne da zaka dinga mini tambaya tamkar kankanuwar yarinya? Idan ma ban ci ba ai cikina ne ko? Tunda baka shawarce ni akan abinda zan ci ba, ka ajiye mini wanda ya yi maka". Ya nisa ya ce "Asiya Toro kenan! Cikin kuka na ce "Komai zaka ce Allah na ganinka ai". A sanyaye ya ce "Kukan na menene Asiya?" Na sake tsananta kukan na ce "Akan me za'a kawo mini alala? Ni bana ci". Ya tausasa murya ya ce"Alalan gwangwani ne, saboda ke har kwai da kifi aka saka a ciki. Daga gidan abokina Abdul aka kawo miki fa, kema kuma kinsan matarsa mai tsabta ce". Da kukan na ce "To ni ina ruwana, ni dai ba zan ci ba, kuma yunwa nake ji tunda kunun ma ban iya sha ba, ya riga ya yi sanyi k'arara." Ya diririce ya ce "Ki yi ha'kuri bari na sa a kai wa Ummi macaroni da kayan miya sai ta daho miki yanzu. Hakan ya yi miki?" Na yi shiru. Ina harara tamkar yana wajen. Ya sassauta ya ce "Please mana Asiya ki ce to". A shak'e na ce "Yanzu d'aya da rabi. Idan ya wuce uku da rabi bazan ci ba, gara yunwar ta kashe ni". Ya dinga fa'din"Na gode sosai, bari na saka a kai mata yanzu. In sha Allah ba zai wuce hakan ba." Ya katse wayar. Na ri'ke wayar, haka kawai sai na tsinci kaina da mamakin yadda Tijjani yake rawar jiki a kaina. Gashi tunda na zo ban ta'ba yi masa wani alheri ko da ta magana mai da'di ba ce. Yadda ya lank'awasa harshe yana rarrashi tabbas yana yi ne tunda ga kasan zuciyarsa. Na fara gasgata sona yake yi ba sha'awa ba. Mintina biyar a tsakani ya sake kira. Na dauka bayan ta kusa tsinkewa. Da sauri ya ce "An tafi kai mata. Na ja mata kunne, na ce ta bar komai ta girka miki, tunda Nina sanya ta. Biyu da rabi zan aika a karbo mini. Dan haka zuwa uku za'a kawo miki in Allah ya yarda". Na yi shiru. Ya numfasa ya ce "Asiya ba ki ce komai ba". "A hankali na ce "Ina ji ai" Ya yi kasa da murya ya ce "Me zan taho miki da shi?" "Bana bu'katar komai na ka". A sanyaye ya ce "Shikenan, amma na siyo miki abin da nasan zaki yi murna". Na kyabe baki tare da fa'din "Hmm to ya yi". "Baki ce na dawo lafiya". A gajiye na ce "Tijjani ni na aike ka ne? Ka dame ni, in ta nine ma kada ka dawo". Kada na dawo Asiya? Saboda ke na yi tafiyar fa! Amma idan na dawo zaki ga ni". Ban bashi amsa ba na kashe wayata. Na ajiye ina jin wani irin abu da bansan menene ba yana mamayata. Uku saura na ji ana buga k'ofar. Na zari hijabi na nufi k'ofar. Yaro ne ri'ke da madaidaicin flash. "Gashi in ji wani a waje". Ya fa'da a hanzarce da alamu sauri yake kada ya yi latti tunda kayan Islamiya ne da jikinsa. Na kar'ba na tura kofar. Kicin ma fara shiga na dauko plate. Sai lokacin na lura da kwalin taliya, macaroni da galan din mai dana manja. Sai wani katon bokiti sosai mai murfi. Na bu'de na ga garin masara ne a tankade. Daga kantar kuwa an jere robobi masu dauke da kuka, kubewa daddawa da yaji. Sai kunshin bakar leda mai dauke da Maggi da onga da kuma gishiri. Na yi tsam da raina. Ina jinjina wannan kokarin. Na sani Kuma Babanmu baya irin wannan al'adar domin shima baya bari a dorawa ango hidima mai yawa. Na tabbatar a kaina aka fara irin wannan hidimar ni din ma saboda Tijjani ya yi. Daga can gefe na sake hango buhun gishiri a cike amma kuma d'aure bakin aka yi. Na saka hannu na ta'ba na ji don na tabbatar ba gishiri ba ne. Ina tabawa kuwa na gane shinkafa ce a ciki. Na girgiza kai ba tare da na furta komai ba. Na dauki abin da zan dauka, na fice. Na zauna ina cin abincin da ya yi mini da'di ya ji kifi da albasa. Na bu'de fridge ga mamakina sai n ganshi cike da pure water da lemon fanta da coke da kowanne zai yi shida. Take na fahimci katon daya ya siya aka hada masa kaloli. Na dauki ruwa da lemo na rufe. Ina ci ina nazarin yadda Tijjani yake ta rawar jiki a kaina. Wayata ta hau kuwwa. Kamar ba zan dauka ba sai kuma na dauka din. Da sauri ya ce "Network dina ne ya dauke. An kawo miki abincin, kin ci?" A shak'e na ce "Ni ban ci ba, yaji ya yi yawa, ga shi salam babu gishiri ko maggi ne oho". Ya diririce ya hau fa'din "haka Ummi zata yi mini? To a kawo miki yoghurt. Kafin na dawo na miki girkin da kaina". Na yi shiru. Cikin rarrashi ya ce "Pls Asiya Toro". Na tunzura na ce "Ai da zaka bar Toron baka tuna da cikina ba. Saboda bani da daraja. Akan me yanzu zaka fitine ni da buge bugen waya da tambayar na ci abinci ko ban ci ba. To bazan ci ba, idan na mutu ma ai baka da asara." Ya harzuka ya ce "Botsarriyar yarinya kawai! Ana taro ki, kina sake nausawa, to kar ki ci din. Allah ne shaidar na yi bakin kokarina". Ai kuwa na zunduma ihu tamkar gaske. Na katse wayar. Ya dinga kira amma naki d'agawa. Ya kira ya kai sau biyar ina gani ban dauka ba. Daga can sai ga text message. Kamar bazan bu'de, sai kuma na bu'de din. "Asiya Toro ki ji tausayina! Ki daina mini irin haka. Kinsan yadda zuciyata take bugawa a dalilin kukanki da kin daukar kirana? Ki yi ha'kuri bazan sake yin tafiya na barki hakan ba. Kuma indai na iso lafiya da kaina zan dafa miki komai kike so". Jikina ya yi sanyi. Tsawon lokaci na kasa gane yanayina, tausayi ya bani ko kuwa mene ne? Na bu'de what'sapp na ga anan ma ya turo mini sakonni. Na kasa bu'de wa domin bana son na sake jin fiye da kasalar da nake ciki. Da yamma lis sai ga shi ya dawo. Na bu'de masa kofa ya shigo dukkan hannuwansa ri'ke da ledoji. Ban yi yun'kurin kar'ba ba. Da walwala ya ce "Asiya Toro babu oyoyo sai kallo mai kama da harara?" Na gintse fuska na yi gaba, na bar shi. Ya biyo ni falon dana shiga. Ya ajiye mini a gabana. Ya fita da sauri sai gashi ya kinkimo kwanon satellite ya ajiye a tsakar gidan ina hango shi ta windo. Da'di ya yi matu'kar kama ni. Domin na kagu na fara kallo. Ya sake fita ya dawo rungume da kwali a kirjinsa da na yi zaton receiver ce. Dayan hannun kuma leda ne. Na yi maza na gyara zamana na yi kamar harkokina kawai nake yi. Ya shigo da sallama na amsa a hankali. Ina mamakin yadda Tijjani yake da yawan sallamah. Ya zauna a kasa a gabana tamkar uwargida da yaronta. Amma girmansa da cikar haibarsa ya sanya bai yi kama da yaron gida a gabana ba. Tunda ni din yar mitsil ce. Yanayinsa yafi kama da na wadda yake neman a amince masa, a gamsu da lamarinsa. Da barin jiki ya tashi ya dauko roba a kicin, da yar wuka hadi da bowl karami irin plastic din nan mai k'wari. Ya debo ruwa a cikin robar. Ya shigo, ya bu'de ledar da tafi kusa da ni. Apple ya ciro guda biyu ya wanke a cikin ruwan, ya saka su a bowl din tare da yar wuk'ar ya miko mini ya ce "Fara da wannan Asiya. Ki rage yunwa kafin na gama miki abincin. Maghariba ta kawo kai sai na dawo daga sallah zan d'ora miki. Me kike son ci?" Ban kar'ba ba, ban kuma tanka ba. Ya ce "Ki kar'ba mana, me yasa kike yi mini haka ne?" Yadda ya yi maganar a dan tunzure, bansan ya aka yi ba, na tsinci kaina da mika hannu na kar'ba. Ya sassauta ya ce "ko na yanka miki?" Ban amsa ba, illah hannu da na saka a cikin robar na wanke. Sannan na dauki Apple din na fara gutsura da bakina. Ya zuba mini ido yana kallon yadda nake cinsa cikin yanga tamkar me cin magani. Ya murmusa ya ce "Yabi yanga". Karon farko da kunne ya ji ya kira ki da Yabi. Na dauke kai na ce "Tsabar adawa da kake yi da hajjina shine ba zaka ce Yabi ba. Yau kuma da bakinka ya subuce ka fa'da din sai da ka ha'da da bita da k'ullin yanga?" Ya fashe da dariya sosai ya ce "Kamar kinsan subutul kalam na yi. Tun fil'azal nafi son ce miki Asiya domin sunan na matu'kar burge ni. Yanzu kuma tunda Jabir haka yake ce miki, na sake kauracewa sunan. Bana adawa da hajjinki, amma fa bazan kira ki da Yabi ba. Ina fatan na samu damar da zan kai ki sauke faralli Asiya. Sai ki zama Hajiya ta sosai tunda hakan shine burinki." Na dauke kai, na gutsuri apple na ce "Da wanne ku'din zaka kai ni Makkah? Ai indai ina tare da kai babu wani alherin da zai same ni, bare alheri irin na zuwa Saudiyyah". Tsawon lokaci ban ji ya ce mini komai ba. Na juyo da kallona gare shi. Na ga jikinsa ya mutu. Duk kuzarin da ya zo da shi ya gudu. Gaba'daya ya zama tamkar an kwara masa ruwan sanyi. Ni kaina sai na ji jikina y mutu lakwas. Tsawon lokaci muna haka tamkar masu zaman makoki. Da k'yar ya yun'kura ya mike ya ce "Na tafi masallaci". Na bishi da ido, ina jin abin da nake ji a kansa na sake mamaya ta. Na kasa gane tausayi yake bani ko kuwa menene? Nasan dai ko ka'dan babu digon sonsa a raina. Da zai dawo ya shigo da k'aramin gas (3kg). Daga bakin kofar falon ya tsaya bayan ya daga labule ya ce "Me zaki ci Asiya?" A hankali na ce "Ni na koshi, akwai macaronin nan a kicin". Bai ce komai ba. Ya saki labulen. Da kansa ya zubo abincin. Sai dai wannan karon a kujerar nesa da ni ya zauna. Bayan ya dauko ruwa da lemun coke. Na kalle shi tamkar wani mai wadata ya hakince ya saka ruwa da lemu a gaba. Ya kammala, ya dube ni bayan ya ha'diye fishins ya ce "Ki dinga jin tsoron Allah Asiya. Yanzu abin da kika yi ya yi daidai kenan? Ki saka na k'ira Ummi na balbale ta da sababin bata yi mini aikin da na saka ta da kyau ba. Ashe ma kin ci kin cika cikin ki, tsabar fitina, da son ki tayar mini da hankali shine ya sanya kike kuka da fa'din abincin bai yi da'di ba?". Na zum'bura baki, na kasa cewa komai. Ya yi k'wafa, bai ce komai ba. Ya sauko ya zauna kan kafet din ya bu'de reciver ya ce "Gashi na siyo miki." Ganin ban amsa ba ya sanya ya cigaba da bude ledojin da ya shigo da su. Kusan duk kayan abinci ne dangisu shinkafa, taliya da macaroni. Sai katon din indomie da kayan shayi. Sai kuma leda mai dauke da sabulun wanki da su omo, makilin da maganin sauro na kunnawa. A hankali ya ce "Ku'din da abokaina suka ha'da mini ne na siyo miki settlite da gas, shine na karo kayan abinci dan mu dan tura sosai kafin su kare." Na juyar da fuskata na ce"Madallah". Ya yi sororo murya a dakushe ya ce "Ba zan yi wani abu da niyyar na sanya ki farin-ciki ki nuna mini kin ji da'di ba Asiya?" Cike da iyashege na fara wage baki, dukkan hakorana a waje, ga idona na zazzarosu tamkar mai motsi a k'wak'walwa. Ina yin hakan, ina cewa "Na yi murna Tijjani. Ka burge ni Tijjani, na ji da'di Tijjani". Sannan na dawo yanayina na zuba masa ido na ce "shike nan?". *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* ✍️ *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES*. *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. *Domin kuwa asalin saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* Ya girgiza kai, bai ce uffan ba, ya tashi ya kwashi kayan abincin ya nufi kicin da su. Ina hangen sa ya dauko farantai ya juye kayan miya da ya barsu a tsakar gida. Ashe har da doya guda uku manya. Sai da ya jide ya adana komai. Sannan ya daga murya ya ce "Zan je sallar isha." Bai jira amsata ba yasa kai ya fita. Na tokara na dauro alwallah dan nima na sallaci isha. Na idar na jima a zaune sannan na shiga daki na yi shirin wanka. Na fito na shirya a nutse. Na dawo falo da nufin na sha ruwa. Aka dawo da wuta. Na kalli receiver dokin a ha'da mini ita ya kama ni. Ina tsaye na gan shi ya dawo, na tsinci kaina da lekensa ta windo. Na ganshi da bargo irin mai sau'kin ku'di da kuma pilo guda daya. Kai tsaye dakin da kayansa suke ciki ya shiga da su. Na dan ji wani iri. Na tsinci kaina da tambayar kaina da cewar wato bai damu sai ya zo dakina ba. Duk da k'arancin shekaruna ni din ma'abociyar karatun littafan Hausa ce mussaman da nake da babbar waya nake karatun littafan online. Ina ganin yanayin yadda angwaye basa daga kafa a wannan fagen. Sannan da yawa an yiwa kawayenmu aure da muka kammala k'aramar sakandire, muna jin labarin zumudin angwaye. Amma shi wannan ko oho. Nan da da nan zuciyata ta baci a dalilin na hakaito*BAKAR TA'ADAR* Da ya saba yake yi! Na ji tsanarsa ta sake tsananta a zuciyata. Na dinga jan tsaki. A haka ya shigo ya same ni. Ya miko mini leda ya ce "Ga shi". Na juya baya ba tare da na kalle shi ba, bare na kar'ba. Ya iso kusa da ni ta yadda muke jin hucin juna. Kamshina ya mamaye wajen, da ace yana shafa turare da sun cakude sun bada kamshi na mussaman. Baya wari, amma kuma ana dan jin tsamin maza ka'dan a tare da shi, wanda rashin tu'amalli da turare ke sababawa. Takaici ya sake k'ume ni. Hawaye ya cika mini ido. Ya nazarce ni. Ya nisa ya ce "Wai menene haka kike mini? Tsabar tsanarsa sai na ji hucin bakinsa mai bashi ne. Zuciyata ta taso na ji tamkar na sheka amai. Na fa'di kan kujerar da bayana na fashe da kuka sosai. Ya matso da sauri da nufin rike ni, na k'walla k'ara sosai. Ya yi maza ya janye hannunsa ya fasa. Ya sassauta ya ce "ki daina yi mini irin haka Asiya. Ubangiji ya sanya mini k'yamar na ji kukanki. Fa'da mini me nake yi miki?" Tsawon lokaci yana dakon amsa ta. Ya kosa da shiruna ya ce "Ki yi ha'kuri komai zai dai-daita mana". Cikin matsanancin kuka na ce "Wallahi ba zai daidaita ba. A hakan ne komai zai dai-daita? Dube ka dan Allah! Ni gaba'daya baka burge ni". Ya murmusa ka'dan, ya mike ya ce "Wata rana zan burge ki In sha Allah". Har ya kai bakin kofa ya ce "Ki ci nama ne, idan kuma ba zaki ci yanzu ba, ki bu'de shi domin akwai albasa a ciki kada ta lalata shi. Ki kara ha'kuri Asiya". Ina ganin ya fice na dinga kuka sosai mai dafa zuciya. Ina jinsa yana ta kiciniyar jawo ruwa a rijiya. Bayan kamar mintina talatin ya dawo ya zauna kusa da ni. K'amshin sabulun wanka kawai na ji a tare da shi ba na turare ba. Cikin rarrashi ya ce "Kuka har yanzu Asiya? Ba zaki yi hakuri ba! Ko wanne bawa da kaddararsa, ba ke ka'dai ba ce, ki tsananta addu'a." Cikin kuka na ce "Addu'a sau milyan nawa zan yi? Ai kaine matsala ta ni kam." Ya yi shiru can ya ce "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Na mike da sauri na bar shi a wajen. Ina shiga d'akin na rufe kofar da k'arfin gaske. Na jima kafin barci ya sure ni. Bansan yadda ya kare a inda na bar shi ba. Washagari kuwa tunda na yi alwallah da asuba da na rufe kofata har shad'aya ina kwance duk da ba barci nake yi ba. Sau biyu yana kwankwasa k'ofar. Amma na share shi. Ban fita ba sai wajen shabiyu da rabi. Shima uzzirin shiga band'aki ne ya uzzira mini. Kan dole na yi shirin wanka. Na fito na tarar da shi a saman katanga yana ta daura kwanon setelite. Ya ha'da zufa sharkaf. Na ja tsaki na shige band'aki. Abin mamaki sai na tarar bayan robar band'akin da take a cike. Ya cika mini botikin wanka ya ajiye a inda ya saba ajiye mini. Na yi shiru ina wasi-wasin yadda saurin fishi irin na Bulkachuwa baya yin tasiri akan sha'anina. Na hakaito yadda yake ta ha'da zufa wanda na tabbatar dan ni yake yi. Abin da nake ji mai kama da tausayinsa ya sake tsananta a tare da ni. Bansan me yasa idan yana kusa da ni nake jin zafinsa ba. Amma ga dukkan alamu rashin iya wanka da gayunsa na cikin cikas dinsa a wajena. Na gama uzzirin na yi wanka sosai. Sadda na fito a falo na hango shi ya kunna talabijin yana ta kokarin saita tashoshi. Na shirya tsaf. Kamshina ya cika dakin. Na hau kakkade dakin. Haka kawai sai na ji tamkar ana kallona. Na juyo ai kuwa sai ganinsa na yi yana jingine da bango ya yi mini zuru. Na b'ata fuska na juya na cigaba da aikina. Ya shigo ya ce "Asiya me zan miki ki daina mua'amalanta ta irin haka? Ko arzikin gaisuwa bani da shi a wajen ki? Me ya yi zafi ne?" Na share shi. Ya tausasa harshe ya ce "Burodi na siyo. Na dafa shayi, na kawo nan, ko zaki fito falo? Da kin daure ma, sai ki zo falon kina karyawa kina kallon tashar da kike so". Ban d'ago ba, na ce "Kallo bai dame ni ba." Ya yi shiru na sakwanni sannan ya saki ajiyar zuciya ya ce "Bari na kawo miki nan to". Ya fita ba tare da ya jira amsa ta ba. Bai jima ba, ya shigo da da biredi da robar butter. Ya ajiye, ya sake juya wa. Ya dawo da kofi yana turiri. Ya ajiye a gabana. Na kalli shayin na ga hadin kauri ya yi masa na sosai. Amma wani sashe na zuciyata ya k'alubalanci had'awar da ya yi. Akan me ba zai kawo mini na ha'da da kaina ba kamar yadda ya mini jiya da shekaranjiya ba? Take na yarda wani k'ullin ya shirya mini. Ya zauna daga k'asa da rarrashi ya ce "sauko ki sha kada ya huce nasan ba kya son shayi idan ya huce." Na zo na zauna kamar da gaske shan zan yi, na dinga juya cokalin cikin shayin. Ya zuba mini ido yana kallon yadda gown din material din Umm Nihla kalar k'wanduwar k'wai ta karbi farar fata ta, dinkin kuma ya yi kyau sosai ya zauna mini. *Umm Nihla mazauniyar Malaysia ce, daga can take turo kayanta masu aminci da rahusa zuwa Kano* *Tana bada daya tana bada sari yadda ke ma zaki sami alheri* *Tuntube ta manhajar Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa* *07020695644* Ba zato kawai na tuntsurar da shayin. Nan da nan kuwa shayin ya fara gangarawa inda yake zaune. Ya zabura ya tashi. Ko ban kalle shi ba na sani ya kai k'ololuwar fusata tunda ya ga ba cikin kuskure ya zube ba. Murya na rawa irin ta tsananin b'acin rai ya ce "Wanne irin wula'kanci ne haka? Idan ba zaki sha ba, ki bar mini mana. Almabozaranci babu kyau. Kin yi dan ki b'ata mini rai, ki saka ni ba'kin ciki! Tabbas hak'kar ki ta cimma ruwa. Raina ya baci k'warai da gaske. Sai dai ki sani, bazan sake yi miki irin wannan kyautatawar ba. Yau kwanan ki uku a gidan nan. Daga yau kin fita daga bakunci a ka'idar shari'a. Dan haka ki fito ki dora abincin rana yunwa nake ji, ko kuma na bar ki da Ubangijin da ya wajaba miki yi mini biyayya". Na fashe da kuka sosai domin ban zaci abin da zai biyo baya ba kenan. Tun fil'azal na tsani ace za'a bar ni da Allah. Cikin kukan na ce "Akan me zaka ha'da mini ba a gabana ba? Na sani ko ka jefa mini wani abu a ciki". Ya ja tsaki mai tsananin gaske. Ya ce "oh ina ganin tala jaurar duniya. Wai ke nan kina zaton zan miki wani abu a dole? Ya girgiza kai ya ce "Babu macen da zan mata hakan. Sai kuma ya fashe da dariya mai sauti sosai. Da murmushi ya ce "Asiya Toro manyan mata. Ki yi ta abu tamkar wata babbar mace. Dan Allah duka shekarun ki nawa ne? Kin wuce sha biyar? Ni kallon kwaila nake yi miki wacce bata gama fitar da halittun ta ba. Wacce bata kai wankan girma ya hau kanta ba. To me kike zaton zan miki da har zan baki wani abu na rashin gaskiya a cikin abin sha?" Ba'kin cikinsa ya sake makure ni. Na sake fashe wa da kuka mai tsananin gaske. Ya sa kai ya fice yana jaddada idan ban zo na dafa masa abin da zai ci ba, ya bar ni da Allan da ya kallafa mini yi masa biyayya. Na jima ina zaune ina kukan ba'kin cikin takaicin da ya cusa mini. Ga cikina sai kiran ciroma yake yi. Ala tilas na tashi na fita bayan na goge fuskata da tissue. Har lokacin yana ta faman hade wayar satellite din a jigin bango. Na wuce shi fuu na fa'da kicin din. Na tsaya ina nazarin me zan dafa ne? A yadda nake jin yunwa zan fi son jalaf din taliya mai dan ruwa ruwa. Dan haka na zabi kayan miyan da suka fara yin laushi na wanke na fara jajjege dan na rasa inda gireta take, duk da akwai wuta zan iya blanding dinsu. Sai dai na fi son na gansu a jajjegen. Na yanka albasa mai yawa. Na bare maggi duk na ajiye a kusa da ni. Na tashi na daurayo tukunya, ya kalle ni, na galla masa harara. Ya yi murmushi tare cewa "The great Asiya a kicin dinta". Na share shi, na shiga falo na dauko naman da ban ci ba a fridge. Na duba na ga ya cire albasar ciki. Na nufi kicin din. Na zuba mai a tukunya. Na zuba albasa. Na jere komai na bu'kata a gabana. Na kalli gas din da yake tsaye sabo dal da shi. Na fara tunanin yadda zan kunna tunda zancen gaskiya ban ta'ba kunnawa ba. Bamu taba amfani da shi a gidanmu ba. Na yi shahadar murda wa sannan na fara kokarin kyasta ashana. Sau biyu ashanar tana karyewa saboda rashin k'warinta. A karo na uku ta k'yastu, na nufi bakin gas din da ita. Ai kuwa gas ya yi wani irin but da karfin gaske! Na furgita, na tsora ainun, na mike na dinga karo da fatali da kayan da na jere a gabana na yi waje a guje cikin ki'dima mai yawa. Ya fito a band'aki ke nan, ya gan ni a guje na yi dakina. Ya biyo ni da sauri. Fa'di yake "mene ne, mene ne?" Ya zuba mini ido yana kallon yadda jikina yake kyarma irin na tsoro sosai. Da sigar salama ya ce "Asiya! Nutsu ki fa'da mini. Mene ne ya ki'dima ki haka?" Ganin na kasa magana ya tashi ya nufi kicin din. Ya tsaya a bakin k'ofar yaga yadda ruwa ya jiqa kasan kicin din. Komai a wancakale tabbacin ta kansu ta bi. Ga gas kuma yana ta yi fahh. Ya rage karfinsa. Sannan ya dora sanwar. Domin ya saba girki tun yana makaranta. Ya gyra wajen. Bai bar kicin din ba sai da ya tsaida ruwan girkin tunda ya ga taliya ta yi niyyar dafawa. Ya koma ya zauna kusa da ita a bakin gadon. Zuwa lokacin ta dan shiga nutsuwar ta. Ya sassauta ya ce"Asiya wai mene ne? Kadangare kika ga ni ko tsaka?" Na zum'bura baki na ce "Wutar abin nan ne ta yo kaina gaba'daya". Ya kwashe da dariya sosai. Hakan kuma ba karamin kular da ni ya yi ba. Cikin bacin rai na ce "Yi dariyar ka son ran ka Tijjani, ai ko k'onewa na yi baka da asara tunda ba sanin darajata ka yi ba". Na fara hawaye. Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi. Nan da nan ya gintse dariyar da yake yi. Ya ce "Very sorry Asiya Toro. Abin ne ya bani dariya yadda kike yar gayu kuma wayayyiya amma gas ya yi miki wula'kanci irin haka?". Sai kawai ya sake tintsire wa da dariyar da ta fi ta farko k'arfi. Ba'kin ciki har mak'oshina nake jinsa. Na rasa me zan yi na sanya takaici akan zuciya da fuskarsa. Kafin na yi magana ya yunkura ya tashi a dalilin kamshin da ya fara cika hancinmu wanda alamu ne na ya tafaso. Bai dawo dakin ba, sai da girkin ya kammala. Ya dawo da plate biyu a hannunsa. Ya dire a k'asa, ya sake fita. Kaamshin girkin ya cika d'akin, hakan ya sake sabunta mini yunwar da nake ji. Ya dawo dauke da pure water da lemo akan tire. Hannunsa kuma da fork guda biyu. Ya zauna ya ja plate daya gabansa ya bu'de murya ya ce "Bismillah Amarya". Na bata rai na ce " Asiya Toro dai. Ina na kai darajar amarya bayan ni din yarinya ce kwaila kuma kankanuwa". Ya murmusa ya ce "Oh wai maganar ciwo ta yi miki ne? Tsakani da Allah ba gaskiya na fa'da ba? " Na girgiza kai ba tare da na kula shi ba. Na sauko na ja abincin da yake jirana. Na kai bakina duk kushena ban isa na ce ga inda girkin yake da tasgado ba. Na dinga zura loma. Sai da ya ga na kusa cinyewa ya kaikaice ya ce "Asiya Toro iyashegen ki yawa gare shi. Jibi yadda kike zabga loma kina zare ido. Me ya janye tunanin zan zuba miki wani abu a ciki Kuma? Kunya ta kamani ka'dan. Amma na daure na yi kamar ban ji komai ba. Na share shi. Sai da na gama na yi gyatsa, na kalle shi na ce "Na tabbatar da Yaya J ne ya dafa abincin nan, zubowa zai yi a waje daya. Sannan ya manta cikinsa har sai ya tabbatar nawa cikin ya cika." Na saci kallonsa na ga har wata zufa ce ta karyo masa. Zuciyata ta fara harbawa da tunanin hukuncin da zai yi a dalilin yadda yanayinsa ya nuna maganar ta buge shi. Ga mamakina sai kawai ya yi yak'e ya ce "Ba ki yi karya ba Asiya! Domin jiya mun je gidansa ni da Salisu a dalilin an sace mashin dinsa. A gabanmu ni da Salisu yake tarairayar Maijidda akan ta daure ta ci ayaba. Kinsan cikinta ya tsufa ba komai take iya ci ba. Ai Jabir kam yana mutuntunta maganar tsohonsa akan Maijidda. Sosai yake sonta yake tattalinta. Har mamaki na dinga yi tare da shakkun idan har ya taba son wata mace kafin ita. Ita ma bata jin kunyar mu din yayunta ba ne sai tabara take yi masa son ranta. Take na gano mata irinsu ba zasu ta'ba barin mijinsu ya yi tunanin wata macen ba. Wanda duk ya samu irinsu ya gama morewa, ga cikar halitta ga shagaba ga kuma biyayyar iyaye da aure. Wanda bai samu irinsu ba ai zai dauwama cikin cizon yatsa ne. Sannan tagomashin biyayyar da suka yiwa iyayensu ya sanya gidansu ya zama gidan farin ciki." Maimakon na b'ata masa rai, sai ya zamana nawa ran ne yafi b'aci. Bayan kod'a Maijidda da ya dinga yi, tare da kwarzanta ta, sai na fahimci yarfe yake yi mini akan ban yiwa nawa tsohon biyayya na mutuntata aurena ba. Na yi shiru na kasa cewa uffan. Ya gaji da jiran kalamina, ya tokara ya tashi. Bai dauke kwanon da ya ci ba, bare ya ha'da da nawa. Ya bar gidan ba tare da ya yi mini sallama kamar yadda ya saba ba. Tun da ya fita bai dawo ba, sai bayan sallar isha. Ga mamakina sai na ji haushin hakan. Rashin dawowar tasa ta mintsinin zuciyata sai dai ban bari ta bayyana akan fuskata ba. Ya leko ni, ina zaune a daki. Bai shigo sosai ba. Ya ajiye mini leda ya juya bayan ya ce "Sai da safe". Bansan ya aka yi ba kuka ya k'wace mini. Ni da kaina ban san dalilin kukan ba. Amma so na yi ya shigo yana lallaba ni, da ro'kon na ci abin da ya siyo, ina botsare masa. Ko duba ledar ban yi ba, na yi kwanciyata bayan na rufe k'ofar dakin. Cikin dare na tashi da wata azababbiyar yunwa. A gigice na janyo ledar na hau cin awara irin manyan nan ga kabeji. Da k'yar na iya janyo leda a lungun gado. Maman kawata Shafa'atu ce ta je Kano ta siyo yajin Annur food mai dan karen dad'i. Shine ta ba ni roba d'aya. *Annur food Delicious* *Ba iya yaji ba har da garin danwake da man Shani, da yajin daddawa* *Tuntube su a wannan lambar dan k'arin bayani 08039183880*. Na sani sadda ya kawo da zafinta. Sai da na cinye tas, sannan jikina ya daina rawar yunwa. Take na tuno ashe jiya iya taliyar nan kawai na sanya a bakina. Na jima barci bai dauke ni ba. Sai kawai na yanke shawarar na doro alwallah na yi nafilah. Na mike ina da tabbacin Gwaggo na kan sallayarta a irin wannan lokacin da bayi suke barci. A hankali na zare sakatar na fita. Abin mamaki sai na ga Tijjani akan barandar yana sallah. Yana sujjada. Na dakata ya idar tunda ba zai yiwu na wuce ta gabansa ba. Na jingina da kyauren kofar dakin nawa. Ina kallon yadda ya kyautata sujjadar. Tsawon lokaci bai dago ba. Wani abu ya sake tsirga mini a kansa. Na tuna a duk sadda Gwaggo ta tashe ni cikin dare dan mu yi nafila. Cewa take yi daure ki tashi ki nemi yardar Ubangiji Yabi. Irin wanna lokacin sai zababbun bayi ne suke rabauta da yin ibada. Duk kuma abin da mai yin ibadar dare yasa a gaba sai ya ga sau'kinsa. Allah da kansa yake saukowa sararin subhana yana shelar ina mai bu'kata na biya masa?" Zuciyata ta sake harbawa domin ni kaina da bana son Tijjani. Kallonsa yana sujjadar nan sai da na ji wani irin abu, to ina kuma Ubangijin da ya kyautata sujjadar saboda shi. Har lokacin kuma bai dago ba. Na sake tuna jawabin Gwaggo da take fadin kada ki ce sai kina cikin damuwa ko bu'kata zaki yi sallar dare. Domin idan ta zame miki dabi'a, to lah shakka duk wata bak'ar k'addara da zata zo miki, sai ta zo da sau'ki, sannan komai kika roka zaki ga biyan bu'kata duk nisan jinkiri. Ban da ma dai dan adam mai shagala ne, ai ya kamata ace yana yawan yin godiya ga Ubangiji bisa dinbin niimomin da ya masa. An yika musulmi, an baka lafiya, an kuma hore maka abin da zaka ci komin kankantar sa. Ashe kuwa ba sai da damuwa za'a yi ibada ba. Na nisa ina jin na fara gajiya da dakonsa. Har zan koma daki sai kuma ya d'ago. Na dinka fatan ace sujjadar karshe ce ba zai koma wata ba. Ai kuwa sai na ga ya zauna, alamun attahiyatu yake yi. Ina ganin ya sallame na yi maza na wuce a dalilin fitsari ya kama ni ba ka'dan ba. Yana zaune har na fito na shige shi. Sai dai Ina wuce wa ya sake mikewa tabbacin dama ya jinkirta mini ne na wuce. Raka'a biyu na yi mai dauke da gajerun surori. Na yi yan adduoina. Ban san me yasa na kasa addu'ar da nake nacin yi ba. Na Ubangiji ya tarwatsa aurenmu. Na tsinci bakina da fa'din Àllah ka mini zabin da zai fi mini alheri. Karon farko da na yi addu'ar da dukkan zuciyata. Na yi addu'oi, na yiwa mahaifana addu'a, na ha'da da al'ummar ma'aiki. Na koma na kwanta ina fa'din "da wanda yayi doguwar sujjada, da wacce ta yi gajeriya, Allah dai ake yiwa, to Ubangiji ka karba mana gaba'daya". *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* ✍️ *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES.* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* Ina kwance ina jin dukkan k'uncin da yake raina yana zagwanye wa da kaso mai yawa. Ban makara sallar asuba ba, a dalilin ya buga mini k'ofa na tashi. Wajen k'arfe takwas da rabi na ji ana kwankwasa k'ofar dakin. Na tashi na bu'de. Na gan shi a tsaye. Ya kalle ni ya ce "Ki zo ki d'ora mini abin karyawa na fara jin yunwa." Na yun'kura da nufin na yab'a masa bak'ar magana. Amma ina ganin yadda ya d'aure fuskar . Sai ya yi mini kwarjini sosai. A sanyaye na kawar da fuskata na ce "Ni bazan sake kunna shi ba". Ga mamakina sai ya sassauta ya ce "Wanko fuskar ki zo na kunna miki. Ai jiyan ma shi kika fara kunnawa kafin ki kyasta ashana. Sa'a ma kika yi ai da gaba'daya jkinki zai bi. Na sake tsorata na ce "gaskiya ka siyo mini gawayi. Idan baka nan wa zai kunna mini?" Ya murmusa ya ce "Zaki iya a hankali." Ya dakata na yi brush, na wanke fuskata, sannan muka nufin kicin din. Cikin nutsuwa ya ce "Sai kin gama hada komai na girkin ki, sai ki kyasta ashana sannan ki murd'a gas din ki. Amma a fara kunna gas da sakwanni kafin a k'yasta ashana hatsarinsa yafi na had'arin mota muni." Ina tsaye ya kunna. Sannan ya fita yana cewa "Sai ki dora abin da zaki yi". Na yi jim ina nazarin abin da zan yi. Sai kuma na yi azamar daukan tukunya na dauraye na d'ora bayan na zuba citta da kaninfari. Na sake nutsawa cikin nazarin me zan yi ne. Idona ya sauka akan doyar da ya zo da ita. Na dauko wuka na yanki ka'dan tunda manyan ne sosai. Ina gama ferewa shayin ya tafasa. Na juye, na mayar da doyar. Ina zaune ina fatan na soya doyar nan ta yi kyau. Zancen gaskiya ba saba soya doya da kwai muka yi ba. Amma kwanaki mun kalla a wata tashar girke girke a YouTube mun gwada a gidan Nazira kuma ta yi kyau. Na dudduba na ga babu k'wai a kicin din. Na fita na gan shi yana ta faman janyo ruwa a rijiya. Na cuna baki na ce "Kwai za'a ba ni". Da walwala ya ce baki kula da shi a fridge ba?" Ban ce komai ba. Na koma kicin na dauko bowl, na nufi falon da shi. Na debo guda hud'u. Cikin ikon Ubangiji na kammala aikin lafiya, kuma ta yi dadi da kyau, k'amshi ya cika gida. Na zuba masa a plate mai zurfi irin na dafaffiyar roba, na dauko robar yaji na zuba masa a gefe. Na dauki flask din shayi na kai masa falon. Na dawo na dauki kofin shayi da cokali da kuma cokali mai yatsu, na kai, sannan na rufe nawa a kicin din da zummar sai na yi wanka. Na fito, na ga ya yi wanka ya shirya yadda ya saba. Ma'ana kaya babu guga. Takaici ya mak'ure ni. Nan da nan idona ya kad'a a dalilin tausayin kaina da ya kama ni. Ni d'an gayu nake so wanda ya iya wanka da soyayya ba marar kintsi irin Tijjani ba. A shak'e na ce masa "Na ajiye maka a falo". Ya share tamkar bai ji ba. Na shige band'akin na rufo kofa da k'arfin gaske. Ya yi sakare domin ba karamin haushi ya ji na wannan tumbatsar da take yi ba. Sannan ta yi magana tamkar da yaronta, bugu da kari ta buga masa kofa tabbacin raini na gaske ta yi masa. Ya ha'diye bacin ran da ya taso masa. Ya isa falon, ya tarar da wani sabon bacin rai. An ajiye masa abinci a bude babu sayawa. Sannan duk farantan tangaran din da ya ga ni ta kasa zuba masa a ciki ta rufe sai a wnanan? Duk yadda doyar ta yi masa kyau a ido, ga kamshin da ya cika hancinsa. Duk irin yunwar da yake ji sai ya ji ba zai iya cin doyar ba. Ya mik'e ya fice ya bar gidan gaba'daya. Na fito na shirya tsaf. Sannan na shiga falon da nufin kwashe kayan sannan na zubo nawa. Sai ganin abincin na yi yadda na bar shi. B'acin rai ya sake baibaye ni. Wato dama ba yunwa yake ji ba? Tsabar k'yashi da adawa da barcina yake yi kawai? Na ja k'wafa. Har zan zauna na cinye, sai kuma na yi tunanin ko sallamah aka yi da shi, ko kuma wani uzziri ya fita, zai dawo ya ci. Na zuba nawa abincin, har na gama bai shigo ba. Dan hakan na dauke, na kai kicin na rufe. Amma zuciyata tamkar ta fa'do k'asa. Na hau shara, ina yi, ina hawaye tare da tir da auren dole. Ina cikin mopping barandar ya shigo da leda a hannunsa. Kai-tsaye dakinsa ya fa'da jim ka'dan na ji yana fa'din"Asiya Toro". Kamar bazan amsa ba, sai kuma na amsa d'in tare da ajiye aikin na nufi inda ya ke. Daga ba'kin k'ofa na ci burki a dalilin yadda kuka yake neman k'wace mini. Ganinsa na yi yana cin masa da k'uli k'uli ga kunun gyad'a a leda yana zuk'a. A tausashe ya ce "Samo abu ki diba idan zaki ci". Na rasa inda zan saka raina, da ba'kin cikinsa. Murya na rawa na ce "Dama ka katse mini barci dan kawai ka saka ni aikin da ba ci zaka yi ba?" Cikin rashin damuwar komai ya ce "Ci zan yi mana". Na kasa bu'de baki na ce uffan, na juya ina jin tamkar na yi ta rusa ihu da kururuwa. Kirjina ya yi nauyi ainun. Na dinga hawaye ina share wa. Tsawon lokaci ina zaune akan barandar nan, na kasa cigaba da aikin. Ya fito da ledar ya kai shara. Ya wanke hannunsa, ya kalle ni ya ce "Sai na dawo Asiya Toro". Ko kallonsa ban yi ba, bare na tanka masa. Shima bai tsaya ba, yasa kai ya fice. Na dinga kuka tamkar dukana ya yi. Yini na yi akan barandar nan. Ina kaico da auren Bulkachuwa. Sallah kawai nake tashi na yi. Sai da na yi sallar la'asar yunwa ta uzzira mini. Na ha'da shayi mai kauri na kwankwada. Ina kallon doyar da ya bar mini bai ko taba ba, amma ban ci ba. Sai bayan isha sosai ya shigo. Hakan ba karamin sake fusata ni ya yi ba. Ina zaune a dakina ido ya yi jawur, ya kumbure saboda kukan dana yini ina yi. Da azama ya iso gare ni yana fa'din "Asiya Toro me ya same ki, kin ga yadda kika zabge kuwa? Ga idon ki tamkar mai fama da matsanancin ciwon apolo. Mene ne yake damun ki?" *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* Da zafin rai na ce "Kai ne ka fitine ni, irin fitinar da ko maki'yata bana fatan a fitine ta irin haka." Na sake rushe wa da kuka tamkar an fa'da mini mutuwar mahaifina. Ya ki'dima ya ce "Me na yi miki? Fa'da mini dan Allah". Takaicinsa ya nemi sark'e mini numfashi. Na kasa magana illah hawaye da yake zuba tamkar famfo. Tsawon lokaci ya yi shiru yana sauraron shesshekar kukana. A sanyaye ya mike, murya babu amo ya ce "ki k'arantawa kan ki k'iyayya ta Asiya! Bai kamata ki kuntata wa zuciyoyinmu irin haka ba. Ki cigaba da addu'a da sannu komai zai wuce." Har ya kai bakin kofa ya ce "kin ci abinci kuwa?" Cikin fishi na ce "Bazan sake cin abinci ba, sai yunwa ta mayar da ni gawa In sha Allah! Ya girgiza kai ya ce "Babu laifi". Maimakon ya yi kwanciyarsa sai na ji yana ta buruntu a kicin. Shude war mintina talatin sai ga shi da bowl yana fa'din "Ki dubi Allah da ma'aiki ki tashi ki ci, ba dan ni Tijjani ba. Dan Allah". Na sassauta kukan domin Gwaggo ta cusa mana yin uzziri matu'kar aka ce saboda Allah. Ya zauna kusa da ni sosai ya miko mini. Cikin rarrashi ya ce "Allah ka yarda da Asiya, ka sata cikin bayin da ka yarda da su". Jikina ya yi sanyi. Na kar'ba, na fara cin indomien da ta yi da'di tamkar ba girkin namiji ba. Ni da nake fa'din bazan ci ba, sai gashi na share ta tas. Da hanzari ya karbi kwanon ya mik'o mini ruwan hannunsa mai rangwamen sanyi. Take na nemi jirin da nake ji na rasa. Na yi gyatsa. Sai kawai na gayra na kwanta. A hankali ya ce "da kin daure kin dan yi tattaki kafin ki kwanta". Ban kula shi ba, a haka barci ya sure ni. Bansan sadda ya tafi nasa makwancin ba. Washagari mirsisi na k'i yin abin kari. Bai matsa mini ba. Ya siyo kosai da kunu ya kawo mini. Kwanaki suka yi ta shud'e wa, har na samu sati a gidan aurena. Har lokacin kuma ban yarda na sake d'ora tukunya ba. Shi kuma ko ya yi fishi, ba ya jure ganina ban ci abinci ba. Kan dole sai ya nemo mini. Ranar da na cika kwanaki goma ya fara gazawa da al'amarina. Ga shi ku'din hannunsa sun tasar ma k'are wa. Ya zaunar da ni ya sassauta murya ya ce "Asiya yanzu a ce abincin da zamu ci ba zaki dinga girka wa ba? Kina kallon kayan miyan can da yawa sun lalace. Ya kike so na dinga yi ne? Idan na fita tun safe na dinga bulayin abin da zan yi na samu taro da sisi dan asirinmu ya rufu amma bazan dawo na tarar da kwanciyar hankali ba? Yini nake cikin zullumi da fargabar halin da kike ciki, da abin da zan dawo na tarar. Me yasa bani da wata alfarma ne a wajen ki?" Na zum'bura baki ainun. Tsawon lokaci ban ce komai ba. Ya numfasa ya ce "Pls Asiya na roke ki, mu zauna lafiya ki kwantar da hankalinki dan Allah". Tsawon lokaci ya dauka yana rarrashi, akan na ce masa na yarda zan dinga yin girki. Amma ban yarda na ce masa komai ba. Ya harzuka ya ce "Allah kai ne shaida ta." Ya tashi ya bar ni. A hakan na cike sati biyu. A wannan lokacin kuma aka fara zuwa mini lalle da kitso. Na rasa a inda zamu dinga zama. Domin tsakr gidan babu bishiya kuma babu rumfa. Baranda kuma idan rana ta bude babu dadin zama. Dakin da kayansa suke nan ne yafi dace wa ya zama dakin da zan dinga yin sana'a ta. Dan haka na shiga na tattara masa kayansa gefe d'aya, na kunna turaren wuta a dalilin kayansa masu datti na zube a k'asan. Na ha'da na d'aure su waje guda. Yini na yi ina lalle. Sai yamma ya dawo gidan da ledar abincin da ya siyo mini. Kallonsa kawai na yi, na gane ya ji haushin cika masa daki da na yi da mata. Ya ajiye abincin ya juya. Sai dare ya dawo lokacin babu kowa. Tuni kuma na share dakin na kintsa shi tamkar ba'a ciki muka yi ba. Fuskarsa a daure ya tarar da ni ya ce "Asiya Toro kada ki kuma shigar mini daki da nufin yin kitso ko lalle". Na cuna baki na ce "Idan na kuma fa?" Ya girgiza kai ya ce "To ki kuma din". Washagari da hantsi sai ga Rafi'a ta shigo mini. Da walwala na karbe ta. Ta dinga fa'din "Amarya ashe haka kika iya kunshi da lalle?" Da murmushi na ce "Ina koya dai, idan kina so sai ki zo na yi miki". Da babbar muryarta ta ce "Ai kuwa na gode sosai". Tijjani na fita na shiga d'akin muka fara yin kunshin. Kafin na gama mata har mutum ukun sun zo. Da azahar ya dawo gidan, ko d'ar ban ji ba, balle na yi fargabar na karya dokar sa. Ga mamakina bai shigo ba, bare ya dauki matakin da nake son ya dauka. Amma sai na ji ya bu'de murya yana kiran Rafi'a daga falon. Ita kuma ta shiga da saurin ta. Wani irin abu ya d'an mintsini zuciyata. Amma na sanya jarumta na boye abin dana ji din. Ina dan jiyo maganganunsu, har na fahimci sun saba dama tunda yayanta abokinsa ne. Bansan me ya ce mata ba, na ga ta fito ta shiga kicin. Abin ya sake buguna. Ban ankara ba na ji ta fara jajjage. Wata babbar mace da na gama sanya wa lallen. Ta kalle ni babu alamun wargi ta ce "Je ki karbi hidimar mijinki a hannun waccar yarinyar tun baki janyo wa kanki sanadin bacin rai ba". Na yi yak'e na ce "Ai tare muke da ita, k'anwarsa ce." Ta saki gauron numfashi ta ce "Tau ya yi babu laifi, na dauka babu sidi bare sadada a tsananinku. Amma dai kada ki fara saka wani lallen, tashi ki je ki marabce shi, ki bashi ruwa sai ki dawo. Ki kula da auren ki da kyau kin ji". Ganin ta haife ni, dan na tabbatar tana da yaran da suka zarta ni. Hakan ya sanya na tashi na yi tamkar na je wajensa, nan kuwa dakina na shiga na zauna bakin gado. Tamkar mai jirana sai gashi ya shigo mini. Ya kaurara murya ya ce "Asiya Toro ba ki ji kashedin da na yi miki ba akan shigar mini daki da mata ba ko?" Na murguda baki na ce "Ban ji ba Tijjani! Ba kuma zan ji ba". Ya ce "Shike nan" Na riga shi barin dakin. Ina kallon yadda ta shirya masa abincin a tray, cikin flask mafi kyau a kicin din. Plate din na tangaran ta saka. Maimakon da ta kai ta fito, sai ta yi zamanta suna hirarsu. A daddafe na kammala lallen. Dan da wata ta zo ma ha'kuri na bata, na ce ina da ayyuka mai yawa ga kuma maigidan na nan. Wani irin makakin ba'kin ciki nake ji har cikin mak'oshina. Duk da bana son Tijjani amma na ji zafin kiran Rafi'a da ya yi. Mussaman umarnin yi masa girki da ya bata. Ina da eani irin kishi tun ina karama ta. Har ta kai Gwaggo kullum cikin yi mini addu'ar samun sassauci take yi. K'asan zuciyata kuma ban yarda kishinsa nake yi ba. Tunda ba wai ina sonsa ba ne. Kawai wula'kanta ni da ya yi ne ya mini ciwo.🤣 Sai da ya gama ta fito da kwanukan abincin. Da murmushi ta ce mini "Na gode sosai Amarya. Sai na sake shigo wa". Ga mamakina na kasa yi mata ko da yak'e ne. Murya a dakushe na ce "Madallah". Da daddare ina falo, ina kallo ya dawo. Sai da ya yi wanka, sannan ya shigo ya zauna. Cikin nutsuwa sosai ya ce "Asiya na ce kada ki kuma shiga mini daki da nufin yin lalle ko kitso amma baki ji ba ko?" Yana rufe baki na ce "Tijjani ban ji ba, ba kuma zan ji ba, ka yi abin da zaka yi marar tsoron Allah kawai". Ya yi mini k'uri ya ce "Me na yi miki na rashin tsoron Allah? Ni ban fa'di hakan akan ki ba, sai ke zaki fa'da mini hakan?" Babu fargaba na ce "Ina da tabbacin bana aikata kaba'ira, kai kuwa kaba'irori nawa kake aikata wa? Tsabar shaharar da ka yi a BAKAKEN TA'ADODI har gidan auren ka ma bai tsira da sharholiyar ka ba". Ransa ya baci. Amma da ya fahimci kishin Rafi'a ne ya k'ume ta, sai farin-ciki ya maye gurbin bakaken kalamanta. Da alamun da Rafi'a zai yi amfani ya dinga rama wula'kanta shi da take yi. Ya girgiza kai ya ce "Sharri dai dan aike ne. Mussaman wanda aka ginasu akan zato da jita jita." A kufule ainun na ce "Ba batun sharri a lamarinka. Iya karshen cuta an yi mini. Amma na barwa Allah al'amurana" Na fa'da hawaye na subuce mini". Ya kasa cevwa komai. Tsawon lokaci mun yi jigum jigum! Sai hawaye da suke tsere a kan fuskata. Babu kuzari ya taso ya dawo kusa da ni sosai ya sassauta murya ya ce "Kinsan bana son kukan ki Asiya! Na tari numfashin sa a zafafe na ce "A gidan uban waye baka son kukan nawa? Makaryaci, mugu, bunsuru..! Ai ban karasa ba, na ji wani irin gigitaccen mari a fuskata. Wanda ya sanya na zunduma ihu a matu'kar ki'dime. Cikin fishi mai yawa ya ce "Kin ci uwar karya kin kwana da yunwa Asiya. Kin yi ka'dan ki zagi ubana, ki wanye lafiya. Ashe togaciyar da na yi miki kwanaki a zauren gida baki ji ba? Wallahi ki mutunta ta kan ki, ki kame bakinki daga zagina. Ni zaki ce wa a gidan uban wa? Ubana zaki zaga? Baki isa ba, rashin kunyar ki ya tsaya a kaina. Ni da kike ganina nasan mutuncin iyayena da gaske, ba wai yaudarar ina sonsu a baki ba, amma na kasa kare musu martabarsu a bayan idonsu ba." Ya mike tsaye ya ri'ke kunnensa alamun gargadi. Da kumfar baki ya ce "Billahillazi kika kuma yi mini lalle a daki sai na wula'kanta ki, ke da gayyar ta ki. Sannan yau ne rana ta karshe da zaki yi gigin zagin iyayena. Ki bari, bana so! Idan kuma kin ki ji, lah shakka ba zaki k'i ga ni ba". Ya tafi ya bar ni ina kuka mai tsananin gaske, domin ba k'aramin shigata marin ya yi ba. Tunda ga wannan lokacin gaba ta k'ullu a tsakaninmu mai tsananin gaske. Ya fita daga al'amarina gaba'daya. Baya bin ta kaina, yana dawowa daga sallar asuba zai fice tun gari bai yi haske ba. Ba zai dawo ba sai wajen Tara. Nan ma yana gama uzzirinsa zai sa kai ya fice. Ba zai dawo ba sai dare. A hakan na fuskanci wajen gini yake zuwa. Fitar asubar ne bansan me yake yi ba. Zuciyata har kissima mini take yi lalata yake fita yi. Dan haka na sake wasarsa, na sake jin haushinsa. Bana girki sai dai na saka almajiri ya siyo mini, abincin siyar wa tunda ana yi a makwabta. Ina samun lalle da kitso. Ban kuma fasa yi a dakin nasa ba. Sai dai kafin ya dawo sun tafi, ni kuma zan gyara masa dakin, sai dai k'amshin muhallabiya ya kama dakin. Bai ta'ba magana ba. Ban sani ba, ko dan bai dawo ya tarar da mu a ciki ba. Ko kuwa ya hakura ne?. Cikin wannan yanayin da muke ciki na yi matu'kar rame wa. Na yi baki. Kullum cikin kuka da b'acin rai na ke. A ranar da na cika wata guda a ranar Dada ta zo ganin dakina. Bulkachuwa da kansa ya dauko ta a mashin ya kawo ta. Ta dinga yaba tsarin dakunan. Amma ta kasa gamsuwa da yanayinmu. A sanyaye ta ce "Mai sunan manya Yabi ta sake kankace wa, ta yi duhu, duk da ita fara ce kal. Kai ma dube ka, babu wani annurin angwanci tare da kai." Ga mamakina sai ya sassauta murya ya ce "Kowa da yadda yake fuskantar kalubalen duniyar nan ai. Me nake da shi da zan jiyar da Asiya da'di bare na samu nutsuwa da ita. Na barwa Allah komai. Idan na mutu Dada na yafe miki wannan ha'din da kika jagoranci aka yi. Cike nake da fargabar kada auren namu ya sake d'aid'aita zumuncin gidan Marina." Dada ta dauki salati tana fa'din "Ashe har yau baku shirya ba? Ashe ba kalau kuke zaune ba, shi yasa ka dinga zille wa idan na ce ka kawo ni gidan ka?". A hankali ya ce "k'alau muke Dada." Ta kalle shi ta ce "Tashi ka bamu wuri." Bai yi musu ba, ya fita din. Ta kalle ni ta ce "Haba Hajja Yabi. Me yasa ba zaki kwantar da hankalin ki ba? Mai sunan manya son ki yake irin son nan mai tsananin gaske. Ban ta'ba ganin abin da ya sanyaya shi irin lamarin ki ba. Tun wanccan satin na je gidan Ubaida tana zaune k'alau da mijinta. Sai ke ce zaki kunyatamu?" Na rushe da kuka sosai na ce "Ita mijinta ai baya wula'kanta ta, baya yi mata sanadin da zata kwana ta yini da yunwa. Mijinta mai kamun kai ne. Amma ni kuwa fa?" Kuka ya ci k'arfina sosai. Duk son kan da Dada ta wanzu tana yi a tsakaninmu da su Bulkachuwa a wannan ranar na ga damuwa mai yawa akan fuskarta. Na ga alhinin halin da ta gan ni a ciki a jikinta Ta bu'de baki ta kira shi. Ya amsa ya shigo. Ta ce "Me ka ke yiwa yarinyar nan haka? Ai farkon zaman bata birkice ba, tunda kowa ya zo sai ya ce Yabi tana zaune cikin walwala kamar ba ita ba. Me ya jefa ta cikin wannan tashin hankalin?" Da rashin kuzari ya ce "Zagi irin na tsamar nama ta yi mini. Hakurina ya k'wace na mare ta. Shike nan fa! kuma yau zancen nan an kai sati biyu. Amma ta taurare ta k'i barin abin ya wuce." Ya fa'da cikin damuwa mai yawa. Dada ta ce "Ai baka rarrashe ta ba. Baka ha'diye fishin ka dan ka kawo masalaha ba." Da sauri ya ce "To na yarda, na yi kuskure, taya ni bata hakuri. Bazan sake dukan ta ba, amma ita ma kada ta sake zagi na". Tausayinsa ya cika Dada domin ta sake fahimtar ya fa'da matsanancin soyayyar Yabi. Ta nisa ta ce "kin ji abin da ya ce Yabi. Ki yi ha'kuri, komai ya wuce ba zai sake ba. Na cigaba da kuka sosai. Ina son na fa'da mata ni girkin da ya sanya aka aka yi masa ne, yafi nukurkusa ta fiye da marin. Amma bansan dalilin da ya sanya na kasa fadar wannan maganar ba. Ta dinga rarrashina tamkar ba Dada da bata yi mini sassauci ba. Sai da na yi shiru. Sannan ta kalle shi a zafafe take yi masa magana. "Idan har ka kuma dukanta, to ka tabbatar zan aikawa uwarka ta zo, tunda ka nuna ban isa ba. Ai ba'a baka ita dan ka dinga gwada mata k'arfi ba. Duka duka ma nawa take ne Yabin? Ba zaka yi hakuri da kuruciyar ta ba?" Ya yi shiru ya kasa bu'de baki ya fa'di abubuwan da nake yi masa. Karshe ya buge da bata hakuri da al'kawarin zai canja. Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. *Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332*. ✍️ *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES.* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. Tsawon lokaci kafin su samu na yi shiru. A kokarin Dada na son na warware sosai, sai ta fasa tafiyar ta ce ya yi tafiyarsa sai yamma ya dawo ya mayar da ita gida. Ya fita, sai kuma ya bu'de baki ya ce"Asiya". Na yi shiru kamar ban ji ba. Dada ta sassauta ta ce "Kiran ki yake yi fa Yabi. Ki na son ki k'one ne? Girman sa yawa ne da shi a wajen ki fa". Na tashi bayan na cuna baki tamkar na buta. Da fishi sosai na tsaya a gabansa. A sanyaye kuma murya k'asa ya ce "Zan je na samo ko kifi ne, ki yi girki dan Allah". Nan da nan na ce "Wallahi bazan dafa da kai ba". Ya ce "Shike nan ki yi muku. Hakan ma na gode sosai". Ya fita na bishi da harara. Ba'kin cikin yadda na takarkare na yi masa doya da k'wai ya k'i ci, ba k'aramin cizo na yake yi ba har yanzu. Sannan girikin da ya sanya aka shigar mini kicin aka yi masa, sai ya gane ni ba irin matan da za'a yi musu hakan ba ne. Bai wani jima ba, ya dawo. Sai da ya shiga kicin din sannan ya fito ya yi dakina. Dada ta zuba mini ido alamun na tashi na bi shi. Akan dole na je din. Ya mik'o mini leda mai d'auke da sink'in sabulun wanka da kwalin TURAREN Ismiyaki. Na kar'ba galala. Ya ce "Idan zata tafi sai ki bata". Na gatsina baki na ajiye a bakin gadon ban ce komai ba, na fita na bar shi a tsaye, ya yi wani iri abin tausayi!. Ya fito ya dan tsokani Dada sannan ya fice. Zafi ya sanya na yiwa Dada shimfida a baranda. Ta fito, muna hirarmu ina gyaran kayan miya. Ina tunanin artabun da zan yi da attaruhu yayin greting. Don kuwa indai na murtsika attaruhu sai na kwana na yini hannuna na yin mini zugi. Kwatsam aka kawo wuta. Cikin karambani da giggiwa na ha'da bilandar na fara markade. Sai da na zuba shinkafa a dalilin ruwa ya tafaso. Sannan na koma wajen Dada. Da murmushi ta ce "Oh ashe dai da rabon za'a samu mai tu'amalli da injin markade na zamani a jikokina". Na yi dariya tare da cewa "Dada kenan. Bari na zauna ki d'ora mini karatu, ina kewar karatun ki." Ta gyatta, na zauna kusa da ita. Ta ce "Tunda Ubangiji ya sanya na ga auren ki har ga ni a gidan ki. To zan 'dora miki karatun da har abada kin wuce yin boranci a idon namiji. Ban ta'ba koya wa kowa wannan addu'ar ba, saboda jarraba namiji ake yi da ita k'warai da gaske. Kema dan ina son ki tsare mijin ki, daga sharholiya ne!". Ban ce komai ba. Ta yi waiwaye dan ta sake samun tabbacin babu me jin abin da zata furta. Ta matso kusa da ni ainun. Murya k'asa kasa ta ce "A yayin da kuka shiga mayafin aure sai ki yi Bismillah ki ce "Allah daraja, MA'AIKIN Allah daraja a taimake ni akan aure. Zan jarraba y'an maza wane.. Ibnu wance. Ki kamo ainihin sunan sa da sunan babar taku, sai ki tofo yawun bakinki akan yatsan sai ki yi matsi da wannan yawun addu'ar. Amma a zuci, zaki yi fa". Ta fa'da da dukkan zuciyar ta. Duk da na saba jin karatun Dada wannan ya yi matu'kar sanya ni mamaki da dariya. Amma na sanya jarumta na maze, na yi k'asa da kaina a zuwan kunya ce ta hana ni sukuni. Ta kuwa dage ta ce "Ba kunya zaki ji ba Yabi! Na baki wannan fahamin ne dan na taimake ki, ku zauna lafiya. Amma fa kada ki yarda ki dinga jansa a k'asa. Domin k'arfin addu'ar yawa ne da shi tamkar yankar wuka take". Na k'yal-k'yale da dariya saboda bilhakki take maganar zan jarabta shi da wannan karatun surkullen. Sai da dariya ta tsagaita mini na ce "Allah ya bada lada Dada. Amma ni bazan yi a kansa ba. Baya sona, bana sonsa. Kowa harkar gabansa yake yi." Ta dauki salati tana fa'din"Ashe har yau baku zama d'aya ba? Tisa ki yayi a gaba yake kallon ki kawai? To idan na tafi zan fara tsayawa wajen Malam Nata'ala na ji ya ya matsayin aurenku. Domin nasan duk ma'auratan da suka shafe kwanaki arba'in basu hadu ba, tabbas aure ya haranta. To ku kwanaki talatin da biyu da aurenku. Zan je na sake jin fatawar kada aje ko auren ya b'aci ba'a sani ba". Na yi shiru domin na kasa gane bayanin na ta. Ban ce komai ba, domin kuwa ban ta'ba jin makancin hakan ba. Ta numfasa ta ce "Yabi kin san duk macen da ta ki d'agawa mijin auren ta k'afa. Zata zama makamashi ne a cikin wutar jahimu?" Na yi shiru tare da b'ata fuska. Ta sake ce wa "Wannan hukuncin lahira ne. A duniya kuwa babu ita babu ganin hasken rayuwa tunda malaiku dubu maitan ne zasu yi ta kabarbari suna d'ebe mata albarka. Kin san kuwa ko limamin unguwarku ne ya tsine miki, kin yi hannun riga ke da walwalar rayuwa bare kuma ma'asumai irin malaikun Allahu". Jikina ya yi sanyi da wannan karatun na karshe. Wanda babu kuskure ko shaci fa'da a cikinsa. Amma da na tuna ai bai ta'ba nema na hana ba, ke nan bana cikin tsinuwar malaiku, sai na samu sau'kin tsoratar da na yi. Kafin ta sake magana na zabura na tashi ina ce wa "Bari na duba girikina". Na tace shinkafa, na yi k'asa da wutar na mayar. Na duba ledar da ya ajiye na ga salak da kuma ledar soyayyen kifi. A gurguje na yanka na wanke da gishiri na bar shi a kwandon tsane wa bayan na rufe. Daidai lokacin na sauke sanwar, na d'ora ta miya. Na juye a flask na fito da tukunyar na jika ta da ruwa. Na ce "Dada mu shiga ki yi kallo. Rana ta fara kusantomu. Ta ce "Zan tashi dai saboda rana, amma ba dan na yi kallon shagala ba. Na kunna na kamo mata wa'azin Malam Guruntun tana saurare can ta nisa ta ce "ya iya karatu kuwa. Amma dai wannan ba namu ba ne ko Yabi?" Cikin k'arfin hali na ce "Musulmi ai d'anuwan musulmi ne Dada. Bare wannan bijimin Malami ne. Ke dai ba ki ji abin da Allah da ma'aiki suka ce ba ne na ki?" "Ta kyabe baki ta ce"Masu daddagen wando ai tsakaninmu da su sai a lahira. Tunda suna raina karamar shehu". Dariya ta kwace mini. Na dinga yi sosai. Na canja tashar cikin sa'a kuwa sai ga sheikh Mak'ari yana bayani irin wanda ta gamsu da shi. Na gama abinci tsaf. Bamu ci ba sai da muka yi salla sannan na kawo mana. Tare ta ce na zuba mana. Muna ci tana yaba girkin nawa. Tana kuma ta yi mini maganganun da suke nuna girman da miji yake da shi. Ban ce uffan ba, sai da ta ce "Ki kwantar da hankalinki ki zauna lafiya. Nan da kwanaki ka'dan zan sake kewayo ku. Idan har kika bari kwanakin auren ki ya kai arba'in baki bari ya ri'ke hannun ki ba. Tabbas zan fa'dawa mahaifin ki. A san halin da kuke ciki. Kada ku fara zaman haranci". Na fara kuka tare da ce wa "Ba ruwan ki Dada! Kada ki ha'da ni da ubana, kada ki janyo mini fishin sa." Ga mamakina sai ta sassauta ta ce "Idan kuwa har irin haka kike gudun fishin uban ki. Kamata ya yi ki guji fishin Allah fiye da hakan. Ai ba Babanku ba ne ya hukunta faruwar al'amarin ba. Allah ne da kansa. Fishin Ubangiji akan bawansa kuwa yana nufin tabarbarewar dukkan al'amuran rayuwa". Na kasa bu'de baki na ce "Bai ta'ba nuna wa yana da bu'katar hakan daga gare ni ba. Saboda yana samu a waje. Sai kawai na sake tsananta kukan da nake yi. Domin har ciki mak'oshina nake jin ba'kin cikin halin da nake ciki. Har la'asar ta kawo kai, bata fasa sakin maganganu ba. Wasu na gaskiya, wasu na barkwanci wasu kuwa masu nauyi ne. Ita kuwa ko a jikinta. Ina kuka sosai amma bata damu ba sai ce wa ta yi "Da kin san kanki ai da tuni kin mayar da shi bita zaizai. Mata irinmu masu k'aramin ruwa ai mafi yawa murza maza muke yi. Kin ga duk haiba da siffar mijin ki. Da kin kwantar da hankalinki, kina masa biyayya, kina ba shi kanki ai wataran ma sai ya shirya zai fita, idan kika ce kada ka fita ce wa zai yi to." Na cuna baki na ce "Da dai ba dan-iskan duniya ba ne". Ta kuwa zabura ta jefe ni da kofin kusa da ita. A ki'dime ta ce "Mijin ki kika zaga kai tsaye babu nadama bare shakka? Tabbas kin kafurta, kin halaka Yabi. Dole sai kin sake karban shahadar shiga musulunci. Na kasa kunshe dariya ta. Na k'yal-k'yale da dariya sosai. Ranta ya baci k'warai da gaske. Ta shiga share hawayen takaici. Murya na rawa ta ce "Ki aikata kaba'ira sannan ki yi dariya? Saboda ku yaran yau babu darhamin imani a zuciyarku?" Na ha'diye dariyar a dalilin kukan gaske take yi. Da sanyin murya na ce "Ki yi hakuri Dada." Ta ce "Na ha'kura amma, ai dole ki sabunta musuluncinki Yabi. In kuwa ba hakan ba, tabbas kin zama arniya. Cikin k'arfin hali na ce "Ba ni kalmar shahadar na sabunta din." Ta rike baki ta ce "Wace ni na shiga sahun Malamai. Ni almajira ce me neman sani. Gaban babban malami za'a kai ki ya baki shahada ki kar'ba. Ko kuma ki yi tuba a gaban mijinki ki nemi afuwa sannan ya baki kalmar ki kar'ba". Na bata rai na ce "Haba Dada tunda ba'a gabansa aka yi ba, ina dalilin sai ya ji. Tunda kin ce na sabawa Allah. Ki bari na ce Astagafirillah! Amma kada ki fa'da masa. Dukana zai yi, son girmansa yawa ne da shi". "To shikenan bazan fa'da masa ba. Amma ki tsananta intigifari Yabi". Daga haka muka yi haramar sallar la'asar. Na tattare kwanukan na share wajen kafin ta fito daga bayi. Mun jima da idar da salla sannan ya dawo. Kallonsa kawai na yi na gane bai ci abinci ba. Dada ta dinga yi masa barka da dawowa. Ya amsa yana murmushi wanda na tabbatar na yak'e ne. Ta zuba masa ido ta ce "Ya na ganka haka ne?" Ya ce "Babu komai. Sauri nake yi kada ki ce ban zo da wuri ba." Bata ba shi amsa ba ta kalle ni. A dole na ce "Sannu da dawo wa". Ya amsa da walwala sosai". Ya ce "Na kai ki yanzu, ko na watsa ruwa?" A tausashe ta ce "Yunwa kake ji, ka fara cin abinci, nasan baka shiri da yunwa". Ya yi k'asa da kansa. Bai ce komai ba. Ta ce "Yabi ki kawo masa ruwa da abinci mana". Na daure fuska matu'ka da gaske sannan na ce "Baya cin abincina ai". Ta fara fa'din "Allahu Akbar kabiran, wa subhanallahi bukuratan wa asila. Wanne irin zama kuke yi ne na kafirci ni Binta? Baya cin abincin ki sai na wa to?" Da yake abin na yi mini ciwo sosai. Cikin rawar murya na ce "Sai na y'ar iska mana." Dada ta kalle ni da kyau tamkar me yin nazari. Sannan ta mayar da kallonsa kansa. Gaba'daya ya yi laushi tabbacin ya buga bai samu abin da ya sanya a bakinsa ba. Tsawon lokaci ta ce "Kira mini lambar Alhaji. Da alamun al'amarin naku ya yi munin da ba zan iya gyara shi ba." Tana rufe baki na fashe da kuka Ina cewa "Saboda son kai sai ki kira mahaifina ki bata ni a wajensa, ki tayar masa da hankali. Alhalin tunda na zo gidan nan ba abin da nake ga ni sai wula'kanci da tozarci. Ai ni an cuce ni karshen cuta kuwa". Na fa'di hakan cikin kuka mai tsananin gaske. Ta saki ajiyar zuciya ta ce "To kira mini Hauwa tunda ita din kin yarda uwar ki ce". Shima cikin sauri ya ce "A a Dada kinsan dai bayan ta zata bi. Sannan fishi zata yi da ni! Yanzun ma ya nake fama ne a rayuwar nan bare kuma ace ina cikin fishin uwa. Rabu da ita kawai Dada. Idan na fa'di na mutu ba shi kenan ba. Sai ta je ta auri wanda take so." *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*. Yadda ya yi maganr ya yi matu'kar dukanmu. Ko ni da ba sonsa nake yi ba. Ya bani tausayi kwarai da gaske. Bare Dada da kowa yasan bata jure ganinsa cikin damuwa. Ta rasa inda zata tsoma ran ta. Ta kasa cewa komai. Can ta ce "Tashi ki kawo masa abinci". Na zum'bura baki ainun na ce "Ba fa ya ci Dada. Akan me zaki ce sai na ba shi, salon ki sa zuciyata tafi hakan b'aci tunda barinsa zai yi". Da sauri ya ce "Wallahi bazan bar shi ba Asiya. Ci zan yi, yunwa nake ji rabona da abinci tun daren jiya. Na gaji da abincin siyarwa, ban saba ba, tun fil'azal." Jikina ya mutu murus. Cikin murya marar amo ta ce "Kin ji ya rantse zai ci". Na sake d'aure fuska ban tanka ba. Ta kalle shi ta ce "Kai me yasa idan ta dafa kake k'in ci?" A hankali ya ce "Zubin wula'kanci ta yi mini. A bu'de kuma a farantin roba". Dada ta fara ce wa "Eh dole ranka ya b'aci, duk namiji sarki ne a gidansa komin kashinsa kuwa. Lalle Yabi wula'kanci da tozarcin ki kabiran ne". Nan da nan ya ce "A a Dada ya kuma zaki sake ankara ta. Ai ban ce ki tayar mata da hankali ba. Ke dai kawai ki rarrashe ta, ai dazu ma kin ce yarinya ce zata daina ne". Ta yi sukuri tana kallonsa cikin tu'ajjibi mai yawa. Jin ya fa'di hakan, na k'ara kukana na ce "Bar ta ta yi son kan da ta saba yi a tsakaninmu. Kuma kai ma dan me baka fa'da mata ka kira budurwarka har falona kun yi hira ba. Me yasa baka fa'da mata bayan hakan da ka yi, bai ishe ka ba. Har umarnin ta yi maka girki a kicin d'ina ka bata?" Na fada cikin kuka sosai. Dada ta dauki salati tana ce wa "A cikin gidan auren ki, ya yi irin wannan ba'kin zunubin? Eh lallai ba laifin ki ba ne, nasa ne. Wato ni a lokacin da nake kamar ki yaushe za'a mini hakan na bar al'amarin salin alin ba tare da na fitarwa da ja'irar jini ba. Na goge hawaye na ce "Ban yi komai ba na kai k'ara wajen Ubangiji. Sannan kuma har abada bazan sake ba shi abincina ba. Ba kuma zan huce ba, daga nan har na tsufa". Dada ta yi maza ta ce "Eh to ba dan ina jin tsoron kada kwanaki arba'in din ta cika auren ya samu karaya ba. Dana goyi bayan wannan tutsun na ki. Amma yanzu ki yi ha'kuri, ki yafe, ki huce! Ubangiji yana son masu afuwa da sassauci. Idan ya kuma ni da kaina ne zan sanar da iyayenku. Ai bazan yarda ki yi irin wannan zaman na kuttu ba". Na girgiza kai na ce "Ai Dada babu maganar huce wa. Babu ni babu sake shiga shirginsa tunda juninsa wula'kanci da nema mini raini ne". Kafin Dada ta yi magana ya yi fit ya ce "Ban san zaki ji haushi ba Asiya. Na rantse ban yi da gayya ba. Amma tunda ban kyauta ba. Allah ya baki hakuri. Ba zan sake ba." Na dauke kai ina harara tamkar idona zasu fa'do k'asa. Ya ce "Dada ki ce ta yi hakuri mana." Ta nisa ta ce "ki yi ha'kuri kin ji. Ta shi ki ba shi abincin ba dan halinsa ba. Dubi Allah, ki duba Manzonsa." Ban sake ce wa komai ba. Na mik'e din. Ban san ya aka yi ba, da na isa kicin din na samu kaina da d'auko plastic plates masu fadi guda biyu. Na zuba masa na rufe na dora cokali a kai. Na dauka na nufi falon. Ina jin Dada na fa'din "kada ka sake kuskuren saka wata ta yi maka girki. Ban da sakarci ma ina kai ina doguwar magana da ita, bare har kasa a yi maka girki akan idon matar ka. Ai gwara da ta murd'e maka. Kasan halin fa'dan ta ai, bare kuma an tsokano ta". Murya ba amo ya ce "ki bar maganar nan, sai na zo dakin ki. Yanzu dai lallaba mini ita Dada kawai". Na shiga na ajiye a gabansa. Ya saki murmushi ya ce " "Madallah da Asiya". Na cuna baki na dauko ruwa na ajiye masa a gabansa na koma gefe na zauna. Ya dauki abincin ya dinga ci tamkar bai ta'ba cin abinci irin hakan ba. Cikin kankanin lokaci ya tashi da uban abincin da na danne farantin da shi. Fanka na kad'awa amma zufa sai yanko masa take yi. Ya ta'ba ruwan ya ji sanyi sosai. A hankali cikin kwantar da murya ya ce "Asiya idan kina da ruwan Lipton taimake ni da shi mana please" . Na dauke kai, kamar bazan amsa ba, sai kuma na tashi na fita ba tare da na ce komai ba. Dada ta bini da ido tana fa'din "Kasaitacciyar mace. K'aramar halitta mai babban al'amari". Sai da na isa kicin na yarda na yi dariya. Na dauko kofi da cokali. Sannan na dauki filas din ruwan zafin. Na sake ajiye wa a gabansa ba tare da na ce komai ba. Na zauna na dauki waya ta ina danne danne. Dada ta ce "Ba ki kawo masa sigari ba." Kafin na yi magana ya ce "Idan zata dafa take zubawa, dan rage masa tasiri." Ta murmusa ta ce "Yabi mutanan turai". Shi ma ya taya ta murmushin. Ni kuwa ban ce komai ba. Ya kammala, ya yi gyatsa tare da hamdala. Ya ce "Har na ji ni a duniya. Na gode sosai Asiya. Allah ya yi miki albarka." Ban amsa ba. Dada ta amsa da sauri tare da fa'din "Barka da arziki Yabi! Kin rabauta tunda kika samu farar addu'a daga mijin ki". Na yi shiru ban tanka ba. Yayin da shi kuma ya mik'e yana cewa "Bari na canja riga na zo na mayar da ke." Yana fita Dada ta ce "Yabi maganar nan ta wuce. Ku zauna lafiya. Ko makaho ya zo gidan nan sai ya gane mijin ki na son ki". Cikin fishi na ce "Baya sona Dada. " Ta murmusa ta ce "Yana son ki. Ke ma da gangan kike inkarin hakan. Yanzu bazan fa'dawa kowa ce wa ba k'alau kuke zaune ba. Amma fa idan na dawo gidan nan, na fahimci baku shirya kanku ba. Ku tabbatar sai na ha'da muku iyayenku da Malamai. Dan bazan yarda da zaman kafirci ba." Na dinga k'unk'unin babu ruwanta da shiga al'amarin da bai shafe ta ba. Ta gyada kai ta ce "komai zaki ce Yabi ki fa'da. Amma ki sani, ni bazan ha'inci shari'ar musulunci ba. Tilas ne ku bi ka'idojin shari'a a kan aurenku." Ya lek'o daga bakin k'ofa ya ce "kin gama Dada, ko na je na dawo bayan maghariba sai na kai ki?" Ta yun'kura tana fa'din "Na gama, yinin ya isa, ba sai na kai almuru a waje ba." Nima na bi bayan ta muka fito. Na kalle shi ya sanya jallabiya. Ko mai bai shafa ba, bare tuarare. Àllah ya sani ina son na dinga jin k'amshin na tashi a jikin mutum. Na shiga daki, na d'auko ledar kayan da ya siyo. Na dauki dubu guda a cikin ku'din da na tara na lalle. Na saka mata a ciki. Na k'ulle. Na sake k'ara wata ledar. Na tarar har sun kusa fita. Na bu'de baki na ce "Dada mun yi sallama ne?" Suka dakata na isa garesu. Na mika mata tare da ce wa "Ga shi Dadarmu na gode da ziyarar ki. Amma Wallahi bakin ki k'anin kafar ki akan sha'aninmu Dada. Idan kuwa kika fa'di wani abu, sai dai a neme ni a rasa." Ta sassauta ta ce "Ayyah Asiya me na ga ni ma ban da alheri? Ai ko da na ce zan fa'di baku zauna lafiya ba. Dan ban fahimta ba ne. Yanzu da na fahimci shine da laifi, ai na fa'di gaskiya. Kawai da ke da shi ku yi kokarin d'abbaka sunna, kada auren naku ya b'aci ba'a ankara ba. Kunya ta yi matu'kar kama ni. Na rasa yadda zan yi, sai kawai na juya da sauri na yi ciki na barsu. Shi kuma ganin hakan ya sanya ya ce "Allah yasa dai ba sai yanzu kika yi mata wannan bitar ba Dada? Domin a zaune zaki yi mata ba a kurarerren lokaci irin haka ba. Idan kuma zaki fasa tafiyar sai bayan Isha da na fi haka gode wa Dada". Ta nuna shi da yatsa ta ce "Tabataccen marar ta ido. Oh ni Binta ina kallon shak'iyanci. Ai gara ma da Asiyan ce matar ka, ita ce maganin ka. Haba kana da fitina Wallahi". Ya yi gum. Ta d'aga murya ta ce "Na tafi Yabi, na gode Allah ya yi albarka. A ci gaba da hakuri." Ina zaune ina kallonsu ta windo har suka fice. Suna tafe a hankali yake jan mashin d'in gudun kada ta subuto tunda ba iya hawa ta yi ba. A hankali take fa'din "Ashe haka zaka yi mana? Akan me zaka kawo wata har gidan auren ka?" Ya ce ba ni na kawo ta ba. Wajenta take zuwa fa. Kuma kunshi take yi, wai ni rage mata aiki nasa aka yi" Ta hassala ta ce kaniyarka da rage mata aikin. To bata so. Kada ka kuma wannan d'anyen aikin." Ya ce "To bazan sake ba, da gaske." Suna isa ana kiran magariba. Dan haka da ya kafe mashin din a zaure bai shiga gidan ba, ya nufi masallaci. Da nutsuwa ya isa kofar Baban Marina ya gaisa da su Gwaggo cikin kunya da girmama wa. Kansa a k'asa ya ce "Gwaggo idan uniform din Asiya na nan wai a bata zata fara koyon dinki" Da sauri ta shiga daki tana ce wa "Sabon yana nan. Tsohon dai Ikilima tana amfani da shi." Jimawa ka'dan ta kawo masa a bak'ar leda. Hannu biyu ya sanya yayin karba. Ya yi godiya, ya yi musu sallama ya tafi. A gurguje ya yiwa Dada sallama ya wuce gidansa. Yana Jin zumudi da d'okin zama kusa da Yabi. Yana son yi mata ba zata. Yana son ya shawo kanta, ya d'ora mata girma ko zata rage tsiwa da zafin kai. *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *08089965176* *07084653262* ✍️. *BAKAR TA'ADA* *45&46* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES.* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *Tallah Tallah Tallah* Shaharriryar marubuciyar nan wacce tanishaɗantar ku a littafin ta mai sunan SAMHA```! ```Ta sake sabon shirin ta, wajan ƙara faranta maku rai' tazo maku da sabon book ɗin ta Wato KECE SANADIN [rayuwa]``` ```Masoyana kufito ku nunamin ƙaunar da kuke cewa, kuna min``` ```farashin KECE SANADIN ₦500 0nly``` ```wacce bata shirya ba kada tamin magana``` ```masu san fara pyarment da wuri gashi, 810353370 kimin screen shot ki turo ta wannan no 08138012334``` ```masu kati kuturo ta wannan layin 08108353370``` *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. 45&46. Ya shiga da kuzari. A falo ya tarar da ita tana kallon tashar Bollywood. Yana wahalar gaske ya ga tana kallon tashoshinmu. Har gara tana kai wa Sunna TV sa'i zuwa sa'i. Ya manta da uniform a cikin but din mashin din. Ya zauna kusa da ita. Ya sassauta ya ce "Asiya Toro babu magana, babu yi mini barka da zuwa?" Na galla masa harara na ce "To ni ina ruwana da kai da zan yi maka magana? Ba gaba mu ke yi ba?" Ya ce "mun shirya ai. Na baki hakuri, kakarmu ta baki, mene ne kuma ya yi saura?" Na ja tsaki mai tsananin gaske na ce "Da wa din ka shirya? Ai ni duk mutumin da zai tozarta ni, ya kuma ta'ba lafiyata da sunan duka to babu ni, babu shi har gaban abada". Na fa'da cikin matsanancin fishi. Jikinsa ya fara mutuwa. Ya numfasa ya ce "Ashe duk maganganun Dada basu shige ki ba? Daga tafiyar ta Asiya zaki fara d'aga mini hankali, mene ne nak'asuna ne da kika washe ni har hakan?" Yana rufe baki na ce"nak'asunka ai birjik ne. Mafi muni baka da kamun kai.". Ya zuba mini ido ya ce "sai me kuma Asiya?" Kai tsaye na ce "Baka burge ni ko kadan. Domin bana jin k'amshi a tare da kai. Baka iya kwalliya ba. Kullum kayan ka babu guga. Kalli faratan hannun ka. Kullum na kalle ka ba'kin ciki ne yake kama ni maimakon farin-ciki." Jikinsa ya yi sanyi kwarai da gaske. Idanuwansa suka canja launi sosai. Murya a dashe ya ce "Sai me kuma?" Na ce "Idan na tuna, na fa'da maka". Ya numfasa ya ce "Duk zan gyara indai sune cikas dina a wajen ki. Idan na sauya din shi ke nan zaki daina tsananta mini?" Na sake shan kunu ban tanka ba. Ya ce "To nima ina da damar da zan fa'di abubuwan da kike yi mini da bana sonsu?". Kamar bazan kula ba. Sai kuma na ce "Baka da damar domin ni ba so nake sai na burge ka ba. Ba kuma so nake ka zauna da ni akan dole ba. Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Shike nan! Amma ina ro'kon ki kada ki sake shiga mini da mata dakina". Na tunzura! Na tashi zaune sosai na galla masa harara na ce "Sannu mai d'aki. Komai dakinka, dakinka. To sai na shiga d'in. Shima ya hassala ainun ya nuna ni da yatsa ya ce "Kada ki fasa Asiya. Ai tunda na gane ba kya son sulhu da sassauci, to mu zuba tsiyatakun mu ga wa zai janye wa wani". Na ja tsaki na ce "Ai ka k'oshi shi yasa ka samu kuzarin yin musayar yawu da ni". Ya juyo a tunzure, ni kuma na zabura na yi shirin kai masa naushi. Dariya ta kama shi ya ce "Wai dambe zaki yi da ni? Ko da yake ai mai hali baya fasa wa." Na ce "oho dai." Ya fita ban sake jin sa ba, sai da asuba ya tashe ni. Da safe ba yadda bai yi ba akan na tafasa masa wani abu, duk da ya shigo da burodi a safiyar, kawai bai dame shi ba ne. Na yi tsallen bad'ake na ce bansan zancen girki ba, gara mu cigaba da zaman doya da manja kawai. Ya shiga ya tafasa farar taliya ya zuba yajin *Annur food* da manja. Ya ci ya fice bai bi ta kaina ba. Sai da na gama komai sannan na d'ora shayi. Na karya na yi wanka. Ina zaune babu wuta, kuma babu kowa. Sai da azahar sai ga y'anmata uku sun zo k'unshi. Muka shiga d'akin da ake ta mini kashedin kada na shiga na fara yi musu. Na gama wa mutum d'aya sai ga Hajiya babbar mace sosai. Dan zata haife ni. Mun saba tuntuni, wani lokacin har gidanta ina zuwa na yi mata, sanadin haka suka saba da Gwaggona. Na marabce ta da murna. Na kammala saka musu. Na kammala yiwa Hajiya a hannu. Sai ga shi ya dawo. Ban san me yasa ba, na ji faduwar gaba ainun. Wata'kila ko dan ya yi ta jaddada mini kada na shigar masa d'akin da nufin yin kunshi ne? Ya lek'o ya tabbatar ban ji maganar sa ba. Ya juya ko gaisuwarsu bai amsa ba. Ya dauko bokiti ya janyo ruwa. Hajiyar ta ce "tashi ki je ki masa sannu". Na ce To" ba dan ina so ba, na yun'kura na fita. Na gan shi ya gama cika bokitin, ya dauko na tsaya ban ce masa kanzil ba. Zuciyata ta tsinke a dalilin yanayinsa ya koma na Bulkachuwa na asali, ba na yanzu da ya koyi sassauci ba. Ya shige ni bai ko kalli inda nake ba. Ya kai ruwansa band'aki. Nima na koma na cigaba da lallena. Mintina biyar sai ga shi ya shigo d'akin babu sallamah. Y'anmatan suka fara gyare gyaren jikinsu yayin da Hajiyar ta rasa yadda zata yi a dalilin duk na yiwa hannuwanta k'unshin. Ba zato ya cire rigarsa ya mak'ale. Zuciyata ta tsinke. Wani irin abu ya tokare ni. Kafin na wartsake sai kawai ya zame dogon wandonsa, ya yi saura daga shi sai singileti da gajeran wando. Hankalina ya kai k'ololuwar tashi lokacin da ya cire singletin. Ya dauki tawul din da yake rataye ya daura a kugunsa. Ban san me ya hana shi zame gajeran wando ba. Yasa kai ya fice zuwa band'aki. Na yi kasa da kaina hawaye ya b'alle mini. *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBE TA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* Gaba'daya y'anmatan suka bi shi da kallo. Wani irin mak'aki ya tokare ni. Na sani zai burgesu tunda Ubangiji ya masa kyakkawar sifa kwarai da gaske. Motsa jikinsa da yake yi, ya sanya jikinsa ya ginu sosai. Wanne irin wula'kanci Tijjani ya yi mini yau? Na fa'da a zuciyata. Matar ta ce "Cire mini lallen nan. Ai bansan maigidan baya so ba. Na tabbatar ba da izininsa kike wannan sana'ar ba. Shiyasa ya dauki wannan k'azamin matakin. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yau na ga lukutar tsiya ni Hadiza." Ta fa'da cikin kad'uwa. Na fara kuka sosai, ina yi, ina cire mata. Ai kuwa ina gamawa ta ja ni jikinta ta mak'ure ta rufe ni da duka tana cewa "wanne irin shak'iyanci kike yi masa da ya janyo miki wannan d'anyen hukuncin. Shin baki da makusanta da suke fa'da miki gaskiya ne? Kowa ya kalle shi yasan yana tsananin son ki. Me kike yi masa?" Dama so nake na yi kukan sosai, ko na samu sau'kin zugin da kirjina yake yi mini. Dan hakan na bu'de baki na dinga canyara ihu. Ita kuwa sai dukana take tamkar ita din Gwaggo ce. Sai kuma ya fito a bazame. Dan ya ga me ya sani irin wannan kukan. Ganina a hannun Hajiyar ta matse ni tana ta mintsini na ya sanya shi ce wa "Na ha'da ki da Allah ki bar ta haka nan Hajiya, k'yale ta" Ai kuwa ta k'yale ni. Ya tsaya daga ba'kin k'ofar ya mika hannu ya d'auko jallabiyarsa da take rataye. Ya yi baya, ya sanya. Ya dawo ba'kin kofar ya ce "Darajar wannan baiwar Allah kika ci, tana gidan. Na rantse miki da yau kin ga k'arshe taurin kai da tsiya." Ya kalli Hajiya ya ce "Na gode sosai, amma dan Allah kada ki sake ta'ba ta. Ki yi ha'kuri". Yasa kai ya bar gidan gaba'daya. Y'anmatan nan suka kasa ce wa komai amma dai gaba'daya sun shiga rud'anin al'amarin da ya faru. Ta tashi, ta fita tana fa'din "Zan je har gidanku na sanar wa Gwaggonki baki shirya zaman aure ba. Gara ta sani kada rana daya ta gan ki kamar jifa kin koma gabanta. Ke ko tunanin halin da take ciki ba kya yi? Tare da kanwar ki aka aurar da ku. Tana zaune k'alau, amma ke kin fitini kanki kin fitine shi." Na dinga kuka ina bata hakuri akan kada ta fa'da wa Gwaggo fishi zata yi da ni. Da k'yar ta yarda ba zata fa'da ba. Bayan ta ce na kira mata shi a waya. Akan dole na kira shi. Na danna speaker. Yana dauka sai ce wa ya yi "Bebina kin daina kukan? Ki yi ha'kuri kin ji. Ai da nasan mutumiyar kirki ce irin haka da bazan yi hakan a gabanta ba". Ba'kin cikinsa ya nemi kassara ni. Na mika mata wayar cikin b'acin rai. Jin muryarta ya sanya ya shiga cikin nutsuwa sosai. Bai bari ta ce komai ya fara bata ha'kurin abin da ya yi. Ta ce "Tambayar ka zan yi. Baka son ta yi k'unshin ne?" Da sauri ya ce "Ina so. Ai bazan hana ta sana'ar da ta kafu da ita ba. Amma dai dole ta bar abin da na ce mata. Na ce kada ta kuma yi mini lalle a d'akina, ta je ta yi a nata d'akin. Shine kawai rikicina da ita". Ta ce "To shike nan. Magana ta k'are." Ta kashe wayar ta murd'e mini kunne tare da ce wa "Dama can dakinsa ne, amma kike masa k'unshi a ciki? Saboda ke tabbataciyar marar kunya ce? Amma yanzu ai kin ga 'karshen tsageranci." Ta saki kunnena ta tashi ta bud'e wadrof d'ina ta ga dukka kayana ne babu nasa ko daya. Ta sake kai kallo ga d'akin ta ga babu alamun hula ko wani abu na miji a ciki. Ta daure fuska ta ce "kwanta na duba ki, wato har yanzu ke budurwa ce ko?" Na rushe da kuka wiwi. Ina fa'din Dan Allah ki yi ha'kuri sanin da na yi ita din mai zafi ce. Sannan ba mai wargi ba ce, y'ay'anta ma shakkarta suke yi ainun. Ta cije ta ce "Kin san Allah sai na ga ni. Ko kuma yanzu na saka Salisu ya dauko mini Gwaggonki tunda ni ba ni da mutunci a wajen ki." Na sake tsananta kukana ina fa'din "Dan Allah Hajiya ki rufa mini asiri. Dama fushi suke yi da ni. Mussaman Babanmu, ki yi hakuri. Kuma ni akan wannan ba laifina ba ne. Na yarda na yi kuskure akan maganar d'akinsa, ba kuma zan sake maimaita wa ba.". Ta saki ajiyar zuciya ta ce "Shikenan na hakura. Amma na baki daga nan zuwa kwanaki uku ki kwaso kayansa ki dawo masa da su nan. Sannan ki kwantar da kai, ki roke shi ya baki iznin zama a d'akin tunda gidan naku babu bishiya ko rumfa. Ba sai na fa'da miki muhimmanci sana'ar ki ba. Komin wadatar miji neman na kai da'di ne da shi. Zaka yi harkokinka kai-tsaye ba sai ka jira an yi maka ba. Bare ke da kika saba yiwa iyayenki hidima a cikin sana'arki". Ina kuka na ce"To. Domin dai na gamsu da maganganunta. Ta sake ce wa "Ki ajiye komai ki rungumi auren ki, kowa da kaddararsa Yabi. Ke taki ma da kyua. Tunda mijin na ki yana son ki da alama kuma yasan me yake yi tunda soyayyar bata rufe masa ido ya sarayar da yancinsa na miji ba. Ki shiga taitayinki. Wadanccan y'anmatan zarata kallon so da fatan ace nasu ne suke binsa da shi. Ki ribaci damarki. Ki rike darajarki tun baki tankwabar da ita ba. Idan a yanzu da yake neman zaman lafiya da ke, kika yarda kuka zauna, to har tsufanku ya dinga kaffa kaffa da ke. Ban ce ba zai bata miki ba, ban ce ba zai kuntata miki ba. Amma dai zaki samu sau'ki, zai kuma din ga shakkar ki botsare masa. Kada ki yarda ki koya masa jure wa fishin ki Yabi". Cikin kuka na sake ce wa "To" Wanda ban san dalilin da ya sanya na kasa daina wa ba. Ta nisa ta sake ce wa "Ban da ma ke din sakarya ce ai cikin hikima zaki gaje can din. Da kin nuna masa nan ne dakinsa ai shike nan. Yanzu kuwa can din da kika raina sai ki ga ya samu wacce zata yarda ta zauna a cikinsa. Sai dai ki ji an kawo masa amarya." Ba k'aramin dukana wannan maganar ta yi ba. Na k'ara sautin kukan da nake yi. Ta ce "Sha sha a haka kamar wayayyiya amma bagidajiya ce. Baki iya komai ba sai kishi. To wai wannan kishin na mene ne tunda ba sonsa kike yi ba? Ya auro uku mana me zai dame ki? Na so bana gidan yau, ya tub'e ya zauna cikin mata na ga yadda zaki yi. Kin san kuma duk masu hankali baza su sake zuwa miki ba. Marasa tunani kuwa sun dinga zuwa, dan su k'ulla alaka da shi". Bata bar gidan ba sai yamma lis, bayan y'an matan sun cire nasu sun tafi. Sai bayan Isha ya dawo. Ya same ni a dakina ina kan abin sallah duk na takura tsabar takaicinsa da yake dafa ni. Ya zauna a kasa kusa da ni. Ya ce "Barka da gida Asiya Toro". Na kasa bu'de baki na ce masa uffan. Domin yadda zuciyata take tafasa sai na ji tamkar na yi ta k'unduma masa ashariya. Yasa dukkan hannunsa ya ru'ko ni yana fa'din "Ba kya gajiya da kuka ne Asiyata?" Ai kuwa ba zato na fara kai masa duka a ko'ina. Ya dinga fa'din"ki yi a hankali kada siraran hannuwan ki su ji ciwo." Na bar dukan domin tabbas hannuwana ne suke mini zafi tunda jikinsa a murd'e yake k'warai da gaske. Kawai sai na fashe da kuka tare da ce wa "Sai Allah ya bi mini hakkina da ka keta a gaban jama'a. Baka da buri irin ace an kai k'arata gaban iyayena. Ka je na barka da Allah ya bi mini kadin zaluncin da kake yi mini. Ban da ka mayar da ni banza ka yi mini hakan? Bayan kwanaki akan idona ka saka aka yi maka girki. Idan tak'amar kicin da kayan abincin naka ne. To kwanukan da tukwanen fa? Ai da sai ka siyo ka kawo mata, ko ta debo na uwarta." Da sauri ya ce "Amma Dada ai ta kashe wannan maganar. Na baki hakuri kuma." Na ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Ri'ke ha'kurin ka bana so. Tunda ka nuna ba ni da iko a cikin gidan da ake ce wa wai nawa ne, sai ka fa'da mini inda zan dinga zama da jama'ata, tunda ka sani a gidan ubana ma ina da inda aka ware mini nake zama na yi sana'ata." Ya koma gefe ya ce "Gidan ki ne ba wai ba ne". Da rawar murya na ce "Wallahi ba nawa ba ne. Domin da nawa ne ba zaka tozarta ni irin haka akan d'aki ba." Ya nisa ya ce "Tsakanin ki da Allah sau nawa ina gargadinki akan dakin? Ai ba sana'a na hana ki ba. Dakin ne ba zai yiwu ace mata suna shigar mini ba. Tunda dai shine dakina zan yi iyakacin kokarina na ba shi kariya irin yadda ake bawa dakin mijin da yake da daraja. Ki zo ki yi anan dakin, ko a falo ba ni da matsala da hakan. Amma wancan dakin baki isa ba, ba ki biyo hanyar da zai zama k'arkashin ikon ki ba Asiya". Na ji tamkar na sharara masa mari. Amma da na tuna maganganun Hajiya. Da alwashin da ta yi na zata fa'da wa su Gwaggo halin da nake ciki. Ya sanya na ha'diye dukkan fishina na ce "Ai shike nan". Ya mik'o mini ledar awara tare da ce wa "Ga shi na san baki ci abinci ba.". Ban kula shi ba. Ya mike ya ce "Sai da safe, yau na gaji likis." Kwana na yi, ina nadamar yadda zan dawo da Tijjani dakin nan alhalin bai nuna yana son ya dawo ba". Washagari bayan na idar da sallah barci me nauyi na yi. Sai wajen goma saura na farka. Na tashi na ga ya ajiye mini burodi. Na ga kuma kusan duk kayansa har wanda ban ga ya sa ba, ya wanke su, ya shanya su a igiya reras. Ashe fitar da yake yi da asuba aiki ya samu a gidan burodi. Kullum ya je suka yi aikin kwabi da d'aure wa. Za'a bashi babban burodi d'aya da donot guda hudu, da ku'di dubu da dari biyar. Idan ya dawo kuma ya huta sai ya fita gurin aikin saka tiles ko na gyaran setlite ko had'awa. Duk abin da ya samu a ranar zai yi. Na burodin ne sau hudu a sati. Dan haka baya rasa yan k'udade hidimar yau da kullum tunda ya k'i jikinsa. Mafi yawa kullum sai ya shigo da taliya daya ko macaroni. Wani lokacin kuma magi rabin leda sai da na ga robar maggin ta sake cika duk da bamu cinye kayan abincin namu ba. Da na yi tsam sai na fahimci baya son kayan abincin su k'are ne. Shi yasa kullum sai ya siyo wani abu ya ajiye akan kayan abincin, duk da har yanzu girkinmu ba kankama ya yi ba, sai na ga dama nake dafa wa. Jiya da garin rogo ya shigo rabin kwano. Ban ce masa komai ba, da na ga ni. Amma har zuciyata na fara gamsuwa Tijjani ba zai bar ni da hidimar gidansa ba, kamar yadda ake hasashe. Sai dai bazan yi saurin shaidar hakan ba sai nan gaba. Shiru bai dawo ba, yan k'unshi suka zo. Na rasa yadda zan yi, rana ta take barandar ba zata zaunu ba tunda inuwa bata zo wajen ba. Ni kuma ina k'yashin yi a falona. Na kasa samun mafita. Kan dole na ce musu "Ba ni da lafiya bazan iya yi ba. Suka tafi suna mini fatan samun lafiya, tunda sun san ni, sun ga kuma ramar da na yi. Suna fita yana shigo wa da alamu sun yi kicibus ma. Na kalle shi na dauke kai. Ya zuba mini ido ya ce "Sai yaushe zaki fara yi mini oyoyo da barka da dawowa ne?" Na gatsina fuska na ce "Eh ai ka yi mini sallama da zaka fice, bare ka saka ran zan yi maka sannu idan ka dawo". Ya girgiza kai ya ce "kullum fa sai na yi miki sallama Asiya. Yau ma sai da na leko na ga barcin na ki ya yi nauyi. Ni kuma wai kada na katse miki shi yasa na fita. Amma ki yi ha'kuri". Na dauke kai na ce "To". Ya mik'o mini leda tare da ce wa "Ungo nasan ki da son gurjiya, ganin ta na yi manya manya da ita. Shine na siyo, na taho na kawo miki". Na kar'ba a hankali na ce "Na gode". Karon farko da na yaba masa har na yi godiya. Da'di ya kama shi ya ce "Nima na gode miki. Ko na zauna na bare miki ne?" Tausayinsa ya kama ni wanda nake kasa gane dalilin raunin da yake kama ni akan sha'aninsa. A hankali na ce "Na hutar da kai" Dadi ya sake kama shi, walwalarsa ta karu. Ya zauna kusa da ni ya ce "Fa'da mini sunan turare mai k'amshi, kuma mai sau'kin ku'di." Kamar bazan kula shi ba. Sai kuma na bu'de baki na ce Dagmar". Ya zuba mini ido sosai sannan ya ce "Na tsani turaren nan, duk yadda yake da dadi mai nutsar da zuciya Asiya. Ya mike ya girgiza kai ya ce "Na gode da wula'kanci! Ai na sha ganin kwalin turaren a dakin Jabir. Shine kike son nima na saka saboda ki dinga jin kamshinsa a tare da ni?" Ba'kin cikin da yake zuciyarsa ya kasa boyuwa. Ya juya ya bar gidan gaba'daya. Kafin na tashi, sai ga shi ya dawo ya kwashe kayansa ya shiga da su dakin ba tare da ya tsaya ninke wa ba. Ya fito a hanzarce ya fice tamkar kububuwa. Abin mamaki sai na ji babu da'di. Yadda idonsa ya canja launi duk sai na damu ainun. Ga shi ban roke ki shi ya bar ni na dinga zama a dakin da yake yi mini tijara a kansa ba. Na tashi na shiga d'akin. Na ga ya zube su akan tabarmar da take shinfide a k'asa. Kamar na ninke sai kuma na fasa. Na janyo na rufe masa. Da yamma sai ga shi ya dawo da cakwal da gawayinsa a leda. A tsakar gidan ya yi shimfida. Ya fita ban san inda ya samo rushi ba. Na ga dai ya zo ya zuba gawayi akai. Tunda ya fara gugar nan bai tashi ba, sai da ya kammala tsab. Ya kalle ni ya ce "kin dafa abincin, ko baki yi ba?" Ba walwala na ce "Na dafa". Ya ce "To a dan bani". Ya fa'da fuskarsa a tamke. Na tashi na zubo masa, na rufe sannan na kawo. A wajen ya ci. Sannan ya kwashe kayansa ya yi dakinsa da su. Zuciyata ta yi nauyi tabbacin da gaske ba zai bar mini dakin ba. Ya fito, ya shiga wanka. Ina zaune a barandar ya fito cikin farar shaddarsa wani irin kamshi sai dukan hancina yake yi. Kamshin da ban ta'ba jin irinsa ba, mai matu'kar da'di. Ya yi kyau tamkar wani hamshakin attajiri. Zuciyata ta buga da irin haduwarsa, ya taje sumar kan nasa da take cike. Gashi bai sanya hula ba. Shaddar ta gogu. Kuma babu dying tunda ya sake waccar mai cibiri cibiri lokacin bikinmu, bai sake b'ata ta ba. Ya dai tara amma babu rini ko murde wa. Na kasa gane me nake ji. Na gan shi a yadda nake son ganinsa. Bai wani tsaya ba ya ce "Sai na dawo ya fice da alama masallaci za shi. Amma ga mamakina bai dawo ba sai da tara ta gota. Sannan da ya shigo ina jinsa da Rafia a zaure da alamu ita ma unguwa ta je a lokacin ta dawo. Da k'arfi ta ce "Ka gaida amarya kwana biyu bana zama ne shi yasa ban shigo ba". Ban ji me ya ce mata, tunda bai daga tasa muryar ba. Wani irin abu mai tsananin gaske ya tokare ni. Shaidan ya shiga zuciyata ya ayyana mini tare suka dawo. Shashanci suka je suka yi abunsu. Hawaye ya b'alle mini. Ya tarar da ni ina matsar k'walla. A rikice ya zauna kusa da ni ya ru'ko ni. Na fizge cikin kuka sosai na ce "Ka je kun gama iskancin kun dawo shine zaka ri'ke ni?" Ya zauna ya ri'ke kansa. Ya kasa ce wa komai. Amma ba k'aramin kidima ya shiga ba. *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*. ✍️ *BAKAR TA'ADA* *47&48* *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* Tsawon lokaci ina kuka shi kuma ya kasa ce wa komai. Da k'yar ya nisa ya ce "Asiya Toro son ki ya zame mini jarabta mai girma. Daga ranar da aka ambata mini za'a bani ke daga ranar ban sake samun y'ancin zuciyata akan lamarin ki ba. Me yasa zaki yi mini irin wannan mummunan zaton?" Ya fa'da cikin b'acin rai matsananci dan har wani haki yake yi. Na cigaba da kuka ban kula shi ba. Ya damk'e ni sosai cikin tsawa ya ce "Ina miki kallon yarinya k'arama kina mini kallon biri boko. Gaba'daya shekarun ki nawa ne a duniya. Ina tausayin k'ank'antar ki, amma ke abin da kika sani ya zarce na manyan y'anmata masu shekaru ashirin da biyar. Kin ture dukkan ka'idojin shari'a, kina ta musguna mini. Babu ragayya a tsakaninmu. Ai ko ban ci darajar aure ba ya kamata na ci na jini. Wallahi na yi zaton ko wani kika ji ya jefe ni da wannan al'amarin sai inda k'arfin ki ya k'are. Amma har da ke a cikin jerin wadanda suke mini yarfe dan na tozarta na yi ba'kin ciki.! Ya numfasa yana maida numfashi tamkar mai mura. Jikina sai bari yake yi a dalilin na shiga zullumin irin damk'e ni da ya yi. Nasan dalilin da ya sanya kike iya kallon idona kike jingina mini wannan Bak'ar TA'ADA. Saboda ban nemi hakkina ba. Ashe tunda ke ba yarinya ba ce kamar yadda nake miki kallo kuskure na yi, da na dauke kai. Tunda kin san kishi kin kuma iya har a kaina da ba sona kike yi ba shike nan, magana ta k'are zan d'ora miki girman da zai sanya ki dinga jin nauyin fa'da mini duk abin da ya zo bakin ki." Na yi muk'us ban da b'ari ba abin da jikina yake yi. Ya sake ni, ya fita. Ai ina ganin ya fita, na zabura na rufe k'ofar da sakata. Na yi shiru ina ta zare ido domin har lokacin zuciya ta bugawa take yi da tsananin gaske. Can na ji yana kwankwasa k'ofar. Na yi bakam a zuwan barci nake yi. Bai tsananta ba, ya juya ya tafi. Da asuba ban yarda na fita ba duk yadda fitsari ya matse ni, sai da na ji fitarsa masallaci sannan na yarda na bu'de k'ofar. Har ya je gidan burodi ya dawo barci bai dauke ni ba. Kamar daga sama na ji muryar Baban Marina a tsakar gidan. Zuciyata ta tsinke sosai. Gumi ya dinga yanko mini. Gaba'daya na tsorata na tabbatar Tijjani ne ya kai k'arata. A sanyaye na bu'de k'ofar, na taya Tijjani marabtarsa. A falo muka sauke shi. Ya amsa gaisuwa ta da walwala na d'an samu kuzari. Domin na lura babu bacin rai a tare da shi. Ganin hakan ya k'arfafa mini guiwa na mike na bu'de firij na d'auko ragowan k'wai uku da ya ragu. Na soya masa a gurguje tunda nasan da burodi. Kafin na gama shirya kofina a tray har shayin ya kusa juyawa. Na dauka na kai gaban Baban. Ina dawowa kuwa shayin har ya tafaso na juye a flask na kai masa. Cikin soyayyar da na kwana biyu ban ga ni ba a dalilin fishin da ya yi da ni akan auren Tijjani. Ya ce "Sannu Yabi. Allah ya yi miki albarka. Na ji da'din yadda na tarar da ku, kuna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Allah ya dauwamar da aurenku, ya baibayeku da albarka ta inda kuka zata da ta inda baku zata ba. Wanzuwar aurenku na cikin burina a wannan duniyar. Ki zauna lafiya, ki yi ha'kuri da kawaici irin na uwarki." Kaina na k'asa amma hawaye nake yi. Tabbas idan da Tijjani zai bu'de baki ya yi masa bayanin yadda muke zaune da bai yi wannan farin-cikin ba. Da bai sanya mini albarka irin hakan ba. Tijjani ya ha'da masa shayi ya ce "Bismillah Baba ka ci abincin Asiya". Da murmushi ya ce "Na riga da na karya, amma tunda Ubangiji ya nufe ni da zuwa gidanku zan ci abin da kuka ba ni. Ina fatan Ubangiji ya buda maka k'ofofin ciyar da iyali cikin sau'ki Tijjani". Nan da nan ya masa da "Ameen Baba". Yana kurb'an shayin Tijjani na yankar biredin yana cusa masa k'wai a ciki, yana mik'a masa. Ba wani sosai ya ci ba. Amma ya shanye shayin. Ya yi hamdala ya ci gaba da sanya albarka cikin marari. Ya ce "Tijjani ina fatan dai lafiya kuke zaune babu damuwa?" Jikina ya d'auki rawa. Amma ga mamakina sai ya ce "Lafiya k'alau muke zaune Baba. Ai Asiya har bayan idonka tana kiyaye tare da girmama umarninka". Da'di ya k'ara kama shi. Ya ce "Alhamdulillah! Allah ka so Asiya, ka sanya soyayyarta da tausayinta a zuciyar mijinta. Shi kuma ka bashi lafiya da jarumta da arziki mai gudana. Àllah ka zaunar da su lafiya, ka basu zuri'a dayyiba." Daga haka ya mik'e ya gyara rigarsa ya ce "Nurun ala nurun a dukkan rayuwar da zaku yi". Tijjani ya bishi suka fita, yayin da na bisu Ina fa'din "A gaida mutanan gidan, Allah ya k'ara lafiya mun gode". K'aran mashin din Tijjani ya tabbatar mini ya tafi mayar da shi ne. Bai dawo ba sai wajen k'arfe d'aya da rabi na tabbatar kuma sai da ya yi sallah. Kai tsaye wanka ya yi, ya sanya jallabiya ya shigo falon, k'amshin turaren da ya tsiri sawa ya bugi hancina. Ya zauna. Na yi kokarin kyautata fuskata na ce "Sannu da dawo wa." Ya kalle ni ya ga na yi kwalliya cikin wani fitinan material. *Wanda Umm Nihla mazauniyar Malaysia take odarsu.* Tuntube ta akan wannan lambar ta *manhajar Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa.*07020695644* Ya ce "Wow Asiya kin yi kyau tamkar yar tsana. Na murmusa na ce "Na gode". Ya numfasa ya ce "Wannan sannun ta ki nasan kin yi saboda rufin asirin da na yi miki ne". Na cuna baki na ce "Yo kai ma ai na rufa maka naka asirin ai". Ya matso kusa da ni ya ce "Fa'da mini rufin asirin da kika yi mini, ni da kin fallasa da ba hakan ba". Na dauke kai ina hura hanci irin na ta'bara da shagwaba. Ya sake susucewa ya ce "Saboda Allah me zaki ce masa ina yi miki na musguna wa?" Cikin yanayin tab'ara na ce "Abubuwa masu yawa, yo ni abubuwan da ka yi mini ban da dai ni din mai hankali ce, da tuni ba'a yi b'atacciya ba". *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* Ya maze ya ce "Ni nasan hankalin ki yawa ne da shi ai". Na sake ce wa "Ban da dai ina tsoron fishin Baba ai da tun ranar da ka sanya aka shigar mini kicin da tun ranar zan bar maka gidan, ita sai ta zauna kawai a madadina". Da sauri ya bar kan kujerar ya gurfana a gabana, ya ru'ko dukkan hannuwana ya sassauta murya ya ce "Asiya" cikin wani irin yanayi. Na kasa amsa wa, karon farko da ya ri'ke ni ban fizge ba. Domin gaba'daya maganganun Baba ya dagargaza ni, ya fahimtar da ni zama da Tijjani tilas ne. Zamana lafiya a gidan aurena yana nufin farin-cikin mahaifina na tabbatar Gwaggo ma ba zata so ta gan ni a gabanta da sunan mutuwar aure ba. Na zum'bura baki na ce "Uum". Ya yi kasa da murya ya ce "kalle ni". Na sake juyar da fuskata ba tare da na kalle shi ba. Da wata irin murya ya ce "Pls mana Asiya Toro". Na zakuda da sauri, na fara kokarin cire hannuna a nasa. Ina ce wa "Ai dai kasan bana son gatsa mini sunana da kake yi." Da azama ya ce "Indai zaki daina yi mini rashin kunya ai daga yanzu na daina fa'da miki. Kwanaki kin ce mini bana goge kaya, bana saka turare. Yanzu na fara yi dan kisan ba abin da bazan yi dan na samu aminci da nutsuwar ki ba. Amma ko ki nuna kin gane na canja, balle ki yaba mini na ji dadi". Na bata rai na ce "Akan me zan yaba? Bayan ba dan ni ka yi ba. Ina ce jiyan da ka fita sai da dare ya raba kana zan ce, idan ta yaba maka ai shike nan" Ya kame baki ya ce "Tabdi jam! Ya bar maganar ya canja da ce wa "Yanzu zan sake ba ki hakuri, ki manta maganar shiga kicin din ki. Na yarda na yi kuskure, dan Allah ki shafe ta a zuciyar ki. Nima na yafe miki zargina da kika yi jiya. Kin ga dai murna da addu'ar da Baban Marina ya yi. Kamata ya yi mu ha'da kanmu mu zauna lafiya". Na bata rai na ce "To ai kai abin haushin ka yawa ne da shi Tijjani. Bana son na ga namiji ya cika kule kulen mata, kai kuma kana tafiya a mashin ma kana iya tsayawa ka yiwa mata magana ko baka sansu ba". Ya sake ru'ko hannuna sosai ya ce "Billahillazi a da ne Asiya. Tunda muka yi aure bana yi, na rantse miki da Allah. Mussaman da kika ce mini mai kamun kai kike so, sai na sake kame wa sosai". Na yi shiru ya ce "shike nan komai ya wuce zamu zauna lafiya, zaki yarda na zama mijin gaske ba na wai ba?" Na ce "Sai ka yarda wanccan dakin ya zama zan yi yadda nake so a cikinsa". Ya ce "Kin san ban iya yaudara ba. Idan kin yarda na zama mijinki na sosai, ai gaba'daya ma ya zama naki, to me zan yi da shi?" Na ce "Ban gane ba?" Ya jima yana kallona har sai da jikina ya amsa sannan murya a dashe tabbacin ya shiga cikin shauki sosai. Ya ce "Idan dakinki ya zama shine nawa, kayana sun koma ciki, kin adanasu tamkar yadda kika adana na ki, sannan a ciki zan dinga kwana, a ciki zan yi komai. Shike nan dakin ya zama na lallen ki da duk bak'on kwana da zamu yi". Gabana ya yanke ya fa'di tamkar yanzu na fara jin ya kamata ya dawo dakina". Na yi k'asa da kaina na kasa ce wa komai. Ya marairaice fuska ya ce "Ki ce to Asiya, na matsu ki zama matar aure ta sosai, na k'osa ki zama babba." Kunya ta kama ni, na rasa yadda zan yi, sai kawai na fara kananun kukan shagwaba tare da ce wa "Ai yanzun ban girma ba kake nufi?" Da sauri ya ce "kin girma mana, shi yasa nake son na sake mayar da ke babba sosai". Na sunkuyar da kai na k'asa domin kunya ce ta sosai ta yi mini k'awanya. Ya dinga murza mini tafin hannuna wanda hakan ba k'aramin abu ya haifar mini a gangar jikina ba. Haka shima gaba'daya ya yi sanyi ido ya canja. Kunya ta sake kama ni. Kan dole sai da ya sake wanka kafin ya tafi sallar la'asar. Nima dai abin da na gani na kasa gane wanka zan yi ko tsarki. Dan haka sai na yi wankan gudun kokwanto. Na dinga mamakin lokacin da muka cinye bamu nemi ko abinci ba. Na shiga kicin na dauko plask din abincin wanda jallof din shinkafa ne. Na koma na dauko plates da cokula. Ya dawo ya tarar da abinci. Ya ce "Kamata ya yi muci a plate daya Asiya". Ga mamakinsa sai ya ji na ce "To." Na zuba mana, muna ci yana yi mini hira kala kala. Muna gamawa ya kalli agogo ya ce kwaso kayan ki na wanke miki". Na girgiza kai na ce "Bar shi zan wanke da kaina". Ya mike ya na ce wa "Bari na debo da kaina. Kan dole na bar masa wankin nan ya yi, ina baranda yana ta faman zuba mini hira. Ni kuma na kasa tanka masa, sai dai eh ko a a. Da daddare yana tafiya sallar isha na rufe k'ofata. Da ya dawo ya ga na rufe. A hankali ya dinga buga mini tare da kiran sunana, amma na kasa bu'de masa. Wata irin fargaba ta dinga ratsa ni. Kan dole ya hakura ya bar ni. Da safe da na fito ya amsa sallamar da na yi masa, kansa na kan doguwar rigata da yake goge wa. Tausayinsa ya tsirga mini, duk yadda na rufe masa k'ofa, kuma ban yarda na bu'de masa ba, bai sanya ya fasa goge mini kayana ba. Gasu nan birjik a gabansa da alamu ya jima yana yi. Tunda rigar da yake kan yi ne ta k'arshe. Sai da na yo brush na ce masa "Ina kwana?". Ya amsa babu yabo babu fallasa" Da ya gama zai fita na ce "Zaka dawo ne da rana?" Ya girgiza kai tare da ce wa "To me zan dawo na yi?" Na yi shiru sai na ce "To idan an zo k'unshi zamu shiga d'akin, kada ka zo ka dizga ni." Ya girgiza kai alamun bai yarda ba. Ya bu'de baki ya ce "Ban yarda ba. Kada ki fara, idan kuma kin ki ji, to ki tabbatar zaki ga abin da baza ki so ba". Na Kwakkabe fuska tare da fa'din "Amma dai kai ne ka ce zai koma nawa". "Na fa'da tabbas. Amma ai na fa'di sharadina. Baki yi abin da na ce ba, dan haka kada ki sake ki kai mini mutane d'aki". Daga hakan ya fita. Ina gama abun da zan yi. Na fara tunanin yau laraba, zan samu masu kunshi sosai har zuwa gobe. Ina matu'kar son sana'a ta, ina samun nisha'di da walwala a cikinta. Sannan ina son na dinga aika wa iyayena wani abu. Idan bana sana'a kuma bazan samu wannan alherin ba. Na tabbatar kuwa matu'kar da kayan Tijjani a dakin da nake son ya zama na zaman sana'ata, to kuwa da sannu zai kore mini jama'a. Na zabura na shiga dakin na dauko jakar kayansa. Na kai ta d'akina. Na sake dauko kwalin makorinin da ya zuba takalmansa a ciki. Na fito da shi tsakar gida na bu'de. Kafa hudu ne da alamu biyu a lokacin aurenmu ya siyesu tunda sabbi ne. Na goge su na kai su daki. Jallabiya da tawul din da suke rataye, na fito da su na shanya tunda da danshin ruwan wanka a tare da su. Bargo da filon kawai na ninke na barsu gefe daya. Na dauko kaskon turaren wuta da yake ci a dakina na saka na sakayo k'ofar. Cikin sauri na d'ora shinkafa da wake. Na kammala na ji almajiri yana bara. Na kira shi na bashi naira dari ya siyo mini salak da kokomba, domin kayan ganye sau'ki ne da su a Toro tunda muna kusa da Jos. Nan da nan ya siyo mini, na bashi guntun burodin jiya. Ina tsaye na yanka na wanke na rufe shi. Na ha'da kwanukan da na bata na wanke. Na shiga wanka. Na shirya cikin doguwar riga cotton mai gajeran hannu. Na saka hular da ta dace da rigar. Na kalli agogo na ga shad'aya ne da rabi. Ai kuwa sai ga wata ta zo kunshi da kitso. Na bude dakin muka shiga, na fara yi mata lallen, cikin kankanin lokaci na gama saka mata. Na dauko kujera a kicin muka fara kitson. Mun yi rabi sai ga tawagar yan mata wajen su bakwai har da amarya. Murna ta kama ni, domin ku'di zan samu ba ka'dan ba. Sannan bana cikin zullumin wula'kancin Tijjani. Ina gama kitson na fara yiwa amaryar tunda nata yafi wahala na salatif ne. Na gama yi mata, na fara yiwa daya cikin kawayen na ji k'arar mashin dinsa. Ya shigo da sallama. A zabure na mike na fita y'an dakin suka bini da kallo. A bakin kofar na tare shi da ce wa "Sannu da dawowa". Bai amsa ba ya sha kunu ya fara kokarin shiga d'akin duk da na tare k'ofar. Baki na rawa na sake ce wa "Sannu da dawo wa, muje ka sha ruwa, ka ga ni". Bai musa ba. Ya yarda ya bini zuwa d'akina. Na nuna masa jakar kayansa da take gefe akan kwalin takalmansa. Na ce "Babu kayan ka a dakin Wallahi. Ka ga tawul dinka ma?" Na d'aga labule ya gan shi akan k'ofa. Ya daure fuska ya ce "Indai a hakan zaki bar mini su, to kawai ki mayar mini abina can." Idona ya ciko da hawayen takaici. Murya na rawa na ce "Kawai dai sana'a ce baka son na yi Tijjani. Ban da haka, ga yadda ka ce na yi, zaka bar mini d'akin, na yi kuma ka ce ba haka ba". Ba wasa ya ce "Ai ba ki adana mini su kamar yadda kika adana na ki ba. Kin ajiye su tamkar suna wancan d'akin dan haka mayar mini su can din kawai." Da sauri na bu'de masa durowar na ce "Ka ga inda na bar maka fa, bana son na bu'de maka kaya ne baka nan. Da sai dai ka dawo ka tarar na jere maka". Ya saki fuskar ya ce "To shike nan. Amma kin yi sallah kuwa?" Na ce "dama d'aya zan k'arisa wa sai na yi kafin na fara yiwa wata". Ya kalli agogo ya ce kusan uku saura, kina neman duniya baki yi abin da aka halicce ki yi ba? Yau ne rana ta k'arshe da za ki ji ana kiran sallah baki bar k'unshi kin yi ba". Na ce "To". Ya ce "Je ki yi alwallah ki zo ki yi sallar a nan". Na fita ban ce komai ba. Yayin da Tijjani ya cigaba da ambaton *RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN.* Cikin farin cikin ganin tasirin addu'ar akan lamarin Yabi. Domin tunda ya ga al'amarin ta babu ragayya, babu soyayyar sa ko kad'an sai ya nace wajen yin wannan adduiakan al'amarin. Ya kuma fara ganin sassauco mai yawa. Mata ku rik'e wannan addu'ar sirrikanta yawa ne da shi. Na idar, na mike na kai masa abincin falo. Na dawo na gan shi kwance shame shame akan gadona. Gabana ya yanke ya fa'di. Saboda ya tube riga daga shi sai gajeran wando. Wani irin tsoronsa ya kama ni a dalilin duk jikinsa gashi ne. Kirjinsa kuwa yafi ko ina gashi. Ranar da ya tub'e a gaban su Hajiya da yake a kidime nake ban ga gashin irin haka ba. Na dauka iya kirjin ne kawai. Murya na rawa na ce "Abinci yana falo". Muryarsa a dashe tabbacin yana jin barci ko wani al'amari daban. Ya ce "Sannu da aiki". Na amsa da ce wa "Na tafi". "Tom, idan na ci zan fita, nasan ba son na lekoku zaki yi ba". "Na ce "Eh. To sai ka dawo din". Na saki labulen na je na cigaba da yi musu. Bai fita ba sai da la'asar ta yi. Sai wajen biyar na gama yi musu tunda na yiwa mutum biyu kitso a cikinsu. Ina gamawa na karkade jikina na wanke hannuna da sabulu. Na shiga kicin, na ga akwai donot sai kawai na dafa shayi na cika filas tunda akwai ragowar abincin rana da na yi Ana kiran magariba suka tafi bayan sun bani kudina. Na kirga na ga alherin da na samu ba ka'dan ba ne. Na ha'dasu na adana. Na yi sallah, sannan na shiga wanka. Nasan sai ya yi isha zai dawo. Amma abin mamaki har goman dare bai shigo ba. Haka kawai sai na fara jin zuciyata tana b'aci. Sai shad'aya saura ya dawo lokacin na gama fusata. Ya shigo ya ga ban ko kula shi ba. Na hau na yi suntum. Ya ce "Asiya na yi ta kiran wayarki a kashe." "Uhum" kawai na ce na kame bakina. Ya ce "Wallahi Maijidda ce zata haihu, haihuwar ta zo da matsala, zan taho, Dada ta ce na kai ta asibitin ta gano ta. To abin ba da'di, ganin mawuyacin halin da take ciki ya sanya Dada kasa barin asibitin, nima kuma sai na yi alkunya na zauna jiranta kada ta ce dama a dole na kai ta". Na ce "Sannu! zaman jiran matar da kake jiran a mutu ka aureta ta haihu ai wajibi ne. Na mike zan bar masa d'akin. Ya yi maza ya ru'ko ni. Ya ce haba Asiyata wacce irin magana ce wannan?" "Na ce k'arya na yi, baka fa'da ba?" Ya ce "Allah ya sauwake, ai na fa'da ne saboda kishin hure miki kunne da yake yi. Amma ni ko d'aura mini wata macen aka yi ba fincike wa zan yi na zura a guje ba." Na saki raina ka'dan. Ya ce "Dazun nan Dada ta gama ce wa yau watan aurensu goma da kwana goma. Cikin Ikon Allah gasu da y'arsu a hannunsu. Baki ji yadda ake ta saka musu albarka tare da diyarsu ba. Su tun a ranar suka manta da komai suka rungumi junansu". Ban kula shi ba. Maimakon ya yi shiru sai ya sake ce wa "Ni da na duba key holder din aurensu na lissafe sai na ga a lissafin bature watansu tara ba kwana uku ma". Kuka ya kwace mini, na ce "Na gode sosai da yarfe Tijjani". Ya marairaice ya ce "Mene ne abin yarfe Asiya? ". Na k'wace na koma gefe ina gunjin kuka. Ya numfasa ya ce "Amma kin san dai bana son kukanki ko?" Na zabura zan ce a gidan uwar wa? Ai ina tuna barin makauniyar da yake yi mini idan na fa'di hakan, na yi maza na ha'diye maganar na buge da jan tsaki da kara k'arfin kukan nawa". Shi da kansa ya a fahimci da zaginsa zan yi, sai kuma na fasa. Ya murmusa ya ce "Ban da abin Asiya Toro wai mene ne abin kuka saboda Allah? Ina ce da kin ji duk abin da ake fa'da miki da yanzu kina da cikin da ya yi daidai da kwanakin auren ki. Kina haihuwa sai dai a fahimci ke ma kin yi biyayya, kin manta da wanda ya manta da ke". Na mik'e na bar masa d'akin. Kai-tsaye band'aki na shiga. Na juyo zan rufe k'ofar na hango shi ya daga labule yana kallona. Sai da na ci kukana, na wanke fuskata na fito. Na ga ya koma ya bar ba'kin kofar. Na lallaba na shige falo na saka sakata na yi kwanciyata akan doguwar kujera bayan na kure gudun fankar. Ina kwance ba abin da nake so irin barci ya sure ni. Amma na kasa, zuciyata sai k'unci take yi. Ban san dalilin k'uncin ba, tunda na laluba ba haihuwar Maijidda ce ta dame ni ba. Jin shiruna ya yi yawa ya sanya ya biyo sawu. Ganin da ya yi k'ofar bayi a bude, ya sanya ya shiga d'akinsa. Nan ma wayam bata ciki. Ya nufi falo ganinsa a rufe, ga fanka na kad'awa da k'arfin gaske ya tabbatar da tana ciki. A fili ya furta "Bilhiillazi an jarrabe ni akan wannan azinanniyar yarinyar. Allah ka hore mini ita". Ya koma ya kwanta, amma barci ya yi masa tutsu. Idan ya tuna jaririyarsu Jabir sai ya ji tamkar ya wayi gari ya ga Yabi ta haifa masa tasa. Ya saki ajiyar zuciya tare da cewa "Wannan yar darun ma, ko sai yaushe zata bari ta girma, rimi rimi na fara shawo kanta, ta sake botsare wa tamkar me bugun aljan. Ya muskuta sai kawai ya tuno uniform din ta da ya karbo sai kawai ya murmusa sosai. Tare da ce wa "gobe da ikon Ubangiji zan rage wannan tutsun na ki na iyashege. Na riga na gaji da kallon ki tamkar hoto". Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* ✍️ *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES.* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* Washagari ko da na fito na tarar ya tafi gidan burodi. Dan haka na k'ira layin Gwaggo. Ta amsa tare da ce wa "Inji dai lafiya kika k'ira ni da duku dukun nan?" Na ce "K'alau Gwaggo. Na gaishe ta, ta amsa. Na k'ara da ce wa "Ki turo mini Anas ya zo ya karbi ku'di, za'a siyo mini lalle da mahallabiya. Sannan salatip din mai kala za'a siyo mini. Zan bashi da ku'di, dubu biyu naki ne, dubu uku kuma ki bawa Baba ya yi cefane, sauran kisa mini a bankina". Ta amsa da "To" tare da saka albarka mai yawa. Sai kuma ta ce "Zan dauki dubu a cikin wanda za'a jefa a bankin na bawa abokan zaman nawa,kowa drmaei biyar ko omo ne sa siya Yabi". A dole na ce "To domin dai mama idna yaranta suka kawo asafi sau tari ma ba'a ji. Idan kuwa an ga ni ma, to mafi yawa baka sanin yadda aka yi da shi. Na kasa komawa barci. Sai kawai na tsiri shara, na gyara ko ina. Sanin zai dawo da burodi ya sanya ban yi haramar dafa wani wani abu ba. Na yi wanka, na shirya, na zauna a falo. Babu wuta bare na yi kallo. Ina ta sake sake har ya dawo. Ya shigo ya kalle ni ya ce "Asiya Toro kina da kunnen k'ashi. Wata'kila dai kin fi son sai na fito na fa'di gaskiyar yadda muke zaune". Na sha kunu ban tanka masa ba. Ya zauna ya ce "Abin da kika yi jiya ya yi dai-dai ke nan? Kin b'ata mini rai. Amma na yafe miki, sai dai ki sani idan kika sake bazan yafe ba". Na sake yin shiru. Ya tashi yana ce wa ni fa yunwa nake ji". Na fito, ganin yana janyo ruwa na tabbatar wanka zai yi, tunda sai zufa yake yi. Bayan aikin k'arfi da da ya yi nasan kuma da gudu gudu yake dawowa saboda ya saba da atisaye. Na duba ledar da ya ajiye, burodin ne da donot din. Sai madara da milo na sacet ko wanne guda daya. Tausayinsa ya kama ni, nasan ni ya siyo wa, shi kuwa sai ya sha ba'kin shayi abinsa. Muka karya, yana ta jana da hira amma na d'ad'are. Ya zabura ya fita da hanzari, alamun ya tuna wani abu. Sai ga shi ya dawo da leda ya mik'o mini. Na kar'ba, na bu'de ganin uniform din makarantana ne. Ya sanya na kalle shi da neman k'arin bayani. Kai-tsaye ya ce "Na karbo miki ne saboda ina da sha'awar ki samu takardar kammala sakandire. Tuni an gama ristar Waec. Amma ta Neco da saura. Idan Ubangiji ya hore mini zan biya miki ki zana. An kusa fara yin tumfirint zaki je ki yi nan da sati biyu". Wani irin farin-ciki ya kama ni marar misaltuwa. Na dinga fa'din "Na gode sosai Tijjani". Domin ban ta'ba hakaito hakan ba, tunda dama ni karatun ba damuna ya yi ba. Amma na ji da'di, zai zama ni ce mace ta farko a gidanmu da nake da takardar kammala sakandire. Ya ce "Amma fa idan kina mini rikicin banza, da rufe k'ofa haka siddan zan fasa ne, tunda alheri misaye ne". Da sauri na ce "Na daina, amma kai ma ka daina yi mini yarfe". Ya kwashe da dariya ya ce "Lallai Asiyata ba yarinya ba ce tunda tasan yarfe har tana jin ciwo idan an yi mata." Na b'ata fuska na ce "Kallon dai mahaukaciya ka ke yi mini kawai". Ya ce "Haba ni yanzu idan za'a tambaye ni kaf gudan Marina wa cece ta fi hankali kina ganin zan tsallake matata ne?" Na dauke fuska ina motsa bakin ni ban yarda ba, da'din baki ne kawai. Ya yi murmushi ya ce "Asiya kin same ni da yawa. Kin shiga zuciyata kin yi kane kane, sai wahalar da ni kike yi. Ko tausayi babu a lamarin ki". Na cuna baki na ce "Gwano baya jin warin jikinsa ai". Ya basar ya ce "Nan da sati uku zan je Toro daurin auren diyar Baba Shehu. Jibi ma zani daurin auren abokina amma bazan kwana ba, idan kuma na ga zan yi dare zan kwana d'aya. Na washe baki na ce "Ka ce na shirya kawai." Ya zuba mini ido ya ce "ke yanzu sai ki bi ni?" Na ce "Ai na je ma na gama. Ya shiga girgiza kai ya ce "Bazan je da ke ba, bana son rikici, wata'kila dai nan da sati ukun na tafi da ke." Na b'ata rai na ce ", Gaskiya ni dai zan je". Ya ce "gaskiya ba zani da ke a hakan ba. Haka kawai ki janyo mini b'acin rai. Babah tana kallon ki zata gane ke d'in budurwa ce kin kuwa san ai ranta b'aci zai yi, ta yi mini fishi mai tsananin gaske". Kunya ta kama ni. Na yi kasa da kaina. Bakina ya mutu murus. Ya sake ce wa "Wata'kila dai bikin Salima na tafi da ke, idan na gamsu da zamanmu". Ban yarda na sake yin magana ba. Ya ce "Ki shirya da yamma idan na dawo zan kai ki, ki yi barka". Babu walwala na ce "Tom". Muka karya, ya yi wanka ya fice. Yau ma na samu y'an lalle, dan ma wasu hakuri na basu, tunda zan fita. Anas ya zo ya karbi sakon. Sai da ya ci abinci sannan na na bar shi ya tafi. Wajen k'arfe biyar ya dawo na shirya na yi fes da ni l. Sosai na yi kyau, rashin nauyin yadin yana sani d'oki sanya shi. Riguna guda biyu masu kyau muka siya a wani plaza sannan muka wuce. A k'ofar gidan muka tarar da Yaya J. Da kansa ya yi mana iso. Ina falon Maijidda su kuma suna tsakar gida suna hirarsu. Zuciyata sai girgiza take yi. Ga shi dai Bulkachuwa ya kere shi a kyaun sifa da k'irar k'arfi. Amma so ba k'arya ba ne. Haka na baro gidan ban yarda na kalle shi sosai ba. A hanya Tijjani sai ce wa yake yi ba ki ga yadda jinjirar ta yi maki kyau a hannunki ba. Ba ki ji sha'awar ki samu ta ki ba?" Ba tare da na zurfafa tunanin komai ba na ce "Na ji mana, sai na ji kamar su bani na tafi da ita". Da sauri ya ce "Maijidda ba zata ba ki ba. Kawai ke ma ki dage ki samu ta ki". Na ce "To Àllah ya ba ni" "Ameen dai Asiyata. Oh har na hango ki kina bata nono". Kunya ta kama ni na yadda ya fa'di sunan mama gatsar gatsar. Duk yadda na dinga ro'kon sa akan muje gidan Marina. Bayan Isha sai mu koma namu gidan k'i ya yi. Da zai shigo gida bayan isha sai ga shi da kaza da yoghurt. Ya tisa ni gaba da zantuka masu nauyi, masu nuni da ya kai k'ololuwar gajiya da zuba mini ido. Na rasa yadda zan yi, domin gaba'daya ya hana ni samun damar da zan gudu na rufe kaina. Tunda ko bandaki da zan shiga bina ya yi ya tsaya a bakin k'ofar. Duk yadda na share lokaci mai yawa ina ciki. Da na fito a zaune na gan shi yana dakona bai gaji ba. Ya ru'ko hannuna. Har cikin dakinmu. Zuciyata sai harba wa take yi. Gaba'daya harshena ya yi mini nauyi. Ya ja ni jikinsa ya rungume sosai tamkar zai mayar da ni ciki. Gaba'daya ma b'oye ni ya yi a jikinsa, tunda ya yi mini rumfa saboda tsayinsa da zatinsa. A hankali ya ce wannan karkarwar da kike fa Asiya? Nutsu, bazan cutar da ke ba". Ni dai na kasa bu'de baki na ce k'ala kanzil. Sallar da ya sanya ni dole. Na bishi ne mun yi babu nutsuwa a tare da ni. Akan sallayar ya shiga b'are b'are. Ina ji, ina gani ya salube mini rigar jikina. Na shiga ki'dima a dalilin abubawan da yake da sassan jikina. Na fara kuka. A ki'dime ya ce "Kada ki zalunce ni, kukan ki na tayar mini da hankali. Na riga, na ku'dira aniyyar yin aure yau, kada ki janyo wa kanki tsinuwar mala'iku.". Jin hakan ya sanya na saddak'ar babu tsumi babu dabara. Yau sai yadda Allah ya yi da ni. Yana jagwalgwala ni yana ce wa "Ai Baban Marina tuni ya dauka mun saba tsintar kanmu a cikin wannan yanayin. Shi yasa ya dinga farin-ciki da roka mana albarkar rayuwa." Da rawar murya na ce "Ka yi mini girma Tijjani, tsoro nake ji kada ka fasa ni". A kunne kamar mai rad'a ya ce "Za ki dauke ni, Ubangiji ne ya shirya komin girman namiji baya gagarar mace ta dauke shi". Da wayo, da rarrashi, da dabara ya samu ya kai ga gaci. Amma ni din ba k'aramin galabaita na yi ba. Domin kuka da shure shurena bai hana shi komai ba, sai da ya tabbatar ya kai inda yake son kai war." Sosai shimfidar ta baci. Wanda bamu lura da hakan ba a lokacin. Ni kam bayan na samu ya rabu da ni, sosoai na bu'de baki nake kuka domin ji na yi k'asan na zugi tamkar an watsa mini borkonon tsidugu. Sannan haka siddan na ji wata irin fargaba ta yanko mini tamkar ina cikin tsaka mai wuya. Dan haka na dinga kuka tamkar raina zai fice. Tun yana rarrashi, har ya hakura ya zuba mini ido. Ya rasa yadda zai yi. Kan dole ya hakura ya bar ni ya je ya yi wanka. Ya dawo kenan aka kawo wuta. Dan haka ya yi sauri ya jona ruwa a yar karama butar dumama ruwa wacce tafi kama da matsakaicin jug. Da k'yar da makyarkyata na yarda zan yi wankan. Ai ina gwada yin tafiya sai kawai na durk'ushe na sake fasa ihu. Domin zafin da ya sake ratsa ni mai tsananin gaske ne. Bai tsaya bata lokaci ba, caraf ya sure ni ya kai ni bayin da kansa. Ya surka mini ruwan sannan ya fice. Ruwan zafi sai ya zama tamkar garwashi dan haka ban yarda na zauna sosai ba. Na watsa na fito. Yana jin bu'de k'ofar ya karaso. Ya sake surata, yana tafe yana manna mini kises bai ko damu da kukana ba. Ina gunjin kuka har barci ya wuce da ni. Ya jima yana kare mata Kallo. A ransa yake tambayar kansa duk barnar da ya yi a baya sai a kuma aka bashi kamilar mace wanda wani namijin bai ta'ba kusantar ta ba. Wata'kila kuma dan ya yi sahihiyin tuba ne. Ya tsinci kansa da fa'din ", Astagafirillah". Ya shinfida sallaya ya fara salla tunda ya yi alwallah da ya yi wanka. Sannan ukun dare ta gota. Ba abin da bai roka ba, inda yafi maimaita wa a addu'ar tasa sai a hore masa lafiya da arzikin da zai sauke hakkin ciyar da Yabi da sauran dawainyarta. Ya dinga ro'kon a cika zuciyarta da sonsa kwatankwacin yadda aka cika tasa zuciyar da kaunarta. Har aka fara kiraye kiraye sallah bai runtsa ba. Yana gaban Ubangiji yana godiya tare da neman rabauta. Sai da ya sallaci raka'aitainil fijir sannan ya tashi Yabi. A hankali ya jata jikinsa ya rungume. Ai kuwa yadda ta yi barci da kuka. Sai kuwa ta tashi da kukan. Ya kankame ta ya ce "Is ok kukan ya isa hakan. Mu je ki yi alwallah, bana son na tafi ban taimake kin yi alwallah ba." Cikin kuka na ce "Da ina da band'aki a ciki ai da ko da rarrafe ne zan je da kaina, ba sai an taimake ni ba". A hankali ya ce "Ko akwai ma zan taimaka miki. Ai nuna kulawa da yabawa a lokacin da ka samu alheri a tare da mutum abu ne mai kyau." Ganin bai tunzura ba, da na yi maganar bandaki sai kawai na rushe da kuka ina cewa "Wayyo bandaki a d'aki nake so ni ". A raunane ya ce "Haba Baby girl, kin shayar da ni farin-ciki, ai bai kamata kuma ki rikita ni irin haka ba. Ki yi ha'kuri, zan miki daki mai bandaki In sha Allah. Amma yanzu ki yi hakuri kin ji". A daddafe dai na yarda ya kai ni, na yi alwallah. Sannan ya tafi masallaci. Ana idar wa ya dawo, duk da yau ba zai je gidan burodi ba, da wucewa zai yi atisaye. Amma ko tashi ban yi akan abun sallata ba. Da rawar jiki ya sure ni, yana ce wa "Barka da safiya My Asi beauty." Ya ta'ba jikina ya ji zafi. Ya fita da sauri, jimawa ka'dan sai gashi ya dawo da kofi mai dauke da shayi, hannunsa kuma da Panadol. Da magiya da ban baki na sha shayin, na ha'diyi magani sannan ya rungume ni tamkar jinjira, muka kwanta. Barci muka yi ainun. Dan kuwa sai bayan shad'aya muka tashi. Shi ya dafa mana indomie. Ya saka kazar jiya a ciki. Da lallashi ya sanya ni yin wanka. Da na fito duk yadda nake ture shi, sai da ya ware tawul din ya shafa mini mai Na runtse idona a dalilin kunya da takaicin sun yi mini rubdugu. Amma shi ko a jikinsa sai yaba laushun fatata da k'oda farina mai kyau ne irin nasa. Ni dai ban kula shi ba. Asalima runtse idona na yi tunda ya riga ya tube ni, yana kare mini kallo tamkar tsohon maye. Yinin ranar bai fita ko'ina ba, sai masallaci wannan kam da azama yake fita. Hatta wayoyinsa kashe su ya yi. Yayin da ni kuma na lanjare, ko motsin kirki na k'i yarda na yi. Yan k'unshi kuwa sai zuwa suke yi. Da kansa ya ke fa'din bata jin da'di, kuma tafiya ma zata yi sai satin sama zata dawo. Dana gaji da jin wannan bayanin nasa, sai na ce shin ina zan tafi ne?". Kansa tsaye ya ce "Hutun lalle zaki tafi. Dan ba zai yiwu muna amarci ana damunmu ba." Na girgiza kai domin kuwa zan ga yadda za'a yi na sake yarda ya gana mini azabar da na sha a hannunsa jiya. Na tabbatar da gayya ya nuna mini rashin tausayi. Kamar jifa ya tafi sallah la'asar sai ga Hajiyar nan. Tana ganina ta gane yanayin da nake ciki. Ta dinga murna tana ce wa "To ko ke fa? Yanzu zai kara son ki, zai kara manne miki. Ke kuma ki yi juriya, ki yi biyayya shi kenan sai ki damk'e shi a hannun ki. Duk wanda zai musguna miki zaki ga ba zai yi k'ima a wajensa ba." Na kasa jure wa na ce "Amma gaskiyar magana ya yi mini yawa Hajiya". Na fa'da ina rusa mata kuka. Ta yi shiru ta ce "Ke kam ranar da zaki haihu da kallo." Ganin da gaske nake kukan ta sassauta ta ce "Iya na yau ne. Da zarar kin zama y'ar gari shi kenan sai rawar kai da falli, da zai dauki lokaci bai nemi ta'ba ki ba sai an ji kanku". Da kuka na ce "Allah ya kyauta na yi hakan Hajiya. Ni bana sonsa, amma an takura, an tursasa ni" Jikinta ya yi sanyi ta ce "ki yi ha'kuri da sannu zaki so shi ne. Kuma ina tabbatar miki kina sonsa ko ya ya ne. Tunda na ga kishi a idon ki ranar da ya yi miki wannan iyashegen." Na yi shiru ba dan na gamsu ba, sai dan ta wuce na yi musu da ita. Ta dinga rarrashina da nasiha. Har ta samu na nutsu. Ta tafi tana ta yi mini addu'ar alheri. Na sani kuma saboda kirkin da Gwaggo take yi mata ne ya sanya ta damu da lamarina. Ta fito da leda a jakarta ta miko mini. Ta ce ki dinga shan wannan, wannan kuma ki dinga shafawa. Na zuba wa magaunnan ido na tabbatar masu daraja ne,na manyan mata ne mussaman da na ga G.H.T. product ne. Ta ce "suna da kyau a wajen wata baiwar nake siyansa, ita ce ta zaba mini su, yayarku Sajida nake siyawa. Shekaranjiya na siya, jiya ta Sako mini a mota. FASEELAT da cika alkawari take, ga shi zata baka kaya masu kyau. Ga lambarta Dan nasan watarana zaki so ki sake siyansu" *07039269802* Na dai ce na gode, amma ba wani abu da zan yi akan Tijjani. Ta tafi babu jimawa ya dawo da leda a hannunsa. Ya zauna kusa da ni. Ya bude kamshin hadadden tsiren da ya yi shura a garin Toro ya bugi hancina. Yawun bakina ya tsinke. Amma na maze tamkar bai bani sha'awa ba. Sai da ya dinga ro'kona sannan na yarda na ci. Da daddare muka kwanta, bai nemi komai ba sai rungume ni da ya yi. Washagari da zai fita sallah ya ce zai wuce wajen aiki sai ya dawo. Na amsa da adawo lafiya. Na bi shi na sanya sakata. Sai wajen tara ya dawo. Shi ne ya tashe ni tunda k'arar kiran wayata da ya yi ne ya tashe ni. Yau bayan madara da milo har da k'wai guda hudu a ledar. Sai da ya yi wanka ya shirya cikin shudiyar shadda da ta sha guga, ga k'amshin turaren da ya fara sanyawa mai da'din kamshi ya baibaiye hancina. Yauma shi ya shiga kicin. Ya soyo kwan. Ya hado shayin da burodi ya kawo gabana. Muka karya. Sannan na yi nawa wankan. Da yake tsamin da jikina ya yi da sau'ki, kwalliya na yi mai sauki. Na kalli fuskata na ga ta d'anyace. Na sake yin fari. Shi kuma baya gajiya wajen kawo hannunsa jikina. Tun lokacin na gane jarabarsa ba k'arama ba ce. Washa gari ya yi sammmako ya fita. Duk tunanina gidan burodi ya tafi. Amma bai dawo ba sai gaf da maghariba. Kayan jikinsa ya tabbatar mini ba a wajen aiki yake ba. Ya mik'o mini ledar hannunsa tare da ce wa "Ga shi in ji Babarki." Ina jin hakan na fasa masa kuka har da dirowa daga kan kujerar. Ya tarairayo ni a gigice. "Saboda Allah fa kin girma Asiya. Yanzu ai kin wuce irin wannan kukan." Da kuka na ce "Amma na ce maka za ni, shine ka tafi babu sallama?" Ya sake rungume ni sosai. Ya sanya kansa a kan wuyana. Cikin rad'a ya ce "Sorry Asiyata. Daga yau bazan sake ba. Takanas ma zan shirya mana zuwa Bulkachuwa. Kwana nawa zaki yi?" A hankali na ce "Sati biyu". Ya lank'awasa harshe yana ce wa "Sati d'aya dai Sweetie". Daga hakan ya dinga kissing dina, har sai da na ji jikina ya amsa sosai, na zame na koma kan kujera. A hakan muka kwashe kwanaki hudu ban yarda an sake ba. A wannan ranar kuma ya rikice akan ya yi iya ha'kurin da zai iya. Kusan k'arfi ma ya sanya mini. Sai me? Gaba'daya sai na ji babu banbanci da na farkon wajen zafi da radadi, na rasa yadda zan yi. Na tattaro dukkan k'arfina wai akan na ingije shi, amma abu ya faskara. A wannan ranar kam har cizo na yi ta gasa masa. Amma bai sanya ya k'yale ni ba, sai da ya yi yadda yake so ya gama. Kukan da na yi a wannan dare ya zarta na ha'duwarmu ta farko. Hankalinsa ya yi mugun tashi. Ya rasa inda zai tsoma ransa. Ya gaji da rarrashi ya zuba mini ido. Can ya nisa cikin rauni sosai ya ce "Asiya irin wannan bacin rai kamar wanda na yi miki fyade. Kin san k'uncin da nake ji kuwa. Kin san yadda kika tayar mini da hankali. Me zan yi miki kin rangwanta mini k'iyayyar da kike yi mini?" Jikina ya yi sanyi. Amma rad'ad'in da nake ji ya hana ni na daina kukan. Ya numfasa ya ce "Ki yi hakuri ko wacce mace da hakan ta girma." Da rawar murya na ce "Billahillazi bazan yi hakuri ka sabauta ni a banza ba. An yi na farko, an yi na biyu to kuwa ba za'a yi na uku da ni ba. Na riga na sani, baka iya yi da y'an k'ananun mata irina ba. Ka saba danne tima tima masu manyan halittu shi yasa nima kake gwada mini rashin imani kana ganin tamkar babbar mace ka samu". Jin ya yi shiru ya sanya na d'ago na kalle shi. Zuciyata ta tsinke a halin da na gan shi. Gaba'daya idanuwansa sun yi jawur tabbacin zuciyarsa ta b'aci ainun da kalaamina. Bai ce komai ba. Ya tashi ya bar dakin. Wanka ya yi, ya dawo dakin ya shimfida abin sallah ya tayar. Yanayinsa ya saka kukan ya tsaya cak. Na rasa gane tausayi yake bani ko kuwa mene ne? Washagari bayan ya dawo daga gidan burodi ya gama duk abin da zai yi mana. Ya kawo mini abin karyawar har d'aki. Fuskarsa babu walwala ya ce "Sai na dawo". Ban amsa ba. A dalilin kuttun da ya shak'e ni. Don me zai fita? Ba zai zauna ya kula da lafiyata ba. Ya tafi bai jira amsawa ta ba. Na dinga kuka. Zuciyata tana kissima mini ai ya samu abin da yake so shi yasa bai damu da ya tsaya na yi wanka ko na karya ba . Da rana ya dawo, ya zauna ya kalle ni. Yayin da ni kuma na d'aure fuska sosai. Ganin hakan ya mik'e shima fursakarsa a d'aure ainun ya ce " Ban samu ku'di na siyo abin da zaki ci ba. Me kike son ci na dafa miki?" Cikin son na wahalar da shi na ce "Faten doya da wake. Sannan da alaihu da kifi a ciki." Ya nisa ya ce "Ba ni da kudin da zan sayi kifi yau. Zan dai je na siyo alaiyahun. Ya fara tafiya da nufin fita. Na bu'de baki na ce "Zo ka kar'ba. Ni ina da kudin". A zafafe ya juyo "Cikin kaushin harshe ya ce "Asiya Toro baki da kudin da zaki yi mini cefane matu'kar ina da lafiya, ina kuma kan k'afafuna. Ba zaki yi ku'din da zaki aike ni, na siyo abu sannan na zo na girka miki ba, har abada kuwa". Ganin yadda ya rikice ya koma Bulkachuwan sa sai na yi maza na kame, domin na sani yana iya dauke ni da mari. Na laluba na kasa gane fishin me yake yi tun dare. To me na yi masa? Ni da ya ganawa azaba ma ban yi masa zafin kai ba sai shi zai dinga yi mini muzurai da hargagi?. Ya yi k'wafa ya fice bayan ya jira na tanka, amma na yi muk'us. Ina ta jin b'ab'atunsa a kicin. Ga mamakina sai ga shi ya kawo mini lafiyayen faten doya da wake a ciki. Ya ji alaiyahu da albasa mai lawashi. Nabi bayansa da kallo. A dalilin bai zauna ba fice wa ya yi. Ina jinsa a kan baranda ya zauna yake cin nasa. Haka kawai sai na ji guiltiness na kama ni to me na yi masa?. Da ya gama bai lek'o ba. Daga inda yake ya ce "Sai anjima". Na rasa gane manufar wannan abin da yake yi. Da daddare ma da ya dawo bayan ya yi wanka. Ya dube ni ya ce "Zaki ci donot da tea ne, ko kuwa da abin da kike son ci?" Cikin kuka na ce "Bazan ci komai ba Tijjani. Na hutar da kai" Na cigaba da gunjin kuka. Da farko kamar ba zai tanka ba. Sai kuma ya kasa jarumtar share ni. Ya ce "Wannan kukan fa? Ko dan na fa'da miki bana so shi yasa kike ta yi, tunda burinki ki kassara ni da ba'kin cikin ki". *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* "Na tsagaita da kukan na ce "Akan me zaka dinga yi mini fishi, alhalin ni ya kamata na yi". Ya zuba mini ido yana yi mini kallo mai tsananin gaske. Cikin b'acin rai ya ce "Idan a duniya akwai abin da na k'i to a jingina mini waccar Bak'ar TA'ADAR ne. Ta yaya kina matar aurena zaki dinga kallon idona kina fa'da mini maganganun da suke neman sabauta ni. Ban da dai kin mayar da ni shasha marar mutunci kya fa'da mini na saba danne mata akan idona?" Jikina ya yi sanyi ganin yadda yake cikin fishi sosai idonsa ya kad'a har k'walla ne kwance a cikinsu. Tabbacin ba karamin k'ona masa rai na yi da kalamun nawa ba. Ban san ya aka yi ba na ce "Allah ya baka hakuri Tijjani". Ina rufe baki ya matso jikina ya ce "Shike nan na yafe miki duniya da lahira. Na huce". Na ce "Amma zan fa'da maka gaskiyar magana". Ya ce "To ina sauraren ki." Na kawar da fuskata na ce "Gaskiya baka iya wannan abin ba. Ba haka ake yi ba, sannan ba haka k'awayena da aka yi musu aure suke ji ba. Domin ni dai ko a littafi idan ina karantawa ba'a shan wannan azabar da kake gana mini. Na tabbatar da haka kowa yake ji da Adda Nazira ta fa'da mini. To ina ganin iyawa ne kawai baka yi ba gaskiya". Ya sake kallona, ba tare ya ce uffan ba, na tabbatar ya rasa me zai ce mini ne. ✍️ *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* *BAKAR TA'ADA* 51&52. Me ya tuna oho. Na ga dai ya ha'diye dukkan fishinsa da mamamkinsa ya ce "Nasan ke ma baki iya ba, bare na kwantar da kai ki koya mini." Na dauke kai na ce "Mu y'an kananu ba'a d'aukar lokaci mai yawa tare da mu." Ya murmusa ya ce "Shike nan next time zan kiyaye." Na sake dauke kai na ce "Ni fa ba zan sake yarda ba". Ya murmusa ya ce "Ai hakan ma na gode". Bai sake tayar da maganar ba. Ya dinga ririta ni. Muka kwana lafiya lau. Washagari zai fita bayan mun karya tunda babu zuwa gidan burodi. Na kalle shi na ce "Ina son zuwa gidan Adda Nazira". Ya girgiza kai ya ce"Ba yanzu ba Asiya". Na bata rai na ce "To sai yaushe?" "Ta kusa haihuwa ai, sai Allah ya sauke ta lafiya. Kya je ganin abin da ta haifa miki". Na tsuke fuska na ce "Gaskiyar magana fa Tijjani ba irin wannan rayuwar nake harin samu ba.". Ya girgiza kai ya ce "Ki gode Allah dai". Na zum'bura baki na ce "Kullum cikin godiyar na ke. Amma yanzu an daina irin wannan takurar fa". Ya kalle ni ya yi murmushi tare da cewa "Asiya Toro manyan mata". Daga haka ya tafi ya bar ni. Kwana hudu a tsakani na warware na cigaba da harkokina har da sana'ata. Shi kuma ya daure bai sake takura ni ba. A haka muka sake kwashe sati. Har lokacin kuma ban sake yarda mun ha'du ba, duk jarabarsa kuwa. Ya rasa yadda zai yi da ni. Domin duk dare sai na sanya panties uku, sannan na saka dogayen wanduna biyu. Na sake saka riga a kai. Duk hilarsa ya kasa cimma ni. Ya gaji da rara-gefe ya koma rarrashi. Amma fir na k'i domin gaba'daya na tsora ta. Da gaske rad'ad'in da nake ji ya wuce misali. Rannan da daddare ya kasa barci. Ya tashe ni, a marairaice yake lallaba ni. Murya a raunane ya ce "Ina jiye miki tsoron tsinuwar mala'iku Asiya." Rai a bace na ce "Ni gaskiya bazan yarda ba, haka kawai ba komai a ciki sai azaba. Daga gunka ne matsalar, tunda ai ba haka ake ji ba, ni ce nake jin hakan." Ya ru'ko ni a diriri ce ya ce "Allah zai taimake ni. In sha Allah yau ba zaki ji zafi ba. Ki yi ha'kuri kin ji. Da ace kin bu'de mini zuciyarki ba zaki ji zafin har haka ba". Duk yadda ya ki'dime da son na aminta da shi fir na bijire, da na ga zai saka mini k'arfi ma. Kuka na dinga yi masa mai tsananin gaske. Ya k'yale ni. Amma barcin da bai yi ba ke nan. Washagari ya tashi da azumi. Amma me? Da ya dawo daga gidan burodi sai gani na yi, ya fito mini da tarkacen filillinkan lallena da na saka aka kawo mini su daga gida. Hatta robar da nake k'wabin sai da ya fito mini da ita. Ya shigo d'akina ya kwashi wasu daga cikin kayansa. Ya mayar can. Ina kallonsa ban ce komai ba. Amma dai kam na shiga damuwa. Domin an jarrabe ni da son sana'a tun ina k'aramata. Ina samun nisha'di a cikin yin lalle da kitso. Na sani kuma ba zai yiwu na mayar da falona wajen dabdalar yin k'unshi da kitso ba. Ya gama uzzirinsa ya yi shirin fita. Ya same ni har cikin falon da nake zaune. Fuskarsa babu walwala ya ce "Asiya kada ki shigar mini daki, ina bu'katarsa. Domin kwanan cikinsa zai fiye mini masalaha ga lafiya ta". Na kalle shi. Yadda ya tsare gida ya sanya na kasa sakar masa bakaken maganganu. Na tsuke fuskata na ce "Al'kawarin ke nan? Ni ba Tijjani ne ya ce ya bar mini d'akin na yi yadda nake so ba?" Ya girgiza kai ya ce "Tijjani ne ya fa'da, yanzu kuma ya fasa sai ya ya?" A kufule na ce "Sai hukuncin mai sab'a al'kawari ya hau kansa". Ya ce "Ya hau din. Tunda dai ba tsinuwar mala'iku zata hau kaina ba ai da sau'ki". Na sake hassala na ce "Wai na tambaye ka mana?". Ya ce "Kunne na jin ki". Babu tsinkaye na ce "Ni a siffofin munafiki ai har da sab'a al'kawari ko?" Da budaddiyar murya ya ce "Eh" , sai kawai ya shammace ni ya dauke ni da mari". Na zunduma ihu ina ce wa "Manzallazi ya saka mini akan wannan zaluncin da kake yi mini". Ya ce "Idan zaki zage ni sau dubu. Ni kuwa zan d'aga miki hannu sau dubu. Shege ka fasa a tsakaninmu. Kuma idan kin cika marar kunya ce ke, to ki shiga mini d'aki da nufin yin k'unshi, ki ga kalar tawa rashin kunyar". Na kasa ce wa komai illah kuka sosai da nake yi. Bai damu da kukan ba, ya saka kai ya fice. Asarar da na yi, a yinin wannan ranar ba ka'dan ba ce. Domin kuwa mutane sun fi goma da suka zo k'unshi ina sallamarsu. Gara ma na yiwa yara uku kitso a falo. Sau uku yana kewayo wa ko zai tarar na shiga, ya wula'kanta ni. Sai kuma ya ga duk zuwan da zai yi bai ga kowa a ciki ba. Kwana biyu muna wannan takun sak'ar. Ga shi na ji a bakin Rafi'a ana ta tumfirint din Neco. Kwana na uku na same shi a d'akinsa da daddare na zauna na sassauta murya na ce "Tijjani ka ce "Zan yi Neco ga shi ana fa'din an kusa rufe yin rigista da tumfirint din". Kai-tsaye ya ce "Na fasa fas. Dama ai ba wai karatun ya dame ki ba ne. Ni ne a kokarin na sanya farin ciki a zuciyar ki ya sanya na ce zaki yi. Ina kuma da sha'awar mace mai ilimi. Yanzu kuma na fasa tunda baki da abin wula'kantawa, sai ni". A sanyaye na ce "Dan Allah Tijjani tunda ka saka mini rai ka bar ni." Ya ja tsaki ya juya ya cigaba da kwanciyarsa. Na tsura masa ido ina jin zuciyata tamkar ta fa'do. Wato ko wanne namiji ya iya tsiyataku masu k'ona rai. Na dinga mamakin me zai sa wula'kancinsa ya yi mini ciwo ne?". Na tashi na bar shi, zuciyata tamkar ta fa'do k'asa. Kullum fishin nasa gaba yake yi ba baya ba. Gaba'daya ya fitittike ya koma wanccan Bulkachuwan da yake dauke kai ga mace in ta nemi yaga shi. Magana ma da k'yar yake yi mini. Tsakaninmu ya shigo mini da cefane. Idan ya samu sararin siyo kayan masarufi kuwa, sai dai na ga yawansu ya k'aru. Ya daina sauraron abincina. Ya kuma daina tambayar me zan ci. Da ya gama uzzirinsa zai sa kai ya fice, nasan dai bai ta'ba fashin kawo mini cefane ba. Sannan bai damu sai na ba shi idan na girka ba. Ranar da babu gidan burodi kuma bai samu aikin da zai yi ba. Zai dawo ya ce mini ki yi wake da shinkafa ko ki dafa taliya da manja. Shi kuwa sai ya jika garin rogonsa ya sha, ya sake fice wa. Wani lokacin tausayinsa ya hana ni sukuni. Na rasa yadda zan yi da shi, ya k'ulla gaba mai yawa a tsakaninmu. Rannan ya ce mini "Ya tafi Bauchi. Da'di ya ratsa ni, domin zan samu na dan yi k'unshi kafin ya dawo garin. K'warai na takura a halin da nake ciki. Ai kuwa mutum uku suka zo, na kai su dakin bayan na kintsa masa kayansa gefe guda. Na dauko bedsheet na rufesu. Na gama yiwa mutum biyu, ina cikin sakawa ta uku. Tamkar jifa sai buga k'ofa na ji. Ban kawo shine ba. Tunda ya ce ya tafi Bauchi. Nasan kuma sai wajen dare zan gan shi. Na fita da sauri ina zaton ko Anas ne. Ina bu'de kofa kawai na ga mutum a tsaye. A gigice na ce "Tijjani ba ka tafi Bauchin ba?" Fuska a daure ya ce "Allah bai yi ba". Na tare hanyar shigowar. Ya ce "menene haka, ba ni hanya band'aki zan shiga". Na diririce. Baki na rawa na ce "Dan Allah, dan darajar Annabi Tijjani ka rufa mini asiri, ka yi hakuri kada ka shiga d'akin lalle. Ya galla mini harara ya ce "Yau munafurci ya tabbata a kan ki, kuma zaki ga k'arshen rashin mutunci Wallahi". Na zabura na ri'ke shi sosai. Murya na rawa na ce "Ka yiwa Àllah da Manzonsa kada ka yi mini haka. Na yarda komai ka ke so zan yi, amma kada ka sake tozarta ni Tijjani". Ya zuba mini ido yana kallon yadda hawaye yake tsere akan fuskata. Ya jijjiga kai ya ce "Shike nan". Sanin bai iya yaudara ba, ya sanya na sake shi ya shiga, ina bin sa a baya. Domin da zai shiga d'akin, ba zai nuna mini ba zai shiga ba. Kai-tsaye falo ya dosa. Na samu nutsuwa a zuciyata. Tsabar nutsuwar da na samu har ruwa na dauko masa. Na kawo masa abincin da na dafa zan ci. Ya hakince tamkar wani basarake. Yana cin magani, komai isa isa yake yinsa. Haka dai na lallaba shi, ya koma harkokinsa. Yana fita na saki gauron numfashi. A fili na ce "Oh Allah. Menene damuwata ne akan abin da zai yi a d'akin da nake shiga zullumi idan zai shiga din?" Na kasa bawa kaina amsa. Na kalli mashin dinsa da yake gefe wanda bai fita da shi ba. Yana fita wasu zugar suka zo. Dan haka har kusan magariba sannan na gama saka musu. A gurguje na yi wanka. An fara kiran isha wacce na saka wa a karshe ta cire ta tafi. Na dinga jin da'din ku'din da na tara. Da na nutsu sai na gane, idan ban dauki matakin dai-dai to a tsakanina da Bulkachuwa ba. Asarar da zan dinga yi a kullum ba ka'dan ba ce. Ba'kin cikin rashin bishiya ko rumfa yana cina. *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*. Ga shi yanzu yanayin damina ne. Idan ruwa bai zuba ba rana ake yi, idan kuma an yi ruwan ba damar zama a waje. Ya shigo na ha'diye haushinsa na yi masa sannu. Na kawo donot da flask din shayi. Sai da muka kammala. Na dauko dukkan cinikin da na yi a ranar. Na tura gabansa. Na sassauta murya na ce "Tijjani ka ga cinikin da na yi yau ka'dai. Na ro'ke ka daina hana ni. Na yarda kullum kana da kaso a cikin ku'din da zan samu". Ya fusata irin sosai din nan. Ya nuna ni da hannu. Ya ce "Ke ce kike mutunta ku'di irin haka. Na kuma sha fa'da miki ce wa baki da kudin da zan sa ido akansu bare har ki yi mini iyashege saboda su. Ya jijjiga kai ya mike tsaye bayan ya dangwarar da kofin shayin. "Da nasan zaki kalli idona ki yi mini irin wannan tayin na raini Billahillazi da dazu ban yarda na karbi ban hakurin ki ba. Amma shike nan. Daga yau din nan bana bu'katar ayi mini lalle da kitso a gidan nan gaba'daya ma". Ina jin hakan na takarkare na ce "Bilhiillazi ba zai yiwu ba, komai kake ji da shi Tijjani, baka isa ka hana ni sana'ar da ka gan ni da ita ba! Duk masifar ka kuwa". Ya murmusa ya ce "Lokacin da aka dauke ki aka ba ni babu shawarata ai ba a ce mini mata zasu dinga yi mini zarya a gida ba. Dan haka yanzu da na ga bazan iya d'auka ba, na dakatar da su". Na sake hassala na ce "To wai dole aka yi maka ka zauna da ni? Na ce ba na sonka, kai ma baka sona, to mu rabu mana. Mugunta ce kawai ta sanya ka ri'ke ni, kake musguna mini." Ya ce "Shike nan bar shi a muguntar ne kawai. Sai dai ki sani na riga na samo wa kaina mafita. Ki saurari abin da zai biyo ba. Ban karbi auren ki ba sai da na kudire wa zuciyata komin rintsi bazan bari mugun halinki ya sanya na kunyata Baban Marina da Babah ba. Ki je ki karaci diban albarkar ki. Ai Ubangijin adalci ya riga ya samar mini mafita a cikin wula'kanta ni da kike yi tun kafin a halicce ni". Daga haka ya fice. Gaba'daya na kasa gane manufar maganganunsa. To wacce manufar ya samo? Na kwana ina tauna maganganun Tijjani. Zuciyata ta yi nauyi a wajen son na fahimci inda ya dosa. Ko dokar da ya sanya mini ta hana ni sana'ata bata tokare mini wuya ba. Irin son na gane mafitar da ya samo. Kwanaki biyun da suka biyo baya, zaman namu ya sake yin tsami bisa dalilai guda biyu. Na farko ya tire kan ra'ayinsa na kada a ayi masa lalle a cikin gidansa. Sannan ya tsiri ya yi wanka ya sheka kwalliyar da ni na koya masa yin ta. Da daddare zai dauki wankakken kaya kuma gogagge ya fesa turaren da duka gidan sai ya amsa tsabar bulbulawar da yake yi, sannan ya fice ko kallon inda nake ba zai yi ba bare ya yi mini sallama. Ba zai dawo ba sai goman dare ta shud'e. Wannan al'amarin ba k'aramin ci mini kwarya yake yi ba. Na rasa inda zan tsoma raina da ba'kin cikin da Tijjani yake guma mini. Mussaman na barina a gida da daddare ni ka'dai kamar mayya. Ranar da muka yi sati a cikin wannan halin. Na bugawa Yaya Ummi waya, ji na babu kuzari ya sanya ta dinga fa'din "Mene ne, me ya same ki Yabi?" Na kasa bu'de baki na ce mata uffan, illah kukan da nake yi mai cin rai, mai kuma sauti sosai. A lokacin kuma dare ne sannan yana gidan. Ya ji ni sarai, tunda a lokacin yana falo. Amma ya yi kamar bai ji ba. Washagari da asuba sai ga Yaya Ummi ta diro mana gidan. Tausayinta ya kama ni. Yargale yargale da ita. Da alamun ma kukana bai barta ta yi barcin kirki ba. Ta same ni kad'ai a dalilin bai dawo masslaci ba. A gigice take tambayar me yake damuna? Murya a dashe tsabar kuka na ce "Tijjani yana shirin kashe ni da raina ne. Haka siddan ina zamana ya saka mini rai zai mayar da ni makaranta na samu shaidar kammala sakandire. Yanzu ya zo ya ce ya fasa. Hakan bai ishe shi ba sai ya ha'da har da soke sana'ata. Sannan dan yasan Baban Marina ba zai saurare ni ba, sai yake amfani da hakan yake musguna mini. Fiye sati yana gaba da ni. Sannan kulllum dare sai ya sheka wanka sannan ya fice ya bar ni a gida sai dare ya raba zai dawo. Ni nasan Bak'ar TA'ADAR sa ya koma. An cuce ni Yaya Ummi." Na fa'da ina rushe wa da kuka sosai. Daidai lokacin kuma ya dawo, amma kukan da Yabi take yi tamkar na mutuwa shi ya hanasu jin motsinsa. Ya zauna a barandar yana son fahimtar abin da yake faruwa. Jikin Yaya Ummi ya yi sanyi. Ta ru'ko hannuna ta ce "Yabi nutsu ki ji ni. Shin me kike masa yake yi miki hakan?". Cikin kuka na ce "Bana yi masa komai". Ta numfasa ta ce "Me yasa kike gaba da shi? Da kina gaishe shi, na tabbatar Yaya Bulkachuwa zai masa miki." Na yi shiru dan kuwa gaskiya ta fa'da. Ta sake ce wa "Da kin ja shi a jikin ki, da ba zai iya fitar da yake yi ba. To me zai yi a wajen bayan yana da d'anyar amarya mai cike da shiriritar kuruciya?" Na bata rai na ce "Kawai saboda ke da shi akwai amana da yarda shi yasa kike shaidar sa a bayan idonsa ni kuma kike bani laifi a kan idona ko?" Na fa'da hawaye na ziraro mini. Ta tsananta ri'ke mini hannu ta ce "Gaskiya ai bata bu'katar ado Yabi. Babu ruwan alk'alami akan kina so ko ba ky so. Kawai girman hakkinsa da ya rataya a kan ki za'a duba. Idan baki sau'ke ba Wallahi halaka zaki yi Yabi. Ni yanzu son nawa mijin nake yi? Amma na yarda kaddara shi ta zaba mini. Dan haka na yi hakuri nake yi masa biyayya, duk da shi din ba duka yake sauke hakkin da shari'a ta gindaya masa ba. Amma na sani ina rabo mai girma a wajen Azza wa jallah". Na tsananta kallonta domin gaskiya ta fa'da. Har zuwa yanzu da ta zarce shekaru goma da aure bata son mijinta, ni shaida ce akan hakan, amma kuma ha'kuri da biyayyar da take yi akan sha'aninsa mai yawa ne. Ta numfasa ta ce "Yabi ba kya yarda da Tijja Yaya Bulkachuwa. Su kuma maza da kike ganinsu komai zaki yi musu na kyautata wa matu'kar ba kya mutunta shinfidarsu, to fa komin kokarin ki a banza ne a idonsu. Saboda haka ki d'auki matakin gyara a tsakaninku." Na nisa na ce "Baya gamawa da wuri Yaya Ummi. Ni gaskiya bazan iya ba." Ta ce "Ahab dama da labarin neman auren da yake yi ya riske ni, sai da na ce na tabbatar ke ce silar k'arin auren sa. Ai sai ki yi tunda al'amarin kishiyata bai saka kin k'yamaci kishiya ba". Wani irin abu ya soki k'irjina, ban san mene ne ba. Amma gaba'daya ji na yi tamkar zan shid'e. Na rushe da kuka mai tsananin gaske. Ta ce "Ai indai kika cigaba da tafiyar da shi a hakan, tabbaskuka na gaba. Ba ki ga Bilkin da yake zuwa wajenta ba, gansamemiya ta yi biyu da rabin ki." Da rawar murya na ce "Me za'a yi da mai BAK'AR TA'ADAH irin ta Tijjani. Aure ko rufa wata biyu ba'a yi ba har ka fara neman wani auren. Na rantse Yaya Ummi sai dai a tsine mini. Amma bazan taba zama da wata macen a k'arkashin ikon Tijjani ba". Ta sake ru'ko hannuna ta ce "Idan kina son ki zauna lafiya, ki yi sana'arki, ki cigaba da tallafa mana. To ki zauna lafiya da mijin ki, ki daina gudunsa, ki yi hakuri da shi watarana sai ki ga kun kai ga babban bigire. Ni fa na dauka ma ciki ne da ke. Jiya nan na je gidan Ubaida na tarar tana ta kwarara amai. Da kaina na rakata asibiti aka tabbatar ciki ne da ita. Kin ga kuma ai kanwar ki ce duk k'uruciyar ki ai kin fita a haife. Jabir din da kike ta kulafacinsa matarsa wata tara ta haihu. Sai ke ce zaki zama shasha wacce bata san me yake mata ciwo ba. Da ace kin kwantar da hankalinki da wata'kila ke ma da na ki cikin a jikinki". Kunya ta rufe ni, na ce "To yanzu dai ki fa'da masa ya bar ni na yi sana'a ta." Ta ce "A yanzu bazan yi masa magana ba. Idan kin canja kin daina gudunsa, bai bar ki ba, sai na yi masa magana. Amma yanzu ai ke ce zaki fara zuwa da gyara". A sanyaye na ce "To". Amma k'irjina tamkar ya fa'do a dalilin nauyin da yayi akan batun tsohuwar budurwar Bulkachuwa wacce aka kai masa ku'din aurenta aka k'i karb'a. Tun lokacin ya fita a harkarta amma ita take ta nacin ya yi hakuri. Tijjani da ya yi bakam yana sauraronsu. Ya saki gauron numfashi yana k'ara ganin hankalin Ummi. Sai dai mamakin da ta bashi a ina ta ji yana zuwa wajen Bilki? Shi yasan tunda aka yiwa su Baban Marina wula'kanci bai sake taka gidansu ba har yau. Idan Ummi ta fa'di hakan da nufin yiwa Yabi barazana. Ya tabbatar liki ta b'allo masa. Duk yadda Yabi take kirarin bata son sa amma kuma kishi take yi akan lamarin sa ba ka'dan ba. Duk da dai ya yi amanna kishi dabi'arta ce. Amma ya tabbatar wannan maganar sai ta ri'ke ta a ranta. Ya saki gauron numfashi yana fatan a sami dai-daito a tsakaninsu. Tsawon lokaci yana sauraronsu, yana jin irin yadda Ummi take ta wasa shi tare da ban baki a madadinsa. Wanda hakan ba k'aramin kaunarta ya k'ara ji ba. Jin tana haramar tafiya ya sanya shi mike wa ya maze tamkar bai ji me suke fa'da ba. Da murmushi ya ce "Ummilolona ke ce da sassafen nan?" Ita ma da walwala ta ce "Eh Yaya Bulkachuwa barka na je nan gabanku ka'dan, shine na biyo na gaisheku ko na yi laifi?" Da sauri ya hau girgiza kai tare da fa'din"kin yi daidai Ummi. Allah ya bada ladan zumunci". Ta ce "Ameen." Ya bita suka fita da kafarsu. Wata'kila har gidanta ya rakata domin ya jima bai shigo ba. Hadari ya hadu mai k'arfin gaske. Daidai lokacin ya dawo tamkar jifa. Sai da ya rufe k'ofar d'akin da yake yi mini isa, ya rufe tagogin falo. Sannan ya shigo d'akina. Na kalle shi na dauke fuska domin haushinsa ya sake kama ni sosai. Ya zauna a gefen gadon ya sanyaya murya ya ce "Albarkacin zuwan Ummi na ajiye fishina. Na huce, komai ya wuce". Na yi kamar ban ji ba. Ya matso jikina sosai ya ru'ko ni, na fizge a fusace na ce "Bana son ka huce Tijjani. Domin dai ni bana ha'da sabgata da marar imani bare kuma tausayi." Ya sassauta ya ce "me na yi na rashin tsoron Allah Asiya?" Murya na rawa ina shirin kece wa kuka na ce "Ban da ka tabbata baka da tausayi mene ne zai sa ka jajibo aure alhalin ko wata biyu baka rufa da yin auren ba. Mene ne hakan inba rashin tsoron Allah da rashin imani ba?." Ya sake matsowa jikina ta yadda bayansa na shafar cikina. Ya yi k'asa da murya ya ce. "Wallahi Asiya Toro tsoron Allah nake ji sosai. Shine shaidar hakan. Asalima saboda ina tsoronsa ya sanya na fara neman auren. Ya zan yi? A d'an zaman da muka yi ya kamata ki fahimci bazan iya ri'ke kaina alhalin ina ganin ki, muna kwana gida d'aya ba. Ke kuma gaba'daya kin bijire , kin k'i saurara ta, tunda ba sona kike yi ba. Sanin zan iya fa'dawa halaka ya sanya na samu wata bazawara mai gajeran buri muke tattauna wa. Idan Allah ya yi zan aure ta. Kin ga shike nan na magance tashin hankalin da yake tsakaninmu, sannan na samu mafita daga hatsarin fa'dawa zina da aurena". Yana rufe baki ba zato na mik'a hannuna na d'auko wata doguwar robar mai ta kokobota. Na kwad'a masa a goshi. Ina kwada masa tare da ce wa "Allah ka yi mini tsari da mugun k'ullin da yake zuciyar wannan bawan naka. Bilhiillazi kana da fitina Tijjani." ✍️ *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. *Assalamu alaikum Bayin ALLAH, kun san ce wa FREE PAGES na littafin ƘALUBALEN RAYUWA ya ƙare? Wanda cigaban littafin KUSKUREN SO na? Kun san dai yadda na nishaɗantar daku a labarin Nafeesar Sufyan? Kuma dai kun san yadda na nishaɗantar DAKU a littafin ISHARA labarin Zainabun Sameer? Littafin ƘWAƊAYI fa? Labarin Zainabun alamaramma? Na san baku manta RAHEELA MAI ƊAN BUJE ta cikin littafin RUGUNTSUMI? Jamaa na rubuta kun karanta kuma kun shaida, alƙalami ne da babu tantama a cikin shi, Jamaa yanzu ma tafe da nake da ɗaya tankar dubu, salon na daban ne? Ba zan so ya wuce ku ba, shiyasa na maku promo ku biya 300 madadin 400 kacal ta wannan hanya 9994468172 Access bank fiddausi musa tare da shaidar biya ta 08036953516 ko 07042277401, domin mu tafi tare, na maku alƙawari, labari ne da zai tsaya zukatan..* 53&54. Ta ko ina nake jifan sa, gaba'daya na hargitse dakin. Da k'yar ya samu ya ri'ke ni ya dauke ni caraf ya d'ora a cinyar sa ya rungume ni tsam tsam. Gaba'daya na shige jikin na yi luf, sai kukana kawai yake tashi, wanda na shagwaba da kishi ne. Cikin rad'a yake ce wa "So ki ke ki illa ta ni ne?" Da k'arfi na ce "Eh. Wata'kila dan ka ga kana da kyau ne ya sanya kake ganin ko wacce mace ka ce kana so, ba zata tankwabar da kai ba. To gara na rugurguza ka. Tunda ni kyaun naka bai rud'e ni na makance akan ka ba" Ya sakar mini wani irin nishi a kunne, sannan ya dan cizar mini shi ka'dan. Yar na ji jikina ya amsa. Na fara fizge fizgen bazan yarda ba, sai nima na cije shi a nasa kunnen. Shi kuma ya dinga dariya yana cakuma ta son ransa. Babu zato ruwa mai k'arfi ya goce. D'akin ya yi duhu saboda ko ina rufe yake gudun kada ruwa ya shigo. Wannan yanayin ya sake susuta Tijjani. Ni kuma na dinga koke-koken jan rai. A ki'dime yake rarrashina. Fa'di yake "ki yi ha'kuri I will be soft and gentle." Ni kuwa sai botsare wa nake yi. Tare da ce wa "Ni dai ba da'de wa zaka yi ba." Da rawar murya ya ce "Nà yarda amma idan kika cije ni, ko kika yi mini fallashasshen kuka. Ki tabbatar kina cikin komar mala'iku". Na yi shiru. Amma zuciyata sai harbawa take yi. Domin har zuciyata nake jin tsoron al'amarin. Ina ji ina ga ni, ya shiga yin yadda ya ga dama da ni. A farkon tafiyar gaba'daya na kankame jikina ina sauraron jin matsanancin zafi. Amma ga mamakina sai ban ji ba. Har na sakankace na saki jikina. Wanda hakan ba k'aramin dadi ya yi masa ba. Ya k'ara haifar masa da kuzari mai yawa. Dan haka lokacin da ya shafe yana abu daya, bai dame ni ba. Bayan ya nutsu. Ya rungume ni yana ta faman sakin kalaman yabo da soyayya. "Asiya da hakan kike yi mini, to me zai sa ma na yi fishi da ke? Bare har na yi tunanin k'arin aure. Na gode sosai, Ubangiji ya sanya albarka a rayuwar ki gaba'daya." Na yi shiru. Amma zuciyata sai kai kawo take yi akan abin da nake son amayar wa. Na kasa jarumtar ha'diyewar murya babu amo na ce "Yo ni ai tunda wula'kanci ka shiryo mini daga yin aure za'a ka fara neman wani dan kawai ka nuna wa duniya bani da wata kima a idonka. Wallahi ba zama zan yi ba. Zaka wayi gari ne ka ga na bace maka." A diririce ya sake ru'ko ni sosai tare da ce wa "Kar ki tayar mini da hankali dan Allah. Na fasa, dama dan na rasa yadda zan yi ne. Amma yanzu indai kin daina yi mini abubuwan da kike yi. Wallahi bazan sake tayar da maganar ba. Ke ko hanyar da ta bi, bazan sake bi ba". Cikin kuka na ce "Daga baya ke nan. Wadanda suka ganka kana zuwa tadi ai tuni sun san baka son Yabi. Dan haka kuwa ba yarda zan yi ba. Ka je ka cigaba da abin da kake yi, ni ma zan samu mafita Wallahi". A raunane ya ce "Bana son kukan ki Asiya! Amma sai ki ta yi mini, dan kawai ki gigita ni. Ban iya yaudara ba. Na ce miki, na fasa, na janye, to ba shikenan ba?" A zabure na ce "Ba shike nan ba". "Da azama ya ce "To fa'da mini yadda za'a yi, me kike so na yi dan ki gamsu?" Na dinga gunjin kuka da na tabbatar yana jijjiga shi. Ya dinga shafa kaina, yana fa'din " Sorry Asiyata! Na ce bazan sake ba, ki yi ha'kuri da gaske na fasa. Dan Allah mu rufe maganar nan haka. Me kike son ci na dafa miki?" Na fara kokarin fizgewa daga rugumar da ya yi mini, amma na kasa. Cikin tab'ara na ce "Bazan ci ba. Yau kwana nawa rabon ma da ka tsaya ka saurare ni akan maganar abinci. Ko na ci, ko kada na ci ai babu ruwan ka". Ya sake sassauta murya ya ce "Wula'kanta ni fa kike yi. Ta ya ya zuciyata zata ji da'din kyautata miki? Yanzu kuwa ai komai yi miki zan yi da kaina". Na cuna baki na ce "Abar maganar abinci. Ka tashi tunda ruwan ya tsaya, ka kwaso kayanka da ka kai mini wanccan d'akin dan kawai kana nema na da jidali". Ya zabura ya tashi. Ya lalubo jallabiyarsa ya d'ora akan gajeran wandon bai ce komai ba ya fice. Ya kwaso su tsab. Ya mayar dasu inda suke. Ya juyo ya ce "Na kwaso, shike nan?" Na bata rai na ce "Ba shike nan ba. Kada mu samu sabani ka sake yi mini hakan. Tijjani ba ruwanka da d'akin can. Nan ne dakinka. Idan kuma zaka dinga fitina ta akan dakin to ka sani zan tattara kayan gadon na mayar maka can din. Tunda nan d'akina ne da shari'a ta ce ka bani shi tilas. Idan anan nake sana'ata ban shiga cikin dakin ba, ai na tsira ko?" Ya yi wani irin murmushin da na fahimci mai harshen damo ne. Ya numfasa ya ce "Namiji ai ba yi masa shamaki a gidansa. Dan haka mu zauna lafiya mu mutuntata juna shine kawai. Amma bazan yarda ina tattala ki, ke kuma ki ce zaki dinga wula'kanta ni, sannan kuma na yi miki yadda kike so." Ya girgiza kai ya ce "Ba haka Tijjani yake ba. Ba kuma zai zama hakan ba". Na kura masa ido na tabbatar iyakacin gaskiyar sa ya fa'da. Na rasa me zance masa domin na tabbatar duk bala'ina. Idan ya kunsa mini ba'kin ciki daya tak kwana zan yi na yini cikin ba'kin ciki mai tsanani. Dan haka sai kawai na buge da sake fashe wa da kukan. Daga inda yake tsaye, ya ce "Allah dai ya taimake ni ki hau ko na samu sau'kin wannan rikicewar da gangan. Idan kina ganin baby a hannunki wata'kila kya daina yi irin wannan sakalcin." Yana rufe baki na fara nuna kaina cikin kuka ina ce wa "Tijjani ni ce sakaliya?" Kafin ya amsa mini na rausayar da kai na ce shike nan na gode da wannan tukuicin". Ya taho da sauri yana kuma dariya. Ya rike k'afafuna ya ce "Ina nufin sakaliyata fa". Na yi tsuka na juya. A sanyaye ya ce "Bana son tsuka Asiya. Amma na yafe miki, ban yi fishi ba". Daga hakan ya koma ya fita. Na tabbatar kuma kicin zai shiga. Ni dai daga nan barci ya sure ni. Sai bu'de ido na yi na ganshi ya yi wanka ya shiraya tsab. D'akin ma ya cika da kamshin turaren nasa. Yana daga jikin sif din yana saka links ya ce "Yanzu dama zan tashe ki, na kai miki ruwan wanka". Ban ce komai ba, na tashi, na daura zani a kirji sannan na saki zanin gadon na sauko. Ya kalle ni babu riga a jikina. Ya ce "Asiya Toro a gabana babu riga. Sai na sake ganin ki wata yar kwaila, a hakan tamkar ba zaki iya komai ba. Nan kuwa al'amarin da yake tare da ke azimin ne". Na cuna baki na ce "Ai ni na gode Allah ma da aka baka yar mitsil din. Kai da rusa rusan mata sai kallo daga nesa. In juninka cusawa mutum takaici ne. Har abada kai da zunduma zunduman mata". Ya murmusa duk da dai yana kokarin shanye dariyarsa. Ya ce "Wato baki ji da'din yabon da na yi ba, sai kika dauki abin da bai yi miki da'di ba, kika yi raddi?" Na share, na dauki tawul na fice abina. Na dawo na tarar da shi ya gyara gadon tsab. Ya share dakin. Na kasa hakuri na ce "Tijjani wai a ina ka iya gyaran gado ne, tunda kullum dakinka na gida a hargitse yake, sai asarrariyar can ta gyara maka shi yake yin fasali". Ya dauko mai yana murmushi ya tarar da ni a bakin gadon. Na yi kamar na hana shi shafa mini mai din sai na fasa kuma. Domin a dan zamanmu na fahimci yana matu'kar son ya shafa mini mai, kafin na sanya komai a jikina. Ina ji ina ga ni ya dinga shafe ni da sunan shafar mai wanda ni kaina ina matu'kar jin sakon nasa a dukkan jikina. Yana cikin murzar tafin kafata. Wanda kafin ya zo kafar ya shafe mintina sha biyar. Murya dakushe tabbacin so yake ya koma ruwa ya ce "Nasiba ce asarrariyar Asiya?" Na fizge kafata na tashi. Na ce "Ina dalilin gatsa sunan matar wani ne Tijjani? Kusan mintina ashirin da yin maganar ashe duk yadda na barka kake yin yadda kake so da sunan shafar mai, zuciyarka na tunanin suntumemiyar halitta ko? Wallahi bazan iya da bala'in ka ba Tijjani! Ganin da gaske na fitittike, zan birkice masa. Jikinsa na bari ya ce "Allah ya baki ha'kuri, na yi kuskure. Sai dai ya kamata ki mini shaidar tun ma kafin a mini babban alherin ba ni auren ki ai na fita a dukkan sha'aninta. Bare kuma yanzu da take matar wani. Dan Allah mu bar maganar, bana sonta. Ki yi hakuri." Ya dauko mini wata riga ya ce "Ga gifts din ki na zama matar aure, tun first night dinmu nw so baki, to bata iso a lokacin ba." Cotton yar kanti. Gaba'daya rigar tafi dacewa da yara y'an shekaru goma. Domin har da teddy wacce aka yi jakar goyo da ita. Sannan da hula irin mai malafar nan. Kalar ruwan hoda (pink )da yarfin filawa mai ruwan lemon tsami (lemon green) ce. Ba karamin kyua ta yi ba. Ya mik'o mini sabon pant. Ya ce na saka miki?" Na juyar da fuska. Ban amsa ba. Sai da na shanye kunyar na na ce "Tijjani da gaske dai kallon yarinya kake mini. Ban da haka wannan rigar ai ta yiwa Iklima ka'dan bare ni. Kasan kuma Anas ne yake bina ba ita ba." Kai-tsaye ya ce "Na sani. Sha'awa ta bani, shine na yi kundubalar d'auko miki ita, rabin ku'din na bayar. Abokina yake kawo su daga China. Ta kusa dubu ashirin, sonta nake yi, saka kawai". Na ce "Tsakani da Allah da atamfa ka siyo mini, yanzu wannan ina zan saka na je da ita?" Ya ce "Ba dan ki sa ki fita na siyo ta ba. Dan ki saka mini na kalle ki a yadda nake son ganin ki ne". Ganin ya b'ata fuska ya sanya na juya na saka pant din. Ina juyowa ya bani sabuwar breziya yar mitsil kalar wando da alamu set ne tare suka zo. Ban ce komai ba na kar'ba. Ina ayyana wato ya riga ya gama gane wacce zata yi mini. Domin duk na lefena sun yi mini yawa duk da k'ananu ne sai dai ko nan gaba. Domin da na aikawa Gwaggo akan ta bayar, dawo mini da su ta yi, ta ce nan gaba zasu yi mini na adanasu. Sai da na shafa hoda na goga jan baki kalar ruwan hoda. Sannan na zura rigar. Ta shige ni tsab. Ta d'an zarce guiwata da ka'dan, kasancewar ba ni da tsayi. Ya ce "Wow This is Asi beauty lady". Na dan yi murmushi. Ban ce komai ba. Da kansa ya sa mini hular ya d'auko sabon turare a cikin kayansa da aka rubuta Active woman. Ya bu'de ya hau fesa mini. Kamshin turaren jikinsa da wanda ya fesa mini suka hadu suak bige ni. Suka isar da wani irin sako akan Tijjani a cikin zuciyata. Shi kuma ganin na koma masa wata yar yarinya kankanuwa ya sanya ya sure ni. Ya yi falo da ni. Yana ta sakin maganganun da suke da nauyin bayyana wa. Komai da barin jiki yake yi mini. Ya ajiye ni akan kujera ya ce "Bari na kawo miki abincin Little Angel." Har cikin zuciyata na ji da'din sunan. Duk sunayen da Bulkachuwa yake fa'da mini babu wanda na ji dadinsa irin little. Domin ya dace da ni k'warai da gaske. Shiru shiru bai dawo ba. Sai na yi kamar na leka shi, sai kuma na fasa. Can sai gashi da tray da ya jero kayan abincin. Da walwala ya ce"Sorry little na bar ki ke ka'dai, ga shi babu wuta bare kallo ya hana ki gundura da zaman jiran kukun naki" Na k'yal-k'yale da dariya na ce "Wai kai ne kukun?". Cikin gamsuwa ya ce "Ba ki aminta ba? To mene ne aikina ban da na fita na yi aiki tukuru dan na nemo miki abin da zaki ci. Idan kuwa ina gida, idai baki bata mini rai ba. Still aiki zan miki dan na hutar da ke shiga kicin kullu yaumin". Na murmusa ba tare da na ce komai ba, domin na yarda da dukkan zuciyarsa ya ke yin maganar. Ya bu'de kwanon abincin ga mamakina sai ganin fanke na yi subu-subu sun soyu sun bada kala mai daukar hankali. Na kalle shi da mamaki na ce "Tijjani yaushe ka iya fanke haka?" Ya saki murmshin jin dadi ya ce "Ki bari sai kin ci sai ki tambayi na iya ko kuwa makwaki na yi". Na sauko ya ha'da mini shayi mai madara da milo. Shi kuma ya zuba bak'i. Muka fara cin fanke wanda ba karamin dadi ya yi ba. Na kalle shi na ce "Ya yi da'di sosai. Na ji har da k'wai da madara ka saka. Maimakon ka bar madara ka zuba a shayinka." Ya rausayar da kai ya ce "Ke dai ki sha my little". Ya kashe mini ido sannan ya ce "Ai ina ganin amfaninta. Addu'a nake yi sosai na samu damar da zan daina siyo miki ta sacet. So nake kullum ki sha ta ruwa gwangwani guda. Ta yadda ba zaki dinga gazawa da al'amarina ba". Kunya ta yi matu'kar kama ni. Na sanya dukkan hannuna na rufe fuskata, ina wani irin murmushin da bansan ta inda yake bullowa ba. Da k'yar na cigaba da cin abincin bayan ya ce "Duk a wajen Baba na koyi girki. Yadda kika ga Aliyu da Nasiru suna hidima irin ta y'ay'a mata nima irin wannan goyon ta yi mini. Kullum fa'di take yi, tunda bata samu mace ba, ba zai yiwu a ce ba zamu tallafa mata da kaomai ba. Kullum cikin fa'da mana take yi mu koyi aikin gida dan wataran mu taimaki iyalinmu. Annabin Rahma da yafi kowa daraja yana tallafawa iyalinsa. Ba mallakewa ba ne dan namiji ya yiwa mace hidimar girki, wanki, ko ta shara ba. Amma kuma ta ce "Ban da wanke wanke wannan na yan daudu ne". Muka k'yal-k'yale da dariya domin kuwa munsan kawai ra'ayinta ne amma babu aibu idan mutum ya yi. Ya ce "rigar nan fa ta yi miki kyua my little. Tamkar na dauwama ina kallon ki". Na murmusa ka'dan tare da ce wa"Thank you" a gayance. Na marairaice na ce "Ya maganar tomfirint din?" Cikin nutsuwa ya ce "zuwa wani satin zan kai ki da kaina". Na fa'dada murmushi na ce "Na gode Tijjani". Ga mamakina sai na ji nauyin gatsa sunan da na yi, ta mamaye ni. Karon farko da na ji hakan a rayuwata. Na lura shi kuma yana cikin maza yan ka'dan da basu damu da a fa'di sunansu kai-tsaye ba. Tas muka cinye fanken. Na kwashe kayan dan nasan idan ya mike zai kwashe ne. Na kai wajen wanke wanke na ajiye. Na koma wajensa na ce "Wai da yaushe ka yi kwabin ne?" Ya nisa ya ce"kina barcin gajiyar da na tara miki. Ni fa duk kallon jaruma nake yi miki. Ashe a tsiwa da dambe da sana'ar k'unshi kike da jarumtar". Na girgiza kai na ce "oh haka ka ce? Ai shikenan next time zaka gane ashe dazu ba karamin jarumtar na yi ba". Ya jani jikinsa ya ce "Kin san bana wasa a wannan fannin tsokanar ki nake yi, idan akwai abin da yafi jarumta kin yi dazun". Na kalle shi cikin nauyi nauyi, kunya kunya na ce "ka ji tsoro?" Da sauri ya ce "Na ji". Bai fita ba sai da ya dawo daga sallar azahar. Muka ci abincin da tare muka yi da shi. Sannan ya fita zuwa gidan Alh Ado Naira zai yi musu gyaran satellite tunda aka kawo wuta suke ta yi masa waya. Kamar ana jiran ya fita aka fara zuwa lalle da kitso. Shike nan muka shirya da Tijjani. Wata irin soyayya yake gwada mini mai wuyar samu. Da ya ga na canja fuska zai fara susuce wa, ya dinga jaye jaye magana, ko fita ya yo sai ya dawo. Matu'kar ban ware masa ba, ba zai samu nutsuwa ba. Ni da kaina na sani an jarrabe shi a kaina. Domin gaba'dayana a tsaye ban fi iya ruwan cikinsa ba. Duk zafin ransa baya son mu yi fa'da. Cikin rarrashi yake tafiyar da ni. Komai da rawar jiki yake yi mini. Kullum safiya ya wajaba kansa share duka gidan. Ya sa tsintsiya ya wanke band'akin, sannan ya tashe ni na yi wanka. Mafi yawa da safe da burodi muke karyawa. Dan haka shayin ma sai dai na gan shi a filas ya riga ya dafa. Da nutsu sai na ga ne tunda na daina gudunsa a shimfida shike nan ya tattara dukkan hankalinsa a kaina da lamarina. Baya taba yin dare a waje. Ana idar da sallar isha zai dawo ya rufe gidan shike nan sai gobe. Idan kuwa uzziri ya yanko masa sai ya bugo waya ya sanar mini yana waje kaza. Na ce to tare da addu'ar ya dawo lafiya. Ranar da yan rikicin suke kusa kuwa, na botsare masa idan ya dawo. Ya yi ta barin jiki wajen rarrashi na. Tuni muka fara jarrabawa har mun kusa kammalawa. Da kansa yake kai ni. Idan mun gama sai na yi masa waya ya zo ya dauke ni. Muna tsaka da jarrabawa Nazira ta haifo d'anta lafiyayye. Dan haka zarya nake yi tsakanin makaranta da gidanta. Har aka yi suna yaro ya ci sunan wan mahaifin mijinta Ahamd. Ni da kaina na lank'aya masa Abid. Sosai na yi mata hidima ita da yaronta. Ranar suna wanda a lokacin watan Maijidda biyu da haihuwa, y'arta Sajida ta yi gubibi da ita. Tana hannuna ina kare mata kallo. Na rasa gane da wa take kama a tsakanin itayenta Jabir da Maijidda. Saratu da Firdausi suka shigo. Ita Firdausi ta haihu. Saratu ce ta ke ja itama yau ko gobe. *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* Na kallesu da murmushi na ce "Ni kam da wa Sajida take kama ne?" Kafin na rufe baki Maijidda ta ce "Da Abbanta mana. Yo ko makaho ya shafa ai yasan kama take da Honey. Shiyasa yake kara sonta domin kullum ya dauke ta sai ya ce mata "Ta zabo uwarta da kanta". Gaba'daya jikinmu ya yi sanyi domin kuwa kowa yasan neman magana kawai take yi. Dan haka sai na mikawa Firdausi yarinya na shiga hidimar raba abinci. Amma k'asan zuciyata ya yi nauyi akan lamarin Maijidda. Har aka watse ban sake yarda na zauna a cikinsu ba. Har dare duk mana gidan Nazira. Muna zaune sai ga yaro ya zo ya yi sallamah ya ce "Wai Asiya ta fito su tafi". Na kasa boye masa abin da Maijidda ta yi. Tun a hanya na hau rattaba masa abin da ta yi mini. Maimakon ya bi bayana ya fa'da mini maganganun da zan ji da'di. Sai ce wa ya yi "To mene ne na bacin rai a ciki? Ke ma Ubangiji ya za'ba miki wanda yafi mijinta son ki, to sai me kuma? Ki bar maganar nan inba so kike na ga ne kishinta kike yi har yau ba". Takaici ya kama ni goma da ashirin. Na kame bakina na yi dif. Amma na riga da na harzuka k'warai da gaske. Ga mamakina sai kawai shi ma ya share ni. Muna isa gida ya gama uzzirinsa ya yi kwanciyarsa ya rabu da ni. Ba'kin cikin hakan ya sanya na dinga kukan sharbe. Bai ko motsa ba, bare ya nuna ya ga ne halin da nake ciki. Da kaina na kwanta. Da asuba bayan ya dawo nan ma kwnaciya ya yi bai nemi ni ba kamar yadda ya sabar mini. Ai sai kawai na fashe masa da kuka mai sauti. Ya janyo ni jikinsa ya ce "Yi shiru, na baki hakuri kin ga". Cikin kuka na ce "Akan me zaka yi fatali da ni?" Da rauni a muryarsa ya ce "Akan me har yau baza ki bar kishin Jabir ba? Kina tunanin zan ji dadi idan na ga ne har yau ban yi nasarar shafe shi a ranki ba?" Na yi shiru sai shesshekar kukana ne yake tashi. Haka ya ajiye fishin nasa ya dinga rarrashi tare da shafata cikin nutsuwa. Daga hakan kuma ya shiga yin abin da baya gundara da yinsa. Sannu a hankali muke rayuwa. Duk yadda Bulkachuwa yake tarairaya ta, akwai abin da yake mini wanda yake ci mini tuwo a k'warya. Duk yadda na so na dinga saka mana kifi ko nama a cikin girkinmu ya k'i yarda. Idan kuwa har na bayar aka siyo na girka to zai ci iya abincin ne ya bar mini nama ko kifina. Rannan da na nuna b'acin raina. A zafafe ya nuna mini yatsa. Ya ce "Iya abin da nake da shi zan ba ki, ba kuma zan zauna ki shiga cikin lamarin rik'on gidana ba. Ke dai tunda kina samun ku'di fiye da ni, komai kike so ci akan abin da nake da ikon ba ki, ba zan hana ki ba. Amma ni kada ki ajiye, ko ki ba ni, bana so". Ganin da gaske baya so din, sai na daina. Iya abin da ya siyo shi zamu ci. Da na bi yadda yake so, sai muka samu dai-daito. Domin duk ranar da ya ga kifi ko nama alhalin ba shi ya siyo ba. To fa yini zai yi babu sukini da walwala. Sai dai wani zubin na kan auni mangyada ko manja na zuba a galan din namu, ko na sayi ledar maggi. Wannan bai cika fahimta ba. Tunda wani lokacin zai siyo gwangwani biyu a leda ya juye a ciki. Dan haka a duk lokacin da ya samu sararin siyo kwalba, kwanaki ka'dan nima zan sake siya na zuba. To baya ankarewa da hakan. Abin da na lura bai dauki maganar da aka yi na ce wa ba zai iya ciyar da mu ba da sau'ki. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* ✍️ *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *08089965176* *07084653262* *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633 55&56. Ranar asabar ya dawo da rana. Sai ga shi da macaroni guda biyu hakan ma taliya, da shinkafa mudu guda. Sai sauran kaya danginsu maggi da sauransu. Na karb'e shi da walwala kasancewar ba kasafai nake yin k'unshi asabar da lahadi ba. Sai kitso ne yafi yawa a wadannan kwanakin, saboda ana hutun karshen mako. Doguwar riga ce ta yadin material din *Umm Nihla collection* *07020695644* A lokacin kuwa watanmu kusan bakwai da aure. Da na lura sai na ga kamar ba a cikin nutsuwarsa yake ba. Na gabatar masa da ruwa da abinci. A hankali ya ce "sai na dawo zan ci. Dauko mayafinki mu je gida". Gabana ya takarkare ya buga. A ki'dime na ce "Me ya faru?" Ya numfasa ya ce"Dada ce ta.." Kafin ya karasa na katse shi ta hanyar saka salati mai tsananin gaske. Tare da ce wa "Ta rasu?" Na fara k'walla ina cewa "Dada yau kwana ya k'are Innalillahi wa inna ilaihir rajiun". Allah ka gafarta wa Dada! Ya bu'de baki ya ce "Yaushe na ce "Ta mutu? Kin san yanzu damina ta tsananta. Ta je zagaya wa ne sai shaddar ta rufta da ita. Allah ya sa an ji k'arar ruftawar, da ba haka ba kam, da tuni ba wannan maganar ake yi ba. An ciro ta amma baki ga ba, duk ta daddauje sosai." Bansan ya aka yi ba dariya ta sosai ta k'wace mini. Na dinga k'yal-k'yale wa. Ya yi sak'are yana kallo na. Can ya kasa jurewa dariyar da nake faman yi babu k'ak'kautawa. Ya kalle ni ya ce "Ban da dai lamarinki akwai k'uruciya mene ne abin dariya a ciki? Dada fa na ce miki ta fa'da shadda. Da kuma rai ya yi halinsa me zaki yi?" Cikin dariyata na ce "Kuka zan yi mana. Baban Kasuwa nake yiwa dariya da ya kasa gyara band'akin gyatumarsa da take nuna masa soyayya ta daban shi da ahalinsa." Gau na ji ya hambare mini baki. Ya d'aure fuska ya ce "Idan zaki iya yiwa k'anin ubanki rashin kunya, to amma kuwa ba a gabana ba. Domin kawuna ne k'anin uwata na kuma yarda k'aninta ne. Da zuwa na yi na dauke ki, ki gaisheta ganin kusan kowa na gidan har Ubaida. Amma tunda zaki dawo da rashin kunyar ki, sai ki zauna ki yi ke ka'dai". Ya mike ya fice. Na bishi da gudu. Murya a marairaice na ce "Zan bika Tijjani dan Allah". Ya zuba mini ido yana yi mini kallo mai tsananin gaske. Na sani so yake na ba shi hakuri, ni kuwa ban ga me na yi ba. Ai gaskiya na fa'da. Bayan haka ai ya buge mini baki, dan haka na waske na k'i ban bada ha'kurin. Kallon ya shige ni, na fara bubbuga k'afa. Ina ce wa "Saboda Allah me na yi maka?" Ya jijjiga kai ya yi tafiyarsa, ba tare da ya ce uffan ba. Ni kuwa da na hasaso Dada a masai sai na sake tuntsire wa da dariya. Sai yamma lis ya dawo. Kai tsaye falo ya shiga. Na bi shi ina masa sannu. Na zauna. Ya ce "zubo mini abincin". Na fita na kawo masa, ban zauna ba sai da na dauko masa ruwa a fridge. Sai da ya gama cin abincin. Sannan na kalle shi bayan na d'aure fuska na ce "Ya jikin Dadan kuwa?" Kai-tsaye ya ce "Da sau'ki. Amma ta samu tagarde a hannunta." Na sake yin kalar tausayi na ce "Ayyah! Allah ya bata lafiya." Ya amsa da "ameen" yana daddana wayarsa. Can na nisa na ce "Tijjani wa ya yiwa Dada bik'in kashin da ta kwaso?" Kamar ba zai yi magana ba. Sai kuma ya ce "Gwaggo ce". Na zabura na dafa k'irjina na ce "Gwaggota?" Kansa na k'asa ya ce "ita fa". Kawai sai na fara kuka ina cewa "Na rantse da ina nan bazan bari ba. Duk yadda take tsangwamar ta sai kuma ta zo ta yi mata irin wannan wahala alhalin tana da y'ay'anta birjik?" Kansa na kan wayarsa dai, ya ce "Ai da yake tana mutunta mijinta ne. Baban Marina aikin ya kama, da yake ita mace ta gari ce, sai ta fanshi mijinta". Na zabura na ce "Wallahi ba shi ya kama ba. Ina ce ga Baban Tsakiya nan, ga kuma dan k'wai Baban kasuwa, dukkansu suna da matan auren kuma". A fusace ya ce "To basu yi ba, ita Gwaggo ita ce ta yi domin tafi dacewa ta yi aikin". Na harzuka na ce "Ban gane ba Tijjani. Wato ita ce kaskantacciya kake nufi ko me? Ai ba ita ce babba ba, ga Mama nan". Ya dago ido cikin ido ya ce "Asiya na ce miki da ita aikin yafi dacewa shiyasa ta yi d'in". Na mike na ce "Wallahi aikin bai dace da ita ba kai ma ka sani. Y'ay'an cikinta ne a hak'ku. Baba Maryo fa?" Ga mamakina sai na kasa ambato Baba ta Bulkachuwa. Shima ya mike ya ce "jikinki na yi miki k'aik'ayi Asiya Toro. Bilhiillazi kika yi gigin zaginsu a gabana sai jikinki ya fa'da miki. Bazan dauki wananan mugun halin ba. Ke abu ba zai wuce a wajen ki ba? D'azu dukkansu sai da suka tambaye ki, amma ke kin k'wafesu a cikin zuciyarki". Na ja tsaki na ce "Kana yi mini dukan da jikina ya fa'da mini. Ka tabbatar kai ma sai naka jikin ya fa'da maka. Domin kuwa dai ka daki aurenka tunda shine lasisinka na dukan jikin nawa". Ya kasa ce wa komai. Amma na lura ba k'aramin b'acin rai ya shiga ba. Ya kewaye ni ya fice. Bai dawo gidan ba. Sai wajen goma. Ni kuma tuni na sake fusata. Dan haka da ya dawo ya shigo d'akina ban ko kalle shi ba, bare nasan me yake ciki. Ga mamakina shima bai kalle ni ba, ya koma k'arshen gado ya kwanta. Washagari ma da asuba ya fice, k'ofar d'akin ya buga da k'arfi. Wanda na gane tashina ya yi dan na yi sallar asuba. Ya dawo ya ajiye burodi. Ya ha'da nasa shayin ya karya ya fice. Na yi abinci na ajiye masa na rana, amma bai dawo ba. Da yake lahadi ne. Mutum biyu sun zo lalle, haka kitso ma mutum uku na yiwa. Kafin la'asar babu kowa. Duk da zuciyata babu da'di a dalilin yadda na lura Tijjani ya tsananta fishin da yake yi. Wayata na dauka na shiga manhajar WhatsApp. Sai ganin Umm Nihla ta yi posting hadaddun materials daga Malaysia. Ina matu'kar son irin yadukan. Ba don komai ba, sai dan basu da nauyi, sannan gasu da taushi, ga kuma sau'kin ku'di ainun. Abin burgewa kuma basa kodou sai da ka gaji da su ka bayar. Wani yellow da blue suka tafi da ni. Kai tsaye na ce mata ina sonsu. Ga mamakina duk ku'din basu yi tsanani ba. Ta tambayi a wanne garin nake? Na bata amsa da Toro. Ta ce to sai a saka miki a motar Jos kenan?. Tunda kunfi kusa akan Bauchi. Na ce "A a akwai sister ta Aisha Lame jakadiyar oriflame. Ita zaki aikawa zasu same ni. Ta yi mamakin cewar nasan Aisha Lame. Na ce "To ai yar garinmu ce. Sannan muna da alaka ta wajen kakata da ta haifi Babana. Umm Nihla ta turo emojin mamaki ta ce "Ai kuwa Aisha na da kirki, kafin na bar Nigeria a wajenta nake siyayyar kayan kwalliya da spices. Farashin kayanta mai sau'ki ne ainun". Cikin alfahari na ce "Ai ko anan haka ahalinsu suke, mutane ne masu kirki kwarai da gaske. Nima da aurena ta bani kyautar fame wash. Yanzu kuwa na tura mata ku'din wani zan siya saboda na gane muhimmancinsa". Daga haka ta turo mini asusunta da zan tura ku'din. Sai mamakin yadda duniya ta samu cigaba nake yi. Ina Toro amma na sayi kaya a hannun wacce take zaune a Malaysia. Har na tura ku'din, ta tabbatar mini ta ga ni. Nima kuma ina da tabbacin zuwa gobe zan ji Aisha Lame ta karba mini. Na saki gauron numfashi. Na fara lissafin ku'dina domin so nake na yi k'undubalar fara shafa man oriflame. Idan nafi haka sheki da d'aukar ido zan fi daukar hankalin Tijjani fiye da yanzu. Haka na lalubo lambar Aisha Lame cikin sa'a tana online, ita da kanta ta za'ba mini Wanda yafi dacewa da farare. Itama take na tura mata ku'dinta. Na fa'da kuma za'a kawo mata material d'ina ta ha'do ta aiko aiko mini. Muka yi sallama. Yau ma sai bayan Isha ya dawo. Ban kula shi, shima bai kula ni ba. Kwanaki uku muna fishi da juna. Abin na cina a zuciyata, amma na daure na matse na share shi. Mussaman da bai shata mini layi da dakin sana'ata yadda yake yi a watannin baya ba. A kwana na hudu Gwaggo ta yi mini waya a lokacin ina tare da masu lalle. Muka gaisa ta ce "Yabi ba zaki zo ki gaida Dada ba ne? Kaf yaran gidan nan kowa ya zo ban da ke. Kuma kullum sai Tijjani ya zo ya duba ta. Amma daga ke har shi baku yi hankalin ki zo ki duba ta ba. Sai ta mutu ki zo gaisuwa ne?" Jikina ya yi sanyi na ce "Zan zo. Shine bai ce na zo ba". Da sauri ta ce "Ke ma k'aramab niyya ce da ke. Nasan Tijjani ba zai hana ki zuwa gaida Dada ba". A sanyaye na ce "Ki yi ha'kuri zan zo In sha Allah". Ta saki gauron numfashi ta ce "Ya dai kamata". Sannan ta kashe wayarta. Kamar almara ana idar da azahar ranar sai ya dawo. Cikin sa'a na gama yiwa wacde nake sawa. Saura mutum biyu su kuma dama sai mun yi sallah. Ban yi abinci ba tunda ba dawowa yake yi ba. Ko cefane ne idan ya kawo mini. A k'ofar gida zai bawa yaro ya shigo da shi, ya yi juyawarsa. Na bishi falon. Murya a dakushe na ce "Sannu da dawowa". Ya amsa babu walwala. Sannan ya ce "yunwa nake ji. Me kika dafa?" Na dauke kai na ce "Ban yi komai ba, tunda nasan cikina kawai zan yiwa". Shima tasa fuskar a daure ya ce "To sai ki dora yanzu. Sauri nake yi kuma". Ban ce komai ba, na juya na shiga kicin din. Na dora farin ruwa dan nasan ina da miya a fridge. Daga nan na nufi bayi dan yin alwallah. Sai da na zuba makaroni sannan na yi dakinmu dan yin sallah. Bayan na idar na shiga falon na dauko miya. Na tarar ta nuna. Na ta ce na dauraye. Na dora miyar dan ta d'umama. Na shirya a tire na kai masa. Bai nemi na zauna muci kamar yadda muka saba ba. Nima kuma ban zauna di'n ba. Na tafi na cigaba da yin lallena. Ya gama ya fita. Har dare ina ta sakar yadda za'a yi a gobe na je na gaida Dada. Muna kwnace kowa na k'arshen gado. Dukkanmu mun kasa barci da alamu akwai abin da ya damemu. Ni dai nasan yadda zan fita gobe nake ta tufka da warwara. Tsawon lokaci muna hakan. Sai kuma na ga ya mirgino ya same ni a jikin bangon da na lafe. Bai ta'ba ni ba. Amma ya mannu da ni sosai. Murya k'asa k'asa ya ce "Asiya Toro idan muna fa'da ai bai kamata mu sanya aurenmu a cikin rikicin ba. Kawai mu yi harkar aurenmu. Allah bar shi da safe muci gaba da gabarmu tunda bani da darajar da zaki mini laifi ki bani hakuri". Nan da nan na gano jarumtarsa ta kare ne. So yake mu kebe. Maimakon na yarda tunda nima na kosa da gabar sai kawai na kwabse na ce "Sawa na nawa kuma? Ai tuni ka sanya shi a ciki. Yau kwananka nawa da yin fatali da shi?" Ya ru'ko hannuna a hanzari ya ce "To yau na cire shi Asiya. Mu shiryasu kin ji. Mu din ma, ko yanzu kika bani hakuri mun shirya. Kin bata mini rai. Wai har ki ce mini zan doki aurena. Ai ban zaci har yau ba kya sona ba Asiya". Yadda ya yi maganr sai ta yi matu'kar ta'ba ni. Ban san me yasa yake yawan bani tausayi ba. Na numfasa na ce "Nima ai ka bata mini rai. Akan me zaka dinga duka na? Ko ka dinga yi mini barazana da duka. Ai na dauka ko wani ka ga zai dokar maka jikin nan nawa sai yadda karfinka ya k'are, ba wai kai da kanka ba". Da sauri ya ce "Bilhiillazi ba wanda zai doke ki a duniyar nan na bar shi ya kwashe kalau. Sai ko Gwaggo da Baban Marina. Amma kowa ye zan motsa k'wannjina a kansa. Ni kuma ai ba haka siddan nake dukan ki ba. Sai na ga zaki kuskure. Sannan kuma ai ba mai yawa nake yi ba". Na cuna baki duk da a duhu ne na ce "To ni dai bana so, ka daina". Da sauri ya ce "To. Amma kema ki daina yi mini taurin kai da rashin kunya. Idan na ce miki ya isa, ko bari. To ki bari din kawai". Ban amsa ba, amma na ji, zan kuma kiyaye. Ya nisa ya ce "To me zaki ce mini?" Na fara tirza kafa ina kukan shagwaba tare da cewa"Ai tunda ka buge mini baki shikenan an yi zuza. Kuma ba sharri na yi musu ba. Gaskiya na fa'da.". Ya ru'ko ni ya ce "Amma tunda raina ya baci, kuma har na fa'da miki ba, sai ki rarrashe ni, ki kwantar mini da hankalina ba?" Na dinga k'unk'unin ina fa'din "Ni ba wani rarrashin k'ato da zan yi". Da yake bai ji me nake fa'da ba. Ya jani jikinsa ya rungume. Ya dinga shinshinata tare da sakin maganganun masu nauyi. Ni kuma na cure jikina, na dunk'ule. Na dinga ja masa rai. Ban yarda na sallama masa ba. Sai da na ce "Yaushe zan je na gaida Dada?" Murya na rawa. Ya ce "Kina ce mini sorry gobe zan kai ki tun safe ki yini a can". Da murna na ce "idan ban ce maka ba fa." Ya ce "Zan kai ki, amma minti talatin tana cika zan tiso ki a gaba mu dawo gida". Sanin da na yi da gaske yake yi, ya sanya na bu'de baki cikin walwala na ce "Ka yi hakuri Tijjani". Nan da nan ya sake rungume ni sosai ya ce "Thats my little girl. Na huce, na kuma yafe miki. Daga Nan abubuwan da suka biyo baya masu nauyi ne. Domin Ni da kaina na tabbatar na yi missing Tijjani da jagwalgwalonsa masu sanya ni tsumaye. Abin da ban yi zaton zan yiwa Tijjani ba, sai da na yi masa a wannan daren. Wanda ba karamin gigita shi na yi. Da safe ya tashi ya dinga yi mini hidima da bare-bare. Ni kuma kunya ta yi mini k'awanya. Da wuri muka shirya ya kai ni gida da kansa. Ya kuma ce sai an yi sallah isha zai zo mu tafi. Sai da zamu shiga gidan ya bu'de but din mashin d'insa ya fito da lemon maltina guda biyu da lucozade shima biyu a leda. Ya mik'o mini ya ce "Ki bata". Na kar'ba tare da cewa "Na gode! Ni ban yi tunanin na siya mata komai ba". Bai ce komai ba, muka shiga gidan. Nan kuwa jakar hannuna cike take da omon viva 85kg zan bawa su Gwaggo. Da kuma alwar da zan raba wa kannena. Tare muka gurfana da shi a gaban Dada muna gaisuwa cikin tausayi da alhini. Bansan ai haka ta jigata ba. Kanta har a lokacin a suntume ya ke. Ga hannu a targade ya sha nadi da bendeji. Ga fuska da k'afafuwa duk sun kuje sosai. Duk yadda ta ji jiki, har jikin ya yi yaushi amma bakinta ras. Ta kalle ni ta ce "Ai Yabi Allah ne yasa da sauran kwana a gaba. Gaba'daya ji na yi tamkar wadda k'asa ta dare na afka. Kai wato wanda yake yawaita ro'kon Allah da neman kariya daga tsautsayi da asara zai ga sassauci a lamarinsa. Ni nasan k'addara bata sauya wa. Amma k'arfin addu'a yana rage zafinta. Na gode wa Rabbani da ya sanya ni cikin bayinsa masu yawan ambatonsa masu kuma yawan gode masa." Tijjani ya ce "Haka ne Dadarmu". Ta muskuta, na kalle ta tausayin ta ya sake kama ni a dalilin nasan bata ji dadin zaman ba. Ilai kuwa kafin na yi wani abu. Sai cewa ta yi "Mai sunan manya matso ka gyara mini zaman nawa. Gaba'daya a takure na ke." Da sauri ya matsa cancakat ya cira ta. Ya ce "Asiya sa hannu ki gyara mata zaninta". Na gyra mata din cikin azama". Ya mayar da ita ya tokare mata baya da filo mai tauri. Ta ce "Allah ya yi maka albarka mai sunan manya. Allah ya tsare ka daga tsautsayi da asara. Allah ya sa kafi karfin magauta. Ubangiji ya bu'de maka k'ofofin alheri". Ya dinga amsawa cikin walwala. Na k'ulu, wato Tijjani kawai zata yiwa addu'a. Na daure na ha'diye ban fashe ba. Can ta zuba mini ido. Sai kuma ta koma ga Tijjani ta ce "Mai sunan manya da alama komai ya dai-daita. Wannan haske da sheki da cikar da Yabi ta yi ba iya na abici ba ne kawai. Ana takar ta sosai gaba'daya ta fara bude wa" Ba ni ba, hatta shi kansa maganar ta yi masa nauyi ainun. Ya yi maza ya sunkuyar da kansa ba tare da ya ce uffan ba. Ita kuwa ko a jikinta sai faman murmushi take yi tana fa'din "Alhandulillahi. Allah kasa zan ga jininka kafin duniyata ta kare". Na mike bayan na tura mata ledar gabanta na ce "Ga shi nan Dada. Allah ya k'ara lafiya bari na tafi inda nima za'a yi nan nan da ni. Kin riga kin saba da hubbu ra'as. Tunda muka zauna ba kya ta tawa. Sai mai sunan manya, mai sunan manya. To na barku ku k'arata". Ta k'yal-k'yale da dariya bayan ta ja ledar tana ce wa "Wayyo Yabi mai dogon hannu. Da'dina da ke akwai ungo. Duk cikin jikokina na d'aki ke ce kika kawo mini tsarabar dubiya. Ko wacce da sun zo da mijinta ta ga ya bani dubu ko dari biyar shike nan sai ta ja ta tsuke. Wai suna nufin mazansu sun fanshesu. Har Nasiba haka ta zo mini hannu na dukan cinya. Ita kam mijinta bai zo ba, bare ya bani. Amma mijinki kullum ne. Sai ya kawo mini kunshin nama, ko lemo da ayaba. Ai yanzu na ga ne biki mai zuciya a ke fa'dawa ba mai dukiya ba". Na ce "Ke kuma Dada da son a baki ki ke. Ban da haka ina lafi ma da aka zo aka duba ki?" Na kalli Tijjani na ga ya kyafta mini ido, alamun na bar maganar haka". Na sanya takalmi na ce "masa na yi cikin gida. Sai ka shigo". Na tafi na bar shi tare da ita. Ina jin tana cewa "Ah yarinya ta yi bundum ta yi cikar daki. Ni dama nasan ruwan wankan aure duk zai sanya muku nutsuwa." A zaure muka yi kicibus da Yaya Anwar yayan Nasiba. Na gaishe shi da mutunta wa domin shi d'in kamamme ne. Ya amsa tare da ce wa "Yabin Bulkachuwa yau a gidan Marina? Tunda aka yi aurenku ke ce ban ga kin zo ba. Bulkachuwa ya rufe ki ruf. Ma sha Allah! Allah ya k'ara ha'da zuciyoyinku". Kunya ta kama ni. Na wuce ban ce komai ba. Amma sunan da ya kira ni da shi ya sanya mini wani irin shauki a zuciyata. Duk kame kamena na fara gasgata cewa na fara son Bulkachuwa. Irin son nan mai shiga a hankali ya yi karfi mai tsananin gaske. Ga shi wani irin kishinsa nake yi irin wanda ban ta'ba jin irinsa akan ko wanne namiji ba. Kawai ina waske wa ne dan kar ya fahimci halin da na ke ciki. Tunda shima na fahimci mai iyashege ne. Ina shiga k'ofarmu aka dinga yi mini oyoyo tamkar ba Yabin da kowa ya ga ji da ita ba. Hatta Mama sai da yi mini barka da zuwa cikin sakakkiyar fuska. Inna kuwa sai kiran kananun y'ay'anta take yi tana fa'din "ku je ku yiwa Adda Yabi oyoyo." Na fito da alawa na dinga bawa kowa a hannunsa. Tun fil'azal kyautar alawar da nake yi musu ya sanya suka fi sakewa da ni. Dakin mama na fara shiga na gaisheta na ajiye mata omonta zare guda. Sannan na shiga na Inna na bata nata. Sai kuma na dawo dakinmu na baje. Na fa'da kan gado na fashe da kuka a hankali. Ta zauna jikinta na rawa ta ce "Duk yadda jikinkinki ya nuna kina zaune k'alau ashe ba hakan ba ne. Daga zuwanki zaki daga mini hankali, ki shafe murnar da na ke ciki ta ganin ki, cikin yanayi me kyau?" Na share idon na ce "Ai ke ce "Baki taba zuwa mini ba. Kowa a gidan nan ya je amma ban da ke. Ko har yau fishi ki ke yi da ni Gwaggo?" Ta ri'ke hannuna ta ce "Ba komai a zuciyata game da ke sai alheri mai yawa Yabi. To me zan je na yi miki ne? Babanku ya je. Mama ta je, Inna ta je, yayarki tana zuwa. To su duk kin raina k'ok'arinsu?" Na juyar da fuska na ce "Ban raina ba Gwaggo. Amma ina so ki zo". Ta mike ta ce "Zan zo. Amma sai kin haihu." Na rufe fuskata domin kunya na ji irin sosai din nan. ✍️ *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* 57&58. Yini na yi cikin farin ciki. Domin Baban Marina tunda ya dawo cin abinci da azahar, bai fita ba. Zama ya yi muke hira ni da shi domin ba k'aramin da'din ganina ya yi ba. Sai da aka fara kiran sallar la'asar sannan muka yi sallama ya fice. Sai dare kuwa muka tafi kamar yadda ya yi mini al'kawari. Albarka na sha ta daga wajen mahaifana har da Dada ma. A k'ofar gida ina shirin d'ale wa mashin din, sai ga Baban Tsakiya. Na yi kamar ban gan shi ba, na dauke kai. Tijjani ya mini inkiyar na gaishe shi amma na waske. Sai shine da kansa ya ce "Tijjani wannan ba Yabi ba ce?". Kafin ya ba shi amsa Na rusuna ka'dan na ce "Baban Tsakiya ina yini". Ya ce "Ai har yanzu ba zaki daina kama suna da inkiya ba?" Ban ce komai ba daga hakan. Na haye mashin d'in ko kunyarsa ban ji ba. Duk da yana kallona haka na dafa Tijjani da zan hau din, tunda har yau ba zai shafa mini lafiya ba. Ya kad'a kai ya ce "Tijjani Allah ya k'ara maka hakuri da juriya". Ya kasa amsa masa, amma gaba'daya na ga ya yi wani iri. Kafin ya ja mashin din sai ga J ya fito da alamu tare suke da mahaifin nasa. Ya mika wa Tijjani hannu suka gaisa. Hasken solar da gwamnati ta kafa akan layika ta haske fuskokinmu tunda muna da ita a k'ofar gidanmu. Karon farko da na kalle shi ban ji wani abu na so ko na burge wa ya taso mini ba. Domin ko ranar da muka je gidansa yin barka sai da tsumin sonsa ya taso mini. Na bu'de baki na ce Yaya J ina yini, ya Baby?" Da wani irin yanayi ya ce "Lafiya k'alau Yabi. Ya kike, ya ruwa?" Na amsa da Alhamdulillah". Daga haka Tijjani ya ja mashin dinsa muka wuce. Lafiya k'alau muka isa gidan, muka gama uzzirinmu muka kwanta. Tsawon lokaci ina jiran na ji hannunsa a jikina shiru. Na dinga mutsu mutsu, amma bai motsa ba. Da k'yar na samu barci ya sure ni. Da asuba ma hakan ya yi, ga shi ya riga ya sabar mini da al'amarin dare da asuba basa wuce mu sai idan fashin sallah nake yi. Shi ma sai mun yi abubuwan da zamu samu nutsuwa. Na rasa yadda zan yi, domin kunya ta hana na fara kai hannuna gare shi. Na daure dai nima na share. Muka koma barci. Ni na fara tashi, na gyara gidan, na duba na ga akwai taliyar hausa. Nasan kuma yana sonta sosai. Sai kawai na d'ora jolof d'in ta. Ina shirin gamawa na ga ya fito ya yi band'aki. Can kuma ya fito da brush dinsa ya zauna daga gefe ya yi, sannan ya mayar ya ajiye. Maimakon ya shigo kicin ya taya ni mu k'arasa kamar yadda ya saba sai kawai na ga ya yi falo. Na fara jin wani iri a dalilin sauyinsa. Na dinga tunanin me ya faru. Amma na kasa gano ko na yi masa wani abu. Na gama, na tafasa shayi. Na ha'da komai na kai falon. Muka fara karyawa amma babu doguwar hira yadda ya saba mini. Muna zaune, jigum jigum yaro ya yi sallamah daga ba'kin k'ofa ya ce "Wai ana sallama da Tijjani". Na zabura na ce "Kai shigo". Ya shigo na kare masa kallo, gaba'daya ba zai wuce shekaru takwas ba. Na zare masa ido a dalilin na ji haushin gatsa sunan da ya yi. Na ce "Ba zaka ce ana sallama da maigidan ba sai ka wani gatsa sunasa tamkar sa'an ka. Zaka iya fa'din sunan Babanku gatsal?" Yaron ya yi shiru yana kallona da alamu ma tsorata ya yi kada na rufe shi da duka. Sai lokacin Bulkachuwa ya ce "Kai je ka ce "Ina zuwa". Ya mik'e ya bar ni. Tunda ya fita sai yamma ya dawo. Bai ce mini ga inda ya je ba, nima ban tambaya ba. Na gabatar masa da ruwa da abinci na yi tafiyata wajen k'unshina. Domin na fara jin haushin daddaurewar da yake yi mini haka siddan. Haka da daddare ma ya sake matse wa bai ta'ba ni ba. Kwanaki uku ke nan, muna haka, na fara k'osawa domin gaskiya ya riga ya yi mini sabo a harkar, tun ina turjiya, ina raki har na zama yar hannu da al'amarin nasa. Sannan na fahimci nima irin halittarsa ce da ni. Ina son harkar, ina jin da'din ta. Ban sani ba ko ya fahimci hakan ne shi yasa zai fara yi mini gayya. Sai na yun'kura zan tambaye shi dalilin sauyinsa sai na yi maza na fasa. Ina jaddada wa zuciyata na ja ajina. Shi da yake namiji ma ya yi jarumtar runtsi idonsa daga gare ni, sai ni mace ce zan k'osa?. Dan haka na yi hakuri, na zuba masa ido, amma gaba'daya bana cikin nutsuwa. Mussaman idan ya shek'a kwalliya ya baza turare sai na ji tamkar na yi tsalle na mak'ale shi. Sai ya fita nake samun damar na yi kukana. Ina ayyana wai ni Tijjani yake yiwa wannan wula'kancin haka siddan dan ya fahimci na fara sonsa. Na fara zargin akwai abin da yake yi a waje da ya sanya yake iya kawar da kansa a kaina. Gaba'daya na rasa sukuni. Na yi wani iri. Ranar da muka yi kwana hudu a cikin wannan halin. Gaba'daya ya juye mini, tamkar ba shine mai rawar jiki da tsoron ganin fishina ba. Tamkar ba shine mai kulafacina kamar me ba. Ranar da wuri ya shigo. Na yi wanka na sanya riga da wando silky. Wando iya guiwa rigar ma iya tsayinta kenan wando kawai ta rufe. Na taje gashina da yake a tsefe na mulke shi da man gashi na kwakwa da asalain man alaiyadi. Na dauko turarena na mai maiko na oudi na murtsike hannayena da jikina har ma da gashin. Na sake dauko turaren active woman da Tijjani ya canja mini na bi jikina na feshe. Na saka hula marar nauyi kalar kayan barcin nawa. Na fita na same shi yana kallon labaran NTA Bauchi. Na zauna ya dago ya kalle ni. Domin na tabbatar kamshina ya kai masa caffa mai yawa. Na sassauta na ce "Wai mun b'ata ne?" Cikin nutsuwa ya ce "Da yaushe?" Na yi sakare ina kallonsa. Na numfasa na ce"Ai tambayar ka na yi." Ya girgiza kai ya ce "To ke mun b'ata ne?" Na rasa me zan ce masa ma. Na nisa na ce "Nasan bamu b'ata ba. Amma na ga ka sauya ne". Ya daure fuska ya ce "Tun yaushe na canja d'in?" Na ce "Tun kwanaki hudu, tun ranar da ka kai ni gida". Ya yi shiru tsawon lokaci kafin ya bu'de baki ya ce "Kuma sai yau kike bu'katar sanin dalilin sauyin nawa saboda baki d'auke ni a bakin komai ba?" Ga mamakina sai na shiga rud'u na ce "To ai kai ne zaka fa'da mini." Ya girgiza kai ya ce "Babu damuwa ki cigaba da zaman jiran na fa'da miki". Idona ya ciko da k'walla. Na zuba masa ido sosai na nuna kaina da yatsana na ce "Ni kake wula'kantawa saboda kawai ka shiga ka fita kasa na saba da kai ko?. Ai shike nan na gode". Daga hakan na kifa kaina a hannun kujerar na fashe da kuka mai tsananin gaske. Ya taso da azama ya zauna kusa da ni. Ya ru'ko ni na fizge tare da ce wa "Ba ruwanka da ni, komai kake yi na barwa Allah. Ka cigaba da yi mini wula'kanci komai lokaci ne ai, watarana ba zaka yi ba". Ya sake tarairayo ni jikinsa yana kamo weak points dina. Jikina ya fara tsuma. Amma na sake k'wace wa na mike, cikin muryar kuka na ce "Bana so Tijjani, ka bari na fa'da maka". Na fice na yi d'akina ina kuka sosai. Sai da ya yi wanka sannan ya shigo d'akin har lokacin kuma ina dukunkune ina kuka sosai. Sai da ya yi shafa'i da wutiri sannan ya tarar da ni a gadon. Bai kwanta ba. Ya zauna ya kaurara murya ya ce "Asiya tashi mu yi magana." Na share shi, na k'i na nuna ma na ji shi. Ya saka hannunsa biyu ya d'aga ni ya zaunar da ni. Na sake yun'kurin koma wa na kwanta dan na nuna masa ba ni da lokacinsa, sai kawai na ji ya bu'de murya sosai ya ce "Wallahi idan kika kwanta idan ranki sun kai dubu ki tabbatar sai na bisu d'aya bayan d'aya na b'ata su." Jin ya rantse sai na zauna din. Amma na tattaro dukkan fishi na yab'a a fuskata. Ya jima yana kallon yadda nake tunbatsa. Shima ya d'aure tasa fuskar ya ce "Ki saurare ni da kunnen basira Asiya Toro". Jin ya fadi wannan sunan na sake hassala ainun. Ya furzar da iskar baki ya ce "Ranar da muka je gida kin wula'kanta ni, kin tozarta ni! Watannin baya na fa'da miki, ba zai yiwu a gabana ki wula'kanta iyayenmu ba. Idan kin ture girmansu na k'annen mahaifinki ne, to ki sani baki isa ki ture nasabarsu da ni ba. Ina kuma da hak'kin ki mutunta iyayena. Dole ne, wajibi ne Asiya ki mutunta mini dangin uwata matu'kar kina son mu zauna lafiya. Ba zai yiwu ina aurenki kuma in zuba miki ido ki dinga yin rashin mutunci ba. Bilhiillazi wannan ne karon k'arshe da zaki ga wani cikin iyayenmu ki k'i gaishesu, ko ki yi musu gaisuwar je ka na yi ka". Na fara kuka ina ce wa "To ina ruwanka ne kam. Kai baka ga irin k'iyayyar da suke yi mini ba? Saboda baka kishina, saboda kai sun yarda gyatumarka yar'uwarsu ce shiyasa kake ganin bekena. Duk abubuwan da suke yiwa ubanmu baku da kaico. Ai ka sani ba sai na fa'da ba, ko auren nan nawa sun yi sanadinsa ne dan kawai suna ganin bazan cigaba ba. Amma da sun tabbatar zan samu nutsuwa a cikinsa a sai sun rugurguza shi. Yanzu ma kuwa nasan akwai lokacin da zai zo da zasu rabamu tunda zuciyarsu mai k'yashi ce." Ya buge mini baki ya ce "Kada ki kuskura ki fa'di maganar banza a kansu a gabana. Dole fa ki mutunta su a matsayin surakanki tunda ke kin yanke nasabar da ta hada ku". Cikin gigita na ce "To ka sake ni, bana son yin surukuta da su. Kai ma bana sonka Tijjani". Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* Jikinsa ya yi sanyi domin ya ga matsanancin fishi a tare da ni. Ya numfasa ya ce "Na sani ai ba kya sona Asiya. Ban manta ba, amma na sakankace a d'an zaman da muka yi, zaki iya mini kawaici da alkunya akan abin da kika san zai musguna mini tunda kin sani sarai an jarrabe ni akan son ki. Amma yanzu na gane da gaske ba kya sona tunda akan idona kika k'i gaida Baban Tsakiya cikin mutunci duk da kashedin da nake yi miki da ido. Sannan kika gaida Jabir cikin falli har kina kiransa Yaya alhalin kin kankare zumuntar da ubansa." Na yi shiru domin kam jikina ya yi tub'us. Ya cigaba da ce wa "Saboda shi kina sonsa, kuma yafi ni ku'di shi yasa kike ce masa Yaya ni kuma ki gatsa Tijjani gatsal duk da na girme shi kuma ni ne mijin ki. Asiya ba zamu tab'a daidaita wa da ke ba alhalin kin ri'ke BAK'AK'EN TA'ADODI. Yanzu duk k'uruciyar ki ai k'iris ya rage ki yi sha bakwai. Kin san kuma hukuncin wacce ta bu'de baki ta ce mijinta ya sake ta ba tare da gamshasshen dalili ba. Sannan kina da ra'ayin ruk'au na k'ullaci. Hakan kuma ba siffar mace ta gari ba ce. Kamata ya yi zuciyar mace ta zama mai taushi da sassauci ba mai tauri da tsanani ba." Na ji kunyar kalamansa mussaman akan J. Na tabbatar shi ba na ce masa Yaya. Amma ban da yau ai nafi wata ban kama sunansa ba, sai dai na yi masa magana kawai. Domin na da'de da daina fa'da a dalilin kunya na kama ni tare da nauyin gatsa sunan nasa. Na tura baki na juya baya. Cikin k'unk'uni na ce "To ai kai ma kana da Bak'ar Ta'ada din, akan me tun a ranar ba zaka fa'da mini laifina ba, sai kawai ka k'ulla ce ni, ka tsiri fishi. Ni ba Allan musuru ba, ta ina zan san kuskurena?" Ya matso jikina ya ce "Da kina sona ai tun a lokacin zaki fahimci sauyin nawa, sai ki shawo kaina ki ririta ni, ki mantar da ni b'acin ran da nake ciki. Amma saboda am nothing to you ai share ni kika yi. Kika tattara kika yi wurgi da ni". Na cuna baki na yi shiru. Ya mik'e dukkan k'afafuwan sa. Ya janyo ni ya kwantar a kai. Ya shiga wasa da gyararren gashina. Murya a dak'ushe tabbacin yana cikin kewa ya ce "Bana son abubuwan da kike yi a gabansu. Su din iyaye ne. Ta ko wacce fuska sune a sama da ke. Zan yi hakuri da komai akan sha'anin ki, amma ban da na fito na fito da iyaye, bana so, ki bari." Na yi shiru ban amsa ba. Ya sassauta murya ya ce "kin yi shiru." Na sake yin shiru still. Ya zame ni daga jikinsa ya juya baya ya yi kwanciyarsa. Ina ganin hakan ai kuwa na tak'ark'are na zunduma masa fallashasshen kukan da baya so. Ina ce wa "Tunda juninka k'ullaci ne ka mayar da ni gidanmu kawai". Ya juyo da azama ya ce "Asiya ki cigaba da wula'kanta ni. Amma ki sani komai zaki yi ni ba zan mayar da ke ba, domin ina son ki, ke da ba kya sona sai ki tafiyar ki, hakan kuma ba shine k'arshe farin-ciki a gare ni ba." Na sassauta kukana domin na ga ya hassala sosai. Na dinga yinsa kasa kasa irin mai cin rai din nan. Da ya gaji da jin kukan nawa ya saka hannunsa ya ja ni jikinsa ya ce "Yi shiru Asiyata, amma ba zamu shirya ba sai kin ba ni hakuri dole". Duk yadda na k'agu mu shirya fuska na yi da ce wa "Ai ban maka laifi ba. Sannan ba dan komai nake ce wa Jabir Yaya ba sai dan yana ce mini Yabi ne. Amma kai sai ka dinga ce mini Asiya Toro babu ko sha'awa ma". Ina rufe baki ya ce "Har abada ba zan ce Yabi ba, idan ya so ba Tijjani kawai ba, ki fa'di cikakken sunan nawa Tijjani Yusuf Bulkachuwa! Marar kunya. Shine rannan kika yiwa yaro sababi akan ya k'ira ni da Tijjani to ke d'in kin saya ne bare ki ji ciwon wani bai saya ba. Kuma ni ban damu sai kin saya d'in ba". Na nisa na saki ajiyar zuciya irin wacce ake yi idan an ci kuka sosai. Na ce "Ni fa tuni na samo maka sunan da zan fa'da maka, amma sai na haihu". Maganar ta zo masa a bazata. Ya ru'ko ni ya ce "Kina son haihuwa ne Asiya?" Da sauri na ce "Ina so sosai, domin duk wanda muka taso ko wacce ta haihu. Wadanda aka yi aurenmu tare Nasiba da Ubaida dukkansu ciki ne da su, ni ce kawai ba ni da shi". Na fa'da da karyayyar murya. Ya sassauta ya ce "Asiya haihuwa lokaci ne da sannu ke ma wataran zaki gan ki da naki cikin. Tunda kin daina guduna, sannan nima ina iyakacin k'ok'ari, kawai mu dinga addu'a". Na ce "To. Ka ga Gwaggo ma ta ce ba zata zo gidan nan ba sai na haihu". Ya rungume ni sosai ya ce "In sha Allah zaki haihu Asiyata. Mace kike so ko namiji?" Kai tsaye na ce "Ni dai na samu cikin nafi so. Ko mai na haifa ina so ba ni da za'bi." Ya yi dariya ya ce "Tom shike nan Allah zai bamu In sha Allah! Kawai ki kara zama jaruma, ko sau nawa za'a yi kada ki yi musu ko ki ce kin gaji". Na ce "Da gaske idan na yi haka zan samu cikin ko dai wayo zaka yi mini?" Ya k'yal-k'yale da dariya ya ce "Ba wani wayo gaskiya nake fa'da miki Asiyata". Daga hakan kuma ya shiga kissing d'ina tare da zafafan sakonni masu rikita ni. Sai da ya tabbatar ya rura mini jiki. Sannan ya sake ni ya kwanta tare da ce wa "Au ashe baki ba ni ha'kuri ba fa, bamu shirya ba". A hankali na ce ", Mun shirya mana, ba har ka yi dariya ba yanzu". Ya ce "Ai ba ki bani hakurin da na ce ki ba ni ba". Na fara kukan shagwaba, ya juyo ya ce "To fa'da mini a kunne na ji". Cikin kuka kuka na ce "Allah ya baka hakuri". Ina fa'din hakan ya rungume ni yana cewa"Ameen little girl na ha'kura na huce gaba'daya". Daga hakan kuma ya dinga b'arin jiki a kaina, komai ha'dama ha'dama yake yinsa har na gamsu k'arfin hali ya yi a kwanakin amma ba samu yake yi a waje ba. Domin duk kulafacina sai da na k'osa amma shi bai k'osa din ba". Haka muka cigaba da gurgurawa ciikin rufin asiri. Dai-dai gwargwadon k'arfinsa yana yi mini komai. Matsalar da ta fara damuna har cikin zuciyata rashin samun cikina gashi watanmu goma da aure Nasiba jiya ta haihu Ubaida kuwa har an saka ranar da za'a yi mata tiyata(c.s). Da aka sanar mini da haihuwar yini na yi cikin sanyin jiki. Sai kuma matsalar Rafi'a. Wata guda da kammala karatunta na digiri ta tattaro ta dawo gida gaba'daya. Kusan ko yaushe a k'ofata take. Idan ina k'unshi sai ta hakince a falo da sunan kallo. Ko Tijjani ne ya dawo ba zata tashi ba, sai ma ta yi ta jansa da zancen makaranta su yi ta hirarsu. Ko idan ta ga ya fita sai ita ma ta bi shi su fita tare. Ranar da na yi masa k'orafi ya balbale ni da sababin wai na raina shi, ban yarda da shi ba. Na kame baki na yi shiru, kuma sai da na ba shi hakuri akan hakan. Tunda ya ja ya tsaya ba shine yake zuwa wajenta ba, ba shi yake kiranta ba, tunda bana so ta zo mini gida to na hanata zuwa kawai. Na rasa ta yadda zan kore ta domin dai gaskiyar magana uwarta tana mini kirki da alheri mai yawa a matsayin ta na babba. Bayan haka ita kanta Rafi'a din kirki ne da ita. Bai zame mata komai ba ta yi mini gyaran gida ba. Kawai ni yadda take shige wa Tijjani ne bana so, domin na riga da nasan shi akan lutayen mata. Wadannan matsaloli sai suke neman sauya zaman aurenmu. Domin ni a k'arancin shekaruna dauka na yi Tijjani ne ya ki yi mini cikin kawai. Sannan yana son Rafia. A hankali na fara janye masa, abubuwa suka fara sauya wa a tsakaninmu. Na daina sauraronsa ko na saurare shi ma to kuwa sau daya ne shima ba cikin da'din rai ba. Ranar da na dawo daga sunan Nasiba kuwa. Kuka na zauna na yi masa mai d'aga hankali k'warai da gaske. Ina yi ina ce wa "Akan me zaka matsa mini sai ka ta'ba ni bayan bana so, na riga na gane ba cikin nan zaka yi mini ba, dan haka na gaji da nukurkusata da kake yi babu sassauci babu kuma wani abu da zan samu." Ya zuba mata ido yana kallon yadda take kuka bilhakki. Ya tafi tunanin shekarunta. Watan da ya shud'e ta ciki shekaru sha bakwai. Ke nan akwai k'uruciya mai yawa a tare da ita. Bai kamata kuma ya biye mata ba, domin ya fahimci da dukkan zuciyarta take ganin shine bai mata ciki ba. Ya numfasa ya saki gauron numfashi kafin ya ce "Asiya Allah ne fa mai bayarwa, kuma ba mantawa ya yi damu ba. Kika san tanadin da yake yi mana?" Cikin kuka na ce "Ba wani, ni kawai ciki nake so, ai ko wacce ta haihu saboda mazansu suna sonsu, sai ni ce kawai saboda baka sona, kowa wani gani gani yake yi mini ba'a yi mini ciki ba". Dariya ta so subuce masa, amma ya maze ya ce "Asiya zai yi wahalar gaske a samu wacce ake takarta irin yadda nake yi miki a cikinsu. Kin san da yawan yi ne sanadin samun ciki da yanzu kin haihu sau uku. Amma shi samuwar ciki ai ikon Allah ne." Da rawar murya na ce"Ba wani kawai dai ni ce baka so na samu ba, ga Ubaida nan yarinya da ita jibi za'a ciro mata d'a ko y'arsu, kai ma da su Nasiba ka aura ai da tuni ka yi musu. Ina goge idona na ce "Wallahi na baka nan da wata d'aya, idan ban samu ciki ba to ba zan zauna ba". Ya sake zuba mini ido cikin mamaki mai yawa. Ni kuwa ko d'ar ban ji ba. Ya ha'diye komai ya ce "Shike nan Allah ka taimaki Tijjani ya yiwa Asiya Toro cikin y'an-uku". Na yi maza na ce y'an uku tashi guda? Y'an biyu ko daya ma ya isa." Ya fara ta'ba ni, na bige hannun na ce "Ni fa yau na gaji Wallahi". Ya ce "To shike nan Asiya Toro Allah ya kai mu gobe, tunda ciki kike so ki sani fa babu ke babu hutu, amma na yarda ki huta yau din". *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* ✍️ *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* 59&60. Haka al'amuran suka ci gaba da gudana. Aka ciro wa Ubaida kyakkawar jaririyarsu mai cike da koshin lafiya. Ita kam gida aka tafi da ita. Tunda bata da lafiya. Sai da aka yi sati biyu da haihuwar sannan aka yi taron suna. Ranar sunan na ga dukkan y'anmata da muka taso har ma da k'anwata kowa da d'a ko y'a a hannunta amma ban da ni. Na shige d'akinmu na dinga kuka. Yaya Ummi ce kawai ta gano ni. Dan kuwa ita Gwaggo ma bata dauki hakan a matsala ba ne. Yaya Ummi ce ta dinga ba ni hakuri tare da cewa gaba'daya ma auren naku wata shad'aya ne fa Yabi. Sannan shekarunki shabakwai. Ban da an miki auren wuri ai har yanzu baki isa auren ba, bare aje ga zancen haihuwa. Wadanda suka zarce shekaru goma babu haihuwa fa sai su ce da Ubangiji me? Ki shiga a hankalin ki fa". Sai da ta shawo kaina sannan muka fita cikin jama'a. Watanni uku bayan haihuwar Ubaida mai gidan burodi da Tijjani yake zuwa ya rasu. Magada sun yi yawa a kai dan hakan suka siyar da shi. Wanda ya siya kuwa kabila ne dan haka ya sallami galibin ma'aikatan ya debo nasa y'anuwan ya zuba. Cikin wadanda aka sallama kuwa har da Tijjani. Ban gane aikin da burodin da yake yi rufin asiri ne mai yawa ba, sai bayan an rasa shi. Domin ba'a dauki kwanankin sati ba sai da muka ga gurbinsa. A da bamu da matsalar abin karya wa tunda burodi har yawa yake yi mana. Ga kuma donougt da ita ma bata yanke mana. Ko baki na yi zan basu. Sannan da daddare ba kasafai muke cin abinci ba, sai kawai muci da shayi mu yi kwanciyarmu. Sannu a hankali rashin samun ku'di ya dabaibaye shi k'warai da gaske. Tunda aikin saka tiles sai an samu. Haka na satellite shima hab'o ne. Tsawon wata biyu muna cikin wannan yanayin. Ga shi ya k'i yarda na taimake shi, tunda ni kullum kasuwancina tamkar ba iya mutane ne suke zuwa mini kitso da lalle ba. Saboda yadda Ubangiji ya ba ni jama'a. Tunda kayan abincinmu suka k'are kullum cikin dirka mana garin rogo ko wainar fulawa yake. Tausayi yake ba ni saboda gaba'daya ya zama desperate kullum cikin yawon neman abin da zai yi yake. Wani lokacin na ga ya fita da takardunsa, wani lokacin idan ya fita tun safe sai azahar zai dawo, haka kuma yake dawowa sai dai na gan shi da garin rogo da siga a leda. Ni kuwa sai ya bani filawa a farar leda ya ce ki yi abin da zai samu da ita, ki mini hakuri dan Allah" Rannan na gaji da bin ra'ayinsa muna kwana da yini cikin yunwa. Na ha'da kan ku'din da na samu na kwanaki biyu na rubuta koamai da nake bu'kata a takarda na bawa almaajirina na ce ya je ya ce nawa ne kudinsu. Jimawa ka'dan ya dawo ya ce "Wai dubu sha bakwai da dari shida". Na kirga na ga har da canjn dubu uku ya rage mini. Dan haka na cire canjin na ba shi ya tafi ya karbo mini. Na duba na ga komai ya cika. Na kinkima na kai kicin na shiryasu. Na ba shi gudar dubu akan ya siyo mini gawayi rabin buhu, da kuma danyar kubewa. Domin na tsani siyan abu dan tsurut a leda kullum. Ina da gas amma na bar shi sai iya da safe zamu dinga amfani da shi. Ya siyo mini bushasshe kuma manya dan jos haka ma kubewar. Na ce "To je ka dawo anjima ka'dan." A lokacin kuwa yammaci ne sosai. Dan haka na ha'da wuta na dora tuwon garin masara wanda yana cikin siyayyar da na yi d'azun. Na gama na kwashe na mayar da miya. Magariba tana yi ina kammala wa. Sai da na yi sallah, na yi wanka sannan almajirin ya dawo. Na zuba masa ya tafi. Sai ga Tijjani ya dawo. Ya kalle ni na ci kwalliya ko'ina kamshi ke tashi. Ya kalle ni da alamun tausayi ya ce "Sannu da gida. Ya mik'o mini ledar hannunsa wacce awara ce. Na kar'ba tare da godiya. Na tashi na gabatar mana da abinci, na zuba mana a plate guda. Na ce "Bismillah". Ya girgiza kai ya ce "Na gode". Na zuba masa ido murya na rawa na ce "Ba zaka ci ba, bayan na tabbatar da yunwa a tare da kai! Da rauni sosai ya ce "Ni ni ne mai ciyar da ke, ba wai na zauna ki ciyar da mu ba". Na tashi na koma kusa da shi na ru'ko dukkan hannuwansa na sassauta murya na ce "Ba ciyar da mu zan yi ba. Ubangiji zai buda maka k'ofofin da zaka samu ka sauke nauyin rik'on iyali tunda shi ya wajaba maka. Kana kuma da niyyar yi d'in. Abin da nake so ka fahimta ko aure bai ha'da mu ba, ai jini ya ha'damu. Ko ina wani gidan idan ina da ikon kula wa da iyalinka ai zan yi, bare kuma ni ce iyalin naka, to mene ne amfanin sana'ar da ka bar ni nake yi alhalin ba zata yi maka rana ba?" Ya yi shiru bai ce komai ba, na sake sassauta murya na ce "Dan Allah ka yarje mini na yi iya abin da zan iya yi". Ya saki gauron numfashi ya ce "Idan na amince ya tabbata dai da aka ce ke ce zaki ciyar da mu Asiya. Shike nan zan rasa yancina na mai gida, shike nan zan zama mata, ke ki zama mijin". Ya fa'da murya na rawa ainun. Na durk'ushe a gabansa na ce "Wallahi ba zaka zama ba. Yadda muke hakan zamu cigaba da tafiya kai ne miji. Ni ce mata, zan dinga karban umarni daga gare ka, abin da kake so hakan za'a yi.". Ya yi shiru yana nazari bai ce komai ba. Na matse hannunsa na ce "Pls mana" cikin sigar shagwaba. Ya zuba mini idonsa da ya kad'a sosai ya ce "Asiya zuciyata ba zata nutsu ace kina siya mini abinci a gidan nan ba. Gara dai ki bari na dinga baki abin da aka yassare mini, idan ma zaki kara da abin da kike so to bazan hana ki ba, tunda ban wadatar da ke ba. Amma ni kada ki yi da ni. In sha Allah ko da bashi ne dai bazan kasa baki abin da zaki saka wa ba'kin salatinki ba. Sai idan kin raina". Na kalle shi na gane da gaske yake yi. Na yi k'asa da murya na ce "Anya kasan kalubalen da yake tare da cin bashi kuwa mussaman a waje? Kawai ka yi hakuri tunda dai Ubangiji ya baka matar da ya bata sana'ar hannu mai k'arfi. Ina fatan Ubangiji ya kawo maka aiki ko sana'ar da zaka dogara da ita." Ya girgiza kai tabbacin bai gamsu ba. Na ce "To shike nan ka dinga karban bashin a wajena." Ya gyara zama ya ce "Nawa kika kashe a hidimar tuwon?" Na ce "mu je kicin a lissafa. Ya mike muka je. Na nuna masa komai da aka siyo wanda a k'alla zamu kai wata muna ci a talau ce. "Nawa kika kashe a wannan siyayyar? Na ce dubu sha bakwai da dari shida na. Sai gawayi na dubu daya." Ya ce "To kub'ewar fa?" Na ce "A bar wannan". Ya girgiza kai. Da sauri na ce "Ta naira dari ce." Ya ce "Sha takwas da dari bakwai ke nan ko?" Na ce "Eh" ya ce "In sha Allah zan biya ki, matu'kar ina shakar numfashi." Muka koma falon muka ci abinci ina ta yi masa hira dan ya ware sosai. Wannan kayan abincin da muke da shi sai ya rage masa damuwa mai yawa. Duk da hakan kuma bai yarda ya zauna a gida ba. Kullum sai ya fita. Rannan ya yi sa'a ya samu hada saltelite har gida uku. Da k'arfinsa ya dawo ya mik'o mini dubu biyar ya ce "Ga shi, na rage miki bashin ki. Ya fita ya dawo da leda mai d'auke da soyayyen kifi. Na kar'ba tare da addu'ar Allah ya kara budi. A wannan tsukun gaba'daya a takure nake domin maimakon na samu ninkin tattalin da yake yi mini kafin mu shiga tsananin da muke ciki. Sai ya zamana ni ce nafi rawar kai a kansa domin dai na samar masa nutsuwar shine mijin. Tunda na lura yana kame wa ne dan kada na samu dama a kansa. Na dinga mamakinsa domin gaba'daya ban yi zaton zai mini kallon zan raina shi dan ya shiga halin babu ba. Ya takura kansa sosai, komai kaffa kaffa yake yi. Idan na yi kamar zan yi masa magana sai na ha'diye. Na dinga hakuri ina lallabawa ina binsa a hankali. Hidimar da ta karu a kaina sai ya zama ina ta kokarin fa'dada kasuwancina. A dalilin an kawo wa Tijjani takardar biyan ku'din gida tun kwanakin baya. Na fara tunanin yin Home service domin na samu na tara masa ku'din kafin lokacin da suka diba mana ya cika. Na kalli yatsun hannuna guda biyu gold ne. Daya na wajen kwamishina ne, dayan kuwa da sana'ar tawa na siya. Jiya na bashi daya na ce ya siyar ya biya ku'din ya ce "Ba ya so, kada na sake na siyar da kadarata akan al'amarin da ba hakkina ba ne. Idan kuma na siyar to ba zai karba ba. Da zai fita na tambaye shi zan fita, zan je bayan layinmu. Bai hana ba. Tunda na fita da hantsi ban dawo ba sai yamma lis tunda asabar ce ban cika samun k'unshi a ranar ba sai kitso. Na dawo na tarar da shi a gida. Ya gyara ko ina. A falo na tarar da shi yana kallo. Na yi masa murmushi ya mayar mini a gajarce. Ya kalle ni ya ce "Daga ina kike na ji sai k'amshin muhallibiya kike yi" Zuciyata daya na ce "Wallahi lalle na yiwa wata babbar mace da ahalinta zasu je biki Abuja. Na fito da kudina dubu sha biyar na ajiye masa na ce "Idan Allah ya yarda a satin nan zamu ha'da ku'din da zaka biya gidan". Ya zuba mini ido galala sai kuma ya kad'a kansa ya ce "Babu laifi". Ni ban kawo komai ba. Na tashi na yi kicin da nufin dora girki. Sai na tarar da ya girka ya juye a flask. Ga shi ya mayar da ruwan wanka kan gawayin. Na bu'de na ga ya yi zafi ainun. Na dauko babban flask din da nake zuba ruwan zafi na cika shi. Na ajiye sannan na juye ragowar na shiga wankan. Sai da na shirya na ha'da Mana abincin na kai ina cewa "Yau dai ka zama Yabi, na dawo na tarar ka yi komai sannu da kokari". Ya sake yi mini wani irin kallon da ban gane ma'anarsa ba. Duk da dai yanzu ya canja amma ba musguna mini yake ba, kawai walwala da sukuninsa ne suka ragu, sannan yana yawan yi mini abubuwan da suke kona mini rai ta hanyar shata layi da abin hannuna. Na kalle shi na ce "Sauko mu ci to". Ya girgiza kai ya ce"ci, ni ba yanzu zan ci ba". Na marairaice na ce"To zo ka dinga bani a baki na gaji sosai Wallahi". Ya sake kafe ni da kallon da yafi wadanda ya yi mini. Bai kuma ce komai ba. Na rasa gane manufar hakan sai kawai na fashe masa da kuka mai tsananin gaske. Ya taso ya zauna kusa da ni ya ce "Me na yi miki zaki yi mini irin wannan kukan?" Da kuka sosai na ce "To akan me zaka dinga yi mini kallon tuhuma? Akan me ba zaka zo mu ci abinci tare ba? Na riga da na gane ka tunda ka fahimci na fara sonka shikenan ka nade kafar wando fara yi mini wula'kanci kala kala". Ya matso jikina sosai ya kwantar da ni a kirjinsa ya ce "Da gaske kina sona Asiya?" Na ture shi na zum'bura baki na juyar da fuska gefe. Na kasa bu'de baki na ce uffan. Ya saki gauron numfashi ya ce "Shikenan na daina yi miki wula'kanci, duk da nasan ba na yi din". Da kansa ya zuba mana abincin. Lokaci zuwa lokaci kuma zai debo ya bani a baki. Ko ruwa da ya bula ledar bai sha ba, bakina ya nufa da shi. Na zuke tas na bar masa leda a hannu. Sai wani ya bu'de. Da yake ina siyar da pure water, saboda masu zuwa lalle kawia na tsiri siyar wa kuma sai nake yin ciniki sosai. Na yi gyatsa "Na yi hamdala. Gaba'daya sai jikina ya mutu murus gajiya ta taso mini, ba abin da nake so irin na kwanta na yi barci. Ga shi maghariba ta kawo kai. Na kalli agogo na ga za'a kai minitina arba'in da biyar kafin a kira sallah. Na mik'e na kwashe kwanukan, na hau zaga tsakar gida dan abincin da na ci ya dai-daita. Na koma falon na kwanta a kujera na yi daidai iskar fanka na kad'a ni. Ya taso ya fara bin gabbobina yana dannawa sannu a hankali nake jin da'di a jikina. Ban ankara ba sai kawai ya sure ni yana cewa "mu je daki na wartsake miki gajiyar gaba'daya. Na fara shure shure shi kuma ya ri'ke ni gam. Fadi nake yi "No bazan yarda ka dora mini wata gajiyar ba gaskiya". A kunne ya ce "Amma kinsan na ce idan kina yin gardama komin kankantar ta cikin ba shiga zai yi ba". Nan da nan kuwa na yi muk'us domin har zuciyata so nake na ganni da ciki, so nake na ganni da baby a hannuna kamar yadda nake ganin su Ubaida. Har aka fara kiran sallar Bai samu nutsuwa ba. Kan dole ya tsallake ya bar ni. A gurguje ya yi wanka ya nufi masallaci. Ni kaina a dole na sake wanka na sauke farali. Yau da wuri muka kwanta domin ana idar da sallar isha da ya shigo ya rufe gidan, ni dama a kwance ya tarar da ni. Sai da ya karasa abin da bai ida ba sannan muka yi wanka, muka kwanta wajen tara da rabi. Washagari lafiya muka rabu, da zai fita na ce "Idan fita ta kama ni zan fita. Bai ce komai ba, ni kuma ban yi zaton bai amince ba. Da yake na dora cewar na fara Home service akan status dina. Sai kuwa na dinga samun k'ira akan ana bu'kata ta a wuri kaza. Na za'bi gida biyu, na bawa guda biyu hakuri akan wasu sun rigasu. Na kammala gyaran gidan tsab. Na fice. Wannan ranar har dare sannan na koma gida. A k'ofar gidan na tarar da shi, cikin wani irin yanayi. Yana ganina ya zabura ya mik'e. Ni kuma ganin a waje muke yasa na zarta shi na shige. Sai kawai na tarar da k'ofar tamu da sabon kwad'o. Na jinkirta amma bai shigo ba. Na gaji da tsayuwar jiransa. Na fara hassala ya gan ni amma ya kasa shigowa, yasan kuma ya canja kwad'o. Na gaji na fita na tarar da shi yana zaune tamkar dutse ko motsi ba ya yi. Na ce "K'ofar a rufe take fa". Ko kala bai ce ba. Na sake fusata. Na ce "Ka zo ka bu'de mini". Nan ma tamkar da Dutse nake magana. Allah yasa ma babu kowa a wajen. Zuciyata ta hauro matu'ka da gaske. Duk fa'din tashin da nake yi dan asirinsa ya rufu shi bai ga hakan ba. Murya na rawa na ce "Ni kake yiwa wula'kanci haka?" A fusace ya ce "Wace ce ke? Gida ne bana bu'katar ki a cikinsa ba, ba sai ki koma inda kika fito ba, kin ga kin yi maganin wula'kancina, nima na huta da rainin da kike yi mini". Jikina ya yi matu'kar sanyi, hawaye ya b'alle mini. Murya na rawa na ce yanzu a daren kake so na tafi gida?" Shima murya na rawa ya ce "Ai ni a daren kika dawo mini gida. Dan haka ki koma inda kika fito ko ki je inda zaki, ai dai babu sisin ki wajen kama gidan har yanzu, bare ki yi mini sabon isgilanci". Na fara kuka na ce "Na rantse da Allah Tijjani kai bahago ne na k'arshe. Duk tunanina mu ha'du mu rufawa kanmu asiri wani bai ji ko ba'a gane halin da muke ciki ba, amma gaba'daya ka murde ka canja, ka ki da'din azanci. Dan Allah ka fahimce ni, nifa ba jin da'din yadda kake yi nake ji ba". A tunzure ya ce "Yo dama ni ina da abin da zan jiyar da ke da'di ne?" Na yi sakare ina kallonsa gaba'daya ya juye ya koma wani azababben mutum. A hankali na ce "To zo ka bu'de mini, tunda dare ya yi." Ya girgiza kai ya ce "bana son ganin ki a cikinsa." Na juya na ce "Shike nan na gode". Na fara tafiya ni kad'ai ga shi wajen ba kowa, tsoro ya kama ni, da na ji kamar ana bina. Sai da muka iso wajen hasken solar na juya sai na ga shi ne yake bin bayana. Na tsaya na ce "To mene ne kuma, ba dai ka kore ni ba?" Da sanyin murya ya ce "Bakin titi zan raka ki, kada karnu ka su biki". A tunzure na ce "Allah yasa ma kuraye su kama ni, su cinye ni! Bai ce komai ba, har muka isa inda zan bi na yi gida. Na kalle shi na ce "Yanzu me kake so na fa'dawa Baban Marina?" Kai tsaye ya ce "ki fa'da masa gaskiyar abin da ya faru kawai". Na marairaice na ce "Tunda har ka rako ni nan, nasan ka huce, mu koma gida ka fa'da mini abin da na yi, ba sai ka ce na baka hakuri ba, zan nemi afuwarka". Ya girgiza kai ya ce "A a bana bu'katar ki a gidan ne, ki je gida, ko ki je ki kwana a wajen neman ku'din ki". Ganin zai sake tunzura da yawa yasa na tafi din. Amma tafiya kawai nake yi, bana ko sanin inda zan jefa k'afata. Tashin hankalina ace na je gidan Marina da sunan bacin rai. Na sani masu murnar ganina sai sun fi masu yin jajjabi yawa. Kuka nake yi sosai. Me zan cewa Baba da Gwaggo ni Yabi? Ko Ubaida k'aramarmu ba'a taba tura ta gida da sunan ta yi laifi ba sai ni? Ni kuwa dama akuyata ta yi shura. Ina ganin hanyar da zan bi na isa gidan, amma sai na bi wanda zata kai ni gidan Yaya Ummi. K'arfe tara da rabi na shiga d'akinta tamkar jifa. Cikin sa'a mijinta ya je Jos d'aurin auren yar kaninsa sai gobe litinin zai dawo. Ganina a wannan daren ga kuka ina yi, duk sai ta diriri ce ta dinga fa'din mene ne, daga ina kike?" Ina kuka, na fa'da mata Tijjani ne ya ce "Bazan shigar masa gida ba." Ta dauki salati ta ce "To ke da ina kika je?" Na fa'da mata gaskiya. Ta yi shiru ta ce "Tsakani da Àllah laifinki ne Yabi. Tunda bai amsa miki ba, ai kinsan ba wai yana so ba ne. Sannan me yasa kika yi dare har wajen tara?" Na yi shiru sai kuka kawai nake yi. Domin tskani da Allah ban san ina son Tijjani sosai ba sai yanzu da ya yi min irin wannan hukuncin. Ji nake kamar na yi ta zunduma ihu har kowa ya fahimci rad'ad'in da nake ji. Baya ga haka kuma fishin da na ga ni shinfide a kan fuskarsa ya sake dagula mini lissafi. Cikin kuka na ce "Ni bana son na je gida Yaya Ummi. Baba fishi zai yi da ni, haka ma Gwaggo. Ga magauta su tasa mu gaba da dariya da zunde". Ta nisa ta dauki k'aramar wayarta ta ce "ku'din ciki babu yawa, amma bari na gwada na ga ni. Bugun farko ya dauka tamkar me jira a k'ira shi. Ta gaishe shi da walwala. Sai kuma ta ce "Yaya Bulkachuwa sai ga Yabi ta zo mini a wannan daren, kuma abin mamaki ta ce wai kai ne da kanka ka koreta, ai da sai ka yi hakuri da safe ka tura ta gidan." Dake a sifika ta saka sai na ji ya ce "Na kasa yin wannan tsinkayen Ummilolo. Amma yanzu taimake ni ta kwana a gidan ki, gobe sai ta wuce gida". Da sauri ta ce "A a kasan ni dakina daya ne. Zan dai rako ta, ko mene ne da safe zan dawo mu tattauna tunda dare ya fara yi". Ya yi shiru tabbacin bai gamsu ba. "Ka yi shiru Yaya Bulkachuwa". Ya ja gauron numfashi ya ce "Kunyar ki nake ji ne Ummilolo. Kada ki shiga wannan maganar. Ba ke ce zaki yi alkalancin nan ba. Domin ban dauki al'amarin da sau'ki ba". Ta sassauta ta ce "Ai tunda na gan ta na sani baka dauke shi da wasa ba. Amma tunda na yi maka waya ai sai ka mini lamini tunda ni da kai ai kasan tun fil'azal bata b'aci." Ya ce "To shike nan". Da walwala ta ce"Yauwa Yaya Bulkachuwa rabin raina na gode". Daidai lokacin kuma ku'din wayarta ya k'are. Ta ce "Ai bu'kata ta biya." Kafin ta yi mini magana, sai ga shi ya biyo bayanta. Tana dauka ya ce "Yi zaman ki Ummi ai ba zai yiwu ki fito b'akatatan a wannan lokacin ba. Bari na wakilce ki, na zo da kaina. Amma ki fa'da wa mijinki gobe, ki zo mu zauna". Ta ce "Na kuwa gode! Gobe da ikon Ubangiji da wuri zan zo". Ya ce "Na gode, ki gaida yaran namu". Ba a wani dauki lokaci mai yawa ba, sai ga shi ya k'ira ya ce ya zo. Ta raka ni har soron gidan sannan ta juya tunda k'ofar gidan nasu tamkar kasuwa yake shaguna ne reras gefe kuma teburan masu sayar da nama na gaba kuma masu kayan miya. A mashin dinsa ya zo. Na haye ba tare da na ce komai ba. *End of part 2.* *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *08089965176* *07084653262* *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES.* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *08089965176* *07084653262* Har muka isa gidan ba wanda ya yi magana. Kai tsaye daki ya shige ya yi kwanciyarsa. Ni kuma na shiga kicin na sama wa kaina abin da zan ci. Sannan na yi wanka. Na gyara jikina sosai, na isa dakin na tsaya gaban madubi na bi ko ina na goga turare. Na tarar da shi idon sa biyu. Na zauna na tausasa murya na ce "Fa'da mini abin da na yi, mu shirya kafin Yaya Ummi ta zo". Ko motsi bai yi ba, bare ya yi magana. Na zuba masa ido ina tuna yadda yake rawar jiki da tsoron fishina. Amma tunda ya fahimci na fa'da komar sa shikenan abu ka'dan zai fitittike ya yi mini fishi. Na kai hannu na fara shafa sumar kansa da nufin lallashi tunda na gane shi mutum ne mai son a rarrashe shi tamkar mace. Da kakkausar murya ya ce "Bari Asiya Toro". Nan da nan kuwa na cire hannun nawa domin gargadi ya yi mini mai kauri. Haka muka kwana duk rai babu da'di. K'arfe takwas sai ga Yaya Ummi da alamu tare suka fito da yaranta yan makaranta su suka wuce ita ta taho nan. A falo muka zauna. Ita ta fara ce wa Yaya Bulkachuwa ka ga yadda ka koma kuwa me yake faruwa ne?" Ga mamakina yana bu'de baki sai ce wa ya yi "Ba'kin cikin Asiya ne yake neman kassara ni". Gabana ya takarkare ya fadi. Me nake yi masa ni Yabi?" Yaya Ummi ta ce "me ya faru haka Yaya Bulkachuwa?" Na kasa kunne sosai dan na fahimci abin da zai ce da kyau. Sai ji na yi ya fara rattabo laifukan da nake yi. Cikin nutsuwa ya ce "Ummi tunda aka rufe gidan burodi da nake zuwa na shiga yanayin rashin ku'di. Har ta kai bana iya yin abin da ya kamata. A farko rimi rimi Asiya ta ke ha'kuri da duk abin da zan kawo. Tare zata sarrafa mu ci, ko da garin kwakai ne. Amma tafiyar bata yi nisa ba sai ta fara gazawa. Ta fara raina kokarina saboda an riga an cusa mata akidar watarana ita ce zata rike mini gidan. Komai zan siyo na bata ba zata yi amfani da shi ba. Kwanaki na siyo sabulun wanka Gif har yau bata ta'ba ba, ta bayar an siyo mata wanda ya dace da ita. Duk ban ce komai ba. Sai shekaranjiya kuma ta ce mini zata fita, ban zaci wai gida gida zata dinga bi tamkar dilalliya ba. Tun safe da ta fita sai yamma lis ta dawo wai ashe gida je ta dinga bi tana yin k'unshi ana biyanta saboda kawai ta fahimtar da kowa ita ce take ri'ke da ni! Ya nisa ya zarce da fa'din tana shigo wa ta tarar na yi komai Kamar yadda ta sani tun farko ni aikin gida bai zame mini komai ba, amma kinsan me ta ce mini?" Yaya Ummi ta girgiza kai cikin sanyin jiki. "Tana bude baki sai ce mini ta yi wai na zama Yabi. Wato na zama mace mai zaman gida, ita kuma ta zama namiji mai fita ya yi gwagwarmaya. Duk yadda maganar ta buge ni hakan na daure na ha'diye maganar na kawar mata da kai! Ya fa'da yana hucin b'acin rai. Gaba'daya jikina ya mutu, zufa sai keto mini take yi. Na tabbatar duk abubuwan da ya lissafo ina yinsu tabbas. Amma ko ka'dan a zuciyata ban daukesu zasu b'ata masa rai ba. Domin ko ka'dan ban yi da nufin wula'kanci ko na muzanci ba. Asalima ni na yi ne da nufin kyautatawa. Kafin Yaya Ummi ta ce komai sai ya cigaba da fa'din "Jiya kuma ta ce mini zata fita ban amsa mata ba. Sai kawai na dawo na tarar bata gidan, tun azahar nake zaman jiranta bata dawo ba sai tara saura. Fa'da mini Ummi me ta mayar da ni, me kuma take nufi da ni ne?" Yaya Ummi ta yi shiru ta rasa abin fa'da domin ta fahimci ransa ba k'aramin baci ya yi ba. Sai kawai ta buge da ba shi hakuri tare da ce wa"Tabbas ta yi kurakure, amma ka yi hakuri zata kiyaye." Ya girgiza kai ya ce "Ba fa zan yi hakuri ba tunda ba zan dauki wadannan BAK'AK'EN TA'ADODIN da ta fara tsirarsu tun daga yanzu ba. Gara manyammu su san halin da muke ciki kada abu marar da'di ya faru ace na bawa marar d'a kunya." Yaya Ummi ta yi maza ta ce haba dai, haba dai Yaya Bulkachuwa ba abin da zai faru sai alheri. Ai gata nan duk ta ji abin da ka fa'da, za kuma ta kiyaye." Ya girgiza kai ya ce "Kin san kafiyarta, ba ji zata yi ba, ni kuma ba zan yarda ba. Kin ga gara komai a yi shi a bayyane ba sai abu ya yi tsananin da rayuka zasu baci da yawa ba". Ni gaba'daya ma mamaki ya ba ni, ya fitittike akan sai na tafi, ita kuma Yaya Ummi sai wani lallab'a shi ta ke yi. Yo ni ban da ina jin tsoron al'amarin da zan fuskanta a gidnman Marina ma zunde da dariya, da ba'kin cikin da zan jefa iyayena da na girgije na bar masa gidansa. Ta kallo ni tare da mini signal din na ba shi hakuri. Na dauke kai na juyar da fuskata. Domin nima na hauro ai komai nake yi dominsa ne. Amma tunda shi ba zan yi masa alheri ya yaba ba, sai dai ya bini da sarhutu to shi kenan na daina yin komai. Fita k'unshi da sunan Home service kuwa na soke sai ya nemo wani laifin kuma. A k'asa zuciyata kuma sai hirji nake yi tare da fatan Yaya Ummi ta kashe wannan matsalar domin duk yadda na hauro nake kurarin zan iya tafiya din, zuciyata tafi son zaman, nafo son ya huce ko ba dan ahalin Marina ba. A karan kaina na damu da fishinsa. Da k'yar Yaya Ummi ta shawo kansa ya ha'kura da maganar sai mun je gaban Baban Marina. Ta bu'de murya ta ce "Ki ba shi hakuri". Fuska a daure, amma cikin azama na ce "Allah ya baka hakuri". Daga haka na tsuke fuskata da bakina. Tare muka karya da ita. Sai da zai fita suka tafi tare ya sauke ta a gidanta. Ban zauna ba sai da na yi abinci na zuba a flask. Na gyara ko ina, sannan na fara yiwa wata da ta zo k'unshi. Bai dawo ba sai yamma, kafin lokacin kuwa na yiwa mutum hudu duk sun tafi. Budurwa d'aya ce ta rage da yake ita zan mata bak'i da kuma kitso. Da azama na saki kitson na fita ina yi masa barka da dawo wa, domin ya tsani ya dawo ban bar abin da nake yi, na je gare shi ba. Idan wani ne ya fa'da mini Bulkachuwa zai dinga yi mini irin wannan mulkin mallakar zan k'arya ta shi kai tsaye. Ni da kaina mamakin kaina na ke yi. Na yadda nake rawar jiki a kansa. Wata'kila kuma yadda yake sarrafa ni ne sirrin. Gabadaya tsoron fishinsa nake yi tamkar me. Ya mik'o mini ledar hannunsa mai dauke da karas da atile. Hannu biyu nasa na kar'ba na dinga fa'din "Na gode, Allah ya k'ara budi.". Na wanke hannuna, na yi kicin na ha'da abincinsa na kai masa. Na debo pure water masu sanyi guda biyu na saka a plate. Na ajiye a gabansa. Na fita na debo masa karas da atilen na zuba a bowl na wanke na kai gabansa. Na dan yi jim na kalle shi yana cin abincinsa cikin nutsuwa. A hankali na ce "zan je na k'arisa kitso." Da walwala ya ce "To". Na fita, a raina kuwa sai fa'din nake yi sarkin son mulkin tsiya. Kai Tijjani baka bai ni haka ba, Yasin" Da daddare ya dinga laluba ta, na maze ban yi masa abin da nake yi masa ba. Ya fara ce wa "Amma dai kin san bana son haka, sannan kuma kin san kin ci bashina jiya". Da sauri na ce "Ba wani bashin ka da na ci. Kai ne ka kawar da kai, alhalin ka ce ko mun yi fa'da kada mu saka aurenmu a ciki. Amma jiya sai da ka saka su tsundum." Cikin kwantar da murya ya ce "Hankalina ne ya tashi matu'ka da gaske. A ce matar aurena tana garanranba a gidajen mutane har almuru da sunan sana'a? Ai k'arshen tozarci ke nan. Amma ai na ha'kura kin san ina sonki fiye da komai Asiya. Ban so wani abu a duniyar nan da ya zarta ki ba. Uwa da ubana ne kawai a gaban ki. Dan haka ki daina damun kanki akan wasu matan. Ba sonsu nake yi ba. Da gaske ba wacce nake so a zuciyata sai ke. Amma zan iya ganin wata ta burge ni ko ta bani sha'awa a dalilin Ubangiji ya sanya sha'awar mace sama da d'aya a zuciyar mazaje. Kullum ina ro'kon Ubangiji ya tsare ni da sha'awar wata macen fiye da ke. Duk sadda na ga wata zata burge ni ko ta ba ni sha'awa gida zan garzayo na ga halalina, na yi abin da nake so da ita. Ke dai idan kin gan ni afujajan na dawo miki, to ban da musu da bijire wa da sunan jan aji". Dan haka ki saki ranki da ni, ke nake so, ke ce halaliya ta, da ke nake fatan na rayu muddin rai". Na fara k'ananun hawaye na ce "To kuma nufinka korata da ka yi da daddare a ganduna ne? Ya tafi a bilis?" Ya tarairayo ni cikin rad'a ya ce "Ai ya wuce tunda da kaina na je na dawo da ke". Na fara turza k'afa ina fa'din "Alkur'an ban yarda ba". Ya sheke da dariya ya ce "Dole sai kin nuna mini kina da alaka da mutanan Gwaram da Birin kudu domin a bakinsu nake jin wannan rantsuwar". Na ce "To mahaifiyata ta fito daga yankin ai kuwa kasan jininsu ce". Ya ce "Haka ne. To yanzu me zan yi ki yarda ki huce". Na shiru ina tunani sai kawai na ce "Yi mini kukan zakara". Ya ce "kukan sa wanne a ciki?" Na ce "oh kukan zakaran kala kala ne?" *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. Ya ce "Yana cara idan afijir ya keto, yana yi yayin kiran sallar farillah akwai kuma wanda yake yi idan ya ga kaza yana kyarkyarar ta, yana hilar ta dan ya samu hadin kanta". Kunya ta kama ni na ce "Yi mini wanda yake yi idan alfijir ya keto kawai". Ya kuwa ce "Alkur'an ba shi zan yi ba tunda ni ma yanzu kyarkyarar ki nake yi". Kafin na ce komai ya tak'arkare ya fara wani irin gurnani yan kur kur sai ya kuma ya yi cara tamkar dai zakaran gaske kafin na ankara ya turmushe ni irin yadda zakara yake dank'ar kaza. Washagari da walwala muka tashi ya dawo Tijjanin da yake kaffa kaffa da ni. Sai ririta ni yake yi. Komai shi ya yi har abin karyawa. Na kalle shi cikin nutsuwa bayan ya d'ora ni akan cinya yana shinshinata tamkar maye. Na kama gemunsa na ce "Wannan shine .... d'ina. Amma ba shine na jiya da shekaranjiya ba". Dariya mai yawa ta k'wace masa ya ce "sabo da Allah little mene ne wani dash dash? Ki ce Tijjanin da kika saba fa'da mana tunda har yau ba ni da k'imar da za'a sakaya mini suna". Na yi murmushi na ce "Ai tunda na yi al'kawarin sai na haihu da na saka maka suna, to fa sai na haihun. Idan ka matsu kawai nan da sati na fara amai, ka kai ni asibiti ana gwada ni ace ciki ne, tun a ranar zan fara fa'din sunan na ka". Ya kankame ni sosai yana dariya kwarai da gaske. Ya ce "Nan da shekaru goma masu zuwa zan tisa ki a gaba ina miki bitar wadannan kalaman a lokacin kin kai ashirin da bakwai. Na ce "ko zuwa lokacin y'ay'a nawa na haifa?" Ya zuba mini ido ya ce "Allah yasa sun kai uku" Na ce "Haba dash dash ina laifin hudu ma. Nifa ina son yara da yawa." Ya yi kissing din goshina ya ce "Allah ya bamu masu albarka. Nima ina so. Amma kin san dole control zamu yi bazan yarda ki tara yara da yawa ki man ce da sha'anina ba". Na yi k'asa da murya na ce "Kai ne fa bebina na farko ta ya ya zan mance ka? To ko y'ay'a dari na haifa kai ne a gabansu. Ni burina na haifo mai kama da kai ma". Nan da nan kuma sai na rufe fuskata alamun kunya ta rufar mini. Shi kuma da'din kalamaina ya yi matu'kar kama shi. Ya samu nutsuwar da gaske ina sonsa yanzu. Ya rungume ni tsam tsam ya kasa cewa komai. Ya sakar mini nishin da yake rura mini jiki. Ya ce "Ni kuma na fi son ki haifo mini little girl mai kama da ke. Amma ba mafad'aciya irin Asiya Toro ba". Na cuna baki na ce "Yo ai ni fa'da na sai an tab'o ni". Ya ce "Amma Asiya ai ni bana tab'o ki kike rikice mini. Yanzun nan zamu rabu k'alau. Idan na dawo sai na ga kina share ni, ko mu yini lafiya, idan mun kwanta ki hau buge mini hannu kina ture ni. Haka ake yi?" Na ce "Amma ai sai ka dade baka dawo ba ne, nake share ka. Zuciyata tana harbawa da k'arfi tare da raya mini tadi ka tsaya yi". Ya dad'a ruk'o ni sosai cikin rarrashi ya ce "Shaid'an ne yake wasa da ke Asiya. Kuma dai ai babu kyau a yanke wa mutum hukunci da zato. Ki dinga sassauta mini, da gaske bana son fishin ki, bana son mu dinga fad'a". Na dauke kai bayan na tura baki na ce "Ai kai ne, kake murde mini tunda ka fahimci ka fara shiga raina. Idan ba wuta wuta nake yi maka ba, ba k'aramin jana zaka yi a k'asa ba." Ya kwashe da dariya mai tsananin gaske. Ya ce "Asiyaty an buga an bar ki. Wato da iron hand zaki yi handling d'ina." Na ce "Ai dama yaya Ummi ta ce "Nan gaba sai ka mini fiye da abubuwan da na yi maka. Ilai kuwa na fara ga ni. A buge wa Asiya baki. A zabge Asiya da mari. A dinga yiwa Asiya iyakar daki a gidanta. A rufe wa Asiya gida. Aka fitittke sai ta tafi gida. An fara jawa Asiya rai. Sai an jagwalgwalata sai a juya baya a ce sai ta bada hak'uri. An ki yiwa Asiya ciki. Idan Asiya bata saki lalle ko kitso ta taso ta yi barka da dawowa ba, a yi mata fishi. Asiya ba son a dinga gatsa sunan ta da na garinta take yi ba. Amma haka za'a daddage ana ce mata Asiya Toro. Ai Wallahi na yi laushi. Ina matukar hak'uri. Ban ma sake maka fuska gabadaya ba kake yi mini hakan ina kuma a ce lako lako nake?" Ya jima yana kallona da matsanancin mamaki. Sai kuma dariyar da bai shirya ba ta sake k'wace masa. Ya dinga yi, ni kuwa na ce "Yi dariyar ka son ranka. Allah ne ya ara maka dama. Ka zuba ruwa a k'asa ka sha. Ka same ni da yawa". Ai kuwa ya jima yana yi, sai ya yi shiru sai ya kalle ni ya ce "Ah aha". Ko ya ce ",Na k'i yi miki ciki ko Asiya?" Sai ya sake kyalkyale wa da dariya. Sai da ya nutsu ya ce "Little ki daina yi mini wuta wuta kin ji. Idan kina son ki damke ni, kawai ki kiyaye abin da bana so. Ki kuma dage wajen yin abubuwan da nake so. Ciki kuwa zan miki, ki k'ara hak'uri lokaci ne kin ji". Na ce "To! Amma kai ma kada ka sake ce wa na tafi gida. Ai kasan Baban Marina ba dad'i zai ji ba. Ni kuma magauta su tisa ni a gaba da habaici da gori." Ya kankame ni ya ce "Har abada ba zan sake ce wa ki tafi ba Asiya. Duk laifin da zaki yi mini kuwa. Matukar kin yarda na haramta miki zuwa gidajen mutane da sunan sana'a. Bana so, ba kuma zan dauka ba". Da azama na ce "Bazan sake yi ba har abada". Dad'i ya kama shi ya dinga kissing d'in kunne na, yana fad'in "I cherish you dear " *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* ✍️ *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* *Watanni shida a gaba*. Zuwa lokacin duk kaucen kaucen Tijjani na kada na shiga harkar ri'ke masa gida ta ci tura. Duk yadda baya son ya karbi ku'dina abin ya faskara domin samun ku'di ba k'aramin wahala yake ga talaka a wannan lokacin da aka janye tallafin mai a Nijeriya ba. Mafi yawa masu kananun sana'u sun shiga halin ni y'asu bare kuma wanda sana'ar sa hab'o ce ma'ana sai an samu za'a yi. Duk da k'arancin shekaruna na fahimci matu'kar Tijjani zai fita ya dawo gida ba tare da ya ru'ko wani abu komai kankantar sa ba, to kuwa a wannan ranar ba zan gane kansa ba. Duk yadda zan yi masa rawar jiki da haba haba dan na samar masa da nutsuwlar bai gaza ba, ba kuma laifi ba ne dan ya fita ya dawo bai samo wani abu ya kawo mini ba. Kullum sai na fa'da masa cinikin da nake yi da nake samun makudan k'udade na yi imani mafita Ubangiji ya kawo mana, domin ba ni ka'dai ba ce wacce ta iya lallai a garin Toro. Amma duk macen da ta tunbatsa, duk macen da ta isa ko ta kai ta kawo to kuwa wajena take yin k'unshi da kitso. Sannan mafi yawa basa ba ni adadin ku'dina sai sun yi mini k'ari. Idan ya bu'de baki sai ya ce "Ko ke ce Zainab Shamsuna ai ba'a ce na zauna na nad'e k'afar wando ki yi mini komai ba. Ubangiji ya ce na ciyar da ke, na tufatar da ke gwargwadon k'arfina." Na nisa na ce "Haka ne! To a maimakon ka dinga tayar da hankalinka, nima kana tayar mini da nawa. Mu yi wata ka'ida mana". Ya zuba mini ido yana saurarona. Na ce "Ka dinga siyar da lalle da mahallabiya da salatip. Ni kuma sai na dinga siya a wajen ka. Pure water ma da nake siyar wa sai ya koma naka ne zan dinga siyar maka". Ya ce na yarda zan siyar da lalle amma ba zan siyar da ruwa ba tunda ai fridge din ba nawa ba ne". Na ri'ke hannunsa na ce "Ashe kayana ba naka ba ne? Rannan a kunne na wata cikin y'anuwana take ta fa'din matu'kar mace da namiji igiyar aure ta zarge su ai komai da suke da shi ya zama mallakin junansu. Ta kalli idona ta ce mussaman idan ta haifa masa y'ay'a to ba wani sauran iyaka a tsakanin abubuwan da suka mallaka." Na nisa na ce "Kana nufin wannan yarfen da aka yi mini, ni da kai ba kamar sauran ma'aurata ba ne? Abuna ba naka ba ne. Kai ma abin ka ba nawa ba ne saboda ni ban haihu ba?" Na fa'da da rawar murya. Jikinsa ya yi sanyi ya janyo ni jikinsa ya ce "Kina dai son ki yi mini rikici ne little ban da haka menene abin kuka? Duka ma shekarar ki nawa ne? Ni fa a halin da nake ciki ma ban shirya karban bebi ba. Hidimar ki ka'dai tana gagarata ina kuma da jariririn da bai san babu ba. Amma idan haihuwar ta zo ina so, kawai dai zan so ace bebinmu sun zo a lokacin da komai ya dai-daita mini ta yadda zan musu hidima sosai". Na yi shiru na ce "Ka sare da yawa ne. Amma da sannu Allah zai kawo mafita." Ya saki gauron numfashi ya ce "Ai al'amuran k'asar ne ya lalace komai sai da hanya, hanyar ma sai ka biya makudan k'udade kafin ka samu aikin gwamnati." Na ce "Idan Allah ya k'addara abu rabon bawa ne komin tsanani sai ya same shi". Da haka na lallaba shi na samu kwanciyar hankali, domin ni rashin ku'dinsa baya damuna irin idan ya takure ya k'i sukuni. Nafi son soyayya, nafi son walwala. Bana kuma samun hakan sai idan yana kawo wani abu, domin ya riga ya k'yamaci ace ni ce nake ciyar da mu. Washagari da wuri ya fita. Bai dawo ba sai yamma lis. Wani abun mamaki da buhun sabon lalle irin mai L din nan ya dawo har buhu uku amma d'anye ne. Na kalle shi na ga ya yi laga laga. Tabbacin da kansa ya shiga jeji ya samo. Tausayinsa ya yi matu'kar kama ni. Hawaye ya cika mini ido, a zuciyata sai addu'a nake yi masa akan Ubangiji ya hore masa hanyar da zai ri'ke gidansa cikin sau'ki. Da k'yar na ha'diye kukan nawa na dinga yi masa sannu. Ya zauna akan baranda ya ce "Asiya na gaji sosai ga k'aya ta yi ta suka na." Da tausayi na ce "Sannu, Ubangiji ya baka lada, ya kuma sanya wa neman ka albarka." Na dauko masa ruwa ya sha. Na kalle shi ya yi kaca kaca da shi. Har kan gashinsa k'ura ne. Na ce "Bari na juyo maka ruwa wanka ga shi akan gawayi. Da kai ya amsa mini. Na sirka ruwan na kai masa bandaki. Ya shiga ya yi. Ya fito ya jika kayan da ya cire. Sannan ya shiga daki dan ya shirya. Kafin nan kuwa na Kai masa abinci falo. Na zuba omo na sab'e masa kayan na shanya masa. Ya fito ya ga ina shanya. Ya murmusa ya ce "Ni ina ce Asiya Toro ce ta ce Aji dawun ta yiwa k'ato wanki?" Kunya ta kama ni domin na sani tsokana ta ya yi, tare da tuna mini sababin da nake yiwa Nasiba idan tana yi masa wanki. Na dara na ce "Ai har yanzu ma ba zan yi ba, kawai na yi maka ne a matsayinka na mijina kuma bebina". Ya shiga falon yana ce wa "zo mu yi maganar a zaune". Yana cin abinci ina masa fifita. Ya ce "Da wayo da wayo dai so kike ki dinga ce mini Bebi ko?" Na yi gajeriyar dariya na ce "A a ai sunan ka yana zuciyata lokacin kawai nake jira. Amma kai kanka ai kasan bebi ne. Domin abin da kake yi mini ai bebis ne suke yin hakan. Ba dama ka kwanta sai ina kusa da kai. Ko juyi zan yi sai dai mu juya kwanciyar gaba'daya, saboda kana.." sai na kasa fa'da. Ya zuba mini ido ya ce "Fadi mana marar kunya. Me nake yi? Na daure na ce zuke wa bebis din da zan haifa mana abinsu." Ya murmusa ya ce "Ai ba nasu ba ne, nawa ne, idan sun zo dai zan dinga sammu su, idan lokacin shansu ya k'are za'a cire su, su bar mini kayana. Ni ai ba zaki taba yaye ni ba". Na yi dariya na kawar da maganar da ce wa "Wai da kanka ka je yago lallen ne?" Ya ce "Eh. Baban Marina na tambaya ko ina zan dinga samun lalle ina sara. Sai ya kwatanta mini yankin da Ubangiji ya azurta da lalle. D'an na goro ake bawa digacin yankin sai ka je ka yi ta yanka. Shine ma ya bani dubu guda duk da shima fama yake da kansa. Da naki karba kin ga b'acin ran da ya yi? Wai raina shi na yi, shi yasa nake ganin ba zai iya bani abu na kar'ba ba. Nasa hannu biyu na kar'ba ina ba shi ha'kuri, shi kuma yana ta yi mini fararen addu'oin da suka k'arfafa mini guiwa.". Na rausayar da kai na ce "Allah ya bada sa'a, yasa a fara a sa'a". Ya amsa da "Ameen Little". Kwanaki ka'dan lallensa ya bushe. Da kansa ya zauna ya gyara abinsa tsab. Ya ha'de su a buhu biyu. Ya fita da su, ni dai bansan inda ya kai ba sai gani na yi ya dawo da shi ya zama gari mai laushi ainun, kuma ya yi auki domin ba k'aramin yawa ne da shi ba. Ya kusa yin buhu guda. Ganin hakan sai na auni kwano biyu na zauna na k'ulle shi tas. D'aurin hamsin, da d'ari. Duk wanda suka zo k'unshi sai na yi musu tallan ina sayar da lalle, ina k'wabawa mutum yasa a gidansa. Nan ma sai Ubangiji ya sanya albarka domin duk sati sai na k'ulla kwano biyu, nima kuma a satin ina k'arar da fin kwano uku ma. Kafin ka ce miye wannan sai jarin Tijjani ya kafu ya samu na siyo mahallabiya da kwalin salatip. Duk sati kuwa zai je ya yago domin ya gamsu ba k'aramin rufin asiri hakan ya yi masa ba. Tunda duk sati zan ha'da masa ku'dinsa a kalla dubu goma. Idan ya kar'ba kuwa zai siyo kayan abinci da k'ananun abubuwa. Maganar ku'din cefane kuwa da ku'din pure water muke yi. Duk da hakan nawa yana shiga amma ba mai yawa ba ne. A hakan kuma bai fasa fita ya yi sana'a ba idan ya samu. Hankalinmu a kwance yake, mun samu rufin asiri. Tunda ya samu ya biya ku'din gidan amma na watanni shida, rabin shekara. Duk nacin ya kar'ba ya biya na shekarar sai ya biya ni a hankali bai yarda ba. Da na matsa ma sai ce mini ya yi "Allah ya karbi ransa kafin ya ga ranar da zan biya masa ku'din hayar gidan da zai kwana." Daga haka na ja bakina na tsuke. Muna cikin wannan rayuwar mai da'di domin dukkanmu mun gamsu da kokarin junanmu. Na yarda ina amfani da duk abin da ya ba ni, ina iyakacin kokarina ban nuna masa ina bu'katar abu sama da k'arfinsa ba, na kuma ajiye dukkan burikana na son na dinga yin suturu masu tsada. Maimakon haka sai na tattara na sayi dan kunnen gold wanda shi da kansa na bawa ku'di ya siyo mini a Jos. Ko zan yi abu a gidan sai cikin dabara ko kuma na kara masa ku'din lallensa idan sati ya zagayo. Shi kuma tunda ya fahimci burina soyayya irin ta indiyawa sai yake ajiye komai ya yi ta kashe ni da kalolin soyayyar da ko indiyawa ma sai a shiri, tunda suma ai shirin fim ne. Shiri kuwa kowa yasan shirya shi ake yi. Amma a hakan yake lalace mini. Ya zama tamkar mai irin shekaruna. Ko a littafai ba kasafai ake samun irin Bulkachuwa ba. Domin ya iya shiririta kala kala da mata suke son ayi musu. Idan yana gida barin komai yake ya tarairaye ni. Cinyarsa ita ce wajen zama na. Goyo kuwa zai iya goya ni, ya yi shara. Har k'aton baho ya siyo irin tafkeke na masu wankan jego. Ya cika shi da ruwa ya dauke ni ya tsunduma. Ya wanke ni tas. A shimfida kuwa irin murza ni da yake yi, da da'din da yake jiyar da ni dole ma na so shi na rikice a kansa. Domin har cikin zuciyata na fara tunanin da ba shi na aura ba dan ban more ba. Har jin haushin son da na yiwa Yaya J na fara yi. Gaba'daya na gama mutuwa a kansa, ba abin da nake so irin na gan shi a gida idan yamma ta yi. Yanzu da baya fita lahadi a gida yake yini. Da kaina na soke yin lalle da kitso. Komin girman mace bana yi a wannan ranar zan fa'da mata maigidan ya hana yi a wannan ranar. Dan na fahimci ba a daina zuwa ana katse mana jin da'dinmu ba sai nake yawan rubutawa a status d'ina cewar babu lalle ranar lahadi haka ma kitso. Mun yi kyau, mun shak'u da juna, komai yana tafiya dai-dai mussaman da na daina yi masa rikicin bai yi mini ciki ba. Da kansa ya dauke ni muka je asibiti da muka cika shekara guda da aure. Dukkanmu aka auna mu aka tabbatar mana lafiyarmu k'alau cikin ko wanne lokaci zamu iya haihuwa. Shike nan sai na daina damuwa illah iyaka ban daina addu'ar ma samu ciki na haihu ba. Muna cikin wannan yanayin mai da'di Rafi'a ta kammala karatunta na jamaia ta dawo gida gaba'daya. Kusan kullum sai ta shigo mini. A zuciyata bana so amma tunda uwarta ba k'aramin kirki take yi mini ba. Sai nake share wa mussaman ita din ma mai kirki ce. Amma haka kawai nake jin fargabar zakewarta a wajena domin na riga da na sani mijina yana son yan lukataye irin ta. Ni kuma yar firit ce. Sannan bazan yaudari kaina ba, zai iya sha'awarta tunda jikinta rugu rugu ne, kuma bayltw damu ta saka mayafi ba. Tunda tana ganin ba sai ta fita waje da ta shigo ba. Bugu da kari ba Hausawa ba ne. Wasu abubuwan nasu da namu akwai banbanci. Haka dai nake ta daure wa ina ta k'ok'arin ban bar shi da kewa ba. Komai yake so sai na yi masa. Ba kuma na tab'a k'osawa da al'amarinsa duk da nima ina son harkar. Amma bana ja masa rai saboda kada ya ga ni a waje ya yi sha'awa. Ba kuma na nunawa ya gundure ni. Ana cikin haka aka tashi bikin. Ihsan k'anwarsa. Tun saura sati biki na tafi, saboda a fara komai da ni, sannan ni ce zan mata k'unshi da kitso. Babah sai ina ka saka take yi da ni. Yadda ta ga na murje na yi kyau ba karamin da'di ta ji ba. Na sani kuma da a ce da goyo na je mata da tafi haka murna. Shi da kansa ya kai ni. Washagari ya tafi akan sai nan da kwanaki ka'dan zai juyo. Komai sai da na bar masa, hatta miya sai da na soya masa, na yi masa cincin. Kawai tafasa farar taliya ko shinkafa zai yi sai kuwa shayi. Ana gobe biki y'an Toro suka iso. Aka yi hidima cikin rufin asiri taro ya tashi lafiya. Kwanaki biyu a tsakani ya zo muka tafi shake da kayan biki masu yawa. Tunda muka yi aure bamu ta'ba nisa da juna ba sai wannan karon. Duk da dai a Bulkachuwan ma ranar biki sai da ya faki ido ya jani muka je wani waje ya yi abin da zai yi sannan ya dawo da ni. Amma muna isa gida ko hutawa bamu yi ba. Daki ya ja ni bamu fito ba sai da ya samu nutsuwa. Da daddare ina zaune a cinyarsa sai ce mini ya yi "Little baki da nauyi, shafal ban ji kin danne ni ba". Na zabura na kalle shi, gabana ya fa'di sosai. Da rawar murya na ce "Sai yau ka fahimci haka? Wa ka d'ora a cinyar da yanzu baka ji yadda kake so ba?" *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* Ya daburce ya ce "Wallahi babu kowa Yabi". Fa'din Yabi da rudun da ya shiga sai yasa na kasa gasgata shi amma kuma na danne na ha'diye saboda babu kyau zargi. Duk yadda na so na bar maganar amma a zuciyata sai wasi-wasi nake yi. Na kasa samun nutsuwa. Hakan ya fara shafar walwalata. Ban sauya masa ba, ba kuma na bijire masa amma kuma babu shiriritar da nake yi masa a baya. Rannan na ce masa ina son na je gida na yini. Da rawar baki ya ce "To, yaushe zaki je?" Domin ya takura da rashin walwalata. Na ce "Duk ranar da ka ce". Ya ce "To gobe sai na kai ki" Haka kuwa da kansa ya kai ni, muka fara isa k'ofar Dada muka gaisa. Tana ta barkwancinta da karatunta. Ban wani jima ba na tashi na nufi k'ofarmu." Ya shigo suka gaisa ya ce mini zai tafi da yaushe zai zo ya d'auke ni? Na ce "ko yaushe ma". A k'ok"arinsa na son ya kyautata mini sai ya ce "Tom idan an idar da Isha zan zo". Na ce "Allah ya kai mu". Ya tafi. Na yini cikin iyayena cikin nutsuwa da walwala. Da yamma lis Gwaggo da Inna zasu je duba yar kanwar Mama da ta haihu kusa da unguwarmu ne. Dan haka Baban Marina ya ce "Asiya sai ku je tare ki rakasu idan kin dawo sai ki shige gidanki". Na amsa da ce wa "To Babanmu, domin idam Gwaggo ta fita ba jin da'din zaman zan yi a dakin ni ka'dai ba, tunda Ikilima ta tafi Islamiya, shima kuma Baban fita zai yi. Mama kuwa babu wata ma'amala mai yawa a tsakaninmu. Dan haka muka tafi tare. Da muka dawo na yi lungun da zai sada ni da gidana, su kuwa suka mik'e suka koma nasu gidan. Haka kawai nake jin nauyin jiki na saukar mini. Wani irin b'acin rai ya ziyar ce ni da na karyo kwanar da na fara hangen gidanmu. Haka nake tafe ina ta jin fargaba. Ina kuma ayyana abubuwa marasa da'di a zuciyata. Nan da nan na fara ta'awizi ina kore shaid'anin da yake son yin wasan kura da zuciyata. Har cikin zuciyata ina son Tijjani, ina son na rayu da shi. Domin a zaman da muka yi na shekara daya da kusan rabi na tabbatar yana da kyawawan dabi'u. Na farko shi mutum ne mai mutunta sallar farillah. Sannan mai yawan tsayuwar dare ne na shaida hakan. Domin duk lokacin da zai shafe yana tiritiri da ni da daddare, to da zarar k'arfe uku ta yi kuma zai tashi ya yi wanka. Ya yi ta yin munajati da Ubangijinsa, wani lokacin ya matsa mini na tashi, wani zubin kuma ya k'yale ni na yi barcina. Sau tari kuma idan ban tashi ba, da asuba idan ya tashe ni sai ya ce "Tashi ki yi sallar farillah akan lokaci, na raba dare ina roka miki alherin duniya da lahira my little". Bayan hakan na karance shi yana da matu'kar son ya kiyaye ka'idojin da shari'a ta d'ora masa mussaman na ri'ke gida da kula da tarbiyata. Sannan ba shi da mugunta ko ka'dan har yau din nan Tijjani bai ta'ba saka mini ido akan ku'dina ba. Asalima kullum cikin k'ara k'auwame kansa yake yi da abin hannuna. Sannan ya iya Soyayyar da duk taurin zuciyar mace sai ya dargaza ta. Ga kuma girmama iyaye, yana mutuntata manya kwarai da gaske. Wadannan dabi'un da ya siffantu da su ya sanya nake hakuri da inda yake kuskure mini, hakan ne kuma dalilin da yasa na k'i yarda na k'arfafa wa kaina zargin ko ya koma Bak'ar Ta'adar sa ta baya. Na shiga zauren na ga kofar tamu a rufe ruf. Na fara tunanin ai ban fito da mukulli ba, tunda mun yi shi zai zo ya dauke ni. Na zaro waya da nufin na k'ira shi ya zo ya bu'de mini, sannan na wuce k'ofar Maman Safiyanu na jira shi. Sai na jingina da k'yauren k'ofar ga mamakina sai na ga ta bud'u. Na tura a hankali na ga sakata a ture tabbacin an saka bata shiga ba ne. Na shigo a hankali. Amma sai na ci birki na tsaya cikin tsananin tu'ajjibi da mastanancin mamaki mai yawa. Jikina ya d'auki b'ari, zuciyata ta yi nauyi ainun. Amma idona ya bushe k'amas. Na saka hannuna na murtsike idanuwana da tunanin gizo yake yi mini, tare da fatan ace sak'e sak'en zuciyata ne da wasi-wasi irin na shaid'an. Amma ina zahiri nake ganinsu. Tijjani zaune akan baranda yayin da Rafi'a take kan cinyoyinsa da manyan mazaunanta. Ta kwanta luf a kirjinsa, shi kuma idonsa na kan k'irjinta yana kallonsu. A zahiri iya abin da na gani ke nan amma zuciyata sai ta shiga wassafo mini cewar yanzu ma suka sanya tufafinsu. Na ki'dima ainun, amma na kasa yin kwakkwaran motsi, na tsaya cak ina kallonsu tamkar mutum mutumi K'arar faduwar wayata ne ya ankarar da shi. Ya d'ago da fuskarsa ai yana ganina ya yi wani irin zabura ya wancakalar da ita, ta hantsilo ta fa'do kan guiwowinta. A matu'kar rude ya k'araso gare ni. Ya rasa mai zai ce, sai kawai ya zube a gabana guiwa bibbiyu. Ya ru'ko hannuna na kalle shi na ce "Tijjani gizo idona yake yi, ko mafarki nake yi?". A ki'dime ya ce "Zan so a ce mafarkin kike yi Asiya". Daidai lokacin Rafi'a ta zo ta shige sum sum tamkar k'wai ya fashe mata a ciki. Na dinga jin tukukin ba'kin ciki da tashin hankali. Amma kuma idona a soye duk yadda nake son hawaye ya zubo mini abu ya ci tura. Na sunkuya na d'auki waya ta na k'wace hannuna na yi d'akina ina jin jiri na katantanwa da ni. Kai tsaye na hau cire rigar cikina domin zafin da nake ji a zuciyata har jikina yake kutso wa. Zufa sai yanko mini take yi. Na cire komai na d'aura zani. Na zauna amma ban daina jin zafin jiki ba. Na fita har lokacin yana durk'ushe a inda na bar shi. Na dauki botiki na nufi rijiya. Da azama ya tare ni, ya ce " Bana hana ki jan ruwa da kan ki ba?". Ban ce komai ba na matsa gefe ya janyo mini ruwan. Ya kinkima ya kai mini band'akin. Na shiga na yi wanka. Amma dana fito ina goge jikina da tawul, zufar na sake keto mini. Na dauki rigar barci marar nauyi na saka, bayan na saka gajeran wando ta ciki. Na d'aure kaina da dan kwali mai taushi. Kicin na fa'da na hau girki, ina yi ina hailala. Gaba'daya jina nake yi tamkar ba ni ba. Na yi matu'kar kad'uwa da abin da na ga ni a cikin gidan aurena. Ban san falalar kuka ba sai a yau, domin gaba'daya hawayen ya k'i zuba. Shi kuma ya takure, a gefe tamkar ka ce k'yat ya zura a guje. Cikin lokaci k'alilan nadama mai tsananin gaske ta bayyana a dukkan jikinsa. Ya kasa sukuni, da alamu kunya ce ta hana shi sukuni. Tunda ni dai ban bu'de baki na ce masa komai ba. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* ✍️ *Dandano* *DAGA Littafin BAK'AR TA'ADA* *NA SURAYYA DEE* *MARUBUCIYAR HALIN YAU DA SABO DA KAZA* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GICSrs9TfxG1Q6FUXiu1Qg *Ina tallata muku make up artist din Guduyo* *Aisha Lame mai kayan kwalliyar yan gayu*. *Jakadiyar oriflame, duk wani nauyin kayan oriflame tana kawo su cikin farashi mai sau'ki*. *Ba iya kayan kwalliya masu daraja ba, ita din GWANAR sarrafa pop corn ce(gugguru), ni shaida ce ta hakika*. *Sannan tana da spices kasaitatu. Masu mayar da girki ya zama na alfarma* *07036662633*. *INA SANAR MUKU ZAMU BUGA LITTAFIN KANA NAKA ZUWA HARD COPY*. *MASU BU'KATAR MALLAKAR NASU SU TUNTU'BE NI, KO SU TUNTU'BI MARUBUCIYA JANAFTY*. *BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*. Na gama komai na kai falo kamar yadda na saba. Shi kuma ya zama mutum mutumi. Na fito na ce "Ga abinci ko sai ka dawo daga masallaci?" Ya zuba mini ido ya rasa abin fa'da. Ya tashi ya ce "Da sauran lokaci ai." Na zuba mana kamar yadda na I'm. Amma gaba'daya mun kasa ci sai faman juya shi muke yi. Gara ni na ci loma biyu na ji mak'oshina ya cushe na ajiye. Shi kuwa yama kasa kai wa ba'kin nasa. Ya gaji ya kalle ni ya ce Dan Allah Yabi ki yi ha'kuri, ki yafe mini". Ba ja in ja na ce "To". Daga haka kuma ban sake ce wa komai ba. Ya yi maganganu na ban ha'kuri da nuna nadama masu yawa amma ban ko kalle shi ba. Aka kira sallah ban yarda na bu'de baki mun yi magana kamar yadda yake fata. Ya yi alwala ya tafi masallaci. Har muka haramar kwanciya ban bu'de baki na ce k'ala ba. Duk jaye-jayen maganarsa kuwa. Da muka kwanta ya fara lalubata ban hana shi ba, amma ko kwakkwaran motsi ban yi ba. Ya yi duk abin da zai yi dan na motsa ko na mayar masa martani amma tamkar an shuka dusa. Ya gaji ya koma ya kwanta yana fa'din "Innalillahi wa ilaihir rajiun" . Ya ru'ko ni da rawar murya ya ce "Yabi ki yiwa Allah, ki bu'de baki mu yi magana". Yana rufe baki na ce"To". "Asiya ki yi ha'kuri, ki yafe mini, dan Allah, dan Annabi, ki yafe mini". Na yi shiru. Ya sake ce wa Bansan me ya same ni ba Yabi. Dan Allah ki mini uzziri ki yi ha'kuri ki gafar ce ni". Nan ma na ce "To". Ya yi iya ban hakuri, amma ban yarda na ce komai ba. Da gari ya waye da wuri ya dawo daga masallaci ya hau hidimar gyaran gida. Ya yi abin karya wa. Har d'aki ya kawo mini amma ina ci sau daya ban sake kai wa na biyu ba, na ce na koshi. Ya yi shiru ya rasa yadda zai yi. Bai fita ko ina ba. Yini aka yi ana zuwa lalle amma ban iya yiwa ko mutum daya ba. Sai ha'kuri nake basu tare da uzzirin cewa bani da lafiya ne. Hakan da ya ga ni ya sake rib'anya tashin hankalinsa. Domin yasan yadda nake matu'kar son sana'ata. Bana son abin da zai hana ni yin lalle ko kitso. Amma da bakina nake sallamar mutane yasan al'amarin da yake zuciyata ba k'ank'ani ba ne. Kwanaki uku muna cikin wannan halin. Daga ni har shi, mun yi matu'kar rame wa tunda bama iya cin abinci ga rashin nutsuwar zuciya. Ya yi juyin duniya mu yi magana na ki, domin har yau ban yarda na yi masa korafi ba. Komai kuma zai ce sai na amsa da "To". Kullum safiya zan gaishe shi, zan kuma amsa sallamar sa idan ya shigo. Daga hakan kuma bazan sake yarda na ce komai ba. Rashin yin lallen har zuwa lokacin ya fara ta'bamu tunda shi ma baya iya fita, ko ya fitan ma baya nisan kiwo zai dawo. Ranar da aka yi kwanaki biyar da faruwar al'amarin, ya zauna ya bani hakuri tamkar yawun bakinsa zai k'afe. Har da k'wallarsa. Amma ban ce komai ba, sai ma murmushi mai ciwo da na yi na ce masa "To me ka yi ne?" Duk da k'arancin shekaruna amma na fahimci shirun da na yi masa ba k'aramin dafa shi take yi ba. Ba abin da yake so irin na yarda mun yi magana ko da rashin kunya ne na yi masa. Amma ban yi hakan ba. Ni a karan kaina so nake na yi kuka, na caccaba masa maganganun da zasu gasa masa zuciya tamkar yadda ya yi dalilin da tawa zuciyar take gasuwa, amma na kasa. Tsawon sati guda muna cikin wannan matsanancin halin, daga ni har shi mun zama wasu iri. Gidanmu ya koma tamkar na zaman makokin mutuwar uwa mahaifiya. Sannan na k'i yin k'unshi har lokacin. Al'amarin da ya sake damalmala mana komai. Shi kam kawai k'arfin halin da aka san maza da shi ne. Amma kana kallonsa kasan yana dandanar kudarsa da shiruna. Yadda bana cin abinci haka shi ma baya ci. Gara ma ni da daddare na kan yi barci, amma shi duk juyin da zan yi zan gan shi kan sallaya ko yana zaune ko kuma yana sallah. Da asuba ya dawo ya tarar har na koma na kwanta. Ya zauna a bakin gadon. A sanyaye ya ce "Yabi wai a haka zamu rayu ne? Bazan iya wannan rayuwar ba. Ki yiwa Allah da ma'aiki ki bu'de baki ki fa'di duk abin da kike so. Na ro'ke ki ba dan ni ba, da Allah nake ha'da ki." Ko motsi ban yi ba. Bare na tanka masa. Ya tsananta da magiya. Sai kawai ji na yi cak ya dauke ni ya yi nufin d'ora ni kan cinyoyinsa. Ai gaba'daya wani irin k'arfi mai tattare da matsanancin fishi ya taso mini. Da dukkan zuciyata na fisge na ingiza shi ya fadi k'asa warwas. Na dinga huci mai zafi, amma na kasa bu'de baki na yi magana. K'irjina sai harbawa yake yi da tsananin gaske. Ya mik'e ya kafe ni da ido, cikin kad'uwa da tashin hankali. Ya ce "Dan Allah bu'de baki ki yi magana. Fadi me zaki ce, idan kuma na zauna ki mini duka zai fi mini akan irin halin da nake ganin ki, ki yafe wa mijinki, ki yafe wa masoyinki, ki yafe mini, kaddara ce ta hau kaina Asiya". Na juya na kwanta ba tare da na ce uffan ba. Kukan kuma bai zo ba. Ya kasa hakuri ya sake biyo ni inda nake kwance ya hau lalubata, ban hana shi ba, ban kuma yi wani yun'kurin da zan tankwabar da shi ba. Ya yi abin da zai yi. Yana gamawa na lalubi zanina na daura na fice. Wanka na yi, sannan na dawo na kwanta. Bayan na mulke jina da hadadden man oriflame. Wanda jakadiyar kamfani ce ta za'ba mini shi fa kanta, q cewarta shi zai fi dace wa ta tarar fatata. *Kunsan dai Aisha Lame make up artist din Guduyo ce. Yanzu ma bata bata bar fatar Yabi babu gyara ba*. *Kun tandadi fame wash din nan kuwa da na yi ta jaddada muku muhimmancinsa a wajenku?* *Ku tuntu'be ta a wannan lambar dan samun sabbin kayanta masu kyau da farashi mai sau'ki da ya zarta na saura*. *07036662633*. Shi kuma yana kwance sai fa'din "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya ke yi da k'arfi. Yau duk jarumtar sa kasa yin ayyukan gidan ya yi. Dan haka na yi abuna. Na yi abin karyawa har na gama yana kwance. Na d'aga labule na ce "Ka zo mu karya." Yana daga kwancen ya ce "Ko na zo d'in ma ai ba ci muke yi ba. Ki yafici abin da zaki ya fita ki rufe". Wasa wasa yana kwance har azahar, ko wanka bai fito ya yi ba. Abin da ban ta'ba ganin ya yi ba, zama da janaba. Komin dare baya kwanciya sai ya yi wanka. Ko da kuwa zai yi second round. Amma yau safiyar Allah kuma ba barci ba, amma yana nad'e ya kasa tashi bare ko ruwan shayi ya kurb'a. Na sani fishin nawa ne ya fara k'ure malejin jarumtar sa. Ina zaune ina tunanin al'amurar rayuwa sai na ga fitowar sa, d'aure da tawul da k'yar yake daga k'afafuwansa rauni gaba'daya ya bayyana a jikinsa. Da ya tashi dawo wa daga masallaci sai ga shi da Malam liman da Malam mai Tafsiri. Ganin dattawa kuma manyan Malamai na shiga marabatarsu da girmama wa. Shi da kansa ya yi musu jagoranci zuwa falonmu. Na zuba ruwa a k'aramin tray na ajye a gabansu. Na gaishe su cikin ladabi. Suka amsa suna saka mini albarka. Na yun'kura zan tashi na basu waje dan a tunanina wajensa suka zo. Sai kawai na ji sun ce "Ina zaki kuma, ai zuwan na ki ne". Gabana ya yanke ya fa'di to me ya kawosu waje na ni kuwa?" Malam liman ya yi gyaran murya ya yi addu'ar bude taro, ya nemi tsari daga sharrin shaidan da rundunarsa. Sannan ya ro'ki Ubangiji ya sanya albarka a abin da za'a tattauna. Aka amsa da ameen. Ya zarce da cewa "Asiya mijinki ya same mu, ya kawo k'arar kansa da kansa gabanmu. Da bakinsa ya ce ya yi miki laifi da ya amsa sunan laifi. Amma yana ro'kon mu zo mu baki ha'kuri a madadinsa". Na yi k'asa da kaina, ban ce komai ba. Domin ba k'aramin nauyi na ji ya kama ni ba. Akan me zai dauko mini manyan mutane irin haka? Malam liman ya zarce da cewa "falalar hakuri yawa ne da shi Asiya. Mijinki ya yi nadama, irin wacce ake so mumini ya yi. A wannan zamanin idan mutum ya yi kuskure ya yarda ya yin ma, har yake bada ha'kuri ba k'aramin mutumin kirki ba ne. Abin da yasa na yarda na zo kenan da bakinsa ya ce ya yi miki k'aton laifi. Sannan na ga rauni mai yawa a tare da shi, wanda idan ba'a ba shi dauki ba zai iya kwantar da shi. Ki gode wa Allah da ya baki miji mai kiyaye sallah. Sama da shekara da zuwansa unguwar nan ban ta'ba fashin ganinsa a sahun gaba na sallar isha da asubahi ba. Annabin Rahma ya ce wadannan sallolin munafukai basa kiyaye ta. Ki yi hakuri da inda ya gaza mutumin kirki ne, na shaida hakan". Sai lokacin kuka mai tsananin gaske ya k'wace mini, irin kukan da yake ki'dima duk mai sauraronsa, kuka mai dafa zuciya mai sawa a shid'e. Kowa ya yi shiru, illah Tijjani da yake fa'din "Alhamdulillah! Alhamdulillah cikin wani irin yanayi. Domin ya sani rashin kukan da ban samu na yi ba. Da rashin furzar da maganganu. Ya sanya na taurare nake dafa shi ta hanyar zuru. Malam mai Tafsiri da yafi kusa da ni, kuma yafi tsufa, domin ya tsufa ainun, na tabbatar ya haifi kamar Babanmu. Ya d'ora hannunsa a kaina yana shafa mini, cikin muryarsa ta girma ya ce "Yi hakuri jikata. Kara hakuri, Innallaha ma-assabirin. Ki daina irin wannan kukan zai janyo miki ciwo. Yi salati ki samu nutsuwa. Tsawon lokaci yana shafar kaina tare da maganganu masu taushi har na samu nutsuwar. Hannunsa na kaina ya ce "Shin Asiya ta huce ta ha'kura, ta yafe wa mijinta?" Da rawar murya na ce "Akan me zai dauko mini ku? Ni bai mini komai ba, kuma nima ban ce masa ya yi mini wani abu ba." Da azama kuma da cikin rawar murya ya ce "Na yi miki Asiya! Ni nasan ban kyauta ba. Amma ki dubi Allah ki yi ha'kuri. Ki bani dama mu tattauna, mu rufe maganar nan ta wuce". Na kalle shi hawaye na zuba mini na ce "Tunda ka kafe ka yi mini laifi, fadi laifin da bakinka. Fa'da musu su ji". Ya yi k'asa da kansa ya kasa ce wa komai. Na juyar da fuskata na ce "Kun ga ni ba. Ai bai mini laifi ba. In ma ya yi Allah ya yiwa, na tabbatar kuma ya nemi gafarsa tunda kwana yake yi yana ibada. Ni kuwa bai mini komai ba." Malam liman ya ce "Ga shi da bakinki kike shaidar yana kwana sallah anya bai cancanci ki yafe masa ba. Kinsan darajar wanda yake munajati da Allah fil lail kuwa?" Kamar na ce "Amma ibadar tasa bata hana shi ya yi barna ba, bata hana shi ya tozarta ni ta hanyar yin bak'ar TA'ADAR a gidan aurena ba. Amma na kasa bu'de baki na fa'da musu hakan. Ban san da gaske ina son sa ba sai yanzu. Domin bayan matsanancin kishinsa da yake cina, sai na ji bazan iya tona masa asiri ba. Bazan iya fa'dawa wani mahaluki abin da na ga ya aika ta ba. Malam liman ya sake cewa "Ki yi ha'kuri kin ji Asiya. Ki yi koyi da mai sunan ki Nana Asiya. Annabi ya fa'da mana falalar ta. Abin da kuma ya janyo mata babban rabo a wajen Ubangiji imaninta da hakurinta akan mijinta ne. Ki yi hakuri, da sannu Ubangiji zai daidaita muku al'amuranku." Jikina ya mutu tubus. Na ce "To". Suka dinga saka mini albarka da godiya. Malama liman ya mike ya ce "Tunda ta amsa ta huce ai shikenan, kai kuma ka kiyaye, kada ka sake aikata laifinka." Da sauri Tijjani ya ce "In sha Allah! Na gode amma Wallahi bata ha'kura ba, kuna tafiya zata cigaba da fishinta. Nima ta ce mini to yafi a k'irga." Jin haka Malam mai Tafsiri ya sake d'ora hannunsa a kaina ya ce "Asiya na yafe wa mijinki a madadinki, na rufe wannan maganar har abada, shin zaki yi mini wannan lamini, zaki mini wannan mutuntawar?" Yam jikina ya amsa. Wani irin abu ya tsriga mini a zuciyata wadda tun ranar da abin ya faru ya tokare ni. A sanyaye na ce "Shike nan Malam na yarda, na kuma yafe masa". Yana jin hakan. Da k'arfi ya ce "Alhamdulillah! Allah na gode, Allah ka taimake ni, ka tsare ni." Ya matso yana fa'din "na gode Yabi". Na galla masa harara na ce "Wallahi ba dan Malam ne ya yafe maka a madadina ba, da har ka tsufa kamar sa baza ka sake ganin walwala a fuskata bare dariyata. Ba kuma zan sake aminta da kai ba. Amma yanzu ka ci darajar masu daraja". Ya matsa kusa da Malam din ya ce "Na gode sosai Malam. A kuma taya ni da addu'a Allah yasa k'arshen al'amarin kenan. Na gode muku, Allah yasa ku gama lafiya". Suka tafi suna mini godiyar yarda da na yi sun isa da ni. Sai addu'ar mu samu haihuwa mai albarka suke yi mana. Shi kuwa jan kunne da tunasar da shi girman hakkina da yake kansa suke yi. Suna ta jaddada masa idan ya musguna mini da gangan ba zai ga haske a al'amuran sa ba. Ya jima bai dawo ba, da alamun dai har gidajensu ya musu rakiya. Ya dawo ya tarar da ni a falo. Na amsa sallamar sa na d'auke kaina. Ya shigo da d'an kuzarinsa. Ya kalle ni ya ce "little me kike son ci na dafa miki?" Ba walwala a fuskata na ce "Babu". Ya matso ya durk'ushe tamkar mai neman gafara. Ya ce "Kin amsa kin yafe mini, kin amsa kin rufe maganar me zai sa kuma ki basar da ni? Na ro'ki dan darajar Annabi ki yafe mini, dan Allah. Shirun ki bala'i ne. Ki fa'di komai na zuciyar ki, zan ha'diye, na sani ban kyauta ba, amma nima bansan me ya same ni ba." Da kuka na ce "Tun yaushe kuke yin hakan?" Da rawar murya ya ce "Ranar ne kawai, Wallahi shine na farko kuma na k'arshe Asiya." Na ce "Ban yarda ba. Ina ce dama kafin ranar ka ce mini ni bana danne ka yadda kake so?". Ya daburce ya ce "Billahillazi kawai na fa'da ne, amma ba dan ina yin wani abu ba ne. Ki yarda da ni, ki bani wata damar, kada ki yanke aminci da yarda a tsakaninmu dan Allah". Ya fa'da hankalinsa a tashe matu'ka. Ya ru'ko hannuna ya ce "Ki ji tausayina. Zuciyata zata iya bugawa idan kika cigaba da share ni, na yi tuba a wajen Ubangiji, ke ma ga ni durk'ushe a gaban ki, ki yafe mini" Na kafe shi da ido hawaye na zuba. Shima ya zuba mini nasa da suka kada suka yi jawur. Da kuka na ce "Kana tunanin zan samu nutsuwa idan kuna rayuwa da it'a a gida daya, kana ganin zan iya mance wa idan ina ganin gittawar ta?" Ya yi shiru. Na ce "ko ina son na manta ba zai yiwu ba. Dan haka zan fa'da maka gaskiyar magana. Sai dai ka zabi daya a ciikin ni da ita". Ina rufe baki ya ce "wanne irin zabi ne wanda babu azanci a cikinsa? Ta ya ya zaki ce na zaba a cikinku? Ai ke ce tawa, ke nake so, ke nake burin rayuwa da ke, ke kike burge ni." Da rawar murya na ce "Ita kuma tana baka sha'awa, kana son ka ji manyan mazaunanta a k'asanka, kana son kama manyan non..". Ya yi maza ya rufe mini baki jikinsa na bari irin na zullumi. Ya ce "Na zabe ki, ke nake so Yabi Ubangiji ne shaidar ban so wata mace kamar yadda nake son ki ba. Na kuma yi imanin ba zan so wata sama da ke a bayan ki ba." Na goge hawayen idona na ce "muhimmi a gurina ka zama kamamme, idan har son da kake yi mini bai yi tasirin da zai kange ka daga ta'ba haramun ba ai banzar wannan son". Da rawar murya ya ce "Allah ka mayar da ni kamamme. Allah ka yafe mini, Allah na tuba". Tausayinsa ya kama ni yadda yake daga hannuwansa yana ro'kon da dukkan zuciyarsa. Na nisa na ce "Mu fuskanci gaskiya. Idan da gaske sonka nake yi to akwai bu'katar na baka gudumawar da zaka tsira daga fa'dawa halaka. Na yarda na kuma gamsu kana sona. Nima kuma idan gaskiyar zan fa'da ina son ka. Amma na sani ban zo maka a yadda kake fatan matarka ta zo maka ba. Na yi amanna jikina bana manyan mata ba ne. Nan da shekaru goma ma ba zan yi girma shahararre ba. Dan haka ka aure ta kawai". Ya zabura ya ce "Kinsan me kike fa'da kuwa?" Idona ya sake cika da hawaye na ce "Na sani mana, kuma har cikin zuciyata nake nufin hakan" Ya sake ni ya na girgiza kai ya na fa'din bana sonta, bana burin na aure ta, ko ina da halin k'ara auren ma kamammiya nake so wacce bata san namiji ba sai a kaina tamkar yadda na same ki". Maimakon na ji da'di sai na sake shiga rud'u. Da rawar murya na ce "ka tabbatar ba budurwa ba ce? Ashe ba iya abin da na ga ni ya gitta a tsakaninka da ita ba kenan?" Cikin ido ya kalle ni da dukkanin gaskiyar sa ya ce "Na rantse iya abin da ya faru kenan. Amma kuma duk macen da bata san namiji ba ai ba zata dinga shige masa ba. Ba ni na je inda take ba, ita ta kawo kanta. Ko da ina son na ta'ba ta sai amince, kin ga ni kuma ba dole na yi mata ba, da son ranta ne, na tabbatar bani ka'dai ta ke yiwa hakan ba, ba ni ka'dai take sakarwa ba. Dan haka ina cikin nutsuwata bazan auri shasha ballagaza ba". Y'anmata kalubalenku abin da mijin Yabi ya fa'da shine gaskiyar magana, saurayin nan da kike amince yake ta'ba ki ba zai aure ki ba, sai tsananin rabo. Idan rabon auren ya rantse kuwa har ki tsufa a hannunsa ba zaki fita daga zargi da wula'kancinsa ba. Ba shakka wayewar da ta sanya kika bar shi yake lalube ki, to shifa a ballagaza wacce ta saba cudanya da maza daban daban yake miki kallo. Sannan ticket din kaskanci kika yankarwa kanki. Ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali ya yi wanka. *Cikakken labarin zai fara zuwa muku ranar 09/09 wanda a wannan ranar mahaifiyata zata cika shekaru ashirin da uku da barin duniyar nan*. *Dan haka zan yi amfani da wnanan damar dan ku taya ni mika mata addu'oin gafara da rabauta a wajen Ubangiji*. *Na gode sosai Ubangiji ya saka muku da alheri bisa soyayyar da kuke yiwa rubutuna*. *VIP 1K* *REGULAR 500* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM* *ZENITH BANK.* *A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08032773332 KO KUMA 09069067488* *NA GODE SOSAI* ✍️. *ANTI KULSUM BAUCHI HOW FAR?🥰* *KIN TUNA RANAR DA NA CE MIKI INA RUBUTU?😄* 67&68. Na daskare a zaune, wato duk tantirancin namiji shi kamila yake so. Duk yadda zaki sadaukar masa da komai da sunan soyayya shi fa a zuciyarsa ba haka ba ne. A yau na k'ara fahimtar darasin rayuwa. Na kuma k'ara gode wa Allah da na tsallake sirad'in yanmatanci lafiya. Na kalle shi cikin tu'ajjibi na ce "To ka sani Wallahi bazan zauna a cikin gidan nan ba. Matu'kar kana son kwanciyar hankali da walwala to kuwa bana son gidan, ba kuma zan zauna a cikinsa ba." A rikice ya ce "Asiya kin san dai da yadda aka biya ku'din rabin shekara yanzu wata guda tal muka yi, ta ina zan fara neman wani gidan?" Ido cikin ido na ce "koma ta ina ne, na baka nan da sati if not Bilhiillazi bazan ha'kura ba. Sai dai ka nemi ni ka rasa shike nan sai ta tattaro ta maye maka gurbina." Ya yi muk'us ya kasa zaburo mini. Ya nisa ya ce "Haba little nan da sati me zan yi na samo ku'di? Kin san dai ba dawo mini da kudin zasu yi ba, bare na kama wani". Na ce "Sai na baka aro, ka karbi zobena ko dan kunne ka siyar, sai ka biya ni idan ka samu hali". Ban san ya aka yi ba kawai ya fara nuna ni da yatsansa cikin sababi yana fa'din "Nafi karfin ki kama gida na zauna a ciki Asiya. Ba zan yi wannan lalacewar ba, har abada da ikon Allah." Na kafe shi da ido tsawon lokaci har ya fara kame kame. Na nisa na ce "Tijjani ni kake yiwa wannnan shouting din?". Na girgiza kai na ce "Ba laifin ka ba ne. Laifina ne da na yarda da afuwar da Malam ya yi maka ba tare da na bayyana tozarta ni da ka yi ba. Afuwar da aka tilasta ni na yi maka ne ya baka kuzarin yi mini sababi irin haka ko? To Wallahi bazan zauna a gidan nan ba. Komai za'a yi da ni kuwa". Na mik'e na bar shi, ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi. Domin ya ga na koma Yabin Marina marar sassauci. Ban jima da shiga d'akin ba sai ga shi ya biyo ni jikinsa a sanyaye. Ya zauna kusa da ni ya tausasa harshe ya ce "Ke little ba ki fahimce ni ba ne. Ki yi hakuri, zamu tashi, amma pls ba nan da sati daya ba dan Allah." Na ce "To". Ai kuwa nan da nan ya hau fa'din "Na rok'e ki fa Little. Ban son irin wannan to din na ki". Na share shi. Ya dinga jaye-jayen magana amma ban tanka masa ba. Sai kuma ya bani tausayi yadda ya yi shiru ya rasa abin yi. A zuciyata sai hango girman gatan da Ubangiji ya yiwa mazaje nake yi. Domin duk girman laifin da zasu yi wa mace sai Ubangiji ya sanya hakuri da sassauci had'i da rauni a zukatan mataye. Nan da nan mace zata yafe ta kuma manta musganwar miji. Na tuna ranar da ya rufe mini gida dan kawai na je na na yi sana'ar da zan samo masa ku'din da zamu rufa asirinmu. Amma har washagari yana sababin sai na tafi gida. Amma ni na fita unguwa na dawo na tarar yana shek'a ayarsa. Na girgiza kai domin nasan da ace ni ya ga ni a cinyar Yaya J sai ya masa dukan mutuwa tunda ba k'arfinsu daya ba. Ni kuwa zai yi wahalar gaske idan bai sallama ni ba. Na kalle shi na ce "Na tambaye ka?" Ya d'aga mini kai tabbacin eh. A hankali na ce "Idan ni ka ga ni a cinyar wanin ka ya zaka ji?" Ya ce "Wata'kila zuciyata bugawa zata yi, wata'kila kuma na had'u da mummunan hawan jinin da zai kanannad'e ni." Na sake zuba masa ido na ce "Amma me yasa baka yi zaton nima sakamakon hakan zai iya samu na a dalilin ganin wata a jikin ka ba?" Ya fara sosa k'eya. Da k'yar ya ce "Ban san ya aka yi hakan ta faru ba. Ni gaba'daya am upset ma". Na girgiza kai na ce "Hmmm". Muka yi shiru sai kuma na ce "Kuma zaka zauna da ni idan ka gan ni a irin yanayin da na gan ka?" Ba ja in ja ya ce "Ba zan iya ba". Na zuba masa ido ina masa kallo mai tsananin gaske. Na kaurara murya na ce "Amma kuwa son zuciyar ka azimin ne Tijjani." Bai yi inkari ba. Bai ce komai ba, na kuma tabbatar da dukkan zuciyarsa ya bani amsar. Kamar daga sama sai na ji ya ce "Mace daraja ne da ita sai wacce ta wula'kanta kanta. Duk matar auren da zata bada k'ofar da wani namijin zai mata waya, ko doguwar gaisuwa dama ai ba kamammiya ba ce. Ba kuma yadda za'a yi mijinta ya gasgata ta. Bare kuma a ce har ya ga ni da idanuwansa, tabbas ba zai zauna da ita ba, ko kuma idan ya ri'ke ta din ma bisa wani dalilin to fa har abada ba zata ji dadinsa ba." Na sassauta na ce "Amma shi namiji idan yana sharholiyarsa ko da kuwa a cikin gidan aurensa ne dole ne matar ta yi hakuri ta zauna da shi ko?" Ya kasa amsa mini. Na zarce da ce wa "Ana rudarku da cewa duk abin da namiji ya yi ado ne, na mace ne kaico. To ka saurare ni da kyau abin da zan fa'da ka sani sai dai zan sake yi maka matashiya ne na kuma kafa maka hujja tunda yanzu ka sanya an tursasa ni na yafe maka. Laifin namiji baligi da na mace baliga a banagaren barna duk daya ne a fuskar addini tunda duk hukunci iri d'aya Ubangiji ya zartar. Al'amari irin wannan kuma bashi ne in ji Annabin Rahma. Idan mutum ya bata y'ar wani, shima za'a bata tasa. Idan ka yi da matar wani, kai ma za'a yi da taka.! Na kaurara murya na ce "Na yarda baka yi zina ba Tijjani. Amma kana kusantar ta. Kana bin hanyar da ta bi. Ka sani kuma Allah da kansa ce wa ya yi kada mu kusance ta, ba wai kada a aika ta ba. Ina ro'kon ka, ka daina kusantar ta bare tsautsayi ya sanya ka fa'da yin ta da auren ka. Ina jin tsoro da zullumin kada na fara haihuwa a b'ata mini yara. Ina cikin fargaba kada laifin ka ya jefa ni cikin had'arin a lalata ni da aurena". Ya zabura ya ce "To y'ar sarkin mugun fata da jawo bak'in alkaba'i." Na kalle shi na ga ya shiga rud'u a dalilin furucina sosai. Kishinsa ya bani mamaki ainun. Ban ji d'ar ba na ce "Gaskiya na fa'da maka, wacce Annabi ne ya fad'a tun gabannin kakaninmu su iso duniyar. Bayan haka kuma ina son ka sani laifin da ka yi tabbas na ha'kura. Amma ina tabbatar maka idan na sake kama ka da irin wannan laifin to fa ka sani ka kuma ri'ke a zuciyar ka ba zan sake zama da kai ba Wallahi". Ya matso kusa da ni ya rungume ni sosai yana fa'din "Da ikon Ubangiji bazan sake ba Asiya. Ki taya ni addu'a. Ina kuma ro'kon ki sake hakuri, ki shafe wannan al'amarin a zuciyar ki. Wallahi summa Tallahi iya abin da ya faru ke nan, kuma a wannan ranar na ta'ba yin hakan, kada shaidan ya rinjayar miki ce war na saba yi din ne. Na kuma fahimci Ubangiji ya so ni da alheri ne shi yasa ma asirina ya tonu." Na saki ajiyar zuciya mai nauyi na ce "Shike nan Allah ya yafe mana gaba'daya." Ya sake ri'ke ni sosai yana fa'din "Na gode sosai, Allah ya sanya ki cikin bayinsa da yake kar'ba daga gare su." Hawayen da ban san dalilinsa ba ya dinga zuba mini. A hankali na ce "Ameen". Shike nan muka rufe maganar. A ranar ma mutum uku suka zo lalle amma hakuri na basu da gabatar da uzzirin ban warware ba. Domin gaba'daya na rasa karfin zuciyata. Rauni mai yawa nake jin yana bina. Sannan wata irin karaya da al'amarin Tijjani ya haifar mini da gajiya da kasala masu nauyi a zuciyata wanda gangar jikin ta rasa k'arfi da kuzari. Bai ce komai ba. Amma jikinsa shima ya mutu domin ya fahimci k'arfin halin da nake yi iya gangar jikina ne kawai. Da daddare ya ri'ke ni, ya dinga rarrashi, da ban baki irin wanda sai masanin falsafa ne zai dinga harhada kalaman masu nauyi a mizanin masalaha. Na amsa da ce wa "Na ha'kura da gaske." Ya ce "To me yasa ba zaki y lalle ba Asiya? Na sani kuma ke ma kin sani, rufin asiri ne mai yawa sana'ar taki take yiwa jama'a." Murya na rawa na ce "Zuciyata ta karye, jikina babu k'wari." Sai kuma na ke ce da kuka fiye da wadda na yi a gabansu Malam. Ya kasa ce wa komai tsawon lokaci mai yawa ina kukan, shi kuma yana shafata tamkar jinjira. Na jima ina kuka bai hana ni ba. Har sai da kukan ya tsaya cak dan kansa. Na koma ina ajiyar zuciya mai d'auke da shesshek'a. Ya sassauta murya ya ce "Kin yi kuka Asiya da ikon Ubangiji ba zaki sake kuka akan irin wannan al'amarin ba. Ki yi ha'kuri, wannan rufin asirin da kika yi mini, ni ka'dai nasan yadda na sake jin ki a raina. Ni ka'dai nasan yadda girman ki da nauyin ki suka yi mini rubdugu. Ke yarinya ce k'arama amma hankalin ki na manya ne. Kin yi k'ank'anta kin tsunduma cikin irin wannan bak'in-cikin. Ina ro'kon Ubangiji ya sanya wannan ne kukanki na karshe akan wannan matsalar a dukkan rayuwarmu gaba'daya". Na amsa da"Ameen" a hankali. Murya babu amo na ce "Bana son wannan gidan, ba zan yi farin-ciki a cikinsa ba. Ka samo mini wani ko daki daya ne zan zauna". A hankali ya ce "Da ikon Allah zan samo miki, amma ki d'aure zuwa lokaci ka'dan kin ji". Na ce "To shike nan". Ya dinga fa'din Na gode sosai my little. Allah ya bani dama da zan jiyar da ke da'di mai yawa". Na ce ni "Ka tsare mini mutuncina da naka da kuma soyayya da tattali nake so fiye da komai". Ya ce "zan miki Asiya, zan yi kokarin kiyaye ko wacce irin BAK'AR TA'ADAR da zata sanya ki kuka. Yanzu yaushe zaki fara yin k'unshin dan na tabbatar kin huce kin kuma yafe mini?" Na shagwaba na ce "Sai ka yi al'kawarin ba zaka dinga yi mini sababi akan k'aramin abu ba. Bana son shouting". Ya numfasa ya ce "Zan dinga k'ok'arin ina yin fa'dan a hankali. Amma bazan yi al'kawari ba, kin san wani lokacin ha'kurinmu k'wace wa yake yi, abin da zaki fahimta shine sab'awa a zamantakewar aure ba k'iyayya ba ce, matu'kar kuskure ne irin na zaman yau da kullum ko kuma sab'anin ra'ayi". Na ce "Tom shike nan jibi zan fara yi In sha Allah" Ya tsananta rik'on da ya yi mini yana fa'din"Thank you my little girl". Daga hakan kuma ya shiga bai baye ni da zafaffar soyayya mai goge dukkan tsatsar zuciya. Washagari muka yini cikin nutsuwa da walwala mai yawa. Tun safe kuma na yi status da cewar gobe idan Allah ya kai mu zan fara k'unshi. Shike nan na ha'kurkurtar da zuciyata na manta komai. Na rungumi mijina da sana'a ta. Illah iyaka na yanke mua'amala da Rafi'a. Mahaifiyarta kuwa ban fasa gaishe ta ba, ban fasa mutuntata ba. Illah iyaka shiga ne bana yi. Ita ma kuma Rafi'a din ta daina shigo mini. Wata biyu da faruwar hakan na fara wani irin zazzabi mai zafin gaske. Domin kwana nake yi mutsutsukun ciwon jiki. Gaba'daya ji nake tamkar ana kwankwatsa mini kasusuwan jikina. Ga bana iya cin abinci. Haka nake kwana ina yini cikin wannan halin. Sa'armu d'aya akwai kayan abinci tare da mu. Sannan yana k'ulla lallen da siyar da ruwa. Babu matsalar babu sosai a tare da mu. Kwana biyu ina ta shan maganin zazzabi da na rage rad'ad'in ciwo. Amma babu sau'ki kullum gaba ciwo yake yi. Hakan ya sanya shi fita ya yi buga bugarsa ya samo ku'di ya ha'da da wanda muke da shi, ya kai ni asibiti. Yini muka yi domin sai da aka k'ara mini ruwa. Aka yi mini gwaje gwaje. Da yamma aka sallame mu bayan sun tabbatar ina da ciki na wata daya har da sati biyu. Duk yadda nake jin rashin kwarin jiki amma sosai na yi murna. Ni da Tijjani ban san wanda yafi murna da zumudi ba. Muna isa gida na dauki waya na k'ira layin Gwaggo. Tana dauka ta ce "Yabi ya jikin dai?" Da azarbabi na ce "Hmmm Gwaggo ashe duk wannan wahalar da murkususun da nake yi ciki ne da ni!" Ta yi shiru, sai kuma ta ce "Ni kika kira ki fa'da wa hakan Yabi? Wacce irin marar kunya ce ke haka?" Na yi sakare domin ni ban ga wani laifin ba. Ita ce uwata bani da wacce ta fita a halin yanzu. Ita ce mafi kusa na tattauna dukkan farin-cikina da ita. Zan yi kokarin na boye fa'da mata damuwar da nake ciki domin na yi amanna damuwata zata tsayar mata da dukkan farin-cikinta ne. Na sanyaya murya na ce "Gwaggo ki yi ha'kuri. Ina cikin murna ne. Kin san kwanaki a gidan nan aka fa'da mini ce wa Tijjani ya gama zubar da yaransa a titi ni bazan haihu ba. Sannan kuma ke da bakinki kika ce sai na haihu da ki zo ki ga muhallina". Ta sassauta ta ce "To ba sai ki bari na fahimta ba, ko na ji a bakin yayarku ko kuma Nazira". Na ce "To sake yin hakuri Gwaggo ai yanzu na fahimta. Idan zan yi ta biyu, bazan fa'da miki ba. Sai dai kawai a ce miki Yabi ta haihu" Ta ja tsaki ta ce "Allah dai ya baki lafiya" tare da kashe wayarta. Tijjani da yake gefe yana ta faman murmushi ya ce "Burinmu ya cika. Yanzu fa'da mini sunan nawa?" Na yi dariya na ce "Ai sai na haihu". Ya girgiza kai ya ce "Kin ce da zarar kin samu ciki zaki fa'da mini fa". Na ce "Haka ne". Ya ce "To fa'da mini na ji". Na murmusa ka'dan na ce "Abbanta". Ya kwashe da dariya ya ce "Wanne irin suna ne wannan? Duk yadda kika kwadaita mini zakuwar samuwar cikin a iya wannan sunan zan k'are? Abbanta kuma. Wace ce?" Na jingina a jikin kujerar na ce "Bebin mana." Ya sake fa'dada dariyarsa ya ce "To idan namiji ne fa?" Na ce "Ai kuwa sunan da zan fa'da maka mai wuyar samu ne indai namiji na haifo tunda na fa'da maka mai kama da kai nake so". Dadi ya kama shi ya ce "Allah ka kula mini da Asiya. Ka taya ni son ta, ka shiga dukkan kasafinta. Duk al'amarin da zai dunfaro ta, Ubangiji kada ka bar ta da iyawar ta. Na ce "Ameen" a gajiye domin wai maganar da na yi har na gaji na fara haki. Haka nake kwana da yini babu lafiya. Duk dare bama barci kwana muke muna fama. Domin gaba'daya ni dai babu sau'ki. Kwana nake magogo. Haka kuma Tijjani baya runtsawa. Tausa yake yi mini, da fifita idan babu wuta. Tin a lokacin muka fahimci zama iyaye ba karamin al'amari ba ne. Duk yadda na zaku na samu ciki sai da na fara sare wa. Murnata ta fara koma wa ciki dan tsananin wahalar da nake ciki. Al'amura suka fara yi mana tsauri a dalilin ku'di ya fara yanke mana. Haka da safe idan ya tallafa mini na yi wanka, ya shafe mini jiki da man zafi zai fita ya dan yawata. Idan an yi sa'a ya samu aiki ya samo ku'di, zai siyo mini 'dan abin kwadayi. Watarana kuma hakan zai dawo. Baya kuma nisan kiwo, ko ya fita hankalinsa na kai na. Sai na samu sau'ki, sai kuma jikin ya sake rikice wa. Na fara gazawa. Rannan Baban Marina da ya zo duba ni, ya ga yadda na koma gaba'daya na yi yaushi. Ya bashi umarnin ya kai ni gida, ko shima ya d'an huta. Bai musa ba kuwa washagari da hantsi ya dauke ni da jakar kayana ya kai ni gida. Har da siya mini su maltina da madara da indomi da zan dan yi kwanaki ina ci. Wanda na tabbatar ya ha'da da bashi. Da k'yar na shiga muka gaisa da Dada wacce bayyana farincikin da ta yi a dalilin samuwar cikin bata lokaci ne. Ya kira Ikilima ta ri'ke ni zuwa cikin gida. Na sani kuma dan ya mutunta iyayenmu ne ya sanya bai ri'ke ni da kansa ba. Yadda Tijjani ya ha'do ni da shirgi da maganganuwana. Sai ka rantse har cikin zuciyarsa yake nufin na zo na yi goyon ciki a gida. Kwana na biyu a gida na fara samun sau'ki tamkar a gidana ciwon yake. Domin ina barci, da safe kuma ina shan koko na ci dumame. Sannan Gwaggo da kanta take daddana mini jikina. Har gasa mini jiki take yi da tawul. Ga shi duk abubuwan da nake son ci na gargajiya ina samu. Kwatsam ranar da na yi kwana uku sai ga shi ya ce shi ya gaji da rashina sai dai mu koma gida. Na tubure akan sai na ji k'warin jikina. Shima ya kafe. Kuma wai ni ce zan ce ina son komawa gidana. Nan da nan na rantse akan bazan fa'da ba. Ya jijjiga kai ya ce "Shike nan tunda babu taimako da fahimta a tsakaninmu. Ni zan fa'da wa Baban akan na gaji ina son ki koma dakinki. Dama kunya da nauyinsa ne suka sanya na kawo ki." Da yamma ya dawo akan na taimake shi mu koma gida. Ya kasa fa'dawa Baban zai tafi da ni. Na ce "Ni dai na fi son zaman nan". Nan da nan ya tunzura ya ce "Saboda bani da ku'di ko Asiya?" Na kalle shi a razane. Ya ce "Haka ne mana. Inba hakan ba wace ce ta taba zuwa gida dan bata da lafiya a gidan nan?" Na ce "Ubaida bata dawo ba?" Da hanzari ya ce "Amma duk jinyar da ta yi da ciki ai bata dawo ba. Sai da ta haihu. Ke kuwa ai ba haihuwa kika yi ba. Idan ba gazawa ta aka ga ni ba. Mene ne zai sa ayi mini wannan umarnin?" Na sake kallonsa cikin tu'ajjibi na ce "Baban Marina kake fa'dawa hakan ko kuwa wa?" A tunzure ya ce "Asiya na ke fa'dawa saboda ita ce zata ce masa ta samu sau'ki." Idona ya ciko da hawayen takaici na ce "To". Daga hakan na k'ulle bakina ban ce masa komai ba. Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi. Ya ce "Ya muke ciki?" Ko kallonsa ban yi ba. Ya gama zamansa ban sake kula shi ba. Da daddare ma ya dawo, ban yarda na kula shi ba. Domin idan akwai abin da yake b'ata mini rai da shi idan muna magana ya dinga sako babun shi ne. Na kuma lura idan ban taka masa birki ba, ba wanye wa k'alau zamu yi ba. Tunda yana nema ya mayar da ita sara. Washagari sassafe sai ga Babah ta Bulkachuwa ta dira a gidan. Ina daga daki na ji suna gaisawa da Baba. Ya ce " Hauwa kamar ba kwanaki ka'dan da suka shud'e kika zo duba y'arki ba. Me ya sake dawo da ke kuma yanzu? Mata kuna da son sabgar yawo. Ta ce "Ba hakan ba ne Yaya. Shi ne ya mini waya wai jikin Yabi ya yi tsananin da ka ce ya dawo da ita gida. Sai ya ro'ki na zo na zauna masa da ita. Ni kaina hankalina ba kwanciya zai yi ba idan ba zuwa na yi na ganta ba." Baba ya numfasa ya ce "Ai shi Tijjani bai gamsu zan kular masa da iyali dan karan kansa ba, sai ya zargi na yi masa fin k'arfi saboda y'ata ce?". Ta diriri ce ta ce "Haba Yaya ni Wallahi har kasa na ji babu da'di." Ya ce "To ki ji mana. Ban da dai ke ma kin banbanta ta ya ya zaki zo ki ce mini "Zaki dauki matar Tijjani a gaba na?" ✍️ *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. Ta shiga ba shi ha'kuri, shi kuma ya dinga yi mata sababi. Yana fa'din "Da kam nan da kwana biyu na yanke zata koma zan ha'da ta Mamarsu ta je ta zauna da ita ko na sati ne kafin jikinta ya yi k'wari. Amma yanzu na fasa ba zata koma ba. Ki fa'da masa na ri'ke ta, sai ta haihu tunda ba shi da kunya, ya banbanta, ya nuna uwarsa ce ka'dai zata yi wa iyalinsa hidima. Ai kuwa Babah ta dinga ba shi hakuri, ta lallaba ta zame kanta ta bar Tijjani tsundum cikin maganar. Ta shigo d'aki ta duba ni. Ta bani leda mai d'auke da soyayyun kaji. Da kuma soyayyar awara da ta sha yaji mai da'di fal leda (K'ara'i). Na fahimci duk yadda Babah bata shiga al'amarin Bulkachuwa Amma bata dauki abin da ya shafe ni da sau'ki ba. Samuwar cikin jikina kuwa sai na fahimci k'arfin soyayyar da take yi masa. Domin farin cikin da take ciki duk wanda ya rab'e ta sai ya gane hakan. Kusan kullum sai na amsa k'iran abokan arzik'inta. Suna mini sannu da jiki. Daga samuwar cikin zuwa yanzu na manta adadin da ta zo duba ni. A dakin Gwaggo ta shigo ta same ta suka hau cakar juna, tunda k'anwar miji ce. Gwaggo ta ce "Oh ni Asma'u ina ganin kananci a wajen Hauwa. Kina zazzame wa akan sha'anin yara. Amma tunda kika ji zaki yi jika sai b'are b'are kike yi da sintiri a hanya tamkar a kanki za'a fara yin jika". Ta ce "kya yi kya gama. Y'ay'ana nawa ne suka haihu? Yanzu ina ce duk sa'anin aurenta sun haihu dama wandanda suka riga ta auren. Duk ba jikokina ba ne?" Gwaggo ta ce "wace ni na ce ba jikokin ki ba ne. Gani na yi Ummi yar hutun ki ma baki ta'ba zuwa dubiya idan tana laulayi ba, sai idan haihuwa ta yi. Amma Yabi kin zo ganin ta, sau ba adadi sabo..". Ai bata jira saboda me Gwaggo zata ce ba. Ta sunkuci jakarta ta fice tana wani irin murmushin farin-ciki. Tare da ce wa "sai ki yi da wata ai. Ke da ake ganin shirunki da hak'urinki, nan kuwa ba'kinki fal zan ce da bita da k'ulli ne". Washagari ta shiga mota ta juya ba tare da ta ce wa Tijjani komai ba. Ai kuwa kwanaki biyu ya dinga wata irin zarya a cikin gidanmu ta ban mamaki. Baban Marina ya share shi. Rannan da daddare ya murje kunyar sa ya ce "Baba gobe zan zo na d'auki Asiya." Baban ya gyara zama ya ce "Ai haba?" Ya yi wani irin tare da sunkuyar da kansa k'asa ya kasa amsawa. Baba ya numfasa ya ce "Ai k'ure rashin kunyar ka zan yi Tijjani. Wai kai magidanci kada a ga gazawar ka. Shine ka turo mini uwarka dan ka nuna mini ita ce zata maka hidima kai tsaye ko?" Ya yi k'asa da kansa tare da ce wa "Ba haka ba ne Baba". Ya ce "Ya ya ne? Fada mini ina jin ka". Tsawon lokaci bai tanka ba. Baban ya ga ji da shirun sa ya ce "To uwar taka ma da soyayyarka ta rude ta, ta zo zata mini rashin kunya na fatattake ta, bare kuma kai karamin alhaki. Ai tunda ka nuna mini da wajena da wajen Hauwa da banbanci, ni kuma zan nuna maka da kai da Salisu d'aya ne a waje na. Bazan baka Asiya ba sai ta haihu ta yi arba'in". Ya kalli Baban ya ce "Idan na baka hakuri fa Baba, zaka ha'kura ka bani ita?" Kai-tsaye ya ce "Bazan hakura ba." Tijjani ya ce "To ka yi ha'kurin kuskuren da na yi". Ya ce "To na ha'kura Allah ya yafe mana. Ku daina banbanta iyaye. Dukkanmu d'aya ne." Ya ce "To Baba zan kiyaye." Suka yi shiru. Can Tijjani ya ce "Baba ko zaka yi hakuri ka janye zancen sai ta haihu, nan gaba a k'ara wata biyar fa, kafin ma ta haihun". Ya ce "To na ha'kura Tijjani. Allah ya yi muku albarka. Allah ya k'ara ha'da zuciyoyinku. Ya kuma hore maka ikon kula da iyalinka". Ya amw.sa da "Ameen Baba". Washagari da yamma ya zo muka tafi, ni kuma sai fishi nake yi. Muna isa gida ya rungume ni sosai yana ta sakin ajiyar zuciya. Ni kuma na sha mur, na kawar da fuskata gefe guda. Ya ce "Tunda mun dawo ai sai ki huce. Yau kwana uku ko hudu kina mini fishi. Gidan fa gaba'daya zafi ya yi mini da ba kya nan." Nan ma ban kula shi ba. Sai da ya dinga rarrashi da ban baki sannan na bu'de baki na ce "Ai dan ka ga na damu da kai ne shi ne kake musguna mini ta hanyar ce wa dan baka da abin duniya ne nake yi maka wani abu. Tunda haka zaka dinga yi mini kawai ka k'yale ni, kowa ya yi harkarsa". Ya dinga fa'din "ki yi ha'kuri na daina, dan Allah ki huce haka nan". Ya shafa cikina da ya fara tasa wa. Ya ce "Ya bebinmu?" Kawai sai kunya ta kama ni na ture hannunsa na rufe fuskata da hannuwana. Ya sani a jikinsa ya ce "Asiya ina son ki, ina son kasance wa tare da ke muddin rai. Jikina ya yi sanyi na kasa ce wa komai. Amma kalaman sun yi matu'kar tasiri a zuciya da gangar jikina gaba'daya. Ban samu kaina ba sai da cikin ya shiga wata biyar. A lokacin kuma ya fito sosai tamkar ba cikin fari ba. A kan dole nake yin k'unshin, amma sai muka tak'aita iya mutum uku kawai nake yiwa a rana. Amma ina yiwa masu son bak'i da tunda shi babu durk'ushe sosai. Sannan ina yin kitso. Ana kuma siyan lalle. Dai-dai lokacin kuma Tijjani ya fara zuwa Bauchi cikin kasuwar Muda lawal. Ya samu Alhaji Auta aminin mahaifinsa tare ma suke kasuwancin. Kawai dai da tafiyar ta yi nisa sai bai cigaba da bibiyar iyalin marigayin ba. Amma hatta katon fiilin da ya fito a gadon Tijjani a jere suka siye su. A yanzu hakan ma shima nasan filin yana nan. Wajen ya rayu, ya yi daraja ainun. Cikin cire girman kai Tijjani ya yi masa bayanin yana son ya zama cikin yaran shagon ko da ciccire ribabbun kayan miya ne. Domin ya fahimci idan Yabi ta haihu ba k'aramin nauyi ne zai sake hawa kansa ba. Ga shi kuma, kullum rayuwar k'ara tsananta take yi ga talaka. Da sakin fuska ya karb'e shi ya kuma babshi wani bangaren da zai dinga kula da shi. Dan haka sai Tijjani ya zama sai bayan kwana uku yake zuwa Toro. Duk sadda zai je kuma zai je da kayan miya, da kayan abinci. Sannu a hankali yake bin kasuwar yana kuma yin biyayya. Amma ba'a dauki lokaci mai yawa ba sai ya fahimci yadda *BAK'AR TA'ADAR* hassada ta yi katutu a zuciyar jama'a. Mafi yawa yaran shagon sun ha'de masa a dalilin suna ganin maigidan nasu ya daukake shi. Sannan ba ya yarda a yi aikin ha'inci da shi. Domin mafi yawa suna satar kayan su siyar ba tare da sum saka ku'din a shagon ba. Zuwansa sai k'udaden shiga suka karu dan haka Alhaji yake bud'a masa yake yi masa Ihisani. A yanzu da ya wadata su da abinci sai ya koma siyan kayan haihuwa. Duk sadda zai tafi sai ya sayi riguna unisex guda biyu, baya damuwa ko da iri daya ne matu'kar dai kala ta banbanta su. Da ya tara riguna da yawa sai ya koma sayan ragowan kaya. Yau ma Sai da ya biya ya siyi setin robar wanka mai sau'kin ku'di. Ya kalli rukunin masu tsada mother care. Ya ji sun ba shi sha'awa. A fili ya ce "Allah ka hore mini wata haihuwar na siya wa Asiya irin wadannan". Ya kara da setin mai na Nycil. Ya tafi ya hau mota. Bayan ya siya mata tarkacen su fruits dangin mangwaro da su abarba. Sannu a hankali muke rayuwa, har cikina ya shiga watan haihuwa, zuwa lokacin kuma ya canja mini gidan, amma shima na rabin shekara ya kama tunda ya fara tunanin mu koma Bauchi da zama, amma ya ce sai na haihu tukun. Kowa ya kalle ni sai ya yi maganr girman cikina. Har rinjaya ta yake yi. Idan ya tafi Bauchi sai Iklima ta dawo gidana. Sai ya dawo sannan ta tafi. Cikin sa'a haihuwa ta kama ni yana gari, kuma da daddare. Dan haka ya samo abin hawa, muka tafi, sai da aka karb'e ni, aka bani gado. Sannan ya tafi gida ya fa'da. Take Baban Marina ya ha'do shi da Mama akan ta zauna da ni. Har asuba ban haihu ba ina shan azabar duniya. Na yiwa Gwaggo addu'a yafi cikin carbi. Sai da na gama galabaita sannan aka fahimci bazan iya haihuwa da kaina ba. Nan da nan aka shirya ni zuwa d'akin tiyata. Amma muna shiga ciwo ya sake tasowa fiye da ko wanne. Na dinga kururuwa ina salati, tare da fa'din a ce wa "Gwaggo ta yafe mini." Likitocin da zasu yi mini aikin suka rufu a kaina. Ai kuwa sai ga haihuwa gadan gadan. Suka taimaka wajen zaro jinjiri. Yana fito wa ya xika dakin da kuka mai tsananin gaske tamkar gyare. Na fara maida numfashin wahala da gajiya. Ai sai wani sabon ciwon ya taso, gaba'daya na rasa karfina. Take kuma likitocin suka tabbatar ba mabiya ce kawai a cikin ba, akwai sauran halitta. Na fara kuka domin na tabbatar bazan iya sake haihuwa a yanzu ba. Ina kuka ina fa'din "Summa sabila yassara". Daga haka ciwo ya tsananta, na birkice, ga shi na kasa nishi mai tsanani. Da taimakon Allah da na likitocin na biyun ya iso duniya bayan sun k'ara ni. Wahala kan wahala na yi kafin na rabu da cikin da na kwashe watanni tara ina tiriri da shi cikin kalubale kashi kashi. Ban gama wartsake waccar azabar ba, aka shiga yi mini dinki tamkar k'warya. Duk yadda aka yi mini allura kashe rad'ad'i sai da na dinga jin ciwon har cikin kaina. Sai da suka gyaramu sannan aka karbo kayan Bebi a wajen Mama sannan aka fito da mu. Sai hamdala nake yi a zuciyata. Ina sake girmama sha'anin Ubangiji. Ba a taba ce mini tagwaye ne a cikina ba. Na tarar y'anuwa sun zo asibitin da yawa. Na dan ji da'di domin kaf y'ay'an Babanmu da aka aurar da su. Ba wacce ban ga ni ba, har Ubaida kuwa. Ko Yaya Indo da bata sake taka gidana tun ranar da aka kai ni ba, na ganta a wajen. Idona ya cika da k'walla ina ayyana duk yadda shaidan yake shiga cikin al'amarin zumuncin yau, jini yana da tasiri k'warai da gaske. Ina ta waige waige domin zuciyata so take ta ga jariraina, so take kuma ta ga uban y'ay'an. Amma ban gansu ba gaba'daya. Na ha'diye na yi shiru na cigaba da kallonsu d'aya bayan d'aya. Tare da amsa sannun da suke ta faman yi mini. Na jima kafin barci ya sure ni. Na dai farka na tarar da Babah ta Bulkachuwa zaune a gefena tare da Mama. Sannan Inna da Yaya Ummi suna ri'ke da jariran da aka nad'e su da zani iri d'aya. Dada na gefe tana mulmular goro a bakinta, tana kuma jan tasbaha. Da suka ga na farka, suka hau fa'din "sannu, sannu Yabi". Dai-dai lokacin kuma ruwan da ake k'ara mini ya k'are. Wata jamiar kiwon lafiya ta shigo a daidai ta cire mini, tana mini sannu. Da walwala ta ce "Mrs Bulkachuwa ina taya ki murnan samun wad'annan kyawawan jariran. Allah ya rayasu ya baki lafiya". Na yi shiru su kuma ahalina suka amsa da fa'din "Ameen mun gode". Ta kalli Mama ta ce "Zo ki ri'ke ta, ki taimaka mini mu zaunar da ita. Yaranta suna bu'katar nono". Da dabara suka zaunar da ni. Sai da ta tambayi na ji da'din zaman ko na takura a gyara ni?" A hankali na ce "Ya yi". Dada tana ganin malamar asibitin ta karbi yaron hannun Inna. Ta zabura ta ce "Dakata dafta". Kowa ya mayar da hankalinsa kan Dada da ta jawo ledar da ta zo da ita, ta fito da k'ok'o tare da gorar mirinda da kuma wani ruwan maganin a wata gorar daban. Ta yun'kura da k'yar tana dunduk'e ta nufo gadon. Ta kalli jami'ar kiwon lafiyar da take shirin kwantar da jaririri a jikina ta ce "gafara ka'dan". Cike da girmamawa ta kauce tana ce wa "Sannu tare da mamakin me zata yi. Sai dai su yan d'akin sun san me zata yi. Ta saka k'ok'o a cinyata, ta d'aga rigata. Duk da y'an k'ananun nono gare ni, amma tunda cikina ya fara girma suka ciko. Yau kuwa da ruwan nono ya zo sai suka yi girma suka tsaya k'yam tamkar kwakwa. Karon farko da aka bu'de mini nono a bainar jama'a ban kuma ji nauyi mai yawa ba. Ta daidaita ta dinga zuba ruwan robar ta kuma saka hannu tana wanke mini su. Sai kuma ta fara k'ok'arin matsesu tana fa'din sai an cire mataccen nonon da yake lalata jinjirai kafin a basu su sha. Dukkansu babu wanda ya yi inkarin hakan domin suma akan wannan Ta'adar suke. Nan da nan malamar asibitin ta ce "kin wanke Dada ya isa haka". Ta d'ago ta ce "Yarinya me kike fa'da ne? Kina son ki ce wai dak'ashin za'a bari su sha?". Cikin girmama wa ta ce "Eh Dada. Domin alfanunsa mai yawa ne a jikin jariri. Shine rigakafi na farko da Allah subhanahu wa ta'ala ya fara yiwa dan-adam da shi." Dada ta bar komai ta kafe ta da manyan idanuwanta ta ce "To sannun ki, amma su wadannan baza su sha datti ba. Kullum a cikin yiwa Allah da ma'aiki k'arya ku ke. Allah dai ya shiryeku idan zaku shiryu". *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*. Ta sake rank'wafawa da nufin yin abin da ta yi niyya. Ma'aikaciyar ta ce "A a Dada daure ki yi hakuri. A yanzu Asiya ba a hannunku take ba. Tana hannun gwamnati ne da kuma hukumar lafiya. Dan haka duk abin da za'a yi mata dole zai kasance k'arkashin kulawar hukumar asibiti ne. Bijire wa hakan kuma yana iya sawa mu gurfanar da mutum gaban kuliya. Dan haka ki yi ha'kuri ki bar hukuma ta yi aikinta. Wannan karon kam a zabure ta ce "ke yarinya kar ki mini iyashege kin ji. Dan Allah falfala da gudu ki kirawo mini hukumar mu yi arangama domin mutuwa ce ka'dai zata hana ni matse wa Yabi mataccen nono marar amfani, ba ku da kuke yiwa masu jajayen kunne bauta ba." Ta murmusa ka'dan ganin Dada ta kufula da yawa. Ta ce "Dada abin bana b'acin rai ba ne. Ki Fahimci bayanina. A da an rayu cikin duhun kan cewar nonon farko mai kalar rawaya matacce ne kuma mai illah. A yanzu da ilimi ya cika duniya masana kimiyya sun gano d'inbin amfanin da Allah ya ajiye a nonon uwa. Mussaman na awannin farko da haihuwa. Yana rigakafin ciwon hanta, k'oda, huhu. Yana hana tasirin ciwon k'yanda da tarin fuka, da shawara. Yana k'arawa jariri kaifin k'wak'walwa, yana kuma daidaita k'asusuwansu". Dada ta dauki salati tare da cewa "Ni Binta ina ga ni da sauraron kinaya. To da kunsan da hakan amma kuka sake k'ak'alo allaurar da ake daukar watanni ana yiwa yara babu tausayi bare imani da sunan rigakafi ce. Yanzu wanne ne gaskiyar magana kenan?" Malamar ta yi murmushi ta ce ko wanne gaskiya ne Dada". Ta ce "To ku ri'ke gaskiyarku, amma ni ban yarda da ita ba, bare kuma na yi muku biyayya" Da walwala ta ce "Shike nan Dada ki ri'ke fahimtarki. Amma tunda har aka kawo Asiya asibiti to wajibi ne abi ka'idojin hukumar lafiya. Idan ba hakan ba zamu sallame ku ne. Komai ya biyo baya kuma babu ruwanmu. Kafin haka kuma, zan rubuta tirjiyar da kuka yi, idan abu marar da'di ya biyo baya ke ce da d'aukar alhakin komai. Domin na tabbatar za ki ga ni". Nan da nan Dada ta d'auki salati tare da fashe wa da kuka ta koma gefe tana ce wa "Yau ko da wa kike tak'ama sai na yi sharia da ke tunda kika ce zan ga ni." Ita kuwa bata damu ba, da alamu ma dariya Dadan ta bata. Domin sai guntse bakinta take yi. Ta kuma d'ora mini yaron tana nuna mini yadda zan tallafe shi a duk sadda zan shayar da su gudun kada su dinga kware wa ko su kasa samun iska. A lokacin da yaron ya fara tsotso wani irin rad'ad'i ya ratsa ni. Na zabura ta ce "Sannu". Na kasa amasawa, kunyar idon su Babah ya hana na yi kwarmato. A daddafe ya sha. Ta dauke shi, ta dauko d'ayan. Ya fara sha ke nan Tijjani ya iso da kayayyaki a hannunsa. Ya ci birki ya tsaya yana kallon yadda take rurrufe ido tana cije wa ga yaro yana sha. Farin cikin Asiya ta zama uwar y'ay'ansa har biyu tashi guda yana matu'kar saka shi tsumaye. Amma ganin Dada na kuka ya takaita masa murnar da yake ciki. Ya ajiye kayan a gefe ya isa kusa da da ita. Yasa hannu ya ru'ko hannunta da take share hawaye. A tausashe ya ce "Dada kukan me kike yi haka ne? Ina ce d'azu kika dinga rangwad'a murnar alherin da ya samu a cikin alhalinki na samun tagwaye?" Cikin kuka mai yawa ta ce "Ayyah mai sunan manya ai wannan ja'irar yarinya tana neman mayar mini da murnar tawa ciki. Ba yadda ban yi ba kada ta bawa yaran nan dattin nono amma sai da ta kafe ta basu suka shanye. Idan an yi sa'a sun rayu, to tabbas zasu tashi da kukan da baya jin rarrashi ga yawan kumburin ciki, sannan mafi muni suna iya samun tawaya a hankalinsu". Ta ke ce da kuka mai tsananin gaske. Fargaba ta shige shi ainun. A ki'dime ya ce "jariran aka yiwa sanadin raunin k'wak'walwa Dada?" Ta kad'a masa kai tabbacin eh. Tare da ce wa "Kuma Wallahi tunda ta ce mini zan ga ni, sai na yi shari'a da ita ko da me take tak'ama kuwa. Ba zata lahanta mini tattaba kunne, sannan ta bini da mugun k'ulli na kuma ha'kura ba. Ko waye ubanta a garin Toro da kewaye sai mun je gaban gatan marar gata wato kuliya". Ya sake ta ya isa gaban su yana leka yadda a ke bawa yaron nono. A gigice ya ce "Baiwar Allah ya zaki dage sai sun sha abin da zai zame musu illah?" Ya fara k'ok'arin karb'e yaron. Babah ta Bulkachuwa ta yi wani irin tari mai kama da kashedi. Nan da nan ya ankara ya fahimci gargadi ta yi masa. Ya d'aure ya saki yaron. Ya koma gefe amma zuciyarsa ta dinga wani irin tsalle. Dada kuma ta sake tsananta kukan tana fa'din "Duk wannan iyakacin da aka nuna mini akan y'ay'an nan baki ji ciwo ba ashe? Ba ki hana ta ci mutuncin uwarki ba, baki hana ta nakasa rayuwar y'an mala'ikun Lillahi ba. Shi ya zo zai kwatar mana yancinmu ni da su shine zaki hana shi? Eh lallai! To ki je na barwa hukumar asibitin ke, ranar da zamu yi shari'a da su ki zame musu shaida ki kwaye wa uwarki da jikokinki baya". Ta juya ta fice tana kuka bilhakki. Yayin da Babah da Inna da kuma Mama suka bita da nufin lallashi da ban baki a gare ta. D'akin ya yi saura daga mu sai Yaya Ummi. Ya d'auki yaron ya rungume shi tsam tsam. Yana ta tofa masa addu'ar da ta zo bakinsa. Ya kalle ni ya ce "Sannu Asiya! Ubangiji ya yi miki albarka, ya baki lafiya, ya baki hakuri da kuma juriyar raino da tarbiya". Na kalle shi ina jin wata irin soyayyarsa na kekketa ni fiye da ko wanne lokaci. Wata'kila kuma kasancewar sa uban y'ay'an da nake jin kaunarsu har a cikin b'argona yana da alak'a da sake jin ninkin soyayyar sa. Na murmusa na masa ameen a zuciyata. Ya mik'awa Yaya Ummi wanda yake hannunsa ya karbi d'aya yaron da ya kammala sha yanzu a hannun malamar. Cikin nutsuwa ta kalle shi ta ce "Mr Tijjani kada Kaka ta rikita ka." Ta shiga fado masa muhimmancin fara bawa yaro nonon uwa a farkon awanninsa a duniya. Ta sake ce wa "Tunda mu musulmai ne mun yi sa'a kuma muna d'abbaka sunnar manzo. Da zarar uwa ko uba sun tauna dabino sun guntsawa yaronsu a baki bayan sun yi Bismillah. Ba abin da zai fi dace wa da lafiyarsa illah wannan nono da mutanan jiya suka tafi a fahimtar ce wa cuta ce. Babban sirrika ne da Ubangiji ya zuba a ciki". Ya gyada kai cike da gamsuwa. Ya yi mata godiya sosai tare da bata ha'kuri akan maganganun Dada. Ta murmusa ta ce "Ai babu komai nima kafin na fito sai da muka haura da tawa kakar. Sai ana yi musu uzziri. Da zarar sun kai shekarun girma irin haka, sai an sake yin hakuri da sha'aninsu ana mayar da komai zasu ce a matsayin girma ne. Shi kuwa tsufa ba k'aramin nauyi ne da shi ba. Domin Allah da kansa sai da ya yi ta jan kunnenmu a cikin kura'aninsa mai girma akan idan iyayenmu suka kai shekarun girma kada mu fa'da musu munanan kalamai, komai zasu yi mana, kada mu ce musu uffan, balle a yi sa'insa da su". Ya sake ce wa "Haka ne. Na gode sosai". ✍️. *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633*. *Masu fitarwa bazance muku komai ba. Kowa ya yi mai kyau kansa.* *Wacce ta karanta mini labarin nan bata biya ba tabbas ina binta bashi*. *Masu jiran na kammala su had'a mini document, kada ku yi hakan, na ro'ke ki a littafaina na baya amma still baku ji ba.* *Bana son a had'a mini document* *Bana son a had'a mini document* *Wacce kuwa ta hada na kai ta k'ara wajen Ubangiji*. Ta tattara kayanta ta fice ta bamu waje. Ya matso ya zauna a gefen gadon da nake kai. Ya zuba mini ido tare da ce wa "Sannu little. Ban zaci zaki iya haihuwa da kanki ba. Mussaman da na ga Ubaida da Nasiba masu garin jiki sun gaza haihuwar da kansu". A hankali na ce "Haihuwa ikon Allah ke sawa a yi ta lafiya ban da haka kam da iyayenmu basu taramu da yawa haka ba". Ummi da take gefe ta murmusa ta ce "Yabi an je kusa da lahira an dawo." Ya ce "Ummi ai ni da kaina na tausaya mata, haihuwar yara biyu tashi guda, sannan ki gansu manya tamkar ba tagwaye ba? Wani ikon Allah bamu yi zaton yan biyu ba ne, Ubangiji ya boye su ko sikanin din da aka yi bai nuna ba." "Ikon Allah ya fi ga hakan ai" Yaya Ummi ta fa'da a hankali. Ya sake kallona ya ce "Asiya kin ga yaran nan kuwa, kina ganin yadda Ubangiji ya mana kyautar da ba kowa yake yiwa irinta tashi guda ba?" A hankali na ce "Ai ban gansu ba, ba'a bani na ga ni ba, kunya kuma ta hana ni na tambaya". Ya yi hanzarin sake matso wa kusa da ni tare da d'ora mini yaron akan cinya a hankali. Cikin nutsuwa yake ce wa "kalle shi da kyau Asiyata. Kalli ki ga yadda suke kama da ni. Kalle shi, ki masa addu'a, ki kuma gode wa Ubangiji bisa d'inbin baiwar da ya yi mana". Na zuba wa yaron ido. Ina son ga ne kammannin da Tijjani yake fa'da. Amma na kasa tantance wa, domin ni kam bana ga ne kammannin jarirai. Na tsananta kallonsa, ina jin wata irin nutsuwa da kaunar yaron na shigata sannu a hankali. Na saka hannu ina duba yatsun hannunsa da na tabbatar irin nawa ne. A hankali Tijjani ya ce "Yusuf ke nan (Baban Bulkachuwa) ki masa addu'a, shi ne babban". A fili na furta "Allah ya raya shi, ya saka shi cikin bayinsa da yake sonsu. Allah ya masa kyakkawar rayuwa. Allah ya bashi basira da azanci, ya saukaka al'amarinsa, ya kuma ba shi kyakkawan rabo a lahira". "Ameen ameen" Tijjani yake fa'da cikin wani irin yanayi. Da azama ya ce "Ummilolo kawo shi, shi ma ya samu tabararakin addu'ar uwa." Ya dauke wanda ya kira da Yusuf. Yaya Ummi ta d'ora mini na hannunta ta koma gefe. Ya gyara rikon na hannunsa ya ce "Kin ga yadda suke kama da juna ko? Tagwaye ne masu kama da juna kwabo da kwabo(Identical twins)". Na gasgata shi, domin ni kaina idan aka jere mini su bazan iya banbanta su ba a yanzu. Na zuba masa ido tamkar yadda na yiwa d'anuwan sa. A hankali Tijjani ya ce "Muhammad Sani ne wannan(Baban Marina)." Haka kawai na ji tausayi yaron ya shige ni. Kaunar sa ta shiga mamayata. Cikin rauni na ce "Allah ya raya shi, ya sanya shi cikin bayinsa da yake kar'ba daga garesu. Allah ya saukaka al'amarinsa, ya kimsa masa ilimi da azancin sarrafa harshe. Ubangiji ya sa ya dace da kyakkawan rabo a lahira". Shi da Yaya Ummi suna ta fa'din "ameen". Ya sake kusantowa gare ni. Ya ha'demu gaba'daya ya rungume. A fili ya ce "Allah ga ahalina, ka so su, ka taya ni kula da al'amarinsu, ka tsarkake mini su. Ubangiji ka basu kariyar da ni ba zan iya basu ba. Ka zame mini jagoran wajen sauke nauyinsu da ka d'ora mini. Allah ka bawa uwarsu lafiya da juriyar raino da tarbiya. Ina ro'kon ka saukar da albarka a cikin gidanmu da rayuwarmu gaba'daya". Ya dinga kaiwa kuncina da goshina sumba. Jaririn da yake hannuna ya fara mutsu mutsu da k'ananun kuka tabbacin an takure shi. Da azama Tijjani ya janye daga gare ni. Yaya Ummi ta matso da nufin d'aukar yaron. Ya ce "Ashe ba ki fita rarashin Dada ba Ummilolo? Da kika ga sun fice ai sai ke ma ki bi bayansu ki bamu waje". Ta ce "ka gama borin kunyar ka dai". Ya matse ya ce "To ba daukarsa zaki yi ba. Taimaka wa zaki yi ya sha. Da alamu yunwa yake ji sai tsotson hannu yake yi". A hankali ya na ce "A a ai ya d'an sha d'azu. Zafi Wallahi!. Cikin tausayi ya ce "Ki yi ha'kuri, zafin na d'an lokaci ne k'alilan". Kan dole na yarda na ba shi. Shi kuwa yaro sai zuka yake yi babu jinkiri da alamu sai yafi d'an uwansa tsotso. Ana hakan na hannunsa shi ma ya fara nasa sukur sukur din. Ya mike ya saba shi a kafa'da, yana dan juyawa. Daidai nan su Babah suka shigo. Ta kalle shi ta ce "Bawa Ummi shi, ka zo ka tafi. Ka zo ka yi kane kane ko kunyar iyayen pka baka ji". Ya bada yaron ya fice ba tare da ya sake ce wa komai ba. Kwana na yi da yini sannan aka sallame mu. Yara lafiyarsu k'alau. Kai tsaye gida aka zarce da mu. A dakin Gwaggo muke yin jego. Hidima kan hidima Tijjani da mahaifiyarsa suke yi. Har sai da Baban Marina ya ce "Ka bi a sannu Tijjani kada ka yi bashi". Tun kafin ranar suna aka lankayawa Yusuf(Hanif). Muhammad Sani kuma (Hamim) Har ranar suna ta zo aka yi taron sunan tagwaye cikin rufin asiri. Na yi kwalliya da leshi, da kuma kyawawan sabbin material din Umm Nihla.... Har kala biyu. Kyaunsu da sau'kinsu ya sanya Tijjani ya siya mini kala biyu. Leshi kuwa a cikin na lefena na dauka na dinka. Fayyace irin kayan da muka samu ni da yan biyu bata lokaci ne. Domin gadajen Gwaggo duka biyu sai da suka cika da kayayyakin barka. Babbar matsalar da ta fara damuna rashin warke wa ta. Tafiya ta a bubbude. Na je asibiti sun ware d'inkin. Suka ce na dinga kama ruwa da ruwan dumi da dan gishiri a ciki zan warke. Sosai Gwaggo take kula da ni. mun warware mun ciko ni da yara. Na murje tamkar ba yara biyu nake shayarwa ba. Matsala biyu ke damuna ta farko kukan yara. Domin idan dare ya fara nisa suka fara kuka, babu me yin barci a k'ofarmu. Da daya ya fara, d'ayan ma zai dauka, su taru su kidamamu. Basa dainawa sai an yi assalatu. Dada kuwa sai fadi take yi "Ai kuka ma basu fara ba, tunda an riga an yi musu sanadin wahala. Waye zai sha mataccen nono ya share k'alau?" Matsalar ta gaba kuma nake jin na bu'de. Ina jin yadda iska ke shigata. Nasan na karu amma ban yi zaton dinkin ba zai ha'de ni ba. Ga shi ban fasa kama ruwa da ruwan zafi ba. Na kasa jin da'din kaina. Na kasa fa'dawa Gwaggo. Yaya Ummi na zuwa na fa'da mata. Ta ce "na sa a kawo sassake da saiwowi kalakala da ake kawo wa daga chadi." A kunya ce na ce "Na gode. Kwana biyu a tskani sai ga ta dawo da kayan. Da kanta ta dafa mini, ta ware mini butar da zan dinga zuba maganin. Dan kama ruwan da na yi da ruwan maganin har na fara jin da'din jikina. Da zata tafi ta hada kan kayanta ta tafi da su. Ina son na ce ta bani koren maganin da na dafa kazar, amma na kasa a dalilin kunya ta yi mini k'awanya. Na tuna ranar sunan Ubaida yadda su Nasiba da su Maijida suke koda kyaun kayan da suke siya daga Kano ta hannun Yaya Ummi. Na tuna sadda ta bani ina amarya na ki kar'ba. *Masu bu'katar kayan gyara na chadi gangariya, su yi mini magana. 08032773332* Amma da yake Yaya Ummi yar'uwa ce ta gaske sai da ta bani kayan nan duka. Kazar ma ta ce zata daho mini idan na kusa arba'in. Cikin dabara na kirgi ku'din da na samu a barka na sawa y'arta mai d'an dama a aljihunta. A haka na kwashe sati hud'u da haihuwa. Tijjani ya fara rawar kai da son na koma gidanmu haka nan. Tunda na warware. Idan ya fara wannan maganar shiriritar da ita nake yi. Da safe an yiwa yara wanka suna ta barci tamkar basu ne masu kwana ido biyu suna kuka mai tsananin gaske ba. Amma da gari ya waye ba za'a sake jin motsinsu ba. Yini suke suna barci. Ranar da muka yi kwanaki talatin ya iso daga Bauchi. Ya zaune kan sallaya a tsakar d'akin Gwaggo. Ya ci abincin da aka kawo masa. Ya kalle ni ya ce "Little ki girmama al'kawari. Ba irin cika bakin da baki yi mini ba akan idan kin haifi namiji suna na mussaman zaki saka mini. Cikin ikon Ubangiji kin haifo har biyu amma har yau ban ji sunan nawa ba. Anya kin yi daidai kuwa?" Na dauke kai ina murmushin kunya. Tare da ce wa "gaggawa ne da kai. Ka bari sai mun koma gidanmu zan fara fa'da maka." Ya yi murmushi ya ce "Gaskiya na matsu fa'da mini na ji kawai". Na yi dariya na yi shiru. Ya zuba mini ido sosai ya ce "So nake ku koma, mu yi kwanaki ka'dan kafin mu fara ha'da kayanmu. Kin san mun kusa cika wa'adin kudinmu. Bazan sake biya ba. Idan na samu dama a Bauchi nake son na samu k'aramin gida mu koma can. Zirga zirgar zata mini yawa ga tsadar ku'din mota. Zan fa'da wa su Baba zamu k'aura zuwa Bauchi." A sanyaye na ce "Allah ya k'ara budi." Domin na shiga zullumin yadda zan rasa jama'ar da nake da ita, tunda bazan samu jama'a a Bauchi kamar yadda na yi shura a Toro ba. Ya ce "Ameen Asiyata! Amma fa ban bar waccar maganar ba. Dai-dai lokacin Haneef ya fara kuka da alamun razana ya yi. Da azama ya dauko shi, ya shiga tofa masa addu'a. Sai kuwa ya yi shiru. Ya bu'de idonsa kirr yana kallon Babansa. Da murmushi Tijjani ya ce "Halo Babana, how you doing today?" Na murmusa na ce "Kana jiran amsa ne?" Ya ce "ko bai amsa ba, ya ji ni. Yasan yana tare da Babansa ba ki ga ya yi shiru ba?" Na ce "Hakane". Daga hakan ya tsoma hannu a baki ya fara tsotso. Tijjani ya ce "shima shan hannu ya fara?" Na ce "Eh! Shi ne ma yake yi kawai. Hamim din da ya fara, yanzu ya gane nono, baya yarda ya sha hannu, wannan yafi shi hakuri". Ya d'aga shi ya ce "To ba shi ya sha kada a dinga amfani da hakurinsa ana barinsa da yunwa." Na karb'e shi na gyara na fara shayar da shi. Tijjani ya tsura mini ido yana kallon yadda k'irjina suka cika, suna tsaye tunda k'ananu ne. Ya kasa hakuri ya dauko Hamim da yake barcinsa ya ce "Ka ji Momi ta ce "Ba ka da hakuri. Baban Marina da ka ci sunansa kuwa hakurinsa mai yawa ne". Shi bai bu'de ido ba. Barcinsa kawai yake yi. Ya ce "Ta shi kai ma ka sha". Na ce "kana shigowa, ina kwantar da shi. A koshe yake." Ya kankace ido ya ce "Ba kya kewata ko little?" Na ji kunya irin sosai. Na kawar da fuskata ba tare da na ce kanzil ba. Ya yi kasa da murya ya ce "Na yi matu'kar gajiya. Na matsu sosai". Na kasa amsa masa. Ya sake ce wa "Yaushe Baba ya ce zaki koma?". Murya babu amo na ce "idan mun yi arba'in mana. Ai yanzu ma saboda kukan yaran nan ne ya barmu da ana yin sati uku zai tattaramu." Ya nisa ya ce "Idan ta kukansu ne ai zan iya da su Asiyata." Na yi dariya na ce "baka san kalar kukan da suke yi ba ne." Ya ce "Da gaske nake yi miki, zan bar komai na ji da su. Kinsan yadda nake jinsu a raina kuwa?" Na girgiza kai na ce "Ina zan sani? Amma ni da su waye a gaba?" Ya tillike da dariya sosai ya ce "Yanzu kishin ki har da y'ay'an ki Asiya?". Na cuna baki na ce "Yo daga tambaya sai ka hau sarhutu". Ya murmusa ya ce "Yaushe zasu fiki, to wa ya haifa mini su?" Na murmusa ka'dan. Ya ce then fa'da mini sunan da kika ce". "Oh Allah! Bari na fa'da maka tunda kai gajen hakuri gare ka. Baban 2. Shike nan?" Da'di ya kama shi, ya washe baki dukkan hak'oransa suka bayyana ya ce "Na gamsu da suna na mussaman ne. Ke kuma Maman 2?". Na juyar da fuska ina murmushi na ce "A a ni ba Mama ba ce." Ya ce to me ce ce?" "Yaya". Ya sake cewa wanne irin Yaya kuma?. Ko da yake tare zaku taso tunda kin yi haihuwar wuri. Amma dai su ce miki Ammi tunda ba kya son Mama". Na ce "To." Su Hanif basu bar kuka ba sai da muka kusan arba'in. Kafin lokacin kuwa sun yi girma na ban mamaki tamkar sun yi watanni biyu. Amma tunda ana fa'din da Bulkachuwa suke kama dole su yi girma. Ana jibi zamu yi arba'in Baba ya ce a shirya ni, domin ranar da na cika arba'in zan koma dakina. Haka Gwaggo ta hau shirya mini kayanmu, tana ha'de su waje guda. Sannan k'anwar mahaifiyarta ce zata zo ta zauna ta taya ni rainon tagwaye har su dan yi k'wari. Ranar da muka yi arba'in tun da sassafe Tijjani ya zo daukarmu, ko kunyar su Baba baya ji. Baban kuwa bai yarda ya tafi da ni ba. Kayanmu dai ya yi ta diba yana kaiwa. Mama Baba ya ce ta rakamu, bayan ya dauko shatar mota ta fara kaimu asibiti a yiwa yara allurar rigakafi. A cewarsa baza mu hau mashin da jinjirai a kwasar musu sanyi ba. Mamah ta tab'e baki ta ce "Alhaji da alamu dai y'ay'an Yabi sun zarta na kowa daraja a wajen ka". Kai tsaye ya ce "To ai su tudu biyu suka ci, kin san Tijjani ne ubansu. Jikokin Hauwa ne fa". Takaici ya kume ta ainun. Ni kuma na dinga mata kallon ko sai yaushe zata daina Bak'ar Ta'adar rashin ri'ke girmanta. A shekarun ta ai ta wuce ta dinga irin k'ananun maganganu marasa kan gado. Wanda babu azanci a cikinsu sai tarin k'yashi da hassada. Akan dole ta raka ni, a asibitin duk inda muka wulga sai an yi sha'awar tagwaye tare da yi musu addu'a. Wajen goma da rabi na safiya muka gama da asibitin sannan muka zarce gidan. Muka tarar da gidan a gyare tamkar ina ciki. Ban yi mamaki ba domin ya riga ya saba da gyaran gida. Jimawa ka'dan ta yi mini sallama tabi motar ta tafi abin ta. Tijjani ya tisa ni gaba da rawar jiki. A sanyaye na ce "Duk gajiyar asibitin da na sha. Ka bari mana dare ya yi". Ya hau jijjiga kai yana fa'din "Ba zan iya ba. Na yi hakuri Asiya! Ke ma kin sani. Kawai ki bani hadin kai. Da daddare rainon twins zan yi, ke kuma ki yi barcinki son ran ki". A hankali na ce "Dama dai ba Baban 2 ba ne". Ya yi dariya ya ce "me kika ce?" Na girgiza kai tare da cewa "Ban ce komai ba". Ya mikar da ni, ya ja ni zuwa d'akin. Na yi turus ganin su Hamim kwance akan sabuwar katifa madaidaiciya daga gefe. Hakan ya saka dakin ya cike. Na zuba ido ina kallon yadda ya shimfida zanen gado sosia, su kuma ya jere su, duk da akwai tazara a tsakaninsu. Na ce "wannan katifar fa?" Ya ce "Tasu ce. Tunda ba ni da halin siya musu gado, shine na siya musu katifa. Kinsan ba yarda zan yi su dinga shiga tsakiyarmu ba. Can ne makwancinsu. Idan sun yi kuka zan koma na kwanta a cikinsu". Na yi k'aramar dariya ban ce komai ba. Ya ja ni jikinsa ya rungume tsam tsam yana shakar kamshin jikina. Al'amarin da ya biyo baya ba mai sau'ki ba ne. Na gamsu ya yi kewata, na kuma gasgata shi da ya ce a matse ya ke. Duk yadda na takura a dalilin yadda kayan chadi suka saka na matse, na daure na bar shi ya samu nutsuwa. Shi kuma sai fa'din "anya ba cs aka miki ba little? Ni ban ji alamun tana nan twins suka fito ba". Ni dai ban bude baki na ce masa uffan ba, amma ni da kaina na gasgata kyaun saiwowin da na yi amfani da su. Na ji dadin maganin sanyin da na sha ba ka'dan ba. *Domin samun naku kayan gyara na mussaman, ko maganin sanyi sadidan.* *SAIWOWINE da ake kawo su daga Chad da Sudan gangariya. Ku tuntu'be ni a kai-tsaye ta manhajar WhatsApp* 08032773332. *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* *Annur food Delicious Nig* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* *Wannan page din tukuici ne ga masu comments akan littafin BAK'AR TA'ADA* Kwana biyu da komawa ta Muna ta barzar amarci. Yaran kuwa tamkar almara basa kuka. Da sun yi ka'dan suka sha nono sai su yi kwanciyarsu sai an idar da sallar asuba zasu farka. Yana dawowa kuwa zai d'ora mana ruwan wanka. Da aka sa zai juyo, ya taya ni mu yi musu wanka. Ni da kaina na tabbatar zai yi wahalar gaske a samu miji irin Bulkachuwa. Domin duk aiyukan gida ba zai zame masa komai ya yi ba. Ina jin dadin Supplement din FASEELAT. Sun taimake ni wajen gyara mini ruwan nono da sake hade ni. .G H.T duniya ne na yarda *07039269802*. Rainon yaran nan kuwa ba abin da ba ya yi. Kafin na yi musu hidima d'aya ya yi musu biyar. Ko pampars suka bata, ba ya jin komai zai cire ya wanke musu ya saka musu wani. Idan sun yi barci, sai kuma ya dawo yana tiritiri da ni. Tun tafiyar tamu bata yi nisa ba na fara fa'din madallah da aurensa a zuciyata. Ban dai furta a fili ba ne. Kwana duk da kuwa yana da na'kasu, sai dai alherinsa yafi tsiyatakum yawa. Kwana biyar da komawa. Baba Lami ta zo daga kangire. Wacce matsayin kaka ce a wajena. Tunda k'anwar mahaifiyar Gwaggo ce uwa daya uba daya. Ranar da ta zo, a ranar ya koma Bauchi. Cikin sau'ki da rangwame nake rainon yan biyu. Basu da fitina. Sannan Baba lami mace ce mai kazar kazar ainun. Abin da nake yi ka'dan ne. Watana biyu da haihuwa na koma kan sana'a ta. A hankali kuma Tijjani yana samun rufin asiri a zamansa a baucy. Tunda abinci dai baya yanke mana. Iyakar kokarin jarfinsa yana yi. Duk sati zai taho musu da Pampers. Ni kuwa kayan shayi duk sati ne. Idan na ce "Basu kare ba". Ya dinga fa'da akan me bazan dinga shan shayi mai kauri ba, alhalin ina shayar da yara har biyu. Ga su nan su sun yi girma ni kuma na sake zuke wa. Watarana Baba lami ta ce masa ba rashin cin abinci ba ne, wasu matan idan suna shayarwa hakan suke yi. Sai sun ya ye sannan su yi kumari. Baba Lami bata tafi ba sai da muka kwashe watanni kusan biyar a tare. Lokacin su Hanif na da watanni shida. Muka ha'da mata alheri sosai. Sannan suka tafi da Gwaggo da Yaya Ummi bikin da za'a yi a can Kangire. Na so zuwa, amma ya yi mirsisi ya hana. Sannu a hankali muke rayuwa, bamu cika samun matsala ba, tunda kwanakin da yake yi a Bauchi sun fi wanda yake yi a Toro. Kullum idan ya dawo sai ya ce "ki tsananta yimini addu'a little. Mahassada sun kewaye ni a kasuwar nan. Ga shi an rasa gane inda matsalar take kullum Alhajin da muke wajensa sai karayar arziki ya ke samu. Ina jin tsoro k'warai da gaske. Cikin tausayi na ke kwantar masa da hankali da kalamai masu taushi. Wani zuwa da ya yi, ya ce "mu shirya zai kai mu Bulkachuwa mu yi sati. Na dinga murna domin rabona da zuwa tun kafin na haihu. Ga shi yazu watannin su tara har sun fara tsayawa. A yanzu kam na gasgata kama suke yi da Bulkachuwa. Domin suma haka suke dogaye, masu gaba manya. Ba wanda zai ce ni ce uwarsu. Domin manya ne sosai, sannan ni yar tsurut ce sosai. Kawai faratuna suka diba, da kuma yan k'ananun kamanni. Amma kammanin ubansu yafi yawa a tare da su. Tun yanzun kuma halayyarsu ta banbanta. Haneef mai sanyi da hakuri ne. Sai ya yini baka ji kukansa ba. Kafin ya nemi nono sau daya Hamim ya nema sau uku. Zai yi wahalar gaske ya damuki d'anuwansa yasa shi kuka. Amma Hamim kullum cikin nukurkusrsa yake. Ga shi da shegiyar kiwa. Ko wajen Babansu sai ya akan dole yake zuwa. Ko idan ya ga ya dauki Hanif zasu fita. Shi dai kullum yana jikina. Ko k'unshi zan yi, sai dai na ha'da masa kayan wasa a kusa da ni. Ko ya ce ",sai na goye shi. Sabanin Hanif da ba ya yin kiwa. Kowa ya mika masa hannu zuwa yake yi. Shiyasa ma na fi kai shi gidan Yaya Ummi ya yini tunda yanzu ba ni da nisa da ita. Kullum Bulkachuwa sai ya ce halina ya kwaso. Domin mafad'aci ne na gaske, ga kuka. Idan ina mita akan halinsa Gwaggo ma ce wa take yi hakan na yi mata. Haka ta sha fama a goyona. Bana yarda a dauke ni. Ko band'aki zata shiga sai an yi artabu da ni. Da yammaci muka isa Bulkachuwa. Babah sai ina ka saka take yi da ni da yara. Komai ta mika hannu a kai sai ta dauko ta ajiye a gabana. Yara kuwa kayan wasa sabbi sun fi kala uku tamkar dama a wajenta suke. Na kasa ha'kuri na ce "Babah wadanda kayan wasan fa?". Domin ihisan ba a garin take ba. A cikin Bauchi take bari na yi zaton na yaranta ne. Da walwala ta ce "Tunda ya ce zaku zo na siya musu, tunda na ga mai sunan yayan nawa rigimamme ne. Shi dai bai kwaso halin mai sunansa ba. Hanif ne ya kwaso halin mai sunansa." Nasir da yake gefe ya ce "Su Babah ana yabon sunan masoyi". Ya bani dariya na rufe fuskata na dinga yinta. Ta mike sabe da Hanif tana fa'din ja'iran yara bari na baku waje. Shi dai Tijjani bai ce komai ba. Asalima matse wa ya yi ko dariyar bai yi ba. Kwana biyu ya yi, ya barmu ya wuce Bauchi. Bayan dakina da na Gwaggo ba inda nake samun natsuwa irin a dakin Babah. Domin wata irin mua'amala take yi da ni mai dadi da tattali. Bata taba nuna surukunta a tsakaninmu ba. Sai ni ce ma nake jin kunyar yin wasu abubuwan a gabanta. Ita kuwa da taga hakan zata balbale ni da fa'da tana fa'din bata son rashin kunya. Har yaushe na zama matar tasa da zan ture ta a uwa na mata kallon suruka. Na sake na yi komai yadda nake so kamar yadda nake yi tuntuni. Da kanta ta dafa mini kazar da na tabbatar ta mata ce. Kunya ta kama ni. Ita kuwa fadi take ci ki sha romon. Tun lokacin haihuwar na siya na dauka zaku zo yawon arba'in. Tunda baku zo ba. Na ajiye nasan a can ma za'a gyara ki." Na rasa yadda zan yi, ita kuwa ko a jikinta. Ranar da Bulkachuwa ya dawo. Da daddare an hadu a falonta ana ta hira cikin walwala ya kutso da maganar yana son mu koma Bauchi gaba'daya. Ta ce "ka dai kafe. Yanzu kam tunda yaranta sun yi k'wari ba zan hana ba. Allah ya bada sa'a. Dama har da tunanin yadda sana'ar ta zata durk'ushe ne. Amma In sha Allah a can din ma sannu a hankali za'a santa." Ni kuma sai kawo masa abinci abubuwa nake yi. Gaba'daya na kasa sukuni. Babah da kanta ta gane yanzu kam sonsa nake yi da dukkan zuciyata. Washagari ana zaune bayan mun karya. Sai kawai ya kalle ni ya ce "A irin wannan ranar ta shekaru uku baya kika zo har nan kika ce ba kya sona Asiya". Nan da nan na ji tamkar k'asa ta tsage na shige. Kunya ta rufar mini. Na rasa yadda zan yi. Sai kawai na fara kuka ina ce wa "Idan juninka tashin tashina ne, da son sai ka kunyata ni, to ni ba damuwa zan yi ba, kai ne zaka ji kunya Wallahi". Nasiru ma cikin dariya ya ce "Ai kuwa nima na tuna yawun da kika kwalbana masa a fuskarsa. Yau kuwa sai faman girmama lamarinsa kike yi". Na sake rushe wa da kuka ina ce wa "Ai kai dama baka fa'din gaskiya". Babah ta ce "Yo ni ke kika fi ba ni haushi, to kukan na mene ne? Ware wa zaki yi ai ku yaga, suma ki nutsu ki fadi irin nasu al'amarin da baza su so a taso musu shi ba." "Nasiru ya ce "Ni dai babu abin da zata fa'da a kaina, sai dai ko akan mijinta". Tijjani dai tunda ya kunyata ni bai sake ce wa ba. Jimawa ka'dan Babah ta mike ta shiga cikin gida. Nasiru ma ya mike yana ce wa "Hajiya Yabi bari na fece tun Babah bata zo ta fa'da miki wani abu a kaina ba." Ko kula shi ban yi ba. Yana fita na kalli Tijjani na ce "Na gode sosai Baban 2" Ya yi murmushi ya ce "wannan godiyar fa! Ta mece ce?" Na matso hawaye na ce ",Na gode da kunyata ni da ka yi, na gode da wannan sakayyar". Ya dara ka'dan ya ce ",Kin san na fa'da miki lokaci zai zo da zaki ji kunyar abin da kika yi". A hassale na ce ",To mene ne zaka tayar a gabanta? Gaskiya kada ka sake yi mini irin haka. Idan kuwa ba hakan ba kasan kai ma ka mini laifin da ban ta'ba bude wa an ji ba". Nan da nan ya shiga nutsuwarsa ya ce "Ai ni ba da bacin rai na fa'di hakan ba. Amma ba zan sake ba, mu rufe maganar haka nan. Na girgiza kai na juyar da fuskata gefe. Ya shiga kiran sunana a hankali, na ki juyowa. Ya diririce. Ya ce "Asiya wasa fa nake yi miki. Me zai sa mu yi fa'da a gaban Babah". Na ce "Ai so kake ka bakanta ni a wajen ta, shi yasa ka dauko wannan maganar". Ya marairaice ya ce "Billahillazi ba hakan ba ne. Gaba'daya ya rikice jin na lauya magana zan tado da tashin hankali. Ya dinga lallaba ni da son sai na dawo da walwala ta. Ni kuma ina sane na yi masa hakan. Bamu bar garin Bulkachuwa ba sai da muka shafe sati biyu. Da zamu tafi, tamkar wanda muka je fatauci saboda kayan da muka samu. Lafiya k'alau muka isa Toro. Kwana biyu a tsakani ya koma Bauchi. Kwatsam aka tashi da mutuwar mijin Nasiba. Wannan mutuwa ta bigemu, domin babu jinya sai mutuwa. Ashe kasurgumin dan shaye shaye ne. Can wajen sharholiyarsu rikici ya kaure tsakaninsa da abokinsa ai kuwa ya daba masa kwalbar a kahon zuci ya mutu a wajen nan take. Gaba'daya maganar ta cika Toro da kewaye. Na tausayawa Nasiba kwarai da gaske, duk da dama ba zaman dadi take yi da shi ba. Duk cikinmu ita ce bata samu sukuni a gidan aurenta ba. Yaranta biyu Muhsin, da kuma Maryam da bata fi watanni shida da haihuwa ba. *Watanni bakwai a gaba* Zuwa wannan lokacin mun koma Bauchi da zama. A satin nan kuma na yaye yara. Bulkachuwa aka kaiwa Babah su. Kwance nake ina fama da zazzabin da ciwon nono ya zuba mini. Ga kewar yara, abin sai ya hadu ya kwantar da ni. Nasan Hanif ba shi da matsala, amma Hamim kam sai Allah. Rashinsa ya fi takura ni. Tijjani kuwa sai tsokana ta yake da fa'din Hanif ne kawai zai dawo, Hamim ya zama dan Bulkachuwa. Bana ce wa komai amma na sani zolaya ta yake yi. Sai da na sha allurai sannan na warware. Sannu a hankali na shiga saboggina tunda anan Bauchi ma na fara sanuwa a wajen k'unshi da kitso, sai dai ba kaman Toro ba. Matsakaicin gida ya kama, cikin madaidaiciyar unguwa. Cikin nutsuwa da rufin asiri mukr rayuwarmu. Har yau din nan Bulkachuwa tattala ni yake yi. Baya kaunar abin da zai ha'damu rikici sai dole. Baya mini fishin da ya wuce na kwana d'aya. Ni ce dai nake jarumtar share shi na lokaci mai yawa. Duk da ni din ma karfin hali nake yi. Yanzu haka Tijjani yana da nasa teburin a cikin kasuwar ma'ana ba k'arkashin Alhaji yake ba. Watanni uku ya karbi ku'dina ya mallaki wajen flda zai ajiye teburinsa. Zobena daya muka siyar. Yanzu haka jiya ya kai ni na zabi wanda nake so ya siya mini a madadin nawa. Na sani ba dan ya samu damar biyan ba ne, sai dan yana son ya biya ni ne. Hakan kuma bai sa sun rabu da Alhaji Auta ba. Ana cikin haka guda cikin kamfanin sadarwa ya nemi kafa turakan ayyuknasu cikin unguwar da filin Tijjani yake. Gaba'daya mutanan da suke da fili a wajen kowa fata yake a ce su karbi nasa, tunda haya zasu kar'ba. Alhaji Auta har addu'a ya baza a yi masa ko ya samu ya d'an farfado. Kamfani har yanzu zagaye yake tare da wakilinsu da suka san ilimin kimiyya suna ta auna inda zasu fi samun sabis. Gaba'daya Tijjani bai sa hankalinsa a wajen ba. Gara ma jiya ya ce mini ku'din da mutum zai samu a shekara d'aya kacal ba k'ananu ba ne. Ina bu'de baki na ce "Idan akwai alheri a cikin samun da za'a yi, Allah ya saukar a kan filinmu". Ya ce "Kayya! Amma tunda Allah kika ce ai magana ta k'are. Ameen". Muka bar magana a hakan. A wannan tsukun auren su Yaya Ammar da na Yaya Rabiu da su Kaltume ya zo. Muka shirya muka tafi tare. A can muka tarar da Babah da y'an yayenta. Hamim na ganina ya cakume ni, ya cukuikuiye hijabina wai bazan gudu na bar shi ba. Hanif kuwa kawai kwantar da kansa ya yi a jikina. Tijjani ya kalle shi ya ce "Kai ma ka bi bayan d'anuwan ka, baka ta tawa ko?" Ya kalle shi kawai. Ya yafice shi tare da ce wa "zo mana Babana". Ya kuwa isa gare shi ya kwanta. Yayin da Hamim ya rikice sai ya sha nono. Da k'yar Tijjani ya yane shi suka fice. Babah ta ce "Ai ban yi zaton darun d'anuwana ya kai haka ba sai yanzu". Na ce "Ai ba shi da sau'ki Babah. Hanif ya fi sassauci". Ta ce "Babu hadi ma. Allah ya musu albarka ya tsare su. Ki yawaita yi musu addu'ar tsari da kuma kambun baka". Cikin na ce "To". Duk inda na shiga sai an kalle ni. Da na juya baya za a hau zancena. Haka Ikilima ta jiyo mini gulmar da sa'anina da muka taso tare su Saratu su Maijida. Suna fa'din ",Ai gaba'daya Bulkachuwa tsorona yake ji saboda ina da ku'di. Duk kafafar da nake yi da burgar kwalliya da yadikan yan gayu na Umm Nihla collection. Ni nake yiwa kaina ba shi ba ne. Su kuwa sun gode Allah mazajensu ne suke dawainiya da su yadda Allah ya hukunta. Barin Maijidda da a yanzu suke Kaduna. A dalilin Yaya J ya samu aiki a kwalejin kimiyya ta kaduna(Kad-poly). Gaskiya ne duk ta fimu d'aukar ido. Amma kuma ba wai ta fi kowa kwanciyar hankali ba ne. Ko wacce ita tasan yadda take zaune a gidanta. Nasiba tuni ta sake dawowa gidanmu gaban Dada. A yanzu da bata da aure ma tafi walwala da kwanciyar hankali. Tunda yayanta Ammar na kula da ita daidai gwagwado. Sannan iyayen mijinta suna ri'ke da Muhsin cikin kulawa, Maryam din da take shan nono ma sukan yi mata aike lokaci zuwa lokaci. Gaba'daya ta murmure ta dawo da jikinta da ta rasa a baya. Sai daga baya aka gane komai na d'akinta ashe ya siyar tunda mashayi ne kuma dan caca. Da ace wata a k'ofarmu hakan ta same ta da anyi yamididin halin d atake ciki. Amma wannan shiru ake ji. Tallafin da take samu ya sanya take figa take yin y'an sitturu da kayan kwalliya dan haka fes take bata da makusa. Na yi tsuka na ce "Basu da abin yi ne, koma a ya ya na ke rayuwa ai babu ruwansu, tagayyara da ake mana fata kuwa ba zamu shige ta ba in sha Allah." Amma a tunzure nake kwarai da Maijidda. Na kuma ku'dire indai ta sake ta mini maganganun banza yadda ta saba yi mini, idan mun hadu a taro, to a wannan karon zamu sake gwada yar kwanji dan na tuna mata baya. Ta fitine ni da yawa. Nazira da take gefe ta ce "Sanin kina da daraja ne a wajen mijinta ya sanya ta washe ki, ban da haka kina matar wani, ta shafa miki lafiya mana, tunda tasan a musulunci mace bata auren miji biyu. Da a ce Nasiba ce ke, ai da tuni Maijidda ta kusa zama gawa, domin ba abin da zai hana mijinta fitowa neman auren ki, tunda har gobe yana son ki". Da hanzari na ce "Allah suturi bukui. Ai sai yanzu na fahimci tun asali ba wani sonsa na yi ba, shak'uwa ce da soyayyar k'uruciya. Yanzu da na saba mua'amalantar barden namiji irin Baban 2, mai zan yi da dan karamin sauron mijinta? Su je can su k'arata har abada ba zai sake burge ni ba." Dadi ya kama Adda Nazira ta fashe da dariya ta ce "Ina komawa zan fa'dawa Baban su Abid tun yanzu Yabi ta fara fa'din madallah da auren Yaya Bulkachuwa". Kunya ta dan rufar mini na ce "eh ki fa'da masa". Haka aka yi bikin aka gama lafiya. Baba Maryo da kanta wani gani gani take yi mini da ban san dalilinsa ba. Ba dama ta ga Babah ta yi mini wani abu sai ta ce "Ba hakan aka barki ba, da aka tashi kame mata Tijjani har da uwarsa aka ha'da ban da hakan irin wannan gudun zuciyrta da kike yi har ina? Yara na son zuwa wajen uwarsu kin kanekane kin rikesu kina fa'din ta je ta yi hidimar jama'a. Ke kuma kin zama mai raino'. A lokacin da take fa'din haka ina tsaye, wata irin fargaba ta kama ni, domin na hango kishina ke cinta ba ka'dan ba. Na laluba ko na yi mata laifi ne, amma ban ga na yi mata komai ba. Wata'kila zamana lafiya a gidan aurena ne yake mintsinarsu. Tunda da safen nan ma sai da Baban Tsakiya da na kasuwa suka tambaye ni, wai na fa'di irin zaman da nake yi, idan babu dama sai a ha'kura ramar da nake yi ta yi yawa. A dakin Dada a gaban kuma Babah. Na kalle su ina mamakin manufarsu. Domin ni dai jefi jefi Tijjani na matsa mini na kira na gaishe su, ina kuma yi tunda tisa ni yake yi a gaba. Amma su kam tunda na yi aure ba wanda ya ta'ba kirana ya ji lafiyata, ko ya ji ya ya na ke? Baban Marina ne kawai yake mini hakan a cikinsu. Amma abin mamaki sune da fa'din wai na rame tsabar sun saka mini ido suna kuma adawar sun jimu k'alau ni da Tijjani. Na bu'de baki cikin nutsuwa na ce "Satin jiya na yaye yara, na yi fama da zazzabi a dalilin haka. Sannan ni ba ni da matsalar komai ina cikin rufin asiri mai yawa. Allah ya saka muku da alheri bisa bawa Tijjani aurena da kuka yi. Bana fatan sauyi ko a aljannah ne". Baban Kasuwa ya ce "To ya isa zabiya! Mun ji, mun ga ne ba sai kin zarce da rashin kunyar da kika saba ba." Baban Tsakiya kuwa ya ce "Na tashi na basu waje sun sallame ni, dama sun nuna kulawa ne dan sun gane muna zaginsu a bayan idonsu akan basa kula da sha'anin yan k'ofarmu. Amma zan fara yi musu rashin kunya da iyashege." Na fito zan shige Babah da take bawa tagwaye koko da kosai. Suka fashe da kuka wannan karon kukan har da Hanif. Murya babu amo ta ce "Zo ki zauna, yunwa suke ji". Na dawo na zauna shi ke nan kuma suka yi shiru. Suka ci gaba da cin abincinsu. Muna haka Tijjani ya shigo dan haka na sid'ad'a na fice tunda suna ganinsa. Washagari muka koma, daga ni har Tijjani so muke mu tafi da yaranmu. Tunda sun yi sati biyu. Amma kowa ya kasa fa'dawa Babah da ta daure fuska bayan ta fahimci take takenmu. Sai da zamu tafi ta biyo ni har zaure tana fa'din "Zan dawo muku da su, amma sai kin warware kin murje. Kina ganin dai yadda ramar ta ki ta janyo cece kuce. Ki kwantar da hankalinki, nan da wata ma zasu dawo." Kunya ta kama ni, na shagwabe fuska na cuna baki na ce "Ni fa Babah ban damu da su ba, su zauna ma gaba'daya a wajen ki, ba ni da matsalar komai". Ina rufe baki Tijjani ya yi maza ya ce "Bilhiillazi karya take yi miki Babah." Ta gwale shi da ce wa "ko k'arya take yi, ai ta saya, kai da baka da kunya ai ka bu'de ka nuna na baku yaranku". Nan da nan ya yi shiru, ni kuma na yi dariya tare da yi masa gwalo. Da hakan muka rabu, ta koma cikin gida, mu kuma muka tafi. ✍️. *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *Tuni labarin ya fara nisa, yana kuma da dadi da darasi*. *08089965176* *07084653262* Da wuri muka shiga Bauchi. Ya taimake ni muka gyara gidan, muka yi girikin abin da zamu ci. Dai da yamma ya fita. Kwanci tashi asarar mai rai, kwanaki suka yi ta shud'ewa har muka samu sati da dawowa daga Toro. Daga ni har Tijjani bama jin da'din rashin yaranmu a tare da mu. Kewarsu muke yi sosai. Amma dukkanmu kowa ya bar abin a ransa, mun bisu da addu'a. Muna cikin hakan ba zato sai aka kira Tijjani tare da albishir din filinsa kamfanin sadarwa yake bu'kata. Zasu karbi hayar wajen na shekaru uku. Idan wa'adin ya cika, wata'kila su siya gaba'daya ma, matu'kar mutane sun karbi sabon kamfanin da hannu biyu. Farincikin da muke ciki ba ka'dan ba ne. Mussaman da Tijjani ya tabbatar mini ku'din ya isa ya sayi gidan da muke ciki da kuma mota golf da ake yin sufuri da ita. Cikin Ikon Allah kuwa bayan cike cike, da kai komo suka tura masa ku'dinsa cas ta asusunsa na banki. Hassada da bak'in-cikin a wajen masu filaye a wajen tamkar su jefa shi wuta. Hatta Alh Auta bai iya boye ba'kin cikin da ya ji ba.duk da Tijjani ya bashi kyautar dubu dari a cikin ku'din amma hakan bai sa ya gode ya ha'diye ba'kin cikinsa ba. Wani k'aramin gida da yake gabanmu ka'dan, Tijjani ya siya. Sabon gini ne, fenti ne kawai ba'a yi ba. Mai gidan ya d'aga gidan xai siyar a dalilin ya samu wnada ya fishi yalea zai siya. Da yamma muka je na ga gidan. Karamin guda ne ainun. Sai dai kuma an tsara shinda kyau. Kafin udan an shiga daga farkon akwai daki mai dauke da band'aki. Wanda tsarinsa yafi dace wa da na maigidan. Daga ciki kuwa k'aramin tsakar gida ne, sai falo mai dauke da dakuna biyu, ko wanne da bandakinsa. A tsakar gidan akwai kicin da kuma wani band'akin daga gefe. Gidan ya sake kawatuwa a dalilin an zuba masa tayal ta ko'ina. Ta bayan dakunan kuma akwai doguwar hanya, bata bille wa, amma dakuna zasu sami iska, sannan za'a iya daura igiyar shanya a wajen. Farin ciki ya mamaye ni. Yau ga ni zan yi d'aki mai dauke da band'aki a cikinsa. Lallai komai lokaci ne. Ya kalle ni da murmushi ya ce "Ya yi miki?" Na bu'de baki na ce "sosai ma kuwa Baban 2. Ubangiji ya k'ara arziki, yasa rabo ne." Da walwala ya ce "Ameen, tunda ya yi miki bari na je wajen dillalan, mu nemi shaidu a je a biya". Na fa'da jikinsa ina jin farin ciki na walagigi da ni. Na dinga jera masa fararen addu'oin da suke sanya shi farin ciki. Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, ciniki ya fa'da ya yi fentin da ba'a yi ba. Ya sayi katifa ya saka a d'akinsa. Dakina kuwa aka shirya kayan gadona bayan an musu kwaskwarima, katifar gadon muka bari a tsohon gidan kafin mu tare. D'akin yaran kuwa aka saka musu katifarsu da ya siya musu yun suna jarirai. Kujera ya canja mini, tawa ta tsufa da yawa, tunda ba mai tsada ba ce dama. Yanzun ma mai L ce amma mai daraja sosai. Aka makala tibinmu a bango shike nan, domin a kicin a saka firij tunda da fili. Gida ya fito ras. Na dan yi siyayyar kayan kicin wanda zan iya. Na sayi kafet da labule kalar kujerar. Muka ja gida muka rufe. Da kansa ya je Bulkachuwa ya taho da Babah da yara. Ta zo ta ga gidan da Ubangiji ya mallakawa Tijjani cikin sau'ki. Ta dinga hawayen farinciki, tare da addu'ar Ubangiji yasa likkafa ta cigaba. A fili ta ce "Da ikon Allah sai kun yi arzikin da kowa sai ya ci arzikinsa. Ina da yakinin Ubangiji ba zai juyar da addu'ar da nake yi muku ba". A ranar ta tafi, duk yadda muka so ta kwana tare da mu, amma fir ta ki. Ta bar yara, tare da zolayata wai gasu nan su mini sati biyu, zata turo Nasiru ya dauke su. Haka ya je Toro ya sanarwa da iyayenmu alherin da ya samemu, tare da basu Ihisani. Mota guda suka taho ganin gidan da su Baban Tsakiya nasu gasgata Tijjani ya siya ba. Tun wuri ya kawo mini kayan miya da nama ya ce "Ki yi abinci da yawa Asiya. Yau mutanan Toro sun taho ganin gidanmu. Nasiba ta ce mini har da Dada". Na dan ji babu da'din yadda ya ce Nasiba ta fa'da masa. To waya suke yi ko kuwa ya ya? Na daure na ha'diye ban tuhume shi ba. Na hau hidimar aikina. Shi kuma ya ri'ke hannun yara suka tafi siyo ruwa da lemo. Na kammala abincin na yi wanka. Ina cikin shiryawa na ji tsayuwar mota, a gaggauce na gama shirina. Na fito ina marabtasu. Na ri'ke hannun Dada ina yi mata maraba ta mussaman. Tuni su Baban Marina, da Baban Tsakiya har da Baban kasuwa suka isa falo. Baba Maryo na cikinsu. Tare da Tijjani muke ta ajiye musu kwanukan abinci da abin sha. Yadda muke shige da fice muna hidimarsu tare, abin ya yi matu'kar burge Dada da Baban Marina. Domin sai addu'ar alheri suke bin mu da ita. Su kuwa ragowar wani irin kallo suke bin mu da shi wanda na rasa gane inda suka dosa. Domin ba wanda ya taya Dada da Baban Marina albarkar da suke sanya mana. Sai da suka ci, suka gyatse. Suka je masallaci suka yi azahar. Sannan muka d'unguma ganin sabon gida. Dada sai hamdala take yi, yau Ubangiji ya gwada mata ta ga gidan mai sunan manya. Baba Maryo kuwa da ta shiga falon ta leka ta ga dakuna biyu, ko wanne da bayi a ciki. Tana bude baki sai ce wa ta yi "Gida kuwa a yalwace. Ban da wuyar zama irin ta y'ay'an yau. Mace biyu ma sai su yi zamansu wata bata takura wata ba. Tunda akwai turakar maigidan". Zuciyata ta yi matu'kar bugawa, domin na fahimci akwai k'ulli a zuciyarta game da ni, tunda muka je biki na ga tana rawar jiki wajen Babah tare da bagarar da ni, nasan akwai abin da take nufi da ni. Maganar da Tijjani ya fa'da mini dazu na ce wa Nasiba ta ce tare da Dada suka taho, ta sake dawo wa ta rib'anya zullumin da na shiga. Na daure ban ce komai ba illah yak'e da nake yi. Gaba'daya Dada da Baban Marina ne suke yin murna ta fisabidillahi a cikinsu. Baban kasuwa da ya bu'de baki sai ce wa ya yi "To Tijjani gida ya yi kyau. Amma ku shiga a hankalinku, ku dinga jin tsoron Allah. Harkar nan ta neman maza ta zama ruwan dare a tsakanin matasa. Kada ku bari manyanku su rude ku su dinga baku kudade kuna b'ata gobenku". Na kalli Tijjani na ga ya yi kasa da kansa yana fa'din"Da ikon Ubangiji zamu kiyaye iyakokon Ubangiji." Zuciyata ta dinga tsallen na mayar masa da martani. Amma idon Baban Marina, da na Tijjani suka mini cikas. Domin na sani dukkansu baza su mini ta da'di ba, idan na yi masa rashin kunya a gabansu. Ban gama jimamin isgilancin Baban kasuwa ba, sai kuwa Baban Tsakiya ya ce "Haka KUMA a kiyaye cin riba, da shiga kungiyar masu daukar bindiga suna kwace wa jama'a rayukansu da dukiyoyinsu suna azurta kansu. Wannan zamani da wuya ya ke." Dada ta ce "Ina addu'a akan duk rintsi kada a jarrabi iyalina da aikata kaba'ira. Ban san me ya hana Baba Maryo sakin nata bakaken ba. Tunda ita ma bata nufinmu da alheri. Shi dai Baban Marina bai ce musu kala kanzil ba. Sai da suka gama. Ya nisa ya ce "Ubangiji ya yiwa neman ka albarka, ya tsare ka, ya baka arzikin halali mai yawa. Ubangiji ya saukar da farinciki a kanka da iyalinka. Allah ya tsareku gaba'daya, ya shirya muku zuri'a." Na daddage da k'arfi na ce "Ameen Babanmu. Ameen dattijon arziki, uban marayu, har masu uban ma.." Baban Marina ya faki idonsu ya galla mini harara. Gane nufinsa ya sanya na ha'diye sauran maganar da na yi nufin zubarwa. Baban Tsakiya ya kalle ni cikin fishi ya ce "Shi ka'dai ne Ubanku?' Da azama na ce "Duk nan ina da uban da ya fika ne Baba? Kai ne ka d'aura mini aure fa". Ya furzar da iskar baki ya ce "Na dauka kin manta saboda kina ganin kun fara shigo wa gari ai" Kan dole na yi shiru. Ban sake ce wa komai ba. Amma dai kam zuciyata a tunzure take ainun. Muna dawowa suka shiga mota suka tafi. Bayan Tijjani ya saka musu kwanduka kayan miya, ya kuma biya ku'din man da suka zubo a motar. Kan dole nabi bayansa wajen yi musu godiya da addu'ar sauka lafiya. Dan kuwa ba dan tsoron Baban Marina ba da iya shi da Dada zan ware na yi musu godiya da fatan su sauka lafiya. Tunda abin nasu babu arziki. Ban da fitina daga zuwa ganin abin arziki, babu saka albarka, babu fatan alheri, babu nasiha mai da'di. Sai mugun k'ulli ya biyo baya. Har da jinginawa mutum mafi munin zunubi irin luwadi. Kaico ga mutanan da basa furta alheri. Hasara da tabe wa ga masu hassada da k'yashi. Àllah ka shirye masu shiryuwa kawai. Tunda suka tafi Tijjani ya kasa tafiya kasuwa. Kwanciya ya yi har dare, sallah kawai ke fitar da shi. Na sani kuma maganganunsu ne suke dafa shi. Duk da bai yarda ya biye ni mun yi zancensu ba. *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*. Kwananki ka'dan muka tare sabon gidanmu mallakinmu ba wai haya ba. Cikin dare mun gama mua'amalarmu, mun yi wankanmu a cikin d'akinmu. Munana kwance ya kankame ni, a kunne ya rad'a mini "little kamar yau kike mini kukan band'aki a daki kike so. Na ce miki da sannu zan miki, a wanccan lokacin baki gasgata ni ba, sai kika ce wasikar jaki nake yi. Tun daga waccan rana ban sake yin sujjada ban ro'ki Ubangiji ya bani damar da zan miki band'aki a cikin d'aki. Sai ga shi a kusa na samu damar ba tare da zato ko iyawa ta ba." A hankali na ce "Baban 2 kana da tashin tashina Wallahi". Ya yi dariya ya ce "Indai ba sharri ne da ni ba ai da sau'ki Maman 2". Ban gama wartsake wa daga kunyar da ya saka ni a ciki ba. Ya sake baro wata maganar. Ta hanyar ce wa "Na k'osa ki yi ciki little kada ki fara yi mini borin idan ban miki ciki ba zaki tafi ki bar ni". Na kai masa duka a k'irjinsa ina kukan shagwaba tare da fa'din "Bana son irin hakan da ka ke yi mini Baban 2". Ya ri'ke ni yana dariya ya ce "Ba gaskiya na fa'da ba? Kin ga twins sun yi wayo, suna gudunsu ko ina, idan kin samu ciki yanzu babu damuwa, kafin ki haihu sun sake girma. Na ga kuma Babah so take ta rabamu da su. Idan kina da wani a hannun ki ba zaki wani damu ba". Ban ce komai ba. Domin kunya ta yi mini k'awanya. A wannan tsukun da'din da Baban 2 ya jiyar da mu ba ka'dan ba ne. Domin suturun da baya samun sukunin yi mini sai da ya mini matsakaita kala biyar. Kusan karamin lefe ya yi mini. Tunda komai sai da ya siya mini daidai misali. Haka yara ma ya yi musu siyayyar kayan sawa da kayan wasa. Cikin nutsuwa muke rayuwa, ina mutunta shi tare da girmama shi. Haka shima yake kaffa kaffa da ni. Idan ya ga zan rikice masa, zai bar komai ya rarrashe ni, ya kwantar mini da hankali. Domin budin da ya samu, ya sanya shima ya sabunta suturunsa, ya sake zama hadadden gaye. Tunda yanzu ne ya cika shekaru talatin. Ma'ana yana cikin shekarun samartaka da k'arfi. A lokacin ni kuma nake shirin shiga shekaru ashirin. Gaba'daya na kwarzabi raina, domin ina ganin zai iya samo zabgegiya ya aura. Ban ta'ba bu'de baki na yi masa k'orafi ba. Amma a ankare nake matu'ka da gaske. Ba a jima ba motar da ya siya ta golf ta iso. Ya zaunar da ni ya fa'da mini zai fara kai kayan miya garuwa ranakun kasuwanni. Tunda zaman kasuwar yana neman gagarar sa. A dalilin yadda Alh Auta da sauran wadanda suke ganin ya je ya same su a wajen amma ya kere su. Sun ki fahimtar Ubangiji ne yake raba arziki a sadda ya so. Cikin nutsuwa na ce "Wai filin nan naka babba ne da suka karbe shi da ku'di masu nauyi irin hakan?". Shima a nutse ya ce "Babba ne ainun. Idan raba shi za'a yi zai yi fuloti uku manya. Sannan wajen ya yi daraja baya ga hakan a bakin titi wajen yake. Kar kuma ki manta tsawon shekaru biyu suka biya. Shiyasa nake son na juya ku'din da ya yi saura mu dinga samun na abinci da sauran bu'katun yau da kullum. Yaranmu gaba ka'dan makaranta za'a sasu, boko da Islamiya, kin ga duk hidimar ku'di ce. Ga yadda kullum rayuwar take sake tsananta. Akwai bu'katar na yi aiki tuk'uru. Sai na barwa Allah ya taimake ni a inda zan gaza". A sanyaye na ce "Da ikon Allah na zaka gaza ba Baban 2. Ubangiji ya yiwa kokarinka albarka. Ya tsare ka da dukkan sharrin masu sharri. Allah ya raba ka da sharrin karfe da titi." Ya rungume ni sosai ya ce "Ameen Maman 2. Ina son ki, ina alfahari da ke. Allah ya barmu tare cikin aminci". Da rauni na ce "Ameen. Amma kasan ina shiga zullumin kada wata ta zo ta k'wace mini kai?" Na fa'da hawaye na ziraro mini. Ya tsananta rik'on da ya yi mini ya tausasa harshe ya ce "me yasa kika karaya haka Asiya? Ban ji akwai wata mace da zata firgita ki ai. Ni naki ne, a hannunki na ke. Ki daina damuwa da abin da yake gaibu ne. Al'kawarin da zan miki d'aya ne. Har abada kin wuce wula'kancina. Kina da alfarmomi masu yawa da babu wata macen da zata samu irin alfarmomin ki a waje na." Bai bar ni ba. Sai da na samu nutsuwa. Can kuma ya ke ce da dariya ya ce "Ubangiji yana ta kama mini Asiyata. Kamar yau take fa'din me zata yi da Basamude irina. Kin tuna amsar da na baki a ranar?" Na k'yale shi domin yanzu ya riga da ya lakanci tuno mini abubuwan da suke kunyata ni. Bai bar maganar kamar yadda na barta ba sai da ya ce "A lokacin na ce miki akwai ranar da zaki yi kuka akan son basamuden nan. Sannu a hankali komai na fa'da a kanki Ubangiji yana zartarwa. Na share ban yarda na tanka shi ba. Cikin Ikon Allah Tijjani ya fara safarar kai kayan miya kasuwanni daban daban na cikin jahar Bauchi da makwabtanta irin su Jigawa. Da wuri yake fita. Ya je ya kai. Idan zai dawo kuma sai ya lodo mutane. Gaba'daya ya ajiye girman kai, da tunanin yana da kwalin digiri. Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, muka rabu da matsalar babu. Domin sosai yake samun ku'di tunda ba balance yake kai wa ba. Ni ce ma na koya masa dabarar ya dinga ajiye wani abu a banki saboda ko watarana motar zata bukaci gyara. Ko wata lalurar zata gitto bakatatan. Ba ja in ja ya yarda da shawara ta. Akai akai yake yiwa mahaifiyarsa da Baban Marina sako. Dada ma bai barta a baya ba. Wani lokacin idan ya je Jos sai ya tsaya ya musu alheri, sannan ya taho. Hatta su Baban Tsakiya yakan yi musu alheri kai musu kayan miya ko doya. Ku'di ne dai baya basu. Wannan rufin asirin da ya samu ya sanya masu yi masa kallon banza suka shiga nan nan da shi. Akai akai ake bugo masa waya, sabanin lokacin baya da ba'a saka shi cikin mutane bare a tuna da shi. Rannan kwatsam sai ga shi ya dawo da Nasiba tare da akwatinta shake da kayan da suke nuni zata jima tare da mu. Na gama nazarinta. Gaba'daya ta goge ta yi fes da ita. Ta cika ko ina dam tabbacin yanzu tafi samun nutsuwa. Ni ce shaida muka akan son da take yiwa Baban 2. Na ha'diye komai na yi mata uzziri tunda shi so Ubangiji ne yake kitsa shi a zukatan bayinsa. Sannan a lokacin da aka zartar da aurena da shi bata yi mini koamai ba, sai fatan alheri duk da kuwa yadda al'amarin ya buge ta. Dan haka nima a yanzu zan mata kawaici ka'dan. Amma ban da aurensa. Wannan kam bazan iya ba. Na kuma tabbatar da niyyar hakan aka turo ta. Uwarta zata yi komai dan ganin Tijjani ya aure ta ba tare da ta jin kunyar ubana ba. Ta manta yadda ta ture komai ta yi sanadin datse soyayyarsu. A yanzu kuma da ake ganin ya samu mamora shine za'a lika masa ita. Ko kunyar ha'damu kishi bata yi. Kiri-kiri take nuna mini tsana tamkar wadda agola ce ni a gidan haka take yi mini. Da daddare muna kwance gaba'daya na kasa sakin raina. Har shi ma na ji haushinsa ya turnik'e ni, akan wanne dalilin zai dauko ta tunda ga Toro su taho Bauchi? Ya kasa ha'kuri ya ce "Little wai mene ne?" Na yi masa banza. Ya tunzura ya ce "Amma dai kin san na tsani na miki magana ki share ni ko?" Na kasa bu'de baki na ce mass komai a dalilin kuka nake yi irin na sharbe. Jin shesshekar kukana ya sanya ya shiga rud'u. Ya dinga tambayar ba'asin kukan nawa. Sai da na tabbatar na rikita shi matu'ka da gaske sannan na ce masa "A kan me za'a sa ya kawo mini Nasiba gida ba tare da yarda ta ba?" A hankali ya ce "Dada ta ce na taho da ita ta mana kwana biyu. Ita ma kuma ta da'de tana fa'da mini tana son zuwa ta ga sabon gidanmu. Shine yau da ta ce zata biyo ni na ce to". Na tashi na zauna na ce "Hakan ya yi. Wato har waya kuke yi ko Tijjani?" Ya zuba mini ido sosai domin yasan tunda na gatsa sunasa gatsal to zan iya yin komai na rikici a tsakaninmu. Ya sassauta ya ce "Dan ta zo mana bakunta mene ne a ciki?" A tunzure na ce "akwai komai ma. Bana son bakuntar ta, ba kuma zata zauna mini a gida ba". Ga mamakina sai ce mini ya yi "Wai gidan na ki ne?" Na kad'u matu'ka da gaske. A matu'kar sanyaye na ce "A a naka ne mantawa na yi, amma ka tabbatar ba zan yarda da kai alhalin ina ganinku a gida daya ba." Na koma na kwanta, shi ma ya kwanta bayan ya juya mini baya da alamu ya yi matu'kar fusata da na ce Ban yarda da shi ba. Ya sani kuma ina da hujjar da zan guji zamansu a gida daya, mussaman karamin gida irin namu. Washagari muka tashi kowa na ganin laifin d'anuwan sa. Na yi matu'kar boye wa Nasiba halin da muke ciki. Tare da ita muka karya a kwano daya. Tunda shi ya fice bai saurari abincin ba. Da daddare ma hakan muka sake kwana babu jituwa. Domin nasan jira yake na ba shi hakuri, na kuma rarrashe shi. Ni kuwa al'amarin da yake cina ba k'arami ba ne. Ko magana bama yi ni da shi. Ba dan bana son ta fahimci akwai matsala a tsakaninmu ba da ko dakinsa ba zan je ba. Amma ina zuwa bayan mun sha hira ni da ita. Ranar da ta yi kwanaki biyu da daddare mun kwanta. Na bu'de baki na ce "Tijjani gobe bakuwarka zata yi kwanaki uku a gidanka. A ka'idar shari'a kuma bakunta ta kwanaki uku ce. To kasan yadda zaka yi ta bar maka gidan a gobe, ko kuma ka ga abin da baka so". A tunzure ya ce ",Tun yaushe na ga abin da bana so Asiya? Ai tunda babu yarda a tsakaninmu magana ta k'are. Ba kuma zan kore ta a gidana ba. Ni da kika gan ni bana manta alheri komin tarin kalubale da rashin kirkin mutane. Dan haka komai zaki yi Bismillah". Na ce "Hakane. Madallah da Tijjani". Kasan zuciyata kuwa tamkar na tashi na cinnawa gidan wuta haka nake ji. Washa gari ya saka kai ya fice bayan ya amsa gaisuwar ta a tsaitsaye ba tare ma da ya kalle ta ba. Haka kuma yake yi mata tunda ta zo. Mun gama karyawa na kalle ta na ce "Nasiba zan je Kangire dubiya. Wata'kila na kwana, wata'kila kuma na dawo. Na tafi da yaran nan ko na bar miki su?" Zucyarta daya ta ce "Ki barsu mana indai baza su yi rikici ba. Idan suna ganin Babansu baza su yi kuka ba ai babu damuwa". Na ce "Hakane. Na shirya kayana set uku a dan k'aramin akwatina, na yi sallama bayan na yi dabarar tura tagwaye kwaso shanya a baya. Na fice a hankali, bayan na ce mata na bar ki da wahalarsu kuma". Ina jin ta tana fa'din 'yayanki ba nawa ba nawa ba ne ke nan Yabi?" Ban tsaya bata amsa ba gudun kada su fito, su ga tafiya ta. Da azahar ya koma gidan a dalilin ya dawo daga Dass. Ya tarar da yara na kukan neman Amminsu. Ya fahimci Yabi ta fice ta bar gidan babu izininsa. Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi, ransa ya baci ainun. Cikin hikima ya ce "Da nasan da wuri zan dawo ai bazan bari ta fita ba.". Nasiba da take kicin ta ce "Nima da ta ce mini zata iya kwana a can na shiga zullumi." Ya mik'e ya ri'ke hannun yaran suka fita, ya rasa inda zai tsoma ransa da wannan tashin hankalin da ya kewaye shi. "Sha'anin mata yana da gigitarwa. Mene ne abin tafiya ki bar dakinki idan ba kalen masifa ba little?" Ya furta a fili a kuma ki'dime. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* ✍️ *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633* *JAN HANKALI* *BAN YARDA A HADA MINI DOCUMENT BA! BAN AMINCE BA.* *DUK WACCE TA YI HAKAN YANZU, KO BAYAN NA KAMMALA LABARIN NAN, WALLAHI NA KAI TA K'ARA WAJEN UBANGIJI.* *FATAN ALHERI GA* *Aunty Umma Kulsum Muhd Kumo* *Aunty Maryam Saminu Sulaimanu* *Gaisuwa da fatan alheri, na gode sosai da alherinku a gare ni*. *Yabo da godiya ga* *Mamana* *Hajiya Zahra Shehu* *Fatan alheri mai yawa a gare ki da ahalin ki* Tsawon lokaci yana tunanin abin yi. Ya rasa inda zai dosa meman ta. Ya tabbatar ba zata nufi Toro ba. Ya tambayi kansa to ina zata tafi har tana fa'din idan dare ya yi zata kwana?. Kukan Hamim na sake rib'anya tashin hankalin da yake ciki. Ga haushinta, ga zullumin fishinta gaba'daya sun ha'du sun yi masa rubdugu. Ya mike ya shiga gidan, ya tarar ta kammala abincin da take yi. Ransa ya sake b'aci da abin da Yabi ta yi, wato manufarta ta bar musu gidan su yi komai ma. Cikin rashin sukuni ya ce "Ha'da kayan ki zan kai ki tasha ki koma gida. Tafiya ta same ni zuwa gadar mewa. Ba zai yiwu kuma na bar ki ke ka'dai a gidan ba." Cikin nutsuwa ta ce "To". Amma yaran fa?" Cikin rashin sukuni ya ce "Zan kai su wajenta daga can, tunda hanya ce". A hankali ta ce "To ko zamu tafi gaba'daya ina ajiye mu a wajenta sai mu dawo gobe da ita". Da rawar ya ce "A a, mu je dai na kai ki tashar, ba zai yiwu na yi ta yawon kasuwa da ke ba." Tunda ya ajiye ta a tasha yake gararanba a titunan Bauchi. Gaba'daya ya rasa ta inda zai fara nemanta. Nasiba kuwa da ta Isa Toro a gidan Marina ta tarar da gyatumarta tare da Dada. Cikin mamaki Dada ta ce "Ke da kika ce sai an gan ki kuma sai ki dawo, duka duka yaushe kika tafi ne?" Cikin nutsuwa ta ce "Yabin ce ta tafi Kangire dubiya. Shi kuma ya ce na taho tunda kwana zata yi". Dada ta ce "Ikon Allah. Ga kuma uwatata bata fadi wani abu ya samu ba, bare mu yi mata ja je". Sai lokacin Baba Maryo ta ce "Hmm Wallahi ba abin da ya faru, kawai zamanta ne bata so a gidan. Shi kuma da yake salallamamme ne shine ya ce ki taho. Yarinya k'ank'anuwa sai azabar iya barikanci. To duk shure shuren kaza baya hana a dirza mata wuka. Yabi akwai tuggu Wallahi shi yasa na washe ta, bata da kunya ko kad'an bare mutunci". *** Da azahar na dira a Bulkachuwa. Babah sai ganina ta yi kwatsam. A sanyaye ta shiga yi mini barka da zuwa. Sai da na yi sallah ta bani abinci da ruwa, na ta'ba ka'dan na rufe. Ta zuba mini ido ainun. Ta ce "Wai mene ne damuwar ki ne Yabi? Maimakon tunda yanzu ba shayarwa kike yi ba, ki murje ki cike, amma kullum sai fige wa kike yi tamkar wacce ake tsakurarki?." Na yi k'asa da kaina, ba tare da na ce komai ba. A tausashe ta ce "Yanzu me yasa kika taho ba shiri ba komài?" Na fara hawaye, ba tare da na bu'de baki na ce komai ba. Ta ri'ke hannuna ta ce "Da ke da Ihisan daya nake jinku. Dan haka zan fa'da miki gaskiya. Gaba'daya aure hakuri ne. Ba yadda ake so ake ga ni ba. Idan Ubangiji yasa farin yafi ba'kin yawa a cikin zamantakewar sai a yi ta gode wa Allah. A kuma yi hakuri da inda aka kuskure. Idan kuwa ba hakan ba sai ki ga gidan aure ya zama tamkar kurku dan tsanani. Adadin mutuwar aure ya yi ta tunbatsa. Yin sassauci da kawaici babban jigo ne da yake rike da gidajen aure. Cikin kuka na ce "Wallahi ina yi." Ta ce "Na sani. Yanzu fa'da mini abin da ya yi miki har kika kasa hadiye wa" Cikin kuka na tsara mata yadda muka yi da shi, ban yiwa al'amarin kwaskwarima ba. Da kuma kafewar da ya yi sai ta zauna da mu saboda tana da alkairai masu yawa a idonsa. Cikin kuka na ce "Ni kuma Wallahi bazan yarda na zauna da ita ba". Ta yi shiru, na tsawon lokaci kafin ta ce "Tashi ki je d'aki ki yi kwanciyar ki. Kar kisa wannan maganar a ranki. Kina da gaskiya dan hakan zan tsaya miki, da kuwa baki da gaskiya da a yau zan mayar da ke dakinki". Dad'i ya kama ni. Babah ta fahimci irin rad'ad'in da nake ji. Ina kwance ta shigo ta ce "Kuma sai kika bar mata yaran?" Fuska ba walwala na ce "Eh". Ta ce "Da kin taho mini da su, ina cikin kewarsu ainun. Amma bar masa din da kika yi akwai hikima mai yawa tunda ba sha suke yi ba. Kukan Hamim kadai ya ishe su ai. Ki yi zamanki ba wanda zai san kina nan tunda Umman gidan nan tana garinsu tafi wata a can. Ko Nasiru ma baya gari. Aliyu ne ya ce zai zo yau, to kuma ya fasa sai satin sama, saboda zasu je Ibadan". Ta dauki abin da zata dauka ta fice. Tana fa'din "Da ni yake zancen". Sai da dare ya fara ja sannan ya koma gida. Bayan Nasiba ta masa text din ta sauka lafiya. Tunda ta kira shi ya fi sau biyar yana gani amma bai dauka ba. Da asuba ya kira wayar Yaya Ummi. A d'an tsorace ta ce "Yaya Bulkachuwa barka da asuba" Murya na amo ya ce "Ummilolo taimake ni ki bani lambar mijinki na nemi izinin aikenki yanzu zuwa gidan Marina". Ta ce yana jinka ma yanzu haka, na saka ta a sifika ka tambaye shi." Ya bu'de murya cikin ladabi ya gaishe shi. Ya kuma roki alfarmar zai aiki Ummi zuwa gidan akan wani al'amari da tayar masa da hankali. Nan da nan ya ce "Babu komai na amince ta je. Ya mika wayar ga Ummi. Ta ce "Ya ya ne Yaya Bulkachuwa?". Cikin zullumi ya ce "Asiya ce ta yi mini yaji Ummi! Tun jiya ta fice ta bar mini gidan da yara." A zabure ta ce "Subhanallah a kan me Yaya Bulkachuwa?" A sanyaye ya ce "Hmm! Kawai mu bar maganar tattauna wa ki tashi yanzu ki je gidan, ki duba ko ina. Idan kin ganta kada ki nuna komai kawai ki dawo gidanki. Ki fa'da mini sai na taho". Yana rufe baki Ummi ta ce "Gaskiyar magana ban jin Yabi zata iya zuwa gidanmu da sunan yaji. Ta tsani yamididi, tana kuma matu'kar tsoron bacin ran Baban Marina". Ya fesar da iskar damuwa ya ce "To saboda Allah ba kisan inda take ba Ummilolo?" "Wallahi ban sani ba, ko waya bamu yi da ita ba. Amma bari na je sumame gidan Nazira". Da sauri ya ce ",Yauwa Ummilolo, na gode, hanzarta dan Allah". Ta ce "Zan sallami mutanan gidan da abin karyawa tukun". Akan dole ya ce "To." A hanzarce ta gama dumame ta sallami kowa. Kusan da sanda ta shiga gidan Nazira domin ta tabbatar mijinta baya nan. Amma bata ga wata alama mai kama da rashin gaskiya ba. Suka gaisa ta tambayi yara. Ta ce "Daga ina Yaya Ummi?" Ta ce "Mafarkin ki na yi Nazira shi ne na taho dan na ganki, na ga lafiyarki". Da'di ya kama Nazira. Ta ce "Madallah da Yaya Ummi. Kin kuma tarar da ni lafiya, har na karya na yi hidimar gida". Ta mike tana fa'din "Alhamdulillah! Tunda na ganki lafiya bari na tafi". Ta hanzari Nazira ta yi kicin dinta ta juyo mata dafadukan macaroni mai dan dama a madaidaicin filas. Ta ce ga shi ki kaiwa yaran nawa. Na maigidan ne bai tsaya karyawa ba. Ana ta jiransa zasu je Lame. Ya dai sha kunu a tsaitsaye." Ta karba da godiya ta tafi. Maimakon ta zarce gidan ta, gidan Marina ta yiwa tsinke. Duk wani bin kwakkwafinta bata ga ko ganin wata alama da take nuna sun san Yabi bata gidanta ba. Dan haka suma ta yi musu sallama ta tafi ba tare da ta bu'de musu komai ba. Sai da ta isa gidanta sannan ta kira Bulkachuwa ta tabbatar masa Yabi bata zo Toro ba. Ya lalube ta anan Bauchin. A rikice ya ce "Yanzu Ummi abin da Asiya ta yi mini dai-dai ne?" Kai tsaye ta ce "To ai bansan me ya faru ba Yaya Bulkachuwa". Ya ce tsaya ki ji, ki fa'da mini inda nake da laifi, ki kuma fa'di shin ta kyauta mini kenan?" Ta ce "To zan fa'di gaskiya tsakanina da Allah kuwa". Ya numfasa ya shiga koro mata bayani tiryan tiryan na gaskiya. Bata katse shi ba sai da ya gama tsaf ya ce "kin ji abin da ya faru". Ta numfasa ta ce "Ka yarda gaskiyar magana zan fa'da?" Da sauri ya ce na gasgata ki Ummi. Komin tasirin jini na sani zaki yi adalci domin ke din mai kauna ta ce na shaida." Ta ce "Na gode sosai. Amma gaskiyar magana kai ne baka kyauta ba. Kasan Yabi tasan akwai tsohuwar soyayya tsakaninka da Nasiba. Yanzu Kuma bata da aure. Akan wanne dalilin zaka dauke ta da kanka ka kai ta gidanka da sunan ta zauna, ba zama irin na bakunta ba.? Me yasa da Yabi ta ce bakuntar kwanaki uku ta amince ta yi muku baka yarda kun fahimci juna ba? Me yasa ka ankarata ta hanyar ce wa Nasiba tana da darajar da ba zaka kore ta a gidan ka ba?. Tsakanina da Allah wannan maganar ta yi nauyi a zuciya. Ai da sai ka ce mata ita ta kore ta, shi kenan magana ta k'are." A sanyaye ya ce "Na gode na kuma yarda na yi kuskure. Amma me yasa ta zarge ni?" Kai-tsaye Ummi ta ce "Kai ka bada k'ofar. Me yasa dan Nasiba zata zo gidanka sai ta hannunka zata biyo? Ba Yabi ce matar gidan ba? Me yasa sai da kanka zaka kai ta? Me yasa ka kausasa harshen ka akan zamanta?" Ya ce "Yanzu dai Ummilolo Yabi ta yi dai-dai da ta fice ta bar gidan babu izinina?" Ta numfasa sannan ta ce "A fuskar shari'a bata kyauta ba. Amma tunda ni mace ce nasan yadda take jin zafi a zuciyarta bata yi laifi ba, tunda ka nuna wacce bata zama dolen ka ba sai ta zauna mata a gidan ko tana so, ko bata so, ba tare da rarrashi ba". Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Na gode sosai Ummi. Na kuma gamsu da wannan gaskiyar ta ki babu son kai a cikinta. Kuma yanzu hakan tun jiya na saka Nasiba a mota ta dawo Toro. Na sallame ta a kurarerren lokaci ko?" Nan ma Ummi ta ce "Eh, baka girmama ra'ayin matarka ba, sai da ka bari ta yi maka tutsu, hakan kuma zai haifar muku da tazara da tsatsar zuciya mai yawa". Cikin karaya ya ce "Na gode bari na shirya yaran nan, mu fita nemanta, ki taya ni addu'a, gaba'daya yarinyar nan ta gigita ni. Wato Yabi jidalinta mai girma ne." Ummi ta kwashe da dariya ta ce ni fa ban ga laifinta ba Yaya Bulkachuwa. Haka kawai za'a lallaba a yi mata kutse mai dafa zuciya, da saka jinya a gangar jiki". Ya numfasa ya ce "Allah ya sauwake, ni Wallahi babu tunanin komai a zuciyata akan hakan". Ta ce "Kai kasan hakan, mu ina muka san zuciyar ka?" Ya ce "Shi kenan bari na saka d'ambar neman ta." Suka yi sallama, ya kashe wayar tare da zurfafa a tunanin ta inda zai fara nemanta. A daddafe ya yi wanka saboda azabar kukan Hamim. Domin a bakin band'akin ya zauna yake kuka na tashin hankali. Hanif kuma sai ri'ke shi yake alamun wai ya yi shiru. Dan haka ko da ya fito a rikice ya shirya, ya dauki yaran da yake ta gunjin kuka. Yasan kukan neman Amminsu yake yi. Allah ya zuba masa k'ulafacin uwa. Ya gama shawo kan Hamim ya yi shiru, sai kawai Hanif ya fa'di ya dan bugu a goshinsa. Ya fara kuka shi ma. Hamim da dama kukan ba daina shi ya yi gaba'daya ba, sai kawai ya bu'de baki yana taya Hanif. Suka rikice masa ainun. Ya jima kafin ya samu su tsagaita. Shi da kansa ya fahimci d'a sai uwarsa. Duk da yadda ya iya raino. Amma rashin Yabi a tare da su sai komai ya k'wace musu daga shi har y'ay'an sa. Har suka bar gidan bai yanke shawarar inda zai dosa ba. Amma yana hawa titi zuciyarsa ta fi rinjayar masa ya je Bulkachuwa. Dan haka gidan mai ya shiga ya sha mai. Ya siya wa yaran yoghurt da cake. Sannan suka dau hanya. Yana yi yana daukar fasinja dan ya samu sau'kin tsadar mai. Da walwala Babah ta karb'e su. Tana ta tambayar ya aka yi suka baro Yabi a gida ita kad'ai? Ya dan diririce, bayan ya ga rashin wasa a fuskarta. Murya babu karsashi ya ce "Bata jin da'di ne shi yasa bamu taho tare ba, nima kayan miya na kawo nan Dambam". Ta ce "Ayyah me ya same ta? Ko zazzabin damina ne da ko ina yinsa ake yi". A sanyaye ya ce "zazzabin cizon sauro ne, amma da sau'ki rashin k'warin jiki ne kawai." "To Ubangiji ya bata lafiya". Ya amsa da Amin cikin damuwar to ina Yabi ta fantsama kenan? Ya kasa ko da shan ruwan da yake gabansa bare kuma abinci. Yara dai suna ta cin abincinsu. Ta zauna tana fa'da masa sati mai zuwa Aliyu zai je Ibadan yin jarabawar zama likita, tunda karatun likitanci yake yi a jami'ar Jos. A gajarce ya yi murna da fatan alheri. Ta fahimci rudun da ya shiga amma ta matse ta yi kamar bata gane ba. Ya sassauta murya ya ce "Tafiya zan yi, zan bar yaran a nan, zuwa jibi zan dawo". Cikin nutsuwa ta ce "Haka kawai ka dauko su babu shirin zasu zauna ka bar mini su? Uwarsu ba zata ji dadi ba". Ya basar ya ce "Ko ba wajen ki na kawo su ba, har ta yi mini inkarin inda na kai su bare kuma wajen ki ne". Da azama ta ce "Wallahi ba zaka bar su ba, tunda kai ma ba da nufin su kwana ka taho da su ba. Kaya kala daya ka sako musu a leda. Nasan kuma idan sun bata na jikinsu a sauya musu ne iya yau. Ka bari idan ka shiryo su da kayansu sai su zo mini, amma ba haka kawai a shiga hakkin uwa da y'ay'an ta ba". Ya rasa yadda zai yi, a kan dole ya kwashe su suka juya. Ni da nake mak'ale a daki, zuciyata sai tsalle take yi a kan na ga yarana. Da k'yar na daure ban fito ba. Da suka tafi kuwa sai na ji tamkar na ruga a guje na ce "Ga ni nan". Na kwanta lamo. Ina kallon silin. Babah ta shigo yanayin da ta ganni a ciki sai ta yi turus. Ta iso ta zauna a gefen k'afafuwana. Ta sassauta murya ta ce "Nasan zaki so yaranki a tare da ke. Amma ki daure ba jimawa zaki yi ba. So nake ya rikice gaba'daya, ta yadda da kansa zai zo da bakinsa ya fa'da mini ba kya tare da su. Har da ce mini wai kina gida zazzabi kike yi". A hankali na ce "Idon Hamim ya yi ja?" Ta galla mini harara ta mik'e ta na ce wa "Ban sani ba. Idan kuwa haka zaki mini, ki kuntata kanki sai ki zo ki bi bayansu kawai". Ta fice tana ta sababin masifar son y'ay'a da iyayen yau suka mak'alawa zukatansu. Da gaske dai mace tana saurin yin afuwa ga namiji a dalilin yaranta. Domin tun yanzu na fara kewarsu. So nake na bu'de ido na ga suna wasan hawa da sauka a jikina. Na fesar da iskar damuwa. Na sani daga shi har yaran suna cikin kewata mai yawa. Barin ma sarkin kuka da k'ulafaci Hamim. Haka na zauna, ina jin wani irin abu na bina. ** Bulkachuwa kuwa da k'yar ya isa Bauchi domin ya shiga rudun inda zai ga Yabi. Ya kira wayarta yafi sau goma ana fa'da masa a kashe take. Amma ya kasa dainawa. Suna isa gida, dakinta ya dire. Yaran da suka waiwaya basu ganta ba, suka dinga kuka a tare. Shi kansa ji yake tamkar ya bare baki ya tayasu. Gaba'daya azanjinsa ya k'are. Da k'yar ya shawo kansu suka yi shiru. Kwanaki biyu yana tiritiri da su. Sa'ar da ya yi ma ya riga ya saba da hidimarsu. Jiya a Toro suka yini, yana bulayin yiwa gidajen mutane dirar mikiya ko zai ga Yabi. Amma shiru tamkar Malam ya ci shirwa. Komai ya tsaya masa cak. Kan dole ya sake komawa Bulkachuwa da su. Ya rasa ta yadda zai fa'dawa Babah Yabi ta gudu ta barsu. Ya gama kame kamensa ya fa'da mata gaskiya sun samu sabanin fahimta da Yabi ta yi yaji, ya kuma neme ta ya rasa tsawon kwanaki uku kenan. Ta dauki salati mai tsananin gaske. Ta dake ta ce "Yarinyar da ubanta ya damka mini amanarta a hannuna ka yiwa sanadin da ta gudu ta fantsama duniya?" Ya yi tsumu ya rasa me zai ce. Ta ce "Sai ka fa'da mini abin da ka shuka mata har ta kasa ha'diye wa ta bar maka wadannan yaran da suka shiga ranta. Ta tafa hannu tana skae kambaba girman lamarin. Fadi take yi "Duk uwar da tafi ta bar k'ananun y'ay'anta ai ba'kin cikin da take ha'diye wa ba ka'dan ba ne. Tura ce ta kai bango". Ya kasa ce wa komai. Illah zufa da take yanko masa tamkar mai hadiyar kunama. Cikin bacin rai ta ce "Ya ya ina magana ka mini shiru sai zare ido ka ke yi irin na rashin gaskiya". Murya babu amo ya ce "Wallahi ba komai na yi mata ba. Nasiba ce ta zo shike nan ta kwarzabi kanta." "Ta kwarzabi kanta kamar ya ya?" Ta tambaya cikin wani irin yanayi na bacin rai mai yawa. Ya numfasa ya ce "Ce wa ta yi sai na kore ta. Ni kuma na ce bazan kore ta ba. Shi kenan na dawo na tarar ta bar gidan". Ta rausayar da kai ta ce "To ai Yabi ta yi adalci. Sai da ta fa'da maka bata son zamanta. Kai kuma ka nuna kana da bu'katar ta zauna a gidan tunda naka ne. To mene ne kuma dan ta fita ta bar muku gidan ku tabbata a ciki?". Ransa ya baci ainun. Ita ma bata fahimce shi ba. Su duk haka mata su ke da kishi ne?. Basa fahimtar komai matu'kar akan kishi ne. A hankali ya ce "Yanzu dan Nasiba ta zo shi kenan sai ya zama masifa? Ta ce sai ta bar gidan? Duk zamanmu da ita bata gasgata ni ba ke nan? Ni ba kula ta nake yi ba, bare ta ce ta fahimci wani abu a tsakaninmu. Wallahi saboda sababin Yabi ko kallon inda ta ke bana yi. Amma hakan bai yi mata. Shin Nasiba ba zata zo gidana ba, ba yar'uwa ta ba ce?". Babah ta girgiza kai ta ce "K'warai yar'uwar ka ce ta gaske tunda har ka zabi fishin matarka akan ta. Madallah da Yabi bata za'bi zaman muzanci ba. Ta daga hannuwanta sama ta ce "Allah kasa yarinyar nan tana hannu na gari. Allah kasa tana Kangire ko kaduna gidan Jabir". Nan da nan ya muzanta. Ya kasa yin shiru ya ce "Kaduna! Ya fa'da cikin takaici mai yawa. Ya kasa yin shiru da rawar murya ya ce "Na rantse idan aka same ta a Kaduna duk masifarta sai ta ga ne bata iya komai ba". Ta galla masa harara ta ce "To me zaka yi ne? K'arshe dai ka sake ta. Ni kuwa Wallahi tana gama idda zan bada aurenta ga saurayi ma, don bazan yarda ta fita daga ahalina ba." Idonsa ya kad'a ya yi jawur. Da rawar murya ya ce "Babah a gabana kike nuna zaki bawa k'anina auren matata?" Ta bu'de murya ta ce "Na fa'da na ji ruruf!". A matu'kar ki'dime ya ce "Allah ya huci zuciyarki. Allah ya tsare ni aikata irin wannan BAK'AR TA'ADA din". Ya bata tausayi ainun. Amma ta cije ta ce "Akan idona uwar Nasiba ba abin da bata fa'da akan ka ba. Ita ta hana a baka aurenta saboda suna ganin ka baka da mamora. Amma Yaya Sani ya juyawa dukkan nak'asunka ya tursasawa Yabi auren ka sai kuma dan ka fara samun dama, ka fara shiga sahun mutane sai a yi maka shunen ta har cikin gidan Yabi! Ta yi shiru. Saboda yadda zuciyarta take jin tsananin zafin yadda aka tado mata tsumin bacin rai na tsawon lokaci. Ta zuba masa ido wanda rabon da ta yi masa haka ya manta. A kaurare ta ce "Nasiba ba matarka ba ce, ko bayan raina ba zata zama matarka ba. Shari'a ta halasta ka aure ta babu aibu a cikin hakan. Amma kuma shariar da kanta ta ce "ku girmama ra'ayin iyayenku sama da naku. Matu'kar ina da hak'ki akan ka Wallahi na haramta maka ita. Soko marar tunani. Har ka manta tozarcin da uwarta ta yi mini akan maganarku?" Hankalinsa a matu'kar tashe ya ce ", Wallahi Tallahi ba ni da manufar komai akan ta. Dan Allah ku fahimce ni mana" "An k'i a fahimce kan. Ban da sakarci me ya kai ka taho da ita tunda ga Toro har Bauchi ku ka'dai ka kawo ta gidan ka. Ai sai a rasa gane wace ce matar gidan tunda sai ta goyi Yabi da zani tsab. A kan wanne dalilin da ta ce ba zata zauna mata a gida ba, ka kafe sai ta zauna d'in? Ban da munafunci irin na ku na maza. Na gode wa Yabi da ta fahimci bata da daraja a wajen ka. Ta fice ta bar maka gidan". Da rawar murya ya ce "Allah ya huci zuciyar ki. Na yi kuskure a yafe ni dan Allah. Tun ranar kuma Nasiba ta tafi, da kaina na ce tafi din" Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da fad'in "Ta baya ta rago". Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* ✍️ *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!* *REGULAR 500* *VIP 1K* *VIA* *2384876855* *SURAYYA IBRAHIM DAHIRU* *ZENITH BANK* *KO* *7061488065* *SURAYYA DAHIRU IBRAHIM* *OPAY DIGITAL SERVICES.* *TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN* *08032773332* *09069067488*. *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. Ya yi shiru ya kasa ce wa komai. Haka ita ma. Yara ne kawai su ke ta wasa a tsakaninsu. Sai iskar fanka da take kadawa da karfi sosai. Amma hakan bai sa zufa ta daina yanko masa ba. Gaba daya ya shiga rudani mai yawa. Ya rasa inda Yabi ta gudu. Ga magaganun Babah masu tsauri. Wanda hakan yake alamta masa yana cikin fishinta. A sanyaye ya sake bata hak'uri tare da matsar da jakar kayan yaran gabanta. Ya mik'e ya faki kallon yaran da suke wasan tsere a tsakaninsu. Ya ce "Zuwa gobe zan dawo". Galala ta kalle shi ta ce "Dauki jaka da y'aya'nka. Ai ba zai yiwu ka kori uwarsu da baki cikinka ba. Sannan ka saka rai zan maka wahalarsu. Wato na zama shasha ma! Ya koma ya zauna ya sassauta murya ya ce "Haba mana, dan Allah ki ji tausayi na. Gabadaya nutsuwa ta yi mini tutsu. Idan na barsu ma ba wai hutawa zan yi ba. Neman ta zan cigaba da yi. Gobe Kaduna zan tafi". Cikin rashin nutsuwa ta ce "To ka tafi da su, ko ka fara kai su Toro wajen Nasibar sai ka wuce. Amma Wallahi ko gwaggonsu ka kai wa yaran nan, ni da kai ne". Ya yi shiru, idon sa ya kad'a ainun, ya koma ya zauna. Murya babu amo ya ce "Ki yi hakuri dan Allah Babah." Ta jijjiga kai ta ce "A kan Yabi Bilhillazi zan yi matukar saba maka. Zan fita a sha'anin ka gabad'aya." Ya yi shiru. Amma ransa suya yake tamkar ya fad'o kasa. Me ya yiwa Yabi da zata janyo masa irin wannan jidalin? Ya dinga bata hak'uri. Da k'yar ta ce sai ya gano Yabi idan ta huce, sannan ita ma zata hakura." Ya mik'e da sauri yana fad'in "Na gode sosai. Bari na tafi neman ta da ikon Allah zan nemo ta". Daidai lokacin Hamim ya fasa kuka yana nuna windo. Tare suka isa gare shi, suna fad'in mene ne?" Shi dai Hanif yana tsaye, yayin da Hamim yake kuka tare da nuni da saitin windo. Nan da nan zuciyar Baba ta tsinke domin ta gano kayan Yabi yake nuna wa akan igiya. Ma'ana ya gane kayan uwarsu, a ba shi ya rik'e mata. Nan da nan ta dauke kai, ta shiritar da Tijjani da ce wa "Tofa masa addu'a mana, watak'ila shaid'anu ke son bude masa ido. Allah ya tsaremu daga sharrin abin da bama kallonsu". A gigice ya hau tofa masa falaki da nasi. Yaro kuwa sai zabura yake akan zai je ya dauko abin da yake ganin na uwarsa ne. Yayin da Babah take ta hirji tare da addu'ar kada Yabi ta kasa jure kukan Hamim da yake d'ada canyarwa tamkar gyare ta fito. Ita da kanta ta gane irin kukan da Yabin ta yi tana yarinya ya gado. Ta ce "Dauke shi ku tafi. Idan ya ga kun shiga mota zai yi shiru." A raunana ne ya ce "Yadda ya razana hakan zan tafi da shi? Ki yi hakuri na bar su a nan, gobe ko jibi da ikon Allah zan dawo na dauke su. Ko ban ganta ba. Ta ce "A a ba fa zan rike su ba. Ai idan kasan zan rik'e maka yara ka dinga shagulatin bangaro da auren ka kenan. Ina ce lokacin da suke hannuna ka fi uwarsu nuna zalamar na baku su? Yanzu kuwa ba zan karbe su ba." Kamar zai rushe da kuka ya ce "Gobe Kaduna zan je Baba." A gajar ce ta ce "Tafi da su ka kai wa Ihisan. Idan ka dawo ka je ka dauke su". A kan dole ya sunkuya ya dauki Hamim. Ya rike hannun Hanif. Bayan ya saba jakar kayansu. Yadda ya d'ebi yaran da jakarsu sai tausayinsu duka ya kama ta. Suka fita, sai da suka jima da fita. Sannan ta bude dakin da Yabi ta ke. Ta tarar da ita zaune akan gado tana faman goge idonta tabbaccin kuka take yi. Ta k'arisa kusa da ita. Ta ce "Yabi kuka kike dan ina kokarin ya fahimci muhimmancin ki a rayuwar sa da ta y'aya'nsa?" Da wata irin tab'ara da kuka na ce "Ai da sai ki karbe su. Kukan Hamim kad'ai abin dubawa ne". Ta yi galala ta zuba mini ido ta kasa ce wa uffan. Na kuwa matse na ce "To ni dai na huce tunda haka ne. Ai ya yi ta zuwa, na kuma san yana cikin tasku, sai ki zaunar da mu, a mayar da zan ce, ki yi masa fada, mu tafi." Ta jijjiga kai tare da ce wa "Ban yi hakan ba Yabi. Ba kuma zan yi ba". Na kuwa juya na kwanta ina kunkunin bazan sake yin yaji na zo nan ba, tunda ba sulhu zata yi ba". Ta dinga salati tana tafa hannu. Tare da ce wa "Ban ga laifinki ba. Amma zaki ga karshen iyashege. Dauko hijabin ki, ki bisu. Na bata rai tare da daure fuska ainun. Ta sassauta ta ce "Ba fishi na yi ba. Tunda laifin kaina zai juye to kawai ki bisu. Duk tsamin ran da nake taya ki, baki yaba ba, bare ki bani hadin kai mu yi maganinsa da kyau". Murya na rawa na ce "To ai da sai ki karbi yaran Babah". Ta bude murya ta ce "Na ki karbar tasu. Ina ce ke kika barsu a gidansu? Kuma ba a hannun ubansu suke ba tabbatacciyar marar ta ido!" Na yi shiru amma dai fuskata a daure. Kafin ta yi magana sai kukan Hamim muka jiyo tabbacin sun dawo. Kafin Baba ta fita har sun shigo falo. Da azama ta fita tana mini kashedin kada na fito da hannu. ** Turus ta yi ganin Hamim na rike da riga da hijabin Yabi a hannunsa, ya kuma sassauta kukan da yake yi. Sai ajiyar zuciya yake faman saki. Kafin ta ce komai Hanif ya ruga ya dauko takalman Yabi da suke gefen falon. Shi ma ya rik'e. Tijjani ya samu nutsuwa domin ya tabbatar tana gidan. Yayin da Babah ta kasa ce wa komai. Cikin nutsuwa Tijjani ya ce "Ashe ba shaid'anu ya ke nuna mana ba. Kayan ta ya ga ni. Har mun fita ya tsananta kuka, ya kuma k'i yarda ya shiga motar. Sai hannuna yake ja. Na yarda na biyo shi muka dawo, sai kawai ya kai ni baya wajen kayan. Anan na fahimci kayan Yabi ya ga ni. Dan Allah Babah ki yi hakuri, ki ji tausayinsu ki basu uwarsu." Ta yi kicin kicin ta ce "Idan ka ganta ba sai ka daukar musu ita ba. Ai tunda har zaka wulakanta Yabi irin haka, tabbas nima zaka wulakanta ni. Dan haka ba zan zuba ido ka fara mata cin kashi bayan ta gama shanye wahalar ka ba". Ta rik'e hannun yaran ta tura su cikin dakin. Domin sun bata tausayin yadda suka rik'e kayanta gamgam. Kayan da shafa'a ne ya sanya aka barsu har yaran suka ankarar da ubansu. Suna shiga ta janyo k'ofar ta zauna akan kujera, ta tsare gida ainun. Ya rasa ta yadda zai fara yi mata magana. Tsawon lokaci kafin ya tausasa harshe. Ya ce "Ina sake baki hakuri. Tunda wannan ne karon farko da ta kawo miki karata a zamanmu da ita. To ki yi mini uzziri a wannan karon . Ni kuma na miki alkawarin ba zata sake kawo miki karata akan wannan matsalar ba. Ki yi hakuri dan Allah". Jikinta ya yi sanyi. Mussaman da ta zuba masa ido ta ga ya fada ya kuma birkice gabadaya. Ya dinga magiya. Da ban baki tamkar zai rushe da kuka tsabar tsananta rokon da ya yi. Rauni irin ma uwa ya shige ta. Ta furzar da iskar takaici. Ta ce "Ba dan ta yi hankalin tahowa nan ba. Da an yi ta yamididi da murnar ka yi kudi ka fara wulakanta ta. Da wanne idon zamu Kalli iyayenta da suka yi alkunya da kawaicin baka auren ta? Ta dinga yi masa fada da togaciya tamkar zata bige shi. Yayin da shi kuma yake fad'in "Ki yi hakuri zan Kiya ye da ikon Allah". Ta tashi ta nufi daki. Ya yi maza ya mik'e ya bi bayan ta a d'arare tare da fargabar kada ta dakatar da shi. Tana tsakiyar gadon. Yayin da Hamim yake kwance kan cinyarta. Hanif kuwa sarkin hakuri filo kawai ya yi da cinyar jikinsa na kan gadon. Daga ita har yaran kowa ya yi shiru tabbacin suna cikin alhini. Baba ta sassauta murya ta ce "Yabi ga shi nan ku sasanta. Idan kin ga zaki yi hakuri ki bisu to, idan kuwa kin ga ba zaki bisu ba. Ba zan matsa miki ba. Ban san me kike hadiye wa ba". Ya rasa inda zai tsoma ransa. Murya babu amo ya ce "Amma na baki hakuri fa". "Dan ka bani hakuri sai na tirsasa ta?" Ta jijjiga kai tabbacin ba zata mini dole ba. Ya sassauta murya ya kalle ni ya ce "Asiya ki yi hakuri da abin ya faru. Na yi kuskure duk da dai fahimta ta ne baki yi ba". Yana rufe baki na ce "Ba zan fahimta ba." Babah ta yi shiru tana kallonmu. Watak'ila kuma mamakina ta yi na yadda na kame kamar ban gan shi ba tamkar ba yanzu na gama yin tijarar na huce ba ". Ya munfasa ya ce "shi kenan ki yi hakuri." Ya furta a hankali. Babah ta zame ta fice. Yana ganin hakan ya matso kusa da ni ya zauna. Ya rage murya ainun ya ce "Saboda Allah little ya kamata ki bar dakin ki babu iznina?" Na galla masa harara na dauke kai ban ce komai ba. Ya sake tausasa harshe ya ce "Tashi mu tafi, idan mun je gida sai ki yi mini ko wanne irin darun ni kuma zan yi ta rarrashin ki, da kalolin soyayya masu tsayawa a rai." Na ja tsaki tare da fad'in "Na bi soyayya da gudu. Ni yanzu bana son ka, kai ko ganin ka bana kaunar na bude ido na yi". Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Tom shi kenan, ki dawo dakinki dan yaran ki, ko ban ci arzikin komai ba ki dawo dan y'aya'n ki". Na dauke kai na ce "Idan na mutu zasu fasa rayuwa ne?". Ya rik'e kafata da tafi kusa da shi. Na goce da sauri. A tunzure na ce "Kada ka kuma tab'a ni. Ka je ka cigaba da damukar wadanda suke da daraja a wajen ka". A zafafe ya ce "Na cigaba Asiya?". Na dauke kai na ce "Eh". Murya na rawa ya ce "Kin ga na damuk'e ta ne? Me yasa kike son jifa na da wannan mummunar maganar ne?" Ba ja in ja na kalle shi na ce "Saboda ina da hujjoji na gaskiya. Sannan idan ba hakan ba, me yasa zaka kawo mini wannan suntumemiyar cikin gida? Har kuma kana kumfar bakin ba zaka ce ta tafi ba, saboda ta yi maka alkhairai. Fada mini alherorin da ta yi maka dan kuwa ban sansu ba". Ya kafe ni da ido. Cikin matsanancin bacin rai ya ce "saboda kin fahimce ni a baibai shi yasa kika taho babu izinina, sannan kike kallon idona kike jifana da alamarin da kika san na tsani a jingina mini. Me yasa kike son ki dinga tayar mini da hankali ne Asiya?" A tunzure na ce "Saboda ba ni da alheri a wajen ka sai sharri. Yanzu ba sai ka sakawa Nasiba da kalar naka alherin ba. Ni kuma ka bini da irin nawa sharrin ba". *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* Ya jima bai iya ce wa komai ba. Da alamu kokawa yake da zuciyarsa. Domin fishin da ya ke shimfide a fuskarsa ya kai intaha. Tsawon lokaci mun yi shiru. Yaran kuwa duk sun yi barci. Ya munfasa ya ce "Ki yi hakuri. Na baki hakuri. Tashi mu tafi, na yafe miki". Na sake hade rai na ce "Ba na son ka yafe mini, domin ban maka komai ba. Ban zalunce ka ba. Kai ne ka ke shirin zalunta ta. Shi yasa na saukaka maka hanyar rabuwa da ni. Kawai ka sallame ni, ba zan iya zaman zullimi da fargaba ba. Tunda ka fara samun kudi ka ke canjawa. Nan gaba bansan yadda zamu kwashe ba. Gara tun wuri na barka tun baka gama barina ba ". Murya babu amo ya ce "me nake yi miki Asiya?" Baka yi mini komai. Son ka ne ba na yi! Ko dole ne?" Ya mik'e tsaye ya ce "Babu dole, to ba ni yarana". Na rungume Hamim da yake ta barci yana sakin ajiyar zuciya. Na ce "Ba zan bayar ba, dauki Hanif shi kenan an raba." Nan da nan ya hau rantsuwar ba zai bar shi ba. Ba zai raba su ba. Na dage tamkar har cikin zuciyata da gaske nake yi. Sosai muke yin takaddama. Sai da na gama famfa shi. Ya sakankan ce bazan iya yarda ya tafi da su ba. Sai kawai na ce "Dauke su ku tafi, Allah ya shiga al-amarinsu." Nan da nan ya yi turus. Jikinsa ya yi sanyi ainun. Ya zuba mini ido tsawon lokaci, ni kuma na yi kamar ban ga ni ba. Ya koma ya zauna a maimakon mikewar da ya yi, yana kumfar bakin sai na ba shi y'aya'nsa. Ya sassauta murya ya ce "Na baki hak'uri fa little. Ki mini uzziri mana". Murya na rawa na ce "Sau nawa ka ke yi mini laifi ina share wa?" Da sauri ya ce "Da yawa. Ina kuma gode miki. Na kuma dha fad'a miki kina da alfarmomi masu yawa a waje na. Yanzu ki mini hakuri dan Allah. Bazan sake yin hakan ba." Na hirgiza kai tabbacin ban karbi ban bakinsa ba. Ya marairaice ya ce "Haba mana my little angel. Ki huce, kin san fishin ki kassara ni yake yi". Sai lokacin na ji kuka ya zo mini. Na dinga yinsa bilhakki. Tsawon lokaci sannan na daina. Ya saki gauron numfashi ya ce "very sorry little. Nasan kin huce, tashi mu tafi dan Allah". Na girgiza kai na ce "Ni kam bazan koma ba fa. Ai tunda har waya ka ke yi da ita, nasan akwai abin da zai biyo baya. Dan haka ka je na bar mata kawai." Ya diririce ainun. Ya fara musun basa waya. Na zuba masa ido na ce "Waye ya ce mini Nasiba ta ce da Dada za'a zo ganin gida?" Ya ce "Ni ne". "Me yasa ni bata fada mini a wayar ba? Me yasa kullum sai ta kira ka? Me yasa sai kai Tijjani? Tunda bata kirana, bata kiran Yaya Salisu da ragowar. Na tsani rashin kame wa". Ya kasa magana tsawon lokaci. A sanyaye ya ce "Ba ni da bakin magana , am speechless. Abin da zan iya ce wa biyu ne. Ki mini uzziri, ki yi hakuri." Na yi shiru. Cikin rarrashin ya ce "Wallahi duk hasashen da kuke yi ni ban tab'a d'arsa shi a raina ba. Amma na gamsu kin fini gaskiya. Idan kika yarda muka tafi yanzu kuma. Na miki alkawarin har kasa ta rufe idona babu magana mai tsayi a tsakanina da ita bare soyayya ko aure, In sha Allah ". Na yi k'asa da kaina, ban ce komai ba, amma kuma k'ullin zuciyata ya hau warware wa". Ganin rarrashin ya fara tasiri. Ya sake tausasa harshe ya ce "Ai ni na dauka babu abin da zan yi miki, ki yi mini yaji. Tunda baki kai hakan ba ma, na miki babban laifi, kika rufa mini asiri kika yafe mini. Amma yanzu kuma a kan zato da zargi kika tozarta ni. Me yasa zaki munana zato a kaina? Me yasa kika zabi ki janyo mini fishin Babah?" Yana rufe baki na ce "saboda ka fahimci ban dauki alamarin da wasa ba, ka kuma gane yanzu hankali ya fara ratsa ni. Ba komai zan lamunta ba". "A karo na ba adadi ina sake baki hakuri. Allah ya huci zuciyar ki. Dan Allah mu rufe wannan matsalar. Wallahi bazan sake yi miki hakan ba, babu ruwana da ita, ko kallon inda take bazan sake yi ba. Ko na ganta a wajen Dada idan ta gaishe ni, zan amsa ne ba tare da na kalle ta ba, bare na gane me take ciki". Na yi shiru. Ban tanka ba. Ya ce "Haba mana Little"! Na cuna baki na ce "To kuma wayar da kuke yi fa?" Da hanzari ya miko mini wayar yana fad'in duba ki ga ni. Na share lambarta. Na kuma jefe lambar a black list ta yadda ita ma ba zata same ni ba". Na yi shiru ya ce "please mana Little ki ce kin huce, ki ce komai ya wuce". Na dauke kai na ce "To kuma iyakar da ka nuna mini fa? Da ka ce gidan ka ne ba nawa ba?" Da rawar murya ya ce "Kinsan An nadamu ala ma fata? To hakan maganar ta ke. To ni me ma zan yi da gidan da babu ke a cikinsa? Idan wannan maganar ne ta sake b'ata miki rai to ki huce. Na baki gidan ma gabadaya. Ki yi yadda ki ke so a cikinsa. Shi kenan?" Na ce shi kenan, amma bazan koma yau ba". Da hanzari ya ce "A a kada mu yi hakan, yanzu zamu tafi idan ba so kike hankalina yafi hakan tashi ba." A hankali na ce "To kawai sai Babah ta ga zamu tafi? Ka bari idan na fada mata jibi sai ka dawo mu tafi". Da azama ya ce "Wallahi bazan iya ba, kada ki zalunce ni, kin sani bazan iya ba. Tunda mun shirya ina ruwanta da mu?" Ya mik'e yana ce wa "bari na je na fada mata zamu tafi". Na bi bayan sa da kallo. Ina jin fishin da na yi da shi yana warware wa. Na zuba wa yaran ido. Ina rasa ga ne wa nafi so a cikinsu. Dukkansu Abu guda nake ji a kansu. Amma na fi jin tausayin Hamim haka siddan duk da shine fitinanne kuma marar hak'uri. A fili na furta "Allah ka rayamu tare da yaranmu, ka tsare mana su, ka yiwa rayuwarsu albarka". Ina kallon Hanif da yake barcinsa akan gado illah kansa da yake jikina. Ina ayyana mutane masu karamci da sadaukarwa tun suna kananu ake fahimtarsu. Yana wahalar gaske ya ture d'an-uwansa a jikina. Ko abu ya dauka da Hamim ya fara kuka zai ba shi. Haka nan baya damuwa idan na goyi Hamim shi na rik'e hannunsa. A raina sai nake ganin shine yafi dace wa ya amsa sunan Baban Marina. Ko da yake bansan ko Baban Bulkachuwan shi ma haka yake mai hak'urin gaske ne. Na shafa kansa ina ce wa "Allah yasa ka zarce da hak'uri da yakanar ka. Allah ya saukaka muku rayuwarku gabadaya". Na yi shiru ina jin wani irin abu na tsirga mini da bansan ko mene ne ba. A hakan Babah ta shigo, Tijjani na biye da ita a baya. Ta kalle ni ta ce "Wai har kin hakura kin ce zaki bi shi Yabi?" Yadda ta yi maganar sai na kasa amsawa. Nan da nan ya ce "Ta hakura mana Babah. Dan Allah kada ki sauya mata shawara. Na bata hak'uri, ke ma ina sake baki hak'uri." Ta ce "Idan ta ce zata koma ai shike nan. Amma idan ta ni ne ko zata koma sai na kira maza sun taya ni kafa maka hujja". Ya marairaice ya ce "Harshe da hakori ma ana samun sab'ani. Mun fahimci juna yanzu. Na yi alkawarin bazan kuma yi mata hakan ba. Mu rufe wannan matsalar a tsakaninmu dan Allah". Ta kalle ni ta ce "Zaki koma, ko sai mun zauna da iyayensa na nan na fada musu BAK'AR TA'ADAR da yake neman tsiro da ita, kada nan gaba su ce na kashe masa aure". Na kasa magana. Shi kuma fadi yake "Babah mun fa shirya ta fahimce ni, na bata hak'uri." Ta ce "Kasan Allah sai na ji da kunnena sannan zan bari ku tafi. Ai kai yanzu maganar ka ba abin dubawa ce ba". Ya rasa inda zai sa ransa. A kidime ya ce "Asiya taimake ni ki fada mata, kin huce, daure ki ce komai ya wuce. Kalli yadda yaran nan suke barcin nutsuwa a jikin ki. Ko baki hakura dan ni ba, huce saboda su". Dakin ya dauki shiru. Kallon Tijjani kawai za'a yi a gane yana cikin zullimi sosai. Ta sassauta ta ce "me kika ce, zaki koma, ko kuwa?" Na yi k'asa da kaina na ce "Tunda ya gane kurensa, ya janye kalamansa, ya kuma bada hakuri, to ba sai an tara masa jama'a ba. Ai mun ba shi assignment ". Ya yi maza ya ce "Wallahi exam ma kuka ba ni." *Anti Rabi how far?* ✍️ *UMM NIHLA COLLECTIONS* *Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik* *A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu* *Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*. *07020695644* *What's app only*. *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633 Ya juya ga Babah ya ce "To ga shi nan ta fada miki ta hak'ura". Ta fita tana fad'in "Y'aya'nta dai sun raunana ta. Ni kam ban so hakan ba." Gabadaya ya yi sanyi da kalamanta. Yana ganin zasu sa na sake botsare wa. Da sanyin murya ya ce "Mu tafi yanzu ko sai anjima little?" Na dauke kai ban amsa ba. Ya diririce. Ya ce "Mun gama magana fa Asiya". "Sai na shirya kayana". Na fada ba tare da na juyo ba. Ya ce "To bari idan an yi azahar sai mu tafi ko?" Ya fada da sigar da tambaya. Ni kuma na yi bakam. Ya yi shiru yana kallona. Ya saki gauron numfashi ya ce "Ina kayan na ki suke na hada miki?" Ban juyo ba na ce "Suna cikin wadirof din". Ya bude ya fito da jakar kayan nawa. Ya gyara su. Ya ninke wanda Hamim ya dauko a igiya ya saka, sannan ya zuge. Ya zauna yana ta yin mini maganganu da nufin mu yi hira. Ni kuwa sai basarwa na ke yi. Amma bai daina ba. Ya dawo daga masallaci ya tarar yara sun tashi muna falo duka muna cin abinci. Ya zauna shi ma ya zuba nasa. Babah ta sake yi masa fada sosai. Sannan ta hadamu gabadaya ta ja kunnenmu akan mu kara hak'uri da junanmu. Sannan ta gode mini da har yau ban canja mata matsayin da na bata ba. Ta rufe da ce wa "Dama idan kin ga kin gaji to wajena ne mafarki matukar ina raye". Na amsa mata da ce wa "In sha Allah Babah". Ya kasa hak'uri ya ce "Kin bata lasisin ta yiwa zaman aure tustu kawai Babah". Ta girgiza kai ta ce "Matukar za'a tozarta ba. Amma idan akan son zuciya zata yi, ai ba yarda zan yi ba. Kai ba abin kunya ba ne ace anji kanki?" Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Ya ce *Tsautsayi ne. Zan kuma kiyaye. Muka gama sannan muka yi haramar tafiya. Har kofar gida ta rako mu tana sake ba ni hakuri. A hanya kuwa shi da su Hanif suke ta hirarsu, yana ta amsa musu gwarmcin maganarsu. Muka isa gidan. Kaca-kaca yake tabbacin bai samu nutsuwar da yake gyara shi ba. Ya tafi masallaci sallar laasar. Ina idarwa na hau aikin gyara gidan. Ya dawo ya shiga taya ni. Cikin lokaci k'ank'ani muka kammala. Na yi wanka, na shiga kicin na fara hidimar had'a abincin dare. Ya fito sanye da jallabiya sai kamshi yake yi tabbacin shi ma wankan ya yi . Sannan ya yiwa yaran. Ya shigo kicin din ya ja turmi ya zauna. Ya zuba mini ido. Ya ce "Little ba ki huce ba ne? Ban kalle shi ba. Na ce "Me ka ga ni?" Murya babu amo ya ce "Ba ki dawo da walwalar ki ". Na yi k'asa da kaina tare da ce wa "Na huce mana. Kawai zuciyata ce take ta yin wasiwasi mai yawa". Ya mik'e da azama ya rungume ni ta bayana. *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*. Ya rankwafo sosai in ya dora kansa a wuyana ya sassauta murya ya ce "Bai kamata ki yi wasiwasi a kaina ba Little. Kuskure ne wanda ajizanci yake sababa shi. Ki manta wannan al'amarin. Ina cikin matsanancin damuwa da fishin ki. Pls my little angel double sorry ". Na saki ajiyar zuciya tare da ce wa "Allah ya kiyaye na gaba" Ya amsa da "Ameen dear. Allah ya yi miki albarka." Ya dinga kissing d'in kunnena da wuyana da duk inda ya yi masa. Tamkar ya jani daki. Amma kusantawor magariba ya sanya ya hakura a dole. Da daddare yara na yin barci, ya fito da maitarsa a fili. Bai sarara mini ba sai da ya samu nutsuwar da yake so. Kalaman soyayya da na rarrashi ya dinga amayarwa. Wasu ma ni ban tab'a jinsi ba sai a ranar. Ya jadda mini ce wa "Dukkan nasarar da ya samu tana d'amfare da irin gudunmawar da na ba shi a zamanmu. Ya sani bai manta ba, ba kuma zai mance ba. Ni kuma na yi lamo a jikinsa na shige ya rufe ni ruf. Ina jin kalamansa suna warware dukkan damuwata. Ina sake gasgata yana sona, so na hakika. Domin ya shayar da ni kalolin kauna masu tsayawa a rai da gangar jiki gabadaya. Ya kaurara murya ya ce "Ki mini alkawarin baza ki sake barin gidan nan babu izinina ba. Ki mini alkawarin komin runtsi ba zaki juya mini baya, Asiya ki mini alkawarin zaki gasgata ni ko da kowa bai yarda da ni ba. Idan har kin tsaya mini zan yi ta samun cigaba a rayuwata. Amma idan kika juya mini baya ina tabbatar miki komai zai lalace mini ya cakalkale watak'ila ma na shiga rayuwar da tafi wanda na yi a baya muni!" Ya karasa cikin matsanancin damuwa da karaya. Tausayin sa ya baibaye ni. Na nisa na ce "Idan har ka mini alkawarin zaka kame daga kule kulen mata, zaka kiyaye dukkan iyakokin shari'a to mene ne ba zan yi maka ba Baban 2?" Ya sake tsanta rungumar da ya yi mini. Yana fad'in "Na gode sosai Asiyata". Sai kawai na ji hawayensa na sauka a kan goshina. Na shiga rudani mai yawa domin a tsawon lokacin da na shafe tare da shi ban tab'a ganin kukansa ba hana rantsuwa lokacin rikicin Rafi'a. Na ga k'walla a idonsa amma hawaye bai zuba ba . Murya na rawa na ce "mene ne?" Shi ma da rawar murya ya ce "Haka kawai nake ganin kamar duniyata ta zo karshe. Karbar filina da kamfani ya yi, yana neman zame mini fitina. To idan ke ma zaki dinga yi mini irin wannan fishin akan sabanin ra'ayi, ki dinga zargina akan abin da baki ga ni ba. Na tabbatar wata rana za'a wayi gari ne bakin cikin duniya ya mayar da ni gawa". Murya babu amo na ce "Da ikon Ubangiji hakan ba zata faru ba. Ba zan sake yi maka irin haka ba. Ka yi hakuri ". Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa, domin shi din mai son na ba shi hak'uri ne ainun. Ya sake ce wa "na sake rokon ki?" Zuciyata na bugawa ainun na ce "Ina jin ka." Ya ce "Dan Allah ki yi dukkan iyawar ki, kada ki bari yaran nan su tagayyara idan har mutuwa ta yi gaggawa ta sure ni". Ai bansan yadda aka yi ba, kuka ya goce mini mai tayar da hankali domin k'warai ya gigita ni. Maimakon ya kwantar mini da hankali sai ya sake ce wa "Na sani idan na mutu dole zaki yi aure Asiya. Domin a yanzu ne ma kika yi shekaru ashirin. Amma dan Allah, dan darajar ma'aiki ban da Jabir, ban da shi little!". Ya fada da wani irin yanayi na tashin hankali sosai. Kukan da na ke yi ya tsaya cak a dalilin tashin hankalin da ya jefa ni ya wuce kukan hawaye ko na baki. Sai kukan zuci da na gangar jiki. Zufa ta dinga yanko mini tamkar na yi tsere. Na kasa ko da motsi. Tsawon lokaci muna ta fama da sake saken zuciya da fargaba. Murya babu amo na ce "wannan ne tukuicin dawowar da na yi ko Baban 2? Haka kawai ka tayar mini da hankali. Kana nufin mutuwa zaka yi ka bar ni da k'ananun y'aya'n ka Tijjani?" Ya ce "Jikina da zuciyata ke raya mini hakan, amma ai bani da tabbacin hakan domin gaibu ne. Fatana dai ki cigaba da zama jajirtacciya ko bayan babu ni. Akwai mata da yawa da suka sadaukar da kuruciyarsu da jin dadinsu dan inganta goben y'aya'nsu. Ki kula da su, ki saka idon a kan tarbiyarsu, idan Ubangiji ya baki tsawon rai sai suma su raine ki, su ji kan ki". Na sake kece wa da kuka tare da ce wa "Kada ka mini haka Baban 2. Dan Allah ina son na rayu da kai. Ina son twins su girma a tsakanin uwa da uba, bana son na rasa ka. Kai nake fatan ya zame mini miji har a aljanna. Idan mutuwar zata dauke ni, to kawai ta hada ta dauke mu tare." Da sauri ya ce "A a In sha Allah ke zaki rayu, ki zame wa y'aya'nmu bangon jingina. Me yasa ba ki gano girman kalubalen da zasu fuskanta a dalilin rashin uwa da uba ba?." Cikin kuka sosai na ce "Allah ka jinkirta mana rayuwarmu gabadaya". Ganin hankalina ya tashi ainun, sai ya kawar da maganar ya shiga rarrashina da tarairaya ta. Amma gabadaya hankalina bai kwanta ba. Na riga da na ankara matuka da gaske. Washagari haka na tashi sukuku babu kuzari bare walwala. Ya yi shirin tafiya kasuwar Ilela. Zuciyata ta dinga ayyana mini na hana shi fita domin sai nake ganin tamkar ba zai dawo ba. Ai kuwa na fasa masa kukan ba zai fita ba. Duk yadda dinga rarrashina amma ban yarda na amince zai fita ba. Kan dole ya zauna ya fasa fitar. Ya sassauta murya ya ce "Idan Ubangiji ya so ikon sa sai na mutu a kan katifata lafiya lau ba tare da ciwon komai ba." Ina hawaye na ce "Masifa da jafa'in kake jawo mini Tijjani Allah ya yafe maka kawai. Allah yasa kai ne zaka ga gawa ta. In kuwa ba haka ba tabbas sai ka yi mini sababin hawan jinin da zai nannad'e ni na kasa moruwa". Ya numfasa bai ce komai ba, fitar da bai yi ba ke nan. Yaranmu suna ta kai komon farincikin ganina a tare da su. Mu kuma muna cikin wani irin yanayi mai wahalar wa. Kwanaki biyu na rik'e Tijjani a gida. Masallaci kawai nake barinsa ya je. Mukullin motar na boye na hana shi. Na kafe sai ya canja sana'a. Da wa'azi da nasiha da lallashi ya shawo kaina ta hanyar cusa mini tauhidi tare da gasgata hukuncin Ubangiji baya sauyawa. Kawai na dinga fahimtar maganganunsa tare da zama jaruma, mai fuskantar dukkan kalubalen rayuwa da k'arfin zuciya, sai kuma na dage da addu'ar duk runtsi Ubangiji ya tsare mini imani ya kuma shirya mini zuria. Na yarda da nasiharsa. Na ba shi mukullin motar sa. Ranar da ya fara fita, na k'ira wayarsa tafi sau goma, ina tambayar sa inda yake. Kwanaki suka yi ta shud'e wa ba abin da ya samu Tijjani. Sai na fara warware wa. Zullimin da nake ciki ya yi sauki. Yayin da shi kuma yake ta samun nasibi. Domin a yanzu ya bar kasuwa. Amma yana sarar kayan miya ya kai kasuwannin k'auyuka. Idan zai juyo sai ya saro abin da yake sauki a garin ya zo ya siyar a cikin gari. Kafin azahar ya dawo gida. Sai ya sake fito da dabarar kai da karbo sako(Delivery). Sosai yake samun alheri da harkar. Ya fara tafiya Jos ya kai kayan miya da sakonnin jama'a, idan zai dawo ya sake karbo sakonni ya kuma saro dankalin turawa da su atile. Nan da nan sai al'amarin ya karbe shi. Muka canja mu da y'aya'nmu a dalilin wadatar da yake samu. Na fara murje wa, ina haske, suturu suka yawaita mini. Mussaman material din Umm Nihla mazauniyar Malaysia. Bana gajiya da siyan yadinka ta. Saboda rashin nauyinsu da kuma yadda suke shan ruwa babu kode wa. Shi kansa Tijjani yana matukar son na yi masa kwalliya da su.... Yawan fataucin da yake yi tsakanin Bauchi zuwa Jos ya sanya akai akai yake zuwa Toro. Ganin wadatar da yake ciki sai aka fara yi mana sintiri da sunan ziyara ko hutu. Wanda kafin ya shiga wannan rufin asirin ba'a cika tunawa da shi ba. Bare a taimake shi. Nasiba ce dai bai sake yarda ta zo ba, ya yanke dukkan hulda da ita. A wannan tsukun na fahimci al'amarin da yake zuciyar Tijjani, domin yadda yake yiwa Baban Marina hidima ko su Yaya Salisu basa yi masa hakan. Yanzu a gidanmu ana iya soya dankali ko doya. Shi da su Yaya Salisu da Yaya Rabiu suka kwaskware kofar tamu ta farfado. Baban Marina da kansa ya fada mini a waya ce wa Duk satin duniya sai Tijjani ya tura masa kudi. Ban da kayan miya da su dankali da yake kai masa babu gajiya. Haka kuma yake yiwa mahaifiyarsa. Dada kuwa kayan shayi ne da sabulai da turare baya rabata da su. Maimakon a yaba masa sai gabadaya gidan aka hau cece kucen ni na hana shi ya kyautata wa su Baban Tsakiyar da Baban kasuwa sosai. Tunda ai duk daya suke da Baban Marina a wajen sa. Amma suna gani za'a yi ta shiga da kayayyaki kofarsa akai akai. Amma su a leda ne kuma sai jifa jifa. Shin dan yana surukinsa ne, ko kuwa akwai wata alak'a ce da tafi tasu?" Nazira ke tsegunta mini. Tare da bani labarin yadda Baba Maryo take cusa masa Nasiba da fad'in ai ba komai ba ne dan ya hadamu ya aura. Rabon y'aya'n da ta haifa ne ya sanya ba a yi da shi ba. Haka kuma ga rabon y'an biyu a jikin Yabi. Dada dai bata ce wa komai a dalilin tana gudun bacin ran autarta. Yayin da Nasiba bata zafafa ba. Tabbas tana son Bulkachuwa. Idan ya nuna yana sonta a radin kansa zata amince domin ba zata zalunci kanta saboda Yabi ba. Amma ta karaya a dalilin ta fahimci shi kansa a hannun Yabin ya ke. Tunda ta dawo daga gidansa ta zauna ta yi nazari da kyau ta fahimci Yabi ta bar masa gidan ne saboda ya kai ta. Tun daga lokacin kuma bata sake ganin walwalarsa ba. Idan ta gaishe shi zai amsa. Amma ko kallon inda take baya yi, bare ya fahimci me take ciki. Ta kuma tabbatar fishin Yabi yake gudu na gaske. Ita da kanta mamakin yadda yake shiga nutsuwar sa yake idan yana gabanta. Idan kuwa ya zo Toro ta bugo masa waya gabadaya nutsuwa wa yake tamkar uwarsa ce ta masa waya. Ya dinga b'are b'are yana tambayar lafiyarta da ta tagwaye. Sannan ya bawa Dada wayar dan ya tabbatar mata a inda yake. A kasan ranta bata ganin aibun matsananciyar soyayya da gudun zuciyar Yabi da yake yi. Domin ta tabbatar Yabi ta cancanci ya mata irin wannan soyayyar domin ta sadaukar da abubuwa da yawa saboda shi. Ta jure a lokacin da kowa yake gudunsa duk da tirsasata aka yi. Ta rufa masa asiri da sana'arta. Kenan a yanzu da ya fara samun dama, dan ya kyautata mata ba abin birge wa ya yi ba. Abin da ya kamata yake yi. Ta sake yarda ko ya aure ta, ba zata iya da jidalin Yabi ba. Tunda a bayyane yake a hannunta yake. Kawai zaman hak'uri zata yi. Abin da ya dame ta daya ne. Yadda mahaifiyarta ta fantsama nemo mata maganin da za'a karkato da hankalinsa kanta. Kullum a cikin bata rubutu take wanda ta tabbatar sunansa ake rubuce wa. Tana kwance ita kad'ai a daki tana ta nazari tare da alkalancin bai kamata ta aure shi ba. Mafi muni ma ta hanyar asiri. Ta tabbatar mahaifiyarta ce ta yi sanadin raba ta da shi a dalilin ba shi da komai, kuma ba a kintse yake ba. "Yanzu kuma da ya zama mai daraja sai ki cusa masa ni a kan dole?" Ta furta a fili ba tare da ta shirya yin hakan ba. Kunya ta kama Nasiba. Ta ya ya mahaifiyarta zata runtse ido daga yin alkunya ga d'iyar wanta uwa daya uba daya? Ta san zumuncin zamani ya shiga tasgado mai yawa, mussaman na gidansu. Amma tana matukar kaduwa da son kai irin na gyatumarta. Har kunya ta taya ta ji a sadda ta karbo mata taimakon da aka rubuce sunan Tijjani da na uwarsa. Alhalin a sadda yake sonta akan idon uwar tasa ta wulakantasu ta hanyar ce wa d'anta bai kai a ba shi aurenta ba. Amma yanzu wai ba wanda take so ya zama surikinta sai Tijjani, mijin Yabin Baban Marina. Ta sake ce wa "wacce irin BAK'AR TA'ADA ce wannan? Wanne irin son zuciya ne ya yiwa mutanan yau katutu a zuciya?" ✍️ *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* 83&84. Zaune nake ina duba kayan gyara da na siya a wajen Surayya Halin yau. Domin lokacin haihuwar twins a wajen ta Yaya Ummi ta siya mini kayan da suka gyara ni matuka da gaske har Baban 2 ya dinga tambabar ni na haife su kuwa?. Tsumin kwakwa ya tayar mini da kwadayinsa da na jima ina yi. Domin dad'i gare shi. Na dauka na sha. Na tashi na je kicin na dauko gwangwanin Madara ta ruwa na fasa. Domin tunda Tijjani ya fara samun sukuni kullum sai na sha gwangwanin Madara. Ban da sauran abubuwan da suke inganta lafiyar jiki. Na fasa na juye a kofi. Na dawo falo na bude robar koren maganin da na tabbatar da kyaunsa. Na zuba na juya na shanye. Ina hasasho subadin da zan sha yau a wajensa. Na tattara sauran na kulle dan kada na yi over dose. Na dauki waya na k'ira shi. Ya amsa na ce "ka taho ne?" "Eh kina son wani abu ne?" "Ka taho mini da dabino ko kwakwa ". Da azama ya ce "Done my little, ban ji hayaniyar 2 ba". Na ce "gasu nan barci suka yi". Ya ce "Da yammacin nan? Tashe su dan Allah. Bazan yarda da daddare su tisamu a gaba su hana ni hutawa ba". Na kyalkyale da dariya. Domin nasan nufinsa. Na mayar da robar y'aya'n gadali domin sai gobe zan ci tunda bani da kwakwa ko dabino a hannuna. *Akwai kayan Chad masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*. *08032773332*. Sosai muke zamana lafiya da taka tsantsan kan abin da zai janyo mana rikici. Na fahimci yajin da na yi, ya sake sawa Tijjani tsoron mu yi fada. Duk da hakan kuma wani loakcin zai fitittke ya yi mini sababin na raina shi, ko akan abu kad'an sai ya tsiri fishi yana fad'in "Tunda Babah ta bani lasisin na dinga yi masa yaji shi ke nan nake yi masa abin da nake so. Dan na ga ba shi da yadda zai yi. Idan yana irin wannan fishin, wani zubin ya bani dariya. Wani lokacin ya bani mamaki. Idan na so sai na rarrashe shi tunda shi haka yake kamar su Hanif wajen son a ritata shi, a tarairaye shi. Wanii lokacin kuwa na share shi, na fi shi fishi. Idan ya lura da hakan sai ya yi maza ya hadiye nasa fishin ya hau lallaba ni. *Shekara daya a gaba* Kwanci tashi tagwaye suka yi shekaru uku. Haka muke gurgura rayuwa yadda ta zo. Wataran fari, wataran baki. Zuwa lokacin sosai harkokokin Bulkachuwa suka sake mike wa. Ni kaina ina siyar da dankalin turawa da su karas da atile a cikin gida. Ba kuma k'aramin alheri nake samu ba. Tunda shine yake siyo mini babu maganar kudin kawowa. Idan na siyar na cire riba na ba shi kudin sai ya sake siyo mini wasu. A hakan har na tara jarina ba tare da na zuba wani kudin ba. Dan haka na ware kudinsa na ba shi, tare da yi masa bayanin yadda kudaden suka haihu dan haka zan cigaba da yi da nawa. Yana bude baki sai ce wa ya yi wadananan din ma naki ne. Kin tuna bashin da kika yi ta ranta mini a lokacin da bani da shi?". Na girgiza lai na ce " A a tsakanina da kai babu bashi Baban 2. Ba ka dauke ni yadda na dauke ba Wallahi." Da azama ya ce "Na gode, na yarda babu bashi. To na ba ki kyauta. Na murmusa na ce "Ka dai biya ni kawai. Shike nan na gode, Allah ya kara budi da lafiya." Ya amsa da "Ameen maman 2." Ya kanne mini ido tare da ce wa "Na kosa a yiwa su twins Gambo fa". Na yi dariya na mike na bar shi dan yanzu sai ya fara tsokana ta akan abubuwan da na yi ta yi masa a baya. Muna cikin haka babu zato sai ga shi ya zo mini da takardar da take nuni na samu gurbin karatu a kwalejin ilimi ta jihar Bauchi. Ban yi murna ba, domin tun filazal na fi son na yi kasuwanci. Na kuma fahimci Ubangiji ya sanya mini nasibi a cikin juya kudi. To akan me zan damu kaina sai na yi karatun da babu garantin zan ci moriyarsa tunda kullum kasar sake lalace wa take yi. Aikin gwamnati siyar da shi ake yi da makuden kudade, sai kana da hanya ma da ka samu a siyar maka d'in. Bai yi fishi ba, ya zauna ya dinga zayyano mini tasirin ilimi a wajen mace ba dan ta yi aiki ta samu kudi ba ne kawai. Ilimin mace da gogewarta na taimaka mata k'warai wajen bawa yara tarbiya da sanin yadda zata yi cudanya da mutane daban daban. Ya sanyaya murya ya ce "Ki daure ki sawa zuciyar ki soyayyar karatun nan Asiya dan sai kin yi shi. Fata na ke yi ko na mutu a ce ke din kina da wata madagora da zaki rik'e mini y'aya'na. Duk duniya ke nake da tabbacin ba zaki gaza da hidimarsu ba. Daure ki bani hadin kai mana". Na dinga kuka domin idan yana irin wannan maganganun gabadaya kidime wa nake yi. Shi kuma baya fasa fada mini lokaci zuwa lokaci, tamkar mai son na yi haddarsu. Tare muka fara makaranta da su Hanif. Domin Nursery da take cikin college din ya snaya su. Da kansa yake kai mu. Sai ya wuce garin da zai je. Bama koma wa gida sai na gama daukar darussa. Komawa ta makaranta sai ta jawo takaddama mai yawa a cikin gidan Marina. Domin a tarihin gidan ni ce na kammala sakandire har na fara ta gaba da ita da kuma aurena. Dada ta dinga sababin ya rungumi BAK'AR TA'ADAR arna masu barin matansu suna cud'anya da mazaje kullum da sunan neman ilimi. Babu kishi babu komai. Alhalin ma'aiki ya ce wanda baya kishin iyalin sa babu shi babu jin kamshin aljanna. Yanzu gabadaya gidan Marina ni na tsole ido. Rufin asirin da muke ciki ya na matukar mintsinin ahalin gidan. Bana damuwa tunda ba a garin nake ba. Wani abin ma har a yi yamididinsa a gama bana ji bare raina ya baci a banza. Kwatsam sai ga Maijidda a gida, wai ta yi yaji. Al'amarin bai yiwa iyayenta dadi ba. Domin ni da ake son ganina ina cikin tasku da jele da sunan bacin rai ba a tab'a ganin na yi hakan ba. Kuma abin mamaki Jabir din ne ya kawota gidan da kansa. Domin ta k'ure hak'urinsa a yadda ya fada. Ya murje idonsa ya juya ya barta. Hakan ya kawo cece kuce da rashin jituwa a tsakanin Baban Tsakiya da na Kasuwa. Duk yadda suka so boye maganar kada mu ji. Sai da maganar ta fantsama domin aure zai k'ara ita kuwa ta ce bai isa ba, sai dai ya zaba ko ita ko amaryar. Ya so su fahimci juna amma ta tada balli domin da ta ga yarinyar da zai aura tunda dalibar kwalejin da yake koyarwa ce. Ai sai ta gigice domin haka take yar tsurut fara kal tamkar dai abokiyar tagwaitakar Yabi ce. Hankalinta ya rubanya tashi domin ta tabbatar ya sota ne a dalilin yadda suke yanayi da ex love dinsa. Ta kuwa ce ba dai ita ba. Shi kuwa ya ce bata da hurumin zaba masa wacce zai yi zaman aure da ita. Watanni biyu basa cikin zaman lafiya, gabadaya ya murde mata fiye da yadda ta murde. A karshe ya kawo ta gida ya ce ta zauna ta huta tukun. Da ya tafi ya kashe wayarsa da dukkan hanyar da za'a same shi. Baban Kasuwa ya dinga fad'a tare da fad'in tozarcin da Jabir ya yi, da shi yake. Kuma ubansa ya kasa tsawatar masa. Saboda yana jin tsoron sa. Rikici ya kaure a tsakaninsu Dada ta kasa shawo kan matsalar domin Baban kasuwa ya dauka da zafi, kuma dama tafi gudun zuciyarsa. Baban marinar da ba'a saka shi ba, shine ya tuntunbesu bayan Dada ta fad'a masa a dunkule ba a bude ba. Abin mamaki kowa ya ce masa babu komai, duk da Dada ta fad'a masa. Shi kuwa sai ya hak'ura ya zuba musu ido. Bai gane kan al'amarin ba sai da ta yi sati biyu. Da kanta ta je ta durkusa tana kuka ta fad'a masa yadda abubuwan suka kasance, sannan ta roki Baban Marina akan ya bawa Jabir hak'uri. Gabadaya ta shiga damuwa da tunani domin dukkan y'aya'nta uku suna can tare da shi. Mai shan nono kawai ya bar mata. Bata tab'a zaton zai yi mata hakan ba. Duk kokarin Baban Marina ya amsa samun Jabir. Washagari ya tisa ta a gaba ya nufi Kaduna da ita. A ransa ya tabbatar dan tana son komawa dakinta ne. Ba dan hakan ba da bai isa ya yi irin wannan ikon ba. Jabir na ganin sa ya ware fuska ya marce shi da girmamawa. Baban ya dinga yi masa fada tare da tabbatar masa ya yi tsaurin ido. Cikin jin nauyi ya ce "Ka yi hak'uri Baba! Ta kai ni bango ne da yawa. Ni fa dama hak'uri nake yi domin ba hakan nake so ba, amma tunda kaddara da rabo ya ba ni ita, ban zalunce ta ba. Ga ta nan ta fada maka inda na kuskure domin nasan iyakar adalci ina yi mata. Aure kuwa bata isa hana ni yi ba, bata kuma da hurumin zaba mini wacce zan aura domin ni din ba makaho ba ba ne, bare ta ce zata zaba mini wacce zan aura". Baba dai ya yi masa fada tare ce wa "Ka dauke ta ka kai mana ita, ka yi tafiyar ka ai rainamu ka yi Jabiru. Duk cikinmu ka rasa wanda zai maka maganin matsalar sai ta hanyar mayar mana da ita? Ko a lahira wani na cin arzkin wani. Kada ka sake irin haka. Kishi kuma ai dole ta yi, ka rarrashe ta, ka kwantar mata da hankali ba wai ka ankara ta ba." Ya juya ga Maijidda take kuka sosai ya ce "Ke kuma ba ruwan ki da auren sa, matukar yana yi miki adalci, kawai ki yi hakuri ki yi addu'a. Ai kishiya yar uwa ce, ina ruwan ki da ita. Ban da ma sakarci me ya ka ki yin fitina akan wacce ma bata zo hannunsa ba? Kina ahalin gidan Marina ki ce ba kya son kishiya? To ko da kika ga gyatumar ki ita kad'ai ai mu kina ganin kofofinmu mata ne da yawa ba kuma wacce ta kori wata, ko ta hana ta samun arzikin ta." A ranar ya juyo ya dawo. Ba jimawa kuwa Jabir ya yi aurensa. Hakan ba k'aramin tasgado ya janyo a taskanin Baban kasuwa da na Tsakiya ba. Da k'yar aka samu suka fara gaisawa. Kunyar mutane da yadda aka san kansu a hade yake ya sanya suke gaisawa. Da kuma yadda Dada ta yi kuka sosai akan gabar da suke yi da juna. A zahiri sun shirya amma kasan zuciyoyi babu dad'i. Ba yadda zasu yi ne kowa yana ganin shine akan dai dai. Baban Marina dai bai ce kala ba. Domin yanzu da abubuwa suka fara warware masa a dalilin mafi yawa y'aya'nsa muna cikin rufin asiri. Muna had'a abin da za'a ci a k'ofarmu. Tijjani kuwa ya dauke masa cefanen kayan miya da kudin k'ananun bukatu. Hakan ya sake janyo masa bakin jinin da babu yadda za'a yi sai zunde a bayan ido. *** A hakan na cinye shekara d'aya da fara karatun. Na fara nisa a cikin ta biyu. Tun bai shiga jikina ba, har na sanya shi a raina na mayar da hankali, hakan ya faranta ran Tijjani tunda ban sami carry over a shekarar farko ba. A hankali sai nake ganin Tijjani na d'an sauyawa. Sauyin bai shafi mu'amalata da shi ba. Amma yana yawan zuwa Toro. Kusan kullum sai ya je ko da ba zai je Jos ba. Ina ta jin rade radin yadda yanzu yake zama ya yi hira da Nasiba da har yanzu bata yi aure ba. Sai ma kasuwanci da take yi sosai. Kayan gwanjo take siyowa a Jos masu kyau. Har ce mini aka yi yana karbo mata sakon kayan. Tun ina daure wa ina dauke kai daga abubuwan da nake ji har na fara sike wa. A dalilin kullum dare sai ya fita k'ofar gida ya shafe lokaci mai yawa yana waya. Haka nan kaffa kaffa yake da wayarsa abin da baya yi a da. Da na yi masa magana sai ya balbale ni da fad'an na saka masa ido ne. Ban da hakan me yake yi mini? Dan ya yi wayar da bata shafe ni ba a waje shine laifi? Na kasa bude baki na ce komai domin ba ni da hujja. A hankali muka fara samun tazara a tsakaninmu. Na sani bai canja daga kawo mini abubuwan abincin ko na bukata ba. Bai canja a hidimar makaranta ta ko hidimar y'aya'nsa ba. Sannan bai canja mini a mu'amalarmu ta auratayya ba. Har yau din nan a cikin mararina ya ke. Duk da ni din ma kullum a cikin gyara kaina nake da ingantattun kayan Surayya da basu da illah ga lafiya. Sannan ina amfani da kayan g.h.t na FASEELAT. Amma yawan wayar da yake yi da sintirin zuwa Toro, da sabunta mu'amalarsa da Nasiba da nake ta jin rade radinta, tana matukar ci mini tuwo a k'warya. Na rasa wa zan fad'awa ya fahimce ni. Domin da na fadawa Gwaggo ce wa ta yi "Ina ruwan ki da jita jita? Sannan ai bai zai yi aure bai fada ba. Ki rage kishi mussaman kan abin da baki gani ba, zato ne da shati fadi kawai. Haka na hak'ura na cigaba da zuba ido tare da hak'uri. Amma sai nake ta d'ad'are wa da shi. Ko a shimfida bana wani katabus shi zai yi kidansa da rawar sa. Wani lokacin ya tambayi dalilin sauyin nawa cikin kwanciyar hankali. Bana iya ce masa komai sai dai na ce "Ban canja ba, babu komai". Wani lokacin ya ce "Allah ya sauwake. Wani lokacin ya yi tsuka ya juya mini baya tare da fad'in "Zan yi maganin wulakanta ni da kike haka siddan Asiya." Gabadaya mun koma muna ganin laifin junanmu a dalilin kowa bai gamsu da kokarin d'an-uwansa ba. A haka na kammala aji biyu. Twins sun yi wayo sosai tunda sun shiga shekaru biyar. Wani irin wayo da fikira a cikinsu tamkar wanda suke siyo dabara a kasuwa. Gabadaya sun juye ubansu sak. Ga shi suna girma suna sake zama iri d'aya. Ni da kaina ina gane su ne ta halayyarsu. Domin har yau din nan Hanif mai hakuri ne, magana bata dame shi ba. Sabanin Hamim d'an hayaniya kuma mafadaci irina. Har yanzu bai bar kuka ba. Sau biyu ina yin bari. A yanzu haka ina zuwa ganin likita a dalilin hakan. Na karshen nan da na yi Bulkachuwa ce mini ya yi "Ina sane nake bararwa tunda na saka masifa a raina. Ya rasa me yake mini da nake gana masa azaba haka. Kallon sa na yi kawai. Ba tare da na tanka masa ba. Domin na riga da na saka a raina ce wa hakurin da aka yi ta jaddada mini na yi a lokacin aurena. Yanzu ne zan fara shi. Dan haka na rungumi addu'a, y'aya'na da karatuna hadi da sana'ata. Na tattara shi na zuba masa ido yana yin almuransa yadda yake so. Muna cikin wannan zaman na fallasa tafi yabon yawa. Kamfani suka sake biyansa kudin hayar filinsa tunda shekaru uku ta cika. A wannan karon har da kari akan wanccan. Duk yadda muke jin haushin juna sai da ya zauna ya mini bayanin komai. Ya kwashe mu ni da yara zuwa Kano. Ya yi mana siyayya. Muka kwana biyu, muka juyo da kaya niki-niki. Yara na baya duk barci ya sure su. Ya sassauta murya ya ce "Zan canja motar nan. Zan siyo wacce ta fita." A takaice na ce "Allah ya kara budi". Ya zarce da fad'in "Ana mini cinikin wani gida mai kyau a Toro zan siya". Nan ma a gajarce na ce "Allah ya sanya alheri." Daga haka bamu sake magana ba har muka iso Bauchi. A dalilin ya fusata duk yadda ya kwashe ni ya mini hidima bai sa na saki raina ba. Ni kuma ina masa kallon a yanzu yana ganin yafi karfina tunda yana samun duk abin da yake so. Kasuwa tana gara masa ainun. Shi yasa gabadaya yake neman bijire mini. Duk abin da yasan bana so a yanzu baya jin komai ya yi a gabana. Jiya da daddare ina jin sa a waya yana ce wa "Ga ni kike ba zan iya bata wayar ba? Wai me kika dauke ni ne? Bari ki ga na sayi gidan da zan saka.ki a ciki, ki ga yadda zan fito da maganar gabadaya. Namiji dan zai k'ara aure sai a ce ba zai iya ba? Mata nawa ne a gidansu? Nima kuma mahaifina biyu gare shi. Da ba'a karin aure da ba'a haife ni ba, tunda tawa gyatumar ce amarya a gidanmu ". Dai dai nan na fito a bandakin. Nan da nan ya katse wayar tare da ce wa "Zamu cigaba da tattauna wa da safe". Ya katse wayar tare da kashe ta gabadaya. Tun lokacin na sake karaya da shi. Tabbas aure yake nema kuma a Toro tunda har zai sayi gidan da zai saka ta a can. Sannan tun yanzu na dame ta tunda har tana masa shaguben tsorona yake ji ba zai iya aure ba. A raina na shiga yiwa mutanan da suke ganin Bulkachuwa tsorona yake ji Allah ya isa ta fi goma. Domin a yanzu da kowa yake mini kallon ina cikin rufin asiri da jin dad'i a gidansa. Ni kad'ai nasan me nake fuskanta. Nafi samun nutsuwa a lokacin da ba shi da ko sisi. A yanzu ba abin da bani da shi a gidan na cima, tunda ga kan nama, kifi, madara, dankali, doya, bare kuma kayan miya, da duk nau'in kayan abincin. Ruwa da lemo basa yanke wa. Komai baja baja yake ajiye mana. Haka sutura ta wadace ni ainun. Amma kuma bani da nutsuwar da nake da ita a da. Ba ya shiririce mini kamar lokacin baya. Dan haka sai na fi son waccar rayuwar da kowa yake mini kallon tausayi. Babah ta kawo mana ziyara. Ta dinga rarrashi tare da shan cikina akan matsalar da ta sanya bana girma, da na fara murmure wa zan sake tsomare wa. Ban yarda na ce komai ba, saboda nasan ba zata yi masa ta dad'i ba, idan ta tafi kuma ya hau sababin ina had'a shi da uwarsa duk da ba komai yake mini ba, ni ce nake zaluntarsa. Da kanta ta fahimci a yanzu ni da shi kowa harkar gabansa yake yi. Gamu nan ne dai, babu warkajabi irin na da, babu nishadi a tare da mu duk da ba gaba muke yi ba. Da daddare bayan yara sun yi barci ta zaunar da mu tana bincikar matsalarmu a kokarin ta na son ta sulhunta mu ta dinke barakar da kullum take sake bunk'asa a zukatanmu ba tare da mun ankara ba. Tsawon lokaci ban iya bude baki na ce uffan ba. Ta hakura ta koma kansa. Cikin kwanciyar hankali ta tambaye shi me yake faruwa. Ai tamkar gudawa haka ya b'arke da zano laifukana. Ya kaurara murya ya ce "Gata nan gabadaya ta ki sarrafuwa mini. Ko dariya take yi da y'aya'nta idan na zauna a cikinsu ta gintse dariyar ke nan. Idan tana zaune a falo na zauna sai ta san abin da zata kirkiro da zai sa ta tashi ta bar mini wajen. Ba zan mata abu ta nuna ta ji dad'i ba, zata dai ta ce ta gode a takaice. Gabadaya ta fitini kanta ta kuma fitine ni. Gara ma da Allah yasa kika fahimci masifar da d'orawa ranta. Gata nan ta fada miki mene ne bana yi a gidan nan da zata kwarzabe mu irin haka. Yanzu idan na fita har fargabar dawo wa nake yi tsabar yadda take shagulatin bangaro da ni, da dukkan al'amarina. Ban sani ba ko miyagun kawaye suke hure mata kunne. Na tabbatar cikin da baya zama idan ta samu ma akwai dalili, idan an tsananta bincike, tunda ta riga ta taurare mini, ita tasan me take nufi da zaman". Na yi k'asa da kaina ina hawaye mai cin rai. Zuciyata tamkar ta fad'o k'asa idan yana danganta b'arin da nake yi ni ce da alhakin hakan. Babah ta dawo kaina cikin tausasa harshe ta ce "Haba Yabi me zai sa ki abin da baki yi a da ba, sai yanzu da kike girma, kuma Ubangiji yake ta yi muku Alam nasharaha. Me zai sa ki yi haka?" Na fashe da kuka mai ciwo na kasa ce wa koma a dalilin yadda nake gunji da shessheka mai nauyi. Baba ta yi zuru tana kallon yadda nake kukan. Ta koma kansa ta ce "Kai ne kake musguna mata, kai ne ka janye dukkan rarrashi da tarairaiya a tsakaninku saboda kana ganin kana ajiye mata komai na bukata." Ya yi shiru. Ta sake juyo wa gare ni ta ja ni zuwa jikinta tana bubbuga bayana cikin rarrashi. Tsawon lokaci ina kuka su kuma ba wanda ya iya ce wa komai. Sai da na yi kuka sosai, domin tsawon lokaci ina ta son na yi ban samu inda zan yi ba. Shi yasa yanzu na yi shi son raina. Sai da na nutsu sannan ta d'ago ni ta ce ",Fada mini damuwowinki Yabi". Na ce "Babu komai Babah". Na saci kallonsa na ga ya kidime sosai domin ya sani idan har na ce babu komai to kuwa abin da yake raina mai nauyi ne. Irin kukan da na yi kuma ya saka shi zullimi. Babah ta hau fad'in "Wato ban isa ba ko Yabi? Na zaunar da ku dan na ji matsalalolinku amma kin ce babu komai alhalin ko makaho idan ya ji irin kukan da kike yi yasan kina cikin bacin rai." Idona ya sake cika da hawaye na ce "Wallahi Babah ba isa ne baki yi ba, ke ma kin san yadda na dauke ki. Kawai ban san me zan ce ba ne. Abin da na fahimta kawai yanzu ya fi k'arfina ne. A yanzu ya samu damar da zai auro daidai da ra'ayinsa, irin wacce ta dace da shi. Ai dole na ga komai! Dole komai zan yi masa ya zama laifi, dole ya janye dukkan tausayi da sassauci a tsakaninmu, Tunda bana birge shi. Yana zaune da ni ne a kan dole, gane hakan da na yi ya sanya na koma gefe dan na ba shi dama ya yi komai tunda Allah ya ara masa damar." Na goge hawayen da ya zubo mini da hijabin jikina. Babah ta yi shiru tana kallonmu tare da nazari sosai. Ta kasa gane waye yafi gaskiya a tsakaninmu. Amma kalamaina sun yi matukar dukansu gabadaya, shi kansa kallona yake yi ya kasa ce wa uffan. Karshe dai Babah ta rinjayar da gaskiya a tare da ni. A sanyaye ta ce "Ban yi mamaki ba. Domin mafi yawa maza haka suke yi. Da sun samu wadata kuma sai wulakanci ya biyo kan wacce aka sha gwagwarmaya da ita. Ba ko wanne namiji yake yin hakan ba, amma dai masu yin sun zarta marasa yin yawa. Sannu Yabi!" Ta fada cikin wani irin yanayi, mai wuyar fasaltawa. Kalaman Babah suka sake fadada zullimiin da yake ciki. Murya babu amo ya ce "Babah kada kalamanta su rude ki, ki bata lasisin cigaba da gasa ni da ruwan sanyi da take yi. Ubangiji ya bata iya sarrafa harshe. Wallahi ita take k'warata. Satin da ya wuce muka dawo daga Kano. Na kuma shirya mana tafiyar ne dan mu samu sauyin muhalli watak'ila hakan zai sa ta huce daga murdewar da ta yi. Jikina na rawa na dinga siya mata komai na ga ni. Amma Wallahi yadda kika san mugun abu na yi mata haka ta sake botsare wa. Tunda muka dawo ta sake taurare wa. Wai a ce yarinyar mace kankanuwa kamar wannan ta iya BAK'AR TA'ADAR gaba da miji haka siddan?" Na kalle shi na ce "TA'ADAR da baka yi ta sharri a baya, yanzu so kake ka k'ware a kanta. Bana gaishe ka? Masharranci kawai! Babah ta ce ",Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ashe kina iya zagin miji Yabi? A gabana kika ce masa masharranci? Ta jijjiga kai tare da ce wa "Tun baku je ko ina da zaman auren ba kun fara zaman da babu mutunci a ciki?" Ta dinga sababi ta inda ta shiga bata nan take fita ba. Gabadaya ta hadamu ta ki yarda da gaskiyar kowa. Ta kalle ni ta ce "Da kam ni kad'ai nasan wulakancin da zan yi masa a kan abubuwan da yake yi miki. Amma tunda na gane ba ki d'auki tarbiyar gidanmu ta barranta daga zagin mijin aure ba. To ai bani da ta ce wa. Domin na gane dukkanku ne baku da mutunci, dukkanku ne kuke son yiwa auren tawili". Ni da danuwana kuke son ku tozartawa, ku kunyata, ku jefamu cikin bak'in ciki da zunden jama'a ". ✍️ *Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.* *Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐, ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To albishirinki yar uwa!* *UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1 Ta fashe da kuka tana fad'in ai bata san haka zamu yi mata ba. Da bata zo gidanmu ba. So muke mu kunyata ta ita da Baban Marina. Dukkanmu kowa ya shiga tashin hankalin kukan da take yi. Domin kuka ne wanda yake bayyana tsananin bakin cikin da me yinsa yake ciki. Da k'yar na bude baki na ce "Dan Allah ki yi hakuri Babah". Bata kula ni ba, ba kuma ta fasa kukan ba. Da k'yar ta yi shiru. Amma duk juyin da muka yi akan ta yi hak'uri ta tashi ta shiga daki bata ko yi motsi ba bare ta tanka. A wannan ranar na gane ita ma kafaffiya ce ta gaske. Domin kuwa dukkanmu a falon muka kwana a zaune, don bata yarda ko kishingida ta yi ba. Tashin hankalin da muke ciki tamkar idan an tsaga jikinmu ba za a ga jini a ciki ba. Ana idar da sallar asuba kuwa ta fice ko sallama bata yi mini ba. Haka nan Tijjani bai kai ga dawowa ba. Na bita ina fad'in "Dan Allah Babah ki rufa mana asiri ki yi hakuri, ki dawo ki gafarce mu." Tafiya kawai take yi. Muka yi kicibus da shi ya dawo daga masallaci. Duk kokarinmu akan ta dawo bata yarda ba. Duk rokon da Tijjani ya yi akan ya mayar da ita bata tanka ba, bare ta amince. Akan dole na dawo gida a dalilin ya ce na taho saboda mun bar yara. Na zauna ina hawaye domin ban tab'a ganin Babah ta yi fishi irin haka ba tunda na ke. A sururuce na shirya yara, na basu abinci . Amma ko makaranta na kasa tafiya. Kan dole suma suka zauna. Har azahar babu Tijjani babu labarin sa. Na tabbatar bin ta ya yi dan ya bata hak'uri. Tun fil-azal yana gudun bacin ran ta. Bare kuma yau da ta yi matsanancin fishi. Sai la'asar ya dawo gabad'aya ya yi zuru zuru, ya hargitse. Kallon sa kawai na yi na gane bai ci komai ba. A sanyaye na masa sannu. Ya zauna a falon ya amsa mini shi ma a raunane. Kaina a kasa na ce "Ya ya Babah?" Ya ce "Bata huce ba. Ya zuba mini ido ya ce "Asiya taimake ni ki fada mini laifukan da nake yi miki." Na yi shiru na k'i ce wa komai. Ya numfasa ya ce "Wallahi sai kin fada mini, na gaji da wannan jidalin na ki. Komai na yi miki babu gwangwaninta, kin tada hankalina kin tashi na ki. Mene ne haka. Kowa ya gan ki sai ya ce kina cikin damuwa ko jinya mai tsanani. Me nake yi miki hakan?" Na dauke kai daga kallonsa. Ya taso daga inda yake a zaune ya gurfana a gabana. Ya ce "Tun ban miki duka ba, ki bude baki ki fada mini musgunawar da nake yi miki" Na ce "Doke ni kawai, ai ka fi ga hakan ranka ya dade Alhaji". Ya damke ni ya ce "Tunda kika yi mini sanadin da uwata ta yi mini tofin Allah tsine Bilhillazi komai zai iya faruwa a tsakaninmu ". Ganin ya rikice da gaske idonsa ya kad'a tamkar wanda ya sha kayan maye. Yasa na bude baki na ce "Son ka ne bana yi, na gaji, kawai ka sallame ni". Jikinsa ya saki, damkar da ya yi mini ta yi sanyi a dalilin ya rasa karfinsa. Ya zuba mini ido tamkar mai son ya fahimci hakikanin abin da yake cikin zuciyata. Murya babu amo ya ce "mene ne dalilin janye soyayyar da kika yaudare ni da ita, har na yi zaton babu abin da zan yi ki janye ta Asiya?". Ban amsa masa ba. Ya kasa hak'uri ya ce"Mene ne bana yi miki? Duk abin da na gani burina na siyo na kawo miki, ko na siyo wa y'aya'n ki. Wanne nau'in abinci ne bana ajiye miki duk tsadarsa? Wanccan watan kina ce mini kayan Oriflame kike son amfani da shi, haka na daure na ce ki fadawa yar lame din da take siyarwa ta aiko miki, kuma tuni na biya. Da me na rage ki da kika janye samar mini da nutsuwa? Tunda muka dawo gidannan bamu jitu sosai ba, bamu samu nutsuwar da ta dace da mu ba. Na dauka bandakin da na samar miki a cikin daki zai sa ki yi farincikin ki gane komai kike so sannu a hankali zan yi miki shi " Ido cikin ido na kalle shi duk da bai sake ni ba, na ce "Duk wadananan abubuwan da ka lissafa hakkina ne da ya zama wajibi ka yi mini su, ba wai taimakona ka yi ba. Idan kuma yinsu alfarma ce to ka daina bana so. Daki mai bandaki kuma bana sonsa, nafi son wanccan gidan da yake fallen falle mai bandaki a tsakar gida, domin nafi samun gamsuwa da mutuntawa a cikin sa. Ya sake ni yana fad'in "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Asiya sai yaushe mata zaku gane hidimar da take kan namiji ba zata bar shi kullum ya mu'amalance ku yadda kuke so ba? Da din da kike marari ba ni da abin yi ne, ina rayuwa ne a takure saboda bana iya samar miki abubuwan da suka dace da ke. Yanzu kuma da na samu hanyar daukan nuyinmu sai ya zama tashin hankalin? Shi kenan sai ya zama laifin da zaki janye soyayyar da kike yi mini?" Na ce ",Eh dama ai ba son ka nake yi ba. Kirki da ririta ni da kake yi ne ya janyo maka soyayyata. Amma tunda ka janye su, nima na fasa son naka sai ya ya kuma? Har kana kumfar bakin ka kai ni Kano ka mini siyayya to ga kayan can bana so. Tunda har zaka yi waya a cikin dakin da kasan ina ciki kana fad'in baka tsorona, zaka bayar da mamaki akan lamarina. To ina ce sai na damu da kai ko kuma idan na zauna da kai? Sannan zaka tozarta ta ni ta hanyar nunawa duniya ni din ba komai ba ce a wajen ka. Ni kuwa me zaka yi mini na ga farin ka Tijjani?" Ya sake ni a matukar sanyaye. Domin ya gane da dukkan zuciyata na shirya wa ko wacce irin fitina. Ya zauna kawai ya jingina da bango sama da awa bai iya ce wa komai ba. Sallah ta fitar da shi. Ya dawo ya zauna a inda ya tashi, gabadaya ya zube tamkar mai amai da gudawa. A sanyaye ya kalle ni ya ce "Ba ni shayi na sha. Yau ko ruwa ban kai bakina ba. Ban yi masa musu ba na hado na kawo masa. Yaran namu su kansu sai suka zama babu walwala a dalilin sun ganmu a birkice. Yana dawowa daga sallar isha ya rufe gida. Da yake da yaran ya je. Suna dawowa Hamim ya yi barci. Hanif ne ya dan jima yana kallon cartoon kafin shi ma barcin ya sure shi bai sani ba. Har lokacin muna zaune jigum jigum tamkar masu zaman makoki. Ya numfasa ya ce "Asiya mu fahimci juna mana. Ko motsi ban yi ba. Bare na tanka masa. Ya ce "Na rasa gane halin da nake ciki. Gabadaya jina nake yi a juye. Amma mu fahimci juna. Kin ga Babah ta yi fishi da mu mai tsanani. Mu shirya kanmu, gobe sai mu je mu bata hak'uri." Na ce "To". Ya ce "Ban gane to ba Asiya". "Allah wahidun! Me zan ce maka to? Na ce a,a?" Ya kalle ni kawai. Ya mik'e ya sure ni tamkar yar tsana ya yi dakinsa da ni. Yana fad'in "Mu je kan katifa na rarrashe ki, domin na gane rarrashi akan katifa yafi na kan gado ratsa jiki". Na dinga mutsu mutsu tare da son na kwace amma ina. Ya mini kamun kazar kuku. Duk fizge fizgen da nake yi bai kula ba. Sai da ya dangana ni da katifar. Ya bini ya mini rumfa da jikinsa. Karshe ma ya sakar mini nauyinsa ta hanyar danne ni. Na daure na ki na nuna na kosa. Ya bini da kisses da sauran al-amura masu nauyi. Tun ina dauriyar kin karbar rarrashin nasa har na kasa jure wa na fara karba ta hanyar sakar masa jiki da daina ture shi. Sai da ya gama jagwalgwala ni, sannan ya kankance murya ya ce "Da gaske ba kya sona Asiyaty?" Na dauke kai ina jin kunya na kama ni. Domin ni kad'ai nasan yadda nake jin sa a zuciyata. Kawai wulakancinsa ne yake neman kwantar da ni. Sai da yasan yadda ya yi muka shirya, ya zangwanyar da fishin da na yi. Bayan ya jaddada mini, ba abin da yake so nan duniya sama da ni. Cikin saa'a bai mini zancen mutuwa ba. Bamu yi barci ba, a wannan dare, domin ko da muka samu nutsuwa. Maganganu muka cigaba da tattauna wa. Haka ya dinga bani hak'uri tare da rokon na daina yi masa irin wannan fishin mai tsanani. Na daina damun kaina ta hanyar kaurace wa abinci da kuma walwala. Sai da muka karya, muka shirya sannan muka dauki hanyar Bulkachuwa. Da k'yar Babah ta sauraremu. Mun shafe fiye da awa ban da sallamarmu bata sake kallon inda muke ba. Harkokokin ta take yi ita da su Hanif. Su kawai ta bawa ruwa da abinci, mu kuwa ko kallon inda muke bata sake yi ba. Ni na fara yin kundubalar bin ta daki. Yayin da ya biyo bayana, amma ya toge a bakin k'ofar tabbacin jiya bai ji da dad'i a hannunta ba. Na zauna a gefenta. Na lankwasa harshe na ce ",Dan Allah Babah ki yafe mana. Idan ba ki huce ba, ba zamu ga haske ba. Kuma tun jiyan ma mun sasanta kanmu." Sai lokacin ta bude baki ta ce "To ni kuma ina ruwana da al'amarinku? Ni da kika ganni bana shiga kasafin da babu mutunci a cikinsa. A gabana ki zagi mijin ki Yabi?" A sanyaye na ce "Ban zage shi ba Babah". Ta ce "Kalmar da kika fada masa ai zagi ne Na yi shiru. Ta dinga yi mini fad'a tamkar zata doke ni. Ganin ta tsananta ya sanya na ce ",Babah Wallahi ni kad'ai nasan kuttun da yake cusa mini. Yanzu ba dama ya dawo ya zauna mu yi hira, sai dai ya yi da wayarsa, na sani kuma da y'anmata yake yin hirar ni ya bar ni gaho. A Kano kuwa da kunnena na ji yana zancen zai tura gidansu". Ta ce "Akan me ba zai yi aure ba? Akan ki zata zauna, me ce a cikin kishiya ne da kika tsananta wa kanki k'in ta. Allah ya ce su yi mataye sama da d'aya idan zasu iya adalci. An janye ayar ne, ko kuwa rushe ta zaki yi, ki kafirta?" Tana rufe baki na rushe da kuka ina fad'in "Kin bi bayansa ya yi mini kishiya ko Babah?" Ta janyo mafici ta shiga kwada mini tana fad'in "Na bi bayan nasa sakarya. To hakan da kike yi masa ne zai hana shi k'ara auren. Tun yanzu kin tattara kin bar shi, idan ta zo ba sai ta karbe shi gabad'aya ba." Cikin kuka sosai na ce "Babah na rantse da Nasiba yake soyayya. Ya auro kowa amma ban da ita. Ni Wallahi bazan yi kishi da ita ba. Mutuwa zan yi, idan kuwa ban mutu ba, daga ranar da ya aure ta. Billahi a ranar na haramta gare shi!" Na fada cikin matsanancin kuka. Ta saki maficin hannunta ta ruko hannuna ta ce "Ni ma matukar bai nisance ta ba Wallahi sai dai ya nemi wata uwar. Na yafe shi. Share hawayen ki har abada ba zaki yi kishi da ita ba. Na miki wannan alk:awarin". Ya shigo a sanyaye ya durkusa a gabanta ya ce "Ki tsananta yi mini addu'a. Ban san me yasa nake jin ina zakuwa akan lamarinta ba. Idan na je wajenta kwata kwata bana jin sukuni dan tsananin takurar da nake shiga. Ko ganin ta bana son yi. Amma da zarar na taho kuma sai na ji zuciyata tana azalzalar na koma Toro dan na ganta. Ku mini addu'a, ku mini uzziri dan girman Allah. Wallahi addu'ar da nake yi ne ma take saisaita mini al-amurana, amma abubuwan da suka sha kaina masu tsanani ne. Ku taimake ni, kune mafi kusa da ni a yanzu." "Tirkashi" Babah ta furta a fili domin ta fahimci ba haka aka bar shi ba tabbas. Ta nisa ta ce "Allah mun tuba, Allah kada kasa shaid'an ya yi galabar tsinka siriryar igiyar zumucin gidan marina da ta yi saura." Kukana ya tsaya cak a dalilin yadda na ga Babah ta tsorata da furucinsa ainun. Yayin da zuciyata ta shiga zullimi sosai. Ke nan Tijjani da gaske yana burin auren Nasiba. Wani irin k'ullutu mai ciwo ya tokare ni. A matukar sanyaye take fad'in "Zan dage da addu'a, kai ma ka dage da addu'ar da kuma danne yadda kake ji akan lamarinta. Sannan ka saka a ranka ba matar ka ba ce, domin matukar ina raye ba zaka had'a su ba, kai gabadaya ne ma ba zaka aure ta ba. Dalilin da ya hana a baka ita a farko, shine dalilin da yasa ba zaka zama mijinta ba a yanzu" Ta juyo gare ni ta tausasa harshe ta ce "ki yi hakuri kin ji Yabi. Yana cikin canka cakare. Ki tallafe shi har ya tsallake wannan siradin. Mutanan yau da yawansu mugaye ne, zuciyarsu cike take da gilli mai yawa." Na kasa ce wa komai domin na kidime, idan har Tijjani da yake kawaici a gaban Babah zai bude baki ya ce yana zakuwa akan lamarinta a gabanta to lah shakka abin da yake ji babba ne. Hawaye ya dinga tsere a fuskata. Tabbas ina cikin tashin hankali. Bana jin tsoron karawa kishi da ko wacce mace, domin na yi imani namiji baya zama da wacce baya so. Idan kishiya ta kere ka a wani fanni to kai ma da ikon Ubangiji sai ka samu fannin da zaka kere ta. Abu biyu ya dame ni. Nasiba suntumemiyar halitta ce irin matan da suke birge Bulkachuwa. Sannan mahaifiyarta kowa yasan bata barin mazanta haka, a hannunta suke, ko marigayi mijin Nasiba kullum a yunkurin mallake mata shi ta ke. Na tabbatar Tijjani ma za'a yi komai dan ta sha gabana, tunda a yanzu ma da bai aure ta ba idan ta gan ni kamar ta doke ni haka take ji. Da k'yar Babah ta shawo kaina na samu nutsuwa, na daina kuka. Sai yamma muka baro Bulkachuwa. Dan haka sai dare muka iso. Na daure na yi k'arfin zuciya ban cigaba da share shi ba. Na rungume shi da hannu biyu muka cigaba da zama lafiya. Duk dare kuma sai ya fita waje ya yi waya. Idan kuma yana gida baya amsa waya matukar bata shafi kasuwancinsa ba. Asalima kamar ya dakatar da a a kira shi idan yana gida ne. Da kaina na fahimci da gaske ya canja, wulakancin yin waya idan yana gida yanzu ya daina, asalima kaffa kaffa yake kada na tuntsire masa. *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633*. Yayin da ni kuma na tsananta addu'ar Ubangiji ya tsaremu akan duk abin da ake nufi da mu na sharri. Sa'a d'aya har yau Tijjani bai bar sallar dare ba. Yana wahalar gaske ya kwanta bai tashi ya yi nafila ba. Kullum kuma a cikin addu'ar duk kaddarar da zata hau kansa ta zama mai sassauci daga Ubangiji. Na sani asiri zai kama shi, amma na yi imani zai zo da sauki tunda wadatar da ya samu bata sanya ya bar Allah ko ya koma BAK'AR TA'ADAR neman matan da ya yi a baya ba. Na kira gwaggo na fada mata komai na roki ta tsananta yi mini addu'a. Cikin rarrashi ta ce "Ina yi miki Yabi. Zan kuma ninka addu'ar da ne yi miki. Abin da zan fad'a miki shine ki barwa Allah ya yi miki zabi, ba wai ke ki yanke hukuncin idan ya aure ta kin bar shi ba. Allah ne ya halasta dan haka akwai bukatar ki nutsu, kada ki bari Ubangiji ya bar ki da dabarar ki." Da kuka na ce ",To Gwaggo". Cikin rauni ta ce "Allah ya yi miki albarka ya shiga tsakanin ki da duk abin da zai birkita miki auren ki. Da ikon Allah ba za'a kai ki k'asa ba. Kin yi sa'a kina cikin albarkar uwa da uba. Dan haka ki yi ibada tuk'uru ki kuma yi barci da minshari ba abin da zai same ki sai alheri da ke da dukkan zuriar ki Yabi". "Na gode Gwaggo". Na furta cikin rawar murya irin ta kuka. Sannu a hankali na samu sassauci na cire hankalina kan maganar Nasiba da Tijjani. Iyaka dai ban daina addu'a ba, ban daina tofawa Tijjani addu'ar tsari a cikin duk abin da zai ci ko ya sha ba. Na rungumi zaman lafiya a tsakanina da shi. Na rungumi karatuna da y'aya'na. Mussaman a yanzu da nake gaf da kammala N.C.E. Twins sun girma domin suna shirin shiga shekaru shida da haihuwa. A lokacin suna aji daya na firamari. Hanif yafi Hamim kokari domin kullum na daya yake zuwa. Amma kuma ba shi da magana. Yayin da Hamim yake zuwa tsakanin bakwai zuwa goma. Amma kuma ba wanda bai san shi ba, saboda suruntunsa, ya kuma yi sa'a ya iya turanci. Kamar wanda ya girma a cikin masu yi. Surtunsa da fadansa ya sanya a ke fafatawa da shi. Sau tari sai ya yi tsokana ko laifi a hukunta Hanif a madadinsa tunda ba'a gane su. Shi kuma Hanif ba zai ce ba shi ba ne. Ko ni ma yana mini wannan iya shegen. Dan haka na daina binsu a guje. Sai ya manta yana ta surtunsa kamar aku sannan zan rik'e shi. Duk sadda na je Toro bin mu kawai ake yi da ido ni da y'aya'na a dalilin yadda muke fita daban muke daukar ido. Wadanda kuma basa iya boye wa hassadarsu a fili sai da kawai na ji suna fad'in iyalin babban direba shugaban masu kayan gwari na Bauchi gabad'aya. Ko yaushe aka nada masa wannan mukamin? Ni da Nasiba kuwa muna gaisawa, bama gaba sai dai babu doguwar hira. Domin idan ta gan ni sai na ga tana d'ad'are wa bata da katabus duk da bata yi mini kallon raini ko na izgili. Shi yasa nima nake jarumtar mu'amalantar ta da sakakkiyar fuska. Ina kammala rubuta jarabawar karshe. Na fara hutun zirga zirgar da na shafe shekaru uku ina yi. Hatta lalle sai da na tafi hutun wata guda a kokarina na son na dinga yin barci yana isa ta. Da zarar na sallami twins da babansu sun fita da yake shi yake kai su makaranta, sadda zasu tashi idan ya dawo yana gari sai ya dauko su. Idan kuwa baya gari sai su taho da yaran bayan layinmu. Suna fita nake rufe gida na gama abin da zan yi na karya na kwanta na yi barci, bana tashi sai azahar. Daidai wannan lokacin Tijjani ya k'osa na samu ciki. Har ta kai ya fara zargin ni nake yin wani abu dan kada na sake haihuwa. Haka kawai rannan ya tuntsire akan ba zai yadda ba. Daga haihuwa d'aya zan kulle bakin mahaifa, to shi ba yahudu ba ne, ba kuma ba Caine ba ne da za'a kiddidge masa yawan y'aya'n da zai haifa. Ya riga da ya gano hak'uri kawai yake yi, to yanzu kuma ya gaji. Na kalle shi a tausashe na ce "Ashe ba Allah ne ke kawo ciki da haihuwa ba Baban 2?" Da kumfar baki ya ce ",Tun kafin ki zo duniya nasan da hakan Asiya. Akan me duk abokan aurenmu haihuwarsu uku amma ke sau daya tak. Ba dan Allah ya so ya bani biyu tashi guda, da yanzu d'aya ne jallin jal. Gaskiya ni yara da yawa nake so malama." Na sake daure wa na ce "Allah bana shan komai ka yarda da ni". "To akan me ina bakin kokarina ba zaki karbi cikin ba?" Na zuba masa ido cike da fargabar ko dai ya fara afa wani abu ne. Tas na gan shi babu alamun maye ko rashin lafiya. Ido cikin ido na ce "Wato ma ni ce na ki karba ko?" Fuska a daure ya ce "Eh mana. Nima ba haka kika yi ta yi mini sadda baki samu ciki ba, ce wa kike ni ne ban yi miki ba. To nima yanzu kawai ki karba Asiya na gaji, ki yi ciki abin da na sani, na ke kuma son ga ni ke nan". Na yi dariya na daga hannu sama na ce "Allah kasa na samu ciki ya zauna kada ya zube ". Ya saki ransa ya ce "Yanzu kika nemi zaman lafiya tunda kin roki mai bayar wa. Kuma na saka miki doka kullum ki dinga wannan addu'ar idan kin yi sallah." Na gintse dariyar na ce "To mai sunan shehu". Ya harare ni tare da ce wa "Kin dauki umarnina wasa ko?" Na girgiza kai da sauri tare da ce wa "Wace ni da wasa da lamarin ka, indai ba so kake Babah ta ce na raina miji ba". Da haka na lallaba na shiritar da maganar, dan kuwa da na dauka da zafi rikici zamu yi mai yawa. Tunda da gaske ya kosa na haihu kamar bamu da yara kwata kwata. Tun wannan lokacin na tsananta addu'ar na samu ciki ya zauna. Na cigaba da zuwa ganin likitan da na daina zuwa. Na kuma yiwa Aisha lame maganar ta siyo mini Saiwowin maganin sanyi a wajen Surayya 08032773332.* *** Baba Maryo ta isa gidan yar'uwarta a Bulkachuwa da la'asar lis. Babah ta karbe ta da karamci da walwala. Har dare suna hirarsu da ta shafe su. Sai da daddare sun kwanta. Babah a kasa ta yi shimfida yayin da kanwarta yake kan gadon. Cikjn hirarsu ta kutso da maganar Nasiba da Tijjani. Ta ce "Na rasa ga ne inda matsalar take, sai sun shirya ya ce zai tura gidan iyayenta sai kuma magana ta kwanta. Sama da shekara guda yana mata yawo da hankali. Shi bai fito ba, shi kuma ya fantsama mata mane ma". Da madaukakin mamaki ta ce"Ban fahimce ki ba Maryo!" Ta kuwa ce "Maganar y'ar ki da Tijjani mana. Ai gara ki yi magana da waliyyinsa a yi komai a gama na gaji da wannan hirar tasu ba tare da an yiwa lamarin kai ba". Babah ta sandare a zaune, ta cika k'warai da rashin kunyar kanwarta. Amma sai ta ce "To shi ban da ma rashin tunani me zai sa ya nemi Nasiba da sunan soyayya. Ai ita matar manya ce. Sannan ta ya ya zai hada yan'uwan jini kishi?" A ladabce Baba Maryo ta ce "Wa ce ce Nasiba da za'a ce tafi k'arfin Tijjani? Bayan haka zumuntar ta da Yabi ba zai hana su zama kishiyoyi ba, tunda Allah bai hana ba." Ba ja in ja Babah ta ce "Gaskiya ba zai yiwu ya had'a Yabi da Nasiba a matsayin matansa ba". Haka kawai ta fad'a Baba Maryo ta fashe da kuka tare da ce wa "Ta fifita bare akan Nasiba". Babah ta ka'du da furucin yar'uwarta. Ta kasa daure wa ta ce "Wacce baren na fifta?" Ta yi tambayar da dukkan zuciyarta. Da kuka ta ce "Yabi mana. Dama sai da na yi zargin ke ce baki d'aure gindin ya aure ta ba, saboda kina gudun zuciyarta da ta uwatata. To komin abin dai ni ce taki ba Asama'u ba". A sanyaye Babah ta ce "Ni Yabi d'iyar Asama'u ce da ta zo da ita daga wani gidan ko kuwa tare da Yaya Sani ta same ta?" Cikin ko in kula ta ce "Shine ubanta amma ai wata ce ta haife ta. Ni kuwa fa? Jikina Nasiba ta tsaga ta fito. Kuma tun lokacin Annabta zumuncin dangin uwa yafi na uba sahihiyar soyayya da tausayi". *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* ✍️ *Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.* *Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐, ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To albishirinki yar uwa!* *UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1 *KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* Babah ta kasa ce wa komai domin ita gabad'aya ma alamarin tsoro ya shiga bata. Tana kuma mamakin rashin kunya da son kai irin na Maryo. Bata yi zaton son zuciyarta ya kai hakan ba. Ta kasa ce wa uffan saboda tsananin kaduwa da ta yi. Ita kuwa ta dinga kuka tana face majina tamkar Dada ce ta kwanta dama. Washagari ko karyawa bata yi ba ta ce zata juya. Da k'yar Babah ta roke ta akan ta bari ta karya. Rai a bace suka rabu a dalilin Babah ta tabbatar aure kam babu a tsakanin Nasiba da Tijjani. Rai a matukar bace ta isa Toro. Ta gurfana gaban Dada tana kuka tana fad'a mata karya da gaskiyar cin mutuncin da Hauwa ta yi mata. Dada ta taya ta bacin rai tare da rarrashinta tamkar yarinya karama. Tana cin alwashin sai ta ci mutumcinta tunda bata san yakamata ba. Bijirewar da Babah ta yi akan auren tare da fitowa baro baro da ta yi ta ce alamarin ba zai yiwu ba. Sai ya zama d'an zani. Domin hakan ya fusata Baba Maryo tare da cin alwashin sai Tijjani ya auri Nasiba ko zata yi yawo tsirara, ta ga karshen rashin kara da nuna banbanci. Takanas ta tafi cikin jeji can kudu da Jos. Ta samo asiri da surkullen da muradinta zai cika. *Bayan waatanni biyu* A hankali Tijjani ya fara rikice mini fiye da bara. Sai mu kwana gari ya waye bai ce mini uffan ba. Zan masa magana goma bai fi ya amsa ni sau biyu ba a gajarce. Ya daina shayin yin waya a gabana. Yanzu har an kai jallin da zai bawa twins waya su gaishe ta. Duk da dai bai tab'a kama suna ba. Sai ya ga dama yake cin abincina. Jiya ma da na zauna kusa da shi ce mini ya na tashi yana bukatar kad'aici. Murjewar da na yi, nan da nan na fara tsomare wa. Sosai ya murde irin yadda ban taba zaton zai yi ba. Na hakurkurtar da zuciyata na dinga ba shi hak'uri tare da rokon ya fad'a mini laifin da na yi masa. Yana bude baki sai ce wa ya yi "Haihuwa yake so. Tunda ba zan haihu ba, shi aure zai yi, idan zan zauna na zauna idan kuma bazan zauna ba, to bai rik'e ni ba." Na zuba masa idona da suka soye. Na ce "Tsakanin ka da Allah kana mini adalci Tijjani?" Ya hassalo ainun tare da ce wa "Ta ya ya zan yi miki adalci Asiya? To ko kawai zaki yi gaba ko zaki samu adalin?" Na sake daskare wa. Na yi maza na kame bakina domin na gane komai na iya faruwa a tsakaninmu. Amma hawaye ke tsere babu jinkiri kuncina. Ya ja tsaki ya fice ya bar ni. Yana fad'in "Me za'a yi da mace mai rainuwa da azababben kishi. A ce mace ba zata taimake ka ta rufa maka asiri, ta taya ka son abin da kake so ba. Sai sarhutu da mance alheri kawai ta iya ". Na yini cikin bacin rai. Yayin da shi kuma ya yi tafiyarsa Toro da yara bai damu da halin da ya bar ni a ciki ba. Ina kuka na d'auki waya na bugawa Baban Marina karon farko da na yi hakan tunda ya aurar da ni. Na kasa magana sai kuka nake yi masa mai tsuma zuciya. Bai katse ni ba. Sai da na gaji dan kaina na katse wayar. Baban Marina ya dawo gida cikin sanyin jiki a dalilin yadda kukan Yabi ya buge shi. Ya leka kofar Dada dan ya bata man zafin da ya siyo mata sai kawai ya ga Tijjani da Nasiba a gefen bisihiyar zogale suna zance. Dada na daki abin ta. Duk da ba yau ya saba ganinsu ba, amma yau din sai da zuciyarsa ta buga da tsananin gaske. Ya amsa gaisuwarsu cikin k'arfin hali. Ya shiga wajen Dada ya fito, ya fita. Ya zauna kan tabarma amma zufa ta rufe shi. Ya dinga jin wani iri. Duk yadda ya so jurewa kasa wa ya yi. Yana tambayar kansa yanzu Tijjani yana da rigar da za'a bashi aure ke nan?. Ya tuna irin kukan da Yabi ta kira ta yi masa dazu, ya san kuka ne na neman agaji, kuka ne mai harshen damo. Daren ranar ya yi masa tsawo ainun. Washagari ana idar da sallar asuba ya ce Salisu ya raka shi Bauchi. Tamkar jifa haka Yabi ta gansu. Zuciyarta ta karye. Domin ta hango rauni da wata irin soyayyar ta a kan fuskar mahaifinta. Tare da Tijjani suka musu iso zuwa falo. Yana amsa gaisuwarsu ya yi gyaran murya ya ce "Zuwa na yi takanas dan na fad'a miki ce wa ki yi hakuri ki zauna a dakin ki. Ki kuma sauke dukkan hakkina da kika san Ubangiji ya dora miki. Daga nan har zuwa lokacin da Allah ya kaddara muku zaman kada ki yarda ki zalunce shi. Kada kuma ki fito babu izininsa. Aure da kike ga ni darajar sa ta wuce duk zaton mai zato. Sai dai bisa adalcin Ubangiji ya kewaye shi da dokoki da kuma sharudda daban daban. Bai barmu kara zube ba. Ina rokon ki, ki k'ara hak'uri a cikin wannan tsukun da ake son kaimu k'asa da bak'inciki mai tsanani. Idan har kika yarda kika yi hak'uri, ni kuma na miki alkawarin zan jaddada damar da shari'a ta baki na zabin cigaba da zaman ko akasin hakan matukar zalunci da cin fuska ya shigo gidan auren ki". Cikin kuka da rawar murya na ce "To Babanmu". Ina fad'in haka ya mik'e tare da ce wa "Allah ya yi miki albarka. Ya fice bai ko bi takan tagwaye da suke ta rige rigen gaishe shi ba. Yaya Salisu ne kawai ya amsa musu tare da ciro ledar alawowi a aljihunsa ya damka kowa tasa ledar. K'warai Tijjani ya muzanta da yadda suka fice basu bi takansa ba. Ya bi bayansu. Ba jimawa ya shigo ya zauna. Ya ce "Baban Marina ya canja, ya yi bangaranci. To wai a kaina aka fara k'arin aure ne da za'a mini wulakanci irin haka?" *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633 Ban kalle shi bare na ba shi amsa. Maimakon shi ma ya sawa bakinsa linzami tamkar yadda na yi sai ya zarce da ce wa "Baban kasuwa ne kawai mai mace daya, shi ma nasan a dole yake zaune bai k'ara ba. Shi Baban Marina din da yake tunzuri irin haka ai uku ne da shi, shine ni zai nemi hana ni jin yadda a ke ji?" Na kalle shi da fishi sosai na ce "Ya isa haka! Ina rantse maka da Allah Tijjani zamu kwashi y'an kallo. Komai kake ji da shi na wulakanci ya tsaya iya kaina. Amma ka yi kad'an ka tabo alfarmar ubana. Ya wuce hakan Wallahi". Bansan ya aka yi ba jikinsa ya mutu. Ya kasa ce wa uffan. Na ja tsaki mai tsananin gaske na tashi na bar masa wajen. Muka k'ulla gaba sosai. Domin ya kullaci zuwan Baban Marina da kalamansa, dazu har da shaguben laifinsa ya shafi twins a wajen Baban Marina bai kula su ba. Yana wankin kayansu yana mini azanci. Ya kuma zabe iya nasu ya bar mini nawa. Ko kallo bai ishe ni ba. Domin sosai nake jin zafinsa. Ranar da aka tabbatar mini su Baban Tsakiya sun kai masa kudin aure gidan iyayen Nasiba kwana na yi ina kuka. Sassafe na yi Bulkachuwa. Ina zuwa na sake tarar da wani abin alajabin. Fad'a kawai Babah take mini wanda babu rarrashi ko nuna soyayya a ciki. Cikin sanyi ainun ta ce "Haba kina da k'warzaba Yabi. A kanki aka fara yin kishiya ne? Tun yaushe kike jidali?. To ni bazan iya hana shi aure ba. Ni nan da kike ganina kan kishiya aka kawo ni. Mahaifiyar ki ma kan kishiyar ta zo, sannan bayan ita ma ya sake yin wata. Ina dalilin wannan kai komon da kike yi na azina?" Na kafe ta da ido na ce "Har cikin zuciyata nasan ba haka siddan kika mini hakan ba. Allah Ubangiji ya kawo karshen wannanan al'amarin." Na fada ina kuka sosai. Ina kula da yadda kukan nawa ya raunanta amma ta kasa ce wa komai. Haka na dawo Bauchi da kaina. Tare da hak'urin dole. Amma ni kad'ai nasan me nake ji a zuciyata. *Toro* Tunda a kai kudin auren Tijjani gabadaya lafiya ta yiwa Baban Marina karanci. Ba komai ke nukurkisar sa ba illah yadda babu wani mutum d'aya a gidan Marina da ya fito ya nuna rashin dacewar al'amarin. Ya kasa samun Hauwa uwar Tijjani a waya. Kowa murna yake yi da auren. Tun jinyar na sand'arsa a hankali har ta kai ya kwanta. Ba'a samu wanda ya fito ya soki al'amarin a cikin yan'uwansa ba, balle a farga da yadda bakinciki ke sakatarsa. A wannan karon dukkan juriyarsa ta k'are. Ya yi amannar yan'uwansa basa son sa da gaske. Ban da haka mene ne za'a fifita Nasiba akan Yabi da take yar gidan? A cikin wannan yanayin Babah ta Bulkachuwa ta zo garin. A dakinsa ta tarar da shi. Kallon sa kawai ta yi hawaye ya tsinke mata. Domin a cikin sati kacal tsufa ya keto masa na ban mamaki. Tausayi ya kamata, ta sani bakin cikin yadda al'amarin ya juye ne yake neman kassara shi. Mussaman yadda kowa ya koma bangaren uwar Nasiba da ta take komai ta runtse idonta. Babban abin da yake damunta bata san me yasa take jin tamkar idan ba a yi auren Nasiba da Tijjani ba zata dauma a cikin kaico. So take ta bude baki ta barranta kanta daga lamarin amma ta kasa. Murya na rawa ta ce "Sannu Yaya! Ya kalle ta da idanuwansa da suka kad'a. Murya babu amo ya ce "Hauwa Tijjani zai yi aure nan da kwanaki kad'an. Bana inkarin k'arin aurensa domin kuwa yana da sukunin da zai ajiye mace hudu ma. Amma ki sani Wallahi ba zai had'a mini y'aya'na guda biyu kishi ba. Idan har dukkan ku babu mai fitowa ya yi magana to ni na yi. Bazan yarda na mutu na bar Yabi a cikin wannan taskun ba. Domin na san kafatalin ahalin gidannan ba zata samu wanda zai mata adalci irin na uba ba. Ke nake da garantin zaki tsaya mata. To ga shi ke ma an juya miki tunani. Shin kina ganin ya dace na zuba ido ana jifanmu ni da ahalina da sihiri bayan na jure dukkan k'iyayya da warakin da na shafe lokaci mai yawa ana mini ni da zugata?" Kamar a tsaorace ta ce "A a Yaya! Ni kaina ina tambayar kaina me yasa na kasa yin magana? Me yasa nake jin tsoron yin magana? Me yasa tashi d'aya na ji soyayyar al'amarin ta shige ni fiye da komai a yanzu?" Ya jijjiga kai ya ce "Na barwa Allah ya kawo mini dauki. Abin da nake so da ke yanzu. Yau din nan ki shiga mota ki dauko mini Yabi. Saboda ke na bawa Tijjani ita. Kin sani a wanccan lokacin ba shi da rigar da za'a bashi aure, asalima hana shi ake yi gida da dawa. Ke na bawa amanarta, ke na damkawa ita a hannunki. A yau kuma ina son ki dawo mini da ita salin alin yadda na baki ita cikin girma da arziki". Ta fara kuka mai tsananin gaske. Tana fad'in "kada ka yi hakan Yaya. Daure mu bi al'amarin a nutse. Tunda har ka gano sihiri ne, ka taimake ni mu lalubo bakin zaren mana!" Ya yi shiru yana sauraren kukanta. Ya numfasa ya ce "Bayan sihiri ai kin san yadda ni da y'aya'na muka zama saniyar ware. Lokacin da Jabir yake hakilon zai had'a Yabi da Maijidda gabad'aya kowa tofin Allah tsine aka yiwa lamarin. Bansan adadin kashedin da Dada ta yi mini akan na jawa Yabi kunne ba. A gabana Badamasi yake fad'in Jabiru ba zai auri Yabi ba. Iliya kuwa shi ma ya sha fad'in "Daga ranar da aka ce Jabiru zai auri Yabi to a lokacin zai sako masa Maijidda. Amma kuma an zuba ido tare da bada goyon baya a kwace wa Yabi mijin da ba'a yarda aka bata shi ba, sai da aka tabbatar ba shi da mamora. Yanzu kuma da ya samu madogara sai aka ga yafi k'arfin ta. Tunda abin hakane sai ta fito ta basu waje. Adalcin Ubangiji ya ishi kowa. Kuka kawai take yi tana jin yadda tsoro da sanyi yake d'ada girma a zuciyarta. Murya babu amo ta ce "Dan Allah Yaya ka janye umarnin na dauko maka ita. Kasan dai yadda Ubangiji ya mutunta sha'anin aure. Ka yi hak'uri mana har muga karshen wannan waki'ar". Ya yi shiru kamar ya yarda sai kawai ta ji ya ce "Wallahi ba zai had'a su ba. P bi mini kadina. Bare ina fatan na yi tsawon rai dan kawai ran Yabi kad'ai ". Kukanta ya karu. Tana yi tana ce wa "Allah ka warware wannan dambarwar. Ubangiji ka taimaki zumuncin ka fahimtar da ni abin da yake boye. Allah na tuba astagafirillah. Ta mike ta tafi babu waiwaye. Ya bi ta da ido yana gasgata surkullen dabaibaye zuciyarta aka yi. Hawaye mai ciwo ya dinga gangarowa ta kwarmin idonsa. Gwaggo ta shiga ta tarar da shi a hakan. Ta zauna ta ce "Alhaji ba zaka karanta wa kanka damuwa ba? Ina jin tsoron kada ka hadu da ciwon nan mai shanye barin jiki". Murya a karye ya ce "Ban da darajar sallah da salati Asama'u ai da tuni zuciyata ta buga ma gabad'aya. A ce haka zan kare cikin bak'inciki da tashin hankalin cikin yan'uwana? Yanzu na rasa mutum daya da zai yuwa Yabi kara da alkunya duk cikin dangina? Tausayin yarana gabad'aya ne yake neman kassara ni. Idan na mutu haka zasu yi ta tashi fad'i babu mai tsaya musu, yanzu shi ke nan bani da wanda zai kula mini da alamarinsu ko wanda zan damk'asu a hannunsa?" *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* Idonta ya ciko sosai amma ta sanya jarumta ta hadiye. Ta ce "To Alhaji ban da abin ka, duk wanda ka damkasu gare shi ai shima zai mace wata rana. Kawai yi dabarar damkasu a hannun Ubangiji domin shi ne rayayye wanzazze. Ina kuma son ka yiwa Hauwa adalci. Al'amarin ne yafi k'arfinta. Shi kansa Tijjani ai ba'a hayyacinsa yake ba. Idan muka daure muka yi hakuri. Muka taushi Yabi ta yi hak'uri komai zai wuce. Duk abin da aka gina shi da son zuciya baya k'arko". Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Ya ce "Kina nufin na sake tirsasa Yabi ta zauna da Tijjani ko da bata son hakan?" Da sauri ta ce "Eh. Domin babu abin da hak'uri ba zai bayar ba idan aka nutsu." Ido cikin ido ya ce "To a yau kam bazan d'auki shawarar ki ba. Sassauci d'aya zan yi, idan ta ga zata zauna shi ke nan sai na bita da addu'a. Idan kuwa ta ga ba zata zauna ba, to kuwa ko menene zai faru sai dai ya faru amma zan fanshi y'ata." Ta kasa ce wa komai domin ta san da dukkan zuciyarsa yake magana. *Bauchi*. Ina falo kan sallaya na idar da la'asar ina jan tasbaha. Hawaye kuma sai sintiri suke yi. Yayin da Tijjani yake zaune babu sukuni a tare da shi. Yara kuma suna islamiya. Na daga hannuwana sama a fili na ce "Allah kai ne mai sarrafa zuciya, Ubangiji ka sarrafa mini ita ta zama mai hak'uri, Allah ka mini baiwa da juriyar shanye ko wacce irin damuwa ba tare da hakan ya tab'a imanina da lafiyata ba. Ina rokon a cire mini damuwa akan wannan al'amarin domin na zama cikin masu imani da abin da ka hukunta. Allah ka warware mini dukkan abin da zai tunkare ni na sharri. Allah ka bawa Mijina lafiya, ka k'ara masa arziki, ka kare shi daga dukkan mummunar kaddara. Ina rokon a shirya zuriata, a tsare mini su, a kuma sanya su a cikin bayi na gari. Allah ka jik'an iyayena ka musu tukuici da aljanna." Na sake yin salatai da istigifati sannan na shafa. Na jingina da bango ina ta sakin ajiyar zuciya domin gabad'aya ji nake tamkar na ciro ta, ko na huta da azababben ciwon da nake ji. Ya sassauta murya ya ce "Asiya na gode miki. Ki cigaba da yi mini addu'a dan Allah. Ina ji a jikina bani da lafiya. Na kasa gane kaina, ki yi hakuri da ikon Ubangiji komai zai faru bazan bar ki ba Asiya". Cikin kuka na ce "Bari na nawa Tijjani? Sau nawa zaka ga ina kuka ka banzantar da ni, sau nawa kake sanadin sa ni kuka? A da na dauka duk lalacewar giwa ta fi k'arfin kiyashi ya ja ta. Ashe sannu a hankali idan suka yi taron dangi sai su jata su kacaccalata. Amma babu komai na barwa Allah ya zame mini garkuwa." Ya tsugunna a gabana ya ruko hannuna a tausashe ya ce "Ba dan ki gamsu ba, ina rantse miki da Ubangijin Al-arshi bana jin so ko wacce mace da sunan soyayya ko sha'awa a zuciyata sai ke Asiya. Amma bansan me yasa nake jin zuciyata na tafarfasa a dalilin Nasiba ba. Ina jin idan ban aure ta ba bazan samu nutsuwa ba har abada. Ki yi hak'uri kada ki juya mini baya a cikin wannan halin da nake ciki. Masifu sun dabaibaye ni, ikon Allah kad'ai yake rik'e da tunanina. Amma gabadaya bani da sukuni. A gida babu nutsuwa a tsakaninmu, a wajen sana'a ta jifana ake yi. Ga shi an kulle mini zuciya da tunanina. Babban tashin hankalina yadda Baban Marina ya shirya kwace mini ke. Dan Allah little kada ki barmu ni da twins. Ya ya ake son mu yi, k'arfin hali kawai nake yi, amma ni yanzu har na fara fatan mutuwa ta dauke ni na huta da wannan dambarwar". Na kasa kwace hannuna. Wani irin abu ya dinga taso mini. Na gasgata ina son Tijjani k'warai da gaske. Domin saukowar da ya yi, ya mini magana ta rarrashi da tausayawa sai na ji k'ullin zuciyata ya fara kunce wa. Na fara kuka na ce "Ta ya ya zan yarda kana sona Tijjani alhalin kullum sai ka mini abin da zai sa ni kuka? Yaushe rabon da ka zauna ka ji damuwata, hatta yaran nan sun san ka canja mini. A gabansu kake rufe ido ka tsigale ni haka siddan. Kullum a cikin yi musu karyar baka da lafiya na ke dan kada su kullace ka. Yaushe rabon ka da nemi wani abu a tare da ni, me kake so na fahimta tunda nasan baka da hak'uri a wannan fagen?". Ya tsananta rikon da ya yi mini ya ce Na gode da kike rufa mini asiri a idon y'aya'na. Allah ya yi miki albarka. Sannan Allah ne shaidar furucin Baban Marina da yake nuni zai k'wace mini ke ya sanya na rasa k'arfi a tare da ni. Wallahi bana aikata komai na b'arna Asiya". Ban ce komai ba ya sake sassauta murya ya ce "Kin tab'a mini alkawarin ba zaki sake fita daga gidan nan ba sai da izinina, ina son ki samar mini da nutsuwa ta hanyar tabbatar mini har yanzu ma ba zaki fita babu yardata ba. Wallahi Asiya ke ce Tijjani. Ke ce nutsuwata, ke ce rufin asirina idan har kika bar ni, ina tabbatar miki komai zai kwace mini. Masu son nawa ma sai sun guje ni, saboda zan rasa abin da suke so a tare da ni." Na kalle shi hawaye na sintiri akan fuskarsa. Ya jani jikinsa ya rungume yana fad'in "Dan Allah ki yafe mini, ki fahimce ni, ki mini uzziri, ki tsananta yi mini addu'a ". Muka dinga kuka babu mai rarrashin wani. Dukkan jarumtar Tijjani ta k'are gabad'aya. Na kuma gasgata ba a haiyacinsa yake yi mini wani wulakancin ba. A haka yaran suka dawo suka tarar da mu. Hamim ya zuba mana ido. A hankali Tijjani ya sake ni tare da dabarar dauke hawayen sa. Yayin da nawa ya kasa tsayuwa. Hanif ya ce "Ammi Baban 2 yau ma ba shi da lafiyar ne, ya sake yi miki wani abu ne?" Kafin mu amsa masa Hamim ya ce "Lafiyarsa k'alau fa. Ammi ce take ce mana ba shi da lafiya, marar lafiya yana yin fad'a ne?" ✍️ *Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.* *Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐, ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To albishirinki yar uwa!* *UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1 *Oriflame products* *Daga make up artist din Guduyo* *Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame* *Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea* *Akwai pop corn* *07036662633*. Bamu yi mamakin furucinsa ba domin tamkar dan kama haka Hamim ya ke da magana. Ga kafirin wayo tamkar ya shekara goma. A sanyaye Tijjani ya jasu jikinsa dukkansu. Yana gode wa Yabi a zuciyarsa da ta rufe masa k'ofar da y'aya'nsa zasu tsane shi. Domin ya riga ya gane Hamim, ba abin da yake so a duniya sama da Yabi. Hanif ne ba shi da alkibla, bai san wa ya fi so a tsakaninsa da ita ba. Sosai ya tisa mu gaba a da tarairaiya. Rabon da ya yi mini hakan na manta. Gara yara yana ta tasu ni ce dai babu dad'i a tsananinmu. Da wuri ya sa suka kwanta. Suna yin barci kuwa ya ja ni dakinsa. Bamu samu kanmu ba sai tsakiyar dare. Mun tabbatar mun yi kewar junanmu. Haduwar kuma ta yi awon gaba da wani kason bacin ran da ke zukatanmu. Barci na shirin daukemu ya yi azama ya ce "Mu tashi mu kai kukanmu gun Allah. Ya taimake mu ya kawo mana mafita ya kuma yi mana maganin duk abin da zai farrak'amu". Duk yadda na gaji tikis. Haka na daure na yi wanka, na bishi sallar da ya tayar muka dinga yi har sai da lokacin asuba ya yi. Kwanakin da suka biyo baya na samu sassauci domin ya yi matukar rage kyara ta. Sannan ya daina fita ya shafe lokaci yna waya a waje. Watak'ila yana yi ne kafin ya shigo. ** Tunda Babah ta koma Bulkachuwa ta shiga damuwar halin da ta baro d'an uwanta, mahaifin Yabi. Sannan ta shiga alhinin yadda ake ta shirin bikin Tijjani da a Nasiba babu nadamar komai a gidan Marina. Ta kasa gane kanta sai kawai ta durfafi addu'a tare da fatan Ubangiji ya warware dukkan abin da babu alheri. Kwanaki biyu kullum sai ta yi mafarkin wai randar Dada ta sanyi akwai maciji mai dafi a ciki. Kwanaki biyu a jere tana wannan farkin babu tsagaitawa. Tun bata tunawa har ya fara shiga ranta mussaman da take ganin macijin na yunkurin fitowa ya hallaka Dada. Ta kasa katabus ta fara kokwanto akan lamarin. Yayin da ya rage saura sati uku biki. Baban Marina ya mik'e ya fara samun sauki a dalilin yadda Yabi ta kwantar da hankalinta. Takanas ta zo har Toro ta bashi tabbacin zata jure matukar ba Tijjani ne ya sake ta ba, to zata yi dukkan iyawarta ta tsallake dukkan kalubalen da yake gabanta. Murya na rawa ta ce ",Ya kamata ka huta Baba. Ya kamata ka samu nutsuwa, sannan mune zamu yi gwagwarmaya mu tsaywa kanmu. Ranar da babu kai kuma waye zai tare mini fad'a ko ya tsaya mini? Bini da addu'a kawai, na karbi wannan kaddarar da dukkan zuciyata, Allah yasa abokiyar arziki ce". Ya d'ora hannunsa a kaina ya ce "Ina alfahari da haihuwar ki Yabi. Ina samun nutsuwa saboda Ubangiji ya azurta ni da haihuwar ki. Da ikon Allah duk abin da kika saka a gaba na alheri sai kin ga fatahi a cikinsa. Allah ya shirya miki yaranki, Allah ya hore miki mijinki. Ya miki shamaki da dukkan abin da zai cutar da ke, ko ya gigita miki kwanciyar hankalinki". Cikin jarumta na ce "Ameen na gode Baba". ** Mafarkin maciji a randar Dada sai idan bata kwnata barci ba. Kan dole ta shirya ta tafi Toro, a lokacin sati biyu ya rage daurin aurensu Nasiba. Sai didima ake yi tare da kambaba lamarin. Masu adawa da Yabi suna fad'in "Duk d'aya ne to wa za'a ki a tsakaninsu? Tare da fake wa da ce wa rabon aure ai kisa yake yi, gara a yi, kowa rabon ta zata samu". A wannan tsukun na gasgata k'arfin jini domin hatta su Yaya Indo da suke mana yan'ubanci na gaske sun kaurace wa shiga shirgin auren ko taya masu adawa kanzagi da nuna kowa nasa ne a tsakaninmu. Kafatalin y'an k'ofarmu sun kame daga shiga cikin maganar auren gabadaya. Sun janye jikinsu sai isu isu. Ai kuwa mutanan gidan suka yi ca wajen sakin maganganun tare da ce wa "Kamar gaske. Su a tsakaninsu ma suke son ganin wani a uku shine yanzu zasu nuna mana an tab'asu? Suka dinga furzar da maganganun da su Yaya Indo suke fad'a akanmu a baya. Yaya Ummi kuwa ta k'i yarda da yadda ake son a sake gwara kansu. Tunda yawanci a kanta suke gulmar sai kuwa ni da na ke cikin rufin asiri. Suke taya masu yamididin duk abin da aka gani a jikina ni nake yiwa kaina. Da kuma ce wa duk k'afafar da nake yi bana gaban Tijjani domin har yau bai bar iskancin kule kulen mata ba. Na ka'du k'warai da Nazira take mayar mini wadannan maganganun da ake ta fitowa da su tare da ce wa a bakin su Yaya Indo aka fara ji. Amma yanzu sun fitittke wai suna kishin kanwarsu sai ka ce gaske. *** Babah sai dube dube take yi a tsakanin randunar Dada amma bata ga komai ba. Ta kasa samun nutsuwa. Rashin ganin macijin, ga shi bata daina ganisa a mafarkinta ba. A yanzu al'amarin ma yafi ta'azzara ko barcin rana ta yi sai ta ga ni. Tana zaune a gefen randar Aliyu ya k'ira ta a waya wanda a yanzu likita ne a F.M.C Azare. Cikin rauni ya ce "Babah kina yawaita addu'a kuwa? Tunda kika fad'a mini auren Yaya Tijjani da yarinyar nan ban sake samun nutsuwa ba. Anya kuwa! Ke ce da kanki kika mara bayan irin wannan kwamacalar a zuria guda? Duk matan duniya a rasa wacce zai aura sai wannan abar da aka tozarta ki saboda ita?" Ta kasa ce wa komai a dalilin yadda take jin an danne zuciyarta. Ga kuma sanyin da yake bin zuciyarta da gangar jikinta gabad'aya. Ya numfasa ya ce "Ki tsananta addu'ar tsari. Ina yawan mafarkin wani abu kamar tulu ya danne ki. Sannan a k'ofar Dada nake ganin abun. Na kasa gane mene ne shi." Jikinta ya sab'e da rawa. A rarrabe ta ce "ko randa ka ke ga ni?" Kai tsaye ya ce "Abu dai da ake zuba ruwa. Amma ba randa ba ce". Ta ce "Ai kuwa nima kullum sai na ga ni duk yadda aka yi akwsi wani abu a randar nan." Ta katse wayar, ta zabura ta mike ta dauko tabarya. Ta yi a'uziya, tare da ce wa "Innahu Sulaimanu wa Innahu Bismillahir rahamanin Rahim". Ta kuwa fasa gindimemiyar randar da tashi ta yi ta ganta a wajen. Dada ta fashe da kuka tana ce wa "Hauwa kika fasa mini randa ta. Kinsan ke ma kanki tare da aba ta kika gan ni. Kwanaki biyu tak a duniya Malam ya siyo mini ita tare da katangar wankan jegon ki. Amma yau kika fasa mini da gangan?". Ita kuwa tunda ta fasa gumi yake yanko mata. Wani irin abu tamkar kiyashi take jin yana sauka daga kanta. Bakinta ya yi nauyi ainun. Daidai lokacin da Innarsu Ubaida ta shigo yiwa Dada sallama zata gidan suna. Tana ganin ruwa ya jik'a tsakar gidan ga fasasshiyar randa ta hau jaje tana ce wa "Yanzu randar nan mai kafirin sanyi yau ta hadu da ajalinta?" Da kuka Dada ta ce "Eh kuma kisan wulakanci da rainin wayo a hadu da shi. Ta ajiye ledar kayanta, ta shiga kwashe rugurguzun randar. A nan ta ga k'atuwar laya. A tsorace ta ce "Dada a 'kona wannan ko ta tsari ce?" Murya babu amo ta ce "Jefa ta a wuta bansan ko ta mece ce ba. Gidan nan kam ai tuni Malam ya kafe shi. Ba dai mugu ya ga kofar shigowa ba. Ai kuwa ana kona layar Baba ta ji nauyin da zuciyarta ta yi ta ware. Sanyin da yake ratsa ta na tsoro da zullimin yin jayayaya ta ji duk ya gudu. Ta dinga Hamdala. A zuciyarta kuwa sai gasgata surkulle a ka yi mata ita kanta. A haka Tijjani suka shigo tare da Nasiba asibiti suka je yin gwaji. Bin su kawai take yi da ido. Bak'inta sai ambaton "Hasbunallahu wa ni'imal wakil yake yi. Zufa kuma bata fasa feso mata ba. Gabadaya ta shiga alhinin BAK'AR TA'ADAR da y'ar uwarta shakikiya ta aikata a dalilin son kai da na zuciya. Ta zuba ido tana nazarin Tijjani. Gabadaya ya kasa sukuni. Idonsa ya kad'a tamkar gauta. Shima sai zufar yake yi. Ya gaishe ta a sanyaye. Ta amsa masa murya babu amo domin gabad'aya ta duniyata ta yi mata tsanani. Jira take ta ji ya yi sallama ko ta fita. Amma yana zaune, duk da bai sake Bude baki ya yi magana ba. Duk takalarsa da magana da Dada take yi. *Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* Ya dai gaishe ta a gajarce. Tsawon lokaci yana zaune. Rigarsa ta jike ta gaba saboda yadda zurlfa take keto masa tamkar mai hadiyar kunama. Fiye da shudewar mintina talatin yana zaune ba ya um ba ya um um. Gabadaya Babah ta shafa'a da miyar da take yi wa Dada. Sai tashin kauri suka ji a hancinansu. Da azama ta yunkura ta sauke. Sannan ta janye wutar ta kashe. A tausashe ta ce "Dada me za'a d'ora kuma?" Cikin bagararwa Dadan ta ce "Kashe kawai." Domin bata sakar mata fuska a dalilin tana taya autarta Maryo fishin cin mutuncin da suke k'irarin ta yi mata da ta je wajenta takanas. Ta fito da garwashin. Ta kashe sannan ta yayyafa ruwa a murhun ta kashe shi gabad'aya. Ta dawo ta zauna. Sannu a hankali Tijjani ya fara dawowa cikin nutsuwarsa. Gumin da yake yi, ya fara tsane wa. Mintina kad'an ya mik'e ya ce "Zan tafi. Babah yaushe zaki koma?" Da mamaki ta ce "Tukunna." Da hanzari ta fice yana fad'in ",Na tafi Dada". Bai ko bi takan Nasiba ba, bare ya yi mata sallama. Babah ta kasa gane al'amarin domin tamkar mai jinnu haka yake canjawa. Ta hakura ta kudiri aniyar tsananta addu'a domin ta yi imanin Ubangiji ba zai juyar da addu'ar ta ba. Sannu a hankali kwanaki suna ta shude wa har ya zama saura kwanaki goma auren da ake ta cece kuce a kansa. Lefe ne kawai ba a kai ba, an yanke shawarar idan ta je gidansa ya bata domin zuciyoyi sun kai kololuwa wajen fusata. * Da safe bayan ya tafi da yara makaranta, shi kuma ya wuce Dass. Ina zaune a falo ni kad'ai, kuka kawai nake yi, irin kukan nan da yake zuwa ko da baka so ba. Gabad'aya duniyar ta mini zafi. Idan na tuna saura kwanaki 'kalilan na fara raba Bulkachuwa da Nasiba sai na ji ina fatan mutuwa ta dauke ni kawai. Na kifa kai a hannun kujera ina kuka tamkar mai wake, domin bilhakki na Bude baki nake yi. Ba zato waya ta hau kuwwa. Na mika hannu a dalilin Gwaggo kawai na saka taken da yake tashi. Sai da na yi jarumtar shanye kukan sannan na dauka. Murya ta kawai ta ji. Ta tausasa harshe ta ce "Kuka kike yi ne Yabi?" Haka kawai ta fad'a na rushe da kuka mai tsananin gaske. Cikin kuka sosai na ce "Gwoggo ba zan iya ba, zuciyata na mini ciwo, tana zafi mai radadi." Ta numfasa ta ce ",Zaki iya mana. Ai ba a kanki aka fara yin kishiya ba, ba kuma za'a kare a kanki ba". Da rawar murya na ce "Amma dai kishiya irin tawa Gwaggo zan zama cikin mutane kad'an da aka yiwa irin ta. Mena yiwa Tijjani da zai mini irin wannan cin mutuncin a rayuwata?" Da taushi sosai ta ce "Nutsu ki ji ni! Shawara zan ba ki, ba umarni ba, kinsan umarni wajibi ne ki mini biyayya. Ita kuwa shawara sai kin so za ki bi. Amma idan kika bi zai fi miki alheri fiye da barin." Ta nisa tare da ce wa "Duk runtsi kada ki ce mijinki ya sake ki matukar bai keta haddi da alfarmar shari'a ko ta aure ba. Sannan ki yi dukkan iyawar ki, kada ki nuna damuwa ko gazawarki a gaban mahaifin ki Yabi. Ya damu da halin da kike ciki. Ki daure, ba abin da ba zai wuce ba, sai ikon Allah". Na yi shiru illah kukan da nake yi mata tamkar zan shid'e. Cikin jarumta ainun ta ce "Allah ya sassauta miki, ba komai kin ji. To ban da ma kin saka damuwa a ranki ai bai kamata al'amarin duniya ya susuta ki irin haka ba Yabi. Kinsan kalubalen da yake gaban ki kuwa? Kwanciyar kabari kad'ai da muna saka ta a gabanmu da bamu bari kalubalen duniya ya kidima mu ya shagaltar da mu yiwa kanmu tanadin kwanciyar da Ubangiji kad'ai yasan adadin tsayin ta ba. Me yasa kishi ya ke sawa mu manta Annabi ya ce mu yawaita sadaka, sallah da istigifari. Domin ya hango mataye da yawa yan'wuta ne. Kuma tsananta kishi alamu ne, na mace ta barranta kanta daga ayar da Ubangiji ya saukar. Wacce kuwa ta barranta daga imani da ayar Allah. La budda tana cikin hatsarin kafirta matukar bata gaggauta tuba tare da yin hak'uri cikin hukuncin da Ubangiji ya halasta ba." Tsikar jikina ta zuba k'warai da gaske. Na sassauta kukan da nake yi. Ta sake sassauta wa ta ce "Ki yawaita karatun kura'ani domin karanta shi kad'ai yana wanke tsatsar zuciya. Ki yawaita sallah. Ki rungumi y'aya'nki da sana'ar ki. Miji kuwa kada ki zalunce shi, kada ki tauye shi, kada ki hana shi samun nutsuwa da ke ko a gidansa. Illah iyaka ki sassauta zazzafar soyayyar da zata saka ki halaka, ki kuma halaka shi". Na numfasa tare da ajiyar zuciya mai nauyi na ce "To" Ta shiga jero mini albarka. Ta ce "Idan akwai abin da yafi albarka da yafiyar uwa na roki Ubangiji ya yi miki da ke da zuriarki. Idan har Ubangiji baya juyar da addu'ar uwa akan d'anta , to alafamar ma'aiki ba zaki wulakanta a wannan duniyar ba. Duk inda rayuwa zata kai ki, komin tsanani zaki zama cikin rufin asiri mai yawa. Da ikon Allah wani mahaluki ba zai ga gazawar ki ba Yabi". Da rawar murya na ce "Na gode Gwaggo! Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana mai albarka". Na jiyo ajiyar zuciyarra alamun ta samu nutsuwa da yadda na karbi ban hak'uriinta. Ta ce "Ameen, ina tagwaye?" Na ce "suna makaranta". "To ke me kike yi yanzu?" Ta tambayar cike da soyayya mai yawa. A hankali na ce "A zaune kawai nake Gwaggo ". "Tashi ki yi nafila, ki daina bari wannan lokacin mai tsada na wuce ki, baki yi salatul duha ba. Kinsan duk abin da Ubangiji ya rantse da shi mai falala ne, mai daraja ne. Allah ya ce "Wad Duha! Lalle ki yawaita neman gafara da rahamar Allah a wannan lokacin, Ubangiji baya juyar da addu'ar da aka yi ta a wannan sa'ar sai dai jinkiri, ko ya mussnya maka fiye da abin da ka roka alheri". Na ce "To!Da budaddiyar murya. Ina jin soyayyar Gwaggo na sake tunbatsa a dukkan sassan jikina. Kwalla ta zubo mini wacce bata ciwo ba ce, ta tausayinta ne, tare da tausayin wacce duk bata girma da uwa mahaifiya ba. Tabbas soyayyar uwa ita ce mafi kololuwa a wannan duniyar. Muka yi sallama na tashi na dauro alwallah, na yi walaha. Akan sallayar barci ya sure ni, irin wanda na jima ban samu yin sa ba. Akai Babah take yi mini waya, tana tambayar lafiyata da lafiyar yara. Na dinga mamakin yadda ta sauko. Na sani tana sona. Amma a kwanakin baya gabadaya ta canja mini. Yanzu kuma ta dawo mini Babah tawa Mai kaunata. Na dinga mamakin haka, da na ga kaina zai dauki caji Sau kawai nayi Hamdala a raiana tare da rok'on Ubangiji ya sake tsare mu daga sharrin masu tofi a cikin kulle kulle. Da daddare muna kwance a dakinsa yara suna dakinsu da yake cikin falona sun yi barci. Dukkanmu kowa tunanin zuci yake yi. Ba abin da nake so irin na fice na bar gidan Tijjani. Tufka da warwara kawai nake yi. Maganganun Gwaggo sun yi matukar karya lagona. Domin a da na kudire wa raina daga ranar da ya shiga dakin Nasiba ya kwana da ita. Tabbas washegari zan bar shi, bari na har abada tunda nasan Baban Marina zai bani masauki tare da kyakkwar mu'amala a tsakaninmu. Amma yanzu Gwaggo ta mini tilas din cigaba da zama ta hanyar rarrashi da dabara. Na nisa na saki ajiyar zuciya. Daidai lokacin ya ce "Sannu Asiya! Ban kula shi ba, ya ruko ni, na yi bakam tamkar mai barci. A sanyaye ya ce "Zullimi ne yake kama ni from no where! Samar mini da nutsuwa pls. Dan Allah bude baki ki fad'a mini wata kalma da zan samu sassauci a zuciyata. Ina daf da tarwatse wa Asiya". Na ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Tsuntsun da ya ja ruwa". Ya sake rik'e ni ainun. Ya kasa ce wa kanzil. Ajiyar zuciya kawai yake yi. Murya babu amo ya ce "Idan na mutu Asiya dan Allah kada laifina ya shafi twins. Ni kaina bana gane kaina a wasu lokuta, kin ga da hantsi ko yamma sai na ji tamkar ana hura mini huta a kirjina. Da zarar wani aka jima kuma sai na ji duk yadda aka azalzale ni na je Toro sai kuma na ji ke nake son na dawo ma ga ni. Ko dai na haukace ne Asiya?" Da k'arfi sosai na ce "Tunda har kana banbance wasu alamuran da hamkalinka sarai. Kuma ina nan akan bakana, ba zan zauna da kai ba Bulkachuwa. Ana kawo maka Nasiba ka tabbatar na hak'ura da kai". Jikinsa ya dauki rawa. Ya ce "Bazan iya rabuwa da ke ba. Haka kuma idan ban aure ta ba, bazan tab'a samun nutsuwa ba. Ki taimake ni mana". Na ce "zaka ga taimako ganin idon ka. Na rantse maka duk wani sababin duniya ka shiryawa ganinsa. Hala dai ka manta Yabin marina ne Tijjani?". Ga mamakina bai iya taso mini da masifar sa ba. Gabadaya jikinsa ya sake sosai. Washagari na tashi da bala'i ko kallon inda yake ban yi ba. Na yarda da zancen Gwoggo. Amma bazan iya samar masa da nutsuwar da ake so ba. Ya je can ya k'arata da dibar albarkar sa, shi da masu goya masa baya. A wannan safiyar ya mini magana yafi sau goma ban kula shi ba. Na ki yin girki. Shi kuma ba shi da kuzarin da zai yi. Gabadaya ya koma Tijjanin farkon aurenmu. Ba na yanzu da yake masife ni a dalilin ina adawa da k'arin aurensa. Ya kai ya kawo a tsakanin dakinsa da nawa. Ya kasa fita bare na samu na d'an sarara. Tunda gabadaya haushinnsa nake ji mai kama da tsana. Sallah kawai yake fita. Da k'yar ya lallaba ya tafi dauko su Hanif. Da gudu suka shigo. Na yi maza na hadiye damuwar da nake ciki na shiga yi musu oyoyo tare da murmushin yak'e. Na dora musu indomie, bayan na juye musu ruwan wanka. Na kammala yi musu wanka, suka yi sallah. Sannan na juyo mana indomie muka fara ci da su. Hanif ya ce "Baban 2 sauko mu ci". Hamim ya ce "Ba shi da lafiya ai marar lafiya ba ya cin abinci" Takaici ya shake Bulkachuwa. Ya daidai ta zamansa ya ce "Hamim baka tausayina ko kad'an?. Zaka ga tsiya, daga yau Hanif zan dinga siyo wa abina tunda kai uwarka kake so kawai". Da yake mai kwadayi ne sai ya marairaice ya ce "Na daina Baban 2 sauko mu ci to." Bai sauko ba, ya koma ya zauna. Ba tare da ya sake ce wa komai ba. Muka kammala da kansa ya saka musu yunifom din islmamiya ya rakasu waje ya dawo. Ya zauna daf da ni ya ce "Asiya Tsakanin ki da mai rumfa me ya hana ki daukar ciki?" Na hassalo na ce "Saboda na gama haihuwar da kai, sai da wani". Ai kuwa ina rufe baki ya cakume ni yana kokarin murde mini baki. Na dinga zille wa, ina ture shi. Maimakon ya bar ni tunda ya ga kuka nake yi sosai, duk da bai mini komai ba, kuka nake na takaicinsa da na aurensa. Amma bawan Allah bai yarda ya kyale ni ba. Ya sure ni ya yi dakina da ni. Sai da ya yi abin da yake so. Ya tara mini gajiya ya ce "Ya kika ji? Kin hana ni abinci, amma kin dafa muku ke da y'aya'n ki, kun ci. Sai kuma na zarta ki k'arfi da kuzari." Na ja tsaki na juya masa baya, bayan na ja mayafi na lullube jikina. Da daddare ya fita ya siyo tsire mai yawa. Ya dafa shayi ya kawo falo. Ya juye naman a plate ya ce mu sauko mu ci. Shi da yaran suka ci. Ni kuwa ko sha'awar ci ban ji ba, duk da yadda k'amshin ya cika wajen gabad'aya. Washagari har wajen tara yana gida kamar ba zai fita ba. Kamar zan masa magana a dalilin yadda ya bani tausayi, amma da zarar na tuna ba janye wa zai yi ya fasa auren Nasiba ba, sai na ji tsanarsa na sake darsuwa mini. Yana zaune sai waya ake yi masa babu kakkautawa. Kan dole ya yi shirin fita. Murya babu amo ya ce "Zan fita Asiya sai na dawo". Ko motsi ban yi ba bare na masa shi. Ya sa kai ya fice. Sai kuma ya dawo, ya gama kame kame ya fita. Mintina kusan talatin ya sake dawo wa. Ya tarar da ni a zaune. Ya ce "Gabad'aya jikina bana jin dad'i. Ga shi fitar ta zame mini dole. Kano zan je na kai kaya. Amma yau zan dawo komin dare in sha Allah ". Na dauke kai na kasa ce wa A dawo lafiya. Ya fita. Na ja tsaki tare da ce wa "Ka gama shige da ficen ka ba kula ka zan yi ba. Azahar ta tayar da ni. Na yi sallah na d'ora abinci saboda yara. A daddafw na yi shara na gyara dakin. Na fito wanka su Hamim suka dawo. Da yake alhamis ne babu islamiya. Dan haka sai suka debe mini kewa, ban fada nazarin yadda zamana da Nasiba zai kasance ba. Tunda a duniya bani da matsalar da ta wuce hakan. Ban ankara da rashin dawowarsa ba sai wajen goma na dare. Yana wahalar gaske ya yi dare. Idan kuwa hakan ta kasance sai ya bugo mini waya, ko da ni ban masa wayar ba. Na fara tsorata da shadaya ta gota. Zuciyata na bugawa na d'auki waya na k'ira shi. Abin mamaki wayar ta ki shiga, na dage da kira babu kakkautawa. A karshe a ka ce a kashe take gabad'aya. Na shiga zullimi sosai. Mussaman da ya tabbatar mini zai dawo komin dare. Na rasa yadda zan yi. Na Kalli yara na barci. Hamim ya dora kafarsa jikin Hanif. Hawaye ya tsinke mini domin yadda nake jin jiki da zuciyata suna bari, nasan akwai abin da zai biyo baya marar dad'i. Duk yadda na so na tashi na yi sallah kasawa na yi. Daren ya mini tsayi ainun. Domin tunda muka dawo Bauchi bai tab'a tafiyar kwana ya barmu ba. Na dinga kuka ina fad'in "Allah ka taimake ni ka dawo da shi lafiya." Da asuba na cigaba da kiran wayarsa nan ma shiru. Ina idar da sallaj na bugawa kaninsa Aliyu waya na sanar masa Tijjani bai dawo ba, kuma wayarsa a kashe. Ya yi yunkurin kwantar mini da hankali. Na katse wayata na kira Yaya Salisu na shaida masa. Har karfe daya na rana babu labarin sa. Hankali dangi ya fara tashi. Da la'asar sai ga Babah ta Bulkachuwa tare da Aliyu. Kuka kawai muke yi ni da ita. Aka rasa mai bawa wani hak'uri a tsakaninmu. Yayin da Yaya Salisu da Yaya Aliyu suka nufi Kano tun hantsi. Tashin hankalinmu ya sake tsananta da la'asar ta yi babu wani tartibin labari akan Tijjani ko motarsa. Hatta Toro hankakula ya tashi ainun domin tabbas abu marar dad'i ya same shi, mutuwa ko mummunar hadarin da aka kasa gane shi. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai muke ta ambata ni da Babah. Babu abin da yake sake tayar mini da hankali irin idan na kalli twins.. gabadaya sun kasa sukuni. Duk fitinar Hamim ya zauna a gefe ya nutsu tamkar marar lafiya. Maganganunsa da ya dinga yi mini a baya akan mutuwa suka dinga dawo mini. Na fara kuka sosai ina ce wa "Sai da na sakankance ba mutuwa zaka yi ba shine zaka tafi ka bar omu, me yasa zaka tafi yanzu alhalin zukatanmu cike suke da gilli da bacin rai mai tsananin gaske?.". Babah ta kasa ce wa komai illa hawaye da ita ma yake k'waranya daga fuskarta. Ina cikin haka sai ga Yaya Ummi da Mama. Baban Marina ya turo su, su zauna da ni. A dalilin bai san Babah tana tare da ni ba. Ganinsu ya sake rikitini ina sake gasgata abu marar dad'i ya same ni. Ina kuka ina fad'in "Ni Yabi yaushe zan tsallake damuwowi ne a rayuwa ta?" Gabadaya na rikice, sai tausa ta suke yi, duk da Yaya Ummi ma kukan take yi sosai. Sai dare Aliyu ya k'ira Babah. Murya babu sukuni. Ya ce "Al'amarin dai sai hak'uri." Abin da na ji ke nan na yanke jiki na fad'i ban sake gane komai ba. *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* ✍️ *INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA* *ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA.* *SABO LITTAFIN TA ZAI ZO BA DA JIMAWA BA*. *HAKA NAN AKWAI WASU DAGA CIKIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA HAFSAT C SODANGI, SUMA SOFT COPIES* *HAJIYA HANNE ADO ABDULLAHI?* *MARUBUCIYAR WANKA DA GARI DA KUMA WACECE UWA?* *TO ITA MA TAKANAS NA SAMO MUKU LITTAFANTA DOMIN KUN SANI TA YI RUBUTU MASU MA'ANA*. *LITTAFAN DA YAWA, AMMA AKWAI DISCOUNT DOMIN SO NAKE KU YI TA SIYAWA Y'AYA'NKU DA KANNENKU LITTAFAI MASU DARASI DA MA'ANA*. *BA DA JIMAWA BA ZAN ZO MUKU DA SU*. *08032773332*. Na farfado ne na gan ni ana k'ara mini ruwa sai fifita suke mini tare da kuka dukkansu. Baki na rawa na ce "Babah ni din musulma ce! Ki fad'a mini Tijjani ya rasu ne?" Da rawar murya ta ce "Bai ce ya mutu ba Yabi. Amma dai akwai abin da ya same shi marar dad'in ji, tunda har Aliyu ya jinjina lamarin". Na fizge k'arin ruwan na zabura na ture su na tashi. Hijabi na raruma na yi hanyar waje ba tare ma da na saka ba. Yaya Ummi ta ruk'o ni tana fad'in "Ina zaki a wannan halin Yabi?" Da kuka sosai na ce "Kano ba zan tab'a samun nutsuwa ba, matukar ban san halin da yake ciki ba". Fuskar kowa k'walla ce da tashin hankali. Hatta Mama jikinta a sanyaye yake ainun. Da k'yar suka tirsasa ni na hak'ura na zauna. Sai ambaton Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai nake yi. A fili nake fad'in Allah ka kaddara mini na ga dawowar Tijjani cikin gidan nan, ko da ba akan kafafunsa ba ne. Fatana ace yana numfashi. Ubangiji ka rufa mini asiri ni da y'aya'na". Ba abin da yake sake tayar mini da hankali irin yadda Babah ta kasa tsayar da hawayen ta. Akai akai take share hawaye babu kakkautawa. Kwanaki biyu muna cikin wani irin zullimi mai tsananin gaske. Domin duk asibiti da yake cikin Kano su Aliyu sun karade a kwanakin nan amma babu Tijjani babu labarin sa. Kowa ya karaya. A ranar Baban Marina ya taho Bauchi tare da Gwaggo. Nasiha kan nasiha suka shafe lokaci suna yi mini akan yarda da kaddara na yi hak'uri mu bishi da addu'ar idan a raye yake Ubangiji ya tsare mana shi, ya kuma bayyana shi. Idan kuwa rai ya yi halinsa to Allah ya sanar da mu, ya kuma jik'an sa. Na rarrafa na fad'a jikin Baba cikin matsanancin kuka na ce "Sai yaushe zan huta, yaushe ne zan ji dad'in da ake ta fad'in zai same ni? Gabad'aya walagigi yafi yaws a rayuwata Baba! Kalli k'ananun y'aya'n Tijjani wa zai taya ni tarbiyarsu da wahalarsu Baba?" Muryarsa na rawa ya ce "Ubangiji da ya baki su shine jagoran da zai taya ki kulawa da su. Sannan matukar ina numfashi ko y'aya' nawa kika haifa zan kula da su iyakar yadda zan iya, tamkar y'aya'n da na haifa! Yadda ya kare maganar da kuka ya sanya Gwaggo fara kuka duk kuwa da yadda take da jarumta mai yawa. Kowa na falo kuka yake, hatta Mama kuka kuma na gaske ba na ganin ido ba. Tsawon lokaci muna kuka tamkar an tabbatar Tijjani ya k'are. Hanif ya ce "Ku yi hak'uri" Hamim kuwa ya ce "Baban 2 zai dawo a motarsa bai b'ata ba." Gabadaya yaran sun rasa kuzari da karsashi a tare da su. Da yamma mun idar da sallar la'asar Yaya Salisu ya kira Baban Marina da yake zaune a cikinmu tamkar mace. A sanyaye ya ce "Mun samu labarinsa, mun je mun gan shi". Gabadaya dakin muka hau fad'in Alhamdulillah Alhamdulillah! Sai dai Innalillahi wa inna ilaihir rajiun din da Baban Marina yake fad'i ya yi matukar tsorata mu, mussaman ni da zuciyata tamkar ta fad'o k'asa. Na kasa fahimtar bayanin da ake masa. Nasan dai na ji ya ce mun gan shi. Gumi ya dinga keto mini. Ina tambayar zuciyata wanne ibtilai ne ya samu Bulkachuwa irin haka?. Sai da Baban ya ajiye wayar. Tsawon mintina bai iya ce wa komai ba. Gabadaya ya jike da zufa. A sanyaye Gwaggo ta ce "Alhaji fad'a mana halin da ake ciki kada zullimi ya karasa kassara mu. Murya babu amo ya ce "Yana hannun jami'an tsaro. Tun shekaranjiya suke tsare da shi. Kuma damln tsabar raina talakan k'asa suka kashe wayarsa bare wani nasa ya ji halin da yake ciki." Na saki nannuyar ajiyar zuciya, da kuka nake fad'in Allamdulillah! Domin sai na ji tamkar an dauke mini k'atuwar masifar da ta nannad'e ni. Tunda yana da ransa komai mai s'auki ne. Domin ban fahimci ana iya yiwa mutum talala ya zama ba shi da yancin yin komai a rayuwarsa ba. Na kasa yin walwala a dalilin yadda Baban Marina ya yi laushi. Na tabbatar Tijjani na cikin k'ak'ani ka yi. *Toro* Baban kasuwa da Baban Tsakiya zaune a gaban Dada da take kuka face face tana fad'in "Ubangiji ka kare mai sunan manya, ka bayyana shi". Baban Tsakiya ya ce "Ki daina damuwa sai ciwon ya tashi ne? An ce miki a gan shi. Sai dai fitowarsa sai ikon Allah. Tunda laifin da aka kama shi da shi idan a wata k'asar ne take za'a tabbatar masa da haddin kisa." Hannun biyu ta d'ora aka tana kururuwa tana ce wa "Allah ka yi mini dan ma'aiki. Alfarmar Shehu Amadu Tijjani mai karama ka saukakawa wannan yaro". Baban kasuwa ya ce "Allah ne ya yi sakayya ya toni asirinsa. Wai Tijjani ya rasa wadanda zai wulakanta sai mu? A fili yake nuna wa Yaya Sani ne kawunsa da zai yiwa hidima. Akan idonmu zai ta d'orawa yara kayan abinci da kayan miya ana kai wa kofarsa amma mu wayam. Wai shi mai suruki. Alhalin ba akan son ramasa ya bashi auren iblishiyar yarinyar nan ba. Mune muka so a bashi".. Baban Tsakiya ya yi k'uta tare da ce wa "Allah ke nan! Ai duk mai gilli mai son ya wulakanta na gaba da shi ya dinga ganin jarraba ke nan." Dada dai kuka take bil hakki. Domin tun farko tana son Bulkachuwa. Da ya samu wadata kuma ya jiyar da ita dad'i duk da dai ce wa take yi bashi yake biyan ta. Tunda dukiyarta da ya salwantar mata runduna ce babba. Washagari muka dunguma Kano tare da Baban Marina. A babbar hedikwatar y'an sanda ta bonfai muka tarar da shi cikin mawuyacin hali. Hawaye ya tsinke mini. Domin gabad'aya ya fita a hayyacinsa. Babu alamun duka a tare da shi. Amma ya jigata k'warai da gaske. Abin mamaki a wajen muka tarar da su Yaya Jabir ya zo daga Kaduna da kuma Yaya Ammar yayan Nasiba. Duk da shi ma a BAUCHI yake aiki a gidan Yari. Tunda su Yaya Salisu suka fada musu, suka bar komai suka biyo su Kano dan sanin halin da Tijjani yake ciki. Cikin tashin hankali Tijjani ya ke fad'in "Wallahi bana harkar. Ina gida aka mini waya akan na biya na karbi sako a Wunti. Ashe wiwi da koken ce ga shi an kasa samun lambar da aka kira ni da ita. Wallahi ba kayana ba ne, ba ni da alak'a da ita". Ya fad'a idonsa ya kad'a ainun tamkar na rikakken mashayi. Na rushe da kuka riris. Domin dai na riga na gane mun fad'a cikin garari mai girma. Kallon sa na yi na gane iyakar gaskiyarsa yake fad'a babu alamun karya ko kwaskwarima domin ya riga ya bani damar da na fahimci gaskiyar sa da kunbiya kunbiyarsa. Babah ta kasa magana, yayin da Baban Marina ya ce "Tijjani ka fadamana gaskiyar magana, dan musan ta yadda zamu b'ullowa wannan azal d'in. Kasan wahalar da shari'a ma laifi ne babba." Murya na rawa ya ce "Wallahi gaskiyar magana na fad'a. Bana harkar, ba ni da alak'a da kayan da aka kama ni da shi Baba". Gauron numfashi Baba ya yi tare da ambaton "Subhanallah! Baba ta kasa magana duk da idonta a soye yake babu alamun kuka. Na sani kuma tana cikin damuwa ne mai yawa. Na tsugunna a gabansa ya sassauta murya ya ce "Asiya na rantse miki ba ni da alak'a da wannan al'amarin sharrin magauta na had'u da shi. Kaddarar da azal ce ta hau kaina". Na zuba masa ido tamkar ba a gaban iyayenmu muke ba. Shi ma ya zuba mini nasa, tsawon lokaci muna kallon juna. A cikin wannan kallon na tabbatar Tijjani bai aikata laifin da aka jingina masa ba. Na kuma gasgata shi akan gaskiya yake amayarwa. Ni na fara janye idanuwana da hawaye suka cika su taf. Da rawar murya na ce "Na gasgata ka Baban 2! Ina baka tabbas din ko baka samu mutum daya da ya gasgata ka ba. Ni Yabi na yarda bak'in k'azafi aka yi maka, tare da hak'a maka ramin mugunta. Dan haka ina tare da kai cikin ko wanne bigire har mu ga me Ubangiji zai zartar mana". Daga hakan na fara kuka sosai. Yaranmu da suke jikinsa suka yi tsuru tsuru suna kallon yadda nake kuka sosai, shi kuma ya susuce ido ya kad'a. Sai lokacin Babah ta ce "Allah ya warware maka, ya bayyana gaskiyar al'amarin". Yaya Ummi kuwa da Mama kuka suke yi. Gwaggo ce bata um bata um tunda ta yi jaje cikin rauni da kasala bata sake iya magana ba. Muna kallo da lokacin da suka bamu ya cika suka iza keyarsa hannunsa dauke da ankwa tamkar kasurgumin mai laifi. Ni dai har muka dawo BAUCHI ban iya daina kuka ba. Tun ana bani bakin na yi shiru har aka zuba mini ido. Maimakon mu yada zango a BAUCHI sai Baba ya ce a wuce Toro kawai. A k'ofar gida muka tarar da su Baban Tsakiya. Na kalle su na gasgata ce wa Baban Marina ne kawai ubanmu. Ba wanda ya bi bayan Tijjani ko na ahalinsa a cikinsu. Dukkanmu a gaban Dada muka zube tamkar masu neman gafara. Tana kuka, matan cikinmu muna yi, tamkar dai mutuwar fuju'a Tijjani ya yi. *INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA* *ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA. *SABO LITTAFIN TA ZAI ZO BA DA JIMAWA BA* Sai ta dauko salatil fathi sai ta rikice ta dauko ashafa da k'yar dai ta fara karanta casa'a ta sauke ta. Tana yi tana ce wa "Rabbani a saukakawa mai babban suna, a tausayawa wadannan y'aya' nasa". Da k'yar Baban Marina ya hakurkurtar da mu aka daina kukan. A dakin Gwaggo na yada zango. Dakin da nake matukar samun nutsuwa a cikinsa. Amma a yau sai na ji ina cikin matsanancin kunci da zullimi domin sai nake ganin tamkar ana shirin raba ni da Tijjani ne. Na ga tsayin wannan dare tamkar dai ace gawa ce a dakin. Ban yi barci ba. Karfe uku na ga Gwaggo ta fita ta dauro alwallah. Duk yadda na ke cikin zullimi sai da na tuna irin wannan yanayin muka shiga a lokacin da aka zartar mini da hukuncin auren Bulkachuwa. Yau kuma ina kukan bak'in cikin nisanta ni da gidansa da aka yi. Gwaggo tana shigowa da alwalarta, nima na zabura na mik'e na doro alwalar. Muka dinga nafila muna shigar da bukatunmu. Ina kuka hannuwana na sama "Tijjani, Tijjani kawai nake iya fad'a gabad'aya kaina ya kulle. Domin dawo da ni gida ya yi matukar sake tsorata ni. Me yasa za'a raba ni da dakina? Kwanaki biyu kacal a gidan Marina na gane masu farinciki yadda na shiga cikin garari sun rinjayi masu tausayi da rarrashina. A k'ofarmu kam babu wanda yake takura mini ko habaici. Amma da zarar na fita da NIYYAR zuwa wajen Dada sai na samu wanda ya yi mini yarfe ana mini habaicin dama karyar arzikin da a muke yi ba mai tsarki ba ne. Har ta kai bana k'aunar na fita. Amma idan ban je ba sai ta aiko wai na je, a wannan lokacin k'warai Dada take tausayina ni da yara. Kullum a cikin sadaka da addu'a take yiwa Tijjani. Kuka kam bansan wa yafi yi a tsakaninmu ba. Ta damu k'warai har jininta ya hau. Ban sake samun damar gano Tijjani ba har aka yi sati da zuwanmu. A lokacin kuma na fara gazawa. Tashin hankalina na sake hauhawa. Baban Kasuwa da na Tsakiya babu wanda ya tako kafarsa da nufin yi mini jaje. Ashe wai na yi laifi da ban bisu kofofinsu na gaishe su tare da yi musu jaje tunda ai su d'ansu ne tun kafin ya zama mijina. Ni luma damuwata ta girmi tunanin zuwa gaishe gaishe. Sannan mafi yawa a wajen Dada nake ganinsu na kuma gaishe su a mutunce. A lokacin na sake fahimta tare da gasgata idan Baban Marina ya kauce bamu da wanda zai tsaya kai da fata ya tallafemu idan mun shiga cikin kalubalen rayuwa. Tausayin k'ananun y'aya'n Baban Marina ya sake rub'anya tashin hankalina. Gabadaya na zama tamkar wata zararriya, na k'are na fige tamkar kudin guzuri. Bayan addu'ar da nake yi wa Tijjani da y'aya'na, sai na sake tsananta addu'ar Ubangiji ya sanya soyayya da tausayi mai yawa a tsakanin y'aya'n Baban Marina. Domin kam al'amarin Baffaninmu sai shukuran. Kullum mutuwa na daukarmu daya bayan d'aya amma bata zame musu izna ba. Abin da na sake fahimta kawai shaidan da son zuciya gami da hassada ne suka yiwa zumuncin yau k'awanya. Sassaucin rayuwar da Baban Marina ya samu a dalilin y'aya'n sa ya zama wani abin tattaunawa. Kullum a cikin fad'in ai yanzu ya farfado suke. Na tabbatar ba za'a bar ni na ji da ibtilain da ya fad'o mana ba, sai an tusa ni gaba da muzanci kala kala. Dan haka na kudire da na yi sati biyu zan fad'awa Baban Marina zan koma dakina tunda dai Tijjani bai mutu ba. Washagari muka tafi Kano da ni da Nazira da Yaya Salisu. Gabadaya Tijjani ya fita a hayyacinsa. Ina kuka nake fad'in "Basa baka abinci ko?" Ya girgiza kai ya ce "Abin nan da nake fad'a miki. Da zarar hantsi ko yamma, ta yi sai gabad'aya na rikice, zuciyata kamar ta yi bindiga wajen son na tafi Toro na ga Nasiba. Masifar zafin da nake ji a zuciyata da kirjina ya wuce misali ina fatan na mutu kawai Asiya". Na kasa ce wa komai. Yaya Salisu ya ce "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Allah mun tuba." Nazira kuwa kuka take yi tana fad'in "Dama nasan ba haka siddan ka runtse ido ka kafe sai ka aure ta ba." Ni kuwa na zama tamkar mutum mutumi. Domin a yanzu na yarda Tijjani na bukatar na samar masa da nutsuwa. Tunda duk yadda yake cikin wannan tashin hankalin amma yana fad'in yadda yake ji game da al'amarin ta. Na tabbatar ba son zuciya ko tozarci ba ne ya sanya yake fad'a mini yadda yake ji akan Nasiba ba. Cikin tausayi nake kallon sa gabad'aya ya zube, ya yi duhu. Tausayi, so, kauna suka sake yi mini rubdugu a dukkan zuciyata da gangar jikina. Murya a tausashe na ce "Ka tsananta addu'a ka kuma yi hak'uri. Da kaina zan kawo ta ka ganta". Ya zuba mini ya ce "Yaushe?" Na ce "Gobe ko jibi". Ya yi k'asa da kansa ya ce "Goben dai." Da k'arfin hali na ce "To". Ya kidime ya ce "Wanne irin to kike nufi Asiya?" Na ce na gaskiya da gaskiyar magana ". Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa ya ce "Ina twins, me ya hana ki zo da su na gansu?" Idona cike da k'walla na ce "makaranta suka bi yaran gidan." Haka muka ba shi abin da zamu ba shi. Aka tafi da shi. Tuni kuma an saka ranar da za'a gurfanar da shi gaban kotu. Sai dai Yaya Ammar ya tabbatar mana BAUCHI za'a dawo da shi. Tunda a cikin jahar Bauchi aka kama shi. Ba'a san dalilinsu na kawo shi Kano ba tare da sun sanarwa da kowa nasa ba har tsayin kwanaki biyu. Da yammaci sosai muka isa Toro. Muka tarar da Nasiba a k'ofar Dada domin mijin babarta aka kwantar a asibitin koyarwa na jamiar Jos. Lokacin da abin ya faru tana can bata dawo ba, sai yau aka sallame su. Babar tata ta wuce gidanta da marar lafiya. Ni da Nazira muna kallon yadda gabadaya ta takure ta kasa sakat tunda muka shiga. Akwai alamun tasku a tare da ita. Na yi jarumtar ce wa "Nasiba Bulkachuwa na ta jajen ki. Ya damu da rashin ganinki cikin masu zuwa duba shi tare da jajanta masa. Gobe zan koma, sai mu tafi tare ko ya samu nutsuwa". Ta kasa amsawa. Hatta Dada ma na kashe ta da kunya gabad'aya sun rasa me zasu ce. Yanayinsu ya sa na gane suma tamkar an tursasu ne akan sha'anin Tijjani. Washagari kuwa na shirya yara na ce mun tafi Kano. Baba bai so ba, amma saboda lallaba farincikina yake yi bai hana ba. Sai ma ya ce "Ubaidun Inna ya raka ni. K'ofar Dada na dire. Na tisa Nasiba a gaba muka tafi a kan dole ba yadda zata yi. Domin na lura tsoro nake bata. Har muka isa Kano ba wata hira a tsakaninmu. Sai kuma muka hadi da tasgadon y'an sanda. Wai ba zamu gan shi ba, ana yawan yi musu zarya da sunan ganin Tijjani bayan shi mai babban laifi ne. Hanif ya fashe da kuka yana ce wa "Zamu ga Baban 2 dan Allah ". Hamim ma ya fara kuka sosai. Watak'ila tausayi suka bawa wannan babban dansandan sai kawai ya bada umarnin a fito da shi. Ga mamakina sama da mintina goma da isowar Tijjani bai kalli inda Nasiba take zaune ba. Tunda ta gaishe shi ya amsa hankalinsa na kan su Hanif da suke kan cinyarsa bai sake bi ta kanta ba. Ni da yara kawai ya ke kulawa. Na mike na ce "Bari na baku waje tunda idona yasa ka kasa yin hirar". A zabure ya ce "Zan ci mutuncin ki little! Jiya da yau ban ji azabar da nake ji ba. Akwai abin da ake yi mini wanda zalunci ne da k'eta. Alfarmar Annabi kuma Allah zai kawo mini k'arshen al'amarin tunda kwana nake ina fad'awa Ubangijin al'arshi ya warware mini wannan masifar. Ni ko wannan k'azafin da aka yi mini baya gigita ni, kamar yadda al'amarin ta yake gigita ni. Amma akwai Allah." Ba Nasiba ba, ni kaina sai da na ji babu dad'i ainun. Na yi tsuru tsuru na kasa ce wa komai. Domin na tabbatar k'arshen muzanci Tijjani ya yi shi. Amma na sake gasgata surkulle ake yi masa. Ban da haka jiya k'iri k'iri ya fad'a mini yau na kawo masa ita. Ko tunanin rikicin da zan yi masa bai yi ba, saboda an ringa an kidima shi a kanta. Na daure na rakito ta, amma bai ko kalli inda take ba, sai ya b'uge da cin mutunci. Jikina ya mutu domin nasan zata zargi na kwaso ta ne dan na saka mijina ya wulakanta ta a gabana. Tunda a hakan kafatalin gidan Marina sun tafi akan na gama da Bulkachuwa tsorona yake ji. Sai abin da na shimfi'da zai bi. Har fad'i suke idan bana son mutum to ko kallon arziki Tijjani baya masa saboda gudun zuciyata. Ta mike a kasalance ta ce "Bari na jira ku a mota Yabi". Murya babu amo na ce "To". Tana tafiya ya saki dogon tsaki mai karfi da na tabbatar zai je kunnuwanta. Na zuba masa ido ba tare da na iya ce wa komai ba. Da k'yar na ce "To da sun san zasu mayar da kai Bauchin me yasa suka kawo nan?" Ya kalle ni ya ce "Akasi aka samu. Sun tsayar da ni a farko ban tsaya ba. Shine suka harbi tayar motar ikon Allah ne yasa motar bata yi bari da ni ba". Zuciyata ta buga da tsananin gaske na ce "mene ne dalilin ka na k'in tsayawa Baban 2? Ta ya ya kana dan k'asa amma ka ce ba zaka girmama dokar k'asar ba? Ko dai kasan dama baka da gaskiya ne?" Nan da nan ya kidime ya ce "Wallahi Tallahi ina da gaskiya, bansan an saka mini wannan abin ba. Ban sani ba, ki yarda da ni Asiya!. Na saki karfaffan numfashi tare da ce wa "Rashin tsayawar ka ba k'aramin hujja zasu kafa da ita ba. Na yarda da kai". Ya nutsu ya ce "Idan har kin yarda da ni to kowa ma kada ya gasgata ni Asiya! Nasan mahaifuyata zata shaide ni, duk fitina ta bana harkar maye bare kuma a yanzu da na girma. Ba zan shiga safarar abin da nasan illah ce ga al'umma ba. Ina miki ranstuwa da girman Allah ban san mugun abu aka bani ba. Waya kawai aka mini akwai sakon kaya da zan karba a Dutsen tanshi, idan na kai Kano za'a karba a biya ni. Kinsan kuwa ina harkar sakonni(Delivery). Ban tab'a zaton za'a mini kutse a cikin sana'a ta ba. Ni yanzu babban tashin hankalina ke ce. Ban san hukuncin da za'a yanke mini ba little. Kinsan k'asar nan waka sani ne waya sanka." Idona taf da hawaye na ce "Nasan baka aika ta wannan BAK'AR TA'ADAR ba. Da ikon Allah ina tare da kai, komin tsanani". Ya murmusa ya ce "Alhamdulillah! Na samu amincin firgicin da nake ciki. Dan Allah Asiya kada ki canja, kada ki juya mini baya a cikin wannan halin canka cakare da nake ciki." Idonsa ya kad'a sosai ya kasa cigaba da magana alamun ya shiga rudani. Hanif ya ce "Baban 2 kada yi kuka zamu zauna mu taya ka zama. Ammo ta tafi ta barmu tare da kai". Hamim ya ce "No zamu je mu koyo yadda zamu kwace shi daga hannun yan sandan kawai". Na yi k'asa da kaina kawai ina hawaye domin tausayin da suka ba ni ba kad'an ba ne. Ban iya ce musu komai ba. Shine ya yi jarumtar sake rungume su tunda a akan cinyoyinsa suke. Murya na rawa ya ce "Baban 2 baya karya domin wanda ya yi karya ya zagi Allah, Wanda ya zagi Allah kuwa dan wuta ne. Dan haka am innocent, ban yi laifi ba. Sharri aka yi mini. Kowa ya yi sallah ya yi wa Baban 2 addu'ar ya zama free". Suka had'a baki wurin ce wa zamu yi sosai ". A sanyaye muka rabu domin gobe za'a dawo da shi BAUCHI dan shiga kotu. A hanya Nasiba ta sake rasa kuzarin ta, dama kuwa bata iya sake wa a gabana na dade da fahimtar a takure take da ni. Abin da Bulkachuwa ya yi mata kuwa ya sake sanyaya mata jiki. Ina hankalce da ita, ina ganin yadda take son yi mini magana amma ta kasa. Cikin kundubala ta ce "Yabi!. Na amsa da "Na'am" murya babu amo. Ta kalli twins da suke barci a jikina. Ta ce "Idan na ce miki bana son Yaya Bulkachuwa na yi karya domin na girma da son sa, ke ma kin sani. Idan na ce miki a yanzu dole aka mini a kan aurensa zaki yarda?" Ban ce komai ba. Illah ido da na zuba mata. Ta numfasa ta zarce da ce wa "Ni da kaina bani da yadda zan yi ne. Domin kuwa mutane da yawa suna haduwa da kalubalen a hadasu da iyaye karkatattu. Sai dai duk da hakan ba zamu ki sonsu ko janye wa daga gare su ba. Na sani tun farko soyayyar sa gare ni ba mai yawa ba ce, bare yanzu da yake auren ki. Dan Allah ki yi hakuri kada ki datse mu'amala da ni Yabi. Al'amarin zumuncin yau ya shiga rudani mai yawa, amma idan aka yi hak'uri aka danne, aka yi sassauci sai a samu masalaha a duniya, a kuma samu rabauta a duniya. Zan yi iyakar kokarina na fita a harkar mijinki, na yarda Yaya Bulkachuwa ba mijina ba ne, ba kuma zai zama ba. Kada ki ce maganganun da ya yi cin fuska ya yi mini, zahirin gaskiya ya amayar". Na rik'e hannunta murya na rawa na ce "Ban kullece ki ba. Amma idan na ce ban ji ciwon abin da ya faru ba na yi karya. Har abada ba zan iya auren mijin ki ba Nasiba. Amma na hak'ura na barwa Allah ya yi mini zabi akan lamarinku. Tunda ai ba haramun ba ne. Shi yasa na hak'ura na barwa Allah komai". Dukkanmu kowa zuciya ta narke, muka dinga kuka. Ubaid da yake gaban motar ya yi tsaki ya ce "Sai ku yi ai. Amma ai mu kam mun kudire matukar ya aure ta sai ya sako mana ke ko da kuwa a gaban alkali ne". Na daskare da maganar sa. Na tuna na ba shi watanni shida. Gabadaya ma shekarunsa ashirin da uku ne. Amma ya yi magana kamar wani babban wanmu. Sai kuma hawayena ya sake zuba a dalilin yadda maganar auren Nasiba da Bulkachuwa ta zama silar samar da soyayya a tsakanin ahalin Baban Marina. Yan ubancin da manyanmu suke gwada mana ya yi matukar zangwanye wa. Na yarda mafi yawan kalubale ya kan zo da wata nasarar komin kankatarta sai dai idan ba a kula ba, ko an bari hankali ya kwace an yi fishin da ya shallake hankali. ✍️ *Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.* *Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐, ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To albishirinki yar uwa!* *UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1 Annur food Delicious* *Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.* *Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa* *HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna* *Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya* *08039183880* Washagari duku duku Baba Maryo ta zo. Domin na je gaida Dada na juyo muryarta tana ce wa "Ai ko baki bijire mini ba gabad'aya ba zai aure ki ba, wane shi. Ashe dama arzikin da ake ga ni a tare da shi kazami ne? To ba zata sabu ba. Aure kam tabbas ya fasu fas. Dama ai ba so kike ba, tunda kin ringa kin tsorata da iblishiyar mata tasa. To ta je ta samu sai ta tabbata a matar d'an safarar kwaya ita kad'ai. Mutane babu Allah a ransu. Ka dinga neman arziki yaki haram yaki halal. Dama so na yi na nuna wa uwarta da ita Yaya Hauwa iyakarsu. To tunda bai shiryu ba, huta toro an bar musu shi. Watak'ila ma daurin rai da rai za'a yi masa. Ai da a sau'udiyya aka kama shi fille wa d'an banza mai yiwa iyayensa kallon raini za'a yi". A sanyaye Dada ta ce "Ai kuwa mai sunan manya ya yi hankali da girmamawa yake gaida kowa kamar ba shi ba. Kawai dai yana nuna son kai ne, ya fi nan nan da k'ofar Alhaji. To wannan kuma dariyar matarsa yake so, ya za'a yi tunda ya jarabtu akan ta.!" Baba Maryo ta ce "Ban da ni din, ni ce ai ko gaishe ni ba zai yi ba, ya kullace ni ainun. Tunda ake fad'in labarin wadatar da yake ciki, ashana bata tab'a had'a mu ba. Kai ya taka ya je gidana bai san wannan ba. Idan ya gan ni tamkar zai doke ni. Amma yanzu da yake ba shi da kunya har zarya yake yi mini. To na fasa ba shi Nasibar. Ba zai yiwu ba, ya je dai ya k'arata da afiruwar matarsa mai izgili. Kai ahalin Tijjani da Yabi za'a yi majununai, biyu ta had'u y'aya'n iska marasa albarka". Na sake jin cikin rauni Dada ta ce "Yanzu fa sun yi hankali suna girmama kowa. Yabi da kanta jiya ta zo har nan ta tafi da Nasiba wajen mai sunan manya. Kin san idan Yabin da ce ba za'a yi hakan da ita ba". Ta saki tsaki ta ce "Yo tunda ya rikice mata ai dole ta kai ta. Amma daga yau zan yanke komai." Dada ta kame bakin ta. Ita kuwa ta ci gaba da sakin maganganu masu nuni da dama ba Tijjanin take so ya zama surikinta ba. Wadatar da ake kallon ya samu ne ake son su lasa. A yanzu da ya hadu da ibtila'i kuma an janye saboda dama ba da zuciya d'aya aka yi abin da aka yi ba. Na shiga daga bakin kofa na gaida Dada, duk da tana ce wa "iso mana, ina tagwaye ko basu farka ba?" "Eh suna barci Dada". Na gaida Baba Maryo a gajarce. Ta amsa fuska babu walwala. Har na juya sai ce wa ta yi "Yabi ashe haka ya faru da Tijjani?" Na ce "Eh! Sai ji na yi ta ce "To wadannan kadarorin da suke yatsun ki da kunnawan ki sai ki hanzarta kad'ar da su dan ki dauka masa lauya domin dai a gindinki da na iyayen ki ya k'are. Gyatumar sa ma yar amshin shata aka mayar da ita. Watak'ila hakkin ta ne ya sanya yake gani a k'waryarsa. Na juya da nufin bata amsa sai na tuna kanwar mahaifina ce. Ba zai yiwu na yi fad'a da ita a yanzu da hankali ya ratsa ni ba. Nasan kuma dole ni ce a ciki tunda shi da kansa Baban Marina zai ce ai kanwarsa ce ta shiga rigarsa mana. Dan haka sai na hadiye na ce "To Baba Maryo zan yi hakan". Ta tunbatsa domin ta washi mu fad'i sunan ta. *** *BAUCHI* Kotun ta cika makil domin sharioi za'a yi masu daukar hankali. A kuma wannan ranar za'a yanke wa Tijjani hukunci. Da wuri muka iso. Da ni, da Yaya Salisu da Baban Marina da kuma Yaya Salamatu. Sai ko Yaya Ammar da yake Bauchi. Karfe shadaya aka fara shari'arsa. Babu wata hujja da zata wanke Tijjani. Domin lambar da ya ce an k'ira shi da ita kwata kwata bata shiga. Sannan an tambaye shi me yasa da aka ba shi kaya bai bude ya duba ba? Tunda ya dauki delivery a matsayin sana'a. Me yasa ba ya nazarin kauce wa dukkan wata matsala da zata taso. Wajibi ne idan zaka karbi sako, ka duba ka ga mene ne a ciki tunda idan aka kama ka ai kai ne a ciki. Sannan me yasa bai binciki ainihin inda mutumin yake ba?" Lauyan da k'aninsa Aliyu ya daukar masa, ya kasa inkarin hujjojin lauyoyin gwamnati tunda tabbas Tijjani bai yi bincike ba ya karbi kaya. Bai kuma bude ya duba ba. An ba shi abu a d'aure cikin buhu kawai ya danna a mota. Sannan bai san mutum ba. Kawai ance idan ya je Kano za'a karba a biya shi. Sannan lauyan gwamnati ya k'ara kafa hujja da ce wa "saboda Tijjani yasan ba shi da gaskiya ya dauko wiwi da koken mai nauyin tam goma shi yasa ya ki tsayawa da jami'an tsaro suka tsayar da shi wanda hakan rashin da'a ne da raina jami'an tsaron da k'asa ta wakilta su duba shige da ficen al'umma." Na zuba wa Tijjani ido da yana tsaye jikin kantar da ake tsayar da wadanda ake tuhuma. Ya zube aiun, ya sake yin duhu. Zuciyata ta karaya, na hangi rashin sassauci a shari'ar. Ta zo fiye da yadda muka tsammace ta. Domin maganarsa d'aya ce ba shi kayan aka yi, bai san kuma san mutanan ba. Lambar wayar da ya gabatar a matsayin wacce aka kira shi da ita bata yi. Jikin kowa ya yi sanyi. Bayan dogon rubutu da alkalin ya yi. Ya yi gyaran murya ya ce "Duba da hujjojin da lauyan gwamnati da kuna jami'an tsaro suka gabatar kotu ta yanke wa Tijjani hukuncin shekaru biyar a gidan yari babu tara. Bisa kama shi da safarar kwaya wanda hakan ya saba kashi na goma sha takwas b cikin baka. Bayan haka kotu ta sake d'aure shi shekara d'aya bisa cin zarafim jami'an tsaro da ya yi ta hanyar yi musu gaddama. Har ila yau kotu ta daure Tijjani na watanni uku ko tarar dubu ashirin saboda rashin kiyaye kaidojin kasuwanci. Ba zai yiwu mutum yana hulda da jama'a ba amma babu taka tsantsan da sanin me mutum ya dauko ko mai zai kai. Yana cikin dab'iun d'an kasa na gari ya zama yana duba komai yana kuma kiyaye dukkan doka." Ya rattaba hannu akan takardun tare da buga stamfi. Gabadaya ahalinmu hankaliinmu ya yi mummunan tashi. Ni kam kuka na ke yi mai gunza. An daure shi shekaru bakwai babu tara? Wacce irin bak'ar kaddara ce wannan? A harabar kotun muka tsaya da shi tunda Yaya Ammar na cikin ma'aikatam gidan yarin. Na kalle shi sai kawai na fashe da kuka a dalilin raunin da na ga ni ya bayyana masa a dukkan jikinsa da zuciyarsa. Muka zubawa juna ido ba tare da mun tuna daruruwan mutanen da suke wajen ba . A sanyaye ya ce "Asiya shekaru bakwai da yawa. Tashin hankalina bai wuce ke ba. Ba zaki iya ba. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun " Sai kawai hawaye ya ya k'wace masa shabe shabe". Na rik'e hannunsa na ce "Ko shekaru sha bakwai ne zan jira ka Baban 2. Idan har rayuwarmu ta kai zaka fito ka tarar da ni a dakin ka. Zan kiyaye maka amana, zan yi aiki tuk'uru na kular maka da y'aya'n ka. Jarumtar nan da ka ke fad'in na dinga yi, zan nin ka ta daga yau". Baban Marina ya dauke idonsa amma bai iya tsayar da hawayensa ba. Tijjani ya matsa kusa da shi ya ce "Wallahi ban aikata laifin da aka jingina mini ba, rami aka haka mini na fad'a. Ka taimake ni, ba zullimin hukuncin ne ya zautar da ni ba. Fargabar yadda zan iya rasa Asiya ne. Shekaru hudu ne gejin da shari'a ta dibawa mace akan dakon mijinta. Ni kuwa shekaru bakwai aka zarge ni". Hawaye ya cigaba da tsere babu kakkautawa. Baba ya kasa ce wa komai. Su Yaya Salisu kowa hawaye. Cikin k'arfin zuciya na ce "Idan ni ce matsalar ka, to ka kaddara baka da damuwa. Zan jira ka. Ba ka ce ko ka mutu na zama jaruma dan na tallafi y'aya'n ka ba? Zan kiyaye mutuncin ka, zan kuma maye wa y'aya'n ka gurbin ka har zuwa lokacin da zaka dawo ka cigaba da kulawa da mu gabadaya. Ka sa a ranka ban yi kokwanto akan ka ba Tijjani. Na gasgata ka, na yarda da kai." Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Allah ya k'ara lafiya Baba. A sanya ni cikin addu'a. Ni kuma ya mini murmushi kad'an ya ce "Na gode". Daga haka suka tafi da shi. Fir na k'i yarda na koma Toro. Domin idan ina gida tashin hankalina yafi yawa a dalilin ina ganin tamkar Tijjani ya rasu ko mun rabu. Bayan haka karatun yara ya dakata. Baban Marina bai matsa mini ba, jikinsa ya yi laushi ya kamu da mugun tausayinmu. Yaya Indo ta zauna da ni na kwanaki biyu. Komai ita take yi, ta ji da hidimar yara ta kuma yi girki da kwantar mini da hankali. Tun sanadin auren Nasiba muka hade da su. Gabadaya yan k'ofarmu muka dinke, muka dunkule, duk wani tsegmi ya yi s'auki tunda dama manyan namu ne karkatattu. Sai da Babah ta Bulkachuwa ta zo sannan ta tafi. Dada ce ta zartar da umarnin Babah ta zo ta zauna da ni. Cikin alhinin rashin Tijjani da kuma tausayi da kyautatawa muke zaune. Nasirun ta wanda shi Ihisan take bi a kai a kai yake zuwa mana domin dalibi ne a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da take cikjn Bauchi. *Toro*. Anas da yake bin Yabi. Yana bandakin k'ofar Dada yana simince shi a dalilin wanda aka yi mata da ta rubza ya farfashe, ba'a yi aikin aminci ba. Gabadaya Baba Maryo ta shafa'a shaf yana k'ofar, kuma kusa da kicin din da take zaune ne. Ta hau tonon murhun tana ce wa "Allah suturi buk'i da auren mazinaci kuma mai dilar k'waya. Wane mutum na had'a iri da shi cikin sanina?" Kalaman ta suka ja hankalinsa ya ajiye abin aikin ya leko tunda bayin ba me k'yaure ne ba. Ganin da ya yi tana tono ya sake jan hankalinsa k'warai da gaske, ya matso sosai. Yana kallonta k'yar. Ya jima yana zargin Yaya Bulkachuwa ba a bar shi haka siddan akan al'amarin Nasiba ba. Ashe kuwa hakane. Ya sandare cikin tu'aajjibi a lokacin da ya ga ta fito da laya a k'asan murhun ta kyasta mata ashana ta k'one. Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Allah na gode da baka k'addara mini ganin auren ta da mai arzikin bogi ba. Ban da ma dai batan basira me za'a yi ne da wanda aka yiwa bulalar zina a bainar nasi? Lallai na yi mantuwa mai yawa. To na tone ramin da na hak'a tun ban rufta ba. Dama Yabi ce ta dace da shi a wannan duniyar." Daidai lokacin Anas ya kasa jure wa ya yi gyaran murya. Ta waiwaya a ankare. Idanuwansu suka hadu, ta yi wura wura. Ta rasa inda zata tsoma ranta. Shi kuwa sai ya ce "A dinga yin sara ana duban bakin gatari Baba! Da Yaya Bulkachuwa, da Adda Yabi, da kuma Adda Nasiba kamata ya yi ki dauke su abu guda. Ba wai ki nemi rugurguza zaman lafiyarsu dan bukatar kan ki ba. Kin cutar da su duka. Ita kanta Adda Nasibar ai dan ba yadda zata yi ne, akan dole ta bi ra'ayin ki domin tana da darhamin imani a zuciyarta. Ya fara hawaye ya ce "Duk duniya ki rasa wanda zaki yiwa kulunboto ya so diyar ki sai mijin d'iyar Baban Marina! Kaico da Bakar hassada, kaico da mutanan da suke da son zuciya, wacce irin BAK'AR TA'ADA ce haka? Asiri kika yi wa Yaya Bulkachuwa! Innalillahi wa inna ilaihir rajiun " Sai kawai ya fito daga bayin a gigice ya zunduma ihu da dukkan muryarsa tamkar mace ba jarumin namiji ba. Domin ya riga ya gigita da abin da ya ga ni k'warai da gaske. Ta hau tafa hannu tana ce wa "Ashe a maza ma akwai makirai majununai? Zaka ga tsiya da tuggu kuwa! Zan nuna maka uban ka ma ya wuce ya tozarta ni, ya kwaye mini asirina. Zaka gasgata makircin mace aziman ne yau din nan". Sai kawai ta takarkare ta zunduma ihu mai tsananin gaske. Da yake Dada barci take, a firgice ta farka tana fad'in "Waye ya mutu Maryamu? Jin shiru sai kukan Anas da na autarta ya cika mata kunnawan, ita ma sai kawai ta fashe da kukan daga dakinta. Tana fad'in "Allah kasa basu harbe mini "Mai sunan manya ba. Lah ha ilah ha ilallahu! Mintina kalilan jama'a suka taru a k'ofar ta da Dada. Baban Kasuwa da na Tsakiya suna gidan yayin da Baban Marina baya nan. Dan haka a sukwane suka bu sahun ahalin gidan da suke ta shigowa a gigice. Kowa sai tambayar ba'asin kukansu yake yi. Anas sai hadiyar zuciya yake yi ya kasa bude baki ya yi magana. Jikin kowa ya yi sanyi tare da sake shiga rudani mai yawa. Domin kowa yasan Anas ba mai hayaniya ba ne sannan yaro ne mai juriya da hak'uri na gaske. Sun tabbatar ba zai yi kuka irin haka ba tare da ya ga wata masifar, domin a lokacin da yake yaro ma ba mai fitina ko koke koken banza ba ne, bare kuma yanzu da yake da shekara ashirin da biyu, ya zama saurayi na sosai. Baban Kasuwa ya ce "Maryo mene ne haka? Me ya faru ya tambaya zuciyarsa na rawa irin ta zullimi. Ta kuwa karkace ta kara k'arfin kukanta ta ce "Ban san yana makewayi ba. Sai na afka bayin ba tare da na tambaya ko akwai mutum a ciki ba. Babu zato na ga Anas ya gogawa al'aurarsa sabulu yana wasa da ita! Na zauce na fito a sukwane ina hirji. Kunya tasa ya kasa fitowa. Sai yanzu ya yi jihadi ya fito, wai dan na yi masa matashiya akan haramcin hakan shine ya fasa mini ihu yana neman k'ulla mini sharri tunda dama dukkansu y'aya'n Alhaji sun tsananta mini akan Tijjani, mussaman y'aya'n Asma'u da ko gaisuwa sun yanke yi mini dan su nuna mini Yabi ta fini a wajensu. Amma ni ban ga laifinsu ba. Ubansu ne ya yarda ta ni irin haka." Sai ta zarce da sabo n kuka. Su Baban Kasuwa suka d'auki salati tare da ce wa "Muminin kare ne ashe kai. Kullum da kai ake kwatance a gidan nan da ma unguwar baki daya saboda nutsuwar ka da hamlnkalin ka ashe BAK'AR TA'ADAR da kake tafi ta yaranmu da ake yi musu kallon fitinannu ne! Duk yadda aka yi kai ne ka yiwa y'ar wajen Malam Kabiru fyade satin da ya wuce. Yarinya karama da ko magana bata iya ba, aka kasa gano mugun da ya aikata mata aika aikar ashe kai ne". Kuka ya tsayawa Anas cak. Ya Kalli Baba Maryo ya kalli Baban Kasuwa. Yana ta kissima sune k'ananu a cikin iyayensu amma sune suke kan gaba wajen ruguza gidan Marina. Bai gama nazarinsu ba sai ya jiyo Baban Tsakiya ya ce "A a tunda ba mu ga ya haike mata ba, bai kamata mu jingina masa ba, shaidar zina babban al'amari ne. Sannan idan aka ji maganar a bakinmu ai muma mun kunyata domin baza mu ce ba daga gidan nan ya fito ba. Kawai shata masa layi zamu yi da y'aya'nmu kada ya dinga b'ata manaa su bamu ankare ba tunda ya jefa kansa a wannan BAK'AR TA'ADAR ta istimina'i". Yara da manya kowa yabi Anas da kallon tsana da tuhuma. Duk Mama da kanta ta ce "Anas ba lallatacce ba ne. Na tabbatar bai aikata hakan ba Maryo". Sai lokacin ya samu kuzarin Budeibaki ya ce "A a Mama kada ki ce mata komai. Na riga na kai alkalanci gaban Ubangiji. Idan ya tabbata na yi abin d at fada to ku nema mini gafarar Allah. Na kuma yafe mata tozarta ni da ta yi, tunda ai ba hakan ya kamata ta yi mini ba. Idan kuwa ban aikata ba ta mini hakan to da ikon Allah ba zaki mutu da ido ba Baba Maryo ". Ta zunduma ihu tana d'ura masa ashariya. Bai rufe baki ba ya ce "Ganinta na yi ta tono mugun k'ullin da ta yiwa Yaya Bulkachuwa akan ya rikice akan Adda Nasiba. Tana fad'in ta fasa auren tunda dan k'waya ne kuma mazinaci. Ganin na ganta ta k'ona layar shine ta mini hakan. Ba zan zage ki ba, ko a lahira wani kan ci arzikin wani. Ban ci arzikin ubana a wajenki ba. Nima ba zaki ci nasa ba. Kin ci arzikin kasancewar ki uwar Yaya Ammar. Ba dan shi ba, ina rantse miki da girman Ubangiji sai na miki dukan da ko Dada sai ta yi gaske da ta shaida ki. Amma babu komai na barwa Allah komai." Ya mik'e yana tangadi yayin da kowa ya yi tsit. Ya kalli Baban Kasuwa ya ce "D'a na kowa ne Baba". Baban Kasuwa ya ce "Ni kad'ai zaka fad'awa hakan, shima Baban Tsakiya ai ya tofa nasa" Anas ya ce "Ko ya tofa dai bai mini k'azafi ba, gaskiyar fahimtarsa ya fad'a. Dada tana bakin k'ofarta tana kurshegen kuka tana fad'in "Dambarwa ta tsananta a cikin ahalina. Ubangiji na ci albarkacin sallah da salati, ka sassauta, yafe mini, ka shirya mini zuria gabadaya". Har aka gama wannan cecekucen Baban Marina da Gwaggo basu tofa ba. Mama ce ta shiga lamarin ta yi kane kane tunda yanzu yar tsama ce mai tsananin gaske a tsakaninta da Maryo. Baya ga hakan kowa yasan Anas ba zai yi abin da ta fad'a ba. An kuma gasgata shi,asirin da yaga ta tone.ne ya ya sanya ta yi wannan dibar albarkar. Nasiba kuka ba wanda bata yi shi ba. Ammar da yake BAUCHI da ya ji labarin bai dauke shi da muhimmanci ba. Murnar yadda ta kunce k'ullin da ta yi yake yi. Domin yana matukar tausayin yadda Bulkachuwa yake damunsa ya kawo masa Nasiba ya ganta. Yanzu kuwa tunda an warware zai daina, zai samu nutsuwa, tunda wani lokacin har susuce wa yake zufa na karyo masa. Da labari ya zo mana Babah ta ce mini "Tare ta hada ta mana ai, ni tun kwanaki na kubuta. Nawa a kasan randa aka yi mini ta yadda zan zama mai sanyi akan sha'anin. Sannan aka danne mini zuciyata. Shi kuwa a k'asan murhun. Matukar aka hura wuta a murhun ba shi ba sukuni idan bai ganta ba. Kai wacce irin BAK'AR TA'ADA ce haka? Ta fara hawaye. Na taya ta muka yi kukanmu sosai domin ta ba ni tausayi. Da ciwo kwarai ace d'an-uwanka ne zai musguna maka irin haka. A raina kuwa na yafe dukkan musgunawar da Tijjani ya yi mini akan Nasiba. Na sake gasgata ba yin kansa ba ne. Na kuma sake kudire a raina matukar ba Babah ba, wani mahaluki ba zai ji halin da nake ciki da shi ba. Zan jira shi har ya kammala WA'ADIN da zai yi, zan kuma yi gwagwarmaya har komai ya daidaita mana. Karshe na yi jarumtar ce wa "Mu yi hak'uri Babah ai ba kuka zamu yi ba. Alhamdulillah zamu tsananta fad'a, mu kuma sake dage wa da addu'a." Murya babu amo ta ce "Allh ya yi miki albarka, ya kara miki hak'uri, da ikon Allah Ubangiji zai miki sakamakklon alheri na gode sosai" Nafi wata biyu ban warware na fara sabgogina ba. Duk karshen wata zamu je mu gano shi. Aliyu kuwa daidai gwargwado idan karshen wata ya zo zai siyo mana kayan abinci, ya kawo da kansa ya kuma damkawa Babah kudin da zamu rik'e. Ya tisa yara a gaba su fita, ya yo musu siyayya sai ya dawo da su. Shirin aurensa ake yi wannan al'amarin ne ya dakatar da komai. Haka su Yaya Salisu akai akai suke mana aika. Yaya Ammar kuwa duk sadda muka je prison sai ya bawa Yara kudi masu auki, kuma babu jami'in da yake tsaya mana a kai saboda Yaya Ammar. Ba laifi kuma yana leko mu jifa, jifa shi da iyalinsa. Yaya J ma duk watan duniya yana aikowa yara kudi amma bata hannuna ba, ta hannun Yaya Rabiu. Shi kuwa yana turo mini ta asusuna. Idan na yi masa text din godiya sai ya ce ba sai an ji ba. Bamu da wata matsala gagaruma. Amma da tafiya ta fara nisa sai na fahimci dukkan masu tallafa mini kama daga kan mahaifana, Aliyu kanin Tijjani, su Yaya Salisu da J hadi da tsirarrarun dangi masu bamu sabulai kowa yana da nauyi a kansa baza su tabbata suna mana hidima ba . Mussaman da kullum rayuwar take sake tsefe wa. Ina kwnace ni kad'ai a daki yara sun tafi makaranta yayin da Baba take dakinta tana lazimi. Tunani nake yi tare da nazarin kaalaman da Tijjani ya yi ta yi mini a lokacin da nake bacin ran shiga makaranta. Ba abin da yafi tsaya mini a rai fiye da yadda yake ta nanata ni kad'ai ce yake da tabbacin bazan gaza da hidimar y'aya'nsa ba. A lissafi watanninsa tara a tsare. Har lokacin kuma bana aikin komai, ban dogara da komai ba sai wanda dangi suke mana. Tunda na riga na gajiya na kasa yin kitso bare lalle. Na numfasa a fili na furta "Ya kamata na yi hobbasa na taimaki kaina. Na hakurkurtar da zuciyata na fita na siyo kayan kunshi. Na fara posting na fara lalle. Ba'a dauki lokaci ba mutane suka fara dawo mini. Da yake bamu da wasu matsalar sosia, sai na ninka aiken da nake yiwa Babanmu. Tunda aka rufe Tijjani ahalin Baban Marina suka gane Tijjani ke hidimar k'ofar da kaso bakwai cikin goma. Wanda ko ni ban gane hakan ba sai yanzu. Dan haka na dage nake tallafawa Yaya Salisu da Yaya Rabiu rik'e gidan. Gefe ina ajiye dan ajiye wani abu a banki, dan tsaron lalurar da zata zo mini b'akatatan. Na shafe tunanin siyan gidan da nake burin yi. Domin tunda muka yi fad'an da Baban 2 ya ce mini gidansa ne ba nawa ba nake tunanin ya kamata na siyi gidan kaina. Idan na had'a zobuna na da dankunne na na sani ciko zan yi tunda manya ne sosai kowa yasan yadda gold ya tsefe. Zan siya zuwa gaba idan na warware matsalar Tijjani. Sannu a hankali nake samun k'arfin zuciyar rungumar kaddarar da afko mana bakatatan. Mussaman da Baban 2 ya kwantar da hankalinsa ya yi imani da kaddarar da ta same shi. *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* 95&96. *HAJIYA HANNE ADO ABDULLAHI?* *MARUBUCIYAR WANKA DA GARI DA KUMA WACE CE UWA?* *KUN TUNA IRIN BAJINTAR TA AKAN RUBUTUN ADABI DA TARBIYA?* *TO ITA MA TAKANAS NA SAMO MUKU LITTAFANTA DOMIN KUN SANI TA YI RUBUTU MASU MA'ANA*. *LITTAFAN DA YAWA, AMMA AKWAI DISCOUNT DOMIN SO NAKE KU YI TA SIYAWA Y'AYA'NKU DA KANNENKU LITTAFAI MASU DARASI DA MA'ANA*. *INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA* *ZAKU SAME SU SOFT COPIES, A HANNUNA* *SANNAN SABO DAL NA KAN HANYA* *HAKA NAN AKWAI WASU DAGA CIKIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA HAFSAT C SODANGI, SUMA SOFT COPIES KAZALIKA ITAMA SABON LITTAFIN TA MA KAN HANYA* *BA DA JIMAWA BA ZAN ZO MUKU DA SU*. *08032773332* *INA MATUKAR GODIYA BISA ADDU'ARKU DA KUMA KAUNARKU GA RUBUTUNA* *WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE TARE DA GODIYA GA DUKKAN WADANDA SUKA SAKA KUDINSU SUKA SIYI WANNAN LABARIN DON JADDADA MINI SOYAYYA DA KUMA KARFAFA GUIWA* *NA GODE, NA GODE*. Auren Aliyu ya samu tasgado. Ba akan komai ba sai akan an kai suka gidansu amaryar cewar d'an-uwansa dan safarar kwaya me gwamnati ta rufe shi Shima ana kyautara zaton yana da BAK'AR TA'ADA. Muna ji muna ga ni aka hana Yaya Aliyu aure ba a akan laifinsa ba. Dama Kuma Babaiba son inda ya dauko auren ba, yar babban attajirice. A raina na Jin ciwon yadda mutanan yau suke yiwa mutane hukunci da laifin yan'uwansu ko na dangunsu alhalin Allah da kansa baya bawa da laifin mahaifansa bare kuma laifin d'an-uwansa. A zuciyata tamkar na ce masa ya nemi Iklima da a yanzu take kwalejin koyon aikin jinya da ke Azare, tana shekarar karshe. A kansu a aka zurfafa karatu ba tare da aure ba a gidanmu. Sun kammala sakandire babu samarin aure. Hakan ya sanya Jabir samowa kannensa gurbin karatu a inda yake koyarwa. Gabadaya mun tafi a cewa iyayensa suka hana ya had'a da ita. Hakan da muka gani ya sanya ni da su Yaya Salisu muka yi kundubalar saka Iklima a Health Technology Azare. A tsaye take cak, doguwa mai cukar halitta kuma fara tas. Na tabbatar ba zai tankwabe ta ba, amma ina jin tsoron na furta. Dan haka sai na tsiri gayyato ta hutu a karshen watan da na tabbatar yana yi mana jele. Akai akai suke haduwa kuwa. Su yi ta cakar juna tunda shi ma mai zolaya ne. Ni kuwa na dinga fad'in "um um fa Yaya Aliyu kada fa reshe ya juye da mujiya." Wani lokacin ya yi dariya ya waske, wani lokacin kuma ya ce "Ba Wani reshe da zai juye, yarinya kankanuwa, raini dai nake son jawo masa. Baba kuwa idan ta ji ya ce haka sai ta ce "Saboda ka kallafawa ranka son ka auri sa'aninka. Ban da haka ai itacw daidai da kai ". A duk sadda Babah ta fad'i hakan dad'i ne yake matukar kama ni. Ina ganin nasara a kudirina. Matukar yana gidan ita zan saka ta yi masa girki, ta dafa masa zobo. Wani lokacin ya yi godiya ya kwashi girki. Wani lokacin ya ce "Tunda na zama matar yayansa na ture girme mini da ya yi, nake mu'amalantarsa a matsayin k'anina. Ban da haka me yake hana ni na yi masa hidima da kaina sai na saka yarinya ta yi masa." Na yi dariya na ce "Yaya Aliyu ko a lahira wani na cin arzkin wani ai" Ba'a d'auki lokaci mai yawa ba ya fara fad'awa tarkonmu. Domin idan ya zo bai ganta ba, ya dinga tambayar me ya hana ta zuwa. Ko ba hutu suke yi ba, da sauran tambayoyi. Da na fahimci hakan kuwa sai na dakatar da zuwan nata. Domin so nake ya taka ya neme ta a inda take ba wai sai ya ganta dan ya zo ba. Ilai kuwa wanne tudu wanne gangare ya silala yake zuwa daga haka har suka had'a kansu. Tunda aka garkame Tijjani ban yi farin ciki har zuciyata ba sai akan wannan al'amarin. Domin dai Na tabbatar Aliyu mutumin kirki ne. Sannan Babah uwace ta gari bayan haka Ikilima zata auri mai rufin asiri. Zamu sake zargowa k'ofarmu wani hasken. Bugu da kari y'aya'nmu zasu kasance cikinsu guda. Tunda shi da Tijjani daya ne, haka ni da ita. Da maganar ta fasu a gidan Marina a lokacin da iyayensa suka je nema amsa aurenta. Ba abin da ba'a ce ba. Bak'in ciki muraran har ce wa aka yi ai k'aramin likita ne, wasu kuwa cewa suka yi ba ma likita ba ne. Malamin tsafta ne. Shi dai Baban Marina ya ce ya basu. Mu kuma dukkanin y'aya'n sa muka goyi bayan al'amarin. Aka saka aure idan ta kammala makaratan da wata daya, watanni biyar masu zuwa. ** Alhaji Auta yana zaune al'amarin duniya ya sake damalmale masa. Gabadaya kasuwa ta juya masa baya fiye da bara. Fatan da yake yi akan kamfani ya kyamaci filin Tijjani saboda an kama shi da laifi bai ci ba. Har asiri yake nema akan su saki filin amma shiru. Su kuwa kamfani sunce riba suke nema. A wajen suke samun gamsuwa, babu ruwansu da laifin Tijjani. Idna lokacin da zasu biya ya yi, zasu tuntubi iyalinsa. Ya rasa inda zai saka ransa. Jiya aoa kama babban dansa a cikin sahun y'an kidnaffing. Dazu kuma k'aramin dansa aka kama shi da yana yuwa yarinya yar shekaru uku lalata a cikin gidansa. Gabadaya kwanciyar hankali da nutsuwa ta yi masa tutsu. Ya rame, ya zama tamkar mai ciwon sida, tsufa ya keto masa na ban mamaki. Yana kishingide amma damuwa ta yi masa k'awanya. Wai shine naira dubu take yi masa wahalar rik'e wa?. Zullimi ya kama shi, idan akwai Bakar Taadar da ya yi ta dame shi bata wuce had'a kai da aka yi da shi wajen yiwa dan amininsa kazafin da yake kulle tsawon shekara guda ba. Ya yi shiru yana tuna irin yadda Tijjani yake zuwa yana gaishe shi cikin girmamawa. Akai akai yake yi masa alheri a matsayinsa na aminin ubansa kuma ubangidansa a kasuwa. Amma shaid'an da hassada suka saka ya jagoranci zaluncin da aka yi masa. Kuka shabe shabe da hawaye. Ya rasa ta inda zai warware wannan k'ullin da suka yi. Kan dole ya kira diaya abokin sharrin nasa, wanda yaro ne a kansa dan ba zai girme wa Bulkachuwa ba. Ya dauka murya a shak'e ya ce "Alhaji kana mini waya da ta wuce kaidar hankali gaskiyar magana na ke fad'a maka. Nima nema nake idan zan samu, ka fitine ni da bani bani gaskiya". Da zullimi ya ce "Ba rokon zan yi ba Haladu! Maganar Tijjani zan yi maka. Gaskiya na yi abin da ya sha mini kai. A harzuke ya ce "To ni me zan yi maka? Ina ce Kai ka kawo shawarar, Kai ka kitsa yadda za'a yi? Ni kawai na karba a hannunsa tare da bawa haro ya ba shi. Hatta lambar wayar da aka kira shi, kai ka siya tun kuma a ranar ka taune shi. Kai ka yiwa Yan sandar hanya shunensa tare da bada lambar motarsa. Kaine zaka yi dakon zunubin ka. Idan ka yi kuskuren saka ni a ciki kuwa Wallahi sai na bata maka suna a idon duniya. Sannan sai na lahanta ka." Kuka wiwi ta k'wace wa Alhaji Auta tamkar mace. Ta ya ya zai kubutar da Tijjani? *** Yini na yi ina yiwa wata hamshakiyar Hajiya kunshi ita da mukarrabanta. Da zata tafi ta ajiye mini kudi a envelope. Ga mamakina da na bude dubu hamsin na gani a ciki. Duk da sunzo da yawa sosai. Amma tabbas kudina bai kai haka ba. Rub'anya mini ta yi. Ban sani ba ko dan na yi jarumtar yi musu jollof din taliya mai dad'i ne. Na kuma baibaye su da pure water mai sayi tunda Ina siyarwa. Na lura ta ji dad'in yadda na yi musu, sannan ta yaba da kunshin da na yarfawa kakkaurar k'afarta fara tas. Cikin hira nake fad'a mata na iya kwalliya ma sai dai nafi bada k'arfi a lalle da kitso. Kwanaki biyu da tafiyar ta sai ga waya ta k'ira ni akan wani satin zan je gidan gwamnati na yiwa mai dakin gwamna kunshi zata je bikin d'iyar gwamnan Jigawa. Jikina ya sab'e da rawa. Ni Yabi zan je government house a sanadin sana'a ta? A fili na ce "Alhamdulillah! Ubangiji ka bani damar da zan yi amafani da ita na fito da Baban 2. Allah ka yi alkawarin taimakon wanda aka zalunce shi. Ubangiji ka shiga lamarin Tijjani." Na zauna kusa da Babah ina fad'a mata. Ta yi farinciki sosai. Na ce "Idan mun je ganinsa zan fad'a masa, idan bai amince ba zan hak'ura, tunda nasan baya son na dinga zuwa gidajen mutane". Ta zuba mini ido ta ce "Allah ya yi miki albarka, Ubangiji ya kawo mana karshen ibtilain nan. Allah ya dawo da mijin ki, zaman zai yi miki yawa babu miji a tare da ke." Sai kawai ta fashe da kuka sosai. Da rawar murya nake bata hak'uri. Ina ce wa "Zan iya Babah! Zan jira shi, da ikon Allah zai dawo a kusa ma". ** Muna ta shirin tafiya dubo Baban 2 a dalilin a irin wannan ranar ta asabar din k'arshen ko wanne wata muke zuwa duba shi, tare da kai masa kayan shopping tamkar na dan makarantar kwana. Ni nake had'a masa wannan kayan. Kudin lallena da kitso suna tafiya ne a hidimarsa da ta gidanmu domin Yaya Aliyu ne yake rik'e da mu. Daidai da pencir ban san na siyawa su Hanif ba. A yadda na taso a irin gidanmu da babu tausayi da tallafawa na k'asa ban yi zaton Aliyu zai yiwa Bulkachuwa irin wannan zumuncin ba. Na sani hidimar kayan abincinmu da baya mantawa akwai alfarmar mahaifiyarsu a tare da mu. Amma yadda baya mance wa da y'aya'n Tijjani na gamsu ko Babah bata tare da mu zai yi iyakacin kokarinsa. Da na fahimci basu mayar da hankali wajen kai wa Tijjani kayan ciye ciye ba. Ni kuwa sai na mayar da hankali, domin shopping nake yi masa mai sunan shopping. Hatta kifin gwangwani ina siya masa fiye da dozin guda duk wata. Kayan shayi da su conflakes kam ba'a maganarsu. Babah har fad'i take wai kayan suna yin yawa. Biskit irin masu dadin nan kullum na yi lalle sai na siya, kafin lokacin da zamu je, sai na yara masu yawan gaske. Sannan bana raba shi da cincin da cake. Kullum fes muke ganinsa. Illa duhu da ya yi. Amma da dukkan zuciyarsa ya karbi kaddarar da ta fad'o masa. Da wuri muke tafiya, da k'atuwar tabarmarmu. Tunda Yaya Ammar yana cikin manyan gandorurobobin kurkun bamu da matsalar komai. Domin yini muke sai yamma lis muke dawowa. Muna zaune mun gama cin abinci. Ya kalle ni ya ce "Baba lafiya bata zo ba yau?" Na yi murmushi na ce "Ta ce wai takuramu take yi, ba zata zo ba sai wani zuwan". Murya babu amo ya ce "Da ta zo abin ta." "Ni ma hakan na ce mata Wallahi". Ya kalli yaran suna can nesa damu suna kallon bishiyar mangwaro da y'aya'n suka sauko kasa kasa ana iya mika hannu a tsinko. Ya kankance murya ya ce "Little kina kewata ko?" Na yi k'asa da kai, idona ya cicciko domin babu yadda za'a yi mu zo bai mini wannan tambayar ba. Na fahimci ita ce tafi damunsa. Na kalle shi na ce "Ina kewar ka sosai Baban 2. Kullum dare idan na kalli inda kake kwanciya sai na jika filo da hawaye! Amma ina karfafa kaina guiwar cewa tunda muna shakar numfashi daya a wannan duniyar akwai lokacin da zai zo da zaka dawo cikinmu mu cigaba da rayuwa. Ina kuma da tabbacin rayuwar da zamu yi zata Fi wacce muka yi a baya nutsuwa da kwanciyar hankali. Yaya Aliyu yana matukar kokari akan gidanka. Su Yaya Salisu da su Ammar suna taimaka, bamu da matsalar komai sai rashin ka." Ya ce "Ke Baki fad'o naki k'ok'arin ba little ". Na ce "Ka sha fad'a mini, ni kake da tabbacin ba zan gaji da hidimar y'aya'nka ba. So nake ka gane ba y'aya'nka ba kawai kai kanka da mahaifiyarka ba zan gaji da hidimar ku ba, muddin ina numfashi." Ya kasa magana. Sai can ya nisa ya ce "Ina son ki sosai little. Ina rok'on Ubangiji ya taya ni son ki, ya k'ara miki hak'uri da jarumta". Cikin rauni na ce "Ameen" domin ya yi matukar ba ni tausayi. Ya saki ajiyar zuciya ya ce "jiya shekara ta d'aya a nan. Tunanin ki kad'ai yasa nake ganin na dade. Amma ban da hakan ba k'aramin gata aka yi mini ba. Domin tunda nake ban tab'a samun damar da nake yin ibada nake ambaton Ubangiji irin a wannan lokacin ba. Na gamsu akwia hikimar Ubangiji ta sakaye ni a nan. Ba ni kaina ba, ko ke addu'ar da nake yi miki little ta ishe ki, bare kuma y'aya'n ki. Shi yasa ban damu sosai ba, da aka kasa fitar da ni". Na ce "Allah ya karba. Ina kuma ganin tasirin addu'ar ka garemu domin bamu tozarta ba Baban 2." Ya ce "Ki tsananta addu'ar nan ta*RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN.* Kullum ina fad'a miki tasirinta mai yawa ne". Na zuba masa ido, shi ma ya zuba mini tsawon lokaci muna kallon juna, idanuwanmu cike da k'walla. Ya yi k'arfin halin danne nasa hawayen ya hadiye. Ya ce "So nake na gan ki da ciki Little" Nasan yadda kike son haihuwa. Na kuma tabbatar renon ciki da hidimar bebi zaisa ba zaki ga nisan zaman da zan yi ba". Na ce "Ta ya ya hakan zata kasance Baban 2?" Domin ni kaina idan har zan samu cikin zan yi matukar farinciki mai yawa. Ya ce "Kina so?" Na daga kaina da sauri amma ban yarda na d'ago kaina ba. Domin haka kawai na ji kunya ta rufe ni. Ya ce "Shike nan zan roki arzikin Ammar ko zai mini alfarma". Na ce "Me zaka ce masa?" Ya ce "Zaki ji daga baya." Na d'ago na ce "Amma Baban 2 idan na samu ya bare kada ka ce na zubar maka fa, nasan halin ka". Ya dan murmusa ya ce "Ai ina fad'a miki ne dan na rama rikici da tashin hankalin da kika dinga yi mini kafin ki samu cikin twins". Na rufe idanuwana ina dariya sosai". Na ce "wanccan satin dai aka daura auren Nasiba". Ya ja tsaki ya ce "Ammar ya fad'a mini. Ya isa haka kuma". Na yi maza na sauya maganar da ce wa "Ka saurare ni da kyau Baban 2 ". Ya ce "Ina jin ki". Na ce "Jiya wata baiwar Allah ta mini waya akan gobe suna son na je gidan gwamnati na yiwa mai dakin gwamna kunshi. Na ce su saurare ni kad'an. So nake mu tattauna me zaka ce game da hakan. Na fi son na yi komai da yardar ka". Ya yi shiru. Sai kuma ya ce "Kuna da matsalar Wani ma abinci ko ma bukata ne?" Da azama na ce "Wallahi bamu da ita. Kuma Ubangiji yana kawo mini mutane har gida babu yanke wa." Ya ce "To bana son zuwan ki gidan mutane Asiya" Na zuba masa ido na ce "Bajq zuwa, ba Kuma zan je ba. Amma sai nake ganin da ka yi hak'uri na je wannan din. Domin ina son a shiga jikin matar gwamna. Watak'ila ta sanadin ta sai Ubangiji ya fito mini da kai, tunda ka hana ni dauko maka lauyoyi, ka hana ni neman taimakon manyan mutane. Ka bani dama yanzu,tunda ita mace ce kuma komai sai da sabab" Ya yi shiru. Kafin ya nisa ya ce "Tsoro nake ji Asiya. Ina jin tsoro kada ki samu dama mai yawa ki fi k'arfina ki k'asa yi mini hak'uri da kike yi yanzu" Ya fada hankalinsa a tashe ainun. Na ce "Haba mana Baban 2! Me yasa kake wasiwasi a kaina? Har duniya ta nade ni taka ce. Ina fad'a maka idan shekaru hamsin aka daure ka Wallahi zan jure na jira ka. Da bakinka ka fad'a mini akwai iyaye mata da suke sadaukar da kuruciyarsu saboda y'aya'nsu. Ashe ni baka gamsu zan yi irin wannan sadaukarwar idan kasa ta rufe maka ido ba. Tunda ga shi da ranka ma kana kallon ba zan iya sadaukar da komai saboda na reni yayanka ba." Ya girgiza kai ya ce "Ba hakan ba ne Asiya. Na sani zaki yi mini komai. Sannan ke yaranki basi yawa". Na ce "Ba yanzu ka gama mini albishir din zaka samo hanyar da zamu bi mu samo wasu yaran ba? Har na fara tunanin zan ga likita dan a d'ora ni a maganganun da zan zasu taimake ni wajen samun ciki da wuri. Ashe da wasa kake yi, ni kuma have nasa rai". Ya ce "Ba wasa nake yi ba. Na ce "To ka ba ni wannan damar. Bana son na yi abu ba tare da ka sani ba, bana son na bata maka rai Baban 2 ". Ya saki ajiyar zuciya ya ce"Shike nan. Amma tare da yara da Babah za'a dauke ku". Da sauri na ce "Dama tare da su zamu je. Na gode, Allah yasa hakan ya zame mana sanadin alheri". Ya ce "Ameen. Daga haka na shiga ba shi labarin Aliyu da Iklima. Ya murmusa farincikin zuciyarsa ya bayyana akan fuskar sa. Haka muka dinga hira. Har lokacin tafiyarmu ya yi. Hanif ya ce "Baban 2 sai mun sake dawowa. Hamim kuwa ya ce "To bude ka bamu biscuit din naka" Ya kuwa bude ya bawa kowa a hannunsa. Suka had'a baki suna fad'in"Mun gode, Allah ya fito mana da kai! Ya ce "Oya ku je office din Uncle ku ce masa zaku tafi ". Suka ruga a guje, suka nufi office din Yaya Ammar. Ba jimawa ya fito rik'e da hannuwansu. Ya kalle ni ya ce "Zaku tafi Yabi?" Na ce "Eh Yaya mun gode sosai." Ya ce "Dafatan dai kin fad'a masa ya dinga cin abinci. Ba kasafai yake cin abinci ba. Kullum sai na taho masa da abinci daga gida. Amma baya wani cin na kirki." Na yi murmushin kunya na ce "Ina ce wa "Na yi masa". Daga hakan muka taho ya bude mana k'ofa, har titi ya kawomu. Ya tarar mana Napep ya biya sai da ya ga mun tafi sannan ya koma. Muka isa gida na fad'awa Babah ya amince amma ya ce mu je tare. Ta ce "To sai mu je taren. Allah ya tabbatar mana da alheri. Ai kuwa har kofar gida Hajiyar nan ta zo ta kwashe mu ni da zugata. Tunda yara na hutu. Sai gamu daredare cikin fadar gwamnati. Aka baibaye mu da abubuwan motsa baki. Ashe Hajiyar nan mai magana da yawun matar gwamnace. Ba'a bata mana lokaci ba aka yi mana iso zuwa dakin da zamu yi kunshin. Zuciyata tana harbawa na fara yi mata. Sai addu'a nake Ubangiji ya ba ni sa'a na yi wadda zai yi kyau ta kuma yaba. Cikin nutsuwa nake yi. Tana yi tana kallona. Na kammala kunshi. Na fara yarfa mata kitso akan dogin gashinta da ya sha gyara na garari. Na kammala. Ta ce hadinaeta ya dauko matso mata dogon console mirror din da yake gefe. Ta ga yadda na yarfa mata kitso. Ta murmusa alamun ta gansu da abin da ta ga ni. Ta kalle ni ta ce "Kin kammala sakandire ne?" Na kasa amsawa domin na tabbatar k'ank'anta ta ya sanya ta yi zaton ko ban yi Kandi ba. Ta lalli Babah ta ce "Hajiya kar dai bata zuwa makaranta?" A tausashe ta ce "Ta kammala tuntuni. Ta nuna su Hamim da suka lafe a jikinta ta ce "wadannan ai y'aya'nta ne ba kanne ba." Ta dauki salati tare da fad'in "Wonderful. Yanzu ke ce uwar wadannan samarin?" Babah ta ce "Ita ce kinga Kuma sai da shekara biyu a daki sannan ta haife su. Tana shatakwaas ta haife su". First lady ta sake tsananta mamakinta ta ce "Yanzu shekarun yaran nawa tunda masu garin jiki ne ba irin ba ne tsaba" Babah cikin dariya ta ce "Shekarunsu bakwai." Ta sakki ajiyar zuciya tana kallona ta ce "Shekaru ashirin da biyar a wannan yarinyar. Ikon Allah. Tunda na ganta na ce kyakkwar yarinya Allah dai yasa tana zuwa makaranta ba iya sana'a take yi ba. Ashe ba yarinyace ainun yadda na zata ba, ban zaci ta cika sha biyar ba ma." Ta ce kin yi karatu ne bayan na sakandire?" A hankali na daga kaina na ce "Na yi N.C.E a nan college of education. Na karanta Home economics " Ta fadada murmushin ta ta ce "Da kyau! Kina aiki ne?" Na ce "A a takarda ta ta yi kyau amma Ubangiji bai kawo mini sababin samun aikin ba". Ta ce "Ai kuwa kin samu yarinya". Ta Kalli Hajiyar da ta kawo mu ta ce "A buga mata upper. A kai ta women center mafi kusa da ita ta dinga koyawa yaranmu sana'ar kitso da kunshi, hadi da tattalin gida." Daga yau kuma na bata mukamin costume din first lady". Cikin farin ciki Hajiyar take godiya a madadinmu. Ni kuma mamakin murnar da take yi ne ya sandarar da ni domin dai na jima ban ga mutanan da basu da Bakar Taadar kyashi da hassada kamar Hajiya mai magana da yawun matar gwamna ba. Baba ta shiga godiya ita ma. Haka nima na shiga godiya mai yawa, kna hawayen farinciki. Na samu daukaka ta sanadin sana'a. Hatta aikin da na samu arzikin sana'a ne ya janyo mini. Alhamdulillah na dinga ambato babu sassautawa. *Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.* *Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐, ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To albishirinki yar uwa!* *UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1 *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S ONLY*. Da zamu tafi aka zuba mana leshina da atamfofi da kayan yara fall leda. Ga Kuma kayan ciye ciye da soyayyun nama. Sai da na nutsu sai na gane har da material din Malaysian Fabrics na umm Nihla. Ta ce kuma Hajiyar ta sallame ni. Murya na rawa Babah ta ce "Baby wata sallama Kuma. Ai kin nuna mana ke din uwar kowa ce a wannan jahar. Allah ya kare ki, ya dora mijin ki akan magauta. Ya dauwamar da arziki ya shirya muku zuria " Cikin Jin dad'i take fad'in Ameen amen". Har gida Hajiyar ta kawo mu . Ta shigo ta huta. Kafin ta bar gidan Baba ta zayyane mata matsalar da mkue ciki akan lamarin Tijjani. Ta ka'du k'warai da gaske. Sannan ta ce zata shigar da maganar gaban first lady da IZININ UBANGIJI. Ta ajiye envelope tana ce wa "Ga albashin ki na farko costumes din matar gwamna. Kafin kuma ki fara karboa na gwamnati. Cikin satin nan zan kawo miki upper din ki har gida " Na dinga yi mata addu'ar fatan alheri da godiya mai yawa. Ta karbi takarduna ta tafi da su. Kwanaki uku ta dawo mini da upper kamar yadda ta yi alkawarin kawo mini har gida. Sannan women center din unguwarmu aka tura ni. Wnai abin burgewa a weekend ne aikin nawa. Ga albashina da tsoka babu laifi. Sati na zagowa muka tafi wajen Tijjani muka yi masa bayanin halin da ake ciki. Ya yi murna, ya yi fatan alheri. Ya sake jaddada mini bai yarda na dinga zuwa gidajen mutane ba. Gidan gwamnati ya amice Slshima sai tare da Babah zamu je. Da girmamawa nake ce wa to, domin ya samu nutsuwa. Nima kuma bana k'aunar abin da zai bata masa rai. Domin a yanzu na gasgata bayan iyayena ba abin da nake so a duniya irin Tijjani da y'aya'nsa. Hatta uwarsa da y'an uwansa ina jinsu daban a duniyata. Ganin ya amince na ce wa Babah zamu je Toro na KAIWA su Baban Marina su ga upper ta." Ta ce "hakan ya yi. Washagari kuwa muka tafi Toro. Murna kan murna Baban Marina ya yi. Ya dafa kaina ya ce "Nasan zaki yi albarka Yabi. Na sani akwai babban al'amari a tare da ke. Na sani zaki daukaka. Alhamdulillah! Ubangiji ya fito mana da Tijjani. Allah ya shirya miki zuria. Allah yasa albarka a cikin komai na ki. Yadda kike tsaye a kaina da iyalina Ubangiji ya tsaya miki ke da ahalin ki fiye da haka. Asiya ke kad'ai gayya ce a gidan Marina". Na yi k'asa da kaina ina hawaye. Ina Jin rashin Tijjani ne cikas dina. Amma babu abinda ban samu ba na rufin asiri a duniyar nan ba. Kafin ka ce miye wannan sai na fara Tara kudade masu nauyi. Domin dai ban fasa yin lalle a gida ba. Duk wata albashi biyu nake ja. Ga wanda gwamnati zata ba ni. Ga wanda ake ba ni a envelope idan na je gidan gwamnati na yiwa Madam da iyalin ta kunshi da kitso. Bana tab'a su tunda har yau Yaya Aliyu bai tab'a yin lako lako da abincinmu da kuma kula da yara ba. Iya na lalle dai da shi nake hidimar da nake yi. Domin so nake na yiwa Baban Marina ba zata ta ban mamaki. A hankali alherin da ya same ni ya fara shiga kunnuwan mutanan gidan Marina. Nan da nan aka fara cece kuce. Ko a biki aka taru saa'anninmu da na yi musu zarrra zasu yi ta sakin baki a gaban Nazira suna ce wa "Ai yanzu na zama y'ar siyasa ba kuma siyasar ce abin kaico ba. Manyan mata ne suke dauka ta muke sheke ayarmu. Ta ya ya za'a ce wai matar gwamna nake yiwa kunshi. Wace ce ni? A wanne karatun da bai fi cikin cokali ba. Tun Nazira na hak'uri, tana tankawa cikin dad'in rai tana fahimtar da su, har ta shiga yin tashin hankali da duk wanda zai soke ni. Hatta yaran dakin inna k'ananunmu ke nan da a yanzu suke y'anmata matukar suka ji wani ya soke ni sai dai aji na gwabza fad'a. Tunda ce wa suke hi karuwanci nake yi. Gabadaya y'an k'ofarmu ba yadda za'a yi a tab'asu su kyale a yanzu. Ganin hakan sai aka koma fad'in ni ce nake musu huduba tunda nima hakan na yi , sannan na mayar da dukkan ahalin Babanmu agwagi sai abin da na ce tunda na fisu kudi. Dan ma sunsan kudin nawa da ake famkama na kazanta ne. Sannan mugun k'ullin da yake raina ne ya sanya aka gane mijina dilar k'waya ne. Dana zauna na nutsu sai na gane tabbas wata k'iyayyar bata da dalilin yin ta. Mafi yawa hassada ne da kyashi. Ba kuma zai yiwu kowa ya so ka ba. Babbar godiyar da nake tsananta yi ban tab'a zuwa gidan Marina na tsugunna a gaban wani na ce a taimake ni ba. Duk yadda aka yi mini aure dan a kassara ni, sai Ubangiji ya yi kishina. Wahala kam na sha ta, amma ba mai yawa ba ce. Sannan Ubangiji ya yi mini rufin asiri irin wanda ko y'aya' mazan gidanmu basu same shi ba. Mafi girman Niimar da Ubangiji ya yi mini, itace ta lafiya da kuma sana'ar hannu, ya kuma ba ni haihuwa, ya sake ba ni mijin da yake tsananin sona. Bugu da kari ina cikin wadanda Ubangiji ya yi musu gata irin na gam da katar na girma da iyayena guda biyu. Wannan kad'ai babbar niimace a wajen bawa. Domin ko da ban san zafin rashin iyaye ba. Allah ya sani ina matukar tausayin wanda iyayen sa suka rasu domin al'amarin da suke fuskanta mai tsananin gaske ne. Ka ga masu iyaye suna samun TAGOMASHIN addu'a, suna samun tallafi, suna zuwa su yi hira da su, domin sun san zasu boye damuwarsu, sabanin wadanda basu dasu a raye sun dinga tiri tiri da matsalar da ta dame su saboda gudun za'a fantsama matsalarsu a duniya. Da na tattara wadannan ni'imomin sai na ga ba zai yiwu kuma a ce kowa ya so ni ba. Ba zai yiwa kuma na ga yadda nake so ba. Tunda sunnar rayuwa ce kowa da irin k'alubalen da zai fuskanta a duniyarsa. Sai na gamsu kalubalena rufe Tijjani da aka yi. Ina rayuwa babu miji tsawon shekara guda. Sai kuma rashin soyayya daga dangi, da rashin hadin kai a tsakaninmu. Na numfasa na ce Alhamdulillah. Ubangiji ka yi mini komai. Allah ka fito mini da Mijina. Ubangiji a sanya soyayya da tausayi a zukatan ahalin gidan Marina gabad'aya. Domin na riga da na gaji da gutsiri tsoma Wallahi. A haka bikin su Ikilima ya matso. Ta ko ina ba ni da sukuni. Domin da na fad'awa mai dakin gwamna za'a yi auren kanwata. Tana bude baki sai ce wa ta yi mu je da Hajiya na zaba gado da kujeru da kayan dakin koami da koami zata yi. Allah ya dora mata sona da tausayina, mussaman yadda na bata labarin tabbas Tijjani sharri aka yi masa ba halinsa ba ne. Ta yi mini alkawarin za'a fito da shi amma ba tashi guda ba. Na saurare ta. Dan haka komai na garari aka siyawa Iklima. Har Toro kuma ta tura Hajiya ta kai kayan abinci gidanmu ta ce a yi hidimar biki. Ganin yanayin gidan namu ya sanya Hajiya ta sake buda mini a dalilin ta yadda gidan yake na masu k'aramim k'arfi ne ainun. Idan na zauna sai na yi ta ambton Ubangiji domin ya yi mini komai. Mafi Jin dad'i ta yadda ni ce sanadin hadin kan y'an k'ofarmu. A haka aka yi bikin cikin rufin asiri. A cikin BAUCHI ya yi gidansa ba nisa da ganeral hospital din da yake aiki. Ba'a jima ba aka kawo Baban 2 asibiti ba shi da lafiya. Kwanaki biyu na fahimci dan yana da hanya ne har aka fito da shi, ban da hakan ai za'a ba shi magani a sickbay din kurkun. Yaya Aliyu kuwa ya saka aka bashi daki a aminity. Yayin da Yaya Ammar ya yi kane kane shine jami'in da zai zauna da shi a madadin ma'aikatan gidan yarin. Dan haka da rana anan muke yini. Da yamma mu tafi da su Babah. Da daddare kuwa Yaya Aliyu zai zo da kansa ya dauke ni da abinci mu tafi. Ba zan dawo ba sai da safe. Tun ina jin kunyarta har na matse na cigaba da harkar gabana tunda bata taba ce mini komai ko bin ba'asin kwanan da nake yi a asibiti ba. Ragowar saiwowin da aka yiwa Iklima da garin daka na yi ta sha. A gefe kuma Ina hadiyar zabbabun supplement na GHT da FASEELAT ta zaba mini su. Muna kwance akan bargon da na shimfi'da akan tabarma tunda gadon ya yi mana kad'an. Ya ce "Kina shan maganin kuwa?" Na ce "Na kai wata ina sha, da yake an dora ni kan maganin da zai taimaka mini wajen conceiving. Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Allah yasa satin da na yi addu'armu ta cika. Gobe zan koma kin sani. Wato albarkacin Ammar na yafe wa Baba Maryo! Asiya Ammar mutum ne. Kullum sai ya kai mini abinci. Wanccan satin na nuna masa ina son ya mini alfarmar ganin iyalina na kwana d'aya. Ina rufe baki ya ce "Na fara zazzabi, zai yi kokarin a kai ni asibitin waje daga nan sai ki zo." Ki ga irin hadarin da ya runguma saboda ya faranta mini. Tunda idan aka gane shi za'a iya sallamarsa daga aikin ace ya ci Amanar aikinsa. Ki ga yadda ya bamu sati a maimakon kwana d'aya ko biyu." Na numfasa na ce "Ni ma na yafe mata Allah ya shirye mu gabadaya." Ya ce "Ameen! Allah yasa kin harbu little." Na rufe fuskata a kirijinsa. Ya dinga Shafa fatar jikina ya ce man nan na Oriflame ya karbe ki. Jikar Dada dai ta iya zabarwa mutum man da ya dace da shi." Na murmusa cikin jin dadin yabawarsa na ce Aisha lame ai ta k'ware, wajen mayar da mace zama y'ar gayu ta gaske". Ya ce "Na gasgata ki". Washa gari kuwa aka sallame shi. Ina kallon yadda aka tafi da shi. Sai kawia kuka ya kwace mini a dalilin Babah tana gida saboda yara. Aliyu ya dinga ba ni hakuri yana ce wa "To da ba ki samu damar ganinsa ba fa? Sati guda fa ya zo ya yi miki haba dai Yabi. Ki yi hak'uri komai zai wuce. *** *Watanni biyu* Ana cikin haka kwatsam gwamnatin tarayya ta rage lakcarori cikin ikon Ubangiji har da Yaya Jabir aka sallama. Gabadaya mun ji ba dad'i mussaman da yake ya tara iyali. Tunda amaryarsa ma yaranta biyu, Maijidda na da biyar domin haihuwa take akai akai tamkar da gayya. Zaman Kaduna ya gagara tunda dama a quayers yake. Kan dole ya tattaro ya dawo Toro. Na tausaya, na ji babu dad'i dole a aka hak'ura tare da fatan Allah ya kawo wata damar. Baban Tsakiya ya dinga fad'in sa hannu ne. Kuma a cikin wadanda yake zargi har da Baban Kasuwa. Domin ya ce ai tunda Jabir ya kara aure yake ta tsiyace wa. Tabbas hannu aka saka masa. Yayin da Baban Kasuwa da ahalinsa suke murnanr hakan da ya samu Yaya J. Tunda sun tafi a cewar Jabir yana fifita amaryarsa akan Maijidda da take yar'uwasa kuma uwar y'aya'nsa. To yanzu sai ya yi rashin mutuncin su ga ni. Daga Baban Tsakiya har Baban Kasuwa kowa so yake a ce Baban Marina a bayansa yake. Har yau din nan sun fishi kudi. Amma ya fisu gata da rufin asiri . Domin a yanzu yana fita wajen sana'arsa saboda sabo da kuma mike kafa. Amma duk watan duniya sai mun ajiye abincin da za'a ci a kofarsa da kudin cefane. Hatta sabulun wanki da na wanka da zai bawa iyalinsa mun dauke shi. Hadawa muke yi gwagwadon k'arfin mutum. Ni ce sha kundum. Hakan da suke gani kuma sai kowa a cikinsu yake son ya shige masa, ya soki d'an-uwansa a gabansa. Shi kuwa baya biye wani a cikinsu suyi hirar wani. Amma ya karbe su da fuskar afuwa da sassauci yake mauaamala da su. Tunda ba abin da Ubangiji bai masa ba. Jahilci ne ka ce zaka rama sharri da sharri. Bakar Taada ce ka ce zaka maimaitawa wani irin kuskuren da aka yi maka. Mussaman akan zumunci, matukar ana son gyara, matukar ana son cigaba. To a bar BAK'AR TA'ADAR riko da kullaci. Afuwa da yafiya yana kawo soyayya da masalaha a tsakanin jini guda. Tashin tashina kuwa yana dawo da gaba da k'iyayyar juna. Allah ya yafe mu gabadaya. Zaune nake kusa da Babah yayin da Anas yake kan kujera su Hanif suna ta dabdala a jikinsa. Babah ta kalle shi ta ce "Kai bana son iskanci ka ji. Da wasa kake ko kuwa da gaske kake wannan maganar?" Da murmushi ya ce "Wallahi ta makance Babah! Ga mamakinmu sai Babah ta fashe da kuka tana fad'in"Allah mun tuba. Allah ka yafe mana. Ni dai ka shaida na yafe mata. Anas ina rokon arzikin ka, ka yafe mata. Addu'ar da ka yi mata cikin fishi ne Ubangiji ya karba. Ka yi hak'uri. Yau na sake gasgata A guji addu'ar wanda aka zalunta, mussaman idan ya yi ta cikin fishi da neman agajin Allah". Nan da nan ya ce "Na yafe mata. Ko yanzu idonta ya bude zan yi murna, idan bai bude ba kuwa Allah yasa ya zame mata kaffara. Amma ai ko yanzu ta ga karshen sharri. Tsofe tsofe da ita ta yi mini bakin sharri irin wannn. Haba wannan duniyar cike take da rudani. Ace wai jinin ka bai k'i ka tozarta ka yi bak'in ciki ba?" Ta share hawaye tana fad'in "Babu wanda zai mori zumunci sai wanda ya yi hak'uri ya hadiye komai, ya yi sassauci ya kuma yi afuwa. Zumunci da kansa ya roki Zati ya ce "Ubangiji ka jefa wanda ya yanke ni cikin wuta. Ubangiji ka tsananta wa wanda ya tsananta mini. Allah kuma take ya karbi addu'ar zumuncin. Shi yasa Annabi ya yi ta jan kunnenmu akan zumunci. Hatta makoci da aminin iyaye sai da Annabi ya yi ta jan kunnenmu a kansu bare kuma wadda nasabarku guda. Akwai bukatar mu ninka hak'uri da kawaici, hadi da yafiya idan kuwa ba hakan ba, gaisuwa ma sai ta gagara a tsakanin jini guda." Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Da dukkan zuciyata na yafe mata. Na yafe wa kowa. Allah ya cigaba da dafa mana." Ta ce "Ameen na gode Anas. Na gode da ka yarda da maganata Ubangiji ya yi maka albarka". *Ya ce "Ameem Hajiya Babah tamu". ** Jumaa da yamma muka yi Toro. Muka tarar da baba Maryo a zaune a dakinta jikinta ras. Ido kuma gwaragwara amma bata ga ni. Fadi take yi "Na rantse bakin Anas ne ya kama ni. A yiwa ma'aiki a kira mini shi. Wallahi ya fini gaskiya. Hauwa ki yafe mini. Ki roka mini afuwa a wajen Yabi da Tijjani." Ta kece da kuka. Na matsa kusa da ita na ce "Baba ki yi hakuri. Ban kullace ki ba. Na kuma yafe miki. Na Ari bakin Tijjani shi ma ya yafe miki. Allah ha baki lafiya." Babah ma tana kuka ta rik'e hannunta ta ce "Sannu da ibada Maryo! Tuni na yafe miki babu komai a zuciyata game da sha'anin ki. Sai alheri. Allah ya yafe mu gabadaya ya kuma gajarta miki wahala. Sannan Anas ya yafe miki tuni, zan kuma k'ira miki shi ki ji da kunnen ki. A take Babah ta kira Yaya Aliyu ta ce ya bar komai gobe ya zo ya dauke su zuwa asibiti a duba ta da kyau. A Toro Babah ta barmu suka nufi asibitin Jos tare da Yaya Aliyu da kuma Yaya Ammar. Dama Nasiba a can take aure dan haka babu matsalar abinci. Kamar jira jikina yake na zo Toro ai sai kawai na hau wani irin zazzafan zazzabi. Hak'ora na har kad'uwa suke yi. Ga azabar ciwon k'asusuwa. Sai na ji tamkar ana kwankwatsa mini jikina. Kullum jiki sai dada rikice wa yake yi. Amai ya tisa ni a gaba. Ba dama a d'ora tukunya yanzu zan fara amaye amaye. Hankali iyayena ya tashi. Da yake yanzu mamam ta hakurkurtar da zuciyarta ta daina tsiyataku, aka rasa me za'a ce mini. Tunda alamu k'arara na mai shigar ciki sun bayyana mini. Gwaggo ta rasa me zata ce mini. Sai da dare ya yi dare. Ta yi gyaran murya bayan ta gama danna mini jiki ta ce "Yabi alamun shigar ciki nake ga ni a tare da ke" Sanin a cikin zullimi take ya sanya ban tsaya noke noke ba na ce "Ni ma ina kyauta zaton shine Gwaggo". Ta hau salati ta ce "Cikin haihuwa Yabi?" Na ce "Shi fa Gwaggo". Ta dauki sabon salati ta ce "Ta ina kika samu ciki Yabi? Nasan dai da ikon Ubangiji ba zaki yi ashararanci ba, ina kyautata miki zato." Na saki ajiyar zuciya. Ga shi ina jin jiki. Ina nishi na ce "Na gode da kyakkwar shaida Gwaggo". Daga haka na kulle bakina a dalilin yadda nake jin tsananin kwankwatsa a duka jikina. Kan dole ta tashi doro alwallah ta tada sallah. Ganin bata samu nutsuwa ainun ba. Ya sanya bayan ta yi sallama na ce "Gwaggo Zaton da kike kyautata mini tabbas hakane. Kuma hakkun ciki ne. Idan Babah ta zo ki tuntube ta ki ji me zata ce akan hakan". Ta zuba mini ido ta ce "Yabi a gidan kurkun kuka yi cikin ko a ina?" Na fara nishi ina fad'in "Ki bari ta zo, ni ba iya bayanin nan zan yi ba. Dan Allah ki zo ki cigaba da matsa mini kafafuwana". Ta sake daukan salati tare da tafa hannu. Sai nanata iko sai lillahi take yi. Sai ta yi shiru sai ta sake zabura ta d'auki salati tana ce wa "K'warzaba da jarabar yaran yau ta kai kure wa. Ni Asma'u ina kallon zamani". A kan dole ta cigaba da yi mini tausa. Tana yi, tana hirji domin ta shiga mamaki mai yawa. Da safe da Baban Marina ya shigo duba ni. A sanyaye ta ce "cikine da Yabi Alhaji". Babu dar ya ce "Ma sha Allah! Ai rabo ba k'aramin al'amari ba ne. Allah ya raba lafiya". Ta yi galala ta ce "Alhaji na ga baka ka'du ba! Ya murmusa ya ce "kad'uwar me zan yi bayan na gasgata Yabi tamkar yadda na gasgata yunwar cikina. Ita tasan yadda ta had'u da mijinta. Tana da miji kuma dan na ganta da ciki sai na bi ba'asi, akan me?" Ta ce "To ai kowa yasan baya nan, sai kuma a ganta da ciki, kana jin yadda ake daura mata magana haka siddan. Ina kuma a ganta da ciki". Ya ja tsaki ya ce "Idan har kika daka bak'ak'en taadodin jama'a babu abin da zaki yi. Ya mik'e yana ce wa "Sannu Allah ya raba ku lafiya." Ya saka kai ya fice. Satin su baba biyu sannan suka dawo, cikin sa'a ido daya ya budu. Daya ya mutu. Aka yi murna da yi mata barka da arzikin da ta auna. Babah tana zaune a dakin Gwaggo. Yayin da nake kwance akan k'aramin gadon. Na samu sauki, amma jikin babu k'warai. Gwaggo ta ce "ikon Allah Yabi dai ciki ne da ita." Ta dauke kai ta ce "Ho ke kam yanzu kina neman baci da magana. Ina dalilin wannan tuyar da kike yi ne. Nasan da shi tun kafin mu zo." Gwaggo ta sake ce wa "ikon Allah sai kallo. Abin ne yake dafa ni. Wato kinsan komai ke, shi yasa ta ce idan kin zo, na ji a bakin ki". Babah ta mik'e ta ce "Sai ki yi ke kad'ai ina dalilin bin wannan diddigine haka? Mace da mijinta". Da mamaki Gwaggo ta sake ce wa "To wai a kurkun, a ina suke haduwa ni Ma'u! Babah ta fice ta ce "A a nima ban sani ba. Sai ki tambayi mijin nata tunda ita kin saka duk ta sururuce da kunya. Domin ke sai akan girman ki zaki baci da magana, sai ki je ki gano shi, ki tambaye shi yadda aka haihu a ragaya ". Ta fice da sauri. A haka muka sake shafe sati biyu. Yaya Aliyu ya zo ya kwashi yara ya ce tunda ba tafiya zamu yi ba, to ba zasu yi asarar karatunsu ba. Na kuma gane Babah tana son ta zauna da Dada a dalilin ta damu da lalurar da ta sami autarta. Sannu a hankali na fara warware wa. Matan gidanmu sai nan ake yi da ni. Mama da kanta sai ta tambayi abin da zan ci. Na tabbatar ta dad'e da ajiye makamanta. Amma yadda nake tiritiri da rik'e musu gidan ya kara mini kima k'warai da gaske. Ahalin gidanne dai idan muka had'u ko idan na fita da nufin zagaye ake bina da kallon k'urillah da tuhuma. Yara basa iya ce mini komai ba. Amma da kunnena na jiyo matansu Baban Kasuwa da na Tsakiya suna gulmar cikin jikina suna fad'in "iyalin Tijjani bata yi shashanci ba, ai a yi mamaki, irin fasadin da ya yi a doron kasa, sai kurum." Na yi kamar ban ji ba. Domin a yanzu da nake fama da rashin Baban 2 mene ne bazan yi hak'uri a kansa ba? Baban Tsakiya kuwa fama yake da ciwon hawan jini. A dalilin mafi yawan y'aya'nsa sun kangare. Dama dai Jabir ne mai dama, to a lokacin da yake da dama bai bari ya taimaki kowa ba. Domin ko ni a farkon farkon rufe Baban 2 idan ya tura mini kudi sai ya ce "Ba sai an ji ba". Dan haka mafi yawa yanzu ba'a taimakonsa ko tausayinsa domin a lokacin da ya samu ba wanda ya more shi. Sai aka yi mutuwar kasko. Shi kuwa Baban Kasuwa manyan y'aya'nsa guda biyu na farkon mata ne. Amina sai Maijidda. Kuma dukkansu a yanzu kowa fama take a gidanta bare ta taimake shi. Gara ma Maijidda yanzu ne babu ta same su. Aminu na ukun sa'an Anas ne, yanzu suke tasowa. Gabadaya rayuwa ta yi juyin waina. Baban Marina da ake ganin babunsa a yanzu yafi su rufin asiri. Abincinmu yafi na kofofinsu. Ba kuma kudi ya yi ba. A a Y'aya' ne suka taso, muka hutar da shi fafutukar rayuwa. Har yau kuma idan Baban Marina ya samu damar da zai yi mana wasiyya sai ya ce "mu zama masu afuwa da manta sharri, mu kuma rik'e alheri komin kankatarsa. Ko waya ka yi masa sai ya ce "Ba jarumta ba ne fad'a a tsakanin yan'uwan juna. Ba kuma tsoro ba ne idan kai mai gaskiya ka janye ka barwa wanda ya karkace, masalaha ne da takaita rikici. Har ilah yau ba imani ba ne ka yi fatan ganin wani ya shiga mummunan yanayi duk yadda ya zalunce kuwa. Mafi yawan sakayya yanzu tun a duniya Ubangiji yake fara yinta. Matukar kana da gaskiya baka nufi kowa da sharri ba, to sai ka ga alheri komin dade wa. Iri iren wadannan nasihohin ne suka dagargaza mini tunanim son ganin su Baban Tsakiya a halin tagayyara, na huce da su nake nema masu gafarar Ubangiji. Na gamsu idan suna cikin tozarci dole dai jininmu ne kuma gidanmu daya. Nazira akai akai take ziyarta ta. Mu yi hira, ta daho mini abinci, ko ba zata zo ba sai ta aiko mini duk da gidan namu da abinci amma kullum sai ta ciko cooler ta kawo mini. Muna hira na ce "Adda Nazi wai ya ya Saiwowin dahuwar tattabaru din nan kuwa? Ni dai na ga kyaunsu. Ya sabunta ni a wajen Baban 2 sosai". Ta ce "hm kayya bari ke dai suna da kyau. Amma maigidan ne kuzarinsa ba mai yawa ba ne. Na yi dariya na ce ke kuma babu s'auki." Ta ce ba haka ba ne". Na ce To zan karbo miki moringa tea ya dinga sha a shayi ko a lemo, zai sha?" Ta ce "zai sha ba shi da matsa akan hakan. Amma dai Yabi kada ki saka na ba shi abin da zai cutu ko ya hallaka ni" Ta ba ni dariya ainun na ce "Kai Adda Nazi. Garin zogale ne fa sai sai saiwowi marasa illah. Yana da d'an kudi amma yana da kyau ainun". Ta ce shima a kano ne?" Na ce "eh a wajen mai saiwowin ne duka daga Chad take kawosu. *08032773332*. Ta ce "Tom shi ke nan. Na gode." Sai da muka yi wata biyu. Muka koma BAUCHI. A lokacin cikin ya shiga wata na hudu. Tun ina jin kunyar Babah har na hak'ura na ware a dalilin itama mita take yi. Wai a sadda muka yi abin da muka yi, ban yi zaton zan ji kunya ba, sai yanzu? Ranar da muka je Tijjani ya fahimci ciki ne da ni har ya yi k'wari ya kasa magana ya tafi ya yi sujjud shukur. Babah ta koma gefe ta yi kamar bata wajen. Ya dinga murna da yi mini addu'a. Gabadaya na danyace. Na ciko sosai. Duk wata ko ban je gidan gwamnati ba, sai Hajiya ta kawo mini kudin envelope tare da nanata basu manta maganar maigidan ba. Karamci kad'an na yiwa Hajiya, sai ya janyo mini sanadin alheri mai yawa. Na kuma fahimci tausayina take ji da gaske. A haduwarmu Allah kad'ai yasan adadin alherin da nake samu. Su Hamim ta mayar da su tamkar jikokinta. Suna bata sha'awa. Kullum a cikin kawo musu suturu masu kyau take, ga kayan wasa kala kala. A haka rayuwar ta cigaba da garawa har na shiga watan haihuwa. A lokacin kamfani ya sake biyan kudin filin Tijjani. Na yi siyyya mai rai da lafiya amma na kudire ba zan yi Taron suna ba. Ya fad'awa Aliyu yadda za'a yi masa da kudinsa. Yaya Aliyu Kuma Bai fad'a mini yadda za'a ba, Nima ban tambaye shi ba. Bayan ya ce a ware wanda za'a yiwa Baban Marina da mahaifiyarsa hidima. Da ragowar yan'uwan. Ya ce Aliyu ya dauko 250 ya yi wani abin. Cikin ikon Allah watan Muharram da kwana bakwai na haifo yarinya sankaceciya. Jawur da ita tamkar tsada. Wanda ya yi daidai da 1 ga watan goma miladiyya. Babah ce ta karbi haihuwar domin cikin dare ciwon ya tashi. Kafin Aliyu ya zo da mota tuni na haihu ta gyara wajen. Kawai mun je asibitin ne an duba ni. A daren muka dawo gida. Babah ta zuba yarinya ido ta ce "Ke kuma Aliyu kika debo?" Na kalle ta. Domin ni fa bana gane kamar yara. Aliyu ba sosai suke kama da Bulkachuwa ba, sai dai suna yanayi saboda jini d'aya. Ihisan ce suke kama da Tijjani kwabo da kwabo shi yasa su Hanif suke matukar kama da ita. Dan idan muka hadu kowa ita yake zaton ta haife su ba ni ba. Washagari Babah ta d'auki jinjira ta kai wa Tijjani da kanta. Aliyu ne ya kaisu. Tare da su Hamin da suke murnar sun yi KANWA tamkar su mayar da ita ciki. Ya karbe ta cikin kunyar uwarsu. Ya zuba mata ido yana jin sonta da tausayinta na tsaga shi. Zata girma babu soyayyar uba alhalin ba mutuwa ya yi ba. Ya tsinci kansa da ce wa "Allah ka mini sakayya da duk wanda ya k'ulla mini sharrin da aka nesanta ni da iyalina, na kuma rasa y'ancina. Aliyu ya juya domin idonsa ya ciko da k'walla. Babah kuwa tuni take sharbe. Domin ya bata tausayi k'warai da gaske. Murya na rawa ta ce "yi mata addu'a ka kuma yi mata huduba. Ya shiga jero mata addu'oin tsari da albarkar rayuwa. Ya Kalli Aliyu ya ce dauke ta ka yi mata huduba da duk sunan da kake so." Ya saka hannu biyu ya dauke ta ya yi mata kalmar shahada ya lakaba mata Hauwa. Ya mikawa Babah ita yana fad'in sunan ki na zaba mata ". Da sauri ta ce "Ba kuwa sunana zata ci ba. A saka mata Asama'u. Don Yabi tasan mun san alheri, muna kuma gode mata.". Aliyu ya ce "Hakane Babah. Ya sake sabuwar huduba ya rad'a mata Asama'u. Maimakon ya bawa Gwaggo sai ta mika mawa Tijjani domin ta ga bai gaji da kallon ta ba. Ya ce "Aliyu rago nawa zaka yanka mata? Domin gabadaya kai ta kwaso, kamar da ta yi da kai ta shahara." Ya ce "Haka na ga ni, Babah ma ta ce ni ta kwaso. Biyu za'a yanks mata. Ana yaye ta kuwa zan dauke ta". Tijjani ya ce "Yabi kuka zata yi Aliyu. Twins ne naka. Kai na haifawa su, ga shi nan kana ta tiri tiri da su babu gajiyawa. Ko yanzu idan kana so ka wuce da su, amma wannan barta, ita ce zata debe wa Yabi kewar zaman jirana". Babah ta ce "Uhum! Nan da nan ya kame bakinsa domin ya shafa'a da ita." Sun jima kafin su tafi su bar shi cikin alhini. Yarinyar ta shiga ransa fiye da twins. Suna isa suka tarar da mutanan Toro. Gabadaya ahalin Baban Marina ne sai Dada. Da murna ta fad'i sunan jaririyaya. Kowa ya yi murna take Yaya Salamatu ta ce sai a kirata Husna. Na ce "To". Farincikin sunan Gwaggo ya zangwanyar da alhinin da nake ciki. ** Na Dade da gane Dada ba k'aramin son Bulkachuwa take yi ba. Domin sai yanzu na fahimci kafatalin jikokinta tafi sonsa. Tunda bata iya boye son tagwaye. Ni kaina na sake samun daraja ne a wajen ta saboda Tijjani. Kullum ta gan ni sai ta yi kuka. Y'aya'nsa kuwa komai hannunta ya taba sai ta basu. Tana yi tana fad'in "Allah ka yiwa mai babban suna abin da zato bai yi zatonsa ba. Wanda duk ya k'ulla masa wannan salalar tsiyar Allahu ka dabaibaye duniyarsa da firgici da tashin hankali." Kaitsaye Babah ta bawa Dada jinjira. Ta zuba mata ido tana kuka ta ce "Mai sunan manya ya haifi Aliyu. Sai na tuna ranar da aka haife shi. Haka yake sak." Aliyu da yake tsaye a bakin k'ofar ya ce "Dada ikon Allah! A gaban y'aya'na da kannena kike maganar haihuwa ta?" Ta ce "To uwaka ma bana yi zancen haihuwar ta bare kai". Ya ce "Ai shike nan, dama ni ba wai kina sona ba ne . Yaya Tijjani ne na ki. Kin ga da kin bini a hankali gobe dia na zo na kai ki wajensa." Ta marairaice ta ce "A sannu ma zan bika Ali gadanga angon kilima". Ya ce "Assha kin batawa amarya ta sunanta. Amma dai zan zo, ya hau gaishe ta. Sannan suka gaisa da su Mama. Ya ce "Ummi ni da ke waye babba ne?" Ta ce "Mama fad'a masa". Mama ta ce "Ita ce babba ranar sunanta aka haife ka". Ta nuna shi da yatsa ta ce "To ka ji Wallahi ka kiyaye ni" Ya rik'e kiirji ya ce "oh saboda Ikilima zaki dinga zare mini ido? Sannu gyambo uwar son girma! Haka kike yiwa Yaya Tijjani?" Ta ce "Ai shi yayana ne kuma duk da hakan girmama ni yake kamar me saboda ya yarda surkuta gaskiya ne. Sai kawai kukan da take danne wa tunda ta ga jaririyaya ya kwace mata duk da dai wasa suke yi. Kowa ya yi k'asa da kansa ana taya ta kukan da take yi. Domin tun fil-azal idan akwai amintattun da ba cikinsu daya ba a gidan Marina to Yaya Ummi da Bulkachuwa ne. Akwai shakuwa da kauna a tsakaninsu mai yawa. A sanyaye ya ce "Ki yi hak'uri ummilolo! Ai yana fad'in hakan sai kuwa ta sake rushe wa da kuka na sosai. Don kuwa Bulkachuwa kad'ai yake ce mata ummilolo. Daada ma ta bare baki ta shiga taya ta suka dinga yin sa kamar me. Da k'yar suka yi shiru. Aliyu ya tafi jiki a sanyaye. Yana fad'in ba zan sake zolayar ki ba Ummi har sai d'an-uwan ki ya fito. Har dare babu nishadi a tare da mu. *Marubuciya Nazifa Nashe tana sabon littafi mai suna Gaskiyar lamari* *Ku bibiye shi , babu jira, babu nadama*. *Ku tuntube ta a wannan lambar* *08033748387*. *MARUBUCIYA* *BINTA UMAR ABBALE🍒* *Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers* *Tuni labarin ya fara nisa, yana kuma da dadi da darasi*. *08089965176* *07084653262* *𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍✍️ ★ALKALAMIN JIKAR NASHE📲 *GASKIYAR LAMARI* (New Book) Wattpad @Nazeefah381. Arewabooks @nazeefah. *Kina bibiyar wannan kasaitattan labarin kuwa?* *Babu jira babu dako, domin tuni an yi nisa.* *Tuntube marubuciyaar wa wannan lambar* *08033748387* *INA MATUKAR GODIYA GA FANS DINA NA AREWA* *NA JI DAD'IN YADDA KUKA YI SUPPORTING DIN RUBUTUNA. UBANGIJI YA KARFAFE KU, YA SHIRYA ZURIARKU*. *ZAN YI KEWARKU* *GA WADANDA BASU BIBIYI LITTAFAINA NA BAYA NA, ZAN KAWO MUKU SU AREWA AKAN FARASHIN MAI SAUKI*. *Godiya kan godiya ga jama'ar what's app, mussaman wanda suka saka kudinsu suka sayi wannan labarin*. *Na gode sosai, bazan gaji da gode muku ba*. *Yabo da jinjina ga y'an special wadanda nake basu ta private, na gode da soyayyarku ga rubutuna.* Sai washagari aka hak'ura da juyayyin rashin Bulkachuwa. Dada tun asuba ta yi wankan tafiya gano shi. Tana yi tana fad'in "Allah a saukakawa wannan yaro. A jibanci lamarinsa. Ya ci arzikin ma'aiki. Ya ci albarkacim Shehu mai karama". Da wuri ya kawo Iklima. Ya ce "Dada zan dawo idan an yi azahr zan kai ki gano mai sunan manya." Ta ce "Ina ce yanzu zamu tafi Ali?" Ya ce "Ai yanzu baza su bari ma a gan shi ba." Ta kyabe baki ta ce "Ina ce Ammar yana wajen? Ni da nake da kafa har a mini iyaka?" Ya ce "Yi hak'uri, ki bari na dawo, tiyatar haihuwa zan yiwa wata mata karfe tara zan shiga." Ta rausayar da kai ta ce "Shike nan sai ka dawo, ya zan yi?" Da ga dawo kuwa gabadaya suka rankaya ganin Tijjani. Ni da Babah kawai aka bari a gida. Da ga can zasu biya gidan Iklima su bar ta a can. Dada ta kalle shi ta ce "Mai sunan manya kana wuridin *RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN kuwa?" Ya ce "Ina yi sosai, ina kuma ganin tasirin ta Dada. Komai ya saukaka mini, na samu k'arfin zuciya da tawakkali, iyalina kuma suna cikin rufin asiri mai yawa ". Ta ce "Hakane, Hakane! Cikin tausayawa. Sun jima sosai suna shirin tafiya ta cewa su Yaya Ummi su yi gaba tana zuwa. Yaya Ummi ta kalle shi da idonta da suka yi ja. Da rawar murya ta ce "Yaya Bulkachuwa sai mun sake zuwa". Ya yi mata murmushi ya ce "Ummilolona kullum sai kin yi kuka? Kamata ya yi ki gode Allah ina rayuwa. Ban rasa komai ba sai y'ancina. Wanda duk ya zo kurku bisa zalunci sai ya samu daukaka, so ku tsananta yi mini addu'a ba kuka ba". Ta share hawaye ta ce "Allah ya nuna mini ranar da zaka fito Yaya Bulkachuwa sai na yi azumi uku da ikon Allah". Haka kawai ya ji ta bashi tausayi. Tun tana k'arama ta damu da shi ainun. Shima kuwa idan aka dauke Ihisan da su Aliyu ba shi da wata yar'uwar da ta wuce ta. Ya tabbatar ko bai auri Yabi ba, amincinsa da ita mai yawa ne. Sai aurensa da Yabi ya sake girmama amincin nasu domin ya sani, tana son Yabi fiye da komai. Shiyasa ta sake kaunarsa, ta kuma bada gudunmawar shawo masa kan Yabi matuka gaya. Suka tafi, su mama duk jiki ya mutu, tausayi ya ratsa jikin kowa. Sai da suka yi nisa Dada ta sassauta murya ta ce "Mai sunan manya wai anan din akwai d'akin sirri ne, ko kuwa a ina kuke haduwa da Yabi?" Kunya ta kama shi. Ya kasa ce mata komai. Ta ce "A a ba kunya zaka ji ba. Kawai ka fad'a mini domin idan cikin jejin can kuke shiga a samowa jinjirar taimako domin idan aka samu ciki da ranar Allah, kuma a fili irin haka aka yi tarayyar da ciki ya shiga to fa wannan yaron ko yarinyar rashin kunyar da zasu yi sai ya gigita kowa". Dariya ta k'wace masa. Ya yi kad'an ya gintse tare da ce wa "Ki yiwa Allah ki bar maganar nan haka. Ki nemo mata taimakon ki kuma tsananta yi mata addu'oi kawai". Ta saki ajiyar zuciya ta ce"Mai sunan manya abin ne yake ta bani mamaki to ta ina kuke kebe wa ne? Ga yarinya nan ta kwaso Aliyu amma cikin ikon Ubangiji doguwa ce sambal. Dazu ana mata wanka da na zuba mata ido gabobinta irin naka ne sak, haka gashin kanta. Oh ni Binta. Kullum ina kuka da zullimin rashin ka ashe kai baka fasa komai ba?" Ya murmusa ya ce "Kina sauke mini dala'ilalul khairati kuwa?" Da hanzari ta ce "Duk satin duniya kuwa. Ko wacce juma'a nake sauke wa. Kuma hadiyya ce a kanka. Mai sunan manya na ga gurbinka! Dakina a bushe, babu kayan shayi irin naka. Babu sabulai da turaruka irin naka. Ta hau kuka sosai. Jikinsa ya yi sanyi. Ya ce su Baban Kasuwa basa siya miki ne?" Ta ce "suna siya amma har sai sun k'are, kai kuwa kafin su k'are ka kawo wasu. Sabulai da turare masu kyau ba masu s'aukin kudi ba. Amma yanzu fa?" Ya ce "Ammar da Jabir basa yi miki ne Dada?" Ta kyabe baki ta ce "Jabiru kam ai yanzu fama yake yi da kansa. Har ya gama samun damarsa kuwa ban wani more shi ba. Kasan sun k'ullace ni akan ku. Wai nafi sonku. Iyayensa kawai yake yiwa. To yanzu an yi mutuwar kasko, kowa ma ya rasa. Shi kuwa Ammar yana yi mini bazan masa k'aharu ba". Amma sai ta waiwaya ta sassauta murya ta ce "Da uwarsa muke raba daidai. Idan ba'a hannuna ya bani kudi ba kuwa, basa zuwa mini". Ya yi shiru, tausayinta ya kama shi ainun. Abin da ya fahimta Baban Marina da mahaifiyarsa sun fi dukkan y'aya'nta yi mata biyayya da kyautatawa a gareta. Sune kuma wadanda ta rayu tana nuna musu rashin soyayya. Komai sune a baya. Amma kuma shi da kansa ya tabbatar Dada tafi sonsa akan kowa cikin jikokinta. Domin Ammar bai samu sukunin yi mata raddi da fito na fito da ita ba. Da ace shine yake da nutsuwarsa da bai san yadda zata ririta shi ba. Ya tuna sadda zai sadada ya kwashe mata yan kobbonta da kayan amafaninta ya siyar. Bata yi masa fada a gaban jama'a. Bari take sai dare ya raba kowa ya kwanta sannan ta shiga dakinsa su yi sababi, tana yi kuma tana ce wa murya kasa k'asa mai sunan manya kada a gane halin da muke ciki. Shi kuwa sai ya bude muryarsa ya ce "Aji mana tunda sharri zaki k'ala mini saboda kin washe ni. Duk yawan jama'ar gidan nan m, babu mai yi miki sata sai Tijjani! Nan da nan zata bar maganar ta ce "Alfarmar shehu zaka bari. Darajar sunan da ka ambata na yafe maka, Allah ya shirya mini kai, ya tsare ka daga hau da sharrin zamani". Ya nisa ya sake murmusawa ya ce "Ki yi hakuri zan fad'awa Aliyu ya dinga yi miki. Ki kuma cigaba da yi mini addu'a Dada. Sannan ki yafe mini ta'adin da na yi miki a shekarun baya. Da azama ta ce "Wallahi na manta komai. Kuma menene baka yi mini ba da ka samu dama? Aliyu kuwa ai shima a k'ullace yake da ni. Ya sha fad'a mini ina nunawa uwarku butanci. Wanda sharri ne kawai, to wa zai haifi d'a ya ce baya sonsa saboda Allah? Jiya kuwa a gidanka ya ce "Yasan nafi sonka a kansa. Sannan kasan matarsa d'iyar Alhaji ce, su kuwa gabadayansu sun kwashe kayansu a gaban ma'aiki akan sha'anina. Yabi ce kawai take mini sassauci, itama dan tasan ni da kai ba dai mutum ba. Duk tsiyatakunta, duk yadda ka jarabtu a kanta, ba zaka k'i jin kaina ba, ba zaka k'i ni ba! Ta fad'a cikin sigar tausayi. Ya saki gauron numfashi ya ce "Ki yi hakuri Dada. Za'a gyara. Yanzu ki daina damuwa. Sannan kada ki koma Toro. Ki zauna anan BAUCHI ki dan huta. Idan jama'a sun tafi zansa a kawo miki kaji Babah ta gyara miki, ki dinga cin abin ki. Idan sun kusa karewa za'a sake soya miki wasu. Sannan yanzu a hanya za'a siya miki kayan shayin ki, ki ajiye a wajen ki. Naki ne ke kad'ai kada Yabi ta yi miki k'auron nata". Ta yi maza ta ce "A a itama tana yi mini alheri, sannan tunda aka sakaye ka soyayya ta sake kulluwa a tsakaninmu, kullum muka hadu sai mun yi kuka. Kasan yanzu ta yi hankali. Gara na fad'i gaskiya ko ba haka ba". Ya yi dariya ya ce "Ho Dada ta Yabi. Tsoron ta kike ji ne yanzu?" Ta rausayar da kai ta ce "Uum kaidin mata mai yawa ne. Yanzun nan idan ta murde kai ma sai ka juya mini baya a kanta. Barta dai tunda ta nutsu, kuma tana mini ya kamata. A lallaba a tafi a haka, domin na riga na yi imani da kiararin da na ji ubanta yana yi mata. Na ce wa ita kad'ai gayya ce a gidan Marina. Ko kasan kaf zuri'ata babu mai ruwan kudi a hannunsa irin Yabi? Yadda na gasgata karamar Shehu haka na gasgata kudinta na halali ne. Ka ga yadda ta mayar da dakin uwarta ne? To ragowar matan uban ma duk ta yiwa dakunansu kwaskwarima lokacin auren Ubaida. Idan ka ga bajintar da ta yi a auren kuwa sai ka rik'e baki. Matar gwamna har tawaga ta turo su wakilce ta a bikin. Kofarsu tafi ko ina haske da kyawu yanzu, kuma duk ita ce. Ko kai ma irin yadda kake yiwa ubanta ai saboda ita ne. Yabi, Yabi duniya ce? K'aramar halitta sai babban al'amari". Ya kwashe da dariya ainun. Ta ce "Allah kuwa. Mata ai yanzu sun ri'ka. Idan basa yin ka to mijinsu ma ba zai maka kallon rahama ba". Ya sake yin dariya ya ce "Duk zan fad'a mata ne". Ta kyabe baki tare da ce wa "To hudawa cikinka wuka da kanka. Ta jima kafin ta dingisa ta tarar da su a mota suka tafi. ** *Watanni uku a gaba* Zuwa lokacin Husna ta yi gubibi da ita. Shayarwa na matukar ciko da Yabi . Saboda kirjinta suna cika, ita kam tana cikin mata kad'an da goyo yake karbarsu. Bata da matsalar komai sai ta rashin miji. Har zuwa lokacin Dada na tare da su. Ba zato ba tsammani Aliyu ya zo ya kwashe su aka yi musu passport. Sai da passport ya fito yake fad'a musu kudin hayar filling Tijjani ne. Shine kuma ya ce Yabi da Dada su tafi su yi Umrah su yi masa addu'a." Ai kafin ya rufe baki Dada ta zabge da kuka tare da ce wa "Ashe zan koma gabar ni Binta? Hauwa kin iya haihuwa! Shehu ya haifu. Allah ka yiwa Shehu abin da mai zato bai yi zatonsa ba ". Sai kuma ta rushe da kuka wurjajan. Aliyu ya ce "Ganin hakan ya sanya na biyawa tawa uwar sai ku tafi tare" Nan ma Dada ce ta yi fit ta ce "Wayyo Ali Allah ya yi albarka, yasa kai ma ayi maka tagwaye." Ya ce "Ai tuni ya bani Dada. Wadannan da suke gittawa ta gabanki ba nawa ba ne? Ko kuwa dan a gidan Marina kowa d'an da ya haifa ne nasa shiyasa kike ganin sai na haifi wasu tagwayen?" Da yake babu wata shak'uwa a tsakaninsu, asalima tsoro tsoronsa take ji. A sanyaye ta ce "A a kuskure ne, da mantuwa Ali. Yanzu dai ba zamu yi fad'a ba, bayan ka zo mana da babban albishirin da babu irinsa. Allah ya saka da alheri, ya yi muku albarka gabad'aya". Ya ce "Ameen". Babah itama ta yi masa godiya da fatan alheri da bunk'asar arziki. Yabi tana bude baki ta ce "Na dad'e ina son na tura Baban Marina Umrah. Na dad'e ina fatan na yi masa ba zata. Ta ce zan tattara abin da nake da shi a yi tafiyar nan da shi". Idon ta ya ciko da k'walla tana ayyana yadda Baban 2 yake fatan ya kai ta Makkah. Ashe abin na ransa, ashe itace zata riga shi zuwa Sau'udiyya? Hawaye ya tsinke mata. Babah ma ta shiga taya ta. Aliyu ya ce "Maimakon ku yi masa addu'a sai kuma ku yi masa tukuicin kuka?". Cikin kuka sosai Dada ta ce "Kai ku yi kukanku da kyau kun ji ai! Ali ai dole mu yi kuka. Yau sama da shekara Shehu na garkame a haka aka samu rabon Asma'u. Kai rabon haihuwa zazzafa ne". Aliyu ya ce "Kai Dada da fitina kike. Me ya kawo wannan maganar a yanzu kuma? Sannan kuma Yaya Tijjani ne ya koma shehun ko kuwa?" Ta ce "Eh shi fa. Tunda ga y'aya'nsa na girma ai gara na tsayar masa da suna d'aya. To na zabi Alhaji Shehu kawai domin sha Allahu wataran zai zama Alhaji da ikon Ubangiji kuwa". Ya gintse dariyasa ya ce "Ni na tafi, tunda Yabi ta had'a ni da aikin dauko Baban Marina gobe". Sai lokacin na ce "Tare zamu je, zan duba yaron Adda Nazira da ya yi targade." Ya ce "Tom in sha Allah". Babah ta ce "To kuma ya zaka yi da wannan kilifar ne tunda bata isa yaye ba. Watanta uku kacal" Ya ce da ita zaku tafi mana". Dada ta ce "Allahu akabar! Yabi ta haifo Yabi." Ya kwashe da dariya ya ce "A a Dada. Ai Yabi wadda aka haifa a hanyar sau'udiyya dan aikin Hajj ne ko aka je da cikinta. Ita kuwa wannan ai an riga an haife ta, sannan Umrah zaku je ba tawwali ba". Ta ce Hakane, sai ace mata Ummara Husna. Domin na tabbatar sai ta yi jidalin Asiya idan ba'a ce mata Ummarah ba. Oh ashe dai da rabon burin Yabi na zama Hajiya a kusa zai tabbata. Nasan Shehu ya biya mini ne dan na kula da ita, na jagorance ta a wajen sa'ayi da safa da Marwa". Ta bawa Aliyu dariya ainun ya ce "A Ina zaki jagorance ta din? Ai ko ke yanzu kika je d'aya zaku zama, ko wanda ya je bara idan ya koma bana sai ya ga abubuwan da bai san da su ba. Saboda yadda gwamnatin Sau'udiyya ta mayar da hankalinta akan Makkah da Madina gabad'aya. Bare ke mai shekaru ashirin da biyar da zuwa, ina ce da kika je ma ba'a haifi Anas ba?" Ta rausayar da kai ta ce"Ko Yabi yayarsa ma ba'a haife ta ba. Kasan ana daf da aihuwata ta Alhaji ya hadu da sharrin masu zamba cikin aminci, aihuwarta ta zo cikin wani irin yanayi mai tsananin gaske ". Na hauro na ce "Dada kina son fad'an wannan labarin. Nasan idan tafiya ta mika zaki k'arasa abin da kuke fad'a cewar ni na kore masa arzikinsa". Ta kama baki da azama ta ce "Yabi ki yiwa darajar Alhaji da Asma'u kada ki birkice mini. Ko mahaukaci ya ji labarin ki da irin bajintar da kike yiwa uwa da uba ai yasan ke din arzika ce ba wai Yabi ba. Yo duk gidan Marina akwai wanda bai ci arzikinki ba ne? Babu shi Wallahi. Allahu ya huci zuciyar ki. Bazan sake ba. Kai Ali tashi ka yi tafiyar ka, nima alwallah zan yi na yi munajiti da Ubangiji. Kai ma ka yawaita zikirrn ambaton Ubangiji ko na istigifari, ko da kuwa tukin mota kake yi ". Ya yi dariya ya ce "Wato da Yaya Tijjani da Nasiba da Yabi sune maganin Dada." Na dauke kai na ce "Kada ka sani Yaya Aliyu! Baban 2 da Nasiba dai. Tun fil-azal sune zasu yi sa insa da ita ta yi mukus. Amma ni kam menene bata yi mini ba?" Ta yi shiru ya kasa ce wa komai. Sai Babah ce ta fanshe ta da ce wa "To marasa kunya ta yi din. Suma wadancan din waye su da zasu yi maganin uwarmu? Ai tunda aka yi sa'a tana tsananta ibada komai zai daidaita mata." Da haka aka bar maganar domin jikin Dada ya yi sanyi. *INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA* *ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA* *HAKA NAN AKWAI WASU DAGA CIKIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA HAFSAT C SODANGI, SUMA SOFT COPIES* *HAJIYA HANNE ADO ABDULLAHI?* *MARUBUCIYAR WANKA DA GARI DA KUMA WACECE UWA?* *TO ITA MA TAKANAS NA SAMO MUKU LITTAFANTA DOMIN KUN SANI TA YI RUBUTUN MASU MA'ANA*. *LITTAFAN DA YAWA, AMMA AKWAI DISCOUNT DOMIN SO NAKE KU YI TA SIYAWA Y'AYA'NKU DA KANNENKU LITTAFAI MASU DARASI DA MA'ANA*. *BA DA JIMAWA BA ZAN ZO MUKU DA SU*. *0803277333*. Da kaina na je Toro na sanar da Baban Marina cewar Tijjani ya biya mana Umrah ni da Dada Aliyu kuwa ya biyawa Babah. Ni kuma na biya masa. Ya yi k'asa kansa tsawon lokaci bai yi ko da motsi ba bare ya yi magana. Ya jima kafin ya d'ago. Na ga hawaye jagejage a fuskar sa. Nima nawa hawayen ya kwace mini amma ni kam na farincikin yadda Ubangiji ya yiwa fafutukar sana'ata albarka nake yi. Domin bani da burin da ya wuce na sanya Baban Marina farinciki tun ina mitsitsiya ta. Gorin da ake mini, haihuwa ta ce ta tsiyata shi. Da kuma bak'in cikin yadda ya zama koma baya a cikin gidanmu na matuka mintsinin zuciyata. Da k'yar ya yi jarumtar ce wa "Na sha fad'a miki ke kad'ai gayya ce Asiya. Na fad'a miki zaki yi albarka. Na dad'e ina fad'a miki akwai lokacin da zai zo da kowa sai ya so ki har makiyan na ki. Ga shi na fara ganin sakamakon alherin da Ubangiji zai yiwa hak'uri da juriyar da kika yi a rayuwar ki. Allah ya yi miki albarka. Daga nan har kasa ta rufe mini ido na yafe miki, kina cikin farar addu'a ta. Allah yasa y'aya'n ki su yi fiye da ke. Allah ya miki tukuici da alheri. Kin yi hak'urin aure, kin yi juriya. Da ikon Allah ba zaki sake fuskantar tsanani a gaba ba." Ina kuka na ce "Allah ya amsa Babanmu! Na gode Allah ya k'ara lafiya. Ya ce "Ku tafi da gyatumar ki Yabi. Kin ga dukkanku mata ne. Da ikon Allah zaki kai ni." Na girgiza kai na ce "Zata je Baba! Amma wannan kudin na tara kaso uku cikin hudu da sana'ar da na rayu ina yin ta. Kai nake son ka je, dan ka ji dad'i ka kuma godewa Ubangiji da ya jarrabe ka da fitinar yan'uwa. Sai kuma ya baka y'aya'n da zasu sadaukar da komai dan ka yi murmushi. Ka je ka yi mana addu'a. Ka kuma tayamu addu'ar Ubangiji ya kubuto mana da Tijjani ". Sai kuka na sosai ya k'wace mini. Abin mamaki sai shima ya taya ni kukan muka dinga yinsa a hankali. Da yake a dakin Gwaggo yake. Ta shigo da Husna a hannunta da ta fara kukan neman nono. Ta tsaya cak bata miko mini ita ba. Ta sassauta murya ta ce "Ayyah Yabi baki ga kullum girma sake kama shi yake ba? Me yasa kike kasa hak'uri a idan kina gabansa? Kin san yadda kukan ki yake rikita shi kuwa? Kalli irin kukan da yake yi mana. Me yasa kike rasa dukkan jarumtar ki a gabansa?" Na kasa magana. Sai shine ya ce "Ni ne nake rasa dukkan jarumtata akan lamarin Yabi. Tana matukar bani tausayi, kuma dama ita ce raunina a cikin dukkan y'aya'na. Shiyasa Ubangiji yake ta jarabtata akan sha'anin ta. Tafi kowa shiga garari da kalubalen rayuwa. Asma'u ki ji tausayin ta?. Ki sake ninka addu'ar da kike yi mata. Zauna a zaune ki ji al'amarin da ta zo da shi." Yana hawaye ya fad'a mata zuwn nawa albishir na yi masa zai tafi gabas. Yana rufe baki itama ta fara hawaye tana fad'in Allah mun gode. Ina taya Yabi godiyar yadda ka cika mata burin ta, na mayar da Alhaji dakin ka. Allah ka k'ara yaukaka mata arziki, ka shirya mata zuria. Ka mata tsari da dukkan abin da zai cutar da ita ko iyalinta". Ya k'ira Mama da Inna ya fad'a musu alherin da ya same su ya rufe da ce wa kada su fad'awa kowa sai abu ya kankama. Domin tafiya gabar kiran Allah ne. A gurgurje na je gidan Nazira na dubo yaronmu. Da yamma muka juyo da Yaya Aliyu akan gobe Baban zai zo BAUCHI don ayi masa passport. Ba a fito da maganar tafiyarmu ba sai da komai ya kammala ya rage saura kwanaki hudu. Baban Marina da kansa ya fad'awa y'an uwansa cewar zasu tafi Saudiya. Da Yabi da diyarta da Dada Tijjani ya biya musu. Aliyu ya biyawa Hauwa. Shi kuwa Yabi ce ta biya masa. Suka ka'du k'warai. Amma da yake dangantarsu ta yi tsami ainun kowa ya hadiye a ransa tunda yanzu so suke ace kowa yafi kusa da Baban Marina a tsakaninsu. Sannan basu gamsu Yabi ce ta biya ba. Duk da dai sun yi matukar sikewa da lamarinta tun auren Iklima. Zuwan tawagar matar gwamna Toro gidan Marina ba k'aramin cece kuce da girmama lamarin Yabi ya janyo ba. Ranar talata da asuba muka nufi Kano tunda an ce shabiyun rana zamu tashi. Karfe tara a airport din ta yi mana. Aliyu bai tafi ba sai da ya ga tashinmu. Sannan ya juya da twins da Ikilima da suka yo mana rakiya. Hamim sai kukan sharbe yake yi. Hanif sai hak'uri yake ba shi yana ce wa "Mun girma fa Hamim. Ammi ba dadewa zasu yi ba. Ba ta ce addu'a zasu je su yiwa Baban 2 ba? Husna zata raina ka fa". Suka bawa Aliyu tausayi. Haka kawai yaran suke ba shi tausayi ainun. Bai bar Kano ba sai da ya siya musu kayayyakin wasa da na ciye ciye dan su warware gabadaya. Kai tsaye a Madina muka sauka. Mun gaji likis. Dole muka kwanta. Dada sai addu'a take yi tana fad'in "Allah k'amshi ya cika hancina, haske ya cika idona, k'arfi ya yiwa gangar jikina k'awanya, farinciki da imani sun cika zuciyata. Allah ka karawa Annabi daraja. Allah ka karbi addu'ar da zamu yi, ka bamu k'arfin da zamu yi ibada ta gaskiya." Sai ta zauna. Sai ta zabura ta je jikin windo tana leken asumayar masallaci ma'aiki. Tana kuka tana fad'in "Rabbani yadda ka sake yi mini gatan ganin koriyar gubba ta d'an Amina mai wuyar ga ni. Allah kasa zan gan shi da idona. Allah ka bani ikon rokon gafararka idan na shiga rauda. Allah ka shirya mini zuria, ka jefa soyayyya a tsakanin ahalina. Allah na yi tuba. Allah mai babban suna aiko ni ya yi takanas, Ubangiji a karba a sassauta a kubuto da shi albarkacin masoyinka Baban Nana". Duk juyin da zan yi zan ga idonta biyu. Babah kuwa barci ta yi sosai domin bata runtsa ba a jirgi, ita take ta fama da Husna. Daf da asuba muka tashi, muka yi alwallah muka nufi masallaci. A harabar hotel din muka had'u da Baban Marina shima ya fito zai tafi. Na kalle shi cikin sabuwar jallabiyar da na siya masa guda uku a Kano. Ya yi fes da shi. Garin Madina rahama ne. Gabadaya zukatanmu cike suke da shauki da rauni. Duk juyin da muka yi da Dada ta saka silifas din ta. Ce wa ta yi "Wane mutum ta taka k'asar Madina da takalmi? Mu dai da muka ga zamu taka ba zata ce komai ba. Allah ya yafe mu kawai" Kan dole muka k'yale ta. Domin har muka yi kwanaki biyar a a Madina bata yarda ta saka ba. Duk ranar da aka yi ranar juma'a ma haka ta tako. Sai da muka shiga motar tafiya Makkah sannan ta saka takalmi, tana hawaye tana fad'in "Allah ina son na sake dawowa. Idna ban samu damar ba, na yi godiya. Allah karbi addu'ar da muka yi." A Makkah kuwa har tausayi suke bani tunda muka je dukkanmu a masallaci muke kwana. Mu yi sallah, mu yi dawafi. Duk shekarun Dada bata zama. Ko dan yar firit ce irina? Ban sake gasgata komai na Dada na kwaso a halitta ba. Sai a tafiyar nan da muka yi. Kamar da muke yi ta baci. Na tsinci kaina da addu'ar kada Allah yasa na yi halinta idan shekarun girma suka cimma ni. Tunda ta sha fad'ar hatta fad'an da na yi ina karama itama haka ta yi a lokacin kuruciyarta. Baban Marina kullum sai ya ce "Dada yau ki kwanta ki huta, Hauwa ke ma ki huta, Ubangiji ya ji addu'ar mu da ikon Allah Tijjani zai fito. Idan kuwa har muka ga bai fito ba, to tabbas zamansa a can yafi alheri. Ku duba shekarun da Annabin Allah Yusuf. Da'n Annabin Allah Yakub, d'an Annabin Allah Ishaq, d'an Annabin Allah Ibrahim A.s. ya yi a kurkuku. An tambayi Annabin Rahma wanne mutum ne yafi kololuwar daraja da nasaba, sai ya ce D'an uwana Yusuf A.s. Amma ya yi shekaru masu nauyi a sijin. Hakan bai zame masa tawaya ba, sai ma k'ara masa kusanci da Ubangiji ya yi. Bayan ya fito kuma Ubangiji ya karrama shi daga bawa ya koma shugaban kasa, kuma babban d'an majalisar sarki." Dada tana kuka ta ce "Hakane Alhaji amma tunda zan iya bari kawai na yi ibada tuk'uru. Na nemi gafarar Allah, na nemi soyayya da tausayi da afuwa ta wanzu a gidan Marina. Bar ni na yiwa Shehu addu'ar ya fito ya cigaba da walwala cikin iyalinsa. Yabi kad'ai idan na kalla sai na ji kuka, bare y'aya'nsa. Ni dai na yafe maka Alhaji. Kaima ka yafe mini". Sai ta kece da kuka. Ya rik'e ta a jikinsa ya ce "Sha'anin uwa ai mai girma ne Dada. Hakkin haihuwa kad'ai ya isa ayi mata biyayya, a girmama sha'anin ta. A kuma dauwama ana rokar mata alherin duniya da na kiyama. Ban kullaci kowa ba bare ke da aljannata take damafare da sawunki." Cikin kuka ta ce "Albarkar d'aki ka rabauta duniya da lahira Alhaji". ** Kwanakinmu goma a Saudiya. Saura kwanaki biyar mu koma gida. Addu'a kam mun yi ta sai fatan alheri ya biyo baya. Imani ya sake cika mini zuciyata. Na ji sassauci mai yawa akan kullatar da na yiwa mutanan da suke gwada mana rashin kirki. Sai na fahimci afuwa da yafiya suna warkar da zuciya, suna sake girmama mutum a wajen jama'a da wajen Ubangiji. Kwatsam na kunna wayata sai ganin status din danginmu nake babu kakkautawa dauke da hotunan Baban 2 babu kakkautawa Jikina ya sab'e da rawa na kasa gane me suke rubutawa domin gabad'aya na rikice! *Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Saiwowin maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. * Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya* *08032773332* *Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.* *Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐, ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To albishirinki yar uwa!* *UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1 *Kawata Janafty zata yi muku reposting din littafin Zaman Gidanmu*. *Kada a manta da littafan marubutan Dab'i* *Hajiya SALIHA ABUBAKAR ZARIA* *Hajiya Hafsat C SODANGI* *Hajiya Maryam Kabir Mashi* *Hajiya HANNE ADO ABDULLAHI* *INA KAWO MAGANIN GYARA MASU KYAU DAGA CHAD DA SUDAN* *MAGANIN SANYI SADIDAN* *INA AIKAWA KO INA A K'ASAR NAN* *BA ZAI YIWU NA TALLATA MUKU ABIN DA BA SHI DA KYAU KO INGANCI BA. DOMIN SOYAYYA DA AMINCI NE A TSAKANINA DA KU MASOYA RUBUTUNA* *KU JARRABA SAIWOWIN DAHUWAR KAZA DA TATTABARU KU GA NI* *KAZALIKA MAGANIN SANYI DA TSUMIN GORAN TULA BABU NA BIYUNSU* *GA Y'AYA'N GADALI DA YAKE SHA YANZU MAGANI YANZU* *ASALIN DAKA NA EMERGENCY* *DA GUMBA DA KUMA TSUMIN KWAKWA DA ZUMA NA SHARHOLIYA* *TUNTUBE NI KAWAI TA WHAT'S APP.DAN SAMUN BAYANI NA SOSAI* *KU GYARA KANKU, KU GYARA Y'AYA'LNKU* *MASU SHIRIN AURAR DA YARANSU KO KANNENSU A ZO A SAMA MASU KAYA MASU NAGARTA* *08032773332* *NA GODE* *Alhamdulillah! Alhamdulillah!* *Nasararorin da na samu a wannan labarin tabbas daga Allah ne* *Na gode masa da ya bani lafiya da azanci*. *Na gode masa da ya bani ikon sauke nauyinku, na gode da ban ja muku rai ba*. *Idan rayuwa da lafiya sun cigaba da wanzuwa mini zamu sake haduwa a wani sabon littafina*. *Idan kuwa ba'a samu damar hakan ba, to na gode muku gabad'aya da soyayyarku ga rubutuna* *Allah ya shiryemu ya shirya zuria.* *Wallahi ina matukar alfahari da duk wacce ta saka kudinta ta siyi wannan labari*. *Ubangiji ya fini yabawa, ya rufa muku asiri duniya da lahira*. *Lokaci ba zai bani na kama sunan kowa ba*. *Domin shafin ya yi kad'an na zayyano sunayen mutanen da suka yi mini karamci ta sanadin rubutu*. *Labarin Bakar Taada ya janyo mini mutanen da basu san komai ba sai alheri*. *Mahaifina a lokacin da yake raye yana yawan ce mini ke y'ar gata ce Surayya* *Na gasgata shi, domin kullum Ubangiji cikin kewaye ni yake da rufin asiri mai yawa, yana ta had'a ni da mutanan arziki da suke ta mayar da ni gayya a cikin jama'a* *Na gode sosai Allah ya kewaye y'aya'nku da rufin asiri mai yawa*. *Zan yi KEWARKU Wallahi!*. Na nutsu na lalubo na Aliyu sai na ga hoton Bulkachuwa sannan ya rubuta Barka da samun yanci Yaya. Allah yasa wannan al'amarin ya zame maka tsanin shahararka a duniya." Na bude murya sosai na ce "jama'a Tijjani ya fito, an sake shi. Gabadaya na rikice, na rikita su. Da k'yar na nutsu na musu bayani. Dada aka fad'i aka yi sujjuda. Ni da Baba muka yi maza muka but bayanta muma muka yagi sukjadar. Ta zabura ta ce "Haramin zan koma. Duk da dare ne bamu hanata ba, muma muka bi bayan ta. Bayan mun je dakin Baba baya nan tabbacin yana masallaci a can zai kwana. Duk son mun gan shi bamu samu zarafin hakan ba. Sai da gari ya waye muka dawo masauki. Ai kuwa gabadaya muka kutsa dakin da yake ciki. Muka hau rigen yi masa albishir. Muna tare a dakin Aliyu ya kira ni vedio call. Aka gaisa aka yi murna, ya nuno mana fuskar Tijjani da ya kare da hannu. Da k'yar ya ce "Ina gaishe ku gabadaya. Na gode sosai. A kuma sake yiwa Ubangiji godiya. Duk yadda nake jin dad'i a Makkah amma sai na ji kwnanaki hudun da suka rage gabad'aya sun mini tsauri. Ji nake tamkar na bude ido na gan ni a BAUCHI. ** *Yadda al'amarin ya kasance* Rundunar ta gurfanar da Alhaji Auta a gaban kotu domin da kansa ya kai karar kansa ofishin y'an sanda ya tabbatar musu laifinsa akan abin da ya yiwa Tijjani. Cikin kuka ya ce "Na aikata BAK'AR TA'ADA, na bari sharrin zuciya da shaidan sun janyo mini wahala. Tunda aka rufe yaron nan. Al'amarina ya sake kacame mini, kullum masifu sake yi mini k'awanya suke yi. Dan haka na zabi na kubuta daga azabar lahira. Tiryan tiryan ya yiwa y'an sanda bayani yadda ya shirya komai. Take aka k'ira yan jaridu na radio da talabijin ya maimata a gabansu. Nan da nan abu ya watsu a BAUCHI da kewaye ko ina maganar ake yi. Sai Allah wadai ake yi da halin Alh Auta. Wasu kuwa su ce ya yi sa'a ma da ya zabi ya fadi gaskiya ya samu sassaucin kwanciyar kabari. Wasu kuwa su ce Yasin aka yi ta buga masa da alkunut shiyasa ya kasa gaba ya kasa baya har sai da ya fito ya lashe amansa. Mai dakin gwamna na zaune a katafaren falonta tare da mai girma gwamana suna kallon N.T.A BAUCHI. Suna kallon yadda kae nuna Alh Auta kai tsaye (live) yana bayanin tuggun da ya had'a. Take ta tuna labarin da Yabi mai lalle ta yi mata. Nan da nan ta ce "Yallabai ka yi magana a gaggauta sako yaron d aka yiwa kaAmzfin nan babu dogon turanci. Ina sake rokon gwamyta bashi Wani abu na diyya bisa samaye shi da aka yi babu laifinsa. Sannan a gaggauta gurfanar da wannan tsohon banzan a gaban kuliya. Idan ka gaggauta sakinsa tare da yi masa wani alheri jama'a zasu sake son ka su tabbatar adali ne. Tunda a yanzu babu abin da zai dauki hankalin al'ummar BAUCHI irin wannan al'amarin ". Take kuwa ya dauki waya ya yi magana da mahukunta. Kasa da awa daya aka.gata ganin Tijjani a talabijin, tare da jajanta masa. Gwamnati kuma ya bashi kyautar milyan ashirin bisa bata masa lokaci da suna da aka yi. Bayan haka take gwamna ya bashi S.A. wato mai bashi shawara akan gidajen gyaran hali. Ba a jima ba sai ga hukumar kare hakkin dan Adam sun dauke shi aiki. Haka ta costom da kuma hukumar kula da kiyaye safarar k'waya da tu'ammali da ita. N.D.LA. Cikin yini daya tak sai da aka yiwa Tijjani aiki tayin aiki a ma'aikatu biyar. *KAWATA JANAFTY ZATA SAKE REPOSTING DIN ZAMAN GIDANMU, za Kuma ta kai shi AREWA*. Ganin hakan gwamna ya sake ce wa ya bashi aiki a a ma'aikaar aikin Hajj. Da albashi mai tsoka. Wajen da aka bawa Tijjani duk shekara sai ya samu gurbin kujerar aikin hajji d'aya ko biyu. Ga shi babban mai bawa gwamna shawara. Ga milyoyin kudi. An sha wahala, an yi bak'in ciki, amma a karshe sai alheri da daukaka ya biyo ba. Yanzu da aka gurfanar da Alhaji Auta a gaban shari'a sai aka yanke masa kwantankwacin shekarun da Tijjani zai yi. Bisa kama shi da zambo cikin aminci, da kuma yiwa k'asa da jihar BAUCHI zagon kasa. Ga mamakin alkali sai Tijjani ya mike ya ce "Ni dai laifin ya yi mini na yafe masa. Allah shine shaida na yafe masa, ubana ne, sharrin zuciya ne d azal ya hau kansa. Tare suka yi gwagwarmaya da mahaifunay. A saddna naje gabansa da nufin ya taimake ni ya bani sana'a bai ki, ba asalima ya daukake ni a cikin yaransa. Maganar filina d aka karaba ba nasa ba , shaidan ne ya shafi kirijinsa. Da yawa mutane basa iya tsallake tarkon kyashi da hassada. Dan haka na yafe masa. Allah ne shaidar hakan". Mafi yawan mutanan sai da suka yi kuka. Suna ayyana da ace mutane irin su Tijjani ne suka fi yawa a duniyar da ba a shiga tsananin da ake ciki ba. Abin da ya yi ya sake zaburar da jama'a girman afuwa da sassauci. Take kotu ta zabtare shekaru biyar a cikin bakwai aka mayar masa shekaru biyu, wanda wannan hakkin cin amanar gwamnati ne bata yafe ba. Sannan ya zama gargadi ga masu son k'ulla sharri haka siddan. Gabadaya kafafen sadarwa labarin da ake tattunawa akai. Cikin rakiyar jami'an tsaro aka ki shi gidansa. Aliyu ne da su Yaya Salisu da Yaya Ammar suka tarbe shi. A ransa kuwa so ya yi ace ya tarar da Babah da Yabi da kuma Dada. Ya tabbatar ukun nan suna gaba da komai a rayuwarsa. Domin ya sani Dada ta so shi hakikanin soyayya. A daddafe kwanakin suka cika muka tattaro muka dawo cikin tsananin farinciki da murna. Aliyu bai samu sukunin zuwa daukarmu ba. Muna dira ya kira Baban Marina tamkar mai auna lokaci. Ya ce mu dauko shatar mota ta kawomu. Da yake karfe takwas muka sauka a Kano na safiya. Hakan kuwa muka yi. Ban tab'a ganin nisan tazarar Kano zuwa BAUCHI na sai yaiy. Jin na yi gabad'aya na kosa. Haka muka isa Lafiya muka tarar da gida cike da mutanan Toro da na Bulkachuwa. Ana murna tare da dawowa lafiya. Na kalle shi yana kan kujera ya yi wanka yana sanye da k'ananun kayansa. Ya rame kam. Amma ya yi kyau. Ya yi aski saisaye. Ya yi fes, twins suna gefen hagu da damansa ma'ana sum sanya shi a tsakiya. Sai satar kallon juna muke muna murmusshi. Gabadaya mutanan da suka cika gidan sun gundure ni. So nake kawai su kauce su bamu waje. Sai la'asar suka dunguma suka tafi Toro tare da Dada da Baban Marina. Yayin da Aliyu ya tafi da Baba da twins gidansa. Kafin ta koma Bulkachuwa tunda Tijjani ya fito. Bamu samu sararin marabtar juna ba sai da ya dawo daga sallar Isha, ya rufe gidan. Ko da mutanan Toro suka tafi, jama'ar unguwar sai shige dagice suke mana da sunan murna da kuma yi mini sannu da dawowa. Da kansa ya yiwa Husna wanka yana ta tsala kukan kiwa. Daga karshe sai na fahimci da ruwan zafi sosao ya yi mata. Dan haka kukan har da dalili. Ya shafe ya da mantaleta, ya Sha nono. Ba'a jima da yin wankan ba kuwa barci ya sure ta irin mai nauyin nan. Daga haka ya tisa ni a gaba da rawar jiki. Bamu iya ce wa komai ba illa barin da jikinmu yake yi. A matukar matse muke da juna. Abubuwan da suka biyo baya masu nauyi ne. Sai dai bai yarda min yi barci ba, wanka muka yi muka dinga sallar godiya. Dukkanmu kuka muke yi. Domin al'amuran da muka tsallake taimakonsa ne kawai. Ba dan ikon Allah ba da tuni aurenmu ya dad'e da daidaicewa. Muna cikin bala'in asiri sai kuma k'azafi da hassada ya sake gigitamu. Amma cikin hucewar Ubangiji komai ya wuce. Da asuba ma da ya dawo rufe gidan ya sake yi. Dai-dai loakcin Husna ta farka. Na canja mata pampers da ta cika shi da fitsari. Na d'ora ta kan fo. Na gyata ta sha nono sai ta sake komawa barcinta. Na kwantar da ita a gadonta tunda Hajiya mai magana da yawun first lady har gado ta kawo mata na garari lokacin haihuwar ta. Na lallaba na shige jikin Tijjani domin barci da gajiya ne a jikina ainun. Tara muka tashi shima kukan Husna ya tayar da mu. Ya bude ido ya ga na yi mata wanka na ina shirya ta. *Ba da jimawa ba zan kai Sabo da kaza da Kuma Halin Yau arewa*. Ya mik'e ya ce "Asiya rabon da na yi barci haka da safe har na manta. Wato mutum baya gane darajar y'anci sai ya rasa y'ancinsa. Gidan gyaran hali babu dad'i! Masifar da na gani ko makiyina bana fatan ya shiga wajen nan. Sannan babu abin da yake sake rikita ni irin Barnar da ta yi katutu a wannan wajen. A had'a masu k'ananun laifuka da manya. Sannan gwamnati bata yi tsarin yiwa masu laifin allurar kashe sha'awa na wani lokaci ba. Ko kinsan luwadi ya yi yawa a gudajen kurkuku?" Cikin gigita na ce "Subhanallah! Ya rausayar da kai ya ce "Barna kan b'arna sai dai kawai Ubangiji ya yafe mana. Abin tausayi wani abin da ya sata bai fi dubu biyar ba, amma rashin gata ya sanya an daure shi sherkaru sama da goma. Wani sharri ne irin nawa, wanni sawun barawo ya taka. Wani bisa kuskure ya aikata laifin. Amma duk an runtse ido an ki yiusu sassauci ta ya ya rayuwa ba zata tsananta mana ba? Addu'ar wadanda aka zalunce su babu hijabi. Sannan yanke hukunci babu hujja yana janyowa al'umma fishin Ubangiji. Bakar Taada ta shiga ko ina a wannan duniyar Asiya." A raunane na ce "ALLAH ya shiryemu ya kuma kawo mana fita. Na yi matukar tsorata da yadda ake b'arna a gidan da ake masa lakabi da gidan gyaran hali. Kwnanaki biyu da fitowarsa muka sami saukin zaryar jama'a. Takanas aka turo mota daga gidan gwamnati. Domin na yi waya da Hajiya akan ina son zu je mu yiwa first lady godiya. Domin na sani abubuwan da aka yiwa Tijjani na alheri har da arzikina da ya ci. Muna zube a gabanta, muna ta godiya. Mai girma gwamana ya ce "Tijjani kana ta sun gurbin aiki a ma'aikatu daban daban saboda a tayaka alhinin halin da ka shiga. Amma Hajiya ta ce "Wanda muka baka zaka yi. Domin ta dad'e da yiwa matarka al'kawarin zata fito da kai, bisa adalcinmu muka jinkirta sai azumi sai ka shiga sahun wadanda gwamnati zata yafe musu, duk da laifin ka mai girmane. Sai kuma gaskiya ta yi halinta. Hajiya ta roki arzikin na rik'e mata kai da kai da kyau dan matarka ta huce wahalar da ta sha ta rashinka. Dan haka zaka zauna a jihar me dan al'ummarka su amafana da kai." Tijjani ya hau godiya da murna, yayin da kaina ke kasa nake taya shi godiya. Cikin kasaita first lady ta ce "Sai a kula, a kuma rik'e mini diyata da kyau domin samun yarinya jaruma ikarama kamar Asiya za'a dad'e . Mace ce mai kamar maza. Na shiga zullimi akan sha'anin ka. Saboda soyayya da sadaukarwa da na ga ni a wajenta. Tana son ka. Ka rik'e a ranka ba zan laminci ka juya mata baya ba". Ga mamakin Tijjani sai ya ji gwamna ya ce "Hajiya yo me yi miki shara ma ai ta wuce ta yi boranci bare y'ar boko irin wannan mai cike da kuruciya." Tijjani ya ka'du k'warai da gaske. Domin ya fahimci tasirin da uwar dakin Yabi yake da shi a wajen mijinta. Sannan ya gane dukkan alfarmomim da gwamnati ta yi masa da iznin Hajiya ne. Ita kuwa saboda Yabi ta yi hakan. Da gaske nasararorin rayuwarsa na d'amfare da Yabi ne. Ya sake yin kasa da kai ya shiga yi mata godiya tare da ce wa ", Za'a kiyaye Hajiya!. Ni kuwa murya na rawa na ce "Na gode mamana. Na sani mahaifiya daya ce, amma idan mutum ya girmama mutane, ya sanyawa harshensa linzami akan sha'anin da ba nasa ba, sannan ya yi gaskiya da juriya sannu a hankali sai Ubangiji ya bashi uwaye masu yawa. Tabbas ina da mahaifiya. Amma ke din uwa ce a waje na. Allah ya kara miki lafiya. Ina fatan idan kin kammala shekarun biyar din data yi muku saura ki zama first lady din Nigerita ba iya ta jihar Bauchi ba." Dad'i ya kama su daga ita har mijinta. Da barin baki ya ce "Ameen yarinya. Hajiya me za'a bata tukuicin wannan farin fatan da yi mana gabadaya?" Da murmushin kasaita ta ce "A maye mijinta da gurbin Kwamishinan ma'aikatu da ya rasu satin da ya wuce mutane suke ta zawarcin kujerar." Ya ce "Angama ranki ya dad'e Tijjani ka zama kwamsinan ma'aikatu na jaha gabadaya. Zan mika sunanka majalisar zartawa ka zama cikin shirin zasu gayyace ka domin tantace ka". Gabadaya muka rikice da murna da godiya. Yayin da ta ce "Ita kuma a mayar mini da ita wata ma'aikata haka mai dama". Take ya buga waya akan a kai ni college of education a matsayin non academic staff.". Ta sake ce wa idan har na zama first lady din k'asa Asiya ki dinga jin ke ce magajiyata." Na ce "Ina godiya k'warai mamana, alherinki mai yawa ne, ba kya fad'ar magana da zummar wake. Allah ya kai fata mizani". Muka taho cikin rakiyar jami'an ican tsaro. Kafin kace miye har an sanar gwamna ya nada Tijjani Yusuf Bulkachuwa a matsayin kwaishinan aiyukan jihar. Ta ko ina murna ake yi. Da kansa Tijjani ya sake gane al'amarin Yabi babba ne. Tabbas ita ce sababin arzikinsa. Sana'ar lallen dai da aka ce zata rike su itace sanadin zargo musu hamshakan matan da suka sada ta da mai dakin gwamna. Babu abin da zai ce da Yabi da sana'arta sai Hamdala. Zai cigaba da girmamata tare da kauce wa dukkan abin da zai had'a su. Domin ya ga ta k'ra wayo. Ta hadu da manyan mata da zasu yi masa fatafata idan ya ce zai taka ta. A ransa sai fad'i yake gwamna na tattala bacin ran Hajiya, bare ni?. Shi kad'ai ya yi dariya tare da kame bakinsa domin ya fahimci sha'anin babbane. Bayan haka Yabi ta yi hak'uri, ta yi juriya, ta yi masa komai. Shi ma zai yi dukkan iyawarsa ya saka mata da alheri kan alheri. *INA KAWO MAGANIN MATA MASU KYAU DAGA CHAD DA SUDAN* *MAGANIN SANYI SADIDAN* *INA AIKAWA KO INA A K'ASAR NAN* *BA ZAI YIWU NA TALLATA MUKU ABIN DA BA SHI DA KYAU KO INGANCI BA. DOMIN SOYAYYA DA AMINCI NE A TSAKANINA DA KU MASOYA RUBUTUNA* *KU JARRABA SAIWOWIN DAHUWAR KAZA DA TATTABARU KU GA NI* *KAZALIKA MAGANIN SANYI DA TSUMIN GORAN TULA BABU NA BIYUNSU* *GA Y'AYA'N GADALI DA YAKE SHA YANZU MAGANI YANZU* *ASALIN DAKA NA EMERGENCY* *DA GUMBA DA KUMA TSUMIN KWAKWA DA ZUMA NA SHARHOLIYA* *TUNTUBE NI KAWAI TA WHAT'S APP.DAN SAMUN BAYANI NA SOSAI* *KU GYARA KANKU, KU GYARA Y'AYA'LNKU* *MASU SHIRIN AURAR DA YARANSU KO KANNENSU A ZO A SAMA MASU KAYA MASU NAGARTA* *08032773332* *NA GODE Kwa aki uku kacal aka ba shi ya huta. Gidan Marina ya kacame da murna kowa ya boye aibu da gilli aka dinga tseren yi mana murna. Baban Tsakiya da na Kasuwa washagari suka zo sai dai tafiyar kowa daban. Dukansu maganganunsu suna nuni.tare da tuni sune suka had'a auremmu dan mu gane oron alherin da suka yi mana. Baban Tsakiya cikin rauni ya ce "Tijjani danuwanka dai yana zaune babu aiki. Jabiru naka. A duba, ga yaranmu nan ka yiwa Allah ka dubasu. Ka rage banbanci Tijjani. Allah ya shirya zuria." Da zai tafi ya bude murya ya ce "Ina Hajiya Yabin?" Gabana ya Fadi ni ce Hajiya Kuma?" Na saka hijabi na fito na tsugunna na ce ga ni Baba". Ya ce "To ku kula. Ki kuma dage da yiwa mijiki addu'a kinga dai fad'i tashin da muka yi har asirin da aka ta jifanku ya karye. Kada na ji, kada na ga ni. Ki dinga tunawa mijinki game da rashin aikin yayanki Jabiru. Ki kuma cigaba da hak'urin aure nasara tana gaba. Alhaji Babba mura yake shiyasa bamu taho tare ba". Da mamaki na ce"wanene ke nan?" Ya ce "Baban Marina mana" A sanyaye na ce "Ai to, Allah ya bashi lafiya." Ya ce "Ameen." Yafi away da tafiya minda Tijjani bamu iya cewa komai ba. Domin ni tunanin fad'i tashin d Aya ambata sun yi nake yi. A hakan Baban Kasuwa ya iso shima ya gama kamun kafarsa da borin kunyarsa. Abin da yake bani mamaki yadda suka fi karkata akan ni naga farinsu fiye da Tijjani ya ga ni. Na fahimci sun riga sun yi nisa a wajen imani da ce wa sai ina son mutum da Tijjani ya taimake shi. A wannan loakcin mun barji soyayya. Kusan salon gwamna Tijjani ya dauka na wajen ririta ni da mutunta lamarina. Tuni ya canja wa twins makaranta ya kai su wacce ta amsa sunanta. Aikina kuwa bai hana ni ba. Haka nan na kan yi kunshi amma ba irin na da ba. Domin a yanzu mai kololuwar daraja nake yi. First lady da mukarrabanta kad'ai sai ko Hajiyar da ta yi mini sanadin zuwana gidan gwamnati. Watanni uku kafin Tijjani ya gane kan ma'aikatar. Cikin sa'a ya samarwa Yaya J da Yaya Rabiu aiki. Ya daga darajar aikin Yaya Salisu. Hatta Yaya Musa da ya zama shasha ya samo masa aikin security a babban asibitin Bauchi. Ya biyawa Anas da k'aninsa Nasiru karatu suka tafi Sweden karatu. Anas digiri zai yi, Nasiru kuwa PhD. Ba jimawa azumi ya zo, ya tisa ni a gaba da yara muka tafi Umrah da kuma Babah da abokiyar zamanta hadi da Aliyu da matarsa. Fad'in irin jin dad'in da muka yi ma bata lokaci ne. Babah Maryo ce ta kasa zuwa inda muke har yau. Hatta Nasiba ta zo yi mana murna. Ta Kuma ro'ke shi ya sama mata aiki duk da a Jos take. Ya mata alkawri zai saka a bata rubuta kati a asibiti. Domin mijin nata babu. Na kuma san Tijjani zai yi mata wannan kokarin. Domin ma riga da na fahimci shi mutum ne mai saurin afuwa da sassauci. A yanzu haka ya yi amfani da kujerarsa ya fito da Alhji Auta. Ya gyara masa gidansa. Ya mayar da y'ayamsa makaranta. Ya kuma saka masa albashi duk wata. Ya yiwa babbar y:arsa da take da hankali hanyar samun aiki in tunda ta yi karatu. Kuka ba irin wadda Alhaji Auta bai yi ba. Lokacin aikin hajji na zuwa ya biya mini ni da shi, da Aliyu da Yaya Ummi. Da Kuma babbar yarsa da suke uba d'aya. Na so ace Ya biyawa Inna tunda itace babanmu bai samu sukunin kai ta ba. Ya ce zata je amma sai ya kai Gwaggo Umrah ta dawo. Domin ya sani ta taka muhimmiyar rawa wajen dannata a loakcin da shaid'anu da mugaye suka so yin tasiri a rayuwar aurenmu. Ummi kuwa mutumiyarsa ce. Kafin ya kai kowa Hajj sai ya kai ta a gidan Marina. Haka muka dunguma ni da Yaya Ummi muka tafi tare da shi. Duk da yanzu ba a iya cewa komai akanmu akan gidan Marina sai da aka yi yamididin yan dakinmu na ware masa ta kai. Da azumi ya kai Iklma an kasa gane ba dan ni ya kai ta ba,dabida Aliyu ne. Ko wata ce matar.kuwa zata je. Yaya Ummi kuwa ko ba ni ce matarsa ba zai kai ta. Cikin kankanin lokaci sunan Baban Marina ya koma Alhaji babba a wajen yan'uwansa. Ko yaransu ne zasu yi abu zasu ce basu da ta ce wa sai abin da Alhaji Babba ya zartar. Tun ana ganin abin daban har aka saba. Shekarar Bulkachuwa d'aya a matsayin kwaishina ya rushe gidan Marina. Ya yi gini na alfarma na zamani. Kowa part dinsa aka kawata shi, aka zamantar da shi. Kowa anmasa bene. Gefen Dada ne babu bene, gini mai suna hini aka yi. Hatta can ciki inda akace ya zauna da Yabi loakcin auren sai da ka rushe shi aka tamfatsa gini. Gidan Marina ya sake yin fice a Toro. Shi kuwa Juwad g.r.a yake nasa ginin na alfarma. Wanda ha siya da nufin ya saka Nasiba a ciki ya ce ya bawa Yabi halak malak. Gidansu na Bulkachuwa ma ya sha gyara tunda gini ne mai kyau mai aminci. Gata na ban mamaki yake yiwa magaitda abokiyar zamanta. Koami tare yake kai musu sai abin da baaytasa ba. Haka nan sisters dinsa mata ko wacce ya sama mata abin yi,.ya dauki yaransu ya kaisu makarantu daban daban. Ta bangarena hankalina ya kwnata domin na daina zullimi akan sha'anin Tijjani. Hatta saka masa idon da na yi akan sha'anin mata yanzu na janye domin aiyukan da suke gabansa bashi da sukunin wannan lamarin. Na murje na ciko. Na mallaki dukkan abubuwan k'awa na ado da kwalliya. Gwala gwalai manya suturu. Malaysia fabrics na Umm Nihla. Mota. Ga yarana suna karatunsu cikin nutsuwa. A yanzu haka cikine da ni na watanni biyar. Husna ta yi shekaru uka. Ya dankara mana gida mun tare tun bara. Tun lokacin kuma ya dawo da Dada kusa da mu. Part dinta daban. Idan ta gaji sai ta tafi Toro. Haka idan ta gaji da Toro sai ta taho wajenmu. *Yajin Annur duniya ne Hajiya domin na jarraba shi, akwai na garlic, akwai marar garlic, akwai na daddawa, tana yi ga masu jego*. *Akwai man shanu, akwai garin danwake*. *08039183880* A yanzu kowa Hajiya yake ce mini. Burina ya cika. Na kai Gwaggo Umrah, na kaita hajji. Nazira ta je, da su Yaya Salamatu. Mama ta je Umrah. Inna kuwa aikin hajji ta je bara. Baban Kasuwa da na Tsakiya suma sun je Umrah da azumi. Shi kuwa Alhaji babba ta bakinsu duk azumin duniya tunda muka samu dama a can yake yi. Sau uku ke nan. Duk shekara idan zai tafi, zai tafi da matarsa daya. Haka Babah da abokiyar zamanta. Kowa ya yi hakuri da sake saken zuciyarsa, ya yarda da hukuncin Allah baya canjawa zai ga alheri mai yawa. Babah Maryo da kanmu muka kai mata ziyara bisa umarnin Babah. Ta saka ya gyara mata gidanta. Aka sanya y'aya'n ta a makaranta. Tunda Yaya Ammar ne kawai ya yi karatu mai zurfi. Nasiba kuwa tuni ta samu aikinta tana cikin rufin asiri. Haka nan Tijjani ya yi k'ok'ari an daga darajar Ammar a wajen aiki. Amma kunya gabad'aya ta hana Baba Maryo sakewa. Umrar bana ma tare Babah ta ce zasu tafi. Hakan kuwa aka yi. Babah da Bulkachuwa da Baban Marina sun fahimtar da ni yadda saka alheri idan an yi maka sharri na matukar tasiri a dukkan mu'amala mussaman ma a harkar zumunci. Duk yadda lokaci ya yiwa Tijjani karanci, ina da lokaci na mussaman a wajensa. Da zarar ya shigo gidan zai kashe wayoyinsa ya tisa ni a gaba da y'aya'nsa. Soyayyar nan da nake so bai fasa shayar da ni ba. Haka nan a shimfi'da sai ya tsiyayar mini da ruwan kai tas. Da kaina nasan an yiwa Baban 2 baiwar lafiya da kuzari. ** Zaune muke a babban falona ni da dukkan yan'uwana da muka taso tare domin a yanzu kowa so yake ace yana kusa da ni. Hatta Maijidda da Nasiba kuwa. A dalilin na haihu sati hudu baya, sai yau na shirya walima tunda c.s aka yi mini. Na Kalli Nazira na ce Adda Nazira dan Allah ki sam mini kiba. Kin ga yadda kika tara teba kuwa?" Ta ce baki ga Maijidda da Nasiba ba sai ni? Ni maganin rabge tumbi ma nake nema. Na ce "zansa a kawo miki daga Kano." *Bada jimawa ba zan zo muku da littafan Hanne Ado Abdullahi* *Marubuciyar Wanka da gari da Kuma wacece uwa?*. Maijidda ta ce ni kuma na sanyi". Na ce "Tom gangariya ne kuwa maganin sanyin". Iklima da Ubaida suka ce mu dai a kawo mana na gyara kawai". Na ce "kowa zan siya masa wadda yake so. Kayan surayya masu kyau ne na yarda da su. Sannan albarkacin Anti Kulsum free delivery ne ga duk wcce ta ta siya take zaune a jihar Bauchi. Suka ce Hajiya kina da yawan jama'a". Na yi murmushi na ce sana'ata ta had'a ni da mutane masu karamci da kyautatawa dan adam. Ba abin da zance da Allah sai godiya." Daidai lokacin jariri ya tashi wanda ya ci sunan gwamna. Muke kiransa da Halifa. Na Kalli kaina a cikin yan'uwana na ga nice zarra. Mafi yawansu kuma sun sake samun rufin asiri ne ta sanadina. Mahaifiinmu da mahaifiyata sun sake samun daukaka ta sanadina. Matan gidan da ada suka hade mata kai, aka mayar da ita banza yanzu kowa so yake ya hlga dariyarta. Ko wacce so take ta samu shiga a wajenta. A sanadina da Tijjani an samu s'aukiin bak'ak'en taadodin da suka yiwa gidan Marina katutu. Ba'a dinke an zama abu d'aya ba. Amma hassada da jahilci da suka samu gindin zama a gidan yanzu ya yi k'aura. Dada tana nan gar da ita. Umrah duk shekara. Tijjani ya tsaya mata. Ta kuma rungumi istigifari. Komai na ce mata na gyara zata karba babu inkari. Idan na so nishadi ma a wajen ta nake yini tana d'ora mini karatukan ta masu sanya ni dariya da tuna baya. Hatta kangire alherina na isarsu. Har yau din nan da Tijjani ya zama attajiri Ina matukar Jin dadin aikina da kuma sana'a ta domin idan a na je na yiwa first lady kunshi makuden kudade take zuba mini a jaka. Idan zan yiwa dangin uwata alheri bana jiran Tijjani. Duk da shima yana iyakacin kokarinsa. Haka nan yadda nake son ganin dakin Gwaggo da kayan ciye ciye haka nake gani, domin bayan siyayyar kayan abinci na duka gida da Tijjani yake yi. Ina warewa na yiwa uwata hidimar da dace da ita. Suma matan gidan na kan yi musu amma ba kamar ita ba. Tunda dukkan y'aya'n k'ofarmu sai da nasan yadda aka yi aka bawa kowa upper aiki. Duk dai k'ananun ma'aikata ne . Amma dai duk wata zasu ji albashinsu. Hatta Yaya Ummi ta samu aiki a woman center tana koyawa dinki tunda ta iya. Sannan Tijjani ya dauki nauyin karatun y'ayanta biyu maza da suka kammala sakandire a jami'ar Ahamadu Bello da take Zaria. Suna Karantar manyan kwasa kwasai domin sosai suke da hazaka. Har su Maijidda da su Saratu. Nazira kuwa koyarwa take yi tunda ta cigaba da karatunta tunda mijinta dan boko ne. Amaryar Yaya J a gidan radiom Toro ta samu aiki. Tuni ya farfado. Maijidda ce a BAUCHI a amaryar na Toro saboda aikinta. *** Waya muke da Nazira akan maganin rage tumbin ya ya isa gareta. Maimakon ta yi mini godiya sai sababi take yi mini tana ce wa "Yabi ban ga Malaysian Fabrics a ciki ba. Ban ga mayukan Oriflame da maclen da kika mini alkawari ba. Ban ga supplement din GHT na FASEELAT ba. Haka nan babu yajin Annur". Na yi dariya na ce "Adda Nazi ke ce kadai kike gatsa Yabi! Ina ce ke shaidace bayan hajjin da na yi ina ciki, na yi a yanzu kan girmana ma? Ta ja tsaki ta ce "Ba zance Hajiyan ba. Yar mitsitsiya da ke sai son girman tsiya.". Na yi dariya na ce "To kwantar da hankalinki gobe Aish lame zata zo garin zata tsaya ta gaida Dada zata taho miki da su. Kinsan wannan Yaya Ummi aka aikowa ta Jos." Ko ma na baki lambarta sai ki zabi duka abin da kike so yayata". Ta yi dariya ta ce "Yanzu na ji magana. To sai anjima hakima ta Yaya Bulkachuwa ". Na yi dariya na cigaba da karatun littafin *Ya za'a yi?* da nake yi a waya na marubuciya *Binta Abbale*. Labarin ya ja hankalina. Tuni na tura kudina ina paid group din ta dan na ji yadda za'a warware wannan dambarwar. *Tuni kuma nake group din Gaskiyar lamari na Nazeefa Nashe*da yake dad'i kamar kada shafi ya k'are *YA KAMATA ACE Y'AN JAHAR BAUCHI SUN SAYI LITTAFIN NAN RUTUTU KO DAN SU RAMA MINI K'AUNAR DA NAKE YIWA JAHARSU* 🥰 *IDAN KE Y'AR BAUCHI CE MUSSAMAN TORO KO BULKACHUWA AMMA BAKI SIYA BA, NA TAYA KI JIN KUNYAR WANNAN LAMARIN* *Fatan alheri GAREKU GABADAYA*. 😀🥲 Ina kwance kan gado ya shigo yana sab'e da Halifa. Na kalle shi ya zama CIKAKKEN mutum mai cike da Kamala. Tuni na fara hango shi a matsayin gwamnan gobe. Wato jihar BAUCHI ta jima tana yin zatan gwamnoni dogaye farare masu farar aniya. A fili na ce "Allah ga Baban 2 a cigaba da yi masa afuwa da rahama. A Buda masa kirijinsa a bashi ikon sauken nauyin jama'a babu gajiyawa. A cika zuciyarsa da son Hajiya Yabi da tausayinta da mararinta babu gundaura." Ya kwashe da dariya sosai ya ce "Ubangijinma sai kin ce masa ke Hajiya ce?" Na ce "To ai tunda zuwa gabar ne sharadin zama Hajiya ai tuni ita ce tun banzo duniya ba" Ya rungume ni ya ce "Hakane Hajiya little. Ina matukar farinciki da ya burina ya cika na kai ki gabas Hajiya. Dukkan burikan sun cika fatana Allah ya cigaba da bani lafiyar da zan ciyar da ku halali na jiyar da ke dad'in duniya dan ki gane ba komai a gabana da ya wuce ki idan kika cire Babah". Na langabar da kaina a jikknsa na ce "Ina godiya. Ubangiji ka so Tijjani, ka karba daga gare shi. Ina godiya bisa kaddara mini ya zama mijina, ina fatan ka tabbatar mini da shi har a aljanna." Ya dinga Ameen dear Hajiya. Allah ya cigaba da iya miki, ya mayar da makiyanki fadawanki, ya shirya mana zuriarmu. Muddin rai ke ce tauraruwar zuciyata." Daidai lokacin naji dirin mota tabbacin Yara sun dawo, daga school na yi maza na zame nasan Hamim idan bai ganni a falo ba sai ya biyo ni daki. Ilah kuwa ya murda kofa ya shigo. Ya ce "Baban 2 Sannu da gida". "Sannu dai Baban Marina. Tijjani ya fad'a da murmushi. Ya iso gare ni ya rik'e hannuna ya ce "Ammi mun dawo". Na ce "To sannu a je a cire uniform a yi wanka tunda kun yi sallah a school". Ya ce "To ya juya zuwa dakinsu." Yana fita Hanif ya shigo. Ya bude baki ya ce "Baban 2 yau baka je ofis ba?" Ya ce "Hutawa nake yi Baban Bulkachuwa". Ya rik'e baki ya ce "Gaskiya Baban 2 ba'a haka. Babu kyau fashi tamkar tauye mudu ne. Mai tauye mudu kuwa d'an wuta ne". Ya janyo yaron jikinsa ya ce "Na gode da tunasarwa Babana. Zan kiyaye". Ya sake shi ya matso gare ni ya dafa ni ya ce "Ammi sannu da gida ina Husna my dear?" Da murmushi na ce "Tana wajen Dada! Ka je ka yi wanka sai ka je ka ganta." Ya ce "Tom". Ya ja hannun Halifa da yake zaune a k'asa yana wasa da kayan wasan da Tijjani ya ajiye masa. Ya juya ya tafi amma Halifa ya saka kukan sai ya dauke shi. Haka ya dawo ya dauke shi ya tafi da shi. Ni mamakin yadda Halifa yake banbance shi da Hamim nake yi. Kafin na yi magana Bulkachuwa ya ce "Wato Hamim ba k'aramin miskili ba ne. Ke ce kad'ai idan bai ganki ba zai damu. Amma daga ni har yan'uwansa baya damuwa da rashinmu. Gara ma ya damu da Hanif". Na ce "Ai Hamim danja ne, ance ni ya gado, ni kuwa ai mai son jama'a ce. Mussaman yan'uwana ". Ya ce "Hakane shima zai warware. Allah ya shirya mana su gabad'aya. Na ce "Ameen dear". Da daddare daga ni har yara muna wajen Dada ana ga sharholiya cikin farin ciki ya shigo ya gaishe ta a tsaitsaye. Ta ce "Alhaji Shehu daga tsaye yau?" Ya ce na gaji ne Dada. Ina son na kwanta. Ta ce "To babu laifi. Mu kwana lafiya." Ya tafi Yara suka bi bayansa a guje. Ta kalle ni ta ce "Haba Hajiya tashi mana ki bi bayansa. Kya bar shi da yara?" Na ce "Rabu da shi Dada ai yaji na yi masa. Yau tun safe bai kira ya ji lafiyata ba. Na k'ira bai d'aga ba". Ta dauki salati ta ce "Haba Hajiya kinsan hidimarsa mai yawa ne. Ban da abin ki irinsu Shehu ai ba'a samunsu da sakwa sakwa. Tashi ki je ai ki fahimtar da shi cikin hikima kin ji Hajiya Yabi" Na yi dariya na ce "Tom". Na isa falon na tarar da shi da yara akan dining suna cin abincinsu. * Muka kwanta ya ja ni jikinsa yana.ce wa "Sarka mai rikicin gangan Hajiya little". Na share ya ce "wai ke ba zaki girma ba. Kullum sai kin samo laifin da zaki jingina mini? To ki huce komai na yi ma, ba da gangan ba ne. Ki yi hakuri kin ji My Hajiya love?" Dariya ta k'wace mini na ce "Na lura dai yadda kake nacin ce mini Hajiya har da gayya" Shima cikin walwala ya ce "To ba burinki ke nan ba? Zan ta ce miki Hajiya. Kuma duk shekara sai na raka ki umrar azumi tunda Annabi ya ce tamkar aikin hajji ce. Kin ga sai ki ta sabunta Hajiyar ta ki". Muka yi dariyar jin dad'i muna fad'in Allah mun gode maka ka cika ni'imarka a garemu". K'arshe. Alhamdulillah. *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI* *IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*. *SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI* *AKWIA SAIWOWIN SANYI* AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA* *AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU* *AKWIA SAIWOWIN TSUMI* *AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN* *AKWIA PACKAGE DIN AMARYA* *AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO* *AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*. *AKWAI GORAN TULA SYRUP* *AKWAI GORAN TULA FRUIT* *INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA* *, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332* *DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.