❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ BOOK 3 kuma shine na karshe. *Ya Ubangiji ina rokonka da kasa kamar yadda na kammala book 1 da 2 lafiya, ya Allah ka bani aron lokaci da dama na kammala book 3 ɗin ma lafiya, Alhadulillah Alhadulillah Alhadulillah, a ko da yaushe ina kara godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ni'imar da ya yi mani, ina alfari da baiwar da ya yi mani, sannan ina matukar farinciki da hakan, ya Ubangijin kuskuren da yake a cikin wannan ɗan littafin, ya Allah ka ya fe mani shi, Allah ka bamu ikon ilmantarwa, wa'azantarwa, faɗakarwa, har ma da nishaɗantarwa*. *Ina miƙo sakon jinjina ga jajirtattun iyaye na waƴan da suka tsaya kai da fata wajen ganin sun bamu ilimi mai albarka mai kuma amfani, sun inganta rayuwar mu, ina matuƙar alfahari da iyayena, haka zalika ƴan uwana, masoyana kai harma da makiyana, domin kuwa makiyi da munafiki, mahassadi, sune ke kara cicciɓaka izuwa sama*. *To ƴan Group na ƴan amana kuma ban manta da ku ba, saƙon jinjinarku na daban ne, masu yi mani comments kullun ba su gajiya, suna kara mani karfin gwiwa, Alhadulillah, Alhadulillah, ba zan taɓa mantawa da ku ba a rayuwata, ƴan paid group kuma ina godiya, masu danna likes ina godiya, marasa dannawa ma ina godiya, Allah Ubangiji ya bar zumunci mai ɗorewa*. GARGAƊI!! DA BABBAR MURYA!! BAN YARDA BA, KUMA BAN AMINCE BA WATA, WANI, SU KARANTA MANI LITTAFI SU MAI DA SHI AUDIO!! SANNAN DUK WANDA TA KARANTA MANI LITTAFI BA TARE DA TA BIYANI HAKKINA BA, TO ALLAH YA ISA, KUMA SAI ALLAH YA SAKA MANI, IDAN KINA BUƘATAR KARANTA LITTAFI NE GA NUMBERTA 0816 139 0581KI BIYA KI KARANTA HALAK ƊINKI!!. 💋STORY and WRITTEN by FATEEMA ZAHRA MUSA.....✍️💋 E1💋 A zafafe ya ɗago kansa yana mai juyo da idanunsa akan wayar tasa da ta faɗi kasa, tsabar tsorata da fargaba tare da faɗuwar gaba yasa numfashinta ya ɗauke diff, ta yanke jiki ta sulale kasa sumammiya. Tana sulalewa kasa kuma ya yi daidai da dawo da kallonsa kanta da ya yi da nufin ya ɗauketa da wani gigitatcen mari, ganin ta sume yasa ya ciza laɓɓansa rai a ɓace ya miƙe ya fice daga cikin ɗakin, domin ba yadda za'ayi ya daki gawa, e gawa mana, wadda yake sume ai kusan gawa ne, idan ya ce zai daka ma, me zai daka a wajen? Amma ba haka ya so ba, ya sone ya bata lafiyayyen mari da zata sanyata ganin wuta na ci bal, bal, bal, a cikin idonta, domin yau shi ne karo na biyu tana buge mashi wayarsa yana faɗuwa kasa, cox ya kamata a wannan gaɓar ya hukuntata da kyau dan ta kiyayi gaba. Yana fita ya nufi fridge dake a cikin Palon saman domin bai kunna fridge na ɗakinsa ba tun jiya, saboda baya jin daɗi baya shan ruwan sanyi sosai. Ruwa ya ɗauko mai bala'in sanyi gora ɗaya sannan ya juya ya koma bedroom ɗin nasa, yana taku irin na cikakkun jaruman maza, masu lafiya tare da jini a jika. Yana shiga kuma shi ma Areef yana shigowa, a kanta ya tsaya tare da ɓalle bakin robar ruwan, yana daga tsayen ya zazzage mata gaba ɗaya ruwan sanyin nan a kanta, wani irin firgita ta yi tare da tashi a razane tana kurma ihu. Rai a matukar ɓace ya sanya kafa zai yi ball da ita kamar kwallo, tattare iya karfinsa dukka Areef ya yi ya shagabansa tare da riƙe kafar tasa, ko kaɗan babu tausayi a fuskar Lion ɗin, dan buge mashi waya da ta yi a karo na biyu yafi kona mashi rai sama da komai. Hannu yasa ya hankaɗe Areef ɗin in da ya yi baya baya zai faɗi a saman table glass dake a tsakiyar wajen. Cikin zafin nama ya sanya hannu ya riƙo wuyar rigar Areef ɗin, dan kada ya faɗa saman table ɗin, ya san idan har ya faɗa a saman table ɗin to tabbas fashewa zata yi, idan kuma ta fashe ba ƙaramin ciwo zata ji wa Areef ɗin ba, hakan yasa ya yi maza ya riƙo shi, duk fa wannan abin da suke yi Rimsha na a tsakaninsu, har lokacin bata ma dawo cikin hayyacinta ba, sai sambatu take yi tamkar wadda ƙwaƙwalwarta ta taɓu. Riƙo rigar Areef ɗin nan da ya yi ba karamin famawa Areef ɗin ciwon dake a kirjinsa ya yi ba, domin kuwa yadda ya damko wuyar rigar ya haɗa da bandeji wadda aka sanya mashi a inda aka cire mashi bullet ɗin da Lion ɗin ya harbe shi, da yake a kafaɗa ne ta gefen wuyarsa, idan ba ku manta ba, to bandejin tana da ɗan girmar da ta zo mashi har a wajen wuyarsa, hakan yasa da Lion ya damki wuyar rigar ya haɗa da bandejin ya ja wo shi, hakan kuma ya yi sanadiyar ɓarewar bandejin ma gaba ɗaya, ba abin da suka gani sai jini da ya fara zuba yana bin cikinsa har yana zuba a kasa. Shi kuma Areef wani wahalallen ihu ya saki tare da sake jikinsa gaba ɗaya yana ƙoƙarin faɗuwa kasa, a zafafe cikin zafin nama Lion ya jawo shi jikinsa gaba ɗaya dan kada ya faɗi. Ɗan duƙawa ya yi tare da saɓar Areef ɗin a kafaɗarsa ya take ƴan yatsun Rimsha dake a tsakaninsu ya bi ta kai ya wuce ya nufi waje. Ihu azaba ta saki tare kuma da dawowa cikin hayyacinta, dan ba takun wasa ya yi mata ba, idan kuma baku mance ba hannun nata akwai ciwo na chemical da ya sanya mata jiya, ta sha bakar azaba kuwa, domin wannan take ta da ya yin har jini wannan tsage tsagen da hannun nata ya yi wajen ya yi, sai wani irin wahalallen kuka take yi kasa kasa, ga shi kuma tana jin yunwar safe daman. Ta ɗauki almost 10 mins a haka kafin daga bisani ta yunkura da kyar da makyarkyata ta miƙe, godiya ta fara yi ga Allah da ya tsareta, ya sanya Lion bai hukunta ta ba, sannan kuma ta fara ƙoƙarin tattara mashi ɗaki da sauri sauri kada ya zo ya taddata bata gyara ba. Shi kuwa yana fita ɗakin Areef ɗin ya wuce da shi, a in da ya je ya fara ba shi agajin gaggawa, kwata kwata ya mance da wata Rimsha, burinsa kawai ya yi dressing na wannan waje da ya fama ta da kansa, sai famar cizar lallausan laɓɓansa yake yi, gaba ɗaya idanunsan nan sun riƙeɗe sun yi ja alamar bai ji daɗin fama wannan ciwon da ya yi ba, domin kuwa idan ba ku mance ba, ba shi da wani burin da ya wuce ɗan uwan nasa ya sami lafiya, kullun fatarsa da addu'arsa kenan, hakan ya sa ya ji babu daɗi sosai. Ita kuwa tsab ta gyare komai tare da tattare komai ta fitar waje, sannan ta dawo ta ɗaga mashi wayarsa ta ɗaura saman sofa, sai kuma me? Tsayuwa ta yi tana tunanin ya za'ayi ta zubar mashi da abin ci, me kenan zai ci yanzu? Ya ilahi ya lillahi, ga shi bata isa ta je ta ce Mark ya yi wani girki ba, wannan mai fuskar shanun wadda take mutuwar tsoron nasa, ai bata ga fuskar cewa ya yi wani girki ba ma, to kenan yanzu ya zata yi? Kuma dai ta ji Areef ya ce ba su cin abinci a waje, ba su iya cin abincin restaurant ko makamancin shi ba, sai na gida, yanzu sai yaya kenan?. Duk jikinta ya yi wani la'asar kamar an zare mata laka, haka ta juya ta fice daga ɗakin ta nufi nata ɗakin, fuskarta gaba ɗaya ya yi jaga jaga da busasshen hawaye, gaba ɗaya dara daran sleeping eyes nata nan sun kumbura sosai saboda uban kuka da ta ci, kuma idanun nata sun ƙanƙance sosai da sosai saboda kukan. Tana shiga ɗakinta ta haye saman gado tana mai cigaba da furta hasbunallahu wanimal wakil, domin Allah ya kawo mata ɗauki, wannan addu'a ce wadda tana da sauƙin faɗe, kuma gata da babbar aiki, Annabi Muhammad (SAW) da bakinsa ya ce duk girman musifa da bawa ya shiga, matukar ya lizimci faɗin hasbunallahu wanimal wakil ko kuma ya hayyu ya kayyum to fa tabbas Allah zai ya ye mashi wannan musifa da yake a ciki, yawan yin istigifari wato astagfirullah waatubu ilai, yana da tasiri sosai wajen bunƙasa niimomi Ubangiji a tattare da bawa, kada ka je ka ce wani ko wata su maka addu'ar samun arziki ko kuma ka je wajen wani boka neman maganin arziki, ga maganin arziki nan wadda ko kana kwance ka yi shi zaka samu kofofi na ni'imar Allah ba adadi su buɗe maka, kaci halak ɗin ka, idan shago kake da shi a kasu wa to maza ka lizimci yin istigifari, In Sha Allah zaka ga buɗi, a lokacin da aka yi kwana uku a gidan annabi ba'ayi abinci ba, wata ruwa ta ce kwana uku, wata kuma ta ce wata ɗaya, to bari dai muyi amfani dana imamu Malik, kwana uku ba'ayi abinci ba a gidan Annabi, wannan zikiri annabi ya lizimci yi Allah ya buɗa mashi cikin ƙanƙanin lokaci, so Allah ya jarabci annabi ta hanyoyi da dama ba dan komai ba sai dan mu samu magungunar cutukar da suke damun mu a yau, idan mutun ya natsu ya fahimci tarihin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da kyau, zai gane cewa tabbas wa su abubuwa da suka faru da annabi, Allah ya yi hakan ne domin Allah ya fitar mana da mafita da maslaha, kamar dai yadda Allah ya fitar mana da mafita akan sihiri da tsafi ta hanyar bawa sheɗanu dama suka yi galaba akan Annabi, suka yi mashi asiri ta kama shi, a nan ne Allah ya saukar mana da maganin da Mala'iku suka karantawa annabi ya warke, idan zaka karanta shi, to tabbas ba dai ɗan adam ba sai dai Allah wlh, da zarar ka riƙesu to ka fi karfin wani matsafi ko boka, Aljani, dabbobi masu cutarwa, da sai sauransu, fatan mu dai shi ne Allah ya ba mu ikon yi Amin. Wannan addu'a kuma da zaka karanta domin samun kariya daga matsafa, tsafi, sharri da komai da komai ba wani mai wahala bane face (Suratul Ikhlaash) kulhuwallahu ahad kafa uku, Suratul Naas kafa uku, sai Suratul Falaq kafa uku, sannan ku rufe da Ayatul kursiyu kafa ɗaya, kowani bayan Sallar farillah idan kayi, in ma azahar ne ko la'asar, mangariba or isha'i au asuba'i fatan mun gane?. MACE MAI CIKI, WANNAN MAGANI NE DAGA MANZON ALLAH SALLAHU ALAIHI WASALLAMA WADDA NANA MARYAM MAHAIFIYAR ANNABI ISA ALLAH YA CE TA YI AMFANI DA SHI DAN SAMUN HAIHUWA CIKIN SAUƘI, IDAN KINA DA CIKI, CIKIN NAKI YA KAI WATA BAKWAI, TO KI LIZINCI CIN DABINO A KULLUN, IDAN DA SON SAMU ME KI CI GUDA BAKWAI KO WANI SAFIYA KAFIN KI CI KOMAI, DA IZININ ALLAH ZAKI HAIHU BA TARE DA WATA WAHALA BA, BA ZAKI SHA WAHALA BA, ALLAH KUMA ZAI BAWA KE DA ABIN DA ZAKI HAIFA LAFIYA DA IZINSA, ANNABI YA BAWA MATA DA DAMA WANNAN MAGANI, DAN HAKA A CIKIN ILIMIN DA ALLAH YA BANI NIMA NA BAKU ƊAYA DAGA CIKI, IDAN KIN JI DAƊI KI YI MANI ADDU'A DA FATAN ALKHARI TARE DA FATAN NASARA A RAYUWATA DA IYAYENA, INA GODIYA. IN SHA ALLAH MAGUNGUNAR MUSULUNCI IRIN HAKA ZAN RINƘA SAƘO MAKU SHI IYA ILIMIN DA ALLAH YA BANI, DAN KUMA KU KARU, IDAN KINA DA WATA TAMBAYA KI YI MANI ITA KAI TSAYE, KADA KI JE KINA TAMBAYAR WATA, NI NA RUBUTA MAGANIN, NI ZAKI TAMBAYA, ALLAH YA BA MU DACE WA. 09262620621 Shine numberta Ma'assalam.✍️ Story RIMSHA Wani irin barci ne mai shegen daɗi ya kwasheta, sakamakon samun natsuwa da ta yi saboda addu'ar da ta rinƙa yi tare da ambatar sunayen Allah. Baiwar Allah a cikin barcinma sai sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya take yi, yau ta ga karfin addu'a iya ganin idonta, domin kuwa ba dan addu'a da ta rinƙa yi ba, to wlh da sai dai a ɗauki gawarta yadda yau ta yi mashi laifi sosai ɗin nan. A ɓangaren su Jelly kuwa, wato gidan Abbi, zaune suke a palon kasa ita da Hanan, yayin da ita kuma Aunty take faman shirya abinci a saman table, Ayla kuwa tana wajen mijinta domin jiya ta ci bakar wuya a hannunsa, wadda ya ja mata zazzaɓi mai zafi, hakan yasa bai bari ta fito ba, ya zaunar da ita yana jinyar kayarsa. Sai kallo suke yi, ɗan kwana biyun da jelly ta yi har ta koyawa Hanan kallo, jelly shugaba ce a iya kallon Film, ta kware sosai da sosai, duk wasu Indian music ta iya su sanka sanka, ga shegen son rawa kamar wata jikar Michael Jackson, kuma ta iya rawar sosai, sannan kuma bata da ƙiba ne yasa bata jin hauyin jikin tata take takawa son ranta, tana bawa jikinta a jikinsa shi ma. A haka Hjy Batula ta shigo palon ta same su, ta yi wanka ta ci wani haɗaɗɗe kuma tsadadden lace black color, ɗinkin bubu gown, da yake dai gaba ɗaya familyn su daddy kyawawane tamkar wasu turawa or larabawa, haka suke, kuma gidansu two colors ne, akwai farare tas kamar turawa, sannan akwai chocolate color, Abba dai farine tas haka ita ka Hjy Umaiya, amma kuma Imran chocolate color ne irin Rimsha, to haka a gidan Abbi ma, Aafia da Irfan chocolate colors ne, saɓanin Umaisha da take fara tas Kamar ka taɓa ta jini ya fito, kun ga ita ma JEHAN fara ce tas kamar daddynsu, while shi kuma daddyn jelly bai yi tas ɗin ba dai, amma kuma ba chocolate color bane, shi irin farin Nigeria ne, su kuma farin waje ne da su gaskiya, da alama a cikin kakanninsu akwai Bature ko kuma balarabe, ɗaya dai daga ciki, domin kuwa wannan hasken nasu ba na nan bane, na can ne. Sosai Hjy Batula ta fito reras abinta, saman sofar kusa da su ta zo ta zauna tana faɗin "Ke Jalila ina ɗan kwalinki?". Turo bakin nan ta yi kamar biro zata yi magana kenan Ommu ta sauƙo kasa tana surfa uwar masifa akan su rage Volume na Tv ko kuma ta kashe Tv gaba ɗaya. Hanan dai da yake ta san halin ta, sai ta ɗauki remote ta rege Volume ɗin, ko sannu jelly bata ce mata ba, suka cigaba da yin kallonsu, yayin da ita kuma Ommu ta juya ta koma sama dan ta cigaba da abin da take yi, yau ta yi nasarar samun number Umaisha ta hannun Hjy Turai da ta karɓa mata daga wajen Aafia, murna a wajenta ba'a magana, tuni ta kyankyasawa Umaisha abin da take buƙata, da yake uwa da ƴa, kuma babba kam ko yaya babba ne, sai bata sha wahala wajen shawo kan Umaisha ɗin ba, karya ta zuba mata akan cewa ai bata da lafiya ne, tana da ciwo a zuciyarta, aiki za'ayi mata a kasar India, Abbi kuma ya ce ba zai biya kuɗin ba, tun da mijinta yana da kuɗi, idan ba damuwa ko sata ne ta sato mata wajen shi, tun da ba zai rasa ajiye kuɗi a gida ba, ko da bai cika 10 million ɗin lokaci guda ba, ta sato da kaɗan da kaɗan, kada ta yarda ta bari ya gane, da farko Umaisha ta ce a'a zata tambaye shi dan tasan ba zai hana ta ba, yana da kyauta sosai, kuma wa su ma a waje ya yi masu bare ita da take mahaifiyarta, ba zai taɓa hana ta ba, sai dai ma ya ce ta shirya su tafi asibitin a tare, da yake ba wani asibitin da zata je karya ce kawai, sai ta sawa Umaisha ɗin kukan munafurci tana faɗin "Ta ya za'ayi ki bari surukina ya san sirri na? Yanzu so kike ki tonawa Abbinki asirin na yaki biya mani kuɗi a kaini asibiti? Wannan ai abin kunya ne, me yasa ke kam wayuya ce? Ai ba'a gayawa miji sirrin gidan iyaye, domin watara sai ya yi maki gori". Kafe wa Umaisha ta yi akan lallai yaya Akil ba zai yi mata gori ba, saboda ai Abbin babbansa ne, nan fa Ommu ta rinƙa yi mata bayani akan ko uwa ɗaya uba ɗaya kuke da mutun ma, wata rana sai ya yi maka gori, dan haka ta daina wani zancen ba zai yi mata gori ba. To da yake kunsan yadda ƙwaƙwalwar ta Umaisha take, Baiwar Allah ko nonon uwa bata samu damar wani sha ba, ga wahala da ta sha na tasowa a hannun maza da suka reneta, wato Irfan da Abbi, kun san dai renon Namiji da mace daban daban, hakan yasa Ommu ta yi wasa da tunaninta, tare da gwada mata ainahin bariki har sai da ta yarda ta amince zata sato mata kuɗin Akil ɗin idan za su zo gida. BABBAR MAGANA. Kuna ganin Umaisha zata ɗauki kuɗin Akil ba tare da ya sani bane? Kuɗi kuma ba kaɗan ba, lallai ba shakka Ommu tana son kai Umaisha ta baro ta. Mu dai je zuwa. Ommu kuwa abin da ya sanya bata son Akil ɗin ya sani, saboda a baya ta yi zama da Hjy Umaiya ai, ta san Ammie akwai shegen bala'in basira sosai da sosai, ga zafin rai da faɗa, sai dai sai an taɓa ta take faɗar tata, to tana da tabbacin da wuya idan su Akil ba su ga ji wannan basira ta Ammie ba, ta san tsab zai ce ta shirya su tafi asibitin ko kuma ya gane karya take yi, shiyasa ta fito da hanyar sanya Umaisha ɗin sato mata kuɗin kawai, a nata tunanin da wawtarta ta hakane kawai zata sami biyar bukatarta. Lallai da akwai kura kenan, tab ɗi jam. Bayan Aunty ta gama shirya masu abincin ne ta zo ta zauna kusa da Jelly tana faɗin "Jellynmu ba karamin kyau kunshin nan ya yi maki ba". Murmushi ta yi tana faɗin "Aunty da gaske na yi kyau?" "E mana my baby jelly sosai ma kuwa". Jelly zata yi magana kawai a ka sako wakar Sharukhan Kuci kuci hotaye, haba malam ai tuni ta miƙe tare da ɗaukar remote ta kure Volume na Tv tare da jawo hannun Hanan akan su taka tare, kwata kwata bata jin daɗin yin rawa ita kaɗai, ta fi son su taka a tare da wani, abin ya fi bada armashi, lokacin da suke Kano da daddy, idan aka sako waƙa a Tv, haka take saka bawan Allah nan rawan dole ba dan ya so ba, kawai dai dan ya rinƙa ganin farinciki akan fuskar ƴar tasa saboda maraicin ta. Ai kuwa Hanan ma ba son rawar take yi ba, amma saboda bala'i irin na Jelly sai da ta sanya ta rawa, Hjy Batula kam waya ta ɗauka ta kama yi mata video dan tana bala'in Kaunar Jelly fiye da tunanin mai tunani. Sai wani juyi jelly ke yi kamar yadda maciji yake irin wannan nannaɗuwa idan zai hau itace, sai ka rantse da Allah bata da kashi a jikinta, saboda yadda take murɗe jikin nata, wannan idan ba'a san asalinta ba, da sai a ce kanwa ce ko kuma jika ce ga Michael Jackson, saboda iya rawa. Suna tsaka da rawa sai ji suka yi an kashe Tvn, a fusashe ta juyo dan gani wani ɗan uban ne ya yi hakan. Ai kuwa ido huɗu suka yi da Ommu dake tsaye tana yi mata kallon sama da kasa, wani irin kallon banza Jelly ta yi mata kafin ta ce "Ke mai kama da pig na discovery me haɗin ki damu da zaki kashe mana kallon mu? Shin mun haɗa wani alaƙa dake ne?". A fusace Ommu ta nufeta da nufin ta daketa, ai kuwa jelly na tsaye dan dai idan ba ku mance ba, bata da tsoro ga kuma uban rashin kunya tare da tsiwa. Sai da ta bari Ommu ta iso zata daketa, ta gama sake jiki zata kai mata duka ai kuwa da iya karfinta ta sa kafa ta gale kafar Ommu, sai ga Ommu ta zube a kasa, a lokacin kuma dama Hjy Batula ta miƙe zata tare faɗar, zata tare kada a daki Jelly ɗin. Ita kuwa Jelly Ommu na faɗuwa ta sa hannu ta ɗauki remote ɗin da ya faɗi kasa ta kunna Tvn, Allah ya sa har lokacin ba'a gama wakar ba, tamkar bata aikata wani laifin ba, kamar ma bata san komai ba, ta koma taka rawarta kamar wata zautatciya, sai tsale take yi tana direwa ta bar Ommu zube a kasa kamar kayan wanki. Wanda bai san jelly ba, zai ce aljanun bishiyar kuka ne ko tsamiya akanta, domin sune suka fi ko wani aljani iyashege da masifa. Aunty tana ganin hakan tasan za'ayi hayaniyi dan ta san halin Ommu sarai ba bari zata yi ba, dan haka sai ta miƙe ta wuce sama abinta, domin bata son hayaniya da ciwon kai, dama kuma ba wani ƙoshin lafiya ke gare ta ba, da alama kuma laulayin ciki take yi, domin ga alamun ciki sun bayyana sosai a tattare da ita. Cikin zafin nama Ommu ta miƙe tare da damƙo wutar Jelly ta baya, da yake Jelly ta san ta kan iskanci kusfa kusfa, sai ta kurma uban ihun da duk wani halitta dake a cikin gidan sai da ya ji, hakan yasa Ommu ta sake ta ba shiri, domin kar ta jaza wa aurenta matsala, dama yanzu ma yaya, tun jiya ta kasa gane kan Abbi, ya koma ya tare wajen Aunty abinsa, yanzu Aunty tana yi mashi al amura ba wasa, kuma kun san dai ta fi Ommu kayan alatu ato. Kungane ai?. Ai kuwa wannan ihun da jelly ta kurma ya yi sanadiyar fitowar kowa dake a cikin gidan, amma ban da Aunty, dan ita ta san me musabbabin faɗar, dan haka ba ruwanta, ba zama ta zo ba, bare kuma ace ta yi wani abin, ko ma ace ita ta daki Jelly ɗin. Jelly kuwa zubewa kasa ta yi kamar wata ƴar bori, tana ihu tana juyi a tsakiyar palon, ta dafe ciki tana faɗin wayyo cikinta zata mutu Ommu ta fasa mata ciki. Yau Ommu taga bala'in makircin da ya ci uban nata ya shanye, yarinya ƴar karama da irin wannan kirsa, to ina ga ta girma kuma? Ya ilahi ya lalliahi, kwata kwata ba abin da Ommu ta yi mata fa ce wannan riƙota ɗin da ta yi, amma saboda iskanci irin na Jelly wai Ommu ta dake ta a ciki, hakan da ta yi kuma ya yi amfani, domin gobe ko da kuɗi aka bawa Ommu ba zata yi yunkurin ta ɓa ta ba. A razane gaba ɗaya family suka shigo cikin palon, Abbi da daddy har suna rige rigen karisawa wajen da take a kwance sai juyo take yi har da nishin karya. Daddy da yake ya san halinta da iya zuzuta abu, sai bai wani tashi hankalinsa sosai ba, domin yana da tabbacin koda ma Ommu ta daketa ɗin kamar yadda take ikirari, to dukan bai kai yadda ta kai shin nan ba, ya santa sarai gwana ce a iya zugi abu. Abbi kuwa tuni hankalinsa ya yi mugun tashi a in da ya ce da Irfan ya tashi mota su wuce asibiti ita kuma Ommu ta jira dawowarsu ba zai kyaleta ba. Hjy Batula dai yau Jelly ta goge mata hadda tsab, da yake ita ma bata son Ommu sai bata karyata Jelly ɗin ba, Hanan dai yau taga bala'in da ya wuci tunaninta, ita kam Aunty Allah ya rufa mata asiri bata ma san me yake faruwa ba, bare kuma hankalinta ya tashi. Ai kuwa kamar wata ƴar baby haka Irfan ya saɓi jelly a kafaɗa suka nufi motarsa, gaba ɗaya ta tashi hankalin kowa dake a cikin gidan nan, daddynta ma dai daga baya da ya ga kamar da gaske ne sosai abin ya sameta, sai hankalinsa ya tashi sosai da sosai. Haka suka ɗunguma zuwa asibiti suka bar Hjy Batula Hanan da kuma Aunty, sai Hjy khadija a gidan, ita kuma Ayla tana can ɗakin daddy tana barci, bata ma san abin da yake faruwa ba, daddy ya bata magungunarta ta sha, shi ne barci ya yi awon gaba da ita. Bayan sun isa asibiti, Dr ya ɗan dubata sannan ya rubuta masu maganin ciwon ciki, kasan cewar ya ga tana period sai ya yi zaton ciwon cikine na period kawai, haka suka sake ɗunguma suka dawo gida a in da Abbi ya ɓata rai sosai tare da kartawa Ommu warning akan ko inuwar ƴaƴan ƴan uwansa karta kuskura ta sake taɓa wa, duk ma wanda ya kawo gidan nan ya ajiye babu ruwanta da shi, idan tana son zaman lafiya, da yake ta lura auren nata na gargada, sai ta bashi hakuri tare da yi mashi alkawarin ba zata sake ba domin bata da hanyar da zata bi ta nuna mashi karya Jelly take yi mata, tun da sun je asibiti har magani aka bata, Dr bai karyata ba, kuma su Hjy Batula tasan ba za su bi bayanta ba tun da ba shiri suke yi ba, ta san cewa Abbin ma ba zai taɓa yarda da cewa karyan bane tun da Dr bai karyata ba, shiyasa ma bata tsaya jayyayya da shi ba, kawai ta bashi hakuri. Yana fita ta ciro wayarta tare da danna wasu lambobi da suka kasance ba na Nigeria ba, sannan ta danna kira. Wayar ta jima tana yin ringing kafin a ɗauka, kwanciya ta yi a saman gadonta tare da fara magana cikin harshen larabci. "Barka da rana mijina abun alfahari na". (Toh fa babbar magana, miji kuma? To shi kuma Abbi me kenan? Lallai akwai yaki kenan). Daga ɗayan ɓangaren wata murya wadda da ka ji kasan balarabe ne ya ce "Habibi wai sai yaushe zaki dawo ne? Gaskiya na gaji wlh, ina kewar ki sosai, daga zuwa ganin ƴan uwa shikenan kin yi zamanki, idan ba zaki dawo ba ni zan zo in ɗauke ki, akan me zaki tafi ki bar mijinki da kewa? Kinsan da ya nake barci ne? Ga su Suhana duk suna kewar Mummynsu, kin tafi kin barni da aikin kai su school na ɗauko su, to gaskiya ni ki dawo, kuma Suhana tana buƙatar kanwa". (Toh fa, kenan wani aure ta yi ne ko yaya? BABBAR MAGANA, wannan shi ne cakwakiya, ga dai su Suhana a gefe, ga kuma su Aafia a nan, tab ɗi jam, ba abanza bata kula su Aafia ba, Allah sarki bayin Allah, wlh idan kana duniyar nan babu abin da ba zaka gani ba, abubuwan da suka ninninka hakan zaka gani, wannan ma ai mai saukine, idan ka ji wani abin, wlh kwakwalwa ba zata iya ɗauka ba, wlh jama'a muji tsoron, mutuwa gaskiya ce, haka zalika wuta da aljanna, Allah dai yasa mu dace.) "Hayati zan dawo nan ba da jimawa ba, kanwata ce aka kwantar a gadon asibiti, shi ne muke ta fama da yawon zuwa asibiti, amma dai In Sha Allah nan da two months zan dawo ka ji?". Da sauri ya ce cikin marairace murya "Haba Ommu Suhana, two months fa, gaskiya ya yi yawa, ya kike so mu yi da rayuwarmu? Ko so kike mu mutu ne? Ni gaskiya ban yarda ba sai dai mu biyo ki Nigeria ɗin kawai mu zauna a tare, idan ya so idan kin tashi dawowa sai mu dawo a tare....". Da sauri ta tari munfashinsa a in da take cewa "Haba Abu Suhana kayi hakuri mana, ai two months kamar yaune, kai dai kawai ka yi hakuri ka cigaba da kula mana da babys ɗin ku ka ji? Ai ba zan jima ba, kuma nima ina tunaninka sosai da sosai, domin kuwa kasan duk duniya babu wanda nake so sama da kai da Suhail da Suhana, ina bala'in kaunar ƴaƴana fiye da rayuwata, dan Allah ka kula mani da su ka ji?". "To shikenan Ommu Suhana, ba damuwa, na baki izinin ki zauna har sai mama ta samu lafiya sannan ki dawo". Ɗan dafe kanta ta yi kafin ta ce "Ba fa mama ba ce bata da lafiya, ka manta na ce maka mama ta rasu ne? Ai ni bani da iyaye sai dai bappana mahaifin wannan kanwar tawa Hjy Turai, ita ce kuma ai nake jinya, yanzu ma haka ina asibitin ne, kuma kasan iyayen nata sune Sarkin Katsina, to komai cikin tsari akayi, kai dai da ta samu lafiya zan dawo". (Hajiya Turai tana zaune lafiya an ɗaura mata lalurar ciwo, kai duniya ina zaki da mu ne wai?.) "To shikenan Ommu Suhana ba damuwa, ki yi jinyar tata har sai ta samu lafiya sannan ki dawo". Da haka suka yi sallama, ya ɗaura wayar a saman bedside drawer tare da cigaba da abin da yake yi na sanyawa Suhana yatsa a gabanta, yana kwakularta yana faɗin "Banza kada ma ki dawo mana, wannan matsalar ki ce". Suhana yarinya yar shekara biyar duk ya lalata mata rayuwa, tun kafin Ommanta ta taho Nigeria yake fakar idanunta yana sanya yarinyar tana sha mashi gabansa, daga haka ya fara wasa da nata gaban, yanzu kullun abin gaba gaba yake yi, shi kuma Suhail ba zai wuci yaro ɗan shekara bakwai ba, amma dan jaraba ya lalata yaron nan ta bayansa, jarababbene na bugawa a jarida, ita kuma Ommu da yake Allah ba azzalumin bawan sa bane sai dai bawa ya zalinci kansa, sai Allah ya jarabceta da bala'in kaunar Suhana da Suhail ɗin, Allah ya sakawa su Aafia ta wannan hanya, a takaice ma domin su Suhana take zama da wannan mijin nata ba dan komai ba, dan saboda ba shi da kuɗi, ita kuma ba sai na gaya maku ba, mayyar kuɗi ce, da farko yana da kuɗi lokacin da suka yi aure, hakan ne kuma ma yasa ta aure shi, daga baya kuma ya samu karayar arziki, shi ne fa take son rabuwa da shi, kuma tana bala'in kaunar ƴaƴanta da suka haifa da shi, ta san kuma ko mutuwa zata ba zai bata ko ɗaya daga cikinsu ba idan ta ce bata son shi, hakan yasa ta daure ta zauna da shi, amma dai yanzu hankalinta na kan Abbi da yake yanzu kuɗi sun dawo kamar da a hannunsa. A ɓangaren ita ma Ommun, ɗaura wayar ta yi a saman bedside drawer tana faɗin "Ɗan wahala ba zan dawo ɗin ba, kuɗi ma nake nema da zan je in biya katti su kashe mani kai na samu na ɗauke yarana mu dawo gidan nan na har abada, banza shashasha". (To fah waye shashasha a cikinsu kenan? Uhm ni dai na yin gaba sai kun zo.) A ɓangaren Akila kuwa, yau tun safe take zubawa ɓoyayyen masoyinta kuka akan lallai tana son ganin hotonsa, da yake yau bai je school ba, suna manne da waya suna kashe juna da kalaman soyayya, ko palo taki fita bare ayi zancen yin breakfast, ta mance ma kwata kwata da ana cin abinci a duniya, ta narkewa masoyinta tana kashe shi da kalamai yana kasheta da shagwaɓar nan tasa mai rikita zuƙatan masoya. "My heartbeat dole na yi duk wani abin da kike so, amma dai ban so baki hotona ba, na so ne na kawo maki kaina da kaina har gida ta yadda zaki sami damar ganina da kyau, na yi maki alkawarin duk rintsi duk wuya ba zan wuci daga nan zuwa 1 to 4 months ba zan kawo maki kaina har gida, amma dole zan tura maki hotona yanzu domin ki yi farinciki, but da sharaɗi". Cikin shagwaɓa ta ce "Sharaɗin menene kuma Heartbeat?". "Sharaɗin zan sanyawa hoton kala, sannan kuma sau ɗaya zaki kalli hoton". Cike da zumuɗi ta ce "Na yarda, ba dai zan ganka ba?". E ya amsa mata da shi tare da cewa "To ki shiga WhatsApp yanzu zaki gani na turo maki, bari na ga action da zaki ɗauka mu gani, na yi nasara ne ko na faɗin? Ganina ya kori jina ne, ko kuma dai jina ya kori gani na." Ita dai bata amsa ba, cikin zumuɗi ta shiga cikin WhatsApp ɗin, hannunta har kerma yake yi wajen sauri ta buɗe saƙon da ya shigo mata da ɓoyayyen number. Ai kuwa tana buɗewa hotonsa ne yana tsaye a gaban wani tapkeken pool mai girma gaske, mai ɗauke da ruwa sky blue, bai sanyawa hoton nasa color kamar yadda ya faɗa ba, ya turo mata ne a ainahin kalar da a ka ɗauki hoton, da alama kuma dama ya gwada ta ne da ya ce zai sanya mata kala a hoton, dogone sosai yana sanye da wandon soja a jikinsa, sai kuma farar T-shirt, ya sanya bakin glass a face nasa, while yana ɗan duƙe da kansa, a shekaru ba zai wuci 22 years ba, yana da ɗan kiba kaɗan, haka zalika yana da faffaɗar kirji, farine tas da shi, yana da gashi a kwance a hannunsa da yake hannun ne kawai ta bayyana, kafarsa na sanye da wasu shegun home sleepers masu balain kyau, launin brown colar, fuskarsa bata fita sosai ba a hoton, sakamakon ya dukar da kansa yana kallon tsadaddiyar wayar dake a hannunsa, da alama irin gayun nan ne masu ɗaukar wanka, domin zaka gane hakan ne daga yana yin irin askin dake a kansa, wani irin askine wadda shi kaɗai ma ya isa ya sanya mata tsayuwa suna kallonsa, ta ko'ina ya haɗu, amma kuma da alama kamar ba farin ɗan Nigeria bane, amma kuma ya akayi yake bala'in mugu mugun jin bushasshiyar hausa haka? Idan ya yi wata karin magana sai ka rantse da Allah a bakinsa akayi Hausa, da alama dai kamar soja ne, domin yanayinsa ya nuna hakan. Shiru ta zuba mashi ido tana karewa kyakkywar halittarsa kallo, amma kuma a nata ganin ya yi mata mugun kama da gwaggo Batula, harta tsawonsa kusan ita ya ɗauko, sannan yanayin hasken fatarsu, kunsan na gaya maku suma hasken fatarsu ba irin hasken nan Nigeria bane, kuma kada ku mance ita dai Hjy Batula kanuri take aure fari tas da shi kamar Balarabe, sannan yana kama da Abla ƴar autar Hajiya Batula wadda ta kasance tamkar balarabiya saboda haske, kusan a cikinsu su dukka ma, ita Ablan ta fi su haske, ko da yake ita kaɗai Akila ta sani, bata san saura ba, Abla yarinya ce karama sa'anin su Jehan ɗin. Ta jima tana kallon wannan hoton nasa, domin tabbas ta taɓa ganin exactly wannan fuskar, to a ina? Duk da ma bai ɗago kan nasa sosai ba, amma dai tabbas yana mata kama da mutane da dama da ta sani, ciki kuma harda Abbanta. (To fa lallai Akila shi kaɗai ne mai kama da mutane da yawa haka? Anya ba kyansa ne ya ruɗa ki ba kuwa? Ke wannan idan da kinga ainahin fuskar Lion or James ko Michael ina ga suma zaki yi saboda ganin tsantsar ainahin kyau, kai Akila akwai son kyau gaskiya oh ni🤔.) "Heartbeat zuciyata sai bugawa take yi da sauri sauri, please ki gaya mani, shin nayi maki ne ko ban yi maki ba? Wannan dalili yasa nake fargaban tura maki hotona, wlh Heartbeat idan kika ce ban yi maki ba zan iya mutuwa, domin ba ƙaramin kamuwa zuciyata ta yi da sonki ba, dan Allah my heartbeat kada ki ce ban yi maki ba kin ji ko tawan?". Sai lokacin da ta ji voice nasa ne yasa ta gane cewa ashe bai katse kiran ba, ita ta shagala da kallon hotonsa, ta mance da suna waya baki ɗaya. Yar firgita ta yi kafin ta ce "Gaskiya baka yi mani ba, bana son soja kuma bana sonka domin kai ba irin mazan da nake burin aura bane". Ta kai karshen maganar tare da fita daga kan hoton nasa ta ma fita WhatsApp ɗin baki ɗaya tana turo baki kamar biro. Yana daga zaune a bakin katafaren pool daya ɗauki wannan hoton da ya tura mata, ya zura kafafunsa a cikin ruwan yayin da fuskarsa ke sanye da face mask ga uban tulin takardu a saman table a kusa da shi, daga gefe kuma drinks ne da glass cup mai ɗauke da drinks ɗin a ciki, da alama karatu yake yi, hira da ita ne tasa har ya sauƙa daga saman table ɗin ya dawo bakin pool ɗin ba tare da ya lura ba, soyayya daɗi bai ma san time da ya tsunduma kafafunsa a cikin ruwan pool ɗin ba, har sai da ta furta cewa bata son shi ne ya yi wani irin razana wadda ta sanya shi faɗawa cikin pool ɗin ba tare da ya ankara ba, sai dai ya ji shi tsulundum a cikin ruwa. Ita kuma cikin wasa ta gaya mashi hakan bata san wannan kalma tana ƙoƙarin yin kisan kai ba. Da kyar ya iya fitowa daga cikin pool ɗin tare da mai da wayar a kunnensa da yake waterproof ce wayar ma, akwai waterproof a jikinta sai bata yi komai ba. Magiya ya fara yi mata har da hawayensa, ita kuma sai murmushi take yi, daga karshe da ta ji yana kuka sosai sai ta bashi hakuri tare da ce mashi ganinsa da jinsa duk ɗaya ne, dan haka ta ko'ina ya yi mata, yanzu burinta kawai ya gaya mata yaushe zai zo gareta ya kawo mata kanshi suga juna ido da ido. Tsabar daɗi da murna bai san time da ya ce mata next week yana nan zuwa ba, haba ita ma wani irin tsalle ta yi tare da komawa saman gadon ta baje tana sauke numfashi. Kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "Heartbeat kada fa ki yi ki jiwa jikina ciwo, kada ki ragewa halitata quality, dan haka ki bi min kayana a hankali cikin kula idan ba haka ba, wlh yanzu ki ga sojoji a gidanku sun zo sun ɗauko mani ke sun kawo mani ke". Zubur ta miƙe zaune tana faɗin "Dama kai ɗan Nigeria ne? Amma ya na ganka kamar balarabe ko Bature?". Yana ƙoƙarin cire kayan jikinsa da suka jiƙe ya ce "Meyasa kike tambayar ni ɗan Nigeria ne ko ba ɗan Nigeria ba?". Cikin zumuɗi ta ce "Ai na ji ka ce za'a azo a ɗauke ni ne, shi ne abin ya bani mamaki". Cikin nuna ko in kula ya ce "Yah ni ɗan Nigeria ne kuma Yaya ne ko kani ne ga Imran Shikenan?" Shiru ta yi tana tunanin anya kuwa ba wasa da hankali zai yi mata kamar yadda ya saba canzawa ƙwaƙwalwarta tunani akansa ba kuwa? Kai ba gaskiya bane, shi ba ɗan Nigeria bane, to amma idan ba ɗan Nigeria bane a ina ya san gaba ɗaya familynta? A ina ya iya wannan busashiyar hausa da babu miss ɗin? A ina ya yi mata wannan shegiyar farin sanin? Har size na takalmarta ya sani? Breziya pant dukka ya san size nata kamar wani Aljani, daren jiya da suna hira akan aurensu da kayan lefe, shi ne take gaya mashi size na jallabiyar da take sanyawa, bai bari ta karisa ba ya rigata da gaya mata size na komai da komai nata, tasha ruwan mamaki, amma kuma bai bari ta yi mamakin ba bare ta tuhume shi ko ta tambaye shi, sai ya yi saurin canza topic na maganar zuwa hirar su AKil, kuma sau da dama haka yake yi mata dama, idan baya son gaya mata abu ita kuma ta matsa, to sai ya canza mata topic ɗin maganar ya mantar da ita wancan magana da take son sani. Ganin ta lula duniyar tunani ne yasa ya ce "Bari na goge maki tan tama akan tabbas ni ɗan Nigeria ne, yanzu dai ki shiga WhatsApp bari ki ganni cikin ƴan uwana". Ai kuwa da sauri ta shige WhatsApp ɗin dan ta ga me kuma zai sake turo mata. Hotonsa ya sake tura mata kusan irin na ɗazun, yana tsakiyar bakaken fata tsundum, dukkansu kuma manyan mutane ne shi ne kaɗai karami a cikinsu, wannan hoto kuma yana sanye da face mask, sai dai kuma ta gane shi ɗin ne domin ta yi mashi kallon kurilla a hotonsa na baya, shiru ta yi tana kallon mutanen dake a gefensa, tana son tantance da ƴan wace State a Nigeria suka yi kama, sai jin muryarsa ta yi yana cewa. "Me yasa zaki yi tantama da abin da na gaya maki? Shin ina yi maki karya ne? Bana maki karya sai dai na yi maki wasa wadda kuma idan muka gama waya kafin mu yi sallama ina gaya maki wasa nake yi maki akan abu kaza domin kada ki ɗauke ni makaryaci, to dai a wannan ma wasa nake yi maki, sai dai ba zan gaya maki a cikin magana biyun man wanenen wasa ba, ni ɗan Nigeria ne or not, da kuma hotona na tura maki shi ma or not, ki gane da kan ki, ɗaya ne gaskiya ɗaya kuma wasa, na tafi karatu za mu yi waya anji ma, yana da kyau ki rinƙa wasa kwakwalwa kema, maza ki yi tunani a cikin maganganu biyun nan ɗaya gaskiya ce ɗaya kuma wasa, cox sai anjima my bugun zuciya". Turo ɗan bakin nan ta yi kafin ta ce "To ai ni ban ga ji da jin muryar ka ba, dan haka ban sallame ka ba". "Heartbeat karatu fa zan yi please mana?". "No my heartbeat yau na soke karatun ba zaka yi ba, idan kuma ka tafi Allah ka sani ba zan ci abinci ba, kuma daga nan har ka gama karatu ka sake kirana ina kuka" . Cikin sauri ya ce "Subhanallah, rufa mani asiri my bugun zuciya, ni na isa in yi abin da baki so ne? Ba dai karatun ne baki so ba? To an barshi, zan ce HAROON ya rubuta mani Exam ɗin, idan kuma na faɗi Shikenan, amma ba zan damu ba tun da gimbiya ta ce ta sanya ni faɗuwa, in dai zaki yi farinciki ai bana ma buƙatar karatun". HAROON ta maimaita sunan da ya kira, ta yi ta yi da shi akan ya gaya mata sunansa, amma yaki, bata taɓa jin ko da sunan wasa ya kama wani suna na wani dake kusa da shi ba sai yau, ta sha ruwan mamaki sosai jin sunan HAROON kuma a bakinsa, to wai shin waye shi?. Ta yi nisa cikin tunanin da take yi sai jin zazzakar muryarsa ta yi yana faɗin "My heartbeat sarkin tunani, to yanzu kuma tunanin me ake yi?". Da alama bai san ya ambaci wani suna ba a cikin maganar tasa, domin kuwa baya son kwata kwata ta san wani abin da ya dangance shi, ina da ayar tambaya ma akan wannan hoto da ya tura mata, by mistake ya ambaci sunan nan na HAROON, ita kuma ta riƙe sunan tana ta juya shi a ƙwaƙwalwarta, kwata kwata bai kawo cewa ya faɗi wani suna da har ta riƙe take juya shi a ƙwaƙwalwarta haka ba. "Heartbeat na magana nake yi maki fa, haba mana, ko so kike yi na yi maki kuka ne?" Ya kai karshen maganar tare da saka mata kukan shagwaɓa har da kumbura kumatu irin na ƴan shagwaɓar nan. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ce "Sorry my husband to be In Sha Allah, tu ba nake yi, kada ka yi mani kuka ka ji Heartbeat ɗin Heartbeat nasa?". "What? Me kika ce? Dan Allah my Heartbeat ki sake maimaita sunan da kika kirani da shi yanzu kin ji?". "My husband to be In Sha Allah na ce". Ya ilahi ya lalliahi wani irin miƙewa tsaye ya yi, a rikece ya fara magana har yana haɗe words. "Heartbeat kina nufin da gaske zaki aureni? Kina nufin kin yarda kina sona duk da baki taɓa gani na ba? Kin yarda da ni kin bani zuciyarki? Dan Allah ki amsa mani ko zan samu natsuwa, zuciyata sai buga mani take yi da sauri sauri, My Heartbeat please say something to your husband ko zai ji sauki kaɗan". Hannu tasa ta fure fuskarta tana murmushi, cikin tsantsar so da kuma kaunar shi ta ce "Yah, na yarda da kai, duk da ban san ka ba, ban taɓa ganin ka a fili ba, ban san a ina kake ba, shin mutun ne kai ko aljani, ban sani ba, amma na yarda da kai domin har cikin zuciyata ina jin baza ka cutar da ni ba, please ka riƙe mani amana, ka ji ko? Da gaske nake yi ba da wasa ba, wlh ina sonka fiye da tunaninka, bana jin zan iya rayuwa da wani namijin idan ba kai ba, ina sonka sosai wlh". Shiru ya yi kamar an ɗauke wutar nepa, daɗi ya hanashi yin magana, ya rasa ta ina zai fara, wani irin daddaɗar yanayi ya tsinci kansa a ciki mara misaltuwa. Ya ɗauki tsawon minti ɗaya kafin ya ce "Heartbeat kin kasheni yau, anya ma zan iya yin barci yau kuwa? Kai daɗi ba zai barni ba, yau dole na yi sadakar da ba zan iya irga nawa ne na kashe ba, dole gobe na ɗauki azumi, dama na yi wa Allah alkawarin duk ranar da kika karɓi soyayyata, ki ka aminta zaki aureni, to tabbas zan yi azumi goma a jere, domin na nuna godiya ta ga Ubangiji na, idan kuma na zo gida Abba ya bani aurenki, to daga ranar zan ɗauki azumi sai na yi guda talatin cif dan nuna wa Ubangiji na tsantsan farin cikina da godiyata a gare shi na ni'imar da ya yi Mani, ya bani ke a matsayin mata, Heartbeat me kike so na yi maki yanzun nan, ki faɗa mani dan Allah, ni kuma na yi maki alkawarin zan yi maki shi matuƙar bai saɓawa Allah ba, kuma komai wuyarsa zan yi maki, please tell me kin ji bugun zuciya ta?". Kai wayyo daɗi soyayya, to bari mu shaƙata da wagga waƙa na TRIPLETS MUSIC daga bakin ɓoyayyen masoyi. "Nazo ki min kalamai my Heartbeat, ke ɗai a cikin mata Ni na riƙe, kuma ba bari ko canza maganaaaaaaa....... Da ke kaɗai na aminta, babu mai canza ni, ko wuya ko daɗi, zuciyata taki ce, sahiba kuma baby na........ Mmmmmm....... Mmmmmm, Ke ɗin ta dabance, in naji muryarki ko a ina zan wai waiya, kuma in tsaya har sai na ganki heartbeatttt, ke ɗai a cikin mata na zaɓa ne, in babuke to ni ɗin ma dai babu neeee, kuma dole ne in ce maki kizo, ni dake na amince, Heartbeat mai kyawun zance, kin iya zuba kalamai, ga iya shagwaɓa ba'a magana". Wayyo daɗi duniyar nan take Mani, duk in da ka ji ance Heartbeat + Heartbeat tofa mu ɗin ne kawai........ TRIPLETS MUSIC..✍️ PRINCESS TEEMA. STORY💋 A shagwaɓe ta ce "Sai mun yi waya an jima zan gaya maka abin da nake so ka yi mani, amma yanzu ma ka fara mannawa Al Qur'ani mai girma kiss, ma'ana idan mun gama waya ka yi karatun Al Qur'ani mai girma koda shafi biyu ne a cikin suratul Maryam, sannan ka yi mana addu'a ka ji mijina?". Wani irin dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, cike da so da kuma kaunar ta ya ce "Dole ma kuwa, yanzu ma ba sai anjima ba, kuma ina katse kiran alwala zan yi na yi Sallah raka'a biyu dan nuna tsantsar madarar godiya ga ubangijin mu, karatun Al Qur'ani ya zama dole, kuma full suratul Maryam ɗin ma zan karanta maki, ke kuma ki je ki yi tunani akan abin da na ce ki gane na wani magana ne na yi na wasa, wanne ne kuma na gaske, ni ɗan Nigeria ne ko a'a? Sannan kuma hotona ne ko ba nawa ba? Ki je ki yi tunani nima bari na je na aiwatar da Sallah da karatu, ki kula mani da kanki sosai da sosai". Yana kai karshen maganar diff ya katse kiran. Har cikin zuciyarta ta yarda cewa yes hotonsa ne wannan, sai dai bata yarda shi ɗan Nigeria bane dan kalar fatarsa, abin da ta manta da shi kuma shi ne suma family'nsu haka kalar fatar haskensu take, sai dai sun ɗan rage haske saboda rana, kuma bata san daddynsu Rismha bane, da ba zata taɓa musa cewa masoyin ɓoye ba ɗan Nigeria bane, saboda kusan hasken daddyn Rimsha da wanda yake jikin wannan hoto wato masoyin ɓoye, duk kusan ɗaya ne, da kaɗan masoyin ɓoyen ya fi shi, haka zalika shima Hassan wato Azharuddeen daddy Anaya, shima kamar Bature haka yake, a A.B.U ma Bature suke kiransa ko kuma Yellow saboda haskensa. Shiru ta kwanta a saman gadon tana tunanin me mafita, wannene ba gaskiya ba a cikin waɗan nan magana biyun nasa?. A ɓangaren JELLY kuwa, bayan sun dawo bata fi da minti biyu ba ta dawo palo ta cigaba da kallonta da take yi ɗazun, kamar ba ita ba, su Hanan kam basa gajiya da mamakin halin jelly, ita ma Aunty sai lokacin ta dawo palon ta zauna, suka cigaba da hirarsu har zuwa lokacin da su Abbi suka fito dan aci abinci. Bayan sun haɗu a saman table ne, Abbi ya ya ce su ba shi hankalinsu bari ya yi magana da su, dukkansu natsuwa suka yi tare da tattara mashi hankalinsu baki ɗaya a kansa. Kowa na cikin gidan yana saman wannan table ɗin except Ommu da dama already kun san da cewa bata shiga cikinsu, domin ba shi ne ya kawo ta gidan ba, abin da ya kawota daban, shiyasa bata damu da kowa a gidan ba. Gyaran Murya Abbi ya yi tare da fara magana "Batula da ke da Halima ina son gobe ku ɗauki Jalila zuwa gidan yaya babba domin ku gabatar wa da Umaiya ita, sannan ku barta a can dan ta zauna a gidan mijinta, bai kamata mu riƙeta a nan ba, ina kuma kunyar mu tasa Imran bai yi wata magana ba, to dan haka ba zamu zama iyaye masu son kai ba, da ni da Maik da Irfan za mu tafi Katsina idan Allah ya kai mu gobe wajen iyayen Hanan, dan yana da kyau su san abin da ake ciki, idan sun bamu Hanan za mu dawo da ita, idan kuma ba su ba mu ita ba, to a can ma zan ɗauki nauyin karatun ta da komai da komai nata har zuwa ta yi aure, amma dai zan so su ba mu ita ɗin, ban san ya halinsu yake bane, kun san wasu iyayen ba za su yarda da hakan ba, to fatan mu dai Allah yasa dai su aminta su baku ita". Amin gaba ɗayansu suka amsa da shi, sannan daddyn Jelly ya ɗaura da cewa "Yaya Deen ai mun yi magana da Imran ɗin, shi ne ma ya ce mu bar jelly a nan zuwa nan da next week zai zo ya ɗauke ta su wuce gidansa". Salati Abbi ya saka yana mamakin jin wannan magana, daddyn Jelly ya zama kamar wani ƙaramin yaro, yaushe aka taɓa yin haka? Dan suna ƴan uwa kawai shi Imran shi zai zo ya ɗauki jelly ya kaita ga iyayensa? Wannan abu sai ka ce wasan yara, aure fa aka ce!. "Maik ya za'a yi muna da mata a gida kuma a ce Imran ne zai zo ya ɗauki Jalila da kansa ya kai ta ga iyayensa? Wannan ai ya zama wasan yara, kuma kai ma sai ka yarda da hakan? Iyaye fa ai ba abin wasa bane, dan haka Batula da Halima su shirya zuwa gobe su ɗauke ta su kai ta gidan da kansu, sannan su yi mata nasiha sosai dan ta natsu ta san yanzu ita matar aure ce, daga nan su barta su dawo, wannan shi ne umarnina!". Jinjina kai daddy ya yi alamar to ba damuwa, shi kuma Irfan miƙewa ya yi ya nufi waje, gaba ɗaya baya jin daɗin abincin ma, ya rame ƴan kwana biyun nan kamar mara lafiya, baya wani cin abinci sosai, baya da kwanciyar hankali da natsuwa, jiya har kofar gidansu Akila ya je dan ya samu ya tambayeta ko lafiya number bata shi ga, amma da ya je mai gadi ya ce bata nan ta tafi school, ga shi numberta baya shiga tsawon kwana uku kenan, kuma ba sai na sake gaya maku ba kun san da cewa Ammie bata kaunarsu bare ya shiga ya tambayeta ko wani abin ne ya sami wayar Akila ɗin, haka ya juyo kan motarsa ya dawo gida, a wannan daren dai bawan Allah nan bai samu barci ba, kamar yadda ya ga rana haka ya ga wannan dare dai, ya ci bakar wuya na raɗaɗin da zuciyarsa take yi mashi. Yanzu ma haka da ya fice daga palon ɗakinsa ya koma ya kwanta tare da runtse idanu kamar mai barci, dama kuma kun san shi ma'abocin kwanciya a ɗaki ne. Yana fita kuma daddyn Jelly ya bisa da ido ba tare da ya ce da shi ko ubban ba. Sai bayan sun kammala cin abinci matan su tafi ne daddy ya dubi Abbi ya ce "Yaya Deen Irfan da Akila fa soyayya suke yi". Da fara'a Abbi ya ce "Kai haba dai?" tabbatar mashi da hakan daddy ya yi, murna a wajen Abbi ba'a magana, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, sai murmushi yake yi ya ce "Zan je Banki ranar Monday da kai na in samu yaya In gaya Mashi, duk hukuncin da ya yanke shi zamu bi, ni nasan ba zai hana Irfan Akila ba, amma dai sai mun gaya mashi sannan asan abin yi". Sosai suka sha hira tare da ɗan tsakuro hiran abin da ya faru a baya suka tattauna kafin daga bisani kowa ya nufi Part nasa, daddy wanka ya je ya yi sannan ya kira Aunty a waya akan ta turo mashi Ayla bari ya yi mata wanka za su fita ne, dan tun da suka bar saman table sai ta bi su Aunty ɗin zuwa ɗakinsu. Salati Aunty tasa tana mamaki wai bari ya yi wa Ayla wanka, kamar wata jaririya, ta faɗa cikin zolaya. Shima cikin zolaya ya ce "To ai ni a wajena jaririya ce, dan haka dole kinga na rinƙa yi mata wanka ina goya kayana". Dariya Aunty ta yi kafin ta ce "Ko ba goyo ba? Wlh yaya Maik tun da ka yi aure ka sauya, wato ma.....". Bai bari ta karisa ba ya ce "Zaki turo mani ita ne ko kuma na shigo da kaina na ɗauki kayata?". Da sauri ta ce "A'a ai yanzu ma gata nan zuwa". Kashe wayar ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, ya cigaba da shirin da yake yi, a haka Ayla ta shigo ta same shi, wani irin sihirtaccen kyau ta kara yi yarinyar nan, fatar jikinta ya kwanta luwai luwai, ta samu hutu sai wani kara ƙiba take yi abinta, mazaunantan nan sai kara cikowa suke yi, da yake ta kasa take da ƙiba ba ta sama ba. Tana sanye da wandon jeans palazo blue color, da kuma riga high neck t-shirt black color, ta yi kyau sosai, kanta na sanye da ɗan karamin hijabi please call me launin blue color, kalar wandonta kenan, jikin hijabin dukka akwai stones manya manyan masu kyalli sosai, hakan ya karawa hijabin da ita kanta kyau. Yana sauke idanunsa akanta wani irin azababben sha'awarta ne ya kama shi, kashe mata ido ɗaya ya yi tare da yi mata alama akan ta zo, da sauri ta tafi ta faɗa jikinsa tana sauƙe ajiyar zuciya. Shima wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin nan ya zame mata Hijabin jikinta, ya ɗaura hijabin a saman mirror yana wani irin sauke numfashi a hankali hankali. Laluɓeta ya fara yi yana ƙoƙarin capko breast ɗinta, cikin dabara ya ɗauketa sai saman gado, ya manta da cewa shirin fita ya yi, tuni ya cire kayan nasa ya hau sabuwar aiki na wucewa sama jannati.......... Takaitacciyar Nasiha garemu mata, da farko zan fara da TSAFTA!! TSAFTA!! TSAFTA!! a addinance tsabta tana daga cikon addini, a zamanance ita ce garkuwan lafiya, duk macen da bata da tsabfa tabbas kusan da ita da dabba duk ɗaya ce, bambancin kawai tunani, bai kamata kina mace ki saki jiki duk datti ba, Hajiyata mace ƴar kwalliya ce, mace da gyara aka santa, mace ƴar gayu ce, ina kara gaya maku, ke ko nawa ne Hajiya ki kashewa jikinki, in dai a fagen gyara ne, sai kaga wata mace ta zauna fatar jiki duk ya bushe kamar wani bayan kada, haba mana ƴar uwa, me namiji zai taɓa ya ji daɗi haka? Jiki kamar bayan bushasshiyar kifi, kai ina kada ki yarda ki zama guzuma, kayan gyaran nan fa ba wani tsada ne da su ba, kuma ma yafi kyau ki zauna ki haɗa kayan gyaranki da kanki a gida, kama daga sabulun wanka, man shawa masu kyau da inganci, turaruka, dilka da sauransu, kada ki rinƙa sayan na haɗawa a waje, domin kuwa suna mixing nashi da chemicals, wadda idan kika saya kika yi amfani da shi, idan suka yi expire suna kashe matar mace, suna lalata mata jiki, wani daga nan fatarta zata daina karɓar kayan gyara, to yana da kyau duk wasu kayan gyara ki haɗawa kanki da kanki, zan baku kaɗan daga cikin sirrin kayan gyara na addini musulci domin lokaci ya tafi, page na ya kai dai dai munzalin da nake Dakatawa. Abu na farko ki sami ganyen ɗanyar lalle ta Hausa, sannan ki sami dilka, nescafe, kwai (egg) da kuma madara ta ruwa, sai lemon tsami kaɗan, sannan sai zuma and ruwan tumatir kaɗan. Wannan ganyen lallen zaki fara daketa sai ta yi laushi ta fitar da ruwa, sannan ki kwashe ki ajiyeta a gefe, kada fa ki daka a turmi mai yaji Hajiyata, to idan kika daga a cikin mai yaji matsalarki ce, ke zaki je kina ihu Princess Teema tana kwance a gado bata san me yake faruwa ba. Bayan kin kwasheta kin ajiye, sai ki ɗauki kwai ki fasata a wata roba daban, dukka kwan zaki haɗa har da na cikin, wasu suna cire na cikin, amma ki zuba har da shi yafi kyau, idan iya yi ɗaya ne, kwai ɗaya ya isheki. Ki kaɗen kwannan sosai, sannan ki zuba wannan dakakkiyar ganyen lallen, ki sake kaɗesu sosai, ki yi tabbatar ganyen lallen nan ya yi laushi luƙui sosai ta yadda zai haɗe da kwai ɗin. Idan kin kaɗesu sai ki zuba madara ta ruwa, idan ma ta gari ce ta samu, sai a jiƙata, sai ta narke, sannan a zubata a ciki, ruwa kaɗan za'a sanyawa madarar, sai ki sake kaɗewa kafin ki zuba zuma da ruwan tumatir kaɗan, sannan sai a zuba nescafe, na sanyawa a tea, shi wannan nescafe ɗin kala kala ne, akwai mai kyau, akwai mara kyau, to a nemi mai kyau dan a sami biyan buƙata, a haɗesu sosai ta yadda za su game jikinsu, daga karshe sai a matsa ruwan lemon kaɗan dan a kashe karnin kwan, sannan kuma yana kashe kananan dark sport na fata, tana kuma taimakawa fata sosai wajen ganin kananan kuraje sun dai'na fita. Idan aka gamesu suka haɗe sosai, sannan za'a iya zuba kuka kaɗan, is and optional, bayan anyi haka, sai a shafe jiki gaba ɗaya, a barshi ya yi minti talatin, ya bushe, idan ya bushe, sai ki murje jikin naki, Hajiyata tun daga kan murjewa zakiga yadda jikinki ke murjuwa, yana fitar da wasu dattin da ke kanki sai kin yi mamakin ta ina wannan datti ya bayyana. Idan kin murje, sai ki je ki yi wanka, wayyo Allah, zakiga yadda fatarki zata koma, wani irin fresh zaki yi, ki fito luwai luwai, kina glowing Hajiyata.. Lokaci ya tafi, sai mun haɗu a wani page ɗin, In Sha Allah duk sauran wasu kayan gyara suna nan tafe, daga gyaran fatar jiki, har kan gyaran can ciki, ma'ana kayan karin ni'ima na mata da sauransu, amma fa ba alkawari na yi maku ba, idan na sami time zan rinƙa jefo maku a cikin page's ne....... Ma'assalam...✍️ PRINCESS TEEMA💋 ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E3-4 Laluɓeta ya fara yi yana ƙoƙarin capko breast ɗinta, cikin dabara ya ɗauketa sai saman gado, ya manta da cewa shirin fita ya yi, tuni ya cire kayan nasa ya hau sabuwar aiki na wucewa sama jannati. Can kasan maƙoshinsa ya ce "Babyn daddy ya naga kamar daddy ya yi ajiya ne?" Cikin nuna ko in kula domin bata ma san ma'anar maganar tasa ba, ta ce "Daddy ajiyar me kuma? A ina kuma kayi ajiyar?". Miƙewa ya yi daga rumfar da ya yi mata ya zuba mata ido sosai, yana kare mata kallo, tabbas ta kara kyau sosai, amma kuma ba abin da yake tunanin ɗin bane, kawai dai kyau ne na tsantsan kula da take samu daga gare shi. Ganin ba abin da yake tunani bane yasa ya shafa shafaffen cikinta nata tare da haɗe fuskokinsu, kasa kasa ya ce "Jelly ita kaɗai Allah ya bani, ina bala'in son yara, wlh idan na kalli yara a hannun wasu, ji nake tamkar in je in kwacesu, ya Allah ka bani baby a wannan haɗuwar tamu da zamu yi yanzu". Ya kai karshen maganar yana yana mai hauro da hannunsa zuwa saman kirjinta. (Tofa shi kuma Romeo ba abin da ya tsana kamar yara, ga wasu kuma a nan suna nema ido a rufe, Allah ya shirya Romeo da rashin son yara) "Daddy nima ina son yara wlh, musamman ma kanana suna da kyau kamar me". A hankali hankali ya fara shafo breast ɗin nata yana faɗin "Musamman ma idan a kace yaran sun yi kama dake ba, wlh ba ƙaramin kyau za su yi ba". Zata yi magana ya capko bakin nata tare da zura mata harshensa cikin tata ya fara kissing nata. Shiru ta natsu tana biye mashi, yanzu idan da sabo, ta gama sabawa da jarabarsa, tun abin yana damunta har ya dai'na, ta rungumi kaddararta na hakura da jararrabar mijin nata, sai dai kuma shi ba kamar sauran irin mazanmu na yau da kullun bane, mafi yawancin maza suna ɗauka jima'i shi ne kawai aure, shi ba haka yake ɗauka ba, tabbas yana da jarabar tsiya, amma kuma yana ƙoƙarin ya zama cikakken miji, yana ƙoƙarin ya yi koyi da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, domin Annabi har wanke wanke yana taya su Nana A'isha, Nana A'isha da bakinta ta ce har ƴar tsere suna yi da Manzon Allah (S.A.W) a gida, ya kama maza su sani ba iya biyan buƙatarsu a wajen mace, da ciyar da ita da shayar da ita ne kawai ya zamana hakki a kansu ba, ya kamata su nemi sanin tarihin fiyayyen halitta domin su samu gobe mai kyau, ga dai misali akan daddyn Jelly, yana balain kaunarta, yana kula da ita, yana faranta mata, ya mai da ta tamkar wata sarauniya, to yanzu ku gaya mani me ya ragu da shi da yake yi mata hakan? Wlh babu abin da ya ragu da shi, sai ma karuwa da ya yi na samin ɗumbin lada wajen Ubangiji, ya yi koyi da Manzon Rahma, ba ko wani namiji ne zai iya yin hakan ba, amma yana da kyau ku rinƙa kwatantawa koma yayane, domin a rage wasu matsalolin na cikin rayuwar aure, kuma, mata na juyo gare mu, yana da kyau mu gyara halinmu, misali akan Aunty, Ayla, da kuma Umaisha, irin halinsu yasa dole mazajensu ke kyautata masu, hakuri, juriya, riƙo da addini, kyautata mashi, kome ya ce matukar bai saɓawa Allah ba cene mashi to, kuma kiyi mashi a lokacin, kada ki yi gardama ko ki yi musu da shi, ki daure ki jure ki yi biyayya, ko da baki samu jin daɗi yadda kk so a nan duniya ba, ki sani a lahira zaki more, zaki huta, zaki ji daɗi fiye ma da yadda ki ke so ɗin, kada ki yarda ki yi biyu babu, babu duniya kuma babu lahira, kada ki yi koyi da irin halinsu Ommu, ki tabbatar kin yi koyi da halin ɗaya daga cikin waƴan nan Aunty, Ayla, ku kwatatan ku yi tunanin me yasa mazansu ke kyautata masu? Meyasa suke kaunarsu? Saboda sun nunawa mazan nasu cewa sune sarakunansu, sune sama da su, ko wani namiji yana son girmamawa, dan haka mu gyara, Allah Ubangiji yasa mu dace. STORY💋 Sosai ya more kayarsa ko in ce suka mori juna, domin kuwa yanzu ita ma ta kware sosai, ya koya mata, ta zama irinsa. Sun jima kwance manne da juna yana zuba mata kalamai tare da shagwaɓa kamar wani yaro, ya zama tamkar ƙaramin yaro a gaban matar tasa, ba ya wani damuwa da zancen zata raina shi, dan yasan ba haka take ba, shiyasa yake zuba mata shagwaɓarsa son ransa, kuma da yawan maza ba wai basa son yin hakan da matansu bane, kamar yadda na faɗa a baya, gani suke yi kamar idan suka yi hanan da matan nasu, matan za su rainasu, wannan dalili yasa suke tsare gida abinsu, wani ma da ya fara hakan sai ta fara ce mashi ragon namiji, to ƙalu bale garemu mata, ko yau a ka haifi namiji to fa sama yake da ke, ko da kuwa kin kai shakara hamsin, Ubangiji ne ya fifitasu akan mu, mune a kasarsu, ba lallai sai miji bama, ko wani irin namiji sama yake da mace, to ina ga kuma ance mijinki? Wadda shi ne Annabi ya ce, da bawa yana yi wa bawa sujjada, to da tabbas zai yi wa mace umarni ta rinƙa yi wa mijinta domin girmamawa, tabbas Allah ya girmama miji sosai akan mata, ko me miji zai yi maki bai kamata magana ta raini ta shiga tsakaninku ba, tun da Ubangiji da kansa ya bashi wannan girma da kuma power, yana da kyau mu kula da hakan dan kada mu zo duniya a banza kuma mu koma a banza, Annabi ya ce mata sunfi yawa a wutar jahannama, wannan magana kuma kunsan tabbas haka ne, innalillahi wa inna ilaihir rajiun......😭 Ba kuma komai ne yasa mata suka fi yawa a wutar jahannama ba fa ce kin bin umarnin mazajensu, zagin mazajen da kuma rainasu, hakan yasa suka fi yawa a wuta, to dan Allah mai karatun littafi na, kada ki bari ki zama ɗaya daga cikin irin waɗan nan mata, nasihata a gareku shi ne, ku yi hakuri ku daure ku danne, da ki cuci mijinki, wlh gwara shi ya cuceki, kuma ki yi wa Allah ki yafe mashi tare da yi mashi addu'a shiriya, tabbas Allah baya barci, yana ganin komai da yake faru, sai ki ga sanadiyar yafe mashi da kika yi, Allah ya baki gidan aljanna ko da kuwa baki yi aikin shigarta ba, to dan haka ina mai mana nasiha akan hakan, sannan kome zaki yi ki tabbatar domin Allah zaki yi, dan ki samu wannan rabo ta ni'imar Allah, idan ki ka yi domin wani, to ki sani wanin bashi da wuta kuma bashi da aljanna, to is better for you ki yi domin mai wuta da aljanna, dan ki shiga cikin aljannar, Allah Ubangijin ya sa mu dace, ya kuma bamu ikon gyara kura kuran mu, ina kara jaddada mana, muji tsoron Allah, a duk in da muke, mu san Allah yana ganin mu, kuma mutuwa bata da tabbas, tana iya zuwa a ko da yaushe, tana iya ɗaukarki kina tsaka da cin abinci ko aikata wani abin, ace mutuwa ta ɗauki mutun yana aikata saɓon Allah, ina zai tsaya da wannan bala'in,. Akan abin da kika mutu za'a tasheki, kada ki manta a ranar gobe kirayama tabbas ba ke zaki yi magana ba bare ki yi karya, hannun da kika aikata sharri ko alkhairi, shi ne zai yi magana da izinin wadda ya halince shi da mu baki ɗaya, shi zai faɗi abin da kika aikata da shi, haka zalika sauran sassa na gaɓoɓin jikinki, to dan haka mu kiyaye, fatana shi ne mu gudu tare, mu kuma tsira a tare, Allah kuma ya sa hakan Amin, ba zan so ace mai karanta littafi na ta kauce hanya ba, zanji zafin hakan fiye da tunanin mai tunani. YA ALLAH KASA DUK MASU KARANTA BOOKS NA, SU KASANCE NA KIRKI DAN KA HAƊA MU A ALJANNA, IDAN MA AKWAI WANI HALI MARA KYAU DA SUKE YI A ƁOYE, YA ALLAH KA YAFE MASU, KASA SU GYARA DOMIN MU KASANCE A TARE A ALJANNA, INA SON MASU KARATUN LITTATAFAINA💘💋❤️. STORY💋 Sai da ya ga ta fara yi mashi barci a jiki sannan ya ce ta tashi su je su yi wanka, make mashi kafaɗa ta yi, cikin shagwaɓa da magagin barci ta ce "Ni barci nake ji daddy". Shafa kanta ya yi yana faɗin "Babyn daddy, ki hakura na yi maki wanka sannan ki yi barcin ko? Bana son ki yi barci da najasa a jiki, Annabi ya tsawatar akan hakan, ya hanemu da hakan, domin hakan babbar barazace ga lafiyar ɗan adam, idan bawa yana cikin najasa fa to komai yana iya faruwa da shi baby, ciki kuma harda asiri, tsafi, aljanu, shaiɗanu, da dai sauransu, dan haka ki daure daddy ya yi maki wanka, in yaso sai ki zo kiyi ta barcinki har sai time da kike so, ni kuma zan yi zaman jiranki har sai kin tashi daga barcin sannan mu fita unguwar ko?". Duk jikinta ya mutu da jin nasiharsa, hakan yasa ta miƙe, jikinta duk a mace saboda barci, haka ta diro kasa daga saman gadon, sannan suka nufi toilet. After some minutes, ya fito riƙe da hannunta suka nufi gaban mirror, dukkansu suna ɗaure da towel, da alama dai a tare suka yi wankar. Lotion ya shafa mata kafin nan ya sanya mata kananan kayanta tare da fesheta da perfume nasa masu daɗin Kamshi, sannan ya ruƙo hannunta suka wuce saman gado yana faɗin. "To jeki kwanta bari na shirya na zo mu kwanta sai zuwa anjima mu fita ko?". Gyaɗa mashi kai kawai ta yi kafin ta wuce ta haye saman gadon, shi kuma, ya wuce ya nufi gaban mirror dan ya shirya. Kafin ya gama shiri ya dawo, har ta yi barci abinta. Kusa da ita ya zo ya kwanta yana fuskartar sama, kamar mai yin wani tunani. Can kuma kasa kasa ya furta "Ina son sanin su waye iyayenki? Ina son sanin a ina suke? Meyasami babanki? Meyasa mamanki ta rayu dake cikin kunci da wahala duk da cewa ta ce mahaifinki yana da kuɗi? Ina buƙatar waƴan nan amsoshi wadda kuma nasan mamanki ce kawai zata iya bani su!". Shiru ya sake yi yana mai jin tsantsar kaunarta yana kara ratsa shi, tabbas yana bala'in kaunarta, amma kuma yana tsoron samun haihuwa da ita ba tare da ya san tushenta ba, in fact a matikar tsorace yake a duk lokacin da ya haɗa jiki da ita, jarabace kawai irin tasa yasa yake kusan tar ta ɗin, domin kuwa yana ji a jikinsa tabbas tana da alaƙa da su mummyn jelly, damuwarsa ɗaya kada ya kasance wadda ta haramta ne a gare shi ne, yasan mumyn jelly bata da ƙanwa, to yaya abin yake kenan?. Da wannan tunane tunane barci ya kwashe shi, sai wani sauƙe ajiyar zuciya yake yi cikin barci, ita kuwa, Baiwar Allah, cikin kwanciyar hankali take zuba barcinta, numfashinta na fita a hankali. GIDAN ABBO. Tun da suka isa gida, Aafia ta kasa sakin jiki da su, sai wani ƴan kame kame take yi, ba yadda Ummi bata yi ba, amma ina, A'AFIA taki yarda ta saki jikinta, da suka ga haka, sai suka kyaleta, ɗakin Jelly Ummi ta kaita kafin ta dawo ta fara sallamar ƴan biki, shi kuma Nawid ɗakinsa ya wuce abinsa, ya je ya yi wanka ya kwanta yana tunani irin auren da aka yi mashi, gabaɗaya ya mance da zancen Abbo, ita ma Ummi bata kara tambayar ina Abbo ɗin ba, bata kara neman numbersa ba, abin kamar ba lafiya ba, duk sun mance Abbo kam. Gabaɗaya jama'ar da suka zo bikin Ummi ta sallamesu akan anriga da an ɗaura aure an wuce wajen, taki nunawa bakin waje Aafia, ƴan uwanta kawai ta nunawa ita tare da yi masu bayanin abin da ya faru na canjin Amaryar da aka yi, ba karamin daɗi suka ji ba, sun kuma yi alkawarin zasu yi gangami suje su gaishe da Abbi, sannan su yi mashi godiya, sosai Ummi ta ji daɗi, amma kuma har yanzu tana tunanin Jelly, kewarta na nan a cike a cikin ranta, Allah ya jarabceta da son jelly ba kaɗan ba. Har karfe 10 na dare Abbo bai dawo ba, babu shi babu labarinsa, haka zalika su kuma, ba wanda ya sake zancen shi, da alama ya rufe masu baki ne, ya kuma mantar da Nawid abin da ya faru a daren shekaran jiya. Ummi da kanta ta shirya Aafia tsaf, ta yi mata kwalliya tare da bata kayan da ta sayawa jelly wadda zata sanya a ranar shiganta ɗakin miji, da yake Aafia ɗin bata da wani ƙiba, sai kayan suka zauna mata a jikinta sosai, danƙareriyar lace ce, milk color, kwalliyar jikin lace ɗin nan an yi sune da manya manyan zanen fulawa blue color, sannan an zuba mashi wasu shegun Stones masu bala'in kyalli, kuma stones ɗin sun daku da jikin lace ɗin sosai, lace ne mai shegen tsada, sai wani walwali yake, manya manyan abubuwan hannu na gold ta sanya mata a hannu wadda sun kasance nata ne da ta jima da saya ta ajiyewa matar ɗan nata kwaya ɗaya tilo a duniya zai aura, bakaramin kyau Aafia ta yi ba, sai dai idanunta da suka yi ja, alamar ta ci kuka ta ƙoshi, wani dankareren sarkar gold Ummin ta sake ɗaukowa ta sanya mata a wuya, sannan ta bata duk wasu kayan gyara da HJY BATULA ta haɗawa jelly bata gama shanyewa ba, ba musu ta ƙarɓa ta sha, komai Ummi ta ce mata, bata cewa A'a, sun zama kamar raƙumi da akala, a takaice dai, da kayan da aka sayawa Amarya jelly, da shi aka yi wa Aafia amfani, humra masu shagen daɗin kamshi Ummi ta sanya mata. Amarya fa masha Allah, ta yi kyau tamkar ka sace ta ka gudu da ita, sai tashin kamshi take yi, mayafi Ummi ta rufa mata sannan ta riƙo hannunta suka nufi bedroom ɗin Nawid. Da sallama suka shiga cikin ɗakin, sai hawaye Aafia take yi kasa kasa a cikin mayafin, domin kuwa yanzu a duniya babu abin da take tsoro biyun namiji, tamkar yadda take tsoron mutuwa, haka take tsoron haɗa ido da angon nan nata, jikinta sai kerma yake yi, Allah sarki baiwar Allah, ta ɗanɗani bakar azaba a hannun ƴan kidnaping, abin ya zauna a zuciyarta, hakan ya haifar mata da razana a cikin ƙwaƙwalwarta, wannan yasa kuma take mutuwar tsohon maza, ciki kuma har da angon nata, wato Dr Nawid, mutumin da take mutuwar so, yau ya zama mallakinta amma tana ji tamkar kabari aka kawota shiga ɗakin nan nasa da suka yi. Lokacin da suka shigo yana zaune a gaban laptop nasa yana aiki, ya yi wanka yana sanye cikin kayan barci masu kyau brown colar, idanunsa na sanye da medicated glass, hannunsa na riƙe da pen ga kuma tarin takardu a gabansa, laptop ɗin nasa kuma tana ɗaure saman table dake tsakiyar bedroom ɗin nasa, shi kuma yana zaune saman wata sofa irin wadda ake sanya guda biyu a cikin bedroom ɗin nan. Jin sallamar Ummi yasa ya ɗago kansa yana amsawa, cike da kulawa ya yi Maganar. Karisowa cikin ɗakin suka yi, a gefensa Ummi ta zaunar da Aafia, ɗan gyara zama ya yi ta yadda Aafia ɗin zata zauna da kyau, sannan ita kuma Ummi ta koma ɗayar sofar ta zauna. Wani irin razana A'AFIA ta yi lokacin da Ummi ta zaunar da ita kusa da shi, jikinta har wani kerma ya fara yi, kasa ta yi da kanta tana cigaba da hawayenta, abin gwanin ban tausayi, daga Nawid har Ummi ba wanda ya lura da tana hawaye, saboda mayafin ya rufe mata fuska, kuma ta sunkuyar da kanta kasa. Nasiha sosai Ummi ta yi masu kafin ta yi masu sallama ta fice daga ɗakin. Ji Aafia tayi tamkar ta tashi ta bi bayanta, amma ba halin yin hakan, saboda bata da amsan da zata basu idan suka tambayeta lafiya. Ummi na fita ya juyo da kallonsa kanta, cike da kulawa ya ce "Sannunki?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Ina wuni?" Ta faɗa cikin muryar kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Maganar da ta yi tasa ya gane tana kuka, dan haka sai ya juyo da kyau suna fuskantar juna, hannu ya sanya ta buɗe mayafin nata, cikin sanyin murya ya fara magana "Kiyi hakuri, nasan wata kila kema baki so na, wata kila akwai wanda kike so, kila ma har kunyi alkawarin aure, amma ina son kiyi hakuri mu yi wa iyayenmu biyayya, Ummina tana masifar sonki, ke kuma Abbinki yana suna da har ya bani ke, ba zan taɓa mantawa da shi ba, ki dai'na kuka, na miki alkawarin zan riƙe ki hannu bibbiyu, ba zan taɓa saki cikin kunci ba, duk duniya idan kika cire iyayena, yayanki Prof shi ne mutun na uku da nake so, to ko dan Imran zan sanya ki farinciki, yanzu dai dan Allah ki daina kuka kin ji ko? Abar batun dangantakar da yake tsakanin Ummi da Aunty Hadiza, ke kanwata ce domin da ni da Prof duk ɗaya ne, dan haka ki ɗauke ni a matsayin Prof Kinji?". Kara tsananta kukan nata ta yi sosai, domin ita kaɗan tasan ciwon da yake a cikin zuciyarta. Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, kafin ya sanya hannu ya riƙo hannayenta, yana ƙoƙarin yin magana, a razane ta kwace hannayen nata, jikinta ya kara tsananta kermar da yake yi. Bai damu ba, domin yasan waye Imran, yasan shi da addini sosai, so yana tunanin gabaɗaya kannensa haka suke, shiyasa da ta kwace hannunta sai ya yi tunanin ko dan irin faɗan da ake musu a gida tun suna yara akan kada su bari namiji ya taɓa su ne. Cire medicated glass ɗin face nasa ya yi, sannan ya ajiye pen ɗin hannunsa, cikin natsuwa ya fara yi mata nasiha tare da nuna mata cewa shi mijinta ne, ko ya taɓata ba wani matsala, dan haka kada ta damu, har lokacin kukanta kawai take yi bata kula shi ba, da alama kuma bata cikin natsuwarta. Ganin hakan yasa ya jawota jikinsa ya rungumeta yana ɗan bubbuga bayanta, jin nasihar da ya yi mata ne yasa bata tashi daga jikin nasa ba, ta kwanta ta cigaba da kukan da take yi. "A'AFIA baki so nane yasa kike yin wannan kuka haka?" Ya yi maganar can kasa kasan maƙoshinsa, tayi kuka sosai, ta kasa magana, sai dai kuma ta ɗan rage kukan nata yanzu. Hannu yasa ya ɗago haɓarta yana kallon face nata, idanunta a runtse, shiru ya ɗan yi na ƴan mintoci kafin ya ce "Dan Allah me zan yi maki ki dai'na wannan kukan ne? Ni bana son kukan nan, ke amana ce a wajena, sannan kanwata ce ke, kuma matata, idan baki so na ne, ki gaya mani, ni nasan ta yadda zanyi wa Ummi bayanin ta fahimceni, kuma nasan shima Prof nasan zai fahimceni, sannan Abbinki ma zai fahimta, auren dole bashi da wata faida, ni nasan zama da wanda baka so babban ciwo ne, ba kowace zuciya zata iya jurewa ba, to kada ki damu, idan baki sona ko kuma kina da wanda kike so, ki gaya mani kinji kanwata?". Ya kai karshen maganar yana cire mata mayafin jikinta. Girgiza mashi kai ta fara yi, amma dai ta kasa buɗe baki ta yi magana. "Bakiso na ne kike girgiza kai?". Sake girgiza mashi kai ta yi a karo na biyu. "Kina sona?" Nan kuma shiru ta yi mashi bata motsa ba. Shiru shima ya ɗan yi kafin ya zame mata mayafin nata gabaɗaya ya ajiye a gefe. "To meyasa kike kuka?". Sake girgiza mashi kai ta yi, bai takura mata lallai sai ta yi magana ba, domin kuwa yasan ba zata iya yin magana ba, saboda kukan da taci ta ƙoshi. Bayanta ya fara shafawa a hankali hankali yana jin yanayi mai daɗi a tattare da shi, ita kuma tun tana sassauta kukan nata har ta dai'na gabaɗaya, sai ajiyar zuciya na wadda ta ci kuka take sauƙewa. Sun ɗan jima a haka, har barci ya fara ɗaukar ta, "Muje ki kwanta a gado ko?" Can kasa kasa ta jiyo voice nasa. Kasa miƙewa tayi daga jikin nasa, domin kuwa duk jikinta a mace, zuba mata ido ya yi yana mai jin wani irin yanayi da ba zai iya fassara shi ba a tattare da shi. "Kanwata, a nan kike son kwanciya ne?" Ya sake magana kasa kasa kamar mai raɗa. Ɗan motsawa kaɗan ta yi ba tare da ta yi magana ba. "To shikenan ɗan ɗaga kaɗan bari na ɗauke ki mu haura saman gado ko?". Jin abin da ya ce yasa ta yunkura da iya karfinta dukkan, a sukwane ta miƙe daga jikin nasa, nan take wani irin muguwar tsoro ya kamata, abin da ya faru da ita a baya ne ya fara dawo mata, nan take ta birkice mashi, ta fara yin wani irin abu kamar bata da lafiya. A wannan karon sosai ya yi mamakinta, zuba mata idanu ya yi, tana ƙoƙarin miƙewa, cikin sauri ya riƙota yana kallon face nata. Kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro ta sa mashi, sai ƙoƙarin kwace hannunta take yi, dan ta gudu, ko ina zata je?. Miƙewa tsaye ya yi har lokacin yana kallonta, kasancewar shi na babban likita, sai kwakwalwarsa ta fara hasasho mashi matsalarta, domin kuwa wannan abin da take yi, ya yi kama da yarinyar da aka yi wa fyaɗe ta karfin tsiya, wadda hakan kuma dama yana birkita masu kwakwalwa. Cikin sauri ya kori shaiɗan tare da kawar da wannan tunani daga ƙwaƙwalwarsa, dan dai shi yana yi wa familyn Imran kallon salihan bayi, ya yi imanin da wuya a sami hakan a cikin jinin Prof, kuma ko da an samu ma, ya yi Imani ba za su ɓoye wa mijin da yarinyar zata aura ba, abin da bai sani ba, shi ne, gabaɗaya family'n ma mutun uku ne suka san da zancen, kuma da alama suma mutun ukun nan sun mance da zancen ma baki ɗaya. BABBAR MAGANA Jawota jikinsa ya yi ya rungume tare fara gaya mata kalamai wadda za su sanyaya mata rai, ya yi amfani da matsayinsa na cikakken namiji mai ilimi da hankali, kuma ya fita shekaru. Tun tana tureshi har ta hakura ta lafe a jikin nashi, mamaki yake akan me yake damunta, ya san dai a shekarun tan nan kam, tasan me ake nufi da aure, sannan kuma tana da ilimi sosai, amma tana yi mashi wasu irin abubuwa da suka ɗar sa mashi ? (Alamar tambaya) a ransa. Cikin dabara ya yi mata wayo suka koma saman gado, a tare suka kwanta tana jikinsa. Sai lallaɓata yake yi kamar wata kwai a saman tray, Bawan Allah ya rungumi kaddararsa, to amma matsalar idan ya gano ba budurwa bace ita ya kenan?. Suna kwanciya, ba jimawa ta yi barci, sai faman sauƙe ajiyar zuciya take yi a cikin barcin nata. Shi kuma, sai faman shafa bayanta yake yi, yana ɗan bubbugata kamar ƴar baby. Sun jima a haka kafin nan ya lura da uban zufar da take haɗawa saboda lace ɗin jikinta. Cikin dabara ya sanya hannu ya ɗauko remote ɗin Ac. Ya kara gudun, sannan ya mai da remote ɗin, a hankali ya fara bin kayan jikinta da kallo, lace ɗin ya yi mata nauyi ta kwana da su. Cikin dabara ya sanya hannu ya zuge zip ɗin rigar kasa, domin ya rabata da su, ko zata ɗan ji daɗin barcin, har lokacin kuma, tana kwance a jikinsa. Bayan ya zuge zip ɗin kasa, cikin dabara ya mai da ita saman gadon ya kwantar da ita, sannan ya miƙe zaune, hannunsa har kerma yake yi wajen sanya hannunsa ya cire mata rigar tata, ya ɗaura mata a saman bedside drawer, juyowa da zai yi da nufin ya cire mata zanin, karaf sai saman kirjinta idanun nasa suka sauƙa. Shiru ya zuba mata ido yana kallonta yadda take barcinta, ga kirjin nata masha Allah. Ya ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ya daure ya kawar da kansa, ya cire mata sarkar wuyarta da abin hannu cikin dabara, sannan ya kai hannunsa ya zame mata zanin jikinta tare da kashe wutar ɗakin wai dan ma kada ya ganta ta ɗaga mashi hankali, domin baya son kusantar ta a yau, ya lura tana tsorace da shi sosai, ya fi son ya barta har sai ta saki jiki da shi sosai, sannan duk abin da zai faru ya faru. Kwanciya ya yi ɗan nesa da ita tare da jawo bargo ya shiga domin shi sanyi yake ji, ba komai bane kuma ya ja mashi jin sanyi fa ce yanayin na sha'awa da ya tsinci kansa a ciki, juya mata baya ya yi tare da yin addu'ar barci, sannan ya juyo ya tofa mata, kafin ya yi wa kansa, daga nan ya ce asuba ta gari. Yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi. GIDAN LION💋 Tana tsaka da barcinta, can cikin ƙwaƙwalwarta ta fara jiyo karar wayarta, a hankali hankali ta fara jiyo ringin ɗin, ɗan motsawa ta yi tare da gyara kwanciyarta, ta kara jawo lallausan pillow ta rungume a kirjinta, tana mai cigaba da barcinta. Sake kiran wayar aka yi a karo na biyu, a wannan karon har tsakiyar kanta ta jiyo ringing ɗin wayar. Slowly ta faro dara daran fararen sleeping eyes nata waje, wadda suka ɗan sauya launi saboda barci. Cikin sauri ta miƙe zaune ganin yadda rana ta take, wani irin sara mata kanta ya yi, cikin sauri ta dafe kan nata tana karato Alhamdulilahil lazi ahyana bada ma'amatani wa ilaihin nushur.... Ta kai karshen addua'o'in nata tare da sauke idanunta akan wayarta dake saman bedside drawer yake ta faman ringing yana neman agaji. Jikinta duk a mace, hannu ta kai ta ɗauko wayar, My lovely Anaya shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, ɗan washe idanunta ta yi tare da ɗan motsa ɗan bakin nan nata kamar zata yi magana, hakan kuma yasa dimple nata gabaɗaya suka lotsa sosai. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ɗauki kiran, ta kara wayar a kunnenta. Daga ɗayar ɓangaren Anaya ta sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya kafin ta ce "Hello Beautyn Uncle Faisal". Guntun tsaki ta ja kafin ta ce "Anaya bana son magana dake fa". Dariya ta yi tana faɗin "To nima bana son maganar ai, Yanzu na dawo daga school, kuma yau wlh uncle Shitu ne ya zo ya ɗauke mu, na so kiga uncle Shitun nan, saboda na gaya maki yana sonmu sosai, Musamman ni, ya ce ina mashi kama da wata ƴarsa da ta rasu". Wani irin bugawa Rimsha ta ji zuciyarta ya yi jin Anaya ta ambaci sunan Uncle Shitu, sai dai yarinta ya hana ta tayi tunani a kan ko dai nasu Uncle Shitun ne, domin ita ma tana tunanin Uncle Shitun nasu ya mutu, hakan yasa bata taɓa kawowa shi ɗin bane, mafiya yawan lokuta Anaya tana yawan yi mata maganar uncle Shitun wadda ya kasance shi ne yake kaisu school wata rana, haka kuma yana zuwa ɗaukarsu wata rana, shi ne yake kula da gidan Hassan, wato daddy Anaya, da yake idan baku mance ba, Hassan baya zama, sai weekend yake dawowa, to hakan yasa ya wakilta uncle Shitu dan kula mashi da gida, abin da yasa ya yi hakan kuma, saboda shi yasan waye uncle Shitu, yasan tarayarsu da Hosaini sa, shiyasa kawai bai damu ba, ya bar mashi ragamar kula mashi da gidansa, ya san uncle Shitu mutun ne mai gaskiya, kuma ita Rimsha bata taɓa cin karo da shi ba, domin kullun ana riga zuwa ɗaukarta, tana tafiya ta bar Anaya a school, haka lokacin zuwa, tana riga Anaya zuwa school ɗin, to da yake ita bata cika son hayaniya ba, da ta zo school zata wuce class nasu ta zauna, hakan yasa ko an kawo Anaya bata ganin waye ya kawota, kuma ba kowa ce Uncle Shitu yake cewa Anaya tana mashi kama da ƴarsa ba face Jehan, dama idan baku manta ba, na gaya maku ba in da Anaya ta bar Jehan a kamanni, ita Anaya bata san tarihinsu Jehan ba, amma daddynta ya sani, kuma ba wanda ya sanar da su, to shima dai uncle Shitu yana tunanin su Jehan sun mutu ne, hakan yasa yake cewa sun rasu. ALLAH SARKI, WANNAN ZALUNCI DAME TA YI KAMA? SUNA RAYE AMMA KOWA YANA TUNANIN ƊAN UWAN NASA YA MUTU, SABODA SUN SAN ABIN DA YA YI NIYAR HALLAKASU BA ABUNE DA ZA SU IYA ZULLE MASHI BA, SHI MA DADDYN RIMSHA YANA TUNANIN SUN MUTU NE YASA YA BAR KASAR BAKI ƊAYA, HAKA SU MUMMY SUNA TUNANIN YA MUTU, JEHAN NA TUNANIN RIMSHA TA MUTU, SU MUMMY SUNA TUNANIN RIMSHA TA MUTU, SANNAN YANZU SUNA TUNANIN ITA MA JENAN TA MUTU, RIMSHA NA TUNANIN SUMA SUN MUTU, WANNAN AZZALUMI DA YA RABASU ALLAH YA SAKA MASU, SABODA ABIN DUNIYA, KAI INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN, YA ALLAH KASA MUFI KARFIN JUƘATANMU. WANNAN KENAN, MU KOMA KAN LABARI. "Allah sarki Anaya ki gaida mani da uncle Shitu ɗin kin ji, In Sha Allah zamu haɗu" "E mana Rimsha, ai dole ma, yanzu dai me ya sa baki zuwa school ne?". Shiru ta ɗan yi domin bata san me zata ce da Anaya ba,. Jin ta yi shiru ne yasa ta ce "Rimsha, lafiya kuwa?". Ƴar firgita ta yi "Lafiya lou Anaya, In Sha Allah zan zo school gobe kin ji ko?". Jinjina kai ta yi sai dariya take, har ga Allah tana masifar kaunar Rimsha sosai da sosai. HMMM AI JINI BA WASA BA. Haka suka ta hirar school Anaya tana bata labarin yau Uncle Faisal ya yi ta nemanta, kamar zai yi kuka da bata zo ba, kuma ya ce ta bashi number Rismha ɗin, kuma ta bashi, ya ce zai kira. Tuna abin da ya faru tsakanin Areef da A'A SALAHUDDEEN yasa Rimsha ta dafe kirji tare da zaro idanu "Anaya me yasa zaki bashi numberta?". Har lokacin sai murmushi Anaya take yi "Haka kawai mana Rimsha, uncle namu nefa, so kike yi na hana shi number ne?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Tom Shikenan, bari na je na yi wanka na yi sallar azahar, domin wlh tun safe nake barci sai kiran wayarki ne ya tasheni, ko sallah ban yi ba, zamu yi waya anjima kin ji ko?" To ta amsa mata da shi, sannan suka yi sallama. A hankali ta zuro kafafunta kasa ta miƙe ta nufi toilet bayan ta ɗaura wayar saman bedside drawer. Yau duk wani aikinta Imran ne ya yi, kuma Allah yasa Lion yana tare da AREEF bai ma san waye ya yi aikin ba, kuma bai kai ga cin abincin rana ba, harta gyaran ɗakin su Mark Imran ne ya yi, daɗin abin ɗaya shi ne Lion bai sanya camera a gidan ba bare ya kalli cewa Imran ne ya yi aikin, shi kuma Imran baya son wani abin da zai tasheta daga barci ne, shiyasa ya yi aikin, time da ya shigo ɗakinta yaganta ta sami barci, sai ya wuce kawai ya fara yin aikin nata. Wanka ta yi a gurguje ta fito ɗaure da towel, bata tsaya shafa mai ba sai da ta gabatar da sallar azahar, saboda lokaci ya tafi, karfe biyu ta kusa. Sai bayan ta yi sallah ne ta zauna zaman kwalliya, sosai ta zubawa hannunta idanu, tana jin bakin ciki sosai ta kalli hannunta babu kunshi, abin yana ɓata mata rai ba kaɗan ba, amma ya zata yi, dole ta hakura da kunshin matukar tana son zaman lafiya. Tsantsara simple make ɗin ta tayi, tare da feshe jikinta da perfume, sannan ta gyara dark black curly hair ta. Bayan ta gama komai ne ta miƙe ta nufi trolleynta. Wando da riga ta ɗauko, wandon jeans ne pink color, sai riga fara tas mai karamar hannu, kayan sun zauna da kyau a jikinta, tula tulanta masha Allah, sai kara haɓaka suke yi, suna ciko riga, sai dai fa kunsan halinta, akwaita da tattalinsu da ɓoyesu, bata son barinsu ko iska su sha, idan zata sanya riga sai ta sanya vest mai kauri a ciki, kamar wani ya ce zai kalla mata, idan ta rufesu da vest, sai ta sanya riga, ta kware a tattalinsu. Sosai ta fito ta yi kyau over, duk wani namiji mai lafiya idan ya kalleta sai ya sake waigawa ya kalleta, saboda tsantsan kyau da kuma dirin halitta da Allah ya yi mata, shekarunta 14 a duniya, amma kuma idan kaga albarkatun halittarta, sai ka ji zaton 16 years ke gareta, ga bala'in shape na coca cola kamar me. Ɗan karakin hijabi fari ta sanya a kanta, a iya kirji Hijabin nata ya tsaya mata, kara feshe jikinta da perfume nata ta yi, sannan ta ɗauki wayarta ta nufi garden na gidan. Ta sallama ta shiga garden ɗin duk da ta san mawuyacin abu ne ta sami wani a waje, domin bata taɓa cin karo da wani a wajen ba, sai dai kuma kamshin perfume ɗin Lion ne kewaye da wajen, da alama in ma tsakiyar dare, ko kuma safiya lokacin da take zuwa school, yana zama a wajen, abin da bata sani ba shi ne, Lion dai ya fi yawan zama a wajen ma fiye da zaman da yake yi a bedroom nasa, ya fi jin daɗin zama a wajen, wani lokaci ma a wajen yake wuni, kawai dai ba su taɓa cin karo bane, da daddare kuma, sai ya kai karfe 2 na dare zaune a wajen, har Mark ya kulle kofar shi yana waje, idan ya tashi shiga cikin gida, kofar baya yake bi, wata rana kuma, ta gaban yake bi ya sanya Mark tashi daga barci, kuma shi ne ya yi wa Mark ɗin uwarni da ya rinƙa rufe ƙofar, saboda idan baku mance ba, baya Kaunar datti ko miskala zarratin, to kwana biyun nan ana iska, kura na shiga cikin gidan, da alama damuna ta ɗan fara ja baya, shiyasa yake sanya Mark rufe kofofin kawai, to kofar kuma idan aka rufeta, ta rufu kenan, sai an sake sanya fingerprint take buɗe wa, shi kuma saboda isa ba zai sanya yatsarsa ba, sai dai ya tashi Mark ya zo ya sake buɗe mashi. (Kai Lion Bala'i ne, wai ba zai sanya yatsa ya buɗe kofar ba saboda isa, sai dai ya tashi Mark daga barci, wannan mulki da nuna isa da izzar Bala'i da yawa take🤔) Haka zai tashi Mark komai dare, ya zo ya sanya hannu ya buɗe mashi kofar, to ita ma fa kofar bayan a rufe take, ko ya zagaya, sai dai ita ta bayar kana ita sarrafata ko ba sanya fingerprint ɗinka ba, saboda ita ta kasance kamar kofar sirri ce, dama kuma kunsan da yawan manyan gidajen nan, akan yi masu karamin kofar sirri ta baya, wadda bata kara, bata fitar da wani sauti da ɗan adam zai ji, to ana yin tane saboda sirri, Allah ya kiyaye idan wata matsala ta faru a gida, to masu gida sukan iya fita ta cikinta, duk wata baban gida da wuya baka sami kofar sirri a cikinta ba. Saman ɗaya daga cikin tantsama tantsamar, luntsuma luntsuwar kujerun dake a cikin garden ɗin ta zauna, wani iska mai shegen daɗi ne yake kaɗa wa, har wani lumshe idanu take ya, ga kamshin perfume ɗin masoyinta tana shaƙa. Wayarta ta kunna tana ƙoƙarin fara kiran number daddynta da Areef ya sanya mata a cikin waya. Da sallama Imran ya shigo garden ɗin, yana sanye da jallabiya fara tas a jikinsa. Ganinsa ya sanya ta saki cool murmushi, wadda ya sanya fararen hakwaranta bayyana "Ina wuni yaya Imran". Shi ma murmushi ya sakar mata, sannan ya wuce ya zauna gefenta yana kallon yadda ta yi masifar kyau, tunani yake yi akan wlh duk ranar da suka yi ido huɗu da Saif, to fa dole sai ya so ta, ko da ba zai nuna ba, saboda ta ma wuci namiji ya tsaya wani dogon tunani a kanta, duk wani namiji mai lafiya ya ganta fa dole ya sota, shima Imran dai ya cire abin a ransa ne, ya kwallafawa ransa Jelly Shiyasa, haka zalika shi ma Areef, dannewa kawai yake yi, amma har ga Allah yana bala'in jin sonta a ransa, sai dai ya san Saif take so tun tana yarinya, shiyasa yake ƙoƙarin tayata ta cika burinta, Allah sarki Areef bawan Allah, yanzu babbar damuwar shi ne a samu su yi ido huɗu da Saif ɗin, matsalar Saif ɗaya, zai iya zama da mutu tsawon lokaci ba tare da ya san kamannin mutumin ba, ba komai yake ɗaga ido ya kalla ba, yafi yin aiki da kawa zuciya sama da abin da zai kallah da idonsa, Anya Saif bai taɓa yin aiki a hukumar C.I.A ba kuwa? Hukumar C.I.A sune suka fi yawan aiki da kawa zuci fiya da abin da za su kalla da ido, suna aiki ne da tunanin kwakwalwa, shiyasa mafiya yawan lokuta idan za su yi aiki, zaka tarar suna rufe idanunsu dan su nutsa cikin tunanin kwakwalwarsu tare da tattaro kawa zucinsu, ba komai suke amfani da abin da suka kalla ba, haka shi ma Saif, duk abin da ya ɗaga ido ya kalla, to fa wanna abin ya kai makura a kan ya kamata a kalle shi ɗin ne, idan baku manta ba, da kallo ɗaya Areef ya yi mata ya gane ta jima tana son Saif, to haka C.I.A suke, da wuya kuma idan Lion bashi da wani relationship da su, idan kuma basu da shi, to tabbas ya horar da kansa a fagen yawan aiki da kawa zuci. Zuba mata idanu Imran ya yi, sai faman turo ɗan bakin nan nata take yi kamar biro. "Rimsha lafiya kike ta faman fushi haka?" Ya tambaya yana mai kawar da kallonsa daga kanta, dan saboda kada ta fahimci wani abu, kamar yasan zata juyo da nata kallon izuwa kansa. "Yaya Imran, tun ɗazun nake ta gwada number daddy bata shiga, ina son ne in gaisa da shi". Ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya fara magana "Network ne babu kyau, amma ki mashi magana a WhatsApp, idan ya sami numberki, shi zai rinƙa kiranki, domin idan ba shi ya kira ki ba, ba zaki rinƙa iya samunsa a waya ba, Network namu bashi da karfi sosai". Shiru ta yi bata sake magana ba, duniyar tunanin abin da Lion ya yi mata ta faɗa, ya rabata da mahaifinta, tana kewar daddynta, nan take taji hawaye ya fara bin ƙuncinta. Shessheƙar kukanta ya sanya Imran juyo da kallonsa a kanta. "Subhanallah Rimsha lafiya kuwa? Meya faru kike hawaye haka?". Faɗowa ta yi jikinsa ta kwantar da kanta a saman kafaɗarsa, kasa kasa take magana cikin muryar kuka. "Yaya Imran me yasa Yaya Saif zai rabani da daddyna? Me nayi mashi? Shi baya da tausayi ne? Shi bashi da daddy ne? Meyasa zai yi mani haka? Ni ai gara ma ya kasheni da ya rabani da iyayena da ƴan uwana? Me daddyna ya yi mashi da ya cancanci wannan hukunci a gare shi?". Tana kai karshen maganar kuka mai karfi ya zo mata, yau ga daddynta a raye, ita ma a raye, amma karfi da yaji an rabasu. Shafa kanta ya yi cikin sigar rarrashi ya fara magana "Rimsha bappa Hosain ya yi kuskure, ba laifin Saif bane, laifin bappa Hosain ne, tayaya zai yi irin wannan furuci a gare su? Bari na fahimtar da ke wani abu, ki sani tsawon Wannan lokaci da baku tare da bappa yana tare ne da su ne fa, yana gidansu na Washington DC, ya zauna da su, wlh tun kafin su zo nan idan muka yi magana da Areef, ba zai yi magana biyu bai kira mani sunan Musharraf ba, yana matukar son daddynki, haka zalika shima Aseef, wannan son da suke yi wa daddynki yasa Saif ya fara kaunarsa, ki sani wlh ko tsuntsuwa bata isa ta sauƙa a gidansu Saif ba, basu son baki ko kaɗan, amma Allah shi kaɗai yasan dalilin da ya sanya ya sa masu kaunar daddynki a ransu da har suka sanya shima Saif ya fara son shi, sun kula da bappa sosai, sun kyautata mashi, yasan halinsu mai kyau da mara kyau, meyasa zai zo ya yi irin wannan furuci akan su na cewa yasan turawa basu da hankali, basu da hankali suka kula da shi haka? Ai ko dan saboda Aseef da Areef tun da bai san Saif ma yana kaunarsa ba, ko dan Areef bai kamata ya yi wannan magana ba, kuma na ƙara gaya maki Saif yana kaunar bappa saboda yadda ya rinƙa sanya Aseef farincikin, mawuyacin abune ki iya gane idan Saif yana son wani abu, amma su Areef sun gane yana kaunar Bappa, to kinga bappa ya yi kuskure, yes ke ƴarsa ce, yana da kyau ya nuna irin haka a kanki, amma baga mutane irinsu Areef ba, yakamata ya tausasa kalaman shi ne a kan su, ni da ban zauna da su a cikin gidansu na Usa ba ma, nasan cewa wallahil azim su ba manema mata bane, ke su dukka da kike ganinsun nan basu da lokacin mace, harta Areef da kike gani mai sauƙin kannan, yanzu da zaki kawo mashi maganar aure in a serious matter, dariya zai yi ya mai daki baki san me kike yi ba, babu zancen aure ko neman mata a ransu, saboda suna ganin ɓata lokaci ne, kawai ni na yarda wani iko ne na Ubangiji da yasa suke kaunarki, daga Areef har Aseef, Allah ne kawai ya sanya masu kaunarki, to su ba mazinata bane ,basu neman mata, amma bappa ya zo ya masu magana a gatse haka, wai turawa mazinata ne, basu ɗauki zina a bakin komai ba, kinga kuwa dole Saif ya ɓata rai, wlh ina mai tabbatar maki Saif ya yi maku hukunci mai sauƙin daga ke har bappa, kuma ya yi hakan ne saboda ni, dan ni ya sassauta maku hukuncin, to dan haka ki godewa Allah ma da hakan, sannan magana ta karshe ina son ki sani Saif ba mugu kamar yadda kike tunani bane, kawai haka yanayinsa yake, kuma bappa ya ɓata mashi rai ne, dama sai anyi laifi yake yin hukunci, baya hukunta wanda bai yi laifi ba, ina da tabbacin idan ya sauƙo zuciyarsa ta yi sanyi, shi da kansa ba zai so kina mace ƴar musulma kuma kina shiga ɗakin su Mark ba, ba zai so hakan ba, kuma zaki gani, zai dakatar da ke daga yin hakan, ni nasan waye shi fiye da yadda kike zato, amma dai kafin ya sauƙo ya waiwayeki ɗin shi ne aiki, zaki sha wuya kam, da ya sauƙo kuma shikenan zai dakatar dake daga yi wa su Mark aikin, sai dai fa rabaki da bappa kam ya riga da ya yi, an wuce wajen, shi ma aikin abin da yasa na sanya a raina zai dakatar dake, saboda shi musulmi ne, yasan haramcin hakan a addini, ke dai ki yi addu'a kawai, amma ki daina ganin laifin Saif". Ya kai karshen maganar tare da shafa kanta ya gangaro da hannunsa izuwa saman face nata ya goge mata hawaye. Suna cikin haka Areef ya lallaɓo ya iso wajen ya same su, jikin nasa Alhamdulilah, ya sami kulawa daga wajen ɗan uwan nasa sosai, cikin ƙanƙanin lokaci ya sami sauƙin ciwon nasa. A ɗayar kujerar dake fuskantarsu ya zauna yana tambayar Imran me ya yi wa Sarauniyar Triplets ɗin su, ya yi maganar yana zarewa Imran ɗin idanu. Imran bai san time da dariya ta subce mashi ba, ji yadda Areef ya zare mashi waƴan nan dara daran idanun nasa, ai sai ya sa mutun ya gudu, ita ma dai Rimsha ya bata dariya kuma ya bata tsoro, domin kuwa, idan baku mance ba, akwaisu da dara daran idanu kamar ball, zarosu da ya yi kuwa, ai kunga za su kara girma. Ganin ta yi dariya ne yasa shi ma ya saki cool murmushi. "Our Queen dariya yana yi maki kyau sosai over". Ya faɗa cikin sanyin murya. Kasa ta kara yi da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Kai ash eyes nasa ya yi saman hannun nata, wani irin tausayinta ya ji lokacin da ya kalli hannun nata, har lokacin sunanan wasu iri da su, sun ɗanyi wani baki bakin ciwo, alamar wajen yana son warkewa. Sorry ya yi mata tare da gaya mata kalamai da za su sanyaya mata zuciyarta, ya kuma yi mata alkawarin ba zai sake bari ayi mata makamancin haka ba, komai wuya komai daɗi zai yi kokari wajen ganin ya cika alkawarin da ya ɗaukarwa Uncle Hosain ɗinsa na kula da ita. Amma fa da ni da ku munsan sone ya jawo hakan, ita da Imran ne ba su sani ba, ba wani alkawari, kawai sonta yake yi yana dannewa saboda Saif take so, kuma a zahirin gaskiya shi ya fi su Saif sanin menene so, domin kuwa shi ya fi su yawan shige shige, Saif bai san menene so ba, dan kunsan baya shaga irin wannan layin, shima dai Aseef yanzu ba za'a yanke mashi hukunci ba, domin yanzu a sabon mutun yake, yanzu yake tantance daidai da ba daidai ba, Imran da yake wani gaya wa Rimsha su basu son mata, to ga dai Areef ya kamu da soyayya, sanin basu son mata or aure, sanin baya ya yi masu, sai dai auren ne har yanzu bamu sani ba, shin suna da niyar yi ko yaya, ko kuma muce Areef yana da niyar yi, domin shi kaɗai ne ya san me soyayya ma a cikinsu. Kalamansa yasa dukkansu daga ita har Imran ɗin sun ji daɗi, sosai Imran ya yi mashi godiya, girgiza kai ya yi alamar baya son godiya, daga haka suka shiga hira, ta saki jiki sosai, ta mance komai ta biye masu sai hira suke yi, sun ɗauketa kamar wata babbar mace saboda hankalinta da natsuwarta, shiyasa basu damuwa suke sanyara a tsakiyarsu suna hira, ba zata rainasu ba, haka zalika tana da kamala sosai. Suna tsaka da hira Aseef ya kira Areef a waya, wani daɗi na daban Areef ya ji ganin kiran Aseef ɗin, domin kuwa yana zargin Aseef ɗin, yana ji a jikinsa akwai wani abin da yake damun ɗan uwan nasa, ya yi mashi tambayar duniyar nan yaki gaya mashi, sai dai ya ce mashi Exam ne yasa ya shiga damuwa, baya son ya faɗa ne, kuma duk wata hanya da Aseef zai bi dan ya ɓoye damuwarsa ne ko menene Allahu aalam, to fa sai da ya bi wannan hanya, idan ba su da suka yi mashi muguwar farin sani ba, ba zaka taɓa cewa akwai abin da yake damun shi ba dan ya ɓoye. Ɗaukar kiran Areef ya yi yana mai sakarwa ɗan uwan nasa cool murmushi, zaune yake saman irin waƴan nan manyan baloon na gym ɗin nan, ba bu riga a jikinsa, sai dai wata shegiyar ƴar short da bata gama sauƙa zuwa cinyarsa ba, ga shi wandon ta matse shi sosai, ta roba ce, irin dai wannan ɗan short da mafiya yawan masu motsa jiki suke sanyawa, to shi, waƴan nan santala santalan cinyoyin nasa a waje, ga gashin kansa sai kara tsawo yake yi, sai kara komawa sak kamanin su daddy yake yi abinsa, ya kara wani sihirtaccen kyau da sheƙi irin na addinin musulunci. Satar kallon Rimsha Areef ya yi domin kuwa yau da ta ga Aseef a irin wannan shiga, da ta yi suma sau bakwai, ranar ma ba riga kawai ta gan shi, amma sai da ta razana, ina ga kuma yau mai kankanta da har zanen komai nasa ana gani, ai sai suma idan suka yi ido biyu. Dawo da kallonsa ya yi a kan wayar. "Aseef kana buƙatar aure fa". kasa kasa cikin zolaya ya yi maganar. Kin haɗa ido da shi Aseef ya yi, kuma Areef ya lura da rashin son haɗa ido da su da Aseef ɗin yake yi, dan baya son suna mashi kallon kurillah. "My Areef ina kewar kane fa yasa na kira ka". Sake maimaita maganar ɗazun Areef ya yi "Aseef kana buƙatar aure fa". Sai lokacin ya ɗago kai suka kalli juna "To ai sai ku yi mani auren ko?". Jinjina kai Areef ya yi yana faɗin "Ai ko baka faɗa ba, zan sama maka mata a Nigeria in taho maka da ita". Ɗaure fuska sosai ya yi yana faɗin "Ni bana son matan Nigeria, ni ka bar wannan shirmen ya jikinka?". "Am good now, hope kaima everything yana tafiya yadda kake so?". Girgiza kai ya yi alamar a'a ba komai yake tafiya yadda yake so ba. "To me matsalar?". Shiru ya yi, tamkar shi da kansa bai san me matsalarsa ba, abin mamaki take bawa Areef, wai yau Aseef ne da jin kunyarsu, sai wani kau da fuska yake yi, anya lafiyarsa kuwa? Abin al'ajabi kunya a cikin jinin William jacop, suda kwata kwata ma basu san menene ita ɗin ba, kunya Hausa fulani suka santa, ba turawa ba, abin ya ɗaurewa Areef kai, da yake basu san kunya ba, shi ne suke ganin kamar wani abin Aseef yake ɓoye masu, a zahirin gaskiya kuma kunyarsu yake ji yasa yake kasa haɗa ido da su, shi kansa ya rasa me yake damunsa da yasa baya iya haɗa ido da su ɗin. TO FA BABBAR MAGANA, ME YASA ASEEF KE JIN KUNYA KENAN?. "Aseef ashe akwai wani abin da zaka iya hidden mana ka da musani? Ashe akwai abin da bai kamata mu sani ba a dangane da kai?". Cikin sauri ya ɗago kai jin yadda Areef ya yi maganar, hakan ta nuna In a serious matter Areef yake. "No Areef i can't hidden anything for you, trust me ba wani abin da yake damu na, just kawai dai..... " Sai kuma ya yi shiru. "Anywhere just kawai ka riƙe maganarka no need ma ka gaya Mani, yanzu dai ya school?". "Kai Areef sarkin fushi, to ni nace ba zan gaya maka bane?" Ya yi maganar a shagwaɓe. Da mamaki Areef yake kallonsa, wato idan ya tashi tsiyarsa har yanzu bai manta yadda ake shagwaɓa ba kenan. "Areef ba fa wani abu bane yake damuna, just kawai kullun idan na kwanta barci ne, sai na yi mafarkin wata ta yi kissed nawa, kuma ba iya kiss kawai ba, just like husband and wife dai". Wani irin ɗan iskan dariya Areef ya kwashe da shi, wato just like husband and wife, eyye su Aseef husband, bawan Allah shi ne abin dake damunsa, kuma ya kasa gaya masu, Allah Mai iko a gabaɗaya family'n William jacop shi ne kaɗai ya samu albarkar kunya, ya rasa ta ya zai yi ya rabu da wannan ɗan iskar mafarkin. Areef kuwa tsabar mugunta dariya har da riƙe ciki, zuba mashi ido Aseef ya yi yana kallonsa, suma su Rimsha, da mamaki suke bin shi da kallo, dan a gaskiya ba su ji me Aseef ya ce ba, da yake kasa kasa ya yi maganar, kuma na gaya maku kunya yake ji, hakan tasa ma ya yi maganar kasa kasa dan kar wani ya ji. Saboda tsabar iskanci irin na Areef sai ya ce "No Aseef explain it dallah dallah for me, like how husband and wife?". Yana magana yana guntse dariya. Ɗan turo baki ya yi "Kai my blood, Like husband and wife mana, i knew you knew yadda husband and wife suke yi, tun da ka wuceni a karatu, ni fa yanzu nake karanta" "No ni dai I didn't know anything, kawai just explain it for me". Shiru ya ɗan yi kafin ya sunkuyar da kansa kasa, wani irin kunya ce take kara rufe shi, bawan Allah ya ciri tuta, ko ba komai ya zama zakara a cikinsu, tun da har ya yi nasarar samu al'kunya. "She is sleeping on my chest, and she is socking my penis sometimes, and also she is kissing my lips, yesternight she wanted to sock my nipples, amma Allah yasa na hanata, ni bana son this kind of dreams, suna bani haushi, please my blood help me". (Jama'a an sanu wata tana son lalata mana Aseef ɗin mu a cikin mafarki🤔 kunji shegiya,🤣🤣 to ya kamata mu tashi tsaye🤣) Shi kam Areef kamar zai mutu saboda dariya, duk waƴan nan abubuwa sai yanzu Aseef yake saninsu, bai ma san menene aure ba sai da Musharraf ya fara koya mashi irinsu FIQHU da sauran littatafan addini, shi ne ya san ma'anar husband and wife, a gaskiya ciwon Aseef dai bata yi mashi adalci ba wlh, yana da 30 years a duniya amma babu abin da ya sani, sai yanzu da Allah ya ƙaddara yana da rabon jin daɗin rayuwa, shi ne ya sami lafiya har ya fara sanin abubuwa, kai amma abin sam bata yi daɗi ba, sai dai kuma ya yi nasarar samun kunya a lamuransa, duk mutumin da bashi da kunya, wlh da sauransa a addinance, addini bata tafiya sai da al'kunya, sai dai fatanmu Allah yasa su ma Areef da Saif su sami wannan kunya ko da kaɗan ce. "My Areef pls stop laughing at me mana, that's why fa naki gaya maka what's going on, shiyasa na yi hidden na abuna ni kaɗai, amma yanzu kazo kayi forcing ɗina na gaya maka, shi ne kake ta yi mani dariya ko?". Tsagaita dariyar ya yi. "Do you know what Aseef?". Girgiza kai ya yi alamar a'a. "Good, duk abin da ta yi maka a cikin DREAM ɗin just kawai kaima ka yi mata reply, kayi accepting nata, idan ka tashi barci zaka ji you are normal". Ya kai karshen maganar tare da sake kwashewa da dariya. Shiru Aseef ya yi yana kallon sanka sanka walaƙanci da Areef yake yi mashi. Ganin ya yi shiru ne yasa ya ce "Sorry my blood zan gaya maka solution, ka dage ka yi mata fyaɗe da karfi a mafarkin, idan ta ji wuya ba zata sake dawowa ba". Nan ma shiru ya yi bai sake magana ba, dan shi maganar ma kunya take bashi sosai wlh. Shi kuwa Areef sake dariyarsa ya yi, domin kuwa yau Aseef ya kawo mashi sabuwar lamari. After 2mins. "Am so sorry my Aseef" ya faɗa yana daidaita natsuwarsa. "Areef don't worry, ni ban damu ba, tun da kayi dariya, kayi farinciki to bani da wata damuwa, burina dama na ganku kuna farinciki!!". Jinjina kai Areef ya yi, har cikin ransa yana mai jin tsantsan kaunar ɗan uwan nasa, shawara ya fara bashi akan ya rinƙa kwana da alwala, sannan ya rinƙa addu'ar barci sosai, In Sha Allah zai rabu da waƴan nan mafarkai mafarkan na banza, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, daga nan Areef ɗin ya kara tambayarsa akan idan ya tashi barci yana yin wankar tsarki ne ko baya yi, wani irin kunya ce ta sake rufe shi, cike da kulawa ya ce yana yi domin Musharraf ya koya mashi, ya gaya mashi cewa idan mutum ya zubar da spam sai ya yi wankar tsarki, kuma ya mashi bayani sosai a kan yadda ita kanta spam ɗin take da sauransu, daga nan kuma ya koya mashi wankar tsarki, to ta hakan ne ma yasan aure da sauransu. Sosai Areef ya ji daɗi, ya kuma kara jin Kaunar Musharraf sosai da sosai, domin ya bada gudun mawa ba kaɗan ba a rayuwar Aseef, wadda da ba dan shi ba, da abin zai yi masu yawa, domin komai daga farko a ka sake koyawa Aseef, amma cikin hukuncin Allah yanzu komai na tafiya daidai yadda ake so da taimakon Musharraf, kuma hakan ma yasa Lion yake Kaunar Musharraf ɗin, domin duk wani dirama da suke yi da Aseef yana ganinsu ta cikin laptop nasa, ta camerar dake gidan nasu, wadda ya haɗa da laptop ɗin nasa, yasan komai, kuma kunsan family'n William jacop suma basu manta Alkhari ko mai kankantarta. Suna tsaka da hira Lion ya yi wa Imran massage akan Rimsha ta kawo mashi abincin rana, karfe 2:30 ta yi. Wani irin faɗuwar gaba ta ji lokacin da ta ji saƙon Saif ɗin, jikinta har ya fara kerma, dama tana son ta tambayi Imran ɗin wai me Saif ya ci da safe ne, tun da ta zubar mashi da abinci, amma sai Areef ya zo ya shashantar da maganar. Jiki ba kwari ta miƙe ta nufi cikin gida, tun da ta fito garden ɗin, sai binta da wani mayen kallo, da wasu mayun idanunsa gateman yake yi, tamkar zai cinyeta ɗanye. A kitchen ta isko Mark, kamar dai kullun ya ji shigowarta, amma bai ɗago ya kalleta ba, kun dai san halinsa. Wucewa ta yi ta wanke hannayenta, bata ce mashi ko sannu ba, domin ko ta ce mashi ma, baya amsawa, shiyasa kawai ta daina yi mashi magana, sallama ma a cikin zuciya take yi abinta, Cikin natsuwa ta zo ta ɗauki tray ɗin abincin, sai a lokacin ta fara jin wani azababben yunwa na nukurkusan cikinta, sai da ta nufi kaiwa Saif abinci, sannan ta tuna ashe ko abincin safe bata ci ba, kuma ba komai ne yasa ta tuna hakan ba fa ce bala'in tsoro. Addu'a take yi sosai tana tafiya. Gabanta kara tsananta faɗuwa ya yi lokacin da ta kai bakin kofar ɗakinsa. Tsayuwa ta yi tare da daidai ta natsuwarta sosai, ta yi sallama cikin sanyin murya, kamar dai kullum, a cikin zuciya ya amsa sallama, hakan ma saboda yasan mahimmancin sallamar ce yasa yake amsawa, duk wani cikakken musulmi mumini mai bin Allah da Annabi, to fa ya zama mashi dole ne wajibi amsa sallama domin cika addininsa. Jin shiru ne yasa ta yi kamar yadda ta saba, wato ta kutsa kai cikin ɗakin. Tana isa tsakiyar ɗakin karaf idanunta suka sauƙa akansa, wani irin mahaukaciyar razana ta yi wadda ta sanyata sakin tray ɗin abincin ya faɗi kasa. A karo na biyu ta yi mashi kaca kaca da ɗaki, gabaɗaya komai ya watse, wasu kayan abincin har kan gado, ga shi babban abin haushin komai na ɗakin white color ne, harta bed sheet, kuma ta lalata komai, gabaɗaya bed sheet ɗin ya ɓaci. Ba komai bane kuma ya sanyata wannan irin Mahaukaciyar razana fa ce ganin ainahin surar jikinsa da ta yi, yana tsaye ne a gaban mirror, daga shi sai towel a kugunsa, da alama wanka ya fito, iya ta bayansa ta gani yasa ta razana haka, ina ga kuma sun yi ido huɗu ba riga a jikinsa? Ina ga ta gan shi ta gaba babu riga? Ko da yake dole ta razana, domin kuwa ya kai matakin da dole mai zuciya a kusa ya razana da ganin ainahin kyakkywar surar jikinsa, yana da wata sihirtaccen kyau ne na fitan Allah, ga shi ya yi gym sosai, damatsan hannun nan nasa ba'a magana, ga uban faɗin kirji, sannan ga bala'in kwarjini. Turus ta tsaya ta kasa sake ɗaga ido ta kalle shi, haka zalika ta kasa gaba ta kasa baya, sai dukan uku uku zuciyarta ke yi mata, ji take yi ranta na barazanar fita daga gareta, wani irin wahalallen yawu ta haɗiye, wasu zufar wahale suka fara karyo mata a gefe da gefen kunnenta, tsoron kai kallonta a kan ɓarnar da ta yi ma take ji, a wannan karonfa ko kerma jikinta ya kasa yi, yadda zai tabbatar maka tashin hankalin dake sanya kerman jikima, ashe karamin tashin hankali ne, idan tashin hankali ya yi tashin hankali to jikinma kasa motsawa take yi, bare kuma ma har ta yi kerma. Cikin natsuwa yake aikin dake gabansa, wato gyara dark black curly hair sa, tamkar bai san mutun ya shigo cikin ɗakin ba bare har ya yi mashi ɓari, tamkar babu shi a cikin ɗakin, haka ya kasance, amma kuma duk abin da take yi kunsan yana ji tun da shi ba kurma bane. Tana tsaye a wajen tana kallon kasa ta kasa motsawa, har ya kammala gyaran gashinsa ya shafa Lotion nasa, sannan ya feshe jikinsa da perfume nasa. Bayan ya gama, cikin wannan natsuwa tasa mai ɗaukar hankali ya juyo........... ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E5-6 Tana tsaye a wajen tana kallon kasa ta kasa motsawa, har ya kammala gyaran gashinsa, ya shafa Lotion nasa, sannan ya feshe jikinsa da perfume nasa. Bayan ya gama, cikin wannan natsuwa tasa mai ɗaukar hankali ya juyo, ko kallon in da take bai yi ba, dressing room nasa ya nufa, lokacin da ya juyo ita kuma tana kallon kasa, bata ɗago kai ba dan saboda tsantsar bala'in tsoro. Jin ya shiga dressing room ne yasa ta duƙa ta fara kwashe kayan abincin da sauran irin su fruits, sai kuma lokacin ne jikinta ya sami damar yin karma, ta kasa tattare kayan saboda ɓari da jikinta yake yi, sai zata ɗauki abu ta kasa, wani irin wahalallen kuka ta saka kasa kasa, ita ina zata sa ranta ne yau?. Tana a haka har ya fito sanye da wando three quarter fari tas, da kuma riga polo shirt sky blue, ba karamin kyau ya yi wa kayan ba, domin idan baku manta ba, shi fa tsabar kyansa shi yake yi wa kaya kyau, ba wai su suke yi mashi kyau ba. Da ya yi niyyar idan ya fito ya bata punishment mai matikar tsauri da wahala, domin ta shiga hankalinta da kyau, amma kuma ganin yadda jikinta ke kyarma, hannunta sai rawa yake yi, ta kasa ɗaukar kayan abinci, tana duƙe a kasa, hakan yasa ta wuce ya fita, domin idan ya yi wani yunkuri kaɗan yana da tabbacin kisan kai zai yi, saboda ya lura wannan yarinta tsoro ma ya sara mate ne, in dai fagen tsoron ne, kuma tana matukar cin albarkacin Imran da kuma farincikin da daddynta yake sanya Aseef, ba da ban hakan ba, da yanzu wani zance ake yi ba nata ba. Ganin ya fita bai ce mata komai bane ya sanya ta ji jikinta ya ɗan yi kwari, ta tattara karfinta dukka ta miƙe ta hau gyara mashi ɗaki, tana roƙon Allah da ya bata ikon rinƙa faranta mashi, ita kullun suka haɗu cikin laifi take, kullun sai ta yi mashi laifi, dan ma Allah yasa Areef ya taimakonta, ai da ya jima da ɓallahta koma ya hallakata baki ɗaya. Tas ta tattare mashi ko'ina, sannan ta miƙe ta fitar da kayan abincin, ta dawo ta goge ko'ina, sai da ta tabbatar wajen ya yi tsab, sannan ta fice daga ɗakin ta nufi wajen su Imran dan ta gaya masu abin da ta yi, ba zata iya komawa ɗakinta ba, domin tana matukar jin tausayin Saif ɗin, tasan tun da ya ce a kawo mashi abinci, to tabbas yunwa take ji ne, ga shi ta zubar da abincin, na safe ma ta zubar. Kamar yadda ta bar su Imran, haka ta dawo ta samesu, kusa da Imran ta koma ta zauna, cikin harshen turanci ta gaya masu abin da ya faru, shiru Areef ya ɗan yi kafin ya ce ta kira mashi Mark. Cikin sauri ta miƙe ta nufi cikin gida, da kallo suka bita da shi, kowa daga cikinsu da abin da take tunani a kanta. Ta zo zata shiga cikin Palo, suka yi karo da shi yana fitowa, yana tafiya yana latsa wayarsa, yau ma dai sake buge mashi waya ta yi, sai dai wayar bai kai kasa ba ta tare, cike da tsoro ta miƙe mashi wayar, saura kaɗan ta furta karlamar sorry, sai kuma ta tuna Areef ya gaya mata, babu kalmar da Saif ya tsana biyun Sorry, da ta yi gangancin furtawa kuwa, da sai dai a kwasheta sumammiya, dai sai ya ɗauketa da wani mahaukacin mari wadda zai sanyata barin duniyar mutane, amma kuma bata furta ba, cikin girmamawa dai ta miƙa mashi wayar. Ba tare da ya kalleta ba, ya karɓi wayar kawai ya wuce, domin shi ma addu'a yake taya ta da shi akan kada Allah ya sanya taji sauƙar hannunsa a jikinta, domin duk ranar da ya mareta, ko ya daketa, to da wuya ta sake moruwa. Wani irin daɗi ta ji da bai daketa ko ya ɗago ya kalleta ba, yau sau uku kenan ta yi mashi laifi, da safe ta zubar da abinci, haka na rana, sannan ga buge mashi waya yanzu, amma duk ya danne saboda baya son ya yi kisan kai, bala'in tsoron ta yake cetanta a wannan fagen. Kitchen ta koma kira Mark, ta dawo garden ɗin, nan ta same shi a wajen, kuma a in da ta tashi ya zauna, kusa da Imran kenan, turus ta tsaya, ta kasa karisawa. Zuba mata ido Imran ya yi, shi kuma Areef da ya ga hakan sai ya ce ta zo ta zauna kusa da shi, ba musu ta karisa wajen ta zauna kusa da shi ɗin tana satar kallon abun kaunar nata. Sai wani nuku nuku take yi, shi kuwa Saif daga su Imran ɗin har ita tamkar bai san da zamansu a wajen ba, kallonsa na akan wayarsa. Shiru suka kasance a wajen har Mark ya zo, umarnin Areef ya yi mashi a kan ya sake ɗaura wani abincin, domin abincin Lion ta tashi aiki, to ya amsa da shi, daidai lokacin kuma wayar Rimsha dake kusa da Imran ya fara ringing, wayar tana daidai tsakanin Saif da kuma Imran ɗin, saboda a nan ta zauna ɗazun. Jin karar wayar ba karamin haushi ta bashi ba, gashi ta fi kusa da shi, kuma waka ce ringington na wayar, ai kuwa Imran na ƙoƙarin ɗaukar wayar ya riga shi, ɗauka ya yi ya yi wurgi da ita, shi da kansa bai san a ina ya yi wurgi da ita ɗin ba, domin kuwa kallonsa a kan wayarsa ne har lokacin. An yi sa'a kusa da Areef ya wurga wayar, hannu Areef yasa ya yi maza ya capke wayar tare da miƙe mata kayanta, zata miƙe Areef ɗin ya zaunar da ita, ba dan komai ba sai dan yana son Saif ya rinƙa sauraron daddaɗar muryarta. Ɗago kai ta yi tana kallon Areef ɗin da mamakin, me yasa zai hana ta tafiya ta je ta yi wayarta, tsoro take yi kada ta fara waya a nan Saif ya daka mata Tsawa, yanzu ga shi iya ringing na wayar ma kawai ya ji, ya kama ya yi wurgi da ita, to ina ga kuma ya ji tana zuba hira, idan baku manta ba, baya son yawan magana, shima Areef da gangan ya dakatar da ita, yana son ja mata ne kawai. Dubawa da zata yi waye mai kiran nata, sai taga new number ne, sake kira aka yi domin ta baya ta katse, cikin sauri ta ɗauka dan kada Lion ya sake jin ringing na wayar tata, tana kuma tsorace saboda new number ce a ka kirata da shi. "Hello My Rimsha iyayen kauna, wato kin mance dani ko? Kin koma gidan masoyi kin manta da Ni". Cewar AKILA, domin ita ce ta kirata a wayar da sabuwar number, Allah yasa su Areef basu jin Hausa, ba su ji me Akila ta ce ba, shi kam oga dama ko ya ji ba shiga harkar zai yi ba, ita ce ƴar wahala da wahala bai isheta ba, take dakon wahala wai son shi tab hmmm, Wani irin kayatatcen murmushi ta saki har sai da dimple da kuma wushiryarta suka bayyana. "Aunty Akila na yi kewarki, nayi kewarki sosai wlh, yaushe zaki zo mu haɗu?". Ta yi maganar cikin sanyin murya da natsuwa. "Ke dai zan cewa yaushe zaki zo Rimsha, ni kam Heartbeat nawa ya hanani fita, daga school sai gida, bayan haka ya ce ko leƙa waje bai yarda nayi ba". Kara faɗaɗa murmushin kan fuskarta ta yi. "Aunty Akila to ni dai ban san yashe zan zo ba, amma....." Bata kai karshen maganar ba zazzaƙar muryarsa ya katse ta, gently ya furta "Get out!" Ya yi maganar kasa kasa cikin sanyin murya, kuma ya yi maganar ba tare da ya ɗago ya kalleta ba. Cikin sauri ta miƙe ta fice daga wajen, shi dai Areef bai ce komai ba, shi ma Imran ba bakin magana, da ma Allah yasa bai haɗa mata da mari ba ai da sauki. Tana fita bedroom nata ta koma, suka cigaba da hira da Akila, a nan AKILA take gaya mata Hjy Batula zata aiko mata da wasu kayan karin girman breast wadda ta haɗawa jelly, suna da kyau sosai, Hjy Batula ɗin ta ce zata bawa yaya Imran ko yaya Akil su kawo mata, idan sun kawo mata, zata ɗebawa yaya Imran ya kawo mata ita ma ta yi amfani da su, sosai Rimsha ta ji kunya, ta kuma amsa da to, sannan ta daɗa da cewa ta haɗa mata da su kanunfari, citta, kimba, da kuma su na'a'na'a, dan tana son ta rinƙa haɗa tea nata irin wadda mummynta take yi wa daddynsu mai shegen daɗin nan, bata son green tea ɗin su Lion, bata saba sha ba, sai ta ji babu daɗi, ga shi ita ma'abociya shan tea ɗin ne, to Akila ta amsa mata, tare da gaya mata zata bawa driversu ya sawo mata kayan a kasuwa, idan ya kawo mata, sai ta bawa yaya Akil ko yaya Imran su kawo mata, sai murna Rimsha take yi, sun sha hira kamar ba gobe, sosai Akila ta kara zugata akan ta rinƙa shan wanka da kwalliya, kada ta yarda Lion ya bar Nigeria ba tare da ta sato masu zuciyarsa ba, sai murmushi take yi jin Akila ta sosa mata in da yake yi mata kai kayi, ita kuma Akilar ta zage sai kara gaya mata lagon maza take yi, abin da bata sani ba shi ne, LION duk duniya abu ɗaya ya bari a kasani a matsayin rauninsa, wannan abu kuma ba komai bane fashe kaunar TRIPLETS nasa, kaunar ƴan uwansa kawai ya bari jama'a suka sani, bayan haka ko uban da ya haife shi, bai san me raunin ɗan nasa ba, shi Lion bai ma yarda yana da rauni ba a duniya, domin a nashi ganin komai ma zai iya yi, kuma zai iya jure komai ciki kuma har da rashin TRIPLETS ɗin nasa da jama'a suke ganin kamar shi ne rauninsa. TO FA ZAN SO GANIN MENENE RAUNIN LION GASKIYA. Idan muka koma ɓangaren gidan Abbo kuwa. Misalin karfe 5 na asuba Nawid ya farka, abin mamaki sai ya ga bata a kan gadon, a hankali ya miƙe tare da zuro kafafunsa kasan gadon, ya kunna wutar ɗakin, nan take haske ya gauraye ɗakin. Can saman dadduma ya hangota, tana zaune tana karatun Al Qur'ani mai girma, baiwar Allah Akil ya riga da ya saba masu, ɗan zamanta da Akil ta koyi abubuwa da dama dan gane da addini, ciki har da su askar, yin karatun Al Qur'ani mai girma, tashi barci kafin lokacin sallar asuba domin ta gabatar da nafila na raƙatainil fajir, sannan ta gabatar da karatun Al Qur'ani, yin sallar dare, da dai sauransu, ba ƙaramin natsuwa da cigaba ta samu ba. Miƙewa ya yi ya nufi toilet, wanka ya farayi, ya ɗauro alkawala, kusa da ita ya zo ya tsaya, ganin shi yasa ta miƙe hannunta riƙe da Al Qur'ani ta nufi saman sofarsa ta zauna. Tsayuwa ya yi ya gabatar da sallar raƙatainil fajir, sannan ya nufi masallaci, ita kuma ta dawo saman dadduma dan gabatar da sallar Asuba. After some minutes, bayan ta idar da sallah ta yi karatu har rana ya fito, ta yi askars ɗinta, ta miƙe ta nufi waje. Tana ƙokarin fita shi kuma yana ƙoƙarin shigowa, karo suka ɗan yi, da sauri ta yi baya tana sunkuyar da kanta kasa. Zuba mata idanu ya yi yana kallonta sosai. Kasa ta yi da kanta, cikin sanyin murya da girmamawa ta fara magana "Ina kwana yaya Nawid?". Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya amsa mata tare da tambayarta ya kwanan bakunta, cike da kunya ta amsa mashi da lafiya, gabaɗaya kunyarsa take ji, domin ta tashi barci ta tarar ya rabata da kayan jikinta. "Ina zaki je yanzu da sassafen nan?" Ya yi maganar yana kara tsareta da ido. "Wajen Ummi zanje". "A nan ɗin na takura maki ne?" Ya yi maganar cikin zolaya. Girgiza mashi kai ta yi tana faɗin a'a. Wucewa ya yi, ya shige cikin ɗakin. "Zo ki yi kwanciyarki sai zuwa anjima sai kije, yanzu ko da kinje ma, tana barci, bata kai ga tashi ba". Kamar zata yi kuka, haka ta juyo ba dan ta so ba. Saman sofa ta zauna tana wani rakuɓe rakuɓe. Da mamaki yake kallonta, ya rasa meyasa take gudun shi haka, tabbas ƙwaƙwalwarsa tana gaya mashi akwai dalili, domin kuwa shekaruntan nan ta wuce a ce sai an zauna ana yi mata wani karin bayani game da aure, 21 years take da shi a duniya yanzu. Tsareta ya yi da ido, yana son karantarta, domin ya gane menene matsalarta. "Tashi ki zonan". Shi ne abin da ya faɗa. Ba musu ta tashi ta koma kusa da shi ta zauna. "Meyasa kike guduna har haka ne A'AFIA?". Kasa ta yi da kanta. "Babu komai yaya Nawid" ta yi maganar cikin sanyin murya. Hannunta ya riƙo a cikin nasa. "Ni yayanki ne, kada ki mance da Ummi da Aunty Khadijah ƴan uwa ne, dan Allah ki gaya mani menene yake damunki Kin ji? Kada ki damu, kuma kada ki ɓoye mani komai". Ɗan satar kallon shi ta yi ta kasan ido. "Da gaske yaya Nawid babu komai". Gefensa ya nuna mata ba tare da ta sake magana ba, ba musu ta karisa hayewa saman gadon, ta kwanta a gefen nasa, shi ma kwanciya ya yi, ya sanya kansa a saman pillow da ta kwantar da nata kan. "Ba zan ɓoye maki ba, a lokacin da aka bani aurenki, kwata kwata babu sonki ko kaɗan a raina, amma daga daren jiya zuwa yau, Allah ya jarrabeni da sonki, ina fatan kema kin na sona?". Ya yi maganar can kasa kasa maƙoshinsa. Ɗan juyowa ta yi kaɗan "Ina son ka nima yaya Nawid". "Da gaske?" Ya faɗa cikin zolaya, gyaɗa mashi kai ta yi alamar e. "Kada fa dan kinga idona ne yasa kika faɗi hakan, fatan Allah yasa babu wani a zuciyarki". Nan ma cikin zolaya ya yi maganar. "Yaya Nawid ba wai dan ganin idonka bane, wlh da gaske ne ina sonka, kuma ni wlh ban taɓa yin soyayya ba, bani da saurayi ko a school, ni koma a ina bana kula kowa, zaka iya tambaya ma ka ji". Hannu ya kai ya ɗan ja hancinta yana murmushi "To waye zan tambaya ɗin?" "Nima ban sani ba, kawai dai ka tambayi koma waye". Kara juyowa ya yi da kyau ta yadda zai sami damar ganin fuskarta sosai. "Ni ba sai na tambayi kowa ba, domin kuwa, na taɓa kamaki kina soyayya, a kan idona kika sace wa wani sarauyari bawan Allah zuciyarsa da kallo ɗaya". Zaro ido waje ta yi "Yaya Nawid a ina aka yi hakan? Kuma ni Aafia ɗin ce na yi hakan?" Ta kai karshen maganar tana yin narai narai da idanu kamar zata yi kuka. Ɗaure fuska sosai ya yi "E mana, ke ɗin dai, ai a gabana aka yi komai". Shiru ta ɗan yi tare da nutsa ƙwaƙwalwarta a cikin tunani, ita dai tasan wlh bata taɓa tsayawa da wani saurayi ba, bata taɓa soyayya ba, Rufee ta yi ƙoƙarin koya mata soyayya, ta yi ƙoƙarin haɗata da maza, amma idan baku mance ba, ta ki yarda, bata kula kowa, karatu kawai take yi, bata shiga harkar kowa. "Yaya Nawid ni wlh ban tuna yaushe aka yi hakan ba, ni ba zan yi musu da maganarka a kan cewa ba haka bane, amma dai abin da zance kila daga ɗan nesa ka gani, to kila mai kama da ni ce sai kaga kamar ni ce...." Katse ta ya yi da cewa "Ba wata mai kama dake, ke ɗin ce ba wata ba". Shiru ta yi na ɗan lokaci. "Tom shikenan Yaya Nawid na yarda ni ɗin ce, amma ka yi hakuri". Shafa face nata ya yi. "My beautiful wife, jiya ba kin sace zuciyar mijinki da daddare a nan ba, to ai shi ne saurayin da kika sace wa zuciyar, kuma ai kinga a gabana aka yi komai ko?". Bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. Tsareta da ido ya yi, yana kallon yadda take murmushin gwanin ban sha'awa. Ganin yana kallonta sosai ne yasa ta ɗan sauƙe idanunta kasa. "Kunyata kike ji?" Dawo da kallonta kan face nasa ta yi, ɗaga mata gera ɗaya ya yi yana kashe mata ido ɗaya. Kara faɗaɗa murmushin kan face nata ta yi, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, ganin ta yi murmushi, kuma ta ɗan saki jikinta. "Gaskiya fa ina kara yi wa Allah godiya, sannan ina kara yi wa Abbina godiya da ya mallaka mani ke, ya zama dole gobe muje mu gaida shi, na ji daɗin bani ke da ya yi". Hannu tasa ta rufe fuska tana murmushi. Hannun nata ya kama tare da zame shi daga kan face ɗin nata. "Ki daina hana ni ganin fuskar matata, ko fuskarki ce?" Ya tambaya yana ɗaga mata gera ɗaya. Kin yarda ta yi, ta dage sai ta rufe fuskarta, shi kuma ya ce a'a bai yarda ba, haka suka kama kokawar wasa, daga karshe dai ya yi nasarar kame hannayen nata dukka biyu, ya riƙe cikin nashi, tare kuma da mannata da jikinsa yana murmushi, ita ma sai murmushi take yi. "To dai na fiki karfi sai ki rinƙa bina a hankali, idan ba haka ba, zaki sha wahala". Cikin zolaya tare da so da kauna ya yi maganar. "Ai daman Yaya Nawid ka fini karfi mana, bama haɗi ai". Sake hannayen nata ya yi tare da jawota sosai ya matseta a jikinsa, matso da bakinsa ya yi saitin kunnenta, ya fara zuba mata kalaman masu shegen daɗi. Tuni ya mantar da ita wani bakin ciki, cikin kankanin lokaci ya sanya ta saki jiki da shi, tun tana mai da mashi da martani ɗai'ɗai, har ta fara zuba mashi nata salon kalaman kamar, yadda yake zuba mata shi ma, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, wani irin yanayi mai cike da annashuwa ya tsinci kansa a ciki, har cikin ransa yake jin breast ɗin nan nata da suke sokinsa a kirjinsa, dannewa kawai yake yi, ita kuma ta saki jikinta da shi. Haka suka kasance har karfe 7 na safe, sannan ya ce ta tashi su je wajen Ummi, daga nan sai suje kitchen ya tayata yi masu girki. "Yaya Nawid ka iya girki ne?" Ta tambaya da mamaki akan face nata. "Prof ya iya girki ne ko bai iya ba?" Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Kamar dai bai iya ba". Kashe mata ido ɗaya ya yi. "Duk wan da ya ce maki Prof bai iya girki ba, to ya gaya maki ne kawai dan ya ji daɗin bakinsa, amma Prof ba abin da bai iya girkawa ba, sai dai kawai baya son yi ne, amma ba dai ya yi aure ba? Zai yi ne ma ba wanda ya sani, nima da ai bana shiga kitchen, ko hanyarta ma ban sani ba, ban san me da me ma a cikin kitchen ɗin ba, amma yau ba gashi saboda ke zai shiga ba". Ya kai karshen maganar tare da sakinta ya miƙe zaune. Miƙewa ita ma ta yi, ta riga shi sauƙowa kasa, hannunta ya kamata suka nufi wajen, sai hira yake zuba mata, ita kuma sai murmushi take abinta, dama akwai tsohon soyayyarsa a cikin zuciyarta, yau soyayyar ta dawo mata sabuwa. A palo suka isko Ummi, har ta gama haɗa breakfast, ta jere saman table tana jiransu su tashi barci. Ganinta yasa A'AFIA ta kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata, cikin sauri ta karisa wajenta, miƙewa Ummin ta yi, ta tarota tare da runhumeta tana sakar mata wani ƙayatatciyar murmushi, sai murmushi shi ma yake yi, bakinsa yaki rufuwa. A tare suka zauna a saman sofar da ta tashi ta koma ta zauna, har lokacin bata saki surukar tata ba, shi ma wucewa ya yi ya zauna, sai murmushi suke yi, suka gaisa, har lokacin kuma, duk cikinsu ba wanda ya iya tunawa da Abbo, ya rufe masu baki, tamkar an goge masu shi a kwakwarsu. A tare suka hau saman table dan yin breakfast. Bayan sun kammala ne A'AFIA ta miƙe ta tattare kwaninkan ta gyara komai, sannan ta nufi bedroom ɗin Nawid wadda ya kasance nasu a yanzu, ita da shi kenan, yanzu ta iya wasu aikace aikacen gida kaɗan, ciki har da girki, kuma zamanta da Umaisha da Akila ta ɗan koya. Ita kuma Ummi suka cigaba da hira da shi. Tana shiga bedroom ɗin ta fara tattare masu ɗakin dan ta gyara, sai da tattare ko'ina, sannan ta fara ƙoƙarin canza masu zanin gado. Tana faman cire bed sheet ɗin, bata ji shigowarsa ba, sai kawai taga ya sanya hannu yana tayata, da mamaki take kallonsa, kamar AKil, domin shi ma Akil, cire kayansa yake yi, ya sanya na shan iska, ya gyara masu ɗaki, ya kuma wanke toilet, sannan ya raka Umaisha kitchen, tana aiki yana shafe mata tula tula, da yake yanzu Umaisha ɗin take yin girki, sun dai'na sayen abinci, Rimsha ta koya mata wasu, sannan shi ma ya saya mata littatafan girki kala kala, dan kawai ta rinƙa yi masu girki, to a nan Aafia ma ta ɗan koyi aiki. "Meyasa kike kallona haka?" Ya tambaya daidai lokacin da ya karisa cire bed sheet ɗin, ya ɗauka ya nufi wajen zuba kayan datti. "Babu komai" . Jinjina mata kai ya yi. "To jeki ki yi wanka, bari na shinfiɗa mana wani bed ɗin, idan kin fito sai na shiga na yi Nima, ko dai nazo muje mu yi a tare ne?" . Ya yi magana ta karshen cikin zolaya. Da sauri ta nufi toilet ɗin tana girgiza mashi kai alamar a'a, dariya ya yi. "Matsoraciya kawai". Ya faɗa yana ciro masu wani sabon bed sheet daga cikin drawer kayansa. Ko sannu ba ta sake ce mashi ba, da haka ta wuce toilet abinta, binta ya yi da kallo har sai da ta shige, sannan ya zo ya fara aikin gyara gadon, a hankali yake jin kaunarta na karuwa mashi a cikin zuciyarsa. After some minutes ta fito wanka, sai ɗari ɗarin fitowa take yi kada ta same shi a ɗakin, domin kuwa towel ta ɗauro, bata iya ta yi wanka ta sake mayar da kayan dattin da ta cire ba. Ta yi Sa'a kuwa, baya ɗakin. Ganin baya nan yasa ta ji wani irin daɗi ya kulluɓeta, gaban mirror ta wuce, sauri sauri ta fara shafa mayukansa da ta gani a wajen. Tana tsaka da shafa mai ta ji saukar hannunsa a kugunta, har ga Allah bata ji shigowarsa, kofar nasa bata kara, idan an taɓata, wani irin ɗaukewa na wucin gadi numfashinta ya yi, cak ta tsaya da shafa mai ɗin da take yi. Kwanto da kansa ya yi a saman kafadarta, tare da sanya hannunsa ɗaya, ya karɓi Lotion na hannunta da take shafawa, zubawa a hannunsa ya yi, a nutse ya murza man a hannayensa, har lokacin kansa na kwance a saman kafaɗarta, a hannunta ya fara shafa mata man, kafin ya ɗan raba jikinsu, ya fara shafa mata a suk gaɓɓan da ake shafa mai, mutuwar tsaye ta yi, ta kasa ko motsawa. Ya zo daidai wuyarta, yana ƙoƙarin kwance towel na jikinta dan ya shafa mata man, cikin sauri ta kankame towel ɗin, ɗago ido ya yi, ya kalli face nata, cikin sauri ta kawar da kallonta, sake mata towel ɗin ya yi, ya shafa mata man a face nata yana murmushi. "Am so sorry gimbiyata, na yi aikin da baki saka ni ba ko? To ki yi hakuri na taya ki ne kawai, tun da an hanani shafawa kirjin mai Shikenan, na bar maki, shafa masu ga kayan sawarki nan na karɓo maki daga wajen Ummi". Yana kai karshen maganar ya wuce ya nufi toilet dan shi ma ya yi wanka. Bin shi da kallo ta yi, har sai da ya zo zai shiga toilet ɗin, sannan ya ɗan juyo, cikin sauri ta kawar da kallonta, murmushi ya saki kawai, sannan ya shige abinsa, yana juyawa ta dawo da kallonta kansa, har sai da ya shige ta daina ganinsa, sannan ta cigaba da abin da take yi, sai tunanin yadda ya shafa mata Lotion ɗin take yi, har cikin ranta ta ji daɗin hakan, musamman yadda taga yana zuba irin wannan murmushi haka, abin ya tsaya mata a ranta. Wucewa ta yi ta ɗauki kayan da ya ajiye mata a saman gado, wani irin kunya ta ji lokacin da ta kalla har da breziya da pant ya kawo mata. Ɗauka ta yi ta fara sakawa da sauri sauri, doguwar rigar Abaya ce, pink color tare da mayafinta. Tana gama shiryawa Ummi ta buga masu kofar ɗakin, cikin sauri ta karisa bakin kofar ta buɗe, miƙa mata wayarta Ummi ta yi. "Ga shi nan tun ɗazun ake ta kiran ki". Cikin girmamawa ta karɓa tare da yin godiya, juyawa Ummi ta yi ta koma nata bedroom ɗin, ita kuma ta dawo cikin ɗakin. Umaisha ce ta kira a wayar, cike da zumuɗi ta bi kiran, tare da zama a gefen gado. Bugu ɗaya Umaisha ta ɗaga. "Hello Umaisha!" Ta yi maganar cike da so da kuma kaunar ƴar uwar tata, "Aunty Afi ina kwana?" "Lafiya lou Umaisha yasu yaya AKil?" "Suna lafiya, ya Yaya Nawid da kuma Ummi?". Nisawa ta yi tana mai kara faɗaɗa murmushinta "Wlh kowa yana nan lafiya Umaisha, amma lafiya kika kirani da sanyin safiya haka? Ya kuma aka yi yaya Akil ya kyaleki kika yi kira da sanyin safiyar nan". Shiru kaɗan Umaisha ta ɗan yi kafin ta ce "Wlh Aunty Afi satar hanya na yi na kiraki, yanzu haka yaya Akil yana ɗaki yana kwance, nace mashi ina zuwa ne, shi ne nazo kitchen na kiraki, yanzu dai muyi magana da wuri Kinji? Dan kinsan halinsa sarai, yanzu idan ya ji na kira wani da safe haka, faɗa zai yi Mani, zai ce na takurawa ƴan gida suna barcinsu. "Okey to menene faɗi ina jinka?" "Aunty Afi Ommu ne ta kirani jiya, ta ce na ɗauko mata kuɗin yaya Akil har naira million goma, to dama yau da daddare ya ce zamu je gida, kuma nace mata idan zamu zo gida zan kawo mata, dama zan ɗauka mata 2 million ne a cikin kuɗinsa da yake ajiyewa a bedroom nasa, to amma tsoro nake ji, na rasa ya zanyi, na rasa me mafita, na rasa wajen waye zan nemi shawara, dan Allah ki ceceni, wlh ina tsoron ɗaukar abin da ba nawa ba!!". Ta kai karshen maganar tana hawaye. A kule Aafia ta ce "Sai dai uban millon 10, ke Umaisha baki da hankali ko? Ta yaya zaki yarda da wannan abin? Kina da hankali kuwa? Ina ilimin naki yake? Ina karatun da kike yi kullun? Haka Allah ya ce ki yi? Allah bai ce ayi wa iyaye biyayya wajen saɓon sa ba, Ki sani naira ɗaya na mijinki, idan kika ci ba tare da ya baki ba, to fa wuta kika ci, to tun wuri ki dawo hayyacinki Kinji na gaya maki, me yasa ba zata tambayi Abbi ba? Idan ma Abbi yaki bata ai yaya Irfan kam ya zama mashi dole ya bata, to wlh kada ki kuskura ko naira ɗaya na yaya Akil ki taɓa ba tare da ya baki ba?". Tana hawaye ta fara bawa A'AFIA ɗin labarin yadda suka yi da Ommu ɗin da har ta yarda zata ɗauko mata kuɗin, jin hakan yasa jikin Aafia ɗin ya mutuwa, Allah sarki uwa da ƴaƴa kenan, komai lalacewar uwa, in dai tasan ta yadda zata yi magana da yaranta, to tabbas ba makawa zata yi galaba akansu, ta rasa me zata cewa Umaisha ɗin kuma again. "Aunty Afi kina jina?" Ƴar firgita ta yi jin muryar Umaisha ɗin, Baiwar Allah ta shiga duniyar tunani ne, domin ta gasgata zancen Ommu ɗin, musaman ma da ta ji an ce Abbi ya ce ba zai biya mata ba, ta san halinsa sarai, tabbas zai iya cewa ba zai biya ɗin ba, domin yana da zafin rai da saurin fushi, sai dai kuma yana da saurin sauƙowa, abin da bata sani ba shi ne, Ommu karya ta shirya masu da ciwo, domin tasan da ciwo ne kawai zata yi saurin karyar masu da zuciya. Tana ƙoƙarin yin magana ta ji Nawid yana ƙoƙarin fitowa daga toilet, cikin sauri ta sallami Umaishar a kan za su yi waya wani lokaci kawai. Katse kiran ta yi, ta koma ta kwanta tana tunanin mafita, har cikin ranta ta tausayawa Ommun tasu. Gaban mirror ya tsaya, ya gama shafa mai da perfume nasa, sannan ya juyo ya kalleta, cike da zolaya ya ce "Amarya azo a sanyawa ango kaya". Miƙewa zaune ta yi tana sunkuyar da kanta kasa, da kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci akwai abin da ya ɓata mata rai, dan haka sai ya ajiye zancen wasa, cikin natsuwa ya kariso gareta. A saman bedside drawer ya zauna, cike da kulawa ya riƙo hannunta. "Menene kuma kanwata? Waye ya taɓa ki?" Ƙaƙalo murmushi dole ta yi. "Babu komai yaya Nawid" ta bashi amsa. "Are you sure?" Ya yi maganar yana ɗan leƙo face nata, ɗagowa ta yi suka haɗa ido, cool murmushi ta sakar masa domin ta tabbatar mashi da babu komai. "Zaki iya bawa yaya Nawid ɗin ki sumbata a kumatu?" Ya faɗa cikin sigar soyayya. Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e, sannan ta ɗaura da cewa in dai zai sanya shi farinciki zata yi mashi. Sosai ya ji daɗi tare da ɗan juya mata kumatun nashi yana murmushi, kirginta sai bugawa yake yi, amma haka ta daure, ta matso da bakinta, cikin natsuwa ta bashi hot sumbata a kumatun nasa. Kusan a tare suka sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, hannayenta ya riƙo "I really love my wife" "I love too yaya Nawid". Miƙewa ya yi ya koma gaban mirror yana faɗin "To za'a zo a sanya mani kayan ne ko ya ya?". Komawa ta yi ta kwanta "Yaya Nawid ni ai ban iya ba". Girgiza kai kawai ya yi tare da wucewa wajen drawer kayansa. Kayan da yake buƙata ya ɗauka ya wuce toilet, ita kuma ta gyara kwanciyarta tare da kashe wayarta gabaɗaya, a cikin zuciyarta kuwa, ji take yi kamar ta kira Irfan ta gaya mashi abin da Ommu ke buƙata shi ya bata kuɗin, sai dai kuma ta san mawuyacin abu ne Irfan ya bada kuɗin, domin kuwa ya fi Abbi ma yin fushi da Ommu ɗin, ko ganinta baya son yi, kawai dai dan ba yadda zai yi ne, ta zo a matsayin mahaifiyarsa, sai dai hakuri kawai, amma fa tabbas ba zai bata wannan kuɗin ba, shiyasa ma bata tinkare shi ba. A haka Nawid ya fito ya sameta, ya shirya cikin kananan kaya, kusa da ita ya zo ya kwanta tare da fara janta da hira, tun tana biye mashi kaɗan da kaɗan, har ta ware suka fara zuba hira tare da zubawa juna kalman so da kuma kauna. To a ɓangaren gidan Lion kuwa. Rana ta ɗage ta yi sanyi, yamma ta yi, misalin karfe 4 zuwa 5 haka, barcinsa yake yi cikin kwanciyar hankali, daga yanayin kwanciyar da ya yi, zaka fahimci a cikin kwanciyar hankali yake, a hankali hankali yake sauƙe numfashinsa, jikinsa na sanye da pajama launin fari tas, kyakkywar dark black curly hair sa, ya zuba mashi har fuskarsa, bai ɗaure ta bane, hakan yasa ta zubo mashi har kan face nasa, ta rufe mashi fuska sosai, sai sheki gashin nan yake yi, abin mamaki kuma gashin nasa, kusan iri ɗaya dana Rimsha, sai dai nasa bata kai na Rimsha nannaɗuwa kamar indomie ba, ita Rimsha nata ya naɗu sosai. ɗan motsawa ya fara yi tamkar mai mafarki, a hankali ya cigaba da juyawa tamkar wani ke juya shi, ya ɗan ɗauki tsawon minti biyu a haka kafin ya waro dara daran blue eyes nasa waje, wadda kuma farin cikin idanun suka yi ja sosai, da alama barcin bata ishe shi ba. Slowly ta sauƙe idanun nasa a saman ɗakin nasa, kafin daga bisani ya dawo da idanun nasa saman gadon nasa. Shiru ya yi na tsawon mintoci kafin nan ya mai da idanun nasa ya lumshe su, a hankali ya motsa kyawawan lips nasa ya furta "Why mummy, why are you always coming in my dream with useless thinks? Why are you disturbing my life?! Do you want me to do something for you, so that you should forget about me? Oh what?". Shiru ya sake yi na tsawon mintoci da a kallah za su iya kai minti 30. A hankali ya miƙe kuma tare da zama a gefen gadon yana mai tsananta tunani akan cikin daddynsu da mummynsu waye ne mai gaskiya? Me yasa shi kaɗai ne mai yawan mafarkin mum ɗin tasu? Meyasa kuma kullun yake yawan mafarkai marasa kyau ne a kanta? Meyasa take zuwa mashi a siffar da ko wani ɗan adam ba zai so ganin wani nashi a ciki ba? Meyasa take yawan yi mashi ikirarin zata kashe shi a mafarkin? Amma kuma a zahiri tana nuna mutuwar sonsu, tabbas da ya ɗauka shirmen mafarki ne kawai, amma yanzu tsawon shekara 15 yana wannan mafarki bai dai'na ba, babu rana ɗaya da zai kwanta ba tare da ya yi ba, dole wannan Mafarki ta sanya shi cikin ruɗani, menene ainahin makasudin ciwon Michael? Sannan daddy yaki gaya mashi gaskiyar a ina ne gidan magicians (matsafa) da ta kai su, yaki gaya masu in da gidan yake bare su binciki gaskiyar lamarin, ya ce masu ya mance a in da gidan yake, amma abin mamaki shi ne ƴaƴanka har guda uku za'a kai su irin wannan gida dan a salwantar da rayuwarsu, amma har ka iya mancewa da wannan gidan? Abin da mamaki gaskiya, daddy bai yi tsufar da zai yi irin haka ba, dan ma shan wine (giya) ne da ya yi a baya ce ta taɓa mashi lafiyar jikinsa, ba dan haka ba, lafiyayyene sosai, dole dai akwai abin da daddy da mummy suƙe ɓoyewa, wadda ba su son ƴaƴan nasu su sani, Lion bai cika son yana shiga hurumin iyayen nasa ba, kai shi ba iyayensa ba, koma waye baya shiga huruminsa, sai idan abu ya zame mashi dole, amma yanzu a ƴan kwana biyun nan yana ji a jikinsa tabbas dole ya binciko gaskiyar da aka binne tsawon shekaru, bai so hakan ba, domin daga daddyn har mummyn nasu ba wanda yake so a cikinsu, hakan kuma yasa bai shiga wannan faɗa ta su ba, ɗan garama Josephine ɗin ya fi sonta ita a kan daddyn nasu. Shiru ya yi ƙwaƙwalwarsa na tariyo mashi abubuwa da dama dan gane da iyayen nasu, tabbas yana ji a jikinsa mummynsu na sonsu da gaskiya, kuma tamkar ta fi daddy gaskiya, sannan wannan ciwo da Michael ya yi na tsawon shekaru 30, to tabbas daddy yana da sa hannu, domin kuwa yana yawan ganin Musharraf yana magana da Aseef ɗin a kan ciwo, tabbas ba ciwo ce ta tsakani da Allah ba, akwai wata a kasa, to amma babbar abin tambayar a nan shi ne, meyasa ita kuma Josephine ɗin take zuwa mashi a mafarki tsawon shekaru 15, kullun maganarta a cikin mafarki zata kashe su, ba zata taɓa bari su rayu ba, wani lokaci ta yi ƙoƙarin caka mashi wuƙa har sai an riƙe ta, ba mafarki ce da za'a yasar da ita ba, ba mafarki ce da za'a ce shirme ba ce, tsawon shekaru 15 tabbas akwai wata aya da take son isa masu a cikin wannan mafarkin, to menene? Kuma shi ne kaɗai mai yin wannan mafarki. Can wata zuciya ta ce mashi to ko dai kai ba ɗan su bane, da sauri ɗayar ɓangaren na zuciyar ta amsa mashi da no ba zai yi wu ba, dole kai ɗansu ne mana, dole kai ne cikon TRIPLETS na MICHAEL and JAMES, idan kai ba ɗansu bane ta ya za'ayi kuyi irin wannan muguwar kamanni haka? Ai zancen kai ba ɗansu bane ma bai ta so ba, ta ko'ina ku ɗauko iyayen naku, daga Josephine ɗin har William ɗin, ta kowani ɓangare kun ɗauko su, so dole sune iyayenku, sai dai kawai ku nemo wata hanya kuma ta daban da zaku nemowa kanku mafita. Har lokacin shi dai yana ji tamkar ba daddy bane mahaifinsa, domin ko kaɗan baya jin son daddyn nasa, kuma ba shi kaɗai ba dukkansu, duk da wannan uban kammanin dake a kan fuskarsu, amma yana jin tamkar dai shi ubansa daban. TO UBANSA DA BAN KUMA?🤔 A'A KU ƘIRA MANA JOSEPHINE TA ZO TA YI MANA BAYANI, TAYA YA YA ZAMA SHI UBANSA DABAN, KUMA SUKE A TRIPLETS? KO DAI BA TRIPLETS NA GASKE BANE? BABBAR MAGANA WANNAN CAKWAKIYA DA YAWA TAKE. A ɓangaren ita kuma Rimsha, zaune take a palon kasa, har lokacin shigar ɗazun ce a jikinta, abinci take ci cikin natsu, yaya Imran ya saho mata abinci, Mark mugu ya hanata yin girki, wai abincin kasarsu na da wari, ɗan banza ya zo ya zauna mana a kasarmu amma dan iskanci wai abincin mu na da wari. Cikin kwanciyar hankali take taunar abincinta. Sanye cikin fararen kaya masu shegen kyau Malika ta bayyana a gefenta, wani irin haɗaɗɗen murmushi ta saki. "Malika ina kika shiga kwana biyu?" Dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali. "Rimsha ke dai bari, ba zaki gane bane, ina can ana ta faman faɗa a kasarmu, kinsan sarkinmu kwanaki bashi da lafiya, to Allah ya yi mashi rasuwa, shi ne fa ake ta faɗa akan waye zai hau mulki, shiyasa kwana biyu na ɓuya, yanzu ma na ɗan leƙo mu gaisa ne kawai, ba jimawa zan yi ba, zan koma saboda har yanzu bamu samu zaman lafiya ba, duk da cewa Yarima Haruna ya karɓi Mulkin, to amma ƴan uwansa sunki yarda, wannna ya ce shi ne zai riƙi mulki, wannan ma ya ce shi ne, aikin kenan, har yanzu hayaniyar da ake yi kenan. Ita dai Rimsha almara take ɗaukar abin, ji wai harda wani sarkinsu ya mutu ana yaki, to ko a gidan uwar wa suke yakin Oho? Ko dai a saman iska suke yakin ne? Sai tambayar kanta take yi, saboda yarinta irin tata. Ganin haka yasa Malika ta kawar mata da wannan tunani "Ina angonmu Rimsha?." Wani cool murmushi ta saki, an sosa mata in da yake yi mata kaikayi, sosai Malika ta ji daɗin ganin wannan murmushi nata, dama kuma abain da take nema kenan. "Malika dan Allah ina son in tambaye ki". Tsareta da idanu Malika ta yi ba tare da ta yi magana ba. "Malika dan Allah ko kin san ta ya ya aka yi Ayla ta baro Daular Mutuwa? Abin ya tsaya mani a raina, dana tambayeta a waya kuma, ta ce mini ta manta, to dan Allah idan kin sani ki gaya mini". Shiru ta ɗan yi na tsawon lokaci kafin ta fara magana a nutse "E Ayla ta baro Daular Mutuwa ne da taimakon wani daga cikin Daular Mutuwar, sun sha faɗa sosai kafin ya samu ya fito da ita, bayan ya fito da ita kuma, akwai wani ruwan tsafi da ya bata, ni ban san faɗar da suka yi a ciki ba, na dai ga lokacin da ya fito da ita, ya bata ruwan tsafin domin ta sha, tana sha kuma ta zube a wajen sumammiya, bata sake farkawa sai bayan kwana ɗaya, a in da kuma ta farka a kusa da wannan kauye da kuka haɗu, shi kuma wadda ya bata ruwan tsafi ya kuma fito da ita, yana ganin ta suma ya juya ya koma cikin Daular Mutuwa, to kin ji abin da ya faru kenan, abin da yasa kuma ki ka ji cikin Ayla na kumbura a lokacin, wannan ruwa da ya bata ta sha ne, shi ne yasa hakan ta faru kafin ya saketa". Rimsha zata sake magana sai ga Mark ya fito daga cikin Kitchen, karo na farko yau da ya sauƙe idanuwansa a kanta, baya iya ganin Malika, ita kaɗai ce a wajen a idanunsa, ba karamin mamaki ya sha ba ganin irin kyanta, sosai ya kare mata kallo daga sama har kasa, ga idanun nasa dara dara, sai dai suna cikin bakin glass, hakan yasa bata gane yana kallonta ba. "What is your name?" Shi ne abin da ya tambayeta da wata fasasshiyar muryarsa a wajen, mamaki ne ya kamata, dama wannan mai fuskar ɓaunan yana magana? Ai ita ta zaci ma kurma ne wlh. RIMSHA ta bashi amsar, kokarin kiran sunan ya yi a cikin zuciyarsa, amma ya kasa, a maimakon Rimsha, sai ya ce Rishma, ganin sunan ba zata maimaitun mashi bane yasa ya ce ya ta je ta ɗauki abincin oga ya gama haɗawa. Okey ta amsa mashi da shi, ta miƙe cikin natsuwa, yau dai bai tafi ba, ya tsaya binta da kallo, ƴar karama da ita sai shegen kyau kamar ita ta yi kanta, Malika dai ta zuba idanu tana ganin ikon Allah, tare kuma da dariyar mugunta, kome take yi wa dariya oho, ita kaɗai ta barwa kanta sani. Yana tsaye a wajen har ta fito ɗauke da abincin, zata yi wa Malika magana, cikin sauri ta ɗaga mata hannu alamar ta je kawai, idan ta yi magana Mark zai ce ta haukace, tun da shi baya kallon Malika ɗin. Sama ta wuce, shi kuma ya wuce ya koma cikin Kitchen ɗin, dan ya ɗauko abincin Areef, yau kawai ya ji yana son tayata aiki ne, shiyasa zai kaiwa Areef nasa abinci. TO FA YANA SON TAYATA AIKI KUMA? SHI DA BAYA KO MAGANA? HMMMM. A bakin kofarsa ta tsaya kamar kullum, kasa kasa ta yi sallama a nutse, kamar dai kullun shiru, a hankali ta zuro kafafunta cikin daɗin. Daddaɗar kamshin perfume nasa ne ya fara kai mata karo a kofofin hancinta. Shaƙa ta yi ta lumshe idanu, har wani nishaɗi take ji. Babu kowa a cikin daɗin, yau dai taƙi ɗago idanu gudun kada ta ga wani abin mai razanarwa, har sai da ta ajiye mashi abincin nasa a in da ta sa ba ajiye mashi, sannan ta fara ƴan waige waigen ko zata ga ta ina yake. Ganin babu kowa ne yasa ta yi zamanta a wajen tana cigaba da kallon ɗakin, sai dai ta ɗan yi kasa da kanta. Jin kamshin perfume ɗin nasa ya karu a ɗakin ne yasa ta ɗago kanta, ya fito daga dressing room nasa, ya bata baya yana kallon fusataccen fuskarsa a jikin mirror, da alama akwai abin da yake yi, jikinsa na sanye da jallabiya fara tas, kai.... shi dai yana bala'in son farin color a rayuwarsa. Sai satar kallonsa ta kasan ido take yi, duk da bata ga face nashi ba, bata ganshi ta gaba ba, tabbas tasan ya yi wa kayan kyau over, da alama ya rage tsawon gashin kansa, domin yau da ya ɗauke ta, jelar bata da tsawo sosai, ba kamar ko da yaushe ba. Sai bayan ya gama abin da yake yi ne, ya dawo kusa da ita a in da ya saba zama ya zauna, cikin sauri ta fara zuba mashi abincin, can cikin ƙwaƙwalwarta zazzakar sexy voice nasa ya daki dodin kunnenta har cikin ƙwaƙwalwarta. "Give me my photo". Shi ne abin da ya faɗa mata, yau ta tattara natsuwarta sosai, bata son ta cigaba da yi mashi laifi, a bayanan da Imran ya yi mata ta fahimci cewa yes tabbas yana yi wa Imran kara sosai da har take yi mashi irin waɗan nan laifuka ya kyaketa, kuma tana cin albarkacin har da daddynta da yake matukar taimakon ASEEF. Cikin natsuwa ta amsa mashi da okey, sannan ta miƙe ta ɗauko mashi wayar, sai dai jikinta sai kerma yake yi, lokacin da ta zo miƙa mashi wayar hannunta sai kerma yake yi, kallo ɗaya ya yi wa hannun nata ya karɓi wayarsa ya fara aikin latsawa, tun da ya fahimci tana mutsuwar bala'i tsoronsa, sai ya ji a ransa bai kamata ya yi mata magana da karfi ba, zata iya mutuwa idan hakan ta faru, dama kuma magana da karfi ba halinsa bane. Abincin ta zuba ta tura mashi, sai daɗi take ji, yau bata yi mashi laifi ba, ita kaɗai sai murmushi take yi, Allah ma yasa baya ganinta, da sai ya ce ta haukace. Da yake yau ya ji yunwa sosai, bai wani tsaya ɓata lokaci ba, tana tura mashi abincin ya fara ɗeba yana kaiwa ɗan bakinsa a nutse, ita kuwa zama ta yi a gefensa tana tunanin da ace yanzu kawai ya fara bata abincin nan a baki mana, ai da ta ji daɗi. (Kai Rimsha duniya) Shi kuwa tamkar ma bai san da mutun a cikin ɗakin ba, laptop nasa dake a ɗaure saman gado ne sauti dariyar Aseef ya fara fitowa dafa ciki, ba tare da ya ɗago kai ba ya ce ta miƙo mashi laptop ɗin, okey ta amsa mashi da shi, a nutsu ta miƙe ta ɗauko mashi. Saman sofa ta gefensa ya ɗaura laptop ɗin, ita ma tana iya kallon screen ɗin, saboda tana gefensa ɗan nesa da shi, kusan a jere suke za'a ce. Zuba ma laptop ɗin ido ta yi, shi kuma yana cin abinci yana sauraron shirmen Aseef da Musharraf, wai Aseef na koyar Hausa, shi ne suke ta dariya, idan Musharraf ya faɗi wani word Aseef ya kwashe da darita kamar zautatce, wai kalmar ta bashi dariya, idan kuma Musharraf ya ce ya maimaita kalmar, to fa idan ya faɗeta sai Musharraf ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya, domin kuwa harshen Aseef a naɗe take, ba yarensa bane, so baya taɓa faɗa daidai, komai sai ya canza mata muhalli. Rimsha kuwa, daddynta kawai take kallo, yadda yake ta dariya abinsa, suna zaune a wajen basket ball na gidan nasu, Aseef na sanye da wando three quarter, sai farar singlet, shi kuma Daddy, yana sanye ne da full dressing ba ƙanana kamar Aseef ba, sun yi kyau ba kaɗan ba, daddy fa ya kara haske sosai, ainahin hasken fatarsa ta kara bayyana, saboda yanayin kasarsu, akwai sanyi sosai. A ɓangaren Lion kuwa, har cikin ransa yake jin matukar daɗin abin da suke yi, ko ba komai cikin kaso 100 na damuwar da Aseef yake shiga na ciwon nan nasa, daddy na rage mashi kaso 80 daga ciki, a zahirin gaskiya Aseef yana jin matukar raɗaɗi idan har ya tuna cewa ƴan uwansa dukka sun gama karatu, shi babu abin da ya sani, wani lokaci har hawaye yake yi, sai dai daddyn Rimsha yana ƙoƙari wajen nuna mashi ya yarda da kaddararsa, kowa da yadda kaddara take zuwa mashi, hakan kuma yasa daddyn yake zama ya ɓata lokacinsa da komai da komai, ya zage dantse yana koyawa mashi abubuwa, harta assignment idan a ka basu, daddy na kula da shi, domin daddy degree ne ke fareshi shi, so sai ya zama tamkar uncle nashi mai yi mashi lesson, hakan kuma ba ƙaramin daɗi da farinciki ya sanya Areef da Saif ba, abin da yasa ma kenan Lion bai hukunta Rimsha ɗazun ba, ya daure ya yafe mata sabida Imran da kuma babanta. Tana ta kallon Daddynta har ya kammala cin abinci bata sani ba, zazzakar sexy voice nasa ta ji yana faɗin ta bashi ruwa, ta shagala da kallonsu ta mance kula da shi, a hanzarce ta zuba mashi ruwan ta miƙa mashi, karɓa ya zo yi hannunsu ya gogi na juna, ai bata san time da ta saki ruwan ba, Allah dai yasa shi ya riƙe cup ɗin, badan haka ba, da ta yi mashi wanka da ruwan. Bai bi ta kanta ba, ya kai cup ɗin saitin ɗan bakinsa. Sai da ya sha rabin ruwan, sannan ya ajiye, bata gaji da ganin daddynta ba, amma haka ba dan ta so ba, ta tattare kayan ta nufi waje, miƙewa ya yi ya koma saman sofa set mai zaman mutun 2 yana mai matukar jin ƙoshi, ga shi yana cikin farinciki dariyar da Daddy yake sanya Aseef, tamkar Tv haka ya mai dasu yake kallon shirmen nasu, sai dai fa duk da wannan daɗi, fuskarsa a turnuƙe kamar kullum. Ita kuma kitchen ta mayar da kayan abincin kafin ta fito ta wuce wajen Areef dan su ɗan yi hira, daidai zata shiga ɗakin nasa, Malika ta jata baya tana faɗin kada ta shiga, da mamaki ta tambayi dalili, hannunta Malika ta riƙe suka koma saman sofa suka zauna dan su tattauna. A nan take gaya mata Areef baya a cikin hayyacinsa yanzu, Sakamakon yakar wanna kunguya ta matsafan da aka sanya shi a ciki, to abin sai a hankali, idan ta shiga Areef zai iya kasheta, su kyale shi shi kaɗai ɗin dai. A tsorace ta tambayeta shin ko Areef ɗin zai sami lafiya. "Rimsha Areef da izinin Allah ya ma sami lafiya ya gama, Kinga wannan yaki da ake yi, azzaluman nan sun tattaru ne a jikin Areef ɗin ne, dan su yi garkuwa da shi ko zasu tsira, amma hakan ba zai yi wu ba, yanzu dai sun yi nasarar shiga jikin nasa, amma fa nan da ƴan mintuna dole su sake shi ko suna so ko basu ko, domin Saif ya baza malamai ta ko'ina suna yi masu sauƙar Al Qur'ani mai girma tare da addua'o'i, ai dolene ma su rabu da Areef, ko da kuwa uwa ɗaya a ka Haife su". Shiru Rimsha ta ɗan yi, kafin nan ta miƙe da sauri ta nufi sama tana faɗawa Malika bari ta je ta yi sallah saboda Areef, bari ta yi nafila ita ma ta rokar mashi Allah da ya kuɓutar da shi lafiya, tsabar sauri bama ta jira amsar Malika ɗin ba, a hanzarce ta faɗa cikin bedroom nata. Kai tsaye toilet ta nufa, bayan ta ɗauro alwala ta fito sai ta shiffiɗa dadduma tare da sanya hijabi ta tada Sallah. Ita kuma Malika miƙewa ta yi ta fito harabar gidan, ƴan dube dube ta yi kafin ta ɓace ɓat. A ɓangaren gidan Abbi kuwa. kamar yadda Abbi ya faɗa haka aka yi, tun safe suka shirya suka ɗauki Hanan suka nufi Katsina, Aunty da ita da Hjy Batula kuma, suka shirya Jelly suka nufi gidan babban yayansu, wato dai Abban Imran. Hjy Batula ce ta ja motar, Aunty na gidan gaba ita kuma jelly tana gidan baya, sai taunar chewing gum take yi, Hjy Batula ta ce ta yasar da chewing gum ɗin nan, kada ta kuskura ta shiga gidan surukuwa da shi, ta ce to sai sun isa gidan sarakuwar tukun nan ta yasar. A waje suka yi parking na mota, suka fito, Aunty ta riƙo hannunta, ita kuma Hjy Batula tana ƙoƙarin ɗage glasa ɗin motar da sauransu, da Motar Irfan suka zo. Bayan ta fito ne suka nufi cikin gidan, mai gadi bai hanasu shiga ba, domin ya ga kamannin Hjy Batula da Abba. Ciki suka wuce, har lokacin jelly bata yasar da chewing gum ɗin ba, ta dai ɓoye a bakinta, ta daina taunarsa. A palo suka isko Ammie zaune tana kallo a Tv, bakinsu ɗauke da sallama suka shigo, jin sallamarsu yasa ta juyowa domin taga suwaye ne. Ganin Hjy Batula yasa ta ɗaure fuska sosai tana binsu da kallon banza. Ita kuwa jelly tun da suka shigo take karewa palon kallo, baki abin magana ta kasa hakuri sai da ta ce "Gwaggon Batula wannan wani irin gidan kazanta ne haka? Jibi ko'ina da datti, amma dai masu gidan guragu ne basu da kafa da hannu ko?". Aunty ce ta rufe mata baki tana girgiza mata kai. Hannunta ta sanya ta zame na Auntyn daga bakin nata. "Ke Aunty gaskiya ce baki so na faɗa ko me? Wlh gidan nan gidan datti ne, buhun datti ne masu wannan gida, jibi kura wajen Tv nan, kuma a haka a ka kunna Tvn? Aunty wlh datti cuta ce, kazanta tana mugun yi wa lafiya Illah". Dafe kai Aunty ta yi domin tasan kaɗan ma ta gani in dai jelly ce, ita kuma Hjy Batula kasa kasa ta ce mata ta rufewa mutane baki. Ammie dai sai binsu da idanunta kawai take yi, bata ce masu ko sannu ba, bata yi masu iso ba, dan ra'ayin kansu, suka iso ciki. Suna isowa idanun jelly suka sauƙa a kan Ammie ɗin. Zuba mata idanu ta yi tana kallonta, sanye take da wani dogon riga irin na barcin nan, kayan duk datti, sai ta yi kama da mai aikin gidan ne ba matar gida ba, wata mai aikin ma, ba zata iya zama cikin uban datti haka ba. Zama suka yi a saman sofa ba tare da an basu izni ba. Sanin hali yasa Hjy Batula bata tsaya yin wani dogon turanci ba, faka faka kawai ta sanar da Ammien abin da yake tafe da su, ai kuwa wani mahaukacin tsalle Ammie ta yi, ta dire ta ce idan akwai wanda ya isa ya yi wa ɗan ta aure shegiya take, uban mutun ya yi kaɗan, ai ba uban da ya ɗauka mata cikin ɗan ya yi mata naƙuda, ya rene mata shi har ya girma, dan haka kuma babu uban da ya isha ya yi wa ƴaƴanta abin da bai yi mata ba, wlh tun suna shaida juna su fitar mata da jelly daga cikin gidan nan, idan ba haka ba ta sumar da ƴa, yanzu ta sanya su suyi danasanin saninta a rayuwarsu. Aunty kam ta tsorata dan bata son hayaniya, Hjy Batula kuwa already ta san hali, dan haka ko ɗar bata yi ba, ita kuma Jelly wani irin ɗaure fuska ta yi, ba mutunci, rai a jagule ta fara magana. "Wannan mai kama da sumammiyar akuyar fa? Gwaggo Batula wace ce ita da har zata ce a fitar da ni daga cikin gidan nan? Ina cewa shi ne gidansu yaya Imran? Kuma wannan ƴar dattin ba mai aikinsu ba ce? Ko dai a wannan gida masu aiki ma suna da damar yin magana da power kamar haka ne?". Shiru Aunty ta yi dan tasan halin jelly fin haka ma yi zata yi, dama bata ce zata mari Ammie ba ai an yi sa'a. Ita kuma Hjy Batula buge mata baki ta yi kasa kasa ta ce "Ke Jalila surukarki ce fa, mahaifiyar Imran ce". Turo bakin nan ta yi kamar biro. "To gwaggo Batula dan ita ta haifi yaya Imran sai ta ce bata son ganina a fitar da nine? To ni dama waye ya ce ma ta so ni? Ni ma ai ba sonta nake yi ba, kuma ba zan zauna ma a gidan nan ba domin daddy ya taɓa gaya mani she is a wicked" Kalubale gareku iyaye, bai kamata kuna zagin wata ko wani a gaban yara ba, domin baku san wace alaƙa ce zata haɗa ƴaƴanku da waƴan nan mutane ba, gaba tafi baya yawa, wannan haka yake, yanzu dai ga shi nan, daddynta yana zagin Ammie a gabanta, ita kuma ta riƙe, a kwana a tashi ga Ammie ta zama surukuwarta, ku sani duk son da Iman yake yi mata, yafi kaunar farincikin mahaifiyarsa sau dubu, ba zai taɓa yarda ta zagi mahaifiyarsa ba, a kan hakan ana iya kwance wannan aure ma baki ɗaya, to shawara dai ta rage gareku iyaye, ni dai na yi nawa, sai ku kuma ku gyara, dan nasan wannan matsala ce da take damun mu, sai ki ga uwa ta zauna tana zagin makontan ta a gaban ƴaƴanta, kuma ana waje guda, komai ka iya faruwa, ta yi wu ɗan maƙotan ya zo neman aure gidan naku, to ya kenan? Ƴaƴanki ba za su ga uwar da daraja ba, sai ki ga kwana biyu aure ya mutu, ƴa ta raina uwar miji, me ya kawo hakan? Wata kila ta taɓa jin kin ce uwar mijin ƴar datti ce ko ƴar kaza ƴar kaza, babu namijin da zai yarda a raina uwasa da ƴan uwansa, wannan kuskure ne babba muke yi, ya kamata mu gyara......... ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E7-8 Turo bakin nan ta yi kamar biro. "To gwaggo Batula dan ita ta haifi yaya Imran sai ta ce bata son ganina a fitar da nine? To ni dama waye ya ce ma ta so ni? Ni ma ai ba sonta nake yi ba, kuma ba zan zauna ma a gidan nan ba, dan daddy ya taɓa gaya mani she is wicked". Sosai Hjy Batula ta buge mata baki da ɗan karfi, kuka ta saka masu, har da birgima a kasa, taɓe maki Ammie ta yi tana ganin ikon Allah, wai wannan mahaukaciyar ce matar ɗan ta? Ta tambayi kanta da kanta. Ita kuwa Aunty a cikin zuciyarta tana jin da ace Mummy Abla ta kyaleta, bata daketa ba, yanzu ga shi ta sake kwaɓe masu komai. Tsawa Ammie ta daka masu akan su fice mata daga gida tun ransu bai ɓace ba. Waya Hjy Batula ta ciro wayarta ta kira Abbi dan ta sanar da shi abin da yake faruwa, bugu ɗaya ya ɗauki kiran, ba ɓata lokaci ta sanar da shi ga abin da jellyn ta yi, ita kuma Ammie ga reply da ta bata akan ba zata karɓi jelly ɗin ba. Shiru Abbi ya ɗan yi kafin ya yi magana kasa kasa dan kar daddyn Jelly ya ji, yasan hakinsa sarai idan ya ji zai ɓata rai ya ce an wulaƙanta mashi ƴa, hakan yasa ya yi magana kasa kasa dan zaman lafiya yake so ba faɗa ba, umarni ya yi masu a kan su dawo da jelly ɗin gida, idan suka dawo daga Katsina za su kira Imran, sai su san abin yi. To ta amsa da shi, ta yi wa Ammie sallama tare da riƙo hannun jellyn ta miƙar da ita suka nufi waje, wani irin matsiyacin kallon banza Ammie ta bisu da shi, sai da suka ƙurewa ganinta ta koma saman sofa ta zauna tare da ɗauko wayarta. Number Imran ɗin ta fara laluɓa dan ta kirashi, ta bashi umarnin akan idan ma ya auri jelly to ya saketa ko ta tsine mashi albarka, sai dai kash a kashe ta sami number, ta ji babu daɗi sosai, saman sofa ta ɗaura wayar ta cigaba da kallonta. Su kuma bayan sun je mota, sosai Hjy Batula ta yi wa Jelly faɗa tare da nasiha, ta kara mata da cewa, in dai bata girmama Ammie ba, to tabbas yaya Imran ba zai taɓa sonta ba, zai dai'na kulata, zai yi watsi da ita, domin yana Kaunar mahaifiyarsa shi ma, shiru ta yi tana sauraron Hjy Batula tamkar wata mumina, yadda kasan an mata sauƙar karatun Al Qur'ani mai girma a kanta, tsit ta yi, sai da mummy Abla ta gama nasihar, ta tada mota dan su tafi. Suna kama hanya ita kuma Aunty ta ɗaura nata nasihar, dan jelly sai an bita a hankali, ta karfi ba zata taɓa yi wu wa ba, idan ka zare mata ido, ita ma zare maka zata yi, bata da tsoro ko kaɗan, ga uban rashin kunya tamkar a kanta a sauƙe shi. Kai tsaye gida suka koma da ita, tun Hjy Batula bata gama kashe motar ba, jelly ta fito ta wuce ciki abinta, da ido kawai Hjy Batula ta bita da shi, tana mugun tausayawa Imran, gaskiya daddyn Jelly ya yi kuskure, ya biye wa sanyata farinciki ya koya mata ɗabiar da barin shi yanzu ba karamin abu bane, ya biye mata komai take yi baya yi mata faɗa, kawai dan ta yi farinciki, to ga shi dai karshe abin da ya haifar masu, bata ganin kowa da girma sai shi daddyn nata da kuma Imran, shi ma Imran ya ci albarkacin son da take yi mashi ne yasa take ɗan girmama shi, daba dan haka ba, shi ma da a sahun marenan wayonta zata sanya shi. TAB AIKUWA AKWAI GYARA BA KAƊAN BA. GIDAN ABBA💋 Kwance take a saman gatonta bayan ta gama cin abicnin dare ta yi sallar isha kenan, ba abin da take jira face kiran sahibinta, abun begenta, farincikinta, ta lula can duniyar tunanin masoyin nata, sanye take da kayan barci a jikinta, doguwar riga ce launin pink color, ta sanya hular rigar a kanta, ƴan kwana biyun nan da tana samin kwanciyar hankali, har wani ƴar kiba ta yi. Karan ringing na wayarta ne ya daki dodan kunnenta, hakan kuma ya yi sanadiyar dawowarta daga duniyar tunanin sahibin nata da ta faɗa, cikin sauri ta duba kiran, abin mamaki kuma abin al'ajabi kiran Irfan ne yau kuma ya shigo wayar tata, sai kuma a lokacin ne ma ta iya tunawa da wani abu wai sun taɓa yin soyayya da Irfan, nan take ta ji jikinta ya mutu, wani irin rashin daɗi ta ji. Jikinta a sake duk ya mutu, haka ta ɗauki kiran nashi. "Yaya Irfan barka da dare". Dogon numfashi bawan Allah ya ja, tare kuma da sauƙewa a hankali. "Heartbeat ina kika shiga ne? Meyasami wayarki? Nazo gida ban same ki ba". Yadda yake maganar kamar zai yi kuka, abin gwanin ban tausayi, bata san lokacin da hawaye suka fara bin kuncinta ba. "Kayi hakuri yaya Irfan ka ji?" Shi ne kawai abin da ta iya furtawa. "Bakomai Heartbeat ba dai kina nan lafiya ba?" "E ina nan lafiya fatan kai ma kana cikin ƙoƙarin lafiya?". Nisawa ya yi tare da suake ajiyar zuciya "Heartbeat bana cikin ƙoshin lafiya, ji nake yi kamar zuciyata zata fashe ta fito waje a kwana biyun nan da ban jiki ba, please kada ki sake yi mani hakan kin ji ko?". Hawaye take yi sosai, shin me yake shirin faruwa ne, kenan har yanzu Akila bata san soyayyar gaskiya ba, har yanzu ba zata iya tantance wadda take so da gaske da kuma wadda take so dan wani abu ba? To fa akwai gagarumar matsala wlh. "Heartbeat ya na ji kin yi shiru?" "Kayi hakuri yaya Irfan". "Heartbeat me ya faru kike kuka kuma, subhanallahi dan Allah ki dai'na Kinji? Idan baki dai'na ba zuciyata zata yi mani ciwo". Hannu tasa tana goge hawayen nata. "Kada zuciyarka ta yi ciwo yaya Irfan, wlh na dai'na, ka gani na goge hawayen". "Good my heartbeat, to yanzu dai gaya mani menene ya sanyaki kuka ƴar kanwar?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Kai ne ka sanya ni kuka mana" "Subhanallah ni kuma Heartbeat?" Gyaɗa mashi kai tayi tamkar tana a gabansa. "Ni kuma laifin ne nayi da na sanya matata hawaye? Yau wace iriyar ranan bakin cikice a gareni da na sanya matata kuka da kaina? Duk da ban san laifin da na yi ba, ina rokon da ki yi mani afuwa kin ji matar mijinta?". Turo ɗan bakin nan nata ta yi. "Ni yaya Irfan ka dai'na magana ka yi shiru na ƴan mintoci tukun nan". Shirun ya yi ya biye mata, dama haka take yi wa masoyin ɓoye wani lokaci, sai ta ce mashi ya yi shiru na minti goma, haka zai yi ta zama shiru yana sauraron sauƙar numfashinta, ta koyo hakan ne kuma daga wajen jelly, jelly ce mai wannan sabon iskancin tun tana yarinya, lokacin da suka je Kano, haka jelly take sanya daddy ya rufe bakinsa, ba yadda ya iya haka yake yin shiru har sai ta ce to lokacin magana ya yi, sai ya fara magana, to shi ne ita ma Akila ta koya, sai ta rinƙa cewa Heartbeat nata ya yi shiru kaɗan, yanzu kuma ga shi ta yi wa Irfan, shima ya ɗana. Shiru ya yi ta zama har tsawon lokacin da ta ɗeba mashi, kafin ya yi magana, a lokacin kuma ta gama tikar kukanta ta share hawaye. Cigaba da hira suka yi, sun biya bashin tsawon kwanaki da suka ɗauka basa waya, sai misalin karfe 10 ta ce mashi tana jin barci, ba dan yaso ba suka yi sallama bayan ya yi kissing na wayar yana faɗin zai yi kewarta, ita ma kissing na wayar ta yi tana mai kara tabbatar mashi a yanzu ma har ta fara kewarsa, da haka suka yi sallama ba dan sun so ba. Saman bedside drawer ta ɗaura wayar, sai kuma me? Sabon kuka ta rushe da shi, ita kanta ta bata san dalilin yin kukan nata ba, tamkar wata karamar yarinya haka take tiƙa wannan kuka, while ita kuma Ammie tana can tana cika tana batsewa, ta tasa Abba a gaba a kan lallai sai ya nemo mata Imran a daren nan, duk in da ya shiga, maza Abba ya nemo shi, a cikin daren nan zai rabu da jelly dan uwarsa, mamaki Abba yake yi, kullun idan zata zagesu sai dai ta ce Uwarsu ba dan ubansu ba, Ammie duniya mai zaman kanta. Har karfe shaɗaya ta buga Akila na kuka, kuka kuma da bashi da dalili. Sai misalin karfe shaɗaya da rabi sannan wadda nake da tabbacin saboda shi take yin wannan kukan ya kirata. Ƙin ɗaukar kiran ta yi, tamkar ya yi mata wani laifin, ashe dai yasan me ya aikata, dan haka sai shi da kansa ya yi received call ɗin, da kansa kuma ya sarrafa wayar tata, ya kara Volume yadda zata ji shi sosai. "Am so so sorryyyyyyyyyy my heartbeat, ba zan sake ba, dan Allah ki yi shiru Kinji?" Cigaba da kukanta ta yi tamkar bata ji me ya ce ba. "Wayyo matata, please amin afuwa, dan Allah ki yi shiru, wlh ba zan sake ba, zan iya jurar komai amma ban da hawayenki". "Meyasa tun ɗazun baka kirani ba?" Ta faɗa can kasa kasa cikin muryar kuka. "Kiyi hakuri zafin kishi ne yasa ban kiraki ba, na barine sai zuciyata ta ɗan sauƙa, amma na tuba ba zan sake ba, kuma fa heartbeat harda kissing na wayar ke ma kika yi ko? Amma ba komai yanzu dai daina kukan, shi ne babban abin da ya fi damuna". Turo baki ta yi kamar biro, kasa kasa take kunkuni ta yadda ba zai ji ba, tamkar wata ƴar baby, irin idan aka daki yarinya ta gama kukan nan, irin wannan kunkuni da suke kasa kasa da ƴan surutai, shi ita ma take yi. Hakan yasa ya saki cool murmushi. "My Heartbeat sarkin rigima, to ko dai sai nazo na goyaki ne?". Lumshe idanu ta yi tana murmushi tare da rufe fuskarta ga hawaye a fuska. "My heartbeat yau kuma ni ake jin kunya?". Gyaɗa mashi kai kawai ta yi alamar e. "To shikenan ki cigaba da jin kunya ni bani da wata damu, abin da na sani dai shi ne, a ranar da muka yi aure, a ranar zan cire maki kunyar tas na watsar, yanzu dai duk ba ma wannan ba kin ci abinci?". "E naci kai fa ka ci ne?" "A'a My Heartbeat, ni ban ci ba, kuma ba zan iya ciba har sai naji voice naki, yanzu zan ɗauko muci tare, kina bani a baki". Kayatatcen murmushi ne ya bayyana a kan fuskarta, ba komai ne kuma ya haifar mata da murmushin nan ba face yadda ya yi maganar, tamkar wani ɗan yaro, ya iya shagwaɓa sosai da sosai. "My Heartbeat Murmushi yana yi maki bala'in kyau". "To dan Allah nima ina son ganin Murmushinka ka ji Heartbeat ɗina?". A shagwaɓe ta yi maganar. "My heartbeat na yi maki alkawarin zaki ganni, yau ba alhamis ba?" E ta amsa mashi da shi. "To ranar Wednesday zan kawo maki kaina har gida domin ki ganni da kyau, ki kare mani kallo son ranki, ki ɗaukeni videos, ki yi mani hoto, ki ji murya, kiyi yadda kikeso dani gabaɗaya, amma kuma da sharaɗi!". "Sharaɗin ne?" Ta faɗa cikin zumuɗi. "Idan nazo gida, ko a gaban waye zan gaya maki ina son ki, sharaɗin shi ne ba zaki gudu cikin gida ba, zaki tsaya mu kalli juna cikin ido, ki zuba mani shagwaɓa, ki yi alkawarin yin hakan, idan ki ka yi alkawarin yin haka, to nima zan yi alkawarin tabbas zanzo". "Nayi, ba dai alkawari ba? To nayi maka, tabbas ba zan gudu ba, zan tsaya mu sha hira ". Ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce "Ina nan zuwa my Heartbeat, nima ai nafi son ganinki fuska da fuska, hakan zai fi, yanzu dai tsarabar me kike so na kawo maki?". "To ai baka gaya mani kasar da kake ba bare na san me da me ne a kasarku har nace ka kawo Mani". "Heartbeat kasarmu ɗaya, a Nigeria nake ai". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Tom tsarabar goriba zaka kawo Mani ". To ya amsa mata da shi. Mamaki ne ya kamata, wai har da wani cewa to, shi kuma bai kawo komai a ransa ba, ita kuma ta dage shi ba ɗan Nigeria ba ne, shiyasa ta yi mashi wayo dan ya gaya mata kasarsa ta hanyar cewa da ta yi bata san kasarsa ba, bare ta san tsarabar me zai kawo mata, amma ya ce a Naija yake, ta ce goriba ya ce mata to, anya kuwa da gaske yake yi? Anya ya san wannan goriba kuwa? Amma dai zata gani ai, ba dai ranar laraba ya ce ba, to shikenan ai. Ta nutsa duniyar tunanin can ta tsingayo zazzakar muryarsa kasa kasa yana faɗin "My heartbeat ki zo na baki abinci a baki kin ji ko?". "Ka bari sai ranar Wednesday idan kazo sai ka bani a baki ɗin". "Are you serious?" Tabbatar mashi da hakan ta yi, sosai ya ji daɗi kamar me, suna hira yana cin abinci a nutse, sai wuraren karfe 2 na dare suka yi sallama cike da kewa da kuma masifar kaunar juna, ba dan sun so rabuwa ba, dare ne kawai ya yi, daren ma dan ita yake tausayawa yasa ya hakura, baya son ta kasa tashi tayi sallar asuba. GIDAN LION💋 Dare misalin karfe 8, Rimsha, Imran, da kuma Areef, suna zaune a palon sama, Areef dai Alhamdulilah jiki ya yi kyau sosai da sosai, waƴan nan shaiɗanun matsafa sun sake shi da karfin ikon Allah, amma anci kwakwa fa, Lion ya sha baƙar wahala ba kaɗan ba, su TGA sun yi nasarar tarwatsa kunjiyar tsafinsu Josephine ɗin, sai dai sun rasa sojoji da dama, ciki kuma harda babban yaron TGA, shi ma TGA ɗin ya ji ciwo sosai a kefen cikinsa, yanzu haka yana gadon asibiti. To sai dai muche Alhadulillah, an gama da shegun matsafa, yanzu Josephine da Areef sun fita daga koma. Sai hira suke yi cike da kula, da kuma girmama juna, massage Lion ya yi wa Imran akan RIMSHA ta kai mashi abinci, da alama yau ya ji yunwa sosai, bawan Allah yau yasha wahala sosai gaskiya, kawai mutun ba zai taɓa gane hakan a kan face nashi or a yanayinsa bane, domin kuwa kullum a siffa ɗaya yake idan baku mance ba, amma yau saboda waƴan nan ƴan iska matsafa na jikin Areef ya sha wahala over, dan sai da ya yi wa Areef ɗin dannar yankar rago kafin ya samu ya fara yi mashi addua'o'i da karatun Alqur'ani mai girma, ba ƙaramin dambe suka sha ba, Imran kam guduwa ya yi tun da Areef ya maka shi da kasa sau ɗaya, ita kuma Rimsha tana ɗaki tana sallah tana kuka tana riƙon Allah da ya bawa Areef ɗin lafiya. Yanzu dan ance ta kai mashi abin bata damu ba, dan tana ganin ɗazun sun wanye lafiya, a shirmenta wai ta fara gane me Saif yake so, yarinya yarinya ce, har izu yau TRIPLETS nasa ma sun kasa iya tantance abu guda ɗaya da yake so bayan kaunarsu, sai ita ce wai ta gano me yake so, to fa mu dai je zuwa. Miƙewa ta yi ta nufi kitchen, binta da kallo Imran ya yi, ciro wayarsa ya yi domin ya kira tailor da ya bawa ɗin kin kayansu, ya ga ji da kallonta da shigar riga da wando, yana tsoron abin da zai je ya dawo, baya son su yi aikin danasani. Tabbatar mashi tailor ya yi akan tabbas rana ita yau azo a karɓi kayan, to ya amsa da shi kafin su yi sallama, ajiye waya ya yi suka cigaba da hira da Areef. A cikin zuciyarta ta yi sallama a bakin kofar kitchen ɗin, annabi ya ce katabbatar da kana yin sallama ne a in da aka san darajar sallama, a in da ake amsata, kada ka yi sallama a in da za'a walakanta sallamar, to shi Mark ai bai san darajar Sallama ba, kuma ba amsata zai yi ba, shiyasa take yi a cikin zuciya, karisawa cikin kitchen ɗin ta yi, sannu ta yi mashi, tamkar babu shi a cikin kitchen, kamar dai yadda suka saba, bai ɗago kai daga abin da yake yi ya kalleta ba, haka zalika, bai amsa sannun da ta yi mashi ba, kamar wani mai aljanu, ɗazun ya yi mata magana da bai taɓa yi ba, yanzu kuma ta yi mashi yaki amsawa, to Allah ya shirye shi. Wucewa ta yi ta wanke hannunta kafin ta ɗauki abin nasa, har lokacin tamkar babu Mark a cikin kitchen ɗin nan, ficewa ta yi abinta, sanye take da wandon jeans baki ya kamata da ga sama har kasa, jikin wandon akwai kyalli sosai farare a jiki, sai ta sama kuma, top mai dogon hannu ta sanya, launin maroon color, ba karamin kyau ta yi ba, kamar kullun hijabin ɗan karami mai taken please call me ne a jikinta, bakin hijabi ne kalar wandon, kafarta na sanye da takalma flat shoe Maroon color, sai tashin kamshi nata perfume ɗin take yi. Sallama ta yi mashi a bakin kofar ɗakin, yana zaune saman sofa set yana latsa wayarsa, jin ya yi shiru ne yasa ta kutsa kai cikin, tana mai kara kwaɗa wani sallamar. A wannan karon ma saura kaɗan ta saki tray ɗin abincin saboda razana da kallonsa da ta yi, sai dai Allah yasa ta riƙe abincin da kyau sosai, hakan yasa bai ɓare ba. Sanye yake da kayan barci, wando dogo har kasa, sai riga mai guntun hannu, damatsan hannunsa suka firgitata, domin gajartar hannun rigar ta bayyanar da su a waje, kamar dai kullun kunsan yana tashin wannan fitinannen kamshin nasa, da alama yau barci yake ji da wuri, Shiyasa ya buƙaci abicnin da wuri haka, ga alamar hakan ka a face nasa, sai lumshe idanu yake yi, gashin kansa a kwance, ta zubo mashi a fuska kasancewar ya sunkuyar da kai a kan wayarsa. A in da ta saba ajiye mashi abin cin, a nan ta ajiye mashi, saboda neman magana irin nata har da wani ce mashi good evening, ai ko tamkar babu shi a cikin ɗakin bai amsa ba. Ganin hakan yasa kawai ta fara zuba mashi abinci, sai da ta zuba rabi ya sauƙo daga saman sofar ya dawo wajen da yake zama dan cin abincin, ya zauna, abin da ya bata mamaki shi ne kafin ya zauna sai da ya yi bismillahi, tana jiyoshi ya yi kasa kasa, kenan hakan ya nuna duk wasu dokoki da wasu abubuwa da suka danganci addin dan korar shaiɗan a kusa da mutun kenan yana yi, kuma yasan su fa, amma meyasa baya amsa sallama na? Ta tambayi kanta, abin da bata sani ba shi ne, kamar yadda ya yi wannan bismillahi yanzu, to fa haka yake amsa mata sallamarta, sai dai maganar tasa ce idan ba'a kusa da shi sosai kake ba, ba ji zaka yi ba. Bayan ta gama zuba mashi ta tura mashi abincin a gabansa, ba ɓata lokaci ya ɗauki spoon ya fara cin abincin nasu, wani irin kalar green ne abinci, ita ko kallon abincin ma bata son yi, sai mamaki take yi, abin cin wani gubar wani, su kuma nata abincin ne suke jin ko da me sun yafe cin shi. Spoon ɗaya ya kai bakinsa, da kyar ya haɗiye abinci, kawai ma dan baya son dawo da ita ne yasa ya haɗiye da kyar ɗin, ta lura da hakan, da mamaki take satar kallon shi, ko me ya faru da abincin Oho. Ajiye spoon ɗin ya yi tare da ɗaukar wayarsa, kasa ya yi da kansa yana latsawa, zuba mashi idanu kawai ta yi tana kallon yadda ya kara ɗaure fuska sosai, dama yaya lafiyar kura bare kuma ta yi zawo, tabbas akwai abin da ya faru da abincin, wannan irin uban ɗaure fuska da ya yi haka ba'a banza ba. Nan take wani irin tsoron shi ya dira mata a ranta, ji take yi tamkar ta tashi ta gudu, dan ganin ya kara ɗaure fuskar, suna a haka Mark ya shigo ɗakin ya same su, hannunsa rike da bowl mai ɗan girma, gabansa ya zo ya ajiye bowl, ba tare da ya yi magana ba ya juya ya koma wajen hukuncin da aka yanke mashi yanzu, shi mai girkin ma first. Da mamaki take kallon pepper dake cikin bowl ɗin, an wankesu da kyau, ga su fresh, ta rasa me hakan yake nufi, me kuma za'ayi da su. Miƙewa ya yi, ya koma saman sofa ya zauna, gently ya ce ta cinye attarugun nan dukka, zaro idanu waje ta yi, yau ta shiga uku laifin me tayi? Ta tambayi kanta da kanta, abin da bata sani ba shi ne, abinci da ta kawo mashi, yau Mark ya yi kuskuren da bai taɓa yi ba, yaji ta kubce a cikin abinci, shi kuma Lion kwata kwata baya cin yaji, komai kankantar ta saboda gym da yake yi, idan har ya ci yaji takan iya yi mashi mummunar illar a jiki, kuma tun kafin ya fara gym ma, shi baya haɗa hanya da yaji, ba'a taɓa yi mashi girki da ya ji ba sai yau, Mark ya yi kuskure, kuma yau kamar ba lafiya ba, sai bai ɗan ɗana abincin ba, haka ya shiryawa ogan nasa, to ita laifin kawowa kawai ta yi shi ne a kace ta ci attarugun, shi kuma Mark na shi hukuncin wa iya zubillah kwakwalwa ba zata ɗauka ba, kuma babban abin haushin shi ne ma zai hukunta kansa, idan kuma ya yi ɗaya ba daidai ba yasan halin ogan nasa, bai ma isa ya tsallake ba. BABBAR MAGANA MAI GIRKA ABINCI DABAN WAƳAN DA HUKUNCI KE SHAFA SU MA DABAN, KENAN KO MAI KANKANTAR SA HANNUN DA MUTUN YAKE DA SHI A WAJEN YI WA LION KUSKURE YA SHIGA UKU TAB ƊI JAM!!!. Hawaye ta fara yi tare da fara ɗaukar attarugun tana kai wa bakinta, har ga Allah ita ma ba ma abociya cin yaji bane, bata ci ko kaɗan a baya, ɗan zamanta a gidansu Kausar ne ma ta ɗan koyi cin yajin, kunsan Yarabawa da shegen son yaji kamar me, to a nan ta ɗan koya, amma a gida wajen mummynta, bata ci, mummy ma bata ci ne yasa bata sanya masu a cikin abincin, yau ta ga tashin hankali iya ganin idon ta. Kwara ɗaya ta ci harshenta ya ɗaye ya yi jawur kamar wuta, kai gaskiya punishment ɗin soja Bala'i ne, shi saboda sun wahala wajen horo, sai ya rinƙa ganin kamar kowa ma irin sane, sai ya rinƙa ganin kamar komai ya yi wa fararen kaya daidai ne, saboda shi already ya hororu, abin da bata sani ba, duk abin da kake yi, zakaga kowa ma tamkar haka take yi, walau mai kyau walau mara kyau, shiyasa idan sojoji suna hukunta mutun, zaka samu hukuncin na da bala'in tsauri fiye da tunanin mai tunani, su kuma normal ne a wajensu. Tana hawaye ta ɗauko na biyu, ga shi har guda goma ne a cikin bowl ɗin, alama ya yi mata da hannunsa ba tare da ya kalleta ba, akan ta ɗebo ruwan tea nasu mai jafi ta rinƙa korawa da shi, TASHIN SENSE bala'i kan bala'i kenan, zafi kan zafi, ruwan zafi haɗe da attarugu, eyya i pity you RIMSHA, Lion ya kware wajen horarwar mugunta, ba kalar da bai iya ba, attarugun ita kaɗan ta ma yaya bare kuma da ruwan zafi, ya ilahi ya lillahi.........😭 Haka ta ɗebo ruwan tea ɗin, ga shi ya haɗu mata da bata son green tea ɗin nan nasu, wlh yarinyar nan ta yi kuka ne har idanunta suka kumbura, shi kuwa tamkar babu shi a cikin ɗakin, Areef Imran suna Palo, kuma shi Areef ya san me yake faru, abin da yasa bai tinkari Lion ɗin ba, yasan idan ya je ba ƙaramin faɗa za su yi ba, saboda Lion ɗin yana jin yunwa sosai, yana son cin abinci ya yi barci saboda ya gaji, sun ɓata mashi rai sosai, a yadda yake nan babu uban da ya isa ya kwaci Rimsha da Mark a hannunsa har sai sun lashe hukuncin nan tas, to yasan idan ya je fa ba ƙaramin faɗa za su yi ba yau, to wai ita Rimsha me laifinta ne? Dan kawai ta kai mashi abin? Ita ta girka ne? Ita da kitchen ɗin ma bata shiga har sai idan zata je ɗaukar abinci, amma saboda bakar zuciya na fitar hankali shi ne har da haɗawa da ita. Allah sarki duk wanda ya kalleta a halin da take ciki sai ya matsa mata kwallah, lips nata sun tashi daga pink sun yi jawur tamkar nasa lips ɗin, kamar ta sanya masu jan lips stick, sai hawaye take yi, ta kasa sakin kuka mai sauti saboda kada ya ji, idan ya ji zai kara mata wani hukuncin, baiwar Allah idanunta sun yi hawur sun yi luhu luhu. Haka ta cinye attarugun nan tas, hawayene majina ne duk sun haɗe mata waje guda, da dama ma ina ga hawayen jini zata yi. Hijabinta ta kamo bayan ta gama cinyewa, ta shiga goge hawayen nata tare da majinar tana mai dana sanin zuwanta gidan nan ma baki ɗaya, wani irin azababben ciwo kirji ne ya dira mata lokaci guda, ga attarugun da shegen bala'in zafi, ga su manya ba halin ta haɗiye bata tauna ba, dole haka ta taunesu. Duk abin da take yi yana same da ita, sai dai kawai shi ya fi karfi ya ɗaga ido ya kalleta ne a nasa cewar, har yau bai san kamannin fuskarta ba, ɗazun da ya juyo ne ma da tana kallon shi to za su iya yin ido huɗu, dan ita ya fuskanta, amma kuma ta yi kasa sosai da kanta, lokacin da ta yi mashi ɓari da rana kenan, hakan yasa bai ma ga face nata ba ya wuce dressing room, so bai san kalar face na ta ba, amma kuma tabbas ya riƙe wadda ta kira shi da sunan GAR a gidansu Imran a lokacin da ya zo, kuma e lallai yana son sani wace ce wannan, sai dai kuma bai tambayi Imran ba, dan gani yake shirme ne, kuma a haka maganar ta tsaya mashi a rai, abin ne da mamaki yadda ta gane ainahin face na shi ba tare da face mask ba, da yanzu Rimsha zata maimaita wannan suna na GAR to tabbas zai gane ita ɗin ce, abin da yasa yanzu bai gane muryarta ba saboda a ranar yadda ta kira sunan GRA daban da yadda take magana, har wani lankwatsa ta yi wa sunan kamar a bakinta a ka halinci sunan nan ranar, so ita ce magana ɗaya da ta tsaya mashi a ransa tun da ya zo Nigeria, yana ganin shirme ne yasa bai tambayi Imran ba, amma ya kasa mancewa da shirmen kuma. TO FA......🤔 Umarni ya sake yi mata akan ta cinye abincin da ta zuba mashi a cikin plate ɗin, idan ta gama ta kwashi kayan abincin ta fitar mashi a ɗaki, ba musu ta fara cin abincin, tasan baya magana biyu, tana ci harshenta tamkar zai ɗaye saboda azabar zafi, ya yi wani jawur da shi kamar jini, azaban balai take yi mata, lips nata ma suka yi ja bare kuma harshe. Allah ya rufa mata asiri ba dayawa sosai ta zuba mashi abincin ba, hakan yasa ta cinye da wuri, kwashe kayan abincin ta yi tare da nufar waje, har lokacin idanunta na zubar da kwallah sun ki tsayawa. A palo ta isko su Imran kamar yadda ta tafi ta barsu, taki kallon in da suke bare su fahimci wani abin, shi kam Areef da ya san komai dan ya tambayi Mark da taren Spanish dan kada Imran ya ji, zuba mata idanu ya yi yana kallonta cike da tausayawa, Imran kuwa bai wani damu da ya kalleta ba, yana latsa waya, kafin ya ɗago kuma ta wuce izuwa palon kasa. Babu kowa a kitchen ɗin, ga wani abinci kuma an ɗaura a saman wuta, ajiye kayan abincin ta yi, ta nufi fridge, a hanzarce ta fara dubawa ko zata sami Madara ta ruwa, ta ko yi Sa'a akwai, sauri sauri ta ɗauko kwara ɗaya, ga sanyi madarar, ta fasa tare da kafawa a ɗan bakinta ta fara kwankwaɗa, azaba tai azaba, bata san time da ta sha kwankwani biyu ba, jin motsin mutun ne yasa ta farga ma ashe gwangwani biyu ta sha. Mark ne ya shigo cikin kitchen ɗin dan duba girkin da yake yi, idanun nan nasa sun yi jawur, da alama ya sha bakar azaba, kuma shi ma da alama ya ci attarugu over, lips nasa duk da suke jawur yau sun kara ja over, har wani kumbura suka yi, ko kallon in da take bai yi ba, ya wuce gaban gas, mamaki take yi, a ranta tana faɗin "Punishment da zai sanya wannan jibgegen Bature sojan idanunsa su yi ja haka ba karamin abu bane, lallai tabbas Lion ya kware wajen mugunta, fata ɗaya kawai mutun zai, shi ne kada Allah ya haɗa shi da mummunar rana ta haɗuwa da hukuncin Lion, Allah ya rinƙa haɗa shi da ɗayar fuskar Lion ɗin, wato ta adalci ba ta mugunta ba". To amin dai kam, idan ba haka ba, fuskar muguntan Lion ai ko makiyi ba zaka yi mashi wannan mummunar fata ta haɗuwa da face ɗin ba. Goge hawayenta ta yi tare da wucewa ta fice daga kitchen ɗin, yau dai bata yi amai ba da ta ci abincin nasu, azababben raɗaɗin da harshenta yake yi mata ma, ai ya mantar da ita ta ci wani abu wai abinsu. Bata bi ta kansu Imran ba, bedroom nata ta wuce, sauri sauri ta shige toilet, fuskarta ta fara wankewa fes, ta fito tare da canza kayan jikinta zuwa goguwar rigar Abaya launin Navy blue, ta yafo mayafin abayar a kanta, ta nufi Palo. Still a in da ta barsu, a nan ta dawo ta same su, kusa da Imran ta zauna. Ɗan juyowa ya yi ya kalleta. "My first lady yau baki jin barci ne?" Shi ne abin da ya faɗa cikin harshen Hausa, ɗan kwantowa ta ɗan yi a kafaɗarsa, a shagwaɓe ta ce "Yaya Imran dan Allah yaushe zamu je gidan Bappa, wlh tun da naji daddy ya ce su Umaisha ƴan uwana ne ina matukar kaunar ganinsu, dan Allah ka kaina na ga ƴan uwana". Shiru ya yi yana tunani, yanzu ai ko uban Rimsha bai isa ya yi iko da ita ba, yanzu Lion ne sabon uban ta.....🤣 Shi maganar da ta yi ma ta tuna mashi da son tambayar Abbansa da yake yi akan me ya haɗa su faɗa da bappa Hosain, tun da dai sun ce shi bappa Hosain ɗin nasu faɗar daban ne dana su daddyn Jelly, ma'ana shi Daddyn Rimsha tun iyayensu na raye ya yi fushi ya bar gidan, su daddyn jelly kuma, sai bayan auren Abba da Hjy Umaiya, har ma an haifi Imran, sannan suka sami gagarumin matsala a tsakaninsu, amma fa kafin auren Hjy Umaiya ɗin ma akwai wata tangarɗa da suka samu na kin auren, abun dai ya haɗu ne kashi kashi sai ya tadda gaba guda ɗaya. "Yaya Imran ka yi magana mana? Yaushe zaka kai Ni? Wlh ina bala'i kewar Aunty AKILA". Nishawa ya yi tare da sauƙe ajiyar zuciya. "Rimsha gobe zan kawo maki Akila gidan nan ku wuni, ita ma Umaisha zan samu lokaci na ɗauko maki ita, amma fita kam kema kinsan ba zai taɓa yiwu ba, yanzu kin zama sarauniya sai dai a kawo maki duk wanda ki ke da bukatar gani". Narai narai ta yi da ido kamar zata yi kuka, shi dai Areef ya zuba masu idanu ne kawai tun da ba jin me suke faɗe yake yi ba, baya jin Hausa ko kaɗan, sai dai kawai ya yi ta binsu da idanu yana murmushi. "Yaya Imran ya batun zuwa school fa?" Shafa kanta ya yi. "My Rimsha, na gaya maki babu uban da ya isa ya fitar dake daga cikin gidan nan sai idan shi ya bada dama, fitar ki ba zai yi wu ba har sai ya bar Naija, sun kusa komawa ai, na ji jiya yana magana da daddynsu akan maybe next week su shigo Usa ɗin, amma kafin ya koma ma, idan ya sauƙo yana iya barinki ki koma school, abin da nake so dake yanzu shi ne, ki natsu, ki natsu sosai, ki daina rawan kai, ki daina yi mashi laifi, wlh dannewa yake yi, idan kika bari Saif ya yi maki koda bari ɗaya ne, ina mai tabbatar maki sai kin kurmance, to dan haka ki kara natsuwa, ki bi komai a sannu dan ku rabu lafiya, idan ba haka ba kuma, wlh ina mai tabbatar maki zai iya tafiya dake kasarsu ki je kina yi mashi aiki, kuma babu wanda ya isa ya tinkare shi bare ma har ya yi gigin yi mashi maganar ya yi hakuri ya kyale ki, ko daddynki bai isa ba, idan kuka ce kun shigar da shi kara court, to fa court ɗin gabaɗaya ma zai iya ɗaukowa ya kawo maku gida, dan ku ji daɗin shari'ar da kyau, shiyasa kika ga daddynki bai ja da shi ba, saboda bashi da dukiya da kuma power iya ja da shi, to muda gabaɗaya kasarmu ma take a karkashin su, sufa suke juya mu, kinga kuwa ba mu isa ja da shi ba, to kawai shawarar da zan baki, ki natsu ki bi Saif a hankali ku rabu lafiya, Allah ya rabaku lafiya, tun da ya kusa komawa Alhadulillah zamu ce". Ya kai karshen maganar yana shafa kanta. Shiru ta yi tana tunanin zalunci irin na Saif, mutun tamkar ba mutun ba? Kamar dutsene a jirjinsa, sai izzar bala'i, ka nuna isa a abin da take mallakinka har ma da wanda yake ba mallakin ka ba, wannan ai zalunci ne. Ganin ta yi shiru ne yasa Areef ya ce "What are you thinking my sister? What prof told you that make you angry like this?". Kai kallonta kanshi ta yi, tare da ƙaƙalo murmushi dole tana girgiza mashi kai alamar babu komai, da hannu ya yi mata alama akan ta zo, ba musu ta miƙe ta koma kusa da shi ta zauna. Hannayenta ya riƙe a cikin nasa, cikin zolaya ya yi magana da harshen tunaranci. "What lion did to you ya sa ki angry haka?". "Yaya Areef ni ai yaya Saif bai yi mani komai ba, kawai barci nake ji ne". Dawo da kallonsa kan Imran ya yi. "Prof ka koya mani wannan yaren naku, dan gaskiya ba zan yarda ba, kuna cutata da yawa, how zaku yi magana ban ji me kuka ce ba, a maganar taku kuma ka sanya sister ta ta ɓata rai, na tambaya kuma all of you kuna gaya mani ba komai ko?". Dariya ta yi mashi tana mai buga hammar barci. "Serious Areef ba wani magana muka yi ba, ta ce mani ne tana son komawa school, shi ne na ce mata ta yi hakuri Saif ya kusa komawa, idan ya koma shikenan sai ta koma school ɗin". Girgiza kai ya yi, yana mai matukar tausayawa Rimsha, domin kuwa, Lion ba next week zai koma ba, wata aiki ma yake yi a Nigeria, aikin kuma ya shafi Musharraf and gwamnatin Nigeria, albarkacin farincikin da Musharraf yake sanya Aseef yasa Saif kwana biyu da suka wuce ya fara bincike akan tun ainahi menene ya faru da har yarabasu da family'nsa haka, menene ya raba kansu da har yake tunanin family'nsa sun rasu, mutumin kirki kamar haka. A ka'ida irin ta aikin Lion idan zai yi aiki baya tambayar abun da ya faru, dan yasan kowa kansa kawai ya sani, da wuya mutun ya faɗi gaskiyar komai da ya faru, bare ma kuma idan mutun ya yi laifi, to zai yi kokarin ɓoye laifin nasa ne ya bayyana na abokin faɗar nasa, hakan yasa ma baya tambaya, bincikensa kawai yake yi, da kansa yake gano gaskiyar ko wace ɓangaren, ya kuma yanke hukunci da ta dace da ko wace ɓangaren, ɗazun da yamma da suka zauna da Rimsha, ya so tambayarta went last ta rabu da su mummynta, sai kuma ya fasa, dan ya fuskanci kan Rimsha na rawa sosai, shi kuma baya son mutun haka, ba ya zama inuwa ɗaya da mutun mara natsuwa, idan bata gyara ba 1 day 1 time zai yi wurgi da ita waje kawai kowa ya huta. Shi Areef ɗin abin da ya sanya ya gane Saif ya fara bincike a kan case ɗin Musharraf ɗin, jiya ne da ya shiga bedroom ɗin na ɗan uwan nasa, a nan ne ya gani cikin laptop nasa, ya sha mamaki shi ne ya fara binciken tun yaushe Lion ɗin ya fara aikin, sai ya ga ma kwana ɗaya ne da ta wuce, ba wani jimawa bane, sai dai kuma Areef ya sa a ransa Lion zai barta ta cigaba da zuwa school, bari dai su samu ya ɗan sauƙo, idan baku manta ba, Lion yana son karatu, yana son yaga kowa yana karatu, baya son jama'a su zauna a cikin duhun jahilci, so da wuya idan zai hanata zuwa school. Shiru suka yi kowa da abin da yake tunani, suna a haka har Mark ya kammala girki, ya zo ya sanar da Areef ya gama girkin oga, bayan ya gaya masu kuma ya koma kan punishment da Lion ya bashi, yau kwana zai yi a waje, Allah sarki, shima bada son shi bane hakan ta faru, bai so ba, bai ma san ya akayi ya sanya yaji a abincin ba, tun da suke yau shekara almost 10 kenan suna tare, bai taɓa yin kuskure maka mancin haka ba, sai yau, amma Lion bai yi mashi afuwa ba, domin a tsarin Lion babu kuskure sai dai ganganci. TAB DA ALAMA AKWAI ABUBUWA DA DAMA DA ZA'A KAMA LION DA SHI, BAI YARDA AKWAI RAUNI A DUNIYA BA, HAKA BAI YARDA DA KUSKURE BA SAI DAI GANGANCI, BAYA SON YARA BARE SHI YA HAIHU, BAYA SON KALMAR SO, KAI SHI DUK WATA ABIN ARZIKI BAYA SO, A LALLAI DA AKWAI BABBAR RINA A KABA.......🤔 Rimsha dai bata so ba, amma haka ta miƙe ta nufi palon kasa, babu kowa a kitchen ɗin, wanke hannunta ta yi before ta ɗauki abincin. Kamar yadda ta saba, da sallama ta shigo cikin ɗakin, bawan Allah ya yi barci da yunwa, dama barci yake ji tun ɗazun, da alama kuma barcin ɗaukarsa ta yi ba tare da ya shirya ba, ga wayarsa a hannunsa da alama latsawa yake yi barcin ta zo. In da ta saba ajiye mashi abincin, a nan ta ajiye mashi, ta juya ta nufi hanyar fita. Har ta kai tsakiyar ɗakin sai kuma ta nuyo dan ta sake kallon shi, nan take ta ji zuciyarta na ingizata akan ta zo ta rufa mashi bargo ta kashe mashi wutar ɗakin, ta kuma zame wayar nan nasa da ya riƙe ta ajiye mashi a saman bedside drawer. Ai kuwa bata yi wata wata ba, ta tako izuwa gaban gadon, a hankali ta ja mashi wanan katon bargon nasa, da kyar ma ta iya jawo bargon ta rufa mashi zuwa jirjinsa, yau gata ga shi kuma yana barci, amma ta kasa kare mashi kallo, zuciyarta ta karaya, ba zata iya kallon shi ba, idan ta yi hakan kuma ta san zata yi ihu ne, zata firgita sosai, domin rikita mata kwakwalwar yake yi a duk san da ta kalle shi, wani irin kwarjini Allah ya yi mashi. Bayan ta rufa mashi bargon, a hankali ta duƙa a gabansa, har lokacin taki kallon shi, hannu tasa tana ƙoƙarin zame wayar nasa, kirjinta sai dukan uku uku yake yi. Wani irin Mahaukaciyar damka ya kaiwa wuyarta, idanunsa a lumshe bai buɗe su ba, bai kawo cewa ita ba ce, a cikin barci kawai ya ji tana zare wayar a hankali hankali daga hannunsa, shineyasa ya kai mata damƙa, sai kuma ya yi Sa'a ya capki siririn wuyar nan nata. Tsabar razana bata san time da ta kurma ihu ba, ai kuwa rige rige Imran da Areef suka yi wajen shigowa ɗakin, har lokacin bai saki wuyar tata ba, ganin hakan yasa Areef ya gane abin da ya faru, Rimsha bata san cewa Lion bashi da nauyin barci ko kaɗan ba, zai iya yana barci kuna hira a palo ma yana jinku sama sama, haka yake, baya da nauyin barci, kuma a yadda ta zo zame wayar tasa, ta yi mashi abu kamar ɓarawo, a hankali take zameta, wai dan kada ta tashe shi, shi kuma ya damketa, a yanzu dai ko bai buɗe idanunsa ba, ya san wuyar waye ya damƙa, tun lokacin ma da ya damka ɗin, ya ji wuyar ɗan siriri, bata ma kai kaurin singalalalin hannunsa wajen ɗaura agogo ba, tun da ya ji haka ta gane wuyar kanwar Imran ce, sai dai kuma bai sake ta ba, dan a ganin shi ta raina shi ne, a kan me zata ta taɓa mashi waya ko wani abu nashi, shiyasa ya kara shaƙe ta yana da ga kwance, idanu a rufe kamar mai barci, dama ga yunwa yana ji. Da sauri Areef ya kariso wajen, bawan Allah da yake yana cikin ciwo, sai ya kasa ɓanɓare hannun Lion ɗin daga wuyar tata, yasan idan ya sanya karfi sosai, wajen ciwonsa zata iya fara yin jini kuma, cikin sanyi murya ya ce "Saif! Saif mace ce fa, zaka kasheta, ba zata iya jurewa ba". Abin da ya sanya ya gaya mashi hakan kuma, Lion da bakinsa lokacin suna school, Aseef zai daki wata yarinya ya hana shi, bayan ya dakatar da shi ya ɗaura da cewa, ai duk mai dukan waƴan nan halittu ba namiji bane, "Idan har zata daki mace to da sauranka a mazantaka, kuma kai Aseef idan ka daki wannan abar ai ba zata saura ba, halittun da su da kansu ma suna tafiya suna faɗuwa saboda tsabar rashin quality, to ina ga kuma ka ɗaura hannu a jikinsu? Ai ka daki namiji, ka sanya namiji dakakken gwarzo kuka, shi ne ka cika namiji, amma waƴan nan halittu, ka sanya masu mahaukacin tsoron ka kawai, wadda ganinka kawai ma zai sanyasu suma". A lokacin da Lion ya yi wannan magana, yana ganinyar tashensa ne, ya ce yafi karfin ya daki mace, sai dai ya sanya kartin maza kuka, idan kuma kuka lura yana daga cikin abin da yasa yake dannewa baya dukan Rimsha, amma bata ji tana kure shi. Ko da Areef ya yi magana, bai zame hannunsa ba har sai da ya ji yana ƙoƙarin yin kisan kai, a cewarsa yarinyar tana kure iya ɗan hakurin da yake da shi ne, rawan kanta ya yi yawa, yana son saita ta da kyau. Yana saketa ta karisa zama a wajen tana ƙoƙarin sulalewa kasa ta kwanta, da sauri Imran ya kariso ya riƙe mata hannu tare da miƙar da ita suka nufi waje. Gefen gadon Areef ya zauna yana mai bin ɗan uwan nasa da kallo. "Saif idan ba damuwa, zan so ka rinƙa yi wa yarinyar nan uzuri, kaga karamar yarinya ce, kuma mace ce, ƙwaƙwalwarta karami ne, kasan ko kallonka ta yi wani mahaukacin razana take yi, idan ka ɗaura hannunka a jikinta wlh daga ranar ba zata sake moruwa ba". Shiru ya yi bai tanka ba, hannu Areef ɗin ya kai ya toshe mashi hanci da karfi yana faɗin "Har dani zaka yi wa walakancin ne?". Tsawon minti ɗaya yana riƙe da numfashinsa kafin ya sanya hannu ya damki hannun ɗan uwan nasa ya janyo shi da karfi, luuuuuuu Areef ya tafi sai saman kirjinansa, waro blue eyes nasa masu ɗauke da barci ya yi akan face ɗin ɗan uwan nasa, ido huɗu suka yi. Wani irin kallon Saif ya bi shi da shi kafin ya sake shi. "Tashi mashi a jiki" gently ya yi maganar. Kara hayewa jikin nasa Areef ya yi. "Karfi ya ɗaga ni in gani". Lumshe ido ya yi yana jin Bala'in kaunar ƴan uwan nasa. "Areef kana kure ni ko?". "Au haba dai? To shikenan ka ɗauki mataki!". "Okey zan ɗauka ai yanzu dai tashi mani a jiki ka zuba mani abinci, am felling hungry over". Ya yi maganar can kasan maƙoshinsa. "Nifa ba zan tashi ba, karfi ya tashe ni nace". Tamkar abin haɗin baki, suna a haka sai ga kiran Aseef bawan Allah. Da yake wayar tana a hannun Saif ɗin, sai ya kawota saitin face nasa, ganin Aseef ne yasa ya sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, shi ma dai Areef ajiyar zuciyar ya sauƙe, bayin Allah nan suna yi wa junansu wani irin mahaukacin kauna ne wadda baki ba zai iya faɗarta ba, duk ɓacin rai ɗin da ɗaya yake ciki, suna ganin juna zasu wastsake. Areef ne ya sanya hannu ya yi picking call ɗin, har lokacin yana kwance a jikin Lion ɗin. Wani irin ƙayatattacen murmushi Aseef ya saki lokacin da ya kalli fuskokinsu dukkansu biyu, da yake video call yake kiransu, bai cika kiransu normal call ba, kwance yake a saman gadonsa yana sanye da kayan barci milk color, ya yi kyau sosai. Shi ma Areef ƙayatattacen murmushi ya saki, shi kuwa Saif bai yi murmushi ba, amma dai ya ɗan saki wannan ɗaurarriyar fuskar tasa, alamar ya ji daɗi kenan, amma murmushi kam, sam babu ko ɗigonta a fuskarsa. "Wow My TRIPLETS yau kam wace iriyar Sa'a ce dani,? Naga face naku a haɗe waje guda, wlh ina kewarku sosai, ko yaushe na tuno ku sai na yi kuka, shi ma daddy yana kewarku sosai, ni gaskiya zan bar exams ɗin nan na biyo ku, ba zan iya zama ba, i can't gaskiya". Ya kai karshen maganar tamkar zai yi masu kuka. "My shagwaɓati ba, kai Aseef ban san ya zanyi da kai ba, yanzu dai kuka zaka yi mana kenan? To kayi bari na yi recording na ajiye tarihi, gaskiya your future wife tana da aiki, yaron nan har yanzu ba zaka canza ba ko?". Cewar Areef, ya yi maganar cikin zolaya. "Serious kewarku nake yi, kuma ni mata mai shagwaɓa zan aura ai, ta yi ta kuka nima ina taya ta, jiya ma na haɗu da wata beb a white house, sai dai bata iya shagwaɓa ba, sai wani juya min ido kamar wata tsuntsuwa ta iya". Dariya Areef ya kwashe da shi, shi kam Saif kamar wasu Tv haka yake binsu da ido, idan suna irin wannan wasan nasu nishaɗi suke sanya shi, yana son ya kallesu suna farinciki suna dariya, ga shi shi kuma bai iya dariyar ba bare ya yi masu shi ma. "Aseef shiyasa fa na ce maka zan ɗauko maka mace daga nan Nigeria in kawo maka, matan Nigeria fa the are beautiful wlh, and suna da kirki over, ba kaga Our princess ba Rimsha? Ai tana da kirki sosai, kuma tana da kyau, to irinta zan samo maka". Ɗan satar kallon Musharraf dake barci a gefensa ya yi kafin ya ce "Idan har Gimbiyar TRIPLETS tana da sister to kawai ka ɗauko mani ita, in dai jinin Uncle Hosain ne, ina so zan aura". Zaro ido Saif ya yi yana jujjuya sunan da suka kira Rimsha da shi, da yake ya san suna kaunar Musharraf, sai ya yi tunanin hakan yasa suke kaunar Rimsha, sai bai kawo komai a ransa ba, bai taɓa kawowa cewa wai Rimsha na haukar son shi ba, dan shi kallon ƴar karamar yarinya yake yi mata, idan ma aka gaya mashi tana son shi ai sai ya sumar da ita, kuma tabbas zai tsaneta, ace yarinya yar karama har ta san soyayya, dududu shekarunta nawa a duniya? Da har zata fara soyayya, ita da ya kamata yanzu ace ta tsaya tsayin daka tana zuba uban karatu kamar ba gobe, amma wai soyayya. TAB LALLAI LION BAI SAN RIMSHA KAM TUN TANA ƳAR SHEKARA 9 TAKE HAUKAR SON SHI BAN, IDAN YA JI TUN WANNAN LOKACIN KUMA SAI YAYA, YANZU MA YA CE KAMAR HAKA BATA KAI SOYAYYA BA, ƳAR JARIRIYA DA ITA........🤣.... TO INA GA KUMA YASAN TA JIMA A CIKIN SOYAYYARSA? TAB AKWAI AIKI. "Kai Aseef ka kawo good shawara fa, zan tambaya maka Rimsharmu idan tana da sister zan nemota na taho maka da ita, amma kuma sai dai kamar da wuya fa ace tana da sister, domin da uncle ya zo mummynsu kawai ya tambaya, ban ji ya ce ina sister ta ko wani abu makamancin haka ba, amma zan bincika". Aseef zai yi magana zazzakar murya Lion ya katse su da cewa "Haba Areef ka tashi mani a jiki kada ka karya ni mana, kuma ai na ce maka yunwa nake ji ko?". Cikin sauri Aseef ya ce "Kai Areef ka tashi ka bashi abinci mana, please ka yi sauri, nima har kasa na fara jin yunwa". Kwafa Areef ya yi. "Ba zan tashi ba karfi ya tashe ni, kuma abinci dai ba za'a ci ba, tun da yau ya shaƙe mani sister ba zai ci abinci a gidan nan ba". Zaro ido waje Aseef ya yi. "Haba mana Lion meyasa zaka shaƙeta? Ai gwara ni kazo ka shaƙeni, ina fa sonta, sister mu ce fa, ƴar uncle ce fa, muna kaunarta ni da Areef, kuma ya kamata kai ma kaso abin da nake so tun da kana so mu, please ka daina shaƙeta ka ji? Saboda ni zaka yi ka ji my pleasure? Our king". Tamkar bai ji su ba, tabbas yasan suna bala'in kaunar Rimsha, dan ya ga irin zaman da suke yi da Areef, ya ga yadda Areef yake bata kulawa ɗazun, abin ma mamaki yake bashi, sai dai shi kuwa bata ma ishe shi kallo ba. "Areef zan yi maka rashin mutunci fa idan baka tashi mani a jikina ba". Ya faɗa gently. "Areef please stand up mana, ko so kake ka saka ni kuka ne? Ya ce maka yunwa fa yake ji, please ka tashi, dan kaga muna lallaɓaka baka da lafiya ko, to Allah ka tashi ko kuma muyi sama da kai, kuma ai ba zan sake shaƙe sister taka ba, na ari bakin ɗan uwan, na yi magana a madadinsa, dan haka yanzu dai ka tashi maza". Cewar Aseef Kin tashi ya yi tamkar bai ji me suke faɗe ba, sai da ya kalli Lion ya lumshe idanu alamar ransa ya ɗan ɓaci, dan a gaskiya yana jin yunwa sosai, kuma baya son ya yi wurgi da Areef ɗin ne, dan saboda ciwon dake jikinsa, hakan yasa yake mugun tausaya mashi, amma Areef na neman kai shi bango. Ganin ya lumshe idanu ne yasa Aseef ya yi mashi alamar ya tashi ya bashi abinci dan Allah, ko da kuma Aseef bai faɗa ba, to ya zama dole shi ma Areef ɗin ya tashin dan kansa, baya son ɓacin ran ɗan uwan nasa. Miƙewa ya yi tare da dirowa kasa yana faɗin "Ba dan halinku na tashi ba". Har lokacin wayar tana a hannun Saif ne. Wucewa ya yi zuwa wajen da Rimsha ta ajiye abincin, tare da zama ya fara zuba abincin a plate. Miƙewa shi ma Lion ɗin ya yi tare da dirowa kasa ya nufi wajen abincin, sai dariya Aseef yake yi masu, idan Aseef da Areef suka haɗu, kamar wasu tom and Jerry suke komawa, su na wasa da dariya da juna over, kamar wasu ƴaƴan kawu nai, sun haɗe kai sosai, shi kuma Saif sai dai ya yi ta binsu da ido kawai yana jin daɗin yadda suke farinciki. Zama ya yi tare da ɗaukar spoon zai fara cin abincin, karɓe spoon ɗin Areef ya yi tare da ɗebowa ya kai mashi saitin ɗan bakinsa yana faɗin "Ni zan baka first spoon". Kallon gefen ido mai kama da hararar wasa ya wurga mashi kafin ya buɗe ɗan karamin bakin nasa. Zuba mashi abincin Areef ya yi, sai murmushi Aseef yake yi, karɓar spoon ɗin shi ma Lion ɗin ya yi, ya ɗebo abincin ya kawowa ɗan uwan nasa a saitin bakinsa, buɗe baki Areef ya yi ya karɓa, a tare suka fara taunar abinci, Aseef ji yake tamkar ya yi tsuntsu ya zo ya same su, wayyo yana wani irin mahaukacin kewarsu. Abin gwanin burgewa, dama idan suka haɗu, tsantsar kula da nuna kaunar juna suke yi wa kansu, ɗauko wani spoon ɗin Areef ɗin ya yi suka fara cin abincin a tare, sai hira Aseef da Areef suke yi, shi kuma abincin kawai yake ci yana saurarensu. A tare suka cire hannu daga abincin, sun ƙoshi, kusan kuma a tare suka sha ruwa. Miƙewa Areef ya yi tare da kwashe kayan abincin ya fitar, lokacin da ya dawo, Saif ya koma gado ya kwanta tare da ajiye wayarsa a saman bedside drawer yana sauraren Aseef tare kuma da kallonsa. Hayewa gadon shi me ya yi, suka cigaba da hirarsu mai cike da so da kuma kaunar juna, sai zolayar juna suke yi, har Lion ya yi barci ya barsu, daga ƙarshe dai suka yi sallama har da yi wa wayar kiss kamar wasu masoya, tare kuma da furta kalmar i love you wa junansu, abin gwanin burgewa da ban sha'awa, kowa zai yi fatan samun ƴaƴa irinsu masu bala'in kaunar juna haka koma fin hakan. Kashe wayar Areef ya yi tare da ɗaurata saman bedside drawer kusa da lamp, daga nan ya kashe musu wutar ɗakin tare kuma da kara gudun Ac ya kwanta, yau dai a ɗakin ɗan uwansa zai kwana kenan. Yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi. A ɓangaren Imran kuwa, bayan ya maida ita bedroom nata, na shi bedroom ɗin ya wuce, ya ɗauko ɗayar wayarsa ya kunna domin ya kira Abba, dama ya kasheta ne kawai dan baya son damuwar kiraye kirayen jama'a, shiyasa Ammie ta yi ta neman numbersa bata shiga. Bugu ɗaya ya yi wa Abba ya ɗaga, a lokacin kuma Ammie ta yi nisa cikin barci, akwaita da nauyin barci sosai. Cikin girmamawa ya gaida Abban nasa, bayan sun gaisa ne ya ce "Abba dan girman Allah ka gaya mani menene ya haɗaku da bappa Hosain da har ya yi fushi da ku ya baro gida". Shiru Abba ya ɗan yi na ƴan mintoci. "Imran babu komai kawai fushinsa ya yi, kasan shi da bala'in zuciya kamar babanmu, to fa ƴar karamar faɗa ce ta haɗasu da mata a cikin gida, shikenan dan munbi bayan matan munyi mashi faɗa ne ya zuciya ta baro gidan". Tabbas Imran yasan ba haka bane, domin a iya zaman da ya yi da daddyn Rimsha a baya, ya fahimci mutun ne shi mai zurfin tunani da kuma sanin yakamata, haka kawai dan faɗa na mata a cikin gida ba zai yi fushi ya bar ƴan uwansa ba, dole dai akwai wata a kasa, da alama kuma babbar al'amari ce a kasar da yasa suke ɓoyewa, dole akwai abin da suka yi wa daddyn Rimsha da har ya zuciya haka. Jin ya yi shiru yasa Abba ya ce "Imran ka fara barci ne?" "A'a Abba ban yi barci ba". "Okey ai naji ka yi shiru ne, to dai shikenan sai da safe ni barci nake ji, da safe ka kirani mu yi magana akan ƴar wajen Maik". Yana kai karshen maganar ya katse kiran domin ya ga Ammie ta fara motsawa, kada ta tashi ta tsayar masu da bala'i, dama kunsan ido rufe take neman Imran ɗin. A ɓangaren Imran kuwa, ɗaura wayar saman bedside drawer ya yi yana tunanin menene gaskiyar abin da ya faru, waye a cikinsu Abba zai gaya mashi gaskiya? Menene yake faruwa a cikin wannan family'n? Ko dai na tambayi gwaggo Batula ce? No tun da Abba bai faɗa mani ba, ita ma ba zata gaya ba, waye ya kamata na samu ya gaya mani wannan magana. To masu karatun na san zaku so jin me ya haɗa su, tun da Imran bai sani ba, bari ni na gaya maku, a shekarun baya kusan shekara 35 zuwa da 37 baya, mahaifin su daddyn Rimsha, wato kakansu Rimsha........ ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E9-10 To masu karatun na san zaku so jin me ya haɗa su, tun da Imran bai sani ba, bari ni na gaya maku, a shekarun baya kusan shekara 35 zuwa da 37 baya, mahaifin su daddyn Rimsha, wato kakansu Rimsha, Dr Salman Sultan yana da rai a idanun jama'a, domin a yanzu ya zama gawa a idanun kowa da kowa, an rufe babinsa, sun shafe shi, shararren likita ne wadda ya shahara a duniya ta fannin surgery, mutun ne mai ɗunbi dukiya ga kuma tarin masoya ta ko'ina da ina na bugawa a jarida, yana bala'in kaunar ahalinsa, wato family'nsa, mutun ne mai fara'a, saukin kai, mara son hayaniya, son jama'a, kyakkyawar gaske ne kamar dai ƴaƴan nasa, fari ne tas tamkar balarabe, mutumin jahar Bauchi state ne mazauni KADUNA. GARIN KADUNA.💋 Tampatsetsen gida ne wadda ya amsa sunan sa gida, two-storey building ne, wato gidan sama hawa biyu, gate ɗin gidan ma kawai abin kallo ne, gida ne wadda ake wa laƙani da aljannar duniya, gabaɗaya abubuwan da aka yi amfani dasu wajen inganta wannan gida da kawata shi white color ne, da alama mai gidan yana son farin color sosai, tsakar gidan yana da girmar gaske, akwai garden, fillin kwallo, katafaren pool, da kuma parking space, sai wajen wasan yara. Wasu kyawawan fararen samari ne ke wasa a wajen wasan yasa dake a cikin gida, gabaɗaya wajen white color ne, kama da pentin waje, kayan wasan da aka zuba, kujerun lilo na wajen, dokunan wasa, ƙananan motoci da mashuna masu amsani da charji, wadda yaro yana iya hawa ya yi tafiya mai nisa, ke kunar hawa, da sauran abubuwan wasa na yara. Su biyu ne ke wasa a wannan waje, kamanninsu ɗaya, daga gani kasan ƴan biyu ne, fararene tas tamkar larabawa, waƴan nan samari ba su kowa bane a fa ce Azharuddeen da kuma Nawazudden, a lokacin Bama a haifi daddyn jelly ba, haka zalika Hjy Batula, Zahradeen wato Abbi, da kuma Abdulkadir wato Abba, a lokacin suna makaranta, haka ita ma Gwaggo tana makaranta, Abba yana haɗa degreensa ta farko a jami'ar Ahmadu Bello University Zaria, a can zaria yake zama, sai idan an yi hutu ya dawo shi ma time to time ne, haka shi ma Abbi sai hutu yake dawowa, ƴan gata ne na bugawa a jarida, iyayensu na bala'in kaunarsu, suna shagwaɓa su, kome suke so cikin ƙanƙanin lokaci ake yi masu, Mahaifinsu hamshaƙin mai kuɗi ne ba na wasa ba, mahaifiyarsu kuma baturiya ce yar kasan Russia, kuma kamshakiyar mai kuɗi ce ita ma, lokacin da babansu ya je karatu a can suka kulla soyayya, har ya aurota ya dawo da ita, amma kafin su dawo Nigeria sun zauna sosai a Russia, dan sai da suka haifi Abba, Abbi, Gwaggo, da kuma twins, har ma su twins sun girma sun zama samari, a takaice dai su daddyn Rimsha ba'a nan Nigeria a ka haifesu ba, a lokacin da suka fara girma sosai ne kuma Mummynsu ta ce lallai sai sun dawo Nigeria dan su san familyn babansu, haka ba dan Dr Salman ya so ba, ya tattarosu suka taho Nigeria, a in da ya sai gida a Kaduna dan nan yake son zama, bayan ya dawo baifi da wata ɗaya ba, iyaye da ƴan uwa suka ce wlh ba zai yi wu ba, dole ya auri yar gida Nigeria dan kada turawan nan su kwashe komai ɗin sa, haka ba dan ya so ba ya yi wa Na'ura wato mummynsu kishiya da wata ƴar karin Bauci, wadda kuma ƴar kanin babansa ne, kuma shi kanin baban nasu ne ya haɗa wannan aure, Naura wato mummynsu shiru shiru ce, duk da take baturiya tana da halin kirki sosai, bata da yawan magana kuma bata son hayani, kamar dai daddyn Jelly take, shi kuma Dr Salman duk da yake da wannan fara'a fa to akwai shi da zuciyar bala'i, ga saurin fushi kamar me, idan ya yi fushi kuma baya sauƙowa ta daɗi, tun da suka yi aure da Naura bata taɓa yarda ta yi mashi wani laifi ba, dan saboda tasan halinsa ciki da bai, kuma an yi sa'a ita ma irin Aunty ta Abbi ce, bata magana, tana bala'in son ƴaƴanta da mijinta, saboda mijin nata ta musulta, da ta musulta kuma ƴan uwanta suka ce sun yafe ta, wannan dalili yasa tun da ta baro kasarsu bata sake komawa ba, kuma hakan ma yasa ta ce su dawo Nigeria, saboda bata son suna haɗuwa da ƴan uwanta kuma basu yi mata magana, tana jin babu daɗin hakan sosai, tun da tazo Naija bata ma sha'awar ta koma kasarsu, NIGERIA ya yi mata daɗi, in yanke maku labari ta koma gaje, tun da ya auri wannan yar Bauchi shikenan zaman lafiya ta yanke a cikin gidan, faɗar yau daban ta gobe daban, a lokacin Naura tana da karamin ciki, da zarar Amarya ta fara bala'inta Naura zata wuce cikin ɗaki abinta, ga shi a cikin yaranta dukka daga Hassan Sai Hossain ne kawai suke garin Kaduna, shi kuma Dr Salman gabaɗaya ya birkice a lokacin, ya juya ya koma wajen Amarya ya tare abinsa, ko kallon in da Naura take baya yi, yana fin wata bai haɗu da ita ba ko ajikinsa tun da yana da Amarya, kuma bata damuwa baiwar Allah, abin kai daga gani kasan shiryar wa Amarya aka yi daga gida, dan dama family sun ce ba zasu yarda baturiyar nan ta zo ta kwashe komai na ɗan su ba, kasan cewa yafi kowa kuɗi a cikin familynsu, Dr Salman farine tas, amma Naura ta haifo ƴaƴa farare irinta da chocolate irin dangin mijinta, mutanen Bauchi two colors ne, kanne Dr Salman gabaɗaya chocolate colors ne, shi ne kawai fari a cikinsu. A na haka su Abbi suka dawo hutu, to dama gabaɗaya cikin yaran Dr Salman ya fi kaunar daddyn Rimsha da Hassan, sun fi shaƙuwa, ita kuma Amarya bata son hakan, tana jin haushin hakan, shiyasa ta tsani daddyn Rimsha fiye da misali. Dawowar su Abbi gidan yasa suka takawa Amarya birki a kan cin mutuncin da take yi wa mahaifiyarsu, har iƙirarin dukan mutuwa Abba ya yi akan zai yi mata, a kwana a tashi Amarya bata daina ba saboda Dr Salman yana goya mata baya, ta mallake shi, sai kwasan dukiyarsa take yi tana turawa gida Bauchi, dan a cewarsu ai ita ma baturiyar tana kwasa ta aika kasarsu, dan haka ne ma suka turo Amarya da babban shirinsu, abin da basu sani ba shi ne, Naura kusan ma tafi Salman kuɗi, domin iyayenta hamshaƙan masu kuɗi ne, kuma kunsan turawa, tun ƴaƴansu na yara suke sakar masu kuɗi da komai da komai, dan su yi abin da suke so, hakan yasa tana da account mai ɗauke da dubbanin makudan kuɗaɗe, ga kuma zallar ruwan cash a gida. Zaman lafiya dai yaki samuwa a tsakaninsu, dan an turo amarya ce ta kori baturiya ta koma kasarsu, abu sai gaba gaba yake yi, yaki karewa. Wata rana aka wayi gari Amarya ta yi yunkurin dukar Na'ura, a lokacin kuma cikin ta ya kai wata biyar haka, ba imani Amarya ta yi yunkurin dukanta, aikuwa Abba ya yi mata ɗan iskan dukan mutuwa wadda har sai da aka kwantar da ita a gadon asibiti, daga nan ne fa wannan tsohuwar gaba ta faro tushe, dan kuwa da Dr Salman ya dawo ya ce ba zai taɓa yarda ba, da hannunsa ya miƙa Abba a police station aka rufe shi akan ya daki amarya, a wannan rana tamkar Naura zata yi hauka, babban ɗanta a police station, idan ba kaddara da soyayya ba akwai wanda ya isa ya rufe mata yaro ne, gida dukka ya birkice da kuka, Abbi ne kawai baya kuka yake rarrashinsu, Naura tana yi, Hassan da Hossain suna yi, yau sun ga ɗan karamin yaki bayin Allah. Sai da Abba ya yi kwana biyu a rufe aka sako shi, Naura ta jigata sosai da kuka, ta yi nadamar musulta da ta yi, ta bar family'nta, ta bar dukka uban gatanta, ta yarda da Dr Salman, ta biyo shi, yanzu ya ci amanarta, yana azabtar da ita, ta yi danasanin cewa su dawo Nigeria. Abin da bata sani ba, shi ma ba laifinsa bane, iyayensa ne da basu kaunarta, su ne suka shirya dukka wannan abin. Bayan kwana biyar da faruwar abin da ya faru na dukan Amarya da Abba ya yi, masifar Amarya dai ba abin da ya ragu, sai ma abin da ya karu, iskanci kala kala, a ranar da aka sallamota daga asibiti ta dawo gida, tun da ta ɗaura ido a kan daddyn Rimsha Allah ya jarrabeta da wani mummunar nufi a kan shi, ko da yake ba Allah bane ya jarrabeta, ita ce ta ɗaurawa kanta wannan wahala, wani irin azababben sha'awar daddyn Rimsha take yi, domin duk cikinsu ya fi su bala'in farin jini, ga shegen saurin shiga rai kamar me, yadda dai kuga Rimsharsa, shi ta gado, duk in da ya je sai an so shi, ga zahiri kuma kungani, yadda su Lion basu karɓar baki, amma shi sun karɓe shi hannu bibbiyu, to haka yake da shegen shiga rai tun yana yaro, ga bala'in kyau kamar shi ya yi kansa. Amarya dai ta yi iya yinta akan ta yi wa daddyn Rimsha fyaɗe, amma ina abin ya ci tura, duk da yana matashi kuma ɗan tubabbiyar baturiya, ya sami kula ta uwa, ya yi dacen uwa da ta yi mashi tarbiya mai kyau, duk da Naura ainahinta ba musulma ba ce, amma da ta musulta ta riƙi addinin sosai, ta kuma koyi abubuwa da dama tun kafin ta haihu, haka ta koyawa yaranta addini, suka yi riƙo da shi sosai, har ma sun fi ainahin musulman da ba mix. Idan suka je Bauchi kowa baya sonsu, sai su rinƙa ce masu ƴaƴan kafura, kyamatarsu kakanninsu suke yi, suna hantararsu, ita kuma Naura baiwar Allah duk da haka bata hana su zuwa ga dangin babansu, Abba yana da bala'in zuciya kamar babansu, sai ya ce shi wlh ba zai sake zuwa ga dangin babansu ba, ai suna zaginsu, suna ce masu ƴaƴan kafura, idan ya je wlh idan suka ce mashi haka, sai ya yi masu dukan mutuwa, a lokacin yana tashen faɗa kamar hauka, ai kuwa Naura tayi ta yi mashi nasiha a kan kada ya kuskura ya tanka, ba kakanninsa bane masu zagin nasa? To ya yi hakuri komai zai wuce watarana, fir yaki yarda, ya yi ta cika yana batsewa, ya ce shi dai ba zai yarda ba, wlh sai ya sumar da kakan nan nasu in dai bata dai na zaginsu ba, gudun kada ya je ya sumar da tsohuwa a banza ya kara ja mata bakin jini yasa Naura ta yarda ta bashi goyon baya akan ya daina zuwa, haka suma su Abbin suka daina zuwa Bauchi gabaɗaya, daga wannan lokacin suka rufe babin family'n babansu, suka cigaba da rayuwarsu. A kwana a tashi lokaci ya ja, cikin Naurat na da wata 8, Amarya ta je gida Bauchi ta yi sati guda ta dawo, har lokacin kuma babansu yana manne da ita, ya guji Naura, abin ya yi Baiwar Allah yawa, ga shi bata isa ta ce zata koma kasarsu ba, domin kuwa ta watsawa iyayenta da ƴan uwanta kasa a ido, ta yarda da Dr Salman ta biyo shi, shi kuma ya ci amanar yarda, haka ta daure ta cigaba da zama cikin kunci tana kula da tarbiyar ƴaƴanta. Ranar da Amarya ta dawo, tun da su Abban Imran suka yi ido biyu da ita, shikenan suka tare a gindinta suma, ta mallakesu, amma kuma Allah da ikonsa ta kasa mallake daddyn Rimsha da kuma daddy Anaya, ƴan biyun nan ƴan baiwa ne na gasken gaske kuwa, sam abin bai yiwa Amarya daɗi ba, domin ita burinta ne ta mallaki daddyn Rimsha dan ta sami abin da take buƙata, kuma duk mallake babansu da ta yi, baya hana shi kula su Daddy Rimsha, saboda su dai maganin bai kamasu ba, wani lokacin ma Amarya tana kiran shi ya zo su kwanta, zai ce a'a shi yau da yaran shi zai kwana, haka zai wuce ɗakinsu daddy Rimsha, su kaɗai yake kulawa a cikin ƴaƴansa. Sam amarya ta gaza samun sukuni, hakan yasa ta fara neman mafitar ta yadda zata salwantar da rayuwar yara biyun nan. Dududu amaryar fa shekarunta 25 a duniya, iyayenta ke shirya mata duk wata manakisa, su burinsu cin dukiya, da ta je gidan ne ta gaya masu abin da su Abba suke yi mata, har da dukanta da Abba ya yi, shi ne mamanta ta kai sunan su Abba ga malaminsu aka mallakesu dan su samu su mulki gidan, su ƙori Naura su mamaye komai dukiya da kyawawan fararen turawan ƴaƴan. A na tafiya a haka har cikin Naura ya kai wata 9, wata ranar Friday da ta kasance rana mafi bakin ciki a garesu, ranar da daddyn Rimsha ya gaza mancewa da shi, ranar data sanya Naura haihuwa ta shiri, ranar da ta kulla gaba tsakanin su Abba da daddy Rimsha, shi ne ranar da Amarya ta yi wa daddyn Rimsha wani mummunar sharrin wai yana nemanta da iskanci, kuma ta yi galaba akan shi ne ta haryar tabbatar masu da shaida, abin da ya faru shi ne. Kiran shi ta yi ɗaki akan zata aikesa, a lokacin yana tare da mummynsa yana yi mata tausa, bawan Allah bai san komai ba sai Kaunar mummynsa da ƴan uwansa, ba in da ya sani a garin Kaduna sai school nasu, shopping da kuma gidansu, shi kuma Hassan yana ta faman shafa cikin mummyn nasu yana lissafa abin da zata haifa masu, kani ko kanwa, abin gwanin ban sha'awa da burgewa, duk wanda ya kalli yadda suke sai ya ji sun burge shi saboda yadda suke ta zubawa mummynsu hira, har lokacin kuma basu jin hausa sai turanci, suna bala'in kaunar juna tare da cikin mummynsu, sai murmushi suke yi abinsu, su Abbi kuma suna bedroom nasu. Da farko da Amarya ta ce yazo, sai ya ce ba zai je kiran ba, sai da mummynsa ta sanya baki, shi ne ya je. Yana zuwa ta rufe kofa, da karfi ta cire mashi kaya har sai da suka yi kokawa, jin ya fara ihu ne yasa ta fishi ɗaga murya wajen fara ihu ita ma, ta ɗauki kwalbar turaren humra ta buga mashi a goshi da karfin gaske, nan take wajen ta fashe, jini jajawur ya fara wanke mashi fuska, da haka ta gayawa Dr Salman ai shi ya shigo zai yi mata fyaɗe, a garin kare kanta ne ta buga mashi kwalbar turare, da yake ta mallake su Abba, sai suka amsa da haka ne da Dr Salman ya tambayesu, Abba har da cewa ai ranar ma ya ga daddyn Rimsha ɗin yana wasa da gabansa a cikin ɗakinta, ita kuma bata nan lokacin, shi kuma Abbi cewa ya yi ai ranar ma ya gan shi yana ta wasa da breziyarta yana kissing na bra ɗin........ Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun 😭 Allah ka tsinewa asiri albarka. # Ai kuwa ran Dr Salman in ya yi dubu to a ranar ya yi mugun ɓaci, a nan ne kuma ya furta kalamai masu zafi a kan ɗan nasa, nan take ya ce ya yafe shi wa duniya, kuma sai an kai shi prison, sai ya yi zaman yari na shekaru goma, da yake su dokar turawa suka sani, ba na Nigeria ba, wani irin Mahaukaciyar razana da shiga tashin hankali Naura ta shiga, domin tasan dokan turawa ya fi namu a nan tsauri, su idan suka yanke hukunci fa, to sai an yi wannan shekarun, kuma ta ji har shekara goma ɗan nata zai yi a prison cewar babansa, bata san Nigeria kam ɗan ma zai iya gudu daga prison ɗin ba. In takaice maku labari, a wannan ranar dai Allah ne ya kaddara Naura kwananta na gaba, da sai dai a kwashi gawarta, saboda tsantsar bala'in tashin hankali da ta shiga, su Abba kuwa tsab suka bi bayan babansu da Amarya suka share Mummynsu, da alama ma sun mance ita ta haifesu, sai zaginta suke yi ita da daddyn Rimsha, yana jin suna zagin mumnynsa, shi sharrin da akayi mashi bai wani damesa sosai ba kamar yadda Abba da Abbi ke zagin mummynsu. Suna ganin Naura na kuka, amma ko a jikinsu saboda basu a hayyacinsu, tashin hankali da damuwar kada a rufe mata yaro ne yasa ta ɗebo kuɗi masu yawa wadda ita ma bata san adadinsu ba, ta zuba kuɗin a cikin jaka, a lokacin Dr Salman ya kira ƴan'sanda, basu kai ga isowa ba, sai dukan daddyn Rimsha yake yi kamar zai kashe shi, da kyar Naura ta iya kwatarsa, ita kuma Amarya tana ɗaki abinta, yau ranta fes, Hassan kamar zai yi hauka, shi ne kuma ya taya mummyn nasu karɓar Hossain nasa, su Abba suna tsaye suna kallon me yake faru, ko a jikinsu. Da kyar ta ja Daddyn Rimsha zuwa ɗakinta, ga ƙaton ciki wadda da alama ma ta fara naƙuda, tana kuka kamar ranta zai fita, haka shi ma Hassan, tamkar ransa zai fita yake kuka, shi kuma daddyn Rimsha ba'a magana, duk Dr Salman ya fashe mashi baki, ga gaskiya suna gani amma suka take. Ɗakin Amarya Dr Salman ya koma ya kwanta yana jiran dirowar ƴan'sanda dan su tafi da Hossain. Suma su Abba kowa ya wuce ɗakinsa, lallaɓawa Naura ta yi tana naƙuda ta ɗauko jakar kuɗin nan ta bawa daddyn Rimsha ta ce ya gudu ya tafi, da yake shima a zuciye yake a lokacin, ya tsani kowa, sai ya karɓi kuɗin ya gudu, mai gadi ya so tare mashi hanya, ai kuwa ya sakarwa mai gadin kunamunsu na twins ya gudu ya fita daga gidan, bai san ko'ina ba, bai san kowa ba, dan ma dai Allah yasa yana da wayo sosai ga kuma ilimi, sai kuka Hassan yake yi yana cewa shi zai bi ɗan uwansa, amma Naura ta riƙe shi gam, da yake dama sun san yana kuka, sai basu kawo cewa Hossain ya fita ne yasa yake kara wannan mahaukacin ihun ba, sai suka bari a kan dukan da babansu ya yi wa Hossain ɗin ne yasa Hassan ke wannan ihu haka. A TAKAICE DAI WANNAN SHI NE SANDIYAR RABUWAR HASSAN DA HOSSAIN, WANNAN SHI NE ABIN DA YA FARU, SAURA LABARI KUMA ZAI ZO MAKU DAGA BAKIN ABBAN IMRAN, WANNAN MAGANA BA ZA SU MAIMAI TA SHI BANE YASA NA GAYA MAKU ABIN DA YA FARU, SHI KUMA DADDYN RIMSHA BAYAN FITAR SA GIDA INA YA JE? ZAI GAYA MAKU DA BAKINSA, INA NAURA TAKE? ME TA HAIFA A RANAR? YA AKAYI DADDYN JELLY YA YI RAYUWA DA DADDYN RIMSHA DA HAR YAKE IKIRARIN SUN FI KUSANCI DA HOSSAIN ƊIN? INA AMARYA? YA MAKOMARSU ABBA A WANNAN LOKACI? YA AKAYI WANNAN ASIRI DA AMARYA TA YI MASU ABBA YA WARWARE DA HAR A YANZU SUKA SAN KUMA SUKA GANE SUN YI WA DADDYN RIMSHA LAIFI? YA AKAYI DAGA BAYA SU ABBI SUKA RABU HAKA? SAURA LABARI YANA GABA, NA SAN A IYA WANNAN MA KAWAI KUN FAHIMCI IN DA ZANCEN YA DOSA, MU DAI JE ZUWA ZAMU HAƊU A GABA DAN WARWARE KOMAI A TARE. STORY💋 💋GIDAN LION💋 Ajiye wayar Imran ya yi tare da kwanciya a saman gadonsa, tunani cike fal ransa, tabbas yana son sanin menene gaskiyar abin da ya raba iyayensu, meyasa daddyn Rimsha baya son haɗa inuwa ɗaya da su? Amma kuma meyasa yake taimaka masu sosai idan suka shiga damuwa? Imran bai san abin da suka yi mashi bane ta tsaya mashi a zuciya da yasa baya son haɗa inuwa da su, jini ba wasa ba, tabbas yana kaunarsu shiyasa ma yake taimaka masu kuma yake bibiyar lamuransu, amma kuma duk lokacin daya gansu, ba abin da yake tunawa fa ce irin sharrin da suka murje idanunsu a gaban kowa suka yi mashi, wai yana neman matar babansa, waiya zubillah, ya kasa mancewa da wannan abin, yana da Bala'in zuciya sosai. A ɓangaren Rimsha kuwa, bata sami barci ba har wuraren karfe 1, tun da Imran ya dawo da ita ɗaki take kuka, kuma ta rasa dalilin kukan nata, ta rasa me yake yi mata daɗi, da kyar barci ya yi awon gaba da ita. Washegari da misalin karfe 8 wanka ta yi, ta shirya tsab cikin wando da riga kamar dai kullum, sai dai yau, Pakistan ta sanya, rigar ma ta ɗan ɗara gwiwarta, wandon kuma yana da ɗan faɗi, sai mayafin mai ɗan girma, dukkansu launin sky blue ne, ba two colors bane. Bayan ta gama shirin ta fes, sanya perfume nata ta yi, tare da ɗaukar wayarta ta nufi Palo, idanunta har yanzu suna kunbure, saboda ba karya ta sha kuka daren jiya. Ko da ta fito Palo, babu kowa, dan haka sai ta wuce kawai ta nufi garden ɗin gidan. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga, Imran ne kawai yake zaune a wajen. Kayatatcen murmushi ta saki mashi kafin ta ɗaga mashi gaisuwa, da fara ya amsa gaisuwar tata, kusa da shi ta je ta zauna, hira suka fara yi a tsakaninsu, cikin mutunta juna da girmamawa, sai murmushi suke sakarwa junansu gwanin burgewa. Suna tsaka da hira suka ji diran motoncin a cikin gidan, nan take gabaɗaya gidan ya kauraye da jiniya tamkar yaki za'a tafi, jibga jibgan motoci masu numfashi kwara biyar ne cif, kuma dukka motocin sojiji ne masu rai, sabbi gal gal, haka zalika jibga jibgan fararen turawan sojoji ne a saman bayan waɗan nan motocin. A razane ta miƙe tsaye tana ganin yadda waƴan nan jibga jibgan sojojin ke dirowa kasa daga saman bayan motoncinsu, dukkansu fuskar nan tasu babu alamar annuri, ga su da tsawo da kuma murɗaɗun jiki tamkar wasu warriors, su goma sha biyu ne cif cif kamar yadda ya faɗa, mamaki ne ya kamata dama da gaske yake yi da ya ce zai karo wa su sojoji goma sha biyu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun wannan wace iriyar zuciya ce ke gare shi,? Muguntarsa ta wuce gaban misali. Dafata Imran ya yi yana faɗin "Na san abin da kike tunani, bai wuce cewa da gaske ne daman Saif yake yi na karo wasu sojojin ba, to ki sani ni tun ranar da ya yi maganar na san cewa yes confirm sai ya kawo su kamar yadda ya faɗa domin duk abin da kika ji ya faɗa to wlh sai kin yi shi, ko mutuwa zaki yi sai kin yi shi, in ya so daga baya ki mutu, tun da ya ce sai kin yi wa waƴan nan kafuran aiki to fa ba makawa kuma babu mai canza hakan sai shi idan ya yi ra'ayi, ya sauƙo daga dokin zuciya da ya hau, ni yanzu damuwa ta ɗaya, tayaya zaki kasance a cikin waƴan nan kafurai masu fuskar shanun? Ba su da imani da tausayi, abin haushin ma, shi ne shiga ɗakinsu da zaki rinƙa yi, kafurai ne ba musulmai ba, bare na ce za su bi dokar Allah, gaskiya daddy bai kyauta ba maganar da ya gayawa Saif, ga shi yanzu ya ja maki bala'in da in danginmu dukka za su haɗu babu mai fiddaki, amma In Sha Allah komai zai wuce nan da ƴan kwanaki kaɗan, ina da tabbacin zai sauƙo, zuciyar zata yi sanyi". Rushewa tayi da kuka tare da zube gwiwowinta a kasa ta toshe baki da hannayenta dukka biyu, ƙwaƙwalwarta yana tariyo mata irin muguntar da ya rinƙa yi mata, hannu yasa ya ɗagota yana mai rarrashinta. A wannan halin Areef ya shigo garden ɗin ya same su, da fara'a ya shigo, amma ganinta a wannan hali yasa ya ɗaure fuska sosai. "Prof me ka yi mata take kuka?". "Me kuma zan yi mata Areef? Kawai dai taga sojojin nan da Lion ya ce zai kawo ne, to ta ga ya cika maganarsa ne, shi ne take kuka. Murmushi kaɗan ya saki, cikin sigar rarrashi ya fara magana "Our princess ina raye ba zan taɓa barin hakan ta faru ba, ɗan uwana ne fa, na san ta yadda zan bi da shi, kada ki wani damu, In Sha Allah wannan aikin gabaɗaya kin kusa dainawa, daga yau zuwa gobe, zan san ta yadda zan dakatar da shi, ba dai na sami lafiya ba, kawai ki zuba ido ko sha kallo, yanzu dai share hawayenki gimbiyar TRIPLETS". Ba karamin daɗi ta ji ba, cikin sauri ta goge hawayenta tare da fara zuba mashi godiya. Girgiza kai ya yi tare da sanya hannunsa ya ɗan rungumota a gefen jirjinsa, wani iri ta ji a jikinta, shi kuma ko a jikinsa bai damu ba, bai ji komai ba. "Ku zauna mana, Prof ina da magana da kai". Ya faɗa tare da saketa ya zauna saman sofa, kusan a tare ita da Imran suka koma suka zauna. "Prof what is goruba?". Ɗan zaro idanu waje Imran ya yi, tunani ya fara yi, wai a ina Areef kuma ya jiyo sunan goriba? Me kuma zai yi da ita? Dan dai tabbas shi dai ba iya cin gorobar zai yi ba, bai ma santa ba, amma ya zo yana tambaya. "Prof i said what is goroba?". "Areef what are you going to do with the goruba?". Kai tsaye cikin wasa ya ce "My future wife mana zan kaiwa, wai kai Prof ina ruwanka ne? Just kawai tell me what is it, kai ni nama fasa son sani menene, just kawai a kawo mani goroba from now to tomorrow"........ To fa goruba kuma🤔 "To Shikenan za'a kawo maka, ba dai goroba ba? Ai gidanta kazo, Allah yasa ka iya ci". Imran bai yarda a kan wata zai kaiwa ba, domin shi dai yasan TRIPLETS ba ɗaya daga cikinsu da yake da girlfriend, kai idan ma ba Rimsha ba, ba su da wata mace da suke yi wa magana, hakan yasa bai yarda da zancen ya ce wata zai kaiwa ba, ya mayar mawai kila yana son ya gwada ci ne, tun da wani lokaci tana cewa zai ci abincin hausawa, to amma a ina yaga goriba? A ina yaji sunanta da har zai gwada ci ɗin? Shi da ko saninta bai yi ba? Akwai wata a kasa. Areef zai yi magana Imran ya rigashi da cewa "Rimsha Saif na buƙatar abinci, ki je ki kai mashi, dan Allah Rimsha ki kula kin ji ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi tare da amsawa da to, daga haka ta miƙe ta bar wajen, su kuma cigaba da hira suka yi. Kamar kullun Mark ya kammala haɗa mata abincin, hannunta ta wanke kafin ta ɗauka ta wuce izuwa bedroom nasa. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga, yana balcony, ya miƙe a saman ɗaya daga cikin tsadaddun kujerun dake a wajen, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, sai wani Lumshe idanu yake yi kamar mai jin barci, pajama ne a jikinsa, launin army colar, ya saki wannan kyakkyawar dark black curly hairn nan nasa, sai wani kyalli gashin take yi, kwana biyu da suka ɗan yi a Nigeria har ya ɗan yi duhu saboda zafi, fatarsa ta rage haske, sai dai kuma ta kara kyau da kwanciya luf luf kamar matar jariri, ya kara fresh sosai. A in da ta saba ajiye mashi abincin, a nan ta ajiye, ita ma zaman ta yi tana jiran shi, shiru shiru ba shi babu labarinsa, sai ƴan waige waige take yi kamar mai neman wani abin, ji take yi tamkar ta tashi ta ɗan yi mashi taɓe taɓe tun da baya nan, amma sai ta tuna da abin da Imran ya gaya mata kafin ta zo, tuna hakan yasa ta daure ta cigaba da zama jiran shi kawai. Sai da ta kwashi minti 30 a wajen a zaune kafin ya miƙe ya taho, wa iya zubillah, kallo ɗaya ta yi mashi, ta yi saurin kawar da kai, dan kada ya kamata, da yake yana nufota ne, amma ta kasa manta kyawun da ta kallah. A in da ya saba zama ya zo ya zauna, abinci ta zuba ta tura Mashi, ba ɓata lokaci ya ɗauka tare da fara ci, sai satar kallon shi take yi. Ɗan dai'dai ya ci abincin, ya ajiye spoon ɗin tare da yi mata alama da hannu akan ta zuba mashi ruwa, cikin sauri ta zuba ta mika mashi, ba ɓata lokaci ya karɓa ya sha, bayan ya ciro cup ɗin kuma, ya ajiye mata tare da miƙewa ya fice daga ɗakin, cikin sauri ta kwash kayan abincin ita ma ta fita. Kitchen ta mayar da kayan abincin kafin ta dawo in da su Imran suke zaune, zama ta yi suka cigaba da hira. Misalin karfe 10 daidai Imran ya je ya ɗauko AKILA, tun jiya dama Rimsha ta kirata a waya ta gaya mata cewa ta zo mata da kayan tea ɗin, yaya Imran ya ce zata zo su wuni, sai dai a gidan Akil ya je ya ɗaukota, yaki zuwa gida da kansa, domin ya ji labarin kiran da Ammie take mashi ta bakin Akil ɗin, to yaki zuwa, ya fi so sai ya haɗu da Abba sun tattauna kafin ya timkareta, sai Abbansa ya yanke hukuncin me zai ce mata kafin su haɗu kenan, shiyasa ya kira Akil akan ya ɗauko mashi Akilar daga gidan, ya ce wa Ammie za su je wani gari ne haka, domin yana so Akilar ta yi kwana biyu haka a gidan, ta ɗan ɗebewa Rimsha kewa, ai kuwa Akil da ya je, sai ya ce wa Ammie Abuja za su je, ita kuma in dai Akil ko Imran ne za su ɗauki Akilar, to bata damuwa, koma wata ne suje su yi, dan tasan suwa ye ta haifi........... OH WASA WASA AKIL DA IMRAN SUN ZAMA MAKARYATA SABODA SOYAYYA.🤔 SU DA BASU SAN MENENE KARYA BA, BASU YI, SUNA MA TSAWATARWA MASU YI, AMMA YANZU SABODA KAUNAR FAMILY'N ABBANSU SUN FARA KARYA SOSAI....🤔 Da Akil ya je gida ɗaukar Akila, Ammie ta tambaye shi ina Imran, sai ya ce mata ai baya kasar ne ma baki ɗaya, amma ya kusa dawowa, haushi kamar ta yi yaya, haka ta hakura ba dan ta so ba, ta yi kwafa tana jiran dawowar shi, dan dole ya saki jelly, bata san shi ma Akil ɗin yana tare da matarsa ba, in dare ya yi, sai ya dawo gida ya shiga ɗaki kamar mai barci, idan dare ta tsala kowa ya yi barci, sai ya fita ya gudu gidansa wajen Umaisharsa abinsa. (Ƴaƴan Ammie akwai ƴan air wlh🤣) Yau murna a wajen Rimsha ba'a magana, ta rungumi Akila sosai kamar wani ya ce zai rabasu, ita tasan Akila ƴar uwarta ce ta jini, ita kuma Akila bata san hakan ba, kuma ga shi daddynta ya ce kada Imran ya faɗa, hakan tasa bai faɗa ba ya yi shiru, ita ma bata gayawa Akilar ba. Ɗaki suka kule, sai zuba hira suke yi, a in da Akila take bata labarin masoyinta ya ce zai zo ranar Wednesday, tana cikin murna mara misaltuwa, sai murna Rimsha take taya ta, tun da Akila ta zo bata haɗu da Areef ba, haka ma Lion basu haɗu ba, hasalima daga Lion ɗin har Areef ɗin ba su san ma tazo ba, gara Lion ma Imran ya gaya mashi zai je ya ɗauko sister sa wa Rimsha, sai da ya bashi izini tukun nan ya ɗaukota. Tun da tazo sun kasa motsawa ko nan da chan, sun baje a saman gado har sai da aka yi sallar azahar, a sannan ne suka yi wanka tare da sallah, yau Rimsha baki ya ki rufuwa, kuma ga shi yau gidan nasu a cike tab da bakin sojoji, idan ba ka kai zuciya nesa ba, to ba zaka iya zama a cikin waƴan nan jibga jibgan ba, wlh kallonsu ma kawai ya isa ya rinƙa razanaka har rai ya yi halinsa, gasu kamar wasu gumaka, basu magana ko kaɗan. Shiryawa suka yi dukkansu cikin riga da wando, da yake Akila ta fi Rimsha cika sai kayan sam basu dace ta fita da su a haka ba, gara Rimsha, duk da ita ɗin ma bai dace ba cikin zaratan mazan nan ba, musamman yanzu da aka karo wasu, ita zuciya bata da kashi, da Allah yasa mazan ma dukka turawa ne, irin wannan shiga ba bako bane a wajensu, shi ne ma dama shigar matan kasarau, to amma ai yanayin jiki da halittar diri daban daban. Palo suka fito, babu kowa a palon sama, dan haka sai suka nufi kasa, dukkansu suna sanye da ƙaramin hijabi please call me, sai murna suke yi, baki ma ba zai iya faɗen farincikin da bayin Allahn nan suke a ciki ba. A palon kasa suka zauna suna hira, Mark na kitchen yana ta faman aikinsa, sai kallonsa Akila take yi, taga farin Bature tas babu mix. A ɓangaren Gidan Abbo kuwa........ ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E11-12 A ɓangaren Gidan Abbo kuwa. Bayan kwana biyu. A cikin wannan kwana biyun sun yi muguwar sabo a tsakaninsu, Aafia ta saki jiki sosai da shi, ya mantar da ita abin da yake damunta a ranta, har wa yau kuma Abbo dai shiru, ba shi ba labarinsa, kuma su dukka ba wanda ya sake tunawa da zancensa, abin kamar almara, ya rufe masu babinsa a bakunansu da kuma zuƙatansu. Soyayya mai tsabta suke gudanarwa a tsakaninsu, sai dai fa tun daga wannan sumbata ɗaya da ta yi Mashi, ba wani abin da ya sake haɗa su, sai dai ya zauna ya yi ta zuba mata hira yana sanyata nishaɗi, Ummi na matikar kula da Aafia tamkar ita ta haifeta, ko ban faɗa ba kunsani, ta fi Hjy Hadiza sau dubu, dan ita dai Hjy Hadiza bata kula da ƴaƴan ba, kenan abin da nake nufi a nan shi ne, Ummi tana kula da Aafia fiye da uwar da ta haifeta. Ba laifi Aafia na ƙoƙarin shiga kitchen ta taya Ummi aiki, suna yi suna hira, wani lokaci Nawid yana shigowa ya taya su, Ummi ta yi ta tsokanar shi wai yanzu kam ya san hanyar kitchen kenan, da sai dai ya zauna yana isar mutane da Ummi kaza zaki dafa mana yau, yanzu kuma har da shiga kitchen dan ya yi mata, kamar wani jikarta haka Ummi ke tsokanar shi, sai dai ya yi ta Murmushi dan bai san me zai gayawa Ummi ɗin ba. Rayuwarsu abin burgewa da ban sha'awa, sun mai da Ummi kakansu, idan suna wani wasan ba zaka so su dai'na ba, saboda burgewa da ban sha'awa. Kwance take a saman gado da misalin karfe huɗu na yamma, Nawid baya nan, ita kaɗai ce, Ummi na ɗakinta, gabaɗaya ko'ina a gyare tsab, sai kamshi yake tashi. Sanye take da doguwar riga mai shegiyar kyau, launin pink color, duk kuma kayan jelly ce, Ummi ta ce sai sun huta, su shirya zuwa sayan mata kayan lefenta, shiyasa take amfani da na jelly tun da suna yi mata daidai. Tayi simple make up a face nata, sai tashi wani irin fitinannen kamshi take yi, ta ɗaga kai sama da alama wani abin take tunani, karar ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faɗa. A nutse ta miƙa hannu saman bedside drawer ta ɗauko wayar. Umaisha itace mai kirar tata, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ɗauki kiran. "Hello Umaisha". Ta faɗa tana miƙewa zaune a tsakiyar gadon. "Aunty Afi ina ta jiranki tun shekaran jiya baki kirani ba, Allah ma yasa bamu samu damar zuwa gida ba, amma kuma naji yaya Akil ya ce yau zamu je, shi ne na kiraki in ji hukuncin da kika yanke, in ɗaukawa Ommu kuɗin ne ko yaya? Wlh ina jin tsoro sosai". Tana magana tamkar zata yi kuka. "Umaisha shi ne ko sallama babu bare gaisuwa? Ki natsu mana". Kamar zata saka ihu ta ce "Kiyi hakuri Aunty Afi, ina cikin matsananciyar damuwa ce, shiyasa ma na manta da wata gaisuwa, to ina wuni yasu yaya Nawid?". "Lafiya lou ya yaya AKil?" "Yana nan lafiya". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Kina ji Umaisha? Magana ta gaskiya dama ina son in kiraki, kasan cewar kwana biyun nan Yaya Nawid yana nan bai fita bane yasa ban kiraki ba, dama ina Allah Allah kada ki ɗauki kuɗin, to Alhadulillah da Allah yasa ma baku je gidan ba, yanzu dai abin da nake so da ke shi ne, idan kunje gida ki gayawa Ommu yaya Akil bashi da kuɗi, bai ajiye a gida ba, amma duk ranar da ya kawo kuɗin gida, zaki ɗebo mata ko nawa take so, kinga idan kika gaya mata haka ba zata ce kinki ɗauko mata bane, ba zata ɓata rai ko ta yi fushi dake ba, kinga bata isa ta ce a ciro mata a account nashi ba, dole ta hakura ta jira sai ranar da ya kawo kuɗin gida, kafin lokacin kuma zamu nemo wata shawara, amma ba Ommu ba kome zai faru kada ki kuskura ki saci kuɗin mijinki, kai bana mijinki kawai ba, na kowa da kowa ma, kada ki yarda ki ɗauki abin da ba naki ba, duk wanda ya roƙe ki abu, idan ya fi karfin aljihunki, sai ki bashi hakuri babu wani zancen ɓoye ɓoye, kuma duk wani abu idan ya taso kada ki kuskura ki yi gaban kanki, ki gaya mani ko ki gayawa yaya Irfan, idan ba zaki iya gayawa Abbi da yaya Akil ba, kina ji na ko?". Dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali. "Aunty Afi na ji daɗi sosai, kuma ina godiya ga Allah daya bani ƴan uwa masu ƙaunata, nagode da shawararki a gareni, zanyi amfani da ita In Sha Allah". "To shikenan mummyn Abbi in ji yaya Akil na ba, zan ji daɗi fa sosai idan yaya Akil ya cika alkawarinsa ya yi wa Abbi takwara". Dariya sosai Umaisha ta yi, tana matikar kaunar cikin nan nata, ko in ce suna matikar kaunar kayansu ita da mijin nata. Da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin ɗakin, ganin shi yasa ta ce da Umaisha za su yi waya anjima, da haka suka yi sallama. Ɗaura wayar saman bedside drawer ta yi tare da miƙewa da sauri ta nufe shi tana murmushi, sai wani lumshe idanu yake yi alamar a gajiye ya dawo, sanye yake da kayan aikinsa, daga ta ciki kuma suit baki ne kafin ya ɗaura rigar tasu ta likitocin, hannunsa na riƙe da bakar jaka mai shegen kyau, while kafarsa na sanye da cover baƙa, daga ciki kuma bakar safa ce a ciki, ya fito a cikakken likitansa. Karisawa wajensa ta yi tana kara faɗaɗa murmushinta, shi ma murmushi yake sakar mata tare da buɗe mata hannu akan ta yi mashi oyoyo, kin yi mashi tayi, tana zuwa ta karɓi jakar hannunsa, zata juya ya yi maza ya riƙota. "Ina zaki je ba tare da kin yi mani oyoyo da kuma sumbata na welcome back ba?". Kasa ta yi da kanta bata ce mashi komai ba. "Haba matata, na fa gaji sosai, kuma nasha wahala, amma shi ne zaki zo ki karɓi jaka kawai, ba wani ɗan sumbata? Baki san cewa idan kika sumbace ni zan ji gajiyar ta gudu mani ba? please mana". Ya kai karshen maganar a ɗan shagwaɓe. Bata san lokacin da ta juyo ta rungume shi ba, ya iya magana sosai, ta haka kuma yake bi da ita, har ya sanya ta ta yi abinda bata yi niya ba, ta haka yake kore mata duk wata damuwarta, ya mantar da ita komai. Sosai ya sanya hannu biyu ya riƙota da kyau, tare da kara matseta a jikinsa yana mai jin tsantsar farinciki yau ta rungume shi. Sun ɗan jima kaɗan a haka, kafin nan ya sanya hannu ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, idanunta a lumshe. "Kinyi kyau over my mata". Ya faɗa kasa kasa. Duk da idanunta a rufe, sai da ta saki haɗaɗɗen Murmushi, da yawan mata suna son ace sun yi kyau, shi kuma ya kware wajen iya yabon mace, shiyasa ma ta yi saurin kware mashi haka. "Saura sumbata, ko dai yau za'a bani har da kiss ne?". Ya yi maganar cikin sigar zolaya. "Ni fa yaya Nawid ban iya ba". Ita ma cikin sigar zolaya ta yi maganar. "In koya maki ne? Kin bani dama?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. Wani irin daɗi ya ji sosai tare da sakin haɓar tata ya saketa yana faɗin "Bari na yi wanka to, ko dai zaki tayani yi ne?". Da sauri ta juya ta bar wajen tana faɗin "A'a zan dai fitar maka da kayan sakawa, daga nan kuma na ɗauko maka abincinka". Murmushi ya yi tare da karisawa ciki ya fara rage kayan jikinsa. Ita kuma bayan ta ajiye jakar a mazauninsa, sai ta wuce ta fice daga ɗakin ta nufi Palo, binta da kallo ya yi yana mai jin kaunarta na ninkuwa a ransa. Abinci ta ɗauko mashi, da yake yanzu a ɗaki take kawo mashi abinci su ci a tare, Ummi ce ta ce su rinka ci a ɗaki, dan ta lura da shi Nawid yana son suna cin abinci suna wasa da dariya tsakaninsu na masoya, ita kuma Aafia tana jin kunyar yin hakan a gaban Ummin, da yake Ummi mace ce mai adalci, ga lura, sai ta gane hakan, dan haka sai ta ce A'AFIA ta rinƙa kai masu abincin cikin ɗakinsu suci a tare. Lokacin da ta ɗauko abincin ta dawo ɗakin, har ya cire kayansa ya shiga toilet, saman Chinese carpet dake tsakiyar ɗakin ta ajiye masu abincin tare da miƙewa ta nufi drawer kayansa dan fitar mashi da kayan sakawa. Kananan kaya na shan iska ta fitar mashi, a saman bed nasu ta ɗaura kayan, ita ma ta kwanta a gefen kayan tana jiran fitowarsa. After some minutes ya fito ɗaure da towel a kugunsa, tsayuwa ya yi a wajen drawer kayansa tare da zuba mata ido, ita kuwa tana jin fitowar shi, amma taki ɗagowa ta kalle shi. "Mrs Nawid yanzu dai ba za'a taya ni sanya kaya ba?". Gyaɗa mashi kai ta yi tana daga kwance, har lokacin kuma taki ɗago kai. Bai sake magana ba ya kariso wajen gadon, kayansa da ta ajiye mashi ya ɗauka yana mai bin kayan da kallo, har cikin ransa ya ji daɗin kayan da ta fitar mashi, hakan ya nuna lallai tana da kula sosai, a ɗan zamansu kwana biyun nan, har ta fahimci irin kayan da yake son sanyawa idan yana gida, abin ya sanya ya kara jin sonta a ransa. Toilet ya koma dan baya son yin duk wani abin da bata so, yasan ba zata ji daɗi ya sanya kaya a cikin ɗakin tana ciki ba, tun da ba sabawa sosai suka yi ba, hakan yasa ya wuce toilet abinsa, kuma shima a yanzu dai ba zai iya sanya kaya a gabanta ba. A yadda ya barta a haka ya sake fitowa shirye ya sameta, gaban mirror ya tsaya domin ya shafa mayukansa. "Mrs Nawid ki zo ki taya ni shafa mai, idan ba haka ba, Allah zan yi maki alluran barci, dan tun da ba tayani aiki zaki nayi ba, gara kawai idan na dawo na rinƙa yi maki alluran barci sai nayi aikina ni kaɗai, kuma bayan haka zan ɓata dake tun da kina da son kai, ni in tayaki aiki, ke kuma baki son tayani ko?". Cikin zolaya ya yi maganar yana mai taje gemunsa. Miƙewa ta yi tare da zuro kafafunta kasan gadon, kafin nan ta miƙe gabaɗaya, gabansa ta isa ta tsaya tana mai ɗauko Lotion da yake amfani da shi. Da mamaki yake kallonta, bai yi zaton zata shafa mashi ɗin ba, ya zolayeta ne kawai, ashe dai zata yi mashi ɗin, a lallai yau rana ce ta Sa'a a gare shi. "Zan iya rungume matata?" Ya faɗa kasa kasa, shiru ta yi Mashi, mamaki ma yake bata, wai komai zai yi mata sai ya tambayeta sai ka ce ita ta aure shi ba shi ya aureta ba. Ɗan shafa gefen fuskarta ya yi yana mai kara faɗaɗa murmushin kan fuskarsa, ita ma sai murmushi take yi ta wani yi kasa da kai tana murza mai a hannunta. Jawota jikin nasa ya yi, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna. "Dama kin ce na koya maki kiss da sumbata ko?". Shiru ta yi mashi tana runtse idanunta. "To buɗe idanu mu kalli juna sai na koya maki daki daki ta yadda zaki fi iya ɗauka da kyau". Ƙin buɗe idanun nata ta yi, har lokacin kuma tana Murmushi. A hankali ya rankwafo da kansa tare da haɗe fuskokinsu waje guda, jin tana iya shakar numfashinsa ne yasa ta razana sosai, nan take abin da ya faru a baya ya dawo mata sabo, a kiɗime ta fara ƙoƙarin kwace kanta daga gare shi, kara kankameta ya yi, dan shi bai kawo komai a ransa ba, ya yi zaton bata saba bane yasa take son guduwa. Ba tare da ya yi magana ba ya ɗaura bakinsa a saman tata, a nutse ya fara kissing nata, tun tana mutsu mutsu tana neman kwace kanta, har ta hakura ta natsu tsit a jikin nasa, shi kuwa lafiyayyar kiss yake bata tare da kara matseta a jikinsa, sai faman sauƙe numfashi da sauri sauri yake yi, hankali ya kwanta, abin nema ya samu. Sun ɗan jima a haka, ta natsu shiru, duk wasu ƙofofi da gaɓɓai na jikinta suna karɓar wannan daddaɗar saƙon da yake aika masu da shi, tuni ya sanya ta fara fita a hanyacinta. Can ta yi nisa bata jin shi sosai, kamar daga sama ta ji sauƙar hannunsa a kirjinta, wani irin bugu kirjinta ya bada, ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi. Can kasa kasa ta jiyo muryarsa bayan ya zame bakinsa daga nata. "Please kada ki hanani taɓawa, na yi maki alkawari ba zan kai hannuna ciki ba, a iya rigar kawai zan shafasu, bana son ɓacin ranki, idan har baki son na taɓa to na hakura". Allah sarki shi kuma yana ƙoƙarin saka ta farinciki ne dan yana tunanin tana cikin kunci anyi mata auren dole, auren da bata shirya ba, bata san shi ba rana ɗaya kawai aka haɗa auren, ranar da ta fara ganin shi, a ranar ta zama mallakinsa, hakan yasa yake binta a hankali dan ya koya mata son shi, a nasa tunanin fa kenan, abin da bai sani be shi ne, ta jima tana dakon soyayyarsa. Jin abin da ya ce yasa tayi shiru ta natsu, dan kyautatawa iya kyautatawa yana yi mata, koda yaushe bashi da wata burin da ta wuce ya ganta tana murmushi tana farinciki, dole ita ma ta yi ƙoƙarin sanya shi farinciki. Kamar yadda ya faɗa hakan ya yi, bai saɓa maganarsa ba, suna daga cikin rigar ya rinƙa matsasu yana wasa da su, ya kankameta sosai a jikinsa, Allah kaɗai yasan me yake ji, shekarunsa 28 to 29 a duniya yanzu. Sun jima a haka kafin ya saketa ya juya ya nufi toilet ba tare da ya bari sun haɗa ido ba, da alama kunyarta yake ji. Ita kuma, da kyar ta koma saman gado ta kwanta tare da lumshe idanunta tamkar mai yin barci, ban da ajiyar zuciya babu wani abu da take sauƙewa. After some minutes. Wanka ya sake yi tare da shiryawa cikin wasu kananan kayan, sai dai a wannan karon ba ita ta fitar mashi da kayan ba, shi ya zo ya fitar da kansa, ita tun da ta kwanta ta kasa sake motsawa. Bayan ya kammala shirinsa tsab, ya kariso gaban gadon, a hankali ya zauna kusa da ita tare da sanya hannunsa ya fara shafa gashin kanta, da yake kwanciyar da ta yi yasa ɗan kwalinta ya zame kasa, gashinta ya bayyana. "Tashi muje na baki abinci ko matata?". A nutse ya yi maganar, har lokacin taki buɗe idanunta, dan bata san da wani ido zata kalle shi ba. "Yaya Nawid naƙoshi". "Ban yarda ba, kiyi hakuri kin ji? Na san abin da nayi maki ne yasa kika ce haka, to na tuba bazan sake ba, yanzu dai yinwa nake ji, please ki tashi muci ko?". Shiru ta ɗan yi Mashi kafin ta ce "Yaya Nawid da gaske ba zan iya ci ba, kai kaci kawai". Ɗan kwantowa kaɗan ya yi tare da ranƙwafo da kansa daidai saman tata, har suna iya jiyo numfashin juna. "Idan baki ci ba, wlh nima ba zan ci ba, dan Allah kiyi hakuri, na ce maki ba zan kara ba kin ji ko?". Ya kai karshen maganar yana mai gangaro da hannunsa zuwa saman wuyarta. "To yaya Nawid ai kunyarka nake ji ne, ni gaskiya ba zan iya buɗe idanuna na kalleka ba" Murmushi ya yi tare da cewa "To tashi kizo, nayi alkawarin ba zan kalleki ba, zan rufe idanuna ko kuma na kawar da kaina a duk lokacin da na kawo maki spoon ɗin abincin bakinki". To ta amsa da shi tare da miƙewa zaune, shima miƙewa ya yi suka sauƙo daga saman gadon zuwa kasa. Ita ta zuba masu abincin, sai kallonta yake yi, ya kasa cika alkawarin da ya ɗauka na ba zai kalleta ba, ita kuma taki yarda ta kalle shi. Bayan ta gama zuba masu, sai ta zauna a gefensa kamar yadda suka saba zama. Ɗaukar spoon ya yi tare da ɗebar abincin ya kai mata saitin bakinta yana mai tsareta da ido. "Ni yaya Nawid zan ci da kaina". Ba musu ya juya abincin izuwa bakinsa, ɗaukar nata spoon ɗin ta yi suka fara ci a tare, abin gwanin ban sha'awa da burgewa. Bayan sun kammalaci, ta miƙe ta kwashe kayan abincin zuwa Palo, lokacin da ta dawo, ta samu yana waya, shiru ta tsaya kusa da shi tana jin muryar macen da ke fitowa daga cikin wayar tasa, wani irin kululun bakin cikine ya turnuke mata maƙoshi, bata bari ya kammala wayar ba ta fusge tare da bin screen ɗin wayar da kallo. Bata kai ga kallon sunan da ya rubuta ba, sai gani ta yi ya miƙe yana ƙoƙarin kwace wayar, da gudu ta nufi waje bata bari ya kwace wayar ba. Ba ƙaramin daɗi ya ji ba, ta fara kishin shi, kenan ta fara son shi, dan shi idan baku manta ba, yana ganin kamar dole aka yi mata, kuma hakan ya sa ya zage yake koya mata son shi. Da sauri ya bi bayanta, a palo ya sameta zaune kusa da Ummi, tamkar ba ita ce ta karɓe mashi waya yanzu ba, kai kallonsa ya yi izuwa kan hannayenta, babu wayar mamaki ne ya kama shi, ko'ina ta kai wayar oho. "Zo mu tafi ina da magana dake". Ya faɗa yana satar kallon Ummi, make kafaɗa ta yi alamar ba zata zo ba, kashe mata ido ɗaya ya yi tare da ɗan karkata mata kai alamar ta yi hakuri ta zo suje. Gyarawa ta yi ta kwantar da kanta a saman cinyar Ummi tana mai da kallonta izuwa saman Tv da Ummin ke kallo, ba zata zo ɗin ba kenan. "To shikenan bani wayata fita dama zan yi, kiran da ki ka ga anyi mani nan, wata patient a ka kawo a asibiti, abin na gaggawa ne, kuma ni kaɗai ne zan iya dubata, dan haka zan je wata kila na dawo yau, wata kila sai safiyar gobe". Ya kai karshen maganar yana miƙa mata hannunsa akan ta bashi wayar. Ɗan satar kallon Ummi ta yi kafin ta miƙe tsaye ta nufi hanyar ɗakin nasu ba tare da ta yi magana ba, murmushi ya saki while ita ma Ummi murmushin ta yi, tana faɗi a ranta cewa, ai ba zata sake shiga tsakaninsu ba, jiya haka suka yi mata, a kitchen suna aiki ya shigo wai zai taya su, A'AFIA na ɓare maggi zata saka a miya, da ya sanya hannu zai taya ta, sai ta ce "Ummi ki ce yaya Nawid ya bar mani kayana bana soz bai iya ba, baya ɓarewa dukka, yana barin sauran Maggi a ciki". Ita kuwa Ummi sai ta shiga, ta ce ya bar mata kayanta, ai kuwa kafin ta gama ɓare maggin nan ita da kanta ta ce "Yaya Nawid to ɗauka muyi bibbiyu". Daga nan Ummi ta fita harkarsu, bata shiga faɗarsu, yanzu ma da ta shiga ta ce A'AFIA bazata je ɗakin ba ko makamancin haka, ai da sun sake bata kunya, tun da ga shi dai ta miƙe ta wuce ɗakin dan kanta, so ba'a shiga tsakanin mata da miji, idan ma mace ta kawo maki kukanta akan mijinta, kiyi mata addu'a kawai ki bata hakuri, wlh idan kika kuskura kika tayata zaginsa da faɗar laifinsa, tofa zata iya biye maki a lokacin tun da sun yi faɗa da mijin, amma kuma da zarar sun shirya, ki tabbatar abin da kika faɗa na zaginsan nan tsab a kunnensa zata gaya Mashi, idan munafuka ce ma, wlh sai ta kara da karya, kuma zata yi ta riƙe ki a rai na kin zagi mijinta, haka dayawan mata suke, Allah dai yasa mu dace mu kuma gyara. Bin bayanta ya yi, a tsakiyar gado ya iskota ta kwanta ruf da ciki tare da kifa kanta a kan pillow. Saman gadon ya haye shi ma, a hankali ya sanya hannu ya ɗago kanta, Subhanallah zaro idanuwansa waje ya yi yana kallon yadda take hawaye sharɓa sharɓa. "Aafia lafiya kike kuka? Me ya faru kuma?" Ya yi maganar fuskarsa ɗauke da damuwa tare da kulawa a gareta sosai. Shiru ta yi mashi ba tare da ta yi magana ba. "Dan Allah matata ki gaya mini, shin nayi miki wani laifi ne?" Ya kai karshen maganar tare da ɗagota da kyau ya mannata da kirjinsa. "Yaya Nawid kwana fa ka ce zaka je kayi a asibitin, kuma fa ai naji mace ce fa ta kira ka, daman kenan akwai number mata a wayarka?". Allah sarki da yake ta jima tana som shi, hakan yasa take bala'in kishin kayanta, shi kuma bai san hakan ba. "Am so so sorryyyyyyyyyy Matata, na tuba, yanzu dai to tashi muje Asibitin tare domin ki ganewa idanunki, ayi komai a gabanki, mu je tare kuma mu dawo tare ko, amma ki yi shiru dan bana son kukanki". Cikin sauri ya ɗago tana kallon shi, jin ya ce zasu je hospital a tare, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, ganin ta tsare shi da ido ne yasa ya jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abin da ya ce. Cikin sauri ta diro kasa saga saman, ta nufi waje tana murna, miƙewa shi kuma ya yi ya hau shirin zuwa hospital ɗin. Tana fita ɗakin jelly ta wuce, har lokacin Ummi tana Palo tana kallonta. Hijabin jelly ta ɗauko tare da wasu kayan, doguwar riga abaya fara tas, da mayafinta, ta sanya rigar, ta ɗaura mayafin a matsayin ɗan kwali, ta ɗaura ɗan hijabin please call me ɗin a saman, shi ma hijabin fari ne tas, ta yi kyau sosai abinta. Lokacin da ta dawo ɗakin shi ma ya kammala shi, hannunta ya riƙo a kan su tafi, karɓar jakar hannunsa ta yi tare da rataya shi a kafaɗarta, suka nufi waje. A Palon suka tsaya suka yi wa Ummi sallama, addu'a ta yi masu tare da fatan nasara da kuma a dawo lafiya, sosai dai ta yi masu addu'a, sai Amin Amin suke amsawa da shi. Suna fita harabar gidan ya ɗan rungumota a jikinsa, lokacin kuma karfe 6 daidai gari ya ɗan yi duhun mangariba. Da kansa ya buɗe mata gidan gaba na motar ta shiga, bayan ya mai da marfin ya rufe, ya zagayo ta mazaunin driver, ya shiga ya zauna. Zuba mata idanu ya yi ba tare da ya kunna motar ba, jin shiru bai tashi motar ba yasa ta ɗan ɗago dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa idanu, ƙasa ta yi da kai tana Murmushi. "Me ya yasa ki murmushi?". Girgiza kai ta yi alamar babu komai. Matsowa kusa da ita ya yi tare da rankwafo da kansa sai tin tata. "Kin taɓa ganin anyi abu babu dalili ne?". Nan ma dai girgiza mashi kai ta yi alamar a'a. "To menene dalilin?" Nisawa ta yi kafin ta ce "Saboda kayi kyau sosai ne yasa nake murmushi, amma kuma....." Sai ta yi shiru. "Amma kuma menene? Ki karisar da maganar mana?" "Amma kuma bana son wata ta ganka a haka, bana son taga kyan da kayi". "Kenan kishi kike yi?" Girgiza mashi kai ta yi alamar A'a. "Menene wannan idan ba kishi ba?" "No yaya Nawid ba kishi bane, kawai ina kula da kai ne, wai ka manta amarka a ka bani ne?" Zaro ido ya yi yana kallon yadda take zaro magana kamar ba ita ba, eyee wato Amanar shi aka bata, kai jama'a, wasa wasa ita ma ta iya magana sosai. "E kam gaskiya ne, tun da amana ta a ka baki, dole ki kula da ni sosai, yanzu dai bani sumbata sai mu tafi ko? Lokaci na kurewa". Kara faɗaɗa murmushinta tayi tare da matso da ɗan bakinta sai tin kumatunsa da nufin ta sumbace shi. Sai da ya bari ta kawo bakinta, sai ya juyo da face nasa ta sumbace sa a saman lips nasa, tana ƙoƙarin zamewa ya riƙota tare da zura harshensa a cikin bakin nata, ya fara kissing nata. Sun ɗan jima a haka kafin daga bisani ya saketa tare da kunna motar yana wani lumshe idanu, kumawa ta yi ta jingina da jikin kujerar motar, ita ma ta lumshe idanunta kamar mai barci, wani azababben son shi ne ke kara ninkuwa a cikin zuciyarta. A hankali yake tukin, duk bayan minti sai ya juyo ya kalleta, har lokacin idanunta a lumshe. Kasancewar suna tuƙi a hankali sai ya sa basu isa Hospital ɗin da wuri ba. Har suka isa kuma, ta ki yarda su haɗa ido, a tare suka fito suka jera zuwa ciki, sai janta da hira yake yi, tun bata biye mashi sosai, har ta fara biye mishi, dayawa daga cikin nurses ɗin sun yi zaton kanwasa ce, domin basu san ya yi aure ba, kuma akwai kama ta jini a kan fuskokinsu, idan baku manta ba, da Hjy Turai da Hjy Hadiza ƴa da kanwa ce, dole za'a samu kama ta jini. Kai tsaye office nasa ya wuce. Bai kai ga shiga cikin office ɗin ba wasu nurse guda biyu suka nufo shi da sauri, basu bari sun gama karisowa ba suka fara gaya mashi halin da matar da zaayiwa aiki take ciki. Dawo da kallonsa kan Aafia ya yi, cike da kauna ya ce "Ki shiga office ki jirani ko, Bahijja ki raka ta, ki zauna ki kula da ita, ke kuma Ameera muje zuwa ɗakin da aka kwantar da matar". Ya kai karshen maganar tare da wucewa gaba. Wadda aka kira da Ameera ta bi bayan shi, ita kuma Bahijja ta yi gaba tana faɗin "Ke muje ko?". Binta da kallo Aafia ta yi kafin ta maido da kallonta izuwa kan mijin nata, bata kula Bahijja ba har sai da ya kurewa ganinta, sai binta da kallon banza da raini Bahijja take yi, dan bata taɓa tunanin Aafia matar Dr bane, tun da basu ji labarin auren nasa ba, abu ne da aka yi shi lokaci guda. Sai bayan ya kurewa ganinta ne ta tura kofar office ɗin ta shige, bayanta Bahijja ta bi, ta je zata zauna a ainahin kujerar da yake zama, Bahijja ta daka mata tsawa akan wai ta dako kujerar da patient suke zama ta zauna, kujerar Dr iya shi kaɗai ne yake zama a kai. Da yake Aafia ma yar yi ce, ko kallon in da take bata yi ba, domin Bahijja bata kai ta ɗaga idanu ta kalle ta ba, wucewa ta yi ta zauna a saman ainahin kujerar tasa. "Ke baki da hankali ne? Ina matsayin P.A na oga zan yi maki magana ki ki kulani, kanki ɗaya kuwa? Na gaya maki ba wanda yake zama a kujerar Dr sai shi kaɗai, dan haka ki dawo wajen da patient ke zama ki zauna, idan ba haka ba ranki in ya yi dubu zai ɓaci yanzun nan". Har lokacin Aafia bata ɗago ta kalleta ba, sai ma ɗauko wayarta da ta yi tana latsawa. Bahijja ta fusata iya fusata, tun da ta kalli Aafia dama ta ji ta tsaneta, bata sonta, tana tsoron ta ce zata yi mata wani abu kuma, ya zamana suna da kusanci sosai da Dr ya yi mata hukunci, hakan yasa ta zauna a patient chair tana cika tana batsewa, ba dan ta so ba ta hakura. Ita kuwa Aafia ko a jininta, ranta fes, sai ma massage ta yi wa Nawid akan tana son shan black tea kafin ya shigo, yana ganin massage ɗin shi ma ya yi wa Bahijja massage a kan ta haɗawa matarsa Black tea ta bata kafin ya zo. Ba ƙaramin razana ta yi ba lokacin data ga massage ɗin nasa, wai a haɗa wa matarsa tea, kenan Aafia matar sa ce? Ta tambayi kanta, "Kai ina ba matarsa bace, sai dai wadda yake son aura, tun da bamu ji ance ya yi aure ba" ta sake faɗa a cikin zuciyarta tare da miƙewa ta nufi wajen wani kyakkyawar show glass dake cikin office ɗin, kayan tea ne kala kala a ciki. Ruwan zafi ta fara jonawa a hitter, kafin ta haɗa komai da zata buƙata a cikin cup mai shegen kyau. Duk abin da take yi Aafia tana jinta, kawai ɗagowa ta kalleta ne tana ganin kamar bata kai wannan matsayi ba, ta fi karfi kula irinsu Bahijja, dama idan baku mance wace ce Aafia ba, kun san ta akwai ta da jiji da kai, abin da ya faru da ita ne ma yasa ta yi sanyi, ta dawo kamar ba ita ba. Cikin girmamawa Bahijja ta miƙo mata cup ɗin tea ɗin bayan ta kammala haɗawa kenan, bata karɓa ba, sai ta nuna mata saman table ɗin a kan ta ajiye a wajen, hakan ma sai da ta ɗauki ƴan sakanni kafin ta nuna mata ɗin. Haushi tamkar Bahijja ta yanka mata mari, wata ƴar siririya da ita kamar bulala ƴar yarinya da ita Dr ya kawota tana yi masu iskanci, cewar Bahijja a cikin zuciyarta. Ba yadda zata yi, haka ta ajiye mata tare da komawa mazauninta, ta zauna tana mai huci, ko kala Aafia bata ce da ita ba. Suna a haka har aka yi sallar mangariba da isha, a cikin office ɗin Aafia ta yi sallah kasan cewar akwai komai a ciki, ita kuma Bahijja nata office ɗin na P.A da yake kafin ka shigo cikin office ɗin Nawid ɗin, to a nan nata office ɗin yake, a nan ta je ta yi sallah ta dawo, domin Nawid ya ce ta kula mashi da mata sai ya gama aikinsa ya dawo sannan ta wuce, kada ta kuskura ko ƙuda ya taɓa mashi mata............... To fa🤔 Suna zaune shiru kamar kura me, Aafia ta jingina kai da jikin kujerar tare da lumshe idanu kamar mai barci, ita kuma Bahijja tana ta kare mata kallo, tana son taga dame Aafia ta fita ne?. Mata kenan matsalar mu kenan, kowa so take a ce tafi kowa, da zarar mata sun haɗu zasu fara kallon junansu dan suka da me wata tafi su, kowa da irin rayuwarsa, kowa da kalar baiwar da Allah ya yi Mashi, naki baiwar daban, ita ma tata daban, wata kilama baiwarki ta fi tata tsada, kowa da abin da yafi a halitta da kuma rayuwarsa, so bai kamata ki haɗa kanki da kowa ba, ki sanya a zuciyarki ke fa ta dabance, ke kaɗai ce babu irin ki, sai ki zauna lafiya, kada ki duba kowa, ki sanya kawai ko kin duba ba irinki bace, ki kasance mai duba rayuwarki kullun ba na wasu ba, hakan ne zai baki damar ki zauna lafiya cikin kwanciyar hankali, Allah yasa mu gyara. Suna a haka har Dr ya shigo, jin shigowarsa yasa Bahijja ta ɗago kai tana bin shi da kallo, ita kuma Aafia bata motsa ba. "Mrs Nawid kin yi barci ne?". Sai lokacin ta waro idanunta a kansa. Cool murmushi ya sakar mata "Am sorry na barki zaune ko? Amin afuwa ba zan kara ba, aikin ne ya bani wahala yau, yanzu dai muje gida ko? Dan naga har karfe 9 ta yi". Ya kai karshen maganar yana zame hand gloves da suke hannayensa. "Yaya Nawid jikina ya mutu barci nake ji, ba zan iya tashi ba fa". Tayi maganar cikin sanyin murya. Tamkar wasu Tv haka Bahijja ta mai da su, abin haushi kamar ta shaƙe Aafia har sai ta mutu sannan ta saketa take ji, shi kuwa tamkar bai ga Bahijja ɗin ba, ta matarsa kawai yake yi. "To idan ma ba zaki iya tashi ba, ai ni zan iya ɗaukarki cak ko?". Yana magana yana nufar in da take. "Yaya Nawid ina da nauyi fa". Ƴar dariya ya yi kafin ya ce "A hakan? Yadda kike yar siririyar nan? To idan ma kina da nauyi, ni kuma ina da karfi" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e tana da nauyi duk da take ƴar siririyar. "To bari na gwada maki ki gani ina da karfi". Hannu yasa yana ƙoƙarin ɗaukarta, cikin sauri ta ce "Wasa nake yi, zan iya tafiya". Girgiza kai ya yi yana faɗin "A'a ni ban yarda ba, dan haka kawai ɗaukarki zanyi gara ma ki tsaya". Yau Bahijja dai taga ikon Allah, tambayar kanta take yi, dama Dr haka yake? Dama yana dariya? Dama yana magana har haka? Wato sune dama yake ɗaurewa fuska kenan? Lallai yau taga abin mamaki. Shi kuwa ɗaukarta ya yi kamar yadda ya faɗa suka nufi waje, daidai zai fita ya ce da Bahijja ta rufe mashi office da duk abin da ya dace shi ya wuce gida, daga haka ya fice da ita a kafaɗarsa. Da Ido kawai Bahijja ke binsu da shi har suka fita. Tun da ya fito duk in da ya wuce nurses sai sun kalle shi sun sake waigawa, ba ƙaramin mamaki ya basu ba, sai tambayar kansu suke yi akan yaushe ya yi aure, dayawa daga cikinsu dai sun san bashi da kanwa, shi kaɗai ne wajen Umminsa, to a ina ya samo wannan yarinyar kuma?. Shi kam bai bi ta kan kowa ba, kai tsaye motarsa ya wuce da ita, sai ɓoye fuska na rashin kunya take yi. A gidan gaba ya zaunar da ita, ya zagayo mazaunin driver ya shiga. Kasancewar parking space ɗin akwai ɗan duhu, babu haske sosai, sai bai kunna hasken motar ba, ya lallaɓa a cikin duhu ya jawota jikinsa, sosai ya matseta tare da zura hannunsa ta samar wuyar rigarta zuwa ciki. Bata hana shi ba, kuma bata tashi daga jikin nasa ba, breast nata ya kama ya fara shafasu a hankali yana wasa da su, hannayenta tasa dukka biyu ta rungumo shi, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mashi ba, yanzu ta yi accepted na shi kenan, nan take ya fara wasa da ita sosai son ranshi, bata hana shi ba kuma bata taya shi ba, ta yi shiru tana sauraronsa. Har sai da agogon hannunsa ta buga masu karfe 10 ya yi, sannan ya saketa yana mai da numfashi tare da lumshe idanu, ita ma sauke numfashi take yi a hankali hankali, alamar ta karɓi saƙon nasa. Sun ɗauki ƴan mintoci a haka, wadda a kalla zasu kai 10mins. Da kyar ya iya jan motar suka nufi gida. WANNAN KENAN A ƁANGAREN SU A'AFIA, BARI MU LEƘA ƁANGAREN SU LION WATA KILA KAFIN MU DAWO SU AAFIA SUN ISA GIDA. GIDAN LION💋 Yau dai Akila da Rimsha sun sha hira kamar ba gobe. Sai misalin karfe 2 da rabi Rimsha ta ce da Akila ta shiga ɗaki ta kwanta ta jira ta, bari ta kaiwa Lion abinci, to ta amsa mata da shi tare da miƙewa ta nufi cikin ɗakin. Ita kuma ta nufi Kitchen dan ɗaukar abincin. Kamar kullum, wanke hannayenta ta fara yi kafin tazo ta ɗauki abincin, tana tafiya tana addu'ar Allah yasa ta kai lafiya ta kuma dawo lafiya. A bakin kofar ta tsaya ta yo sallama, daga ciki Areef ya amsa sallamar tata tare da bata izinin shigowa, tattara dukkan natsuwar da Allah ya bata ta yi, ta kutsa cikin ɗakin tana kara yi mashi sallama. Imran, Areef, kwance suke a saman gadon Lion suna hira, while shi kuma oga yana zaune saman sofa yana bincike a cikin laptop nasa. In da ta saba ajiye mashi abincin ta nufa, a nutse ta ajiye mashi tare da ɗagowa ta gaida Areef da Imran, da fara'a suka amsa, dirowa kasa Imran ya yi yana faɗin bari ya je ya ɗauko mata abincinta daga gidan Akil, dan tun ɗazun AKil ya yi mashi massage akan Umaisha ta gama abinci ya zo ya ɗauka mata. Cikin zolaya Areef ya ce zai bishi domin yau ya kalli bakin ƴan uwan Prof da bai sani ba, a zafafe Lion ya ɗago da dara daran blue eyes nasa, tare da wurga mashi wani mugun kallo, alamar baka da hankali ne zaka fita?. Dariya ya kwashe da shi, dama dan saboda Lion ɗin ya ɗago ya yi maganar, yasan ba ta yadda za'ayi ya fita da wannan ciwon nasa haka, amma kuma kafarsa na bala'in kaikayi, yana burin fita, har tausayawa kansa yake yi akan idan ya samu lafiya kalar yawon da zai yi, sai ya kewaye gabaɗaya States na Naija, zai je wajajen tarihi da saurasu, har ya gama tsara kalar yawon da zai yi, addu'ar samun lafiya kawai yanzu yake yi........( To fa lallai Areef ya shirya karewa kasarmu kallo) Shi dai Imran bai ce komai ba, ya sa kai ya wuce abinsa, ita kuma Rimsha zama ta yi tana jiran Oga ya sauƙo ta zuba mashi abincin. Sai da ya ɗauki almost 30 mins yana latsa laptop ɗin, ita kuma tana zaune shiru. A hankali cikin natsuwa ya ɗaura laptop ɗin saman hannun sofa tare da miƙewa ya sauƙo kasa, a in da ya saba zama ya zauna. Ta kasar ido ta saci kallonsa, pajama ce launin fara tas a jikinsa, ya kulle gashin kan nan nasa a bayan wuyarsa, wannan fitinannen daddaɗar kamshin nasa dai kamar kullun take, ba canzawa. Yana zama shima Areef ya sauƙo daga saman gadon, ya kariso in da suke yana Murmushi. Abincin ta fara zuba mashi kamar yadda ta saba. "Our Queen zuba mini nima, amma tare zaki zuba mana dake". Cewar Areef, ya yi maganar yana zama kusa da ɗan uwan nasa, shima dai pajama ash color ce a jikinsa. "Yaya Areef ni ai ban iya cin kalar abincinku ba". Ta yi maganar tana turawa Lion abincinsa da ta gama zuba mashi. Kwaikwayon voice nata ya yi yana faɗin "To ai koya miki ci zanyi my Rimsha". Bata san time da dariya ya kubce mata ba, ba iya basajan wajen aiki kawai ya iya ba, ashe har da kwaikwayon murya ya iya, dan kuwa sak siririn voice ɗin nan nata ya yi, shi dai Lion tamkar babu shi a cikin ɗakin, abincinsa kawai yake ci cikin kwanciyar hankali. "Dariyar me kike yi mini? Dan na kwaikwayi zazzakar muryar nan taki ko?". Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a. "Kinsan me my Rimsha?". A'a ta bashi amsa. "Kina da murya mai shegen daɗi, idan kina magana bana son ki daina, just like uncle Musharraf voice naki yake, shima haka voice nasa yake da zaki, sai dai fa kina magana a sanyaye kamar Lion, ke da Lion sam baku son buɗe baki ku yi magana sosai, i don't know why, ko dai bakinku na yi maku zafi ne idan kuka ɗaga murya?". Yana magana yana satar kallon ɗan uwan nasa, wadda tamkar babu shi a cikin ɗakin. Zuba mashi abincin ta yi ta tura mashi a gabansa tana faɗin "Yaya Areef nifa wlh kawai ban san ya akayi maganata take a haka ba". Sai da ya bari ta gama zu ba masu abincin, ta turo masu, sannan ya kira Aseef video call dan su takurawa Lion, yau sai sun sanya shi ya canza magana, dole ya barta ta koma school, yarinya yar karama ace ba zata rinƙa zuwa school ba, cutar ta zaayi. Ya danna video call ɗin yana faɗin "A'a akwai dalili dai, sai ku rinƙa magana kamar baku son yi?". Bugu ɗaya Aseef ya katse kiran ya kirashi, hakan zai tabbar maka da cewa haɗa baki suka yi, sun shiryawa Lion kitimurmura, kuma da alama da wuya ya tsallake masu yau, dan sune rauninsa dama. "Da gaske yaya Areef......" Bata kai karshen maganar ba zazzaƙar sexy voice nasa ya daki dodan kunnenta. "Get out". Sun cika mashi kunne da surutu, ba damar ya kori Areef, amma ita yana da damar korinta. Cikin sauri ta miƙe ta nufi waje, tana jiyo voice ɗin Areef yana faɗin "After 30 mins ki zo ki kwashe kayan abincin". Okey ta amsa da shi tare da ficewa abinta. Kada ku mance da Turanci suke magana. Duk abin da ya faru, Aseef yana jinsu, dan Areef ya yi picking call ɗin. Jawo ɗan ƙaramin kyakkyawar table dake wajen ya yi tare da ɗaura wayar, ya jingina wayar da tissue pack, ta yadda Aseef zai ji daɗin ganinsu su biyun dukka da kyau. "My bloods wlh kewarku zata iya yi mini illah fa, please ku dawo ko kuma ni na taho, saura mani Exam har guda huɗu fa, ni gaskiya almost 2 weeks suka rage ba zan iya jira ba, ya yi mini nisa". Lion bai san time da Areef ya kira Aseef ɗin ba, jin zazzakar murya ɗan uwan nasa yasa shi ya ɗago blue eyes nasa daga kan abincin da yake ci zuwa kan wayar. Zubawa Aseef ɗin idanu ya yi yana kallon yar ramar da ya yi, da alama dai yana yawan tunanin ƴan uwan nasa sosai, Allah sarki bawan Allah, tun da suka taso basu taɓa rabuwa su yi nisa har haka ba sai wannan karon, duk ya shiga damuwa sosai, dan ma Musharraf na rage mashi damuwar, amma duk da haka sai da damuwar ta fito ta hanyar sanya shi rama. "Our pleasure muma muna kewar ka sosai, ban taɓa shiga damuwa sosai irin na wannan karon ba, seriously tamkar na rasa wani ɓangare na jikina haka nake ji, amma dai ka kammala Exam ɗin, 2 weeks ai kamar yau ne". Cewar Lion kenan, kuma tun da yake sai yau ya taɓa yin magana makamanciyar hakan, ya yi ne kuma dan ya kwantarwa da ɗan uwan nasa hankali ya samu ya natsu ya rubuta Exams nasa cikin kwanciyar hankali, sannan kuma har ga Allah yana kewar ɗan uwana nasa over, abin na damunsa a rai, dan dai kawai bai da yawan magana ne yasa ba zaka fahimci hakan ba. Nisawa Areef ya yi kafin ya ce "Ni ba zan iya misilta kewarka da nake yi ba my blood, baki ba zai iya faɗa ba, a kullun ina ji tamkar na yi fiffige kawai na ganni a tare da kai". Turo baki ya yi zai fara yi masu shagwaɓa. Har lokacin Lion bai ɗauke idanunsa daga kan wayar ba, ji yake tamkar ya sanya hannu ya fito da ɗan uwan nasa ta cikin wayar su rungumi juna. "Zaka fara yi mana shagwaɓar kenan ko?" Cewar Areef. "Ni ba wani shagwaɓa da zan yi maku, yanzu dai Lion ina son kayi mini wata alfarma ne ka ji?". Shiru bai yi magana ba, sai dai ya ɗaga mashi gera ɗaya alamar ya ji. Shiru shima Aseef ɗin ya yi ya rasa ta ina zai fara. "Aseef abin da nake so da kai shi ne, ka daina yawan tunaninmu da kake yi, bana son ganinka a ramen nan, idan kana son sanya ni cikin damuwa kuma shikenan". Cewar Lion ya yi maganar yana mai da spoon ɗin hannunsa ya ajiye a cikin plate ɗin abincin. "To Shikenan Lion na yi alkawarin zai dai'na duk wata tunani, zan daure yanzu dai please my blood ina son ka bar Rimsha ta rinƙa zuwa school, ma'ana ta daina yi muku aikin safe, ya zamana iya na rana da dare ne kawai zata rinƙa yi muku, kaga yarinya ce, idan aka yi mata wasa da karatu a yanzu to za'a canzawa rayuwarta akalar shi ne, please ni zakayi wa ba kowa ba, idan ka yi hakan zan yi murna sosai wlh". Ya kai karshen maganar cikin sigar shagwaɓa. Ɗaukar spoon ɗin da Lion ɗin ya ajiye Areef ya yi, ɗibar abincin ya yi tare da kawo wa ɗan uwan nasa a bakinsa, buɗe baki Lion ɗin ya yi ya karɓa yana mai dawo da kallonsa kan Areef ɗin, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, cigaba da bashi abincin a baki Areef ɗin ya yi tamkar wasu mata da miji. Kuka Aseef ya fara yi musu a kan lallai shi gobe zai zo, ya za'ayi yanzu shi ba mai bashi abinci a baki, shi wlh ba zai yarda ba, ya gaji, yanzu ba mai bashi first spoon fa. Girgiza kai Lion ya yi, Aseef sai Allah, yana bala'in kaunarsu fiye da tunanin mai tunani. Shi kuma Areef ɗebo abincin ya yi tare da kawowa saitin wayar yana faɗin "Ɗan nema to maza buɗe bakinka na zuba maka, ba dai first spoon ba? To ga shi nan, har ma da last spoon zaka samu, ɗan babynmu, auntar TRIPLETS, sweetien daddy, pleasure Lion, shagwaɓati kuma damuwati na, ciwon kan Uncle T, ciwon cikin Uncle Herry, matsalar Jonh, addabawa rayuwar Jay, wadda mummy ta fi so, dukka kai kaɗai maza buɗe baki, yi sauri......" Bai kai karshen maganar ba ya yi shiru sakamakon damko gashin kansa da Lion ya yi, da ɗan karfi ya ja mashi gashin nasa. "Wash Lion me nayi maka kuma? Ko mugunta zaka yi mini ne nima, kamar yadda kake yi wa sauran mutane". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Me pleasure na ya yi muku da zaka ce mashi ciwon kan Uncle T, ciwon cikin Uncle Herry, me yake yi masu da ya zama ciwon kansu? Me yasa zaka zage shi?". Cewar Lion. "Kai fa Lion ka iya mugunta, kuma baka son gaskiya, ai ka sani, waye Aseef ya raina biyun Uncle T, ba dole ya rinƙa sanyawa uncle T ɗin ciwon kai ba, duk wata tsiyarsa idan ya ɗebo a kansu yake sauƙewa, mu kuma ya zo nan yana yi mana kuka da shagwaɓa." Cewar Areef, yana magana yana ciza laɓɓansa, saboda zafin riƙe mishi gashi da Lion ɗin ya yi. Kara jan gashin nasa ya yi, har sai da ya yasar da spoon ɗin hannunsa ya damko hannun Lion ɗin da hannayensa dukka biyu yana faɗin "Wash wlh wasa nake yi Mishi, ai kowa yasan pleasure ka bawan Allah ne, mumini, shi da ko magana ma baya yi".......... Oh su Areef an ji wuya har ya sauya zance🤣 Runtse idanu Aseef ya yi, har cikin ransa yake jin wannan wash ɗin da Areef yake faɗa, ji yake yi tamkar shi ake jawa gashin ba Areef ba. "My Lion na yafe mishi, ka sake shi, gashin nasa fa zai iya cirewa, ni wlh na yafe mishi, gara ni ka ja nawa gashin ka sake mishi mashi". Yana magana idanunsa a datse, dan baya son ganin face ɗin ɗan uwan nasa cikin jin raɗaɗin zafin da yake ji. Shiru Lion ya yi tamkar bai ji ba, shi kuwa Areef da ya ji azaba da gaske, bai san time da ya sake jiki ya kwanta a cinyar Lion ɗin ba, hakan kuma ta sanya dole Lion ɗin ya sake shi ba dan ya so ba, ba ta yadda zai yi ya cigaba da riƙe gashin yana kwance a jikinsa. Duk da ya sake shi bai tashi daga cinyar tasa ba, sai ma gyara kwanciya da ya yi yana mai da numfashi, shi kuma Lion ruwa ya ɗauro ya fara sha. After 2 mins "Tashi mini a kafata" Ya faɗa a sanyaye. Ƙin tashi ya yi, a kule ya ce "Wlh ba zan tashi ba, kazo ka cire mini fatar kai ne zaka wani ce na tashi, to naki tashi sai ka yi jinyata". "My Areef please ka tashi kada ya sake ja maka gashi, idan ya sake zan yi kuka wlh". Cewar Aseef, ya yi maganar a shagwaɓe kamar zai yi kuka. Ɗan zaro mashi dara daran blue eyes nasa Lion ya yi, har ɗan tsorata ya yi, saboda da ya zaro idanun nasa, har wani kyalli suka kara yi. Sake turo ɗan bakin nan ya yi "Haba mana Lion me nayi maka kuma da zaka tsorata Ni?". Kara zaro idanun nasa sosai ya yi, a sukwane Aseef ɗin ya datse nasa idanun kamar zai yi kuka. Dama abin da Lion yake so kenan, yana son Aseef ɗin ya runtse idanu domin ya yi mashi kallon tsab, ya kalle shi da kyau, dan ya lura da canzawar ɗan uwan nasu. Sosai yake kare mashi kallo, yasan idan idanunsa a buɗe, ba zai taɓa yarda su kare mashi kallo ba, sai ya zulle masu, wai kunyar ganin cikin idanunsu yake ji. Shi ma Areef juyo da kallonsa izuwa kan wayar ya yi ba tare da ya tashi daga kan cinyar ɗan uwan nasa ba. Cikin Harshen larabci Areef ya ce "Serious fa Aseef ya canza sosai, ji wani irin kyakkyawar kyalli da face nasa take yi, kamar wadda ya shafa baby oil, har wani haske fa ya kara yi na musamman, amma fa kamar akwai zazzaɓi a jikinsa". Jinjina kai Lion ya yi alamar yah zancen Areef haka ne. Jin suna magana da wani yare ne yasa shi waro idanunsa waje. Ɗaukar wayarsa Lion ya yi tare da rubutawa Tyrone massage akan ya duba jikin Aseef, idan zazzaɓi sosai ne ya gaya masu, kuma ko me zai faru ya tabbatar bai daka ta Aseef ɗin ba, ya tabbatar ya yi mishi allura, dan Aseef baya shiri da allura ko kaɗan, baya so, sun san halin kayansu. "My Lion ya batun Sister? Dan Allah ina son ta je school, wlh idan ta koma school zan ji daɗin da ban taɓa ji ba". Ya yi maganar cikin marairacewar murya. Ɗan zuro hannayensa shi ma Areef ya yi, sosai ya harɗe ɗan uwan nasa, while kansa har a lokacin yana a saman cikinyar ɗan uwan nasa, sosai ya riƙe shi yana faɗin "Same here, idan ka kyaleta tana zuwa school zan yi murna sosai". A tare suka sake haɗa baki Areef da Aseef wajen cewa "Please mana Our Lion". Da mamaki yake binsu da kallo, sun tsaya tsayin daka a kan Rimsha tamkar suna da wata alaƙa da ita, anya ba wani abin suke shiryawa ba kuwa? Gaskiya yafara zarginsu. Saka shi a gaba suka yi, sun ki barin shi ya ja wani dogon numfashi sosai, daga karshe dai dole ya amsa masu da to ya ji, wani irin miƙewa Areef ya yi tare da rungumo wayarsa wai ya rungumi Aseef, sai dariya suke yi kamar wasu zararru, Allah sarki suna Kaunar Rimsha over, musamman ma Aseef da idan baku mance ba, zuciyarsa yanzu sabuwa ce, duk abin da a ka bashi yasa a cikinta, to fa da gaske zai riƙeta hannu bibbiyu, dan bai san wasa, karya or yaudara ba, soyayya kawai ya sani, bugu da kari yana tare da Musharraf wadda ya kasance shi ne yake kalla a gabaɗaya Washington DC ya ji daɗi, yana bala'in kaunar Musharraf over, kun ga kuwa dole ya so Rimsha fiye da tunanin mai tunani. Ba ƙaramin daɗin ganin su a cikin farinciki Lion ya yi ba, har cikin ransa ya ji cewa idan Rimsha ta shigo ɗakin nan zai ɗaga idanu yaga wai shin wace ce wannan da ƴan uwansa mafi soyuwa a garesa a duniyar nan suke shiga farincikin da bai taɓa ganinsu a ciki ba saboda ita, yau saboda ita suke irin wannan dariya da murna haka, tabbas bai taɓa ganinsu a irin wannan tsantsar farincikinba, suna dariya amma ba kamar na yau ba, ya ji yana son ganin wace ce ita ɗin, dan tun da suke da ita, take kawo mishi abinci, ko a ce take gidan, bai taɓa kallonta ba, bai san ya kamaninta yake ba, dama idan baku mance ba, shi yakan iya jimawa tare da mutun ba tare da ya ɗago ya kalli face nasa ba, to haka rayuwarsa take. Sun ɗan ɗauki tsawon ƴan mintoci a haka kafin Areef ya maida wayar saman table ya ajiye tare da ɗan tsagaita dariyar. Yana ajiye wayar ya juyo ya rungumi Lion ɗin tare da manna mashi kiss a kumatu, kuka Aseef ya sa masu akan lallai shi ma yana son ya yi kissing nasu, jan dogon hancin Areef Lion ya yi, kasa kasa cikin harshen larabci ya ce "Areef kana jawo mana jangwan gwan ko? Ba zaka bar shi ya natsu ya yi karatu ba ko? Yanzu idan ya ce ba zai zauna ya yi Exams ɗin da suka rage mashi kuma ba fa?". Kara mashi wani kiss ɗin Areef ɗin ya yi yana dariya kawai bai yi magana ba. Shi ma Lion ɗin juyowa ya yi tare da sumbatar ɗan uwan nasa a goshi, ya miƙe ya bar wajen ya koma saman bed nasa, dan ba zai iya jure rigimar Aseef ba. Dawo da kallonsa kan wayar shi kuma Areef ya yi tare da kashewa Aseef ido ɗaya, shi ma Aseef ɗin kashe mashi ido ɗaya ya yi, alama suke yi wa junansu akan sun yi nasara. "Aseef zan kiraka later, yanzu dai jeka yi abin da yake gabanka na practical da daddy". Bai jira amsar ɗan uwan nasa ba ya katse kiran tare da miƙewa ya nufi saman gadon shi ma. Har ya kusa kai wa gadon, sai kuma ya juyo ya dawo, Apple wanda ba'a yanka ba gudarta ya ɗauka tare da nufar gadon. Kusa da ɗan uwan nasa ya kwanta tare da kai Apple ɗin halinsa, a hankali ya datseta kaɗan, yana karewa ɗan uwan nasa kallo. "Lion wlh Nigeria ta karɓeka sosai, ni dai ina son kasarnan over, kawai ku barni a nan, kuma kai ma ba zan so ka koma ba, dan serious soft skin naka ta kara kyau". Juyo da blue eyes nasa ya yi izuwa fuskar ɗan uwan nasa, gently ya fara magana. "Kai Areef ban san wani kalar hukunci zan yi maka ba, dan tabbas...." Bai kai karshen maganar ba ya tura mashi Apple dake hannunsa a ɗan bakin nasa, ya danne da karfe ta yadda dole ba dan ya so ba ya datsi Apple ɗin shima. "Wlh Lion babu wani hukuncin da zaka yi mini, dole a kaina ka fara yi wa mutane afuwa, wai kai a tsarinka babu yafiya ne? To idan ma babu ni yanzu na sanya maka". Yana magana yana kara danna mashi Apple a baki. Da ɗan karfi Lion ɗin ya ture shi tare da furzo mashi da Apple ɗin da ya datsa, dariya Areef ya kwashe da shi, ganin yadda ɗan uwan nasa ya kara tsuke wannan ɗan bakin nasa, alamar apple ɗin bata yi mashi daɗi ba, ya haɗe geran sama da kasa, fuska kamar wani hadari. "Kai fa Areef wasa wasa mugu ne, yanzu da ka sanya ni amai fa?". Ya faɗa yana kara ɗaure fuska. "Ni ne kai, in dai a fagen mugunta ne, to ni Areef ni ne Saif". Yana magana yana ɗaga gera ɗaya. A kule Lion ɗin ta kai hannu zai damƙoshi, da sauri ya faɗa jikinsa yana faɗin "Kafin ka riƙoni na kawo kaina". Hakan kuma ya yi daidai da shigowar Rimsha, dan ta zo ta tattare kayan abincin ta fitar. Komawa Lion ya yi ya kwanta yana sauƙe ajiyar zuciya tare da kara jin tsantsar kaunar ƴan uwan nasa, sune farincikinsa, sune komai nasa a duniyar nan. Shi kuma Areef matsowa ya yi daidai bakin gadon, cikin zolaya ya ce "Sister wai ya naga sai kara kyau kike yi ne? Me sirrin ne? Ko da yake ba ke kaɗai ba, ga Lion ma har wani fresh ya kara yi, Kasarku akwai shegen daɗi, da Lion mace ce sai na ce ciki gare shi yasa ya yi wannan kyau ɗin". Yana magana yana guntse dariya, ita ma maganar dariya ya bata, wai da Lion mace ce sai ya ce ciki gare shi irin wannan kyau da ya kara. Tana tsoron yin magana Oga ya koreta irin ta ɗazun, sai ta yi shiru kawai, sai murmushi take yi ta tattare kayan ta fita waje. Tana fita kamar wani walkiya haka Areef ya tashi a guje, abin da ya sanya ya yi hakan kuma, wani wawan damƙa Lion ya kai mashi a wuya, shi ne ya zulle, dama kuma yasan sai Lion ya shaƙe shi haɗa shi da mace da ya yi, da gangan ya yi maganar dama, dan kawai ya tanka. Abin da ya sanya shi kuma Lion ɗin bai kula shi a gaban Rimsha ba, dan baya son kowa ma yasan yana wasa da ƴan uwansa har haka, kun dai san baya son raini, komai shi ne a sama yake so. "Come here Areef". Ya faɗa yana ɗaure fuska. "Wlh i can't, ni zaka yi wa mugunta, ai suɓutar baki ce, mistake ne". Kara ɗaure fuska sosai ya yi "I said come here ko?". Kashe mashi ash eyes nasa ɗaya ya yi tare da ɗaga gera guda yana faɗin "Haba my sweetheart na fa ce maka mistake ne, haba mana son ɗin daddy, ka manta sunan ko? To ban mance ba, yanzu dai serious yau zan haɗa maka Salmon da kai na tun da Aseef baya nan, shikenan ka hakura?". Kawar da kai ya yi gefe guda, har ga Allah ba zai iya yi wa TRIPLETS nasa komai ba, amma ba dan haka ba, wlh da wani ne ya danganta shi da mace, idan bai kashe shi ba kaɗan ne zai rage mashi, dama ko da Areef ɗin ya zo, bai wuce ya ja mashi gashin kansa da karfi kamar yadda ya saba ba, bayan hakan kuma ba wani abin da zai iya yi masu. Shi kuma Areef sarkin daɗin baki, ko ɗaura pot a wuta bai iya ba, amma yana faɗin wai zai haɗa mishi Salmon, ya faɗa ne dan ya sanya ɗan uwan nasa farinciki, yasan shi ne best abincin da ya fiso tun suna yara, kasan cewar Aseef baya son kifi ne yasa ya daina cin Salmon ɗin gabaɗaya, amma ba wai dan baya so ba, har gobe ita ce best food nasa. Komawa Lion ya yi ya kwanta yana sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, lallaɓowa shi ma ya yi ya dawo saman gadon ya kwanta yana faɗin "My blood akwai in da Rimsha zata rakani gobe, please kada ka ce ba zan je ko'ina ba". Idanunsa a Lumshe ya ce ba in da Areef ɗin zai je, ba zai fita ba har sai ya sami sauƙi, marairace murya ya yi tamkar zai yi kuka, ya dage a kan lallai ya sami sauƙi, kin kula shi Lion ya yi, har ya gaji da magana ya kwanta shiru kamar mai tunanin wani abin. A ɓangaren Rimsha kuwa, tana mai da kayan abinicn kitchen ta nufi bedroom nata, yadda ta bar Akila kwance a saman gado, haka ta dawo ta sameta, kwanciya ita ma ta yi suka cigaba da zuba hira, Akila na kara mata lecture a kan soyayya. Suna tsaka da hira misalin karfe 4:30 bayan sun yi sallar la'asar, masoyin ɓoye ya kira Akila, cikin sauri ta ɗauki kiran, tare da manna wayar a kunnenta......... ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E13-14 Suna tsaka da hira misalin karfe 4:30 bayan sun yi sallar la'asar, masoyin ɓoye ya kira Akila, cikin sauri ta ɗauki kiran, tare da manna wayar a kunnenta. "Heartbeat yau fa tun da safe da muka yi magana ba mu sake yi ba, ina ka shiga ne?" Kamar dai kullun kun san a shagwaɓe ta yi Maganar. Daga ɗayan ɓangaren ya amsa mata shi ma a shagwaɓe. "Am so so sorry my heartbeat, nasan na yi laifi, to amma ba Rimsha ta ɗebe maki kewa ba? Ai Rimsha ta fanshi laifi na ko?". Turo baki ta yi tamkar tana a gaban shi. "Yanzu Heartbeat ita kuma Rimsha a ina ka santa? Yaushe kuma kasan mun haɗu da ita?". "Kai heartbeat to ai ita Rimsha kanwarmu ce, yanzu dai bar zancen Rimsha yakika wuni? Ya fama da kewa na?". Shiru ta yi a cikin zuciyarta tana maimaita kalmar ita Rimsha kanwarsu ce? Me hakan yake nufi kuma?. Jin tayi shiru ne yasan ta faɗa duniyar tunani, idan ya canka daidai kuma, tunani take yi a kan maganar da ya ce na Rimsha kanwarsu ce, dan haka sai ya katse mata tunani da cewa "Heartbeat kamar yadda kika ji na faɗa Rimsha kanwar mu ce, yas kanwar mu ce kamar yadda kike kema kanwa a gare ni, abin da yasa nace Rimsha kanwar mu ce kuma, ba komai bane face dan saboda na fita shekaru, kuma kema kin fita shekaru, kin ga kuwa ai kanwarmu ce ni da ke ko? Wai kin manta duk abin da kike so nima zan so shi ne? To idan kin manta na tuna miki, a cikin zuciyata na ji cewa kina Kaunar Rimsha sosai, shiyasa na kirata da kanwarmu kai tsaye". Murmushi ta sakar mashi kafin ta ce "Wai ka saya mini goribar da nace ne?". Kai tsaye ya ce mata "Prof bai kawo ba tukun nan". Da yake bata san waye suke cewa Prof ɗin ba, sai ta ce "Tom shikenan ka ce mishi ya haɗo mini da aduwa". Maimaita sunan aduwar ya yi kafin ya amsa mata da okey. Ita dai Rimsha kamar Tv haka ta mai da su, sai kallon ikon Allah take yi, ji yadda Akila take wani tsuke fuska tana zuba shagwaɓa tamkar wata baby, lallai ma, abin mamaki ma ya bawa Baiwar Allah nan Rimsha. Ita kuwa Akila da alama ta mance da Rimsha a cikin ɗakin, kamar yadda suka saba da sahibin nata, ta zage sai zuba hira da shagwaɓar ta take yi har sai lokacin sallar mangariba suka yi sallama, ɗagowa da zata yi already Rimsha ta yi barci a gefenta, bata san time da ta saki cool murmushi ba. A hankali ta tashi Rimsha ɗin akan su je su yi sallar mangariba ba, da kyar ta iya tashi dan barcin yana a idanunta sosai. Bayan sun yi sallah ne suka koma suka zauna a saman gadon suka cigaba da zuba hirarsu kamar yadda suka saba. Wayar Rimsha dake ɗaure saman bedside drawer ne ya fara kara alamar shegowar kira, kasan cewar Akila ta fi kusa da wayar sai ta ɗauko ta miƙa mata. Anaya ce mai kirar tata, cike da farinciki da zumuɗi ta ɗauki kiran. "Hello Anaya? Ykk?" Da fara'a ita ma Anaya ta ce "Lafiya lou Rimsha yasu Yaya Imran naki?" "Suna nan lafiya lou ina su yaya Feroz da mummy, daddy, Uncle Shitu da Zaira?" "Suna nan lafiya Uncle Shitu gobe da asuba zai je Maiduguri ya duba su Gwaggo Aisha, tun da suka koma Maiduguri basu sake dawowa ba, ina kewarsu wlh, gobe daddy ne zai kai mu school dan ya zo yau, da uncle Shitu ya gaya mashi zai je duba su Gwaggo Aisha, shi ne ya zo dan ya kula da mu kafin uncle Shitu ya dawo nan da kwana biyu". Ta kai karshen maganar tana ɗan dariya. Nasan baku gane suwa ye Anaya take Magana a kai ba, Gwaggo Aisha dai ba kowa bace fa ce Gwaggon Jehan, sai mummyn su Rimsha, na san zaku yi mamakin ya aka yi suka haɗu da Uncle Shitu da kuma daddy Anaya, to ku saurara, ya akayi suka haɗu da daddy Anaya zai zo maku a gaba, shi kuma uncle Shitu dama kun san already yana tare da daddy Anaya kafin su mummy su zo, wai shin menene yake tsakanin Uncle Shitu da su mummyn Rimsha? Uncle Shitu yaya ne ga mummy'n Rimsha, ɗan bappanta ne, sai dai shi Mahaifin mummy Rimsha ya yi wayo ne a Niger ba'a Nigeria ba, tun yana saurayi ya tafi Niger kasuwanci, daga nan bai sake dawowa Nigeria ba har sai da ya auri mahaifiyar mummyn Rimsha wadda ta kasance ƴar Niger ɗin ce, bayan auren nasu ne ya ɗaukota zuwa Maiduguri Nigeria dan taga ƴan uwansa, lokacin da ya zo kuma ya samu yayan sa Mahaifin uncle Shitu ya samu karuwar yaro wato uncle Shitu, a lokacin har ya yi wayo, dan zai shekaru 10 haka, da suka zo komawa Niger ya so komawa da uncle Shitu, amma yayan nasa yaki, ba dan yaso ba ya koma ba tare da uncle Shitu ɗin ba, tun daga lokacin kuma bai sake zuwa Nigeria ba har sai da suka haifi Mummyn Rimsha tana da shekara biyar a duniya suka zo Nigeria, a lokacin uncle Shitu yana da 15 to 16 years, da suka tashi koma a wannan karon, sun tafi da uncle Shitu ɗin, dan ya je ya ga in da suke ya yi masu hutu ya dawo, ba ƙaramin jin daɗin zaman Niger uncle Shitu ya yi ba, ba dan yaso ba ya dawo NIGERIA, tun daga nan kuma ba su sake jin ya su mummyn Rimsha suke ba, har bayan shakaru 7, lokacin mummyn Rimsha tana da shakaru 12 zuwa 13 a duniya, shi kuma uncle Shitu 22 to 23 years yake da shi kenan, a lokacin ya shirya yaje Niger ɗin bisa umarnin Mahaifinsa akan ya je ya dubo mashi ɗan uwansa ya yake, a lokacin yana 100 level karatu a Ahmadu Bello University, hutu yake zuwa Maiduguri, da yazo hutun ne ya je Niger duba bappan nasa, a nan ya sami mummunar labari na ce wa, bappansa Allah ya yi mashi rasuwa shekara ɗaya da ta wuce, ya sha kuka ba kaɗan ba, ya so su dawo tare da mummyn Rimsha da mahaifiyarta, amma iyayenta wato kakannin mummyn Rimsha sun ki yarda, haka ya hakura ya dawo ya sanar da gida abin da ya faru, sun sha kuka sosai kuma sun ji haushin mahaifiyar mummyn Rimsha da ta kasa turo ɗan aika ko ta nemi waya ta gaya masu rasuwar ɗan uwan nasu, sun ji ba daɗi ainun, hakan yasa suka yi fushi suka ce ba zasu karɓo mummyn Rimsha ɗin ba, sun yi fushi da mahaifiyarta, kun san Shuwa Arab su ma sun iya fushi ba kaɗan ba, daga nan kuma basu sake bibiyar ya Mummy Rimsha take ba, sun watsar da su, basu sake sanin ya suke ba sai yanzu da ta kai kanta da kanta ga dangin mahaifin nata, to shi ne suka sake sanyata a idanunsu..... KUNJI ALAƘAR DAKE TSAKANIN UNCLE SHITU DA MUMMY RIMSHA, YA AKAYI MUMMY RIMSHA TA AURI DADDY RIMSHA? YA AKAYI TA ZO NIGERIA? INA MAHAIFIYARTA? MEYASA BATA TAƁA ZANCEN MAHAIFIYAR TATA BA? MEYASA BATA KOMA NIGER BA BAYAN ƁATAR DADDY RIMSHA? DUK AMSA ZAI ZO MAKU DAGA BAKIN DADDY RIMSHA DA UNCLE SHITU, YANZU DAI NA FAYYACE MAKU ALAƘAR TA DA UNCLE SHITU NE A TAKAICE DAN KU GANE ME MATSAYINSA A WAJEN SU RIMSHA, DAN HAKA MU KOMA KAN LABARIN MU. STORY💋 "Allah sarki Anaya ni dai ina son ganin Gwaggo Aisha nan naki, wlh ko dan takura mini da zancensu da kike yi ma dole naso ganinsu" . Ta yi maganar tana mai dafe kirjinta, ta rasa dalilin da yasa duk lokacin da Anaya take bata labarin ƴan uwanta sai ta rinƙa jin gabanta yana faɗuwa, kirjinta na bugawa da sauri sauri, wani lokaci har sai ta dafe kirji nata take samun sauƙi. A ɓangaren ita ma Anaya duk lokacin data kalli Rimsha sai gabanta ya faɗi, da yake dukka dai yara ne sai ba wanda ya kawo komai a ransa, kuma sosai Anaya tana ganin muguwar Kamannin dake tsakanin Rimsha da kuma Gwaggo Maryam wadda ta kasace mummy Rimsha ɗin kenan, amma bata taɓa gayawa Rimsha ba, sau da dama tana zucci zuccin gaya mata tana yi mata kama da Gwaggon ta Maryam matar uncle ɗinta, sai dai idan sun haɗu sai hiran school ko hirar wani abin, Anaya ta na mancewa da zancen kullum. "Rimsha In Sha Allah zaki kalli su Gwaggo Aisha, kin san me? ". A'a ta bata amsa. "Idan su Gwaggo Aisha suka sake zuwa zan ce daddy ya kawo ni gidanku mu ɗauko ki, kizo ku gaisa, jiya ma munyi waya da Gwaggo Aisha ta ce mini zasu zo azumi, kuma kinga azumi ya kusa, tun da an kusa babban zaɓe, to suna zuwa zan gaya miki, wlh suna da kirki kuma suna son mu sosai, musamman ma ni, gwaggon A'isha ta fi sona fiye da kowa, dan nayi kama da ita, naso su zauna damu a gidan nan, amma suka ce a'a, daddy ma ba yadda bai yi ba, sunki yarda suka ce sun fi son Maiduguri, shi ne kawai daddy ya barsu a can yana saya musu duk wani abin da suke so ya tura musu can, amma zan gaya miki gaskiyar meyasa basu son zama damu, wlh mummymu ce bata son su, tana zaginsu, shi ne suka ce zasu koma Maiduguri, kuma gwaggo A'isha ta ce kada na gayawa daddy mummy ta zagesu, da nace sai na gaya, amma sai na fasa dan kar gwaggo A'isha ta ji na daɗi". Anaya sarki magana, faɗi ba'a tambaye ki ba, sai mamaki Akila take yi na irin shegen surutun nan na Anaya, duk ta gama tune asirin gidan nasu kamar wadda aka tambaya, ta zube komai a faranti abinta. Ita dai Rimsha da yake ba mai cika son surutu bane, tun tana amsawa Anaya har ta dawo binta da to, a'a, da kuma e, wani lokaci ma girgiza kai kawai take yi tamkar Anaya ɗin na a gabanta. Sai dariya kasa kasa Akila take yi, dan ta tula Rimsha ta gaji da surutun Anaya, ita kuma Anaya tamkar yanzu ma ta fara, babu niyar dakatawa a lamuranta. Sai da aka kira sallar issha, cikin sauri Rimsha ta sallameta tana sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya tare da godiya ga Allah ta tsira daga takurar Anaya, ita kuwa Anaya cewa ta yi idan ta yi Sallah zata sake kiran ta, da okey kawai Rimsha ta bita da shi, ba dai idan ta kira ɗin sai ta ɗauka ne zata ji surutun ba? To wlh ba zata ɗauka ba, ta faɗa a ranta tana turo ɗan bakin, da haka ta nufi toilet dan yin alwala. Bayan ta fito Akila ta shiga ita ma. A tare suka yi sallar mangariba suka zauna har lokacin issha ya yi, bayan sun yi issha ne Rimsha ta miƙe dan ta kaiwa Lion abinci, ita kuma Akila ta haye saman gado tare da jawo wayarta dan ta yi hira da masoyinta a WhatsApp, tun da yanzu ya bata damar tana iya yi mishi massage a WhatsApp, amma ko a WhatsApp ɗin numbersa a rufe take. Kamar kullum, Kitchen ta nufa dan ɗaukar abincin, bayan ta wanke hannayenta ta ɗauka a nutse, ba tare da ta ce da Mark ko sannu ba, shi ma ko sannu bai ce mata ba, kamar kullu ko kallon in da take bai yi ba. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga ɗakin, yanzu ta daina tsayuwar jiran sai an amsa mata sallamar ta, tana zuwa zata yi sallama ta faɗa. Babu kowa a ɗakin, da alama sun fita, a in da ta saba ajiye abincin, a nan taje ta ajiye tare da zama tana tunanin ina kuma suka shiga. Bata gama rufe tunanin nata ba ya shigo cikin ɗakin yana mai yin sallama kasa kasa, da mamaki ta amsa sallamar kasa kasa ita ma, kenan dama idan zai shigo ɗakin nasa yana yin sallama? Ta tambayi kanta tana ɗan satar kallon shi, yes idan zai shiga ɗakin nasa yana yin sallama, duk da yasan babu kowa a ciki, amma yana yin Sallama saboda sunnah ce ta annabi yin hakan, idan kayi sallama mala'ikun rahma zasu amsa maka idan ba mutane, yanzu ma bai san da ita a cikin ɗakin ba, ya dai yi sallamarsa ne kamar yadda ya saba. Ta kasar ido ya kalli inuwarta, hakan ya tabbatar mashi da mutun a cikin ɗakin, kwata kwata ya manta da ya ce zai kalleta idan ta shigo, zai kalli wacece su Areef suke so haka?, Allah sarki sabo tirken wawa, ya saba da ɗabi'arsa na rashin ɗaga idanu ya kalli abu, da wuya ya dai'na. Da yake yana jin yunwa, sai ya wuce wajen da ya saba zama ya zauna, yana zama gabaɗaya wutar gidan ta ɗauke diff tamkar dama wutar nepa ce, mamaki ne ya kama shi, ta ya akayi engine nan ya mutu? Tun da yazo Naija da aka ɗauke nepa sau ɗaya aka yi wajen 3 hours ba'a dawo da shi ba, daga nan ya yi watsi da nepa ya saho wani tampatsetsen engine wuta, mai matukar gudu da bada wuta mai karfi, baya shiri da zafi, Shiyasa ba zai iya zama babu wuta ba. Wani irin mugun tsoro ne ya dira mata a ranta ganin duhu ya mayaye ko'ina na cikin ɗakin, kun santa da tsoron bala'i, shi kuma jingina kansa da jikin sofar dake kusa da shi ya yi tare da waro idabunsa sosai yana kallon gabansa, ma'ana yana kallon in da yake fuskanta. Shiru shiru wutar bata dawo ba, shi kuma bai kunna wutar wayarsa ba, yana jin ta yadda take wani jan numfashin tsoro a hankali hankali, alamar ta tsorata over. Almost 10 mins shiru babu wuta babu labarinsa, sai raba idanu take yi, shi kuma har jikinsa ta fara haɗa zufa, ya tsani zafi fiye da tunanin mai tunani, Sojoji goma sha huɗu da su Mark a gidan amma wuta ta ɗauke har tsawon minti goma basu duba me matsalar ba?. Guntun tsaki ya ja tare da ɗago kan nasa da nufin ya miƙe ya nufi wajen, kwatsam sai ga hasken wutar ta dawo, wani mahaukaciyar ihu ta kurma tare da sulalewa kasa sumammiya. Da mamaki ya kalleta kwance a kasar, ko me ya sumar da ita Oho, yarinya tamkar mai aljanu, tamkar kanta biyu, da yake tana kwance ne sai bai samu damar ganin face nata ba, kuma irin kwanciyar da ta yi, ta ɗaura hannunta ɗaya a saman kumatunta, dan lokacin da take kurma ihun sai da ta dafe kumatun nata da hannayenta dukka biyu, ba komai ne kuma ya sanyata ihu da suma ba fa ce ganin cikin kwanyar idanunsa da ta yi, tana fuskantarsa, ga shi da yake a duhune idanun nasa a buɗe suke sosai, kuma shima yadda ya yunkura zai tashi ita yake fuskanta, hakan yasa ta kalli tsakiyar kwayar idanun nasa, ba ƙaramin razanata suka yi ba, saboda hasken wutar yasa kwayar idanun sun kara kyalli. Komawa ya yi ya zauna, har ya kai hannu zai ɗauki ruwa ya zazzage mata a kai, nan take zuciyarsa ta tunano mashi da irin farincikin da TRIPLETS nasa suka shiga ɗazun a ta dalilinta, har ga Allah yaji daɗin da bai taɓa ji ba na ganinsu a wannan farincikin, tuna hakan yasa ya fasa zazzaga mata ruwan sanyi, dan kada ta cutu sosai, idan ya zazzaga mata wannan ruwa mai uban sanyi, to fa a haukace zata tashi, idan ba'a yi Sa'a bama, tana iya hayewa kansa, dan fita zata yi a hayyacinta. A na haka sai ga Areef ya shigo ɗakin shima yanzu ya idar da sallah, daman sun rabu da Lion ne, shi ya wuce bedroom nasa dan yin Sallah a can, Imran, Lion kuma suka wuce masallaci. Wajensu ya nufo dansu ci abinci, yanzu kusan gabaɗaya ya tare a ɗakin ɗan uwan nasa. "Kai subhanallah Lion menene ya sami sister kuma?" Tamkar babu shi a ɗakin, bai amsa ba, sai ma yunkurawa da ya yi zai miƙe ya bar wajen, cikin sauri Areef ɗin ya ce "Please zauna bari ni nayi serving naka ko?". Ba musu ya koma ya zauna dan yunwa yake ji, ɗaukarta cak Areef ya fara yi yana ciza laɓɓansa alamar zafi kafaɗarsa ke mashi, dan akwai sauran ciwo sosai, ko sannu Lion bai ce mashi ba, ai shi ba ƙaramin yaro bane, yasan abin da ya dace da shi, da kuma wanda bai dace ba, idan ya yi wa kansa illah ma shi ya jiwo. Saman sofa dake a cikin ɗakin ya kwantar da ita tare da dawowa wajen ɗan uwan nasa yana cizar lallausan laɓɓansa. Abinci ya zuba masu suka ci a tare kamar ɗazun, bayan sun kammala ya kwashe kayan abincin ya ɗaura saman table dake cikin ɗakin. A tare suka miƙe Lion ya nufi toilet shi kuma ya haye saman bed, ita kuma tana sume a samar sofa. Wanka Lion ya yi tare da fitowa ya shirya cikin kayan barcinsa riga da wando masu shegen kyau ga laushi kamar auduga, ba su da nauyi ko kaɗan, kamar dai kullum launin white color ne, bai ɗaure kyakkyawar gashin kansa ba, ya barshi zube sai kyalli yake yi yana tashin kamshi. Saman gadon ya dawo ya kwanta yana zuba uban kamshi, yana kwanciya Areef ya miƙe ya nufi toilet ɗin dan shima ya yi wanka, saboda ciwon dake a kirjinsa shi ba wanka yake yi kamar kowa ya yi ta zuba ruwa ba, no a hankali yake yi ta yadda ruwar ba zata taɓa bandejin dake wajen ba, har ta taba ciwon, hakan yasa idan ya shiga wanka sai ya ɗauki almost 1 hour kafin ya kammala, daki daki yake yin komai. Shiryawa ya yi cikin kayan barcin Lion, a ƴan kwanakin nan ma kayan ɗan uwan nasa yake yawan sawa, dan kusan ya tare a ya dawo ɗakin Lion ɗin, idan ya shigo baya fita har sai idan zai yi wani abin, kayan barcin launin black color ya sanya, bai cika sanya farin abu ba a yanzu, sabida ciwon nan nasa, baya son ganin stain na jini a jikin kayansa, so ya fi sanya Black colar or brawn, wadda ba zasu fitar da shaidar abu ba, duk kaunar da yake yi wa white color ya hakura. Saman gadon yazo ya kwanta kusa da ɗan uwan nasa, har lokacin Rimsha tana sume kwance saman sofa, da alama shi ma Areef ɗin ya mance da ita a wajen. A kwanciyar tasu suna fuskantar juna, Lion idanunsa a lumshe, shi kuma Areef ya tsare shi da idanu yana kare mashi kallo tare da godiya ga ubangijin daya yi masu wannan kyakkyawar halittar haka, Lion kyakkyawar gaske ne kamar shi ya yi kansa, har ta ƴan uwan nasa yaba kyansa suke yi, da yake su basu ganin nasu kyau ɗin sai nashi, dama kuma haka ne, baka cika ganin abu ba idan a jikinka yake, kafi ganin kyaunsa a jikin wani, to suma haka ne sunfi ganin kyan juna, ɗaya yaga na ɗaya haka. Daga karshe Areef ya juya tare da ɗauko wayarsa daya ɗaura saman bedside drawer ya shiga latsawa, dan kwata kwata baya jin barci, shi kuma Lion da alama barci yake ji sosai, Shiyasa ma ya yi barcinsa abinsa. Ita kuwa Akila tana kwance tana chatting da masoyinta, bata wani damu ba dan Rimsha bata dawo ba, while shi kuma Imran yana ɗakinsa yana shirin barci. ☠️DAULAR MUTUWA☠️ A YAU DAULAR MUTUWA TAKE KARA SHEKARA GUDA A KAN SHEKARUN HASSASATA DA AKA YI. Sai murna suke yi, an kawata gidan tamkar ba gidan ba, sun yi amfani da tsafinsu wajen sauya gine ginen dake a cikin gidan, sun fito da sabbin gine gine tare da sabon penti, ga wasu baloon da kayan kyalkyali da aka zuba, tamkar wajen party, kai idan ba ance maka nan DAULAR MUTUWA bane ba zaka taɓa ganewa ba, saboda tsantsar kyan da ya yi, su barbushi duk sun zama kyawawan matasa masu jini a jika, ma'ana sun koma aihanin halittar da Allah ya yi masu, kyawawan matasan kabilar Ebo ne, duk wanda ya san Ebo ya sansu da tsawo da kuma ƙiba, mafiya yawancinsu farere ne kuma kyawawa, to suma haka suke, fararene tas kyawawa, ga tsawo da ƙiba, suna da kirar karfi tamkar masu ɗaka karfe, ma'ana masu yin gym, kuma ba wani gym da suke yi, halittace kawai da mafiya yawan mazan Ebo haka suke. Fadar QUEEN an kawata shi da wani irin mahaukacin kyakkyawar zazzafar kwalliya, komai na cikin fadar Navy blue ne, ga wasu tsala tsalar kujeru da suka yi amfani da tsafinsu wajen kyara su, idan ka kalli fadar QUEEN sai ka yi zaton wani katafaren Daula mai tarin arziki na wani hamshakin basarake ne. A cikin fadar akwai wani hawa step 3 haka, a saman step ɗin ne a ka kawata wa QUEEN kujeran da zata zauna, sai dai kujerun guda biyu ne a wajen ba ɗaya ba. Sai shagali ake yi, su baba da yake sun saba gani duk shekara sai basu wani damu ba.... WAI SHIN MENENE MAKASUDIN HASSASA DAULAR MUTUWA NE? kamar yadda na gaya maku a baya, ta kabilar Ebo ce, sun hassasata ne ma dan tsafe tsafensu na samun makudan kuɗaɗe, suna ɗebo yara daga arewa zuwa wajen, da wuya ka samu ɗan gudu a cikin waƴan da ke cikin gidan, ko da gigin wasa ba zaka taɓa gani sun yi kuskuren kamo ƙabilar tasu ba, suna tsafi sosai da jikin mutane, ba iya yara ba, har da manya wanda ya yi sake da addininsa, yanzu matsafa sunyi yawa a duniya fiye da tunanin mai tunani, sai a riƙe ibada dan a tsiranwa gaidinsu, suna shan jini sannan kuma suna cin namar mutane, suna sayarwa wasu gidan matsafar wani sassa na ɗan adam idan suka buƙata dan yin tsafinsu, a caf faɗin kasar nan da wuya a samu gidan matsafa da suka kaisu girma da komai da komai, sun shahara ta wannan ɓangaren ba kaɗan ba, duk wanda ya shiga wannan gida baya fita, an rufe babinsa.... MU KOMA KAN LABARIN MU. Murna a wajensu ba'a magana, wata kyakkyawar halitta ce ta fito daga wani katafaren kyakkyawar ɗaki, wannan halitta mace ce, a shakaru ba zata wuci 22 years ba, tana da tsawo sosai, amma bata da ƙiba sosai, ga shape kamar ita ta yi kanta, fara ce tas, ga hancin nan ɗan siriri kamar karas, ya zauna sosai da kyau a saman kyakkyawar farin fuskar tata, ɗan bakin nan nata ɗan karami, lips nata launin dark purple, kyau iya kyau wannar matar ta yi, sanye take da doguwar riga launin black color, rigar tata tana ja har kasa, rigar irin weeding gown ɗin nan, kanta babu ɗan kwali, ta zuba gashin nan nata har gadon baya, tamkar ita ta bawa kanta wannan kyakkyawar gashin, ga shi irin gashi mai gazar gazar ɗin nan ne, sai ya kwanto mata har baya. Wannan mata ba kowa bace fa ce QUEEN. Saman ɗaya daga cikin kujerun da aka tana da mata ta nufa, ga wasu kyawawan fararen samari guda biyu suna take mata baya, sai kasa da kai su barbushi suke yi alamar girmamawa, a gabaɗaya cikin fadar QUEEN ɗin ita ce karama, amma kuma ita kowa yake durkusawa dan girmamawa, har sai da ta zauna a saman kujerarta suma suka zazzauna a nasu kujerun. Tana zama bai fi da minti 5 ba, mahaifiyarta ta fito, wadda ita kuma dattijuwa ce da a kalla zata iya kai 45 to 50 years haka, da kallo ɗaya zaka yi mata kasan cewa yes tabbas ita ta haifi Queen, ba komai zai sanya ka yi tunanin hakan ba face muguwar kamannin dake a kan fuskokinsu. Tana takawa bodyguards guda biyu suna take mata baya kamar dai yadda suka rako QUEEN, har sai da ta zauna bodyguard ɗin suka juya zuwa ta bayansu suka tsaitsaya dan tabbatar da tsaro a kansu. Cikin yarensu mahaifiyar QUEEN ta buɗe musu taron, kowa yana zauna saman tsadaddun kujerun, sun sha kwalliya na ƙin karawa, suna da yawa sosai, a kallah sojijin ko in ce dakarun QUEEN zasu iya kai su 50 haka, dukkansu babu wani yare na daban a ciki, duk yarensu ne, hakan zai tabbatar maka da ba ƙaramin shiri suka yi wa wannan bakin azzalumin gidan ba. Cikin yaren su suka gudanar da komai, sun ɗauki tsawon lokacin suna magana, wadda a kallah zai kai awa uku zuwa biyar haka, sai tattauna suke yi, da alama suna kara yin shawara ta yadda zasu kara buɗa gidan ne, ta yadda zasu inganta shi ya kara girma fiye da tunanin mai tunani, shi ne abin da suke tattaunawa, kowa yana kawo shawararsa a kan ga yadda zasu yi. QUEEN dai shiru bata ce ko uppan ba, mahaifiyar ta ke magana, daga karshe ma mahaifiyar tata ce ta yanke shawarar ga matsayar da zasu tafi a kan shi dan su kara faɗaɗa gidan nasu...... BASU SAN CEWA ALLAH BAI YI ALKAWARIN TALLAFAWA AZZALUMAI BA, ALLAH BAYA BARCI, YANA GANIN KOMAI DAKE FARUWA, WANNAN TSINANNEN GIDA BA ZAI CIGABA BA, YA DAI CIGABA A BAYA, SUN CI LOKACIN SU DA DAMARSU A BAYA, A YANZU IN SHA ALLAH SAI YA RUGUJE, BA ZASU SAKE YIN MASARA BA, BA ZASU SAKE KASHE KOWA BA, BA ZASU SAKE TSAFI DA KOWA BA, AZZALUMAI TSINANNU. Duk wannan taron da suka yi babu Duna babu alamar sa, wai shin ina duna ɗin? Ina suka kai shi? To muje dai zuwa, koma me zamu ji a gaba. Sai da dare ya tsala sosai suka tashi taron nasu, sun ci sun sha, sun ƙoshi sun yi hani'an, an cashe anyi murna sun sha sharholiya, abin ba'a cewa komai. Sai bayan sun tashi taron mafiya yawa daga cikinsu suka koma kamanninsu na matsafan dan sun ce yafi yi musu daɗi, wasu kuma sun zauna a ainahin kamannin da suke da shi na kyawawan matasa. QUEEN ma bata koma kamannin tsafi ba tukunnan, haka ita ma mahaifiyarta, da alama su kam basu son wannan tsiffa tasu ta matsafar, to koma yaya ne zamu ji a gaba,. Da ainahin kamanninta Queen ta bar wajen zuwa katafaren daular yin barcinta, tana barin wajen taro ya watse, kowa ya wuce bakin aikinsa. TO KUN JI ABIN DA YAKE FARUWA A DAULAR MUTUWA, BARI MU LEƘA WASHINGTON DC DAN JIN YA AKE CIKI NE. WASHINGTON DC💋 Tafiya suke yi a cikin mota, Aseef da kansa yake tuƙa motar, shi kuma Musharraf yana gefensa suna hira. "Kana ji uncle Hosain? Dama ai na gaya maka, sai na kwashi rabin kuɗin account ɗin uncle T na yi ta sadaka da su, ko Allah zai dube shi da idon rahama yasa ya musulunta, wannan kafurar zuciya ta ragu, to in gaya maka yau a account nasa na kwashi kuɗi na zuba a nawa, nan da anjuma zaka ji ya kirani akan me zan yi da uban kuɗin da na ɗeban nan, ai tun da suka sanar da ni sirrin bankin su, wlh ko ba su so sai sunyi sadaka, musamman ma uncle T da Uncle Herry, basu taɓa kyauta wa wani ba, sai pastor, shi kawai suke bawa kuɗin su". Dariya Musharraf ya yi sosai kafin ya tsagaita ya ce "Wlh Aseef ka zama lashe money, ina ga nan gaba kaɗan sai sun canza gabaɗaya tsarin bankinsu saboda kai, duk sai ka talauta mutane ko? To kai ma dai Allah ya sanya ka gama karatun nan lafiya ka fara aiki ka tara naka kuɗin, sai ka fita daga layin lashe moneys". Yana ƙoƙarin juya kan motar ya sauƙa daga kan titin da suke izuwa titin kasa ya ce "Uncle ba zaka gane bane, basu yin sadaka ne shiyasa nake yi masu, kuma ai kuɗin su ba zai kare ba tun da kullun wasu ne suke shigowa, duk cikin mu fa, daga Saif sai Areef ne kawai suke yin sadaka, shi ma daddy da kake ganin nan, wlh pastor kawai yake bawa kuɗinsa, bayan pastor kuma sai ni da nake cin kuɗin, ko suna so ko ba su so, kuma dole su bani na ci". Kara faɗaɗa murmushinsa ya yi "My Aseef ka cigaba da yi musu addu'a, In Sha Allah everything will be okey nan ba da jimawa ba". Ɗan ɗaure fuska kaɗan ya yi. "Uncle Hossain wlh wannan bakar zuciya da kake gani, ni nasan daga wajen wannan Roshan ɗin suka gado shi, ko ban ji tarihin kakan nan namuba, nasan shi ne mai shegen bakar zuciya tamkar shaiɗanun farko, kai uncle Hossain baka ji sunansa bane? Wai fa Roshan, daga ji kasan anyi tsiya ba na wasa ba, ni ban ma son jin tarihinsa, ban son sanin komai, dan nasan bakin mugune da wani idanunsa a wajen, ya ma yi Sa'a Allah yasa idanunsa irin na Lion blue color, dan hakan yasa nake raga mashi, ba da ban haka ba, da sai na ce Allah ya kara mishi azaba tun da bai musulta ba ya mutu". Yana magana yana ɗaure fuska. (Kai jama'a to me kakansu kuma ya yi mishi da ya kare mishi tanaji har haka?🤔 Allah ya shirya Aseef Wlh, wai da ya ce Allah ya kara mishi azaba🤣 to ai ka riga da ka faɗa sai dai kar a kara🤣) "ASEEF abin da nake so da kai kana jina?" Gyaɗa mishi kai ya yi ba tare da ya yi magana ba. "Yauwa, musulmi ba zai taɓa zama cikakken musulmi har ya shiga aljanna ba sai yana kiyaye harshensa, Annabi da kansa ya yi wa duk wandan ya kiyaye abu biyu zuwa uku alkawarin shiga aljanna babu fashi, na farko, ka kiyaye abun dake tsakanin hakwaranka na sama da na kasa, wato harshe kenan, idan har kana iya kiyaye harshenka, to ana sa ran ka samu babban rabo, abu na biyu ka kiyaye abun dake tsakanin kafafunka, wato al'auranka, muddin ka kiyaye gabanka baka aikata zina ba, muna yi maka kyakkyawar zaton da samun Rahmar Ubangiji, abu na uku gani, ka kiyaye idanunka wajen zuwa lallai sai ka leƙa abin da ya zama haramun, misali kallon fina finan banza da tsiraicin wani, mutane biyu kawai Allah ya yafewa da su kalli tsiraicin juna, mata da miji, bayansu duk wanda zai zo a baya tofa akwai matsala, uwa tana iya yi wa ƴaƴanta wanka suna yara ta kalli tsiraicin su kafin sukai munzalin haramta ita ma a gareta, idan ba ya zama dole ba, Aseef ina son ka san wani abu guda wadda duk wanda ya sanya hakan a ransa dole ya tuba ya koma ga Allah, ina son ka saurareni da kyau, Ubangiji bai bawa kowa daman sanin aikinsa ya karɓu ko bai karɓu ba, ka kwana kana sallah, kana azumi, zakka, hajji, ba abin da baka yi a manya manyan ayyuka Alkhari, sadaka, amma kada ka kuskura ka saki jikin cewa wannan aikin naka tana karɓuwa, domin me? Saboda baka sani ba wata kila akwai in da ka tabka babban kuskuren da ya shafe dukkan ayyukan alkharin nan naka, idan bawa yana da hankali bai kamata ya saki jiki da duniya ba, saboda baka da tabbacin abin da aka turoka a duniyan ka yi shi mai kyau kuma an karɓa, Aseef muddin aikinka bai karɓuba ka shiga uku ka lalace, bari kaji Annabi da kansa akwai lokacin da Allah ya sauƙar mishi da aya ya daka mishi warning akan yana shiga abin da bai kamata ya shiga ba, a lokacin sai da annabi ya shiga tsananin tashin hankali na abin da ya faru, to shi kaga ɗan gata ne, Allah yana son shi da Rahma har hakan ta faru, zaka iya zuwa kana tapka babban kuskure da zai goge duk wani aikinka ba tare da ka sani ba, Sahabban annabi ban cire maka ko ɗaya ba, harta waƴan da suka san makomansu ɗin, waƴan da suka san aljanna zasu tafi irinsu Sayyidina Abubakar, Omar, Usman, Ali, ɗalhatu binu Ubaidullahi, abu ubidu binu zarrai da sauransu, su kansu idan aka kira lahira jikinsu kerma yake yi, kuka suke yi suna kara neman gafara da sassauci wajen ubangiji, wannan kawai bai isa yasa bawa ya kasance cikin tashin hankali a kullun ba? Manyan Sahabban da suka san yes aljanna zasu tafi, suna kuka idan suka ji annabi ya fara magana a kan lahira, to mu da ko rabin su a aikin Alkhari bamu yi ba, sai kaga bawa ya samu waje ya kwanta ana kiran sallah yana zaune tamkar wani kurma, ya ilahi ya lillahi, wlh bai kamata bawa ya zauna cikin kwanciyar hankali har ma ya yi tunanin cutar da wani ba, mutuwa gaskiya ce, tashin alkiyama gaskiya ce, yau ina kakaninmu? Wasu ina iyayenmu? Ina kannenmu? Wasu ina yayyunmu? Idan ka juya kaga matsalar dake a kewaye da kai ma kawan ya isa ya sanya ka kara jin tsoron Allah ka girgiza, ya isa ya sanya ka kara komawa ga Allah dan samun rabauta, kafin Annbi ya rasu, da Sahabbai suka tambaye shi ya Rasulullah yaushe za'ayi tashin alkiyama, ya ce da su sanin gaibu sai lillahi, Allah ne kaɗai ya barwa kansa sani, amma akwai misali da Ubangiji ya yi mini, zan yi muku shi dan ku kotanta, mikar da yatsun hannunsa gabaɗaya ya yi, kun dai san yatsun hannu ɗaya ta fi ɗaya, sai ya ɗauki babba ta tsakiya da kuma manuniyar yatsa, ya mikar da su sosai, ya ce da sahabbansa abin da ta regewa duniya ta tashi bai wuce ɗan wannan fifikon dake tsakanin yatsarsa ta tsakiya da kuma manuniya ba, ku duba ɗan ratan dake tsakanin yatsunnan, a lokacin annabi yace abin da ta ragewa duniya kenan, bare kuma yanzu da ya yi shekara 1445 da yin wannan maganar, to ku lissafa abin da ya saura kenan, a lokacin da Sahabbai suka ji wannan magana, hankalinsu ya yi mummunar tashi, masu kuka suna yi, annabi ya yi ƙoƙarin kwantar musu da hankali ta hanyar nunawa su sayyidina Abubakar cewa su fa ƴan aljanna ne, amma ina sunki yin shiru, suka ce idan ba sun ga kansu a cikin aljanna ba, sun karɓi takardansu da hannun dama, baza su taɓa daina kuka suna neman gafara da sassauci wajen ubangiji ba, ɗan adam ako da yaushe mai kuskure ne, tana iya yiwuwa su je su aikata wani abin da zai shefe musu aikin alkharinsu na baya, to su da suke Sahabbai ma kenan, ina ga mu da ba ɗaya kanwar biyu? Sai kaga mutun sai wani jiji da kai yake yi yana faɗi kamar ba nan da ɗan lokaci kaɗan cikin kasa zan koma ba, jama'a duk wasu masifa da suka zo a cikin Al Qur'ani mai girma da hadisan Manzon (S.A.W) da suke nuna almomin tashin alkiyama ne, to wlh sai bayyana suke yi, me ba'ayi yanzu? An maida zina abin kwalliya! An mai da luwaɗi gasa! An mai da lesbian sana'a! Saɓon Allah ya zama har tinƙawo da shi ake yi! Uba ya nemi ƴa ya kwanta da ita, yaya ya yi wa kanwarsa ciki, makwabci ya yi wa ƴar makwabcinsa ciki, mata su kashe mazansu a kan shirmen banza, ba'a ɗauki ran a bakin komai ba, matan aure suna zina, Maza na cin amanar matansu, namiji ya auri yarinya kuma ya zagayo ya yi wa kanwarta ciki, wasu ma tamkar a garin dabbobi suke, ka auri yarinya sannan ka kwanta da uwarta, ya ilahi ya lillahi, me ba'ayi?! Cutar mutane an mai da shi yanzu tamkar wani ilimi, har koyan danfara ake yi, karya na gudu kana bin shi a guje sai ka kamo shi, dole dole sai anyi karya, zalunci da hasada na gudu kuna binsu ku kamo su, dole dole sai an zalunci jama'a, kashe mutane kamar kiyashi ya zama contract! Gasa ta gina manya manyan gine gine a duniya ta bayyana, wadda annabi da bakinsa ya faɗa tana daga cikin manya manyan almomi na tashin alkiyama, masifu kala kala sai bayyana suke yi, shi kansa wannan faɗa ta yahudawa da musulmai ya zo mana a cikin Al Qur'ani mai girma? Kafin tashin Alkiyama sai anyi shi, duk wasu alamomi sun bayyana, jama'a muji tsoron Allah, mu tsaya tsayin daka dan gina lahirarmu, bai kamata hankalinmu ya kwanta mu saki jiki da duniya ba, har sai ranar da muka karɓi takardanmu da hannun dama, mu lizimci yin istigifari dan idan munyi laifi ma Allah ya yafe mana, a kowace rana ku rinƙa tuna mutuwa fiye da yadda kake tunanin abinci, dan mutuwa tafi abincin saurin zuwa, idan kwana ya kare ko tafiya kake zaka tsallaka babbar titi sai an zare ranka, second ɗaya mala'ika azarailu baya karawa bawa wajen zare rai, ko a ina yake kuwa, shi kuma abinci kana iya jira har sai an kammala, to dan haka mu lura, mu tuba mu koma ga Allah, zunubanmu ya yi yawa, Allah gafurun rahim ne, amma ku sani a yanzu ne kuke da damar tuba kafin lokaci ya kure, a lahira ko kabari ba'a tuba, iya duniya Allah yake karɓar tuba".... Yana magana yana hawaye bibbiyu, duk dakiyar zuciya irin na daddyn Rimsha sai da ya yi hawaye ba kaɗan ba, haka zalika shi ma Aseef, paka motar ya yi a gefen titi tun lokacin da daddyn Rimsha ya fara maganar, ya kifa kansa da jikin steering motar, hawaye yake yi sosai, wani na bin wani, duk sai ya ji duniyar ma ta ishe shi, ya ji jikinsa gabaɗaya ya mutu, me bawa zai nema a duniyar nan da ta wuce lahirarsa? Me zai tsayar da bawa yin wasu shirme a duniyar nan? Ya ilahi ya lillahi, gaskiya duk wanda ya zo duniya, ya mutu ya tafi wuta to tabbas shi ya so, shi yaga dama, kuma ya zama babban mai asara number ɗaya a duniya, dan Allah ya bamu lokaci da kuma dama, Allah Arrahaman ne, mai rahma a kan bayinsa, tabbas wannan hakane, Allah ne kaɗai zaka yi babban laifi ya kuma baka damar tuba ka koma gare shi, ka sake yi ya sake baka damar tuba, duk dan ka samu rahmarsa, ba wanda zai yi wa bawa haka sai mahaliccinsa, wani ma nan a unguwarku idan yana jin haushinka, haka kawai sai ya ɗauki gaba da kai ba gaira ba dalili, idan kayi kuskure yi mashi laifi kaɗan, to ka shiga uku, ba zai taɓa yafe maka ba, sai ya ɗau fansa, kunga ya tabbata idan ka mutu ka shiga wuta kai kaso. Sosai suke kuka duk cikinsu babu mai iya rarrashin wani, sun jima a haka kafin Musharraf ya ɗauki robar ruwa ya fita ya wanke fuskarsa ya dawo. Yana dawowa ya hau rarrashin Aseef, da kyar ya samu ya yi shiru, sai shessheƙar kuka tare da ajiyar zuciya yake sauƙewa, idanuwansa sunyi jawur kamar wuta, abinku da farar fata, har wani ja kumatunsa ya yi, tamkar wadda a ka wawwankawa marika. Sun ɗauki almost 1 hour a wajen kafin su dawo daidai, kunna motar Aseef ya yi suka nufi in da zasu je, wato white house. Yau duk fara'a irin ta Aseef, da yake yi wa sojoji da ƴan'sandan white house dariya da kyauta, yau dai ba wanda ya ga hakwaransa a waje, kyauta dai kamar yadda ya saba ya zube masu kuɗaɗe ba kaɗan ba, duk sai mamaki suke yi, sun sha jinin jikinsu ganin yanayin da suka jima basu ganshi a ciki ba, wato yanayi na ɗaure fuska, tun lokacin ciwon shi da yake ɗaure fuska, babu damar tambayarsa ko lafiya, haka suka haƙura suka fara raba kuɗin da ya basu. Yau bai shiga fadar shugaban kasa ba, kai tsaye cikin gida ya nufa abinsa, bai jira a yi mishi iso ba, ya wuce izuwa babbar palo ya yi zamansa saman wata danƙareriyar sofa, masu bala'in kyau da ɗaukar idanu, sofar ta haɗu iya haɗuwa, a gefensa Musharraf ya zauna suka yi shiru, yau ba hira da dariya, dama shi Aseef akwai wata guntuwar zazzaɓi a jikinsa, sai abin ta haɗu mishi, kansa ya fara yi mishi ciwo, haka ya daure ya kwanta a saman sofar tare da tada kai da cinyar Musharraf, kyakkyawar gashin kansa Musharraf ɗin ya fara shafa mishi yana yi addua'o'i tare da tofa shi, sau da dama haka suke yi, duk lokacin da Aseef zai tada kai da cinyarsa, tofa sai ya yi ta tofa mishi addua'o'i sosai da sosai, kuma ga shi Aseef ɗin bashi da wani wajen kwanciya biyun cinyar Musharraf ɗin. Suna a haka wata kyakkyawar budurwa ta sauƙo daga sama, kyakkyawa ce sosai, farace tas, daga gani kuma tana da alaƙa da su, dan kuwa kamannin His excellency ne a kan face nata, da alama jikarsa ce, kamar yadda suma su Lion ɗin suke jikokinsa, ba karya tana da kyau kam, idanunta farare tas tamkar madara, sai dai ƴar siriri ya ce sosai, kunsan zubin turawa dama, sirarane sosai, to haka ita ma take, tana sanye da wasu shegun kananan kaya, kun dai san yadda dressing nasu yake, wando da riga ne da suka kamata, a kafarta kuwa, wasu shegun high heel ne masu matukar kyau da tsada, da ganinta zata yi jiji da kai ba kaɗan ba, hannunta na riƙe da wata danƙareriyar wayarta, sai wani ɗan siririn jaka wadda ba zai wuci ɗaukar iya ATM card ba. Ta gabansu ta zo zata wuce ba tare da ta ɗago ta kalli su waye a wajen ba, kallonta na a kan wayarta, da alama dai wannan izza da jiji da kan nasu na gado ne, a jininsu yake, dan kuwa ita ma bata ɗago ta kallesu ba. "Ke Jessie wuce ki gayawa uncle ina nan kiran me yake yi mini". Cewar Aseef, ya yi maganar yana yi wa yarinyar kallon banza. Da sauri ta juyo jin zazzakar muryarsa, ganin shi yasa ta taho da sauri ta faɗa saman jikinsa tana faɗin "Michael i really missed you, long time ina ka shiga?". Ɗaure fuskar nan sosai ya yi, tamkar bai taɓa sanin menene dariya ba, sai ya dawo sak Lion. "Tashi mini a jikina da wuri, kuma sunana ba Michael ba!". Ya faɗa yana mai kara ɗaure fuska kamar hadari. Da sauri ta ɗago idanu tana kallonsa jin yadda ya yi magana a kausashe, da yake Musharraf yasan halinsu sai bai wani damu ba, ya san abin da ya fi hakan ma zasu iya ai katawa, dan ta kwanta a jikin Aseef ba wani abin bane, ai ƙaramin alhakine hakan. Babu tsoro ko kaɗan a face nata, matso da fuskarta sai tin nasa ta yi, sai murmushi take yi tana ƙoƙarin kai mishi kiss a laɓɓansa, cikin zafin nama ya hankaɗe da karfi, abunku da yar siririr ba nauyi, sai gata a kasa kamar wata kayan wanki, a fusace ya yi kanta da nufin ya daketa, da sauri Musharraf ya ruƙe shi yana mai bashi hakuri, ina ai kwace hannunsa da Musharraf ya riƙe ya yi, jinin William jacop ne ke gudu a jikinsa, dukkansu akwai zuciyar bala'in, sun gado ne daga iyayensu. Bai saurari Musharraf ba ya fara ball da ita, dama haushinta yake ji, wai tun tana yarinya ta kafe sai shi ko kuma Lion zata aura, idan baku mance ba His excellency ya taɓa zuwa gida har ya ce da daddy ya ce wa Lion ya zo ya kalli Jessie idan ta yi mishi sai a haɗasu aure, har daddy ya ce shi yana tsoro sai dai shi His excellency ɗin ya yi mishi magana, shima yaki, to wannan ita ce Jessie da ake magana a kanta, tun tana yarinya ta kafe lallai sai su, ko Lion ko Aseef, dan Areef kam ma bata san kammaninsa ba, tun ainahi bai cika zuwa white house ba, bai ma santa ba, kai ubanta ma bai sani ba bare ita, Lion da Aseef ke zuwa white house, su ta sani yasa ta kafe sai su, mahaifin ta baban abokin shawarar His excellency ne, kuma ɗan uwansa na jini ne, Jessie ta kasance jika ce a wajensa. Sai ihu take yi, Aseef kuma ta bashi haushi, yana tsaka da tunanin lahiransa zata zo tana ƙoƙarin saƙe ɓata mishi duniyar nasa ma baki ɗaya, idanunsa sun rufe ya zaro belt ɗin wandonsa ya hau jibganta kamar an aikosa. KU DAGA GANI KUNSAN BA IYA YUNKURIN YI MISHI DA TA YI BANE YASA YAKE YI MATA WANNAN ƊAN ISKAN DUKA, DA AKWAI WATA A KASA, DOLE AKWAI ABIN DA YA TAƁA HAƊASU YASA YAKE JIN HAUSHINTA HAR HAKA. Jin kukanta yasa mutanen gidan suka fito, ganin abin da yake faruwa yasa Madam matar His excellency ta ɗauko waya ta kira His excellency dan yazo ya ceci Jessie. Ko da shi ma ya zo bai iya karɓar Jessie ɗin ba, dan Aseef ya rufe ido sosai ta ko'ina yake kai mata duka, duk wanda ya yi gigin tinkararsa shima zai samu rabon nashi bulalar. Waya His excellency ya ɗauko dan ya kira Lion, shi kaɗai zai iya dakatar da Aseef, ko da ya kira Lion ɗin da farko ya ce to ya kashe ta mana shi ina ruwansa, yasan idan da bata je in da Aseef ɗin yake ba, ba zai kamata ya daka ba, sai dai His excellency ya yi ta lallaɓa shi sannan ya ce a bawa Musharraf wayar, cikin sauri suka miƙawa Musharraf, a nitse ya karɓa tare da karawa kunnensa. Magana na minti ɗaya Lion ya yi wa Musharraf ɗin kafin ya ce su sanya mishi wayar a hand-free, ba musu suka sanya wayar. "My pleasure". Ya furta a nitse, cak Aseef ya tsaya tare da juyowa yana bin wayar da kallo, sai sauke uban haki yake yi tamkar wadda ya ci uban gudu ya ƙoshi. "Ku koma gida". Shi ne abin da Lion ya sake faɗa daga nan ya katse kiran, jefar da belt ɗin hannun nasa a tsakiyar palon ya yi tare da tahowa ya rungumi Musharraf kamar shi aka daka, hannunsa Musharraf ya riƙe suka fita daga palon, binsu da kallo His excellency ya yi, dama ya kira shi ne a kan zancen Jessie ɗin, ya kira shi ne a kan yazo ya ganta su shirya kansu, ga shi ya zo ya mata shegen duka kamar an aiko shi, dama daga jin yadda ya ce mata ke jeki gayawa His excellency ina nan, daga nan ya kamata kusan haushinta yake ji, abin ku da farar fata musamman ma fatar mace ba kwari, duk jikinta ya yi ruɗu ruɗu na zanen belt ɗin, ta yi wani jawur da ita kamar ka taɓa jini ya fallatsa, tamkar ruɓaɓɓen jan tumatir, sai hakuri mutanen gida suke bata, His excellency yasa aka kwasheta zuwa asibiti dan a dubata. Su kuwa suna fita kai tsaye wajen motarsu suka nufa, a mazaunin passenger ya buɗewa Aseef akan ya shiga, shi kuma ya shiga mazaunin driver dan ya jasu. "Uncle Hossain ka dawo nan bari na tuƙamu ko?". Yana magana yana haki kamar wadda ya yi gudu. "No Aseef Saif ya ce ni na tuƙa motar, dan haka kawai ka bari na tuƙa mu zuwa gida ko?" "Uncle daman ka iya mota ne?". Gyaɗa mishi kai ya yi tare da kunna motar suka bar gidan, suna tafiya a hanya yana bashi labarin rayuwarsa na Nigeria, har takatar shigaban kasa da ya nema da sauransu, abin da ya faru da shi na rabuwarsa da su Abba da kuma abin da ya faru da shi na rabuwarsa da su Rimsha ne kawai bai gaya mishi ba. Har suka isa gida suna hira, Aseef har ya mance da ya jibgi Jessie,. Suna shiga gida bayan sunyi parking a parking space, a tare suka karisa cikin palo har zuwa bedroom nasu, a nan ne kowannensu ya wuce toilet nasa dan ya yi wanka. Kusan a tare suka fito daga wanka, dukkansu pajama suka sanya, da yake shi ma daddyn Rimshan ba wani ƙiba ne da shi ba, duk dai irin zubin turawan ne, sai pajama ta yi mishi kyau over. Saman gado suka haye Aseef ya ɗauko littatafan addini dan su cigaba da karatu, ba musu Musharraf ya cigaba da koya mishi karatu yana kara gaya mishi girman Allah, shiru ya nitsu yana saurara. WANNAN KENAN ABIN DA YAKE FARUWA A WASHINGTON DC, BARI KU LEƘA NIGERIA GIDAN LION MU GANI ME YAKE FARUWA. GIDAN LION💋 Yau dai Rimsha a ɗakin Lion saman sofa ta kwana, Areef, Lion suna kan gado, da alama sun mance da ita gabaɗaya. Ita kuma Akila ta yi hiranta da masoyin ɓoye har barci ya ɗauketa, bata damu dan Rimsha bata dawo ba, dan ita bakuwa ce bata san yanda tsarin gidan yake ba, ta yi zaton ma sai tsakiyar dare Rimshar ke dawowa, yau ta yi barci da wuri, bata kai karfe 9 ba, barci ya saceta wayar na gefenta, ba dan masoyin nata ya so ba ya rabu da ita ta yi barcin. A bangaren Imran kuwa, bayan ya yi wanka ya shirya shirin barci ya kwanta tare da jawo wayarsa ya kira number daddyn Jelly dan ya yi hira da matar tasa, amma ina number a kashe, mamaki ne ya kama shi, a ransa ya yarda cewa ita ta kashe wayar, yasan tabbas wayar tana hannunta, kuma kaɗan daga aikinta, yanzu wani abin take shiryawa kenan. Bai damu ba ya ajiye wayar a gefensa ya ce zuwa anjima zai sake kiranta. Bai kai karfe 10 ba barci ta yi awon gaba da shi ba tare da ya shirya ba. Can cikin barci, har tsakiyar kansa ya tsinkayo ringing ɗin wayar tasa, ɗan motsawa ya yi tare da ɗan juyawa kaɗan, kira ta farko ta katse ta biyu ta sake shigowa, a hankali ya waro idanunsa yana kallon saman ɗakin, idanun nasa sun yi jawur dasu saboda barci bai ishe shi ba. Miƙewa ya yi tare da salatin annabi kafin ya ɗaura da addu'ar tashi daga barci, a hankali ya zura hannu ya ɗauko wayar tasa, ya kawota daidai saitin fuskarsa. Ganin number daddyn Jelly ne yasa ya ɗan washe idanunsa tare da kai kallonsa kan time dake jikin wayar, karfe shabiyu da rabi, ɗan zaro idanu waje ya yi, kafin ya yi picking call ɗin kiran ta katse. A gaggauce ya bi kiran, bugu ɗaya ta ɗauka, manna wayar a kunnensa ya yi, ban da sautin kukanta babu wani abin da yake tashi daga ta cikin wayar. Hankali a tashe ya miƙe zaune tare da yaye bargon da ya lulluɓa, bawan Allah har haɗe kalmomi yake yi wajen tambayarta me yake faruwa, me aka yi mata? Kara rushe mishi da kuka mai sauti ta yi, har da shessheƙa. Bai san lokacin da ya diro kasa daga saman gadon ba, cikin matsanancin tashin hankali mara misaltuwa yake kara tambayarta menene ya faru? Ina daddy yake?, Ina su Abbi? Wani abu ne ya same su?. Cikin kuka ta ce "Yaya Imran ni kazo yanzun nan, idan ka ɗan jima kaɗan mutuwa zan yi". "Subhanallah to naji zanzo yanzu, amma menene yake faruwa? Ina daddy? Wani abu ya same su ne? Idan baki gaya mini ba ba zan iya tuƙi ba WLH, hankali ba zai taɓa kwanciya ba". Kara sautin kukan nata ta yi tana faɗin "Kai dai kazo yanzu mana, idan ba haka wlh zan mutu, wayyo mummyna, nashiga ukuna na lalace". A firgice ya fita daga ɗakin, ko kashe wayar bai yi ba, tunaninsa kuma bata bashi cewa ya kira Abbi ko zai san me yake faru ba, ta rigada ta kiɗima shi sosai, Bawan Allah. Har ya kai tsakiyar palon sama, sai ya juyo ya dawo dan ya ɗauki key ɗin motarsa. A gaggauce ya fice daga ɗakin bayan ya ɗau key ɗin, kai tsaye bakin gate ya nufa, gateman yana zaune a bakin aikinsa, cikin fitar hayyaci ya bashi umarnin ya buɗe mishi gate, ganin yanayin da yake ciki yasa gateman ɗin ya yi wa Lion massage akan Prof zai fita kuma ga yanayin da yake ciki, da yake sam Lion bashi da nauyin barci har cikin tsakiyar kansa ya ji shigowar saƙon, sai dai bai duba ba, saboda idan baku manta ba, baya haɗa abu biyu lokaci guda, baya aikin kaza lokacin kaza, yanzu lokacin barci ne, dan haka babu wani abin da zai duba kuma. Shi kuma Imran cikin motarsa ya wuce tare da kunnata, ganin Lion bai yi mashi reply bane yasa gateman ɗin ya buɗe wa Imran ɗin gate, saboda duk wanda yake tare da Lion yasan shirun shi ma magana ce, baya shiru babu dalili, haka zalika baya magana babu dalili, a nasu faɗen idan har baya son Imran ya fita zai yi musu reply da su hana shi fita, idan ya yi shiru kuma yana nufin su barshi ya fita kenan. Kai tsaye gidan Abbi ya nufa, wani irin mahaukacin gudu yake shararawa a kan titin nan, har lokacin bai katse kiran ba, ita ma bata katse ba, tana jin duk abin da yake yi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya isa gidan, horn ya fara zubawa ba ɗaga kafa, ba ƙaramin tsorota mai gadin ya yi ba, da sauri ya taso har yana haɗawa da gudu ya zo ya buɗe mishi gate ɗin. A gaggauce ya danna hancin motar cikin gidan, ya kasa karisawa parking space na gidan ma, a tsakiyar gidan ya paka motar tare da fitowa da gudu, Allah ma yasa ya iso lafiya, kuma da yake darene babu motocin sosai a kan hanyan, da rana ne sai Allah kaɗai yasan me zai faru a irin yadda ya fiton nan, ga uban gudu da ya rinƙa shararawa. Kai tsaye cikin palo ya nufa, da mamakinsa sai ya ga kofar palon a buɗe, ba ɓata lokaci ya afka ciki kawai, sai haki yake yi bawan Allah. Wani irin birki ya ja ya tsaya turus yana ganin ikon Allah, zaune take saman sofa tana shan ice cream, kayan barci ne doguwar riga zuwa gwiwarta a jikinta, a wannan daren take shan ice cream mai uban sanyin nan, ta tsantsara make up kamar ba ita ba, sai tashin kamshi take yi, ta yi kyau sosai da sosai. Ganinsa yasa ta ajiye ice cream ɗin ta nufe shi da sauri tana faɗin "Haba yaya Imran rabon da na ganka tun yaushe?" Ta kai karshen maganar tare da faɗawa a saman kirjinsa tana turo baki. Tabbas ya yarda da maganar daddynta da yake cewa idan ka biyewa jelly, in bata kasheka ba, to zata haukata ka, yanzu wannan abin da ta yi mashi da yazo da karar kwana ai da shikenan sai dai a kwashi gawarsa, dubi yadda ya rinƙa sharara gudu a kan hanya, ba dan Allah ya tsare ya kawo shi lafiya ba ai da wani zancen ake yi yanzu ba nashi ba, zuciyarsa sai harbawa da sauri sauri take yi, da mai ƙaramin zuciya ne ma bugawa zuciyar tasa zata yi. A kule ya ce "Me yake faruwa kika kirani kina kuka?" Ba ko ɗar ɗar ta ce "Kewa mana, kewarka nake yi, wlh har ciwo zuciyata take yi mini, ka daɗe fa baka zo gidan nan ba, me nayi maka da zaka hana ni ganin fuskarka da kai kanka? Sai dai kayi ta kirana a waya ko?". Haushi tamkar ya sakar mata mari, amma ba komai zai yi mata abin da ya fi mari zafi, ya lura idan ba mai da ita cikakkiyar mace ya yi ba, ba zata taɓa yin hankali ba, zata yabawa aya zakinta yau wlh, ba tare da ya yi magana ba ya ɗauketa suka nufi waje, bata tambaye shi ina zai kai ta ba, sai ma kwanciya da ta yi a kirjinsa. Kai tsaye cikin motarsa ya sanyata a gidan gaba, har lokacin bata tambaye shi ba, shi ma bai yi magana ba, da gudu ya figi motar suka bar gidan suka nufi gidan Lion, matsowa ta yi ta kwantar da kanta a saman kafaɗarsa tana lumshe dara daran idanunta tare da shaƙar kamshin jikinsa........ ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E15-16 Kai tsaye cikin motarsa ya sanyata a gidan gaba, har lokacin bata tambaye shi ba, shi ma bai yi magana ba, da gudu ya figi motar suka bar gidan suka nufi gidan Lion, matsowa ta yi ta kwantar da kanta a saman kafaɗarsa tana lumshe dara daran idanunta tare da shaƙar kamshin jikinsa. Su Abbi kuwa, suna can suna barci basu san me yake faruwa ba. Wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kai hannunsa yana shafo kanta yana tuki da hannu ɗaya, rage guduwar motar ya yi dan kada a je a sami matsala. "Yaya Imran Allah nayi kewarka fa sosai, ka kai sati baka zo gida ba, kullum sai ka rinƙa cemin zaka zo zaka zo, amma shiru, yau dan ban san in da kake bane da sai na je na same ka". Allah sarki da iya gaskiyarta take kaunarsa kamar yadda yake kaunarta, bayan daddynta shi ne mutun na biyu da yake cikin zuciyarta, shi ne ko da yaushe yake ce mata zaizo zaizo kuma baya zuwa ɗin, shiyasa yau ta yi mishi wannan tsiyar dan ta samu ganin shi. "Haba jelly shi ne zaki yi mini irin wannan wasan? Idan da wani abin ya faru da ni fa? Kin san a wani hali na baro gida kuwa? Kin san halin da kika jefani kuwa? Kin san da ya na kariso gidan bappa kuwa? Gaskiya bai kamata ki yi mini haka ba, kuma ko da sunan wasa kada ki sake yi wa wani haka, ba iya ni kaɗai ba, kowa da kowa kada ki sake yi mishi irin wannan wasa, babu kyau, zaki iya sanya mutun ya mutu ko ya suma kin ji ko?". Ya yi maganar cikin sanyin murya, yasan yarinta ce ke damunta, kuma ya haɗu da kaunarsa da take yi, nan take ya ji zuciyarsa ta yi sanyi, saɓanin ɗazun da yake jin haushinta, yake kuma jin zuciyarsa na tafasa kamar zata faso jirjinsa ta ɓullo waje. Rungumo shi sosai tayi tare da manna mishi kiss a kumatu tana faɗin "To yaya Imran ba zan sake ba, amma kai ma dan Allah kada ka sake kin zuwa na ganka, idan kayi mini hakan Allah zan yi kuka". Horn ya yi a bakin gate ɗin gidan Lion yana shafa kanta, kasa kasa ya ce "Ba zan sake ba, yanzu ma aiki ne ya yi mini yawa yasa ban zo gareki ba, amma badan haka ba ai kema kin sa dole na zo wajen matata ko? Kin san fa ina masifar kaunarki, dole na kai kaina gareki farincikina". Murmushi ta fara yi mishi tana turo ɗan bakin nan nata kamar na daddynta, daidai lokacin gateman ya wangale mugu gate ɗin. Cikin natsuwa ya kutsa hancin motar cikin gida, kai tsaye parking space ya nufa. Bayan ya kashe motar ne ya juyo suna fuskantar juna. "Wannan kwalliyarfa?" Ɗan turo baki tayi. "Yaya Imran dan kai mana nayi, Aunty ce ta koya mini, dama nasan idan na kiraka zaka zo ne shiyasa nayi maka kwalliya idan kazo ka gani". Ba ƙaramin daɗi ya ji ba, hakan yasa ya jawota jikinsa sosai tare da rungumeta da kyau. "My jelly ina matukar kaunar ki, ina son ki matata, ba'a son raina nayi nisa dake ba, kullun cikin tunani da kuma kewarki nake, bana taɓa jin farinciki har sai na kalli hotonki, wai baki gani bana iya barci da daddare har sai na ji muryarki ne?" Shigewa jikinsa da kyau da kyau ta yi, a shagwaɓe ta ce "To yaya Imran ai nima kasan ina sonka ko?". Jinnina mata kai ya yi alamar e. "To tashi mu shiga ciki muje ɗaki ki kwanta a jikin nawa sarkin son jiki". Dariya ta yi tana ɓoye fuska na rashin kunya. Buɗe kofar motar ya yi tare da zuro kafafunsa waje, ita ma miƙewa ta yi daga jikin nasa ta buɗe nata kofar ta fito waje. Hannunta ya kama suka wuce cikin gida, sai zuba mishi surutu da shagwaɓa take yi, tun baya biye mata har ya fara biye mata. Suna shiga ɗaki ta sake shi ta haye gado tana miƙa, kwata kwata bata san kunyar miji ba, dan ita ɗauka ma take yi da yaya Imran da daddynta ɗaya ne a haukarta da yarintar ta, tana ganin ba wani abu bane, komai ta yi a gaban yaya Imran daidai ne. Bajewa ta yi abinta, ga rigar barcin tata bai gama rufe mata cinyarta ba, ta sha gyara sosai, skin nata har wani sheki yake yi, fatarta ta yi wani luwai kuwai da ita, ga tsantsi tamkar fatar jariri, ta buɗe mashi santala santalan cinyoyin nan nata a waje, daga ta samar rigar kuma, rabin tudun tula tulanta a waje, gasu sun sha gyara tamkar an hura balo balo, kamar an dasasu a wajen, ko da yake dashen Allah ne, ga wani balaƴaƴƴen sihirtaccen kyau da ta kara, ya haɗu kuma da ta yi make up, abin ba'a magana sai dai ace Masha Allah. Nan take ya nemi natsuwarsa ya rasa, lokacin guda ya fara jin wani irin azababben sha'awarta ta kama shi, dama can dannewa yake yi yana fama da lemon tsami, har sauya launi idanunsa suka yi, ba ƙaramin ƙoƙari yake yi ba wajen dannewa ya hakura idan ya ga koda hoton tane, idan baku mance ba, gabaɗaya abokansa cewa suke yi auren rage zafi ya yi saboda azababben sha'awar da yake da shi, har tsokanarsa suke yi akan lemon tsami ta daina yi mishi aiki saboda abin ya fi karfinsa............🤣 Hayewa saman gadon ya yi cikin sauri bayan ya kashe wutar ɗakin kenan, kusa da ita ya kwanta tare da tada kai da pillow da ta tada nata kan. Jin numfashinsa na fita da sauri sauri ne yasa ta ce "Yaya Imran lafiya kuwa?" Ɗan juyowa ya yi suna fuskantar juna. "Ba komai kwanta kiyi barci". Sarkin son jiki, juyowa ta yi tare da shigewa cikin jikinsa da kyau tana faɗin "To mu yi barci tare dai, wai ma yaya Imran wannan gidan waye ne? Ko shi ne gidan ka? Amma kuma su Gwaggo Batula suka kaini wani gida na daban mai shegen datti da wari, ita ma mai aikin gidan yar datti ce, ga masifa kamar kanwar tsigai?". Yatsarsa ɗaya ya ɗauka saman ɗan bakin nata. "Shiiiiiii ki yi shiru, baki ga dare ya yi bane? Ki yi barci sai da safe zan baki amsa". Bakin nata ta buɗe tare da capko yatsar nasa ta fara tsotsa tana ɗan ciza a hankali hankali, tamkar allura ta tsira mishi, cikin sauri ya kwace yatsar nasa tare da jawota jikinsa, sosai ya matseta, a cikin duhun ya fara laluɓar lips nata. Yana capkowa ya fara tsotsa kamar sweet, bata hana shi ba, sai ma capko nashi da ta yi ita ma ta shiga tsotsa, ba ƙaramin kara ɗaga mishi hankali ta yi ba, hannu ya zura ta saman wuyar rigarta ya capko tula tulanta, wadda guda ɗaya ya cika mashi hannu tap, kara narke mishi ta yi tare da ɗaura hannunta a saman bayansa. Sosai yake matsa breast ɗin nata son ranshi, sai wani irin numfashi da sauri sauri yake sakar mata, cikin dabara ya saki breast ɗin nata tare da kwance igiyar rigar ya rabata da shi, hakan ne kuma zai bashi damar ganin tula tulan nata a filin Allah. Zame bakinsa daga nata ya yi tare da mai da shi saman breast ɗin nata, shansu ya fara yi ba kakkautawa, yana shan ɗaya yana matsa ɗaya, da ta ji wuya sai ta fara yi mishi kuka tana ƙoƙarin ture shi, ina kara kakkameta ya yi yana zuba mata sambatu. Da gaske yake son shigarta yau, sai dai kuma lokacin da ya zo shiga sai ya tarar da har lokacin tana period, sam bai ji daɗi ba, yaso buɗe kayarsa a daren nan, ba dan ya so ba ya hakura ya yi wasa da ita ta yadda zai samu gamsuwa, daga nan ya rarrasheta. Sai da ya sami natsuwa ya kyaleta tare da miƙewa ya nufi toilet dan yin wanka, ita kuma ta shige cikin bargo ta lafe luf, kafin ya fito daga wanka har ta yi barci abinta, ga fuska bushe da hawaye, tasha kukan matse tula tula da ya yi. Shiryawa ya yi cikin wasu kayan barcin, ya haye saman gadon asuba ta gari. A ɓangaren gidan Akil kuwa, bayan Umaisha ta kammala waya da Aafia ɗakinsu ta koma, kwance ta isko shi saman gado yana fuskantar sama, kusa da shi ta zo ta kwanta tana faɗin "Yaya Akil tunanin me kake yi ne?". Dawo da kallonsa kanta ya yi, cike da so da kauna ya fara magana "Wife menene yake damunki? Meye Matsalar?" Zazzare wannan dara daran idanun nasu na gado wadda suka gado daga Na'urat da Dr Salman ta fara yi, da Dr Salman da Na'urat duk ba baya ba wajen dara daran idanu kamar ball, shiyasa abin ya bi family gabaɗaya, dayawa daga cikinsu akwai idanun kamar zasu faɗo kasa, musamman JEHAN da Rimsha, jelly da kuma AKILA, ita Jehan ma, girman idanun nata ba'a magana, idan baku mance ba sak daddynta take kama, shi kuma sak Na'urat yake kama. Ƴan kame kame ta fara yi mishi, zuba mata nashi dara daran idanun ya yi yana kallon tsantsar rashin gaskiya a tattare da ita, ya yi mata farin sani fiye da tunanin mai tunani, ya san abin da zata iya aikatawa da Wanda ba zata iya ba. Sake mai maita tambayar da ya yi mata da farko ya yi. "Yaya Akil babu komai fa". "Ba zaki gaya mini ba kenan ko?" Ɗago idanu ta yi tamkar zata yi kuka. "Wlh yaya Akil babu komai". A fusace ya ɗaga hannu zai mareta na rantsewar da ta yi a kan karya, sai kuma ya dakata, rai a ɓace yake kare mata kallo, ba ƙaramin haushi ya ji ba, ashe akwai abin da zata iya ɓoye mishi dan kada ya sani? Bata san cewa duk abin da take yi yana sane da ita ba, tun ranar da Ommu ta kirata a kan maganar kuɗin har zuwa yau yasan komai, ya yi mata shiru ne dan ya ga gudun ruwanta, yana son kuma ya ga ya ta ɗauke shi, mahimmancinsa ya kai yadda yake tunani ne ko dai da saura, ya ji daɗi sosai lokacin da ta kafe take gayawa Ommu alkharansa da kuma tabbatar mata da ba zai hanata kuɗin ba, hakan ya tabbatar mishi da ko a bayan idanunsa alkharinsa take faɗa ba kishiyarta ba, haka zalika ya ji makutar daɗin shawarar da Aafia ta bata, shi ba ɗaukar kuɗin ne damuwansa ba, no yana son Umaisha ɗin ta fahinci dokar Allah, sata ba abu bane mai kyau, kuma ya yi nasara tun da Aafia ta fahimtar da ita hakan, yasan matar tasa sai a hankali, gata yar Auta, gata rainon maza, ga rashin kulawar uwa, ƙwaƙwalwar tata sai a hankali, shiyasa wani lokaci yake binta da idanu kawai, yana kwatanta ƙwaƙwalwar tata tana kara buɗuwa ne ko ko jiya eyau, ba laifi tana kara buɗuwa sosai da sosai, musamman yanzu da Aafia take bata shawari da sauransu, ga Akila na kara mata lecture kala kala, duk kuma abin da suke yi da Akila da Aafia, duk shawarar da suke bata yana ji, kuma yana sane dasu, wani lokaci ya yi dariya, wani lokaci yayi ta mamakin a ina Akila ta koyo wannan abin dukka, ya sa a ransa nan gaba kaɗan zai aurar da AKILA, dan ta san komai, irin wannan lecture nata ko matan aure da suka shekara biyar zuwa goma a ɗakin miji sai haka. Yau dai Umaisha da Akil sun sami saɓani, kunsan mace mai ƙaramin ciki babu abin da ba zata iya aikatawa ba, hakan yasa yau ta mayarwa da Akil martani, har da ce mishi Bayahude, kalmar ta yi mishi zafi, amma ya yi mata uzuri saboda cikin nata, yana da ilimin sosai, yasan duk wata rigima ta mai ciki, ya san me yake yi sarai, hakan yasa sai bai kulata sosai ba, kuma bai yi fushi sosai ba, sai dai fa ya ji zafin maganganun da ta gaya mishi, dan kawai ya dage sai ta gaya mishi abin da yake damunta, yana son ji daga bakin ta ne, ita kuma ta kafe akan babu komai. Ransa a matukar ɓace ya ce mata wlh yau ba sai gobe ba zai yi yaji, kuma ba zai dawo gidan nan ba sai bayan wata guda, a kule ta ce mishi "Dan Allah yaya Akil kar ka dawo, ka tafi da haka ma, kai daman baka san na gaji da ganinka a cikin gidan nan bane? To idan ma baka sani ba yau na sanar da kai, da wani idonka kamar ball ɗin mota, sai ka rinƙa wani kallona, to ka wuce ka tafi kada ka sake dawowa". Tana masifar idanunta a rufe, ji yake yi tamkar ya ɗauketa da mari, amma ya danne ya yi mata uzuri saboda babynsa, yasan duk babynsa ne ya haddasa mata wannan masifar, saboda ma ba halinta bane ko iyawa bata yi ba, amma duk da haka ya kuduri niyar sai ya yi maganinta. Miƙewa ya yi tare da sauƙowa kasa daga saman gadon, drawer kayansa ya nufa, kaya kala biyar ya ɗauka masu kyau da tsada, kuma dukka manyan kaya ne babu kanana, ya zuba su a cikin wani kyakkyawar jakarsa tare da ɗauka ya fice mata daga ɗakin, har ya fita sai surfa masifa take yi idanu a rufe, da alama ma bata san ya fita ba. Sai bayan ƴan mintuna da tafiyarsa ne, da ta ji shiru sai ta waro idanun nata waje, ganin wayam babu kowa ne yasa ta ja guntun tsaki tare da komawa ta kwanta a saman gadon ta rungumo pillow, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita, sai faman sauke nauyayyar ajiyar zuciya yake yi cikin barci. (Akil da Umaisha manya, abin ba sauki🤣) MU KOMA GIDAN LION DAN JIN YADDA AKE CIKI. Misalin karfe 2 na dare, sanyi A.C ne fara ratsa dukkannin ilahirin jikinta, har cikkin kashi ɓargo da jijiya take jiyo wannan bala'in sanyin, ta jima a hakan kafin ta waro idanunta a hankali, kai tsaye saman ɗakin ta fara kallo, a hankali take jiyo sautin zazzaƙar muryarsa yana tashi, rera karatun Al Qur'ani mai girma yake yi cikin surarul Mai'da, ba karamin iya rairai kira'a ya yi ba. A hankali ta juyo da dara daran sleeping eyes ɗin nata izuwa ta in da take jiyo wannan zazzakar murya tasa, tsaye yake saman dadduma yana fuskartar gabas, jikinsa na sanye da jallabiya fara tas, blue light dake ɗakin ba ƙaramin kara bayyanar da kyan fuskarsa ta yi ba, ya ƙulle gashin kan nan nasa, jin abin Rimsha take yi tamkar a mafarkinta da ta saba yi, bata yarda a zahiri bane, dan haka sai ta tsare shi da idanu tana kare mashi kallo. A haka Areef ya fito daga cikin toilet ya isko ta, shima Alwala ya ɗauro, da alama ya yi wanka, dan ya cire kayan barcin jikinsa, ya zura farar kalla ash color. Bai lura da idanunta a buɗe ba, wucewa ya yi, gefen ɗan uwan nasa yazo ya tsaya tare da ta da hiƙama ya tada kabbara, da yake daddumar irin manyan nan ne masu faɗi ga bala'in laushi, sai ta ishe su suka tsaya a tare. Ganin Areef yasa ta yarda ba mafarki take yi ba, a hankali ta miƙe zaune, har wani jiri take ji, sanyin Ac ne ya farfaɗo da ita. Sai da ta bari Lion ya yi sujjada ta miƙe da sauri ta nufi waje, sai tangal tangal take yi kamar zata faɗi kasa sabida yunwa, bata ci abincin dare ba, haka ta jure ta kame jikinta ta nufi waje. Kai tsaye bedroom nata ta wuce, Akila nata sharara barci kamar bata duniyar mutane, sai wani sauƙe numfashi take yi a hankali hankali, gefenta ta je ta haye ta kwanta, ta so ta yi nafila koda raka'a huɗu ne, amma ina barci ya ci karfinta, sai kawai ta hakura ta kwanta, ranta cike da mamakin hali irin na Saif, duk wani abu da cikakken musulmi mai imani ya kamata ya yi, Saif yana yin shi, sai shegen bakar zuciya kamar kafuran farko, bashi da Imani da tausayi a cewarta. Ranta cike da tunanin zazzakar sexy voice nasa har barci ya yi awon gana da ita. Washegari gari da misalin karfe 8: 30. A hankali ya waro ash eyes nasa a kan fuskar ɗan uwan nasa, zuba mishi idanu ya yi yana kare mishi kallo, hannu ya kai cike da tsokana zai ja hancin ɗan uwan nasa, kamar daga sama ya damki hannun nasa yana girgiza mishi kai alamar kada ya kuskura. "Good morning my Lion". Ya yi maganar cikin zolaya, har lokacin bai buɗe idanunsa ba, dan yau barci sosai yake ji. Sake kai hannu ya yi zai taɓa shi, can kasa kasa da murya irin na mai barci ya ce "Wai meyasa nikam kake takura mini ne Areef?" Matsowa kusa da kunnensa ya yi, kamar mai raɗa ya furta "So mana, son ka yasa nake takura maka". Shammatarsa Lion ɗin ya yi idanu a rufe ya damƙo gashin kan ɗan uwan nasa. Ƴar kara ya yi yana faɗin "Kai kai kai wlh yau ba zan kyakeka ba, amma dai please ɗan sake mini gashin, ko dan saboda kai wlh dole na yanke gashi nan ya huta, muguntarka a kan gashin nan ta fara isata". Lion bashi da wajen kamawa a jikin ƴan uwan nasa sai wannan gashin nasu, da shi yake morarsu. Waro dara daran blue eyes nasa masu ɗauke da barci ya yi, kai tsaye fuskar ɗan uwan nasa ya sauƙe su. "Wai kai Areef me ma ya dawo da kai ɗakin nan ne?". Sai ciza laɓɓansa yake yi saboda zafi. "Ni da ɗakina ka ce me ya dawo dani, ai ni na dawo nan kenan". "Baka isa ba, yau zaka bar ɗakin nan saboda kana takura mini". Yana riƙe mishi da gashinsa yana ja amma bakinsa yake mutuwa. "Wlh Lion babu in da zanje, sai dai kai ka canza ɗaki, ni nan ɗakin ne ya yi mini". Kara jan gashim nasa da karfi Lion ɗin ya yi. Da sauri ya ce "Wash daddyna, haba mana ɗan kyakkyawan mu, beautytin TRIPLETS, kai fa babynmu ne, to sake ni". Zubawa face ɗin Areef ɗin idanu ya yi, mamaki yake yi na irin gasken da shi kuma ya kara, shi Lion ya ɗan yi duhu saboda zafi, shi kuma Areef ya kara haske, hakan zai tabbatar maka kowa da yanayin jikinsa, kowa da abin da ta fi karɓar jikinsa, sai kaga wani ya sha magani ta yi mishi, kai kuma idan ka sha, ba zata yi maka ba, saboda yanayin jikin daban daban. "Haba mana Lion ka sake ni mana, kai ne fa farincikin mu, shi ne ni kuma kake saka ni kuka, ba komai mai rama mini na nan zuwa". Shiru dai Lion bai tanka shi ba, kuma bai sake shi ba, dama sai su yi magana wajen sau uku ba ya tankawa. "Wlh Lion ka jira ka gani duk wannan abin da kake yi mini mai rana mini na nan zuwa, shiyasa fa kaga nake kula da i......." Sai kuma ya yi shiru, dan yasan idan ya karisar da wannan magana ba zasu wanye lafiya a ɗakin nan ba, kuma ya ja ma Rimsha sabuwar wahala da bala'i, dai in ba'a sa'a bama Lion sai ya koreta daga gidan nan ko kuma ya haɗata da aikin azaba, tuna hakan yasa ya yanke maganar. Tsab Lion ya san karkashin harshensa, yasan abin da yake son faɗe, sai dai bai san a kan waye Areef ɗin yake magana ba, mace ce ko naiji, oho bai san mishi ba, abin da yasa bai damu ba ma kenan, kuma shi yana ganin ai inaaa, ba wadda ya isa ya ɗaga mishi murya a duniyar nan. "Lion wai ba zaka sake ni ba?". "Areef Allah kana kure ni, idan ka bari wata rana na yi maka wata capka ba zaka ga da kyau ba". Ya kai karshen maganar yana sakin gashin. Areef zai yi magana Imran ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, a tare suka amsa sallamar. Saman gadon nasu shima ya haye, kallo ɗaya Areef ya yi mishi ya kwashe da dariya. Da mamaki Imran yake kallon yadda Areef ɗin ke dariya kamar ba lafiya ba, shi kuwa Lion da yake yasan me Areef yake yi wa dariya sai ya kawar da kansa gefe guda, dan da Areef da Imran sai dai shiriyar Allah za'a neman musu, da kallo ɗaya shi ma Lion ya yi wa Imran ɗin ya fahimci matsalar, amma bai bi ta kansu ba, sai ya kawar da kansa gefe guda. "Areef ban san iskanci fa, me kake yi wa dariya kuma?". Bai tanka ba har sai da ya yi dariyarsa mai isarsa, ya tsagaita na ƴan mintoci kafin ya ce "Wai Prof ni kam ba kana da mata ba?" Gyaɗa mishi kai ya yi alamar e. "To me yasa ba zaka ɗauko kayarka ba, kake wahalar da kanka, kasan illar yin hakan kuwa? Tana da illar sosai ga lafiya wlh, tun muna school na gaya maka kada ka daka ta Lion da Aseef basu san daɗin duniya ba, idan ka biye musu zaka mutu a bushe kamar itace". Wani damka Lion ya kai mishi a gashi kai again, Areef ya yi mugun sako shi a gaba kwana biyun nan, dan iskanci ko wani misali ya tashi yi sai ya kwatanta da shi, yanzu shi da Aseef ne basu san daɗin duniya ba kenan? To me daɗin duniyar?. Shi kuwa faɗawa jikin ɗan uwan nasa ya yi yana dariya. "Allah Lion baka son gaskiya, yanzu ba gaskiya na faɗa bane? Duk wanda ya biye muku kai da Aseef to zai mutu kamar bushasshiyar kifi or itace, idan kuma ka ce ba haka ba to me yasa......." Kasa karisa maganar ya yi saboda wani dalili nashi na kansa. "Ni kam Areef ni sa'an ka ne? Ni abokin wasan kane?" Ya faɗa yana ɗaure fuska alamar ba wasa. Shi kuwa Areef cikin dariya ya ce "Yes kai Sa'a na ne mana, abokin wasa kuma ai daga kai da Aseef sai Prof". Shiru ya yi bai sake tanka musu ba, dan ya lura idan ya biyewa Areef yana iya yi mishi illah, ko kuma su yi faɗa, dama an samu shekaru basu yi faɗa ba, a lokacin da suke ƴan 22 to 23 years, kullun na Allah ne sai sun yi faɗa, lokacin shi ma Areef akwai zafin zuciya, Lion bala'in zuciya rashin hakuri, Aseef zuciya, kun san lokacin ciwonsa, to haka zasu yi ta faɗa duk gidan ba mai iya raba su, sai sun jiwa kansu ciwo sun daku iya dakuwa ga junansu, sannan su hakura idan sun gaji, idan suka fara faɗa ko Uncle T tsoron tinkararsu yake yi kada su haɗa da shi, daddy kuwa har kuka yake yi idan sun fara, dan yasan ba shakka sai sun jiwa kansu ciwo, dan dukkansu ba baya ba wajen karfi ga zuciyar bala'i, ɗaya ya ce ba zai hakura ba, idan aka mishi sai ya rama, idan ya rama shima wadda aka rama ya ce ba zai bari ba, babu hakuri ko ɗaga kafa, haka zasu yi ta yi, amma yanzu Alhamdulila sun samu tsawon shekaru a kallah 6 basu yi faɗa ba, kuma duk da wannan faɗa da suke yi fa basu cin abincin idan har ɗaya daga cikinsu baya nan, a tare suke komai, har kwana ɗaki ɗaya suke yi, gado ne uku a cikin ɗakin nasu a lokacin, tun ainahi suna kaunar junansu fiye da tunanin mai tunani, sai dai kunsan dama ana samun faɗa irin haka a tsakanin ƴan uwa, musamman ma twins or Triplets. STORY💋 "Yauwa Prof menene Aduwa?". Cewar Areef. Shiru ya ɗan yi yana tunanin menene ma wannan aduwar. Katse mishi tunani ya yi da cewa "To koma menene ka haɗa da aduwa da goribar ka kawo mini da wuri fa" "Tom za'a kawo yau ma zan je kasuwar barci ba za'a rasa ba". Okey ya amsa da shi, daga nan ba su sake yi wa juna magana ba, suna kwanta shiru. Can after some minutes Areef ya ce "Prof na mance ka ce da sister ta shirya zuwa Monday ta koma school". Ɗan satar kallon Lion dake kwance yana fuskantar gefe da su ya yi, kafin ya ce "Okey amma naji matukar daɗi over wlh". Ya kai karshen maganar tare da shafa kyakkyawar dark black curly hair Lion ɗin. Juyo da blue eyes nasa ya yi a kansu. Ganin irin murmushin dake a kan fuskar Imran da kuma ɗan uwan nasa yasa ya ji daɗi sosai, yana son ganin Imran cikin farinciki kamar yadda yake son ganin TRIPLETS nasa, har cikin ransa yake jin Kaunar shi, bai taɓa son wani bayan TRIPLETS nasa kamar yadda ya so Imran ba. Haka suka cigaba da nishaɗi suna hira, duk da bai sanya musu baki ba, yana matikar jin daɗin yadda suke hira da dariya haka. AFTER SOME DAYS GIDAN HAJIYAR DAƊI 😭. Tsawon kwanaki uku kenan yau su JEHAN suna rufe a cikin toilet, babu ruwa babu abinci, duk sun fita hayyacinsu, duk kyankyani irin na Jehan jiya sai da ta sha ruwan famfom toilet ɗin dan ta ceci rayuwarta kada ta mutu, sai kuka Adiva take yi, Allah sarki bata saba ba, ga yinwa ga kishin ruwa, sun yi ƙoƙarin buɗe kofar toilet ɗin amma abin ya ci tura, idan baku mance ba ta baya Zinariya suka rufe su, duk sun yi tsuru tsuru da su abin tausayi, sun fita hayyacinsu, tsabar yunwa tasa basu gani sosai, A'isha dai ta yi dana sanin biyewa Jehan, sun buga kofar toilet nan har suka gaji, ko motsin mutane basu ji ba, tamkar basu a duniya, tamkar babu kowa a gidan, Jehan ta yi kokarin buge wurar dake jikin window toilet ɗin dan taga me a wajen, sai taga akwai karafuna ta waje a jikin window, ba halin fita, kuma duk a cikin gidan window yake, ba a waje bane. Idanuwan Jehan sun ƙanƙance sun yi jawur, da akwai dama, da ta yi kuka ita ma, amma ta daure tana rarrashin Adiva, banda sunan Allah babu abinda take kira, ta rasa madafa, sai yanzu zantukan daddynta ke dawo mata a cikin kunnenta, lokacin da yake neman takara, yana yawan gayawa uncle Shitu, idan zaka yi gyara ko kana son dakatar da wata ɓarna a ƙasar nan, to kada ka yarda ko da sunan wasa ka fitar sa nufin ka, dan akwai wasu shegun kuraye da dama da basu son a kawo gyara, su burinsu kawai a ɓata, kansu kawai suka sani, idan zasu ji daɗi to kowa ma ya mutu in yana so, idan ka kuskura ka fitar da nufinka na kawo gyara, to zaka ɓata, kuma ɓata ta har abada, za'a rufe babinka, za'a shafeka tamkar ba'a taɓa yin ka ba, jama'ar dake goya maka baya ma, duk zasu juya maka baya, a kullum jama'a suna amfani da abin da suka ji, ko kuma abin da aka shirya musu karya a kansa suka kalla, ba zasu taɓa yin tunani da kwakwalwarsu ba, da zarar ka shirya musu ƴar karamar karya tsab zasu yarda su hau kai su zauna, sai ka rasa wani irin kwakwalwa ce da mutanen mu, sai ka rasa me yake damunsu, ga gaskiya suna gani sai su take, shi ne babbar matsalar ƴan kasarmu, da suna da zuciyar tsayawa a kan gaskiya, dagiya a kan adalci, cire son zuciya, cin hanci da rashawa, su daina duba ɗan karamin abin da za'a basu, su duba al'ummarsu, su duba cewa wannan ɗan abin da za'a basu zai kare su sake komawa wahala, amma idan suka tsaya tsayin daga a kan ayi adalci, a kawo gyara, a dakatar da ɓarna, to ko basu sami komai ba, adalci ta tabbata zasu ji daɗin rayuwa fiye da tunanin mai tunani, a ƙasar nan ba'a yaki da rashin gaskiya gaba da gaba, idan ka kuskura ka yi gigin yin hakan, to zaka yi danasanin zuwarka duniya, ta karkashin kasa ake yakar tsinannu shegu, ta karkashin kasa ta in da basu zata ba, ta nan zaka yaki duk wasu kuraye marasa adalci masu tauye gaskiya. Tuna zantikan daddynta yasa ta fara hawaye, yau ne ta tabbatar da abin da daddyn nata yake faɗe, sai dai kayi yaƙin sunkuru da rashin gaskiya, ba dai ka yi gaba da gaba ba. Ganin tana hawaye yasa Adiva ta dafata tana faɗin "Jehan lafiya kike hawaye haka?". Girgiza kai ta fara yi kafin ta fara magana. "Adiva daddy ya yi gaskiya, yanzu kinga da muna nuna zamu yaki gidan nan ta karfin tsiya, kinga mun kare a cikin toilet, daman daddy ya ce ta karkashin kasa ake yakar rashin adalci, yanzu na gane nufin daddy, hawayen da nake yi kuma saboda daddyna nake yin shi, daddyna ina yake? Yana raye ne ko ya mutu? Bana jin ya mutu Adiva, bana jin hakan a jikina, na fi zaton yana wani wajen yana rayuwa, ya Allah ka kare mini iyayena da ƴan uwana, Rimsha ƴar uwata ɗaya tilo a duniya, ko a ina take yanzu Oho, ita ma ina ji a jikina tana raye, tana wani wajen, Allah sarki, Allah ka kawo mana mafita". Ta kai karshen maganar tana goge hawayen fuskarta. A cikin wannan kwana uku da suka yi a rufe, sallah ma a zaune suke yin shi a cikin toilet ɗin, ita Jehan azumi take ɗauka a gabaɗaya kwana ukun, shiyasa abin ya yi mata sauki, su A'isha kuwa, ruwan toilet ɗin suke wuni sha ba abinci, cikinsu ya yi ta ciwo kamar zasu mutu, haka zasu wuni suna hawaye, da daddare kuwa, Adiva da Maryam cikin baf ɗin wanka suke shagewa su kwanta, ita kuwa Jehan a zaune take kwana, idan barci ya kwasheta har faɗuwa take yi wani lokacin, Aisha kuwa, a kasa mai gabaɗaya take kwanciya dan suna wanke toilet ɗin, Bayin Allah nan abin tausayi, duk wanda ya gansu sai ya matsa musu kwallah, har wani shegiyar rama suke yi. Su kuwa su Zinariya, suna can suna harkokin gabansu, sun kawo sabbin ƴan mata da wasu sabbin matan aure ƴan hannu, kuɗi nata kara shigowa kamar ba gobe, sun bar bayin Allah a cikin toilet, tamkar ba rayuka suka rufe a ciki ba, Allah dai ya yi mana maganinsu ya toni asirin tsinannu shegu. In Sha Allah sai sun girbi abin da suka shuka, zasu ɗanɗani ƙuɗarsu kuwa. WANNAN KENAN A GIDAN HAJIYAR DAƊI BARI MU LEƘA GIDAN LION DAN JIN YA AKE CIKI. AFTER SOME DAYS. Yau ma dai tsala wanka suka yi, suka shirya cikin kananan kaya, a yau ne kuma Imran ya tafi karɓo musu ɗin kinsu dake wajen tela, yana fita ba jimawa suka shirya cikin wando jeans ash color mai shegen kyau, ta ɗan kamasu daga ta sama, ta kasar kuma ta buɗe, riga kuma top ce pink color, sun yi kyau sosai kamar ka sace su ka gudu da su, Rimsha zata ɗaure gashin kanta Akila ta hanata, wai ta sake shi kamar ba Indiya, kuma kun san yadda gashin nata yake, sak gashin kakanta Na'urat, abin ba'a cewa komai sai dai Masha Allah. Haka ta biyewa Akila ta saki gashin har gadon baya, perfume ɗin Akila suka sanya a jikinsu, Rimsha ta fito kamar baturiya sai dai hasken fatar ne kawai da bata da shi kamar nasu, ita kuma Akila da yake gashin ta bai kai na Rimsha tsawo ba, sai ta ɗaure shi tare da sanya ɗan ƙaramin handkerchief ta ɗara a gaban goshinta, tsakiyar kanta a waje. Da farko Rimsha ta ce ba zata fita babu ɗan kwali ba, daga ƙarshe kuma da Akilar ta yi ta zugata, sai ta yarda suka nufi waje a hakan. Babu kowa a palon sama, dan haka sai suka sauƙa kasa, nan ma babu kowa, waje gabaɗaya suka nufa, ita kuma Jelly tana can tana barci abinta. Garden ɗin gidan suka nufa, sai satar kallon sojojin da Lion ya karo Akila take yi, ita kuma Rimsha tsoronsu ma take ji, fuskokinsu kamar wasu shanaye a ɗaure, ita kuma Akila kyau take kalla, taga fararen turawa, ga tsawo ga murɗewar jiki, shiyasa take ta faman satar kallonsu. A ƴan kwana biyun nan dukka Imran ne yake yin aikin Rimsha na gyara ɗakin Lion da na su Mark, dan har ga Allah Rimsha bata iya gyaran ɗaki ba, bata san yadda ake yi ba, bare ma gyaran gado, sam bata iya ba, a hankali hankali dai tana koya. Babu kowa a garden ɗin, zama suka yi, Rimsha ta ce bari ta ɗauko masu ice cream su sha, dan su ji daɗin hira, to Akila ta amsa mata da shi, miƙewa ta yi ta koma cikin gida, ita kuma Akila ta zauna shiru sai kalle kalle take yi, garden ɗin ya haɗu iya haɗawa ba karya. Daga karshe ta ɗauko wayarta ta fara latsawa. Fitar Rimsha ke da wuya, sai ga Areef sanye yake da Army trouser, da kuma farar T-shirt, ya yi kyau sosai, yau da alama yana ji da tsiya, domin kuwa ya yi kitso guda bibbiyu ta gefe da gefen kunnuwansa, kuma ba ƙaramin kyau suka yi mishi ba, sauran gashin nasa kuma, ya tara a tsakiyar kansa ya ɗaure, hannunsa na riƙe da wani cup mai shegen kyau, sai tiririn hayaki ne ke fita daga cikin cup ɗin, da alama coffee ne a ciki, kafafunsa na sanye cikin home sleepers masu shegen laushi launin ash color, ɗayar hannunsa na riƙe da wayarsa yana latsawa, da alama kuma wani saƙon yake turawa. Kwata kwata bai san da mutun a cikin garden ɗin ba, sai ya shiga da sallah kasa kasa ta yadda babu wanda zai iya ji, ita dai kanta na kan wayarta tana karanta saƙon ɓoyayyen masoyinta. Bai lura da ita ba, wucewa ya yi zai zauna, kwatsam ta ɗago kai dan jin ɗan motsi da ta yi, shi ma kuma a lokacin ne ya lura da ita, a razane ta......... ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E17-18 Bai lura da ita ba, wucewa ya yi zai zauna, kwatsam ta ɗago kai dan jin ɗan motsi da ta yi, shi ma kuma a lokacin ne ya lura da ita, a razane ta miƙe tsaye tana kallon shi, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, shi kuma cool murmushi ya saki kafin ya zauna a in da yake son zama tare da ajiye cup ɗin hannunsa. "Why are you standing?" Ya faɗa cikin sanyin murya, ya yi maganar kuma yana ƙoƙarin fara latsa wayarsa. A hankali ta koma ta zauna tana kare mishi kallo, tabbas wannan shi ne a hoton da ɓoyayyen masoyi ya tura mata, sai dai hoton tun yana ɗan 22 years kenan? Ta tambayi kanta da kanta, duk da bata kalli fuskarsa sosai ba a hoton, tabbas soyayyar da take yi mishi ta gaskiya ce, tabbas ko a ina zata iya gane shi, tabbas ma shi ne, TO FA BABBAR MAGANA. "Prof sister right?" Ya faɗa yana mai dawo da kallonsa a kanta, da kyar ta ɗaga mashi kai alamar e, mamaki take yi yadda ya nuna kamar bai gane ta ba, kenan yana tunanin ita ba zata iya gane shi bane dan ya tura mata hotonsa yana ɗan 22 years ko yaya yake nufi? Ta sake tambayar kanta da kanta, tambayar kuma da bata da amsarsa. "Heartbeat right?" Ya sake tambayarta, kara zaro idanunta waje sosai kamar zasu firfito su faɗi kasa ta yi, domin sai yanzu ma ta ji wannan zazzakar murya tasa, kuma wlh yadda ya kira Heartbeat ɗin nan, haka yake kiranta a waya, tabbas shi ne, daddaɗar muryarsa ne, kyau nasa ne, komai da komai na sa ne, ta kasa magana, sai kare mishi kallo take yi, yanzu tambaya biyu ya yi mata bata amsa ba. Ganin tana ta kallon shi ne yasa ya kashe mata ido ɗaya tare da ɗaga mata gera ɗaya yana faɗin "Nayi maki kyau ne?" Duk maganar da yake yi cikin harshen turanci yake yi, babu hausa ko ɗigo a bakinsa, watakila yana tunanin bata gane shi bane yasa bai yi hausa ba, ko kuma dai ya abin yake ne? Na kasa ganewa. "Heartbeat ki yi magana mana? Why ki ke ta kallona haka? Shin na yi wani laifi ne, ko dai kina so na ne?". Ya kai karshen maganar cikin zolaya. Miƙewa ta yi da sauri dan ta gudu da nufin ta bar wajen, in dai shi ne ɓoyayyen masoyi to bata son shin, domin dama idan baku mance ba, ta ce bata son maza masu yin gym, kuma shi Areef tamkar Lion yake, yana yin gym sosai da sosai. Ganin zata gudu ne yasa ya yi saurin miƙewa ya riƙo hannunta yana kare mata kallo. "Heartbeat what is the problem? Why ina yi maki magana you refuse to amsa me, and then kina ta kallona, daga karshe ki tashi zaki gudu, menene matsalar, ko dai kin fasa so na ɗin ne?" Ya faɗa yana ɗaga mata gera ɗaya alamar zolaya. Ƙoƙarin kwace kanta take yi dan ta gudu, da karfi ya jawota jikinsa har sai da ta buge shi a ciwonsa, wash ya ɗan furta da karfi. Zuba mashi ido ta yi tana kare mashi kallo, ya riƙera sosai, sai kare mata kallo from Head to toe shi ma yake yi, wani tunani ne ya faɗo mata, tun da bai nuna ya santa ba, ita ma ta biye mashi a haka taga karshen me zai yi, ba dai ya ce ranar Wednesday zai zo gida ba, to ai gobe ne Wednesday, ta biye a je a bai santa ba, zata ga ranar Wednesday idan ya zo gida kuma me zai sake ce mata, dan dai ita ta san wlh shi ne wannan, ko kaffara ba zata yi ba, kallon ƙurillah ta yi wa hotonsa, wannan brawn hair ɗin nasa, sannan ga muryarsa, yadda ya kirata da Heartbeat yanzu, tamkar yadda yake faɗa ne a waya, ga shi yanzu ya ce ko ta dai'na son shi ne, akwai hujjoji da dama da suke tabbatar mata da tabbas ko rantsuwa ta yi ba zata yi kaffara ba shi ɗin ne. Yin wannan tunani yasa kasa kasa ta ce "To sake ni na gaya maka". Da hausa ta yi maganar, amma kuma tamkar ya ji me ta ce, sai ya sake ta tare da komawa ya zauna a saman sofar, domin sosai yaji zafin buge mashi ciwon nan da tayi. Komawa itama ta yi ta zauna a saman nata sofar in da ta tashi. Zuba mata waƴan nan shegun rikitattun dara daran ash eyes ɗin nasa ya yi, duk yasa ta tsargu, sai wasu ƴan kame kame take yi, mamaki ne ya rufe shi, wai ita heartbeat me matsalar ta ne? Ya tambayi kansa. Ita kuma Rimsha tana barin wajen da nufi ta je ta kawo masu ice cream, a palo ta haɗu da Imran ya dawo daga karɓo musu kaya, zai fita ita kuma ta shigo palon kenan, sai ya ce ta je ta kaiwa Saif abincin rana, mamaki tayi sosai akan meyasa daga jiya zuwa yau Lion yake cin abicni akan lokaci, kuma yake barci a kan lokaci, Meyasa? Abin da bata sani ba shi ne, dama tarin tulin aiki da rashin kwanciyar hankali yasa baya samun damar cin abinci, amma yanzu Alhamdulila da mumnynsa da ɗan uwansa sun tsira daga wajen waƴan nan tsinannun matsafan, babu wata aiki da ta rage mashi fa ce aikin daddynta daya fara last week, yanzu ya samu kwanciyar hankali sosai, domin shi ƴan iskan Nigeria bai ɗaukesu a wata tsiya ba, gani case ɗin daddynta yake yi kamar cin kaza ne, dama yakin da su TAG za su je ne yasa bai mai da hankali a kan aikin daddyn nata ba, ya tattara hankalinsa a kan nasarar su TAG ɗin, yanzu kuma tun jiya bai sake duba case ɗin ba, yana ɗan busy na tura gawarwakin sojojin da a ka kashe zuwa ga iyalansu da sauran abin da ya dace a matsayinsa na babba, to a takaice dai yanzu ya sami kwanciyar hankali yana da damar cin abinci sosai da kuma samun barci akan lokaci. To kun ji abin da yasa tun da Rimsha ta bar garden bata dawo ba. Shiru suka zauna a garden ɗin, tunani kala kala ne cike fal a cikin ranta, shi kuma ya tsareta da idanu sai kallonta yake yi kamar zai cinyeta ɗanye, tamkar mai son yin wata magana, amma kuma bai ce komai ba. Ganin ta yi kasa da kai ta yi shiru ne yasa ya ɗauko cup ɗin coffee ɗinsa yana faɗin "Zo na baki coffee a baki to, kila idan na baki, zaki iya yi mini magana" . Har wayau cikin harshen turanci ya yi maganar. Kara rikicewa ta yi, wlh haka yake ce mata a waya, sai ya ce ta zo ya bata coffee a baki, amma yanzu ya nuna kamar bai gane ta ba, lallai ma mutumin nan ya kware a iya basaja, shi ɗin number ɗaya ne. Shi kuma ya kasa hakuri ya shareta, yana son ta saki jiki su yi hira, dan haka sai ya miƙe ya dawo kusa da ita, a saman sofar ya zauna yana faɗin "To buɗe baki na zuba maki". Yana magana yana kawo mata cup ɗin saitin ɗan bakinta. "Na ƙoshi ni kam!" Shi ne abin da ta faɗa, kuma cikin harshen Hausa ta yi maganar, ga mamakinta sai ta ji ya ce "No open your mouth". Shi kuma dai da turanci yake magana, kwata kwata yaki furta ko word ɗaya da Hausa, amma kuma ga dukkan alamu dai yana jin yaren, tun da ga shi idan ta yi magana yana ji har yana amsa mata da English. A wannan hali Imran ya shigo ya same su, har cikin ransa bai ji daɗin dressing dake a jikinta ba, ya ji haushi sosai, yana ƙoƙarin hana Rimsha yin irin wannan shiga, ita kuma ta zo ta yi, sai dai bai damu ba dan ya ganta kusa da Areef, yasan halin Areef sarai da wasa da dariya, kuma Areef ya yi mata farin sani, ita ce bata san shi ba, tun suna makaranta Imran ɗin yake yawan basu labarin Heartbeat ɗin sa, idan sun je yin shopping na school, in ya ga wani color irin wadda take so, yana ce masu ga irin color da my Heartbeat take so, a takaice dai Areef ya santa sosai, ita ce bata san shi ba, bata taɓa ganinsu face to face ba, yanzu haka akwai hotunan ita Akilar ita da Imran da Akil duk akwai hotunansu a wayar Areef ɗin, yana ma da hotonta tun bata kai haka ba, lokacin tana karama, lokacin suna school da Imran, idan ta turo ma Imran ɗin hoton, sai Areef ɗin ya ce ya tura mashi zai ajiye hoton kanwarsa, duk lokacin da ya je Nigeria in ya ganta a hanya ya ganeta, wasa wasa Areef ya tara hotunanta dayawa a email nasa, idan baku manta ba shi dai Areef na kowa ne, ya iya zama da mutane sosai da sosai. Ganin Imran yasa ta miƙe da sauri zata rungume shi, sai ta tuna idan ta rungume shi yau sai sunyi faɗa da masoyin nata, domin kuwa ko hannunta wani ya taɓa sai sunyi faɗa da shi, sai ya yi fushi, kuma bata son fushinsa ko kaɗan, dan haka sai ta fasa rungumar yayan nata, ta tsaya a gefensa tana karewa Areef kallo. Mamaki sosai Imran ya yi akan meyasa bata rungume shi ba, bayan kuma ta saba yin hakan?. Hannunta ya riƙe suka zauna yana mai yi mata faɗa akan irin wannan shiga da ta yi, sai binsu da ash eyes nasan nan yake yi, yana ta murmushi. "Prof where is my Rimsha?" Ya tambaya yana ƙoƙarin kunna hasken screen ɗin wayarsa. "Ta je kaiwa Saif abinci". Cool murmushi ya saki kafin ya ce "Saif!! Saif!! Hmmm wlh Saif idan Allah ya tashi kama shi ba zai yi mashi da kyau ba, ya yi laifi dayawa wlh, Allah dai ya yafe mashi, ni bana da wani damuwa, dan na san our Queen tana da kirki, shiyasa ma fa na zaɓa mashi ita, tana da hakurin jure halinsa, zata jure, yana da saurin hawa, shi ma wannan zata jure, zuciyar bala'i, zata jure, nuna tsantsar isa akan abin da ba mallakinsa ba, ya dage sai ya juya kowa da kowa ya zama kamar uban kowa, shima zata jure, sai dai kuma kasan me nake tunani Prof?". Girgiza kai ya yi alamar A'a. "Yana da matukar wuyar gaske uncle Hosain ya bawa ɗan uwana Rimsha". "Meyasa ka ce haka Areef?". "Hmmmm kai baka san faɗar dake tsakanin uncle da Lion bane, ni ranar da uncle ya zo aka ce sister ƴarsa ce, ba abin da ya faɗo mani a raina face wannan rikici dake a tsakaninsu, Lion fa ya mayar da uncle kamar wani yaron shi ne, fata na dai Allah ya daidai ta su kafin nan". Amin suka amsa da shi, daga nan suka yi shiru kowa da abin da yake tunani, shi Areef yana tunanin da ace idan Lion ya gama warware case ɗin Musharraf ya ɗauki mataki a kai, to da zai gayawa Musharraf ɗin, wata kila ya yafe mashi, mari da kuma abubuwa da ya yi mashi, sai dai shi Lion baya abu ya faɗa, kamar yadda bai tambayesu menene gaskiyar abin da ya faru ba, to haka idan ya binciko gaskiya ba gaya masu zai yi ba, idan ma yaga suna da laifi, sai dai ya sanya a hukuntasu ba tare da sun san waye ya hukunta su ɗin ba, kuma a kan me aka hukuntasu ɗin, mafiya yawancin lokuta haka yake yi akan wadda suke tare, shi wani irin bahagon mutun ne da baka gane mishi, idan kuma haka ne akwai gagarumin matsala, domin shi ma daddyn Rimsha zuciya gare shi kamar me, tun da ga shi har yau ya kasa mance abin da su Abba suka yi mashi, kuma yana sane sun yi nadama, duk da haka ya riƙesu a rai, to fa da alama haka ya riƙe Lion ma a rai. RIMSHA💋 Kai tsaye kitchen ta nufa, kamar kullum sai da ta wanke hannunta kafin ta ɗauki abincin ta fito, a bakin kofa ta tsaya ta yi mashi sallama, yana ciki, yana zaune a bakin bed nasa yana fuskartar kofar shigowa. Kutsa kai cikin ɗakin ta yi, ta kasan idanunsa ya kalleta, bai ga fuskarta ba, saboda bai ɗago ba, a yadda ya kalleta ba zai wuce ya kalli daga kafafunta zuwa kugunta ba, sai dai shi ma kugun nata tray ɗin abinci da ta ɗauka ya rufe shi. A in da ta saba ajiye Mishi ta je ta ajiye tare da zama tana jiran shi. Shiru shiru almost 20 mins yana zaune a haka, har ta fiddaran zai ci abincin, sai kuma ta gan shi ya miƙe ya nufeta, ita ma dai ta kasan idanunta ta saci kallonsa, yau sanye yake da short zuwa cinyoyinsa, daga ta sama kuma polo t-shirt ne, dukka farare ne tas tamkar yanzu ya cirosu daga ledarsu, kyawawan fararen cinyoyinsa masu ɗauke da bakin lallausan kwantaccen gashi a waje. Tun da ya taso daga saman gadon take kallon kyawawan fararen kafafunsa har ya iso in da take, a in da ya saba zama ya zo ya zauna, saboda tsabar kyan fararen kafafunsa sai ka rantse da Allah bai taɓa taka kasa ba saboda haske da kuma kyan ƙafafuwansu, sai santin su take yi tana yabasu a cikin zuciyarta. Abinci ta zuba mishi kamar ko yaushe, yau ɗan gefenta da ɗan nisa ya zauna, ta dukar da kanta kasa tana zuba mishi wasu daga cikin cimarsu, shi kuma ya ɗago kai zai kalli abin da take zuba Mishi ɗin, karaf sai saman kyakkyawar dark black curly hairnta dara daran blue eyes nasa suka sauƙa, gashi Akila ta hana ta sanya ɗankwali, ta saki gashin har baya, mai da kallonsa kan plate ɗin ya yi, gently ya ce "Is okey". A nitse ta dagata da zuba mishi, ya ɗan yi mamaki, idan tana aiki tana yin komai a nitse, amma idan ba aiki take yi ba akwai bala'in shegen rawar kai kamar me, to me yasa hakan kenan?. Spoon ya ɗauka ya fara cin abincinsa kamar yadda ya saba, ita kuwa yatsun kafarsa kawai ta zubawa idanu, har ga Allah sun yi mata mugun kyau ba kaɗan ba, ji take yi kamar ta sanya hannu ta shafosu. Yana tsaka da cin abincin Aseef ya kira shi video call, da hannu ya yi mata nuni a kan ta miƙo mashi wayar ba tare da ya yi magana ba, cikin natsuwa ta miƙe ta nufi saman bedside drawer, ta ɗauki ta dawo ta miƙa mishi. Karɓa ya yi tare da yin picking na call ɗin, saman table da Areef ya ajiye wayar ranar, shi ma a nan ya ɗaura tasa yana cigaba da cin abincinsa. Ganin Rimsha yasa Aseef sakin kayatatcen murmushi. "Our Queen!" Ya ambaci sunanta da ɗan karfi, jin muryarsa yasa ta ɗago kai da sauri, cool murmushi ta sakar mishi, sai kuma ta sake ɗaure fuska tare da ɗan komawa baya kamar taga abin tsoro, da mamaki yake kallonta yadda ta ɗaure fuska lokaci guda. "Lafiya Rimsha? Kina murmushi kuma kika sake ɗaure fuska, me ya faru?" Ya yi magana yana shafa gashin jikin coper da Lucky dane kusa da shi, ɗan turo makin nan nata ta yi, a shagwaɓe ta ce "Yaya Aseef waƴan nan karnikan kusa da kai ne suka bani tsoro ai, bana son su". Ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce "Okey to bari na fita daga ɗakin nasu sai mu yi magana ko? Idan na fita zaki yi mini dariya ai ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e zata yi mishi. Miƙewa ya yi daga shi sai shot da singlet farare tas a jikinsa, waje ya nufa, haushi su Lucky suka fara daga mishi alamar basu son ya fita, da sauri ta toshe kunnuwanta tare da kawar da kallonta daga kan wayar zuwa gefe, shi kuwa Lion tamkar babu shi a cikin ɗakin, abincinsa kawai yake ci cikin kwanciyar hankali. After some minutes, a hankali ta zame hannayen nata da kunnuwanta da ta toshe tare da mai do da kallonta a kan wayar. "Sarkin tsoro". Ya ambata yana ɗaga mata gera ɗaya, wow Aseef shi ma fa ba dai kyau ba, bakin nan nasa ɗan ƙaramin. Cikin zolaya da wata kwaɓaɓiyar Hausarsa da ya koyo wajen Musharraf ya ce "Ina kowa (ina kwana)". Bata san lokacin da dariya ya subce mata ba, wai ina kowa, babu kowa ne to. Tana tsaka da dariya ta tsingayo zazzakar muryarsa ya daki dodon kunnenta "give me water". Cikin sauri ta daidai ta natsuwarta tare zuba mishi ruwa ta miƙa mishi, karɓa ya yi tare da kaiwa ɗan bakinsa ya fara sha. Cigaba da janta da hira Aseef ya yi, ba dan ta so ba ta rinƙa biye mishi, tana tsoron kada Lion ya koreta a ɗakin ne idan ta cika surutu, abin da bata sani ba shi ne, matikar pleasure sa (farincikinsa) zai yi farinciki ya yi murmushi, to zai iya jure surutun nata, shi bai damu da kowa ya shiga kunci ba, matikar TRIPLETS nasa suna farinciki to bukatarsa ta gama biya a duniya. Sun sha hira da Aseef sosai, ta rinƙa cin gyaransa a kwabaɓɓiyar hausar nan tasa, sai dariya yake yi har da kyakyatawa, sai da ya kammala cin abincin zai miƙe ya ɗauki wayarsa ba tare da kalli in da take ba ya wuce saman sofa ya zauna, ita kuma fara haɗa kayan abincin ta yi. Yana zama Aseef ya sa mishi kuka akan shi bai gaji da magana da Rimsha ba, tamkar bai ji me Aseef ɗin ya ce, ya yi banza da shi, daga karshe ma katse kiran ya yi tare da ajiye wayar a gefensa yana mai kishingiɗa a saman sofar. Kwashe kayan abincin tas ta yi tare da ficewa daga ɗakin ta nufi waje, kitchen ta fara komawa ta ajiye kayan kafin ta wuce garden wajensu Akila. Tasha ruwan mamakin ganin Imran da Areef a wajen, duk da cewa tasan wajen zamansu ne, amma bata yi zaton ganinsu yanzu a wajen ba. Kusa da Akila ta je ta zauna, da fara'a Areef ya ce ya mata "Our Queen gaskiya yau kin yi kyau over". Ba ƙaramin faduwar gaba Akila take ji ba a duk san da ta saurari muryarsa, to me yake nufi da ya nuna bai gane ta ba? Ko dai ya fi son ya kai kansa da kansa gida ne? Sai jerowa kanata da kanta tambayoyi take yi. Wayarta dake hannunta ne ya ɗan yi kara alamar shigowar saƙo, jikinta duk a mace ta kunna hasken screen ɗin wayar dan ta duba saƙon wanene. Ganin saƙon ɓoyayyen masoyi ne yasa ta ɗago da sauri ta kalli Areef, kansa na duke a kan wayarsa yana latsawa, da alama dai shi ma wani saƙon yake turawa, ko yake rubutawa, dawo da kallonta a kan wayar tata ta yi, password ɗin wayar ta fara cire wa, kai tsaye saƙon ta buɗe. "My heartbeat sarkin ruɗu da son sanya ƙwaƙwalwarta a cikin tunani, yanzu me na tunanin ni ne ko bani bane? Bayan kin rigada kin san ni, shiyasa fa tun farko naki turo miki hotona, dan bana son ki ganni a wani waje ma ki gane ni har sai na kawo miki kaina gida, amma kika takura mini na turo miki hotona, duk da haka sai kin sake shiga ruɗu a kai na?". Zaro idanu ta yi tana karanta saƙon, da hausa ya rubuta mata kamar yadda ya saba, ita kam gaskiya yanzu ta kara tsorata da lamarinsa, ta sare sosai, anya zata iya jurewa ta cigaba da nuna mishi tamkar bata gane shi ba kuwa? Anya ma zata iya cigaba da soyayya da shi kuwa? Ta tambayi kanta, wani ɓangare na zuciyarta ne ya bata amsa da cewa, to ya zaki yi tun da kina son shi, ko dai akwai wani da kike yi wa rabin son da kike yi mishi ne?. Shiru ta yi ta rasa ina zata sanya rayuwarta ta ji daɗi, har lokacin sai dukan uku uku kirjinta yake yi, su Rimsha sun lula duniyar hira sun barta a duniyar tunani, kwata kwata bata jin me suke faɗe, daga karshe ma miƙewa ta yi ta nufi waje, Imran na kiranta amma ina bata ji ba, bata tare da su. Binta da ash eyes nasa ya yi yana kare mata kallo har ta fice, dawo da kallonsa a kan wayarsa ya yi tare da cigaba da abin da yake yi na latsa wayar, da sauri Rimsha ta miƙe ta bi bayanta, su kuma su Imran suka cigaba da hiran da suke yi. A ɗaki zaune saman tsakiyar gado ta iso ka, kusa da ita ta zo ta zauna tare da taɓata tana faɗin "Aunty Akila lafiya kuwa?". Ƴar firgita ta yi tare da juyowa suna fuskantar juna, idanuwanta cike tap da kwallah, babu ɓoye ɓoye babu komai ta fara bawa Rimsha labarin halin da take ciki, yanzu ta rasa mafita, tana magana tana hawaye. Dafata Rimsha ta yi ta fara bata hakuri, wani saƙon ne ya sake shigowa wayar Akilar a wannan lokacin, kin buɗewa ta yi, ta ce ita ko mutuwa zata yi sai dai ta mutu, amma ɓoyayyen masoyi ta hakura da shi, karɓar wayar Rimsha ta yi ta buɗe saƙon, rubutu ne kamar haka. "Am so so sorryyyyyyyyyy my heartbeat, na san nayi wasa sosai da ƙwaƙwalwarki, amma ki yi mini afuwa, ba zan sake ba, wlh waya ta yi kaɗan wajen ɗaukar sorry dake cike a bakina, girman laifin da nayi, sorry a waya ya yi kaɗan ya goge shi, ki bani dama gobe kamar yadda na faɗa zanzo har gida, na yi alkawarin zangoge dukkan laifukana, dan Allah kada ki yi fushi dani, kin san cewa kece bugun numfashina ko? Tun ba yau ba ina gaya miki hakan, kin ɗauka wasa nake yi ne ko kuma kawai kalamai ne irin na masoya da suka saba faɗa? To idan haka kike ɗaukar kalamaina ki daina, duk abin da zan gaya miki na kalmar soyayya, wallahil azim da gaske nake yi, da gaske daga karkashin zuciyata take, ni ban taɓa soyayya ba sai a kanki, tun hotonki na farko da Prof ya turo mini na kamu da son ki, ban sanki ba, ban san halinki ba, amma zuciyata ta kamu da masifaffen Kaunarki, mace ta yi mana illar da ba za mu taɓa mancewa da shi bane, Shiyasa dana kamu da sonki na zaɓi na gwadaki ta wannan hanyar, ban taɓa yarda da mace ba sai a kanki ke da Rimsha, dan Allah ki fahimceni, ki gane abin da nake nufi, ki gane abin da ya sanya na saka miki idanu da kuma duk wani motsin da zaki yi ina gani, ki gane dalilin da ya sanya naki gaya miki ni waye, ina son ne ki soni domin Allah ba dan wani abu ba, ina son ne ki soni kamar yadda nake son ki, hakan yasa nayi miki wasa da hankali na kuma ki gaya miki waye ni, amma ai hotona na gaskiya na tura miki dan bana son ganinki cikin damuwa, kin shiga damuwa sosai a kan kina son gani na, hankan yasa na baki hotona tun na 22 years, na tuba My Heartbeat, ki fahimceni bugun zuciyata, wlh ba zan sake ba, yanzu komai zan rinƙa gaya miki gaskiya ne, ba zan sake ɓoye miki komai ba, i really love you more than anything except my TRIPLETS and Prof, idan kika ciresu, kece mutun ta farko a zuciyata, wlh ban taɓa rokan wani abu a wajen wani ba sai soyayyarki, ban taɓa cewa wani sorry ba sai a kanki, ki yi hakuri ki karɓi sorry na dan kinyi breaking record ɗin TRIPLETS, yau na ce miki sorry". A karshen massage ɗin ya sanya mata emojin kuka da kuma tambarin zuciya. A bayyane Rimsha ta karanta mata komai, shiru ta yi har lokacin tana ruwan hawaye, tabbas tana yi mishi wani irin mahaukacin makauniyar soyayya, wadda ko kanta bata yi wa irin wannan soyayya, amma kuma har cikin ranta tana jin tamkar taraiyarsu ba zata yiwu ba. To me yasa take jin hakan❓ Sosai Rimsha take rarrashinta tare da bata baki, cikin sanyin murya tare da sigar rarrashi ta fara magana "Aunty Akila in dai ɗaya daga cikin TRIPLETS ne, in dai yaya Areef ne yake sonki, wlh ina mai baki shawara da iya gaskiyata da basirata, ina mai gaya miki ki yarda da shi, ba wai dan wani abu ba, ba wai dan ina bin bayansu ba, ni nasan waye yaya Areef a ɗan zama na da shi, wlh, wlh mutumin kirki ne da samun na biyunsa zai yi matukar wahala, ko yaya Imran ne ya ji wannan magana shawarar da zai baki kenan, ni san duk wanda zaki tambaya halin yaya Areef ba zaki taɓa samun ɗaya na banza ba, bashi da matsala ko kaɗan a rayuwarsa, ina da tabbacin duk wata mace mai bala'in buri a kan miji, to da zarar ta zo kan TRIPLETS burinta ya kare, su ɗin burin ko wace cikakkiyar hamshakiyar mace mai hankali da sanin ya kamata ne, su ɗin burin ko wace uwa ce, kowa zata so samun ƴaƴa irinsu, kaunar junansu, ba'a magana, wlh idan kika shiga cikin rayuwar TRIPLETS ba ƙaramin daɗi zaki ji ba, ina ga sau da dama zaki rinƙa mance a wata duniya kike, saboda kyawun halinsu da kuma kula da zaki rinƙa samu, ki sani yadda suke kaunar junan nan nasu haka zasu kaunace ki idan kika shigo cikinsu, wlh ina da tabbacin idan kika auri yaya Areef to harta yaya Saif sai ya soki, duk abin da ɗaya daga cikinsu yake so, ko da basu so suna hakuri su bi son ɗayan nasu, ta hakan suke kara tabbatar da kaunar dake a tsakaninsu, ni wlh ba zanso ki ce ki na fushi da yaya Areef ba, na san son shi kam ba zaki taɓa dainawa ba, ko me zai yi miki, dan haka suke da shegen shiga rai kuma basu fita, idan ma kika ce zaki ciresu, to mutuwa zaki yi a banza, tun last week nake ƙoƙarin cire son yaya Saif a raina, amma ina abin ma karuwa yake yi, dana matsa ma sai naji rayuwata tana barazanar barin gangar jikina, ba dan naso ba haka na hakura dolen dole, to nasan ba zaki taɓa iya cire son yaya Areef a zuciyarki ba, idan kika matsa sai kin cire ma, wlh zaki iya mutuwa, dan haka ki hakura kawai ki karɓe shi dan ya cancanci a so shi ɗin, ni dai Aunty.......". Bata kai karshen maganar ba Akilar ta rufe mata baki tana faɗin "Na yarda da zancensa da ya ce ke kanwarsa ce, ga shi yanzu kinzo sai yabon shi kike yi, dan Allah ki yi shiru ki kyaleni na ji da abin da nake ki kinji ko? Bakin ku ɗaya ai da shi, dama ya gaya mini ke kanwarsa ce, kinga kuwa ai ba zaki so laifin yayanki ba daman". Sosai Rimsha ta ji ba daɗi, maganar Akilar ta yi mata zafi, kenan Akila tana nufin bata sonta ne yasa take bin bayan Areef ko yaya?. Miƙewa ta yi da nufin ta fice daga cikin ɗakin, da sauri Akilar ta riƙo hannunta tana faɗin "Kiyi hakuri Rimsha, da wasa nayi maganar kin ji ko?" Tana magana tana ƙaƙalo murmushi dole. Da yake Rimsha mace ce mai kyakkywar zuciya, sai ta hakura ta dawo ta zauna, kuma har ga Allah tana kaunar Akilar over, musamman ma da yanzu ta san cewa ƴar uwanta ce, ƴar bappanta ce, sai son ya karun mata a ziciyarta. "Rimsha ko dan farincikinki zan yi yadda kika bani shawara, amma kuma ba zan gaya miki yadda zan yi wa Heartbeat ba, dan saboda nasan yana jina, zai ji komai da muka faɗa, dan haka kawai na barwa zuciyata sanin hakan, sai dai ki sani ba zan guje shi ba, ba kuma zan canza mishi ba, abu ɗaya zan yi mishi wadda sai nayi zaki gani". Sosai Rimsha ta ji daɗi, ita kaunar da take yi wa Akilar ce ma tasa take yi mata kwaɗayin samun ɗaya daga cikin TRIPLETS, saboda tasan zata sami kula fiye da tunanin mai tunani, zata sami farinciki sosai da sosai. Shiru suka ɗan yi na ƴan mintoci kafin Akila ta ɗauki wayarta tare da miƙewa ta shiga toilet, fuskarta ta wanko tare da fitowa ta kara tsantsara make up, zuba mata idanu Rimsha tayi tana ganin ikon Allah. Bayan ta kammaya ta ɗauki hoto kala biyu a wayar tata, tayi kyau sosai da sosai, ta fito a sak jinin Dr Salman da kuma barrister Naurat, feshe jikinta da perfume nata masu daɗin Kamshi ta yi kafin ta ce da Rimshan ta tashi su koma garden. Ba musu ta tashi, sai dai kuma bata gaji da binta da idanu ba, sai mamaki take yi, irin wannan sauyi lokaci guda haka. A yadda suka bar su Imran, haka suka dawo suka same su, sallama suka yi musu, har suna haɗa baki wajen amsawa, zuba mata idanu Areef ya yi har sai da ta zauna a saman sofa, cike da zolaya ya ce "Sarkin rigima, Prof this your sister fa ba'a magana, rigimammiya ce number ɗaya, Aseef part 2". Yana magana yana wannan murmushin nasa mai kayatarwa tare da ɗaukar hankali. Cool murmushi ta sakar mishi kafin ta ce "Saboda ni auta ce ai yasa dole nayi rigima ko ba haka ba yaya Imran?". Cikin harshen turanci suke magana ba Hausa ba. Gyaɗa mata kai Imran ya yi yana faɗin "Yes Our Heartbeat ke auta ce dole ki yi shagwaɓa, mu kuma mu kara shagwaɓa ki". Shima dai Imran da turanci ya yi maganar, sai murmushi suke yi dukkansu, Akila ta nuna kwata kwata ita ma bata gane shi ba, tun da haka ya nuna mata. "Heartbeat ki shirya gobe da safe Akil zai mai dake gida kin ji ko?". Cewar Imran. Da sauri Rimsha ta ɗago kamar zata yi kuka, rarrashinta Imran ya fara yi tare da yi mata alkawarin bayan kwana biyu zai sake ɗauko mata ita, zai kawota su yi wata guda, ba dan ta so ba ta hakura. Haka suka ci-gaba da yin hirarsu mai cike da nishaɗi tare da bawa juna kulawa cikakka, kayatattun murmushi ne ɗauke a kan fuskar ko wannansu, hakan zai tabbatar maka ba ƙaramin jin daɗin hirar suke yi ba, abin ba'a magana, shi kuma oga yana bedroom nasa yana bincike a kan wani sojansu da a ka kashe, a jikinsa an sami wani tambari na kungiyar ƴan ta'adda, to yana bincike yaga gano gaskiya, shin sojansun ɗan leƙen asirin ƴan'ta'adda ne ko yaya abin yake, ita kuma jelly tana can har yanzu tana barci, kuka ta sha iya son ranta kafin barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, ta gama period jiya, amma taki yarda da yaya Imran, da yazo zai shigeta sai ta yi ta yi mishi kuka, haka zai hakura ya kyaleta ba dan ya so ba, ɗazun ma abin da ya haɗasu kenan, ta sha kuka har barci ya ɗauketa, ta kafe akan ba zai taɓa mata tula tulanta ba dan suna yi mata zafi, shi kuma bawan Allah zafi sun haɗu sun yi mishi yawa, ya kasa jurewa, ɗan wasan da yake yi ma ya sami sauƙi, yanzu ta hana shi yi, abun sun haɗe mishi, baya son ya yi mata ta karfi dan kada ya sanya mata tsoron abin, shiyasa yake binta a hankali yake hakura, duk da ya hakura ya kyaketa dan baya son yi mata dole, amma sai da ta tasa shi a gaba ta rinƙa kuka yana rarrashinta, shi ne har barci ya ɗauketa, to daga barcin ne bata tashi ba har yanzu. TO KUN JI YADDA GIDAN LION YAKE, BARI MU LEƘA GIDAN ABBI DAN MUGA ME SUKE CIKI, ZUWA ANJIMA SAI MU DAWO, SHIN YA SU ABBI SUKA DAWO DAGA KATSINA❓ BARI DAI MU LEƘA MU GANI. GIDAN ABBI 💋 A ranar da suka je Katsina a ranar suka dawo, sun yi sa'a sosai da yake baban Sadiq mayen san kuɗi ne, sai ya basu Hanan dan ya ga ruwan kuɗi, har mamaki daddyn Jelly ya rinƙa yi na yadda bai san su bai san suwaye su ba ya ɗauke ƴa sukutum ɗungurumgum ya miƙa musu, Maman Sadiq ta yi ƙoƙarin hana shi, amma ina shi ya ga ruwan kuɗi, ta yi ƙoƙarin gaya mishi kila ƴan mafiya ne, kila kuma sayar da Hanan ɗin zasu je su yi, nan ma ya rufe idanu ya murje gaskiya ya ɗauki Hanan ya miƙa musu, Abbi kam daɗi ya rinƙa ji abinsa, shi kuma daddyn Jelly nasiha sosai ya yi wa baban Sadiq ɗin tare da tunatar da shi Hanan fa tana da babban hakki a kansa, a ranar alkiyama sai Allah ya yi mishi tambayoyi akan ta, yanzu da ya ɗauketa ɗungurumgum ya basu bai san suwaye su ba idan ya mutu Allah ya tambaye shi ina amanar da ya bashi ya ƴarinya Hanan me zai ce? Kenan cewa Allah zai yi ya kyautar da ita ko ya'ya? Dama an bashi ita ne dan ya kyautar da ita? Ya sani fa ba iya iyaye bane kawai ke da hakki a kan ƴaƴa, suma ƴaƴa suna da hakki sosai a kan iyayensu, tun daga ranar da aka haife yaro har izuwa ranar da zai koma ga mahaliccinsu sai Ubangiji ya tambayeka ya ka kula da su, cinsu, shansu, tarbiyarsu, iliminsu, sutura da sauransu, abin ku da jahilci, sai ya ce e shi dai ya ji ba dai sun ce sunan son Hanan ɗin ba? To gata ya basu, idan kuma wani munafurci da iskanci zasu kawo mishi ne to su ajiye mishi yarinya su wuce su bashi waje. Jin hakan yasa suka kyale shi, ya yi nisa ba zai ji kira ba, jahilci babu daɗi, haka suka ɗauke ta, Abbi ya bashi 200k suka kamo hanyarsu ta dawowa gida, sai washe baki yake yi ya sami kuɗi, yau ba'a magana, sai ruwan Albarka yake sanyawa Hanan ɗin ta kawo mishi mai bashi kuɗi, bai wani damu da rasuwar maman Hanan ɗin ba ma, shi dai buƙata ta biya tunda ga kuɗi, duk wannan abin da ya faru Sadiq da Yusuf basu nan, Yusuf yana shagonsa, kasuwancin nasa Allah ya saka mata albarka, sai haɓaka take yi, shi kuma Sadiq yana gareji, har kwallah sai da Maman Sadiq ta yi, ta rinƙa haɗa su Abbi da Allah akan kada su cutar da Hanan, Irfan ne ya rinƙa bata hakuri tare da yi mata alkawarin babu abin da zai faru sai alkhari In Sha Allah, da hakan suka baro Katsina suka nufi KD Suna shiga gida kowa ya wuce Part nasa, daddyn Jelly ya wuce part nasa shi da Irfan, da suka shiga ciki kuma Irfan ya wuce bedroom nasa, dama kun san shi sarkin ƙulewa a cikin ɗaki ne, kullum yana ƙule yana kwance abinsa, baya son hayaniya, shi kuma daddy jelly toilet ya nufa dan ya yi wanka, Ayla bata nan, tana can cikin gida wajensu Aunty. Aunty da ta ga sun da wo da Hanan, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, baiwa Allah, ta tsala wankanta suna zaune a palo ita da Ayla, danƙareriyar lace ce pink color, ɗinkin riga da skit ne a jikinta, kayan sun zauna mata da kyau sosai, ba ƙaramin kyau ta yi ba, ta sha make up iya make up abinta, sai tashin ni'imantaccen kamshi take yi, ga wani kyakkyawar ɗaurin ture kaga tsiya data ɗaura, ganinsa ya sa ta miƙe da sauri tana yi mishi sannu da dawowa, ita ma Ayla ta sha kwalliya ba kaɗan ba, sai wani kara sihirtaccen kyau take yi, ta yi fresh sosai, ga kamshin da take zubawa, sai dai ita doguwar riga ce a jikinta, yaunin maroon color, da yake akwai duwatsu masu kyalli a jikin rigar, sai ta kara mata wani shegen kyau sosai. Sai murmushi suke yi dukkansu, cikin sauri ita ma Aylar ta miƙe tare da yi wa Abbi sannu da zuwa suka gaisa ta gaisa da Hanan kafin ta zame cikin dabara ta gudu wajen mijinta, tun ɗazun take kewarsa, ta damu sosai, bai taɓa yin nisa da ita na awa ɗaya ba, sai ga shi yau wajen awa 8 basu tare, ta damu sosai, shiyasa bata ji kunyar su Abbi ba ta zame ta gudu abinta, sai dariya Abbi da Aunty suke yi mata domin sunga fitarta. Ɗan zungurin Aunty Abbi ya yi kasa kasa ya ce "Kinga yadda ake yi wa miji ko? Ya zamana kullum marmarin shin zaki rinƙa yi, babu jin kunyar kowa kina ji ko?" Dariya ta yi tare da rungume shi tana faɗin "To bana yi maka ne?" Jan hancinta ya yi "Kina yi mini mana, amma ki kara, wancan ya yi mini kaɗan". Ganin haka yasa Hanan ta zame sumui sumui ta basu waje, ta haura sama zuwa ɗakin da yake mallakinta a yanzu, lokacin ita ma Jelly tana nan, tana ɗakin kwance tana barci, kada ku manta mun ɗan koma baya ne kaɗan a gidan Abbin, dan kuji me suka faru a kwanakin da suka wuce, ita kuma Hjy Batula ta je kaiwa Aafia ziyara dan ta dubo wani hali take ciki, kamar kullum Ommu tana ɗakinta. "Halima wai yanaga sai kara haske kike yi ne?" Ya tambaya yana kare mata kallo, zata yi magana kenan suka jiyo Ommu daga ta bayansu saman bene tana surfa uwar masifa da murya kamar babanin akuya. "Yanzu cin amanar taku har ta kai ranar kwanana ku tsaya a palo kuna iskancinku ta yadda ma zan gani kenan ko? Wato na zo na gani da kyau kunci amanata ko? To Allah ya isa kuma sai Allah ya saka mini, ke kuma Halima ki jira ki gani, bakar munafuka, ai kinsan yau a ɗakina yake, shegiya kullun kina wani sunnar da kai kamar ta Allah ashe Musa ne baki fir'auna a zuci ko? Bakar azzaluma algunguma kullum cikin faɗar Allah ya ce Annabi ya ce kike, amma baki amfani da abin da kike faɗa, yanzu idan da ke malamar Allah da Annabi ce ai da ko kallon shi kin san haramun ne a wajenki yau kam tun da a ɗakina yake, mayya kin bi kin cinye mini kurwar miji, ya tattare ya tare a wajenki, to wlh ta Allah ba taki ba, ki gama tsafinki da asirinki duk haka zaki ganni ni Deeje ki barni, na fi karfin yarinya sai dai Uwar yarinya, wlh idan......" Bata kai karshen maganar ganin zata tara musu jama'a yasa Abbi ya daka mata wata uwar tsawa mai firgitarwa. "Hadiza kina shan giyar wake ne? Kanki ɗaya ne ko akwai motsi a ciki? Kin san me kike faɗa kuwa? Kin san me kike yi kuwa? To idan ma kanki ba ɗaya ba ni zan dawo miki da shi ɗaya yanzun nan, ki sani ba zan iya wannan halin naki ba, kuma Halima ba zan iya raba makwanci da ita har na rinƙa raba muku kwana ba, kin manta shekaru nawa kika sa kafa kika yi fatali da aurenki kika bar gidan nan ne? To a wancan lokacin baki san da hakkin nawa ba kenan ko?, A wancan lokaci baki san da raba kwana zai zo ba kenan sai yanzu ko?, Ko dama kina tunanin zan yi ta zaman jiranki ne?, Idan haka kike tunani to kin tabbata mai ƙwaƙwalwar kifi, kinje kin yi ta yawace yawacenki na tsawon shekaru kin dawo, ban ce miki komai ba, na ɗaga miki kafa saboda albarkacin ƴaƴan dake a tsakaninmu, yanzu kin dawo kina son sake ɗaga mini hankali ki takurawa matata farincikina ko? To ina son ki sani ba zan iya rabuwa daidai da kwana ɗaya da matata mai sona domin Allah ba, Halima ita ce farincikina dan haka ki je na sake ki saki ɗaya". Ya yi maganar cikin faɗa da zafin zuciya, ya kai karshen maganar tare da riƙo hannun Aunty suka nufi saman benen. Ta gefenta suka raɓa suka wuce, mamaki ne ko tsoro waya san mata, ta dai kasa magana, sai binsu da idanu take yi, jin abin take yi tamkar a mafarki, ita yau Abbi ya saka, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, ta furta a cikin ranta tare da juyawa jiki a mace ta koma cikin bedroom nata zuciyarta cike taf da tunanin mafita. Shi kuwa Abbi yana shiga bedroom nasa toilet nufa dan ya yi wannan, duk zafin rai da ɓacin ran da Ommu ta sanya mishi a Palo, yana shigowa cikin ɗakinsa ya ji sanyi a zuciyarsa, Aunty ta gyara mishi ko'ina, sai tashin wani fitinannen daddaɗar kamshin air freshener ɗakin yake yi, ga wani daddaɗar sanyin Ac dake gudu a tsaka tsakiya, daddaɗar sanyin Ac da ni'imantaccen kamshi idan suka haɗu ya kuke tunanin abin zai kasance? Ai abin sai wanda ya ji. Nan take ya nemi ɓacin ran nasa ya rasa, wani muguwar soyayyar Aunty ce ta karu mishi a cikin zuciyarsa, sai albarka ya ke zuba mata a cikin zuciya, da haka ya shiga cikin toilet, ita kuma ta hau fitar mishi da kayan sakawa, Baiwar Allah har ciwo kanta ya fara yi mata saboda hayaniyar da Ommu ta yi yanzu, da Ommu ta fara bala'in, ta yi ƙoƙarin guduwa ta haye sama, Abbin ne ya riƙeta ya dakatar da ita, dan yana son ta rinƙa rage tsoron nan nata, ta cika shiru shiru da bala'in tsoro, shiyasa duk wanda ya ɗebo rashin mutumcinsa sai ya sauƙe a kanta, to yana da kyau ta koyi faɗa ko kaɗan ne, dan ta rinƙa kwatarwa da kanta ƴanci, shiga ɗaki tana kuka ba shi ne mafita ba, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce idan aka yi maka abu ka ji ba zaka iya hakuri ba, ka rama daidai da abin da aka yi maka, kada ka kuskura ka kara koda kwayar zarrace a kan abin da aka yi maka ɗin, daidai zaka rama, wannan shi ne ka'ida ta musulci, amma idan zaka iya yafewa, to yafiyar dai tafi, zaka sami Rahmar Ubangiji, Allah kasa mu a cikinta. A ɓangaren Ayla kuwa, tana fita wajen mijinta ta nufa, lokacin yana wanka, kai tsaye wajen drawer kayansa ta nufa, kananan kaya ta fitar mishi da su, da yake ba wani iya aikin kirki ta yi ba, sai gyaran ɗakin nata bai yi kyau sosai ba, amma ta yi ƙoƙari, ta shinfiɗa musu gado ta yi shara iya yadda ta iya, kada ku mance irin rayuwar da ta taso a ciki, bata zauna a gida ba bare ta koyi wani aiki, iya abin da ta koya a gidan su Kausar sai kuma wadda Aunty ke ɗan koya mata a yanzu shi kaɗai ta iya. A saman gado ta ɗaura mishi kayan, ita ma ta zauna a gefen kayan tana jiran fitowarsa,. Yana fitowa da kyakkyawar fuskarta ya fara tozali, cool murmushi ya sakar mata kafin ya buɗe mata hannayensa akan ta zo, da sauri ta miƙe ta nufe shi, rungumeta ya yi sosai suna sakin Murmushi a tare. "Nayi kewarki sosai my baby". Ya faɗa kasa kasa. "Daddy nima nayi kewarka, har ciwo sai da kaina fa ya yi dan baka dawo da wuri ba". Ta yi maganar a shagwaɓe. "Subhanallah ciwo kuma?" Ya tambaya yana ɗago haɓarta, gyaɗa mishi kai ta yi alamar e. "Ayya Sorry ba zan sake tafiya wani waje mai nisa na barki ba, idan zan tafi to kafata kafarki, idan ba haka ba, na fasa zuwa". Murmushi ta sakar mishi tare da kara lafewa a jikinsa, tana jin daɗin wannan damshin ruwan jikin nasa dake taɓata, ya lura da hakan, cikin sauri ya sake ɗago haɓarta suna kallon juna, tabbas idan ya canka daidai ciki gareta, dan ga alamominsa dukka sun bayyana a tattare da ita, wani irin mummunar faɗuwar gaba ya ji lokacin da ya tuna menene silar mutuwar mummyn jelly, Haihuwa, haihuwa ta zo yi Allah ya karɓi kayansa, kwata kwata ma ya mance da zancen kamanni dake tsakaninta da mummy'n Jelly ɗin, shi dai murna ya fara yi ya samu abin da yake so. Sakinta ya yi tare da nufar gaban mirror, cikin sauri ya shirya tare da yi wa Allah sujudur shukur, sai bin shi da idanu take yi, bayan ya kammala ya zo ya runhumeta sosai a jikinsa yana zuba mata godiya da sambatun me take so ya yi mata, mamaki ne ya kamata, me yake faruwa ne kuma? Ta tambayi kanta. Zaunar da ita a bakin gado ya yi tare da riƙo hannunta, cike da so da Kauna ya fara magana. "Babyn daddy kina jina ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e "Nine auta a wajen mamana, bayan ni babu wasu, mamana tana sona fiye da tunaninki, amma a haka ta barni tana kuka ta tafi, ba ma wannan ba nake son gaya miki, kinga ni bani da kani kuma Allah bai bani yara da yawa ba, jelly kawai gareni, zan so ki haifa mini yara dozen da zan rinƙa kallah ina jin daɗi, ina rage zafin kewar mamata". Ya yi maganar idanunsa cike tab da kwallah. Da yake yarinya ce sai bata hango tsantsar ciwo dake cikin rayuwarsa ba, bata hango irin bakin cikin da yake ciki ba, ta ɗauka kawai irin kwallan da ya saba yi ne, bata san wannan kwallah mafi azaba bane a gare shi ba. "Daddy dama gwaggo Batula ba kanwar ka bace?" Ta faɗa tana rufe mishi idanun dan hawayen dake ciki su zubo ta goge mishi. "Batula kanwata ce amma mamanmu ba ɗaya ba, baki ji nace miki nine auta a wajen mamanmu ba ne? Ba a wajen babanmu na ce ba, wajen mamata, ni ne auta". "Daddy to ina mamanka da babanka, dan Allah ka kaini ina son ganinsu". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Babana ya rasu, mamata kuma tana a in da bamu isa mun yi gigin tinkarar wajen ba, so kawai ki bar zancen, just kawai ki yi musu addu'a Allah ya jikan baba, mama kuma Allah ya fitar da ita zance ne ko kuma me oho dai, kawai ki yi musu addu'a da ta dace da su, amma itama mama fa bamu da tabbacin tana raye a yanzu ko ta mutu, kawai ki yi musu addu'ar Allah ya jikansu baki ɗaya". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya shiga toilet dan ya je ya yi kuka sosai ko zai sami saukin abin da yake ji a ransa. Allah sarki sunga rayuwa iya ganin idanunsu, musamman ma shi da yake Auta, an rabashi da mahaifiyarsa tun yana yaro ƙarami, tun bai wuci 2 to 3 years ba, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, yafi su Abbi gabaɗaya shiga kuncin rayuwa, ga shi lokacin da ya fara girma ya dawo hannun Abbi, Ommu ta azabtar da rayuwarsa, ya zo ya yi aure da wuri ba dan ya shirya ba, sai dan samun mafita, a auren ma sai da ya fiskanci matsalar dangin matar tasa, shekara ɗaya da aurensa suna tsaka da son juna da matar Allah ya karɓi kayansa a lokacin haihuwa, ya yarda da kaddararsa bawan Allah, ya jure ya cigaba da addu'a, ya riƙi jelly hannu bibbiyu, baban Muneer ya zo ya sake jefa rayuwarsa a cikin kunci, bayan haka jelly ta ɓata, ya sha bakar wahalar da har jinya sai da ya yi, ya sake gane ta, a gabaɗaya rayuwarsa, waje uku ne ya ji daɗi, na farko rayuwar da ya yi ɗan kalilan da daddyn Rimsha, sai rayuwar shekara ɗaya na aurensa da mummyn jelly, sai kuma yanzu da ya sake aure ya auri Ayla, sune iya jin daɗi da ya samu a gabaɗaya rayuwarsa, amma duk da haka bai sare ba, ya dukufa ya koma ga Allah, bai ce wani ne ko wata suka yi mishi wani abin ba, ya yarda jarabawace daga Allah, kuma a wajen Allah kawai yake neman taimako. Sai da ya yi kuka sosai kafin ya wanke fuskarsa ya fito ya dawo cikin ɗakin, kwance ya sameta a saman gadon har ta yi barci, abin ku da mai ƙaramin ciki, saurin barci. Kusa da ita ya zo ya zauna tare da shafa kanta ya karanto mata addua'o'i sosai ya tofa mata, sosai yake jin tsantsar kaunarta a cikin zuciyarsa. Ya jima yana kallonta kafin ya haura saman gadon da kyau ya gyara mata kwanciya tare da rufa mata bargo dan garin akwai hadari da iskar ruwan sama. Alwala ya wuce ya ɗauro a toilet tare da simfiɗa dadduma ya tada sallar la'asar da bai samu ya yi ba. A ɓangaren gidan Lion kuwa. Misalin Karfe 8 na dare, zaune suke ita da Akila a ɗakinta suna hira, tana sanye da Abaya mai shegen kyau launin pink color, ita kuma Akila atampha ce ɗin kin doguwar riga a jikinta, Akila ta zuba mata make up tamkar waƴan da zasu je party ko gidan bikin, bata ɗaure kyakkyawar dark black curly hair'nta ba, ta sake shi har gadon bayanta, sai ta yafa mayafin gyalen a kanta, sai tashin kamshi suke zubawa, Akila na ta bata labarin kyawu irin na kakanta Naurat, bata san cewa kakansu ɗaya ba, da yake ita Rimshan ta sani, sai kara tambayarta take yi da waye kakan nasu take kama, kuma dan Allah a ina ta san kakar tasu, nan Akila ta gaya mata a hoto ta santa, Abba yana da hotonta tun tana budurwa har aurensu da Dr Salman da bayan aure duk yana da hotunan, kamar zata yi kuka ta ce "Dan Allah Aunty Akila ki ɗauki hoton a waya ki turomin ko ta WhatsApp ne in ganta kin ji?" To ta amsa mata da shi, har mamaki Akilar take yi na yadda Rimsha ta damu sosai a kan maganar kakar tasu, tambayar kanta take yi sai ka ce Rimsha na da wani alaƙa da kakar tasu. Suna tsaka da hira Imran ya shigo ya sanar da Rimsha ta je ta kaiwa Saif abinci, cikin sauri ta miƙe tana faɗin "Aunty Akila ina zuwa". Riƙo hannunta Akilar ta yi tana faɗin "A'a Rimsha ki jirani yau muje naga masoyin nan naki". Zata yi magana Imran ya rigata da cewa "A'a Heartbeat ki zauna ki jirata". Ba musu ta amsa da to, da sauri Rimsha ta wuce, sai da ta fita shi ma ya fice daga ɗakin suka bar Akilar ita kaɗai, wayarta ta jawo ta fara latsawa. Kamar kullum Kitchen ta wuce ta ɗauko abincin, da sallama ta shiga ɗakin nasa, yana zaune saman bed nasa, jikinsa na sanye da wandon jeans baki da T-shirt fara tas, high neck t-shirt ne mai dogon hannu, ya ɗaure dark black curly hair'n nan nasa a bayan wuya, da alama yau yana cikin bakinciki, dan fusataccen fuskar nan tasa har wani kyalli take yi, saboda bala'in ɗaureta da ya yi, bata kalli in da yake ba, dan tana tsoron kada su haɗa ido ko ta kalli cikin idonsa ya tsorata ta. In da ta saba ajiye mishi abincin ta je ta ajiye, tana zama bai fi da minti biyar ba sai ga shi ya miƙe ya iso in da take, a in da ya saba zama ya zauna tare da lanƙwashe kyawawan fararen kafafunsa. Abincin ta fara zuba mishi, while shi kuma ya zubawa yatsun hannunsa idanu yana kallon, A hankali ya juyo da kallonsa a kanta da nufin ya kalli abin da take zuba mashi a cikin plate ɗin, dan yau ba komai zai ci ba, akwai abin da baya sha'awar ci yau, yana ɗago dara daran blue eyes nasa kai tsaye suka sauƙa a saman kirjinta wadda kuma anyi sa'a wuyar abayar tata ta gangaro kasa kaɗan, hakan ya yi sanadiyar bayyanar sunansa dake a waje, sai dai sunan bai fito sosai ba, sakamakon ba sosai wuyar rigar tata ta yi kasa ba, iya sunan GRA ne kaɗai ya bayyana, saura ba su fito ba, dawo da kallonsa ya yi a kan fuskarta wadda shi ne kallonta na farko da ya fara yi a rayuwar zaman da suka yi, sun ɗan jima a tare amma bai taɓa ganin face nata ba sai yau, wannan kallon da ya yi mata kuma tayi daidai da ɗagowar kanta domin ta saci kallonsa ko me yake yi. Ido cikin ido suka kalli juna yau, wani irin bugu da karfi kirjinta ya yi, yau ta kalli cikin tsakiyar kwayar idanunsa, a sukwane ta yi kasa da kanta yayin da shi kuma ya sanya hannunsa ya zame mayafin dake a kanta tare da riƙo rip ɗin gaban rigar tata domin ya zuge kasa ta yadda zai samu damar ganin abin da ta rubuta a kirjin nata da kyau. A razane ta miƙe da nufin ta gudu ta bar ɗakin, cikin zafin nama ya riƙo hannunta tare da fisgota da karfi, ai kuwa yana fisgota sai saman kirjinsa ta faɗa, ko kaɗan bai ji komai ba tamkar wani dutse, ita kuwa suma ne kawai bata yi ba, amma har wani fitsari take ji ya zo mata da wani uban gudu tamkar zai zuba mata a pant nata, duk ta kiɗime ta fita hayyacinta, bata san time da ta saki wani marayan kuka ba wadda daga ji kasan cewa kukan tsoro ne ainun. Shi bai wani damu dan tana jikinsa ba, abin da yake gabansa kawai yake yi, abin da ya yi niya kenan wato ganin me ta rubuta a wajen domin zuciyarsa na gaya mashi sunan sane da gaske kamar yadda ya gani. Hannu ya kai ya damki zip ɗin rigar nata da nufin ya zuge, cikin sauri ta kai hannu bibbiyu ta kankame gaban rigar tata, ta hana shi zugewa, tana yi tana matsalar kwallah bibbiyu. Gently ya ce "Remove your hands". Jin sexy voice nasa mai haukatar da tunani mai sauraro saboda daɗi, ba karamin haukata ta ya yi ba, bata ma san time da ta zame hannayen nata ba, sai dai ji ta yi ya zuge zip ɗin kasa har zuwa shafaffen cikinta, datse idanunta ta yi da kyau, wani irin azababben kunyarsa ne ya kamata, yau wani ya kallan mata tula-tulanta, kuma gata a kwance a jikinsa, abin haushi ma namiji ba mace ƴar uwarta ba, kuma namijin ma ba muharraminta ba, babu abin da ya haɗa su, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, shi ne kawai abin da ta iya furtawa a cikin zuciyarta. Shi kuwa bai wani damu ba, hasalima bai kai idanunsa kan tula tulan nata ba, abin da yake bukatar gani shi kawai ya zubawa idanu yana karantawa tare da jan kyakkyawar farar vest ɗin jikinta kasa dan ya gani da kyau. Tsab ya karance kafin ya dawo da kallonsa a kan kyakkyawar face nata da ya sha make up sosai yau, ta datse idanu gam tamkar zata fasa su, saboda matse su da ta yi, gabaɗaya ilahirin jikinta karma yake yi, kuma tabbas ya lura da hakan............... ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E19-20 Tsab ya karance kafin ya dawo da kallonsa a kan kyakkyawar face nata da ya sha make up sosai yau, ta datse idanu gam tamkar zata fasa su, saboda matse su da ta yi, gabaɗaya ilahirin jikinta karma yake yi, kuma tabbas ya lura da hakan, daidai lokacin kuma Areef ya shigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama irin ta addinin Musulunci, bai lura da ita a jikin ɗan uwan nasa ba sakamakon sun bawa kofar shigowa baya. Jin sallamar Areef yasa ya saki vest ɗin nata tare da sakinta, daidai lokacin shi kuma Areef ya kariso wajen, ya sha ruwan mamakin ganinta a jikin Lion ɗin, bai yi tunanin wani abin Lion ɗin ya duba a jikin nata ba, bai ma lura da zip ɗin rigarta a zuge kasa ba, da yake kunsan akwai vest, hakan yasa bai gane ba, amma dai kansa ya ƙulle, ya san dai dole akwai abin da ya kawo ta jikin Lion ɗin, to menene wannan?. Zama ya yi kusa da ɗan uwan nasa har lokacin bai kau da idanunsa daga kansu ba, ita kuma idanunta a datse har lokacin, shi kuma Lion tun shigowar Areef yake kallon face nata yana nazarin wani abin, yes tabbas akwai abin da yake nazari dan gane da face ɗin nan nata, tabbas ya taɓa kallon mai irin wannan fuska sak a tare da Josephine, to wace ce? Ya tambayi kansa. "Stand up from my body!" Shi ne abin da ya furta a nutse. Jikinta sai kerma yake yi ta miƙe daga jikin nasa ta sauƙa kasa, har ga Allah ganin sunansa yasa gabaɗaya ya ji wani iri, jikinsa ya yi sanyi, amma yana da bukatar ya tabbatar da tun yaushe aka yi wannan zane dan ya lura kamar ba na yanzu bane, idan zanen ya jima kenan hakan yana nufin dan Allah aka yi shi, idan kuma bai jima ba, akwai dalilin yin ta. Cike da tsoro da fargaba idanunta a rufe bata lura da Areef ba, ta nufi hanyar fita daga ɗakin, har lokacin jikinta na karma, da kyar take iya taka kafafunta ta riƙe kanta dan kada ta zube kasa. "Come here". Ya furta tare da dawo da kallonsa a kan Areef. Da kyar ta iya juyowa ta nufo shi tana mai kallon kasa, ta ki yarda ta ɗago kanta bare ma su yi ido huɗu. In da ta saba zama, a nan ta koma ta zauna. "What is your Name?" Ya tambaya yana ɗauko wayarsa. Gabaɗaya ta nemi natsuwarta ta rasa, ta rasa ina zata sanya ranta ta ji daɗi, ta rasa me yake yi mata daɗi, da kyar murya na rawa ta bashi amsa da "My name is Rimsha". Shi dai Areef sai mamaki yake yi, wai me ya haɗa su ne? Ya kasa ganewa fa, a fitar da shi daga duhu. "Yaushe kika yi wannan zanen? Kuma me yasa kika yi ta?". Yana maganar yana tura saƙo a watarsa zuwa ga Aseef. Cike da tsoro da fargaba, bata san lokacin da ta ce mishi last week ta yi ba, ta rikice ta manta ko yaushe nema ta yi zanen. Jin ta ambaci last week yasa ya ce ta ɗauko mishi chemical da ya zubawa mata a lallen hannunta ranar bari ya zuba ya goge zanen, wani irin mahaukacin razana ta yi tare da sakin kuka mai sauti, ita kaɗai tasan azabar dake tattare da wannan shegiyar chemical ɗin, shi dai Areef ya zubawa sarautar Allah idanu kawai yana kare musu kallo, tun da an rasa me fidda shi daga duhu. Ɗago dara daran blue eyes nasa ya yi tare da sauƙesu a kanta, nan take ta natsu sit tare da haɗiye kukan nata, ta nemi kukan ta rasa, tuni ya gudu, wargi ma ai waje ya samu, ba tare da ya yi magana ba ya mai da kallonsa izuwa saman drawer da chemical ɗin yake ciki, ta gane nufinsa, wato ba zai maimai ta maganarsa ba kenan. Jiki ba kwari ta miƙe ta nufi wajen drawer, shi kuma Areef ya sanya hannu bibbiyu ya tallaɓo kumatunsa ta yadda zai ji daɗin mai dasu Tv'nsa kawai, tun da an rasa mai fidda shi duhu. Ɗauko chemical ɗin ta yi tazo ta miƙa mishi tare da zube gwiwowinta a kasa, karɓa ya yi tare da buɗewa, gently ya ce ta cire rigar tata sannan ta sanya hannu ta tare chemical ɗin ta zuba a kirjin nata da kanta, shi kuma zai zuba mata a hannun, kuka take yi baiwar Allah, hawayen nan wani na bin wani, kara tsananta kermar jikinta ya yi, idanunta tamkar zasu firfito su faɗo kasa, hannayen nata sun kasa tsayawa wajen jan vest ɗin nata zuwa kasa, tsantsar kerma da jikinta yake yi ne, yasa komai nata ya kasa tsayawa waje guda, duk wata zuciya mai imani idan ta ga halin da take a ciki sai ta matsa mata kwallah, amma shi kuma Lion tamkar wani mai zuciyar dutse, ko kaɗan bai ji tausayinta ba. "Lion wai me yake faruwa ne?". Cewar Areef ya yi maganar yana kamo hannunta dake ta faman kerma ta ɗaura a saman kirjinta ta kasa jan vest ɗin nata kasa, shiru Lion bai tanka mishi ba, riƙota da kyau Areef ɗin ya yi tare da jawota ta dawo kusa da shi, har lokacin kuma kallon ɗan uwan nasa yake yi, ya kasa kawar da kansa yana jiran amsa. "Sister me yake faruwa? Me ya haɗaki da Lion?". Kasa magana ta yi, kuka yaci karfinta Baiwar Allah, hawayen nata ya fara goge mata yana mai kara jawota jikinsa. Daga ita har shi sai da suka yi wani mahaukacin razana jin tsawar da Lion ɗin ya daka musu akan ta bashi hannunta ya zuba mata chemical ɗin nan ta zuba a kirjinta, tsabar razana bata san lokacin da ta kankame Areef da hannayenta dukkan biyu ba, ganin ta fita a hayyacinta sosai ne yasa Areef ɗin ya rungumota sosai a jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta. "Saif me yake faruwa ne? Me ta yi maka?". A karo na biyu ma shiru ya yi bai tanka ba, miƙewa da ita a jikinsa Areef ɗin ya yi, bayan sun miƙe tsaye sai ya saɓata a kafaɗarsa dan ya lura ba zata iya tafiya ba, kuma ya lura muddin bai fitar da ita daga ɗakin nan ba tana iya mutuwa saboda tsabar razana. Bai ce da su komai ba har suka fice daga ɗakin, ya yi hakan ne kuma dan saboda baya son ja in ja da Areef ɗin, duk abin da zai yi yana yin shi ne da lissafi, baya taɓa yi wa TRIPLETS nasa faɗa ko magana mara daɗi a gaban wani, dan baya son kowa yasan tsakaninsa da ƴan uwansa, ko ranar da ya ce Mark ya sanyata tsalle kwaɗo Areef ya hana, yana sane, abin da yasa bai yi magana a lokacin ba, baya son su Mark su raina TRIPLETS nasa, yana son tamkar yadda kowani securitynsa zasu ji maganarsa, to haka zasu ji maganar TRIPLETS nasa, yasan cewa idan ya yi magana a lokacin Mark zai raina Areef ɗin, zai zama idan Areef ya yi magana ba zai ɗauki maganar da muhimmanci ba, hakan yasa ya yi shiru sai da Areef ɗin ya shigo ɗaki ya same sa ne ya yi mishi faɗa tare da gaya mishi baya son ya rinƙa shiga irin wannan magana, idan ya bawa wani punishment to baya son su rinƙa saka baki, haka kuma ya saba yi musu, daga shi sai su yake yi musu faɗa, ko Imran baya bari yasan tsakaninsa da TRIPLETS nasa, yanzu ma yana jiran Areef ɗin ne ya dawo, kuma ma abin da yasa bai karfafa dole sai ya sanya mata chemical ɗin ba, saboda yasan zanen ba na yanzu bane, rikicewa da shiga ruɗu ne yasa ta ce na yanzu ne, amma a matsayinsa na babban soja ya san tabbas ba na yanzu bane, an jima da yin shi, to shiyasa bai karfafa dole sai ya zuba mata ba, ku kunsan da ya karfafa wane Areef ya karɓeta daga hannunsa, ba'ayi wadda zai iya karɓarta ba, bugu da kari fuskarta, wannan fuska tata ta sanya shi cikin tunani, akwai wani ɓoyayyen sirri a tarrare da face ɗin tata a cewarsa, bai kawo cewa son shi ne yasa ta yi zanen sunan ba, dan a yadda yake ganinta, kallon karamar yarinya yake yi mata, bata san menene ma soyayya ba, kuma kuma masu karatu kunsan a lokacin da ta yi wannan zanen ta yi ne ba dan tana son shi ba, ta yi ne kawai dan yana burgerta, a lokacin bata iya banbance soyayya da burgewa ba. (Amma kuma da ta tara hannunta da gaske fa zai zuba mata chemical ɗin nan, gaskiya Lion halinsa sai shi, baka gane gabansa bare bayansa🤔) Kai tsaye ɗakinta Areef ya wuce da ita, zaune ya isko Akila tana aikin latsa waya, ganinsa ɗauke da Rimshar yasa ta miƙe tsaye tana tambayarsa ko lafiya, bai ce da ita komai ba, ya wuce ya kwantar da ita a saman gado tare da zama a gefenta yana kallon yadda jikinta ke uban kerma tamkar mazari. Gently ya fara magana "Rimsha ya isa haka nan, ki dai'na wannan kukan, yanzu ki tashi ki gaya mini gaskiya me ya faru tsakaninki da Lion? Me ya haɗa ku?". Ta ɗauki tsawon a kallah minti goma kafin ta iya dawo da natsuwarta, da kyar ta tattaro sauran muryar da ya rage mata, cikin shasshekar kuka ta fara magana "Yaya Areef ba zan ɓoye maka ba, dan ya kalli zanen dake a kan kirjina ne ya ce zai zuba mini chemical na goge shi". "Zan iya ganin wani zane ne?" Ya tambaya yana kallon kirjin nata, sai yanzu ya lura da zip ɗin rigarta a zuge kasa, abin ku da Turawa, kwata kwata basu san menene kunya ba a rayuwarsu, Akila kam ta zuba musu idanu kawai tana kare musu kallo. Da kyar ta iya miƙewa zaune tare da sanya hannu cike da kunya ta ɗanyi kasa da vest ɗin jikinta kaɗan zuwa rabin tudun tula tulan nata, ta nuna mishi zanen, zuba wa zanen idanu ya yi yana karantawa. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Lallai da kuwa Lion ya tabka babban kuskuren da ba zai iya gyarawa ba a rayuwarmu, yanzu idan ma ban da shi da neman magana, ko in ce da san gallazawa rai, ai yasan wannan zane daga ido ma ba ta yanzu bace, kowa ya ga wannan zane yasan ta jima, abinda har ta fara bin fatar jikinki, amma ba komai ina mai baki hakuri a madadinsa, kuma In Sha Allah daga yau kin dai'na zuwa in da yake, Aseef yana nan zuwa gobe, dama shi ne mai kai mishi abinci, zaki huta my sister, rabu da shi Allah yana ganin mu ai". Ya kai karshen maganar yana jawo mata zip ɗin rigar tata sama, sam bai ji daɗin abin da ɗan uwan nasa ya yi ba, yasan da cewa yana sane zanen ya jima, kawai bakar mugunta ce sai ya gallazawa ƴar mutane Baiwar Allah, amma ba komai zai gane kurensa, zai ɗanɗani ƙuɗarsa ne. Bayan ya gama ja mata zip ɗin rigar ya goge mata hawaye tas kafin ya miƙe tsaye yana mai dawo da kallonsa a kan Akila da ta tsare shi da idanu. "Heartbeat sarkin rigima, yanzu kuma wani sabon rigima zaki yi mini?" Ya yi maganar cikin zolaya, kuma duk cikin harshen turanci suke magana. Ɗan rufe fuska ta yi da hannunta tana murmushi bata ce komai ba, wucewa ya yi ya fice daga ɗakin ya koma wajen ɗan uwan nasa. Yana fita ta koma ta kwanta ƙwaƙwalwarta na tariyo mata abin da ya faro, kwayar idanunsa kawai take gani cikin nata, matsowa kusa da ita Akila ta yi ta shiga rarrashinta tare da bata baki. A ɓangaren Areef kuwa, abinci ya je ya zubawa ɗan uwan nasa, a tare suka ci suka ƙoshi, da kansa ya tattare kayan ya fitar tare da dawowa ya ɗauki chemical ɗin ya mai da shi mazauninsa, a lokacin shi kuma Lion already ya koma saman bed nasa ya kwanta, abu biyu suka tsaya mishi a zuciya tun zuwan shi NIGERIA, na farko Yarinyar da ta kira sunansa kai tsaye a ranar da ya sauƙa gidansu Imran, har cikin ransa yanzu da ya ga sunansa a kirjin Rimsha zuciyarsa ya bashi ita ce wannan yarinya, abu na biyu kuma fuskarta, tabbas ya taɓa kallon mai irin wannan fuska sak a tare da Josephine, to waye kenan? Wan can dai ba yarinya ba ce tare da Josephine, dattijuwa ce, kada ku mance kowa da yadda yake kallon mutum, wani zai ga kayi mishi kama da wani na shi, kai kuma ba zaka ga kamannin ba, to shi dai tabbas ya ga mai irin wannan fuska tata sak a tare da Josephine, sai dai ya rasa a ina ne ya taɓa ganin nasu tare, shiru ya yi yana faɗaɗa tunaninsa a ina ne ya ga hakan. Gefensa Areef ya zo ya zauna tare da ɗan taɓa shi, juyo da dara daran blue eyes nasa ya yi izuwa kan Areef ɗin, shiru bai ce komai ba, cikin natsuwa Areef ya fara magana. "My blood na san kana son farincikin mu fiye da naka, na san kana son abin da muke so, na san baka da wani burin da ta wuce ka ganmu a cikin farinciki, duk in da muka je muna alfahari da hakan, muna jin daɗin hakan, dan Allah yau ina neman Alfarma a wajenka, ba dan ni zaka yi ba, please and please dan girman Allah zaka yi, ina son ka rinƙa danne zuciyarka a kan sister, wlh tana da problem a kanta, ta shiga ta shin hankali, ko in ce taga tashin hankali da ya wuce shekarunta, ya wuci girman ƙwaƙwalwarta, hakan yasa take da yawan razana, to please tana tsoronka kamar ta mutu, tana tsoron ganin kwayar idanunka, idan har ka cigaba da kallonta ma kawai wlh kana iya ɗaukar gawarta, ni zaka yi wa, ina kaunarta, ina kaunarta fiye da tunaninka, idan tana farinciki nima ina yi, idan ta yi kuka, ko ban yi a zahiri ba, ina yi a cikin zuciyata, kasan dai bawa baya sanyawa kansa soyayya ko? To ba ni na sanyawa kaina sonta ita da mahaifinta ba, Allah ya jarrabeni da hakan, ka taimaka mini tun da Aseef zai zo gobe, ina son sister ta daina kawo maka abinci, ta daina zuwa kusa da kai, yanzu haka dole Prof ya ɗauketa zuwa asibiti, idan ba haka ba, akwai gagarumin matsala". Ya kai karshen maganar cikin wata iriyar murya mai ɗauke da damuwa ainun, tabbas duk abin da yake damun Rimsha ya sani, baiwar Allah bala'in da ta rinƙa gani na Daular Mutuwa ya birkita mata kwakwalwa, ko shi Dr Nawid bai gano ainahin damunwanta ba, wlh bala'in dake Daular Mutuwa ya fi karfin ƙwaƙwalwarta ya ɗauka, hakan ya haifar mata da razana, Areef ya gano hakan ne ta hanyar dubata da ya taɓa yi da bata da lafiya, hakan yasa take yawan suma, kuma Areef ya yi gaskiya idan ta cigaba da zama inuwa ɗaya da Lion to wata rana za'a iya ɗaukar gawarta a wajen. Shiru ya yi bai tanka ɗan uwan nasa ba, shima Areef ɗin shiru ya yi, almost 30 mins suna haka kafin Lion ya ce "Haka kake so?" Gyaɗa mishi kai ya yi alamar e, jinjina kai ya yi alamar to ya yi accepted, wani irin farinciki ne ya dira mishi a cikin zuciyarsa, da sauri ya rungumi ɗan uwan nasa yana zuba mishi ruwan godiya tare da ruwan Albarka, shikenan yanzu Rimsha ta tashi daga ƴar aiki, ta yi free wow abin ya yi daɗi, yau saboda Areef Lion ya canza magana, saboda faricniki TRIPLETS kai abin ya kayatar. Sun jima suna hira, ko da sunan wasa Lion bai sanar da Areef face ɗin Rimsha ya yi mishi kama da na wata da ya taɓa gani tare da Josephine ba, ya bar abin a ransa zan yi bincike a kan idan ya sami lokaci, yau dai kwanan faricniki Areef ya yi, shi kuma Saif mafarkin Josephine kamar kullum ya kwana yana yi. A ɓangaren Rimsha da Akila kuwa, Rimsha dai barci ɓarawo ne ya yi awon gaba da ita, ita kuma Akila sai da suka yi waya da Umaisha kafin ta raba dare da sahibin nata suna hira, sai Misalin karfe 2 na dare suka hakura ba dan sun so ba, ko kaɗan a hirar tasu bata kawo mishi zancen cewa ta gane shi ko makamancin haka ba, shima bai kawo mata zancen ba, sun dai zuba soyayyarsu kamar yadda suka saba. Wayar da suka yi da Umaisha ba komai bane face magana a kan yajin da Akil ya yi, mu koma baya kaɗan mu ji tattaunawar tasu kafin mu cigaba da tafiya. Kiranta Umaisha ta yi, tamkar zata yi kuka ta fara magana "Hello Heartbeat". Cike da kulawa Akilar ta ce "Aunty Umaisha ta yaya Akil, to ya ake ciki ne? Ya naji muryarki haka? Ko dai babyna ne yake addaba miki? Kin san nina yi mishi huɗuba ai, na ce ya tabbatar yana takura miki sosai, ya yi ta naushinki a ciki har sai kin yabawa aya zakinta". Tana magana tana murmushi, turnuke fuska Umaisha ɗin ta yi, tamkar zata yi kuka ta ce "Ni Heartbeat ba wannan ba, dan girman Allah wata alfarma nake nema daga gare ki". Da sauri ta ce "Wace alfatma kuma?" "Dan Allah heartbeat ki kira mani shi a waya, ki ce mashi wlh na tuba bazan kara ba, tun fa da safe ya yi fushi ya fita, kuma wlh kafin ya fita sai da ya ce mini ya yi yaji sai ya yi sati biyu ko wata ɗaya zai dawo, na ɗauka wasa yake yi kuma raina a ɓace na ce mashi kada ma ya dawo ma in yana so, ashe wlh da gaske yake yi, yanzu na kirashi yafi miss call hamsin ya ki ɗagawa, kuma wlh ni nasan yana ganin kirata, ɗauka ce kawai ba zai yi ba, na yi mashi massages har na gaji babu reply, dan girman Allah ki kirashi nasan zai ɗauki kiranki, ba zan taɓa iya yin barci ba har sai ya dawo". Kwashewa da dariya Akila ta yi har da riƙe ciki, iskanci Umaisha da Akil ya wuce misali. "Heartbeat ki tausaya mini ko dan saboda babynki". Tana magana murya a dashe taci kuka ta ƙoshi, ita kuma Akila tsabar shakiyanci tana binta da to na iyashege, sai da Umaishar ta gama maganarta tas, sannan Akilar ta ce "Kai amma yaya Akil ya iya, wato ma shi ne ya yi yaji kenan? Wayyo cikina, ai kaɗan ma kika gani, ba ke duk abin da na gaya maki baki ɗauka ba, wlh yaya Akil ustadz ne, koyi da annabi yake yi, shiyasa shi ya yi yaji ya bar miki gidan, nasan yana masallaci a yanzu, ya tare a can, abin da zai faru kawai ki jira sai ya cika wa'adinsa da ya ɗebe". Ta kai karshen maganar tare da sake kwashewa da dariyar shakiyanci, katse kiran kawai Umaisha ta yi, dan ta lura Akila zata kara mata zafi a kan zafi ne. Bayan ta katse kiran ne Akilar ta jawo bargo ta shiga kafin nan ta rubutawa Akil massage a kan halin da Matarsa ke ciki, bayan ya tura mishi ne bai fi da minti goma ba masoyin nata ya kira, shi ne suka fara hira har karfe biyu na dare, to kun ji yadda a ka yi. Washegari karfe 8 na safe, Akil ya zo ya ɗauki Akila ya mai da ita gida, kamar yadda Imran ya faɗa, sun sha kukan rabuwa da Rimsha kamar ba gobe, sai da Areef ya ja Rimsha zuwa cikin gida, ita kuma Akila Imran ya turata cikin motar Akil suka nufi gida. Ɗaki Areef ya mayar da Rimsha tare da yi mata albishir a kan daga yau ta bar aiki, school kawai zata rinƙa zuwa ta dawo, sai wanka da tsala kwalliya, sai kuma barci, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, dama kamar zata yi kuka, daurewa kawai take yi tana yin wannan aiki, amma badan haka ba, Allah ne kaɗai yasan yadda take ji a duk san da ta ɗauki abincin da nufin ta kai wa Lion. Ganin sai murmushi take baki yaki rufuwa ne yasa shi ya miƙe tare da ficewa daga ɗakin yana mai jin tsantsar kaunarta a ransa. Bin bayansa da kallo ta yi har ya kure wa ganin ta ya fice daga ɗakin, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare buga uban tagumi, ta rasa me yake damunta, daga jiya zuwa yau, a hankali hankali soyayyar da take yi wa Saif yana juyawa ya koma kan Areef ne ko Aseef ne ta rasa, ita kanta ta rasa me yake damunta, ko wace zuciya tana son mai kyautata mata, tabbas son da take yi wa Saif kaso 40 cikin ɗari ya dawo kan Aseef da Areef, sai dai a cikinsu ta rasa tantance waye ne take yi wa son aure, waye kuma take yi wa son kyautatawar da suke yi mata, shekarunta bai kai ta iya tantance hakan ba, ba karya suna bata kulawar da ko motsi ta yi sai sun tambayeta akwai wani abin ne idan suna kusa, shi kuma Aseef idan suna yin video call kenan, ba su taɓa barinta ta zauna shiru har ma ta yi wani tunanin da zai sanyata bakin ciki, tabbas tana son su ba kaɗan ba, ba zata iya yin wuni guda bata ga Aseef or Areef, idan bata yi Video call da Aseef ba, to zata kalli Areef, musamman ma shi Areef ɗin wanda suka yi mugun sabo na kin karawa, kuna ganin dai yadda suke da ita, kuma idan ba ku manta ba, shi Areef ɗin shi ya fara bata kulawa kafin Aseef ya biyo bayansa, shi ya kula mata da daddynta tamkar ɗan uwan shi, wannan matsala tata tana neman zama mata gagarumar matsala, domin ta rasa wa take so so na aure, waye kuma yake yi wa son kyautatawa a cikin TRIPLETS. Yana fita abinci ya je ya ɗaukawa ɗan uwan nasa daga kitchen zuwa ɗakinsa, kamar dai kullum a tare suka ci abincin cikin nishaɗi da kaunar juna, bayan sun kammala suka koma saman bed dan su cigaba da hira, bayan Areef ya gyare wajen kenan, Allah sarki karfi da ya ji Areef ya koyi aikin da bai kamata ace shi ne yake yi ba, before bai iya ba sam, yanzu kuma Alhamdulila yana ƙoƙartawa ya yi. Misalin karfe biyu na rana, taci kwalliya kamar ba gobe, ta sanya ɗaya daga cikin ɗinkunan da Imran ya ɗinka musu, wata shegiyar ɗinkin riga da skit a kayi mata, kayan sun zauna tsam a jikinta tamkar dan ita aka yi shi, ya bi shape ɗinta sosai da sosai, bata iya ɗaura ɗankwalin atampha ba, sai kawai ta yafa abinta a saman kanta, ta yi kyau iya kyau. Palon sama ta fito ta zauna tana jiran Imran ya fito zai kai ta wajen gyaran gashi, yau tana ji tamkar ta yi kumshi idan suka je gyaran gashin tun da yanzu ta daina yi wa Saif aiki, farinciki a wajenta ba'a magana, tana zaune shiru ga wayarta na a gefenta, ko me ta tuna sai kuma idanunta suka cika tap da kwallah, wayar tata ta laluɓo. Kunna hasken screen ɗin wayar ta yi, bayan ta cire password ɗin contact ta shiga, number Anaya ta fara kira, bugu ɗaya Anaya ta ɗaga dan lokacin ta dawo daga school, murya a gajiye ta ce "Rimsha ina wuni?". Tamkar zata fashe da kuka ta ce "Anaya, Anaya yau GAR ya kallah mini......." Sai kuma ta kasa karisawa ta yi shiru. "Rimsha waye kuma GAR? Me kuma ya kallah miki ɗin". Girgiza kai ta fara yi tamkar Anaya ɗin na a gabanta "Babu komai Anaya zamu yi waya anjima". Ta kai karshen maganar ba tare da ta jira Amsar da Anaya ɗin zata bata ba, ta yi maza ta katse kiran. Ajiye wayar a gefenta ta yi tare da buga uban tagumi tana tunani, abin da Lion ya yi matan nan, ya yi mata zafi ba ɗan kaɗan ba, kuma dai kunsan yadda take tattalin tula tulan nan nata, bata son ko iska su sha, idan zata sanya kaya sai ta rufesu da vest, bata bari ko alamarsu a gani, kawai ya zo ya wani buɗe mata su ya kalle kamar nashi ko an aike shi, yau da tana da dama sai ta kifa mishi maruka ko biyar ne haka, kila ta huce takaicin da take ciki, idan ta tuna shikenan ya kallesu, sai ta ji tamkar ta aza hannu a kai ta yi ta kurma ihu ko zata ji sauƙi a cikin rayuwarta. Tana tsaka da tunani ta ji alamar gudu ana haurowa saman benen, kai kallonta izuwa wajen ta yi dan taga su wanene. Coper, Lucky, Winston, da kuma Brady da wasu irin mahaukatan gudu suka hauro palon saman. Tana yin ido huɗu da su bata san time da ta miƙe da wani mahaukacin gudu ba, ta ruɗe sosai, bata san time data faɗa ɗakinsa a maimakon na Imran ba, dan ba zata iya shiga ɗakinta ba, salon su bita su yi mata wani abin, gwara ɗakin Imran, duk wuya zai tare mata, ba zai bari su taɓata ba, ba zai bari su cije ta ba, sai aka samu akasi, ta fito daga ruwan zafi ta faɗa wuta, shi ne shiga ɗakin Lion da tayi kenan. Yana tsaye a gaban mirror daga shi sai towel a kugunsa, kai tsaye wajensa ta nufa, su kuwa tana miƙewa suka rufa mata baya, dan su karnuka dama amfani suke yi da kamshin jikin mutun su nemo in da yake, Lion suke nema, ba ruwansu da ita, ita ce ta tsorata sosai, musamman ma Brady in da ya yi kewar Lion sosai, ai a guje ya nufi ɗakin Lion ɗin. Ita kuma idanunta a rufe ta faɗa jikinsa ta baya tare da kankame shi sosai tana ihu, gently ya juyo tare da juyo da ita ta gabansa dan taga waye ta riƙe, ina ai idanunta a rufe, haushin su Brady yana kara haukata mata kwakwalwa, wani irin damka ta yi mishi tare da harɗe hannayenta a kugunsa ta kewayo da su ta bayansa, kanta a saman kirjinsa, ta kara ƙanƙame shi sosai ta yadda ba zai iya ɓanɓareta daga jikin nasa ba, ta manne kamar chewing gum, tare da datse idanunta gam A fusace yake ƙoƙarin daka mata tsawa Brady ya yi kansu da gudun gaske, wani razanannen ihu ta saki tare da sake yin tsit tamkar an ɗauke wutar nepa, sarkin tsoro kenan number ɗaya. Daka suwa Brady ya yi ya haye jikinsa yana kuka a hankali, ga Rimsha a ɓari guda ga Brady a ɓari guda, daidai lokacin Aseef ya shigo cikin ɗaki Areef na biye da shi a baya, su coper suna gefensu, shi Aseef ya ce ba zai iya tafiya mai nisa ya bar su coper ba, shiyasa ya tattarosu abinsa, tamkar sun dawo NIGERIA ne da zama. Karisowa wajen ɗan uwan nasu suka yi, fuskokinsu ɗauke da tsantsan faricniki tare da kayatatcen murmushi,. Rimsha na ƙoƙarin sulalewa ta zube kasa dan bai riƙeta ba, kuma ta suma jikinta ya saki, yana jinta bai tare ta ba, a cewarsa me haɗin shi da ita, Aseef da Areef har suna rige rigen tareta, mamaki ne ya kama shi, kamata ya yi Aseef ya rungume shi ya yi mishi oyoyo amma suna rige rigen ɗaukar Rimsha, wai anya lafiyarsu kuwa? Ya tambayi kansa, yana tsaresu da ido. Areef ne ya tareta, shi kuma Aseef ya dakawa Brady tsawa a kan ya sauƙa a jikin Lion ɗin bari shi ya rumgumi ɗan uwansa, da yake sabo tirken wawa, sun saba sai Brady ya sauka shi kuma ya rumgumi ɗan uwan nasa, rike shi sosai Lion ɗin ya yi yana shafa kansa, gently ya ce "Ya hanya?" Kiss ya yi wa ɗan uwan nasa a kumatu yana faɗin "Ai Exams dana haɗa nayi lokaci guda ya fi wannan tafiya wahala". Dariya Areef ya yi lokacin yana kwantar da ita a saman gadon Lion ɗin. Da mamaki Lion ya bishi da kallo, wai me TRIPLETS suke nufi da shi ne? Ya tambayi kansa, kai kallonsa kan ta ya yi tare da dawo da kallon nasa a kan Areef ɗin. Cool murmushi Areef ya sakar mishi kafin ya ce "A filina ta kwanta ai ba'a fillinka ba". Girgiza kai ya yi wato ma suna sane suke yi mishi abin da suka ga dama, bai damu sosai ba dan yana ɗauka cewa Areef yana sonta ne, soyayya irin ta aure suke yi, shiyasa sau da dama baya damuwa da irin hakan, kuma tabbas ya ga tsantsar kaunarta da sonta a idanun ɗan uwan nasa, to babban abin tambayar a nan shi ne, wannan suna da ta rubuta a kirjinta fa? Ya tambayi kansa da kansa, tabbas yana da tabbacin Areef yana sonta, kuma yaga yadda suke da ita da Areef ɗin gwanin ban sha'awa, baza'a ce bata son shi ba, to ya abin yake kenan? Ya sake tambayar kansa da kansa. TO FA BABBAR MAGANA SHI LION SABODA SHAƘUWAR DAKE TSAKANIN TA DA AREEF YASA YANA TUNANIN SOYAYYA SUKE YI, KUMA IDAN BAKU MANTA BA TABBAS AREEF YANA SONTA, KAWAI DAN YASAN ƊAN UWANSA TAKE SO NE YASA YA HAKURA, SHI LION SABODA TSANTSAR KAUNAR TRIPLETS NASA YASA YAGA TSANTSAR SOYAYYAR RIMSHAR A CIKIN KWAYAR IDANUN AREEF ƊIN, HAKAN YASA YA GASGATA TUNANIN DA YAKE YI A KAN SHAƘUWAR TASU, YA KENAN WANNAN SHI NE CAKWAKIYA, ITA MA DAI KUNJI YANZU TA FARA SON AREEF ƊIN, MU DAI JE ZUWA. "Je kayi wanka ka shirya sai ka zo ka ci abinci". Cewar Lion, ya yi maganar yana kallon Aseef. "Lion a kira masu gyara ɗaki, su zo su sanya mana bed guda uku a cikin bedroom ɗin nan ka ji?" Cewar Areef. Shiru ya yi musu tamkar bai ji su ba, zasu fara saka shi a gaba kenan, wai gado guda uku, ya bi uku da gudu, kowa ɗakinsa zai wuce iya shegensun nan. Wucewa Aseef ya yi izuwa cikin toilet, shi kuma Areef ya tattara su Brady ya nufi waje da su, oga kuma, ya cigaba da abin da yake yi na shafa Lotion nasa. Bayan ya kammala ya wuce dressing room nasa, ita kuma tana kwance a saman bed nasa, yau gata a bed ɗin Lion a matsayin budurwar Areef, lallai akwai cakwakiya ba ɗan karami ba wai. After some hours💋 Shirye cikin wani shegiyar wandon jeans mai bala'in kyau da tsada Aseef ya fito, wandon launin blue, sai kuma riga launin ash color, ya yi matukar kyau sosai kamar ba shi ba, sai tashin kamshi perfume ɗin ɗan uwansa yake yi, yanzu saboda tsiya perfume ɗin Lion yake sakawa, tun da ya sami lafiya shikenan ya koyi takurawa Lion shima, ya bi kafar Areef, diamond watch nasu na TRIPLETS yau ya ɗauko ya sanya a hannunsa, dama idan baku mance ba Lion ya karɓe watch ɗin gabaɗaya ya ajiye, to ya je ɗaukar agogon Lion ɗin sai ya ga diamond watch nasu, hakan yasa ya ɗauke shi kawai, glass kuma, baki ya ɗauko wadda baka iya ganin kwayar idanunsa, kuma glass ɗin ba ƙaramin kyau ta yi mishi ba, sarkansu na nan a wuyarsa ko in ce a wuyoyinsu. Bayan ya kammala shiri tsab ya fito daga dressing room ɗin zuwa cikin ɗakin, babu kowa a cikin ɗakin sai Rimsha dake sume, saman gadon ya hau tare da shafa fuskarta yana ambatar sunanta kasa kasa, shiru bata farka ba, sauƙowa kasa ya yi tare da buɗe fridge ya ɗauko ruwa mai sanyi, kaɗan ya tarfo a hannunsa tare da shafa mata a fuskarta, da yake a nitse ya yi mata, sai ta farka a nitse, ganin shi da black glass ya rufe kwayar idanunsa ba zata iya tantancewa ba sai ta yi zaton Lion ne, abin da mamaki yadda mutane ke kallon fuskokin mutane da dama a fuskar Aseef, dama akwai irin mutanen nan, sai dai basu da yawa a duniya, wadda idan ka kallesu dole sai sun yi maka kama da wani naka, haka halittar fuskarta ke. Kokarin sauƙa kasa ta yi dan ta gudu kada ya yi mata hukunci, riƙo hannunta ya yi yana mai ambatar sunanta, jin muryarsa yasa ta tsaya tare da ambatar sunansa yaya Aseef, shi kuma mamaki take bashi yadda take banbanta voice nasa dana Areef, ta yi musu farin sani yarinyar nan, ko bata ga face nasu ba, tana iya banbanta voice nasu, akwai ta da kwakwalwa over. "Waye ya ce miki ni ne? Areef ne fa". Ya faɗa cikin zolaya, dariya mara sauti ta yi ba tare da ta yi magana ba, yana riƙe da hannunta ɗaya cikin nasa ya ciro wayarsa da ɗayan hannu ya fara kiran number daddynta video call. Bugu ɗaya daddyn nata ya ɗauka, yana zaune kusa da pool yana karatun husnul Muslim, ganinta yasa ya saki wani ƙayatattacen murmushi har sai da dimples nasa suka lotsa sosai, ita ma murmushi take yi sosai tamkar ta shiga ta jawo daddyn nata ra rungume haka take ji. Sai binsu da ido Aseef yake yi yana murmushi, cikin harshen Hausa suka gaisa tare da fara hira, sai dariya take yi ta manta ma a ina take, almost 30 mins suna hira haka kafin Aseef ya ce "Uncle zan kira anjuma yanzu zata rakani wani waje ne". Da turanci ya yi maganar, okey Musharraf ya amsa da shi, diff ya katse kiran tare da cewa "To tashi muje ki rakani unguwa", ɗan zaro idanu ta yi, "Unguwa kuma yaya Aseef?". Gera ɗaya ya ɗaga mata alamar e, okey ta amsa mishi tare da miƙewa ta sauƙo kasa, har lokacin bai saki hannun nata ba, tamkar wasu mata da miji haka ya riƙe hannunta suka fita waje. A palon sama ya cikaro da Areef yana ƙoƙarin shiga bedroom ɗin. "Kai, kai, kai, Aseef ina zaka je haka?" Ya yi maganar yana kare mishi kallo, ba karya ya yi kyau sosai. "To sarkin sa ido ina ruwanka da ni, ni dai yanzu bani saƙona ka gani". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce Okey, bai wani damu ba, dan yasan Aseef da Musharraf babu ɓoye ɓoye a tsakaninsu, wata kila Musharraf ne ya gaya mishi in da wasu ƴan uwansa suke zai je duba su. Juyawa ya yi a tare suka sauƙa palon kasa, Lion yana garden zaune, Aseef da Rimsha suka wuce zuwa garden ɗin, shi kuma Areef ya wuce cikin bedroom nasa. A ɓangaren Lion ɗin ma haka ne, da ya ce mishi zai je unguwa Rimsha zata raka shi, ya yi tunanin wajen wasu daga cikin ƴan uwan Musharraf zai je, tun da ɗan Kaduna ne Musharraf ɗin, sai bai hana shi fita ba. Riƙo hannunta ya yi suka koma cikin gida Imran da jelly kuma basu nan sun tafi gidan Abbi, dama tare zasu fita da Rimshan, ganin tana barci a ɗakin Lion yasa ya tafi abinsa, dan shi bai ɗauka a sume take ba, ya yi zaton barci take yi. Ɗakin dake kusa dana Areef a palon kasa ya wuce da ita, har lokaci bata ɗaura ɗankwalin nata ba, dan bata iya ba, lokacin da suka yi rayuwa da daddynta bata sanya atampha, sai blouse da sauransu, hakan yasa bata iya ba. "Yaya Aseef ina zamu je?" Ta tambaya tana kallon uban akwatin da yake ƙoƙarin jawowa da hannu ɗaya. "Sarkin tambaya, ki bari idan muka je zaki gani, yanzu dai idan mun dawo wancan akwatin shi ne tsarabarki, sai ki zo ki ɗauka dan ni bani da karfi". Dariya ta yi, akwatin da yake hannunsa yake ja yanzu ma ai tafi tata da ya nuna girma, amma wai bashi da karfi, shima ya iya abin dariya. Harabar gidan suka fito, da sauri wani soja ɗaya daga cikin shabiyu da Lion ya karon nan, ya nufosu ya karɓa mishi akwatin zuwa bayan motarsa, har lokacin kuma bai saki hannunta ba, yana rike da ita kamar an ce mishi zata gudun mishi ne. Yana isa wajen motar da zai fita da ita wadda Lion ya saya tun farkon zuwansa, sai ga Areef ya fito da wata kwali mai ɗan girma a hannunsa, a gidan baya na motar kusa da akwatin ya sanya mishi kwalin yana faɗin idan ya je ya gaishe mishi da ƴan uwan Musharraf, shima idan ya sami lafiya zaizo ya gansu har gida, okey kawai ya amsa mishi da shi, shi kaɗai ya barwa kansa sanin in da zai je, ya ɓoyewa ƴan uwan nasa, shi kaɗai yasan dalilin ɓoyewar tasa. Gida gaba yasa Rimsha shi ma ya shiga mazaunin driver, Mark ya yi ƙoƙarin cewa zai raka shi, ya tuƙa su, amma yaki yarda, da su Areef suka tambaye shi yasan wajen ne, sai ya ce e ya sani shi dai su kyale shi, kada su sake tambayar shi ai shi ba yaro bane, haka suka kyale shi dan tun da Lion bai saka baki ba to sun san komai normal ne. A hankali ya ja motar suka bar gidan, ita dai Rimsha ta zuba idanu tana ganin ikon Allah, sai tafiya yake yi yana kallon wayarsa kamar ya san hanya, da alama kuma ya kunna goggle map ne. Sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa lafin su kai kofar gidansu Akila, da mamaki ta juyo tana kallon shi, wai a ina kuma yasan gidan su Akila?. Shiru dai bata ce mishi komai ba, dan tana tunanin daddynta ne ya ce yazo ya gaishesu tun da Abban Imran yayan daddy ɗin ne. Shi ma bai yi magana ba sai ɗayar wayarsa da ya ɗauko ya kira number Akila ɗin, bugu ɗaya ta ɗauka. "Hello My Heartbeat". Ya faɗa yana kallon anguwar ta cikin black glass ɗinsa. Shagwaɓe murya tayi tamkar zata yi kuka ta ce "Wai Heartbeat har yanzu baka iso bane? Nifa wlh na gaji". Ta kai karshen maganar idanunta sun ciko tap da kwallah, tana tsaye a kusa da gadonta, ta ci kwalliya sosai da sosai tamkar ba ita ba, atampha ta sanya ɗinkin riga da skit, abin kuma kamar haɗin baki, sak irin kayan jikin Rimsha, da yake tare Imran ya yi musu ɗinkin, ta yi kyau fiye da tunanin mai tunani, kun santa dama da iya tsara make up ba'a magana, sai dai bata yi make up irin na hauka da zai mai da ita kamar aljana ko bebin roba ba, mai kyau ta yi, tana ta tashin ni'imantaccen kamshi. "Sarkin rigima, ni kada ki yi mini kuka, kada ki ɓata mani kwalliya, yanzu dai abin hawa nake nema, nan da 1 hour zan iso". Cikin sauri ta ce "No ni ka gaya mani a in da kake, zan sanya driver ya ɗauko ka kawai". "Ina bakin gate ɗin gidanku". Ya bata amsa a takaice. Wani irin tsalle ta yi ta dire a tsakiyar gadonta, yau zata ga zaɓin zuciyarta, wayyo Allah daɗi kasheta, zata gan shi ido da ido, tunani ta fara yi ya zasu yi ido huɗu da shi, anya kuwa zata iya? Amma dole ta je su ga juna ko dan taga ya zai yi da ya rinƙa nuna mata bai gane ta ba jiya har da cewa baya jin Hausa, abin da bata sani ba shi ne, yes Areef baya jin hausa kamar yadda ya gaya mata, maganar da ta yi a garden ko baka jin yare zaka fahimci me take nufi tun da a kan hakan suke maganar, bare kuma shi da yake babban jami'i, haka shi ma Aseef ɗin bana jin Hausar, akwai dai wani abu, amma basu jin Hausa, kuma abin ne ma ya haɗe mata ya birkita mata kwakwalwa ta yadda ta ɗauka yes Areef ɗin ne. Mayafinta ta ɗauka ta nufo waje, a palo ta sami Ammie, ba ɓoye ɓoye ta gaya wa Ammie in da zata je wajen saurayinta, da farko Ammie ta hanata fita, daga karshe kuma da ta ga ƴar tata ta damu sai ta ce to ta je kada ta jima, sai murna take yi ta fito waje. Tun da mai gadi ya ɓuɗe mata gate ta fito ya tsareta da idanu ta cikin glass, bata kai ga karisowa wajen motarsu ba, ya buɗe kofar motar ya fito, a zuciyarta ta ambaci tabbas shi ne, da yake ya sanya bakin glass bata ga kalar kwayar idanunsa daban dana Areef ba, bata saba ganinsu a tare ba, ba zata iya banbance su lokaci guda haka ba, kuma jini ba wasa ba, sannan kuma TRIPLETS ai ba karya ba, dole akwai wannan kama da idan ba a tare ka gansu ba, ba zaka iya banbanta su ba, amma fa ta ruɗewa kyau iya kyau, ta birkice, kuma tabbas a Areef ta ɗauke shi, shi kuma Aseef ne, cakwakiya kenan, ita dai Rimsha idanu kawai take binsu da shi, abin ya ɗaure mata kai, to wai shin wanene mason Akilar a cikinsu? Alamu dai sun nuna ba Areef bane, kamar yadda ya nuna mata da farko bai ganeta ba, bai da alaƙa da da ita, to hakan ne, yana da gaskiya. TUN FARKO YA KAMATA KU ƊAUKI HASKEN WAYE MASOYIN AKILA A CIKINSU, WAYE TRIPLETS SUKE CEWA HEARTBEAT ƊIN SU❓ WAYE AUTANSU❓ IDAN BAKU MANTA BA YANA YAWAN CE MATA HEARTBEAT+HEARTBEAT, FATAN KUN GANE❓ SAURA KUMA ITA MA AKILAR TA GANE Da fara'a ta kariso wajensa, da yake polo t-shirt ya sanya sai bata banbance yanayin jikinsu ba, cikin harshen Hausa ta ce mishi "Sannu da zuwa sarkin basaja, yanzu ma zaka ce mini baka gane ni ba ko?" Ta yi Maganar cikin zolaya. Cikin harshen turanci ya ce mata "Kiyi magana da English ni bana jin Hausa". Babbar magana, to fa, ya tabbata basa jin hausa, amma ya akayi yake magana da ita a waya da Hausa,? To ko dai ba shi bane? Anya kuwa, kaina ya kulle sai Allah ya kaimu Monday da rai da lafiya dan jin ya wannan cakwakiya take, baya jin hausa kuma?🤔 Wayyo heartbeat+ Heartbeat, Auta+ Auta, Shagwaɓa+ Shagwaɓa, Kuka+ Kuka, Iya soyayya+ Iya soyayya, Tsarkakkan zuciya + Tsarkakkan zuciya. Ya kuke ganin Abin❓ Akwai cakwakiya a TRIPLETS sosai gaskiya. ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E21-22 Cikin harshen turanci ya ce mata "Kiyi magana da English ni bana jin Hausa". Babbar magana, to fa, ya tabbata basa jin hausa, amma ya akayi yake magana da ita a waya da Hausa,? To ko dai ba shi bane? Anya kuwa, kaina ya kulle, baya jin hausa kuma?🤔 Da mamaki ta zaro idanu tana kallon shi, baya jin Hausa kuma? Ta maimaita a ranta. "Why are you surprised after I told you I'm not understanding hausa?". Ya yi maganar yana tsareta sosai da idanunsa, da yake a cikin bakar glass ne, sai bata fahimci yana ganinta ɗin ba. "How am I sure that you are not understanding after all we are chatting with hausa?". Wayarsa ya ciro ba tare da ya yi magana ba, numberta ya fara kira, ɗagowa tayi ta kalle shi, alama ya yi mata da hannu a kan ta ɗauki kiran. Jim ta ɗan yi kafin ta ɗauki kiran, kara wayar a kunnensa ya yi, cikin harshen turanci ya ce mata "Hello my heartbeat good afternoon". Abin mamaki ita kuma sai ta ji maganar nasa da Hausa ya zo mata wayar tata, domin ta gasgata maganar abin da take ji, sai ta ce mishi cikin harshen Hausa "My heartbeat ina kewarka sosai". A cikin wayarsa ta ji muryarta na magana da English, babbar magana to me hakan yake nufi?. A sukwane ta cire wayar daka kunnenta tana bin screen ɗin da kallo, shi kuma kallon rikitatciyar face nata kawai yake yi, da dai yaga bata da niyar magana ta shiga ruɗu sosai, sai ya ɗan matso kusa da ita, cikin shagwaɓa da harshen turanci ya fara magana "Sarkin shiga ruɗu ba, to ke yanzu a wannan ɗan abin me na shiga ruɗu fisabillilahi?". Ɗago idanuwanta ta yi tare da sauƙesu a kansa, "My heartbeat dole zan shiga ruɗu, taya hakan ta faru please,? How comes ni zanyi magana da Hausa kai kuma zaka ji da English, kuma ga shi murya ta ce da komai, sak yadda nayi magana, amma kuma ba da yaren da nayi ba yaje maka". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Na sha wahala sosai kafin na iya canzawa number ki language, sai da naje company musamman a ka buga mini wayar nan, lokacin da na je sayawa uncle Musharraf waya, a lokacin nasa aka buka mini ita, na kuma sanya a saka mata wannan tsari, ina sonki, kuma bana son ki san ni waye, ina sone in yi miki magana da yarenki dan hankalinki ya fi kwanciya da ni, dan ki karɓeni hannu bibbiyu, nasan idan na kiraki na fara magana da yarena, ba zaki wani ɗaukeni da muhimmanci ba, hasalima cemin zaki yi wrong number ne, saboda keɗin mai daraja yarenki ne, kuma hakan ya kamata kowani ɗan adam ya kasance, ya zama mai daraja yaren iyaye da kakanninsa, kada ya zama mai aron yare, sai dai a ari tasa yaren, kada ya yarda shi ya ari na wasu, wannan dalili yasa na sanya aka saka mini wannan tsari a wayata, dan koba komai idan kika ji nayi magana da Hausa, tabbas zaki saurareni, ko da kuwa ba zaki so ni ba, albarkacin wannan yare naki da nayi zaki bani dama, kuma nayi nasara, albarkacin magana da Hausar tasa kin bani dama, kin kula har na shiga zuciyarki, amma ina mai baki hakuri a kan hakan, nasan ban kyauta ba, yanzu dai kin ji, wayata ke canza maganar da na yi daga English ya baki da Hausa, shiyasa Hausar take fito miki a kema na fiki iyawa ai, dan ba mutun yake yi ba, computer yake yi". Ya kai karshen maganar cikin zolaya yana ɗaga mata gera ɗaya. Ɗaure fuska ta yi tamkar ba ita ce mai murmushi yanzun nan ba, a kule ta ce "A ina ka san ni? Waye ya baka number ta?". Zuba mata idanu ya yi na ƴan mintoci kafin ya ɗan gyara tsayuwarsa cike da kulawa ya fara magana. "Haba My heartbeat why sudden changed on your face, from smile to mood? Don't you know that i really like your smile? Please put smile on your face, so that I can get peace of mind". Kin kula shi ta yi, sai ma juyawa da ta yi da nufin ta koma cikin gida, ita a dole ta yi fushi da shi. Cikin sauri ya riƙo hannunta, gabaɗayansu sai da suka ji wani shock, abin ku da zuciyoyin masoya, ya riƙe hannun Rimsha bai ji komai ba, dan ba ita ce ainahin wadda zuciyarsa ke marari ba, ita ma tana riƙe hannayen ƴan uwanta, bata jin komai sai na shi yau, har wani irin yarr suka ji a jikinsu lokaci guda. "Please My heartbeat am so so sorry, okey don't change your face again, I will amsa you like this". Kasa kasa ta ce ya sakar mata hannu, kara marairace murya ya yi tamkar zai yi kuka, a shagwaɓa ya ce "Okey zan saki, amma please promise me that you can't go anywhere without my parmition?" Jinjina mishi kai ta yi alamar ta yi alkawarin ba zata tafi ba. Sakin hannun nata ya yi tare da cigaba da magana "Before na fara kiranki a waya i have had some of your pictures that your brother sent to me last, ɗin kenan, so first time of seeing your pictures i fall in love with you, i bought this my phone second day of seeing your pictures, 3 day lokacin kuna gidan uncle naku, you are together with your sisters, uncles and your brothers, prof called me on video, wen I saw you, sai na ji i can't control my self or stop my self izuwa ga kiranki, already lokacin an haɗa mini wayar, Prof bai katse video call ɗin ba, ina kallonki na tura miki massage na farko a tsakanina dake, ina ganin action naki time ɗin, to kin ji yadda abin ya fara, please don't be angry with me, kin ji my heartbeat, my pleasure part 4". "Part 4 kuma?" Ta maimaita, jinjina mata kai ya yi alamar yah part 4. "Why part 4? Who is the part 1, 2 and the 3?" Murmushi ya saki wadda ta kara bayyanar da tsantsar kyan da Allah ya ba shi, Allah ya yi halitta a kan TRIPLETS. Ba ƙaramin rikitata murmushinsa ya yi ba, dama tun ɗazun sai faman satar kallon shi take yi, ya haɗu ta ko'ina, ai baza ma ta iya kwatanta shi da kowa a cikin zuciyarta ba, ba zata iya fushi da shi ba, yanzu tsantsar kaunarsa ma karuwa sosai ta yi a cikin zuciyarta, sai addu'ar Allah ya mallaka mata shi take yi. "My TRIPLETS the are part 1 of my pleasures, and then your brother, prof part 2, my uncle Hossain part 3, then you part 4, then rest". Da mamaki cikin zola ta ce "Yanzu ko kunyata baka ji ba a gaba zaka ce nice part 4". Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "Yes My heartbeat, do you want me to lied to you ne? Ni bana yiwa wanda nake so karya, kai not only wanda nake so, everybody bana yi wa kowa karya, yanzu idan nace kece farincikina sama da Triplets na zaki yarda?". Girgiza Mishi kai ta yi alamar a'a. "To kingani, ba amfanin na gaya miki maganar da nasan ba zaki yarda da shi ba, wadda sai dai ki amsa mini dan jin daɗi na kawai, is better ka gayawa mutun gaskiya ko da zai ji ba daɗi, daga baya zai gane gaskiya na gaya Mishi". Sosai ta karajin kaunarsa ya ninku a cikin zuciyarta. "Heartbeat what of Rimsha? Last time you told me tha she is your sister, and then you didn't mention her a cikin pleasures naka, why?". Ɗan juyawa ya yi ya kalli cikin motar tasa, da yake bakin glass ne, baka iya ganin mutumin da yake daga ta ciki, sai shi na ciki ne zai iya ganinka. "My heartbeat idan nace my TRIPLETS i mean with her insert, Rimsha ita ce cikon TRIPLETS, In Sha Allah matar Saif ɗin mu ce, kinga kuma idan babu Saif to babu TRIPLETS, idan akwai Saif to akwai Rimsha kuma akwai Triplets, fatan kin gane?" Jinjina mishi kai ta yi almar yes ta gane, kuma ba ƙaramin daɗin maganarsa ta ji ba, gaskiya Rimsha ta sami gurbi mai shegen tsada a zuciyar Areef da Aseef, wannan gurbi da ta samu kuma, zamu iya cewa tafi daddynsu samun matsayi, tashin sense. Ita dai Rimsha ta zubawa satautar Allah idanu tana kallonsu, har barci ya fara ɗaukarta baiwar Allah. "Heartbeat amma ya akayi kake iya controlling na wayata ko da yaushe, and then komai na yi kana gani". Shagwaɓe murya ya yi tamkar zai yi mata kuka. "Ke Heartbeat kin cika tambaya sosai, ni ba ɗaya daga cikin Triplets bane? Sakawa na yi a datsa mini camerar wayarki, a kayi yi mini connecting da laptop na, Tyrone babban yaron Lion ne ya yi wannan aiki, kuma na gaya mishi kada ya gayawa kowa, akwai sirri a tsakanin mu, shiyasa duk in da zaki je matikar kina tare da wayarki to sai na ga abin da kike yi, sai dai idan camerar wayar taki bata zauna saitin in da zan ganki ba, amma fa wani lokaci kawai ina cankar abin ne da kike yi ne da kai, dan wani lokaci a saman bedside drawer kike ajiye wayar taki, kuma ba kifa wayar kike yi ba, kina danne camerar a kasa, bana samin ganinki da kyau, sai na canka kawai, batun controlling na wayar ki ma Tyrone ne ya yi wannan aikin, so please stop asking me some questions kin ji?". Ya kai karshen maganar tamkar zai yi kuka. "Amma fa Heartbeat ka yi wasa da kwakwalwata sosai, ba dan Rimsha ba serious fushi da kai zanyi, amma Rimsha ta ceceka". Ɗan langwaɓar da kansa ya yi a shagwaɓe ya ce "Heartbeat let's enter inside the car, ni na gaji da wannan ranar, serious tun ɗazun yake damuna, na daure ne saboda ke". Ɗan kallon motar ta yi kafin ta ce "No ni a ranar nake son ka tsaya". Cool murmushi ya sakar mata "Okey i like everything you like, let's stay here ɗin kawai, kuma da kika yi magana ma ya fi daɗi". Murmushi ta saki ita ma, har cikin zuciyarta ta ji matuƙar daɗin zancensa, ya iya magana kamar ba gobe, dama ta ce su tsaya a nan ne dan ta gwada shi, dan taga shin zai iya yi mata gardama ko a'a, to ga shi dai duk abin da take so shi yake so, soyayya ruwan zuwa. "Amma wannan hoton da ka turomini kana cikin Hausa mens ɗin fa?" Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Pic ɗin Triplets na ne, ba ni bane, ni before bana son black peoples ko kaɗan, a baya mutun ɗaya daga cikin mu ne yake kula kowa har da black peoples, to hoton sa ne ba nawa ba, ni da Lion bamu so, amma yanzu da muka musulta, muna son kowa, mun gane kowa ɗan adam ne mai ƴanci". Shiru ta yi tana tunani, tana son gane banbancinsa da hoton, ta dage dole dole sai ta gano banbancin dake tsakanin TRIPLETS, ga shi kuma iya kalar kwayar idanun Areef kawai ta sani, bata san na Lion ido da ido ba, bata san na shi Aseef ɗin ba. "My heartbeat you look so gorgeous more than everyday". Ya yi maganar kasa kasa cikin sigar soyayya da kauna, yana ji tamkar idan bai mai da ita cikin zuciyarsa ba, ba zai taɓa samin kwanciyar hankali ba. Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "My heartbeat am surprised lokacin da na ganka, ba zan ɓoye maka ba har yanzu na kasa yarda da cewa wai kamar kai ne kake so na, tun da na ganka, na tabbatar kai ne, daga nan na shiga ruɗu akan soyayyar da kake ikirarin kana yi mini". Tana magana tana wasa da yatsun hannunta. Hannun nata ya riƙo cikin nasa, a hankali yake murza ƴan yatsun nata, har cikin tsakiyar kansa yake jin wani irin yanayi mara misaltuwa, a ɓangarenta itama hakan ne, wani irin baƙon yanayi take ji. "Me yasa kika ce haka my heartbeat?" Yana magana yana kallon face nata sosai, nisawa ta yi kafin ta fara magana a nitse, "Naga ko rabin ka ban yi a kyau ba, kuma gaka kai Bature ne, wadda ya fito cikin kyawawan fararen turawan, wadda farinsu babu ko miss, idan muka tashi kwatance kyau a nan cewa muke yi kyakkyawa kamar baturiya, saboda kyanku yasa kuke bamu sha'awa, amma duk da haka ka tsallakesu kazo har Nigeria, Nigeria ma Kaduna, ka ce ni kake so, ni fa a haka fara ce a gidan mu, ko in ce a danginmu, amma yanzu kallah da na zo kusa da kai, na dawo baka, hasken ka ya dishashe nawa, wannan dalilin yasa naji zuciyata ta karaya, na ji anya kuwa ba mafarki nake yi ba? Ko kuma wasa kake yi mini ba, sannan bugu da kari, ga kuɗi mulki kai komai ma kun haɗa, dan Allah Heartbeat ka gaya mini gaskiyar me kake so a waje na? Ni nasan ba soyayya bace ta kawoka waje na, zuciyata ta tsorata wlh". Ta kai karshen maganar hawaye na zuba daga idanunta. Shiru ya ɗan yi kafin ya jingina da jikin motar tare da lumshe dara daran brawn eyes nasa, hakan yasa dogayen eyelashes nasa suka kara bayyana, zuba mishi idanu ta yi tana hawaye tana jiran amsa daga gare shi, kun sani na sani har ga Allah tana bala'in kaunar shi kafin ta san waye shi, ganin shi ido da ido yasa ta ji zuciyarta ta karaya, a nata ganin ya fi karfinta, sai dai idan wani abin kawai yake so da ita, dama jira take ta tabbatar da shi ɗin ne, to yanzu ya kawo mata kansa, ta tabbatar da yes shi ne, a zahiri ma yafi kyau fiye da hoton, duk da hoton ma tun yana ɗan 20 years ne, ta ruɗe da kyansa sosai, kuɗi, kwarjini, shiyasa take ganin kamar ba son gaskiya yake yi mata ba. Almost 10 mins suna a haka, a hankali ya duƙo da kansa yana kallonta, ita ma shi take kallo, ya rasa da wani baki zai yi mata magana, mai da kallonsa izuwa kasa ya yi, da yake unguwa ce ta manyan mutane, titi har cikin unguwa, ga titin fes babu datti, hakan yasa ya zube gwiwowinsa a kasa a gabanta, duk wanda ya san turawa yasan yin hakan ɗabi'arsu ce, su zube gwiwowinsu a kasa dan bayyanar da soyayyansu. A razane ta koma baya ganin ya zube gwiwowinsa a kasa a gabanta, duk da tasan ɗabi'arsu ce yin hakan, ba wani abu bane, amma sam bata yi tsammanin haka daga gare shi ba, dan a nata tunanin bata kai wannan matsayin ba, bata kai ya zube mata gwiwowinsa a kasa ba, duba da irin tarin dukiya da suke da shi, ita kanta Rimsha da ta san halinsu ta girgiza ganin ya zube gwiwowinsa a kasa, ta razana ainun, bata taɓa tsammanin hakan daga gare shi ba, ko a mafarki, bata san lokacin da idanunta suka washe ba, gabaɗaya barcin cikinsu ya gudu, zaro idanun nata ta yi tare da matsowa jikin glass ɗin motar sosai tana kallon wanan abin al'ajabin, yau ga ɗaya daga cikin TRIPLETS na THE GENERAL OF THE ARMY ya zube a kasa a gaban mace, ina ma wannan abin a Washington DC ta faru, da gabaɗaya gari ta ɗauka izuwa yanzu. "My Heartbeat trust me, from the button of my heart nake sonki, serious babu wasa, ni bana son turawa, ke Allah ya zaɓa mini, kin san cewa ko TRIPLETS na ban gaya musu ina sonki ba, dama nace sai nazo Naija zan gaya musu, amma zumuɗin in zo in ganki ido da ido ya hanani tsayawa na basu lokaci na, muyi hira har na gaya musu, uncle Hosain kaɗai na gayawa, kuma shi ne ya kara mini confidence a kanki, he told me that ke ƴarsa ce, ƴar yayansa, kina da farar zuciya, zaki iya tambayarsa, da gaske nake sonki, yasan komai, please stop doubting a kai'na, kiyi hakuri ki yarda dani, ni bana karya, duk abin da nayi miki a baya na gaya miki dalilin yinsa, kuma idan da bana sonki ba zan ɓata lokaci na wajen zuwa in da kike ba, saboda ke na haɗa Exams uku a lokacin guda nayi, kuma ba rana ɗaya za'ayi su ba, ni ne nace dole a bani nayi a rana ɗaya, dan nayi miki alkawarin zan kawo miki kai'na yau, bana son saɓa miki alkawarin dana ɗauka miki, Shiyasa nayi hakan, ko kaɗan banji daɗi ba da zuciyarki ta fara tunanin ko ba da gaske nake sonki ba, please ki gaya mini wasa kike yi kinji ko?". Ina ta kasa magana, har lokacin ganin abin take yi tamkar a mafarki, ta kasa yarda da abin da take gani, ji take yi tamkar ta gudu ta koma cikin gida, dan ta tsorata sosai. Ganin bata yi magana bane yasa ya ɗan rarrafo da gwiwowinsa a kasa, ya matso kusa da ita, hannayenta ya riƙo cikin nasa, a wannan karon a shagwaɓa ya yi magana, "Please My heartbeat talk to me now, zuciyata tana bugawa da sauri sauri, ji nake yi like zan mutu, i need your amsa now please". A hankali ita ma ta zube gwiwowinta kasa a gabansa, cikin sanyin murya ta fara magana "Already you knew that i really love you, wadda zata soka ba tare da sanin waye kai ba, ita ce masoyiya ta gaskiya, sanin waye kai a yanzu ne ya girgiza ni, ya sa naji tamkar matsayina bai kai a soni ɗin ba, amma ka dai'na tunanin zan dai'na sonka, never wlh, because kai ne first love ɗina". Rimsha dai ta mai da su Tv, sai kallonsu take yi gwanin burgewa, da yake anguwa manya ne, babu mutane, kowa yana harkan gabansa, sai ɗai ɗai kun motoci dake wucewa lokaci zuwa lokaci. "Yanzu you trust me ko?" Jinjina mishi kai ta yi alamar e, saboda tsabar daɗi bai san time da ya matsa hannayenta dake cikin nashi ba, sai da ya ji ta ambaci wash ya farga tare da ɗan sassauta riƙon da ya yi musu. Kada ku manta fa, ita Akila a ɗaukarta da Areef take magana ba Aseef ba, bata ma san Aseef ɗin ba, ya kenan idan ta san ba wanda take tunani bane kuma? Mu dai je zuwa, Areef Rimsha ta yaba mata kyawawan halayensa ba Aseef ba. Miƙewa tsaye ta yi tare da jan jannunsa dake cikin nata sama, alamar ya miƙe shi ma, ba musu ya miƙe tare da ɗan duƙawa yana kakkaɓe mata ɗan kuran da ya hau saman skit nata wajen da ta duƙa, ita dai har yanzu mamaki take yi, bata san cewa yes yadda take ganin turawa a Tv wajen kula da soyayyansu da abin da suke so hakan suke a zahiri ba, ta ɗauka a iya Tv ne, bata san a zahiri ma hakan suke ba, in dai suna son abu, to suna bashi tsantsan kula da iya iyawarsu. Sai bayan ya kammala kakkaɓe mata ya miƙe ne ita ma ta ɗan duka ta goge mishi wajen gwiwowinsa daya zube su kasa, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, har da sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya ya yi lokacin da ta fara kakkaɓe mishi. Bayan ta Kammala ta miƙe tsaye suna fuskantar juna, ganin ta kafe shi da dara daran nan nata na gado ne yasa ya ɗan kyasta mata yatsunsa guda biyu a saman face nata, ɗan runtse idanun nata ta yi tana murmushi. "Kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa". Ya faɗa yana murmushi, ita dai har yanzu bata yarda ba, idan ya ce ita kyakkywace, dan tana ganin ai daga cikin ƴan uwansa Turawa ya fito, a wawtarta da shirmenta, tana ganin daga kan turawa kyau ya kare, bata san cewa a ko'ina akwai kyawawan gaske ba, kamar dai ita ɗin, sai a tara turawa 50 ba'a a sami mai kyanta a cikinsu ba, hasken fatar kawai zasu fita da shi, kyau kam iya kyau Allah ya zubawa jinin Dr Salman da barrister Naurat, Ba fulatani da Baturiya, ya kuke tunanin haɗin zai fita, ai kunga suma madaran kyau ne a wajen. Turo ɗan bakin nan nata kamar biro ta yi, cikin shagwaɓa ta ce "Ni Heartbeat ka dai'na ce mini kyakkyawan nan, dan nasan kawai kana faɗa ne dan ka ji daɗin bakin ka". Shima turo mata ɗan bakin nasa ya yi, tare da shagwaɓe murya "No serious nake gaya miki, you are so very gorgeous more than your expectations wlh". Shiru kawai ta yi ba dan ta yarda ba. Sake kyasta mata yatsun sa guda biyu ya yi a fuska "Ga fa goribar ki a mota, na sanya Areef ya nemo mini tun kafin nazo, shi kuma ya sanya Prof ya nemo, a takaice dai ga shi nan na kawo miki, amma me ake yi da shi?". Jim ta ɗan yi tana maimaita sunan Areef, idan bata manta ba, idan kuma ƙwaƙwalwarta ya bata daidai sunan Areef Rimsha ta kira wadda ta ambata a matsayin masoyin ɓoye, to amma me yasa yanzu kuma ya ce ya sanya Areef ya memo mishi goriba, to shi kuma waye? Ko dai su dukka sunansu Areef Areef ne? Abin ya ɗan ɗaure mata kai. Shi kuwa bai lura da yanayin da ta shiga na tunani ba, sai hira yake yi mata. "My heartbeat dan Allah yanzu zaka iya gaya mini sunanka?" Ta tambaya tana mai da kallonta kasa. Kai tsaye ya ce mata Aseef, maimaita sunan ta yi, sai ta ji da Aseef da Areef ai ba banbanci, hakan yana nufin ita ce bata ji sunan da Rimsha ta kira da kyau bane koyaya ne? Ta sake shiga ruɗu, sunan sunzo kusan iri ɗaya, wai me yake faruwa ne? Ta kasa gane komai. To fa Akila ta kasa gane komai, shawara kawai ki bisu a duk yadda suka zo miki, idan ma kin gansu dukkansu biyu, duk sunan da yazo bakinki, in ma Aseef or Areef duk maka musu kawai, ai dole su amsa tun da suka rikita mini ƙwaƙwalwa, Allah sarki Baiwar Allah sai ma kin gansu su biyun da black glass, a nan ne zaki yi ainahin rikicewa, a dai Nigeria idan ba Rimsha da Imran ba, ba mai iya banbanta su.......🤣 Ita ma Rimsha Allah ne kaɗai yasan baiwar dake gareta, yasa take iya banbantasu, shi kuma Imran ya sansu tun ba'a kai haka ba. "Heartbeat Ammie ta ce kada na jima, zan koma gida ba dan ina son rabuwa da kai ba, sai dan kada na tsallake maganar mahaifiyata, ka kula mini da kanka, zamu yi waya ko? Yanzu ai zaka dai'na ɓoye mini number ko?". Jim ya ɗan yi kafin ya wuce ya buɗe bayan motarsa ya fito mata da kwalin goribarta da kuma kawatin da ya yi mata tsaraba, already Rimsha ta jima da yin barci abinta, kwata kwata Akila bata san cewa tare yazo da Rimsha ba, shi kuma hira ta yi daɗi ya manta ya gayawa Akila ɗin tare suke da Rimshar. "Heartbeat ya kamata ka je ka gaida Ammie fa idan ka sake zuwa". Yana jawo akwatin zuwa gabanta ya ce "Okey zan je idan na sake zuwa, yanzu dai ga kayanki, zaki iya ɗauka ne ko dai na kai miki ciki?". Kada ku manta duk maganar da suke yi cikin harshen turanci suke yinsa, sannan karin wani haske, kada ku manta da Naurat da Dr Salman da farko a kasar Russia suke zaune, a can a ka haifi su Abba, to suma basu jin hausa sai da suka dawo Nigeria, hakan yasa su Jehan babu hausa a bakinsu sosai, dan iyayen nasu ma basu cika yin hausar ba, to suma su Akila turanci ya fi zama a bakinsu sama da Hausa, amma kuma sunfi kaunar yaren Hausa sama da turancin, shiyasa suke magana da Hausar idan suka haɗu da su Aafia, dan sun ce Hausa tafi musu ko wace yare a duniya, a takaice dai family'n Dr Salman duk gayyan ƴan yin turanci ne, na yi muku bayani ne dan kada ku ce to a ina suke jin American English da suke magana da TRIPLETS, to suma tushensu dai English ɗin turawan ne, shi suka iya, fatan kun gane?. Da sauri ta buɗe kwalin goribar dan ta tabbatar da gaskiya, tabbas kuwa goriba ce da aduwa very fresh a ciki, gwanin ban sha'awa, ɗagowa ta yi tana kallon shi, while shima ita yake kallo. "Me ake yi da su My heartbeat?" Ya tambaya yana zura hannu a cikin aljihun wandonsa. "Ci ake yi". Waro dara daran brawn eyes nasa ya yi yana kallon goribar, maimaita kalmar ci ya yi a filli, jinjina mishi kai ta yi tana mai tabbatar mishi da ci kuwa. Hannu ya miƙe mata, a kan ta bashi guda ɗaya, bari ya ci ya ji, shi da abincin Nigeria mai shegen daɗi da Musharraf yake girkawa a Washington DC ma, ya kasa ci bare kuma goriba. Da farko kin bashi ta yi, sai da ya fara zuba mata shagwaɓa kamar zai yi kuka, sannan ta ɗauko goriba ɗaya aduwa ɗaya ta miƙa mishi, karɓa ya yi tare da kaiwa bakinsa da nufin ya gutsiri goribar, dan a wanke take kuma tana cikin leda kafin a sanyata cikin kwalin, sannan a cikin fridge Areef ya sanyata, a tunaninsa fruits ne kamar irinsu Apple, shiyasa ya sanya Mark ya wanketa tas, aka zuba a leda sannan aka sanya a cikin fridge ɗin, wai dan karta ruɓe kafin Aseef ɗin yazo. (Wayyo cikina, goruba yaga gata, har da fridge 🤣 Wayyo rashin sani yafi dare duhu🤣🥱) A tunaninsa laushi take da shi kamar apple, sai da ya kai bakinsa sai ya ji abu kamar dutse, da sauri ya fitar yana furta subhanallah, ya tsuke ɗan bakin nan nasa, tare da haɗa geran sama da ta katsa, tsabar dariyar mugunta Akila bata san lokaci da ta yi baya tana ƙoƙarin faɗuwa ba. Bata kai ga faɗuwa ba ya yi maza ya riƙo hannunta ɗaya, har lokacin yana tsuke da ɗan bakin nan, ya je ya gabtari dutse ta kusa cire mishi hakwara a cewarsa, gata da shegen bauri kamar me, bai yi Sa'a ba, ya sami mai bauri a maimaikon zaki, tufarwa ya fara yi yana goge bakinsa da hannunsa, har lokacin sai dariya take yi mishi. A shagwaɓe ya ce "Heartbeat stop laughing for me now". Yadda ya yi maganar ma, dariya ya kara bata, har da sanya hannu ta dafe cikinta saboda dariyar. Turo ɗan bakin ya yi yana ƙoƙarin saka mata kukan shagwaɓa, cikin sauri ta tsayar da dariyar tana faɗin "Am so so sorryyyyyyyyyy my heartbeat". Turo ɗan bakin ya karayi sosai, bai ce da ita komai ba, sai aikin zubar da yawu yake yi, tana son ta yi dariya, tana tsoron rigimarsa kuma, haka ta danne ta yi shiru suka yi sallama, ba dan sun so rabuwa da juna ba, sai dan kada Ammie ta yi faɗa. Har bakin gate ya ja mata trolley tsarabar da ya yi mata, ya kai mata, ita kuma ta ɗauki kwalin goribarta,. A bakin gate ɗin ma tsayuwa suka yi na ƴan mintoci da a kallah zasu kai 20 haka, kwata kwata basu son rabuwa da juna, umarni ya yi wa mai gadin a kan ya shigar mata da trolley da kuma kwalin goribar dukka cikin gida, hannayenta dukka biyu ya riƙo cikin nasa, abin ku da turawa, su yin hakan a wajensu ba wani abu bane, anyi sa'a ma da bai ce zai rungumeta ba, ita ma kuma bata hana shi riƙe hannayen nata da yake yi ba, ta biye mishi kawai, dan tana ganin ba zai wuce yin hakan ba, a iya hannu kawai zai tsaya. Cike da kulawa da tsantsar kaunarta ya fara magana "My heartbeat zan yi kewarki, ji nake yi tamkar ba zan iya wannan rabuwa da zamu yi ba, ni gaskiya ba zan iya jimawa sosai ba, tun da nazo Kasarku kafin mu koma ayi mana aure kawai, ki gayawa daddynki, zanzo na ganshi, ya saka mini lokaci, amma kafin nan zan yi magana da Pleasures ɗina". Kasa ta yi da kanta tana amsa mishi da okey, gabaɗaya ta koya mishi kunya, a wajenta ya koya, har yake jin kunyar TRIPLETS nasa. Daga haka ya saki hannayen nata tare da binta da idanu har ta shige cikin gida, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya zuwa wajen motarsa. Lokacin da ya shigo cikin motar Rimsha sai zuba barcinta take yi kamar ba gobe, ƴar murmushi ya yi tare da shafa lallausan kyakkyawar gashin kannan nasa yana furta mata kalmar sorry kasa kasa. Cikin natsuwa ya tada motar ya nufi gida, lokacin yamma ta yi sosai, almost karfe 6. Lokacin da suka koma gida, Imran da jelly sun dawo, Areef yana zaune a saman ɗaya daga cikin kujerun shan iska dake wajen pool na gidan, Lion yana cikin bedroom nasa, haka suma Imran da jelly ɗin, suna cikin bedroom nasu, sai iya shege kala kala jelly ke zuba mishi, bawan Allah shi kuma sai biye mata yake yi, dan ba yadda ya iya da ita. Bayan ya yi parking na motar ne ya juyo da kallonsa a kanta, a hankali ta fara motsawa kafin ta buɗe dara daran sleeping eyes nata masu ɗauke da barci, ganin su a gida yasa ta juyo gefe dan ta ga a ina take, karaf suka yi idu huɗu, cool murmushi ya sakar mata yana furta kalmar sorry, murmushi ta mai da mishi ita ma kafin ta ce "Yaya Aseef am waiting for you ne fa, ina son ka gama magana da Aunty Akila, i wan to talk to her, amma shi ne ka dawo dani gida bamu yi magana ba ko?". Ɗan kama kunnansa ya yi yana mai kara maimaita mata kalmar sorry tare da ɗaurawa da gobe zai kaita ai kada ta damu, okey ta amsa mishi da shi kafin ta buɗe kofar motar ta fito waje. Shi me fitowa ya yi tare da nufar wajen pool ɗin dan ya hango Areef a wajen, ita kuma cikin gida ta nufa, dan ta je wajen Imran duk da cewa ba wani shiri sosai suke yi da jelly ba, jelly na kishi da ita, da farko suna zaman lafiya, daga baya da ta fahimci Imran yana bawa Rimshan kulawa sosai, duk wani motsi idan ta yi sai ya tambayeta me take so, tun daga nan jelly ɗin ta fara kishi da ita, ta ja baya da ita sosai, idan ma Rimshar na yi mata magana bata cika wani amsawa ba, sai tayi kamar bata ji ba, hakan yasa Rimshar bata cika shiga harkan ta ba, bata son ma su haɗu sai idan ya zama dole, dan ba zata iya masifar jelly ba, kuma koba komai jelly ta girmeta, ta bata a kallah shekaru 2, sa'ar jehan ce ita, shiyasa bata biye mata, kuma ita Rimsha dama bata iya faɗa ba, bata iya masifa ba, ita dai a barta da soyayya kawai, shi ta fi iyawa, shima ɗin Akila ke kara koya mata. ASEEF Da sauri ya karisa ya rungumi ɗan uwan nasa yana faɗin ya yi kewarsa, ture shi Areef ɗin ya yi yana faɗin "Sai yanzu ne kayi kewa na ɗin ko? Tun ɗazun baka yi ba wato? Tukun nan ma ina ka je? Ina ne mai mahimmancin da ya fi maka zama tare da mu a ranar da kazo, bayan kasan muna kawarka sosai? Koma inane ba zaka iya hakura sai gobe ba ko? To yau munyi hannun riga". Ya kai karshen maganar yana mai da kallonsa a kan wayarsa da yake latsawa. Shiru Aseef ɗin ya ɗan yi, yana tunanin abin da zai gaya mishi da zata sanya shi dariya, yasan bai kyauta ba, yasan suna kewarsa sosai da sosai, amma haka ya tsallakesu ya tafi wajen Akila, ya kasa hakura sai gobe ya je ya ganta, kuma da ya je ya kasa barin wajen nata da wuri, da farko ya yi niyar idan ya je ba zai wuce ya yi minti 30 ba ya dawo, sai kuma gobe ya je su ga juna da kyau, amma ya je ya yi almost 2 hours a wajen nata, sam ba haka ya so ba, yanzu haka yasan Lion ma bai ji daɗi ba, dan yasan shi ne bugun zuciyarsu, kuma farincikinsu. "Wlh Areef she is gorgeous". Ya faɗa yana murmushi tare da goya hannayensa a saman kirjinsa. Da sauri Areef ɗin ya miƙe yana faɗin "Who is she please?". Wani kallon gefen ido ya wurga mishi dama yasan idan ya kawo wannan zance ɗan uwan nasa zai sauƙo. "Wlh she is gorgeous". Ya sake maimaita maganar ta ɗazun. Cikin zumuɗi ya sake tambayarsa wace ce kyakkyawar, kuma a ina take, son ta yake yi ne ko ya ya. Kara faɗaɗa murmushin nasa ya yi kafin ya sake cewa "Wlh she is gorgeous". Ɗaure fuska sosai Areef ya yi dan ya fahimci iskanci sabo Aseef yake ji da shi, zai wani tsaya yana gaya mashi she is gorgeous, to waye gorgeous ɗin an tambaye shi yana ta kara maimaita magana ɗaya, ga shi shi kuma a ƙage yake da ya ji wace ce wannan da Aseef yake yabonta haka. "Aseef ban son iskanci fa, i said who is she ko? Tun ɗazun sai maimaita magana ɗaya kake yi, she is gorgeous, she is gorgeous, to na gaji da jin hakan". Cigaba da murmushinsa ya yi yana faɗin "Wlh she is gorgeous". Areef ya zo har wuya, a fusace ya ɗaga hannu zai kai mashi duka, kaucewa ya yi yana faɗin "Haba mana, kai fa mugu ne, na ce maka wlh she is gorgeous, my cow da na saya jiya a Washington DC mana, wadda Saif ya ce kada a kawo mashi gida, kada na kuskura na zo da ita kasarnan, to ita ce kyakkyawar". Wani irin harzuƙa Areef ya yi, a guje ya raka shi dan ba zai kyale shi ba, shima da gudu ya wuce zuwa cikin gida, kai tsaye sai bedroom na Lion. Yana zuwa ya faɗa saman bed yana dariya har da riƙe ciki, idan ya tuna yadda Areef ya ɗaure fuska dan ya ji shanuwa ce kyakkyawar ba abin da yake zata ba, sai ya kara tuntsurewa da dariya. Saif yana zaune a gefen bed ɗin, jikinsa na sanye da farar jellabiya, ya ɗaure gashin kan nan nasa, fuska dai kamar kullum, a fusace, a ɗaure tamau, tamkar hadari, yau dai rubutu yake yi a cikin wani takarda mai girman gaske, mai kama da diary, sai tashin fitinannen daddaɗar kamshi perfume ɗin nan nasa yake yi, ko kallon in da Aseef ɗin yake bai yi ba. Shi ma Areef yana shigo kan gadon ya faɗa yana faɗin, "Allah ka tashi muje ka fara frog jump dan ba zan kyaleka ba". "Ni ban iya frog jump ba, amma tun da Lion ya iya zai karɓa mini tun da ni pleasure'nsa ne, ba zai bari na sha wahala ba". Yana magana yana turo baki, jan gashinsa da karfi Areef ɗin ya yi kamar yadda Lion yake yi mishi shima. A shagwaɓe ya sa ihu yana turo baki tare da kumbura kumatu, ko sannu Lion bai ce musu ba, ganin bai kula su ba yasa Areef hakan bata yi mishi ba, dan ya fi son yaga yana takurawa Lion ɗin sosai, yana sanya shi yin magana. Sakin Aseef ɗin ya yi, ya koma kusa da Lion ɗin dan ya saka shi magana, shi baya son ya ga ɗan uwan nasa yana zaune shiru, ya fi son yaga yana sanya shi magana ko ba yawa. "Lion wai ya batun bed guda ukun nan ne? Ka sanya a zo a zuba mana su a nan mana, dare fa yana yi". Ko sannu bai ce mishi ba, dan wlh ba zasu zauna mishi a ɗaki ba, yanzu ma ya yake karewa da su bare kuma a ce sun dawo ɗakin, ai hawan jini zasu saka mishi, yasan ko zai mutu sai sunyi ta saka shi magana. Shima Aseef miƙewa ya yi ya dawo ɗayan gefen ɗan uwan nasa, suka saka shi a tsakiya kamar masu shirin bashi shawara mai mahimmanci, har lokacin bai ɗago ya kallesu ba, Allah ne kaɗai yasan abin da yake tunani da kuma abin da yake cikin zuciyarsa, duk yadda suke da saboda da Lion ba zaka taɓa gane ina ya dasa ba, ba zai taɓa baka wani sign da zai nuna maka alamar in ya dosa ba, sai dai kai kayi ta hasashe dan kanka, harta su dad nasa hasashensa kawai suke yi a kansa, ɗan gara ma Triplets ɗin nasa, suna iya cankan abu daidai a kansa, yanzu haka sai Allah kaɗai yasan me yake rubutawa, ko sun duba ma, ba zasu gane kan zancen ba, tun da ba littafi ne karami ba, shiyasa basu sha wahalar duba abin da yake rubutawa ɗin ba, ga shi da shegen good handwriting kamar computer, ga bala'in iya rubutu da sauri, kafin su karanta layi ɗaya, ya sake rubuta wani layi ɗayan ya wuce wajen. A ɓangaren Rimsha kuwa, kofar ɗakin Imran ta nufa, da sallama ɗauke a bakinta ta tsaya a bakin kofar tana jiran izinin shigowa, daga ta cikin ɗakin jelly ta amsa mata da "To ƴar anace, yaya Imran yana wanka, idan kina son yin magana da shi, sai ki jira shi a waje ai". Ta kai karshen maganar tana jan tsaki. Har cikin zuciyarta maganar ta yi mata zafi, kuma hakan ma kaɗan ne daga maganganun da jelly ɗin ke gaya mata, yanzu ma da tasan baya cikin ɗakin ba zata je wajen ba, dan tana jin zafin maganganun jelly sosai, kuma kunsan halin jelly, number 1 ce a rashin kunya. Rai a ɓace ta juya ta koma cikin ɗakinta, tason ta yi magana da Imran akan zuwa gyaran gashin nan nata, dan kan nata na damunta, ta kuduri niyar ba zata sake zuwa wajen Imran neman wani abin ba, dan tana zargin da gangan ɗazun jelly ta ce mishi lallai su je gidan Abbi, dan kawai ta ji yace zai kai Rimshar gyaran gashi, shi ne ta bijiro da nata dan kada a kai Rimshar, ta yanke wa kanta hukunci zata rinƙa fita da kanta ta je tunda yanzu ta yi free, zata tambayi Akila sunan anguwar da ake gyaran gashin dan ta rinƙa kai kanta da kanta kawai zai fi mata. Tana shiga bedroom nata zuciya cike fal da tunani, toilet ta wuce dan ta yi wanka, bayan ta kammala ta shirya cikin ɗaya daga cikin ɗinkunan da Imran ya yi musu, dogowar riga ce ɗinki ya zauna mata sosai a jikinta, fesa perfume nata ta yi tare da ɗaukar wayarta ta nufi garden na gidan. Tana zama cikinta ya fara kukan yunwa, shiru tayi tana sauraron yadda cikin nata ke ƙu,lu,lu,lu, wato kuman yunwar kenan, tunani take yi a irin rayuwar da zata shiga yanzu kuma, ji take yi tamkar ta roƙi Areef yasa a mayar da ita kusa da daddynta, ko kuma ta koma gidan Akil, wani ɓangare na zuciyarta ne ya bata amsa da ita ma Umaisha kishi take yi da ke ai, tamkar zata yi kuka tuna hakan da ta yi, a kule ta ce wai me yake faruwa da ita ne? Ko wace mace sai ta ce tana kishi da ita, to ita tace tana son mazansu ne? Abin gwanin ban tausayi, can wani ɓangare na zuciyarta ya tuna mata to ko dai ta koma gidan Abbi ne?, Nan ma ɗayar ɓangare na zuciyar tane ya bata amsa da anya zata iya yin nisa da Saif kuwa? Anya zata iya jure wuni guda ba tare da ta ganshi ba kuwa? Anya hakan zai yiwu kuwa? Bama Saif ba, shima Areef anya zata iya rabuwa da shi kuwa?, Tuna hakan yasa ta fara ruwan hawaye, ga yunwa, ba wadda zata iya gayawa tana ji, yaya Imran ne kawai, shi kuma yanzu jelly ta yi musu tsakani. Tana cikin wannan hali sai ga jelly da Imran sun nufo garden ɗin, sunci kwalliya, Imran na sanye da kananan kaya, wato wandon jeans baka da t-shirt blue, ita kuma jelly riga da skit ne a jikin nata, skit ɗin ruwan kasa da ratsin fari, riga fari, kayan sun ɗan kamata, amma ba sosai ba, ba karya sun yi kyau sosai, yau Imran ya sanyata dole sai ta saka ɗankwali a kanta, hakan yasa bata ji daɗi ba, sai turo baki take yi, ita a dole ta ji haushi. Ganin su yasa ta yi saurin goge hawayen fuskarta tare da ƙaƙalo murmushi dole dan kada Imran ya gane komai, tasan yana yi mata iya iyawarsa, baya bari ta shiga kunci, yanzu ma duk abin da yake faruwa tsakaninta da jelly bai da masaniya a kai, idan ya sani zai ɗauki mataki, ba zai bari hakan ta cigaba da faruwa ba, idan baku manta ba, kunsan jelly da iya makirci da kirsa, to bata yi wa Rimsha abu a in da ta san Imran ɗin zai gani ko kuma ya ji, sai ta faki idonsa take tsula tsiyarta, ɗazun ma da yake toilet ta yi wa Rimsha wannan maganar, ta san cewa ruwa na zuba, karar ruwan ba zai bari ya ji maganar ba, shiyasa ta yi. Ganinta a garden ɗin yasa shi sakin kayatatcen murmushi yana faɗin "Rimsha yaushe kuka dawo?" "Yaya Imran yanzu ba jimawa muka dawo". Kusa da ita ya zo ya zauna "Ai mun dawo daga gidan Abbi na tambayi Areef ina kike, sai ya ce mini kun fita ke da Aseef, fatan dai kun dawo lafiya?" Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "Lafiya lou Alhadulillah". "Kina jin yunwa ko?" Ɗan satar kallon Jellyn ta yi kafin ta gyaɗa mishi kai alamar e "Am so so sorryyyyyyyyyy, gaskiya rayuwar gidan nan akwai wahala a gareki, ke baki iya cin abincinsu ba, su kuma basu son warin naki, ni kinga na iya cin abincinsu dan a kasarsu nayi karatu, amma ba komai ai kwanaki kaɗan ya rage mana a nan ɗin, zaki jure ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e. "Good to tashi ki ɗauko mayafinki mu je gidan Akil a tare, tun da dai ke kince baki son abincin restaurant, ai aiki ya gammu da yawon zuwa gidan Akil ko gidan Abbi ɗaukar abinci". Ɗan motsa lallausan lips nata ta yi tamkar wadda take son yin murmushin, nan take dimple nata dukka biyu suka lotsa, wani irin fitinannen kyau na ɗaukar hankali ta kara, tana ƙoƙarin mikewa ta nufi cikin gida dan ɗauko mayafin nata, sai ga Aseef da Areef sun jero tamkar wasu taurari, sai walwali suke yi, Lion ya gaji da surutunsu ya haɗasu da Allah su fita mishi a ɗaki, sanin girman Allah yasa suka hakura suka kyale shi ya sha iska, ba dan haka ba, yau ba zasu rabu da shi ba. Har wani daddaɗar nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe ganinsu, ta rasa me yasa take jin tsantsar farinciki idan ta gansu, ta rasa me yasa take jin duk wani damuwarta ya gudu da zarar ta yi tozali da kyawawan fuskokinsu masu ɗauke da annuri ta murmushi. A ɓangaren shima Areef, ganin ta a wajen yasa ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya da ta sanya Aseef juyowa yana kallon shi. Gefenta ya je ya zauna shi kuma Aseef ya zauna a wani kujera na daban, ita kuma jelly tana ta faman kumbura kuma tu, ita a dole ta ji haushin kula Rimsha da Imran ya yi. "Our Queen me yake damunki? Waye ya taɓa mana ke?". Cewar Areef, da kallo ɗaya ya yi mata abinku da jami'i, tuni ya fahimci akwai abin da yake damunta. Ɗan zaro idanu Imran ya yi yana kallonta, har lokacin kuma shi dai bai ga alamar wata damuwa a face nata ba, shi ma Aseef da kallo ɗaya ya yi mata ya ga damuwa kwance a cikin idanunta, da yake idan baku manta ba, Triplets akwai baiwa, akwai kwakwalwa, sun gaji brain wajen Dr William jacop. "Yaya Areef babu abin da yake damuna fa". Ta yi maganar tana kara ƙaƙalo murmushi a kan fuskar tata, dan ta tabbatar musu da babu komai ɗin. Kallon Areef Aseef ya yi while shima Areef ɗin shi yake kallo, daga bisani suka juya suka kalli Imran wadda shima ya tsaresu da ido sosai, yana kallonsu, yana son sanin me yake damun kanwar tasa. "Yaya Imran mu tafi ɗaki barci nake ji" muryar Jelly ce ta katse musu shirun da suka yi suna tunani, kallonta gabaɗayansu suka except Areef, shi dawo da kallonsa a kan Rimsha ya yi, a nan ne kuma ya fahimci jelly ce matsalar gimbiyar tasu, domin kuwa wannan magana da jelly ta yi, ta sake jefa fuskar Rimsha cikin damuwa da tunani, fahimtar hakan yasa ya ɗan yi shiru yana tunani mafita, tabbatas ba zai taɓa yarda da duk wani abin da zai sanya Rimsha cikin ɓacin rai ba, zai yarda da komai a gidan amma ban da hakan. "Rimsha me zaki ci in sayo Miki". Cewar Imran, ya yi maganar ba tare da ya tanka maganar jelly da ta faɗa na su tafi ɗaki ba, sai dai bai gama rufe baki ba jelly ta kuma katse shi da su tashi su tafi ɗaki, ta yi hakan ne kuma dan kada Imran ya sahowa Rimsha abinci ko ya ɗauketa su fito, kishi kumallon mata, ko wace mace tana da shi, sai dai na wata ya fi na wata, ayi wa Jelly uzuri, ta ga hankalin yaya Imran ɗin ta na ƙoƙarin rabuwa biyu ne, ta ga yafi kula da Rimsha sama da ita da take matarsa, kuma take gani ita ta kasance kanwarsa, Rimsha kuma babu abin da ya haɗa su tun da bata ma san waye bappan nasu Hosain ba. "Jelly ki bari bari na je ya sayowa Rimsha abinci ko na ɗauko mata a gidan Akil, ki je ɗakin ki kwanta ina zuwa". Babu kunya bare tsoron Allah ta sa mishi kuka wai cikinta na ciwo, shi dai Areef binsu kawai yake da ido yana karantarsu, shi kuma Aseef ganin tana kuka yasa ya tambayi Imran ɗin menene matsalar, Shi Areef duk da baya jin Hausa, zama yau da gobe da su, yasa idan suka yi magana yana fahimtar in da maganar ta dosa, sannan kuma yana karantar yanayinsu, ta hakan yake gane a kan me suke maganar. Kanta Imran ya yi yana tambayarta ko lafiya, kuka take yi tsakaninta da Allah, hawaye wani na bin wani ta dafe cikin nata. A hankali Rimsha ta faki idanunsu ta miƙe tana son barin wajen dan kada zuciya ya ɗebeta ta kifawa jelly mari, dan kayan haushin jelly ya isheta, sanin halinta da zuciya yasa bata son haɗuwa da Jelly'n, dan bata son suyi faɗa a matsayinsu na ƴan uwan juna. Sosai Areef ya ji babu daɗin hakan, dan yasan Rimsha bata da wanda yafi Imran, shine farincikinta a yanzu, amma wata tazo tana kutse a tsakaninsu. Tana miƙewa ya riƙo hannunta, da sauri ta juyo duk da ta san shi ɗin ne, girgiza mata kai ya yi alamar a'a ta dawo ta zauna, ba musu ta koma ta zauna, shi kuma Imran ya ɗauki jelly a kan zai kaita ɗaki ya rarrasheta ya dawo. Suna barin wajen Rimsha ta fara hawaye, tana mamakin jelly yarinya yar karama da ita ko a ina ta koyi wannan banza hali na kirsa da makirci oho, ɗan riƙota a gefen kirjinsa ya yi, yana goge mata hawaye tare da bata baki, da mamaki cike fal ransa Aseef ya miƙe ya dawo kusa da su dan ya ji wai shin menene matsalar. Ɗan langwaɓar da kanta a gefen kirjin nasa ta yi tana mai jin bakin ciki a cikin zuciyarta, zama a gefenta a in da Imran ya tashi Aseef ya yi, fuskarsa ɗauke da damuwa ya fara tambayar me yake faruwa, ba ɓoye ɓoye Areef ya sanar da shi duk abin da ya fahimta, cikin sauri ta ɗago kanta daga gefen kirjin nasa, tana kallon face nasa, mamaki take yi waye ya gaya mishi abin da yake damunta, kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Kina mamaki ne? Ina kaunarki ai, dole na iya gane me yake damunki, kuma duk da bana jin yarenku, ina fahimtar akan me kuke tattaunawa, yanzu dai jeki ɗauko mayafinki muje wajen cin abincin, Aseef zai ja mota, Lion ba zai hanani fita ba, dama abin da yasa yake hana fita, dan ni kaɗai ne, kada na fita wani abin ya same ni, ko kuma na fama ciwona, yanzu Aseef yana nan, babu abin da zai faru In Sha Allah, kuma daga yau kada ki sake tambayar Prof wani abu, duk abin da kikeso, Aseef yana nan idan ni ba na kusa, kin ji ko?". Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e ta ji. "Yanzu nauyinki a kan mu yake, dole mu kula dake tamkar yadda zamu kula da kanmu, Aseef ɗauko makullin mota ka sanar da Lion zamu je restaurant, ke kuma jeki ɗauko mayafi". Kusan a tare suka miƙe Ita da Aseef ɗin, hannunta ya riƙo suka nufi cikin gida yana tambayarta shekarunta, 14 years 3 months ta bashi amsa, sai mamaki yake yi, ƴar karama da ita, lallai akwai kura. A palon sama suka rabu, ita ta shiga ɗakinta, shi kuma ya shiga ɗakin Lion. Jim kaɗan suka fito kusan tare, sake riƙe hannunta ya yi a cikin nasa yana faɗin "Wannan abin da kuke rufe jikinku da shi, ba karamin kyau yake yi muku ba". Sai murmushi take yi ba tare da ta yi magana ba suka nufi waje. A yadda suka bar Areef haka suka dawo suka same shi, yana ganinsu ya miƙe a kan su tafi, fitowa balcony ɗakinsa Lion ya yi dan yaga tafiyarsu, yana ji da ƴan uwan nan nasa over, har ga Allah bai so Areef ya fara fita yanzu ba, saboda jikin nasa da saura, amma shi kuma yana bala'in son yaga ya fita, ya son ganin cikin Naijan nan ya take, Hakan yasa Lion ɗin ya hakura kawai ya kyale shi su fita. Kiran Imran a waya Areef ya yi, ya tambaye shi a wani location restaurant ɗin da suke sayan abincin yake, ba musu ya gaya musu, bai kuma tambayesu me zasu je yi a can ba, dan yasan ba makawa Rimsha zasu je sayawa abinci. Kunna goggle map Aseef ya yi a wayarsa tun kafin su bar gidan, Rimsha ta so zama a gidan baya na motar, amma Areef ya ce lallai ta dawo gidan gaba su zauna a tare, shi kuma Aseef ya tukasu. Bata yi musu da shi ba, ta dawo kusa da shi ta zauna, duk abin da suke yi a kan idanun Lion suke yi, a kan idanunsa suka bar gidan, sai tsokanar Rimsha Areef yake yi, suna ta murmushi. Kai tsaye wajen wani katafaren restaurant suka shiga, suna parking suka fito kusan a tare, nan take kallo ya dawo kansu, kun san mutanenmu idan suka ga Turawa, sai kallonsu jama'a suke yi, su kuwa kwata kwata basu son wannan kallo da jama'a suke yi musu, dama kuma kunsan kallo bashi da daɗi ko kaɗan, idan mutun yana kallonka gabaɗaya sai ka tsargu, sai ka fara tunanin ko dai wani abin da bai kamata bane a jikinka yasa suke kallonka. Saman tsadaddun kujerun dake wajen suka zauna, nan take masu karɓar order suka nufo wajen nasu. "Rimsha ki basu order abin da kike buƙata". Cewar Areef, shi dai Aseef ya yi kasa da kai yana latsa wayarsa, da alama chatting yake yi da Heartbeat nasa. Daidai lokacin aka fara kiraye kirayen sallar mangariba, umarni Areef ya yi musu a kan su yi mata takeaway ne kawai su wuce da shi gida, mangariba ya yi, sai dai abin dariya kuma abin haushin shi ne, babu mai ko biyar a jininsu, kuma ba ta yadda zasu yi su yi wa masu restaurant ɗin transfer, ko da aka kawo musu takeaway ɗin da bill ɗinsu, kallon Aseef Areef ya yi, shi ma a lokacin ya ɗago kansa dan ya kalli ɗan uwan nasa, da wani kuɗi zasu biya to? Suka tambayi kansu da kansu a cikin zuƙatansu, ita ma Rimsha sai kallonsu take yi tana kankame da laidar takeaway ɗin nata abinta. Su kuwa masu karɓar kuɗi suna tsaye suna jira, dan kuwa ba zasu yafe ba, ice cream da suka sanyawa Rimsha ma kawai almost 10k bare azo kan saura abubuwa ga abinci. Dariya ne ya subcewa Rimsha lokacin da ta gane me matsalar, zuba mata idanu Areef ya yi yana kallon yadda take dariyar, ba ƙaramin burge shi ta yi ba, shi ma dai Aseef dariya abin ya bashi, wai su a dole sun zo sayan abinci, sun manta ba'a Washington DC suke ba. Babbar magana yanzu ya zasu yi? Su mayar da abincin ne ko yaya za'ayi? Ga shi ita kuma Rimsha ta kankame ledar ta abinta, jira kawai take yi su biya su tafi, har ta kotsa ta fara shan ice cream dake cikin, ga shi har da pizza ta ce a sanya mata........... ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E23-24 Suna a wannan hali sai ga Mark ya shigo cikin wajen, fusataccen fuskar nan tasa tamkar face ɗin shanu, yana sanye da wandon jeans black color da t-shirt maroon, faffaɗar kirjin nan nasa a buɗe irin na ogan nasa, tamkar wani zaki, ya sanya bakar glass a idanunsa, ba wasa a tattare da shi ka ɗigo, ganin shi ma kawai ya isa ya razanar da duk wata halitta mai rai. Kai tsaye in da suke ya nufo, cikin girmamawa ya gaida su tare da miƙawa masu karɓar kuɗin rafar kuɗi ƴan dubu dubu, wadda a kallah zasu kai 100k, ko basu tambaya ba sun san Lion ya aiko shi, dan idan ba Lion ba, ba wanda ya isa ya sanya Mark fita daga gidan, ya bar bakin aikinsa, dama tun da suka fita Lion ya kira Mark ya bashi kuɗi a kan ya bi bayansu da shi, dan yasan basu da ko biyar a jikinsu, kuma yasan ba ta yadda za'ayi su yi transfer, su sun mance da hakan, amma shi tsabar kauna da kuma kula da su da yake yi bai manta ba, yana ankare dasu, shiyasa ya yi musu hakan, dan kada wata matsala ta biyo baya, Areef kawai yake jiyewa, ciwon nan nasa, tun da suka fita yake jin wani iri a ransa, yadda Areef ɗin ke jijjiga jikin nan nasa, ciwon nasa na jijjika, to shi ma haka Lion ɗin yake jin wannan jijjiga a jikinsa, tamkar ciwon a jikin nasa yake ba Areef ba, ya kyalesu su fita ne dan su yi farinciki, tun da sun nuna hakan suke so, bai taɓa hanasu abin da suke so ba, sai idan ya tabbatar da in suka yi abin zasu cutu matuƙa, shi ne zai taka musu birki, ba dan yaso ba, sai dan kada su cutu. Tun da Mark ya miƙa kuɗin, Aseef ya riƙo hannunta suka nufi waje, shima Areef miƙewa ya yi ba tare da ya kalli in da Mark ɗin yake ba, ya bi bayansu. Motarsu suka shiga, da gudu Aseef ya ja motar dan lokacin sallah ya yi, da mugun gudu shi ma Mark ya fito ya rufa musu baya, da motar da yazo da ita. Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gida, saboda irin uban gudun da suke shararawa, dama idan baku mance ba, Aseef ya iya guduwa da mota kamar ba gobe. Suna yin parking ta fito ta nufi bedroom nata dan ta yi sallah, a tsakar gida suka yi karo da Lion da Imran zasu tafi masallaci, bin su Aseef da Areef ɗin suka yi, zasu je su yi alwala a can ɗin kawai. A palon sama taci karo da jelly, ko sannu bata ce mata ba, da alama ta rako Imran ne, ta kula da shi har ya fita dan kada ya kula Rimshar. (Kai jama'a Jelly duniya, wato har waje take rako Imran ta tsare shi dan kada ya kula Rimsha 🤣) Bedroom nata ta nufa, binta da kallon banza jelly'n ta yi bata ce da ita komai ba. Tana shiga bedroom ɗin nata, toilet ta nufa dan yin alwala, tare da ɗaura ledar takeaway ɗinta a saman bedside drawer. Bayan ta yi ta zo ta shinfiɗa dadduma ta tada sallah abinta. A ɓangaren gidan Akil kuwa, wasa wasa har shabiyun dare shiru ba Akil babu labarinsa, Umaisha tayi kuka ne har ta godewa Allah, sai uban haɗa zufa take yi, duk da sanyin Ac dake gudu a cikin ɗakin, ta jigata sosai, ta kuma kasa yin barci, a ɓangaren shi ma Akil ɗin ya sha bakar wahala, dan bai saba kwana ba tare da ya taɓa tula tula ba, tun ranar da ya yi aure har zuwa yau, ya kasa runtsawa, sai juyi yake yi a saman gadonsa dake bedroom nasa a gidan Abba, ya jigata sosai, kuma yaga massage ɗin Akila, ya basar ne kawai, irin shi zai daure ya yi koda sati ɗayar nan ne haka, amma ina kwana ɗaya ma ya kasa jurewa, da ya gaji da kwanciya zai miƙe zaune yana haɗa zufa, gabaɗaya ya rasa ina zai sanya ransa ya ji daɗi, daga karshe dai miƙewa ya yi tare da zura jallabiya ya ɗauki makullin motarsa ya fito palo. Babu kowa a Palon, kai tsaye waje ya nufa, su Ammie sun jima da yin barci abinsu, motarsa ya je ya shiga ya nufi gidansa. Lokacin da ya isa gida, tana zaune a palo sai kuka take yi, kwata kwata hawayenta ya dai'na zuba daga idanunta, sai shessheƙar ne kawai zaka ji, shi zai tabbatar maka da kuka take yi, amma hawaye kam ya dai'na zuba gabaɗaya. Tana jin tsayuwar motarsa, amma ta kasa tashi saboda wani irin jiri da take ji yana ɗebanta, hakura ta yi ta cigaba da zama a in da take har ya shigo cikin palon, da farko bedroom nasu zai wuce, jin shessheƙar kuka a palo yasa ya tsaya tare da kunna wutar palon, ya tsorata sosai ganin yadda har idanunta suka kumbura, bai yi zaton kukan da Akila ta rubuta mishi a massage take yi ya kai har hakan ba, ya yi zaton irin kukan kullun ne da ta saba yi mishi. Da sauri ya kariso in da take yana ambatar sunanta, "Wife! Wife". Kara rushe mishi da kuka ta yi, yana zuwa ya runhumeta yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi tare da zama a gefenta, ina ai sai da ta gan shi ne ma ta ji sabon kuka ya zo mata mai karfi, yi take yi yana rarrashinta, sai da ta bashi wahala kafin ta tsagaita da kukan, ɗaukarta ya yi suka nufi toilet, ko abinci bata ci ba, dan ta kasa ci ɗin, wanka ya fara yi mata kafin ya fito ya shiryata cikin kayan barci masu kyau, sosai ya yi nadamar abin da ya aikata, bai yi zaton zata wahala har haka ba, da yanzu cikin nasu ya zube waye gari ya wayanwa to? Ya tambayi kansa da kansa, dan yasan damuwa tana ɗaya daga cikin abin da take hana ciki zama a jikin mace. Bayan sun shirya da kansa ya rinƙa bata abinci a baki yana rarrashinta, a wannan dare dai basu suka kwanta ba sai karfe 3 na dare, sai lokacin suka gama duk abin da zasu yi, sai sauke ajiyar zuciya take yi, har lokacin sai kara rarrashinta yake yi, ba shi ya sami kwanciyar hankali ba har sai da ya ga tayi barci cikin kwanciyar hankali kwance a kirjinsa tana faman sauke ajiyar zuciya, a sannan ne ya samu natsuwa tare da yin addu'ar barci ya shafa musu ita da shi baki ɗaya. ASUBA TA GARI. GIDAN LION💋 Bayan ta yi sallar mangariba da issha, sai ta ɗauki abincinta ta fito palo dan taci tare da Aseef, shi ne abokin yin ta dama, kuma dama kafin su rabu ya tafi masallaci ta ce mishi idan ya dawo zasu ci abinci tare, okey ya amsa mata da shi, to shi ne yanzu zata je garden su ci abincin a tare idan zai iya. Duk da tasan babu kowa a garden ɗin, sai da ta tsara sallamarta irin ta addinin musulunci, tana sa kai zata shiga ciki, ita kuma jelly tana fitowa, karo suka yi, baya kaɗan ta yi tana ce wa Jellyn sannu, dan ita ce ta bugeta, rai a ɓace jelly ta ɗaga hannun zata mareta, dan dama haushinta take ji, kamar daga sama ta ji an riƙe hannun nata, Rimshar ta gama rintse idanunta gam tana jiran saukar mari sai ta ji shiru. A hankali ta waro dara daran fararen sleeping eyes nata a kan jelly, da mamaki take kallonta, cikin sauri kuma ta ɗan juya gefenta ganin jelly'n na kallon hannun nata, muryarta har rawa yake yi wajen furta "Yaya Areef". Yana tsaye ya rasa wani hukunci zai yi wa Jelly yau, ji yake tamkar ya murɗe hannun nata ya karye shi gida biyu, yau sai ta ɗanɗana kuɗarta, dawowansa daga masallaci kenan ya ce bari ya zo garden ɗin, dan yasan da wuya ba zai sami Gimbiyar tasu a wajen ba, yanzu a gabaɗaya gidan bata da wani wajen zama da ya wuci wannan wajen, shiyasa ya nufo wajen kai tsaye da fara'arsa, cike da kwarin gwiwar zai same zaune tana cikin farinciki, Aseef da Imran sun wuce ciki, shi Aseef ya je ya yi wanka ya sako kayan shan iska, dan ya ce zafi ta yi yawa, shi kuma Imran wajen Jellyn ya nufa, dan bai taɓa tunanin a wannan lokacin zai sameta a garden ba, ya fi zaton tana ɗaki, dan ita sarkin kallo ce, sai ta wuni a cikin ɗaki tana kallon film a Tv dake cikin ɗakin, bata wani cika fitowa waje ba. Sun kai almost 2 mins tsaye a wajen, ba ƙaramin razana jelly ta yi da ganin face nasa ba, tun da take da su a gidan sai dai taga wucewarsu, bata taɓa yin ido huɗu da su ba, kuma shi ma Areef dama da Rimsha kawai yake wasa da dariya har haka bayan TRIPLETS nasa da Imran, bai cika yiwa mutanen da suka zo baki magana ba, idan suka yi mishi magana, yana amsawa saɓanin Lion da ko kallon in da suke ma bai ishe shi ba, a takaice dai bata taɓa yin gaba da gaba da ɗaya daga cikinsu ba, sai dai bayansu take gani. Nan take ta sha jinin jikinta, tayi narai narai da ido, dan dama duk rashin kunyar mai rashin kunya sai dai idan bai yi ido huɗu da fusatattun fuskokin zakunan jikin William jacop ba, ga fuskokin nasu mai cike tap da bala'in kwarjini mai haukata mutane kamar me, ganin ya yi shiru bai saki hannun nata ba, bai kuma yi mata hukuncin da yake da burin ya yi mata ba, yana tunanin ya ɗaga mata kafa saboda auren dake kanta ne ko kuma ya karyeta kawai?. A hankali cikin sanyin murya Rimsha ta sake ambatar sunansa "Yaya Areef". Dawo da dara daran ash eyes nasa kanta ya yi, tare da sakin hannun jelly'n ya wuce zuwa cikin garden ɗin, da gudu jelly ta watsa zuwa cikin gida, ita kuma Rimsha bayansa ta bi zuwa cikin garden ɗin. A ɗan gefensa ta zauna tana mai ɗaga mishi gaisuwa, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, bai amsa gaisuwar tata ba sai ya ce "Daga yau duk wanda ya yi kuskuren marinki, in ma a gidan nan ko a waje, ki rama, idan kika kuskura kika bari wata ta mare ki baki rama ba, to gaskiya zan yi miki hukunci, ko Mark ne ya mare ki, ki rama ki ce ya zo ya rama a kai'na, kina ji na ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi, sai faman sauke numfashi yake yi tare da nisawa, tamkar shi aka yi niyar mara, gabaɗaya ya ji babu daɗi, yaso ɓalle hannun Jelly wlh, bai so ta yi wannan babban kuskure na yunkurin marin Rimsha ya barta ba, yau dai taci albarkacin igiyoyi ukun dake kanta, ba dan haka ba, da yanzu haka tana gadon asibiti. Suna tsaka da hitarsu sai da Aseef, sanye yake da gajeren wando jeans baki zuwa gwiwarsa, sai riga mai ƙaramin hannu sky blue, kusa da ita ya zo ya zauna sai tashin kamshi yake yi, kamar ko da yaushe, sai aikin latsan waya yake yi, yana chatting da bugun zuciyarsa. Shammatarsa Areef ya yi ya kwace wayar yana faɗin "Tun da kazo kafi bawa wayarnan mahimmanci sama da ni, wai me kake yi ne a cikinta ne?". Dawo da kallonsa kan Rimsha ya yi yana faɗin "To ka duba mana ka gani, ba wani abu bane hira nake da matata faricniki na, our Queen ina abincin mu?". Ya yi maganar yana ɗaga mata wannan kyakkyawar cikakken gerar tasa, gata baka kirin cike da gashi. Zata yi magana kenan Areef ya katse ta da cewa "What? Me nake ganin nan, dan Allah da gaske ne abin da nake gani Aseef". Rimsha ce ta amsa mishi da "E mana yaya Areef da gaske ne, ai ni naga komai" tana magana tana dariya. Ɗan leƙo face nata ya yi kafin ya ce "Wow our Queen kin ga ɗan bakin nan naki kamar baya magana ko? Ashe dai kin iya sa ido, wato kallona kike yi lokacin da nake hira da Heartbeat ko? Amma shi ne da na dawo cikin mota kika yi kamar mai barci ko? To Allah ya kamaki yanzu, har da wani cemin yaya Aseef ina son yin magana da Aunty Akila amma baka tashe ni ba, eyye wato barcin karya aka yi mini kenan? Ni ne ban gane ba, to ba zan bari ba, sai na zane ki". Zata yi magana ya ɗaure kyakkyawar farin yatsansa a saman lips nata yana faɗin shiiiiiiiiii ta yi mishi shiru. Buge hannunsa Areef ya yi yana faɗin "Ba wani shirun da zata yi maka, ka jimin mutun, ka dai'na taɓa mata baki, zo nan ma ka gaya mini tun yaushe wannan abin ya fara faruwa ban sani ba, ka barni a gantale ban san komai ba, shi ne dan iya shege zaka wani cemin kana mafarkin mace ko? To dama kana zuba irin wannan kalaman soyayya ya za'ayi ba zaka yi mafarki ba, lallai ma ka sha da rabona". Cikin sauri ta ce "Yaya Areef nasan komai, duk abin da ya faɗa wa Aunty Akila ina jinsa, ni zan gaya maka". Aseef zai sake yin magana Lion ya shigo wajen bakinsa ɗauke da sallama kasa kasa, yana sanye da pajama launin fari tas, tamkar yanzu ya fitar dasu daga ledarsu, yau shima sarkar wuyarsa tana a waje saman rigar kamar yadda Aseef yake yi, bai barta a ta ciki ba, ya yi kyau over, kujera daban ɗan gefe dasu ya je ya zauna, hannunsa na riƙe da laptop da kuma wayarsa. Ganinsa yasa suka watsar da zancen shirmen da suke yi dan sanya Rimsha dariya, Areef baya son Lion ya rinƙa kallonta kullum a cikin shirme da yarinta, gwara su rinƙa yin abu serious a gaban shi, dan ya dai'na yi mata kallon small baby. Abinci Areef ya ce ta kawo musu suci, miƙewa ta yi ta nufi cikin gida, jim kaɗan ta dawo hannunta ɗauke da plates and spoons. A in da ta tashi, nan ta koma ta zauna tana Murmushi tare da satar kallon Lion ɗin, da yake wajen gabaɗaya wasu shegun fitillune masu ɗan karen haske, sai ya yi tamkar rana, ko'ina gauraye yake da haskensu, ta yadda ko allurarka ce ta faɗi zaka iya ganin kayanka, hakan yasa suke ganin komai tankar. Abincin ta fara zuba musu, fried rice ce and pepper chicken, abin ba'a magana, sai tashin daddaɗar kamshi yake yi, shi dai Aseef ji yake kamar ba zai iya ci ba, amma ya daure dan ta yi farinciki, kuma dan Lion yana wajen yasa ya ɗauki spoon, suka matso da ɗaya daga cikin tables dake wajen, suka ɗaura plate ɗin, sun sanyata a tsakiya kamar ƴar karamar kanwarsu da suke uwa ɗaya uba ɗaya. Ɗibar spoon na farko Areef ya yi ya kai mata saitin ɗan bakinta yana faɗin "Have my first spoon our Queen". Da sauri Aseef ya matso da bakinsa ya cinye abincin yana faɗin "Ba wanda ya isa ya yi having na first spoon naka sai ni, dan wulakanci shi ne zaka bata ko? To na cin ye in ga abin da za'ayi". Dariya sosai ta kwashe da shi, ganin yadda yake tsuke baki saboda abincin, kuma ga shi sai masifa yake yi yaki yin shiru. Duk abin da suke yi Lion yana jinsu sarai, amma bai ɗago ya kallesu ba, sai dai ya sanya a ransa idan har suka iya cin wannan abincin Nigeria da Rimsha ta zuba musu to tabbas ya jinjina mata, dan kuwa yana kallon yadda Musharraf ke fama da Aseef a Washington DC a kan cin abincin Naija, kullum Aseef ya ɗanɗana sai ya yi amai, shi kuma Areef sau ɗaya ya ɗanɗana a wajen Imran, daga nan bai sake kwatantawa ba, yanzu idan ya tabbata sunci na hannun Rimsha, to ba makawa yarinyar nan ta kai matakin da shi ma ya kamata ya ɗauketa da mahimmanci, dan kuwa bayan shi babu mai saka TRIPLETS nasa murmushi kamar ita, har mamakinsu yake yi. Allah mai iko, ya sanya maka soyayyar wanda baka sani ba, ya kuma sanya maka tausayin wadda baku haɗa komai ba, wani ma baka san shi ba rana ta farko da fara ganinsa da kai, sai gaji duk duniya idan ba shi ba, ba zaka taɓa samun kwanciyar hankali, baku haɗa komai da mutun ba, yana iya zama shi ne farincikinka, kamar dai su yanzu, basu son mata kwata kwata, harta maza basu so, basu son kowa ya raɓesu, lokaci gudu suka kamu da kunamarta, kauna irin ta ƴan uwan taka, ganinta da idanun ma kawai tana sanyasu matukar farinciki , rana tsaka suka santa, basu haɗa komai da ita ba, amma ta zama ita ce farincikinsu, suna kaunarta kauna irin ta addinin musulunci, Allah mai iko. TO FA BABBAR MAGANA MU DAI LEƘA GIDAN HAJIYAR DAƊI MU DAWO, WATA KILA ZASU IYA CIN ABINCIN KO KUMA AKASIN HAKAN, AMMA KUMA CIN ABICNIN NAN BA ABU BANE MAI SAUKI A WAJENSU, SANNAN KUMA BASU SAN ABIN DA LION YA KUDURA A RANSA BA, DA SUN SANI, DA ZASU YI KOKARI SU DANNE SUCI ABICNIN KO DA KUWA YAYA NE MA. GIDAN HAJIYAR DAƊI😭💔 A rana ta huɗu da suka kasance a cikin toilet ɗin, sun gama jigata, sun wahala, ita kam Aisha ma rai yana dab da yin halinsa, dan wani azababben rashin lafiya da take fama da shi, Jehan, Adiva, sun yi wani uban rama kamar masu ciwon kanjamau, ita kuma Maryam dama ta saba da wahala, daga cikinta ta fito, abin da ya fi hakan ma Baiwar Allah ta fuskanta, duk sun fita hayyacinsu, gashin kan jehan kamar na mahaukaciya ya dawo, ba tajewa, ba saka mai, sai zuba mishi ruwa da take yi tana wankewa, hakan yasa ya dankare kamar shekar tsuntsu, ba ƙaramin azabtuwa bayin Allah n nan suka yi ba, duk wanda ya gansu a cikin wannan hali sai ya matsa musu kwallah, ga shi kaya kala ɗaiɗai ne a jikinsu, ko wanka basu yi, dan ba ta yadda za'ayi su yi wanka a idanun junansu, ita dai Aisha ko a jikinta, a gabansu take tuɓewa ta yi wanka dan ta saba da bariki, Jehan baiwar Allah, ita da kanta bata son kallon jikinta saboda datti, duk tsabta irin nata da tsanar datti, yau ta kasance cikin datti tsumu tsumu, kwana uku cikin na huɗu ba wanka, gata da uban kyankyani sai aikin tufar da yawu, idan baku manta ba, dirty boys take cewa su Sadiq, dan bata son datti komai kankantarsa, ba wai dan su Sadiq suna da datti yasa take ce musu hakan ba, a'a ai Sadiq yana da tsabta sosai, kayan jikinsu ne da ya koɗe yasa take ganin kamar datti ne, shiyasa take ce musu hakan, dan komai kankantar datti bata son shi, iya cutuwa Jehan ta cutu a wannan bakar gidan, ta azabtu ba karya, ko da iya dattin nan a ka barta an cutar da rayuwata, abin da baka saba ba, ta yi kukan zuci har ta gaji, amma taki bari hawayenta ya zuba a fili, dan a nata ganin hawaye nuna kasawa ne da sarewa, ita kuma bata kasa ba, kuma bata sare ba, ta ce ko mutuwa zata yi sai dai ta mutu, amma sai ta yi iya kan bakin ƙoƙarita wajen ruguje wannan bakin gida ne tsinannu karuwan banza karuwan hofi, ba abin da yafi sakata cikin matsanancin bakin ciki irin ƙodar ƴaƴan mutane da ake sayarwa a kasashen waje, a kama yara matasa a cire musu wani ɓangare na daga halittar da Ubangiji ya yi musu a sayar, wannan bakin zalunci da me ya yi kama? Da matan aure masu yin zina, sun mai da abin sana'a, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, irin wannan lukutin masifa da me ta yi kama?, Wannan hajiyar daɗi akwai tsinanniya ta karshe a duniya, muguwa bakar azzaluma, tsinanniya, Jehan dai abin ya tsaya mata a rai, musaman laifuka biyun nan, matan aure dake zina, da kuma sai da wasu sassa na ɗan adam ba tare da izinin iyayen su ba ko da sanin yaran da ake yi, su ne manyan laifukan da suka tsaya mata kam a ranta a yanzu, in takaice muku Jehan ta dai'na tunanin daddy'n da sauransu, yanzu tunanin yadda zata ci uban hajiyar daɗi kawai take yi. Da yamma misalin karfe biyar suna zaune jugum jugum, sai lumfashi sama sama Aisha take yi, ga jikin nan nata ya yi zafi jau kamar wuta, duk suna kanta sai sannu suke yi mata, tana kwance cikin baff ɗin wanka, sai rawan sanyi take yi, ga shi babu abin da zasu rufata da shi, sai addua'o'i Jehan take ta faman tofa mata, da kyar take iya motsa bakinta, can kasa kasa ta ce "Jehan wlh kin cuceni, da ban biye maganarki ba, ai da yanzu ina zaune lafiya ta Lou cikin jin daɗi, amma yanzu ga shi zan mutu a cikin toilet saboda bala'in yunwa da kishin ruwa, ga wahala ta sanyi babu wajen kwanciya bare rufuwa, sai dai mu kwanta a tiles haka, dole sanyi ta kama mu, yanzu waye gari ya wayanwa?". Tana magana siraran zafafan hawaye na bin kuncinta ta gefe da gefen kunnenta. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara magana a nutse, duk yunwa ya kwakulesu, da kyar ita ma voice nata yake fita, "A'isha ban cuce ki ba, kuma abin da ya faru a yanzu kamata ya yi ma ya zama miki darasi, kamata ya yi ma ki ɗauki haske, yanzu tsakaninki da Allah kuɗi zai kai naira nawa kika kawowa wannan tsinanniyar gidan? Na san ba zaki iya kirgawa ba, duk da wannan kuɗi da kika kawo musu, bai sa sun ji tausayinki sun san suna karuwa dake ba, bai sa sun agaza miki sun yafe miki ba, ina son ki sani A'isha, sun gama dake ne, yanzu baki da amfani a wajensu, sun san cewa yanzu ba'a yayinki, sun gama ɗebar abin da zasu ɗeba a tattare dake, yanzu kin tashi aiki, ke da bakin ki a nan kika gaya mini, idan mace ta ragwargwaɓe zuwa suke yi su jefar da ita a wani garin, hakan yana nufin kenan idan mace ta gama biya musu bukatarsu to bata da amfani a wajensu, ki godewa Allah da ya nuna miki da idanunki kika gani tun da sauran numfashinki, wlh Aisha bariki bata da wata amfani, jiya dai kinga yayinki ake yi, kowa rububinki yake yi, yau kuma fa? Kowa ya gujeki, saboda komai naki ya kare, da zama kikayi, kika hakura kika yi aure, wlh koma ya zaki koma, sai an ganki da daraja tun da a ɗakin mijinki ki ke, yanzu fa? Ina mai tabbatar miki idan kika mutu, tamkar idan dabba ya mutu haka zasu ɗauke ki su jefar, kin sani ba wai baki sani ba, ke da bakin ki kike bani labari, to yana da kyau ki sani, duk wata ƴar bariki or ɗan bariki, mutuwar walanci suke yi, a lalace suke karewa, yana da kyau ki nitsar da tunaninki waje guda, ki san abin da kike yi, baa yin kuɗi da jiki, duk wanda ya ce miki ana yi karya yake yi miki, kuɗin ba zasu yi albarka ba, ni ina son ki tuba ne, ki koma ga Allah, ina miki sha'awar samun rahmar Ubangiji, yanzu sai Allah ne kaɗai yasan me yake damunki, wata kila wani cuta wani kafurin mutun ya sanya miki, kinga kuma su ba damuwrasu bane, idan cuta ta kamaki, ki mutu dan kanki, su dai tun da kin biya kuɗin da suka saye ki, to babu ruwansu, wlh yana da kyau duk masu shirin faɗawa irin wannan rayuwa ta bariki su sani babu wata nasara a saɓon Allah, babu in da zaka je, babu kuma abin da zaka cinma matukar zaka kauce hanyar Allah Manzonsa, duk wuya duk daɗi, ka tsaya a faɗar Allah da Manzonsa, to a nan ne zaka ci riba biyu, wato duniya da lahira, wlh ko yau na mutu, ba zan taɓa danasanin zuwata duniya ba, saboda ina iya kan bakin ƙoƙarina wajen ganin na tsaya a kan koyarwar manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, ban taɓa batawa iyayena rai ba, bantaɓa bari Sallah ya wuce ni ba, azumi, sadaka, dukka ina iya bakin ƙoƙari, har na rabu da iyayena albarka suke saka mini, to me yafi wannan a duniya? Ni nasan jarabawa ce Allah ya jarrabeni da shi na zuwa na wannan gidan, idan da na gaya miki ni ƴar wace ce, ke da kanki zaki ce eh tabbas jarabawa ce Allah ya jarrabeni da shi, kuma ina ƙoƙarin naga na ci wannan jarabawa, bana neman taimakon kowa sai na mahaliccina, baya barci, yana kallon duk abin da yake faruwa damu, da izininsa kuma zai kawo mana mafita, zai dafa mana, dan addu'a bata faɗuwa kasa banza, sai dai jinkirin amsawa, to ina mai........". Bata kai karshen maganar ba ta dakata sakamon buɗe kofar da ta ji ana yi, cikin sauri suka miƙe tsaye da kyar, wani irin jiri ne ya ɗebesu saboda bala'in yunwa, cikin sauri ta dafe bango dan kada ta faɗi kasa, da kyar da kyar suke jan numfashi, idanu duk sun rena fata, dama Jehan akwai dara daran idanu, da ta rame sai suka kara fitowa kwala kwala da su. Zinariya ce ta buɗe kofar, kamar kullun kajeren jeans fashion trouser ne a jikinta, sai riga mai hannun vest baki, tasha wannan uwar make up ɗin nata, ga uban attachment da ta zuba a kai kamar wani bukkar shaiɗanu, fuska kamar an ɗaye bayan kadangare, saboda bleaching ta cinye fatar, naman fuskar ta yi jawur, sai kuma ta rinƙa damɓara uban Foundation, abin kamar kayi ta kwara amai idan ka gani, ga wani uban hujin hanci da ta yi, sai ta wani tabka katon ɗangunne kamar na Indiyawa, to su indiyawa yana musu kyau idan suka sanya, ita kuwa, sai ya yi mata wani sundumdum a fuska kamar garman shanu, abu ba kyan gani, babban abin haushi kuma abin amai shi ne eyelashes da suke labkawa, abu kamar bindin kaza, a tsaitsaye yana zagin wadda suke kallah, harta Hajiyar daɗi irin dressing nata kena, kayan haushi, kamar ya finciko wannan uban ɗan kunnan na hancin nan nasu ka tuge har da hancin kowa ma ya huta shegu, sai uban warin man bleaching suke yi, kamshin turaren da suka sanya daban, warin man bleaching daban, dama kuma haka yake yi, shegen wari masu bleaching nan suke yi, ko sun sanya turare baya kau da warin, sune basu ganewa, na kusa da su kuma basu gaya musu gaskiya, dan tsoron kada su ɓata alakar dake tsakaninsu, hmmmm ai duk abin da Allah ya haramta ka ce zaka yi, to fa kana tsaka mai wuya, ka rinƙa faɗawa wahala da masifu kala kala, Allah dai ya karemu, yasa mu tsaya a iya in da Ubangiji ya tsai damu Amin. Kallon banza ta watsa musu kafin ta ce "Ku wuce ku fito". Ta kai karshen maganar tare da juyawa ta nufi waje, "Ai na ɗauka barinmu zaku yi mu mutu a ciki, ban yi zaton zaku buɗe mu ba ai". Cewar Jehan da baki baya shiru, da kyar maganar yake fita, amma sai ta yi tsiwa. "Ke kada ki kuskura ki ce zaki gaya mini wata magana a nan, wlh yanzun nan sai mu saɓa miki kamanni, ke wato bakin ki ba zai yi shiru ba ko?, To wlh ki sani nan bariki kikazo, akwai iyayen iyayenki a rashin kunya, yanzu zamu gyara miki zama, ku yi maza ku fito min nan tun ban ci uban yarinya ba dan ubanta!". Tana magana tana hura hanci takar balo balo, dama ga hancin ba'a magana. "Babu in da zanje, kuma da kike wannan magana dama an gaya miki ni mara tarbiya ce irinki da zaki ce kunfini rashin kunya, wlh ina mai baku shawara da kuji tsoron Allah, ku sani akwai mutuwa, dan ba zance muku akwai tsufa, saboda kun rigada kun tsufa kun tsofe, ke a yadda kike yanzun nan saboda Allah ba kamata ya yi a ce ewar haka kina saman dadduma kina addu'a Allah yasa ki cika da imani ba, duk kin tsufa kin zagwanye, kadangarun bariki sun zuke miki ruwan kai da jinin jiki, amma har yanzu sheiɗan na zugaki na cewa kina da mamora ko? To wlh ki sani babu wata mamora da ta rage a jikinki face azaba da kika tana da wa kanki da kanki, ke da kanki idan zaki gayawa kanki gaskiya ki ajiye zancen sheiɗan a gefe, kin san cewa bai wuci taku biyu ya rage miki zuwa kabari ba, shekarunki nawa a duniyar nan? Kin taɓa waigawa ki duba a waƴan nan shekarun na baya da kika yi me kika aikata na alkhari? Wai ko dai kema kina ɗaya daga cikin waƴan da suke tunanin sun zo duniya kenan babu komawa? To idan ma kina ɗaya daga ciki ki sani dai duniya kam akwai ranar barinta, mutuwa gaskiya ce, yanzu ma tana iya ɗauke ki, bata jira sai an shirya, da a shirya da kar a shirya duk sai ta ɗauka idan lokacin ya yi, babu kuma uban da ya isa ya hanata ɗauka, to tun da sauran ni'ima ta numfashi da Ubangiji ya yi muku is better for you da ki tuba, ki tuba ki koma ga Allah, Allah gafurur rahim ne, zai karɓi tubanki!!". A fusace ta juyo ta dawo cikin toilet ɗin, ranta a matukar ɓace ta ɗaga hannu zata zabga mata mari, nan take zuciyarta ya tuna mata da Hajiyar daɗi na dawowa gobe, hakan ce kuma tasa ta buɗe su, idan Hajiyar daɗi ta dawo da sami wani tabo a jikin su ukun nan, wato JEHAN, ADIVA, MARYAM, su da aka kawo sabbin, basu biya kuɗinsu ba, to sai ta yi wa su Zinariyar mummunar hukunci, dan kuwa ita bata ɗaukar asara, bata yarda da asara ko mai kankantar sa, shiyasa suka yi sauri tun yau suka buɗe su Jehan ɗin, zasu duba lafiyarsu da sauran abin da ya dace kafin hajiya ta iso ta same su lafiya, daga nan kuma su umarce su da kada su kuskura su gayawa hajiya abin da suka yi musu, idan ba haka ba wlh sai sun bi dare sun kashe su. BARIKI KENAN, BABU MUTUNCI KO KAƊAN. Tuna hakan yasa bata bari Jehan ɗin ba, ta juya rai a ɓace ta koma cikin ɗakin tana jiran fitowarsu, da kyar Maryam da Adiva suka iya jan kafafunsu suka fito cikin ɗakin, ita kuma A'isha ko motsin kirki bata iya yi, komawa kusa da ita Jehan ta yi ta zauna, sai jiransu Zinariya take yi, amma shiru Jehan taki fitowa, daga karshe dai ta taso ta dawo cikin toilet ɗin, cike da bada umarni ta ce "Ke Jehan ki wuce mu tafi". A kule rai a matukar ɓace ta ce "Babu in da zanje marasa imani kawai, wlh in dai baku ɗauki A'isha kun kaita cikin bedroom kun kwantar da ita a gadonta ba, to sai dai mu mutu ni da ita a nan!". Basu da zaɓi dole su fito da Aisha ba dan sun so ba, da farko basu yi niyar ko kallon in da take ba, amma da Jehan ta kafe akan sai sun fitar da ita zata fito ita ma, dan dole suka yi hakan dan gudun su yi laifi wajen Hajiya. Bayan sun fitar da ita zuwa saman gadonta ne ita ma Jehan ɗin ta fito, dama sai da Zinariya ta kira wata wai tattabara tazo ta tayata fitar da A'isha, to suna fitar da ita tattabara ta koma bakin aikinta, ita kuma Zinariya ta tasasu a gaba tamkar wata uwarsu tana basu umarni kamar haka. "Wlh ko da gigin wasa, idan wata ta kuskura ta sanar da hajiya abin da ya faru da ku, to sai na lahira ya fi ku jin daɗi, shekarunku sun yi kaɗan da su ɗauki azabata, zan iya kashe rayinya wlh". Cike da confidence babu tsoro ko kaɗan a tattare da ita Jehan ta mai da mata da martani kamar haka "Saboda ke ce uwar mu ba, ai dole ki saka mu a gaba kina wani bamu umarni, ke bari ki ji in gaya miki fa, a bariki babu uwa, a bariki babu babba, duk wanda ya taka, kai ma ka taka shi, ko da kuwa shi ya koya maka bariki, kina tunanin bansan komai dan gane da bariki bane? To idan haka kike tunani ki canza, kowa babban kansa ne a bariki, kowa ga shin kansa zai ci, bari ki ji nayi yawo a Media fiye da tunaninki, sannan ke daga ganina baki ga kalar jahila ba, babu wadda ta isa ta zana mini ga abin da zan yi, tun asalina abin da nayi niya nake yi, to kuma a haka zan rayu a cikin gidan nan, da kuma kike maganar zaki kashe mu idan muka faɗa, an gaya miki rayukanmu a hannunki yake ne? Babu wanda ya isa ya kashe wani har sai kwanansa ya kare, duk wanda kika ga an kashe, to kwanansa ne ya kare, ko ba'a kashe shi ba zai mutu a wannan lokaci, sai maganar azabtar damu da kike yi, ke baki san mu kafuwar Allah bane? Duk azaban da kuka yi mana, kuka kullemu a cikin toilet babu ci har na tsawon kwana uku da wuni ɗaya, kuka buɗe mu babu abin da ya same mu, daga nan ya kamata ki sani kafuwar Allah ne ba na ɗan adam ba, sannan kina da wuta da aljanna ne? Tun da baki da ko ɗaya ai shekenan duk wani azabanki na banza ne, ni ba zan gaji da gaya miki ki ji tsoron Allah ki sani akwai lahira, akwai ranar da zaki biya duk wani abin da kika yi, ranar da babu uban da ya isa ya tare miki, kuɗi ba zasu tsinana miki komai ba a wannan rana, kina da sauran lokaci da zaki iya tuba, to kada ki bari dama ya kubce miki, sai magana ta karshe, wlh zaman ki lafiya a gidan nan shi ne ki dai'na nuna mana wani izza kamar ke kika haifemu, idan ba haka ba, na yi miki alkawarin wlh ni zan sanya ki ki fara danasanin zuwanki duniya a rayuwarki, da ni kike magana JEHAN NAWAZUDDEN SALMAN SULTAN, ni kai'na wani lokaci tsoron kai'na nake ji, dan haka zaman ki lafiya ki fita harkata, idan kuma kika ki, wlh na juyo muka sanya kafar wando ɗaya, Allah sarki, sunanki sorry". Duk wannan magana da Jehan take yin shi fa, bala'in tsoro ne cike fal a ranta, kamar yadda kuka sani ne, kwarin gwiwar a iya baki ne kawai, ita dai kawai ta yi Imani da cewa duk tsoron mutun da kake ji, idan ka dake ka nuna baka shakkarsa ba kuma ka tsoronsa, to tabbas sai fara shakkarka har ma ya ji tsoron naka, kuma haka ne, rayuwa idan ka nuna kana tsoron abu, to tabbas yafi tsoratar da kai, amma idan ka dake, ka nuna jan wuya, to fa ba makawa zai fara tsoronka, zai yi ta tunanin ko ka taki wani abin ne. Duk rashin kunya irin ta Zinariya yau dai sai da ta ji tsoron Jehan ya kamata, mamaki take yi tare da tunanin anya ba wani abu Jehan ta taka ba kuwa? Abin ya fara ɗaure mata kai, shiru ta yi bata sake ce da su komai ba, wannan shi ne gaba ma da gabanta. Suna a wannan hali Yar gwal ta shigo ɗakin ɗauke da abinci kala biyu, na Jehan daban, nasu Adiva daban, nan ma ba karamin dirama suka sha ba, dan Jehan ta ce wlh idan sun ga ta ci abinci, to tare da su Adiva zata ci, ba zata ci wannan abincin da suke bata ita kaɗai ɗin ba, domin kuwa tun da suka kafe sai taci shi tun farkon zuwanta, daga nan tasan tabbas akwai wani abu a cikinsa, ba haka kawai ba, to kuma ba zata ci ba, ba yadda basu buga ba, ta kafe ta ce sai dai yunwa ya kasheta, ƴar gwal har ta fara yunkurin ƙoƙarin zata dake ta, Zinariya ta dakatar da ita, ba dan sun so ba, sai dan saboda kada yunwa ya kashe Jehan Hajiyar daɗi ta sanya su biya, haka suka hakura suka fita da abincin Jehan ɗin, suka ce taci nasu Adivar, hakan kuma ya kara tabbatarwa da Jehan tabbas akwai abin da suka zuba a ciki, idan da babu komai ai da zasu juye musu abincin ne su haɗa musu su ce su ci, amma sun koma da shi, to akwai wani abu a kasa. Allah dai ya kyauta. Suna fita su Adiva suka fara cin abincin hannu baka hannu kwarya, bayin Allah sun wahala, ita ma Jehan ɗin hannu baka hannu kyarta ta fara cin abincin, jolof rice ce, ta ji kayan haɗi ba karya, ko wanka basu tsaya yi ba, sai da suka kusan cin ye abincin, Jehan ta ɗauki tray ɗin ta dawo kusa da A'isha dake kwance tamkar babu rai a tattare da ita, dan ta bata abincin a baki. Zama ta yi a gefenta tare da fara ambatar sunanta a nutse, "A'isha, A'isha". Shiru bata amsa ba, taɓata ta fara yi tana mai cigaba da ambatar sunanta, nan ma shiru bata amsa ba, a razane ta fara jinjigata da karfi tana kiran sunanta, da sauri suma su Adiva suka yi kanta dan su ga menene ya same ta, ina shiru bata ko motsi, da gudu Jehan ta diro kasa daga saman gadon ta nufi waje. Bata zame ko'ina ba sai office ɗin Zinariya, zaune ta iskota saman kujera tana shan lemun kwalba mai sanyi, a ruɗe ta gaya mata abin da yake faruwa da A'isha, babu ko tsoron Allah a cikin zuciyarta bare tausayi ta ce "To ina ruwana dan bata motsi? Ta mutu mana idan ta ga dama". Hankalinta kwance ta yi wannan magana. Tsabar bakin cikin Jehan bata san lokaci da ta yi wani irin mahaukacin kukan kura ta damko wuyar rigarta ba, idanunta sun rufe, rashin imanin gidan nan ya wuci tunanin mai tunani, zuciyarta tafasa yake yi tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje, ga idanunta dama sun kara girma sabida rama, yanzu kuma sun yi jawur kamar wuta, zarosu waje ta yi sosai tare da shaƙe wuyar Zinariyar da iya karfinta na karshe, cikin tsawa ta ce "Tabbas idan A'isha ta mutu wlh ba zan barki ba, baku da imani, baku da tausayi, me A'isha bata yi muku ba a gidannan?, jikinta fa kuka sayar kuka sami kuɗi, yau an wani gari tana kwance rai a hannun Allah ne zaku ce babu ruwanku da ita? Wlh kukam ko kun tuba Allah ba zai barku ba, domin nasan akwai yara da dama da suka mutu a dalilinku, to ku sani Allah baya yafe hakkin wani, iya laifin tsakaninku da shi kawai yake yafewa, to taya zaku nemo yafiyar waƴan da suka mutu? Wlh ku bakaƙen azzalumai ne, macuta, makirai, kuma kafurai, sheiɗanu kai komai da komai ma, da izinin Allah sai Allah ya kawo karshenku tsinannu, baku babu ganin Annabi, wlh mutuwar walakanci zaku yi, ko kare sai ya fiku mutuwa mai daraja, Allah ya tsine muku albarka, ya kwashewa iyayen da suka aifeku albarka, da haihuwar irinku gara ɓarinku, shegu mugayen iri kawai". Tana magana tana hawaye wani nabin wani, ji take yi wani mahaukacin jiri na ɗibarta, saboda tsantsar ɓacin rai, da alama kuma ta fita a hayyacinta, dan wannan surutai da take yi bata san tana yinsu ba, abin ya yi mata muguwar ciwo, dama kun san halinta, zata iya ɗaukar komai banda cin zalin wani bawa, bata ganin za'ayi rashin adalci ta bari, kuma hakan ne yazama sanadiyar shigarta kaddarori da dama, saboda taimakon Hanan ta yi wa FAROOQ karyar ta yi recorded nasa, daga nan ya turo a kasheta, hakan ya yi sanadiyar zuwanta wannan gida, ta shiga bala'i kala kala a kan taimakon wasu, kun san da hakan!. Da Iya karfinta na ƙarshe Zinariya ta sa hannu zata kwaci wuyarta, amma ina ta kasa, sabon jini da tsohon jini ba ɗaya ba, duk ta ragwargwaɓe maneji take yi dama, Jehan tazo tana ƙokarin karisa ta. suna cikin wannan hali sai ga ƴar gwal, ganin abin da yake faruwa yasa ta kariso ciki da gudu ta yi kansu, tana zuwa ta kwashe kafafun Jehan ta zube kasa Zinariya ta bita ta faɗa kanta, dan kuwa taki sakin wuyar tata, Jehan akwai taurin rai da taurin kai ga taurin zuciya over. Kokawa suka fara yi ƴar gwal na ƙoƙarin kwatar Zinariya, ita kuma Zinariya tana ƙoƙarin baƙontar lahira, Jehan kuwa ta kankameta gam taki saki, kwalbar lemon da Zinariya ke sha kafin Jehan ɗin ta shigo, ƴar gwal ta ɗauko da niyar ta kwalawa Jehan a kai, Jehan kuwa sai da ta daidai ci daidai zata kwala mata, sai ta juya da Zinariyar, kwas kake ji yar gwal ta kwalawa Zinariya a kanta, ga shi da iya karfinta na ƙarshe ta saki kwalbar dan ta fasawa Jehan kai, sai ga shi reshe ta juye da mujiya, nan take kan Zinariyar ya fashe, shi ma kwalbar ya fashe, da alama kuma ya shiga kan Zinariyar, jini ne ya fara zuba kamar wani famfo, a zabure Jehan ta saketa tare da sanya karfin da ya rage mata ta tureta gefe guda ta miƙewa tana tangal tangal kamar zata faɗi, ta nufi waje zata fita, jawota ƴar gwal ta yi da nufin ta daketa, nan take ta fara yi musu hauka hauka, ta nuna musu ta fita a hayyacinta, duk abin da ta samu ɗauka take tana harbin ƴar gwal da shi, hatta laptop ɗin Zinariya na shigar da bayanan kuɗin da aka samu bayan tafiyar hajiya da sauransu Jehan ta ɗauka ta yi wurgi da shi, kan kace me ta fasawa ƴar gwal baki, watsi da komai na cikin office ɗin ta fara yi, a guje ƴar gwal ta watsa waje tana ihun a kawo kara ɗauki mahaukaciya, Jehan ta haukace, da gudu Jehan ɗin ta bi bayanta, suka bar Zinariya kwance rashe rashe a cikin jini, ko motsi bata yi, da alama dai ta mutu ne ko suma. Wani katon katako Jehan taci karo da shi a tsakiyar gidan, ɗauka ta yi a fusace ta cigaba da bin ƴar gwal, yau haukace musu tuburan ta yi, a takaice dai da kyar da makyarkyata a ka iya kama Jehan, sai da su tattabara da su zillaziya suka sanya hannu, bayan sun danneta ne, Ƴar gwal na daga laɓe a bayan sauran matan gidan da suka taru, tana loƙo su baki a fashe yana jini, har ya kumbura suntum kamar ruɓaɓɓen alale ta ce "Kada ku sake ta, ku saka sarka ku ɗaureta sosai, wlh mahaukaciya ce, ina ga a mahaukatan ma wannan ta karshe ce, a mahaukatan ma ina ga babu irinta, ku danneta da kyau, ku kula fa kada kuma ta kashe ku". Tana magana tana zare idanu, yau tasha bugu. Haka su tattabara suka sa karfi suka ɗaure Jehan da kyau, sannan suka ɗauketa zuwa ɗakinsu, daga nan jama'a ko wacce ta koma ɗakinta, ita kuma ƴar gwal da su zanƙaɗaziya suka nufi wajen Zinariya dan suje su kai mata agajin gaggawa. Yau dai anyi ƙaramin yaki a gidar Hajiyar daɗi, matan gidan kowa sai mamakin Jehan yake yi, saboda kowacce tana bala'in mutuwar tsoron su Zinariya kamar me, ba wace ta isa ta ɗaga musu yatsa or murya, yau an wayi gari Jehan ta yi musu hauka hauka ta ragargaji banzaye, ai kunga dole su yi mamaki GA A'ISHA KWANCE KO TA MUTU KO TANA RAYE OHO😭😭 WANNAN BALAIN DAME YA YI KAMA? ALLAH KA KAWO MANA KARSHEN DUK WASU AZZALUMAI DAKE FAƊIN DUNIYA BAKI ƊAYA, NI DAI NA TAFI GIDAN ABBO, WATA KILA KAFIN NA DAWO KOMAI YA ƊAN LAFA A WANNAN BAKIN GIDAN, KO KAƊAN BAI KAMATA A KIRA WANNAN GIDA DA GIDAN KARUWAI BA, KAMATA YA YI A KIRASHI DA BAKIN GIDA, GIDAN ZALINCI DA AZZALUMAI😭. GIDAN ABBO💋❤️ Misalin karfe 5 na yamma, aiki take yi a kitchen, yayin da ita kuma Ummi take faman gyaran palo, sanye take da doguwar riga ashe color, ta yi kyau sosai, tana samun kulawar mijinta dana surukuwarta, sai wani kara haske take tana ƙiba, tana aiki tana tunanin mijin nata, kayan miya take gyarawa, ta bawa kofar shigowa baya, sai tunani take yi na ya akayi bai dawo ba har yanzu, ko dai aiki ne ya yi mishi yawa. Bata idasa tunanin nata ba ta ji an rufe mata idanu ta baya, ko bata juya ba ta san shi ne, domin kuwa Ummi dai ba zata yi mata hakan ba, cool murmushi ta saki, "Yaya Nawid yau fa kayi latti". Ta yi maganar cikin sanyin murya, ƙayatattacen murmushi ya sakar mata tare da kwanto da kansa a saman bayanta yana faɗin "Ke dai bari, ai nasan nayi laifi, shiyasa ma zan fara bada hakuri tun yanzu, nayi kewarki sosai fa". "Ni kam ba zan iya misilta irin adadin kewarka da nayi ba, tun ɗazun tunaninka nake yi, amma me ya sa ka jima har haka? Bayan kuma kace mini karfe 4 zaka dawo". Zame hannayen nasa daga saman idanunta ya yi tare da mayar da hannu ɗaya saman shafaffen cikinta yana ɗan shafawa, ɗauke wuta ta yi na wucin gadi tare da ajiye kayan niyar dake hannunta ta juyo da sauri. Tana juyowa ya jawota jikinsa ya rungume, a tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya na kewar juna, "Me ka sayo mini a hanya?" Ta yi maganar kasa kasa, "Kayan daɗi na sayo Miki, amma sai dare zan baki, yanzu dai yunwa nake ji, da kuma gajiya, zaki yi mini tausa ko?" Ya kai karshen maganar yana ɗan raba jikinsu, "Ni ban iya tausa ba ai". "Shima zan koya miki kamar yadda na koya miki kiss, yanzu dai a bani kiss na barka da dawo kafin a kawo mini abinci". "Yaya Nawid ka bari mana kaga fa Ummi tana Palo, kowani lokaci daga yanzu zata iya shigowa cikin kitchen ɗin nan, idan ta ganmu fa?" Jan dogon hancinta ya yi, "Waye ya ce miki Ummi zata shigo? Ai tana ganina na shigo Kitchen ɗin, sai da muka gaisa ta yi mini sannu da dawowa, kuma tasan idan na shigo sai na taɓa ki, Kinga kuwa ba zata shigo ba dan ita zata ji kunya, kin san Katsina da kunya, amma ni bani da shi". Dariya ta kwashe da shi, wai shi bashi da shi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ta faɗa a cikin ranta. "Ni ki daina dariyar nan ki bani hot kiss bari na je nayi wanka". "Rufe idanunka to" ta yi maganar tare da tsagaita dariyar da take yi. Ba musu ya datse idanun nasa tare da matso mata da bakinsa, ɗan ɗaga kafanta kaɗan tayi, ta yadda zata kamo shi tsawo, cikin natsuwa ta kai bakinta sai tin nashi ta fara kissing na kayanta, kamar jira yake yi ya jawota jikinsa tare da fara matsa mata breast ɗinta ta saman rigar nata, kankame shi ta yi ta zura hannayenta dukka biyu a bayansa, cikin sauri ya juyar da kiss ɗin ya dawo shi yake kissing nata ba ita take kissing nashi ba, sosai yake matse mata breast nata yana wani sakin numfashi da sauri da sauri. Sun ɗan jima a haka, sai da ya fara fita a hayyacinsa tukunnan ta kwace kanta tare da juyawa ta koma kan aikin da take yi, duk abin da suke yi Ummi na gyaran palo tana jinsu, dan palon ba nisa da Kitchen ɗin, idan da sabo ta saba da tsiyarsu, wani lokaci ma a gabanta idan ya shigo Kitchen ɗin yake sumbatar Aafia a kumatu, sai dai ta kawar da kanta kamar bata gansu ba, bata son su matsa kusa da ita ne, da farko Nawid ya ce zasu koma gidansa, ita taki yarda, ta ce a'a su zauna kusa da ita, Baiwar Allah kuma bata takura musu, komai suke so suyi, sai ma kara musu kwarin gwiwa da take yi a kullum. Da kyar ya iya barin kitchen ɗin ya nufi bedroom nasu, a palo ya wuce Ummi bai ce mata komai ba ita ma bata ce mishi komai ba, yana shiga ɗaki ya ajiye jakarsa tare da nufar toilet dan yin wanka, ita kuma sauri sauri ta karisa wanke kayan miyar ta fara haɗa mishi abinci dan ta kai mishi........... ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E25-26 Da kyar ya iya barin kitchen ɗin ya nufi bedroom nasu, a palo ya wuce Ummi bai ce mata komai ba, ita ma bata ce mishi komai ba, yana shiga ɗaki ya ajiye jakarsa tare da nufar toilet dan yin wanka, ita kuma sauri sauri ta karisa wanke kayan miyar ta fara haɗa mishi abinci dan ta kai mishi. Lokacin da kai abincin ya fito daga wanka yana tsaye a gaban mirror, ta cikin mirror ya zuba mata idanu yana kallonta, in da ta saba ajiye musu abinci, a nan ta je ta ajiye, zata fice daga ɗakin ya ambaci sunanta kasa kasa, juyowa ta yi tana kallon shi. "Baki fitar mini da kayan sakawa bafa," cikin zolaya ya yi maganar, ba musu ta dawo wajen drawer kayan nasa, kananan kaya ta fitar mishi, tana ƙoƙarin juyawa ta nufe shi, sai ji ta yi ta buge shi, da sauri ta ɗago kai, bai bari ta kalli face nasa ba, ya yi saurin jawota jikinsa, "Wai ni sister yaushe ne zaki barni nayi wasa dake son raina ne?" Ya yi maganar kamar mai yin raɗa. Shiru ta yi bata amsa shi ba, sai wani ɓoye fuska a kirjinsa take yi, bayanta ya fara shafawa a hankali yana sauke numfashi, shiru ta kwanta a jikinsa bata motsaba har sai da ya saketa dan kan shi, yana sakinta fa miƙa mishi kayan nasa, karɓa ya yi ya nufi toilet, ita kuma kitchen ta koma. A palo ta haɗu da Ummi, zata wuce kitchen ta dakatar da ita ta hanyar cewa "A'a Aafia ki bar girkin zan je in karisa, ki je ki kula da mijinki tun da ya dawo". Kasa ta yi da kai, a dole ta ji kunya, sumui sumui ta juya ta koma, dama ita ma tana son zama ta kula da kayanta, dan kawai kada Ummi ta ce ta bar mata girki daga kai abinci ne yasa ta fito, badan haka ba, ta fiso mijinta ya ci abinci a gabanta, dan ta san adadin komai da yake buƙata, ma'ana tasan adadin cinsa da sauransu, dama kuma yana da kyau ku san adadin abincin da mijinku yake ci, dan kada ki rinƙa labta mishi abin da ba zai iya cinyewa ba, ki zuba mishi abin da ya fi karfin cikinsa, ko kuma wadda ta yi mishi kaɗan, sai ya zo yana a kara mishi ko daɗin ji babu, wai a kara. Lokacin da ta dawo ɗakin shi ma ya fito daga toilet ɗin shirye cikin kayan data fitar mishi ɗin, ya yi kyau sosai, ya fito a cikakken saurayinsa, duba time ya yi 5:30, in da ya saba zama ya je ya zauna, cikin natsuwa ta karisa in da yake, abincin ta fata zuba musu, bayan ta gama ne suka fara ci a tare, cike da so da kaunar juna, da kuma kula da juna, sai zuba mata hira mai shegen daɗi yake yi, ita kuma sai bin shi da murmushi take yi har suka kammala. Miƙewa ta yi ta tattare kayan abincin ta nufi waje, Ummi tana kitchen tana faman zuba soyayyar nama a cikin miyar da Aafia ɗin ke haɗawa. "Ummi bari na karɓa miki". Ta faɗa bayan ta ajiye kayan abincin. "A'a Aafia ai kin yi abinci, miyar kuma bari na karisa, ke dai jeki ki kula da mijinki, Allah ya yi muku albarka, ya dawwamar min da rayuwarku a cikin tsantsar farinciki". Amin ta amsa da shi tare da yi wa Ummin godiya ta juya ta koma ɗakinsu. Kwance ta isko shi saman doguwar kujeran, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ya zuba wa Tv dake manne a jikin bango idanu. Daidai saitin kansa ta zo ta sanya hannu ta ɗan ɗaga kannasa ta zauna tare da ɗaura kan nasa a saman cinyarta, juyo da kallonsa a kanta ya yi suna fuskantar juna. "Sister kinsan duk wani abu da nake so, Allah ya yi miki albarka, kina sanya ni farinciki sosai da sosai, ba abin da zan ce sai dai nayi ta yi miki addu'ar fatan alkhari". Hannu tasa tana shafa face nasa, cikin sanyin murya ta ce "Yaya Nawid farincikin da kake sanya ni yafi wadda nake sanya ka, fata na dai Allah ya kare min kai a duk in da kake, Allah yasa kada wata mace taga kyanka sai muni, ya zamana ni kaɗai zan ga kayana" "Eyee wato ma dai addu'a kike yi na kashe mini kasuwa ko? To ban yarda ba, haka kawai? Ni bana so, ina laifin ki ce mata kyawawa zuƙa zuƙa kamar ke haka, guda uku su makale suce sai ni, ai kinga......." Bai kai karshen maganar ba ta rufe mishi baki da hannunta, a kule ta ce "Haka ma zaka ce?" Girgiza mata kai ya yi alamar a'a, tun da ba halin yin magana, ta rufe mishi baki. Miƙewa ta yi tare da kwantar mishi da kansa a saman sofa ta nufi gado ta kwanta, irin ta yi fushin nan, da sauri ya miƙe ya bi bayanta yana ambatar sunanta, kin kulashi ta yi, ta yi kwanciyar ruf da ciki, tare da kwantar da kanta a saman pillow. Saman bayanta ya haye ya kwanta tare da kwanto da kansa a saman kafaɗarta, murya a sanyaye ya fara magana "Haba my sweetheart, me yasa zaki ɓata ranki bayan kinsan wasa nake yi miki, nifa ke kaɗai kin ishe ni, bana son wata, please tashi kiyi mini tausa kin ji ko? Na tuba ba zan kara ba". Ɗan ɗago kanta ta yi, da sauri ya sauƙa a kan nata, pillow ta ɗauka ta fara bugun shi da shi, tana kumbura kumatu, sai dariya yake yi gwanin ban sha'awa, shammatarta ya yi ya haɗeta ita da pillow gabaɗaya ya rungume yana dariya, shigewa jikinsa da kyau ta yi tana murmushi,. "Eyyee ranar nace kishi kike yi, kin ce ba haka ba, to yau kuma menene? Ko dai shi ma wannan ba kishi bane?" "A'a yaya Nawid, ba kishi bane, ni bana kishi ai, na gaya maka kula da kai ne, wai ka manta amanarka a ka bani ne?". Hancinta ya ja zai yi magana aka fara kiraye kirayen sallar mangariba, shiru ya yi yana salatin annabi yayin da ita ma take yi, sai bayan an idar da kiran sallah ne suka yi addu'a da ya kamata. Sauƙowa kasa ya yi daga saman gadon ya nufi toilet dan ya ɗauro alwala, ita ma sauƙowa ta yi ta fiddo mishi da jallabiya, bayan ya fito, ya ɗauki jallabiyar ya koma toilet ɗin, jim kaɗan ya fito sanye da ita ya nufi masallaci, amma kafin ya tafi sai da ya manna mata hot sumbata a kumatu, ita ma ta mishi reply, sannan ya wuce zuwa masallacin, ita kuma ta haye gado ta kwanta dan yau bata sallah. A ɓangaren gidan Abbi kuwa. DADDYN JELLY & AYLA. Wasa wasa laulayi ya kankama, kwata kwata bata cin wani abincin kirki, cikin nata mai mugun zaɓar abinci ne, ga uban laulayi, cikin ƴan kwanakin da basu fi biyar da bayyanar cikin ba, har ta yi wani uban rama, kullun sai kwanciya a kasa tana bin sanyin tiles, ba wan da bai tausaya mata ba, shi kam daddy ma ba'a magana, kullum yana tare da ita, da ta yi motsi zai tambaye ta ko wani abin take so, ya dai'na fita ko nan da cikin gida wajen su Abbi, babban abincin da ta fi ci a yanzu shi ne yalo, dan haka daddy ya jibge mata su dayawa a cikin fridge, da yaga sun kusa karewa, zai sayo wasu, yana ji da cikin nan nasa, yana ririta kayansa, dama ko ban faɗa ba kum sani, kunsan Ayla raguwa ce number ɗaya, yanzu ma ragwancin take zuba mishi ba karya, haka zai yi ta biye mata, dama da lafiyarta ma shi yake yi mata komai, ina ga kuma yanzu da lalura ta samu, ai sallah ne kawai yake barinta ta yi da kanta, sai kuma shiga toilet, amma harta kaya, shi yake sanya mata bayan ya yi mata wanka, ta dawo jaririyarsa da gaske, dan ma yana da ƙoƙarin yi, baya damuwa, har rama shi ma ya yi saboda wahalar da cikin nan yake basu, da kyar yake iya lallaɓata ta ci abinci, nan ma sai ya nuna mata zai yi kuka, da zarar ta ci kuma zata yi ta kwarara amai tamkar zata amayar da ƴan hanjinta, tana azabtuwa ba karya. Da misalin karfe 8 na safe, tana zaune a tsakiyar gadonsu, jikinta na sanye da wata ƴar shimin rigar barci da bata wuci zuwa cinyarta ba, hannun rigar ƴan sirara ne kamar igiya, kayan suna da kyau sosai da sosai, ta rame ta yi wata fayau da ita, fuskar nan kamar ba ita ba, sai ido zaka gani. Daddy na gaban mirror yana fesa perfume, yana shirye cikin kananan kaya, wandon jeans ash color da riga baka, ya yi kyau sosai, bini bini zai kalleta ta cikin mirror, ita ma sai bin shi take yi da idanu irin Allah sarkin nan, ganin tana ta kallon shi ne yasa ya juyo yana sakar mata murmushi. "Babyn daddy akwai abin da kike so ne?" Kayatatcen murmushi ta sakar mishi tana girgiza mishi kai alamar a'a "Ki tuna dai da kyau, idan akwai ki gayawa daddy yanzu zan kawo miki". Nisawa ta yi kafin ta ce "Daddy wai dama haka ciki yake da wahala ne?" Ajiyar zuciya ya sauke tare da girgiza mata kai alamar a'a. "Ba kowani ciki bane yake da wahala baby, kinga cikin jelly kwata kwata bamu san ma da shi ba har sai da ya kai almost wata 3, a sannan ne ya bayyanar da kansa, to ko wani ciki da yanayin yadda yake zuwa mace, ke dai kiyi addu'a Allah ya baki lafiya, sannan kuma Allah ya bamu ƴaƴa masu albarka, next time In Sha Allah zai zo miki da sauƙi, yanzu ma da izinin Allah da ya kai wata uku zai rage miki duk wannan laulayin kin ji ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e ta ji. "Yauwa babyn daddynta, yanzu dai tuna da kyau babyna baya buƙatar komai?". "E daddy baya buƙata". "In kawo miki yalo?" Cikin sauri ta gyaɗa mishi kai alamar e ya kawo mata, ƴar murmushi ya yi yana faɗin "Ba baby ya ce baya buƙatar komai ba? Ya akayi yanzu kuma zai ci yalo?" Hannayenta dukka biyu tasa ya rufe fuskarta tana dariya. Takowa ya yi ya nufi wajen ɗan madaidaicin fridge ɗin nasu, buɗewa ya yi tare da fito mata da yalo guda biyu, a gefenta ya je ya zauna tare da ɗan rungumota a jikinsa yana kai mata yalon saitin ɗan bakin nata, kaɗan ta ɗan gutsira ta fara tauna tana mai mugun jin daɗin yalon sosai da sosai. "Daddy kai ma kaci mana?" To ya amsa mata da shi tare da kaiwa bakinsa, kwata kwata baya son yalon, amma tun da ita ta ce ya ci, dole ya jarraba ko dan ta yi farinciki. Shi ma kaɗan ya gutsira ya fara tauna, sai murmushi take yi, ya sake kai mata bakinta ta gutsira, da haka haka ya yi ta bata a baki har ta cinye tas. "In karo miki wani ne?" Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a, jinjina mata kai ya yi tare da manna mata sumbata a goshinta yana faɗin "Muje yawo ne baby?" "Daddy yawo kuma a ina?" Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Gidan yayana Hassan da kuma yawo a gari, wajen hutawa, wajen wasanni da sauransu". "Daddy dama kana da wani yaya ne bayan Abbi?" Gyaɗa mata kai ya yi yana faɗin "E ai Abbi ma ba shi bane babba, baban Imran shi ne babba, shi ma kafin shi akwai wadda ya rasu Abdulkarim, sai Abba sannan Abbi, bayan su ina da yayyu biyu, Hassan da Hossain, bamu san in da Hossain yake ba, ya guje mu, shi kuma yaya Hassan gidansa na nan Kaduna, bana son zuwa gidan ne, amma yau dan saboda ke zan je, zan kai ki wajen shi, sai dai kuma duk abin da matarsa zata ce miki, ki yi mata shiru kawai, akwai ta da surutu da baki kamar Sadiya". Ya kai karshen maganar cikin zolaya, dan shi da kansa yasan Aunty tana da halin kirki, idan yana son tsokanar tane sai ya ce ta cika yawan magana da shisshigi. Ƴar dariya ta yi. "Daddy ai ita Aunty bata da yawan magana". Shafa face nata ya yi tare da miƙewa ya ɗauko mata wasu kaya masu shegen kyau, doguwar riga ce da mayafinta, da kansa ya sanya mata tare da riƙo hannunta suka fita, shi dama already a shirya yake, palon Abbi suka nufa, sun yi kyau sosai sai ramar nan da suka yi ne ta so ta ɓata musu kwalliyar nasu. Aunty ce kaɗai a palo tana shirya musu breakfast, ganinsu yasa ta saki wani ƙayatattacen murmushi tana yi musu barka da safiya, ita kuma Ommu tana can bedroom nata dan bata bar gidan na, duk da Abbi ya saketa, tana nan bata motsa ba, shi kuma Abbi bai sake bi ta kanta ba, bai sake kula ta ba tamkar bai san tana nan ɗin ba. "Sadiya ɗauko mini key ɗin motar yaya bari mu fita, daga nan ki sanar mishi na tafi gidan yaya Hassan". Da mamaki Aunty take kallon shi "Yaya Hassan kuma?" Ta maimaita a filli, gyaɗa mata kai ya yi, "Waye yaya Hassan ɗin? Ko dai yaya babba ne?" Girgiza mata kai ya yi yana faɗin "A'a yaya babba daban, yaya Hassan daban, yaya Hassan shi ne ai ɗan uwan yaya Hossain". Ba karamin ruwan mamaki ta sha ba, a ranta ta ce ko su nawa ne a wajen iyayen nasu Allah masani, wata kila ma akwai wasu da basu bayyana ba, amma to meyasa suka yi wannan uwar watsewa hakan? Ta tambayi kanta da kanta, tambayar kuma da bata da amsar shi. Cike da tunani ta nufi sama dan ta ɗauko mishi key ɗin, shi kuma ya zaunar da babynsa a saman sofa dan kada ta wahala da tsayuwa. "Daddy palon nan yana wari". Ta yi maganar baiwar Allah tana toshe hanci, shi komai ta yi muguwar tausayi take bashi, Allah sarki kowa yasan ba halin ta bane, ita da ko magana bata cika yi sosai ba, daga to sai a'a, da wuya kaji ta ɗaga murya tana magana, kusa da ita ya dawo ya zauna, cikin tsantsar kaunarta ya fara rarrashinta akan ta daure bari Aunty ta kawo mishi key ɗin su tafi, ba dan ta so ba ta amsa mishi da to, haka suka zauna sai faman toshe hanci take yi har Aunty ta fito. Tun bata kariso wajen da suke ba, ya miƙe cikin sauri ya nufeta, key ɗin ya karɓa bai tsaya ya jira abin da zata ce ba, cikin sauri ya zo ya kama hannunta suka fita, yana jiyo sautin muryar Aunty tana faɗin "Abbi ya ce ka gaida mishi da yaya Hassan ɗin". A waje ya amsa mata da to, baya son duk wani abin da zai ɗaga wa babynsa hankali har ya sakata amai, ita kuma Aunty komawa ta yi saman table ta cigaba da abin da take yi, ita ma tana fama da ɗan ƙaramin cikinta, sai dai ita nata babu laulayi, ta yi sa'a, sai barci da kasala da yake sakata, bayan haka babu wani abin, ko amai bata yi har sai idan bata yi sa'a ba ta ci ta ƙoshi sosai. Idan muka koma ɓangaren Hanan, sosai take jin daɗin zamanta a gidan Abbi, yanzu shirye shiryen sakata a makaranta ake yi, har wani fresh ta kara abinta, Abbi ya saya mata waya, dama da suka je Katsina ta karɓi number Yusuf wadda ya kasance shi ne kaɗai mai waya a gidan, shi ɗin ma bai jima da saya ba, daya ga ya sami riba sosai a shagon nasa ne, sai ya sayeta, irin waƴan nan Tecno nan ne, masu babban kai ɗin nan, shi kam Sadiq ko a jikinsa, bai wani damu da sayan waya ba, shi dai burinsa yaga ya ginawa mahaifiyarsa gida ta bar wannan gida na amarya gidan gori kullum, ko kayan sakawa bai damu da ya saya ya saka a jikinsa ba, tara kuɗinsa yake yi ba ji ba gani, shi dai ya yi gini su fita daga wannan gida ko hankalinsa zai kwanta, da yake niyarsa mai kyau ce, Allah yana dafa mishi, yana samu ba karya, ko wace rana yana iya samun 2000, or 1500, or 1000 haka, idan ka ganshi ya kashe kuɗi, to Mahaifiyar tasu ya sayawa wani abin, ita kuma Hanan babban waya mai kyau da tsada Abbi ya saya mata, tana kiran Yusuf su gaisa da su maman Sadiq har shi kansa Sadiq ɗin, a hankali hankali Aunty ke koya mata ƴadda zata yi amfani da wayar, ita kuwa Ommu kamar yadda kuka sani ne, bata fita waje kwata kwata, idan kunganta a palo, to ko dai zata ɗauki abinci, ko kuma zata fita ta tafi unguwa, bacin haka kullum tana maƙale a cikin ɗaki kamar wata mara gaskiya, haka zalika kullum sai ta kira Umaisha a kan batun kuɗin nan, dan tana son komawa in da ta fito, tana son ta je ta kwaso mafi soyowar ƴaƴa a gareta, ita kuma Umaisha A'afia ta hanata ɗaukar kuɗin, ga shi Ommu ta takura mata, baiwar Allah ta rasa ya zata yi, har ƴar rama ta yi, shi kuma Akil ya zuba musu idanu yana kallonsu tun da taki gaya mishi abin da yake faruwa, bai tuna mata ya sani ba, dan idan ya kuskura ya nuna mata ya sani, zata fahimci kamar yana biniyarta ne, abin zai zama kaman zargi a tsakaninsu, zata daina yarda da shi, haka zalika ko magana take yi da ƴan uwanta, zata rinƙa shiga ruɗu da damuwar ko dai yana kallonta, ko dai yana jinta, bazata sake yarda ta saki jiki ta yi magana da wani nata ba, dan zata tunanin zai ji ta, hakan ba karamar matsala zata haifar musu ba, shiyasa ya yi shiru, kuma yana son fitar da ita daga cikin damuwar da take ciki, yana son ta faɗa mishi da bakinta sai ya bata mafita, amma ita kuma ta kafe ta ki faɗa, dan Ommu ta ce mata idan ta faɗa zai yi mata gori, shi ne ta adana sirrinta kada ya yi mata gori. A ɓangaren Irfan kuwa, har yanzu yana fama da dakon soyayyar Akila, sai dai ya fawwalawa Allah komai, baya kiranta a waya, dan ko ya kira ba zai same ta ba, kuma kunsan bai isa ya ce zai je gidansu ba, Hjy Umaiya ba zata yarda ba, kullum yana Sallah yana roƙan Allah da ya zaɓa mishi abin da yafi zama mishi alkhari a rayuwarsa baki ɗaya, wani kayan haushi, kullum son Akila ninkuwa take yi a cikin zuciyarsa, bawan Allah duk ya rame, bai cika zuwa aiki bama, ya barwa Abbi companynsa, shi kuma Abbi bai kawo komai a ransa ba, ya yi tunanin abubuwa ne suka riƙe ɗan nasa, dan ya ce yana son ya cigaba da karatu, a tunanin Abbi shi ne yasa ya shiga busy kwana biyu, bai san cewa ɗan nasa faɗa yake ta faman yi da zuciyarsa ba. Idan muka koma ɓangaren gidan Lion kuwa. Sai dariya Rimsha take yi musu, abincin ta ɗebo a cikin spoon nata ta kaiwa Areef saitin ɗan bakinsa tana faɗin "Yaya Areef to ni tun da yaya Aseef ya cinye mini first spoon ɗin da ka bani, ni bari na baka nawa". Buɗe ɗan bakin nasa ya yi yana ƙoƙarin karɓa, da sauri Aseef ya matso ya karɓe yana faɗin "Kowa a cikin gidan nan ni ne zan rinƙa cin first spoon na shi, shi ma Lion ai ni yake fara bawa, dan haka kema ni zaki fara bawa". Duka Areef ya kai mishi, da sauri ya kauce yana dariya "Areef wlh idan ka taɓa ni yanzu ina da mai rama mini, zata shigar da kai kara court na gaya maka, dan ba zata yarda ko kuda ya taɓa ni bata yi mishi hukunci ba". Turo ɗan bakin nan Rimsha ta yi, a shagwaɓe ta ce "Yaya Areef buɗe baki bari na baka second spoon to, rabu da yaya Aseef ɗin nan, mun ɓata da shi". Ba musu ya buɗe baki, ɗabowa ta yi ta kai mishi sai tin bakinsa, karɓa ya yi tare da karɓar spoon ɗin nata, a hankali ya fara taunar abincin, ɗebowa ya yi shima ya kawo mata saitin bakinta, bata kai ga karɓa ba, Aseef ya tura mata nashi da ya ɗebo yana faɗin "Nawa zata fara ci". Haushi kamar Areef ya kifa mishi mari, Aseef ba dai neman magana ba, ya iya kamar me, bayan ya zuba mata a bakin nata ne ya zare spoon ɗin ya sake ɗebar wani abincin tare da miƙewa ya nufi wajen Lion, binshi da idanu suka shi, shi Areef yasan in dai Aseef ne ya bawa Lion abu, to ko baya so zai ci, ita kuma Rimsha har ta fara tunanin yadda zai yi ball da spoon ɗin, bata san cewa Aseef pleasure sa bane. Kusa da shi ya karisa tare da kawo mishi spoon ɗin saitin ɗan bakinsa, kin buɗe baki ya yi, dan ko warinta baya son ji, ya ga kokarinsu ma da suka iya cin har two two spoon's, kuma ya jinjinawa Rimsha kamar yadda ya faɗa, shagwaɓe murya ya yi kamar zai yi kuka "Please mana my pleasure, idan baka ci bafa, ba ni ba barci yau, haba mana son ɗin daddy". Idan suka kira shi da wannan sunan na son yana tuna mishi abubuwa da dama da suka wuce, suna ne da daddynsa yake kiran shi da shi tun ranar da aka haife shi, har ya kai 13 years kafin daddy ya dai'na kiran sunan, ba kuma wai ya daina gabaɗaya ba, a'a yana kira, amma sai idan yana rarrashin shi a kan abu, sai ya rinƙa ce mishi haba my son, ka yi kaza mana, to sunan tana da matukar muhimmanci a wajensa. Ba dan yaso ba ya buɗe baki ya karɓi abincin, a nutse ya tauna yana mai jin wani irin yanayi a tattare da shi, wai yau shi ne ya ci abincin Naija, abincin ma na Rimsha, gaskiya TRIPLETS ba su kyauta mishi ba, shi kuwa Aseef da yake gwani ne a neman magana har da wani cewa ya karo Mishi ne ko kuma ya ɗauko mishi har da plate ɗin ma baki ɗaya, buɗan bakinsa sai ya ce a'a ba iya plate ɗin ba kawai, ya ɗauko mishi har da mai abincin ne ya manta, Aseef da iya shege, yana sane sarai magana Lion ya gaya mishi, amma saboda neman rigima sai ya je ya kamo hannunta, shi dai Areef sai binsu da idanu yake yi, kusa da shi Lion ɗin ya zaunar da ita tare da riƙo hannun ta ya sanya cikin na Lion ɗin yana faɗin "To ga mai abincin nan". Rai a matukar ɓace ya kwace hannunsa tare da kaiwa Aseef ɗin damka a wuya, ya miƙe tsaye, da karfi ya shaƙesa, Areef kuwa gyara zamansa da kyau ya yi ko ajikinsa, dan sun fi kusa, shi nashi ido ne kawai, a guje ta miƙe zata bar wajen, da hannu guda ya damkota tare da dawo da ita kusa da Aseef ɗin, shi kansa ya rasa wani irin hukunci zai yi musu, yau ransa ya ɓaci sosai tun da har ya iya shake Aseef mai gabaɗaya, wlh Areef ko a jikinsa, Tv ma ya mai dasu, har da guntun murmushi, dama yasan za'ayi hakan, shi ma Aseef ɗin ganganci ne sai kace bai san halin ɗan uwan nasu ba, zai ja a kashe ƴar mutane a banza. ASEEF Da kyar ya iya buɗe baki ya ce "Lion ka shake ni, ita kam ka sake ta, ai ba laifinta bane, bata san komai ba, ni nayi laifi". Sai lokacin ya dawo da kallonsa kanta dan yaga wai shi wannan wace iriyar yarinya ce, cikin tsawa ya ce mata "Me kika yi musu da har suke sonki fiye da kansu?!" Ya yi maganar tare da zame hannunsa daga wuyar Aseef ɗin ya damko nata wuyar, dama ga wuyan nata ɗan siriri, dogo zai yi daɗin shaƙa, "Ba dake nake magana bane?!" Ya sake daga mata tsawa, tamkar zata saki fitsari a wando, ta yi bala'in tsorata na karshe, ya shaƙeta sosai ba ta yadda za'ayi ta yi magana, sai girgiza mishi kai take yi, hawaye wani na bin wani daga idanunta zuwa kuncinta. Zubawa face nata ido ya yi, wannan fuska nata a duk san da ya gani sai tsikar jikinsa ya tashi, tabbas koma wace ce mai irin wannan face ɗin tata, tana da matukar muhimmanci a rayuwarsu, ya zama dole ya san wace ce, shiru ya yi yana kallonta ba ko kyaftawa, ya kasa kawar da kallonsa, duk da hakan yana sa tsikar jikinsa gabaɗaya ya rinƙa tashi, tabbas akwai wani sirri tattare da wannan yarinya, ba'a banza su Areef suke sonta har haka ba, ga shi shima yanzu ya tashi da zafinsa zai mata hukunci, daga ganin face nata ya ji jikinsa ya mutu, dole akwai dalili. Ganin ya yi shiru yana kare mata kallo ne yasa Areef miƙewa ya kariso wajen nasu, shi ma Aseef ido yake binsu da shi, sai mamaki yake yi na irin kallon da Lion yake yi mata, ga shi kuma ya shaketa bai sake ta ba, kamar zata mutu, shi kuma sai ƙoƙarin karantar face ɗin nan nata yake yi ko zai iya tunano wace ce mai irin shi, a ina kuma yake yawan ganinsu da Josephine, dan baya son ya tambayi Josephine kai tsaye, yafi so sai ya yi bincike a kan faɗar tsakaninta da daddynsu ya gano mai gaskiya kafin ya yi magana da ita, amma wannan mai face irin na Rimshan ta tsaya mishi a ransa, ta hana shi sukuni, duk yadda aka yi, alaƙa mai karfi ne a tsakaninsu. "Lion ka sakar mata wuya kada ta mutu". Shi ne abin da Areef ya faɗa da ya kariso wajen, jin voice ɗin ɗan uwan nasa yasa ya zame hannun nasa da wuyarta tare da juyawa da sauri ya bar wajen, bin shi da kallo suka yi, da sauri ita ma ta bar wajen dan ta tsorata da irin kallon da yake yi mata, ba shaƙeta da ya yi bane ma ya dameta, tsoronsa ya fi wannan shaƙewa rikitata, ƙanƙame wuyar tata da hannayenta dukka biyu tayi, da kyar take numfashi ta nufi bedroom nata. Aseef ne ya matso kusa da Areef ɗin yana faɗin "Me yake damun Lion ne? Ko dai yana son sister ne". Nisawa Areef ya yi "Ko kusa ko alama, a yanzu dai babu sonta ko ɗigo a ransa, ina ganin dai akwai abin da yake nema a tattare da ita, idan hasashena ya zama gaskiya a matsayina na jami'i, ko dai tana yi mishi kama da wata da ta tsaya mishi a rai, ko kuma akwai abin da yake bincika a kanta, akwai dai wani abin a kasa, amma ba soyayya bace, sai dai ina fatan hakan ya zama soyayya a tsakaninsu, tabbas zai bukace ta dan bincike, ina fatan hakan ya zama sanadiyar faɗawar shi soyayya da ita, ina son ganin ta cikin farinciki, ina son ganin ta sami abin da take so, ya Allah ya tabbatar mana nan ba da jimawa ba". Shiru Aseef ya yi, ya shiga duniyar tunani, ko Amin ɗin ma bai iya amsawa da shi ba, to wace ce Lion zai rinƙa gani tana yi mishi kama da sister? Aseef ne ya yi wa kansa wannan tambayar a cikin zuciyarsa. Sun jima tsaye a wajen suna tattaunawa, daga bisani Areef ya ɗaukawa Rimsha abincinta ya bi bayanta da shi, dan yasan yunwa take ji, shi kuma Aseef ɗakin Lion ɗin ya nufa bayan ya ɗauka mishi laptop nasa da wayarsa da ya bari a garden ɗin. Kwance ya iskota a saman bed nata, ta yi shiru tana tunanin yadda ta ga fuskarsa kusa da kusa yau, sai taga ya yi mata kama da wani wadda ta sani, sai dai ta rasa wanene, yau kewar ƴan uwanta ya dawo mata sabo, tunani take yi ko a wace duniya suke yanzu Oho. Gefen bed ɗin ya zauna tare da ɗaura mata abincinta a saman bedside drawer, rarrashinta ya fara yi yana bata hakuri tare da yi mata alkawarin akan Lion ba zai sake yi mata hakan ba, dan kuwa, idan ya canka daidai, mai irin wannan fuska tata tabbas ta tsayawa Lion a rai, kuma da alama a yinwa ce yake da ya san wace ce, so zai rinƙa binta a hankali. Da kyar ta ƙaƙalo murmushi dole ta yi mishi tare da miƙewa zaune, abincin ya ɗauko ya miƙa mata, kusan a tare suka ci, dan sai da ya taya ta ci, saboda ita yau har daɗin abincin ya ji, sai da ya tabbatar da ta ƙoshi tap, ya miƙe ya nufi waje yana yi mata sai da safe. Yana fitowa palon sama suka ci karo da Imran da jelly, cike da kulawa ya ce "Prof ina kuma zaku je a daren nan?". Ganin shi yasa jelly ta ɓuya a bayan Imran, dan mutuwar tsoron shi take yi, har wani duhu duhu ta fara gani. Ƴar murmushi ya yi yana faɗin "Jelly ta ce mini ba zata zauna a ɗakin sama ba, wai kuna nan sama, tsoronku take ji, dan haka mu koma ɗakin kasa". Jinjina mishi kai ya yi tare da wucewa ya shiga ɗakin Lion ba tare da ya sake yin magana ba. Zaune suka isko Lion a saman gado, duk wasu kaya na mummynsa da ta bar mishi ya watsasu yana dubawa, da mamaki Areef yake bin kayan da kallo, kwata kwata ma shi bai san da waƴan nan kaya nata ba, ga shi babu hoto a ciki ko gwara ɗaya da zai gani ko dai a cikin kawayenta ne mai irin wannan fuska take, wani zuciya ce ta ce mishi to ya ɗauki Rimsha a hoto mana ya turawa Josephine ɗin, ya tambayeta wace ce mai irin wannan face ɗin, nan take ya ɗaure fuska yana faɗin no, shi baya neman taimakon kowa, komai da kansa yake yi, ɗauko hotunan Josephine ɗin ya yi daga cikin wannan ɗan akwatin, lokacin tun tana budurwa, duk hotunan ita kaɗai ce, babu ita da kawa ko ƴar uwa, a lokacin face nata sak na Aseef, ba karya Josephine kyakkyawar gaske ce, hancin nan nata kamar ita ta yi wa kanta, ga ɗan karamin red mouth nata irin na Lion ɗin sak. Hotunan daddynsa ya kuma kwasowa, lokacin daddy na saurayi, yadda kasan Lion photo copynsa ne, da yana saurayi sak Lion ɗin, dama ga kalar idanunsu ɗaya, su dai su Areef zama suka yi suka zuba mishi idanu suna ganin ikon Allah ikon gaske, duk ya watsa komai da komai, sai dai babu komai a ciki da ya danganci abi da yake son sani, kwashe su ya yi ya mayar, da nufin idan ya gama bincike a kan daddyn Rimsha zai waiwayesu, koma wace ce kuma kome alaƙarsu sai ya gano, dan ba ta yadda za'ayi yana kallon Rimsha tsikar jikinsa na tashi kamar ba lafiya ba ace kuma babu wani abu a tsakaninsu, ina ba zai yiwu ba. Bayan ya mayar da kayan kyakkyawar mazaunin da ya yi musu, toilet ya wuce dan ya yi wanka, ruwa mai sanyi ya sakarwa kansa dan ya samu zuciyarsa ta yi sanyi, yana shiga toilet Areef ya ɗauko laptop nasa ya fara bincike a cikinta dan ya gane menene ainahin matsalar ɗan uwan nasa, shi kuma Aseef abinci ya wuce ya je ya ɗauko musu dan su ci. After some minutes, bayan ya kammala shiri cikin kayan barcinsa masu shegen kyau da tsada, sai tashin kamshi yake zubawa kamar me, wajen abincin ya nufa, suna zaune suna jiransa, Aseef shi ya yi serving nasu a plate guda, a nutse suka fara cin abincin, ba wanda ya ce da ɗan uwansa ko uppan, har suka kammala cin abincin suka miƙe, Lion ne ya fara tashi ya haye bed nasa, Aseef ya kwashe kayan abincin ya fitar, ya dawo ya gyara wajen. Dukkansu gadon Lion ɗin suka haye dan su sanya shi nishaɗi, sun san yana cikin damuwa, sun ko yi nasara, sai da suka saka shi nishaɗi, suka sanya ya mance duk wani abin da yake damunsa, Allah sarki ƴan uwa rabin jiki, sai dai kuma har gobe yaki ya yi koda murmushi ne su gani, abin yana damun Aseef sosai, shi kam Areef normal ne, ko a jikinsa, ba dai ya tabbatar da ɗan uwan nasa ya yi murna ba? Hankalinsa ya kwanta, to ba sai ya yi murmushi ba. Da kyar suka rabu da ɗan uwan nasu suka koma ɗakin Areef, Aseef ya ce ba zai kwana shi kaɗai ba, tare suka kwana da Areef, suna kwanciya ba jimawa Areef ya yi barci, shi kuma ya hau aikin waya da Heartbeat nasa, sai zuba mata shagwaɓa yake yi, tana zuba mishi nata ita ma, kamar dai yadda suka saba, haka suka raba dare, sai misalin karfe 3 na dare suka yi sallama ya yi mata sai da safe, kwata kwata bai so su rabu ba, dare ne ya yi sosai yasa ya hakura, yana ajiye wayar ya yi addu'ar barci, ba jimawa barcin ta yi awon gaba da shi. ASUBA TA GARI. Washegari da safe, misalin karfe 8, ta tsara wankanta cikin pakistan na Indiyawa, ta yi kyau sosai, wandon farine tas mai ɗan faɗin, riga kuma launin blue, mayafin ma blue ne kalar rigar, ta yi kyau sosai ba kaɗan ba, sai tashin kamshi take yi abinta. Palo ta fito, babu kowa, kai tsaye ta nufi garden dan tasan da wuya idan bata same su a can ba, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga wajen, suna zaune su biyun, kowannensu yana latsa wayarsa, sun yi shiga iri ɗaya, ga shi dukkansu sun sanya black glass a face nasu, no respect, idan har ba irin Rimsha da ta yi musu farin sani ba, to da wuya mutun ya iya banbantasu, wandunan jean ne blue color a jikkunansu, sai kuma riguna polo t-shirt farare tas, ga gashin kan nasu ma iri ɗaya, dukka brown hair ne, sai dai na Aseef ya fi shiga brown sosai, na Areef ya ɗan yi haske, amma sai ka lura zaka gane hakan. Ganinta yasa suka saki cool murmushi a tare, ita ma cool murmushi ta sakar musu tare da karisawa ciki, kamar abin haɗin baki suka wani matsa mata tsakiyarsu akan tazo ta zauna, zata wuce zuwa ɗayar kujerar Areef ya jawota ta zauna a tsakanin nasu. "Good morning my lovely brothers". Cikin sanyin murya ta yi maganar, Areef ne ya iya amsa mata, shi kuwa Aseef yana can duniyar sahibar tasa, baya tare da su, "Muje sayan abinci ko?". Cewar Areef "Yaya Areef zaka ci abincin ne?" Gyaɗa mata kai ya yi alamar e zai ci. "Yaya Areef da gaske kana son abincin mu?" Ta yi maganar cikin zumuɗi, fuska ɗauke da mamaki. "Sosai our Queen, wlh abincinku is so sweet, jiya baki ga naci ba? Amma matsalar ni bana son abincin restaurant ne, idan zaki rinƙa girka mana, to zan rinƙa ci sosai, bamu taɓa cin abincin restaurant ba sai jiya, duk wuya duk daɗi a gida muke cin abinci, idan tafiya ta kamamu, muna tafiya da mai yi mana girki, duk in da muka je, shi zai yi mana girki". "Yaya Areef to ai wannan Mark ɗin ya hanani yin girki, ranar da nayi ya zubar" "Akan me zai zubar miki?!" Ya faɗa a ɗan zafafe, "Nima ban sani ba". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Okey yanzu dai zamu je mu sayo abincin, amma in the afternoon ke zaki girka mana, nima kuma zan taya ki yin girkin, jeki wajen Lion ki ce nace ya baki kuɗi zamu je sayan abu, daga nan sai mu je wajen gyaran gashi ko?". Cike da mamaki ta ce "Yaya Areef waye ya ce maka ina son a gyara mini gashi na?" Kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Ai duk abin da yake da mahimmanci a wajenka, to ya zama maka dole ne ka rinƙa gane abin da yake buƙata, ke dai jeki ki karɓo mana kuɗi kizo, zan baki mamaki yau, zan saya miki abubuwan da kike buƙata wadda baki san kina da buƙata ba". Shiru ta ɗan yi tana tunanin ta yadda zata shiga ɗakin Lion ta ce ya bata kuɗi, ɗan dafa ta ya yi yana faɗin "Ki je babu abin da zai faru". Mamaki ne ya kara kamata, wai shi yaya Areef ɗin nan waye yake gaya mishi abin da yake zuciyar tane? Bata san da babban jam'i hukumar sirri take tare ba. Jiki ba kwari ta miƙe ta nufi bedroom ɗin na Lion, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga, babu kowa a ɗakin, ɗan leke leke ta yi mishi, shiru babu kowa, juyawa ta yi zata fita kenan wayarsa dake saman bed nasa ya fara kara alamar shegowar kira, Babu ko tsoro ta juyo ta dawo wajen wayar nasa, video call ne, ake kira, My dad shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, ba tsoro bare tunanin me zai je ya zo, kwata kwata ta manta wayar waye zata ɗauka, zuciya ya ɗebeta, shaiɗan ya zugata, ɗaukar wayar tayi, taɓe taɓe ta fara yi har ta yi picking call ɗin, a matukar razane ta saki wayar ya faɗa a kan gadon, hakan ya faru ne kuma sakamakon yin ido huɗu da blue eyes na daddy da ta yi, sai dai kuma bata kawar da kanta daga kallon shi da take yi ba, yana zaune a saman bed nasa, ya yi kewar ɗan nasa ne yasa ya kira, ganin ta yasa ya yi muguwar ɗaure fuska da bai taɓa yin irin shi ba, wani uban tsawa ya daka mata akan ina mai wayar? Me kuma ya haɗa ta da wayar? Cikin tsoro ta fara tattaɓa screen ɗin wayar dan ta katse kiran, hannunta sai kerma yake yi, kirjinta na dukan uku uku, sai yanzu da aikin gama ya rigada ya gama ta tuna da wayar waye ma ta taɓa, hankali a matukar tashe take ta faman katse kiran, sai magana daddy yake yi mata bata amsa ba, da kyar ta samu ta katse kiran tare da kwasawa da gudu ta nufi waje. Bata zame ko'ina ba sai garden, yadda ta barsu haka ta dawo ta same su, a bakin garden ɗin ta tsaya ta daidai ta natsuwarta kafin ta shiga, bata bari su Areef sun gane abin da ta yi ba, a nutse ta ce mishi Lion baya ɗakin, taɓa Aseef ya yi tare da ce mishi ya je ya ɗauko musu kuɗin su tafi kawai. Okey ya amsa da shi tare da miƙewa ya nufi cikin gida, shi kuma ya miƙe ya riƙo hannunta suka nufi wajen mota, da shigarsu bai fi 2 mins ba, sai ga Aseef ɗin ya dawo hannunsa riƙe da key ɗin motar da kuma kuɗin, mazaunin driver ya shiga tare da kunna motar, tun kafin su iso gateman ya wangale musu gate ɗin, da gudu ya kutsa hancin motar waje, sai dukan uku uku kirjinta yake yi, addu'a take yi Allah yasa kada Lion ya gane ta ɗauki wayar............ TO SAI DAI MU CE AMIN, AMMA DA KAMAR WUYA DAI. ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E27-28 "Ina muka nufa Areef?" Cewar Aseef, kallon Rimsha dake ta faman kallon titi ya yi, "Sister ina zamu fara zuwa? Super market ko kuma restaurant?". Jin voice ɗinsa sai da ya sanya gabanta ya yi wani mummunar faɗuwa. "Restaurant" ta bashi amsa tana kallon hanya. "On Monday zaki fara zuwa school ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar eh, dogon hancinta ya yana faɗin "To kin dai shirya ko?" E ta bashi amsa, shi kam Aseef sai tuki yake yi yana latsa waya, ga shi sai zabga uban gudu yake yi kamar babu gobe, ɗan uwan nasa kuma bai wani damu da ya hana shi taɓa waya yana tuki ba, ya mance cewa nan fa ba Washington DC bane, a Washington DC ne idan aka ga motocin gidansu sun hau hanya, abubuwan hawa ke kaucewa su basu hanya, shiyasa suke yin duk irin tukin gangancin da suke so a kan hanya, dan babu wani abin hawa da zai keta da gabansu, a nan Nigeria kuwa, basu san gidan jajayen wuya suka zo ba, yo ko doka ce a ka kafa ƴan Nigeria irin haka, ai sai sunci uwar dokar sun kora da ruwan mai sanyi daga fridge, koma uban waye yazo wucewa a kan titi ƴan Naija babu ruwansu wucewa zasu yi, idan ya ga dama ya wuce ko ya tsaya matsalar sa ce, su dai sun rigada sun wuce. Restaurant da suka je jiya, shi yauma suka je, yau dai a nan suka ci abincin, sai kallonsu jama'a suke yi, sun ga masu jajayen kunnuwa, fararen tattabaru, kyawawan gaske, kamar dai ko yaushe sai aikin latsa waya yake yi, yana makale da Heartbeat nasa suna hira, ya hanata ko motsawa, Rimsha da Areef sai zuba hira suma suke yi, cikin natsuwa suka ci abinci, sai dai Aseef bai ci ba, ya ce ba zai iya ba, Areef ne kaɗai ya tayata ci. Bayan sun kammala Areef ya biya kuɗin suka fito daga wajen suka nufi super market, suna tafiya suna hira, sai bata labarin Washington DC Areef yake yi, tana ta murmushi. Tasha ruwan mamaki lokacin da suka je super market ɗin nan, kayayyakin da take mutuwar so Areef ya rinƙa zaɓa mata, sai tunani take yi a kan waye ya gaya mishi abin da take so kenan, har da takalma high heels irin wanda take so ya kwasa mata, ta sha sayayya iya sayayya ba karya, a nan ne Aseef yake gaya mata ai shi ma ya saya mata kaya, har da abin wuya irin nasu da ya ce zai sa a buga mata, to ya bugo ya zo mata da shi, yana cikin wannan akwaitin da ya ce ta ɗauka jiya bata ɗauka ba, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, cike da murna ta ce su koma gida, dan ta je ta kalli kayan, to suka amsa mata tare da nufar wajen biyan kuɗi. Areef ne ya biya, ma'aikatan wajen suka ɗauka masu kayan zuwa wajen motarsu, a gidan baya suka sanya kayan, kamar yadda suka zo, ita da Areef a kujerar gaba, shi kuma Aseef driver, haka suka sake shiga suka nufi gida, sun manta da batun gyaran gashi. Suna tsaka da tafiya a hanya daddy ya kira number Aseef, ya sha ruwan mamakin ganin call ɗin daddy da safiyar nan, yana can yana tunanin ko lafiya daddy ya kira shi, sai da wayar ta kutsa matsewa, ya yi maza ya ɗauka tare da sanyata a hand-free dan yana tuƙi. "Hello daddy good morning?". Wani irin mahaukacin tsawa ya daka mishi wadda ya sanya shi taka birki a tsakiyar titi, saura kaɗan motar dake biye da su a bayansu ta dake su, sai Allah yasa ta kauce, daga Rimsha har Areef sai da kansu ya bugu da jikin glass ɗin motar, saboda irin birkin da ya ja babu excuse. "Michael wace ce ta ɗauki wayar Romeo yanzun da na kira shi?! Na sake ina kiran shi baya ɗagawa, shin a ina ma kuke tukunnan?!!". A razane ya ɗago yana kallonta, dan yasan ita ce ba makawa, daddynsu bai taɓa yi musu magana cikin irin wannan matsanancin siga mai cike da tashin hankali ba, to menene matsalar?. Nan take shi ma tsantsar bala'in ɓacin rai ya bayyana a saman fuskarsa, tabbas yasan yau ba ƙaramin yaki za'a sha ba a Washington DC, dan kuwa idan daddy ya san suna Nigeria akwai bala'i ba kaɗan ba, sun ce mishi suna Spain ne wajen James, ba zai taɓa yarda su yi nisa har Nigeria ba, fatansu dai Allah yasa kada ciwonsa ya tashi, shi kansa Areef yau idan ransa ya yi dubu to ta ɓata mishi, ina ga kuma Romeo? Shi da ta ɗaga kiran na shi, Aseef jikinsa har rawa yake yi saboda tsantsar ɓacin rai, ji yake yi yau idan bai ɓalla yarinyar nan ba, ba zai sami kwanciyar hankali ba, yarinya bata ji sam, me ya kai ki taɓa waya ke da akace ki karɓo kuɗi?. "Daddy am coming". Yana kai karshen maganar ba tare da ya jira me daddy zai ce ba ya yi diff ya katse kiran, a fusace ya juyo da kallonsa kanta, cikin ɓacin rai da kakkausar murya ya fara magana "Me yasa kika taɓa wayar Lion? Kin san abin da zaki jawo mana kuwa?!". Ɗaga mishi hannu Areef ya yi alamar ya yi shiru, ba musu ya yi shirun, da hannu ya sake nuna mishi hanya a kan su tafi sun tsaya a kan hanya, kunna motar ya yi zuciyarsa na tafasa, bawan Allah baya son ɓacin rai sam, amma yau sai da Rimsha ta ɓata mishi rai, shi ma Areef dannewa kawai ya yi dan ko sun ce dukanta zasu yi ma, a cewarsa me zai daka a jikinta, abu kamar ka lometa ka kora ruwa. Tsantsar bakin ciki ya hana Areef magana, dama kunsan ance mai hakuri, shiru shiru, mai fara'a, bai iya shiga ɓacin rai ba, idan ransa ya ɓaci sai ya jijjiga kowa dake kusa da shi, hakan yasa ya daure ya yi shiru yana karanta لَا إلَهَ إلَّا اللهُ وحْدَهُ لَا شَرِيكَ لهُ، لهُ المُلْكُ ولهُ الحَمْدُ، وهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيْرٌ. [عشر مرات](١)أو [مرة واحدة](٢). Dan ya sami zuciyarsa ta yi sanyi cikin ƙanƙanin lokaci, idan ba haka ba, zai iya yi wa Rimsha mari ɗaya ba tashi, dan kule shi, fitinarta ya yi yawa. Shiru suka yi babu wanda ya sake ce da wani ko uppan, haka har suka isa gida, suna parking na motar ta fito ta nufi cikin gida dan ta je ta yi wanka ta cire kayan jikin nan nata, ice cream ya ɗan zuba mata a kan kayan, har ta kai kofar shiga Palo, sai kuma ta juyo da sauri ta dawo, Areef yana tsaye ya ɗan jingina da jikin motar yana binta da kallo, shi kuma Aseef ya zagaya ta wajen pool a in da yake zaton zai sami Lion a wajen, gaban Areef ta dawo, cikin sanyin murya ta fara magana "Yaya Areef dan Allah kayi hakuri, ba zan sake ba, ka bawa yaya Aseef hakuri, dan naga ransa ya ɓaci sosai, In Sha Allah ba zan sake ba". Tana magana tana murza ƴan yatsun hannunta. Hannun nata ya kamo cikin nashi, "Ba komai ki rinƙa kula Kinji? Laifi nane da na aike ki ɗakin, da ya kamata naje da kaina ne, laifin ki ke kuma da kika taɓa wayar, ki sani zuciyar Lion ba irin tamu bace, mu muna iya controlling namu, shi kuma ba haka yake ba, idan kika yi mishi abin da ya ɓata mishi rai, a lokacin zai buɗe miki aiki, kuma na sha gaya miki hakan, kada ki kuskura ki shiga gonarsa, yanzu kinga dole zai ɓata rai, ko in ce miki zamu ɓata rai, daddynmu bai san muna Nigeria ba, ba zai taɓa yarda mu zo Africa ba, dan ta yi nisa da shi sosai, yanzu yana tunanin muna Spain ne, shiyasa ya hakura ya daure ya zauna a Usa, daddy ba zai iya nisa damu har haka ba, bai taɓa ba kuma ba zai iya ba, idan har yasan Nigeria muke, ba zai taɓa yarda ba, zai ce sai ya biyo mu ko kuma mu dawo yau yau ɗin nan ba sai gobe ba, kuma kinga akwai aikin da muke yi a nan, yanzu dai shiga ciki, amma dai akwai matsala". Duk jikinta ya yi sanyi da jin maganarsa, ta yi kuskure, su kuma basu son daddy ya ce zai zo Nigeria, dan yanayin jikinsa, tafiya mai tsawo ba karamar wahala zai sha ba, jiki a mace ta nufi cikin gidan dan yin wanka, tana shiga bedroom nata ta wuce toilet. A ɓangaren Aseef kuwa, yana isa wajen pool ɗin shi kuma Lion yana fitowa zai nufi cikin gida, a tare suka jera zuwa cikin gidan, kwata kwata bai gaya mishi abin da yake faruwa ba, a palon kasa suka rabu ya wuce bedroom ɗin Areef, shi kuma Lion ya haura sama zuwa nasa bedroom. Yana shiga cikin ɗakin ya ɗan tsaya shiru yana tunanin me ya kawo wannan yarinyar yau kuma ɗakinsa, dan ya tsinci kamshin perfume nata a cikin nasa, dressing room nasa ya wuce. After some minutes ya fito sanye da wandon jeans fara tas zuwa gwiwarsa, sai riga polo t-shirt ita ma fara tas, ba ƙaramin kyau ya yi ba, saman bed nasa ya zo ya zauna, sai tashin kamshi yake yi, ɗan bakin nan nasa kamar ya sanya jan janbaki, sai wani kyalli ɗan bakin nasa yake yi. Wayarsa ya ɗauka, ya sha ruwan mamaki lokacin da ya kalli miss call ɗin daddy almost 10, shiru ya ɗan yi kafin ya cire password ɗin wayar, ɗan waro idanunsa waje ya yi lokacin da ya kalli an yi picking na first call da daddy ya yi, bai kawo komai a ransa ba, ya yi tunanin ma Aseef ne ya yi picking, cikin kwanciyar hankali ya fara kiran daddyn video call, tamkar jiransa dad yake yi, bugu ɗaya ya ɗauka, fuskar nan nasa a ɗaure tamau, yau ya fito a ainahin dangerous Boss ɗinsa, zuba mishi idanu Lion ya yi yana kallon shi, bai ce ko uppan ba. "Who is she Romeo?" Shi ne tambayar da ya fara yi mishi, shiru ya yi bai amsa ba. "Me haɗinta da kai? Meyasa wayarka zai kasance a hannunta?" Nan ma shiru ya yi bai yi magana ba, sai bin daddyn nasa da ido kawai yake yi. Tsawa daddyn ya daka mishi "Am i not talking to you?!" Ɗan zaro idanu kaɗan ya yi yana mamakin, wai yau shi daddy yake yi wa tsawa har haka lallai. "Romeo am i your mate?!" Nisawa ya yi kafin gently ya fara magana "Daddy i don't know what to say, because i don't know what you are talking about ". "Romeo how comes za'a ce mace ta ɗauki wayar ka kuma ka ce you don't know her, how this can be possible?". Shiru ya yi dan shi ba zai iya wannan surutu na daddy ba. "Romeo a ina kuke yanzu haka?" Kai tsaye ya amsa mishi da "Nigeria". "Nigeria kuma?" Jinjina mishi kai ya yi alamar tabbatarwa. "Okey yanzun nan ku haɗa kayanku ku dawo, yau ba sai gobe ba, kuma i really hate this girl that a saw koma wace ce". "Ba zai yiwu ba daddy, sai na kammala abin da nake yi zamu dawo". Ya yi magana a nitse cikin kwanciyar hankali. A fusace dad ya miƙe tsaye, cikin fushi da kausashiyar murya ya fara magana, "Romeo I'm your father who born you not your friend or your Triplets!! So is better for you ka san irin maganar da zaka rinƙa gaya mini". Shi ma a wannan karon ranshi ya ɓaci, baya son hayaniya ko kaɗan, daddy ya zo yana ta wani daga mishi tsawa, a fusace ya miƙe tsaye, cikin tsawa da ɗaga murya ya mayarwa da dad amsa kamar haka "I'm so what dad, am so what if it is you had born me? Take me back to your womb!" Tashin hankali da ba'a sama mata date. "Romeo are you hard what you said? Are you forget who you're talking with?!!". "Am talking with father of TRIPLETS so what,?". Babbar magana!!. Dafe saitin zuciyarsa daddyn ya yi, cikin kunan rai ya buɗe baki da kyar ya furta "Romeo umarni nake baka yau ba sai gobe ba ku dawo Usa". "Daddy ba zan dawo ko'ina ba har sai na kammala abin da nake yi, so ya rage naka ka hakura ko ka ɗauki mataki, ni dai na gama maganata, ba kai zaka rinƙa gaya mini abin da zan yi ba, a matsayina na soja aiki yana iya kaini ko ina, so ba umarninka zan bi a kan aikina ba that's all!!". Shaiɗan da zuciya sun ɗebesa sosai yau "Romeo so kake yi ka kashe ni ko?". Shiru ya yi dan idan ya ce zai buɗe baki zasu yi kaca kaca da dad ne, saboda babu wanda ya isa ya ce mishi ga abin da zai yi, sai wanda ya yi niyar yi, a cewarsa, daga karshe ma katse kiran ya yi tare da yin wurgi da wayar a saman gado, cikin zafin nama ya nufi waje, kyawawan gashin dake kwance a hannunsa har wani miƙewa suke yi saboda ɓacin rai, Rimsha ta raina shi da har zata ɗauka mishi waya, ga shi tasa dad ya zo yana yi mishi hayaniya a kai, kuma kowa yasan shi mutun ne da baya son magana ma bare hayani ya, ta ja ransa ya ɓaci ya mayarwa da daddynsa magana, duk da cewa su yin hakan ma a wajensu ba wani laifi bane, wai dan yara su mayarwa da iyaye magana, ba su ɗauke shi a matsayin wani laifi ba, domin tun farko a kan hakan iyayen ke renan ƴaƴan, su sunma yi ƙoƙarin da har suke iya dannewa suna yiwa dad ɗin su biyayya, amma ba dan haka ba kowa yasan yadda ainahin rayuwar turawa yake, yara suna da dama da ƴancin yin komai da suke so, doka ce a dokonin kasarsu, ciki kuwa har da rufe iyaye a prison yara suna yi, a takaice dai da yara da iyaye su duk ɗaya ne a wajensu. ALHADULILLAH DA ALLAH YA YI MU A WAJEN DA MUKE YIN KASA DA MURYA A GABAN IYAYENMU, WANNAN MA KAƊAI BABBAR NI'IMA CE A GARE MU. Yana fita bai zame ko'ina ba sai bedroom nata, lokacin da ya sako kansa ya shigo ɗakin, ita kuma ta fito daga toilet ɗaure da towel a kirjinta, da alama wanka ta yi, ganinsa yasa ta watsa a guje ta koma cikin toilet ɗin, da karfi ta banko kofar har da murza key, rai a matuƙar ɓace ya karisa wajen kofar, da karfi ya sanya kafa ya take kofar, wani irin jijjiga ta yi bata buɗe ba, sake ɗan komawa baya ya yi, a zafafe ya take ta da karfi, sai ga kofar ta ɓalle, ihu ta kurma ganin hakan, takawa ya yi cikin zafin nama ya damko gashin kanta, dama ga shi babu ɗankwali a kan nata, ta saki gashin har baya, jawota ya yi da gashi har zuwa tsakiyar ɗakin, wurgi da ita a kasa ya yi, rai a matukar ɓace ya daka mata tsawar ta yi mishi shiru kokuma ya take ta a wajen har sai ta mutu. Jin hakan yasa ta miƙe a guje dan ta bar ɗaki, tasan a wannan yanayi da yake ciki tsab zai iya aikata duk abin da ya faɗa. Wani irin mahaukacin damƙa ya yi wa wuyarta, sosai ya shaƙeta tare da zaro mata dara daran blue eyes ɗin nan nasa, gently ya yi magana. "Waye ya ce ki taɓa mini waya?". Ba bakin magana, sai ma ƙoƙarin jawo numfashinta da take yi domin ta rayu, ita ko da iya idanunsa da ya zaro mata ma ya barta, to zata iya mutuwa, ba sai ya kara mata wani azaban ba, a yau ne ta fara nadamar saninsa a rayuwarta, zata mutu ba tare da ta sake haɗuwa da su mummy ba, da kaɗan da kaɗan ta fara dai na kallo, wani irin duhune ya turnuke idanunta, har lokacin kuma bai saki wuyar tata ba, yau ta kure shi, ya jima yana danne zuciyarsa dan kada ya yi kisan kai, dama ya san duk ranar da ya sauƙe hannunsa a jikinta da nufin hukunci, tofa tabbas sai dai gawarta, tana yi mishi Laifuka da dama yana dannewa saboda Triplets, Imran da kuma daddynta. "Ba dake nake magana bane?!". Ya mance ba ta yadda za'ayi ta yi magana, ya shaƙeta sosai, sai fafutuka take numfashinta yana gaf da ɗaukewa, idanunta har sun yi jawur da su kamar wuta, ga hawaye wani na bin wani, abin gwanin ban tausayi, sai dai shi ko ɗingon tausayin babu a zuciyarsa, sau da dama yana ɗaukar kowa kamar soja, hakan kuma ba ƙaramin cutar da mutane yake yi ba. A hankali towel dake jikinta ya warware ya gangaro kasa, yana ƙoƙarin faɗuwa, a zafafe ya sanya ɗayar hannunsa ya tare mata a daidai cikinta, runtse idanunsa ya yi, yarinyar nan tana neman kure zuciyarsa, idan ya biyewa zuciyarsa tabbas zai halakata, gently ya hauro mata da towel ɗin sama ba tare da ya buɗe idanunsa ba, bai kuma saki wuyar nata ba, ya kawo towel ɗin daidai saitin kirjinta, a zafafe ya kuma saki towel ɗin ta zame ta faɗi kasa. Ba komai bane yasa ya saki face hannunsa da ya sauƙa a saman tula tulanta, ita kanta sai da ta waro dara daran idanunta waje, tamkar zasu faɗi kasa, nan take ta ji ta watsake, a karo na farko ya kallah, yanzu kuma ya taɓa, wayyo Allah wani irin kululun bankinciki ne ya ziyarci zuciyarta, ji ta yi gabaɗaya ta tsane shi, shi kuma wannan taɓasu da ya yi, sun sanya ya ji wani irin mahaukacin shock a jikinsa, daga tafin kafarsa har izuwa tsakiyar kansa sai da ya amsa, ko kusa ko alama bai taɓa taɓa kirjin wata mace ba a rayuwarsa, jinsu ya yi wani iri, sun buga mishi kwakwalwar kansa ba kaɗan ba, wani irin yanayi mara misaltuwa ya ji a jikinsa, gently ya zame hannunsa daga wuyar nata tare da juya mata baya ba tare da ya buɗe idanun nasa ba, cike da ɓacin rai ya sanya hannu ya fara watsa gashin kansa yana ciza lallausan laɓɓansa na kasa. Yana sakinta ta zube kasa tana tari tamkar maƙoshinta zai fashe, yasan kallon tsiraicin mutun a musulci haramun ne, hakan yasa ya juya mata bayan, kuma saboda hakan yasa ya sake ta, ba dan haka ba yau sai dai a ɗauki gawarta, ita kuma tari take yi tamkar ba zata rayu ba, duk da halin da take ciki bai hanata lallaɓawa ta ɗauki towel nata ta ɗaura ba, gabaɗaya ilahirin jikinta kerma yake yi, ta gama tsorata da lamarinsa, ta sadaddaƙar mutuwa zata yi yau, bawan Allah yana da ƙoƙari wajen ganin ya kula da addininsa, sai idan abu yafi karfinsa ne yake take wa, amma gaskiya yana ƙoƙarin sosai, duk da yake Bature kuma krista a baya, yanzu ya riƙi addinin musulunci sosai, hannu bibbiyu ba wasa. A wannan hali Areef ya shigo ya same su, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke dan yasan dama za'ayi hakan, shiyasa ma da ya je ɗakin Lion bai same shi ba, ya nufo ɗakinta dan ya dubata shin tana lafiya. Karisowa cikin ɗakin ya yi, wajen ta kai tsaye ya nufa, har lokacin tari take yi tamkar ranta zai fita, ta dafe kirjinta da hannayenta dukka biyu, da sauri ya juya ya koma Palo, ruwa mai sanyi ya ɗauko mata tare da dawowa ya zo ya miƙa mata, shi kuma Lion a zafafe ya juya ya fice daga ɗakin, bai sake kallon in da take ba, yau Allah ya ceceta, tsiraicinta ya ceceta, bin shi da kallo Areef ya yi har sai da ya fita, dawo da kallonsa kanta ya yi, a hankali ya buɗe ruwan ya rinƙa bata, ta fita a hanyacinta sosai, idanuwanta tamkar ba ita ba, yau ta ji kamshin mutuwa. Ta kasa tashi har sai da Areef ɗin ya taimaka mata ta miƙe, a gefen gado ya zaunar da ita tare da juyawa ya fice daga ɗakin yabi bayan ɗan uwan nasa. Sai da ta ɗauki good 30 mins zaune a wajen tamkar an shuka dusa, da kyar ta iya dawowa daidai, bayan ta dawo daidai ɗin ma, sai da ta kara 30 mins zauna a wajen kafin ta iya lallaɓawa ta miƙe zuwa wajen trolleynta, wandon jeans baki ta ɗauko da riga pink color mai dogon hannu, har lokacin jikinta na kerma, da kyar ta iya sanya kayan, bayan ta kammala komai da komai, hawa saman gado ta yi ta kwanta tana tunanin yadda taji sauƙan hannunsa a saman kirjin nata, runtse idanunta gam ta yi tana hawaye, abin ya yi mata ciwo, ita ai gara ya yi ta shaketa har ta mutu da taɓa mata su da ya yi, kwata kwata bata yi la'akari da cewa abin da ya tare mata ya fi tula tulan hatsarin a gani ba, ta ji uban shaƙa bata san cewa towel ɗin ya gangara zai faɗi ne ya tare mata ba, a wawtarta da shirmenta, da gangan da saninsa ya sa hannu ya taɓa mata su, tunanin hakan yasa ta ji bata son sake haɗa idanu da shi. Haka ta kwanta tana hawaye har barci ya yi awon gaba da ita, a ɓangaren sa shi kuma oga yana fita bedroom nasa ya koma, toilet ya wuce, ruwan sanyi ya zuba a kansa, bayan ya fito, sai da ya sha robar ruwa mai bala'in sanyi har guda biyu, sannan ne ya ɗan samu zuciyarsa ta ɗan sauƙa, pajama ya sanya a jikinsa ya hau gado ya kwanta, a lokacin Areef baya ɗakin, dan ya shigo ya samu yana toilet sai ya fice zuwa wajen su Brady, sai kuka suke yi tun ɗazun, da alama wani abin suke so, ga shi Aseef yasa sarka ya ɗaure su, yana zuwa ya kwance su, kanshi suka haye suna haushi, barema Brady da yafi kowa kuka a cikinsu, kamar wasu mutane haka Areef ya zauna yana rarrashinsu. Shi kuma Aseef yana riƙe da waya yana magana da daddy, da kyar ya samu ya kwantarwa da daddy hankali ya kuma bashi hakuri na abin da Lion ya yi mishi, shi kam Areef ko a jikinsa, dan ma laifi daddyn ya gani, saboda ya sani sarai Lion baya son shi, yana hakuri ne kawai yana yi mishi biyayya a matsayinsa na uba, amma ya zo ya tsaya yana yi mishi hayaniya a kai, ai dole ta kwaɓe musu dama, sai ka ce bai san halin ɗan nasa ba, ya san komai domin ai renonsa ne yaran, shi ya ɗaurasu a kan wannan turba, tun suna yara ya basu horon kada su yarda wani ya ɗaga musu murya, to dama ita rayuwa haka take, duk abin da ka koyawa yaro a kwana a tashi watarana sai ya yi maka, shiyasa ake so ka ɗaura yara a kan turba mai kyau, dan idan suka tashi yi maka ka ga mai kyau, Allah dai yasa mu dace. After some hours. Da yamma misalin karfe 4:30, sanye da wando jeans pink color da riga fari mai ƙaramin hannu ta fito Palo, ta ɗaure wannan kyakkyawar bakin gashin nata, sai kyalli face nata yake yi, hannunta na riƙe da wayarta, da alama ta ci kuka har ta ƙoshi, dan ga idanunta nan sun kumbura, sun yi jawur ta kasan. Palon kasa ta nufa, babu kowa, gidan shiru, ko'ina a gyare yake tsab tamkar hannu bai taɓa taɓa komai dake wajen ba, kamar daga leda aka ciro komai, fitinannen kamshi air freshener ne ke tashi ta ko'ina, ga blue light da sanyin Ac, abin ba'a magana, ya ƙayatar ba kaɗan ba. Sai buga hammar yunwa take yi, dan bata ci abincin rana ba, ta sha barci kamar ba gobe, shi kuma Imran ya tafi shopping shi da Jelly, dan ta matsa mishi a kan lallai suje su sayi kaya, shi ne ya ɗauketa suka tafi. Mark na kitchen yana aikinsa, kamar dai kullum fuskar nan tasa tamkar na ogansa, babu annuri ko kaɗan, basu san wani abu wai shi murmushi ba, bare dariya kwata kwata a rayuwarsu, ɗaure fuska da bada umarni kawai suka iya. Kallo ɗaya ta yi mishi ta kawar da kanta, dan haushin kowa na gidan take ji, tun da Lion ya taɓa mata tula tula shikenan ta tsani kowa, yanzu ma yunwa ne ya fito da ita, ba dan haka ba, ta ce ba zata sake fitowa waje ba, ba zata sake kula kowa ba, yarinta kenan, shi kuma Areef bawan Allah lokacin da take barci sau biyu yana zuwa ya dubata bata tashi ba, lokacin cin abicin rana ya je ya dubata, dama zai ce mata su je su sayi abinci ne, sai ya samu bata tashi ba, ita kuma ashe fushi take yi da kowa, har da su masu saya mata abincin ma gabaɗaya. (Wayyo cikina wlh Rimsha zata kashe ni da dariya 🤣 ƴar kaniya idan ta yi fushi da su to waye zai saya mata abincin?🤣 Kuruci dangin hauka) Tana fita harabar gidan suka yi ido huɗu da Brady dake tsaye a harabar gidan, tun safe da Areef ya kwancesu bai sake ɗaure su ba, akwai ta da bala'in tsoron kare, bare kuma Brady da ya kasance renon soja, ai sai a hankali, Lion ya rene shi a irin halin sojoji, akwai shi da faɗa na bala'i, baka kula shi ba ma zai kula ka, idan ba TRIPLETS ba, baya ragawa kowa ɗan banzan karen nan. Ihu ta kurma tare da juyawa a guje ta koma cikin in da ta fito, ai kuwa shima da gudu ya bi bayanta yana daka haushi, dama kunsan ka'idan karnuka ne hakan, idan mutun ya gudu zasu bishi, bare shi Brady da dama ko bata gudu ba sai ya bita ɗin dan bala'in faɗa, a guje ta haura sama tana ihu, shi ma a guje ya haura yana haushi. Daidai tsakiyar palon suka ci karo da Lion ya fito zai sauƙa kasa, yana shirye cikin wasu shegun tsadaddun kananan kaya, da alama fita zai yi, yau ma kamar jiya, sarkarsa na saman riga ba a ciki ba, black glass ne a idanunsa, sai tashin kamshi yake yi kamar anyi ɓarin turare a jikinsa, ya yi kyau over tamkar shi ya yi kansa. Bata lokacin da ta ƙanƙame shi da iya karfinta tana ihu ba, a guje Brady ya yi kanta yana ƙoƙarin kai mata cizo, wani irin mahaukaciyar damka ta yi wa Lion ɗin a kirjinsa, da alama bata ma san waye ta rungume ba, hankali ya tashi sosai idanunta sun rufe, bata gani, ita dai a rabata da wannan bala'in, wato Brady. Yana ƙoƙarin kai mata cizo Lion ya tare shi da hannu ɗaya, gently ya yi mishi magana da English a kan ya bari, tsalle ya yi ya taka kafaɗarta ya haye jikin Lion ɗin yana wani girgiza kamar wadda ya je farauta ya dawo, ɗan banzan balaƴaƴen kare, ko da yake a haka a hore shi. "Sake ni". Ya faɗa a nutse, shiru bata amsa ba kuma bata sake shin ba, ɗan duƙo da kansa ya yi a kan face nata, sai yaga ta sume mishi a jiki, ashe lokacin da Brady ya zo zai cijeta, bala'in tsoro yasa numfashinta ya ɗauke, ɗan ciza laɓɓansa ya yi tare da cewa Brady ya sauƙa mishi a jiki, ba musu ya diro kasa sai wani girgiza na iya shege yake yi. Ji ya yi tamkar ya yi wurgi da ita kawai ya yi tafiyarsa, amma kuma sai ya kasa yin hakan, ɗan rage tsawonsa ya yi tare da ɗaukarta cak ya nufi saman sofa, har zai kwantar da ita a wajenku ko me ya tuna sai ya fasa, ya nufi bedroom nata, saman gadonta ya kwantar da ita, zai miƙe kenan sarkarsa ya dawo da shi, dan kuwa sarkar nasa ya makale a cikin nata sarkar dake ta cikin rigarta, ɗaukarta da ya yi yasa sarkar wuyarsa ya shiga rigarta. Guntun tsaki ya ja tare da ɗan jan wuyar rigar nata kasa ya fito da nata sarkar, gently ya warware su ya zame nasa, miƙewar da zai idanunsa suka sake sauƙa a saman sunansa dake rubuce a tudun tula tulanta, shiru ya ɗan tsaya yana karewa sunan kallo, daga bisani kuma ya dawo da kallonsa a kan face nata, har wani shock ya ji lokacin da ya kallin face ɗin nata, yau taso ma ta yi mishi kama da Josephine, ɗan shafa kansa ya yi yana mamakin wannan fuskar tata, fuskar ce abu ta farko da ta tsaya mishi a rai, ya gane cewa ita ce ta kira sunan shi a gidansu Imran, dan ranar da ta kira Anaya a waya zata gaya mata cewa ya kallan mata breast, a ranar ya gane ita ta kira sunansa, da ta kira Anaya ta ce Anaya GAR ya kalla mini.. sai kuma ta yi shiru, yana cikin bedroom nasa yana jinta, yaji GAR da ta faɗa, tamkar a bakinta a ha halicci sunan, ta iya kira kamar ba gobe. Gently ya juya zai bar ɗaki, idanu ɗuhu suka yi da Areef dake tsaye a bakin kofar shigo, tun lokacin da Lion ɗin ya shigo da ita shi ma ya shigo, dan ihun da ta yi ta gudu Brady ya bi bayanta, lokacin yana garden, ya ji ihun nata ne ya biyo bayanta, yana haurowa Palon sama lokacin shi kuma Lion ya ɗaukota zai kai bedroom nata. Ko sannu bai ce da Areef ɗin ba ya wuce ya fice abinsa, mamaki Areef yake yi, wai me haɗin breast ɗin Rimsha da Lion ne, duk idan zasu yi karo to fa breast ɗin nan nata ne a gaba, sai ya kallesu, wannan wace iriyar kaddara ce? Ya tambayi kansa, suku nasu kaddarar a haka tazo kenan?. Juyawa shima ya yi ya fita, a harabar gidan ya isko Lion ɗin da Mark zasu fita, ga hadari na tasowa, alamar ruwan sama za'ayi, har walkiya ta fara wanzuwa a sararin samaniya, garden ya koma abinsa, shi kuma Lion ya wuce suka fita da Mark, Aseef kuma yana ta shararra barci bawan Allah. ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E29-30 A ɓangaren gidan Hajiyar daɗi kuwa, ranga ranga suka kwashi Zinariya suka fita da ita daga gidan, sai Allah ne kaɗai yasan in da zasu kai ta, ita kuwa Jehan, bayan sun kaita ɗaki sun fito, miƙewa ta yi zaune tare da cewa Adiva, "Adiva zo ki kwance ni kin ji?". Da farko Adiva taki, ta ce tana tsoro kada su Zinariya su zo su mata ɗan banzan duka, sai da Jehan ɗin ta yi ta kara mata karfin gwiwa sannan ta yarda ya zo ta kwaceta ɗin, "Bani ruwan sha Maryam". Da sauri ta ɗauko mata ruwan a fridge, tun da ta kafa kai bata ɗaga ba har sai da ta shanye ruwan nan tas, sai faman sauke nauyayyar ajiyar zuciyar take yi, ita kanta ta wahala, ina ga su Zinariya kuma? Abin ai ba'a magana, sun wahala ba kaɗan ba. Jugum jugum suka yi, dukkansu idanu sun rena fata, bare ma Adiva da bata saba da shan wahala ba, renon madara da ice cream, jiki duk madara, yau ta kare a gidan karuwai, wannan shi ne ake kira da rashin sani yafi dare duhu, ga iyayensu a can suna haukar nemansu, ga su sukuma a nan, ana ƙoƙarin lalata musu rayuwa a sakasu a harkar bariki, gabaɗaƴansu ma sun ɗauka iyayen nasu sun mutu, ya Allah kasa mu fi karfin zukatanmu. "Adiva ina wayar nan taki? Ɗauko ki saka mana ita a charji, bana son komai ya sameta, dan akwai abubuwan da na ajiye masu mahimmanci a cikinta". Cewar Jehan kenan, da sauri ta miƙe ta shiga cikin toilet ta ɗauko wayar, dan a can suka barota, da kyar ita kuma Jehan ɗin ta lallaɓa ta shiga toilet dan ta yi wanka ko jikinta ya sami kwari. Kusa da A'isha da bata ko motsi Adiva ta zo ta zauna tare da zuba mata idanu, bayan ta yi wanka ta fito, kayan Adiva ta sake sakawa a jikinta kafin ta haye gadon Aisha ɗin, jugum jugum suka yi suna kallonta, fuskarta ya yi wani irin haske tamkar babu rai a jikinta, ga face ɗin natan ya kumbura kamar an hura balo balo, tunani Jehan take yi anya ba wani cutar wani alhajin ya sanyawa A'isha ba kuwa? Ji yadda take ta kumbura kamar ana hurata, anya ma akwai rai a jikinta kuwa? Anya akwai sauran numfashi a tattare da ita kuwa?. Sai tunane tunane take yi, abin ya ɗaure mata kai, ga shi ita ba iya gane matatciya da rayayyiya zata yi ba, basu da wata madafa, ba magani ba asibiti. Sun jima zaune a wannan yanayi kafin a kira sallar mangariba, Jehan ce ta fara tashi ta ɗauro alwala ta fito, tana fita Adiva ta shiga, daga cikin su ƴar gwal kuwa, babu wacce ta sake shigowa cikin ɗakin nasu, basu sake jin ɗuriyar kowa a gidan ba, tamkar babu kowa. Bayan sun idar da sallar mangariba sai suka zauna saman daddumar suna karatun Alqur'ani mai girma, har sai da aka kira sallar issha suka tashi suka gabatar da sallah, Maryam da Adiva suka je suka ɗauko musu abinci bayan sun idar da sallar kenan. A tare suka ci abincin, Allah sarki yau ban da A'isha, abin gwanin ban tausayi, bayan sun gama ci, ko wace ta haye saman gadonta, ita kam Adiva gadon jenan ta haye dan tana tsoro, addu'ar barci suka yi, ba jimawa Adiva da Maryam suka yi barci, ita kuwa Jehan yadda taga rana, haka ta ga dare, ta kasa rintsawa, Allah ne kaɗai yasan me take tunani da bata yi barci ba, har wa yau A'isha bata motsa ba. Washegari da safe kamar yadda suka saba, bayan sun yi sallar asuba suka gyara ɗakin nasu, suka yi wanka sannan suka zo suka zauna saman gadajensu, sai latsa waya Jehan take yi kamar mai tura wani saƙon. Da misalin karfe tara na safe, suna zaune jugum jugum sun tasa A'isha a gaba, har lokacin bata motsa ba. A hankali aka turo kofar ɗakin nasu, wata hamshakiyar mace ce, mace wadda ta amsa sunanta mace, sanye take da wata shegiyar lace wadda ta amsa sunanta lace, ta haɗu lace ɗin nan, da alama zata yi bala'in tsada, wuya da hannayenta duk shaƙe suke da kayan ado na gwalagwalai, fara ce tas, amma farin mai ce, tana da faɗin fuska sosai, kafarta na sanye da wani tsadadden haɗadɗen plat shoe mai bala'i kyan gaske, ta ko'ina a jikin matan nan dukiya ce a narke a wajen, kanta ba ɗankwali, ta zuba uban attachment har baya, da kallo ɗaya zaka yi mata kasan ba bahaushiya bace, in ma bayarabiya or Ebo, egala, ɗaya daga ciki dai, ga wani uban make up da ta sha, eyelashes nan ba'a magana, kamar bindin kaza, hancin nan nata a haje a fuskar tata, irin matan nan ne masu cika ido, idan ka gansu sai sun cika maka idanu ta yadda zaka kasa yi musu gardama a kan abu, akwaita kuma da katon tunbi kamar mai ciki wata tara, tana da kiɓa ba cancan sosai ba, idanunta dara dara, irin waƴan nan idanun da suke tamkar a waje haka, gula gula da su, gasu jawur tamkar ƴar shaye shaye, sai tashin wani irin warin maganin gargajiya take yi, da alama wani turaren magani ta banka a jikin nata, dan ga kamshin perfume nata a gefe, shi kuma maganin warinsa na gefe. Babu ko sallama ta kutso cikin ɗakin, zuba mata idanu suka yi har ta iso wajen bakin gadon nasu, tun da suka ɗaura idanunsu a kanta suka kasa ɗaukewa, da alama kuma gabaɗayansu sunyi la'asar, duk jikinsu ya mutu tamkar wani abin ta yi musu, da alama dai ba haka kawai ta shigo ba. Gefen gadon ta zauna, cikin sanyin murya ta fara magana cikin harshen turanci, da alama babu Hausa a bakinta, "My daughters ya kuke ta kallon mummynku haka? Tamkar kunga wata bakuwa daga wata duniya? Ba zaku gaishe ni bane? Mummynku ce fa, ni ce mahaifiyar ku yanzu". Har suna haɗa baki wajen ɗaga mata gaisuwa, har lokacin kuma basu kawar da kallonsu daga kanta ba, wani irin shu'umin murmushi ta saki "Yauwa daughters ko ku fa? Ai yana da kyau ku rinƙa respect na mum ɗin ku, Jehan me ya same ki naga bakinki kamar ya ɗan kunbura?". Hannu ta kai ta taɓa bakin nata tana faɗin "Mummy babu komai" "No daughter ki gaya mini idan wata ko wani ne suka taɓaki a gidan nan, yanzu zan sanya ayi musu hukunci!" Girgiza kai ta shiga yi tana faɗin "Da gaske mummy babu komai". Dawo da kallonta kan A'isha dake kwance tamkar gawa ta yi, a ɗan ruɗe ta furta "Oh my god, me ya sami my daughter A'isha kuma?". Cikin sauri Adiva, Jehan suka haɗa baki wajen cewa "Muma bamu sani ba mummy". Miƙewa tsaye ta yi, da ganinta kasan anci duniya da tsinke, bariki ta zauna, goggiya ce, duk wani tantiranci ta iya shi, makirci, kirsa suma sara mata suke yi, nan take ta nuna musu ta birkice, ta shiga tsantsar tashin hankali da halin da A'ishar take a ciki, hankalin ya yi mummunar tashi, har da wani kyarkyatar karya, tare da ciro wayarta ta danna kira, cikin wani yare ta yi magana, bayan ta gama wayar ta koma ta zauna tare da fara shafa fuskar A'ishar tana faman ambatar "Oh my daughter, yau ina zan sa kai'na, dole a zo a kai mini ita Hospital, oloni". Bayin Allah sun ɗauka da gaske ne, ko da yake ba wani abin da za su iya yi, ta rufe musu baki ruf, yanzu sai abin da ta ce shi zasu yi, ba su isa su tsallake maganarta ba....... INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN JUSTICE FOR JEHAN, ADIVA AND MARYAM, SUN SHIGA KOMA SUMA, DUK WANI MAI IMANI DOLE YA YI MUSU KWALLAH, SUN SHIGA HANNUN WANNAN MAKIRA.😭 Ba'afi minti 5 da yin wannan waya da ta yi ba, sai ga wasu mata sun shigo cikin ɗakin su biyu, mata ne amma masu kirar maza, duk layinsu ɗaya da hajiyar, cikin wannan yare nasu ta sake yi musu magana, tsawon minti uku suna maganar, daga bisani suka ɗauki A'isha suka fita da ita, Jehan, Adiva, Maryam, babu wacce ta iya tambayar ina za'a kai A'ishar, sun zuba ido kawai suna kallo, har aka fice da ita, juyowa garesu Hajiyar daɗin ta yi. "My daughter's kada ku damu magani za'a je a yi mata, Hospital zasu kai ta, dole nayi jinyar daughter ai, kada ku ji komai, nan ba da jimawa ba, zata dawo gareku, yanzu dai kunci abinci ne?" Har wa yau cikin harshen turanci ta yi maganar. E suka amsa mata da shi. Girgiza kai ta yi tana faɗin "No daughters bari na sa a kawo muku wani abincin, ai ina gidan nan, kada ku damu dole zaku yi abin da kuka ga dama, tun da mummynku ta dawo shikenan ai, zaku ji daɗi, Jehan idan kun gama cin abinci ki shirya mu je super market a sayo miki kayayyaki masu shegen kyau da kuma sauran duk abin da kike buƙata". Da murnarta ta amsa da okey, Allah sarki kun shiga koma sai addu'a. Waya ta sake yi a kan a kawo musu wani abincin, a wannan karonma da wannan yaren nasu ta yi maganar ba da English ba, da alama dai bata son su san me take faɗe ne yasa take magana da wannan yare, hakan na nufin magana a kan A'isha ma wani abin ta shirya kenan, babbar magana, lallai wannan mata ta kai duk in da ake neman makira shegiya. Matan da suka fita da A'isha, sune suka kawo musu abinci, tasa su ta yi a gaba da daɗaɗan kalamai masu ratsa zuciya, har sai da suka cinye abincin nan tas, daga maganar Hajiyar daɗi zaka san tantiriyar karuwa ce mai lasisi, dan ta iya tsara zance da daɗin baki sai ka ce karuwan zamanin farko, yanzu zata saye zuciyar mutun ko da bai yi niya ba, sai wanda Allah ya tsare, hakan yasa take samu galaba sosai a fannin jawo matan aure zuwa wannan tsinanniyar harka, da wannan daɗin bakin nata, ga shegen iya zuba zance, ta fito a tsohuwar karuwar tata, nan take take saye zukatan matan aure, ta halakar da su, ta kaisu ta baro, ya ilahi ya lillihi, Allah ka kare mu da mu da zuria'ar mu baki ɗaya, ya Allah kasa duk halin da zamu shiga imani da tsoronka ya tabbata a zuƙatanmu, ire iren su Hajiyar daɗi su suka fi komai yawa a rayuwarmu ta yau, Allah ka yi mana tsari da su. Sai da ta tabbatar sun ƙoshi haniƙan, da kanta dan tsabar makircin ta buɗe musu ruwan sha tare da lemon kwalba, su kuwa bayin Allah komai tace, da okey kawai suke amsa mata, abin gwanin a zubar musu da kwalla, bayan sun kammala komai ta yi musu sallama har da basu sunbata a goshi, da wani bakinta da ya yi bakinkirin saboda busar shisha da su sigari da sauran kayan buguwa, basu ji kyamar bakin ba, haka suka bari ta sumbace su ta fice daga ɗakin tana wani cewa "Am going to miss you my daughter's, amma zan dawo nan da two hours". Har suna rige rigen amsa mata da okey. Tana fita Jehan ta kwanta tana sauke numfashi cikin kwanciyar hankali, suma ko wacce ta haye saman bed nata ta kwanta, da alama sun mance da A'isha, an rufe musu babinta, sai murna jenan take yi zasu fita sayayya da mummynsu wato Hajiyar daɗi, tashin hankali da ba'a sanya mishi rana. Masu karatu shin ku a tunaninku me ya sami D.P.O ne?, ko dai ta mance wace ce ita ne? Anya lafiya kuwa? Akwai cakwakiya gaskiya, in dai haka ne Hajiyar daɗi ta ɗauki hakkin jama'a sosai a kanta, da alama rufewa mutane baki take yi, ba ji ba gani, dole sai maganarta kawai kowa zai bi, sai Allah ne kaɗai yasan adadin mutanen dake cikin gidan nan wadda basu son zaman gidan, Allah ne kaɗai yasan adadin matan da suke kuka a cikin zuƙatansu basu son wannan harka, wlh ba kowa zai so yin harkan nan ba, kunga ita ma Jehan bata zo da niyar son wannan harka ba, hasalima yakarsu ta yi niyar yi, amma sai ga shi reshe ta juye da mujiya, da alama ta koma tana supporting nasu fa, ko ya makomanta zai kasance cikin wannan bakin gida? Mu dai je zuwa, mu waiwayi gidan Abba mu dawo. GIDAN ABBA💋 A bakin kofar palo mai gadi ya ajiyewa Akila trolley tsarabar da Aseef ya kawo mata, da kanta ta ja zuwa cikin palon, yadda ta bar Ammie hakan ta dawo ta same ta, tsakiyar palon ta jawo akwatin ta kawo shi, zuba mata idanu Ammie ta yi tana kallon ikon Allah, bayan ta ajiye akwatin ta koma ta ɗauko kwalin goribarta, shima a tsakiyar palon ta ajiye shi, sai wani sakin uban murmushi take yi baki yaki rufuwa, har lokacin Ammie bata tanka ta ba. "Ammie heartbeat ne ya kawo mini wannan tsaraba fa". "To Akila heartbeat kuma?" Gyaɗa mata kai ta yi baki yaki rufuwa, "Waye shi heartbeat ɗin?" Kusa da ita ta zo ta zaune tare da kwantar da kanta a saman cinyar Ammien nata tana faɗin "Ammie zan baki labarinsa daga baya, yanzu dai ya ce zai zo ya gaishe ki idan ya sake dawowa, har da Abba ya ce zai je ya gaidar, bari dai na buɗe tsarabar nasa in gani". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi trolleyn, zuba mata idanu kawai Ammie ta yi tana mamakin ƴar tata, wannan murmushi dake a kan fuskar ya isa ya bayyanar da tsantsar kaunar masoyin nata da take yi. Kwantar da trolley ta yi, tare da zuge zip ɗin, da wata katuwar teddy ta fara cin karo, teddyn nan ta haɗu tamkar ɗan mutun, fari tas da ita, a gaban teddyn daidai wajen wuyarta an yi rubutu da jan kala, Heartbeat+ Heartbeat, wani irin haɗaɗɗen murmushi ne ya kubce mata, yasan abin da take so ashe, ya santa da teddy akwai amana, ga wannan teddy ma ta tsaru iya tsuruwa, da alama shi ya bada yadda yake so aka buga mishi, sai kamshin perfume ɗin Lion take yi, tsabar murna, jikinta har rawa yake yi wajen ciro teddyn daga ledarta, ta wani rungume a kirjinta tamkar Heartbeat ɗin nata ta rungumi, da yake Ammie ta san halinta da shegen kaunar teddy's, sai bata yi mamaki ba, in dai a kan teddy ne fin haka ma zata yi, a wajenta wannan teddy ya fi mata komai dake cikin akwaitin, da kyar ta yarda ta ajiye shi ta fara fito da sauran kayan. Nan ta sake cin karo da wani haɗaɗe flowers mai girma, ya kusa kai girman teddyn nata, flowers yana nan round, an shirya shi datsan datsan, ba karya shi ma ya yi, dukka kayan cikin akwaitin nan kamshin perfume ɗin Lion suke yi, perfume ɗin da idan ya kama kaya baya saki, sai dai abin mamaki Ammie bata ce bata son kamshin ba, sai ma shaka da take yi tana lumshe idanu, amma kuma da alama kamshin ya canza abubuwa da dama daga cikin gidan, duk wasu aljanu dake kusa sun gudu, har wani haske gidan ya kara yi, to me hakan yake nufi? Ita dai Ammie duk abin da waƴan nan dodannin basu so, suna sawa ita ma ta ji bata so, to ya akayi take son wannan kamshin, su kuma sun gudu da suka jita? Akwai ayar tambaya a nan gaskiya, ba mai amsa mana kuma sai ita Ammien da kanta, mu dai je zuwa. A jikin flower an rubuta i really love you my heartbeat, da farin kala aka yi rubutun, shi kuma flower ja ne, a wannan karon Ammie ta kasa hakuri sai da ta ce "Heartbeat hala Bature ne ya kawo miki wannan kyauta?". Cikin sauri da mamaki ta gyaɗa kai tana faɗin "Ammie shi ne ya aka yi kika gane to?". Karo na farko da ta saki cool murmushi, cak Akila ta tsaya tana kallonta, yau tsawon shekaru 15 kenan rabon da taga Ammiensu tana murmushi, kullum fuskarta a ɗaure, tun tana yarinya da take mata wasa da dariya, daga ta fara girma Shikenan duk wata annuri ta kau daga fuskar mahaifiyar tasu, Allah sarki abin tausayi. "Akila kenan ai soyayya da Bature daban yake da kowa a duniyar nan, su duk in da zasu yi soyayya baza su ɓuya ba, haka zalika kyautarsu a soyayya bata ɓuya, abin da zance miki na karshe shi ne ki shirya wajen tara flowers, dan zaki samesu babu adadi, idan ba Bature ba waye zai tsaya irin wannan soyayya, bahaushe zai wani sayo miki flower ne? Ai su ɓata lokaci da shirme ne a wajensu, yanzu idan kika ji uban tsadar wannan flower dake hannunki sai kin tsorata, da za'a canza kuɗi da kuɗin Nigeria, sai ya saya miki ƙaramin gida, tab ai ni nina san Bature, ke baki san tarihin Abbanki ba ko,? Lokacin da muke soyayya da shi, bashi da babbar kyauta biyun flower, a lokacin ma kakanku tana nan, kinga shi ma Abbanku har ya yi girma ya yi wayo yana cikin turawa kafin su dawo nan, to yanzu ne zama cikin Hausawa ya sauya shi, amma duk wani ɗabiunsa a baya irin nasu ne, shima Bature ne ai kinga ni". Zaro wannan dara daran idanun nasu na gado ta yi, tana mamaki, ba abin da yafi bata dariya da mamaki wai Abbanta ma soyayyar flower ya yi, dan iya shege sai ta rufe idanu tana imagine ga Abba nan ya zo ya duƙa yana miƙawa Ammie flower, kamar wata zararriya haka ta tuntsure da dariya har da faɗuwa kasa, Ammie kamar wata aljana, ta san me take yi wa dariyar, sai ta shareta tamkar bata sani ba. Sai da ta yi mai isarta ta tsagaita tare da ajiye flower ta cigaba dan fitar da sauran kayan, set na wasu ɗankara dankaran shegun chain ta fitar, a jere suke guda goma sha biyu, dukkansu na zallar madarar zinari ne babu mix, sai wani irin bala'in kyalli suke yi, suna ɗaukar ido ba karya, ko wanne da irin design nasa, ita kanta Ammie ta tsorata da ganinsu, tsadar bala'i gaske suke da shi, ko wani guda ɗaya bala'in tsada ke gare shi, ga shi har goma sha biyu set ɗin baki ɗaya ya saya mata, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ai Ammie bata san lokacin da ta tambayeta da ɗan waye take soyayya ba, ɗan shugaban kasa ne ko waye, da yake ita Akilar bata san tsadar chain ɗin ba, sai bata wani ɗaga hankalinta sosai da ganinsu ba,. "Lafiya Ammie kike tambayata da waye nake soyayya?". "Akila kin san tsadar chain ɗin hannunki nan kuwa?" Girgiza kai ta yi tana faɗin "Ammie ba ɗan shugaban kasa bane, amma jikan shugaban kasa ne, kuma ke baki ganin news ma bare nace zan yi miki kwatancen shi ki gane shi, da kina kallon Tv ne idan na kira miki sunan ɗan uwansa zaki iya saninsu". Hannu tasa ta karɓi chains ɗin tana kara kare musu kallo, farkon soyayyarta da Abba ya saya mata irin shi guda ɗaya, ita kuma Akila set baki ɗaya tabɗijam. Cigaba da watsa tarukucen kayan ta yi, a nan ta sake fito da diamond Ring mai bala'in tsada, kafin ta fitar da wani tambarin Heartbeat mai bala'in kyau fari tas, tamkar balo balo a ka hura, haka heart ɗin yake, amma ba balo balo bane, yana da karfin da ba zai fasu ta daɗi ba har sai dai idan yanka shi za'ayi, Heartbeat+Heartbeat ne a rubuce a gaban heart ɗin, an yi rubutun da jan kala, rungume heart ɗin ta yi a kirjinta, ita duk tsadar waɗan nan abubuwa basu wani dameta ba, tafi kaunar teddy, Heart, da kuma flower nan, sun fi shiga ranta, Heartbeat nata ya san abin da take so da wanda bata so. Miƙewa ta yi da sauri ta nufi bedroom nata ta bar Ammie da tulin kaya a gaba, har zata shiga sai kuma ta dawo ta ɗauki teddynta, sai murmushi take yi ta haye saman bed nata tare da fito da wayarta, massage ta yi mishi a WhatsApp a kan ya kirata yanzu. Ba'afi minti ɗaya da shigar massage ɗin ba, sai ga kiransa da numbersa na ainahi ba unknown number ba, cikin zumuɗi ta ɗaga kiran, a shagwaɓe ta fara magana. "Heartbeat, heartbeat Allah har na fara kewarka over". Cikin shagwaɓa shi ma ya fara magana "In zo in ɗauko ki mu dawo gidan mu ne?" Da yake su Turawa a wajensu dan budurwa ta dawo gidan saurayi da zama ba wani laifi bane, bai san nan kam Nigeria bane, kasar musulci, ko za'ayi hakan ma sai dai a ɓoye kuma ba da sanin iyaye ba, a takaice dai sai wadda iyaye suka yi wa baki ne zata yi hakan, wadda aka cewa jeki kya gani, Allah ka tsaremu da jin wannan mummunar kalma daga bakin iyayenmu masu albarka Amin. "A'a Heartbeat ka zo dai mu yi hira, idan mun gama sai ka yi wa Abbana magana". "Heartbeat ina nan zuwa wajen Abba, dole ne kuma nazo nayi magana da shi, dan gaskiya ba zan iya komawa ba tare da aurenki ba". Cool murmushi ta saki tana ɓuye fuska "Amma Heartbeat in tambaye ka mana?". Yana daga kwance ya miƙe zaune yana faɗin "To ina jinki". "Yanzu me kake yi?" "Ina kwance daga ni sai shot and single, kizo mu kwanta tare". Rufe fuska ta yi, ko me ya aiketa ta tambaye shi Oho, ai ga shi nan ta sami amsa daidai da tambayarta. Kawar da zancen ta yi da cewa "Heartbeat dan Allah zaka iya gaya mini me yasa kake sona?". "Kyau, saboda kyanki mana". Ya bata amsa a full voice nasa, ba shagwaɓa a cikinta ko kaɗan. "Heartbeat kyau kuma?" Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "Eh mana, nasan idan na gaya miki wani abu akasin haka, nasan zuciyarki ba zata yarda ba, so kawai ki riƙe wannan amsar, ni kuma na barwa kaina sanin me yasa nake sonki, da kuma irin son da nake yi miki ɗin". "Dan Allah Heartbeat ka gaya mini, wlh zan yarda da kai, ina son nasan asalin dalilin da yasa kake so na ne". Nisawa ya yi kafin ya ce "To Shikenan, babu wani dalili, Allah ne ya jarrabeni da sonki a kallon farko, dan haka saboda Allah nake sonki, adadin son da nake yi miki kuma, ba zai faɗu a bakin nan nawa ba, na barwa zuciyata sanin hakan". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Wani kalar abinci kafi so?" Shagwaɓe murya ya yi tare da yin kasa sosai da voice ɗin nasa tamkar wani na yi mishi laɓe "Ni ba abincin da nafi so zaki tambaye ni ba" "Me yasa ba abinci zan tambaye ka ba? To me zan tambaye ka?" Ta yi maganar ita ma a shagwaɓe kamar yadda ya yi mata. Ɗan turo ɗan bakin nan nasa ya yi tamkar yana a gabanta, "Abinci ai bashi da wata faidar ki san me nafi so tun da ba ke zaki rinƙa yi mini girki ba, baki iya irin abincin mu ba ai, muna da masu yi mana girki". "Haka ne amma ai yana da kyau nasan duk wasu abubuwan da kafi so tun da ni dai ka rigada ka gama sanin nawa ko?" Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Abubuwan da nafi so ai basu da yawa, na farko Triplets na, na biyu uncle Hosain, na uku Prof, na huɗu ke, a aikace kuma karatun Alqur'ani mai girma, sallah azumi, and then ina jin daɗin in ga ina sadaka sosai, abubuwan da nafi a tattare da ke kuma ko in ce a tattare da aure, first soyayya, and then your ball's, your eyes, mouth and rest". Shiru ta yi, sai jujjuya kalamansa take yi a cikin ƙwaƙwalwarta, wai meyasa Turawa kam basu da kunya ne? Ta tambayi kanta, wai ball's nata yake so, ko a ina ya gansu oho mishi. "What are you thinking?" Ya katse mata tunanin nata. Dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali, "Nothing my heartbeat". "Okey good kin ji abubuwan da nafi, and then ina son kiss sosai, i really like your lips, idan kina magana am feeling like nayi kissing naki". Hannu tasa ta toshe bakinta tana faɗin "Heartbeat mu ai a kasar nan ba'a kissing na mace har sai an ɗaura musu aure". "Serious?" Ya tambayeta ko a jikinsa, jinjina mishi kai ta yi alamar tabbatarwa. "Okey ba damuwa ai, ke matata ce, very soon zaki zama, mu a kasar mu zaki iya kiss na kowa normal ne, amma tun da ina kasarku zan bi dokanku, zan jure, amma fa idan muna tare ki daina turomin ɗan bakin nan naki, idan ba haka ba, seriously zan yi kissing nashi ba zan iya jurewa ba". Cool murmushi ta saki jin yadda ya yi maganar, a shagwaɓe sosai, ga shi ya yi kasa da murya da alama Areef bai yi nisa da shi ba, ko yana toilet or balcony haka. "Heartbeat ba dokar kasar mu bace ta hana ayi kissing na mace kafin Aure". "To dokar waye ne hakan?" Yadda yake maganar irin bai damun nan ba, yana cikin farinciki komai normal, "Dokar Allah ce Heartbeat, babu kyau ka taɓa jikin macen da ba muharramarka ba, ba sai budurwarka ba, kowa ma, in dai ba muharramarka bace, babu kyau ka taɓa ta, shi kuma kiss matarka kawai zaka yi wa". "Tsaya tsaya heartbeat to ai ni har daddyna ina kissing na shi, my TRIPLETS muna sumbatar juna". Nisawa ta yi, cikin jin kunya ta ce "Heartbeat ba irin wancan sumbata da kake yi wa su daddy ba, no ina nufin kiss baki da baki, ka sha lips nata ta sha naka, shi ne matarka kawai ya halakta ka yi wa hakan". Shiru ya ɗan yi wannan maganar tata ta jefa shi cikin wani yanayi, "Heartbeat ya kayi shiru?". "Babu komai just am feeling like i want to hug you ne". Dama ta san za'ayi hakan, shiyasa ta sake tambayarsa, ta san shi sarai ɗan nema, ranar ma haka suka yi da ita, daga ta ce mishi me yake yi, sai ya ce mata yana kwance rungume da pillow yana tunaninta, tsautsayi ya sa ta ce mishi gata nan zuwa su kwanta, shikenan ya birkice mata wai yana jin feeling, ga shi su basu san kunya ba, baya ɓoye abu, karara ya fito ya gaya mata gaskiyar abin da yake ji, wai a hakan kuma gara shi sau dubu da sauran, shi ta koya mishi kunya, Lion da Areef kam sai addu'a dan kwata kwata basu san hanyar da kunya ta bi bama. Shi ne da magana ita da jin kunya. "Heartbeat kin iya tausa?" Zazzaƙar muryarsa ya katse mata tunani, "E na iya me ya faru". "Zaki rinƙa yi mini? Ni fa seriously ina son tausa sosai, and then ina son macen da ta iya soyayya da shagwaɓa sosai kamar dai ke ɗin nan" "Kasan me my heartbeat?" A'a ya bata amsa, "Kayi addu'a Allah ya kai mu ranar da zamu mallaki juna, nama alkawari zan maka soyayyar da sai kayi kuka dan daɗi". "Serious?" Jinjina mishi kai ta yi alamar tabbatar mishi da abin da take faɗa. Kukan shagwaɓa ya sa mata yana faɗin "Ni gaskiya ba zan yarda ba, dole ayi sauri azo a kawo mini ke gida na, duk abin da za'ayi ayi da wuri, ina son soyayya sosai, ina son naga kin zama mallakina". Yana magana yana turo baki tamkar yana a gabanta, ga kukan shagwaɓa da yake yi mata, ita ma kukan shagwaɓar ta sa mishi "Heartbeat nima ina son naga ka zama mallakina ai". "Uhm uhm da gaske kike yi Heartbeat?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar eh da gaske take yi. "Waye yake kiranka a waya tun ɗazun nake jin kara". Ta faɗa tana turɓune fuska, "Ɗayar wayata ce fa, Haroon ne yake ƙirana". "Waye kuma Haroon?" "Class mate". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "To kaɗauki kiran mana, wata kila wani abin zai gaya maka mai mahimmanci da ya shafi school". Girgiza kai ya yi yana faɗin "Duk wani abin da zai faɗa mini bai kai kwatar hirar da nake yi dake mahinmanci ba, idan ba Lion or Areef bane suka kirani a yanzu ba, ba wanda ya isa ya sani na kula shi a lokacin da nake magana da ke, so ki kyale shi, idan mun gama magana zan kira shi". "My heartbeat wata kila fa abin yana da mahimmanci sosai tun da ga shi sai kiran ka yake ta yi". Ta yi maganar a shagwaɓe tana Murmushi, har cikin karkashin zuciyarta ta ji daɗin maganarsa, tana jin daɗin irin yadda ya ɗauketa da matukar mahinmanci a rayuwarsa. "Seriously ba zan ɗauki kiran nan ba, ki kyale shi kawai, yanzu ke so kike yi mahimmancin wani yafi naki? Kin san yadda nake jinki a zuciyata kuwa? Ba zaki gane bane, ke dai Allah ya mallakamin ke ina ga a sannan ne zaki gane irin yadda nake sonki, yanzu ko na yi miki bayani ba zaki ɗauki haske ba". Wani irin ƙayatattacen murmushi ta saki tare da rungume pillow dake kusa da ita, wani irin azababben kaunarsa ne yake kara ninkuwa a cikin zuciyarta, addu'a take yi Allah ya mallaka mata shi, yadda yake son soyayyar nan ga shi ɗan shagwaɓa ɗan soyayya, zasu haukata juna, "Heartbeat" ya ambaci sunanta tamkar zai sa mata kuka, kasa sosai ta yi da murya cikin wani irin siga mai ruɗar da mai sauraro ta amsa da "Na'am my heartbeat". "Wai meyasa kike yin shiru ne,? Me kike tunani? Nifa bana son koda na second ɗaya ki hanani jin wannan zazzakar sexy voice ɗin naki, idan kika sake yin shiru serious kuka zan yi miki". "My shagwaɓati ni kada kayi mini kuka, ai kasan ba zan so kukan ba ko?" "To in dai haka ne kada ki sake yi mini shiru, ko kuma yanzun nan ki ganni a cikin bedroom naki". "Yanzu idan nace kazo zaka zo?" Turo ɗan bakin nan ya yi "Why not my heartbeat,? Ai ko karfe 2 dare kika ce nazo ya zama dole nazo". Mirginawa ta yi ta sake murginowa tare da kankame pillow sosai a kirjinta, tana sauke numfashi a hankali hankali, sai Allah ne kaɗai yasan abin da take ji a ziciyarta a kansa, ta haukace sosai a kan soyayyarsa, a ɓangarensa shima hakan ne, ya zurma over a kanta, ya tafi dayawa, zallar madarar soyayya yake mata wadda babu mix ko ɗigo, idan suna waya ji yake yi tamkar idan bai mayar da ita cikin zuciyarsa ba, ba zai taɓa samin sauƙi ba, shi kaɗai yasan me yake ji. Sautin kukan shagwaɓarsa ne ya dawo da ita daga cikin duniyar tunanin da ta faɗa, cikin sanyin murya tare da wani irin shagwaɓa mai tafiya da duk wanda aka yi domin shi "Heartbeat me ya faru kuma kake kuka?". Kin yi mata magana ya yi tamkar bai ji ta ba. "Haba my heartbeat, to na tuba ba zan sake ba". Nan ma shiru ya yi mata bai yi magana ba, kukan shagwaɓar ita ma ta fara yi mishi, can kasa kasa ta tsinkayo muryarsa yana magana a shagwaɓe "Heartbeat ni bana son kukan nan naki kin sani ko?" "To ba kai ma kana kuka ba? Dole nima nayi ai". Tana magana tana kumbura kumatu. "To na dai'na kema ki dai'na, amma kuma ai kece kika sakani kuka, na ce miki ki dai'na yi mini shiru idan muna waya, amma sai ki yi ta yin shiru, to idan kin yi shirun tunanin waye kike yi?" Sarkin kishi ba, ta faɗa a ranta, akwai shi da bala'in kishi kamar me, ko Imran ta kira a waya suka jima suna hira sai ya yi ta yi mata faɗa wai shi baya son ta jima tana hira da kowa sai shi kaɗai, baya son kishiya, komai nashi daban ne, kada ta haɗa shi da kowa, duk da Imran yake yayanta shi baya son su jima suna hira, idan kana son kaga ɓacin ransa cikin ƙanƙanin lokaci ka ce mishi ga Akila da Irfan suna waya, tamkar zai yi hauka haka yake zama, har kuka yake yi mata akan baya so, shiyasa ya hanata zuwa gidan Abbi kwata kwata, da Imran ya ce suje, sai ta ce mishi kanta na ciwo ba zata iya zuwa ba, haka Imran da jelly suka tafi, ita kuma ta kwanta tana shan hira da sahibin nata har ya iso gareta, a takaice dai yanzu ya hanata zuwa gidan Abbi ne dan kada ta haɗu da Irfan, dan kishin bala'i, ya ce idan ta cigaba da kula Irfan sai ya harbe shi da bindiga kowa ma ya huta. Wayyo Allah soyayya daɗi, Allah sarki Irfan, da a harbe shi da bindiga ba gara ta hakura ta dai'na kula shi ba?, Shiyasa ta hakura ta dai'na kusantar shi dan ya rayu. Idan muka koma ɓangaren gidan Lion kuwa, After some hours, a hankali ta waro dara daran idanunta da suke jawur da su, kai tsaye sai cikin tsakiyar kwayar Amber eyes ɗin Brady dake saman bed ɗin nata, a haukace ta miƙe zaune, haushi ya daka mata yana mai ɗaga kai sama, kamshin Lion ya biyo, idan baku manta ba ta taɓa ɗaukar rigar sanyin Lion a ɗakin Imran, to dama kunsan karnika suna bin kamshin mutun ne, rigar Lion ya biyo zuwa ɗakin nata, ihu ta kurma cikin fitar hayyaci ta diro kasa daga saman gadon ta nufi waje, da farko bai yi niyar binta ba, dan shi kamshin Lion ya biyo, neman ta in da kamshin yake a ɗakin nata yake yi, bai bi ta kanta ba, amma ganin ta watsa a guje ta yi waje yasa ya rufa mata baya da gudun gaske. A haukace ta nufi palon kasa, babu kowa hakan yasa ta nufi waje, gidan shiru, sai kurma ihu take yi, daidai lokacin motarsu ta danno kai cikin gidan, saura kaɗan Mark ya bi ta kanta, ga hadiri sosai a garin, iska ruwan sama ya dawo da su, a zafafe ya taka birki wadda sai da ya sanya kan Lion buguwa da jikin kujerar gaba na motar, dan a baya yake zaune, cikin ɓacin rai ya ɗago kansa dan ya ga me yasa Mark ya taka birki haka, a lokacin ita kuma ta bugu da jikin gabatar motar tana ƙoƙarin zubewa kasa, rai a matukar ɓace ya buɗe kofar motar ya fito da nufin ya yi ball da ita, dan bai san me ya biyota ya sa ta shiga gabansu a haka ba, da shi ne ke tuka motar nan a cewarsa bi ta kanta zai yi dan bata da hankali. Yana fitowa ya nufeta, cikin ɓacin rai ya damki gashin kanta tare da miƙar da ita tsaye yana ƙoƙarin yin wurgi da ita, dan tana yawan shiga harkarsa, daidai lokacin Brady ya kariso waje, haka zalika Areef da Aseef, daidai lokacin suka fito da sauri dan jin ihunta da suka yi, shi ne suka fito suga menene ya same ta. Da gudun gaske Brady ya yi kanta da nufin cizo, a haukace ta damko kirjin Lion ɗin da hannayenta dukka biyu, ta kankame shi sosai tana ihu, wani irin yanayi mara misaltuwa yaji a jikinsa, daga kansa har izuwa tafin kafarsa sai da ta amsa, domin kuwa ɓul ɓul ɗin breast nasa ta damko bata sani ba, ta riƙesu sosai, ga shi sai faman cusa kanta a kirjin nasa take yi tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, cak ya ji duniya ta tsaya mishi, ya kasa dakatar da Brady dake ƙoƙarin cizonta, ya kuma kasa yin wurgi da ita da ya yi niyar yi ɗin, Mark dake cikin mota yana kallon me yake faruwa, cikin sauri ya cire wannan black glass ɗin nasa yana kara zaro dara daran hezal eyes nasa, duk sauran sojojin dake gidan ido suka zaro suna kallon ogan nasu, abin da ko a mafarki basu taɓa yin gigin mafarkin mace zata taɓa shi bai taketa har sai ta kasa motsi ta mutu ba, sai ga shi yau a zahiri da rana tsaka a gaban kowa, mace ta rungume shi har haka ba tare da ya yi wurgi da ita ba, Allah ne kaɗai yasan adadin mata nawa ya yi kwallo da su da suka yi gigin yunkurin taɓa shi, basu ma kai ga taɓa jikin nasa ba, yunkuri kawai suka yi, ya take su, babu macen or Namiji bayan TRIPLETS da suka taɓa yi mishi makamancin abin da Rimsha ta yi mishi, fusataccen fuskarsa mai raza mutane ne ma ke hana wasu kusantar shi, amma da alama ita wannan yarinya bata san waye ta runguma ba, duk wannan tunanin sojojinsa suke yi a cikin zuƙatansu. Shi kuma Aseef da ya ga da gaske Brady cizonta zai yi, sai ya daka mishi tsawa da turanci, munafukin kare mafaɗaci, yana jin tsawar Aseef ya yi wani irin girgiza tare da daka tsalle ya haye jikin Lion ɗin, ya sauƙe mata bindinsa a bayanta, a lokacin kuma Lion ɗin ya daka mata wani mahaukacin tsawa a kan ta sake shi, ya yi maganar tare da yakaceta daga jikin nasa ya yi wurgi da ita gefe guda, wani irin wahalallen ihu ta saki dan ta bugu, da sauri Brady ya diro kasa daga jikin nasa ya nufeta, dan a nasa ilimin tun da Lion ya yi mata hakan to mai laifi ce ita. Ganin Brady ya yi kanta yasa ta kurma wani razanannen ihu tare da miƙewa ta watsawa a guje ta nufi waje, ita da kanta bata san in da ta nufa ba, taku biyu Areef ya yi ya riƙota, dan ya lura ta fita a hayyacinta sosai, kankame shi ta yi idanunta a datse gam, tamkar zata fashe su, sai kuka take yi, abin gwanin ban tausayi. Ganin Areef ya rungumeta yasa Brady ya dawo jikin Lion ya ɗane abinsa yana wani girgiza, wucewa Lion ɗin ya yi ba tare da ya sake juyowa in da suke ba, ya shige cikin palo, har lokacin kuma Brady na jikinsa, rarrashinta Areef ya fara yi tare da bata hakuri, ba ƙaramin tausayi ta bawa Aseef ba, da sauri shima ya kariso wajen suka haɗu suna rarrashinta, da kyar suka samu ta yi shiru tare da lafewa a kirjin Areef ɗin tana shasshekar kuka, gabaɗaya sojojin dake gidan burinsu ɗaya, shi ne su san wace ce ita, dan kansu ya ɗaure sosai, me yasa su Areef suke rarrashinta har haka? A iya saninsu da TRIPLETS kwata kwata basu son mata, basu son kowa, to wace ce ita? Shi ne abin da kawai suke son sani, Mark ma fitowa ya yi ya nufi cikin gida. Ɗaukarta Areef ya yi suka wuce zuwa palo, har lokacin baiwar Allah jikinta sai kerma yake yi, suna shiga palo kuma suka isko su Lucky da suka fito daga bedroom na Areef yanzu, kara kankame Areef ɗin ta yi sosai tana sake sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. "Aseef ka ɗaure karnikan nan, kuma ya kamata a dai'na kwancesu tun da tana tsoronsu, a bari a hankali hankali har sai ta dai'na tsoronsu, sai a rinƙa sakesu". Cewar Areef, Okey Aseef ya amsa da shi, tamkar karnikan sun ji abin da Areef ɗin ya ce na a ɗaure su, da gudu suka watsa suka yi waje dan kada ya ɗaure su ɗin, sai kiransu yake yi suka ki kula shi, suma sun fi son a barsu su sakata su wala abinsu, su shiga ko'ina su fito, su yi ɓarna son ransu. Binsu wajen ya yi, da kyar ya samu ya yi musu dabara ya ɗauresu ya dawo, da kyar ta yarda ta rabu da jikin Areef ta koma saman sofa ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, "Our Queen ya kamata ki dai'na wannan tsoron naki, dan kinga matar GAR muke fatan ki zama, bai kamata ace kina da tsoro har haka ba, kuma shi Brady da kike gani, ina mai tabbatar miki da cewa Lion ba zai taɓa rabuwa da wannan karen ba, sai dai mutuwa ta raba su, shi ya reni kayansa, yana son shi fiye da tunaninki, to is better ki daina jin tsoronsa". Shiru ta yi tana tunanin wai shin waye ta rungume da farko ne? A tunaninta Areef ne, sai kuma yanzu ta fara tunanin tamkar jikin ba ɗaya dana Areef ba, wancan jikinsa tafi cika sosai, sai yanzu abubuwan suke dawo mata. Shiru suka zuba mata idanu suna kallonta, shi Aseef ma daga barci ya taso, duk jikinsa a mace, a ɓangaren Lion kuwa, yana shiga bedroom nasa toilet ya nufa, har lokacin Brady na tare da shi, yaki barinsa. Wanka ya yi tare da Bradyn, suka fito, duk in da ya saka kafarsa shi ma Brady sai ya saka nasa, kamar wasu twins, dama kwana biyu ai sun yi missed na juna, Brady sai Lion, Lion sai Brady, mutu ka raba. Yana tsaka da sanya kaya ruwansa kamar da bakin kwarya ta kece, shiryawa ya yi cikin wani ɗan ƙaramin shot mai irin kama jikin nan, launin sky blue, sai ƴar singlet fara tas, ba ƙaramin daɗin ruwan saman nan ya ji ba, dan garin akwai zafi sosai, kwana biyu dama ba'ayi ruwan ba, da alama damunar ta fara ja baya ne, kun san shi dama da son tsayawa a balcony yana kallon zuban ruwan sama, yau ma hakan ce ta faru, bayan ya gama shi kai tsaye ya nufi balcony, sai tsalle Brady yake yi, da alama shi ma ya ji daɗin ruwan saman. Tsayuwa ya yi yana kallon yadda ruwan ke kwarara tamkar da bakin kwarya, kamar ance mishi ya kalli kasa, can ya hangota kamar wata kifi tana juyi a cikin ruwan, ɗan waro idanunsa waje ya yi yana kallon ikon Allah, abin da ya faru shi ne, suna tsaka da hira da su Areef ruwan saman ya kece, shi ne ta tashi a guje ta yi waje, sun ɗaukama wani abin zata ɗauko, suna zaune suna jiranta, ita kuma ta je ta shige cikin ruwa abinta, idan baku mance ba akwai ta da son shiga ruwan sama ba kaɗan ba, bata ganin ruwa ta hakura bata shiga ba. Sosai ya tsareta da dara daran blue eyes ɗin nan nasa babu ko kyaftawa, ta yi kyau sosai a cikin ruwan, har da wani ɗaga kai sama take yi ruwan na zuba mata a fuska, ba ƙaramin nishaɗi take ciki ba. "Rimsha sarkin son ruwa". Cewar Malika da ta bayyana a yanzu, da sauri ta juyo, ganin Malikar yasa ta saki kayatatcen murmushi tana faɗin "Malika ai kema kina son ruwan, kullum a kayi sai kin shiga". Ɗan dariya ta yi kafin ta ce "To shikenan dai yanzu dai ya isa haka wanka a ruwan nan, fita kada mura ya kama mini ke". Da mamaki Lion ke kallota, shi a iya ita kaɗai yake gani, bai ga Malika ba, ga shi sai zuba surutu take yi tana dariya, tunani ya fara yi anya kuwa yarinyar nan kanta ɗaya? Anya babu wani motsi a kan nan nata kuwa?, Wani ɓangare na zuciyarsa ne ya amsa mishi da to kai me naka a ciki? Guntun tsaki ya ja tare da juyawa ya bar waje zuwa cikin bedroom nasa, saman bed nasa ya haye, cikin sauri Brady ya daka tsalle ya haye jikinsa, bargo ya ja musu ya rufesu zuwa daidai ciki, shi kuma Brady iya kansa ne kawai a waje, a hankali ya lumshe dara daran blue eyes ɗin nasa, ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi. Ita kuma Rimsha sai da Areef ya ji shiru ya biyota wajen, ba ƙaramin ruwan mamaki ya sha ba ganin ta a cikin ruwan, tasata a gaba ya yi tare da yi mata faɗa akan shiga ruwan da ta yi, hakuri ta fara bashi, sam bai ji daɗi ba, ya ce ta je ta yi wanka da ruwan zafi ta canza kaya kada mura ya kamata, sai su je sayan abinci, okey ta amsa mishi da shi, ta wuce sama sai ɗigar da ruwa take yi, shi kuma ya wuce bedroom nasa, zuciyarsa cike taf da tunanin irin ganin da ya yi mata a jike da ruwa, komai na ga halittar ta ya bayyana saboda kayan sun manne da jikinta, gabaɗaya tula tulanta sun bayyana sosai, abin ya tsaya mishi a rai, shi kuma Aseef waya ya ɗauka tare da kiran Akila ya wuce bedroom da ta kasance mallakinsa, dan su zuba soyayya da Heartbeat nasa. Yana shiga ya haye gado tare da shigewa cikin bargo yana manna waya a kunne, "Hello My heartbeat".............. ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ 💋HEARTBEAT+ HEARTBEAT 💋 E31-32 Yana shiga ya haye gado tare da shigewa cikin bargo yana manna wayar a kunnensa, "Hello My heartbeat". Daga ɗayan ɓangaren tana daga cikin bargo ita ma saboda ruwan dake zuba tamkar da bakin kwarya, gari ya yi mugun sanyi, "My Shagwaɓati tamkar ta shiga cikin zuciyata kasan kewarka nake yi a yanzu haka". Kasa ya kara yi da murya, "Ai zuciyoyinmu a haɗe suke, dole zan san wani halin bugun zuciyata take ciki, yanzu dai yasu Ammie?" "Sunanan lafiya lou ina su Rimsha?". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Hmmm Rimsha ta Saif uwar rigima ba, tana ɗaki, yanzu ta gama zuba mana rigima, amma in tambaye ki mana?". "Allah yasa na sani". Ta bashi amsa, "Kina tsoron karnika ko baki yi?" "Tab ai ni idan na gansu a kusa da nima zan iya suma". Dafe kansa ya yi yana salati a cikin zuciyarsa, Rimsha part two kenan, shi yanzu ya zai yi? Ga shi dai ba zai iya rabuwa da su Lucky ba gaskiya, duk wuya, duk daɗi suna tare, yana kaunar kayansa. "Shagwaɓati ya kayi shiru?". Shagwaɓe mata murya ya yi tamkar zai yi kuka "Heartbeat sanyi nake ji sosai, ki zo mu kwanta tare, na san idan kina nan for sure ba zan ji sanyi ba". Kara jan bargonta sosai ta yi, cikin sigar soyayya mai tafiya da tunanin mutum ta ce "Tom shikenan ka yi mana addu'a In sha Allah ba za'a sake yin wani ruwan sama ban zama mallakinka ba". Nisawa ya yi, ba ƙaramin daɗi maganarta ya yi mishi ba, yana son kullun ya rinƙa jin kalmar zai mallaketa, idan ta gaya mishi hakan ji yake yi tamkar ya kamota ya mayar da ita cikin cikinsa ko zai sami natsuwa. "Heartbeat In Sha Allah ke mallakina ce, nan ba da jimawa ba hakan zata faru, yanzu dai a ina zan sami Abba?". "Banki, yana banki a can zaka same shi". "Okey tom gobe zan zo gida da yamma me zaki bani?" Kara lafewa ta yi a gadonta, ta kule cikin bargon. "Me kake so?" "Ke mana my heartbeat, ke nake so". "Kai my shagwaɓati to ai ni taka ce". Jawo pillow ya yi ya rungume da kyau a kirjinsa, ji yake yi tamkar ita ya kankame, ga yadda ruwan saman ke zuba abin ba'a cewa komai, "Heartbeat kina shagwaɓa ni sosai fa". Turo ɗan bakin nan ta yi kamar biro "To ai dama kai my shagwaɓatina ne, dole zan shagwaɓa ka sosai". "Serious?" jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "Yah seriously, dole na shagwaɓa ka, sai ma munyi aure, zaka sha soyayya, sai ka kasa fita waje". Kukan shagwaɓa ya saka mata, a hankali ta fara ambata sunansa "My shagwaɓati, my shagwaɓati!" Kin amsa mata ya yi, sai uhm uhm yake ce mata. "Please my shagwaɓati ka yi magana mana". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Ni gaskiya ba zan yarda ba, Allah aure nake so, ni dole a aura mini ke". Kwaikwayar maganarsa ta yi ta maimaita abin da ya faɗa "Ni gaskiya ba zan yarda ba, Allah aure nake so, ni dole a aura mini ke". "Ni Heartbeat serious nake gaya miki, ki dai'na wasa". Ya yi maganar tamkar zai fashe mata da kuka, sake kwaikwayarsa ta yi, daga muryar har maganar da ya yi, "Ni Heartbeat serious nake gaya miki, ki dai'na wasa". "Uhm uhm kai heartbeat ki dai'na kwaikwayona nace miki ko?" Sake kwaikwayon na shi ta yi, kuka ya saka mata tare da katse kiran. Cool murmushi ta saki tana faɗin "Ɗan rigima kawai, nima ai na iya". Ta kai karshen maganar tare da fara kiran layin nasa tun da ya buɗe mata, wayar ta yi ringing har ta katse bai ɗaga ba, tana katsewa sai ga shi ya biyo kiran nata, "Ɗan rigima" ta faɗa kafin ta ɗauki kiran. "My heartbeat i want to see your face now". Shi ne abin da ya faɗa bayan ta ɗaga kiran, "Video call?" Ta tambaye shi, yes ya bata amsa, "Okey in kira ka ne ko zaka kira ni?" "No bari ni na kira ki". Okey ta amsa mishi da shi, juya kiran ya yi zuwa video call, cikin zumuɗi ta ɗaga, dan ita ma tana mugun son ta kalli face nasa, bata gajiya sam sam ga ganinsa, ya haɗu ne ta ko'ina, irin mijin da take burin aura kenan su kashe juna amma da soyayya da kauna tare da shagwaɓa. Kayatatcen murmushi suka sakarwa junansu lokacin da suka sauke idanu a kan juna, cikin sanyin murya ta ce "My shagwaɓati ka yi kyau sosai, kasarmu ta karɓe ka". "Ba dole Kasarku ta karɓe ni ba, tun da kina cikin kasar, yanzu dai ɗan yi kasa da bargon nan bari naga face naki da kyau". Kara jawo bargon sama ta yi har zuwa wajen idanunta, cikin sigar zolaya da shagwaɓa ta ce "Ni kunyarka nake ji". Rumtse idanu ya yi, kasa kasa ya furta "Wato ba zaki dai'na yi mini irin wannan wasa bako? For sure watarana sai kin saka ni zuwa gidanku 2 na dare". Ɗan zato idanu waje ta yi "To ai da gaske kunyarka nake ji my shagwaɓati". Turo mata ɗan bakin nan nasa ya yi "Uhm uhm wai fisabillilahi ba zaki bari ba? So kike yi ki sanya ni kuka ko?" Ɗan gangaro da bargon zuwa kirjinta ta yi, tana murmushi tare da faɗin "Sarkin rigimana to ai gani nan ka ganni, yanzu dai ba shikenan ba?". Shiru ya yi bai yi magana ba, ya zuba mata idanuwansa babu ko kyaftawa, "Lafiya kake kallona haka?". Gera ɗaya ya ɗaga mata tare da kashe mata ido ɗaya, ɗan zaro idanu ta yi tana kallonsa, "Wai me ya faru ne shagwaɓati? Kayi magana mana". Nisawa ya yi tare da shagwaɓe fuska kamar zai yi kuka, bai ce mata komai ba. "Shagwaɓati wai ba zaka yi magana ba?". Ji yake yi tamkar ya jawota ya rungume, shi kaɗan yasan me yake ji a cikin zuciyarsa, ta yi matukar tafiya da imaninsa, ya tsareta da waƴan nan idanuwan nasa, a hankali ya lumshe su ya sake buɗewa a kan face ɗin nata, ba ƙaramin rikita ta ya yi ba yadda ya lumshe idanun, sai ya kara kyau over, tsantsar madarar kyau ne ya bayyana, ga zara zaran eyelashes nasa wadda suke tamkar ya kara dana kanti saboda tsawo, sak irin na Lion, kuma irin na Josephine. "Heartbeat ban san me zance miki bane, shiyasa na yi shiru, idan nace zan yi magana zan iya yin kuka, kina rikitani sosai my one and only". Kara kudundunewa ta yi a cikin bargon, murya kasa kasa kamar wani nayi mata laɓe ta ce "Heartbeat kai ne kake rikita ni dayawa wlh, ban san ya zan kwatanta maka yanayin kyanka ba, ni na rasa ma me zan ce". Sake lumshe idanunsa ya yi zuciyarsa na kara macewa a kanta, ya kara narke mata sosai. "My shagwaɓati idan kana lumshe idanun nan naka kana kara birkita mini ƙwaƙwalwa fa". A tsananin shagwaɓe ta yi maganar, nisawa ya yi, cikin sanyin murya ya fara magana "Rufe idanunki bari na baki wani surprise". Okey ta amsa mishi tare da datse idanun nata, waro idanunsa ya yi a hankali, zuba mata idanun ya yi sosai yana kare mata kallo, ga shi kuma high neck t-shirt ne a jikinta, rigar ta kamata sosai, kana iya ganin shape nata sosai, kanta babu ɗankwali, ta saki gashin nan nata da ya sha gyara sai kyalli yake yi, ga kamshin shampoo ta sai tashi yake yi, ya ɗauki ƴan sakanni yana kallon face nata kafin a hankali ya dawo da kallonsa izuwa kirjinta daidai in da ta tsaida bargon nata, ɗan daidai tsakiyar breast nata, zuba musu idanu ya yi na second goma, daga bisani ya mai da kallonsa izuwa saman kanta. Ya shagala da kallonta zazzakar muryarta ta katse mishi tunani da cewa "My shagwaɓati in buɗe idanun nawa ne?" Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali "Ban gama kare miki kallo ba ai, ɗan ja mini bargon nan ƙasa mana". Cikin sauri ta waro idanunta a cikin nasa, kashe mata shanyayyum idanun nan nasa ɗaya ya yi, idanun sun zama tamkar wadda ya sha wani abin ko kuma yake jin barci, turo baki ta yi tare da saka mishi kukan shagwaɓa akan ita ba zata yarda ba, dan me zai kare mata kallo, rarrashinta ya fara yi yana ce mata sorry, sai da ta ɗan wahalar da shi kafin ta yarda ta yi shirun. "My rigimati ba, ki cigaba da bani wahala, baby's ɗina zasu rama mini, ƴar rigima kawai". "Kai kuma ɗan shagwaɓa kawai, nima ai baby's ɗin nawa zasu rama mini, Allah yasa first born na ya fika shagwaɓa, ya rama mini abin da kake yi mini". Kafeta ya yi da ido bai yi magana ba, "Zan so ganin ranar da baby's ɗina zasu takura maka, su rama mini duk shagwaɓar da kake yi mini". "Ni da ke waye yafi wani Shagwaɓa?". Yadda ya yi maganar ba zaka taɓa cewa shi ya yi taba, ba zaka yi tunanin ya motsa lallausan lips nasa ba, a hankali ya fitar da words ɗin, ya yi maganar kuma yana yi mata signal da gera ɗaya, abin gwanin ban sha'awa. "Kai mana, ai ka fini iya shagwaɓa, kai karshe ne a wannan fannin". Girgiza kai kawai ya yi, shi kaɗai yasan me yake ji yadda yake kwancen nan, tana sane sarai da halin da ya shiga, tun da ta buɗe idanunta lokacin da ya ce ta rufe, tun a sannan ta fahimci ya shiga wani yanayi, shiyasa ma yake kasa yin magana, idan ta yi mishi magana, sai dai ya bita da ido, sai ta yi sau biyu yake amsa ɗaya, ga shi ya kasa kawar da kallonsa daga kanta, a nata shirmen kuma, da ƙaramin tunaninta, idan ta barshi yana kallonta suka cigaba da yin video call ɗin, zai sami natsuwa, dan haka take kallo a film, sai ta yi tunanin hakan ne a gaske, bata san cewa kara mishi raɗaɗi take yi ba, musamman ma idan ta yi magana, har cikin ransa yake ji, idan ta motsa laɓɓanta har wani shock yake ji, wani irin sanyi ne ke kara ratsa shi tana karuwa mishi har cikin tsakiyar kansa, bawan Allah yana cikin yanayi, ga ruwan sama. A hankali ya lumshe dara daran idanunsa, tare da kara jawo pillow ya kara rungumewa a jirjinsa sosai, zuba mishi idanu ta yi tana kare mishi kallo daga face nasa har zuwa kyakkyawar lallausan wuyarsa, ita kanta lips nasa kyau suke yi mata ba karya, mai do da kallonta izuwa kyakkyawar brown sajen dake kwance a gefen kumatunsa ta yi, ya gyara sajen ta zama ƴar siriya, gwanin burgewa, gashin gerarsa sun kusa haɗewa saboda cika, gasu gazar gazar a kwance luf, da yake ba da hannunsa ya riƙe wayar ba, ya jinginata ne da jikin pillow dake kusa da shi, hakan ne ya basu damar ganin juna da kyau da kyau. A hankali sautin saukar numfashinsa irin na mai barci ya fara ratsa dodan kunnenta, alamar ya yi barci, ajiyar zuciya ta sauke yau ta sami damar kare mishi kallo tsab, ji take yi tamkar ta sanya hannu ta shafi kyakkyawar fuskar nan tasa ko zata ji sauƙi a ranta, kunsan idan mutun ya lumshe idanu to gashin idanunsa suna kara bayyana sosai, to shi ma dai haka nasa suka yi, sun bayyana sosai, ba ƙaramin tafiya da imaninta suka yi ba. Ta ɗauki almost 30 mins tana kallon shi kafin ita ma barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, sun bar wayoyin nasu a kunne........ SOYAYYA RUWAN ZUMA. After some days. GIDAN LION💋 Misalin karfe biyu na dare, duniya gabaɗaya ya yi shiru, mafiya yawan bayin Allah suna barci, kalilan masu kwaɗayin ni'imar Allah, kuma masu wayo suna a kan dadduma suna sallah or karatun Alqur'ani mai girma, cikinsu kuma har da Lion, Aseef, Areef, da kuma Imran, ita kuma Rimsha yau wani irin azababben barci mai matukar nauyin gaske ne ya ɗauketa, tun da ta yi sallar issha ta ɓige da yin wannan barci, da kyar ma ta iya dawowa saman gado, dan tun daga kan dadduma ta fara barcin, ko abinci bata ci ba, Areef ya zo tambayarta me zata ci yau, sai ya samu tana barci, bawan Allah bai tashe ta ba, ya kyale. Daidai lokacin da agogo ta buga karfe 2 daidai, a wani irin haukace ta farka daga barci tana ambatar sunan Jehan!! Jehan!! tamkar ba lafiya ba, sai zufa take haɗawa tamkar wadda ta yi tsere da dawakai masu uban gudu a tsakiyar rana, salati ta fara yi tare da karanta يَنْفُثُ عَن يَسَارِهِ (ثَلاثاً). يَسْتَعِيْذُ بِااللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ، وَ مِنْ شَرِّ مَا رَأَى (ثَلاثَ مَرَّاتٍ). لَا يُحَدِّثُ بِهَا أحَداً. يتحَوَّلُ عَنْ جَنْبِهِ الَّذِي كَانَ عَلَيْهِ Addu'a ce mai matuƙar muhimmanci idan mutun ya yi mummunar mafarki, Allah zai kareka daga faɗawa irin wannan mafarki tare da kawo maka saukin a cikin zuciyarka, mummunar mafarki ta yi a kan ƴar uwar tata, gani ta yi gata can cikin ukuba da wahala ta rayuwa, hawaye ta fara yi domin kewarta ya dawo mata, komai ya dawo mata sabo, nan take kuma tsoro ya dira mata a ranta, dan yadda ta kalli fuskar Jehan a cikin mafarkin nan ba ƙaramin ɗaga mata hankali tare da tsoratata ya yi ba. Almost 10 mins tana hawaye, can kome ta tuna, sai ta diro kasa da sauri tare da ɗaukar wayarta ta kunna wutar wayar, toilet ta nufa, a gurguje ta ɗauro alwala, dadduma ta fitar tare da shinfiɗawa, ta zura zumbulelen hijabi har kasa a saman kayan barcin nata, cikin natsuwa ta tada sallah, tana yi tana kuka tana rokon Allah da ya kare mata ƴar uwarta a duk in da take, a sujjadarta ta karshe ta zubawa Allah kirari tare da yi wa jenan addu'a ba kaɗan ba, tana yi tana ruwan hawaye tamkar an buɗe famfo, sai da ta ji zuciyarta ya ɗan sami natsuwa kafin ta rufe da salatin annabi ta ɗago daga sujjadar tare da fara yin tahiya. Idan kana son addu'ar ka ta karɓu cikin ƙanƙanin lokaci, annabi (S.A.W) ya ce kayi ta cikin sujjada, idan ka kafa goshi a kasa, Allah ya fi saurin karɓarta, dan zata tafi ne tare da sallarka, sannan yana da kyau kafin kayi addu'a ka fara zubawa Allah kirari, Allah kai ne Arrahaman mai rahma a kan bayi, kai ne algaffaru mai gafartawa bayin ka, ya Ubangiji na babu wanda ya isa ya bani abin da baka bani ba, babu kuma wanda ya isa ya hana abin da ka bani, babu abin da ya isa ya motsa a dukka faɗin sammai da ƙassai ba tare da izininka ba ya Allah, ina tawassuli da sunanka tsarkaka, bani da tsumi bani da dabara, na miƙa wuyata a gare ka ina rokon da ka biya mini buƙata ta kaza, irin wannan makamancin kirarin, ya kamata ku rinƙa yi wa Ubangiji, akwai wasu da dama, na muku misali ne da iya wannan, dan dayawa basu san yadda ake yi wa Ubangiji kirari ba, ita kanta rokar biyan buƙata dayawa basu san ya akeyi ba, wasu kawai su zo ne su faɗi bukatarsu tamkar a gaban ƴaƴansu suke, ko iyayenka idan kana son abu a wajensu sai ka rusunar da kai bare Ubangijin talikai, mai kowa mai komai, sannan ana son kafin ka fara addu'a ka fara buɗeta da salatin annabi, wasu malamai sun ce a tsakiyar addu'ar ma ana karanta salatin annabi, amma dai a karshe ma da salatin annabi ake rufewa, matikar kayi irin wannan babu jimawa zaka samu biyan buƙata, Allah kasa mu cikin wanda Annabi zai ceta a ranar gobe kiyama, Allah ka kara mana ilimi mai albarka mai amfani. Tun da ta farka bata sake mayar da barci ba har sai da ta yi sallar asuba, da yake ta kwana tana sallah, sai barci ya cika mata idanu, tana yin sallar asuba ta ɓige da barci a saman dadduma, fuskarta gabaɗaya jaga jaga da kusasshen hawaye, idanuwanta har sun ɗan kumbura saboda kuka. AREEF Misalin karfe 6:30 fitowa ya yi daga ɗakinsa zuwa bedroom ɗin Aseef, da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin ɗakin, can naɗe saman bed nasa ya hango shi, ya wani kankame pillow a kirjinsa, ga ɗaya kuma ya tashi kansa da ita, ɗaya a tsakanin kafafunsa, sai zuba barci yake yi cikin kwanciyar hankali, da alama daren jiya ya kwana yana waya bai yi barci ba, sai yanzu yake biyan barcin. A hankali ya kariso cikin ɗakin izuwa bakin gadon, zubawa ɗan uwan nasa idanu sosai ya yi yana kallon shi yadda yake barci furkarsa ɗauke da annuri, sai kyalli yake yi yana wani kwailin, kamar mai mafarkin wani abin. Ya ɗan jima a haka yana tunanin ya tashe shi ne ko kada ya tashe shi. Can wani abin ya faɗo mishi cikin tunaninsa a in da ya saki cool murmushi kafin ya haye saman gadon tare da sanya hannu a hankali ya zame pillow dake a tsakanin kafafun shi, sai guntse dariyar mugunta yake yi domin yasan yau za su kwashi ƴan kallo ba kaɗan ba, idan ya yi mishi abin da yake da niyar yin nan. Yana ƙoƙarin kai pillow saman fuskar ɗan uwan nasa ya toshe mishi numfashi, cak ya riƙe pillow da hannu ɗaya idanunsa a rufe kamar mai barci. Guntun tsaki ya ja kafin ya ce "Dama in the first place dana shigo na yi tunanin baka yi barci ba, oya stand up". Wani kayatatcen murmushi ya saki ba tare da ya buɗe ido ba ya fara magana tamkar mai sambatun magagin barci "Heartbeat i really love you so much, kada ki manta ki rufe kofa kada Areef ɗan gulma ya leƙo, kin san...." Bai barshi ya karisa ba, ya kai mashi duka yana faɗin "Waye kuma ɗan gulma?". Wani irin miƙewa ya yi ya rungume shi yana faɗin "Kai mana, muna tsaka da soyayya da heartbeat zaka tashe ni ko? To yanzu ba gulmar ka zo yi bane?" Hararar wasa ya watsa mishi tare da sauƙowa daga gadon ya nufi waje, "Ka shirya by 7 zamu kai sister school, zan je naga school ɗin, bari nayi magana da Prof ina zuwa". Okey ya amsa mishi da shi tare da komawa ya kwanta yana murmushi kamar wadda aka cewa ga amaryar ka can ana kawo maka ita. A ɓangaren Lion kuwa, yau ya zuba kwalliya ta musamman, da alama akwai in da zai je, ya yi wani azababben kyau na wuce misali, kananan kaya ne a jikin nasa kamar kullum, sai dai waƴan nan daga ganinsu kasan sun amsa sunansu kaya ba karya, masu shegen tsada ne, yanzu yana yawan barin sarkarsa a waje samar sigarsa mai mai kon a ta ciki, da alama hakan ta fi yi mishi daɗi, Brady na goye a bayansa, sun fito tsakiyar palo sama kenan Brady ya yi tsalle ya diro kasa yana daka haushi, zuba mishi idanu Lion ɗin ya yi yana kare mishi kallo, cikin harshen turanci ya yi mishi magana a kan su tafi komai na gidan nan kamshin perfume nasa yake yi, saboda ya gane me Brady ɗin yake yi wa haushi, kamshin perfume nasa ya ji yo a ɗakin Rimsha na wancan rigar sanyi, to shi ne yake haushin shi ba zai tafi ba sai ya fito da rigar, tamkar rigar sane ɗan kaniya. Da kyar ya yarda ya biyo Lion ɗin suka sauƙa kasa, babu kowa a palon kasan sai Mark dake kitchen, jin kamshin perfume ɗin ogan nasa ta karu a palon ne yasa ya gane ogan nasa ya fito, ɗauko kayan abincin da ya gama haɗawa ya yi izuwa palo, a saman dinning table ya shirya su kafin ya juyo izuwa wajen ogan nasa, shiru suka yi dukkansu biyu, dama already kun sani, dukkansu sarakan zama shiru ne, zasu iya shekara su biyun nan ba tare da sun ce da junansu uppan ba, kuma suna tare waje guda, hakan suke kamar wasu kurame, ga Mark kullum cikin bakar glass yana rufe sexy Hazel eyes nasa, dan idanun nasa zaka tara turawa 1000 baka sami biyu masu irin idon ba, idanun yana nan tamkar green eyes ne, sai dai bai kai green eyes shiga color ba, combination ne na green da brown, sune suka bada Hazel, yana da bala'in kyau sosai, ga shi shima akwa mangan idanu ga karfin gani, kullum yana cikin black glass abinsa, sai ka rantse baya kallon komai, saboda sau ɗaya yake kallon abu baya kuma mai da kallonsa sai in an sami kuskure, to shi ogansa ma baya kallon abin, Lion zaku jima tare da shi ba tare da ya ɗago ya ganka ba, daga motsin mugun yake iya zayyana shi a ransa, idan kuna tare yau da gobe, yanayin yadda mutun yake motsi a kusa da shi, ta hakan ya gane Rimsha tana da bala'in rawar kai, bata da natsuwa. Sun jima tsaye a haka kafin Lion ya yi gaba ba tare da ya ce da Mark ɗin uppan ba, rufa mishi baya Mark ɗin ya yi, motarsa ya je ya shiga, sai tsalle Brady yake yi, da alama daɗi yake ji zasu je yawo, gidan gaba Mark ya shiga tare da yi wa motar key suka bar gidan, tana tsaye a jikin window ɗakinta tana kallonsu, tun ɗazun ta tashi daga barci dan zata je school, makarantar yana ranta, shiyasa bata yi wani barcin kirki ba ta farka, yau Lion ya yi mata wani masifaffe kuma azababben kyau ba kaɗan ba, ta kafe shi da idu har suka bar gidan, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya zuwa toilet. A gurguje ta yi wanka tare da fitowa ta shirya cikin uniform nata, ba ƙaramin kyau ta yi ba, a palon kasa ta isko Areef yana tsaye yana waya, da alama da daddynsu yake magana, gefensa ta zo ta tsaya tana jiran ya kammala, after some minutes, ya Kammala wayar tare da riƙo hannunta cikin nasa yana faɗin "Kyakkyawar gimbiyar TRIPLETS ya aka yi ne?". "Good morning lovely brother". Ɗan leƙo face nata ya yi, ta yi kyau sosai da sosai, "Shikenan an gama shiri muje ko?" Kai ta gyaɗa mishi alamar e "To yanzu dai zo muje saman table na koya miki cin abincin kasarmu kafin mu tafi ko?". Ba zata iya yi mishi musu ba, kai ta gyaɗa mishi tana faɗin Okey. Abincin da Mark ya shirya musu ya fara zuba mata ɗaya daga ciki, sai bin shi da ido take yi, "Me yasa ki kuka daren jiya kuma?" Ɗan zaro idanu waje ta yi, tana mamakin waye ya gaya mishi ta yi kuka kuma, "Ki dai'na mamaki idanunki suka nuna mini kin yi kuka, yanzu dai gaya mini dalili, da daddare dai nasan ba wanda zai shiga ɗakin ki har ya yi miki wani abin, to me matsalar?". A maimakon ta gaya mishi halin da take ciki na ɓatar ƴar uwarta, dan ko banza ba zai yarda ba sai ya nemota, amma sai ta ɓoye mishi tare da ce mishi karatun Alqur'ani mai girma ta yi ya sanyata kuka, ya gamsu da maganarta, dan ko shi idan yana karatu, yana tuna girman Allah, da wasu bayi dake bijirewa umarni Allah sai ya yi musu kwallah, sai dai a jikinsa yana jin tamkar tana da damuwa, bai cika son matsa mata a kan abu ba, dan haka sai ya kyaleta tare da tura mata abincin da ya zuba a plate ɗin a gabanta a kan ta ci. "Yaya Areef ina tare zamu ci?" "Haka kike so?" Gyaɗa mishi kai ta yi, okey ya amsa mata da shi tare da ɗauko spoon ya ɗabo first spoon ya kai mata saitin ɗan bakinta yana faɗin "Buɗe baki ki karɓi first spoon na". Bata kai ga buɗe baki ba Aseef da ya fito yanzu ya yi maza ya zo ya cinye yana murmushi, harararsa ya yi kafin ya sake ɗebo mata wani abincin, zama shi kuma ya yi a ɗayar gefenta ya zamana sun sakata a tsakiya, a shagwaɓe ya ce "Sister saura first spoon naki, ɗebo ki bani naci". Ba musu ta ɗebo mishi, dan tasan halinsa sarai, yanzu ba ƙaramin aikin shi bane ya sanya musu kukan shagwaɓa a nan, bayan ta bashi sai ya ɗauko spoon nasa shi ma, ita ya fara bawa kafin Areef, daga nan suka fara ciki a tare, wasa wasa Rimsha bata san time da cikinta ya cika tap da abincin nasu ba, sun mantar da ita me ma take ci, sai hira suke yi mata gwanin ban sha'awa. To mu ɗan koma baya kaɗan, a daren jiya, ba iya Rimsha ce kawai ta yi mafarkin Jehan na cikin wani hali ba, har ta daddynsu, mummynsu, Gwaggo duk sun yi, hakan yasa gabaɗayansu suka kwana a saman dadduma suna kaiwa Allah kukansu, musamman ma daddynsu da yafi kowa shiga tashin hankali, dan shi nashi mafarkin a tsantsar mummunar yanayi Jehan ɗin ta zo mishi, ya tsorata sosai, wai gata nan tana kuka an mata fyaɗe, tana kwance cikin jini, ga sarka a hannu da kafa an ɗaureta ana zaneta da wasu irin dogayen bulalu masu shiga jiki, duk in da aka zana mata sai wajen ya yi jajir ya tara jini, da yake ita fara ce tas, kunsan duk Uba na gari ya ga yarsa cikin wannan hali ko a mafarki ne ma dole hankalinsa ya yi mummunar tashi ba kaɗan ba, hakan yasa yau ya tashi da azumi a bakinsa dan ya roka mata Allah da ya tsareta a duk in da take, yasan in makamancin haka ya faru da ita zai iya mutuwa saboda bugawar zuciya, wlh bawan Allah nan har wani ƴar rama ya yi, duk ya yi sanyi jikinsa ya mutu, kuka ne kawai bai yi ba. A ɓangaren mummy da gwaggo ma hakan ne, da azumi a bakinsu suka tashi, duk da su mafarkinta da suka yi bai kai na daddy muni ba, bayin Allah basu kaiwa kowa kukansu sai ubangijin taliƙai, da abu ya damesu zasu ɗauro alwala su kaiwa Allah damuwarsa, shiyasa a kullum suke cin nasara a kan makiya, badan suna addu'a ba ai da an rufe bakinsu, da Rimsha ba zata iya fitowa daga Daular Mutuwa ba, karfin addu'a ya fito da ita, shi ya juyar da hankalin duna har ya taimaka musu suka fita, suka yi breaking na record ɗin Daular Mutuwar, haka shi ma daddy, badan karfin addu'a ba da an jima da kashe shi, su ma su mum ɗin hakan ne, uncle Shitu, dukkansu karfin addu'a ke cetarsu a ko da yaushe, to yanzu ga Jehan ma sun dukufu a kanta, yadda suka dukufan nan kuwa wane uwar Hajiyar daɗi dan ubanta, tsafinta ya yi kaɗan, masu kai kara wajen Ubangiji sun fi yawa, karfin addu'ar bayin Allah ya fi karfinta, Allah dai ya basu Nasara, Amin. Mu cigaba da labari. Bayan sun kammala cin abincin Areef ya riƙo hannunta yana kallon jakar bayanta, suka nufi waje, shi kuma Aseef sai da ya koma bedroom nasa ya ɗauko wayarsa da key ɗin mota ya fito, a cikin motar ya iskosu zaune suna jiransa, sai hira suke zubawa kamar wasu kawaye, mazaunin driver ya shiga, bai kai ga tada motar ba sai ga Imran da jelly su fito, gidan baya suka shiga, Areef na ya kirasu akan su tafi tare, suna shiga Aseef ya yi wa motar key, gaisuwa Rimsha ta fara ɗagawa Imran, da fara'a sosai a kan face nasa ya amsa, tare da tambayarta ya take, ita ma sai murmushi take yi ta amsa. "Aunty jalila ina kwana?" Ta ɗagawa jelly gaisuwa, cikin mutunci Jellyn ta amsa mata, da alama ta natsu ne, tana bala'in tsoron TRIPLETS, bare ma kuma da taga Rimshar na zaune kusa da Areef ɗin a kujerar gaba, sai ta kara natsuwa sit kamar bata a wajen, shi kansa Imran sai da ya sha ruwan mamakin me yasa ta natsu sit daga shigowarsu cikin motar, kamar zai yi magana sai kuma ya danne, sai wani kankame shi take yi tana satar kallon Areef da tamkar bai san da zamanta a cikin motar ba, idan ta kalli Areef ɗin sai ta sake juyawa ga Aseef ta kasa banbance waye ne a cikinsu ya yi yunkurin marinta rannan. Sai hira Areef da Rimsha suke yi suna dariya har suka iso school ɗin, shi kam Aseef yana tuƙi yana latsa waya, Heartbeat na kashe shi da love, tana kudundune a cikin bargo ta lafe a gado sai zuba mishi iya shege take yi, duk ya birkice mata, da kyar ma ya iya tuƙa motar har suka isa. A parking space na makarantar suka tsaya, dawo da kallonsa kan Rimsha Areef ya yi cikin sanyin murya ya fara magana "Ki kula mana da kanki sosai, zamu dawo mu ɗauke ki idan time ya yi, ki je class mu bari mu duba shigaban makarantar naku". Da yake ba da wannan motar ta saba zuwa ba, sai Anaya bata san ita aka kawo ba, motar Imran Anaya ta sani, tana class, amma kafin ta shiga class ɗin taga tsayuwar motar, sai dai bata kai kallonta wajen ba, dan tasan bata san motar ba, da alama ita ma Anaya bata shiga abin da bai shafe ta ba. "Yaya Areef zan yi kewarku sosai". Ta faɗa a ɗan shagwaɓe, leƙo face nata ya yi, cikin zolaya ya ce "Za'ayi kewarmu ne ko za'ayi kewar Saif?" Rufe fuska ta yi da hannayenta tana faɗin "A'a dukkanku dai". "Au ashe dai shi ma Saif za'ayi kewarsa kenan?" Cewar Aseef, shi ma cikin zolaya ya yi maganar, "E mana yaya Aseef, zan yi kewarsa sosai, dan ma na ganshi ɗazun kafin ya fita". Murmushi suka yi a tare har da Imran, a nan ne kuma jelly ta fahimci ita Rimsha ba son Imran take yi ba, tana da wadda take so kenan, gabaɗaya sai ta ji babu daɗi abin da ta yi mata, dama an ce rashin sani ya fi dare duhu, to ita jelly abin da ya faru kenan tsakaninta da Rimshan tashin sani. Sumbata Areef ya yi mata a lallausan kumatunta yana faɗin "Nima zan yi kewarki sosai, ina jin kamar ba zan iya wuni guda ban ganki ba". Wani irin kunya ta ji, su kuma kun sani ba sai na sake faɗa ba, sumbatar mutun or kiss ba wani abu bane a wajensu ga koma waye, shiyasa ma ya sumbace ta ɗin. Ganin ta yi shiru ne yasa ya ce "Ba zaki sumbace ni ba nima? Haka zaki tafi mu rabu?". Bata da zaɓi, dole ita ma ta juya ta sumbace shi a kumatu, tana kokarin cewa Areef ya fita bari ita ma ta fita dan ita ce a ciki, sai ta ji saukar wani sumbata a kumatunta na Aseef, juyowa shi ma ta yi tare da bashi sumbatar, cool murmushi ya sakar mata kafin ya buɗe kofar motar ya fita yana faɗa mata ta kula musu da kanta sosai. Kusan a tare mazan suka fita daga motar, dan su je office ɗin shugaban makarantar, ita kuma jelly tana ciki tana jiransu, Rimsha na ƙoƙarin fita jelly ta riƙo hannunta tare da ce mata "Ki yi hakuri da abubuwan da suka faru kin ji Rimsha?". Cool murmushi ta sakar mata kafin ta ce "Babu komai Aunty Jalila, ni daman ban riƙe ki a cikin zuciyata ba, nasan rashin fahimta ce". Rungumar juna suka yi kafin nan ta saketa ta fita tana yi mata bye bye, da ido jelly take binta da shi babu ko kyaftawa, yau taga Rimsha ta yi mata kama da daddynta, Allah sarki bata san ƴar uwarta bace, dole akwai kama ta jini. Class nasu ta nufa, da sallama kasa kasa ta shiga, wani ihu Anaya ta yi tare da tahowa da gudu ta rungumeta tana dariya, "Dama na ce yau In Sha Allah zaki zo". Ita ma dariyar take yi, ƴan class sai binsu da kallo suke yi, dan sun san halinsu a tare, Anaya na bala'in Kaunar Rimsha haka ita ma Rimshar. Wucewa suka yi suka je suka zauna a mazauninsu, dama kowa da kujerarsa, sai dai suna kusa sosai da juna, "Rimsha ya kamata ki je ki roƙi uncles su baki test ɗin da suka wuce daga na last Monday zuwa yau fa ki yi, dan kinga suna da yawa, almost test 7 fa". Cewar Anaya. Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Anaya ni English and mathematics nafi ji, yanzu dai ki rakani office ɗin Mr Emmanuel bari na roƙe shi ya bani English na yi, wlh ranar da kika gaya mini anyi test na English da kyar na iya barci". Murmushi ta yi tana faɗin "Kai Rimsha saboda English ɗin kika fi iyawa ba? Dole ki damu ai, amma gaskiya ni ba zan je office ɗin Mr Emmanuel ba, dan kin san halinsa sarai da bala'i, yanzu idan munje mu biyu ma yana iya kin baki ya ce waye ya ce muzo mu biyu, kin san fa ba'a shiga mishi office bibbiyu, mutun ɗaya ne, kema ki yi addu'a kafin ki je, bakin mugu azzalumi, sannan kuma uncle Faisal na jiranki, ba idan ya kiraki baki ɗauka ba, zaki yi bayani". Guntun tsaki ta ja tare da miƙewa ta miƙawa Anaya ɗin school bag nata tana turo baki ta nufi waje, haushin uncle Faisal ɗin nan take ji, kamar ta yi ta kifa mishi mari, a wawa, wawa take kallon shi ma, dan kawai yana nan shiru shiru da shi. Tana fita ta hango motar su Areef ya bar makarantar, ajiyar zuciya ta sauke tare da wucewa ta nufi office ɗin, a bakin kofa ta yi excuse kasa kasa tare da tura kofar ta shiga, wani irin mahaukacin birki ta ja babu shiri, zaro idanuwanta waje ta yi tana kallon abin da kwakwalwarta ya kasa ɗauka, Mr Emmanuel tare da wata student ƴar ss 2 ne ko 3 suna romancing na juna, ya cire mata rigar uniform yana wasa da breast nata, ita kuma yarinyar sai wasa da gabansa take yi, matashiyar budurwa ce wadda zata iya kai 19 to 20 years haka, gata kyakkyawa ba laifi, fara ce tas, kuma da alama musulma ce, dan kunsan hasken musulci baya ɓuya a fuskar bawa. A wani irin razane suka ɗaugo kai jin an buɗe kofar, guntun tsaki yarinyar ya ja tare da ɗaukar rigar uniform nata tana maidawa jikinta, da gudu Rimsha ta juya tana ruwan hawaye, to me abin kuka? Binta da kallo Mr Emmanuel ya yi, ita kuma yarinyar sai faman mayar da kayanta take yi, damko rigar uniform ɗin nata ya yi, cikin murya mai kama da na ƴan shaye shayen da turanci ya ce "Ina zaki je Fadila? Ai ban gama ba". Kara jan dogon tsaki ta yi tana faɗin "Mr Emmanuel ka bari sai an shiga class zan sato hanya nazo". Shafa breast ɗin nata dake tsaye kyam ya yi tare da lumshe idanu, kamar wani tsohon maye yana wani lashe baki. Ba dan ya so ba ya barta ta fice daga office ɗin bayan ta gama mayar da kayanta kenan. Tana fita ya lumshe idanu yana tunano Rimsha a cikin zuciyarsa, tun ranar da ya ɗaura waƴan nan shegun idanu nasa a kanta ita da Anaya yake haɗiye yawu, ya yi ƙoƙarin jan Anaya da wannan shashancin, sai dai bai sami dama ba, dan kullum tana tare da Rimsha, kuma kullum suna cikin class basu cika fita sosai ba, yasan idan ya fara da Anaya zai yi nasara, dan da alama bata da ilimin addini sosai, kuma akwai yarinta sosai a kanta, ita kuma Rimsha ba sai na gaya muku ba, ta san komai dan mummynsu babu kunya babu ɓoye ɓoye ta sanar musu da komai, ta faɗaɗa musu ilimi dan gujewa irin hakan, shiyasa ake son uwa ta rinƙa jan ƴaƴanta a jiki, ya zama daga bakinta suka san komai ba daga bakin kawaye or wani waje ba, baya son idan ya tinkari Anaya Rimsha ta sani, ya fi son kafin ta sani ya rigada ya lalata Anaya ɗin, Shiyasa bai yi wargin tinkararsu lokacin da suke tare ba, ya bari yana jiran wata ƴar dama, lokacin da Rimsha ta daina zuwa school, kwata kwata baya samun damar ganin Anaya ɗin, sai ya zo class nasu karantar da su, bata fitowa, bata da abokiyar hira, da an tashi breakfast ko ya aika a kirata ba zasu ganta ba, a dokar makarantar kuma ba'a yarda wani malami ya kira ɗaliba lokacin da suke class ba, sai dai ita ɗalibar ta fita a sace, idan aka kamata kuma zata yi bayani, a takaice dai Mr Emmanuel Anaya yake son fara lalatawa kafin Rimsha, dan idan Rimsha ta san kudurinsa, zata zuga Anaya ta kuma tsawatar mata a kan kada ta yarda da shi, tsab ya gama karantarsu jira yake ya sami ƴar dama ya cinma burinsa. Rimsha tana barin office na shi class nasu ta nufa, tana tafiya tana hawaye, abin ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, ace wannan kafurin yana lalata ƴar musulma, ta ji zafin hakan ba kaɗan ba, shi ne kuma abin da ya sanyata hawaye, sai da ta zo kofar class nasu ta tsaya tare da goge hawayenta tsab kafin ta shiga ciki, saman chairnta ta je zauna tana kasa da kanta dan kada Anaya ta gane ta yi kuka. "Rimsha me ya faru ne? Me ya same ki? Mr Emmanuel ya yi miki muguntar tasa ko? Azzalumin wannan mutumin akwai bakin mugu, ya ce ba zan baki ki rubuta bako? Ko dai dukanki ya yi ne". Cewar Anaya. Girgiza kai ta yi tare da miƙewa da sauri ta riƙo hannun Anaya ɗin suka nufi waje, binsu da kallo ƴan class suka yi har suka fice, suna fita suka haɗu da Uncle Faisal, gaisuwa suka ɗaga mishi, da fara'a ya amsa tare da tambayar Rimsha ya jiki, satar kallon Anaya ta yi tana mamakin ita kuma yaushe ta yi rashin lafiya? Kashe mata ido ɗaya Anaya ɗin ta yi alamar ita ce ta ce mishi bata da lafiya ne yasa bata zo school ba kwana biyu, ganin hakan yasa ta amsa mishi da ta ji sauki. "Ayya Allah ya kara sauki, na yi ta kiran numberki da Anaya ta bani dan na yi miki sannu ya jiki, sai dai kuma baki ɗauka ba". Kasa ta yi da kanta tana faɗin "Wayar ce bata a hannuna, tana hannun yayana ne, bai cika bani ita ba, Shiyasa ban ɗauka ba". "Okey tom shikenan yanzu dai ina zaku je?". Ƴan kame kame suka fara yi, dan suma basu san in da zasu je ba, ganin hakan yasa ya yi tunanin ko toilet zasu je ne, dan haka sai ya wuce yana faɗin "To ku kula dai sosai, kuma ku dawo da wuri dan kunga lokacin shiga class ya yi, muna da class daku yanzu, daga nan ma class naku zan shiga". Okey suka amsa mishi da shi tare da wucewa suka nufi ta hanyar toilets ɗin, shi kuma ya wuce cikin class nasu. A kusa da toilet suka tsaya shiru, sai kallonta Anaya take yi da mamaki, ita kuma ta rasa ta ya zata gayawa Anaya ɗin abin da take son gaya mata, suna tsaye a wajen sai ga Fadila ta nufo su, wani irin faɗuwar gaba ta ji lokacin da idanuwanta suka sauƙa a kan Fadila ɗin. Daga ɗan nesa da su ta tsaya, da hannu ta yi musu alama a kan su zo nan, ba musu suka nufeta dan senior su ce, dole su girmamata su kuma bi umarninta. Wallon walaƙanci ta fara yi musu kafin nan a walakance a yamutse ta ce "Ke ya sunanki?!" Ta yi maganar cike da izza, ta yi shi kuma tana kallon Rimsha. "Rimsha Nawazudden Sal......." Bata kai karshen maganar ba ta ɗaga mata hannu tana faɗin "Ban ce ki gaya mini sunan tsoho ba, iya sunanki kawai na tambaya, ina son ki buɗe kunnanki da kyau ki saurare ni!, Nasan kin ga abin da ya faru a office ɗin Mr Emmanuel, to wlh ina mai daka miki warning da kada ki kuskura naji maganar nan a wani waje, idan ba haka ba, wlh zan iya sakawa a ɓatar mini dake, kuma a ɓatar da banza, dan haka kibi a hankali". Shiru ta yi, bata ce da ita komai ba, dan bata san me zata ce da ita ɗin ba, wannan rayuwa tana wahalar da ita sosai, ita muguwar tausayi ma Fadila ɗin take bata, tana ta tunane tunane har Fadila ta bar wajen ba sani ba. Dafata Anaya ta yi tana faɗin "Rimsha me yake faruwa ne? Me ya haɗa ki da Fadila?" Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "Muje class Anaya, idan mun fita break zan gaya miki abin da ya faru". Okey ta amsa mata, a tare suka jera zuwa cikin class ɗin, lokacin already uncle Faisal har ya fara yi musu karatu, sannu suka yi mishi tare da wucewa zauwa mazauninsu, sai kus, kus, kus ƴan class ɗin suke yi akan su Rimshar da uncle Faisal, dan na gaya muku dokace idan an rigada an shiga class student basu fita, sai ga shi su sun fita kuma sun dawo uncle Faisal bai ce dasu komai ba bare ma ya hukunta su, hakan ya kawo cecekuce a wajen ƴan aji, sai dai duk cecekucen nasu, basu bari uncle ɗin ya ji ba, iya tsakaninsu ne kawai. A ɓangaren su Areef kuwa, suna komawa gida, cikin mutunta juna suka yi sallama, hannun jelly Imran ya riƙo zuwa bedroom nasu, Aseef kuwa, juya kan motar ya yi ya sake fita daga gidan, da alama wajen heartbeat zai je, Areef ɗakin Lion kai tsaye ya wuce ya kwanta. Suna shiga bedroom Imran ya jawota jikinsa yana faɗin "My jelly gaskiya hakurina ya kare, wai ba zaki tausaya mini bane? Ko so kike yi ne na auri wata matar?". Kuka ta saka mishi a kan lallai ita kada ya sake yin zancen wata mace, "To jelly ai ba zan iya jurewa bane, ina shan wahala sosai, in dai baki son na kara wani aure, to sai dai ki barni na rinƙa wasa dake". "Iya wasa?" Ta tambaye shi tana kallon kasa. "Eh iya wasa kawai, ba zan wuce hakan ba". Hannu ta zura cikin rigarsa tana shafa jirjinsa tare da lafewa a jikin nasa ta yi shiru, gata da shegen son kwanciya a jikinsa kamar wata mage, sai kuma ta ce lallai kada ya taɓa mata tula tula ma bare kuma babban lamari ya wakana, sai dai ta yi ta shafa mishi kirji tana jefa shi cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa, bawan Allah haka zai yi ta juyi a saman gado idan ta yi barci, sam baya son ya yi mata dole, ya fi so ne ya yi mata komai a hankali da kuma yardar ta. Ɗaukarta ya yi suka koma saman gado, sai kara shigewa jikinsa take yi, cikin dabara ya ɗago da haɓarta tare da haɗe bakinsu waje guda, ga shi ita ma ta iya kiss ɗin sosai, yana yi mata tana taya shi, sai ya fara fita a hayyacinsa kuma, sai ta saka mishi kuka alamar bata yarda ba, to a yau ma dai da ya haɗe bakin nasu, ba musu ta shiga kissing nashi cikin salo, shafa wuyarta ya fara yi yana gangarowa a hankali hankali har zuwa saman breast ɗin nata, tana jinsa bata hana shi ba, ba kuma ta yi wani motsi da zai nuna ta ji shi ɗin ba. A hankali ya fara shafasu yana ɗan matsasu, hannunta ta zura ta rungumo shi ta baya sosai, kara kankameta shi ma ya yi tare da zame bakinsa daga nata ya mayar saman wuyarta, nan take ya fara rikita ta da salon shi, ita ma ɗin dai ta taya shi, dan kuwa ta ɗauki lecture Akila da kyau da kyau, taya shi ɗin da take yi kuma ba ƙaramin kara haukata shi take yi ba, tun daga saman wuyarta yana gangarowa har izuwa bakin nipples nata, cikin salo ya capko ɗaya, yayin da ya sanya hannunsa ɗaya yana ƙoƙarin zuge zip ɗin wandon dake jikinta dan ya rabata da shi, murya can kasa kasa ta ce mishi "Yaya Imran ka cire rigar kan nan botir ɗin yana ji mini ciwo a kirjina". Bai iya amsa mata ba sai dai miƙewa da ya yi ya cire rigar tare da kashe wutar ɗakin, da yake gabaɗaya window curtains ɗin a sake suke, sai ɗakin ya yi duhu babu haske, cire mata rigar jikinta ita ma ya yi, sai dai bai cire mata wandon ba, ya bar mata kayanta dan ya ce mata iya wasa kawai zai yi, yasan idan ya yi gigin cire mata wandon tsab zasu yi faɗa yanzun nan, zata ce ba zata yarda ba, dan haka a hankali zai bita. Bayan ya cire mata rigar ne ya yi mata runfa da kirjinsa, hannunsa dukka biyu yasa ya capko tula tulan nata, a hankali ya fara wasa da su yana kallon face nata, ta runtse idanunta ruf tana ɗan turo baki, alamar dai tana jin abin da yake mata ɗin har cikin ƙwaƙwalwarta, cigaba da yi ya yi yana mai ɗan lasar wuyarta...... ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ *Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta* E33-34 Sai da ya tabbatar ta fita a hayyacinta, ya ruɗar da ita da salonsa, cikin dabara ya zame wandon jikin nata, ko kaɗan bata ji lokacin da ya cire ba, hayewa kanta da kyau ya yi tare da haɗe bakinsu waje guda dan kada ta yi mishi ihu idan ya shiga, ya kudura a ransa kome zata yi yau sai ya buɗe kayansa, idan bai buɗeta ba tabbas ba zata dai'na hana shi kanta ba, wasa ya cigaba da yi da harshensa a cikin bakinta, sai ƙoƙarin kama harshen nasa take yi yana zulle mata, duk dan ya ɗauke mata hankali ne. Cikin dabara ya mai da hannunsa kasa tare da kama bananarsa ya ɗan buɗe kafafunta ya zura abarsa, yana zurawa ya kankameta da kyau tare da kara manne bakinsu sosai, ƙoƙarin kwace bakinta ta fara yi dan ta yi mishi ihu, amma ina yaki sakinta, dan ba zai iya hakura ba yau, a hankali ya fara sucking nata, duka ta fara kai mishi a baya tana son kwace bakinta ya hanata, bai damu da dukan shi da take yi ba, ya cigaba da abin da yake yi yana mai kara manne bakinsu waje guda. Da kyar da kyar take numfashi hawaye wani na bin wani ta gefe da gefen kunnenta, kasa kasa ya furta mata kalmar sorry, yasan yau ba ƙaramin dirama zasu sha ba, yau sai sun yi ɗan karamin yaki, to amma ya zai yi, bashi da zaɓi dole ne ya karɓi hakkinsa dan kada ya cutu, ta kankame jikinta sosai da sosai, hakan ya haifar mata da zubar da jini sosai, saboda ya ɗan jimata ciwo, da farko a hankali ya fara yi mata, da tafiya ta yi tafiya, sai salon ya canza, bai san time da ya fara yi mata da karfi karfi ba, ga shi ta kankame jikinta da kyau, zame bakin nasa ya yi daga nata dan ya sami damar yin abin da yake buƙata da kyau, sai dai fa yana zame bakin nasa ya sanya hannunsa a saman bakin nata ya rufe dan kada ta yi mishi ihu, ta sha bakar wahala shi ma kuma ya sha wahala, dan kusan kokawa suka yi da ita, ga shi ta kankame jikinta, hakan ya basu bakar wahala dukkansu biyu. Sai da ya tabbatar ya mai da ita cikakkiyar mace, ya samu natsuwa sannan ya saketa tare da koma ya kwanta a gefenta, a lokacin kuma babu bakin yin ihu, duk ta yi laushi, numfashi ma da kyar take fitarwa bare kuma ihu, hawaye kam wani na bin wani, idanuwanta a runtse ruf, ta datsesu da karfin gaske, ban da shessheƙar kuka babu abin da zaka ji. Almost 10 mins yana kwance kafin ya lallaɓa ya miƙe, sai sauke numfashi a hankali hankali yake yi, yau ya sami abin da ya jima yake marari, ya sami abin da ya yi renon shi almost 12 years, buri ya cika, har wani kyalli face nasa take yi, daf da ita ya matso, murya kasa kasa ya fara magana "Am so so sorry my wife, na tuba ba zan sake ba". Tamkar babu ita a cikin ɗaki, ko motsawa bata yi ba, bare ya saka ran zata yi magana, sosai ya rinƙa rarrashinta yana bata baki, amma ina, ban da hawayen nan dai babu wani abin da take yi. Daga karshe dai ya hakura ya miƙe ya nufi toilet, ruwa mai zafi ya haɗa tare da dawowa ya ɗauketa, bai direta a ko'ina ba sai cikin ruwan, a wahale ta kara sautin kukan nata tare da kankame shi da karfi tana wani irin numfashi wadda dole ta baka tausayi, ya tausaya mata sosai, kasa sosai ya yi da murya ya cigaba da bata hakuri har ya yi mata wanka ya gama. Ɗaki ya dawo da ita, a saman sofa ya kwantar da ita sannan ya cire bed sheet ɗin ya shinfiɗa musu wani, har lokacin idanunta a rufe ruf, taki buɗewa sai kuka wahala kasa kasa take yi, saman gadon ya mayar da ita tare da rufa mata bargo dan yaga tana rawan sanyi sosai, toilet ya wuce ya yi wanka shi ma tare da fitowa ya shirya cikin wando three quarter fari da riga baki. Saman gadon ya dawo ya kwanta, a hankali ya fara ambatar sunanta, jin bata amsa ba kuma ta daina kukan da take yi ne yasa ya matso kusa da ita tare da ɗaura hannunsa a saman fuskarta yana sake ambatar sunan nata, da sauri ya ɗauke hannunsa jin irin zafin da jikinta ya yi, waro idanu ya yi yana kallonta, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, da alama barci ta yi, ga kuma zazzaɓi mai zafi ya rufeta, miƙewa zaune ya yi tare da zuro kafafunsa kasan gado kafin ya miƙe baki ɗaya ya nufi waje. Babu kowa a palon kasan, haurawa sama ya yi, a lokacin Lion ya dawo, bedroom nasa ya shiga, kwance ya isko Areef a saman gado yana zuba barci cikin kwanciyar hankali, shi kuma Lion yana balcony yana waya da TGA, key ɗin motarsa da ya bari jiya da daddare a ɗakin ya ɗauka ya nufi waje, kai tsaye pharmacy ya nufa, ya san cewa bai isa ya tinkari Lion da wannan magana ba, shiyasa bai nemi magani a wajensa ba ya nufi pharmacy kawai ya je ya haɗa mata maganin a can, Lion baya irin wannan wasan da su, ɗan gara ma da TRIPLETS nasa, wani lokaci idan yana jin yin hira da su yana tsokanar Areef ya ce mishi jarabarsa ta yi yawa, dole ya yi mishi tiyata ya cire mishi, Areef bawan Allah sai ya yi dariya ya ce in dai bai cirewa kansa ba, to shi ma babu mai cire mishi, baya irin wannan magana ma da Aseef kwata kwata, iya Areef ɗin ne kawai suke hakan, shi ma sai yana cikin nishaɗi sosai na wuce misali. A ɓangaren Rimsha kuwa, bayan uncle Faisal ya fita class ɗin nasu, Mr Emmanuel ya shigo ya raba musu papersu na test, yana fita kuma aka buga break time, cikin zumuɗi Anaya ta buɗe paperta dan taga nawa ta ci, ga mamakinta sai taga zero ya bata, zaro idanu ta yi tana kallonsu, nan take idanun nata suka cika tab da kwallah, dan kuwa tasan amsa daidai ta rubuta, tun da take bata taɓa samin ko 50 / 60 ba, 60/60 take samu kullum, sai tast na Mr Emmanuel ne zai wani bata zero, to me ta yi ba daidai ba? Ace gabaɗaya ta faɗi kai ba zai taɓa yiwu ba, dole idan ta faɗi wani zata ci wani. Student duk kowacce ta kama kanta zuwa waje dan su yi breakfast, ɗago kai Rimsha ta yi tare da sauke idanunta a kan Anaya ɗin tana faɗin "Anaya mu je top shop zan sayi sweet na melody da kuma conacaf....." Bata kai karshen maganar ba ta dakata sakamakon ganin yanayin da Anaya ɗin ke a ciki, idanun sun cika tab da kwallah. "Anaya lafiya idanunki suka cika da kwallah?" Miƙa mata paper ta yi ba tare da ta yi magana ba, damuwarta ɗaya ,daddynta ba zai taɓa yarda ba, ɗan boko ne tsantsa, bai basu ilimin addini kamar yadda ya basu na boko ba, mahaifiyarsu ma ƴar boko ce, degree gareta a ɓangaren computer engineering, so sun mai da hankali wajen bawa yaran kulawa ta fannin boko, yau idan ta kai wa mummynta wannan paper ta shiga uku da faɗa, daddynta ma idan ya dawo ba kyaleta zai yi ba, ko marking ɗaya suka faɗi a makaranta, sai iyayen nasu sunyi musu faɗa sosai tare da ce musu su tabbatar next time sun dawo da marking ɗayar nan, idan baku manta ba Azharuddeen Bature professor ne, kun ga kuwa boko ta zauna fiye da tunanin mai tunani, Allah kuma ya bawa yaran kwakwalwa, Anaya akwai su da basira na wuce misali, kullum ita ce first class, bata taɓa zuwa second ba, sai dai zuwan Rimsha school ɗin yanzu, da alama za su yi takara ba kaɗan ba, dan ilimin nasu kusan ɗaya ne za'a ce, kuma kun san dai dukkansu jikoki ne ga manyan ƴan boko, Barrister Naurat tare da Dr Salman, an sha boko an ƙoshi, akwai basira ba kaɗan ba. Zaro idanu Rimsha ta yi tana kallon paper, tun da take da Anaya bata taɓa kallon ta faɗi ko kwara ɗaya ba, fara karatan questions ɗin ta yi yana duba amsar da Anaya ɗin ta rubuta, tabbas duk da bata nan aka yi test ɗin, amma ta san wannan amsa da Anaya ta rubutu correct amsa ne, to me matsalar kenan? Ta tambayi kanta, ita kam Anaya tuni ta fara ruwan hawaye, zuciyarta na yi mata kuna ba kaɗan ba. Miƙewa Rimshan ta yi daga saman nata chair ta dawo saman table ɗin Anayar ta zauna, rarrashinta ta fara yi tare da bata shawara a kan ta je ta tambaye shi me yasa zai sanya mata zaro bayan kuma correct amsa ta rubuta mishi, ba ƙaramin daɗin shawarar ta ji ba, goge hawayenta ta yi tare da miƙewa ta karɓi paper ta nufi waje, har zata fita Rimsha ta yi saurin dakatar da ita tuna abin da ya faru ɗazun, abin da ta gani da idanunta ba jita jita ba. "Anaya ɗan zo". Ba musu ta juyo ta dawo, sai murmushi take yi tamkar ba ita ce ta gama kuka yanzu ba, burinta kawai ta isa gare shi ya gyara mata sakamakonta ya bata taci, idan ba haka ba zata iya suma, dan sun ɗauki boko da mahimmanci sosai. Kusa da Rimshar ta zo ta tsaya tana faɗin "Me kuma ya faru kika kirani Rimsha?" Nisawa ta yi kafin ta fara bata labarin abin da ta gani, daga karshe ta ce mata ta kula da kanta sosai, da yake ita ba ilimin addini gare ta ba, bata san illar hakan ba, kuma tana yawan kallace kallacen fina finan Turawa, sai bata wani ɗauki abin a matsayin wani babban abu ba, bata ma damu ba idan ance za'a rabata da budurcinta, dan bata san amfaninsa ba, film da take gani duk tana ɗauka ma abu ne mai kyau, to abun ku da iyaye tantagaryun ƴan boko, kullum suna wajen aiki, basu da lokacin yaran bare ma har su tsaya yi musu bayani a kan irin wannan matsala, tsakaninsu da yaran sai dai idan sun kawo assessment su taya su yi, bacin haka sai duba takardun makarantar nasu dan suga me aka rubuta, ko me suka koya yau, so a takaice dai ita Anaya bata ma san me ainahin amfanin budurcin ba bare ma ta ji ciwo dan an rabata da shi. Cikin nuna ko in kula ta amsawa Rimshar da "To suma irin na India film suke yi kenan? Ki ce mun samu India a Nigeria". Baki wangale Rimsha ke kallonta, ko a jikinta wai an yakushi kakkausa, "Anaya kina da hankali kuwa? Kin san me kike faɗa kuwa? To wlh bari ki ji na gaya miki, idan babu wannan abin da na gaya miki, to babu mace". Zaro waƴan nan dara daran idanun nata na gadon Dr Salman ta yi, dan suma sun gaji idanu kam ba karya, daga dara daran idanun nan nasu zaka iya gane cewa jinin Dr Salman ne, zama ta yi saman chair ɗin ta tana faɗin "Rimsha kenan mutuwa mace zata yi ko kuma me na ji kince idan babu shi ba mace". Ganin ba zata fahinci abin da take nufi bane yasa tai amfani da ƙwaƙwalwarta da basirar da Allah ya bata, tun da ta fahimci tabbas Anaya ɗin ta tsorata da jin babu mace, to bari ta yi amfani da hakan ta tsoratata dan ta kare mutuncinta, idan ta ce zata tsaya yi mata nasiha da bayani a kan me ake nufi da budurci, to tabbas ba zata fahinci komai ba a cikin ƙaramin lokaci haka, dan babu komai a kanta sai boko, dan haka sai ta ce mata "Tabbas Anaya, idan akwai abin da ya fi mutuwa ma mace zata yi, kuma idan kika yarda wani namiji ya taɓa ki ba ɗan uwanki na jini ba, zaki fara rashin lafiya mai tsanani, ko an kai ki asibiti ba zaki warke ba, kuraje zasu fito su ɓata miki jiki, daga nan sai ki mutu, idan kuma kika bari wani namiji ya yi zina dake, to a wajen ba sai kin motsa ba zaki mutu, ba zaki sake kallon su mummy ba, dan haka kada ki yarda Mr Emmanuel ya taɓa ki, kinga shi krista ne ma, yana taɓaki kaɗan dodansu na church zai shanye jininki ki mutu, dan haka sai ki kula sosai, kada ki yarda kowa ya taɓaki". Zaro idanuwan nan ta yi tamkar zasu faɗo kasa, muryarta har rawa yake yi, ta gama tsorata, har wani zufa ta fara haɗawa, hankali a tashe ta ce "Yanzu Rimsha ita ma Fadila zata mutu?" "Kwarai kuwa, nan bada jimawa ba, dan haka kema idan kina son ki mutu to ki yarda wani ya taɓaki". Narai narai ta yi da idanu tamkar zata yi kuka, duk ta rasa me yake yi mata daɗi a duniyar baki ɗaya, yanzu shikenan idan wani ya taɓata zata mutu, Allah ya sota ma ita ba wanda ya taɓa taɓata sai yaya Feroz ɗinsu da daddy, ko Uncle Shitu bai taɓa taɓata ba, yau ta shiga uku ta lalace, duk wannan a zuciya take zantukan nan. Ganin ta tsoratata sosai ne yasa Rimshar ta fara rarrashinta tare da kara mata karfin gwiwa da shawari ta yadda zata kula da kanta, daga karshe ta ce mata dama idan kana yaro wani ya taɓaka hakan ba zai faru da kai ba, sai ka girma ka fata period ne idan wani ya taɓaka zaka mutu, da yake ta san Anaya ɗin ta fara period, sai ta fito mata ta wannan hanyar, shiru ta yi tana tunanin tabbas last period ɗin da ta yi lokacin mummyn Rimshan sun zo gidansu sun ɗan yi kwana biyu, tabbas da ta gane tana yi ta tsawatar mata a kan kada ta yarda wani namiji ya taɓa ta, tuna hakan yasa ta kara gasgata zance Rimshar, bayan mummyn Rimsha ma, mai aikin gidansu ta yi mata faɗa sosai a kan kada ta kula maza, ita kuma mummynta tana can wajen Aiki, idan ta fita da safe sai karfe 6 na yamma take dawowa, dan haka bata sanin me ma yake wakana a cikin gidan, ranar da Anaya ɗin ma ta fara period ɗin, mummyn nasu bata sani ba, bata nan, mai aikinsu ne ta taimaka ta nuna mata komai, da mummyn ta dawo, iya always da sabbin pant ta bada aka sayo mata, daga haka ba wani bayani da ta kara mata, da alama ita ma mummyn babu ilimin addini sai zallar boko ne a kanta, irin waƴan nan iyaye na Anaya su suka fi yawa a duniyar mu ta yau, dan girman Allah mata mu kula, ƴaƴa hakki ne a kanku da Allah zai tambaye ku ranar gobe kiyama, amma wasu sai su zaɓi abin banza na duniya su yi watsi da tarbiyar ƴaƴansu, idan kuɗi ya bugasu sai su wani ɗebo ƴan aiki, Allah ba ƴan aiki zai tambaya ba, iyaye zai tambaya, ƴarki mace ki jata a jiki ku zama kawaye, duk wata matsalarta ya zama ke zata fara gayawa kafin kowa, kada ki yarda ace ƴarki tana da wata Aminiya da zata rinƙa gayawa sirrinta ba ke ba, ko da sunan wasa kada ki yarda da hakan, dan Allah iyaye a gyara, kada kuɗi da jin daɗin duniya su ruɗeki, akwai mutuwa a tafi a bar duk wani kuɗi da jin daɗin, Allah ya kyauta yasa mu dace ya kuma sa mu gyara, kuna dai ganin mummyn Rimsha baiwar Allah, dalilin tarbiya da ta basu yau ga shi nan anwayi gari al'umma da dama suna amfanuwa da ƴaƴa nata, badan Rimsha ba ya kuke tunanin rayuwar Anaya zai tafi? Ba dan Jehan ba ya kuke tunanin rayuwar Hanan, Maryam, Adiva, zasu kare? Ku duba irin kasadar da Jehan ta ɗauka a kan Maryam, duk dan me? Dan ta kare mata mutuncinta, da mummynsu bata gaya musu mahimmancin shi ba zasu matsa su shiga kasada dan kula da nasu har wanda ba nasu bane? Da ba'a gaya musu amfaninsa ba za su damu da kula da shi har haka ne? Da bata basu tarbiya ba, ya kuke tunanin rayuwarsu zai kasance? Ku duba yadda suka gogi wahalar rayuwa, Rimsha ta sha zullewa maza ga irinsu boda jamiu, duk dan me? Dan an gaya musu mahimmancinsa, so yana da kyau tun yara basu girma sosai ba, da sun ɗan fara hankali, ki zaunar da su, ki nitsar dasu, ki gaya musu amfaninsa, idan ta kama ki haɗa musu da tsoratarwa, duk dan rayuwarsu ne, a raba yara da kawaye, zina ta yi yawa, lesbian, wannan abu yana yi mini ciwo, yana damuna a cikin zuciyata, kaga yarinya ƴar 15 to 16 years ta san lesbian tana kuma yi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allahumma ajirni fi musibati, kuma duk abin da yarinya zata yi idan kuka bincika sanadiyar kawayen banza ne, ku duba rayuwar Aafia, dan Allah kirana a gareku iyaye, ku kula da ƴaƴa, ban da kawaye na kara faɗa, a rabasu da kawaye, tun tana karama ki cusa mata tsanar kawaye, idan ta tashi da shi shikenan kin huta, dan Allah a ja yara a jiki, waƴan nan bala'i na yanzu sun yi yawa, saɓon Allah ya yi yawa, Allah yasa mu gyara amin. Anaya dai duk ta firgi ce ta tsorata, da kyar Rimsha ta shawo kanta ta yarda zata je office ɗin Mr Emmanuel ɗin, da farko ta ce ta fasa zuwa, ta hakura ta karɓi zero ɗin, sai da ta yi ta bata baki sannan ta miƙe jiki ba kwari duk a mace, tayi ligis ta nufi office ɗin nasa, ita kuma Rimsha ta gyara zama tana jiranta ta dawo su je top shop. Baki ɗauke da excuse ta shiga office ɗin, yana zaune ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ganinta yasa ya saki cool murmushi yana faɗin "I knew dama zaki zo, me matsalar?". Saman kujera ta zauna, jikinta sai kerma yake yi, murya a sanyaye ta fara magana "Mr Emmanuel i came to complain about my test results". Kafeta da shegun idanun nan nasa masu kama dana mujiya ya yi, yana kallonta tare da lashe baki kamar wani tsohon maye, idan baku manta ba na gaya muku, bayan halittar dara daran idanu da suka gada har da breast and hips, to ita ma fa Anaya akwai shi, sak Jehan ɗin ne ba maraba, duk lafiyayyen namiji idan ya gansu sai ya kyatsa. Miƙa mata hannu ya yi akan ta bashi paper ya gani, ba musu ta miƙo mishi hannunta sai rawa yake, karɓa ya yi tare da ajiyewa a gefe, a maimakon ya buɗe ya duba, sai bai duba ba, cike da maitarta ya fara magana da wata shegiyar muryarsa kamar an tada injin niƙa, tamkar wadda ya jima a cikin harkar shaye shaye. "Anaya Azharuddeen Bature, na sani, nasan kinci questions naki dukkan, amma kuma ai ni baki ci nawa rajarabawar bane yasa na baki zero a can". Ɗan zaro idanu ta yi tana tambayarsa wani jarabawa kuma bayan wadda ya rubuta musu suka yi, ko dai ya yi wani bata sani bane? Da yake babu Allah a zuciyar bare ayi zancen kunya, sai ya fito kwaro kwaro ya gaya mata irin abin da yake da buƙata su yi kafin ya bata result mai kyau, a razane ta ce mishi ba zai yi wu ba, kai tsaye shi kuma ya ce mata to ba zata taɓa cin test na shi ba, kullum idan ta yi zero zata samu, idan dai har bata bashi kanta ba, to wlh ta shirya karɓar zero kullum, idan kuma ta shirya bashi kanta ko yanzu ne, to ta shiga toilet na shi dake cikin office ɗin zai zo ya sameta, tsabar rashin kunya har da ce mata ya yi ba zata jima ba, ba zai fi minti 20 ba anyi an gama, kuma kada ta damu ba wanda zai gane, dan ba zai yi mata yadda wani zai gane ba, da gudu ta miƙe ta yi waje dan ma kada ya ce zai taɓata, sai dukan uku uku kirjinta yake yi, har wani sara mata kanta yake yi, yanzu me zata cewa daddy da mummynta akan wannan test ɗin?. Amma fa yadda Anaya ta yarda da boko ta ke kuma so, da Rimsha bata yi mata hakan ba, da tabbas dan ta ci test nata zata yarda mishi da abin da yake nema, dan dai kunga, da farko da Rimshar ta gaya mata, ba ta ɗauki abin a wani matsala ba, Allah dai ya sota da rahma ya kuma tsareta a yau kam, sai dai bamu san me gaba zata haifar ba. Kuka ne mai karfi ya kubce mata, a ɗari ta shiga class ɗin nasu, Rimsha na ganinta ta miƙe a razane tana ambatar sunanta tare da tambayarta lafiya, zuwa ta yi ya rungumeta tana kuka ba tare da ta yi magana ba, jijjigata Rimsha ta fara yi tana ambatar sunanta, "Anaya lafiya kuwa? Ki yi mini magana mana, dan girman Allah ki gaya mini kada ki saka na suma, kin ɗaga mini hankali sosai, wani abin ya yi miki ne?". Cikin kuka ta gaya mata duk abin da ya faru daga A har Z ta feɗe mata biri har wutsiya, daga karshe ta ɗaura da cewa ita test nata ne ma ya dame ta, yanzu Mr Emmanuel ya ce ba zai sake bata result mai kyau ba, ta shiga uku ya zata yi. Goge mata hawayen nata ta fara yi tana rarrashinta tare da bata hakuri akan kada ta damu dan ya bata zero, ta barshi da Allah, zai saka mata, idan ta je gida ta kwana sallah ta kai kukanta ga Allah, zai yi mata maganin shi, da kyar ta samu ta rarrasheta ta yi shiru, a yau dai basu fita break ba har a ka dawo class, duk sun yi jugum jugum da su, abin gwanin ban tausayi, Rimsha abin ya shiga jininta sosai, ta san ita ma da wuya idan ba zero zai yi ta bata ba, yau duk wani karatu da aka yi musu, bai wani shiga kansu ba, har lokacin tashi ya yi, Rimsha aka fara zuwa ɗauka, tana ganin motarsu ta ce da Anaya ta zo su gaisa da ƴan uwanta, da murna Anayan ta bita suka je, sai dai ga mamakinsu sai suka ga Mark ne kawai ya zo, ta so ta tambaye shi inasu yaya Areef, amma ba sai na gaya muku ba, kun san halinsa sarai, bata ga fuskar tambaya ba, ko kallon in da take ma bai yi ba, Anaya tana ce mishi good afternoon sir, amma ina ko kallonsu bai yi ba bare su saka ran zai amsa musu. Ɗan zunguran Rimshar ta yi kasa kasa ta ce "Rimsha a ina kuma kika samo Bature? Ko dai ɗan uwan ki ne? Dama kuna da ƴan uwa turawa ne?". Da yake bata taɓa bata labarin TRIPLETS ba, ita tana da siriri sosai, iya hirar school kawai take yarda su yi ban da na gida, wani lokaci har faɗa Anaya ɗin take yi mata ta ce wato ba zata bata labarin ƴan uwanta bako, sai dai ta yi murmushi ta ce zata bata mana, da haka suke rabuwa. Yanzu ma murmushi ta yi tare da shigewa cikin motar tana faɗin "Idan nazo gobe zan gaya miki, amma dai ba ɗan uwana bane, soja ne mai yi wa su yaya Areef girki". Ɗan sake leƙo shi Anaya ɗin ta yi, har ga Allah ya yi mugun shiga ranta, ta ji tana bala'in son shi, shi kuwa Rimsha na shiga ya kunna motar ya wuce suka bar Anaya tsaye tana ɗaga musu hannu. Suna fita school ɗin uncle Shitu na danno hancin kan nasa motar, ya zo ɗaukar Anaya, Rimsha hankalinta na kan jakarta tana ɗan duba takardunta, bata gan shi ba, sun yi saɓani. Uban gudu sosai Mark yake shararawa a kan titin nan, suna mantawa nan a Nigeria suke, ba Washington DC ba ne, Allah ya tsare suka isa gida lafiya lou, yana kashe motar a parking space ta riga shi fitowa ta nufi cikin gida, binta da kallo gateman ya yi, babu kowa a palon kasa, kai tsaye sama ta nufa. Tana saka kafarta a saman benen shi ma yana sako kafarsa Brady na makale a bayan shi, dan bashi da wajen zama sai ya ɗane bayan Lion ɗin, ya iya tsiya sosai karen nan, baya taɓa yarda ya tafi da kafafunsa in dai ba dole ba, tun yana ɗan jariri Lion ya saba da goya shi a baya, shiyasa da ya girma ma yaki dena hayewa, ko Lion ya ce ya sauƙa ya tafi da kafa sai yaki kamar wani yaro, duk wata tsiya karen nan ya iya shi sanka sanka, da alama garden zasu je, yana ganinta ya diro kasa daga bayan Lion ɗin, kunsan karnika da shegen son shinshina mutun su ji ko daga ina ya fito, kun san su kamshi suke bi. Ganin ya diro kasa yasa ta fara ja da baya da baya, ko sannu Lion bai ce mishi ba, bata ankara ba sai ji ta yi ta buge mutun ta baya, da sauri ta juya dan ganin waye ne. Areef ne daga shi sai singlet da three quarter, yau garin ana zafi, rana ta take, kallon Lion dake ta tafiyarsa ko kallon in da suke bai yi ba ya yi, shi kuma Brady duk da Areef ya zo bai dena nufota ba, zuba mishi ido Areef ya yi sai da ya kariso wajen yana ƙoƙarin fara shinshinarta, wani wawan mari Areef ɗin ya kai mishi a kumatunsa, da karfi ya daka haushin da ya sanya Lion da ya yi gaba juyowa dan ya ga me ya same shi. Kara mishi wani marin Areef ɗin ya yi, cikin harshen turanci ya tambaye shi me Rimsha ta yi mishi da yake takura mata a gidan nan? Ta shiga harkarsa ne? Ko kuma ta taɓa kula shi ne? Sit ya natsu tamkar yaro da aka nitsar ake yi wa faɗa da nasiha mai ratsa jiki, kun san fa suma dabbobi suna jin magana sosai,. Abin ya ɓatawa Lion rai, dan me akan wata Rimsha za'a marin masa Bradynsa, dan haka cikin harshen turanci ya ce da Brady "B fight for your ride!". Yana kai karshen maganar ya fice daga palon abinsa. Ai kuwa tamkar alluran soja ya yi wa Brady ɗin, nan take ya daka haushi tare da yin tsalle ya haye jikin Areef ɗin ya fara kai mishi yagushi a fuska, ba ji ba gani yake yagushin shi, ƙoƙarin kama hannun nasa Areef ya yi, amma ina yaki yarda ya bada damar yin hakan, daga jikin Areef ɗin ya sake daka tsalle zuwa jikin Rimsha dake tsaye a wajen, ita ma yagushi ya fara kai mata ta ko'ina, yana yi yana daka uban haushi kamar ba gobe, da ganga kuma Lion ya ce mishi hakan, dan yasan Areef ba zai iya kama shi ta sauƙi ba, horon sojoji gare shi, ya horu ba karya, idan baku manta ba na gaya muku mafaɗaci ne na a mutu, kama shi ba abune mai sauki ba, yana da wayo over, dama shi Lion ɗin ne ya ce mishi ya rinƙa jin maganar TRIPLETS nasa, shiyasa yake raga musu, yanzu kuma tun da an ce ya kwaci ƴancinsa ai shikenan. Sai ihu Rimsha take yi ta zube kasa tana birgima, ganin zai yi mata illah sosai ne yasa Areef ɗin nufarsa a zafafe, ransa a matukar ɓace ya yi ƙoƙarin kama shi, da yake yasan idan ya kama shi ba zai yi mishi da daɗi ba, sai da ya bari ya iso yana ƙoƙarin damko shi, sai ya daka wani uban tsalle ya haye saman kan Areef ɗin ya rufe mishi idanu da gashin jikinsa, kokawa suka fara yi ba kaɗan ba, a tsatsan ɓacin rai Areef ya yi wurgi da shi, ya bugu da jikin bango ya faɗi kasa, wani mahaukacin haushi ya sake dakawa tare da miƙewa ya yi wani girgiza, a guje ya sake mufarsu, Areef bawan Allah ba zai iya faɗa da shi bane saboda ciwon dake kirjinsa, bai gama warkewa ba, shiyasa ma Bradyn ya bashi wahala, baya iya ɗaga hannunsa sosai dan a gefen kafaɗa ne ciwon take, kuma Lion yana sane da hakan ya ce Bradyn ya kwatan wa kansa ƴanci, yasan a yanzu haka Brady zai ji musu ciwo sosai, da dai Areef yana da lafiya ne, da wane kaniyar Brady ya iya taɓasu ma, tuni zai yi wurgi da ɗan banza ko ya murɗe mishi wuya ya mutu kowa ma ya huta da masifarsa. Yana nufosu da gudu Aseef da ya fito tun ɗazun ya zuba musu idanu ya sha gabansa, shi kuma Areef bama ta su yake yi ba, ya duƙa yana rarrashin Rimsha da Brady ya yagushiwa hannu, fuskarta ya so yagusa da waƴan nan shegun faratun nasa masu tsini, shi ne ta sanya hannunta ta tare face ɗin nata yagushin ya sauƙa a hannun nata, sai jini yake yi, shi ne Areef ya tsugunna yana bata hakuri tare da riƙo hannun nata yana dubawa. Shi kuma Brady, faɗa suka fara yi da Aseef gadan gadan, sai wani ƙoƙarin yagushin Aseef yake yi, ai kuwa Aseef ya yi wurgi da ɗan banza, da gudu ya sake tashi ta nufo shi, a karo na biyu kuwa, maƙogoronsa Aseef ɗin ya damko, da karfi ya shaƙesa tare da zare mishi ido, cikin harshen turanci dai ya ce mishi "Au ka manta ni na sayo ku kenan? Da ni zaka yi faɗa? Ko Areef da ka jiwa ciwo dan bashi da lafiya ne mara kunyar banza, idan baka rabu da mu ka bar palon nan ba Allah sai na murɗe maka wuya ka mutu mun jefar da banza". Haushi ya daga mishi da karfi, mari shi kuma ya kifa mishi a fuska tare da damko hannayensa dukka biyu ya sake yin wurgi da shi a jikin bango, a wannan karon dai a hankali ya yi haushin, alamar ya jigata kuma ya wahala, ko kallon in da yake Aseef ɗin bai yi ba ya nufi su Areef dake ta faman yi wa Rimsha sannu. Kusa da ita shi ma ya zo ya tsugunna tare da kamo hannun nata yana mata sannu, sai kuka take yi, shi ma Areef ya sha yagushi a fuska ba karya, miƙar da ita Aseef ya yi a kan suje ya saka mata magani, ba musu ta bi shi, shi kuma Areef ya ɗauka mata jakar school nata, suka karisa hayewa saman suka bar Brady kwance a kasa yana mayar da numfashi, ya wahala, ba karamin buga shi da bango Aseef ya yi ba, dan ma ya yi sa'a Areef ba shi da lafiya ai da murɗe wuyarsa zai yi ya mutu, dan yanzu tun da ya fara takurawa Rimsha Areef ɗin baya son shi, ita kuma abin da bata gane ba, idan ta gansu kada ta gudu, in ta gudu sai sun bita, amma da ta gansu zata zura a guje dan tsoro. Sun zo zasu shiga ɗakin Lion ɗin ta tsaya, kallonta suka yi "Lafiya Rimsha?" Areef ya tambaya, cikin muryar kuka ta ce "Yaya Areef ina tsoron shiga ɗakin yaya Saif ni kam, zan zauna a nan palo kawai". Ɗan lumshe idanunsa ya yi tare da sake warosu a kanta, da hannu ya yi mata nuni da ta shiga ba damuwa, bata son yin musu da babban mutun, dan haka sai ta shiga kawai. A saman bakin bed nasa Aseef ya zaunar da ita tare da ɗauko A box, saman bedside drawer ya ɗaura A box ɗin kafin ya fara buɗe wa yana duba magani, zama gefenta Areef ya yi, Aseef ne ya yi musu dressing na wajen tare da taimakon Areef ɗin, shi ya nuna mishi maganin da zai yi musu amfani da shi da sauransu. Rimsha ta sha kuka ba karya, dan maganin yana da zafi, sai rarrashinta suke yi, Aseef ya rakata har ɗaki sannan ya dawo, a ɓangaren Lion kuwa, sam bai ji daɗin saka Brady da ya yi da ya yi faɗa da Areef ba, dan kuwa yasan tsab zai yi wa Areef lahani, amma ba yadda ya iya zuciya ce ta ɗebe shi, ya ji babu daɗi yadda Areef ɗin ya fifita Rimsha da ya sani jiya jiya a kan Brady da suka jima. (kai gaskiya Lion da sauranka, saboda wakalanci dan baka ɗauki ɗan adam da daraja ba shi ne zaka ce kare ya fi ta, a fifita kare sama da mutun kenan? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wannan rashin sanin darajar mutun har ina? Gaskiya ya kamata ace Lion ko ba yawa ne ka san darajan mutun.) A ɓangaren Imran kuwa, lokacin da ya fita, pharmacy ya je ya haɗo mata magunguna ya dawo, har lokacin barcin wahala take yi, kiran Akila ya yi a waya ya tambayeta ina dollyn Jellyn, ta gaya mishi tana nan, ta bawa mai gadi ya zai fi kula da ita, dan wata rana idan tana da class ta tafi school babu mai bawa dollyn abinci, okey ya amsa mata da shi tare da ce mata zai zo ya ɗauka da daddare, tom ta amsa mishi da shi, ruwa mai sanyi ya tsaya a palo ya ɗauko mata tare da komawa cikin bedroom ɗin nasu, gefenta ya zauna jikin nata ya tsananta zafi over, har lokacin sai ajiyar zuciya take sauƙewa, wani irin mugun tausayinta da so da kaunarta ne suke kara ratsa shi, a hankali ya fara ƙoƙarin tashinta dan ta sha magani, yana yi kirjinsa na dukan uku uku dan yasan za'ayi dirama ba karya. Da yake bata da lafiya sosai, sai bata wani bi ta kansa ba, ko da ta tashi, kuka kasa kasa kawai ta sa mishi, rarrashinta ya rinƙa yi tare da bata magani, karɓa ta yi ta watsa a baki, shi kuma ya sanya mata ruwa a baki, bayan ta gama ta koma ta kwanta tana kuka kasa kasa, yau dai bakin tsiwa ya mutu murus, kukan ma baya fita sosai. Kusa da ita ya kwanta, sai rarraahinta yake yi, da haka har wani barcin ya ɗauketa, kun san mai zazzaɓi da yin barci minti minti, shiru ya zuba mata idanu yana kallonta yadda take barci tana ajiyar zuciya, zubawa ɗan bakin tsiwar nan idanu ya yi, a hankali furta "Allah yasa daga haka bakin ya yi sanyi".......... To nima dai da Amin na amsa maka dan gaskiya idan bai yi sanyi ba akwai matsala kana ruwa. A ɓangaren Rimsha kuwa, uniform nata ta cire tare da wucewa toilet dan ta yi wanka, har lokacin hannun nata yana ɗan yi mata zogi kaɗan kaɗan. Bayan ta gama wanka, ta shirya cikin doguwar riga abaya baka ta haye gado, yunwa take ji amma tana tsoron fitowa waje, a wannan hali Areef ya shigo ya same ta, lallaɓata ya yi ta miƙe su je su ci abinci, bata yi mishi musu ba dan yunwa take ji dama, tsoro ne ya hanata fita. A palon kasa suka isko Aseef saman table yana jiransu, zama suka yi, kamar dai yadda suka zauna da safe, sun sakata a tsakiya, Mark ne ya zo ya yi serving nasu, bata musa ba, ta ci abincin nasu, yau kam ma kusan irin abincin Nigeria ne, shinkafa ce tasu ta can zara zara, sun dafata koriya shar, ta ji nama ba karya, sai wasu daga cikin kayan lambunsu da suke amfani da shi da sauran ingredient nasu, ta ci sosai dan ba karya ta ji yunwa, bayan sun kammala suka miƙe Areef ya ce ta zo su je garden, ba dan ta so ba ta bisu, yanzu tsoron Lion da Brady take yi sosai ba karya. Zaune suka isko shi yana waya da daddynsu, daddy ya ce yana son ya zo Nigeria, shi kuma ya ce a'a ba yanzu ba, daddy ba zai iya jure rashinsu a kusa da shi ba, amma hakan ya hakura ba dan ya so ba, Brady na kwance a jikinsa, ya sha wahala ne yasa ya lafe a kirjin Lion ɗin tare da lumshe idanu. Ita da Areef kujera ɗaya suka zauna, shi kuma Aseef kusa da Lion ya je ya zauna yana wani murmushi, yana son gayawa Lion ya je ya nema mishi auren AKila, amma ya fi son ya sami lokaci na musamman ya gaya mishi. (Jama'a Lion da zuwa neman aure, Wayyo cikina anya kuwa wannan abin zata yuwu?🤣 Ba gara ma Areef ɗin ba, kuma dai ji yadda Lion yake cewa Imran ya kula da waƴan nan halittu🤣 wayaga Lion a wajen Abba ya je neman aure🤣) 💋GIDAN ABBA💋 ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ *Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta* E35-36💋 💋GIDAN ABBA💋 Tun da Ammie ta shaki kamshin perfume ɗin Lion sabuwar rayuwa ya shigeta, duk wasu aljanun dake gidan da wasu dodannin sun gudu, rayuwarta ta bayane ya fara dawo mata, Baiwar Allah ashe duk rayuwar da tayi tsawon shekarun nan bata cikin hayyacinta, bata sani ba, yanzu ne ta dawo normal. Wani daddaɗar kamshi air freshener ne yake tashi tun daga cikin babban palon kasa har zuwa harabar gidan, ko'ina na palon a tsananin gyare yake tsab, sai tashin kamshi ko'ina yake yi, har wani kyalli kayan cikin palon suke yi saboda tsantsar gyara da suka sha, gidan shiru da alama Akila ta tafi school. Baki ɗauke da sallama Abba ya shigo cikin palon, ko kaɗan babu alamar mamaki a kan fuskarsa, domin kuwa shi ma yanzu ya dawo cikin hayyacinsa, abin da yasa kuma bai yi mamakin gyara palon da aka yi ba, saboda already yasan Ammie ba kazamiya ba ce, mace ce mai bala'in tsabta na amutu, akwaita da son gyara, ga bala'in son kamshi, shiru shiru bata son hayaniya, sai dai fa idan ka taɓota, zaka gane annabi ya faku, bata da fara'a sosai, amma ba laifi tana ɗan murmushi, yanzu gabaɗayansu ita da Abba sun dawo cikin hayyacinsu sanadiyyar turaren Lion........NASAN KOWA A ƘAGE YAKE DA YA JI TARIHIN AMMIE, TO KU GYARA ZAMA IN SHA ALLAH TARIHINTA NA NAN TAFE NAN BA DA JIMAWA BA, NIMA NA ƘAGU NAJI MENENE MATSALARTA? ME TAYIWA WAƳAN NAN SHAIƊANUN ALJANUN SUKE AZABTAR DA ITA HAR HAKA, GA DUKKAN ALAMU DAI SUN NUNA MUTUNIYAR KIRKI CE A RAYUWARTA TA BAYA, TO MENENE YASA HAKAN YAKE FARUWA DA ITA? KU KASANCE DA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA DAN JIN YADDA KOMAI YA WAKANA. Sama ya nufa yana mai shaƙan kamshin air freshener mai bala'in daɗi da yake fitowa daga cikin bedrooms nasu, a ƙage yake da ya shiga cikin ɗakin nasu, ɗakin Ammien ya fara nufa, baki ɗauke da sallama ya shiga, tana zaune saman dadduma ta idar da sallar azahar tana addu'a, ko'ina a cikin ɗakin nan a gyare yake tsab, ga azababben daddaɗar kamshi da kuma sanyin Ac mai ratsa zuciya yana tashi. Sai wani lumshe idanu yake yi ya kariso cikin ɗaki, da sauri ta miƙe tare da nufo shi tana yi mishi sannu da dawowa cikin harshen turanci, da yauwa ya amsa mata tare da rungumota, ta sha kwalliya da wata danƙareriyar doguwar riga mai bala'in kyau da tsada, bata yi wani make up sosai ba, dan ba wani son make up ɗin take yi ba, iya ka powder ta murza da kwalli, ta ɗaura gyalen rigar a kanta kafin ta sanya hijabi, dukkansu bayin Allah sun shiga sabuwar rayuwa, da alama ma sun mance da rayuwar da suka yi a baya, idan kuma basu mance ba, to akwai wani abu a kasa, amma lokaci ne zai nuna mana komai, dan abin da mamaki yadda Abba bai yi mamakin sauyawarta ba, duk da eh yasan haka take a baya, amma basu nuna wata alamu da zata nuna cewa sun san sun yi rayuwa cikin kazanta da wahala ba, ko da yake dama idan dodannin ma suka zo suka zanesu, mantar da su komai suke yi, koma dai me lokaci zai nuna mana menene yake faruwa? Menene gaskiyar lamari?. Sannu da zuwa ta yi mishi, shi kuma cike da nuna so da kulawa ya tambayeta ina su Imran, AKil, AKila, basu dawo bane?, Da mamaki cikin harshen turanci ta ce "Su Imran ban san in da suke ba, Akila kuma ta tafi school, amma ka kira mini Imran ɗin a waya, ya zo maza, ko ina suka shige Oho". Sai da ta yi maganar ya tuna Akil ya gaya mishi zai koma Madina sati mai zuwa, ya sha'afa da zancen baki ɗaya sai da ta yi maganarsu yanzu. To ya amsa mata da shi tare da ciro waya ya kira number Imran ɗin, bugu ɗaya ya ɗaga, cikin girmamawa ya gaishe da Abban nasa, da fara'a sosai a kan fuskarsa ya amsa tare da ce mishi "Ina kake ne Imran?" "Abba ina gidan Saif ne lafiya?" Nisawa ya yi kafin ya ce "Tom ka zo Ammie ku na buƙatar ganinka yanzu". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Abba jelly ce bata da lafiya, babu ta yadda za'ayi na tafi na barta". "Me ya sameta?" Ya faɗa yana ɗan zaro idanu, ita ma Ammien zaro idanu waje ta yi tana kallonsa tana jiran ta ji me ya faru. Ƴan kame kame ya fara yi musu, daga nan Abban ya fahimci menene matsalar, dan haka sai ya ce zuwa yamma idan ta sami lafiya ya taho da ita, da mamaki ya ce "Abba Ammie ba zai zama matsala da ita ba?" "E babu komai ka taho da ita". Okey ya amsa da shi, katse kiran Abban ya yi tare da juyowa yana kallonta yadda ta tsare shi da ido tana jiran ta ji menene yake faru, Ammie ba karya kyakkyawa ce idan baku manta ba, gata fara tas mai ɗan ƙaramin jiki, idan ka ganta, ba zaka bata bata shekarun nan nata ba, ba zata taɓa cewa ita ta haifi Imran, Akil ba, amma za'a iya cewa ita ta haifi AKila, nan ma ba kowa ne zai yarda ba, dan ba karya ta mori jiki mai kyau. "Me yake faruwa Abban Imran?". Still dai cikin harshen turanci ta yi maganar, to fa akwai ayar tambaya a nan, kenan bata jin hausa ne ko kuma yaya ne? Ko dai dama ba su yin magana da hausa ne before ta fara ciwo? To Allah masani mu dai je zuwa, koma menene munanan zamu ji komai daga biri har wutsiya. "Ɗan ki fa ya angwance ne, idan an sami baby sai ki shirya zama kaka". Ya faɗa yana mai sakinta ya nufi toilet, da sauri ta sake shan gabansa tana faɗin "Ban gane ya angwance ba? Yaushe ya yi aure kuma?". Ɗan shafa kan ta ya yi cikin zoyala ya ce "Au a bayanan da na yi miki jiya ban gaya miki sun yi aure ba ko?". Da sauri ta gyaɗa mishi ka alamar e "To da Imran da Akil duk sun yi aure". "Kai, kai, kai a lallai tom waye suka aura ban sani ba?" Kai tsaye ya gaya mata su waye ne matan nasu, fuskarta ɗauke da fara'a ta ce "Tom ka kirasu duk su kawo mini matan nasu nan yau ɗin nan ba sai gobe ba, su kawo mini surukaina mu zauna". Jinjina mata kai ya yi babu ko ɗigon alamar mamaki a face nasa, da alama dai jiya sun yi zama da ita ne, tun da kunji ya ce a bayanan da ya yi mata bai gaya mata su Imran sun yi aure bako? Hakan na nufin jiya ya mata bayanin wasu abubuwa shiyasa baya mamaki. Toilet ya shiga ita kuma ta wuce ta fitar mishi da kayan sakawa tare da zama saman gefen bed tana jiransa ya fito. A ɓangaren gidan Lion kuwa. Da misalin karfe 4 na yamma, suna zaune a garden suna hira, Aseef, Areef, Rimsha, dukkansu fuskokinsu ɗauke da murmushin, da gani kasan suna jin daɗin kasancewa a tare, sun nutsa cikin hiran da suke yi ne Areef ya ce da Rimsha "Our Queen jeki ki ɗauki abincin Lion ki kai mishi ɗakinsa kin ji?". Zaro wannan fararen dara daran sleeping eyes ɗin nata ta yi, ba ita kaɗai ba har da Aseef, shi ma ya sha ruwan mamaki har sai da ya zaro idanu waje. "Yaya Areef abincin yaya Saif kuma?" Ta yi maganar tamkar zata sa kuka, shafa kan ta ya yi cike da kulawa ya ce "E sister abincin shi, kada ki damu ba zai hanaki zuwa school ba, na rana da dare kawai zaki rinƙa kai mishi, da safe Mark zai kai ki school, yau Aseef yana barci, ni kuma ba zan iya tuki bane yasa Mark ya je ya ɗauko ki, shi kuma Prof matarsa bata da lafiya, shi ne nace ya zauna kusa da ita, to daga yanzu Mark ne zai rinƙa kai ki school, tashi ki je ki kai mishi abincin da wuri, tun ɗazun kinga ya yi mini massage". Tom ta amsa mishi da shi tare da miƙewa jiki ba kwari ta nufi cikin gidan, kamar dai kullum kananan kaya ne a jikinta, wando jeans baki da t-shirt maroon, ta ɗaura wani ɗan ƙaramin gyale baki na doguwar rigarta a kanta. Bayan tafiyarta Aseef ya dubi Areef ya ce "Areef what is going on ne? Me yasa zata kaiwa Lion abinci?". Wayarsa ya ɗauko ya fara latsawa yana faɗin "Bincike mana, bincike a kan face ɗin nan nata Lion ɗin yake yi, ai dama na gaya maka zai buƙa ce ta a kusa da shi, sai dai ba zai ce mata ga abin da yake yi bane, kuma ka bita yanzu ka gani, ka san me nake tunani?" . Girgiza kai ya yi alamar a'a "Idan ta je ɗakin, zai rinƙa yawan ganin face nata dan aikinsa, da aikin babanta, ina mishi mummunar addu'a da ya faɗa tarko, wlh duk wadda ya kalli sister sai ya ji yana sonta, shi ma kuma zai sota In Sha Allah, mu zuba ido mu gani, ina tunanin ma ni kam nan ba da jimawa ba hakan zata faru, dan zaka kalla zai ɗan saki jiki da ita, sannan kuma zai so ta rinƙa zama kusa da shi, abin da yasa kuma zai so zamantaa kusa da shi, kasan halinsa, yafi karfin ya nemi alfarma or ya tambayi wani mutun wani abu, to akwai tambayoyin da ya kamata ya yi mata, amma ba zai yi ba saboda idan ya yi hakan kamar ya nemi alfarma a wajenta ne, zai yi amfani ne da zaman da take yi kusa da shi ya binciko amsoshin tambayoyinsa da kansa". Shiru Aseef dai ya ɗan yi kafin ya ce "Ni ma fa ina son in sami special time, lokacin da yake cikin farinciki na gaya mishi batun aure na, ya je ya nema mini aure heartbeat". A sukawane ya juyo da ash eyes nasa zuwa kan Aseef ɗin, cikin sauri ya ce "Amma Aseef yau ka sha wine (giya) ko?" "Wine kuma?" Ya faɗa yana zaro idanu. "E mana wine, yo idan ba wadda ya sha wine ba, waye zai ce Lion ya je ya nema mishi aure, hmmm wlh na rantse ba zan yi kaffara ba, idan kayi ganganci yi mishi magana ma ba zai kula kaba, idan kuma ka matsa ya kula ka ya je, to fa ka sani da kai da Heartbeat har abada, dan kuwa izza da isa zai je ya nunawa iyayenta, ko ma ya ce a ɗauko mishi iyayen nata a kawo su har nan, idan hakan ta faru kuma Heartbeat ɗin taka zata dai'na sonka, dan su a nan kasar basu yarda a raina iyayensu, suna bin umarnin iyayensu sosai, ba zata taɓa yarda tana ji tana gani Lion ya sanya a ɗauko iyayenta kamar wasu yaransa a kawo su gidan nan ba, kuma ta yarda ta cigaba da zama da kai ba, na dai gaya maka, gwara ka canza hanya dan Lion kam ba zai je neman alfarman a baka aure ba, yanzu fa na gama gaya maka, wasu tambayoyi yake son yi wa Rimsha, amma saboda yafi karfin neman wani abu wajen wani, shi ne gara ta rinƙa zama kusa da shi tana kai mishi abinci daga motsinta da yanayinta har ya fahinci abubuwan da yake so, na buɗe laptop nasa jiya, na rasa a ina ya samo hotunan kusan gabaɗaya family'n uncle Hossain, har da mahaifin Prof naga hotonsa a can, ina ga fa babban al'amari ne kuma babban case ne ba kaɗan ba, dan daga bayanan da naga ya samu akwai rikici ba kaɗan ba, Rimsha ita kaɗai ce wadda take da kusanci da uncle Hosain, kaga ko Prof bai da kusanci da shi sosai, shiyasa Lion ya zaɓeta, ba dan haka ba Prof ma ya wadatar, amma Prof bai san Komai game da uncle ba, kuma ba sai na sake gaya maka ba, Kasan Lion ba zai tambayi uncle Hossain wani abu dan gane da binciken ba, ita dai Rimsha ta hannunta zai sami biyan bukatarsa, mu dai namu idanu kawai". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa yana mai jin tausayin Aseef ɗin, dan kuwa yasan Lion ba zai je neman auren nan ba, idan kuma suka matsa, to sai dai yasa a tattaro mishi iyayen yarinya a kawo mishi, su zo nan su karɓi sadakin ƴarsu, su kuma bada auren a nan a ɗaura iya su kawai, babbar magana lallai akwai kallo. Areef na tafi Aseef ɗin ya ciro wayarsa ya fara kiran daddyn Rimsha, bugu ɗaya ya katse ya kira shi, yana ɗauka ya saka mishi kukan shagwaɓa, daga ɗayan ɓangaren yana daga zaune saman sofa a part ɗin Aseef ɗin na Washington DC sanye da kayan barci masu kyau da tsada ya fara magana a nitse "Haba mana ɗan auta, waye ya taɓa mana kai kuma da kake kuka?". Shagwaɓe fuska ya yi "Uncle ni wlh kawai ka zo Nigeria mu je neman auren heartbeat, ba zan taɓa yarda ba, Lion ba zai neman mini aurenta ba, kuma ni aure nake son yi da wuri, dan haka kawai kazo Nigeria gobe sai mu je wajen Abbanta". "To shikenan yanzu dai a dai'na yi mini kuka, ba dai auren AKila ba ce? To ka kwantar da hankalinka, Akila taka ce, ba sai nazo Nigeria ba, ni kaina ina da damar aura maka ita, amma sai na gayawa baban nata duk da nake da daman, yanzu dai duk ranar da ka shirya zuwa ganin Abban nata, idan ka je ka kirani a waya ka haɗa mu, zan yi magana da shi, dolema ai a baka Heartbeat ɗin ka, idan ba haka ba mu hana kowa kwanciyar hankali, mu takurawa kowa". Ya kai karshen maganar cikin zolaya. Cool murmushi ya saki yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya, sai yanzu ya ji daɗi a ransa, shiyasa yake bala'in kaunar uncle Hosain ɗin nan, duk yadda zai bi ya faranta mishi rai ya sani, yana kula da shi ba ɗan kaɗan ba, yana son farincikinsa sosai tamkar kaninsa na jini. "To shikenan Uncle zanje wajen Abban nata gobe In Sha Allah". Okey daddyn Rimsha ya amsa mishi da shi, daga nan suka shiga hirar duniya abinsu da kuma kewar juna, yana yi yana karawa Aseef ɗin karatu, Aseef da daddyn Rimsha sai Allah, suna matikar kaunar junansu ba kaɗan ba. A ɓangaren Rimsha kuwa, Kitchen ta nufa, hannunta ta wanke kafin ta ɗauki abincin, ga mamakinta yau da ta cewa Mark sannu ya ce mata Okey, tambayar kanta ta yi to ko dan ta jima bata shigo Kitchen ɗin bane yasa ya amsa mata yau kuma? Oho mishi mutun kamar wani aljani, daga shi har ogan nasa baka taɓa gane musu, kamar waƴan da ake pappasu, yau ka gansu fari, gobe kuma baki, sai ma ka rasa gane ina ne alkiblarsu dan bakin hali. Duk wannan masifa fa a cikin zuciyarta take yin shi, Mark na kona mata rai da abin da yake yi matan nan, dan iskanci yau ka gan shi fari, gobe kuma baki, ji take kamar ta yi ta tsitsinkawa ɗan banza mari har sai wannan farar ɓul ɓul ɗin kumatun nasa sun yi jawur kamar tumatiri ruɓaɓɓe ko zata ji daɗi. Shi dai ko kallon in da take ma bai yi ba, kawai yau en amsawar ne suka zo shiyasa ya ce mata okey ba tare da ya kalli in da take ba. Wucewa ta yi zuwa bedroom ɗin Lion, a bakin kofa ta tsaya ta yi sallama, can kasa kasa da ta kasa kunne ta ji ya amsa kamar baya son buɗe baki ya yi magana, kutsa kai ciki ta yi tana mai jin kirjinta na dukan uku uku, a in da ta saba ajiye mishi, nan ta nufa ta ajiye tare da zama, ta wutsiyar idanunsa ya kalleta. Yau dai da zamanta a wajen bai fi minti biyar ba sai ga shi ya miƙe ya nufota, gefenta ya zauna a in da ya saba zama kenan, cike da kasada da tsoro ta ce mishi "Good evening". Bai amsa ba amma dai ya gyaɗa mata kai, da yake tana duƙe ba kallonsa take yi ba, sai bata san ya yi hakan ba, abinci ta fara zuba mishi, kamar dai yadda ta saba, bayan ta kammala ta tura mishi a gabansa, spoon ya ɗauka ya fara ci. Shiru ta zauna tana ɗan satar kallon kyawawan fararen kafafunsa da ya lanƙwashesu dan yin zaman cin abinci ta sunnah, wato kamar yadda annabi yake yi kenan. Can kasa kasa kamar a mafarki zazzakar muryarsa ya daki dodan kunnenta a kan ta miƙo mishi wayarsa da laptop nasa, okey ta amsa tare da miƙewa a nitse. Tana miƙewa ya ɗago dara daran blue eyes nasa ya bita da kallo, ɗauko laptop ɗin ta yi tare da wayar, har lokacin bai kawar da kallonsa a kanta ba, zubawa face nata idanu ya yi yana son yaga action ɗin da zata ɗauka lokacin da zata kalli home screen na laptop ɗin. aura kaɗan ta saki laptop ɗin ya faɗi kasa ya tarwatse lokacin da idanunta suka sauƙa a kan screen ɗin, ta sha ruwan mamaki sosai ganin wata kyakkyawar farar baturiya mai kama da daddynta sak babu maraba, ba dan ta ganta da gashi ba ma, da sai ta ce wannan daddynta ne, sun yi kama sosai over, tsayuwa ta yi tana kallon matar ta manta ma da shi ya aiketa, ta mance ma da a ɗakinsa take, ga shi dai matar ba babbar mace bace bare tace ko yar daddynta ne ko wani abu, a yadda take ganin matar ba zata wuci 28 years ba, da alama ma budurwa ce, tariyo fuskar ƴan uwan daddynta da ta sani gabaɗaya ta fara yi a cikin ƙwaƙwalwarta, duk wadda ta tuno sai taga baya kama da wannan mata sosai sai daddynta, ba dan wannan mata ta fi Jehan shekaru ba, da sai ta ce Jehan ce, dan kuwa babu maraba. Ganin wannan ta shiga duniyar tunani ba zata kawo mishi laptop ɗin bane yasa ya yi mata gyaran murya tare da ɗauke kallonsa daga kanta. A hanzarce ta ɗago tana kallonsa, jikinta duk ya mutu, da sauri ta kariso wajen nasa tare da zama kafin ta miƙa mishi laptop ɗin, hannu yasa zai karɓa hannunsu ya goge na juna, cikin sauri ta sake mishi dan wani irin shock da ta ji, shi kuwa ko a jikinsa ya karɓa ya ajiye a gefensa wajen da ya saba ajiyewa, kasa kasa ya ce ta bashi ruwa, a hanzarce ta zuba ta miƙa mishi, still ya zo karɓa hannayensu ya sake haɗuwa, cikin sauri ta sakar mishi cup ɗin, shi kuma bai kai ga riƙewa da kyau ba, ruwan gabaɗaya ya zube mishi a saman cinyarsa, gently ya ɗago da idanunsa ya sauƙe a kan face nata dan yaga wai me matsalar yarinyar nan ne? Dan hannunsu ya taɓe na juna take haukace mishi haka. Daidai lokacin da ya ɗago idanu, ita ma ta ɗago nata dan ta kalli wani irin action ne a kan face nasa da ta zubar mishi da ruwan, yau a karo na biyu suka kalli juna ido cikin ido, da sauri ta yi kasa da kallonta, shiru ya ɗan yi kafin ya ce da ita ta miƙo mishi hannunta bari ya gani, a razane ta ɗago kanta, nan take idanunta suka cika da kwallah, addu'a take yi Allah yasa ba wani hukunci zai yi wa hannun nata ba dan ta zuba mishi ruwa a jiki, shi kam tambayar kansa yake yi wai me matsalar yarinyar nan ne? Daga ya ce ta bashi hannu har ta fara kwallah, daga hannunta ya taɓe nasa ta zubar mishi da ruwa a jiki, ba dan akwai abin da yake son sani a tattare da ita ba ai da ya bata hukunci mai tsanani, yariya kamar ba lafiya take ba. Jikinta har ya fara kerma ta miƙo mishi hannun nata tare da runtse idanu, nan take hawayen da suka cika mata idanu suka gangaro saman kuncinta, kallon second biyar ya yi wa hannun nata kafin ya kai nashi hannun ya kama natan, waro dara daran sleeping eyes nata waje ta yi, jujjuya hannun nata ya yi kamar mai neman wani abu, ga yatsun nata zara zara da su sak irin na Areef, ya ɗan yi mamaki ganin irin ƴatsun Areef a tattare da nata, amma bai wani damu ba, dan ba yadda Allah baya halittar bawa, shi dai ya riƙe hannunta ne dan ya ga wai me matsalar ta dan hannun nata ya ɗan taɓa nashi har take yi mishi ɓarna, baya son hukunta ta, dan haka baya son ta yi mishi ɓarna ta ɓata mishi rai, baya son abin da zai dakatar da shi daga binciken da yake yi, shiyasa zai kawar da duk wani abin da zai ja ta yi mishi wani ɓarnan da ba daidai ba har ya hukunta ta. Almost second 30 yana riƙe da hannun nata yana jujjuyawa kafin daga bisani ya saketa tare da maido da kallonsa zuwa saman face nata, da sauri ta yi kasa da idanunta, "Dama ganganci yasa kike yi mini ba daidai ba?" Shi ne abin da ya faɗa, girgiza mishi kai ta yi har lokacin tana hawaye, "To me matsalarki dan hannunki ya taɓa nawa zaki zuba mini ruwa a jiki?". "Babu komai". Ta bashi amsa, shiru ya yi daga nan bai sake magana ba, sai ma miƙewa da ya yi ya nufi dressing room nasa dan ya canza kaya, bin shi da kallo ta yi tana mamakin wai shin yau wace iriyar sa'a ne taci a rayuwarta da har ta yi mishi laifi bai hukunta ta ba, ita da ko bata yi laifi ba in dai ta biyo hanyar da aka yi mishi laifi a wajen to sai ya hukunta ta, anya yau lafiya yake kuwa? To ko dai mala'ikun rahma da imani sun rokawa zuciyarsa samun imani da rahmar ne? Ta tambayi kanta, bata san akwai abin da yake nema a tattare da ita bane yasa bai yi hakan ba, yo idan ba dan haka ba ai da wani zance ake yi yanzu. Tana zaune a wajen har ya fito, gently tamkar baya son motsa laɓɓansa ya furta ta kwashe kayan abincin ta fitar ta dawo ta gyara mishi gado da kuma ɗakin baki ɗaya, ɗan zaro idanu ta yi cike da mamaki, ita da ko yadda ake gyaran ma bata iya ba, ga komai na ɗakinsa sai an bisu daki daki, idan kayi mishi kuskure ɗaya ka shiga uku, amma ya zata yi ? Ai dole yau ta zo ta zage dantse ta yi mishi. A hanzarce ta kwashi komai ta fitar, shi kuma saman sofa ya koma ya zauna tare da jawo laptop nasa, zarginsa ya tabbata gaskiya, tun daga irin kallon da ya ga Rimsha tana yi wa wannan mata, to wace ce wai? Mu dai kasance a tare zaku san koma wace ce. Bai taɓa ɗaga idanu ya karewa daddynta kallo ba, idan suna shirme shi da Aseef lokacin da Aseef ɗin yake Washington DC ma, sai dai ya kunna yana jinsu yana wani abin, ba zama yake yi yana karewa face nasu kallo ba, amma duk da haka ya fahimci wannan mata tana kama da daddyn Rimsha ɗin sosai, shiyasa ya yi wa Rimsha hakan dan ya tabbatar, dole daddyn Rimsha yana da relationship da wannan matar, cigaba da aikinsa ya yi, hoton daddyn Jelly ya fitar yana bincike a kansa, da kuma yaushe ne suka rabu da daddyn Rimsha ɗin, dan yanzu case ɗin daddyn Rimsha yake da waƴan da suka zauna da shi kafin ya rabu da family'nsa, dan yana son gane ainahin me ya rabasu har haka, kuma kun san daddyn Jelly ya zauna da daddyn Rimshan kafin daga baya su rabu. Ita kuma bayan ta fitar da kayan abinci, dawowa ta yi dan ta yi aikin da ya sakata, gadonsa ta fara nufa, abin dariya abin tausayi, girman gadon ma ta fara tsayawa tana karewa kallo, yanzu ita ta yaya zata shinfiɗa wannan gadon? Ta tambayi kanta, zazzakar sexy voice nasa ne ya daki dodan kunnenta a in da yake ce mata ta ɗauko wani sabon bed sheet ɗin daga dressing room nasa, sai ta cire na saman gadon ta shinfiɗa sabon, okey ta amsa mishi da shi tare da nufar room ɗin,. Ba karamar ƴar kallo ta zama ba lokacin da ta shiga cikin room ɗin, dan ma bata ga na Washington DC ba, wannan ai kaɗan ne, dama idan baku manta ba, shi ɗan gayu ne, ɗan son kwalliya ne, akwai kaya over, komai na shi a shirye suke datsan datsan gwanin ban sha'awa, ko mai wajen ajeyesu daban, set by set, agogon nan suna jere cikin wani tsadadden show glass mai bala'in kyau, babu kalar agogon da babu a wajen, haka takalma, kaya ne masu bala'in tsada shirye a wajen, kamar an ce ta ɗago kai, idanunta suka sauƙa a saman ɓangaren shot nasa, ita kanta ba zata iya kirga yawansu ba, ga fararen singlet a gefe da yawa, mafiya yawan kayan dake wajen farare ne, yau dai ta zama ƴar kauye a dressing room na shi na Nigeria, idan ta ga na Washington DC kuma ina ga kasa fita zata yi idan ta shiga. Da kyar ta iya gano wajen sets na bed sheets ɗin, babu ƙaramin bed sheet ko ɗaya a wajen, dukka manya manya ne masu duvet, da kyar ta iya ciro wani kato launin milk color, yana cikin jakarsa mai bala'in kyau, ko da ta ciro shi ta kasa ɗauka, ya fi karfinta, yanzu a kalla ta ɗauki 20 mins a cikin dressing room nan tun daga shigowarta zuwa yanzu, ta rasa ta yadda zata ɗauki duv ɗin nan dan yafi karfinta, daga karshe dai ta yanke shawarar jan shi a kasa zuwa bakin gadon sai ta buɗe ta fito da su ɗai'ɗai, haka kuwa ta yi, yana zaune ya ganta sai faman jan abu take yi kamar mai jawo akuya, ko sannu bai ce mata ba, har bakin gadon ta kawo, sannan ta buɗe zip ɗin jakar ta fara ƙoƙarin fito da kananan irin su rigar pillow cases da sauransu, badan tana da tsowa ba, da Lion ya ce shekarunta 11 a duniya, ga rashin karfi, abin gwanin ban dariya yadda ta jawo bed sheet ɗin. Sai da ta fitar da su pillow cases ɗin kuma, sai ta tuna ashe bata cire bed sheet ɗin dake saman gadon ba, mayar da su cikin jakar ta yi tare da fara ƙoƙarin cire wannan katon bargonsa dake saman gadon, irin waƴan nan bargon ne wadda idan mutun ya shige ciki ma ba za'a taɓa zaton yana ciki ba, saboda girma da tudun bargon, ga shi kuma jikin bargon mai irin jikin magen nan ne, bala'in laushi gare shi kamar me. Dukka iya karfinta ta sa zata ja bargon kasa, ai kuwa sai gata a saman gadon baki ɗayanta, dan kuwa bargon yaki jawuwa, yana da girma over ga bala'in nauyi, sautin dariya ta ji daga bayanta, ko bata ɗago ba tasan Aseef ne, shi kuwa Lion tamkar babu shi a ɗakin, aikinsa kawai yake yi. Ba ƙaramin dariya ta bawa Aseef ba, bare ma yadda bargon ya rinjayeta ta faɗa saman gadon, Rimsha ba karfi sam, karisowa wajenta ya yi yana dariya, cikin zolaya ya ce "Ki zo na ara miki karfina ƴar piritu". Da kyar ta iya miƙewa, a shagwaɓe ta ce "Allah yaya Aseef bana so, ai ina da karfi, bari kuma ka gani sai na cire bargon nan yau" Sake da karkarewa ta yi wajen jawo bargon dan ta sauke shi kasa, a karo na biyu ma sai gata a saman gadon ta faɗa, bushewa da dariyar zolaya ya yi har sai da ya sanya Lion ɗagowa ya kallesu, wayarsa ya ciro yana faɗin "Oya sake gwada ɗagawa bari nayi miki video, zan ajiye tarihi ne, idan kin yi aure kin haihu zan nunawa yaranki, in ce musu mummynsu raguwa ce ta karshe, babansu kuma jarumi ne na karshe, sannan uncle nasu Aseef ma jarumi ne". Ya kai karshen maganar yana dariya, kumbura kumatu ta yi a shagwaɓe "Yaya Aseef na ce maka bana so ko?" Ta yi maganar tamkar zata saka mishi kuka. "Oh, oh, oh our Queen ba sai kin yi mini kuka ba, bari na sauke miki kin ji ko ƴar sistotonmu?". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannunsa dukka biyu na ɗauki bargon, bin shi da kallo ta yi tana mamakin wannan uban nauyin dukka ya ɗauka, saman sofa kusa da Lion ɗin ya ajiye bargon tare da dawowa ya tayata cire bed sheet ya kuma fito mata da wadda ta ɗako daga cikin jakar ya ɗaura mata a saman bed ɗin yana faɗin "Tom na gama aikina ko?". Murmushi ta sakar mishi tana faɗin "Yaya Aseef nima fa zan fara koyan training dan nayi karfi kamar kai". Nufar Lion ya yi yana faɗin "Tom shikenan, nan ba da jimawa ba zaki fara koya". Okey ta amsa mishi da shi tare da juyawa ta fara ƙoƙarin warware ƙaramin bed sheet ɗin dan ta shinfiɗa. Abin dariya abin tausayi, sai haɗa zufa take yi ta kasa shinfiɗa gadon da kyau, sai ta jawo nan ta ga can ya ɓaci, tamkar zata saka ihu, shi kuma Aseef ya koma kusa da Lion ya zauna, hankalinsa na a kan wayarsa yana chatting da Heartbeat, baya kallonta bare ya zo ya taimaka mata, ta zagaye gadon nan yafi sau goma ta kasa shin fiɗa bed sheet ɗin, daga karshe dai, ta saman gadon ta fara bi dan kafafunta sun gaji da zagayawa ta nan ta kuma zagayowa, ga gadon da uban girma. A wannan hali Areef ya shigo ya same ta, ba ƙaramin dariya ta bashi ba, sai uban haɗa zuba take yi baiwar Allah, dawo da kallonsa kan su Lion ya yi, aikin gabansu kawai suke yi tamkar basu san da ita a cikin ɗakin ba, karisowa ya yi yazo ya sanya hannu suka fara yi bibbiyu, sai murmushi yake yi mata, duk ta firgice kamar wadda ta wuni tana tikar aikin wahala. Bayan sun shin faɗa ƙaramin bed sheet ɗin, sai ya ɗauko mata duvet ɗin ya gyara shi da kyau kafin ya shinfiɗa, dan yasan ba zata iya shin fiɗawa ba, ya yi mata girma, ba ƙaramin kyau gadon nan ya yi ba, ba'a taɓa shinfiɗa wa gadon bed sheet milk color ba sai yau, kullum daga fari sai sky blue mai haske, banbancinsa da farin kaɗan ne, ita ta jera mishi kananan pillows dake zuwa da bed sheet ɗin, su kam ta iya jerasu ba kaɗan ba, ta ɗauki wannan mai design of heart ɗin ta sanya a gaba tsakiyar masu four corner, sai ta ɗauko dogon kuma ta sanya a bayan masu four cornern, mai Heart ɗin dai ya zamana shi ne a gaba, shi kuma Areef wucewa ya yi ya cicciɓo wannan uban bargon, a tsakiyar ɗakin ya tsaya ya maɗe bargon gida huɗu, sannan ya ɗaura saman gadon kusa da pillows ɗin daga ɗan gefe, wani uban tudu bargon ya yi naɗe shi da aka yi, shi ma Areef ɗin da kyar ya naɗe saboda ciwonsa, dan ma ɗazun ya sha magani ya kuma shafa magani a wajen, shi ne ya ji wasau ta ɗan sake shi, ba laifi kuma ciwon tana warkewa sosai ba karya. Bayan sun kammala ya koma kusa da ƴan uwan nasa dake ta faman aikin gabansu ya zauna, Lion yana fama da laptop shi kuma Aseef waya, tamkar babu su a cikin ɗakin, ita kuma kayan shara da mopping ta ɗauko, yadda kasan ta iya aiki sosai, sai wani zagewa take yi, shara ta fara yi, har ta gama bata ga datti ko ɗaya da ta sharo ba, mamaki ma take yi, wai a hakan kuma kullum sai an share ɗakin har sau uku, ko me suke sharewa oho, mutun ne sai shegen bala'in kyamar datti kamar me, sai zancen zuci take yi har ta fara mopping ɗin, shi ma dai ka tulluka, dan babu wani abin da ta goge, ko'ina tsab yake, amma dan bala'i da shegen son tsabta wai sai an share an yi mishi mopping, kai wannan Saif ɗin akwai kusfa da kakale kakale. Da ta kammala har zata fita waje, sai kuma ta tuna ai bata sanya musu turare air freshener ba, ta san halinsa sarai yanzu duk kamshin dake karaɗe da ko'ina a cikin ɗakin nan, zai iya cewa bai yi mishi ba sai an kara, wannan ba dan ta gan shi da kafufunsa yana taka kasa ba, da sai ta ce baya taka kasa kuma bai taɓa takawa ba, dan abin nasa ne sai shi ɗin, dama mai yin aiki a karkashinsa ai sai ya shirya ba kaɗan ba, sai ya kai zuciya nesa can kololuwa, kayi kuskure kaɗan kasha bakar wahala, dan ma dai yanzu ba aikin take yi a karkashin sa ba, akwai dalilin na zuwanta ɗakin, ya fi karfin ya tambayi Musharraf abu shi ne yake amfani da ita. Dressing room ɗin nasa ta koma bayan ta mayar da kayan sharar, turarruka kala kala ta samu, wasu ma da alama bai san ya kamshinsu yake ba, ya dai sa an sayo mashi ya zube su a wajen, kuma kullum air freshener ɗaya yake amfani da shi, dan yafi son kamshin sa, bai taɓa gwada sauran ya ji ya suke ba, tun da wancan ta yi mishi ai shikenan kuma. Dubawa ta fara yi, dan ita bata ma san da wanne yake amfani ba, ɗaya baya ɗaya ta rinƙa ɗauka tana buɗewa ta ji kamshin ya yake, dukkansu suna da bala'in daɗi, har da mai kamshin mangoro a cikinsu, nitsuwa ta yi ta zaɓa mishi dai'dai da ra'ayinta, wadda ya kwanta mata a rai ta kuma ji daɗin kamshinsa ba kaɗan ba, cikin zumuɗi ta ɗauke shi ta fito cikin ɗaki, lungu da saƙo ta fara bi tana fesawa. Kusan a tare dukkansu TRIPLETS ɗin suka ɗago kansu jin daddaɗar kamshin da ya daki kofofin hancinsu, Aseef, Areef kallonta suke yi, shi kuma Lion kallon air freshener hannunta yake yi, kamshin ya kayatar da su ba kaɗan ba, har wani lumshe idanu Lion ya yi. Tsab ta gama fesa musu tare da mayarwa, ta fito zata nufi waje, Areef ya kirata a kan tazo ta zauna su yi hira, okey ta amsa mishi da shi tare da dawowa ta zauna kusa da shi, cikin zolaya ya ce "Sister yau kin canzawa ɗakin mu kalar kamshinsa". Zata yi magana Brady ya shigo yana wani haushi, da ga gani wani abin ya je ya aikata, a guje ya nufi jikin Lion, hayewa ya yi tare da sauke bindinsa a saman laptop ɗin da yake aiki, ɗan matsar da laptop ɗin gefe ya yi tare da rungume Brady ɗin da kyau, kasa kasa ya ce mishi ina ya je tun ɗazun, haushi ya yi tamkar mai bada amsar in da ya je ɗin, baki ta saki tana kallon ikon Allah, Lion baya magana amma kuma har da tambayar Brady ina ya je tun ɗazun, ba karamin burgeta kuma suka yi ba, hakan ya tabbatar mata da ba son wasa Lion yake yi wa karen nan nasa ba. Ƴar kara laptop nasa ta yi alamar shigowar saƙo, a tare gabaɗayansu suka kai kallonsu kan laptop ɗin, a zafafe ta miƙe tsaye tana ambatar sunan mummynta, dan kuwa hoton mummynta ne ya bayyana a kan screen ɗin laptop ɗin, da alama browsing yake yi Brady ya shigo, bata gama buɗuwa ba ya kawar da laptop ɗin ya rungumi Brady ɗin, shi ne yanzu ta buɗe yasa laptop ɗin kara alamar ya gama. Binta da kallo dukkansu suka yi banda Lion, dan shi tamkar bai san da ita a wajen ba, shi ma Brady har da wani juyowa da sauri yana kallonta dan tsabar gulma, "Is she your mum?". Cewar Areef, gyaɗa mishi kai ta yi alamar e, hannu ya kai ya ɗauko laptop ɗin tare da matso mata da shi gabanta da kyau dan ta gani, tabbas mummynta ne, sanye take da lace milk color, ta sha kyau sosai, tana zaune a cikin palonsu na gidansu dake Abuja, ko a ina ya samo hoton oho mishi, ga shi dai a gidansu na Abuja ne nan, kai Lion kamar wani aljani haka yake. Miƙa musu hannu Lion ya yi akan su ba shi laptop na shi, ba musu suka miƙa mishi, can kasa kasa ya yi wa Brady magana a kan ya sauƙa mishi a jiki bari ya cigaba da aikin da yake yi, kin sauƙa ya yi tamkar bai ji ba, fita harkarsa ya yi ya cigaba da aikinsa, dan ba shi da lokacin biye mishi, haka suka zauna, ita da Areef suna hira kasa kasa, Lion yana aiki, Aseef yana latsa waya har aka kira sallar mangariba. Kusan a tare su ukun suka miƙe, ita kuma bata tashi ba, tana jiransu su fita tukunnan, dan kada ta yi ta karo da su. Har cikin ransa Lion ya ji daɗin ganin yadda gadonsa ya yi tsantsar kyau da bed sheet milk color, sai dai bai nuna a filli ba, toilet ya wuce ya ɗauro alwala ya fito, tsalle Brady ya fara yi a kan lallai sai ya bishi, bai musa ba ya ɗauke shi, da mamaki su Areef suke kallon shi ta ya za'ayi ya tafi da kare masallaci? Sai dai basu yi mishi magana ba. Sai da suka fito palon kasa ya ce da Brady ɗin ya zauna yana zuwa, da kyar ya yarda ya zauna, su kuma suka nufi masallaci, suna fita ita ma ta miƙe ta fice zuwa nata ɗakin. A palon sama ta haɗu da Imran, "Yauwa Rimsha wajen ki zan je dama, zan je gida ni da Jelly, da naso mu tafi da ke, amma Areef ya ce a'a, dan haka ki kula da kanki sosai sai mun dawo". Okey ta amsa mishi da shi tare da yi mishi addu'ar Allah ya kaisu lafiya ya kuma dawo da su lafiya, Amin ya amsa da shi, ta wuce bedroom nata shi kuma ya juya ya koma kasa, har lokacin Jelly tana zazzaɓi, idan ta sha magani ya sauƙa, anjima kaɗan kuma ya sake dawowa, amma dole haka zai ɗauketa ba dan ya so ba, sai dan ya je ya amsa kiran iyayensa. A ɓangaren su Lion kuwa, bayan sun yi sallar mangariba da issha, tsayuwa Lion ya yi a waje ɗan nesa da gidan nasu yana waya da Tga a kan idan ya sami sauƙi ya taho mishi da daddyn Rimsha nan Nigeria, shi kuma Aseef cikin gida ya je ya ɗauko mota ya fita, Areef kuma ya koma cikin gidan dan suje su ci abinci da Rimsha, ya ga kwana biyun nan tana barci da wuri, dan sabida school. Yana shigowa gida Brady ya fara yi mishi haushin ina Lion, buɗe mishi gate ya yi tare da yi mishi nuni da hanyar in da Lion ɗin yake, da yake ya san su kamshi suke bi, tsab zai iya gano Lion ɗin, sai bai damu ba ya sake shi, da gudu ya fice abinsa, shi kuma Areef ya koma wajen Rimsha. Yana zuwa ya haye jikin Lion ɗin yana wani kuka kasa kasa, shafa lallausan gashin jikinsa Lion ɗin ya fara yi yana cigaba da wayarsa, fita shi ma yake son ya yi, shiyasa bai koma cikin gidan ba, kuma ba da motar gida yake son fita ba, ya sanya a kawo mishi sabuwar mota, akwai abin da zai je dubawa ne da ya shafi aikinsa, sai dai fa da Rimsha yake son fitar, dan ita ce ta san abin da yake nema ɗin wadda bai bayyana shi ba, ko ina zasu je,? Shi ya barwa kansa sani. Kamar daga sama ya ji an fisge wayar nasa, gently ya ɗago idanu, tuni ɓarawon ya watsa a guje abinsa, su biyu ne matasa, irin gayun nan ne masu yawo wando kugu a sake, da alama kuma suna ɗan taɓa shaye shaye, wani irin mahaukacin dirowa kasa Brady ya yi yana wani girgiza ya rufa musu baya, shi kam Lion gyara tsayuwarsa ya yi yana mamaki tare da tunanin wannan rayuwa, wai ace matasa yara masu jini a jika ba zasu je su nemi aikin yi ba sai su zauna sata?, Zuciya duk ta mutu, gaskiya wannan abin yana ƙona mishi rai, ya tsani ya ga mai matatciyar zuciya, ya fi son yaga kowa ya zama jarumi, ya tsayawa kansa har ma da wasu. Brady kuwa haukata su ya yi, ko ban faɗa ba na san kunsan Brady mugu ne mafaɗaci, wannan wandon nasu da suke tafiya ƙugu a sake sai da ya zamo zuwa kafafunsu, dan kuwa duk da sun yasar da wayar Brady ɗin ya ɗauka, yaki barin binsu, sai haukata su yake yi ga wayar Lion ɗin a bakinsa ya riƙe gam, duk ya ruɗa jama'ar da suka biyo hanyar, ga shi bashi da tsoro ko kaɗan, baka isa ka razana shi ya gudu ba, sai dai ya kara haukata kai mai razana shi ɗin........ ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ *Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta* Dedicated to A'isha Baita Jiddah💋 E37-38💋 A takaice dai sai dai Brady ya haukatasu, har sai da suka bar layin baki ɗaya, ɗaya daga cikinsu ma har cikin kwata sai da ya faɗa, ga wando na faɗuwa, abin gwanin ban tausayi gwanin ban dariya, basu san cewa Brady ɗin ba zai cijesu ba, saboda akwai waya a bakin nasa, kawai bala'i ne irin nasa yasa ya wahalar da su ya ki kyalesu har sai da ya tabbatar da numfashi ma da kyar suke iya fitar da shi, sannan ya kyalesu ya dawo wajen Lion. Tsaye ya isko Lion ɗin a wajen bai ko motsa ba, tsalle ya yi ya haye jikinsa tare da miƙo mishi wayar, karɓar wayar ya yi yana yi mishi faɗa akan meyasa ya hau mishi jiki bayan ƙafarsa akwai datti, tsabar iya shege irin na shi sai ya wani riko Lion ɗin a wuya yana wani mimmiƙewa, shafa jikinsa ya fara yi tare da nufar gida, bai yi niyar komawa cikin gida ba, hasalima ɓuyanwa Brady ɗin ya yi dan ya tafi in da yake son zuwa, ya so ne kawai a kawo mishi mota Areef ya haɗo mishi trolleynsa, ya fito mishi da Rimsha su tafi, amma Brady ya ɓata mishi jiki dole ya koma ya sake yin wanka ya kuma yi mishi wayo ya gudu. Babu kowa a palon kasa da sama, cikin bedroom nasa ya wuce, daddaɗar kamshin air freshener ne ta daki hancinsa, shaƙa ya yi tare da lumshe idanuwansa ya sake buɗewa, abin da ya faru shi ne, bayan ta yi sallar issha ta sake dawowa ta gyara mishi ɗakin tare da kawar mishi da laptop nasa zuwa saman bedside drawer, ta gyare wajen sofar sannan ta kara mishi air freshener mai shegen daɗin kamshi irin na ɗazun, ba ƙaramin daɗi ya ji ba. Toilet ya wuce da Brady ɗin, wanka ya yi tare da wankewa Bradyn kafa da sauransu, bayan sun fito dressing room nasa ya nufa, shiryawa cikin pajama milk color ya yi, ya ɗaura jacket mai ɗan girma a kai tare da ɗaukar wata ƴar karamar kyakkyawar trolley ya zuba kaya kala shidda a ciki, kala biyu ne cikakkun tsadaddun kaya jeans and T-shirt, kala biyu kuma three quarters ne masu bala'in kyau da tsada da T-shirt nasu, sai pajama guda ɗaya da kuma kayan barci guda uku da ya zuba daga baya, diamond watch nasa na TRIPLETS ya ɗauko tare da perfume nasa guda ɗaya, sai karamar kyakkyawar farar towel, shots and singles, da saukan kayan buƙata nasa, dukka ya shirya cikin trolleyn, bayan ya kammala ya sanya wani haɗaɗɗen cover shoe mai bala'in tsada kalar pajamar jikinsa wato fara, ya yi kyau ba karya, sai tashin fitinannen daddaɗar kamshin perfume nasa yake yi, ya ɗaure kyakkyawar dark black curly hair sa a bayan wuya, ya ɗauki pistol gun, daga karshe ya sanya face mask a face nasa. Jawo trolley ya yi zuwa cikin ɗakin, lokacin Brady ya fice waje, ba ƙaramin daɗi ya ji ba ganin Brady baya ɗakin, dan ba tafiya da shi zai yi ba, massage ya yi wa Mark a kan ya ɗaure mishi Brady ɗin kada ya ga tafiyarsu, sannan ya yi wa Areef massage a kan ya turo mishi Rimsha ta same shi a waje gate baki ɗaya, ya wuce ya ɗauki laptop nasa ya sanya a cikin trolleyn ta gefe, yana gamawa ya nufi waje abinsa. Babu kowa a palon sama da kasan baki ɗaya, waje ya nufa kai tsaye, gabaɗaya sojojin dake gidan suka fara sara mishi, har suna rige rigen karɓar trolley dake hannunsa, hannu ya ɗaga musu alamar baya buƙata, buɗe mishi gate gateman ɗin ya yi, cikin taku mai nuna isa da izza ya nufi waje,. Ɗan nesa da gidan ya tsaya yana latsa wayarsa, alamar massage yake rubutawa. Sanye take da kananan kaya dai kamar kullum, akwaita da son kananan kaya dan su ta taso tana sakawa, lokacin da daddynta, mummynta suke nan, shi ne kayansu ko da yaushe, shiyasa bata iya jurar saka wasu kaya sai su, wandon jeans ne pink color, sai riga fari, wandon akwai kyalli sosai a jikinsa, shi kuma rigar high neck t-shirt ne, ga rigar ya kamata sosai, da yake ita ba saka breziya take yi ba, sai gabaɗaya shatin tula tulan ya bayyana, dan ma ta sanya vest a ciki, bata saka bra sai vest, kanta na ɗaure da pink ɗin ɗankwali, gyalen abayar tane ta ɗaura a kan nata, ta yi kyau sosai, sai zuba kamshi ita ma take yi, a tsorace ta fito wajen, kafin ta fito sai da gateman ya tsayar da ita, a kan ba zata fita ba, sai da ta gaya mishi Lion ne yake kiranta yana waje, sannan ya bata hanya dan yasan yanzu Lion ɗin ya fita. Ganin shi a ɗan nesa da gidan ga trolley a kusa da shi ba karamin mamaki ya bata ba, ɗan kunna hasken screen ɗin wayarta ta yi dan ta duba time, 8:20 cikin natsuwa ta karisa in da yake tsaye ɗin, cikin girmamawa ta ce mishi "Gani nan yaya Saif". Ko sannu bai ce mata ba, sai latsa waya yake yi, bai kuma kalli in da take ba, shiru ta tsaya a gefensa tana addu'ar Allah yasa lafiya. Tsayuwar minti goma suka yi a wajen sai ga wata danƙareriyar bakar mota kirar jeeb mai bakar glass ta paka a gabansu, sai kyalli motar take yi tamkar yanzu a ka fito da ita daga laidarta. Wani jibgegen Baturen soja ne ya fito daga cikin motar, gabansa ya kariso cikin girmamawa ya miƙa mishi key ɗin motar yana risinar da kansa kasa, karɓa ya yi tare da ɗaga wa sojan hannu alamar ya je kawai, cikin sauri ya bar wajen ya nufi cikin gida, shi kuma Lion ɗin gidan baya na motar ya buɗe ya sanya trolleynsa kafin ya buɗe mazaunin driver ya shiga, ita dai tana tsaye tana ganin ikon Allah, bayan ya shiga ya kunna motar ne ya danna mata horn alamar ta shigo, da yake ita ma renon ice cream da madara ce ta gane nufinsa, sai ta buɗe gidan baya zata shiga, gently ya ce "Ni driver ki ne?". Da sauri ta girgiza mishi kai tare da rufe kofar ta dawo gaba ta shiga, tana shiga ya bawa motar wuta suka ɗauki hanyar barin cikin Kaduna, da yake ita bata san ta ina ake shigowa Kadunar or fita ba, sai bata san fita zasu yi ba, ta ɗauka wani waje zasu je a cikin gari kawai su dawo, ga shi shi ya ɗauki trolley da kaya, ita kuma daga ita sai na jikinta da waya a hannunta, lallai akwai case kenan, mu dai je zuwa. A ɓangaren daddy jelly kuwa, suna barin gidan Abbi kai tsaye gidansu Anaya suka nufa, babu kowa sai mai aiki da Zaira da ta dawo daga school yanzu ba jimawa, bata da lafiya ne aka dawo da ita gida, school nasu daban daban da Anaya, su karfe 1 suke tashi, Anaya kuma karfe 2 , da farko school nasu ɗaya, daga baya daddynsu ya raba musu. Sam daddyn Jelly bai ji daɗi ba, ya so su sami daddyn Anaya dan yana da magana da shi, amma baya nan yana Zaria, haka suka yi musu sallama suka nufi wajen shan ice cream, suna tafiya yana ta jan ta da hira, ta yi lamo a jikin kujera tana ganin hanya, a hankali yake tukin dan kula da lafiyarta, duk yadda ta ɗan motsa sai ya tambayeta ko lafiya, gyaɗa mishi kai kawai take yi alamar e tana lafiya, cigaba da tafiya yake yi yana satar kallonta. Daidai bakin wani ɗan karamin kasuwa irin na bakin hanya wadda yake a unguwa haka, ba za'a kira shi da kasuwa ba, dan ba girma gare shi na, irin waje ne haka da masu sayar da kayan miya su tumatiri da sauransu ke kafawa a bakin hanya ta cikin unguwa haka, daidai zasu wuce wajen a tsananin razane ta miƙe zaune tana faɗin "Daddy ka tsaya ga mamata can!.". Ba shiri ya ja wata iriyar birki, tun bai gama tsayar da motar ba ta buɗe ta fito da gudu, saura kaɗan wata motar ta taketa, Allah ya takaita mai motar ya kama birki, ita kam bata bi ta kan motar ba, wajen maman nata kawai ta nufa a guje, burinta kawai ta isa gareta. Zaune take a kusa da masu sayar da kayan miyar, tana ɗauke da kwanon bara a hannunta, ta yafo wani koɗaɗɗe kuma jemammen zaninta a kanta, ga wasu uban gudaje dake binta saboda dattin dake jinta, tamkar mahaukaciya haka take zaune a wajen, da alama ta murji bakar wahala na wuce misali, kuma da alama har yanzu bata da lafiya, ta rame sosai, fuskar nan tata duk ya mokaɗe saboda rama, wasu kasusuwar wahala ne suka bayyana a saman face ɗin nata, tamkar mai cutar kanjamau. Tun bata karisa wajen ba take ambatar mama, mama, mama, a hanzarce ita ma matar ta ɗago kanta dan ko mutuwa ta yi ta dawo ba zata taɓa mantawa da muryar ƴar ta ɗaya tilo a duniya ba, a guje ta zo ta rungumeta tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro tare da ambatar sunan maman nata, ita ma maman rungumeta ta yi tuni hawaye suka wanke mata fuska baja baja. A wannan hali daddy ya iskosu bayan ya yi parking na motar da kyau, gabaɗaya jama'ar dake wajen hankalinsu ya dawo kansu, harta masu sayar da kayan miya a wajen dukkansu hankalinsu ya karkato izuwa kansu, sai kuka Ayla take yi tamkar ranta zai fita, ita ma maman kuka take yi ta kasa magana, an rasa mai rarrashin ɗan uwa. Shi kansa daddy sai da idanunsa suka kawo kwallah, uwa ba wasa ba, almost shekara 4 kenan yanzu basu tare, ai dole su yi kuka, ko da ace ma rabuwar daɗi suka yi bare kuma rabuwar wahala, sace Ayla ɗin akayi idan baku manta ba, kun ga kuwa rabuwar wahala rabuwar da basu shirya ba suka yi shi. Sai da daddy ya ga kukan da take yi ɗin ya yi yawa, zai iya illatata, sai ya matso kusa da su tare da tsugunnawa a gaban nasu ya sanya hannunsa ya jawo Ayla ɗin zuwa jikinsa, juyowa ta yi ta kankame shi tana kuka tana faɗin "Daddy mamata ce, wlh ita ce, ita ce daddy!". Hannu yasa yana goge mata hawaye yana faɗin "Ya isa haka babyn daddy, ya isa kukan, ba shi ya kamata ki yi yanzu ba, murna zaki yi tun da mama ta bayyana, ki godewa Allah da ya bayyyana mana ita, dan Allah ki yi shiru kin ji ko?". Da yake bata yi mishi musu, bata saba ba kuma bata taɓa yi ba, sai ta yi ƙoƙarin haɗiye kukan nata, amma hawayen sunki tsayawa, ganin hakan ga kuma jama'a sun rufesu wasu ma har sun fara ɗaukarsu a video, sai ya miƙe tare da ita a jikinsa yana faɗin "Mama dan Allah ki tashi muje ko?". Bata musa mishi ba, ta miƙe ta bi shi, dan tun da ta kalle shi tare da ƴarta, tasan shi ne ya taimaki ƴar tata kenan, dan haka ba macuci bane, shiyasa ta yarda ta bishi zuwa cikin mota, jama'a da gulma sai video suke yi musu dan a sami na yin posting a media, yanzu da abu ya fara faruwa a waje, a maimakon jama'a su jajanta, sai su ɗauko waya su fara ɗauka, ko da kuwa accident aka yi a waje, Allah dai ya kyau. Gidan baya maman ta shiga, ita kuma Ayla ya sanya ta a gidan gaba, dan baya son barinta ta je wajen mama ta cigaba da yin kukan nan nata, tana ɗaga mishi hankalin, shiyasa ya rabasu, kunna motar ya yi ya nufi gida, an fasa zuwa yawon, har lokacin sai kuka Ayla take yi, ita ma maman nata sai hawaye take yi, da yake yanzu ba hira suke ba, sai ya zuba gudu sosai da motar, cikin ɗan ƙanƙacin lokaci suka isa gida, kai tsaye part ɗin Abbi suka nufa, yaki yarda ya bar Ayla ta je jikin mamanta, dan baya son kukan da take yin nan ko kaɗan, dan haka sai ya rungume kayansa suka shiga cikin palon. Aunty ce kawai a ciki tana zaune saman sofa bayan sun kammala cin abinci kenan, tana ganinsu ta miƙe tana yi musu sannu da dawowa, ganin wata a tattare da su yasa ta kara faɗaɗa fara'arta tana yi musu sannu da zuwa, saman sofa daddy ya zauna da Ayla a jikinsa sai aikin rarrashinta yake yi, ita kuma maman nata zata zauna a kasa ya ce mata a'a ta zauna a saman sofa, ganin Ayla na cin uban kuka haka yasa Aunty ta kariso wajensu da sauri tana tambayar ko lafiya, cike da kulawa daddy ya gaya mata abin da ya faru, sannan ya ɗaura mata da cewa ta kai maman Aylar ɗaki ta yi wanka ta ci abinci, ta huta zuwa anjima zasu yi magana, daga karshe ya tambayeta ina Abbi? Ya fita ta bashi amsa Kafin ta nufi maman Aylar tana faɗin "Muje ko? Ki dai'na kukan haka ya isa". Allah sarki Aunty baiwar Allah, ita dai ba ruwanta, koma waye aka kawo, in dai mijijta da ƴan uwansa ne, hannu bibbiyu take karɓarsu, bata da wata matsala a rayuwarta, ba kyashi bare hassada, haka ta riƙo hannun maman Aylar, bata damu da dattin da yake jikinta ba, ta wuce da ita zuwa ɗakin Hanan. Shi kuma daddy rarrashin babyn nasa ya cigaba da yi yana gaya mata ai murna zata yi, wannan abin faranciki ne ya same su, dan haka ta kwantar da hankalinta, shi ya fi kowa ma murna, dan ko ba komai yanzu zai san su waye familyn babyn nasa da har take masa kama da tsohuwar matarsa wato mummyn Jelly. Da kyar ya lallaɓata suka wuce bedroom nasu dan ya je ya sakata tayi barci kada kanta ya yi ciwo, yasan yanzu tana lokacin barci ne saboda cikin nata, da ta kwanta kaɗan sai barci, abin ba sauki sam. A ɓangaren matafiya kuwa. Rimsha tun tana iya ganin mutane har ta dai'na, gabaɗaya sun fita garin Kaduna sun ɗauki hanyar Abuja, tsoro ne ya kamata, amma tuna cewa duk wuya ba zai taɓa cutar da ita ba, yasa ta hakura ta lafe a jikin kujerar motar, shi kuwa sharara uban gudu yake yi tamkar ba gobe, ban da hanya babu abin da yake kallah. Dai'dai wajen checkpoint na sojiji bayan ka fita Kaduna ta wajajen jare, a nan suka tsayar da su, a lokacin ma ta yi barci abinta. Tun da ɗaya daga cikin sojojin nan ya dallah wutar torch light ɗinsa ya kalli motarsu, yasa a ransa sun yi kamu zasu samu kuɗi, dan kuwa ba ƙaramin mota bane wannan, nufarsu ya yi kai tsaye, da yake glass ɗin motar a sauke take kasa, sai ya danna musu torch light a cikin motar kai tsaye, har sai da Lion ya ɗan rintse idanunsa saboda bala'in hasken light ɗin. Da sauri sojan ya haska Rimsha bayan ya haska Lion ɗin kenan, da mamakinsa sai ya ga ita chocolate color ce, shi kuma Lion Bature kamar ka taɓa jini ya zuba saboda haske, ga shi ita karamar yarinya, bugu da kari tana barci, fusataccen face ɗin Lion kuma idan ka kallah wani lokaci zaka rantse irin bakaken mugayen nan ne masu kashe mutane ba gaira ba dalili, dan haka sai sojan ya tuhume shi da satar yara, wato ya sato Rimsha kenan, kuma a yanayin da suke ɗin nan dole za'ayi mishi irin wannan tuhuma, cikin wannan dare ya ɗauko ƴa mace sun nufi Abuja, kuma kunsan dole wanda bai san su ba ya yi tunanin hakan, to da yake shi ma soja ne, yasan a kan aikinsu suke, sai bai wani nuna musu karfi ko ya dake su ba, hakan da suka yi dama shi ne dai'dai, gently ya ce musu wannan sister sane cikin Abuja zasu je, kwata kwata baya son a gane waye shi, dan shi bai zo Nigeria dan a gane ne yana ƙasar ba, yasan idan ya cire face mask na face nasa to tabbas ko basu san face nasa ba zasu san shi ne. Kin yarda sojojin suka yi, suka ce sam sai ya tashi Rimsha su ji daga bakinta, ya tasheta a gabansu, ta ya za'ayi yana Bature ɗan haure zai ce musu bakar fata kanwarsa ce,? Ai wannan hankali ba zai ɗauka ba, babu wata kama da take nuna wannan kanwarsa ce, ko suna da alaƙa da ita, dan haka ko ya tashe ta, ko kuma ya miƙa musu ita ya kawo wani abu na cin hanci kenan, sai su yafe mishi ya tafi ya barta a wajensu, da farko ya ɗauka faɗa suke yi a kan gaskiya, sai yanzu ya fahimci in da zancen ya dosa, ashe marasa gaskiya ne ma, ba suna faɗa dan kare kasarsu daga miyagu bane ma, dan aljihunsu suke yi ashe. Cike da izza ya ce bai ga uban da ya isa ya tashi Rimsha a nan ba, kuma wlh su basu hanya su wuce ko kuma ya yi musu abin da sai sun yi danasanin zuwarsu duniya, cike da izza shi ma ɗayan sojan ya sanya gindin bindigarsa zai taɓa kumatun ta da shi ya tashe ta, ɗayan kuma ya ja kofar motar zai buɗe, sai surfa masifa suke yi, wai ai ɗan haure ne, ya hauro musu kasa ba ta hanyar da ta dace ba, dan haka sai ya ɗanɗani kuɗarsa yau. Bai kai ga taɓata da bindigar ba ta farka saboda surutansu da ya yi yawa, shi kuma Lion sai ƙoƙarin dannar zuciyarsa yake yi dan abin da yake gabansa ya fi masa sauraran waƴan nan banzaye muhimmanci a cewarsa, miƙewa ta yi zaune tana murje idanunta. Tsawa sojan ya daka mata wadda ya sanyata firgita, shi kuma Lion wayarsa ya ɗauko ya fara latsawa, dan shi bashi da lokacin sauraran waƴan nan marasa hankali da basu san aikinsu ba a cewarsa,. "Ke waye wannan kuma ina zai kai ki?" Ɗaya daga cikin soldiers ɗin ne suka mata magana cikin tsawa, a firgice cikin magagin barci murya na rawa ta basu amsa da cewa "Yayana nane ya ce zan raka shi wani waje ne, amma ni ban san wajen ba". Dawo da kallonsu kan shi suka yi, sai latsa waya yake yi, zasu yi magana wani daga cikin sojojin da alama babbansu ne ya kariso wajen, cikin girmamawa ya ce da Lion su tafi, ya samu kira daga sama, su kuma sojojin su bashi hakuri, bai jira wani hakurinsu ba, dan idan baku manta ba, ya tsani kalmar sorry a rayuwarsa, da gudun gaske ya ja motarsa ya bar wajen, yana barin wajen kuma suka sake samin kiran waya an soke aikinsu baki ɗaya, an koresu daga aiki kenan, gabaɗayansu da suke wajen, a nan dai ya yi musu amfani da karfin ikonsa ne ba karfin damtse ba, ya fahimci sojojin irinsu masu karɓar cin hanci, sam basu da wata amfani a hukuma, domin kuwa, ba kasa da al'umma suke yi wa aiki ba, aljihunsu da cikinsu suke yi wa aiki, to yana da kyau su bar aikin al'umma su je su nemi aikin cikin nasu, dan aikin soja aikin kasa da al'umma ne, da mutane masu kishin kasa kishin kansu da al'ummarsu ya dace ba banzaye irin waƴan can ba. Cigaba da sharara gudunsa yake yi, sun yi nisa sosai har ma sun kusa shiga Abuja, sautin garuwar hakwaranta ne ya saka shi waigowa ya kalleta, tun da ya bar wajen sojojin nan ya ɗage glass ɗin motar saboda sanyi da ya fara sauƙa, amma a haka wai rawan sanyi take yi, da farko kamar ba zai kula ta ba, sai ya tuna idan wani abin ya sameta shikenan shirin shi ya ruguje, dan ba zata iya fita ba, tuna hakan yasa ya yi parking na motar a gefen titi ya cire jacket ɗin jikinsa ya rufa mata a jikinta, sai zuba barci take yi, kunna motar ya yi ya cigaba da tafiya dan sun kusa shiga, kamar a mafarki ta ji kamshin perfume nasa sosai yana ratsata, ga kuma ɗumi da ta ji, karayin lamo ta yi a jikin kujerar tana sauke numfashi a hankali hankali cikin kwanciyar hankali. Misalin karfe 11 dai'dai suka shiga cikin garin Abuja, kai tsaye gidansu ya nufa, tamkar already ya san hanya, amma kuma bincike ya yi ya gane location na gida, sai ya yi amfani da google map, sai zuba barci take yi bata san ma sun iso ba, da yazo shiga babban gate na duplex apartment ɗin sai da aka charje motarsa tsab, bai hanasu ba, dan ma baya son wasu su san ya shiga gidansu Rimsha ɗin, baya son kowa ya sani. Bayan sun gama charjewa, kai tsaye kofar gidan ya nufa, rufe take gate ɗin, ga wani zabgegen kwaɗo da aka sanya a babban gate na shigar da mota, parking ya yi a bakin gate ɗin, gently ya fito ya nufi wajen gate ɗin, ga mamakinsa sai yaga babu kura ko wata alama da zata nuna an jima ba'a shiga gidan ba, alamu sun nuna akwai masu zuwa gidan, shiru ya ɗan zubawa kwaɗon idanu, gently ya kai hannunsa har kamar zai taɓa kwaɗon, sai kuma ya fasa ya juya zuwa wajen motar tasa dake kunne, juyawa da zai yi sai ya kalli mutun daga gidan kusa da su ya leƙo ya kuma koma, bai bi ta kansu ba ya koma cikin motarsa. After some minutes ya fito ya dawo gaban gate ɗin, wani ɗan ƙaramin kwalba da ya ɗauko ya buɗe ya zubawa kwaɗon ruwan dake cikin kwalbar, nan take kwaɗon ta ɓalle gida biyu gate ɗin ta buɗe, daddyn Rimsha ya cika mai sa'a da har Lion ya tsaya tsayin daka a kan case nasa har haka, dan ma dai idan ya ce zai yi abu, to wuya ko akasinta bata sanya shi ya juya baya, muddin ya fara abu, to sai ya kai in da yake buƙata, komai wuya komai daɗi baya sarewa kuma baya gajiyawa, akwai shi da taurin zuciya na bala'i, ga zafa a kan aikinsa da ya sa a gaba, rashin tsoro, tashin tausayi, karfin da kuma zafin zuciya, baya tankwaruwa kamar yadda baya juyuwa, in ya miƙe, ya miƙe kenan har sai in shi ya ga damar zama. Da kansa ya buɗe gate ɗin sannan ya koma ya shigo da motar ciki, babu ko tsoro a ransa, yana sane sarai akwai masu shigowa gidan, da alama ma ƴan shaye shaye ne, ko kuma wasu criminals, sun mai da gidan gidan maɓoyansu idan suka aikata wani laifi. A parking space na gidan ya yi parking na motarsa, a nitse ya fito yana bin ko'ina da kallo, tabbas hasashensa gaskiya ce, akwai masu zuwa gidan, dan ga tayan motoci nan alamu sun nuna ma kwana biyu da suka wuce waƴan nan motoci suka shiga, suka kuma fita, da yake akwai taɓo na ruwan sama a jikin tayun ne sai ya bada shati sosai, da hasken screen ɗin wayarsa ya haska yake gani, dan gidan babu wuta, da alama an yanke wutar gidan an cire baki ɗaya. Ya ɗauki almost 10 mins yana ƴan dube dubensa kafin daga bisani ya dawo cikin motar, da hannu ɗaya ya saɓeta a kafaɗarsa dan yanzu kula da ita zai yi sosai kada wani abin ya sameta, dan ya cinma abin da yake son cin ma wa, trolleynsa ya zaro da ɗayar hannun nasa ya ja zuwa cikin palon, da yake suma kofar palon nasu mai amfani da fingerprint ne, sai ya saki trolleyn nasa ya sanya hannu a aljihunsa ya fito da wata kati, har lokacin tana kwance a saman kafaɗarsa tana zuba barci, ta wahala baiwar Allah tafiyar dare, Lion sai Allah bai tashi yin tafiyar ba sai dare. Sanya card ɗin mai kama da ATM card ya yi a daidai saitin fingerprint na kofar, nan take kofar ta buɗe, gyara ɗaukarta da ya yi da kyau ya yi sannan ya ja trolleyn zuwa ciki, palon kawai duhu sosai, a haka ya shiga zuwa tsakiyar palon, kafin ya saki trolleyn ya ciro wayarsa ya haska, saman doguwar sofa ya kwantar da ita, sannan ya ja trolleynsa ya haura sama tamkar already ya san gidan, ɗakin daddynta kai tsaye ya nufa, komai yana nan yadda suka barshi, da alama masu shigowa gidan basu shiga cikin bedrooms sai iya tsakar gida or palo. Ƴan dube dube ya yi a ɗakin kafin ya wuce zuwa toilet, wanka ya yi, Allah yasa akwai ruwa sosai, da ruwan sanyi ya yi wankar tasa, ya fito, shiryawa ya yi cikin kayan barci masu kyau da tsada farare tas, ya sanya perfume nasa sannan ya fito zuwa balcony dake tsakanin bedroom ɗin mum da na dad ɗin, kun san irin gine ginenmu a nan, mafiya yawanci balcony ɗaya ake yi wa gida, saɓanin ginin turawa da ko wani bedroom yana da balconynsa, a nan ɗin ma akwai manya gidaje masu irin wannan, sai dai ba sosai bane, to suma dai gidansu Rimsha, balcony babba guda ɗaya suke da shi tsakanin bedroom ɗin mum da dad. Wajen ya nufa ya tsaya, zafi yake ji sosai shi, shiru ya tsaya yana kallon gidaje guda biyu dake makwabtaka da nasu Rimshar, nazari yake yi a kan waƴan nan gida guda biyun, a tunaninsa dole suna da saka baki a abin da ya faru da family'n Nawazudden, ace suna makwabta duk wannan abin da ya faru kuma basu sani ba? Sannan basu yi jajen ina family'n suka ɓata lokaci guda haka ba? Tabbas akwai sa bakinsu, suna da masaniya a kan komai, koma ace matan gidan basu sani ba, to tabbas mazansu sun san komai, ai Nawazudden ba mutun ne da za'a ce zama da shi babu daɗi ba da har zai ɓata basu shiga damuwa ba. Ya nitsa cikin tunanin lamarin sai yaga kamar dirowar mutane cikin gidan, da yake dugune babu haske, ba ka iya gani sosai, dan ma neighbors ɗinsu akwai wuta suna ɗan haske gidan kaɗan, tabbas karti ne har guda uku suka diro cikin gidan, tafiyar sanɗo suka fara yi kamar ɓarayi, da ga gani kasan sun sami labarin an buɗe gidan Nawazudden ne, shi ne suka biyo koma wane ne. Da farko bai yi niyar nufarsu ba, ya yi niyyar ya kyalesu su kawo kansu gare shi ne a balcony su same shi, ya ci ubansu a wajen ya watsasu ƙasa, amma tuna Rimsha tana palo yasa ya yi saurin juyawa ya nufi palon. Dai'dai zai saka kafarsa a benen ya sauƙa izuwa polon, ya ji takun sahunsu, suna haurowa saman benen daga can kasa, to da yake benen kusan guda biyu ne, ɗaya ya kwanto a kan ɗaya kamar cross, yana kuma da ɗan tsawo benen, sai ya fasa sauƙa ya laɓe a wajen kofar ɗakin mum yana jiran su iso ya yi musu kisan mummuke, sai dai fa zuciyarsa na tuna mishi Rimsha da ya bari kwance a palo tana barci, kada su illatata kafin su hauro, duk da cewa suma sun shigo ne a duhu suna wani sanɗa, da wuya su ganta, kuma shigowa da suka yi a duhu sun yi shi ne dan kada wadda yake cikin gidan ya gansu, suma da alama kisan mummuke suke son yi wa duk wadda suka samu a cikin. Dai'dai lokacin ita kuma ta buɗe kofar dakin mum ta fito sanye da kayan barcinta a jikinta, lokacin da ya haura sama ashe ta farka, da yake wayarta na aljihun wandonta ne, sai ta kunna wutar wayar ta haura sama, ta sha mamakin ganinta a cikin gidansu, sai dai bata wani damu ba, dan tasan duk abin da Lion zai yi to da dalili. Ta fito ne riƙe da wayarta a hannunta tana faman kunna haske torch light ɗin wayar, bata lura da shi a wajen ba, tana kokarin nufar benen ta sauƙa kasa, cikin sauri ya jawota jikinsa tare da sanya hannunsa ya toshe mata baki, dan yasan zata iya yi mishi ihu, kaɗan ne daga halin mata, da sun ɗan tsorata sai ihu, ɗayar hannunsa yasa ya karɓi wayar nata ya tura cikin aljihun wandon kayan barcinsa, tun lokacin da ya jawota jikinsa ta gane shi ne ta hanyar kamshin perfume nasa, sai dai ba zata iya kwanciya a jikin nasa ba, ba kuma zata iya ce mishi ya sake taba. Ta nutsa cikin tunanin me mafita a gareta, zazzakar sexy voice nasa ya daki dodan kunnenta can kasa kasa gently ya furta "Ki kwanta shiru". Ya yi maganar yana zame hannunsa daga bakin nata, da ɗayar hannunsa kuma yana kwantar mata da kanta a faffaɗar kirjinsa. A wannan lokacin kuma mutanen suka kariso wajen, cikin dabara ya kara yin baya kaɗan da ita, baya ganinsu saboda duhu, amma da lumshe da kuma takun tafiyarsu yake iya irga su nawa ne a wajen, kai tsaye bedroom na daddy suka nufa, sai da ya bari sun wuce sun shiga, sai ya damki na baya ya toshe mishi baki tare da murɗe mishi wuya ya zube kasa gawa a wajen, kasa kasa ya ce mata ta sake shi ta koma ɗakin mummynta yana zuwa, ai ina kara kankame shi ta yi, da Iya karfinta dukka ta rike shi, da ta mutu a hannun waƴan nan azzalumin, gara shi ya kasheta sai ya fi mata sauƙi, ko ba komai ta mutu a hannun masoyinta. Dama already yasan za'ayi hakan, yasan ta da bala'in muguwar tsoro, dan bincike da ya yi a kan ƴaƴan Nawazudden, babu wanda ya kaita tsoro, ba yadda bai yi ba, fir taki sakinsa, ta ce sai dai su mutu tare, ba shi da zaɓi dole ya goyata a bayan shi, domin ba zai yarda wani abin ya same ta ba, idan wani abu ya sameta shikenan, ba zai sami damar kama wadda ya zo kamawa ba, idan baku manta ba, lokacin da uncle Shitu ya ce su gudu, ya ce kada su yadda su bari a san suna raye, hakan zai nuna muku cewa mai neman hallakar da jinin Nawazudden a yinwace yake da neman Family'n Nawazudden ɗin, to Lion kuma zai yi amfani da Rimsha ne dan ya kama mutumin, ya san da cewa mutumin idan ya sami labarin ga ɗaya daga cikin familyn Nawazudden nan ta zo Abuja, to dole koma a ina ya ɓuya zai bayyana dan ya kashe Rimsha, a nan ne kuma Lion yake son kama shi cike da hujja, shi ne dalilin zuwansu Abuja, to kunga idan wani abin ya sameta, ko ta ji ciwo, ai ba yadda za'ayi ta fita har a san tana raye, har a ganta a kaiwa mutumin labari ya zo farautarta, yanzu mutanen nan da suka zo, basu san suwaye ne suka zo gidan ba, su dai an ce musu koma wanenen ya shiga gidan Nawazudden su kashe shi, aikinsu kenan, su saka idanu a kan gidan, shi ne da suka sami labarin yau wani ya shigo, suka biyu sahu dan su kashe shi, kunji abin da ya faru, mu koma kan labarinmu. Dole haka ya goyata a bayansa ya bi bayansu, wasan duhu suka fara yi yana yi musu kisan ɗai'ɗai, ta kankame shi tamkar zata shige cikin jikinsa, ta lafe a bayan nasa kamar babu ita, jikinta sai kerma yake yi, duk abin da take ciki yana jinta, yana jin duk abin da take yi,. A haka ya rinƙa yi musu kisa mummuke har ya gama da su ukun dukka, ciro wayarta da ya karɓa ya yi daga aljihunsa, ya kunna wutar wayan, palo ya sauko har lokacin tana bayansa, kofar palon ya je ya rufe, maimakon ya fara rufe gate ɗin gidan, sai ya bar gate ɗin a buɗe ya rufe iya palo kawai ya koma balcony. Gently ya ce ta sauƙa mishi a baya, kara kankame shi ta yi ita gaskiya ba zata sauƙa ba, dan bata yarda mutanen sun kare ba, sauƙo da ita ya yi, a sukawane ta kara faɗawa saman faffaɗar kirjinsa ta rungume shi sosai tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, ba karya ta tsorata iya tsorata, bata yarda mutanen sun kare ba, tana jin kamar akwai wasu, kuma wasu ma zasu sake zuwa, duk tsoronsa da take ji yau sai dai ya kasheta amma ba zata bar jikinsa ba, nisawa ya yi kafin gently ya ce "To sake ni bari na ɗauko mattress sai mu kwanta". Tamkar bata jin me yake faɗa, jikinta sai kerma yake yi, yau shi ne karo na farko da wani ya taɓa bashi tausayi a rayuwarsa, a cikin wannan hali da take ciki dole ta baka tausayi, kuma tabbas ya jinjina mata, a kananun shekarun nan nata ta iya jure duk wannan bala'i da suka shiga lokaci guda, ya jinjinawa karfin imaninta, ba ko wace zuciya bace zata ɗauki abin da ta ɗauka, tana da 14 years ƴar gata uwa da uba, kamata ya yi ace yanzu tana kwance jikin mahaifiyarta tana jin ɗuminta, amma ko in da mahaifiyar tata take ma bata sani ba, tana raye ko ta mutu? Allah masani, ba ƙaramin ƙoƙarin Rimsha ta yi ba, baki ma ba zai iya misulta irin kokari da karfin imani da take da shi ba, hakan yasa bai yi mata tsawa ba, ya saɓeta a kafaɗarsa zuwa cikin bedroom ɗin na daddynta, ya yi mata uzuri sosai saboda halin da ta tsinci kanta a ciki, ga shi yau a gabanta ya kashe mutane har guda uku, kuma cikin duhu, ai dole ta tsorata, dole yau ya yi mata uzuri. Mattress na gadon daddy ya ɗauko, dan ba zai iya kwana a cikin ɗaki ba, zafi ya yi yawa, ga shi babu wuta a gidan, akwai engine wuta, sai dai babu mai a cikinta. Balcony ya kawo mattress ɗin ya shinfiɗa, tana kankame da wuyarsa taki sakinsa, har lokacin kuka mai tsuma rai take yi, sai faman sauke wani irin numfashin wahala take yi. Bayan ya shinfiɗa mattress ɗin a kasa, sai ya koma ya ɗauko bed sheet ya dawo, bai ɓata bakinsa wajen cewa ta sauka jikinsa ya shinfita bed sheet ba, dan yasan ba zata sauƙa ba, duk yadda take tsoronsan nan ace yau ta haye jikinsa haka, shima ya san bala'in ya kai bala'i a gareta, kuma dama dole ta tsorota, ga uban duhu kamar me. A haka dai ya lallaɓa ya shinfiɗa bed sheet ɗin, sannan ya koma ya ɗauko wayarsa tare da pistol gun da ya taho da shi suka dawo balcony ɗin, "Sauka ki kwanta to". Ya faɗa a nutse. Kada ku manta cikin harshen turanci TRIPLETS suke magana. Ina ai ko motsawa ba zata iya yi ba, ita dai yau duk bala'i ba zata rabu da shi ba, sai dai su mutu tare, ji ya yi tamkar ya yi wurgi da ita kasan benen nan dan haushi, amma ina ba dama, dole ya lallaɓata matikar yana son ya cinma abin da yake so, bugu da kari kuma yanzu a hannunsa take, shi ya fito da ita daga gida, duk abin da ya sameta, hakkin ya rataya ne a wuyarsa, so dole ya kula da lafiyarta. Bashi da zaɓi dole ya kwanta da ita a saman mattress ɗin, tana manne da kirjinsa kam taki saki, ta kamkame rigarsa ta gefe da gefen cikinsa, sai sauke ajiyar zuciya take yi, gabaɗaya ta ji gidan nasu ma ya fita a ranta, ta tsani gidan, ita dai ya mayar da ita wajen yaya Imran, da farko ta yi murnar ganinta a gidan nasu sosai, amma yanzu bata so. Shiru suka kwanta yana jin saukar numfashinta a wuyarsa har barci ya ɗauketa, lokacin da ya sami kwanciyar hankali dare ta tsala wuraren karfe 2 har lokacin tana a jikinsa, bai yi barci ba idanuwansa biyu, sannu a hankali ya fara jin wani irin yanayi a tattare da shi na kwanciyar da ta yi a jikin nasa, ɗazun duk bai ji komai ba saboda da shi da ita duk hankalinsu ba'a kwance yake ba, yanzu ita tama yi barci, shi kuma ya sami natsuwa sosai shiyasa. Ɗan ɗago kansa ya yi tare da laluɓar wayarta ya kunna hasken screen ɗin, fuskarta ya haske, duk ya yi jaga jaga da busasshen hawaye, anci kuka an ƙoshi. Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali kafin ya juya da ita ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa dan ya sauketa daga jikin nasa, da kyar ya iya zame hannayenta daga riƙon da ta yi mishi. Bayan ya kwantar da ita ya jawo bed sheet ɗin ta gefenta ya rufa mata tare da juyawa ya bata baya. Jim kaɗan barci ta ɗauke shi shima, ko tsoron kwana a cikin gidan bai ji ba, ga gawarwakin da ya kashe a ciki, ko da yake, dama kama su ya zo yi shiyasa bai sauƙa a hotel ba ya sauƙa a nan gidan dan ya kama azzalumai ɓata gari. Can misalin karfe 4 na dare, karan sautin garuwar hakwaranta waje guda ne suka farkar da shi daga barci nasa, kun san dama shi bashi da nauyin barci, abu kaɗan ya yi motsi kusa da shi zai farka, rawan sanyi take yi sosai da sosai saboda sanyin asuba ya fara sauka, hakwaranta sai garuwa da juna suke yi, gabaɗaya ilahirin jikinta rawa yake yi, barci cike da idanuwansa sosai, da kyar ya warosu a kanta, lokacin kuma hasken wata ya ɗago sosai, shiyasa ma sanyin ta yi yawa, juyawa ya yi gabas da yamma babu wani abin da zai sake rufeta da shi, ba zai iya miƙewa zuwa cikin ɗaki ba, dan wani irin azababben barci dake damunsa, jikinsa sam babu kwari, bashi da zaɓi dole ya jawota jikinsa dan sanyin ya yi mata sauki, yasan ko ya ce ta tashi ta tafi ɗaki ɓata bakinsa zai yi, wannan uwar tsoro ai tana tashinta ma zata yi tsalle ta ɗane shi dan bala'in tsoro, haka ya jawota jikinsa ya kara tattare bed sheet ɗin gefen nata ya rufeta da kyau, shi kuma dai bai ji wani sanyi ba, hasalima zafi zafi kaɗa kaɗan yake ji, dama kun san su kam ai sarakan sanyi ne, sun saba da sanyin da ya ninninka wannan mai kankara ma. A haka dai suka cigaba da barcinsu, gently ya mayar da idanunsa ya lumshe su ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi. Bashi ya farka ba har sai karfe 5:30, a nan ma ba karamar dirama suka sha ba, taki rabuwa da shi, sai da ya daka mata tsawa sannan ta dawo cikin hankalinta tare da takurewa a saman mattress ɗin tana kuka ƙasa ƙasa, shi kuma ya wuce toilet ɗin daddy ya ɗauro alwala dan lokaci anata sallah a masallatai, bayan ya fito ne ita ma ta miƙe cike da tsoro ta nufi cikin, tana bala'in tsoron haɗuwa da wani dan dai bata yarda ba wasu mutanen ba, kuma tana tsoron Lion ɗin, haka ta daure baiwar Allah ta nufi bedroom nasu ita da Jehan, wanka ta yi sauri sauri ta fito ta shirya cikin wata ƴar doguwar rigarta wadda da kaɗan ya wuce gwiwarta, da rigar tana kai mata har kasa, amma yanzu da ta ɗauko shi ya yi mata guntu, dan an jima ai rabonta da kayanta na gidan, rigar tana da dogon hannu, jikinta kuma kamar rigar sanyi yake, ma'ana yana da kauri, sai dai ta roba ce, tana kama jiki, ta bi jikinta ta kwanta luf, shape nata ya fito sosai da sosai, daga shape na sama har na kasa. Zumbulelen hijabi ta zumbula har kasa, da sauri ta fesa perfume ta fito ta nufi balcony ɗin, a lokacin kuma karfe 6 da rabi ta yi, in da ya shinfiɗa dadduna ta nufa, yana kwance saman mattress ɗin, da alama ya mayar da barci ne, dan akwai barci sosai a idanunsa, sam taki kallon in da yake. Sallah ta yi tare da zama ta fara askar har zuwa karfe 8, rana ya ɗago sosai, lallaɓawa ta yi cike da tsoro ta nufi kitchen nasu, zuciyarta sai dukan uku uku yake yi, haka ta wuce gawarwakin mutanen daren jiya ta nufi kitchen. Komai yana nan yadda yake, akwai gas akwai komai, kayan tea ɗin da mum take haɗawa dad ta buɗe drawer ta ɗebo, yunwa take ji sosai, wanke pot ta yi tare da zuba ruwa ta ɗaura tea ɗin. Bayan ta ɗaura sai ta koma palo ta cire hijabin jikinta ta ɗaura saman sofa sannan ta dawo kitchen ɗin, tsayuwa ta yi kusa da gas ɗin har sai da tea ɗin ya tafasa dai'dai yadda take buƙata, cike da tsoro da kuma fargabar me zai je ya zo ta ɗauko cup ɗin daddynta guda biyu masu bala'in kyau ta zuba musu tea ɗin bayan ta tace kayan ciki kenan, saman tray ta jerasu, shi sai ta ɗauko mishi madara da suga tare da milo, dan black tea ne ta girka, zuciyarta sai harbawa yake yi ta nufi sama da kayan tea ɗin. Bata same shi a wajen ba, kusa da mattress ɗin ta ajiye tray ɗin tare da juyawa da gudu zata bar wajen, dan ta tsorata rashin ganin shi a wajen, da yake tana gallon ƙasa ne sai ta yi karo da shi bata sani ba, faffaɗar kirjinsa kanta ya daka, shigowarsa wajen kenan ya je ya yi wanka ne ya shirya cikin wandon jeans baki da polo shirt sky blue, ya yi kyau over, ya saki gashin kannan nasa. Baya ta yi zata faɗi ya sanya hannunsa ɗaya ya riƙo wuyar rigarta, hakan kuma ya yi sanadiyar bayyanar sunansa dake saman tudun tula tulanta, jawota ya yi ya tsayar da ita da kafafunsa kafin ya wuce zuwa wajen mattress ɗin, a gefe ya zauna tare da jawo wayarsa ya kira his excellency a kan ya sanya a turo ƴan sanda da fararen kaya su zo su kwashi gawarwakin nan da ya kashe jiya, abin da yasa ya kashe su dukka ba tare da bar ko guda ɗaya dan ya samu wasu bayanai daga wajen shi ba shi ne, su waƴan nan ba wani abin da suka sani fa ce a kirasu a waya a ce musu suje su kashe wane, hasalima basu san da waye suke waya ba, umarni kawai suke jira sai kuma diran kuɗi a account nasu, dan haka babu wasu bayanai da suka sani, kashe su shi ne dai'dai, shiyasa ya ɓarar da shegu, mugun iri ɓata gari. Cikin sanyin murya cike da tsoro ta ce "Yaya Saif ga tea". Bai amsa ba kuma bai ɗago ya kalleta ba har His excellency ya ɗaga kiran nasa, kara wayar ya yi a kunnensa ya fara magana a nitse cikin kwanciyar hankali, yana fitar da words one by one, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yadda yake motsa kyawawan lallausan red lips nasa, ba zaka taɓa cewa shi yake maganar ba, magana cike da class ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ *Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta* Dedicated to Maman Yasmin💋 E39-40💋 Cikin sanyin murya cike da tsoro ta ce "Yaya Saif ga tea". Bai amsa ba kuma bai ɗago ya kalleta ba har His excellency ya ɗaga kiran nasa, kara wayar ya yi a kunnensa ya fara magana a nitse cikin kwanciyar hankali, yana fitar da words one by one, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yadda yake motsa kyawawan lallausan red lips nasa, ba zaka taɓa cewa shi yake maganar ba, magana cike da class. Bayan ya kammala ya ajiye wayar a gefe tare da yin kasa da kansa kamar mai tunanin wani abin, daddaɗar kamshi su kaninfarin da chitta dake cikin tea ɗin sai dukan hancinsa yake yi, har ga Allah kamshin ta yi mugun yi mishi daɗi, ita kuma tana tsaye kamar wata soja, wani irin kara suka ji tamkar fashewar glass a palon kasa, a guje ta watso ta haye saman mattress ɗin ta ɓuya a bayansa, har da kankame shi ta yi, mamaki ne ya kama shi, wai wannan wace iriyar yarinya ce, tsoronta ya yi yawa, ko motsawa bai yi ba. Sun ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ya yunkura zai miƙe dan ya je ya ga menene ya fashe a palon. Kankame shi sosai ta yi, ba ƙaramin haushi ta bashi ba, ya tsani mutun matsoraci, a ɗan fusace ya juyo tare da fisgota da karfi, gabaɗaya ta tafi sai saman faffaɗar kirjinsa, damko wuyarta ya yi yana ƙoƙarin fara magana, zaro idanunta waje ta yi a matukar tsorace, ba ƙaramin kyau razananniyar face ɗin nata ta yi mishi ba, musaman ma da ta zaro idanun nan nata, ga su sleeping eyes dara dara, ga su farare tas kamar audiga, ya tsani ganin matsoraci, amma yau fuskar matsoraciya ta burge shi, tsoron ya yi wa face ɗin nata kyau, sake ta ya yi tare da miƙewa ya nufi palon kasan, ita kuma kwanciya ta yi a wajen ta takure waje guda, jikinta sai wani kerma yake yi. Babu kowa palon kasa, daga in da yake tsaye ya hango cikin kitchen, ashe cup ɗin daddy da ta ɗauka bata mai da drawer da kyau ta rufe ba, kuma ta jawo tray ɗin cups ɗin baki baki dan tsawonta bai karisa kaiwa can ba, to shi ne tray ɗin ya faɗo gabaɗaya glass cups ɗin suka fashe, guntun tsaki ya ja tare da juyawa ya koma saman. A in da ya tashi ya koma ya zauna, cup ɗin tea ɗaya ya ɗauka cikin natsuwa ya ɗan zuba sugar kaɗan ya fara sha, dan kamshin tea ɗin ya yi mugun tafiya da shi, haka zalika ɗanɗanon tea ɗin ta yi mishi daɗi, kuma yunwa yake ji sosai yasa shi ya sha, idan baku manta ba, bai ci abincin daren jiya ba. Ba ƙaramin daɗi ta ji ba, Lion ya sha tea ɗin da ta girka mishi, har wani nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da miƙewa zaune a tsakiyar mattress ɗin tana ɗan satar kallon shi, da yake suna kusan a jerene waje guda, sai dai da ɗan rata a tsakaninsu. Wayarsa ce ta fara kara alamar shigowar kira, yana dubawa sai yaga Aseef ne, nisawa ya yi, ba ƙaramin daɗin kiran nan ya ji ba, yana kewarsu sosai da sosai, ɗaukar kiran ya yi, suna haɗe su dukkansu biyu kwance a saman bed nasa, cool murmushi Aseef ya saki, shi dai Areef bai da yawan fara'a, amma akwai kyan zuciya kamar me, zuciyar zinari ke gare shi, ba kowa da kowa yake samun ni'ima da baiwar zuciya irin makamanciyar tasa ba. Kamar abin haɗin baki, har suna rige rigen tambayar ina Rimsha, Lion ya ɗan yi mamaki, wai ba za su tambaye shi ya yake ba, ya ya isa garin da ba nasu ba, ya ya kwana, sai ina Rimsha suke tambaya?, Ko gaisawa basu yi ba, su dai ina Rimsha kawai, lallai Rimsha ba ƙaramin samun damar mallake zuciyar ƴan uwansa ta yi ba,. Shiru ya yi musu bai tanka ba, turo baki Aseef ya yi tare da saka mishi kukan shagwaɓa a kan lallai shi sai an nuna mishi Rimsha. "Ka sha maganinka Areef?" Shi ne abin da ya ce dasu, gyaɗa mishi kai ya yi yana mai kara tambayarsa dan Allah ina Rimsharsu take. "Yau ya kamata ka cire bandejin dake wajen ciwon ai, yanzu komai normal ne". Ya sake faɗa a sanyaye, tamkar bai ji tambayarsa Rimsha da suke yi ɗin ba, amsa mishi da okey Areef ɗin ya yi tare da sake tambayarsa ina Rimsha a karo na uku. Shiru ya yi bai amsa ba, cikin zoyala Areef ɗin ya sake cewa "Wai Saif me ya faru ne na ganka kamar sabon ango? Sai wani kyalli face naka take yi, ko dai garin Abujan ne ta yi daɗi sosai?". Kwashewa da dariya Aseef ya yi yana faɗin "Ni dan Allah ka nuna mini my Rimsha, ita nake son gani, idan ba haka ba, wlh bani ba cin abinci yau". Ya san halin Aseef sarai, zai aikata ya ki cin abincin. Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, ya fahimci ba za su barshi ya yi numfashin or ya sha iska ba matikar bai nuna musu in da take ba, da alama kuma idan bai nuna musu ita ɗin ba, ko abinci ba zasu ci ba, yadda suka kafe da sanyin safiyar nan suke wani tambayarsa ita, wannan kenan dan ita suka kira shi ba dan lafiyarsa ba, ita suka kira su kallah ba wai su tambaye shi ko ya isa lafiya ba, lallai ma sun shahara, yanzu Rimsha ta zama kamar kishiyarsa a zuciyarsu. Gently ya ɗan waigo tare da ɗago dara daran blue eyes nasa ya sauƙesu a kanta, tana zaune shiru kamar mai tunanin wani abin, ba karya ta yi kyau sosai cikin kayan jikin nan nata, gabaɗaya shape nata sun bayyana, ga shi ba'a magana in dai wajen shape ne, akwai shi sosai, ƙasa ta yi da kanta dan kada su haɗa idanu, yatsun hannunta ta fara wasa da shi kamar wata mara gaskiya, zazzaƙar sexy voice nasa ne ya ratsa dodan kunnenta, calmly ya furta ta zo nan, ba musu ta matso gefen shi sosai tana wani yin kasa da kai, Aseef yana ganinta ya furta "Our Queen!" Shi kuma Areef ajiyar zuciya ya sauke. Jin muryar Aseef yasa ta ɗago kanta, wani irin kyakkyawar kayatatcen cool murmushi ta saki wadda sai da dimple nata suka yi wani irin lotsawa na musamman, siririn wishiryarta dake tsakanin fararen hakwaranta ya bayyana, ba zaka taɓa cewa abinci ko wani abin ya taɓa ratsa cikin hakwaran nan nata ba saboda haskensu, sai kyalli suke yi, suna shan wankewa ne da kayan wanke baki masu inganci, shiyasa suke tas. Shagwaɓe murya ya yi yana faɗin "Our Queen ina missing naki over wlh, yau ba zanci first spoon naki bafa". Ita ma shagwaɓe murya ta yi kamar dai yadda ya yi mata magana, tamkar zata yi kuka ta ce "Nima ina kewarku sosai, Yaya Areef dan Allah ku shigo mota kawai ku biyo mu, zan fi jin daɗi, yanzu wlh ina tsoron gidan sosai, akwai wasu mutane, dan Allah kuzo zan fi jin sanyi". Yadda tayi maganar sai da ta sanya Lion ɗin waigowa ya kalleta, ga shi tana magana dimple nata na wani irin lotsawa, duk wanda ya kalleta sai ta burge shi, ga shagwaɓa da take zubawa Aseef, abin ba'a cewa komai, yau har cikin zuciyarsa sai da ya ji ta burge shi, kawar da kallonsa ya yi daga kan nata tare da cigaba da shan tea ɗin nasa ya kawar da wayar daga face nasa zuwa saitin tata. "Kina so mu zo ne my Rimsha?" Cewar Areef, da sauri ta gyaɗa mishi kai alamar e, "To shikenan zamu zo, amma ke da kike tare da Lion me abin tsoro? Kada ki damu, ni nasan waye ɗan uwana, yana kaunarmu kuma yana kaunar dik abin da muke kauna, muna kaunarki ya sani, ba zai taɓa watsa mana kasa a idanu ba, yana son ganin mu cikin farinciki fiye da kansa, so ki kwantar da hankalinki, dole zai baki farinciki dan yasan idan ya yi hakan kamar mu ya yi wa, in kin yi farinciki tamkar mune muka yi, akasin hakan ma, mune muka yi"......... A nan wajen Areef ya yi amfani da basira ne ya ɗaure Lion da magana, ya gayawa Rimsha Lion yana sonsu fiye da kansa, dan haka zai kula da ita, ya san cewa idan ya faɗi hakan, kenan suna da kwarin gwiwa sosai a kan shi, hakan zai sa Lion ɗin ya bata kulawa dan kada ya watsawa ƴan uwan nasa kasa a idanu, Areef ba dai basira ba, akwai basirar na wuce misali. Zata yi magana Lion ya miƙa mata waƴar tare da miƙewa ya bar wajen zuwa ɗakin daddynta, yana tafiya Areef ya ce "Kina ji sister?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e tana ji, "Lion ba ya cin abincin restaurant, ba ma zai taɓa ci ba komai wuya komai daɗi, duk in da zai je in dai ba mai yi mishi girki, to Maltina da kyau sune kawai suke zama abincinsa, dan su hannun baya taɓa cikinsu a cewarsa, kinga kwai ma ko an dafa ai ba'a taɓa cikin ba sai bayan, bayan kuma ɓarewa za'ayi a zubar, dan haka ki rinƙa dafa mishi kwai, dan Allah kada ki bari ɗan uwana ya zauna da yunwa, wlh bashi da juriyar yunwa, sai dai baya cin abinci sosai, iya Maltina idan ya sha, yana iya ƙoshi, amma idan lokacin cin abincinsa ya yi zai shiga damuwa dan baya jure yunwa, ki rinƙa bashi Maltina da kwai, na san ba zai iya cin abincinku na Nigeria ba, dan haka ba sai kin sha wahalar girkawa ba kin ji ko?" "To yaya Areef amma yanzu da na bashi tea namu na nan ya sha wlh, ka ga cup nashi ma har ya kusa shanyewa, kaɗan ya rage". Ba Areef kawai ba, har ta Aseef sai da ya zaro idanu waje, anya kuwa,? Aseef ya tambayi kansa da kansa a cikin zuciyarsa, Areef kuwa cewa ya yi "Ba abin mamaki bane dan ya sha, na san yunwa yake ji shiyasa ya sha, na gaya miki baya da juriyar yunwa ko kaɗan, dole zai sha dan bashi da mafita, ba zai iya cin abincin waje ba duk wuya duk daɗi, yanzu kuna da Maltina a gidan naku ne ko babu?". Ɗan waigawa ta yi tana kallon shi yana nufota ya fito daga bedroom na daddynta, "Yaya Areef babu, babu Maltina kuma babu wuta a gidan". Zai yi magana Lion ya miƙa mata hannu a kan ta bashi wayarsa, babu musu ta miƙa mishi cikin girmamawa a kuma nitse. "Areef zan fita ne, sai na dawo". Ya kai karshen maganar tare da katse kiran ba tare da ya jira amsarsu ba, pistol gun da ya ajiye daren jiya ya ɗauka ya nufi hanyar palon kasa dan ya sauƙa fita zai yi zuwa unguwa. Zazzaƙar muryarta ne ya katse shi tare da sanya shi juyowa babu shiri. "Yaya Saif tsoro nake ji, dan Allah kada ka fita ka barni, ina jin tsoron gidan sosai". Ta yi maganar a nutse, a shagwaɓe, can kasa kasa kuma, sannan ta yi maganar tana sunkuyar da kai katsa dan bata son kallon face nasa bare ma taga action ɗin da zai ɗauka. Shiru ya ɗan kalleta na ƴan sakanni, maganar Areef ne ta dawo mishi kunnansa, yana son mu fiye da kansa kuma yana son farincikinmu, ba zai taɓa bari ki shiga kunci ba, dan yasan idan kin yi farinciki to tamkar mune muka yi, tuna hakan yasa ya juya ya cigaba da tafiya, binshi da kallo ta yi idanunta sun ciko tab da kwallah, tana bala'in tsoron zaman gidan ita kaɗai, bai juyo ba kuma bai yi mata magana ba har ya sauƙa ya fita daga palon baki ɗaya, juyowa ta yi ta balcony tana kallon shi ya zo wajen motarsa, shiru ya ɗan tsaya bai shiga ba, can kuma sai ya ɗago kansa sama kamar yasan tana kallon shi, da hannu ya yi mata alama a kan ta zo su tafi, da sauri ta miƙe, tsabar murna bata ma san lokacin da hawayen da suka cika mata idanu suka zubo ba, ɗakinsu ta koma ta ɗauko ɗan ƙaramin farin hijabi ta sanya a saman kanta, ta yi kyau over, baiwar Allah ko tea ɗin ma ita bata sha ba, kuma tana jin yunwa sosai kamar ta mutu, amma ba halin ta ce zata tsaya shan tea ɗin, dan ba zai jirata ba. Ta wutsiyar idanunsa yake kallonta tun da ta fito, sai da ta kariso gabansa, calmly ya ce ta buɗe musu gate, da okey ta amsa mishi tare da wucewa ta je ta buɗe gate ɗin, shi kuma ya shiga motar ya tada ta, waje ya nufa, bayan ta fita ne ya tsaya yana jiranta, sai da ta rufe gate ɗin sannan ta zo da sauri ta shiga gidan gaba, sai tashin kamshi take yi. Da gudu ya ja motar, bayan sun kusa kaiwa babbar gate ne ya ciro face mask ya sanya a face nasa, dan yasan idan sun isa gate ɗin sai ya sauƙe glass ɗin motar, miƙa mata face mask ɗaya ya yi a kan ta saka, dan baya son su tsayar da su tambayarta yaushe ta dawo da sauransu, dan ba wanda bai san ƴaƴan Nawazudden ba a wajen, suma masu tsaron babbar gate ɗin sun santa tun da kullum daddy na kaisu school. Haka kuwa aka yi, da suka zo sai da aka tsayar da su, suka yi binciken da zasu yi sannan suka fice, suna fita ya kunna goggle map a wayarsa ya ɗauki hanya kawai abinsa, sun yi nisa da tafiyar da suke yi sai ya lura ana bin bayansu, wata bakar mota ce ta fara biyo su tun ɗazun, ɗan juyowa ya yi ya kalleta ta cikin mirror, sarkin tsoro sai kallon hanya take yi, kasa kasa ya ce ta ɗaura seat belt nata, okey ta amsa tare da ɗaura wa, shi ma ɗaurawa ya yi tare da canza hanya daga kan hanyar da yake ya sauƙa izuwa ɗayar hanyar ya kuma kara gudun motar sosai, bata wani damu ba, dan dama bata san ina zasu je ba. Gudu ya yi ta shararawa har suka fita bayan gari, a ɗan wani daji ya paka motar tasa tare da ce mata ta zauna a ciki kada ta fita, dama yasan in dai suka fita sai an bi bayansu, da gangan ya ce ta buɗe mishi gate, dan ta fito a waje ne ta shiga motar tasa, yana son kowa ya san ta dawo, idan suka sani kuma sai an biyo bayansu, wannan dalilin yasa ya ɗauko pistol gun nasa. Ta cikin mirror yake kallon wannan bakar motar, ɗan nesa da nasu suma suka paka, suma bakar glass ce da motar tasu, baka iya ganin mutanen da suke ciki, baya son fita, dan kada su gudu, yana da tabbacin basu san shi ne a cikin motar ba, Rimsha suka biyo, dan ita ce ya shiga motar a waje, shi tun daga cikin gida ya shiga, ita kuwa sarkin tsoro tuni ta tsorata ganinsu a daji, jikinta har wani karma ya fara yi, ta manta ita ƴar soyayya ce, yau ga daji daɗin soyayya amma kuma jikinta na kerma. Tana can tana tunani zazzakar sexy voice nasa ya katse mata tunani da cewa "Cire face mask na fuskarki ki fita ki zagaya wajen bishiyoyin ɗan bayan mun can ina zuwa". Ba musu ta cire ta kuma fita, ya yi mata haka ne, dan yana son mutanen su fito, yana son sanin ko su waye ne, tabbas idan ya fito suka ganshi zasu gudu in basu riƙe makamai ba, idan kuma suka gudu da wuya su sake biyo Rimshar ta wannan hanya, sai dai su canza salo, hakan kuma zai sanya shi ya jima a garin nan, baya son wuce kwana uku bai gama komai ya koma ba, idan ita ta fita, zasu yi tunanin bari su lallaɓa su kasheta su cika aikinsu, dan shi ɗan ta'adda kullum gani yake yi zai yi nasara, baya taɓa hangen zai faɗi, shiyasa basu nadama sai sunga mutuwa ɓaro ɓaro. Tana fita ta nufi wasu bishiyoyi dogaye da suke ɗan nesa da motarsu ta ɗan bayar motar amma, ma'ana tsakanin motarsu da na waƴan da suka biyo su, mutane huɗu ne suka biyosu, dukkansu fuskokinsu sanye da mask, ga kuma bakaken suit kamar zasu je church or party, suna ganin fitowarta ɗaya daga cikinsu ya ce "Oga wlh ita ce, yanzu saura mu san ita da waye a cikin motar, mahaifiyarta ce ko waye?". Wanda aka kira da ogan ya amsa da cewa "Dole ita da mahaifiyarta ce mana, kun san dai Nawazudden kam ya jima a lahira, shi ma Shitu hakane, dama ita da Mahaifiyarta da ƴar uwarta suka rage, kuma kunsan Nawazudden ba shi da ƴan uwa, duk waƴan da suka san shi sun ce shi kaɗai suka sani, maraya ne tsintatcen mage, zuwa Abuja neman aikin yi fa ya yi, ɗan cirani ne bai da kowa, ita ma matar tasa marainiya ce basu da kowa, amma ba zamu yi gangancin tinkarar motarsu ba har sai mun san dame suke tafe, yanzu dai ku sauƙa mu kashe yarinyar, idan muka bita cikin dajin muka kasheta kunga dole mahaifiyar tata koma wace ce ta fito idan ta ji shiru yarinyar bata dawo ba, dole na cikin motar ta fito dan zuwa nemanta, kunga a nan ne zamu gane da waye suke tafe, sai mu haɗesu duk mu kashe, yanzu ku fita mu je". To suka amsa tare da buɗe kofofin motar suka fito, jahilci ya fi hauka, ya Allah ka bamu ilimi mai albarka mai amfani, kowa ya tsaya ya nemi ilimi, idan ba jahilci ba, ta ya za'ayi ku kalli mota danƙareriyar har haka ta faka a cikin daji kuma kuyi tunanin su ba'a shirye suka zo ba? Tabbas jahilai ke yin ta'addanci, mai ilimi wadda yasan me yake yi, yasan Allah da girmansa, da hukuncisa, ya yi imani da ranar tashin kiya ma, ya kuma yarda da Allah da Manzonsa, tabbas ba zai kashe rai ba, wasu dama sunan musulmai ne kawai ke garesu, amma babu ilimin da suke da shi, sun dai san ana cewa Allah da annabi, amma basu ma san menene Allah ba, me zai yi musu idan suka saɓa mishi, ko an gaya musu da fatar baki, ba zasu ɗauka gaskiya bace, saboda tun farko ba'a faro musu ginin daga farko ba, kowa ya tsaya ya nemi ilimi, dan jahilci ya fi hauka, Allah kasa mu dace ka kuma bamu ilimi mai albarka mai amfani. Tun da suka fito yake kallonsu ta cikin mirror motar, har suka nufi in da ta nufa, kuma babban jahilcin da suka yi, sai suka fito su dukkansu suka je kashe karamar yarinya, abin ma ba tsari sam, suna yin abu ne best on tunaninsu na jahilai. Sai da ya bari sun kurewa ganinsa, sannan ya fito tare da bin bayansu, tana zaune saman wani ɗan dutse ta yi shiru tana tunanin ko me yasa yaya Saif ya ce ta zo nan ta zauna oho, bata ankara ba sai ganin karti huɗu ta yi a kanta, a razane ta miƙe, nan take idanunta suka fara kwallah, ga shi ɗan ƙaramin hijabi ta saka suna kallon gabaɗaya suran jikinta, lumshe idanu ogan nasu ya yi kafin ya ce "Ni kam ma wlh ta yi mini, dama matata ta tafi gidansu tun last week, dan haka ku kama min ita bari na rage zafi kafin mu aikata in da aka aika babanta". Yana magana yana cire botir ɗin suit ɗin jikinsa, tana ƙoƙarin wage baki ta yi ihu idanunta suka sauka a kan Lion dake tsaye a bayansu yana kare musu kallo, yatsa ɗaya ya ɗaura mata a saman bakinsa alamar ta yi shiru, ba musu ta yi shiru duk da a tsananin tsorace take, amma ba zata iya kin bin maganarsa ba dole ta haɗiye ta danne. Nufar ta maza biyu suka yi da nufin su kamata wa ogansu, sai kallon Lion take yi babu ko kyaftawa, bai yi ko motsi ba yana tsaye yana kare musu kallo, ganin ta zubawa waje guda idanu ne ya saka su juyawa da sauri dan suga me take kallo, ganin cikakken gwarzon namiji a tsaye yasa suka juya da kyau dan su tabbatar da wa da idanunsu abin da suke kallo. Kallon ogan nasu suka yi, shima cikin sauri ya juya dan yaga me suke kallah, ganin Lion ba ƙaramin razana su ya yi ba, amma saboda su basu lissafin faɗuwa a rayuwarsu, sai ogan ya basar kirjinsa na dukan uku uku ya ce "To me dan kunga wannan zaku tsorata? Daga gani ma kasan dadironta ne, baka gan shi Bature ba ne, mayun mata kenan, kada ku ji komai ai ance turawa basu da quality, saboda fararen fata ance su basu da quality, ku cimin ubansa ni kuma bari na buɗe mata aiki dan a hannu nake, da gani ma nasan ɗan iskancan ya rigani buɗe mata aiki tun da gida ɗaya suke kuma babu kowa a cikin gidan, ku kunsan ba zai ga irin wannan kayan ya bari ba, har na fara lissafin yanzu zan buɗe budurcin mata na 20 fa kenan, na kusa na cika 20 ɗin nan na kusa kamo Oga, amma yanzu wannan bata cikin lissafi dan nasan ya buɗeta, har yanzu dai a 19 nake". Yana surutu yana wani haɗa zufa, daga gani a tsorace yake ɗan banzan. Shi kuma Lion tamkar ya ji me suka ce, dan da hausa suka yi magana ba English ba, kamar ya ji su ya tsareta da idanu yana kallon kayan da aka ce ya gani ba zai kyale ba, from head to toe yake kare mata kallo, lokacin guda sai da ya ji wani iri a jikinsa. (Anya Lion baya jin Hausa kuwa? Na fara tantanma a kansa🤔) Tun da yake da ita bai taɓa karewa surar jikinta kallo ba sai yau, tsab ya kalleta kafin ya maido da kallonsa kansu, ganin suna ƙoƙarin kamata ne yasa ya yi mata alama da hannu a kan ta zo, da gudu ta watsa ta nufe shi, tana zuwa kuma saman faffaɗar kirjinsa ta faɗa tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, jikinta sai kerma yake yi ta tsorata sosai. Juyawa ogan nasu ya yi yana faɗin "Ai na gaya muku wlh dadironta ne, idan ba haka ba me ya haɗa shi da ita? Ba ga shi ta rungume shi ba, Nawazudden da matarsa dai basu da ƴan uwa, to a ina ta samo wannan Baturen kuma? Kuje ku kamo min ita a matse nake, shi kuma ku tura shi in da ba'a dawowa". Rashin sani yafi dare duhu, da gudu suka nufe shi dan su kamota, kara kankame shi gam ta yi tana kara sakin kuka mai sauti, wani mara kunya daga cikinsu ne ya sanya hannu zai fisgota daga jikin Lion ɗin, carap ya capke hannun nasa tare da murɗe shi baya kafin ya sanya kafa ya kwashe kafafunsa ya faɗi kasa, calmly ya ce "Sake ni ki koma mota ki zauna". Sakin nasa ta yi da gudu ta juya ta nufi motar, wani katon itace ogan nasu ya ɗauka ya harbeta da shi, sai kanta ya sameta, ihu ta fasa kafin ta faɗi kasa a cikin ciyayi, shi kuma Lion yana ƙoƙarin murɗewa waƴan nan da suka zo kamata ɗin wuya, bai damu dan ogan ya harbeta ta faɗi ba, kuma bai juya ya kalleta ba, bai bi ta kanta ba, jibgan waƴan nan kawai yake yi kamar an aikosa, a takaice sai da ya kashe su tas ya rage daga shi sai ogan nasu, yana ƙoƙarin guduwa ogan nasu, ya damko wuyarsa ta baya tare da kwashe kafafunsa ya zube kasa a wajen. Babu tausayi babu imani haka ya kama hannun ogan nasu ya kakkarya kamar ba lafiya ba, sannan ya kama kafarsa ta dama ita ma ya karya ta, kafin nan ya zauna a saman dutsen da Rimsha ta zauna, cikin harshen turanci ya tambaye shi ina ogansu baki ɗaya yake? Sai ihu yake yi babu bakin magana, pistol gun nasa ya fitar ya saka mishi a dai'dai saitin ido ya sake maimaita mishi tambayar da ya yi mishi, yau shi ne karo na farko da Lion ya maimaita magana, cikin bakar azaba ya amsa mishi da Hausa a kan shi baya jin English, ciro wayarsa ya yi ya ɗauki fuskar mutumin hoto, kafin nan ya harbe shi da bindigar hannunsa a dai'dai tsakiyar goshinsa, sannan ya miƙe ya nufi in da take kwance kamar gawa. Tsugunnawa ya yi a kusa da ita, ta yi kwanciyar ruf da ciki, remote ɗin motar tasu ya fitar tare da dannawa kujerar motar ta kwanta, gently ya miƙe tare da saɓarta a saman kafaɗarsa zuwa filin motar, yana zuwa ya buɗe already kujerar ta kwanta, kwantar da ita ya yi tare da rufe kofar ya koma ta ɗayar ɓangaren ya shiga, ɗan baya kaɗan ya yi da kujerarsa yadda zai dawo dai'dai da saitin kan nata, hijabin jikinta ya fara cirewa, buguwa ce ta yi daga ta ciki, ta waje bata ji ciwo ba. Saman kujerar baya ya ɗaura hijabin kafin ya zuba mata idanu yana kallonta, hannu yasa ya tattara dark black curly hair nan nata ya dawo da shi ta gaba dan ya ga in da ta bugu ɗin, ciwo a cikin kai babbar musifa ce, akwai azaba, hannu ya kai saman wajen da itacen ya taɓata, wajen ta ɗan kumbura, shiru ya ɗan yi kamar mai wani tunani, can kuma sai ya saki gashin nata tare da mayar mata da shi baya, fuskarta ta yi fayau da ita kamar mara lafiya, wayarsa ce ta fara kara, His excellency ne yake kiran shi, ɗauka ya yi tare da komawa ya jingina bayansa da jikin motar suna magana a kan ƴansandar da ya buƙata sun je gidan kuma baya nan. Lumshe dara daran blue eyes nasa ya yi kafin ya sake warosu a hankali, calmly ya ce su yi aikinsu kawai, ba sai lallai idan yana nan ba ai, su kwashe gawarwakin su fita da su, shi ya fita ne amma yanzu shi ma zai dawo, kuma dama baya son haɗuwa da kowa, dan haka kafin ya dawo su kwashe komai tas, daga haka suka yi sallama da shi, ya katse kiran ya ajiye wayar a gefe guda, robar ruwan dake kusa da shi ya ɗauko, tarfo ruwan a hannunsa ya yi tare da shafa mata a fuska. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da jan dogon numfashi ta sauke a hankali, zuba mata idanuwansa ya yi yana kallon yadda take motswa a hankali tana son farkawa, miƙa ta yi sosai tare da juyawa saura kaɗan ta faɗi kasa ya tareta da hannu ɗaya, bata san cewa ba'a saman bed take ba, saman kujera ne, a hankali ta waro dara daran sleeping eyes nata kai tsaye sai cikin idanunsa, da sauri ta mayar da su ta datse gam, dan har gobe tsoron ganin cikin kwayar idanunsa take yi, rufe robar ruwan ya yi tare da juyawa da kyau yana ƙoƙarin kunna motar, ɗaura rubar ruwan ya yi a mazauninsa kafin ya ɗaga nata kujerar nata. Walkiya da rugugin hadari ne suka fara wanzuwa a sararin samaniya, kunna motar ya yi suka nufi hanyar da suka bi su ka zo, wani katafaren super market suka nufa, kayan drinks ya saya da su fruits, sai kwai, ita kuma ya ce ta ɗauki abin da take so, kayan sakawa ya ɗauka, wandunan jeans da sauransu, sai wasu high heels guda biyu da ta ɗauka, ganin irin man wanke kansa yasa ta ɗauka mishi har guda biyu, shi kuma bai gani ba, dan bai je wajen ba, idan baku manta ba ta taɓa shiga toilet nasa, bata da mantuwa, bata manta kalar mayukan da ta gani a cikin toilet ɗin ba, da yake duk rabin kayan da muke amfani da su a kasar nan na kasar waje ne, kuma super market ɗin banbane sosai, sai ta sami irin shampoo ɗin nasa, ita ma ta ɗaukawa kanta ɗaya dan ta yi amfani da su ta gani, basu wani kwashi kaya sosai ba, amma sai da ta saki baki jin irin uban kuɗin da aka kira musu zasu biya, batasan mayukan nan da ta ɗauka sune masu uban tsada ba, ga shi har guda uku ta kwasa abinta, tambayarsu ya yi zasu karɓi dollars, e suka amsa mishi da shi, bata key ɗin motar ya yi a kan ta je ta ɗauko kuɗi a ciki mota, har ta nufi waje, kome ya tuna sai ya ce ta dawo, karɓar key ɗin ya yi ya tafi da kansa. Jim kaɗan ya dawo tana tsaye a wajen, lissafi suka buga mishi ya kirga ya basu, ma'aikatan wajen ne suka kwasa musu kayan zuwa cikin mota, ba ɓata lokaci suka shiga suka bar wajen, suna fita wajen motar Hajiyar daɗi na danno kai ita da Jehan sun zo sayayya, dama idan baku manta ba sun ce zasu zo sayayya, to shi ne suka zo, sun kuma yi babbar saɓani da su Lion, da yake dukkansu bakaƙen glass ne da motar tasu kamar wasu marasa gaskiya, sannan ita Jehan tana gidan baya suna hira da wata yarinya sabuwar zuwa da kuma Adiva, sun baro Maryam a gida, A'isha kuma shiru har yanzu, ba su sake jin ɗuriyarta ba. Gida Lion ya nufa, amma kafin nan sai da ya tsaya ya sayi jarkar man fetur guda dan su kunna engine, hadari ne sosai ya taso kafin su isa gida, lokacin da suka isa ta sauƙa ta buɗe mishi gate har an fara yayyafin ruwa, yana shigo da motar ruwan saman ta kece kamar da bakin kwarya, tsalle ta buga tare da nufar wajen kwano in da ruwa ke zuba sosai ta tsaya, sai murmushi take yi, sarkin son ruwa, ta manta ma bata kulle gate ɗin ba, zuba mata idanu ya yi yana kallon ikon Allah, yarinya ne kamar wata kifi, sai shegen son shiga ruwa, wannan ma ya ga akwai pool a gidan nasu, idan linƙaya take so to ta shiga mana, amma ita ba haka take so ba, ta fi so ne taga ruwan na zubo mata daga kanta har zuwa kasa, ta yi ta juyi yana zubo mata, ba ƙaramin daɗin hakan take ji ba, har wani garɗi, garɗi barci, barci take ji idan tana cikin ruwan sama. Sosai ya tsareta da ido, ba ƙaramin burge shi kuma ta yi ba, yadda take juyi a cikin ruwan ba'a magana, kowa ya ganta sai ya sake waigawa ya kallah. Almost 30 mins yana cikin mota ita kuma tana cikin ruwa, da ya ga ruwan ba shi da niyar tsagaitawa ga kuma mattress sun bari a sama da wuya idan bai jike bama, kuma yana son zuwa ya kunna engine dan ya sanya su Maltina a fridge su yi sanyi ya sha, yana jin yunwa, hakan yasa ya buɗe kofar motar kawai ya fito, a rumfar parking space ɗin ya tsaya yana kara kare mata kallo, wato ita fa ko kwana ruwan sama zai yi ita ma zata iya kwana a cikinsa, kwata kwata bata wani tunanin illar hakan, nufar gate ɗin ya yi ruwa na jiƙa shi ya je ya jawo dan ya rufe, jin karar gate ɗin yasa ta juyo ga gate ɗin da sauri, ganin shi ne yake ƙoƙarin rufewa yasa ta nufe shi da sauri ta ma mance da zancen rufewa, hannu tasa da nufi bari ta karɓe shi ta rufewa, bai kula ta ba ya rufe tare da miƙewa, ita ma miƙewa ta yi tana son ta ce mishi ya yi hakuri, tana tsoro dan ta ji an ce baya son kalmar sorry. Da hannu ya yi mata nuni da ta wuce cikin gida, okey ta amsa tare da juyawa da sauri zata bar waje, tsantsi ne ya ɗebeta ta yi baya ta faɗi kasa, saboda ta juya da sauri dan ta tafi, tiles ɗin kuma akwai ruwa sosai, ga jikinta da ruwa, ga ruwan kuma yana zuba, zaman ƴan bori ta yi a kasan ta kasa miƙewa, da farko kamar ba zai kulata ba zai wuce, sai ya tuna anjuma akwai in da zai je da ita, dole ya tabbatar tana lafiya kafin lokacin, tuna hakan yasa ya juyo ya miƙa mata hannansa a kan ta kama ta miƙe, ba musu ta kama, sai dai ta kasa miƙewa, saboda ba karya ta bugu, zafi take ji, ganin hakan yasa shi ya kama hannunta ya fisgota da karfi ta miƙe tare da faɗawa saman faffaɗar kirjinsa, ga ruwa na zuba kamar ba gobe, ƴar kara ta saki dan kuwa fisgota da ya yin nan ya yi mata zafi, hannunta ya yi mata zafi, sannan kuma mazaunanta da ta bugu suma sun mata zafi, zuba mata idanu ya yi ga sanyin ruwan saman na ratsa shi, wani irin yanayi mai daɗi ya tsinci kansa a ciki, ita kuma sai aikin turo baki take yi tana ƴar kara, Bin ɗan bakin nata da kallo ya yi, ba ƙaramin kyau lips nata suka yi mishi ba, yadda ruwa ke zuba a kansu, ƙoƙarin raba jikinsa da nata ya yi dan ya je ya zuba mai a engine ya tayar, cikin sauri ta kankame shi tana faɗin "Wlh yaya Saif ba zan iya takawa ba, Allah na bugu sosai". Sak yadda Aseef yake magana idan iya shegensa sun motsa, haka ta yi magana ita ma, tana yi tana turo baki, Aseef ya gama koya mata tsiyar nan tasa, har cikin ransa ya ji wannan magana da ta yi, lumshe idanunsa ya yi yana mai ɗaga kansa sama ruwa yana sauka a saman face ɗin nasa, ɗaga kai ɗin nan da ya yi wannan kashin na wuyar maza nasa ta bayyana, tsabar rashin ji irin nata bata yi tunanin me zai je ya zo ba, sai ta kai hannu ta taɓa ƙashin, ga bala'in tsoronsa kuma kamar zai kasheta, amma sai uban rashinji cike a kanta. A sukwane ya sauƙo da kan nasa kasa tare da sauke kallonsa a saman face nata, nan take ta yi narai narai da idanu, jikinta ya fara kerma ta fara nadamar hakan da ta yi, kullum sai ta yi laifi take fara danasani, lokacin da zata yi bata danasani har sai ta yi, yama rasa wani irin hukunci zai yi mata, baya son ya taɓa lafiyar jikinta sam, dan anjima da daddare akwai in da zasu je, kuma wannan waje ne mai matukar muhimmanci wadda yasa ran dole zai sami wanda yake nema a wajen, to wani hukunci zai yi mata ta ji ba daɗi sosai ba tare da ya taɓa lafiyarta ba? Ya tambayi kansa. Tsareta da idanu ya yi, can zuciyarsa ta tuna mishi da abin da ya faru ranar da ya taɓa tula tulanta by mistake, abin ya yi mata ciwo sosai har ta kira Anaya a waya dan ta gaya mata, har kuka sai da ta yi, tuna hakan ne yasa yasa hannun shi ɗaya ya matso da ita jikinsa sosai, har lokacin ruwan saman bai tsagaita ba ko kaɗan, ɗayar hannunsa ya sanya ya gangaro da wuyar rigarta zuwa kasan breast ɗin nata, nan take sunansa ya bayyana, ga shi da ruwa ya jiƙa zanen sai suka kara fitowa ɓaro ɓaro, kankame shi ta yi tana ɓuye kirjin nata a jikinsa, ba zata iya guduwa ba dan ba karya ta bugu, da karfi ya ɗan raba jikinsu tare da sanya hannusa ɗaya ya damki breast ɗin nata gu ɗaya, ihu ta kurma mishi shima sakinta ya yi ba shiri, dan wani irin shock da ya ji, runtse idanunta gam ta yi tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a kalla mata su ma bare taɓawa, ji ta yi kamar ta tsinke shi da mari sai dai ya kasheta idan zai kasheta mugu kawai. Shi kuma ba zai iya shiga cikin gida ya barta a nan ba, saboda lafiyarta dan fitar da zasu yi, dole haka ya saɓeta a kafaɗarsa tana kuka ya wuce da ita ciki, yau idan ranta ya yi dubu to ya ɓaci, kuka take yi ba kaɗan ba, a tsakiyar palo ya sauketa tare da komawa waje ya fito da fetur ɗin zuwa wajen engine, zubawa ya yi ya tayar sun yi sa'a ba abin da ya sami engine ɗin. Bayan ya kunna wuta ya zo ne ya wuce ciki, yadda ya barta haka ya dawo ya sameta, alamar abin ya yi mata mugunciwo sosai, sai kuka take yi, ko kallon in da take bai yi ba ya haura sama abinsa, ya ji daɗi da ya kona mata rai ba tare da ya taɓa lafiyar jikinta ba, zaman dirshan ta yi a wajen tana kuka tana jan Allah ya isanta a cikin zuciyarta, Fridge na ɗakin daddy ya fara kunnawa kafin ya sake saukowa kasa zuwa wajen mota ya kwaso kayan drinks da suka sawo ya dawo, a cikin fridge ɗin ya zuba su, har lokacin tana zaune a palo tana kuka, tamkar bai san da zaman ta a wajen ba, toilet ya nufa ya yi wanka tare da shiryawa cikin pajama ya fito zuwa balcony dan ya duba mattress ɗin, ya jike sharkaf da ruwa, ɗagawa ya yi ya tsayar a tsaye tare da jingina shi da jikin karafunan wajen, sannan ya nufi bedroom ɗin mum, nata mattress ɗin ya ɗauko zuwa bedroom ɗin dad, da yake girman gadon nasu ɗaya, kunna Ac ya yi sannan ya shinfiɗa bed sheet ya haye ya kwanta tare da ɗauko wayarsa da ya ɗaura a saman bedside drawer tun shigowarsa, da yake wayar tasa wata Prof ce sai bata yi komai ba da ruwan sama ya jiƙasu, ɗan latsa wayar kaɗan ya yi kafin barci ta yi awon gaba da shi, ita kuma sai da ta gama cin kukanta har sai da idanunta suka kumbura, sannan ta miƙe zuwa bedroom nasu ta yi wanka tare da shiryawa cikin wasu shegun riga da wando, jeans ne baki mai bala'in kyau, ya kamata sosai duk da yake na Jehan ce, amma ta ɗan yi kiba shiyasa ya matseta sosai, sai ƴar riga mai karamar hannu fara, hand dryer ta ɗauko tare da junawa ta busar da gashinta, cike da tsoro ta fito ta nufi ɗakin daddyn nata, dan wlh ko za'a kasheta ba zata kwanta ita kaɗai a ɗaki ba, salon wasu karti su shigo, gara mata shi ɗin dai duk da tana jin haushinsa, ga shi baya rufe gidan, sai ya bari a buɗe kayansa, ko alamar tsoro babu a tattare da shi. Da sallama ta shiga cikin ɗakin, sai faman kumbure kumbure take yi, already lokacin ma ya jima da yin barci abinsa, harararsa ta yi tare da kara jan Allah ya isa a cikin zuciyarta kafin ta kwanta saman sofa tana mai jin kuna a cikin ranta, ga bala'in yunwa. A ɓangaren gidan Hajiyar daɗi kuwa, bayan sun dawo daga super market ɗin, sun sha sayayya ba karya, Jehan sai murna take yi ba kaɗan ba, a hankali Hjy ta turo kofa ta shigo cikin ɗakin nasu, daga ɗan bakin kofa ta tsaya tana faɗin "Jehan". "Na'am mummyn". Ta amsa tana miƙewa zaune, "Ki shirya, ki tsantsara kwalliya mai shegen kyau kina da bako". Cool murmushi ta saki, ita da bata murmushi a baya, "To mummy wani irin kaya zan saka?". Shiru Hajiyar ta ɗan yi kafin ta ce "Baƙon na musamman ne, ɗaya ne daga cikin jigo na wannan gida, kusan zan ce miki shi ya kafa mu da har muka kai izuwa yanzu, ya nuna ra'ayinsa a kanki sosai, dan haka ki saka short zuwa gwiwa, da kuma riga mai karamin hannu ma it's okey". Da fara'ata ta amsa da to tare da miƙewa ta shige toilet, ita kuma Hajiyar ta nufi waje, Maryam Adiva duk suna baje a sama gado sun yi ɗai'ɗai daga su sai guntayen wando zuwa cinya da ƴar riga da bata wuci cibiya ba, sai taunar chewing gum suke yi. Wanka ta yi ta fito ta shirya kamar yadda suka yi da Hjy, sai murmushi su Adiva suke yi suna yaba kyan da ta yi, wayar Adivar ta ɗauka tare da nufar waje, sai sheki gashin kanta yake yi, ya sha gyara sosai a fitar da suka yi ɗazun, ta yi kyau kam ba karya, office ɗin Hjy ta nufa, sai murmushi take yi, ba sallama ta afka ciki, Hjy na zaune a saman dankareren lallausan kujerarta, ga sanyin Ac na bugata, Hamshakiya mandiya, sai wani washe baki take yi taga ruwan kuɗi. Ganin Jehan ɗin yasa ta kara washe baki tana faɗin "Jehan ga alhajin da yake bukatarki, ya ce ma tafiya zaku yi da shi sai jibi zai dawo da ke". Ba musu ta amsa da okey mummy tare da juyawa ta kai kallonta kansa, wani irin bugu gabanta ya bada, zaro idanun nan nata ta yi tana kallon shi da mamaki, ko mutuwa ta yi ta dawo ba zata manta da wannan fuska tasa ba a rayuwarta, ganin face ɗin nasa kuma yasa ta tuna da wace ce ita, me ya kawota gidan, menene yake faruwa, da ni daku munsan addu'ar da iyayenta suke yi mata ne ya yi sanadiyar dawowarta cikin hayyacinta, amma ita bata sani ba, bata kuma nuna musu ta dawo cikin hayyacinta ɗin ba, sai ta ce to su je ta shirya, magani Hjy ta bata akan idan taje kafin su kwanta da alhajin ta sha dan gudun ɗaukar ciki, ba musu ta karɓa tare da wucewa ta yi gaba tana tunanin yadda zata ɓullowa lamarin, duk sai ta ji wani irin, dressing nan da ta yi sam bata ji daɗin shi ba, amma saboda akwai abin da ta kudurta a ranta, sai ta daure ta shanye, bata nuna kamar kayan sun sanyata bakin ciki ba. Shi kuma alhajin ya miƙe zai bi bayanta Hjy ta tsayar da shi tana yi mishi magana a kan dan Allah kada ya bari Jahan ta ɗauki ciki, wani irin shu'umin murmushi ya yi, dan shi yasan me ya shirya a kan Jehan ɗin, yasan Nawazudden sosai, akwai ƴar tsama a tsakaninsu, so amfani da Jehan ɗin zai yi ya zuba mata tsafi a ciki ta mutu dan babanta ya yi mishi wani laifi da ta shafe su can, sai dai bai nunawa Hjy hakan ba, ya ce mata ba komai zai kula, da haka suka yi sallama ya bi Jehan suka fita. Tun da suka ɗauki hanya barin gidan ta kurawa hanyar idanu sai kallo take yi, shi kuma Alhajin bai lura ba yana tuki, da haka har suka fita garin Abuja suka ɗauki hanyar Kaduna. Sai karfe 8 na dare suka shiga garin Kaduna, kai tsaye wani katafaren gidansa dake unguwar su Lion ya nufa da ita, guest house ne, akwai ƴan'sanda biyu dake tsaron gidan, da kuma ƴar aiki guda ɗaya, hakan zai nuna maka babban mutun ne sosai, da alama kuma ya aminta da waƴan da suke cikin gidan ne. Ciki suka shige, tana biye da shi babu musu kamar wata rakumi da akala. Cikin wani tampatsetsen bedroom ya shiga da ita, sai kallon hanya take yi, duk in da suka bi ta gani kuma ta haddace, suna shiga ya fara cire kayan jikinsa, ya rage daga shi sai shot kafin ya shiga cikin toilet dan yin haɗe haɗensa na tsafin nasa, tana zaune tana tunanin me mafita, me yakamata ta yi? Can wani idea ya faɗo mata na wani labari da ta taɓa cin karo da shi a Media, wata ta yi wa mijinta, shiru ta yi tana jiran fitowarsa, tsabar ma mugunta ya shirya mata sai bai ce ta yi wanka ba, sauri sauri kawai yake yi ya aiwatar da abin da yake so, saman gado ya hau tare da cire shot nasa yana faɗin ta zo mana, tsirara haihuwar uwasa ya yi a gabanta, yau shi ne karo na biyu da ta ga wannan tashin hankali, amma ta daure ta danne bata nuna mishi zata tirje ba, cikin dakiyar zuciya ta ce "Ina son shan ruwa mai sanyi da fruits kafin mu yi komai, kai baka ga hanyar da muka sha bane? Ai ina jin yunwa". Ɗan kwaɓe fuska ya yi kafin ya ɗauko waya ya kira mai aiki a kan ta kawo mata, "Yauwa Alhaji bana son a yanka mini fruits ɗin dan ina da kyankyani sosai, ni zan yanka da kai'na dan bana son datti". Dariya ya yi yana faɗin "Ai dama baki yi kalar datti ba". Murmushi dole ita ma ta yi tana mai duba time a wayar Adiva dake hannunta, shi kam ko a jikinsa, dan yasan sai Hjy ta saye imaninsu ta yadda basu yi wa mutun musu kafin ta fara ɗaurasu a network, Jehan kuma akwai basira, ta fahimci hakan ne shiyasa ma bata nuna musu ita ta fita daga tarkonsu ba, tana ciki ba zata yi musu musu ba ta nuna. Ba kunya ba tsoron Allah mutumin nan yana kwance tsirara har mai aikin nan nasa ta kawo mishi abin da ya bukata, da alama shi da mai aikin ma suna sheke ayarsu tun da bai rufe jikinsa ba har ta shigo. Saman bedside drawer ta ɗaura tray ɗin tare da yi wa Jehan sannu ta juya ta fita, fruits ne irinsu Apple ayaba lemu da sauransu, sai wata ƴar madaidaiciyar wuƙa mai kaifin bala'i tare da robar ruwa mai sanyi da glass cup kwara ɗaya a saman tray ɗin. Natowa Jehan ɗin ta yi tare da fara ɗaukar ruwa ta yi bismillahi ta buɗe robar ta sha, dai'dai lokacin kuma a ka kira shi a waya, da yake wayar tana kusa da shi sai ya ɗaukota yana faɗin "Bari ma na sanyata a airplane mode dan kada a takura mana da kiraye kiraye muna tsaka da jin daɗin mu, mutane basu san lokacin da ya dace su kira mutun ba, su dai idan bukatarsu ya taso shikenan........" Bai kai karshen maganar ba ya ji wani bakin azaba ya ziyarcesa, da iya karfinta ta sanya wukar da aka kawo mata dan yanka fruits ta yanke mishi gabansa wato bananarsa, daga tushensa ta yanke ba ma sama sama ba. Tana yankewa ta yi wurgi da wukar tare da ɗaukar wayarta ta fisge nashi dake hannunsa ma ta haɗa dukka biyu ta nufi waje da uban hudu,. Ihu ya kurma tare yunkurawa, amma ya kasa tashi, nan take jini ya fara gangarowa, ihu ya cigaba da waje muryar nan tasa yana kurmawa. Jin ihunsa yasa ƴan'sandan dake bakin gate suka nufo ciki da gudu, ita ma mai aikin da gudu ta nufo ɗakin, laɓewa bayan wani ɗaki Jehan ɗin ta yi, tana ganin ƴar'sandan suka wuce zuwa ɗakin nasa, bayan sun wuce ne ta fito a guje gabaɗaya jikinta kermar tsoro yake yi, gudun cetar rai zata yi, fitowar da ta yi kuma ashe mai aiki ta ganta, da gudu ta kira ƴan'sandan tana gaya musu gata can gata can, kafin su zo ma tuni ta isa bakin gate, sai dai gate ɗin a rufe yake da kwaɗo, tsabar bala'in tashin hankali da take ciki, bata san lokacin da ta kama gate ɗin ta haye ta dira waje ba, gabaɗaya wayoyin saman ginin sun ji mata ciwo, amma bala'in da take ciki yafi wannan, tasan idan suka kamata a cikin wannan gida to sai dai gawarta ya fita, ta san wadda ta yi wa wannan aika aikan ba ƙaramin mutun bane, ƴaƴan Farooq ne uwa ɗaya Uba ɗaya, idan baku manta Farooq wanda ya yi kokarin lalata rayuwar Hanan a Katsina na ba, to yayansa ne wannan alhajin..........Dama idan bala'i ta yi balai zaka yi abin da ba ka taɓa zaton zaka yi shi ba, yanzu dai bala'i tasa Jehan haura saman gate, dama haka ne, in kaga bala'i ba abin da ba zaka iya yi ba, san da zaka yi ma, ba zaka sani ba, sai daga baya bayan ka samu natsuwa zaka yi ta mamakin ya akayi kayi abu kaza? Allah dai ya raba mu da bala'i. A guje ƴan'sandan suka buɗe gate ɗin suka rufa mata baya, a haukace ta hau saman hanya tana gudu ga kanta babu ɗan kwali, saura kaɗan wata danƙareriyar mota ta takata, har ta ɗan bugeta ta faɗi kasa ma, da alama ta ɗan ji ciwo, dan ma dai Allah yasa driver motar ɗan hannu ne, ya iya tuki sosai, shiyasa ya yi nasarar taka birki a cikin wannan yanayi, ganin ta faɗi kasa ne yasa matukin motar ya fito da sauri ya nufo ta, dan ya ganta karamar yarinya ce, ba wata babbar mata bace. Zaro dara daran brawn eyes nasa ya yi yana faɗin "Areef kazo ka kallah ta ɗan ji ciwo fa, ka zo ka dubata, kuma ka ga wasu ne suke binta". Yana zaune a gaban mota, shi dai burinsa azo a kai shi wajen heartbeat yau ya ganta su gaisa, amma Aseef zai ɓata musu lokaci, tun da bata ji ciwo ba sosai ba Allah ya tsare basu bugeta sosai ba, ba sai ya wuce su tafi ba, me na wani kiran shi ya zo ya ganta. Dama sun ce da Akila suna zuwa ne, yau za su je su gaisa da Ammie, ita kuma Akila ta gaisa da Areef, shi ne suka shirya tsab za su je. Ganin sai kiransa Aseef ɗin yake yi ne yasa shi fitowa yana jan tsaki, Aseef ya ɓata mishi rai, dai'dai lokacin kuma ƴan'sandan suka iso wajen, da yake unguwar na manya ne, kun san babu jama'a, kowa yana cikin gida.......... Yaya makomar wannan lamari zai kasance? Anya alhajin nan zai rayu kuwa? Shin Jehan ta kyauta kuwa? Aseef, Areef zasu taimaka mata kuwa? Alhajin zai kyaleta kuwa? Ga kuma kaninsa Farooq dama yana nemanta, Jehan ta tara maki ta ko'ina, Ya makomarsu Adiva? Shin Lion zai kama wadda ya je nema kuwa? To bari dai na barku haka sai mun haɗu on Monday idan mai dukka ya kaimu ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ *Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta* E41-42💋 Ganin sai kiransa Aseef ɗin yake yi ne yasa shi fitowa yana jan tsaki, Aseef ya ɓata mishi rai, dai'dai lokacin kuma ƴan'sandan suka iso wajen, da yake unguwar na manya ne, kun san babu jama'a, kowa yana cikin gida, kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa yana faɗin "Me yasa kake ta kirana ne wai?". Ita kuma buguwar da ta yi nan ne yasa ta ke ganin jiri jiri bata wani jin me suke faɗe sosai. Miƙewa ta yi tana wani tangal tangal kamar zata faɗi, ta gaji over, ga uban gudu da ta sha, baiwar Allah ga dirar da ta yi ta saman gate kafarta na ciwo, bugu da kari duk ta kukkuje jikinta da wayar dake saman gate ɗin, ta ji ciwo,. A sugwane Aseef ya ce "Areef wlh she is resembling uncle face, they look alike, i think sister Rimsha ce, daughter uncle ce ita ma, kalli face nata ka gani". Hararar shi Areef ɗin ya yi yana faɗin "Zaka wuce mu tafi ne ko kana gaya mini she look like Uncle,? Wai ka manta nan kasarsu uncle ne? To dole akwai masu kama da shi over, so please let's go ina son mu dawo na kira Lion dan nayi magana da my Rimsha, ina missing nata over, tun safe bamu yi magana ba fa". Katse su ƴan'sandan da suka iso yanzu suka yi da cewa "Ke wuce mu tafi". Maganar da suka yi kuma yasa Areef da Aseef ɗin gabaɗaya juyo da kallonsu a kansu, da kallo ɗaya Areef ya yi musu ya fahimci marasa gaskiya ne, shi ma Aseef a nasa tunanin ya san dole wani abin zasu yi mata, duba kuma da irin shigar da yake jikinta, wata kila fyaɗe suka yi kokarin yi mata ta ki yarda, shi ne ta gudu suka bita, a tunanin Aseef kenan, shi kam Areef kai tsaye yasan basu da gaskiya. Kokarin kamata suka yi Aseef ya ce ba zai yi wu ba, wlh babu wanda ya isa ya kamata, dan ta yi mishi kama da uncle Hosain sosai, ko da ba ƴar uwarsa bace, to dole zai taimaka mata saboda albarkacin kamar da fuskarta ta yi da shi, dan haka sai ya tsaya tsayin daka a kan lallai ba zasu tafi da ita ba. Jingina da jikin motar Areef ya koma ya yi, tare da goya hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa yana kallon karfi hali irin na Aseef, shi ya dage a dole lallai sai ya tafi da ita, yarinyar da bai san ta ba, kawai daga ganin wasu sun bi yo ta a cikin daren nan ya wani tsaya shi dole sai ya taimaketa, ga shi ba shi da karfin ko na ɗaga kwalin sweet, su kuma ƴan'sandan da suka biyota sun ce lallai sai sun tafi da ita, domin kuwa ta aikata laifin da dole su kasheta. Wani dogon tsaki Areef ɗin ya ja Aseef yana ɓata mashi lokaci, ya ƙosa ya koma gida ya kalli ya Rimsha ta wuni yau su yi video call, yana kewarta sosai da sosai. Yana tsaka da tunani bai ankara ba sai jin wani kara na sauƙar mari mai sauti ya yi. Cikin sauri ya ɗago kai tare da kai kallonsa kansu Aseef ɗin, ɗaya daga cikin ƴan'sandan ne ya wanke Aseef da wani mahaukacin mari, da sauri Aseef ɗin ya dafe kuncinsa da hannunsa, idanunsa sun yi jajawur domin ba karya ya maru sosai. Kan ka ce me ɗayan ya sake kwashe kafafunsa a in da ya zube kasa a waje, nan fa suka yi yunkurin yi mashi ɗan iskan duka domin su tafi da ita. Wani irin mugun bakin ɓacin rai Areef ya ji wadda tasa bai ma san lokacin da ya raba jikinsa da jikin motar ba ya yi kansu a zafafe. Cikin zafin nama ya hau jibgansu tare da watsi da su kamar an aikosa, nan take ya koma ainahin waye shi, wato ya koma jam'in C.I.A cikakkun jarumai masu bada rayukansu akan al'ummarsu, kafin ma su shiga aikin sai sun sanya hannu akan sun sayar da rayukansu, ba su tsoron a mutu ko ayi rai, jininsu a tafashe yake a ko da yaushe, sun sami horo iya horo na wuce misali. Rai a matukar ɓace ya yage rigar jikinsa domin tana takura mashi wajen jibgarsu yadda ya kamata, haka ya cigaba da ba su a jikinsu. Shi kuma Aseef sarkin tausayi, bai ma damu da wani hali Areef ɗin yake ciki ba, bayan kuma shi ya jangwalo faɗar, miƙe wa ya yi abinsa ya riƙo hannunta yana yi mata sannu. Duk ilahirin jikinta sai kerma yake yi, dama a tsorace take, ganin suna faɗa kuma yasa ta kara tsorata sosai, ta fara kuka. Hannunta ya ja suka karisa wajen motarsu yana faɗin "Kada ki ji komai tsab Areef ɗina zai yi masu dukan mutuwa, ke dai yanzu shiga mota bari ya gama jibgansu ya zo mu maida ke gidanku..." Bai kai karshen maganar ba ya ga an wurgo mutun kusa da shi, ai kuwa a guje shima ya shige cikin mota yana faɗin "Ya Subhanallah, Allah ka rufamin asiri da irin wannan duka na Areef, ka kama mutane sai jibga kake yi kamar an aiko ka, ni dai ina daga ciki, ka tabbatar ka ba su jikinsu sosai kafin ka zo mu wuce, amma fa ka yi sauri dan ina kewar My Rimsha wlh, zan je na kirata video call". Da yake ita Jehan ɗin ta ɗan bugu kuma ga tashin hankali da take ci, sai bata ma sauraron abin da suke faɗe, ta dafe kanta da hannayenta dukka biyu, ban da wash babu wani abin da take furtawa, kan nata ne dama ya bugu da jikin motar tasu. Lilis Areef ya yi wa ƴan'sandan kafin ya taho ya shiga cikin motar, a kujerar gaba ya zauna yana ɗan dafe wajen ciwonsa, dan ɗaga hannunsa da ya yi ta yin nan ya ɗan ji zafin ciwon ba kaɗan ba. Yana shiga Aseef ya ja motar suka koma gida, da yake ma basu da nisa da gidan, daga in da suke suna hangen gidan, dan fitowarsu kenan suka ci karo da ita. Sai da suka shiga cikin gida kuma Aseef ɗin ya ce "Areef ai da mun fara mayar da ita gidansu kafin mu dawo ko?" Fita daga cikin motar Areef ɗin ya yi ba tare da ya yi magana ba, burinsa kawai ya karisa cikin gida ya shafa maganinsa ya kuma sha na shansa dan ya fama ciwon nasa. Dawo da kallonsa kanta ya yi, har lokacin tana dafe da kanta ta yi shiru da alama bata dawo dai'dai ba, "Ni ba zan ji daɗin kai ki gida ni kaɗai ba, amma ki zo mu shiga ciki, idan Areef ya ɗan ji sauki sai mu kai ki gida, daga nan dai zuwa 9 zai ji dai'dai In Sha Allah, yanzu ki fito mu je ciki". Shiru bata amsa mishi ba, kada ku manta da turanci yake magana. Ganin bata amsa bane yasa ya fito tare da buɗe gidan bayan ya riƙo hannunta zuwa cikin gida, da kyar ta iya fitowa daga cikin motar, ba musu ta bi shi kamar wasu yaya da kanwa, kai tsaye ɗakin da su Imran suka baro a sama ya kai ta, da farko ya so kaita ɗakin Rimsha, sai kuma ya tuna Rimsha daban ce basu haɗa ta da kowa, dan haka sai ya kaita tsohon ɗakin Imran da suka fara zama. A bakin gado ya zaunar da ita, sai kallonta yake yi, shi dai ko ma yaya yasan wannan dai tabbas tana da alaƙa da uncle Hosain ɗinsa, dan sun yi kama over, amma dai bari Areef ya samu ya dawo dai'dai shi ma ya ganta dole zai ga kamannin, sai tunane tunane yake yi, bai ma san lokacin da ta kwanta ba sai dai ɗago kai ya yi ya ganta tana sharar barcin wahala, ɗago dara daran brawn eyes nasa ya yi ya sauƙesu a kan Ac dake ɗakin, rage mata gudun ya yi kafin ya rufa mata bargo zuwa cikinta ya juya ya fita zuwa wajen Areef dan ya ga a wani hali yake ciki. Ɗakin Lion ya nufa, Areef ɗin na toilet yana wanka, ga A box a saman bedside drawer ya ajiye, da alama ya yi dressing na ciwon nasa ne kafin ya shiga wanka, saman bed ya haye tare da jawo wayarsa dan ya kira Lion ya zuba mishi shagwaɓa kaɗan, ya takura mishi. Har zai fara kiran number kuma sai ya tuna Heartbeat na can tana jiran zuwansu, dan haka sai ya fasa kiran Lion ɗin ya kirata dan ya sanar da ita sai gobe da safe zasu zo, tun da Areef ya ɗan ji ciwo. Bugu ɗaya ta ɗauka cikin zumuɗi a shagwaɓe ta fara magana "Hello my shagwaɓati kun iso ne?" Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, yadda ta yi maganar ta tafi da shi ba kaɗan ba, "Heartbeat ki yi hakuri ba zamu sami damar zuwa yau ba sai gobe". Kuka ta saka mishi a kan lallai ita wlh ba zata yarda ba, in dai yana son farincikinta to yazo yanzun nan, shiru ya yi yana sauraron shagwaɓar da take zuba mishi har sai da ta kai aya, sannan ya fara magana a nutse "Heartbeat muna hanyar zuwa fa muka sami accident, mun buge wata ƴarinya ce wadda tasa dole muka juyo zuwa gida, so please ki yi hakuri zuwa gobe kinji ko my rigimati?". Zubur ta miƙe daga kwanciyar da take tana dafe kirji tare da zaro idanu waje, "Amma dai baku ji ciwo bako?" Ta tambaya hankali a tashe, "Calm down My heartbeat, babu abin da ya same mu, Allah ya tsare yarinyar ce kawai muka ɗan jiwa ciwo, ita ma ba sosai bane, shi ne muka dawo gida dan mu dubata". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Ya yarinyar take to? Babban mata ce ko dai karama?". Da yake shi bai san kishin mata ya yake ba, sai ya zauna ya zayyana mata yadda ya ga Jehan ɗin tas, budurwa ce kamar ita ga kuma irin kayan da ta sanya, kyakkyawace sosai mai kama da uncle ɗinsa, da sauransu. Kuka ta sa mishi tana faɗin Wlh sun ɓata kada ya sake kiranta tun da har da riƙe irin kayan da yarinyar ta saka, kenan ma wato ya yi ta kallon yarinyar ko? To wlh ba zata yafe mishi kallon wata da ya yi ba, tana kuka tana surutai, shi kam yau yaga bala'i, dan bai san mata haka suke da kishi ba, dafe kansa ya yi tare da fara rarrashinta dan bashi da mafita. Kin yarda ta yi ta katse kiranta tana kuka hawaye bibbiyu, sake kiran nata ya yi, kin ɗagawa ta yi, ta yi fushi da shi, tamkar zai yi kuka, duk ta rikita shi, ba zai iya jurar tashin hankalinta ko ɓacin ranta ba, zai iya ɗaukar komai amma banda wannan. Cigaba da kiranta ya yi, amma taki ɗauka, sai sharɓar kuka take yi kamar ba gobe, ɗauko wayar Areef ya yi ya kirata da shi, call na farko bata ɗauka ba saboda taga new number ne, sai a karo na biyu ta ɗauka, ban da shessheƙar kuka babu abin da yake jiyowa daga cikin wayar, cikin sanyin murya ya fara magana "Am really sorry my heartbeat, you knew ni ba zan taɓa kula kowa ba sai ke, bani da wani interest a kan wata mace sai ke, please ba zan iya jure kukan ki ba, zaki haifar mini da babbar matsala a cikin zuciyata, ki dai'na dan Allah". Kun sani na sani turawa basu yin mata biyu, mace ɗaya ce, sai dai masu bin matan banza zaki samesu da wata ta waje, amma matar aure ɗaya ce, kawai rigima ce irin ta heartbeat, da kuma tana tunanin zai iya canzata ya auri wata, tun da dama kunga tana tantama a kan son da yake yi mata, tana ganin kamar bata kai ya so taɓa, bata da wani abin da ya kai ya so ta domin shi, da sun yi aure ba zata damu ba dan tasan ba kishiya, yanzu kuwa zata iya damuwa dan a girlfriend nasa take, yana iya canzawa. Shiru ta dai'na kukan, amma bata yi mishi magana ba, "My rigimati zaki sha chocolate na kawo miki yanzu?". Ya faɗa a shagwaɓe, shiru taki amsa mishi, "Muyi Video call?" Nan ma shiru ta yi bata amsa ba, juya kiran ya yi zuwa video call. Sai da kiran ya kusa ya katsewa ta ɗauka, tana kwance ta tada kai da pillow tana wani turo baki tare da kumbura kumatu. "My rigimati, kaga ɗan bakinta a wajen sai rigima, yanzu dai sai da kika yi mini asarar hawayena ko? Ba komai zan rama ne, bari na zo da safe sai na matse ɗan bakin nan, ki cigaba da turo mini shi". Shiru ta ki kula shi kuma taki ɗagowa su haɗa idanu. "Haba mana my rigimati, wai ba zaki ɗago ki kalle ni ba? Haba mana ƴar kyakkyawata, ƴar babyna, kaga hancinta kamar karas idanu kamar madara masu kyan gaske, ga wani ɗan siririn saje a gefe zai yi mini daɗin wasa da shi". Kukan shagwaɓa ta saka mishi tana faɗin "Ni Allah ka bari bana so". Narke mata murya ya yi tamkar zai yi kuka ya ce "Ni gaskiya ba zan bari ba, ni da kayana dan na yaba sai ya zama wani abin,? Bakiga ma da kika yi maganar nan ba yadda ɗan bakin nan ya yi mini kyau kamar in jawo ki in tsotse kayana kamar sweet". Hararar wasa ta wurga mishi ta kasan idanu, tana murmushi kasa kasa, ya iya magana idan ya yi niyar yi, idan kuma baya jin yin maganar sai ya yi ta binta da okey or not, amma gwani ne wajen iya zuba kalaman soyayya, ya san duk ta yadda zai bi ya kwantar mata da hankali idan ta ɓata rai. "Kin san me nake tunani My heartbeat?" Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a bata sani ba, "Ranar da na mallake ki ko? Akwai wani abu". Kawar mishi da zancen ta yi da cewa "Ina Areef?" Dan tasan halinsa sarai yanzu zai kawo mata wasu maganganun da zasu sakata jin kunya, shi kuma hakan ba laifi bane a wajensa, bata ganin laifinsa dan ya yi ire-iren wannan magana, saboda tasan halin Turawa ne hakan, tana yi mishi uzuri sannan tana ƙoƙarin koya mishi dai'na yin hakan tana kuma ƙoƙarin canza mishi topic na magana idan ya ɗauko zancen, ta san yanzu ba ƙaramin aikinsa bane ya ce mata idan ya malllaketa, ranar da aka kawota a gaban kowa zai yi mata kaza zai yi mata kaza su kiss da sauruansu, ita kuma kunyar irin maganganun take ji sosai shiyasa bata so. "Areef yana toilet yana wanka". Bawan Allah da yake shi wankansa ba irin na kowa bane, dole ya bi komai a hankali saboda ciwonsa yasa yake jimawa a toilet idan ya shiga. "Tom gaskiya ya kamata nayi hira da shi ko ta wayane yau tun da baku sami damar zuwa ba". Okey ya amsa mata da shi, "To ɗago ki kalleni". Make mishi kafaɗa ta yi alamar a'a b zata ɗago ba, "Please mana my heartbeat". Ya faɗa a tsananin shagwaɓe, "To ka rufe idanunka idan kana son ganin na ɗago kai". Ba musu ya rufe idanun nasa, dama a yunwace da son kallon face nasa take, dan haka sai ta ɗago ta zuba mishi idanu tana kallon face nasa kamar ta kai hannu ta shafa, shi kuma ya datse idanunsa gam dan bin abin da take so, saboda farincikinta. "My shagwaɓati ka kara kyau sosai, Allah har wani kyalli face naka take yi". Waro dara daran brawn eyes nasa ya yi kai tsaye sai cikin nata, lokacin guda suka sakarwa da juna wani kayatatcen murmushi mai sanya zuciyoyin masoya nishaɗi ya kuma mantar da su a wani duniya suke, "I really love you my wife to be In Sha Allah". Ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya, wani irin kallon soyayya ta wurga mishi mai ɗan ɗauke da harara kaɗan irin na masoya tana faɗin "My shagwaɓati ina ganin daga mum, dad, Triplets a masu sonka sai ni,". Cikin zoyala ya ce "Au dama baki fi Triplets sona ba?". Gyaɗa mishi kai ta yi tana faɗin "E mana, yanzu idan nace maka nafi Triplets naka sonka zaka yarda?" Girgiza mata kai ya yi alamar a'a ba zai yarda ba, dan duk wanda zai so shi, to fa wlh yazo a bayansu Lion, "To ka gani ai, ba yadda za'ayi in yi maka karya, gaskiya na gaya maka". Zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda take motsa lips nata da suke pink color, ga shi ta sanya lips balm, sai suka kara wani kyalli sosai, ba ƙaramin ɗaukar hankalinsa suka yi ba, yana bala'in son ya yi kissing nata. "Me kake kallon haka kuma?" Nisawa ya yi kafin ya ce "Babu komai kawai dai ina son na yi miki kiss ne". Turo mishi ɗan bakin nata ta yi tana faɗin "To Bismillah". Wani irin dogon numfashi yaja tare da saukewa a hankali kafin ya lumshe dara daran idanunsa, shi kaɗai yasan me yake ji, gyara kwanciyarsa ya yi tare da rungumo pillow yana faɗin "Ni kike yi wa kwalele ko? Zaki sani bari na riƙe ki". Yadda ya yi maganar tamkar baya son motsa laɓɓansa, can kasa kasa ya yi ta, murmushi ta yi yana ce mishi sorry ba zata kara ba, shiru ya yi bai tankata ba, dan ta jefa shi cikin yanayi, haka suka cigaba da hirarsu cike da nishaɗi suna farantawa juna rai, sai dai baya wani yin magana sosai, daga yes sai no yake binta da shi. A ɓangaren Lion kuwa, wato Abuja. A razane ta farka daga barcin da take yi tana kurma ihu, mummunar mafarki ta yi wai ga kartin jiya sun dawo sun kamata, dirowa kasa ta yi daga samar sofar, tare da nufar gadonsa, baya nan, sake tsorata ta yi, a guje ta watsa ta nufi waje, sai dukan uku uku kirjinta yake yi, ya jima da farkawa daga barci har ya yi wasu uzurorin gabansa. Palo ta nufa, a dai'dai tsakiyar benen suka yi karo da shi ta buga kanta a tsayayyen faffaɗar kirjin nan nasa, baya baya ta yi tana kara kurma ihu, duk a tsananin firgice take, zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda take firgicen ga idanunta a datse, mamaki ma yake wai me ya sameta ne haka? Ita da ya bari take zuba barci cikin kwanciyar hankali, anya kanta ɗaya kuwa? Ya tambayi kansa, dama zai haura sama ne ya je ya yi alwala azahar ta yi, ya yi sallah. Raɓawa gefenta ya yi yana mai wucewa sama abinsa, har gobe ɗaukar ƙaramar yarinya yake yi mata, bai taɓa ɗaukarta a mace ba, shiyasa baya damuwa sosai yake taɓa ta kamar jiya kenan da ya ɗauketa. Da gudu ta bi bayansa dan a tsorace take, toilet ɗin daddy ya nufa, alwala ya ɗauro tare da fitowa, ga mamakinsa sai yaga ta shinfiɗa mishi dadduma, ya ji daɗin hakan a cikin zuciya, amma a fili kuma shiru, ba wata alamar da ya nuna hakan. Bayan sun yi sallar baki ɗayansu, fita ya yi zuwa palo ya barota a cikin ɗakin tana askar, har zai wuce zuwa palon kasa sai kuma ya ce bari ya duba sauran ɗakunan dake cikin gidan, maybe akwai abin da zata amfane shi a bincikensa. Ɗakin mum ya fara shiga, ƴan dube dube ya yi, babu wani abin tuhuma, har zai fita sai ya tuna bai buɗe drawer mirror ba, dawowa ya yi ya buɗe, hotunane a cike a ciki, tun daga kan iyayen Naurat, iyayen Dr Salman har zuwa Rimsha wadda ta kasance Auta a cikin family'n Dr Salman ɗin, duk cikinsu ita ce karama, autar kowa ce, idan baku manta ba, daddynta yana bibiyar rayuwar ƴan uwansa sosai har yana taimaka musu, to a nanne ya samo hotunansu da su da ƴaƴansu, su Imran dukka, su basu san nashi ƴaƴan ba, amma shi ya san su bakiɗaya. Bashi da lokacin tsayawa kallon hutuna, dan haka sai ya kwashesu a kan idan ya koma Kaduna ya natsu zai duba, da haka ya fita zuwa ɗakin dake kusa dana mum ɗin, wanda kuma ya kasance nasu Rimshan ne kenan. Ya sha ruwan mamakin ganin uban zanen face nasa a cikin duk wata drawer da ya buɗe a cikin ɗakin, ɗaukar zane ɗaya ya yi yana dubawa, sak shi aka zana har da sanya mishi blue color a idanunsa ta yi kamar blue eyes, tunawa ya yi da sunanta dake saman kirjinta, to me hakan yake nufi kenan? Ya tambayi kansa, dan shi bai yarda Rimsha ta san soyayya ba, ƴar baby yake ɗaukarta wadda bata wuce goyo wajen iyayenta ba, bai ma ɗauka ita ce ta yi waƴan nan zane ba, dan yana ganin kamar bata kai iya zane har haka ba, babban abin kuma daya ɗaure mishi kai shi ne dukka zanen sun jima, alamu sun nuna ba yanzu aka yi su ba, to ya akayi suka san face nasa kafin ya zo? Ya sake tambayarsa kansa da kansa, shiru ya yi yana tunanin shin waye ne ma ya yi zanukan nan bakiɗaya?. Drawer kayanta da ya buɗe ne ya ci karo da wata katuwar cardboard paper fara tas, an nannaɗeta da kyau sosai, an yi mata ajiya na musamman. Zarota ya yi tare da buɗewa, zanen face nasan ne dai a jiki, sai dai kuma a jikin wannan cardboard paper ya sami amsa a kan wacece ta yi zanen, dan kuwa bayan ta zana face nasa da girma, sai ta zana nata face ɗin karami a kasa dai'dai wajen wuyarsa ta gefen dama, daga gefen hagu kuma ta yi rubutu da biro da manyan baki kamar haka GAR MY PLEASURE MY WORLD, I REALLY LIKE TO SEE YOUR FACE, AM SURE, SOON I WILL SEE YOU IN SHA ALLAH. Ba karamin mugu mugun kyau handwriting nata ya yi mishi ba, ƴar karama da ita sai good handwriting kamar me, shi bai wani ɗauki zancen da ke rubuce da mahimmanci ba, dan ba sanin me soyayya ya yi ba. Calmly ya motsa kyawawan laɓɓansa ya furta "Who are you?". Dum dum gabanta ya bada bugu domin bata yi zaton ya san da shigowarsa ba, tun ɗazun ta shigo ta tsaya tana kallonsa, tsoro yasa da ta gama askar ta biyo bayansa, yana shigowa ba jimawa ta shigo, bata san cewa tun shigowarta ya san da ita ba. "How are you assuming my face before seeing me face to face?" Ya kai karshen maganar tare da juyowa gareta hannunsa na riƙe da paper, har ga Allah bai taɓa shan ruwan mamaki irin na yau ba, ya za'ayi bata taɓa kallon shi ba ta zauna ta kawata shi a ranta, ta kuma zana shi, sannan kuma zanen ya fita sak shi? Ko da kana kallon abu da wuya ka zana shi ya fita sak yadda yake a zahiri, amma ita bata na kallah bane ta zana har haka? Abin da ban mamaki, kuma abin ya tsaya mishi a ransa ba kaɗan ba, ya ji har can kasar zuciyarsa, ya aka yi hakan ta faru? Da ma ace ta taɓa ganin shi ne koda sau ɗaya to da sauki, amma ko da sunan wasa bata taɓa ganin face nasa ba, kawai dai tana kawata wa ne a ranta yadda zai iya kasancewa a zahiri, sai kuma ga shi sak har da sajensa bata bari ba, gashin gera, kai komai tamkar camera ce ta ɗauke shi ba zane ba, ba karya ya fita sak tamkar ka kira shi ya amsa. Tsareta da waƴan nan dara daran blue eyes ɗin nasa ya yi yana kare mata kallo yana jiran amsa, har cikin ransa yau ta yi mushi mugun kyau, ga razananniyar face ɗin nan nata yanzu ma a tsorace take, bai san me yasa ba idan ta tsorata take yi mishi bala'in kyau, baya son matsorata, a kanta face na matsorata yake yi mishi kyau, yanzu ma ba karya ta tsorata da jin tambayar da ya yi mata, dama ga tsoron gidan da take ji, dai suka haɗe mata waje guda, ta ɗan tsuke ɗan bakin nan nata tana ɗan zaro idanu, sai dai kasa take kallo taki yarda su haɗa idanu ko ta kalli fuskarsa. Takowa ya yi ya nufota, dama tana ta kusa da bangon ɗakin ne ta wajen kofar shigowa, ganin shi yana nufota ne yasa murya na rawa ta ce "Ni wlh ban san ya akayi na iya zana ka ba, kawai ina kawata yadda zaka kasance a zahiri ne yasa nake zane best on yadda na kawata kyan naka, bayan haka ban san komai ba wlh"., Bai tsaya daga tinkarota da yake yi ba, saboda bai gamsu da zancenta ba, a cewarsa ba ta yanda za'ayi hakan ya yi wu, gara ma da ace babbar mace ce za'a iya cewa ta girma ta yi hankalin da zata iya kawata abin da yake cikin face mask and black glass, amma yarinya kamar wannan da bata wuce a rinƙa goyonta ba, yaushe ma ta san mai kyau da mara kyau da har zata iya kawata shi?. (E lallai Romeo ya raina Rimsha, wai yarinyar da bata wuce a goya ba?🤔 Lallai bai san mukam a Naija kamar Rimshan nan tsab za'a yi mata aure ta zauna bane?) Ganin ya matso daf da ita ne yasa ta ja baya ta mannu da bangon, zuciyarta sai dukan uku uku yake yi tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje, sai karanto duk wani addu'an da ya zo bakinta take yi, idan muka leƙa nashi ɓangaren, har can kasar zuciyarsa wlh zanen ya yi matukar burgesa dan ya fita ne ba karya, har blue eyes ɗin sai da ta sanya blue color, nace muku kamar camera aka sanya aka ɗauke shi kawai, so ya ji daɗi ba kaɗan ba, amma yana son ta amsa mishi a ina ta san shi kafin ta gan shi a zahiri. Daf da ita sosai ya matso har tana iya jiyo sautin numfashinsa, shi baya jiyo nata dan tana kasa da shi ne, ita kuma ya rankwafo mata da kansa ne, dole zata ji yo numfashinsa,. "Ba zaki gaya mini gaskiya ba?" Zazzaƙar muryarsa ya sake dakan dodan kunnenta. Ɗan ɗago kai ta yi tana kallon sarkar dake kirjinsa, ɗayar hannunsa riƙe da hotunan da ya kwaso a ɗakin mum, ɗayan kuma riƙe da cardboard paper zanen, haɗe cardboard paper da hotunan ya yi a hannu guda ya riƙe, ya sanya ɗayar hannun nasa ya ruƙo sarkar dake wuyarta yana ganin chain ɗin, ya kusa yin kama da nasu, amma kamar yadda Aseef ya gaya mata da akwai banbanci sosai haka ne, nata round ne nasu Heart, nata akwai mix nasu zallar zinari ne. Sake sarkar ya yi tare da ɗago haɓarta suna fuskantar juna, runtse idanunta ta yi gam, "Zaki bani amsa ne ko sai na karya ki?" Yana magana yana karewa face nata kallo, a hankali ta motsa laɓɓanta ta furta "Wlh yaya Saif ni ban san ya akayi ba, kawai dai idan na zauna ina tunanin yadda kyanka zai iya kasancewa ne a zahiri, shi ne yasa nake zanawa, bayan haka wlh babu wani abin dana sani, please kada ka dakeni, zan ƙona dukka zanen in baka so". Shiru ya zubawa lips nata idanu, yana kallon yadda take motsasu har ta kai ƙarshen maganar nata. "Ya za'ayi ki zanani tsab yadda nake a zahiri harta yawan sajen dake fuskata sai da kika zana kuma kice a iya tunani kika sanni?". Ya yi maganar tare da kara rage tsawonsa, ya ɗan kara rankwafowa kanta kaɗan. "Wlh yaya Saif iya gaskiya kenan na gaya maka, bayan haka babu wani abin, kuma duk wanda zai gaya maka wani abu bayan haka to karya ce, ni kai'na idan na gaya maka wani abu bayan haka to wlh karya nayi maka". "Open your eyes". Ya faɗa a sanyaye can kasa kasa, ba musu ta waro dara daran sleeping eyes ɗin nata, kai tsaye sai cikin idanunsa, da sauri ta kawar da kallonta zuwa saman faffaɗar kirjinsa, sakin haɓar tata ya yi yana mai buɗe zanen ya sake gani, har lokacin suna nan daf da juna kamar zata shige jikinsa. Zubawa zanen face nata dake jikin paper idanu ya yi, ita kanta sak kanta ta zana, harta sleeping eyes nata bata bari ba, tun daga jiya zuwa yau da ya kare mata kallo, babu wani abin da yake mishi kyau a tattare da ita sama da wannan idanun nata, suna da bala'in kyau over, gasu farare tas, sun yi mishi kyau sosai har ya ji yana son ajiye hotonsu a wayarsa, sai dai bai nuna hakan a fili ba. Ɗan baya ya ja yana ƙoƙarin barin wajen zazzakar muryarta ta katse shi da cewa "Yaya Saif in kona zanen dukka?". Juyowa ya yi da kallonsa a kanta "Time da kika zana kin gaya mini ne?". Girgiza kai ta yi tana kallo ta bayansa, Malika ce ta bayyana a wajen, kara zaro dara daran fararen sleeping natan nan ta yi, hakan ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, tana mamaki ne na ganin Malika, shi kuma hakan ya yi mishi kyau sosai dan kuwa ya karawa idanun nata kyau, juyawa ya yi ya bar wajen ya nufi waje, da sauri ta bi bayansa dan ba zata biyewa Malika ba wasu karti su zo su kamata, murmushi Malika ta yi, dan bata ga laifinta ba, irin yadda ake farautar rayuwar nan nata ai dole ta rinƙa binshi duk in da zai je, idan ba haka ba ta jita a in da ba'a dawowa. Cikin trolleynsa ya je ya sanya hotunan da kuma zanen nata, kafin ya zauna a gefen bed nasa ya kira daddynsa a waya, lokacin da ta shigo yana waya da daddy, "Jeki ki kawo mini fruits". Ya faɗa tare da cigaba da magana da daddyn nasa. "Kai da waye Romeo? Na ji kamar mace ka ambata". Cewar daddyn, kai tsaye ya ce mishi "Ni da sister su Aseef ne". (Wato shi ba sister shi bace kenan? Kai Romeo duniya ne wlh). "Who is Aseef?" Da yake idan baku manta ba shi daddy bai san sun musulunta ba, so bai san Michael ya koma Aseef, James ya koma Areef ba, "Daddy what is your business about them?" Ya faɗa yana ƙoƙarin jawo laptop nasa dake ɗan nesa da shi. Ba karamin ruwan mamaki daddy ya sha ba, baki ba zai iya misilta irin mamakin da daddyn ya sha ba, yau Romeo ne inuwa ɗaya da mace? Kai anya kuwa yaransa ne kuwa? Dole ya zo Nigeria dan ya tabbatar ba wani abin aka yi musu suka canza ba, ranar ya kira waya mace ta ɗauka, yanzu kuma ya ji yana cewa mace ta kawo mishi fruits, to ko dai ɗan nasa ya fara neman mata ne? Ya tambayi kansa. Cikin sauri ɗaƴar ɓangare na zuciyar tasa ta bashi amsa da ina, Romeo ba shi da lokacin duk wata mace a duniya, akwai dai wani abin a kasa, ya kira Michael zai sami amsa, idan baku manta ba Michael da ya sani a baya, baya karya, kuma baya ɓoye abu, komai ka tambaye shi kai tsaye zai gaya maka ba wata kona kona, bai san cewa yanzu Aseef yake ba Michael ba, yanzu ya san me ake cewa sirrinta abu, ya san abin da ya kamata ya faɗa da wanda bai kamata ba. Zazzaƙar sexy voice ɗin ɗan nasa ne ya katse mishi tunani a in da yake magana da Rimsha, "Ni zan yanka fruits ɗin kenan?". Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a, tare da tsugunnawa a gaban bedside drawer ta fara yanka mishi. "Romeo i want to see your face now". Cewar daddyn, Okey ya amsa mishi da shi tare da juya kiran zuwa video call, kira ɗaya ya ɗauka, yana zaune a palon kasa shi da uncle Herry, kamar kullum suna shan tea suna kallon labarai a Tv. "Romeo ina son ganin yarinyar nan da kake magana da ita yanzu". Ba musu ya juya mishi wayar zuwa kanta tana faman yanka mishi apple, gyaran murya ya yi mata ta ɗago dan daddy ya kalli face nata da kyau, tana ɗagowa suka yi ido biyu da juna, wani irin haɗe rai daddyn ya yi tare da ɗaure fuska kamar hadari, da ɗan tsawa ya ce "Romeo na gaya maka bana son yarinyar nan, because bana son bakaken fata, bana son ta zo kusa da ku". Gently ya amsa da cewa "Dama ni son ku nake bi ne?, Ni dama abin da kowa baya so ni shi nake son aikatawa". Babbar magana, abin da ba'a so shi yake so shi kuma? Wannan wani irin mutun ne? Shi dai yaga yana ɓatawa kowa rai kenan shi ne burinsa ko yaya?, Shi wato daban yake da kowa, abin da jama'a basa so, shi yake so, lallai akwai aiki. "Romeo i said a hate this girl, kuma kada ta sake zuwa kusa da ku, bari ka ji da turawa ƴan uwanku kawai zaku yi mu'amala banda baƙaƙen fata". Shiru ya yi tamkar ba zai amsa ba. Almost 2 mins daddy na surfa bala'i baya son bakaken fata. Calmly ya fara magana "Dad ban taɓa jin cewa da mutun or da mace nake tare ba ma, amma yanzu da kayi magana ka ce baka sonta, sai naji ashe da mace nake zaune, kuma na ji daɗin zama da ita da baka sonta, wannan matsalar ka ce kana sonta or not, ni dai zama da ita ba fashi har sai na kammala abin da nake yi". "Romeo kana son ka rinƙa ɓata mini rai ko? To ina nan zuwa Nigeria gobe". "Babu in da zaka zo daddy, ban yi tunani akan hakan ba, kuma ba za'ayi ba". "Romeo for sure dole nazo". Shiru ya yi bai sake tankawa ba, dan idan ya biyewa daddy zasu yi kaca kaca ne, saboda wlh shi babu wanda ya isa ya juya shi ko ya ce mishi ga abin da zai yi a rayuwarsa, idan ya yi magana ya yi kenan, duk bala'in da za'ayi sai dai ayi baya canzawa, zai ga ta yadda daddyn zai zo ba tare da izininsa ba, abin da ko gidan nasu ma ba wanda ya isa ya fita idan bai bada izini ba. Ita kuma ba ƙaramin tsorata ta yi ba jin yadda suke sa in sa da daddyn nasa, duk da ta san cewa su a wajensu yin hakan ba wani abu bane ma, zaka iya samun uba da ɗa ma suna dambe, amma kafiya irin na Lion ɗin ne yake bata mamaki, idan ya kafe a kan abu ba mai tanƙwara shi, idan ya yi magana ba sauyawa, wannan wani irin mutun ne,? Wai abin da ba'a so shi kuma shi yake aikatawa, wannan kalma ta tsaya mata a rai, da ta yi tunani kuma sai ta ga haka ne, duk rayuwarsa idan aka ce ba'a son abu to sai ya yi, a iya zaman da ta yi da shi, ta fahimci hakan, da daddynta ya ce baya son ta zauna a gidansu ne, shi kuma ya ce sai ta zauna, da daddynsa ya ce baya son su zauna a Naija, shi kuma ya ce sai sun zauna, wannan bala'in da me ta yi kama?, Mutun kamar ba mutun ba, ba zaka taɓa gane mishi ba, yau fari gobe bakin kirin, duk zuciyar da ta yadda da shi ma a kan zai iya sauyawa to ta yaudari kanta, a cewarta. Jingina wayar tasa ya yi da jikin pillow ta yadda daddy'n zai sami damar ganinsa da kyau, ya miƙe ya nufi toilet, jim kaɗan ya fito ya wanke hannayensa, a in da ya tashi, a nan ya koma ya zauna tare da ɗaukar apple da ta yanka mishi ya fara kai wa ɗan bakinsa, "Romeo ka sani a duniya babu wanda ya kai bakaken fata mugunta, ka dai'na cin abin hannunsu dan kada su cutar mini da kai". Cewar daddyn. Ko sannu bai ce ba, sai ma kara ɗauko wani salan lemu da ya yi ya kai bakinsa, dan shi bashi da lokacin biyewa daddyn nasa a cewarsa, sai hana shi daddy yake yi, amma saboda an nuna ba'a so, sai ya ce ai tun da yake shan fruits ma bai taɓa shan mai daɗin wannan ba, dan haka ta karo mishi, tamkar daddy zai yi hauka ya katse kiran dan ya kira Michael wato Aseef, sai dai fa duk da haka ko kaɗan daddy bai yi nadamar irin horon renon da ya basu ba, shi ya koya musu hakan, yanzu da suke yi Mishi, yana mugun jin ba daɗi, amma bai taɓa yin danasanin irin tarbiyar da ya yi musu ba, da yake ɗabi'arsu ce yin hakan,......LALLAI DADDY DA SAURANKA, IN DAI BAKA YI NADAMA BA, TO DA SAURANKA, KA KOYAWA YARA KADA SU YARDA WANI YA ƊAGA MUSU MURYA A DUNIYA, ANYA KA NEMI ZAMAN LAFIYA KUWA? ALHADULILLAH, ALLAH MUN GODEMA DA KA BAMU IYAYE MASU TSAWATAR MANA A KAN DAI'DAI DA BA DAI'DAI BA, ALLAH KA KARA MUSU LAFIYA, KA JIKAN WAƳAN DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA, KA BAMU IKON CIGABA DA YI MUSU BIYAYYA MUNA FARANTA MUSU. Misalin karfe 8 na dare bayan sun ci abincin dare sun yi sallah, ita indomie da kwai ta girka ta ci, shi kuma fruits ya sha sai Maltina guda ɗaya, ya ce ta shirya zasu je wani waje na musamman, okey ta amsa mishi da shi sai murna take yi zasu fita, wanka ta tsara, har da zama a gaban mirror ta tsantsara make up ba karya, bata sanya janbaki ba, lips balm kawai ya sanya, ta yi kyau over na wuce misali, kamar dai kullum wandon jeans baki mai bala'in kyau ta ɗauko tare da riga maroon color mai doguwar hannu, high neck ce rigar, ta sanya a jikinta, kayan sun kamata sosai, da yake shima rigar kamar roba haka take, bayan ta sanya sai ta ciro wani dankareren turban cap nata baki kalar wandon ta sanya a kan nata bayan ta ɗaure dark black curly hair ta kenan, hular kamar ɗaurin gwaggwaro aka yi shi, ba karya ta fito kamar ka saceta ka gudu da ita, sauri sauri ta sanya perfume a jikinta ta fito zuwa bedroom ɗin daddyn nata, har ta fita sai kuma ta dawo ta ɗauki Booth ɗin Jehan ta sanya a kafarta, launin maroon color ce kalar rigarta kenan. Tsaye a gaban mirror ta isko shi ya kammala shiryawa cikin wando jeans shi ma, da kuma T-shirt, ba karya shi ma ya fita over, ya ɗaure gashin kan nan nasa, fuskarsa sanye da black face mask tare da p-cap, yana kallon fusataccen fuskarsa a jikin mirror, sai tashin fitinannen daddaɗar kamshin perfume nasa yake yi, har wani curly sosai soft skin nasa yake yi, idanun nan nasa sun kara wani kyau ba kaɗan ba, lips nasa har wani sheki suke yi kamar wadda ya sanya lips balm. Sallama ta yi mishi, kamar lullum kasa kasa ya amsa ba tare da ya juyo ba kuma bai kalli in da take ba, sai da ya kammala kallon face ɗin nasa kafin ya wuce ya nufi waje ba tare da ya kalli in da take ba, da sauri ta bi bayansa, mota suka je suka shiga, ita ta buɗe musu gate sai da ya fitar da motar sannan ta rufe ta zo ta shiga suka wuce. Cikin natsuwa yake tuki, bai yi gudu ba ko da sunan wasa, da alama akwai dalilin yin hakan, yana tuki yana duba diamond watch nasa dake ɗaure a hannunsa, alamar yana duba time, hakan yana nufin akwai lokacin da yake son isa wajen da zasu je ɗin, wayar tane ya fara kara, a ɗan tsorace ta ɗauki kiran, tana tsoron kada ya yi mata tsawa, ya ce akan me zata ɗauki kira?, Anaya ce take kiranta, Allah sarki taga yau bata zo school ba, shi ne ta kira ta ji dalili. Kara wayar a kunnanta ta yi can kasa kasa ta ce "Hello Anaya". Daga ɗayan ɓangaren Anaya ta amsa da "Rimsha ina wuni?" "Lafiya lou Alhadulillah yasu Zaira?" Da lafiya ta amsa mata kafin ta ɗaura da tambayarta ya bata zo school ba yau, ɗan satar kallonsa ta yi kafin ta ce "Babu komai zan zo jibi In Sha Allah". "Rimsha kina ganin fa mun gama test Exam zamu fara on Monday, amma sai wasa da zuwa school kike yi ko? Kina son ki zo last ko?" "A'a Anaya, In Sha Allah ba zanzo Last ba, ki rinƙa taya ni da addu'a". Nisawa ta yi kafin ta amsa da "To zan rinƙa tayaki, amma dai kema ki dage sosai". "Okey my Anaya ina godiya yanzu muna hanya ne idan mun koma gida zan kira ki". Tana ƙoƙarin katse kiran ta katseta da cewa "Rimsha ina wannan Baturen? Allah jiya nayi mafarkinsa, gaskiya yana da kyau sosai wlh, ga shi shiru shiru kamar yaya Feroz, dan Allah ina yake, ki turomin hotonsa idan kina da shi". Juyawa ta yi gabaɗaya ta zubawa Lion idanu tana faɗin "Tom zan ɗauka miki shi hoto idan bai sani ba na turomiki". "To dan Allah Rimsha yau ba sai gobe ba". Zata yi magana ta ga Lion ya yi parking na motar a parking space na wani wajen da bata san ko ina bane, cikin sauri ta katse kiran tare da zubawa wajen idanu tana kare mishi kallo, ga dukkan alamu clubs ne, ga ƴan mata da samari birjib a ko'ina na harabar wajen, mafiya yawan matan suna shaye shaye, ga sigari a hannunsu suna busawa, dressing ɗin jikunansu na banza, wasu ma da su da tsirara duk ɗaya ne, sai dai fa clubs ɗin a sihirtaccen waje yake, da alama clubs ne na manyan mutane ƴan sharholiya, dan gabaɗaya dankara dankaran tsadaddun motoci masu numfashi ne cike a parking space na wajen, sannan gabaɗaya ƴaƴan da suke wajen komai na jikinsu masu zafi ne, masu tsadar gaske, haka zalika wayoyin hannunsu masu zafi ne. A sukawane ta dawo da kallonta kansa, sai latsa waya yake yi bai bi ta kanta ba, jim kaɗan ya fito da bakar glass ya sanya a face nasa bayan kuma ga face mask, da alama baya son a gane shi ne, domin kuwa ya sanya hands gloves, kafarsa kuma tana cikin Booth, da alama shiri ne duk abin da ya yin nan. Bayan ya sanya glass ɗin ne ya ce da ita suje, bai tsaya sauraronta ba ya fice daga cikin motar, ya ɗan yi gaba ya barta a baya, tana fitowa samari suka fara kewayeta suka tare mata gaba, ga shi tayi irin dressing na karuwan ita ma, daga mai cewa jimana ƴan mata, sai mai cewa nariga, sun sha gabanta sun hanata bin shi, sai kakkauce musu take yi tana son wucewa sun hanata, da alama kuma dayawa daga cikinsu a buge suke, sun sha sun bugu sosai, sai wani layin maye suke yi mata, baki duk warin giya. Ta ruɗe ta rasa ya zata yi, bata ankara ba sai ji ta yi an jawo hannunta ta faɗa saman kirjin mutu, tun daga yanayin faffaɗar kirjinsa ta fahimci shi ne, nufa cikin ainahin wajen ya yi da ita, tana manne a jirjinsa, dan ya lura idan ba rungumeta ya yi ba, ba zasu daina tare ta suna taɓa ta tare da shafe mata jiki ba, shi kuma baya son a gane shi, shiyasa bai yi yunkurin ɗagawa kowa murya ba, kawai ya rungumeta a kirjinsa dan su yi saurin kammala abin da ya kawo su. Sosai ta kankame shi tana shakar numfashinsa, ɗan sauko da kansa kasa ya yi yana kallonta, sarkin tsoro duk ta bi ta tsorata, abin da bata saba gani ba, sai ya yi mata wani banbara kwai. Bayan sun shiga waje, sai kuma ya ji ba zai iya sanyata wannan aikin ba, ba zai iya sanyata zuwa ga mutumin dan ta fito mishi da shi ya kama shi ba, baya son shiga ya kamashi saboda wani dalili nashi na kansa, amfani da ita yake son yi wajen kama shi, yasan idan ya kalleta dole zai biyota, dan a haukace yake da neman sauran family'n Nawazudden da suka rage, ɗan raba jikinsu ya yi yana kallonta, yadda ta yi shigar tata marabanta da waƴan da suke wajen kaɗan ne, shi ba ma shigar kayanta ne a gabansa ba, idan ya raba jikinta da nashi kafin ta isa ga mutumin samari da dama zasu tare ta, zasu yi ta rungumarta suna shafata, ita kuma sarkin tsoro tsab zata ɓata musu shiri, dan zata iya waje baki ta yi ta ihu a cikin jama'a har komai ya lalace. Shiru ya yi yana tunanin me mafita kenan? Dan tun da ya sako kafarsa a cikin nan ya ji gaskiya ba zai iya tura ta ba, ya zuba mata idanu, amma a zahiri ba ita yake kallo ba, tunani yake yi, da yake dai a cikin glass idanun nasa suke, sai ka yi, zaton ita yake kallo. Wasu samari ne ke nufo in da suke, sun sha sun bugu suna ta tangal tangal suna layi tamkar zasu faɗi kasa, sun zo dai'dai kusa da su, cikin sauri ya mai data jikinsa ya rungumeta dan kada su bangajeta ta faɗi kasa ta fara yi mishi ihu a nan, wannan mai da ita da ya yi sai da ya ji shock ba kaɗan ba, dan da karfi ya jawota jikin nasa har sai da ta buge shi sosai a kirjinsa, waje ya juya da ita, cikin mota ya mayar da ita kafin ya fito ya rufe motar da key dan kada wasu ma su nufeta ta yi mishi hauka, takure jikinta waje guda ta yi tana kallon yadda ƴan mata da samari ke shagawagi a wajen ga uban kiɗa da yake tashi kamar zai ɗauke garin. Ta yi lamo a jikin kujera tana tunanin me ya kawo su wannan waje kuma, me Lion zai yi a nan?, Bata ankaraba sai gani ta yi gabaɗaya wutar clubs ɗin ta ɗauke, zaro idanunta waje ta yi tana faman kallon guys dake ta kunna hasken wutar tsadaddun wayoyinsu. A cikin duhun ta ji an buɗe gidan baya na motar tasu, ba ƙaramin bugu ziciyarta ya bada ba, jin alamar shigowar mutun a gidan bayan ne yasa bugun gaban nata ya kara tsananta, sai ƙoƙarin dannewa take yi, lokaci guda kuma ta sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya shaƙar numfashin mai ɗauke da daddaɗar kamshin perfume nasa da ta yi ne yasa hakan, ashe shi ne ya buɗe gidan bayan ya sanya mutumin da ya zo kamawa a ciki, ya yi wa mutumin ɗaurin goro tare da ɗaure mishi baki da wata tsumma wadda a wajen ya samu. Gidan gaba ya zo ya shiga ya tada motar da gudun gaske suka bar clubs ɗin, har lokacin kuma wutar bai dawo ba, security dake wajen ma da karfin kakinsa ya yi amfani wajen wuce su, wato dai waya suka samu daga sama a kan akwai mota mai kira kaza zata zo fita, da ta zo a bata hanya ta fita, tun shigowarsu ya shirya hakan, lokacin da ya yi parking na mota kafin ya fito ya tsaya ya tura saƙo zuwa ga His excellency, shiyasa yana zuwa kawai aka bashi hanya ya fice abinsa. Bai zame ko'ina ba sai gida, suna zuwa ya fito yana faɗin "Ki ɗauki abin da zaki ɗauka daga nan sai Kaduna". Ya kai karshen maganar tare da wucewa cikin gida dan ya ɗauki abin da yake da bukatar ɗauka, sun bar mutumin a cikin motar ɗaure ko motsi bai isa ya yi ba, dan ɗaurin mutuwa ya yi mishi, da sauri ita ma ta fito, har lokacin enginen wuta a kunne, zanensa da ta yi a baya ta ɗeba, tare da wasu hotuna da ta ajiye a drawersu, sai kayan haɗa tea na mum da take haɗawa dad ta ɗeba dayawa da dai sauran kayan da zata buƙata, trolley Jehan ta ɗauko ta shirya komai a ciki tare da nufar waje. A cikin mota a wajen gate bakiɗaya ta isko shi, sanya trolley ta yi a cikin motar gidan baya kusa damutumin kafin ta dawo zata rufe gate ɗin, tana kokarin jan gate ɗin ta rufe sai ganin shi ta yi ya fito daga cikin motar ya nufota da nufin ya rufe gate ɗin, komawa baya ta yi ta tsaya tana kallon shi, ciki ya koma ya kashe engine tare da cire wayar sannan ya dawo ya rufe ƙaramin gate ɗin ta ciki da sakata kafin ya fito ya jawo babbar, wata danƙareriyar sarka ya sanya a jikin babbar gate ɗin, irin sarka ce da ake ɗaure manyan ɓarayi, ita ya fitar daga cikin boot na motarsa ya sanya wa babbar gate ɗin ta waje, sannan ya danna wata sabuwar kwaɗo da ya saya a shopping da suka yi ɗazun, sai da ya tabbatar ya yi wa gate ɗin ɗauri mai kyau kafin ya rufeta tare da juyawa ya nufi motar, da sauri ita ma ta juya ta shige ciki. Da gudun gaske ya figi motar ya bar wajen, kai tsaye hanyar Kaduna suka nufa, sai sharara uban gudu yake yi tamkar zasu tashi sama, ita kuwa tuni ta lafe a jikin kujera sai barci abinta, duk wani checking point da ya wuce da karfin kakinsa ya yi amfani wajen wucewa ta yarda ba su tsayarda shi wajen bincikar motarsa da sauransu ba. Sai karfe 12 suka shiga Kaduna kai tsaye gida ya wuce, su Aseef sun jima da yin barci bayin Allah, ita ma Jehan tana can tana zuba barcin wahala Baiwar Allah, ta azabtu ba karya, ko wanka bata yi ba bare kuma cin abinci, tun wannan barci da ta yi time da Aseef ya kaita ɗakin, tun shi bata farka ba. Suna shiga gidan ya miƙawa Mark mutumin, dan suna shiga cikin gidan Mark ya nufosu da sauri yana yi wa ogan nasa welcome, Mark ɗan amana, ɗan ba ruwana, yana bala'in kaunar ogan nan nasa, dan halinsu kusan ɗaya. Umarni ya yi mishi a kan ya ɗauki mutumin ya cigaba da kula da shi yana bashi hukunci mai kyau zuwa lokacin da Nawazudden zai diro Naija, dan yana son haɗesu waje guda ne, kafin ya san abin da ya dace ya yi next. Ita kuma Rimsha, sai barci take zubawa abinta, ba ta da labarin sun iso gida ma, kashe motar ya yi ya fito zuwa cikin gida, har ya kai tsakiyar harabar gidan, sai ya tuna ashe da ita suke tare, ɗan juyawa ya yi ya gani ko Mark na kusa ya buɗe mota ya tasheta, sai yaga walam babu Mark, ba dan ya so ba ya juya zuwa wajen motar, kofar side nata ya buɗe yana tunanin wai menene ma sunanta oho, hannu yasa yana ɗan bubbuga jikin kujerar, shiru bata farka ba, ganin zata ɓata mishi lokaci ne, ga shi yana son zuwa ya yi wanka tare da cin abincin ya kwanta, hakan yasa ya saɓeta a kafaɗarsa zuwa cikin kawai. Da yake dare ta yi sosai, shiru kake ji, bedroom nata ya kai ta, saman bed ya kwantar da ita, ba tare da ya bi ta kanta ba ko ya kalli in da take ba ya juya sai bedroom nasa. Kayan jininsa ya fara cirewa, ya rage daga shi sai short sannan ya nufi toilet dan yin wanka, yau har cikin ɗaki Mark ya kawo mishi abinci saboda TRIPLETS sun yi barci, babu mai kawo mishi. Bayan ya kammala wanka, ya yi shiri cikin kayan barcinsa mai bala'in kyau da tsada, abincin Mark ya zuba mishi, ya ci mai ɗan yawa saboda yunwa da yake ji, bayan ya kammala ya sha lemu saboda abincin ta yi digesting, miƙewa ya yi ya nufi waje, shi kuma Mark ya kwashi kayan abincin ya nufi kitchen. Palon kasa ya sauƙo, bedroom ɗin Areef ya fara shiga, tare ya samesu saman bed suna zuba barci, Aseef ga waya a hannunsa, da alama chatting yake yi barci ta yi awon gaba da shi, Allah sarki yana bala'in kaunar ƴan uwan nan nasa, ba zai iya yin barci ba tare da ya shigo ya duba lafiyarsu ba. Saman bedside drawer ya zauna tare da fara karanto addua'o'i yana tofa musu, barci suke yi cikin kwanciyar hankali, dukkansu fuskokinsu ɗauke da annuri, da alama cikin matsanancin farinciki barcin ya ɗaukesu, gently ya karɓi wayar hannu Aseef tare da ajiyewa a gefe yana mai cigaba da tofa musu addu'a, zubawa ciwon Areef idanu ya yi yana kallon yadda ya shafa maganin a wajen, da kallo ɗaya ya yi wa wajen yasan Areef faɗa ya je ya yi ya fama wannan ciwon, har ya kai hannu kamar zai taɓa, sai kuma ya fasa dan baya son su tashi daga wannan barcin farincikin da suke yi. Ya ɗan jima yana yi musu addua'o'i kafin ya miƙe, gently ya kaiwa Areef sumbata a goshi yana mai jin tsantsar kaunarsu a ransa, a nitse ya zagayo ta ɗayar ɓangaren da Aseef yake, shi ma ya bashi sumbata, cike da so da kaunarsu fal a cikin ransa ya wuce ya nufi nasa bedroom ɗin, saman bed nasa ya haye ya kwanta, duk a gajiye yake sosai, wayarsa ya jawo ya kashe kafin ya yi addu'ar barci ya shafa, a hankali ya lumshe dara daran blue eyes nasa, after some minutes idanuwansa a lumshe ya sanya hannu ya laluɓo remote ɗin Ac ya kara gudu tare da jawo bargonsa zuwa cikinsa ya kashe wutar ɗakin tare da kunna lamp dake bedside drawers masu bada wuta sky blue, babu jimawa barci ya yi awon gaba da shi, a hankali yake sauke numfashi cikin kwanciyar hankali, da gani ba ƙaramin jin daɗin barcin yake yi ba. A ɓangaren gidan Abba kuwa, lokacin da Imran ya isa da jelly, dai'dai lokacin shi ma Akil ya danno hancin motarsa tare da Umaisha.............. ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ *Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta* E43-44💋 A ɓangaren gidan Abba kuwa, lokacin da Imran ya isa da jelly, dai'dai lokacin shi ma Akil ya danno hancin motarsa tare da Umaisharsa, a tare suka fito daga cikin motocin nasu, ɗaukar jelly Imran ya yi dan idan ya ce ta tafi da kafarta, zasu jima basu shiga ciki ba, kun santa dama da iya zuzuta abu, tsabar iskanci idan ya ce ta taka kafa sai taki, yes tana jin zafi amma har da karawa ta yi, rufa musu baya su Akil suka yi, sai da ya isa tsakiyar palo ya sauƙeta tare da zaunar da ita saman sofa ya juyo ya miƙawa Akil hannu dan su yi musabaha. Fuska ɗauke da fara'a Akil ɗin ya miƙa mishi hannu suka gaisaz Umaisha ta dawo kusa da jelly ta zauna tana faɗin "Yaya Imran ina wuni?" Da fara'a sosai a face nasa ya amsa da "Lafiya lou ya karfin jiki". Dan Akil ya gaya mishi bata jin daɗi, da lafiya ta amsa mishi. Gin motsinsu yasa Akila fitowa dan taga su waye ne, ganin sune yasa ta kurma ihu ta taho da gudu ta rungume Umaisha da jelly ta faɗa jikinsu tana dariya, zama Imran da Akil suka yi saman sofa mai zaman mutun uku Imran yana faɗin "Ke Heartbeat zaki yi ki karya mini mata ko? To maza ki tashi a jikinta bata da lafiya". Rungumeta jelly ɗin ta yi tana faɗin "Aunty Akila wlh jikina ciwo yake yi mini". Kara rungume sosai Akilar ta yi tana yi mata sannu duk da bata san menene yake damunta ɗin ba, a wannan hali Ammie da Abba suka sauƙo daga sama suka samesu. Da sauri Ammie ta kariso wajen tana faɗin "Ku nuna mini wace ce ƴar Maik a cikinsu?". Akila ce ta nuna mata Jelly, murmushi kaɗan ta yi dan idan baku manta ba, bata da yawan fara'a sosai, "A dole ƴar Maik ta zama haka ai, Maik namu, kai amma ina kewarsa wlh, ya ce Ammie idan kika kuskura yau kika yi mana irin miyar rannan sai na yi miki saki uku". Tana magana tana ɗan murmushi. Kallon juna Akil da Imran suka yi suna mamakin mahaifiyar tasu, ya akayi yanzu kuma take son family'n Abbansu? Anya Ammie sune kuwa? Kai akwai dai wani abin, ita kanta Akila ta sha ruwan mamaki, kashe musu ido Abba ya yi akan kada su yi mata wata magana da bata dace ba, kada su kuskura su tuna mata ta taɓa cewa bata son family'nsa, dan idan suka tuna mata za'a iya samun matsala tun da yanzu ne ta sami lafiyar ba'a jimaba, to tana iya komawa ruwa idan suka mata wata magana. Ganin abin da Abban nasu ya nuna musu na su yi shiru ne yasa suka yi shiru suka danne mamakinsu. Hannun jelly ta riƙo tana faɗin "Tashi na ganki, ai ƴar Maik ƴar ɗakina ce, babanki a hannuna ya zauna tun yana ɗan shekara 10 zuwa 18 sanan ya koma wajen Deen, saboda Deen ya matsa lallai dole ya koma wajensa, ban so rabuwa da shi ba a lokacin, amma ba yadda zan yi ne, Deen ya kureni a lokacin, sai dai ko da ya koma wajen Deen ɗin yana yawan zuwa wajena mu wuni dan ya fi son zama da ni shi ma". Miƙewa Jellyn ta yi da nufin ta bita zuwa saman nata kujerar, ƴar kara ta saka lokacin data fara ɗaga kafarta. Cikin sauri Imran ya ce "Ammie bata da lafiya fa". Yana magana yana sunkuyar da kai kasa, tuna abin da Abba ya gaya mata na yaronta ya angwance ne yasa ta kalle shi tana watsa mishi harara, tare da riƙo hannun Umaisha dake ta binsu da kallo, mamakin Ammi ya hanata yin magana, ganin abin take kamar ba gaske bane, dan idan baku manta ba, ita ta gasu ba kaɗan ba a hannun Ammie, sai dai kuma ita Ammie bazata iya tuna cewa ta wahalar da ita ba, Allah sarki rayuwa kenan, yanzu ga shi Umaisha ɗin ta riƙeta a ranta sosai. Rungumosu dukkansu biyu ta yi a gefe da gefen kafadarta tare da karisawa da su zuwa saman sofa mai zaman mutun uku a hankali, tare da su ta zauna tana mai tsananin jin kaunarsu a ranta, wai surukunta ne waƴan nan, matan ƴaƴanta, kai farinciki ba'a magana. Zama saman sofa mai zaman mutun 2 Abba ya yi yana binsu da kallo, Akila dai ta lula duniyar chatting da sahibinta dan tun ɗazun yake ta tura mata saƙonnin soyayya da su flowers ta WhatsApp. "Abban Imran bari mu haura sama da matar Imran ina zuwa". Cewar Ammie, ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta riko hannun jelly'n dan ta mikar da ita, bayan ta miƙe ta ɗan rungumota suka nufi sama, dan ta san matsalar, Jellyn bata shiga ruwan zafi mai kyau bane, daga ita har Imran ɗin ba wanda ya yi tunanin idan ta shiga ruwan zafi tana gasa gaban nata da kyau zata sami sauƙi. Suna haurawa sama su kuma su Imran suka fara gaishe da Abban. Bedroom nata ta wuce da ita, saman bakin gado ta zaunar da ita kafin ta nufi toilet, sai sannu take ce mata, ruwa mai zafi daidai ta haɗa mata tare da zuba mata wasu sinadarai nata da take amfani da su, ciki har da man zogale, da man zaitun, na tane wadda ta jima take amfani da su tun kafin ta sami wannan matsalar, bayan ta samu matsala bata amfani dasu, jiya Abba ya sake sayo mata su tun da ta dawo cikin hayyacinta, sai ta cigaba da amfani da su kamar da, suna gyara mace sosai, bayan ta kammala, daga karshe ta zuba mata ruwan jikakken sassaken mangoro da take jiƙawa, dan yana matikar kashe sanyin gabar mace ba kaɗan ba, bare ma ita jelly da take yanzu aka buɗeta, tana buƙatar ire iren su dan kada a sami wata matsala. Dawowa cikin ɗakin ta yi, da kanta ta cire mata kayan jikinta, Jellyn bata yi mata kaddama ba, dan idan baku manta ba, ita jelly rainon namiji ne, duk da daddyn ya tsawatar mata a kan wada ta yarda wani ya taɓata ma bare ya cire mata kaya, amma ta san wannan maman Imran ne babu damuwa, kuma ita jelly bata da kunya ko kaɗan, shi ne yasa bata yi wani gardama ba, ta tsaya ta cire mata komai tas, ya rage daga ita sai pant ta kama hannunta zuwa cikin toilet ɗin, Allah sarki duniya kenan, yau ta sami sabuwar uwa, Allahu Akbar Allah mai yin yadda ya so da bawansa, ya bashi a lokacin da yake so, ya kuma karɓa a lokacin da yake so, ya karɓi mahaifiyarta tun ranar da ta zo duniya, yau kuma cikin ni'imarsa ya sake bata wata uwar, ba abin da zamu ce sai dai Alhadulillah. Sai da suka isa bakin baf ɗin ne ta tsaya ta cire mata pant ɗin nata kafin ta ce to ta shiga, da yake jikin nata dai ba kwari, bata musawa Ammie ba, sai okey kawai take binta da shi, da yake da turanci Ammien take yi mata magana. Da kyar ta iya zama a cikin ruwan saboda zafin shi, sai Weldon Ammien take ta ce mata, ganin ta ɗan jima ruwan yana ratsata sosai ne yasa Ammien ta fita zuwa palon kasa, hira ta samesu suna ta zubawa. "Akila ta shi ki kawo mini kayanki ɗakina yanzu". "Okey my Ammie" . Ta amsa tare da miƙewa ta nufi saman. Dawo da kallonta a kan Akil Ammien ta yi tana faɗin "Son kar dai ka gaya mini abin da nake hasashe gaskiya ce?". Da sauri ya ɗago yana kallonta da mamaki "Ammie me kike hasashe kuma?" "Matarka ciki gareta mana". Ɗan kasa ya yi da kansa yana faɗin "E Ammie gaskiya ce, zai kai wata wajen biyu ma yanzu". Zaro idanu ta yi tare da nufar in da Umaisha ɗin take zaune tana faɗin "Wayyo shi ne a rasa wanda zai yi mini albishir a cikin ku? Ni yau ina zan saka kai'na saboda tsantsar farinciki, Allah nagode maka, ya Allah Alhadulillah". Tana magana ta rungume Umaisha ɗin sosai tana mai jin tsantsar farinciki, ita kuma Umaishar ta kasa sakin jiki da ita, sai ɗan murmushi da take yi, a zahirin gaskiya tsoron Ammie take yi kamar ta mutu, dan ma tafiyar Ammie sama da ta yi da jelly Abba ya ɗan yi musu bayani a kan abubuwan da suka faru a baya Ammien bata cikin hayyacinta ne, amma duk da haka ita ta kasa sakin jiki da Ita. Ammie kuwa yau murna a wajenta ba'a magana, Imran ya angwance, ya kawo mata jinyar amayar tasa, shi kuma Akil ya kawo mata tsarabar yaron ciki, kai abin sai godiya, yau murmushi bakinta yaki rufuwa, sai godiya take zubawa Allah tare da kirari mara adadi, haka ta tasa Umaisha a gaba a kan me zata ci? Me take jin ƙoɗayi? Me baby yake so? Ta faɗi koma me ne yanzu aiki da gamawa za'a kawo mata, to da yake na gaya muku Umaisha ta kasa sakin jikinta, sai ta rinƙa nokewa tana faɗin babu komai, babu abin da take so, kuma a zahirin gaskiya tun da suka shigo da ta ji kamshin girkin Ammien take haɗiyar yawu, cikinta har wani kulle mata yake yi saboda yadda daddaɗar kamshin yake dukan hancinta, burinta kawai ta ci wannan girki, sai dai kash ta kasa sanar da kowa abin da yake ranta, ta so su keɓe da mijinta ta gaya mishi, amma ba hali, yanzu kuma an tambayeta me take so ta kasa faɗa ta ce babu komai. Sai da Ammie ta yi maya tambaya yafi baki goma, amma amsa ɗaya, shi ne babu komai, sai da Abba ya ce wai ta kyaleta mana ko dole sai ta cusa mata sha'awar abu ne, sannan ne ta kyaleta ta koma wajen jelly dan ta dubata. Kamar yadda ta barta haka ta dawo ta sameta, ruwan ya yi sanyi, riƙo hannunta ta yi tare da taimaka mata ta fito daga cikin baff ɗin ta tsaya a gefe guda, buɗe ruwan Ammien ta yi ya fita tare da haɗa wani mai ɗan ɗumi ta ce ta shiga bari ta yi mata wanka, ba musu ta shiga, Ammie da ƙoƙari tas ta kwanketa, dan ita gani take Akila ma bata wuce ta kamata ta yi mata wanka ba, kunga Akila kuma ai ta girmi jelly wajen da shekaru uku kenan. Bayan ta kammala ta tsaneta da toilet tare da ɗaura mata mai ɗan girma a kirjinta ta ja hannunta zuwa cikin ɗakin, gaban mirror ta tsayar da ita a in da ta shafe ta da mayuka masu kyau da tsada, sannan ta zuba mata turaruka masu kyau da daɗin kamshi kafin ta ɗauko kayan da Akila ta ajiye mata a saman gado ta dawo gaban mirror, har da bra Akila ta kawo mata, dan haka sai ta shirya ƴar tata tsab tare da sanya mata bra ɗin, dama suna nan tula tulan ba a sanya bra bama, da aka sanya ba'a magana, sai suka kara cika waje, simple make up ta yi mata tare da kara fesa mata turare a saman doguwar rigar tata da ta sanya mata, ba karya ta haɗu iya haɗuwa, yafa mata gyalen rigar ta yi tare da riƙo hannunta suka nufi palo, Masha Allah yanzu kafan nata ya sake mata, gaba nata ma ya dai'na yi mata zafi, ya dawo dai'dai. Tun daga suka sako kafarsu a saman benen Imran ya zubawa tauraruwar tasa idanu, ta yi kyau ba karya, ji yake yi tamkar ya tashi ya rungumo kayarsa, amma ina ba hali, dole ya danne dan saboda su Abba, kuma ya ga ma sai harararsa ta gefen ido take yi, da alama zasu sha dirama ba kaɗan ba, dan fushi take yi da shi. Saman sofar da Umaisha take Ammie ta zauna tare da zaunar da ita a gefenta, ya zama da Jellyn da Umaisha sun sakata a tsakiya, ita kuma Akila ta je ta tada kai da cinyar Abba tana aikin latsa waya, shi dai Imran ya san latsa wayar me take yi, dan shi ya haɗa komai, yana taya kanwar tasa murnar samun ɗaya daga cikin TRIPLETS da ta yi, yasan zata more ta ji daɗi, hankalinta zai kwanta sosai, zata sami soyayya mai tsabta wadda babu mix, dan duk TRIPLETS basu karya kuma basu yaudara, idan suna son abu, to zasu yi mushi mahaukacin so ne, za kuma su zage dantse sosai wajen kula da duk wani motsin wannan abin, ga dai misali a kan ita Akilar, duk wani motsinta Aseef yana sane da ita, kuma yana matuƙar kulawa da ita over, to haka suke idan suna son abu, idan kuma suka tsani abu, to fa wannan abin ya shiga uku, zai sha bakar wahala ba kaɗan ba, dan ko ganin mai kama da shi suka yi sai sun zage shi, haka suke, shiyasa Imran yake tayata murna na samin Aseef a matsayin masoyi da ta yi. Kada ku manta duk in da Akila zata je tana rungume da wannan teddy ɗin nata na tsarabar masoyin nata, a ɓangaren Umaisha kuwa, ta ƙosa kuma ta matsu Ammie ta ce azo a ci abinci, rashin sani yafi dare duhu, ita kuma Ammie da yake bata sani ba, sai bata kawo zancen abincin bama kwata kwata a kanta, dan a nata ganin yaran nata ba baki bane, idan suna son cin abinci ai dole su nufi table su ce a zuba musu, to ita kam Umaisha ta gasu, tsoron ma magana take yi dan kada ya zama laifi, Ammien ta daketa, Allah sarki. Haka suka rinƙa zuba hira cikin nishaɗi har sai da lokacin sallar issha ta yi, a tare Abba, Imran, AKil, suka nufi masallaci, su kuma matan suka haura sama, Akila, Umaisha, suka nufi bedroom ɗin Akilar, ita kuma jelly Ammie ta riƙo hannunta suka nufi nata ɗakin. A ɓangaren gidan Abbi kuwa, bayan wasu ƴan kwanaki, gabaɗayansu zaune suke a palo, Ayla ta tada kai da cinyar mijinta tana lumshe idanu tamkar mai jin barci, Aunty ma hakan ne, ta tada kai da cinyar Abbi tana kallon Tv, maman Ayla tana zauna saman nata sofa daban suna kallon labaran safe a Tv, har wani haske ta kara ta yi kyau kwana biyu da ta yi a gidan, tana samun hutu ga cima mai kyau, nan take ta fara murmurewa tana kiba abinta, ashe ita Ayla ta biyo wajen yin ƴar ƙiba, Hanan tana zaune kusa da maman Aylar tana latsa wayarta, da alama dai chatting take yi, suna cikin matsananciyar nishaɗi ba kaɗan ba, Irfan yana zaune kusa da daddyn Jelly amma ba a kujera ɗaya ba, kowa da nasa kujerar, kowa da abin da yake yi, Ommu wato Hjy Hadiza tana cikin bedroom nata tana barcin asara da ta saba yi. Gyaran murya Abbi ya yi tare da fara magana a nutse "Yanzu ya mata ki bamu labarinki, da kuma labarin Aliya tun da kin ɗan huta ai ko?". Shiru ta ɗan yi, sai dai ga dukkan alamu ta shiga damuwa jin tambayar Abbin, amma bata da zaɓi dole ta basu labari,. Ɗago kai ta yi tana ƙoƙarin fara yin magana sai suka ji sallama daga bakin kofar shigowa. Har suna haɗa baki wajen amsawa, A'A SALAHUDDEEN ne ya shigo, sai murmushi yake yi, jikinsa na sanye da wata danƙareriyar shadda mai bala'in kyau da tsada launin sky blue, ya sha bakar hula da bakar takalmi, ɗinkin half jampa ne, ba karya ya fito ya yi kyau sosai abinsa. Karisowa cikin palon ya yi, sai sannu da zuwa suke yi mishi, yauwa ya rinƙa amsawa da shi, kusa da Irfan ya zauna tare da miƙawa Irfan ɗin hannu dan su gaisa, miƙo mishi ya yi suka gaisa, daga nan ya ɗagawa su Abbi ma gaisuwa, da fara'a ɗauke a kan fuskar ko wannensu suka amsa mishi da lafiya, Hanan ta ɗaga mishi gaisuwa bayan sun gama gaisawa da su Abbi kenan, shi ma da fara'a ya amsa mata. Shiru palon ya yi kowa da abin da yake tunani, can A'A ya katse musu shirun da tambayar daddyn Jelly ina ƴarsa take? Wato jelly, cool murmushi ya saki yana faɗin "Jelly tana can wajen mijinta ai". Ɗan zaro idanu ya yi, sai kuma ya yi kasa da kai yana faɗin "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun yanzu rashin zumuncinmu har ya kai Jalila ta isa aure ban sani ba? Kenan yanzu zan iya haɗuwa da ita a hanya ban gane ita ɗin bace fa na wuce, kai amma abin bai yi mini daɗi ba, amma dai dole a wannan karon zan je na kalleta dan gaba, dan kuma mu gyara laifin da muka yi a baya, gaskiya ban yi wa Aunty Umaima adalci ba". Irfan ne ta caɓi zancen da cewa "E gaskiya kam baka kyauta ba". "Rufe mini baki, ba duk haka kuke ba". Cewar Abbi, shiru ya yi yana ɗan sosa kai, dan kuwa yasan haka suke, shi yanzu bai san ya kalar ƴaƴan Azharuddeen Bature wato su Anaya suke ba, zai iya haɗuwa da su a hanya ya wuce su wuce bai san su bane, gara A'A ma ace basu gari ɗaya, shi kuma da shi da su Anaya gari ɗaya unguwa ce ta raba, to ko yayan su Anaya ɗin Feroz da ya kasance babba ma, matashin saurayi kamarsu bai san shi ba bare mata yara dake cikin gida, haka zalika bai san ko ɗaya daga cikin ƴaƴan Hjy Batula ba, shi su Imran kawai ya sani, dama daddyn Rimsha kam ba'a sanya ƴa'ƴansa a lissafi, dan saboda babu wanda ya san shi ne ma Hossain... Matasa kuji tsoron Allah ku daina zubar da zumunci, wlh gaskiya ce zumunci tana hana bawa tsallake gadar siraɗi, to kada ku yarda ku zama ɗaya daga cikin waƴan da zumunci zai riƙe a ranar gobe kiyama, ku kasance masu ziyartar ƴan uwanku, dayawa daga cikin matasa da sun girma dai shikenan, sai su watsar da kowa, suna ganin kamar zubar da girma ne zuwa gidan kawune da bappanu, hakan ba dai'dai bane wlh, kuskure ne babban ku ke yi, yana da kyau ku gyara dan mu gudu tare mu tsira tare, Allah ya bamu dacewa, mu dai mata ko dan biki muna sada zumunci, mu an san mu da zumunci ba karya. Sai wani sunkuyar da kai suke yi, A'A ne ya ce "Gaskiya dai Abbi dukkanmu mun yi babban kuskure, dan haka ya zama dole yanzu mu gyara da izinin Allah". Caɓe zancen Irfan ya yi da cewa "E gaskiya kam, ni yanzu ma weekend zan shirya na je Maiduguri wajen gwaggo Batula, idan na dawo zan yi yawo a gabaɗaya dangi har Bauchi zan je dan na gyara kuskurena". "Ba zaka je har kasar Russia bane sai iya Bauchi kawai? Ya kamata ka je ka gano mana ƴan uwan mummy ai". Cewar daddyn Jelly, ya yi maganar cikin zolaya. Zaro idanun nan nasa na gado ya yi yana faɗin "Russia kuma? Ai sai dai a mafarki, yadda kuka bani labarin ƴan uwan Barrister Naurat ɗin nan balaƴaƴƴu ne, ina ni ina tinkararsu, salon su sauke haushin musuluntar da ita da Dr Salman ya yi a kai'na, su kamani su peɗeni da raina, bappa Maik kasan fa har ƴanzu nasan mugu mugun haushin gabaɗaya family'n Dr suke ji, tsoho ya rasu ya barmu da gaba mara iya ka, ai tsakanina da Barrister sai dai nayi mata addu'a wlh, Allah ya jiƙanta a koma ina take, amma ƴan uwanta, ni ban ma sansu ba, kai kaddara ma bamu da wata alaƙa". Dariya gabaɗaya palon suka saka A'A yana faɗin "Wlh da gaskiyarka, kasar Russia ba wasa ba, yanzu idan ka kawo musu wargi za'a ɗauki gawarka, bare ma Dr da ya yi babbar laifi ya shiga ya ɗauko ƴar cikin kasar ya musultar da ita ya kuma kawota Nigeria, tab ai akwai kura ba kaɗan ba, ku da shiga Russia sai dai a Tv wlh". Shi da Abbi da daddyn Jelly sai murmushi suke yi, dan sun san fin haka ne ma zata faru idan jininsu ya tinkari ƴan uwan Barrister, domin sun san ƴan uwan nata a manya manyan abokan gaba suke ɗaukarsu, babu yafiya, ko yanzu suka je suna iya kashesu har lahira, kuma sun kashesu sun kashe banza, babu mai tankawa dan su ƴan Nigeria ne bakaken fata a cewar ƴan uwan. "Abbi ni fa magana nazo nayi da kai". Cewar A'A, yana magana yana wani sunkuyar da kai kasa, "To Ahmad in zo kenan ne?" Girgiza kai ya yi yana faɗin "A'a Abbi a nan ma ya yi, zan iya maganar ai, zan fi jin daɗi nayi a gaban kowa, sannan ga yaya Maik a kusa". "Okey tom ina jinka". Shiru ya ɗan yi kamar mai wani tunani, can kuma ya ce "Dama Abbi auren ƴarka nazo nema, a gaskiya ba zan ɓoye maka ba ina sonta, tun last zuwana da nayi, na kasa faɗa maka ne kawai, amma yanzu naji ba zan iya cigaba da ɓoyewa ba, gara nazo na nemi izini kawai". Yana magana yana kallon Hanan dake ta faman buga game a waya, miƙewa zaune Aunty ta yi tana faɗin "A'a gaskiya, ai auren Hanan a wajena za'a nema ba wajen Abbi ba, ni zan bada ita". Jin an ambaci sunanta yasa ta ɗago kanta, karaf sai cikin idon A'A, kawar da kallon nata ta yi zuwa kan Aunty, dan ita bata ɗauka ma zancen a kanta ake yi ba idan ba da ta ji Aunty ɗin ta yi ambaci sunanta ba. Daddyn jelly ne ya katse su da cewa "Kai duk ku lafa haka nan, Hanan dai ƴata ce, kuma idan har tana son kanina Ahmad to na bata, Ahmad ga Hanan ka tambayeta idan tana sonka to shikenan, ka kawo mini sadakinta ni zan isar da shi Katsina da kai'na". "Wannan gaskiya ne, Ahmad ga Hanan idan tana sonka, to zamu shige maka gaba zuwa Katsina, nasan ba za'a hanamu aurenta ba". Cewar Abbi. Shiru palon ya yi kowa ya zubawa Hanan da A'A idanu, sai wani kasa da kai take yi, shi kuma ya tsareta da ido babu ko kyaftawa. Hanan, ya ambaci sunanta, kin ɗago kai ta yi, sai ma kara kasa da kai da ta yi, abin ku da jinin Turawa, su Abbi dukkansu babu kunya a lamarinsu, duk Naurat suka biyo, idan baku manta ba su Turawa dama haka suke, a gaban iyaye ake shan soyayya, suma iyayen a gaban ƴaƴa suke shan love nasu son ransu, to shi ne yasa abin sam babu kunya a cikinsa, su A'A ma gabaɗaya cikin turawa suka yi karatun, so babu wata kunya a lamusansu, wannan dalilin ne ma yasa zaku sami Abbi da Aunty a palon kasa suna soyayyya, Aunty ta tada kai da cinyarsa ko a jikinsu, shiyasa suke zuba love iya son ransu har su daddyn jelly babu mai jin kunya yin soyayyya, misali lokacin da su Akil suka zo da matansu, ai kunga haɗuwa suke yi a palo, kowa yana kula da matarsa babu kunya, to uzuri zaku yi musu, suma ruwa biyu ne ba ɗaya ba, shiyasa suke a haka, kuma su su Abbi idan baku manta ba, a can suka taso har sai da suka zama manyan samari kafin su dawo nan, daddyn Jelly shi kaɗai Naurat ta haifa a Nigeria, shiyasa idan kuka lurama duk cikinsu shi ne kaɗai mai ɗan kunya, kuma yana nuna kunyarsa a fili kowa ya san shi da ita, amma hakan baya nufin shima ɗabi'ar Turawan ya kyale shi, a'a akwaita sosai, ciki kuma har da zuba love babu kama hannun yaro, kuna dai ganinsa shi da Jelly'nsa ma bare kuma Ayla da take matarsa, ai abin nasu a jini yake. "Kina sona Hanan?" Ya yi maganar yana kara tsareta da idanun, da yake ita kam jinin Katsina da mutan Kaduna ne, akwai kunya a lamuranta, sai ta kasa magana, tana son tashi ta bar wajen ma ta kasa, saboda tana ganin idan ta tashi za'a ce ta dawo, kuma ga kowa yana kallonta, dan haka sai ta cusa kanta cikin cinyoyinta tana murmushi, dan tana son A'A, ya yi mata, kuma shi ma irin mijin da kowacce mace zata buƙata ne, akwai kyau sosai na jinin Hausa Fulani, akwai kuɗi, ga ilimin addini da boko ba kaɗan ba, nitsastse da shi, bashi da hayaniya, so har cikin ranta tana kaunarsa, tun ranar ma da ya zo ya yi mata kyau sosai, ta rinƙa satar kallonsa. Aunty ce ta katsesu da cewa "A'a fa Hanan kada ki yi mana hakan, ya muna shirin komawa India zaki wani ɓoye fuska, ki ɗago ki gaya mishi gaskiya kina son shi ko yaya?". Ta yi maganar cikin zolaya, shi dai Irfan sai murmushi yake yi bawan Allah, duk ya rame kamar mai wani ciwon, kuma ba wani ciwo da yake damunsa, kawai rashin samun kwanciyar hankali ne ta sako shi a gaba. "Kada ku takurawa ƴa ta" Cewar daddyn Jelly, hannu A'A ya saka ya karɓi wayar da yake hannunta, numbersa ya sanya a wayar tata ya yi flashing, sai ga number tata ta shigo wayarsa, mai da mata da wayar tata ya yi a cikin hannun nata yana faɗin "Yaya Maik ku kyaleta ne, zuwa gobe zan dawo muku da amsa". Ita dai maman Ayla sai kallon A'A take yi, ita kuma Aylar sai zuba barci take yi a cinyar mijin nata, kunsan yanzu tana mumzalin barci ne, da ta kwanta kaɗan sai barci abinta. A'A na ƙoƙarin sake yin magana aka sako labarai a Tv, "Ku kara mana Volume". Cewar Abbi, Aunty ce ta kara Volume ɗin, natsuwa suka yi dukkansu dan saurara, wata ƴar jarida ce ke magana kamar haka "A safiyar yau ne Allah ya yi wa shararren ɗan siyasarnan wato ABUBAKAR SALAHUDDEEN rasuwa, ya rasu ne kuma sakamakon taimakon da ya je yi, duk wanda ya san ABUBAKAR SALAHUDDEEN ya san shi mutun ne mai taimakon talakawa, yana kan hanyarsa ta zuwa gidan hutawarsa dake cikin Kaduna ya hangi wata yarinya a bakin titi tana zaune tana kuka, matashiyar budurwa ce da zata kai shekaru 18 zuwa 19 a duniya, ganin hakan kun san shi da taimakon yasa ya ce a tsayar da mota, da kansa ya fita ya nufi in da wannan yarinyar take zaune tana kuka, dan kunsan duk mai hankali ya ga yarinya budurwa da daddare a kan hanya tana kuka dole zai tambayeta ko me ya faru, yana isa wajenta dan ya tambayeta me ya faru, yarinyarnan ta zaro wuƙa mai kaifin bala'in ta shammacesa ta daɓa mishi da iya karfinta a cikinsa, daga shi sai wasu ƴan'sanda biyu dama suka tafi, nan take ya yi kokarin faɗuwa kasa ƴan'sandan suka riƙe shi, a nan ne ita kuma yarinyar ta gudu, dan babu security sosai a tattare da shi lokacin, gidan hutawarsa zai je ya huta, shiyasa bai ɗebi securitys ba, dama kun san mafiya yawancin lokaci haka yake yi, daga nan ƴan'sandan suka ɗauke shi zuwa asibitin, tun a hanya Allah ya yi mishi cikawa, ya ce ga garinku, a safiyar yau muka sami labari, ita kuma yarinyar ta gudu, sai dai an yi nasarar samun hoton fuskarta, a yanzu haka jami'an tsaron su bazama nemanta, wannan shi ne hoton ABUBAKAR SALAHUDDEEN tare da makashiyarsa JEHAN NAWAZUDDEN, da ƴan'sanda suka sami hotonta ne, a nan ne muka san cewa ƴar gidan Nawazudden ce, wanda ya kasance tsohon ɗan takarar shugaban kasa da ya rasu ta hanyar haɗari, sai abin mamaki a nan shi ne, Nawazudden dai ya mutu da shi da family'nsa dukka, to bamu san ya akayi ita kuma Jehan ta kasance a raye ba, hukuma suna nan suna bincike, kome yake ciki zamu rinƙa kawo muku labarai a kai a kai, ku kasance damu, mun gode da sauraran mu". Babbar magana, masu karatu, akwai lauje cikin naɗi, da ni da ku duk mun san cewa wannan labaran ba gaskiya bace, da farko Jehan bata kai 19 years ba 16 to 17 years gareta, na biyu kun san ba'a kan hanya ta daɓa mishi wuƙa ba, a cikin gida ne, kuma ba ɗaɓa mishi wukar a ciki ta yi ba, yanke mishi gaba ta yi, amma ya akayi cikin ƙanƙanin lokaci a ka juye maganganun dukka, kenan dan a rufawa ABUBAKAR SALAHUDDEEN asiri ne a matsayinsa na ɗan siyasa ne a kace hakan ko kuma yaya abin yake,? Lallai an shiryawa Jehan kadar zare ba na wasa ba, daga ganin wannan abin babban shiri ne daga abokan gaban mahaifinta, dan yanzu faɗar ta koma ta siyasa, ba abin da zamu ce sai dai Allah ya kuɓutar da Jehan, mu dai je zuwa, komai zai warware a hankali, ku kasance da alkaramin Fateema Zahra Musa dan jin yadda zata kasance. A wani irin mahaukacin razane A'A ya miƙe tsaye, dan ABUBAKAR SALAHUDDEEN ba kowa bane face mahaifinsa da ya haifesa, AHMAD ABUBAKAR SALAHUDDEEN shi ne suke ce mishi A'A, miƙewa su Abba ma suka yi dan su taushe shi, saboda duk sun san mahaifinsa ne, miƙewa ita ma maman Ayla ta yi tana faɗin "Alhadulillah, Alhadulillah, Alhadulillah, Allah na gode maka da ka muna mini mutuwar Abubakar kafin na bar duniya, azzalumin, mugu, macuci, banso ka mutu a haka ba, na so ne ka mutu a walaƙance, wanda ko kare sai ya fika daraja, bakin shaiɗani". Tana magana tamkar wadda ta zare, da alama farinciki ne ya yi mata yawa. Kwantar da Ayla a hankali daddyn Jelly ya yi tare da miƙewa yana faɗin "Mama lafiya me yake faruwa,? Menene tsakaninki da Abubakar kuma?". Nisawa ta yi tana ta uban murmushi wadda tun da ta zo gidan bata taɓa yin shi ba "Abdul Malik wannan Abubakar ɗin da kake gani ba mutun bane, shaiɗan ne yazo a siffar mutun, ba kuna tambayata waye uban Aliya ba,? To shi ne, shi ne uban Aliya". Tashin sense da ba'a saka miki date. Nan take kallo ya dawo kanta, gabaɗaya palo suka zuba mata ido, Ayla baiwar Allah sai zuba barci take yi, bata san me yake faruwa ba. "Shi ne mahaifin Ayla kuma?" Cewar Abbi, "Kwarai kuwa shi ne uban Aliya, babu wata tantanma, bakin azzalumin, ai naso Aliya ta girma ta kai mishi kanta da kanta ne, idan ya isa yanzu kuma ya ce ba yarsa bace, ai da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, da ya tashi bani ita sai ya bani ita kaman uban nata sak, babu in da ta baro shi, lokacin da take cikin cikina, ya ce ba cikinsa bane, ni kuma nasan ba mazinaciya bace, ban taɓa zina ba sai da shi, bayan shi ni ban taɓa kusantar wani ɗa na miji ba, nasan cikinsa ne, amma ya ce ba nashi bane, ya barni cikin bakin azaba da wahala, saboda son kai irin nasa, to ga shi yanzu babu wanda ya isa ya ɗaga idanu ya kalli Aliya ya kuma kalli Abubakar ya ce ba ubanta bane, kama harta idanunsa bata bari ba". Tana magana tana murmushi yau zuciyarta fari tas. Cikin dakiya Abbi ya ce "Dan Allah ki yi mana bayani dallah dallah yadda zamu gane, ya akayi ya zama mahaifin Aliya? Kun taɓa yin aure da shi ne?". Dariya ta yi kamar zautatciya, da alama ta cutu sosai na abin da ya yi mata, da alama yau farincikin ya zautar da ita baiwar Allah, bata jin komai yau sai murna, dan haka bata damu ba zata iya wangale komai yau, dan tasan ko bata faɗa yau ba, to dole gobe ta faɗa, dan dole mijin Ayla ya buƙaci jin tarihinta. Dan haka nan take ta buɗe musu aiki mai gabaɗaya "Ni ban taɓa yin aure ba, Aliya shegiya ce kuma ga ubanta nan a gabanku yanzu aka gama labarai a kansa, yanzu ni bana jin komai a raina, ko yanzu na mutu hankalina ya kwanta, ABUBAKAR SALAHUDDEEN bakin azzalumin, kune kuke kallonsa kamar mutumin kirki, saboda ya sanya fatar ɓauna ya lulluɓewa duniya laifukan da yake aikatawa, da Abubakar da Farooq wlh ko sun tuba sai sun ɗanɗani azaban Allah, dan kuwa akwai da yawan al'umma da suka mutu ta sanadiyarsu, waƴan nan azzaluman guda biyu, wlh sai Allah......" Bata kai karshen maganar ba A'A ya ɗaga hannu zai zabga mata mari, cak ta riƙe hannunsa tana kare mishi kallo. "Saboda ina faɗar gaskiya a kan ubanka shi ne zaka mare ni? To kai kanka ka kalli kanka da kanka ka kalli Aliya dake kwance tana barci zaka iya banbanta fuskarka da tata ne? Bari ka ji idan kayi kuskuren marina, wlh, wlh, wlh, sai na kwantowa gabaɗaya juri'arku ruwan da ba zaku iya tsayar da shi ba, wlh sai na bankaɗo dukka laifukan ubanka da ɗan uwansa wa duniya, sai ya zama baku da idanun fita ku kalli jama'a saboda kunya, wasunku ma bakin cikine zai kashe su, idan kuma kace ba haka ba to Bismillah zaka gane shayi ruwa ne wlh, dama na rufe ne dan saboda kada ya kashe mini ƴa ta, na ɓuya ne dan kada ya kalli Aliya ya kasheta, shiyasa ban fito na nunawa duniya ɓarnar da suke yi ba, amma yanzu kabi a hankali!!". WANNAN SHI NE TASHIN HANKALI, BABBAR MAGANA. Wani irin azababben kululun bakin cikine yasa A'A zubewa kasa tamkar gawa baya numfashi, kansa su Abbi suka yi suna ambatar sunansa, amma ina ko motsawa bai yi ba, ruwa Irfan ya ɗauko mai sanyi a fridge ya zo ya zuba mishi, amma ina ko motsi bai yi ba, daga karshe dai suka kwashe shi zuwa asibiti dan ceto rayuwarsa. Ita kuma maman Ayla sama ta haura ta nufi ɗaki abinta, dan yau zuciyarta fes, Aunty kam taga tashin hankali yau, Hanan kuwa tun da aka fara hayaniyar ta bar palon, ta koma bedroom nata, dan bata son hayaniya ita ma,. Yanzu babbar abin tambayar a nan shi ne, a ina maman Ayla ta san mahaifin A'A? Menene yasa kuma ya ce ba cikinsa bane? Akwai lauje cikin naɗi, amma muje zuwa, zata warware mana komai ta bamu labarin yadda akayi komai, yanzu dai bari mu leƙa gidan Lion dan ganin wani hali suke ciki, wata kila kafin mu dawo wannan family sun ɗan sami kwanciyar hankali. Misalin karfe 8 na safe, shirye suke cikin shiga iri ɗaya, sai dai wandon Areef ya fi shiga kalar brown sosai, na Aseef ya yi light, zaune suke a garden da alama dai shirin zuwa wani wajen suka yi, zubawa Aseef dara daran ash eyes nasa ya yi yana kallon yadda fuskarsa take wani kyalli, da alama yana cikin farinciki over, sai aikin latsa waya yake yi. "Wai Aseef yana ga sai wani fresh kake yi ne? Seriously Naija ta karɓeka kai da Lion, sai wani kyalli face naka take yi, zo ka gaya mini me sirrin ne?". Bai ɗagoba, yana ta faman aikin latsa waya, sai murmushi yake yi Heartbeat ta yi kira. "Kana ji Areef, Heartbeat ce ta yi mini ciki, shiyasa kaga nake wannan kyan". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa dan Akila ta ce yazo yanzu. Areef ya gama fahimtar tun da Aseef ya fara soyayya ya dawo mara mutunci, da an yi mishi magana zai shere mutane, ko kuma ya mayar musu da amsar iya shege, yanzu me na wani cewa wai heartbeat ce ta yi mishi ciki daga tambaya? Gaskiya abin da ban haushi. Yana can yana tunani sai ya ji tashin motar ɗan uwan nasa, alamar da gaske barin gidan zai yi, tafiya zai yi kenan, miƙewa ya yi da sauri ya nufe shi dan tare zasu je su gaida Ammie ya kalli heartbeat ɗin shi ma. Lokacin da ya isa wajen, Aseef ɗin ya kashe motar ya fito zai nufi cikin gida, "Ina kuma zaka je mu tafi mana?" Ɗan juyowa ya yi yana faɗin "Yauwa Areef zo dan Allah, zo muje ka kallah wani abin". Ba musu ya bi bayansa, kai tsaye ɗakin da Jehan take suka nufa, ita kuma Rimsha, sai zuba barci take yi abinta, shi ma Lion haka, da alama dukkansu a tsananin gajiye suke. Da sallama ya shigo cikin ɗakin, tana zaune a bakin gado ta farka, tun da Areef ya ɗaura idanunsa a kanta ya ce tabbas gaskiyar Aseef ne, duk yadda aka yi wannan jinin Uncle Hosain ce, akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu, dan kamar ta yi yawa, amma bari su je wajen heartbeat su dawo, tun da Rimsha tana nan zata warware musu komai ai. Sannu suka yi mata, sai binsu da idanu kawai take yi, tana mamakin me kuma ya kawota gidan Turawa? Ko dai a kasar turai take ne? To yaushe a ka kaita can? Iya saninta a Nigeria take. Ganin taki yin magana ne yasa Areef ya ce "Kila bata magana ne, yanzu dai muje mu dawo, zan gayawa sister ta kula da ita kafin mu dawo sai mu san abin yi". Okey Aseef ya amsa, ya kuma ji matsananci daɗi da Areef ya yarda da cewa tabbas tana da alaƙa da uncle ɗin su, ya yi murna da hakan, juyawa suka yi suka fice daga ɗakin zuwa na Rimsha, ganin sai zuba barci take yi ne yasa Areef ya rubuta massage a wayarta a kan idan ta tashi akwai bakuwa dake ɗakin Imran, ta ɗan taimaka mata kafin su dawo, daga haka suka nufi waje dan su je wajen heartbeat, Lion kuwa tare suka yi sallar asuba da shi, dan haka sun san yana lafiya yana barci, sai ba su shiga ba bare su tashe shi suka wuce. Sai misalin karfe 9 Rimsha ta farka daga barcin gajiya da take yi, da kyar ta sauko kasa ta nufi toilet dan yin wanka. A gurguje ta yi wanka tare da shiryawa cikin kananan kaya ta fito da nufin ta duba su Areef dan su ci abinci yunwa take ji, ganin babu kowa a gidan ne yasa ta dawo cikin ɗaki ta ɗauki wayarta dan ta kira Areef ɗin, a nan ne ta ci karo da sakon da ya ajiye mata na bakuwar da suke da ita, fasa kiran nasa ta yi ta ce bari ta fara duba bakuwar tana zuwa, fitowa ta yi ta nufi bedroom ɗin. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga, a sukawane ta sanya hannu tana murje idanunta dan ta tabbatarwa da kanta abin da take kalla gaskiya ce ko ba gaskiya bace, ita ma Jehan ɗin a razane ta miƙe tsaye tana mai murza idanunta dan ta tabbatarwa da kanta ba mafarki take yi ba. "Jehan". Rimshar ta ambaci sunanta, tare da tafiya da gudu ta rungumeta, ita ma rungumeta sosai ta yi suka shiga kewaye ɗakin suna ruwan hawaye. "Rimsha dama kina raye?" Ta faɗa tana kwallah. "Ina raye Jehan, ina raye, dama kema kina nan Kaduna? Shi ne Sadiq bai gaya mini ba". "Rimsha bana Kaduna, dogon labarine zan baki daga baya, yanzu dai ina su mummy?" Ta yi maganar tana raba jikinsu. "Ban san in da suke ba, daddy kawai na san in da yake". "What daddy kuma?!!" Ta faɗa tana zaro idanu kamar zasu faɗi kasa, "E Jehan daddy, yana nan, yana raye bai mutu ba". Zata yi magana kenan suka ji jiniyar motocin ƴan'sanda ya karaɗe ko'ina a cikin anguwar, da alama jiga jigan ƴan'sanda ne, da alama kuma suna da yawa, dan motocin nasu manya ne, jiniya ya karaɗe ko'ina tamkar filin yaki suka nufa, kallon juna suka yi, "Zo mu je waje mu gani menene". Cewar Rimshar, da yake Jehan bata da tsoro ko kaɗan a fili, ga karfin hali da dakiya sai ta bita suka nufi waje dan suga menene. Daga bakin kofar palon kasa suka tsaya suna hangen gate ɗin gidan, amma kafin su fito sai da Jehan ta sanya doguwar rigar Rimsha, dan idan baku manta ba, ba wani kayan arzikine a jikinta ba, daga three quarter sai ƴar vest, shiyasa ta ce ba zata fita a haka ba duk da bata san su waye ne a gidan ba, sai da Rimsha ta ɗauko mata doguwar rigarta ɗaya, ta sanya sannan suka nufo wajen. Can suka hango gateman yana dirama da ƴan'sandan a kan lallai ba zasu shigo cikin gidan nan ba, su kuma sun kafe sai sun shigo, daga Rimsha har Jehan basu san menene yake gudana ba, garama Jehan bata yi mamakin ganin ƴan'sadan ba. Waya gateman ɗin ya yi wa Lion da ƴan'sandan suka matsa, a lokacin shi ma ya tashi daga barci, ya fito daga wanka kenan, yana tsaye a gaban mirror ɗaure da towel a kugunsa, umarnin ya bawa gateman ɗin da ya bar ƴan'sandan su kama yarinyar tun da a kan aikinsu suke, shi yasan menene doka, dan sune doka, sune suke tsawatarwa da abi doka, tun da sunce kisan kai ta yi to su kamata, kuma sai ya ji dalilin da yasa su Aseef zasu kawo mishi mai laifi gida. To fa kada ku ga laifinsa, a kan dai'dai yake, doka ce dole a matsayinsu na masu doka su girmama dokan kafin na kasa da su subita, ba zai ce kada su kamata ba tun da shi bai san wacece ita ba, bai kuma san gaskiya a kan me ya faru ba, kuma kunga news ɗin da suka baza a gari a kan daɓa wa ABUBAKAR SALAHUDDEEN ɗin wuka ta yi a ciki, kuma ko su Aseef ne zasu yarda da yes ta daɓa mishi ɗin, dan kuwa a kan hanya suka ganta ana binta, basu san daga ina ta fito ba, sai dai idan sun yi bincike mai tsanani ne suna iya gane gaskiya, amma yanzu dai duk yarda zasu yi akan abin da ta yi kenan, babbar magana. WANNAN ABIN DA ƊAURE KAI YAKE AMMA MUKE ZUWA, DAN JIN DALILIN DA YASA AKA JUYA LABARIN YA KOMA KARYA, SUKA BINNE NA GASKIYAR. Shigowa police biyu suka yi, mace ɗaya namiji ɗaya, in da su Jehan suke tsaye suka nufa, ko motsi Jehan ɗin bata yi ba, babu kuma alamar tsoro ko ɗigo a ranta, ita kuwa Rimsha ta tsorata sosai, sai ambatar sunan ta take yi tana tambayarta ko lafiya, su koma cikin ɗaki, amma ina ko motsawa Jehan ɗin bata yi ba, kamar wadda ta taki wata tsiya. Kamata macen ta zo ta yi tana faɗin "Wuce mu tafi". Kankameta Rimsha ta yi tana kuka tana faɗin "Dan Allah kada ku tafimin da ita, wlh bata aikata laifin komai ba, dan girman Allah ku sake mini ita, wayyo Allah na, nashiga uku, daddy kazo ka hanasu tafiya da Jehan, zasu tafi da ita". Jehan ɗin kuwa, ko a jikinta tamkar ba ita ba, kamar bata san hukuma ne suka zo kamata ba, tsakaninta da Allah Rimsha take kuka kamar ranta zai fita, haka suka tafi da Jehan ɗin tana ji tana gani, da gudu ta koma cikin gida ta ɗauki wayarta dan ta kira su Areef ko daddynta, har wani jiri take gani, dama ga yunwa. Number Areef ta kira, bugu ɗaya ya ɗauka, a haukace ta kasa natsuwa ta fara gaya mishi abin da yake faruwa, zaro idanuwansa ya yi yana tambayarta dama tana da sister ne? Kenan gaskiyar Aseef da ya ce Sister ta ce?. Muryarta na rawa ta gaya mishi e tana da sister, su biyu daddy ya haifa, cikin kwanciyar hankali ya ce "To ya isa haka kuka, ba dai ƴar uncle bace? To kada ki ji komai dole ma su dawo da ita, bari na dawo muyi magana da Lion, wai laifin me ma tayi musu ne?" Da kyar ta iya furta "Ban sani ba, ban sani ba yaya Areef, kawai sun tafi da ita ne, kuma nima basu gaya mini abin da ta yi musu ba". "To shikenan ya isa ki kwantar da hankalinki, ina nan juyowa yanzu, na ma fasa zuwa wajen Heartbeat ɗin, Aseef zai je shi kaɗai, bari na hau abin hawa na dawo". Okey ta amsa mishi da shi, katse kiran ya yi dan baya son jin kukanta, Allah sarki bawan Allah. Ɗaura wayar saman bedside drawer ta yi tare da kifa kanta da jikin gado tana mai cigaba da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, duk da ta yarda da Areef, tasan idan ya ce abu to zai aikata, sai dai hankalinta ya kasa kwanciya ne dan tasan idan Lion bai bada goyon baya ba, shi ma Areef ɗin dole ya hakura, abin da bata sani ba shi ne, His excellency dukkansu kakansu ne, suna da damar su ce mushi ga abin da suke so ya yi musu, sai dai wani hanzari ba gudu ba, abin da ya shafi doka, shi kanshi his excellency sai ya nemi jin ta bakin Lion, sai abin da ya yanke zasu yi amfani da shi, babbar magana, akwai kura fa....... A wannan hali Areef ya shigo ya sameta, ko kaɗan bai ji daɗin ganin tana kuka har haka ba, rarrashinta ya fara yi tare da yi mata alkawarin kada ta damu dole sisterta zata fito da izinin Allah, amma bari ya yi magana da Lion zai je police station ɗin yanzu da kansa dan ya ji laifin da ta aikata da har zasu kamata, idan ma laifin babba ne to ya yi mata alkawarin zai tsaya tsayin daka ya yi bincike a kan case ɗin sai in da karfinsa ya kare, ma'ana sai in da hujjojinsa suka kare, dan yasan Lion ba zai taɓa tallafawa rashin gaskiya ba, duk wuya duk daɗi yana bayan gaskiya.... TOFA GASKIYA A WANNAN LAMARI BINCIKO GASKIYA BA KARAMIN WAHALA BANE A WAJEN AREEF, DAN JEHAN BATA DA SHAIDAR BA'A KAN HANYA TA KASHE ABUBAKAR SALAHUDDEEN BA, KUMA SUN ƊAURETA TA YADDA FITA ZAI YI MATA WAHALA, DOLE TA KAWO SHAIDAR A GIDA TA KASHE SHI GA KUMA DALILINTA, SAI DAI KUNA GANIN JENAN ZATA IYA DA WANNAN SHARI'AR? ZATA IYA KAWO SHAIDAR KUWA? Da kyar ya lallaɓata ta yi shiru, miƙewa ya yi ya nufi bedroom ɗin Lion,. Zaune saman sofa ya isko shi yana....... ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E45-46💋 Da kyar ya lallaɓata ta yi shiru, miƙewa ya yi ya nufi bedroom ɗin Lion,. Zaune saman sofa ya isko shi yana latsa waya, kusa da shi ya zauna, cike da kulawa ya ce "Good morning". Shiru bai amsa mishi ba, dama ya san ba amsawar zai yi ba, dan haka sai ya cigaba da cewa "Zanje police station na dawo". Jinjina mishi kai ya yi alamar okey ya ji, "Idan na dawo zamu yi magana da kai". Nan ma jinjina mishi kai ya yi, ya kuma barshi ya shiga case ɗin ne dan ya gano Jehan ƴar Nawazudden ce, sai dai ko da take ƴarsa idan har bata gaskiya, to shi babu ruwansa, ba zai shiga rigimar ba, yanzu kuma ba zai yi bincike a kan case ɗin nata ba, dan a kan na babanta yake har yanzu tukunnan, da saura bai kammala ba, wani sabon babi ma ya buɗe a kan binciken nasa, idan baku manta ba, baya haɗa abubuwa biyu, ko wanne da lokacin yinsa, idan ya fara sai ya kammala yake capko wani, shiyasa bai damu ba dan Areef ɗin zai shiga, saboda shi ba zai shi ga ba sai ya gama wadda yake kai, ya kuma lura ana son nunawa yarinyar fin karfi ne, shiyasa ya kyasu da Areef ɗin. "Me yasa ka yin faɗa jiya? Kuma da waye kuka yi faɗar?" Ya yi maganar ba tare da ya ɗago da kallonsa ba, "Waƴan da suka biyo yarinyar ne suka nemi yi mini ba dai'dai ba, shi ne na taka musu birki". Shiru ya yi tamkar ba zai sake yin magana ba, can kuma sai ya ce "Yana da kyau ka dai'na wasa da ciwon nan naka, ka san me zai iya biyowa baya idan har baka bari wajen nan ya warke ba, wajen zai iya ci ya tafi kai tsaye ya huda zuciyarka, yana da kyau ka kula sosai". Jinjina mishi kai ya yi, dan shi ma ya sani, tabbas idan ya yi wasa da wannan ciwo, to rayuwarsa tana cikin babbar haɗari, sai dai fa ko mutuwa zai yi sai da ya mutu amma babu wanda ya isa ya taɓa Aseef a duniyar nan ya kyale shi, da wani suka daka zai iya kawar da kai, amma Aseef ba zai taɓa yiwuwa ba, sun mari kyakkyawa kuma lallausan fuskar da bata taɓa shan mari ba, da yake shi Areef ɗin bai san da cewa Lion ya taɓa marin Aseef ɗin ba, so yana ganin ai babu wanda ya taɓa kusantar wannan kyakkyawar fuska ko da sunan wasa da sunan zai mara. Miƙewa ya yi tare da mannawa Lion ɗin sumbata a kumatu yana faɗin "Zamu je da Mark". Jinjina mishi kai ya yi tare da mai do mishi da martanin sumbata shi ma, kai TRIPLETS suna kaunar junansu na wuce misali wlh. Waje ya nufa, kafin ya fita sai da ya sake komawa ɗakin Rimsha dan ya sake rarrashinta, nan fa ta kafe mishi a kan lallai sai ta bishi sun tafi tare, ba yadda ya iya, in dai yana son farincikinta to dole ne ya tafi tare da ita. Hannunta ya kama suka nufi palon kasa, a kitchen ya isko Mark, nan ya sanar da shi zai jasu zuwa police station mafi kusa, okey ya amsa cikin girmamawa yana risinar da kansa kasa. Kai tsaye police station na kusa da su suka nufa, ita da Areef a gidan baya suka zauna, sai kwantar mata da hankali yake yi yana karfafa mata gwiwa a kan kada ta damu lallai Jehan ɗinsu zata fito, ɗan kwantar da kanta a kafaɗarsa ta yi tana lumshe idanu tare da shaƙar daddaɗar kamshin perfume nasa, hannu yasa ya ɗan shafa lallausan kumatunta yana faɗin "Sarkin saurin kuka, ya kamata ki zama jaruma, ke da kike da ni, ai bai kamata ki shiga damuwa dan ƴan'sanda su kama sisterki ba, kin san dole zan tsaya mata tun da ƴar uncle ce, ni kuma ki ɗauke ni tamkar Lion, dan in na tsaya dole Lion ya hakura shi ma ya tsaya, dan ba zai iya ganina cikin damuwa ba, ni kuma ba zan iya ganinki a cikin damuwa ba". Da irin waƴan nan daɗaɗan kalamai ya yi ta amfani wajen kwantar mata da hankali har ta saki jikinta sosai da shi. Ko da suka isa police station ɗin, ƴan'sandan suka sanar da su ba nan a ka kawo ta ba, tana sama da su, tambaya ya yi suka yi mishi kwatance ya kunna goggle map suka ɗauki hanya, sai dai kuma abin mamaki ko da suka je wajen sai aka ce musu bata nan an wuce da ita kai tsaye prison, dan ba ƙaramin laifi ta aikata ba, bai tsaya tambaya me ta aikata ba ya ce da Mark su je prison ɗin, wani ɗan'sandan ne ya sanar da shi ai ba za'a bar kowa ya ganta ba, ko kallon in da suke bai yi ba, dan bai ga uban da ya isa ya hana shi ganinta ba, waya ya yi wa Lion a kan yana son ganinta, ya taimaka ya shirya haɗuwarsu kafin su isa prison ɗin, da farko kamar ba zai yi ba, sai kuma tunanin kyautata musu da irin tsantsar kauna da daddyn Rimsha yake nunawa TRIPLETS nasa ta faɗo masa, ya kuma tuna irin Kaunar da TRIPLETS ɗin suke yi wa daddyn, hakan yasa ya amsa da okey tare da ciro waya kai tsaye ya kira president na Nigeria, dan yanzu Already sun san da yana cikin kasar, sun san shi ne ya zo, so mafiya yawan lokuta baya kiran His excellency a nan kawai yake shirya duk abin da yake so. Ko da suka isa prison da aka kai ta, wani ganduroba ne ya yi musu jagora zuwa ciki, sai mamaki Rimsha take yi, wai ba da ance ba za su sami damar ganinta ba? To ya aka yi da kansu suke yi musu jagoranci zuwa ciki kuma? Sai tambayar kanta take yi, bata san cewa duk da ba kasarsu bace suna da daman yin abin da ya fi ɗan kasa, saboda sun fito daga babbar kasa, kuma ga His excellency ai dole ma a yi musu abin da ya fi na ɗan kasa, sun fi ƴan kasa samun ƴanci. Office ɗin ogansu ya wuce suka zauna, idan ba dan su manya bane, yaushe za'ace yarinyar da ta kashe ɗan takarar shugaban kasa ace har wasu zasu iya samin damar ganinta, kai abin da abin mamaki. Har cikin office ɗin Mark ya bisu, dan hakki ne a wuyarsa da ya kula da Areef kada ya bari wani abin ya taɓa shi, saman doguwar kujerar dake cikin office ɗin Areef da Rimsha suka zauna, shi kuma Mark yana tsaye tamkar wani robot. Ba'a ɓata musu lokaci wajen fito da ita ba, da gudu Rimsha ta miƙe zata je wajenta, cikin sauri Areef ya riƙeta yana girgiza mata kai, shi tun daga farkon case ɗin ma ya fahimci akwai zalinci a ciki, na farko a kallon da ya yi wa jenan bata kai shakarun da za'ayi mata irin wannan hukuncin ba, na biyu yadda suka zuba mata tsaro kamar wata kungurumiyar ƴar ta'adda, na uku yadda suka wuce da ita prison kai tsaye tamkar dama jira suke yi su kamata, akwai wasu kananan dalili dai, amma waƴan nan sune manya, yadda case ɗin nata ya tafi ma sam ba tsari, dan sun yi abin ne a yunwacen suna son kamata, sai kuma suka fitowa da duniya hakan, mai basira tsab zai iya gane ina suka dosa, sai dai fa Areef bai damu sosai ba, dan yana ganin kamar mu kuma dokokin kasar mu ce a hakan kenan, shiyasa bai damu ba, ya fi son ya ji magana daga bakinta, dan ya yi imanin gabaɗaya jikin Nawazudden ba zasu yi karya ba, ya yarda da su, ya yi wa Uncle nashi kyakkyawar yarda. Kasan carpet dake wajen ta zauna, hannunta na sanye cikin sarka wadda ya tafi har kafarta, shiru Areef ya ɗan zubawa sarkar idanu yana kallonsu, shi dai ya san gunguma gunguman ƴan ta'addan kasa da kasa suke ɗaurewa da irin wannan sarka, amma an tashi an lafkawa ƴar yarinyar da bata wuce goyo ba a cewarsa. Wani ganduroba ɗaya daga cikin waƴan da suka fito da ita ne ya ce "Sir kuna da only 10 mins". Bai bi ta kansu ba, dan bai ga uban da ya isa ya saka mishi time a rayuwarsa ba, idan suka yi wasa ma sai ya ce ba zai bar nan ba sai da ita ya ga karshen iskanci, idan ya ce lalllai ba zai tafi ba sai da ita, ai dole Lion ya zo, kuma dole His excellency ya saka baki, dan sufa kasar American tsuntsuwar kasarsu ma ranta na da muguwar daraja bare kuma mutun ɗan cikin kasarsu, mutun ɗin ma jika ga His excellency ai dole ma su tursasa kasar Nigeria a bawa Areef Jehan dan ya bar wajen kada wani abin ya same shi, amma ba zai yi hakan ba, dan yasan doka kuma ba zai taka ba, saboda suke faɗa kullum abi doka, suke kama masu karya doka su hukunta, to idan su basu bi ba, waye zai bi kenan? Ai kowa ma take dokar zai yi, idan ba doka kuma ai ba al'umma. Cikin sanyin murya ya tambayeta ya sunanta, kin magana ta yi, tamkar bata ji shi ba, sai kallon kasa take yi abinta, kallon Rimsha ya yi yana faɗin "Our Queen bata magana ne?" "Wlh tana magana yaya Areef, bari ka ji na tambayeta". Sauƙowa kasan ta yi kusa da ita, tana hawaye ta fara magana tare da riƙo hannunsu cikin na juna "Jehan dan Allah ki yi mishi magana, ki gaya mishi gaskiyar abin da ya faru, wlh zai taimaka miki, kinga shi ya taimaka mini ya kuma taimakawa daddy, nasan kema ba zai barki ba". Jin ta ambaci daddy yasa Jehan ɗin ɗago dara daran idanunta da suke farare tas babu ko alamar ɗigon hawaye, suna bushe garau kamar bata san me ake tuhumarta da shi ba, har wani haske idanun nata ma suka kara, shi kansa Areef ya sha ruwan mamaki dakiya irin nata, gata yarinya karama, ga ta a prison, sannan jikinta duk ya sha sarkuna a ɗaure kafa da hannu, amma a haka ko a jikinta, bugu da kari gata mace, abin dole a jinjina mata, kuma ayi mamaki, idan da wata mace ce ai ta rinƙa ihu kenan ganinta a hannun hukuma. Shi ma dai sauƙowa ya yi dan ya kama Rimsha ta dai'na kuka, mamaki ne ya kama Mark yadda Areef yake bala'in kaunar su Rimsha, ko a mafarki bai taɓa tunanin ɗaya daga cikin TRIPLETS zai yi hakan ba, ya sauƙo ya zauna a saman carpet sabida Rimsha, abin dole ga wadda ya sansu a baya ya yi mamaki over. "Jehan wlh daddy ya yarda da shi sosai, ki yi mishi magana kin ji". Cewar Rimsha, kuma da harshen Hausa ta yi maganar nata, jinjina mata kai Jehan ɗin ta yi alamar to. "My name is Jehan Nawazudden Salman Sultan". Ta bashi amsa, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke dan kuwa har voice nata sak na daddynta ne, babu in da ta baro shi, hannun Rimsha ya kama suka koma saman sofa suka zauna, baya son ganinta tana kuka. "Okey Jehan zaki iya gaya mini a kan wani laifi suke tuhumarki da kuma gaskiyar abin da ya faru". Ba musu ta gaya mishi a kan laifin kisan kai suke tuhumarta da shi, ba ƙaramin tsorata Rimsha ta yi ba, shi dai Mark ya zuba musu idanu ne yana kallon ikon Allah, Jehan na magana kamar wata babbar jarumar soja, babu tsoro ko ɗarɗar a muryarta, kai tsaye ta ce kisan kai lallai. "Okey to da gaske kece kika yi kisan ne?" Jinjina mishi kai ta yi alamar e ita ta yi, Rimsha bata san lokacin da ta kurma ihu ba, da karfi ta ce "Wlh karya ne, ni nasan wacece ƴar uwata, tana da faɗa sosai, amma wlh ko kaza ba zata iya kashewa ba, karya ne". Rungumota Areef ya yi yana ƙoƙarin miƙewa dan komai ya lalace tun da Jehan ta amsa da bakinta ita ta yi kisan, shikenan kuma. Har zai miƙe sai kuma ya koma ya zauna yana karewa Jehan ɗin kallo, yarinyar nan ko a jikinta wai an yakushi kakkausa. Mark ne ya yi gyaran murya cikin girmamawa ya ce "Sir am sorry to say amma wannan yarinyar ba ita ta yi kisan nan ba, ko da ita tayi to akwai dalili mai karfi ko kuma by mistake ne". Jinjina mishi kai ya yi alamar ya gamsu, shi ma ya yi tunanin hakan shiyasa ya fasa tafiya ya dawo ya zauna, cikin sanyin murya ya sake tambayarta ko zata gaya musu ya akayi ta yi kisan, nan ne kuma Rimsha ta yi shiru ta nitsu tana son jin ta ya akayi hakan ta faru. Ba musu ta gaya musu tsab, sai dai bata gaya musu daga ina ya ɗauko ta ba, ta dai ce musu ya ɗaukota ne da nufin ya yi mata fyaɗe ya kai ta gidan shi, shi ne ita kuma ta yanke bananarsa, dai'dai lokacin da ta furta ta yanke bananan nan, gabaɗaya gandurobobi uku dake wajen sai da suka sanya hannu a gabansu dan su ji nasu yana nan kam ko, harta shi kan shi Mark sai da ya sanya hannu a saitin gabansa yana mamakin karfin hali irin na yarinyar nan, har zata iya kallon gaban babban namiji ta saka wuƙa ta yanke?, Wannan da horon sojoji ta samu ba karamar soja mara imani za'ayi ba a duniya, sai ta kafa tarihi a duniyar hukuma, wai ta yanke, ko a jikinta ta faɗa kai tsaye, Areef bai taɓa shan ruwan mamaki irin na yau ba, suna hukunta masu yin fyaɗe ta wannan hanya na yanke musu gaba, amma ita fa mace ce kuma yarinya karama, abin ya bashi mamaki sosai, bare ma yadda ta faɗi komai dallah dallah a nitse cikin kwanciyar hankali, ita kam Rimsha tsit ta nasu ta ji abin da ya goge mata lissafin ƙwaƙwalwa yau, lallai jenan ta wuce tunanin mai tunani. Gyaran murya ya yi, lokacin guda kaunarta ya shiga ransa, yana bala'in son mutun jarumi mai dakiya, son gaskiya, adalici da taurin zuciya, mai ƙoƙarin kare kansa a koma ina ne, shi abin da Jehan ta yi, ta yi mishi dai'dai, hakan kuma yasa ya ji sonta a cikin zuciyarsa, ta burge shi ba kaɗan ba. "Lokacin da abin ya faru, waye da waye ne a cikin gidan?" Nan ma ba musu ta bashi amsa tare da ɗaura mishi da cewa ai ƴan'sandan ne suka biyota shi da Aseef suka bugeta da mota, sai yanzu ya gama fahimtar case ɗin ma, ashe da bakin hukuma mutumin yake lallata ƴaƴan mutane, a dole dama su yi wa Jehan irin wannan sharri, dan idan gaskiya ta fito, har su kansu hukumar sun shiga uku, dan sune masu tsaron mutumin ai. "Okey tom ba damuwa zan sake dawowa zuwa anjima or gobe dan in yi miki wasu tambayoyi". Ya bata amsa tare da miƙewa ya riƙo hannun Rimsha, binsu da ido ta yi, har ya ɗan yi gaba sai kuma ya dawo ya tsugunna a gabanta tare da riƙo haɓarta ya ɗan ɗago suna fuskantar juna, "Kyakkyawa mai kama da uncle na, ki kula sosai dan nikam na samu jarumar sister". Ya faɗa tare da miƙewa, kun san shi dama da wasa da dariya idan ya yi niya, harara ta wurga mishi, kashe mata ido ɗaya ya yi yana ɗan murmushi, jawo hannun Rimsha ya yi yana faɗin "Muje hai sister, wannan mai kama da uncle ɗin mafaɗaciya ce sosai". Rufa musu baya Mark ya yi, ita kuma Jehan suka mayar da ita cikin prison ɗin. Suna tsaka da tafiya Mark ya ce "Sir is seeing like this girl bata kai 19 years da suka faɗa ba, amma how comes suka ce she is 19 years old?" Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da cewa "Dukka maganganu ma da suka faɗa ai ba gaskiya ba ce, i really trust my uncle, ni nasan family'nsa ba zasu yi karya ba, na fi yin aiki da kawa zucina fiye da abin da naji kuma na gani, wani lokaci zaka ji karya kuma ka ga karya, amma shi kawa zuci gaskiya yake zayyano maka, duk abin da Jehan ta faɗa shi ne gaskiya, kawai sun juya maganar ne saboda wani dalili nasu da ban yi tunani a kan shi ba, sai dai kuma ina tunanin sun ce she is 19 years old ne dan idan an je court su yanke mata hukuncin kisa, or something like this, dole ma akwai makarkashiya a wannan case ɗin, dole shirya kasheta aka yi, da yuwuwar dama an jima ana farautarta, abune wadda yake a bayyane ga mai ƙwaƙwalwa, zai iya gane ina aka dosa, amma zan yi ƙoƙarin wajen ganin na duba case ɗin, sai dai fa zasu yi saurin kaita court, dan idan ka lura komai da suke yi, suna yin shi ne best on they are on choice, ba wai doka suke bi ba, so zasu kaita court da wuri dan a yanke mata hukunci, kuma ka zuba ido ka gani, ita kanta court ɗin zata yi saurin kula da case ɗin, za kuma ta yi saurin yanke mata hukunci, saboda an shirya hakan, a nawa ganin kamar uncle yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sanya aka kullah mata wannan sharrin, amma bari mu koma zan yi binciken wai shin da waye da waye ne ma uncle ya tsaya takara a lokacin da yake neman mulki, dole da sa hannun manya, akwai dai wani abin gaskiya". "Amma sir if that is the case, i think za su yi kokarin kasheta a prison ɗin ma, because na lura yarinyar bata da tsoro ko kaɗan, idan suke je court zata iya faɗar gaskiya, kuma da alama ba zata ji tsoron barazana ba idan aka yi mata". Jinjina kai ya yi yana faɗin "Yes ba zata ji tsoron barazana ba, and then ba zata yi magana a court ba, saboda bata da hujja, kuma kasan abin an shirya mata gadar zare ne, duk ta yanda zasu yi suga bata yi magana a court ba, za su dan su rufe bakinta, kuma dai ita ma ba zata yi ba, tana da ilimi, she knew what she is doing, tasan ba'a magana a court matikar babu hujja, batun kasheta a prison kuma, ba za su yi hakan ba, saboda yin hakan da za su yi, zai iya tona musu asiri, ina da yakinin akwai abin da suke son cinmawa ne, akwai abin da suke son nunawa duniya game da uncle da kuma family'nsa, amma koma me ne zan duba na gani, ai idan sun san wata basu san wata ba, daga ta sama zan biyo musu, bari dai na bincika na tabbatar da gaskiyar ta duk da bana shayi a kan nata, amma zan duba". Shiru suka yi, Mark ya nitsa cikin nazari da tunani a kan case ɗin, shi kuma Areef yana tunani a kan kyakkyawar fuskarta mai kama da daddynta, dan shi wannan case ɗin ko kaɗan bata dame shi ba, yasan cewa dole ma sai sun saketa dan ubansu, ko suna so ko basu so, amma yana son ya bi komai ne bisa doka, baya son taka doka, ba dan haka ba ai da tuni ya karɓata. A ɓangaren Aseef kuwa, kai tsaye cikin gida ya shiga da motarsa, dan heartbeat ta ce ya shigo, tana tsaye a window ɗakinta tana kallon shi, waya ya ɗauko ya kirata a kan ya shigo, cikin zolaya ta ce ya kalli sama, da sauri ya ɗago kai yana kallonta, cool murmushi suka sakarwa junansu kafin ta ce mishi tana zuwa, sai kuma ta katse kiran ta nufi kasa. A palo da isko Ammie, cike da murna ta sanar mata da Heartbeat ya iso, okey ta amsa mata tare da ce mata to ya shigo mana, sai murmushi take yi ta nufi wajen nasa. Tun da ta fito ya tsareta da idanu yana kare mata kallo, sai yanzu yake ganin tsantsar kamanta da Jehan da ya baro a gida, dan shi bai san an kamata ba, Areef bai gaya mishi ba, ya ce mishi dai zai je gida ne kawai, ganin kamanninsu yasa ya kara yardanwa kansa da lallai Jehan ƴar uwar uncle ce, duk yadda aka yi akwai alaƙa ta jini, to kunsan fa kowa da yadda yake kallon mutun, shi dai Aseef ya ga kamannin Jehan da AKila, amma ba lallai ya zamana suna kama sosai kamar yadda ya gani ba, jini ne kawai da ko'ina baya ɓuya. Sai da ta kariso kusa da motar kafin nan ya fito yana sakar mata kayatatcen murmushi, "Good morning my shagwaɓati". Ta faɗa tana Murmushi, tsareta ya yi da idanu bai yi magana ba, tana sanye da abaya mai bala'in kyau launin maroon color, ta yafa mayafin nata a kanta, kafarta na sanye da plat shoe kalar kayan nata, simple make up ta yi, ta yi kyau over. "To me kuma kake ta wani kallona?" Ta yi maganar a shagwaɓe tana turo baki. Nisawa ya yi kafin ya ce "Sarkin rigima, to ɗago ki kalleni" Make mishi kafaɗa ta yi tana wasa da ƴan ƴatsun hannunta, "Ba zaki ɗago ba?" Kai ta gyaɗa mishi alamar e, hannu yasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, runtse idanunta ta yi tana mai jin kirjinta na bugawa da sauri sauri kamar ya ce zai yi mata wani abin. "Shi ne kika rufe ido?" Gera ta ɗaga mishi alamar e, hannunta ya riƙo cikin nasa ba tare da ya saki haɓar tata ba "Me yasa ne kika ciki rigima?" Turo baki ta yi tana faɗin "Me yasa kai kuma ka cika shagwaɓa ne?" Ɗan rankwafowa kaɗan ya yi a kanta, kasa kasa ya ce "Wai bana ce ki dai'na turo mini ɗan bakin nan ba? Ko so kike yi na sha kaya na ne?". Cikin sauri ta waro idanunta waje sai cikin nasa, murmushi ya saki yana faɗin "To ba ga shi yanzu na sanya kin buɗe idanun ba, sarkin rigima kawai". Ya kai karshen maganar tare da sakin haɓar tata yana murmushi, wani irin harara ta masoya ta wurga mishi tare da kwace hannunta daga cikin nashi tana ƙoƙarin juyawa ta bar wajen. Cikin sauri ya riƙo hannun nata yana faɗin "To yanzu kuma me nayi da za'ayi mini rigima? Kin san fa jiya kin saka ni ciwon kai, Allah kin iya rigima sosai Heartbeat, idan Areef yasan kina sakani ciwon kai ba zai kyale ki ba, sai ya baki punishment, sai dai ni kuma ba zan yarda ba, da a hukunta mini ke ai gara a zaneni". Wani irin shock ta ji lokacin da ya matse hannun nata a cikin nasa yana magana, buɗe tafin hannunta ya yi yana shafawa a hankali kamar mai murza mata mai, yana yi yana magana cikin kwanciyar hankali abinsa. "Kazo muje ka gaishe da Ammie tukun nan". Tsareta ya yi da idanu yana kallon lallausan lips ɗin nan nata, har ga Allah suna burge shi, kuma yana son yi mata kiss, amma saboda ya girmama al'adun Hausawa yasa ya daure, ya jure dan farincikinta. "To ni Heartbeat ki bari mana na kalle ki sosai kafin mu shiga ciki". Ya yi maganar a shagwaɓe sosai. "Kai ko". Ta faɗa tana kama yatsun hannunsa da yake murza mata fatar cikin tafin hannunta da shi, "Wai kai ina ruwanka da hannuna ne?" Ɗan matsowa ya yi yana faɗin "Laushinsu daɗi yake yi mini idan ina taɓawa, shiyasa nake son in yi ta shafasu". Kallon so ta wurga mishi tana mai buɗe tafin nasa hannun ta ji nasa laushin ya yake da zai takura wa nata hannun. Bawan Allah baya wani aikin wahala, kullum yana cikin hutu, soft skin nasa ma har wani sheki yake yi bare fatar cikin hannunsa, ai ba'a magana, akwai laushi sosai da sosai, ɗan murza fatar ta yi har sai da ya furta wash, sake shi ta yi tana faɗin "Naka hannun ma ae yafi nawa laushi, amma saboda neman rigima sai ka rinƙa taɓa mini nawa ko?" "Naki ne ko nawa?". Ya faɗa yana ɗan juyar da tsayuwarsa da kyau ya dawo suna fuskantar juna da kyau da kyau. "Innalillahi My shagwaɓati me ya sameka a kumatu? Ya naga shatin yatsun wani kuma a face naka? Marinka aka yi?". A ruɗe take jero mishi tambayoyin, ba karya marin da ɗan'sandan nan ya yi mishi ya maru, wajen ta yi jawur kamar ka taɓa jini ya zuba, da yake tun da ya shigo bai juya da kyau bane yasa bata gani ba, yanzu kuma ya juya suna fuskantar juna da kyau, hakan yasa ta gani. Bai ɓoye mata komai ba ya gaya mata abin da ya faru da kuma wanda ya mare shi, tambaya ɗaya ta yi mishi shi ne Lion ya sani, girgiza mata kai ya yi alamar a'a tare da sake riƙo hannunta yana faɗin "Ni ki dai'na maganar, ai Areef ya hukunta su, bana ma son Lion ya ji, dan nasan ba zai taɓa kyalesu ba, yanzu dai ki rufe idanunki bari na baki surprise". Ba musu ta rufe idanun nata, komawa cikin mota ya yi, jim kaɗan ya fito tare da dawowa gabanta, mai gadi dai ya mayar da su kamar wasu Tv, yana kallon ikon Allah, sai kallon Aseef yake yi, yau yaga Bature, fari tas kamar madara. Zube gwiwowinsa ya yi a kasa a gabanta tare da buɗe wani ɗan akwai mai ɗauke da dankareren diamond ring, sai kyalli yake yi yana ɗaukar idanu, baki mai gadi ya sake yau yana kallon American film a zahiri. Umarni ya bata a kan ta buɗe idanunta, ba musu ta warosu a hankali, kai tsaye dai kan zobben ta sauke idanun nata, da sauri ta mayar da kallonta kan face nasa, cool murmushi ya sakar mata tare da ciro ring ɗin ya kama hannunta ya sanya mata a yatsanta na kusa da babba na tsakiya, wani irin sihirtaccen kyau hannun nata ya kara yi, kai hannun nata saitin ɗan bakinsa ya yi tare da sumbatarta, wani irin shock suka ji dukkansu biyu, miƙewa ya yi tare da jingina da jikin motar yana lumshe idanu. "My shagwaɓati ka kawo naka ring ɗin na saka maka mana?". Ta faɗa tana kai hannun nata kusan bakinta ta sumbaci zobben, "No ni bana sanya ring ai, amma zan saka na auren mu, a kasarmu idan ka saka ring yana nufin kai mai aure ne, abin da ya sanya kema na saka miki, dan naga ku a nan kuma sawa ne, naga akwai a hannun our Rimsha, to shiyasa kema na saka miki, amma ni a'a bana ma sanyawa, baya burgeni, chain kawai nake sakawa, shi ma da ne yanzu bana sakawa sai na mummynmu ne kawai a wuyana". Ya kai karshen maganar tare da fito mata da sarkar mum ɗin nasu dan ta gani, zubawa sarkar idanu ta yi tana kallon shi, tabbas ta taɓa ganin irin wannan sarka sak, babu banbanci ko kaɗan, to a ina? Shiru ta yi tana tunani, shi kuma mayar da sarkar ya yi yana faɗin "Ina su Prof?" Suna ciki ta bashi amsa yayin da take ƙoƙarin tunani wai daga ina ta taɓa ganin wannan sarka, sai ya yi mata kamar a hoton kakansu Naurat ta taɓa gani, yes tabbas a wuyar Naurat ta taɓa ganin wannan sarkar, akwai wani hoton Naurat ita da kanwarta autarsu, so dukkansu ita da kanwar nata suna sanye da irin sarkar nan. "Okey muje bari na gaishe da Ammie sai nazo na koma ko?" "Koma wa kuma?" Ta tambaya tana turo baki, hannu yasa ya shafa lips nata na kasa yana faɗin "Wai ke bana ce ki dai'na turo mini ɗan bakin nan ba? Very soon zan sha kayana ki cihaba", Kama hannun nasa ta yi tana kallon kyawawan fararen yatsunsa, ga farcensa sai kyalli suke yi farare tas, ga wani kayatatcen brawn ɗin gashi kwance a saman yatsun nasa, haka zalika hannunsa, gabaɗaya kyawawan kwantatcen gashi ne sosai a wajen, "My shagwaɓati wlh yatsun hannunka suna yi mini kyau over". "To meyasa zaki wahalar da kanki wajen cewa suna yi miki kyau bayan mallakinki ne?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da sumbatar yatsun nasa tana murmushi, wannan sumbata har cikin ransa ya jita, lumshe idanu ya yi yana mai sauke nauyayyar ajiyar zuciya. "Muje ko?" Ta faɗa tare da sakin hannun nasa ta yi gaba, zura hannayen nasa ya yi a cikin aljihunsa ya bi bayanta yana kallon yadda take tafiya a nitse kamar bata son taka kasa, ta kara tafiya da imaninsa ba kaɗan ba. Bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin palon, zaune ta isko Ammie, Imran, Akil suna hira, iso ta yi mishi tare da wucewa kusa da Imran ta zauna, karisowa ciki ya yi, Imran ya fara miƙawa hannu kafin Akil, da yake shi bai san al'adar Hausawa ba sai nasu ya sani, sai ya miƙawa Ammie ma hanu dansu gaisa, bata yi mamaki ba, suma su Imran basu yi mamaki ba, sunma ga kokarin sa da bai ce zai rungumi Ammien bama, dan su runguma a wajensu kamar nuna murna da ganin mutun ne ba wani abin ba, Akila dai ta sha mamaki, kuma ta yi nadama da bata gaya mishi yadda zai yi wa Ammie ba idan ya shigo. Ba musu Ammie ta miƙa mishi hannu suka gaisa dan ita ma mijin nata Baturen ne, duk kanwar ja ce, Bismillah ta yi mishi da ya zauna saman sofa, zama ya yi kafin su fara ƴan tattaunawa, a haka Abba ya sauko kasa ya same su, ya yi shirin zuwa office, Umaisha tana kitchen Jelly tana barci, Umaishar ta ce lallai sai ta taya Ammie aiki, shi ne ta shiga tana ɗan goge goge. Ganin Abba yasa ya miƙe ya bashi hannu, ba musu Abba ya miƙa mishi hannu suka gaisa, ɗan rungume Abban kaɗan ya yi kamar yadda suka saba yi a kasarsu, shi ma Abban mayar mishi da martanin hakan ya yi dan duk ɗaya ne, da gani ba tambaya, komawa ya yi ya zauna abinsa yana kallon heartbeat nasa, sai murmushi take yi. Abba ne ya tambayi Imran a ina suka samo Bature ruwansu mummynsu wato Na'urat kuma? Dan duk ɗaya ne, kai tsaye Imra ya ce mishi saurayin Akila ne, shiru Abba ya ɗan yi kafin ya ce " Saurayin Akila kuma?" Jinjina mishi kai Imran ɗin ya yi ba tare da ya wani damu ba. "Akila kam ai na riga da nayi mata miji". "What?!!" Imran ya faɗa tare da miƙewa, ita kan ta Ammie sai da ta miƙe, Akil ma dai tambaya ya yi akan miji kuma,? Shi ma Aseef miƙewa ya yi da yake da turanci suka yi maganar. "Abba ban gane ka yi wa Akila miji ba? Waye ka bata to? Ka yi mana bayani". Cewar Imran, yana magana yana kallon Aseef da ya tsaresu da idanu, yasan idan hakan ta tabbata lallai akwai yaki kenan, babbar magana. "E Imran kamar yadda ka ji dai haka ne, kwana uku da suka wuce Deen da Maik sun same ni a office akan maganar Irfan da Akila suna son junansu, na yi murna sosai, na kuma bawa Irfan aurenta, Friday mai zuwa za'a ɗaura aure, ranar Wednesday gabaɗaya iyalan gidan Deen zasu tattaro su dawo nan dan ayi komai waje guda, sai bayan biki zasu koma, Batula tana zuwa jibi, mantawa nayi ban gaya muku ba, amma an gama shirya komai ai". Tashin sense da ba'a saka mishi date, zube gwiwowinsa a kasa Aseef ya yi, nan take hawaye suka fara wanke mishi fuska cikin sanyin murya ya ce "Please Abba kada ka yi hakan, am very sure heartbeat bata son Irfan, ni ba zan iya rayuwa ba idan ka hana ni ita, please and please ka taimake mu, na san ita ma heartbeat ba zata iya rayuwa da kowa ba sai ni, wlh muna son junanmu over, ni kayi mini duk abin da zaka yi mini amma kada ka hanani auren Heartbeat, ba zan iya jurewa ba, ba kuma zan iya ɗauka ba". Yana magana hawaye wani na bin wani, Ammie bata san lokacin da hawaye ya fara bin kuncinta ba ita ma, dan dole Aseef ya bawa mutun tausayi a yanayin yadda yake magana. Zubewa kasa ita ma Akilar ta yi, tana kuka tamkar ba gobe, hawaye wani na bin wani "Abba wlh ni bana soyayya da yaya Irfan, ni Heartbeat nake so, dan Allah kada ka aura mini yaya Irfan, Allah bana son shi". Imran sarkin saurin kuka tuni ya fara yi musu hawaye, dan shi yasan menene soyayya, yasan wahalarta, ya kuma ɗanɗana, Akil kuwa tunani yake yi tun da Akila ta buɗe baki ta ce bata son Irfan to gaskiya bai ga dalilin da zaisa a aure mata shi ba, aure ba abin wasa bane, ba abu ne da ake yin shi shekara ɗaya ko biyu ya kare ba, rayuwa ce ta har abada, zama da wadda baka so yafi komai wahala da azaba a duniyar nan, dan haka iyaye ku ji tsoron Allah ku dai'na yiwa yara dole, zama da wanda zuciya bata so babbar barazace ga rayuwar yarinya, ya kan sakata ta yi abubun da kowa zai zo ya yi dana sani daga baya, to maganin bari kada asoma, ku sani dai Allah zai tambayeku. "Abba dan Allah ka duba wannan magana da kyau". Cewar Imran. "Imran ya kake so na yi to? Deen fa nace maka, bappanku Deen fa!, Shi da kansa ya zo ya nemanwa Irfan aurenta, yana da damar da zai aurawa Irfan ɗin ita ko ban sani ba, ba shi ya ɗaura muku aure ba? Nasan time da ya ɗaura muku ne? Ai ban sani ba, to haka ita ma Akilar zai iya aurar da ita ba tare da sanina ba, kuma bani da abin cewa, amma duk da haka ya wanke kafa ya zo ya nemi auren ta, na kuma ɗauka na bashi, yau saura kwana takwas kenan a ɗaura auren, kenan so kuke nace mishi na fasa bashi wani na waje zan bawa ne ko yaya?". Shiru palon ya yi, ban da shasshekar kuka Heartbeat and Heartbeat babu wani abin da yake tashi, su Imran dai sun rasa bakin magana, sun san ba ta yadda za'ayi Abba ya ce wa Abbi ya fasa bawa Irfan wani daga waje zai bamawa, hakan sam ba abune mai yiwuwa ba. Suna tsaka da tunani basu ankara ba sai ganin Aseef suka yi ya sulale kasa sumamme, ihu Akila ta kurma ta yi kansa tana ambatar sunansa Heartbeat!! Heartbeat, kamata Akil ya yi ya rungumeta a jikinsa tare da bubbuga bayanta dan ta samu ta natsu. Da gudu Umaisha ta fito daga cikin kitchen dan ta zo taga me yake faruwa ake ihu haka, Abba, Imran a zafafe suka yi kansa, sai kiran sunansa Aseef, Aseef Imran yake yi, amma ina shiru, ruwa Ammie ta ɗauko a fridge Abba ya karɓa ya tarbo a hannu ya shafa mishi a fuska, shi kuma Akil sama ya wuce da Akila dan kada ta karawa Aseef ɗin zafi a kan zafi, ga ciwo ga kuma kukanta, wucewa Abba ya yi yana faɗin "Ana jiransa a office tun ɗazun, bari ya je". Okey suka amsa mishi da shi, sauri yake yi sosai, kuma baya son tsayawa ne, dan baya son ganin halin da Aseef da Akila suke ciki, saboda yasan duk wuya duk daɗi ba zai canza magana ba, ba zai iya hana Irfan ya ɗauki Akila ya bawa wani bare ba, amma fa har can kasar zuciyarsa shi ma yana son bawa ƴar tasa zaɓinta, amma ba dama ne kawai, bashi da yadda zai yi, jini ba karya ba. Sai rarrashinsa Imran yake yi, amma ina yaki yin shiru, sai ruwan hawaye yake yi bawan Allah, ba zai iya jure rashin Akila ba, ita ɗin ta zame masa wani ɓari na rayuwarsa, ita ce first love ɗinsa,. Sai da Imran ya ce ya yi mishi alkawarin zai shawo mishi kan Abba, duk wuya In Sha Allah Akila matarsa ce, sannan ne ya ɗan hakura ya dai'na ruwan hawaye, ita ma Ammie karfafa mishi gwiwa ta yi a kan kada ya damu, da izinin Allah Akila tasa ce, tun da har ta furta bata son Irfan to kada ya damu zasu shawo kan Abba idan ya dawo, da haka dai suka samu suka lallaɓa shi ya daure ya hakura ɗin. Imran ya ce su je ya tuka shi zuwa gida, okey ya amsa tare da cewa Imran ɗin dan Allah kada ya gayawa su Areef, idan ya gaya musu yasan Lion zai ce sai dai ya rabu da Heartbeat ɗin tun da haka ne abin, to dan haka kada ya gaya musu, okey ya amsa mishi da shi, da haka ya yi wa Ammie sallama sai hakuri take bashi suka nufi gida. Yana komawa bedroom nasa ya wuce ya haye gado saboda tsananin ciwo da kansa yake yi mishi, bai kula kowa ba yau a gidan, yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi, sai sauke ajiyar zuciya yake yi cikin barci, shi kuma Areef yana can yana faman bincike a kan case ɗin Jehan. Da misalin karfe 8:30 na dare, bayan sun gama cin abinci, da kyar Rimsha ta ci abinci, nan ma har sai da Areef ya ɓata rai sannan ta yarda ta ci, shi ma dai Aseef ba wani abincin kirki ya ci ba, dan ma dai Imran ya sake kiransa a waya ya kara kwantar mishi da hankali ne yasa ya yarda ya ci abincin, da kuma baya son su Lion su gane yana cikin damuwa, dan Lion ba zai goyi bayansa ba, zai ce akan mace har zai ɗaga hankalinsa, shi bai san so ba, ganin abin banza yake yi mata. Wanka ta yi ta shirya cikin wani wando da bai karisa kai mata idon sahu na kafarta ba, sai riga mai karamar hannu mai shegen kyau, ɗaura handkerchief ta yi a kanta, ta yi kyau ba karya, sai dai fa kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana cikin matsananciyar damuwa, plat shoe ta sanya a kafarta tare da nufar waje, ban da tunanin jenan babu wani abu da take yi, garden ta nufa dan ta rage wa kanta raɗaɗin abin da take ji, gabaɗaya blue light ne kunne a garden ɗin, saman sofa ta kwanta tana tunane tunane har barci ya yi awon gaba da ita, sai misalin karfe 11 na dare da sanyin ya ratsata ne ta farka, a hankali ta waro dara daran sleeping eyes nata, ganin a cikin garden take yasa ta miƙe a tsorace, bata lura da akwai mutun a cikin garden ɗin ba kawai ta nufi cikin gida, sai dai kash Mark ya rufe gabaɗaya kofofin gidan, ga shi bata fito da wayarta ba bare ta kira Areef, ga kofar ko ta yi knocking ba lallai su ji ba, kuma ma tana tsoron yin knocking ɗin dan kada Lion ya tashi daga barci. Ta jima tsaye a wajen tana tunanin mafita, can ta ɗan ji motsin su Brady, dake ɗaure a kusa da ta wajen pool, a guje ta juya ta koma garden ɗin, saman sofar da ta tashi nan ta koma ta kwanta tare da takure jikinta waje guda, ga sanyi ga kuma tsoro, sai ta takure sosai, ta datse idanunta gam tamkar zata fasa su, jikinta har wani kerma yake yi, duk abin da take yi yana kallonta, dama idan baku manta ba, wajen zamansa kenan da daddare, wani lokaci sai ya kai karfe 2 na dare a wajen, so yanzu ma yana zaune yana aikin latsa waya, da ya gaji sai ya kishingiɗa a saman doguwar sofa dake kusa da shi, sai dai tsawonsa ta fi ta sofar, dan haka sai ya ɗan naɗe kafa, duk wani motsinta yana gani, amma ita bata san da shi a cikin garden ɗin ba, da haka barci ɓarawo ya sake ɗaukarta, ta takure jikinta over. Can cikin dare misalin karfe 1 sanyi ya sauƙo sosai, sai dai ita kuma ɗumi take ji yana ratsata ba sanyi ba, wani irin daɗin barci take ji abinta, miƙa ta yi da nufin bari ta juya daga yanayin kwanciyar da take, sai ta ji wuyarta na ɗan yi mata zafi, waro idanunta waje ta yi, idanun nata ɗauke suke sosai da barci, still dai a cikin garden ɗin take, yunkurawa ta yi zata miƙe sai ta ji kamar ba jikin sofa ta dafa ba mutun ta dafa, da yake akwai hasken blue light a wajen sai ta kai kallonta in da ta dafa kafin ta ɗago kanta izuwa kansa, yana zaune ya jingina kansa da jikin headboard na sofar, da alama shi ma barci ne ta yi awon gaba da shi. Abin da ya faru, da misalin karfe 12 na dare, sai rawan sanyi take yi, hakwaranta na garuwa da na juna sosai, kasa jure jin sautin hakwaran nata ya yi, suna toshe mishi kunne, hakan yasa ya miƙe tare da dawowa saman sofar da take kwance, sofar ta yi musu kaɗan, dan haka sai ya ɗaga kanta ya ɗaura saman cinyarsa bayan ya zauna kenan, sannan ya cire jacket dake jikinsa ya rufa mata, da yake jacket ɗin nasa yana da girma sai ta rufe ta da kyau, ga kuma kauri jacket ɗin, cigaba da latsa wayarsa ya yi har barci ta yi awon gaba da shi shi ma, to shi ne abin da ya faru, ya yi mata hakan ne kuma a cewarsa yanzu tausayi take bashi saboda irin wahalar rayuwa da ta sha, idan baku manta ba a Abuja ya faɗa, ita ce mutun ta farko da ta fara mashi tausayi a rayuwarsa. (To mudai je zuwa daga tausayi se me readers?) Ganin shi ne ba karamin ruwan mamaki ta sha ba, tunani ta fara yi a kan yaushe ya zo garden ɗin kuma? Bata san tun karfe 9 yana wajen ba, kai kallonta saman jacket nasa dake rufe da jikinta ta yi, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, da yake zuciya bata da kashi, sai ta ce yaya Saif yana da kirki, har ta manta abubuwan da suka faru a baya, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yadda yake barci cikin kwanciyar hankali, Allah ya yi halitta, kyau iya kyau, tsabar rashin ji irin nata sai ta kai hannu ta shafi kumatunsa, kada ku manta bashi da nauyin barci, tun motsinta na farko da ta yi lokacin da ta yi miƙa tana son juyawa kafin ta farka kenan, to motsin nata ya farkar da shi, sai dai da yake barcin yana kan shi sosai ne sai bai buɗe idanu ba, ya cigaba da lumshe su dan kada barcin ya watse mishi. Daga ita har shi sai da suka ji wani irin yarrrrr a jikinsu lokacin da ta shafa lallausa kuma kyakkyawar kumatunsa, sai dai ko motsawa bai yi ba, hannunta na kerma saboda rashin ji sai da ta sake kai hannu saman dark black curly hair, shafawa ta yi a hankali har zuwa sajensa, a hankali ta gangaro da hannunta zuwa saman lallausan laɓɓansa, tana ɗaura hannun nata a lips ɗin nasa caraf ya cafke hannun nata ba tare da ya buɗe idanu ba, ba ƙaramin razana ta yi ba, a zafafe ta yi yunkurin sauƙa daga saman sofar ta gudu. (to ki gudu ki je ina? Ba kin iya neman bala'i ba? Baki jin magana ai sai ki tsaya ayi wace za'ayi) Riƙe hannun nata da kyau ya yi tare da sauko da kansa sai tin face nata, a hankali ya waro dara daran blue eyes nasa masu ɗauke da barci a saman razananniyar face ɗin tata, datse idanunta ta yi tana addu'ar Allah yasa kada ya ce zai dake ta, Allah yasa ya yafe mata, wai mema ya kai ta ne? Wani ɓangare na zuciyarta ne ya ce mata kyau mana, kyansa ya kai ki taɓa shi,. "Open your eyes". Ya faɗa a sanyaye, ya yi maganar can kasar maƙoshinsa, da ni da ku dukka mun san idanun nata yake son kallo, suna matukar burgesa, izza ta hana shi ya nuna sun burge shi, dama duk wanda ya kalli sleeping eyes nata dole su burge shi, ga su dara daran farare tas kamar audiga, dole su ɗauki hankali dan idanun duniya ne, bare ma idan ta tsorata ta zarosu ai ba'a magana, zata sanya samari da ƴan mata faɗawa cikin kwata, dole idan ta tsorata ta burge mutun, ko dan kara zarosu da take yi. Tsuke ɗan bakin nan nata ta yi tare da waro idanun nata a hankali, kai tsaye sai cikin nasa idon, ita tana bala'in son na shi idon, shi ma yana son nata, ɗan kawar da kallonta ta yi daga cikin kwayar idanun nasa zuwa saman lips nasa da suke red color sosai............. ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E47-48💋 Tsuke ɗan bakin nan nata ta yi tare da waro idanun nata a hankali, kai tsaye sai cikin nasa idon, ita tana bala'in son na shi idon, shi ma yana son nata, ɗan kawar da kallonta ta yi daga cikin kwayar idanun nasa zuwa saman lips nasa da suke red color sosai, ita dai a duniya wannan lallausa kuma kyakkyawan lips ɗin nasa suna bala'in burgeta, ji take yi kamar ta sa hannu ta taɓa, shi kuma ya zubawa idanunta kallo babu ko kyaftawa, kamar mai nazarin wani abin a tattare da ita. Slowly ya dawo da kallonsa saman beautiful lips nata sa suke pink color, ga shi ta tsuke ɗan bakin nata alamar a tsorace take, "Me haɗinki da face na?" Ya faɗa can kasan maƙoshinsa, girgiza mishi kai ta fara yi tana faɗin "Babu komai". Wani irin yanayi ya ji yadda ta motsa lips ɗin nata, shi bai san menene soyayya ba, bayan kaunar TRIPLETS nasa bai san wani so ko kauna or tausayin wani ba, ita ce ta farko da ya fara tausayawa bayan TRIPLETS nasa, wannan yanayin da yake ji a jikinsa idan tana kusa da shi, yana danganta hakan da tausayin da take bashi, idan baku manta ba shi a budurwar Areef ma yake ɗaukarta, dan ba karya ya san ɗan uwan nasa yana sonta, sai dai fa ganin abin ma a hauka yake yi, yana ganin Areef bai san me yake yi ba da zai ce yana son ƴar yarinyar nan da bata wuce a goya ba, to me abin so a wajen?. (A lallau Lion ya yi mugun raina Rimsha, wai bai san cewa Rimsha tsab za'a iya yi mata aure kuma ta zauna bane? Ya je Gombe ya ga ikon Allah, gombawa ayi hakuri gaskiya ce🤪) Sake hannun nata da ya riƙe ya yi tare da mayar da kansa jikin headboard na sofar ya lumshe idanunsa, barci yake ji sosai, jikinsa duk a mace, ya kasa miƙewa ya shige ciki, idan kuma bai shiga ba, ita ma ba ta haryar da zata shiga. Saboda tsiya irin tata da kuma tsoron wajen da take ji, sai ta mayar da kanta a hankali saman cinyar tasa ta kwanta tare da kara jawo jacket ɗin nasa ta rufe jikinta da kyau tana shakar daddaɗar kamshin perfume nasa, wani irin farinciki na wuce misali ta tsinci kanta a ciki, sai sakin murmushi take yi abinta, yau gata a cinyar abin kaunarta, kai abin ba'a magana, idan baku manta ba, ranar da ta kwana a saman kirjinsa a Abuja bata cikin hayyacinta, tana tsorace sosai, so bata sani ba, yau kuma tana cikin hayyacinta. A can cikin gida kuwa, mu koma baya kaɗan, lokacin da suka gama cin abinci, Areef ya ɗauki laptop ɗin Aseef ya kule cikin bedroom nasa yana bincike da ƴan dube dubensa na wasu bayanai da ya kwaso a kan Family'n Nawazudden ɗin daga laptop na Lion, shi kuma Aseef bedroom nasa ya koma. Bayan ya haye saman gado, gabaɗaya bawan Allah ya rasa me yake yi mishi daɗi, duniya har wani juya mishi take yi, wayarsa ya jawo tare da fara kiran number heartbeat, dan ita ce kaɗai zata sanya shi farinciki a rayuwarsa ta yanzu, bugu ɗaya ta ɗauka, baiwar Allah ta ci kuka har ta godewa Allah. Tana ɗauka wani kukan ta saka mishi, dafe kansa dake yi masa barazanar tarwatsewa ya yi, murya a dashe can ƙasa ƙasa ya fara magana "My heartbeat please and please ki yi shiru, idan ba haka ba, kina iya jefani cikin damuwar da zata iya yin sanadiyar rayuwata, ni kukanki ya fi zama mini bala'i a kan hanani ke da akayi, please ki daina kin ji? Kada ki ɗauka daɗin baki ne nake yi miki, duk abin da zai fito daga cikin bakina ki sani tsantsar gaskiya ce wadda babu mix ko ɗigo, na san idan ban same ki ba, mutuwa zan yi, yanzu dai ki yi shiru kin ji ko?". Tsabar kukar da ta sha, voice nata sam baya fita sosai, da kyar ta ce mishi, "Wlh Heartbeat kukan ne yaki tsayawa, idan har na ce zan tsayar da shi sai yaki, hawayena sun ki dai'na zuba, kai'na ciwo yake yi mini sosai, komai ya tsaya mini cak, duniya gabaɗaya juya mini take yi". Miƙewa zaune ya yi tare da nufar wajen da ya ajiye key ɗin motarsa yana faɗin "To shikenan, yanzu dai kinci abinci ne?" Girgiza mishi kai ta yi tamkar tana a gabansa, "Baki ci ba?". Ya yi maganar tare da ɗaukar key ɗin motar ya fice daga ɗakin "E ban ci ba, Heartbeat ni fa ba zan iya cin abincin bane, ko na saka a bakina ba zai wuce wuyana ba". Kitchen ya shiga, da kansa ya ɗebi abinci daga cikin na Lion ya zuba mata a cikin wani dankareren kula mai bala'in kyau, dan yasan dama Lion baya cin ko rabin abincin da ake zubawa a kular tasa, shiyasa ya ɗeba mata, spoon ɗaya ya ɗauko tare da fitowa ya nufi motarsa, da gudun gaske ya tada motar ya fice, a lokacin ita ma Rismha tana ɗakinta kenan tun da baya muka koma. Sai rarrashinta yake yi a wayar ba tare da ya gaya mata yana zuwa gidansu ba, duk magana idan ya yi sai ruwan hawaye ya kara tsananta a fuskarta, ita kaɗai tasan raɗaɗin azabar da take ji, ba zata iya rabu da shi ba gaskiya. "Heartbeat wai ba zaki dai'na wannan kuka ba har sai kin saka ni yi nima ko?". "Kayi hakuri zan dai'na, amma ko na goge hawayen sai wasu sun zubo ne". "Okey to fito gani a waje". Ya kai karshen maganar tare da yin parking na motarsa a ɗan nesa da gidan nasu. Zubur ta miƙe daga kwanciyar da take, nan take hawayen nata suka kara tsananta, dirowa kasa ta yi daga saman gadon wayar tana manne a kunnanta, kayan barci ne a jikinta, riga da wando ne masu laushi launin brown color, suna da bala'in kyau ba kaɗan ba, hijabi ta ɗauko zuwa gwiwarta ta sanya a jikinta tare da fitowa ta nufi bedroom ɗin Ammie, har lokacin tana ruwan hawaye, ba ɓoye ɓoye ta sanar da Ammie ga Aseef ya zo zata je wajensa, Allah sarki uwa da ƴa, ita kanta dama ta shiga damuwa matuka a kan halin da ƴar tata ta shiga, dan haka sai ta yar je mata akan ta je suga juna, sai dai kada ta jima dan taga Abba ya kusa dawowa, dan ma ya biya wajen Abbi ne ai da ya jima da dawowa, idan ya dawo ya sameta a waje da Aseef kuma zai yi faɗa sosai, dan ya gaya musu ya yi mata miji, to ta amsa mata da shi, ta juya har lokacin sai ruwan hawaye take yi, binta da kallo Ammien ta yi tana mai matukar tausaya mata, dan tasan wannan aure nata da Irfan babu mai rusa shi, yanzu ma ta barta ta je wajen Aseef ɗin ne dan tana da yakinin idan ta je zata rage damuwa, zata samu ta yi barcin daren yau. Tun da ya hango fitowarta daga gida shi ma ya fito daga cikin motarsa, jingina da jikin motar ya yi tare da zuba mata idanu yana kallon ta, wani azababben kaunarta ne yake kara ninku mishi a cikin farfajiyar zuciyarsa, har ta kariso gabansa ba tare da ya sani ba, yana can yana tunanin mafita, zazzakar muryarta dake dashe sabida kuka ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya faɗa. "Sannu da zuwa ina wuni?" Shi ne abin da ta faɗa. Ganin har lokacin hawaye na a kan fuskarta ne yasa ya ce "Har yanzu baki dai'na yin kukan ba?" Kasa ta yi da kanta tana faɗin "Heartbeat na gaya maka kukan ne yaki tsayawa wlh, ko na goge hawayen sai ya dawo". Hannunta ya kama tare da jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, tun daga tsakiyar kansu har zuwa tafin kafarsu sai da suka ji wani irin shock, daurewa ya yi tare da ɗago haɓarta ya sanya kyakyawar farar hannunsa yana goge mata hawaye, tuni kukan nata ya tsaya cak, tun da ta faɗa saman kirjinsa ta nemi kukan ta rasa. "To kinga na yanzu na goge miki hawayen dukka, kada ki bari wani ya fito kinji my rigimati?". Gyaɗa mishi kai ta yi alamar ta ji, nisawa ya yi yana tunani, a matsayinsa na namiji, dole shi ya ɓoye tashin hankalinsa da damuwarsa dan ya kwantar mata da hankali, idan ya nuna mata tsantsar bala'in da yake ciki abin zai yi mata yawa, to dole ya danne sosai. "Me kike wani kallona haka?". Ya yi maganar a shagwaɓe dan ya mantar da ita damuwar da suke ciki, ɗan kwantar da kanta a saman kirjin nasa ta yi tana jan hanci bata ce komai ba, a hankali ya fara shafa bayanta kaɗan kaɗan, jin hakan yasa ta tashi daga jikin nasa cikin sauri tana koran shaiɗan ɗin da yake son ya shiga tsakaninsu, bai damu ba dan ta tashi daga jikin nasa, dama shi burinsa kawai ta yi shiru ta dai'na kuka, to kuma ya yi nasarar tsayar da hawayen nata. "Zo mu shiga cikin mota kin ji ko?" Da farko taki yarda, sai da taga kamar bai ji daɗin hakan bane yasa ta ce to su je, gidan gaba ya buɗe mata ta shi, bayan ya rufe sai ya zagayo ta mazaunin driver ya shiga, wutar dake kan titin unguwar tana haska har cikin motar ta su, kular abincin ya ɗauko daga gidan baya tare da kawowa tsakaninsu, zuba mishi idanu ta yi tana kallon ikon Allah, buɗe abincin ya yi, wani irin daddaɗar kamshin ne ya daki hancinta, da yake ita kam tana cin ire iren abincin a manyan restaurant da suke sayan abinci, sai bata wani damu ba. Ɗiba ya fara yi yana kai mata sai tin ɗan bakinta, tun tana nokewa har ta saki jiki tana karɓa, sai zuba mata hira masu daɗi yake yi har ta ci abincin sosai ba tare da ta sani ba, tissue paper ya ɗauko ya goge mata baki tare da rufe kular bayan ya tabbatar ta ƙoshi, ruwa ya sake ɗaukowa a kusa da su ya buɗe ya kai mata sai tin ɗan bakinta, kallon shi ta yi, kashe mata ido ɗaya ya yi kafin ya ce "Wai har yanzu duk da na tura miki hoton mu mu dukka uku kin kallemu, har yanzu ina yi miki kama da su sosai ta yadda baki banbantamu kamar yadda kika ce da farko?". Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "E wlh ni kullum na kalli hoton sai in kalli kamar mutun ɗaya ne a wajen, ido ne kawai yake banbanta ku, na rasa wlh, sai dai Lion ya fiku cika, kuma kaman ya fiku tsawo ma". Kai mata ruwan bakinta ya yi ta karɓa ta fara sha. "Kin san menene?" Girgiza mishi kai ta yi tana kan shan ruwan. "Da ni da su ko a cikin duhu Rimsha tana iya banbanta mu, mafiya yawan lokuta daddy da ya haifemu idan yana magana a palo da Areef dake cikin bedroom, idan na amsa daga cikin bedroom ɗin a madadin Areef, to wlh baya gane ni na amsa, basu rabe muryata da ta Areef, duk duniya dama Lion ne kawai yake iya rabe muryoyinmu, na sha ruwan mamaki lokacin da Rimsha ta iya rabe muryoyinmu a rana ta farkonta da ganinmu, to haka take banbanta mu ko a cikin duhu, wani lokaci idan na rufe mata fuska ta baya zaki ji ta ambaci sunana, idan na ce waye ya gaya miki Areef ne fa ba Aseef ba, zata kafe lallai dole ni ne ba Areef bane, , shi kan shi Areef ya sha ruwan mamakin banbanta mu da Rimsha take yi a cikin duhu, bare ma masoyinta Lion, bata haɗa shi da kowa ba, karfi da ya ji ta rabamu, ko cikin zolaya idan na ce mata Saif ne bayan na rufe mata ido, zaki ji tana cewa, kai ina GAR ya fi haka, kai in takaice miki kome kika yi wa Rimsha dan ki rikitata a kanmu sai ta rabe miki mu tsab wlh, na rasa wani irin baiwa ke gareta, shi ma Areef ya gwadata har ya gaji ya hakura, su uncle T duk basu rabeni da Areef idan nayi magana, amma ita ina raba mu take yi tsab". Dariya ta kwashe da shi tana faɗin "Kai ai dole Rimsha ta yi muku farin sani kafin ganinku, kasan yadda take kaunar Lion kuwa? Hmm banga laifinta ba dan ta ce muku bata haɗa shi da kowa ba, ai kai ma ban haɗa ka da kowa ba, gaskiya sosai Rimsha akwai kwakwalwa na wuce misali, gata da natsuwa sosai". Hannayenta ya riƙo bayan ya ajiye robar ruwan, tsareta da idanu ya yi yana faɗin "Wace Rimshar ce mai natsuwa? Sai dai idan wata Rimsha a gidanku, amma mu na gidanmu kamar battery ake saka mata, tana da fitina ga neman rigima wajen Saif, watara Allah sai ya sumar da yarinyar nan ina da tabbaci". Murmushi ta yi tana wasa da ƴan yatsun hannunsa masu bala'in ɗaukar hankali, "Duk abin da kaga Rimsha tana yi wa Lion ni na gaya mata wlh, ni na san cewa yaro mai kiriniya yana da saurin shiga rai, na san idan tana yawan shiga harkarsa tana taɓa mishi abubuwa bai aiketa ba, dole watarana ya ɗago ido ya kalleta, a kwana a tashi dole ya fara sonta, Allah Rimsha ta sha bakar wahala akan soyayyarsa, idan ba shi ta aura ba, wlh aurenta ba zai taɓa zuwa ko'ina ba, tun tana da 9 years a duniya take haukar kallon shi a Tv, ni nasan a yadda yake ɗin nan, ba zai yi saurin ɗaura hannunsa a jikin mace da sunan duka ba, shiyasa na bata wannan shawarar ko kuma in ce maka kullum nake kara bata hakan idan mun yi waya, ta dai'na jin tsoronsa, ta rinƙa taɓa mishi wasu abubuwa nasa ba zai taɓa dukanta ba, amma a nawa ganin da nake masa fa kenan, bacin haka, wlh Rimsha nitsatsiya ce sosai, kuma idan ka lura ai Lion ɗin kawai take yi wa rashin ji ɗin, to ni nake zugata". Nisawa ya yi yana faɗin "Yes da wuya Lion ya ɗaura hannunsa a jikinta da nufin duka gaskiya, ko ni ai ba zan daki mace ba, to wai me ma zaka daka a jikin mace? Ka je ka sumar ko ka kashe ƴar mutane a banza, mace ai bata da wajen duka a jikinta, shi Lion ma ya ce faɗuwa ce babba ga namiji ya sanya hannunsa a jikin mace da sunan duka, yo Allah na tuba Lion da yake mari manyan zaratan maza su faɗi su suma ina ga Rimsha kuma? Ai idan ya mareta sai mutuwa, gaskiya ma ba zai yiwu ba, duka kam a'a ba zai daketa ba, idan ta cika matsa mishi dai, sai dai ya bata punishment irin su frog jump da sauransu". Ya kai karshen maganar tare da kai hannunta dake cikin nasa saitin ɗan bakinsa ya sumbata. Kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "I really love my heartbeat, kece bugun numfashina, idan bake to babu ni". Buɗe tafin hannunta ta yi tare da ɗaura nasa hannun a saman natan, yazama kamar sun tafa da juna kenan, cikin shagwaɓa ta ce "Promise me that ba zaka taɓa barina ba duk wuya duk daɗi". Matso da fuskarsa daf da tata ya yi "I promised you that ko me wuya ko me daɗi ni naki ne, a kanki zan tsaya ba ja baya". Cool murmushi ta saki har sai da gaf teeth nata suka bayyana Heartbeat ya ambaci sunanta a tsananin sanyaye, ita ma a sanyaye ta amsa mishi, "Fito da harshenki dukka waje bari na gani". Ba musu ta fito da ita, tana da tsawo sosai harshen nata, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce tom ta mayar, mayarwa ta yi tana tambayarsa menene yasa ya ce ta fitar, jan dogon hancinta ya yi yana faɗin "Sai gaba zan gaya miki dalili". Make kafaɗa ta yi a kan lallai bata yarda ba sai ya gaya mata ita dai, kara matsowa kusa da ita sosai ya yi har suna iya jiyo sautin numfashin juna, "Ba kin ce na dai'na irin maganar sai mun yi aure ba?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e, "To kin gani ki bari sai mun yi aure sannan zan gaya miki dalili". Turo baki ta yi taso jin meyasa ya kalle mata harshe, amma ba komai ai, yanzu ma da ya ce sai sun yi aure tun da ta ce ya dai'na irin wannan magana, ta fahimci ina ya dosa, sai dai bata san me na'amar hakan ba, ta dai fahimci duk zancene da ya shafi ma'aurata. "My shagwaɓati zan koma gida kada Abba na ya dawo ya sameni a waje, zai yi faɗa sosai, Ammie ta ce kada na jima". Har cikin ransa sai da ya ji wani raɗaɗin zafi, amma haka ya danne tare da gaya mata kalamai masu daɗi dan kada ta shiga gida ta shiga cikin damuwa koma ta yi kuka, sai da ya tabbatar ya sanya ta farinciki sosai har da dariya kafin ya ce to suje ya taka mata zuwa bakin gate. A tare suka fito suka nufi gidan, sai hira yake zuba mata, burinsa ta mance da komai ta yi barcin cikin farinciki. Sai da suka je bakin gate ne ya ɗan jawota jikinsa ya rungume, dan su a kasarsu hakan ma sallama ce, ɗan shafa lallausan kumatunsa tayi kafin ta raba jikinsu ta wuce zuwa cikin gida, binta da kallo ya yi har sai da ta shiga palo sannan ya bawa mai gadi dama ya rude gate ɗin, ya juya zuciyarsa cike tab da bakin ciki, shi kaɗai yasan me yake ji. Cikin mota ya koma ya zauna tare da kifa kansa da jikin steering motar yana jin zuciyarsa na tafasa kamar zata kone, yanzu ko hawayen ma ya nema ya rasa, saboda bala'in ta kai mishi bala'i. Ya jima a haka kafin ya kunna motar zuwa gida, yana kan hanya ta kira shi a waya dan ta ji ko ya isa lafiya, kin ɗauka ya yi har sai da ya koma sannan ya kirata suka cigaba da hira suna farantawa juna rai tare da kara nitsawa cikin kogin soyayyar juna. Shi kuma Areef yana can yana ta bincikensa, ya tasa hoton Jehan da ya ɗauko daga laptop ɗin Lion yana kare mata kallo, shi dai wlh ta shiga ransa ba kaɗan ba, musamman idan ya kalli idanun nan nata masu kama dana daddynta, suna matukar burgesa, abin da baku sani ba gabaɗaya TRIPLETS Allah ya jarrabesu da bala'in kaunar manya manyan idanu, suna ɗaukar hankalinsu sosai, bare ma idan idanun suka kasance farare tas abin ba'a magana, ga family'n Dr Salman kuwa gabaɗayansu ba baya ba wajen manya manyan dara daran idanu, shi ne yasa Lion yake bala'in son idanun Rimsha, sun kasance manya manyan farare tas, ga su sleeping eyes, ai dole ma ya so su, dan abin nasu a jini yake. A ɓangaren Rimsha da Lion kuwa, barci gabaɗayansu suka koma, iska mai daɗi yana kaɗa shi, ita kuma sanyi iskar ya yi mata, a hankali yayyafin ruwan sama ya fara sauka a kansu, wajen akwai runfa ta yadda ruwa ba zai shiga ba, to amma ruwan da iska sosai yake tafe yasa iskar yake kaɗo ruwan har ciki yake taɓa su. A hankali ya waro dara daran blue eyes nasa tare da sauko da kansa kaɗan, karaf sai saman kyakkyawar fuskarta ya sauƙesu, sai zuba barci take yi kamar ba gobe, lumshe idanun nasa ya yi tare da sake buɗe su a kan face ɗin tata, shiru ya yi yana tariyo makusantar Josephine da ya sani ko zai ga mai irin wannan face ɗin, shi dai yasan tabbas ya taɓa ganin matar tare da Josephine to wace ce? A hankali ya kwantar mata da kanta a saman sofa tare da miƙewa ya nufi wajen fridge dake wajen, ruwa mai sanyi ya ɗauko, dawowa ya yi ya zauna a saman wata sofa daban, nan take ruwan sama ta kece kamar da bakin kwarya, shan ruwan tas ya yi tare da ajiye robar ruwar ya kishingiɗa a saman sofar tare da fito da wayarsa ya fara latsawa, a haka har suka kai asuba, ga ruwan sama yaki tsayawa, yana son komawa cikin gida ya ɗauro alwala zuwa masallaci, amma ina ruwa kamar da bakin kwarya yake zuba. Da yake ita ma jikinta ya saba tashi da asuba, sai ga shi ta farka, tare da miƙewa zaune, wani azababben sanyi ne ya bugeta lokacin guda, cikin sauri ta takure jikinta waje guda, baiwar Allah ta yi barci mai nauyi bata ma san ana ruwan sama ba, jin zuban ruwa yasa ta fara waije waije dan nemo ina yake, can saman sofa ta ganshi a kwance yana latsa waya, ware jacket ɗin nasa ta yi tare da sanyawa a jikinta ta takure waje guda tana rawan sanyi, jacket ɗin ya yi mata yawa sosai. Shiru shiru har aka yi sallar asuba, shi kuwa yana kwance abinsa daga shi sai T-shirt polo da jeans sky blue, amma baya jin wani sanyi, ita ce dai ta takure kanta, dama kuma kun san yanayi ba ɗaya ba, shi ya saba da sanyi mai kankara, dole ba zai ji komai ba a wannan sanyi tamu ta nan. Karar sautin garuwar hakwaranta yasa shi ɗago idanunsa izuwa kanta, mamaki yake yi wai ita wannan wace iriyar mutun ce? Yanzu sanyin me ake yi a nan da har zata rinƙa bari har haka? Kai anya ba wani cuta yake damunta ba kuwa?. Ayya shi bai san mu a wajenmu wannan sanyi ne sosai mai ratsa kashi ba. Cigaba da latsa wayarsa ya yi bai sake bi ta kanta ba har gari ta fara haske, sannan ne ruwan saman ya tsagaita, lokacin karfe 5:44, miƙewa ya yi ya wuce izuwa cikin gida, da sauri ta miƙe ta bi bayansa, a tare suka shige, kai tsaye ya nufi bedroom nasa ita ma ta nufi nata. Sallah dukkansu biyu suka yi dan lokaci ya kure, haka zalika kusan a tare suka shiga wanka, dan a tare suka dawo cikin gidan, bayan ya yi wanka ya fito, shiryawa ya yi cikin pajama launin white color, saman bakin bed nasa ya zauna yana ƙoƙarin kiran number Areef sai gasu sun shigo a tare kamar abin haɗin baki. Saman sofa suka zauna, cikin sanyin murya da nuna kula da juna suka ɗaga mishi gaisuwa, shiru ya yi bai amsa ba, can kuma sai ya ɗago da kallonsa zuwa kan Aseef, da ya dukar da kansa kasa kamar mai tunanin wani abin, ga kuma waya a hannunsa kamar mai latsawa, sai dai ga dukkan alamu ba wayar ma yake kallo ba, ya shiga duniyar tunani ne. Zuba mishi idanu sosai ya yi yana kare mishi kallo, har yanzu akwai ragowar shatin yatsun ɗan'sandan nan da ya mare shi a fuskarsa, wajen ya yi ja. "Who slapped you?". Ya faɗa yana ɗaure fuska sosai, dama ga fuskar ba'a magana, tamkar hadari kullum, ƴar firgita ya yi tare da fara latsa wayarsa daka hannunsa, shi ya mance ma da marin nasa da akayi, yanzu bala'in da yake ciki tafi karfin mari. "Wani ɗan'sanda ne ya mare shi". Cewar Areef, "A kan me?!" Ya faɗa a tsawace, sai lokacin ya ɗago kansa tare da kai kallonsa kan fuskar ɗan uwan nasa. Ɓacin rai iya ɓacin rai Lion ya ji, akan me wani zai ɗaura hannunsa a saman kyakkyawar fuskar heartbeat nasu,? To koma waye uban shi sai ya karɓi hukunci wlh, dan bayan shi ba wanda ya taɓa ɗora hannu a saman wannan kyakkyawa kuma lallausar kumatun, shi ma sau ɗaya ya taɓa marin shi, kuma da dalilin, so dan haka bai ga dalilin da wani mahaluki zai ɗaura hannunsa a jikin TRIPLETS nasa ba kuma ya kyale shi, ba'ayi wannan mutumin ba a duniya a cewarsa. Nan take Areef ya gaya mishi duk yadda aka yi, abin ya fara damunsa yanzu, wato kenan a kan Jehan wani ya mare shi? Wai shi ya rasa gane me matsalar TRIPLETS nasa da jinin Nawazudden ne, shi gaskiya yanzu sun fara ɓata mishi rai, ya fara jin ya tsani Nawazudden ɗin ma, akan me dalilinsa ƴan uwansa mafi soyuwa a garesa zasu rinƙa shiga haɗari, gaskiya shi ba zai yarda da hakan ba, dole ya taka musu birki kuma ya ɗauki mata, sai dai fa abin da bai sani ba shi ne, ya makaro, dan shi kan shi soyayyar Nawazudden ɗin tana cikin zuciyarsa, shi ne bai sani ba dan bai san menene ma soyayyar ba, amma tabbas shi ma yana kaunar Nawazudden da family'nsa, dama idan baku manta ba, da Rimsha da babanta muguwar shiga ran bala'i ke garesu, idan ka zauna da su to dole sai sun shiga ranka ta yadda zaka kaunace su ba tare ma da ka sani ba, to shi ɗin ma hakan ce, yana bala'in Kaunar Nawazudden ɗin, shi ne bai gane ba, kuma cire son Nawazudden a ransa ba abu bane mai yiwuwa a saukake yadda yake faɗe a baki, su kuma su Aseef sun riga da sun yi nisa, ba zasu iya dai'na son uncle nasu ba, ya zamo wani ɓari na jikinsu. TO FA BABBAR MAGANA SHI KUMA LION KISHIN BALA'I KE GARE SHI NA FITAR HANKALI, YANZU YA FARA KISHIN TSAKANIN ƳAN UWANSA DA DADDYN RIMSHA NE KO YAYA? DAN WANNAN DAI ALAMAR KISHI CE. Shiru suka yi gabaɗayansu ba wanda ya sake yin magana, after some minutes Areef ya miƙe yana faɗin "Zan je prison tare da Mark ina dawowa". Zaro idanu Aseef ya yi yana faɗin "Prison kuma? Me zaka je yi a can". Nufar waje ya yi yana faɗin "Ƴar uncle zan je gani". Zai miƙe ya bishi Lion ya riƙo hannunsa tare da juyowa suna fuskantar juna. "What is wrong with you?" Ya faɗa a sanyaye yana kuma tsare shi da blue eyes nasa. Girgiza kai ya fara yi yana faɗin "Nothing". Shiru ya yi bai sake magana ba, dan dama baya tambayarsu abu ya sake maimaitawa, shi kuma Aseef ɗin ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi dole ya yi dan ya tabbatarwa da ɗan uwan nasa ba komai, ya san cewa idan har Lion ɗin yasan cewa a kan mace ya shiga wannan damuwa har haka, to fa shi da auren Heartbeat har abada, dan wlh Lion sai ya wargaza komai, zai ce dama ai yasan mata balai ce, daga haka kuma sun jawa Rimsha, abubuwa dai zasu kwaɓe sosai, shiyasa ya gwammaci ya ɓuye damuwarsa shi kaɗai, ko Areef ba zai gayawa ba, dan yasan dukka bakinsu ɗaya ne, idan Areef ya ji, to tamkar a kunnen Lion ne, dan sai ya gaya mishi, haka suke gabaɗayansu, ko shi Areef ya gayawa magana ya ce kada ya gayawa kowa, to fa sai ya gayawa Lion, wuyarta dai a faɗa mishi ɗin ne, ana faɗa zai labartawa Lion ɗin, shi ma Lion ɗin wani lokaci yana gayawa Areef ɗin magana idan ta shafesu or daddy, a takaice dai dukkansu bakinsu ɗaya ne, so mafi alkhari a gareka idan baka son ɗaya daga cikinsu yasan da magana, to ka ɓoye kayanka a cikinka, dan soyayyar da yake tsakanin TRIPLETS ya wuci wasa, sun wuci tunanin mai tunani. A palon sama Areef ya ci karo da Rimsha tana riƙe da Jacket ɗin Lion da ya rufa mata daren jiya, "Good morning my lovely brother". Ta faɗa tana ɗan murmushi, "Morning our Queen ina zaki je?" "Zan mayarwa da yaya Saif rigarsa ce". Shiru ya ɗan yi yana kallon rigar kafin ya ce "Okey je ki dawo ina jiranki a wajen mota ki zo mu je wajen sister a prison". Cike da murna ta amsa mishi da to, da sauri ta wuce zuwa cikin ɗakin, shi kuma ya wuce zuwa kasa. 💋PRISONERS💋 Ɗakin da suka kai Jehan ɗaki ne mai ɗauke da mata guda uku da ita huɗu, biyu daga cikin matan, manya ne masu ɗan shekaru wanda a kallah zasu kai 28 haka, ɗayar kuma matashiya ce. Da yake bata san su ba, sai tana ɗari ɗari da su, saman gadon da ya kasance mallakinta ta zauna a bakin tana tunanin yadda zata yi da gidar Hjyr daɗi, ita ba halin da take ciki bane ma ya dameta, su Adiva dake gidan Hjyr daɗi sune a gabanta, da kuma yadda zata yi ta rusa gidan, a cewarta bata bukatar taimakon kowa, dan bata yarda da kowa ba, su kansu hukuma bata yarda da su ba, a cewarta ɓata gari sun yi yawa a ciki, dan haka sai ta natsu ta samu aboki na kirki wadda ta san ba na banza bane daga cikin hukuma kafin ta bashi hujojin da take da su, yanzu bukatarta ta fita daga cikin prison ɗin nan ne, idan ta fita, zata fara bincike a kan hukuma dan nemawa kan tafita, kafin nan kuma sai ta tabbatar da ta tsaya da kafafunta ta yadda zata ci uban Hjyr daɗi babu surki, ta tsani matar tamkar ta sanya wuƙa ta cinke mata maƙogoron wuya kowa ya huta. Ɗaya daga cikin matan dake cikin ɗakin ne ta katse mata tunani da cewa "Yarinya sannunki da zuwa gidan holewa da shagali tare da sharholi, amma gaki ƴar karamar yarinya har haka laifin me kika yi da ya cancanci a kawo ki nan?". Ɗaya daga cikinsu ne ta sake katseta da cewa "To ya wuci kisa ne, kin san fa yaran yanzu duk ƴan ta'adda ne, bar ganinta yarinya hmmm wannan daga ganin idanunta a bushen nan ba karamar ɓarna zata yi ba a duniya". Ita dai shiru bata tanka musu ba, miƙewa matar da ta fara maganar ta yi ta dawo kusa da ita ta zauna tana faɗin "Ki saki jikinki, nan gidan jin daɗi ne ai, ki zama jan wuya dan ki zama zakarar gwajin dafi a gidan nan, a nan ba'a yin shiru shiru, wlh idan kika yi shiru shiru azabtuwa zaki yi, ki buɗe baki ki yi magana, yanzu dai gaya mini laifin me kika aikata da har aka kawo ki nan?". (Niko na ce baki san da waye kike magana ba gaskiya, jehan ai ba shiru shiru ba ce, kawai bakunta ce, amma daga baya zaku san wace ce ita ai) Juyowa Jehan ɗin ta yi ta dafa matar tana faɗin "To ke laifin me kika yi da har aka kawo gidan yarin?". Babu alamar shakka ko tsoro, nadama bare kuma sarewa a tattare da matar, idanunta a tsaitsaye, a bushe garau, ta ce "Kishiyata mana na zubawa shinkafar ɓera taci ita da ƴaƴanta biyu suka mutu, ni kuma aka wucu dani nan, ni wlh wannan gidan ma ya fi mini daɗin zama, amma wai fa kashe ni za'ayi, kawai zaman ɗan lokaci nake yi a nan, kuma da kike ganina a cikin ɗakin nan, nine mai ƙaramin laifi, wancan kuma ban san me ta yi ba, mun tambayeta sai ta ce babu komai, to babu komai za'a kawota nan ne?". Ai kuwa Jehan bata san time da ta sake ta ba, baya kaɗan ta ja tana kare mata kallo, jibi yadda ta furta ta yi kisan tamkar wadda ta kashe kaji ko tattabaru, ba mutane ba, anya wasu suna son samun rahmar Ubangiji ko yaya take kuwa? Kai gaskiya wasu dai sun rantse dole dole sai sun tabbata a wutar jahannama, a haka kuma wai ita ce mai karamin laifi da suke ikirari a cikin waƴan da suke a ɗakin before Jehan ɗin, wannan bala'i da me ta yi kama?. Kallon banza Asiya wadda ta yi magana ɗazun ta wurgawa Jehan ɗin kafin ta ce "Me kika wani ja baya dan kinji abin da Raliya ta ce? Ai ke karamar ƴar iska ce, mu kam ai jiga jigai ne, dan haka ma ki daina tsoro na gaya maki, a duniyar yanzu kada ki ji tsoron kowa nake gaya miki, ki zama jaruma kamar dai mu?". Da alama wannan Asiyar ƴar wiwi ce, ƴar hauce ba kaɗan ba, tana abu kamar wata jikar kauraye. Shiru Jehan ta yi tana tunanin in dai zata zauna a nan, to ya zama dole ta fito da halinta na baya, domin ta lura gabaɗaya ƴan gidan nan tantiran ƴan iska ne, to dole ta koma ainahin jinin Nawazudden ɗinta dan su ci uban juna, daga zuwanta yau taga bala'in da ya sha gaban tunaninta, ji bi yadda suke faɗar laifukansu da bakinsu sanka sanka, lallai duniya abin tsoro ce, ba dole mu rinƙa shiga masifu kala kala ba. Matsowa kusa da ita ɗayar da bata yi magana ba take shiru shiru mai suna Ameera ta yi tana faɗin "Ni ban san sunanki ba, amma dai koma ya sunanki ina son ki sani wlh ban aikata wani laifi ba aka kawo ni nan, zaluntata aka yi, kawai fin karfi a ka nuna mini". Juyowa Jehan ɗin ta yi suna fuskantar juna da Ameera ɗin, yarinya yar matashiya da ba zata wuci 21 years ba, zuba mata idanu Jehan ɗin ta yi, da alama yarinyar tana da ilimi kuma ta yi karatu. "To me yasa aka kawo ki nan?" Miƙewa ta yi ta dawo saman gadon Jehan ɗin tana faɗin "Wani yaron amshakin mai kuɗi ne ya yi wa wata yarinya fyaɗe, shi ne iyayen yarinyar suka kai kara court, dana ji labari a matsayina na ƴar jarida mai son tallafawa kasar, sai na nemi zantawa da yarinyar, ni gaskiya ƴar talakawa ce, da kyar da suɗin goshi iyayena suka iya biya mini kuɗi nayi karatu, iya diploma na tsaya a karatu na, Allah ya sa dai ina da rabo na sami aiki, to kamar dai yadda kika sani ne a duniyar yanzu mai kuɗi shi ne mutun, talaka kuma bawa ne, haka aka tauyewa yarinyar nan hakkinta, aka rufe case ɗin da wasu kananan shaidu wai dama yarinyar bin maza take yi, shi yaron lokacin da abin ya faru ma baya kasar, kawai dai talauci ne ya yi wa iyayenta yawa yasa suka yi wa yaro wannan sharri dan su sami kuɗi, iyayen yaro suka saye alkali ya basu gaskiya, har da ɗaurawa iyayen yarinya diya da zasu biya wai dan sun ɓata wa yaro suna, ni kuma dana ga haka sai na yi ƙoƙarin zantawa da yarinyar, na samu hujoji daga wajenta shi ne nayi ƙoƙarin bankaɗo gaskiya, daga haka ne fa suka ɗaura mini sharrin ina dillancin kwayoyi, ni ban san taya akayi kwayoyin maye suka shiga jakata har gidan mu ba, ina dawowa daga wajen aiki ƴan'sanda suka kamani wai sun sami information a kan ina dillancin manya manyan kayan maye, daga haka court ta yanke mini hukuncin ɗaurin rai da rai a nan gidan, dan ba kananan kayan maye aka samu a jakata ba, ban san hawa ba ban san sauƙa ba, sai dai na ganni a nan, yanzu sai Allah kaɗai ya san ya iyaye na suke, yau watana uku kenan a nan, kanina ne kawai ya taɓa zuwa sau ɗaya farkon rufeni da aka yi, ya ce mini baba yana asibiti, tun daga ranar ni ban sake ganin kowa nawa ba". Ta kai karshen maganar tana sharar kwallah dake zubo mata, ita kam Jehan ta rasa ya zata yi da waƴan nan abubuwa, can gidan Hjyr daɗi ga Maryam da take son ta kama ubanta ta yi mishi ɗan yen hukunci, nan kuma ga Ameera, wannan bala'i da me ya yi kama ne wai? Dariya Asiya ta kwashe da shi har da shewa tana tafa hannu, ita ma dai Raliya dariya ta kwashe da shi tana faɗin "Yo idan ban da abin ɗan talaka da neman saka kai cikin masifa, ina ke ina nemo wasu hujjoji dan ki tona mishi asiri fisabillilahi? To ai shikenan yanzu ga shi ai kin kare a wannan gida ɗaurin rai da rai, dama wannan abin ne kike ɓoyewa kika ki gaya mana laifinki? Wlh na zaci ma kan wani kika fille ko kin kwakwale idanun wani jaririn ne? Ashe ke salihar baiwa ce ma ban sani ba, to ai ga shi yanzu zaki kare gabaɗaya kuruciyarki har tsufa zuwa mutuwa a nan, kuba ƴan shisshigi ba? Ɗan talaka da bai iya samun karamar dama ko ya take ba, to yanzu ai sai ki baza shaidar kowa ya gani". Ta kai karshen maganar tare da sake tuntsurewa da dariya. A walaƙance Jehan ta kalleta ta watsar kafin ta ce "Ke dai anyi dabba jahila wlh, an gaya miki shi talaka ba mutun bane? To idan baki sani ba ki sani, wani talaka da yake yawo a cikin bola sai ki tarar ya fi shugaban kasa samun matsayi a wajen ubangiji, ki zama mai yin fariya da aikata aikin Allah ba saɓon Allah ba, ki bugi kirji ki ce kina da kusanci da Ubangijinki ta gefen sallah, azumi, Zakka, sadaka, da sauransu, ba ki daki kirji kina cewa kin fi wani abu kaza na duniya ba, Allah da ya baki ba wani abin kika yi mishi ya baki ba, haka suma waƴan da bai bawa din ba, ba wani abin suka yi mishi ya hana su ba, bai manta da kowa ba, yana sane da dukka bayinsa, so ki zama mai fariya da kin fi kowa aikata aikin Allah ba kin fi wata or wani samin wani abu na duniya ba, banza ballagaza kawai, wadda bata san ciwon kanta ba". Ta kai karshen maganar rai a matukar ɓace. A fusace Raliyar ta damko wuyar rigarta tana faɗin "Bani da mutunci, wlh yanzun nan sai na saɓa miki kamanin, ke har kin isa ki ɗaga mini murya a cikin ɗakin nan dan ubanki?". Buge hannun nata jenan ɗin ta yi, a walakance ta ce "Ke ma kika ce baki da mutunci bare kuma ni, to da kike kallona hakan nan, sam ban san menene mutunci ba, na fiki zama mara kunya, dan haka ina mai baki shawara wlh tun wuri ki kama kanki babu ruwanki da ni, bana shiga harkar kowa, amma idan mutu ya shiga tawa, to fa ya sani duk girmansa bana shayin na bi ta kan mutun na take banza!!". A harzuƙe Raliyar ta miƙe tare da sake riƙo mata wuyar riga ta ɗaga hannu da nufin marinta, cak Jehan ɗin ta riƙe hannun nata tare da miƙewa ita ma tana faɗin "Wlh idan kika yi gigin marina bazaki sake marin wata ba a duniyar nan, an gaya miki ni irin kishiryaki da kika kashe ne? To ni ba haka nake ba, ni kaɗai na gayyya ce mai zaman kanta, idan kina so ki jawa kanki bala'in da gabaɗaya zuria'arku ba zasu iya ɗauka ba kuma to Bismillah zaki iya sanya hannunki a jikina". Abinku da prison, Asiya tana makale saman gadonta tana zuga Raliya a kan kada ta yarda wannan ƴar yarinya ta ɗaga mata murya, ita taki yarda ta sauƙo ta shiga faɗar dan tana tsoron idan gandurobobin sun ji ana faɗa suka zo, su haɗa da ita su yi mata hukunci, shi ne taki saukowa ta shiga, tana daga sama tana kara hura wutar abin. Miƙewa Ameera ta yi tana rokonsu a kan dan Allah su bari, ita kuwa Raliya har cikin ranta ta tsorata da jin kalaman Jehan, tana ganin kamar Jehan ɗin ta taki wani tsiyar ne, dama kunsan irin wannan idan baka san mutun ba irin haka ta kasance a tsakaninku, to zaka rinƙa ganin kamar ya taki wani abin ne, tsoron da ta ji ne yasa da Ameera ta basu hakuri, sai ta hakura ta saki Jehan ɗin ta koma saman gadonta ta kwanta, ita ma Jehan komawa saman nata gadon ta yi ta zauna tana tunanin yadda zata ɓullowa waƴan nan abubuwa da suka sha kanta. Gefenta Ameera ta zauna tana tambayarta a kan me ta aikata da har aka kawo ta nan, ba musu ta gaya mata ga abin da ta yi, daga Raliya har Asiya sai da suka ce eh!! Da karfi, wato ta yanke gabansa gabaɗaya, Jehan da iya shege har da iya gaya musu gabaɗaya ta cire bata rage ba, dafe kirji Ameera ta yi tana jinjina mata irin wannan aiki, ita da take da 21 years a duniya ma yaushe zata iya kallon namiji babba zindir ba kaya bare har ta kama ta yanke, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ai gani da ido ma kawai babbar bala'i ce, duk wata mace a ranar da ta fara kalla sai ta shiga tsoro bare ita Jehan da take ƙaramar yarinya, kuma abin mamaki idan tana magana hankalinta a matukar kwance, tamkar ba ita ta aikata ba, to yau dai sun ji labarin da ya goge musu hadda, daga haka ɗakin ya yi tsin kowa da abin da yake tunani a cikin ransa. A ɓangaren Rimsha kuwa, bayan ta shiga ɗakin da sallama ɗauke a bakinta, Aseef ne ya amsa mata sallamar tata, kusa da Lion ɗin ta zo ta tsaya tana faɗin "Good morning Yaya Saif and yaya Aseef". Bai amsa ba kuma bai ɗago ba, Aseef dai ya amsa amma bai ɗago ba. Miƙa mishi rigar tasa ta yi tana faɗin "Ga shi nan Nagode". Sai lokacin ya ɗago da kallonsa kai tsaye sai saman idanunta, dan suke yake son kallah, yanzu gabaɗaya ma haushin family'n Nawazudden ɗin ya fara ji, dan suna jefa mishi TRIPLETS nasa cikin haɗari, ya kuma sanya a ransa sai an yanke hannun wannan ɗan'sanda da ya mari Aseef ɗin, dan ba zai barshi ba, bai ga wanda ya isa ya taɓa masa TRIPLETS nasa kuma ya kyale shi ba. Kallonsu na ƴan sakanni ya yi kafin ya dawo da kallonsa saman rigar da take riƙe da shi ɗin, shiru ya ɗan yi, ya kalli rigar kafin ya mai da kallonsa kan abin da yake yi, bai ce da ita komai ba, kuma ba shi da niyar yin maganar ma baki ɗaya. Shiru ta tsaya tana jiran ta ji me zai ce. Ganin Lion ɗin bai da niyar yin magana ne yasa Aseef ya karɓi rigar yana faɗin "Sarkin rigima me kuma kika je ki ka taɓo ya shiga miki idanunki? Ko kuka kika yi ne?" Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin "Barci dai nake ji". "Daren jiya baki yi barci bane?". Ɗan satar kallon Lion ta yi kafin ta ce "Nayi amma dai ina jin wani ne sosai". Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "To jeki kiyi ko?". Okey ta amsa mishi tare da juyawa ta nufi waje da sauri dan ta je wajen Areef su tafi wajen Jehan, duk da tsananin barci da take ji tana son kallon ƴar uwanta, dole ta danne ta je wajenta. Cikin bedroom nata ta koma ta kwasanwa Jehan ɗin kayan sakawarta wajen kala biyar, ta haɗa mata da hijabin sallah har kasa, guda biyu, ta ɗauka mata daddumarta ta haɗa, duk dai abin da ta san ƴar uwar tata zata buƙata sai da ta ɗauka mata ta zuba a cikin school bag nata ta ɗauka ta fito waje. A cikin mota ta isko Areef da Mark suna jiranta, tana shiga Mark ya kunna motar suka bar gidan, sai hira suke yi shi da ita har suka isa prison ɗin, kamar dai jiya haka aka rakasu har ciki, in da suka zauna jiya yau ma a nan suka zauna. Ba'a ɓata musu lokaci ba aka fito musu da Jehan ɗin, gaisawa suka yi da Rimsha kafin ta ɗagawa Areef da Mark gaisuwa, har yau tana cike fal da confidence, babu fa alamar sarewa ko karaya a tattare da ita, cike take da kwarin gwiwa, Areef bai yi mamankin ganin bata yi laushi ba, dan a bincike a kan ta da ya yi daren jiya, ya gano tun ainahinta ma mafaɗaciya ce, ga zafin rai, ga kuma taurin kai, bata magana ta canza, bata da fara'a ko kaɗan, so silent take, bata shiga abin da bai shafeta, sai dai idan taga za'ayi zalinci to fa sai in da karfinta ya kare, hakan nema ya kara karfafa mishi gwiwa a kan lallai tana da gaskiya kuma zai taimaka mata, zai tsaya mata. "Jehan zaki iya yi mini kwantancen gidan mutumin, wato in da abin ya faru?". Cewar Areef ɗin. Shiru ta yi kamar mai tunani, can kuma sai ta girgiza mishi kai tana faɗin "No daga nan ba zan iya yi maka kwantance ba, sai dai idan naje unguwar zan gane gidan, ni ban taɓa zuwa Kaduna ba sai wannan karon, ban san ya yake ba tare na iya kwatantawa". Shiru ya zuba mata idanu yana kallon yadda take magana, shi dai kome ta yi wlh burge shi take yi, "Okey yanzu abin da ya kawo ni nan, ina son duk wanda zai zo nan ya ce yana son yin magana dake, to kada ki yarda, kada ki kuskura ki bawa kowa damar yin magana da ke, ko da an sanyaki fitowa dole, to idan kin fito ko sun yi miki tambayoyi amsa ɗaya zaki basu shi ne baki san komai ba, daga haka kada ki kara kada ki rage, nasan akwai lauyoyin da zasu buƙaci ganinki or ƴan jarida, da sauran manyan mutane, na san kamar yadda kike da makiya suma makiyan naki suna da makiya masu son ganin bayansu, so wasu zasu samu damar amfani dake dan cimma burinsu a ɓangaren siyasa, dan na ga yanzu faɗar taku ta koma ta siyasa ce, dan haka ki kula, kada ki kuskura ki buɗe baki ga kowa". Jinjina mishi kai ta yi alamar to ta ji, miƙa mata jakar kayan Rimsha ta yi suka miƙe dan su tafi, ita ma Jehan ɗin miƙewa ta yi dan ta koma ciki. Kamar jiya har ya ɗan yi gaba, sai kuma ya sake dawowa tare da riƙo haɓarta yana faɗin "Shi ne baki tambayi sunana ba ko?" Kallon gefen ido mai kama da harara ta watsa mishi kafin ta ce "To me sunanka zai kara mini?". Kashe mata ido ɗaya ya yi tare da yi mata signal da gera ɗaya yana faɗin "Wai ke jiya baki yi tunani na bane? Ni fa na kwana tunaninki". Shiru bata tanka mishi ba, dan a cewarta bata da lokacin shirmensa, dama kuma idan baku manta ba, ita haka take, bata san wani abu wai shi shauki or wasa da dariya ba, tsare gida kawai ta iya. "Au ba zaki yi magana ba?" Nan ma shiru ta yi, tana kokarin buge hannunsa da ya riƙe haɓarta da shi. "Sarkin faɗa, ai jiya duk naga tarihinki tun kina ƴar shekara 2 a duniya, kika rinƙa takurawa my Rimsha da masifa a baya ko? To zan rama mata ai, mai rama mata ya zo, masifaffa kawai, ni kada ki ce zaki yi mini dan maganinki zan yi, yanzu dai ki ajiye sunana dan zai yi miki amfani, sunan babyn baby kin ji ko?" Zaro idanu Rimsha ta yi tana maimaita sunan babyn baby kuma? Ga shi dai da Hausa ya faɗi babyn baby, to ko a ina ya jiyo sunan oho mishi, shi da ba jin Hausa yake yi ba, ita yanzu ta ma dai'na mamaki a kan TRIPLETS dan sun wuci tunanin mai tunani, idan ka biye musu mamaki ne zai kashe ka, wai babyn baby dan iya shege. Harara ta watsa mishi kafin ta sa kai ta wuce abinta, juyawa ya yi ya riƙo hannun Rimsha yana faɗin "Wannan ƴar diramace, ta iya juyawa mutun idanunta fararen nan, kuma suna da kyau idanun sosai kamar na uncle na". Ita dai Rimsha ko a jikinta tun da ta zo ta ga Jehan tana nan lafiya lukui ai shikenan. Suna barin prison ɗin suka nufi gida, shiru suka yi a cikin motar Areef yana tunani a kan Jehan, shi kuma Mark yana tunaninsa na daban, ita kuma Rimsha kamar kullum ne, kun sani tunanin Lion take yi. A ɓangaren gidan Abbo kuwa waton gidan su Nawid ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ *Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta* E49-50💋 A ɓangaren gidan Abbo kuwa waton gidan su Nawid, har yanzu dai Abbo shiru ba shi ba labarinsa, soyayya babu kama hannun yaro suke zubawa a tsakaninsu, A'afia ta saki jiki sosai da Dr Nawid, ta mance ma da abin da ya taɓa faruwa da ita a rayuwarta ta baya, ta shiga sabuwar yaruwa mai cike da nishaɗi da annashuwa, mijinta na nuna mata so, surukuwarta na nuna mata tsantsar kula, hankalinta ya kwanta over. Yau ta kama ranar Friday, tun misalin karfe 5 ta kammala komai nata, ta Shiryawa mijin nata duk wani abin da ta san zai buƙata saboda yau da wuri zai dawo daga wajen aiki, ba zai kai mangariba ba, tsara wanka ta yi tsab ta zuba kwalliya sosai da sosai, doguwar riga baka mai kama jiki ta sanya, ta haye saman bed nata ta yi shiru tana tunane tunane yadda zata yi da batun Ommunsu na case nata ita da Umaisha, gaskiya ba zata iya barin Umaisha ta yi sata ba, idan Ommu ta cika matsawa to ita gaskiya zata sanar da Abbi da kuma Irfan sai dai duk abin da zai faru ya faru, ita ta jawa kanta da kanta. Ta nutsa cikin tunanin kamar a mafarki ta ji ya kwanto a jikinta yana faɗin "Me kike tunani har nayi sallama baki amsa mini ba?". Kayatatcen murmushi ta sakar mishi tana shafa kumatunsa tana faɗin "Kai mana my mijina, kai nake tunani, to barka da dawowa ya aiki? Ya su Bahijja?" Ɗan jan dogon hancinta na gadon turawa ya yi yana faɗin "Sarkin kishi ba, kullum sai an ce yasu Bahijja, ni nasan ba dan kiji ya suke kike wani tambayata ba, kawai dai dan kiji na kallesu ko na kula su ne, to ki sani ni bana kula mata haka yadda kike tunani, ina fa sane da abin da nake yi, dama da kike gani sometimes nake cewa zan kula mace dan na nemi matar aure ce, na gaji da zama a gwauro, to yanzu kuma tun da Allah ya bani mata saliha, kamila, mai kaunata tsakani da Allah tare da bani kulawa, to ina ruwana da wasu matan kuma? Ni tun ainahima su Bahijja a ƴan aikina suke, basu taɓa wuce wannan matsayin ba, idan da ina kulasu ai da na jima da yin aure, to ba ko wace mace nake ɗaga idanu na kalla ba ma, sai a rage kishi". Ya kai karshen maganar tare da bata sumbata a kumatu, kashe murya ta yi a ɗan shagwaɓe ta ce "Ni fa nace maka ba kishi nake yi ba, kawai dai kula da kai nake yi ne". Matso da face nasa daf da tata sosai ya yi, harshensa ya fitar yana ɗan lasan lips nata cikin salo da kwarewa irin nasu na likitoci, dan sun kware a sanin sirrin mata da iya sarrafasu, a hankali ya zura harshen nasa cikin bakinta yana jujjuyawa, nisawa ta yi tare da fara yin kissing nasa da kyau da kyau, kankameta ya yi cikin dabara ya fara laluɓar breast nata dake ta faman sokinsa a kirji daman, ta saman wuyar rigarta ya zura hannunsa ciki ya capko ɗaya, cikin salo ya fara murzasu yana wani lumshe idanu kamar mai jin barci, zura hannunta ta yi cikin gashin kansa ta shiga shafawa har zuwa wuyarsa, nan take ya birkice mata. Zame rigar jikin nata ya fara yi, bata damu ba, dan ita ta mance ma da ana wani abu wai sex a rayuwar aure, kullum zasu yi wasa iya wasa da shi, amma bai taɓa kwatanta shigarta ba, shiyasa ko da ya rabata da kayan jikinta bata wani damuwa, wasa da ita ya fara yi sosai yana sauke numfashi, ita ma bata yi kasa a gwiwa ba wajen taya shi tare da ruɗar da shi ya kara fita a hayyacinsa sosai, surutai ya rinƙa zuba mata tare da sambatu, har duhun mangariba ya fara saukowa, miƙewa daga kan nata ya yi tare da kashe wutar ɗakin ya fara cire kayan jikinsa. Tana kwance shiru yadda ya barta, ya gama rabata da komai na daga jikinta, da yake akwai duhun mangariba sai ya zama da ya kashe wutar ɗakin bata iya ganinsa sosai. Tas ya cire kayan jikinsa bai rage komai ba, dawowa saman gadon ya yi tare da hayewa kanta ya cigaba da abin da yake yi, ta ɗan tsorata lokacin da ta ji saukar jikinsa a nata kuma babu short, idan suna wasa baya cire short nasa gaskiya, iya kayan yake ragewa, wani lokaci ma ko singlet nasa baya cirewa, amma yau gabaɗaya ya cire komai, abin ya bata mamaki. Tana can tana tunani bata ankaraba sai ji ta yi ya shigeta, zaro idanu waje ta yi kusan a tare suka zaro idanun nasu, shi ya yi hakan ne dan ya ji ta ba'a budurwa ba, ita kuma ta yi hakan ne dan tsorata da shigarta da ya yi, shiru ya ɗan yi kafin kuma ya fasa abin da ya yi niyar yi ɗin ya zare jikinsa daga nata, ita har ga Allah ma ta manta da abin da ya faru da ita a baya, ya mantar da ita komai da soyayyarsa. Kwanciya ya yi a gefenta yana mayar da numfashi tare da yin ruf da ciki a saman gadon, bata motsa daga in da take ba, shi kuma juyi ya fara yi har aka yi sallar mangariba, sun yi shiru dukkansu, can tamkar a mafarki ta tsinkayo muryarsa cikin dodan kunnenta yana faɗin "Aafia ina kika kai budurcin ki? Waye kika bamawa? Waye kika sadaukarmawa?". TASHIN HANKALI, WANNAN TAMBAYA CE DA DUK WATA MACE A DUNIYA BA ZATA TAƁA SON MIJINTA NA SUNNA YA YI MATA SHI BA, KO WACE MACE ZATA SO NE TA ZAMA MAI DARAJA DA KIMA A WAJEN MIJINTA, IDAN BABU WANNAN ABIN, TO BABU WATA DARAJA DA KIMA A TATTARE DA MACE, KOMAI ABINKI BA ZAKI TAƁA SON KIJI IRIN WANNAN TAMBAYA DAGA BAKIN MIJINKI BA, DAN HAKA MATA MU KULA, IYAYE A KULA SOSAI, KI KULA DA MUTUNCINKI DAN KI GUJEWA IRIN WANNAN TAMBAYA, DA ZARAR KIN SAMI IRIN WANNAN TAMBAYA DAGA FARKO TO SHIKENAN KE KAM KIN GAMA YAWO, KE DA DARAJA I IDONSA KAM SAI DAI KI HANGA A MAKOTA, YANA DA KYAU MU KARA TSANANTA KULA, ITA DAI AAFIA KADDARACE TA FAƊA MATA, TO AMMA SHI BAI SAN DA HAKAN BA, DOLE YA YI MATA TAMBAYAR DAN YA JI MENENE YA FARU? DUK WANI NAMIJI A DUNIYA TAKAMARSA WANNAN ABIN NE, IDAN BAKU SANI BA KU SANI ALFAHIRI YAKE YI DA SHI IDAN YA SAMU, HAR YA MUTU YANA ALFAHARI DA SHI YA KARƁI BUDURCIN MATARSA, ALLAH YA KARA TSAREMU A DUK IN DA MUKE. Wani dum dum gabanta ya bada bugu, wasu zafafan hawaye ne suka fara bin kuncinta, ta rasa me zata ce da shi, a nashi ɓangaren kuwa, tunani yake yi a kan su Imran, gabaɗaya sai ya ji kimarsu Imran ɗin ta ragu a idanunsa, bawan Allah bai san cewa shi Imran ma bai san da maganar ba, harta Abbi da ya haifeta bai san da maganar ba, da ya sani zai yi gaggawar sanar da shi, kuma ba zai aura mishi ita ba har sai ya sanar da shi idan ha aminci, iya daddyn Jelly, Irfan da Akil ne kawai suka san da maganar, su ma bayin Allah sun mance da zancen ne baki ɗaya, da basu mance ba, zasu sanar da shi tun da wuri. "Ba zaki bani amsa ba?" Ya yi maganar tare da miƙewa zaune, ban da hawaye babu abin da take yi, ta kasa magana, yau abin ya dawo mata sabo, ta tuna komai a cikin ƙwaƙwalwarta, ya ilahi ya lillahi. Ganin bata da niyar yin magana yasa ya ce "Amma dai gaskiya baki yi wa su Abbi adalci ba, kin cucesu kin zaluncesu, dama shiyasa kike guduna dan kada rana irin ta yau ta zo? Baki kyauta musu ba, nima kuma kin cuceni baki kyauta mini ba, amma babu komai". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi toilet dan ya yi wanka ya yi sallah lokacin sallar isha ta kusa, dan anyi mangariba kam tun ɗazun, sai kuka take yi, ta rasa bakin magana, kada kuga laifin Dr bai san gaskiyan abin da ya faru bane, ya ma yi mata da sauki da bai sameta a yadda yake tunani ba ya hakura, da wani namijin ne sai ya haɗa mata da mari, amma shi ya danne saboda da Mahaifiyarsa da tata ƴa da kanwa ce, ga shi ta kasance kanwa ce ga babban amininsa ɗaya tilo a duniya, hakan yasa ya daure ya danne abin, amma fa ba karya ya yi mishi ciwo ba kaɗan ba. Tana kwance har ya fito ya shirya tare da yin sallar mangariba sannan ya fice daga ɗakin zuwa masallaci dan ya yi sallar issha, bayan tafiyarsa ne ta miƙe da kyar ta nufi toilet, har lokacin kuka take yi, wanka tayi tare da ɗauro alwala, fitowa ta yi ta shirya cikin doguwar riga, ta zuba hijabi, ta tada sallah, bayan ta idar ne ta kunna wutar ɗakin tare da gyara gadon fes kafin ta sanya air freshener a ɗakin, har lokacin tana cikin tsananin damuwa na wuce misali. Bayan ta kammala ta hau gadon ta kwanta, ko wajen Ummi yau ta ji bata bukatar fita, gara mata ta yi kwanciyarta a cikin ɗaki kawai, Ummi kuma tana palo tana jiran su zo su yi hira, dama haka suka saba yi, idan sun ci abinci sai su fito su sha hira zuwa karfe tara kowa ya wuce bedroom nasa, to yau dai hayewa saman bed nata ta yi ta kwanta tana tunanin abubuwan da suka faru da ita a rayuwarta ta baya, sai yanzu take jin cewa Rufee ta cuceta, ta gama da rayuwarta, da alama dai asirin da Rufee ta yi mata ya sake ta ne, to anya ba bokan bane ya mutu ko kuma Rufee ne ta fito ta warware asirin da kanta? Mu dai je zuwa zamu ji komai. A ɓangaren Dr ma, da kyar ya iya yin sallah dan ɓacin rai, shi da tun farko ta gaya mishi ita ba budurwa bace ai da ya fi mishi, matsalar kuma da aka samu shi babban likita ne, duk wasu matsaloli na mata ya sani, dole zai gane ita ba budurwa ba ce, idan kuma da kansa ya gane dama dole a sami irin wannan matsala, farkon abin da zai fara tunani ma to da waye ta kwanta? Wani irin mutun ne? Yana ɗauke da wani ciwo or not? Ita ɗin lafiya take or not? Koma dai akwai karamin ciki a jikinta? Tambayoyi dai kala kala zai yi ta yi wa kansa wanda kuma daga haka babu samun yarda kenan a tsakaninsu, dan zai yi ta tunanin ai bin maza take yi, ya Allah ka tsare mana imaninmu mutincinmu da martabanmu, masu yi wa yaran mutane fyaɗe ku dubi girman Allah ku daina, ku daina lalata ƴaƴan mutane, kuna cutar rayuwarsu, kuna ruguza musu duk wani farinciki, kuna rusa musu jin daɗi kamar sauran mata, kusa su fiskancin tsangwama wajen mijinsu da sauran ƴan uwa, ku ji tsoron Allah ku dai'na, akwai kiyama, akwai lahira ranar da zaku biya duk abin da kuka ci, akwai mutuwa, sannan ko baku mutuba akwai tsufa, bugu da kari kuma zaku haifi ƴaƴan nan ko ba jima ko ba daɗe, kuma maza kuji tsoron Allah ku rinƙa jin kan ƴaƴan da aka zalunta aka yi wa fyaɗe idan kun auresu, ku sani ba laifinsu bane, ku tausaya musu Allah zai biya ku, Allah ka bamu dacewa. Sai misalin karfe 9 ya shigo gida abin da bai taɓa yi ba, a ko da yaushe idan ya je masallaci burinsa kawai ya yi sallah ya dawo wajen matarsa da mahaifiyarsa, sai ga shi yau kuma ko da ya yi sallah ya yi zamansa a masallaci har karfe tara sannan ya dawo, ta shiga damuwa sosai na ganin bai dawo ba, har kamar zata kira shi a waya, sai kuma ta fasa ta danne ta cigaba da kwanciya kawai tana jiransa. A palo ya isko Ummi tana ƙoƙarin shiga bedroom nata dan lokacin barcinta ya yi, da mamaki take kallonsa na fitowa daga waje da ya yi, sannu tare da barka da dare ya yi mata kafin ya nufi bedroom nasu, da mamaki ta bishi da kallo. "Nawid lafiya kuwa? Ya A'afia bata fito ba yau, na yi tunanin bari naje na dubata sai kuma na tuna kila kana ciki ne, amma ya ka fito daga waje kuma? Ga dukkan alamu kuma kana cikin damuwa, lafiya me yake faruwa? Ko dai A'afia ɗin ce bata da lafiya?". A rikice take jera mishi tambayoyin nata. Ƙaƙalo murmushi dole ya yi yana faɗin "Ummi ki kwantar da hankalinki babu komai, A'afia ce take ɗan jin zazzaɓi kuma nayi mata allura tana barci, dan haka babu komai, ki je ki yi barci". Murmushi ita ma ta yi a cikin zuciyarta tana faɗin Allah yasa cikine da surukuwar tata, kullum tana yi musu addu'ar Allah ya basu ciki mai albarka, Nawid shi kaɗai Allah ya bata, tana yi mishi addu'a shi kuma ya haifo mata ko dozen ne haka, zata riƙe su baki ɗaya, sai hamdala take ga Allah ta wuce bedroom nata bayan ta yi wa Aafia ɗin addu'ar samun sauki cikin gaggawa. Shi ma wucewa ya yi nasu bedroom ɗin yana amsawa da Amin ya Allah, kwance ya iskota saman bed, sam bai bi ta kanta ba ya wuce saman sofa ya zauna tare da jawo takardunsa da laptop nasa ya fara aiki, cike da tsoro ta ce mishi ta zuba mishi abinci, ko kallon in da take bai yi ba bare ta sa ran zai amsa mata, cigaba da abin da yake yi kawai ya yi har zuwa karfe 11, bata yi barci ba, shi kuma bai ci abincin ba, ita ma bata ci ba saboda tare suka saba ci, sai 11:30 ya tattare komai ya wuce toilet, wanka ya yi tare da shirin kwanciya ya zo saman bed ɗin ya ɗauki pillow da bargo ya koma saman sofa ya yi kwanciyarsa, yana jin yunwa sosai haka ya kwanta, ita ma tana jin yunwa sosai haka ta kwanta, sai misalin karfe 2 na dare ta samu barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, shi kuma sai karfe 4 ya iya yin barci, nan ma da kyar, sai tunani yake yi a kan waye A'afia ta baiwa mutuncinta, kishi ya hana shi barci, abin ya tsaya mishi a ransa sosai, rashin sani ya fi dare duhu. A ɓangaren gidan Lion kuwa, yau gabaɗaya Network sai rawa yake yi, shi kuma Lion yana son ya yi magana da Tyrone dan ya ɗauko mishi daddyn Rimsha su taho tare, jikin TGA har yanzu akwai sauran ciwo jikinsa da tafiya zai yi mishi wahala, shi kuma Lion yana bukatar daddyn Rimsha da wuri dan yana tantanma a kan wanda ya kama, ƴan biyu ne masu kama ɗaya, daddyn Rimsha ne kawai zai iya rabe wanene daga cikinsu abokin faɗan nasa, bayan haka akwai wasu abubuwa da yake son tasa daddyn Rimsha a gaba ya yi mishi bayani a kai, magana ce da ta shafi Na'urat mahaifiyarsu, yana son kammala case ɗin da wuri ya koma kasarsu dan ya ɗauki lokaci a nan, hakan kuma sam bai yi mishi ba, so yana son kashe komai ya shafe rikicin dan daddyn Rimsha ya dawo cikin family'nsa su yi zaman farinciki. Bayan ya yi sallar mangariba da issha ya dawo, ya yi ƙoƙarin samun Tyrone a waya amma abin ya ci tura, rai a matukar ɓace ya nufi wajen gate baki ɗaya dan ya nemi wajen da akwai Network, dan shi dai dole sai ya yi wannan call ɗin tana da mahimmanci, baya son daddyn Rimsha ya wuce kwana biyu bai shigo Naija ba. Haushi Brady ya fara yi mishi a kan lallai sai ya bishi, ɗaure fuska sosai ya yi tare da cewa Mark ya kwance mishi karen sa, waye zai wani ɗaure mishi sweetheart ɗinsa dan iskanci, bai san cewa Areef yasa Aseef ya ɗaure shi ba dan kada ya takurawa Rimsha, shi ne suka ɗaure shi. Kwance shi Mark ya yi, da gudu ya taho ya rungume Lion ɗin yana wani kuka kasa kasa, shafa jikinsa ya fara yi alamar rarrashi tun da an yi mishi ba dai'dai ba, an kama an wani ɗaure shi an hana shi jin daɗin duniyarsa, ya sha alwashin Allah duk wanda ya sake ɗaure mishi sweetheart ɗinsa dai ya hukunta shi, ko da kuwa Aseef ne, akan me su suna jin daɗin rayuwarsu suna sake wa shi kuma zasu takura mishi? To wlh ba zai yiwu ba, dole ya taka musu birki. Lion da Brady mutuka raba, akwai kauna da amana ba kaɗan ba, wanda yake son mutuwa cikin sauki to ya yi ƙoƙarin cutar da wannan sweetheart Bradyn ya ga ikon god, cikin sauki kuma cikin sauri zai wuce lahira. Waje ya nufa da shi yana cigaba da shafa jikinsa, lafewa ya yi a jikin Lion ɗin alamar ya hakura kenan, kai Brady duniya, ya samu horo iya horo, wani lokaci idan yana abu kamar mutun. Sun ɗan yi tafiya mai nisa tsakaninsu da gidan nasu kafin ya tsaya kusa da wani restaurant yana duba Network ko ya zo, Brady na manne a kirjinsa kamar wani yaronsa, ya kuwa yi Sa'a wajen akwai Network, number Tyrone ya kira, bugu ɗaya ya ɗaga, ba tare da ɓata lokaci ba ya sanar da shi on Monday ya taho mishi da daddyn Rimsha Nigeria, okey ya amsa cikin girmamawa, yana katse kiran nasa Brady ya diro kasa daga jikinsa ya nufi wasu guys dake tsaye su biyu ta gefensu ta ɗan baya kaɗan, da yake Lion ya rungume shi a kirjinsa ne shi yana iya kallon abin da yake bayan Lion ɗin, shi kuma Lion yana kallon gaba ne, shiyasa ya kallin guys ɗin. Da farko zai kira Brady ɗin, sai kuma ya fasa dan ya san horon da ya bawa karen nasa, na farko baya kwaɗayi, na biyu baya bin mutane a hanya, shi baya yarda ma da kowa kamar ogan nasa, sannan baya yin abu babu dalili, ko Rimsha da yake takurawa ita ce take gudunsa, take yin abu kamar mara gaskiya, to a irin hoton da ya samu kuma idan ya kalli mara gaskiya dole zai bishi, shiyasa idan ta gudu yake binta. Zuba mishi ido Lion ɗin ya yi yana kallon ikon Allah bayan ya ɗan juyo garesu kenan, yana zuwa ya yi tsalle ya sanya bakinsa ya kwace wayar dake hannun guy ɗin, yana kwacewa ya nufo Lion da gudu ya kawo mishi wayar tare da hayewa jikinsa, karɓa ya yi tare da juyo screen ɗin wayar dan ya gani menene Bradyn ɗin ya gani, yasan dai haka kawai ba zai kawo mishi wayar mutane ba. Hoton Rimsha ne tana tsaye sanye da wani wandon jeans baki mai bala'in kyau sai ƴar t-shirt fara tas mai ratsin baki a jiki, ta saki dark black curly hair nan nata har gadon baya, ta yi kyau over kamar ka saceta ku gudu, ka je ka ajiyeta kayi ta kallo, ga shi ta ɗan ɗaga idanunta sama, sleeping eyes ɗin sun fito sosai a hoton, ta ɗan motsa laɓɓanta kaɗan dimple nata ya bayyana, da alama hoton bata jima da yin shi ba suka rabu da iyayenta, dan a gidansu na Abuja ta yi hoton tsaye wajen pool nasu. Zubawa hoton idanu ya yi sai haushi a hankali hankali Brady yake yi mishi, Abin da ya faru shi ne, guys ɗin suna tsaye ta bayansu shi kuma Brady yana kallonsu, ya kalli lokacin da suka buɗe hoton, shi kuma kare baya mantuwa, musamman ma irin Brady da ya samu horo, so ya san Rimsha sosai, ya san a gidansu take, dole idan ya ga hotonta zai ganeta, dan su karnika akwai rike mutun, in dai sun san mutu wlh ko shekara zasu yi basu gan shi ba, to duk ranar da suka haɗu sai sun gane shi, haka zasu yi ta hawa jikinsa suna nuna murnar ganinsa da suka yi. Ya ɗan ɗauki ƴan mintoci da zasu kai a kallah biyu yana kallon hoton kafin ya fita daga kan hoton, sai ya kallima ashe a WhatsApp na mutumin aka turo mishi hoton, ɗago kai ya yi dan ya kalli guys ɗin, sai ya kalli wayam sun gudu, dan su da kansu ba su ga wajen da zasu tinkara suce ya basu wayarsu ba, kuma sun san su masu laifi ne, dama duk wani mara gaskiya da ya ji ɗan motsi zai gudu. Ganin basu nan yasa ya dawo da kallonsa kan wayar ya fara bin chatting na guy ɗin da wanda ya turo mishi hoton, dan ya ga me hoton Rimsha yake yi a wajensu? Me kuma za'ayi da ita?. Voice dake saman hoton, wadda aka fara turowa kafin hoton ya buɗe, cikin harshen Hausa mutumin ya yi magana, da wata muryarsa kamar na hamshakan bugaggu ƴan kwaya ya ce "Ni ban san in da take ba, kawai dai ku nemota, iya abin da na sani shi ne, ita Jehan ta turawa video na da ta ɗauka, dan haka ku nemota, ku tabbatar kun karɓa mini video na, idan taki ku kasheta, ni zan ji da Jehan tun da tana prison, dolema na san hukuncin kisa za'a yanke mata tun da Abubakar jaja ya mutu, zan turo muku hotonta wadda na sha bakar wahala kafin na samu, na wahala kafin na gane ƴaƴan Nawazudden ne, akwai wan da ya ce mini tabbas ya taɓa ganin ita Rimshar a Kaduna, na tura mishi hoton ta ne sai ya ce wlh tana Kaduna, shiyasa na nemo ku, dan haka ku nemota, idan kuka kuskura kuka bari video na ya fita wlh sai kun mutu". Shi ne abin da yake cikin voice ɗin, sai dai kafin ya gama jin voice ɗin wayar ta shiga key. Kashe hasken screen ɗin wayar ya yi tare da zubawa screen ɗin idanu yana karantar wajajen da aka fi yawan taɓawa a kan screen ɗin, sune zasu iya kasancewa password na wayar, dan in da ake yawan taɓawa dan buɗe password ɗin, dole zata yi daban da sauran jikin screen ɗin. Ganin babu haske sosai da zata ishe shi ya kalli abin da yake son kallah ne yasa ya nufi gida dan ya buɗe wayar ya yi bincike a cikinta. A bakin gate ta waje ya isko Mark, da mamaki ya tambaye shi me yake yi a waje kuma? Bawan Allah ɗan amana sai ya ce kawai ya fito ne dan hankalinsa ya kasa kwanciya ogansa yana waje, shi ne ya fito dan ya jira shi a nan ya kuma duba lafiyarsa, har cikin ransa ya ji daɗi sosai, umarni ya yi mishi a kan to suje ciki, hannu yasa yana ƙoƙarin ɗaukar Brady da ya wani kanainaye wuyar Lion ɗin kamar wani ya ce zai kwace mishi shi, da yake Mark mutuminsa ne, sai ya saki Lion ɗin ya koma wajen Mark ɗin yana yi mishi kuka a hankali alamar yana bashi labarin yaga hoton Rimsha a wani waje, da yake Mark ɗin ma ya yi mishi farin sani sai ya ce da Lion me Brady ya gani, shiru Lion ɗin bai tanka mishi ba, hakan yasa ya gane abin bai shafi kowa ba kenan, case ɗin na ogan nasa ne shi kaɗai. Palo suka nufa, tun da ya sako kai cikin palon daddaɗar kamshin kayan tea ɗin da Rimsha ta dafa mishi a Abuja ya daki hancinsu dukkansu biyu, harta Mark ya ji mugu mugun daɗin kamshin, shaka suka yi suka lumshe idanu, bai yi magana ba har sai da suka shiga tsakiyar palon. Suna kaiwa tsakiyar palon ya juyo tare da sauƙe dara daran idanunsa a kan Mark ɗin, ya kuma dakata daga tafiyar da yake yi. Ƙasa da kai Mark ɗin ya yi tare da fara ƴan kame kame, tun ba'ayi mishi magana ba ya yi saurin fara magana cikin girmamawa. "Sorry sir am not the one and I don't know how it happened, it might be prof sister". Shiru ya yi bai yi magana ba, bai kuma ɗauke idanunsa ba, bai kuma juya ya cigaba da tafiyar da yake yi ba, da alama tunani yake yi a kan hakan. Almost 5 mins suna a haka, gently ya mayar da kallonsa izuwa hanyar kitchen na ƴan sakanni babu ko kyaftawa, daga bisani kuma ya juya ya cigaba da tafiya dan zuwa in da yake da niyar zuwa wato bedroom nasa. Sauke Brady Mark ya yi tare da nufar kitchen ɗin dan ya ga waye ne ya yi wannan aiki da ya canzawa gidan daga kamshin abincinsu zuwa na kayan tea, ba kowa bace ta yi aikin nan fa ce Rimsha, ganin Mark ɗin baya kitchen ɗin ne yasa ta zo ta tafasa tea ɗin ta abinta, shi ne kamshi ya bule daga kitchen ɗin har palon. Lion kuwa yana shiga bedroom nasa ya iskota ta ajiye mishi abinci tana jiransa, ta wutsiyar idanu ya kalleta kafin ya wuce zuwa dressing room nasa, Jim kaɗan ya fito sanye da pajama launin white color, dama already kafin ya fita neman Network ya yi wanka ne ya zura jallabiya bai tsaya shiryawa ba, dan yana matuƙar son ya yi magana da Tyrone. Zama ya zo ya yi a in da ya saba zama, calmly ya ce ta kawo mishi laptop nasa, da sauri ta ɗauko ta miƙa mishi, abincin ya ce ta zuba mishi kafin ya shiga ƙoƙarin buɗe wayar mutumin, tana tsaka da zuba mishi abincin ne zazzakar sexy voice nasa ya daki dodan kunnenta a in da yake ce mata "Daga yau ban yarda ki sake fita ko ina ba, school Mark zai kai ki ya kuma ɗauko ki, shi ma school ɗin idan kin je kada ki kuskura ki yarda da kowa, ko wani ya kira ki kije ko makamancin hakan, ko da su Areef ban yarda ki sake bi ki fita ba". Okey ta amsa mishi da shi, can kuma wani tunani ya faɗo mishi, to me zai hana ya haɗa ta da soja ɗaya kawai ya rinƙa tsaronta a school ɗin, tun da Jehan ta rigada ta jefa mata rayuwarta cikin haɗari, yanzu sai Allah kaɗai yasan adadin mutanen da wannan azzalumin ya turawa hotunanta a kan su kamota ta kawo video da Jehan ta zuba mishi karya akan ta turawa Rimshar, idan baku manta ba, lokacin da Jehan ta yi wa Alhajin can na gidan hajiyar daɗi video, ta ce mishi ta turawa ƴar uwarta Rimsha, to kuma dama kunsan manya mutane irin waƴan nan ba zasu bar abu makamancin haka ya fita ba, dan idan ya fita sun san shikenan rayuwarsu tana kwale kwale, shi ne to yasa aka nemo mishi hoton Rimsha yanzu kuma yasa a kamota a karɓa mishi videonsa, shi kuma zai ji da jehan. Gaskiya Jehan ta tara makiya ta ko'ina, yanzu ga shi ta tsundumo Rimsha da bata san komai bama a ciki, shiyasa wani lokaci ake son kafin ka yi abu ka yi tunani, tunani ma mai zurfi a kan me zai je ya zo, Jehan ta yi babban kuskure a nan tun da ta san babban mutun ne, ba zai taɓa rabuwa da ita tana riƙe da videonsa tsiraicinsa ba, to ya kamata mu rinƙa tunani wani lokaci kafin mu yanke hukunci. Abincin ta zuba mishi ya ci mai ɗan yawa kafin ya cigaba da abin da yake yi, ta miƙe zata kwashe kayan abincin ya ce mata idan ta kai ta dawo, okey ta amsa cike da mamaki ta nufi wajen. Tana shiga kitchen ɗin suka yi ido huɗu da Mark, ga shi yau bai sanya glass ba, Hazel eyes nasa dara daran nan yau dai a waje suna shan iska, mamakin idanun nasa ta yi, bata taɓa ganin irinsu ba, ajiye kayan abincin ta yi bata kula shi ba kamar dai kullum, zata fita ya ambaci sunanta, da mamaki ta juyo, wai dama Mark mai kama da robot ɗin nan dumkum ba magana nan ya san sunanta ne? Ta tambayi kanta da kanta. Tambayarta ya yi a kan waye ya ce ta yi girki a kitchen ɗin nan? Turo baki ta yi kafin ta ce mishi Areef ne ya ce ta yi, daga haka ya yi shiru bai sake yin magana ba, sa kai ta yi ta wuce abinta, ɗakin Lion ɗin ta koma dan amsa kiran da yake yi mata. A gefensa ta je ta zauna abinta, ya sha ruwan mamaki yadda ta wani zauna a gefensa ko a jikinta, can kuma ko me ta tuna ne ta miƙe da sauri ta fito zuwa bedroom nata, cup ɗin tea ɗinta ta ɗauka ta dawo bedroom ɗin nasa, in da ta tashi ta koma ta zauna. A hankali ta fara shan tea ɗin tana jiran ta ji kiran me ya yi mata, shi kuma ya buɗe wayar mutumin sai bincike yake yi a ciki, a hankali hankali kamshin tea ɗin ta yake dakan masa hanci, har cikin zuciyarsa yake son kamshin, akwai daɗi sosai. Almost 5 mins suna a haka, da yake tea ɗin akwai zafi a hankali take sha, Juyowa ya yi suna fuskantar juna tare da juyo da laptop nasa mai ɗauke da wani hoto, "Kin san wannan fuskar?" Ya tambayeta, shiru ta yi tana kallon mutumin, shi kuma ya tsareta da idanu yana kallon sleeping eyes nata, sai dai kuma nazari yake yi a kan face ɗin nata, "A'a ban san shi ba". Dama ya san da wuya ta san shi, dan ita ko Media bata damu da hawa ba, daga karatun boko sai na Islamiyya, shi ne kawai abin da take yi kullum, ko kallon film bata damu da yi sosai ba, idan kaga tana kallo to labarai ake yi a kan jaruminta GAR wato shi kenan. Ɗago dara daran sleeping eyes nata ta yi dan ta saci kallonsa, kai tsaye sai cikin idanunsa suka sauka, dan kuwa ita yake kallo, ya rasa me yasa yake son kallon face nata, ɗan saukar da idanunta kaɗan ta yi izuwa saman lips nasa, shi kam yana mamakin yawan kallon lips nasa da take yi idan suna kallon juna, hannu ya kai gently ya karɓi cup ɗin tea ɗin hannunta tare da kaiwa ɗan bakinsa, mamaki ne ya kamata, dama zai sha ne? Ta tambayi kanta, bata taɓa tunanin hakan ba, kai gaskiya ba zata manta wannan rana ba a cikin rayuwarta. Ganin ta saki baki tana kallonsa ne yasa ya kyasta mata yatsunsa a saman fuska, ƴar firgita ta yi tare da turo mishi ɗan bakin nan nata, sai ya yi mata kamar da Aseef sarkin shagwaɓa take tare, ita ma bari ta zuba mishi nata shagwaɓar, ta manta da GAR take tare ba Aseef ɗin ba. Shi kuma tun ranar da ya kare mata kallon a Abuja in da ƴan ta'addan nan suka biyosu, tun lokacin take burge shi sosai, komai ta yi kyau yake yi mata, yarinyar akwai shiga rai, zanensa da ya gani ta yi kuma ba ƙaramin kara burgesa ta yi ba, Allah sarki komai taurin zuciya tana son mai kyautata mata, kyautatawa ke sanya duk taurin zuciya ta yi laushi, ai dole ma ta burgeka, dan ma baka san cewa har a Daular Mutuwa ta rinƙa zana fuskarka ba, ai da sai ta burgeka fiye da hakan ma, bugu da kari ga TRIPLETS naka abin kaunarka suna bala'in kaunarta, ai dole ta burgeka. Kurɓa ɗaya ya yi wa tea ɗin ya miƙo mata kayanta, dan ta sanya madara a ciki, shi kuma baya so, bai son madara a cewarsa tana da karni sosai, dama kamshin su kaninfari ya ɗebesa ya sha. "Yaya Saif in haɗa maka wani ne?". Shiru ya yi bai tanka ta ba, zubawa laɓɓanta idanu ya yi, yadda ta motsasu gabaɗaya dimples nata sai da suka lotsa, ba ƙaramin ɗaukar hankalinsa suka yi ba, ɗan sunkuyar da kanta kasa ta yi tana wasa da ƴan ƴatsun hannunta, zubawa kyakkyawar dark black curly hairnta idanu ya yi yana kare musu kallo, sai sheƙi yake yi yana ɗaukar hankalin mai kallo, ga wasu gashi baki siɗif kwance a saman goshinta ya yi mata kamar hula ta kifa, ga saje ɗan siriri gwanin burgewa a gefe da gefen kunnenta, kawar da kallonsa ya yi daga kan nata zuwa kan laptop nasa. "Jeki dressing room ki kawo mini trolley da muka yi tafiya da shi". Okey ta amsa tare da miƙewa, binta da kallo ta wutsiyar idanunsa ya yi, komai nata gwanin burgewa, sai dai shi fa yaki yardanwa zuciyarsa tana burgesa, kokarin tursasa zuciyar tasa ma yake yi da ta dai'na cewa tana burgesa ɗin. TAB LALLAI KANA DA BABBAR AIKI IN DAI KUWA HAKA NE!! AI ITA ZUCIYA BA'A TURSASA MATA, DOLE ABI YADDA TAKE SO KO TA HANA MUTUN YIN BARCI!. Kawo mishi Trolley ta yi, buɗewa ya yi tare da fito da hotunan da ya kwaso daga Abuja, ta sha ruwan mamakin ganin hotunan, tunani ma take yi a kan a ina ya samosu? Dan ita bata san da zaman hotunan a gidansu ba. Hoton Naurat ya ɗauko tare da ɗago idanu yana kallon Rimshar, suna kama kuwa, ya sha ruwan mamakin ganin hakan, jini ba wasa ba, a wannan lokaci Aseef ya shigo ya samesu, kusa da su ya zo ya zauna yana bin hotunan da kallo, su dayawan da a kallah zasu kai 45, ba shi da lokacin ɓatawa wajen ganinsu dan haka sai ya duba na Naurat da Azharuddeen Bature da kuma na Rimshar, ya kwashi sauran ya mayar cikin akwatin. "Yaya Saif in tafi?" Ta faɗa tana ɗago ido dan ta saci kallonsa, yana ƙoƙarin snapping ɗin hoton Naurat da ya ɗauko yanzu a wayarsa ya jinjina mata kai alamar tana iya tafiya ba tare da ya yi magana ba kuma bai ɗago ya kalleta ba. Aseef ne ya riƙo hannunta yana faɗin "Ki tafi zuwa ina dan kinga na zo ko?" Ya kai karshen maganar tare da ɗan jawota jikinsa yana cigaba da cewa "Yanzu kin dai'na kulani sosai ko? Shikenan ai tun da ga Jehan ta zo zan koma abota da ita". Ya yi maganar a shagwaɓe. Hannu ta kai saman gashin kansa tana faɗin "Yaya Aseef da gaske ban dai'na kula ka ba, kai ne dai yanzu baka kulani". Ɗan rankwafo mata da kai sosai ya yi dan ta cigaba da watsa mishi gashin yana faɗin "No ba wani nan dan kin ji nace ga Jehan ko? Kishi kike yi ko? To na gano ki". "Yaya Aseef wai meyasa kake son yanke gashin nan naka ne? Ka rinƙa barin shi kamar nasu yaya Areef da yaya Saif mana, wlh ba ƙaramin kyau zai yi maka ba". "No ni damuna yake yi ai, idan ya yi yawa yana takura mini". Cigaba da watsa gashin nasa ta yi, a hankali ta ɗago idanu dan ta saci kallon masoyin nata, karaf suka haɗa idanu, wani irin mugun kallo ya wurga mata wadda ya sanyata sakin gashin ba shirin, dama tana magana ne tana satar kallon shi, dan tana bala'in jin daɗin kallon face nasa, gently ya ce ta fita mishi a ɗaki tana toshe mishi kunne da magana, tana damunsa. Miƙewa ta yi da nufin ta fita, hannunta Aseef ya riƙo yana faɗin "Jani na miƙe mu fita tare zan je wajen Areef". Ɗan satar kallon Lion ɗin ta sake yi, kansa yana duke yana aikin dake gabansa, a shagwaɓe ta ce "Yaya Aseef ba zan iya janka ba, dan kayi nauyi, wash Allah na". Dariya ya kwashe da shi yana faɗin "Raguwa kawai, bata da karfin komai". Sake turo baki ta yi zata yi magana Lion ya daka mata wata uwar tsawa wadda ya sanyata ficewa da sauri "Get out i said!!". A ɗari ta fice, shi kuma Aseef kukan shagwaɓa ya saka mishi yana faɗin "Wai Lion me haka ne? Na ce ta ɗaga ni ka zo ka koreta". Banza da shi ya yi bai tanka ba, ya cigaba da abin da yake yi kayansa. Tana fita bedroom nata ta wuce, jikinta har wani karma yake yi, ta tsorata da jin yadda ya daka mata tsawa har haka, bai taɓa yi mata tsawa haka ba sai yau, bata taɓa jin muryarsa da sauti ta fita ba sai yau. Wanka ta yi tare da yin shirin barci ta kwanta tana tunanin zata je school gobe, murna cike fal ranta. Shi kuma Aseef da ya gama zuba shagwaɓarsa son ransa Lion ɗin bai kula shi ba, sai ya miƙe ya nufi ɗakin Areef, bai san cewa Lion kam ransa a ɓace ma yake ba, ko me ya ɓata mishi rai cikin ɗan ƙanƙanin lokaci haka? Ko dai aikin da yake yi ne ya gano wani abin da bata yi mishi daɗi ba? Shiyasa yaki kula shagwaɓatin nasu, dan yasan idan ya buɗe baki zai iya marinsa ma. TO FA BABBAR MAGANA MARI KUMA? SHAGWAƁATIN NAMU? KAI LION BAKA SON ZAMAN LAFIYA. ASEEF Ga mamakinsa sai ya kalli bedroom na Areef ba kowa, toilet ya nufa dan ya leƙo ko dan uwan nasa yana ciki, nan ma babu kowa (Kai da yanzu yana ciki toilet ɗin haka zai leƙa shi kenan?🤔) Waje ya nufo dan ya tambayi Mark, nan wani soja ya ce mishi gaskiya bai ga Mark ɗin ba, waya ya ciro ya kira number ɗan uwan nasa, tare da duba time almost karfe 11 yanzu, to ina Areef zai je a daren nan haka? Ga kuma ba wani ƙoshin lafiya ke gare shi ba?. Bugu ɗaya ya ɗaga, a gurguje ya ce mishi, ya je wani waje ne shi da Mark amma ba zai jima ba yana nan dawowa, okey ya amsa tare da yi mishi addu'ar a dawo lafiya sannan ya wuce nasa bedroom ɗin, wanka ya yi kafin ya yi shirin yin barci, sannan ya jawo wayarsa tare da lalauɓo number heartbeat nasa dan su kwantarwa da juna hankalinki su sha soyayyarsu. A ɓangaren su Jehan kuwa, ba yadda Ameera bata yi da ita ba akan ta zo su je karɓar abinci lokacin da ake rabon abincin, amma ina ta kafe a kan ita ba zata je ba, kuma Allah ya kiyaye ta ci wannan abincin, abin kyama, haka Ameeran ta hakura ta kyaleta tare da nufar wajen karɓar abincin, ita kuma ta wuni da yunwa, da daddare ma haka ta zauna ba abinci, ta ki yarda ta ci abincin nasu, ga yunwa kuma tana ji kamar ta mutu, amma saboda kafiya da taurin zuciyar bala'i ta hana kanta ci. Su kuwa suka ci abincinsu tas kafin su haye gado ba sallah bare salati suka kwanta, ita kuwa sai da ta je ta yi wanka a toilet na prison ɗin, ba laifi akwai tsabta sosai toilet ɗin, matan suna wankewa, bayan ta yi wanka ta ɗauro alwala, kayan da Rimsha ta kawo mata ta sanya ɗaya daga ciki tare da tambayar Ameera ina ne gabas, nuna mata ta yi ta zumbula hijabinta ta tada sallah, da ta yi mangariba ta idar bata tashi a wajen ba har sai da ta yi issha, ta jima zaune tana askar tare da addua'o'i kala kala dan neman taimakon Ubangiji, sai misalin karfe 9 ta haye saman gadonta bayan ta naɗe daddumar ta mayar cikin jakar, kafin ma ta shigo da jakar sai da gandurobobin suka cajeta fes sannan suka bata. kwanciya ta yi cikinta na mata murɗan yunwa, har wani jiri jiri take gani. Can misalin ƙarfe 11:20 ta sauko daga saman gadonta dan ta je ta ɗauro alwala ta zo ta yi sallar nafila, dan yunwa ya hanata barci Baiwar Allah. Toilet ta nufa, sarki ta yi tare da ɗauro alwala ta fito, dai'dai zata shiga hanyar da zai kaita ɗakinsu babu kowa a wajen, ko tsoro bata ji ba, ga shi dare ne kowa ya kule cikin ɗakinsa, kamar daga sama ta ga mutun a gabanta, da yake akwai hasken wata sosai, sai ta gane waye ne, kallon gefen ido ta yi mishi kafin ta kara ɗaure fuska sosai tana faɗin "Malam lafiya zaka wani zo ka tare mini gabana?". Yatsa ya ɗaura mata a saman lips nata yana faɗin "Not malam it's babyn baby". Kallon uku goma ta watsa mishi kafin ta ce "Bani hanya na wuce!". Matsowa kusa da ita sosai ya yi "Babu in da zaki wuce ki je, wai ke baki murmushi ne sai faɗa kullum ki ka iya?". Banza ta yi da shi bata sake tankawa ba. Raɓawa gefensa ta yi zata wuce, cikin sauri ya sake shan gabanta, har cikin ranta tana bala'in tsoronsa, dan ganin fuskarsa ma razana ta yake yi, idan baku manta ba, TRIPLETS akwai kwarjini sosai, amma saboda dakiya irin tata ne take dannewa ta nuna kamar ma bata ji komai ba, daga ta ciki kuma, har wani dukan uku uku kirjinta yake yi na bala'in tsoronsa. "Wai kai me na tare maka ne da zaka zo ka takura mini?". Matsowa kusa sosai ya yi da ita, har yana iya jiyo sautin numfashinta, "Tambayar me kika yi mini kike yi? To ki saurara, me yasa kika shiga cikin tunanina kika watsa mini lissafin ƙwaƙwalwata? Ya zama komai nake yi sai na kallin wannan kyakkyawa kuma fusataccen fuskar taki mai kama da unclena? Ga idanun nan naki sun saka ni a gaba da tunani, na kasa barci sai su nake tunawa, shi ne yasa nazo in ganki, ni anya ma ba zan ɗauke ki kawai mu tafi ba? Kai na fara jin hakan a raina, amma dai yanzu faɗa mini ke kina tunanin face na?". Wani muguwar harara ta watsa mishi kafin ta ce "Waye kai da zan yi tunaninka? Kuma sai na rasa waye ma zan yi tunani sai kai? Lallai baka da aiki, ni ka bani hanya na wuce hai!!". With full confidence take yin maganar. "Komai kika yi ni burgeni kike yi, ji yadda kike tsaro magana kamar wata brigadier general na sojoji, ji ɗan bakinta a wajen ban da tsiwa babu abin da ta iya, idan kika cigaba da yi mini haka for sure sai na shanye wannan ɗan bakin, ni ki gaya mini kalamai masu daɗi bari na wuce zuwa gida hai!". Ya kai karshen maganar yana ɗaure fuska, tunani ta fara yi to ko dai ta yi mishi ihu ne? Amma kuma ai tun da ya shigo har in da take hakan ya nuna cewa gandurobobin sun san da zuwansa, so ko ta yi ihu ba amfani, wannan bala'in dame ta yi kama? Zai wani takura mata, dan iskanci wai sunansa babyn baby. Tana can tana tunani bata ankara ba sai jinta ta yi a jikinsa ya jawota yana faɗin "Zaki gaya mini kalamai masu sanya mutun love and romance dream ne ko dai ya ya?". Duk da tsoronsa da take ji bai hanata wage baki zata yi mishi ihu dan ya sake ta ba, ta san yadda ya riƙeta ɗin nan ba zata iya kwace kanta ba, kada ku manta su rungumar mace a wajensu ba laifi bane. Cikin sauri ya toshe mata baki yana faɗin "Masifaffiya kawai, ni ki natsu ko dai wlh na shanye bakin nan naki, maza yanzu ki ce I love you my baby tare da wasu kalamai dan na samu na tafi Aseef sai kirana yake yi, ya damu sosai dan ina waje, bai san ina wajen wadda ta takura tunanina bane". Ya kai karshen maganar tare da sakinta ya kuma zame hannunsa daga bakin nata, dan ya fara shiga wani yanayi, da gudu ta raɓa gefensa ta wuce tana mai jin haushinsa, a kan me zai wani rungumeta? Har da ce mishi mugu azzalumi ta yi, shi kuwa juyowa ya yi tare da goya hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa yana binta da kallo har ta shiga ɗakinsu, murmushi kaɗan ya yi kafin ya ce "Sarkin faɗa, zaki dai'na ne, na rinƙa takura miki kenan, waye ya ce kiyi kama da uncle na? Ai tun da kika yi kama da shi kin shiga uku da ni, ba dai kin nuna baki so abin da nake yi miki ba? To mu zuba mu gani". Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya nufi office ɗin shugaban gandurobobin, sallama ya yi mishi kafin ya ce da Mark da yake zaune su tafi, gaba ya yi Mark ɗin ya rufa mishi baya suka nufi motarsu. Gida kai tsaye suka wuce, a lokacin kuma Aseef bawan Allah ya gama rarrashin AKila, dan sai kuka take yi mishi, ta sanar da shi cewa su Abbi zasu dawo gidansu da zama gobe dan shirye shiryen bikin tun da goben saura kwana shidda kenan, ya shiga tashin hankali na wuce misali, amma haka ya daure ya danne ya yi ta rarrashinta tare da bata hakuri ya kuma kara mata kwarin gwiwa a kan su kaiwa Allah kukansu, su kuma bashi zaɓi, In Sha Allah komai zai zo musu da sauki, da kyar dai ya samu ta ɗan kwantar da hankalinta har suka ɗan yi hira, bayan sun yi sallama misalin karfe 1 kenan, barci gabaɗaya ya kaurace daga idanun bawan Allah nan, ya shiga tsananin damuwa ya rasa mafita, gaskiya shi ba zai iya rabuwa da ita ba, koma yaya ne, dole ya san abin yi a kan hakan. Ko da Areef ya dawo, bai bari ya gane halin da yake ciki ba, da ya ji motsin shi ma, barcin karya ya yi, hakan yasa Areef ɗin ya shigo ya yi mishi addu'a kawai ya juya zuwa nashi bedroom ɗin, sai da ya yi wanka ya yi shiri cikin kayan barci kafin ya kwanta zuciyarsa cike da tunanin Jehan ƴar diramarsa, da haka barci ya kwashe shi ba tare da ya leƙa Lion ba. A ɓangaren Lion kuwa.......... ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ *Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta* E51-52💋 A ɓangaren Lion kuwa, ba shi ya kwanta barci ba har sai da ya tabbatar ya kammala da case ɗin nan, sai da ya san ya gano wanene yasa a nemo mishi Rimsha, sannan ne ya tattare komai ya kashe laptop ɗin tare da miƙewa ta nufi toilet, wanka ya yi tare da fitowa ya shirya cikin kayan barcinsa masu bala'in kyau da tsada, ya feshe jikinsa da perfume nasa mai kwantar da hankalin mai shaƙa, zai wuce zuwa saman bed nasa sai ya kalli trolley da ya ce Rimsha ta ɗauko mishi ɗazun, dan haka sai ya ɗauki trolley da nufin ya mayar dressing room, bayan ya shiga dressing room ɗin sai ya lura zip ɗin trolleyn bata rufu da kyau ba, zugeta gabaɗaya ya sake yi ya buɗe, zanensa da ta yi wanda ya ɗauko daga Abuja ya buɗe yana kallo, ba karya fa ya zanu a zanen kamar ka kira shi ya amsa, shafa fusataccen fuskarsa ya yi kafin ya dawo da kallonsa kan face nata dake jikin zanen, ba karya ita ma ta zanu na wuce misali, zubawa sleeping eyes nata idanu ya yi na ƴan sakanni kafin ya mayar da shi ciki ya ja zip ɗin ya juya zuwa cikin bedroom ɗin. Saman bed nasa ya haye tare da jawo bargo zuwa saitin cikinsa, ya kara gudun Ac kafin ya kashe wutar ɗakin, a hankali ya lumshe dara daran blue eyes nasa, ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi, asuba ta gari. After some days, (bayan wasu ƴan kwanaki) A cikin ƴan kwanakin nan da suka wuce abubuwa da dama sun faru, an miƙa case ɗin Jehan court, suna ta ƙoƙarin su ga sun yanke mata hukunci a kan lokaci, shi kuma Areef yana bincike sosai dan ya gane gaskiya, ya je har gidan mutumin in da abin ya faru, ya yi bincikensa, yana ƙoƙarin haɗa hujjoji da kyau da kyau. Tsakanin Akila da Aseef kuwa, abubuwa sai kara taɓarɓare musu yake yi, komai ya lalace musu, yau saura kwana uku aurenta da Irfan, a ɓangaren Lion da Rimsha kuwa, yanzu suna zaman lafiya, ta dai'na yi mishi rashin ji, tana bin duk abin da yake so, tana ƙoƙarin ganin bata ɓata mishi rai ba, so yana gudanar da aikinsa yadda ya dace, wani lokaci ya kirata kusan tare zasu yi aiki, baya tambayarta, sai dai ya zaunar da ita kusa da shi yana aiki tana kallon shi, daga nan yake fahimtar abubuwan da yake son samu amsoshi a kansu, wasa wasa shaƙuwa tana shiga tsakaninsu saboda yawan zama tare da suke yi, yanzu har ta kai kusan koda yaushe suna tare saboda aikin nan nasa, sai dai fa duk da haka yaki yardanwa zuciyarsa tana burgesa, kullum ƙoƙarin ƙaryata zuciyar tasa yake yi, dan a cewarsa bai ga wata halitta da zata burge shi ba bayan TRIPLETS nasa, su kaɗai suke burge shi, a ɓangaren school nata kuwa, kullum Mark ne yake kaita ya kuma kula da ita sai sun tashi ya dawo da ita, da yake yanzu suna Exam ne, karfe 12 suke dawowa, kullum sai Anaya ta yi wa Mark magana, tun baya amsawa har ya dawo amsa mata, idan ta ce good morning sai ya ce how are you, ba ƙaramin daɗi take ji ba da ya fara amsa mata ɗin. GIDAN LION💋 Sanye take da uniform nata ta sauko zuwa palon kasa, kitchen ta nufa, Mark ta samu a cikin kitchen ɗin yana zubawa Lion abinci, wajen ajiye kwanikansu ta nufa, kula ta ɗauki mai kyan gaske, kusa da shi ta zo ta tsaya, cikin natsuwa ta ce ya zuba mata abinci a ciki, ba musu ya karɓa ya zuba mata, dan shi aikinsa ya girka, duk mai so ya zuba mishi, ɗauka ta yi tare da ɗauko ruwa mai sanyi da drinks guda biyu a cikin fridge, ta haɗo da fruits da ba'a yanka ba, sai kuma spoon guda ɗaya, duk ta zuba su cikin kwandon ɗaukar abinci ta ɗauka ta fito zuwa palo. Babu kowa a palon dan haka sai ta nufi bedroom ɗin Aseef kai tsaye, yana kwance tamkar mara lafiya, yau saura kwana uku auren AKila, su Abbi duk su dawo gidan Abba, shirye shirye ake yi babu kama hannun yaro, ya shiga tashin hankali na wuce misali, ya kira daddyn Rimsha, shi ma ya yi magana da Abba amma a matsayin yaya ga Aseef ba Hosain ba, Abba ya bashi hakuri a kan ya rigada ya bawa Irfan aurenta, hakan yasa kullum Aseef ɗin yana cikin ciwon kai, ita kuma Akila zazzaɓi, shi kuma Lion baya zama kwana biyun nan, Areef yana fama da case ɗin Jehan, dukkansu basu da kwancinyar hankalin da zasu iya fahimtar ɗan uwan nasu yana cikin wani hali, suna jin ba daɗi a jikunsu sakamakon damuwar da Aseef ɗin yake ciki, amma sun bar abin a matsayin busyn da suke fama da shi kwana biyu ne, basu kawo a ransu cewa wani abin ne yake faruwa da Aseef ɗin ba. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin ɗakin, yana kwance da idanu kawai ya bita, har ƴar rama ya yi, kusa da shi ta zauna, cikin sanyin murya ta ɗaga mishi gaisuwa, ƙaƙalo murmushi dole ya yi kafin ya amsa, kasa ta yi da kanta tana tunanin yadda zata yi ta aike shi. "Rimsha lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana miƙewa zaune, "Yaya Aseef dama ina son ne dan Allah ka kaiwa Jehan wannan abincin a prison". Shafa kanta ya yi yana faɗin "Tom shikenan, kina murna gobe daddy zai zo ko?" Kai ta gyaɗa mishi alamar e, karɓar abincin ya yi tare da miƙewa tsaye, cikin ɗari-ɗari ta ce "Yaya Aseef baka da lafiya ne?". Gyaɗa mata kai ya yi yana faɗin "Kaina ne yake yi mini ciwo, amma na ji sauki, kin yi breakfast ne?" Jinjina mishi kai ta yi alamar e ta yi. "Okey tom ko zamu je na sauke ki a school ɗin kafin na wuce prison ɗin?". Girgiza mishi kai yi kafin ta ce "A'a yaya Aseef ka kaiwa Jehan ɗin dai, yaya Areef ya ce mini bata cin abincin da ake girkawa a prison ɗin, daren jiya ma da ya je bata da lafiya, kuma ta ki gaya mishi me yake damunta, sai da wata ƴar ɗakinsu ta gaya mishi ai bata cin abinci ne, yunwa ne ya kwantar da ita, shi ne ya ce kullum na rinƙa dafa mata irin abincinmu na nan zai rinƙa kai mata, yau nayi latti shi ne ban tsaya yi mata girkin ba na karɓa mata wajen Mark, na fito kuma sai naga yaya Areef ɗin baya nan, nasan kuma tana jin yunwa sosai, shi ne ka kai mata kawai Mark zai kai ni school ɗin". Jinjina mata kai ya yi yana mai yaba mata tare da gaya mata ai dama bai kamata Jehan ta ci abincin da ake dafawa a Prison ba, ta wuce hakan ai, amma dai yanzu bari ya kai mata da wuri ita kuma ta je ta samu Mark su wuce zuwa school lokaci na kara tafiya, okey ta amsa mishi da shi kafin ta miƙe ta nufi waje, shi kuma ya ɗauko makullin mota ya fito zuwa nashi motar. Bedroom nata ta koma ta ɗauko school bag sabo da Areef ya saya mata, dan nata kam ta kaiwa Jehan kaya a ciki, palon kasa ta nufo, tana sanya kafarta a saman benen shi kuma yana haurowa rungume da Brady a kirjinsa, da alama daga wani wajen suka fito, yana ganinta ya diro kasa daga jikin Lion ɗin yana wani girgiza na iya shege. Har ta fara ja da baya zata gudu sai ta tuna da huɗubar Akila, akan ta dai'na gudun karen, ta rinƙa nuna mishi bata tsoron shi, idan ya matsa mata sai ta rungumi Lion ɗin suga ta tsiya, tuna hakan yasa sai bata gudu ba ta tsaya, sai da Bradyn ya isota ya daka tsalle zai hau jikinta, cikin sauri ta kauce mishi tare da faɗawa saman faffaɗar kirjin Lion ɗin, dan ta ga karshen tsiyarsa, karen ya rainata da yawa. Haushi ya fara daka mata a kan me zata taɓa mishi jikin Lion nasa, shi kuma Lion cak ya tsaya yana kallon wannan ikon Allah. Kankame shi ta yi sosai tare da cusa kanta a cikin kirjin nasa, tsalle Bradyn ya yi ya haye kanta da nufin ya sakata ta sake mishi Lion ɗinsa, ai jikinsa ne shi kaɗai, shi kaɗai zai rinƙa kwanciya a kirjin Lion ɗin, dan haka ta sake shi ko ya cijeta. Gently ya sanya hannunsa ya rabata da jikinsa yana kallon face nata, ta datse idanu gam tamkar zata fasa su, ga kuma Brady a saman bayanta wajen school bag nata ya ki sauƙa, kiris ya rage ta saki fitsari a wando dan azaban tsoro, calmly ya ce da sweetheart ɗin nasa ya sauka daga jikinta, girgiza ya yi alamar shi gaskiya ba zai sauƙa ba, waye ya ce ta hau mishi kirjinsa in da yake kwanciya, dan haka sai ya bata azaba, yana ƙoƙarin sake yin magana sai ya ji tana ƙoƙarin zubawa kasa alamar ta suma dan bala'in tsoro. Tallabota da kyau ya yi yana mai kara ɗaure fuska sosai ya ce da Brady ya sauka, ganin ya ɗaure fuska sosai ne yasa ba dan ya so ba ya diro kasa yana wani kuka mara sauti irin ya ji haushin nan, an ɓata mishi rai. Hannunsa ɗaya ya kai ya riƙo lallausan kumatunta yana ɗan girgizawa, ina ta sume, kawar da kallonsa ya yi daga kanta zuwa kan sweetheart ɗin nasa, ruwa ya ce mishi ya je ya kawo mishi, ya yi maganar tare da saɓarta a kafaɗarsa suka karisa saman benen, bedroom nasa ya wuce da ita, saman sofa ya shimfiɗeta tare da zama kusa da ita. Yana zama ba jimawa sai ga Bradyn da ruwa roba ɗaya mai sanyi a bakinsa ya riƙo, karɓa ya yi tare da buɗewa, kaɗan ya tarbo a hannunsa ya shafa mata a fuska, doguwar numfashi ta ja tare da saukewa a hankali, gently ta waro idanunta kai tsaye sai cikin nasa idanun dan kuwa ita yake kallo, zubawa juna idanu suka yi, da alama ita tana ɗauka a mafarki take kallonsa, dan da alama bata dawo normal ba, shi kuma Allah ne kaɗai yasan me yake tunani da ya tsareta da rikitattun dara daran idanun nan nasa. Sun ɗauki a kallah minti ɗaya suna kallon juna babu ko kyaftawa, haushin Brady ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya faɗa, miƙewa ya yi tare da nufar toilet, ita kuma lumshe idanunta ta yi tare da sake buɗe su dan ta tabbatarwa da kanta ba mafarki take yi ba, ganin yes da gaske a cikin ɗakinsa take ne yasa ta miƙe jiki ba kwari, already Brady ya bi Lion ɗin cikin toilet. Kyawawan kafafuwanta ta zuro kasa kafin ta miƙe ta nufi waje, a harabar gidan ta isko Mark yana jiranta, gidan baya na motar ta shiga, shi kuma mazaunin driver, kunna motar ya yi suka nufi school. Suna yin parking a parking space na school ɗin Anaya ta taho da sauri, ita ta buɗewa Rimsha motar, fitowa ta yi suka rungumi juna, dukkansu fuskokinsu ɗauke da kayatatcen murmushi da zata tabbatar maka da suna tsantsan kaunar junansu sosai, farinciki a wajen su ba'a misiltawa. Leƙowa Anaya ta yi ta gaban motar ta ce mishi good morning, ba tare da ya kalli in da take ba ya amsa tare da tambayarta ya take, da fara'a ta amsa mishi da lafiya lou Alhadulillah, daga haka bai sake magana ba, kuma har lokacin bai ɗago ya kallesu ba, shi dama irin ogan sa ne, in da suka saka gaba nan kawai suke kalla, ba ruwansu da juye juye. Rungume da juna suka nufi class nasu, yau Exams biyu suke da shi, ɗaya na Mr Emmanuel ne, ɗayar kuma na Mss Deborah, na mss Deborah ne farko, Mr Emmanuel nasa ne na karshe. Dukkansu sun sha jinin jikinsu lokacin da suke rubuta Exam na Mr Emmanuel, ba dan komai ba sai dan sun san faɗuwa za su yi, sun san ba zai basu marking mai kyau ba, fuskokinsu ya rage yelwan farinciki sosai, sun shiga damuwa, amma haka suka daure suka rubuta tsakaninsu da Allah, suka sanya abin da suka sani na amsa, kujerar zamansu daban daban, amma abin mamaki amsa iri ɗaya suka rubuta, hakan ne zai nuna maka kwakwalwarsu ɗaya, akwai basira na wuce misali. Exam nasa shi ne na karshe da suka rubuta, daga nan suka tashi zuwa gida, har wajen mota Anaya ta rakota dan ta sake ganin Mark, yana zaune ya buɗe kofar motar ta gefensa ya zuro kafafunsa waje yana latsa waya, a duk cikin sojojin Lion ba wanda Lion ɗin ya yarda da shi sai Mark, shi ma dai ba wani yarda 100 ya ba shi ba, sai dai kawai ya fi sauran sojojin samu waje a zuciyar Lion ɗin ne, suna shiri sosai saboda hali ya zo ɗaya. Rungume juna suka yi kafin ta saketa ta shiga cikin motar suna yi wa juna bye bye, a hankali ya dawo da kafafunsa cikin motar dan su tafi, yana ɗago idanunsa ta cikin mirror motar karaf idanun nasa suka sauka a kan face nata, ta buga uban tagumi a kujerar baya, sai bye bye Anaya take yi mata bata amsa ba, kawar da kallonsa ya yi yana tunanin me ya sameta, dan kallo ɗaya ya yi mata yasan tana cikin ɓacin rai da damuwa, wani tunanine ya faɗo mishi na ya kalli Anaya mana ko ita ma tana cikin ɓacin rai ɗin, tuna hakan yasa ya ɗan ɗago kansa tare da juyowa ya kalleta, karaf suka haɗa idanu, dan kuwa shi take kallo, kawar da kansa ya yi yana tunanin to me ya samesu, kamar zai tambayesu sai kuma ya tuna hakan bata cikin aikinsa, amma har cikin ransa bai ji daɗin ganin damuwar da suke ciki ba, ko dan kaunar da su Aseef suke yi wa Rimsha dole ne ya tsaya tsayin daka ya bata kulawa dan yana bala'in kaunar TRIPLETS shi ma fiye da tunanin mai tunani, bugu da kari kuma ita ce mace ta farko da ya fara gani tare da ogansa, duk da bai san menene yake tsakaninsu ba, a yadda ya fahimta yake kuma tunani, dole tana da matsayi a wajen ogan nasa, sannan a ƴan kwanakin nan yana yawan ganinsu inuwa ɗaya, wani lokaci zai gansu a garden zaune, Lion na zaune tana zaune kusa da shi kamar wasu wa da kanwa, hakan ya kara tabbatar mishi lallai tana da mahimmanci a wajen Lion ɗin, amma a tunaninsa ne hakan, so dole ya kula da ita kamar yadda yake kula da ogan nasa. Har ya tada motar sai ya ji kai ina gara dai ya tsaya tun suna tare su biyun ya ji menene matsalarsa ne wai, kashe motar ya yi duk da yana tsoron yin hakan tun da Lion bai bashi umarni ba, amma ya daure ya ce mata "Rashmee menene yake damunki? Me ya faru a cikin class ɗin naku? Dan da kuka fito waje dai ban ga wani abu ba!". Da yake baya kiran sunan Rimsha sai dai ya ce Rashmee, kada ku manta da English ya yi magana. Daga ita har Anayar sai da suka zaro idanu waje kamar zasu faɗo kasa, mamaki Anaya take yi dama haka muryarsa take? Dama ya iya magana kenan? Lallai ma Mark. Kallon Anaya ta yi tana tunanin ta gaya mishi ne ko kada ta gaya mishi, cikin sauri Anayar ta gaya mishi cewa Mr Emmanuel ne yake kin basu Marking nasu dai'dai da abin da suka rubuta, sai ya basu zero kullum, kuma amsa dai'dai suke rubutawa dan suna kallon paper ƴan class da yake bawa marking duk amsar iri ɗaya ce. Cikin sanyin murya ya ce ta bashi paper test ɗin nata bari ya gani, a hanzarce ta sauke jakar bayanta tare da buɗewa ta fito da paper ta miƙa mishi, karɓa ya yi yana dubawa, tabbas dukka amsar da ta rubuta daidai ne, amma kuma zero ya bata, kara ɗaure fuskarsa sosai ya yi, dama ga fuskar ba'a magana a ɗaure take tamau, ɗago da kallonsa ya yi zuwa kan ta, cikin sanyin murya ya ce su kai shi office ɗin Mr Emmanuel ɗin bari ya ga ɗan uban waye ne shi ya kuma ji a kan me zai tauye musu marking nasu. Okey suka amsa mishi da shi, fitowa ya yi Rimsha ta biyo bayansa, daga manyan student har yara sai kallon shi suke yi sun ga Bature fari kal kamar ka taɓa jini ya zuba, tuni ƴan matan suka fara santinsa, shi kuwa abin da kuka sani ne, in da yake takawa kawai yake kalla, bai ɗago idanu ba ma bare ya ga wata yarinya or wani uncle, gabansa kawai ya zubawa idanu, karin abin burgewa da shi, yana tafiya ne a bubbuɗe kamar ogan nasa wato Lion, irin tafiyarsu ɗaya, kuma tafiyar tana ɗaukar hankali ba kaɗan ba, yana da kyau da burge mutane, dan tafiya ce da take nuna cikakkun jarumai masu jini a jika ne, babu wasa a lamuransu ko kaɗan. Suna gaba yana biye da su har office ɗin Mr Emmanuel, ba ko excuse ya shiga office ɗin fuskar nan tasa tamkar hadari, babu alamar wasa a tattare da shi. Ba ƙaramin razana Mr Emmanuel ya yi da kallon shi ba, ya tsorata ainun, jikinsa har kerma ya fara yi, a razane ya tambaye shi lafiya, yana magana yana zaro idanu wanda zai nuna maka tsantsar rashin gaskiya a tattare da shi, sannan yana magana murya na kerma da sarkewa, da kyar ma ya iya furta maganar. Ko kallon arziki Mark ɗin bai yi mishi ba, dama can shi ba kallo mutane da arziki yake yi ba, cike da isa ya miƙa mishi paper ba tare da ya yi magana ba, hannu yasa ya karɓa ya buɗe dan ya gani. Ganin wannan paper ta Anaya ɗin ce yasa ya ɗago ya dubi Mark ɗin, ina ai bai ga wajen wargi ba, yasan idan ya yi wani abin da ba dai'dai ba yanzu zai ji shi a in da ba'a dawowa, dan haka cikin sanyin murya ya ce "Am sorry sir it's a mistake, amma yanzu zan gyara". Ko sannu dai bai ce mishi ba, shiru ma magana ce, dan a cewarsa bai ga abin da zai buɗe baki ya ɓata wajen magana da wannan banza kazami da bai wuce ya yi ball da shi ba. (Wannan ma Mr Emmanuel baka haɗu da zakunan William jacop ba, ashe da fitsari zaka yi a wando, to ka yi fatar kada ka haɗu da su kuwa, Mark ma kawai ya razana ka, ina ga kuma manyan shegun? Wato Lion and Areef 🤔) Cikin sauri ya gyara mata marking nata, da mutunci ya miƙa mata paper, karɓa ta yi tare da daka tsalle ta rungumi Rimsha suna dariya kamar wasu zautattu, Allah sarki bayin Allah sun yi murna ba kaɗan ba. Ganin Mark yana tsaye bai motsa bane yasa Rimsha ta ɗago tana kallon shi, to me ya tsayar da shi kuma ba zai zo su tafi ba? Ta tambayi kanta. Shi kuwa Mr Emmanuel ganin hakan yasa ya gane abin da Mark ɗin yake nufi, wato ya shigar da marking na Anayar cikin list da zai sanya a result nata yanzu a gabansu yana ganinsa, hakan yasa cikin sauri ya fito da list na marking ɗin ya dubo sunanta, mugu har ya sanya mata zero a wajen, a gabansu ya canza zuwa 60/60 kamar yadda ta ci. Juyowa Mark ɗin ya yi garesu, sun rungumi juna sai murna suke yi, can kasa kasa ya yi magana "Shikenan ina naki paper Rashmee?". Nan take face nata ya sauya, cikin sanyi murya ta ce "Ni yaki bani na rubuta, tun ranar da na dawo school na roke shi amma yaki bani, dama ni bana nan aka yi test ɗin". Juyowa gare shi ya yi, tun kafin ya yi magana tuni ya fito mata da question paper ya miƙa mata hannunsa har rawa yake yi, karɓa ta yi tana murna, da hannu Mark ya nuna mata saman sofa akan ta zauna ta rubuta da wuri su wuce gida zai je ya yi girki. Tana tsaka da rubuta wa daddyn Anaya ya zo ɗaukarta, Zaira ce ta shigo office ɗin kiranta dan wata student ta gayawa daddyn ta gansu sun shiga office ɗin Mr Emmanuel, cike da murna ta sake rungumar Rimshar tare da bata kiss a kumatu tana murna, tsabar farinciki Juyowa ta yi ta rungumi Mark ɗin ma da yake tsaye kamar Robot tare da furta mishi ta gode sosai, Allah sarki ita ɗin ma bata ɗauki rungumar a matsayin laifi ba, ba ilimin addini sai zallar boko babu surki. Har cikin ransa ya ji wannan rugumarsa da ta yi, babu wata mace da ta taɓa zuwa kusa da shi ma bare har ya kai ga sun yi musabaha ta hannu da hannu ma bare kuma runguma, babu wannan macen, yau Anaya ta rungume shi, har wani shock ya ji a jikinsa, sakinsa ta yi tare da juyawa cike da murna tana yi wa Rimsha bye bye, juyawa shi ma ya yi ya bita da kallo yana mamakin irin tsantsar murnar dake kan face nata, kamar wadda aka yi wa wani hamshaƙin kyauta na gani na faɗa, bai san cewa ta ɗauki boko ne da matukar mahimmanci fiye da tunanin mai tunani ba, wannan paper tun ranar da Mr Emmanuel ya bata ta kasa nunawa daddynta dan tana tsoron ya ga ta ci zero, ba zai yi farinciki ba, haka mum ɗinta, to yanzu kuma an gyara mata marking ɗin, ai dole ta yi murna over. Ita kuma Rimsha tana son zuwa su gaisa da daddyn Anaya, sai dai ba dama, Mark na jiranta ta gama rubuta test da wuri su wuce, bata ji daɗin hakan ba sam, ta so ganin daddyn Anayar, dan Zaira ta ce daddy da uncle Shitu ne suka zo a tare, sam ba haka ta so ba, amma dole tahakura. Shi kuma sai da Anayar ta kurewa ganinsa ya dawo da kallonsa kan abinda Rimsha take rubutawa, ya yi mamakin ganin yadda take tsara amsar kamar wata computer, ya jinjinawa kaifin basira da kwakwalwarta ba kaɗan ba. Sai 12:40 ta kammala, lokacin kuma hadari ya haɗu sosai a garin, miƙawa Mr Emmanuel ta yi, da sauri ya karɓa ya bata marking yadda ya dace tare da shigar da list, sannan ne Mark ya ce suje, tasa ta gaba ya yi suka wuce, binsu da kallo Mr Emmanuel ɗin ya yi yana sauke ajiyar zuciya, sai dai fa a cikin zuciyarsa ya kudurci niyar tun da suka yi mishi haka shi kuma wlh sai ya lalata Rimsha da Anayar baki ɗaya, ko da kuwa zai mutu sai dai ya mutu sai ya san hanyar da zai bi wajen ganin ya cimma burinsa na lalatasu ɗin, to ance mai son abinka ya fika wayo, Allah dai yasa mu dace. Lokacin da suka fito student ɗaiɗaiku ne suka rage a cikin school ɗin, dayawansu iyayensu sun zo sun ɗauke su, saura waƴan da iyayensu ke lattin zuwa. Kai tsaye motarsu suka nufa, gidan baya ta shiga, shi kuma ya wuce mazaunin driver. Suna fita school ɗin aka fara yayyafin ruwan sama, wani irin farinciki ne ya dira mata a ranta lokacin da ta ga ruwa, ji ta yi tamkar ta ce mishi ya tsaya ta shiga cikin ruwan dan Allah, sai dai tana tsoro sosai, dan ma yau sun yi babbar sa'a da har ya yi musu magana kuma ya tsaya musu a kan matsalarsu har komai ya warware, dannewa ta yi har suka isa gida. Yana yin parking ba motar, tun bai gama kashe ta ba, da sauri ta ajiye school bag nata da ɗan hijabinta da bai gama rufe kirji ba a saman kujerar motar, a hanzarce ta buɗe kofar motar ta fito, har tana haɗawa da gudu wajen shigewa cikin ruwan, juyi ta fara yi a ciki tana tsalle. Shi kuma Mark wayarsa ya ciro ya fara latsawa dan baya jin zai iya fita a cikin ruwan nan, zuba ruwan yake yi sosai, gabaɗaya ilahirin sojojin dake gidan suna tsaye a host na gidan, ga ruwan saman very fresh. Sai juyi take kamar wata ƴar tsana, bata ankaraba Juyowa da zata yi sai ji ta yi buge mutun, da yake ta yi ta juyi ya yi mata kamar ajijiya, sai jiri ya ɗebeta zata faɗi kasa, wuyar rigarta ya riƙo yana kallon face nata, dawowarsa kenan, tana can tana juyi bata ma ga shigowar motarsu ba, sauri yake yi ba zai iya jiran ruwa ya ɗauke bane yasa ya fito daga cikin motar ya keto ta cikin ruwan dan ya shiga cikin gida, wasu takardu yake son ɗauka zai sake fita ne, su ya dawo ɗauka ya koma shiyasa yake sauri. Da yake ruwa na zuba mata a fuska ta kasa buɗe idanunta ma bare taga wanene, ga shi kuma bai ɗago da ita ba, ya dai riƙe wuyar rigar tata, sai dai kuma har cikin ranta ta ji cewa yes tabbas shi ne, dan idan ba shi ba babu mai riƙeta a wuyar riga idan zata faɗi, idan Areef ne hannunta yake riƙewa ko kuma ya rungumota, shi kam Aseef ma gabaɗaya yake rungumota a jikinsa, bayan su ukun nan kuma gabaɗaya gidan ko da daga sama bene zata faɗo babu mai ɗaura hannunsa a jikinta, ta rasa meyasa sojijin gidan gabaɗaya suke respect nata over, duk da dama basu kallon mutane, amma ita rashin kallonta da suke yi ma na daban ne, kamar waƴan da aka yi wa warning a kanta, ba ta san cewa ba wanda ya yi musu warning, kawai suna bala'in tsoron ogan nasu ne, suna kuma mugun respecting nasa fiye da tunanin mai tunani, kamar yadda suke yi masa kuma haka suke yi wa su Aseef, duk wanda Lion ɗin ya ɗaga idanu ya kallah har ma ya zauna inuwa ɗaya da shi to haka suke respecting nasa, ko da sunan wasa basu kuskura su kusanci abin da ya kasance Lion ɗin yana amfani da shi, hakan yasa suke nesanta kansu da koda kallonta ne, dan suna ganinta tare da su Aseef sosai, ga shi suna rungumeta suna wasa da dariya, abin da basu taɓa yi da wata mace ba a rayuwarsu, sannan kuma yanzu tana zama tare da Lion ɗin dan aikin da yake yi, hakan yasa gabaɗaya sojojin suka ɗauketa a matsayin ko budurwar ɗaya daga cikin TRIPLETS ɗin ne, ko kuma matar ɗaya daga ciki ne ma, shiyasa suke bata wannan respect ɗin. Zuba mata idanu sosai ya yi yana kallon yadda ruwan nan yake sauka mata a kan face nata, wani irin azababben kyau lips nata suka yi mishi, yadda ruwan yake sauka a kansu yasa suka kara pink over kamar ta sanya lips stick, irin lips na kakanta Naurat sak, ga su da laushi kamar fure, ƴan kanana da su, na kasa ya fi na sama girma kaɗan. Shi kam Mark ajiye wayarsa ya yi tare da zubawa ogan nasa idanu yana faɗin "Da alama oga ya faɗa tarkon mace fa, ji yadda yake kallonta babu ko kyaftawa, amma gaskiya so bata yi mishi adalci ba, wannan ƴar yarinyar haka da bata wuce goyo ba". Sai zancen zuci yake yi shi kaɗai a cikin mota yana kallon ikon god, tunanin rungumarsa da Anaya ta yi ɗazun ne ya faɗo mishi a ransa, shiru ya yi yana jin yadda ya jita a jikinsa, wani irin yanayi ya ji har tsakiyar kansa, face ɗinta ya fara tunanowa a cikin ƙwaƙwalwarsa, ga sanyin ruwan sama na kara ratsa shu, nan take ya faɗa wani yanayi na soyayya. TAB OGA DA YARONSA FA SUNA RUWA, AMMA FA SUNKI YARDAWA KANSU DA HAKAN, DAN YARA SUKE ƊAUKAR SU RIMSHA, E KAM AKWAI AIKI BABBA MA KUWA, GA DAI YARINYA TA SANYA MARK TUNANI, SHI KUMA OGA YA TSARE YARINYA DA IDANU. A hankali ta motsa laɓɓanta tare da ɗan turosu gaba alamar shagwaɓa, nan take dimples nata suka yi wani irin lotsawa sosai, har cikin zuciyarsa ya ji hakan. Ganin ba zai ɗagota bane yasa ta yi kokarin ɗagowa da kanta duk da tasan a yadda ta riƙeta ɗin ba zata iya ɗagowar ba, amma ta kwatanta, hakan ya sanya ya fisgota da karfi ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, hannu ta sanya tana ƙoƙarin sharce ruwan face nata dan ta buɗe idanu ta kalli waye ne, duk da ta san shi ne, dan wannan faffaɗar kirjin shi kaɗai ne mai irinsa a cikin TRIPLETS, daga shi sai Areef mai bi masa, fisgota ɗin da ya yi kuma ya sanya gashin kanta dake jike sharkaf yana zubar da ruwa ya watsu mata har saman kirjin nasa, ɗan dagowan nan da ta yi dan ta sharce ruwan face nata sai gabaɗaya gashin nata suka dawo face nata, sun rufe mata idanu, abin gwanin burgewa. Gently ya kai hannunsa ya kawar mata da gashin zuwa gefen kunnenta tare da sakinta ya nufi cikin gida, Juyowa ta yi tana kallonsa, har ya ɗan yi gaba kuma ko me ya tuna ya juyo, taku biyu ya yi ya dawo in da yake tsaye, ta yi mutuwar tsaye tana kallonsa, gashin kan nata ya zo ya damke tare da tasata a gaba a kan ta wuce zuwa cikin gida, ta fita daga cikin ruwan. Ai kuwa kukan shagwaɓa ta saka mishi dan ita gaskiya duk bala'i bata son a rabata da ruwan saman nan, gara mata ya daketa, amma dai ya barta a cikin ruwan nan sai an ɗauke. Ganin bai kulata bane da gaske ciki zai wuce da ita yasa ta juyo da kyau ta rungume shi sosai tare da kankame shi tana yi mishi kukan shagwaɓa, tun da Areef ya gaya mata Lion ba zai taɓa dukanta ba ta saki jiki da shi sosai, tana zuba mishi shagwaɓa san ranta, yanzu ta san shi baya dukan mata, ya fi karfin sanya hannunsa a jikin mace dan duka, amma kuma yana bada punishment ai idan bai yi duka ba. Kin kulata ya yi tamkar bai san tana yi ba, amma fa a zahirin gaskiya yana bala'in jin daɗin shagwaɓarta over, musamman ma idan ta haɗu da Aseef a ɗakinsa, ai abin ba'a magana, ba ƙaramin burgesa suke yi ba idan suna yi, sai dai ba zaka taɓa gane yana burgesa ɗin ba, saboda dama kun san shi ba'a taɓa gane halin da yake ciki. Ƙoƙarin zubawa kasa ta yi ta zauna dan ya saketa, da hannu ɗaya yasa ya ɗauketa cak ya saɓa a kafaɗa ya nufi cikin palo abinsa, duk abin da suke yi gabaɗaya sojijin nasa suna kallonsu, sai dai basu yi mamaki ba, dan jiya ma sun ga fin haka yadda suka gansu tare a garden yana bincike tana zaune a kusa da shi, daga karshe ta yi barci tare da kwantar da kanta a saman kafaɗarsa, da ya ga haka sai ya gyara mata kwanciya zuwa saman cikyarsa ya cigaba da aikin da yake yi, dan kada wuyarta ta yi ciwo ne ya yi mata hakan, so sun ga komai jiya da yamma, bayan ya kammala aikin da yake yi kuma ya ɗauketa cak zuwa cikin palo, a saman sofa ya kwantar da ita kafin ya wuce cikin bedroom nasa, a cewarsa yanzu lafiyarta tana da matukar muhimmanci a gare shi ya kula da shi dan akwai tafiyar da zasu yi nan da kwana bakwai, shiyasa yake bata kulawa, a hankali shakuwa tana shiga tsakaninsu ba tare da ya sani ba, ita kam dama ai ta jima a ciki. Sama ya haura da ita, kai tsaye bedroom nasa ya nufa, sai kukan shagwaɓa take zuba mishi tamkar babu shi a wajen, sam bai kula ta ba, jikinsu duk sai zubar da ruwa yake yi. A tsakiyar bedroom nasa ya sauketa tare da kara ɗaure fusataccen fuskar nan tasa sosai kamar hadari, cike da bada umarni ya fara magana a nitse cikin sanyin murya "Idan na sake ganinki a cikin ruwan sama sai ranki ya yi mummunar ɓaci, ki je ki kawo mini birth certificate na ƴar uwarki bari na gani". Natsuwa ta yi tsit dan bata ga alamar wasa a tattare da face nasa ba, har gobe kuma tana mutuwar tsoronsa, sai dai tana dannewa ne sakamakon kwarin gwiwa da take samu daga Aseef, Areef da kuma Akila, suna karfafa mata gwiwa sosai tare da kara gaya mata ta daina jin tsoronsa dan ba zai taɓa dukanta ba, baya dukan mata, ta rinƙa yi mishi abubuwa da zai rinƙa sanya shi magana, a haka idan ya saba da ita, to fa duk ranar da bai ganta ba dole zai shiga damuwa, zai ce yau dai ba wanda zata saka shi magana, hakan zai sanya ya ji ba zai iya yin nesa da ita ba, daga haka kuma shakuwa ce zata shiga tsakaninsu mai karfi, da alama kuma shawarsu Areef ta yi aiki, dan kuwa shakuwar tana ta kara yawaita sosai a tsakaninsu. Juyawa ta yi da nufin ta fita tsantsin ruwan jikinsu da ya zuba a tiles ɗin ne ya ɗebeta dama ga kafarta da ruwa, tafiya ta yi luuuu zata faɗi, a zafafe ya tareta ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa ta baya, dan idan ya barta ta yi wannan mummunar faɗuwa da wuya idan ba zata samu karaya ba, ba'a saiti ta tafi zata faɗi ɗin ba, so dole tasa ya tareta dan kada ta karye ta ja mishi dakatar da tafiyar da zai yi. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan juyo kaɗan, da yake gabaɗaya ta jike sharkaf, sai ya zamana kayan jikin nata sun manneta sosai, hakan yasa gabaɗaya ilahirin albarkatun jikinta suka bayyana, ɗan zuba mata idanu ya yi yana kallon shafaffen plat tummynta, tamkar bata taɓa zuba abinci a ciki ba. Zura hannunsa ya yi ta saman kugunta a in da ya juyo da ita da kyau suna fuskantar juna, wani irin ɗauke wuta ta yi na wucin gadin jin saukar hannun nasa a kugun nata. Calmly ya fara magana, a hankali yake motsa lips ɗin nasa ta yadda ba zata taɓa tunanin shi ne ma yake maganar ba, dan bakinsa bai motsa ba, shiyasa kullum maganarsa yake can kasa kasa baya ɗaga murya. "Meyasa baki ji ne? Why kika cika rawan kai over haka? Why ba zaki rinƙa abu a hankali ba?". Turo mishi ɗan bakin nan ta yi tana kallon kasa, hannu ya kai ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, idanunta yake son kallah dan ya yi missed nasu, tun safe da ya kalla bai sake kallo ba. Yana ɗago haɓar tata ta yi maza ta datse idanun nata, ɗan rankwafowa kanta kaɗan ya yi tare da matso da face nasa saitin tata kaɗan, zaro idanunsa waje kaɗan ya yi kafin ya ce "Open your eyes". Ba yadda zata yi haka ta warosu waje, kai tsaye sai cikin nasa, dama ga shi ya zarosu kaɗan, wani irin razana ta yi wadda ya sanya ta kurma ihu sai kuma ta yi shiru diff kamar na ɗauke wutar nepa, har gobe tana tsoron ƙwayar idanunsa sosai, bare ma ya zarosu ai dole ta tsorota, dan idanun nasa har wani kyalli suke yi, bare ma idan ya zarosu waje, ba'a magana dole idan baka saba ganinsu ba ka tsorata. Da yake bai riketa ba sai ta yi kokarin zubewa kasa, a zafafe ya riƙota da kyau tare da tallaɓota yana mamakin wai ita wannan yarinyar me matsalarta ne? Sai shegen tsoro kamar farar kura, karkaɗa mata ruwan dake dark black curly hairnsa dake ɗiga ya yi a face nata, amma ina shiru hata motsa ba, ɗan zuba mata idanu ya yi na ƴan sakanni kafin ya kwantar da ita a kasa a wajen tare da tsugunnawa a kusa da ita bayan ya ɗauko ruwa daga fridge. Ga mamakinsa ya zuba mata ruwa sosai, amma shiru bata farfaɗo ba, hakan ya samo asali ne kuma na riƙeta da Malika ta yi ta hanata farkawa, shi bai sani bai, baya ganinta, amma ita tana ganinsa, Malika aljanace mai kirki sosai, musulma ce shiyasa bata gudun perfume ɗinsa, dama shaiɗanun aljanu yake kora ba na kirki ba, ita tana da kirki sosai. Ya yi ya yi ta farka amma ina shiru, Malika da iya shege ta hanata farkawa da tana son ya hura nata iska ne da bakinsa a cikin bakinta dan dama idan dai bata farka ba bashi da zaɓi dole sai hakan, shiyasa Malikar ta riƙeta, dan tasan muddin ya haɗa bakinsa da nata ya hura mata iska to fa da wuya ya tsallake bai faɗa tarkon sonta ba, dan ya rinƙa tuna wannan abin kenan a ransa, Allah sarki bawan Allah bai sani ba tarko Malika ta kafa mishi dan tana bala'in kaunar Rimshar, ta gaji da kallonta tana wahalar dakon soyayyarsa, yanzu kam ya kamata ace ya fara jinta a ransa, kullum sai ta zauna ta yi ta tunanin yadda zata taimakawa Rimshar a kan soyayyarta, duk ranar da Rimshar ta kasance tare da shi, to da daddare sai ta yi mafarki, tana shan wahalar wannan soyayya ba kaɗan ba, dan dai yarinya ce mai tawakkali yasa ta fawwalawa Allah komai bata nuna damuwarta a fili, ta samu tarbiya na kin karawa wajen mummy da daddy duka, shi kam daddy barin gida ya yi mishi amfani, dan da ya bar gidan bai wani taso da ɗabiun turawan nan kamar Hassan nasa ba, shi ya canza ya fita daban a cikinsu, idan baku manta ba harta Abbi a baya baya wani kula dasu Aafia da tarbiyarsu, zasu yi irin dressing ɗin da suke so suje school baya wani damuwa, bai ma san suna yi ba, duk cikin su dai su Rimsha ne suka sami tarbiya sama da kowa, sai su Imran wanda su kuma Hjy Umaiya ce ta basu tarbiya ba Abba ba, dan shi ma Abban duk kanwar ja ce shi da su Abbin. Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallonta kafin ya rankwafo da kansa dai'dai saitin tata sosai yana jin kamar ba zai iya hura mata isaka ba gaskiya, amma zuciyarsa tana ta ingiza shi a kan dole dole sai ya hura mata ta farka, idan ba haka ba zuciyar tasa ba zata kwanta ba. Ba dan ya so ba ya sunkuyo gabaɗaya tare da kai hannunsa ɗaya saman lallausan kumatunta, a hankali ya matse kumatun nata dan ɗan bakin nata ya buɗe, matso da bakinsa ya yi tare da ɗaurasa saman tata, wani irin azababben shock ya ji tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafin ƙafarsa, da kyar ya iya dannewa ya karisa ɗaura lips ɗin nasa saman tata, wani irin daddaɗar laushi lips nata suke da shi over ba'a magana, wani irin kasala ne ta sauko mishi lokaci guda, da kyar ya hura mata iskar dan jikinsa ya mutu. Ya hura mata na farko shiru bata farka ba, ya kara na biyu, nan ma shiru bata farka ba, sai da ya kara manne bakin nasu da kyau ya ɗan hura mata da ɗan karfi. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, a sukwane ya raba bakin nasu tare da miƙewa tsaye dan baya ma son ta san meyafaru. Wani irin tsalle Malika ta yi tana dariya kamar wata zautatciya, da yake babu mai jinta ko da ta yi magana, sai ta fara surutanta a fili "Wlh Saif ka shiga uku, tun da ka hura mata iskar nan, ba kai ba barci dare yau, ka rinƙa mafarkin lips ɗin nan nata kenan, ko zaka mutu wlh dole a yanzu sonta ya shigeka, ko ka shirya ko baka shirya ba, dole a ƴan kwanakin nan zaka karɓi bakon yanayin da baka da zaɓi ba yadda zaka yi dole ka karɓe shi hannu bibbiyu, Allah ya cika mini burina yau na haɗa soyayyar Rimsha, zaka yi bayani sai ka tashi tsakar dare kana tunaninta ka kasa barci, ba ita kake cewa yarinyar da bata wuce a goya ba ko? Ai kuwa yanzu zaka ga yarinya, zaka fara goyata amma a kirjinka a matsayin masoyiya ba'a bayanka ba, Allah sarki har ka ban tausayi, bawan Allah baka san menene soyayya ba, zaka wahala kafin ga iya gane soyayyar kuwa, kai dai zaka ji duniya kana son ta kasance tare da kai amma ba zaka san so bane, amma dai ka ban tausayi kaɗan, wayyo ni Malika daɗi zai kashe ni yau, dole na je na bawa Haruna labari". Ta kai karshen maganar tare da sake kwashewa da dariya har da durkushewa kasa tana rike ciki saboda dariyar mugunta ta yi mata over. Shi kuwa ganin ta farka ne ya wuce ya nufi toilet dan ya yi wanka ya zo ya fita zuwa in da zai je, dan gobe Monday za'a yankewa Jehan hukunci a court, shiyasa ya buƙaci birth certificate nata dan ya duba date of birth nata, yaga a court zaman da suka yi ranar Alhamis an ce tana da 18 to 19 years, shi kuma a iya binciken da ya yi, da auren daddy da mumnynta ma kwata kwata yanzu 17 to 18 years ne, to ya akayi ita ta kai 19 years? Daga ji kasan shiri ne, domin kuwa koda daga zuwa mummy ta samu cikinta yanzu sai dai a ce mata 17 years take da shi, dan ciki ma sai ya yi wata tara, dan haka dole ya takawa lauyoyi da alkalin birki, shi ne ma abin da ya dawo da shi gidan. Duk abin da ya faru a ɗakin a kan idanun Aseef ya faru, ya shigo duba Lion ɗin ne sai ya kalle shi yana ƙoƙarin hura mata iska, shi ne ya koma da baya, dan idan ya bari ya gan shi, to fa ba zai hura mata iskar nan ba sai dai ta mutu, shi ne yasa ya koma baya ya laɓe yana kallonsu tare da yi wa Allah godiya da Allah ya nuna mishi wannan rana da Lion yake damuwa da Rismha har haka, har zai hura mata iskan bakinsa a cikin nata dan ta tashi, kai ai dole su yi wa Allah godiya. Sai bayan ya ga Lion ɗin ya miƙe zai nufi toilet ne ya gudu ya koma ɗakinsa dan kada ya gan shi, yasan idan ya gan shi to fa ya jawa Rimsha ne, zai fara yin fushi da ita ya koreta a kusa da shi dan kada hakan ya sake faruwa ma bare wani ya gan shi. LION DUNIYA. Hannu ta kai saman idanunta tana ɗan murjesu, da kyar ta warosu waje, a hankali ta miƙe zaune tana tunanin ina kuma ya nufa, lallaɓawa ta yi ta miƙe zuwa bedroom nata, toilet ta nufa ta yi wanka tare da ɗauro alwalar sallar azahar, abaya ta zura dan gabatar da sallah. Sai bayan ta yi sallar ne ta zauna tsantsara kwalliya, wandon jeans ash color ta sanya mai bala'in kyau, ta sama kuma riga maroon ta sanya, ta yi kyau over, ta busar da gashinta da hand dryer, tare da shafa masa mayukanta masu bala'in kamshi, tana cikin ƙoƙarin ɗaure gashin ne ta tuna da shampoos da ta ɗauka mishi a shopping da suka yi a Abuja, da sauri ta saki gashin nata ta nufi trolleyn da ta daho da shi, buɗewa ta yi ta cirosu, cool murmushi ta saki kafin ta miƙe ta nufi gaban mirror dan ta karisa shirinta, saman drawer mirror ta ɗaura shampoos ɗin ta karisa komai, ta yi kyau over, sai tashin kamshi sosai take yi. Bata ɗaure dark black curly hairnta ba, dan yaki ɗauruwa sam, yana da bala'in tsantsi, sai ta sake shi kamar wata Baturiya abinta, bata ɗaura ɗankwalin ba, dan tana sauri ta kai mishi shampoos ɗin. Kwasansu ta yi har ta kai bakin kofa, sai ta tuna cewa ai ya ce ta kai mishi birth certificate ɗin Jehan, hakan yasa ta dawo da sauri ta sake bincika akwaitin dan ta duba, cash bata samu ba, babu a ciki, yana Abuja, ta ji babu daɗi, jikinta har ya mutu duk da bata san me zai yi da birth certificate ɗin ba, haka ta miƙe zuwa bedroom ɗin nasa. Da sallama ɗauke a bakinta ta shigo, baya cikin ɗakin, ganin hakan yasa ta lallaɓa ta nufi toilet nasa, sauri sauri ta ajiye masa shampoos ɗin, dan tasan idan ta bashi hannu da hannu zai ce baya so, dan shi ba'a mishi goninta, komai ka yi mishi baka burge shi, ba'a yi mishi sai abin da ya ce ayi, shima abin da ya ce ayi ɗin baya taɓa yabawa koda shi ɗin ya ce ayi, haka yake a murɗe, shiyasa ta zaɓi ta kai mishi toilet ɗin ba tare da ya sani ba, sai dai kawai ya zo ya gani. Sauri sauri ta ajiye mishi ta fito, yana cikin dressing room yana sanya kaya, saman sofa ta zauna, sai kuma ta kalli bed nasa ya ɗan hargitse alamar tun da ya tashi da safe ma bai sake komawa ya kwanta ba, kuma da alama Areef bai dawo gidan ba bare ya gyara mishi, shi kuma Aseef bawan Allah yana fama da kansa, bashi da kwanciyar hankalin da zai iya wannan aiki, ko da ma yana cikin kwanciyar hankali ba abin da ya iya, Areef ne bawan Allah dama mai yi, shi Aseef sai dai kwanciya da iya zuba shagwaɓa kamar ba gobe. Miƙewa ta yi ta nufi bed ɗin dan ta gyara mishi, ta yi sa'a yau wannan gibgegen bargon nasa tana ninke, ba'a warwareta ba, gadon ta fara gyara mishi har lokacin ana ruwan sama sosai, garin ya yi sanyi sosai, tana jin sanyi amma bata sanya jacket ba, dan bata da shi tana kuma jin tsoron saka nasa da ta taɓa ɗauka a wajen Imran kada Brady ya biyo ta ya haukatata, shi ne ta shafawa kanta salama da zaman lafiya ta hakura bata saka ba, da sanyin haka ta jure. Tsab ta gyara mishi gadon kafin ta zo ta ɗauko tsintsiya da mopper, ruwan da suka zubar a shigowarsu ɗasun da suna ɗigar ruwa, shi ta fara gogewa kafin ta fara share ɗakin, babu wani dattin komai kamar dai kullum. A haka ya fito ya sameta, kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa, ya shirya cikin wandon jeans fari tas tamkar yanzu ya ciro ta a ledarta, ta sama kuma high neck t-shirt ne shi ma fari tas ya sanya, da yake rigar ta kama shi sosai, hakan yasa faffaɗar kirjin nan nasa ta bayyana kamar na zaki, ga breast nasa da suke ɓul ɓul, ya yi kyau sosai, shi ma ya busar da gashin kansa da hand dryer, sai kyalli gashin yake yi, ya ɗaure a bayan wuyarsa, ya ɗaura rigar ruwa a saman kayan nasa, kafarsa na sanye da bakaken takalma masu kama da slippers, sai dai waƴan nan suna da laushi sosai, sannan kuma an yi su ne kamar cover shoe ta samansu, jikinsu kuma kamar jikin mage, haka takalmar suke, suna da bala'in kyau ga tsada, sai zuba kamshi yake yi kamar ba gobe. Bakin bed nasa ya zauna yana duba time a wayarsa, dressing room nasa ta nufi ita kuma, jim kaɗan ta fito riƙe da air freshener a hannunta, lungu da saƙo dake ɗakin bakiɗaya sai da ta bi ta fesa, har cikin ransa ya ji wannan daddaɗar kamshin air freshener data zaɓa mishi, sai dai a fuska kamar yadda kuka sani ne, ba zaka taɓa gane hakan ba. Bayan ta gama ta mayar ne ta dawo kusa da shi ta tsaya, bai ce mata komai ba, kuma bai ɗago ya kalleta ba, shagwaɓe murya ta yi tana faɗin "Yaya Saif in ta fi ne?". Tamkar babu shi a cikin ɗakin, ita kuma ta manta abin da ma ta zo gaya mishi shi ne bata ga birth certificate na Jehan ba, sai ta tsaya shiru kawai, abin ya yi mata kamar shi ya kirata ne. Ganin bashi da niyar kulata or ya ɗago ya kalleta ne yasa ta zauna a saman bedside drawer, kirjinta na dukan uku uku na tsoronsa, amma haka ta daure ta zauna abinta, ita dai tun da ance mata baya dukan mata, ya fi karfin ya ɗaura hannunsa a jikin mace dan duka, shikenan ta dai'na damuwa idan zata yi mishi wasu abubuwa, a shirmenta wai in dai iya punishment me to bata damu ba, bata san cewa punishment nasa ya fi dukan azaba ba. A tare Aseef da Areef suka shigo suka same su, wani irin azababben kyau suka yi musu na yadda suka zauna shi a bakin bed ita a bedside drawer, cool murmushi Areef ya saki har cikin ransa ya ji wani irin daɗi, gefen Lion ɗin ya zo ya zauna yana faɗin "Our Queen kin ga irin azababben kyau ɗin da kika yi kuwa? Gaskiya kyau ɗin nan ya wuci a zauna a gida, muje ki rakani unguwa". A sukwane ta ɗago ta kalli Lion ɗin, dan ya hanata fita idan baku manta ba, tamkar babu shi a ɗakin yana ta aikin duba waya. Hayewa saman bed ɗin Aseef ya yi, ta bayansu ya kwanta, bawan Allah ko zama ba zai iya wani yi ba, dan azaban jiri da yake ji, rabonsa da ya sanya abincin kirki a cikinsa yau kwana uku, kullum sai dai ya ɗan tsakura kaɗan dan kar ya mutu, ya sha ruwa ya kora da Maltina shikenan. "Our Queen lafiya baki amsa ba?". Areef ya sake tambayarta, murmushin dole ta ƙaƙalo tana faɗin "Yaya Areef ina wuni?". Da yake shi ya fi kusa da ita sai ya sanya hannu ya ɗan buge bakintan yana faɗin "Tambayar da na yi miki shi zaki bani amsa". Kukan shagwaɓa ta saka mishi tana murje ɗan bakin nata, "Sarkin rigima zo na rarrasheki". Ya faɗa tare da jawota jikinsa yana cigaba da cewa "Zo muje zan saya miki chocolate kala kala na biya buge bakin da nayi". "Yaya Areef ba chocolate ba, hoton Jehan zaka ɗauko ka nuna mini, wlh jiya har mafarkinta nayi, ina son sanin ya take". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai, shafa lallausan dark black curly hair'nta ya yi har zuwa bayanta yana faɗin "To zamu je dai tare ki ganta, daga nan muje yawo ki kaini gidansu Prof ina son naga ƴan uwan uncle". Yana magana yana ƙoƙarin tara mata lallausan gashin nan nata ya ɗaure mata, rabin jikinta na zaune saman cinyarsa rabi kuma saman bed, dan irin jawota da ya yi, sai ta ɗan kwantar da kanta a saman kirjinsa. "Bari na tara wannan gashin na ɗaure miki dan ainahin kyanki ya kara fitowa Our Queen, ke fa da bikinki hmm ko da yake faɗe ɓatawa, Allah dai ya kai mu......". Bai kai karshen maganar ba Lion ya daka musu wani mahaukacin tsawa wanda ya sanyata miƙewa ba shiri, a kule ya yi tsawar, ransa a matukar ɓace, "Get out!!" Shi ne abin da ya faɗa, a cewarsa suna damunsa da surutu, sun toshe mishi kunne. Ganin yadda ta miƙe a razane ne yasa Areef ya riƙo hannunta yana kallon ɗan uwan nasa da mamaki, ya riƙo hannunta ne kuma dan yasan halinta sarai da razana, yanzu tana iya sumewa a wajen ma bakiɗata, ba karamin ruwan mamakin jin tsawar Areef ɗin ya yi ba, tun da yake da ɗan uwan nasa yau shekara talatin da ɗaya, bai taɓa jin voice na ɗan uwan nasa mai sauti haka ba, kullun kasa kasa yake magana, ko sojojinsa baya yi musu tsawa, da idanu ma kawai idan ya kallesu sun san sauran, sun karanci ogan nasu tsab, wani shiru ma idan ya yi sun san me yake nufi, so shi tun ainahinsa ma haka yake baya ɗaga murna, baya magana da sauti, ga muryarsa da bala'in daɗin sauraro, amma sai rowarta ya iya. Ita ma da yake ta saba da Areef fiye da kowa, bata wani damuwa da duk wani abin da zai yi mata, dan tasan ba zai taɓa cutar da ita ba, shiyasa ma take kwanciya a jikinsa da sauransu, ganin ya riƙo hannunta yasa ta tsaya ta natsu jikinta na kerma kamar me. Shi kansa Aseef dake kwance ta bayansu yana fama da kansa sai da ya miƙe zaune, jin tsawar ta ɗan uwansa yasa ya nemi damuwar tasa ma ya rasa ina ta nufa?, Ya ji abin da bai taɓa ji ba a tare da TRIPLETS nasa. "Lion lafiya kuwa?". Cewar Areef. Ko sannu bai ce musu ba, ko ɗago kai ma bai yi ba bare su saka ran zai amsa, dawo da kallonsa kanta Areef ɗin ya yi sai kallon Lion ɗin take yi, shi dai sun kulle mishi kai, ɗan Juyowa ya yi ya kalli Aseef ko zai yi mishi cikakken bayani. Tsabar tsiya irin na Aseef ɗin sai ya matso kusa da Lion ɗin sosai tare da sanya hannayensa dukka biyu ya tushewa ɗan uwan nasa kunne wai dan kada ya ji abin da zasu ce shi da Areef. "Ka toshewa sister ma kunne kada ta ji me zan ce mana". Cewar Aseef ɗin. Jawota jikinsa Areef ɗin ya yi don ya toshe mata kunne, dan shi dai yana son jin gulma ato, dole ya toshe mata kunne. A zafafe Lion ya juyo ya damko wuyar Aseef ɗin, ransa a matukar ɓace ya shaƙesa sosai, da sauri Areef ya miƙe tsaye tare da sakinta, ko a mafarki bai taɓa mafarkin Lion zai shake Aseef ɗin ko ya ɗaura hannu a jikinsa da nufin duka ko wani abu makamancin haka ba, sai ga shi yau ya shakesa sosai, saketa ya yi tare da hayewa saman bed ɗin dan ya kwaci Aseef ɗin, ita kam yau ta ga bala'i, yadda nan take Lion ya canza musu daga Saif ya koma Lion na gaske. Tamkar jira yake yi Areef ɗin ya zo, sai ya saki Aseef ɗin ya damko wuyar Areef ɗin, da alama fa ɓacin ran dama na Areef ne ba na Aseef ba. Shiru Areef ɗin ya zuba mishi idanunsa da suka yi jawur kamar wuta yana jin shakar da ya yi mishi har cikin zuciyarsa, yana shan azaba amma bai motsa ba bare ya yi yunkurin kwatar kansa, sai ma tsare shi da idanu da ya yi yana karantar yanayinsa dan ya gane ɓacin ran na menene ne haka?. Sai da ya tabbatar ɗan uwan nasa ya galabaita sosai kafin ya sake shi tare da miƙewa, da farko ya yi kamar zai nufi toilet, sai kuma ya juyo ya damko gashin kanta a in da take tsaye ta yi sumar tsaye, dan ta tsorata ganin ya shake Areef da Aseef yau, bata san a baya faɗa suke yi sosai ba, suna kaunar junansu, amma dama kunsan TRIPLETS or TWINS suna faɗa sosai dan suna ganin kansu ɗaya, to ɗaya ba zai yarda ɗaya ya nuna mishi fifiko ba, amma su da suka girma sosai sun dai'na gaskiya, sun jima basu yi ba na gaya muku a baya, ita dai Rimsha ita ce bata sani ba, shi ne abin ya yi mata wani iri hakan nan. "Ban ce ki fita mini a ɗakin nan ba?" Ya faɗa murya can kasa kasa, ya yi maganar kuma har lokacin yana damke da dark black curly hairnta, dan gashin nata ya damko ba wuyarta ba, narai narai ta yi da idanu kamar zata yi kuka, zafi sosai gashin yake yi mata, ko kusa Areef bai yi yunkurin kwatar ta ba, dan yana zargin ɓacin ran ɗan uwan nasa yana da nasaba da rungumeta da ya yi or something like this, koma yaya yana dai da nasaba da ita, idan kuwa haka ne, Lion ɗin ba zai taɓa yi mata abin da zai cutar da ita ba, zai dai hukunta ta iya hukuncin irin nasa, amma ba zata cutu ba, shi ne yasa ya zuba musu idanu kawai, shi kam Aseef dama tun da aka sake shi ya koma ya kwanta ya basu baya abinsa, dan shi bala'in da yake ciki ma kawai ya ishe shi, ba zai iya ɗaukar wani ba kuma, kada ya mutu lokacin mutuwarsa bata yi ba. Tsareta da idanu ya yi yana jiran amsa, a hankali ta motsa kyawawan laɓɓanta ta furta "Ka ce na fita, yanzu zan fita ɗin". Ganin yadda lips nata suke motsi dimples nata suke lotsawa ne yasa ya tuna abin da ya faru ɗazun na iska da ya hura mata cikin ɗan bakin nata, wani irin zirr ya ji a jikinsa tuna abin, sakinta ya yi ba tare da ya yi magana ba, da gudu ta juya ta fita, dama Malika ta faɗa, dole sai abin ya yi ta dawowa mishi cikin tunaninsa, dan abu ne da bai taɓa yi ba a rayuwarsa, so dole ya ji wani iri, dama mace da namiji kamar kararrawa suke, duk lokacin da suka haɗu dole sai zuciya ta bada sautin bugawar kararrawa, haka halittar take, musamman kuma yadda ya ji lips ɗin nata da bala'in laushi kamar me, ai dole ya tsaya mishi a rai. (Gaskiya Malika bata kyauta mishi ba, Allah ya sakawa bawan Allah, yana zaman zamansa muguwa ta ɗarsa mishi abin da bai taɓa ji ba a zuciyarsa😭 justice for Lion, ta iya shirya kitimurmura Malikar nan wlh, duk wani tsiya ta san shi, yanzu sai Allah ma kaɗai yasan me ta yi ta shiryawa da har aka kawo wannan matakin😌) Hanyar fita ya nufa, har ya yi gaba sai kuma ya juyo da kallonsa kan Aseef dake kwance ya basu baya, calmly ya ce "A karo na karshe zan tanbaye ka, me yake damunka?" Juyawa Areef ya yi ga Aseef ɗin, yayin da shi ma ya juyo ga ƴan uwan nasa, kasa kasa ya furta "Zazzaɓi and ciwon kai". Ɗan zaro idanu Areef ɗin ya yi tare da kai hannunsa saman lallausan kumatunsa dan ya ji akwai zazzaɓin ne ko babu, tabbas akwai ta a jikinsa, dan ga jikin nan ya yi zafi sosai, dawo da kallonsa kan Lion ɗin ya yi, gera ɗaya Lion ɗin ya ɗaga mishi alamar ya ake ciki? Jinjina mishi kai ya yi yana bashi tabbacin yes da akwai zazzaɓin a jikinsa, Juyowa ya yi ya dawo saman bed ɗin, hayewa ya yi tare da tallaɓo kan Aseef ɗin yana kallon cikin kwayar idanunsa. Nan take dukkansu biyu suka shiga damuwa, A box Areef ya ɗauko dan su duba shi, shiru Lion ɗin ya yi yana tunanin cewa wannan zazzaɓi na Aseef ba zazzaɓin kwayar cuta ba ce, sai dai idan zazzaɓin tashin hankali ko makamancinsa, dan kuwa idan da zazzaɓin kwayar cuta ce dole za su ji a jikinsu na farko, na biyu kuma dole yanayin Aseef ɗin zai canza. Shi kuma Areef sai ƙoƙarin haɗa kayan aiki yake yi. Kuka Aseef ɗin ya saka musu a kan shi dai ba za su yi mishi allura ba, ya warke dan haka su kyale shi, hannu Lion ya ɗagawa Areef a kan kada ya haɗa komai, da mamaki yake kallonsa, kwantar da kan Aseef ɗin ya yi a saman pillow tare da ɗan kwantowa kusa da shi yana faɗin "Menene ainahin abin da yake damunka?". Dama shi Aseef yariga da ya san tsab Lion zai iya gane zazzaɓin kwayar cuta da kuma ta firgici or tashin hankali, sai dai bai ɗauka da wuri haka zai gane ba, amma duk da haka sai ya kafe musu a kan shi babu wani abin da yake damunsa, hakan yasa Lion ɗin ya ce a kira mishi daddy Rimsha, dan yasan dole ne ma shi yasan menene yake damun ɗan uwan nasu, Areef na kokarin kiransa a waya, sai kuma ya ce no ya barshi kawai koma menene zai sani ne, shi kuma Aseef ya jira shi yana nan dawowa zai yi bayani ne tun da yaki gaya mishi gaskiya. Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya sauko kasa ya nufi waje dan aikin da yake yi bai karisa ba, ya dawo ɗaukar wasu abubuwa ne tare da birth certificate na Jehan. Yana fita Areef ya dawo kusa da Aseef ɗin dan ya lallaɓa shi ko zai gaya mishi menene yake damunsa, nan ma dai kin faɗe ya yi, ya kafe a kan shi fa kansa ne yake ciwo da zazzaɓi, bayan haka kuma babu wani abu da ya sani, dole tasa Areef ɗin ya hakura ya kyale shi ba dan ya so, saukowa ya yi ya nufi waje, cikin sanyin murya Aseef ɗin ya ce "Areef please zo ka yi mini alluran barci". A sukwane ya juyo yana kallonsa da mamaki, wai me yake damun sa ne?. Tunani cike fal ransa ya zo ya haɗa alluran ya yi mishi, bawan Allah yau tsawon kwana uku baya samun isasshen barci, yana son kuma ya yi barcin dan ya hutawa ransa, amma ina abin ya fi karfinsa, hakan yasa kawai ya ce ayi mishi alluran barci ko ya ɗan samu ya rintsa. Aikuwa ana yi mishi ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi, Areef ya ɗauki tsawon lokacin yana kallonsa kafin ya miƙe ya fice daga ɗakin ya nufi nasa bedroom ɗin dan ya yi wanka ya je wajen Jehan a prison, gobe court zata yanke mata hukunci. A ɓangaren Rimsha kuwa, tana fita bedroom nata ta koma.......... ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ *Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta* E53-54💋 A ɓangaren Rimsha kuwa, tana fita bedroom nata ta koma, saman gado ta haye tana tunanin wai shi yaya Saif ɗin nan wani irin mutun ne? Sai ka rasa me yake damunsa sam. Shi kuwa waje ya nufa dan ya je in da yake bukatar zuwa, har ya kai tsakiyar palon kasa sai ya tuna bai karɓi birth certificate ɗin Jehan ba, juyuwa ya yi ya nufo saman, bedroom nata kai tsaye ya nufa. Kasa kasa ya yi sallama kafin ya faɗa, bata ji sallamar tasa ba sai dai ta ji daddaɗar kamshin perfume nasa da ya ziyarci hancinta, cikin sauri ta ɗago da kallonta zuwa bakin kofar shigowa, a bakin kofa ta ciki ya tsaya yana ɗan latsa wayarsa, zubur ta miƙe zaune tana kallon shi, tamkar ba bedroom nata ya shigo ba, ta ruɗe ta rasa me zata ce mishi, muryarta na rawa ta ce "Yaya Saif sannu da zuwa ina wuni?". (Wayyo cikina 🤣 wai yaya Saif sannu da zuwa ina wuni) Tamkar babu shi a wajen, ko kallon in da take bai yi ba, duk ya rikitata, dirowa kasa ta yi daga saman bed ɗin nata ta nufo shi, kusa da shi ta tsaya tana son tambayarsa me ya zo yi, kwata kwata ta manta da cewa ya ce ta bashi birth certificate na jenan, sai wani ƴan kame kame take yi, shi kuma ya kware wajen gindayar da mutane, yanzu ma dai shirun gindayarwar ya yi mata. Sai da ya ɗauki good 5 mins yana tsaye kafin ya ɗago da kallonsa a kanta, kasa ta yi da kai, zubawa kyakkyawar dark black curly hairnta idanu ya yi, ba ƙaramin kyau gashin suke yi mishi ba, sai wani murza yatsun hannunta take yi alamar duk a tsarge take. "Ina birth certificate da na ce ki kawo mini?". Cikin sauri ta ɗago idanunta ta saukesu a saman faffaɗar kirjinsa, "Ban gani ba ne, yana Abuja". Ta yi maganar cikin natsuwa, mamakin natsuwarta wani lokaci yake yi, wata zubin kuma sai ka ganta kamar wanda aka sakawa battery, rawan kai kamar me. Ganin bai tafi bane yasa ta ɗan ɗago ido dan ta saci kallonsa, caraf suka haɗa idanu, kasa ta sake yi da kanta tare da takure kanta ta ɗan turo baki, wannan turo bakin da ta yi nan take ta tuna mishi da abin da ya faru ɗazun na iska da ya hura mata, laushin da lips nata suke da shi ne kawai yake yi mishi yawo a cikin kwakwalwarsa. Tuna hakan kuma yasa ya juya ya fice daga ɗakin, bin bayansa da kallo ta yi har ya isa tsakiyar palon saman, a nan ne kuma suka haɗu da Areef da ya fito daga bedroom nasa bayan ya yi wa Aseef allura kenan. Tsayar da shi Areef ɗin ya yi yana faɗin "Gobe za'a yankewa baby hukunci fa, kuma ka san kai tsaye hukuncin kisa zasu yanke mata, yanzu me abin yi? Ka dai san tana da gaskiya ko? Kare kanta zata yi ta kashe shi bisa kuskure, kuma kasan wannan hukuncin da ta yi mishi dai'dai ne, dan ko kai ka kama irin shi, wannan hukuncin zaka yi mishi". A takaice ya ce "To ina ruwana da case ɗin?". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya sauka kasa abinsa, bin bayansa Areef ɗin ya yi ba tare da wata damuwa ba dan yasan Lion ɗin ba zai taɓa bari a kasheta ba, dan kuwa yasan tana da gaskiya, kuma mugun iri ta kashe, shiyasa bai wani damu ba ya bi bayansa suka sauka kasa ya wuce bedroom nasa. Ita kuwa Rimsha tun da ta ji abin da suka tattauna hankalinta ya yi kummunar tashi, nan take hawaye suka fara wanke mata fuska, shikenan za'a kashe Jehan kenan? Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, ba zata iya jurar wannan bala'in ba, saman bed nata ta koma ta kwanta, hawaye tamkar ruwan famfo haka yake gudu a face nata, ji take yi duniya na juya mata, har wani duhu duhu take gani yana gilma mata ta cikin idanunta, daga Lion ɗin har Areef ɗin ba wanda ya san ta ji abin da suka tattauna, da sun ji Areef ba zai tafi ba har sai ya tabbatar ya kwantar mata da hankali. Haka ta kwanta har aka kira sallar la'asar, jiki duk a mace, da kyar ma ta iya mikewa ta yi sallar, bayan ta idar ta yi wanka ta shirya cikin Abaya sannan ta fito zuwa kitchen dan ta ɗauki abincinsa ta kai masa, tun karfe 3 ta ji dawowarsa, amma ta san ba zai ci abincin a lokacin ba, shi ne yasa ta yi kwanciyarta kawai. Kitchen ta nufa, tsaye ta isko Mark yana latsa wayarsa, sannu ta yi mishi, bai amsa ba, bai kuma ɗago ya kalleta ba, tamkar dai babu shi a wajen kamar kullum, wanke hannunta ta yi ta ɗauki abincin ta fito ta nufi bedroom ɗin nasa. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga, yana zaune saman bed nasa ya jingina da jikin headboard na gadon tare da rufa bargo zuwa daidai saitin cikinsa yana latsa waya. In da ta saba ajiye mishi abincin ta nufa, ajiyewa ta yi tana ƙoƙarin zama kenan muryarsa ya daki dodan kunnenta. "Kawo mini fruits kawai is okey". Ya yi maganar ba tare da ya ɗago ya kalli in da take ba. Okey ta amsa mishi da shi tare da ɗauko mishi ta nufo shi, saman bedside drawer ta ɗaura plate ɗin tare da zama a saman carpet ɗin dake wajen, cike da tsoro ta ce "Yaya Saif ina son zuwa prison in ga Jehan". Shiru ya yi bai kulata ba, almost 10 mins suna haka, sannan ne ya ce zata iya tafiya bedroom nata, kuma kada ta kuskura ta fita daga gidan nan, ba zata je prison ɗin ba. Da sauri ta miƙe ta nufi waje, tana shiga bedroom nata ta faɗa a saman gado tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, shikenan idan ma kashe Jehan ɗin za'ayi ita ba zata sake kallonta ba, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wannan bala'i da me tayi kama? Ji ta yi kamar ta rataye kanta dan bakin ciki, har wani irin shasshekar kuka take yi wadda daga ji kasan zuciyarta a kusa take, kiris take jira ta yi bindiga. Shi kuwa ko a jikinsa ya sha fruits nasa kafin ya gyara kwanciyarsa da kyau tare da lumshe idanunsa kamar mai barci. A ɓangaren Areef kuwa, wanka ya tsara ya nufi prison ɗin shi da Donald ɗaya daga cikin sojojin Lion, a lokacin Mark yana aiki shi ne yasa ba su tafi tare ba. Sai da suka biya super market ya saya mata wasu abubuwa da yake ra'ayi, sannan ya fito suka nufi prison ɗin Office ɗin shugaban gandurobobin ya zauna tare da bukatar ganinta, ba ɓata lokaci kamar dai kullum suka fito da ita, sun zuba mata sarkoki a hannu, dama idan za su fito da babban mai laifi haka suke yi. A kasa saman carpet ɗin gandurobar ta zaunar da ita, hankalinta a kwance tamkar ba ita za'a yankewa hukunci gobe ba, Ameera da ba ita za'a yankewa hukunci ba ma, ta shiga tashin hankali sosai, duk bayan minti ɗaya sai ta ce "Yanzu Jehan ke sam baki damu ba? Kuma kin san hukuncin kisa zasu yanke miki fa ko?". Tsaki take ja tana faɗin "To idan su suka riƙe raina ba sai su kashe ni ɗin in gani ba, wai ma su suke da wuta ko aljanna ne? Ni fa Ameera ki daina damuna, duk wanda kika ga ya mutu to lokacinsa ne ya yi, idan lokaci kuma ya yi, ko a saman kadon kuɗi da mulki kike kwance sai kin mutu, to idan mutun ya san haka me zai wani takura wa kansa? Ke ni bari ki ji wlh ni bana ma ɗaukar alkalinma kamar mutun bare har na ɗaga idanu na kalle shi, ni dai nasan ga abin da na yi, so wannan tsakanina ne da ubangijina, idan sun cuceni a nan sun nuna mini fin karfi, suma suna nan zasu zo in da zasu turani ɗin, tun da babu wanda Allah ya ce zai tabbata a duniya, kowa sai ya mutu, dan haka za su mutu su zo su same ni suma, a nan ne kuma mai karfin iko, malikiyaumiddin mamallakin ranar sakamako zai karɓa mini hakkina, lokacin kuma babu wata rai da zata iya musawa ta ce bata yi kaza ba, ko kuskure aka samu, duk babu wannan korafin, ranar hukunci ne da ubangiji subhanahu wata'ala zai yanke ta dai'dai da abin da kowa ya yi, idan ta yi maka daɗi, ka yi da kyau kenan a duniya, kuma da haka zaka yi ta kallon mai kyau har abada, idan bata yi maka daɗi ba, to fa farkon kofar rashin jin daɗin rayuwarka ce ta buɗe har Illah Masha Allah, so dan haka ki dai'na takurawa kanki muddin kin san da mai wuta da aljanna kika dogara ba kato ba!!". Baki Ameera take sakewa tana ganin ikon Allah ita dai, duk a tsorace take, amma ita da za'a yankewa hukunci ko a jikinta, hankalinta kwance tamkar wanda take gidan iyayenta tana shan Ac mai sanyi. STORY💋 Zuba mata idanu sosai Areef ya yi yana kallon ramar da ta yi, sam baya son hakan, ba karya ta rame saboda zaɓar abinci da take yi, ji yake yi kamar ba zai iya hakuri ba, gara mishi kawai ya ɗauketa su tafi gida, amma yasan Lion ba zai yarda da hakan ba, dan ya saɓa doka, hakan yasa yake daurewa kawai yake kawar da kansa ya barta a prison ɗin. Kallon shugaban gandurobobin ya yi, cikin natsuwa ya ce "Zaka iya bamu waje dan zan yi magana ta sirri ne da matata". Wani kallon sama da kasa ta wurga mishi, wai mata, ko waye ya bashi ita oho mishi. Kashe mata ido ɗaya ya yi yana mata signal da gera ɗaya, guntun tsaki ta ja, dan duk lokacin da ya yi irin hakan, kama yake yi mata da tantiran maza irin ƴan duniyar nan, sai ya wani kashe ido ɗaya kamar wani tantirin ɗan iska, shi kuma ya saba abin ne sakamakon zaman da ya yi cikin ƴan ta'addan da ƴan iska, shi ne ya koyi abin, sai kuma ta zamo mishi jiki, har idan bai yi ba ma baya jin daɗi. Miƙewa shugaban gandurobobin ya yi ya nufi waje, kallon Donald ya yi, tun bai yi magana ba shi ma ya fice da sauri abinsa. Dawo da kallonsa kanta ya yi, cikin zolaya ya fara magana "Tun da ba zaki gaishe ni ba ni bari na gaishe ki? Ya jiki?". Kasa kasa ta amsa mishi da ta ji sauki. "Wai da gaske baby har yanzu baki fara tunanina ba?". Ya yi maganar murya a sanyaye, kuma can kasa kasa ya yi maganar, harara ta watsa mishi ba tare da ta yi magana ba, dan a cewarta bata da lokacin ɓata bakinta na magana da shi, ga shi sai bala'in tsoronsa dake ji cike fal ranta, a fili kuma sai karfin halin bala'i. Miƙa mata ledar hannunsa na shopping da ya yi mata ya yi yana faɗin "Okey tom shikenan yanzu dai bari na gama da case ɗin naki, dole zan koya miki tunanina, amma first yanzu dai karɓi wannan". Kin ɗagowa ma ta yi ta kalle shi bare ta yi ƙoƙarin karɓar ledar duk da hannunta ma dama da sarka a ɗaure, hakan yasa ya ɗaura mata ledar a saman cinyarta yana kara kare mata kallo, kyakkyawan gashin kan nan nata da ya sha gyara a gidan Hjyr daɗi kafin ta biyo Abubakar jaja, sai kyalli gashin yake yi in da ya leƙo ta cikin hijabin nata. Hannu ya kai ya ɗan zame hijabin nata zuwa baya, ya sauke shi kenan daga kanta zuwa wuyarta, abin haushi shi ne hannunta ɗaure da sarka ba ta yadda zata yi ta buge hannunsa ko ta hana shi ya ta ɓata, ɗaure fuska sosai ta yi tana faɗin "Kada ka taɓa mini gashi". "Gashin ki ne ko nawa?" Harararsa ta gefen idanunta ta yi bata sake ce da shi komai ba, dan ko wani amsa ta bashi sai ya sake kawo mata wata maganar kuma, rufin asirinta kawai shi ne ta yi shiru. Hannun ya sanya yana tara mata gashin nata yana faɗin "Uncle nawa yana zuwa gobe, dole na san abin yi, bana son uncle na ya zo ya same ki a nan, amma In Sha Allah nasan Lion ba zai taɓa bari a yanke miki hukuncin kisa ba, nima kuma ba zan bari ba, ki kula mini da kanki sosai, kada ki ji komai, gobe yiwar haka muna tare a gida, tare zamu ci abincin rana". Ko sannu bata ce mishi ba har ya tare mata gashin nata, pil ɗin da yake ɗaure gashin kansa da shi ya zaro ya sanya mata a kan nata yana faɗin "Bana son ki rinƙa sake gashin nan naki haka, nafi son ki rinƙa ɗaure mini shi kina ɓoye mini shi, kada ki bari kowa ya kalla mini abina, nawa ne ni kaɗai". Mamaki ne ya kamata ganin yadda gashin nasa ya zubo mishi har kafaɗarsa kamar wata mace, dama bata san gashinsa yana da tsawo har haka ba, dan baya barinsa a sake, kullum a tare a bayan wuya ya sanya mata ɗan karamin pil ya ɗaure, ba zaka taɓa tunanin yana da tsawon gashi har haka ba, ya fi Lion tsawon gashi sosai, dan shi Lion yana rage tsawon nasa, baya bari ta wuce mishi bayan wuya, shi kuma Areef ɗin baya ragewa, ya bar kayansa ta kai har baya abinsa, yana kashe mata kuɗi over yana gyarata, kuɗin shampoos na gyaran gashinsa kawai ta isa ta sayawa mutum dankareren gida, ba karamin kuɗi suke kashewa gashin nasu ba, kowa da ra'ayinsa a cikinsu, shi Aseef ma ai dukka yake tankewa abinsa, baya son wahala, Lion rage tsawon, shi kuma har baya ya bar abinsa. Zubawa gashin nasa idanu ta yi tana mamaki, ya fi nata tsawo. Bayan ya ɗaure mata nata ne ya tara nasan ya kulle a bayan wuyar nasa, duk da ya san zata warware, bai wani damu ba tun da ya ɗaure mata nata, gashin TRIPLETS akwai bala'in tsantsi ne sosai, hakan yasa dole idan zai ɗaure gashin nasa sai ya sanya pil, idan ba haka ba, warwarewa zata yi. Hira ya ɗan yi mata na ƴan mintoci da basu wuce 10 ba, sannan ya yi mata sallama tare da rankwafowa ya manna mata sumbata a goshinta yana faɗin "Ki kula mana da kanki, ina son uncle ya zo ya sameki cikin ƙoshin lafiya, dan haka ki kula". Kallon uku goma ta watsa mishi, ko a jikinsa ya nufi waje abinsa yana yi mata bye bye. Yana fita ba'afi da minti uku ba sai ga gandurobobin suka dawo ciki, macen da ta fito da ita, ita ta mayar da ita tare da ɗaukar ledar da ya bata, sai da suka je bakin kofar ɗakin nasu, sannan suka cire mata sarkar da suka ɗaure ta tare da karɓar ledar da Areef ɗin ya bata dan su zuba me a ciki, always ne da pants a ciki, sake baki ta yi tana kallon always ɗin da matar ta fitar, ko waye ya gaya mishi yau period nata ya zo da safe? Kai wato ma ya saka mata ido na wuce misali kenan? Ta tsaya sai tunane tunane take yi, sai magana gandurobar take yi mata a kan ta shiga ciki, amma ina ta lula duniyar tunani waye ya gaya mishi yau tana period kuma?. Sai da gandurobar ta taɓata sannan ne ta dawo daga duniyar tunanin nata, Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta karɓi kedar ta wuce ciki, rufesu matar ta yi tare da juyawa ta bar wajen. Shi kuma Areef yana barin prison ɗin gidansu Imran ya nufa dan ya riga da ya gaya wa Imran ɗin yana zuwa yau. Gidan cike yake da ƴan biki, part ɗin Imran ɗin suka wuce, Akila tana ciki tana kwance bata da lafiya, zazzaɓi kamar zai kasheta, har Abbi ya ce ko za'a ɗaga bikin ne, Abba ya ce a'a ayi kawai ta je ta yi jinyar a gidanta, da yake shi ya san me matsalar, Ammie dai raba dare take yi tana rokan Allah da ya kawowa ƴar tata mafita, ya zaɓa mata abin da ya fi zama mata alkhari, bata wani nuna damuwa ba. Lokacin da Areef ya shiga cikin palon, Imran, daddyn Jelly, AKil, Irfan, Dr Nawid, duk suna zaune saman sofa suna zuba hira, da yake yana sanye da black glass sai Akil bai iya rabe shi da Aseef ba, ya ɗauka ma Aseef ne, dan haka sai ya ɗan kawar da kansa, dan sam baya son haɗa idanu da Aseef, ya kasa manta zubewa a kasa a gabansa da Aseef ya yi kwana uku da suka wuce, lokacin su Abbi ba su dawo gidan ba, ya zo wajen Akila hira ne, har cikin palo ya shiga dan Abba baya nan, Akil ɗin ya fito zai fita zai je unguwa, shi ne ya zube gwiwowinsa a gabansa yana rokonsa da dan Allah ya rokan mishi Abba, wlh ba zai iya rabuwa da Akila ba, idan aka rabasu zai iya mutuwa, wannan abin ya tsayawa Akil sosai a rai, yadda ya kalli fuskar Aseef a wannan rana, ban da tsantsar soyayyar Akila babu wani abin da yake cikin idanunsa, bawan Allah. Lallai rayuwa ba ta yadda bata zuwa wa bawa, yau a kan mace, a kan soyayya har ɗaya daga cikin TRIPLETS jinin William jacop, TRIPLETS ga The General Of Armys yake zube gwiwowinsa a kasa yana rokan kada a raba shi da ita? Ya ilahi ya lillahi, duk wata zuciya mai imani sai ta zubarwa da Aseef kwallah na halin da yake ciki, tabbas yana cikin halin mutuwa ko rayuwa, domin kuwa ya yi mummunar zurmawa over ne a soyayyar AKila. Da yake shi Areef bai san komai ba, sai ya miƙa musu hannu dan su yi musabaha fuska ɗauke da murmushi, sosai Akil ya sha mamaki, sai kallonsa yake yi, ya kuma kasa gane cewa ba Aseef bane Areef ne, kila da ya cire glass ɗin face nasa ne ya iya gane shi ta kalar kwayar idanunsa. Haka suka cigaba da hira Areef yana ta kallonsu dan baya jin Hausa, bai san me suke cewa ba. A nan ya yi sallar mangariba da issha sannan ya yi musu sallama ya nufi prison dan ya sake duba Jehan su yi sallama sai gobe, yana fita sai da Akil ya tambayi Imran ya akayi Aseef ya hakura ya wastsake? Nan yake gaya mishi wannan ba Aseef bane, Areef ne, ya sha mamaki irin tsantsar kamar da suka yi mishi har ya kasa raɓesu, shi kuma Dr Nawid ya sha mamakin dama wannan TRIPLETS na Lion ne, su Lion kawai suka sani, shi ma ba face nasa suka sani ba, bai taɓa ganinsu a zahiri ba sai yau, ga shi har musabaha suka yi ba tare da ya san shi ba ne. A ɓangaren Lion kuwa, bayan ya yi sallar mangariba da issha bedroom nasa ya wuce dan yunwa yake ji sosai, zaune ya iskota ta kawo mishi abinci tana jiransa. Wajen da ya saba zama ya je ya zauna tare da bata umarnin ta zuba mishi abinci, ba musu ta zuba mishi ta turo mishi a gabansa, ɗaukar spoon ya yi ya fara ci, shiru ta yi tana tunanin ƴar uwar tata, kamar saukar aradu haka ta ji zazzakar muryarsa ya daki dodan kunnenta. "What is wrong with you?". Shi ne abin da ya faɗa cikin sanyin murya. Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin "Nothing". "Saboda na hanaki zuwa prison ko?" Nan ma girgiza mishi kai ta yi alamar a'a, ga idanunta kuma har sun kumbura saboda kuka, dole dama zai gane tana cikin damuwa ta kuma yi kuka sosai, saboda idanun nata, kuma kunsan yadda yake tsantsar kaunar ganin idanun nan nata, dole dama zai ɗago ya kallesu, idan ya gansu a kumbure kuma ai dole ya tambaya. Shiru ya yi bai sake yin magana ba har ya kammala cin abincinsa ya tashi ya fita daga gidan, waje gabaɗaya ya nufa, a waje Mark ya fito da mota ya same shi, akwai in da za su je ne. Kwashe kayan abincin ta yi ta mayar kitchen kafin ta koma bedroom nata ta ɗan kwanta, da misalin karfe 10, Lion bai dawo ba haka shi ma Areef, Aseef kuma har lokacin yana ta barci alluran bata sake shi ba. Sam ta kasa barci, ban da tunanin Jehan ba wani abin da take yi, a haka har 11 gari ya yi shiru, kasa jurewa ta yi ta diro kasa daga saman bed ɗin nata, mayafin abayar tata ta ɗauka ta yafa a kanta tare da nufar waje, gabaɗaya sojojin sai kewaye suke yi a cikin harabar gidan dan tabbatar da tsaro, wucesu ta yi ta nufi gate, kwata kwata ta manta Lion ya ce kada ta kuskura ta fita, idanunta sun rufe, ban da tunanin Jehan babu wani abin da take yi. Hanata fita gateman ya yi, karya ta zuba mishi a in da ta ce mishi Areef ne yake kiranta yana waje, da yake ta san Areef ɗin baya nan. Jin hakan yasa ya buɗe mata gate ɗin ta fita, tafiya ta fara yi bata san ina ta dosa ba, ita dai prison kawai take son zuwa abinta. Har ta fita daga layin nasu ba tare da ta sani ba, sai a lokacin ne kuma ta tuna ashe bata san hanyar zuwa prison ɗin ba ma, ga shi babu abin hawa, bugu da kari babu kuɗi a hannunta. Daurewa ta yi ta cigaba da tafiya abinta, ta ɗan kara tafiya can ta ci karo da irin matasan nan ƴan shaye shaye, wuka suka zare mata a kan ta basu kuɗin jikinta, dan a tunaninsu irin karuwan nan ne ita. Kuka ta fara yi jikinta na kerma, ga shi ba abin da ta fito da shi, ko wayarta bata ɗauko ba bare ta basu su rabu da ita, cikin kuka ta ce musu ita bata da kuɗi, ɗaya daga cikinsu ya ce ta yi shiru ta dai'na yi musu kuka ko su kasheta, a yadda take kyakkyawan nan ne zata ce musu bata da kuɗi? Kenan a banza mazan suke kwasanta ne? Duk wannan kyau ɗin nata su kwasa ba biya? Ina karya take yi, ta basu kuɗi ko kuma su kasheta,. Rantse musu da Allah ya rinƙa yi a kan wlh ita bata da kuɗi, jikinta sai kerma yake yi, tana kuka kamar ranta zai fita tare da danasanin fitowarta. Wuƙa ɗaya daga cikinsu ya fitar dan ya caka mata a ciki tun da taki basu kuɗi, cikin sauri wani daga cikin ya dakatar da shi yana faɗin "Kai wawa ne fa, ba gara muma mu ɗan kwasa na banzan ba tun da ba kuɗi, ka ga karamar yarinya ne, wato wayo mazan suke yi mata su kwashi daɗi basu biyanta, daga ganin wannan yarinyar irin yaran nan ne da uwarsu ta mutu suke hannun matar uba haka, shi ne yasa take fitowa bin maza, idan ba haka ba, ba yadda za'ayi uwarta tana raye ka ganta a yawon ta zubar a cikin daren nan, ka ganta kyakkyawa dan haka muma mu kwashi rabonmu tun da ba kuɗi". Amsa mishi suka yi da e haka ne ya kawo shawara mai kyau gaskiya. Jin hakan yasa ta yi ƙoƙarin guduwa ta kuma yi musu ihu, damko mayafin abayarta kanta suka yi, da sauri ta cire musu mayafin ta fara gudu dan ta tsira, ina ai tana mace ba zata iya guje musu ba, tuni suka damko gashin kanta, janta suka fara yi da gashin dan tsabar mugunta, ɗaya daga cikinsu ya toshe mata baki, cikin ma gudanar ruwa dake gefe da gefen titi wato lambatu suka yi ƙoƙarin shigar da ita, da yake babu ruwa a ciki, duk ruwan saman da aka yi ya ganganre ya tafi, wajen har ma ya bushe, ga shi ya yi fresh saboda ruwa ya wanke shi. Yana riƙe da gashin kanta gam, da shi yake janta yana ƙoƙarin shigar da ita ciki, ya toshe mata baki, ita kuma ta yi yarda ta shiga, haushi hakan yasa wanda ya ciro wuka ɗazun ya sake cirowa dan ya yanke mata wani sashe na daga jikinta ko kuma ya caka mata a ciki ta yadda zata zube kasa su shugar da ita, koma ta mutu su za su iya biyan buƙatarsu, cike da mugunta ya yi yunkurin caka mata wukar a cinya, cap Lion ya damki hannunsa, wani irin baya ya yi da hannun ya murɗe da karfi ji kake kas ya karya kashi, ihun azaba ya saki. Saketa wanda ya riƙeta ɗin ya yi suka yi ƙoƙarin guduwa, kap nasu Mark ya damkosu, da yake sun ɗan yi shaye shayensu babu wani kuzarin kirfi a tattare da su, kwallo da su sosai Mark ya yi kafin ya haɗesu ya cire wandon ɗaya daga cikinsu ya yage shi ya ɗauresu da kyau kamar wasu goro. Abin da ya faru, lokacin da yaran suka tareta, a lokacin motar Lion ta wuce su, sai dai bai kawo cewa ita ɗin ba ce, ya dai ga mace da maza suna tsaye, a tunaninsa ma duk tare suke, hira suke yi da yake ta bawa hanyar baya, sai dai fa da kallo ɗaya ya yi wa bayan nata ya ji cewa ita ce a zuciyarsa, sanin ita tana gida ba zata taɓa fitowa bane yasa ya kawar da tunanin a ransa suka wuce, bayan ya koma gida ya buƙaci shan fruits, ya kira Areef a waya dan ya sanyata ta kawo mishi tun da shi bashi da numberta, sau uku Areef yana kiran numberta bata ɗauka ba, shi ne ya sake kiran Lion ɗin ya ce dan Allah ya dubata a ɗakinta ko lafiya bata ɗaukar waya, da farko ya share ya kwanta, sai kuma ya tuna da yarinyar da ya gani tsaye cikin mazan nan tabbas bayanta ya yi maka da nata. Tuna hakan yasa ya fito ya shiga bedroom ɗin nata, bata nan, palo ya fito zuwa waje ya tambayi gateman, a nan ne yake gaya mishi ai ta fita, wani mahaukacin mari ya sakarwa gateman ɗin wanda ya sanya shi sumewa, tsawa ya dakawa sojijin dake wajen a kan hauka suke yi ne da zasu bar wani ya fita daga cikin gidan nan ba tare da saninsa ba, kasa suka yi da kansu suna tsoron ce mishi yarinyar ta ce Areef ne ya kirata, in da ya harzukannan zai iya yanke musu mummunar hukunci, dan haka sai suka ja bakinsu suka yi shiru. Tuna cewa tana tare da mazan can yasa bai bi ta kansu ba ya ce Mark ya fito da mota suje, to shi ne abin da ya faru a gida da har ya iya sanin in da take ha zo. RIMSHA Suna sakinta ta zube gwiwowinta a kasa a wajen, kuka ta saka dan tasan yau ta mutu a hannunsa, daga yanayin tsayuwar da ya yi ma tun bata kai kallonta ga face nasa ba tasan babu mai kwatarta yau, a zafafe rai a matukar ɓace sai huci yake yi ya damko wuyarta, jan ta ya yi har zuwa wajen mota, a gidan baya ya wurgata kafin ya shiga mazaunin driver, ya ja motar ya bar Mark ɗin a wajen, shi yasan ta yadda zai yi ya dawo gida tare da tantiran yaran da ya kama. A guje ya figi motar tun bai karisa wajen gate ba yake danna musu uban horn, a zafafe sojojin nasa har suna rige rigen buɗe mishi gate ɗin gidan, da wani irin mahaukacin gudu ya danna hancin motar, sai huci yake kamar wani zaki, yau Rimsha ta kure shi, har zai ce kada ta fita kuma ta saka kafa ta fita, kenan tafi karfin shi ya yi mata magana, ta raina shi kenan, dole yau ya kashe yarinyar nan a cewarsa, dan babu wanda ya taɓa yi mishi abin da ta yi mishi. Dani da ku duk mun san azababben bala'in kishi ne na waƴan can matasan sun taɓata, shi ne yake damunsa, ba wani dan ya ce kada ta fita ta fita, shi ne dai yake ganin ai raina shi ta yi, ya ce kada ta fita ta fita, mu kuma mun san kishin bala'i ne irin nasa. Tun bai kashe motar ba ta fito a guje ta nufi cikin gida, dan tasan yau tashiga ɗari ba uku ba. Kai tsaye bedroom nata ta nufa, banko kofar ta yi tare da murza key ta je ta haye gado tana kuka tare da danasanin abin da ta yi, shi ma dai bai kashe motar ba ya fito a zafafe, cikin zafin nama yake taku ya bi bayanta, wani soja ne ya zo ya kashe mishi motar. Kai tsaye bedroom ɗin nata ya nufa, jin kofar a rufe yasa ya yi baya ya take kofar da karfi, wani irin jijjiga ta yi bata buɗe ba, sake yin baya ya yi ya take ta da karfi sai ga kofar a kasa ta ruguzo, ihu ta kurma tare da miƙewa, ta rasa ina zata sanya ranta, ga kofar toilet nata already ya ɓalle mata shi ranar, wajen ɓuya dai ya kare, yau tashi ga ukunta. Ihu take yi kamar mahaukaciya, a zafafe cikin takun jarumta ya shigo cikin ɗakin, gudu ta fara yi tana ƙokarin neman ina zata ɓuya, Aseef yana can yana barci ya sha allura bai san me yake faruwa ba, bawan Allah duk tsoronsa da allura yau da kansa ya ce ayi mishi, daga nan zaka san bala'in ta kai mishi bala'i. Dai'dai lokacin motar Areef ya danno kai cikin gidan, damkota shi kuma Lion ɗin ya yi, ya jata har zuwa bedroom nasa, a tsakiyar ɗakin ya yi wurgi da ita, belt na wandonsa ya fara cirewa, dan wlh yau sai ya yi mata azababben dukar mutuwa, idan ta yi sa'a ta rayu to, idan kuma ta mutu ita ta ji yo a cewarsa, har lokacin ihu take yi ta kasa magana. Jin ihunta yasa Areef ya karisa haurowa benen da sauri, dama yana haurowa zai zo wajen Lion ɗin ne. Yana shigo ya ga abin da yake faruwa, kai tsaye ɗan uwan nasa ya nufa yana tambayarsa me yake faruwa? Me ta yi mishi? Ko kallon in da yake bai yi ba ya zaro belt nasa tare da nufarta gadan gadan, da sauri Areef ɗin ya tare gabansa yana faɗin. "Sister ki gudu, Lion dan girman Allah kada ka ce zata taɓa lafiyar Rimsha yanzu, wlh zaka iya kasheta har lahira, dan girman Allah ka yafe mata sai zuwa da safe ka yi mata hukunci duk da ma ban san me ta yi maka ba". Ko kallon in da Areef ɗin yake bai yi ba, yau idan bai ga Rimsha ta dai'na numfashi ba, wlh ba zai taɓa jin sanyi a ransa ba, da duka zai kasheta, tun da ita bata jin magana, dan kawai sun yi tafiya ya ɗan sake mata fuska shi ne har take ƙoƙarin kawo raini a tsakaninsu? Ya ce kada ta yi abu ta kama ta yi, wlh babu mai karɓarta yau, sai ta gane annabi ya faku, sau tari dama ɗaukar karamar yarinya yake yi mata shiyasa yake kawar da kansa a kan wasu abubuwa da take yi mishi, bai taɓa ɗaukarta a cikakkiyar babbar mace ba, idan ba ku manta ba a baya duk zaman da suka yi da ita a gidan bai taɓa ɗaga idanu ya kalleta ba sai a ƴan kwanakin nan sanadiyar tafiyar da suka yi ne daya kare mata kallo, a nan ne ya fahimci ta fara girma, kuma hakan yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sanya yake ƙoƙarin hanata kusantar su Areef kamar da, dan kun sani duk da yake Bature shi mutun ne mai kula da addininsa sosai, yana daraja addininsa, wannan dalili yasa yake taka musu birki ya kuma nuna mata ce yanzu ta girma dole ta dai'na zama a jikinsu Aseef kamar da tun da su ba dutse bane, ko yaya suna jin shauki, shi ne ma yasa ɗazun ya daka musu tsawa dan kada ta koma jikin Areef ɗin ta zauna, ita kuma bata ɗaukar hakan kamar wani abin, dan idan baku manta ba, da farko bata yarda ya rungumeta, amma a hankali ya saba mata da hakan, da ta fahimci ba cutar da ita zai yi ba sai ta saki jiki da shi, bugu da kari kuma taga daddynta ya yarda da shi sosai, shiyasa ta sake musu ta ɗaukesu tamkar yayyunta na jini, ga kuma karin yarinta a kanta. Wani mahaukacin tsawa ya dakawa Areef ɗin a kan ya matsa mishi a gabansa ko ya yi mishi illah, kin matsawa ya yi yana faɗin "Rimsha ki gudu". Da gudu ta miƙe zata yi waje, ture Areef ɗin gefe ya yi da karfi tare da damko gashin kanta ya janyota baya da karfi, kafin ya hankaɗata ta faɗi kasa, ihun azaba ta sakar mishi, na gashi ta da ya ja, kokarin riƙesa Areef ya yi amma ina ya kasa, dan yau ran maza ya ɓaci over, baya ji kuma baya gani, almakashi ya ɗauko daga cikin drawer da chemical nasa suke, wurga mata ya yi yana faɗin "Ɗauka ki yanke gashin nan gabaki ɗaga ki zubar". Babbar magana, saboda waƴan can sun taɓa gashin sun kamata da gashin ne za ta yanke? Lallai Lion akwai bala'in kishi na wuce misali. Ta kasa koda motsawa saboda tsananin tsoro da tashin hankali, yanzu gabaɗaya kukanta ma ya dai'na fita, yau taga tashin hankali, bata taɓa tunanin haka Lion yake da zuciya na bala'in fitar hankali ba, lallai ma, kuma a hakan ma saboda ita mace ce yasa bai wani hau ba, dan yasan duka ɗaya kwakkwara idan ya yi mata, ba zata tashi ba, da namiji ne ya yi mishi laifi ai data ga bala'in da ya sha gaban tunaninta. Ganin haka yasa Areef ya juya ya fice daga cikin ɗakin dan yasa in dai Lion ya hau to duk duniya ba mai iya dannarsa, mafita ɗaya, shi ne su yi mishi allura, amma idan ya ce zai tare shi ma zasu yi faɗa ne, zai yi mishi illar a banza, ga shi dama ba lafiya gare shi ba, ko da yana da lafiya ma Lion ya fi karfinsa, idan suka sami ɓacin rana suka yi faɗa shi yake dakuwa dan karfin ba ɗaya ba, kuma yanzu a halin da Lion yake ciki ba zai ma tuna cewa Areef ɗin yana da wani ciwo ba ya tausaya mishi, idan ya tare mishi gaba tsab zai yi mishi dukan mutuwa, ko sun haɗu sun haɗa karfi da Tga basu iya riƙe shi idan ya fusata, alluran dai ita ce mafita. Bedroom nasa ya koma, alluran ya haɗa na barci mai karfi na 30 mins, ɗaya daga cikin alluransa da ake masa time da yake jinya ne, lokacin da ya dawo bedroom ɗin Rimsha ta kasa motsawa har lokacin, shi kuma yana ƙoƙarin naɗa belt nasa zai zaneta. "Ki yanke gashin nan nace!!" Tsawa ya daka mata wanda ya sanyata warwarewa, a sukwane ta ɗauki almakashin da nufin ta fara datse gashin nata, hawayenta har sun kafe dan azaba, hannunta ma da kyar ya iya riƙe almakashin saboda kerma da gabaɗaya ilahirin jikinta yake yi. Shammatarsa Areef ɗin ya yi ya caka mishi alluran a hannu wajen damatsansa tare da zira mishi ruwanta a cikin jikinsa, da yake abune da suka saba yi, sun san yadda suke yi, alluran yana nan ɗan karami da shi, ba zama ka taɓa cewa allura bane, suna amfani da shi wajen kama manyan ƴan ta'addan idan sun shiga yakin sunkuru, da sun yi wa mutun ba zai fi second goma ba zai zube kasa. A fusace Lion ɗin ya juyo ya damko wuyar Areef ɗin da karfi, sai kuma a hankali idanunsa suka rufe alamar barci, yana ƙoƙarin zubawa kasa, duk da ciwon da yake kirjin Areef ɗin bai hana shi tare ɗan uwan nasa ba ya faɗa saman kirjinsa, wash ya furta da ɗan karfi, dan ya ji zafin ciwon nasa, da kyar ya iya kai Lion ɗin saman bed nasa ya kwantar da shi kusa da Aseef kafin ya zauna a bakin gadon yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya. Miƙa mata hannu ya yi a kan ta bashi almakashin da yake hannunta, ba musu ta rarrafo zuwa gabansa ta miƙa mishi, karɓa ya yi yana sake sauke nauyayyar ajiyar zuciya. "Kawo mini ruwa". Ya faɗa yana ajiye almakashin a gefe, da kyar ta iya miƙewa ta nufi fridge dake cikin ɗakin, ruwa ta ɗauko mishi mai sanyi ta kawo, karɓa ya yi tare da buɗewa ya kafa kai, sai da ya shanye dukka kafin ya cire kansa. "Me ya haɗaki da Lion?". Ba ɓoye ɓoye ta gaya mishi, bakin ciki tamkar ya tsinka mata mari, a fusace shi ma ya fara magana "Kina hauka ne zaki fita gidan nan da wannan dare haka? Kin san hanyar zuwa prison ɗin ne? Kin san da wa zaki haɗu a hanya? Da ace Lion bai ganki ba me kike tunanin zai faru? Gaskiya kin yi laifi sosai wlh, ya kamata nima na zane ki, idan ma ya hanaki zuwa ba sai ki kirani a waya ki gaya mini ba, idan kina son lallai sai kinga ƴar uwarta ki, ai akwai hanyoyi da dama da zan haɗa ki da ita wanda ba sai lallai ki take maganar da Lion ya gaya miki ba, to ki sani wlh Lion yana iya kin saka baki a case ɗin ƴar uwar taki dalilin laifin nan da kika yi mishi, me yasa kike son ɓata komai da kan ki ne? Meyasa ba zaki gaya mini ba? Kin taɓa gaya mini ga abin da kike so ban samo miki hanyar da zaki same shi bane?". Girgiza kai ta yi tana hawaye tana bashi hakuri, faɗa ya yi mata sosai a kan kada ta sake yin irin wannan gangancin, duniyar yanzu sai a hankali, tsab yarancan zasu lalata mata rayuwa, yanzu ta je ta yi wanka ta kwanta zuwa gobe ko ta wani hali zai haɗata da Jehan ɗin. Kallon Lion dake kwance ta yi ta kasa motsawa, ya gane nufinta dan haka sai ya ce "Kije babu wani abu, idan ya tashi zai zama normal, zuciyar zata sauka, amma kada ki kara irin wannan kuskuren, sannan kada ki yarda nan kusa ya sake ganin gashin nan naki, dan wlh kika bari ya gani sai ya yanke shi dukka ya zubar, ki kyale shi sai ya huce na kwana biyu, ai wlh kin ma yi muguwar sa'a, na ma kara fahimtar wani abu a tsakaninku, ba dan haka ba Allah yau da sai dai wata ba ke ba, gateman kuma sai dai mu ce Allah ya jikansa, ki sani kuma idan ya mutu nauyin na kanki dan ke kika yi mishi karya kika sanya ya karya aikinsa, sai ki san yadda zaki yi ki shawo kan Lion ɗin kada ya yi mishi hukunci, dan yanzu Lion sai ya fi jin maganarki sama da tawa, je ki yi wanka ki kwanta sai da safe". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi waje dan ya je ya yi wanka ya zo ya duba lafiyar Aseef kafin ya kwanta. Da kyar ta iya miƙewa, zubawa Lion ɗin idanu ta yi yadda yake barci ga fuskarnan a ɗaure tamau tamkar hadari, rai a matukar ɓace, wani irin azababben so da kaunarsa ne yake kara shigarta kamar me, matsowa kusa da shi ta yi, kasa kasa ta fara magana tare da tsugunnawa a kusa da gadon "Kayi hakuri ba zan sake ba, na san nayi laifi sosai, ban ji daɗin ɓata maka rai da nayi ba, amma In Sha Allah ba zan sake ba, ka sani ni koma me ina sonka, kuma ba zan dai'na ba, wannan ita ce kaddarata ni kuma". Ta kai karshen maganar tare da riƙo hannunsa guda ɗaya a cikin nata, ga Aseef kwance a gefensa yana sharara barci. Zubawa yatsun hannun nasa idanu ta yi tana kare musu kallo, kyau iya kyau, sai sheki farcensa suke yi ga su farare tas kamar madara, hannunsa laushi sosai kamar bai taɓa yin wani aiki ba. Ta ɗan jima tana kallon hannun nasa kafin ta sake shi ta miƙe ta nufi waje. A gurguje ta yi wanka ta fito ta shirya cikin kayan barcinta masu kyau, dogon wando ne da riga mai dogon hannu, launin pink color, fesa perfume nata ta yi tare da hayewa gado ta kwanta, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita dan ta gaji, ta wahala ba karya. After 1 day👌 Daddyn Rimsha bai samu damar tashi a jiya ba, sai yau ya taso shi da Tyrone, Tga dai har yanzu yana fama da jinya, ba karya ya wahala a wajen yakar wannan kungiya ta su Areef. Shiri tsab Aseef ya yi cikin wandon jeans baki da polo t-shirt sky blue, ya yi kyau sosai, ya ɗan sami lafiya da kwarinjiki, kiran Akila ya yi a waya ya ce mata ga shi nan zuwa gidansu, dan ba zai iya hakuri yau kwana uku bai ganta ba, ba zai iya cika kwana na huɗu ba, ga shi gobe ɗaurin aurenta, tsabar kuka da zazzaɓin da take yi, sam muryarta baya fita, su Umaisha duk suna a tare da ita, amma ina ko sannu bata iya ce musu, sai aikin gyara Hjy Batula take yi mata, amma ba uhm bare uhm, yau za'ayi mata kunshi na amare, shi kuma Irfan bai wani damu sai ya rinƙa hira da ita ko ya kirata a waya ba, a cewarsa tun da bata da lafiya gara ya kyaleta kawai, hakan yasa baya damuwa da kiranta yake kyaleta. Jin Aseef zai zo yasa ta tashi da kyar ta shiga bedroom ɗin Ammie dan ta sanar da ita, bata yin komai sai da yardan mahaifiyar tata, Aunty, Hjy Batula, Ammie ta samu a cikin ɗakin, sannu ta yi musu kafin ta ce "Ammie ina son yin magana dake". Okey ta amsa tare da miƙewa ta zo ta riƙo hannunta suka nufi waje, har wani jiri baiwar Allah take gani. Bedroom ɗin Abba ta shiga da ita, da yake baya nan suna can shi da Abbi suna nasu shirye shiryen, kun san yadda bikin turawa, da uba da ƴaƴan duk haɗewa suke yi sai ka rasa gane ina iyayen suke ina yaran, to wannan ma haka ne, dan Abba da Abbi dai duk ɗabi'ar tana tare da da su, dan sune manya sun girma sosai a kasar Russia kafin su dawo Naija, so ɗabi'ar ta fi zama a jikinsu sosai. "Akila lafiya?" Ammie ta tambaya, da kyar ta iya gaya mata Aseef ne ya kirata a kan yana zuwa, shiru Ammie ta ɗan yi kafin ta ce "To Akila ba zan hanaki zuwa wajensa ba, amma dai ki san ta in da zaki bi ki fita kada a ganki, kin ga jama'a suna cike, kada ki ja mana magana, kuma ki ce da Aseef ɗin ya tsayar da motarsa a can nesa da gidan nan, wlh duk lokacin da na yi sallah ina rokan miki mafita, Aseef dai shi ne idan na tuna zaki aura hankali yake kwanciya ba Irfan ba, shiyasa bana hanaki kula shi, dan ina ji a jikina kamar da shi za'a ɗaura auren nan gobe ba Irfan ba, amma Allah shi ne masanin gaibu, ba zan taɓa son a baki abin da baki so ba, ki je ki gan shi, amma kada ki jima, ki kuma kwantar mishi da hankali sosai, dan yadda na ganshi kwana huɗu da suka wuce sai da nayi mishi kwallah". Allah sarki babu mai fahimtarka sama da Mahaifiyarka a duniyar nan, uwa ta wuce wasa, babu mai son abin da zaka so sama da mahaifiya, ita ke sadaukar da farincikinta dan ƴaƴanta, uwa baban jigoce ga rayuwar ɗan adam, Allah ka jikan iyayenmu da suka rigamu gidan gaskiya, waƴan da suke raye Allah ka kara musu lafiya, ka kuma bamu ikon yi musu biyayya mu bisu sau da kafa. Rungume Ammie nata ta yi tana ruwan hawaye, ita kaɗai tasan me take ji a ziciyarta, wlh tasan idan aka ce yau an ɗaura aurenta da wanin Aseef shikenan tata tazo karshe. Ɗan raba jikinsu Ammie ta yi tana faɗin "Kije kada su Halima su yi tunanin wani abin muke faɗa da bamu yi magana a idanunsu ba, ki kula dai kada ki bari Abbanki or wani ya ganki, idan kika bari hakan ta faru kin san sauran, komai sai ya lalace miki, zaki haɗu da fushin mahaifinki sosai". Okey ta amsa da shi tare da juyawa ta fice da sauri, bedroom na Akil ta nufa, kayan Umaisha ta sanya, dama na gaya muku a baya idan baku manta ba, da Umaisha da Akila da Rimsha yanayin jikinsu kusan ɗaya, shape nasu ɗaya, dan haka kayan Umaisha sai ya zauna ɗam a jikinta tamkar nata ne dama bana Umaisha ɗin ba, ɗinkin riga da skit ne, kayan sun fita sosai. Bedroom nata ta koma ta ɗauko bayafinta, dan Umaisha bata da mayafi, sai zumbula zumbulan hijabai har kasa, ita kuma ba zata iya saka hijabi ba gaskiya a cewarta, cikin dabara ta ɗauki mayafin bata bari su Umaisha ɗin sun ga me ta ɗauka ba, sai murna suke yi yau ta ji sauki har ta sanya kaya masu kyau, sai fara'a Umaisha take yi, Jelly kam tana kwance shiru kamar wata malamar islamiya, da alama dai malaikun natsuwa ne suka yi mata addu'a. Bata wani kula su ba ta nufi waje tana faɗa musu tana zuwa, bedroom ɗin Akil ɗin ta sake komawa ta ɗauko face mask ta sanya a face nata tare da fesa perfume nasa, akwai mutane sosai a palo, haka ta zo ta wucesu, wasu sun gane ita ce wasu kuma basu gane ba. A harabar gidan ma akwai jama'a amma haka ta ketasu ta wuce zuwa waje, da yake a harabar gidan sai hidima da aikace aikace suke yi, sai basu lura da ita ba, su kuma su Irfan su part ɗin Imran, waje ta nufa, ta yi tafi mai ɗan nisa kaɗan, amma tana iya hango gidan nasu, sannan ta tsaya tare da kiran shi a waya a kan ga in da zai sameta kada ya je kofar gida, okey ya amsa mata. Bata fi minti 10 da tsayuwa ba sai ga shi nan ya danno hancin motarsa, a hankali yake tuka motar, hakan zai sa ka gane yana cikin tsantsar mawuyacin yanayi. Cikin sauri ta buɗe kofar motar ta shiga gidan gaba dan kada wani ma ya ganta, ko yaya Akil ya ganta, Alhamdulila glass ɗin motar ma baka ce, ta kuma yi sa'a ba wanda ya ganta ɗin, ruwa ya ɗauko a roba ya miƙa mata dan ya ga tana haki kamar wadda ta yi gudu, karɓa ta yi tare da cire face mask ɗin face nata, ta kafa ruwan a bakinta, ta sha mai ɗan yawa kafin ta cire ta mayar ta rufe tare da miƙa mishi, karɓa ya yi ya ajiye. Zuba mata idanu ya yi na ƴan mintoci kafin nan ya ce "Heartbeat kin ga yadda kika rame kuwa? Ba zan iya juran hakan ba gaskiya". Ɗago dara daran idanunta na gadon nan ta yi, da ta rame ma sai idanun nata suka kara fitowa dara dara da su over, zuba mishi ido sosai ta yi, shi ma ya rame sosai, na shi ramar ma ya fi nata, duk yana harkitse. "My shagwaɓati hakuri zamu yi, mu fawwalawa Allah komai, In Sha Allah idan mu rabon juna ne Allah zai kawo mana mafita, matar mutun ai kabarinsa ne". Nisawa ya yi kafin nan ya riƙo hannayenta tare da matsowa kusa da ita, zuba mata ido sosai ya yi while ita kuma tana kallon kasa. A nutse cikin sanyin murya ya fara magana "Yanzu da gaske Heartbeat Abba ba zai canza magana ba? Da gaske Abba ba zai bani ke ba? Please ki ce mashi zan yi duk abin da yake so, dan Allah kada ya rabani dake, wlh zan iya mutuwa idan hakan ta faru, please my heartbeat ki ji tausayina, ni ban san menene soyayya ba sai a kanki, ban taɓa yin soyayya ba sai a kanki, tun rana ta farko da prof ya tura mini hotonki nayi bala'in kamuwa da kuanarki, wlh zuciyata ba zata iya jure rashinki ba, ba zan iya ba, ki tausayawa rayuwata, wlh nafi kowa sonki, na fi shi ma Irfan ɗin sonki, please my heartbeat ki rarrashi Abba, kome yake so nayi mashi in dai bai saɓawa Allah ba, to zan yi mashi dan ya bani ke, kin ji ko?". Ya kai karshen maganar yana zubar da kwallah. Hawaye ne suka fara gangaromata daga eyes nata zuwa face nata, ta kasa ɗago kai ta kalle shi, tabbas bata san me yake cikin zuciyarsa ba, amma dai tana da yakinin idan bai same ta ɗin ba, kamar yadda ya faɗa, mutuwa zai yi, ta tabbatar da yana yi mata wani irin mahaukacin so, kuma ita ma a nata ɓangaren tabbas idan ba shi ɗin ta aura ba, zuciyarta zata ita bugawa, shi ne zuciyarta ta aminta da shi, shi ne zaɓinta, bazata iya rayuwa da wani namijin bayan shi ba. Ganin tana hawaye ba ƙaramin ɗaga mashi hankali ta yi ba, cikin sauri ya sake hannayenta tare da ɗago haɓarta suna fuskantar juna, muryarsa har sarkewa yake yi wajen cewa "My Heartbeat please and please ki yi shiru, ki yi hakuri kada ki kara mini zafi a kan zafi, zan iya jure komai amma ban da kukanki heartbeat nawa, wlh hawayenki na bakin ciki, daidai yake da ana caka mini wuƙa a kahon zuciyata, zafi nake ji my heartbeat idan kina kuka, ni zan iya ɗaukar komai ban da kukanki, ki daina please". Yana magana yana hawaye shi ma. Cikin kuka ta ce "My shagwaɓati kukan ka yafi nawa zama tashin hankali da bala'i a gare ni, ka daina dan Allah, wlh idan kana hawaye zuciyata zata iya bugawa ka ji?". Bai san time da ya jawota jikinsa ba, wani irin shock suka ji su dukkansu biyu, dannewa ya yi tare da fara rarrashinta cikin salo da dabara tare da natsuwa, tamkar kara ingiza ta yake yi, sai kara kukan take yi, ta lafe a kirjinsa tana jan hanci tare da shaƙar daddaɗar kamshin perfume nasa mai kwantar mata da hankali. Hannu yasa ya ɗago haɓarta daga saman faffaɗar kirjin nasa, ya zama suna fuskantar juna, goge mata hawaye ya shiga yi yana mai cigaba da rarrashinta, kukanta babbar bala'i ce a gare shi, zuciyarsa ba zata ɗauka ba. Ganin taki daina ruwan hawayen ne yasa ya ranƙwafo kanta sosai tare da fito da harshensa ya fara lashe hawayen nata, cak ta tsaya da kukan nata sakamakon wani irin baƙon yanayi da ta ji na sanya harshensa a kan fuskarta da ya yi. Shi kuwa tas ya lashe hawayen nata kafin ya ɗago da brawn eyes nasa ya sauƙesu cikin tata fararen idanun. Da kyar ya ƙaƙalo murmushin dole dan ya sanya ta farinciki, zuba mishi ido ta yi, ba ko kyaftawa, shi ma dai zuba mata dara daran idanuwansa ya yi yana mai kare mata kallo. Sun ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ya matso da fuskarsa daf da tata sosai ta yadda suna iya jiyo numfashin juna, can kasan maƙoshinsa da kyar ya iya furta "Can i kiss you one my heartbeat?". Wani irin faɗuwar gaba ta ji jin yadda ya yi maganar, ji take yi tamkar rabuwa da shi zata yi, ta kasa magana, ta dai zuba mashi ido kawai. Ganin bata yi magana bane yasa ya matso da lausasan laɓɓansa zuwa saman tata, wani dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali, yayin da shi kuma ya sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, a hankali cikin natsuwa ya haɗe bakinsu ya shiga kissing nata. Sumar zaune ta yi mishi, ko da sunan wasa ba wanda ya taɓa kissing nata, bata ma san ya ake ji ba idan aka yi kiss sai yau, tana dai karance karance novel nata, da kalle kallen film, amma bata taɓa ji a zahiri ba. Shi kuwa kara jawota jikinsa ya yi tare da rungumota da kyau da kyau, kissing nata yake yi babu kama hannun yaro, cikin dabara ya zame mata mayafin kanta tare da ɗankwalinta baki ɗaya, shi ma bai taɓa yin kiss ba, bai san ya ake ji ba sai yau, kuma yau ɗin ma ya haɗu da ya yi wa macen da ya fi kauna a duniya, wow abin ba'a magana. Shafa kyakkywar gashin kanta da ya sha gyaran biki ya shiga yi yana mai kara matseta a jikinsa bakinsu na a cikin na juna. Sosai ya yi kissing nata, ita kuma ta yi mashi sumar zaune, duk jikinta ya mutu, ko motsin kirki ta kasa yi, bata ankaraba sai jin sauƙar hannunsa ta yi a saman breast nata, cikin sauri ta kwace bakinta tare da ja baya daga jikin nasa tana mai laluɓar ɗankwalinta. Idanunwansa sun yi jawur, murya na rawa ya ce "My heartbeat lafiya kuwa? Me yasa zaki hanani?". Shiru ta kasa yi mishi magana, sai faman ɗaura ɗankwalinta take yi, tanayi tana hawaye, ji take yi kamar shikenan zata rabu da shi. Tana ƙoƙarin mayar da mayafin nata ya yi saurin riƙewa yana faɗin "My heartbeat talk to me now". Sai a lokacin ta ɗago idanuwanta wadda suke cike tap da ruwan hawaye, ga shi wasu kuma suna zuba mata a saman face nata, wani na bin wani. "Ya subhanallah, Heartbeat me ya faru kuma kike sake yin kuka haka? Saboda na yi kissed naki ne? To idan saboda haka ne ki yi hakuri, na tuba, bazan kara ba, kin ji ko? Please ki daina kuka". Kin yi mishi magana ta yi, da sauri ta sakin mishi mayafin tare da fita daga cikin motar, da gudu ta nufi gida tana sakin kuka mai sauti, tasan ko zata mutu Abba ba zai canza magana ba, dole gobe a ɗaura aurenta da Irfan, ga shi kuma ta zo ta yarda Heartbeat nata ya yi mata kiss, yanzu me makoman hakan kenan? Taci amanar yaya Irfan ko dai yaya?. Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun. Cikin sauri da zafin nama shi ma ya fito daga cikin motar, hannunsa na riƙe da mayafinta da ta bar mishi. Kafin ya fito har ta shige ciki gida, kifa kansa ya yi a jikin motar yana kuka tare da dana sanin kissed ɗin nata da ya yi, a tunaninsa hakan ce tasa ta gudu, kuma hakan ce ta sakata kuka sosai. Ya jima a wajen ya kasa motsawa, banda ruwan hawaye babu abin da yake yi, lokaci guda duk ilahirin jikinsa ya yi zafi jau alamar zazzaɓi, zuciyarsa tamkar zata fashe, sai da ya kwashi good 30 mins a haka, da kyar ya iya lallaɓawa ya shiga cikin motar. Wayarsa ya ɗauko ya fara kiran number ta, dan ya rarrasheta ta yi shiru, yasan halinta sarai, yanzu tana can tana kuka, ba zai iya tafiya ba idan har bai rarrasheta ta yi shiru ba. Sau uku yana kiranta bata ɗauka ba, sai a na huɗun ne ta ɗauka, ban da kuka babu wani sauti dake fitowa daga cikin wayar, dafe kansa dake barazanar tarwatsewa ya yi, zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri, da kyar yake fitar da numfashi mai zafin zazzaɓi, su dukkansu biyu sun kurɓi gubar soyayya, hawaye babbiyu yake zuba mishi daga idanunsa, ya kasa magana, ita ma ta kasa magana, dukkansu sai kuka suke yi wa juna,..... To fa, waye kenan zai rarrashi ɗan uwa? HEARTBEAT+ HEATHER ƴan auta kenan, kuma shagwaɓaɓɓu, bugun zuciyar family'ns guda biyu, sanyin idanunyar mutane da dama, BABBAR MAGANA akwai kallo da. ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ *Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta* 💋Dedicated to My comments section groups people's🌹 E55-56💋 Jin irin sautin numfashinsa dake fita ta cikin wayar ne yasa ta tsagaita da dukan da take yi, a ruɗe cikin tashin hankali ta ambaci sunansa, shiru ya kasa amsawa, sake kiransa ta yi hawaye wani na bin wani a fuskarta, tana kwance a saman bed ɗin Akil, nan ma shiru, sau uku tana kira bai amsa ba, dan ba zai iya magana ba. A tsananin razane ta miƙe zaune tare da dirowa kasa ta nufi waje, tamkar wata zararriya haka ta nufi waje babu ko mayafi a jikinta, ƴan biki suna ta hidimar gabansu, sai aikace aikacen girke girke da sauransu suke yi, haka ta keta mutane ta nufi waje. A guje ta nufi motar tasa, ya kifa kai da jikin steering motar yana wani irin numfashi wanda da ka ji kasan da kyar yake fitar da ita, a tsananin tashin hankali ta buɗe motar ta shiga, sunansa ta rinƙa ambata Heartbeat! Heartbeat, amma ina ya kasa amsawa, jijjiga shi ta fara yi, jin irin azababben zafin da jikinsa ya yi yasa ta kara tsorata sosai tare da yin yunkurin ɗago kansa daga jikin steering dan ta kalli face nasa. Tana ɗago shi ya sake mata jiki ya kwanta a saman kafaɗarta yana fitar da numfashi mai tsananin zafi, girgiza kumatunsa ta fara yi tana ambatar sunansa, ina ko motsin kirki baya yi, ban da wannan numfashin da yake fitarwa babu wani abin da zaka ji a tattare da shi, wayar dake hannunsa ta karɓa dan ta kira ɗaya daga cikin ƴan uwansa su zo kada ya mutu. Kash wayar da akwai password a jikinta, tamkar zuciyarta zata fashe ta fito waje haka take ji, cikin fitar hayyaci ta fara lalauɓar number Imran a wayarta da ta fito da ita, har lokacin ko motsawa bai yi ba. Bugu ɗaya ta yi wa Imran ya ɗauka, kuka ya hanata wani maganar kirki. "Yaya Imran ka zo, kazo Heartbeat zai mutu". "Akila ki natsu ki yi mini magana, na zo ina kuma?". Da kyar ta iya cewa "Kazo waje, yana waje". Daga haka ta katse kiran ta cigaba da ambatar sunansa. Tana kashe wayar sai ga shi ya fito da sauri, nufo motar tasu ya yi, cikin sauri ya buɗe kofar ɓangaren da take, ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin abin da yake faruwa, ina ai idan wani abin ya sami Aseef a dalilin familynsu ya san sun shiga uku da Lion, dan ba zai taɓa ɗaukar wannan kaddara ba, shi da likitoci ma suka tabbatar mishi da Aseef ɗin ya mutu a baya, amma ya kafe ya ce sam ba za'a binne shi ba, ba wanda zai sanya mishi ɗan uwa a rami, bare kuma yanzu Aseef ya mutu sanadiyar AKila, ai wlh duk sai Lion ya kashe su har lahira, idan ma bai haɗa da mai gadi da kowa da kowa ba, ai duk wanda ma ya zo bikin nan sai ya mutu. Fita ya ce ta yi bari ya duba Aseef ɗin, da kyar ta iya raba jikinta da na shi, ta kwantar da shi a jikin headboard na kujerar ta fito, sai kuka take gwanin ban tausayi, shi ga cikin motar ya yi yana ambatar sunansa, amma ina ba zai iya amsawa, ya rigada ya kurɓi gabar soyayya. "Akila ki koma cikin gida bari na mayar da shi gida dan ayi gaggawar duba lafiyarsa kin ji?". Durkushewa a kasa a wajen ta yi tana kuka kamar ranta zai fita, cikin kuka ta ce "Yaya Imran dan Allah ka tafi da ni, wlh ba zan iya zama ban san halin da yake ciki ba". Tana magana tana dafe kirjinta da yake yi mata tsananin ciwo tamkar zata mutu. "A'a Akila ki je gida, idan na tafi dake abin ba zai yi mana kyau ba dukkanmu, ke dai ki je gida, baki san waye kike tare da shi ba ne shiyasa kike cewa na tafi da ke, so ki koma kawai". A gudu ta miƙe ta nufi gida, binta da kallo ya yi yana matuƙar tausaya musu, ya rasa ya zai yi, tunani yake a kan wlh dukkansu biyu zasu iya mutuwa fa idan ba'a duba wannan lamari ba. Fitowa ya yi daga cikin motar ya dawo ta ɓangaren da Aseef ɗin yake ciki, ya buɗe kofar, da kyar ya iya fito da shi ya mayar da shi gidan baya, sannan ya shiga mazaunin driver ya tada motar, da gudun gaske ya figita dan su isa gida da wuri, idan ba haka ba daga yanzu zuwa ko wani lokaci suna iya rasa Aseef ɗin bakiɗaya. Horn ɗaya ya yi Donald ya buɗe mishi gate ɗin, dan gateman kam yana gadon asibiti bai farfaɗo ba, ciki ya danno hancin motar, yana kasheta ya fito da sauri ya nufi cikin gida, ya kuwa yi sa'a ya sami Areef da daddyn Rimsha a palo suna hira, Rimsha kuma ta tafi school bata nan daddynta ya iso, sai dai ta dawo ta same shi kawai, Jehan tana ɗaki tana barci. Cikin tsananin tashin hankali ya ce da Areef "Ina Lion?" Miƙewa Areef ɗin ya yi yana kallonsa da mamaki na lafiya?. Lion baya nan ya fita neman Aseef ɗin ne, dan ya yi ta kiran numbersa bata shiga, suna zaune suka ji su coper suna ta daka haushi, hakan yasa Lion ɗin yasan Aseef baya lafiya, shi ne ya yi ƙoƙarin neman numbersa network babu kyau, bai same shi ba, wannan dalilin yasa ya fita nemansa. Areef na kokarin tambayarsa ko lafiya ya shigo a birkice haka, sai suka ji tsayuwar motar Lion a harabar gidan, da sauri Imran ɗin ya juya, dan ba zai gayawa Areef me ake ciki ba, yasan ba zai iya ɗaukar Aseef ba saboda ciwonsa, dan haka sai ya nufi wajen kawai. Da sauri suka rufa mishi baya, Lion na shigowa shi kuma yana fita, karo suka yi, baya yaɗan yi yana gaya mishi ya zo ya fito da Aseef daga cikin mota, ya yi sauri dan yana bukatar taimakon gaggawa, ɗan zaro idanu ya yi, ya ma kasa tambayar me ya sami ɗan uwan nasa, dan ba zai iya jin mummunar labari a kan TRIPLETS nasa ba, bai shiryawa hakan ba, kuma ba shi da wannan juriyar gaskiya. Cikin sauri suka rankaya zuwa wajen motar, a zafafe Areef ya buɗe kofar ɓangaren da Aseef ɗin yake ciki, dan jikinsa har tsuma take yi yana son ya ga menene ya sami ɗan uwansa. Yana zaune kansa na jingine da jikin headboard na kujerar, tamkar babu rai a jikinsa, da alama ya suma ne, ga kuma mayafin Akilar a hannunsa bai saki ba, ya riƙe gam. Areef zai taɓa shi Lion ya dakatar da shi tare da kai hannu dukka biyu ya tallaɓo shi, Imran kam baya ya yi yana jiran ya ga saukar aradu kawai, dan kuwa yasan akwai yaki yau ba kaɗan ba, wani abu ya sami Aseef dalilin AKila, tab aikuwa Akila zata mutu a tunaninsa. Ciki Lion ya wuce da shi bayan ya saɓa shi a kafaɗarsa, har lokacin mayafin Akilar na hannunsa, saman bed nasa a bedroom nasa ya kwantar da shi, kallon juna Imran da Areef suka yi, yana ƙoƙarin tambayarsa menene ya sami ɗan uwan nasa, sexy voice ɗin Lion ya katse shi da cewa "Bani ruwa Areef". Da sauri ya nufi fridge. Roba ɗaya mai sanyi ya ɗauko ya dawo ya miƙa mishi, karɓa ya yi tare da buɗewa ya tarfo a hannunsa, a fuska ya shafawa Aseef ɗin, shiru bai motsa ba, sake tarfowa ya yi ya shafa masa, nan ma shiru, sai a karo na uku ne ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali, sai kuma kuka ya biyo baya, dukkansu zuba mishi idanu suka yi suna kallon ikon Allah. Kuka yake yi sosai, idanuwansa a datse gam ya fara sambatu. "Ki ce da Abba wlh zan iya mutuwa, ba zan iya jurewa ba, ki yafe mini dukkan abin da nayi miki a rayuwar da muka yi tare, ni nasan yau ba sai gobe ba zan rayu ba, mutuwa zan yi, zuciyata tana yi mini zafi sosai, mutuwa zan yi my heartbeat, ba zan rayu ba, idan na mutu ki rinƙa yi mini addu'a kin ji? Kuma kada ki manta dani, kin ga dai kin yi mini alkawarin ba zaki rabu da ni ba ko? Kuma ba zaki manta da ni ba, to dan Allah kada ki manta da ni, ki cika alkawari". Juyowa Lion ya yi da kallonsa zuwa kan Areef while shi kuma Areef ɗin ya juya yana kallon Imran, shi kuma Imran daddyn Rimsha yake kallo. "Me ya sami my pleasure?!" Lion ya tambaya cikin tsawa. A tare dukkansu suka dawo da kallonsu kan shi. Jin muryar Lion ɗin yasa Aseef ɗin dakatawa daga sambatun da yake yi, a hankali ya waro idanuwansa da suka riƙiɗe suka yi ja sosai na wuce misali, da kyar ya kai hannunsa ya riƙo hannun Lion ɗin, jin ya kama hannunsa yasa ya juyo da kallonsa kansa. Zuba mishi idanu ya yi kafin ya kankame hannunsa cikin na shi, "My pleasure what is happening? What is wrong with you? Who break your heart?" Cewar Lion ɗin kenan. Ba ɓoye ɓoye ya gaya mishi komai, tun farkon ganinsa da Akika har yau da suka yi sallamar bankwana, daga karshe ya rufe da cewa "Ba zan iya rabuwa da ita ba Lion, mutuwa zan yi yau na sani, aurenta za'a ɗaura da wani, ba zan iya juran hakan ba, burina a duniya bai wuce na aureta muyi rayuwa a tare ba, shi ne burina na karshe kuma zan mutu da shi ban cika ba, zafi zuciyata take yi mini sosai, ku yafe mini duk abin da na taɓa muku a rayuwarmu, ni na san ba zan tashi ba, ina ji a jikina mutuwa zan yi, zafi nake ji my TRIPLETS, ban san ya zan yi ba, jikina ciwo yake yi mini, amma dan Allah idan na mutu, in kun zo binne ni ku sakani da mayafin Heartbeat data bar mini, shi ne abinta ɗaya kawai da nake da shi, dan haka ku rufeni a rami da shi". Yana magana yana tari tare da fitar da wani irin numfashi mara daɗin ji na zafin zazzaɓi. Duk taurin zuciya irin na daddyn Rimsha sai da ya yi hawaye, Imran kam tuni dama hawaye ya wanke mishi fuska sosai. A ɓangaren Akila kuwa, bata kai ga shiga gida ba Abba ya ganta, ganin haka yasa ya ce da Abbi ya taro dukka mazan gidan yau za'a ɗaura auren nan, dan kuwa ya ga komai, ya ga motar Aseef, shiyasa dan gudun abin ya zama matsala ya san halin Turawa yanzu Aseef yana iya ɗaukarta su tafi kasarsu ma ko kuma ya biya bukatarsa da ita, shiyasa dan gujewa hakan ya ce a ɗaura auren yau kowa ya huta, bai san cewa Aseef kam soyayyar gaskiya yake yi mata ba, tsakani da Allah yake sonta babu wasa ko kaɗan, so ba zai taɓa kwanciya da ita ba tare da aure ba, lokacin da yake krista ma bai yi zina ba, baruwansa da mata, yanzu da ya musulta ya san girman Allah ba zai taɓa aikata hakan ba. Lokacin da ta samu labarin Abba ya ce yau za'a ɗaura aurenta, a haukace ta nemo wayarta ta fara kiran number Aseef ɗin, sai kuka take yi. Sau uku ta kira bai ɗauka ba dan wayar ya barta a mota, number Imran ta kira, bugu ɗaya ya ɗauka dan ya ji tana lafiya ne ko yaya, saboda shi ma bai cire rai akan dole sai ta cutu ba, hakan ma yasa ya ɗauki kira, sai kuma ya yi rashin sa'a wayar tasa volume tata a kure, harta Aseef ɗin dake kwance yana iya jiyo komai da ta faɗa. A tsananin ruɗe ta ce "Yaya Imran zan mutu, yaya Imran ka taimake ni, Abba ya ce yau za'a ɗaura auren, ya ce yanzu ba sai anjuma ba, wlh mutuwa zan yi, ka haɗani da Heartbeat zan yi magana da shi wata kila shi ne zai zama magana ta da shi ta karshe kenan a duniya, dan nasan mutuwa sanyi, dan Allah....." Diff ya kashe wayar ba zai iya bari ta karisa maganar ba, zuciyarsa ba zata iya ɗauka ba. Shi kuwa Aseef yana jin abin da ta ce hankalinsa ba karamin kara tashi ta yi ba, nan take ya fara murkusoso tamkar wanda ake zarewa rai, ya kankame hannun Lion a cikin nasa, ganin hakan yasa Lion ɗin ya ɗan danne shi ya fara karanto mishi kalmar shahada dan yasan duk idan rai ta zo fita haka bawa yake yi, so ba zai so ɗan uwansa ya tafi ba tare da kalmar shahada a bakinsa ba, gara kome yake ji ya danne ya bashi kalmar shahadar zai fi dan hakan ne cikakkiyar soyayya kenan. Areef kam ganin abin yake tamkar mafarki ne, dan haka ya kasa motsawa daga in da yake tsaye, a hankali Aseef ɗin ya fara karɓar kalmar shahadar, da kyar ya kai na farko ya sake farowa, sai karanto mishi Lion ɗin yake yi ya ɗan dannesa kaɗan. Bai kai karshen kalmar shahadar ta biyu ɗin da yake karanto mashi ba, ya yi shiru diff tamkar an ɗauke wutar nepa, rai ya yi halinsa. Wani irin kururuwa Areef ya kurma tare da yin kan gadon a zafafe yana faɗin "No Aseef no, kada ka mutu, ka tashi, na yi maka alkawarin ko raina zan bada domin cika maka burinka na auren Heartbeat naka, ka tashi, ba zan iya jure rashinka ba". Yana magana yana jijjiga gawar Aseef ɗin da iya karfinsa na karshe. Mikewa Lion ya yi ya fice daga cikin ɗakin da sauri, domin zuciyarsa ta kasa jure ganin abin da yake faruwa, motarsa ya je ya shiga, da kansa ya tuƙa ya fita a gidan da wani mahaukacin gudu, da alama ya fita a hayyacinsa sosai, Mark ya yi ƙokarin karɓa mishi tukun dan ya dawo da Rimsha yanzu, amma ina bai bi ta kan kowa ba ya figi motar ya yi waje. Da sauri Imran da daddy suka yi kan gadon suna ƙoƙarin jan Areef ɗin baya dan ya dai'na jijjga gawar Aseef ɗin kada ya yi mishi illah. Idonsa ya rufe, baya ji kuma baya gani, shi dai kawai ɗan uwansa ya tashi, bai san suwaye ne suka riƙe shi ba kawai ya yi watsi da su tare da kurma wani irin mahaukacin ihu tamkar kururuwar maƴinwacin zaki, da karfi karfi ya cigaba da danne kirjin Aseef ɗin yana ambato sunansa tare da faɗi kada ya mutu ya tashi. Tamkar zautatce haka Areef ya zama a wannan rana. Duk abin da yake faruwa Tyrone ya sani, dan haka sai ya kira Tga a waya ya sanar da shi Michael ya mutu, cikin ƙanƙanin lokaci labarin ya fara bazuwa, duk sojijin dake gidan sun samu labarin. A yau family'n William jacop sun ga matsanancin tashin hankali na kin karawa. John ya yi suma sau ba adadi da suka samu labari ta bakin Tyrone, dan ya san me yake faruwa, shi ne ya sanar da Tga, shi kuma ya sanar musu, Jay kam tun da ya zube akan gwiwowinsa a tsakiyar palon kasa bai kara motsawa daga wajen ba, shin ko yana raye ko shima ya mutu, Allah masani, TGA kuwa duk taurin zuciya irin tasa yau sai da ya yi kwallar da ta kasa tsayawa, sun ki faɗawa daddy abin da yake faru, domin sun san idan ya ji labari, to fa tabbas za'ayi gawa biyu, Josephine kuwa lokacin da ta samu labari karamin hauka ta yi masu wadda sai da Areef ya sanya aka rufeta a ɗaki, lokacin da Rimsha ta dawo daga school ta sami labari da yake shabiyu suke dawowa yanzu, ta yi suma ya kai sau uku saboda tsananin tashin hankali, wannan bala'i da me ta yi kama?, Imran ma kuka ya sha tamkar ƙaramin yaro. A ɓangaren daddyn Rimsha kuwa, ai kusan ya fi kowa hauka, domin idan ba ku manta ba, kusan za'ace ya fi su Areef shaƙuwa da Aseef ɗin a yanzu, idan baku mance ba komai a tare suke yi, hakan tasa sau biyu yana suma, ya yi kuka har idanunsa suka kumbura suka yi luhu luhu, ga shi sun yi jawur tamkar wuta, Jehan da bata san shi ba ma ta zubar da kwallah ganin halin da jama'ar gidan suka shiga. Lion kuwa tun da ya sa kafa ya fita daga gidan bai kara dawowa ba, sai jiransa suke yi ya dawo ayiwa Aseef sutura a kai shi makwancinsa, amma shiru, sun kira wayarsa har sun gaji a kashe, sosai hankalin Areef ya tashi na rashin samun Lion ɗin a waya, tunani ya fara yi kada ace wani abin ne ya same shi fa, domin kuwa da kansa ya tuka mota ya fita daga gidan, kuma da alama baya cikin hayyacinsa time da ya fita. Mukoma baya kaɗan dan jin ya akayi jenan ta dawo gidan, mu koma jiya kenan da za'a yanke mata hukunci. Lokacin da Lion ya tashi daga barcin wannan allura da Areef ya yi mishi, ya ɗan ji komai ya ragu, zuciyar ta sauka, amma fa abin yana ransa, sai dai dama idan aka yi maka laifi, in baka yi hukunci a lokacin ba, to kana iya yafe lafin dan abin ya ɗan sauka, shi ma hakan ce ta faru da shi, toilet ya nufa ya yi wanka kafin ya fito ya shirya cikin kayan barcinsa ya zo ya kwanta, ba jikawa ya yi barci na gaskiya ba na allura ba. Washegari da safe Rimsha ta shirya zuwa school, kamar kullum Mark ne ya kaita, kwata kwata bata haɗu da Lion ba, shi ma kuma bai zauna ba, tun asuba ya fita zuwa Abuja, sai karfe 11 ya dawo, Areef kuma ya tafi court dan hukuncin da za'a yankewa Jehan. Da misalin karfe 12:30, Rimsha tana tsaye a bedroom ɗin Lion tana gyara mishi bed nasa, ba jimawa ta dawo daga school, ko abinci bata ci ba ta hau wannan gyara, tana ta aikintaTv dake manne a bango yana magana, labarai ake yi, ta kasa kunne tana jin abin da suke faɗe duk da bata ganinsu aikin da take yi kawai take kalla, tamkar saukar aradu yaka ta ji ana faɗin hukuncin da aka yankewa Jehan a labaran, wato hukuncin kisa ta hanyar rataya, hakan yasa ta yanke jiki ta faɗa saman bed ɗin da take gyarawa, saboda tsantsar tashin hankali, a lokacin Lion ɗin yana zaune saman sofa yana latsa laptop, shi abin ma mamaki ya bashi, ta ya ya za'ayi irin wannan shari'ar haka? Abu sai kace wasu marasa ilimi, amma bai wani damu ba, shi bincike ma yake yi akan wanda Jehan ɗin ta kashe, a nan ne kuma ya gano gaskiyar cewa ABUBAKAR SALAHUDDEEN shi ne mai gidan wanda ya kamo daga clubs ɗin nan, wato wanda Mark yake horarwa yanzu, ABUBAKAR SALAHUDDEEN shi ne ya basu contract na kashe daddyn Rimsha, wanda ya kamo babban yaron Abubakar jaja ɗin ne, babbar magana, Jehan ya kashe wanda ya yi yunkurin tarwatsa musu family koma a ce ya tarwatsa, ta kashe shi bata san waye shi ba, lallai idan Allah ya tashi kama bawa baya gaya mishi ga ta in da zai bi ya kama shi, yanzu shi Abubakar kafin ya rasu, lokacin da yake cin duniyarsa, idan aka ce mishi ƴar cikin Nawazudden ce zata kashe shi, wlh ba zai yarda ba, dan yana ganin ya fi karfin Nawazudden ma bare ƴarsa, amma da Allah ya tashi kama shi, sai ya haɗa shi da ƴar makiyinshi, shi ya santa, amma ita bata san shi ne ya tarwatsa musu gida ba, ta dai san abokin takarar mahaifinta ne, bayan haka batasan wani abu ba, bata san yana da alaƙa da mahaifinta ta wata fuska bayan siyasa ba, Allah mai iko, ga shi ta ɗauka musu fansa cikin rashin sani. Ganin wanda ta kashe shi ne ya tarwatsa musu gida yasa Lion ya ciro wayarsa ya kira His excellency, cikin natsuwa ya sanar da shi, ya sanar da president na Nigeria yana bukatar court ta wanke Jehan duniya kowa ya gani, bayan haka ƴan'sandan da suka ɗauketa su dawo mishi da ita har cikin gidan nan kamar yadda suka ɗauketa. Haka kuwa aka yi, duk abin da ya bukata an yi mishi, dan kakan nasa yasan jikan nasa baya yanke hukunci da kai haka kawai, duk abin da yake yi yana tsawaita tunani da bincike, kuma a kan gaskiya yake aiwatar da komai, hakan yasa a ka wanke Jehan daga idon duniya kamar yadda suka yi mata sharri, sai Allah yasan waye mai tsara musu magana, nan take suka juya maganar da cewa ai ba Jehan ba ce ta yi kisan, kuskure a ka samu, Jehan ta je wucewa ne a lokacin ta taka sahun ɓarawo, dan haka wanda ta yi kisa daban, ana nan ana bincike za'a nemota, ita kuma Jehan court ta wanketa tare da bata hakuri na abin da ya faru, daga karshe court tana kara jinjinawa Nawazudden tare da yi mishi fatan samun aljanna, nan take duniya ta ɗauki zancen gaskiya ne, kowa ya dai'na ganin laifin Jehan, ƴan'sanda mota uku ne suka ɗaukota zuwa gidan Lion ɗin, da mutunci suka sauketa suka juya. Suna sauketa Areef ya iso wajen da matarsa shi da Donal, fita ya yi daga cikin motar bayan ya sa Donal ta taka birki, cikin sanyin murya ya ce mata su shiga cikin gidan Rimsha tana can tana jiranta, harara ta wurga mishi kafin ta wuce gaba abinta, ɗaya daga cikin sojojin ne ya buɗe musu gate, lokacin Rismha tana sume kwance saman bed ɗin Lion. Bedroom ɗin Rimshar Areef ya rakata, ganin bata ciki ne yasa ya ce "ki zauna bari na duba miki ita a bedroom ɗin Lion", ko sannu bata ce mishi ba ta samu waje ta zauna abinta tana wani kwaɓe fuska. Lokacin da ya shigo bedroom ɗin Lion ɗin, shi kuma ya miƙe daga saman sofa ya nufi toilet, ya yi mamakin ganin Rimsha a kwance a gado, shi a ɗaukarda barci take yi, sai da ya matso kusa da ita sannan ya san ba barci take yi ba suma ta yi, jin saukar ruwa a toilet ya sa ya gane Lion yana ciki, fridge ya nufa ya ɗauko ruwa mai sanyi da zuba mata ta fuska, duk a gajiye yake, jikinsa har ciwo yake yi mishi, ya sha fama ba kaɗan ba, kullun yana zarya tsakanin prison da gida, wani lokaci ma da daddare, Alhadulillah dai yanzu komai ya wuce ai. Yana shafa mata ruwan ta farka a tsananin razane tana ambatar sunan Jehan, riƙota ya yi yana faɗin "Our Queen ki natsu, baby ta dawo tana ɗaki". Zuba mishi ido ta yi tana jin abin kamar a mafarki, jin motsin Lion yana fitowa ne yasa ya saketa dan baya son duk wani abin da zai kawo mishi matsala tsakaninsa da ɗan uwansa, tun da ya lura azababben kishi ɗan uwan nasa yake yi idan suka taɓata, sai ya fara ja baya da ita, kuma ko kaɗan bai ga laifin Lion ɗin ba dan ya yi kishj, domin kuwa haka suke dukkansu uku, shi ma yanzu misali idan Lion ya taɓa Jehan gaskiya zai ji babu daɗi, so dan haka shi ma gara ya kiyayewa ɗan uwan nasa matarsa dan shi ya rigada ya bashi ita. Ta yi mamkin irin saketa da ya yi tare da ɗan matsawa baya kaɗan daga kusa da ita, ganin Lion ya fito ne yasa ta fahimci dalilin sakin nata da ya yi, kallo ɗaya ya wurga musu ya kawar da kansa kafin ya wuce zuwa dressing room abinsa, daga kallo ɗayan ba kari. "Zo muje ki ga baby ita ma tana ɗaukin ganinki". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya yi gaba, da sauri ta diro kasa ta bi bayansa, bakinsa ɗauke da sallama ya shigo cikin bedroom ɗin. Da gudu Rimshar ta tafi ta rungume yar uwarta tana kuka, ita ma runguneta ta yi suna jin abin kamar a mafarki, shi kam tsayuwa ya yi ya zuba musu idanu yana kallonsu fuskarsa ɗauke da fara'a, yana jin daɗin ganin irin tsantsar farincikin da suke ciki, abin ba'a magana, mai saurin kuka ma sai ya zubar musu da kwallah. Rimsha an sha kuka kamar ba gobe, sai rarrashinta Jehan ɗin take yi tana goge mata hawaye. Cikin zolaya ya ce "Au baby ashe kin iya rarrashin mutun? Wato ni ne kike yi wa wannan kallo na up and down ɗin ko?". Harara ta watsa mishi bata kula shi ba. Dukar wasa Rimsha ta kai mata a kafaɗa tana faɗin "Ki dai'na hararar mini yaya na gaya miki, idan ba haka sai mun cire idonki ɗaya". Guntun tsaki ta ja tare da miƙewa ta nufi toilet abinta ta barsu a wajen, dawo da kallonsa kan Rimshar ya yi yana faɗin "Me kika ce mata? Wai ku ba zaku dai'na magana da yaren nan naku da bana ji bane?". Murmushi ta sake idanunta ɗauke da sauran ruwan hawaye ta gaya mishi abin da ta ce wa Jehan ɗin, murmushi shi ma ya yi kafin ya ce "Ni kam tana burgeni sosai idan tana wannan tsare gidan nata, haka idan tana faɗa ba karamin burgeni take yi ba, ina jin daɗi sosai, ki kyleta zata sha tsokana a wajena ba kaɗan ba ai, tun da na san me bata so, bari ma uncle ya zo gobe zaki ga abin da zan yi mata, da idonta irin wanda nake so a wajen". Dariya Rimsha ta yi, wannan wai ya zageta kenan, wai da idonta irin wanda yake so, kai Areef duniya. Haka suka kasance cikin farinciki, wunin wannan ranar dai cikin tsantsar farinciki suka wuni, ko palo Jehan bata leƙa ba, tana bedroom ɗin Rimsha tana kudundune cikin bargo abinta, tana faman sauke gajiya da wahala bayan ta yi wanka ta ci abinci kenan, ta sha barci kamar ba gobe dan ta tsallake rijiya da baya wlh, Rimaha kuwa tana fita ta kaiwa Lion abinci da sauransu, da ta gama zata dawo wajen ƴar uwarta su zauna, duk da ba hira suke yi ba amma ta fi son ta ganta tare da ita, idan baku manta ba, Jehan bata da yawan magana, shi ne yasa basu yin wani hira, shiru suke zama kamar kurame, sai idan Rimshar ta gaji ne ma zata jefo mata tambaya ɗaya biyu, wani lokaci ta amsa, wani lokaci kuma sai ta ce "Wai ke Rimsha ba zaki bar bakinki ya zauna shiru bane? To idan ke baki gaji da tambaya ba, ni na gaji da bada amsa, dan haka ki kyaleni, idan kina cigaba da takura mini zan kai miki duka gaskiya!". Sai dai ta yi dariya ta yi shiru, dan idan da sabo ta saba da Jehan ciki da bai, tsab ta san halinta, bata son yawan surutu kamar daddy da Gwaggo, basu da yawan magana, idan ka cika matsa musu da magana ma mari zasu kai maka, to ita ma hakan take, ita kuma tana son jin labarin in da Jehan ɗin ta yi rayuwa, amma sam taki bata haɗin kai ta gaya mata, dole ta hakura ba dan ta so ba, haka suka yi kwanan tsantsar faricniki. Washegari da safe, Rimsha ta shirya ta tafi school dan yau saura kwana huɗu su gama exams, ita kuma Jehan ta kule a cikin ɗaki, da Rimsha ta zo tafiya ta fito waje ta yi mata rakiya zuwa wajen mota, suka rungumi juna suka yi sallama, Areef yana yi mata magana, sam taki kula shi ta wuce ta koma ɗaki ta yi kwanciyarta, da yake ya shirya nemanta da tsokana sai ya bita ɗakin, haka ya tasata a gaba ya rinƙa yi mata duk wani abin da bata so, har sai da ta kusa yin kuka sannan ya kyaleta ya fito. Shi kuma Aseef a lokacin ne ya shirya ya tafi wajen Akila kenan. Lokacin da daddynta ya sauƙa a airport, har bedroom nata ya zo ta ce mata ta shirya suje ɗauko daddy, kamar zata ce mishi ba zata je ba, amma sai ta kasa dan a matukar yunwace take da son ganin daddyn nata, haka ta shirya tsab suka nufi airport ɗin. Lokacin da suka yi parking na motarsu a Airport ɗin basu ga daddyn ba, fitowa ya yi dan ya duba shi, Donal ne ya kawo su airport ɗin, can ya hango shi tsaye shi da Tyrone, da sauri fuska ɗauke da fara'a ya karisa wajensu, rungumar juna suka yi shi da daddyn kafin Tyrone ya ɗaga hannu ya sara mishi, sai murmushi suke yi dukkansu. Ganin ya ga daddyn ne yasa ta fito da sauri, tsabar farincikin bata san lokaci da ta tafi da gudu zata rungumi daddyn ba, shi kuma daddy bai ganta ba, kwata kwata bai ma san tana tare da su ba, hankalinsa yana kan Areef, da gudu ta zo zata rungune shi, cikin sauri Areef ɗin ya shiga tsakaninsu ta rungume shi, haushi kamar ta kifa mishi mari, shi kuma daddy dariya abin ya bashi, ga kuma tsantsar murnan ganinta, yaso shi ta runguma, sai dai ba zai iya cewa Areef meyasa ya yi mata haka ba, sai ya danne yana dariya. Tashi ta yi daga jikin nasa a fusace ta ɗaga hannu zata kai mishi duka dan ya kureta ba kaɗan ba, kada ku manta daga ta ciki bala'in tsoronsa take ji. Cikin sauri daddy ya riƙe hannun nata tare da jawota jikinsa yana faɗin "Yi hakuri babyn daddynta". Juyowa Areef ɗin ya yi yana dariya sosai har da riƙe ciki, dan yau ya kureta, zuba mishi ido daddy ya yi yana mamaki, tun da yake da su bai taɓa kallon Areef ya yi dariya irin wannan mai sauti haka ba, yana dai murmushi, ya ma fisu dukka yawan murmushi kafin Aseef ya sami lafiya, amma dariya haka mai sauti har da rike ciki gaskiya bai taɓa gani ba. Shi kuma Jehan ce ta bashi dariya, yadda ta ɗaure fuska har da ɗaga hannu wai zata kai mishi duka, to a ɗan hannun nan nata ma idan ta dake shi me zai ji ne wai? Ya tambayi kansa, abin da hannun nata ɗan siriri kamar muciya shi ne zata kai duka, gaskiya ta bashi dariya, daddy ya rungumeta yana ta kallon Areef, yau yaga abin mamaki, kuma Areef ɗin ya yi mugun kyau da yana dariya, harta Tyrone sake baki ya yi yana kallonsa ga trolleynsa dana daddyn a hannunsa. Shi kam daddy ya kotsa ya ji labarin a ina suka sami Jehan? Yana son suje gida ya haɗa ƴaƴansa ya rungume, yau murna a wajensa ba'a magana, ji ya yi kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha dan daɗi. Sai da Areef ya yi dariyarsa mai isarsa kafin ya tsagaita ya ce "Uncle let's go, wannan babyn ƴar dirama ce". Kallon banza ta watsa mishi tare da jan guntun tsaki, shi dai daddy yana ganin ikon god yau, Jehan sarkin faɗa, Areef sarkin neman tsokana wannan abin yana bada sugar. Hannunta ya kama suka nufi mota, daddy, Jehan da shi Areef ɗin, a baya suka zauna, Tyrone ya zauna a gidan gaba, Donal ya tashi motar sai gida, sai hararsa take yi, ga shi ita ce a tsakiya. Sai zuba hira daddy da Areef ɗin suke yi tamkar wasu abokan juna, cikin hiran nasu ne ya ce "Uncle this our baby ta iya faɗa over". Murmushi daddy ya yi yana faɗin "Gadon faɗar ta yi ai, dole ne ma a samu masu faɗa a family'nmu da yawa, dan kuwa babana mafaɗaci ne number ɗaya, ta gefen mamana akwai su Trump wanda sun kasance ƴan uwanta ne, dukkansu sarakan faɗa da zafin rai ne sosai, duk ma mamanmu ita ce kaɗai bata da faɗa cikin ƴan uwan nata, haka babban yayanmu Abban su Imran, yana da faɗa sosai ga bala'in zuciya, yanzu ne ya yi sanyi, amma da, tab ba'a magana, shiyasa shi ma ya samu mafaɗaci ɗaya wato Akil, Abbi ma yana da faɗa, duk yanzu da girma ya kamasu ne suka yi sanyi, ban da haka ai ba'a magana, haka sisterta A'isha ita ma number ɗaya ce a faɗa, ina ga ma ita Jehan ta biyo, ga Jalilan Maik ma ta gada, so kaga faɗa ai gadon shi ta yi, ita dai My Rimsha ba ruwanta da faɗa, shiru take abinta, kowa nata ne". Capke zancen ya yi da cewa "Yes uncle our Queen bata da faɗa, shiru take ma, sai da na koya mata yawan magana". Mamaki Jehan take yi wato dama shi ya koyawa Rimsha ɗan banzan surutun nan kenan, shigen ɗan ƙaramin bakinsa a wajen, ba zakaga baki ba sai rashin mutunci da surutu yana takurawa ƴaƴan mutane, da wani idonsa kamar ball ɗin mota, wlh zan yi maganin shi ne, sai zancen zuci take yi su kuma suna ta zuba hirarsu har suka isa gida. A tare suka fito suka jera zuwa cikin gida, Areef ne ya riƙe trolleyn daddyn. Bedroom na sama in da Jehan ta fara zama farko, wato ɗakin Imran na farko, nan Areef ya kai daddy, kusa da ƴaƴansa abinsa, zata shiga bedroom ɗin ya tare mata baki kofa ya ce ta koma, kallon sama da kasa ta yi mishi kafin ta ce "Ni ka bani hanya na wuce hai". Kwaikwayar maganar tata ya yi yana murmushi, ji tayi kamar ta shakesa dan haushi, ga kuma bala'in tsoronsa da take ji. "Wuce ki bani guri a nan, ba zaki shiga bedroom ɗin nan ba, uncle zai yi wanka ne ya kwanta ya huta, dan haka ki wuce naki bedroom ɗin ko na ɗauke ki na kai ki". Bata da zaɓi dole ta koma, dan tasan ƙaramin aikinsa ne ya ɗauketa cak ya kaita ɗin kamar yadda ya faɗa, dan haka sai ta shafawa kanta lafiya ta wuce abinta. Tana shiga bedroom ɗin ta haye gadonsu ta kwanta, ba jimawa barci ya ɗauketa, shi kuma daddy wanka ya yi, ya shirya cikin kananan kaya abinsa, dan yanzu kwata kwata baya wani saka manyan kaya, ya zama irinsu sak, kuma dama yana sanya kannanan kayan sosai, sai dai zama dasu yasa ma gabaɗaya ya manta da manyan kaya ma a duniya. Bayan ya kammala sai ya fito palon saman, zaune a saman sofa ya isko Areef ga abinci ya jera mishi a kasa saman carpet yana jiransa. Da fara'a ya kariso wajen suka zauna suna hira suna cin abinci a tare, bayan sun kammala Areef ɗin da kansa ya kwashe kayan ya mayar kitchen, duk abin da suke yi Lion yana ciki yana jinsu, amma tamkar babu shi a gidan, yana can yana harkar gabansa. A lokacin ne kuma su coper suka fara kuka suna daka haushi da karfi, fitowa Lion ɗin ya yi yana tambayar ina Aseef yake? Kowa sai dai ya ce bai san in da yake ba, hakan yasa ya kira numbersa network babu kyau bata shiga, shi ne ya ɗauki mota ya fita nemansa, su kuma su Areef suka zauna a palon suna jiran dawowarsa, dan Lion ɗin ya ce kada su fita. TO WANNAN SHI NE ABIN DA YA FARU DAGA JIYA ZUWA YAU, MU KOMA KAN LABARINMU TUN DA KUNJI YADDA AKA YI KOMAI. Sai jiran Lion suke yi, amma shiru, Areef dai bawan Allah tamkar zai yi hauka, ya kira Lion har ya gaji ya yi wurgi da wayar, sai rarrashinsa tare da kwantar mishi da hankali daddyn Rimsha yake yi, duk da shi ma dai ya kasa ɗaukar abin, amma yana ƙoƙarin ganin ya jure, yau duk tsiwa irin na Jehan sai da ta yi sanyi ta rinƙa rarrashin Rimsha, ta kwanta a jikinta ta yi lamo, ban da ruwan hawaye ba wani abin da take yi, gida fa yau ya girgiza, gabaɗaya sojijin gidan sai da suka sha jinin jikinsu suka yi laushi, Mark idanun nan nasa sun yi jawur tamkar wuta, alamar shi ma ya shiga tsananin tashin hankali, domin kuwa duk wanda ya zauna da TRIPLETS ko da na kwana ɗaya ne, dole a yau idan ya ji labarin abin da ya faru zai yi musu kuka, dan dole zai san tsananin kaunar da suke yi wa junansu, dole a tausayawa Areef da Lion. Da misalin karfe 1 Tyrone ya shigo cikin bedroom ɗin ya kira daddyn Rimsha suka fita waje, har lokacin gawar Aseef tana kwance a saman gadon, ba wanda ya taɓa shi, dole sai Lion ya dawo. A ɓangaren Lion ɗin kuwa yana barin gidan kai tsaye gidansu Imran ya nufa, maza cike a kofar gidan ya samu suna kokarin ɗaura aure, bai bi ta kan kowa ba, ya yi parking na motarsa ya fito cikin takun katsaita, izza da kuma isa, idanuwansa tamkar wuta aka sanya a cikinsu saboda tsananin ja da suka yi, yau gabaɗaya fuskarsa a hargitse take, ganinsa kawai sai ya sanya mai karamin zuciya suma, babu alamar annuri ko tausayi ko kaɗan a face nasa, yau yana cikin tsantsar tashin hankali na wuce misali wanda babu mix ko kaɗan. Bai bi ta kan kowa ba ya wuce cikin gida kai tsaye tamkar gidansa ne, baki su Abba suka buɗe suna ganin ikon Allah, daga ganinsa Abba yasan dole ɗan uwan Aseef ne, shi ma Akil hakance, yasan ɗan uwan Aseef ne, dan haka sai suka miƙe a tare shi da Abba suka nufi cikin gidan dan suga me Lion kuma zai yi, da sauri su Abbi suka rufa musu baya, shi kuma Imran yana gidan Lion ɗin bai dawo ba. Kai tsaye cikin palo Lion ya wuce, ya wuce kowa dake wajen bai ce ko sannu ba, ko sallama ma bai yi ba, dan yau babu mutunci a tattare da shi. Mata ne cike a cikin palon, ba sallama ya faɗa, da kallo ɗaya ya yi wa Ammie dake tsaye a wajen bene zata haura sama ya gane ita ce mahaufiyar Imran, dan akwai Kamanni. Cikin wata iriyar murya ta nuna isa da izza ya ce "Ke ina ƴarki?". Da yake ita ma taga kamanin Aseef a tattare da shi sai ta ce mishi "Tana cikin ɗakin can". Ta yi imanin su Aseef ba zasu cutar da su ba, kuma ita ma Aseef take son ƴar tata ta aura tun da shi ne zaɓinta, gabaɗaya palon ya yi tsit tamkar waƴan da ruwa ya ci su, sun zuba mishi ido suna ganin ikon Allah, ba wadda ta iya buɗe baki bare ta yi magana, dan basu ga wajen wargi ba, ko jaruman maza a yanayin da yake nan basu da kwarin gwiwar iya yi mishi magana bare mata. Bai sake cewa komai ba ya nufi bedroom ɗin Akil da Ammie ta nuna mishi, babu ko sallam ya faɗa cikin ɗakin, tana kwance saman gado tana kuka kamar ranta zai fita, har wani irin shassheka take yi kamar mai numfashin fitar rai, ma'ana mai magagin mutuwa kenan. Yana zuwa ya damƙo hannunta ya jata, miƙewa ta yi, ta diro kasa, jan hannunta ya yi suka fito ba tare da ya ce komai ba, da yake ita tana ganin hotonsa a wajen Aseef ta san shi, hotonsu su ukun ne ma a kan screen ɗin wayar Aseef ɗin, sannan ya turo mata hotunansu da dama, so ta san fuskar Lion sosai, bata musa ba ta bishi dan a tunaninta wajen Aseef zai kaita, shiyasa ta bishi dan bata da burin da ya wuce ta san wani hali Heartbeat ɗin nata yake ciki. A tsakiyar palon kasa yaci karo da su Abba da suka shigo yanzu, ko kallon in da suke bai yi ba, ya nufi waje da ita, duk cikinsu an rasa mai karfin zuciyar tare gabansa ya tambaye shi ina zai kaita, duk rashin kunya da zafi irin na Akil yau ya kasa tare gaban Lion ya tambaye shi ina zai kai mishi sistersa, ido kawai suka bishi da shi dan basu ga alamar imani or tausayi ko wargi a tattare da Lion ɗin ba, basu ga fuskar da zasu iya tinkararsa ba. Sai bayan ya fita da ita ne suka bi bayansa, shi dai Abbi yau yaga ikon Allah bawan Allah shi bai san komai ba, su Abba da suka sani basu yi mamaki sosai ba, abu ɗaya ne ya ɗaure musu kai a nan shi ne ina zai kai ta? Me zai yi mata. Yana zuwa ya turata gidan baya na motarsa, shi kuma ya shiga mazaunin driver tare da ciro kuɗi mai uban yawa ya dubi su Abba da suke nufo motar tasa, rai a matukar ɓace da suka iso ya dubesu can kasa kasa ya ce "A cikin wanene ubanta?" Kallon juna suka yi. Daddyn Jelly ne ya yi ta maza ya ce "Lafiya? wai me yake faruwa ne?" Ko kallon in da suke bai sake yi ba, ya mai da hankalinsa yana ƙoƙarin kunna motar, shi ma Abba fa bai wani damu ba, dan yana son ƴarsa sosai, yana son farincikinta, yana son ta auri wanda take so, kawai dai dan ba yadda zai yi ne, ɗan uwa ba wasa ba, ba zai iya hana Irfan ya bawa Aseef ba bayan ya bata Irfan ɗin, amma abin na yi mishi ciwo, shi ne ya danne ya hanata zaɓin nata, shiyasa yanzu da Lion ya zo bai wani damu sosai ba, abu ɗaya yake son ji shi ne ina za'a kai ta?. "Tun da ba zaku gaya mini waye ubanta ba, ku karɓi wannan kuɗin shi ne sadakin ƴarku, zan ɗaura mata aure da gawar Aseef, aurenta shi ne burinsa na karshe dole na cika mishi, bayan haka ku saurari dawowata a karo na biyu dan sai kun biya ran Aseef wlh". Ya kai karshen maganar tare da watsa musu kuɗin ya ja motar da gudu ya yi gaba abinsa ya barsu tsaye sun kasa magana. Ita kuma Akila tun da ta ji ya ambaci gawar Aseef numfashinta ya ɗauke diff tamkar an ɗauke wutar nepa, ta sume, tamkar ba mutun ya ɗauko ba, ko kallon in da take bai yi ba, kai tsaye babban masallaci ya nufa da ita, bayan ya je ne ya kira Tyrone a kan ya kawo mishi daddyn Rimsha ya zo ya zama waliyinta, shi kuma zai zama waliyin gawar Aseef. BABBAR MAGANA WANNAN SHI NE NUNA TSANTSAR ISA A KAN ABIN DA BA MALLAKINKA BA. Shi dai TRIPLETS nasa ne kawai mutane? Baya ɗaukar kowa da daraja bayan su ɗin? Lallai akwai aiki babba ma kuwa, daddy ya yi kuskure babba na irin tarbiyar da ya basu. Bayan an kawo mishi daddyn Rimsha ya gaya mishi abin da yake da buƙata, sosai daddy ya ji daɗi dan kuwa shi ma ya ji muguwar zafin raba su da Abba ya yi, sai dai kuma da ya tuna Aseef ɗin ya rasu, sai wasu zafafan hawaye suka fara gangaro mishi a saman kuncinsa, shikenan yanzu Aseef ya tafi ya barsu? Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, tunani ya fara yi wai shin an taɓa ɗaura aure da gawa ne?. Amma ya zai yi, ya zama mishi dole ya yi accepting dan ba'a yi wa Lion musu. Haka ya zo ya zama walinta aka ɗaura auren, yau ga ikon Allah Lion ba shi ya haifi yarinya ba, amma saboda isa da izza ya fi karfin ya nemi alfarma ya roƙa a bashi cikin salama, kawai ya ɗauko yarinya tana sume ya ɗaura mata aure, wannan izza anya akwai biyunta a duniya kuwa? Daga karshe dai an ɗaura aure Akila da gawar Aseef wannan shi ne tashin sense da ba'a saka mishi date. Sadaka ya yi mai tarin yawa a Masallacin bayan an ɗaura auren, kafin su shiga mota da nufin su koma gida a je a yiwa Aseef sutura, gidan baya daddyn Rimsha ya shiga in da Akilar take, shi kuma ya shiga gidan gaba. Suna shiga daddyn Rimsha ya ga Akilar tana sume, hakan yasa ya ɗauko ruwan dake gaban motar ya yayyafa mata, shi kuma Lion ya kunna motar da nufin su wuce gida. A razane ta farka tana ambatar "Heartbeat bai mutu ba, ni nasan bai mutu ba, wlh yana raye, ya yi mini alkawarin zai rayu dani, ni nasan ba zai karya mini alkawarina ba, wlh ba zai mutu ba, dan girman Allah ku ce mutuwa ta barshi ni ta zo ta ɗauke ni, Wayyo Abbana nashiga uku!". Da alama ta fita a hayyacinta sosai, riketa daddyn Rimsha ya yi yana rarrashinta sosai, shi kuwa Lion jin surutanta yasa ya kara gudun motar, kamar yadda zuciyarsa take tafasa haka yake kara taka motar shi ma, ba ƙaramin tsorota daddy ya yi da irin gudun da yake shararawa ba, kada su je su yi accident. Shi kuma bawan Allah zuciyarsa ne take tamkar zata fashe yasa yake taka motar da karfi, Allah dai ya tsare sun isa gida lafiya, yau dai gabaɗaya gidan daga kan sojiji har cikin gida kowa jugum jugum yake kamar ruwa ya cinyesu. Yana kashe motar ya fito ya buɗe kofar gidan bayan ya damko hannunta, ba musu ta fito, jan ta ya yi zuwa cikin gida, da sauri daddy ya bi bayansu, kai tsaye bedroom nasa ya wuce da ita in da Aseef yake kwance kenan. Har lokacin tana kuka tana sambatu kamar zautatciya, yana zuwa ya saketa a kan gawar Aseef ɗin tare da juyawa ya basu baya yana ciza laɓɓansa, shi kaɗai yasan me yake ji a cikin zuciyarsa. Imran da Areef duk miƙewa suka yi suna kallon Lion ɗin, ita kuwa tana ganin Aseef a gaban gadon ta dai'dai fuskarsa ta zube gwiwowinta a kasa tana kuka, cikin fitar hayyaci ta fara sambatu tana ambatar sunansa. "My shagwaɓati, ka tashi, ni nasan wlh baka mutu ba, na san ba zaka mutu ka barni ba, ka tashi ko kuma ka dauke ni mu tafi tare, bana son kowa sai kai, ai na gaya maka ba zan rabu da kai ba, kuma ni na cika alkawari, ba zan rabu da kai ba, ka manta kai ma ka ce ba zaka rabu da ni bane? To kai ma ka tashi ka cika mini alkawarina, ka manta kai mai cika alkawari ne? To idan ka manta ma na tuna maka, saboda kayi mini alkawarin zaka kawo mini kanka yasa ka haɗa Exams naka gabaɗaya ka yi su lokaci guda dan ka cika mini alkawarin da ka ɗauka, to nasan yanzu ma zaka cika mini, please ka tashi ka ganni nazo!". Yadda take surutan nata bata a cikin hayyacinta, kawai magana take yi bata san me take faɗe ba. Hannu ta kai saman fuskarsa tana grigiza shi tana sake ambatar sunansa, kasa jurewa Imran ya yi da sauri ya fice daga cikin ɗakin yana ruwan hawaye, shi kuma Areef matsowa ya yi kusa da ita da nufin ya kamata ta daina girgiza Aseef ɗin. Dogon numfashi Lion yaja tare da saukewa a hankali, shi kwata kwata bai san da soyayyarsu ba, ai da Aseef ya gaya mishi da tuni zai sanya a ɗauko Akilar da iyayenta a ɗaura musu aure, ai duk abin da TRIPLETS nasa suke so to fa dole ne a basu idan ana son zaman lafiya, yanzu ga shi yazo a tunaninsa na banza ya sanya zuciyarsa ta buga, ya je yana tunanin Lion ɗin zai hana shi sonta, bai san ba haka bane, in dai ya san yana sonta da gaske babu wasa ai dole ya san ta yanda zai bi ya mallaka mishi ita, dan farincikinsu shi ne nashi. Jin abin da yake faruwa na Areef yana kokarin kamata tana tirjewa ita lalllai sai dai a barta a wajen heartbeat nata ne yasa Lion ɗin ya nufi hanyar fita dan tana kara mishi zafin rashin ɗan uwan nasa ne a zuciyarsa. Yana yin taku biyu sai ya tsaya cak tare da juyowa a sukwane ya dubi Aseef ɗin dake kwace, shi ma Areef sakinta ya yi yana kallon Aseef ɗin kafin daga bisani ya dawo da kallonsa kan Lion ɗin, dai'dai lokacin shi ma Lion ɗin ya dawo da kallonsa kan Areef ɗin, gera ɗaya ya ɗaga mishi alamar yane?. Jinjina mishi kai Areef ɗin ya yi alamar duk ɗaya ne, a tare suka ji bugun zuciyar, a zafafe ya dawo wajen bed ɗin, dan wannan bugawar da zuciyarsu ta yi a tare tana da nasaba da Aseef, saboda duk abin da ya sami ɗayansu sai sun ji hakan a tare, shiyasa ma ya dawo dan ya duba ko dai Aseef ɗin bai mutu bane. Duba shi ya fara yi a zafafe babu kama hannun yaro, shi ma Areef hayewa saman bed ɗin ya yi suka fara bincikarsa ko zasu gano wani abin. Daddyn Rimsha kuma zuwa ya yi ya riƙo Akila dan kada ta hanasu yin aiki, sai kuka take yi, duk rashin son hayaniya ta Lion yau ya daure yana jin kukan AKila bai yi magana ba, domin kuwa Aseef yana mahaukacin sonta, dole su kula da ita dan ɗan uwansu, dama idan baku manta ba Rimsha ta taɓa gayawa Akilar, in dai ɗaya daga cikin TRIPLETS yana sonta ya aureta, to dukkansu uku zasu so ta har da shi ma Lion ɗin, dan suna son abin da ɗayansu yake so, bare kuma yanzu da take matar Aseef ɗin, ai dole sun danne su shanye, bugu da kari ga irin rabuwar yankar kauna da aka yi musu, ai kukanta mai hujja ne, dole ta yi, dole suma su danne su barta ta yi ko zata samu sauki a ranta. Sun ɗan ɗauki lokaci suna bincikar Aseef ɗin, amma ina babu wata alama da take nuna yana raye, can kamar daga sama suka ji saukar hannunsa, nan take numfashin ya fara fita da sauri da sauri kirjinsa na harbawa da karfi karfi, a zafafe Areef ya diro kasa daga saman bed ɗin ya nufi wajen drawers dake wajen mirror dan ya kawo oxygen su saka mishi numfashin ta daidaita, ya kuwa yi sa'a suna da shi, dan suna tafiya da abubuwa irin haka saboda tsaro, duk wasu kayan taimakon gaggawa da ta shafi lafiya suna tafiya da shi dan yanayin aikinsu, tana iya yiwuwa a harbi wani daga cikinsu da bindiga ko makamancin haka, to shi ne dalilin da yasa duk in da zasu je suke ɗaban kayan kula da lafiya na agajin gaggawa. Sanya mishi Lion ya karɓa ya yi dan numfashin ta dai'dai ta, sun kuwa yi sa'a ta daidaita, sai dai bai buɗe idanu ba, kamar ma bai farka ba, sun dai tabbatar yana raye bai mutu ba, kifa kai Areef ya yi a bayan Lion yana sauke numfashi tare da zuba ɗinbin godiya ga ubangiji da ya sanya Aseef bai mutu ba, da ya mutu ai da sun shaga uku, Juyowa Lion ɗin ya yi suka rungumi juna, Allah ne kaɗai yasan irin farincikin dake cikin zukatansu a yanzu. Sosai suka kankame juna, har ƴar washewa idanun Lion ya yi, bayin Allah suna mutuwar kaunar junansu, ita ma Akila shiru ta yi dan ganin Aseef yana numfashi, daddyn Rimsha ba'a magana, murna a wajensa ya wuce misali, Allah sarki ita kam Rimsha tana cikin bedroom nata kwance a jikin Jehan tana ruwan hawaye bata san me yake faruwa ba, bata san cewa doguwar suma mai kama da mutuwa Aseef ya yi ba, ta ɗauka ya mutu baiwar Allah, abokin shagwaɓarta da zuba hira, sun yi sabo sosai da shi, shiyasa take kuka har haka, sai rarrashinta Jehan take yi dan ta yi mugun bata tausayi. Wunin ranar dai a cikin bedroom ɗin suka wuni, Akila taki yarda ta matsa daga jikin gadon, gani take yi idan ta tashi wani abin zai same shi, shi kuma har lokacin bai farfaɗo ba, yana dai numfashi, Lion, Areef duk basu matsa daga wajen ba, suma suna ganin kamar idan suka matsa wani abin zai same shi, cikin ƙanƙanin lokaci labari ya sake isanwa Mutanen Washington DC akan Aseef bai mutu ba, nan ne fa su John suka ce su gaskiya za su zo su ganshi da idanunsu, Lion bai hanasu zuwa ba, daddy ma da bai san me yake faruwa ba ya kafe sai ya biyo su John sun zo tare, shi ma Lion ya barshi yazo dan ya lura hakurin daddyn nasa ya fara karewa a kan rashinsu a kusa da shi, kada ciwonsa ta yi ta kara cigaba, yanzu sun fara murna sauki ya samu, to kada a koma gidan jiya gara ya bar shi ya zo ɗin, shi ne yasa ya kyale su suzo tare, shi kuma Tga sai ya kara samun sauki nan da next week. Da misalin karfe 6 na yamma, duk sun haɗu a cikin bedroom ɗin Lion, harta su Rimsha sun zo, Lion, Areef suna saman bed kusa da ɗan uwansu, ita kuma Akila tana zaune saman bedside drawer tana ta kallon mijin nata ba ko kyafta idanu, hayaniya ne ya fara tashi a waje, sojoji ne da su Abba sun biyo AKila, Abba ne da Abbi sai daddyn Jelly, Irfan da kuma Akil da ya yi musu jagora, sojojin sun hanasu shiga gidan ne, shi kuma Abba ɗan zafin rai ya ce dole sai ya shiga ya je ya ɗauko ƴarsa. Jin hayaniyar yasa Areef miƙewa ya nufi wajen, dai'dai lokacin kuma ɗaya daga cikin sojojin ya ɗaga bindiga zai harbi Abba a kafa dan ya ce sai ya shiga, daka musu tsawa Areef ɗin ya yi yana faɗin suna hauka ne zasu harbi mutun basu san waye shi ba? Laifin me ya yi musu zasu harbe shi? Sorry sir suka fara ce mishi. Bai sake bi ta kansu ba ya yi wa su Abba iso zuwa cikin gidan cikin mutunci yana mai basu hakurin abin da sojojin suka yi musu ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E57-58💋 Bai sake bi ta kansu ba ya yi wa su Abba iso zuwa cikin gidan, cikin mutunci yana mai basu hakurin abin da sojojin suka yi musu, a palon kasa ya sauƙesu, dan bai san da me suka zo ba, kada su je palon sama ya zamana da ɗaga murya suka zo Lion ya jiyo su suna ɗaga murya ya zo ya kwaɓe komai, dan kaɗan daga aikinsa idan suka ɗaga murya ya sanya a basu hukunci mai tsanani, bayan kuma shi ya je ya ɗauko musu yarinya kamar shi ya haifa musu ita, so yanzu sun rigada sun zama family ɗaya tun da dai Akila da Aseef aure ya ɗauru ba warwarewa, yana da kyau su daraja iyayen Akilar, kuma yana da kyau su basu kulawa tun da suna da damar da kuma power yin hakan. Zama shi ma ya yi cikin sanyin murya ya ɗagawa Abba da Abbi gaisuwa, fuska ba yabo ba fallasa suka amsa, miƙawa daddyn Jelly hannu ya yi dan su gaisa saboda suna kusa da juna, ya raina daddyn Jelly yana yi mishi kallon matashi dan ya ganshi ɗan kwalisah, yana yi mishi kallo kamar su yake, bai san ba haka bane, daddyn Jelly ya girmesu da almost shekaru 8, kawai yana da karamin jiki ne da kuma kyau irin na Naurat, shi ne har da wani miƙa mishi hannu ya yi dan yana ganin ai duk sa'annin juna ne su. Miƙawa Irfan da Akil ma hannu ya yi suka gaisa, Abba ne ya fara cewa sun zo ɗaukar Akila ce, cikin nuna ko in kula ya ce "Akila ai matar aure ce, ba ta yadda za'ayi ta fita ba tare da izinin Aseef ba, amma kuyi hakuri idan Aseef ɗin ya farka zan gaya mishi ya kawo muku ita har gida ku ganta". Har cikin ransa Abba ya ji daɗi da ƴarsa ta auri zaɓinta, amma kuma sai ya ɓoye tare da ɗaure fuska yana faɗin "Ban gane matar aure ba? Waye ya isa ya ɗaurawa ƴata aure ba da izinina ba? Ai hakan sam ba zai yiwu ba, idan ma an ɗaura dole a warware kuma bai ma ɗauru ba tun da ni ubanta ban bayar ba, kuma babu waliyi". Karɓar zancen Abbi ya yi da cewa "Tayaya za'ayi ma ace an ɗaurawa yarinya aure ba tare da izinin iyayenta ba? Wannan aure bai yiwu ba, kawai ku bamu ƴarmu mu tafi dan ba hanayina ko wani abin bane ya kawo mu". Akil dai shiru ya zuba musu idanu, dan shi ransa fes kanwarsa ta auri zaɓin ranta, shi ai sun faranta mishi rai, yadda yake mugun kaunar Heartbeat ɗin nan, ai baya son ɓacin ranta sam, so dan haka shi bama zai saka baki ba. Shiru Areef ya yi yana jinsu suna ta surfa zance son ransu, su dai dole a kira musu Akila su tafi da ita, ya rasa me zai ce musu bawan Allah, sai kawai ya bisu da ido, shi dai ba zai iya yi musu rashin kunya ba, ba kuma zai gaya musu magana mara daɗi ba, shiyasa ya bisu da idanu kawai. Tamkar saukar aradu suka ji sexy voice ɗin Lion yana faɗin "Ina da bukar ku yi mini shiru ban son hayaniya!" Ya yi maganar yana saukowa kasan, bin shi da idanu suka yi har ya sauko zuwa kasan, daddyn Rimsha tare da Imran ma a tare suka sauko, Jehan da Rimsha suma a tare suka sauko. Nufar hanyar fita daga palon Lion ɗin ya yi ba tare da ya sake ganin in da suke ba. "Lion sun zo suna son tafiya da matar Aseef ne fa". Cewar Areef, tamkar bai ji me Areef ɗin ya faɗa ba ya cigaba da tafiyarsa. Sai da ya kai bakin kofar fita daga palon sannan ya ce "To ba sai su ɗauke ɗin in gani ba". Ya kai karshen maganar yana ƙoƙarin sa kai ya fita. "Wai taya za'ayi ace kun ɗaurawa yarinya aure ba tare da yardar iyayenta bane? To ku sani auren bai yiwu ba, dan bata da waliyi, dole ku bamu ƴarmu". Cewar Abbi, Juyowa Lion ɗin ya yi yana kare wa Abbin kallo, ganin bai ma ga in da zai mara a face ɗin Abbin bane yasa ya kawar da kallonsa, dan a cewarsa idan ya mari Abbin zai suma ko mutuwa. "Zaku iya tafiya dan bana son abin da zai takurawa Aseef a yanzu, yarinya kuma ta riga da ta yi aure, idan kunga ta fita daga gidan nan, to ita da mijinta ne!". Shi ne abin da Lion ɗin ya ce da su. "Wlh ba zai yiwu ba, dole sai kun bamu ƴar mu, babu wanda ya isa ya tsara mana ga abin da zamu yi a rayuwarmu, dan haka baku isa ku ce ga abin da zamu yi ko abin da ƴarmu zata yi ba". Cewar Abbi. Shiru ya yi bai sake magana ba, dan shi maganarsa mai tsada ce, ba mai arha da zai tsaya bada amsa a kan komai da suka faɗa ba. Ganin Abin yana neman kwaɓewa ne yasa Areef ya yi saurin cewa "Please uncles ku kwantar da hankakinku mu fahimci juna, komai ai mai sauki ne". Cikin kunar rai Abba ya ce "Babu zancen mu kwantar da hankali a nan". Dan ba karya ya ji babu daɗi abin da Lion ya yi musu, a cewar Abban ai ya rainasu ne, basu san cewa shi a haka yake ɗaukar kowa bama, su yama yi musu da sauki dan sun bawa ɗan uwansa abin da ya fi so, da wasu can ne wlh basu isa su shigo cikin gidansa har cikin palo suce zasu saka magana a saman nasa maganar ba, wane kaniyarsu, amma su koba komai sanadiyarsu Aseef zai yi farinciki, dama kuma shi Lion baya rena alkhari kuma baya mantawa, shiyasa ya ɗauki zane ɗaya daga cikin wanda Rimsha ta yi mishi ya ajiye a wajensa dan baya rena alkhari kuma baya mantawa. Abbi zai sake yin magana daddyn Rimsha ya yi saurin taresu cikin yaren Tatar wato yaren mahaifiyarsu Naurat dan ma kada su Rimsha su ji abin da zai faɗa, "Yaya Babba dan Allah ya isa haka, kuyi hakuri kada ku sanya wannan abin a ranku, kada ku yi abin ya zama wani babban case, waƴan nan da kuke gani haka suke, haka Allah ya yi su, idan kuka matsa kune zaku sha wahala, dan baku da wani abin da zaku yi sai hakuri, dan Allah ku bar maganar nan haka ya isa, ku yi hakuri, ni Hossain nina basu auren AKila, ni ne waliyinta, ko ban kai na aurar da ƴarka bane yaya?". Babbar magana, zuba mishi idanu suka yi sun kasa magana. Miƙewa daddyn Jelly ya yi yana faɗin "Yaya Hossain, dama na faɗa musu wlh kai ne His excellency Nawazudden, amma shi ne ka ce mana ba kai bane ko?". Ɗan kawar da kansa ya yi yana faɗin "Yanzu ma dan farincikin Aseef yasa na gaya muku ni ne ai, yanzu tun da kunsan waliyin AKila sai ku kyale mini Aseef na ya huta, kun kusa kashe mini shi, da shikenan ya mutu fa, da kuwa sai kun biya dan da ba zan yafe muku ba!" Ya yi maganar on a serious note. Abba da Abbi dai sun kasa yin magana, dan kuwa sun rasa da bakin da zasu fara yi mishi magana har su nemi gafararsa, shi kuma Lion wucewa ya yi ya fita abinsa. Ganin su Abbi sun kasa yin magana ne yasa ya ce "Yaya lafiya kuwa?" Shiru suka yi ba wanda ya yi magana, karisowa kusa da su ya yi yana sake tambayarsu me yasa suka yi shiru, su kuwa abin da ya faru a baya ne ya dawo musu sabo, kallon Jehan da Rimsha dake tsaye ya yi cikin harshen turanci ya ce "Kuzo ga bappanunku yau kam na bayyana muku su". Kallon Rimsha Jehan ta yi da mamaki, ita kuwa ko a jikinta, dan idan bamu manta ba kafin daddy ya kowa Washington DC ya gaya mata Imran yayanta ne, dan haka ta sani, sai bata wani damu ba. Karisowa wajen suka yi, ita dai Jehan tana ta mamaki, wai dama daddynsu yana da ƴan uwa ne? Ita ta ɗauka ma shi maraya ne bashi da kowa kamar yadda mutane suke faɗe, yau dai ga shi ya nuna musu su. Kusa da Abbi Rimsha ta zo ta zauna dan shi ta sani, shi ne take zuwa gidansa da Imran, bata san Abba ba, rungumeta Abbin ya yi tamkar zai yi kuka, ita kuwa Jehan taki zuwa wajen kowa, ta tsaya a tsakiyar palon tana binsu da idanu, hannu Abba ya miƙa mata a kan ta zo, ɗan juyawa ta yi dan ta kalli daddynta caraf suka haɗa ido da Areef, kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Me kike wani kallona? Da wani idonki a wajen". Guntun tsaki ta ja kafin ta karisa wajen Abban tana faɗin "To me zan kallah a tattare da kai dama, mummunar fuska ko me?". Daddynta ne ya yi saurin cewa "Ke baby wlh ki kiyayeni, bai fiki kyau bane da zaki ce mishi mummuna?". Murmushi Areef ɗin ya yi kafin ya ce "Yes my uncle i love you so much, gaya mata na fita kyau, ita ma ta sani ai, har da satar kallona take yi taga fine guy, bata san ina ganin duk abin da take yi ba ne ai?". Turo baki ta yi tare da miƙewa daga wajen Abban zata bar palon dan sun ɓata mata rai, cikin sauri daddyn Jelly ya riƙota yana faɗin "Rabu da su hai, sun taɓa ganin namiji yafi mace kyau ne? Ai ke karshe ce a kyau, baki ga idonsa kamar ball bane?". Ɗan yake ta yi kafin ta ce "Yes nima ga bappana zai karɓa mini". Rimsha ne ta karɓi zancen da cewa "Wlh bappa yaya Areef ya fita kyau, jiba kanta kato fa, shi kuma nasa daidai, ga gashinta kamar na Gwaggo ba kyau, idonta kamar na......". Bata kai karshen ba daddyn Jelly ya wurga mata harara yana faɗin "Saboda tafiki kyau ne kike kishi ko?". "No uncle gaskiya baby bata fi Our Queen kyau ba, ita fa Queen ita kaɗai ce, daga ita babu wata kyakkyawa a duniya, kawai fa babyn nan dan ta yi sa'a ne nake kulata, kuma ta yi sa'a ta ɗan yi kama da uncle shi ne ta yi kyau". Cewar Areef, miƙewa Jehan ɗin ta yi fuuuu kamar wata kunfa ta fita daga palon tana faɗin zata kama Rismha ne, wlh sai ta cire mata hakoran gaba, ta zama bata da hakori, dariya Abbi ya yi yana jin tsantsar farinciki a ransa. Nisawa Abba ya yi tare da fara ƙoƙarin bawa daddyn Rimsha hakuri, dakatar da shi daddyn ya yi yana faɗin "Komai ya wuce, dan haka a barshi a ya wucen kawai, please kada ku dawo da komai, bana son tuna komai, ni har ga Allah na yafe muku, so ku manta da komai". Jinjina mishi kai suka yi, Akil da Irfan dai sai binsu da idanu kawai suke yi, shi kuma Imran tun ɗazun ya fita amsa wayar jelly da ta kira shi da layin Ammie, dan har yanzu bata da waya. Hira suka fara zubawa, sam daddyn Rimsha yaki yarda su dawo mishi da abin da ya wuce, sun so ya gaya musu a ina ya yi rayuwa, bayan barinsa gida ina ya je, amma ya nuna sam baya son maganar, dan haka sai suka kyale shi sai zuwa gaba idan ya saki jiki da su sosai, sai su tambaye shi. A ɓangaren cikin bedroom na Lion kuwa, wato wajen Aseef, su Lion suna fita Akila ta matso kusa da mijin nata, dai'dai saitin kunnensa ta kai ɗan bakinta, a hankali ta fara yi mishi magana kamar mai raɗa. "My shagwaɓati, please ka tashi kaji? Ka tashi ka kalleni in ganka, ina kewar muryarka, tun fa da safe da naji ban sake ji ba, kana so ne na yi rashin lafiya? To ni dai gaskiya ka tashi ko nayi maka kuka, kuma idan na fara kuka ba zan yi shiru ba, ina son jin shagwaɓarka mijina, ni gaskiya ka tashi". Da yake Lion ya sanar da Areef ya ɗaura musu aure a gabanta tana ji, shi ne ta san cewa mijinta ne, ba dan haka ba bazata sani ba, dan a lokacin da aka ɗaura auren tana sume bata sani ba, bawa Areef labari da ya yi ne ta ji. Ɗan kwanto da kanta a saman kirjinsa ta yi tana mai kara cigaba da magana "Wai ba zaka tashi ba har sai na fara kukan gaske ne? Yanzu fa kai mallakina ne, nima kuma mallakinka ne, to ka tashi mana my shagwaɓati, ka tashi bari nayi maka tausar ka ji? Uhm uhm". Sai kukan shagwaɓa da ba hawaye take yi mishi, shiru bai motsa ba. A haka har aka kira sallar mangariba, tana wajen har lokacin kuma kanta a saman kirjinsa, sai zuba mishi shagwaɓa da surutu a hankali kamar mai raɗa take yi, a haka Lion ya shigo ya same su, kallo ɗaya ya yi musu ya kawar da kansa tare da nufar toilet dan ya yi alwala su je masallaci, bata san Lion ya shigo bama, tana can duniyar surutu ga shagwaɓatin nata. "My shagwaɓati ka tashi to na baka abinci a baki, tun fa da safe baka ci komai ba, nima yunwa nake ji mijina, amma ba zan iya cin komai ba sai abin da ka bani da kanka, to ka tashi ka bani a baki dan naci". Duk surutun da take yi Lion yana jinta, ita ce bata san ya shigo ba. Alwala ya yi yazo ya fice bai bi ta kansu ba, su Abba ma duk sun tafi masallaci, gidan ya rage daga ita Akilar, Aseef, Rimsha, sai kuma Jehan. Har lokacin tana kwance da kanta a saman kirjinsa tana surutu. Kamar daga sama ta fara jin shasshekar kukansa, dama ya suma ne yana kuka, dan haka sai ya tashi da kuka, a hankali kukan take fita, da kaɗan da kaɗan yana karuwa, ɗago kanta daga kirjin nasa ta yi tana ambatar sunansa, amma bai kulata ba sai famar shasshekar kuka yake yi yana yin wani abu kamar shaƙuwa. Ta jima tana ambatar sunansa kafin nan ya tsaya da kukan cak, da alama ya ji muryarta ne yasa ya yi wannan shiru yana sauraron. Mayar da kanta saman kirjin nasa ta yi tana faɗin "My shagwaɓati ka dai'na kuka ka buɗe idanunka ka ji? Ai yanzu kam gani nan nazo". A hankali ya waro dara daran idanuwansa waje, idanun nasa sun yi jawur da su alamar yana cikin ciwo, bata san ya buɗe idanu ba, ta ɗan kifa kai a saman kirjinsa tana surutai abinta, zuba mata idanu ya yi babu ko kyaftawa, ganin abin yake yi tamkar mafarki ne, ɗakin Lion ɗin ya fara bi da kallo dan ya tabbatar da in da yake, a hankali ya sanya hannu ya zame oxygen dake hancinsa, numfashin nasa yanzu ta yi dai'dai. Hannu ya ɗaura saman kanta dan ya tabbatar ba gizo take yi mishi ba, da sauri ta ɗago jin saukar hannun nasa a kanta, ganin ya buɗe idanu ne yasa ta mike zaune gabaɗaya tana kallon shi, shi ma kallonta yake yi babu ko kyaftawa. Shigowar Areef ne ya sanya ita ta miƙe ta koma saman bedside drawer ta zauna tare da kawar da kallonta daga kansa zuwa kasa, tana mugun jin kunyar TRIPLETS nasa, su kuma bata san basu san menene ma kunya ba sam, basu san hanyarta ba sam. Shi kuwa har lokacin idanunsa yana kanta, sai kallonta yake yi. Saman bed ɗin Areef ya hau yana faɗin "Sarkin shagwaɓa sarkin kuka, yanzu ma daga farfaɗowa sai da kayi ko? To yanzu dai ka kara girma ka zama family man sai ka dai'na yi mana wasu tsiyar". Kallon gefen ido ya wurgawa Areef ɗin kafin calmly ya ce "Ni har gobe autan daddy ne, kuma pleasure TRIPLETS, sannan heartbeat ɗin su uncle T, dan haka babu ruwanka da ni". "Au lallai ka warke, to sai ka tashi ka bar mana ɗaki". Kuka ya saka musu yana turo baki. "Au haka ne our pleasure to ya isa our ɗan auta, ba sai ka zuba mini sabon shagwaɓa ba, dan nasan da ka suman nan wani sabon salo kazo da shi". "Wlh bari Lion ya zo sai ya rama mini". "Sai dai ya rame maka ba dai ramawa ba". Kuka ya sake saka musu hakan kuma ya yi daidai da shigowar Lion ɗin. Karisowa bakin gadon ya yi yana kallon Areef dake faman sauka, damko gashin kansa ya yi calmly ya ce "Me kayi mishi?". A shagwaɓe Aseef ɗin ya ce "My Lion zagina ya yi tayi". Ita dai AKila ta buɗe baki tana kallon kauna irin na TRIPLETS, suna masifar son junansu, ji yadda suke wasa da raha a tsakaninsu gwanin ban sha'awa da burgewa, wani idan zaka kashe shi ma cemaka zai yi Lion kurma ne baya magana, dan basu taɓa ji ya yi ba, amma kana shiga ɗaki ka same shi da TRIPLETS nasa, abin ba'a magana, duk da ba wani biye musu yake yi ba, amma yana magana kaɗan. "Me zan yi mishi in rama maka?" Ya faɗa yana kara jan gashin Areef ɗin da karfi, "Ni wlh Lion saboda kai zan datse wannan gashi dukka, ka takurawa kaina haka kawai, amma kuma naga alamar my baby tana son gashi ba zai yanke ba". Cewar Areef. Shi dai Aseef lallaɓawa ya yi da kyar ya miƙe zaune, ya zubawa Akila idanu yana kallonta. "My pleasure ka faɗa mini me zan yi mishi?" Lion ya tambaya ya ƙoƙarin cirewa Areef ɗin wani ɗan abu da ya kallah a jikin gashin nasa. Runtse ido Akila ta yi kasa kasa ta yi mishi alama da ya ce a saki Areef dan yana jin zafin gashinsa da Lion ɗin ya kama, ga shi sai faman cija laɓɓa yake yi alamar zafi. "My Lion zuwa da safe sai ka bashi punishment mai kyau". Cewar Areef, ya yi maganar yana wurgawa Areef ɗin harara. "Baby ta ce idona kamar ball, to ga mai idon ball nan tazo ta gani, diba idanunka Aseef kamar kwan lantarki". Cewar Areef da ake riƙe da gashinsa ba'a saki ba amma yana sake neman wani tsokana saboda ya saba tsokanar Aseef ɗin sosai wani lokaci. Sake shi Lion ɗin ya yi tare da zama a gefen Aseef ɗin yana kare mishi kallo. "How are you feeling now?" Ya tambaya yana dawo da kallonsa kan Areef, hayewa gadon Areef ɗin ya yi tare da sanya hannunsa a saman kan Aseef ɗin dan ya ji zazzaɓin jikin nasa. Kwanto da kai Aseef ɗin ya yi a kafaɗan Lion ɗin a shagwaɓe ya ce "Heartbeat ta zo na dai'na jin ciwo ai". Kasa ta yi da kanta tana wasa da yatsun hannunta, shi kuma Areef kallonta ya yi kafin ya ce "Kina jina?". Ɗago kai ta yi suka haɗa idanu kafin ta ɗan kawar gefe tana faɗa mishi e tana jinsa. "Aseef shi ne farincikinmu, shi ne komai namu, muna kaunarsa fiye da yanda muke kaunar kanmu, kinga ya nuna yana sonki sosai, kema nasan kina son shi, to zamu baki amarsa, please ki kula mana da shi sosai, kada ki bari yaji ɓacin rai, kinga muma bamu barin ɓacin rai ya samu waje a zuciyarsa, kullum yana yawan bani labarin irin farincin da kike sanya shi, to dan Allah ki ɗore a haka, dukkanmu haka da kike gani kafin muzo Nigeria babu wanda ya taɓa yarda da mace ta raɓemu, saboda muna ganin ku macuta ne, a kan matan Nigeria muka fara sakewa da mace, saboda duk ƴan Nigeria waƴan da muka yi alaƙa dasu bana banza, mutanen kirki ne, hakan ne kuma yasa muka yarda ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba, ko ina akwai na kirki, kada ki yi breaking heart namu! Ki riƙe wannan shaida da muka yi muku, kin so Aseef tun baki san waye shi ba, hakan ma tasa Lion ya ɗaura muku aure, dan mun san soyayyar gaskiya kike yi mishi, so please ku cigaba a haka, idan ya yi miki abin da bai yi miki daɗi ba, ki zo ki same ni ki sanar da ni, shi ma idan kika yi mishi ba dai'dai ba ya zo ya gaya mini, nine alkali a tsakaninku, sannan ki kula mana da kanki sosai kinji ko ƴar autarmu?" Ɗagowa ta yi tana mamakin ya ce mata ƴar autarsu. "Kina mamaki ne? Ai ke yanzu autarmu ce tun da auta kika aura". Kwanto da kansa Aseef ya yi a saman cinyar Lion yana faɗin "My Lion yanzu da gaske ka aura mini my heartbeat tawa?" Shafa kyakkyawar face nasa Lion ɗin ya yi kafin ya ce "Je ka yi wanka ka yi sallah sai kazo kaci abinci". Miƙewa ya yi tare da rungumo Lion ɗin yana zuba mishi godiya tare da sumbata a kumatu. Sumbatarsa shi ma Lion ɗin ya yi suna jin tsantsar farinciki tare da kaunar juna. "Aseef ka je ka yi wanka kazo ka kai matarka wajen parents nata su ganta zasu koma, ni na tsayar da su, na ce sai sunci abinci an kawo musu ita sun gaisa, so ka yi sauri". Cewar Areef, ya yi maganar tare da miƙewa ya nufi waje, miƙewa shi ma Lion ya yi tare da ɗaukar wayarsa ya shiga balcony dan ya yi waya da daddynsa. Suna fita ya zuba mata ido yana kallon yadda take aikin murza yatsun hannunta. "So kike ki nemi magana dani ko?". Ya faɗa with his full voice babu shagwaɓa a cikinta, ɗago kai ta yi suka zubawa juna idanu, har lokacin tana murza yatsun hannunta. Matsowa ya yi kusa da ita tare da kama hannun nata yana faɗin "Wai ke me yasa kike son neman magana da ni ne? Sai ki yi murje mini yatsuna ko? Bayan kuma kinsan ni yakamata nayi hakan ko?" A wannan karon ya yi maganar a shagwaɓe. Ɗan turo baki ta yi zata yi magana Rimsha ta shigo cikin ɗakin bakinta ɗauke da sallama, a tare suka amsa mata sallamar, kusa da su ta zo ta tsaya tare da gaishe da Aseef da jiki kafin ta ce "Aunty Akila ya ya Areef ya ce kizo muje ɗakina ki yi wanka ki shirya kafin yaya Aseef ya shirya su Abba suna jiranku". Sakin hannayen Akilar ya yi tare da riƙo na Rimshar yana faɗin "Me ya kumbura miki idanu our Queen?". Ɗan murmushi ta yi kafin ta ce "Kuka na yi ne da aka ce ka rasu". Ɗan rungumota ya yi yana bata hakuri, da yake shi bai san cewa Lion yana jin kishi idan suka yi hakan ba, shiyasa har yanzu bai dena rungumar tata ba, Areef dai ya dai'na bawan Allah, dan ya karanci ɗan uwan nasa tsab. "Muje ko our Queen?" Cewar Akikar, ta miƙe dan su tafi ya yi maza ya saki Rimsha ya riƙo hannunta ɗaya yana faɗin "Shi ne zaki tafi babu sumbata bare kiss". Kallon Rimshar Akilar ta yi kafin ta dawo da kallonta kansa, duk ya jefasu cikin kunya shi ko a jikinsa, hankalinsa a kwance ya faɗi maganar. "Aunty Akila idan kin fito wannan ɗakin, ɗakin da yake kallon wannan ɗin shi ne namu". Cewar Rimsha ta kai karshen maganar tare da juyawa abinta ta fita, dan ba zata iya tsayuwa ba, irin wannan kalamai na Aseef ai sai shi AKila ɗin. "Heartbeat ka sanya Rimsha jin kunya ta gudu". Janyota ya yi ta faɗa saman jikinsa yana faɗin "Ke dai kika sanyata ta gudu ni babu ruwana, yanzu dai a bani sumbata". Kallon balcony ɗin ta yi in da Lion yake kenan, sumbatar lallausan kumatunta ya yi kafin ya ce "Shi fa Lion babu ruwan sa da mu, dan haka ki ma dai'na kula shi, ko shekara zaki yi a cikin ɗakinsa wlh ba lallai ya ɗago idanu ya kalle ki ba, dan haka ni a bani sumbata ki dai'na wahalar mini da kanki". "To rufe idanunka". Ba musu ya rufe ruff, a kumatu ta manna mishi haɗaɗɗiyar sumbata tare da miƙewa daga jikin nasa ta nufi waje da sauri dan kada ma ya ce zai yi mata wani abin da ya fi sumbata ga su Abba na jiransu. Ƙayatattacen murmushi ya saki yana binta da kallo har ta fita, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya miƙe da nufin ya shiga toilet ɗin, wani irin jiri ne ta ɗebesa ya faɗa saman bed ɗin, dafe kansa ya yi dan wani irin sara mishi da ta yi, shiru ya ɗan kwanta na ƴan mintoci da basu wuce biyar ba kafin ya sake ƙoƙarin miƙewa, still akwai jiri sosai a tattare da shi, hakura ya yi da miƙewa ya zauna yana mayar da numfashi. After some minutes ya kira Lion akan ya zo ya taimaka mishi ya shiga toilet jiri sosai yake ji, cikin natsuwa ya shigo cikin ɗakin. Ya miƙe bari ya gani ya ce mishi, mikewa da zai yi ya sake yunkurin faɗuwa saboda jirin, tare shi ya yi yana kare mishi kallo, wato dai bai dawo normal ba har yanzu, sai sun bashi treatment na musamman, dama ai irin wannan yankar kauna da aka yi musu dole suyi rashin lafiya. Tallafa mishi ya yi zuwa toilet ɗin, da kansa ya haɗa mishi komai da komai, daga karshe ma sai ya ce bari ya yi mishi wankan kawai, da yake shi ma Aseef ɗin sarkin shagwaɓa ne sai ya ce Okey, can kuma kome Lion ɗin ya tuna, sai ya ce no ya fasa yi mishi ya yi kawai da kansa, turo baki ya yi yana faɗin shi fa ba zai iya ba, jikinsa duk ciwo yake yi mishi, ko sabulun wanka ba zai iya rikewa ba, ba zai iya zuba su shampoos a gashinsa ba, kai mikewa ma ba zai iya yi ba, Lion ɗin ya yi mishi wankar kawai, sam bai kula shi ba ya fice daga toilet ɗin ya barshi, dan Aseef sai Allah. Da yaga da gaske Lion ba zai yi mishi wanka ba sai ya lallaɓa ya yi, a wannan karon ba shagwaɓa ba ne, da gaske yana fama da bala'in jiri ne da ko miƙewa ba zai iya yi ba, shi ne yasa ya yarda ayi mishi wankar, amma da yaki yi mishi haka ya lallaɓa ya yi wa kansa, da dafa bango ya isa wajen kyawawan fararen towels dake gere a ma'ajiyarsu ya ɗauko ɗaya ya ɗaura a kugunsa, bawan Allah da kyar ya fito daga cikin toilet ɗin, Areef kawai ya samu a cikin ɗakin. Yana ganin ɗan uwan nasa nata faman dafa bango ya miƙe da sauri ya kariso gare shi yana tambayar ko lafiya, kukan shagwaɓa ya saka mishi yana faɗin "Bana iya tafiya ne, idan na sake bangon zan faɗi saboda jiri". Cikin zolaya ya ce "Zaka sha allurai kenan". "Kai fa Areef mugu ne wlh, to ba sai ku yi ta yi mini alluran ba, kada ku bari sai kunga na mutu". Rungumo shi ya yi yana faɗin "Haba our heartbeat, kasan fa lafiyarka shi ne kwanciyar hankali a gare mu, alluran dole ce zata sanya ayi ai". Ko sannu bai sake cewa ba, ya cigaba da turo baki. Saman mirror chair ya zaunar da shi tare da fara shafa mishi Lotions na Lion masu daɗin kamshi kyau da kuma tsada, a wannan hali Lion ɗin ya shigo hannunsa rike da farar jallabiya ya same su, miƙawa Areef jallabiyar fara kal da ita ya yi yana faɗin ya sanyawa Aseef ita, a bedroom ɗin Aseef ɗin ya je ya ɗauko mishi, karɓa ya yi ashe da short da singlet a jiki, sai suka faɗi kasa dan a tunaninsa jallabiya ce kawai ya karɓa. Ɗauka ya yi tare da shirya ɗan uwan nasa ya shunfiɗa mishi dadduma tare da taimaka mishi zuwa saman daddumar ya zaunar da shi, dole a zaune zai yi sallah dan ba zai iya tsayuwa ba, jiri zata kayar da shi, shi kuma Lion balcony ya koma ya zauna ya cigaba da abin da yake yi. A can Palo kuma sai hira su Abba suke yi, yanzu sun saki jiki da daddyn Rimsha, dan ya nuna musu babu komai, komai ya wuce, za su tafi gida Areef ya ce sam sai sun tsaya, haka ba dan sun so ba suka tsaya suka ci abinci, da yake su sun saba cin irin abincin a Russia, san basu wani ji komai ba, Mark ne ya yi serving nasu, da farko sun ki yarda su ci abinci, sai da daddyn Rimsha ya saka baki, hakan tasa suka hakura suka ci, shi dai Irfan bai ce komai ba, ya yi shiru, dan shi dama ba shi da yawan magana, daga um sai umum, har cikin ransa ya ji zafin rasa AKila, amma bai nunawa iyaye nasa ba, da suka bashi hakuri ma bai ce komai ba, bawan Allah ya danne sosai, amma fa har azzaɓi yake ji mai zafi, sai dai bai bari sun gane bane. Bayan Aseef ya gama idar da salla ne Areef ya taimaka mishi zuwa palo wajen su Abba dan ya gaisa da surukan nasa, ita ma Akila ta yi wanka ta yi sallah yanzu tana shiri, kayan Rimsha ta sanya, da yake Abaya ce sai suka ɗan yi mata daidai, ita dai Jehan tana kwance saman bed ko sannu bata ce da Akilar ba, ita ma Akilar da yake tana sauri bata kula ta ba, a tunaninta ma barci Jehan ɗin take yi. A can palo kuwa, da fara'a suka tarbi Aseef dan sun ga yadda daddyn Rimsha yake kaunarsa, so ko dan ɗan uwansu Hosain dole zasu so Aseef, cikin mutunci suka gaisa, sai murmushi daddyn Rimsha yake yi, yau Aseef ya sami AKila. Da zuwansa palon bai fi da 5mins ba Rimsha ta fito tare da AKila, ita kam Jehan tana ɗaki, ta ce ba zata zo ba dan suna cika mata kunne da surutu, so gara mata ta yi ta kwanciyarta a cikin ɗakin. Tun da ta shigo Aseef ya tsareta da idanu yana kallonta, ta yi kyau sosai abinta, kusa da Abba ta je ta zauna, ita kuma Rimsha ta juya ta koma sama dan ta je ta gyarawa Lion ɗakinsa. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin ɗakin, yana balcony yana zaune, amma kuma zucuyarsa yana son ganinta, dan yau basu da kwanciyar hankali basu haɗu ba sam. Gyaran bed ta fara yi mishi kafin ta share ɗakin duk da ba datti, ta yi mopping da kyau, ita ma tana kewarsa, tana begen ganin kyakkyawar fuskarsa, sai dai bata san yana cikin ɗakin ba, ta yi tunanin ya fita ne, dan haka data gama gyaran sai ta haye saman sofa ta kwanta tana mai da numfashi, ta gaji sosai ɗan wannan aiki da ta yi. Ta ɗauki a kallah 10 mins kwance a wajen tana hutawa, ta yi shiru tana kallon sama, yanayin kwanciyar da ta yi kuma yasa wani ɓangare na daga cikin zanen sunansa da ta yi a kirjinta ya fito, saboda ta kwanta ne a mike tana kallon sama, so kunsan yadda wuyar normal abaya kuma take, tana da ɗan girma, bare ita da bata gama cika sosai ba, wuyar ta yi mata yawa kaɗan. Sam bata ji shigowarsa cikin ɗakin ba sai ganin inuwar mutun ta yi a wajen mirror ta wutsiyar idanunta, da sauri ta miƙe zaune tana faɗin "Yaya Saif in kawo maka abinci?". Ko sannu bai ce mata ba, miƙewa ta yi zata fice daga cikin ɗakin, zazzakar muryarsa ne ya daki dodan kunnenta. "Yaushe zaku gama exams?" Ya yi maganar ba tare da ya juyo ba, amma yana kallonta ta cikin mirror, ita ce dai bata kallon face nasa sai bayansa. "Saura kwana uku ne yau nake tunani". Ta bashi amsa, Jinjina mata kai ya yi dan yana son barinta ta kammala Exams nata kafin su yi tafiya, baya wasa da karatu, yana ɗaukar ilimi da daraja da mahimmanci over, shiyasa baya yi mata wasa da karatunta. "Yaya Saif in kawo maka abinci?". Ta sake tambayarsa. "Ki kai mini garden". Ya faɗa tare da wucewa ya nufi toilet. Wani irin daɗi ta ji yau ta yi magana har sau biyu da shi kuma dukka ya amsa, da idan ya amsa sau ɗaya ko zaka shekara kana sake yi mishi magana ba zai sake amsawa ba. Palo ta nufa, sai nasiha ta tarar su Abba suke yi wa Akila da Aseef, kasa kunne ta yi tana jin abin da suke faɗe da ta shiga kitchen ɗin, sai kuka Akila take yi ta kwanto kanta a cinyar Abba, faɗa sosai suka yi mata, har ta daddyn Jelly sai da ya yi mata faɗa, sannan suka dawo kan Aseef ɗin shi ma suka yi mishi nasiha sosai a kan aure, sosai ya natsu yana jin su har suka kammala, cikin sanyin murya ya ce "Nagode sosai uncles, kuma nayi muku alkawarin In Sha Allah zan kula da Heartbeat sosai, zan kula da duk wasu hakokinta da ya rataya a kai'na, ba zan iya biyanku ba abin da kuka yi mini, sai dai nayi muku addu'ar samun rahmar Ubangiji a duk in da kuke, bani da wasu kalmomi da zan yi muku godiya da shi face addu'ar nan dai". Areef ne ya karɓi zancen da cewa "Gaskiya mun gode sosai da irin halakci da kuka nuna mana, we really appreciate Allah ya biya ku da mafificin alkhari". Amin suka amsa da shi kafin su ce daddyn Rimsha ya rufe musu taron da addu'a zasu tafi, shi dai Lion duk abin da suke yi yana ciki abinsa, bai ma san suna yi ba, ya yi wanka yana shiryawa cikin kayan barci, abin da ya faru tsakaninsa da Rimsha ne yake ta yi mishi yawo a kwakwalwarsa, idan ya tuna ya hura mata iska a baki sai zuciyarsa ta amsa, lallausan laɓɓanta sun tsaya mishi a rai sosai, kamar yadda Malika ta yi tunanin zai faru, hakan kuwa ya faru, sun tsaya mishi a rai ba kaɗan ba. Ita kuma Rimsha da ta gama jin nasihar sai ta kwashi kayan abincin ta wuce garden da su, bayan ta kai ne ta dawo ta yi wanka tare da shiryawa cikin kayan barci riga mai dogon hannu da kuma wando dogo, sai ta ɗauki hijabi ta sanya a saman kayan bayan ta gama fesa perfume a jikinta, sai zuba kamshi take yi, ta yi kyau abinta sosai. Garden ɗin ta koma, har lokacin bai zo ba, zama ta yi saman sofa dan ta jira shi, su kuma su Abba, bayan sun kammala addu'a da duk wani nasiha da zasu yi, suka yi musu sallama, har wajen motocinsu dake wajen gate daddyn Rimsha da Areef suka rakasu, sun bar Akila da Aseef a palon, sai kuka take zubawa. Ba zai iya miƙewa ya je kusa da ita ba bawan Allah, jiri yake gani, dan haka sai ya rinƙa rarrashinta daga in da yake zaunen har su Areef suka dawo suka same su, daddyn Rimsha ne ya rungumota ya rinƙa bata hakuri yana rarrashinta, shi kuma Areef ya taimakawa Aseef ɗin zuwa bedroom ɗin Lion dan su bashi abinci da kulawa ta musamman dan tabbas akwai ciwo a jikinsa. Suna shiga bedroom ɗin shi kuma Lion yana fitowa shirye cikin kayan barci masu kyau da tsada, riga ce da doguwar wando masu bala'in laushi, sai dai ya ɗaura jacket a saman kayan nasa, dama haka yake yi in dai zai ke garden, yana sanya jacket saboda cikin dare sanyi mai ratsa kashi yana sauka a wajen. Ko sannu bai ce musu ba ya wuce zuwa palon kasa sai zuba daddaɗar kamshi yake yi. A nan ya wuce Akila da daddyn Rimsha ko kallon in da suke bai yi ba. Da sallama kasa kasa ya shiga garden ɗin, tana zaune tana taunar chewing gum da Anaya ta bata dayawa a school yau, shi ne ta zubasu a cikin jakarta take aikin tauna guda biyu, shakar daddaɗar kamshin perfume nasa ta yi tare da lumshe idanu. Saman sofa ya zauna ba tare da ya yi mata magana ba, miƙewa ta yi ta dawo kusa da shi ta zauna tare da fara zuba mishi abincin, bayan ta zuba mishi ta tura mishi ne ya ce ta je ta kawo mishi laptop nasa a bedroom nasa, okey ta amsa mishi da shi tare da miƙewa. Kunna wutar screen ɗin wayarsa ya yi ya duba time 9:30pm jawo abincin ya yi ya fara ci cikin natsuwa da class, a haka ta dawo ta same shi, kusa da shi ta ajiye mishi laptop ɗin tare da komawa saman sofa ta kwanta tana tunanin yadda zata kaya a ranar da zasu gama exams, suna da party a school ɗin nasu, tasan daddynta, yaya Areef, yaya Aseef duk zasu je, amma ta so ace Lion ma zai je, sai dai ko a mafarki ta san ba zai taɓa yiwuwa ba, dan kuwa bata ga mai sanya shi zuwa ba, bama wanda ya isa ya tinkare shi da maganar, amma bata da burin da ya wuce ya je ɗin. Wayarta ne ya fara kara, dubawa da zata yi sai ta ga new number ne, kamar ba zata ɗauka ba, sai kuma ta ɗauka, karawa ta yi a kunnenta a sanyaye kasa kasa ta ce "Hello". "Kin fara barci ne Rimsha". Daga ɗayan ɓangaren uncle Faisal ya faɗa, "Aa uncle ban yi barci ba ina wuni". "Lafiya lou ya karatun exams?" "Lafiya lou Alhadulillah" ta bashi amsa tana kallon yadda Lion yake cin abincinsa cikin kwanciyar hankali. "Yau dai nayi sa'a da kika ɗauki kirana, ban san meyasa baki son ɗaukar kirana ba Rimsha". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Babu komai uncle ai wayar ce bata hannuna shiyasa, amma kai ma kasan ai ba zan ki ɗaukar call naka ba, kuma.......". Bata kai karshen maganar ba ta tsaya cak sakamakon ido da Lion ya wurga mata, ga shi dare ne idanun nasa sun kara kyalli, nan take ta nemi natsuwarta ta rasa, duk tabi ta dibirbir ce, bai ce da ita komai ba, ya dai tsareta da idanu yana kallon face nata, duk da ta kawar da kallonta daga kansa, amma ta kasa cigaba da yiwa uncle Faisal ɗin magana, sai hello, hello yake ta cewa, amma ta kasa amsawa. Almost 2 mins suna haka, bai kawar da kallonsa daga kanta ba, ita kuma bata cigaba da wayar ba, shi kuma uncle Faisal bai katse kiran ba, dan a cewarsa idan ya katse da wuya ya sake samu ta ɗauki kiransa, so gara ya saurara ya ji. Hannu Lion ɗin ya miƙa mata a kan ta bashi wayar tata ba tare da ya yi magana ba, ba musu ta miƙe ta karisa gabansa, cikin natsuwa ta miƙa mishi wayar, karɓa ya yi tare da cewa ta zuba mishi ruwa. Mamaki take yi, ta fara tantama a kan Lion gaskiya, duk yadda aka yi yana jin Hausa, domin kuwa duk maganar da suka yi da uncle Faisal da hausa suka yi shi, idan ba ya ji me suka ce ba, me zai sa ya karɓi wayarta? To me ma zai yi da wayar? Sai tambayoyi take jerawa kanta har ta gama zuba mishi ruwan ta miƙa mishi. Shi kuma bai bi ta kan call ɗin da suke yi ba ya ajiye wayar a gefensa tare da karɓar ruwan ya kafa a bakinsa, abin da ya faru tana can tana waya ya ce ta bashi ruwa bata ji ba, shi ne ya ɗago ya tsareta da idanu, da ya ga bata da niyar zuwa ta zuba mishi ruwan, sai ya ce ta kawo mishi wayar daga yau ya kwaceta kenan. Sai magana uncle Faisal yake yi, Lion ɗin ya ajiye wayar ma bai kula ta ba, zata kwashe kayan abin ne ya ce mata ta zauna ta cinye sauran abincin da ya rage, dama tana jin yunwa sosai, dan haka sai ta zauna ta fara ci, shi ma Lion ɗin yasan tana jin yunwa sosai ne shiyasa ya ce ta zauna ta ci, yasan duk wanda yake gidan nan yau to da yunwa ya wuni, dan basu da kwanciyar hankali, basu bi ta kan abinci ba sam. Tana tsaka da cin abincin ne Brady ya shigo cikin garden ɗin da gudu, wani irin girgiza ya yi na ganin Lion, da gudu ya haye jikinsa, da gani yana cikin tsantsar farinciki, shafa jikinsa Lion ɗin ya fara yi yana ƙoƙarin ɗauko wayarsa kira ya shigo wayar Rimshar, number uncle Faisal ne. Da farko kamar ba zai kula ba, sai kuma ya yi picking call ɗin tare da sanya wayar a hand-free, daga ɗayan ɓangaren uncle Faisal ya fara magana "Gimbiya sarautar mata, yau rana ta ce mai sa'a, ban yi tunanin zaki sake ɗaukar kiran ba, gaskiya naji daɗi kuma nayi sa'a, ɗazun ya akayi kika yi shiru muna magana?" Wannan karonfa uncle Faisal da turanci ya yi maganar tasa dukka. Ɗago ido Lion ya yi yana kallon Brady, ita kuma kwarewa ta yi ta fara tari kamar wata mara gaskiya, ɗaukar wayar ya yi tare da bin number uncle Faisal ɗin da kallo, kallo ɗaya ya haddace number a kansa, sai hello uncle Faisal ɗin yake ta faɗa, katse kiran ya yi tare da yunkurin miƙewa zaune, dan ya fi karfin ya yi magana da uncle Faisal ɗin, tsabar tsadar maganarsa ba kowa yake samu jin voice nasa ba, wani abin ba sai ya yi magana ba yake ɗaukar mataki a kai, in ji sojojinsa suka ce shirunsa ma magana ce. Sauka daga jikinsa Brady ya yi dan ya bashi damar miƙewa. "Waye shi?!" Shi ne tambayar da ya wurga mata, wani irin haɗiyar wahalallen yawu ta yi, "Uncle namu ne" da kyar ta iya bashi amsar, tunani ya fara yi a ransa, au dama su uncle ɗin an tura musu yara ne dan su yi ta kiransu a waya suna gaya musu wasu maganganu marasa kan gado? Dama ba karatu suke koya musu bane ko yaya? Yanzu shi da girmansa yana malami ne zai kira karamar yarinyar da yake koyarwa yana faɗan hakan? Anya malan ƴan Nigerian nan kansu ɗaya kuwa?. A fili kuwa ɗaure fuska sosai ya yi dama fuska ba'a magana, kullum a ɗaure take. "Dama ba karatu kike zuwa yi a school ɗin ba kenan?". Ɗago kai ta yi dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa idanu, ganin yadda fuskarsa take ne yasa ta miƙe a guje dan ta bar wajen, saboda kada ya naɗa mata duka, ai yanzu tsoronsa ya kara ninkuwa a ranta tun shekaran jiya da ya kusa kasheta, ba dan Areef ba da yanzu idan bata cikin kabari to tana gadon asibiti. Wani wawan damka ya kai mata a ciki tare da jawota baya, tafiya ta yi luuuu sai saman faffaɗar kirjinsa ta faɗa, wash ta furta da karfi, shi kuma hannu yasa ya damko wuyarta ta saman hijabin, rai a matukar ɓace ya ce "Me kike zuwa yi a school?" Girgiza mishi kai ta fara yi ta ji shaƙa, nan take ta fara ganin wasu hayaniya suna gilma mata ta cikin idanu, shi kuwa ransa kara ɓaci yake yi idan ya tuna cewa yanzu idan ta je school kenan tsayawa take yi da maza suna hira, har da basu number wayarta, wato ta yi girman da zata yi hira da namiji? To ta ce mishi menene ma?. Tuna hakan yasa ya kara shaketa da karfi har sai da harshenta ya fito waje sosai, "Me kike zuwa yi a school?!" Ya sake tambayarta idanunsa sun riƙiɗe sun yi jawur da su, sai ƙoƙarin bubbuga hannunsa take yi dan ya saketa kada ta mutu, idanuwanta sun yi jawur kamar jini, sun ciko da kwallah tab, azababben kishi ya rufe mishi idanu zai yi kisan kai a banza. Ganin zata mutu da gaske ne shi kuma bai ma damu ba yasa Brady ya fara daka mishi haushi yana kokarin cire hannunsa daga wuyarta, tabbas da ya kara minti ɗaya shake da ita ba makawa mutuwa za ta yi, dan kuwa ta shaku ba karya, ya matse wuyarne na wuce misali ta yadda ko numfashi baya wuce nata. Sai da ya tabbatar ta galabaita ta kusa mutuwa sannan ya saketa yana wani huci kamar mayinwacin zaki. Kokarin kama shi ta fara yi dan ta miƙe ta sauka daga jikinsa, ruwa kawai take son sha, yau a karo na biyu ta ji kamshin lahira dukka kuma a hannunsa, ranar ta farko shaketa da ya yi a bedroom nata lokacin da ta ɗauki kiran daddynsa, sai dai fa shakar yau ta fi shan azaba, dar har sai da harshenta ya zazzago waje, ta kusa bakuntar lahira. Damko wuyar rigarsa ta kirjinsa ta yi cikin fitar hayyaci tana kokarin mikewa ta kasa, ta riƙe wuyarta da hannu ɗaya, sai ruwan hawaye take yi, babu karya ta azabtu na wuce misali. Duk azababben bakin kishin da yake ji, bai hana ya ji tausayinta ba ganin halin da take ciki, ciza laɓɓansa ya yi tare da ɗauko ruwa a cikin kayan abincin ya buɗe bakin robar, tallabo kanta ya yi a gefen kirjinsa ya kafa mata robar a bakinta, sha ta fara yi babu kama hannun yaro, sai wani irin numfashin take yi, ta fita a hayyacinta sosai, komai bibbiyu take gani, harta shi kansa bibbiyu take kallonsa. Allah sarki ita kuma nata kaddaran kenan, wannan azababben bakin kishin nasa, da shi take azabtuwa matuka, idan ya damketa sai ta ji kamshin lahira. Sai da ta shanye ruwan tas kafin ya cire mata robar daga bakinta, yana cire mata ta lafe a kirjin nasa tare da runtse idanunta tana sauke nauyayyar ajiyar zuciya, da alama har yanzu bata dawo daidai ba. Sake kiran wayar tata uncle Faisal ya yi a karo na uku, wani irin wurgi ya yi da wayar ta daki jikin glass dake kewaye da wajen ta tarwatse, jin hakan yasa ta yi kokarin barin jikin nasa, rikota ya yi da karfi yana sake tambayarta me take zuwa yi a school dama?. Ganin hakan yasa ta kwanta a kirjin nasa kawai tana kuka kasa kasa mara sauti mai tsuma zuciyar mai sauraro, sai dai sam shi kam bata tsuma mishi zuciya ba gaskiya, azababben kishi ya rufe mishi ido. "Yaya Saif wlh bana kula shi, shi ne nan yake yi mini magana, kuma ni bani na bashi numberta ba, wlh Anaya ce ta bashi, ka kira shi ka tambaye shi ko ya kirani bana ɗauka, wlh ni karatu nake zuwa yi a school ba wani abu ba, zaka iya tambayar Mark ka ji, Allah banda karatu babu wani abin da nake yi". Da kyar take yin maganar muryarta na gargada, ta kai karshen maganar tana sakin kuka mai sauti sosai, ta wahala sosai ƴar kaniya. (Tab uncle Faisal ma kenan, to ina ga ya ji labarin Mr Emmanuel kuma da abin da yake yi musu kuma?🤔 Ina ga lahira ne kawai zata yi bako) Har cikin ransa ya ji sanyi dan ya yarda da maganarta, yasan bata yin karya, idan kaji ta yi karya to da kwakkwaran dalilinta na yin hakan, so ya yarda da abin da ta faɗa yanzu, ya kuma ji sanyi sosai a ransa, dan haka sai ya sauke Nauyayyar ajiyar zuciya tare da lumshe idanunsa, sai a lokacin ne kuma ya fara jin sautin kukan nata yana ratsa shi, har cikin ransa ya ji ba zai iya jure kukan nata ba, waro idanuwansa ya yi a saman face nata, idanunta a datse gam. Zuba mata idanu sosai ya yi yana kallonta, nan take tunanin laushin laɓɓanta ya dawo mishi cikin ƙwaƙwalwarsa, kai kallonsa saman Lips ɗin nata ya yi yana jin wani irin yanayi a jikinsa, ji yake yi tamkar ya kai hannu ya taɓa su, ga shi yadda take kukan hancinta ya toshe saboda tana kwance ga kuma kuka, dole ta baki take numfashi, so time to time tana motsa laɓɓan nata dan fitar da numfashi, duk kuma time ɗin da ta motsa su sai dimples nata sun lotsa, ba karya suna kara tafiya da imaninsa ba kaɗan ba, duk abin da yake saman face nata ba karamin kyau yake yi mishi ba. Motsa laɓɓanta ta yi dan ta ja hanci, nan take dimples nata suka yi wani irin lotsawa sosai, bai san time da zuciya ta ɗebe shi ya sanya yatsarsa ɗaya a cikin ramin dimple ɗin nata ba, suna yi mishi tsantsar kyau, sam shi ma yanzu baya cikin hayyacinsa, ya yi nisa a kallon abubuwan da suke burge shi, bugu da kari gata kwance a kirjinsa, ai dole ma ta sanya shi shiga wani duniya. BAKA GA KOMAI BA, AN GAYAMAKA MATA WASA NE? Ɗan motsa latsan nasa ya yi a cikin ramin dimple ɗin nata yana mai jin wani irin yanayi, bata san lokacin da ta tsayar da kukun nata ba jin hannunsa a face nata, tana tsoron ta waro idanu su haɗa ido da shi, dan haka sai ta danne duk da cewa tana son kallon meyasa ya sanya yatsansa a dimple ɗin nata, a hankali ya ɗan shafa kumatunta tare da shafo hawayen nata, shiru ta natsu tana jinsa, bawan Allah ya fita a hayyacinsa, yau ma a karo na biyu ya faɗa tarkon mace. (A gaskiya Justice for Lion😭 Malika bamu yafe ba, kina son lalata bawan Allah😭 anyi breaking heart nawa a garden ɗin nan💔😭😌) Babban yatsansa ya ɗaura saman lips nata yana ɗan shafawa a hankali tare da lumshe dara daran blue nasa, dan shi kaɗai yasan me yake ji, while har lokacin hannunsa ɗayar tana saman lallausan kumatunta. Ta kasa jurewa hakan yasa ta buɗe idanunta dan ta ga wai shi ne ko an canza shi ne? Ko dai yana neman in da zai yanke mata ne yau kuma a jikin nata. (Wayyo cikina, Rimsha da Lion duniya🤣 wai yana neman in da zai yanke omg, wlh salonku daban yake da kowa💃) Ganin idanuwansa a lumshe ne yasa ta tsare shi da idanu tana mamakin abin da yake yi a face ɗin nata, tunani ta fara yi to ko dai Malik ce ta shaga jikinsa? Bata san ita ma Malika tana can tana zuba soyayya a duniyarsu ba, yau kwana wajen uku ma Malika bata sauko duniyar mutane ba, kawai dai yanayi ne da kuma tarkon da Malikan ta kafa mishi da farko ya kuma faɗa, su ne kawai suka sanya yake yi mata hakan. A hankali ya zura latsar tasa cikin bakin nata tare da fitar da chewing gum da yake ciki ya jefar a kasa sannan ya cigaba da ɗan murza laɓɓan nata, da alama fa wlh baya cikin hayyacinsa, hannunsa dake saman kumatunta ya zame a hankali tare da mayar da shi saman............. ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ 💋Dedicated to myself...✍️🔥❤️ E59-60💋 A hankali ya zura latsar tasa cikin bakin nata tare da fitar da chewing gum da yake ciki ya jefar a kasa, sannan ya cigaba da ɗan murza laɓɓan nata, da alama fa wlh baya cikin hayyacinsa, hannunsa dake saman kumatunta ya zame a hankali tare da mayar da shi saman kanta, a hankali ya zame hijabinta daga kanta zuwa wuyarta, lallausan dark black curly hairnta ya fara shafawa har lokacin idanuwansa a lumshe. Ita dai ta zuba mishi ido tana kallon ikon Allah yau, ta kasa koda motsawa, gangaro da hannunsa ya yi zuwa saman dogon wuyarta da yake yawan shakewa, a hankali ya fara shafa wuyar tata yana wani irin numfashi, abin da bai taɓa yi ba a rayuwarsa bai ma taɓa tunanin zai taɓa kwatantawa ba, daidai in da ya shaketa ɗazun ya tsayar da hannunsa shiru kamar mai tunanin wani abin, sai kuma ya zame hannun nasa gabaɗaya daga jikinta ya mayar cikin dark black curly hairnsa ya fara watsawa, miƙewa ta yi daga jikinsa a hankali, bai hanata ba dan da alama ya shiga duniyar tunani, bai ma ji mikewan nata ba. Wajen wayarta ta nufa, a hankali ta ɗauko, screen ɗin ya yi raga raga ya tarwatse, ta ji babu daɗi, amma bata ce komai ba, kwanikan abincin ta zo ta kwashe ta nufi cikin gida hijabin yana wuyarta bata mayar kanta ba, shi kuma a hankali ya fara sauke numfashi mai ɗauke da wasu abubuwa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa. Shi kuma Brady ya kama kansa ya tafi yawo, dan dama baya wani zama waje guda, yanzu ma daga wajen Aseef ya fito. Ko da ta je shiga cikin gida kofar palon a rufa, ajiye kayan abincin a wajen ta yi tare da dawowa garden ɗin, ɗan gefensa ta tsaya tana kallonsa, a hankali yake sauke numfashi irin na mai barci, da alama ya yi barci, lallaɓawa ta yi ta ɗauki wayarsa dan ta kira daddynta ko kuma Areef ya zo ya buɗe mata kofa. Wayar da akwai password a jikinta, kokarin gwada buɗewa ta yi tana ɗan satar kallon shi, sunan Aseef ta fara sakawa, nan take wayar ta fara kara dan wrong password aka saka mata, wani irin razana ta yi jin yadda wayar take kara tamkar jiniyar motar ƴan'sanda, a hanzarce ta ɗago dara daran sleeping eyes nata ta saukesu a kansa, ko motsawa bai yi ba, amma dai ya farka daga barcin dan bashi da nauyin barci. Jikinta na kerma ta mayar mishi da wayar ta ajiye tare da komawa saman sofar dake kusa da shi ta zauna tana tunanin ko dai ta je ta buga kofar ne wani ya zo ya buɗe mata? Sai dai ko ta buga ma ba zasu ji ba. A can cikin gida kuwa, bayan tafiyar su Abba, bedroom ɗin su Jehan Areef ya wuce dan ya je ya tsokane ta kamar yadda ya saba yi bayan ya kai Aseef bedroom ɗin Lion ya duba lafiyarsa tare da bashi abinci kenan. Da sallama ɗauke a bakinsa ya faɗa cikin ɗakin, tana kwance ta yi shiru tana tunanin duniya, ta manta da wayar Adiva dana Abubakar jaja da ta ɗauko, wayoyin suna ɗakin da daddynta ya sauka, suna bayan gado ta ajiye su, sai dai duk sun mutu babu charji. Saman bedside drawer ya zo ya zauna yana faɗin "Tashi muje na baki abincin a baki dan nasan yunwa kike ji". Tamkar babu ita a ɗaki, sam bata kula shi ba, hannu ya kai ya ja dogon hancinta yana faɗin "Wai ke baki dariya ne? Ni na gaji da kallon face naki tamkar na Lion ɗin nan, na je ɗakin Lion naga Tiger face, kema nazo wajen ki naga Tiger face, ina kuke son na saka raina naji daɗi to? To ni nagaji gaskiya!". Still ko sannu bata ce mishi ba. Zai sake yin magana sai ga daddynta ya shigo rike da hannun Akila, kara faɗaɗa murmushin kan face nasa ya yi kafin ya ce "Uncle ka ce baby ta tashi muje na bata abinci ko kuma na ɗauke na je na yi mata ɗure kamar baby". Ƙayatatcen murmushi daddyn ya saki yana faɗin "Ai dole ma ta tashi amma yanzu bari ta rarrashi ƴar uwarta tukunnan, ina Rimsha?". Kallon Jehan ɗin suka yi suna jiran amsar ina Rimsha, turo baki tayi kafin ta ce "Daddy Rimsha ta tafi kaiwa wani wai yaya Saif abinci, wai daddy waye shi? Kuma ita Rimsha dama ƴar aiki ce?". Ta kai karshen maganar tare da mikewa zaune tana cigaba da cewa "Wai yarinyar nan ina cewa kada ta je tana ce mini bata shirya mutuwa ba, ban gane bata shirya mutuwa bane? Kisa akeyi a gidan ne ko yaya? Shi ne nake jiran ta dawo ta yi mini bayani". Kallon Areef daddyn ya yi yana faɗin "Sai ka gaya mata waye Saif". Wayarsa ya ciro tare da fito da hoton Lion ɗin ya nuna mata, kallon hoton ta yi ba tare da ta karɓi wayar ba, wani irin mummunar faɗuwar gaba ta ji ganin fusataccen fuskarsa, nan take ta sha jinin jikinta, dan kuwa wlh ganin face ɗin Lion a ɗaure dole ya raza mutun, ga uban kwarjini da Allah ya yi wa TRIPLETS kamar me, shi ma Areef ɗin dannewa kawai take yi tana yi mishi abin da taga dama dan taga yana dariya ta kuma san bazai yi mata komai ba, amma mugun tsoronsa take ji, sai ɗan banzan farinjini garesu TRIPLETS ɗin nan kamar su suka bawa kansu, ko'ina zasu shiga sai an so su, amma kusantarsu kuma ba kowa yake iyawa ba sai wanda suka so, suka ja shi a jiki. Shiru ta yi bata sake yin magana ba, dan kuwa bata san me zata ce ba, a bata ga laifin Rimsha ba, dole ta ce bata shirya mutuwa ba, wannan mai fuska kamar Tiger face ɗin, a haɗe kamar hadari, yadda damisa bai san murmushi ba shi ma haka bai san menene ko da yake ba bare murmushi har a kai ga dariya, duk bai sansu ba kuma bai taɓa yi ba, bai ma iya ba, bashi da wani sassauci a rayuwarsa, dama dole za'a iya samun haka daga gare shi, dan kuwa matsayin GENERAL OF THE ARMY ba wasa ba, duk wasu sojoji da kuka sani a duniyar nan, duk girman mukamansu kama daga kan BRIGADIER GENERAL, GENERAL, LIEUTENANT GENERAL, MAJOR GENERAL, da sauransu, duk a karkashinsa suke, daga kan mukaminsa babu wani mukami ta sama, shi ne kololuwa, star biyar ke gare shi, shi ne on top, so dama dole a ganshi haka, dan ya tsallake abubuwa da dama kafin ya taka wannan matsayi, ba irin horar da mutane da bayyi ba, kisa ba kalar wanda bai yi ba, babu wani masifa da tashin hankali da bai gani ba, horo kuwa ba'a magana irin horon da ya samu, duk wata wahala ya ganta, dama dole a samu rashin tausayi a tattare da shi, dan tun yana gani yana jin tausayi har zuciyar ta bushi babu komai a cikinta face zallar aiwatar da aiki babu ɗar ko wasa, dole idan aka gansa a razana, dole ya razana maza, dan shi ma ya razana kafin ya taka matsayin, damma dai babu abin da musulci ya bari, musulci rahma ce babba da babu irinta, ta sanya mishi imani, ta sanya ya sauya, lokacin da yake krista, ya ilahi ya lillihi, a lokacin Lion zai iya ɗaure mutun yana yankar wasu sassa na jikinsa har ya kashe shi da haka idan ya yi mishi laifi, babu imani ko ɗigo ko miskala zarratin a ransa, idan babu imani kuma ai babu tausayi, lokacin kam bawani bawa mai imani da zai so jin irin rashin imaninsa da zafin zuciyarsa, baya ɗagawa kowa kafa, haka zalika baya ganin kowa kamar mutun bayan TRIPLETS, tun fil azar bashi da tsaro, ga aiki kamar agogo idan ya yi ra'ayin yi, idan kuma bai yi ra'ayi ba, to fa ba'a haifi wanda ya isa ya ce ya yi ba, ambatar sunansa a waje ba ƙaramin razanar da mutane yake, dayawan sojoji da criminals da ace Lion ya yanke musu hukuncin da za'ayi musu idan suka yi laifi, gara su harbe kansu da kansu da bindiga su mutu yafi musu sauki, dan rashin imaninsa ba'a magana, daddynsa sam bai ishe shi kallo ba, su uncle T sun sha bakar wahala a hannunsa, dan idan suka yi mishi kuskure sai ya bankaresu kamar wasu kajin da za'a gasa, ya yi musu mummunar ɗauri, ya barsu tun safe har gobe da safe ko motsi basu yi, wani lokaci idan ya sanya aka kwancesu ko mikewa basu iya yi, suna zaune ma suna faɗuwa dan azaban wahala ga yunwa da kishi, sai ya shanyasu a rana kamar wasu kayan wanki, a hakan ma dan su na gida ne, duk wata horo na mugunta babu kalar wanda bai iya ba, idan baku manta ba akwai lokacin da daddy ya kirashi a waya da ya ɗauka, ranar daddyn ya yi murna over har yake cewa ba zai manta da wannan rana ba yau Romeo ya ɗauki kiransa, to a lokacin ya musulta ne, ya san hakkin iyaye a kan ƴaƴansu, shiyasa yake ƙoƙarin saukewa, bayan daddynsa su uncle Herry gabaɗaya tsoron tinkararsa da karamar magana ma suke yi, ganin face nasa razanasu yake yi a lokaci, baya magana ya canza koda kuwa mutane goma zasu mutu sanadiyar wannan hukunci da ya yanke, to fa sai dai komai ya faru ya rigada ya yi ta kenan, babu mai iya kusantar shima bare ya tankwara shi, sai dai bayan TRIPLETS nasa yana son kakansa His excellency, amma duk da haka bata hana idan suka sami saɓanin ra'ayi ya yanke abin da yake so, kakan nasu kuma Allah ya jarrabesa da bala'in son Lion ɗin kamar ba gobe, kunsan Turawa idan suna son abu ba'a magana, hakan tasa yake biye mishi, idan nace zan tsaya gaya muku wanene Lion lokacin da yake krista yake amsa sunan Romeo or GAR wlh zamu kwana mu wuni bamu yi ko kwata ba, dan fa ya yi rashin imani tsantsar ta, ga bala'in zuciya na wuce misali, ga azababben kishi tun suna school, baya taɓa bari wani na wucesa a kan abu saboda kishi, shiyasa yake zuwa na farko a komai, dan idan wani ya wuce shi ko da marking ɗaya ne, to ranar baya iya barci saboda azababben kishi da zuciya, sai yaga ya wuce kowa a class ɗin yake samun kwanciyar hankali, haka a wajen aiki kafin ya zama babban baya yarda a wucesa, ga kafiyar bala'i kamar ba gobe, taurin rai da kuma taurin kai kamar me, kai fi ɗaya ne tak!! Ga bala'in tsanar musulmai da bakaken fata, amma lokaci guda kaunar addinin ta yi mishi mummunar shiga sanadiyar Imran, wannan shi ne dalilin musultar, kira'ar AlQur'ani mai girma ce ta ja ra'ayinsa, jin yadda Imran yake rerata ta yi mugun tafiya da shi lokaci guda, da Allah ya kaddara yana da rabon samun rahma sai ya fara karatunta kafin ya musulunta, ya kuma yi bincike sosai a kan addinin tare da karanta littattafan musulci, sai da ya tabbatar da addinin ita ce ta gaskiya kafin ya karɓi kalmar shahada, so silent da shi baya magana kuma baya son hayaniya!!. Da Lion bai musulunta ba lallai akwai aiki ba kaɗan ba, dan kafurar zuciya ke gare shi na bala'i, bugu da kari ga irin tarbiyar da suka samu, ga abin da suka taso a kai na sune sama da kowa a cewar daddynsu, ba wanda ya isa ya ɗaga musu murya, amma yanzu Alhamdulila komai ya yi sauki sosai, am very very proud to be a Muslim wlh, musulci duniya ne, daga kansa kuma babu ma na kusa da shi, shi kaɗai ne, addini mai sauki daɗi ga sakamako mai kyau idan kayi aiki wato aljanna, jama'a aljanna fa babu mai iya kwatanta muku ni'imominta, jama'a ayi aikin Alkhari a shigeta fisabillilahi, dan wlh duniya ba komai bane, aljanna wayyo Allah, Allah ka bamu ita da ni da duk masu karanta littafina dama musulman duniya bakiɗaya, kai idan Allah ya yi ka tsinci kanka a cikin musulci to harka mutu kada ka dai'na gode mishi, yanzu idan ba dan musulci ba ya kuke tunanin rayuwar Lion zai kasance?. (Komai na Lion ya canza kamar ba shi ba, ga shi Malika ta kara sauya mana shi😭 ta mayar da shi ɗan soyayya😭 justice for Lion, gaskiya babu karya Rimsha da iyayenta sun ciri tuta a cikin rayuwar Lion duba da irin rayuwarsa a baya na tsanar musulmai da bakaken fata, sunci albarkacin TRIPLETS nasa ne sosai,) STORY💋 Mayar da wayarsa aljihu Areef ya yi tare da miƙewa ya nufi waje, yana fita ya shiga bedroom ɗin daddyn ya haye saman bed nasa ya kwanta, shi kuma daddy zaunar da Akilar ya yi a kusa da Jehan ɗin yana faɗin "To Jehan ga ƴar uwarki, ki kula da ita kafin Rimsha ta dawo". Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya fita zuwa bedroom nasa. Kwance ya isko Areef yana ɗan latsa wayarsa, yana ganinsa ya miƙe zaune, gefen bed ɗin ya zo ya zauna yana kallon Areef ɗin kamar mai son cewa wani abin, kwanto da kansa ya yi a saman cinyar daddyn yana faɗin "Uncle I really missed you wlh". Shafa gashin kansa daddyn ya fara yana faɗin "Gaskiya dai nima na yi tsananin kewarka my Tiger, ya aiki? Kayi nasara ko?". Jinjina mishi kai ya yi kafin ya ce "I don't know the reason why nake kaunarka uncle, ko Lion na kasa gaya mishi aikin da nake yi a lokacin, amma kai ban ɓoye maka komai ba, kai idan na tuna abin yana bani mamaki fa, gaskiya i really like you my uncle". "I really like you too my Tiger, yanzu dai gaya mini kayi nasara ne? Amma fa ka sakani a cikin damuwa a lokacin, bare ma da na ga halin da Aseef ya shiga na rashinka, har nace gaskiya zan gaya musu gaskiyar in da kake kawai suje su ɗauko ka, sai kuma na tuna nayi maka alkawarin ba zan gayawa kowa ba, amma na sha wuyar danne wannan sirrin naka, dan na kasa jurar ganin tashin hankali da Aseef ya shiga gaskiya". Murmushi ya yi kafin ya shiga bashi labarin yadda komai ya faru tun shigarsa Kasar Spain har izuwa shigarsa South Africa, da kuma isowarsa Nigeria, da kama shi da aka yi a Naija, yadda Lion ya karɓo shi da komai da komai, daga karshe ya gaya mishi ya yi nasara sai dai Lion ya cire shi a cikin hukumar C I A, yanzu haka idan ya sami sauki aikin soja zai fara, Lion ya ce baya son C I A sam. Ba ƙaramin jinjina mishi daddyn ya yi ba tare da zuba mishi addua'o'i da fatan samun nasara, gaskiya daddyn Rimsha ya bawa Areef gudumawa ba kaɗan ba a nasarorin da ya samu, kwana sallah yake yi yana rokan Allah da ya kare Areef ɗin a duk in da yake, ya bashi nasara, ba dan addu'ar da yake kwan yi mishi ba, ai da sun jima da kashe shi a Nigeria, duk azumin da daddy yake a Washington DC Areef ɗin yake yi wa dan ya roka mishi Allah ya tsare shi ya dawo da shi lafiya, da yake ya gaya mishi har in da zai je da kuma aikin da zai je ya yi, shiyasa Allah ya jarrabi TRIPLETS ɗin da kaunar daddyn har ta Lion, dan ya yi musu aikin Alkhari kuma a ɓoye ba tare da sun sani ba, babu aikin da Ubangiji ya fi karɓa da wuri yake baka sakamakon da wuri irin ka kyautatawa bawa ba tare da sanin kowa ba, ka taimakawa bawa ba tare da sanin kowa ba sai Allah kawai, ko shi bawan kada ka gaya mishi kai kayi mishi kaza, to idan Allah ya tashi biyanka zai biyaka ne ta in da kai ma baka yi tsammani ba, shiyasa ga shi yanzu Allah ya jarrabi Lion da abubuwa da dama dan taimakawa daddyn ba tare da sun sani ba, bugu da kari ga soyayyar Rimsha wanda shi kansa Lion ɗin bai san yana yin soyayyar ba, bai san ta ya akayi ta shigesa ba, shi dai kawai yasan baya son wani ya raɓeta ne kawai, amma bai taɓa yarda cewa soyayya bane, dan bai ma san soyayyar ba bare ya ce ita ɗin ce, kawai tana burgesa. "Uncle do you know something?" Girgiza kai ya yi yana mai cigaba da shafa gashin nasa. "Gaskiya ba zan ɓoye maka ba I fall in love with your daughter seriously, and then aurenta nake son yi ba da jimawa ba, so na zaɓi na gaya maka ne tun da wuri". Jan hancinsa daddyn ya yi yana faɗin "I knew, I knew you love her, dama na zuba maka idanu ne kawai ina ganin gudun ruwanka". Cool murmushi ya saki kafin ya ce "Kai uncle ka cika gane mutun serious". "To ba dole na gane mutun ba yana kalle mini yarinya a gabana baya jin kunyata". Kara faɗaɗa murmushinsa ya yi "Allah uncle ka dai'na mana, ni fa bana wani kallonta sosai". "Kana kallonta kam ai na ganka". "Kai uncle, kai uncle, to shikenan ni dai bana son wani ya kula mini ita ne shiyasa na gaya maka da wuri, dan duk wanda ya kulata serious zan cire mishi ido". "Sarakan kishi ba, to ka kwantar da hankalinka kamar ka aureta ka gama, in dai Jehan ce to na baka ita, ko na mutu yau ka ce na bada wasiya a ɗaura muku aure, taka ce kai kaɗai". "That is my uncle, shiyasa nake sonka over, much kauna my lovely uncle". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya sumbaci daddyn a kumatu yana murmushi sosai tamkar bakinsa ba zai rufu ba. Shi ma daddy murmushi sosai yake yi dan har ga Allah yana kaunar Areef ba kaɗan ba, kuma yana taya Jehan murnar samun mutun mai zuciyar zinari irin shi. Haka suka cigaba da hira cikin so da kauna tare da mutunta juna. A ɓangaren Aseef kuwa, bayan ya kammala cin abincin nasa ne ya kira number Rimsha, amma a kashe dan a lokacin Lion ya fasa wayar, kira number Areef ya yi a kan ya turo mishi Heartbeat nasa yana son ganinta, a lokacin suna ta hira da daddyn Rimsha, haka ya miƙe ya nufi bedroom ɗin nasu dan ya kirata, ya ce da daddyn Rimsha yana dawowa su cigaba da hira, ai yau ba barci, an jima ba'a haɗu ba, sai sun yi ta mayar da zancen baya. Lokacin da ya shiga ɗakin nasu, ta gama shiri cikin kayan barcin Rimsha zata kwanta kenan ya ce ta je ɗakin Lion Aseef yana kiranta, bawan Allah baya iya miƙewa saboda jiri, ga azababben ciwon kai. Cikin jin kunya ta amsa mishi da to, komawa wajen daddyn Rimsha ya yi bai kula Jehan ba dan ya ga idanunta a lumshe, a tunaninsa barci take yi, shi ne yasa bai kulata ba ya fice. Hijabin Rimsha ta ɗauka ta sanya a saman kayan barcin nata kafin ta fito waje sai zuba kamshi take yi abinta. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin bedroom ɗin, cike da so da kauna ya amsa mata, saman bedside drawer ta zo ta zauna tana kallon shi kasa kasa tare da tambayarsa ya jiki?. "Kin ci abinci ne?" Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a, hannu ya miƙe mata a kan ta bashi kular abinci da plate ɗin da ya gama cin abincin a ciki yanzu, a nutse ta miƙa mishi, ɗan kallon kayan jikinta ya yi ta kasan hijabin, ganin kayan barci ne yasa ya ce "Baki ci abinci ba zaki kwanta daman?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e, "To meyasa?" Ya yi tambayar yana zuba mata abincin. "To ai ban san a ina abincin yake bane, kuma ban san waye mai girkawa ba". Shiru ya yi dan yasan Rimsha tana wajen Lion ne badan haka ba da zata bata abinci. Mai ɗan yawa ya zuba mata abincin tare da ajiye kulan a kasa ya ɗago dara daran idanunsa yana kallonta. "Zoki zauna na baki". Ya yi maganar tare da nuna mata saman cinyarsa, ɗan zaro idanu ta yi kafin ta ce "Kai da baka da lafiya?". Gera ɗaya ya ɗaga mata alamar e shi da bashi da lafiya ɗin dai tazo ta zauna. "A'a ka bari sai ka samu sauki, yanzu dai ka bani na ci a nan, idan ka samu sauki sai na rinƙa zama a kafar taka kana bani a baki ina baka". Shagwaɓe murya ya yi yana faɗin "Wai ba yanzu su Abba suka gama cewa kada ki yi mini musu ba? Ba sun ce komai nace ki ce okey ba? Shi ne daga tafiyarsu zaki fara ce mini a'a ko?". Girgiza mishi kai tayi alamar a'a tare da miƙewa ta zauna a saman cinyar tasa tana faɗin "Kayi hakuri ba zan sake ba". "Tom Allah ya yi miki albarka". Murmushin ta saki wato ya ɗauki nasihar daddyn Jelly kenan, dan daddyn Jelly ne ya ce mishi ya kasance mai yawan sakawa matarsa Albarka dan addu'arsa a gareta mai karɓuwa ce, idan yana saka mata albarka, to zata yi Albarka sosai, idan kuma ta yi Albarka gidansa ne ta gyaru, dan mace ita ce gida, idan ta yi albarka gida, arziki da komai na miji zai yi albarka, idan kuma ta lallace, to fa miji ko da babban malami ne zaku ganshi sai a hankali, yana tafiya yana magana shi kaɗai kamar zararre dan matar ta haukata shi saboda rashin albarka, Allah kasa maza su zama masu sanyawa matansu Albarka kamar yadda Annabi yake sanyawa su nana A'isha a kullum, Allah kasa mazanmu gabaɗaya ban cire kowa ba da masu aure da marasa aure har yara, Allah kasa su rinƙa koyi da annabin rahma a dukkannin lamuransu dan gyara gobensu. Abincin ya fara bata a baki, cikin natsuwa ta fara karɓa tana ci, sai kallonta yake yi yana murmushi, ita ma yau ba zata iya misilta farincikin da take ciki ba. Ta ci abincin mai ɗan yawa dan tun safe rabonta da abin, cin abinci ta ƙoshi kuma tun ranar da Abba ya ce ya bawa Irfan aurenta, daga ranar ta dai'na cin abinci ta koshi sai dai ta ɗan tsakura kawai dan kada yunwa ya kasheta, yau kuma gata a zaune a saman cinyar Heartbeat nata, yana bata abicni a baki, kai Allah iko kenan, wannan rana ba zasu taɓa mantawa da shi ba dukkansu biyu. Sai da ya tabbatar ta ƙoshi sosai sannan ya kyaleta tare da bata ruwa ta sha. "My shagwaɓati zan je in yi brush, amma bani da brush ɗin ma a nan gidan". Sumbatar kumatunta ya yi kafin ya ce "Jeki bedroom na kiyi, sai ki yi amfani da brush na ko?". "To ban san ina ne bedroom ɗin naka ba ai". Yadda ta yi maganar a shagwaɓe, kwaikwayon muryarta ya yi tare da yi mata kwatancen bedroom ɗin nasa. Miƙewa ta yi tare da ɗaukar kayan abincin ta nufi waje, binta da kallo ya yi yana faɗin kada fa ta jima, okey ta amsa mishi da shi, kwanciya ya yi tare da jawo bargo zuwa cikinsa, yana son tashi ya sanya ɗaya daga cikin kayan barcin Lion ya yi brush amma ba zai iya ba saboda jiri, dole haka ya kwanta da jallabiyar ba dan ya so ba. After some minutes ta dawo bakinta ɗauke da sallama hannunta rike da brush ɗin nasa da wani kwano mai ɗan girma sai roban ruwa guda ɗaya, ba ƙaramin daɗi ya ji ba dama yana tunanin yadda zai yi ya shiga toilet ɗin Lion ya yi brush tun da akwai brush da dama a ciki sabbi. Saman bedside drawer ta zauna tana faɗin "My shagwaɓati naga akwai brushs dayawa a cikin toilet ɗin naka, kuma dukka sabbi ne". Ɗan shagwaɓe murya ya yi. "E na sani amma da nawa wanda nake amfani da shi nake son ki goge bakin ai". Cool murmushi ta saki dan kuwa da shi ɗin ta yi amfani abinta, ga na mijinta me zata yi da sabo? Ai babu. Miƙa mishi brush ɗin ta yi tana faɗin "To kai ma ga shi nan ka yi". Make mata kafaɗa ya yi. "No ni ke zaki yi mini idan ba haka ba ba zan yi ba". A tsananin shagwaɓe ya yi maganar. Ba musu ta miƙe ta dawo gefen gadon tare da sanya mishi kwanon a saitin gemunsa kafin ta sanya mishi brush ɗin ta fara goge mishi kyawawa kuma fararen hakwaran nasa, farare tas dasu kamar audiga, ga su a shirye kamar shiryayyun masara, datsan datsan da su gwanin ban sha'awa. Tas ta goge mishi tare da bashi ruwan roban da ta kawo ya kurkure baki, mikewa ta yi ta nufi wajen dressing room ɗin Lion ɗin bayan ta ajiye kwanon a kasa ta bashi brush ɗin a hannunsa ya rike mata, ta sha ruwan mamakin ganin dressing room ɗin, ƴar kauye ta zama a ciki, da kyar ta iya dannewa ta ɗauko wani ɗan karamin towel fari ta ciro shi daga cikin ledarsa tas da shi. Bakin nasa ta zo ta goge mishi da towel ɗin kafin ta karɓi brush ɗin ta haɗa da kwanon ta ɗauka ta nufi waje, Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana binta da kallo tare da yiwa Ubangiji godiya daya mallaka mishi ita, tana da hankali ga sanin darajan mijinta, ta san ta yadda zata kula da kayanta. Bakinta ɗauke da sallama ta dawo cikin ɗakin, saman bedside drawer ta zauna tana kallon shi, hannu yasa ya nuna mata gefensa a kan ta zo ta zauna, da farko kamar zata ce mishi a'a, sai kuma ta tuna nasihar su Abba kada ta yi mishi musu, dan haka sai ta miƙe ta koma kusa da shi ɗin. A hankali ya kai hannu ya cire mata hijabin jikinta tare da ɗaura shi saman bedside drawer. "Meyasa zaki wahalar mini da kanki wajen saka wannan abin kuma?" Murmushin kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba. Ɗan taɓata ya yi ganin tana hamma tare da nuna mata saman kirjinsa a kan ta kwanta, kallon shi ta yi tana turo baki, shagwaɓe murya ya yi tamakar zai saka mata kuka "Wai ba Areef ya ce na baki kulawa bane? Yanzu ki zo ki kwanta na baki kulawa har ki yi barci mana, dan naga barci kike ji". Ɗan kallon ɗakin ta yi kafin ta ce "My shagwaɓati ina cewa wannan ɗakin Lion ne?". Jinjina mata kai ya yi alamar e ɗakin Lion ne. "To meyasa zamu kwana a ciki? Shi kuma a ina zai kwana?". Hannu ya kai ya jawota jikinsa, kasa kasa ya ce "Shi Lion ai yana da wajen kwana da yawa a gidan nan, kada ki damu, yasan muna nan ba zai dawo ba, baki ga ya sanya jacket kafin ya fita bane? Har kayan barci ya sanya kafin ya fita, baya sanya kayan barci har sai idan zai kwanta, ko garden zai je da normal kaya yake zuwa, amma yau da kayan barci ya fita, so ya sallami ɗakin nan kenan, ya bar mini ni da ke, sai gobe zamu koma bedroom namu, yau dai muna nan. Lafewa ta yi a kirjin nasa tana shakar daddaɗar kamshin perfume ɗin Lion dake jikinsa, dan yau da shi ya yi amfani, sauke bargon kasa ya yi tare da ɗan gyara mata ta kwanta da kyau a jikin nasa kafin ya hauro da bargon ya rufesu zuwa kirjinsa, iya kanta kawai ya bar mata a waje, ɗauko remote na Ac ya yi tare da kara gudun sannan ya kashe wutar ɗakin ya kunna lamp mai bada sky blue light. "My rigimati". Ya ambaci sunanta kasa kasa, a shagwaɓe ta amsa mishi da na'am my shagwaɓati, "Barci zaki yi baki bani hot kiss ba?" Ɗan ɗago kanta ta yi tana kallon shi. "Ni ɗazun da safe ma waye ya ce kayi mini kiss?". "Lips naki ne ko nawa?" Ya faɗa a shagwaɓe, mayar da kanta ta yi ta kwantar a saman kirjin nasa tana murmushi sosai, tana bala'in kaunar mijin nan nata shagwaɓatin ta. Hannunsa ya ɗaura saman hulan kayan barcin dake kanta, a hankali ya zame hular daga kan nata ya ajiye a gefe, shafa lallausan gashin kanta ya fara yi yana gangarowa har zuwan bayanta, cikin shagwaɓa yake gaya mata kalamai masu daɗi tare da tayata murnar yau sun mallaki juna, hannu ita ma ta ɗaura saman kansa tana shafa gashinsa tare da bashi amsar duk wata kalma ta so da ya gaya mata, sai murmushi suke yi, ransu fes, a hankali yake ta juyar da ita tana komawa rabin jikinta a saman bed ɗin har suka zama irin kwanciyar nan na suna fuskantar juna, matso da face nasa daf da tata ya yi yana faɗin "Da nace ki bani hot kiss kin ki yanzu ai zan sha kayana". Ɗan turo bakin nata ta yi tana faɗin "Ni bari ma na tashi na tafi ɗakin mu, sai da safe, ai na tayaka hira haka ya isa". Hannu ɗaya ya sanya ya rufe mata idanu tare da ɗaura lips nasa saman tata ya fara bata kiss, nauyayyar ajiyar zuciya suka sauke su dukkansu biyu a tare, kara jawota jikinsa ya yi ita kuma ta ɗaura hannunta ɗaya a saman bayansa tana mai mayar mishi da martanin kiss ɗin da yake yi mata. Shafa bayanta ya fara yi har zuwa saman mazaunanta, harshenta ta zura cikin bakinsa tana wasa da nasa harshen, shafa mazaunan nata ya fara yi yana kara narke mata, a hankali ya zame hannunsa dake saman idanunta ya mayar saman breast nata, caraf ta capke hannun nasa tare da kwace bakinta tana faɗin "Uhm uhm kai my shagwaɓatina, wai ba zaka barni nayi barci bane? Na gaji fa". Kukan shagwaɓa ya sanya mata "Ni to kiyi barcin ki mana na hanaki me? Ni ki barni na taɓa kayana". Ita ma kukan shagwaɓar ta saka mishi. "Ni gaskiya ba zan barka ba, ka taɓa ganin ana taɓa mutun kuma ya yi barci ne? Ai idan kana taɓani ba zan yi barci ba, please mana my shagwaɓati, barci nake ji sosai, Allah na gaji dayawa". Lumshe idanuwansa ya yi yana faɗin "To ki barni na taɓa sau ɗaya zan barki, kinga da safe ma kin hanani taɓawa ko? Da safe ba mallakina bane, yanzu kuma mallaki na ne, please mana My rigimati, sau ɗaya fa". Sakin hannun nasa ta yi tare da kwantar da kanta a gefen kirjin nasa. "Kin yarda na taɓa?" Ya tambayeta a tsananin shagwaɓe, bawan Allah sam baya son ya yi mata abin da bata so, shi farincikinta ya fi mishi komai. Jinjina mishi kai ta yi almar ta yarda, sumbatar goshinta ya yi. "I really love you my wife, my heartbeat, My rigimati". "I love you too my shagwaɓati". Ta faɗa cikin muryar barci, dan barci sosai take ki baiwar Allah, ta gaji, ta sha wahala, hannu ya kai ya ɗan shafa bayanta kafin ya dawo da hannun nasa saman breast ɗin nata, Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke jin su irin wanda yake ra'ayi, suna cike ɓul ɓul tamkar an hura balo balo. A hankali ya ɗan matsa mata su kafin ya sakesu ya jawota jikinsa sosai yana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya fara shafa bayanta har barci ya yi awon gaba da su bakiɗaya, suna cikin tsantsar farinciki na wuce misali. A ɓangaren daddyn Rimsha da Areef kuwa, hira suka rinƙa zubawa suna kwance har barci ya kwashe su, yau dai Areef a ɗakin daddy ya kwana. A can waje kuwa wato garden, bayan ta gama zamanta sai ta miƙe da taga babu sarki sai Allah, lokacin kuma Already duk sun yi barci, kusa da shi ta zo ta zauna, sai zuba barcinsa yake yi cikin kwanciyar hankali ya jingina kansa da jikin headboard na sofar. "Yaya Saif dan Allah ɗan bani wayarka bari na kira yaya Areef ya zo ya buɗe mini kofa, ko na buga kofar nasan ba zasu ji ba". Shiru bai amsa mata ba, ya ji duk abin da ta ce, dan tana zama a kusa da shi ya farka, sai dai bai buɗe idanunsa bane kawai, amma ya farka. Miƙewa ya yi ya gyara kwanciyarsa a saman sofar tare da laluɓar wayar tasa idanu a rufe ya cire mata password ɗin wayar ya miƙa mata, miƙewa ta yi daga saman sofar dan ta bashi damar mike kafafunsa da kyau, duk da cewa ma yafi sofar tsawo dama, amma idan ya miƙe kafafun dai zai fi jin daɗin kwanciyar. Karɓar wayar ta yi, gabaɗaya babu app ko guda a cikin wayar, sake baki ta yi tana tunanin ina apps ɗin kuma suke? Ina wajen contact da sauruansu? Bata san wayar muguwar security ke gareta ba, apps ɗin suna nan, amma sai idan shi ya fitar mata da wanda zata yi amfani da shi, duk suna karkashin tsaro ne, babu mai ganinsu sai idan ya fitar mata da contact ɗin zata ganshi, idan yana so kuma dukka zai iya fitarwa lokaci guda, duk yadda yake so zai iya sarrafa wayarsa. Tsugunnawa ta yi a kusa da shi cikin sanyin murya ta ce "Yaya Saif ban kalli contract ɗin ba". Shi gabaɗaya ma ya manta bai fitar mata ba, karɓar wayar ya yi har lokacin idanunsa a lumshe, babbar yatsansa ya daura a saman screen ɗin ya ɗan ja kasa sai ga apps ɗin gabaɗaya sun fito, karɓa ta yi tare da shiga contact, My pleasure ta gani, shi ta kira, number Aseef ne, wayar tana cikin mota a rufe, ta yi ringin har ya kaste ba'a ɗaga ba, sake kira ta yi, nan ma shiru, har sau huɗu tana kira ba'a ɗauka ba, shiga can cikin contracts ɗin nasa ta yi dan ta duba number Aseef, a tunaninta na Areef ta kira, ta san cewa su biyu ne a duniyar nan zai yi saving numbersu da haka. Our heartbeat ta sake cin karo da shi, murmushi ta saki dan a tunaninta number Aseef ɗin kenan, ta yi gaskiya tunaninta gaskiya ne, number Aseef ɗin ne, amma numbersa na Washington DC ne, wanda ta kira da farko kuma na nan Nigeria ne, number a kashe take, guntun tsaki taja jin bata shiga, yanzu a tunaninta ta kira Aseef da Areef kenan, bata san dukka number Aseef kawai ta kira ba. Number daddynta ta fara rubutawa dan ta haddace a kanta, ga mamakinta sai taga ya yi saving da sunan Uncle, shiru ta yi tana tunanin kenan shi ma ya ɗauki daddynta uncle nasa kamar yadda su Aseef suka ɗauke shi ne? Abin ya bata mamaki, kiran number ta yi, a kashe dan number Washington DC ne ba zata yi amfani a Nigeria ba, shiru ta yi tana tunanin waye zata kira kuma. Ganin babu ne yasa ta fara bincika mishi contact nasa tana ganin sunayen da ya yi saving numbobi mutane, daga uncle T, uncle Herry, Jay, John, General, su Major, Captain Peter da dai sauransu, su ne dai a wayar babu wata suna mai daɗi bayan nasu Aseef, shi ma Imran Prof ya sanya mishi, Josephine kuwa mummy ya sanya mata, amma kuma baya kiranta mummyn a baki, sai dai ya ce mata Josephine, duk da ma da wuya kaji ya yi maganar ta, amma idan zai yi Josephine ɗin yake faɗe a baki, amma ya yi saving num ɗinta da mummy, da alama lokacin da ya musulta ne ma ya sanya numberta a wayarsa har ya sanya mata mummyn, dan kuwa a baya bashi ma da numberta sam, kuma tun da ya musulta bai yi maganarta ba, wata kila yanzu tun da ya musulta zai iya ce mata mummyn kamar yadda ya yi saving numberta, shi ɗin ne baka gane mishi!. Ta wuce number Areef da ya yi saving da My pleasure, sai dai ta ɗauka number da ta kira da farko ne, sai bata gwada kira ba, yana barci tana yi mishi bincike a contracts nasa. Sai da ta ji wayar ta buga karfe 11 daidai sannan ta ajiye mishi a kusa da shi tare da komawa ɗayar sofar ta takure waje guda danma yau akwai hijabi a jikinta, duk da ba mai girma bane bai kai gwiwowinta ba, amma ya ɗan tare mata sanyi kaɗan, ta takure saboda tsoro, da kyar ta iya samu barci ya yi awon gaba da ita, gabanta sai faɗuwa yake yi. Can wuraren asuba irin karfe huɗun nan ta farka tare da waro idanunta waje, a hankali ta miƙe zaune tana kallon in da yake kwance, ga mamakinta sai bata ga jacket a jikinsa ba, ɗan waigawa da zata yi, sai taga jacket ɗin a jininta ya rufa mata, shiru ta yi tana tunanin yaushe aka yi hakan kuma? Bata san cikin dare irin karfe 1 nan ta dame shi da rawan sanyi ne ya je ya rufa mata jacket ɗin nasa ba, sai kakkarwa take yi hakwaranta na garuwa waje guda, shi kuma hakan yana hana shi yin barci, dan komai kankantar motsi yana farkar da shi daga barcin nasa, hakan yasa ya farka ya cire jacket ɗin ya sanya mata, shi ne ta samu ta cigaba da barci cikin salama, shi ma ya samu barci mai daɗi cikin salama ba tare da takurarta ba. Wani irin daɗi ta ji ganin hakan, ɗaukar jacket ɗin ta yi ta manna mishi kiss tare da sanyawa a jikinta tana bin garin da kallo, akwai hasken farin wata, tun farkawarta ta farkar da shi, motsinta ya tashe shi, sai dai bai buɗe idanu ba. Ai dama dole Lion ba zai yi nauyin barci ba, General Of the army fa, ai ba'a barci ya kai wannan mukami ba, tun bai kai mukamin ba suka saba da rashin nauyin barci saboda jiran harin abokan gaba a koda yaushe, lokacin da suke bakin iyaka, a kowani lokaci abokan gaba suna iya farmakansu, hakan yasa basu da nauyin barci, komai kankantar motsi zai tashe su, abin tun daga training suka samo shi, shi yanzu ba wani aiki yake yi bama ya kai mukamin hutu, sai dai aikin da ya ga dama ya saka kansa zai yi, amma rashin nauyin barcin tabi jikinsa, ya zamar masa jiki abin, ko yaya ka motsa kusa da shi sai ya ji, sai dai ya basar ya cigaba da lumshe idanunsa kawai har barcin ta sake ɗaukarsa. Haka suka kasance har asuba, sai da ya fara jin kiraye kirayen sallah ne ya miƙe ya nufi cikin gida, da sauri ta bi bayansa, bedroom na kasa ɗaya sabon da ba'a taɓa shiga ba, nan ya shiga dan ya yi wanka da alwala, akwai bedroom a kasa wanda mutun bai taɓa shiga ba, komai na ciki sabo ne, amma yaki zuwa ya kwana a ciki, gara mishi garden, dama kuma already kwanan garden kam ya saba, dan raba dare yake yi a wajen, wani lokaci sai karfe 2 yake shiga cikin gida, kusan za'a ce kawai kwana a ciki yake yi. Wanka da alwala ya yi tare da fitowa ya nufi bedroom nasa dan ya canza kayan jikinsa zuwa jallabiya, shi ba ruwansa dan su Aseef suna ciki, matsalarsu ce, dan ya ga Aseef ɗin yana son bedroom ɗin nasan ne ma yasa ya bar musu. Sai zuba barcinsu suke yi rungume da juna a cikin bargo, ko kallon in da suke bai yi ba ya wuce dressing room. Jim kaɗan ya fito sanye da jallabiya fara tas ya fito ya nufi masallaci, a palon kasa ya cikaro da Areef da daddyn Rimsha, ko kallon in da suke suma bai yi ba ya wuce abinsa zuwa masallaci. Ita kuma bedroom nasu ta koma, Jehan na ta zuba barci, toilet ta nufa, tsarki da alwala ta ɗauro tare da fitowa ta shinfiɗa dadduma bayan ta saka katon hijabi ta tada sallah. Sai bayan ta idar ne ta tashi Jehan dan ta yi sallah, da kyar ta tashi tana yatsine fuska, ita kuma hawa gado ta yi ta kwanta zuwa karfe 6 ta tashi ta yi shirin zuwa school, Mark ne ya kaita kamar kullum, har ta tafi school ɗin kuma basu haɗu da Lion ba. Yau jirginsu daddyn Lion ya ɗaga da misalin karfe 10 na safe daga Washington DC zuwa Naija, to sai dai muce Allah ya kawo ku lafiya, sun bar uncle T a gida yana jinya. Da misalin karfe 10:30 Lion yana zaune a gefen bed nasa, Aseef kuwa Areef ya mayar da shi bedroom nasa, Akila tana tare da mijinta, Areef da daddyn Rimsha suna zaune a palon sama suna hira, ita kuma Jehan tana ɗaki dan bata son fitowa Areef ya takura mata, haushi ma yake bata ɗan rainin wayo a cewarta. Kiran number Areef Lion ya yi dan ya zo su yi magana, ganin kiran yasa ya miƙe yana faɗin "Uncle ina zuwa ka jirani". Okey ya amsa da shi, duk abin da suke faɗe Lion yana jinsu sarai dan a palon sama suke kusa da bedroom nasa. Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga bedroom ɗin, kallo ɗaya Lion ɗin ya yi mishi ya kawar da kansa izuwa saman wayarsa, laptop nasa tana garden sun barota a can. A gefensa Areef ɗin ya zauna yana yi mishi good morning, cikin mutunci da kaunar juna suka gaisa, sai murmushi Areef yake zubawa daddy ya bashi auren Jehan. "Areef zan yi tafiya zuwa kasar Russia nan da kwana uku, so ka kula da su daddy da kowa, zan tafi da ɗaya daga cikin yaran nan, ko ƙaramar ko babbar, nafi son ma na tafi da babbar dan ita ce mai kama da ubanta, na gaya maka tun yau ne dan iya yau ɗin ne kawai nake da time na zaman magana, akwai sauran abubuwan da zan kammala kafin na tafi, so ina busy". Zaro idanu ya yi yana faɗin "Lion Russia kuma?!". Shiru bai amsa mishi ba. "Amma dai kasan bamu shiri da kasar Russia ko kaɗan ko? Kana jami'e zaka shiga kasar, to mema zaka je yi a can?". Ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya amsa mishi da "Kakansu zan ɗauko, ƴar Russia ce ai, so tana wajen iyayenta sun kamata sun rufeta a ɗaki dole dole sai ta zama kafura kafin su saketa tayi rayuwa kamar ko". Shiru Areef ya yi yana tunanin wannan bala'i da Lion yake neman jefa kansa, ya sani basu ko ga maciji da kasar Russia, ƙasar America da Russia sam basu shiri ko kaɗan, babu mutunci a tsakaninsu, sannan ya ce zai shiga cikin kasar ya ɗauko ƴar cikin kasar, dama ga shi family'nta a kule suke da Family'n Dr Salman, ya je su sauke haushin a kansa, dan cewa ma zasu yi ko shima ɗin family'n Dr Salman ɗin ne, tun daga nesa su harbe shi da bindiga ko su yi mishi wani abin, lallai kam akwai ƙura, amma kuma yana da kyau a ɗauko Na'urat ɗin dan kada su sanyata ta yi ridda, sai dai fa daddy ba zai taɓa yarda ayi wannan tafiya ba, barema idan ya ji akan abin da ake rikici ƴan uwan Naurat sun hasala sun fusata an musuluntar musu da ƴar uwa, idan baku manta ba ya tsani musulmai, ya ji labarin sun kamata sun rufe tsawon shekaru taki yarda ta zama krista, haushi kamar su rataye kansu ne Lion ya ce zai shiga har cikin gidansu ya ɗaukota, anya kuwa hakan zai yiwu? Akwai babban haɗari gaskiya, da wuya ma gwamnatin kasar ta barshi ya shiga cikin kasar, ina bama zai yiwu ba. "Kai sarkin tunani, ta ruwa zan shiga kasar, kuma na gaya maka zan tafi da yarinya ɗaya dan mu sami jituwa tsakanina da matar, so ka kula sosai". Da yake yasan Lion idan ya yi magana baya canzawa sai ya ce "Allah ya bada sa'a ya kare mana kai, amma fa Lion to sai dai ka tafi da Rimsha ba dai Jehan ba, ni ba zan iya yin kwana ɗaya ban ga baby ba". "Dama da farko da ita naso tafiya, amma tsoronta ya yi yawa shiyasa nace zan tafi da babbar". Tsuke fuska ya yi yana faɗin "Wlh hakuri zaka yi ka tafi da ita ɗin dai, baby kam babu in da zata je gaskiya, idan ba kana son wlh nabi bayanku ba in ka tafi da ita". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Bari na sanya Mark ya shirya sojoji biyar da shi Mark ɗin shida kenan, sun isa dan kula da jirgin ruwan da zamu tafi da shi". Nan take wani tunani ya faɗowa Areef, to in dai haka ne ta jirgin tuwa zasu bi ai ya sami hanyar da zai sanya Lion ya yi aure cikin sauki, amma bari ya gwada duk da yasan da wuya ya amince. Nisawa ya yi tare da fara magana a tsantsar nitse kamar wani malami mai yin wa'azi. "Lion in dai haka ne to bai kamata ka tafi da Rimsha a haka ba, kasan dai ba ta yadda za'ayi ta zauna a cikin sojoji ko? Dole a kusa da kai zata zauna, duk da akwai wasu ɗakuna a cikin jirgin, amma a kusa da kai zata zauna dan tsaron lafiyarta da kuma kula da ita, ba zai yiwu ka barta a wani ɗaki daban kai kana wani daban ba, dole a ɗakinka zata zauna, kuma kasanta dama da bala'in tsoro sosai, baza ta taɓa yarda a cikin waƴan nan tabka tabkan takun da zaku keta cikin jirgin ruwa yana tafiya ta yarda ta kwanta a ɗaki ita kaɗai ba, zata yi ta ganin kamar mutuwa zata yi ko zata nitse cikin ruwa, kasan tafiya a cikin ruwa fa sai wanda ya daure, ruwa yana da giggiwar ɗibar mutun kamar jiri idan yana da yawa, so zata tsorata sosai, idan kuma a ɗakinka zata zauna kaga a matsayinta na mace ba muharramarka ba haramun ne a addini, so yanzu kawai a ɗaura muku aure yadda zata zauna a ɗakin naka ba tare da wani tsinuwar mala'iku ya sauka a kanku ba, idan kun dawo daga tafiya zaka iya sakinta tun da kun gama aikin". Guntun tsaki ya ja tare da ɗaukar wayarsa ya fara latsawa dan Areef bashi da hankali ya lura, aure kuma shi? Abu kamar hauka ko wasan yara, haba ai shi bashi da lokacin yin aure, bashi ma da lokacin mace, gani yake yi Areef ya samu matsala ne a kwakwalwarsa, so bai kamata ma ya bashi amsar wannan shirme da hauka ba. Shi kuwa Areef dan ya karawa abin armashi da kara haɓakata dan ya tabbatar da zancensa har da mikewa ya nufi waje yana faɗin "Bari na fara yin magana da uncle zan dawo mu karisa maganar mu". Ko kallon in da yake bai yi ba, dan bama da Rimshar zai tafi ba, da Jehan ɗin zai tafi dan tafi dakiya da rashin tsoro, Rimsha tana ganin wani bala'in ai rungume shi zata yi ta hana shi cetansu da kuma cetanta, ta ja a ci galaba a kansu, yasan kuma ba ƙaramin yaki za'ayi ba kafin ya shiga kasar Russia, akwai cakwakiya, ya yi alkawarin kuma sai ya kammala case ɗin Nawazudden tas zai koma kasarsu, yana son haɗa shi da kowa da kowa nasa su koma kamar da ne. Wannan aiki idan ba General Of Army ba waye zai iya shi? Su kansu su daddyn basu san in da mahaifiyarsu take ba, amma har ya nemota zai je ɗauko ta, zai shiga gagarumin haɗari saboda su, gaskiya daddyn Rimsha ya ciri tuta, Lion ya yi mishi abubuwa da yawa, sai dai shi kuma daddyn yana kullace da Lion ɗin na abin da ya faru a tsakaninsu, bawan Allah bai san gagarumin taimakon da Lion ɗin ya yi mishi bane, da ya sani ba zai kulkace shi ba. Zama Areef ya yi kusa da daddy yana faɗin "Uncle ina so ne ka bawa Lion auren Rimsha zasu yi tafiya, idan suka dawo zai saketa, kaga bai dace su yi tafiya a haka ba suna matsayin da sukenan, Rimsha ta girma ai". Areef ya tabbaka babban kuskure a maganarsa da ya ce a bawa Lion auren Rimsha zasu yi tafiya ne, idan ya dawo zai saketa, sai kace wata kayan wanki ko kayan gwanjo, wani uba ne zai yarda da hakan? Ƴar cikinsa fa, Rimsha 14 years a mayar da ita bazawara ne kenan ko yaya? Haba maganar ta yi muni over, ai wlh koda ba zai saketa bama daddy ba zai bashi aurenta ba bare kuma har da wani cewa idan suka dawo zai saketa kamar wata kaza, maganar ta konawa daddy rai over, shi kuma Areef bai yi mishi bayanin Lion da wuya ya saketa ɗin ba, tarko Areef ɗin ya kafa mishi dan ya kamu da sonta ai, shi kawai ya faɗi maganar ne dan yana tunanin daddyn yasan komai da yake wakana, bai san cewa tun da ya zo ai bai samu zama dasu Rimshar ba bare ya fahimci akwai kusanci tsakaninta da Lion ɗin. Rai a matukar ɓace shi ma daddyn ya tabbaka babban kuskure wanda ya dawo yana danasani mara amfani, dan kuwa cikin fushi ya ce "Wlh Allah ya sauwaka na bawa Saif auren ƴata, koda ma yana sonta ba zan bashi ita ba bare kuma baya sonta, tafiya zasu yi idan ya dawo ya sake ta, ita ɗin an gaya maka kayan wanki ce? Ko kaza ce? Wlh ba zan bashi ba, ko namutu sai na bada wasiha kada a bashi ƴata". Dama kuma duk wani uba na kirki zai ji zafin magana irin haka idan akayi ta a kan ƴarsa, sai dai daddyn a in da ya yi kuskure yasan halin Lion ɗin, amma yana bari zuciya ta ɗebesa tasa ya yi abin da zai na danasani daga baya, ya san cewa idan Lion ya ce abu to ba yadda ya iya da shi sai hakuri, amma haka wani lokaci idan ya hau dokin zuciya idanunsa suka rufewa ya faɗi kalamai masu zafi. To a wannan rana ma tarihi ce ta maimaita kanta, domin kuwa Lion ya ji duk abin da suka faɗa, hakan ta sanya shi ya fito cikin kunan rai ya yi wasu maganganu masu zafi ga daddyn. "Ba zan auri ƴar ka ba saboda baka so ko? To wai kai baka san ni duk abin da ba'a so shi nake yi ba ne? Bani da ra'ayin yin aure a rayuwata, amma a yau yanzu ba sai anjuma ba za'a ɗaura aurena da ƴarka, sannan ka sani zan yi tafiya da ita kamar yadda Areef ya faɗa, da ba da ita zan tafi ba, amma yanzu da kayi magana da ita zan tafi, sannan kuma kai ne waliyin da zaka karɓi wannan auren kuma ka bayar ko kana so ko baka so! Daga karshe kuma sai ka fara azumin kaffara na rantsuwar da kayi ba zan aureta ba!!". Tashin hankali, danasani daddy ya farayi na maganganun da ya yi, domin kuwa ya sani auren Rimsha da Lion yau babu fashi kamar yadda Lion ɗin ya faɗa, shikenan yanzu ya ɓatawa ƴarsa rayuwa da kansa da kalamansa? Magana kalilan ta sanya ya cuci yarsa, yana shirin ko ace ya jefata cikin wahala? La ilahi ya lilliahi. Shi kam Areef sam bai so abin ya zo musu a karo na biyu ma da haka ba, ya so ne su fahimci juna, bai san meyasa sam daddyn Rimsha da Lion basu shiri ba, basu haɗuwa inuwa ɗaya, daddy zuciya da saurin hawa, idan ya hau kuma baya iya controlling kansa, sannan bugu da kari shima yana da izza, shi kuma Lion duk balai idan ka ɗaga mishi murya tofa sai ya sanya kayi laushi, bare kuma daddy da yake faɗan maganganu masu zafi akan Lion ɗin, ai dole bazasu shirya ba, dole kullum idan suka haɗu sai ta kwaɓe musu, idan bai yi sa'a bama ya jawa Rimsha bala'i kenan, dan da wuya idan Lion ba zai azabtar da ita ba, dan daddynta ya ji kunan rai sosai, sai dai kuma ta wani ɓangaren Areef ɗin ya ji daɗi da Lion ɗin ya amince zai aureta, babban abin jin daɗi na gaba kuma, Lion idan ya yi niyar yin abu fa to baya fasawa, saboda kayi niya ka sake fasawa ma shi yana ganin ai kaskanci ne da nuna faɗuwa, ka zubar da girmanka, dan haka wannan hatsaniya data faru a tsakaninsu bai sa ya ce zai fasa ɗauko Naurat da haɗa daddyn da family'nsa ba, laifin wani baya shafan wani, idan ya ɗauko Na'urat ba iya daddy kawai ya yi wa ba harda surukansa wato su Abbi. Makudan daloli wato dollars ya ɗebo daga ɗakinsa wanda shi kansa bai san adadin yawansu ba, yazo ya zubewa daddyn a kan shi ne sadakin Rimsha, wayarsa ya ɗauko ya kira Sultan limamin masallacinsa na Washington DC, ya sanya wayar a hand-free, Sultan ya zama mishi waliyi, daddy dole ba dan ya so ba ya bada auren Rimsha Sultan ya karɓa aka ɗaura aure take a wajen a Washington DC wato cikin Masallacin su Sultan ɗin. TASHIN HANKALI, YAU AKE YINTA, DADDY KA JAWO BABBAN AIKI, ALLAH YA CECI ƳAR TAHALIKAN NAN KADA YA CE ZAI HUKUNTATA DAN UBANTA YA JI HAUSHI DA ƁACIN RAI. Wannan shi ne tashin hankali Rimsha tana school suna rubuta Exams, sam bata san me yake faruwa ba, ita ma Jehan tana can tana zuba barci, bata san ƴar uwarta ta zama matar aure ba, ba wanda ya sani daga daddyn, Areef, sai Lion ɗin, murna a wajen Areef kam ba'a magana, yau ransa fes, bai wani damu ba, dan yasan Lion ɗin ya fara sonta, dan haka yana sa ran wannan tafiya da zasu yi su kara samu kusancin da zai kamu da tsantsar kaunarta ta yadda ba zai iya rabuwa da ita ba dole ya dawo ya bawa daddynta hakuri in dai yana sonta, tashin hankali Lion da bada hakuri! Anya kuwa Areef baka manta waye shi ba? Mutumin da ya tsani ma a ce mishi sorry shi ne zai ce sorry? To dai zamu gani, amma da kamar wuya gaskiya. Aseef yana can yana zuba barci Akila tana kwance a gefensa tana tunanin rayuwa, sam basu san ne yake faruwa ba, basu san an ɗaura aure a palon sama ba, daddy ya bada auren Rimsha a dole ba dan yana so ba, an nuna mishi fin karfi da isa. E lallai, Lion ya nuna fin karfi da isa da izza ya aurawa Aseef AKil, yanzu kuma da karfi ya nuna isa ya auri Rimsha. GASKIYA INA JIYEWA LION WLH HMM. Lallai akwai gagarumin matsala, anya William jacop zai yi accepting na Rimsha da Akila kuwa a matsayin surukai? Kun dai sai tun farko ya nuna ya tsani Rimsha over, tab lallai daga Rimshar har Akilar suna tsaka mai wuya kuwa, dan William jacop ba taya baya bane! *DANGEROUS BOSS* ɗin ne da gaske idan baya son abu, akwai dai matsala, akwai yaki, ache acikin TRIPLETS nasa sanyin idanuwansa biyu daga ciki sunyi aure kuma ba Turawa suka aura ba bakaƙen fata? Tab akwai gagarumin matsala ba kaɗan ba wlh. LION Bedroom nasa ya koma bayan an ɗaura auren ya yi kwanciyarsa abinsa hankakinsa kwance yana tunanin ta hanyar da ya kamata ya shiga cikin kasar Russia, zai iya zuwa da private jet nasa, amma ra'ayinsa ne ya zaɓi tafiya da jirgin ruwan saboda wasu dalilai nasa na kansa, gaskiya bai so tafiya da Rimsha ba, da Jehan ya so dan bata da tsoro, daddy ya canza komai da wasu banzayen kalamansa. Yau saura kwana uku ya yi tafiyar ga daddy yana hanyar zuwa, Rimsha saura kwana uku suma su kammala Exams, zai zama ranar da zasu kammala a ranar zasu tafi, amma anya daddy zai aminta da tafiyar nan kuwa? Akwai fa kura? Dan kuwa wannan tafiya babbar haɗari ce ga Lion, sai dai shi dama duk abin da aka ce ba'a so, shi kuma shi yake so, zaman ka lafiya ma kada ka ce mishi baka son abu, kana ce mashi to fa sai anyi wannan abin sai dai ka mutu, gaskiya akwai gagarumin matsala tsakaninsa da daddynsa, dan ba zai taɓa yarda ya shiga wannan kasada ba........ ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E61-62💋 A ɓangaren Rimsha kuwa, wato school, sun rubuta Exams na farko lafiya, sai murna suke yi sun kusa kammalawa, sai dai fa yau tun da ta je school bata cikin mood mai kyau, har sai da Anaya ta gane ta tambayeta dalili, kaƙalo murmushi dole ta yi. "Anaya babu wani abin da yake damuna, kawai kai'na ne yake yi mini ciwo sosai". Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa dan ta je cikin mota ta ɗauko ruwa, da sauri Anayar ta miƙe ta bi bayanta tana yi mata sannu Allah ya sawwaka. Suna tafe suna hira saura musu paper ɗaya su koma gida, sai murna Anaya take yi zata ga Mark. Kamar dai kullum yana aikin latsan waya, sannu ta yi mishi, ɗago idanu ya yi ya sauƙesu a kanta, har wani irin yarr ya ji a jikinsa, sai murmushin take yi abinta, ita kuma Rimsha ta buɗe gidan baya ta zauna tana shan ruwan da ta ɗauko a gaban motar, zama ta yi ta kyau dan babu kyau shan ruwa a tsaye, Annabi ya hana, ka samu waje ka zauna kasha, dan ruwa cikin ƙanƙanin lokaci yana iya kashe bawa idan kayi mishi shan garaje. Ɗan kawar da kansa ya yi ba tare da ya amsa sannun ba, har cikin zuciyarsa yake jin yarinyar tana mugun burgesa, bare ma idan tana murmushi, da dimple nata irin na Azharuddeen Bature wato daddynta, idan baku manta ba, da daddynta da daddyn Rimsha duk suna da dimple, Rimsha ta gado, ita ma Anaya ta gado, ba ƙaramin kyau kuma ya yi musu ba, sai ma idan suna magana ko suna murmushi, dayawa daga cikin student suna tsananin ganin kamanninsu, sai dai da yake su basu kula kowa, ba wata student da ta taɓa tinkararsu ta ce suna kama. Suna tsaye a wajen sai ga Fadila ta kariso wajen rai a matukar ɓace cikin fushi, da yake Rimsha tana cikin mota sai Fadilar bata ganta ba ta ga iya Anaya kawai. Damko wuyar rigar Anayar ta yi tana faɗin "Ke dan ubanki a baki wani ɗan iskan kika ji cewa ina zuwa office ɗin Mr Emmanuel na zauna muyi romancing juna da har da zaki gayawa su Zee? Dan sun ce a bakinki suka ji". Da yake ita ma Anayar ƴar yi ce, ba tayar baya bace sai ta ce "Da kika rena tsoho shi ne kika zo nan kina kwashe mishi albarka ko? To ki sani tsoho kika zaga ba ni ba, kuma da kike magana a kan office ɗin Mr Emmanuel karya akayi baki je ɗin bane? Bani na gayawa su Zee ba, amma tun da kin ce ni ne, to ni ɗin ne ki yi abin da zaki yi, angaya miki..." Bata kai karshen maganar ba ta dakata sakamakon ɗaga hannu da Fadilar ta yi zata zabga mata mari. Runtse idanuwanta ta yi tana jiran saukar marin, ta tsuke fuska sosai alamar ta tsorata, jin shiru marin bai sauko bane yasa ta yi yunkurin buɗe idanunta dan taga me ya dakatar da Fadilar, bata kai ga buɗe idanun ba, sai ji ta yi Fadilar ta sakar mata wuyar rigar tata da ta rike, da sauri ta waro idanun dai'dai lokacin ta ji kara mai sauti na saukar mari. Tana buɗe idanu sai kan face ɗin Mark da Rimsha dake tsaye a gefensa tana zaro waƴan nan dara daran sleeping eyes ɗin nata, ga kuma Fadilar a baje a kasa kamar kayan wanki bata numfashi, da alama ta suma ne, da sauri ta dawo da kallonta kan face ɗinsa, daidai lokacin shi ma ya ɗago Hazel eyes nasa ta cikin glass yana kallonta, bata san yana kallonta ba, dan yana cikin bakar glass, dan haka sai ta tsare shi da ido, shi ma ya tsareta da idanu yana kallon razananniyar face nata, yadda ta tsorata dan ta sadaukar marinta Fadila za ta yi. "Anaya mu tafi ko?" Rimsha ta katse musu kallon juna da suke yi, ta kuma yi maganar a tsorace na ganin Mark ya mari Fadila har ta suma. Hannu ya miƙawa Anayar alamar ta zo, sake baki Rimsha ta yi tana ganin ikon god, ko me zai yi mata da zai ce ta zo kuma. Ita ma Anayar ta tsorata bare ma yadda taga face nasa a ɗaure sosai, dama haka yake kullum, amma yau da ya mari Fadila ya kara ɗaure fuskar sosai, sai ta ji tsoron kada ya daketa ko ya yi mata wani abin. Hakan yasa ta kasa yarda ta miƙa mishi hannunta, gabaɗaya ma sai ta kawar da kallonta daga kansa tana ƴan kame kame, ganin hakan yasa shi ya riko hannun nata tare da janta suka nufi office ɗin shugaban makarantar dan ya sumar da Fadila, ya san cewa case ɗin zai iya shafar su daga ita har Rimshar, idan kuma ya shafesu gida zasu sami labari, dole su Aseef zasu tuhumesa har Lion ya ji, case ɗin zai iya zama babba, shiyasa ya zaɓi ya kashe wutar da kansa kamar yadda ya kunna ba sai ta girma ba. Waye ya lura da Mark ya ki yarda ya rike hannun Rimsha sai dai Anaya⁉️ Da sauri Rimsha ta rufa musu baya suka bar Fadilar a wajen ga kofofin motar a buɗe, wani irin daɗi sosai yau Anaya take ji, hannunsa laushi sosai kamar baya wani aiki, ga skin ɗin nasa sai sheki yake, jawur da shi kamar ka taɓa jini ya zuba, a nashi ɓangaren ma laushin hannunta ba ƙaramin daɗi ya yi mishi ba. Abin da ya faru dukka ya sanar da shugaban makarantar tare da gaya mishi ya san yadda zai yi da Fadila, idan ta farfaɗo ya yi mata iya ka da su Rimsha, tun wuri ya taka mata birki kafin gida su sami labari, idan ba haka ba, ya kuskura ya bari gida suka ji ana takurawa Queen nasu, to tabbas wannan makaranta za'a iya rufeta na har abada a dalilin taɓa Rimsha, sannan su Rimshar babu ruwansu a sumar da Fadila da ya yi, hasalima basu san komai ba, dan yasan za'a iya cewa su suka ja komai ya faru, to dan haka su babu ruwansu, okey ya amsa musu da shi, fitowa suka yi Mark ɗin ya tambayesu sun kammala paper ne su wuce gida?. Rimsha ce ta bashi amsar a'a, shiru ya yi bai sake yi mata magana ba, dan kamar tsoron yin magana da ita yake yi, ya fi mishi alkhari da jin daɗi idan ya yi magana Anaya ta bashi amsa ba Rimsha ba, dan kuwa tabbas ya gano ogansa yana son yarinyar nan, yanayin yadda yake ganinsu suna gudanar da rayuwarsu a cikin gidan, tsab ya fahimci so ne a tsakaninsu kamar yadda a yanzu ya gane cewa shi ma fa ya kamu da son Anaya ba karya, kwata kwata baya son idanuwansa su yi mishi kuskure ganin ko da in da Rimsha take, baya son ta yi mishi magana, haka zalika shi ma baya son ya yi mata, sai idan ya zama dole, ya san wanene Lion, ya san shi da mahaukacin kishi na bala'i, so ba zai so wani abin da zata haɗosa da shi ba, dan bai shirya mutuwa ba gaskiya......WLH MARK DA GASKIYAR KA INA DALILI IRIN WANNAN KISHI AI HMMM. Class nasu suka wuce shi kuma ya koma wajen motar, zubawa Anaya idanu ya yi yana kallon yadda take tafiya tana juyowa ta saci kallonsa, duk in ta yi tafiya ɗaya biyu sai ta juyo ta kalle shi, yana kallonta bata san yana kallonta ba saboda glass ɗin face nasa, wani irin sonta ne yake kara shigansa, da yake shi ya san so, ya ma taɓa yin soyayya da wata Baturiya ƴar kasar London da suka haɗu a school tun kafin ya kai wannan mukami da yake kai, lokacin suna school ne ma, ya so yarinyar sosai, amma mutuwa ta rabasu, ya sha kukan mutuwarta kamar ba gobe, accident ta yi da motarta da babban mota a hanyarta ta zuwa school, tun daga kanta kuma bai sake ɗaga idanu ya kalli wata mace ba har ya fara aikin soja, daga nan ya mayar da hankalinsa a kan aikinsa ya watsar da komai, kokarinsa yasa Lion ya dawo da shi kusa da shi, sai dai fa iyayen Mark ƴan ƙasar Russia ne ba ƴan Usa bane, zama ya zaunar da su tun lokacin kasashen biyu suna shiri, har dai suka zama ƴan kasa, to shi dai Mark ɗan Usa ne dan a nan aka haifesa ya girma, a takaice ma bai taɓa zuwa Russia ba, sai dai iyayensa su bashi labarin ƴan uwansu, amma bai taɓa zuwa ba har iyayensa suka mutu, dan haka shi bai san kowa na daga family'n iyayen nasa da ido ba, amma yana da hotonansu da dama a wajensa, ba karya Mark mutumin kirki ne sosai, baya shiga harkan kowa, baya da surutu shiru shiru, ga rikon amana kamar me, yanayin rayuwarsa zaka rantse da Allah cikakken musulmi ne ba krista ba, amma krista ne, wannan shi ne tarihinsa. Yana zaune a wajen har wasu student suka zo suka ɗauki Fadila daga wajen aka wuce da ita zuwa hospital na cikin makarantar. Bayan sun kammala Exam ɗin ne Anaya ta rako Rimsha zuwa wajen mota dan ta sake kallon Mark, bye bye ta yi musu kafin ta ce da Mark ta gode, jinjina mata kai ya yi tare da cire glass ɗin face nasa ya ɗago idanunsa ya saukesu a kanta, abin da ya sanya ya cire glass ɗin dan ta san yana kallonta, yana da bukatar haɗa idanu da ita. "What is your name?" Ya tambaya yana ɗaura glass ɗin nasa a saman wayarsa, "My name is Anaya". "Anaya wow nice name, my name is Michael amma ana kirana da Mark, Long story ne sunan Mark tun daga school ya samo asali, nice to meet you beb". Ya kai karshen maganar tare da miƙa mata hannunsa dan su gaisa, miƙa mishi hannu ta yi tana murmushi, shi ma ɗan motsa ɗan ƙaramin bakin nan nasa ya yi ya ɗan yi yake na gefen fuska, alamar ya ji daɗin kenan fa, hakan shi ne ya ji tsantsar farinciki kenan tab. Ita dai Rimsha ko a jikinta, dan kuwa dama Anaya tana takura mata da wlh tana son shi, so yanzu ai ga shi nan sun gaisa kila zata barta ta huta, tunanin Lion ɗin ta ma ta shiga yi, nan take abin da ya faru daren jiya ya dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, shiru ta yi, shi ne ma abin da ya sanyata yau tun da ta zo school bata wani jin daɗin jikinta, abin ya tsaya mata a ranta sosai. Gaisawa suka yi kafin ya yi mata sallama tare da mayar da glass nasa ya kunna motar, har zasu bar wajen kome ya tunane ya sake ɗauko wayarsa ya miƙa mata a kan ta sanya mishi numberta, ba musu ta karɓa ta sanya mishi, karɓa ya yi tare da yi mata bye bye ya ja motar suka bar school ɗin, sai daɗi take yi, baki yaki rufuwa, haka ta yi ta ɗaga musu hannu har suka bar school ɗin, sannan ta koma wajen da take tsayuwa ta jira daddynta ta tsaya a wajen. Dai'dai lokacin da Mark ya yi parking na motarsa a cikin gida, shi kuma Lion ya danno hancin nasa motar sun dawo daga airport ɗauko su daddy, mota biyu suka yi, Lion shi da daddy suna zaune a gidan baya Tyrone ne ya tuka su, Jay, John da kuma uncle Herry suna ɗayar motar wani soja ne yake tukasu, sam su daddy basu lura da ita ba dan Mark yana kashe mota ta fito ta shiga cikin gida da sauri dan tana jin fitsari, shi kuma Lion ya kalleta dan tun da suka shigo gidan ya zubawa motar da Mark ɗin ya ja ido, tunani yake yi a kan ya kamata su sayi sabbin motoci, wannan da Mark yake kaita school ma ya tsufa. Aseef bai je airport ɗin ba sakamon bashi da lafiya, basu ma gaya mishi daddy na hanya ba, sun kyale shi kawai, shi kuma Areef Lion ya aike shi Abuja gidansu daddyn Rimsha a kan ya kwaso mishi wasu daga cikin takardu na Naurat, dan ya gansu a ɗakin daddy, takardun makarantarta har da katin ƴar kasa na Nigeria da kuma na Russia, duk ya gansu, shi ne ya aika shi ya kwaso mishi su dan zai yi amfani da su, da Donal suka tafi, so bai san su daddy sun iso ba. Cikin gida suka nufa daddy burinsa kawai yaga shalelensa wato Michael a idonsa mu kuma Aseef a idanunmu. Suna shiga palon kasa ya fara tambayar Lion ina Michael nasa? Dama Lion ɗin ya gaya mishi Michael ɗin bashi da lafiya ne yasa bai zo Airport ba, shiyasa ma ya matsa ya ganshi ya ga a wani hali yake ciki. Nuna mishi bedroom ɗin Aseef ɗin ya yi tare da wucewa ya haura sama abinsa, dan shi baya son ciwon kai wato hayaniya, yasan kuma idan daddy da Aseef suka haɗu, ciwon kai zasu saka mishi da surutu kamar ba gobe. Bedroom ɗin Aseef ɗin daddyn ya nufa da fara'arsa da kuma zafansa na son yaga ɗan nasa farincikinsa, rufa mishi baya su Jay suka yi dan suma su kalli Michael ɗin. Babu ko excuse ya faɗa cikin bedroom ɗin, Akila na gyaran gado shi kuma Aseef yana cikin toilet yana wanka, yanzu suka tashi daga barci rana da ya ɗebesu, shi ne ta hau gyaran musu ɗaki shi kuma ya wuce toilet. Ganinta yasa daddy ya ɗaure fuska over, duk da take fara tas kuma fari irin na turawar, amma da yake akwai mix na jinin bakar fata, wato Ammie a jikinta, sai ta zamana baka a gabansu, hakan yasa daddy ya tsaneta sosai, barema da ya kalli ba Rimsha ba ce sai ya kara jin haushi over, kenan hakan yana nufin bayan Rimsha da take tare da Lion wanda ya zo da niyar raba su akwai wata? Kenan dukka ƴaƴansa suna tare da bakaƙen fata? To kuwa ba zai yiwu ba, shi dai dole ƴaƴansa da Turawa kawai zasu yi hulɗa. Tsawa ya daka mata a kan wacece ita?! Sautin zubar ruwan da yake zuba a toilet ɗin ne yasa Aseef bai ji me yake faruwa ba, ganin face ɗin daddy ba ƙaramin razana ta ya yi ba, domin kuwa shi ma dai Tiger face gare shi wajen ɗaure fuska, akwai shi da zuciya da iya tsare gida ba kaɗan ba, bare ma idan aka ci karo da abin da baya so, ai ba'a magana. Cikin girmamawa da rawar murya ta yi musu sannu da zuwa, domin kuwa, ko ba'a gaya mata waye su ba, ta san dole mahaifin TRIPLETS ne, dan jini ba karya ba, akwai kamanni na wuce misali a tsakanin fuskar daddyn da yaran nasa, ga idanunsa irin na Lion sak, ai ga maihankali ma da gani babu tambaya zai san ubansu ne. Tsawa ya sake daka mata a kan wacece ita? Me kuma ya kawota gidan ɗansa har cikin bedroom ɗin ɗaya daga cikin ƴaƴan nasa? A iya saninsa ko sojojin Lion basu shiga musu ɗaki dan rashin yarda da mutane da suke yi, sun tsani mata, mace bata taɓa raɓarsu ba, yau rana tsaka mace a ɗakin Michael tana gyara mishi gado, ai dole ya ji ko ƴar uban wanene?!. Murya na rawa ta amsa mishi da ita matar Heartbeat ne, dan a gaskiya ba karya Akila bata rike sunan Aseef ba, sau ɗaya ya taɓa gaya mata sunansa, kuma ta manta, Heartbeat take kiransa tun farko, kuma sunan ne ya zauna a bakinta, dan haka sai ta ce ita matar Heartbeat ne. Da yake shi ma daddyn haka yake kiran Michael ɗin nasa, wato Heartbeat, sai ya gane wato ita matar Michael ne, tab lallai akwai rikici. Cikin fushi ya ɗauketa da wani wawan mari wanda ya sanyata juyi ta faɗa saman gadon, wani irin azababben ihu ta saki dan ta maru ba karya, nan take yatsun daddy biyar reras suka fito ɓaro ɓaro a saman kumatunta, dan ita ma a Nigeria fara ce tas, a gabansu ne take baka dan su babu mix a jininsu tarr suke. Jay, Uncle Herry da suke tsaye a bayansa duk sun ji daɗin abin da daddy ya yi dan suma suna kyamar bakaƙen fata, shi kuma John har cikin ransa bai ji daɗi ba, dan kuwa tun da ya ganta a ɗakin Michael yasan cewa Michael yana sonta kenan, to duk abin da Michael yake so shi ma yana so, ba ruwansa da kabilarci or faɗar addini, shi dai yana kaunar Michael dan tare suka taso, komai tare suke yi a baya, dan haka kaunar a jini take. To masu karatu a yanzu dai dole mu mayarwa da su Michael sunansu na farko, domin su daddy basu san sun musulunta ba, kuma kunga dama basu son su daddyn su sani, bamu san dalilinsu ba, za dai muji komai a gaba, yanzu dai shi daddy Michael yake kira, so dole bakinsa zamu rubuta ba namu ba. Da sauri John ya karisa wajen da take kwance ta dafe kumatunta tana kuka, cikin sauri ya sanya hannu ya ɗan ɗagota yana faɗin "Haba daddy why zaka mareta haka? You know fa tun da ka ganta a nan Michael yana sonta ne, to kuma bai kamata ka daki abin da Michael yake so ba gaskiya, ni wlh ina sonta tun da Michael yana sonta". Wani irin mahaukacin tsawa ya dakawa John ɗin wanda ya sanya shi razana har ya saki hannunta da ya riƙe, wannan tsawar ce kuma ta sanya Aseef dake toilet ya ji abin da yake faruwa, tsaida ruwan da yake zuba ya yi yana son jin menene yake faruwa?. Faɗa daddy ya fara yi a kan lallai Akila ta tashi ta bar gidan nan yanzu! Babbar magana, Me ya kawo hakan? Duk tsana ce? To ina ga kuma ya ji shi ma Lion ya auri bakar fatar? Akila da take fara tas kamar Naurat ma ya kira ta baka ina ga kuma Rimsha da take da kala mai tsada a duniya wato chocolate color? Ita kam kamar gawayi zai kalleta kenan? Ina ga ita tsanar da zai yi mata ma sai yafi na kowa, dan ita ce kawai chocolate a cikinsu dake gidan, Jehan ma fara ce tas irin farar fatar Naurat, e lallai da akwai case ba kaɗan ba, dan kuwa bana jin Aseef dai zai rabu da Akila, bama zai yiwu ba, dan ana rabasu mutuwa zai yi, sai dai Akila ta hakura ta jure azaban daddy, dan yadda ya tsanesun nan zasu wahala da alama!!. Jin voice na daddynsa ne yasa ya ajiye brush dake hannunsa, dama already ya gama wanka yana shirya brushs dake wajen ne da AKila ta watsasu da safe bata gyara ba, ruwa kuma yana ta zuba bai kashe ba, dama sai ya gama zai kashe ya fita, jin voice ɗin na daddyn ne yasa ya ajiye brush ɗin tare da ɗauko karamar towel ya ɗaura a saman kansa dan goge gashinsa, dama already ya ɗaura babba a kugunsa. Da kyar ya fito wajen, har lokacin bai gama warwarewa ba, ya dai samu jirin ta sake shi, yana iya shiga toilet da kansa, amma jikinsa babu wani kwarin kirki. Ganin abin da yake faruwa ne yasa ya kariso wajen da sauri tare da kama hannun Akilar ya mikar da ita yana kallon face nata yadda yatsun daddy ya fito ɓaro ɓaro, hakan kuma ya yi daidai da shigowar Lion da Areef da ya dawo daga Abuja yanzu, jin daddyn na surfa masifa ne yasa suka shigo dan su ga me yake faruwa. Rungume matarsa Aseef ya yi yana bata hakuri ba tare da ya ce da daddy komai ba, ya san dai wlh babu abin da ta yi wa daddy ya mare ta, dan haka ba sai ya tambayi ba'asi ba. Daga Lion har Areef sun san cewa wlh babu abin da Akila ta yi wa daddy ya shinfiɗa mata yatsunsa biyar ɗin nan a face nata har haka, already dama sun san shi da tsanar bakaƙen fata, to a tunaninsu hakan ce tasa ya wanke mata fuska da mari, Baiwar Allah har wasu taurari ta gani, ta sha marin Dr William Dangerous Boss. Tsawa ya dakawa Aseef ɗin a kan ya saketa ta zo ta bar gidan nan, da sauri ya ɗago brawn eyes nasa da suka yi ja ya saukesu a kan Lion dake tsaye yana ganin wannan iko irin na daddy, sai ka ce shi zai zauna da ita. Areef ne ya katsesu da cewa "Daddy what is happening here? Why are you shouting like that? Kabi komai a hankali mana". A kule ya jiyo ga Areef ɗin yana tambayarsa au tsawa ma kenan yake shi, ihu yake yi ma kenan? E lallai sun raina shi. "James ina son wannan yarinyar ta bar gidan nan yanzu nan, I don't want to see her close to my son". "Sorry daddy, I can't live without her, gaskiya ni a bar mini matata". Cewar Aseef, ya yi maganar da kyar saboda tsananin ciwo da kansa yake yi mishi. Ganin yadda yake faman ciza laɓɓansa ne yasa Lion ya fahimci har yanzu fa akwai ciwo a tarrare da shi sosai, so bai kamata su ɗaga mishi hankali ba, dan haka sai ya dubi daddyn nasa ya ce "Daddy babu abin da zai raba Michael da matarsa, yana sonta, ita ma tana son shi, so banga abin da zai rabasu ba, ko da Michael ya ce baya sonta yau, to wlh dole ya zauna da ita dan kuwa tana son shi, a kansa ta kusa mutuwa, bai isa ma ya ce ba zai zauna da ita ba, ko ya dai'na sonta, so daddy kowa ya wuce bedroom nasa bana son wata hayaniya!!". Tsawa ya daka musu tare da buga saman bedside drawer yana faɗin ba zai yiwu ba, dole yau wannan munafukar yarinyar ta bar gidan nan. Banza da shi Lion ya yi bai sake yin magana ba tamkar babu shi a wajen, ba zai wani ɓata bakinsa ba wajen yin wani magana, saboda bai ga uban da ya isa ya raba Aseef da matarsa ba, ba daddy ba yau ko Jacop Roshan ne zai fito daga cikin kabari to sai ya barwa Aseef matarsa. Tashin sense, Jacop Roshan da kansa kuma yau? E lallai Lion ya yi nisa. Nisawa Areef ya yi kafin ya ce "Dad please and please ka dai'na faɗin haka, seriously Michael yana son matarsa, and then....." Wani irin razanannen tsawa daddyn ya daka mishi wanda ya sanya shi dakatawa da maganar, sam Areef baya son ganin ran daddyn ya ɓaci, amma kuma yana kure shi, sai danne zuciyarsa yake yi dan kada ya zama ya yi mishi irin abin da Lion yake yi mishi, idan aka ce sun haɗu sun zama iri ɗaya waye zai taushi daddyn kenan? Amma kuma daddyn yana neman kure hakurinsa gaskiya, taya zai yi ya ce shi baya son matar Aseef sai dai su rabu? To shi zai zauna masa da matar ne? Wlh tsohon nan ɗan neman bala'i ne, to sun ce basu son turawa ƴan uwan nasu bakaken fata suke so ana dole ne? Dama ya samu Aseef ɗin ya yi auren ne zai wani takura musu, idan da irin Jay Aseef ɗin ya yi musu ya kawo musu ɗan shege ba shikenan ba?!. Shi kuwa Aseef ya rungume Akila dake ta faman kuka ta sha mari yau, sai rarrashinta yake yi. "Michael ɗauketa ku je zuwa bedroom na dan na ga kamar zaka faɗi, idan kun je ka rufe kofar with key". Cewar Lion, dan ya luran Aseef ɗin kamar zai zube kasa saboda rashin kwarin jiki, ga kuma hayaniyar daddy sannan ga Akila a rungume a jikin nasa tana kuka, abubuwan sun yi mishi yawa bawan Allah. Sam daddy ya hanasu wucewa, shi dai ya kafe lallai baya son bakaken fata, sai da ya ga ran zakunan nasa wato Lion da Areef ya ɓaci, face nasu ta sauya, ya san ba zata yi musu kyau ba, sannan ne ya shafawa kansa ruwan sanyi ya bawa Michael hanya, amma fa ya kuduri niyar wlh sai ya rabasu, dan shi bazai yi mix na jini da kowa ba face ƴan uwansa...... E akwai kura in dai haka ne kam. Wucewa Aseef ɗin ya yi zuwa bedroom ɗin Lion, a hankali yake tafiya gudun kada ya faɗi, sai shessheƙar kuka Akilar take yi, ita kuma Rimsha tana cikin bedroom nata suna zuba dirama da Jehan a kan zuwa wajen Lion ta yi dare haka, dan jiya a kullace da Rimshar ta yi barci, ta jirata har wajen 11 bata dawo ba har barci ya yi awon gaba da ita, da safe kuma Rimshar ta tafi school basu haɗu ba, dama jiranta take yi ta dawo school sai ta gaya mata uban da take zuwa yi wajensa har dare haka? To shi ne diramar da suke yi, Rimsha dai ta kafe akan ita wlh babu wani abin da take yi bayan kai mishi abinci, ita kuma Jehan ta ce karya take yi munafuka, kai abinci ne sai ta shafe awa huɗu a can, to wlh ba zai yiwu ba, ta shiga hankalinta da kyau idan ba haka ba sai ta yi mata ɗan iskan dukan mutuwa sai dai duk abin da zai faru ya faru. Da yake ita ma Rimshar akwai zuciyar sai ta ce "Kinga ne Jehan duk wannan magana ba ni zaki yi wa ba, ki je ki sami Yaya Saif ɗin ki gaya mishi, domin shi ne mai tsayar da ni, kuma ni ban isa in ce mishi a'a ba, so kila idan kika yi mishi magana zai ji sai ya dai'na tsayar da ni". "Rimsha ba zan yi mishi magana ba dan bani da wani haɗi da shi! Ke kuma na isa in saka ki kuma in hana ki, wlh idan kika sake wuce minti 30 a wajensa sai ranki ya ɓaci!!". Ta yi maganar cikin fushi da ɓacin rai, dan kuwa abin ya kona mata rai yadda jiya Rimshar ta jima bata dawo ɗaki ba har ta yi barci, wannan ma fa bata san cewa tare a garden ɗin suka kwana ba, ta yi tunanin Rimshar ta dawo cikin dare bayan ta yi barci kenan. Miƙewa Rimshar ta yi tare da riko hannuta zuwa palon sama, dai'dai lokacin kuma Lion da Areef sun hauro sama bayan sun gama case da daddy Areef ya kai shi masauki, shi ne suka nufo bedroom ɗin Lion ɗin dan su tattauna a tsakaninsu su ukun. Da hannu Rimsha ta nunawa Jehan ɗin Lion tana faɗin "Wannan shi ne yaya Saif, sai ki gaya mishi ya dai'na rikeni ina jimawa a ɗakinsa". Ko kallon in da suke Lion ɗin bai yi ba ya wuce zuwa kofar bedroom nasa yana knocking a hankali dan Aseef ya rufe kofar da key, ita kuwa Jehan ta sha jinin jikinta sosai ganin Lion, ashe bata ga komai a hoto ba, a zahiri ma kwarjininsa yafi yawa, wani irin azababben tsoronsa ne ya dira mata a ranta, dan kuwa bata ga wajen wasa ba, dan ma ko kallonsu bai yi ba, Areef ne ya tsaya yana tambayarsu me yake faruwa? Ba ɓoye ɓoye Rimshar ta gaya mishi abin da yake faruwa. Da hannu ya yi wa Rimshar alama a kan ta koma bedroom nata bari ya yi magana da Jehan ɗin, a lokacin kuma Akila ta buɗewa Lion kofar bedroom ɗin ya shige abinsa. Wucewa Rimsha ta yi ta koma ciki, juyawa ita ma Jehan ɗin ta yi da nufin ta koma ciki, da sauri ya riko hannunta yana faɗin "Wai ke meyasa kika cika faɗa da neman rigima ne?". Harara ta watsa mishi tare da fisge hannunta ta juya zuwa ɗakin dan ta je ta jibgi Rimsha akan ta kawota gaban Lion, haka kawai ta sanya ta sai faɗuwar gaba take yi tun da ta ganshi, dan haka ba zata kyaleta ba wlh. Da sauri ya bi bayanta zuwa cikin ɗakin, dan yanda ya kallin ta juya a fusacen nan yasan tana iya aikata wani abin ga Queen nasu. Dai'dai lokacin da ya shigo ta ɗaga hannu zata mari Rimshar dan fa a fusace take, rike hannun nata ya yi tare da ɗaure fuska sosai cikin nuna isa ya ce. "Ki natsu ko kuma na nitsar dake yanzun nan". Ganin ya ɗaure fuska ya koma kamar Lion ne dama kuma ga bala'in tsoronsa da take ji, hakan yasa ta natsun kamar yadda ya faɗa, dan kuwa wlh tsab zai iya ajiye soyayya a gefe ya gyara mata kuskure idan ta yi, yana da wasa da dariya ga waƴan da ya ga damar yi da su, amma fa idan ka yi mishi ba dai'dai ba abin da baya so, wlh tsab zai canza maka daga Areef zuwa TRIPLETS ɗin General Of The Army, yanzu zai yi maka hukunci. "Our Queen jeki zuwa wajen daddy ina zuwa nima yanzu". Ya yi maganar tare da sakin hannun Jehan ɗin ya nuna mata waje saman gefen gadon a kan ta zauna, bata musa mishi ba ta zauna, dan tasan ko daddy ta kaiwa karansa bai wuce ya ce mata yayanta ne ta bi abin da ya ce ba, so is better kawai ta bin ya fi. "Ba da wasa nake miki ba, idan kika yi kuskure dukan Rimsha serious ko ni ban isa in tare miki wannan faɗar ba, dan idan garin nan kap zasu haɗu bana jin zasu iya tare miki, idan kika ga Lion bai sumar dake ba, to sai dai idan Rimshar ce da kanta ta shiga tsakaninku, ki sani Lion yana da damar yi miki duk hukuncin da ya ga dama idan kika taɓa ta saboda matarsa ce, akwai aure a tsakaninsu, so baki da damar dukanta, bare kuma da hujjar taki ta zama a kan dan ta je wajensa ne, to ki sani mijinta ne, ita kanta bata san mijinta bane, kuma ban ce ki gaya mata ba, ki kyaleta kamar yadda uncle ya ce kada a gaya mata, abin da yasa kema na gaya miki, dan ba zan iya juran wani abin ya same ki bane, na san in dai kika taɓata a yadda Lion yake yanzu sonta na ɗawainiya da shi ba tare da ya sani ba, tsab zai iya yi miki illah, ba zan iya juran hakan ba ni kuma shiyasa kawai na gaya miki, tun wuri ma ki sani, dan haka ki cire idanunki a kansu babu ruwanki da su". Hakika ta tsorata da jin cewa akwai aure a kan Rimsha, abin ya girgiza ta, to ya akayi hakan ta faru? Ta tambayi kanta, lallai kuwa abin da mamaki, baiwar Allah Rimsha ita bata ma sani ba, ga shi daddy ya ce kada a gaya mata, ko meyasa ya ce hakan? Ta sake tambayar kanta. Ganin ta shiga duniyar tunani ne yasa ya hura mata iskar bakinsa a fuska yana faɗin "Faɗa mini ke kuma yaushe kike son muyi aure?". Kallon uku goma ta wurga mishi kafin ta ce "Me kuma aure? Sunan wani abinci ne? Idan ma abinci ne bana ci, dan daga jin sunan abincin ba zai yi daɗi ba". Da yake shi ma ɗan yi ne sai ya matso kusa da ita sosai, kasa kasa kamar mai raɗa ya fara magana "Yes sunan abinci ne aure, abinci kuma mai daɗi ma kuwa, kuma ko zaki yi yaya sai kinci, kuma ni zan baki da hannuna, dan haka ki fara shirin aure tun yanzu, bari dai Lion ya je lafiya ya dawo lafiya, daga nan sai aurenmu, yanzu bani da kwanciyar hankali yin aure har sai ɗan uwana ya dawo lafiya, ji wani ɗan bakinta a wajen, zaki ga abinci ne iya ganin idonki masifaffa mafaɗaciya kawai, Allah ko har na hangoki kina goye da baby'sna a bayanki, zakuwa ki yi matukar kyau da hakan, Allah ya sanya ki haifi 5 baby's lokaci guda, dan ni ina matukar son baby's Lion ne baya so, shi ma kawai dan baya son hayaniya ne, amma nasan idan baby's nasa ne dole zai so a nawa tunanin". Miƙewa ta yi dan ta lura Areef fa ya fita iya iskanci, duk wani mannin haukarta to ya ninkata, ko da me ta zo wlh ya fita, Hmmm ga shi Bature babu kunya ko ɗigo a lamuransu, bugu da kari ya yi rayuwa waje daban daban, ai dole ma taga abin da ya minka haka, idan bata yi hankali ba ma ta biye mishi suna magana, wlh watara sai ya gaya mata abin da yafi karfin ƙwaƙwalwarta, rufin asirinta ɗaya idan yana magana ta yi shiru, idan ba haka ba, duk wani amsa da zata bashi, yadda zai fassara shi daban, dan sai ya kara gishiri da su maggi, ya tsara kalmar da kyau kafin ya bata amsa wanda zai sanyata yin shiru bata shirya ba, ga shegen iya magana a wajensa na wuce misali, kai a takaice komai ya haɗa, idan shiru shiru ne ma tsab zaka samu a wajensa, dan wlh bashi da magana sai da waƴan da yaga dama, maganar tasa ta ganin dama ce, wani lokaci ko da Aseef idan bai ga dama ba baya tanka mishi magana idan yana yi mishi, shi ɗan naga dama ne over. Ganin ta miƙene yasa shi ma ya miƙe yana faɗin "Jiba idanunta a wajen kamar na Aseef, sai ka ce ball, amma suna mugun yi mini kyau fa". Ko sannu bata ce mishi ba ta nufi waje dan ta je wajen daddynta, rufa mata baya ya yi yana faɗin "Wow baby ko ta baya ma ke haɗaɗɗiya ce, gaskiya kin iya tafiya fa, see beautiful shape!" Tsayawa ta yi ta fasa tafiyar haushi kamar ta shake mishi wuya ta yi ta kifa mishi maruka a wannan jajir ɗin kumatun nasa ko zata huce, ashe dama tafiyarta yake kallo dan iskanci, wannan mutumin ɗan iska ne gaskiya, ta faɗa a cikin zuciyarta tana wani zabga mishi harara. Shi kuwa murmushi ya sakar mata yana jin wani irin tsantsar nishaɗi idan yana tsokanar ta, da gangan ya ce mata hakan dan kawai yaga tana hararsa tana juya dara daran fararen idanun nan nata, ba ƙaramin tafiya da imaninsa suke yi ba idan tana hararsa, so yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa yake yawan tsokanarta, da hararar. "Mu je mana". Ya faɗa yana karewa kirjinta kallo, ga shi babu hijabi a jikinta, daga ita sai doguwar rigar abaya, sai dai ita tana sanya breziya, yanzu ma ta yi amfani da guda ɗaya cikin wanda Akila ta taɓa ɗaukawa Rimsha lokacin da Imran ya kaisu shopping, Rimsha bata taɓa bi ta kansu ba, dan bata sakawa, da vest kawai take amfani, amma ita tana sanyawa dan breast nata sun ciko sosai, dama kun san tana da halittarsu sosai ita ma, so shiyasa take sakawa, hakan kuma ba ƙaramin kyau ya kara mata ba, ya kara bayyanar mata da shape nata, bata sanya ɗankwali ba, dan idan baku manta ba Jehan bata son ɗankwali sai idan ya zama dole, idan baku manta ba kullum faɗarta da mummy kenan a kan ɗankwali, so yanzu ma ta saki kyakkywar gashin nata ba ta ɗaure ba. Ganin yana karewa kirjinta kallo ne yasa bata da zaɓi dole ta cigaba da tafiya dan ta gujewa kallon da yake yi mata ɗin, cool murmushi ya saki yana mai jin tsantsar kaunarta har cikin ransa, yana son ƴar diramar nan tasa so na wuce misali. Rufa mata baya ya yi har zuwa bedroom ɗin daddy. Daddy da Rimsha suna saman bed suna hira, yana zaune Rimsha ta tada kai da cikyarsa. Da sauri ta haye gadon tana faɗin Rimsha ta tashi mata bari ta kwanta idan ya so ita kuma sai ta kwanta ta kafofin daddyn, yau ga karfin hali. Juyowa Rimshar ta yi ta rungumi daddyn tana faɗi wlh bazata tashi ba, ai ko addinin musulunci ya yi hani da ka sami mutun a waje yana zaune ka ce ya tashi ka zauna, koda kuwa ka girme shi to bai kamata ka tashe shi ba, yin hakan zalinci ne, addinin musulunci kuma baya goyon bayan zalunci, ya yi hani da shi, kuma ya tsawatar da babbar murya, dan haka ita gaskiya bazata tashi ba dan magana ake ta addini bata girma ba. A kule ta ce "To sarkin wa'azi, ban nemi ki yi mini wa'azi a nan ba, dan haka ni ki tashi ko kuma wlh naja kafarki ya yasar dake a kasa, dama can ai ni nake kwanciya a cinyar daddy da Gwaggo, ke kuma mummy wata rana ki haɗa da Gwaggo, dan haka wlh ki tashi tun wuri". Shi dai daddy sai murmushi yake yi abinsa, wato har yanzu da suka girma ma ba zasu dai'na wannan faɗar ba, abu tun suna yara, kamar wasu tom and Jerry. Kai uba mai daɗi kenan, Allah ka sakawa iyayenmu da gidan aljanna. Hayewa saman gadon shi ma ya yi yana faɗin "Our Queen maza tashi ki bani waje dan dukkanku yanzu ba kafarku ba ne, nawa ne ni kaɗai". Ba musu ta miƙe ta bashi waje, kwanciya ya yi abinsa, shafa lallausan gashinsa daddyn ya fara yi suka fara zuba hira, miƙewa Rimshar ta yi ta nufi waje abinta dan ta leƙo masoyinta tana kewarsa. Ita kuma Jehan haushi kamar ta kifawa Areef ɗin mari, haka ta matso ta kwantar da kanta a kafaɗar daddyn tana turo baki, daddy dai yana ganin ikon Allah wajen ƴan diramar nan tasa, wato Areef da Jehan sai Allah, yanzu da gangan ya ce zai kwanta a cinyar daddyn dan yaga ta ce zata kwanta, saboda neman tsokana ya wani haye ya kwanta, sam ya manta magana zasu yi da Lion da Aseef, ya zo yana ta neman tsokanar Jehan. A ɓangaren su Aseef kuwa, lokacin da suka shiga bedroom ɗin na Lion, saman bed ya haye tare da sakin Akilar yana mai cigaba da yi mata sannu, saman bedside drawer ta zauna tana ɓoye fuska dan bata son ganinsa ba riga, wani irin kunyarsa take ji, sosai ya lura da hakan, sai ya ce ta zo. Ba musu ta haye saman bed ɗin, jawota saman kirjin nasa ya yi yana faɗin "Kunyar kallon mijinki a haka kike ji?". Gyaɗa mishi kai ta yi tana sake ɓoye fuska, "Au kin manta cewa kafin muyi aure kin yi alkawarin zaki yi mini wanka kuma tare zamu rinƙa yi dake kullum ne?". Dukan wasa ta kai mishi a kirjin nasa, cikin tsantsar shagwaɓa ta fara magana kasa kasa kamar mai raɗa. "To ai ba yanzu ba, sai gaba". Kai tsaye ya ce mata "Sai nayi disvirgin naki?". Zaro idanu ta yi tana mamakin rashin kunya irin tasu, wai su kwata kwata basu san kunya ba, magana sam bata yi musu nauyin faɗa? (Ni kuwa nace ai Aseef ma mai sauki ne yana da ɗan sauran nasa kunya da kika koya mishi, rashin kunya ai sai Lion da Areef) "Baki bani amsa ba?". Ya yi maganar yana ɗago haɓarta dan su fiskancin juna, shiru ta yi tare da rufe idanunta dan har ga Allah bata da amsar da zata bashi, ya sanya ma ta kara jin kunyarsa sosai. "In dai sai nayi disvirgin naki ne zaki fara yi mini soyayyar da kika faɗa to ni gaskiya dole yau zan yi hakan". Ya yi maganar a shagwaɓe sosai, wasa ta fara yi da yatsunta a saman kirjin nasa tana turo baki tare da faɗin "Ni dai Heartbeat ka dai'na faɗin haka dan Allah, Allah bana so". "Bakin so me?" Ya tambaya yana ɗan kama hannun nata ya mayar saman breast nasa. "Maganar da kake yi mana, bana so ka bari". "Baki son nayi disvirgin naki?". Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e, "Why to?" Babu komai ta bashi amsa, "Serious?" Ya yi maganar cikin wata iriyar murya dake nuna tsantar tsokana ta masoya, jinjina mishi kai ta yi almar e da gaske take yi. "Tom shikenan naji ba zan yi yau ba, amma gaba zanyi idan na sami lafiya, dan gaskiya ba zan iya kyaleki ba, ina son in karɓi virgin ɗina sosai". Yatsa ta ɗaura a saman lips nasa alamar ya yi shiru, ta yi hakan tana gyara kwanciyar a jikin nasa da kyau, ɗan bakin nasa ya buɗe tare da capko yatsar nata ya fara ɗan ciza a hankali yana shafa bayanta har zuwa kumatunta in da ta sha marin daddy. "Am so sorry my rigimati". Ya faɗa tare da cire yatsar tata daga bakin nasa, nisawa ta yi kafin ta ce mishi babu komai ai daddynsa tamkar daddynta yake, so yana da damar da zai iya dukanta kamar yanda zai dake shi shi ma, dan haka kada ya damu ita ta yafewa daddyn tun lokacin. Rungumeta ya yi sosai yana mai jin tsantar farinciki tare da jin wani azababben kaunarta yana kara ratsa shi, ita ma rungume shi ta yi tana murmushi. "Can I kiss you?". Ya yi mata maganar cikin raɗa a kunne, ɗan ɗagowa ta yi suna kallon juna, zubawa lips nasa idanu ta yi, sun kara ja sosai alamar ya ɗan cizasu saboda daɗin rungumarsa da ta yi. Gera ɗaya ya ɗaga mata yana faɗin "Do you love it?" Ya yi maganar yana nuna mata lips ɗin nasa. Kai ta gyaɗa mishi alamar e tana son lips ɗin nasa, dan ba karya suna da kyau sosai, akwai abubuwa da ya kasace a jikin TRIPLETS iri ɗaya ne sak babu banbanci, ciki har da kafarsu, lips nasu da sauransu, dama kunsan dole a sami hakan dan mahaifa ɗaya ba wasa ba, hakan yasa duk wanda ya gansu sai ya ji lips nasu ya burge shi, dan fa ba karya akwai kyau, shiyasa Rimsha take yawan kallon na Lion, sai dai ita fa Rimsha na Lion ɗin ne kawai yake burgeta, bata taɓa ɗaga ido ta kalli na TRIPLETS nasa ba, ita dai nasa kawai. SO KENAN, NA KOWA BAYA BURGETA SAI NASA, YANZU KUMA SUN ZAMA MALLAKINTA BA TARE DA TA SANI BA. Yana ƙoƙarin fara kissing nata Lion ya yi musu knocking na kofar, sauka gadon ta yi ta je ta buɗe mishi, ko kallon in da take bai yi ba ya shige cikin ɗakin, bayansa ta biyo ta zo ta zauna a saman bedside drawer. "Kai my rigimati, ni kizo ki kwanta a jikina kamar ɗazun hai". Ya yi maganar a shagwaɓe, ɗan satar kallon Lion dake ƙoƙarin fito da A box daga mazauninsa ta yi, kafin ta grigiza mishi kai alamar a'a bazata zo ba tun da Lion yana nan. Kukan shagwaɓa ya saka mata yana faɗin "Wai ke meyasa kike yin wannan abin ne? Ni fa bana son wannan kunyar". Shiru ta yi bata yi magana ba. A gefensa Lion ɗin ya zauna tare da fara duba shi bai ce musu ko sannu ba, dan shi bashi ne a gabansa ba, lafiyar ɗan uwan nasa ne a gabansa, shi ne abin da ya fi damunsa. Haka suka kasance har ya kammala duba shi tare da yi mishi alluran barci sannan ya miƙe ya fice gabaɗaya daga bedroom ɗin ya koma garden dan ya kwanta ya huta. Yana fita ita ma ta haye saman bed ɗin kusa da mijin nata ta kwanta, dan tana tsoron ta koma bedroom nasu daddy ya sake dawowa. 💋AFTER SOME HOURS❤️ Da misalin karfe 8 na dare, taci wankanta ta tsara kwalliya kamar me, ta yi kyau sosai, sai tashin kamshi take yi, yau barci take ji sosai saboda ta gaji, ga shi gobe akwai school zasu yi Exams na karshe, jibi partynsu, dan haka sai ta sanya kayan barcinta riga da wando launin white color masu masifan kyau, akan idan ta dawo daga wajen Lion kawai ta kwanta abinta ba sai ta tsaya shiri ba, kayan barcin jikinsu yana da tsantsi sosai ga laushi, hijabi har zuwa gwiwarta ta ɗauko ta sanya a jikin nata tare da kara fesa perfume nata sannan ta fito ta nufi kitchen dan ta ɗauki abincin Lion ta kai mishi, ita kuma Jehan tana wajen daddy suna hira, Aseef ya koma bedroom nasa shi da Heartbeat, Areef yana bedroom ɗin daddynsa suna hira. Bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin ɗakin, shiru babu kowa, a in da ta saba zama ta je ta zauna tare da ajiye abincin tana jiran zuwansa, kamar wanda aka mintsina sai ta ce bari ta buɗe kular yau taga me Mark ya girka musu, dan yanzu abincin Lion ɗin take ci, bata zuwa kitchen ɗiban wani, na kular tasa dai idan ya gama ci shi take ci. A hankali ta buɗe kular tana leƙawa kamar daga sama taga mutun ya faɗo cikin ɗakin babu ko excuse, ba ƙaramin razana ta yi ba, hakan yasa ta saki marfin kular tare da mikewa kamar wata mara gaskiya. Ɗaure fuska sosai daddyn ya yi yana kare mata kallo kafin ya daka mata tsawar me ya kawota bedroom ɗin ɗansa? Wacece ita kuma me zata yi mishi a cikin abinci data buɗe? Me tazo yi?. Baya baya ta farayi dan ta gudu ta fita, daddyn ma ya fara binta tare da kara tambayarta me take yi a cikin ɗakin ɗansa, ta tsorata sosai da ganin shi, musamman da ya zare mata dara daran blue eyes nan nasa irin na Lion ɗin, ga shi kuma an samu akasi ta buɗe kular abincin ne ya shigo, shiyasa ya ce sam wani abin zata yi wa ɗansa, dama bakaƙen fata mugaye ne a cewarsa. Hawaye ta farayi tana ja da baya bata ankaraba sai ji ta yi ta bugi mutun, ta kasa juyawa ta ga wanene dan saboda bala'in tsoron daddyn, sai dai har cikin ranta ta ji cewa Lion ne, dan daga kamshin perfume nasa ta gane, duk da cewa yanzu su Areef duk da perfume ɗin nasa suke amfani, amma ya fi kama jikinsa shi, idan ya doso waje dole sai kamshin ta bule ko'ina lungu da saƙo. Tsawa daddyn ya daka mata wanda ya sanyata watsawa a guje da nufin ta fita ɗakin, cikin sauri Lion ɗin ya rikota ta kugunta tare da jawota jikinsa dan ya rabata faɗa da daddyn kada abin da ya faru da Akila na marinta da daddyn ya yi ya faru da ita itama, so is better ya takawa abin birki ya kuma gayawa daddyn cewa shi ya sakata duk wani abin da take yi a cikin bedroom ɗin nasa, dan haka babu ruwansa da ita. Narai narai ta yi da idanu ta kasa juyowa ta kalli Lion ɗin, ɗan rankwafo da kansa ya yi daidai saitin kunnenta kasa kasa ya ce ta je ta zuba mishi abinci dan yana jin yunwa, ya yi maganar tare da sakinta yana kallon daddyn. "Dad let's go and eat". Ya faɗa tare da nufar saman bed ya ajiye laptop nasa da duk wasu kayayyaki na mummynsa da ya je ya yi bincike a kansu a garden. "Romeo ni ba zanci abincin nan ba, kuma kai ma ba zakaci ba, dan ban yarda da abincin ba". Shiru ya yi bai tanka ba, bayan ya gama ajiye kayan ne ya wuce zuwa in da ya saba zama ya zauna, a nitse ya ce "Dad why kake son problem ne? This girl she is our sister, since before now muna tare, and then karamar yarinya ce sosai why are you thinking or expecting cewa zata cutar damu? Me wannan innocent face ɗin ta sani? Gaskiya kana son wahalar da kanka dad, you know cewa tun da ka ganta a bedroom na ai nasan ba zata cutar da mu ɗin bane, so please stop all this thing that you are doing, kazo kawai muci abinci". Jinjina mishi kai daddyn ya yi alamar ya gamsu da maganarsa yana faɗin "Okey tom i agreed, amma ni zanje naci abinci dasu Herry a saman dinning table kamar yadda muka saba ci". Kai kawai ya gyaɗa mishi ba tare da ya yi magana ba, juyawa ya yi ya fice daga cikin ɗakin ya nufi wajen uncle Herry. Zuba mishi abincin ta yi ta tura mishi, spoon ya ɗauko ya faraci a nitse ba tare da ya kalli in da take ba, sai dai fa yana tsananin son kallon cikin idanunta, ya yi kewarsu sosai yau, ita ma sai satar kallon shi take yi, tana kewar fine face nasa, sam bai ɗago ya ganta ba har ya kammala cin abincin ya mike ya bar waje ya nufi waje gabaɗaya. Kayan abincin ta kwashe zuwa waje, kitchen ta mayar da su, ko sannu bata ce da Mark ba, dan ta lura yanzu sam baya son ta rinƙa yi mishi magana, hakan yasa ko sannu bata ce mishi ba ta wuce ta fito abinta. Bedroom nasu ta yi niyar komawa, tamkar wadda aka cewa ta juya ya kalli cikin bedroom nasa, kai tsaye saman bed nasa ta kallah, kayan da ya ajiye ta gani, sanin cewa baya cikin ɗakin ne yasa bata ji tsoro ba ta shige ciki dan ta kalli menene ya ajiye a wajen. Gefen bed nasa ta zauna, ko'ina na cikin ɗakin fes yana tashin kamshi, kayan mummyn nasa ta fara dubawa, wannan takarda da yake son sanin wace yarece a rubuce a jiki ta ɗauka tare da hoton Josephine ɗin tana kallo, da yake kowa da yadda yake kallon mutun, sai ita kuma ta kalli Josephine ɗin sak Lion ɗin tamkar an tsaga kara, banbancin kawai kalar kwayar idanu ne, amma ta yi mata muguwar kama da shi, hakan yasa ta fahinci cewa lallai wannan mummynsa ne ko kuma sisters, dan kunga a lokacin da Josephine ɗin ta yi hoton tana budurwa, shiyasa Rimshar ta kirata da sistersa, ta yi kyau sosai a hoton ba karya. Zubawa sarkar wuyarta idanu ta yi tana kallon shi da mamaki, tunani ta fara yi a kan a ina ta taɓa kallon sarkar nan bayan wuyar TRIPLETS, tabbas sai da ta ganshi yanzu a wuyar Josephine ɗin ne ma ta tuna wlh ta taɓa kallon irin sarkar, to amma a ina? Ta mance dan lokaci bata yi wayo haka ba, matso da hoton sosai ta yi kusa da ita, a nan ne ta fahinci da sarkar wuyar Josephine ɗin da ta wuyar Lion yana da banbanci kaɗan, na wuyar Josephine ɗin akwai rubutu a tsakiyar sannan ya fi nasu girma, tun da Lion yake bai taɓa kurewa hoton kallo har yasan da rubutu a jikin sarkar ba, sai ita yau dan tsabar fitina. Zubawa rubutun idanu ta yi tana son karanta menene a rubuce a wajen, shiru ta yi tana tariyo sarkar Lion dan shi ma ɗin nasan kamar akwai rubutu wlh, sam dukkansu ba wanda ya taɓa lura da rubutun dake jikin sarkar, dan ba karya rubutun kanane sosai, idan ba ka mayar da hankali sosai ba bazaka gani ba, tabbas tana da bukatar sake kallon sarkar Lion dan taga me aka rubuta, ga dai na Josephine rubutun ba da English bane, da yare ne, hakan na nufin kenan Josephine tana da yare? Dan kuwa wannan sarka dai ita da kanta ta sanya aka buka mata, ba kamar sauran sarkoki yake ba, kuma da alama tabbas akwai dalilin da ya sanya ta sa aka buga mata wannan sarka, alamomi da dama sun nuna hakan, na farko rubutun dake jikin sarkar, na biyu da yare aka yi rubutun, na uku meyasa ta cire tambarin heart na sarka ɗaya ta rike a wajenta, sai ta bawa TRIPLETS babu shi? Meyasa zata yi hakan? Hakan na nufin tabbas akwai sakon da take son isar musu ne wanda ta san da bakinta ba zai isa garesu ba, tasan ba zasu taɓa sauraranta ba idan suka girma, hasashe ta yi hakan yasa ta yi musu haka, ga shi kuma hasashenta ya zama gaskiya, sam sunki bata dama su saurareta, bata wani damu ba, dan tasan duk lokacin da Lion ya natsu, ya kuma mallaki hankalin kansa sosai, ya lura da abubuwan da ta bar musu, to dole shi da kansa zai zo in da take dan neman wasu amsoshi wanda ita ce kawai zata bashi wannan amsoshin, a nata hasashen kenan, kuma hakan ce take shirin faruwa, dan kuwa idan baku manta ba, a dube duben da Lion yake yi kwanaki har yaso yasa a kawo mishi ita dan ya yi mata wasu tambayoyi, case ɗin daddyn Rimsha data kunno kai tasa ya watsar da zancen mummyn nasa, yanzu kuma ya gama da case ɗin daddy, abin da ya rage ɗauko Na'urat ce wanda kuma ya san in da take, sai mummy wanda ita ma yasan in da take, so a takaice ya gama da case ɗin daddy Shiyasa yau ya fito da kayan mummyn nasa yana bincika dan gaskiya yana son sanin gaskiyar abin da yake faruwa a tsakaninta da daddy, yana da bukatar amsoshi da dama daga wajenta, ciki kuma har da fassarar abin da ta rubuta a takardan nan dan shi bai san wani yare bane wannan, shiyasa ma taki rubuta mishi da yaren da zai gane dan dolensa ya je neman faffasar yaren a wajenta, tarko ta kafa musu sosai ta yadda in dai sun mallaki hankalin kansu to dole zasu nemeta a koma ina ne su kai kansu gareta. Ganin ba zata iya karanta abin da yake rubuce a jikin sarkar ba ne yasa ta ajiye hoton tana santin kyau irin na Josephine, dan fa ba karya kyakkyawace ajin farko. Takardan sakon wasikar da ta rubuta musu ta fara budewa dan ta kalli me a ciki, wow ta furta ganin wani irin good handwriting, abin mamaki kuma handwriting ɗin sak irin nata, yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya da suka je Abuja Lion ya ɗauki takardanta na makaranta guda ɗaya ba tare da saninta ba, saboda wlh handwriting nata da wannan handwriting da aka rubuta sakon nan babu banbanci, da yake ita tasan yadda daddynta yake rubutu, sai ta kalli ma handwriting ɗin tafi kama ta tasa sosai, dama gadon rubutun daga wajensa ta yi. Ƙoƙarin fara karanta sakon ta yi sai ta fahimci bada turanci bane, haka ta rinƙa kwaɓawa tana karantawa, ba abin da ta gane ko ɗaya, dan dama yare idan ba naka ba ai ko haɗa kalma ka karanta ba iyawa zaka yi ba. A karshen rubutun ne da ta karanta sai taga an rubuta da turanci wajen da aka sanya i really love you my pleasures, and i will going to miss you more than your expectations. Shiru ta yi tana tunanin irin wannan rubutu haka kamar yaren aljanu, ta kasa karanta komai, sai wasu kalmomi take haɗawa kamar tana tsinewa kanta ne da yaren, irin wannan abu haka anya ba yaren aljanu bane kuwa?. Ta yi nisa cikin tunanin da take yi sai jin motsinsa ta yi a palon sama alamar yana shigowa cikin bedroom ɗin, a guje ta miƙe ta nufi toilet ta ɓuya a bayan wasu kyawawan fararen towals dake gere a wajen kusa da show glass na su mayukan wanke kansa. Kasa kasa ya yi sallama tare da wucewa dressing room nasa, kayan jikinsa ya cire kafin ya ɗauko wani towel mai azababben kyau fari tas ya ɗaura a kugunsa ya fito ya nufi toilet ɗin da ya yi wanka ya yi shirin barci. Yana shigowa ta runtse idanunta kirjinta na dukan uku uku, yau tashiga uku ta lalace a cewarta. Wajen brush nasa ya nufa, haɗa mayukan goge bakinsa ya yi tare da fara yi cikin natsuwa, bayan ya kammala sai ya nufi wajen tampatsetsen baf ɗin wankansa dan ya haɗa ruwa, ruwan zafi ya fara zubawa zuwa daidai rabin baf ɗin kafin ya cikata da ruwan sanyi, sannan ya ɗebo sabulansa kala kala ya zuba a cikin ruwan, kunsan dama su Turawa yadda suke wanka, mafiya yawan lokuta sun fi zuba zabulan wankansu a cikin baf ɗin sai ruwan ta yi kunfa over suke shiga, sai su goge jikinsu da kyau kafin su fito idan sun kammala su shiga shower dan ɗauraye jiki, suna son tsunduma cikin ruwan kumfar sosai, suna kuma ɗan jimawa a cikin ruwan idan suka shiga, shiyasa basu cika amfani da sabulai irin namu ba, sun fi yin amfani da sabulai na ruwa. Bayan ya zuba duk wasu soaps nasa da sauran kayan wankansa, tsab ya kammala komai, duk abin da yake yi tana kallon shi, tsabar dukan uku uku da kirjinta yake yi yasa gabaɗaya gaɓoɓin jikinta sun yi sanyi, sun kasa ɗaukarta, dap take da ta zube kasa dan wlh ba zata iya ba, a hakan ma dan ya bata baya ne yake harkokinsa, ba ta gabansa take kallon ba, da ta gaba ne ina ga sai suma. Yana ƙoƙarin kwance towel ɗin dake kugunsa dan ya shiga ya yi wanka ne, ta ji ina bazata iya jurewa ba, dan haka sai ta fito daga bayan towels ɗin da gudu gaske ta nufi waje, taku biyu ya yi ya damkota ta shafaffen cikin nan nata, dama tun shigowarsa ɗakin yasan ta shigo mishi, duk kuma abin da ta yi ta taɓa mishi ya gani kuma yasan an taɓa, sai dai bai yi tunanin a toilet ɗin ta ɓuya bane, ya yi tunanin dressing room ta shiga da ta ji motsin nasa, lokacin da ya shigo toilet ɗin ya ji kamshin perfume nata, so ya yi tunanin nan ma shigowa kawai ta yi ta mishi taɓe taɓe kamar a cikin ɗakin, bai kawo ɓuya ta yi a ciki ba, sai da ya je zai ɗauki brush ne ya ganta, amma ya yi kamar bai ganta ba ya yi brush nasa zai fara wanka ko a jikinsa. "What brought you in to my room?. Me ya kawoki cikin bedroom na?" Ya yi maganar a nutse cikin wannan cool sexy voice ɗin nasa. A hankali ta juyo suna fuskantar juna har lokacin hannunsa a saman flat tummynta ya riketa sosai ta wajen, gabaɗaya ilahirin jikinta kerma yake yi, harta laɓɓanta ɓari suke yi dan bala'in tsoro. Ya ilahi ya lillahi, wani irin mahaukacin razana ta yi na ganin surar jikinsa a zahiri ba riga, musamman faffaɗar kirjinsa, ga wannan baƙin gashi dake kwance a iya tsakiyar ɓul ɓul ɗin breast nasa, gashi bashi da yawa, ɗan daidai tsakiyar breast ɗin nasa ne, ga breast ɗin ba sai na sake gaya muku ba, suna nan ɓul ɓul saboda training da yake yi, damatsansa kamar zasu fashe, a cike suke tab, ga wasu siraran jijiyoyi ɓaro ɓaro a saman damatsan nasa alamar cikar jarumin namiji kenan. Datse idanunwanta gam ta yi kirjinta na dukan tara tara, jikinta na kara tsananta kerma da yake yi, iya razana ta yi ba karya, soft skin nasa ma kawai abin kallo ne yadda yake wani sheki tamkar fatar jariri, kamar bai taɓa fita waje ba, ga jikin nasa da tsantsar daddaɗar kamshin perfume nasa da already ya rigada ya kama fatarsa gam, ko bai saka ba yana zuba kamshin. Duka dukanta bata wuce dai'dai tsakiyar ɓul ɓul ɗin breast nasa a tsawo ba, kanta ya tsaya a dai'dai breast ɗin nasa, dan ba karya Lion yana da tsawo sosai irin daddynsa, biyunsa kuma Areef, Aseef ma yafi Imran tsawo sai dai bai kaisu ba, so tanannan ƴar dai'dai a gabansa, musamman idan ya mannata da faffaɗar kirjinsa da ya ji training ya koshi, sai ta lafe luf a gefe guda. "Open your eyes". Ya faɗa murya can kasan maƙoshinsa, ya yi maganar kuma yana cire hijabin jikin nata dan sai haɗa uban zufa take yi, ta tsorata over ƴar kaniya, yana cirewa nan take zanen sunansa dake saman tudun breast nata ya bayyana, da yake ta yadda ya damko cikin nata yasa wuyar rigar kayan barcin jikin nata ya yi kasa, tudun breast ɗin nata sun bayyana sosai, zubawa sunan idanu ya yi yana kallon yadda zanen ya zauna ɗas tamkar da shi aka haifeta. A tsananin shagwaɓe ta ce "Yaya Saif na tuba wlh, ba zan iya buɗe idanuna ba, ba zan iya kallonka a haka ba, na yarda idan ka fito wanka ka shirya, to koma wani irin hukunci ne a lokacin ka yi mini zan karɓa, amma yanzu Allah ba zan iya buɗe idanuna ba, kuma na maka alkawarin ba zan sake taɓa maka komai naka ba, ba ma zan sake shigowa ɗakinka ba idan ba abinci zan kawo ba, wlh tsautsayi ne yasa yanzu ma na taɓa abubuwan da na taɓa, wayyo daddyna nashiga uku yau kam, yaya Areef kazo ka ceceni". Ta kai karshen maganar hawaye na zuba daga idanunta, danasanin abin da ta yi ta farayi, me ma ya aiketa ta taɓa mishi abubuwa? Ga shi har da kayan mummynsa tsab ta buɗe komai. Yadda ta zuba shagwaɓa over wajen yi mishi magana tasa ya ji gabaɗaya jikinsa ya mutu, ba zai iya yi mata wani hukunci ba, da ya yi niyar hukunta ta sosai, dan babu wanda ya taɓa taɓa mishi abin da ta taɓa yau, ko su Aseef basu san da shi ba, amma sigar da ta yi mishi magana da shi yasa ya ji ya hakura.......... E LALLAI SOYAYYA NA ƊAWAINIYA DA ZUCIYAR LION BA TARE DA YA SANI BA TA BAKIN AREEF, IDAN BA SOYAYYA BA ME ZAISA TA YI MISHI LAIFI YA CE YA YAFE MATA? MUTUMIN DA A BAYA KO BATA YI MISHI LAIFI BA MA IDAN TA BIYO TA HANYAR DA AKAYI MISHI LAIFI SAI TA KARƁI HUKUNCI, BA SHAKKA LION KA FAƊA TARKON KARAMAR YARINYA. A hankali shasshekar kukanta ya fara ratsa zuciyarsa, ɗan ɗago idanun nasa ya yi daga saman zanen sunan nasa zuwa kyakkywar fuskarta, ganin yadda hawaye wani na abin wani suke zarya a face ɗin nata ne yasa ya ji sam babu daɗi a cikin zuciyarsa, ga shi ta datse idanu gam tamkar zata fasasu, hakan bai yi mishi daɗi ba, baya son ganin hawayen, bai san lokacin daya ɗago hannunsa ya ɗaura saman lallausan kumatun nata ba, a maimakon ya goge mata hawaye, a'a shi salon rarrashinsa daban ne, yasan ko ya goge hawayen ma wasu ne zasu zubo, so kukan ya kamata ya dakatar ba goge hawaye ba, kara jawota jikinsa ya yi da ɗayar hannunsa dake saman cikinta, ta shiga firgici sam bata ma san da hannunsa a saman cikin nata ba. A hankali ya sanya latsarsa guda ɗaya a........ ❤️❤️TRIPLETS❤️❤️ E63-64💋 A hankali ya sanya latsarsa guda ɗaya a saman lips nata dake ta faman kerma kamar mai rawan sanyi, ɗan murza lips ɗin nata ya fara yi tare da zame hannunsa dake saman cikinta ya mayar saman mazaunanta ta baya dan ya ji daɗin rikota da kyau. Saukar hannunsa a saman mazaunan nata ne yasa ta waro idanunta ba shiri, kai tsaye sai cikin dara daran blue eyes nasa idanun nata suka sauka, dan kuwa ya tsareta da idanu yana kallonta, wani irin azababben sonta ne yake kara ratsa shi ba tare da ya shirya ba, wani irin daddaɗar yanayi yake jin kansa a ciki mara misaltuwa. Har lokacin idanunta suna zubar da kwallah zuwa saman face nata bata dai'na ba, zame hannunsa ya yi daga saman lips ɗin nata a hankali ya gangaro da shi zuwa saman lallausan wuyarta, blinking idanunta sau biyu ta yi dan ta tabbatar wa da kanta ba mafarki take yi ba, tunani ta fara yi wai ko dai akwai wani abin da ya shiga kansa ne? Anya yaya Saif ɗin da ta sani ne kuwa? Anya Malika bata yi mishi wani abin ba kuwa?. Tana can tana tunani sai jin saukar lallausan hannunsa ta yi a saman tudun tula tulan ya sanya yatsa ɗaya babbar cikin yana shafa sunan nasa dai'dai in da ta rubuta GAR, kasa ɗaukar hakan ta yi, bata san lokacin da numfashinta ya tsaya cak ba saboda razana da shiga yanayin da bata taɓa tsintar kanta a ciki ba. Tana ƙoƙarin zubewa kasa ya rikota da kyau da hannunsa dake saman mazaunanta, dawo da kallonsa saman face nata ya yi yana kallon yadda ta sha kuka, ta sume mishi a jiki sarkin tsoro. Ranƙwafo da kansa sosai ya yi daidai saitin face nata, shiru ya ɗan yi kamar mai tunanin wani abin, can kuma sai ya ɗan ɗaga kai tare da sanya hannu ya goge mata hawayen kafin ya ɗauketa cak a saman kafaɗarsa ya fito da ita zuwa cikin ɗakin. A saman bed nasa ya ahinfiɗeta kafin ya koma cikin toilet ɗin dan ya yi wanka. After 45 mins, ya fito shirye cikin tsadaddun kaya barcinsa farar tas, sai shaki soft skin nasa yake yi sosai, yana ta zuba kamshi. Saman bed ɗin ya nufa kamar zai zuba mata ruwa, kome ya tuna sai kuma ya fasa ya nufi waje dan ya duba ƴan uwansa da kuma daddy. After some minutes ya dawo, sai da ya bisu ɗaya bayan ɗaya ya duba su sannan ya dawo, har Aseef sai da ya yi musu knocking suka buɗe ya duba lafiyar Aseef ɗin kafin ya dawo bedroom ɗin nasa. Saman bed ɗin ya haye bayan ya ɗauko ruwa roba ɗaya daga cikin fridge, ya buɗe robar ruwan yana ƙoƙarin tarbowa a hannunsa dan ya zuba mata ta tashi ta koma bedroom nata, bai kai ga yin hakan ba daddynsa ya shigo bedroom ɗin dan yana son ya yi magana da ɗan nasa, ganin daddyn yasa ya tsaya bai zuba mata ruwanba yana bin daddyn da kallo. "Son me yarinyar nan kuma take yi a saman bed naka?". Shiru ya yi bai tanka mishi ba. "Son ka tasheta ta fita magana nazo in yi da kai, kuma kasan cewa nace bana son yarinyar nan since before nazo nan ko? To dan haka bana sonta! Bana son ganinta a kusa da kai! Dan haka yanzu ba sai anjuma ba ka tasheta ta fita a ɗakin nan, kuma kada ta sake zuwa dan bana sonta kusa da kai". Yanayin yanda daddyn yake magana sai ya ga kamar daddyn yana wani nuna mishi isa da izza ne, shi kuma kun sani ba sai na sake faɗa ba, baka isa ka nuna isa a gabansa ba, kuma shi daddyn shi ya basu wannan tarbiya, dan haka iyaye ku ji tsoron Allah ku bawa ƴaƴanku tarbiya da zata sanya su yi abin alkhari, ku sani duk abin da kuka koya musu wlh sai sun yi muku shi a kwana a tashi, to dan haka ku koya musu alkhari dan kuma kuga alkhari, kada ki yarda ko irin gulmar da yara suke kawowa irin idan sun je gidan mutane duk abin da ya faru suzo suna gaya miki, kada ki yarda, tun wuri ki taka musu birki, da sun fara ki hanasu ki ce waye ya tambayeku? Idan ba haka ba, wlh haka zasu tashi da wannan kananun maganganu da gulma da munafurci, a kwana a tashi kema sai sun yi miki, Allah dai ya dafa mana ya bamu ikon aikata alkhari a duniyarmu dan muga lahira mai kyau. Jin yanda daddyn ya yi mishi magana cikin nuna isa ne yasa ya fasa zuba mata ruwan ma bakiɗaya, tare da yin kwanciyarsa bayan ya ajiye ruwan a saman bedside drawer, ya jawo bargo zuwa dai'dai cikinsa, ganin bargon ya rufe har kanta ne yasa ya mike ya gyara mata kwanciya a in da ya ɗaura kanta a saman pillow dake manne da jikin headboard na gadon, sannan ya ja musu bargo dan shi bashi ma da lokacin yin wata magana da daddaren nan bare ya biyewa daddy su yi. Ganin hakan yasa daddy ya ɓata rai sosai ya fara faɗa babu kama hannun yaro, shiru ya yi bai tanka ba tamkar babu shi a ɗakin. Sai da yaji surutun daddy fa yana neman sanya shi ciwon kai, a fusace ya miƙeq zaune, cikin nuna isa da izza ya fara magana "Daddy do you know what? She is my wife yanzu da nake maka magana matata ce, a da bani da niyar kulata, amma tun da ka ce baka son ganinta a kusa da ni, as from today ta dawo bedroom ɗin nan da zama kenan, ko waje ba zata fita ba idan ta dawo school, kuma zan kula da ita saboda baka sonta, wai ka manta cewa ni abin da ba'a so ne ni kuma nake so? To idan ka manta na tuna maka, tun da baka sonta dole zan kulata, zaka iya tafiya yanzu barci nake ji, ita kuma matata ce babu wanda ya isa ya canza hakan!". Tashin hankali, a tsananin razane daddyn ya miƙe, cikin fushi shi ma ya fara magana "Romeo ni fa na haifeka ba kai ka haifeni ba, to ina mai baka umarni da ka fitar da yarinyar nan daga cikin bedroom naka, in fact daga gidan nan baki ɗaya, na ce bana sonta ko?". Shiru ya yi bai sake yin magana ba, sai ma kwanciyarsa da ya yi tare da jawota jikinsa tun da daddyn ya ce baya son ta zo kusa da shi, to barima ya rungumeta suyi barci tare sai ya ga karshen tsiya, shin daddyn zai mutu ne ko yaya? Mutun sam baya son zaman lafiya?. Bakin ciki tamkar daddyn ya haɗiyi zuciya ya mutu, Allah dai yasa yanzu ya sami sauki sosai, da yanzu ciwonsa ya tashi saboda tsananin azabar ɓacin rai, ko kallon in da yake Lion ɗin bai sake yi ba, hannu ma ya ɗaura a saman bayanta yana shafawa a hankali tare da lumshe idanuwansa kamar mai barci. Daddy bashi da zaɓi dole ya juya ya fita daga ɗakin, domin kuwa babu yanda ya iya da Lion, dole dai ya hakura ne. Daddyn yana fita ya rabata da jikinsa tare da juya mata baya ya yi kwanciyarsa, batun bedroom nasa kuma ta dawo kenan kamar yadda ya faɗa, dan baya magana ya canza, bare ma kuma da ya zamana daddyn yana gidan, ai ko dan ya cika maganar tasa dole ta zauna a bedroom ɗin. Yana juyawa ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi, dama ita kam already tana sume baiwar Allah. A ɓangaren Aseef kuwa bayan sun yi sallah sun ci abinci ne suka wuce kasa abinsu. Suna shiga bedroom nasu ya rufe kofar da key dan ma kada daddy ya caza mishi kai, Lion ne ya ce mishi ya sanya key a kofar dan kada su tayar mishi da hankali ba lafiya gare shi ba. Wanka ya yi tare da shiryawa cikin kayan barcinsa launin ash color masu bala'in kyau da tsada, kafewa ya yi a kan lallai sai ya yi wa Akila wanka, ita kuma ta ki yarda, kuka ya saka mata shi gaskiya ba zai yarda ba, ai ita matarsa ce to me zata ɓoye mishi? Ba kayansa bane wai?. Cikin shagwaɓa ta ce "Kai my shagwaɓatina, kayan kane mana, amma ai yanzu baka da lafiya ne, ni gaskiya ka bari sai ka warke". Kin yarda ya yi ya cigaba da zuba mata kukan shagwaɓa tare da kwanciya a saman gadon ya bata baya ya yi ruf da ciki wai ya yi fushi. Lallaɓawa ta yi, cikin salon so ta haye saman bayansa tare da kawo bakinta saitin kunnensa tana hura mishi iska a hankali, kara tsananta shagwaɓar tasa ya yi yana faɗin "Kome zaki yi mini ba zan saurareki ba har sai kin barni nayi miki wanka". Kumatunsa ta sumbata tare da ɗan jan gemunsa tana faɗin "Yanzu ka tashi daga shagwaɓati ka koma rigimati Allah, wlh ka cika rigima sosai, ni Allah ba zan yarda ba". Shiru ya yi bai tankata ba. Hannu ta cusa cikin gashin kansa ta fara shafawa har zuwa fuskarsa wuyarsa dukka, cikin salo mai ɗaukar hankali ta zuro harshenta waje ta fara yi mishi tafiyar tsutsa a wuya, tuni ya manta da fushi ya juya da ita ta koma saman bed ɗin, jawota jikinsa ya yi tare da fara bata sakonni na musamman, kukan shagwaɓa ta sanya mishi tana faɗin ya barta bari ta yi wanka, haɗe bakinsu waje guda ya yi tare da fara bata hot kiss, cikin dabara ya zura hannunsa cikin rigarta ya fara aikin matsa abubuwan da yafi kauna, biye mishi ta yi tana yi mishi kiss ɗin ita ma, nan take ta ruɗa bawan Allah ya fara zuba mata shagwaɓa babu kama hannun yaro. Da kyar ta samu ta kwaci kanta ta nufi toilet ɗin, tana shiga ta rufo kofar da key dan ma kada ya biyota, kwanciya ya yi yana jiranta ta dawo dan shi kiss ɗin bai ishe shi ba gaskiya. After some minutes ta fito ɗaure da towel a kirjinta, kiranta ya yi a kan ta zo haka da towel ɗin, make mishi kafaɗa ta yi tare da nufar dressing room nasa, kayan barcinsa riga da wando ta fitar dan tasa, saboda ta manta bata ɗauko kayan daga ɗakin su Rimsha ba. Tana ƙoƙarin sanya kayan ne kamar daga sama ta ji ya zuro hannunsa daga ta bayanta zuwa ta gaba ya kwance towel ɗin, ko yaushe ya taso ya zo? Ta tambayi kanta, damke towel ɗin ta yi tare da juyowa gare shi, rungumota ya yi yana zuba mata shagwaɓa a kan shi ta daina hana shi taɓa kayansa, idan ba haka ba gaskiya zai yi mata kuka. "Wace kuka kuma bayan wanda kake yi mini yanzu?" Ta faɗa a shagwaɓe, hannunsa dukka biyu yasa ya riko breast nata bakiɗaya tare da kawo bakinsa saitin kunnenta kasa kasa ya ce "Yanzu ai kukan soyayya nake yi miki, idan kika cigaba da hanani kukan gaske zan yi". Ya kai karshen maganar tare da sumbatar wuyarta. "To dan Allah my shagwaɓatina ka bari na sanya kaya sai mu koma bedroom saman gado, a nan sai kayi duk abin da kake so". "Promise?" Gyaɗa mishi kai ta yi, sakinta ya yi tare da juyawa zuwa cikin bedroom ɗin. Saurin sauri ta shirya ta fito zuwa gaban mirror, kayan nasa sun yi mata kyau sosai duk da cewa sun fita, sun yi mata yawa, amma ba karya ta yi kyau, Lotion nasa ta shafa a jikinta tare da perfume irin na Lion daya ɗebo musu daga ɗakin Lion ɗin, sai tashin kamshi take yi ta dawo saman bed ɗin. Kamar jiranta yake yi ya fara murzata son ransa, bata hana shi ba, dan tasa idan ta hana shi ma kuka zai saka mata, to gara kawai ta bar mishi kayansa ya murza son ransa, babu in da bai yi wasa da shi ba a jikinta har gabanta, sai dai bai yi yunkurin shigarta ba, a iya wasa ya tsaya, tana kwance tana jinsa, duk yanda ya juyata haka take juya mishi, sai da ya sami natsuwa sannan ya rabu da ita tare da kwanciya ya jawota jikinsa yana zuba mata albarka har barci ya yi awon gaba da su. Shi kuwa Areef sai da ya tsokani Jehan sosai kamar yanda suka saba sannan ya nufi bedroom ɗin daddy, bayan ya duba shi suka yi sallama ya wuce nasa bedroom ɗin dan kwanciya. Asuba ta gari. Washegari kamar kullum, haka suka tashi, sai da Lion ya dawo sallar asuba ne ya shafawa Rimsha ruwa ta farfaɗo, ta sha ruwan mamakin ganinta a bedroom nasa, wanka ya ce ta yi sannan ta yi sallah ta shirya zuwa school, okey ta amsa tare da dirowa kasa daga saman bed ɗin ta nufi waje, calmly ya ce mata a toilet nasa zata yi wanka, dan kuwa kamar yanda ya gayawa daddy ta dawo bedroom nasa nan, to hakan ce, baya saɓa maganarsa. Mamaki kamar zata cinye ɗan yatsanta, yau me ya shiga kansa ne? Ta tambayi kanta, bata san diramar da suka sha daren jiya shi da daddy bane, ita dai tana mugun mamakin abin ne. Toilet ɗin nasa ta dawo ta shige, shi kuma kwanciya ya yi tare da jawo bargo ya lumshe idanunsa dan ya mayar da barci, ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi, ita kuma bayan ta yi wanka ta fito, bedroom nasu ta nufa, da yake ya yi barci, bai san fita ta yi ba, ya ji motsinta, yana tunanin dressing room ta shiga, shiyasa bai buɗe idanu ba, ya cigaba da barcinsa, bata san ya ce ba zata sake fita daga bedroom ɗin ba idan ba school zata je ba. BABBAR MAGANA LALLAI AKWAI CAKWAKIYA ZAMAN CIKIN ƊAKI YA KAMATA KENAN, DADDY YA JA MATA AIKI. Shiryawa cikin uniform nata ta yi, sun sha guga sosai, ita tun da take a gidan bata taɓa sanin waye mai yi musu wanki ba, kullum idan ta dawo gida zata cire uniform nata, amma kafin nan da awa biyu an wanke uniform ɗin an goge an dawo mata da shi cikin bedroom nata, haka duk kayan da ta cire, tun abin yana bata mamaki har ta dai'na mamakin, komai ya zama mata jiki. Kitchen ta nufa ta sami Mark, abinci ta ce ya zuba mata bari ta ci su tafi, bai amsa mata ba sai dai ya zuba mata kawai, saman table ɗin palon sama ta koma ta zauna, a nan Areef ya iskota, yana zama daddynta ya fito shi ma, gaishe su ta yi cike da fara'a tana faɗa musu su tayata da addu'a yau zasu rubuta Exams na karshe, okey suka amsa mata tare da yi mata fatan alheri. Zama suka yi kusa da ita suna tayata hira, a nan ne ta cewa daddy idan ta dawo school zai kaita shopping dan ta sayi kayan partynsu da sauran abubuwa, ita Indian dressing zata yi, dan ana yawan ce mata hakan a school, saboda dark black curly hairnta irin na Naurat, shiyasa suke ce mata ƴar india, to gobe dressing na Indiyawa za ta yi, daddy ya kaita shopping ta sawo sari mai kyau da sauran kayan indiyawa. Kallon Areef ya yi, while shi ma Areef ɗin shi yake kallah, babu wanda ya isa a gidan nan ya ce zai ɗauketa su je shopping ba tare da izinin Lion ba, kai ai da wuya ma ya yarda koda sun tambaya. Shiru suka yi mata an rasa mai bakin yin magana, cike da damuwa ta ce "Daddy lafiya kuka yi shiru kuna kallon juna?". Ƙaƙalo murmushi dole suka yi dukkansu biyu Areef yana faɗin "Ba komai yanzu dai idan kin gama cin abinci ki je ki sami Lion ki tambaye shi zamu je shopping anjuma, idan ya barki to, idan bai barki ba kada ki ji tsoro ki saka mishi kuka, ki ce kowa zai yi shiri mai kyau ya je school amma ke baki da kaya, ki yi mishi kuka sosai har da hawaye zai barki". Shiru ta yi tana tunano abin da ya faru daren jiya, abin ya ɗaure mata kai ta yadda akayi yanzu baya son ganin kukanta sam. Ganin ta yi shiru ne yasa daddyn ya ce "Ba komai tun da Areef ya ce kiyi hakan ki yi kinji ko?" Gyaɗa musu kai ta yi tana ƴar murmushi, amma zuciyarta cike yake fal da tunanin abin da ya faru jiya a tsakaninta da masoyin nata, tunani take yi wannan abin sam ba dai'dai bane, bai kamata yaya Saif ya rinƙa taɓata haka ba, ita ai ba muharramarsa ba ce, sai yanzu karatun mummynta suke dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, da duk ta manta, sai dai kuma abin haushi kome zai yi mata bata isa ta yi mishi wani magana ba, solution a nan kawai shi ne ta rinƙa gudunsa, ya zama suna wasar ƴar ɓuya, kada ta bari suna haɗuwa, idan ta kai mishi abinci ta rinƙa kawar da kanta gefe tana kuma sanya hijabi har kasa, bayan haka da ya gama cin abinci ta kwashe kayan da wuri ta bar ɗakin, idan ba haka ba zata kauce hanyar Allah a nata tunanin. Tuna hakan yasa duk ta ji babu daɗi, istigifari ta fara yi na yardan da ta yi a baya yana taɓata itama tana kwanciya a jikinsa, nan take idanunta suka cika tap da kwallah, ita da take faɗa kada ayi saɓon Allah wai yau ita ce har ta yarda wani ya taɓata, sam bata ji daɗi ba kuma shaiɗan bai yi mata adalci ba, bakin azzalumin. Daddy da Areef suna ta zuba hira basu lura da ita ba har ta mike ta bar wajen ta nufi bedroom nata, sai zuba barci ta sami Jehan tana yi, hijabi har kasa ta ɗauko ta sanya a jikinta tare da wucewa zuwa bedroom ɗin nasa dan ta yi mishi magana a kan zuwansu shopping ɗin. Bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin bedroom ɗin, yana balcony ta hangosa, wucewa ta yi zuwa wajen, yana sanye da three quarter zuwa gwiwa da polo t-shirt, dukkansu fararene tas, tana mamakin irin yanda yake kaunar white color a rayuwarsa. Yana zaune saman ɗaya daga cikin kyawawan tsadaddun sofas dake wajen, hannunsa rike da robar ruwa, ya yi shiru kamar mai tunani. Gefensa ta zo ta zauna tana faɗin "Good morning yaya Saif". Bai amsa ba kuma bai ɗago ya kalleta ba, ɗan sunkuyar da kanta kasa ta yi cikin girmamawa ta ce "Yaya Saif dama a kan batun partynmu da zamu yi a school ne, to ni bani da kayan da zan saka, shi ne nake son su yaya Areef su kaini shopping na zabi kayan, ton shi ne nake neman izini". Shiru bai tanka mata ba, tamkar babu shi a wajen. Ganin hakan yasa ta saka mishi kukan shagwaɓa sosai tana faɗin "Allah kai yaya Saif ɗin nan sai mutun ya yi maka magana ka share shi". Yadda ta yi maganar ne yasa dole sai da ya juyo gareta ba tare da ya shirya ba, hawayen da ya gani a saman face nata ne yasa sam ya ji babu daɗi, zuba mata idanu ya yi bai ce komai ba. Ganin hakan yasa ta kara tsananta kukan shagwaɓar tata tare da miƙewa da nufin ta bar wajen. Hannunta ya riko tare da jawota jikinsa, ɗago haɓarta ya yi can kasan maƙoshinsa ya furta "Yaushe kika zama rigimammiya haka ne?". Ɗan turo baki tayi kamar yanda take yi wa Aseef, tuni ta manta da cewa yanzu ta gama istigifari a palo, kai jama'a shaiɗan la'ananne ne, makiyin mu ne, dan haka kuyi taka tsantsan da shi, kurinƙa yawan neman tsari da shi daga wajen Allah, duk da cewa mijinta ne ba ta sani ba, amma har shaiɗan ya mantar da ita tuban da ta yi a palo, da yanzu ba mijinta bane haka shaiɗan ɗin zai yi ta amfani da damarsa har ya cinwa burisan na ganin ya sanyasu saɓon Allah, Allah ka kare mu daga sharrin la'ananne shaiɗan. "To ba kai ne sai mutun yana yi maka magana sai kaki kula shi ba". Yadda ta turo baki ta yi maganar cikin shagwaɓa sosai, ba ƙaramin burgesa ta yi ba, hannu ya kai saman face nata ya goge mata guntun hawayen da suka zubo. "Idan kin dawo daga school Areef zai kai ki shopping ɗin, shikenan?" Gyaɗa mishi kai ta yi tana sakin cool murmushi, nan take kyawawan dimples nata masu tafiya da hankalinsa suka lotsa, yatsa ɗaya ya sanya a ciki yana kallon face nata, bata san time da wani sabon murmushi ya sake kubce mata ba, shi dai yana jin daɗi idan tana murmushi, amma bai iya yi ba, bai taɓa kwatantawa ba, bata burge shi ma ya yi, sai dai ita ɗin. Wayarsa ce ta buga musu time karfe bakwai dai'dai ta cika, rankwafowa da kansa ya yi cikin sanyin murya a nitse ya fara magana "Daga yau bedroom nan shi ne ya zama naki, idan kin dawo daga school a nan zaki zauna ban yarda ki fita ko palo ba, idan abinci ne ma zan sanya Aseef yasa matarsa ta kawo miki, akwai waya a cikin dressing room na idan kin dawo ki ɗauke shi saboda idan kina son wani abin sai ki kira number Aseef or Areef or daddynki, amma ke ban yarda ki fita ko palo ba". Zaro idanu waje ta yi sosai, bazata fita ko palo ba kuma? Wannan wani irin abu ne? Wai shin ita matarsa ce? Ko dai yaya Saif aljanu sun shiga kansa ne? Anya kuwa lafiya? Haka ta rinƙa jerowa kanta tambayoyi. Ganin ta zaro idanu ta shiga duniyar tunani ne yasa ya hura mata iskar bakinsa a fuska, lumshe idanun nata a hankali ta yi tare da sake buɗesu a kan face nasa, wani irin kunyarsa ma ta ji ganin yanda yake kallonta. "Tashi ki je Mark yana jiranki". Ya kai karshen maganar tare da ɗago haɓarta sosai ta yadda fuskokinsu ya kasance daf da juna, dan idan baku manta ba dama ya ranƙwafo kanta. Kerma jikinta ya fara yi, Lips nata suna wani ɓari kamar mai rawan sanyi, mamaki ne ya kamashi wai meyasa ta cika tsoro ne yarinyar nan? A haka kuma zai tafi da ita? Ya sake tambayar kansa, to amma ya zai yi tun da ya rigada ya ce wa daddynta dole da ita zai tafi, ga shi shi kuma baya saɓa magana idan ya yi, hakan tasa dole dai da ita zai tafin. Runtse idanunta ta yi while shi kuma ya kara ranƙwafo da kansa sosai a saman tata yana kallon yadda laɓɓanta ke ɓari, ji ya yi tamkar ya sumbacesu, sai ingiza shi zuciyarsa take yi, ita kuma ta datse idanun tana addu'ar Allah ya yafe mata. Sun ɗan jima a haka yana jin zogi a zuciyarsa na lallai ya sumbaci lips ɗin nan nata, ɗan ɗago kansa kaɗan ya yi tare da kai mata sumbata a goshi kafin ya mike zaune da kyau yana mayar da kallonsa kan wayarsa da call ɗin Mark yake shigowa. "Mark na jiranki time yana tafiya". Ya faɗa tare da ɗaukar wayar, da kyar ta iya buɗe idanunta tana tunanin yanda ta ji saukar lallausan laɓɓansa a saman goshinta, suna da laushi over, zuba musu idanu ta yi tana kallon yanda yake ɗan cizasu kaɗan kaɗan kamar mai nazarin wani abin. Jin bata tashi daga jikin nasa bane yasa ya dawo da kallonsa kanta, a hanzarce ta yi yunkurin tashi dan ta gudu, ya gane sarai lips nasa take kallo, sai ya yi kamar ma bai gani ba ya basar, mikewa ta yi ta nufi waje, cigaba da rubuta massage da yake yi wa Mark ya yi, sai da ya kammala ne ya shiga part na hotunansa, hoton shi tare da TRIPLETS nasa ya zubawa idanu yana kallo yana kuma tariyo fuskar Rimsha, Jehan da kuma Akila a cikin ƙwaƙwalwarsa, sai Allah kaɗai yasan me yake tunani a cikin zuciyarsa. Ita kuwa tana fita bedroom nata ta koma ta cire hijabin jikinta kafin ta karisa shiryawa ta ɗauko school bag nata ta fito waje, already Mark yana cikin mota yana jiranta, shiga ta yi, har zasu fita Mark ya tsayar da motar a dai'dai bakin gate ɗin gidan yana gayawa Tyrone idan Lion ya fito ya sanar da shi ɗaya daga cikin yaran nan da suka kama ranar waƴan da suka so yi wa Rimsha fyaɗe fa kamar ya mutu, dan tun jiya baya sumfashi, ya zuba mishi ruwa har ya gaji amma shiru bai farka ba, so idan Lion ya fito ya gaya mishi, Okey Tyrone ya amsa da shi sannan suka wuce. Ita kam Rimsha mamaki ne ya hanata sakat, wai dama yaran har yanzu suna nan? Gaskiya Mark mugu ne na karshe wlh, yanzu shi ne ya rinƙa azabtar da su har ɗaya ya mutu kenan? Amma sun yi mugun bata tausayi, duk da tasan a yanda yarannan suke yawo da makami to ba makawa sun taɓa kashe wani, sun sha jiwa al'ummar mummunar rauni, dan babu imani a tattare da su, amma wlh sun bata tausayi, dan da ka shiga hannun Lion da Mark dan hukunci, wlh gara ka rataye kanka da kanka ya fi maka, dan duk iskancinka tun a horo na farko zaka yi nadamar zuwanka duniya, sun san kan mutunta over. Suna yin parking a school Anya ta taho da gudu suka rungumi juna suna dariya, zuba mata idanu Mark ya yi yana kallon murmushi dake kan fuskarta, sam bata kula shi ba sai da ta gama yi wa Rimshar ta oyoyo sannan ta juyo gare shi tana murmushi. "Good morning sir". Ta faɗa tana kawar da kallonta daga kansa, kin amsawa ya yi, sake maimaitawa ta yi, nan ma dai yaki amsawa, sai a karo na uku ne ya ce "Ba zan amsa ba, ai kin san laifin da kika yi mini, dan haka ina fushi". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "To kayi hakuri". Shiru bai amsa ba, sake maimaita mishi good morning ɗin ta yi. "Waye ya ce jiya ki kashe mini waya?" Ya tambaya yana cire glass ɗin face nasa, kara faɗaɗa murmushinta ta yi tana faɗin "To ba kai ne ba kayi mini wani maganar da sai da kasa na kashe wayar baki ɗaya". Zubawa ɗan bakin nata idanu ya yi yana kallon yanda take magana, ita dai Rimsha yau taga ikon Allah, wai dama Mark yana magana haka? Wai dama ya iya magana kenan? Ai ita ta ɗauka daga okey sai no ya iya, sai ga shi yau suna zuba hira da Anaya har da wani wai ya yi fushi dan an kashe mishi waya, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, nan take kuma tunanin Lion ya faɗo mata a ranta na yanda ya canza kwana biyun nan, haɗa abin waje guda ta yi wato da canzawar Mark da kuma canzawar Lion, ta haɗesu waje guda tana tunanin tabbas da Mark da Lion ɗin basu da lafiya ne kila, dole da akwai wani abin a kasa. Tana can tana tunani ita kuma Anaya tana rarrashin masoyin nata, dan fa ya ce shi ya yi fushi gaskiya, a kan me zata kashe mishi waya daren jiya suna tsaka da hira, daga karshe dai sai da ta buɗe motar ta shiga ta zauna ta bashi hakuri da kyau sannan ya hakura tare da miƙa mata hannu suka gaisa, ganin abin nasu azimun ne yasa Rimsha ta yi gaba abinta tana faɗin Anayar ta sameta a cikin class ita bata iya tsayawa. Cikin zolaya ya ce "Kinga kin kori matar oga ko?". Yar dariya ta yi tana faɗin "Au matar oga ce ma kenan?". Jinjina mata kai ya yi. "Yes matar oga ce, amma fa nina aura mishi ita, shi bai ce yana sonta ba, kawai nina lura da yana sonta ne yasa nake ce mata matar oga". "E lallai ka iya sa ido kam". Ta kai karshen maganar tare da fitowa daga cikin motar ta nufi class nasu tana yi mishi bye bye, ɗaga hannu ya yi shi ma yana yi mata tare da zuba mata idanu har ta kurewa ganinsa ta shiga class nasu. Ajiyar zuciya ya sauke tare da ciro wayarsa ya fara latsawa kamar dai kullum. After some hours gidan Lion . Fitowa daga bedroom nasa ya yi hannunsa rike da wayarsa, yana sanye da pajama ya nufi bedroom ɗin daddy, dai'dai zai shiga Areef ya kariso wajen shi ma zai je wajen daddyn ne, a tare suka shiga. Kwance a saman bed suka isko daddyn nasu yana kallon kwallo a Tv, shi kuma Aseef yana bedroom nasa shi da AKila, ya ce ta shirya suje ya saya mata kaya kafin Lion ya dawo daga tafiya sai su haɗa musu akwatinsu tun da ta ce mishi mu a al'adar mu anayin lefe, to yanzu dai zasu je sayan kayan da zata rinƙa sakawa ne kafin Lion ya dawo su sami kwanciyar hankali sai a sayi koma me, ta kafe sam ba zasu fita ba ya bari sai ya sami lafiya, ai zata rinƙa sanya kayan Rimsha, shi kuma ya ce no akwai kayan da yake da ra'ayin ta rinƙa sanya mishi ne ba irin na Rimsha ba, shi baya son dogayen riguna, hakan yasa ta lallaɓa ta je ta gayawa Areef dan gaskiya bata son ya fita, seriously bashi da lafiya, Allah ma yasa yana da sauran kwana a gaba ai da hanashi aurenta da akayi ba abin da zai hana shi mutuwa, abin ya taɓa shi ba karya. Da ta gayawa Areef ne sai ya ce Okey to kada ta damu ta kyale shi su gama shiri, dama zai kai Rimsha yin shopping anjuma idan ta dawo daga school Lion ya sanar da shi, to sai su tafi tare, shi ne ta dawo suke shiryawa tare. Gefen daddyn Areef ya zauna, shi kuma Lion a saman sofa ya zauna yana faɗin "Dad zan yi tafiya gobe, do you want something from me?". Dawo da kallonsa kan shi daddyn ya yi yana girgiza mishi kai alamar baya bukatar komai. "Okey to ba lallai mu sake samun time na zama da kai ba, dan daga nan Abuja zan je, na sanya a shirya mini jirgin ruwa, so ina busy gaskiya, na wuce wata kila da daddare zan shigo idan na dawo da wuri". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye da nufin ya fita. Jin ya ambaci jirgin ruwa ne yasa daddyn ya ce "Wai Romeo ina ne zaka je?". Kai tsaye ya amsa mishi da Russia. A tsananin razane daddyn ya diro kasa daga saman gadon nasa yana mai maimaita sunan Russia. "No Romeo, kasan me kake faɗa kuwa? Russia fa? Ba zai yiwu ba gaskiya! Ba zaka je ba, bana son ka sake yin maganar ma a nan, koma me zai kai'ka to ka hakura!!". Ya yi maganar yana ɗaure fuska sosai. Cikin kwanciyar hankali ya ce "Dad already na gama shiri so sai na dawo kawai, amma zuwa ban ga abin da zai hanani ba". "Romeo na ce maka bana son, bana da bukata, kuma ba zaka je ba!!". "Daddy dama ai ba sonka nake bi ba, ba bukatar ka nake so ba, tafiya ce sai na yi, aiki ne zai kai ni can, so ba umarninka zan bi ba!!". Cikin tsantsar ɓacin rai ya ce "To zamu gani, idan ka isa ka je mu gani" "Zaka gani dai, tafiya babu fashi, ka sa na kara jin son tafiyar ma da kace baka so, ni duk abinda ba'a so shi nake so!!" Tashin hankali, daddy fa ya sha jinin jikinsa, domin wannan kalma da Lion yake yawan faɗa na duk abin da ba'a so shi kuma shi yake so, to best kalmar daddyn ne lokacin da yake tashen samartaka, ya kware a furta kalmar kamar ba gobe, ya azabtar da mutane da dama ta dalilin wannan kalma, so yanzu abin ya fara damunsa gaskiya, dan kuwa Lion ya fi shi kwarewa a iya furta wannan kalma da kuma aiki da ita, wannan shi ne ɗan na gada ya fi ɗan na koya, abu fa ya fara damun daddy ba karya, wannan shi ne ramakon gayya ta fi ta gayya zafi!!. Da sauri Areef ya mike ya karisa wajen ɗan uwan nasa yana faɗin "Lion please and please ka fasa wannan tafiyar, tun da daddy ya kafe baya so, kuma kai kanka kasan irin mummunar alaƙar da take a tsakaninmu da kasar Russia, so ka hakura kawai tun da ya nuna baya so, kuma wlh nima bana so, kirjina har dukan uku uku yake yi idan na tuna zaka yi tafiya kuma ga in da zaka je". Wani irin mahaukacin razanannen tsawa ya dagawa Areef ɗin ransa a ɓace, cikin fushi ya fara magana "Areef ai ni dama abin da ba'a so shi nake aikatawa, ya rage nashi ya yi mini fatan alkhari or not!, Ka gaya mishi tafiya babu fashi, duk abin da zai faru ya faru!!". Ya kai karshen maganar tare da nufar kofar fita, da sauri Areef ɗin ya sha gabansa yana faɗin "Gaskiya babu in da zaka je, dan bamu shirya rasa ka ba!". Wani mahaukacin damka ya kaiwa Areef ɗin a wuya, rai a matukar ɓace, nan take wasu siraran jijiyoyi suka bayyana mishi a wuyarsa, har wani zufa yake haɗawa, idanuwansa sun yi jajir yau daddy ya nuna mishi isa har da wani cewa to ya tafi ɗin ya gani, kuwa zasu gani iya ganin idanunsu, tafiya dai babu fashi. A kausashe ya ce "Ko ku shirya rasa ni ko akasin haka, sai na tafi, ka bani hanya tun ban yi ball da kai ba!!". Rai a matukar ɓace shi ma Areef ɗin ya damko wuyar Lion ɗin, sai huci yake yi ya ce "Lion babu in da zaka je wlh!!". Ganin suna ƙoƙarin fara faɗa ne yasa daddyn ya yi saurin zuwa ya shiga tsakaninsu yana ƙoƙarin rabasu, dan kuwa yasan faɗarsu idan ta fara babu kyan gani sam, duk sai sun jiwa kansu ciwo, sai sun yi wa kansu fata fata, babu tausayi suke jibgan junansu tamkar ba jini ne a jikinsu ba, idan suka fara faɗa, zaka rantse da Allah wasu shahararrun abokan gaba ne, mafiya yawan lokuta sai Lion ya gama illata Areef sannan yake hakura, wani lokaci ma sai ya sumar da Areef ɗin sannan ya ɗaukesa juna word room ya fara bashi taimakon gaggawa, haka suke kamar wasu zakuna a dokar dawa idan suna faɗa. Jan Areef daddy ya yi dan yasan shi ne mai hakurin da zai iya dannarsa kuma ya danne ya hakura, shi kuwa Lion ina ai idan ya zuciya baya ji baya gani, shiyasa daddyn bai yi yunkurin tinkararsa ba. Sakinsa Lion ɗin ya yi tare da nufar waje abinsa, shi kuma Areef daddy ya mayar da shi saman bed tare da ɗauko mishi ruwa mai sanyi daga cikin fridge, karɓar ruwan ya yi tare da buɗewa ya kafa a ɗan bakinsa yana mai jin zafi a zuciyarsa, sam baya son tafiyar ta Lion wlh, amma ya zai yi? Dole ya hakura, dan kome zasu yi wlh sai ya tafi kamar yanda ya faɗa. Lion kuwa yana barin bedroom ɗin ɗakinsa ya nufa, wanka ya yi tare da shiryawa ya fito shi da Tyrone suka nufi Abuja dan ta Lagos zai fita kasar, shirye shiryen kuma daga Abuja aka farota. A ɓangaren su Rimsha kuwa, sun rubuta Exams lafiya lou, sai murna suke yi, Anaya ta bawa Rimsha wani haɗaɗɗen yaji da mummyn Rimsha ta kawo musu daga Maiduguri, yaji yana da bala'in daɗi sosai, dama tana kawo musu duk idan zata zo, to wannan karon dai da yake Anaya tana tare da Rimsha sai ta deɓo mata dayawa ta bata, sosai Rimshar ta ji daɗi dan rabonta da cin yaji tun suna Abuja tare da su mummyn nata, idan baku manta ba a gidan Lion ba'a dafa abinci da ya ji, dan basu ci dukkansu, suna yin gym basu isa da cin yaji ba, zai yi musu mummunar illah dan gym ɗin da suke yi ba irin na kananan yara bane. Sai murnar samun yajin take yi ta karɓa Anayar ta yi mata rakiya har wajen mota, sai bayan ta yi mata bye bye ne ta juyo ga Mark, ya zuba mata idanu yana kallonta, cool murmushi ta sakar mishi tana yi mishi bye bye. Waya ya ɗauko ya fara ɗaukarta hoto tana murmushi wani wajen kuma ta rufe fuska da hannunta, a wani wajen ta turo baki tana faɗa mishi bata so, hotuna dai kala kala ba iya ka ya ɗauketa, ita dai Rimsha wannan abin yana bata mamaki, har ƴar zazzaɓi zazzaɓi ta rinƙa ji na ganin irin sauyin Lion da Mark, gara ma shi Lion ba lokaci guda ya sauya ba, da kaɗan da kaɗan abin ya kama shi, tun zuwansu Abuja da suka dawo, a hankali komai ya sauya mishi, amma har yanzu dai kaso 70 na cikin halinsa na baya yana nan, a hankali hankali dai yana sauyawa, shi kuma Mark lokacin guda ya sauyawa iya Anaya kawai kamar yanda shi ma Lion ɗin iya ita Rimshar ce kawai take ganin ya ɗan canza mata, bayan ita babu wanda ya canzawa, kamar dai yadda yake a baya haka yake a yanzu ga kowa, shi ma Mark hakan yake ga kowa banda Anayarsa, ita kaɗai yake sake mata har su yi magana. Sai da ya ɗauketa hoto iya son ransa kafin ya ɗan matso da face nasa ta glass ɗin motar yana magana kasa kasa, sam dukkansu basu ji me ya faɗa ba, dan haka sai Anayar ta matso kusa da shi sosai tare da ɗan rankwafowa kansa tana tambayarsa me ya ce, da yake su basu san me kunya ba a rayuwarsu, sai ya sumbaceta a kumatu yana faɗin abin da ya ce kenan ta zo ya sumbaceta su yi bye bye, sam Rimsha bata ga abin da ya yi ba, dan tana ciki, kuma ta mayar da hankalinta kan students dake safa da marwa a wajen, ita kuma Anaya rufe fuska ta yi tana murmushi ta bar wajen da sauri, komawa cikin motar da kyau ya yi tare da kunnata ya ja suka bar waje zuciyarsa cike da tunaninta. After some minutes, bayan ta yi wanka ta ci abinci ne ta ɗauko sim card nata ta nufi bedroom ɗin Lion, bakinta ɗauke da sallama ta shiga, baya nan yana Abuja basu dawo ba, dressing room nasa ta shiga ta ɗauko wata danƙareriyar waya mai bala'in tsada, wayar ta yi mata kyau over, kunnata ta yi sai taga hotonsa ne a saman screen ta fuskar wayar, yana zaune a bakin pool nasu na Washington DC, daga shi sai kayan shan iska, farare tas masu bala'in kyau, kafarsa na sanye da wasu takalma masu bala'in kyau irin home sleepers ɗin nan, ya ɗaure gashin kansa ya bar wannan guntu na gaban goshin, idanunsa akwai glass blue color, ya yi kyau over. Ba karamar daɗi ta ji ba, sumbatar wayar ta yi tana murmushi, kai kallonta saman wayar ta yi sai taga akwai sim card a cikinta, shiru ta ɗan yi tana tunanin to sim ɗin waye? Ta cire ta sanya nata ne ko kuma dai ta barshi a ciki kamar yanda ta gani?. Ganin babu mai bata amsa ne yasa ta fito daga cikin room ɗin zuwa cikin ɗakin tare da zama a gefen gadonsa, tunani ta fara yi wai shin ina yake ne ma? Ina ya tafi? Ganin shi ma babu mai bata amsa ne yasa ta miƙe ta fita zuwa wajen Areef dan su tafi shopping bayan ta sanya sim card ɗin nata. A ɗakin daddynta ta isko Areef ɗin, ya tasa Jehan a gaba sai tsokanar yake yi daddy nayi musu dariya, saman gadon ita ma ta haye tana faɗin "Yaya Areef mu tafi". Kallon kayan jikinta ya yi kafin ya ce "Jeki saka wannan abin da kuke sakawa har kasan nan, irin wanda kika saka da safe, ki rufe jikinki kaf". Okey ta amsa mishi tare da cewa "Daddy yaya Saif ya ce na koma ɗakinsa da zama, ya ce ko palo bai yarda na fita ba, yanzu ma shi ne ya ce yaya Areef ya kai ni shopping". Ta yi maganar tamkar zata yi kuka. Jinjina mata kai daddyn ya yi yana faɗin "Duk abin da ya ce miki to kibi umarninsa kin ji ko my daughter?". Gyaɗa mishi kai ta yi zuciyarta cike fal da mamaki. "Allah ya yi miki albarka my siha". Amin ta amsa da shi, duk jikinta a mace, Areef ya lura da hakan, dan haka sai ya yi ƙoƙarin sanyata farinciki, da haka ya ce da Jehan ta shirya suje shopping ɗin, kai tsaye ta ce bazata je ba, bai tilastata ba, ya rabu da ita suka tafi shi da Rimsha sai Aseef da AKila, sun bar daddynsu daddyn Rimsha dasu uncle Herry a gida. Sun sha sayayya ba kaɗan ba, duk kuma abin da suka saya Lion ne ya biya kuɗin, dan a ɗakinsa Areef ya ɗebo musu kuɗin, Aseef kayan shanawa dana barci kawai ya ɗebawa Heartbeat nasa, ita ma Rimsha ta ɗauki kananan kaya sosai, sai kuma jallabiyoyi da perfume, sai hijabai guda biyu da kuma kayan Indian ta da zata sanya gobe, daga karshe ta ɗauki vest dozen ɗaya farare tas. Shi kuma Areef ya sayawa Jehan kaya da yawa, ciki kuma har da breziya da su pants, dan yasan size nata gabaɗaya, idan baku manta ba da tana prison ya saya mata pants, kuma ba wani bane ya gaya mishi size nata, da idanunsa ya auna kawai, ganinta yasa ya gane girman komai, da haka sai ya saya mata komai dai'dai ma'auninsa. Sun sha sayayya ba karya sannan suka dawo gida. Har ɗaki Areef ya kaiwa Jehan ɗin kayan, ita kuma Rimsha ta wuce bedroom ɗin Lion da gabaɗaya kayanta da suka sayo, a dressing room nasa ta shirya komai, Aseef da Akila suka wuce bedroom nasu. Bayan ta kammala komai ta ci abinci ta yi wanka ne ta haye saman sofa ta yi kwanciyarta dan ta yi barci, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita. A ɓangaren Jehan kuwa, sun sha dirama da Areef, data ga kayan da ya saya mata ne ma yasa ta kara yarda wlh shi ɗan iska ne da gaske, ji ta yi ta kara tsanarsa, idan ba iskanci ba me na saya mata su breziya? Shi kuma dai yasan matarsa ce tun da daddy ya bashi aurenta, kuma har sadakinta ya biya, ba ɓata lokaci ya bawa daddyn bakudan kuɗaɗe daloli daya kwaso a wajen Lion, shi kansa bai san nawa bane, kawai ya zubewa daddy a matsayin sune sadakinta, shiyasa baya shayin ya yi mata duk abin da ya yi niya. Da misalin karfe 8 na dare, sosai Rimsha ta shiga damuwa ganin Lion yau sam bata gan shi a gidan ba, ta rasa waye kuma zata tambaya, ta yi barcin ta har ta tashi ta yi wanka, ta je kitchen ta ɗauko mishi abincinsa ta zo ta yi sallar mangariba da issha, amma shiru bai dawo ba, kunna wayarta ta yi tana duba time, shiga cikin wayar ta yi tana dubawa, da alama wayarsa ce da ya taɓa amfani da ita, dan akwai hotonansa dayawa a ciki, sai dai kuma wayar ta yi kama da sabuwa ce sosai, bayan hotonsa babu wani abin da yake cikin wayar. Shiru ta yi tana tunanin ina kuma ya shiga, ga shi bata san numbersa ba bare ta kira shi, komawa ta yi ta kishingiɗa a saman sofa tana tunanin mafita. Can kasan maƙoshinsa ya yi sallama tare da shigowa cikin ɗakin, tamkar ta watsa a guje ta yi mishi oyoyo haka take ji, ba karamin daɗin ganinsa ta ji ba. Sannu da dawowa ta yi mishi, sam bai amsa ba kuma bai bi ta kanta ba, da alama ransa a ɓace ya dawo, toilet ya nufa, shiru ta yi tana tunanin yanda face nasa, ta razana ba kaɗan ba, dan da alama a kusa zuciyarsa take yau. Wanka ya yi tare da fitowa ya shiga dressing room, tana zauna a wajen har ya fito cikin shirin kayan barci, saman bed nasa ya haye ba tare da ya bi ta kanta ba, cike da tsoro ta ce mishi "Yaya Saif in zuba maka abincin". Har cikin ransa ya ji dama dama najin sautin voice nata da ya yi, ga shi ta yi maganar cikin natsuwa, voice ɗin nata kuma da akwai shagwaɓa a cikinta. Shiru ya yi bai tanka ba, mikewa ta yi cike da tsoro ta dawo saman bedside drawer, jikinta har kerma yake yi saboda tsoro, amma sai ta daure ta ɗan shagwaɓe murya kasa kasa a nitse ta ce "Ayya Yaya Saif in saka maka abincin ne?". Waro dara daran blue eyes da suke jawur ya yi a saman face nata, ta tsorata da ganin idanunsa ba kaɗan ba, shi kuma ya ji duk wani ɓacin ransa ya gudu da ya ga kyakyawan face nata, sai ya ji wani sanyi a cikin ransa. A hankali ya lumshe idanun nasa tare da sake buɗesu akanta, still dai ita ɗin ce, Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da mikewa zaune ya yi shiru kamar mai tunanin wani abin. Zuba mishi idanu ta yi ya ɗan ɗauki lokaci a haka kafin nan ya jinjina mata kai alamar ta zuba mishi abincin, ganin kyakkyawar fuskarta yasa ya ji zai iya cin abincin, saɓanin yanda ya shigo cikin ɓacin rai, sam bashi da niyar sanya wani abin a bakinsa, ya yi niyar ya yi barci ne kawai. Amma sai ga shi a dalilinta ya ci abincin mai yawa ma, dan yana jin yunwa sosai, tun fitarsa da safe bai ci komai ba sai Maltina, dole dama ya ji yunwa over, ba ƙaramin daɗi ta ji ba ganin ya ci abinci, mikewa ya yi ya nufi toilet ya yi brush ya fito, zama ita kuma ta yi ta ci abincin kaɗan kafin ta kwashi kayan abincin da nufin ta mayar kitchen, ba tare da ya kalli in da take ba ya ce ta bar kayan abincin a wajen ai ya hanata fita ko nan da palo, so ta yi kwanciyarta duk time da Areef ya shigo zai fita da kayan abincin. Ba dan ta so ba hakan ba ta ajiye kayan tare da kwanciya a saman sofa, kayan barci ne a jikinta sai ta ɗaura hijabi a sama, shi kuma saman bed nasa ya haye ya kwanta ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi dan a gajiye ya dawo, ita kam mamaki da al'ajabin wannan al'amari ya hana yin barci Baiwar Allah, bare ma yanda daddynta ya bada goyon baya ta kwana a ɗakin mutumin da ba muharraminta ba, ba mijinta ba, abin ya ɗaure mata kai sai take ganin kamar ba daddyn nata bane, kamar an canza mata shi, ko kuma ciwon dake damun Lion da Mark ne yake damun daddyn nata shi ma. Tunani dai kala kala cike fal ranta har karfe 1, da kyar ta samu barci ya yi awon gaba da ita. Karfe biyu daidai Lion ya tashi ya fara sallolinsa kamar yanda ya saba, bai mayar da barci na sai da ya yi sallar asuba, ita kuma da ta yi sallar asuba ta hau shirin zuwa school saboda partynsu. Yana barci amma yana jin duk wani motsinta, tsab ta shirya ta yi wani irin azababben kyau tamkar ba Indiya, sai ta saki gashin kan nan nata har gadon baya bata ɗaure ba, sam bata san ita matar aure bace, ta yi dressing nata son ranta, ba karya ta fito ɗas. Fitowa ta yi zuwa kitchen ta karɓi abinci, yau Mark duk rashin kallonta da baya so yi sai da ya kalle ta ya sake waigawa, dan fa ta fita, duk wanda ya kalleta a gidan sai ya sake waigawa ya kalleta, ga sarin nata launin pink color abin ba'a magana. Saman table ta zauna ta ci abincin nata, tsabar murnar zuwa partyn nan ko neman su daddynta bata yi ba, haka ta tafi school basu haɗu da Lion ba, kuma bata nemi su daddy ba, ita kam kawai ta yi tafiyarta, ta kuma tafi da wayar da Lion ɗin ya bata dan su yi hotuna da classmate nata da Anayarta, dama sun yi da Anaya shigar India zasu yi, ita Anayar ce ma ta tsayar musu da kalar da zasu saka. Haka Mark ya buɗe baki yana ganin kyau ɗin da Anaya ta yi, kamar wasu tagwaye, tamkar ka sace su ka gudu da su, kyau iya kyau ba'a magana. Mark yana zaune a wajen har motarsu Areef ta iso, dama sun ce mata zasu zo, Aseef, Areef, daddynta, Akila, da kuma Jehan, ta sha faɗa wajen daddy ba kaɗan ba da bata sanya ɗankwali ba, sam bai ga fitowarta daga gida ba da ba zai bari ta fito babu ɗankwali ba, shi kam Aseef ko a jikinsa yana tare da rigimatinsa suna aikin da suka saba, wato zubawa juna shagwaɓa, Areef kuwa ba abin da ya ayyana a ransa irin a samu ɓacin lokacin Lion ya ce zai zo wajen nan, wlh Rimsha ta shiga uku, mai kwatarta sai Allah, dan wlh idan bata yi sa'a ba karshen gashin nan nata ne ya zo, shi kansa ya yi kishin ganin yanda idanun dubbanin jama'a har da iyayen yara manyan mutane suke kanta, suna kallonta, duk in da ta juya kowa ita yake kallo, lallai Allah dai yasa kada wata kaddarar ta kawo Lion nan, dan idan bai tashi jama'a da boom ba abu kaɗan ne zai hana, amma tabbas zai tashi kwakwalwar Rimsha da tunaninta, sai ta yabawa aya zakinta ba kaɗan ba, ga shi dan iskanci har da wani saka wasu siraran jigida masu bala'in kyalli da kyau suna ɗaukar hankali mutane a kugunta ta saman kayan, kun san dama suna ɗaura sarka a saman sarin, to ita ba ɗaya bama ta ɗaura almost guda biyar sirara ta zuba a wajen. Areef dai yana taya ɗan uwansa kishi, ya kasa jurewa sai ya mike ya bar wajen dan ya kira numberta ta fito daga wajen cikin rufin asiri su koma gida, kash babu network, wayar ta ki shiga, hotuna take ta ɗauka da Anaya da classmate nata, anata gabatar da abubuwa. After some minutes ta nemi Anaya a wajen ta rasa, ɗan waige waige ta fara yi bata ganta ba, wata classmate nasu dake kusa da ita mai suna Aisha ta tambaya ina Anaya? Cikin nuna kulawa ta bata amsa da Mr Emmanuel ya aiko an kirata, ɗan zaro idanu ta yi tana mamakin yanda akayi Anaya ta bar wajen ba tare da ta gaya mata ba, ko da yake jama'a sun yi yawa, to amma me Mr Emmanuel zai yi mata kowa yana tsaka da shagali?. Tuna banzan hali irin nasa ne yasa ta sauko daga saman step ɗin da sauri ta fito daga cikin hall ɗin, kai tsaye office nasa ta nufa, shi kuma Areef yana ta baya wajen motocinsu yana gwada kiran numberta, Aseef da daddy tare da su Jehan suna zauna a saman kujerun da aka tanadawa iyaye, sam a cikinsu babu wanda ya lura da ta bar hall ɗin, da yake sai zuba hira Aseef da daddy suke yi kwana biyu basu haɗu ba. Ko da ta shiga office ɗin babu kowa a ciki, har ta juya zata fita sai ta kalli takalmar Anayar guda ɗaya a dai'dai wajen table chairnsa, da sauri ta karisa wajen tana kallon takalmin, hakan na nufin kenan tabbas Anaya ta shigo office ɗin, to ina take? Ta tambaya tare da ɗagowa tana bin office ɗin da kallo, tuna cewa ya taɓa cewa Anayar ta shiga cikin toilet ne yasa ta yi saurin karisawa bakin kofar toilet ɗin tana knocking. Kamar jira yake yi ayi knocking, cikin kankanin lokaci ya buɗe kofar daga ta ciki, yana buɗewa kuma ya fesa mata wani farar powder a fuska, nan take ta zube kasa sumammiya, dariya ya yi yana faɗin "Dama nasan dole zaki zo neman Anaya dan ɗaya bata tafiya sai da ɗaya, shiyasa na zauna zaman jiran zuwanki dan na haɗa ku lokaci guda nayi abin da nake so, nasan daga yau zamu tafi hutu ba zan sami cika burina a kanku ba, to dole nayi amfani da damata ta yau". Yana surutu yana ƙoƙarin ɗagota dan ya shigar da ita cikin toilet ɗin, daddaɗar kamshin perfume ɗin Lion da bai taɓa jin irinta ba ne ta daki kofofin hancinsa wanda ya sanya shi ɗago kai cikin sauri dan yaga daga ta ina wannan fitinannen daddaɗar kamshin ya fito. Yana ɗago ido suka yi 4 eyes da blue eyes na Lion dake tsaye a bakin kofar shigowa, hannunsa na rike da wayarsa Mark yana tsaye a ta bayansa, shi Lion ya biyota ɗaukarta su wuce ne, idan baku manta ba suna da tafiya yau, shi kuma Mark dama aikinsa ne kula da ita, so ya kalli time da ta shiga office ɗin, shi ne da Lion ya zo ya ce ina take Mark ya kirata su tafi, sai ya ce tana office na uncle nasu, ba zai iya jira ba, shi ne ya fito da kansa dan ya ɗauketa su wuce, shi kuma Areef ganin Lion yasa ya shiga tashin hankali, dan kuwa yasan Rimsha ta shiga uku.........E KAM TA SHIGA UKU HAKA ZALIKA WAƳAN DA SUKA SHIGA UKUN ALLAH YA YI YAWA DA SU A SCHOOL ƊIN, CIKI HAR DA DADDYNTA DAN BASHI DA HANYAR WANKE KANSA, KO ZAI MUTU ZA'ACE AI YAGA DRESSING DA TA YI, TO JUSTICE FOR MUTANE DAYAWA. E 65-66💋 Ganin idanun Lion ba karamin razana ya yi ba, dama abin da kuka sani ne, duk dakiyar mutun da kwarin zuciyarsa yana yin idanu biyu da Lion sai ya razana, dan blue eyes yanayin su ma tun ainahi idanu ne masu firgitarwa bare ace dara dara ga masu shi fuska a ɗaure, dole a hantar maza ta kaɗa sosai. Sakinta ya yi tare da watsawa a guje ya koma cikin toilet ɗin ya rufo kofar tare da murza key. Wani irin huci Lion yake fitarwa tare da furzar da wani iska mai azababben zafi daga bakinsa, idan ya runtse idanunsa kawai ganin yanda Mr Emmanuel ya riko hannayenta zai ɗaga ta yake yi, jin zuciyarsa yake yi tamkar zata faso kirjinsa ta fito waje, har wani irin tsuma jikinsa yake yi tsabar tsananin ɓacin rai, gabaɗaya gashin jikinsa sun miƙe tsaye saboda halin da ya shiga, shi kansa Mark da already ya san halinsa, amma yau ya razana, dan gaskiya bai taɓa ganin ogan nasa ya yi irin wannan zuciya haka ba, yana zuciya a baya amma baya kai haka, dan ko bai zuciya bama hukuncinsa bata da kyan gani bare kuma ace ya zuciya, so bai cika bari yana zuciya yana hawa sosai bama, dan idan fa ya zuciya ya hau kifar da komai yake yi, babu wanda ya isa ya tinkaresa ma bare ya dakatar da shi. Kofar toilet ɗin ya nufa da wani irin taku na nuna isa da jarunta, da sauri Mark ya bi bayansa, cikin fushi ya yi wa kofar wata mahaukaciyar taku, sai ga kofar ta ruguje ta faɗi kasa ta cikin toilet ɗin, sam bai shiga cikin toilet ɗin ba, dan kyama gabaɗaya office ɗin ya bashi, ba dan Rimsha ba wlh yafi karfin shiga irin wannan dattin wajen a cewarsa, kuma kunsani already baya son datti komai kankantar shi, baya shiri da datti sam, shiyasa yaki shiga cikin toilet ɗin dan yasan zai yi amai, haka gabaɗaya TRIPLETS suke da wannan azababben kyamar, idan suka ga abin da bai yi musu ba, to sai sun yi amai ko a ina ne. Ta gefen idnaunsa ya kalli Mark, Mark ya gane karatun ma'ana shi ya shiga ya fito da Mr Emmanuel kenan, da sauri ya shiga, ba shiri ya ja birki ganin Anaya kwance cikin baf ɗin wanka babu kaya a jikinta, wani irin azababben harbawa zuciyarsa ta yi lokaci guda, dafe kansa dake barazanar tarwatsewa lokaci guda ya yi, nan take idanunsa suka yi jajir tamkar wuta, kawar da kallonsa daga kanta ya yi zuwa kan Mr Emmanuel dake manne da jikin bango yana zare idanu kamar ɓera a tarko. Kayanta ya ɗauka ya rufa mata a jikinta kafin ya damko wuyar rigar Mr Emmanuel ɗin ya ja shi zuwa wajen, har wani ruwa mai kama da hawaye ne suka kwanto mishi a cikin idanunsa, tun bayan mutuwar budurwarsa bai sake shiga tashin hankali irin na yau ba, bai taɓa shiga ɓacin rai irin na yau ba, har wani irin numfashi yake yi mai kama da shasshekar kuka, zuciyarsa na harbawa da sauri sauri ji yake yi tamkar zai zube kasa, kafafunsa suna ƙoƙarin kasa ɗaukarsa saboda abin da ya gani. Mikawa Lion shi ya yi tare da ɗan yin gaba kaɗan dan zuciyarsa gab take da tarwatsewa, da kallo daya Lion ya yi wa Mark ɗin ya fahimci yau ran Mark ya kai kololuwa wajen ɓaci, yau tsawon shekaru 5 suna tare bai taɓa ganinsa a cikin irin wannan hali ba sai yau, hakan yasa ya fahimci dole akwai abin da ya gani a cikin toilet ɗin ne da ta jefa shi cikin wannan yanayi haka. Amma sai ya basar tare da damko wutar Mr Emmanuel ya ɗaga shi sama tare da shakesa sosai, wurgi da shi ya yi a can gefe guda, yana mai jin kuna a cikin zuciyarsa. Wani irin karfi Mark ya ji ya zo mishi lokaci guda, har haɗa zufa yake yi, watsi ya fara yi da computers da kuma gabaɗaya takardun dake cikin office ɗin dan tsabar ɓacin rai, Lion kuma yana aikin jibgar Mr Emmanuel, sake ɗaga shi ya yi, ya yi wurgi da shi ta gefe guda. Yana yin wurgi da shi Mark ɗin ya tinkare shi gadan gadan tare da damƙo wuyarsa da rigar jikinsa bakiɗaya ya haɗe ya shaƙosa tare da yin sama da shi ya sake wurga shi kusa da Lion ɗin, tamkar kwallo haka suka mayar da Mr Emmanuel a cikin office ɗin nasa, gabaɗaya sai buga shi suke yi, suna haɗe shi da jikin bango ne chairs dake office ɗin da sauransu, duk wasu takardu, desktop computers ba abin da ya rage da ransa, komai ya tarwatse, ko kwallo suka samu ba zasu buga shi kamar yadda suka buga Mr Emmanuel a yau ba, shi kam Mark idan ya tuna yanayin daya ga Anaya a ciki sai ya ji kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu, hakan tasa ya ji wlh ko gawar Mr Emmanuel ba zai iya bari ba, a haukace dai suka yi mishi duka har rai ya yi halinsa basu sani ba, dan kusa dukkansu sun shaki bakin ciki ne na wuce misali, sai da suka karya mishi kafafu da hannaye, shi Lion ma ya kasa hakura har sai da ya ɗaga shi sama ya ɓalla mishi baya da jikin wata table dake cikin office ɗin, sannan ne suka rabu da gawarsa, dukkansu biyu an rasa mai ɗaga idanu ya kalli su Rimsha, wani azababben kishi ne yake cin zuciyarsu, shi dai Lion idan ya lumshi idanu sai kawai yaga lokacin da Mr Emmanuel ya kama hannunta, wannan abin idan ya tuna ji yake tamkar ya haɗiyi zuciya kawai ya mutu sai ta fi mishi sauki, shi kuma Mark yanayin da ya sami Anaya yake tunawa, sai ya ji kamar yasa bindiga ya harbi kansa ko zai huce, duk idan suka tuna sai sun sake taka gawar Mr Emmanuel, da alama dai sun fita a hayyacinsu sosai, tsantsar kishi ne yake ɗawainiya da su. Sun jima a haka kafin Lion ya nufi wajen da take kwance, ji ya yi kamar kawai ya yanke hannun nata da Mr Emmanuel ya taɓa dan haushi, dukawa ya yi ya saɓeta a kafaɗarsa ya nufi waje, sam bai san da Anaya a cikin toilet ɗin ba. Ganin ya fita ne yasa Mark ya nufi cikin toilet ɗin, da kansa ya mayar mata da kayanta kaf, wasu zafafan hawaye ne suka fara gangaro mishi a face nasa, tabbas ya san cewa Mr Emmanuel bai yi mata komai ba, dan da alama ya gama cire mata kayan ne Rimsha ta shigo ta yi musu knocking, amma duk da haka, zafin ya cire mata kayan ne yasa shi cikin wannan hali da yake ciki, dole ya yi hawaye, dan wani lokaci idan bakin ciki ta yi maka yawa, idan baka zubar da kwallah ba, to kana iya haɗiyar zuciya ka mutu, zubar da kwallah ne rufin asirinka, shi zai taimaka ya rage maka raɗaɗin da kake ji a cikin zuciyarka, shi ma dai Mark hakan ce ta kasance da shi........... Tab da ace Lion ne ya sami Rimsha kamar yanda Mark ya sami Anaya, da ina ga yau kashe kansa kawai zai yi dan kishi🤔😭😌 Kallon face nata ya yi, tunanin powder daya hura musu ɗin yake yi, powder ce mai haɗari da suke hana amfani da ita, goge hawayen face nasa ya yi tare da ɗaukarta a saman kafaɗarsa ha bi bayan Lion. A cikin motarsa Lion ya shifiɗeta a gidan baya tare da bawa sojojinsa guda biyar da ya zo da su umarnin a kan su kama mishi gabaɗaya malaman da suke cikin school ɗin nan, su kuma students ɗin su rufe su a cikin hall ɗin, cikin girmamawa suka karɓi umarni tare da wucewa. Su daddy suna tsaka da kallon party, anata abubuwa kawai basu ankara ba suka ga diran jibga jibgan Turawan sojojin Lion, gasu da tsawo da faɗin kirji kamar wasu zakuna, farare tas tamkar ka taɓa jini ya zuba, sai dai fa fuskokinsu babu alamar imani ko ɗigo a wajen, shi ma Areef a lokacin ya dawo yana cikin hall ɗin, ya kasa sukuni dan yana jiyewa Rimsha abin da zai biyo baya, ya kasa gayawa daddy Lion ya zo. A ɓangaren Mark kuwa, shi ma a cikin mota ya kwantar da Anaya, sai lokacin Lion ya fahimci dalilin da ya sanya Mark cikin tashin hankali haka, shiru ya yi bai tanka musu ba. Mu koma baya kaɗan, da daddyn Rimsha da daddyn Anaya duk sun zo taron, sai dai basu haɗu ba, shi dai daddyn Anaya yana ta kallon Rimsha, ya kuma kuduri niyar idan suka tashi taro sai ya kirata sun yi magana, dan duk yanda akayi wannan ƴar Hosain ɗinsa ne, tana kama da mummynta da yake tare da ita a gidansa yanzu, shi daddyn Rimsha ya ga kalli Hassan ɗin nasa, amma kun sani dama can yaki yardan musu da shi ne Hosain, dan haka sai bai kula daddyn Anaya ba, ya yi kamar ma bai ganshi ba, Anayar kawai yake ta kallo, ta girma sosai, hotonta da yake da shi lokacin bata wuce 12 years ba, yanzu kuma 16 years take da shi, har cikin ransa yake jin kaunar Anayar dan kamanninsu ta ɗauko, irin Jehan ce sak, da daddyn Rimsha da daddyn Anaya fa ba karya akwai kamanin, da suke yara ma ba'a banbantasu, sai da suka girma ne kamannin ya ragu, to haka Jehan da Anayar suke kamani, ga su dai ba twins ba, amma kowa ta ɗauko babanta, sai suka zama twins ɗin kawai. Gabaɗaya malaman makaranta sai da waƴan nan jibga jibgan sojojinsa da zasu tafi da su Russia suka kamasu, dukkansu sai da suka sanyasu suka zube gwiwowinsu a kasa, yau dai anyi yaki a cikin school ɗin, ba wanda hankalinsa bai tashi ba, shi dama uncle Faisal tun washe garin ranar da ya kira Rimsha a waya ya wuce gadon asibiti, dan Mark ne ya yi mishi wani ɗan iskan duka bisa umarnin Lion, yanzu ko in da kansa yake ma bai sani ba, so baya school ɗin. Tun da TRIPLETS suka ga abin da yake faruwa, tun da suka ga sojojin sun san lallai an yiwa Lion ba daidai ba, shi kam Areef ya san komai dan ya bisu wajen, sai da ya kalli sun nika Mr Emmanuel lilis ne ya dawo cikin hall ɗin ya rasa ma me zai ce da su Aseef. Tambayarsa Aseef ya yi a kan me akayiwa Lion yasa aka kama malamai gabaɗaya? Ba ɓoye ɓoye Areef ɗin ya sanar musu da abin da yake faruwa, sosai daddy ya shiga tashin hankali, a hanzarce har yana haɗe words ya tambayi Areef ɗin amma babu abin da ya sami Rimsha ko? Basu yi mata wani abu ba ko? Babu abin da suka yi mata Areef ɗin ya bashi amsa, Allah sarki uba mai daɗi, shi dai burinsa ya ji babu abin da akayi mata kawai. Da mamaki Aseef ya tambayi Areef ɗin to su kuma malaman makarantar me ruwansu da za'a haɗa da su, a kule Areef ɗin ya bashi amsa da cewa "Akwai ruwansu kam azzalumai, ace suna da malami irin wannan mai lalata ɗalibai kuma su ce basu sani ba? Ai yau ni zan yankewa shugaban makarantar nan abin da baby ta yankewa wancan kazamin". Jinjina kai Aseef ɗin ya yi tare da riko hannun heartbeat nasa suka nufi hanyar fita daga cikin hall ɗin, dan ya je wajen motarsu ya duba ɗan uwansa, cikin girmamawa sojoji biyu da suka tare bakin hall ɗin suka bashi hanya suna sara mishi. "Uncle muje wajensu Lion, tsayuwa a nan sam bai dace damu ba" . Ya kai karshen maganar tare da riko hannun Jehan dan su nufi waje, bata kwace hannun nata ba, dan kuwa tana bala'in tsoron sojijin da suka tare kofar nan, kada ta je ta kwace hannunta su hanata fita, sai kawai ta bishi suka nufi wajen. Suna fita ta kwace hannunta, shi ma bai wani damu ba, burinsa kawai su isa ga Lion. Tattare malaman gabaɗaya sojojin suka yi, sauran students da parents nasu kuma suka rufesu a cikin hall ɗin. Lion yana tsaye yana waya cikin fushi, da alama a kan tafiyar tasu yake magana, zasu bi jirgi sama ne zuwa Lagos, daga nan sai su shiga jirgin ruwan, so an gama shirya komai shi kaɗai ake jira, sai kiransa suke yi a waya, shi ne suka kara ɓata mishi rai yake kwashe musu albarka da kyau da kyau. Tsayuwa su Aseef duka zo suka yi kusa da shi, Akila ta kankame Aseef sosai saboda tsananin tsoron Lion, bare ma yanda taga face nasa yau, ai rike mijinta kam ta yi abinta, daddyn Rimsha da Areef kuma sun jingina da jikin motarsu Tyrone suna kallon Lion ɗin, yau fa Jehan kusa da Areef sosai ta tsaya saboda tsoron Lion, tasan ko daddynta bai isa ya yi magana ba, so gara mata Areef ɗin dai duk bala'i, ta san dai idan ta kama shi shi ne ta kama dahir...... Wayyo rashin kunya ma ashe waje yake samu. Ganin yanda Lion yake magana cikin fushi da faɗa faɗa ne yasa Jehan ɗin ta yi mugun tsorata, dama tsoronsa kamar ta mutu, yau kuma ga shi ya kara ɗaure fuska over yana faɗa, sai dai fa duk faɗan da yake yi kasa kasa yake magana, bai iya ɗaga murya a magana ba sai idan ya zama dole. Bayan ya kammala wayar ne ya juyo garesu, ganin daddy a wajen yasa zuciyarsa ta kara hasala ba kaɗan ba, cikin fushi ya nufo daddyn, a kausashe ya ce da shi dama kenan yana ganin Rimsha ta fita da irin shigar jikintan nan?! Ga sarin ma bai gama rufe mata cikinta ba, wato ya san komai ya zuba mata idanu ko? To tukun nan ma me ta je yi a office ɗin Mr Emmanuel? Dole yau su karɓi hukunci baki ɗayansu. Cikin sauri Areef ya ari bakin daddy ya ci mishi albasa, dan baya son ta sake kwaɓe musu a karo na huɗu, yana son ya ga suna zaman lafiya da mutunta juna. "Lion seriously uncle bai san time da ta zo school ba, mu daga baya muka zo, kuma ka dai'na tambayar me ya kaita office na Mr Emmanuel, kasan fa uncle nasu ne, so maybe kiranta ya yi, kadai san sister ba zata je office nasa haka kawai ba, sannan kuma......". Hannu ya ɗaga mishi yana faɗin "Ba da kai nake magana ba!". Dafe kai Areef ɗin ya yi yana mamakin wai meyasa daddyn Rimsha da Lion basu shiri ne? Meyasa Lion ya raina daddy har haka ne? Why yake yi mishi haka? Mutun ya ɗauki yaransa guda biyu da Allah ya bashi su kawai a duniya ya basu aurensu amma Lion baya ɗaga mishi kafa, a gaskiya wannan karon bai ga abin da zai sa ya bari ayiwa daddy wani hukunci ba, dan kuwa bashi da laifi, bai san Rimsha ta fita haka ba, kuma Lion ɗin yasan hakan, yasan cewa daddy ba tarbiya ta banza ya bawa yaransa ba, shi mutun ne mai kula, a gabaɗaya ƴan uwansa ma shi ne ya fi bawa ƴaƴansa ilimin addini da kuma tarbiyarsu mai kyau, so yasan tarihinsu, ya san komai, kawai dai rashin jituwa da basu yi da daddyn ne yasa ya kasa yi mishi adalci, da kuma azababben kishi da ya rufe mishi idanu. Zai sake yin magana sojojinsa da malaman makarantar suka iso wajen, hakan yasa ya danne maganar tare da bawa Areef umarni a kan zai turo wasu sojojin a wuce mishi da malaman gabaɗaya gida, sojojinsa su fara basu hulunci idan ya hau hanya ma'ana idan sun shiga ruwa zai waiwayesu dan yaga hukuncin da ya dace da su, so Areef ɗin ya kula da komai sauri yake yi yanzu, shi kuma daddy ya jira dawowarsa, dan ba zai kyale shi ba!!. Umarni ya yi wa su Mark a kan su shiga motocinsu su tafi, okey suka amsa, cikin girmamawa Mark ya ce yana son ya mayar da Anaya gidansu, da yake shi ma Lion ɗin yana son Mark ɗin saboda zaman amana da suka yi, sai ya ce to su shiga mota sai su fara biyawa ta gidan nasu kafin su wuce airport, ya san gidan ne, yasani ya amsa da shi dan jiya ta yi mishi kwatance a waya da ya ce mata zai zo, so sai ya yi amfani da google map ya duba sunan unguwar tasu, ya ji daɗi sosai. Ko da suka je gidan uncle Shitu da ya dawo daga tafiya yanzu suka samu, mika mishi Anayar Mark ya yi ba tare da ya yi magana ba suka wuce, lokacin Rimsha tana sume bata sami damar ganin uncle Shitu ba, ga shi su mummynta ma sun zo jiya dan azumi ya kawo kai, daddyn Anayar ya ce sai dai su zo nan su yi azumi, shi ne suka zo, da yake tana cikin motar Lion ne, ga kuma bakin glass ne da motar, sai basu sami damar ganinta ba. Da haka suka wuce airport, suna barin school ɗin sauran sojojinsa shidda take gida suka yi wa makarantar dirar mikiya, dama idan baku manta ba sojoji 12 ya kawo, da Mark 13 sai gateman nasa 14, so gateman da Mark ba'a sanyasu a lissafi, kun ga kenan sojoji 12 ne dai, to dama gateman ba shi da lafiya ɗaya daga cikin sojojin ne ya karɓi aikin nasa wanda shi ne cikon sojoji biyar da ya tafi da su Mark ya cike shidda. Suna zuwa airport jirginsu ya ɗaga dan dama an gama shirya komai, su kuma malaman makarantar sojijin suka tasasu a gaba suka wuce da su, daddy da su Aseef suka shiga cikin motocinsu suka koma gida. After some hours suka yi leading a garin Lagos, ba ɓata lokaci suka nufi bakin ruwa, Rimsha bata ɗauki kaya ba, bata ma san da tafiyar ba, shi kuma ya shirya duk wani abin da zai buƙata akwai uku, sai dai akwati ɗayar tata ce, kayan da suka saya jiya ya shirya mata a ciki, sai ya ɗauki kayanta da ya gani a cikin dressing room nasa dukka ya zuba mata a ciki har da uniform nata, kamar zai shiga bedroom nasu ya kwaso mata wasu, sai kuma ya fasa, ya ɗauki iya waɗan nan dake bedroom ɗin nasa kaf. Brady na biye da shi a bayansa ya saɓi Rimshar a kafaɗa suka shiga dankareren jirgin ruwan. Jirgin ya haɗu haɗuwa ta wuce misali, akwai ɗakuna da dama a ciki, kitchens, toilets da duk wani abin bunata tamkar gida, tsadaddun beds ne a cikin ɗakunan, ko wani ɗaki akwai sofa guda ɗaya a cikinta da table, gadon ma kawai abin kallo ne, nera ta yi kuka a kan jirgin nan, daga Washington DC aka turo mishi ita, ya ce baya son na nan, His excellency ya shirya mishi komai, shi ma fa His excellency baya son tafiyar, kawai ba yanda ya iya da jikan nasa ne dole ya hakura. Bedroom nasa komai a cikinta fari ne tas, sai sheki komai yake yi, duk abubuwan da suke ciki sababbi ne gal a laidansu, gadon nasa wani irin laushi ne da shi, ga wani dankareren bed sheet fari tas dake shinfiɗe a kai, ga wasu kyawawan pillows masu laushi kamar audiga, kai abin dai ba'a magana, tamkar bedroom nasa na gida haka shi ma wannan yake, har da su pool wajen wasanni, kananan mashunan shiga ruwa koda wata matsala ta taso irin ko jirgin ya fashe da sauransu, akwai kananan jirage da mashunan shiga ruwan dan tsirar da rai, akwai su parachute da sauran kayan shiga cikin ruwa kala kala, akwai wuta da engine jirgin ke bawa cikin jirgin kamar wutar nepa, a takaice dai tamkar gida hakan jirgin take,. Saman bed nasa ya shinfiɗeta sai tsalle Brady yake yi, yana leƙa ruwa ta glass ɗin dake cikin ɗakin nasu, bango guda a gefen dama dafaffen glass ne mai karfin gaske da kana iya ganin cikin ruwan da komai da komai dake wajen, nan Brady ya je ya tsaya abinsa. Toilet Lion ya nufa, wanka ya yi tare da fitowa, already sun fara tafiya tun da ya shiga cikin jirgin, sojojinsa kuma sun rarrabune a kowani ɓangare na jirgin, hannunsu na rike da manya manyan jiga jigan makamai masu numfashi, wanda basu saɓa saiti. Bayan ya yi wanka ya fito ne ya shirya cikin pajama tare da fitowa waje ya ce da sojojin nasa su yi wanka su cire kakin jikinsun nan su sanya fararen kaya, okey suka amsa cikin girmamawa. Komawa ciki ya yi sai tashin kamshi yake yi, Mark kuwa tuni ya yi wanka ya shiga kitchen dan ya yi musu girki. A box Lion ya ɗauko daga cikin akwatin kayansa, ya nufo saman bed in da take kwance, a gefenta ya zauna, wayar dake kankame a hannunta ya fara karɓa ya ajiye a gefe guda, da kyar ya iya zaro wayar daga irin kankame shi da ta yi, allurar da zai iya karya karfin powder da Mr Emmanuel ya shaka mata ya fara haɗawa, tana shimfiɗe kamar gawa a saman bed ɗin, wani abu sai suma, duk bala'i tsoron alkura irin tata yau Lion ya yi mata allura a jijiyar hannu lafiya lou. Gabaɗaya ma haushinta yake ji, wayarsa ya ɗauka ya kira Areef a kan yasa a buɗe students ɗin nan sannan a jefar da gawar Mr Emmanuel kada ma a binnesa, a bawa karnika shi. Okey Areef ya amsa da shi. Yana kashe wayar ta fara motsi alamar tana son farkawa, miƙewa ya yi kamar zai bar wajen, sai kuma ya koma ya zauna dan ya san a haukace zata farka, ya zai yi? Ba zai iya barinta ta je ta afka wani waje ba, dole dai ya dawo ya zauna kusa da ita yana jiran ta farka. Juyi ta fara yi tana sambatu kafin ta waro idanunta da suka yi ja tamkar ƴar shaye shaye, wani irin azababben zufa ne ya fara karyo mata, a tsananin razane ta farka tare da yunkurawa zata sauka, alluran yana sanya ta tana ganin abu da girma, komai da girma yake zuwa mata, hakan zai sa duk kankantar abin da ta gani zata ganshi da girma har ta yi ƙoƙarin kauce mishi dan a tunaninta babba ne, a haka zata iya faɗawa wani wajen. Tana ƙoƙarin sauka daga gadon ya rikota, wani irin wahalallen kuma ta saka mishi tana sauke numfashi da sauri sauri, tana ƙoƙarin kwace kanta, nan take wasu zufa suka fara tsatsafo mata daga gefe da gefen kunnenta, yanayin yanda take kukan gwanin ban tausayi, ba shiri ya jawota jikinsa dan kwata kwata bata a hayyacinta, rungume sosai ya yi tana kukan kasa kasa mara sauti. Sun ɗan jima a haka mafin karfin alluran ya fara yin kasa, har lokacin bata dai na wannan wahalallen kukan ba, Brady kuwa tuni ya nufi waje, can wajen Mark ya je dan ya bashi abinci yana jin yunwa. Lokacin guda ta yi shiru kukan ya ɗauke diff, ta kwanta shiru a saman faffasar kirjin nasa idanunta a buɗe kamar mai tunanin wani abin, can kasan maƙoshinsa ya furta "Meesha". Ɗago idanu ta yi tare da saukesu a kan kyakkyawar face nasa, hawayen da suka cika mata idanu ne suka fara zubowa a saman face ɗin nata, sai lokacin ta sami damar furta "Ina Anaya take? Dan Allah yaya Saif ka taimaketa, kada ka bari Mr Emmanuel ya yi mata komai". Tana magana tana shakewa saboda kuka, voice nata ma sam baya fita. Hannu ya kai saman face ɗin nata ya ɗago haɓarta da kyau suna fuskantar juna. "Tana gida kuma bai yi mata komai ba". Ya bata amsa a takaice, cak ta tsaya da kukan nata tare da zaro idanu da suke jawur tana kallo wuyarsa, can kuma kome ta tuna sai ta yunkura zata tashi. Riketa ya yi yana faɗin "Me ya kaiki office nasa?!" Ya yi maganar murya a ɗan kausashe, lafewa ta yi a kirjin nasa tun da ya hanata sauka, murya a dashe ta fara bashi labari tun lokacin da ta dawo school ɗin da abin da ya shiga tsakaninsu da kuma abin da Mark ya yi mishi, daga karshe ta rufe da labarin abin da ya faru yau na ta je office ɗin ne neman Anaya. Iya ɓacin rai ya ji ɓacin rai, sai yaga kamar ma ai bai yi wa Mr Emmanuel hukuncin da ta dace ba, fin haka ya kamata su yi mishi, ciza lallausan laɓɓansa na kasa ya yi yana ɗan shafa kansa. "Meyasa kika yi irin wannan dressing ɗin kika je school?!". Shiru ta ɗan yi tana wasa da butirin rigan jikinsa. "Bazaki bani amsa ba sai na hukunta ki?!" Cikin natsuwa ta gaya mishi dama sun ce zasu yi irin dressing ɗin ne ita da Anaya, shi ne yasa suka yi, amma ta tuba ba zata sake ba. Can kasa kasa ya furta "Without head tight!". Shiru ta yi bata bashi amsa ba, ita da kanta ta san tayi kuskure, ta rasa me ya shiga kanta da har ta fito babu ɗankwalin, zame hannunta daga saman botirin nasa ta yi zuwa saman cikinta dake murɗa mata tamkar mai jin yunwa, ɗan dafe cikin ta yi tana jin ciwon kai. Zuba mata idanu ya yi yana kallonta kamar ya mareta yake ji, dan ya ji haushi ba kaɗan ba, sai dai fa yasan idan ya mareta wlh idan ta sume mishi sai ta fi sati bata tashi ba, hakan yasa ya danne kawai. Tamkar zata yi kuka cikin shagwaɓa ta ce "Yaya Saif ina jin yunwa sosai har cikina yana murɗa mini". Yanda ta yi maganar har cikin ransa ya ji, hakan yasa ya saketa tare da cewa "Jeki ki yi wanka bari Mark ya kawo abinci". Okey ta amsa mishi da shi tare da miƙewa daga jikin nasa, sai dai kuma tana sauka kasan gadon jiri ya ɗebeta ta faɗo saman bed ɗin, ɗan zuba mata idanu ya yi, shi kansa yanzu ya san cewa har zuciyarsa dole akwai wata alaƙa tsakaninsu, shiyasa ya dai'na yaki da zuciyar tasa ma wajen yin ƙoƙarin cireta da tunaninta, ya hakura kawai ya karɓi kaddararsa, mu koma baya kaɗan, abin da ya sanya daren jiya ya dawo cikin ɓacin rai kenan. Ya yi tafiya zuwa Abuja, so tun da ya tafi ya kasa samun sukuni, banda tunaninta babu wani abin da yake yi, ya yi iya kokarinsa wajen ganin ya kawar da tunaninta a cikin ƙwaƙwalwarsa, amma ina abin ya citura, ya wuni bai ganta ba, gabaɗaya ya rasa sukuninsa, hakan ce ta ɓata mishi rai ba kaɗan ba, dan ma Allah yasa yana da hotonta a wayarsa, wannan hoton ne na wayar mutumin can da ya ce a nemo mishi ita, so hoton ce ta rage mishi raɗaɗin kewarta da yake ta fama da shi. Sai dai fa yaki yardawa kansa sonta yake yi, shi dai ya bari a wata alaƙa kawai or tausayi, dan a cewarsa bai ga abin da zai so a wajenta ba, sai dai idan renonta zai yi. Lokacin da ya dawo gida, ya dawo ne da niyar ya taka mata birki a kan kada ya sake ganinta a in da yake, kada ta bari ya sake ganinta a gidan nan, duk yanda zata yi ta yi kada su haɗu, baya son ganinta, amma da ya shigo cikin bedroom nasa ya sameta, sai ya ji ba zai iya aikata hakan ba, shi ne ya wuce ya yi wanka ya yi shirin barci ya kwanta, yana jin yunwa amma yaki cin abinci saboda yana yaki da zuciyarsa wajen cireta, lokacin da ta yi mishi magana sai ya ji ya mance da komai hakan tasa dole ya ci abincin ba dan ya so ba. So yanzu ya fahimci dole akwai wata alaƙa mai karfi a tsakaninsu, ya kuma hakura ya dai'na tilastawa zuciyarsa a kan ta dai'na tunaninta, dan ya gano hakan ba zai yiwu ba, ya yi sake face nata ya zauna a cikin zuciyar tasa ta yanda ba zai ciru ba, shi ne ya hakura ya karɓi kaddararsa. Mu koma kan labarinmu. Miƙewa ya yi ya ɗauketa a kafaɗarsa zuwa cikin toilet ɗin, saman wani kyakkyawan chair ya zaunar da ita kafin ya haɗa mata ruwan wankan da kansa, bayan ya kammala ya sauketa kasa daga saman chair ɗin tare da kwance mata sarin ya cire pil dake jikin wanda ta yafo a kafaɗarta, sannan ya fara warware mata shi, bayan ya cire shi ne ya yi ƙoƙarin cire mata vest ɗin jikinta, daga ta kasa kuma irin short ɗin nan ne masu matse mutun mai jikinsa roba shi ta sanya. Yana damko vest ɗin da nufin ya cire, bata san lokacin da a sukwane ta sanya hannunta ta rike dan kada ya cire ba, ko a jikinsa ya sake mata ya juya ya fice abinsa, saman bed ya haye bayan ya ɗaura sarin nata a saman sofa, wayarsa ya ɗauko ya yi wa Mark text a kan ya kawo musu abinci, yana gama rubutawa ya kwanta yana tunanin irin nasa kaddarar kenan, wai tunanin wannan halitta a cikin zuciyarsa tab, babban bakin ciki shi ma ɗaya shi ne wai wannan ƴar yarinyar, wannan kam renonta kawai zai yi ne ko ya ya? Ya rasa me ma yake tunani a kanta, shi dai face nata kawai ne yake yi mishi yawo a kwakwalwarsa, idan kuma ya yi ƙoƙarin tilastawa kansa rabuwa da tunaninta to fa ba makawa zai cutar da kansa ne a banza, kuma ba dai'na tunanin zai yi ba............ Eh to lallai Lion har yanzu da sauranka ba kaɗan ba, wato har yanzu baka dai'na ganin mata a halitta ba, to dai ga karamar halitta na neman zautar da kai😌🙃 Da gudu Brady ya shigo ya haye jikinsa, Mark ya bashi abinci ya ci ya ƙoshi abinsa, sai murna yake yi, shafa gashinsa ya fara yi, ita kuma tun da ta shiga toilet ɗin sai ta fahimci ba'a toilet na gida take ba, mamaki ne cike fal ranta, haka ya lallaɓa ta karisa wajen baf ɗin wankar, shiga ciki ta yi tare da fara yin wanka. After some minutes Mark ya shigo musu da abinci cikin wasu tsadaddun kayan abinci masu tsananin kyan gaske, akwai table na cin abinci ɗan madaidai ci a cikin ɗakin, sai tashin kamshi abincin yake yi tun ma ba'a buɗe shi ba, a saman table ɗin ya ɗaura musu abincin, yana fita ita ma ta fito daga cikin toilet ɗin daure da towel fari kal mai bala'in kyau da tsada, da yake towel nasa ne yana da ɗan girma, sai ya saukan mata har zuwa gwiwa, tsayuwa ta yi tana tunanin wai a ina ma suke ne? Sam bata lura da glass ɗin dake gefe ba, ƴan waige waige ta fara yi can ta hango trolleys guda uku, ɗago kai da zata yi idanunta suka sauka a kan glass ɗin, baki ta saki tana kallon tabkeken ruwan da suke ciki, a hankali ta ɗaga idanu sama tana kallon saman ɗakin nasu, ta rasa gane a ina suke, tunani ta fara yi ta saka kaya ta shirya sai ta fita waje ta duba, da wannan tunani ta nufi kusa da gadon. Idanunsa a lumshe kamar mai barci, kusa da shi ta zauna cikin natsuwa ta ce "Yaya Saif kayan sakawa". Tana tsoron taɓa mishi trolleys ɗin nasa ne kada ya yi mata faɗa, shiyasa gara ta tambaye shi, dan yanzu ma tasan tabbas ta ɓata mishi rai, taga hakan a face nasa, so tana gudun kara yin wani laifi. Shiru bai amsa ba kuma bai ɗago kai ba, sai Brady ne sarkin gulma ya ɗago kai yana kallonta, harara ta watsa mishi ta tsani karen nan tun da yake takura mata. Haushi ya daka mata shi kuma yana ƙoƙarin tashi daga jikin Lion ɗin dan ya yi kanta, rike shi Lion ɗin ya yi ba tare da ya buɗe idanu ba, can kasan maƙoshinsa ya ce "Me kika yi mishi?" Mamaki ne ya kamata, lallai Brady ya cika munafukin, yanzu dan ta harare shi, shi ne dama zai mike ya yi kanta? Wato har Lion ma ya gane anyi mishi wani abin kenan? Wannan kare akwai ɗan iska, ɗan bala'i ne, abu kamar wani mutun, yasan komai. "Babu abin da nayi mishi fa". Ta faɗa tana kumbura kumatu ita a dole ta ji haushi. Haushi ya kuma dakawa irin kamar karya take yin nan, baki ta saki tana ganin ikon Allah wajen karen nan, shi kuma Lion rungume shi ya yi yana shafa jikinsa alamar lallarashi, harara ta watsa musu dukkansu biyu a cikin zuciyarta tana faɗin "Kasan yanda zaka bi da kare a hankali, kasan yanda zaka rarrashi kare da yake dabba, amma saboda mugunta da zalinci baka san ta yanda zaka yi magana da mutane cikin girmamawa da tausasawa ba, ba abin na sami bulala wlh na zaneka ba, iskancin kawai". A fili kuma shagwaɓe murya ta yi tamkar zata yi kuka ta fara magana "Yaya Saif wlh garin akwai sanyi sosai, kayan sakawa, Allah sanyi nake ji ba kaɗan ba". Mikewa zaune ya yi tare da Bradyn nasa a jikinsa, waro idanuwansa ya yi a kanta, kasa ta yi da kallonta, shi kuma zubawa dogon wuyarta idanu ya yi yana mata wani irin kallo, murza yatsun hannunta ta shiga yi tana wasu ƴan kame kame kamar mara gaskiya, duk kunya ta isheta, bata yi tunanin zai tashi ba, da yake tasan halinsa sai dai ya yi magana daga kwance idanu a rufe, so bata yi tunanin zai tashi ba, shi kuma ya tashi ne ma dan ya sauka kasa ya ci abinci bayan ya gaya mata ga in da kayanta suke kenan, yunwa shi ma yake ji. Ganin bai yi magana bane yasa ta ɗan ɗago kallonta dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa idanu, wani irin azababben kunya ta ji, da sauri ta miƙe dan ta bar wajen ta koma cikin toilet ɗin kawai, hannu yasa ya riƙota a kugu, kasa ta yi da kallonta tana jin kirjinta na bugawa da sauri da sauri, kasa jurewa ya yi har sai da ya jawota jikinsa, kusa da Brady ta kwanta a gefen kirjin nasa kenan, haushi Brady ya fara yi alamar ta tashi mishi a jikinsa, ai jikin Lion nasa ne shi kaɗai, cikin faɗa ya tashi yana daka haushi tare da yin kanta da nufi zai cijeta da gaske, ihu ta kurma tare da rike Lion ɗin kam, zubawa Bradyn idanu ya yi yana kallon haukan da yake yi. Sai da ya ga da gaske zai kai mata cizo ne ya hana shi ta hanyar yi mishi magana, da sauri ya dawo kusa da face nasa yana wani buɗe baki shi ala dole cizo zai yi. Magana Lion ɗin ya yi mishi a cikin kunne ta yadda Rimsha ba zata ji me suka ce ba, wani girgiza ya yi tare da daka tsalle ya diro kasa ya koma saman sofa ya kwanta kamar mai jin barci. Ita kuma ta kankame shi sosai tana kuka kasa kasa, shiru ya yi yana jin kukan nata, har ga Allah bashi da yawan magana, bai ma iya dogon magana ba, so ba zai wani iya magana da ita da baki ba wajen rarrashi, sai kawai ya ɗagota da kyau ya gyara mata kwanciya a kirjin nasa yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi, rike shi ta yi a gefen kafaɗarsa tana sauke ajiyar zuciya, hannu ya kai yana goge mata hawaye. Ganin taki dai'na kukan ne yasa ya ce "Ya isa haka to sarkin rigima". Ya yi maganar kasa kasa, ɗago idanunta ta yi tare da kan nata gabaɗaya daga saman kirjin nasa, ƴan waige waige ta fara yi tana neman Bradyn, zuba mata idanu kawai ya yi tamkar kurma haka ya yi yana kallonta. Ganin Bradyn baya saman bed ɗin ne yasa ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da ɗan ɗagowa dan ta saci kallonsa, 4 eyes suka yi da blue eyes nasa, tana ƙoƙarin kawar da kallonta daga kansa ya sanya hannu ya tallaɓo haɓarta yana mai karewa face nata kallo, runtse idanu ta yi gam. "Meesha". Ya furta kasa kasa, na'am ta amsa mishi amma taki buɗe idanu, shi kuma sleeping eyes ɗin yake son kallah ta kama ta rufe mishi kayansa. Shiru ya yi yana tunanin me zai yi mata ta buɗe idanun nan ya yi ta kallonsu, ranƙwafowa kanta ya yi tare da haɗe gashinsa da nata, wani irin tsorata ta yi, nan take jikinta ya fara kerma, tunani take yi wai me kuma zai yi mata?. Zazzakar muryarsa ne ya katse mata tunani da cewa "Open your eyes". Turo ɗan bakin nan ta yi har sai da ya taɓa nasa lips ɗin da yake fuskokinsu a haɗe, a tsananin shagwaɓe ta ce "Allah yaya Saif ni ba zan iya ganin cikin idanunka ba, sai dai ka rufe ido ni kuma na buɗe". Jikinta na kerma take maganar, kamar yanda jikinta yake kerma kuma haka laɓɓanta suke kerma, ba ƙaramin tsuma shi suka yi ba yanda suke kerman nan, ga shi yanayin yanda take motsasu tana magana, ya ilahi ya lillahi har wani irin shock yake ji a jikinsa, uwa uba ga shagwaɓar da take zuba mishi wajen yin magana, ta gama kwance mishi lissafin ƙwaƙwalwa. Sam bai san time da ya ɗaura lallausan lips nasa a saman.......... E 67-68 Sam bai san time da ya ɗaura lallausan lips nasa a saman tata ba, wani irin azababben daɗi laushin lips nata suka yi mishi, ita kuwa a sukwane ta waro idanunta waje sosai, kai tsaye sai cikin nasa idanu, da yake shi bai san menene kunya ba, tsareta da idanu ya yi tare da capko lips nata na kasa ya fara sha, ita kam babu shiri ta mayar da idamunta ta datse gam tamkar zata fashesu, wani irin harbawa kirjinta yake tamkar zuciyarta zai fasa kirjinta ya fito waje, baiwar Allah sam bata taɓa jin makamancin abin da take ji yau ba, ruɗu da shiga firgici yasa sam bata jin abin da yake yi mata, da alama ma ta fita a hayyacinta bata tare da ya sani ba. Shi kuwa kissing nata yake yi cikin kwanciyar hankali da natsuwa, hannu ɗaya yasa ya tallaɓo wuyarta da kyau, har wani irin azababben shock yake ji daga kansa har tafin ƙafarsa, nan take duk wasu kofofi na feeling a jikinsa da suka shafe shakaru talati a rufe, nan take suka fara buɗewa a yau, gabaɗaya tsikar jikinsa miƙewa ya yi, wani sabon bakon yanayi yake karɓa a jikinsa, shekara talatin bai san da hakan ba sai yau da ko'ina ya buɗe a jikinsa, ba ita kaɗai ce ta fita a hayyacinta ba, har da shi bawan Allah, 30 years yana cutar da rayuwarsa ba tare da ya sani ba, ba wani abin da ya sani fa ce hukunci, kisa da ɗaure fuska sai bada umarni, bacin haka bashi da wani feeling a rayuwarsa, a yau ne ya fahimci waye ne ma shi bakiɗaya. A hankali ya mayar da hannun nasa ta bayan wutarta a in da ya yi sama da shi zuwa cikin gashin kanta ta bayan, cikin natsuwa ya kwanta da ita a jikinsa yana cigaba da shan lips ɗin nata cikin salo da natsuwa, ko motsi ta kasa yi, da alama bata a duniyar nan bakiɗaya, ɗaga ɗayan hannunsa ya yi tare da ɗaura shi a saman mazaunanta zuwa kugunta yana ɗan shafawa a hankali, nan take numfashinsa ya sauya, har lokacin kuma yana kallon face nata sosai, ganin tana hawaye ne yasa cikin natsuwa ya zame bakin nasa daga tata, tare da juyawa da ita ta koma saman gadon ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa. Can kasan maƙoshinsa da kyar ya iya furta "Meesha". Bata amsa ba, kuma bata buɗe idanun nata ba, hawaye ne kawai ke gangaro mata daga idanun nata, sai Allah kaɗai yasan me take tunani Baiwar Allah, hannu ya kai sama face nata yana ɗan taɓa kumatunta, yana ambatar Meesha, sam kamar ba ta a wajen ko motsi ta ki yi. "Why are you crying Meesha?" Ya tambaya yana goge mata hawayen nata, wayarsa ce ta fara ruri alamar shigowar kira, kai kallonsa kan wayar ya yi, Areef ne yake kiransa, kuma video call ne, komawa ya yi ɗan gefe saman pillownsa ya kwanta tare da ɗauko wayar, idanunsa sun yi jawur kamar jini, sai sauke nauyayyar ajiyar zuciya yake yi. Picking call ɗin ya yi dan yasan idan bai ɗauka ba Areef ba zai taɓa barinsa ya yi numfashin da kyau ba, dan ya rinƙa kira kenan ba kakkautawa, ya kiransu ne kuma dan ya ji sun isa Lagos ɗin lafiya dai ko?. Yana ɗauka cool murmushi Areef ɗin ya sakar mishi yana zaune a bedroom ɗin su Rimsha, da alama ya je tsokanar Jehan ne. Assalamu alaikum ya yi wa Lion ɗin yana ɗan daga hannu sama zuwa saitin face nasa a yanda suke gaisuwa kenan, shi ma Lion ɗin amsa mishi sallamar da hakan ya yi. "Ya hanya ya kuma our Queen?". Cewar Areef ɗin, ya yi maganar yana murmushi, sai yanzu Lion ya fara fahimtar dalilin da yasa su Areef suke cewa Rimsha Queen or Gimbiyar TRIPLETS, tabbas idan hasashensa gaskiya ne dalilin shi suke ce mata hakan. "Lion meyake faruwa ne? Me ya sami idanunka? Ina sister take? Baka yi mata hukunci ba ko? Ina fatan ka yi mata afuwa?". Areef ya jera mishi tambayoyi. Ɗan dawo da blue eyes nasa kanta ya yi ta miƙe ta sauko kasan gadon ba tare da ta kalli in da yake ba, tun da ta ji ya yi picking call ta dai'na kukan nata, shi ne ma ta mike ta sauko, toilet ta nufa har lokacin tana hawaye sai dai ba sautin kuka, da kyar take iya ɗaga kafarta saboda gabaɗaya ilahirin jikinta a mace, gaɓoɓin jikinta tamkar an yanke su an rabasu da jijiyar jininta. "Lion lafiya kuwa?" Areef ɗin ya sake katse mishi kallonta da yake yi. Dawo da kallonsa kan wayar ya yi yana faɗin "Kai ba jami'e bane? To sai ka canka ni ka dai'na tambayata yakake? Ina my pleasure?". Kara faɗaɗa murmushin fuskarsa Areef ɗin ya yi kafin ya ce "Kasan dai zan iya ganewan ai, yanzu dai kun isa lafiya? Ina sister?". Jinjina mishi kai ya yi alamar lafiya ba tare da ya yi magana ba. "Ina sister ina kewarta sosai?". Ɗan ɗaure fuska ya yi yana faɗin "Idan kana kewarta ai sai ka nemeta ko? Ai bani zaka tambaya ba tun da baka bani ajiyarta ba". "Sarkin faɗa mai da wukar ni ka nuna mini ita mu gaisa dan Allah, ko dai nima kishi kake yi da ni ne a kanta?". Shiru ya yi bai sake tanka mishi ba, sai magana Areef ɗin yake ta yi mishi ya yi banza da shi, almost 10 mins suka a haka kafin ya ce "Am coming Areef ba sai ka katse kiran ba". Ya kai karshen maganar tare da ajiye wayar a saman bedside drawer ba tare da ya jira amsar Areef ɗin ba ya miƙe zaune tare da zuro kafafunsa kasa ya miƙe tsaye. Toilet ɗin ya nufa dan ya dubata, zaune ya iskota saman chair tana kuka ta kifa kai da gwigwarta, cikin natsuwa ya karisa wajen nata, hannu yasa ya ɗauketa cancak ya nufi waje da ita, sam taki ɗago kanta bare ta buɗe idanunta, ta san cewa shi ne, so sai bata wani damu ba. Saman sofa kusa da Brady ya sauƙeta tare da juyawa ya nufi wajen trolleyns ɗin, jin numfashin Brady yasa ta buɗe idanu, ganinta kusa da shi yasa ta miƙe da gudu ta nufi Lion ɗin, jin gudunta yasa ya juyo, yana juyowa ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa tana kuka mai ɗan sauti, shi sam ya manta ma tana tsoron Bradyn, da yake ya saba da sweetheart ɗin nasa, sai yana ganin kamar kowa ma ya saba da shi kuma baya tsoronsa. Kankame shi sosai ta yi har sai da ta saukar mishi da kasala a jiki, dan yanzu fa duk wasu ƙofofin feeling a jikinsa sun buɗe, abu kaɗan zai iya sanya shi ya ji feeling, dan fa ba'a magana ta wannan fannin oga ne, dama dan bai sani bane bai kuma taɓa kwatantawa ba, shi ne abin baya damunsa, ga kuma yanayin training da aikin da yake yi, shiyasa bashi da feeling ɗin sai yanzu da ita ta zama sanadiyar buɗewa kofofin nasa, yanzu da zarar ta taɓa shi gabaɗaya jikinsa zai amsa ta taɓa shi saɓanin da da zai iya kwana da ita a jikinsa normal ne babu wani abin da zai ji. Shafa kanta ya yi yana kallon kyakkyawan wuyarta, yana son dogon wuyar nan nata, hannu yasa ya ɗan raba jikinsu ba tare da ya yi magana ba, hannunta ya riko zuwa wajen trolleys ɗin, da hannu ya nuna mata nata tare da wucewa zuwa saman bed ɗin. Tsugunnawa ta yi a gaban trolleys ɗin ta kwantar da wanda ya ce shi ne nata, zuge zip ɗin ta yi tare da fara duba kayan sakawa, shi kuma wayar nasa ya koma ya ɗauka suka cigaba da hira da Areef, zuba mishi idanu Areef ɗin ya yi yana kallon tsantsar soyayyar Rimsha dake kwance a cikin idanun nasa, harara ya watsawa Areef ɗin yana faɗin "Kallon fa?". "Kewarka nake yi mana, ba dole na kalle ka ba, yanzu ka yi mini nisa, anya zan iya jurewa kuwa? Anya nima ba zan ɗauki babyna mu bi jirgin ruwan nan ba? Nasan dai zamu sha soyayya kafin mu iso in da kuke". Magana ya gaya mishi a fakaice, da yake shi ya iya magana a dunkule kuma cikin hikima, tabbas yana zargin Lion ɗin ne, dan a yanayin yanda ya kalli kwayar idanunsa tamkar wanda yake tsaka da kwanciya da mace aka katse shi, sannan ya ce yana son ganin Rimsha an haka shi saɓani da idan ya ce yana son ganinta za'a juya mishi camera ya kalleta, ko lokacin da suka je Abuja idan ya kirasu, da ya ce yana son ganinta za'a juya mishi camera, yau kuma ya tambayi ina take yafi baki goma Lion ɗin yaki kula shi, ya san dai akwai wata a kasa, ga shi kuma ɗan bakin Lion ɗin ya yi kamar an tsotse a cewarsa, ya san ɗan uwansa farin sani, ya san yanda lips nasu yake, so bai taɓa ganin lips nasa a haka ba, ji yanda suka kara ja sosai alamar anyi kiss, shi ne yake gaya mishi magana a takaice..........GASKIYA AREEF ƊAN BAIWA NE KUMA ƊAN SAKA IDO BA KAƊAN BA. Shiru dai Lion ɗin bai tanka mishi ba, hankalinsa ma baya kan Areef ɗin sam, yana kanta da take faman shiryawa, cikin toilet ta shiga ta sanya kaya, sai ta fito ta tsaya a wajen trolleys ɗin tana shafa Lotions nata daya kwaso mata, so shi ne hankalin Lion ɗin yake kanta, yana kallon duk motsin da take yi, yanzu ta dai'na kukan da take yi ɗin, da ta shiga toilet ma ta wanke face nata fes kafin ta zo ta shafa Lotion ɗin. Bayan ta kammala ne ta nufi hanyar fita daga ɗakin, taki yarda ta kalli in da yake, wandon jeans baki ta sanya da t-shirt fari tas, kayan sun kamata sosai, da yake curly hairnta yana da tsantsi sosai baya ɗauruwa sai an sanya mishi pil, ita kuma ta duba cikin kayan babu pil ɗin, sai ta saki gashin haka abinta, ta dai gyara shi ya yi kyau. Tamkar a mafarki ta ji zazzakar muryarsa yana faɗin "Come here". Juyowa ta yi ba musu ta nufi gadon, amma sam taki ɗago idanu ta kalle shi, sai kumbura kumatu take yi, yau an yi mata kiss kuma a cewarta ba muharraminta ba, ba mijinta ba, ba komai ba, abin ya kona mata rai har ya sanyata kuka. Da hannu ya nuna mata kusa da shi a kan ta zo ta zauna, ba musu ta hau gadon dan tasan bata isa ta yi mishi musu ba, ko tayi ma wahala zata sha kuma babu wani riba, dan ko tana so ko bata so dole ta yi abin da yake so ya kuma ce ta yi. Ɗan karkato da wayar ya yi zuwa saitin face nata, cool murmushi Areef ɗin ya saki yana faɗin "Our Queen ya da ɓata rai haka? Ko baki son yin magana da ni ne?". Jin muryarsa yasa ta ɗago kai tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya ta saki wani ƙayatattacen murmushi tana rufe fuska da hannunta ga idanunta da suka yi ja saboda kuka. Shiru suka zuba mata idanu su dukkansu biyu, Areef yana mamakin me Lion ya yi mata take ta faman kumbura kumatu haka? Ga idanu sun yi ja alamar ta yi kuka, to me ya yi mata? Tun da ya gano dai ba da shi take fushin ba, shi kuma Lion yana kallon irin sihirtaccen kyau da ta kara da take murmushin. "Yaya Areef where is Jehan?". Kara faɗaɗa murmushin fuskarsa ya yi yana juya mata wayar shi ma, Jehan ɗin tana zaune a bakin gado, fuska a ɗaure kamar kullum, sai turo baki take yi, alamar dai dole Areef ya sanyata zama a wajen ba dan ta so ba. "Jehan dan Allah ina son yin magana dake ne". Ta yi maganar cikin harshen Hausa dan kada su ji me zata faɗa, jin voice nata yasa Jehan ɗin ta ɗago idanu tana kallon wayar, "Wace magana kuma? Faɗi ina jin ki". Ta bata amsa. Miƙa mata wayar Lion ɗin ya yi ya miƙe ya fita waje dan ya yi magana da sojojinsa, cikin sanyin murya ta fara magana tamkar zata yi kuka. "Jehan wlh yaya Saif kiss ya ya mini, kuma ya taɓa mini kirjina ranar, na shiga uku na, ni kuma ban isa in hana shi ba, kuma kin dai san haramun ne ya taɓani ko?" Tana magana tana ruwan hawaye. Saboda iskanci irin na Jehan sai ta ɗaure fuska kamar wata soja tana faɗin "Kin ga Rimsha wlh ban son iskanci, to idan ya yi miki kema ba sai ki yi mishi ba, ai kome ya taɓa miki kema yi mishi kawai zaki yi, wlh ni kada ki sake kawo mini wani zancen banza, waye ma ya ce ki kirani? Lokacin da kike zuwa wajensa a bedroom nasa ku shafe awa huɗu kuna tare duk baki san da haka ba sai yau ko? To ki shafawa kanki ruwan sanyi kawai ki cigaba da yin haramun ɗin". Ta bata amsar tamkar bata san cewa matar aure bace, sam bata nuna mata wani alama da zai nuna hakan ba, idan baku manta ba Areef ya ce kada ta gaya mata in ji daddy, to shi ne bata nuna mata wata alama da zata nuna ita ɗin matarsa ba ce. Goge hawayen fuskarta ta yi tana ƙoƙarin sauka daga gadon dan a cewarta sam Jehan bata sonta, ba zata kula da matsalar ta ba. Muryar Areef ne ya dakatar da ita a in da yake cewa "Our Queen what is the problem? Ni ya kamata ki gayawa ba Jehan ba, rabu da masifaffa mafaɗaciyar nan, menene ya faru kike kuka?". Ganin zata iya shiga wuta ne yasa bata da zaɓi dole ta gaya mishi ko zata sami mafita, wani irin daɗi sosai ya ji, a cikin zuciyarsa ya ce dama daga ganin lips na Lion ai ansan kiss ya yi ɗan rainin wayo, zan yi bayani ne, ya kama ƴar mutane yana shanye mata baki bayan ya gama yi wa babanta rashin mutunci, wlh Lion ina tausaya maka. A zahiri kuma cewa ya yi "Rimsha ki kwantar da hankalinki, Lion fa mijinki ne, uncle ya ce kada na gaya miki, amma tun da an zo wannan gaɓar ba zan iya ɓoye miki ba, amma kada ki nunawa uncle na gaya miki, dan baya son ɗaga miki hankali ne yasa ya ce kada a gaya miki, yana tunanin zaki shiga damuwa idan kika sami labari, bai san cewa kina son Lion ba, ni kuma ban gaya mishi ba, saboda bamu samu lokaci ba, yanzu abin da nake so dake ki yi wa mijinki biyayya, ki kula mana da shi sosai kamar yanda na sanki, zan turomiki video in da aka ɗaura auren naki ma a palo ranar, amma ta wayarki zan turo miki, dan bana son Lion yasan na ɗauki video, to dan haka ki kula, asha soyayya lafiya ƴar soyayya, amma ki rinƙa gayawa baby nima ta rinƙa gaya mini kalaman soyayya, idan ba haka ba, muma jirgin ruwa zamu hau". Cool murmushi ta saki tana ɓoye fuska na rashin kunya, wai ita a dole ta ji kunya, guntun tsaki Jehan ta ja zata mike ta bar wajen, cikin sauri ya rikota yana faɗin "Sister zan kiraki ta wayarki anjuma". Ya kai karshen maganar tare da katse kiran. Wani irin daɗi na wuce misali ta tsinci kanta a ciki, mikewa ta yi ta diro kasa daga saman gadon ta nufi waje, tana ƙoƙarin fita shi kuma yana shigowa, karo suka yi ta ɗan yi baya kaɗan dan ta bashi hanya ya wuce, tsayuwa ya yi yana kare mata kallo, ta yi kyau sosai da ita, wayarsa ta miƙo mishi sai murmushi take yi baki yaki rufuwa tana wani sunkuyar da kai kasa, mamaki yake yi na abin da ya sanya murmushi haka kamar ba ita ce mai zuba kuka yanzu ba, tuna cewa da Areef ta yi waya, yasan fin murmushi ma zata yi in dai Areef ne, karɓar wayar ya yi yana faɗin ta zo ta zuba mishi abincin, okey ta amsa mishi da shi tare da juyawa ta koma cikin bedroom ɗin. Ya fa sha ruwan mamakin ganin yanda take ta uban murmushi kamar ba lafiya ba, abincin ta zuba mishi tare da tura mishi a gabansa, cike da murna ta miƙe da nufin ta fita, calmly ya ce ta zo ta zauna taci abincin mana, ba ɗazun ta ce tana jin yunwa ba? Ina ai murnar sanin shi mijinta ne yasa ta ƙoshi ma, sam ta nemi yunwa ta rasa, ya gudu, ta ƙoshi ta bashi amsa tare da ficewa waje dan ya kalli a ina suke. Ba ƙaramin razana ta yi ba ganin irin tabkeken tekun da suke ciki, ihu ta kurma dan ta razana ba kaɗan ba, ta yi ihun kuma tana runtse idanu tare da ɗaura hannu ta toshe kunnuwanta. Da sauri sojoji biyu suka yi kanta dan a tunaninsu wani abin ne, shi kuwa Lion kai ya ɗaga yana kallon Tv dake manne a cikin ɗakin wanda yake haɗe da camera da zaka iya kallon waje, da farko sam bai yi niyyar tashi ba, amma ganin sojojinsa sun nufeta yasa ya mike ya bar abincin ya nufi wajen. Dai'dai lokacin da ya fito su ma sojojin suka iso wajen, ganin shi yasa suka yi baya dama basu yi tunanin yana kusa bane yasa dole suka nufeta dan su tabbatar da tana lafiya ba wata matsala, a cikin ruwa suke so ko wani lokaci ana iya samun matsa, wata kila wani abin ta gani shiyasa ma suka yi yunkurin kawo mata taimakon gaggawa. Wani irin mugun kallo ya watsa mata wanda ya sanyata haɗa malaman jikinta tare da wucewa sumui sumui ta koma cikin ɗakin nasu, bin bayanta ya yi ya wuce saman bed ya kwanta, cike da tsoro ta ce "Yaya Saif abincin fa? Naga baka ci ko rabi ba". Shiru ya yi bai tanka mata ba, bata san cewa in dai ya fara cin abin baya tashi ba, idan kuma ya tashi to fa ya hakura da abincin kenan sai dai kuma wani lokacin. Ganin bai kulata bane yasa ta tattare kayan abincin tas ta haɗesu waje guda, tana son kwanciya Brady na banci a saman sofa, ita kuma tana tsoron hawa gadon nasa, wayarta ta ɗauka tare da shinfiɗa dadduma a kasa ta zauna ta fara kiran number Akila dan su yi waya, lokacin da kiran ya shigo wayar Akilar, sai shagwaɓa Aseef yake zuba mata a kan shi gaskiya tare zasu yi wanka, idan ba haka ba ba zai ci abinci ba, sai biye mishi take yi ita ma tana zuba mishi shagwaɓa, har mantawa suke yi da duniyar da suke ciki idan suna tare suna zuba shagwaɓar nan tasu, ji suke yi tamkar su cinye juna dan so da kauna. Da farko ya ce bazata ɗauki kiran ba har sai ta amsa mishi da zasu yi wanka tare, zai yi mata ta yi mishi, yana kwance saman bed daga shi sai short da singlet, ita kuma kayansa ne pajama a jikinta, taki sanya wanda ya saya mata a shopping, dan ta ce wlh ba zata iya saka su ba, duk kayan bana mutunci a ciki, daga ƴar pant mai haɗe da bra sai pant mai igiyoyi, ta ce bazata iya sakawa ba, shi kuma ya ce ya fahimci sai ya yi disvirgin nata zasu shirya, hakuri ta rinƙa bashi kafin ya hakura ya kyaleta ɗazun kenan, sai da ma ta haɗa mishi da kukan gaske, sannan ne ya ce ya hakura ya barta sai Lion ya dawo. Ganin kiran Rimsha ne yasa ya barta ta ɗauka, da farko ya hanata, cikin zumuɗi ta ɗauka tare da sanya wayar a hand-free dan tasan mijin nata ba hausa yake ji ba. "Aunty Akila ina wuni". Da fara'a ta amsa da lafiya tare da tambayarta ya angonta, da mamaki ta ce "Aunty Akila kenan kema kin sani?" Jinjina mata kai ta yi tana faɗin "E mana na sani, Heartbeat ya gaya mini, shi ma kuma Yaya Areef ne ya gaya mishi. Ɓoye fuska ta yi kamar tana gaban Akilar tana wani murmushi. "Kai Aunty Akila shi ne ni baki gaya mini bako?" "Ke ban son tsiya ta ina zan gaya miki ɗin? Ke da a gidan nan lokacin da kike nan ba mai ganinki, da kin dawo daga school kin wuce wajen mijin naki, to Allah dai yasa kina kula mana da yayan namu sosai, ba ki zauna ki na yi mishi shirme ba, kin san fa shi yana da wuyar sha'ani kuma ba shi da shi in ji heartbeat". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Aunty Akila ni ai yau ne ma yaya Areef ya gaya mini". "Kai dama ɓoye miki suka yi zasu cuci yayana a banza ko? Lallaima waye da ɗanyen aikin nan kuma?". Kai tsaye ta bata amsa da daddy ne ya ce a ɓoye mata, jin cewa bappanta ne yasa ta waske da cewa. "To shikenan hakan ma bappa ya yi dai'dai, yanzu dai ba kin sani ba? Sai ki ɗaura ɗamarar kula mana da yaya sosai, ki tabbatar kina sanya shi farinciki, kada ki yarda ki bari ya shiga damuwa, kullum ki rinƙa kasancewa kusa da shi, dama ke ba mai son manyan kaya ba ne, so ki rinƙa zuba mishi wankar irin su short zuwa cinyar nan da sauransu, ki tashin kansa, kin san zuciyar sojoji sai kin yi da gaske, dan a bushe zuciyar take sosai, zaki sha wahala kafin ki zuba mata ruwa ta yi laushi, bar ganin misali ace yana sonki, wlh kika yi mishi ba dai'dai ba tsab zai manta da soyayya ya yi ball da ke, so kada ki yi la'akari da cewa dan yana sonki zaki yi mishi wasu abubuwa da zasu ɓata mishi rai, ko ki ce zaki gwada shi, irinsu ba'a gwadasu wlh, idan kika yi kuskuren yin haka kuwa idan baki yi sa'a ba kina iya rasa wani abu na daga halittar ki, sai dai daga baya su dawo suna danasani mara amfani ke sun rigada zuciya ta ɗebesu sun cutar dake, to kamar yanda na sanki da natsuwa, kowani namiji yana son mace mai natsuwa ba mai rawan kai ba, kin fini sanin waye shi, ki sami kamar kwana uku kina yawan zama kusa da shi dan ki karanci abubuwan da ya fi so, da kin karanta shikenan ina mai tabbatar miki yaya Saif ba zai yi miki wahalar Juyowa gabaɗaya gareki ba, ko wani namiji da abin da ya fi so a tattare da mace, iya abin da na sani dai shi ne babu namijin da baya son mace mai shagwaɓa, wannan shagwaɓar shi yake banbanta mace da na miji, ko ya nuna miki a zahiri baya so, wlh a cikin zuciyarsa daɗi yake ji idan kinayi, zaki ga wasu mazan idan kina yin shagwaɓa zasu nuna kamar basu so basu damu ba, wlh suna jin daɗi sosai, akwai wasu kuma matan ne sam basu iya shagwaɓar ba, wata zaki ga sai yana cikin ɓacin rai ta zo tana wani turo mishi baki ita a dole zata yi mishi shagwaɓa, irin haka idan aka samu ɓacin rana sai ki ga ya tsinka mata mari dan ransa a ɓace yake, so komai yana da lokacin da zaki yi wa namiji, yanzu dai ki karanto mana yaya Saif tsab sai musan ta yanda zamu yi maganinsa, babban shawarar da zan baki a nan dai shi ne, kada ki yarda yana saman gado kina saman kujera, mallakinki ne mijinki ne, ato yana sama kina sama, idan da damama ki shige jikin kayanki kina masa wasa, a lokacin zaki iya zuba mishi shagwaɓa son ranki dan yana kwance ne ba abin da yake yi sai tunaninki or tunanin duniya, dan haka ki mantar da shi a wani duniya yake da salon shagwaɓarki, kinga yanzu ku biyu ne, ki rinƙa rikita mishi kwakwalwa da wanka na shegun kaya masu watsa mishi tunaninsa, kin san dai ba sai na gaya miki ba bai taɓa yin soyayya ba, so yanzu fa ko da kin rumgume shi ba zai ce miki komai ba, ba zai wani damu ba koda kin kwanta a jikinsa, ba zai ce miki ki tashi ba, ba kuma zai ɓata rai ba, ba duka ba zagi, haka zalika babu harara, so kawai wani lokaci idan yana tsaye ki haye bayansa ki kwanta, zaki ga sai dai ma ya sanya hannu ya rikoki da kyau, amma fa ki rinƙa fahimtar sai idan baya cikin ɓacin rai zaki yi mishi hakan, bari na gaya miki idan yana cikin ɓacin rai yanda zaki rarrashe kayanki cikin sauki ya sauko ba tare da ya sani ba, ya manta komai ya afka duniyar da kika ja shi ciki, idan yana cikin ɓacin rai ki........." Kwace wayar Aseef ya yi yana mamakin irin surutun da take zubawa babu ko hutawa, ga shi baya jin me take faɗa tun da ba Hausa yake ji ba, sai magana kawai yake ganin tana yi kamar calbi ya tsinke. Kuka ta saka mishi tana faɗin "Kai My shagwaɓati ni ka bani wayata bamu gama ba". Da yake bai katse kiran ba Rimsha tana jinsu duk irin shagwaɓar da Akilar take zubawa. "Ni gaskiya ba zan baki ba, ki huta da maganar haka ya isa mana, tukun nan ma me kike gayawa Mrs Lion ɗin?" Turo baki ta yi tare da yin ƙoƙarin sauka daga gadon, jawota jikinsa ya yi yana faɗin "Haba my sarkin rigima to ina zaki je baki bani kiss ba? Ni fa Allah kuka zan yi miki idan kina yi mini rowar kayana". "Ni my heartbeat ka sakeni mun ɓata, ina tsaka da bawa kanwata lecture ne zaka hanani, so kake ta sha wuya wajen Yaya Saif ko?". Hararar wasa ya wurga mata yana faɗin "Ni ma a nan ba wuya kike bani ba ne? Wato ita ma koya mata yanda zata wahalar mini da my pleasure na kike yi ko? Allah ba zan yarda ba!". Zata sake yin wani magana ya haɗe bakinsu waje guda, dukan wasa ta fara kai mishi a kirjinsa tana ƙoƙarin kwace bakinta, ƴan rigima biyu aka haɗa a wajen ne, sun iya rigima ba kaɗan ba. Jin abin nasu azimun ne yasa Rimsha ta lallaɓa ta katse kiranta cikin rufin asiri tare da miƙewa ta koma saman bed ɗin ta kwanta kusa da shi cike da tsoron abin da zai iya aikata mata, tuni ya jima da yin barci abinsa, hakan ce tasa ta miƙe ta yi kwanciyar rigingine tare da zubawa face nasa idanu, sam bata san shi bashi da nauyin barci ba, bata san duk motsinta yana ji ba. A hankali kamar wata ɓarauniya cikin sanɗo ta kai yatsarta saman lips nasa ta ɗan taɓa, ganin bai motsa bane yasa ta ɗan sake taɓawa, duk yana jinta sai dai barci ya sha kansa ya kasa buɗe idanu. Matso da face nata daf da nasa ta yi, sumbatar lallausan kumatunsa ta yi, shiru bai motsa ba, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake kai ɗan bakin nata saman nasa lallausan lips ɗin, a tunaninta yana zuba barci, sumbatar lallausan laɓɓansa ta so ta yi, sai da ya barta ta kawo ɗan bakin nata zata sumbacesa ya waro dara daran idanunsa waje, gasu sun yi jawur saboda barci, a sukwane ta miƙe dan ta diro kasa daga gadon ta gudu, hannu yasa ya rikota tare da jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, runtse idanunta ta yi tana faɗin ta tuba ba zata sake ba, nadama ta fara yi na menene ma ya kawota wajensa?. (Ni kuwa na ce shagwarar Akila ya kawo ki mana) Hannunsa ɗaya ya ɗaura a saman bayanta tare da mayar da idanunsa ya lumshe, dan barci yake ji over, ganin hakan ba abin da zai yi mata yasa ta kwantar da kanta a saman kirjin nasa tana shaƙar daddaɗar kamshin perfume nasa, a hankali ya cusa hannunsa cikin gashin kanta yana ɗan watsawa idanunsa a lumshe, barci yake ji sosai amma tana neman hana shi yin barcin nasa. A ɓangaren gidan Abbo kuwa, bari mu leka mu dawo, kafin nan wata kila Lion ya yi barci ya taso ko kuma Rimsha ta hana shi yi, bari dai mu je gidan Abbon mu dawo sai muga me ake ciki. A saman sofa Dr Nawid ya kwana, zamu koma baya ne dan jin me ya wakana, bayan ya yi sallar asuba sam bai mayar da barci ba, wanka ya yi tare da yin shirin zuwa office dan baya da bukatar cigaba da jimawa a cikin gidan, idan yana kallon face ɗin Aafia ransa yana kara ɓaci, kishi tana motsawa. Bayan ya kammala shirinsa zai fita ne ta sauko daga saman bed ɗin ta sha gabansa tare da zube gwiwowinta a kasa tana ruwan hawaye tana bashi hakuri, da kyar ya iya magana saboda ɓacin rai. "Hakurin me kuma zaki bani A'afia? Ni tambaya ɗaya nayi miki, ki gaya mini a ina kika kai budurcinki? Kin ki ki bani amsa, to me kuma kike son na sake ce miki?". Cikin kuka ta ce "Zan gaya maka, amma ka zauna dan Allah muyi magana a nutse". Bai musa mata ba ya koma ya zauna a saman sofa yana kallonta, kusa da shi ita ma ta zauna amma a kasa saman carpet, tana kuka kamar ranta zai fita ta fara bashi labarin duk abin da ya faru daga farko har karshe, tunawa ya yi da lokacin da Umminsa ta ce mishi kidnappers sun kama ƴar gidan babarsa Hjy Hadiza, kenan dama Aafia ce? Ya tambayi kansa, yes yasan da zancen an kamata, kuma yasan lokacin da aka karɓota Ummi ta bashi labari, da yake tana yawan bashi labarin ƴan uwanta idan suka zauna, hakan yasa yake da labarinsu duk da bai taɓa zuwa in da suke ba, har cikin ransa ya ji sanyi kuma ya ji tausayinta, amma sai ya ce to ta kira mishi daddyn Jelly bari ya yi magana da shi, ba musu ta kira mishi shi a waya ta bashi. Cikin girmamawa ya gaishe shi kafin ya ɗaura mishi da dalilin da yasa ya kira shi, tabbatar mishi da hakan daddyn Jelly ya yi tare kuma da bashi hakuri na mantawa da suka yi basu gaya mishi ba, har lokacin tana kuka sosai, wani mugun tausayinta ne ya kama shi, katse kiran ya yi bayan sun yi sallama da daddyn, saukowa kasa saman carpet ɗin shi ma ya yi tare da rungumota yana bata hakuri yana kuma rarrashinta, da yasan haka ne ai ba zai yi abin da ya yi mata ba, rungume shi ita ma ta yi tana mai cigaba da kukanta sosai. A cikin kunne ya raɗa mata ta yi kuka sosai dan ta rage ciwon dake cikin zuciyarta, ya yi maganar yana kara rungumeta da kyau. Sai da ya barta ta yi kuka kamar na minti goma sannan ya hau rarrashinta yana faɗin to kukan ya isa haka yanzu kam, ai ta yi na kuɗinta, sam ta kasa dai'na kukan nata, da ya ga dai ba zata dai'na ba sai ya ɗago haɓarta ya haɗe bakinsu waje guda tare da sanya hannunsa yana goge mata hawaye idanun nata, shiru ta yi tana wani irin jan numfashi irin na wanda ta sha kuka ta ƙoshi. Sai da ya yi kissing nata sosai sannan ya saketa tare da ce mata ta shirya ta raka shi office, a zahirin gaskiya gwadata yake son ya je ya yi gudun kar a samu matsala ta wata cuta ko makamancin haka, tun da fyaɗe ne, kuma ba ita kaɗai suka taɓa yi wa ba, suna yi wa mata da yawa, so ba za'a rasa cuta a jikinsu ba, amma sam bai bari ta gane abin da zai yi mata ba kenan, dan baya son ya sake ganinta cikin damuwa, shi yasan ta ƴan da zai bi da ita ya ɗebi jininta ba tare da ta kawo wani tunani a cikin zuciyarta ba. Kasa tashi ta yi saboda duk karfin jikinta ya kare, ga shi yanzu suka tashi barci bata ci komai ba, ta kuma zo ta ci kuka kamar ba gobe. Miƙewa ya yi tare da cire suit dake jikinsa ya ɗauketa cak zuwa cikin toilet ɗin, da kansa ya haɗa mata ruwan wanka tare da cewa zata iya yi ne ko sai ya yi mata?. Da sauri ta ce zata iya yi, murmushi ya yi tare da juyawa ya fita ya bata waje. Wankar ta yi, shi kuma yana fitowa wajen Ummi ya nufa, tana kitchen tana ƙoƙarin haɗa musu breakfast, tayata aikin ya fara yi suna gaisawa, cike da damuwa ta tambaye shi ya jikin Aafia? Da sauki ya bata amsa yana juya mata miyarta, abin gwanin burgewa, yanzu A'afia ta koya mishi shiga kitchen yana taya Ummi aiki, ya zamana ko ita Aafia bata a kitchen ɗin, to shi zai shiga ya taya mahaifiyar tasa, sune ake kira da nice family, Abbo kuwa ya mantar da su shi ma kwata kwata a rayuwarsu, babu wanda ya yi yunkurin nemansa, sun rufe babinsa. Bayan ta fito daga wanka, shiryawa cikin Abaya launin Navy blue da zanen fari ta gaban ta yi, ta sanya ɗan hijabinta na please call me fari a kanta, ta fito waje, a kitchen ta iskosu, cikin girmamawa ta gaishe da Ummi, sai yi mata sannu ya jiki Ummi take yi, satar kallon shi ta yi, kashe mata ido ɗaya ya yi yana yi mata alamar ta amsa kawai, amsawa da lafiya ta ji sauki ta yi tana wani sunkuyar da kai kasa, sosai Ummi ta ji daɗi tare da yi musu fatan alkhari, sai dai ta fahimci Aafia ɗin ta yi kuka, amma da yake tasan ciwon mata, dama anayi ana kuka ne, sai ta mayar ai duk ciwon ne ya saka ta kuka, dan haka sai bata nemi jin ba'asin kukan ba. A tare suka yi aikin suka kammala, Ummi ta yi ta yi da Aafia a kan ta koma cikin bedroom nata ta kwanta, amma ta ce a'a zata yi aiki, shi ma Dr yana son ta yi aikin dan ta ɗan jinjiga jinin jikinta saboda ya sami abin da yake so. Sai karfe 7 dai'dai suka kammala girke girke nasu tare da wucewa palo dan su yi breakfast cikin jin daɗi. Bayan sun kammala suka yi wa Ummi sallama kamar kullum har bakin kofar palo ta rakasu a in da ta yi musu addua'o'i sosai sannan ta dawo cikin, sai sunkuyar da kai kasa Aafia take yi dan kunyarsa take ji sosai, sarai ya lura da hakan shiyasa da ya yi parking na motar tasa a cikin hospital ɗin bai fita ba, ya tsaya ya zuba mata idanu, sai wani ƴan kame kame take yi, daga karshe dai sai ta yi ƙoƙarin buɗe motar ta fito tun da shi bai fita ba. Jawota jikinsa ya yi yana faɗin "Ina zaki je bayan mijinki bai fita ba?" Yana magana yana shafa bayanta, "Office naka zan je". Ta bashi amsa, a hankali ta yi maganar. "Wajen waye zaki je a office ɗin tun da ni ina nan?". Shiru ta yi bata bashi amsa ba, dan bata san me zata ce ba. A'afia, ya ambaci sunanta, na'am ta amsa mishi kasa kasa. "Kiyi hakuri da abin da ya faru kinji? Ki saki jikinki kamar da komai ya wuce, rashin sani ne ya jawo nayi miki irin wasu tambayoyi da yanzu ni kai'na bana son tunasu". Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta bashi hakuri ita ma a kan rashin gaya mishi da bata yi ba. "Zan sami kiss ɗaya kafin mu tafi?". Sam baya ji a jikinsa ta ɗauki wata cuta, shiyasa ma yake wasu abubuwa da ita, kwararren likita ne, so bai ga alamar cuta a tattare da ita ba, kawai dai zai gwada ta saboda tsaro ne, dan kuma tabbatarwa. "Kai yaya Nawid ai ni ban iya kiss ba". "Sai na sake koya miki ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e, hannu ya kai ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna. "Duba idonta a wajen, har kin rame kwana ɗaya, a kan ki na fara son mace siririya fa, da sam basu burgeni, amma yanzu idan kika yi kwalliya sai naga kin fi masu kiba kyau sosai, kwalliya tafi zama a wajen masu jiki irin naki". Juya idanunta sama ta yi tana faɗin "Cigaba da zugani, idan ka tashi ka auro ƴar lukuta, wata kila ma idan nayi kwalliyar daurewa kawai kake yi kana kallona ba dan na burgeka ba". Ƴatsa ɗaya yasa ya buge mata baki yana faɗin "Haka zaki ce?" Shiru ta yi bata kula shi ba. "Oh gimbiyata to yi hakuri na tuba". "Gaskiya ba zan hakura ba sai na rama". Ta faɗa a sanyaye. "To shikenan na yarda rama sai mu tafi". Ya kai karshen maganar tare da ɗago mata bakinsa a kan ta rama, "To ka rufe idanunka". "To ai kema idanunki a buɗe nayi miki". Turo baki ta yi tana faɗin "A'a ni ban yarda ba sai ka rufe idanu". Ba musu ya rufe yana faɗin na rufe, sumbata ta kai mishi a saman bakin nasa tana ƙoƙarin zamewa ya capkota, dama yasan abin da zata yi mishi kenan, ƴar kara ta saka mishi dan bata yi zaton zai kamata ba, shi kuwa tas ya san me zata yi ne ya kuma shirya ta yanda zai rikota ɗin, kissing nata ya fara yi tare da rungumeta sosai a jikinsa, duk abin da suke yi su Bahijja suna sama ta window office nasa suna kallonsu, da yake asibitin hawa uku ne, shi office nasa tana can sama kololuwa, ita kam Bahijja tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu take ji dan bakin ciki, mamaki ma suke yi wai dama Dr ɗan love ne kenan? Ya zuba son ransa a gida sun zo nan ɗin ma ba zai raɓu da matar tasa ba, wannan anyi jarababbe in ji Bahijja................. Ba wani jarababbe kishi kawai take yi dan bata samu ba😌🤣💃 Sai da ya yi kissing na kayansa son ransa kafin ya saketa yana faɗin su je, fitowa ta yi kusan a tare suka fito, rufe motar ya yi ta karɓa mishi jakarsa, shi kuma ya riko hannunta suka nufi ciki, sai kallonsu jama'a suke yi saboda sun yi dace da juna ba kaɗan ba, jini ba wasa ba har wani kama suke yi, sai da ya kusa shiga office ɗin ne su Bahijja suka haɗa malaman jikinsu waje guda, ta koma office nata na bakin kofar shiga office ɗin nasa zuciyarta cike da bakin ciki. Ko da suka zo shiga ko kallon in da take Aafia bata yi ba, sam jininsu bai haɗu ba ko kaɗan, cikin girmamawa ta gaishe da Dr kafin ta ce "Aunty ina kwana" sannunki kawai A'afia ta ce mata sannan suka shige ciki. Dabara ya yi mata ya ɗebi jininta da nufin zai yi mata test a kan wata cuta da ta shigo yanzu, har da ce mata shi ma zai yi wa kansa, gudun ya kawar mata da zargi haka ya ja jininsa a gabanta ba dan zai yi amfani da shi ba, sai dan kawai kada ya sa ta ji wani irin a cikin zuciyarta, ya fi so ta manta da komai. Laboratory ya nufa yana faɗa mata yana zuwa ta jira shi, yana zuwa ya ajiye nasa jinin a gefe ya fara aiki a kan nata dan shi ne a gabansa ba nasa ba, tsab ya gwadata, babu wata cuta dake tattare da ita, hamdala ya yi ga Allah cike da farinciki ya dawo office ɗin nasa, yana zuwa ya rungumeta yana jin tsantsar farinciki, ta yi mamakin irin murnar da yake yi, ita ma sai ta rungume shi suka cigaba da abin da suka saba, yau kuma tun da ta rako shi office ɗin ai shekenan, aiki kuma a lalace zai yi shi. Idan muka koma gidan Lion kuwa, zaune Jehan take a palon sama ita kaɗai tana tunanin duniya, Areef da daddynta sun fita........ E69-70 Idan muka koma gidan Lion kuwa, zaune Jehan take a palon sama ita kaɗai tana tunanin duniya, Areef da daddynta sun fita, Aseef da Akila suna cikin ɗakin, sai zubawa juna shagwaɓa suke yi, Akila ta ce ya kaita wajen Ammienta, shi kuma ya ce sai ta yarda ya yi mata wanka sannan zai kai ta, diramar da suke yi kenan sama da 40 mins, idan ta fara kuka sai ya rarrasheta, idan ta yi shiru ta ce zasu je, sai ya ce a'a sai ta yarda, idan ta sake saka mishi kuka shi ma sai ya saka mata ya kwanta ya ce ya yi fushi, haka zata yi ta aikin rarrashi har ya sake hakura, abin nasu kamar wasan yara, sam yanzu baya kula Areef, yana can yana zuba love ɗin sa, shi ma Areef ɗin bai zauna ba two days, yana faman busy ga tsokanar babyn nasa da yake yi, duk bayan ƴan mintuna sai ya tsokane ta. Sam yau ta ji babu daɗin da bata ji ɗuriyarsa ba, sun jima da fita da daddy, yau bai tsokane ta ba, sai ta ji babu daɗi, tana zaune a palon sama tana shan yoghurt mai sanyi, kamar daga sama ta ga mutun ya hauro saman zai shiga bedroom ɗin Lion, kallo ɗaya ta yi mishi ta kawar da kanta tare da cigaba da abin da take yi. "Who are you?" Muryarsa tamkar saukar aradu haka ta ji shi, ɗago idanu ta yi tana kallon cikin blue eyes nasa babu ko ɗar a tattare da ita, ta sani ko ba'a faɗa mata ba, daga ganin shi tasan daddynsu Areef ne, dan kuwa akwai kamanin, amma da yake ya nuna mata rainin wayo sai ta yi banza da shi kamar bata a wajen, tsawa ya daka mata yana mai sake tambayarta wace ce ita, mikewa ta yi ta ɗauki yogurt nata ta nufi bedroom ɗin daddynta dan a cewarta bata da lokacin bashi amsa, saboda idan baku manta ba, ita mutun ce da idan ka bita a hankali zaku zauna lafiya, amma idan ka nuna mata rainin wayo da izza ko isa, to ko bata yi maka rashin kunya ba, zata mai da kai mahaukaci, sai ka yi ta magana ba zata tanka ba, idan ka cika matsa mata ma, sai ta tashi ta baka waje, idan ƴan rashin mutuncinta suna kusa kuma, sai ta sauke maka kwando kwando kafin ta wuce, to shi dai daddy ya yi sa'a bata yi mishi rashin mutuncin ba, ta ɗauki yogurt nata ta wuce ta bashi waje, saboda tsoron ƴaƴansa ne yasa bata kula shi ba, tasan idan ta yi mishi rashin kunya ko mari ɗaya Areef ya yi mata ba zata tashi ba, sai ta kama kanta. Baki ya buɗe yana ganin ikon Allah, yau yaga mace mai irin halin Lion a cewarsa, banbancin ba yawa, ji har da wani ɗaure fuska kamar wata ubansa, abin ya bashi mamaki, shiru ya yi kamar mai tunanin wani abin. Ya jima tsaye a wajen kafin ya shige cikin bedroom ɗin na Lion, dan yasan shi dai yanzu ba yanda zai yi da bakaƙen fatan nan, tun da Lion ya ce ba zasu bar gidan ba, to zaman lafiyarsa kawai ya fita harkarsu, idan ya matsa to wlh zai ja wa kansa matsalar da ba zai iya ɗauka ba, shi ne ya haɗa malaman jikinsa baya shiga harkarsu daddyn Rimshan sam, sai dai yana nan yana tunanin ta yanda zai raba ƴaƴan nasa da waƴan nan mutane wato bakaken fata. Da misalin karfe 8 na dare, daddyn Rimsha, Areef, da kuma Jehan suna zauna a palon sama suna hira, sun dawo daga unguwar da suka je, gidan daddy na nan Kadunan suka je suka duba, dan Areef ya ce da Tga idan zai zo ya zo mishi da takardan yarjejeniyar da Lion da daddy suka yi akan lallai daddy zai yi shekaru huɗu a karkashin Lion ɗin, so ya kawo mishi takardan da hannunsa zai yage ta kafin Lion ɗin ya dawo, domin ya samawa daddyn ƴanci, ya gaji da kallon abin da Lion yake yi mishi, shi ne daddyn ya ce to zai koma gidansa na nan Kadunar, amma ya yi wa Areef alkawarin za'a ɗaura aurensa da Jehan kafin ya bar gidan, so zai tafi ya barta a nan, hakan tasa Areef ɗin ya ji daɗi ba kaɗan ba, to shi ne suka je ganin gidan suka kuma saka masu decoration na gida suka zo suka gyara komai, a ka wanke ko'ina da ina. Areef da daddy sai hira suke yi, ita kuma Jehan tana kallon India film a Tv, Areef ya tada kai da cinyar daddy suna zuba hira kamar wasu abokai, a hankali daddyn ya kwantar mishi da kansa a saman sofa tare da mikewa yana faɗin yana zuwa bari ya yi wanka ya yi shirin barci dan barci yake ji, okey Areef ɗin ya amsa mishi da shi yana hararar Jehan dake kallon shi, ita ma hararar shi ta yi tana turo baki, motsa laɓɓansa a hankali ya yi ya furta zan kamaki ne, kallon up and down ta yi mishi tare da murguɗa baki, shi dai daddy sa kai ya yi ya wuce abinsa, dan shi diramar tasu ma wlh daɗi take yi mishi, abin yana burge shi. Daddyn yana barin waje suka mai da hankalinsu gabaɗayansu a kan Tv, dama ita already kallon take yi, shi kuma tafiyar daddyn yasa dole ya yi kallo lafin ya dawo, dan yasan ko ya yi mata magana ba zata amsa ba, to ba sai ma ya yi mata ba, su yi kallo kawai dan bai jin tsokanar yau. Kamar da ga sama aka hasko masoyan Indiyawa suna kissing na juna a cikin Tvn, juyowa ya yi yana kallonta yayin da ita ma ta juyo ta saci kallonsa, tamkar ta nitse cikin kasa saboda kunya, gera ɗaya ya ɗaga mata alamar yane, kallon sama da kasa ta yi mishi tare da kawar da kanta gefe dan bata son ma ta sake kallon Tvn tun da sun sako abin kunya, dama ba'ayi hakan bama ya ta kare da ɗan iskan nan a cewarta. Zazzaƙar muryarsa ne ya katse ta da cewa "In zo nima ki yi mini?". A sukwane ta dawo da kallonta kan nasa, me zata yi mishi kenan? Ta tambayi katan, tana tsaka da tunani sai ganin shi ta yi ta miƙe ya nufota yana faɗin "Kiss mana, shi zaki yi mini". Ai bata san lokacin da ta mike da gudu ta bi bayan daddynta ba, sai dai ina bata kai ga shiga ɗakin daddyn ba ya sha gabanta yana faɗin "Allah ba zaki je waken uncle ba, sai dai ki tafi bedroom naki ko kuma ki yi mini kiss". Tamkar ta shakesa haka take ji saboda haushi. "Amma baby wlh lips naki zai yi daɗin kiss ba kaɗan ba, bari dai na gwada mu ji". Yana magana ya matsowa kusa da ita, a sukawane ta juya ta shige cikin bedroom nasu tana ɗaure fuska, murmushi ya yi yana faɗin "Ba yanzu ba, amma gaba tabbas zan yi hakan, yanzu dai tsona ce kawai". Ya kai karshen maganar tare da nufar ɗakin daddyn, dan basu gama hira ba, yana shiga ya haye saman bed ya kwanta, ita ma saman gadonta ta haye ta kwanta tana tunanin idan anjima kaɗan ta yi in Areef ɗin ya koma bedroom nasa zata je ta gayawa daddy wlh ya rabata da Areef ko kuma ta bar gidan nan. Da wannan tunani ta miƙe ta yi wanka ta shirya cikin kayan barci riga da wando, ta yi kyau sosai na wuce misali, sai zuba kamshi take yi, dama kunsanta akwai ta da son kamshi kuma bata son datti ko kaɗan, saman bed nata ta kwanta har karfe 11 na dare, sannan ta miƙe ta lallaɓo a hankali kamar wata ɓarauniya ta nufi bedroom ɗin na daddy. Tazo zata shiga ɗakin kenan shi kuma yana fitowa, a bakin kofa suka yi karo, bata kula shi ba, ta sa kai zata wuce cikin ɗakin, hannu yasa ya tare kofar ɗakin tare da gyara tsayuwarsa a wajen ya tare mata hanya. Idan da sabo ta saba da iskancinsa dan haka sai ta ce "Malam ka bani hanya zan wuce ne". Tsare ta ya yi da idanuwan nan nasa, ya wani kashe su kamar wanda ya yi shaye shaye, sai mata wani irin mayen kallon yake yi from head to toe ba tare da ya yi magana ba. Ganin ba shi da niyar yin magana kuma bashi da niyar bata hanya ne yasa ta ce "Wai kai dan Allah me na maka ne kake addabama rayuwata?". Sai da ya ɗauki good 2mins yana ta mata wani shegen kallon kafin ya matso kusa da ita sosai, murya kasa kasa ya fara magana "Saboda kin ki kice mini I love you, sannan kuma kin ki ki fara kirana Babyn baby, dan haka ba zan daina takura miki ba". Da wani irin kallon banza ta juyo da kallonta kanshi, ji tayi kamar ta wanka wa lallausan kumatun nan nasa mari, ga kumatun ya yi jawur luwai luwai zai yi daɗin mari, amma ba zata iya ba, a zahirin gaskiya daurewa take yi kawai tana magana da shi, amma bala'in tsoronsa take ji kamar zata mutu daga ta ciki, ga bala'in kwarjinin da yake yi mata. Jin ta yi shiru ne ya sa ya sake matsowa da ɗan bakin nan nasa saitin kunnanta kamar mai raɗa. "Baby kin girma daidai yanda nake so fa, komai ya cika daidai, kinga twins ball's ɗin nan naki, daidai haka nake so, sun isheni". Da sauri ta ɗago tana kallon shi, kashe mata ido ɗaya ya yi yana wani ɗaga gera guda, ɗan juyawa ta yi ta kalli kofar ɗakin daddyn, shi ko kunyar daddy ya ji abin da yake faɗa ma baya ji. Ganin tana kallon ɗakin ne yasa ya kara matsowa kusa da ita sosai, ta yanda har suna iya juyo numfashin juna "Daddy ya san ke matata ce ai, ya bani ke, dan haka normal ne, yanzu dai bani hot kiss kamar wanda muka gani ɗazun a Tv, zan je na kira Lion mu ga juna daga nan nayi barci" Harara ta banka mishi tare da faɗin "Bani hanya na wuce!". Dafe saitin zuciyarsa ya yi yana faɗin "Wash Allah kin kashe ni da kika yi maganar nan, wai ni baby me nayi miki ne da baki so na?". A kule ta ce "Saboda kai ɗan iska ne, kuma wlh ko ka bani hanya na wuce, ko kuma na yi maka ihun kwarto a tsakar daren nan". Wani irin cool murmushi ya saki yana shafa kansa ya ce "Good idea kin ga daga nan sai a ɗaura mana aure, na yi mata a sama, amma shawaran nan ta yi bari ki ga na yi miki kwartancin ma da wuri yadda za'a fi yin saurin ɗaura aure". Ya kai karshen maganar yana jawota jikinsa. Kware baki ta yi zata yi ihu da gaske, cikin sauri ya toshe mata bakin da hannunsa ɗaya, dan baya son ta tashi daddy daga barci, bawan Allah ya jima da yin barci abinsa. Kasa kasa ya ce "Idan kika yi ihu Allah sai na yi maganinki a cikin daren nan, tukunnan ma me ya fito da ke? Kuma me zaki je yi wajen uncle?". Ya kai karshen maganar tare da zame hannunsa daga bakin nata. Wani irin yanayi take ji yana ratsata, namiji bai taɓa taɓa jikinta ba, sai wannan ɗan bala'in a cewarta, sai kokarin kwace kanta take yi, shi kuwa da hannu ɗaya ya riƙe kugunta ya mannata da kirjinsa, ta kasa kwacewa. "Ki natsu ki gaya mini me ya fito dake? Kuma me zaki je yi wajen uncle?". Ta san halinshi sarai idan bata ba shi amsa ba to ko kwana za su yi a nan ba zai sake ta ba, hakan yasa ta turo baki rai a ɓace ta fara magana. "Ni da daddyna shi ne kake tambayar me zan je yi a wajen shi? To ganin shi zan je yi" girgiza kai ya yi yana ɗan raba jikinsa da nata, dan ta fara jefa shi cikin yanayi. "No correct amsar abin da ya fito da ke zaki gaya mani, idan ba haka ba yau a cikin bedroom na zaki kwana". Kamar ta shakesa saboda haushi, kumatu a kunbure ta ce "Karar ka zan kai mashi, dan ya rabani da kai, ka addabawa rayuwata, na ga ji". Sake ta ya yi yana murmushi ya ce "Au haka ne dama? Lallai kice na kara takura miki kenan? Tom gara da mum tana nan idan kika kaimata karata shi ne wata kila zan ɗan barki ki huta na kwana biyu, amma uncle kam kara hura wuta zai yi, kisani daga yau kullun da safe sai kin zo bedroomna na ganki tukunnan kafin ki ga kowa, nine mutun na farko da za ki fara gani kafin kowa, kin ji na gaya miki, sannan ina miki albishir da ki sani takura yanzu na fara yi miki ba fashi, daga yanzu sabbin salo zan fitar in ga mai kwatarki my babyn babynta". Ya kai karshen maganar yana ɗaga gera ɗaya. Kallon sama da kasa ta yi mishi rai a ɓace ta ce "Allah zai saka mini kuma wlh ban....." Bai bari ta karisa ba ya yi sauri sake jawota jikinsa yana faɗin "Kina karisawa sai na yi miki abin muka yi ido huɗu dake da ni a Tv ɗazun". Tuna abin yasa ta yi sauri kama bakinta ta yi shiru ba ta yi magana ba, zuba mata wayan nan idanun nasa ya yi yana kallon face nata. "Jehan why are you so beautiful like my uncle? Gaskiya kina caza mini kai sosai, anytime tunanin ki ne kawai yake zuwa mani cikin brain ɗina, seriously i really love you, ni na gaji da abin da kike yi mini, ina son ki gaya mini why baki so na? Why kika tsani gani na? Me na yi miki? Ko akwai irin type na mijin da kike so ne? Please tell me the reason, idan ba haka ba zaki cutar da ni sosai". Karo na farko da ya fara yi mata magana cikin natsuwa da kuma serious akan abu, babu tsokana ko muryar raha a cikin maganar, in a serious matter ya yi maganar, hakan yasa ta ɗago tana kallon fuskarsa, shi ma ita yake kallo babu ko kyaftawa, alamar amsa kawai yake jira. "I don't know the reason why, but ba kai kaɗai ba, ni bana son kowa, banyarda da soyayya ba". Matso da fuskarsa ya yi daf da tata har suna iya jiyo numfashin juna, kwata kwata sun mance ma a kofar ɗakin daddy suke wannan diramar ta su. Ƙoƙarin kawar da kanta gefe ta yi, amma sai ya hanata ta hanyar haɗe goshinsa da nata, hancinsu yana gogan na juna. "Zaki yarda mu yi wani game da ke?" Ya yi maganar kamar mai yin raɗa, cikin sanyin murya. Zubawa laullausan laɓɓansa idanu ta yi tana kallon yanda yake motsasu idan zai yi magana, gasu jawur kamar ya sanya jan jan baki, ga laushi kamar me, sai sheki suke yi tamkar an sanya musu lips balm. "Kiyi magana mana!". Ba ƙaramin tafiya da imaninta lips nasa suka yi ba, abin ya ɗauki hakankalinta, "Jehan why kika yi shiru? Talk now, zaki yarda mu yi game?". Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a bata so, raba fuskokin nasu ya yi tare da ɗan ja baya yana faɗin "Okey jeki ki kwanta ki kyale uncle ya yi barci, da safe sai ki zo ku yi magana ko?". A wannan karon ma a nutse da ainahin voice nasa ya yi mata magana. Juyawa ta yi ba musu ta nufi bedroom ɗin nata, har ta kusa shiga sai kuma ta ɗan juyo dan ta saci kallonsa, har cikin zuciyarta take jin daɗin kallon kyakkywar face nasa. Tana juyowa suka haɗa idanu, dan kuwa ita ya tsare da kallo. Cikin sauri ta juya tare da karisa shiga cikin bedroom ɗin nasu, cool murmushi shi kuma ya saki tare da wucewa nashi bedroom ɗin yana mai jin tsantsar kaunarta a cikin zuciyarsa, ƴar diramarsa, har kewarsa ta yi yau, ya fahimci matsalarta a yanzu, ba wai bata son shi ba ne, no bata san menene ma soyayyar ba, bata taɓa yi ba, bata san ya ake yi ba, bata da wasa da dariya bare wani ya iya gane idan ta shiga feeling na soyayya, ba wanda yake gane ina ta dosa saboda rashin sakewa da mutane da bata yi, hakan yasa yake yawan tsokanarta dan ta saba da wasa da dariya, so yake yi ya canza mata rayuwar da ta taso a kanta, wannan shi ne dalilin tsokanarta da yake yawan yi. A ɓangaren ƴan rigima kuwa, sai bayan sun yi sallar isha sun ci abinci ne Aseef ya kira Lion Video call dan su ga juna, yau dai tare suka ciyar da juna abinci shi da rigimatin nasa, a baki ya rinƙa bata ita ma tana bashi, yau sam sun ƙi zuwa dining table su ci abincin, su Areef ne kawai suka haɗu da su daddy aka haɗe gabaɗaya a table, shi Aseef ya ce a ɗaki zasu ci dan a saman table ɗin Akila zata bashi kunya, zata ki yarda ta karɓi abinci a baki idan ya bata, zata ce tana jin kunyar daddy alhalin shi kuma daddyn bai san kunya ba, su ba ruwansu ko kiss Aseef zai yi mata a wajen ma, kai idan ta kama ma abin da ya fi kiss ma su yi ba abin da ya dami su daddy, amma ita ta kafe sam kunyar daddy take ji, shi ne ya ɗauko musu abincin zuwa bedroom ɗin nasu, bayan sunci sai suka yi wanka suka yi shirin kwanciya, yau dai shi ya zaɓa mata kayan barcin da yake son ta saka mishi, ba dan ta so ba ta karɓa sai dan ba zata iya cigaba da yin musu da shi a koda yaushe ba. Wasu shegun riga ne mai ƙaramin hannu zuwa cibiya da ƴar wando zuwa cinya, jikin kayan suna da tsantsi sosai, sai yabawa kyan da ta yi yake ta yi har suka haye gado ya kira Lion don su gaisa, suna tsaka da hira da Lion ɗin ne ya ce mata ta zo su gaisa, ganin kayan jikinta ta yi kafin ya jawo bargo zuwa kirjinta, sannan ya juyo da wayar kanta, good evening ta ce mishi cikin girmamawa, amsa ɗaya ya bata kafin ya ce da Aseef ɗin good night, bai jira amsarsu ba ya katse kiran, murmushi Aseef ɗin ya saki yana faɗin "My rigimati Allah kin ciri tuta da har Lion ya amsa miki gaisuwa, dama da gangan na ce kizo ku gaisa dan naga shin zai amsawa matata ne ko ba zai amsa ba, amma kuma kin saka shi ya ce mini good night bamu gama waya ba, ban fa gaji da ganin shi ba". Turo bari ta yi tana faɗin "Allah Heartbeat kai ko, yanzu haka dama kake zama ka yi ta zubawa yaya Saif shagwaɓa ko? Ji yanda ka rinƙa yi mishi magana kamar da ni kake magana". Kasa kasa ya ce mata "To ai ni autansu ne, kuma ni pleasure su ne, dole su biye mini yanda nake so". "To ai yanzu yaya Saif zai dai'na shagwaɓaka tun da shi ma ya samu mai shagwaɓa shi". Murmushi ya yi yana faɗin "Ai ni har abada ba zasu dai'na shagwaɓa ni ba, matsayin sister daban, matsayi na daban kin gane ai?". Zata sake yin magana ya jawota jikinsa kasa kasa kamar mai raɗa ya fara magana "Ki bar maganarsu Lion, yanzu maganata zaki yi, me zaki bani yau kuma?" "Me kake so?" Ta yi maganar a shagwaɓe, a kunne ya raɗa mata abin da yake so ɗin, zaro idanu ta yi zata yi magana ya yi maza ya haɗe bakinsu tare da jan bargon gabaɗaya ya rufesu har kansu. ASUBA TA GARI. A ɓangaren Lion kuwa, barci ya koma saboda barcin ne a idanunsa sosai, sai shakar daddaɗar kamshin perfume nasa take yi ta lafe a saman kirjin nasa har ita ma barci ya ɗauketa, basu suka farka ba sai karfe biyu, ita ce ta fara farkawa, a hankali ta waro idanunta waje, da yake ta sha barci dai idanun suka yi ja, zubawa kyakkywar fuskarsa idanu ta yi tana kallon yanda yake sauke numfashi a hankali hankali cikin natsuwa. Cikin sanɗa ta lallaɓa zata sauka daga jikin nasa, cap ya rikota domin kuwa tun farkawarta shi ma ya farka, a hankali ya waro idanuwansa a saman face nata, runtse ido ta yi tana sakin cool murmushin da bata san dalilin yin shi ba, haka kawai ta ji murmushin ya zo mata. Sakinta ya yi tare da yunkurawa zai miƙe, sauka ta yi daga jikin nasa ta diro kasa daga saman gadon ta nufi toilet, wayarsa ya ɗauko dan ya duba time, 2:02pm, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya zuro kafafunsa kasa, duk jikinsa a mace, toilet ɗin shi ma ya nufa dan ya yi wanka tare da ɗauro alwala dan gabatar da sallar azahar. Kai tsaye ya shige cikin toilet ɗin, wani ihu ta kurma tana daga cikin baf ɗin wanka, sam bata yi zaton zai shigo ba, ko da ya shigo kuma bai bi ta kanta ba, bai ma san tana cikin baf ɗin ba sai da ta kurma ihun ne ya kai kallonsa wajen, ɗan zuba mata idanu ya yi ta takure jiki waje guda ita a dole ta ɓoye jikinta, girgiza kai kawai ya yi tare da wucewa ya ɗauki brush, dan shi mamaki ma yarinyar nan take bashi, ko me zata ɓoye oho mata. Ta kasa cigaba da yin wankar tata, shi kuma bai sake bi ta kanta ba ya yi brush ya kammala sannan ya ɗauko wani baf na wanka irin tafi da gidan kannan, baf ɗin yana da bala'in kyau sosai tamkar ainahin baf yake, sake baki ta yi tana kallon ikon Allah, tunanin take yi a cikin zuciyarta ba dai wanka zai yi ba shi ma?. Bata ankara ba tana can tana tunani sai ta ga ya haɗa ruwa yana cire kayan jikinsa, shi ko ajikinsa ba abin da ya damesa, dama ita ce ta san kunya, shi dai bai san wannan ba. Ganin da gaske ya cire riga ai bata san lokacin data zunduma ihu ta datse idanunta gam ba, juyowa ya yi yana kallonta, tunani yake yi wai wannan yarinyar bata da matsala a cikin ƙwaƙwalwarta kuwa?. Ihunta ya sanya Brady shigowa cikin toilet ɗin da gudu yana wani girgiza, jikin Lion ɗin ya haye yana son jin me ake wa ihu, rungumesa ya yi suka nufi wajen baf ɗin nata dan su duba ko lafiya take ihu haka. Wani ihun ta sake kurmawa ganin suna nufota, sam bai tsaya da tafiyar da yake yi ba har ya isa in da take ɗin, ta datse idanu gam ta kuma ɓoye tula tulanta da hannu ta dungule jiki waje guda, cikin ruwan ya zubawa idanu dan ya ga ko wani abin ne a ciki, ganin ba komai ne yasa ya dawo da kallonsa kanta, "Are you okey kuwa?". Ya faɗa a sanyaye. Cikin kuka ta ce "Ni dan Allah yaya Saif ka tafi". Juyawa ya yi abinsa Brady na makale a kirjinsa, komawa ya yi wajen baf ɗin wankansa, tare da cewa Brady ya sauka mishi a jiki bari ya yi wanka lokacin sallah na wucewa, hannu tasa ta kunna ruwa mai sanyi dan ya cika mata baf ɗin sosai ta lume a ciki. Bai sake bi ta kanta ba ya cire singlet nasa, ganin ainahin kyakkyawa kuma kakkarfan suran jikinsa a waje yasa bata san lokacin da ta ce "Yaya Saif dan Allah ka bari na gama wanka ka ji ko? Wlh zan iya mutu idan ka ce zaka yi wanka ina nan". Tana magana idanunta a rufe ruf, shi kam yana mamaki har yana tunanin wlh Rimsha bata da lafiya, dole a duba lafiyar ƙwaƙwalwarta, bai san cewa kunya take ji ba, ita akwai kunya ta jinin fulanin Bauchi wato Dr Salman a jikinta, ga kuma mummynta mutanen Maiduguri, ita ba irin shi ba ce, tana da kunya sosai, ba zata iya ganin wannan ɗanyen aiki ba. Da farko kamar ba zai fasa abin da ya yi niya ba, jin tana kuka kasa kasa mai tsuma zuciyar mai sauraro ne yasa ya fasa yin wankar, yau karo na farko a rayuwarsa da ya yi niyar yin abu kuma ya fasa, yau ita ce rana ta farko da aka ce mishi ba'a son abu kuma bai aikata ba, idan baku manta ba, duk abin da ba'a so shi yake aikatawa, to yau dai Rimsha ta ce bata so kuma ya hakura bai aikata ba, tun da yake a rayuwarsa shekaru talatin cikin talatin da ɗaya bai taɓa ja baya a maganarsa ba sai yau ɗin, babbar magana...... E lallai mata sarakuna ne, mace sarauniya ce, yau dai akan mace ya canza ra'ayi, a kan mace ya fasa yin abin da ya yi niya har ma ya fara aikatawa, ina daddynsa? Ina su Areef? Yau su zo suga ikon Allah, yau da daddynsa na nan sai ya ce wannan ba Romeonsa ba ne, an canza shi ne. Waje ya nufa, yana fitowa kuma ya bar ɗakin bakiɗaya, ita kuma yana fita ta fara wanka da saur sauri kamar ya ce mata zai dawo ne. Bayan ta kammala ta ɗauro towel nasa ta fito waje, sauri sauri ta shafa Lotions nata tare da sanya perfume, wani ɗan ƙaramin wandon jeans ta ɗauko wanda ba zai wuce zuwa gwiwarta ba, sai ƴar riga ce mara nauyi, har lokacin bai dawo ɗakin ba, shiryawa ta yi cikin kayan nata sannan ta fara duba cikin akwaitin babu hijabi sam, kamar zata yi kuka ta ɗauko wani sabon bed sheet daga cikin drawer dake cikin ɗakin ta rufe jikinta ta yi sallah, bayan ta kammala ne ta zauna tana addu'a tare da yi wa iyayenta fatan Allah ya tsaresu a duk in da suke, haka shi ma Lion ta yi mishi addu'a sosai kafin ta miƙe tare da naɗe bed sheet ɗin ta mayar cikin drawer. Saman sofa ta zauna tana tunanin ko ta kira number Anaya ne ta ji ya take, da wannan tunani ta ɗauko wayarta da sauri ta fara kiran number, amma ina a kashe dan kuwa a office ɗin Mr Emmanuel ta baro wayar, tamkar zata yi kuka ta mayar da wayar tata ta ajiye. Tana ajiyewa ta fara jin saukar ruwan sama, har lokacin Lion bai dawo cikin ɗakin ba, wani irin tsallen murna ta yi tare da fitowa waje da gudu, sam ita ta manta da dressing dake jikinta, kowa yasan tsakanin Rimsha da ruwan sama akwai amana, kanta babu ɗankwali ga wandon jikinta zuwa iya gwiwa, sannan shi ma rigar tata mai ƙaramin hannu ne a iya kafaɗa, ga shi ba shi da wani kaurin kirki, kuma ba laifinta bane, irin kayan ne kawai a cikin akwatin, dan su ta ɗauko a wajen shopping da suka je da su Areef, shi kuma ya kwasa ya zuba mata kawai ba tare da ya san ma wasu irin kaya ba ne. Cikin ruwan ta shiga har da leko da kanta ta cikin tekun tana yi wa ruwan sama magana kamar wata zararriya, kasan jirgin cikin ruwan kenan ta rinƙa leƙo kanta kamar zata tafi ta faɗa cikin tekun ta kai ta kai, ga ruwan saman yana jiƙata, sai murna take yi tana dariya kamar wata zautatciya. Almost 10 mins tana a haka, kamar daga ta ji daddaɗar kamshin perfume nasa, a hanzarce ta juyo dan ta kalli kofar ɗakinsu, caraf suka yi 4 eyes yana tsaye a bayanta yana kallonta, ga ruwan sama shi ma yana jiƙa shi, ƴar waige waige ta fara yi, gabaɗaya sojojin nasa da ta fito ta samu a wajen basu nan, tsoron yanda ta ga fuskarsa ne ya kamata, sam babu alamar wasa a tattare da shi, ya haɗe gerar sama da ta kasa alamar yana cikin ɓacin rai. Takowa ya yi ya nufota, baya baya ta fara yi jikinta na kerma, ta sha jinin jikinta, ya ji haushi sosai lokacin da ya fito ya sameta tana wanka a cikin ruwan ga kuma sojojinsa a tsaye, duk da cewa aikinsu kawai suke yi basu bi ta kanta ba, amma abin ya bakanta mishi rai, dole ya yi mata hukunci dan gobe kada ta kara. Sai da ta kai karshen jirgin ta gefe ne ta tsaya tana zare idanu, ta yi narai narai da idanun kamar zata yi kuka. Yana zuwa wajen ya damko gashin kanta tare da janta zuwa wajen matakalar shiga jirgin, sauke matakalar kasa ya yi izuwa cikin ruwan, taku biyu ya yi a saman step ɗin, sai da ya je bakin ruwan, sannan ya juyar da ita tare da turata cikin ruwan, bata kai ga faɗawa ba cikin sauri ya riko hannunta kamar zata faɗa cikin tekun, wani azababben ihu ta kurma tare da kankame hannunsa da karfe, kasa kasa ya ce "Ba ruwa kike so ba? Ai sai ki shi ga". Girgiza mishi kai ta fara yi tana kuka kamar ranta zai fita, ƴar kaniya ta ga mutuwa muraranta. Sake hannun nata ya yi dan ta faɗa cikin tekun yana faɗin ta sake shi ta faɗa ciki sai ta yi wankan da kyau, ina ai rike shi ta yi gam tana ihu kamar maƙoshinta zai ɓalle, jin ihunta yasa Mark fitowa daga cikin bedroom nasa, ganin ita da Lion ɗin ne yasa ya koma cikin sanɗa dan ma kada ogan nasa ya gan shi. Har cikin ransa ta bashi tausayi yanda take ihu ta kuma ƙanƙame shi kamar zata shige jikin hannun nasa, ga kuma ruwan sama na sauka a saman face nata, amma idan ya tuna yanda ta fito tana wanka ga sojojinsa a wajen sai ya ji wani kululun bakin ciki a cikin zuciyarsa, a fusace ya damki gashin kanta da gaske ya yi yunkurin jefata cikin ruwan, a sukwane ta saki hannun nasa ta rungume shi, tun da ya ɗan ɗagota kaɗan, zata iya rungumar shi, shi ne ta rungume shi tana kuka. Ƙoƙarin raba jikinsa da ita ya yi dan ya jefata cikin ruwan ko da sau ɗaya ne ta ɗanɗani azaba gobe ba zata sake ba, sai ta sha azaba zai cirota, amma ina taki sakinsa, sosai ta rike shi tana ihu tana faɗin wlh ta tuba daga yau ba zata sake shiga cikin ruwan sama ba, ita har abada ma ta tsani ruwa, sosai take kuka tamkar ranta zai fita. Kasa jure kukan nata ya yi, ya kasa dannewa ba dan ya so ba ya haura da ita zuwa tsakiyar jirgin in da ta tsaya ɗazun take wanka, ɗage matakalar ya yi sama yana ɗan shafa bayanta alamar rarrashi. Ta shige kirjinsa sosai tana wani irin marayar kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, ɗagota cancak ya yi zuwa saman kirjinsa, kwantar da kanta a saman kafaɗarsa ta yi tana wani irin wahalallen numfashi, ɗan juyo da face nasa ya yi suna fuskantar juna, zuba mata idanu ya yi yana kallon yanda ta lafe shiru idanu a rufe. "Meesha". Ya ambaci sunanta, kin amsawa ta yi dan ba zata iya ba, hannu ya kai ya tattara mata gashinta da ya barbazu mata har saman face nata, sake ambatar sunan nata ya yi, har lokacin bata amsa ba, matso da face nasa daf da tata ya yi yana mai sake ambatar sunan tata, tana jinsa amma taki amsawa, dan ya bata haushi ba kaɗan ba, a cikin zuciyarta ta ce wlh ba zata dai'na shiga ruwan sama ba ya kasheta idan yana so. Tana can tana tunani sai jin saukar hannunsa a saman kumatunta ta yi, ɗan shafawa ya yi kafin ya dawo da yatsansa guda ɗaya saman lips nata da suka yi pink sosai saboda ruwan saman dake zuwa a kansu, wani irin laushi ya ji lips ɗin nata sun kara yi saboda ruwa ya jiƙasu. Dawo da ita ta gabansa ya yi tare da ɗaurata a saman wani kyakkyawan chair dake wajen kusa da su, a hankali ya haɗe fuskokinsu waje guda, can kasan maƙoshinsa ya fara magana a nutse "Meesha meyasa kika cika son ruwa har haka ne? Kuma ruwan ma bana pool ba, ba na toilet ki yi wanka kamar kowa ba, a'a ruwan sama mai sanyi har haka why?" Yana magana yana kallon idanunta dake rufe gam. Turo ɗan bakin nan nata ta yi, a tsananin shagwaɓe ta fara magana "Kai yaya Saif ni ma fa ban sani ba, kawai ina son ruwan ne, kuma yana yi mini daɗin shiga, Allah ko dare idan ana ruwa shiga nake yi, daddy ma hakura ya yi ya kyaleni ina shiga". Yanda take magana tana kara turo baki. Harshensa ya fitar tare da ɗaurawa saman lips ɗin nata ba tare da ya sake yin magana ba, hannu ta kai ta saƙalo wuyarsa idanun nata a rufe har lokacin, wannan saƙalo wuyar nasa da ta yi tamakar ta kunna shi ne, cikin natsuwa ya kama lips nata ya fara kissing ga ruwan sama na sauka a kansu, shiru ta yi tana tunano zantukan Akila tun kan lecture da ta rinƙa bawa su jelly, Umaisha da ita kanta, daɗi ta ji sosai yau dai GAR mijinta ne na sunnah, tuna hakan yasa ta fara yin wasa da hannunta a wuyar nasa, sai dai fa tabbas tana tsoronsa har yau har gobe, amma da yake ta kudurta a ranta tana son shi, ga kuma yarinta a kanta, ga rashin mummynta, ta yi aure babu uwa a kusa da zata gaya mata abin da ya dace ta yi, hakan yasa kawai take amfani da duk abin da ya zo mata a cikin ƙwaƙwalwarta, dan ma tana da kwakwalwa da basira bata manta abubuwa, duk wasu karatu da mummy ta koya mata bata manta ba, sai dai ai mummyn bata yi mata karatu a kan aure ba, so bata san komai ta wannan ɓangaren ba sai wanda Akila ta koya mata, ta ɗauka a iya soyayyar kawai ake tsayawa, shi kawai za'ayi ta zubawa kamar ba gobe. Wani irin azababben shock ya ji sosai lokacin da ta fara shafa mishi wuyarsa, waro dara daran blue eyes nasa waje sosai ya yi a kan face nata, sai ya kallima idanunta a rufe ruf take abin, tuni ya sauketa daga saman chair ɗin ya dawo da ita saman kirjinsa tare da cigaba da kissing nata babu kama hannun yaro, gabaɗayansu jinsu suke yi tamkar ba'a duniya suke ba, bedroom nasu ya koma da ita tare da zame ɗan bakin nasa daga tatan. Sai zubar ruwa suke yi, sauketa a tsakiyar ɗakin ya yi tare nufar trolleys ɗinsa ya fito da kayansa pajama launin white ya nufi toilet. Ita ma kayan jikinta ta cire a hanzarce kafin ya fito ta canza zuwa wasu ƙananan kayan, sannan ta ɗauko mopper ta goge ɗakin. Yana fitowa ya haye saman gado ya kwanta tare da jawo bargo ya kara gudun Ac, kansa ciwo yake yi mishi saboda ruwan saman da ta dakesa. Bayan ta gama wayarta ta ɗauka ta koma saman sofa ta kwanta tare da fara kallon hotunansa dake cikin wayar tana kara jin tsantsar kaunarsa, da gudu Brady ya shigo cikin ɗakin, zai haye saman bed sai ya kalli hoton Lion a wayarta tana kallo, da gudu ya haye jikinta tare da kwace wayar tata, ihu ta kurma tare da miƙewa dan sam bata ga shigowarsa ba, shi kuwa dirowa kasa ya yi wayar tana a bakinsa ya haye saman bed ya bawa Lion wayar dan ya ga hotonsa da take kallo. Ita kuwa wani marayar kuka ta saka dan ta tsorata ba karya, kun san idan abu ya razana mutun sosai, daga baya ya fahimci abin bai kamata ya razana ba, akwai wani irin kukan da yake saki mai tsuma zuciyar mai sauraro, to ita ma hakan ta yi. Shi kuma Lion karɓar wayar ya yi yana ganin hoton nasa da take kallo, Brady ya tona mata asiri. Jin kukanta yasa ya ce da Brady ya je ya kira mishi ita, dirowa kasa ya yi ya nufota, hannunta ya zo yana ƙoƙarin kamawa da bakinsa ya ja ta dan ya kaita wajen Lion ɗin, ihu ta sake kurmawa tare da miƙewa tsaye ta haye saman bed ɗin da gudu, dan tasan ba in da zata je ta tsiranwa Brady sai wajen Lion ɗin dai, shi kaɗai ne mai dakatar da shi, a tunaninta cizonta ya zo yi, bata san aikoshi akayi ya kirata ba. Tana zuwa ta haye jikinsa ta ƙanƙame shi tana kuka, rungumeta ya yi tare da kiran Brady dan ya zo ya haɗasu su zama abokan ko zai huta da wannan bala'in nasu, ya gaji da rabasu faɗa. Da gudu ya haye bed ɗin, shafa jikinsa ya fara yi kasa kasa ya furta "Meesha". Cikin kuka ta amsa mishi da na'am, "Ɗago kai ku gaisa da Brady daga yau ku zama friend". Girgiza kai ta fara yi tana kuka ta ce "Bana so, ni kam bana son shi yaya Saif, dan Allah ka ce ya tafi, wlh bana son ganin shi, wayyo daddyna, mummyna, gwaggona, Jehan, wlh bana son shi". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce da Brady ya kyaleta zuwa anjuma idan ta gama kukan kila ta yarda su zama abokai, dan dole ne idan yana son zaman lafiya a cikin jirgin nan to ya cirewa Rimsha tsoron karen nan, idan ba haka ba, wata rana zata iya faɗawa cikin tekun nan saboda tsoro da razana, so dole ya cire mata tsoron da su zauna lafiya. Sauka kasa Bradyn ya yi ya nufi wajen Mark abinsa, ita kuma har lokacin kuka take yi ta kankame mijin nata gam kamar nace zan kwace mata shi, hannu ya ɗaura saman bayanta yana ɗan bubbugata alamar rarrashi........... ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne. KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ 👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊ *Domin samun karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581* 71-72 Sauka kasa Bradyn ya yi ya nufi wajen Mark abinsa, ita kuma har lokacin kuka take yi ta kankame mijin nata gam kamar nace zan kwace mata shi, hannu ya ɗaura saman bayanta yana ɗan bubbugata alamar rarrashi. Meesha, ya amsaci sunanta a hankali, cikin kuka ta amsa mishi da na'am. "Why baki son ku zama friend da Brady?" Hannunta ɗaya ta ɗaura a saman kirjin nasa tana faɗin "Wlh mugu ne, baka ga ranar abin da ya yi wa su yaya Areef ba ne? Ni nasan ko mun zama friend watarana sai ya cijeni tun da ya jiwa yaya Areef da suka saba ma ciwo". "To amma ai baya yiwa mutun komai har sai idan ni na ce ya yi, ko Areef ɗin da ya jiwa ciwo ma ai ni nasaka shi ko?". Yana magana yana shafa bayanta da hannu ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ya kai saman face nata yana goge mata hawayen nata. "Uhm ni gaskiya yaya Saif bana son shi koma dai yaya". Cigaba da share mata hawayen ya yi yana faɗin "It's okey, tashi to tun da Bradyn ya tafi". Make mishi kafaɗa ta yi ba tare da ta yi magana ba "Bazaki tashi ba?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e bazata tashi ba. "Why ba zaki tashi ba?". Tamkar zata ce saboda jikin mijinta ne, sai kuma ta fasa ta ce "Ba zan iya tashin bane, jikina duk a mace yake". Zuba mata idanu ya yi yana kallon yanda take faman turo baki tana magana. Yatsa ya ɗaura a saman lips ɗin nata yana ɗan murza su, kara turo bakin nata sosai ta yi tana wasa da hannunta a saman kirjinsa, tana yi mishi tamkar tana zana zane a wajen, ɗan gyara mata kwanciya ya yi a jikin nasa ta yanda zai sami damar buɗe tula tulanta, hannu ya kai ya ɗan yi kasa da wuyar rigar zuwa saman tudunsu, a hankali ya shafa zanen sunan nasa, can kasan maƙoshinsa ya furta "Waye ya zana miki wannan zane?". Ɗan ɗago idanu ta yi dan ta saci kallonsa saboda yanda ta ji ya ya kuke maganar alamar baya cikin mood mai kyau. Tana ɗagowa karaf suka haɗa idanu, kasa ta yi da nata tana faɗin "Wata mata ce a garinsu Kausar". "Kuma sai kika buɗe mata jikinki ta yi zanen? Sannan a rasa ina za'a buɗe mata ta zana sai nan wajen?". Ɗan saƙalo wuyarsa ta yi dan ta miƙe ta bar jikin nasa saboda ta ji yanayin maganarsa ya fara sauyawa, kada ya je ya zaneta ko ta sha mari, gara mata ta yi nesa da shi idan ya so ta amsa mishi tambayar a can, idan ta kama duka ne kafin ya miƙe ya capkota ta zunduma waje a guje abinta, sai dai ina tana ƙoƙarin miƙewa ya ɗaura hannu a saman bayanta tare da mayar da ita ta kwanta dan dole ba dan ta so ba. "Ba yanzu kika ce ba zaki iya tashi ba? Amsa my question first ma dai". Har lokacin hannunta na a sakale a wuyarsa bata saki ba, ɗan shafa wuyar tasa ta fara yi tana tunano shawarar da gwaggo take gayawa mummy idan ran daddy ya ɓaci abin da zata yi mishi ya sauko cikin ƙanƙanin lokaci, yau karatun gwaggo take tunanowa, nan take zuciyarta ta amince mata da shi ma ta yi mishi hakan ko zai sauko yanda ya fara yi mata magana da zafan nan, kishinsa ya motsa. Tuna hakan yasa ta cigaba da shafa wuyan nasa a hankali tana haurawa zuwa baki bakin gashin kansa ta sake sauko da hannunta zuwa saman bayansa. "Yaya Saif lokacin fa da aka yi mini zanen ina karama, ban kai haka ba, lokacin kamar ma ban cika 13 years ba". Ta yi maganar tana ɗago da dara daran sleeping eyes ɗin nan nata, ga su sun kara wani irin fari tas da su kamar audiga. Tana ɗago idanu ya ɗago haɓarta shi kuma ta yanda zasu ji daɗin ganin juna da kyau, hannunsa dake saman bayanta ya zura cikin rigarta yana shafa lallausan bayan nata, kwanciya ya yi da ita a jikinsa har lokacin yana kallon cikin kwayar idanunta da ta saukesu kasa tana ɗan kallon gefe hannunta na saman wuyarsa, cikin ɗarɗar ta ɗaura hannu a saman ƙashin maƙoshinsa, wani irin zirr ya ji a jikinsa, bai san time da ya rungumeta sosai a jikin nasa kamar wani ya ce zai kwace mishi ita ba. "Meesha" Ya ambaci sunanta a hankali, ɗago kai ta yi da nufin ta amsa, tana ɗagowa ya haɗe ɗan bakinsa da nata, wani irin guguwace ta ɗebeta zuwa wata duniya, dan kuwa a kiss da ya yi mata yau karo na uku, biyun dukka bata cikin hayyacinta, ba zata iya wani gane me ma ta ji ba, yanzu kuwa tana cikin natsuwarta, sai jinta ta yi tamkar wanda aka zarewa laka, sumar kwance ta yi tana jin lallausan lips nasa dake yawo a tsakanin laɓɓanta na sama da na kasa, jin abin take yi tamkar a mafarki ko a tunani. Sai da ta ji saukar hannunsa a saman mazaunanta ne ta dawo daga duniyar da ta afka, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke cikin tsoro jikinta na kerma ta yi ƙoƙarin kissing na shi ita ma dan laushin lips nasa sun kiɗimata over, tana son ta ji, dama idan baku manta ba, ɗan bakin nan nasa yana ɗaya daga cikin abin da take bala'in kauna a face nasa. Hannunta dukkan biyu tasa ta tallabo kumatunsa tare da capko lips ɗin nasa ta datse idanunta gam dan ma kada ta ga wani irin yanayi ne zai bayyana a saman face nasa. Tana fara kissing nasa bai san time da ya waro dara daran idanunsa waje sosai ba, ga idanun nasa sun yi jawur kamar wuta. Ganin da gaske ita ce take kissing nasa yasa ya lumshe idanunsa saboda wani azababben daɗi dake ratsa shi, ji yake yi tamkar ya mayar da ita cikin cikinsa, duk wannan abin da yake faruwa sam baya cikin hayyacinsa, ya jima da afkawa duniyar sama jannati, ga shi ta zo ta kara rikita masa ƙwaƙwalwarsa da kissing nasa da ta fara yi. Ita ma kuma laushin laɓɓansa ya jata zuwa duniyar da ya faɗa wato duniyar sama jannati, sam bata ji bata gani ta fita a hayyacinta, kissing nashi take yi babu kama hannun yaro, hannunta ya kama ya ɗaura a kansa, watsa gashin nasa ta shiga yi tana kara lafewa a jikinsa, nan take sautin numfashinsa ya sauya, hannu ɗaya ya ɗaura a saman gashin kanta yana ɗan shafawa izuwa bayanta. Call ɗin daddynsa ne ya dawo da su daga duniyar da suka faɗa, sakin lips ɗin nasa ta yi tana ƙoƙarin sauka daga jikin nasa, rikota ya yi idanunsa a lumshe ya mayar da ita saman kirjin nasa yana sauke numfashi a hankali hankali, call na farko ya katse na biyu ya sake shigowa, sam baya ji kamar zai iya ɗaukar kiran, cigaba da shafa bayanta ya yi yana wani sauke nauyayyar ajiyar zuciya. "Yaya Saif ana kiran wayarka, in ɗauko maka ne?" Ta yi maganar cikin sanyin murya, shiru bai amsa mata ba, kira na uku ne ya sake shigowa da alama dai daddy yana bukatar yin magana da shi cikin gaggawa ne. "Yaya Saif kayi magana mana, sai mutun ya yi ta yi maka magana amma ka share shi". A wannan karon ta yi maganar a shagwaɓe sosai. Waro idanunsa da suke jawur da su ya yi, can kasan maƙoshinsa ya furta "Ni ban san yaushe kika zama irin Aseef ba a wajen magana". Turo baki ta yi tana faɗin "Kai yaya Saif ni dama haka nake maganata". Tana magana idanu a rufe ruf, shiru ya yi bai sake yin magana ba ya zubawa face nata idanu yana jin wani iri a cikin zuciyarsa, tabbas face ɗin Rimsha da Jehan suna gefa shi cikin yanayi a duk lokacin da ya kallesu, musamman ita Rimsha ya rasa me dalilin da yasa yake jinsu a cikin zuciyarsa. Call ɗin daddy na biyar ne ya sake shigowa, hannu ya miƙa saman bedside drawer ya ɗauko wayar, video call ne, dad ya kira ne dan ya ga ɗan nasa ya ji kuma ya tafiyar tasu ta kasance, ko a jikinsa ya ɗauki kiran tana kwance a saman kirjin nasa yana shafa kanta zuwa bayanta da hannunsa, ta lafe abinta idanu a rufe. Lokacin da ya ɗauki kira suka yi 4 eyes da dad ɗin, wani irin murje idanunsa daddyn ya yi dan ya sake ganin wai shin abin da yake ganin nan gaskiya ce ko mafarki ne, mace a kwance a saman kirjin Lion, bayan haka kuma yana shafa lallausan gashin kanta? Anya ba mafarki yake yi ko kuma gizo idanunsa suke yi mishi ba kuwa? Ya tambayi kansa da kansa. Shi kuwa Lion ko a jikinsa, ita ma bata san cewa ya ɗauki kiran ba, bata san cewa Video call bane, haka zalika bata san cewa daddynsa ba ne, idan baku manta ba idanunta a rufe ruf. "Why are you looking at me like that daddy?". Ya tambaya yana dawo da kallonsa a saman face ɗin uncle Herry dake kusa da daddyn. "Romeo what do I see? tell me that it's not what am thinking, tell me it's a dream not reality". Cikin tsananin tashin hankali ya yi maganar Jin voice ɗin daddyn yasa ta waro idanunta waje da sauri, karaf sai cikin idanun daddy, domin kuwa wayar tana saitin face nata da yake ya ɗan yi baya da wayar ta yanda zai kalli daddyn nasa da kyau. Ganin shi yasa ta yunkura da gudu zata sauka daga jikin mijin nata, riketa ya yi tare da mayar da ita yana faɗin "Ina zaki je kuma?". Kallon wayar ta yi ta kasa magana, mayar da kallonsa a kan daddyn ya yi yana faɗin "This is the reason why you called me dad? You called me to ask me if you are dreaming or not, Why didn't you ask Aseef or Areef?". Tashin sense, wato ma shi Lion ya nuna sam bai san me daddy yake yi wa mamaki ba. "Romeo why do you always want to see me sad?". Shiru ya yi bai tanka ba, dan bai san me zai ce ba, ita kuma ta datse idanunta gam tare da juyar da fuskarta gefe guda dan ma kada daddyn ya yi ta kallonta. Jin ya yi shiru ne yasa daddyn ya tausasa muryarsa dan yasan wannan shiru na Lion ba alkhairi bane a gareshi, zata iya kwaɓe musu ne kaca kasa, so sai ya tausasa muryarsa tare da canza maganar yana faɗin "How is your journey?" Jinjina mishi kai ya yi alamar komai normal ba tare da ya yi magana ba. "Okey good where is Brady?". Shiru ya yi na almost 2 mins tamkar ba zai yi magana ba, sai can kuma ya ce "Daddy how are and how was your body?" Idan da sabo sun saba da halinsa, kullum ba wani canji a tattare da shi, tun da ya taso har izuwa yau hakance, idan ka yi mishi tambaya bata yi mishi ba baya amsawa sai dai ya yi maka magana akan abin da yake gabansa kawai, Rimsha ce kawai a duniya taga canji a tattare da shi, bayan ita ko TRIPLETS nasa babu wani canji da suka gani, yanda yake a baya hakan yake yanzu ma, babu wata annuri ko tausayi bare girmama ɗan adam a lamuransa, so har yanzu kamar baya yake amsawa daddyn nasu ma, idan ka yi mishi magana sai ya ɗauki mintuna yake amsawa, a hakan ma idan ya ga damar amsawar kenan, idan bai ga dama ba sai dai ka jira amsa har ka gaji ka hakura, Rimsha ita ce mutun ta farko da yake amsawa magana idan ta yi mishi a tsakanin ƴan sakanni, ko su Aseef sai ya ɗauki lokaci, wani lokacin ma baya amsa musu sai dai ya jinjina musu kai kawai alamar ya ji, shi ma jinjina kai ɗin ba kowa yake samu ba. "Am fine my son what of u?". Nan ma jinjina mishi kai ya yi alamar yana normal. "Romeo wai me zaka je yi a kasar Russia ne? Baka faɗa mini abin da zai kai ka ba". "Daddy do you have any relationship with Russia ne da ka damu haka?". Cikin sauri ya girgiza mishi kai alamar a'a, yanayin yanda ya amsa mishi da sauri ma sai da yasa Lion ɗin zargin wani abin, amma sai ya basar da cewa "To dad you don't have any relationship with then amma kake takura wa kanka har haka?". Shiru ya yi dan yasan waye ɗan nasa, idan suka cigaba da jan magana zai iya sanya shi ma ya faɗi abin da bai yi niyya ba. Tun da suka fara magana daddyn yake son tambayarsa meyasa idanunsa suka yi jawur har haka, amma gudun amsar da ɗan nasa zai ba shi ne yasa ya danne, dan kuwa idan ya ji cewa ɗansa ya haɗa jini da bakar fata, ma'ana ya kwanta da Rimsha ne to fa gaskiya zuciyarsa zata iya bugawa ya mutu, dan ya yi wa bakaƙen fata mummunar tsana, a hakan ma bai san cewa su musulmai bane, da ya san su Rimsha musulmai ne ai da bala'in ta fi hakan, tsanar sai ta ninka hakan, kuma yasan halin Lion baya karya, duk abin da ya tambaye shi amsa kai tsaye zai bashi, babu shayi ko wani ɗar, so yana iya gaya mishi kaza ne ya faru, dan su ba kunya ce ke garesu ba, rufin asirinsa kada ya jiyowa kansa bala'i ne yasa ya danne ya yi shiru tsit bai tambayi dalilin jan idanun nasa ba, yanzu ma da yake ganinta a saman kirjin ɗan nasa tamkar zai mutu da bakin ciki haka yake ji, har wani harbawa zuciyarsa take yi, bare ya ji wani labari daban, ai abin ba'a cewa komai, sai dai fa zuciyarsa sai zargin hakan take yi mishi, duk da yasan canzawan launin idanu ga namiji ba lallai sai idan sha'awarsa ta motsa ba, akwai dalilan da suke kawo hakan, ciki kuma har da ɓacin rai, wahala da kuma gajiya, barci, rana da sauransu. Jin saukar hawayenta a saman kirjin nasa ne yasa ya dawo da kallonsa kanta, kuka take yi hawaye wani na bin wani, ita kanta bata san dalilin yin kukan nata ba. Meesha ya ambaci sunanta, can kasa kasa ta amsa mishi na'am. "Why are you crying?". Shi dai daddy ya saki baki yana ganin ikon Allah, tunani ma yake yi wai ko dai ba da ɗansa yake magana bane? Ko dai an canza mishi Lion nasa ne?. Shiru bata yi magana ba dan bata san me zata ce ba, bakin ciki take ji yanda daddynsa yake nuna musu kiyayya karara, ita dai tasan babu wanda ya isa ya halicci koda ɗan yatsa a duniyar nan, da fari da baki dukka Allah ne ya yi su, kuma da ya yi su bai ce baya son baki ko kuma yafi son fari ba, ba wanda ya fi so face wanda ya fi tsoronsa ya kuma fi bauta mishi tare da aikin alkhairai, amma ta rasa meyasa wasu suke cewa basu son bakake fata sai farare, su sanya wasu suna kauce hanyar Allah ta hanyar yin bleaching na fatarsu dan su burge mutane, yin hakan babban kuskure tare da gefa kai ga hala, duk wanda ya canza halitta daga yanda Ubangiji ya halicci shi to ya jira sakamako mai girma na azaba da Ubangiji ya tanada mishi, ba sai kin canza wani abin daga cikin halittarki ba zaki sami abin da kike so, Allah baya sanyawa bawa abin da bata dace da shi ba, kowa abin da ya dace da shi ake ba shi, ku ɗauki darasi a kan Rimsha, ita dai gata chocolate color, bata taɓa raina halitta ko kalar fata da Allah ya yi mata ba, kullum tana gode mishi da ni'imar da ya yi mata, ga shi ya yi mata sakayya ta hanyar bata jarumin miji fari tas tamkar daga kansa an gama haske da kyau, komai ya haɗa, kuɗi, mulki, isa, izza, kyau na wuce misali, hasken fata na wuce misali, hutu, mukami mai girma, gashin kansa bakinkirin mai bala'in kyau har tsakiyar bayansa idan da zai bari bai yanke ba, fuskarsa kawai ya isheta ta zauna ta yi ta kallo daga safe har yamma saboda kyau, kalar idanunsa mai tsada wanda kowa yake burin mallaka, idan ta zo kusa da shi bakakirin take zama, amma a haka Allah ya jarrabe shi da sonta, duk duniya ita kaɗai take jin wani irin muryarsa da ba wanda ya taɓa yi wa magana da shi, ita kaɗai take yi mishi magana ya amsa kai tsaye ba sai ya ja lokaci ba, ita kaɗai take zuba mishi shagwaɓa kuma ya burge shi, mutumin da a baya babu wani abin da yake burge shi sama da aikinsa, baya ɗaukar komai da daraja face TRIPLETS nasa da kuma aikinsa, sai daddynsu, amma yau an wayi gari ta shigo cikin rayuwarsa a in da ta zama ciwon TRIPLETS ɗin nasa, wato cikonsa kenan, dan ita ce shi, wasu abubuwa ma ya fi sake mata sama da TRIPLETS nasa, to bai kamata ku canza daga halittar da Allah ya yi muku dan burge wasu ba, idan wani bai so ki a haka ba, Allah zai kawo miki wanda ya ninninka shi, Allah dai ya bamu dacewa yasa ku gane gaskiya ku dai'na cutar kanku, ku canza halittarma sam baku kyau, sai ku zama kamar wasu dodanni, dan babu wanda ya isa ya haɗa na Allah da na kari na kanti, da kunsan munin da kuke yi idan kuka canza wani abin na daga halittarku, wlh da ko kusa ko alama ba zaku yi ba, Allah ya yi mana kyakkywan karshe. Katse kiran ya yi tare da kashe wayarsa bakiɗaya dan kada su dame shi da kira, ɗago haɓarta ya yi yana tambayarta meya faru take kuka. "Yaya Saif menene laifin mu da daddy zai ce baya son bakaken fata? Mune muka yi kanmu?". Shiru ya yi yana tunani, tana da gaskiya, shi bai ga abin ki a bakin fata ba, shi dukka ma ɗaya yake ɗaukarsu, kafin ya musulunta ne lokacin da yake krista ne yake wannan kabilanci, amma da ya musulta yasan da fari da baki dukka Allah ne ya yi su, daga nan bai sake cewa baya son baki ba, kowa ma shi ba ruwansa, idan aiki ta haɗasu to za'a yi kawai, sannan a kan Rimsha ya kara jin yana son bakaken fata over, domin kuwa ita dai chocolate color ce, color mai tsada a duniya, amma ba wata macen da yake ji a ransa biyunta, tana bala'in yi mishi kyau kuma tana burgesa, Turawa ƴan uwansa sam basu burgesa ko kaɗan. Goge mata hawayen nata ya yi ba tare da ya bata amsa ba ya ce "Jeki ci abinci bari na kira Mark ya kawo miki". Da mamaki ta ɗago tana kallonsa, ko yaushe yasan cewa tana jin yunwa kuma?. "Why kike yin mamaki? Ai ba iya aikin soja kawai na iya ba, harda karantar mutane, ki ci abinci ki zo ki gaya mini why are you watching my pic's like film?". Yana magana yana kunna wayarsa dan ya yi wa Mark massage ya kawo musu abinci. "Kai yaya Saif, ashe kai ma ka iya sa ido ko? To ni ai bana kallon hotonka" Shiru bai sake yin magana ba, hannunsa ta riko cikin nata tana kallon ƴatsun hannun nasa, dama tana burin ta ga ta taɓa waƴan nan kyawawan latsun nasa, ga su tamkar ka latsa jini ya fita, zuba musu idanu ta yi tana kallonsu babu ko kyaftawa, shi kuma zubawa idanun nata ido ya yi yana kallonsu cike da kaunarsu, a duniya yana bala'in kaunar sleeping ɗin nan nata. Mark ne ya katse musu kallon da suke yi ta hanyar shigowa bakinsa ɗauke da excuse, kallo ɗaya ya yi musu ya yi saurin kawar da kallonsa tamkar bai gansu ba, saman table ɗin ya ajiye kayan abincin tare da ɗan tsayawa a gefe guda, bawan Allah yana son ya tambayeta ko tana da number wani daga cikin ƴan uwan Anaya dan ya kira ya ji ya lafiyarta tun da number Anaya ɗin bata shiga, sai dai yana bala'in tsoron yi mata magana, bai ma san taya zai fara tambayarta ba, yana tsoron Lion sosai, ita kuma tana da number daddyn Anaya ɗin har da mummunta da yaya Feroz dukka, sai dai bata kawo cewa yana da bukatar ya yi magana da su ba, sai ƴan kame kame yake yi tun da ya shigo ɗakin. "Is there any problem Mark?". Ya tambaya yana ɗan sauketa daga jikin nasa, kankame shi ta yi taki sauka dan tana son yin magana da shi idan Mark ɗin ya fita, so ta ɗauka ko zai sauketa ne ya fita tare da Mark ɗin, shi ne ta rike shi, kallonta ya yi kafin ya barta a jikin nasa ya mai da kallonsa kan Mark ɗin. "Sir i want to talk to Madam". Ya faɗa cikin tsoro, daga jin muryarsa kasan a tsananin tsorace ya yi maganar, ba karamar shahada ya yi ba, ya kasa samun sukuni ne, duk abin da yake yi tunanin Anayar ce kawai a cikin ƙwaƙwalwarsa, yana da bukatar ya yi magana da ita idan ba haka ba za'a iya samun matsala, dan har kansa ta fara yi mishi ciwo wuni ɗaya kawai, dama duk wanda ya san turawa yasan basu iya faɗawa soyayya ba, idan suka faɗa fa to komai suna iya sadaukarwa a kan wannan soyayyar tasu, gabaɗaya zuciyarsu suke bawa wanda suke so, suna kula da soyayyar tasu sama da yanda suke kula da kansu, ko dabbobi suke so to fa kular da zasu basu sai ka saki baki kana kallo, dan kula ce ta wuce misali, so su haka soke, shiyasa shi ma Mark ya rasa sukuninsa, ya rasa duk wata jin daɗi wuni yau kawai. "What do you want to tell her?". Yana magana tamkar yanda yake magana da su da baya, cikin bada umarni da nuna isa tamkar ba shi ne ya gama rarrashin Rimsha yanzu ba, dama fuska kam tamkar kullum haka yake, ko ita Rimshar bai sauya mata face nasa ba, hakan na nufin halittarsa ce Tiger face, babu wasa kuma babu alamar murmushi ma bare dariya. "Sir i want to ask her about her friend, I want to ask her if she has a number of her own". Sai lokacin ta gane bawan Allah yana so ne ya yi magana da Anaya, ɗago kai ta yi da nufin ta yi mishi magana, wani kallo Lion ɗin ya wurga mata wanda ya sanyata haɗiye maganar ta koma ta kwanta luf a saman kirjin nasa. Shiru ya yi na tsawo almost 2 mins kafin nan kasa kasa ya ambaci sunanta Meesha, yadda ya yi maganar kasa kasa ko Mark ɗin bai ji me ya ce ba, ita ma dan tana saman kirjinsa ne da ba zata ji ba, na'am ta amsa ba tare da ta ɗago ba "Do you have the number he is looking for?" Jinjina mishi kai ta yi alamar e, ya hanata magana ta hanyar sanya yatsansa ɗaya a cikin bakinta yana wasa da language nata, sam baya son ta yi magana, na'am ɗin da ta ce ma kasa kasa maganar ya fita saboda yatsar nasa dake bakin nata. Tsotsar yatsan nasa ta fara yi kamar sweet tana ɗan ciza mishi, tamkar wanda aka watsawa ruwan kankara haka yake ji a jikinsa, duk ta saukar mishi da kasala, dan fa ba karya yana da azababben sha'awa, kawai dan dama bai san da hakan ba ne, bai taɓa kwatantawa ba, yanzu kuma da gabaɗaya komai nasa ta buɗe da ta taɓa shi kaɗan komai yake motsa mishi, sai dai baya ɗaukar hakan a matsayin wani abin azo a gani ma, dan idan zaka kashe shi bai san me yake tsakaninsa da Rimsha ba, shi dai kawai tana burgesa, batun kiss kuma wannan abu ne da kun riga da kun sani su fa kiss a wajensu ba wata tsiya ba ce, ko ba masoya ba suna yi, so ko ba son yarinya kake yi ba su suna iya kissing nata, amma fa shi ya fara yardan wa kansa tabbas akwai wani abin a tsakaninsu, idan zuciyarsa ta ce mishi so ne, sai ya ce a'a shi bayan TRIPLETS nasa ba zai so kowa ba, kawai abota ce or tausayi a tsakaninsu, haka a koda yaushe yake ƙoƙarin tursasawa zuciyarsa da ta yarda da hakan............Tab akwai aiki kenan, ka gama kissed na yarinya ka ce abota ko tausayi, zaka yi bayani da yarenku na Spanish ne or turancin da kuka fi iya wa ne wlh, mu dai je zuwa ba dai yanzu kana iya jin feeling ba? Zaka ga abota.🤣🤣 Ɗauko wayarta daga saman bedside drawer in da ya ajiye ɗazun da Brady ya kawo mishi ya yi, miƙawa Mark ɗin ya yi yana faɗin ya je ya duba number, cike da murna har yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya ya zo ya karɓa tare da nufa waje. Mark ɗin yana fita Lion ɗin ya zame hannunsa daga bakinta dan ba ƙaramin ɗaga mishi hankali take yi ba da irin ɗan ciza ƴatsar nasa da take yi. Ɗago kanta ta yi tana faɗin "Yaya Saif meyasa Mark zai rinƙa shigowa ɗakin nan kai tsaye?". Shiru ya yi dan shi ma sam bai ji daɗin hakan ba, bai so Mark ɗin ya shigo ya samesu a haka ba, ga shi ba wani kayan kirki ne a jikinta ba, amma da yake sun saba da hakan ne yasa bai ce da Mark ɗin ya fita ba, ya saba ɗakinsa ne shi kaɗai, kuma Mark ɗin yana shigowa duk lokacin da ya buƙacesa ba tare da wani shamaki ba, shiyasa yanzu ma ya shigo ba wata shamaki abin sabo ne. "Yaya Saif ni kam bana son ya rinƙa shigowa, ya tsaya a waje zan rinƙa zuwa na karɓi abincin ko kuma zan je kitchen ɗin na rinƙa ɗauka da kai......". Bata kai karshen maganar ba ya wurga mata wani shegen harara da dara daran idanun nan nasa, hakan yasa ta shanye maganar. "Ki je ki karɓo a hannunsa?". Ya maimaita maganar yana mai cigaba da wurga mata kallo mai kama da harara. Ba ƙaramin razana ta yi ba, nan take ta sha jinin jikinta, tunani take yi wai yaushe yaya Saif ɗin nan nata zai yi koda murmushi ne a rayuwarsa? Wlh face nasa a ɗaure kullum ɗin nan yana razanata ba kaɗan ba, daurewa kawai take yi dan tasan ba zai taɓa lafiyar jikinta ba. Girgiza mishi kai ta yi tana mai datse idanunta gam. "Tashi ki je ki ci abinci". Jin ya faɗi hakan ne yasa ta waro idanun nata tare da yunkurawa zata tashi, har zata miƙe sai ta tuna zancen Akila, komawa ta yi ta manna mishi haɗaɗɗiyar sumbata a saman lallausan kumatunsa tana sakin cool murmushi tare da runtse idanunta, nan take dimples nata suka lotsa. Sosai ta kara tafiya da imaninsa, tamkar zai sake jawota jikin nasa, sai kuma ya fasa dan yana son ta ci abinci. Kiƙewa ta yi zuwa wajen trolleynta ta ɗauko yajin da Anaya ta bata dan ta saka shi cikin kayan da suka yi sayya shi kuma Lion ya haɗo da shi ya zuba cikin trolleyn. Bayan ta ɗauka saman table ta wuce ta zauna dan ta fara cin abincin. Kiran Areef Video call ne ya shigo wayar tasa, ganin kiran yasa ya ji dama ya sake kashe wayar dan barci yake son ya yi, amma ba zai iya kin ɗaukar kiran TRIPLETS nasa ba a ko wani hali yake ciki, sannan da ya ga kiranma sai da zuciyarsa ta harba tamkar ɗaya daga cikinsu yana cikin tashin hankali da damuwa, hakan ce tasa ya ɗauka da wuri dan ya ji menene. Yana ɗauka a matuƙar ruɗe Areef ya fara magana. "Lion ka kawo agajin gaggawa, matar Aseef tana gaf da mutuwa, poison ta ci, gabaɗaya sun haɗu a palo da su daddy suna cin abinci kawai ta zube kasa kumfa na fita daga bakinta, i think masu girkin ne suka sanya poison ɗin, yanzu dai na yi iya kan bakin ƙoƙarina wajen ganin na ceci rayuwarta, amma tamkar ana kara poisonin ɗin ta ne, abin sai karuwa yake yi tamkar kara cin gubar take yi, abin ya ɗaure mini kai ya kuma sha gaban tunanina, please ka kawo mana agajin gaggawa na wata hanya da zamu ceceta kada ta mutu". Shiru ya ɗan yi na ƴan mintocin da ba su wuce biyu ba, sai azalzala mishi Areef yake yi da ya yi magana, amma shi kuma ya yi shiru yana ɗan tunani, can kuma sai ya ce "How comes za'ace matar Aseef ta ci poison? Taya za'ayi ace kowa a gidan ya ci abincin lafiya lou sai ita ce kawai ta ci poison a ciki? Wannan ba laifin masu yin girki ba ne, laifin daga cikin masu cin abincin yake tun da kowa a gidan ya ci abincin lafiya lou! Amma ba tare da Aseef ta ci abincin bane?". A ruɗe Areef ɗin ya amsa mishi da "Wlh i don't know, ina ga kamar tare suka ci abincin, ni bana gidan kirana Aseef ɗin ya yi a waya a kan na yi sauri nazo na ceci rayuwarta kada ta mutu, so ban san ya abin ya kasance ba". "Shi Aseef ɗin kuma yana nan lafiya?" "Yes yana nan lafiya, shi fa ya kirani a waya da kansa!". Mayar da kallonsa kan Rimsha dake ta faman haɗa spoons waje guda ya yi, ɗan zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda take zuba yaji a gabanta tana tsince namar dake cikin abincin tana tarawa a gefe guda alamar bata son ci, dawo da kallonsa saman face nata ya yi, yana kallon yanda take murnar cin yajin da take yi, nan take kwakwalwarsa ya ayyana mishi Akila ce zaune a wannan waje ba Rimsha ba, tunani ya fara yi na yadda akayi ta ci guba ita kaɗai a gidan, yanda Rimsha ta zuba wannan yaji a gabanta zai zamana haka aka zuba guba a gaban Akilar lokacin da suke cin abinci, to waye ya yi hakan? Ta ya za'ayi gabaɗaya family'n suna saman table ɗin cin abincin a tare har a zuba mata guba a gabanta babu wanda ya gani? Wannan abu ne mai wuyar ganewa mai kuma ɗaure kai. "Where is she?" Ya tambaya yana mai sake jinjina al'amarin a ransa tare da dawo da kallonsa kan wayar. "Tana bedroom ɗin Aseef ɗin". "Okey take da camera to her place let me see her". Okey ya amsa mishi da shi tare da ɗaukar wayar da sauri ya nufi bedroom ɗin na Aseef. Gabaɗaya ƴan gidan suna cikin bedroom ɗin, harta daddyn Rimsha da Jehan, hankalin kowa ya yi mummunar tashi, musamman ma daddyn Lion ya shiga tashin hankali sosai bare ma da ya ga yanda Aseef ya haukace musu suna neman rasa shi gabaɗaya, ga kuma Akilar tana ta faman ta shake wuyarta tamkar ba zata rayu ba, kowa dake cikin ɗakin sai da ya yi mata hawaye, harta uncle Herry da su Jay, dama shi kam John already yana sonta, dan haka ya sha kuka ba kaɗan ba, ita ma Jehan sai da ta zubarwa da Akilar kwallah sosai yau, Aseef kam ba'a magana, dan haukace musu gabaɗaya ya yi, sai da daddyn Rimsha ya rungume shi sosai ya hana shi taɓata, amma yaki yana ta ƙoƙarin kwace kansa, John ya zo ya haɗu suka rike shi sosai, sai kuka yake yi musu yana faɗin, shi ma dan Allah a bashi poison ɗin yasa su kwanta tare da Heartbeat nasa, idan ma mutuwa ne sai su mutu tare, wlh idan ta mutu shi ba zai iya rayuwa ba, dan girman Allah a agaza shi ma a bashi gubarnan, da farko ma cewa ya yi sam sai ya yi mata kiss sun raba gubar tare, da kyar Areef ya janyesa daga wajen nata ya miƙa shi wa daddyn Rimsha, bawan Allah duk ya birkice ya fita a hayyacinsa, Akila ke ciwo amma ya fita shiga tashin hankali, har wani jiri yake ji kirjinsa na harbawa da karfi karfi, yanzu duk jikinsa ya mutu kamar wani gawa haka ya kwanta a jikin daddyn Rimsha, hawayen da yake fita daga idanunsa ne zai tabbatar maka da bai mutu ba yana da rai. Daddyn Lion a matsayinsa na babban likita ma ya kasa shawo kan matsalar Akilar, mummunar guba aka bata, wanda ba zai kashe ta a lokaci guda ba sai ya gama nakasata ya wahalar da ita tare da kashe duk wasu kwayoyin halittarta, sannan ya kasheta, Saman gadon Areef ya haye da wayar tare da juyawa Lion camerar dan ya ganta da kyau, shiru ya zuba mata idanu yana kallonta, sai fama take yi abin gwanin ban tausayi, idanuwanta tamkar zasu fito waje saboda zarosu da take yi, bakinta, hancinta duk suna fitar da jini mai kauri tamkar ba jini ba, tsabar kaurin jinin ma har wani pink pink ya yi, alamar gubar ta fara azabtar da ita, ta fara ratsa jininta da kyau............... WAYE KUKE TUNANIN YA BAWA AKILA GUBA A CIKIN WANNAN FAMILY'N⁉️ ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne. KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ 👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊ *Domin samun karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581* 73 Zuba musu idanu gabaɗayansu Lion ya yi yana karantar face ɗin kowa, dukkansu babu wanda alamar rashin gaskiya yake a tattare da shi, wani irin azababben tari da Akilar ta fara yi ne ya sanya Lion ɗin dawo da kallonsa a kanta, gabaɗaya hankalin kowa ya dawo kanta, dukkansu sun yi shiru suna sauraron su ji me Lion zai ce kuma, shi dai daddy ya yi iya yinsa a matsayinsa na likita shiru, shi ma Areef ya jarraba, amma poison ɗin ma karuwa yake yi sosai. Almost 2 mins Lion yana kare mata kallo kafin calmly ya ce "Areef kwance mata chain ɗin nan da yake wuyarta ka saka mini shi a cikin ruwa". Miƙawa daddyn Rimsha wayar tasa ya yi a kan ya rike mishi da kyau ta yanda Lion ɗin zai ji daɗin ganin abin da suke yi, matsowa kusa da ita sosai ya yi tare da sanya hannunsa ya ɗan ɗago kanta yana furta Bismillahirrahmanin a cikin zuciyarsa, gabaɗaya sun zaro idanu suna ganin ikon Allah. "John help me with water inside bowl". Cewar Areef ɗin, ya yi maganar yana cire mata chain ɗin. A sukwane John ya nufi hanyar fita, dakatar da shi Lion ya yi tare da cewa Aseef ya tashi ya kawo ruwan ba John ba, da mamaki su daddyn Rimsha suke kallonsa, me Lion yake shirin aikatawa kenan? Menene yake faruwa? Tambayoyin da suke yi wa kansu kenan. Shi ma Areef ya ɗan yi mamaki, amma sanin halin ɗan uwan nasa yasa bai wani damu ba, yasan komai sai da dalilin Lion yake yin shi, kuma tun da ya ji haka to fa akwai matsala kenan. Kallon daddyn Rimsha Areef ɗin ya yi tun bai yi magana ba daddyn ya fara ƙoƙarin tashin Aseef ɗin a kan ya tashi ya kawo ruwa, kasa tashi ya yi dan gabakiɗaya ilahirin jikinsa ya mutu, sai kerma kamar mai zazzaɓi jikin nasa yake yi, ko motsi ba zai iya yi ba, shi kaɗai yasan me yake ji bawan Allah, tabbas idan Akila ta mutu Aseef zai bita, domin kuwa son da yake yi mata ya wuce gaban misali. "Lion Aseef fa ba zai iya kiƙewa ba". Areef ya faɗa yana ƙoƙarin sauka daga gadon hannunsa rike da chain ɗin da ya kwance daga wuyar tata. Shiru Lion ɗin ya ɗan yi na tsawon 3 mins kafin ya ce "Okey keep the chain behind this your uncle, then ka je ka ɗebo ruwan because da kai da Aseef all abu ɗaya ne". Okey ya amsa mishi da shi tare da ajiye chain ɗin a bayan daddyn Rimsha saman bedside drawer kenan, da yake daddyn yana ta gaban bedside drawer ne saman sofar dake kusa da gadon. Ruwa ya je ya ɗebo a bowl tare da dawowa cikin ɗakin, kafin ya dawo Lion ya ce da daddynsa ya fara treating na Akilar yanzu za su iya shawo kan matsalar, ana cire mata chain ɗin ta sume a wajen har lokacin kuma bakinta na fitar da kumfa mai haɗe da jini, ba ɓata lokaci daddy ya fara ƙoƙarin ceto rayuwarta, shi kuma Areef ya zo ya sanya chain ɗin a cikin ruwan da ya kawo, kafin ya sanya sai da ya furta Bismillahirrahmanin rahim a cikin ziciyarsa sannan ya saka chain ɗin, da wuya Areef ya yi abu ba tare da sunan Allah a bakinsa ba bawan Allah, komai zai yi sai ya ambaci mahaliccinmu. Wani irin ajijiya ruwan robar ya yi tare da fallatsuwa sama tamkar an watsa shi, sannan ya koma cikin robar babu ko ɗaya da ya ɗiga a kasa duk irin tashi sama da ya yi, duk cikin ɗakin sun yi matukar tsorata ban da daddyn Rimsha da yake dake yana furta sunan Allah, shi kansa Lion da yake kallonsu sunan Allah ya furta a cikin zuciyarsa, dan kuwa wannan abin sai Allah ne kawai zai iya kare bawansa daga sharrinsu. Suratul Aaraf Areef ya fara karantawa a cikin ziciyarsa yana mai cigaba da kallon ruwan yanda yake wani irin juyawa da karfi karfi yana fitar da kumfa tamkar mutum ya ci guba, tsit ɗakin ya yi daddy yana ta ƙoƙarin ceto rayuwar Akila, ya ɗan tsaga wutarta kaɗan dan ya samu aikinsa ta yi mishi cikin ƙanƙanin lokaci, idan ba haka ba tana iya mutuwa nan take. Areef bai matsa daga wajen ba, yana dake yana kiran sunan Allah har sai da ruwan nan ta gama ajijiyarta bakiɗaya ta koma ta natsu tsin, chain ɗin ya kwanta a kasar ruwan, juyowa ya yi yana kallon Lion da ya zuba musu idanu yana kallonsu. "Waye ya bata wannan chain ɗin?!". Cewar Lion ɗin, ya faɗa a tsawace, ya yi maganar kuma yana mayar da kallonsa a kan Brady da ya shigo yanzu yana ƙoƙarin haukata Rimsha, ya kawo mata wayar Mark ne, ya je ya sami Mark ɗin yana kallon hoton Anaya, shi ne ya kwace wayar ya kawo mata ta gani, dan yasan a wayarta kawai ya taɓa kallon hoton Anaya ɗin, ita kaɗai ya taɓa gani tana kallon hoton, to yau kuma sai ya ga Mark yana kallo, shi ne ya kwace wayar ya kawo mata, ita kuma ta yi muguwar tsorata na hawa jikinta da ya yi yana miƙa mata wayar ta ɗauka cizonta zai yi. Da gudun gaske ta miƙe daga saman table ɗin ta haye saman bed ɗin wajen Lion tana kuka kasa kasa. Sam bai ji komai ba ko a jikinsa su daddy su Jehan duk suna kallon shi ta cikin camera ya runhumeta yana ɗan bubbuga bayanta, jin kukanta yasa dukka suka ɗago suka zubawa wayar idanu, harta Jehan ɗagowa ta yi cikin sauri dan ta kalli me ya sami ƴar uwar tata take kurma ihu haka, shi ma daddynta ɗagowa ya yi yana kallon wayar da yake Areef ya karɓi wayar dan ya nunawa Lion ɗin yanda chain ɗin ta koma. Ganin ta haye jikinsa tana kuka ne yasa suka saki baki har su John suna ganin ikon Allah, shi ma daddynta dai mamaki ya yi, har da kara waro idanu yana kallon shin wai da gaske ne Rimsha ce ta haye jikin Lion har haka? To me ya tsoratata da ta hau jikinsa haka? Shi ne abin da daddynta yake tambaya, haurowar Brady saman gadon ne yasa suka fahimci dalilin yin ihun nata da kuma kukan da take yi yanzu. "Areef i said waye ya bata chain ɗin nan?". Yana magana yana cigaba da bubbuga bayan Meeshar tasa dan ta yi shiru, ya kara ɗaure fuska sosai, sam babu alamar wasa a tattare da shi, nan take kowa dake kallonsa ya sha jinin jikinsa, duk suna tunanin waye ya bata chain ɗin, dan kuwa wannan kara ɗaure fusataccen fuskar nan nasa da Lion ya yi da alama za su ji ne a jikinsu. "Lion i don't know, ita kaɗai ce zata bamu wannan amsar". Cikin rawar murya John ya amsa da "Ni na bawa Aseef ya bata". Tashin hankali, ya zaɓi ya bada masa ta gaskiya ce, dan kuwa yasan Lion dai ba'a yi mishi karya kuma baka isa ya ɓoye mishi abu ba, idan ma kayi kuskuren yin hakan to ka kwana da shirin tabbas zai gamo koma me ka ɓoye, idan kuma ya gano da kansa to fa zai ninninka maka hukuncin ne a kan wanda ya yi niyar yi maka a baya. A razane gabaɗaya ɗakin suka mai da kallonsu a kan John ɗin, cikin tsawa tare da ɓacin rai Areef ya ce "Kai ne kenan kake son kashe mini my pleasure? Dan ba matarsa zaka kashe ba, shi zaka kashe, saboda idan ta mutu shi ma ba zai rayu ba!!". Ya kai karshen maganar tare da nufar John ɗin gadan gadan, da karfin gaske ya damko wuyarsa ya shaƙe shi yana faɗin "Before ka kashe shi ni bari na kasheka!!". Tsawa Lion ya daka mishi yana faɗin ya sake shi, da mamaki ya juyo da ash eyes nasa da suka rikiɗe suka yi jawur Saboda tsantsar ɓacin rai. "Lion cewa fa ka yi na sake shi? Heartbeat namu fa ya yi ƙoƙarin hallakawa, a haka zan kyale shi?". "Areef i said ka sake shi, calm down mana, ya kamata a ko da yaushe ka yi aiki tamkar jami'i ba mutun kamar kowa ba!". Ciza laɓɓansa ya yi da karfi tare da furzar da iska mai tsananin zafi daga bakinsa, ba haka ya so ba, ya so ne yau ya kashe John da hannunsa, amma tun da Lion ya ce ya sake shi yasan akwai dalili, dan haka sai ya sake shi ɗin yana wani huci tamkar shi ma John ɗin ba ɗan uwansa bane, su dai su ukun nan sune kawai ƴan uwa, a kan junansu zasu iya kisan kai!. Ita kuma Rimsha jin maganar Areef ne yasa ta ɗago kai daga saman kirjin nasa tana kallon wayar hannunsa, ganin su daddynta bakiɗaya a wajen ne yasa ta yunkura ta gyara kwanciyarta da kyau a saman kirjin nasa tana kallon daddyn nata, shi ma ita yake kallo tamkar ya sa hannu ya jawota ya rungume, tana son ta yi musu magana, amma ba hali domin Lion yana magana da Areef, ba su isa su saka musu baki or su yi wata magana ba har sai sun kammala, ɗagawa daddyn nata hannu kawai ta yi tana sakin kayatatcen murmushi. Sam daddy bai murmusa ba, dan suna cikin tashin hankali, ta yi mamakin ganin daddyn nata bai yi murmushi ba, Baiwar Allah bata san me yake faruwa ba. "John who give you this chain?". Cewar Lion, Bawan Allah ya ji shakar manya, tuni ya jiyo kamshin mutuwa, har wani jawur idanunsa suka yi yana fitar da kwallah. Da kyar ya iya buɗe baki ya ce "Jo....sep....hine ne ta bani su guda uku a kan na bawa matar Michael da kuma wannan da take kusa da kai sai wannan ɗayar." Ya kai karshen maganar tare da nuna Jehan, da kyar ya iya furta sunan Josephine ɗin saboda wani irin azababben shake mishi wuya da aka yi, ji ya yi tamkar ana zare mishi jijiyoyin wuyar nasa, wannan ma dan Allah yasa suna tare da Musulmai ne a cikin ɗakin, da su kaɗai ne kila kashe John ɗin za'ayi. BABBAR MAGANA WANNAN SHI NE TASHIN HANKALI, JOSEPHINE KUMA? TO A INA TA SAN SU AKILA? WAYE YA GAYA MATA ƳAƳAN NATA SUN YI AURE? ME HAKAN YAKE NUFI? WANNAN SHI NE CAKWAKIYA, SHI WAI A TSAKANIN JOSEPHINE DA WILLIAM WAYE MAI GASKIYA NE? MU DAI JE ZUWA. "Areef ku bashi ruwa ya sha". Cewar Lion, da sauri Jay ya ɗauko ruwan daga cikin fridge ya kawo musu, a cikin zuciya Areef ɗin ya yi bismillahi tare da yin tamkar zai sha ruwan ya tofa ayoyi biyar na farkon suratul baƙara ba tare da sun ankara ba, sannan ya bawa John ɗin dan ya sha, abin da yasa ya yi hakan saboda kowa da yake cikin ɗakin ya lura da irin mawuyacin halin da John ɗin ya shiga na shake shi da aka yi lokaci guda, so shi ne ya taimaka mishi dan su sami abin da suke so. Kowa da yake wajen ya shiga tashin hankali jin cewa daga wajen Josephine sarkar ta fito, shi kuwa Lion ko a jikinsa, kallon Areef ya yi yana faɗin "Why kake magana da ita a ɓoye ba tare da na sani ba? Kana tunanin na zan gane ba ko?". Ya yi mishi magana ta sigar da ba wanda zai gane nufinsa, dan ya yi maganar ne a matsayinsu na jami'ai wanda ko daddynsu bai gane me ya ce ba, saboda ba baki da baki ya faɗa ba, da laɓɓansa kawai ya motsa suka yi ƴar kurma, da yake Areef ɗin yana kallonsa. Shi kuwa daddynsu jin John ya ce Josephine ce ta bada chain ɗin ba ƙaramin razana ya yi ba, saukowa kasa daga saman gadon ya yi yana mai kara tambayar John ɗin wace Josephine? Kuma a ina ya ga Josephine ɗin?. Katsesu Lion ya yi da cewa "Its okey dad, komai ya wuce, ni zan yi bincike a kai, dan haka kada ku sake tambayar John, kada wanda ya sake tayar da maganar nan, Areef go out let's talk". Gabaɗaya ɗakin jikinsu ya yi sanyi, daddyn Rimsha da yake ta ƙoƙarin ya ga sun yafe wa mahaifiyar tasu dan a nashi hangen ba ita ce mai laifi ba daddynsu ne da laifi, amma sai ga shi yau kuma ta yi wani abin da duk mai hankali ya san me hakan yake nufi, kenan da gaske tana tsafi? Kenan ba kungiyar matsafa ɗaya ta shiga ba ne ko ya ya abin yake? Wannan chain da aka cire a wuyar Akila chain ne mai matuƙar haɗari, yana haɗe ne da guba mai karfin da samun maganinsa yana da matuƙar wahala a duniya, sannan an tsafe chain ɗin sosai ta yanda ba wan da zai ga ne cewa na tsafi ne, Aseef ya taɓa chain ɗin har ya ɗaura mata a wuya lokacin da zasu fita zuwa wajen cin abinci, amma lafiya lou ya ci abincin ba tare da wata tangarɗa ba, ita kuma ɗan shafa chain ɗin da ta yi tana ta cewa ya yi kyau ya yi kyau tana yaba kyautar surukar tata tana murmushi, shi ne musabbabin kunnuwar gubar dan dama saboda ita aka yi shi, dalilin kenan da ya sa tana fara cin abincin poison ɗin ya hau kanta ta fara fitar da kumfa, dan ita jinin Hajiya Umaiya ce ma yasa abin bai yi mata kaca kaca lokaci guda ba, da su Rimsha ne izuwa yanzu namar jikinsu ma sai ya zama green color saboda karfi gubar nan haɗe da tsafi, ba sai na gaya muku ba, kun san jinin Hajiya Umaiya baya taɓuwa, yanzu ma dan abin mai bala'in karfi ne yasa ya jijjiga Akilar har haka, amma babu wani ciwo da ya ji mata daga ta ciki, babban nasarar da suka yi kuma lokacin da ta faɗi tana fitar da kumfa a palo, sai ya zamana Aseef ɗin ne kawai ya ɗauketa, daddyn Rimsha ya taɓata lokacin da suka shigo da ita ɗaki, amma shi saboda ya yi askar na safe sai abin bai shafe shi ba, an yi sa'a Jehan bata taɓa ta ba, da wlh sai gawa, su dai jinin William ɗin su suka taɓa ta, shiyasa duk abin bai kama su ba, dan ba dan su aka haɗa ba, dan bakaƙen fata dake kewaye da su aka yi. Jugum jugum suka zauna a cikin ɗakin, shi kuma daddynsu Lion ya koma wajenta dan ya cigaba da bata kulawa, duk wannan abin da suke yi Aseef yana kwance idanunsa biyu, amma ko motsi baya yi, daddyn Rimsha ya tsorata sosai, tunaninsa kuma damuwarsa ɗaya shi ne Allah yasa kada su ja ƙwaƙwalwar Aseef ta koma kamar ta baya, sai tayarwa da bawan Allah hankali suke yi, suna jefa shi cikin masifa da bala'i, lokacin aurensa da Akila ya sha dakyar bawan Allah nan, yanzu kuma sun sake jefa shi cikin masifar da ta fi ta baya, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, a garin haukarsu na cewa basu son bakaƙen fata ga shi zasu kashe ƴaƴan nasu da kansu, dan kuwa a ƴanda TRIPLETS suke a yanzu, wlh duk wanda aka ce ta mutu daga cikin matansu, to fa sai ta Allah da wuya idan suma basu mutu ba ko wani abin ya same su, dan fa sun kamu da muguwar soyayya mara jin magana, bata sauraron maganar kowa sai na masoyan nasu, fatan mu dai Allah yasa waƴan nan masu jajayen kunnuwa su gane gaskiya su hakura kawai su kyale TRIPLETS da farincikinsu wato matansu. Sai addua'o'i daddyn Rimsha yake tofa Aseef ɗin, amma ko motsi bai yi ba, kuma idanunsa biyu yana kallon kowa a cikin ɗakin, yanzu ma sam ya dai'na hawayen da yake yi tamkar ba shi ba, sai dai jawur ɗin da idanun nasa suka yi kamar wuta ne zai nuna maka yana cikin tsananin tashin hankali. Areef yana fita waje Lion ya ce mishi "Ka bani amsar tambayar da na yi maka, meyasa kake magana da ita?". "Nothing kawai dai ina so ne naga ko da ba zan je kusa da ita ba, in rinƙa kiranta a waya mu gaisa, in kuma ji idan tana buƙatar wani abin, shi ne kawai yasa nake kiranta". "To meyasa ka gaya mata Aseef ya yi aure?". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Seriously Lion ban gaya mata Aseef ya yi aure ba, ba mu yin irin wannan hirar da ita, gaisawa kawai muke yi sai in tambayeta ko tana bukatar wani abin, amma ana gobe su dad zasu zo Nigeria ta ce mini zata bawa John gift ya kawowa matan da zamu aura a matsayinta na suruka, ni ban tambayeta waye ya gaya mata zamu yi aure ba, dan ban cika jan magana da ita ba, ban kuma ce mata a'a ba, sai na ce mata to kawai zan gayawa John ɗin ya je ya karɓa, bayan mun gama magana da ita na sanar da TGA ya ce da John ya je New York ya karɓo mini saƙon, so ni daga nan na fita harkarsu, ban san ya karɓa ko bai karɓa ba, ban san ya suka yi ba, ban kuma san menene ta ba shi ba, so ban san ya aka yi ya bawa matar Aseef ba". Nisawa Lion ɗin ya yi kafin ya ce da Rimsha dake kwance a jikinsa "Ina kyautar da John ya baki?" Ɗan ɗago kai ta yi tare da yin shiru tamkar mai tunani dan ita ta manta ma da in da ta ajiye abin. Zuba mata idanu suka yi daga shi har Areef ɗin suna kallonta, wani irin giyar soyayyarta ne take kara fusgar Lion, musamman da ta ɗaga dara daran idanun nan nata sama tana tunanin in da ta ajiye chain ɗin, hakan ba ƙaramin tafiya da imaninsa over ya yi ba. "Sister kin manta da ni ko?" Cewar Areef, sauko da idanunta a kansa ta yi tana ƙoƙarin yin magana Lion ya rufe mata baki yana faɗin ta bashi amsar abin da ya tambayeta first tukun nan. "Yaya Saif kyautar da John ya bani fa ina ga yana gida cikin drawer kayanmu, dan zan tafi school ne da safe ya bani, sai na kai ɗakinmu na ajiye na tafi, daga school kuma sai nan muka zo ai, so yana cikin drawer". "Da ke da waye ya bamawa?". Kwantar da kanta a saman kinjin nasa ta yi tana faɗin "Lokacin ni da Jehan ne kawai a palon saman, ya bawa Jehan ɗin ta ce bata buƙata, na ce ta karɓa mana ta ajiye ta ce mini bata yi ra'ayi ba kuma ba zata karɓa ba, shi ne ni na karɓa dukka biyun har da natan a kan idan na dawo daga school zan lallaɓata ta karɓa". Nauyayyar ajiyar zuciya Areef ya sauke, shi dai masifar Jehan ta yi mishi rana ato, shiyasa yake bala'in son masifar nan tata, dan kuwa tana tsare kanta daga shiga bala'i sosai, da yanzu irin Rimshar ce ita, ai da ta karɓa ta koma ɗaki ta buɗe kwalin ta ciro shi ta saka a wuyarta, ai da tana ciro shi ma zata zube kasa kafin a kawo mata wani taimako ta mutu, amma sai Allah yasa ita ɗin ba komai ne take kulawa ba, wannan abin ya yi mishi daɗi, ya ji ya kara sonta sosai, wlh da Rimsha ba school zata tafi a lokacin ba, da tsab zata je ɗaki ta buɗe kwalin ta cirosu dan ta ga menene a ciki ki, kai Jehan duniya ce, mace mai jan aji da tsare gida da halin ko in kula ga masifa da faɗa ma ta yi a rayuwar nan, musamman irin ita Jehan ɗin da idan ka iya zama da ita zaku zauna lafiya, raini ne bata so, bazata shiga harkar ka ba, kai ma kada ka shiga tata, abin da yasa kenan bata karɓi kyautar John ɗin ba, saboda a cewarta babu wani abin da masu jajayen kunnuwar nan zasu bata da bata da shi, ita tafi karfin wani ma ya yi mata kyauta, bare ma yanda suke dirama da Areef ai ba zata karɓa ba dama. "Areef sai ka je ka ɗauki chain ɗin dukka biyu ka haɗa dana matar Aseef ɗin ka kai mini bedroom na sai na dawo, na gaji da wannan bala'i na daddy da mummy, amma bari na dawo duk sai na yi maganinsu, ka ajiye komai yanda ya dace sannan ka kwantar da case ɗin sai na dawo, ka da ka sake kiranta a waya kuma daga yau, za mu yi waya anjuma!!". Okey ya amsa mishi da shi, sannan suka yi sallama. Cikin shagwaɓa ta ce "Yaya Areef wato ma katse kiran ka zaka yi ko? Ina jiran ku gama magana shi ne har da cewa yaya Saif sai anjuma kenan?". Tana magana har da turo baki, "Sorry our Queen, ai naga kamar baki tare da ni ne shiyasa na ce bari na barki sai kin sauko ki ɗauki wayarki". Areef sarkin iya magana a dunkule, nan ma magana ya gaya mata daga ita har Lion ɗin, dan Lion ne ya ce mishi zasu yi waya anjima abin da bai taɓa ce mishi ba, hakan na nufin yanzu lokacin matarsa ce kenan, ita kuma ta wani lafe a saman kirjin mijin nata tana wasa da yatsun hannunsa ta ce wai zata yi magana da shi, lallai sun raina mishi wayo nema, shi ne ya yi musu magana a dunkule, wai sai ta sauko ma'ana sai sun dawo cikin hayyacinsu sai ta neme shi, kai Areef ba dai iya magana da sa ido ba. "Kai yaya Areef ɗazun fa na yi maka magana". Miƙa mata wayar Lion ya yi tare da sauketa daga jikinsa ya miƙe ya nufi waje, dan hiran Areef da Rimsha sai su, so yana son ya yi magana da sojojinsa. Shigewa cikin bargo ta yi suka fara zuba hira da Areef ɗin, yana magana yana nufar bedroom nasu dan ya je ya kwaso chains ɗin. Yana shiga ita kuma Jehan tana fitowa, ta sha wanka fes tamkar ba ita ce ya gama ruwan hawaye ɗazun a ɗakin Aseef wajen Akila ba, ta shirya cikin wani shegen dogon riga mai bala'in kyau launin pink color, ta yafo mayafinsa a kanta, kyau iya kyau ta yi, bata yin make up, saboda su natural beauty ke garesu ita da Rimsha, halittar idanunsu ma tamkar waƴan da suka sa kwalli, lips nasu pink color ne sosai irin na Naurat, gashin gerarsu tamkar an zana, ga dogon hanci har baka, kyakyawan kuma bakin saje kwance musu a gefe da gefen fuskarsu, to me zasu kara a face ɗin nasu? Ai babu, komai normal ne. Tare mata hanya ya yi yana tambayarta da ta yi wannan uban kyau haka ina zata je, ko sannu bata ce mishi ba, ɗaure fuska sosai ya yi dan kishinsa ta motsa shi ma, ta zauna ya yi irin wannan haɗuwa haka kuma ta ce zata fita yana tambayarta ba zata ba shi amsa ba, to wlh bata isa ba, cikin nuna isa ya ce ina zata je?!. Jin yanda ya yi maganar babu wasa a lamuransa ne yasa ta ɗago ta kalle shi, wani irin dukan uku uku kirjinta ya yi ganin ya ɗaure fuska sosai, cikin sanyin murya ta ce "Zan je ne daddy ya kaini wajen yin lalle da gyaran jiki". Tana magana tana turo ɗan bakin kamar wanda aka sanya magana dole. Katse wayar da suke yi da Rimsha ya yi tare da gyara tsayuwarsa a bakin kofar yana kare mata kallo. "Malam ka bani hanya na wuce". Duk in zata yi magana da shi bata taɓa kallon cikin idanunsa ta gaya mishi magana, a'a tana kallon kasa take duk wannan rashin kunya da take yi mishi, bata da kwarin gwiwar iya kallon cikin idanunsa. "Please kada ki yi lallen kin ji ko? Wlh dukkanmu TRIPLETS ba mu kaunar wannan abin ko kaɗan, idan kika yi zan yi amai sosai, akan hakan kuma ranar Saif ya yi wa sisterta mummunar hukunci, dan ta yi lalle, haka Allah ya yi mu, kyama yake bamu sosai da sosai". Kallon sama da kasa ta yi mashi kafin ta ce "To ni dama ina ruwana da ku? Ko dai ina da wani relationship da kai ne? Ni dan Allah bani hanya na wuce hai, kada ku so lalle dan Allah" A karshen maganar tata sai ta yi da Hausa yanda ba zai ji ba, ta ce "Ai ko dan na ganka cikin bakin ciki, wlh dole sai na yi lalle, ba dai yau na ji abin da baka so ba? To kana tsaka mai wuya, lalle kullum ba fashi, iskancin banza dana wufi, ba Saif ba zan ga uban da ya isa ya hukuntani a gidan nan dan na yi lalle". Ta kai karshen maganar tana jan tsaki tare da raɓawa gefensa ta nufi hanyar fita daga ɗakin. Cikin sauri ya sha gabanta yana faɗin "Seriously i can't believe it gaskiya, ki ajiye zancen lallen nan dan ba zan yarda ba, in fact baza ma ki fita ba". "Wai kai uban me muka haɗa da kai ne da kake addabawa rayuwata? Me na tare maka? Meyasa sai ni kaɗai ka takurawa a duk waƴan da suke cikin gidan nan?". "Because I love you mana, shiyasa nake takura miki, kuma ba zan daina ba har sai ranar da kema kika furta mini kalmar you love me, idan kuma kika ki, to for sure za'a ɗaura auren mu this week, ni wlh na fi karfin ma naje neman aure, sai dai nasa a ɗauko mini yarinya a kawo mini ita, ni kuma na turawa babanta sadaki tare da bawa Sultan umarni akan ya ɗaura auren kawai, amma ke abin da yasa nake binki a hankali, saboda kaunarki nake yi ba so ba, kuma saboda ke ƴar uncle ce, dole nayi abin da zai sanya uncle na farinciki, amma ban da haka wlh nafi karfin neman soyayyar mace!". "To dama waye ya kiraka a nan? Ba sai ka kara gaba ka nemi wata matar ba, ni dai ma ce bana.....". Ta kasa karisa maganar saboda nauyi da kalmar ta yi mata, a kullum mummynsu tana ja musu kunne a kan su tinkari mutun baki da baki su ce basu son shi, saboda ɗan adam ba abin yarda bane, zuciya bata da kashi, karya ne a duniya ka ce kasan mutum 100, hakan ba zai yiwu ba, ka dai san abin da ya yi niya ka sani dangane da shi, amma mutum shi kaɗai yasan zuciyarsa ya san wanene shi, so kuskure ne babba ka ce da mutum baka son shi a gaban idanunsa, baka san me zai iya aikata maka ba, ko a bayan idanunsa ma bai kamata ka faɗa ba, dan maganar tana iya koma mishi, idan baka son shi sai ka bar abin a ranka kai kaɗai kada ka kuskura ka gayawa wata or wani, Allah kasa mu dace. "Meyasa baki karisa maganar ba?". Ya tambaya yana matsowa kusa da ita, shiru ta yi bata ba shi amsa ba. "Jehan ni fa wannan faɗar ta ki ma kara saka mini kaunarki yake yi a cikin zuciyata". A duk lokacin da furta kalmar sunan Jehan, har cikin ranta take jin sunan, ya iya kira tamkar a bakinsa aka halicci sunan, idan ya kira har wani sanyi take ji a zuciyarta, sai dai kuma bai cika kiran sunan ba, sai idan zai yi mata magana serious ba wasa ba, shi ne zai ambaci sunan dan ya san idan ya ambata, zata natsu ta bashi hankalinta. (Bari mu bar waƴan nan ƴan diramar mu je mu leƙa su Meesha mu dawo, kafin nan kila Jehan ta tafi wajen lalle, dan fa ta ce sai ta yi🤣 ana life a TRIPLETS wlh, yau abin nema ya samu, Jehan ta gano abin da Areef baya so, Malam Areef ka shiga uku👊🤣🤣 zamu dawo nan da ƴan mintoci, dalili tasa dole mu bar wajen nasu yanzu.) Lion yana fita daga cikin bedroom ɗin nasu ya ci karo da Mark dake zaune saman chair dake kusa da bedroom ɗin nasu ya yi shiru, bawan Allah Brady ya kwace mishi waya ya kai wa Rimsha. Ko kallon in da yake Lion ɗin bai yi ba ya wuce wajen sauran sojojin dan ya yi magana da su, ita kuma Rimsha ta kwanta tana ta yi mishi taɓe taɓe a wayar tasa, Brady ya koma saman table yana cinye abincin da ta gudu ta bari, ga wayar Mark a saman table ɗin, ɗan kaniyar kare bai mayar mishi ba, yabar Mark ɗin a cikin tunani. A haka Lion ya shigo ya samesu, sam bata san da Bradyn a cikin ɗakin ba, a tunaninta ya bi Lion, cikin harshen Spanish ya ce da Bradyn ya ɗauki wayar Mark ya mayar mishi da kayansa, haushi ya ɗan yi alamar amsawa kenan kafin ya ɗauki wayar da sauri ya nufi waje. Shi kuma Lion saman bed ɗin ya hau tare da sanya hannu ya karɓi wayarsa, hotonsa take ta faman kallo abinta, hannu tasa ta rufe idanunta tana murmushi, ta ji kunya ya kamata tana kallon hotonsa a karo na biyu kenan yau kawai. Yatsa ɗaya ya sanya mata a ciki dimple nata da suka lotsa yana kallon ɗan bakinta da take zuba murmushi, ga fararen hakwaranta da suke tas tamkar audiga, kamar bata taɓa cin wani abin ba saboda haskensu. Shiru suka yi almost 5 mins a haka kafin ta ɗan zame hannun nata a hankali ta buɗe idanunta ta saci kallon shi, karaf suka haɗa idanu, da sauri ta mayar da hannayenta dukka biyu a saman face ɗin nata tana cigaba da murmushi, hannu ɗaya ya kai ya zame hannun nata yana faɗin ta buɗe idanu. Turo baki ta yi tana faɗin "Yaya Saif Allah kunyarka nake ji, ni ba zan iya buɗe idanuna na kalli cikin naka ba". Sunan kunyar ma yau ya fara jinta, dan haka sai ya ɗaura hannunsa a saman lallausan kumatunta tare da rankwafowa kanta yana faɗin "Open your eyes i said". Tamkar zata yi kuka ta waro idanun nata waje tana turo baki kamar biro, yaya Saif ɗin nan nata ya cika takurawa mutun, a cewarta. Zubawa laɓɓansa idanu ta yi tana kallon yanda suka yi ja sosai, shi kuma ya zuba nata idanu ido yana kallon kwayar idanunta, kiran sallar da wayarsa ta fara yi ne yasa ya ɗan kawar da kallonsa izuwa kan wayar tasa, lokacin sallah ya yi, mikewa ya yi dan baya wasa da lokacin sallah sam, kome yake yi da lokaci ya yi zai ajiye dan gabatar da sallah, shi yasa akoda yaushe yake yin nasara a kan makiyansa, saboda baya jinkiri wajen gaishe da ubangijinsa, shiyasa ubangiji ma baya jinkiri wajen biya mishi bukatunsa, wannan faɗi ne na Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, matukar zaka yi aikin Alkhari da bautar Allah a kan lokaci, to shi ma ubangiji zai zama mai amsa maka buƙatunka a kan lokaci, sallah ba abin wasa bane ƴan uwa, shi ne aiki na farko da ake fara bincika a ranar tashin kiyama, idan ta yi kyau, to fa ana sa ran ka tsira, idan bata yi kyau ba, kofar azabarka ce ta buɗe, Allah ka bamu ikon yin sallah a kan lokaci. After some hours, bayan sun yi sallar isha, Mark ya kawo musu abinci, kin ci ta yi, shi kuma ya ci ya ƙoshi dan bai san cewa fushi take yi ba, da ya ce ta zo taci abincin, sai ta ce mishi ta ƙoshi, dan haka sai ya ci kayansa kuma ita ta yi serving ɗin shi. Bayan ya kammala ta haɗa kayan abincin zata fitar da su ya ce ta barsu a wajen Mark ya zo ya ɗauka, kuka ta saka mishi tana turo baki, idanu ya zuba mata yana kallon ikon god, sai da ya ga da gaske take kukan nata ga hawaye wani na bin wani ne yasa ya ce "Lafiya dai ko?". Kara sautin kukan nata ta yi tana cigaba da turo baki. Ɗan dafe kansa ya yi, shi dai bai san yaushe Rimsha ta dawo irin Aseef ba, yarinya sai shagwaɓa kamar ba gobe, amma dai tana burge shi over idan tana yi, har wani sanyi yake ji a cikin zuciyarsa. Ɗaukarta ya yi cancak suka nufi saman bed yana tambayarta menene ya sameta. "Yaya Saif to ba kai ne ba?". Tsareta ya yi da idanu ba tare da ya sake yin magana ba. "Na ce maka ni bana son Mark ya rinƙa kawo mana abinci, zan je in rinƙa ɗaukowa, amma shi ne ka bari yanzu ma ya shigo mana da abincin, kuma ka ce ya zo ya kwashe kayan abinci, shiyasa na yi fushi kuma ba zan ci abincin ba". A tsananin shagwaɓe ta yi maganar, yanda ta yi maganar kuma dole shi ne ya amsa mata da okey ba dan ya so ba, saboda ta saukar mishi da kasala, ta sanya shi shiga cikin yanayi, ta rikita mishi kwakwalwa da shagwaɓar tata, uwa uba da ta kai karshen maganar sai da ta sanya ɗan bakinta a saman kumatunsa ta ɗan ciza dan ta huce haushi, hakan da ta yi ba ƙaramin kara birkita mishi lissafin ƙwaƙwalwa ta yi ba. Saman bed ɗin ya sauketa tare da nufar toilet yana faɗin, to ta je ta ci abinci, Mark ba zai sake shigowa ba, shi zai ɗauko abincin da kansa tun da haka take so. Sosai ta ji daɗi, shi dai Lion akwai tsananin kishi, ba zai iya barinta ta fita ta keta cikin sojojin nan ta shiga kitchen wajen Mark ta ɗauki abinci ba, gara mishi Mark ɗin ya kawo mishi abincin kofar bedroom nasu shi ya fita ya karɓar, e lallai Rimsha ta ciri tuta ko a iya haka, dalilinta ne yau zai rinƙa karɓo musu abinci da kansa?!! Abin da mamaki, kishi dai yau ta yi amfani. Wanka ya yi ya shirya cikin kayan barci ya zo ya kwanta tare da jawo wayarsa yana tunanin me zai hana ya fara bincike a kan Josephine yanzu tun da baya aikin komai?. Ita kuma abincin ta ci ta gama, sannan ta wuce toilet ta yi wanka tare da yin shirin barci sannan ta hau saman sofa ta kwanta sai zuba kamshi take yi, ga kayan barcin nata ma wasu irin kaya ne wanda suke ƴan sharara sharara marasa nauyi, riga ce mai ƙaramar hannu kamar na vest, sai dogon wando har kasa. Har ta kwnata ta sake miƙewa ta feshe musu cikin bedroom ɗin nasu da air freshener mai bala'in daɗin kamshi wanda Lion ya ɗauko musu, bayan ta kammala ta zo ta kwanta a saman sofa, shi kuma Brady yana wajen Mark, dama shi yawonsa yake tafiya sai lokacin da ya ga dama yake shigowa, yau kam ma da gangan Mark ɗin ya rike shi su yi hira tare, dan yau ba'a gida suke ba, babu su Tyrone, ba abokan hira, shi ne ya rike Bradyn dan ya rage mishi kewa. Yana ƙoƙarin miƙewa ya ɗauko laptop nasa dan ya fara bincikar tsakanin daddynsa da Josephine wai waye ne mai gaskiya a cikinsu? Wannan abin ya fara damun shi sosai gaskiya, yana da bukatar sanin gaskiya a yanzu kam. Bai kai ga miƙewa ba Malika ta fito a siffar dodo ta tsorata Rimshar, tana tsaka da tunanin Lion ɗinta kawai taga abu ya fito kamar wani shaiɗani ga kawo ɗaya a tsakiyar kai, idanu kamar zasu zazzago waje, wani mahaukacin ihu ta kurma tare da mikewa a guje ta nufi saman gadon, ta san dai duk wani bala'in da ya ta so Lion ɗinta ne kawai zai iya tare mata, shiyasa shi kaɗai take nufa idan wani abin ya taso. Yana ƙoƙarin miƙewa ta haye jikinsa tana ihu, shi kuma bawan Allah bai ga komai ba, dan Malika wa iya Rimshar kawai ya fitowa, da yake tasan ba zasu ji ta ba, sai ta yi dariya tana faɗin "Ƴar kaniya kawai, zaki wani zo ki kwanta a saman sofa ki bar mana angon mu shi kaɗai a saman gado, wato baki ji nasihar Akila ba kenan? Mu samu da kyar mun tayaki yaki a kan soyayyar taki ne har kika samu nasara shi ne kike kokarin watsa mana kasa a idanu ki ruguje komai ta hanyar yin nesa da shi ko? To mu zuba da ni da ke ƴar nema". Ta kai karshen maganar tare da kwashewa da dariya sannan ta ɓace ɓat kamar wata walkiya. Ita kuwa Rimsha ta kankame shi sosai tamkar zata koma cikin jikinsa, sai ihu take kurmawa kamar ba lafiya ba, su kansu sojojin Lion ɗin sai da suka yi mamakin irin ihun da take yi, yarinya kamar kanta akwai motsi, basu san cewa Malika ce ke yi mata tsiya wani lokacin ba, ta razanata tasa ana yi mata kallon mahaukaciya ko tana da matsala a kwakwalwa. Ganin yanda jikinta yake kerma sosai ga kuma kuka da take yi ne yasa ya ɗago kai dan ya ga ko dai Brady ne ya tsoratata, bawan Allah shi bai ga komai ba, ɗago haɓarta ya yi dan ya rarrasheta ta yi shiru ta gaya mishi menene, amma ina ta ki yin shiru, dan fa ba karya ta tsorata iya tsorata, irin wannan halitta da daddare haka ya fito maka ba tare da ka shriya ba, dole kwakwalwa ta juye. Sai ambatar sunanta Meesha yake yi, amma ina sam bata jin shi, sai ihu sosai take yi, hakan yasa ya haɗe bakinsa da nata dan ya sata ta yi shiru, kara kankame shi ta yi tana jan numfashi da kyar da kyar. Sai da ya tabbatar da ta sami natsuwa ta yi shiru sannan ya saketa yana mai ɗago haɓarta, ta runtse idanu gam hawaye na zuba daga idanun nata. "Meesha why are you crying?" Cikin kuka murya a dashe ta fara magana da kyar da kyar "Yaya Saif dodo na gani fa". Sake ɗago idanu ya yi yana bin ɗakin da kallo, ganin ba komai ne yasa ya fara tofa mata addua'o'i kawai, dan a tunaninsa tsorata ta yi, dama ya san ta da shegen tsoro, ga shi kuma ta ga a cikin ruwa suke, kila ta fara barci ne ta yi mafarkin sun nitse cikin ruwa, shi ne ta farka take yi mishi ihu wai dodo ta gani, ko a ina taga dodon ƴar rigima kawai, haka yake ta tunani a ransa. Yana tofa mata addu'a yana shafa bayanta a hankali hankali alamar ta yi barci to. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne. KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ 👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊ *Domin samun karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581* 74 Yana tofa mata addu'a yana shafa bayanta a hankali hankali alamar ta yi barci to. Cikin ɗan ƙanƙacin lokaci ta samu natsuwa sosai saboda karfin addu'a, sai sauke ajiyar zuciya take yi tana jan hanci, ta ci kuka ba karya. Jin ta samu natsuwa ta kara lafewa a jikin nasa tamkar mai jin barci ne yasa ya ɗan rankwafo da kansa a kanta tare da dakatawa daga addu'ar da yake tofa mata. Can kasan maƙoshinsa tamkar mai raɗa ya furta "Meesha". Ɗan ɗago kanta ta yi tana kallon lallausan laɓɓansa, ta kasa kallon cikin kwayar idanunsa, "Are you okey now?". Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "Yes am okey, amma kuma ina jin sanyi sosai yaya Saif". Kallon yanda take aiki tura ɗan bakin nata ya yi. "Meyasa kika cike tsoro har haka ne?". A shagwaɓe ta ce "Ni fa yaya Saif ba tsoro nake ji ba, da gaske ne naga dodo irin wanda gwaggo take bamu labarin shi a tatsuniya". Sam bai gane in da zancen nata ya dosa ba, wai ana basu labari a tatsuniya, kai Rimsha duniya. Canza topic ɗin maganar ya yi da cewa "Anywhere, yanzu dai a duk lokacin da kika tsorata, ki kasance sunan Allah shi ne abu na farko da zaki fara ambata ba ihu ba, idan kina ihu a duk lokacin da kika tsorata hakan zai bawa shaiɗanun aljanun dake kawaye da ke su iya shiga jikinki har su cutar dake, so be careful". "Tom yaya Saif zan kiyaye". Ya ji daɗin amsar da ta bashi, bata yi ƙoƙarin kare kanta ta hanyar yi mishi musu ko wani abin ba, yasan ita mai addini ce, yasan ta tsorata sosai ne da har ta manta bata furta sunan Allah, amma sam bata yi ƙoƙarin gaya mishi ta tsorata ne yasa ta kiɗime bata yi hakan ba, sai kawai ta amsa mishi da to zata gyara, ya ji mugun daɗi, dayawa daga jikin maza haka suke, sun san komai, amma zasu rufe idanu suyi ta faɗa a kan abin da suka san bake kika yi shi ba, idan baki yi masu musu ba, kika basu hakuri, wlh ba ƙaramin daɗi suke ji ba, zai wuni a cikin zuciyarsa yana sanya miki Albarka, idan kuwa kika yi ƙoƙarin kare kanki dan ki gaya mishi gaskiya, to zaku yi faɗa ne a banza dan ba zai karɓi kuskurensa a wannan lokaci ba, so yana da kyau mata ku lura a kan hakan, ba ko wani lokaci zaku yi musu da su wajen sawa su gane baku da laifi ba, sun san komai, wannan hallitta ce da Allah ya yi musu na ba zasu nuna sun sani ɗin ba, zasu ga kamar idan suka yi hakan zaki renasu ko makamancin haka, ya kamata mata mu waye a kan karatun maza, mu karancesu tsab. "Why are you always looking at my lips?". Ya tambayeta yana ɗauko wayarsa da ta yi ƴar kara alamar shigowar saƙo. Massage ne da ɓoyayyiyar number, gargaɗi ake yi mishi da babbar murya a kan kada ya yarda ya tonowa kansa abin da zai bin ne kansa da kansa, guntun tsaki ya ja tare da goge saƙon ya ajiye wayar a ransa yana faɗin Wai su kam basu sam shi abin da ba'a so shi yake aikatawa ba ne? To wlh sai ya yi bincike ya gano wasu kungiyar matsafa ne Josephine take ciki, yana da yakinin sune suka turo mishi wannan shirmen banzan da wofin, sun ja ma ya ji yana bala'in kaunar binciken yanzu, kuma sai ya yi idan sun isa kada su bari ya kwana yau, iskancin kawai, har shi za'ayiwa barazana, to wlh sun ma taɓowa kansu ne, sai ya yi abin da basu taɓa zato ba, amma ya ɗan yi mamakin a ina suka samu numbersa, sai dai bai damu ba dan yasan number Nigeria ne, da numbersa na Usa ne wlh wane kaniyarsu su iya turo mishi saƙo kuma har ta shigo, ba zata shiga ba ko sun tura, dan ba kowani shirme yake shiga wayarsa ba. Yana tunani yana shafa bayan matar tasa yana jiran ta bashi amsar meyasa take yawan kalle mishi lips. "Allah yaya Saif lips ɗin naka ne suna yi mini kyau". "Serious?" Ya yi maganar yana ɗaga gera ɗaya, tamkar walkiya ta ga ɗaga gerar tasa, dan ta wutsiyar idanunta ta ga hakan, cikin sauri ta ɗago da kallonta zuwa saman face nasa da kyau, dan ta tabbatarwa da kanta da gaske gera ɗaya ya ɗaga irin na Areef ne?. Tana ɗago idanu ya sake ɗaga mata gera ɗaya ba tare da ya yi magana ba, ba ƙaramin ruwan mamaki ta sha ba, wato shi ma ya iya ɗaga gera guda kenan? Lallaima yaya Saif ɗin nan, wato dai babu abin da bai iya ba shi ma, kawai yi ne ba zai yi ba, amma yanzu ga shi da lokacin yi ɗin ya yi ai yana yi. Number Sultan ya kira dan ya gaya mishi su fara sauke mishi Alqur'ani mai girma dan zai sake komawa wannan shegen case ɗin na matsafa, a ko da yaushe shiyasa Lion yake nasara a rayuwarsa, ga shi dai shi Bature ne kuma krista ne ya musulunta, amma duk abin da zai yi Allah yake fara sakowa a gabansa kafin komai, Allah kaɗai yake kaiwa kukansa, baya tsoron wani mahaluki a duniyar nan, baya shakkar kowa. Sai dai fa abin mamakin duk da wannan abin da ya faru sun fi jin Josephine ɗin a ransu sama da daddy, sun rasa meyasa suka fi kaunarta. Bugu ɗaya Sultan ya ɗauka, cikin sanyin murya suka gaisa, sannan ya gaya mishi buƙatarsa, shiru Sultan ɗin ya ɗan yi kafin ya ce mishi "Amma Saif da ka bari sai ka koma tukun nan, akwai haɗari sosai, saboda kaga in da ka nufa yanzu waje ne mai haɗari, sannan tafiya kake yi a cikin ruwa, kasan kuma a cikin ruwan nan babu abin da babu, akwai shaiɗanun aljanu sosai, kuma aiki ne da ya shafi tsafi da shaiɗanun aljanu, ni dai a nawa shawarar zan so ka bari sai ka fita daga cikin ruwan nan, ka koma gida lafiya lou, sai mu ɗaura ko?". Kallon Rimsha dake ta faman kallonsa ya yi yana tunanin wannan ƴar rigimar tasa ma ba zata iya ɗaukar wannan kasada ba, tana jin motsi zata zunduma mishi ihu ta hana shi yin aiki, so Sultan yana da gaskiya, ko dan ma Rimsha zai hakura sai ya koma ɗin, kuma yana ganin girman Sultan sosai, dattijo ne sosai wanda a kallah zai iya kai shekaru 60 zuwa 70, sai mai taimakinsa wato ladan ɗinsa wanda sunansu iri ɗaya da Sultan ɗin, shi ma baban mutun ne, so ba karya Lion yana ganin mutuncin Sultan tun lokacin da ya musulta. Hakan ta sa ya ce "Okey uncle i will think about it". Addua'o'i sosai kamar yanda ya saba Sultan ɗin ya yi mishi, shiru ya yi yana sauraron addua'o'i suna ratsa shi tare da sanyaya mishi zuciya, har sai da ya kai karshe sannan ya amsa mishi da Amin uncle......... Ai ko dan addua'o'i da Sultan yake zuba mishi ma dole zuciyarsa ta yi ta sanyi tana rage zafi, dole ya sauƙo, ai addu'ar manyan malamai ba wasa ba. Karin wata haske na abin da baku sani ba, perfume ɗin Lion Sultan yake haɗa mishi ita, shiyasa basu shiri da duk wani shaiɗanin aljani, basu haɗuwa waje guda, to Sultan yake haɗa mishi ita haɗi na musamman, shi ya zaɓi irin kamshin da yake so, sannan Sultan yake tofe mishi ita da addua'o'i masu karfin gaske kafin ya bashi, ainahin turaren daga Dubai yake sayosu ya kawowa Sultan ɗin, idan ya gama haɗa mishi su sai ya kira shi a waya a kan ya aiko a ɗauka mishi, to kun ji tushen perfume ɗin nan, duk wani shaiɗanin aljani ba zai taɓa zama kusa da wannan perfume ɗin ba, ko aljanune a jikinka in dai masu cutarwa ne shaiɗanu da an shaka maka zasu gudu. Da haka suka yi sallama ya ajiye wayar yana mai dawo da kallonsa a kanta, cikin sauri ta runtse idanu tana murmushi, ba ƙaramin kyau ta yi ba, hannunta ya riko cikin nasa yana kallon ƴan yatsun nata, tunanin maganarta na ɗazun ne ya faɗo mishi a ransa, a in da take cewa yaya Saif lokacin fa da aka yi mini wannan zanen ina yarinya ce, tunani ya yi wato ita yanzu ji take yi ta girma kenan ko? Wai da tana yarinya, kai wannan ƴar rigimar tasa akwai ta da iya magana da son girman, yanzu ma bata wuce a goyata ba wai da tana yarinya yanzu ta girma tab su babba manya. "Yaya Saif nace maka sanyi fa nake ji?". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai, shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Har a jikin nawa da kike kwance ma?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e tana faɗin "To ai yaya Saif kai ma kayan narci ne a jikinka ba jacket ba, shiyasa nake jin sanyi, da Jacket ne zan shiga ciki ba zan ji sanyi ba". Shiru ya yi bai yi magana ba sai dai ya gyara kwanciyarsa da ita a jikin nasa tare da ja musu bargo zuwa wuyanta shi kuma karjinsa. Tamkar mai yi mata raɗa ya furta "To sauka mini a jikina". Make kafaɗa ta yi tana faɗin "Ni a'a gaskiya, ina tsoron dodan can Allah, haka kawai na sauka ya kamani, gara mini dai jikin naka duk wuya". Yanda take magana ba ƙaramin gigita shi ta yi ba, zuro hannunsa waje ya yi daga ta cikin bargon ya kashe wutar ɗakin ta hanyar yin amfani da remote dake saman bedside drawer, sannan ya kunna green light dake manne a sama kusa da farin wutar. "Yaya Saif in tambayeka?". Shiru ya yi bai amsa mata ba, dan sam baya jin yin magana. "Uhm uhm yaya Saif ka amsa mini mana". Yatsarsa manuniya ya sanya mata a cikin ɗan bakin nata yana wasa da harshenta dan ta dai'na damun shi da surutu, tsotsar yatsan nasa ta fara yi tana ɗan cizawa, kwace kayansa ya yi dan kada ta jefa shi cikin wani hali, kukan shagwaɓa ta saka mishi mara dalili. Shiru ya ɗan yi na ƴan mintocin da ba su wuce 2 ba, kafin nan ya ɗan juya kaɗan da ita a in da ya sauketa daga saman kirjin nasa ya zamana suna fuskantar juna, matso da face nasa daf da tata ya yi yana yi mata wani irin mayen kallon, da yake darene sai idanun nasa suka kara haske, ga kuma hasken green light na ɗakin. Cikin sauri ta runtse idanunta dan ba zata iya gani shi ba. Haɗe fuskokinsu ya yi waje guda yana mai lumshe idanunsa shi ma, a hankali ya fitar da harshensa izuwa saman lallausan laɓɓanta na kasa yana ɗan tattaɓa lips ɗin nata, wani irin yanayi ta shiga, buɗe ɗan bakin nata ta yi da nufin ta kama harshen nasa, janyewa baya ya yi yaki bata, idanunta a datse gam ta turo mishi ɗan bakin alamar shagwaɓa, bata ji daɗi ba da yaki bata. Sake zuro harshen nasa ya yi zuwa saman lips ɗin nata, a hankali yake ɗan wasa da harshen a saman lips ɗin ba tare da ya kai cikin bakinta ba, sake kokarin kama harshen nasa ta yi, ina nan ma janyewa baya ya yi bai bari ta kama ba, kukan shagwaɓa ta saka mishi tana ɗan bubbuga kirjinsa, sam bai kulata ba a karo na uku ma ya sake zuro harshen nasa zuwa saman lips ɗinta, a wannan karon ta ci alwashin sai ta kama harshen, ƙoƙarin kamawa ta yi yana ɗan janyewa kaɗan kaɗan yana janta da wayo har ta matso kusa da shi sosai, a in da ya ɗaga kai daga rankwafowa da ya yi a kanta, ya zamana yana miƙe. Kuka ta saka mishi tana kokarin barin jikin nasa, rikota ya yi tare da zura harshen nasa cikin ɗan bakin nata yana tsotsar lips nata na kasa, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da cizan harshen nasa dan ta huce takaicin wasa da hankalin da ya yi mata, bai san time da ya furta wash ba jin yanda ta cije shi, zame harshen nasa ya yi tare da kara mannata sosai da jikinsa yana shafa bayanta, har cikin ransa yake jin irin sokinsa da breast nata suke yi a kirjinsa, a da ya rainasu sosai, yanzu kuwa ga shi suna tsokale mishi zuciya, musamman ma idan ya matseta sosai a jikin nasa, shi kaɗai yasan me yake ji, dama kun sani ita ba saka breziya take yi ba, to yau ko vest ɗin ma bata saka ba dan kayan barci ne a jikinta. Hannu ya ɗaura a saman mazaunanta da suke matuƙar ɗaukar hankalinsa, kowa ya san matan Turawa basu da mazaunan mai girma sosai, sai dai shape da hips, amma basu da halittar mazaunan, akwai ɗaiɗaiku da suke da shi, amma ba su da yawa, hakan yasa nata suke matuƙar ɗaukar hankalinsa, dan ita fa tana da su sosai, a cike suke ga shape kamar me, musamman idan ta sanya kayan da suka ɗan kamata suka fito da su sosai, suna burg shi over, a duk halittar jikinta sun fi burg shi, shiyasa yake yawan taɓasu, ga soft skin nata da bala'in laushi tamkar fatar jariri, shi kaɗai yasan abin da yake ji a duk lokacin da yake taɓa skin nata, ko da hannunta ne kuwa. Shafasu ya rinƙa yi a hankali hankali har ya zura hannunsa ciki ta yanda zai sami damar shafasu da kyau, waro idanunta waje ta yi jin ya zura hannunsa ta baya a cikin wandon barcin nata, idanunsa a lumshe yana bata wani irin hot kiss cikin natsuwa mai mantar da masoyi a wani duniya yake ciki, komai nasa cikin natsuwa da kwanciyar hankali yake yi, zame hannun nasa daga mazaunanta ya yi tare da haurowa zuwa saman bayanta har izuwa gashin kanta, suman kwance ta yi mishi ta kasa wani kataɓus, ko ɗan kissing na shi da take yi ma yanzu ta dakata tana bin shi da kallo. Kamar daga sama taga yasa ɗayar hannunsa ya rufe mata idanu yana zame ɗan bakin nasa daga tata, cool murmushi ta saki, wato dai bai rufe idanunsa sosai ba yana kallon duk irin kallon da take yi mishi, Allah yaya Saif ɗin nan ma sam baka gane mishi, ta faɗa a cikin zuciyarta. "Meeeesha". Ya ambaci sunanta cikin wata iriyar murya da bai taɓa yin magana da ita ba, bai taɓa sanin ma yana da ita ba, a tsananin sanyaye muryar ta fita, ya kira sunan kuma da salo a cikin voice ɗin nasa, duk da cewa dama kullum a wani irin salo yake kiran sunan, sai ya ja sunan cikin natsuwa da jan hankali yake ambata, amma fa na yau daban ne, ita kanta sai da ta ji tamkar ba shi ba ne ya kirata, yanayin jan sunan da ya yi ma yau har da kara mata wasali, ga kuma zazzakar sexy voice ɗin nasa a tsananin nutse da kwance tamkar mai jan numfashi ne ya amsaci sunan, bugu da kari ga barci da tsananin sha'awa a tattare da muryar tasa, sai hakan ya bada wata kala mai tafiya da imanin masoya. "Na'am yaya Saif". Ta amsa mishi ita kuma a tsananin shagwaɓe tana shafa lallausan sajensa, wani irin daɗi yake ji na shafa sajen nasa da take yi. "Kwanta ki yi barci dare ya yi". Ya faɗa tare da manna mata haɗaɗɗiyar sumbata a lallausan kumatunta, ita ma sumbatar ta manna mishi a kumatun nasa tana ɗan murmushi. Shafa bayanta a cigaba da yi har barci ya yi awon gaba da ita, shi kuwa bai yi barci ba har karfe biyu na dare, a hankali ya ɗan yunkuro tare da raba jikinsa da nata, cikin natsuwa ya kwantar da ita a gefe tare da miƙewa zaune ya zuro kyawawan fararen kafafunsa kasan gadon kafin ya miƙe gabaɗaya ya nufi toilet. Wanka ya yi tare da ɗauro alwala ya fito, Sallah ya fara yi yana karatun Alqur'ani mai girma har aka kira sallar asuba a wayarsa, bayan ya yi sallar rakatainil fajir ne ya yi asuba sannan ya yi askar kafin ya mike ya nufi bed ɗin ya kwanta tare da tashinta a kan ta je ta yi sallah, miƙewa ta yi duk jikinta yana yi mata ciwo, wanka ita ma ta yi tare da ɗauro alwala ta zo ta yi sallah. Bayan ta idar ta yi askar kafin ta miƙe ta nufi bed ɗin ita ma, already ya yi barci abinsa, dan bai samu dama ya yi na dare ba, kusa da shi ta zo ya kwanta tana ɗan satar kallonsa har barci ya yi awon gaba da ita. A ɓangaren su Jehan kuwa, ɗaure fuska sosai Areef ya yi cikin nuna isa ya ce "To zo ki wuce ki je ko yi lallen in gani". Jin yanda ya yi magana ne yasa ta ɗago idanu tana kallonsa, babu ko alamar wasa a tattare da shi, nan take ta sha jinin jikinta, shiru ta yi tana tunanin to ko dai ya ji abin da ta ce da hausa ne? Bata san shi ɗin ɗan baiwa ne yana da kwakwalwa sosai ba, yana iya karantar yanayin da mutun ya yi magana a ciki sai ya gane me mutun yake son faɗa ko da baya jin yare, ko da bai gane duka ba yana cankar wasu ɗaiɗai, idan mutun yana cikin ɓacin rai ne ya yi magana, so zai iya cankar a kan me ya yi maganar, kuma bugu da kari zamansa a tare da su yau da gobe tasa yana jin wasu kalmomi masu sauki daga cikin Hausa waƴan da ake yawa ambata irinsu zo, tafi, ba zanzo ba, bana so, ina so, zan ci, ba zan ci ba, da sauran kalmomi da ita Jehan ɗin ita da Rimsha da daddy suke yawan amfani da su, so yasan wannan, ko da ta ce sai ta yi lalle, ya ji me ta ce, ya san ma'anar sai na yi, shiyasa ya ce mata to ta zo ta wuce ta je ta yi lallen ya gani. "Jehan am i your mate? Da har ni zan ce miki ba zaki yi abu ba kuma ki ce zaki yi, ni sa'anki ne? Ko don ina yawan wasa dake ne yasa kike ƙoƙarin gaya mini duk wani abin da ya zo bakinki?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Kayi hakuri". Ta yi maganar sam bata kalli in da yake ba, sa kai ya yi ya wuce zuwa cikin bedroom ɗin abinsa, shi ma bai sake bi ta kanta ba, idan baku manta ba babu abin da TRIPLETS suka tsana a duniya irin raini, basu son raini ko kaɗan, kullum yana wasa da ita baya damuwa da duk abin da take gaya mishi saboda yasan bada gaske take yi ba, cikin wasa take yi ita ma kamar yanda yake yi, amma yau kuma da gaske ta gaya mishi maganar shiyasa abin ya bashi haushi, ta raina shi kenan da har zai ce mata ga abin da baya so kuma ta ce sai ta yi, yanda ta yi magana da gasken nan yasan sai ta yin ne dan yasan wace ce ita, shiyasa ya gaya mata abin da ya gaya mata shi ma ya kuma ɓata rai. Chains ɗin ya ɗauko ya zo ya wuceta tana tsaye ya fice zuwa bedroom ɗin Lion ba tare da ya kalli in da take ba, ajiyesu ya je ya yi sannan ya koma bedroom ɗin Aseef ya ɗauko na Akilar ya zo ya haɗa, ita kuma Akila har lokacin tana sume, Aseef kuma ya samu barci bawan Allah, daddyn Rimsha ya kwantar mishi da kansa a saman sofa tare da gyara mishi kwanciyar sannan ya wuce nasa bedroom ɗin. Areef bayan ya kai chain ɗin ya dawo cikin bedroom ɗin a in da ya haɗe hannunsa da kyau ya ɗauki Aseef ɗin cak daga saman sofa zuwa saman bed kusa da matarsa, dan yafi sofar tsawo, wuyarsa zai yi ciwo a yanayin kwanciyar da ya yi, shi ne yasa ya ɗauke shi, su daddy duk sun koma bedroom nasu dan a bar Akila ta huta kada su dameta da hayaniya, daddyn ne ma bayan ya gama dubata ya ce a kyaleta ta huta, shi ne dalilin da yasa suka fice bakiɗayansu. Bedroom ɗin daddyn Rimsha ya nufa dan su ɗan yi hira bayan ya gama gyarawa Aseef da Akilar kwanciya, har da ja musu bargo ya yi dan ya lura kamar sanyi suke ji. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga cikin ɗakin, kwance ya isko Jehan saman cinyar daddy cikin yaren Hausa tana gayawa daddyn abin da ta yi wa Areef ɗin yau, ta ce daddy ya bashi hakuri dan ya ɓata rai sosai, duk yanda yake bala'in kaunarta amma yau ya shareta dan ya nuna mata kuskurenta na raini da take neman kawowa a tsakaninsu, sam ita ma bata ji daɗin abin da ta yi ɗin ba, shi ne take gayawa daddy har idanunta sun ciko da kwallah. Saman bed ɗin ya hau yana faɗin "Uncle sannu da ƙoƙari". Murmushin ya yi kafin ya ce "Areef Jehan zata je gidan yayana Deen ta gaishe su, please ka kai min ita ka ji?". Kallonta ya yi kafin ya ce "Uncle this your daughter ƴar rigima ce, yanzu kuma me zata je yi a gidan mutane? Salon ta je tana ɗaure musu fuska tare da basu command tamkar wata Captain na sojoji ko? Serious uncle ina ji a jikina duk yanda aka yi wannan yarinyar jininmu ce, kana ganinta tamkar ita take bin Lion a haihuwa, wannan da namiji ne banbancinta da Lion kaɗan ne, to kaga mu Lion abin a jininmu yake, gadon faɗar muka yi daga wajen daddynmu, ita kuma ya akayi ta zama irinmu, bata magana, ga bala'in tsare gida, ga faɗa da bala'in zuciya, iya bada command, son girma, kai komai ma". Murmushi daddy ya yi yana faɗin "Ita ma gado wajen kakanta ta yi ai, da kuma ƴan uwan mummynmu su uncle Trump, uncle Alex iyayen bala'i". "To shikenan Uncle ta shirya mu tafi ko?". Ya yi maganar yana kallonta. Cikin harshen Hausa daddy ya ce mata "Tashi kije ki shirya sai ki zo ku tafi gidan Abbi ki gaishe su, idan kuna tafiya a hanya sai ki bashi hakuri, yana da saukin kai kuma zai hakura, ki daina yi mishi gardama Jehan, Areef ba zai taɓa cutar dake ba, kuma yana sonki da gaske, wlh babu wata mace da ta isa ta tsaya tana yi mishi abin da kike yi mishi yana hakura, so ki daina kin ji? Ki rinƙa girmama shi, ki dai'na idan ya yi magana ki ce zaki bashi amsa ko da ma cikin wasa ne, kin ji ko? Ai ya fiki shekaru nesa ba kusa ba, so ki rinƙa girmama babba". Jinjina kai ta yi tana ɗan turo baki ta ce to daddy tare da miƙewa dan ta je ta shirya. Tana fita daddy ya dubi Areef ɗin ya fara magana cikin natsuwa "Nasan kana hakuri da halin Jehan, amma ka kara hakuri ka ji?". Murmushi ya yi yana faɗin "Uncle ni fa bata taɓa yi mini wani abin da ba dai'dai ba, ni halin nata ma mugun burgeni yake yi, na san cewa a haka take, shiyasa nake ƙoƙarin canzata izuwa yanda kowa yake rayuwa, ta dai'na takura kanta tana ɗaure fuska, murmushi rahmace kuma baiwa ce, ta dai'na gudun mutane tana zama ita kaɗai a ɗaki, shi ne yasa nake son na koya mata wasa da dariya, so ni bana jin komai a kan abin da yake a tsakaninmu, ni nabi ta hakan, idan ina so zan iya canza hanya, dan haka kada ka damu our daddy". Ajiyar zuciya ya sauke yana kwarara musu ruwan albarka, Amin Amin ya rinƙa amsawa da shi, a haka ta dawo ta samesu, wayar daddy ta karɓa kafin ta ce su je, okey ya amsa mata tare da miƙewa ya fito suna yi wa daddy sallama, sai kallonta yake yi da waƴan nan dara daran ash eyes ɗin nasa, ba karya ta yi kyau sosai na wuce misali, doguwar riga dai ta sanya kamar ɗazun, sai dai na yanzu ash color ne tare da yafa mayafin a kanta. Gidan gaba na motar ta shiga ta zauna, kallon sama ya yi yana kallon yanda wani bakinkirin ɗin hadari yake tasowa, ɗan kallonta ya yi kafin ya shiga cikin motar ya zauna a mazaunin driver, yanzu ya sami sauki yana iya tuki da kansa. Kunna motar ya yi suka nufi waje, tun kafin su iso gateman ya wangale musu gate ɗin, cikin natsuwa ya danna hancin motar waje. Sai shakar daddaɗar kamshin perfume nasa take yi, sun yi tafiya mai nisa tsakaninsu da gida kafin ya ce mata "Ina ne gidan? Ko dai gidansu Prof ne?". Tana ta aikin danna wayar daddy da ta karɓa, hankalinta baya a kansa, sam bata ji abin da ya ce ba, kashe motar ya yi a gefen hanya tare da juyo da kallonsa bakiɗaya a kanta, sai latsa waya take yi tana buga game. Hannu ya kai ya karɓi wayar dai'dai lokacin kuma ruwan sama ta ɓarke tammar da bakin kwarya, ɗago idanu ta yi tana kallonsa, kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Sai ki bar mijinki shi kaɗai yana ta magana ke kuma kina latsa waya ko? To maza gaya mini hanyar gidan mu tafi kin ga ruwan saman nan da karfi da kuma iska ya zo". A kule ta ce "Nima ai ban san gidan ba". Ta ji haushin ya kwace mata waya ne tana tsaka da buga game. "Baki san gidan ba kuma?". Ya tambaya da mamaki, banza ta yi da shi bata sake yin magana ba. Kunna motar ya yi suka cigaba da tafiya ba tare da ya bata wayar daddyn ba, wani irin azababben iska da ruwa mai karfi ake yi wanda ya sanya shi dole ya yi parking na motar a gefen hanya dan gudun haɗari, baya iya ganin gabansa saboda iska da karfin ruwan. Jingina ya yi da jikin kujerar motar yana sauke numfashi a hankali. "Malam ka bani wayata". Ta faɗa cikin no respect, sam yaki kulata dan yanda ta yi maganar bai yi mishi daɗi ba, duk da yasan cewa ita haka take magana cikin nuna isa, amma yana da kyau ya fara gyara mata magana idan ta yi, idan ba haka ba akwai matsala babba. Sai magana take yi mishi ya sherata bai kulata ba, da taga ba zai kulata ba, sai ta yi yunkurin buɗe motar ta fita mishi daga cikin motarsa dan a cewarta ai ya raina ta ne, ko dan yana ganin ta shiga motarsa ne, ai a gida bai taɓa yi mata hakan ba, yanzu kuma wato dan yasan ba'a gida bane kuma ta shiga motarsa, shi ne zai yi mata walaƙanci......... Mata kenan, shi kuma yau ta haka ta fassara shi, bawan Allah ba hakan yake nufi ba shi kuma. Ganin kofar motar a rufene yasa ta juyo a fusace ranta a ɓace, dama kunsanta da saurin hawa ga zuciyar bala'in, Areef ya rainata yau, ba zata sake shiga motarsa ba, a kule ta ce "Ka buɗe mini motar nan na fita". Ta faɗa cikin ɓacin rai. Ɗan zaro ido waje ya yi kafin ya ce "Baki da hankali ne da zaki fita a cikin wannan uban ruwan sama dake zuba kamar da bakin kwarya? Kuma baki ganin a kan hanya muke ne? Kina fa sane iska da kuma karfin ruwan saman nan ya sanya muka dakata da tafiya har sai ruwan ya tsagaita". Sosai ta ɗaure fuska tana faɗin "Ka buɗe mani mota ni dai na ce". Shiru ya jingina kansa da jikin headboard na kujerar motar yana shakan daddaɗar kamshin perfume nata dake kwantar mishi da hankali, yaki sake tankata. Ganin hakan yasa ta yi kokarin buɗe kofar motar domin ta fita waje, dawo da kallonsa kanta ya yi yana kare mata kallo tare da mamakin yaushe yarinyar nan ta zama mai shegen gardama ta kuma raina shi har haka ne?. Ganin da gaske take yi sai ta fita yasa ya sakar mata kunamarsu na TRIPLETS a daidai hannun marfin motar. Ihu ta kurma tare da sake hannun motar ta faɗa jikinsa tana kuka, sosai ta kankame shi tare da runtse idanunta gam, kunamar ya ɗaga mata hankali, ta tsorata ba karya. Wani irin yanayi mai wuyar fassarawa ya ji a jikinsa, gabaɗaya ya kasa motsawa, sam bai yi zaton zata faɗa jikinsa haka ba, ya zaci jaruma ce bata tsoron komai, ashe damisar kwalice, ga tsoro ga ban tsoro. Ita kuma sai kara kankame shi take yi tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Kaɗan kaɗan ya ke jiyo sautin kukan nata har ta fara ratsa shi da kyau, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya sanya hannunsa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, can kasan maƙoshinsa ya fara magana a nutse. "Am so so sorry my baby, ban taɓa tunanin zaki tsorata haka ba, shiyasa ma na sakar miki kunamar, kuma saboda na san ba zata cijeki bane, amma dai ki yi hakuri, na tuba ba zan kara ba". Jin cewa kunamarsa ce kuma da gangan ya sakarmata ya sa ta miƙe daga jikinsa a zafafe, rai a matuƙar ɓace ta sanya hannunta ta buɗe Kofar ta fice abinta. Ganin ta fita a cikin wannan uban ruwan saman yasa ya yi saurin buɗe kofar motar shi ma ya fito waje tare da bin bayanta da gudu yana faɗin "Dan Allah ki yi hakuri, na amince ki yi mini duk hukuncin da zaki yi mini amma kada ki hukunta mini kanki da shiga cikin wannan ruwan sama mai bala'in sanyin, dan Allah ki dawo, na yarda baki so na, muje a haka, ni dai ki zo ki shiga mota mu koma gida". Gabanta ya tare tana wannan surutan. Rai a matuƙar ɓace, kun san ta dama da shegiyar kafiya kamar kafuran farko, bata san ta yi magana ta canza ba, hakan yasa ta ce "Ka bani hanya na wuce ko kuma wlh na zabga maka mari". A zahirin gaskiya kamar dai yadda kuka sani ne, mugun tsoron shi take yi, dakiya ce kawai irin tata take nuna mishi bata tsoron komai, amma daga ta ciki, idan suka haɗa ido har wani fitsari take ji saboda tsoro, ko a mafarki ba zata iya kuskuren marin shi ba. Da yake su dukawa mace ƙaramin abune a wajensu wanda ma ya zama masu kamar jiki, ko flowers za su bata sai sun duƙa sai dai masu girman kai a cikinsu irin masu zuciyar Lion, sune ba su duƙawa, irin su ma ai mace da na miji ma duk ba su ishe su kallo ba. Zube gwiwowinsa a kasa a gabanta ya yi tare da riƙe kunnuwansa da hannayensa yana faɗin "Am so so sorry, na gaya miki ba zan kara ba ko? Please ki yafe mini". Raɓawa ta yi ta gefensa zata wuce abinta. Cikin sauri ya miƙe ya tare gabanta yana faɗin "Yanzu idan kika tafi a cikin ruwan nan ina zaki je? Kin san dai baki san hanyar gida bako? To ko dan haka ki yi hakuri na mai dake, ko dan uncle na kinji ko?". Kin yi mishi magana ta yi tare da sake raɓawa ta gefensa ta wuce, a zafafe ya sureta ta baya kamar ƴar baby ya yi wajen mota da ita, abin da bata wuce ya ɗaga ta da hannu ɗaya ba ta tsaya tana ɓata mashi lokaci ruwan sama na dukansu. Sai bugun shi take yi a hannunsa akan ya sauƙeta, amma ina yaki har sai da ya kaita wajen motar, ya sauƙeta tare da buɗe kofar motar ya turata ciki ya rufo kofar. Yana ƙoƙarin zagayawa ta ɗayar kofar sai ya ga tana ƙoƙarin buɗewa ta fito, da sauri ya sake dawowa wajen kofar tata, ya sanya hannu ya maida karfin ya rufe tare da jingina bayansa a jikin marfin ruwan sama na dukansa daga tsakiyar kansa, bawan Allah ya gwammaci ruwan sama ta yi mishi duka akan ya barta ta fito ruwa ya daketa. Almost 10 mins yana jingine da jikin marfin motar ruwa na dukar tsakiyar kansa, ita kuma tana ciki ta yi shiru, ta rasa abin yi. Ganin zai illata kansa da gaske ne yasa ta ji tsoron hakan, jikinta ya yi mugun sanyi, wani irin so yake yi mata haka? ya gwammace shi ya cutu har haka akan ita ta fita ruwan ya taɓata, lallai wannan ya kai masoyin da dole ko wace zuciya ta yi maraba da shi, shi ne irin masoyin da ko wace zuciya take begen samu a duniyar nan. Jiki a mace ta yi mishi knocking na glass ɗin motar, ya ci bakar wahala, idanunsa duk sun yi jawur saboda ruwan saman, kun san dama idan mutun ya shiga cikin ruwa mai yawa sosai haka, to idanunsa suna yin ja sosai. Slowly ya juyo tare da kifa kansa a jikin glass ɗin motar bayan ya rage tsawonsa kenan, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yanda idanun nasa suka sauya, da alama ya wahala over, wani mugun tausayinsa ne ya dira mata a ranta, alama ta yi mishi da hannu akan ya shigo ciki. Kara rage tsawonsa sosai ya yi, ya dawo daidai da tata yadda take zaune a cikin motar. Ko ya yi magana ba zata ji shi ba saboda glass ɗin a rufe, hakan yasa ya yi amfani da motsa lallausan laɓɓansa ya tambayeta akan ta yi alkawarin idan ya tashi a wajen ba zata fito ba? Cikin sauri ta gyaɗa mashi kai alamar e, cool murmushi ya sakar mata, ɗan sunkuyar da kanta kasa ta yi tana wasa da hannunta. Da sauri ya bar wajen jikinsa sai zubar da ruwa yake yi, kofar side nasa ya je ya buɗe ya shiga, duk sun jika kujerun motar, wani irin sanyi sosai yake ji, sam bai damu da kan shi ba, ita yake jiyewa saboda ita ma ta jike sosai, tsaki ya ja yana kallon motar tasu, ba irin motarsa na Washington DC ba ne, da yanzu ya canza sanyi zuwa zafi saboda ita. Shiru suka zauna har ruwan ya ɗan tsagaita, sai satar kallon shi take yi, yana da kyau over, take faɗa a cikin zuciyarta, shi kuma ya lumshe idanu yana tunano irin sanyin da take ji bawan Allah. Da yaga ruwan ya ɗan rage karfi ne sai ya kun motar suka nufi wani tampatsetsen super market, shi kaɗai ya fito daga cikin motar tare da rufeta ya nufi cikin super market ɗin, kaya ya saya suka bashi ɗaki ya canza, sannan ya saya mata doguwar riga da Jacket ya kawo mata, karɓa ta yi tana kallon kayan, sun yi kyau sosai. Komawa cikin super market ɗin ya yi dan ya bata dama ta canza kayanta, da yake bakin glass ne da motar ta su, bata yi musu ba ta canza dan bala'in sanyi take ji. After 10 mins ya dawo hannunsa rike da cups guda biyu masu ɗauke da hot coffee da ya saya daga cikin restaurant dake manne da super market ɗin. Cikin motar ya shiga har lokacin ana ruwan sama, miƙa mata guda ɗaya ya yi, da kamar ba zata karɓa ba, amma tuna cewa daddy ya ce Areef ba zai taɓa cutar da ita ba ne yasa ta karɓa tare da ce mishi thank you, jinjina mata kai kawai ya yi tare da ɗan kurɓar nasa, wani irin azababben amai ne ya ji ya zo mishi, sam ɗanɗanon coffee ɗin da kuma yanayin wajen bai yi mishi ba, buɗe motar ya yi ya fara aikin tikar amai, anyi ruwan sama ya kalli kan hanya ya yi caɓa caɓa shi ne duk hanlinsa ya tashi dan basu son datti ga bala'in kyama, wurgi ya yi da cup ɗin ya yi amai sosai, da mamaki take da kallon shi har ya kammala ya wanke ɗan bakinsa, sannu ta yi mishi ya amsa cike da murna na ta yi mishi magana a nutse, sannan ya kunna motar suka nufi gida tun da dukkansu babu wanda ya san hanyar gidan Abbin, dama zai kira Imran ne ya gaya mishi, to ruwan saman nan tasa ya ce su koma gida kawai. Ko da suka koma gida ya yi parking a parking space na gidan, tana ƙoƙarin fita dan ta keta ruwan saman ta shiga cikin gida, cikin sauri ya rufe kofar yana kallonta, ita ma Juyowa ta yi tana kallonsa. "Malam dan Allah ka barni na shiga cikin gida, wlh sanyi nake ji sosai, ga shi kuma ruwan saman nan da alama ba yanzu zai dakata ba". Ban da kallonta ba wani abin da yake yi, ga shi ba damar ta tafi ya hana ta, turo baki ta yi ta juya tana kallon gaban ta, ta ɗauke kanta daga kallon shi. Ɗan kwantar da kansa a jikin kujarar ya yi tare da lumshe idanuwansa kasa kasa ya furta "Komai kika yi kyau yake maki, kina ɗaukar alhakina sosai, please my baby ki karɓi soyayyata kin ji? I don't want to force you akan abin da baki so, kin san cewa a yau idan ina so a ɗaura mana aure ko cikin dare ne sai an ɗaura, ba mai hanawa, kin san uncle ya gama yi mini koma, ya bani ke, amma ni bana son auren mu ya kasance baki so na, bana son ayi miki dole, duk da cewa na san dole ma zaki soni idan muka yi auren, amma ba irin wannan soyayya nake da bukata ba, ina son ki soni tun kafin mu yi aure, please kada ki ce a'a a tambaya ta karshe da zan yi maki, kina so na?". Ya kai karshen maganar tare da waro idanuwansa a kan kyakkyawar fuskarta. Shiru ta yi bata iya ba shi amsa ba, lallai ta san cewa ya haɗa komai da duk wata cikakkiyar mace zata buƙata a tattare da namiji, matsalar a nan shine ita bata yarda da soyayya ba, bata son aure, domin tana ganin irin wahalar da matan aure suke sha, ta yi rayuwa a in da tasan menene aure wato gidan Hjyr daɗi, taga yanda matan aure suke afkawa zinace zinace da halaka kansu saboda matsalar maza, shi ne dalilin da yasa ta ce ita kam ba zata yi aure ba, amma ba wai dan nata son shi ba. Ganin ta yi mishi shiru ne ya sa ya ɗan matso kusa da ita sosai, ruwan saman na kara karfin zuban da yake yi, hannayenta dukka biyu ya riƙo cikin nasa, ba shiri ya saketa saboda wani irin ɗumi mai daɗi da ya ji daga hannun nata, barci yake ji sosai sai lumshe idanuwansa yake yi, calmly ya ce "Tun da kin kasa yin magana, idan kina so na ki zauna a tare da ni a nan har ruwa ya ɗauke, idan kuma baki sona, zaki iya fita cikin ruwan ki tafi cikin palo". Ai tun bai gama rufe baki ba, tayi ƙoƙarin buɗe kofar motar da niyar fita, a zafafe ya jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, dan kada ta fita ruwa ya jiƙata, mamakin hali irin nata ya fara yi, tunani yake anya ba zai kai ta ayi mata ruƙiyya ba ko wani aljanin ne ya aureta?. Saboda daɗin ɗumin jikinta ga sanyin ruwan sama ya sa ya lumshe idanuwansa tare da kara kankamata a saman kirjin nasa yana sauke numfashi a hankali hankali. Kasancewar ya kankameta sosai ba halin ta kwace kanta, kasa kasa ta ce "Malam ka sake ni bana so". Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe, shiru ya yi bai tanka ta ba, dan bashi da abin da zai ce mata, jikinsa duk ya kara mutuwa dalilin kwanciya da ta yi a jikin nasa, ga kuma wani bala'in daɗi na ɗumin jikinta, abin ba'a magana, har wani barci mai matuƙar ni'ima ce take ƙoƙarin ɗaukarsa. "My Jehan please kada ki azabtar da bawan Allah da bai san komai ba sai tsantsar soyayyarki, even for the sake of uncle ki soni kin ji? Amma kuma ina da tambaya meyasa baki so na? Shin bancancanci a soni bane?". Ya yi maganar can kasan maƙoshinsa, da kyar muryar tasa take fita, tamkar mai magagin barci. Tamkar a mafarki haka yaji zazzaƙa kuma daddaɗar muryarta tana faɗin "Ka wuce ma mace ta tsaya yi maka wata magana na bata sonka ko makamancin haka, kuma ai ni ban taɓa cewa bana sonka ba, soyayya da aure ne ni bana so, amma ina sonka tamkar yanda nake son Rimsha". Duk da bata furta mishi so irin na mata da miji ba, tabbas ya ji daɗin kalamanta hakan yasa ya kara matseta a jikinsa sosai tare da ɗan rankwafo da kansa a kanta yana ɗan ɗaura hannunsa a saman bayanta. "Meyasa baki son soyayya?". "Saboda soyayya karya ce, yau idan ka ce kana sona muka yi aure, after some days or months, mind naka zai canza daga kai'na zuwa kan wata or something else, like dai baban Maryam na gidan hajiyar daɗi, shi ne kawai yasa ni ban yarda da soyayya ba, is better for me na zauna da daddyna". Tabbas ya fahimci tsantsan yarinta ce a cikin maganar tata, dan abu ya faru da wata kawai sai ki yi tunanin kamar da kowa ma haka ne, baga misali a kan mummynki da daddynki ba, shi ya dai'na sonta ne?, Amma sai bai nuna mata hakan ba, sai ya yi amfani da yarintar tata dan ya canza mata tunani. "Yes kina da gaskiya, haka ne duniyar yanzu, amma ni yanzu dai ki yarda mu buga wani game kin ji ko my diramati?". Yana magana yana ɗan shafa bayanta. "Tom shikenan na yarda, amma na minti nawa?". "One week ma it's okey for me". Ɗan zaro idanu ta yi tana faɗin "Game ne har one week? To da wayar waye zamu buga". Ɗan jan dogon hancinta ya yi yana faɗin "Ba da waya ba, a reality zamu buga game ɗin, soyayyar wasa na sati ɗaya zamu yi, zaki kasance ke girlfriend ɗita ce for only one week, duk abin da na ce zaki rinƙa amsa mini cikin so da kauna, and then zaki rinƙa yi mini like ni boyfriend naki ne a zahiri, ko da baki taɓa jini na ba, for example idan zan fita na ce mini zan fita, you can pray for me and tell me some romantic words like yanda girlfriend take yi wa boyfriend nata, kin gane ai?". Shiru ta ɗan yi tana tunani abin. "Sarkin tunani, kowa ai yana bedroom nasa ko? To haka zamu kasance, idan dai mun haɗu a palo ne zamu yi soyayya like boyfriend and girlfriend, idan muka kai one week muna buga game ɗin nan, to daga lokacin zan dai'na kulaki, zan dawo yayanki not masoyi, do you agree?". Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "One week kawai ko? Daga nan kuma zaka dai'na takura mini kana kulani ka yi alkawari?" Hannunta ya riko cikin nasa yana faɗin "Yes nayi alkawari zan dai'na takura miki kuma zan dai'na kulaki". Jinjina kai ta yi tana son tashi daga jikin nasa. Hannunsa dukka biyu ya ɗaura a saman bayanta yana faɗin "Ina zaki je kuma? Ai yanzu kin zama girlfriend na for one week, so a jikina zaki kwanta mu yi hira". "Dama girlfriend and boyfriend suna kwanciya a jikin juna ne?" Ta tambaya tana ɗago kanta dan ta kalli face nasa. "Yes mana baki sani ba? To mu a kasarmu haka ake yi". A takaice ta ce mishi "To mu kuma a kasarmu ba haka ake yi ba, kuma nan kasarmu ne ba naku ba, dan haka dokarmu zaka bi!". "Okey na ji zan bi dokarku, amma for now dai ki kwanta shiru mu ɗan yi soyayya kafin ruwa ya ɗauke mu shiga ciki sai ki dai'na zama a jikin nawa". Ya kai karshen maganar tare da mayar da kan nata ya kwantar a saman kirjin nasa yana ɗan shafa........... ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 *KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*. *KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ 👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊ *Domin samun karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581* 75 Ya kai karshen maganar tare da mayar da kan nata ya kwantar a saman kirjin nasa yana ɗan shafa bayanta zuwa saman kanta. "No ni ban yarda ba gaskiya, ni dai ka bari na tashi". "Talk to me like my girlfriend not like sister kin ji ko? Ko kin manta mun fara game daga yanzu ne?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "To shikenan amma ai ni haka na iya magana". Jinjina kai ya yi yana faɗin "Okey i will going to teach you how to talk to me like your real boyfriend or your husband okey?". Gyaɗa mishi kai ta yi tana dai son ta tashi daga jikin nan nasa dan sam hankalinta bai kwanta da kwanciya a jikinsa or taɓa jikinsa ba. Katse mata tunani ya yi da cewa "Idan muka je ciki zaki busar mini da gashi na with hand dryer?". Ɗan zaro dara daran idanun nan nata ta yi tana faɗin "Kai a'a gaskiya". Ɗan shafa kumatunta ya yi kafin ya ce "A gaban uncle fa za'ayi hakan kin yarda?". Nan ma shiru ta ɗan yi kafin ta ce "E to tunda a gaban daddy ne in dai bai ce komai ba, bai hana ba na yarda". "Serious?". Jinjina mishi kai ta yi. "I really love you my baby". Ya faɗa yana murmushi, shiru ta yi bata bashi amsa ba, "To ya bazaki bani amsa ba? Ba nace miki I love you ba, kema ya kamata ki ce mini I love you too my baby, ko kin manta yanzu ke girlfriend ɗita ce?". A sanyaye ya yi maganar. "I love you too my baby". Ta faɗa a normal yanda take magana, girgiza mata kai ya yi yana faɗin "Not like that mana baby, ki faɗa da salon soyayya kamar yanda na gaya miki, idan ba haka ba ni ba zan yarda ba". Ɗan turo baki ta yi tana faɗin "Allah ni ban san ya zan yi ba, ni fa a haka na iya maganata". Tabbas ta san yanda ake magana cike da soyayya, ta yi zaman gidan Hajiyar daɗi idan baku manta ba, kuma tun ainahi ita mai yawace yawace a media ce, babu wani abin da bata sani ba, kawai yi mishi ne ba zata yi ba, dan tana ganin like shirmene ka zauna kana wani kwantar da murya dan yin magana da wani, kana wani kirkiro salo na karya da banza. "To shikenan ki rinƙa yi a hakan ma yana yi mini daɗi". "Da gaske?" Ta faɗa a sanyaye, ɗago idanu ya yi yana kallonta, har cikin ransa ya ji daɗin yanda ta ce da gasken, dan ta yi maganar a sanyaye kamar ba ita ba, da alama ta fara kwaikwayon yanda yake magana ne. "Zaki rakani unguwa anjuma?". "Unguwar ina kuma?". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Wajen masoya". Jinjina mishi kai ta yi alamar e zata je, "Yauwa my baby sarkin rigimata wani irin kwalliya zaki yi mini?". Da kamar ba zata amsa ba, sai kuma ta tuna game suke yi, dan haka sai ta ce "Wani iri kake so?". Wani irin azababben daɗi mara misaltuwa yake ji, matso da ɗan bakinsa zuwa wajen kunnenta ya yi, a hankali kasa kasa kamar mai raɗa ya fara magana "Kin san fa ke kyakkyawace ko baki yi kwalliya ba, komai naki natural ne, dan haka ki saka mini wannan kayan naku masu zanen nan, wanda ranar kika saka, yana nan something like drawing aka yi a jiki da wasu abubuwa da aka saka miki a gaban rigar kin gane shi?". Sarai ta gane atamfar Rimsha da Imran ya bada aka zuba mata ɗinki riga da sket mai bala'in kyau da ta saka ranar yake magana, amma saboda ta wahalar da shi sai ta ce mishi ita bata gane ba, haka ya zage yana ta faman yi mata kwatancen atampha, amma sai ta tununa sam ita bata gane ba, daga karshe da yake yana da basira sai ya gane wahalar da shi kawai take yi, bawan Allah shi bai san atampha ba, matan kasarsu da kananan kaya suke amfani, ba ruwansu da atampha, shi kuma yana yi mishi kyau tun ranar da ya fara gani a jikin Rimsha, hakan yasa yake so ta saka mishi. Da ya fahimci cewa ta gane nufinsa kawai wasa da hankali take yi tana wahalar da shi, sai ya yi ƙoƙarin jan dogon hancinta da karfi dan shi ma ya rama, da sauri ta miƙe daga jikin nasa dan ta gudu zuwa waje ta nufi cikin palo dan ruwan saman ya tsagaita, kuma ta ga nufinsa jan mata hanci zai yi, da zafi idan ya ja mata, shi ne zata gudu. Ina rikota ya yi yana faɗin "Ina zaki je? Wato dama wahalar da ni kike son yi ko?". Girgiza mishi kai ta yi tana ɗan murmushi, zubawa mirmishi nata idanu ya yi yana kallo, ko ba komai yau kawai ya yi nasara da har ya sakata tana murmushi kuma ta ɗan saki jiki da shi tana wasa, kai wannan abin ya yi mishi mugun daɗi wlh. "Kayi hakuri to". Girgiza kai ya yi yana faɗin "Idan zaki yi mini magana ki rinƙa cewa baby, ai haka lovers suke yi, ko kin manta muna game ne?". Girgiza kai ta yi kafin ta ce "To shikenan ka yi hakuri babyna". Wani irin azababben daɗi ya ji tana ratsa shi, bawan Allah yana tsananin sonta, tamkar yanda Akila ta kasance kaddarar Aseef ce ita, ta zama kamar wata bugun numfashisa, to haka shi ma Areef Jehan take bugun numfashisa, dama su basu iya so ba, idan suna son abu gabaɗaya suke tafiya mishi. "Mu je cikin gida ko?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e, ɗan sumbatar lallausan kumatunta ya yi yana faɗin "To muje tun da ruwan ya tsagaita". Ya kai karshen maganar tare da sakinta, da sauri ta fita ta yi gaba abinta, fitowa ya yi shi ma ya bi bayanta yana kare mata kallo hannunsa na rike da wayar daddy da kuma nasa. A palon sama suka isko daddynta yana zaune shiru ya buga uban tagumi, kusa da shi suka zauna, tamkar abin haɗin baki suka sanya shi a tsakiya, ya ji matukar daɗin ganinsu a tare haka, ƙoƙarin kwanciya a cinyar daddyn ta yi, da sauri ya rigata kwanciya yana bawa daddyn labarin sun je basu san hanyar gidan Abbin ba sunka dawo. Shi kuma daddyn tambayarsa ya yi me ya jika mishi gashin kansa? Ko dai ya shiga ruwa ne? Miƙewa zaune ya yi yana faɗin "Uncle kada ka tambaya ka ji? Ban san me zan ce maka ba, ba zan iya yi maka karya ba, kuma bana son na gaya maka gaskiya, iya abin da na san zan iya cemaka shi ne ba wata matsala bane kawai, ka ji my uncle?". Shafa kan nasa daddyn ya yi yana ɗan kallon Jehan ɗin, ita ma gashin kanta a jike, a matsayinsa na babba ya fahimci in da suka dosa, ya san wace ce Jehan yanzu gardama ta yi mishi ta sanya shi shiga cikin ruwa, tuna hakan yasa sam bai ji daɗi ba kuma ya kudurta a ransa sai ya yi mata faɗa sosai, dan ya lura rainin da ta yi wa Areef ɗin nan yana neman ya yi yawa, so yana da kyau ya tsawatar mata. "Uncle baby ta ce zata busar mini da gashina with hand dryer, amma ta ce sai da izininka, ka bamu izini?". Ya yi maganar yana miƙewa tsaye, jinjina mishi kai daddyn ya yi yana faɗin ya basu izini, ya san waye Areef, so baya damuwa dan za su keɓe da ita, Jehan ai matarsa ce, ita ce dai bata sani ba, kuma ya ce kada a gaya mata sai ya gama tsokanarta son ransa, amma matarsa ce tun ranar da suka fita da shi da daddyn zuwa gidan daddyn na nan Kadunar, a lokacin sun biya gidan Abba, a nan ne daddyn yake sanar da Abba ya yi wa Jehan miji, ya kuma aurar da Rimsha, da yake Abba mutun ne shi ma mai son farincikin ƴan uwan nasa, ya ji daɗi sosai, lokacin su daddyn Jelly suna gidan a in da Abbi ya ce to a ɗaura auren kawai dan su ba ruwansu da bidia, ya tambayi Areef ɗin a ɗaura? Ya ce e a ɗaura tun da su Abba sun ce a ɗaura, sai dai baya son a gayawa kowa har sai in Lion ya dawo, dama ya bari sai ya dawo ne za'ayi auren, amma tun da sun ce to a ɗaura sai a bar maganar iya tsakaninsu, shiyasa a ƴan kwanakin nan yake taɓa jikinta yake kuma wasa da ita fiye da a baya, a baya sam baya taɓa jikinta kuma baya bata umarni, yanzu kuwa kun dai gani da safe in da ya yi mata magana cikin bada umarni da nuna isa, shiyasa kuma daddyn ya ce ya kaita gidan Abbi da kansa, domin kuwa yasan TRIPLETS da kishi, Areef ba zai yarda wani ya ɗauketa zuwa gidan Abbin ba, so matarsa ce halak malak kawai wasa da ita yake yi son ransa, yana son su saba ta kuma faɗa tarkon sonsa sosai. (TRIPLETS gidan mamaki, kullum cikin bazata nake baku ko? To ga auren Areef ma ya zo muku a bazata😌🙄 ku jira akwai saura bazata da yawa masu tashin kai su birkita muku lissafin kwakwalwa fiye da baya suna zuwa, ku dai'na wahalar da kanku wajen cankan me zai faru a gaba a cikin littafina, dan fa ni ɗin ta daban ce,👊😹 haka zalika labarina ko in ce labaraina dan har da na gaba in da rai da lafiya, labaraina salonsu daban ne da kowa, labarina ya wuci nan🤪👊 ku dai jira, anya kun taɓa......... Bari dai na barku sai mun haɗu a next book ɗin kawai, akwai tashin kwakwalwa dan fa shi da dafasa yake tafe ba da zafi ba, tafasa yake yi!!!!!.) Miƙewa ya yi tare da riko hannunta yana faɗin "Uncle ya bada izini zo mu je ki busar mini ko?". Ɗan kallon daddyn ta yi, jinjina mata kai ya yi a kan ta je ba komai, mamaki take yi yanda daddyn nata yake haɗa ta da wani namijin da ba muharraminta ba, abin ya fara ɗaure mata, ita dai tasan tun suna yara daddy yake tsawatar musu a kan maza, amma how comes zai ce ta rinƙa bin wani yanzu kuma?. Bedroom nasa ya wuce da ita, a nan ta ga abin mamaki, duniya guda, komai yana nan clear tamkar sabo, sai tashin kamshi komai yake yi ga hasken wuta ta ko'ina a cikin ɗakin, saman mirror chair ya zauna tare da zame pil da yake rike mishi da gashin nasa ya sake ta zuba mishi har tsakiyar gadon bayansa, wani irin kyau ya kara sosai, ya tafi da imaninta sosai. Nuna mata in da hand dryer yake ya yi, ba musu ta ɗauko ta dawo kusa da shi, jonawa suka yi yana faɗin to ta fara busar mishi. Ai da sauri ta fara dan tana bala'in son taɓa gashin nasa, ya yi matukar burgeta, kamar wata mace har tsakiyar bayansa, ga tsantsi a kwance luf, zuba mata idanu shi kuma ya yi ta cikin mirror yana kallonta yana jin tsantsar daɗin yanda take cakuɗa gashin nasa. Ya shagala da kallonta bai san lokacin da ta kammala ba, sai dai gani ya yi ta ajiye dryer tana ƙoƙarin nufar hanyar fita, da sauri ya riko hannunta yana faɗin "Saura ni kuma na busar miki da naki". Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin ita bata so zata je ɗaki ta yi wa kanta. "Haba baby bafa haka boyfriend and girlfriend suke yi ba, please ni ki zauna na yi miki kin ji ko babyna?". Ba dan ta so ba ya miƙe daga wajen ita kuma ta zauna. Da hannunsa ya zame mayafin kanta tare da ɗauko dryer ya fara busar mata, har cikin ranta take jin tsantsar daɗin hakan. Tsab ya busar mata kafin ya ajiye dryer tare da kasheta, tana ƙokarin ta miƙe dan ta tafi ya mayar da ita yana faɗin "Wait for me mana, ai ban gama ba, ke ce kika yi mini rowa kika ki gyarawa boyfriend naki gashinsa da kyau, amma ni ki jirani ki gani". Shiru bata ce da shi komai ba. Mayukan gashinsa ya ɗauko ya fara shafa mata a kan nata tare da turaren gashi, nan take gashin ya fara kyalli yana wani kara tsantsi, bayan ya kammala ya tara a bayan wuyarta ya sanya pil nasa ya kama mata da shi, a hankali ya kwanto da kansa a saman kafaɗarta tare da matso da face nasa kusa da tata sannan ya ɗago idanu yana kallon kansu a mirror, sun yi matuƙar kyau da ɗaukar hankali over, sun dace fiye da tunanin mai tunani, kasa ta yi da nata idanu duk da tana son kallon fuskokin nasu, ita kanta sun burgeta bare kuma shi da ya jima a cikin kogin sonta. "My baby you are really beauty over wlh, gaskiya na yi dace, please ɗago idanu ki kalle ni mana, kada ki yi mini musu game muke yi". Bata san time da murmushi ya subce mata ba, wato ya san zata yi musu kenan shiyasa ya yi saurin cewa kada ta yi mishi musu game suke yi, kai gaskiya Areef ya gama karantarta tsab ba kari. Hannayensa dukka biyu ya ɗaura a gefe da gefen wuyarta tare da ɗan masto da lallausan laɓɓansa kusa da kunnenta ya fara magana can kasa kasa kamar mai raɗa. "A duk lokacin da kika yi murmushi ina ji na tamkar ba'a duniya nake ba, gaskiya murmushinki yana yi mini kyau over my baby". Abin ku da zuciyar mace, duk in da mace take tana son yabo, shiyasa ya yi saurin tafiya da imaninta. "Yanzu dai ɗago idanu ki kalleni kin ji my beauty?". Ɗan ɗago idanunta ta yi tana faɗin "Ai kai ma kana da kyau sosai". "Da gaske?" Jinjina mishi kai ta yi alamar tabbatarwa, "Amma ai ban kai ki kyau ba ko?". Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin "Seriously ka fin....." Bai bari ta karisa ba ya rufe mata baki da lallausan hannunsa yana faɗin "Zaki yi saɓofa". Shiru ta yi bata yi magana ba, dan har ga Allah bata son yawan magana, kawai dan ya ce game ne yasa take ƙoƙarin taga ta yi magana, ya ce mata idan bata yi mishi kamar yanda yake yi mata ba, to ta faɗi game ɗin, ita kuma bata son faɗuwa sai dai nasara, shi ne yasa ta dage, amma ba dan haka ba, wlh Jehan bata da yawan magana sam, bata ma iya surutun ba. "Baby meyasa kika yi shiru?". Babu komai ta bashi amsa, zuba mata idanu ya yi yana jin tamkar kawai ya yi kissing nata, amma ina bayason hakan a tsakaninsu yanzu har sai ta fara son shi sosai. "Yaya Areef in tafi ɗaki?". Ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya ce "Babyn baby ne sunana, ki daina ce mini yaya now we are playing a game, ni ba yayanki ba ne a wannan wasa, ni babynki ne, dan haka call me baby direct". Nisawa ta yi kafin ta ce "Baby zan iya tafiya ɗaki?". "Har kin gaji da nine my baby?". Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a. "To why kike son ki tafi ɗaki?". Bata son ce mishi saboda tsare mutuncinta ne, sai ta ce mishi "I want to go and do something, ina jin sanyi over, kuma kaga ka ce zan raka unguwa ko?". Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce "Haka ne my baby, to shikenan I will going to miss you, ki kula mini da kanki, i really love you more than your expectations". Kasa kasa ta bashi amsa tun bai tambaya ba, dan tasan zai tambaya ɗin. "I love you too my baby". Wani irin daɗi ya ji sosai, ji yake yi tamkar ya mayar da ita cikin cikinsa dan tsabar murna. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar fita, tana son ta juyo ta kalle shi, amma kuma bata son ta juyo su haɗa idanu, dan ta san confirm yana kallonta, haka dai ta daure ta fita ba dan ta so bata samu damar sake kallonsa ba. Shi kuwa ya tsareta da idanu ta cikin mirror har ya fita. Tana fita ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da nufar toilet dan ya yi wanka saboda ruwan saman da ya jiƙasu, ita ma toilet ta nufa lokacin da ta shigo ɗakin nasu kenan dan ta yi wanka. A ɓangaren Rimsha kuwa, sai misalin karfe 10 na safe ta farka daga barcin farincikin da ya ɗauketa, a hankali ta waro idanunta waje, baya ɗakin ya fita, miƙewa zaune ta yi tare da zuro kafafunta kasan gadon kafin ta miƙe tsaye gabaɗaya, toilet ta nufa, a gurguje ta yi wanka tare da fitowa ta nufi wajen trolleys nasu. Wasu shegun riga da wando ta ɗauko, wandon jeans ne pink color mai rastin fari a jiki, daga ta saman wandon ya kamata sosai a in da ya bayyanar mata da kyakkyawan shape nata, kasan kuma a buɗe yake kamar palozo, rigar kuma high neck t-shirt ne wanda jikinsa gabaɗaya roba ce ta kamata sosai launin fari tas, ta sanya vest daga ciki kafin ta sanya rigar, kasan cewar babu ɗan kwali a cikin akwaitin sai ta gyara gashinta ta hanyar amfani da mayukansa, ta sako shi har bayanta yana wani kyalli, ta yi kyau over, perfume nasa ta ɗauka ta sanya a jikinta dan bata ga nata ba, dama guda ɗaya ya ɗauko mata, so ya shige cikin kaya sai ta saka nasa kawai, bedroom slippers nasa ta sanya dan ita bata da shi. Bedroom ɗin ta gyara musu tsab tare da gyara musu gado kafin ta feshe ɗakin da wani shegen daddaɗar air freshener mai tashin kai da kamshi, ta kara gudun Ac sannan ta sake komawa wajen trolleys ɗin ta kara gyara jikinta. Ba karya ta haɗu iya haɗawa, ta saki gashin nan tamkar ba Indiya, ta so ta ɗan yi simple make up, sai dai babu kayan make up ɗin a cikin trolleyn. Haka ta nufo waje, ga abinci a saman table a jere, an jera musu komai tun kafin ta tashi, amma sam bata bi ta kan abincin ba ta nufi waje. Wani ni'imantaccen iska mai matuƙar daɗin gaske ne ya fara kaɗata tun lokacin da ta sako kafarta wajen bedroom ɗin, ɗan waige waige ta fara yi tana wani lumshe idanu saboda daɗin iskan. Can ta hango mijin nata yana tsaye ya goya hannu a saman faffaɗar kirjinsa yana kallon ruwa ya bata baya tamkar mai tunanin wani abin, jikinsa na sanye da pajama launin sky blue mai matuƙar kyau, a ko da yaushe yana nan tsab tamkar a lokacin yake ciro kayan da zai yi amfani da su daga laida saboda bala'in tsabtarsa. Da sauri ta karisa wajen da yake tana tunano maganar Akila da take cewa idan yana tsaye ki rinƙa hayewa jikinsa babu abin da zai yi miki, haka kuwa aka yi, tana zuwa ta rungume shi ya baya tare da kwantar da kanta a saman bayansa, tamkar abin haɗin baki a tare gabaɗaya sojojin nasa suka juya musu baya, tamkar waƴan da ya bawa umarni, haka suka yi maza suka juya baya dan ma kada su kallesu, abin ya yi mugun burgeta ya kuma bata mamaki yanda ya zamana sun juya a tare tamkar waƴan da aka bawa umarni. Shi kuwa nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke ta wani kwantar da kanta a saman bayansa, a hankali ya juyo da jikinsa gareta, wani irin sanyi ya ji a cikin zuciyarsa lokacin da ya ɗaura idanunsa a kan kyakkyawar fuskarta, fara kallonta ya yi from head to toe, babu karya ta haɗu, ta kuma jijjiga daular birnin zuciyarsa, musamman yanda ta saki gashin nan nata tamkar wata Baturiya. Ganin ya tsareta da idanu ne yasa ta faɗa saman kirjin nasa tana faɗin "Good morning my lovely brother". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai kuma can kasa kasa, ɗaga idanunsa ya yi a in da ya kai kallonsa kan sojojinsa da suka juya musu baya har da runtse idanu bayin Allah, shi Mark dama yana cikin ɗaki ya samu damar magana da Anaya ta wayar mummynta, sai yau ya gane number mummyn nata tun lokacin da Lion ya bashi wayar, abin ka da ba wayarka ba, ba kuma ka san da wani suna aka yi saving number ba, bai kuma isa ya zo ya ce zai tambayi da wani suna aka yi saving ba, shi ne kawai ya yi ta nema bawan Allah sai yau ya gane, so yana ciki suna zuba soyayya da beb nasa. "Yaya Saif ba zaka amsa gaisuwa ta bane?" Wannan karonma a shagwaɓe ta yi maganar, hannu yasa ya ɗauketa cancak zuwa saman kirjinsa suka nufi cikin bedroom nasa, dan kuwa ita kaɗai ya canzawa, bayan ita babu wanda ya ga alamar canji ko da sunan wasa a tattare da shi, hakan yasa ma ya ɗauketa suka nufi ɗaki dan kada ma ya yi magana sojojin nasa su ji, sai dai fa suma sojojin sun san ogan nasu ya faɗa tarkon son ƙaramar yarinya, dan kuwa babu wata mace a duniya da ta isa ta tinkare shi ma bare kuma har ta kwanta a jikinsa haka ba tare da ya yi wurgi da ita a cikin wannan ruwan tekun ba, amma ita Rimsha lafiya lou ta kwanta, ga shi kuma har da ɗaukarta ya yi suka wuce ciki, ko daga nan sun san oga fa ya shiga tarkon mata. Bai direta ko'ina ba sai saman bed nasu, in da ya kwanta da ita a jikin nasa, ya ji tsantsar farinciki na yanda ta gyara gadon nan fes ga wani daddaɗar kamshin air freshener da ta fesa musu mai kwantar da hankalin mai shaƙa. "Kada ki sake fita wajen nan ki na ji na?". Ya yi maganar cikin bada umarni kamar baya, kuma ya yi maganar yana ɗaure fuska sosai. Jinjina mishi kai ta yi tana amsawa da okey, ya bata tsoro yanda ya ɗaure fusataccen fuskar nan nasa yana magana, dama ga fuskar kullum a ɗaure, idan ya kara ɗaurewa har wani fitsari take ji, ta sha jinin jikinta, shi kuwa sam lokacin da ta zo ta rungume shi bai ji daɗi ba, kawai ba zai iya daka mata tsawa ko makamancin hakan ba ne yasa ya kyaleta, amma sam bai so ta rungume shi a gaban sojojinsa ba, saboda shi baya son raini ko kaɗan, ko da yake rungumarta a gaban su daddy, ya san ko giyar wake suka sha basu isa su yi mishi wani magana ba ne, kuma a cikinsu babu mai karfin gwiwar da zai iya ɗaukarsa a hoto ya ɗaura a media duniya ta gani saɓanin idan tana rungumarsa a waje gaban kowa, za'a iya samun wani ya ɗauke shi hoto ta ja mishi raini.............. Tab Lion duniya, amma dai ka yi kokarin da ka iya canza mata ita kaɗai ɗin ma, dama ita kaɗai ya kamata ta ga wasu abubuwa naka, a matsayinka na babba a cikinsu kam dama bai kamata ta ja su rai'naka ba. Bugu da kari ga bala'in kishin yanda ta fito ta wuce sojojin ta zo in da yake, ya ji kishi sosai, shiyasa ya ce kada ta sake fitowa waje baya so. Yunkurawa ya yi zai sauka daga gadon zai kuma sauketa daga jikin nasa ya fita waje, cikin sauri ta kara ƙanƙame shi tana faɗin "Yaya Saif to ai baka amsa mishi gaisuwar tawa ba". Komawa ya yi ya kwanta yana kare mata kallo. Shiru ta yi dan taga gudun ruwansa, shin zai amsa ne ko zai cigaba da kallonta ne kawai. Almost 5 mins suna a haka bai ce ko uppan ba yana ta kallonta, kukan shagwaɓa ta saka mishi tana turo ɗan bakin. Nisawa ya yi a nutse ya fara magana. "A duk lokacin da nake tare dake, wlh Aseef ne kawai yake yi mini yawo a cikin kwakwalwata, ina kewar shi sosai, duk wani abin da yake yi mini na tsiya shi kike yi mini yanzu, that is the reason why nake jin daɗin ganinki a kusa da ni". Ya yi maganar a sanyaye cikin natsuwa da kwanciyar hankali, babu wata hayaniya a voice nasa. Cool murmushi ta sakar mishi tana faɗin "To shikenan ka ɗauka ni ce shi, dama kuma ai ni renonsa ne". A yanzu ma yanda ta yi maganar kamar Aseef ɗin, tana yi tana turo baki, yatsa ɗaya ya tura mata cikin dimple nata yana kara jawota jikinsa, duk sai ya ji yana bala'in kewar TRIPLETS nasa, wani azababben son su ne yake karuwa mishi a cikin zuciyarsa bawan Allah. Hannu ta kai ta kama ɗan guntun gashin nan nasa dake gaban goshinsa tana wasa da shi, shi dai shiru ya zuba mata idanu dan bai san me zai ce ba, bai wani iya dogon magana ba, sai dai idan ta yi ya bata amsa, amma dan kansa kam bai san me zai ce ba. Wayarsa ce ta yi kara, ɗaukowa ya yi, Video call ne kuma TGA ne yake kiransa, su dai sun fi jin daɗin su yi video call suna kallon juna. Ganin hoton TGA yasa ta ce "Yaya Saif wannan TGA ne ko?". Ɗan zaro idanunsa waje ya yi yana mamakin a ina kuma ta san TGA?. Ba ƙaramin tsoratata ya yi ba yanda ya zaro idanun nan nasa, runtse nata idanun ta yi. Katse kiran ya yi tare da ajiye wayar, yana wani abin ba zai yi wani ba.......... LION DUNIYA WATO YANA WANI ABIN BA ZAI YI WANI BA.🤣🤣 KO DA YAKE DAMA WANNAN DOKARSA CE BAYA HAƊA ABUBUWA BIYU LOKACI GUDA, A TSANAKE YAKE KOMAI. "A ina kika san TGA?". Ya tambaya yana tsareta da idanu. Labari ta fara bashi cikin shagwaɓa tun kallonsu da take yi a Tv lokacin tana ƴar shekara 9, yanda aka yi ta iya banbanta su da yanda ta yi ƙoƙarin banbantawa ƴan gidansu su kowa ya kasa ganewa sai ita kaɗai, ita kaɗai ta iya rabesu, da yanda aka yi ta fara zanensa, dukka ta bashi labari. Shiru ya yi ya kuma sha jinin jikinsa gaskiya, bai taɓa tunani a duniya bayan TRIPLETS nasa za'a samu mai yi mishi mahaukacin soyayya irinta ba, tub tana 9 years, kai, kai, kai, kuma har ta iya rabe shi da TGA abin da ko mutane a waje basu iya rabesu, idan ba a tare ka gansu ba ba zaka iya rabasu ba, idan suna tare suna da banbanci sosai, amma idan ganin daban daban zaka yi musu ba zaka taɓa ganin banbancin ba, amma ita har ta iya ganewa ba tare da ta taɓa ganinsu a tare ko ta taɓa ganin face nasu babu face mask ba, lallai tabbas ta cancanci a jinjina mata. Sai dai kuma fa ya ji a jikinsa wannan kaifin kwakwalwa da take da shi tabbas irin nasu ne, irin kwakwalwar TRIPLETS gareta, tamkar wata twins, dama da TWINS da TRIPLETS Allah ya basu baiwa over, mafiya yawan lokuta abin da zasu yi ba kowani ɗan adam ne yake iya yin shi ba, ga su da kaifin kwakwalwa kamar ba gobe, sai dai idan basu sami kula bane kwakwalwar da basirar tasu take tafiya a banza, amma wlh baiwa garesu na wuce misali, ga shi wani abin cutarwa baya saurin kamasu, Allah yana tsaresu. Tunanin cewa daddynta TWINS ne ya faɗo mishi, tuna hakan yasa ya ce kila kwakwalwar daddyn nata ta gado, shafa kanta ya yi ba tare da ya yi magana ba yana tunanin yanda Areef ya rinƙa bashi labarin yanda ta iya rabesu shi da Aseef, ko a cikin duhu suka yi magana tana iya rabesu, abin da ko daddynsu baya iya rabe muryansu da Aseef da Areef ɗin, amma ita tsab take rabe kowa, ko da rufe mata idanu suka yi ta baya idan ta taɓa fuskarsu zuwa hannunsu tana rabesu tsab, abin ya yi mugun burge shi ba kaɗan ba, wani irin azababben kaunarta ne yake kara shigarsa ba tare da ya sani ba, yau dai bayan TRIPLETS nasa ya samu mai son shi dan Allah, wanda ta so shi ba tare da ta san waye shi ba, ba kuma ta taɓa ganin ainahin face nasa ba, kawai dai tana son shi da zuciya ɗaya. Wani irin rumgume sosai ya yi a jikinsa yana godewa Allah da yasa bai zuba mata chemical a kirjinta ya goge zanen sunan nasa da tayi ba, dan kuwa yanzu ya gane tana da dalilinta na yin zanen, kuma gaskiya ta cancanci ya yi wa zanen nan wani kyauta na musamman, ya ji tsantsar kaunar zanen a ransa ba kaɗan ba. Juyawa ya yi da ita a in da ya yi mata rumfa da faffaɗar kirjin nasa, yau wani irin farinciki mara misaltuwa yake ciki, sai dai fa duk da haka face nasa a ɗaure, kuma ba zaka taɓa gane yana cikin farincikin ba, ko ita bata gane ba dan ba wani canji a face nasa. Hannu ya kai saman mararta wajen shafaffen plat tummynta, wani irin dogon numfashi ta ja tare da runtse idanunta gam tana sauke numfashin a hankali. Zubawa face nata idanu ya yi while a hankali yake yawo da hannunsa a saman shafaffen cikin nata. "Meeeesha". Ya ambata cikin sarkewar murya a kuma nutse tamkar kullum. Na'am ta amsa mishi da shi. "Why anytime idan muna tare kike son rufe idanunki? Yanzu kuma baki son kallo GAR again ne?". Cikin sauri ta girgiza mishi kai tana faɗin "Ina matuƙar son kallonka, kawai ina jin kunya ne". "Meye kuma kunya?". Ya tambaya yana haurar da hannunsa da kuma rigar nata sama, dan zanen sunansa yake son gani dama, rigar jikinta high neck ne, so dole sai ta kasa zai ɗaga rigar idan yana son kallon zanen, ya kamu da kaunar zanen over. "Yaya Saif baka san kunya ba?". Jinjina mata kai ya yi alamar e yana faɗin yes shi bai sani ba, turo baki ta yi tana faɗin "To ai ni ban san taya zan gaya maka me kunya ba, amma dai ba zan iya haɗa idanu da kai ba". "Why to?". "Uhm uhm haka kawai mana nima ban san dalili ba, haka kawai nima nake jin ba zan iya ba.....". Jin saukar lallausan laɓɓansa a saman kumatunta ya bata sumbata ne yasa ta yi shiru, yanayin yanda ta yi maganar ne ta yi matuƙar burge shi yasa har ya sumbaceta, musaman idan ta ce mishi uhm uhm sai ya ji tamkar ta yi ta yi mishi irin hakan kada ta dai'na. Ɗage rigar nata ya yi gabaɗaya har zuwa wuyarta, nan take ɗan ƙaramin farin vest nata ya bayyana, wuyar vest ɗin ya ja kasa gabaɗaya ya bayyanar mata da tula tulanta dukka, daga ita har shi a tare suka ja dogon numfashi, datse idanunta sosai ta kara yi tamkar zata fashesu, shi kuwa zubawa face nata ido ya yi yana kallon yanda ta runtse idanu gam haka kamar ba lafiya ba. Dawo da kallonsa saman tula tulan nata ya yi, bai taɓa ganinsu gabaɗaya a waje haka ba sai yau, mafiya yawan lokuta iya tudun da zanen sunansa yake kawai yake buɗewa, yau kuma gabaɗaya ya buɗesu, wani irin shock ya ji tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafin ƙafarsa, hannu ɗaya ya ɗaura a saman zanen yana ɗan shafawa, takure jikinta waje guda tayi tana jin wani irin yanayi a tattare da ita. Ɗan bakinsa ya kai saman zanen ya sumbata, shi da kansa ya kasa ɗagowa saboda wani irin...... Da ya ɗebesa, ita kam ai ba'a magana, misilta halin da ta shiga ba zai yi wu ba, shi ma ɗin dai hakan ce. Da kyar ya iya ɗagowa tare da kai ɗan bakinsa direct saman lallausan laɓɓanta, kissing nata ya fara yi cikin natsuwa da kwancinyar hankalin, ga kuma salo mai jan hankali, a tare suke fitar da numfashi, sai dai nashi numfashin ya fi nata fita da sauri sauri. Sai da ya yi mai isarsa sannan ya saketa tare da kwanciya kusa da ita yana mai kara jawota jikinsa, sam baya son ya kai hannunsa ya taɓa breast nata, shi kaɗai ya san dalilinsa na kin taɓawa, sai dai ya shafa iya wajen zanen kawai, amma ko da sunan wasa bai taɓa yin gigin wasa da su ko ya taɓasu ba, yau ɗin ma hakance, rungumeta ya yi kawai tare da lumshe idanunsa tamkar mai jin barci, haka suka kasance cikin tsantsar farinciki manne da juna, suna kara jin tsantsar kaunar juna. After some hours bayan sun yi sallar mangariba da issha, dukkansu sun yi shirin barci cikin kayan barcinsu masu kyau da tsada, shi ya ci abinci tun ɗazun, ita kuma ta tsaya zuba hira da Anaya bata ci ba sai yanzu, bayan ta kammala ta yi komai sai ta hau saman sofa ta kwanta tana kokarin kiran number Areef dan ya haɗata da daddy da kuma Jehan. Shi kuma Lion yana kwance saman bed yana latsa wayarsa. Da gudu Brady ya shigo cikin ɗakin tare da hayewa saman bed ɗin yana wani rungume Lion ɗin, yau sun yi kewar juna, rungume shi Lion ɗin ma ya yi yana sumbatarsa kafin ya sake shi ya cigaba da latsa wayarsa. Kamar daga sama Bradyn ya kwace wayar daga hannunsa da gudu ya sauka gadon ya haye jikin Rimsha a in da ya ɗaura mata wayar a saman jikinta. Ihu ita kuma ta kurma kafin ta miƙe ma ya sauka daga jikin nata ya yi waje dan yasan idan Lion ya kama shi wlh ba zai yi mishi ta daɗi ba, shi ne yasa ya gudu, yasan yau ya yi laifi, kuma shi irin horon da aka bashi kenan ato. Ganin ya sauka daga jikinta ne yasa ta natsu tare da sanya hannu ta ɗauki wayar Lion ɗin da ya ajiye mata a jikinta ta juyo da screen ɗin dan ta gani, hotonta Lion ɗin yake kallo yasa Brady ya kwace wayar ya kawo mata dan ta gani, shiru ta yi cikin ɗari ɗari ta ɗan ɗago idanunta dan ta saci kallon shi, sai faman sauke nauyayyar ajiyar zuciya take yi, tabbas ta ji daɗi na ganin cewa yana kallon hotonta, dama kenan yana da hoton nata? Bata san cewa har a laptop nasa ma da akwai su ba, da kansa ya nemo ba wanda ya bashi. Tana ɗago idanu kasaf suka haɗa ido, dan kuwa ya tsareta da idanu yana kallonta, cool murmushi ta saki tana sunkuyar da kanta kasa, ɗan lumshe idanunsa ya yi yana tunanin kalar hukuncin da zai yi wa Brady yau, ga dai Bradyn ya gudu abinsa, dama ya san zai sha hukunci, shi ne ya tsere tun wuri, wata kila kafin ya dawo zuciyar Lion ta sauka.............. Wayyo cikina Allah ya yafewa Brady, yau zai sha lugude wajen Lion, ya tona mishi asiri shi ma, amma kuma fa idan kun lura wlh da gangan Bradyn ya yi mishi hakan tun da harda tserewa dan kada a kama shi, kenan ya san komai.....🤣🤣 Ko da yake dama horon Lion ɗin ne, shi ya koya mishi yin hakan!!. Jin ya yi shiru bai yi magana bane yasa ta miƙe dan ta kai mishi wayarsa, kusa da shi ta je ta tsaya tare da miƙa mishi wayar cikin girmamawa, a maimakon ya karɓi wayar sai ya jawota jikinsa ita da wayar bakiɗaya, ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, a tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, dukkansu biyu sunyi kewar juna. Cikin dabara ya karɓi wayar tasa tare da kasheta bakiɗaya ya ɗaura saman bedside drawer, kashe wutar ɗakin ya yi tare da kunna green light sannan ya ja musu bargo zuwa wuyarta shi kuma kirjinsa. Can kasan maƙoshinsa ya furta......... ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 *KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*. *KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ 👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊ *Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 09162620621* https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S 76 Can kasan maƙoshinsa ya furta "Why are you smelling dan kin ga ina ganin hotonki?". Kasa kasa kamar mai raɗa ta fara magana "Ai dole zan yi kuma na yi mamaki, dan ban ma taɓa tunanin kana da hoton nawa ba ne". Shiru ya yi yana cigaba da shafa gashin kanta. "Yaya Saif a ina ka sami hotona?". Ɗan juyawa da ita ya yi yana mai rankwafowa kanta, a kunne ya raɗa mata magana a hankali, cool murmushi ta saki tare da ɗago kai ta sumbaci lallausan kumatunsa, lumshe idanunsa ya yi tare da sake warosu a kanta, ya ji daɗin sumbatar sosai. Sake matso da ɗan bakinsa kusa da kunnenta ya yi cikin natsuwa ya furta "Wani kyauta kike so nayi miki dan wannan zanen ya cancanci kyauta". Juya fararen idanunta sama ta yi tamkar wata mai tunani, zuba mata ido shi kuma ya yi yana kallonta, har ga Allah yarintarta yana mugun burge shi, komai take yi cikin yarinta, hakan ba ƙaramin tafiya da shi yake yi ba. "Yaya Saif sai dai na tambayi yaya Areef ko yaya Aseef". Kasa jurewa ya yi sai da ya sumbaci dimple nata kafin ya lumshe idanu tamkar mai barci. "In tambayesu yaya Saif?". Hannu ya sanya a saman lips nata alamar ta yi shiru ta yi barci dare ya yi, saƙalo wuyarsa ta yi da hannu ɗaya tare da lumshe idanu ita ma. Basu kai ga yin barci ba Brady ya dawo cikin ɗakin, saman bed ya haye tare da hayewa jikin Lion ɗin, ihu ta kurma tana kokarin Miƙewa ya yi saurin rikota yana waro idanunsa waje, ganin Brady ne yasa ya mai da idanunsa ya lumshe tare da mayar da ita saman kirjinsa, cikin harshen Spanish ya yi wa Bradyn magana a kan ko ya kwanta ya yi barci ko kuma idan ya kama shi sai ya yi mishi punishment na laifin da ya yi mishi ɗazun, yanzu ma dan ya yi sa'a sun rigada sun kwanta ne, da sai ya yi punishing na shi sosai. Ba musu ya kwanta kusa da Lion ɗin yana wani kuka kasa kasa, yasan idan Lion ya kama shi ba zai yi mishi ta daɗi ba, to rufin asirinsa kawai ta kwanta shiru. Cikin tsantsar shagwaɓa ta ce "Yaya Saif Allah ina tsoron kwana da shi gado ɗaya, ni to zan koma saman sofa". Bata gama rufe baki bama Bradyn ya miƙe ya diro kasa tare da ficewa waje da gudu, dama shi ai baya kwanciya waje guda, yanzu ma neman magana ya kawo shi, abin da yawonsa yake tafiya, Mark ne kawai yake iya yi mishi dabara ya rike shi har su yi barci tare, ƙoƙari irin na Mark har kallo yake kunna mishi na training ɗin sojoji a wayarsa ya saka shi kallo, idan yana kallo sai ya yi ta tsalle yana zuro harshe waje, shiyasa suke mugun shiri da Mark ɗin, yanzu ma wajensa ya tafi dan su je su sha kallon film, dama ya leƙo ne yaga ya Lion nasa yake. Ganin ya fita ne yasa ta koma ta kwanta shiru tana tunane tunane har barci ya yi awon gaba da ita, shi ma ba jimawa barci ta ɗauke shi suna manne da juna. A ɓangaren su Areef kuwa, wanka ya yi ita ma ta yi wanka, cikin atamfar ta shirya, da yake kayan Rimsha ne sai suka kamata sosai, dan ma kayan an yi wa Rimshar su da tsawo, dama sket ɗin yana ja mata har kasa, ita kuma Jehan ɗin sai tsawon ya yi mata dai'dai, riga kuma tamkar dan ita akayi ba dan Rimsha ba, dama Rimsha taki saka kayan dan anyi mata breast cup a jikin kayan, kuma mai ɗan girma aka yi mata, shi ne yasa taki sakasu tun da ta gwada sau ɗaya, ita kuwa Jehan sun zauna mata sosai ɗas. Mayafin Abayar Rimsha pink color kalar atamphar ta ɗauka ta yafa a jikinta tare da feshe jikin nata da perfume ɗin Rimsha mai matuƙar kamshi da daɗi, saman bed nata ta haye tana tunanin su Adiva da Maryam, ko a wani hali suke ciki yanzu? Bayin Allan har idanunta sun ciko da kwallah. A ɓangaren shi kuma Areef, cikin kananan kaya wandon jeans baki da t-shirt blue ya sanya, ya yi matuƙar kyau, gaban mirror ya zo ya tsaya tare da kara gyara gashin kansa sannan ya ɗaure bayan ya shafa mayukansa, ya yi kyau na wuce misali. Wayarsa da kuma wayar daddy da ya karɓa a hannunta ɗazun ya ɗauko tare da fitowa waje ya nufi bedroom ɗin daddyn Rimsha, sallama ya je ya yi mishi a kan zasu fita ba zasu dawo ba kuma sai dare dan haka daddy ya kula da kansa sosai, ya kai karshen maganar tare da miƙa mishi wayarsa, addu'a sosai daddyn ya yi musu tare da fatan a dawo lafiya, amin ya amsa da shi kafin ya mannawa daddyn sumbata a kumatu yana gaya mishi yana kaunarsa, sumbatar shi ma daddyn ya yi mishi yana mai do mishi da kalmar shi na yana kaunarsa, da haka suka yi sallama ya fito zuwa ɗakin matar tasa kuma ƴar diramarsa. Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo, tana kwance ta yi nisa cikin duniyar tunani ga hawaye na bin kuncinta, sam bata ji shigowarsa ba, saman bedside drawer ya zauna cikin zolaya ya ce "Kin gama shiri shi ne ba zaki zo wajena bako? Wato sai kin wahalar da ni k....." Bai kai karshen maganar ba ya ga hawaye a kuncinta wani na bin wani, nan fa hankalinsa ya yi mummunar tashi, sunanta ya ambata, amma ina ta yi nisa sam bata tare da shi. Mikewa ya yi ya dawo bakin bed ɗin yana mai sake ambatar sunanta, bata amsa ba, hannu ya kai saman face nata da nufin ya goge mata hawayen, a razane ta tashi dan bata san ya shigo ba. "Jehan lafiya kike kuka?". Ya faɗa cikin wata iriyar murya wanda da ka jita kasan hankalinsa a tashe yake. Goge hawayen nata ta yi wani na fitowa tana faɗin "Ina tunanin rayuwa ne, yanzu komai ya wuce kamar ba'ayi ba, ina kewar mummyna". Yanda ta yi maganar cikin kasalalliyar murya, duk wanda ya ji dole ya tausaya mata. "Mummy tana raye ne daman?". Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "E tana raye, mun rabu da ita a Katsina, amma Rimsha ta ce mini bata Katsina wai ta tafi Maiduguri, jiya na tambayi daddy ya ce mini yasa ana nemanta, ya ce mini ya yi magana da su Abba ana nemanta a Maidugurin, ina kewarta sosai wlh". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Amma kina da hoton ta ne?". Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin "A'a bani da shi, amma idan ka kalli Rimsha tamkar ita ka kallah, mutane suna yawan cewa suna kama sosai". Girgiza kai ya yi kafin ya ce "Ki dai'na cewa mutane suna cewa tana kama da ita, ba lallai suna kama ba, kowa da yanayin yanda yake kallon mutun, ni baki sani bama, da Aseef Rimsha take yi mini kamanni, dan dai shi fari ne kawai, so kowa da yanda yake kallon mutun, dan haka ba lallai Rimsha tana kama da mum ba, wata kila masu cewa tana kama da ita ɗin su ne kawai suke ganin hakan, yanzu dai zan tambayi uncle hoton mum ɗin zamu nemota cikin ƙanƙanin lokaci, amma promise me that ba zaki sake yin kuka a kan ɓatar mum ba". Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin ba zata sake ba, hannu ya kai saman face ɗin nata ya goge mata hawayen yana faɗin "Muje toilet na wanke miki face naki sai mu tafi". Make mishi kafaɗa ta yi tana faɗin "A'a ka bari zan wanke da kai'na?". "Haka kike so?". Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e haka take so, mikewa ya yi ya koma saman bedside drawer yana mai cemata ta je yana jiranta. Zuro kafafunta kasa ta yi kafin ta miƙe ta nufi cikin toilet ɗin, da kallo ya bita yana kallon kyakyawan halittar da Allah ya yi mata, diri iya diri suna da shi ba karya, lumshe idanuwansa ya yi yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya. Wake face nata ta yi ta fito ta tsaya a gaban mirror, mai ta shafa kafin ta gyara mayafinta ta ce su je, shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Baby why not ba zaki saka wannan hijabin naku ba?". Girgiza kai ta yi tana faɗin "Ni bana son hijabin ne". Miƙewa ya yi tare da nufota yana faɗin "Haba my beauty, hijabin ai yafi yi miki kyau, please dan ni zaki saka kinji ko? Bana son kowa ya kalli kyanki ne, kin manta yanzu ke girlfriend ɗita ce? To ni kaɗai zan kalli kyanki ai". Ya kai karshen maganar tare da matsowa kusa da ita, ajiyar zuciya ta sauke tare da nufar cikin drawer wayansu ba tare da ta yi magana ba. Da sauri ya karisa wajen yana faɗin shi zai zaɓa mata, bata yi mishi kaddama ba, ta zuba mishi idanu ya ɗauko mata wani pink color, kalar zanen flowers ɗin dake jikin kayan nata. Miƙa mata ya yi ta karɓa tana ƙoƙarin sakawa, hannu yasa ya tayata sakawa, ta fito chas a cikin hijabin, ta yi matuƙar kyau over, waya ya fitar yana yaba kyanta tare da cewa bari ya yi mata hoto, har wani sanyi zuciyarta ta yi na irin yabon da yake yi mata, mata akwai son yabo, tuni ta bada kai ya ɗauketa hotuna kala kala. Hannunta ya kama yana faɗin suje, ɗan kwace hannun nata ta yi tare da yin gaba ya rufa mata baya, bedroom ɗin daddynta ta shiga dan ta yi mishi sallama, zaunar da ita ya yi cikin harshen Hausa ya yi mata faɗa sosai tare da nasiha, daga karshe ya ja mata kunne a kan rainin da take ƙoƙarin yi wa Areef, sannan ya ruɗe mata da cewa a matsayinsa na babanta yana umartanta da duk abin da Areef ya ce kada ta kuskura ta yi mishi gardama, idan ta yi hakan to ta sani fa ransa ne zai yi mummunar ɓaci ba na Areef ba, dan haka ta kiyayye, to ta amsa mishi kafin ta sake tambayarsa komai fa ya ce idan Areef ya ce ta yi kuma sai ta yi?. Ya fahimci in da zancen nata ya dosa, dan haka sai ya yi mata yanda zata gane, ya ce mata Areef ba zai taɓa yin abin da bai da ce ba, ba zai taɓa sakata ta kauce hanyar Allah ba, shi mutun ne ma da idan ya ga zata kauce hanyar Allah zai tsawatar mata idan ta kama ma zai haɗa mata da duka, dan haka kada ta damu ta yi duk abin da ya ce kawai ba tare da ɗarɗar ko shakka ba. Shi dai Areef bawan Allah sam baya jin Hausa bayan waƴan can kalmomi, dan haka sai ya zuba musu idanu yana kallon ikon Allah, sai magana daddy yake yi, shi gani ma yake yi kamar basu san me suke faɗe ba, abinku da ba yaren shi ba. Sai da daddy ya gama yi mata faɗa tsab sannan ya yi musu addu'a da fatan alkhari daga nan suka fito, tana gaba yana binta a baya, sam taki yarda ta jera da shi. Bedroom ɗin Aseef ya nufa, bayin Allah har lokacin barci suke zubawa, daga shi har Akilar tasa ba wanda ya motsa daga cikinsu, sun ci wahala kamar ba gobe. Saman bed ɗin nasu ya hau a in da ya tofa musu addua'o'i sosai da sosai, ita kuma tana tsaye a gefe tana kallon shi da mamaki, sai yanzu ne ta gasgata zancen daddynta da yake yawan cewa Areef ba zai cutar dake ba, ashe bawan Allah ne, yana da addini sosai, da a ɗan iska take ɗaukarsa, bata san shi kam na kwarai ne da samun irin shi ma akwai wahala ba, mai zuciyar zinari. Sai da ya kammala ne ya sauko tare da riko hannunta yana faɗin "Gaskiya yanzu kam a tare zamu jera, ai haka boyfriend and girlfriend suke yi, suna tafiya suna zuba love, to kema haka zaki rinƙa yi mini kin ji ko?". Gyaɗa mishi kai ta yi ba tare da ta yi magana ba. Wucewa suka yi waje har wajen mota, gidan gaba ta shiga shi ma mazaunin driver ya zauna, sun yi matukar kyau over abinsu. Kunna motar ya yi suka bar gidan, ta yi shiru tana tunanin duniya, yau Adiva da Maryam kawai take tunani, tunaninta ɗaya lokaci ya yi da ya kamata ta san abin yi dan wargaza gidan Hjyr daɗi, to amma waye take da shi wanda zai tallafa mata a duniyarnan? Sam ko daddynta bata son gayawa, dan a cewarta bata son ta sake jefa shi cikin bala'i, a bayama lokacin da yake da kuɗi yake harin mulkar kasan ma dan ya yi takun saka da su Abubakar jaja shi ne aka ne mi ɓatar da shi da kuma shafe babinsa bakiɗaya, bare yanzu kuma da komai nasa ya ruguje babu hukuma a hannunsa babu komai, idan ta gaya mishi ma wlh zata sa ransa ne kawai ya ɓaci a banza kuma babu yanda zai yi, domin kuwa gidan Hjyr daɗi dai su Abubakar jaja ne suka kafa, to a karo na biyu bata son daddynta ya sake shiga bala'in su, kuma tana da gaskiya aka ce idan maciji ya sareka, to ko igiya ka gani dole ka tsorata, kada ku manta shi Farooq yana raye, so tana tsoron sake jefa daddynta cikin bala'i, shi ne yasa ta kasa gaya mishi, a hakan ma bata san cewa ba iya takarar siyasa ce kawai tasa Abubakar jaja ya yi niyar shafe daddynta a doron duniya ba, akwai tsama a tsakaninsu na kamasu da daddy ya yi suna safaran mata da kananan yara, suna fitar da yara waje ba da izinin iyayensu ba, a sayar musu da koda, sai su zaɓi matasanmu masu jini a jika, waƴan da suke fama da talauci suna neman abin da zasu ci a fujajan, talakawa waƴan da basu da ilimi basu san darajar kodarsu ba, su yaudaresu da sunan zasu basu kuɗi gida da sauransu, su fitar da yara waje a je a cire musu koda ɗaya, sannan suna safarar mata su fitar da su kasashen Turawa su kai su gidan karuwai su karɓi kuɗi, su yaudaresu da sunan aiki, kuma duk mafiya yawan aiki Hjyr daɗi take gudanar da shi, zata yi shiga ta mutunci ta je ta yaudari mata da sunan aiki, daga kin yarda shikenan sai idan Allah ya ƙaddara zaki dawo lafiya, wata ma sai ta kamu da cuta suke kwasota su dawo da ita, kananan yara suna yi musu alluran shakafashe su sanyasu karuwanci, ga safarar kayan maye su shigo da shi ta ɓarauniyar hanya, haka zalika suna shigo da mugayen makamai ta ɓarauniyar hanya su sayarwa ƴan ta'adda ayi ta kashe talakawa, so daddy ya taɓa kamasu a kan wannan aiki, a lokacin kuma kowa shi yake so, shi za'a zaɓa, ya ci alwashin idan har ya hau mulki wlh sai ya tarwatsasu, ba yanda Abubakar ɗin bai yi ba a kan daddyn ya dawo cikinsu, amma sam ya kafe yaki yarda, ya ce shi talakawa zai yi wa aiki kuma sai ya tarwatsa azzalumai da yardan Allah, kuma sun san batun zaɓe shi zai ci, sun kuma san shi da zuciya idan ya ce zai yi abu to fa sai ya yi, tabbas sai ya wargazasu, hakan tasa suka nemi ɓatar da shi su shafe babinsa baki ɗaya a duniya, amma da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne, komai daren daɗewa zalunci bata tabbata sai ta ruguje, sai Allah yasa Jehan ce ma ta zama sanadiyar mutuwar Abubakar ɗin wanda ko a mafarki ya yi mafarkin ƴar Nawazudden ce zata kashe shi idan ya farka sai ya yi ta dariya dan ba zai yarda ba, sun yi niyar kashe Nawazudden lokacin da uncle Shitu ya biyosu, da gindin bindiga suka daki uncle Shitun a kai sanadiyar haka kansa ya fashe, shi ma sun so kashe shi, amma Allah bai yi ba ya kuɓuta da kyar, ya juya kan motarsa ya samu ya gudu, Allah ya yi yana da rabon shan ruwa a gaba shi ma, a dai'dai lokacin ne kuma daddy ya yi wa mummy massage a kan su gudu dan ba sojoji ba ne suka kama shi, abokan hamaiya ne, mum tana cikin ruɗu bata ga saƙon ba har sai da suka bar Abujan. Kafin su yi yunkurin kashe daddyn sai da Abubakar jajan ya zo har gabansa ya sake yi mishi ta yi na shiga cikinsu a karo na karshe, nan ma saboda karfin zuciya irin na daddyn da karfin imani ya riki Allah yana ganin mutuwa amma ya ce shi ba zai yarda ba, shi gaskiya kawai ya riƙe, ya riki Allah kuma ba zai ci amanar talakawa ba, hakan tasa Abubakar ɗin ya ce a kashe shi kuma a kashe family'nsa, dan idan familynsa suna raye ya san su sarai gwaggo ba zata taɓa yarda ba, ko an kawo gawarsa zasu shigar da kara kuma dama kunsan gwaggon Jehan da iya faɗa, zata ce sai an binciko mata ya akayi ya mutu, idan ma ance mata accident ne zata ce sai an bincika, ita ma mummy ba zata bari ba, zasu kafe sai an bincika, idan kuma ba'a dawo da gawarba, nan ma zasu fito duniya wa ƴan jarida su yi sanarwa Nawazudden ya ɓata, ga shi kuma su suke da goyan bayan al'umma a lokacin, za a bi bayansu sosai, za'a bazama nemansa har gaskiya ta bayyana, shi ne yasa ya ce a kashe gabaɗaya harda family'n nasa. Wani maharbi ne ya ceci daddy daga hannunsu, da sun kashe shi, wannan maharbi ya jima a wajen yana taimakon mutane da ake kawosu za'a kashe, tsohon maharbi ne sosai wanda baya saɓa saiti, da ba'a nan yake da zama ba, daga baya ya dawo wajen da zama, shi ya ceci daddy a in da ya harbesu da kwari da baka ya kuma fito suka yi fito na fito da shi, a lokacin Abubakar jajan ya bar wajen dan ya ce a kashe daddyn sai ya tafi, wannan maharbin ya kashe su gabaɗaya, suma sun yi ƙoƙarin harbinsa da bindiga, amma ina bindiga bata cinsa, ko bullet ɗaya bata iya taɓa shi ba, kowa yasan dayawa daga cikin maharba suna tsafi, ba dukkansu bane akwai waƴan da basu yi, to shi yana yin tsafi shiyasa bullet bata cinsa, kuma ya dai'na harbin ma yanzu, ya koma wajen ne kawai da zama abinsa dan ya rinƙa taimakon mutane, daddy ya yi kwana biyu a wajensa kafin su rabu a in da daddyn ya ce mishi zai dawo zuwa nan da wani ɗan lokacin, to ya amsa mishi da shi suka yi sallama cikin mutunci, yana bala'in kaunar daddyn, idan baku manta ba dama shi daddy da daddyn Anaya bala'in shiga rai ke garesu, to haka daddy ya shiga ran wannan maharbi sosai in da suka yi zaman mutunci kuma rabuwar mutunci cike da kaunar juna. Daga nan da daddy ya bar wajen ya dawo Abuja a in da maharbin ne ya taimaka mishi da kuɗin mota, lokacin da ya dawo babu su mummy, uncle Shitu ya saka su a motar Katsina, ganin basu nan ne yasa ya ji ba zai iya zama ba, komai nasa ya lalace, idan babu su mummy ai babu shi, ba zai iya zama ba, sune komai na shi, dan a tunaninsa kashe su akayi, yasan babu in da za su je a duniyar nan, basu da kowa, hakan tasa ya je banki ya ciri kuɗi dayawa ya fita kasarnan ta ɓarauniyar hanya dan komai na shi na cikin gida su passport da sauransu, so dole sai ta ɓarauniyar hanya zai bi, dan gidan nasa an sanya mata kwaɗo da sarka an rufe. WANNAN SHI NE ABIN DA YA FARU DA DADDY BAYAN RABUWAR SHI DA SU MUMNY, KO BAN TSAYA NA YI DOGON BAYANI BA NASAN KUN FAHINCI IN DA ZANCEN YA DOSA KO? TO MU CIGABA DA STORYN MU. ❤️AREEF and JEHAN💋 Wani katafaren wajen shakatawa ya yi parking na motarsa, waje ne na ƴaƴan shugaban kasa, gwamnoni, ministocin, ƴan majalisu, sarakuna da sauran manya kusoshin gwamnati, wajen ya kawatu iya kawatu ba karya, ba zaka taɓa tunanin a cikin Nigeria kake ba idan ka shiga wajen, zaka yi tunanin irin a Dubai or saudiyan nan kake, an narka dukiya na kin karawa wajen kawata wannan waje ba karya, tsayawa zayyana muku kawatuwar wajen nan ma sai ya cinye mana ɗan space ɗin da ya rage mana, dan haka ku kawata a ranku kawai abin sai wanda ya gani. Mamaki ta rinƙa yi a kan yaushe ya san wannan wajen kuma? Sai ka ce wani ɗan Kasa, ya wani kawosu nan?. Manya manyan dankara dankaran shegun shadaddun motoci ne suke shawaji a wajen, sai kaga wata shegiyar mota wanda sai ka rantse da Allah ba'a kan kasa take tafiya ba saboda haɗuwa, da ta yi parking sai kaga wata ƴar figaggiyar yarinya ce zata fito daga ciki wanda bata wuce ka hureta ta faɗi ba, irin yarannan masu zubin taliya, sai aukin taunan chewing gum suna wani yi wa mutane kallon kaskanci da walaƙanci. Fitowa ya yi abinsa tare da ce mata ta zo su je, ita dai duk ta tsorata da ganin wajen, har da su pool a cikin wajen, ga abubuwan more rayuwa tamkar baza'a mutu ba, tun da ya sako kafarsa waje mata da maza suke kallon shi tamkar zasu cinye shi saboda kallo, ba karya ya yi kyau sosai. Jingina da jikin motar ya yi yana jiran ta fito, sam taki fitowa, sai da ya ji shiru ne ya zagaya ta side nata, duk in da ya yi motsi idanuwa ne rututu na mata da maza a kan shi, sun ga masu jajayen kunnuwa, akwai fafare da dama a wajen, amma kunsan Turawa da shegen farinjini a wajen mu, kuma uwa uba ga shi kyakkyawa matashi lafiyayye mai jini a jika ɗaya tamkar da dubu, ai tuni kallo ya dawo kansa babu ko kyaftawa, wasu ma har cewa suke yi basu taɓa kallon kyakkyawa irin shi ba, mata dayawa sun afka tarkon kaunarsa, sai haɗiye yawu suke yi kamar wasu kanne mayu, sun ga ɗan achan achan, ga kuɗi ga mulki, kyau tamkar shi ya yi kansa. Buɗe mata kofar side ɗin nata ya yi yana faɗin ta fito su tafi, ya yi maganar yana miƙa mata hannu, cikin sanyin jiki ta bashi hannunta ya rikota ta fito, nan fa kallo kuma ya dawo biyu, dan da dama daga cikin jama'ar wajen Jehan da Areef sun yi musu muguwar kama, idan baku manta ba ita dai Jehan farace tas tamkar Naurat, sai dai fa duk da haka a gabansa ita ɗin baka ce, haskensa yana dishashe nata, dan shi ziryan Bature ne babu mix, ita kuma akwai. Sai kallonsu a akeyi, tamkar bai san menene murmushi ba haka Areef ya zama yau, ya ɗaure fuskar nan tamau kai ka ce ba shi ba ne, babu alamar annuri a tattare da shi, duk waƴan da suke wajen sun sha jinin jikinsu, kuma kallon da ya ga suna yi musu ne yasa ya ɗaure fuska babu wasa, ita kanta Jehan ɗin ta tsorata da ganin yanda ya wani ɗaure fuskar nan tamau tamkar bai san menene ma murmushi ba, sai ya dawo mata sak Lion. Cikin wajen cin abincinsu suka shiga, wasu shegun tsadaddun kujeru ne waƴan da suka amsa sunansu kujeru, ga bala'in laushi kamar menene, komai na cikin wajen launin ash da baki ne, Jehan fa yau ta sha jinin jikinta, ta ga manyan mata masu class yanda suke kallon Areef kamar su cinye shi ɗanye, ko kyafta idanu daga kansa sun kasa yi, sun ga kyau iya kyau, shi kuma bawan Allah, ko kallon in da suke ma bai yi ba, ya kafe kallonsa a kan Jehan ɗinsa, ita kaɗai yake so babu canji, duk sai ta ji wani iri a jikinta. Kayan cima kala kala da dama aka kawo musu, kusa da juna suka zauna sosai, sai kallon yanda mata suke kalle mata shi take yi, duk matan dake cikin wajen cin abincin ma idanunsu ya dawo kansa. Ɗauko kankana ya yi daga cikin fruits da aka kawo musu, cikin zolaya ya ce "Mu bamu cin abincin restaurant or wani waje, mu abincin gida kawai muke ci, amma dalilin Rimsha mun ci a restaurant ranar, yanzu kuma dalilinki zan sake ci". Ɗan kasa ta yi da kanta tana faɗin "Au dama kun taɓa zuwa nan da Rimsha ne?". Girgiza mata kai ya yi yana faɗin "A'a muna zuwa yawo dai, amma bamu taɓa zuwa nan ba, wajen nan ai na boyfriend and girlfriend ne or something like that, Rimsha kuma sisterta ta ce ai, ya za'ayi......". Bai karisa ba wata figaggiyar yarinya ta yi musu sallama a kansu, sam bai ɗago idanu ya kalleta ba, Jehan ɗin ce ta ɗago idanu tana kallonta. Hannu ta miƙa mishi tana mai gabatar mishi da kanta, ita kam Jehan sake baki ta yi tana kallon wannan yarinya mai tallar kai haka, dama tun da ta shigo ta ji wasu ƴan mata su uku da suke zaune kusa da su ta baya suna magana cikin harshen Hausa a kan ɗaya ta ce wlh sai ta tinkare shi ko me zai faru ya faru, ɗayar ta ce Allah da budurwarsa yake tare, musa mata suka yi a kan sam Jehan ba budurwarsa ba ce kanwarsa ce, dan sun yi kama kuma wannan yarinyar ai ta yi karama ace budurwarsa, kina ganin matashi lafiyayye kyakkyawa ga kirar karfi da lafiya mai class kamar wannan me zai yi da wannan ƴar yarinyar a budurwa? Caraf ɗayar ta capke tana faɗin "Amma ai kinsan yarinyar tana da kyan da dole zai sota ko? Ni fa duk cikin wajen nan idan gaskiya za'abi wlh ban ga mai kyan yarinyar nan ba". Tsaki ɗayar ta yi tana faɗin koma wacece wlh ita sai ta je ta kula shi, to shi ne ta zo, saura sun ce wlh ba zasu iya ba, suna tsoron dan sunga face nasa babu alamar wasa a tattare da shi, ita dai ta ce ko za'a kasheta sai ta zo. Kankanar hannunsa ya kaiwa Jehan ɗin saitin ɗan bakinta yana faɗin ta karɓa ta sha, kallon yarinyar da take tsaye musu a kai ɗin kawai take yi, hannu ya kai ya rufe mata idanu yana tura mata kankana a baki, sam tamkar bai san da yarinyar a wajen ba, wani irin kunya yarinyar ta ji, ya yi mata kalakanci na karshe da cin fuska, ya tsinkata a cikin mutane, shi kuma lokacin yin magana da ita ne ba shi da shi, bai ga abin kulawa a wajen ba, bata kai ya ɗaga idanu ma ya kalleta ba a cewarsa. Haka ta juya jiki ba kwari kunya kamar ta shige cikin kasa ta bar wajen, shi kuwa cigaba da bawa ƴar diramarsa fruits ya yi tare da zame hannunsa daga saman idanun nata, kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Ni ba zaki bani a baki ba ne? Ko kin manta am your boyfriend ne?". Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin "A'a ban manta ba, ai kai ne baka ce na baka ba". Ɗan matso da face nasa daf da tata ya yi yana faɗin "Ai ba sai nace ba mana, haba baby". Salar yankar apple ta ɗauko ta kai mishi saitin ɗan bakin nasa ba tare da ta yi magana ba, buɗe baki ya yi ya karɓa ba tare da ya barɓa dukka a cikin bakin nasa ba, sai ya ɗan ciza kaɗan ya rike, kallon shi ta yi tana kallon yanda ya ɗan rike apple ɗin da fararen hakwaransa yaki kaiwa cikin bakinsa, bata ankara ba sai ji ta yi ya jawota jikinsa tare da haɗe fuskokinsu ya kai mata apple da ya rike da kyawawan hakwaransan bakinta, hakan da ya yi ya sanya mata da yawa a wajen sun zubar da abin sha da yake hannunsu, yasa samari da dama jin kunya dan basu iya soyayya ba!. Ita kuwa ya tashi kanta, dan bata taɓa tunanin zai yi mata hakan ba, bata da zaɓi dole ta karɓa ko dan kada ta tsinka shi a cikin mutane, amma ya bata kunya, ko da ta karɓa kuma sam bai rabe fuskokin nasu ba, ya zuba mata idanu yana kallon yanda take taunar apple ɗin. "Baby to bani apple ɗina, dama na baki ne ki tauna mini". Ya faɗa cikin sanyin murya, batasan time da murmushi ya kubce mata ba. "Apple naka dai na cinye, sai dai ka ɗauki wani". Ita ma ta bashi amsa a sanyaye. "Ni bana son wani na cikin bakinki nake so". Make mishi kafaɗa ta yi tana fito mishi da harshe dan ya gani ta taune ta kusa haɗiyewa, shammatarta ya yi ya kama harshen nata da bakinsa, da sauri ta kwace kayanta tana turo baki. Cool murmushi ya saki tare da raba fuskokin nasu, tamkar wasu film aka mayar da su a cikin wajen, tsantsar madarar soyayya yake zuba mata, ya kuma yi mata wayo ta biye mishi ba dan ta so ba, haka suka kasance cikin tsantsar farinciki a wannan wajen, suna ta tashin kan masoyan da suke wajen. A ɓangaren Rimsha da Lion kuwa yau ma dai kamar jiya, sai misalin karfe 10 na safe ta farka daga barcin nata, sai dai fa yau ba dan ra'ayin kanta ta farka ba, wani azababben ciwon ciki ne ya tasheta, kuka ta fara yi tana juyi a saman bed ɗin, shi kuma Lion baya nan yana waje kamar dai jiya yana kallon hanya, sun yi nisa sosai a tafiyar tasu, sun kusa isa in da yake son su kai. Juyi take yi a saman bed ɗin tana hawaye, a haka Brady ya shigo ya sameta, ta kasa buɗe murya ma bare ta yi kuka mai sauti da zai sa Lion or wani ya jita. Ganin yanda take juyi yasa Bradyn ya haye gadon da gudu yana tattaɓata, yau duk tsoronta da shi sai da ta yi la'asar, ta ji tana gani yana taɓata amma ta kasa motsawa ma bare ta gudun mishi, shi kuwa ya shiga damuwar ganin halin da take ciki, sai ƙoƙarin janta yake yi dan ta miƙe, amma ta kasa, da gudu ya diro kasa daga saman gadon ya nufi waje. Bai zame ko'ina ba sai wajen Lion, jikinsa ya haye yana yi mishi nuni da cikin bedroom ɗin yana haushi da karfi karfi, da yake sun san halinsa, shi ya reni kayansa sai ya gane karatun nasa, ya fahimci akwai matsala a cikin ɗakin, rungume shi ya yi tare da juyawa suka nufi ɗakin a tare, sai haushi yake yi da karfi karfi. Suna shigo Bradyn ya sauka daga jikin nasa ya haye saman bed ɗin yana cigaba da yin haushinsa, karisowa wajen Lion ɗin ya yi, hayewa saman bed ɗin shi ma ya yi tare da sanya hannu ya ɗagota, kuka take yi sosai ta dafe cikinta, hannunta dake saman cikin nata ha zame tare da ɗaura nashi a wajen yana kallon face nata. "Meesha menene yake damunki?". Ya faɗa yana mai cigaba da kallon face nata yana kuma shafa mararta a hankali hankali. Da kyar cikin kuka ta amsa mishi da cikinta ne yake yi mata ciwo. "Kin taɓa yin period ne?". Ya tambaya. Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a, ɗan rungumota ya yi a kirjinsa yana shafa bayanta a hankali dan ya san matsalar kenan, yanzu sai dai su jira lokacin zuwan shi kafin ya bata magani da allura. Kankame shi sosai ta yi tana kuka shi ma Brady yana tayata kuka, Allah sarki yaji tausayinta, duk da yake kare ya ji ba daɗin ganinta tana kuka kuma cikin wani hali, duk sai shi ma ya shiga cikin damuwa, yau abokiyar faɗa bata da lafiya. Kun sani a duniya babu kalmar da Lion ya tsani ji kamar sorry, ya tsani wannan kalmar, ko a faɗa mishi ita ko shi ya faɗa, bai taɓa cewa wani sorry ba, idan kuma wani ya ce mishi to sai ya hukunta shi mummunar hukunci ma, amma yau an wayi gari shi da bakinsa yake cewa Rimsha sorry yana shafa marar tata a hankali hankali, haƙiƙa ya tausaya mata dan yanda take murkusoso sai ta baka tausayi, ita kuma da azababben ciwon mara ya zo mata. Cigaba da kukanta ta yi tana kara shigewa jikinsa tare da kankame shi. Almost 40 mins tana a wannan hali kafin period ɗin nata ya zo, ta jigata ainun, ta wahala ba karya, ta sha kuka kamar ba gobe, duk da ya zo kuma marar tata bai dai'na ciwo ba, sai sambatu take yi mishi a kan ita wlh bata son period ɗin nan, dama ai lokacin da Ayla zata fara period ita ta ce bata so, dan Allah yaya Saif ya ce period ɗin ya tafi, mutuwa zata yi idan bai tafi ba, ciwo cikinta yake yi, wayyo mummynta, daddynta, ita yau ta shiga uku zata mutu. GA ABIN DARIYA GA ABIN TAUSAYI. Banda sorry hard luck babu abin da yake ce mata, sai dai ya shiga damuwa mara misaltuwa na ganinta cikin ciwo har haka, shi kansa ya ji ya tsani period ɗin nata dan da alama zai wahalar da ita over, shi kuma yanzu zuciyarsa ba zata iya jure ganinta cikin wahala ba, ga shi ba yadda zai yi, dole dai wannan sorry shi zai yi ta ce mata yana rungume da ita, dan shi dai period dole ya zo ato, ya barta tanata sambatun nata dan zai rage mata raɗaɗi ba kaɗan ba. Ganin jinin ya zo ne yasa ya kwantar da ita tare da miƙewa ya sauko kasa, duk ta ɓata mishi jiki, sam bai damu ba, a matsayinsa na babban soja jini ba bakon abu ba ne a wajensa, abin da ya fi jini ma ya tsallake kafin ya taka matsayin da yake kai a yanzu, so duk wani soja da zai ce baya son ganin jini or yana kyamar jini ma to ba soja bane, ragon namiji ne! Su da suke fasa mutun da bindiga ma jininsa ya wanke musu fuska!, Me dan jinin mace ya taɓa su? Amma dai baya son ganin jinin a jikinsa, ya so ya canza kayan amma sai ya ce bari ya gama dubata ya tabbatar ta ji sauki kafin ya yi wanka, idan ba haka ba ko da ya yi wanka ya canza kaya ya sake dawowa wajenta ma sake ɓaci da jinin zai yi, dan ba always ba ne garesu a cikin jirgin!. A box ya ɗauko ya dawo saman gadon, nan fa suka fara rikici da ita, dan kuka ta saka mishi a kan wlh ita bata son allura, jinjina kai ya yi yana faɗin e lallai ta sami lafiya ba shakka, da farko kamar zai yi mata tsawa, amma kuma sai ya danne dan tana cikin ciwo ne, lallaɓata ya yi cikin dabara ya yi mata alluran tare da bata magunguna dan ta sha, da kansa ya ɗauko mata ruwa ta sha maganin sannan ya ɗauketa zuwa toilet, har lokacin tana fama da ciwon ciki, sai dai ya ragu ba kamar na ɗazun ba. Haɗa mata ruwa ya yi ya ce ta yi wanka, fita ya yi ya bata waje, da kyar ta iya cire kayan jikinta ta yi wankar, shi kuma cikin bedroom ɗin ya dawo a in da da kansa ya cire bed sheet ɗin da ya ɓaci shi ma da jini saboda kwantar da ita da ya yi ya je ya ɗauko A box, ba zai iya sanya Mark ya yi wannan aiki ba saboda tsananin kishi, to gara mishi ya yi da kansa dan ma kada wani ya kalli jinin nata........ LION DUNIYA SARKIN KISHI, DAGA KANKA AN RUFE KOFA IN DAI FAGEN KISHI NE!!. Canza bed sheet ɗin ya yi dai'dai lokacin ita kuma ta fito wanka ɗaure da towel tana wani layi ta dafe ciki saboda azaban ciwo da yake yi mata, bai ce mata komai ba ya wuce ya shiga cikin toilet ɗin, wanka ya yi ya fito, kwance saman sofa ya iskota ta sanya kaya, ta yi shiru tana sauraron yanda marar nata yake murɗa mata tamkar zata mutu, hawaye wani na bin wani a face nata, kayansa ya ɗauka tare da komawa cikin toilet ɗin ya shirya, pajama ce fara tas ya sanya a jikinsa. Bayan ya fito kuma sai ya tsaya shiru yana tunanin yanda zai yi da ita, basu da always a cikin jirgin, ga shi kuma jirgin nasu ne su kaɗai ba na kasuwa ba ne bare ya ce ko su tambayi wasu, wani ɓangare na zuciyarsa ce ta ce mishi to ya aika Mark ya sayo musu a ɗaya daga cikin garuruwan da suke kusa da su mana, sai Mark ɗin ya yi amfani da mashin na ruwan dake ciki kin jirgin ya je ya sayo ya dawo ya samesu. Girgiza kai ya yi kishi ba zata iya barinsa ya aiki wani ya sayo mishi always da pant nata ba, haƙiƙa idan har Mark ya rike su da hannunsa to wlh ba zata yi amfani da su ba, tunani ya yi to ko dai ya je da kansa? Nan ma kishi ba zai barshi ya iya tafiya ya barta ita kaɗai cikin zaratan sojojin nan ba, to shi ya zai yi yau? Ya tambayi kansa, bai isa kuma ya ce zai ɗauketa su tafi ba, dan bata da lafiya sosai, kuma a gaskiya ba zai iya yin nisa da ita ba yanda take wannan murkusoso na ciwon marar......... TO JAMA'A SAI KU BAWA LION SHAWARA, KISHI BA ZATA BARSHI YA IYA AIKAN MARK YA SAYO ALWAYS DA PANT BA, HAKA ZALIKA KISHI BA ZATA IYA BARIN SHI YA JE DA KANSA YA BARTA ITA KAƊAI CIKIN SOJOJI BA, GA SHI BATA DA LAFIYA, BA ZAI IYA NISA DA ITA BA, TO YAKENAN ZAI YI? KU BASHI MAFITA, NI DAI NA HAƊA KAYANA ZUWA GIDAN ABBI DAN NA DUBA SU AYLA SUKE. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 *KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*. *KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ ❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋) *Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581* https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S 77 ❤️GIDAN ABBI💋 Mu koma baya dan jin abubuwan da suka faru, a lokacin da su Abbi suka kai A'A SALAHUDDEEN Asibiti, sum kira babban yayansa KABIR SALAHUDDEEN a kan ya zo ya ga halin da kaninsa yake ciki, waya ya yi wa maman Anisa da take cikin Kd a kan ta yi sauri ta isa asibitin dan ta duba halin da A'A ɗin yake cikin kafin su zo tun da su a Abuja suke, idan baku manta maman Anisa ba, ita ce wanda A'A ya gayawa su Rimsha Ayla tana kama da kanwarsa Anisa da take cikin KD, to ita ce Kabir ɗin ya kira dan ta zo ta kula da shi. Sai da maman Anisar ta zo sannan su Abbi suka dawo gida suka barta da A'A. Bayan sun dawo gida sun ci abinci sun ɗan huta, sai Abbi ya buƙaci maman Ayla da ta zo ta basu labarin abin da ya faru da yaya kuma akayi ta san *ABUBAKAR SALAHUDDEEN* ita dai Ayla baiwar Allah sai barcinta take yi abinta, Aunty da ƙoƙari har da rufa mata bargo ta zo ta yi tare da rage mata gudun Ac palon. Haɗuwa suka yi a palon da Abbi da daddyn Jelly sai maman Aylar, Ayla kuwa tana saman sofa tana barci, Aunty kuma miƙewa ta yi ta bar musu palon dan ita bata son jin labari mai taɓa zuciya, ita irin mutanen nan ne masu saka abu a rai, idan har labarin maman Ayla yana da taɓa zuciya to wlh idan ta ji zata jima bata manta da shi ba, shi ne yasa rufin asirrinta kawai ta bar palon dan zaman lafiyarta da abin da yake cikinta, ita kuwa Hjy Hadiza tana can cikin bedroom nata tana aikin kullewa da warwarewa na yanda zata yi da Abbi, ta dai ki barin gidan, ɗan balaraben mijinta kuma sai kiranta yake yi a waya a kan shi zai biyota Nigeria, kullun cikin waske mishi take yi, tana kwantar mishi da hankali da duniyancinta a kan ta kusa dawowa, ba dan yana so ba yake hakura, amma yana bala'in son ta dawo dan ƴarta Suhana ta kamu da ciwo wanda yana tsoron kai ta aisbiti dan kada asirinsa ya tonu, shi ne yasa yake son maman ta dawo, a haukarsa idan ta dawo zata san yanda zata yi ta yi jinyar ƴarta ba sai sun kaita asibiti ba, ya kuma ki yarda ya gaya mata basu da lafiya, sai dai ya yi ta damunta a kan ta dawo kawai. Abbi ne ya yi gyaran murya a in da ya ce da maman Ayla ta basu labarin abin da ya faru, shi dai daddyn Jelly labarin ma bata dame shi ya ji ba, shi dai yanzu tun da ya gano alaƙar da take tsakanin Ayla da mummyn jelly to Alhadulillah, yanzu ya fahimci akwai aure a tsakaninsa da Aylarsa, to shi bai ma son jin wani labari na bakin ciki, amma da yake Abbi ne ya ce ta basu labarin sai ya hakura ya zauna yana sauraro. Labari ta fara basu kamar haka, "Ni dai asalina ƴar garin Bauchi ce, karatu ne ya kawoni Zaria Kaduna state, iyayena masu kuɗi ne dai'dai gwargwado, mahaifina babban malami ne, mu uku iyayenmu suka haifa, ni ce ta biyu bayan yayana babba sai autarmu Aliya wanda na mayar mata da sunan Ayla kenan, a kullum idan aka yi hutu ina komawa gida, ina zaune ne a hostel namu, ina karatu babu kama hannun yaro, iyaye na kuma kullum idan muka yi waya suna yi mini faɗa a kan na kula da mutuncin kaina, a duk in da nake na ji tsoron Allah, na sani mutuwa zata iya riskana a kowani lokaci, na sani abin da na aikata ko a gaban idanunsu ko a baya to a baya ɓuyarwa Allah, yana ganin komai kuma a ranar tashin alkiyama tamkar Tv haka za'a buɗe rayuwata wa jama'ar duniya bakiɗaya su kallah, to dan haka na kula da duk abin da zan aikata, ina ɗaukar maganarsu sosai musamman mahaifiyata da ta kware wajen iya nasiha mai ratsa jiki. So wasa wasa na fara yin kawaye a makarantar, da farko bani da ko ɗaya, daga baya na yi wata kawa malama nitsatsiya mai sunan Maryam, mun cigaba da rayuwa tare da ita muna karatunmu lafiya Lou, bamu kula kowa. Akwai wani malami da ya nemi ya samu kusanci da mu, amma mun ki bashi kofa, harkar gabanmu kawai muke yi, a taikaice dai har Abida ta zo ta shiga cikin rayuwarmu, Abida ita ce mafarin rugujewar rayuwarmu, ita ta fara koya mana shan kayan maye irin su kwaya da sauransu, yanda akayi ta fara koya mana kuwa shi ne, idan mun je class mun dawo, irin muna complain na mun gajin nan, to sai ta bamu ta ce mu sha rabin kwalba gajiyar zata sakemu, tun muna ki dan bamu ma san menene ba har muka fara sha, abin ku da kayan shaye shaye, fara shi ne wahala, da ka fara zaka ji ba zaka iya dai'na wa ba, zaka ji idan baka sha ba zaka iya mutuwa, to muma haka ce ta kasance da mu, ba mu iya wuni bamu sha ba, abin har ya zama mana jiki. Kwance tashi babu wuya a wajen Allah har wani matashi ya shigo cikin tafiyar ta mu mai suna Anwar, mun yi rayuwa da Anwar na tsawon watanni da basu fi biyu ba, to ashe shi kam ba tsakani da Allah ya shiga cikinmu ba, ashe irin mazannan ne masu kaiwa manyan masu kuɗi ƴan mata dan su yi lalata da su, a hankali ya fara yi mana inviting na harkar, sam muka ki yarda, a lokacin kuma ya turawa Abubakar salahuddeen hoto na, tun da ya ganni kuma ya ce na yi mishi yana bukatar a kawo mishi ni. Ba irin kuɗin da Anwar bai nuna mini ba, amma naki yarda dan ina bala'in tsoron iyaye na da kuma yayana, a barni dai a iya kayan mayen nawa, to da suka ga wannan hanya yaki shi kuma Abubakar ya kwallafa ransa a kai'na, sai ya fito da kansa ya nuna yana so na ne da aure, da yake ni ban san cewa shi ne Anwar yake yi wa aiki ba, sai na karɓi soyayyarsa, mun yi soyayya sosai amma kusan zan ce muku soyayyar ta sirri ce, dan har mamaki nake yi watarana a kan baya taɓa zuwa wajena da rana sai da daddare, yana yin abu tamkar mara gaskiya, kuma a lokacin sam bai shiga siyasa ba. A hankali yana jana da kalamai na yaudara irin na mazan banza da idan suna son abu a wajen mace ba irin kwatar da murya da marairaicewa da basu yi, tun ina ɗari ɗari da shi har na saki jiki muna hira tare da zuba soyayya, karatuna ya ja baya sosai saboda kayan mayen da nake sha, sam kwakwalwata bata ɗaukar karatu, da anyi karatu after 10 mins na mance komai, na zama wata iri da ni, haka zalika ita ma Maryam ta zama sai a hankali, ita kam Abida dama ai ta saba, so bata jin komai, su mamana kuwa, sai na fi sati ban nemesu a waya ba, sai idan su suka gaji da kansu suka kirani, idan na ɗauka sai nayi musu karya na ce musu wlh lectures ne suka ɗauki zafi yanzu, abubuwa ne sun sha kai'na, suna yi mini uzuri, haka mama zata yi ta yi mini nasiha duk a banza, dan a wannan lokacin nasihar ma sam bata shiga kai'na, a yanda nake ma ji nake yi mama fa tana takura mini, idan kuma ta cigaba to watara zan buɗe mata aiki ko da tawayar ne. Haka muka cigaba da rayuwa har Abubakar ya fara cewa na raka shi shopping da sauransu idan ya zo Zaria, ba a Zaria yake ba zuwa yake yi, ni ban san garin shi ba daga farko, sai daga bayana na san cewa shi ɗan Kano ne, da tafiya ta yi nisa ne ya gabatar mini da kaninsa Farooq duk dan na kara yarda da shi sosai, ya kuma yi sa'a dan na kara yarda da shi over, na saki jiki aurena zai yi da gaske kamar yanda yake faɗa, haka zan raka shi shopping muje mu dawo lafiya lou, wani lokaci ma tare da Farooq ɗin muke zuwa, so yana da gidan hutawa a Zaria, a lokacin sau ɗaya da muna dawowa daga shopping ya ce mu biya ta gidan dan mu ɗan huta, to a nan ne nasan da gidan. In takaice muku labari Abubakar da Farooq sai da suka yaudareni suka zuba mini kwaya a cikin abin sha a cikin school namu da ya zo muna hira da shi, tare da Farooq suka zo ranar, sun saka mini kwayar barcin bayan na sha na yi barci a cikin motar ne suka ɗauke ni muka fita zuwa gidansa, ban taɓa kawowa zai sanya mini kwaya a abin sha ba, na yarda da shi sosai da sosai, hakan yasa nake karɓar abin hannunsa na sha. Ban sake sanin in da kaina yake ba tun da na sha lemun da ya bani sai farkawa na yi na ganni a cikin ɗakinsa na gidan hutawarsa, shi kuma yana kwance kusa da ni yana barci abinsa, ya bani kwaya na sha na yi barci ya lalata mini rayuwa, ya yi mini fyaɗe, na yi kuka sosai, ban da mamana babu wanda nake tunani, na san idan ta san da haka zata iya mutuwa, ta bamu tarbiya iya karfin iyawarta. Ko da na tashe shi daga barci sai ya nuna mini ai ba wata matsala ni matarsa ce In Sha Allah, yaudara ta ɗan bariki, da naki yarda ina ta kuka sai ya kira Farooq ya zo suka haɗu suka yi mini daɗin baki har na sake yarda da shi. Haka muka cigaba da rayuwa, mun cigaba da zuba soyayya tamkar ba gobe, bayan shi ni bana kula kowa, bai canza mini ba bai kuma gujeni ba har sai da ciki ya bayyana a jikina, nan fa rikici ya ɓarke a tsakaninmu, ya ce shi wlh ba cikinsa ba ne, ni kuma nasan shi kaɗai ne na taɓa kwanciya da shi, nan fa ya ce shi wlh ba cikinsa ba ne na nemi uban cikina kuma shi ya fasa aure na dan ba zai auri ragowar wasu ba, amma taimako ɗaya zai yi mini shi ne ya bani makudan kuɗaɗe na kuma zubar da cikin ko zan sami mijin aure, dan babu wanda zai aure ni idan ya ganni da ciki ko kuma ya ji labarin na taɓa yin ciki, to rufin asirina shi ne na zubar, ni kuma na kafe na ce wlh ba zan zubar ba, nan ne fa ya yi yunkurin kashe ni, ya aiko wasu maza biyu dan su kashe ni, Allah ya tseratar da ni, na sha da kyar. Sanin cewa shi ya aiko a kashe ni yasa na tura mishi da sakon Video da na ɗauke mu ni da shi a gidan hutawar tasa muna shan soyayyarmu, ina da ire iren videos ɗin da yawa dana ɗauka ba tare da saninsa ba, ganin video yasa hankalinsa ya yi mummunar tashi, a karo na biyu ya sake aikowa da a rufe babin rayuwata, da Allah yasa nan ma ina da rabon rayuwa a gaba, na tsira sanadiyyar ƴan'sanda da suka fito patrol, hakan tasa na haɗa kayana na koma Bauchi dan na je na reni cikina, na yi alkawarin wlh ba zan zubar da cikin ba sai na haifa, ina komawa Bauchi nan kuma babana ya ce wlh wane ubana, sai dai na koma in da na fito, ba zan zauna mishi da cikin shege a gida ba, ace yana matsayin babban malami a unguwa kowa yana girmama shi kawai sai ƴar cikinsa na ɗauke da cikin shege!, Na zubar mishi da mutunci, to wlh ba zai yi wu ba, na yi maza na je na nemi wani uban shi ya sallamani wa duniya, haka yayanmu babba ma ya rinƙa zagina, mamana ce kawai take ta kuka tana bawa babana hakura a kan ya hakura idan na tafi yanzu ina zan je? Fir babanmu ya murje idanu ya ce duk in da nake so na je amma ba'a gidansa ba. Haka na kwashi jiki na koma cikin Kaduna, da kuɗin da Abubukar ɗin ya bani na kama gida na zauna a in da na cigaba da renon cikina, muna zaman mutunci da ƴan unguwa, dan a tunaninsu ni bazawara ce da mijina ya rasu ko muka rabu, a yanda suke ganina da mutunci babu wanda yake yi mini kallon mai cikin shege. Bani da kowa haka na zauna cikin kunci tare da kewar kanwata da mamana, Allah sarki kanwata ko kallon karshe ba mu yi wa juna ba, lokacin da na je gida tana makaranta bata sani ba, shi ne yasa dana haifi ƴa mace na yi mata takwara Aliya ina kiranta Ayla, ko kaɗan banga laifin babana ba, domin kuwa da farko baya son naje makarantar, ni ne nan na kafe zan je, sai da muka yi yarjejeniya da shi a kan zan tsare mutunci na, sannan ne ya barni na je, amma na rusa komai. Haka na cigaba da rayuwa komai yana kare mini, duk kuɗin da Abubakar ɗin ya bani suna ta karewa dan ba juyasu nake yi ba, sai dai na zara na kashe, har ta kai ta kawo bani da abincin da zanci, kuɗin haya ya kare, ga Ayla tana karama bata fi shekara ɗaya ba lokacin, bani da zaɓi dole na kwashe gabaɗaya videos ɗin da na yi wa Abubakar daga kan wayata na zuba a cikin memory card a in da na ɓoye memory a wani wajen da na san ko yanzu na je wajen memoryn na nan, shi kuma wayar na sayar, a kwana a tashi shi ma kuɗin wayar ta kare a sayan abinci, nan fa na fara shiga kangin bauta da wahala, kuɗin haka ya kare, haka na sayar da wasu daga cikin kayan amfanina su gas da sauransu a in da na tashi daga unguwar da nake ɗin dan a wannan lokaci ba zan iya biyan kuɗin hayar wannan gida har naira 70k ba, shi ne na bar gidan na bar unguwar mutanen kirki na je na kama wani ƴar kango naira dubu 10 a shekara, duk kayana na wancan gidan na kwasosu zuwa wannan kangon, a takaice dai mun rayu cikin kunci da wahala ni da Ayla har na fara ciwo, haka yarinyar nan ta taso cikin kunci da bakin ciki, ba makarantar boko, gara Arabic ma lokacin da nake da lafiya ina koya mata sosai, kuma tana ɗaukar, sai dai na fi koya mata addua'o'i da sauransu, unguwar da muka koma sai su rinƙa ce mata shegiya idan ta fito, bata sakewa ta yi wasa koda a tsakar gida ne, sai dai a ɗaki, dan gidan ba mu kaɗai bane, akwai wasu matan da nasu yaran, to yaran suna tsangwamanta, kuma iyayen basu ce musu komai, haka zan wuni ina kuka tare da danasani na zuwata duniya, baiwar Allah bata san komai ba ta rayu cikin kunci da wahala tare da bakim ciki, lokacin da na san mahaifinta ya shiga siyasa, kara ɓoye kai'na na yi daga gare shi, dan kada ya kashe mini Ayla, na san cewa duk in da ya ganta sai ya san ƴarsa ce, dan kuwa babu in da ta barshi a kamanni, harta murya, kullum idan na ganta, sai na yi kuka ba kaɗan ba, saboda fuskar Abubukar da nake gani a tattare da ita, ban sake komawa gidanmu ba har yau da nake yi muku magana, lokacin da Ayla ta ɓata, aka sace mini ita, haukace kawai ban yi ba, Allah ne kawai ya kaddara ina da sauran rayuwa a gaba, amma da na jima da mutuwa saboda bakin ciki, ga shi bana iya tafiya a lokacin bare na je na nemota, na azabtu ba kaɗan ba, a haka har Allah ya haɗani da wata mata ta taimakeni, irin matan nan ne masu taimako bayin Allah, ita ta kaini asibiti, ban san waye ya bata labarina ba, kawai ina kwance a cikin ɗaki rai a hannun Allah ta zo ta ce mini daga kunguyarsu na tallafawa marayu da gajiyayyu ta zo, haka suka ɗauke ni zuwa aisbiti, bayan na warke ina iya tafiya da kafata, na yi tsantsar farinciki a in da na fara neman Ayla ido rufe, ban ganta ba, ban san a ina zan sameta ba, amma kullum addu'a ta ɗaya shi ne Allah ya kare mini ita a duk in da take, ban taɓa cire tsammani zamu haɗu zan ganta ba, bani da sana'ar komai hakan tasa dole na koma bara, bani da gidan da zan zauna dan kuwa gidan da muke ciki bayan na warke daga ciwo, na baro asibiti kenan, da na koma sai naga babu gidan an rushe shi, hakan tasa na fara kwana a kasan gada kawai, a takaice wannan shi ne labarina dana Ayla, na san saura abubuwan da suka faru kunji daga bakin ita Aylar?". Ta kai karshen maganar tana sharar kwallah. Daga Abbi har daddyn Jelly sai da suka yi kwallah, shi kam daddy dama kun san shi da saurin kuka, dan haka kukansa ya fi na kowa yawa, ya zubar da hawaye har da shessheka yana sauke ajiyar zuciya, sun tausaya mata sosai, shi kuma daddy ya kara jin tsantsar kaunar Ayla over fiye da a baya, ya tausayawa rayuwarta ba kaɗan ba, baiwar Allah ashe haka taci bakar ukubar rayuwa, kai gaskiya Ayla tana da tawakkali sosai yarinyarnan, da wata ce ai da yanzu wani labari ake yi ba wannan ba. Jin sautin kukan Ayla ne yasa dukkansu suka ɗago kai da sauri tare da kai kallonsu kanta, kuka take yi na wuce misali, ta jima da farkawa daga barci, duk labarin da mamanta ta bayar ta ji komai, baiwar Allah hawaye tamkar ruwan famfo haka yake bin kuncinta, tana daga kwance sam bata motsa ba. Da sauri daddy ya dawo kusa da ita dan ya rarrasheta, Abbi da maman nata duk dawowa kusa da ita suka yi, zama daddy ya yi saman sofar tata tare da ɗagota ya rungume yana rarrashinta, shi dama tun farko bai so ma ya tsaya ya ji labarin ba, ya so a bar komai kawai ya wuce dan baya son tashin hankali, ga shi yanzu sun sa babynsa ta ji komai tana kuka, yasan yanzu abin zai tsaya mata a ranta ga kuma ƙaramin ciki, da wanne ɗaya zata ji? Duk irin ukuban da wahalar da ta sha a baya bai kamata yanzu su barta ta sake yin kukan bakin ciki ba a rayuwarta. Dukkansu haɗuwa suka yi suna rarrashinta, da kyar suka samu ta yi shiru, ruwa mai sanyi Abbi ya ɗauko mata, karɓa daddy ya yi tare da buɗe mata ya bata a baki, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, duk wata zuciya mai imani sai ta tausayawa Ayla da mamanta, sun ga rayuwa ba karya. Ɗaukarta daddy ya yi suka bar palon dan sam baya son abin da zai sa yaganta cikin damuwa, gara su koma Part nasu ya sanyata farinciki, Abbi kuma rarrashin maman Aylar ya yi a in da yake gaya mata ai ga shi nan Allah ya saka mata, ta yi hakuri komai ya wuce, kuma In Sha Allah shi da kansa zai mayar da ita gida wajen iyayenta, zai yi musu bayani tare da nasiha, da izinin Allah za su yafe mata, dan haka ta dai'na damuwa ta koma ɗaki ta kwanta ta huta, godiya ta yi mishi mai tarin yawa kafin ta miƙe ta haura sama, shi ma miƙewa ya yi ya haura sama wajen Aunty..........TO JAMA'A KUN JI LABARIN AYLA, KUMA KUN JI ALAƘARTA DA MUMMYN JELLY, MUMMYN JELLY DAI ƳA CE GA FAROOQ SALAHUDDEEN KANIN ABUBAKAR SALAHUDDEEN, SO DA AYLA DA MAMAN JELLY CAUSINS SISTERS NE, FATAN KUN GA NE? BA SAI NA TSAYA DOGON BAYANI BA, NASAN KUN GANE IN DA MUKA DOSA, SHAWARATA A NAN SHI NE MATA MU JI TSORON ALLAH A DAI'NA SHAYE SHAYE, WANNAN SHAYE SHAYE DUK SHI YA JEFA RAYUWAR MAMAN AYLA CIKIN GARARI, DOMIN DA BATA FARA SHAYE SHAYE BA, DA KWAKWALWARTA YANA NAN GARAU BA ZATA BIYEWA SAMARI BA, KADA KU MANTA KO MATA BATA BIYEWA DA FARKO, KARATU KAWAI TAKE YI, SANADIYAR SHAYE SHAYE NE HAR TA YI ABOKI NAMIJI WATO ANWAR, YA SHIGO CIKIN RAYUWARTA YA TARWATSA MATA DUK WATA FARINCIKI NATA WANDA HAR YAU BATA SAKE SAMUN FARINCIKI BA A RAYUWARTA, YA LALATA MATA KOMAI, SANNAN SHAWARATA GA ƳAN MATA, KU SANI SHI FA NAMIJI ƊAN YAUDARA BASHI DA KAMMANI, TAMKAR YANDA MUGU BASHI DA KAMANNI, TO SHI MA MAYAUDARI HAKA NE, ZAI IYA YAUDARARKI TA KO WACE SIGA, BAR GANIN KINA DA WAYO, WLH ƊAN BARIKI YA WUCI TUNANINKI, ABU MAFI SAUKI DA ZAKI YI KI GUJEWA FAƊAWA TARKONSA SHI NE ADDU'A, ALLAH NE KAWAI WLH ZAI IYA TSAREKI DAGA SHARRIN ƊAN BARIKI KUMA ƊAN DUNIYA, WLH DUK WAYONKI IDAN ƊAN DUNIYA YANA SON CINMA BURINSA A KAN KI TOFA SAI YA YI, DAN HAKA DA ALLAH KAWAI ZAKI HAƊASU, SHI ZAI TSAREKI DAGA SHARRINSU, BASU DA KAMANI BARE KI CE IDAN KIN GANSU ZAKI GUDU, A DUK LOKACIN DA KIKA KAFA GOSHINKI A KASA DA NUFIN SUJJADA TA SALLAH IN MA NAFILA KO FARILLAH, TO KADA KI YARDA KI ƊAGO DAGA SUJJADAR NAN BA TARE DA KIN ROKI ALLAH DAYA KAREKI DAGA SHARRIN MAZAN BANZA BA. ALLAH UBANGIJI DUK HALIN DA ZAMU SHIGA, YA ALLAH KA TAUSAYA MANA KA BARMU DA IMANINMU. STORY💋 ❤️LION and RIMSHA💋 Almost 2 mins yana tsaye yana ɗan tunani kafin ya wuce ya ɗauki wayarsa, kusa da ita ya dawo ya zauna tare da fara latsa wayar tasa, da amala sako yake turawa, lallaɓowa ta yi a in da ta ɗaura kanta a saman cikyarsa tana hawaye, ɗaura hannunsa a saman face nata ya yi ba tare da ya yi magana ba yana cigaba da latsa wayarsa da hannu ɗaya. Sai da ya kammala abin da yake yi sannan ya ajiye wayar a gefe tare da dawo da kallonsa kanta, goge mata hawayen nata ya yi yana faɗin "Gaskiya Meesha ke raguwace". Turo baki ta yi tana cigaba da hawaye ta ce "Allah Noori ni ba raguwa ba ce, ka san yanda nake ji kuwa? Ciwo sosai marata take yi fa". Maimaita sunan Noorin ya yi a fili ba tare da ya sake ce mata komai ba. Zame hannunsa daga saman face nata ya yi tare da mayar da shi zuwa saman marar tata yana mai cigaba da kallon face nata, runtse idanunta gam ta yi tana jan dogon numfashi, shiru ya yi yana karanto mata addu'ar da annbi ya bawa Nana Fateema a lokacin da take fama da rashin lafiya, duk wanda ya karanta wannan addu'a sau uku ya tofa a hannunsa ya shafa a wajen da yake yi mishi ciwon, to fa duk karfin ciwo in dai bana ajali bane sai ya yi diff ya ɗauke tamkar an ɗauke wutar nepa, wannan addu'a bata da wahala kuma bata tsawo amma akwai aiki sosai. *YA HAYYU YA KAYYUMU BI RAHMATIKA ASTAGISU ASLILI SHANIN KULLAHU WALATAKIL ILAH NAFSA ƊARFATA AIN*. Wannan ita ce addu'ar, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce da Nana Fateema a duk lokacin da ta ji ciwo kai or ciki ko dai wani ɓangare daga jikinta, to ta karanta shi sau uku ta tofa a hannunta sai ta shafa a wajen da yake yi mata ciwon, da izinin Allah zata sami sauki nan take ba sai anjum. Wannan addu'a ya fara kasanto mata yana shafa mata a marar tata, shiru ta lafe a saman cinyar tasa tana jinsa, Allah da ikonsa yana yi mata wannan addu'a ba'afi da minti ɗaya ba ta ji tamkar anyi ruwa an ɗauke, ciwon ya tafi gabaɗaya, lumshe idanunta ta yi tare mai riko yatsun hannunsa cikin nata. "Are you okey?". Ya yi maganar dai tamkar kullum, wato cikin sanyin murya. Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "Allah Noori ciwon dukka ya tafi". "To sai a dai'na ruwan hawayen ko?". Cool murmushi ta saki tana ɗan murza ɗan ƙaramin yatsansa da ta riƙo. "Tashi kici abinci". Girgiza mishi kai ta yi alamar ta ƙoshi. "Idan mace tana period bata zama da yunwa". Waro idanunta ta yi tana kallon shi, ko a ina ya san wannan karatu kuma? Ta tambayi kanta, bata san cewa shi ma ai ya iya aikin likita da ya koya daga wajen daddynsa, ya san abubuwan da suke yi wa mutun illah ga lafiya, ya san komai kawai dai dan bata shafe shi ba ne yasa baya bi ta kai, kuma kunga shi bai taɓa kula mace ba bare ku san ya sani ko bai sani ba, sai yanzu da suke tare ne yake fito da saninsa a kan abubuwa da yake gigita ƙwaƙwalwarta dan bata taɓa tunanin ya sani ɗin ba...... YO DAMA SHI LION WAYE YAKE GANE IN DA YA DOSA? AI KO YA SANI BA ZAKA TAƁA SANIN YA SANI ƊIN BA HAR SAI IDAN SHI YA FITO YA NUNA MAKA YA SANI, SHI A RAYUWARSA MA BAYA TAƁA BARIN WATA ALAMA DA ZATA NUNAWA MUTUN GA HALIN DA YAKE CIKI KO GA IN DA YA DOSA, DUK SA IDONKA BA ZAKA TAƁA GANE MISHI BA!!. Ganin ta ɓata sofar da jini ne yasa ya miƙe ya kwantar mata da kanta a saman sofar ta nufi wajen table ɗin cin abincin nasu, ba zai yiwu ta tashi ba saboda jinin da yake jikinta, dole shi zai ɗauko mata abincin dan tun jiya rabonta da abinci, so yanzu kuma a halin da take ciki ga shi sabon fara period ne dole ta ci abu mai ɗumi dan kada ta samu matsala, idan mace tana period sam zama da yunwa ba nata ba ne, idan ta zauna da yunwa mugun lalata mace yake yi ba kaɗan ba, so haɗari ne babba ga ƴa mace ta zauna da yunwa a irin wannan lokaci, ya san da haka shiyasa ya gwammaci gara ya ɗebo mata abincin ya bata. Zuba abincin a plate ya yi tare da ɗaba mata green tea mai zafi sai tiriri yake yi sosai, jawo ɗan ƙaramin table dake kusa da sofar ya yi zuwa gabanta a in da ya ɗaura mata abincin a sama sannan ya nufi waje yana faɗin ta cinye dukka kafin ya dawo. Da kyar ta miƙe zaune saboda kullewa da cikinta ya yi na azababben yunwa, tea ɗin ta fara sha, duk da bata son tea ɗin nasu, amma ta sha dan ya ce ta cinye komai. Shi kuma waje ya nufa wajen sojojin nasa, almost 10 mins ya ɗauka yana magana da su kafin ya koma cikin ɗakin, saman bed ya hau ya kwanta dan har ga Allah baya son ganin yanda ta ɓata jikinta, ga shi basu da zaɓi dan ba pad dai a cikin jirgin, wayarsa ya sake ɗauka ya latsa na tsawon 5mins kafin ya ajiye saman bedside drawer, lumshe idanunsa ya yi yana tunane tunane har barci ya ɗan ɗaukesa. Ita kuma ta gama cin abincinta tas kafin ta matsar da table ɗin sannan ta koma ta kwanta, sam bata ma lura da ta ɓata saman sofar ba, ita ma tana kwanciya ba jimawa barci ya ɗauke ta. AFTER SOME HOURS💋 Karar sautin Helicopter ne ya tashe shi daga barcin da yake yi na tsawon awanni, ita kuma da yake tana da ɗan nauyin barci, sam bata motsa ba, a hankali ya waro idanunsa waje ba tare da ya miƙe ba, duk jikinsa a mace, har mamakin irin barci da ya sha yau yake yi, ya jima bai yi barci na tsawon awanni haka ba, ko sallar azahar bai yi ba, kuma barcin nasa ta ɗan yi nauyi yau. Wani dankareren Helicopter ne ya tsaya a tsakiyar saitin jirgin ruwan nasu ta sama, Helicopter ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali launin army uniform, daga ganin Helicopter kasan na manya ne, dan fa ya kawatu iya kawatuwa. Sako matakar Helicopter suka yi kasa izuwa cikin jirgin ruwan, wata kyakkyawar Baturiya doguwa jajir da ita ce ta fito daga cikin Helicopter ta biyo matalar, gashin kanta har baya bakinkirin, jikinta na sanye da kayan sojoji, kayan sun yi mata kyau sosai, babbar mace ce da akalla zata kai 35 years haka, Taku uku ta yi a saman matalar Helicopter wata macen soja ta leƙo daga ta ciki ta miƙa mata wani dankareren akwati mai matukar kyau da tsananin tsada, kasa da Helicopter kaɗan driver ya kara yi dan matan tamkar ba zata iya ɗaukar trolleyn ba, trolleyn ya yi mata girma, dan ma soja ce, da hannu ɗaya ta rike trolley ta kuma riƙe matalakar saukowar da hannu ɗaya tana sauka. Karisowa wajen Mark ya yi da nufin ya karɓa mata trolleyn tun da ta kusa isa kasa, girgiza mishi kai ta yi alamar ya bari kawai, Mark ya santa sojansu ce, sai dai kuma bai taɓa yi mata magana ba sai yau, ta sha mamaki ita ma duk da ta san cewa dan trolleyn ya yi mata magana. Da kyar dai ta sauko kasa, tana gama saukowa Helicopter ta tashi sama dan ta ɗan yi zagaye kafin ta dawo ta ɗauketa. Cikin harshen Spanish ta tambayi Mark da ina Lion? Kallon bedroom nasu ya yi kafin ya ce ta jira sai time da ya fito, tana ƙoƙarin sake yin magana idanunta suka sauka a kansa yana tsaye a kofar bedroom ɗin nasu, fuskar nan tasa tamkar hadari a ɗaure tamau, dama shi bai san menene murmushi ba a rayuwarsa, gabaɗaya sojojin kara natsuwa suka yi suka sha jinin jikinsu, wasu malaman natsuwa ne suka shiga jikinsu lokaci guda, nan take suka kame waje guda, ɗaga hannu macen sojan nan ta yi cikin girmamawa tare da tsoro sosai a tattare da ita ta sara mishi, shi kuma kallon Mark da ya kame ma yake yi, ya ga wani irin kyalli face ɗin Mark ɗin yake yi, sai aikin ɗan ciza laɓɓansa yake yi tamkar ba lafiya ba, hankakinsa da kallonsa sam baya a kan matar. Daga jiya zuwa yau ya lura da Mark fa sai a hankali, shi kaɗai sai ya rinƙa wasu abubuwa tamkar mara gaskiya, bai san Mark ya shiga hannun Anaya dumu dumu ba ne, birgita mishi ƙwaƙwalwa take yi da shagwaɓa da kalaman soyayya, shi ne bawan Allah duk ya damu su koma ya je ya ga babyn nasa. Hannu ya miƙawa macen sojan a kan ta kawo mishi trolleyn ba tare da ya yi magana ba, cikin hanzari tare da taku irin na jaruman sojojin da suka sami tsantsar horo ta kariso gabansa, sai da ta sake kamewa kam ta sara mishi kafin ta miƙa mishi trolleyn, sam bai karɓa ba bai kuma ɗaga ido ya kalleta ba, hankalinsa ya koma a kan wayarsa dake hannunsa, ya barta rike da trolleyn for almost 5 mins, ga trolleyn da bala'in nauyi, ta gaji amma ba damar ta nuna hakan, daurewa ta yi har sai da ya kara tsayuwar 2 mins kafin ya yi mata alama da hannu a kan ta ajiye ta wuce mishi ta bashi waje, sam bai yi magana ba dan nuna tsantsar isa da izza. A hanzarce ta ajiye mishi ta juya ta koma wajen da ta sauko dan ta jira Helicopter ta dawo ta ɗauke ta, ya ɗauki almost 2 mins ba tare da ya motsa ba yana latsa wayarsa cike da nuna isa, tamkar ba shi ne ya gama cewa Meesha yanzu a cikin ɗaki ba, ko da yake dama Meeshansa kawai ya canzawa, ita kaɗai taga canji a tattare da shi, da ya bar wajen ta, to ya koma ainahin Lion ɗin nasa, sai ya wani kara ɗaure fuska na wuce misali, ga uban nuna isa da izza babu abin da ya ragu. Ɗaukar trolley ya yi zuwa ciki, gabaɗaya sojojin sun yi mamakin me zai yi da trolley,? Saboda sun san wanene shi, baya sayan kaya a hanya, idan zai yi tafiya yana shirya komai da zata ishe shi, harta ita kanta soja mace da ta kawo trolley bata san menene a ciki ba, ita dai an kawo mata trolley har cikin office nata aka ce ta shiga jirgi zu je zata kaiwa GAR, amma bata san me a ciki ba, duk abin da yake ciki wannan kyakkyawa tsadadden kuma haɗaɗen trolley to Josephine ne ta sayo shi, ita ta je da kanta ta yi sayayya, a lokacin da zata je ita da kanta bata san me zata je saya ba, ita dai tana zaune sojoji biyu suka zo har cikin gida suka ɗauketa zuwa super market, sai da suka shiga super market ɗin ne Lion ɗin ya yi mata massage a kan ga abin da zata ɗauka mishi a super market ɗin, ta sha ruwan mamakin ganin saƙonsa, bata taɓa tunanin ya san da numberta a duniya ba, dole dai ba dan ta so ba ta yi wannan sayayya na abin da ya rubuta mata tas, bata yi mamakin ganin ya rubuta mata ta ɗauka mishi kayan mata har da su pad ba, domin duk wani motsin yaran nata tana iya sani, amma ba kowani lokaci ba, time to time haka dai, Lion shi ne yake yawan zulle mata sosai dama, dan ya fi TRIPLETS nasa riko da addini fiye da tunanin mai tunani, bata iya bincikar halin da yake ciki, kuma bata taɓa iya gane mishi, kullum a siffa ɗaya yanayi ɗaya take ganin shi, Aseef kuwa bawan Allah da yake yanzu ma yake koyan karatun addinin bai yi nisa ba, sai ya zamana duk wata bala'i take farawa ta kansa, shi kuma Areef Allah yana kare shi daga duk wata sharri saboda kyakkyawar zuciyarsa ta zinari kuma shi ma yana da riko da addini sosai duk da bai kai Lion ilimin addinin ba, amma yana iya ka bakin kokarinsa, Lion shi ne ya zurfafa bincike sosai a kan addinin musulunci shiyasa ya fisu ilimi na wuce misali. So Josephine bata yi mamaki ba dan ya ce ta zaɓo mishi kayan mata, ta san yana tare da mace, abin da ya bata mamaki a nan shi ne karfin izzarsa da nuna isa irin na yaron nata, wato shi ko ana so ko ba'a so idan yana son abu to fa sai an shi, gata dai a nata wawtar wai ita take juyasu, amma shi kuma shi ne yake ainahin controlling nata ko tana so ko bata so, bata isa ta ɗaura wata magana a saman nasa maganar ba, idan ya yi magana dole ne a yi, yanzu dan tsabar isa irin nasa tana zaune a gidanta yasa aka ɗaukota aka kawota super market, kuma ba yanda ta iya dole ne ta yi wannan sayayya idan tana son zamanta lafiya, kuma duk abin da ya rubuta dole haka zata ɗauko mishi su masu kyau ko ranta ya ɓaci a banza, ita dai tana ganin gararin rayuwa, sun haifi ƴaƴan amma ƴaƴan su ne suke juyasu, ko da yake ba laifin ƴaƴan ba ne, laifin su ne dan su suka basu tarbiya irin haka, so dole su ɗauki koma me yaran zasu yi a yanzu, dan sun makaro tunfarko, itace tun yana ɗanye ake tankwara shi, idan aka kuskura aka bari ya bushe to ba zai tankwaru ba sai dai ya karye, Allah ka bawa ko wace mace ikon bawa ƴaƴanta tarbiya irin na koyarwar manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama dan amfanuwan kanta. A takaice dai Josephine ce ta yi dukkan sayayyar cikin trolleyn nan, bayan ta kammala ta shirya su cikin trolleyn sai ta bawa soja mace dake biye da ita ta ɗauko suka fito, sojan ta wuce office nasu ita kuma Josephine ɗayar sojar ta mayar da ita gida aka cigaba da tsaronta, dan Lion ya hanata fita ko nan da can, kullum tana gida zaratan sojoji biyu suna gadinta. Wajen da trolleys nasu yake ya nufa ya ajiye trolley, kusa da ita ya dawo, sai zuba barci take yi abinta, hankali a kwance, ɗan zuba mata waƴan nan dara daran blue eyes ɗin nasa ya yi na ƴan mintoci kafin ya sanya hannu ya saɓeta a kafaɗarsa tamkar wata ƴar baby ya nufi toilet da ita. Daddaɗar kamshin perfume nasa ne ya fara kai mata karo a hancinta lokacin da ta farka sanadiyar jin da ta yi an ɗauketa, a hankali ta waro dara daran sleeping eyes nata a saman face nasa, hankalinsa baya a kanata haka zalika kallonsa, yana kan wajen da yake son zaunar da ita, amma ya san tana kallon shi. Hannu tasa ta saƙalo wuyarsa tana ɗan turo baki, jin saukar hannun nata a wuyarsa ne yasa ya sauko da idanunsa kanta, cikin sauri ta runtse nata idanun, tsayuwa ya yi daga tafiyar da yake yi ya zuba mata idanu. "Open your eyes". Ya faɗa a tsakanin sanyaye. A hankali tamkar mara gaskiya ta ɗan buɗe idanun nata tana kara turo mishi baki. Zuba mata ido ya yi na ƴan mintoci kafin ya ɗaurata a saman chair dake cikin toilet ɗin. Ɗan ɗaukanta da ya yi har ta ɓata mishi jiki, da yake idan baku manta ba shi rabin kayansa dukka fararene, shi ne yasa take saurin ɓata shi. Wucewa ya yi ya haɗa ruwan wanka sannan ya nufi hanyar fita yana ce mata ta yi wanka ta zo ta sanya kaya, okey ta amsa mishi da shi, ficewa ya yi zuwa ɗayar ɗakin shi ma dan ya yi wanka. Ta riga shi fitowa daga wankar, ko da ta fito taga sofar da ta kwanta a kai ya ɓaci da jini, sai ta ɗauko towel fari mai kyau irin na goge sumar kai idan an yi wankar nan, ta ɗauko sabulai masu kamshi sosai, ta zo ta zuba tare da ruwa kaɗan ta goge tas, nan take wajen ta fara zuba kamshi sosai saboda karfin kamshin sabulan, bata sanya kaya a jikinta ba har sai da ta gyare musu ɗakin tsab, air freshener har kala uku ta fesa musu sannan ta ɗan kara gudun Ac, wani haɗaɗɗen kamshi tare da sanyin Ac mai ratsa zuciya ne yake tashi a ɗakin. Lotions nasa ta je ta fitar tare da zama ta fara shafawa sai ga shi ya shigo ɗakin cikin shigar wando three quarter fari tas da kuma polo t-shirt sky blue, ya yi matuƙar kyau tamkar shi ya yi kansa, ya ɗaure dark black curly hairnsa a baya, ya bar wannan guntu na gaban goshin nasa, face nasa har wani kyalli yake yi, soft skin ɗin nan nasa ya kara kwanciya luff tamkar bai taɓa taka kasa ya fita waje ba, sai wani sheki fatar tasa take yi, alama ce ta ya kara samu kwanciyar hankali over fiye da na baya. Sosai yau ta zuba mishi idanu tana kallo shi, ya yi wani irin azababben kyau ne na wuce misali, ji take yi tamkar ta tashi ta je ta rungume shi ta kuma sumbaci ɗan bakin nan nasa, dan kuwa lips nasa har wani kyalli suke yi tamkar ya sanya musu lips balm, sun kara ja sosai. Ya tsaya a tsakiyar bedroom ɗin yana ɗan latsa waya. Kasa jurewa ta yi da sauri ta miƙe ta zo ta faɗa jikinsa. Nauyayyar ajiyar zuciya suka sauke a tare kafin ya buɗe hannunsa ya rungumeta da kyau a saman faffaɗar kirjinsa, sam ta manta ma da cewa towel ne a jikin nata, ga gashin kanta bai gama bushewa ba, akwai ruwa ruwa a jikinsa, shi ma gashin kansa da ɗan ruwa a jikinsa, dan bai busar da shi ba, da ya goge da towel kawai sai ya barta dan yana son ya zo ya bata pad kada ta saka kaya ta sake ɓata jikinta, yasan idan ba shi ya zo ya bata da kansa ba, to ba zata taɓa trolley ɗin ba, kayanta kawai zata ɗauka dan bata da shisshigi a kan abin da bai shafeta ba. Lumshe idanunsa ya yi yana shaƙar daddaɗar kamshin air freshener da ta fesa musu ga kuma sanyin Ac dake ratsa mishi zuciya, shi kaɗai yasan me yake ji. Hannu ya ɗaura a saman bayanta kasa kasa ya ce "Muje na baki kayan sakawa". Ya yi maganar a tsananin sanyaye kamar dai kullum, ya kuma yi maganar yana waro idanunsa a kanta. Sakinsa ta yi ta nufi wajen trolleys ɗin tana faɗin "Noori yau kai ne zaka zaɓa mini kaya?". Tana magana cikin tsantsar yarinta, hakan ba ƙaramin burge shi take yi ba, sai dai shiru ya yi bai yi magana ba, ya kariso wajen trolley ɗin. Wanda sojan can ta kawo mishi ya kwantar a in da ya zuge zip ɗin ya buɗe, manya manyan teddy guda biyu farare kal kal masu matukar kyau da kuma girma sosai ya fara cin karo da shi a cikin trolleyn, kallo ɗaya ya yi musu ya kawar da kansa, shi dai bai cewa Josephine ta saya mishi teddy ba, ita kuma ta saya mishi ne dan ta nuna mishi cewa Rimsha fa baby ce da bata wuce ta yi wasa da teddy ba, sako ta aiko mishi a fakaice, ya gane nufinta sarai amma sai ya yi tamkar bai gane ba. Yana ciro teddy ya ajiye a gefe Rimshar ta kariso wajen da sauri tana zuba uban murmushi cike da murna ta ɗauki teddy ɗaya, ta ji tsantsar farinciki, rabonta da su tun a Abuja lokacin da daddynta yake sayo musu suyi ta faɗa ita da Jehan akansu. Zancen Josephine ya tabbata, Rimsha fa yarinya ce da bata wuce wasa da teddy ba, ga shi kuwa ta ɗauki abinta tana ta murmushi har da yi wa teddyn magana tamkar da mutun take tare. Girgiza kai kawai ya yi ya cigaba da duba kayan ba tare da ya fitar dasu daga cikin trolleyn ba, yes komai ya yi, yanda ya rubuta haka ya sayosu, wata ƙatuwar leda mai ɗauke da pad a ciki ya fitar tare da ɗauko kwalin pant guda ɗaya, miƙa mata ya yi yana faɗin ta ajiye teddyn nan ta je ta shirya, karɓa ta yi tana kallon pad ɗin da mamaki, ita fa bata san taya ma ake sanya always a jikin pant ba, bata taɓa ganin yanda ake yi ba, shiru ta tsaya ta kasa motsawa, gyara kayan cikin trolley ya yi tare da jan zip ɗin ya rufe, sannan ya miƙe tsaye da nufin ya bar wajen. Ganin tana tsaye tana ta kallon always ɗin ne yasa ya ɗan zuba mata idanu, sarai ya gane bata san ya ake amfani da shi ba ne, amma sai ya yi tamkar bai gane ba ya yi wucewarsa ya barta tsaye a nan rike da su ta saki baki ta rasa ta ina zata fara, ita tunani ma take yi na ya akayi a wancan ranar Ayla ta yi amfani da nata ma? Bata sani ba, dan ai Ayla ba'a gabanta take sakawa ba, a toilet take sakawa. Tamkar zata yi kuka ta juyo da kallonta a kansa, yana kwance saman bed ya lumshe idanunsa tare da ɗaura hannu ɗaya a saman goshinsa tamkar mai yin barci. "Noori Allah ni ban iya saka wannan abin ba". Ta yi maganar tamkar zata yi kuka, tamkar babu shi a cikin ɗakin, sam bai kulata ba, shiru ta yi tana tunanin mafita. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 *KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*. *KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ ❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋) *Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581* 78 "Noori Allah ni ban iya saka wannan abin ba". Ta yi maganar tamkar zata yi kuka. Tamkar babu shi a cikin ɗakin, sam bai kulata ba, shiru ta yi tana tunanin mafita. Kukan shagwaɓa ta saka mishi daga baya wanda ya sanya shi buɗe idanunsa ba tare da ya shiryawa hakan ba, bubbuga kafa ta fara yi a kasa tana turo baki tana faɗin "Uhm uhm ni yanzu Noori to ya zan yi? Allah cikina ma ya sake fara ciwo, wayyo mummyna, ina kike ne? Kizo ki koya mini yanda zan saka wannan abin". Ɗan sake lumshe idanu ya yi, ba yanda ya iya, wannan shagwaɓa tata dai tana matuƙar ɗaukar hankalinsa tare da jan ra'ayinsa ya sake jin yana son kasancewa tare da ita a koda yaushe. Hannu ya miƙe mata a kan ta bashi pad da pant ɗin, cikin wani irin yauki da shagwaɓa ta kariso gabansa, sai turo baki take yi tana kumbura kumatu. Miƙewa zaune ya yi yana kallon face nata, komai yarinyar nan ta yi a duniyarnan burge shi take yi, wai shin me matsalarsa ne? Ya tambayi kansa. Cikin yanga kamar yanda AKila ta gaya mata ta miƙa mishi pad ɗin, karɓa ya yi tare da ajiyewa a gefensa har lokacin ya kasa kawar da kallonsa daga kanta, yangar tata ma ba ƙaramin burge shi ya yi ba, yarinya karama sai iyayi kala kala, bai san cewa duk Akila take koya mata waƴan nan abubuwa ba. "Bani kwalin mana". Ya faɗa a sanyaye. Dama da gangan taki miƙa mishi kwalin pant ɗin, ta bari ne ta ji zai iya kiran sunan pant ɗin ne ko ba zai iya ba, sai kuma ta ji bai faɗi sunan ba, kawai ya ce ta bashi kwalin. Turo baki ta yi a tsakanin shagwaɓe ta ce "Noori wai dama me a cikin kwalin ne?". Ayya Rimsha da gaske yarinya ce, bata san tunaninsa ya wuce nan ba, shi baya sauraron maganar saman harshen mutun, karkashin harshensa yake karanta, hakan da ta yi mishi sai ya ji tamkar ta rai'na shi ne or ta mayar da shi bai san me yake yi ba, abin ya ɓata mishi rai da har yasa hannu ya damko towel ɗin jikinta da nufin ya jawota dan ya dallah mata koda mari ɗaya ne yau ta san shi fa ba abokin wasan ta bane. Duk yanda kuke da TRIPLETS kada ka kuskura ka bari wata alama ta rainin ta shiga tsakaninka da su, duk mutuncin da kuke yi kuma duk yan da suka kai ga sonka, muddin ka yi musu wargi kaɗan da zata nuna ka rainasu, to wlh nan take za su manta da soyayyar nan su yi maka abin da zaka yi danasanin zuwanka duniya, haka suke tun suna yara, haka kuma suka taso har izuwa yanzu. Lion sam baya dukan mata, amma wlh a yanda Rimsha ta yi mishi wannan magana tsab zai dallah mata mahaukacin mari da zai sata suma ko sau uku ne, maganar tata akwai rainin wayo a ciki, sai dai ita bata kalli hakan ta fuskar rainin wayo ba, rashin sani ne, bata san taya zata sanya shi ya kira mata sunan pant ɗin ba, shi ne ta tambaye shi ta wannan hanyar, tana ganin hoton pant da sunansa a jikin kwalin amma dan rainin wayo zata tambaye shi, dole ya ji haushi. Ƙoƙarin guduwa ta yi a in da ya fisgota da karfi har sai da ta bugu da jikin bedside drawer, karan azaba ta saka mishi wanda ya sanya shi sakinta. Allah sarki ta rigada ta zama rauninsa, ta shige jikinsa sosai a lokacin da bai sani ba, soyayyarta ya yi mishi over a zuciya, so ba zai iya ganinta cikin wani hali kuma ya sake yunkurin kara mata wani hukuncin ba, ganin ta bugu da jikin drawer ne yasa ya saketa, ya kyaleta ba dan ya so ba, a sonsa kam ya bata mari koda guda ɗaya ne mai rai da lafiya. Kasa miƙewa ta yi dan ta bugu sosai, kuka ta sanya mai tsuma zuciyar mai sauraro, bai bi ta kanta ba ya ɗauki kwalin pant ɗin, da farko ma ya yi niyar kin sanya mata pad ɗin a jikin pant ɗin, amma da ya tuna zata ɓata mishi waje da jini ne yasa ya ɗauko dan ya sanya mata. Kuka take yi sosai amma ko a jikinsa, pant ɗin ya fitar tare da ciwo always ɗaya, calmly ya ce ta tashi ta kalli yanda ake yi dan daga wannan ba zai sake saka mata ba, bala'in tsoronsa yasa ta miƙe da kyar dan ta kallah, hawaye wani na bin wani, zantukan AKila kawai take tunawa, in da take ce mata wlh idan kika yi mishi ba dai'dai ba tsab zai manta da soyayyar da yake yi miki ya hukunta hukunci mai tsanani, sai dai daga baya ya ji babu daɗi or ya yi danasani, amma a lokacin kam ba makawa sai ya hukuntaki, dan na lura haka zuciyar TRIPLETS gabaɗaya suke, sun iya canzawa lokaci guda su manta da duk wata alaƙa da take a tsakaninsu da mutun su bashi hukunci mai tsanani, sai da ga baya idan sun sauko daga dokin zuciyar ne kuma sai su ji ba daɗi. Cire ledar pad ɗin ya yi tare da buɗe pant ɗin ya sanya mata a ciki, kunya tamkar zata shige cikin kasa, shi kuwa da yake jinin turawa, ko a jikinsa, tamkar ma bai san me ya rike ba, sam babu ko ɗigo na alamar kunya a tattare da shi. Ga pant ɗin fari tas da shi mai shegen kyau, jikinsa laushi sosai. Ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, sai dai ta yi mamakin yanda aka yi aka sayo mata pant dai'dai size ɗinta, bata san da idanunsa ya aunata a in da ya rubutawa Josephine size da yake bukata ba, hausawa sun ce ido ba mudu ba amma ya san kima, to haka ne, in dai zaka kalli abu da idanu to ba sai ka auna ba, kana iya kimantawa, amma sai masu basira sosai. Bayan ya kammala sakawa ya miƙa mata tare da komawa ya kwanta ba tare da ya ɗaga idanu ya sake kallon in da take ba. Duk jikinta ya yi mugun sanyi tamkar wanda ciwon mutuwar gaɓoɓi ya kamata, ta ji babu daɗin ganin ya yi fushi da ita, ɗaukar ledar pad da kwalin pant ɗin ta yi ta nufi wajen trolleys ɗin. Ajiyesu ta je tayi tare da ɗaukar kayan sakawarta ta nufi toilet. Jim kaɗan ta fito ta shirya cikin haɗaɗɗun kananan kayanta, wandon jeans ne guntu bai ma karisa rufe mata cinyarta ba, irin wandunan nan ne wanda suke tsayawa a dai'dai tsakiyar cinya, sai ƴar riga mara nauyi da ta tsaya mata a kugunta, rigar tana da ƙaramar hannu zuwa iya kafaɗa. Ɗan kwana biyu da suka yi a cikin ruwan nan, har wani sihirtaccen kyau ta kara, wajen ya karɓeta sosai, soft skin nata ya kara kwanciya luwai luwai, tsantsar tsadadden kalar fatarta wato chocolate color ya kara bayyana da kyau da kyau, ba karamin azababben kyau hakan ya kara mata ba, ga idanu farare tas kamar farin cikin kwai, ga su dara dara kuma sleeping eyes, ai abin ba'a magana, dole ma Lion ya rinƙa kasa ɗauke idanunsa daga kanta, kusamman idan ta motsa kyawawan laɓɓan nan nata, nan take haɗaɗɗun dimples nata suke lotsawa, wow ai dole ya rinƙa kafeta da blue eyes nasa babu ko kyaftawa, bawan Allah ya yi mummunar zurmawa a cikin kogin soyayyarta ba tare da ya ankara ba. Gyara kyakkyawar gashin kanta ta yi tare da zuba perfume nasa a jikinta tamkar babu gobe. Jiki ba kwari ta nufo wajen bed ɗin, yana kwance irin kwanciyar da ya yi ɗazun. Ta wajen kusa da bedside drawer ta zo ta tsugunna a gabansa, cikin sanyin murya da shagwaɓa sosai a cikin muryar tata ta fara magana tare da riƙo hannunsa ɗaya a cikin nata. "Ban taɓa tunanin akwai wata bakar rana da zata zo a duniyar nan da zansa ka ji babu daɗi ba, ba zan iya yafewa kaina ba har sai idan ka yafe mini, ina cikin damuwa da kuncin zuciya, kai nake gani nayi farinciki, na tuba ba zan sake ba, ka yi hakuri ka ji Noori? Am so so sorryyyyyyyy, na yi alkawarin ba zan sake ba". Tana magana tana kuka, duk wannan abubuwa da ta faɗa mishi wlh caf kalaman mummynta ga daddynta ta ɗauko, tana jinsu wani lokaci idan daddy ya shigo gida cikin ɓacin rai, mummy ba ita ta ɓata mishi rai ba, amma da yake ita mace ta gari ce, sai ta je ta yi ta bashi hakuri tamkar yanda manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya umarci mace ta gari da ta yi wa mijinta, to shi ne ita ma ta haddace yau take yi wa Noorinta. Tabbas har cikin ransa ya ji daɗi, bai taɓa jin kalmar sorry ta yi mishi daɗi ba a duniya sai yau da ya fito daga bakinta, ya tsani kalmar fiye da tunanin mai tunani, amma yau da ta faɗa, kalmar ta yi mishi mugun daɗi, dan a tsananin shagwaɓe ta furta kalmar, sai dai ya ɗan yi mamakin a ina ta koyo maganganu masu daɗi da ma'ana haka? A ina ta jiyosu?. Ƴar yarinya da ita amma ta iya abubuwa da zata saye zuciyar mutun duk taurin ransa.......MATA!! MATA!! MATA!! ALLAH YA BAMU BAIWA, DUK TAURIN ABU MUNA IYA SANYA SHI YA YI LAUSHI CIKIN ƘANƘANIN LOKACI IDAN MUKA YI RA'AYI! TO UBANGIJI ALLAH YA KARA MANA HAZAKA DA BAIWA😌🙃 Zazzakar muryarta ne ya sake katse mishi tunani da cewa "Noori na Allah idan baka yafe mini ba yau daga yanzu har sanda zaka yafe mini zan yi ta marin kai'na ne, kuma zanyi ta kuka har sai hawayena sun kare, sannan kuma ba zan yafewa kai'na ba, please mijina ka yafe mini.....". Bata kai karshen maganar ba ta yanketa sakamakon wani irin waro idanun waje da ya yi, bai taɓa tunanin ta san cewa shi mijinta bane, bugu da kari bai taɓa tunanin koda ta sani ma zata iya furta mishi kalmar miji a haka ko shakka babu ba, ko ɗazun da ta ce mishi Noorinta wato haskenta ya bashi mamaki, dan bai yi zaton tana da wannan kwarin gwiwa ba, bai san cewa Akila ta gama ɗaurata a kan hanya ba, ita kuma tun da ta san ba zai taɓa lafiyar jikinta ba, shikenan sai ta saki jiki tana zuba mishi kalamai son ranta. Wani irin razana ta yi na ganin ya waro idanun nasa waje, har wani kyalli suka kara yi na zarosu da ya yi. A hanzarce ta miƙe dan ta gudu, a tunaninta dukanta zai yi or something like that, shi ne yasa zata gudu. Tana ƙoƙarin sakin hannunsa da ta rike ya yi maza ya riko nata hannun tare da jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, kara ɗaure fuska sosai ya yi tamkar hadari. Calmly ya furta "Waye ya gaya miki ni mijinki ne?". Da yake tun da ya kamota ta runtse idanunta, sai bata san ya kara ɗaure fuska ba, bataga action da ya ɗauka ba, magana kuma da normal yanda yake yi mata magana a sanyaye ya yi shi, so bata ji wani canji ba, dan haka sai ta turo baki cikin shagwaɓa ta fara magana. "To.... To.... To Noori kai ba mijin nawa ba ne? Uhm uhm ni Allah ka matse ni da yawa, zaka fasa mini kirji fa". Ya ilahi ya lillahi, ai yanda ta yi wannan magana tamkar ta kwala mishi guduma ne a tsakiyar kansa, amma fa gudumar soyayya, tamkar ta caka mishi mashi ne a kahon zuciyarsa na tsantsar kaunarta, yanda take motsa laɓɓanta tana magana ya ilahi, shi kaɗai yasan irin azababben sha'awarta tare da kaunarta da yake ji. Lumshe idanunsa ya yi ya kasa jurewa har sai da ya matso da face nasa izuwa saman tata. Idanunta a runtse sai zuba mishi shagwaɓa take yi tare da turo ɗan bakin, ba zai iya jurar ganin yanda take motsa lips ɗin nata ba, dan haka sai ya sanya yatsarsa ɗaya a samansu dan ta yi shiru yana mai lumshe idanu, saƙalo wuyarsa ta yi da hannunta ɗaya tare da ɗaura ɗayar hannun nata a saman kirjinsa daidai saitin ɓul ɓul ɗinsa. "Noori yanzu maganar ma ba zaka barni na yi ba?". Kara ingiza mishi zuciya ta yi da wannan magana tata, matseta sosai ya yi a jikinsa yana jin wani irin azababben yanayi mai azabar daɗin gaske tana ratsa shi. "Noori ka bari....." Yatsar tasa ya zura mata cikin bakin nata tare da danne mata tongue yana sauke numfashi a hankali. Cikin natsuwa da sanyin murya, can kasar maƙoshinsa ya furta "Meeesha Keep quiet". Cikin salon da shi kansa bai san ya iya ta ba ya yi maganar. Wani irin daɗin yanda ya yi maganar ta ji. Sam baya son ta cigaba da magana tana daɗa jefa shi cikin yanayi mara misaltuwa, yanzu ma komai ya miƙe mishi, bai san time da gabansa ta tsaya kyam ba, irin hakan yake gudu yasa sam baya son yawan wasa or yawan taɓata, yasan waye shi, shiyasa ko da sunan wasa baya kuskura ya taɓa breast nata ko ya yi wasa mai ɗan tsawo da ita, kallon yarinya sosai yake yi mata, kada ya cika taɓata ya jawa kansa bala'i, Rimsha ba zata iya da jarabarsa ba a ƴan shekarun nan nata, shiyasa sam baya wuce ya yi mata kisa ko ya rungumeta, dan tsaro, kada ya je ya kashe ƴar mutane a banza a cikin jirgin ruwan nan, shiyasa yake kame kansa, amma ita kuma tana son hayewa jikinsa, tana son rungume shi, ba dan komai take yin hakan ba sai dan tsantsar kaunarshi da take yi, ta yi mishi wani irin mahaukaci kuma makawon so a rayuwarta, shi ne yasa yanzu da ya zama mallakinta kuma tasan ba zai yi mata komai da ya shafi duka ko tsawa ba sai tana yawan rumgume shi, ta san gabaɗaya TRIPLETS basu dukan mata, dukan mace sai namiji rago da bai sai ciwon kansa ba, mace bata da wajen duka a jikinta dama. Shiru ta lafe a jikin nasa, shi ma shiru ya yi yana jin azababben sha'awarta da ta motsa, komai ya tsaya mishi cak, bawan Allah ta jefa shi cikin yanayi. A ɓangaren Jehan da Areef kuwa, soyayya babu kama hannun yaro Areef yake zuba mata ba karya, haka zai yi mata wayo ta yi ta biye mishi ba tare da ta sani ba, yana yi mata dabara tana kara zurmawa cikin son shi, daddynta kuwa ko a jikinsa, murna ma yake yi sosai da hakan, ya fi kowa farinciki. Idan muka koma ɓangaren gidan Abbo kuwa, soyayya babu kama hannun yaro Dr da Aafia suke zubawa, Ummi kuwa tana kara musu goyon baya ta hanyar bawa A'afia shawari da sauransu. A ɓangaren su Jelly kuwa, yanzu fa jelly ta ɗan natsu sosai, amma sai dai ba dan Allah fa ta natsun ba, maza take karɓa a hannun Imran, baya ɗaga mata kafa ko kaɗan, morar kayansa yake yi son ransa, Ammie kam aikinta gyara da kasasu da ruwan zafi, hankalinta kwance, da anci abincin dare zata kaɗasu ɗakin mazajensu, kuma dole su tafi ko sunki ko sun so. Umaisha da Akil kam dama kunsan mayun juna ne, Akil ya koya mata, su dama a manne suke tamkar chewing gum, cikin nasu ya fara girma ma basu hakura ba, sai sun murji juna son ransu sannan Akil ya shafa cikin tare da zuba mishi addu'a har da cewa Allah yasa yaron nasu ya gaji babansa.................... (Ni kuwa sai na ce ba Amin ba, wannan jaraba har ina? Idan ya gaji babansa ai mun bonu idan kuka zo TRIPLETS return 🤣🤣 kunsan fa ance ɗan na gada yafi ɗan na koya, to ni dai na ce wlh ba Amin ba, kada ya gaji babansa da mamansa gaskiya, ina zamu tsaya idan ya yi gadon wannan irin ɗanyen aikin nasu? Kufa readers me kuka ce?😌🧐) Ita kuwa Umaisha da ya yi addu'ar sai ta ce Amin da sauri, su dai su Imran shiru basu sami ciki ba har yanzu. Idan muka koma gidan Lion na Kaduna kuma....... ❤️AFTER SOME DAY'S💋 A ɓangaren Aseef da Akila kuwa sai dai mu ce Alhamdulila, dan fa sauki kam ya samu ba karya, Akila ta warke garau, ta samu kula na musamman daga wajen Dr William jacop, shiyasa cikin ƴan kwanaki kaɗan ta sami sauki, shi ma Aseef daddyn nasa ya kashe lokacin a kansa ba karya, ya kula da shi fiye da tunanin kai tunani, sai da ya tabbatar ya yi treating ɗin duk wata cuta da ya gani a tattare da ɗan nasa. A takaice dai duk sai da ya fitar da su daga cikin haɗari, sannan ne ya ɗan samu natsuwa, yana bala'in kaunar TRIPLETS nasa, yanzu ya fahimci idan wani abin ya sami matansu fa to yana iya rasasu, shi ne yasa ya saduda kawai ba dan yana so ba ya karɓi bakaƙen fatar a matsayin surukai, dole tasa kawai ya hakura dan kada ya rasa ko mutun ɗaya daga cikin TRIPLETS nasa, farincikin rayuwarsa, kuma su ne duniyarsa bakiɗaya. Areef da Jehan game fa yanata tafiya, yanzu saura ƴan kwanaki da basu fi uku ba a gama game ɗin, ya sanya ta saki jiki da shi sosai fiye da tunanin mai tunani, suna hira, sai dai har yanzu bata dariya kuma bata da yawan magana wanda hakan kuma halittarta ce. Yau ma dai kamar kullum tana kwance cikin bedroom nata ya iskota, yanzu ta tashi daga barcin safe. Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo, cike da kulawa ta amsa mishi sallamar, saman bedside drawer ya zauna. Zuba mata idanu ya yi yana kallon kayan jikinta. Kayan barci ne marasa nauyi a jikin nata, tana da breast masu matuƙar ɗaukar hankali, dan kuwa sun cika kirjin nata fam, idan ta sanya kaya ko ba breziya sai su yi tamkar zasu fasa rigar saboda cika, idan baku manta ba dama fa sun gaji girman breast da kuma hips, so dukkansu kusan hakan suke, A'afia ce kawai ƴar caras a cikinsu, ita ce bata da cika sosai, amma dukkansu ba baya ba wajen cikansu. Ganin sai kallonta yake yi ne yasa ta ɗan meke daga kwanciyar da take tana faɗin "Kallon fa?". Ɗan matsowa kusa da ita ya yi yana faɗin "Girlfriend ɗita nake kallo mana". Shiru ta yi bata sake ce mishi komai ba na ɗan lokacin, shi ma shiru ya zuba mata idanu yana kallonta. "Yau kuma ina zaka je?". "Ina dai zamu je ko?". Hararsa ta yi tana faɗin "Ni babu in da zanje". Kashe mata ido ɗaya ya yi kamar yanda ya saba yana ɗaga jera ɗaya, cikin sanyin murya ya ce "To shikenan bari na je na shirya na yi tafiya ta". Adawo lafiya ta bashi amsa, miƙewa ya yi tamkar zai fita sai kuma ya juyo tare da manna mata sumbata a goshinta yana murmushi, yunkurawa ta yi dan ta buge bakinsa, da sauri ya wuce tamkar dama yasan zata yi mishi hakan, ko da yake dama da gangan ya sumbace ta ɗin, dan ya san bata so. Yana fita bedroom ɗin daddynta ya nufa, kwance ya isko daddy yana tunanin mummy, yana kewarta over to over fiye da tunanin mai tunani, dan ma yana da dakiya ne da kuma jarunta yasa ya iya jure rashin ta, rashin mace kamar mummy ba kowa zai iya jurewa ba, ƴar marainiyar Allah ta iya kula da miji fiye da tunanin mai tunani, ta riga da ta kashe zuciyar daddyn da soyayyarta, baya tunanin kowa sai ita, ba zai iya jure rashinta ba, musamman ma da ya ji tana raye daga bakinsu Jehan, tun daga nan ya shiga damuwar a ina take?. Saman bed Areef ɗin ya zauna yana ƙoƙarin fara magana sai ga ƴar diramar tasa ta shigo ita ma, dama tun da ta tashi daga barci take son zuwa ta duba daddyn nata, amma ta kasa tashi saboda kasala, sai da mijin nata ya zo ya tasheta sannan ne ta iya fitowa. Still kayan barcin ne a jikinta, duk idan ta yi taku ɗaya sai gabaɗaya ilahirin jikinta ya girgiza saboda yanayin kayan barci nata, kasa jure hakan oga fa ya yi, shi gaskiya ya gaji da dannewa, ya fara sarewa, yana son rungume kayansa suyi barci tare yana jin ɗuminta. Duk abin da suke ciki daddynta yana ganinsu, kawai ya zuba musu idanu ne yana ganin gudun ruwansu, ya san cewa Areef fa ba zai iya jurewa ba, dan fa shi ma Lion part two ne, akwai shi da jaraba sannan kuma yana bala'in sonta fiye da tunanin mai tunani, haka zalika ita ɗin ma sarai daddyn yasan ta kamu da son Areef ɗin, kawai wahalar da kansu suke yi, amma ya zuba musu ido ya ga karshen game ɗin nan nasu sai ya san abin yi, dan ba zai yarda Jehan ta rinƙa ɗaukar alhakin Areef bawan Allah a banza ba, so dole ya san abin yi idan game nan ta zo karshe gaskiya. Kusa da daddyn ta zauna tana wani yamutse fuska tamkar wanda aka yi wa dole ta fito waje. Kasa jurewa Areef ya yi, yana son ya ɗan rungumota amma haka kawai sai ya ji nauyin daddy yau kuma, hakan yasa ya miƙe yana faɗin "Baby ki kawo mini fruits da ruwa mai sanyi ɗaki na, ki yi sauri fa!" Yana magana yana kallonta. A hankali ta motsa laɓɓanta ta furta wata kalma ta yadda sautin ba zai fita ba, sai dai mai kallonta ya karanci me ta faɗa daga yadda ta motsa laɓɓan, baza'a kawo ba, shi ne abin da ta faɗa. Mai da kallonsa kan daddy dake kwance ya yi yana faɗin "Uncle ka dai ji wai ba zata kawo mini ba ko?" Cikin sauri ta ce "Daddy wlh ban ce ba, ai baka ji na yi magana ba ko?". "E to tashi ki je ki kai mashi kin ji?" Cewar daddy'n. To ta amsa tare da miƙewa tana turo baki. Gaba ya yi ya fice daga ɗakin yana jin nishaɗi, dan dama idan bai tsokaneta ta turo bakin nan ba, kwata kwata baya jin daɗin rayuwa, ya fi so ya ga ya tasata a gaba yana mata abu tana turo baki, ba ƙaramin daɗin hakan yake ji ba. A ɓangaren ta kuwa, Allah ya kiyaye ta aure shi take yi a cikin zuciyarta, amma idan ta tuna abu ɗaya sai ta fasa wato daddynta, shi ne duniyarta komai nata....... YARINYA KINA CEWA ALLAH YA KIYAYE KI AURE SHI, BAKI SAN CEWA MIJINKI BANE MA A YANZU. Palon kasa ta nufa tana turo baki, kanta sam babu ɗanlwali ta saki gashin nan gwanin burgewa, kitchen ta nufa, plate ta ɗauko ta shirya mishi fruits ɗin, tun da take tare da daddynta da mummynta a Abuja, bata taɓa shiga kitchen ba sai da ta rabu da su. Haɗa komai ta yi ta ɗauka ta nufi bedroom ɗin nasa, duk in da ta taka kafa sai jikinta ya yi rawa, musamman mazaunanta da breast nata wanda bata sanya breziya ba, dan idan zata yi barci dama bata sakawa, kuma kunga bata jima da tashi daga barci ba. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga bedroom ɗin nasa tana turo baki irin alamar an yi mata dolennan. Baya cikin ɗakin, saman bedside drawer ta je ta ɗaura mishi plate ɗin a in da ta zauna a gefen bed nasa tana jiransa, tasan cewa ko ta tafi sai ya sake dawo da ita, dan zai ce wlh ba zai sha ko ruwan ba sai ta zo ta zuba mishi da kanta, haka daddy zai sakata ta sake dawowa, to gara ma kawai ta zauna ta jira shi. Ta yi shiru sai kallon ɗakin take yi a ranta tana yaba tsantsar tsabta irin na TRIPLETS, duk tsabtarka idan ka zo gabansu to fa tamkar kazami haka za'a ganka saboda tsabtarsu ya wuce misali. TO BARI MU LEƘA RIMSHA DA LION WATA KILA KAFIN MU DAWO AREEF YA DAWO DAGA IN DA YA JE. JIRGIN RUWAN💋 Zaune take a saman bed nasa, tana shirye cikin kayan barci masu tsantsar kyau farare tas, ɗaya ne daga cikin kayan da Josephine ta yi mata sayayya kwana huɗu da suka wuce kenan, kayan suna da matukar kyau, jikinsu tamkar audiga saboda laushi, kusan iri ɗaya ne da na shi. Shi kuma yana waje yana magana da Mark, ita kuma ta kule saman bed a in da ta rufe rabin jikinta da lallausan bargonsa ta sanya Bluetooth nasa ɗaya a kunnenta hannunta na rike da wayarta a in da ta shiga cikin Vidmate tana duba wakoki. Har zata wuce sai ta yi play ɗin wani waka, jin cewa ta san wakar ne yasa ta yi downloading nata zuwa kan wayarta, tana gama ɗaukota sai ta fita daga Vidmate ɗin ta shiga gallery, wakar ta yi playing tare da fita ta shiga kan hoton jarumin mijin nata dan ta kafe shi da ido. A hankali ta fara ɗan kaɗa kai tana ɗan bibiye wakar har aka zo wajen wata baiti. Da ɗan karfi ta ɗaga murya tana bibiye wakar tana kaɗa kai "A kanka bani jin kunya, ace na haukace a soyayya, samun irinka akwai wuya a wannan zamani duniya, a kanka zan yi komai, in bada rayuwata, kai ne jarumina....". Bata kai karshen ba juyowa da idonta da zata yi suka yi 4 eyes da shi, yana tsaye a bakin kofar bedroom ɗin, tun ɗazun ya shigo ya tsaya yana kallon yanda ta tasa hotonsa a gaba ta sanya Bluetooth nasa tana bibiye wakar. A ransa ya ce e lallai sauki ya samu ba karya, yau period nata ya ɗauke, amma har yanzu kafin ya fita daga cikin bedroom ɗin sai da ta yi mishi kukan ciwon ciki, magani ya bata kafin ya fita zuwa wajen Mark, amma kafin ya dawo har ta sami sauki ta fara bin waka. Ganinsa yasa a sukwane ta kwanta tare da jawo bargo ta rufe har kanta gabaɗaya, wai ita a dole ta ji kunya, sai murmushi take yi ita kaɗai a cikin bargon. Karisowa cikin bedroom ɗin ya yi tare da nufar bed ɗin. Hayewa ya yi ya kwanta tare da jan bargon shi ma ya shiga, sannan ya karɓa wayar tata ya kashe ta yana yi mata faɗa a kan kunna waka bayan ta san barci zasu yi, hakuri ta bashi tare da yi mishi alkawarin ba zata sake jin waka da daddare ba, sumbatar kumatunta ya yi yana jawota jikinsa ya lumshe idanunsa, ba jimawa barci ya yi awon gaba da su bakiɗaya.. ASUBA TA GARI. Washegari da safe, da misalin karfe 10 na safe ta farka daga barcin safenta, miƙewa ta yi ta nufi toilet. Kamar kullum baya cikin bedroom ɗin, wanka ta yi tare da fitowa ta shirya cikin wasu tsadaddun riga da wando, shi ma ɗaya daga cikin kayan da Josephine ta saya mata ne, ta yi kyau sosai, ta gyara gashin kanta a in da ta sake shi har gadon bayanta, gyara musu ɗakin ta yi fes, duk da cewa babu wani datti, amma saboda tsanin halin mijin nata da mugun son tsabta baya son datti, sai ya zama duk bayan ƴan awanni sai ta sake goge ɗakin ta gyara ko'ina ta kara musu air freshener, yana ɗaya daga cikin abin da yasa yake kara sonta, saboda tsabtarta. Zama ta yi saman sofa tare da ɗauko wayarta tana ƙoƙarin kiran number Areef dan ta tambaye shi kyautar me zata ce Lion ya yi mata a zanen nata. Kamar daga sama ta ji an kwace wayar, ko bata ɗaga kai ba ta san shi ne. Ganin Areef take kira yasa ya kara ɗaure fuska yana ce mata a kan me zata kira Areef da safen nan? Bata yi mamaki ba dan jiya ma ya hanata kiran daddy da safe, ya ce ta bari sai da rana kada ta takurawa mutane da kira wata kila suna barci, sai dai fa tana son yin magana da Jehan sosai. Turo bakin nan nata ta yi kamar zata yi kuka. Kusa da ita ya zauna yana faɗin ta kawo musu breakfast su yi dan jirginsu ya kusa shiga Russia, dan haka ta shirya, turo bakin nan ta kara yi tare da miƙewa ta nufi wajen table ɗin, abincin ta dauko musu, yau tana tsantsar ji da rigima ba kaɗan ba. A gabansa ta ajiye abincin tare da fara zuba mishi a plate. Sanyayyar muryarsa ne ya daki dodan kunnenta a in da yake tambayarta me yake damunta?. Da yake rigima take ji da shi yau sai ta miƙe da sauri da nufin ta bar wajen tana wani matsu fuska. Cikin sauri ya riƙo hannunta tare da jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, wani irin yarrr suka ji su dukkansu biyu tamkar basu taɓa taɓa jikin juna ba. Zubawa face nata waƴan nan dara daran idanun nasa masu rikitarwar ya yi, yana kallon yadda take turo ɗan bakin nan nata, ba ƙaramin kyau lallausan lips ɗin nata suka yi mashi ba yau, har wani irin tsuma jikinsa yake yi ganin lips ɗin tata da ya yi. Can kasar maƙoshinsa ya ce "Me yake damunki?". Kasa ta yi da kanta tare da shigewa jikin nasa sosai. Yin hakan da ta yi ba ƙaramin kara rikita shi ta yi ba, wani irin yanayi ya tsinci kansa a ciki. Da kyar ya iya sako hannunsa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, runtse idanunta ta yi dan har gobe tsoron ganin cikin kwayar dara daran blue eyes ɗin nan nasa take yi. Ya ɗan ɗauki mintuna yana kallon face nata kafin ya tsinci kansa da matso da nasa face ɗin izuwa saman tata. Jin hakan na face nasa a saman tata ba ƙaramin shiga cikin yanayi ta yi ba, wanda kuma hakan yasa ta waro idanuwanta waje, karaf sai cikin nasa idanun, domin kuwa fuskokinsu a haɗe yana kallon idanun nata. Da sauri ta mayar ta runtsesu tare da kankame shi, saboda wani azababben bugu da zuciyarta yake yi, yanayin da ta gan shi a ciki yau fa gaskiya ya ɗan razanata, idanun nan nasa sun rikiɗe sun yi jawur sosai yau. Sai bugu kirjinta yake yi, kuma babu halin ta sanya hannu ta dafe kirjin nata, sakamakon tana kwance a jikinsa, kuma ya rankwafo kanta, shiyasa kawai ta kankame shi ko zata samu sauƙin abin da take ji. Hannu ya sanya slowly ya ɗan shafi lips ɗin nata, har lokacin kuma face nasa yana nan daf da tata, sai ingiza shi zuciyarsa take yi akan lallai ya yi kissing na breast nata da suka ciko fam yana kallon tudunsu ta saman wuyar rigarta, idan fa bai yi kissing nasu ba, ba shi ba kwanciyar hankali, domin kuwa ba abin da wannan zuciya tasa take so a yanzu sama da hakan. Ya ɗauki tsawon mintuna 10 a haka kafin daga bisani slowly ya kai lallausan laɓɓansa saman tata da nufin sumbata. Lokacin da lips ɗin nasa suka sauƙa a saman tata, wani irin kankame shi ta yi da karfi wanda hakan kuma ta yi sanadiyar kara ingiza zuciyarsa ta yadda ya capko lips nata na kasa ya fara sha babu kama hannun yaro. Daga ita har shi yau wani irin bakon yanayi suke ji a jikinsu, dukkansu ji suke yi tamkar basu taɓa taɓa jikin juna ba, musamman ma ita da ta gama period jiya, abin sai ya yi mata wani iri, tana jin sauyi sosai a tattare da ita wanda bata taɓa ji ba. Wani irin laushi mai shegen daɗi Allah ya zubawa lips nasa, kamar fure hakan suke, shi ma kuma a nashi ɓangaren wani irin bala'in daɗin da bai taɓa jin makamancin shi ba yau ya ji a tattare da lips ɗin tata duk da yana kissing nata a baya, amma yau sai ya ji komai daban tamkar yau ya fara. A zafafe ya matseta a jikinsa tare da cigaba da kissing nata da zafa zafansa dan yanzu ya dai'na yi a hankali. Bata san time da ta damko ɓul ɓul ɗin breast nasa ba, saboda shiga wani irin yanayi mara misaltuwa da tayi, baiwar Allah ta yi period ita ma duk wasu kofofi masu karɓar sako a jikinta sun buɗe, shi ne sauyin da ta ji a tattare da ita, idan ya taɓata sai ta ji tamkar shocking na wutar nepa ne ya ja ta, yanzu a garin kokarin kankame rigarsa ta kirjinsa take yi, saboda ta sami sauki, to abunku da suma breast ɗin nasa suna cike ɓul ɓul, sai kawai ta riƙosu tare da rigar. Yin hakan da ta yi kuwa, ba ƙaramin aika mishi da wani saƙo har tsakiyar kansa ba tayi, wani irin abu ya ji har cikin tsakiyar kansa tamkar wadda aka kwalawa guduma da mugun karfi a kan nasa, kun san yadda ake ji idan a ka buga maka abu a tsakiyar kai, shi ma dai haka ya ji wannan saƙon nata na riƙo ɓul ɓul ɗin breast ɗinsa da ta yi. Ai kuwa a zafafe ya kara karfin kissing ɗin nata da yake yi, zafa zafa tare da cusa hannayensa dukka biyu cikin gashin kanta, ya fara watsasu yana cusa hannayen nasa cikin fatar kanta. Dama abin da yake gudu kenan yasa baya yawan wasa da ita, baya son jawa kansa wahala, yasan tabbas Rimsha a ƴanda take yanzun nan ba zata iya jurewa jarabarsa ba, so kada ya zo ya fara abin da ba zai yiwu ba ya jawa kansa wahala. Gabaɗaya ta rasa ina zata sanya ranta, ta kiɗime sosai, Noorinta yana neman sumar da ita yau, duk sai ji take yi tamkar shocking na wutar nepa idan ya taɓata. A zafafe cikin fitar hayyaci ya zamo da hannunsa ɗaya daga saman kan nata ya mai do da shi izuwa saman wuyarta, shi ma dai da zafa zafa cikin zafin nama yake shafata, ita kuwa sai faman kara kankame ɓul ɓul ɗin breast nasa take yi, ta ruɗe sosai, hakan da take yi ne kuma yake kara ingiza shi, saboda tana yi mashi kamar matsa mashi su take yi, yadda take ƙanƙame su ɗin. Bai ma san time da ta miƙe da ita zuwa saman katafaren gadonsu ba, kwanciya da ita ya yi bakinsa na cikin tata. Rumfa ya yi mata da faffaɗar kirjinsa har kuma lokacin bakinsu na manne dana juna, hannu yasa yana ƙoƙarin laluɓar tula tulanta cikin yanayi da ba zan iya fassara ya yake ba. Jinsu a cikin riga ne yasa ya damki wuyar rigar cikin zafin nama tare da raba bakinsu, yasa hannu ya tsaga rigar daga sama har kasa ya direta. Ba ƙaramin tsorata tayi ba jin ya yage mata riga, duk da idanunta a rufe bata ganin halin da yake ciki, ta yi matuƙar razana, nan take jikinta ya fara kerma, a tsorace ta fara ambato sunansa can kasa kasan maƙoshinta domin muryarta ta dashe sosai, bata wani fita. "Noori, Noori, Noori, ka bari mana, Yaya Saif me kake yi haka ne?". Ina baya jinta dan kuwa ya yi nisa. Bayan ya yage rigar ma ya tarar da wata farar vest mai shegen kyau a ciki, ita ma yageta ya yi da karfin tsiya, tare da capko abin da yake nema da hannunsa ɗaya, while shi kuma ɗayan hannun nasa ya mayar da shi saman kanta, ya tallaɓota da kyau ta yadda zai ji daɗin yin abin da yake so. Wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe lokacin da hannunsa ya sauƙa a saman lallausasan tula tulan nata, wani irin duniya ya shiga, da zafa zafa ya fara matsesu, kun san yadda jininsa yake a tafashe, to haka yake yi mata komai a tafashe, a zafafe. Da kyar ya iya samun kan nipple nata saboda babu wanda ya taɓa taɓasu bare su yi yunkurin fitowa, kun san dai yadda take ɓoye kayanta, sabbine kal a leda, tamkar basu da baki saboda ƙanƙantar bakin nasu. Wani wahalallen kara ta saka mishi lokacin da ya gano ƴan bakin nipples ɗin ya fara murjesu, zafi ne ya ziyarce ta yasa ta saka mashi kuka, mai da lallausan lips nasa ya yi saman wuyarta, lasheta ya fara yi yana yi mata wasa da harshensa a wajen, while hannunsa kuma yana a kan nipple nata. Tun tana kuka da kyar da kyar saboda rashin fita da muryarta baya yi, har ta fara samu muryar ta sake ta, tana kuka da ɗan karfi karfi, shi kuwa daga saman wuyarta yake lasheta yana gangarowa izuwa saman kirjin nata, sai wani gurnani yake yi tamkar wani zaki, ga shi komai a zafafe yake yi mata. Manyan tambayoyin dake a cikin zuciyarta shi ne, yaushe Yaya Saif ya iya wannan abin dukka? Waye ya koya mashi? A ina kuma ya iya? Shi da yake shiru shiru, ko magana baya yi. Shi ne tambayoyin da take yi wa kanta da kanta, wanda kuma bata da amsarsu. Tana kukanta da ɗan karfi karfi tana tunane tunane kuma a cikin zuciyarta, kamar daga sama ta ji saukar lallausan lips nasa a saman tula tulan nata, ya capko nipple ɗin nata ɗaya, ya fara sha, while hannunsa kuma yana a kan ɗayar. Dakarkarewa ta yi da iya karfinta ta kurma ihu domin zafi take ji. Wannan ihun nata tamkar sugar ta kara mishi a abin, shi ne abin da yake guda dama, ya san cewa ku mai ihun da zata yi idan ya yi niyar yin abu fa sai ya yi, ba zai wani damu da ihunta ba, idan tana ihun ma kara ingiza zuciyarsa zata yi har ya kai in da bai zata ba, bugu da kari komai ihun da zata yi a cikin sojojinsa babu wanda ya isa ya yi gigin shigo mishi cikin ɗaki, so zai yi abin da ya ga dama, hakan yasa yake gudun yin wasa da ita ma dan kada ya kashe ƴar mutane a cikin ruwan nan. Kara matseta ya yi a jikinsa tare da zame ɗan bakin nasa daga saman nipple ɗin tata. A hankali ya maido da bakin nasa saman tata ya cigaba da kissing nata. Ƙoƙarin ture shi ta fara yi, amma ina ko motsa shi ta kasa yi, shi kuma da sauri ya kara kankameta da kyau da kyau. Can kasa kasan maƙoshinsa ya fara sambatu da wannan rikitattiyar sexy voice ɗin nasa mai rikita mai sauraro, ga shi yana cikin yanayi sai muryar tasa ta kara wani irin azababben daɗi. "My Meesha, My Meesha, please play with my balls for me, (ɓul ɓul ɗin breast nasa kenan) it making me very very sweet feeling about you". Cak ta tsaya da kukan nata tana sauraron sambatun da yake zuba mata. Mamaki ne ya daɗa kamata, wai dama kenan yasan abin da ake cewa kusantar mace? Ko dai yaya abin yake ne? Ko dai yau ma mafarki take yi ne? Ta tambayi kanta a cikin zuciyarta. (Rimsha da tambayar iskanci take wlh, yo shekarunsa nawa a duniya da ba zai sani ba? Bayyi karatun addini bane? Bai yi na boko bane? Kuma koma bai yi karatu ba akwai munzalin da idan bawa ya kai wannan lokaci, Ubangiji yana sanya mishi sha'awar wannan abin a cikin jikinsa, halittace a jini yake.) Tana tsaka da tunani bata ankaraba sai jin lallausan ɗan bakinsa ta yi a saman cibiyarta, ya zura harshensa ciki yana jujjuyawa tare da wasa da wajen yana ɗan danna jibiyar tata ciki da harshen nasa. A wannan karon ta kasa jurewa har sai da ta saki ihu mai sauti. Ina ko a jikinsa, tamkar bai ma ji ta yi ba, sai ma kara capko tula tulanta da hannunsa dukka biyu da ya yi, while har lokacin bakinsa na a saman cibiyarta. Mutsu mutsu ta shiga yi, tana neman kwace kanta, amma ina ta kasa, domin kuwa ko da hannu ɗaya ya riƙeta ba zata iya kwace kanta ba, bare kuma ya yi mata runfa da jikinsa. Haka ta hakura ta danne ta jure ta zubawa sarautar Allah ido kawai. Shi kuwa haka ya cigaba da juyata yana wasa da ita son ransa, ya kware wajen sarrafa mace ta yadda ko bata so dole ta bada kai bori ya hau, sai dai kuma duk wannan wasa da ita da ya yi tamkar bai san da wani abu wai shi kusantar mace ba, kwata kwata bai tunkari gabanta ba, sai dai birkita mata lissafin ƙwaƙwalwa da ya yi da wasanninsa har sai da ta suma. Baiwar Allah bata taɓa jin irin wannan abin ba, bugu da kari yanzu ma ta fara period, kuma jiya ta kammala dole dama a sami irin haka a tattare da ita. Shin me ya sanya Rimsha suma? Daɗi ne ko kuma tsoro da fargabar ganin ya yi abin da bai taɓa kwatantawa ba a duniya ba ne?. Ni dai na fi tunanin sumar birkita mata lissafin ƙwaƙwalwarta da ya yi da wasanninsa ta yi, domin tun farko jikinta ya nuna hakan, ta karɓi saƙonsa ne har ya yi mata over, ya sanyata suma ba shiri. Ko da ta suma bai kyaleta ba har sai da ya kai lokacin da yake buƙata, ya samu natsuwa, sannan ya zame bakinsa daga saman nipple nata tare da komawa gefenta ya kwata, ya jawota jikinsa yana mai sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya. Runtse idanuwansa da suke jawur tamkar wuta ya yi. A hankali ya motsa lallausan laɓɓansa tamkar yana son furta wata magana, sai dai kuma bai furta ba, ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa tare da ɗan ciza laɓɓansa ya sanya hannunsa ɗaya ya shafa kyakkywar dark black curly hairnta izuwa bayanta. A hankali ya furta. "Matsoraciya kuma raguwa kawai, daga wasa har da suma". Ya kai karshen maganar tare da kara matseta a jikinsa, dan fa shi yanzu ma yake ji tamkar....... Zata fashe saboda tsayuwa da ta yi kyam, duk wasan da ya yi da ita abar tasa taki kwanciya, kawai ya kyaleta ne dan kada ya fita cikin hayyacinsa sosai ya afka mata, yasan confirm idan ya kusanceta a yanzu za'a iya ɗaukar gawarta........SHI FA LION ƊIN NAN YA RAI'NA RIMSHARMU DA YAWA😌 HABA WANNAN IRIN RASHIN MUTUNCI HAR INA? ZAI RINƘA WANI CE MATA YARINYA😌🥺 READERS KU GAYA MISHI MUFA A NIGERIA KAMAR RIMSHA 14 YEARS BA YARINYA BA CE, KUMA ZATA IYA ƊAUKAR AL' AMURA,🙃👊 SAI DAI SHI ƊIN NE YA YI A HANKALI, KADA YA KASHE MANA ITA, YA KAMATA WILLIAM JACOP YA FARA RENON JIKOKI YANZU, DAN YA KWARE A IYA RAINO, KADA KU MANTA SHI YA RENI TRIPLETS ƊIN NASA.🤧😂 A can kasan zuciyarsa kuwa, wani tunanin yake yi na daban wanda bai bawa kowa daman sanin me yake tunani ɗin ba. Haka suka kasance har tsawon good 30 mins, kafin ya sauketa daga jikin nasa ya miƙe ya ɗauko ruwa dan ya yayyafa mata ta farfaɗo. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 *KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*. *KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 79 TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ ❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋) *Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581* Haka suka kasance har tsawon good 30 mins, kafin ya sauketa daga jikin nasa ya miƙe ya ɗauko ruwa dan ya yayyafa mata ta farfaɗo. Saman bed ɗin ya dawo. Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallon face nata kafin ya tarfo ruwan a hannunsa. A nutse ya sha mata a face ɗin nata. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan motsa kaɗan. Rufe robar ruwan ya yi ya ɗaurata a saman bedside drawer yana mai cigaba da kallon face nata. Slowly ta waro idanunta da suka yi ja saboda kukan da ta sha kafin ta suma. Kai tsaye sai saman face nasa ta sauke idanun nata. Kawar da kallonta ta yi tana turo baki ita a dole ta yi fushi. Zazzakar muryarsa ne ya katseta da cewa "What happened to your eyes?". A sukwane ta juyo da kallonta kansa. Lallai ma wato ma kenan bai san me ya semeta ba? Yana so ya ce duk kukan da ta yi bai ji bane?. Lallai ma yaya Saif ɗin nan ya kware ya shahara. Hannu ya kai saman face ɗin nata a in da ya kyasta mata kyawawan fararen yatsunsa. Lumshe idanunta ta yi tare da kara turo baki. Yau wani irin rigima na daban take ji da shi, dan haka sai ta yunkura zata mike dan ta yi fushi da shi. Ganin zata sauka daga saman bed ɗin ne yasa ya jawota jikinsa yana mamakin yaushe Meeshan nan tasa ta zama rigimammiya har haka ne? Sai son rigima da zuba mishi shagwaɓa, ga saurin fushi na iya shege da take yi mishi. Amma fa hakan da take yi ba ƙaramin kara nutsawa can cikin farfajiyar zuciyarsa take yi ba, mugu mugun burge shi take yi idan tana rigima, shagwaɓa or fushi. Musamman ma idan ta turo baki ta ce ta yi fushi da shi, ba karamin tafiya da shi take yi ba. "Where are you going?". Ya faɗa a sanyaye. "To ba kai ne ba?". Ta faɗa idanunta na cikowa da kwallah na zallar madarar shagwaɓa. "Me ni kuma nayi?". Hawayen ne suka fara zubo mata a saman kuncinta. A tsananin shagwaɓe ta ce "Ɗazun ina ta ce maka ka bari kaki, ka sakani kuka, amma yanzu sai ka ce me ya sami idanuna? Bayan kuma kai ne fa ka sakani kuka, kuma ga shi ina ta kiranka kaki ka amsa mini, uhm uhm ni Allah mun ɓata da kai." Shi kam idanu kawai ya zuba mata yana kallon ikon Allah, sam baya ma jin abin da take faɗa, hankalinsa ya tafi wani tunani da ban, wannan irin magana tata shi ne yake kara tsananta azababben sha'awarta da yake ji. Ganin bai tanka mata bane yasa ta yunkura zata miƙe daga jikin nasa ta sauka kasan gadon. Rikota ya yi yana mai cigaba da kallon ɗan guntun hawayen shagwaɓar dake face nata. "Look at me." Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa. Make mishi kafaɗa ta yi tana ƙoƙarin kara shigewa jikinsa da kwantar da kanta da kyau a saman breast nasa. Sai a lokacin ta lura ashe babu riga a jikinta. A hanzarce ta rungume shi dan ta ɓuye breast nata, kuruci dangin hauka kenan. Shi kansa ya ɗan yi mamakin yin hakan da ta yi, amma sam bai kawo cewa breast nata take ɓoyewa ba, rungumar shi ɗin da ta yin ne ya ɗan bashi mamaki. Meesha, ya ambaci sunanta. "Na'am noori." Ta amsa kasa kasa. "Tashi ki yi wanka ki shirya kici abinci, kin ji jirginmu yana buga alamar mun iso madakata, so tashi ki ci abincin." "Zaka bani a baki?." Ta yi maganar tana ɗan ɗago kanta tare da runtse idanu. Ya ɗan yi mamakin jin maganar tata, amma kuma shi ma zai so ya bata a bakin dan sam kwana biyun nan tana mugun wasa da cin abinci, wani lokaci ma sai ya yi mata magana take cin ɗan kaɗan ta bar saura. "Noori zaka baki a baki?." Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "Idan har zaki iya kallon face na a lokacin da nake baki ɗin." Turo bakin sosai ta yi tana faɗin "Kawai dai ba zaka bani ba zaka ce mini." Shiru ya yi bai amsa mata ba. A duniya wannan kunya tata tana matuƙar burge shi, yanda take kin yarda su haɗa ido, da kuma idan abu ya bata kunya sai da rufe fuska da hannu tana murmushi, ba ƙaramin jin daɗin hakan yake yi ba. Shiru tayi tana tunanin yanda zata yi mishi yau ya bata abinci a baki, ta san dai ba zata iya ganin face nasa suna fuskantar juna ba, to me yakamata ta yi?. Miƙewa ya yi da ita a jikinsa suka sauko kasan bed ɗin. Ɗan zaro idanu ta yi tana kallon lallausan wuyarsa while shi kuma yana kallon hanyar da yake tafiya. Ta shagala da kallonsa sai jinta ta yi a cikin ruwa tsulumdum, kankame wuyarsa ta yi tana ƙoƙarin saka mishi kukan shagwaɓa. Yatsa ɗaya ya ɗaura a saman lips ɗin nata yana girgiza mata kai. Yanzu ba lokacin wasa bane, lokacin ya kure musu har sun isa madakatarsu a tafiya. Matso da face nasa ya yi daf da tata a in da ya manna mata kyakkyawar sumbata a lips ɗin nata kafin ya juya ya fita zuwa ɗaya daga cikin bedrooms dake cikin jirgin dan shi ma ya yi wanka. Bin bayansa da kallo ta yi har sai da ya kurewa ganinta. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani sabon azababben son mijin nata yana kara ratsata. Juyawa ta yi ta fara wanka, kafin nan sai da ta tsaya ta zubawa breast nata idanu tana tariyo duk abubuwan da suka faru ɗazun. Lokaci guda ta saki cool murmushi tuna irin abin da ya yi ta faɗa ɗazun, har da cewa ta yi mishi wasa da breast nasa, yanzu idan ka ce shi ne ya ce hakan zai ce wlh ba shi bane, dan ba'a cikin hayyacinsa ya faɗa ba, ya manta komai yanzu. Wanka ta yi tare da fitowa ta nufo cikin bedroom ɗin. Mamaki ne ya kamata ganin ya fitar mata da kaya ya ɗaura a saman bed kafin ya fice daga cikin ɗakin. Karisowa wajen bed ɗin ta yi tare da ɗaukar kayan tana dubawa. Shiru ta yi a in da ta faɗa duniyar tunanin a ina kuma ya samo abaya? Ko dai a cikin kayan da Josephine ta saya mata ne?. Wani ɓangare na zuciyarta ne ya ce ina ai a kayan da Josephine ta saya mata babu abaya, gabaɗaya kananan kaya ne irin nasu na turawa, to shi a ina ya samo wannan abaya har da karamin hijabi fari tas? Sai zuba uban murmushi kayan suke yi sosai. Ganin tunani ba wani mafita da zai bata ne yasa ta wuce zuwa wajen trolleys ɗin hannunta rike da kayan nata. A hanzarce ta shirya, abayar ya yi matukar yi mata kyau, ga ta dai'dai da jikinta tamkar dan ita aka yi shi. Da yake gashin kanta ya jike sai ta yi ƙoƙarin jona hand dryer ɗakin dan ta busar, amma ina yaki yi, hakan yasa ta hakura a in da ta yafo mayafin abayar kawai ta fito waje dan ta duba a wani ɗaki yake ta je ta ce ya zo ya jona mata hand dryer. Tana sako kafarta wajen bedroom ɗin gabaki ɗaya sojojin nasa suka juya, lokaci guda suka bata baya. Ta sha ruwan mamaki na ganin hakan, barema yanda suka yi a tare, abin sai ya kayatar over. Bedroom dake kusa da nasu ta nufa. Har zata yi sallama sai ta hango shi saman mirror chair yana busar da gashin kansa da hand dryer. A cikin zuciyarta ta yi sallamar dan kada ya ji. A hankali ta lallaɓo zuwa ciki kamar wata ɓarauniya. Jikinsa na sanye da wani irin haɗaɗɗen jeans fari tas da kuma high neck t-shirt sky blue, ya yi matuƙar kyau over, sai tashin wani azababben kamshi yake yi. Lallaɓawa ta yi har ta ƙariso in da yake, da yake yana zaune ne sai tsawonta ya kai tana iya kallon kan nasa. Hannu ɗaya ta cusa cikin gashin nasa tare da saka ɗayan hannun ta karɓi hand dryer daga hannunsa. Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗago idanunsa ta cikin mirror yana kallonta. Ta yi kyau over, sai satar kallon shi take yi bata san yana kallon ta ba. Wani irin lumshe idanunta tayi tare da sake warosu a saman kan nasa. Gashin nasa ya yi mugun yi mata kyau. Shi kuma da yake kallonta ta cikin mirror har wani irin tsuma jikinsa ya yi na ganin yanda ta yi da sleeping eyes ɗin nan nata, dama idan baku manta ba, sune abu na farko da suka fara jan shi izuwa gareta, yana bala'in sonsu musamman idan tana jujjuyasu, haba ai har wani irin duniya yake lulawa a lokacin. Busar mishi da gashin ta fara yi, tana yi tana cakuɗa hannunta cikin kan nasa. A hankali ya lumshe idanunsa saboda wani irin daɗi da yake ji yana ratse dukkanin ilahirin jikinsa. Ita kanta daɗin taɓa mishi gashin take ji saboda yanda yake da tsananin laushi ga tsantsi kamar me. A hankali ta kai ɗan bakinta ta sumbaci gashi tana sauke ajiyar zuciya. Yana jin duk abin da take yi mishi, jin saukar sumbatar ne yasa ya ɗan waro shanyayyun idanunsa waje. Zuba mata idanu ya yi yana kallon yanda take murmushin tana shafa gashin nasa. Ƴan mintuna ta ɗauka tana busar mishi dan ya fara yi dama, ita karisawa kawai ta yi. Bayan ta kammala ta shafa mishi mayukansa dake saman mirror a wajen, lokacin da ta je ɗaukar mayukan ne ta fahimci ashe yana kallonta ta cikin mirror. Wani irin kunya ne ya kamata, kenan ya kalli sumbatar gashinsa da ta yi? Ta tambayi kanta. Lokaci guda ta sanya hannu ta rufe face nata tana murmushi. Shi dai har lokacin bai kawar da kallonsa daga kanta ba. Sai da ta yi kora da kunyarta ya isheta sannan ta shafa mishi mayukan tare da tara gashin nasa waje guda. Da kyar ta iya ɗaurewa saboda bala'in tsantsi, sai da ya sanya hannu ya taimaka mata. Tun da yake a rayuwarsa bai taɓa ganin gashin kansa ta yi mishi tsantsar kyau irin na yau da ta gyara mishi ba. Bai san cewa matar aure tana da baiwa na wuce misali, kome ta taɓa in dai wa mijinta zata yi wa, to fa kyansa na daban ne, zaka ga namiji zai fita waje ya sayi abinci naira dubu ɗaya, amma zai cinye shi kaɗai wani lokaci ma bai koshi ba, amma da zai bawa matarsa wannan dubu ɗayan ya ce ta dafa musu abinci, da izinin Allah sai ta yi wannan abin da wannan dubu ɗayar su ci su koshi har ya yi saura, kaɗan kenan daga cikin ni'imomin da Allah ya yi wa matar aure wanda ba kowa ne ya san da su ba, sunanan bila adadi, idan nace zan tsaya zayyano muku baiwarsu, to sai mu cike littafin TRIPLETS fam bamu kammala ba, zai cinye mana ɗan sauran filinmu, dan haka a takaice matan aure dai Allah ya yi musu baiwa na daban, sai dai dayawa daga cikinsu basu san ta yaya za su yi amfani da baiwar ba, to Allah ya buɗawa kowacce ƙwaƙwalwarta ta iya sarrafa mijinta da kyau ta yanda zasu mori juna, mu dai muna iyaka bakin ƙoƙarin mu wajen ganin mun buɗe muku wasu abubuwa da baku sani ba dan ku gyara gidajenku!!. Zazzakar muryarta ne ya katse shi da cewa "Noori na iya gyarawa? Ya yi maka kyau?." Ta kai karshen maganar tare da zuro hannayenta ta saman wuyarsa izuwa kirjinsa tana kwanto da kanta a saman kafaɗarsa. Lumshe idanu ya yi tare da sake buɗesu a kanta, ta kwantar da kanta shiru tana jiran amsa. Hannun nata dake saman kirjinsa ya riko a in da ya jawota ta dawo ta gabansa. Saman cinyarsa ya nuna mata a kan ta zauna ba tare da ya yi magana ba. Ba musu ta zauna tana mai cigaba da murmushi. Zame mayafin abayar dake kanta ya yi a in da ya ajiye shi a gefe guda saman mirror, da yake ya fita tsawo sosai sai ya zamana da ta zauna a cinyar nasa yana iya kallon tsakiyar kanta sosai. Hand dryer ya ɗauko tare da sake kunnata ya fara busar mata da gashi. Wani irin haɗaɗɗen murmushi ta saki lokacin da ta ji abin da yake yi mata. Duniya kenan, yau GAR ne yake busar mata da gashin kanta? Allah mai iko mai yin yanda ya so da bayinsa, yau dai gata a saman cikyar mutumin da take mahaukacin kauna tun tana yarinya, bugu da kari yanzu ya zama mallakinta, mijinta ne shi ɗin, ga tsantsar kulawa da yake bata, sam bata damuwa da tsantsar kishinta da yake yi, domin Areef ya gaya mata sai ana son abu ne ake kishinsa, to ta kwantar da hankalinta, idan Lion baya sonta ko kallon hanyar da take ma ba zai yi ba, so ne yaja yake kishin, kuma ta godewa Allah ma da ya bata namiji mai kishinta har haka, hakan na nufin shi ɗin mai tsantsar kula ne, zai bata kulawa fiye da tunanin mai tunani, duk wani motsi idan ta yi sai ya so jin menene yake damunta, ko dan kada wani ya raɓeta zai zamana kullum yana son ta kasance kusa da shi, haka zalika zai bata soyayya mai tsayawa a rai ta yanda bazama ta ga wani soyayyar a Tv ko a wani waje bama har ya burgeta, duk wani abin da ya san zata kallah a waje ya burgeta, to fa zai yi ƙoƙarin ya ga ya yi mata shi fiye da yanda ake yi a wajen dan kishin kada na wajen ya burgeta, kaɗan kenan daga cikin baiwa da falalar samun namiji mai kishi, ko takalmar sakawanki ba zai bari wani ya gani ba dan kishi. Meesha, ya ambaci sunanta a hankali, ya kuma yi maganar dai'dai lokacin da yake kashe hand dryer yana tara mata gashin nata dan ya ɗaure. "Na'am Noori." "Tashi muje kici abinci sai mu wuce an gama shirya komai mu ake jira." "Noori na koshi mu tafi kawai." "No zaki ci, because ba zan bari kici abincin gidansu kakanki ba idan munje, the are not Muslim, so zai iya kasancewa suna cin something da ba dai'dai ba a musulce." Zaro idanu waje ta yi tare da juyowa gare shi tana faɗin "Noori dama wajen kakana muka zo?". Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, sake juyawa ta yi tana fuskantar mirror tare da sakin wani ƙayatatcen murmushi. "Noori yanzu zan ga kakana wanda ta haifi daddyna? Tana gidan nasu ne? Da.....". Bata kai karshen maganar ba idanunta suka sauka cikin nasa ta cikin mirror. Cikin sauri ta runtse nata tana murmushi, bata san cewa ya tsareta da kallo ba. Ɗan kwanto da kansa a saman kafaɗarta ya yi tare da daidaita fuskokinsu waje guda. Calmly ya furta "Open your eyes." A hankali tamkar mai tsoron wani abin ta ɗan waro idanun nata waje. Kai tsaye sai saman fuskokinsu ta cikin mirror. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana kallon yanda suka yi wani azababben kyau, haɗin ya yi matuƙar dacewa, chocolate color and white color, abin ba'a magana. "Are you interested?." Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa, kuma ya yi maganar yana ɗaga mata gera ɗaya. Jinjina mishi kai ta yi alamar e, ɗaura hannunsa a saman shafaffen cikinta ya yi yana ɗan shafawa a hankali. Cike da tsokana ta sanya hannu ta shafo kyakkyawan sajensa zuwa wuyansa suna kallon juna ta cikin mirror. Yau dai ta daure tana kallon face nasa, amma ba cikin kwayar idanunsa ba. "Noori." Ta ambaci sunansa. Tsareta da idanu ya yi ba tare da ya amsa ba. "Noori ina ka samo abaya?." Shiru ya ɗan yi na ƴan mintoci kafin ya ɗan juyo da kansa hakan tasa ɗan bakinsa ya kasance a saitin kunnenta. Raɗa ya fara yi mata a kunnen nata a hankali. Kyakkyawan murmushi ta sakar mishi tare da juyowa ta rungume shi da kyau. Yatsa ya sanya mata a cikin dimple nata yana jin tsananin farinciki a tattare da shi. Sumbata ta kai mishi a wuyarsa ita ma tana cikin tsananin farinciki. Maganar da ya gaya mata a kunne ya yi matuƙar sanyata farinciki fiye da tunanin mai tunani. (Ko me ya gaya mata?🤔 Amma muje dai zuwa zata fito fili ne ma muji.) Hannunsa ɗaya ya ɗaura a saman bayanta a in da ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna. Sai sakin murmushi take yi. "Why kike son yin smiling har haka?." Ɗan turo baki ta yi, a wannan karon bata runtse idanunta ba, sai ma ɗaga su sama da ta yi tana jujjuya su. A shagwaɓe ta ce "To Noori murmushin nawa baya yi maka kyau ne na dai'na yi?." Shiru ya ɗan zuba mata idanu kafin ya bata amsa da cewa "Yana yi mini kyau over to over." "To Noori kai ma dan Allah ka yi murmushin ko sau ɗaya ne mana, ban taɓa ganin ko da sunan wasa kayi murmushin ba, tun da nake karama ina kallonka a Tv, fuskarka a ɗaure tamau na santa, har kuma izuwa yau a ɗauren take, ina son in gani ko da sau ɗaya ne kayi murmushin." Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallonta kafin ya amsa mata da "I don't know how to do it, that is the reason why ban taɓa yi ba, even my pleasure yana son nayi, amma i don't know how to do." Shiru ta yi tana ɗan tunani yanda ya furta my pleasure wato Aseef, ashe dama ya iya kiran sunan soyayya, wato shi TRIPLETS nasa kawai ya iya sakawa wannan suna kenan?. Bata san ita ma sunan da yake kiranta ɗin suna ne na musamma ba, shi kaɗai yasan dalilin da yasa ya sanya mata wannan suna haka. "Noori in koya maka yanda ake yi zaka yi mini?." Girgiza mata kai ya yi yana faɗin no. "To why baka son na koya maka?." Ta tambaya kamar zata yi kuka. Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da "Because bazata yi mini kyau ba, smile is for women only, ba zan iya yi ba ko da kin koya mini." "To Noori idan ina son kayi fa?." Ɗan jan kumatunta ya yi yana faɗin "Zaki haɗa har da nawa sai ki rinƙa yi, it's okey ko?." Turo baki tayi tana tunani, kila ita kuma haka ne kaddararta, kila har ta mutu ta koma ga Allah ba zata taɓa ganin murmushi mijin nan nata ba, wato ma ita ce zata yi nashi murmushin? To fuskarsu ɗaya ne? Allah yaya Saif ɗin nan ya iya abu shi ma. Duk wannan zantuka a cikin zuciyarta take yin su. Miƙewa ya yi tare da ita a jikinsa. Hannu tasa ta saƙalo wuyarsa tana kara lafewa a kirjinsa. Yana fitowa sojojin nasa suka sake juya musu baya cikin girmamawa. Tsananin tsoron ganin Rimsha suke yi, dan Mark ya ja musu kunne a kan kallonta, ya gaya musu kanwar oga ce, shi dai bai san cewa matar oga ce ma bakiɗaya ba, dan bai san da batun auren ba, ya dai san ogansa fa ya kamu da sonta, gudun kada ya yi ɓaran ɓarama ne yasa ya ce wa sojojin kanwar oga ne kawai. Sun sha ruwan mamakin jin hakan, amma basu da zaɓin da ya wuce su yi shiru, dan basu isa su tambayi Mark ɗin a kan yaushe oga kuma ya samu kanwa ba? Tun da su dai sun san TRIPLETS su kaɗai Josephine ta haifa, kuma ya za'ayi kanwar ogar ma ta kasance bakar fata kuma ƴar Nigeria? Amma da yake su dai umarni kawai suke bi sai suka yarda a kan kanwar oga ne, shi ne yasa suke mugun bata girma. Kun dai san suma ba yara ba ne, tsab sun fahimci soyayya ce mai zafi tsakanin ogan nasu da ƴar yarinyar nan, hakan tasa suke kara respecting nata fiye da tunanin mai tunani. Saman table chair a cikin bedroom nasu ya sauƙeta, zama ya yi a gefenta saman ɗayan kujerar. Abincin ta fara zuba musu cikin natsuwa. Mikewa ya yi ya ɗauko wayarsa a in da ya turawa driver jirgin nasu sako da su dakata tun da tun ɗazun jirgin yake yi musu alamar sun iso madakata. Dama sojojinsa a tsananin tsorace suke na ganin sun fara haura iyaka kuma Lion ɗin yana sane. Amma bai ce a dakatar da jirgin ba, ba su san yana can yana zuba soyayyarsa bane yasa ya mance ma da sun isa madakatarsu, ga shi ƙasar da suka zo dama sai a hankali, to ace kuma tun daga farkon shiga kasa sun fara karya musu doka? Ai abin ba zai yi musu kyau ba, amma saboda isa irin na Lion sai da ya gama shan love nasa tas sannan na ce su dakata. Bayin Allan suna ganin rayuwa, basu isa su yi komai ba sai da izininsa Allah sarki. In da ya tashi ya dawo ya zauna, ta gama zuba abinci, spoon ya ɗauka ya ɗebo da nufin ya kai bakinsa. Kuka ta saka mishi tana kumbura kumatu irin na shagwaɓa. Fasa kai abincin bakinsa ya yi a in da ya juyo ya tsareta da ido. Gabaɗaya ta zama ƴar rigima yarinyar nan, ya faɗa a ransa. Ganin bai yi magana ba ne yasa ta tsananta kukan nata tana mai turo baki. "Meesha what happened? Why are crying?." "To Noori ba kai ne ba, a gida fa idan kuna cin abinci da su yaya Aseef, sai ka bawa yaya Aseef first spoon naka cikin soyayya da kaunar juna, yanzu kuma ba yaya Aseef shi ne ni ba zaka bani first spoon ɗin naka ba ko? Yanzu fa ni ce yaya Aseef naka tun da baya nan?." Tana magana tana hawaye kamar da gaske. Ɗago hannunsa ya yi a in da ya duba time a jikin diamond watch nasu na TRIPLETS. Jawota jikinsa ya yi yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi, bai yi magana ba sai dai ya ɗan matso mata da spoon ɗin alamar to ta karɓi first spoon ɗin nasa. Cool murmushi ta saki ga wasu guntun hawaye na iya shege a kumatunta. Kaɗan ta karɓi abincin ta bar mishi sauran a spoon ɗin tana faɗin "To kai kuma ka ci wannan." Girgiza kai kawai ya yi tare da kai spoon ɗin bakinsa ya cinye. Lokaci na tafiya ita kuma ta zauna tana zuba mishi shagwaɓa tana kara cinye musu lokacin. Hakan yasa kawai ya fara bata abincin a baki dan su yi sauri, ya lura idan ba haka ya yi mata ba tabbas ba zasu bar cikin jirgin nan da wuri ba. Sai da ya tabbatar ta ƙoshi tap sannan ya kyaleta tare da miƙewa ya ce su je. Kuka ta saka mishi a kan shi ya bai ci abincin ba, rarrashinta ya fara yi tare da ɗaukarta cak ya ɗauki Maltina ɗaya suka nufi waje. Sai zuba mishi shagwaɓa take yi a kan ita dai sai ya ci abinci gaskiya, shi kenan zai zauna da yunwa ko yaya?. Sam bai kulata ba, ya kyaleta tamkar bai san tana yi ba. Sai da suka fito wajen ne ya sauketa tare da riko hannunta, dan yasanta da shegen tsoro, ko a wajen saukarsu ma zata iya bashi matsala. Haka kuwa aka yi, shegen tsoronta yasa ta kasa sauka daga jirgin, dan tana ganin kamar ruwan dake bakin tekun ma yana da zurfi. Girgiza kai ya yi tare da ɗaukarta ya saɓa a saman kafaɗa. Sai da suka sauka ya sauketa yana tunani wai shi kam anya ba horon sojoji zai fara bawa yarinyar nan ba kuwa? Yarinya sai hangen tsoro kamar farar kura. Gaisawa da jami'an bakin ruwa su Mark suka yi. Tsayuwa Mark ya yi yana magana da su, shi kuwa Lion wucewarsa ya yi abinsa rike da hannunta suka nufi wata hanya. Tambayarsu Password da sauransu Jami'an suka fara yi. Sam Mark bai nuna musu kamar suma jami'ai ba ne, kawai ya fitar da password ɗin ya miƙa musu da sauran abubuwan da suka buƙata. Bin Lion da kallon suka yi suna mamakin yanayin jikinsa, ya yi musu kama da GAR na kasar America, basu san cewa shi ɗin ba ne. A takaice dai suka kammala komai da Mark ya zo ya sami su Lion suka wuce zuwa wani waje dake can gefe da tekun. Tamkar gida wajen yake. Basu kai ga karisawa wajen ba ma jibga jibgan motoci har shidda suka nufosu. Mamaki Rimsha take yi na motocin waye kuma waƴan nan, gabaɗaya motocin bakake ne sai kyalli suke yi tamkar sabbi. Dakatawa suka yi da tafiya har sai da motocin suka iso garesu suka yi parking. Buɗe mishi gidan baya na motar tsakiya Mark ya yi yana mai sara mishi. Hannunta ya saki kafin ya nuna mata cikin motar dan ta shiga. Cikin sauri ta shige ta zauna kafin shi ma ya shiga. Kara sara mishi Mark ɗin ya yi tare da rufe kofar motar sannan ya juyo ya nufi motar dake kusa da nasu amma ta baya. Yana ƙoƙarin buɗe kofar motar ne wani kyakkyawan matashin Bature fari kal da shi mai kirar karfi ya fito daga cikin motar. Kyakkyawan gaske ne, Allah mai halitta kamanninsa ɗaya sak da Aseef, kamar an tsaga kara. Shi kansa Mark sai da ya ɗan yi jim yana ganin wannan matashi, ya yi kama da Aseef sosai da sosai. Shiru ya ɗan yi yana karewa matashin kallo. Sai daga baya ya fahimci wannan ya fi Aseef shekaru, kuma shi idanunsa Sapphire blue ne, while na Lion kuma Sky blue, sapphire blue ta fi shiga kala sosai. Duk da cewa Turawa kusan kamanninsu ɗaya dama, amma dai wannan ya yi kama over da Aseef, harta gashin kansu brown color iri ɗaya, idanun ne kawai banbanci sai shekaru da ya fisu. Ɗan rungumo shi matashin ya yi yana faɗin "Michael Trump?." Jinjina mishi kai Mark ya yi alamar e haka ne shi ne Michael Trump. Cike da fara'a ya ce "My name is Alex Trump, nice to meet you my brother." Shiru Mark ya ɗan yi yana jujjuya sunan iyayen nasu, ya ji sunan iri ɗaya ne, dukkansu Trump, Trump kamar abin haɗin baki. Abin da bai sani ba shi ne sunan kakansu ne Trump ɗin hakan tasa aka yawai ta masu irin wannan sunan a family'n, dayawa daga cikin uncles nasa sun yi wa kakan nasu takwara, shi ne yasa shi ma Alex ɗin sunan babansa ya zama Trump. Jin motar da Lion yake ciki sun danna musu horn ne yasa Mark ya ce su shiga ciki sa karisa magana a hanya, sake rungumo shi Alex ɗin ya yi kafin su shige ciki. A tare motocin suka tashi zuwa cikin gari. Sai tambayarsa Alex yake yi a kan ina zasu je ne? Me kuma suka zo yi a kasarsu?. Shiru ya yi bai bashi amsa ba, dan idan baku manta ba shi ma fa Mark kamar gunki yake wajen rashin magana, baya son surutu sam. Haka Alex ya gaji da magana ba amsa ya kyale shi kawai ya zubawa hanya idanu yana kallon in da zasu je ɗin kawai. Ita kuwa Rimsha tun da suka sako kafarsu cikin kasar Russia wani azababben sanyi ya turnuketa. Shi dai Lion ko a jikinsa dama sun saba da sanyi, ita kam bata saba ba sai ta dunkule waje guda abinta. A ɓangaren Jehan da Areef kuwa, wato Nigeria gidan Lion na Kaduna. Tana zaune a bakin bed ɗin nasa har ya shigo cikin bedroom ɗin ya sameta, wajen Aseef ya je dama. Saman bed ɗin ya haye tare da jingina bayansa da jikin headboard na gadon, ɗan Juyowa ta yi tana kallon shi kafin daga bisa ta mayar da kallonta a saman plate ɗin fruits ɗin da ta kawo. Ƙoƙarin kai hannu take yi dan ta ɗauko ruwan ta zuba mishi a cikin glass cup. Ɗan gyaran murya ya yi mata wanda ya sanyata mayar da kallonta kansa. Hannu ya miƙa mata a kan ta bashi nata hannun bari ya gani. Ba musu ta miƙa mishi hannun nata, rikewa ya yi da kyau kafin ya fisgota ta tafi luuu ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa. Kusan a tare suka furta wash. Shi ya furta ne saboda ta buge mishi wajen ciwonsa sosai, ita kuma ta furta ne saboda yanda ya fisgota har wani jiri ta kallah, sai da ta ji hannunta da ya ja ɗin ya yi mata zafi sosai. Ɗaure fuska sosai ta yi tamkar bata san menene murmushi ba. A kule ta ce "Me hakan kuma?." Shiru ya yi mata bai tanka ta ba, sai ma kara matseta da ya yi a jikin nasa yana sauke numfashi a hankali. Ƙoƙarin kwace kanta ta yi dan ta bar ɗakin. Amma ina ta kasa saboda ya riketa da hannu ɗaya da kyau. "Please ka sakeni bana so, ni ba yar iska ba ce, dan haka ka sake ni wlh ko kuma nayi maka ihun kwarto." Leƙo face nata ya yi yana kallon yanda take magana with her full confidence kuma cikin masifa. "Zaki iya yi mini ihu ne?." Ya faɗa a sanyaye. "Me zai hana in dai baka sake ni ba." "Tom shikenan ɗan yi ihun bari naji, kinga daga nan sai na danneki a ɗakin nan babu mai kwatarki, kin dai san ko kin yi ihu ma uncle ba zai ji ba, dan yana sama, su kuma sojojin da suke kasa ba ruwansu da ihunki, haka zalika su daddy da su John, dan haka kina yi zan danneki a cikin ɗakin nan sai nayi miki hot kiss son rai'na, dama kin san na gaya miki ina son nayi kissing naki ko? To ki yi ihu zaki ga abin da zan yi miki yau Allah kuwa, ina ga sai na baki baby a yau ɗin nan." Zaro idanu waje ta yi, ta san halinsa sarai, tsab wlh zai aikata duk abin da ya faɗa, ƙaramin aikinsa ne ya danneta ɗin ya yi abin da yake so kamar yanda ya ce, rufin asirinta kawai ta bishi a hankali su rabu lafiya, ko ta yi ihu ta bakin nasa a banza ne, dan babu mai shigo mishi ɗaki ba tare da izininsa ba sai TRIPLETS nasa, to kuma Lion baya nan, shi kuma Aseef yana tare da matarsa suna aikin da suka saba, wato shagwaɓa wa junansu, dan haka bama zai bar matarsa ya zo dan ya ji ihunta ba. Ganin ta yi shiru tana tunani ne yasa ya ɗan matso da bakinsa kusa da kunnenta, can kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "Ko dai idan nayi miki fyaɗen na baki baby zaki yanke mini bananata kamar yanda kika yi wa wancan kazamin mutun ne?." Jinjina mishi kai ta yi tare da kara ɗaure fuska tana faɗin "Sosaima, me zai hana na yanke?." Cool murmushi ya saki tare da miƙewa ya kwanta da ita. Cikin salo ya juya da ita a in da ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa. Kasa kasa ya ce "To bari na gwada yi miki fyaɗen sai kema ki gwada yanke mini mu gani, amma fa ni nawa ba irin na wancan kazamin mutumi da kika yanke bane, shi ai ya tsufa ni kuma ban tsufa ba, matashi ne ni mai jini a jika, kuma jarumin gaske, dan haka sai kin samo wuka mai kaifi sosai kafin ki iya yanke mini nawa." Dama an ce duk iskancinka akwai ubanka a iyawa, to ita dai Jehan ga ubanta a iya shege ta gani, dan haka sai ta nemi sulhu kawai dan su gyarota ta samu ta bar ɗakinsa ba tare da wata hayaniya ba, ta san wlh tsab zai iya aikata duk abin da ya ce, ba ƙaramin aikinsa bane ya mai da ita cikakkiyar mace a yanzun nan. Karo na farko a rayuwarta da ta fara bawa wani hakuri ta kuma yi magana cikin girmamawa da ladabi. "Dan Allah kayi hakuri, ba bazan iya ganin naka bama bare na yanke, ni dai please ka kyaleni na tafi ka ji my boyfriend?." "Are you sure am your boyfriend?." Ya yi maganar yana ɗaga mata gera ɗaya. Jinjina mishi kai ta yi alamar tabbatarwa. "Okey give me a hot kiss first." Turo baki ta yi cikin natsuwa ta ce "No mu a nan yin hakan haramun ne, ka bari tukun nan sai gaba." "Gaba yaushe kenan?." Shiru ta yi tana tunanin wani irin wayo kuma zata yi mishi again...... Kai jama'a wai wayo Jenan zata yi wa Areef. Innalillahi gaskiya Jehan baki san waye Areef ba ne shiyasa zaki ce zaki yi mishi wayo, tab yo ai ko daddynki ba zai ce zai yi mishi wayo ba bare ke, duba ga irin yanayin rayuwar da ya yi, ya zauna da mutane daban daban, ba abin da bai sani ba sai dai ya nuna bai sani ɗin ba. "Amsa me, gaba yaushe kenan?" Ya katse mata tunanin da take yi. Ɗago idanu ta yi tana kallon face nasa kafin ta ce "Gaba idan muka yi aure." Ɗan zaro idanu waje ya yi kafin ya ce "Aure? Are you sure zaki aureni?." Jinjina mishi kai ta yi alamar e, ita dai burinta kawai ya saketa ta samu ta gudu ta bar mishi ɗakin, a tunaninta idan ta ce zata aure shi ta yi mishi wayon da hakan zai sa ya kyaleta tun da dama ya jima yana cewa ta yarda ta aure shi. Rashin sani yafi dare duhu, bata ma san already ai ita mallakinsa ba ne. Shi kuma yanayi mata irin hakan ne dan ta koyi girmama na gaba da ita, ta kuma koyi bawa wanda ta yi wa laifi hakuri, ga shi dai yau a dalilinsa ta bada hakuri, abin da bata taɓa yi ba, kuma ta yi magana cikin girmamawa, dama hakan yake so, komai cikin dabara yake koya mata, ba hayaniya ba ɓacin rai. Kara matso da face nasa ya yi daf da tata sosai yana sakin cool murmushi kafin ya fara magana, duk abin da take yi da abin da take gaya mishi ya san ina ta dosa, ya san da cewa idan an barta wai wayo take son yi mishi, amma sai ya nuna mata bai san komai ba, da yake shi ma ɗan duniya ne. "Amma kina so na ne da kika yarda zaki aure ni? Or you wanted to play with my heart?." Yana magana yana kara matso da face nasa kusa da face nata sosai. Tsabar tsorata na ganin yanda ya matso kusa da ita sosai har suna iya jiyo numfashin juna, yasa har wani in'ina ta fara yi, maganarta na rarrabewa. Kun san dai babu wani namijin da ya taɓa gigin kwatanta yi mata abin da ya yi mata yanzu, dole ma Maganar tata taki fita straight. "E... A'a... Dama........... ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 *KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*. *KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ ❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋) *Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581* E80 Tsabar tsorata na ganin yanda ya matso kusa da ita sosai har suna iya jiyo numfashin juna, yasa har wani in'ina ta fara yi, maganarta na rarrabewa. Kun san dai babu wani namijin da ya taɓa gigin kwatanta yi mata abin da ya yi mata a yanzu, dole ma Maganar tata taki fita straight. "E... A'a... Dama... na ji ina sonka.... Sonka ɗin ne ji.......". Yatsa ɗaya ya ɗaura mata a saman lips nata jin yanda take ta zuba mishi magana wani a saman wani, sam bai ma gane me take faɗa ba. "Calm down, ki natsu ki yi magana, ni ai yanzu ban fara yi miki komai ba tukun nan, ba kin ce zaki aure ni ba?". Da sauri ta jinjina mishi kai tana kara tsuke fuska alamar tsantsar tsoronsa ya bayyana a saman face ɗin tata. "Okey ai tun da zaki aure ni ba zan yi miki komai ba, yanzu dai saki jikin ki sai ki yi mini magana a nutse ko?." Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "To dan Allah ka bari na koma koda saman bedside drawer ne sai muyi magana kaji ko?." Sumbatar kumatunta ya yi yana mai kara jin tsantsar kaunarta har cikin karkashin zuciyarsa. "Jehan you are so beautiful, i don't know the reason why duk time da na kalleki am feeling like in ɗaukeki cancak in sanya ki a cikin zuciyata, so that ki kalli irin tsantsar kaunarki da yake ciki, amma i don't why kike bani headache, i ask you several times a kan ki gaya mini season da ya sanya baki so na, amma you refuse to tell me, a koda yaushe kina kawo mini bad season wanda ke da kanki you know i can't accept it, saboda all season da kike kawowa, ba wan da hankali zai kama ba ne, yanzu ina son ki gaya mini menene matsalarki?." Hakika kalamansa sun ratsa ziciyarta sosai, ya iya magana a nutse wanda ko baka so sai ta ratsa maka can cikin zuciyarka. A nutse ta fara magana. "Ni kawai bana son rabuwa da daddy na ne." "That is the only reason?." Jinjina mishi kai ta yi alamar e. "Okey tom shikenan i will do something about it, yanzu dai ba wannan ba, kinga yau saura kwana uku mu gama game ko?". Jinjina mishi kai tayi alamar e. "Okey to zaki rakani unguwa please?." Ɗan turo baki ta yi tana girgiza kai alamar a'a bazata je ba. Why ya tambaya. "Nothing kawai ba zan je ba ne." "Even wajen duba mum zanje?." Zaro idanu waje ta yi tana faɗin "A'a zanje nan kam." Cool murmushi ya saki kafin ya sake cewa "I really like your lips and your eyes, kai i like everything about you, because you are special." "Same here, i like your attitude, you are a very very good person, you have a gold heart, beautiful life, like the way my dad said." Ta kai karshen maganar cikin sanyayyar murya. "Really?." Ya tambaya da mamaki a kan face nasa. Bai taɓa tunanin zata ce mishi mutumin kirki ba, akoda yaushe ya ɗauka kallon ɗan iska take yi mishi kamar yanda ta faro tun daga farko. "Yeah you're a good person, most a time daddy bashi da wani magana idan ba naka ba, hakan ce tasa nima na yardanwa kaina you are a special, daddy baya zama da kowa, before shi ko friend bai da shi, mum da Gwaggo sune friend nasa, sai ni da Rimsha, uncle Shitu PA sa ne, kuma yayan mum, sam daddy baya da yawan surutu, haka kuma baya yarda da mutane, amma i was surprised lokacin da naji yana yawan maganarka." Shiru ya zuba mata idanu har sai da ta kai karshen maganar tata. Nisawa ya yi yana ƙoƙarin yin magana suka ji hayaniya a palon kasan. Ɗan kai kallonsa bakin kofar shigowa ya yi tare da sake dawo da kallonsa kanta. Zaro idanu ita ma ta yi tana jin surutan da ake yi a palon, tamkar faɗa suke yi. "Muje ko baby? Muje muga suwaye ne." Ya faɗa tare da manna mata sumbata a kumatu, sannan ya mike daga rumfar da ya yi mata. Cikin hanzari ita ma ta miƙe ta sauko kasa. Ta riga shi fita wajen dan tsabar saurin ta je ta ga menene, shi kuma ya tsaya sai da ya sha ruwan da ta kawo mishi. Tana fitowa suka yi 4 eyes da mai irin face ɗin Lion kuma irin idanun Areef ɗan diramarta. Wani irin mummunar faɗuwar gaba ta ji, da farko ma ta ɗauka Lion ɗin ne, sai da ta kalli idanuwansa sannan ta gane wannan fa ash eyes gare shi ba blue ba. Asbunallahu wani'imal wakil ta furta a ranta jin yanda gabanta ya yi mummunar faɗuwa da ganinsa. Gabaɗaya family sun yi cirko cirko suna tsaye, Aseef na rungume da Akila dake ta faman kwallah, ita ma ta kankame shi gam. Yanzun nan dirowar TGA cikin gidan kenan, yana shigowa palo ya cikaro da Aseef da Akila suna cin abinci, shi ne fa ya ce lallai sai Akila ta bar gidan dan baya son ganin bakar fata, to diramar da ake yi kenan, kuma kun san TGA renon Lion ne, sam bashi da sauki, bashi da imani bare tausayi, bashi da mutunci. Yanzu da za'a barshi tsab zai kashe Akila har lahira a wajen nan. Shi kuma Aseef ya rungume matarsa ya ce wlh babu in da zata je, dan ita ce farincikinsa, in dai zata bar gidan, to fa tare zasu tafi da shi gabaɗaya, zasu bar musu gidan, dan duk wanda ya ce baya son Akila a cikinsu, to shi ma kawai suce basu son shi, domin shi da ita babu banbanci, matarsa ce kuma yana son kayansa!!. Babbar magana, yau ake yinta. Jin motsin fitowar Jehan yasa gabaɗaya suka dawo da kallonsu a kanta. Zaro idanu waje TGA ɗin ya yi yana mai kare mata kallo. "Okey wato bama mutun ɗaya bane, akwai wata ma kenan? Wai su waye ne waƴan nan ƙazaman?!!." Cewar TGAn, kuma ya yi maganar cikin tsawa. Ba ƙaramin tsorata Jehan ta yi ba, dan taga basu da wani banbanci da Lion, duk jirgi ɗaya ya kwasosu a iya ɗaure fusataccen fuskar nan tasu. Jikinta har kerma ya fara yi, da sauri ta juya dan ta gudu ta koma ɗakin Areef ɗinta, duk tsiya shi dai ya fi mata. Tana juyowa suka yi karo dan yanzu ya fito ya tsaya a bayanta bata sani ba. Ɗan baya kaɗan ta yi kamar zata faɗi. Rikota ya yi tare da jawota jikinsa yana ɗaure fuska sosai. "James who are those dirty peoples?." Cewar TGA. Nisawa ya yi kafin ya ce "Michael ɗauki matarka ku koma ɗaki." Ajiyar zuciya ya sauke tare da raba jikinsu yana ƙoƙarin kamo hannunta. Wani irin mahaukacin tsawa TGA ɗin ya daka musu wanda ya sanya Aseef ɗin dakatawa ba shiri. "Babu in da wannan kazama zata bi Michael, barin gidan nan zata yi." Rai a tsananin ɓace Areef ya fara magana tare da sakin Jehan ɗin yana karisowa kusa da TGA ɗin. "Uncle T wai in tambayeku mana? Me Michael ya yi muku ne a duniyar nan da bazaku barshi ya huta ba? Me ya yi muku? Duk wani bala'i idan kuka ɗebo a kansa kuke fara saukewa, ku barshi ya huta haka mana, okey ko so kuke ya koma gidan jiya ko? So kuke sai damuwa da ɓacin rai ya yi mishi yawa a cikin kwakwalwarsa ya sake rikiɗewa ya zama muku irin Michael da kuka sani a baya ko? Meyasa baku son zaman lafiya ne? To wannan dai matarsa ce, kuma duk gidan nan banga uban da ya isa ya rabasu ba, idan kuma ka ce ba haka ba to ka rabasu bari na gani!!." Gabaɗaya palon sun yi tsit suna sauraron wannan bala'in, wannan abin da taɓa zuciya yake, bawan Allah Aseef, shi suka rai'na, duk wani iskanci a kansa suke fara saukewa, dan kawai sun ga yanzu ya tashi daga Michael ya koma Aseef, ya zama so silent, ai da a baya ne ko giyan wake suka sha basu isa su kawo mishi wargi ba, yanzun nan zai aika mutun a in da baa dawowa. Readers kuma shaidu ne, kun san halinsa na baya ai, baya ɗaukar wargi. "James ni kake gayawa magana haka?." Cikin tsawa ya ce "Uncle T na gaya maka, kuma ba iya magana ba in dai ka matsa a kan batun matar Michael to sai na yi maka abin da sai kayi dana sanin sani na, Michael shi ne rayuwarmu kuma farincikinmu, duk abin da ya taɓa shi to mu ukun dukka ya taɓa, dan haka ya isa ɗaga mishi hankali da kuke yi, ku zaɓa ɗaya cikin biyu, ko dai ku kyale shi ya zauna cikin farinciki da zabin zuciyarsa, ko kuma duk wanda ya ɗaga mishi hankali ni kuma zan hana shi barci, dama kwanciyar hankali bakiɗaya!!." Yau fa an kure hakurin Areef, duk cikin palon ba wanda bai tsorata ba na ganin yanda ya rikiɗe yake magana cikin zafin rai tamkar Lion, dama mai hakuri bai iya faɗa ba. Daddynsu ne ya katse su da cewa "General is okey, James please ku je bedroom naku, my heartbeat ɗauki matar taka ku tafi bedroom naku kaji? Don't feel bad my son ka ji ko?." TGA zai yi magana daddyn ya ɗaga mishi hannu yana faɗin "General it's not a joke, it's a command!!." Yan da daddy ya yi maganar cikin tsawa ne yasa TGA ɗin hakura ya haɗiye maganar da yake son yi. Cikin fushi ya wuce fuuuu zuwa sama. Kallon Aseef daddyn nasu ya yi yana mai sake ce mishi su wuce bedroom nasu. Okey ya amsa tare da riko hannun Akilar suka wuce. Bayan sun tafi ne daddyn ya dawo da kallonsa a kan Areef yana faɗin "Ina son ku sanya Michael farinciki a koda yaushe, because this two days an ɓata mishi rai over, kuma bana son hakan, na san cewa da kai da Romeo kune zaku fi kowa sanya shi farinciki, so ina da bukatar hakan daga wajenku." Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya koma bedroom nasa. Su uncle Herry suka rufa mishi baya, daddyn Rimsha ma komawa nasa bedroom ɗin ya yi yana mamakin hali irin nasu. Dawo da kallonsa kan Jehan dake tsaye a bayansa ta bakin kofar bedroom nasa Areef ya yi. Tsantsar tsoro ne a bayyane a kan face nata, yau dai taga bala'i, dama haka Areef ɗin yake da iya faɗa? Ta tambayi kanta, ita ai ganin shiru shiru take yi mishi, bata taɓa tunanin ya iya faɗa har haka ba, ji yanda yake magana da uncle T kamar wani ɗansa, cikin faɗa da nuna tsantar isa da izza, nan take wani azababben tsoronsa ya sake kamata, ta kara shan jinin jikinta. Har ya ƙariso in da take ba tare da ta sani ba, ta luluka can duniyar tunani. Sai da ta jita a saman kirjinsa sannan ta farga ashe ya iso gareta. Shiru ta kwanta a jikin nasa saboda dukan uku uku da kirjin nata yake yi, har ga Allah ta tsorata da ganin uncle T ga kuma bala'in da suka yi da Areef. A wannan karon dai bata yi ƙoƙarin kwace kanta ba, sai ma kwanciya da ta yi tana mai da numfashi, kafafunta gabaɗaya sun yi mata nauyi, dan fa a gaskiya sai mai karfin zuciya ne zai iya kallon Lion da TGA suna faɗa a waje, idan kana wajen to kana iya suma dan faɗarsu bashi da kyan gani ko miskala zarratin, yanzu zasu aika mutun in da ba'a dawowa idan aka yi wargi. Areef bawan Allah akwai saurin fahimta, ya fahimci ta tsorata sosai ne yasa ya rungumeta, dan ta ɗan sami natsuwa, jinjina mata a cikin zuciyarsa ma yake yi da har ta iya tsayuwa ta kalli bala'in TGA, ta yi ƙoƙari sosai. Sai da ya ji ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya ne sannan ya saketa tare da riko hannunta suka koma cikin bedroom ɗin yana faɗin ta zo suje su sha fruits a tare. Sam bata yi mishi musu ba saboda har lokacin bata gama warwarewa ba. A tare suka jera zuwa cikin ɗakin. A ɓangaren Aseef da Akila kuwa. Bayan sun shiga cikin bedroom nasu, saman bed ya zaunar da ita tare da zama a gefenta dan ya rarrasheta. Baiwar Allah tana ganin rayuwa a wajen waƴan nan masu jajayen kunnuwa, su kuma nasu kaddarar kenan, matsalar dangin miji, duk TGA yasa ta fita a hayyacinta, gabaɗaya surutan ma da ya rinƙa yi bata jinsa, tun da ya daka mata tsawa ta farko lokacin da ya shigo cikin palon, daga nan ta faɗa rashin hayyacinta na wucin gadin. "My heartbeat dan Allah ki dai'na wannan kukan kinji ko? Ba dai kina so na ba?." Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e tana son shi. "To shikenan it's okey, ki kwantar da hankalinki, da ni kaɗai zaki zauna ba da su ba, dan haka babu ruwanki da su kin ji ko?." Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "My shagwaɓati yanzu idan suka rabani da kai fa? Kaga kowa naka ya ce baya sona, ina tsoron su rabamu ne, seriously ba zan iya rayuwa babu kai ba." Baiwar Allah tana magana hawaye zafafe suna bin kuncinta. Matsowa ya yi a in da ya rungumota sosai a saman kirjinsa. Murya cikin sigar rarrashi ya fara magana yana ɗan shafa bayanta a hankali hankali zuwa kasa. "My heartbeat, babu wanda zai rabamu da izinin Allah, ke tawa ce kamar yanda nake naki ke kaɗai, har mu mutu babu rabuwa, ki dai'na damuwa kinji matata farincikina?." Hannu tasa tare da rungumo shi da kyau, a hankali ta kara shigewa jikinsa tana faɗin "Tom shikenan my shagwaɓatina." Cikin zolaya muryarsa ɗauke da zallar madarar shagwaɓa ya ce "Kina tsoron rasa fine guy ko?." Turo baki ta yi tana faɗin "Kafara ko?." "A'a ni ban fara komai ba, kawai gaskiya na faɗa, kina tsoron rasa kyakkyawa babyn daddynsa kuma pleasure TRIPLETS ko?." Dukan wasa ta fara kai mishi a kirji nasa tana faɗin "Mun ɓata da kai tun da sharri zaka yi mini." Ta kai karshen maganar tana kokarin miƙewa daga jikin nasa. A hanzarce ya rikota yana mai kara matseta a jikin nasa. "Am so so sorryyyyyyyy sarkin rigimata, na tuba." Ɗago kanta ta yi tare da kama kunnensa ta ja da karfi. Ƴar kara ya saki yana ɗan turo baki. "Allah ba zan kyaleki ba, kawai dan kinga kunena yafi naki kyau ko? Shi ne zaki cire mini shi?." Ya kai karshen maganar tare da karisa haurawa saman bed ɗin. Yana hawa ya jawota jikin nasa. A tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya, juyowa ya yi tare da yi mata rumfa da kirjinsa. A shagwaɓe ta ce "Za ka fara ko?." "Kayanki ne ko nawa?." Ya bata amsa shi ma a shagwaɓe. "A'a kayanka ne ranka ya dade." Hararar soyayya ya wurga mata kafin ya kai hannunsa izuwa saman breast nata. A hankali ya lumshe idanunsa saboda wani daɗin da yaji ta mamaye shi. "My rigimati wai yaushe zaki barni nayi dis virgin naki ne? Ni fa ina son karɓar kayana." Kukan shagwaɓa ta saka mishi tana faɗin "Ni to ka bari na huta mana? Wai ma yaushe aka yi auren ne? Ban gama hutawa daga gajiyar biki ba, sai ga kuma gajiyar ciwo, yau fa kwanana biyu da tashi daga ciwo, to ka bari sai na huta." Kuka ya saka mata a kan shi Allah bai yarda ba, yana son yaga yana shiga jikinta sosai. Sanin halin kayanta yasa ta shige jikinsa sosai ta fara rarrashin shi. Akila sai Aseef, Aseef sai AKila, ba mai iya su sai junansu, haka zasu zauna suyi ta zubawa juna shagwaɓa kamar me, abin gwanin burgewa. A kunne ya raɗa mata to ya hakura, amma next week yana son su je wajen Ammie su gaishe ta. Da murna ta ƙanƙame shi sosai tana zuba mishi godiya. Tureta ya yi tare da miƙewa zaune ya bata baya yana faɗin "Kafin mu yi aure ma kin fi so, kin fi bani kulawa, yanzu dan nace zamu je wajen Ammie ji yanda kika rikeni sosai, amma idan ba haka ba sai ki ce kina jin kunyata, ko fa wanka baki yarda mu yi tare, kuma ke kika yi mini alkawarin idan muka yi aure zaki yi mini soyayya sosai." Cikin shagwaɓa ya yi maganar tasa. Matsowa ta yi a in da ta kwantar da kanta a saman bayansa tare da zuro hannayenta ta saman cikinsa. Murya a sanyaye ɗauke da shagwaɓa ta fara magana. "Kayi hakuri kaji my shagwaɓatina, nayi alkawarin ba zan sake ba, komai kake so zanyi maka, ba zan sake cewa ina jin kunya ba, zan kula da kai sosai." "Are you sure?." Ya yi maganar ba tare da ya juyo gareta ba. "Yes my heartbeat, kai ne fa bugun zuciyata kuma bugun zuciyar kowa dake gidan nan, please ka dai'na ɓata rai, na san idan ka ɓata rai yaya Saif da yaya Areef ma zasu ji hakan a jikinsu." Turo ɗan red lips nasan nan ya yi tare da juyowa ya mannata da kirjinsa. A hankali ya fara shafa bayanta yana faɗin "Tom shikenan na dai'na ɓata rai, me zaki bani yau?." "Me kake so?." Shiru ya ɗan yi kafin ya matso da bakinsa dai'dai saitin kunnenta. Can kasa kasa ya furta "Abin daɗi." Lulukawa duniyar tunanin menene kuma abin daɗi ta yi. Matsowa da bakinsa ya yi zuwa saman kumatunta, sumbatarta ya yi yana faɗin "Sarkin tunani ba, har yanzu baki dai'na tunanin ba kenan? Ni ba sai kin tuna menene abin daɗi ba, in anjuma ya yi da kai'na zan ɗauki kayana, yanzu dai tashi muje ki karisa cin abincinki.". Zaro idanu waje ta yi, a tsananin tsorace ta ce "A'a ni ina tsoron uncle T, nama ƙoshi da abincin." Cikin nuna ko in kula ya ce "Ki dai'na tsoron Uncle T fa, dan wlh ina ga miki bashi da hankali ne, ni ko ba'a gaya mini ba nasan uncle T ɗin nan Roshan kakansu ya gado, mutun sai bakar bala'in tsiya, to ko Lion yanzu da ya musulunta ya rage faɗa, amma shi uncle T kamar busar shaiɗan ake yi mishi a kai, Allah ni nasan wannan Roshan ɗin ne ya ɓatasu, dan naji ance shi ma Roshan ɗin a lokacin shi sam baya ɗaga kafa, dan haka ke ai ba ruwanki da uncle T." Shiru ta ɗan yi kafin ta sake fara magana cikin natsuwa da kuma sigar da zai fahimceta cikin sauki. "My heartbeat kana ji ko? Please ka dai'na cewa uncle T haka kaji? Duba yanayinsa zaka yi, bashi da wani laifi duba da irin tasowan da suka yi kenan, a addinin musulunci komai lalacewan uncle T a matsayin daddynka yake tun da kanin daddyn ne, baku da wanda ya fishi, idan har baka son uncle T to zai zama daddy ba zai taɓa jin daɗi ba, dan shi ma yana son ƴan uwan nasa, kaga yanzu misali duk yanda kake sona idan nace bana son su yaya Saif zaka zauna da Ni?." Girgiza mata kai ya yi yana faɗin "A'a ba zan zauna da kema koda kuwa zan mutu idan kika tafi, to gara na mutu da na zauna da wanda bata son TRIPLETS nawa." "Good, to ka sani shi ma daddy haka yake son uncle T kamar yanda kuke son junanku, jini ɗaya ba wasa ba, uwa ɗaya uba ɗaya ba wasa ba, ina da tabbacin daddy yana matuƙar son uncle T, kuma shi ma uncle T ɗin yana matukar kaunar daddyn, duba ga irin yanda ya girmama daddyn ɗazun, kaga umarni daddyn ya bashi a kan ya yi shiru, amma haka ya yi shirun ba dan yana so ba, hakan zai tabbatar maka da yana son yayan nasa kuma yana jin maganarsa komai wuya komai daɗi, baka ganin kullum daddyn da uncle Herry suna tare ne?." Jinjina mata kai ya yi alamar e kullum suna tare. "To ai saboda yana sonsu ne bashi da biyunsu a duniya yasa kullum yake tare da su, in dai kuka yi wa Uncle T or uncle Herry abu, to ku sani tamkar daddy kuka yi wa, dan sai ya fisu shiga bakinciki, sai dai kawai ba zai nuna muku bane." A wannan gaɓar sai ta yi amfani da ilimi, bata ce mishi daddy ba zai nuna musu ɓacin ransa bane dan yasan irin tarbiyar da ya basu tsab zasu iya hayayyako mishi ba, sai bata ce hakan ba, duk da a zamanta da su ta lura da hakan, ta lura tun farko daddyn ne ya tabbaka babban kuskuren da ba zai taɓa gyaruwa ba, dan mawuyacin abune yanda suka girman a hakan nan ya sake cewa zai iya juya su, ina ba zai yiwu ba, bare ma da suka yi aure yanzu, ai shi dai daddy sai dai kawai muce Allah ya bashi jikoki masu jin maganarsa da bin umarninnsa, ƴaƴa kam sai dai hakuri ya ɓata komai da kansa tun farko. Rungume sosai ya yi yana mai kara jin kaunarta a ransa, a koda yaushe tana kara mishi ilimi dan gane da addinin musulunci, wannan shi ne amfanin ka auri mace mai ilimi, ko baka mori ilimin nata ba, ƴaƴanka zasu mora. Shi dama ina ya wani san cewa da daddynsa da uncle T duk ɗaya ne, ai shi kawai daddynsa shi ne mutun tun da shi ne ya haife shi, amma yanzu ta fahimtar da shi kuma ya gane ya kuma ji daɗi. "To muje ki karisa cin abinci ko, sai kizo ki kira our Queen, tun jiya fa take ta kiranki a waya, ta yi miki miss call sosai lokacin da bamu da lafiya, daga karshe ina rokan Allah daya sauke miki ni'imarsa mara adadi a tattare da ke my heartbeat kuma my rigimati". Ɗago kai ta yi suna fuskantar juna. "To haka zamu tafi baka bani hot kiss ba?." Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da kara rungumeta sosai, dama abin da yake so kenan, rakinta yasa bai ce zai yi mata ba, yanzu idan ya ce zai yi mata sai ta tsaya ta yi ta raki, amma Alhadulillah tun da ita ta ce da bakinta ya yi mata, sai ya kwanta da ita a jikinsa kafin ya fara kissing ɗin nata. Yau dai sam bata ji kunyarsa ba kamar yanda ta ce mishi ba zata sake cewa tana jin kunyan nasa ba, haka kuwa aka yi, fara taya shi kiss ɗin ta yi tare da rungume shi sosai. Wani irin azababben daɗi ya ji na musamman, tun da suka yi aure sai yau ta bashi goyon bayan ɗari bisa dari. Hannu yasa ya fara wasa da breast nata dake matuƙar burge shi amma tana yi mishi rowa, to yau dai ta bashi, da kanta ma take taya shi ta hanyar gaya mishi kalamai masu daɗi. Romancing nata ya fara yi babu kama hannun yaro, haka ita ma ta zage dan kada ya kureta, amma sai dai ina ba zata haɗa kanta da shi ba, dan sufa zallar madarar soyayya wanda babu mix ko ɗigo a jininsu yake, gadon shi suka yi, kawai dan dai a yanayin yanda suka taso ne yasa basu ma sha'awar soyayyar, da ace mummynsu na tare da su, ai da dukkansu manyan ƴan soyayya ta duniya zasu zama, duba da irin soyayyar da daddynsu ya zuba lokacin yana saurayi, tamkar zasu cinye juna da mum ɗin tasu, lokaci guda kuma sai Allah ne kaɗai yasan me ya rabasu, sanadiyar hakan daddyn ya fara shan wine (giya) dan ya rage takaicin rabuwa da suka yi, hakan har ta yi mishi mummunar illah, bugu da kari kowa yasan dama su Turawa ai mayun love ne, bautawa soyayya suke na wuce misali. Tun tana ƙoƙarin kure shi har ta kasa ta hakura ta lafe a jikinsa shiru tana karɓar saƙon da yake aika mata, ita ma dai saura kaɗan ta suma ba iya Rimsha kawai ba, ita Rimsha ma ai dan mai sauki Lion ya yi mata, kada ku manta bai cika son wasa da ita ba, yana yin komai a hankali kaɗan kaɗan da taka tsantsan, amma a hakan ma sai da ta suma, ina ga kuma ya saki jiki ya yi wasa da ita son ransa?. To ita ma Akila kusan hakan suka kare da Aseef, har sai da ta yi mishi kukan daɗi, ya kiɗimata over, dama goyon bayanta ne da bai samu ba yasa yake ɗaga mata kafa dan baya son yi mata abin da bata so, amma yanzu ai sai ya sanyata suma saboda daɗi. Da kyar ya hakura ya kyaleta ba dan ya so ba, sai dan kukan da take yi mishi. Kwanciya ya yi da ita a jikinsa yana shafa bayanta alamar rarrashi yana kuma mai da numfashi. Akila manya ita da ta ce zata sanya shi kuka sai ga shi daga wasan farko ita ta yi kukan. Sai rarrashinta yake yi yana gaya mata kalamai masu ratsa zuciya, da haka har barci ya ɗauketa lafe a kirjinsa. Ganin ta yi barci ne yasa ya shafi kumatunta yana faɗin "Ƴar rigima kawai, idan baki yi mini rigima ba sam baki jin daɗi na lura." Ya kai karshen maganar tare da gyara mata kwanciya da kyau da kyau shi ma ya lumshe idanunsa alamar barcin zai yi............. Rigimati da shagwaɓati sai Allah, suna tsantsar kaunar junansu, soyayyarsu mai tsabta ce, suna matukar girmama duk abinda ɗayansu yake so, bugu da kari suna girmama juna sosai, ga kula da addini da kuma mutunta ƴan uwan juna, da nuna musu soyayya. Ba abin da zamu ce sai dai Allah ya bar su tare cikin Kaunar juna da farinciki. A ɓangaren kasar Russia kuwa. Ganin yanda ta takure jikinta waje guda tana rawan sanyi ne yasa Lion ya jawota jikinsa, ga shi ko jacket bai saka ba bare ya rufeta da shi. Ba tare da ya kallin driver dake tukasu ba ya ce da shi ya kashe Ac'n motar. A hanzarce ya kasheta. Ko da aka kashe bata dai'na kermar sanyi ba, ɗaukanta ya yi cancak ya dawo da ita saman cinyarsa dan ta sami damar shiga jikinsa sosai ko sanyin jikin nata zai ragu. Shi dai bodyguard dake tukasu ɗin sai satar kallonsu yake yi ta cikin mirror, sun yi matuƙar burge shi, a tunaninsa ma yaya da kanwarsa ce, duk da ya kalleta chocolate color, bai yi amfani da kalar fatarta ba, dan akwai black Americans ai, kawai sai ya yi amfani da kyan da Allah ya yi mata ya haɗasu suka zama yaya da kanwa, kwata kwata bai kawo cewa mata da miji bane, dan yanda ya ganta yar karama, ko kusa ko alama bai ma kawo mata aure kusa ba, a nasa tunanin ma bata wuce 11 years ba, dama kunsan su kamar Rimsha dai gaskiya yarinya ce sosai a wajensu, idan ana maganar aurema ko kusan kiran irinsu Akila ma baza'a yi ba bare Rimsha. Meesha, ya ambaci sunanta. Kasa kasa ta amsa mishi da na'am, "Are you okey now?." Turo baki ta yi tana girgiza mishi kai alamar a'a. Shafa bayanta ya yi yana mamakin halinta irin na Aseef. Allah sarki Aseef ne yake yi musu wannan tsiya, idan bashi da lafiya suka yi treating nasa, idan sun tambaye shi are you okey? Sai ya ce musu no, ba ya taɓa ce musu ya ji sauki, kullum no yake ce musu, da farko sai su ɗaga hankalinsu su yi ta sake duba shi, amma daga baya da suka gane tsagen iya shege ne da zallar madarar shagwaɓa sai kawai su kyale shi, kuma har gobe idan bai da lafiya suka tambaye shi ya ji sauki zai ce musu no, shi bai ji saukin komai, idan ma suka yi sa'a bai haɗa musu da kuka ba. To ita ma Rimsha shi ne take yi mishi yau, wai no, ta tuna mishi Aseef, dayawa daga cikin ɗabi'unta irin na Aseef ɗin ne, shi ne yasa a duk lokacin da yake tare da ita baya kewarsu sosai. Tuna cewa irin halin Aseef kenan sai ya kyaleta ita da no ɗin nata. Cikin girmamawa bodyguard dake tukasu ya tambaye shi yanzu kuma sai wani hanya zasu bi?. A takaice ya yi mishi bayani, karawa motar gudu ya yi a in da cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gidansu Na'urat ɗin. Shiru bodyguard ɗin ya yi yana mamakin dama gidansu za su kenan? Dama bakinsu ne kenan?. Toh fah!!. Gida ne mai matuƙar girman gaske, ina da tabbacin yana daga cikin manya manyan gidajen da ake ji da su a kasar, hawa huɗu ne suma gidan nasu tamkar gidan Lion na Washington DC , sai dai gidan Lion ya fi nasu girma nesa ba kusa ba. Wasu jibga jibgan bodyguards fararen Turawa tas da su ne suke shawagi a cikin harabar gidan. Ko'ina ka kai kallonka sai ka ga farin Baturen bodyguard yana kewaye a wajen, dukka bodyguards ɗin suna sanye cikin suit bakake tare da takalma cover baka, hand gloves baki, kowannansu da akwai face mask baki da black glass a face nasu, gabadayansu babu mai fuskar alamar dariya a tattare da su, kunsan mafiya yawan bodyguards dama masu kirar karfi ake zaɓowa, to suma waƴan nan masu jajayen kunnuwa haka suke, ga tsawo ga cika ido. Gidan ne na tiles da glass, yanzu na kara tabbatarwa da aka ce Naurat tafi Dr Salman kuɗi, irin wannan aljannar duniya, Allah sarki su amarya basu sani ba suka ce wai Naurat dan kuɗin shi ta aure shi, ta biyo shi cin arziki, tana sace mishi kuɗin tana turawa iyayenta, to su zo suga aljannar duniya a nan, idan suka zo wannan gida ai sai su ɓata a ciki su yi wata basu ma san a wani part suke ba. Ita kam Rimsha ta saki baki ne tana kare kauyancinta......... Ni kuwa na ce dan ma baki je gidan mijinki na Washington DC ba ne, da bazaki yi kauyanci a nan ba, dan nan ba komai bane idan aka danganta shi da nasu. Ya ɗan jima a cikin motar kafin ya ambaci sunanta, dai'dai lokacin kuma Mark ya buɗe mishi kofar motar. Alex ya sha mamakin ganin cewa gidansu suka zo, to me ya kawo su kenan?. Shi ne tambayar da yake yi wa kansa. "Let's go Meesha." Ya faɗa tare da nuna mata hanyar fita yana latsa waya. Da sauri ta fito waje, shi kuma Mark a hanzarce ya matsa ya bata hanya. Fitowa shi ma Lion ɗin ya yi a in da yake ta aikin latsa waya, da alama wani abin yake shiryawa, dan fa har gobe ba'a gane ina ya dosa. Bayan ya kammala latsa wayar ne ya dubi sojojinsa da suka zo, cikin yaren Spanish ya yi musu magana a kan dukkansu shiddan su zauna a waje bari ya zo. Shiru bodyguards ɗin suka yi suna jin wani yaren da basu sani ba. Riko hannunta ya yi tare da cewa Mark su je ko. Ba musu Mark ya rufa mishi baya. Tamkar ya san hanyar shiga cikin gidan, haka ya wuce gaba ya je ya buɗe kofar. Kafin ya zo kasar sai da ya sami hoton zanen takardan gidan ya gama kare mata kallo, ya karanci komai sannan ya kama hanya, ba da ka kawai yake aiki ba, ya shirya abubu da dama ba tare da sanin kowa ba, dan haka a shirye tsab ya zo, su daddy ne suke ganin kamar idan ya zo za'a iya samun matsala, amma shi yasan me ya shirya kafin nan ma ya ce zai zo. Ya san ainahin mahaifin Naurat babban soja ne da kasar take alfahari da shi, hakan yasa bodyguards suka yawaita a cikin gidan duk da baya raye ya mutu. Ita dai Rimsha sai kalle kalle take yi abinta, yau tana gani ikon Allah. Tun da suka sako kafarsu cikin babbar palon gidan ta fara cin karo da masu kama da daddynta da kuma daddyn Anaya, dan Anaya ta tura mata hoton daddynta lokacin suna cikin jirgin ruwa, ba ƙaramin ruɗewa ta yi ba na ganin daddyn Anayar yana kama da daddynta sak, a lokacin ta yi ƙoƙarin kiran number Anayar dan ta gaya mata daddynta yana kama da nata, amma kash number bata shiga, shi ne ta hakura a kan sai ta koma gida sannan ta je gidansu kawai. Wasu kyawawan matasa ne kamar dai Alex su biyu suna zaune a saman sofa suna hira, gabaɗaya komai na cikin palon blue color ne, tsala tsalan sofa set uku ne a cikin palon, tamkar ba'a duniya mutun yake ba, haka zai ji idan ya shiga irin wannan palon, ya sha komai na kayan alatu. Bai bi ta kan kowa ba yana shigowa ya saki hannun Rimsha ya haura saman bene tamkar gidansa. Waƴan nan matasa sun sha ruwan mamaki na ganin ya wuce sama kai tsaye bai ce musu ko sannu ba. Sai dai basu ce komai ba duba da suna yi mishi kallon yana kama da ƴan gidan nasu, musamman ma da ya kasance Alex yana da blue eyes irin na kakansu, sai suke kallon yana kama da Alex ɗin, shi kuma Alex kallon mai kama da Aseef Mark yake yi mishi, wannan shi ne cakwakiya!!..... To shi dai Lion da Dr William jacop yake kama, har kwayar idanu da tsawo dukka, Aseef kuma ya fi kama da Josephine, Areef da su uncle T. Amma kuma sai a rinƙa cewa Aseef yana kama da mutane da yawa, to ko dai ita Josephine ɗin tana da ƴan uwan da bamu sani ba ne? Dan ita ce dai Aseef ya biyo a kama, kuma ita ce dai bamu san kowa nata ba. Wannan shi ne cakwakiya ni dai nayi gaba sai kun zo........ Amma kuma fa ana iya samun mutane irin Aseef, wanda idan ka ga face nasu dole zasu yi maka kama da wani wanda ka sani, akwai masu irin wannan baiwa a duniya, sai dai basu da yawa ne, zaka rinƙa ganin face ɗin mutane da dama a tattare da su. Takurewa waje guda Rimsha ta yi, ta tsorata sosai. Shi kuma akwai dalilin da yasa ya barta a wajen ya haura sama, ya san idan ya haura da ita akwai bala'i, ƙwaƙwalwarta ba zai iya ɗaukar abin da zata gani ba, ba zata iya daurewa ta jure ta rufe baki ta barshi ya aikata abin da zai yi ba, shi ne yasa gara mishi ya barta a cikin palon tun da gidan kakanta ne. Da yake da safe ne gabaɗaya ahalin gidan suna nan basu fita wajen aiki ba, kowannansu yana dakinsa, hakan kuma ya yi mishi dai'dai yanda yake so, dan so yake ya yi musu tsatsauran hukunci ko da kaɗan ne, saboda sun bashi haushi, kuma ya ɗauko Na'urat a gaban kowa ya tafi da ita, sai yaga karshen iskancin nasu, duk sai ya koya musu hankali a cewarsa. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 *KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*. *KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 *Dedicated to Sadiya. Ubangiji Allah subhanahu wata'ala ya baki haihuwa, ya baki ƴaƴa kyawawan gaske masu albarka, Allah ya baki waƴan da zaki ce yi su yi bari su bari, Allah ya sa wannan jinkirin rashin haihuwar ta zama miki alkhari.* TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ ❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋) *Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581* E81 After some minutes da ba su wuce 40 ba, sai ga shi ya sauko kasa. A in da ya barta a nan ya dawo ya sameta. Cikin harshen Spanish ya ce da Mark ya ɗaure mishi matasa biyun nan dake zaune a saman sofa...... Bai kai karshen maganar ba idanuwansa suka sauka a kan Alex dake bayan Mark ɗin yana tsaye. Ɗan zaro idanu ya yi yana kallon shi. Shi kansa da kallon farko ya ɗauka Aseef ne, sai da ya kalle shi da kyau ya fahimci ba Aseef ɗin ba ne, amma ba karya sun yi kama na wuce misali. Kawar da kansa ya yi tare da miƙa mata hannu, da sauri ta taho ta faɗa jikinsa. Na san za ku so jin me ya je ya yi a sama, to ku saurara, binsu ya yi ɗaki ɗaki ya yi musu ɗaurin goro tare da ɗaure musu baki kamar an aikosa, kamar wasu kaji haka ya yi musu, harta tsofaffin wato yayyun Naurat ɗin bai bari ba, cikin dabara da salon iya aiki ya yi musu hakan ba tare da ya sami wata matsala ta sun yi mishi ihu ko makamancinsa ba, yakin sunkuru ya yi musu. To shi ne abin da ya je ya yi a saman ya dawo, yasan idan suka tafi da Rimsha tsab zata yi ihu ta tona mishi asiri, shiyasa ya bar Brady a mota. Idan taga ya toshewa mutun baki kuka zata fara yi, shi ne yasa ya barta a kasa tare da Mark, ya san waye Mark, haka kawai Allah ya sanya mishi kaunar Mark ɗin a cikin zuciyarsa, baya yarda da kowa, amma Mark yana da kusanci da zuciyarsa sosai, yana jinsa sosai a ransa. Massage ya yi wa sojojinsa a kan su shigo dan su fito mishi da kowa dake cikin ɗakunan da ya bi ya ɗauresu kamar kajin nan, ya san idan ba haka ya yi musu ba, to wlh ba za'a sami fahimta a tsakaninsu ba, za su iya kira mishi sojoji su tada yaki a tsakaninsu, shi dai baya barin ko ta kwana, idan aka kawo mishi wargi to fa zai yi ba dai'dai, kuma kakansa His excellency ya ce ya bi komai a hankali har ya shiga ya fito, babu wata hukuma da zata tare shi dan ya shirya musu makarkashiya, dama kuma kunsan kasar America gwana ce wajen shirya shiryen sheyen abubuwa, to shi ne yasa ma kuka ga ya shigo kasar lafiya lou, kuma shi ne yasa ya ɗauresu dan ya yi komai a tsanake. Ɗaukarta cancak ya yi suka koma saman. Bai zame da ita ko'ina ba sai ɗaki na karshe a sama bakiɗaya. Da akwai key a jikin kofar, dan haka sai ya murɗa ya buɗe. Bakinsa ɗauke da sallama suka shiga ciki. Jin sallama yau a gidan GENERAL TRUMP ne yasa a hanzarce ta ɗago kanta. Tana daga zaune saman bed ta kifa kai da gwiwowinta, da alama tana cikin tsananin damuwa. Dattijuwa ce, amma da yake jikin Turawa baya saurin nuna tsufa, suna da jiki mai kyau, sai tsufanta bai wani bayyana ba, idan ka ganta zaka ce 35 years gareta, gata kuma da ƙaramin jiki mai shegen kyau. Kyakkyawar gaske ce, fara tas tamkar ka taɓa jini ya zuba, ga dark black curly hair har bayanta a kwance. Ashe ita Rimsha ta ɗauko a gashi. Tsawon shekaru 33 tana kulle a cikin wannan ɗaki, ko waje bata leƙawa, babban yayansu wanda Lion ya fara ɗaurewa yanzu shi ne ya rufeta a cikin ɗakin, suna azabtar da ita a kan lallai sai ta dawo kafura ta fita daga addinin Musulunci, ita kuma ta ce sai dai su kasheta, amma wlh ba zata yi ridda ta zama krista ba, ta rigada ta musulta kenan, bata ga wanda ya isa ya mai da ita krista ba, shi ne suka rufeta, abin ci ne kawai yake sanyawa suke buɗeta. Duk kudin nan nasu dan bakin mugunta sau ɗaya suke bata abinci a rana, ruwa ma ɗan kaɗan suke bata, ta azabtu matika na tsawon waɗan nan shekaru, amma duk da haka bata ji kamar ma zata iya fita daga cikin addinin musulunci ba, sun hanata hijabi dan kada ta yi sallah, amma a hakan sai ta yafa wani abin ta yi, dai'dai da rana ɗaya lokacin sallah bai taɓa wuce ta ba. Daga karshe dai suka hakura suka barta a cikin ɗakin rufe kawai suna bata abinci sau ɗaya. Naurat ta sha bakar wahala sosai a rayuwarta, tasha na Amarya a Nigeria, ta kuma sha na ƴan uwanta a nan, ita da ta taso ƴar gata sosai, saboda su uku ne kawai mata a cikin yaran GENERAL TRUMP goma sha uku, goman dukka zaratan maza ne, su uku ne mata, da ita da kannenta mata biyu wanda su basu zaune a Russia ma, tun asali a America suka yi karatu, so suna can da zama basu dawo nan ba har yanzu, ita kaɗai mace ta rayuwa da daddynta, ya yi mata gata fiye da tunanin mai tunani kafin ya mutu ƴan uwanta maza su cigaba da kula da ita, haɗurwarta da Dr Salman a shopping ya fara canza komai, shi ne kuma mafarin wahalarta har zuwa yanzu. Karisowa cikin ɗakin ya yi tare da sauke Rimsha kasa. A gefen bed ɗin nata kusa da ita ya zauna, haka kawai Allah ya sanya mishi kaunar dattijuwan nan har cikin ransa, musamman idan ya tuna irin gwagwarmayar da ta sha a kan cewa ba zata bar addinin musulunci ba, sai ya ji ya kara kaunarta over. Cikin harshen turanci ya fara yi mata magana a nutse. Ya gaya mata ɗaukarta ya zo yi su koma Nigeria. Kin yarda da shi ta yi, duba da shi ma Bature ne, kafewa ta yi a kan cewa ita bata san Nigeria ba kuma bata da wata alaƙa da Nigeria. Baiwar Allah muryarta ma da kyar yake fitowa saboda jimawa da ta yi bata magana da kowa. Da hannu ya yi wa Rimsha alama a kan ta zo, da sauri ta kariso kusa da shi ta zauna. Dama kamar yasan Na'urat zata yi mishi gardama, shi ne yasa ya taho da Rimsha, idan baku manta ba da Jehan ya so zuwa ma, dan ita ce mai kama da daddynta, a wani ɓangare kuma yana son zuwa da Rimsha dan launin fatarta irin nasu family'n Dr Salman, yanda Na'urat ta sha wahalar nan baya jin kamar zai yi mata dole a rayuwarta, shi ne yasa yake binta a hankali. Cikin sanyin murya ya sake gaya mata da gaske shi ba cutar da ita zai yi ba, tafiya da ita ya zo ya yi dan ya mayar da ita cikin ƴaƴanta, hakan ce ma tasa ya zo mata da jikanta ƴar Nawazudden ɗinta dan ta shaida, ya san cewa ko zata manta kowa, to ba zata manta Nawazudden ba, dan shi ne ɗa mafi soyuwa a gareta. Ai kuwa duk kin yarda da ta yi da shi, jin ya ambaci sunan daddyn Rimsha sai da ta ɗago sosai tana kare musu kallo, sai dai fa ita a yanayin yanda take kallon face ɗin Lion da ƴan uwanta na nan yake yi mata kama, amma ganin Rimsha yasa ta ji ta yarda da su, duk da cewa Rimsha bata wani kama da daddyn nata, sai dai kama ta jini, da mum take kama. Kara yi mata bayani ya yi a nutse dallah dallah yanda zata fahimta, yanda kuma rikicin tsufa ba zai sanya ta kasa ganewa ba. A takaice dai ya yi babban sa'a ta yarda da shi dalilin Rimsha, dan haka sai ta amince zata bishi. Ya ji matuƙar daɗi sosai, shi da kansa ya taimaka mata ta miƙe tare da saukowa kasan bed ɗin. Sai murna Rimsha take yi yau ta ga kakanta mai tsananin kama da daddynta. Riko hannunta Naurat ɗin ta yi tana ji tamkar hannun Nawazudden ta rike, tana bala'in kaunar daddyn Rimsha da daddyn Anaya, tafi sonsu sama da kowa a cikin ƴaƴan nata. A hankali suka fito palo, nan ya iske kowa na gidan, gabaɗayansu sojojin sun fito da su sun zube su a palon. Sun yi mugun bashi haushi ne na izayar da suka rinƙa yiwa ƴar tahalikan nan na tsawon shekaru, ya so ne ma ya yanke wa kowannesu koda kunne ɗaiɗai ne, amma kuma yana sauri, dan haka sai ya kyale su kawai. Har ya kai bakin kofar palon rike da hannun Naurat ɗin ita kuma tana rike da hannun Rimsha. A hankali ya juyo ya ce da Mark ya kwance Alex da shi zasu tafi. Cikin girmamawa Mark ya ce yana neman alfarma Lion ya yi hakuri ya sanya a kwancesu, dan saboda uncles nasa ne, ƴan uwan daddynsa ne, dukka ya sansu ta cikin hoto, yana da hoton kowannansu, Alex ɗin ne kawai dama suke waya da shi, kuma Mark ɗin ne ya nemo number Alex ɗin dalilin wannan zuwa da za su yi. Shiru Lion ɗin ya yi yana mamakin, Allah mai iko, yau dai ga Mark a cikin family'nsa, Mark ɗin ma jikan gidan ne kamar dai su Rimshan. Jinjina mishi kai ya yi yana faɗin, ya barsu idan sun tafi za'a kwancesu, dan sun ɓata mishi rai fa. Haka ba dan ya so ba ya kyalesu, ya kwance iya Alex ɗin kawai sojojin suka sanya shi a gaba suka bar palon. Wani karfin hali sai wajen Lion, ya shigo har cikin kasarsu, kuma cikin gidansu, ya kuma ɗauki ƴar uwarsu da suka rufe tsawon shekaru, kuma a gaban idanunsu, ya kuma sa kafa ya fita, ba yanda suka iya da shi, wato a duniya idan kai wani nema fa ka ji daɗi, idan kana da goyon bayan manya daga sama ba abin da ba zaka aikata ba, kuma ka zauna lafiya, Allah ya yi wa dukkanin musulman duniya bakiɗaya arziki mai albarka mai kuma amfani. Koda bodyguards na gidan suka gansu, ko sannu basu ce musu ba, dan sun ga da ɗan gida suke tare, ga kuma Naurat, sai dai abin mamaki Alex ya kasa iya gayawa bodyguards ɗin abin da yake faruwa a cikin gida dan su hana su Lion fita, ya rasa ya akayi bakinsa ta yi mishi muguwar nauyi. A takaice dai haka suka sake fita daga gidan cikin waƴan nan motocin da suka zo ɗin, suka koma cikin jirgin ruwansu. Ba ɓata lokaci suka ɗauki hanyar komawa gida. Naurat a ɗakinsu ta zauna, dan ya kula da ita, yana jin tsantar kaunarta a ransa. After some hours. Bayan sun kama hanyar ne, jirgin ruwan nasu ya tashi, a nan ne yasa Mark ya turo mishi Alex. Har cikin ɗakin nasu Alex ɗin ya zo, saman sofa ya ce mishi ya zauna, ita kuma Naurat tana zaune saman bed nasu, Rimsha ta tada kai da cinyarta tana mai jin tsantar farinciki. A saman bedside drawer shi kuma Lion ɗin ya zauna. ❤️PRINCESS TEEMA💋......✍️ A nutse ya fara magana cikin harshen turanci, a in da ya gayawa Brr Na'urat cewa Alex fa yaronta ne ba ɗan yayanta TRUMP ba, zaro idanu ta yi tana mai gaya mishi ai ita yaron da ta haifa ya mutu, girgiza mata kai ya yi yana faɗin. "A binciken da nayi bai mutu ba, karya suka yi miki da ya mutu dan ma kada watara ya zo kawo miki abinci ki gaya mishi kece mamansa kuma ya musulta, shi ne yasa suka ce miki ya mutu, amma Alex ɗan ki ne, shi ne wanda kika baro Nigeria ba tare da kin san kina da cikinsa ba, sai da kika dawo nan da watanni kika san da hakan, so ba Abdul Malik ba ne autanki, Alex ne!." Babbar magana, zancen Lion gaskiya ne, bayan Naurat ta haifi cikin da daddyn Rimsha ya barota da shi, wato cikin daddyn Jelly, yana da shekara ɗaya da rabi a duniya sun sake samun kyakkyawar alaƙa da Dr Salman, da alama a lokacin asirin da amarya ta yi mishi ne ya karye, sun kowa kamar da, suna soyayya tare da kula da yaransu, suna kuma neman daddyn Rimsha, a lokacin shi kuma daddyn Rimshan yana Niger tare da abokinsa. Bayan wata uku da samun jituwar tasu suka sake komawa gidan jiya, faɗa kullum kullum, a lokacin ne kuma amarya ta karo sabon walaƙanci a in da ta mayar da Naurat ɗin ƴar aikinta, ganin ba zata iya jurewa ba ne yasa ta kira yayanta TRUMP a waya wato wanda aka ce shi ne mahaifin Alex yanzu, shi ne suka zo suka ɗauketa ta baro daddyn Jelly a hannun su Abba yana yaro, bai gama cika 2 years ba lokacin, sam bata san da shigar cikin Alex ɗin ba a lokacin, dan lokacin cikin bai kai ko wata ɗaya ba. Sai bayan ta koma Russia ne da ƴan watannin da ba su yi biyu ba, nan ta fahimci ciki ne da ita, a lokacin kuma tana shan azaba wajen ƴan uwanta, wanda hakan ya zama tana danasanin biyosu, dan fa mugaye ne kuma mafaɗata ne na karshe, basu da sauki ko kaɗan ga zafin ran bala'i, ta ce gara mata gidan Dr Salman sau dubu a kan abin da ƴan uwanta suke yi mata dan taki yin ridda. A takaice dai haka ta yi rayuwa cikin kunci har cikin Alex ya girma, lokacin da take nakuda ba wanda ya kulata a cikinsu sai matar kaninta ɗaya, ita ta taimaka mata har ta haihu, bayan ta aihu ne kuma suka zo suka ɗauki yaron, after some minutes suka dawo suka ce mata ai ya mutu saboda bata je asibiti ba, alhalin karya suke yi mata, basu so ne ta koyawa yaron addinin musulunci. Haka suka reni Alex cikin so da kauna a in da da ya taso suka ce mishi ai yayan Naurat ɗin shi ne babansa, shi kuma ya tafi a hakan, basu barin shi yana kai mata abinci, kowa zai kai mata abinci a gidan amma banda shi, dan sun san uwa da ɗa ba wasa ba, wani lokaci ma dan walaƙanci barinta suke yi ta kwana da yunwa sai su ce sun manta ne da ita yasa basu kai mata abinci ba, izaya kala kala suka rinƙa yi wa ƴar tahaliƙan nan, sai dai Allah ya saka mata kawai. Daga ita har Alex ɗin sun rasa bakin magana, Allah sarki yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ma Alex ɗin ya kasa gayawa bodyguards ɗin sacesu su Lion za su yi, uwa ba wasa ba, yau Allah ya ƙaddara ne zai gane ba Trump ba ne babansa. Sosai ya rinƙa kuka da hawayensa, sai tunanin irin izayar da suka rinƙa yi mata ya fara yi, ya ma kasa ɗaga idanu ya kalleta tsabar shiga tashin hankali da damuwa ga kuma murna a gefe. Kifa kansa kawai ya yi da jikin sofa yana kuka. Ita ma Na'urat ɗin kuka take yi sosai, ƴan uwanta sun cutar da ita sosai, yanzu ace ɗanta na cikinta ne ya taso a krista tsawon shekaru? Bai san komai ba dan gane da addinin babansa, wannan abin ya yi mugun yi mata zafi. Amma fa kuma abin mamaki shi ne, Alex ya fita daban a cikin ƴaƴan TRUMP ɗin, shi ne yasa ma wani lokaci yake jin kamar ba su ne iyayensa ba, na farko yana da kirki sosai shi, jinin Hausa Fulani Bauchi state kenan, wato Dr Salman, yana da son mutane da saukin kai, yana da fara'a tamkar Dr Salman, wani lokaci idan aka taɓo shi yana da zafin rai, sak da ainahin babansa, so abin yana bawa su ƴaƴan TRUMP ɗin ma mamaki, sai dai duk cikin ƴaƴan Brr ɗin babu wanda ya kai Alex ɗin fitowa sak Turawa babu mix, sak kakansu GENERAL TRUMP wato mahaifin Naurat kenan. Shi dai Lion ya yi shiru yana kallon yanda suke ta shan kuka dukkansu, ita ma Rimsha ta yi hawaye sosai na jin wannan labari nasu mai taɓa zuciya, mutun mahaifiyarsa tana raye amma dan bakin zalinci an hana ta bashi nono? Aka rinƙa ɗirkawa bawan Allah madara, Allah sarki, wlh zalinci bai yi ba, duk abinsu dai yau ga shi ya haɗu da mahaifiyar tasa, kuma da izinin Allah sai ya musulunta, bakinciki ya kashesu. Sun sha kuka kamar ba gobe, shi dai Lion bai iya ce da su komai ba, bai ma san me zai ce musu ba, haka ya zuba musu idanu suka yi kukan har ya ishe su. Sannan Alex ɗin ya mike ya dawo kusa Brr. Mikewa Rimsha ta yi daga saman cinyar tata ta bashi waje. Yana zuwa ya rungumeta yana jin tamkar ya koma ya kashe uncles nan nasa bakiɗaya na irin izayar da suka yi mata, zuciyarsa sai tafasa yake yi tamkar zata fashe. Rungume shi Brr Naurat ɗin ta yi tana rarrashinsa har sai da ya yi shiru. Miƙewa Lion ya yi tare da riko hannun Rimsha suka bar musu ɗakin zuwa na kusa da su, dan su basu dama su tattauna. Shi ma Lion ɗin yana son ya yi sallar azahar dan lokaci ta yi. Rimsha tamkar zata yi kuka haka ta biyo shi, sam bata son rabuwa da kakanta, amma ba yanda ta iya. Suna shiga cikin bedroom ɗin ya saki hannunta tare da nufar toilet. Zama ta yi a saman bakin bed ɗin tana jiran shi ya fito. Wanka ya yi tare da ɗauro alwala ya fito. Ganin face nata a ɗaure tamau ne yasa ya ce lafiya take wannan ɗaure fuska, turo baki ta yi tana faɗa mishi ita wajen kakanta take son zuwa, da hannu ya nuna mata hanyar tafiya. Da sauri ta miƙe ta fita, har ta kusa kifawa saboda sauri. Shi kam ko a jikinsa, dadduma kawai ya ɗauko tare da shumfuɗawa dan ya gabatar da sallah. Tana zuwa ta sami sun gama shan kukan suna tattaunawa, hayewa saman bed ɗin ta yi tare da komawa ta kwanta saman cinyar Brr. Kallonta Alex ɗin ya yi yana tambayar Brr wace ce ita. A takaice ta bashi labarin su daddyn Rimshan wato ƴan uwansa. Sosai ya ji tsananin kaunarsu a ransa. Shafa kumatun Rimshar ya yi yana mai jin kaunarta ita ma, ƴar autar family'n Dr Salman kenan. Duk familyn Dr ita ce karama, ita ce autarsu, daga ita sai Zaira kanwar Anaya, sannan Jehan da Anaya wanda su shekarunsu ɗaya, ratar ƴan watanni ne kawai. Shi kuwa Mark yana can yana hira da Anaya a waya, a in da yake gaya mata nan da kwana huɗu zasu dawo dan tafiyar tasu ta canza salo. Sai murna take yi ya ce zai zo gidansu. Shi Mark sam bai san cewa ba za'a bashi auren Anaya ba har sai ya musulunta, ya ɗauka za'a iya bashi ita a haka, shiyasa ma har da ce mata zai zo yaga daddynta........ E lallai akwai chakwakiya. After some hours. Da misalin karfe 8 na dare, bayan sun yi sallar isha kenan, gabaɗaya kewar mijin nata ya isheta, ga shi tana kunyar barin Brr Naurat ta je wajen shi, shi kuma sam yaki zuwa in da suke, ya kule a cikin bedroom nasa yana aikin latsa laptop nasa, Brady na kwance kusa da shi. Brady na Mark, kwana biyun nan duk a wajen Mark yake kwana, sam yanzu ya rage zuwa wajen Lion ɗin, sai jefi jefi, Mark ya saye shi ta hanyar kunna mishi kallo a waya da sauransu, shi ne ya saye zuciyarsa. Alex yana tare da Mark a waje suna hirar yanda Mark ya yi rayuwa da kuma mutuwar iyayensa wato causing ɗin Alex ɗin kenan, Mark zai kira Alex uncle dan causin ɗin daddynsa ne. Cikin harshen turanci Brr Naurat take ta tambayar Rimsha labarin daddynta da sauransu. Sai hira Rimahar take zuba mata na mutanen Nigeria, amma fa hankalinta na wajen tunanin mijinta, duk ta damu, tun da rana bata sake saka shi a idanunta ba. Sarai Naurat ta lura da tana cikin damuwa, hakan yasa ta yi ƙoƙarin tambayarta me yake damunta. Babu komai ta ce mata, a haka har Mark ya kawo musu abinci. Kin cin abincin ta yi dan tana tunanin zata je su ci da mijinta. Muryar Brr ɗin ce ta katse mata tunani da cewa "Wanene wannan da ya ɗauko ni ɗin?." Shiru ta yi ta rasa me zata ce, ta ce mata mijinta ne ko ta ce mata me?. Ganin ta yi shiru ne yasa ta ce "Kunyata kike ji ne?." Girgiza kai ta yi alamar a'a. Murmushin Brr ta saki har sai da dimple nata irin na ƴaƴanta Nawazudden da Azharuddeen ya bayana, dama a wajenta su daddyn Rimsha suka ɗauko dimple da gaf teeth. "Rimsha kunyata mana kike ji, ai na san ku mutanen Nigeria sai ku rinƙa cewa wai kuna jin kunyar abu, haka kakanki Dr yake yi wani lokaci, to amma idan har kina jin kunyata haka a kansa, hakan na nufin kuna da wata alaƙa da kusa kenan?." Shiru ta yi tana murmushi tare da sanya hannu ta rufe fuska. "Rimsha kada ki ce mini aure Nawazudden ya yi miki? A ƴar yarinyar kin nan? Duk da a family'n Dr nasan suna aurar da yara 12 to 13 years ma, amma ai su a kauye suke, ba su ma yi karatu ba, shi kuma Nawazudden me ya haɗa shi da irin wannan al'adar ta kakanin nasa? Ai kinyi yarinya da yawa." Ita dai bata ce komai ba bayan wannan rufe fuska da ta yi. "Amma kuma gaskiya na yi miki murna na samun miji irin wannan bawan Allah, yana da kirki sosai." (Ni kuwa na ce ke dai kin yi sa'a da kika ga fuskar kirkin nasa, dan haka ki yi fata kada ki haɗu da ainahin true colornsa, idan kika kuskura kika yi ido huɗu da ainahinsa, daga ranar ba zaki ma sake yin maganarsa ba, saboda haushi da zai baki, ya kuma birkita miki tunani.) "To amma Rimsha shi ne kika zauna a nan baki je wajen shi ba?." Tana magana tana cin abincin cikin natsuwa. Baki ɗauke da excuse Alex ya shigo cikin ɗakin. Jin abin da Brr ta ce ne yasa ya ce "Mum a kan me kuke magana ne?." Cikin nuna ko in kula ta bashi labari. Zaro idanu ya yi yana mamakin ƴar Rimshan nan ne aka yi wa aure? Kare mata kallo ya fara yi daga sama har kasa, shi dai bai ga abin da za'a aurar ba, kuma aure ma ga namiji kamar Lion? Wannan ai sai ya kasheta kawai a karon farko, sake baki ya yi yana jinjina al'amarin. Bai san cewa sune suke rena Rimsha ba, suna yi mata kallon yarinya, to su biyota ɗaki suga yanda take sanya Lion ɗin sambatu da kuma sauka daga layi, yo ai kamar yanda namiji baya kaɗan haka ita ma mace bata kaɗan, in dai ta wuce 13 years kuma ta samu tarbiya ai shikenan an gama. Katse mishi tunani Brr ta yi da cewa ya zo su ci abinci, ita kuma Rimsha ta tashi ta wuce wajen mijin nata. Jiki ba kwari ta miƙe ta fita tana yi musu sai da safe. Shi kuma Alex kusa da mum ɗin tasa ya zo ya zauna saman ɗaya daga cikin kujerun table ɗin. Cikin tsantsar soyayya irin ta uwa da ɗa suka fara cin abincin a tare. Ita kuma Rimsha baki ɗauke da sallama ta shigo cikin ɗakin nasu. Tamkar babu shi a cikin ɗakin, ko kallon in da take bai yi ba, kamar ma bai san da shigowarta ba. Toilet ta wuce sai wani ɗari ɗari take yi. A gurguje ta yi wanka tare da fitowa, ta yi mamakin ganin trolleys nasu a cikin bedroom ɗin, bata san cewa shi ya ɗaukosu tun da rana ba, tana can tana surutu da kakanta. Cikin wasu shegun kayan barci ta shirya, masu matuƙar ɗaukar hankalin, riga ce zuwa iya dai'dai santala santalan cinyoyinta, daga ta saman rigar hannun vest ce gareta, gabaɗaya tudun tula tulanta a waje, bugu da kari rigar ƴar shara shara ce bata da kauri, ainahin zanen shatin tula tulan nata ma a waje, har kan nipples nata shatinsa ya bayyana. Sake gashin kanta ta yi har baya tare da zuba perfume nasa a jikinta. Sai wani irin sheki santala santalan cinyoyinta suke yi, ta shafesu da Lotion nasa, ita kanta sai sheki take yi. Shi kuwa hankalinsa yana kan laptop nasa, da alama dai wani aiki mai muhimmanci yake yi. Saman table ta nufa, dan already shi ya ci abincinsa. Zama ta yi tare da zuba abincin ɗan kaɗan. A nutse ta fara ci tana satar kallonsa. Shi ma kayan barci ne launin white color a jikinsa, ya yi matuƙar kyau over, ya saki dark black curly hairnsa, sai ɗan ciza laɓɓansa yake yi a hankali, da alama aikin yana ɗan bashi wahala. Gabar rigar barcin nasa a buɗe ne mai wuyar V, faffaɗar kirjinsa a waje, wannan kyakkyawa kuma kwantatcen bakin gashi nan na kirjin nasa a kwance luf yana wani sheƙi. Jin azababben kamshin perfume ɗin ya kai mishi karo a hancinsa ne yasa ya ɗan ɗago idanunsa izuwa kanta, dai'dai lokacin ita ma ta ɗago dan ta saci kallon shi. Karaf suka haɗa idanu. Kasa ta yi da nata tana ɗan murmushi, shi kuwa zuba mata idanu ya yi yana kallon ikon Allah, wani irin azababben kyau na wuce misali ta yi. Duk sai ta ji ta tsargu saboda kallonta da yake yi, wani irin kunya ce ta ji ta lulluɓeta, ƴan kame kame ta fara yi tana wani yin abu kamar mara gaskiya, dama kun san idan mutun ya tsareka da ido yana kallonka, duk sai ka tsargu, to ita ma haka ce. Kasa cigaba da cin abincin ta yi a in da ta miƙe kawai ta nufe shi tana wani sunnar da kai kasa tare da ɓoye fuska na rashin kunya. Time da zata sanya kayan bata yi tunanin cewa zata ji kunya idan ya gani ba, sai yanzu ne take wani sunnar da kai na rashin kunya. Tana zuwa ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa tana cigana da ɓoye fuska. Haushi Brady ya fara daka mata na a kan me zata kwanta mishi a jikin Lion ɗinsa. Tamkar bata ji yanayi ba, sai ma kara saƙalo wuyarsa da ta yi tana wani ɗan turo baki tare da yi mishi yauki da yanga. Cikin dabara ya kawar da laptop ɗin daga gabansa zuwa saman bedside drawer, hannu bibbiyu yasa ya rungumota da kyau yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya. Ba karya ya yi kewarta sosai, kawai wannan aikin ne ta sha kansa da ta sanya bai je ya ɗaukota ba, ita ma ta yi kewar shi sosai, dan haka yana rungumeta ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya. "Noori Allah nayi kewarka sosai yau." Ta yi maganar tamkar zata saka mishi kuka. Ɗan ɗago haɓarta ya yi suna fuskantar juna. "To ba gani yanzu kin zo gare ni ba?." Jinjina mishi kai ta yi tana mai kara rungumo shi sosai. Haɗe fuskokinsu waje guda ya yi yana kara kare mata kallo. "Noori meyasa kake yawan son kallona?." Ta tambaye shi a shagwaɓe. Dirowa kasa Brady ya yi ya wuce zuwa wajen Mark abinsa, dan ya lura Lion fa ba tashi yake yi ba. Ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya bata amsa da cewa "Because you are mine." Zaro idanu waje ta yi, bata taɓa tunanin zai ce ita mallakinsa ba ne, kai Lion da abin mamaki yake, baka taɓa game mishi, idan ya yi wani abin sai kaga kamar ba shi ba. Ganin ta zaro idanu ne yasa ya ɗaura lips nasa a saman tata tare da fara kissing nata a nutse. Tamkar jira take yi ita ma ta fara mayar mishi da martani. Kankame juna sosai suka yi. A hankali ya fara romancing nata, daga karshe sai ya kwanta tare da ita a jikin nasa a in da ya ja musu bargo suka kule a ciki, a nan ne ya fara romancing nata da zafa zafa. Tun tana ƙoƙarin taya shi har ta kasa dan ya kureta, tuni ya rabata da kayan jikinta ya shiga murzarta da kyau da kyau, sai dai fa yanayi yana taka tsantsan dan tsaro, bai zurfafa da yawa ba. A haka ƴar lallaɓawar ma sai da ta yi mishi kuka, yana birkita mata tunani ne sosai. Kuka ta rinƙa yi mishi shi kuma yana zuba mata sambatu. Sai da ya ɗan ji sauki sauki a jikinsa, sannan ya rabu da ita tare da kwanciya gefe ya jawota jikinsa, kashe wutar ɗakin ya yi da kuma kara musu gudun Ac. Kankame shi ta yi tare da lafewa shiru tana shakar daddaɗar kamshinsa har barci ya yi awon gaba da ita. Shi ma ba jimawa barci ta ɗauke shi. ASUBA TA GARI. AFTER SOME DAY'S💋 ❤️PRINCESS TEEMA💋......✍️ AREEF AND JEHAN. Yau ta kama Monday, kuma a yau ne game nasu ya zo ƙarshe. Tun safe da misalin karfe 7 ya shirya ya bar gidan, ba komai yasa ya bar gidan ba sai dan ya yi maganinta kuma ya tantance tana son shi ne ko bata son shi. Tana can cikin bedroom nata tana zuba barcin da ta saba, dan ita wani lokaci ma sai 11 na safe take tashi daga barci, sam bata san tsiyar da gogan nata ya shirya mata ba. Aseef da Akila ma sai zuba barcinsu suke yi. Wannan gida dai kun sani ba sai na sake faɗa ba, gida ne na yara jiki dukka madara iyaye jiki dukka madara, ba ƴaƴan malam shehu ba ne, sai su yi ta zuba barcinsu son ransu, sai time da suka ga dama suke tashi, ba wanda zai tashesu daga barci, idan yunwa ta tasheka ma to sojoji masu yin girki dai sun gama aikinsu, bayin Allan tun karfe 7 suke gama komai su jere a saman table, amma mutanen gidan nan ne su zo su ci ya zama tashin hankali, wasu ma sai 12 suke cin abincin, irinsu daddyn Rimsha kenan, ita kuwa Jehan duk time ɗin da ta tashi barcin take ci. Haka suma Aseef da Akila, duk time da suka tashi suke ci. Shi kuwa daddynsu Lion, wani lokaci ma ba cin abincin safen yake yi ba, sai dai su sha green tea shi da uncle Herry. Mutane ne dai gasu nan kala kala, iri irin ra'ayi sun iya, kowa da kalar tasa, ba zaka taɓa sanin ina ma suka dosa ba, kowa kawai abin da ya zo mishi cikin ƙwaƙwalwarsa yake aikatawa. Shi John ma ai dama sai ya sha giya ya bugu da daddare tukun nan yake yin barci, shiyasa idan ya fara barcin safe baya tashi da wuri, wani lokaci sai karfe 2 ko 3 na rana, sai lokacin da giyar ta sake shi, ga shi baya yi mata shan wasa. Shi kuwa Jay ɗan ba ruwana, matarsa yake kira a waya su yi ta zuba soyayya har dare ya tsala, wani lokaci ma sai asuba ya gabato yake hakura su yi barci, shiyasa shi ma baya tashi da wuri, sai ya kai 10 or 11, kai a takaice ma duk gidan ba mai tashi barci kasa da karfe 8 sai masu aiki, sojoji, sai kuma Lion da shi dama bai damu da yin barcin safe ba. Lokacin da Rimsha take zuwa school ne tana tashi da wuri. Yanzu ma duk sai zuba barcinsu suke yi, shi uncle T tun ranar da ya zo, ya saka kafa ya bar gidan bai kara dawowa ba, ya tafi yawonsa, sai Allah kaɗai ya san mishi in da ya tafi. Da misalin karfe 11 dai'dai ta farka daga barci. Ko da ta farka ta jima a kwance har 11:30, sannan ne ta lallaɓa a hankali ta sauko kasan bed ɗin, ta nufi toilet. Wanka ta yi tare da dawowa ta shirya cikin wandon jeans baki da t-shirt maroon. Ta yi kyau sosai, dama ita bata son manyan kaya, kuma dama bata saba sakawa ba idan baku manta rayuwarsu a baya ba. Fitowa ta yi ta nufi bedroom ɗin daddynta, a duk tunaninta zata sami Areef a wajen, dan yau da kewarsa da kuma tunaninsa tare da begen son ganinsa ta tashi. Amma ko da ta shiga baya nan, daddyn nata kawai ta samu kwance a saman bed yana latsa wayarsa, sai murmushi yake yi. Chatting suke yi da Rimsha, amma sam bata gaya mishi sun ɗauko Na'urat ba, dan Lion ya ce kada ta gayawa kowa, hakan yasa bata faɗa ba. Sai zubawa daddyn nata shagwaɓa take yi a kan tana kewarsa, shi kuwa ya ce mata ba wani nan, ba tana tare da GAR ba? Yasan ba wani kewarsu da take yi, kawai wayancewa take son ta yi mishi dan ya ce mata yana kewarta. Voice ta yi mishi a in da take zuba mishi kukan shagwaɓa a kan lallai ita wlh tana kewar shi over. Guntun tsaki Jehan ta ja tana ji kamar ta damƙo Rimshar nan ta bata a jikinta, saboda a cewarta duka Rimsha take so, wani kayan takaice har da kuka a cikin voice ɗin. Shi dai daddy da yake ya san matsalar baby Jehan ɗin tasa, sai ya miƙe zaune tare da ajiye wayar a gefe yana ce mata sarkin rigima an tashi?. Turo baki ta yi tana ce mishi "Good morning dad." "Morning my daughter how are you doing?." Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Daddy i wanted to eat something, am feeling hungry." Ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufo palo. Kasa ta nufa dan a can table na kasan ake jere abinci. Zuba kalar wanda take so ta je ta yi, ga abincin kala kala sama da kala goma jere cike a saman table ɗin, zaɓa ta yi wanda ya yi dai'dai da ra'ayinta, sannan ta ɗeba tare da haɗo duk wasu abin da zata buƙata ta koma saman. Bedroom ɗin daddy ta koma, saman lallausan carpet na kusa da bed ɗin ta zauna tare da zube abincin a kasan, har lokacin bata cire tsammani Areef zai shigo cikin ɗakin ba, sai dai kuma har ta ci abincin ta kammala sam bai shigo ba. Hira suka yi ta zubawa da daddy bayan ta kammala har zuwa azahar, a nan ne suka yi sallama ta koma bedroom nata dan ta yi sallah. Shi ma daddy ya miƙe ya shiga toilet. Bayan ta idar da sallah ne sai ta fara tunanin to yau ina Areef ya je? Kuma ga daddynta a gida bai fita ba bare ace sun fita tare, to shi ina ya je?. Haka dai abu ya fara tsamari har zuwa la'asar bata gan shi ba, ta kuma kasa tambayar daddynta ina yake, ta kasa cin abincin rana, ta shiga damuwa sosai da sosai na wuce misali. Hayewa saman bed nata ta yi da yamma kenan bayan ta yi sallar la'asar. Duk ta damu fiye da tunanin mai tunani, kwanciya shiru ta yi tana tunanin abubuwan da suka rinƙa faruwa a tsakaninta da shi, bata san time da ruwan hawaye ya fara bin kuncinta ba, ta kasa goge hawayen, haka ta barshi ya cigaba da zuba, idan ta rufe idanu face nasa kawai take gani yana murmushi, tana jin yunwa amma ta kasa iya cin abinci. Wasa wasa har ta yi sallar isha bai dawo gidan ba, abin ya isheta har ta fito zuwa bedroom nasa dan ta duba shi. Ko da ta je babu shi babu alamarsa. Bedroom nata ta koma, yau ta kasa zuwa su yi hira da daddynta ma. Tana zuwa ta haye saman bed nata ta hau kuka, yunwa kamar zai kasheta amma sam ko kallon in da abincin yake ma ta kasa, ga shi bata da phone numbersa. Hawaye ne wani na bin wani a saman kuncinta tana daga kwancen, Allah sarki wlh har faɗawa ta yi na wuni ɗaya, har ta ɗan rame, idanunta sun kara fitowa sosai, kun san idan mutun ya rame idanunsa suna kara girma, to ita ma hakan ce ta kasance da ita. Har karfe 10 na dare bai dawo ba, ita kuma bata dai'na ruwan hawaye ba, ga uban yunwa, sai dai idan ta gaji da kwanciya ta juya ta nan, idan ta sake gajiya ta juyo, duk ta jike lallausan pillownta da hawaye. Duk wannan halin da ta shiga daddynta yana sane da ita, amma sam bai kulata ba, saboda shi da kansa ya ji daɗin abin da Areef ɗin ya yi mata, yanzu ai zata san cewa yana da matsayi a cikin zuciyarta. Tana tsaka da kukanta hawaye wani na bin wani, ta luluƙa duniyar tunaninsa. Tamkar daga sama ta ji ana goge mata hawaye, sam bata ji shigowar mutun ba. A hanzarce ta waro idanunta sosai tare da miƙewa zaune. 4 eyes suka yi da shi yana zaune saman bedside drawer, hannunsa na rike da handkerchief fari kal mai bala'in laushi kamar audiga. "Jehan meyasame ki kike kuka?." Kai Areef ɗan duniya ne number ɗaya, wato ya nuna irin shi bai san komai ɗin nan ba. Wani irin harara ta wurga mishi da idanunta da suke jawur saboda kukanta da ta ci ta koshi. A hanzarce ta diro kasa daga saman gadon tare da nufar hanyar barin ɗakin wai bata son ganin shi. Cool murmushi ya saki tare da miƙewa da sauri ya tare gabanta. "Jehan What is wrong with you ne? Ina yi miki magana, you have to be amsa me first before ki fita ko? Ko kin manta ni yayanki ne?." Haushi tamkar ta rataye kanta, raɓawa gefensa ta yi zata wuce tana wani hucin da ita kanta bata san dalilin yin shi ba. ❤️PRINCESS TEEMA💋......✍️ Sake tare gabanta ya yi tare da zube gwiwowinsa a kasa ya kuma kama kunnensa yana faɗin "Am so so sorryyyyyyyy my sister, bana son naga sister ta cikin ɓacin rai, yanzu kinga na duka kasa ina baki hakuri, to kiyi hakuri ki tsaya ki gaya mini waye ya taɓaki muje na rama miki? Ai yayanki yana nan." Da gudu ta juya ta koma saman bed ɗin nata tare da faɗawa tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, wanda ita kanta bata san dalilin yin kukan nata ba. Da sauri ya miƙe ya rufa mata baya, saman bed ɗin ya hau dan kukan nata har cikin ransa yake ji, ba zai iya jurewa ba. Ɗagota ya yi tare da mannata da kirjinsa yana tallaɓo kanta da kyau da kyau. Idanunta a rufe ta fara kai mishi dukan huce takaici, tana yi tana kukanta, kankameta sosai ya yi a jikinsa yana bubbuga bayanta alamar rarrashi, sam taki yin shiru dan kukan zuciya take yi, tana yi tana wani irin shessheƙa wanda zai nuna maka zuciyar mutun a kusa yake, an kure hakurinta. Ganin haka ne na taki yin shiru ne yasa ya kwanta da ita tare da yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa a in da ya haɗe bakinsu waje guda ya fara kissing nata. Tamkar an ɗauke wutar nepa haka ta dakata cak da kukan da kuma dukan nasa da take yi. Da sauri ta kai hannunta saman idanunta ta murjesu da kyau, dan ta tabbatarwa da kanta ba fa mafarki take yi ba, tabbas namiji ne yake kissing nata. Wani irin azababben bakin ciki ne ta ji, a kule tasa karfinta dukka ta ture shi daga kanta. Da yake bai saka karfi a wajen kwanciyar tasu ba, dan bai yi tunanin zata ture shi ba, sai ya zamana da ta ture shi ɗin ya kuma turu, ya sauka daga kanta. A zafafe ta diro kasa daga saman gadon tare da nufar waje da gudu tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Gabaɗaya ya kasa mikewa ya bi bayanta, duk kasala ta sauka mishi a jikinsa, kwanciya kawai ya yi a saman bed ɗin yana sauke numfashi a hankali hankali, da haka har barci ɓarawo ya ɗauke shi a wajen. Ita kuma bedroom na daddynta ta shiga da gudu tana kuka. Tana zuwa ta faɗa jikin daddyn nata. Hankali a tashe yake tambayarta menene yake faruwa? Ko dai wani abin ne ya sami Areef. Cikin kuka take gaya mishi wlh Areef ɗan iska ne, kiss ya yi mata. Sam daddy bai san time da murmushi ma ta subce mishi ba, Areef da Jahan abin nasu ma sai ka rasa ta ina zaka ɓullo musu, amma dai yau kam bari ya kashe wannan wutar bakiɗaya. Rarrashinta ya fara yi tare da bata labarin Areef fa mijinta ne, shi ba ɗan iska ba ne, matarsa ya taɓa. Karo na farko a rayuwarta da ta ji wani azababben kunya ya kamata. Hannu tasa ta rufe fuskata tare da miƙewa da gudu ta bar ɗakin, sai yanzu ma take jin kunyar abin da ta gayawa daddyn nata. Shi dai daddy ina ruwansa da iya shegensu? Ba dai ya gaya mata gaskiya ba yau? To ta je su karata a can, ƴan rigima ne ai dukkansu biyu daga ita har Areef ɗin. Bedroom nata ta koma, a nan ta same shi ya yi mata barci a saman bed nata, bawan Allah ya gaji sosai. Kusa da shi ta zo ta zauna tana kare mishi kallo. Ita da kanta ta san Areef yama wuce irin mazan da mata suke burin mallaka, kyakkyawan gaske, natural beauty. Yana ta zuba barcinsa cikin kwanciyar hankali. Kayan jikinsa ta fara bi da kallo, da alama daga dawowarsa ko bedroom nasa bai shiga ba ya zo wajenta, dan ba kayan barci bane a jikinsa, shi ma da tsananin kewarta ya wuni. Wandon jeans ne da polo t-shirt a jikinsa, sai takalma Booth a kafarsa. Miƙewa ta yi a hankali tare da komawa kusa da kyawawan kafafunsa. A nutse ta kwance igiyar takalmar nasa tare da cire mishi su, ta ajiye a kasa. Ɗan motsawa ya yi kamar zai farka, tsit ta yi tana kallon shi. Bai farka ba sai dai ma ya gyara kwanciyarsa, ya cigaba da barci. Ta jima tana ta kare mishi kallo kafin ta miƙe ta ɗauko bargo da pillow ta dawo kasa ta kwanta abinta, ta bar mishi gadon, duk yunwan da take ji ma ta neme shi ta rasa, da haka barci ya ɗauketa ita ma cikin farinciki. Washegari da asuba, ko da ta farka sai ta kalleta a saman bed, shi kuma baya ɗakin, ko ba'a gaya mata ba ta san shi ya mayar da ita sama gadon. Dama kun san su TRIPLETS sun saba sallar dare, ya farka dan ya yi sallah ne ya ganta kwance a kasa, shi ne ya mayar da ita saman bed shi kuma ya koma bedroom nasa. Ta ji daɗi sosai. Toilet ta nufa, wanka ta fara yi kafin ta ɗauro alwala. Bayan ta idar da sallah ta sake kwanciya dan ta yi barcinta. Ba ita ta farka ba sai karfe 9. Wanka ta yi ta shirya cikin kananan kaya ta nufo waje dan ta je ta gaishe da daddynta, ta kuma yi breakfast, dan da wani azababben yunwa ta tashi. Dai'dai zata shiga bedroom ɗin na daddy shi kuma yana fitowa. Ɗaure fuska sosai ta yi tare da wucewa bata ce mishi ko sannu ba. Shi ma ɗaure fuska ya yi ya wuce abinsa. (Areef bai san Jehan ta san cewa shi mijinta bane yanzu, har da ɗaure mata fuska ya yi, ya wuce, irin yanzu ya zama yaya babban nan, boss baya son raini, lallai yanzu ne ma za'a fara sabon dirama, kuma sabon wasa, da alama ita ma zata wana shi.😂) Sai dai fa daga shi har ita ɗin suna wucewa kuma suka sake juyowa a in da suka lallaɓo a hankali dan su zo su leƙa juna. Yana leƙo cikin bedroom ɗin daddyn ita kuma ta leƙo waje, karaf suka haɗa ido. A sukawane ta juya da sauri dan ta wuce ciki. Cikin zafin nama ya rikota yana mai jawota jikinsa. Duka ta kai mishi a kirji na huce haushi meyasa ya leƙota. Kama hannun nata ya yi tare da kaiwa ɗan bakinsa ya sumbata yana faɗin. "Da ni da ke waye ne ya leƙo wani da kike jin haushi? Kawai kinga handsome guy ya wuce kin kasa hakuri kin zo zaki leƙa shi ko? To Allah ya kamaki." Wani irin kallo ta wurga mishi kafin ta ce ".............. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 *KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*. *KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 *Dedicated to Sadiya. Ubangiji Allah subhanahu wata'ala ya baki haihuwa, ya baki ƴaƴa kyawawan gaske masu albarka, Allah ya baki waƴan da zaki ce yi su yi bari su bari, Allah ya sa wannan jinkirin rashin haihuwar ta zama miki alkhari.* 82 TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ ❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋) *Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581* After some minutes da ba su wuce 40 ba, sai ga shi ya sauko kasa. A in da ya barta a nan ya dawo ya sameta. Cikin harshen Spanish ya ce da Mark ya ɗaure mishi matasa biyun nan dake zaune a saman sofa...... Bai kai karshen maganar ba idanuwansa suka sauka a kan Alex dake bayan Mark ɗin yana tsaye. Ɗan zaro idanu ya yi yana kallon shi. Shi kansa da kallon farko ya ɗauka Aseef ne, sai da ya kalle shi da kyau ya fahimci ba Aseef ɗin ba ne, amma ba karya sun yi kama na wuce misali. Kawar da kansa ya yi tare da miƙa mata hannu, da sauri ta taho ta faɗa jikinsa. Na san za ku so jin me ya je ya yi a sama, to ku saurara, binsu ya yi ɗaki ɗaki ya yi musu ɗaurin goro tare da ɗaure musu baki kamar an aikosa, kamar wasu kaji haka ya yi musu, harta tsofaffin wato yayyun Naurat ɗin bai bari ba, cikin dabara da salon iya aiki ya yi musu hakan ba tare da ya sami wata matsala ta sun yi mishi ihu ko makamancinsa ba, yakin sunkuru ya yi musu. To shi ne abin da ya je ya yi a saman ya dawo, yasan idan suka tafi da Rimsha tsab zata yi ihu ta tona mishi asiri, shiyasa ya bar Brady a mota. Idan taga ya toshewa mutun baki kuka zata fara yi, shi ne yasa ya barta a kasa tare da Mark, ya san waye Mark, haka kawai Allah ya sanya mishi kaunar Mark ɗin a cikin zuciyarsa, baya yarda da kowa, amma Mark yana da kusanci da zuciyarsa sosai, yana jinsa sosai a ransa. Massage ya yi wa sojojinsa a kan su shigo dan su fito mishi da kowa dake cikin ɗakunan da ya bi ya ɗauresu kamar kajin nan, ya san idan ba haka ya yi musu ba, to wlh ba za'a sami fahimta a tsakaninsu ba, za su iya kira mishi sojoji su tada yaki a tsakaninsu, shi dai baya barin ko ta kwana, idan aka kawo mishi wargi to fa zai yi ba dai'dai, kuma kakansa His excellency ya ce ya bi komai a hankali har ya shiga ya fito, babu wata hukuma da zata tare shi dan ya shirya musu makarkashiya, dama kuma kunsan kasar America gwana ce wajen shirya shiryen sheyen abubuwa, to shi ne yasa ma kuka ga ya shigo kasar lafiya lou, kuma shi ne yasa ya ɗauresu dan ya yi komai a tsanake. Ɗaukarta cancak ya yi suka koma saman. Bai zame da ita ko'ina ba sai ɗaki na karshe a sama bakiɗaya. Da akwai key a jikin kofar, dan haka sai ya murɗa ya buɗe. Bakinsa ɗauke da sallama suka shiga ciki. Jin sallama yau a gidan GENERAL TRUMP ne yasa a hanzarce ta ɗago kanta. Tana daga zaune saman bed ta kifa kai da gwiwowinta, da alama tana cikin tsananin damuwa. Dattijuwa ce, amma da yake jikin Turawa baya saurin nuna tsufa, suna da jiki mai kyau, sai tsufanta bai wani bayyana ba, idan ka ganta zaka ce 35 years gareta, gata kuma da ƙaramin jiki mai shegen kyau. Kyakkyawar gaske ce, fara tas tamkar ka taɓa jini ya zuba, ga dark black curly hair har bayanta a kwance. Ashe ita Rimsha ta ɗauko a gashi. Tsawon shekaru 33 tana kulle a cikin wannan ɗaki, ko waje bata leƙawa, babban yayansu wanda Lion ya fara ɗaurewa yanzu shi ne ya rufeta a cikin ɗakin, suna azabtar da ita a kan lallai sai ta dawo kafura ta fita daga addinin Musulunci, ita kuma ta ce sai dai su kasheta, amma wlh ba zata yi ridda ta zama krista ba, ta rigada ta musulta kenan, bata ga wanda ya isa ya mai da ita krista ba, shi ne suka rufeta, abin ci ne kawai yake sanyawa suke buɗeta. Duk kudin nan nasu dan bakin mugunta sau ɗaya suke bata abinci a rana, ruwa ma ɗan kaɗan suke bata, ta azabtu matika na tsawon waɗan nan shekaru, amma duk da haka bata ji kamar ma zata iya fita daga cikin addinin musulunci ba, sun hanata hijabi dan kada ta yi sallah, amma a hakan sai ta yafa wani abin ta yi, dai'dai da rana ɗaya lokacin sallah bai taɓa wuce ta ba. Daga karshe dai suka hakura suka barta a cikin ɗakin rufe kawai suna bata abinci sau ɗaya. Naurat ta sha bakar wahala sosai a rayuwarta, tasha na Amarya a Nigeria, ta kuma sha na ƴan uwanta a nan, ita da ta taso ƴar gata sosai, saboda su uku ne kawai mata a cikin yaran GENERAL TRUMP goma sha uku, goman dukka zaratan maza ne, su uku ne mata, da ita da kannenta mata biyu wanda su basu zaune a Russia ma, tun asali a America suka yi karatu, so suna can da zama basu dawo nan ba har yanzu, ita kaɗai mace ta rayuwa da daddynta, ya yi mata gata fiye da tunanin mai tunani kafin ya mutu ƴan uwanta maza su cigaba da kula da ita, haɗurwarta da Dr Salman a shopping ya fara canza komai, shi ne kuma mafarin wahalarta har zuwa yanzu. Karisowa cikin ɗakin ya yi tare da sauke Rimsha kasa. A gefen bed ɗin nata kusa da ita ya zauna, haka kawai Allah ya sanya mishi kaunar dattijuwan nan har cikin ransa, musamman idan ya tuna irin gwagwarmayar da ta sha a kan cewa ba zata bar addinin musulunci ba, sai ya ji ya kara kaunarta over. Cikin harshen turanci ya fara yi mata magana a nutse. Ya gaya mata ɗaukarta ya zo yi su koma Nigeria. Kin yarda da shi ta yi, duba da shi ma Bature ne, kafewa ta yi a kan cewa ita bata san Nigeria ba kuma bata da wata alaƙa da Nigeria. Baiwar Allah muryarta ma da kyar yake fitowa saboda jimawa da ta yi bata magana da kowa. Da hannu ya yi wa Rimsha alama a kan ta zo, da sauri ta kariso kusa da shi ta zauna. Dama kamar yasan Na'urat zata yi mishi gardama, shi ne yasa ya taho da Rimsha, idan baku manta ba da Jehan ya so zuwa ma, dan ita ce mai kama da daddynta, a wani ɓangare kuma yana son zuwa da Rimsha dan launin fatarta irin nasu family'n Dr Salman, yanda Na'urat ta sha wahalar nan baya jin kamar zai yi mata dole a rayuwarta, shi ne yasa yake binta a hankali. Cikin sanyin murya ya sake gaya mata da gaske shi ba cutar da ita zai yi ba, tafiya da ita ya zo ya yi dan ya mayar da ita cikin ƴaƴanta, hakan ce ma tasa ya zo mata da jikanta ƴar Nawazudden ɗinta dan ta shaida, ya san cewa ko zata manta kowa, to ba zata manta Nawazudden ba, dan shi ne ɗa mafi soyuwa a gareta. Ai kuwa duk kin yarda da ta yi da shi, jin ya ambaci sunan daddyn Rimsha sai da ta ɗago sosai tana kare musu kallo, sai dai fa ita a yanayin yanda take kallon face ɗin Lion da ƴan uwanta na nan yake yi mata kama, amma ganin Rimsha yasa ta ji ta yarda da su, duk da cewa Rimsha bata wani kama da daddyn nata, sai dai kama ta jini, da mum take kama. Kara yi mata bayani ya yi a nutse dallah dallah yanda zata fahimta, yanda kuma rikicin tsufa ba zai sanya ta kasa ganewa ba. A takaice dai ya yi babban sa'a ta yarda da shi dalilin Rimsha, dan haka sai ta amince zata bishi. Ya ji matuƙar daɗi sosai, shi da kansa ya taimaka mata ta miƙe tare da saukowa kasan bed ɗin. Sai murna Rimsha take yi yau ta ga kakanta mai tsananin kama da daddynta. Riko hannunta Naurat ɗin ta yi tana ji tamkar hannun Nawazudden ta rike, tana bala'in kaunar daddyn Rimsha da daddyn Anaya, tafi sonsu sama da kowa a cikin ƴaƴan nata. A hankali suka fito palo, nan ya iske kowa na gidan, gabaɗayansu sojojin sun fito da su sun zube su a palon. Sun yi mugun bashi haushi ne na izayar da suka rinƙa yiwa ƴar tahalikan nan na tsawon shekaru, ya so ne ma ya yanke wa kowannesu koda kunne ɗaiɗai ne, amma kuma yana sauri, dan haka sai ya kyale su kawai. Har ya kai bakin kofar palon rike da hannun Naurat ɗin ita kuma tana rike da hannun Rimsha. A hankali ya juyo ya ce da Mark ya kwance Alex da shi zasu tafi. Cikin girmamawa Mark ya ce yana neman alfarma Lion ya yi hakuri ya sanya a kwancesu, dan saboda uncles nasa ne, ƴan uwan daddynsa ne, dukka ya sansu ta cikin hoto, yana da hoton kowannansu, Alex ɗin ne kawai dama suke waya da shi, kuma Mark ɗin ne ya nemo number Alex ɗin dalilin wannan zuwa da za su yi. Shiru Lion ɗin ya yi yana mamakin, Allah mai iko, yau dai ga Mark a cikin family'nsa, Mark ɗin ma jikan gidan ne kamar dai su Rimshan. Jinjina mishi kai ya yi yana faɗin, ya barsu idan sun tafi za'a kwancesu, dan sun ɓata mishi rai fa. Haka ba dan ya so ba ya kyalesu, ya kwance iya Alex ɗin kawai sojojin suka sanya shi a gaba suka bar palon. Wani karfin hali sai wajen Lion, ya shigo har cikin kasarsu, kuma cikin gidansu, ya kuma ɗauki ƴar uwarsu da suka rufe tsawon shekaru, kuma a gaban idanunsu, ya kuma sa kafa ya fita, ba yanda suka iya da shi, wato a duniya idan kai wani nema fa ka ji daɗi, idan kana da goyon bayan manya daga sama ba abin da ba zaka aikata ba, kuma ka zauna lafiya, Allah ya yi wa dukkanin musulman duniya bakiɗaya arziki mai albarka mai kuma amfani. Koda bodyguards na gidan suka gansu, ko sannu basu ce musu ba, dan sun ga da ɗan gida suke tare, ga kuma Naurat, sai dai abin mamaki Alex ya kasa iya gayawa bodyguards ɗin abin da yake faruwa a cikin gida dan su hana su Lion fita, ya rasa ya akayi bakinsa ta yi mishi muguwar nauyi. A takaice dai haka suka sake fita daga gidan cikin waƴan nan motocin da suka zo ɗin, suka koma cikin jirgin ruwansu. Ba ɓata lokaci suka ɗauki hanyar komawa gida. Naurat a ɗakinsu ta zauna, dan ya kula da ita, yana jin tsantar kaunarta a ransa. After some hours. Bayan sun kama hanyar ne, jirgin ruwan nasu ya tashi, a nan ne yasa Mark ya turo mishi Alex. Har cikin ɗakin nasu Alex ɗin ya zo, saman sofa ya ce mishi ya zauna, ita kuma Naurat tana zaune saman bed nasu, Rimsha ta tada kai da cinyarta tana mai jin tsantar farinciki. A saman bedside drawer shi kuma Lion ɗin ya zauna. ❤️PRINCESS TEEMA💋......✍️ A nutse ya fara magana cikin harshen turanci, a in da ya gayawa Brr Na'urat cewa Alex fa yaronta ne ba ɗan yayanta TRUMP ba, zaro idanu ta yi tana mai gaya mishi ai ita yaron da ta haifa ya mutu, girgiza mata kai ya yi yana faɗin. "A binciken da nayi bai mutu ba, karya suka yi miki da ya mutu dan ma kada watara ya zo kawo miki abinci ki gaya mishi kece mamansa kuma ya musulta, shi ne yasa suka ce miki ya mutu, amma Alex ɗan ki ne, shi ne wanda kika baro Nigeria ba tare da kin san kina da cikinsa ba, sai da kika dawo nan da watanni kika san da hakan, so ba Abdul Malik ba ne autanki, Alex ne!." Babbar magana, zancen Lion gaskiya ne, bayan Naurat ta haifi cikin da daddyn Rimsha ya barota da shi, wato cikin daddyn Jelly, yana da shekara ɗaya da rabi a duniya sun sake samun kyakkyawar alaƙa da Dr Salman, da alama a lokacin asirin da amarya ta yi mishi ne ya karye, sun kowa kamar da, suna soyayya tare da kula da yaransu, suna kuma neman daddyn Rimsha, a lokacin shi kuma daddyn Rimshan yana Niger tare da abokinsa. Bayan wata uku da samun jituwar tasu suka sake komawa gidan jiya, faɗa kullum kullum, a lokacin ne kuma amarya ta karo sabon walaƙanci a in da ta mayar da Naurat ɗin ƴar aikinta, ganin ba zata iya jurewa ba ne yasa ta kira yayanta TRUMP a waya wato wanda aka ce shi ne mahaifin Alex yanzu, shi ne suka zo suka ɗauketa ta baro daddyn Jelly a hannun su Abba yana yaro, bai gama cika 2 years ba lokacin, sam bata san da shigar cikin Alex ɗin ba a lokacin, dan lokacin cikin bai kai ko wata ɗaya ba. Sai bayan ta koma Russia ne da ƴan watannin da ba su yi biyu ba, nan ta fahimci ciki ne da ita, a lokacin kuma tana shan azaba wajen ƴan uwanta, wanda hakan ya zama tana danasanin biyosu, dan fa mugaye ne kuma mafaɗata ne na karshe, basu da sauki ko kaɗan ga zafin ran bala'i, ta ce gara mata gidan Dr Salman sau dubu a kan abin da ƴan uwanta suke yi mata dan taki yin ridda. A takaice dai haka ta yi rayuwa cikin kunci har cikin Alex ya girma, lokacin da take nakuda ba wanda ya kulata a cikinsu sai matar kaninta ɗaya, ita ta taimaka mata har ta haihu, bayan ta aihu ne kuma suka zo suka ɗauki yaron, after some minutes suka dawo suka ce mata ai ya mutu saboda bata je asibiti ba, alhalin karya suke yi mata, basu so ne ta koyawa yaron addinin musulunci. Haka suka reni Alex cikin so da kauna a in da da ya taso suka ce mishi ai yayan Naurat ɗin shi ne babansa, shi kuma ya tafi a hakan, basu barin shi yana kai mata abinci, kowa zai kai mata abinci a gidan amma banda shi, dan sun san uwa da ɗa ba wasa ba, wani lokaci ma dan walaƙanci barinta suke yi ta kwana da yunwa sai su ce sun manta ne da ita yasa basu kai mata abinci ba, izaya kala kala suka rinƙa yi wa ƴar tahaliƙan nan, sai dai Allah ya saka mata kawai. Daga ita har Alex ɗin sun rasa bakin magana, Allah sarki yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ma Alex ɗin ya kasa gayawa bodyguards ɗin sacesu su Lion za su yi, uwa ba wasa ba, yau Allah ya ƙaddara ne zai gane ba Trump ba ne babansa. Sosai ya rinƙa kuka da hawayensa, sai tunanin irin izayar da suka rinƙa yi mata ya fara yi, ya ma kasa ɗaga idanu ya kalleta tsabar shiga tashin hankali da damuwa ga kuma murna a gefe. Kifa kansa kawai ya yi da jikin sofa yana kuka. Ita ma Na'urat ɗin kuka take yi sosai, ƴan uwanta sun cutar da ita sosai, yanzu ace ɗanta na cikinta ne ya taso a krista tsawon shekaru? Bai san komai ba dan gane da addinin babansa, wannan abin ya yi mugun yi mata zafi. Amma fa kuma abin mamaki shi ne, Alex ya fita daban a cikin ƴaƴan TRUMP ɗin, shi ne yasa ma wani lokaci yake jin kamar ba su ne iyayensa ba, na farko yana da kirki sosai shi, jinin Hausa Fulani Bauchi state kenan, wato Dr Salman, yana da son mutane da saukin kai, yana da fara'a tamkar Dr Salman, wani lokaci idan aka taɓo shi yana da zafin rai, sak da ainahin babansa, so abin yana bawa su ƴaƴan TRUMP ɗin ma mamaki, sai dai duk cikin ƴaƴan Brr ɗin babu wanda ya kai Alex ɗin fitowa sak Turawa babu mix, sak kakansu GENERAL TRUMP wato mahaifin Naurat kenan. Shi dai Lion ya yi shiru yana kallon yanda suke ta shan kuka dukkansu, ita ma Rimsha ta yi hawaye sosai na jin wannan labari nasu mai taɓa zuciya, mutun mahaifiyarsa tana raye amma dan bakin zalinci an hana ta bashi nono? Aka rinƙa ɗirkawa bawan Allah madara, Allah sarki, wlh zalinci bai yi ba, duk abinsu dai yau ga shi ya haɗu da mahaifiyar tasa, kuma da izinin Allah sai ya musulunta, bakinciki ya kashesu. Sun sha kuka kamar ba gobe, shi dai Lion bai iya ce da su komai ba, bai ma san me zai ce musu ba, haka ya zuba musu idanu suka yi kukan har ya ishe su. Sannan Alex ɗin ya mike ya dawo kusa Brr. Mikewa Rimsha ta yi daga saman cinyar tata ta bashi waje. Yana zuwa ya rungumeta yana jin tamkar ya koma ya kashe uncles nan nasa bakiɗaya na irin izayar da suka yi mata, zuciyarsa sai tafasa yake yi tamkar zata fashe. Rungume shi Brr Naurat ɗin ta yi tana rarrashinsa har sai da ya yi shiru. Miƙewa Lion ya yi tare da riko hannun Rimsha suka bar musu ɗakin zuwa na kusa da su, dan su basu dama su tattauna. Shi ma Lion ɗin yana son ya yi sallar azahar dan lokaci ta yi. Rimsha tamkar zata yi kuka haka ta biyo shi, sam bata son rabuwa da kakanta, amma ba yanda ta iya. Suna shiga cikin bedroom ɗin ya saki hannunta tare da nufar toilet. Zama ta yi a saman bakin bed ɗin tana jiran shi ya fito. Wanka ya yi tare da ɗauro alwala ya fito. Ganin face nata a ɗaure tamau ne yasa ya ce lafiya take wannan ɗaure fuska, turo baki ta yi tana faɗa mishi ita wajen kakanta take son zuwa, da hannu ya nuna mata hanyar tafiya. Da sauri ta miƙe ta fita, har ta kusa kifawa saboda sauri. Shi kam ko a jikinsa, dadduma kawai ya ɗauko tare da shumfuɗawa dan ya gabatar da sallah. Tana zuwa ta sami sun gama shan kukan suna tattaunawa, hayewa saman bed ɗin ta yi tare da komawa ta kwanta saman cinyar Brr. Kallonta Alex ɗin ya yi yana tambayar Brr wace ce ita. A takaice ta bashi labarin su daddyn Rimshan wato ƴan uwansa. Sosai ya ji tsananin kaunarsu a ransa. Shafa kumatun Rimshar ya yi yana mai jin kaunarta ita ma, ƴar autar family'n Dr Salman kenan. Duk familyn Dr ita ce karama, ita ce autarsu, daga ita sai Zaira kanwar Anaya, sannan Jehan da Anaya wanda su shekarunsu ɗaya, ratar ƴan watanni ne kawai. Shi kuwa Mark yana can yana hira da Anaya a waya, a in da yake gaya mata nan da kwana huɗu zasu dawo dan tafiyar tasu ta canza salo. Sai murna take yi ya ce zai zo gidansu. Shi Mark sam bai san cewa ba za'a bashi auren Anaya ba har sai ya musulunta, ya ɗauka za'a iya bashi ita a haka, shiyasa ma har da ce mata zai zo yaga daddynta........ E lallai akwai chakwakiya. After some hours. Da misalin karfe 8 na dare, bayan sun yi sallar isha kenan, gabaɗaya kewar mijin nata ya isheta, ga shi tana kunyar barin Brr Naurat ta je wajen shi, shi kuma sam yaki zuwa in da suke, ya kule a cikin bedroom nasa yana aikin latsa laptop nasa, Brady na kwance kusa da shi. Brady na Mark, kwana biyun nan duk a wajen Mark yake kwana, sam yanzu ya rage zuwa wajen Lion ɗin, sai jefi jefi, Mark ya saye shi ta hanyar kunna mishi kallo a waya da sauransu, shi ne ya saye zuciyarsa. Alex yana tare da Mark a waje suna hirar yanda Mark ya yi rayuwa da kuma mutuwar iyayensa wato causing ɗin Alex ɗin kenan, Mark zai kira Alex uncle dan causin ɗin daddynsa ne. Cikin harshen turanci Brr Naurat take ta tambayar Rimsha labarin daddynta da sauransu. Sai hira Rimahar take zuba mata na mutanen Nigeria, amma fa hankalinta na wajen tunanin mijinta, duk ta damu, tun da rana bata sake saka shi a idanunta ba. Sarai Naurat ta lura da tana cikin damuwa, hakan yasa ta yi ƙoƙarin tambayarta me yake damunta. Babu komai ta ce mata, a haka har Mark ya kawo musu abinci. Kin cin abincin ta yi dan tana tunanin zata je su ci da mijinta. Muryar Brr ɗin ce ta katse mata tunani da cewa "Wanene wannan da ya ɗauko ni ɗin?." Shiru ta yi ta rasa me zata ce, ta ce mata mijinta ne ko ta ce mata me?. Ganin ta yi shiru ne yasa ta ce "Kunyata kike ji ne?." Girgiza kai ta yi alamar a'a. Murmushin Brr ta saki har sai da dimple nata irin na ƴaƴanta Nawazudden da Azharuddeen ya bayana, dama a wajenta su daddyn Rimsha suka ɗauko dimple da gaf teeth. "Rimsha kunyata mana kike ji, ai na san ku mutanen Nigeria sai ku rinƙa cewa wai kuna jin kunyar abu, haka kakanki Dr yake yi wani lokaci, to amma idan har kina jin kunyata haka a kansa, hakan na nufin kuna da wata alaƙa da kusa kenan?." Shiru ta yi tana murmushi tare da sanya hannu ta rufe fuska. "Rimsha kada ki ce mini aure Nawazudden ya yi miki? A ƴar yarinyar kin nan? Duk da a family'n Dr nasan suna aurar da yara 12 to 13 years ma, amma ai su a kauye suke, ba su ma yi karatu ba, shi kuma Nawazudden me ya haɗa shi da irin wannan al'adar ta kakanin nasa? Ai kinyi yarinya da yawa." Ita dai bata ce komai ba bayan wannan rufe fuska da ta yi. "Amma kuma gaskiya na yi miki murna na samun miji irin wannan bawan Allah, yana da kirki sosai." (Ni kuwa na ce ke dai kin yi sa'a da kika ga fuskar kirkin nasa, dan haka ki yi fata kada ki haɗu da ainahin true colornsa, idan kika kuskura kika yi ido huɗu da ainahinsa, daga ranar ba zaki ma sake yin maganarsa ba, saboda haushi da zai baki, ya kuma birkita miki tunani.) "To amma Rimsha shi ne kika zauna a nan baki je wajen shi ba?." Tana magana tana cin abincin cikin natsuwa. Baki ɗauke da excuse Alex ya shigo cikin ɗakin. Jin abin da Brr ta ce ne yasa ya ce "Mum a kan me kuke magana ne?." Cikin nuna ko in kula ta bashi labari. Zaro idanu ya yi yana mamakin ƴar Rimshan nan ne aka yi wa aure? Kare mata kallo ya fara yi daga sama har kasa, shi dai bai ga abin da za'a aurar ba, kuma aure ma ga namiji kamar Lion? Wannan ai sai ya kasheta kawai a karon farko, sake baki ya yi yana jinjina al'amarin. Bai san cewa sune suke rena Rimsha ba, suna yi mata kallon yarinya, to su biyota ɗaki suga yanda take sanya Lion ɗin sambatu da kuma sauka daga layi, yo ai kamar yanda namiji baya kaɗan haka ita ma mace bata kaɗan, in dai ta wuce 13 years kuma ta samu tarbiya ai shikenan an gama. Katse mishi tunani Brr ta yi da cewa ya zo su ci abinci, ita kuma Rimsha ta tashi ta wuce wajen mijin nata. Jiki ba kwari ta miƙe ta fita tana yi musu sai da safe. Shi kuma Alex kusa da mum ɗin tasa ya zo ya zauna saman ɗaya daga cikin kujerun table ɗin. Cikin tsantsar soyayya irin ta uwa da ɗa suka fara cin abincin a tare. Ita kuma Rimsha baki ɗauke da sallama ta shigo cikin ɗakin nasu. Tamkar babu shi a cikin ɗakin, ko kallon in da take bai yi ba, kamar ma bai san da shigowarta ba. Toilet ta wuce sai wani ɗari ɗari take yi. A gurguje ta yi wanka tare da fitowa, ta yi mamakin ganin trolleys nasu a cikin bedroom ɗin, bata san cewa shi ya ɗaukosu tun da rana ba, tana can tana surutu da kakanta. Cikin wasu shegun kayan barci ta shirya, masu matuƙar ɗaukar hankalin, riga ce zuwa iya dai'dai santala santalan cinyoyinta, daga ta saman rigar hannun vest ce gareta, gabaɗaya tudun tula tulanta a waje, bugu da kari rigar ƴar shara shara ce bata da kauri, ainahin zanen shatin tula tulan nata ma a waje, har kan nipples nata shatinsa ya bayyana. Sake gashin kanta ta yi har baya tare da zuba perfume nasa a jikinta. Sai wani irin sheki santala santalan cinyoyinta suke yi, ta shafesu da Lotion nasa, ita kanta sai sheki take yi. Shi kuwa hankalinsa yana kan laptop nasa, da alama dai wani aiki mai muhimmanci yake yi. Saman table ta nufa, dan already shi ya ci abincinsa. Zama ta yi tare da zuba abincin ɗan kaɗan. A nutse ta fara ci tana satar kallonsa. Shi ma kayan barci ne launin white color a jikinsa, ya yi matuƙar kyau over, ya saki dark black curly hairnsa, sai ɗan ciza laɓɓansa yake yi a hankali, da alama aikin yana ɗan bashi wahala. Gabar rigar barcin nasa a buɗe ne mai wuyar V, faffaɗar kirjinsa a waje, wannan kyakkyawa kuma kwantatcen bakin gashi nan na kirjin nasa a kwance luf yana wani sheƙi. Jin azababben kamshin perfume ɗin ya kai mishi karo a hancinsa ne yasa ya ɗan ɗago idanunsa izuwa kanta, dai'dai lokacin ita ma ta ɗago dan ta saci kallon shi. Karaf suka haɗa idanu. Kasa ta yi da nata tana ɗan murmushi, shi kuwa zuba mata idanu ya yi yana kallon ikon Allah, wani irin azababben kyau na wuce misali ta yi. Duk sai ta ji ta tsargu saboda kallonta da yake yi, wani irin kunya ce ta ji ta lulluɓeta, ƴan kame kame ta fara yi tana wani yin abu kamar mara gaskiya, dama kun san idan mutun ya tsareka da ido yana kallonka, duk sai ka tsargu, to ita ma haka ce. Kasa cigaba da cin abincin ta yi a in da ta miƙe kawai ta nufe shi tana wani sunnar da kai kasa tare da ɓoye fuska na rashin kunya. Time da zata sanya kayan bata yi tunanin cewa zata ji kunya idan ya gani ba, sai yanzu ne take wani sunnar da kai na rashin kunya. Tana zuwa ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa tana cigana da ɓoye fuska. Haushi Brady ya fara daka mata na a kan me zata kwanta mishi a jikin Lion ɗinsa. Tamkar bata ji yanayi ba, sai ma kara saƙalo wuyarsa da ta yi tana wani ɗan turo baki tare da yi mishi yauki da yanga. Cikin dabara ya kawar da laptop ɗin daga gabansa zuwa saman bedside drawer, hannu bibbiyu yasa ya rungumota da kyau yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya. Ba karya ya yi kewarta sosai, kawai wannan aikin ne ta sha kansa da ta sanya bai je ya ɗaukota ba, ita ma ta yi kewar shi sosai, dan haka yana rungumeta ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya. "Noori Allah nayi kewarka sosai yau." Ta yi maganar tamkar zata saka mishi kuka. Ɗan ɗago haɓarta ya yi suna fuskantar juna. "To ba gani yanzu kin zo gare ni ba?." Jinjina mishi kai ta yi tana mai kara rungumo shi sosai. Haɗe fuskokinsu waje guda ya yi yana kara kare mata kallo. "Noori meyasa kake yawan son kallona?." Ta tambaye shi a shagwaɓe. Dirowa kasa Brady ya yi ya wuce zuwa wajen Mark abinsa, dan ya lura Lion fa ba tashi yake yi ba. Ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya bata amsa da cewa "Because you are mine." Zaro idanu waje ta yi, bata taɓa tunanin zai ce ita mallakinsa ba ne, kai Lion da abin mamaki yake, baka taɓa game mishi, idan ya yi wani abin sai kaga kamar ba shi ba. Ganin ta zaro idanu ne yasa ya ɗaura lips nasa a saman tata tare da fara kissing nata a nutse. Tamkar jira take yi ita ma ta fara mayar mishi da martani. Kankame juna sosai suka yi. A hankali ya fara romancing nata, daga karshe sai ya kwanta tare da ita a jikin nasa a in da ya ja musu bargo suka kule a ciki, a nan ne ya fara romancing nata da zafa zafa. Tun tana ƙoƙarin taya shi har ta kasa dan ya kureta, tuni ya rabata da kayan jikinta ya shiga murzarta da kyau da kyau, sai dai fa yanayi yana taka tsantsan dan tsaro, bai zurfafa da yawa ba. A haka ƴar lallaɓawar ma sai da ta yi mishi kuka, yana birkita mata tunani ne sosai. Kuka ta rinƙa yi mishi shi kuma yana zuba mata sambatu. Sai da ya ɗan ji sauki sauki a jikinsa, sannan ya rabu da ita tare da kwanciya gefe ya jawota jikinsa, kashe wutar ɗakin ya yi da kuma kara musu gudun Ac. Kankame shi ta yi tare da lafewa shiru tana shakar daddaɗar kamshinsa har barci ya yi awon gaba da ita. Shi ma ba jimawa barci ta ɗauke shi. ASUBA TA GARI. AFTER SOME DAY'S💋 ❤️PRINCESS TEEMA💋......✍️ AREEF AND JEHAN. Yau ta kama Monday, kuma a yau ne game nasu ya zo ƙarshe. Tun safe da misalin karfe 7 ya shirya ya bar gidan, ba komai yasa ya bar gidan ba sai dan ya yi maganinta kuma ya tantance tana son shi ne ko bata son shi. Tana can cikin bedroom nata tana zuba barcin da ta saba, dan ita wani lokaci ma sai 11 na safe take tashi daga barci, sam bata san tsiyar da gogan nata ya shirya mata ba. Aseef da Akila ma sai zuba barcinsu suke yi. Wannan gida dai kun sani ba sai na sake faɗa ba, gida ne na yara jiki dukka madara iyaye jiki dukka madara, ba ƴaƴan malam shehu ba ne, sai su yi ta zuba barcinsu son ransu, sai time da suka ga dama suke tashi, ba wanda zai tashesu daga barci, idan yunwa ta tasheka ma to sojoji masu yin girki dai sun gama aikinsu, bayin Allan tun karfe 7 suke gama komai su jere a saman table, amma mutanen gidan nan ne su zo su ci ya zama tashin hankali, wasu ma sai 12 suke cin abincin, irinsu daddyn Rimsha kenan, ita kuwa Jehan duk time ɗin da ta tashi barcin take ci. Haka suma Aseef da Akila, duk time da suka tashi suke ci. Shi kuwa daddynsu Lion, wani lokaci ma ba cin abincin safen yake yi ba, sai dai su sha green tea shi da uncle Herry. Mutane ne dai gasu nan kala kala, iri irin ra'ayi sun iya, kowa da kalar tasa, ba zaka taɓa sanin ina ma suka dosa ba, kowa kawai abin da ya zo mishi cikin ƙwaƙwalwarsa yake aikatawa. Shi John ma ai dama sai ya sha giya ya bugu da daddare tukun nan yake yin barci, shiyasa idan ya fara barcin safe baya tashi da wuri, wani lokaci sai karfe 2 ko 3 na rana, sai lokacin da giyar ta sake shi, ga shi baya yi mata shan wasa. Shi kuwa Jay ɗan ba ruwana, matarsa yake kira a waya su yi ta zuba soyayya har dare ya tsala, wani lokaci ma sai asuba ya gabato yake hakura su yi barci, shiyasa shi ma baya tashi da wuri, sai ya kai 10 or 11, kai a takaice ma duk gidan ba mai tashi barci kasa da karfe 8 sai masu aiki, sojoji, sai kuma Lion da shi dama bai damu da yin barcin safe ba. Lokacin da Rimsha take zuwa school ne tana tashi da wuri. Yanzu ma duk sai zuba barcinsu suke yi, shi uncle T tun ranar da ya zo, ya saka kafa ya bar gidan bai kara dawowa ba, ya tafi yawonsa, sai Allah kaɗai ya san mishi in da ya tafi. Da misalin karfe 11 dai'dai ta farka daga barci. Ko da ta farka ta jima a kwance har 11:30, sannan ne ta lallaɓa a hankali ta sauko kasan bed ɗin, ta nufi toilet. Wanka ta yi tare da dawowa ta shirya cikin wandon jeans baki da t-shirt maroon. Ta yi kyau sosai, dama ita bata son manyan kaya, kuma dama bata saba sakawa ba idan baku manta rayuwarsu a baya ba. Fitowa ta yi ta nufi bedroom ɗin daddynta, a duk tunaninta zata sami Areef a wajen, dan yau da kewarsa da kuma tunaninsa tare da begen son ganinsa ta tashi. Amma ko da ta shiga baya nan, daddyn nata kawai ta samu kwance a saman bed yana latsa wayarsa, sai murmushi yake yi. Chatting suke yi da Rimsha, amma sam bata gaya mishi sun ɗauko Na'urat ba, dan Lion ya ce kada ta gayawa kowa, hakan yasa bata faɗa ba. Sai zubawa daddyn nata shagwaɓa take yi a kan tana kewarsa, shi kuwa ya ce mata ba wani nan, ba tana tare da GAR ba? Yasan ba wani kewarsu da take yi, kawai wayancewa take son ta yi mishi dan ya ce mata yana kewarta. Voice ta yi mishi a in da take zuba mishi kukan shagwaɓa a kan lallai ita wlh tana kewar shi over. Guntun tsaki Jehan ta ja tana ji kamar ta damƙo Rimshar nan ta bata a jikinta, saboda a cewarta duka Rimsha take so, wani kayan takaice har da kuka a cikin voice ɗin. Shi dai daddy da yake ya san matsalar baby Jehan ɗin tasa, sai ya miƙe zaune tare da ajiye wayar a gefe yana ce mata sarkin rigima an tashi?. Turo baki ta yi tana ce mishi "Good morning dad." "Morning my daughter how are you doing?." Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Daddy i wanted to eat something, am feeling hungry." Ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufo palo. Kasa ta nufa dan a can table na kasan ake jere abinci. Zuba kalar wanda take so ta je ta yi, ga abincin kala kala sama da kala goma jere cike a saman table ɗin, zaɓa ta yi wanda ya yi dai'dai da ra'ayinta, sannan ta ɗeba tare da haɗo duk wasu abin da zata buƙata ta koma saman. Bedroom ɗin daddy ta koma, saman lallausan carpet na kusa da bed ɗin ta zauna tare da zube abincin a kasan, har lokacin bata cire tsammani Areef zai shigo cikin ɗakin ba, sai dai kuma har ta ci abincin ta kammala sam bai shigo ba. Hira suka yi ta zubawa da daddy bayan ta kammala har zuwa azahar, a nan ne suka yi sallama ta koma bedroom nata dan ta yi sallah. Shi ma daddy ya miƙe ya shiga toilet. Bayan ta idar da sallah ne sai ta fara tunanin to yau ina Areef ya je? Kuma ga daddynta a gida bai fita ba bare ace sun fita tare, to shi ina ya je?. Haka dai abu ya fara tsamari har zuwa la'asar bata gan shi ba, ta kuma kasa tambayar daddynta ina yake, ta kasa cin abincin rana, ta shiga damuwa sosai da sosai na wuce misali. Hayewa saman bed nata ta yi da yamma kenan bayan ta yi sallar la'asar. Duk ta damu fiye da tunanin mai tunani, kwanciya shiru ta yi tana tunanin abubuwan da suka rinƙa faruwa a tsakaninta da shi, bata san time da ruwan hawaye ya fara bin kuncinta ba, ta kasa goge hawayen, haka ta barshi ya cigaba da zuba, idan ta rufe idanu face nasa kawai take gani yana murmushi, tana jin yunwa amma ta kasa iya cin abinci. Wasa wasa har ta yi sallar isha bai dawo gidan ba, abin ya isheta har ta fito zuwa bedroom nasa dan ta duba shi. Ko da ta je babu shi babu alamarsa. Bedroom nata ta koma, yau ta kasa zuwa su yi hira da daddynta ma. Tana zuwa ta haye saman bed nata ta hau kuka, yunwa kamar zai kasheta amma sam ko kallon in da abincin yake ma ta kasa, ga shi bata da phone numbersa. Hawaye ne wani na bin wani a saman kuncinta tana daga kwancen, Allah sarki wlh har faɗawa ta yi na wuni ɗaya, har ta ɗan rame, idanunta sun kara fitowa sosai, kun san idan mutun ya rame idanunsa suna kara girma, to ita ma hakan ce ta kasance da ita. Har karfe 10 na dare bai dawo ba, ita kuma bata dai'na ruwan hawaye ba, ga uban yunwa, sai dai idan ta gaji da kwanciya ta juya ta nan, idan ta sake gajiya ta juyo, duk ta jike lallausan pillownta da hawaye. Duk wannan halin da ta shiga daddynta yana sane da ita, amma sam bai kulata ba, saboda shi da kansa ya ji daɗin abin da Areef ɗin ya yi mata, yanzu ai zata san cewa yana da matsayi a cikin zuciyarta. Tana tsaka da kukanta hawaye wani na bin wani, ta luluƙa duniyar tunaninsa. Tamkar daga sama ta ji ana goge mata hawaye, sam bata ji shigowar mutun ba. A hanzarce ta waro idanunta sosai tare da miƙewa zaune. 4 eyes suka yi da shi yana zaune saman bedside drawer, hannunsa na rike da handkerchief fari kal mai bala'in laushi kamar audiga. "Jehan meyasame ki kike kuka?." Kai Areef ɗan duniya ne number ɗaya, wato ya nuna irin shi bai san komai ɗin nan ba. Wani irin harara ta wurga mishi da idanunta da suke jawur saboda kukanta da ta ci ta koshi. A hanzarce ta diro kasa daga saman gadon tare da nufar hanyar barin ɗakin wai bata son ganin shi. Cool murmushi ya saki tare da miƙewa da sauri ya tare gabanta. "Jehan What is wrong with you ne? Ina yi miki magana, you have to be amsa me first before ki fita ko? Ko kin manta ni yayanki ne?." Haushi tamkar ta rataye kanta, raɓawa gefensa ta yi zata wuce tana wani hucin da ita kanta bata san dalilin yin shi ba. ❤️PRINCESS TEEMA💋......✍️ Sake tare gabanta ya yi tare da zube gwiwowinsa a kasa ya kuma kama kunnensa yana faɗin "Am so so sorryyyyyyyy my sister, bana son naga sister ta cikin ɓacin rai, yanzu kinga na duka kasa ina baki hakuri, to kiyi hakuri ki tsaya ki gaya mini waye ya taɓaki muje na rama miki? Ai yayanki yana nan." Da gudu ta juya ta koma saman bed ɗin nata tare da faɗawa tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, wanda ita kanta bata san dalilin yin kukan nata ba. Da sauri ya miƙe ya rufa mata baya, saman bed ɗin ya hau dan kukan nata har cikin ransa yake ji, ba zai iya jurewa ba. Ɗagota ya yi tare da mannata da kirjinsa yana tallaɓo kanta da kyau da kyau. Idanunta a rufe ta fara kai mishi dukan huce takaici, tana yi tana kukanta, kankameta sosai ya yi a jikinsa yana bubbuga bayanta alamar rarrashi, sam taki yin shiru dan kukan zuciya take yi, tana yi tana wani irin shessheƙa wanda zai nuna maka zuciyar mutun a kusa yake, an kure hakurinta. Ganin haka ne na taki yin shiru ne yasa ya kwanta da ita tare da yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa a in da ya haɗe bakinsu waje guda ya fara kissing nata. Tamkar an ɗauke wutar nepa haka ta dakata cak da kukan da kuma dukan nasa da take yi. Da sauri ta kai hannunta saman idanunta ta murjesu da kyau, dan ta tabbatarwa da kanta ba fa mafarki take yi ba, tabbas namiji ne yake kissing nata. Wani irin azababben bakin ciki ne ta ji, a kule tasa karfinta dukka ta ture shi daga kanta. Da yake bai saka karfi a wajen kwanciyar tasu ba, dan bai yi tunanin zata ture shi ba, sai ya zamana da ta ture shi ɗin ya kuma turu, ya sauka daga kanta. A zafafe ta diro kasa daga saman gadon tare da nufar waje da gudu tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Gabaɗaya ya kasa mikewa ya bi bayanta, duk kasala ta sauka mishi a jikinsa, kwanciya kawai ya yi a saman bed ɗin yana sauke numfashi a hankali hankali, da haka har barci ɓarawo ya ɗauke shi a wajen. Ita kuma bedroom na daddynta ta shiga da gudu tana kuka. Tana zuwa ta faɗa jikin daddyn nata. Hankali a tashe yake tambayarta menene yake faruwa? Ko dai wani abin ne ya sami Areef. Cikin kuka take gaya mishi wlh Areef ɗan iska ne, kiss ya yi mata. Sam daddy bai san time da murmushi ma ta subce mishi ba, Areef da Jahan abin nasu ma sai ka rasa ta ina zaka ɓullo musu, amma dai yau kam bari ya kashe wannan wutar bakiɗaya. Rarrashinta ya fara yi tare da bata labarin Areef fa mijinta ne, shi ba ɗan iska ba ne, matarsa ya taɓa. Karo na farko a rayuwarta da ta ji wani azababben kunya ya kamata. Hannu tasa ta rufe fuskata tare da miƙewa da gudu ta bar ɗakin, sai yanzu ma take jin kunyar abin da ta gayawa daddyn nata. Shi dai daddy ina ruwansa da iya shegensu? Ba dai ya gaya mata gaskiya ba yau? To ta je su karata a can, ƴan rigima ne ai dukkansu biyu daga ita har Areef ɗin. Bedroom nata ta koma, a nan ta same shi ya yi mata barci a saman bed nata, bawan Allah ya gaji sosai. Kusa da shi ta zo ta zauna tana kare mishi kallo. Ita da kanta ta san Areef yama wuce irin mazan da mata suke burin mallaka, kyakkyawan gaske, natural beauty. Yana ta zuba barcinsa cikin kwanciyar hankali. Kayan jikinsa ta fara bi da kallo, da alama daga dawowarsa ko bedroom nasa bai shiga ba ya zo wajenta, dan ba kayan barci bane a jikinsa, shi ma da tsananin kewarta ya wuni. Wandon jeans ne da polo t-shirt a jikinsa, sai takalma Booth a kafarsa. Miƙewa ta yi a hankali tare da komawa kusa da kyawawan kafafunsa. A nutse ta kwance igiyar takalmar nasa tare da cire mishi su, ta ajiye a kasa. Ɗan motsawa ya yi kamar zai farka, tsit ta yi tana kallon shi. Bai farka ba sai dai ma ya gyara kwanciyarsa, ya cigaba da barci. Ta jima tana ta kare mishi kallo kafin ta miƙe ta ɗauko bargo da pillow ta dawo kasa ta kwanta abinta, ta bar mishi gadon, duk yunwan da take ji ma ta neme shi ta rasa, da haka barci ya ɗauketa ita ma cikin farinciki. Washegari da asuba, ko da ta farka sai ta kalleta a saman bed, shi kuma baya ɗakin, ko ba'a gaya mata ba ta san shi ya mayar da ita sama gadon. Dama kun san su TRIPLETS sun saba sallar dare, ya farka dan ya yi sallah ne ya ganta kwance a kasa, shi ne ya mayar da ita saman bed shi kuma ya koma bedroom nasa. Ta ji daɗi sosai. Toilet ta nufa, wanka ta fara yi kafin ta ɗauro alwala. Bayan ta idar da sallah ta sake kwanciya dan ta yi barcinta. Ba ita ta farka ba sai karfe 9. Wanka ta yi ta shirya cikin kananan kaya ta nufo waje dan ta je ta gaishe da daddynta, ta kuma yi breakfast, dan da wani azababben yunwa ta tashi. Dai'dai zata shiga bedroom ɗin na daddy shi kuma yana fitowa. Ɗaure fuska sosai ta yi tare da wucewa bata ce mishi ko sannu ba. Shi ma ɗaure fuska ya yi ya wuce abinsa. (Areef bai san Jehan ta san cewa shi mijinta bane yanzu, har da ɗaure mata fuska ya yi, ya wuce, irin yanzu ya zama yaya babban nan, boss baya son raini, lallai yanzu ne ma za'a fara sabon dirama, kuma sabon wasa, da alama ita ma zata wana shi.😂) Sai dai fa daga shi har ita ɗin suna wucewa kuma suka sake juyowa a in da suka lallaɓo a hankali dan su zo su leƙa juna. Yana leƙo cikin bedroom ɗin daddyn ita kuma ta leƙo waje, karaf suka haɗa ido. A sukawane ta juya da sauri dan ta wuce ciki. Cikin zafin nama ya rikota yana mai jawota jikinsa. Duka ta kai mishi a kirji na huce haushi meyasa ya leƙota. Kama hannun nata ya yi tare da kaiwa ɗan bakinsa ya sumbata yana faɗin. "Da ni da ke waye ne ya leƙo wani da kike jin haushi? Kawai kinga handsome guy ya wuce kin kasa hakuri kin zo zaki leƙa shi ko? To Allah ya kamaki." Wani irin kallo ta wurga mishi kafin ta ce ".............. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥 *KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*. *KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*. ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S ❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥 83 TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️ ❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋) *Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581* ❤️Dedicated to myself.....✍️💋 "Da ni da ke waye ne ya leƙo wani da kike jin haushi? Kawai kinga handsome guy ya wuce kin kasa hakuri kin zo zaki leƙa shi ko? To Allah ya kamaki." Wani irin kallo ta wurga mishi kafin ta ce "Au da gaske?." Gyaɗa mata kai ya yi yana faɗin "E mana". Shiru ta ɗan yi Kafin ta ce "Okey rufe idanunka bari na gani da ni da kai waye ne ya leƙo wani". Kasa kasa ya ce "Wayo zaki yi mini ne yauwa?." Juya idanunta sama ta yi tambayar mai tunanin wani abin. Shiru ya zuba mata idanun yana kallonta tare da kara kankameta sosai. Ɗan ɗago kafafunta ta yi dan tsawonta ya yi daidai da na shi, amma bata iya cinwa kunnensa ba, magana take son gaya mishi dama. Ganin hakan yasa ya ɗan rakwafo kaɗan dan ya bata damar faɗan abin da take son faɗa. Kara ɗaga kafafunta ta yi a in da ta cinwa kunnen nasa. Kasa kasa kamar mai raɗa ta fara yi mishi magana a cikin kunnen nasa. Zaro idanu waje ya yi yana sauraronta, bai san time da ya saketa daga rungumar da ya yi mata dan ya sami damar kallon face nata ba. Shafa gefen kunatunsa ta yi tare da wucewa da sauri izuwa cikin ɗakin daddyn nata tana murmushi. Shi kuma sai Allah kaɗai yasan me ta gaya mishi da ya sanya shi ya yi suman tsaye, kamar ba shi ba, haka ya lula duniyar tunani. Almost 2 mins yana tsaye a haka kafin daga bisani ya bi bayanta izuwa bedroom ɗin. Kwance saman bed ya iskota tana zubawa daddy hira. Kusa da ita ya zauna yana faɗin "Uncle wannan Jehan ɗin ko?." "Me kuma ta sake yi maka?." Zai yi magana suka haɗa ido da ita, kashe mishi ido ɗaya ta yi tare da haɗa mishi da harara. Shiru ya ɗan yi, can kuma kome ya tuna, sai ya saki cool murmushi tare da miƙewa yana faɗin "Uncle tom ka ce ta kawo mini breakfast na ɗaki, ba zan iya ci a palo ba." Zaro idanu ta yi tana faɗin "A'a daddy, gaskiya ni ba zan je bedroom nasa ba". Kallon shi daddyn ya yi tare da cewa "Just ka bata umarni kai tsaye, daga yau ba sai ka ce nace mata ta yi kaza ba, ka wuce sai ka sani na saka ta yin abu, idan ka ce ta yi ma ya wadatar." Matsowa ya yi tare da sumbatar daddyn a kumatu yana faɗin "Love you my uncle" "Love you too my son." Harara ta bishi da shi tana turo baki. Kashe mata ido ɗaya ya yi yana mai cigaba da murmushi. Ficewa ya yi daga ɗakin abinsa. Yana fita daddyn ya ce ta tashi ta je ta kai mishi abincin. Ba dan ta so ba ta mike, sam bata son su keɓe saboda tasan abin da ta gaya mishi a kunne ba zai barta ba, sai ya yi mata ba dai'dai ba. Kamar zata yi kuka ta nufo wajen. Saman table na palon kasa ta nufa, abincin da ranta yake so ta haɗa mishi tare da ɗauka ta nufi ɗakin nasa. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga, yana zaune a bakin bed nasa yana waya da Lion a kan gobe zasu shigo Nigeria, sai murna yake yi, ya yi kewar Lion ɗin sosai, ya jima bai ji rigimar Rimsha ba, ga shi yanzu ta zama rigimammiya number ɗaya. "Lion am feeling like something is going wrong". Cewar Areef ɗin kenan. Daga ɗayan ɓangaren Lion ɗin ya amsa mishi da cewa "Same here, amma just keep praying kawai, everything will going to be normal In Sha Allah". Yana magana yana bawa Rimsha abinci a baki, tana zaune saman cinyarsa daga ita sai wata ƴar shimin riga mara nauyi. Da alama ma bata jima da farkawa daga barci ba, wanka kawai ta yi. Ya ce ta zo ta ci abinci ne taki ta gudu wajen Brr, shi kuma da bai san menene kunya ba, sai ya je ya saɓota a kafarsa ya wuce da ita toilet, wanka ta yi ta fito ta shirya, ta ci abinci ta tsaya tana wasa, shi ne yake ciyar da ita......SOYAYYA RUWAN ZUMA.😞 "Okey zamu yi waya anjuma". Cewar Areef ɗin, Okey shi ma Lion ɗin ya amsa da shi tare da katse kiran. Dawo da ash eyes nasa a kanta ya yi, ta ɗaura mishi breakfast ɗin a saman carpet ta zauna saman bedside drawer tana kallon kasa kamar wata malama. "Au yanzu kin fara jin kunyata kenan?". Ya faɗa a sanyaye. Shiru bata amsa mishi ba. Matsowa kusa da ita ya yi tare da riko hannayenta da take ta wani murjesu. "First yanzu gaya mini jiya ni yaushe na shafa miki breast? Amsar shi zaki fara bani kafin na saura". Ɗago idanu ta yi izuwa saman face nasa, a hankali ta furta "Time da ka mayar da ni saman bed mana, ka ɗauka ban...." Bata kai karshen maganar ba ya fisgoga ta faɗa saman kirjinsa. "Breast ɗin naki ne ko nawa?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Ni ai ban ce naka ba ne, kuma ban ce nawa bane, kawai dai da ka ce naga handsome guy na zo ina leka shi ne, shi ne sai na gaya maka ai kai ne ma kake leƙani har abin da ya fi leƙawa". "Jehan who teach you how to talk?". Kwantar da kanta a saman kirjinsa ta yi tana faɗin "Ni dama can na iya magana ta, kawai ban gadamar yi bane, amma ba abin da ban iya ba". "Harda love kin iya?". Gyaɗa mishi kai ta yi tare da cewa "Ni fa na zauna a gidan Hjyr daɗi, so komai ma na iya". "Ina ne kuma gidan Hjyr daɗi?." Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Ba zaka sani ba ko da na gaya maka, yanzu dai sakeni bari na je na yi breakfast ina jin yunwa". "Zan iya baki breakfast ɗin?". Yunkurawa ta yi zata tashi daga jikin nasa tana faɗin "A'a zanci kayana da kai'na". "Why baki son na baki?". Ɗago kanta ta yi, a kunne ta raɗa mishi cewa saboda bata son ya cigaba da kare mata kallo kamar yanda ya saba. Wato kenan dama duk abin da yake yi mata tana sane, lallama Jehan ta iya mannin hauka. Jan hancinta ya yi tare da gyara mata zama a jikin nasa yana faɗin "Idan na kallah ɗin idonki ne?". Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a. "Okey to me ruwanki?". "Babu komai". Ta bashi amsa. Matso da plate ɗin abincin ya yi tare da fara bata a baki. Ba dan taso ba, dan dole ta karɓa ta fara ci. Sai da ya tabbatar ta ƙoshi, sannan ya saketa yana faɗin to tashi bari naje nayi wanka na shirya da akwai in da zanje. Da sauri ta ce "Ina zaka je?". Cool murmushi ya saki yana faɗin "Ai ba zan sake yi miki irin na jiya ba, my baby uwar rigima, jiya saboda ban dawo da wuri bane har da kukanta, ji ɗan bakinta a wajen". Dukan wasa ta kai mishi a kirji tare da miƙewa dan ta sauƙa daga jikin nasa. Rikota ya yi yana faɗin "To me abin fushi ƴar babyna, idan kina so ai sai mu tafi tare ko?". "Ni ba zan je ba". Ta bashi amsa a takaice. "Serious?". Kai ta gyaɗa mishi alamar e. "To shikenan na yarda, amma kafin in tafi zaki zo muyi sallama ko?". "A'a ba zan zo ba". Why ya tambaya. Ƙoƙarin barin jikin nasa ta fara yi tana faɗin "Mu a al'adarmu ta Hausa Fulani, mace bata bin namiji zuwa in da yake, sai dai shi ya kawo kansa gareta, wannan shi ne cikakken ɗabia ta Hausa Fulani". "Really?". Tabbatar mishi ta yi da hakan. "Okey are you Hausa or Fulani?". "Hausa and Fulani all are the same thing, my mum is shuwa Arab and kanuri, her father is shuwa Arab from borno Maiduguri, her mother is kanuri, my dad is Hausa Fulani." "Your dad is not Hausa Fulani". "Why are you saying that my dad is not Hausa Fulani?". Ta yi maganar da mamaki a kan face nata. "Because your grandma is not Hausa Fulani, she is from Russia, so your dad is not Hausa Fulani". Yau ta ga karfin hali, dole shi sai ya mayar mata da daddynta Bature, wai an gaya mishi yaren mama yafi na baba karfi ne? Bai san yaren uba shi ne power ba? Kuma Dr Salman dai Hausa Fulanin Bauchi state ne. Amma bata ja da shi ba, dan ta san zai kafe a kan lallai daddynta jinsinsu ne, wato Turawa, ba bakin fata ba ne, dan haka sai ta kyale shi. "What are you thinking?". Hannu ta ɗaura mishi a saman face nasa tare da ɗan shafa lallausan kumatunsa tana faɗin "My brother, am thinking about you". "Do you believe that am your brother?". Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "Yes i did". Tsareta da ido ya yi na ƴan sakanni kafin ya ce "Okey now kin manta ku baku kwanciya a jikin namiji har haka ne?". Ɗago idanu ta yi sosai izuwa saman face nasa tana faɗin "Ba kowani namiji ba ai, is halal na kwanta a jikinka". A takaice ya ce mata because? "Because your are my brother". Ta bashi amsa ita ma a takaice............. E lallai yau ake yinta, duk sun mannawa juna hauka kenan, Areef da Jehan akwai ƴan duniya wlh. "Okey in dai haka ne can i have a one kiss?". Why not?. Ta bashi amsa tana ɗaga mishi gera. Ɗan zaro idanu ya yi yana faɗin "Oh now you believe that zaki iya kissing nawa?". "Close your eyes and see mana, ai kai yayana ne, ko nayi kiss naka ba wata matsala". "Oh dama ana kissing na yaya ne?". Girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce "Ba'a yi, amma kai special ne, dan haka close your eyes ka gani". Dan ya gwadata kuma ya tabbatar da abin da take faɗa, shin zata yi ko ba zata yi ba, sai ya runtse idanun nasa. Ɗan ɗagowa ta yi a in da ta kara tsawonta tare da dafa cinyarsa ta saƙalo wuyarsa da hannunta ɗaya, runtse idanu ta yi kafin ta matso da face nata daf da tashi, zuciyarta tamkar zata fashe ta fito waje saboda tsananin tsoro, amma haka ta daure ta ɗaura lips nata a saman nasa. Wani irin dogon numfashi ya ja wanda sai da ya sanya ta buɗe idanunta, kankame jikinta ta yi waje guda tana jin tamkar ba zata iya ba, amma saboda ta kure shi sai ta daure, a hankali ta fara shan lips nasa na kasa. Bai san time ɗin da a sukwane ya waro idanunsa waje ba, ta datse nata idanun gam tana kissing nasa cikin kwanciyar hankali. Kasa jurewa ya yi a zafafe ya kankameta sosai a jikinsa tare da juyawa suka koma saman bed ɗin da kyau. Bai taɓa zaton da gaske zata aikata abin da ta faɗa ba, duba da ita mace ce mai tsare mutuncinta over, fiye da tunanin mai tunani, abin da bai sani ba shi ne, dan ta san shi mijinta ne yasa, ba dan haka ba, wlh ko kusa ko alama, wani ma ya kawo mata zancen banza ba sai ta zubar mishi da hakwara ba, tana da kula da kanta over, shi ne abin shi ma ya ɗaure mishi kai, a koda yaushe yana yi mata addu'a sosai idan ya yi sallah, yana sanya mata albarka tare da fatan alkhairi na irin ƙoƙarin tsare mutuncinta da take yi, hakan yasa ma kullum sonta yake mugu mugun karuwa a ransa. Idan ka dubi rayuwar Jehan ta fiskar ilimi da basira, zaka fahimci ita mace ce da duk wani namiji a duniya zai yi burin ya sami irinta, ba ita kaɗai ba, duk ƴaƴan Nawazuddeen, saboda mum ta yi iyaka bakin ƙoƙarinta wajen basu tarbiya ba karya. Zura harshensa ya yi cikin bakinta, ya fara bata nashi salon. Tun ba'a je ko'ina ba ta nemi ta gudu, amma ina ta makaro, dan kuwa riketa gam ya yi tare da fara shafa wasu sassa na jikinta, fara kokarin ambatar sunansa ta yi, amma ina bai amsa ba. Nan take idanuwansa suka sauya launi. Cikin fitar hanyaci ya kamo breast nata ta saman rigar tata. Wani irin numfashi mai wuyar fassaruwa ya fara sakar mata. Nan take tsoro ya kamata ta fara kiran sunansa da karfi karfi. Amma ina bai amsa mata ba. Ganin yana ƙoƙarin cire mata kayan jikinta ne yasa ta dakarkare ta gabza mishi cizo a hannu, ko kaɗan bai ji komai ba, tamkar ba shi ta ciza ba. Kuka ta fara yi mishi tana bubbuga shi a kan dan Allah ya kyaleta. Duk abin da take yi na rakin yana jinta, dan bai zurfafa da yawa ba bare ya fita a hayyacinsa, da gangan ya barta ta yi ta yi yaga iya gudun ruwanta. Can kuma wani tunani ya faɗo mishi, idan har ya yi mata hakan kuma zata fara gudun shi, ɗan sakin jikin da ta yi da shi ma zata janye. Tuna hakan ne yasa ya matso da bakinsa kusa da kunnenta. Raɗa ya fara yi mata a hankali yana faɗin "Wato har yanzu baki daina rigimar ba ko? To na kyaleki, amma kuma ai ke kika fara ko?". Yana magana yana goge mata hawaye. "Bana son wannan kukan sam my baby, ki daina kin ji ko? Yana taɓa mini zuciya sosai". Ko sannu bata ce mishi ba har ya gama goge mata hawayen tare da gyara mata rigarta da ya fara kokarin cirewa. Sumbata ya kai mata a kumatu kafin ya ce to ta tashi ta je ta yi wanka, dan ya san abin da zata ce kenan. Ya kai karshen maganar tare da sauka daga kanta. Runtse idanuwanta ta yi tare da mikewa zaune, wani irin sabon azababen kaunarsa take ji yana ratsata. Jiki ba kwari ta miƙe ta kwashe kayan abincin ta nufi waje. Da kallo ya bita har ta fita kafin ya koma ya kwanta tare da kifawa ya jawo pillow ya rungume tamkar ita ya runguma. AFTER ONE DAYS.💋 A ɓangaren Aseef da Akila kuwa, yau za su je wajen Ammie, sai murna Akila take yi, shi ma sai tayata yake yi. Amma fa kamar yanda kuka sani ne, an sha dirama a wajen yin wanka, ya ce shi dai lallai sai ya yi mata wankar nan, ita kuma ta ce a'a, daga karshe dai suka yi yarjejeniya a kan idan suka dawo da daddare zasu yi tare, haka ta amince mishi, sai dai shi kuma ya kudurci niyar tun da yau Lion zai shigo, tabbas idan suka dawo da daddare sai ya yi dis virgin nata, Allah yau ba zai kyaleta ba, amma bai bari ta gane ma ya yi niyar yin hakan ba, ya dai kyaleta a kan idan suka dawo da daddare za su yi wanka a tare, shi kaɗai ya barwa kansa sanin abin da ya shirya mata. Zata gane shayi ruwa ne, za kuma ta gane annabi ya faku. Haka suka shirya cike tab da kula da juna suka nufi gidan Ammie, Areef ya so su je tare, amma sai ya ce su je kawai dan akwai wani surprise da ya shiryawa daddyn Rimsha anjuma kaɗan, idan bakin sun iso zai zo tare da daddyn da kuma Jehan. Da haka suka yi sallama da su, suka wuce wajen Ammie. A ɓangaren Lion da Rimsha kuwa, abin ba'a magana, yanzu ya zamana anytime suna manne da juna, ko tana kwance a jikinsa saman faffaɗar kirjinsa, ko kuma ta tada kai da cinyarsa, yana aiki a laptop tana taɓa mishi saje, idan ta cika damun shi da yawa, sai ya ture laptop ɗin ya jawota jikinsa, daga nan zai fara romancing nata cikin taka tsantsan. Na'urat tana samun kulawa over daga wajensu, suna matuƙar kaunar tsohuwar, dan fa kowa ya san Brr mutuniyar kirkice over, duk wanda ya ji tarihinta sai ya kaunaceta. Alex da Mark sun yi muguwar sabo, sun zama kamar wasu twins, har waya da Anaya Alex yana yi, su gaisa, sai dai bai san cewa Anayar ƴar yayansa Hassan wato Azharuddin ba ne, shi ma dai Mark har yanzu bai san alaƙar dake a tsaninsa da su Rimsha ba, shi dai yaga an ɗauko Naurat, tun da Lion bai yi mishi wani karin bayani ba, sai ya yi shiru shi ma, kuma sam bai tambayi Alex ɗin ba, dan baya shiga abin da bai shafe shi ba, kowa ya sani dan ma soyayyar Anaya tasa ya ɗan canza har yake iya magana mai ɗan tsawo da mutanen, ban da haka ai shi kamar robot ma yake. Rayuwarsa gwanin birgewa, baya shiga harkar kowa, idan kuma ka shiga tasa, to zaka yi danasani. RIMSHA Zaune take saman sofa daga ita sai wasu shegun kayan shan iska, wandon ɗan guntu wanda ko rabin santala santalan cinyoyinta bai kai ba, sai riga zuwa iya cibiya, daga ta sama hannun vest rigar yake da shi, ta sako gashin nan har gadon baya, hannunta na rike da wayarsa tana latsawa, da alama chatting take yi ko da daddynta, ko Areef or Aseef. Sai zuba murmushi take yi kyawawan dimples nata suna ta lotsawa. Tamkar daga sama ta ji ya zuro hannunsa ta bayanta izuwa saman shafaffen cikinta da tamkar bata taɓa zuba mishi abinci ba. Sake jiki ta yi ta kwanta a saman faffaɗar kirjinsa tana mai kara faɗaɗa murmushinta. Matso da ɗan bakinsa saitin kunnenta ya yi yana faɗin sun kusa shiga Nigeria me zata bashi?. Ajiye wayar a gefe ta yi tare da juyowa ta shige jikinsa da kyau tana faɗin "Me kake so?". Shafa kanta izuwa bayanta ya fara yi, sanye yake da wando three cuter da polo t-shirt, shi ma bai ɗaure gashin kansa ba. A kunne ya raɗa mata abin da yake so tamkar wani nayi musu laɓe. Ɗan zaro idanu ta yi waje kafin ta ce "To shikenan na yarda, amma kuma ai ina....". Bai bari ta karisa maganar ba ya ɗaura latsa ɗaya a saman lips ɗin nata tare da ɗaukarta cak suka wuce gado. Saƙalo wuyarsa ta yi a in da suka kwanta tare, rumfa ya yi mata da faffaɗar kirjinsa yana kallon cikin kwayar idanunta, while ita kuma tana kallon wuyansa. Daga saman cibiyarta ya fara kissing nata har zuwa saman wuyarta, lumshe idanu ta yi tare da sanya hannu ta fara shafa mishi kyakkyawan gashin kansa. Romancing nata ya fara yi son ransa, bata hana shi ba, sai hawaye da take yi. Har sai da ya samu ɗan sauki sauki sannan ya kyaleta. Ɗaukarta ya sake yi suka nufi pool dake cikin jirgin, ta baya kenan. Ruwan ciki akwai zafi dai'dai yanda suke wanka. Sundumata ya yi a ciki da gabaɗaya kayan jikinta, ƴar kara ta saka mishi dan ruwan da akwai ɗan zafi, ya yi mata yawa zafin. Shiga ciki ya yi tare da jawota jikinsa yana yi mata sorry na zafin da ta ji. Hannu ta ɗaura saman ɓul ɓul ɗin breast nasa tana faɗin "Noori kirjinka a cike sosai". "Kina son kallonsu a zahiri ne?". Cikin sauri ta girgiza mishi kai alamar a'a. Ɗan shafa fusatatcen face nasa ya yi yana faɗin "Why?". Ba komai, ta bashi amsa. Hannu ya kai saman hannun rigarta, zamesu ya yi ta saman kafaɗarta suka sauko kasa zuwa wajen hannunta. Zamesu gabaɗaya ya yi rigar ta dawo saman cikinta. Hannunsa dukka biyu yasa ya riko tula tulanta, ko wanne da hannunsa ɗaya ya riko shi. Runtse idanunta gam ta yi. Da ɗan karfi ya matsa mata su har sai da ta ce "Wash Noori akwai zafi". A hankali ya lumshe idanuwansa tare da sake buɗesu a kanta. Sake tula tulan ya yi yana mai kara jawota jikinsa. Shafa zanen sunansa ya fara yi yana mai jin matuƙar kaunar zanen. Meesha, ya ambaci sunanta. "Na'am My Noori". Ta amsa tana ɗan murmushi. "I like this your tattoo". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce mishi ba tattoo ba ne, wani abin ne da yarabawa suke kwaɓawa. Shiru ya yi yana mai cigaba da shafa wajen na tsawon lokaci. Sun jima manne da juna a cikin ruwan kafin su fito. Bedroom nasu suka koma a in da suka tsara shirinsu cikin kayan mutunci, dan sun kusa shigowa Nigeria. A ɓangaren su Areef kuwa, sai misalin ƙarfe biyu ya ce da daddyn Rimsha ya shirya su je unguwa. Sam daddyn bai kawo komai a ransa ba, shiryawa ya yi suka nufi gidan Abba. Areef ɗin ne ya ja motar, sam Jehan taki yarda ta zauna a gidan gaba, a baya ta zauna, daddynta ya zauna a gaba. Ko da suka je gidan Aseef da Imran basu nan, sun je gidan Abbi, Akila, Umaisha, Jelly kawai suka samu a palo, shi Akil ya ma yi tafiya zuwa Abuja yau da safe, yana shirye shiryen komawa Madina. Su na shiga palon bakinsu ɗauke da sallama, da sauri Akila ta miƙe ta nufo Jehan tana yi mata ayoyo, dama kwana biyun nan suna shiri sosai. Rungume juna suka yi tare da karisawa cikin palon. Ina Aseef, Areef ya tambayi Akilar, kasa ta yi da kai wai ita a dole tana jin kunyar yayan miji, cikin girmamawa ta ce mishi sun tafi da yaya Imran. Okey ya amsa mata tare da ɗaukar wayarsa da call ya shigo yanzu ya nufi waje yana cewa su daddyn yana zuwa. Hira suka cigaba da yi har Ammie ta fito ta same su, cikin mutunci suka gaisa, Akila ce ta gaya mata daddyn Rimsha shi ne bappansu Hossain. Kara faɗaɗa murmushinta ta yi tana sake ɗaga mishi gaisuwa. Wancan karon da ya zo basu haɗu da ita ba, ta so su gaisa, amma tana barci, shi ne yasa bata san shi ba. Cikin farinciki suka cigaba da zuba kiransu har lokacin da Areef, Abba, Mummyn Rimsha da kuma gwaggo suka shigo cikin palon bakinsu ɗauke da sallama. Areef ne ya binciko in da suke, dama idan baku manta ba su mummyn sun zo Kaduna saboda azumi ya kusa, sun zo yin azumi gidansu Anaya, shi kuma Areef da farko ma ba su mummyn ya je bincika a gidan ba, ganin cewa daddyn Anayar yana tsananin kama da daddyn Rimsha ne yasa ya fara bibiyarsa dan ya san wanene shi, tun a school ɗin su Rimsha ranar ya ga daddyn Anayar. Rana ta farko da ya fara zuwa gidan ya sha ruwan mamakin ganin Anaya, da farko ya ɗauka Jehan ce, sai da ya kalleta da kyau, sai yaga Jehan ta fita haske, ta kuma fita cika, shi ne kawai banbancinsu, banda haka suna kama over. A ranar da ya je sun gaisa da daddyn Anaya a in da ya yi mishi tambayoyi a kan ko ya san su Abba, bai nuna mishi cewa suna tare da daddyn Rimsha ba. Amsa mishi daddyn Anayar ya yi da e su Abba ai yayyunsa ne, ya sansu, sai dai baya zuwa in da suke, kuma ya yi alkawarin ba zai sake zuwa in da suke ba har sai sun nemo mishi Hosain ɗinsa. Sosai Areef ya ji matuƙar daɗin maganar daddyn Anayar. Shi kuma daddyn Anayar ya bashi wannan amsa ne dan yana tunanin kila wani abin ne ya sami su Abba da yasa har Areef ya zo bincike, a tunaninsa da kuma kallon da yake yi wa Areef, babban jami'in ne, shi ne yasa bai ɓoye mishi ba ya bashi amsa ta gaskiya. Ko da ya dawo gida, sam bai nunawa daddyn Rimsha ya je wajen daddyn Anaya ba, ya kyalesu dan sai ya gama binciken da yake yi. Zuwansa gidan na karshe jiya da ya ce Jehan ta zo su je unguwa ta ce ba zata je ba, to wannan fita da ya yi gidansu Anayar ya je, ya kuwa yi sa'a daddyn Anayar ya ce su shiga cikin palo. Suna shiga shi ne yaga mummy da gwaggo suna hira, dama idan baku manta ba, ya ce zai karɓi hotonta a wajen daddyn Rimsha, to ya karɓa, shi ne yasa da ya ganta, ya gane ta, amma bai nuna mata ya gane ta ba, kuma bai nuna mata ya san mijinta ba, dan yasan ba ma zasu yarda da hakan ba, sai ya kyaleta ya zo ya gayawa Abbansu Imran. Sam bai je ɗaukota ba, sai ya bari Abban ya je ya ɗaukota da kansa, dan idan shi ne, tabbas mum zata biyo shi. To wannan shi ne surprise da ya shiryawa daddyn Rimsha. Ai kuwa ya ga tsantsan farincikin daddyn Rimsha da bai taɓa gani ba. Gwaggo sarkin masifa, da farko ta ce wlh ita ba zata shigo gidan Abba ba, ai ita da Abba har abada, sun yi hannun riga. Sai da Areef ya fito ya yi mata daɗin baki, shi ne ta yarda ta shigo, dama wannan ɗaukar waya da Areef ɗin ya yi ya fita, waje ya je dan Abba ne ya kira shi a kan gwaggo ta ce wlh ba zata shigo ba, ta tsani gidan..........To meyasa gwaggo zata tsani gidan yayanta kuma? Mu dai je zuwa, amma fa akwai rina a gaba ba kaɗan ba, akwai cakwakiyoyi na wuce misali, ku gyara zama dan ƙwaƙwalwarku ta iya ɗaukar wasu abubuwa, cakwakiyar gidan Hjyr Umaiya ma na dodannin nan kawai ya wuce tunaninku gaskiya. Gwaggo har da kukanta na ganin daddyn Rimsha. Allah sarki rayuwa kenan, palo ya cika da tsantsan farinciki, tuni Jehan ta haye jikin gwaggo, dama kun san ita ai ta gwaggo ce, bata wani turmushe mummynta kamar yanda ta turmushe jikin gwaggo ba, sau ɗaya ta rungumi mum, daga nan ta haye jikin gwaggo ta kwanta kamar wata jaririya. Ita ma gwaggo dama kunsanta da goyawa Jehan ɗin baya, idan kana neman bala'in gwaggo to ka taɓa Jehan, nan zaka ga ruwan bala'i da masifa kwando kwando, kai gwaggo ba dai faɗa ba wlh, akwaita da zafin rai ga karfin hali, isa da kuma izza, duk ta haɗe kamar wata jinin sarauta, dama ita Jehan ta gado, shiyasa suke shiri, sai hali yazo ɗaya ake abota. Sai wani lallaɓa Jehan ɗin gwaggon take yi, ita kuma Jehan ɗin tana zuba mata ruwan shagwaɓa. Har wani taɓe baki Areef ya yi yana mamaki, wai dama Jehan ta iya shagwaɓa har haka? Dama tana magana har haka?..... Bai san cewa ainahi dama ita idan ba da gwaggo ba, ko da mummynta bata sakewa ta yi hira, idan kana son kaga tana magana, to ka ganta tare da gwaggon, ai shagwaɓa kwando kwando take zubawa gwaggo, ita kuma tana biye mata. Ansha kuka kamar ba gobe. Sai da komai ya ɗan lafa ne gwaggon ta ce wai ina Rimshar ta ne, bata ga ƴar autarta ba, uwar rigima da kukan. Tamkar jira Jehan take yi a tambaya, nan ta fara bawa gwaggo labarin duk abinda ya faru na auren Lion da Rimshar. Nan fa gwaggo ta yi tsalle ta dire, ta ce idan an isa me take, bata uban da ya isa ya yi musu wannan iskanci ba, kamar Rimshar ce za'a aurar? To wlh ba zata saku ba bindiga a ruwa, da sake wlh. Hakuri daddy ya fara bata. Ina taki sauraran shi, ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, sai hura hanci sama take yi. Abba ya yi ƙoƙarin saka baki, amma ina ta murje idanu sam ta ce wlh ba zai yiwu ba. Dama ita gwaggo fa idan ta fara ballin bala'inta, to wlh kowa a cikinsu sarara mata suke yi, sai time da ta sauko...... Gwaggo fa ita ta ɗauko ainahin jinin TRUMP, wato mutanen Russia, mahaifin Naurat, ita ta gadosu in dai fagen zafin rai da faɗa ne, ga bakar zuciya ta faɗa. Shi dai daddyn Rimsha sanin halin Lion yasa ya cigaba da bata hakuri. A kule ta ce "Allah Nawazudden ka kiyayeni, ina magana kana magana ko?. Yau sai naga waye ubansa a garinnan, dole na ɗauko Rimsha yanzu, wai ce mishi aka yi bata da gata ne? Ko dai kwararota aka yi daga ruwa? Ko daga jikin bishiya ta fito da zai ce ya aureta ba tare da yardan iyayenta ba? To wlh ba daga jikin bishiya ta fito ba, da iyayenta cike ciff suna raye, ƴar gata ce na wuce misali, dan haka dole ya zo ya nemi izini daga wajen mu, ke Jehan wuce muje ki kaini in da suke, mu zai gwadawa isa, to wlh gidan isa da izza ya zo, ba'a yi wa familyn Dr Salman wannan iskanci a zauna lafiya!!.". Cikin sanyin murya tare da rarrashi daddyn ya sake cewa "Dan Allah ki tsaya nayi miki bayani dallah dallah yanda zaki fahimta, ba yanda kike tunani ba ne fa, ba haka.....". "Nawazudden wai yaushe muka zama abokan wasa ne da kai?." Shiru ya yi bai sake magana ba, dan yasan halinta sarai da uban iya bala'i, yanzu zasu hau sama jannati su diro, bazata fahimce shi ba, yanda ta fusatannan, dama ita haka take, idan fa ta hau dokin zuciya, to sai dai a daure a bi umarninta kawai.........WANNAN GWAGGON AKWAI RUWAN BALA'I😌 Shi dai Areef bawan Allah da yake baya jin Hausa, sam bai san me ake faɗa ba, bai san cewa zage mishi ɗan uwa suke yi ba, sai binsu da kallo kawai yake yi yana mamakin bala'i masifa irin na ƴan uwan daddyn. Ita dai Jehan ko a jikinta, sai ma kara shigewa jikin gwaggonta take yi, yo ita ai ko yanzu a je a ɗauko Rimshar, me ya yi mata zafi?......... E kam babu abin da ya yi miki zafi, sai Lion ya zubar miki da hakwara gabaɗaya ne zaki gane ba abin da ya yi miki zafi. "Jehan ta shi muje gidan". Cewar gwaggon, ta yi maganar tana ƙoƙarin miƙewa. Shi dai Abba da yake yanzu sulhu yake nema da ƴan uwan nasa, sai bai hanata ba, dan yasan ba shiri suke yi da ita ba, zata ma iya gaya mishi magana duk da yake babban yayansu, dan kafin su rabu, ba'ayi rabuwar daɗin rai da ita ba, ya san ya yi musu laifi, kome suka yi mishi suna kan gaskiyarsu, kuma ba zai ga laifinsu ba, dan fa ba'a magana a kan abubuwan da suka wuce, sun yi muni da yawa, musammanma ita gwaggo da take mace, sam bai kamata ya yi mata abin da ya yi mata ba. Allah sarki, shi ma ba laifinsa ba ne......... Nasan kowacecce a cikinku zata so jin wai me ya haɗasu da gwaggo kuma? To kubi komai a sannu, dan idan ba'a sannu kuka bi ba, ba zaku fahimci komai ba, PRINCESS TEEMA zata warware muku komai cikin natsuwa, yanzu dai ku biyoni kawai, dan akwai rina a gaba ba kaɗan kaɗan bama, yanzu komai zai ɗau zafi, saboda yanzu familyn suka haɗu, akwai cakwakiya, yanzu wasan ma ya fara!!. ❤️PRINCESS TEEMA....✍️💋 Daddy yana son ya gaya mata Lion baya nan, amma sam taki sauraronsa, haka ta ce su tashi su kaita gidan, idan ma ba zasu kai ta ba, to su bata key ɗin mota Jehan ta nuna mata hanya ta kai kanta. Cikin mutunci daddy ya ce a'a ba sai ta kai ga haka ba, su je ya kaita. Mum da Ammie dai faɗar gwaggo ba bakon abu bane a wajensu, ita mum ma ai ta san komai, akwai lokacin da wani malami a makaranta ya zane Jehan dan ta make wata ɗaliba, ai kuwa gwaggo ta figi mota ta je ta sauke mishi ruwan aradu a kai, daga ranar ba malamin da ya sake gigin dukan ƴaƴan Nawazuddeen, idan baku manta ba zamansu a Katsina ma fa anyi irin hakan, Jehan zata ɗauko faɗa, ita kuma ta tare mata, tana da zafin rai ne over. Haka suka ɗunguma zuwa gidan Lion gabaɗayansu, har da Ammie da bata fita, yau ta bi su, dan bala'in faɗar gwaggo abin kallo ne, kuma dole ne ma su rakata, dan kada ta je ita kaɗai Lion ya kasheta babu mai kwatanta. (Hasbunallahu wani'imal wakil😂 gwaggo duniya mai zaman kanta😂😂) Suna shiga palon sama a gidan Lion ɗin suka isko bala'in da ya wuce karfin tunaninsu. Gabaɗaya waƴan da suke gidan suna palon saman. Daddysu Lion, Uncle Herry, Jay, da kuma John, sune a palon. Ga Lion da ya diro yanzu ya shake TGA kamar zai kashe shi, babu Rimsha a wajen, tana bedroom ɗin Lion ɗin, dan ba zata iya ganin wannan bala'in ba, shi ne ta gudu abinta. Nasan zaku so jin me ya haɗa Lion da TGA faɗa, to ku saurara. Idan baku manta ba kwana biyu da suka wuce, Lion yana yawan bincike a laptop nasa, to ba komai yake bincika ba fa ce case ɗin mum da daddynsu, abin da ya haɗasu faɗa. Abin da yasa yake binciken dan yaga sun kusa isa Nigeria ne, shi ne yasa ya fara. To da ɓangaren mum ɗin nasu ya fara bincikawa, a nan ne ya cikaro da kullum weekend sai TGA ya je wajenta, abin ya yi mugun ɗaure mishi kai, shi dai ya san a baya ko mai kama da ita TGA baya son gani, shi ne ma yake cewa a kasheta idan ta zo gidan, to kenan me yake yawan zuwa yi a wajenta? Me yake kai shi?. Ga shi kuma babu camera a cikin gidan nata, a iya bakin gate kawai Lion ɗin ya sanya camerar, to bai san me suka yi a cikin gidan ba idan TGA ɗin ya je. Shi ne yasa tun kafin ya iso Nigeria ya kira TGA ɗin a waya a kan duk in da yake ya tabbatar kafin ya shigo yana gida, dan yana son ganin shi cikin gaggawa. So a takaice dai suna shigowa a palon sama ya isko TGA ɗin, shi ne ya tsaya ya tambaye shi me yake zuwa yi wajen Josephine? Wajen matar da ya fi tsana a duniya sama da kowa!. Kin faɗa mishi TGA ɗin ya yi, a in da ya fara yi mishi kame kame, to shi ne ya shake shi, ko ya gaya mishi gaskiya ko kuma ya kashe shi, faɗar da suke yi kenan. Su daddyn Rimsha suna shigowa Imran da Aseef suka biyo bayansu, kusan a tare suka shigo gidan. Ita kuma Naurat tana zaune a saman sofa gefe guda tana kallonsu, ta kasa magana. Alex da Mark suna waje filin sauran sojojinsa. Ita kuwa gwaggo ko a jikinta, tamkar bata san ana faɗa a palon ba, ba abin da ya dameta da su, ita dai abin da ta zo yi kawai zata yi. Cikin fushi ta ce "Ku nuna mini wani isasshe ne mijin Rimshar?". Nan take kallo ya koma kanta. Sam ba wanda ya lura da Naurat dake wajen, gida ya kacame da hayaniya. A wani irin mahaukacin tsananin razane gwaggo ta furta "Dr William!!". A yanayin yanda ta kira sunansa da karfi harta Lion ɗin sai da ya juyo da kallonsa kanta. Ɗan zaro idanu daddynsu Lion ɗin ya yi yana kallonta, zuba musu idanu kowa na palon ya yi yana kallonsu. "Wace ce ke?". Shi tambayar da daddyn Lion ɗin ya yi mata. Wani irin shewa da dariyar takaice ta yi kafin ta ce "Dr William ni kake cewa waye ni ko? Ko da yake hakan ba baƙon abu bane a wajen ka, kuma dama ai bani da wata alaƙa da kai a yanzu, dan haka yanzu bama wannan ba, ina ƴaƴana suke bakin azzalumi? Ko suma baka sansu ba?". Zaro idanu ya yi sosai yana kallonta kafin ya sake cewa. Wai wacece ita? Kuma wani ƴaƴa take magana a kansu?. Wani irin kallon banza ta watsa mishi tana faɗin "Nan kasarmu ka zo! Ko da yake baka san cewa ni ƴar Nigeria ba ce ko? To yau ka sani, nan a kasarmu kake! Dan haka ka shiga hankalinka da kyau! Ka gaya mini ina *TRIPLETS* na? Ko ka gaya mini in da suke, ko kuma kayi danasanin sanina a rayuwarka! Wlh wannan karon sai ka bani ƴaƴana, azzalumi, jinin shaiɗan kawai! Can kasarku ce, shi ne yasa na barka, amma nan kasar mu ce, zaka ga yanda ake tijara sanka sanka!! Zaka san da ƴar Nigeria kake yi!!". Tashin hankali!!. Duk waƴannan maganganun da ta yi, ta yi shi ne cikin harshen turanci, dan tasan William dai baya jin Hausa. Jin wannan bala'in da ƙwaƙwalwa take ƙoƙarin kasa ɗauka ne yasa Lion ya saki TGA tare da juyowa da kyau yana kallon daddyn nasa da gwaggo. Aseef kuwa tambayar kansa yake yi to wasu TRIPLETS ake magana a kansu kenan?. (Ni ko na ce ku mana🤣 akwai wasu TRIPLETS bayan ku ne?😌😒) A fusace Areef ya dakawa gwaggon tsawa yana mai gaya mata ta shiga hankalinta, ya isheta zagin daddynsu da take yi. Sai a lokacin ta ɗago kai tana kalli Areef ɗin, wani irin bugu kirjinta ya yi, shi kansa Areef ɗin sai da ya ji matuƙar bugu a kirjinsa na haɗa idanu da ita da ya yi. "Daddynku? Hmmm daddynku ko kuma bakin shaiɗan mai wutsiya? Dr William ai ba mutun bane, shaiɗan ne a suffar mutun, ni ƴaƴana kawai zai bani yau, bani da wata alaƙa da shi kuma!!". Aseef ne ya katseta da cewa "Wasu ƴaƴa naki kuma? Mu daddynmu bayan mu bashi da wasu ƴaƴan, iya mu TRIPLETS ne kawai ƴaƴansa". Zaro idanu ta yi tana faɗin "Au cemin zaka yi kune ƴaƴan nawa, ba shakka ga shi kuwa ka yi kama da Abban Imran, hasken kawai zaka gwada mishi". Areef duk da zuciyarsa na dukan uku uku a kanta, bai hana shi tinkararta dan ya sharara mata mari ko da guda ɗaya bane, wai ko zata dawo cikin hayyacinta. Dan su a mahaukaciya suka ɗauketa. Yau dai family sun ga bala'in da ya sha gaban tunaninsu. Ita dai Naurat tana zaune tana binsu da kallo, a matsayinta na Brr tana karantar kowa dake wajen, tana son gane mai gaskiya, kuma Allah da ikonsa, da yake hayaniya ya yi yawa, ba su lura da Naurat ɗin a wajen ba. Da gaske gaske Areef ya nufota tare da ɗaga hannu zai mareta. Tsawa Lion ya daka mishi a kan kada ya kuskura. Cak ya tsaya yana kallon Lion ɗin. Gabaɗaya palon kallo ya koma kan Lion ɗin, da gudu ita ma Rimsha ta fito daga bedroom ɗin nasu ta zo ta tsaya a bakin kofa tana kallon wannan bala'in da ya sha gaban tunaninta. Zazzaƙar sexy voice na Lion ɗin ne ya daki dodan kunne kowa da yake cikin palon, cikin sanyin murya ya ce "Wannan mata tana da gaskiya, dole tasan daddy, idan bata san shi ba ya akayi ta kira sunansa kai tsaye? Ya akayi ta san yana da TRIPLETS har take ikirarin ƴaƴanta ne?". Cikin sauri Areef ya ce "Lion ka san me kake faɗa kuwa? Kenan kana nufin wannan mata tana da gaskiya ita ce ta haifemu? To idan haka kake tunani what about Josephine? Ya za'ayi ace ba Josephine ba ce mum ɗin mu? Kada ka manta da ita Aseef ya yi kama sosai, tana kama da mu, shi ma kamar karya ce?". TASHIN SENSE, WANNAN SHI NE TASHIN HANKALI MADARARTA Shiru Lion ɗin ya ɗan yi na ƴan mintuna kafin ya ce "Ban yarda ita ta haife mu ba, amma dole ta san daddy, kuma dole suna da alaƙa, dan haka daddyn ne zai gaya mana gaskiya!!". Nan take kallo ya koma kan daddyn suna jiran amsa. A nutse ya ce musu "Ni ban san wannan matar ba, bayan Josephine ni bani da wata mata". Tashin hankali!!. Dawo da kallon shi kan gwaggo Lion ɗin ya yi yana ƙoƙarin sake yin magana ta riga shi da cewa "Wa ce Josephine ɗin? Ba dai Josephine da na sani ba?". A takaice daddyn ya ce mata ai Josephine dai guda ɗaya ne shi ma ya sani a rayuwarsa. Dariyar takaici wanda aka ce yafi kuka ciwo gwaggon ta yi mai isar ta kafin ta ce "Dr William baka tsoron Allah sam sam a rayuwarka, zafa ka mutu watarana, to bari ku ji, da Josephine Jacob Roshan da William Jacob Roshan, da Herry Jacob Roshan, sai Tyson Jacob Roshan, bari ku ji uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, dama ai dole ku yi kama da Josephine, dan kanwar uban ku ce!! Bakin mugu azzalumi kawai"........ TO FA JOSEPHINE DA WILLIAM UWARSU ƊAYA UBANSU ƊAYA KUMA? TA YAYA HAKAN ZAI KASANCE? WANNAN WANI IRIN CAKWAKIYA CE? SHIN A INA MA GWAGGO TA SAN DR WILLIAM? YA AKAYI JOSEPHINE TA ZAMA UWAR TRIPLETS? MEYASA DR WILLIAM ƊIN YA TSANE JOSEPHINE ƊIN? TO YA AKAYI TGA YAKE ZUWA WAJEN JOSEPHINE BAYA KUMA YA TSANETA? YA AKAYI JOSEPHINE DA DR WILLIAM SUKA YI ZAMAN AURE TARE DA SOYAYYA IDAN AN CE UWARSU ƊAYA UBANSU ƊAYA? AI BABU AURE A TSAKANIN WAƳAN DA SUKA FITO CIKI ƊAYA, DUK DA WASU TURAWAN RAYUWARSU KAMAR TA DABBOBI SUKE YI, AMMA AI SU MASU ILIMI NE SOSAI, KUMA YANZU AI AN WAYE OVER, TO IDAN MA HAKA NE SU UNCLE HERRY BASU SANI BENE DA SUKA BAR JOSEPHINE ƊIN TA YI ZAMAN AURE DA DR WILLIAM? IDAN HAR DA GASKE GWAGGO CE UWAR TRIPLETS TO MEYASA TA RABU DA SU? A INA KUMA TA RABU DA SU? ME YA KAITA KASARSU? KO DAI ZUWA NIGERIA DR WILLIAM ƊIN YA YI?. TANA TA IKIRARIN CEWA WILLIAM JACOB BAKIN AZZALUMI NE, A INA TA SAN SHI DA HAR TA SAN SHI AZZALUMI NE? GWAGGO TA TAƁA AURE NE KO DAI TRIPLETS ƊIN SHEGU NE? DAN DAI KUN SAN BABU AURE A TSAKANIN KARUFI NAMIJI DA MUSULMA MACE!! WAYE NE MA YA ƊAURA MUSU AUREN DA HAR SU ABBA BASU SANI BA? TO TA YA AKAYI SUKA SAMI TRIPLETS? GA SHI DAI TA CE DR WILLIAM ƊIN NE UBANSU, DA BAKINTA TA FAƊI HAKAN, TO A YAUSHE TA HAIFI ƳAƳA HAR UKU SU DADDYN RIMSHA BASU SANI BA? BA ZAI YI WU ACE DADDYN RIMSHA BAI SAN TANA DA ƳAƳA BA, YA AKAYI SU LION ƊIN BASU SAN CEWA JOSEPHINE KANWAR UBANSU BANE?. WILLIAM JACOB KRISTA, AISHA DR SALMAN SULTAN WATO GWAGGO MUSULMA, KUMA ACE SUNE IYAYEN TRIPLETS? ANYA KUWA HAKAN ZAI YI WU? KAI ƘWAƘWALWA MA FA BA ZATA ƊAUKI WANNAN CAKWAKIYA BA. GASKIYA AKWAI RINA A KABA BA KAƊAN BA, KAI AI BA MA IYA RINA BA, AKWAI RINONI A KABOBI MARASA ADADI!!!. *❤️PRINCESS TEEMA......✍️💋 A KODA YAUSHE NI ƊIN TA DABAN CE, SHIYASA KOMAI NAWA YAKE NA DABAN NE😍😌😂 TRIPLETS GIDAN SURPRISE DA CAZA ƘWAƘWALWA TARE DA ABIN MAMAKI, NA YAU KUMA KUN JI TA YANDA YA ZO🤔🧐😌 TO KU GYARA ZAMA SOSAI DAN MU JI KOMAI A TARE* *DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA WANNAN KAYATATCEN KUMA SHAHRARREN LITTAFIN NAWA MAI SUNA TRIPLETS, HANZARTA KI YI MINI MAGANA TA WANNAN NUMBER 0816 139 0581, DAN KADA AYI TAFIYAR PRINCESS TEEMA BABU KE, AKWAI LABARAI MASU TASHIN ƘWAƘWALWA DA SUKA SHA GABAN TUNANINKI, NISHAƊANTARWA, ILMANTAR, FAƊAKARWA TARE DA WA'AZANTARWA, DUK SAI PRINCESS TEEMA.💋 KADA KI YARDA ACE KINA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA KUMA BAKI TARE DA PRINCESS TEEMA💋 LABARAINA SUN SHA BANBAN DA SALON LABARAN DA KUKA SANI, KUMA SHAIDA NE KO MY READERS?❤️🧐 TO MU JE ZUWA, BAYAN TRIPLETS AKWAI MAI ZAFI GASKE, MAI TAFASA DA ZAI SHA GABAN TUNANINKU, ZAI TAFI DA ZUCIYOYINKU BA NA WASA BA.❤️ TRUST ME MY PEOPLE'S, TAFIYATA BA ZAKI JI KUNYA BA, BA ZAKI TAƁA DANASANI BA, BANA BAWA READERS KUNYA, GA DAƊIN LABARI HAR BAYAN KUNNE😍😂 IDAN KINA KARATUN LITTAFINA HAR WANI BARCI BARCI ZAKI JI SABODA DAƊI😂🧐 GA UPDATE A KAN LOKACIN⏲️😍🧐 GA UBAN YAWAN READ MORE❤️💋 KO WANI PAGE KUMA SAI KIN KARU DA ABUBUWA DA DAMA MASU AMFANI KUMA KI NISHAƊANTU,❤️💋 KO YA KUKA CE READERS?.* *TAMMAT BI HAMDILLAH, NAN NA KAWO KARSHEN BOOK 3, SAI MUN HAƊU A BOOK 4. NA SO LITTAFIN YA TSAYA MINI A BOOK 3, AMMA KASAN CEWAR DOGON LABARI NE YASA HAR MUKA TAFI BOOK 4, IN SHA ALLAH SHI NE NA KARSHE.* SIGN BY PRINCESS TEEMA....✍️💋❤️❤️ SSG Palace Gujungu