🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Da sunan Allah mai rahma mai jinkai Allah Kasa kamar yadda nafara littafin nan lafiya na gamashi lafiya🤲 Allah kabamu zaman lfy a qasarmu, ka ji6inci lamuranmu ya Allah, karka barmu da kanmu🤲 (Amin) Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 001 Safa da marwa yai tayi a tsakar falon, hannuwanshi goye a bayanshi. Kallo daya zaka yimashi kasan yana cikin tsananin damuwar da yake Neman mafita. Tsaki yasake ja a karo na ba adadi. "Kai impossible wlh!" Yafada cikin qaraji. "Wlh bazai ta6a yiwuwaba... Bankrupt? Ni? Ni? The whole Alhaji Shamsu bankrupt kema barazana? No, bazai yiwuba, dole insamu mafita, dolene!" Ya kai zancen yana kaiwa bango naushi. Qara kai dubanshi yayi ga agogo, 5:55pm. Tsaki yaja don lokacin be mashi gudu, cigaba yayi da parade dinshi har saida agogon yabuga 6 dot. Hannu na kyarma ya dauki wayarshi dake kan center table yashiga Neman lambar, har zufa yake don bala'i. Saida takusan tsinkewa sannan aka Daga. "Hello sir" muryar wata ta doki kunnenshi. "Hi Helen...so what's up, komai yayi daidai" ya tambaya yana dan Waro idanu kamar mai jin tsoro. "Yes sir, at last ya Baka appointment..." "Really?!.. Oh am grateful, thank you thank you Helen" yafada yana katseta. "It ok Sir, Saidai fa sai ranar Monday kuma yace 8 dot zai ganka kuma kasan baison sa6a..." Qara katseta yayi da "ohh don't worry, Tun seven ma zanzo, thanks zan maki kyauta idan komai yatafi successfully" "Alright sir, bye and thanks" "Ni keda godiya" yafada yana latse wayar. Zubewa yayi kan cushion din bayanshi yana sauke ajiyar zuciya. "Wuhh! Allah na godema, atleast nafara jiyo qamshin nasara" "Don Monday, duka duka yau Friday, ay ko nanda sati yace injira zan jira indai zan samu nasara, Nidai Allah ka dorani akanshi kabani sa'a, bari in rama sallolina, Haba tension ba dadi" Haka yayi gaba yana 'yan sabbatunshi, sai lokacin yasamu kwanciyar hankalin yin sallolinshi na azahar da la'asar. ********************************* "Ok.. Insha Allah... No you don't have to worry ai munada cika alqawari insha Allah... Sosaima and I bet you zakuji dadin mu'amala damu...hhhh mu keda godiya.... Alright bye thanks for patronizing us" Katse wayar tayi tana sauke ajiyar zuciya. "E be like say wannan satin sai munfi shiga chakwakiya" tafada tana kallon wata budurwa dake gabanta riqeda wani qaton littafi da Biro. Murmushi budurwar tayi tace " wallahi kau ma'am, nima naga alama " "Hmm yanzufa sufee's family mukayi waya dasu Wai suna buqatar snacks na birthdayn autarsu, kuma this coming Friday, sati daya kenan, ga order din bikin sir Wilson, Wanda ko farawama bamuyiba" "Aikaudai don yanzu haka bamu gama na ordern savannah hotel ba" inji budurwa tana kada kai. "Wuhh! Ba damuwa ai, kin gane maryam, kawai yawan ma'aikata zamuyi yadda komai zai tafi fast and smoothly, kinsan an sanmu da cika alqawari banaso mu 6ata wannan image din namu" Maryam tace "hakane ma'am, hakanma yakamata Ayi" "So kije kiyi Duk yadda ya dace, ni zan tsara komai zan turomiki anjima ta email..." Ringing din wayarta ya katseta. Dauka tayi tana duba mai kiranta. Da hannu tayima maryam nuni da tana iya tafiya, Dan russunawa tayi sannan tajuya tafice tareda janyo kofar. Daga wayar tayi cikin fara'a "Assalamu alaikum" "Wa alaiki salam, jewel" aka amsa ta dayan bangaren ciki fara'a. Cikin jindadin yanayinda taji muryarshi tace "Na'am sweet daddy, ina wuni?" "Lfy jewel, ya kike? Ya aiki" Marairaicewa tayi tana cewa "as usual dad, ganinan kamar inyi kolo saboda gajiya" Dariya yayi yace " maganinki ai, ba yadda banyi dakeba akan kiyi White collar job kina zaune cikin AC babu wahalar komai abiyaki Duk wata da albashi mai tsoka kinqi, yanzu ai ga irinta nan" Itama dariyar tayi tana jujjuyawa saman kujera don inda sabo tasaba da qorafin daddy. "Yanzu daddy ya lbr?" Ta tambaya trying to switch the topic. "Akwai lbr shalele, mai dadi kuwa" yafada cikin zumudi. "Haba?!" Itama ta tambaya cikin zumudi. "Wlh, kawai ki qaraso kisha labari" yafada yana yar dariya. "Aikau yanzu zaka ganni Dama nayi closing" "To saikin zo shalele" Kit ta katse wayar tana murmushi. Saurin tashi tayi tana tattara komatsanta, ta qosa taje taji meya chanza mood din daddynta, yau dasafe ko magana beson yi sbd damuwa, dakyar ta tausashi ta tattausan kalamai sannan tasamu yayi break, Amma yanzu shine hardasu dariya, lallai addu'arta ya qarbu. Rataye jakar tayi ta gyara rolling din gyalenta ta feshe kanta da turarenta mai sanyin qamshi sannan tafita. Bakwana tayi da ma'aikatanta kamar ba itace boss dinsu ba sannan ta hau motarta ta kama hanyar gida...✍ Ummin fasihu ce 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILS👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah kabamu zaman lfy aqasarmu, ka yayemana wannan cuta (covid19)🤲 Ya Allah ka ji6anci lamuranmu karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 002 "Kai alhamdulilah! Amma daddy na tayaka murna!" Tafada cikin murna tana rungumo kafadunshi. "Ai shalele nafiki murna, Allah dai ya dorani kanshi, naji ance Dan ji da Kaine, shegen kanshine, jibi yadda gaban wahala kafin ya hada mana appointment" yafada yana yatsina fuska. "Ai tunda dai kwalliya tabiya kudin sabulu shikenan ai, chan ta matse mishi" "Ai kwalliyar bata kaiga biyan kudin sabulun ba kidai tayani addu'a" "Insha Allah daddy, komai zaizo da sauki, Allah will be in control" "Ai ingayamiki, Saidai na hada azahar da la'asar, kasama sallan nayi sbd fargabadon nasan koda nayima sai nayi kwa6a" Dan shan mur tayi tace "Haba Dad kawai sbd abin duniya saika qi yin Sallah kan lokacin?" "Wlh shalele nashiga tension ne, shiyasama nakasa tashi nayi" "Haba Dad, ai Allah baya dorama bawa abinda be iyawa, memakon ace a lokacin tension din zaka yawaita ibada ko Allah zai jiqanka ya dafama?" Ta qarashe mgnr tana turo baki. "Au nafa manta da ustaziya nake mgn, yi hqr to, kamar yadda nafada tension ne, hakan bazai sake faruwaba" ya fada cikin sigar lallashi. Sake turo baki tayi tana cewa "ai Dama haka kake cewa, dad kafison abun duniya bisa na lahira, please karage, money Is not everything, marassa shi na living life dinsu comfortably, da arziqin duniya so kwara na qiyama tunda itace dawwamamma" "Hmm you won't understand, wlh kudi Sune komai, idan kanadasu kanada komai don duniya da mai kudi take harka, yanzu duba wannan guy din is just 25+ ga yadda aka gayamin Amma bakiga yadda ake binshiba, a haife na haifeshi Amma ji wulaqancin dayayiman, muryarshima kadai haryanzu banjiba, Saidai muyi magana da secretary dinshi, Duk me yaja wannan? Money" Dan ta6e baki tayi tace "manzon Allah dai yace Ku nemi duniya kamar bazaku mutuba haka zalika Ku nemi lahira kamar bazaku wayi gari a duniyaba" "To naji ustazziya, alarramiya SAUDATU" Murmushi tayi tamiqe tana Dan miqa. "Dad zan haye Kaga magrib ta gabato, zan watsa sai inyi Sallah" "Ok nima bari inwuce masjid, Adai tuna damu a addu'a, Allah ya dorani kanshi" Dariya tayi tace "kai daddy? Insha Allah yama doraka, Kaga amfanin self dependent, ni yanzu waya isa yatadamin hankali, wuri nawane, nice boss din kaina, business nawane, ba bashi, ba barazana..." "Anji wuce kije kiyi Sallah wahallaliya, wannan aikine ko wahala?" Haurawa tafarayi tana dariya "ai dad Neman halak da wahala" "Kyaji dashi" yafada yana ficewa. Saida akayi isha'i sannan yadawo gida inda yayi addu'a sosai na Allah yabashi sa'a akan wannan mutumin don yasan idan yarasa wannan damar to ya kad'e har ganyenshi. Abinci sukaci duka danyi fira sannan kowa yawuce makwancinshi. Washegari Saturday, babu mai zuwa aiki cikinsu, yau gida SAUDART ta wuni, tayi musu girki kamar yadda al'adarta take, dukda sunada yan aiki hakan baisa idan tana gida taqi tayasu musanmman fannin girki. Girki shine favourite hobby na saudart don hakama yasa tana kammala degree dinta tasa daddynta ya budemata qaton bakery idan take hada dangin snacks tana siyar wa. Saudart macece maison Neman gashin kanta tanada ra'ayi na rashin dogaro da wasu, shiyasa Duk nacin daddy yabarta tayi yadda takeso. Washegari Sunday, shima babu aiki, fita tayi zuwa gidan mamanta, kasancewar sun rabune da daddy tayi aure wani wuri (zakuji bayanin komai nan gaba) Acan ta wuni har magrib sannan tadawo gida tahau ayukka a laptop inda Duk ta gama arrangement na gobe...✍ Ashaanty ce 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah kabamu zaman lfy aqasarmu, ka yayemana wannan cutar (covid 19) Please yan uwa mu tashi tsaye wajen roqon Allah akan wannan masifar data afkamana, kuma mubi hanyoyin kiyayeta, wlh covid 19 is real, prevention is better than cure Allah ka ji6anci lamuranmu karka barmu da kanmu🤲. Story written by Ashaanty love ( ummin fasihu) 003 MONDAY Ranar da kowane mahaluki zai tashi busy Bayan hutun weekend. Hakan take a 6angarensu Alhaji Shamsu, dashi da diyarshi basu koma barciba Bayan sallar asuba Ita tana shirin zuwa bakery dinta don tantance sabbin ma'aikatan dasukayi applying while Alhaji Shamsu na shirin haduwarsu da life saver dinshi kamar yadda ya rad'a mashi. Seven daidai taji ana kwankwasa mata kofa. Zage zip din jakkar laptop dinta tayi tanufi kofar da sauri jin ba'a bar bubbugowaba. Tana budewa fuskar daddynta ya bayyana. A mammakince take kallonshi. "Dad? Lfy?" Ta tambaya cikin mammaki. Hararar wasa ya gallamata "Da akayi me?" "Naganka ciki shiri" "To da cikin me kikeson ganina? Mtcheew Nidai am off" yafada zai juya. Saurin tsayar dashi tayi dacewa "please kajira mutafi tare, nima na shirya bari na dauko laptop" "Mtcheew kiyi sauri fa" yafada yana duba wristwatch dinshi. Sauri tayi ta dauko tafito suka sauka inda sai anan tasamu zarafin gaisheshi ya amsa ataqaice don Duk hankalinshi baya taredashi. Gannin ta nufi dinning yasashi cewa "where are you going to?" "Dad breakfast zamuyi ko?" Tsaki yaja yajuya yana cewa "in that case, bye saimun hade" Saurin biyoshi tayi tana mashi magiyar yabari su karya Amma ko tankata beyiba. Tasan Dama za'a Rina Dama haka daddy yake indai Abu na ranshi ko abincin kirki be iyaci, kuma ya dinga tsaki kenan kamar wani tsaka. Rakoshi tayi har bakin motarshi, leqowa tayi Bayan yazauna ciki tace "dad Allah yabada sa'a, Amma please kaci wani Abu don Allah" "Amin, insha Allah" ya amsata yana tada motar. Ja tayi baya tabishi da iso harya fice Daga gidan. Ajiyar zuciya tayi sannan tanufi motarta itama ta shiga tabata wuta ta fice. A.A INTERNATIONAL ENTERPRISES Tsaki yaja a karo na ba adadi yana kallon wrist watch nashi. "Wai Helen are you sure yau yace inzo? Wannan wulaqancin dame yayi kama, ace Tun seven thirty inanan yanzu har nine thirty?" "Please kayi hqr sir, wlh nima narasa dalilin rashin zuwanshi haryanzu kuma wlh boss Beda African time" "Mtcheew, wannan ai wulaqanci ne, ki kirashi mana, mutane sai wucewa suke suna Kallona wannan ai ba girmana bane" Waro idanu tayi tace "me? Kace injawa kaina firing, kawai kayi hqr, kamayi hqrin kwanaki bare yan awwanni" Ya bude baki zaiyi magana, maganar ta maqale sanadin shigowarsu. Saurin gyara zama yai yana sakin fuska. As usual, fuska a tamke yashigo, ko kula da Helen mai gaisheshi beyiba bare Alhaji daketa yaqe baki. Wucesu yayi mutane hudu na takemishi baya, daya daukeda suitcase dinshi while others na empty handed. Saida yashige sannan Alhajin ya kalli Helen yace "to ya? Nashiga?" Harara ta 6alla mashi batareda tasaniba. "Lallaima sir, babu iso babu komai?" Daidai nan qattin dasuka rakashi uku suka fito banda daya Wanda Dama ba bodyguard bane ko ga yanayin shiga zaka gane. Tattara wasu files tayi tace "5mins sir" Kada mata kai yayi yabita da kallo harta shige, ajiyar zuciya ya sauke yana addu'ar samun nasara cikin zuciya. Bayan minti goma, sai gata tafito daukeda wasu files din. Binta da kallo yayi harta ajiye saman desk dinta sannan tajuyo tace "Sir kana iya shiga" Gabanshine yafadi, ya rasa dalilin nervousness din dayakeji Tun wayewar garin yau. Miqewa yayi a sanyaye ya nufi kofar Knocking biyu yayi sannan akayi mishi iso. Ahankali ya tura kofar yana summoning din courage dinshi. Da sallama yashiga, amsa sallamar dayan mutumin dake ciki kawai ya iyaji shiko gogan ko dago kai beyiba. "Bismillah" inji dayan mutumin yana nunamishi kujerar dake facing dinsu. Ja yayi ya zauna sannan ya miqama mutumin hannu sukayi musabaha, juyowa yayi wajen gogan ya miqamishi hannu shima don su gaisa. ************************************** Duk yadda take zaton aikin zai ca6emusu yawuce hakan. Sosai suka Zage wajen tantance sabbin ma'aikatan tareda rarrabasu bangarorin da yadace. Idan Kaga Saudart lokacin saita burgeka sbd kazar kazar dinta, ga iya mu'amala da jama'a, take ta saye zuqatan sabbin ma'aikatan, haka taita zagaya bangarorin bakery din, idan ka ganta Baka cewa itace mai bakery din don har 6il6ishin flour ke akwai ajikin apron dinta. Haka sukaita zagaye suna distributing aiki...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan cuta (covid19) Ya Allah karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 004 Kallo yabi hannun dake sagale a iska kamar Wanda yaga kashi sannan ya maida kallonshi kan system din gabanshi yana cigaba da danne dannenshi. Wani Abu Alhaji shamsu taji ya ratsashi Daga kai zuwa tafin kafa, ga wani dunkulalen Abu daya tokareshi a maqoshi. Tunda yake ba'a ta6a wulaqantashi irin nayauba, he felt totally embarrassed. Saurin kama hannun da har yanzu yakasa ajiyewa dayan mutumin yayi yana yar dariya. "Sorry Alhaji shamsu, kasan yanzu musabaha is so risky sbd wannan cuta (covid19), he's trying to be preventive ne" Murmushin yaqe Alhaji shamsu yayi Wanda iyakarshi le6e yace "hakanma Nada kyau" "To ni sunana Sadeeq Umar, P.A na wannan companyn, wannan kuma is the C.O.E na A.A ENTERPRISES, MR ASHRAF AUWAL by name" inji mutumin cikin sakin fuska. "Nice meeting you, am ALHAJI SHAMSU AHMAD KANKIYA by name, c.e.o na A.S GALLERY" "Na'am, satin daya gabata kazo mana dawata magana Wanda bamu idataba kasancewar Mr Ashraf bayanan, so yanzu zamuso ka sake fadin dalilin zuwanka idan ba damuwa" Ajiyar zuciya Alhaji shamsu yasaki ya d'an saci kallon MR ASHRAF dake busy operating din system dinshi. "Like I said earlier, company na ne yake cikin barazanar bankruptcy, akwai tarin bank's loan damukebi gashi abubuwa suna ja baya sakamakon wannan cuta ta covid19, yanzu haka bank are on our necks, ga sauran shareholders naneman janyewa sbd yanayin abubuwan shine nazo kozan samu loan awajenku sbd preventing company na from collapsing" ya ida yana addu'ar samun nasara cikin zuciyarshi. Shiru ne ya d'an ratsa office din sannan Mr sadeeq yace "Idan na fahimceka bashi kakeso mubaka ko?" "Yes, haka nake nufi" "So kamar nawa? Kuma yaushe zaka biya?" "Inason kamar 30million Naira idan so samune" "30million?!" Inji sadeeq yanadan ware iso "Eh, cos zanyi settling din bank da 20million kingin kuma zamusa mu fargado da company din" yafada cikin nutsuwa Shiru yasake ratsa wajen kuma haryanzu gogan ko dagowa beyiba. "Ok sir a ganinka zuwa yaushe zaka biya? Cos the money is so huge da bazamu so sa6a alqawariba" "Insha Allah nan da shekara daya. Bazaima kaiba idan an samu yadda akeso kuma insha Allah babu sa6a alqawari tsakaninmu" yafada acikin zuciyarshi kuma tantama yake akan anya wancan ba kurma bane? "Ok sir, zamu duba, kana iya dawowa jibi idan babu damuwa don jin yadda muka tattauna akai" Miqamashi hannu Alhaji shamsu yayi yana cewa "Shikenan, Allah yakaimu, am grateful" "You're welcome" sadeeq ya amsa da murmushi fuskarshi. Bankwana yayi dasu sannan yafice Daga office din zuciyarshi Tabb da wasiwasin ko buqatarshi zata biya ko A'a. Motarshi yashiga be zarce ko inaba sai company nashi don settling wasu abubuwa. *********************************** "Good, yanzu sauransu Sufee's su za6i kalan cake dasukeso, ki turamusu wadannan samples din su za6i choice dinsu, shikuma na sir Wilson afara hada komai da ake buqata, kinsan kwana uku kawai ke garemu" inji Saudart dake danne danne akan system din gabanta. "Yes ma'am, yanzu given za'a aika na hotel din?" Inji maryam "Ehh, ai saura finishing touch, idan bamu idaba yau nasan zuwa gobe mun kammala, yanzu kije kiyi sending din samples din sannan kiyi listing din abubuwan da bamu dasu" "Ok ma'am" inji maryam a ladabce sannan tafice. Cigaba tayi da danne dannenta tanayi tana sipping din tea kakaura, rurin wayarta ya katse mata abinda take...✍ Please manage babu chaji🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan cuta (covid19)🤲 Ya Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 005 "Assalam alaikum" tafada cikin fara'a "Wa'alaiki sallam shalele" shima ya amsa cikin fara'a. "Dad, you sound happy, how far?" Ta tambaya cikin zumudi "Hhhh, komai daidai Saidai kin dawo, akwai labari" "Really! Please d'an fesamin dad, komai yatafi daidai?!" "Eh.. Kusan hakan, Saidai kindawo kawai" "To Dad kana ina yanzu?" "Ina office, ina settling din wasu abubuwa" "Ok dad, saina dawo din, take care uhn?" "Ok sweetheart" Ding.. Ta katse kiran 'Seems yasamu nasara, he sound happy' tafada cikin ranta. Maida hankali tayi ga abinda take, ba ita tasamu kantaba sai lokacin closing. As usual bakwana tayi da staffs dinta sannan ta nufi gida looking very exhausted. HOURS LATER zaune suke a dining sunacin abinci, saudart sanye cikin loose gown while Alhaji cikin ash din jallabiya, kallo daya Zakayi musu kasan suna tattauna wani Abu mai muhinmmanci ne. Ajiyar zuciya Saudart tayi tace "dad karka damu insha Allah zasu baka, just be hopeful" "Allah ya yadda, don wlh Sune last hope dina, yanzu ace misali bansamuba ya kike tunani zanyi da tarin basussukan kaina? Kinsan banki basusan qaddaraba, idan nace in biyasu gabadaya rubdugu zanma company din, ga kingin Masu hannun jari, dame zan biyasu kudin dasuka zuba a kamfanin? Kashi ba wasu qadarori nataraba, zan shiga chakwakiya ba kadan ba" "Kabar fadin haka dad, insha Allah hakanma bazai faruba. Kaidai ka dage da addu'a insha Allah komai zai warware cikin sauqi" tace cikin sigar lallashi. "Allah ya yarda shalele, kidai dinga tayani addu'a" "Insha Allah" "So ya bakery, Mrs chef?" Yafada cikin sigar tsokana "Kai dad, bakery alhamdulilah, komai na tafiya daidai..." Nan tashiga bashi lbrin yadda bakery din, ahaka har suka gama cin abincin, sannan sukayima juna saida safe kowa yawuce makwancinshi. Tuesday was uneventful a 6angaren Dad, while Saudart a 6angarenta yauma she's busy, bata samu kantaba saida yamma liqis. Haka takoma gida tasamu Dad dinta cikin tarradadin yadda gobe zata kasance. Kamar koda yaushe kwantar masa da hankali taitayi har saida ta tabbatar hankalinshi yadan kwanta, haka ta raya Rabin Daren tana yimashi addu'ar samun nasara. WEDNESDAY Dayake yau haduwar marecene sa6anin na ranan, yau Saudart kadai tafita dasafe, saida ta tabbatar yaci abinci kuma ta qara kwantar mishi da hankali sannan tafice bakery dinta. ************************************** "Wannan kwalailaita ko mace sai haka, please Ashraf kayi da jiki mutafi, Wai halan Baka duba time ne?" Inji sadeeq cikin qosawa. Ko nuna alamun yajishi beyiba bare ya tanka. "Ni wlh narasa gane kanka, kaida bakada Africa time Amma akan wannan mutumin kazama wani.." "Ohhhh! Please sadeeq🙏 Wai kai bakinka baya zugine sbd surutu? Dan Allah free me, Dan Allah" ya fada kamar zaiyi kuka. "Oh nine.." "Dalla shut up mallam, nace shut up, mgnarce bana so, zaka samun headache, idan bazai iya jiraba then off he go, bani nakawoshiba so bazan hanashi tafiya haka zalika bazai hanani harkan gabana ba, idan ka takuramin sai in Daga appointment din zuwa next month, try me and see" yafada daringly. Daga hannaye sama sadeeq yayi alamun surrender sannan yajuya yacigaba da kallon t.v sbd yasan qaramin aikinshine ya aikata abinda yace din. Saida yaqara wasting kusan 30mins sannan yagama shirya wa, izuwa yanzu qiris yarage sadeeq yafashe don haushi. "Shall we?" Inji Ashraf yana gyara necktie dinshi. Banza yayi dashi saima tashin dayayi fuuu yawuce waje. Ta6e baki Ashraf yayi sannan shima yabishi abaya. Mota daya suka shiga da sadeeq dayan kuma bodyguards dinsune aciki suka cilla kan kwalta. ************************************** "Sir munyi nazari akan buqatar ka, kuma mun yarda zamu Baka adadin daka buqata ko fin haka, Saidai da sharadi Bamusan idan ka amince" inji sadeeq Murnar Alhaji taso komawa ciki, kallon sadeeq yayi sannan ya maida kallonshi kan Ashraf dake faman jujjuyawa kan kujera idanunshi lumshe. "Inaji, wane sharadi kenan?" Inji Alhajin "Bansan yadda zaka dauki zancennan ba but believe me, it's just business, bamuda wata manufa akan hakan, zamu Baka loan na 30 million Naira ko fin hakan na shekara daya zaka maidosu ciff babu d'ori babu ragi Saidai kamar yadda kasani bakada abinda zamuyi holding akan idan Baka biyamuba zamu fanshe ta wajen, koba hakaba?" "Hakane" inji Alhaji "Shine mukayi shawara why not muyi haka, muyi trade by barter, mubaka kudin kaikuma kabamu wani abun dazamu riqe harsaika maido kudin sannan mubaka" yafada cikin nutsuwa. "Me kenan?" Alhaji ya tambaya cikin rashin fahimta. Kallon Ashraf sadeeq yayi Wanda haryanzu yana jujjuyawane akan kujera sannan ya maido dubanshi ga Alhajin. "Diyarka" ya bashi amsa ataqaice. "Diyata?" Ya tambaya cikin rashin fahimta. "Eh ina nufin kabamu diyarka saimu Baka kudin.." "Wait, nufinku inbaku diyata sbd kudi? Ko nufinku son kudi zaisa in lallata rayuwar 'yata? This is unbelievable!" Alhaji ya katseshi cikin tsananin mammaki. "Calm down Alhaji, ba nufina kenanba, you misunderstand us, abinda nake nufi shine zakaba Sir Ashraf auren diyarka bisa yarjejeniyar daka biyashi kudin shi zai sakoma ita, babu abinda zai shiga tsakaninsu, kawai sunan an daura aurene, zai Baka bashin har zuwa 50million idan kana so, all you'll do is sign a contract with him, Amma fa bawai tilas bane, Mr shamsu remember kanada option, this is just...Business" yaqarashe zancen yana mai stressing din business din. Shiru Alhaji yayi don kanshi yayi mugun kullewa, contract? Aure? AUREN KWANGILA fa kenan? To meye ribarsu? Shikuma meye ribarshi? Tambayoyin daketa mashi kara kaina akai kenan. "Alhaji kayi shiru" inji sadeeq dake kallonshi. Dagowa yayi yana kallon Ashraf, yes he's handsome, damn hot! Irin namijin da kowacce mace zataso samu a matsayin miji, ga kuma uwa uba kudi, he's damn rich, zaici riba idan Ashraf yazama sirikinshi koda na kwana dayane, gaggarumin riba kuwa, Amma shi Ashraf din meye ribarshi idan yayi hakan? Dolene yanada manufarshi nayin haka, meye manufarshi to? "I'll take your silence as NO" Inji sadeeq. "No, bawai nayi rejecting bane, Saidai shi meye ribarshi idan yayi hakan? Nasan akwai wata manufa akai" inji Alhaji shamsu. "Good. Kayi tunani mai kyau, dolene yanada manufa, eh yanada ita, as you can see, Ashraf matashine mai ji da kudi da kyau, he's clocking 28 yrs wata mai zuwa, iyayenshi sun tasoshi gaba da mgnr aure har suka bashi wasu adadi lokuta na idan be kawo mataba zasu hanashi da wadda sukeso, shikuma wacce yakeso na schooling ne, sai nanda shekaru 2 zata gama, so shine daya bincika yaga kanada 'ya yaga why not ya aureta, AUREN KWANGILA, Inyaso daka biyashi saiya saketa at that time kuma yarinyar dayakeso is over sai kawai ya aureta, this is just a CONTRACT MARRIAGE, kamar yadda nafadama babu abinda zai shiga tsakaninsu, yadda ka kawota haka zaka amsheta" Shiru Alhaji shamsu yayi yana sauraronshi, yana kuma hada kalmominshi yana rarrabawa, abunka da businessman harya fara hango hanyoyin samun ribarshi na sosai ma, yes akwai riba, huge riba, babba ma kuwa. "Kai muke sauraro, ka amincene? Koko musami wani?" Inji sadeeq. Qara kallon Ashraf yayi Wanda a wannan karon shima shi yake kallo yana jiran amsarshi, nima nayi kasaqe da Biro a hannu ina jiran amsarshi. Bakajin komai a office din sai qarar A.C Sauke ajiyar zuciya yayi sannan ahankali ya bude baki yace......✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan cuta (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 006 Sauke ajiyar zuciya yayi sannan ahankali ya bude baki yace "Idan nace kubani lokaci inyi tunani fa?" Wannan karon Ashraf yayi magana cikin husky cool voice dinshi "You can have your time to think, is not as if tilastama akeyi, wannan deal ne kawai Wanda bazai yiwuba sai duka 6angarorin sun amince kuma sunyi sign, ni, kai sai daughtern ka, kanada ikon janyewa it's your right, Saidai remember millions of people are outside waiting for opportunity irin wannan, idan beyimaba karka ji kunyar fada. Am good with any of your answer" ya qarashe zancen yana qara balancing a kujerarshi. Ajiyar zuciya Alhaji yayi. 'Thank God. At least fargabana na aurama diyata kurma ya kau' yafada cikin zuciyarshi. "Babu matsala insha Allah, kawai dai kubani time inyi tunani" "Zuwa yaushe?" Inji sadeeq "Nan da Monday insha Allah" "To Allah yakaimu" "Amin thanks, I'll get going" "Alright mungode sir" "You're welcome" yafada yana miqewa tsaye tareda miqama sadeeq hannu sukayi musabaha sannan ya d'an sack kallon Ashraf sannan yafice. Kallon juna Ashraf da Sadeeq sukayi Bayan sun rakashi da idanu. "Did you think the jerk will accept?" Inji Ashraf cikin yamutsa fuska. "Ina jiyo qamshin nasara dai, he won't afford to loose this opportunity, besides wazai the whole SIR ASHRAF?" Murmushin gefen baki yayi yana sake balancing a kujerar. "It better be" yafada yana shafa sajenshi ahankali murmushin still a fuskarshi. **************************************** Tuqi yake Amma kwata kwata hankalinshi na wani wajen. AUREN KWANGILA? Contract marriage? Da familyn A.A? diyata tazama daya Daga cikin familyn A.A? Wow! What an incredible opportunity! Ni? In-law din A.A family? As for me banda problem but Saudart... Shiru yayi yana tuna aqidar Saudart na tsanar mutuwar aure, koyaya taji aure yamutu saita shiga damuwa da 6acin rai, musanmman idan antara iyalai. Tashin datayi cikin broken family yasa ta tsani mutuwar aure, lokaci da dama takan gayamishi ra'ayinta na son yin auren MUTU-KA-RABA, Akoda yaushe maganarta baya wuce "Dad katayani da addu'a Allah yabani miji na gari, ko bashi da kyau bashida arziqi ya kasance mai kyan hali, Wanda zamu Gina ingantacciyar zuri'a nan gaba, Wanda zamu hadu muba 'ya'yanmu tarbiyya, Wanda mutuwace kawai zata rabamu" Wani sa'in ya kan tsokaneta da marar kunya tana fadamashi irin wannan mgnan a matsayinshi na mahaifinta. Takan yi dariya lokuta da Dama tana rufe fuska sannan tace "Dad, ai gaskiyane, Aure wajibine ga dukkan musulmi Duk cikarka bazaka ta6a zama cikkake mai darajaba saikayi aure, name zanji kunya Bayan nasan koba dade koba jima saina yi auren? Hakan daya tuno ba qaramin tada mashi hankali yayiba. Me zaice mata? Zan hadaki AUREN KWANGILA da A.A sbd farfadowar company na? Impossible! Bazai iya kiyasta tashin hankalin fasata shigaba idan taji hakan, aure? Na Wanda bata saniba kuma bata ta6a ganiba? Kuma qarin gishiri a ciwo Aure na taqaittacen lokaci? Kai da kamar wuya. Haka yaita tunane tunanenshi harya iso gida jikinshi yayi matuqar la'asar. Shidai abinda yasani no matter what, bazai bar wannan damar ta wuceshiba. WAIWAYE (Adon tafiya🕴) Manage please🙏 Ummin fasihu ce 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan cuta (covid19)🤲 Ya Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 007 WAIWAYE (Adon tafiya🕴) Alhaji shamsu d'ane tilo ga Mallam yahya. Su yan asalin garin kanjiyane dake jahar katsina. Tun yana Dan shekara shida mahaifinshi yakaishi cikin birnin katsina almajiranci. A makaranta wani babban malami wato mallam Ballo. Haka suke rayuwa a wannan makarantar Wanda yawanci abincin dazasuci sai sunje bara suke samu, wani sa'in idan basu samuba haka suke haqura su kwanta kasancewar iyayensu basu wani had'osu da abincin kirkiba, gashi shima malamin ta kanshi yake don bazai iya daukar nauyinsuba kasancewar shima bamai wani hali bane ga d'aliban dayawa. Haka rayuwa ta kasance basa komawa qauyensu saiga damina don taimakawa iyayen da noma, da kaka tayi sai asake turosu da guzurin dabe taka kara ya karyaba. Rayuwa suke irin na sakakku wadanda babu mai tsawata Masu sai malaminsu shima a lokacin karatu, wani sa'in karatun ma ba dauka sukeyiba saboda ai sai ciki ya dauka sannan za'a maganar karatu, wani sa'in saisun yi aikatau sannan zasu sami abinci. Haka rayuwarsu ta kasance wani sa'in tufafin dazasu sa sai sunyi bara suke samu shima dakyar, wasu kau Kayan jikinsu sbd tsabar datti ko zanen Kayan ba'a gani, wasu kuma kaya sun 6e66ere Masu ajiki Amma babu halin dinkawa. Acikin wannan rayuwar wasu suke kauce hanya su fada munanan hali batareda an ankaraba tunda babu Masu sanyamusu ido, sai aga ba'a samo karatunba kuma 'ya'ya sun kangare sun gaggari al'umma. Shamsu shi Allah ya tsareshi da fadawa irin wadanan halin Saidai yataso da kwadayin abin duniya, kudi ko ta hanyar haram ne yanabi yasamesu, gashi da tarin karatu Saidai be amfaneshiba. Duk buga bugan dazaiyi yasamu kudi saiyayi don a tunaninshi kudi shine komai, idan kanada kudi to kowama kana iya takawa. Tun yana komawa kauyensu Duk damina don taya babbanshi noma har ya daina. Alokacin dakowa ke komawa kauye sai shi yashige cikin gari yana buga buganshi na Neman kudi, wani sa'in ya kwana a tasha wani sa'in a massalaci. Babu yadda babanshi beyi dashiba don ya dinga leqosu koda sau dayane a shekara Amma firr yaqi, don aganinshi baya iya zaman kauye kuma, yasaba da riqe kudi da cin Abu mai maski mezeje yi kauye? Abun ba qaramin damun mallam Yahya yayiba gashi shine d'a talin qwal nashi. Haka ya haqura yazuba mashi idanu don yariga ya kangare bawai maganar kowa yakejiba. Shamsu likafa taji gaba, Tun yana buga buganshi a katsina harya koma kano jin can anfi kasuwanci kuma anfi samun kudi. Wani babban shago yasamu aiki na yaron shago inda ake siyarda Cosmetics Kala kala. Sosai yake samun kudi don shagon shahararene kuma mai shagon na sallama mai tsoka. Dayake Shamsu Allah yayimashi farin jinin mutane, cikin d'an qanqanin lokaci yasan kwastamomi dayawa, kusan kowa yasanshi saboda barkwancishi da iya mu'amala. Ahankali ahankali yafara yiwa ubangidan nashi cuwa, yana mashi rinto, wani sa'in idan aka aikashi saro kaya saiya Dora nashi Asama kokuma wurin Saidawa ya qara akai. Dayake uban gidan nashi ya yarda dashi kuma becika sa ido sosaiba, beyi saurin ganewaba, saida yayi mashi mummunar 6anna, sbd Duk kusan customers dinshi sunbar zuwa sbd yadda kayanshi suke tsada. Ataqaice dai shago yarushe babu riba kullum sai faduwa, Daga qarshe Saidai ya sallami yaran shagon gabadaya yarufe shagon sbd rashin jari. Shamsu daketa Tara kudaden dayake samu wajen rintonshi, yasamu wani qaramin shago cikin kasuwar yabude shima yazuba irin Kayan da oganshi ke Saidawa ada. Ahankali ahankali, kasuwancinshi yadinga ha66aka, Allah yasa mashi albarka a kasuwancinshi. Abu qarami yakoma babba Tun yana sari garuruwa harya fara fita qasashen waje. Cikin shekara biyar ya bude wani qaton company mai suna A.S GALLERY Duk abinda akeso na Kayan alatu yana Saidawa. Company nashi yazama shaharare Wanda ake tutiya dashi garin kano. Wata shekara yadai runtse ido yayi aikin hajji shima sbd matsa mishi da abokan kasuwancinshi kemashi na yaqi aikin hajji. Haka dukiyar Alhaji shamsu yacigaba da bunqasa Wanda Duk yawanci na ha'incine don sosai ya kware wajen ha'intar mutane. Saidai abinka ga Dan kauye, Duk tarin dukiyarshi beta6a marmarin sayan kadaroriba sbd gaba kokuma yabude reshe awani wajen, Shidai Duk abinda yasamu ya narkawa company dinshi. Ana haka rasuwar mallam yahya ta riskeshi, sosai ya girgiza don rabonshi da kankiya harya manta, yana dai yimusu aike bakin gwargwado. Ba shiri yanufi qauyen, yayi kuka sosai jin baban nashi yadade kwance ba lfy, haka yaita Neman gafarar inno (mahaifiyarshi) harta yafe mashi. Bayan Arba'in ya tarkata inno sai kanon dabo don acewarshi bazai iya cigaba da zama a kauyeba. Shekara daya da rasuwar mallam inno ma tabishi, babu laifi mutuwar ta girgizashi na Dan lokaci sannan yacigaba da rayuwarshi. Yana Dan shekara 32 yayi aure ya auri wata shuwa Arab Wanda suka hadu da ita awata tafiya dayayi Maiduguri. Mace mai kyau, hankali da tarbiyya. Bayan shekara ta sulu6o Masu da kyakyawar baby mai kammaninta sak masha Allah. Saidai Tun Daga sannan suka fara samun sa6ani dashi a dalilin sata dayayi Wai tacire mahaifarta beson haihuwa diya daya ta isheshi. Wai 'ya'ya babu abinda suke jawowa sai talauci. Itakau firr taqiya Wanda hakan yaja mummunan sa6ani tsakaninsu Wanda Daga qarshe suka rabu da Abu yaqi dadi. SAUDART Nada shekara biyar Alhaji shamsu ya amsota sbd yaji mahaifiyarta zatayi aure acewarshi 'yarshi baza taje wani gida agolanciba. Saida aka kai ruwa rana sannan suka bashi ita da sharadin sai ta dinga zuwa Duk sati suna ganinta kuma yasata both islamiya da boko. Soyayya sosai Alhaji shamsu ke nunama Saudart, wata irin shaquwa ke tsakaninsu na qin qarawa don sunfi shaquwa dashi bisaga mamanta. Ya sakata both islamiyar da boko, Duk wani gata da diya zata samu wajen iyayenta tana samu don Saudart tadauko dukan halin iyayenta. Kyaun fuska da hali na mamanta sai farinjini da siye zuciya irinna bbanta. Tun tana yar shekara sha biyar tasauke Al qur'ani mai girma, a fannin boko kau tanada kwalin degree a fannin economics. Saudart Tun tana yarinya ta tsani mutuwar aure, don shine silan rabuwanta da daya Daga iyayenta. Tsanar yaqara karfine dataji a islamiya malaminsu ya gayamusu babu abinda Allah ya tsana kamar mutuwar aure don har sama girgiza take. Tin alokacin take addu'ar Allah yabata miji nagari Wanda mutuwa kadai zata rabasu. Tana gama degree dinta ta matsama daddynta ya bude mata bakery, sbd tsananin son datakema girki, da farko yaqi yarda don yafison tayi aikin office Amma data matsamashi dole yabude mata Wanda nan da nan Allah yasamata albarka a harkar har tayi fice a garin, babu Wanda beson ALHAIRI BAKERY ba. Ana haka wannan cuta (covid19) tashigo duniya harta 6illa Nigeria Wanda hakan baqaramin rushe tattalin arziqin qasa yayi, cikin wadanda abun yashafa harda Alhaji shamsu don komai ya karye sakamakon rufe border da akayi. Ga tarin basussukan da ake binshi na banki haka yasa dole yanemi taimakon shahararen kamfanin nan na A.A ENTERPRISES. Saiga kuma yadda abun ya kasance...✍ Sorry babu dai editing🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan cutar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 008 Cigaban labari📖 Yau Saudart tafi zama busy saboda ita dakanta ke tsara cake din bikin Sir Wilson, abubuwa take cikin qwarewa while wasu tsirarun ma'aikata na gefe suna qara daukar kwas. Aiki take Amma hankalinta na wajen daddynta. Tun dazu take jiran kiranshi Amma shiru, Allah Allah take ta ida ta dawo gida, abindama yaja delay rashin samun kalar colouring dasukeso dawuri da tuni angama an hada da kingin snacks da akayi delivering dazu. 6:30pm ta kammala cake din, sai tashin wow! Wow!! Kakeji a dakin kamar jiniyar motar ambulance sbd haduwar cake din. "Wow ma'am! This is the best cake I've ever set eyes on" inji wani mai suna Farouq yana tafawa. Nan kowa yabi sahu sunata tafa mata. Yar dariya tayi sannan tad'an dramatically tana cewa "thank you, thank you". Ba ita tabar bakeryn ba sai 7:00pm Duk hankalinta yayi gida. 'Meyasa dad be kiraniba? I hope all is well' tafada acikin zuciya. Da sallama tashiga parlourn, can ta hango daddy a dining yana sipping din coffee. Dadi taji ganinshi cikin nishadi babu damuwar komai. Amsamata sallamar yayi cikin fara'a saikuma yasha mur yana kai dubanshi ga wall clock. Dan Waro idanu tayi tana Dan dariya ciki ciki yayinda ta qarasa wajenshi tana rungumo kafadunshi. "Sorry dad, am late, wlh wani aiki ya tsayar dani" Hararar wasa yayimata. "Silly girl, harna fara damuwa danaji shiru" yafada yana dungure mata kai. Shafa kan take tana turo baki "Ai Dad Baka damu daniba, ko ka kira kaji lfy?" Murmushi yayi yace "ai ina cikin shawarar kiranki sai gaki" Jan kujera tayi ta zauna kusa dashi. "So daddy how far? Guess ansamu nasara. Yadda kake washe bakinnan nasan ba banzaba" Bugu yakai mata ta kauce tana dariya. "Lallai kin maisheni kakanki ko?" "Am sorry, Nidai ya kuka kaya?" "Lau.. Tashi kiyi Sallah mufita, akwai outing yau" Wani ihu tabuga tana tsalle "Yeee! Kace anci nasara? Kai alhamdulilah! Dad am soo happy!" Tafada tana rungumarshi. Dariya yayi yana janyeta. "Tukunna dai, kidai je kiyi sallar ki shirya" "Yanzu kuwa" tafada tareda yin hanyar dakinta da sauri harda hadawa da Dan gudu. Binta yayi da kallo harta kule, Ajiyar zuciya yayi yana sake qarfafama kanshi gwiwa. Sosai Saudart taji dadin outing din don wurare daban daban suka je na shaqatawa, sannan sukaje wani had'ad'en restaurant sukaci abinci Daga qarshe suka biya shopping mall sukayi shopping Wanda Duk yawanci Kayan data kwasa dad dinta na siyarwa kawai shiya matsa saita saya. Agajiye liqis suka dawo gida. Saida kowa ya watsa yayi sallar isha'i sannan suka dawo parlour suna kallo suna hira. Soyake ya dauko mata maganar daketa cin ranshi Tun dazu Amma yakasa. Can ya nisa ya kalleta da yanayi na seriousness yace "SAUDATU" Dumm gabanta yafadi dajin yakira ainahin sunanta. Kasa kai cokalin ice cream din tayi a baki ta ajiye sannan ta maida hankalinta kanshi. Shiru ya ratsa falon yana tunanin yadda zaiyi mata presenting din maganar, can ya nisa yace "Saudatu, baki tambayi yadda muka qare dasu mutanenki ba" Ajiyar zuciya tasauke da qarfi "Kai dad, harka bani tsoro, to ya kuka qare ba cewa kayi sun bakaba?" "Eh sun bani Amma basu baniba" Kallon rashin fahimta tayimashi "Ya hausan sun Baka, basu bakaba?" "Abinda yafaru shine....." Cikin qwarewa da baiwarshi ta dadin baki ya labarta mata Duk yadda sukayi dasu Sadeeq. Tunda yafara magana ta zubamashi idanu tana kallo ko blinking batayi don ita harga Allah batasan inda yadosaba. Koda yakai aya batabar kallon shiba. Shima kallonta yake don ganin reaction dinta Amma she's expressionless. Kamo hannunta guda yayi yana Dan murzawa. "Are you there shalele?" Sai alokacin tayi blinking, ahankali ta motsa baki tace "I don't get you dad, kaina ya kulle" Murmushi yayi sannan yafito mata 6aro2 yace "I mean so suke inbashi ke akan yarjejeniya Dana biya zai maidomin ke, ma'ana you guys are having contract marriage" Zaro idanu tad'an yi sannan ga mammakinshi tafashe da dariya harda tafawa. "Lol.. Amma dad mahaukatane ko? I guess company mahaukatane idan ba hakaba ina aka ta6a wannan irin auren? Ko a film ma banta6a ganiba, gaskiya a binciki brain dinsu" Shiru Dad yayi yana kallon yadda tama maida abun wasa. "Jewel this is not funny, please let be serious" yafada yana qoqarin danne 6acin ranshi. "Ok..ok, naji sai kace musu me daddy?" "Subani lokaci inyi tunani akai" "Tunani? Tunani fa kace Dad? Meye abin Tsayawa tunani anan, amsar a Afili take, idan su jahilai ne mu ba jahilai bane, the amsa is capital NO!" Tafada itama cikin son danne 6acin ranta Amma deep down she's boiling. Kamo dayan hannun nata yayi yahada biyu sannan a tausashe yace "shalele, please listen, ahalin yanzu banida za6in da yawuce..." "Wait Dad.., come again, bamuda me? Bakada za6i fa kace? Don't tell me kana shirin yadda da jahilcinsune" ta katseshi tana kallonshi unbelievable. "Saudart... Wannan ba jahilci bane, banida choice, sokike inzauna in nade hannu ina kallon company na yayi collapsing a gaban idanuna?" Shiru tayi don she's speechless ma, kallon shi kawai take cikeda rashin yarda. Matsa hannunta yafarayi a tausashe. "Kinyi shiru shalele, please say something, yanzu kece last hope dina. Please speak up" "Dad me zance? Ka kasheni da raini, nakasa yarda da abinda nakeji Daga gareka" "Saudart auren nan ba dadewa zaiyiba, zanyi iyakar qoqarina wajen ganin na hada kudin dawuri, bazaki wuce 6months ba" Fizge hannunta tayi ba shiri "Dad! Are you kidding me? AUREN KWANGILA? Ni? Dad kasan abinda Allah yafi tsana shine mutuwar aure? Wannan ma agefe, Dad atunanina kafi kowa sanina, kafi kowa sanin ra'ayina, kasan ra'ayina na aure.." Katseta yayi dacewa "sanin hakan yasa na yarda da sharadin babu abinda zai shiga tsakaninku, believe me I.." "Noo!" Ta katseshi da karfi tana toshe kunnuwanta. "Shalele.." Miqewa tayi bashiri still hannunta dade da kunnuwa, idanunta nakawo ruwa. "I said No! Bazai yiwuba! Impossible!" Saita juya dagudu tanufi stairs kuka ba kufce mata. Binta yayi yana kwalamata kira Amma inaa shigewa tayi dakin tarufe harda sa sakata, sannan taruga tafada kan gado tana gunjin kuka. Naushin iska yayi yana fadin "shit! Shit!! Shit!!!"...✍ No editing🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan cuta (covid19) Allah ka ji6anci lamuranmu karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 009 Aranar babu wanda yayi barcin kirki cikinsu, musanmman Saudart data kusan kwana tana kuka. Da asuba a kasalance ta tashi tayi Sallah ko lazimi Kasa yi tayi barci ya dauketa akan sallayar saboda rashin isashen barci datayi jiya. Sai 8:00am ta farka, wanka tashiga Bayan yan mintuna tafito sannan tayi shirin aiki a kasalance, har yanzu takasa yarda da abinda yafaru jiya. Ahankali take saukowa a stairs din hannunta daya da waya danyen kuma rataye da side bag. Dago kai yayi yakai dubanshi saitinda yajiyo takunta. Kallo daya yayi mata yagane kukan datayi jiya ba kadan bane saboda yada idanun suka dan kumbura gashi basu ida washewaba. Tunda suka hada idanu ta kauda kai sannan tanufoshi a kasalance. "Ina kwana Dad" ta gaisheshi in a formal way. Kamo hannunta yayi zai zaunar daita kusadashi ta janye cikin wayancewa. "Dad, am late, zan wuce aiki" Kara kamo hannunta yayi yace "break fa, baki karya ba" "Am ok" ta amsa ataqaice. "No, dole kici wani Abu, please sit down" Zata bude baki tayi musu yayi saurin katseta da "Please.." Babu musu ta ja kujerar ta zauna, da kanshi yayi serving dinta sannan ya turamata gabanta. Ba musu tajawo abincin tashiga ci Saidai Duk yadda yaso su hada ido taqi yarda. Tutturawa taitayi har saida taci rabi sannan ta ture plate din tana goge bakinta da tissue. Kamo hannunta guda yayi ganin tana niyyar tashi hakan yasa ta fasa tashin Saidai ko dagowa batayiba. "Shalele?.... Fushi kike da Daddynki?" Shiru tayi kanta Kasa "Am so sorry shalele, banyi hakan don 6atamiki raiba. Kawai banida za6ine, shalele ko jiya saida akayiman barazana ta waya, ga banki kema kifini sanin halinda nake ciki Basai nasake miki bayaniba" yafada a tausashe yana murza hannunta. Har yanzu shiru tayi batace komai ba kuma bata dagoba. "Shalele idan da inada yadda zanyi nima Tun farko zanyi rejecting dinsu Amma a halin yanzu they are my last hope" "Dan ba'aso mutum na fidda rai akan rahmar ubangiji, arziqi da rashinshi Duk na Allah ne, saboda bamason talauci saimu sa6ama Allah? Shin wayau zamu yima Allah? Kasani Allah yasan damu Kuma yasan halinda muke ciki, akwai wadanda suka fimu shiga matsala kuma sun dauki qaddara, why not Muma muyi koyi dasu? Dad wannan kwata kwata is not an option, haram ne" "Shalele, Allah na yafewa Duk Wanda ya nemi yafiyarshi, zamu nemi yafiyar Allah Bayan mungama komai, Allah gafurun raheem ne" Shiru Saudart tayi don takaici yama hanata magana "Say something please jewel" Janye hannunta tayi Daga riqonshi tace "Dad bazan iyaba, tunda bazaka iya rungumar qaddara nizan siyarda bakery dina saikayi settling din komai, inyaso saina nemi aiki" Da ada ne zai yarda Amma yanzu babu abinda yakeso kamar yazama surukin A.A so maganar siyarda bakery ma be tasoba. "Shalele siyarda bakery dinki won't help, kawai amincewarki ne kadai zai taimakeni" "Then am sorry, bazan iyaba" tafada ta tashi afusace zata wuce. Kamo hannunta yayi da sauri tareda juyota da d'an karfi "Don't you dare walk out on me ok?! Ina miki magana zaki wani tashi min ki wuce, ni tsaranki ne?!" Yafada 6acin ran dayake dannewa yaqi dannuwa. Kallonshi take idanunta suka kawo ruwa don tunda take beta6a yimata maganaba cikin wannan yanayin. "Dad?.." "It ok, kina iya tafiya, atunanina ke mai sharemin hawayena ce, a tunanina ke mai rufamin asiri ce but am made a mistake!" "Dad..." Saikuma ta fashe da kuka. "Go! Kawai ki tafi nagode" yafada yana barin parlourn Dama gidan gabadaya. Kuka Saudart keyi kamar ranta zai fita, tarasa gane meyasa idanun daddynta yarufe har haka. Bakeryn dabata fitaba kenan, ranar taci kuka har ta godewa Allah. Saidai tayima 'yan bakery dinta qaryar batajin dadi sannan ta wakilta P.A dinta tayi taking charge. Yini tayi cikin qunci ranar tayita jiran dawowar daddy Amma hartayi barci be dawoba. Washegari ma Tun kafin tafito yafita. Duniya tayima Saudart zafi don kwata kwata Dad yafita harkarta. Abinda be ta6a yi mataba, kullum cikin kuka take don bema barin su hadu, koda sun hadu baya amsa gaisuwarta barema azarce sa magana, Dama yaganta zai fice ko yashige dakinshi beqara fitowa. Dukda damuwar datake ciki na shariyar daddy hakan be sata jin zata amince da buqatarshi ba, she's stubborn, tagado taurin kan maminta ne. Yau Monday dawuri tashirya cikin wata gown din atamfa mai A, sannan ta yane kanta da kyale mai dan girma. Sosai tayi kyau dukda kallo daya zaka yimata kasan tana cikin damuwa. Fitowa tayi falo, kamar yadda tayi zato Dad yariga yafita. Itama Sakai tayi tafita batareda ta kula breakfast da'aka jeramataba. Motarta tashiga sannan ta karya motar hanyar company din A.A ENTERPRISES. Dole ayita yau taqare, tagaji da attitude da daddynta kebata. Bazata iya juraba kuma, dolene yau taga A.A......✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annoba (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 010 Cikin kwarewa tashigo da motar cikin qatuwar haraban shahararen company nan datake tajin labarinshi. Parking tayi a parking space sannan tafito ahankali. Cikin wayencewa take qarema makeken qayattacen company din kallo tana tasbihi ga Allah. Kallo daya zakayima kamfanin kasan mallakin tattacen mai kudi ne don Duk inda ka wulga glass ne, kamar dashi akayi ginin. Hatta entrance door ma na glass ne. A wajen sanitizing hannu taje ta wanke hannunta kamar yadda yake doka akowani wajen da za'ayi cud'anya da mutane Tun shigowar wannan cutar (covid19), sannan taje wajen kofar ta latsa botton yabude sannan tashiga yarufe sannan tasake budewa taciki. 'Masha Allah' ta furta tunda tasa kafarta tashiga ciki. Watakan wani Sanyi mai dadi ya bugeta mai cakud'e da sanyayan qamshi. Zuqar iska tayi ahankali tana lumshe idanu sannan ta furzar. Cikin natsuwa take takawa zuwa wajen receptionist dake gefe tanayi tana qarema wajen kallo a wayance, kujeru dake jefi jefi awajen ma abun kallone. Wajen receptionist din tanufa, mace mai fara'a ta gaisheta. "Welcome to A.A ENTERPRISES ma'am how may I help you" tafada fuskarta washe. Dan Gyaran murya Saudart tayi sannan tace "thanks you, please I want to be directed to the C.E.O office" "Ok ma'am, here you are" inji receptionist din tana miqamata wani card. Amsa tayi tayimata godiya sannan tabar wajen tana kallon card din. Wajen lift tanufa tayi typing din floor number din a sannan tashiga. Cikin yan sakanni harya kaita, kofar tabude tafito. Qauyancinta kusan fitowa fili yayi saboda haduwar wajen yawuce misali. Sai yanzu taga can Kasa Ashe nafilane a kyau. Cikin natsuwa ta taka zuwa desk din secretary din wanda hankalinta ke kan system din gabanta. Ganin kamar ba musulma bace sakamakon 6ingillalun kayanta da uban gashin doki data tilama kai yasata cewa "Hi" Maimakon sallama. Dagowa Helen tayi tana kallonta, wata kyakyawar budurwa tagani mai mugun shiga rai, gatadai bawani ado tayiba ko kwalliyar hauka Amma ita kanta ta burgeta. She looks so simple and unique. "Hello, how may I help you?" Ta amsa tanamata wani kallon raini don atunaninta irin yanmatan nanne Masu kawo Kansu wa boss nata dukda taga wannan kamar nitsatsace koga decent shigartama. Dukda ta lura da kallon rainin da matar ke binta dashi hakan besata nuna komai ba tace "Yes, please inason ganin C.E.O ne" Wani kallon up and down tasake binta dashi zuciyarta fall Kishi don itama a haukanta son boss take. "Kunada appointment ne?" Ta tambaya a d'age. "No Amma what I want to discuss with him is very important" inji Saudart da jikinta yafara Sanyi da yanayin kallon dataga matar ke binta dashi. "Boss baya ganin mutum saida appointment so am sorry kya iya tafiya idan kika samu appointment dashi saiki dawo" Ta maida hankalinta ga system din gabanta. Shiru Saudart tadanyi tana nazarin me zatace mata tabari taganshi don sosai takeson ganawa dashi. "Please I really.." Katseta Helen tayi da "what? Waiku mata meyasa bakuda ajine, ayita koranku Amma kuyita naci, ke yanzu bakiji kunyaba? Kin wani wanko kafa kinzo gun namiji har office? Da anyi magana kuce Muslim, Masu tsoron Allah, ina tsoron Allahn yake? Kitafi kafin yafito don mutuncinki zaici don ba irin yan iskan mazannan bane" Sosai kan Saudart ya kulle, Wai tsaya me take shirin kirantane? Kafin tasamu zarafin magana kofar office din C.E.O din ya bude saigashi yafito cikin shigar suit baqi da shirt din ciki fari. Turus yayi ganinsu tsaitsaye kasancewar tashi Helen tayi tana zazzaga mata bala'in. Kallon Saudart yatsaya yi na yan daqiqu sannan ya kalli Helen "Helen, what's going on here?" Cikin ladabi tafara cewa "Sir, Wai Mr A.A take son gani kuma basuda appointment Sir" Kallon Saudart yayi dake kallonsu itama yace "hello miss" Dakyar ta iya cewa Hi saboda yadda takeji, she felt totally embarrassed jin yadda Helen ta fassarata. "Mr A.A zaki gani?" Ya tambaya a tausashe Kamar tace A'a tafasa saikuma ta daure tace "Yes Amma ba prob tunda sai an samu appointment dashi, am sorry" tafada tana niyyar juyawa. Saurin tsaidata sadeeq yayi dacewa "wait please, am so sorry. Ba haka bane bari inyimiki iso" Juyo tayi asanyaye tace "A'a ba matsala fa, zan naimi appointment" "No please ki tsaya bari nayimiki iso" yafada yana juyawa da sauri ya bude kofar daya fito ya shige. Da kallon mammaki Helen tabishi dashi. Itakau Saudart dadi taji koba komai zata samu damar rama wulaqancin da Helen tayimata. "Hey.. Atunanina kallo daya za'ayima ni dake a tantace wa ya cancanci sunan karuwa, Saudart tafi karfin tabi namiji Saidai subita, maza dayawa sun mutu mata Masu kyau kudi da aji mezatayi da tsoho akwala (atunaninta tsohone mai kamfanin) So it's better ki dinga tauna kalamanki kafin ki furtasu don mata suna suka tara". Daidai nan sadeeq yafito yana fadin " bismillah madam" Wani kallo tasake watsama Helen sannan tabishi abaya tabar Helen hangame da mouth😨 Ahankali tasanya kafarta cikin office din wani daddadan qamshi namata marhabin. Saida tashiga sannan sadeeq yafita yana rufomusu kofar. Tsayuwa tayi takasa gaba takasa baya don jitayi Duk qarfin gwiwarta data shigo dashi ya zirare. Batama son dago idanu ta kalleshi don bata buqatar haka. Haka taita Tsayuwa kanta Kasa tana jiran ayimata iso Amma shiru. Shima 6angaren Ashraf hakan take don tunda sadeeq yazo ya kyankyasa masa ya tsinci kanshi cikin 6acin rai. Wato like father like daughter, yadda uban keda kwadayi hakama Diyar tunda gashi takawo kanta, hakan yasa yaqi dagowa ya kalleta tunda tashigo. Jin shirun yayi yawa yasamu dagowa lokaci daya, caraf suka hada idanu👀 Gaban Saudart yafadi tayi saurin janyewa don bashi tayi zaton ganiba. 'Wannan ne A.A din ko d'anshi ne?' Tambayar datayima kanta kenan. Shikau ko a kwalar shirt dinshi don bawani Tsayawa qaremata kallo yayi ba. "Good morning..sir" tafada cikin rawar murya. Shiru yayi kamar bazai amsaba sai can kuma yace "Morning" Ganin Beda niyyar yimata iso yasata summoning courage ta qaraso gabanshi taja kujera tana fadin "may I?" Banza yayi da ita itama bata jira amsarshiba tazauna don Allah Allah take tayi abinda yakawota takoma. Shiru ya ratsa office din, tanata kokwanton tayi maganane kota bari yafara. Ganin wankin hula nason kaita dare yasata yin karfin halin cewa "Ehm.. Am Saudart shamsu by name" Shiru tayi ganin ya dago yazubamata cat eyes dinshi daya kusan rikitata. Janye idanu tayi saurin yi sannan dakyar tasake bude baki tace "Ni diyar Alhaji shamsu kankiya ce" "Uhum?" Ya buqaceta cikin tsareta da idanu. "How may I help you Miss Shamsu?" Jitayi ta takura da kallon qurrillar dayake binta dashi, cikin inda inda tafara cewa "Akan.. Akan previous maganarku da Daddy ne, na...na.. Auren...auren contract... Shine..." "Shine kikazo yimin godiya Dana za6i nayi hakan da babanki? Koko shine yasa kikazo nuna jindadinki nazama mai sa'ar dazata aureni" ya katseta dafadin haka cikin raini. 'What!' Tafada azuciyarta. Dagowa tayi ta kalleshi shima ita yake kallo "No..no ba haka bane..." "To yayane?" Ya sake katseta "Kinzone don ki ganni kiji sanyine koko kinzo don kiyi selfie dani asamu abin dorawa a status? Ko kinzo ne don kina buqatar kudi?" "What!" Wannan karon tayi exclaiming Afili. "Ok nawa kikeso, Dama nasani Basai kinzoba, nasan Duk macenda wannan opportunity din yasameta saitaji kamar ta kashe kanta don dadi, Saidai dafatan tsohon naki yaga yamiki this is a contract marriage, babu abinda zai shiga tsakaninmu, zan baki kudi, da suna don Daga inda kika aureni kinyi suna Amma bazan baki kaina ba, am not that cheap, babban goro.... Ni mai tsadane, wutsiyar raqumi ke kanki kinsan tayi nesa da qasa, don haka karkiyi crossing limit dinki, yes..as I was saying nawa kike buqata diyar Shamsu?" Saudart was shocked, dumbfounded, angry and overall embarrassed. Kallonshi take idanunta na canza launi from pure with to red. Tunda take ba'a ta6a cimata mutunciba irin na yau. Bata ankaraba taji saukar Abu a fuskarta, razana tayi tabi abin da kallo inda yafadi taga wrapper yan dubu dubune guda biyu. "Dauka ki 6acemin" yafada yana maida hankalinshi kan system din gabanshi. "What!" Taqara exclaiming tana miqewa tsaye...✍ No editing🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 011 "What!" Taqara exclaiming tana miqewa tsaye ilahirin jikinta duk cira yake. "Me?..." Tafada tana nuna kanta da yatsa hawaye na taruwa a idanunta. "How dare you? How dare you?!" Tafada muryarta na cracking. Wani kallo ya watsamata sannan yaja dogon tsaki yana cewa "Dalla mallama fitarmin a office ko kudin ne basu ishekiba?" Jiki na rawa ta tsugguna ta kwaso kudaden tana mai yage paper da akayi bundling dinsu. Be ankaraba yaji watsin kudaden a fuskarshi. Saurin dagowa yayi yana kallonta a mammakince. Watsi tafarayi da files din kan table dinshi wanda hakan yasashi saurin miqewa yana kallonta. "Hey! Kinyi haukane?!" "How dare you!" Itama ta daka mishi tsawa. "Ni zaka ciwa mutunci? Who the hell did you think you are?! Uhm? Gayamin!" Nunashi da yatsa tayi dake rawa don Duk ilahirin jikinta rawa yake abinka da mai zuciya. Ga hawayen dasukaqi Tsayawa. "Kayi kadan, kayi kadan ka wulaqantani! Kayi kadan nabika, me kake dashi dazan bika? You have nothing! Ni ba kallon namiji nake makaba don bakakai akiraka da namijiba haka zalika bakakai darajar maceba. Yes nazo nan don maganar contract whatever, Amma ba don komai ba don infadama bakakai standard din zaka mallakeniba koda daidai da second dayane. Bakada wannan quality din, and also kudinka basu isa susani kallonkaba saboda I don't fucking care about your goddamn money! Kai suka Dama ni ko ajikina, lastly kasan wanda zaka dinga ma wulaqanci domin yayinda wasu ke binka kamar yadda kake ikirari wasu ko sanin ka wanzu a duniyarnan basuyiba" Ashraf dayayi mutuwar tsaye beko motsi yakasa cewa komai don he never expect this. Dakyar yabude baki yana nuna kanshi da yatsa "Ni? Kinsan koni waye?.." "Go to hell! To hell with you and your personality, bansan ko kai wayeba kuma I don't fucking care!" Ta ida atsawace hawaye na gudu afuskarta sosai kamar Wanda aka laqadama shegen duka. Daukar handbag dinta tayi sannan ta watsa mishi wani kallon tsana da rinnanun idanunshi tabuga tsaki tareda fadin "Bloody idiot" Fuu tafice tana banging kofar da karfi. Har tsakar kanshi yaji tsakinta da zagin dakuma bugawar kofar. Bin inda tabi tafita yake da kallo kamar haryanzu tana wajen, zuciyarshi inbanda bugawa babu abinda take ga wani suya na musanmman da take. Daidai yafito Daga office dinshi dauke da files yaga wucewarta dagudu. Saurin binta yayi Amma ina harta shige elevator. Tsaki yaja cikin takaici, saida fa yayi warning Ashraf karya cimata mutunci, a fusace ya nufi kofar office din Ashraf da niyyar rufeshi da masifa. Turus yayi ganin yadda office din yakoma kamar na mahaukata, ga Ashraf gefe be ida dawowa hayyacinshiba. "Ashraf?" Yakira sunanshi yana dafa kafadunshi Bayan ya qarasa wajenshi. Dagowa yayi ya kalleshi, gaban sadeeq yafadi ganin yadda launin idanunshi suka canza. "Ashraf menene? Meya faru?" Ya tambayeshi a rude yana kamo hannunshi. Fizgewa yayi cikin zafin nama yana watsa mashi jajjayen idanunshi dasuka koma kamar gauta. Hanyar toilet yanufa cikin sassarfa yabude yashige sannan shima ya turo kofar da karfi. Sadeeq tsaye yayi yana kallon ikon Allah, 'to me yafaru?' Abinda yaita tambayar kanshi kenan. Dagudu taqarasa wajen motarta tashige, kifa kanta tayi kan steering tana cigaba da kukanta. 'Dama wannan ne daddynta keson ta aura? Lallai' "Shine kikazo yimin godiya Dana za6i inyi hakan da mahaifinki?" Maganar Ashraf yashiga amsa kuwa a kunnenta "Koko kinzone don muyi selfie kisamu abin dorawa a status?" Cizan yatsanta manuniya tayi da qarfi hawaye nazuba. Bata ta6a danasanin yin Abu a rayuwar taba kamar yau. Lallai aikau Duk abinda daddy Saidai yayi don wlh bazata ta6a yarda da buqatarshi ba. Afusace ta tada motar tadau hanyar bakery dinta. ********************************** Yau 'yan bakery sunci ubansu don rikitasu Saudart tayi, Abu kadan saita rufe mutum da fada kamar zata cinyeshi, sunsha mammaki, matarda ba ruwanta tashige cikin ma'aikatanta Ayi raha Ayi fira? Ko maryam P.A dinta tsoron tunkararta take da magana don sau biyu kenan tana masifeta. Haka yau bakery yazama ba dadi don kowa yasan yau ran boss a6ace yake hakan yasa kowa ke taka tsantsan daita. Koda aka tashi ficewarta tayi batareda sunyi sallama kamar yadda ta sababa. Kawai haryanzu haushi takeji, ga maganganunshi sai eoching a kunanta yake. A dining ta iske daddy yana cin abinci, gaisheshi kawai tayi ta haura sama unlike da dazataita binshi a marairaice. Hakan yasa daddy sanin Duk yadda akayi anta6otane don idan Saudart tayi zuciya bakyau, abinka damai hqr. "Ashraf Wai Meya faruwane, kavarni ina 6a66atu kamar wani dan iska" inji sadeeq afusace. Ko motsawa Ashraf beyiba Daga balancing dayayi a kujera idanunshi lumshe. "Ashraf!" "What?!" Ya fada a tsawace kamar wanda aka tsakura. "Wai meke damunka Ashraf?" Inji sadeeq cikin mammaki. "You know what? Nakusan maqureka a office dinnan wlh, ina ruwanka dani? Spare me mana, aah aah?" Yafada afusace. "Kaifa dan iska ne wlh, mekayiwa diyar mutane tafita tana kuka" Harara ya dalla mashi yace "sainaji shaquri sannan, mtcheew, abeg kira wannan tsohon banzan kace wlh nanda kwanaki uku idan bezoba zanyi cancelling din deal dinmu ne" A mammakince yace "meyasa?" "Shine nace sainaji qarfin maqara, get out abeg!" Ba yadda ya iya ya tashi ya fice don yasan halin mutumin nashi. Jingina yayi da kujerarshi yana d'an jujjuyawa "hmm you're in hot soup, I swear" yafada yana tauna le6en qasa...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annoba (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 013 Kwanaki biyu kenan rabonda tasa daddynta ido, sanda zata fito bayanan bata kuma sanin dawowarshi. Yau ranar Alhamis, as usual tadawo Daga aikine agajiye. Dakyar ta iya kai motar wajen parking tayi parking. A kasalance ta fito ta rufe motar. Wata mota tagani a parking space din Wanda ba tasu bace. Tsayawa tayi tana kallon motar taba tunanin to ta wanene? Wucewa tayi ta murda kofan falon tashiga da sallama. Tarin dataji Anayi ba qauqautawa ne, yasata jin ta wartsake nan take. "Dad?.." Tafada idanunta waje. Da sauri tanufi part dinshi tana kwala mishi kira. Murda kofar tayi tashiga, Turus tayi tareda saurin rufe bakinta da tafin hannu. Dad ne kwance yana tari kamar na fitar rai ga doctor ya duqufa kanshi yana qoqarin shawo kan tarin. "Daddy!" Tafada da qarfi tayi wurgi da handbag dinta taruga wajenshi. Kamoshi tayi tana kuka ganin yadda yake tarin Duk ilahirin jikinshi rawa na rawa. "Nashiga uku daddy, doctor what's happening to my daddy?" Tafada cikin kuka sosai. "Please miss Saudart kiyi hqr kifita" "No!" Tafada tana qara rugumoshi tana kuka sosai. "Please kinaso muyi loosing dinshi? Kibari nayi aikina" Jin hakan yasata janyewa Amma still tana kuka. "Kifita please, kijira waje, komai zaiyi daidai insha Allah" Badon tasoba tafita tasamu wata kujera ta zauna tana kuka. Meke damun daddynta? Dama bayada lfy? Tun yaushema yafara rashin lfy? Anya kau ta kyautama kanta? Ace mahaifinta suna gida daya Amma harya kwanta ciwo bata saniba? Haka taita jerama kanta tambayoyi tana kuka. Bayan kusan mintuna ashirin sai gashi doctorn yafito yana yarfe gumi. Da sauri tamiqe tana kallonshi "Doctor ya yake? Is he fine? Please tell me he is, please" "Miss Saudart, ki kwantar da hankalinki please, zauna zamuyi magana" Zama tayi hawaye nabin kuncinta "Saudart garin yaya kuka barshi har yakai wannan stage din batareda kun kaishi asibitiba?" Kan Saudart yasake kullewa "Doctor meke damunshi ne? Wlh bansan baya lfy ba" "Really? Kuma kuna kwana under roof daya ace bakida masaniya akan lfyanshi?" Kasa amsawa tayi sai kuka. "Well am sorry, Amma daddynki yakamu da ciwon zuciya" Waro dara daran idanunta tayi tana toshe bakinta da hannu tana girgiza kai unbelievably "No, it can't be" "Yes miss Saudart, daddynki yakamu da ciwon zuciya sanadin damuwa, damuwa tamishi yawa har yayi sanadin stressing din zuciyarshi yanzu haka gab take da bugawa" "No!!" Saikuma tafashe da kuka abin tausayi. "Nashiga uku ni Saudatu, daddy idan katafi kabarni ya zanyi?" "Bazai tafiba insha Allah idan kuna kiyayewa, Ku kiyayi 6atamishi rai, Ku dinga yimashi abinda zai faranta mishi, sbd next time yasamu wani attack din sai Allah" Kuka take afujanjan, badai akan wannan auren contract dinba yakamu da ciwon zuciya ba? Badai tasoshi gaba yan banki sukayi ba? Ita Saudart ina hankalinta yatafi ta za6i tayi nisa da daddynta a lokacin dayafi buqatarta? Kaico. "Ga magunguna can na ajiye a bedside locker akwai prescription dinsu ajiki, a dinga kulawa da maganinshi and I repeat aguji 6ata ranshi" Daga haka yayi mata sallama yafice. Ta dade zaune awajen tana kuka sannan ta lalla6a ta tashi tashiga dakin daddyn. Ahankali taqaraso wajenshi tana kallonshi, kukane yakusan kufce mata tayi saurin dade baki don karta tadashi. Zama tayi gabanshi ta riqo hannunshi tana murzawa ahankali. "Dad ka yafemin, nakasa share maka hawaye ka yafemin" tafada cikin muryar kuka. Saida tayi mai isanta sannan ta share hawayenta. "Daddy insha Allah bazan ta6a bijirema ba, badai akan bashin bankiba? Insha Allah nizan sharema hawayenka. Gobe insha Allah zanje in saka bakery na kasuwa, banga amfaninshi ba idan inada damar siyar wa in taimakekaba. Insha Allah damuwar ka tazo qarshe" Don tsabar takaici jiyayi kamar yabuga uban tsaki Daga inda yake kwance. Wai wacce iriyar yarinya ce wannan mai kunnen qashi? Wato har lanbon ciwonma bazai sata Amincewa da qudurinshiba? Tsaki yaja azuciyarshi, jiyake kamar yatashi yaita kifeta da Mari. Wai bakery? Ana batun arziqi waketa tsinannen bakery can. Haka taita sabbatunta shikau sai qumuwa yake da takaici Saidai ba halin yako motsa. Aka ta kwana tana kulada Alhaji Washegari kau tayi waya dawani wanda tasani akan maganar siyarda bakery dinta. Saidai me? Duk inda akaje Saidai ayimasu tayin wulaqanci. Tun tana daukar abin wasa har abun yafara bata tsoro, kwata kwata highest din tayin 5million. Sosai tashiga damuwa, Duk inda akaje Saidai suce ai yanzu abubuwa sun rage daraja, corona virus. Abinda batasaniba, daddynta ne keda sa hannu awannan abin, shi yasa akebin kwakwafinta Duk inda taje siyar wa saisu saye mutanen akan suyimata tayin wulaqanci. Saidai naci da taurin kan Saudart yaqi bari ta hqr. Ganin wankin hula na naiman kaishi dare yasashi watarana burkuce mata, aman jini yadinga yi ba kakkautawa. Hankalin Saudart yatashi ainun idan banda kuka babu abinda take. Koda takira doctor fada yayita mata kan idan Alhaji yamutu itace. Haka taita kuka ganin dai babu sarki sai Allah tafara sabbatu. "Wlh nayarda, nayarda zanyi auren, please kace yatashi" Saura kadan Alhajin yabuga tsalle don dadi. "At last, at long last" yaita nannatawa aranshi. Tofa? Burin Alhaji shamsu fah yacika, zaizamo sirukin Sir A.A 😅 Cikin kwana biyu ya warke sumul sai nan nan yakeda Saudart, itako kwata kwata tarasa abinda kemata dadi. She can't believe ta yarda da AUREN KWANGILA da wannan monster dinba. Jitake Dama mutuwa tayi tahuta. Ada batasan qiyayyaba, ko wuqa aka samata awuya akace tafadi maqiyinta daya bata iyawa. Amma yanzu qiyayar datakema Ashraf bata misaltuwa, shine sanadin rugujewar farincikinta, shine silan rushewar burinta na aure mutu-ka-raba, uwa uba shine silan sa6awa ubangijinta. She soo much hate him. With passion. MONDAY Su Alhaji shamsu yau ko barci ba'a komaba Bayan asuba, sai shirin ganawa da A.A ake. Yau za'ayi signing din contract din auren...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, Karka barmu da kanmu🤲 Wannan page din nakune Mamman mama, sis hajara, Maman Ameerah, maman areefullah and lastly sisto ta ummie amaryar baba sama'ilanta😜 Ina yinku irin wujiga wujiga dinnan, nagode da addu'oinku gareni🙏 Ga page nan nakune kuyi yadda kukaga Dama dashi🤷‍♀ Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 014 Kwankwasa kofarta da'akayi ne ya tsaidata Daga shafa man datake. Hijabi tazura tanufi kofar tabude. Fuskar daddynta yayi mata maraba washe da fara'a. Itama washe fuskarta tayi tana matsawa gefe don yashigo. "A'a? Inyee? Dad wannan hadewa haka kamar wanda zaya gana da president?" Dariya yayi sannan yace "Ai wanda zamu gana dashi dinma yakai President dinma koma yafi sbd shi gumin kanshi yakeci bawai na al'umma ba, besides yanaga baki shiryaba?" "Wlh Dad yanzu zan shirya, ai duka yanzu eight fa, inada sauran time" "Bamuda time shalele, we ought to be there by 9" "Wai Dad sai cewa 'mu' kake, dawa dawa?" "Ni da ke mana" "Tofa? Fita zamuyi Dama?" "Mtcheew, kin cika shirme shalele, nufinki bakisan yau zamuje signing din contract dinba?" Sororo tayi tana kallonshi "Contract?" "Mtcheew, Wai meke damunki ne, nufinki bakisan yau ake signing din AUREN KWANGILARKU BA" Gabanta ne yafadi, dagaske kenan aurennan will push through? "Kinyi shiru?" "Dad yanzu fisabillilah kai zakaje shi bazai zoba, Dad indirectly zuwa tallana fa kake" "Ya ilahi Saudart, don girman Allah kibar maido hannun agogo baya, Nike nema wajenshi so nizan je" yafada cikin Fushi. "To Allah ya tsare, nikam bani zuwa, kuma please daddy karkace zaka tilastani don Dama auren bawani kwanta min yayiba" tafada tana zama gefen gado ta cigaba da shafa kafanta mai. "Shalele ni kikema haka don kinga ina Neman Abu awajenki?" Kamar wanda yacema tafara. Aikau saita fashe da kuka, harda shesheka kamar wanda akayima tsinannan duka. Sakin baki Alhaji yayi yana kallonta. Ganin abin nata bana qarewa bane, saiya zauna kusada ita yajata jikinshi ya hau rarrashi. "Shikenan Shikenan, Basai kinje ba, kibar kukan haka, kiyi shiru please" Dakyar yasamu tayi shiru sannan yafice yatafi shi kadai. Tashi tayi Bayan fitarshi. "Ca6di! Wlh bana fatan wani Abu yasake hadani da wannan jerk din, tsinemin akayi?" A gurguje ta shirya itama tafice bakery dinta. *********************************************** "No way! Wannan Abu mu uku yashafa, don haka mu uku zamuyi sign kamar yadda kagani a paper" "Nasani Mr A.A Amma kamar yadda na fadama bata jindadi ne, da daita zanzo" "To sai abari saita warke sai Ayi, yanzu kai kayi sign din naka, idan ta warware saitazo tayi nata sannan zakaji alert" inji Ashraf da yake ganinma Alhaji shamsu yayi mugun raina mishi wayau. Shiru Alhaji shamsu yayi yana tunani "Look is not as if ina tilastama neba, idan wannan abin bazai yiwuba abarshi please" "No..no bahaka vane Mr A.A, kawo inyi signing, insha Allah zuwa gobe idan ta warware zatazo tayi nata" Yafada yana amsar paper, ya karanta sharuddan kamar dai yadda Dama yasani sannan yasa hannu wajen da yakamata yasa. "Gashi insha Allah gobe zataso" injishi yana miqama Sadeeq da tundazun ko A bece ba. "To Allah yakaimu" inji sadeeq while Ashraf yawani lumshe idanu kamar maijin barci. Bayan tafiyarshi sadeeq ya kalli Ashraf da idanunshi ke lumshe haryanzu. "Wai! Gaskiya yarinyar nan yar jin kai ce,komai saitaja aji?" "Get out!" "Toni menayi kuma?" Yafada cikin dariya. "Kasan Allah ubanka zanci, nace out!!" Harara ya galla mashi sannan yafita yana gunguni. ************************************* WASHEGARI A kasalance take shirinta nayau, haryanzu abinda yafaru tsakaninta da Dad jiya yaqi sakinta. Sosai jiya daddy ya burkuce mata jiya don tace baza taje tayi sign ba. A jiya tasan dayan 6aren daddynta, don be raga mataba tatass yamata abin ba dadinji. Bata ta6a tunanin akan dan Abu irin wannan dad zai mata tijara irin najiya ba. Don dole ta amince zataje don bazata iya da masifar Dad ba. Shirya wa tayi cikin wani sky blue Arabian gown ta nade kanta da gyallen rigar sannan ta rataye side bag dinta sky blue. Masha Allah tayi kyau musanmman data kwama baqin shade a idanu mai taken NO RESPECT. saukowa tayi ahankali, a dining ta ga dad zaune yana kari, kallo daya yayi mata ya dauke kai. Murmushi tayi taqaraso wajenshi tana cire glass din idonta. "Good morning dad" "Morning" ya amsa kamar mai ciwon baki. Jawo plate din gabanshi tayi tasaka fork itama tanaci. Ci kanki bece daitaba. Ganin haka yasa ta dago ta kalleshi a marairaice. "Dad!" Shiru "Dad don Allah kayi hqr, fushin ka agareni masifa ce" Nanma shiru. "Please Dad Kaga Daga nanma can na nufa, kayi hqr" Dukda yaji dadi Amma ko nunawa beyiba saima banza dayayi daita. Kuka tafara ahankali, saurin dagowa yayi tareda jawoya ajiki yana rarrashi don ga yadda tayi kyau dinnan beson tayi kuka kwalliyar ta6aci🤔 "It ok sweetheart, ya isa please, na haqura" Shima saida yasha fama sannan ta hqr. Har mota ya rakata yanata samata albarka. Shiga tayi ta dagamashi hannu sannan ta tada motar ta fice cikin tuqi mai burgewa. Naunnauyan ajiyar zuciya Alhaji yasaki yana girgiza kai, Saudart? Hmn halinta sai ita. Tuqi take tana saqe saqe, she can't believe Wai zuwa zatayi tayi signing din aurenta da wanda kwata kwata besan darajar mutane ba. Lallai, aikau yau she won't take shit, idan yayimata ramawa zatayi don ba tsoronshi ba takeji. Tsaki taja, yanzu me zeta cemishi idan taje? Nazo signing din contract din auren mu? Mezai dauketa? Mai binshi din dagaske? Gashi tagama ikirarin bekai standard din mallakarta dadai da second dayaba, nezai dauketa yanzu? "Kai wlh daddy kagama dani!" Tafada tana dukan steering Saudart Nada sanyin hali Saidai bata jurar wulaqanci, Duk yadda kuke daita ka nemi raina mata wayau yanzu kunyi sama Ku tiqo qasa. Tanada hqr haka kuma tanada zafi sosai, shiyasa ko a qawaye shakkar 6atamata rai ake. Danna hancin motarta tayi cikin harabar company din Bayan an wangale mata gate din. Yau company din bewani yimata kyau ba. Tafi minti biyar amotar takasa fitowa kawai fargabar shiga take, dayake ruwa ruwace har hawaye sunfara kwanciya a kwarin idanunta. "Dad ka gama dani, ka gama dani" haka taita nanatawa. Saida ta tattaro sauran jarumtarta sannan ta bude murfin kofar tafito ahankali....✍ Sorry nasan yayi kadan ba chaji🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 015 Maida murfin kofar tayi tarufe sannan ta kulle motar. Zaro baqin shade dinta tayi ta qwama a fuska wannan yakusan rufe Rabin fuskar sannan ta gyara zaman side bag dinta. Ahankali cikin wani taku tanufi main entrance din. Sanitizing din hannunta tayi sannan ta shiga ciki. Direct elevator tanufa don ta riqe number floor din. Cikin yan daqiqu abin yatsaya alamun anzo. Ahankali tasanyo kafa tafito elevator din gabanta na bugun uku uku. Allah yasani dauriya kawai take don zuciyarta fall take da fargaba. Kamar kwanaki, Helen nanan mazauninta anci gayu cikin Riga da 6ingil din skirt, ga tulin gashin doki data tilama kai anmata style din baby face dashi. Fuska a tamke ta qaraso wajen wanda qamshin turarenta ne ya fargar da Helen zuwanta. Gaban Helen ne yafadi datayi tozali da wata unique super duper cutie, dukda shigarta simple ce ba qaramin kyau tayiba, gashi bawani kwalliya tayiba Amma kyan datayi baya misaltuwa. "Is your boss around?" Inji Saudart cikin tsantseni. "Yy..yes" "Ok? Tell him yayi baquwa" Tafada tana zama kan daya Daga kujerun wajen ta Dora kafa daya bisa daya. Shiru kamar bazata tafiba, saikuma tatuna da haduwarsu na ranan, dan haka ta tashi tanufi office din. "Yes? Come in" inji sadeeq dake tareda Ashraf yana nunamishi wani project dazakuyi presenting a wani meeting. Helen ce tashigo jiki a sanyaye. Gaishesu tafarayi sannan tace "sir kayi baquwa?" "Who?" "I don't know her name Amma seems Sir sadeeq yasanta" Kallon juna sadeeq da Ashraf sukayi "Ni?" "Yes sir, wannan lady din ta ranan?" Waro idanu yayi "OMG!she's here, Alhaji shamsu's daughter, she made it at last" inji sadeeq cikin murna. Kunya da takaici Yakama Ashraf, ji yadda yake Neman zubda mashi aji gaban wannan arniyar? "Je kice tashigo" inji sadeeq da bemasan Ashraf nayi ba. Juyawa tayi a ladabce 'Alhaji shamsu's daughter? Dama diyarshi ce?' Abinda yaita yawo azuciyarta kenan. Yadda ta barta haka ta taddata sai wani kada kafaffu take ahankali. "Kina iya shiga" inji Helen tana mata wani kallo marar fassara. Ko a jikinta, ta tashi cikin nutsuwa ta gyara zaman kayanta sannan tanufi office din. Ahankali ta bubbuga sau uku, sadeeq ne zaije ya bude mata Ashraf ya riqo hannunshi. "Dan ubanka idan wannan rawar kan zakayiman zan koraka, idiot" Sake bubbugowa akayi, ganin Ashraf Beda niyyar amsawa yasa sadeeq kware baki yana cewa "Come in" Ajiyar zuciya tasaki sannan ta runtse idanunta ta murda kofar ahankali, tashige. "Ya subhanalillah!" Inji sadeeq cikin zuciya dayayi tozali da Saudart. "Wow! Ta hadu ta hadu ta hadu!!!" Duk a zuciya yake zancenshi azahiri kuwa murmushi yake mata. Shikau gogan kamar yadda kuka zata kanshi nakan system din gabanshi. Sallama tayi ciki ciki, amsawa sadeeq yayi cikin fara'a yana mata iso. Ashraf kamar ya shaqeshi don takaicin yadda yake wani rawar kafa. A yangace tanufo kujerar da sadeeq yaja mata idanunta akan Ashraf Amma kasancewar baqin glass na idanunta ba'a ganewa. Zama tayi ahankali sannan ta Dora kafa daya bisa daya. "Ok boss, zan tafi in ida arrangement din" inji sadeeq yana tattara files din. 'What?' Yafada azuciyarshi, Amma mugun dan air ne sadeeq, nufinshi barinsu zaiyi su kadai. Be ankaraba yaji qarar rufewar kofa alamun harya fita. Wani irin shiru office din yadauka, itama kanta Saudart bataso tafiyar sadeeq ba don da niyyarta ta tambayi ina file din wajenshi tayi sign tafice don vataso ko kalma daya ya hadata da Ashraf. Kusan mintuna biyar Amma shiru babu wanda ya motsa cikinsu, shi yana danne danne a system, ita tana shafe shafe a waya. Minti biyar...Goma...Sha biyar Amma still ba wanda ya motsa. Kowanne jira yake dan uwanshi yafara motsi. Saudart takaici kamar tayi kuka, saitayi kamar tayimashi magana saikuma tafasa. Shima hakan take a wajenshi, jiyake kamar yayi me? (Ni Duk nafisu jin takaici, Wai wannan wane irin wulaqanci ne zasu barni sagale da Biro a hannu😠) Ganin wankin hula na naiman kaita dare yasata motsawa, ahankali cikin yanga mai tattare da jin haushi tace "Bani paper din inyi sign, Inada abinyi" Murmushi Ashraf yayi cikin zuciyarshi, at last ta karaya. Dago sharp cat eyes dinshi yayi ya doramata su a karo na farko tunda tashigo. Ko seconds biyu beyiba yakuma dauke kai yacigaba da danne dannenshi. Kutt! Lallai ma Tashi tayi da niyyar ficewa don bazata iya jure wulaqancin shiba. "Kina fita deal cancelled" yafada still hankalinshi kan computer Dakatawa tayi zuciyarta na suya, gaskiya Dad yagama daita, wannan wulaqancin har ina. Juyowa tayi tana kallonshi Jitake kamar ta rufeshi da duka. "Look mallam inada abubuwan yi, let me sign the damn paper and leave" Dagowa yayi Daga system din tareda komawa yayi balancing sosai a kujerar kamar irin dan sarkinnan. Zubamata cat eyes dinshi yayi ya qureta da kallo. Dukda glass din idanunta sun kareta Amma hakan be hanata jin tsinin idanunshi ba akanta. "The paper?!" Tafada tsakankanin haqora cikin jin haushi don ko motsawa beyi yawani zubamata na mujiya. "Paper? Which paper?" Ya tambaya cikin isa. "Wanda kayi blackmailing din Dad na dashi mana, kabani inyi signing inyi tafiyata" "Ba haka dad dinki yayi sadda yazo jiyaba, he begged for it, so kema ki roqa idan kinaso idan kuma bakiso?.." Saiya Daga kafadu sama alamun fine🤷‍♂ Shiru tayi tana kallonshi unbelievable, ta roqa? Yadda daddynta ya roqa? Kenan daddy strooping low yayi ya roqeshi? Innalillahi Dad yagama da ita. Hawaye taji yana naiman saukomata, ga wani nauyi da zuciyarta tayi. Qoqarin maida hawayen take don bataso yaga saukarsu yayinda tsanarshi sai qara farashi yake azuciyarshi. "Miss shamsu, kina 6atamin time, beg me to marry you" yafada yana jindadin moment din don yasan ba qaramin wulaqanci yake shufka mataba. Yasan babu yadda za'ayi tayi rejecting dinshi ko don daddynta, don Duk yadda akayi harta yarda yanada masaniya akai kuma yasan yanzuma forcing dinta Alhaji shamsu yayi hartazo. Lumshe idanu Saudart tayi tana qoqarin saita muryarta "Look, you don't have the idea of how I hate you, stop pushing it, give the paper let me sign and leave, am suffocating here" tafada muryarta nadan cracking. Tashi tsaye yayi ya tako ya zagayo gabanta cikin takun qasaita. "Really? Kin tsaneni Amma kikazo Neman aurena? Wannan wacce iriyar tsana ce" Hadiye wani Abu daya toshemata maqoshi tayi kafin tace "Ba aurenka nazo nemaba, albarka mahaifi nazo nema don nasan darajarshi da matsayinshi if not ko sanin da wanzuwarka bazan yiba bare ko kallo ka isheni" tafada idanunta na qara durar ruwa. "Then ki nemi albarkar dakyau, kiyi biyyaya gareni kamar yadda uban naki yayi, beg!" Ya ida zancen cikin rad'a Kasa riqe hawayen tayi, saurin kauda kai gefe tayi don karyagansu. Jitake kamar tamutu don takaici. Murmushin gefen baki yayi na mugunta ganin tana hawaye, Dama ya dauki alwashin saita raina kanta haduwarsu nagaba. "Kinada minti daya kacal kiyi abinda yakawo ki ki fitarmin office don numfashinama sarqewa yake saboda odour" Lumshe idanu tayi tana qara bama hawayenta damar gangara. Shiru tayi atsaye still idanunta lumshe. "10 seconds to go" yafada yana kallon agogo Bayan yakoma yayi balancing a kujera yana kallon yadda take hawaye. Jan hanci tayi sannan ta goge fuskarta da hanki. "Mr A.A kabani paper inyi signing.... Please" tafada tana sake lumshe idanunta tacikin glass. Wani dadi Ashraf yaji jin tace please. Amma saiya wani dago yana kallonta. "Ban jiba come again" Kuka takeso tayi Amma ta dake. "Nace kabani paper inyi signing please" "Beg with Hausa" yafada yana enjoying din moment din. "Dan Allah..." Murmushi yasaki na gefen baki sannan ya taso yasake zagayowa wajenta. "In taimaka miki in baki?" Wasu sabbin hawaye suka sake gangaro mata. "Ehh" ta amsa murya na rawa "Ehh what?" Yafada yana kafeta da idanu fuskarshi fall murmushin mugunta "Ehh...Sir" Furzar da iska yayi yana lumshe idanu cikin jindadi sannan ya budesu akanta. Kanta na sadde Kasa hawaye na diga zuciyarta na wani irin zafi. "Yanzu kinsan koni wanene?" Ya tambaya "Yes" "Yes what?" "Yes sir" tafada tana girgiza kai ahankali don takaici. "Yakamata kisan gabama da gabanta, nafi qarfin cakuri cici irinki, kamar yadda nafada abaya wutsiyar raqumi tayi nesa da kasa , so maintain ok?" Nan ya dauko wata paper acikin wani file ya ajiye mata gaban desk dinta. "Gashi na taimaka nabaki ba don halinki ba ko dan kinkai, sign and get lost" Cize lips dinta nakasa tayi sannan ta dauki pen din hannunta nadan rawa, batareda ta karanta shirmen da'aka rubutaba tanemi inda zatasa hannu ta Dora hannu sama. Shiru kamar bazatayiba saita daure tayi signing zuciyarta na wani irin karta. Ajiye pen din tayi tana sauke ajiyar zuciya. Shima dauka yayi yayi sign inda yakamata sannan yace "DEAL!" Yana buga stamp akai. Bata ankaraba taji ya fizgo hannunta na dama, saurin dagowa tayi tana kicin kicin kwace hannunta Amma takasa. Wani box yafiddo a aljihunshi da hannu daya dayan na riqeda hannunta. Budewa yayi sannan yafiddo wani hadadden zobe mai kyau yazuramata a yatsa ta karshe. Kukane ya kufce mata zuciyarta kamar ana haura wuta. "Welcome, welcome to the famous's world, ba suna kikeso ba zakiyi suna" Yafada haryanzu yaqi sakin hannun. Zaremata glass din idanunta yayi yana kallonta. "Idan kika zare wannan ring din... Deal cancelled! Kuma kinsan har tsinemiki kwadayayyen babanki na iyayi" Yayi wurgi da hannun a kyamace. "Get lost, gobe by four zan aiko driver ya dauko ki ki kasance cikin shiri. GET LOST!" Yafada yana komawa bisa kujerar shi. Ahankali ta dago idanunta ta zubamashi, gabanshi ne yafadi ganin kallon tsantsan tsana datake mashi. "Mekuma kike jira, ki 6acemin nace" Glass dinta ta dauka Daga kan desk din still tana kallonshi sannan ahankali ta bude baki cikin wata iriyar murya tace "I HATE YOU....WITH PASSION" sannan tajuya tafice cikin sassarfa. Bin kofar yake da kallo kamar still tananan, zuciyarshi namashi saqe saqe. Unlike ranan yau ahankali tafito, ta maida glass dinta don haka babu Wanda yasan yanayin fuskarta. Wuce Helen tayi ko kallonta batayi ba, itakau Helen tabita da kallon tuhuma. Mota tashiga ta tada sannan ta figeta da wani irin gudu ta halba titi...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19) Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 016 Tuqi take Amma ita kanta tasan kariyar Allah ce kawai ke tareda ita, Jitake kamar tacire zuciyarta ta jefar saboda radadi 'He blackmailed me' 'He made me beg' 'He forced me' Wasu hawaye suka qara gangarowa fuskarta ta sharesu afusace. Qara gudun motar tayi, batayi koina ba sai gidan maminta (inda take aure) Budemata gate akayi ta Danna hancin motarta ciki. A parking space tayi parking Saidai takasa fitowa, Duk Jitake jikinta kamar ba nataba , ga wani Sara da kanta keyi. Tafi minti biyar ahakan sannan tasamu tafito dakyar hannu daya dafe da kai. Kwankwasa kofar tayi sannan ta murda tashiga da sallama. Babu kowa a falon kasancewar Duk qannenta ('ya'yan mamy) suna Maiduguri wajen kakansu Hutu. Su biyar mamy ta Haifa a wannan gidan. Aminulah dan shekara 16, sai kamalideen dan shekara 14, sai Ibrahim 11, habeeb 09 sai auta Abdul baseet 05. Saudart nason qannenta sosai suma haka suna sonta sosai, Duk weekend idan tazo fira suke sha kamar me? Akwai shaquwa sosai tsakaninsu. Zubewa tayi kan three seater din falon tana dafe kai. Tafi mintuna biyar ahakan kafin mamynta tafito Daga kitchen da alama girki take. Da farko bata lura daita ba saida tashigo falon sosai, tsoro taso bata data ga mutum kwance a falo. Saida ta qaraso sannan tagane Saudart ce "Saudart?" Bude jajjayen idanunta dasukayi mata nauyi tayi ta kalleta saita tashi zaune a kasalance. Qarasowa mamy tayi ta zauna itama daf da ita. "Saudart lafiya?" "Mamy ina wuni?" "Lfy lau, meya sameki ne? Ji idanunki, ga muryar ki ma" "Mamy bana jindadi ne" tafada tana kallon qasa. "Kamar ya? Kallo daya za'a yimiki asan kinyi kuka, fadamin menene" Girgiza kai tayi alamun babu komai. "Wajen aikinkine?" Nanma girgiza kai tayi "Ko babanki ne?" Murmushin takaici tayi sannan tace "Mum please, nace babu komai, bana jindadi ne, kaina ke ciwo" tafada tana dafe kai. "To Allah ya sauwaqe taso kishiga daki kisha magani ki kwanta. Na musu ta tashi tabita wani daki, acan mamy ta bata magani sannan ta umarceta da ta kwanta tasamu barci. Kasa barcin tayi koda mammyn tafita. Qurawa ceiling kawai tayi tana tunane tunane. Motsi kadan saita girgiza kai tana murmushin takaici. Ahaka barci ya dauketa. Bata farkaba sai four shima mamy ta tadata tayi Sallah, da to kawai ta amsa dukda ba sallar takeba. Watsa ruwa tayi a bandakin dakin sannan tafito. Saida ta cika cikinta bam sannan ta bar gidan Bayan mamy tata bara shawarwari Masu amfani. Gida tanufa kai tsaye, yanzu tarage jin zugin zuciyarta. Horn daya tayi aka Budemata. Da sallama tashiga falo ta hango dad zaune yana amsa waya "Ok hang on zan kiraka" yafada yana tsinke wayar sannan ya miqe yanufota yana dariya. Rungumeta yayi cikin jindadi yana ta suburbuda mata albarka don burinshi yacika, harma yaji alert. Itadai Saudart iyakarta murmushi Wanda bana komai bane saina takaici. Sai nan nan yake da ita, lokacin barci ma dakanshi yakaita daki yayi mata addu'a sannan yakashe mata wuta yajawo mata kofa. Murmushin takaici tasakeyi tana girgiza kai. Ta dade kafin barci Yaa dauketa, don data runtse ido abinda yafaru dazu take gani. Dakyar tasamu barci ya dauketa can biyun dare. Asuba tagari😴 Washegari bata wani damun kanta wajen shirin bakery ba, don bazata jeba, wanka kawai tayi ta kintsa kanta sannan tahau yin aiki a laptop. Haryanzu fuskarta a cunkushe yake don haryanzu bata warwareba Daga abinda yafaru jiya. Zobe kuwa bata cire shiba, yana a yatsarta ko meyasa oho? Daddy ma yau be fitaba Wai zai tayata zaman gida tunda batajin dadi. Saidai waya dayake tayi da mutane akan business, kallo daya zaka mashi kasan yana cikin farinciki. Hakan yasa itama Saudart taji Dama Dama don farincikin daddynta natane. 3:40 Suna zaune a falo, Saudart na kallo Alhaji na aiki a laptop sukaji qarar door bell. Tashi tayi tana cewa "bari naduba" Koda tabude maigadi tagani tsaye, fuska a washe suka gaisa tana tambayarshi lfy? "Hajiya wani ne yazo daukanki" "Wani?" "Eh hajiya" "Tofah wanene?" Alhaji shamsu shima yataso "Shalele menene?" "Dad Wai wani yazo daukata Wai" "Dauka? Waye?" "Wlh Alhaji nima bansanshiba" "Cemashi ya qaraso" Sunanan tsaye saiga wani saurayi ya qaraso cikin shigar suit. A ladabce ya gaida Alhaji, ya amsa itadai Saudart nata ido. "Tofah, kaikuma Daga ina?" "Sir, sir A.A yace nazo na dauko madam" Kallon juna Saudart da Alhaji sukayi. Sai asannan Saudart ta tuna dayace mata zai aiko driver qarfe hudu, ca6 aikau za'a yita. "Shalele, dagaske ne?" "Tayaya za'ayi insani daddy? Nima bansaniba, kai kaje ka sake tambaya qila 6atan hanya kayi" Tafada tana komawa ciki. Alhaji ya maido kallonshi kan saurayin "ka tabbata nan aka aikoka?" "Eh Sir, nanne" "Ok kajira ina zuwa" Hmm yau ake yinta, don firr Saudart taqi yarda da buqatar daddy "Dad ya kakeso danine? Ni matarshi ce dazai wani aiko azo a dauko ni? Gidan ubanwa ma zai kaini? Dad kaima kasan this is not proper" "Saudart..." "Daddy nayima biyyaya, bada son rainaba na amince da AUREN KWANGILA, ka tilastani nayima biyyaya, Dan Allah karka tilastamin wannan saboda ina gudun in bijirema" "Saudart, wannan fa abin ba komai bane kawai..." "Agarekane ba komai ba dad, agarekane ba komai ba, daddy ka daina sona, Baka sona, kafi son kudi akaina? Kafison dukiya akaina? Kafison farantama wani akaina?" Saikuma tafashe da kuka. Sosai jikin daddy yayi Sanyi, rungumota yayi yafara rarrashinta cikin baiwarshi ta dadin baki. Yasha wahala kafin yashawo Kanta ta yarda zataje. Fita yayi yabata wuri don tashirya. Yana fita ta Dora babin kukanta saida tayi mai isanta sannan tashige bayi tayi wanka. Da gangan taita Jan jiki sai wajajen 4:30pm tagama shirin. Izuwa yanzu Daga Alhajin har drivern sungaji dajira. Ahankali ta sauko, yauma kamar jiya idanunta dode cikin NO RESPECT Sakin baki daddy yayi ganin irin masifataccen kyan datayi. Sanye take ciki Jan less mai touches din baqi, anmata style din Riga fitted da skirt mai wrapper, gashi ta cogale kallabin Kayan tayi daurin ture Kaga tsiya, sai baqin gyale a kafada yayinda ta lullu6a fuskarta da baqin shade. Tayi kyau harta gaji dukda bawani kwalliya tayiba. Fuskar nan a tamke, kana ganinta kasan bazata bar kota yiniba bare ta kwana. Yau saita gwadama A.A ko mema ake kiranshi wacece Saudart, yanzu bayada dammar blackmailing dinta tunda yariga ya turama dad kudaden. "Wow! Sweetheart you look soo takeaway!" Dan ta6e baki tayi sannan tace thanks ahankali. "To kuyi maza kutafi please Saudart behave" Bata amsaba tafice taje tasamu driver Wanda harya gaji da ji ranta. Gaangaan!! Yau akeyinta, sainaga ruwan comments zanyi typing, idan basu gamsheniba kuma zakuji shiru. Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Wannan page din nakine ummin bilal da Duk members din AUREN KWANGILA NOVEL GROUP Amma fa banda yan le6el😏 Ngd da addu'o'inku agareni🙏 Allah yabar zumunci🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 017 Cikin wani irin taku ta qarasa motar kafin tayi yunqurin budewa har driver din ya Budemata kofar baya aladabce harda dan russunawa. Ta6e baki tayi sannan tashiga, rufewa yayi ya zagayo gaba yashiga. Dad keta faman Daga mata hannu, yitayi kamar bata ganiba ahaka suka fice. Ta6e baki Alhaji shamsu yayi, "kedai kika sani mutum arziqi na kiranshi yana guduwa" Yaja tsaki yakoma ciki. Shiru motar tayi, babu mai magana, tunda Saudart take bata ta6a shiga irin wannan motarba, watakau tahadu harta gaji, gashi kamar ba tafiya takeba don ko alamun tafiya bakaji. Ga Sanyi mai hade da qamshi mai dadi Wanda ke saurin sa barci yakamaka idan Baka sababa. Itama Saudart saida tayi dagaske don karta 6ingire, watakan idan kana cikin motar bakama sanin ana wani Abu waishi rana Awaje. Haka taita kallon waje ta window hankali kwance, ganin ba hanyar A.A ENTERPRISES yabiba yasata muskutawa tace "Mallam Wai ina zaka kaini ne haka?" Cikin ladabi yace "Kiyi haquri madam mun kusa zuwa" Afusace tace "bashi na tambayekaba, where are you taking me to nace" "Kiyi hqr madam mun kusa" yafada yana shan wata corner. Masifa tashiga zazzaga mashi akan ya maidata inda ya daukota koya ajiyeta bata zuwa. Shidai ko uffan beceba harta gaji tayi shiru. A Gaban wani tangamemen gate ya tsaya yana horn. Saida akayi scanning dinsu sannan gate din ya budu suka shiga. Tun cikin motar tasaki baki tana kallon wajen. Tunda take bata ta6a ganin qayattacen waje irin wannan ba, Waima ahakan tana cikine bata fitoba. "Madam munzo, please come out" inji drivern da har yazagayo yabude mata. Wani kallo ta watsa mashi Wanda bemasan tanayi ba saboda glass din daya kare idanunta. "Are you serious? Nan inane ka kawoni?" Kafin yasamu zarafin amsamata tajiyo muryar wani nacewa "A'a? Harkun iso?" Daga kai tayi ta kalleshi taga Ashe Wanda take ganine a office din A.A (sadeeq) Cikin fara'a yadan qara Budemata murfin kofar yana cewa "Bismillah gimbiya" Cikin tsuke fuska tace "Wai inane nan? Kuma me nakeyi anan?" "Yi hqr madam, wani dan shagalin nasarar da companynmu da kingin rassashi yasamu muka hada shine kema aka gayyaceki" yafada cikin fara'a. Kamar tasake mgn saikuma tayi shiru. "Please kiyi hqr kifito" Kamar bazata fitoba sai can ta ziro kafarta a yangace tafito. 'Ya sallam!' Tayi exclaiming ganin zallar haduwa da wajen yayi. Ga furranni ata koina. Allah ya taimaketa akwai glass a idanunta da an lura da kauyancinta. "Ma'am mu qarasa yana cikin waccan motar" inji sadeeq yana nuna wata dalleliyar mota fara qall Bin inda ya nunamata tayi da kallo sannan ta kauda kai. "Please ma'am Ku kadai ake jira a hall din" Cikin tsantseni tace "shi bazai iya fitowa bane, am going nowhere" ta maida Kallonta kan wayar hannunta tana shafawa. 'Lallai ahe wannan tafishi ma girman kai' yafada cikin zuciyarshi. "Ok bari na kirashi" saiya juya yanufi inda motar take. Ashraf Dama tundazu su yake kallo, ganin sadeeq yataho shi kadai yasa ranshi qara 6aci. Dama gashi famm yake saboda latti dasukayi gashi yanzu tana botsarewa, lallai saiya koyamata hankali. Kwankwasa glass din motar yasashi sakin siririn tsaki yana kauda kai. Budewa Sadeeq yayi yana cewa "to saika fito gimbiya dai taqi Qarasowa" Banza yayi dashi ko kallo be isheshi ba. "Ashraf?" Wani kallo ya watsa mashi yasake dauke kai. "Please Wai bakusan kun tara mutane bane? Haba jira babu dadi" Nan ma shiru. "Wohoho Ashraf for goodness sake dakai fa Nike" Harara ya watsa mishi yana cewa "cancel the gathering" "Me?! Are you serious?!" Yafada cikin Waro idanu Harara yasake watsa mishi "you heard me ai" "Haba Ashraf? Ka gama tara mutane kayi wasting din time dinsu sai kuma ka soke taruwar, wannan wane irin wulaqanci ne" "Look sadeeq karfa ka manta matsayinka, the fact that kai abokinane bazai Baka damar mayar dani shashasha ba, am still your boss!" Yafada tsakankannin haqora cikin Fushi. "Kayi hqr Ashraf Amma..." "Just shut up! Tagama 6atamin lokaci sannan tace bazata qarasoba? Ita wacece? Na ta6a jiran mace? Kai shaidane ban ta6aba sai akanta saikuma tanemi rainamin hankali? Cancel the damn party kazo mutafi!" Kallonshi kawai sadeeq keyi ganin dagaske fah yake nufin Ayi cancelling din partyn Bayan Duk manyan mutane aka tara, lallai aikau bazata sa6uba. Kwantar dakai yayi yaita roqonshi harya yarda dakyar yafito. Izuwa yanzu har biyar darabi tayi. Saudart nacikin motar don bazata juri Tsayuwa ba, itama a 6angarenta aqule take, lallai wannan gayen dan wulaqanci ne, Dama sawa yayi akawota don ya shanyata. Ta cikin motar ta hango fitowarshi, ta6e baki tayi tana kauda kai. Sanye yake cikin farar suit qall, sai jar shirt dake ciki da Jan necktie irin dan qaraminnan, sai hanki ja daya dan leqo ta aljihun gaba. Wow, gaskiya A.A haddadene👌 ba qaramin kyau shigar sukayi mashi ba. Tare suka taho da Sadeeq dake Bayan Ashraf. Suna isowa wajen dazasu bi su shiga ciki yaja ya tsaya hannaye zube cikin aljihu, fuska tamke ga shima uban baqin shade daya kwama. Ganin haka yasa sadeeq qarasawa motar Saudart don tahowa da ita. Saida tasake Jan aji sannan tafito itama sannan suka tako wajen Ashraf. Shikau Sadeeq sai ayyana yadda dan zamansu zai kaya don ya lura dukansu yan jin Kaine. Koda sukazo wajenshi ko gefenshi bata kallaba kamar yadda shima yayi kamar besan da itaba. "Ina zuwa" inji Sadeeq yayi gaba don zuwa sanarda isowarsu. Haka suka tsaya ko nuna alamun sunsan da zaman juna basuyiba. Daga nesa idan ka hangesu saisun burgeka don dukkansu sun hadu ba karya ga kayansu daya kusan marching. Ita jaa da baqi shi fari da jaa. Yadda yabarsu haka ya tardasu. "Please Ku qaraso" Nanma rasa wanda zai fara takawa akayi "Please Ku ake jira kuyi hqr" inji Sadeeq daya gaji da dramar su. Nan Saudart taci girma tafara takawa sannan fa dan jinkan shima yatako. "Please kubar tafiya aware kufa fiancée ne" Babu Wanda ya tankamashi suka cigaba da tafiya. Haka suka qarasa entrance din, DJ na hangosu ya saki wani kida mai dadi. Take kallo yakoma kansu, kowa na yaba haduwarsu. Tafi aka dauka hall din anatayi har suka qarasa wajen zamansu. 'Ashe surprise Sir A.A zaiyi Masu? Ashe da masoyiyarshi zaizo wannan party din' haka kowa yaita saqawa yayinda mafi yawan matan dake hall din Kishi ya cika musu zuciya. Mutane sukayi tazura mazauninsu Bayan sun zauna suna tayasu Murnar nasarar d company dinsu yayi da kuma taya Murnar samun mata. Sai a sannan Ashraf yayi danasanin daukota don shifa yayi hakanne don ya gwadamata koshi wanene dakuma yadda yakeda iko. Hasken flashes din hotuna kawai ke haskemasu fuska. Ashraf kamar koda yaushe fuskarshi a tamke itakau Saudart babu yabo babu fallasa idan kuma akayi congratulating dinta sai tadan saki murmushi. Ji take kamar ta tashi ta ruga don sosai tajita ta takura. Dakyar akasamu mutane suka koma suka zazzauna. Nan m.c yahau jawabin abinda ya tarasu cikin harshen turanci. Itadai Saudart kawai tana wajen ne Amma hankalinta Duk yayi gida, Jitake wama yasa ta yarda Tun farko da zywan? Duk inda ka wurga idanu yan media ne Masu dauka wannan mostly sunfi daukar su Ashraf. Ashraf kau abinne yaso juyemashi don ba haka yasoba. So yayi yakawota don ta raina kanta kuma beta6a tunanin yan jarida zasu hallarci wajen ba. Kawai yakawotane don taga matsayinshi dakuma ikonshi. Bayan jawaben nan aka shiga ci dasha, kowa da zaune a tebyr dinshi yana dan ta6a wani Abu. Hakan take awajensu Ashraf. Dukda babu mai cin komai cikinsu, kowa da abinda yasha mishi kai. Sadeeq ne yaqaraso wajen dawasu yan jarida biyu. "Sir, gawasu yan media zasuyima kai da sarauniyarka tambayoyi" inji Sadeeq aladabce Saidai deep down dariya yake mishi. Takaici ya hana Ashraf cewa komai don sai yanzu yasan Sadeeq ne ya gayyato mashi yan jaridar nan. "Sir wane irin farinciki kake ciki ayau?" Inji wani yana saita mic dinshi gabanshi Shiru yayi kamar bazeyi mgnba saiya daure cikin muryarshi mai dadin amo yace "Ina cikin farinciki sosai" "Sir wannan ne karo na farko da akafara ganinka da mace, ko zaka iya gayamana matsayinta agareka?" Inji wani nakusada nafarkon. Nanma shiru, "Lallai Sadeeq you are in hot soup" yafada cikin zuciyarshi Can cikin murya qasa qasa yace "She's my fiancée" "Wow congratulations... Ma'am zaki iya fadamana farincikin dakike ciki?" Suka maida akalar tambayar wajen Saudart. Jimm tadanyi sannan itama ayangace tace "Ina cikin farinciki sosai" "Ma'am wani matsayine sir A.A ke dashi awajenki" Murmushi tadan saki "Kamar yadda yafada am he's fiancée" "Wow.. Zaki iya fadamana farkon haduwarku?" Woo! Nabani, tafada cikin zuciyarta "Eh" "Ok muna jinki ma'am" "Mun fara haduwane a bakery dina" tafada kai tsaye "Wane bakery kenan?" Inji dayan. "Alhairi bakery" "Omg, badai kece mai alhairi bread ba?" Inji dayan cikin mammaki. "Yes nice" ta amsa cikin basarwa. Ashraf na gefe takaici kamar yayi hauka. "Me sir A.A yajeyi a bakeryn?" Murmushin gefen baki tayi irin Wanda shima yakeyi. "Me zaije yi kau? Yaje Isar da saqon zuciyarshi ne" "Wow! Me hakan ke nufi?" Inji dayan sai setasu da camera ake. Dukda tagaji da tambayoyin Amma burinta na quntatawa Ashraf yasa tace "Ina nufin yazone donyayi fighting for his love" "Wow amazing! Sir Ashraf hakane?" Inji dayan yana saita Ashraf da mic. Jiyayi kamar ya nutse don kunya don Dama tunda suka fara hankalin kowa yadawo Kansu. Babu damar musawa yayi murmushi yana kada kai. "Sir idan hakane akwai inda kafara ganinta kenan harka fola Mata, inane kafara ganinta?" Ca6, da ace ana ganin zuciya da kunga yadda zuciyar Ashraf ke tafarfasa. "A cinema" yafada ahankali, dukda cikin Fushi yake hakan be nunaba a fuskarshi. Lallai wlh saita gane kurenta, shi take zubarma girma agaban jama'a? Wai har binta bakery ko ubanmi ma yayi? "Wow gaskiya labarin haduwarku yayi dadi, ma'am da Sir A.A yazo wajenki da qoqon bararshi ya kikaji?" Kutt.. Qoqon me? Inji Ashraf cikin zuciya. Cikin basarwa Saudart tace "well as expected nayi mammakin hakan, ganin yanayin halinmu ba dayaba. At first naqi yarda da soyayyarshi gaskiya ce Amma ganin yadda yaketa zarya bakery dina Dama gidanmu yasani giving abun a second thought, ahankali ahankali nafara kulashi har yayi nasarar yaqar zuciyata da soyayyarshi" tafada murmushin mugunta fall fuskarta Wohoho nan hall din ya rude da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinshi, Shidai Ashraf komawa yayi yayi balancing akan kujerar tareda lumshe idanu, zuciyarshi kamar ana hura wuta. dakyar hall din yayi shiru sannan daya Daga cikin yan jardan yace "yanzu zaki iya fadamana wane matsayin yake dashi azuciyarki?" Murmushi tadan saki a kunyace sannan tace "Yanada babban matsayi azuciyata sbd mutum neshi mai iya tarairaya, iya tarairayarshi da kulawarshi yasani fara sonshi, gaskiya am lucky to have such a caring guy" Caraf dan jaridan yayi yace "shima he is lucky wajen samun kyakyawar sarauniya irinki, kou Mr A.A?" Bude idanunshi yayi tacikin glass wadda ba'a ma hango idanun. A hankali yace "Yeah...am indeed.. Lucky" Tafi aka dauka gabadaya hall din, sai haskesu da flashes ake, wasu dan iyayi har zuwa wajensu suke sudau selfie. Wasu yan rawar kan kau sai liqema Saudart suke ala dole zasu qulla abota da masoyiyar the famous billionaire A.A Itakau Saudart ko ajikinta, ko babu komai ta rama koda kadanne cikin wulaqancin da Ashraf yayi Mata don haka jinta take wasai. Oga kau a zahiri kawai yake garas Amma karka tona zuciyarshi, jiyake kamar ya tashi yabar hall din, Allah Allah yake agama damn gathering din...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Wannan page din nakine ummin bilal da Duk members din AUREN KWANGILA NOVEL GROUP Amma fa banda yan le6el😏 Ngd da addu'o'inku agareni🙏 Allah yabar zumunci🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 017 Cikin wani irin taku ta qarasa motar kafin tayi yunqurin budewa har driver din ya Budemata kofar baya aladabce harda dan russunawa. Ta6e baki tayi sannan tashiga, rufewa yayi ya zagayo gaba yashiga. Dad keta faman Daga mata hannu, yitayi kamar bata ganiba ahaka suka fice. Ta6e baki Alhaji shamsu yayi, "kedai kika sani mutum arziqi na kiranshi yana guduwa" Yaja tsaki yakoma ciki. Shiru motar tayi, babu mai magana, tunda Saudart take bata ta6a shiga irin wannan motarba, watakau tahadu harta gaji, gashi kamar ba tafiya takeba don ko alamun tafiya bakaji. Ga Sanyi mai hade da qamshi mai dadi Wanda ke saurin sa barci yakamaka idan Baka sababa. Itama Saudart saida tayi dagaske don karta 6ingire, watakan idan kana cikin motar bakama sanin ana wani Abu waishi rana Awaje. Haka taita kallon waje ta window hankali kwance, ganin ba hanyar A.A ENTERPRISES yabiba yasata muskutawa tace "Mallam Wai ina zaka kaini ne haka?" Cikin ladabi yace "Kiyi haquri madam mun kusa zuwa" Afusace tace "bashi na tambayekaba, where are you taking me to nace" "Kiyi hqr madam mun kusa" yafada yana shan wata corner. Masifa tashiga zazzaga mashi akan ya maidata inda ya daukota koya ajiyeta bata zuwa. Shidai ko uffan beceba harta gaji tayi shiru. A Gaban wani tangamemen gate ya tsaya yana horn. Saida akayi scanning dinsu sannan gate din ya budu suka shiga. Tun cikin motar tasaki baki tana kallon wajen. Tunda take bata ta6a ganin qayattacen waje irin wannan ba, Waima ahakan tana cikine bata fitoba. "Madam munzo, please come out" inji drivern da har yazagayo yabude mata. Wani kallo ta watsa mashi Wanda bemasan tanayi ba saboda glass din daya kare idanunta. "Are you serious? Nan inane ka kawoni?" Kafin yasamu zarafin amsamata tajiyo muryar wani nacewa "A'a? Harkun iso?" Daga kai tayi ta kalleshi taga Ashe Wanda take ganine a office din A.A (sadeeq) Cikin fara'a yadan qara Budemata murfin kofar yana cewa "Bismillah gimbiya" Cikin tsuke fuska tace "Wai inane nan? Kuma me nakeyi anan?" "Yi hqr madam, wani dan shagalin nasarar da companynmu da kingin rassashi yasamu muka hada shine kema aka gayyaceki" yafada cikin fara'a. Kamar tasake mgn saikuma tayi shiru. "Please kiyi hqr kifito" Kamar bazata fitoba sai can ta ziro kafarta a yangace tafito. 'Ya sallam!' Tayi exclaiming ganin zallar haduwa da wajen yayi. Ga furranni ata koina. Allah ya taimaketa akwai glass a idanunta da an lura da kauyancinta. "Ma'am mu qarasa yana cikin waccan motar" inji sadeeq yana nuna wata dalleliyar mota fara qall Bin inda ya nunamata tayi da kallo sannan ta kauda kai. "Please ma'am Ku kadai ake jira a hall din" Cikin tsantseni tace "shi bazai iya fitowa bane, am going nowhere" ta maida Kallonta kan wayar hannunta tana shafawa. 'Lallai ahe wannan tafishi ma girman kai' yafada cikin zuciyarshi. "Ok bari na kirashi" saiya juya yanufi inda motar take. Ashraf Dama tundazu su yake kallo, ganin sadeeq yataho shi kadai yasa ranshi qara 6aci. Dama gashi famm yake saboda latti dasukayi gashi yanzu tana botsarewa, lallai saiya koyamata hankali. Kwankwasa glass din motar yasashi sakin siririn tsaki yana kauda kai. Budewa Sadeeq yayi yana cewa "to saika fito gimbiya dai taqi Qarasowa" Banza yayi dashi ko kallo be isheshi ba. "Ashraf?" Wani kallo ya watsa mashi yasake dauke kai. "Please Wai bakusan kun tara mutane bane? Haba jira babu dadi" Nan ma shiru. "Wohoho Ashraf for goodness sake dakai fa Nike" Harara ya watsa mishi yana cewa "cancel the gathering" "Me?! Are you serious?!" Yafada cikin Waro idanu Harara yasake watsa mishi "you heard me ai" "Haba Ashraf? Ka gama tara mutane kayi wasting din time dinsu sai kuma ka soke taruwar, wannan wane irin wulaqanci ne" "Look sadeeq karfa ka manta matsayinka, the fact that kai abokinane bazai Baka damar mayar dani shashasha ba, am still your boss!" Yafada tsakankannin haqora cikin Fushi. "Kayi hqr Ashraf Amma..." "Just shut up! Tagama 6atamin lokaci sannan tace bazata qarasoba? Ita wacece? Na ta6a jiran mace? Kai shaidane ban ta6aba sai akanta saikuma tanemi rainamin hankali? Cancel the damn party kazo mutafi!" Kallonshi kawai sadeeq keyi ganin dagaske fah yake nufin Ayi cancelling din partyn Bayan Duk manyan mutane aka tara, lallai aikau bazata sa6uba. Kwantar dakai yayi yaita roqonshi harya yarda dakyar yafito. Izuwa yanzu har biyar darabi tayi. Saudart nacikin motar don bazata juri Tsayuwa ba, itama a 6angarenta aqule take, lallai wannan gayen dan wulaqanci ne, Dama sawa yayi akawota don ya shanyata. Ta cikin motar ta hango fitowarshi, ta6e baki tayi tana kauda kai. Sanye yake cikin farar suit qall, sai jar shirt dake ciki da Jan necktie irin dan qaraminnan, sai hanki ja daya dan leqo ta aljihun gaba. Wow, gaskiya A.A haddadene👌 ba qaramin kyau shigar sukayi mashi ba. Tare suka taho da Sadeeq dake Bayan Ashraf. Suna isowa wajen dazasu bi su shiga ciki yaja ya tsaya hannaye zube cikin aljihu, fuska tamke ga shima uban baqin shade daya kwama. Ganin haka yasa sadeeq qarasawa motar Saudart don tahowa da ita. Saida tasake Jan aji sannan tafito itama sannan suka tako wajen Ashraf. Shikau Sadeeq sai ayyana yadda dan zamansu zai kaya don ya lura dukansu yan jin Kaine. Koda sukazo wajenshi ko gefenshi bata kallaba kamar yadda shima yayi kamar besan da itaba. "Ina zuwa" inji Sadeeq yayi gaba don zuwa sanarda isowarsu. Haka suka tsaya ko nuna alamun sunsan da zaman juna basuyiba. Daga nesa idan ka hangesu saisun burgeka don dukkansu sun hadu ba karya ga kayansu daya kusan marching. Ita jaa da baqi shi fari da jaa. Yadda yabarsu haka ya tardasu. "Please Ku qaraso" Nanma rasa wanda zai fara takawa akayi "Please Ku ake jira kuyi hqr" inji Sadeeq daya gaji da dramar su. Nan Saudart taci girma tafara takawa sannan fa dan jinkan shima yatako. "Please kubar tafiya aware kufa fiancée ne" Babu Wanda ya tankamashi suka cigaba da tafiya. Haka suka qarasa entrance din, DJ na hangosu ya saki wani kida mai dadi. Take kallo yakoma kansu, kowa na yaba haduwarsu. Tafi aka dauka hall din anatayi har suka qarasa wajen zamansu. 'Ashe surprise Sir A.A zaiyi Masu? Ashe da masoyiyarshi zaizo wannan party din' haka kowa yaita saqawa yayinda mafi yawan matan dake hall din Kishi ya cika musu zuciya. Mutane sukayi tazura mazauninsu Bayan sun zauna suna tayasu Murnar nasarar d company dinsu yayi da kuma taya Murnar samun mata. Sai a sannan Ashraf yayi danasanin daukota don shifa yayi hakanne don ya gwadamata koshi wanene dakuma yadda yakeda iko. Hasken flashes din hotuna kawai ke haskemasu fuska. Ashraf kamar koda yaushe fuskarshi a tamke itakau Saudart babu yabo babu fallasa idan kuma akayi congratulating dinta sai tadan saki murmushi. Ji take kamar ta tashi ta ruga don sosai tajita ta takura. Dakyar akasamu mutane suka koma suka zazzauna. Nan m.c yahau jawabin abinda ya tarasu cikin harshen turanci. Itadai Saudart kawai tana wajen ne Amma hankalinta Duk yayi gida, Jitake wama yasa ta yarda Tun farko da zywan? Duk inda ka wurga idanu yan media ne Masu dauka wannan mostly sunfi daukar su Ashraf. Ashraf kau abinne yaso juyemashi don ba haka yasoba. So yayi yakawota don ta raina kanta kuma beta6a tunanin yan jarida zasu hallarci wajen ba. Kawai yakawotane don taga matsayinshi dakuma ikonshi. Bayan jawaben nan aka shiga ci dasha, kowa da zaune a tebyr dinshi yana dan ta6a wani Abu. Hakan take awajensu Ashraf. Dukda babu mai cin komai cikinsu, kowa da abinda yasha mishi kai. Sadeeq ne yaqaraso wajen dawasu yan jarida biyu. "Sir, gawasu yan media zasuyima kai da sarauniyarka tambayoyi" inji Sadeeq aladabce Saidai deep down dariya yake mishi. Takaici ya hana Ashraf cewa komai don sai yanzu yasan Sadeeq ne ya gayyato mashi yan jaridar nan. "Sir wane irin farinciki kake ciki ayau?" Inji wani yana saita mic dinshi gabanshi Shiru yayi kamar bazeyi mgnba saiya daure cikin muryarshi mai dadin amo yace "Ina cikin farinciki sosai" "Sir wannan ne karo na farko da akafara ganinka da mace, ko zaka iya gayamana matsayinta agareka?" Inji wani nakusada nafarkon. Nanma shiru, "Lallai Sadeeq you are in hot soup" yafada cikin zuciyarshi Can cikin murya qasa qasa yace "She's my fiancée" "Wow congratulations... Ma'am zaki iya fadamana farincikin dakike ciki?" Suka maida akalar tambayar wajen Saudart. Jimm tadanyi sannan itama ayangace tace "Ina cikin farinciki sosai" "Ma'am wani matsayine sir A.A ke dashi awajenki" Murmushi tadan saki "Kamar yadda yafada am he's fiancée" "Wow.. Zaki iya fadamana farkon haduwarku?" Woo! Nabani, tafada cikin zuciyarta "Eh" "Ok muna jinki ma'am" "Mun fara haduwane a bakery dina" tafada kai tsaye "Wane bakery kenan?" Inji dayan. "Alhairi bakery" "Omg, badai kece mai alhairi bread ba?" Inji dayan cikin mammaki. "Yes nice" ta amsa cikin basarwa. Ashraf na gefe takaici kamar yayi hauka. "Me sir A.A yajeyi a bakeryn?" Murmushin gefen baki tayi irin Wanda shima yakeyi. "Me zaije yi kau? Yaje Isar da saqon zuciyarshi ne" "Wow! Me hakan ke nufi?" Inji dayan sai setasu da camera ake. Dukda tagaji da tambayoyin Amma burinta na quntatawa Ashraf yasa tace "Ina nufin yazone donyayi fighting for his love" "Wow amazing! Sir Ashraf hakane?" Inji dayan yana saita Ashraf da mic. Jiyayi kamar ya nutse don kunya don Dama tunda suka fara hankalin kowa yadawo Kansu. Babu damar musawa yayi murmushi yana kada kai. "Sir idan hakane akwai inda kafara ganinta kenan harka fola Mata, inane kafara ganinta?" Ca6, da ace ana ganin zuciya da kunga yadda zuciyar Ashraf ke tafarfasa. "A cinema" yafada ahankali, dukda cikin Fushi yake hakan be nunaba a fuskarshi. Lallai wlh saita gane kurenta, shi take zubarma girma agaban jama'a? Wai har binta bakery ko ubanmi ma yayi? "Wow gaskiya labarin haduwarku yayi dadi, ma'am da Sir A.A yazo wajenki da qoqon bararshi ya kikaji?" Kutt.. Qoqon me? Inji Ashraf cikin zuciya. Cikin basarwa Saudart tace "well as expected nayi mammakin hakan, ganin yanayin halinmu ba dayaba. At first naqi yarda da soyayyarshi gaskiya ce Amma ganin yadda yaketa zarya bakery dina Dama gidanmu yasani giving abun a second thought, ahankali ahankali nafara kulashi har yayi nasarar yaqar zuciyata da soyayyarshi" tafada murmushin mugunta fall fuskarta Wohoho nan hall din ya rude da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinshi, Shidai Ashraf komawa yayi yayi balancing akan kujerar tareda lumshe idanu, zuciyarshi kamar ana hura wuta. dakyar hall din yayi shiru sannan daya Daga cikin yan jardan yace "yanzu zaki iya fadamana wane matsayin yake dashi azuciyarki?" Murmushi tadan saki a kunyace sannan tace "Yanada babban matsayi azuciyata sbd mutum neshi mai iya tarairaya, iya tarairayarshi da kulawarshi yasani fara sonshi, gaskiya am lucky to have such a caring guy" Caraf dan jaridan yayi yace "shima he is lucky wajen samun kyakyawar sarauniya irinki, kou Mr A.A?" Bude idanunshi yayi tacikin glass wadda ba'a ma hango idanun. A hankali yace "Yeah...am indeed.. Lucky" Tafi aka dauka gabadaya hall din, sai haskesu da flashes ake, wasu dan iyayi har zuwa wajensu suke sudau selfie. Wasu yan rawar kan kau sai liqema Saudart suke ala dole zasu qulla abota da masoyiyar the famous billionaire A.A Itakau Saudart ko ajikinta, ko babu komai ta rama koda kadanne cikin wulaqancin da Ashraf yayi Mata don haka jinta take wasai. Oga kau a zahiri kawai yake garas Amma karka tona zuciyarshi, jiyake kamar ya tashi yabar hall din, Allah Allah yake agama damn gathering din...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 Allah ka yayemana wannan cuta (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 019 "Wuuhh! Soyayya ruwan Zuma! Ashe dai da gaskiyar Hamisu breaker dayace soyayya bata kyale kowaba, cabdi zarkad'i! Ahe dai Duk fafa din yaya ana buga love agefe? Wow!" Tafada tana zooming din hoton daidai fuskar Saudart. "Soo cute! Kai wlh tafi yaya kyau ji bakin, dama ni" tafada tana qarewa pics din kallo. "Lallai saisu Suzy azo abar daydreaming din samun yaya, ga Wanda ta damata ta shanye nan a kyau." Tasake fada tana shiga WhatsApp dinta. Direct wajen status dinta tanufa ta Dora hotunansu kowane da caption dinshi. Dariya ta fashe dashi tana cewa "yau wasu zasuyi mushe, zan bugi zuciyar wasu" Ta fita ta shiga Instagram dinta nanma ta Dora hotunansu. Kan kace me? Liking sukaita shigowa ba kakkautawa, da comments, kowa na fadin albarkacin bakinshi na haduwar dasukayi. Itadai baby dadi kawai takeji at least yaya zaiyi aure yabar musu gidan ta sarara dakyau. "Lallai su alarrama yaya, ka hana wasu soyewa Ashe kai kanacan kana babbakewa. Ca6! Naso inga fuskar yaya ana kalaman soyayya, hhhh lallai soyayya manya" Haka taita sabbatunta tana bin comments din mutane tana karantawa cikin jindadi. Ahankali ta turo kofar tashigo, babu kowa falon hakan yasa ta qarasa ciki. Zaune ta tardashi kan gado ya tankwashe kafaffu yana aiki akan laptop dinshi. Dagowa yayi suka hada ido nan Kowanne yasakarma juna murmushi. "Ummy dakanki? Da kin aiko nazo" yafada yana matsarda laptop din Daga gabanshi. Zama Ummy tayi gefen gadon tana murmushi. "A'a babana, ba gashi nazoba? Tundazu nake baza idanu kozaka shigo Amma shiru shiyasa nabiyo sahu" "Wlh Ummy wani aiki nakeyi saura kadan ma in qarasa shut ban fitoba, ina kwana" yafada yana matsowa kusada ita tareda yin matashin kai da kafarta. "Lfy lau, ya gajiyan jiya? Shine kadawo ko kashigo?" "Wlh Ummy agajiye nadawo ne kuma nayi tunanin kun Riga kunyi barci ne" "Ayyah, to ya partyn ya tafi?" Ta tambaya tana shafar sumanshi dake kwance luff luff. "Great, anyi taro lfy an tashi lfy" "Yayi kyau, shine kuma mu Saidai muji a salensa? Daka fara gwada mana budurwarka gwara ka fara gwadama duniya?" Shiru yayi don dama yasan arina. "Dakaifa nake son, yanzu fisabillilah Saidai muga photonku kaida budurwarka a t.v ko sanin da ita bamuyiba? Ka kyauta kenan?" "Ummy bahaka bane.." "To yaya ne? Uhm? Wato mu munanan kabarmu munata haukanmu Duk yarinyar Dana kawoma kace bata yimakaba Ashe kanacan kana campaign wani wajen" "Ummmy..." "It ok, ai hakanma daidai ne, ni dama bason tilastama nakeba, nafi son ka za6o za6inka, kuma gaskiya tayima, ina ganinta ta kwanta min, yaushe zaka kawota muganta" "Haba Ummy Bayan ganin da kuka yimata yanzu?" Yafada yana turo baki zuciyarshi fall da haushi. Dungure mishi kai tayi "Wato rowarta zakayi mana ko? To Baka isaba, dolene ka kawota muganta tunda Allah ya tona asirinka, Ayi a sanya biki Ayi auren dama ka isheni da shagwa6arka, gwara ka qara gaba matarka taji dakai niba inji da autata" tafada cikin sigar tsokana. Tashi zaune yayi yana turo baki cikin shagwa6a. "Dama Ummy batun yauba nasan kin gaji daniba, ba komai" yafada yana juyamata baya. Dariya Ummy tayi tace "atoh ba dole in gaji dakaiba mutum godai godai dashi sai ta6ara, kaiba autaba Amma ka kwacema autata autanci, oya tashi muje muyi break" Tafada tana kamo kunnenshi, Dan qara yasaki cikin raki, hakan besa tasakeshi ba har saida suka fito sukazo har dining. Baby daketa faman maida yadda akayi a wani group dinta mai taken CLASSIC LADIES akan hotunan data Dora a status. Ganin fitowarsu yasata saurin kulle datar ta ta ajiye wayar ta nutsu. Sai kicin kicin kwace kunnenshi yake ganin Baby a dining Amma Ummy taqi saki saida ya zauna sannan tasakeshi sannan itama ta zauna kusadashi. "Ina kwana yaya?" Inji baby a nutse. Cikin cin magani yace "lfy" Ta6e baki tayi cikin zuciyarta tana cewa "kaji dashi, Amma da agaban babyn taka kake da fuska kamar gonar auduga" Serving dinshi Ummy tayi ta turamashi, shima turomata yayi yana tsuke baki. Girgiza kai tayi tace "matarka dai tabani, wannan ta6arar taka ai ko auta albarka" Baby cikin zuciyarta tace "aikau dai, ai harna tausaya mata, Kodayake mace fa shu'umace idan tasan takan aiki shi zaizama bawanta, Nidai Allah yasa Ayi agama dawuri kona sarara, kai zamusha biki sai gwargwarona ya dinga yima mutane daquwa, zamu sha zanku" Duk cikin zuciya take wannan zancen azahiri kau murmushi take. "Ke!" Firgigit tayi Daga daydreaming dinta ta dago ta kalleshi. "Get lost!" Yafada bawasa a fuskarshi "Haba son. Metayi kuma?" Shiru yayi bece komaiba Shan ruwa tayi sannan tamiqe ta dauki wayarta tabar wajen don shine rufin asirinta don kallon dayake watsamata ya isheta. "Hmm Allah ya shiryeka son, yarabaka da wannan baqin ran" Bece komaiba ya cigaba da amsar abincin datake feeding dinshi. Shiga daki tayi tana gunagunai tana harare harare. Ringing din wayarta ne ya katseta Ganin mai kiranta yasata sakin ihu sannan ta Daga. Ihu aka saki Daga dayan 6angaren, itama tasaki nata sannan suka kyalkyale da dariya kamar sabbin kamu. "Shegiya, haka akayi? Dazu nahau naga hotuna" "Kedai bari sis, na dasa bomb" inji baby tana dariya. "Aikau yadasu, hawo kiga bala'i. Gasu team dinsu Suzy can sai ashar suke saki, group ya hargitse" Waro idanu baby tayi "Haba?" "Shegiya ai kyace hakan Bayan kin dasa bomb kin tsere" "Wlh Ummy takirani nafita yin break Amma bari nahau.." Ding.. Ta katse wayar, har kyarma take wajen bude data tashiga WhatsApp. Waro idanu tayi ganin massage sunfi 200 Daga saukanta zuwa yanzu. Bi taita yi tana kallon abubuwan dasuke tattaunawa akai tanacin dariya saboda yadda su team Suzy suka fito da Kishi qarara suna masifa. Saida tagama bi sannan ta tura wani sticker na baby tana hura chewing gum. Ai ana ganinta group yaqara hargitsewa, nan Abu yadawo sabo don tsagerune suka hadu, sai shaqiyanci suke suna qara cusama qawayen Suzy haushi. "Babban goro sai magogin karfe, sama tayiwa yaro nisa Saidai yatada kai yayi kallo, yayana alluran cikin ruwane, ruwanma na kogi mai rabo ke dauka" inji baby cikin shaqiyanci Teema qawarta dasuka gama waya yanzu tace "Fadi da ihu ki qara da wayyo yar uwa, yayanmu sai balarabiya mai natural kyau ba dangin bleaching da qonewar fata ba" Wata cikin qawayen Suzy tace "Ji tura kai ba kwarjini, su kalan dangi anji jiki, Wai yayanmu lol" Baby tayi charaf tace "Ai kalan dangima iyawace, idan fitsari banxane kazama tayi" Wata princess Amee cikin qawayen baby tace "Anayi ina jin nice ana bari inajin haushi" ta Dora sticker gwalo. Haka sukayitayi Daga baya taranmasu qawayen baby sukayi kasancewar qawayen Suzy bawani yawa ke garesuba, gashi sun fisu baki. Dole suka sauka suka kyalesu. Duk abinda ake Suzy na kallo tana kuma saurare. Ta Kasa yarda da abinda takeji kuma take gani. Ashraf dinta? Ashraf dinta dawata? Ashraf dako kallo saitayi dagaske yake kallonta shine take ganin pics dinshi da wata da sunan ita zai aura? Cabdi aikau za'a yita...✍ Wata sabuwa😳 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Yaa Allah ka yayemana wannan annobar (covid19) Ya Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 020 Girrr! Girrr!! Girrr!!! Kamar bazata daukaba saikuma ta Daga ta kara a kunne batareda tayi magana ba. "Suzy? Wai ina kika shiga ne abubuwa nata faruwa baki ko fitowa, shin kinma san abinda ke faruwa kuwa? Ki hau yanar gizo kisha news" "Nasani Beebah, a tunaninki Duk abinnan da'akayi bansaniba?" "Au kinma sani kenan, to zokiga yadda waccan qallemar ke cimana mutunci a group da ita da tsinnanun qawayenta" "Duk Nagani beebah yanzu ni batasu Nike ba, wlh ni kadai nasan yadda nakeji acikin zuciyata, beebah Ashraf yaci amanata, Ashe Duk abinda nake aikin banzane yana can yana bin wata?" "Hmm kya qara gani ai, ina kaiki kina kauce hanya, a tunaninki shima ba zuciya ke cikin kirjinshiba da bazai fada son wataba?" "Hmm wlh beebah am broken, tunda naga wannan abun Nike cikin damuwa, nama Kasa tashi inyi komai, beebah kiban shawara, please me zanyi? Mezanyi in mallaki Ashraf? Me zanyi in mallakeshi ni kadai?" Ta ida zancen tana sakin kuka. "Kuka? Kuka fa kike Suzy?" "To mezanyi beebah, I've loose Ashraf for good" "Ya da saurin karaya? Ashraf nakine ke daya, ki sanya wannan aranki, babu wacce ta isa ta rabaki dashi. Kedai kawai ki cigaba da bin Duk yadda nace" Haka taita rarrashinta har tasamu tayi shiru sannan sukayi bankwana akan zata shigo su tattauna akan lamarin. Saukowa take tana tafe tana zira hannun hijabinta. Sanye take cikin atamfa mai zanen kalar fari da purple, dinki Riga da skirt pieces, sai farar three quarter din hijab mai hannu wanda yake daidai gwiwa. A falo ta tarda daddy yana kallo. Qamshin turarenta ya fargar dashi isowarta. "Wow shalele, kinyi kyau" Dariya tayi tana qarasawa wajenshi ta zauna kusadashi. "Daddy ina kwana?" "Lfy qalau shalele, ya gajiyan jiya" Shiru tayi bata amsaba. "Shalele kinga yadda aketa nuna hotunanku a t.v kuwa? Cab! Wlh kunyi kyau gashi sai nannata sunanki ake dakuma bakery dinki kinga ko anan ma kinyi tallar bakery dinki ga wadanda basu saniba" Hmm kawai ta iya cewa tana kauda kai. "Shalele, wannan auren alhairine agareki kai ga dukkanmu gabadaya, ji Tun kafin Ayi auren ma harmun fara ribantuwa inaga anyi auren." "Hmm dad sai wani nanata Kalmar aurennan kake kamar wani mai dorewa, auren da na lokaci ne?" "Eh na lokaci ne, Amma ai kana naka Allah na nashi, wayasani ko yazama dorarren" "God forbid! Allah ya tsareni, ko maza sun qare bazan iya zama dashiba Wai da sunan aure na dindindin, me zanyi da wanda besan darajar mutane ba" "Haba shalele, ki dinga yiwa mutane uzuri, a yanzu bazaki fahimci halayenshi ba saikun zauna tare" "Aikaudai, dad bari Kaga in qarasa, na kwana biyu ban leqa bakery ba" "To Shikenan Allah ya karemin ke sweetheart" Peck tayimashi tana cewa "Amin sweet daddy". Tunda tashigo bakery din ta lura da irin kallon da ake binta dashi Wanda bata saba ganiba. Sharewa tayi ta cigaba da aikin gabanta, tana nan zaune maryam P.A dinta tashigo da sallama. Dagowa tayi tana amsawa fuska sake. Gaisheta maryam tayi cikin girmamawa sannan tafara gabatar mata da ordern da akayi kwana biyun da batazoba. Saidai Saudart nalura da kallon da maryam din kemata wanda yasha banban dana. Saida suka gama, har maryam tajuya zata tafi saikuma ta tsaya. " uhum? Wani Abu?" Inji Saudart "A'a ma'am, kawai..kawai tayaki murna zanyi" "Murna? Ta me?" "Yau.. Yau dasafe naga hotunanku da fiancée dinki, congratulations" Sai a sannan Saudart tasan dalilin kallon da aketa binta dashi. "Oh thanks" "Allah ya sanya alhairi yakawo zuri'a dayyiba" "Ok jeki Ku qarasa dan Allah kinsan ba isashen time ne garemu ba" tafada batareda ta amsa addu'arta ba A ladabce ta juya tafice, ta6e baki tayi, ta maida hankalinta kan aikin gabanta. Wajajen karfe uku tana tsaka da aiki aka bubbugo kofa "Yes come in" tace kanta kan rubutun datake. Maryam ce tashigo "Ma'am kinyi baqi" "Baqi?" "Yes ma'am" "To? Kishigo dasu" Da to ta amsa tafita can saigata tasake shigowa dawasu yanmata biyu biye a bayanta. "Yeah! Antynmu!" Inji Baby tana rugawa wajen Saudart ta rungumeta. Kasa motsawa Saudart tayi don mammaki. Sakinta baby tayi tana dan jabaya tana kallonta. "Wow! Wlh anty kinfi kyauma azahiri, Wai kin ganki?" "Mtcheew Wai baby zaki nutsu ne kokuwa?" Inji teema da takaicin rawar kanta "Ke dalla malama kyaleni, na dade ina addu'a Allah ya bayanamin ita ko tazo ta daukeshi sutafi nima in wala, yau naganta kuma saiki hanani murna?" "Mtcheew, ke kika sani ai... Ina yini anty" inji teema tana kallon Saudart da tundazu binsu kawai take da kallo. Murmushi ta qaqaro ta amsa tana cewa "bismillah Ku zauna mana" Harara suka gallama juna teema da baby sannan baby taja kujera takawo kusada Saudart tazauna tana cewa "Kusada anty ta zan zauna" Ta6e baki teema tayi tana harararta. "Dadin abin ba taki kadai bace" Murmushi Saudart tayi dukda haryanzu bata ganesuba Amma sai gani take kamar ta ta6a ganin fuskar baby wani waje Amma takasa tunawa. Ido tayima maryam akan akawomusu abin ta6awa. "Sannunku yanmata" Tare suka amsa da Yauwa, baby na dorawa da "Ina wuni antyna ta kaina" Murmushi tayi sannan ta amsa da "Lfy qalau... Saidai ban wayekuba" Caraf baby tace "laa anty baby ce halan yasha baki labarina nidince baki ta6a ganiba" Kan Saudart ne ta kulle "Baby?" Kallon teema baby tayi itakuma ta antayamata gwalo. "Wato dan wulaqanci ko maganata baya miki kenan, kai yaya Ashraf?" Jin ta ambaci sunanshi yasata gane kosu waye, sai yanzu taga Ashe kammanin take gani a fuskarta. "Ba kece uwar cusa kai ba kwarjini ba? Ai kadanma kika gani" inji teema tana mata dariya. "To waya Kasa dake? Yar sa eyes kawai" saikuma tajuyo kan Saudart. "Anty ni sunana baby qanwar lovely dinki, Amma kina iya kirana da mhiz Meebee sunan da nikeso aringa kirana kenan Daga yanzu, baby yayi kauyanci dayawa, koba hakaba?" Tafada tana kallon teema daketa antayamata Harara tundazu "Bansaniba, waike kam baki iya aro nutsuwa kona d'an lokaci bane? Gabanfa surukarki kike?" Waro idanu tayi sannan tayi saurin kada kai sannan tajuyo kamar saliha tana sunsunne kai. "Mun sameku lfy in-law?" Kamar me ta6in hankali takuma zabura ta gyara zama tana antayama teema Harara. "No way! Bawani kunya, nadade ina jiran tazo tarabamu da jalli joga kuma yau inganta kice zaki hanani bayyana murnata? Bakida hankali" Yar dariya ta kufcewa Saudart daketa kallon ikon Allah tundazu. Itama baby tawani maqe murya tana kwaikwayon dariyarta. "Kai anty kin iya dariya, wannan da ita kadaima kina iya siye zuciyar kowama" tasake maqe murya tana qara dariyar. Dariya Saudart tayi tana girgiza kai, lallai wannan uwar rawar kan ce kanwar A.A? Lallai tahuta dabata dauko baqin halin yayanta ba. "Anty kiyi hqr wlh haka take wani sa'in kamar sabuwar kamu" Dariya Saudart tasakeyi tace "A'a qanwata ba sabuwar kamu bace, ko baby" Turo baki baby tayi "mhiz meebee dai anty" Daga gira Saudart tayi tana cewa "oops na manta, mhiz meebee" "Yauwa antyna, wlh bakiji yadda sunan yayi dadiba abakinki" "Kamar yadda nake fadamiki kafin wannan amebo din ta katseni, ni qanwar lovely dinki ce, kuma auta agidanmu. Ina schooling a Ahmad bello uni, yanzu haka ina level 200, best colour dina pink, best food dina shashaka, ingayamiki har saceni kina iyayi da ita, best hobby dina kwalliya, I can do make up for devil ma, bana tara tarkacen qawaye, wannan itace ma nake dan maneji daita, a rayuwa babu mai takurani kamar lovely dinki, ya matsa mini, kiyi hqr fa nasan da ciwo a kushe masoyinka Amma bakin gaskiya ta nake fada, dan Allah ki taimaka ki aureshi Kitafi dashi wlh dama nagaji dashi ya isheni sbd..." Dundu teema takaimata abaya har saida ta duqe. "Wlh bakiyiba baby, shegiya naga Wanda zai qara rakaki wani waje" inji teema tana harararta. "Anty kin ganiko?" Saudart dataci dariyar dramar su tace "Haba kyaleta, yanzu dai ga wannan kudan ta6a" tafada tanama maryam ido dake tsaye tundazu tana dariyar dramar baby akan ta qaraso. Qarasowa tayi ta ajiyemusu , snacks ne wadda sukeyi da drinks. Gutsira daya baby tayi ta Waro idanu, tauna take tana lumshe idanu harda wani rausaya kai. Teema kau kamar taita kifamata mari don takaici. "Wow anty, anan akeyin snacks dinnan?" Kadamata kai Saudart tayi tana murmushi. "Wow yummy, insha Allah anan za'ayi mana snacks din birthday dina kou?" Ta qarashe zancen tana kallon teema. Guzurin Harara tasamu awajenta hakan yasata kauda kai. Haka taita zuba surutunta hankali kwance, Saudart kau sosai baby kebata dariya saboda surutunta da rawar kanta. Tun bata biyemata harta fara biyemata, Tass ta cinye snacks dinta yayinda teema tarage itama kawai saboda kunya, itakau baby ko a jikinta acewarta ai antynta ce bawani kunyarta dazataji. Haka Saudart ta zagaya dasu bakery din part part, sosai baby ta dinga santi tana yaba bakery din itadai Saudart dariya ne nata. Saida suka zagaye koina a bakery din sannan suka dawo nanfa baby tafara daukarta hoto. Ta dauketa ita kadai suyi selfie gabadaya. Haka sukayitayi Tun teema na Dari Dari harta ware itama ganin yadda Saudart ta saki jiki dasu, abinka da wayyaya. Sai anan Saudart tagane Ashe Duk jirgi daya ya kwasosu don zani ce ta tarda muje. Sai qarfe biyar suka bar bakery din Bayan sunyi exchanging din number sannan Kowanne tacika mashi shopping bag da kala kalan snacks. Haka suka dawo gida sunata labarin kirkin Saudart...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19) Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Sorry for the late post, wata hidimace ta tasomana yanzu qila sau daya zan dinga post arana, Amma idan nasamu sarari zaku samu ko sau biyune. Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 021 Knocking da akayi a kofarshi yasashi dagowa. Sake knocking akayi, ahankali ya bude baki kamar mai ciwon baki yace "Yes? Come in" Ahankali aka bude kofar aka shigo, haryanzu be dago kaiba ta kalli mai shigowa ba don Duk a tunaninshi Sadeeq ne yagama wasan 6uyar dayake dashi yazo. "Hellooo my man" Hakan yasashi dagowa ahankali, idanunshi ne suka sauka akanta. Kamar kullum tana cikin tsukakkun kaya, wando high waist baqi da shoulder less vest fara sai rolling din dan yalolon gyale fari datayi. Cikin karairaya fuska dauke da murmushin barikanci ta qaraso gabanshi taja kujera ta zauna, kafa daya kan daya. Dauke kanshi yayi batareda yace mata uffan ba yacigaba da harkan gabanshi. "Man?.. Ya kake?" Banza yayi daita "My... Am talking" Sai alokacin ya dago ya kalleta Saidai qala bece ba. "Man, Baka maraba da zuwana ne?" Nanma shiru Saidai bebar kallontaba. Narke fuska tayi cikin duniyanci "Man, why are you giving me tough time? Meyasa kakeda riqo? Nasan nayi kuskure ada, Amma izuwa yanzu ya cancanta ace ka yafemin, man nobody is above mistake kaima kasani, am sorry, nayi nadama please give me another chance" ta qarasa zancen tana qaqalo hawaye Maida kallonshi yayi akan abinda yakeyi batareda ya sake bi takanta ba. "Man.." "Look Suzy, please get out, why zakizo kina distracting dina? The last time I checked na hanaki zuwa office dina, then why zaki addabeni?" Yafada cikin Fushi "Haba man, what happen to us, da ba haka kakemin ba, nasan nayi laifi, kuma na tuba, ko Allah mukayiwa laifi muka tuba muka roqi yafiyarshi yana yafemana, bare mutum" "Ni laifi kikayi min? Bakiyimin komaiba, idanma kinyi na yafemaki, Shikenan?" Yafada cikin qosawa. "Ba Shikenan ba, yakamata mukoma yadda muke da idan dagaske ka yafemin din" "Wannan kuma ne ake kira impossible tense, idan an mutu ba'a dawowa baby, so forget" Kukan munafirci ta fashe dashi "Look, this is an office ba kasuwa ba, please get out" "Man.." "Out or I Call the security" "Yanzu Ashraf ni kake kora? Nice fa, suzyn ka" "Ada kenan, that's past tense, yanzu nasan kinfini sanin matsayinki awajena, and don't forget very soon zanyi aure to the love of my life, nasan kina sane da hakan, so please get out before I throw up" Shiru tayi takasa cewa komai sai kallonshi datake ga hawaye sai bin kuncinta suke. Ganin yafara danna landline nakusadashi alamun zaiyi kira yasata tashi afusace. "Ok muzuba mugani. Zan fita Basai ka hadani da qatin banzaba, zan fita office dinka Amma bazaka ta6a fiddani a rayuwarkaba, I will hunt you till eternity, kai nawane ko kaqi ko kaso so is better kama so" "Naji fita" "Zan fita din ne, zan fita!" Tafada tana daukar Jakarta ta fice a hasale. Guntun tsaki yaja sannan ya maida hankalinshi saman system dinshi. Bayan mintuna biyar sai gashi an sake knocking, be dagoba bare ya amsa. Sake knocking din akayi nanma shiru hakan yasa mai knocking din budewa yashigo. Kobe dagoba yasan Sadeeq ne. Qarasowa Sadeeq yayi sai rarraba idanu yake alamun rashin gaskiya sannan yaja kujera ya zauna. Ko dagowa ya kalleshi beyiba bare yasa ran zai tankashi. "Sir A.A barka da warhaka" inji Sadeeq kamar wani na Allah. Dagowa Ashraf yayi ya antayamishi wata uwar Harara. "Ka gama guje gujen?" Dariya kesan kufce mashi yayi saurin maidata "Guje guje kuma sir?" "Zakaci ubanka ne, wato dan ka maidani sa'anka kawani gayyatomin yan jarida ko and to add salt to injury ka tafiyanka da drivern ko?" Yar dariya Sadeeq yayi sannan yace "Afuwan sir, wlh tsoro naji, ganin antayen hararan da kakemin yasa naji tsoro nagudu, Amma kaika maidata gida?" Wata uwar Harara yasake lafta mishi "Zakasan Wanda ya maidata ne idan wannan watan kaji muqui" Zaro idanu Sadeeq yayi "Haba ranka shi dade, wlh natuba,ka riqemin salary ai kagama dani, please Allah ya huci zuciyarka" "Zakayi bayanine" "Haba ango mai jiran bed wajen amaryarshi Saudart, please inci alfarmar antyn tawa mana" Jifanshi yayi da pen din hannunshi "Kasake kiramin sunan nan a office dina saina sa6amaka" "Ohh sorry to masoyi a wajen Suzy baby yar kwalisa" Tamke fuskarshi Ashraf yayi ba alamun wasa. "Ina wasa dakaine Sadeeq, ka mance agaban boss dinka kake? Tafi nayi suspending dinka na wata daya" Wani tsalle Sadeeq yayi sai agabanshi "Sus- me? Haba boss Dan Allah kayi hqr natuba" Saida ya wanashi sosai sannan ya haqura. "Ashraf naga fitowar Suzy Daga office dinnan, metazo yi?" "Bansaniba" "Please mana" "Kacika gulma ko?" "Ba gulma bace wlh, please gayamin" Resting yayi a kujerarshi yana dan jujjuyawa "Wai tazo inbata second chance" "To bata din zakayi?" Harara ya gallamashi "No chance in hell dude" "Hmm Baka ganin yakamata Ayi a daura auren nan ko ta sararamaka?" Banza yayi dashi. "Ashraf magana Nike, kabashi kudin yanzu shi yarage yabaka" "To yanzu nizanje in tunamashi abinda yakamata yayi? Yafini sani ai" "To ai shima kai yake jira, jai zaka tura asa rana ko?" "Babu inda zan tura" "Mtcheew, wani sa'in idan kayi wani abun kamar aita dukanka" "Go ahead ai kana iya dukan nawan ma" "Yanzu dai tell Ummy kasamu wanda kakeso atura Ayi magana aure kakeso" Wani mugun kallo ya watsa mashi "Are you kidding me?" Dariya Sadeeq yayi yana cewa "Allah ya yayema wannan dabi'ar, Harara kamar tsohuwar faruwa" Bugu Ashraf yakai mashi yayi saurin kaucewa yana dariya "Get out" "Naji Amma wlh kayi yadda nace" "Bazanyiba idan kai bakada kunya ni inada" "To kunyatu, ya za'ayi kenan?" "Ta inda aka hau tanan za'a sauka" "Meaning?" "Bansaniba" "To nima ban ganeba" "Kar Allah yasa kagane" "Amin Amma.." "Out!" Yabude baki zai sake magana ya katseshi ta hanyar Jifanshi da pen "Out!!" Da dariya yafice office din. Shima murmushi yayi yana girgiza kai, Sadeeq? Ciwon kai. Shiru yayi yana tunanin maganar da Sadeeq yafada mashi yanzu 'Eh auren nan kawai zaisa Suzy tabar liqemashi, dolene Ayi auren kusa kusa don yaji dadin fara daukar fansa akan babban maqiyinshi. ****************************************** Su baby ankoma gida an Tisa Ummy gaba sai zubamata surutu suke suna bata labarin Saudart da kirkinta, nan suka shiga nunamata hotunan dasukayi, Masha Allah kawai Ummy ke fadi saboda ba qaramin shiga ranta yarinyar tayiba, kallo daya zakayimata kasan tanada nutsuwa. Nan suka fiddo snacks din sunaci suna santi harda Ummy, sosai ta qagara itama ta ganta. Da daddare fa group din CLASSIC LADIES ya qara hargitsewa saboda pics din da baby ta tura Wanda sukayi a bakery dazu Kowanne da caption dinshi, nanfa akayi caaa kowa na fadin albarkacin bakinshi. Masu yabawa na yabawa Masu kushewa na kushewa, yan a la6e gefe asha dariya nayi. Duk abinda ake Suzy Nagani, baqinciki kamar tayi bindiga. Haka taita zooming din hotunan Saudart tana bin kowane lungu da saqonta da kallo, takaici fall zuciyarta. ***************************************** Kwance take kan gadonta ruff da ciki ta tada kai da tafikan hannayenta tazubama wani littafi idanu tana karantawa. Sanye take cikin pink din Kayan barci Riga da Wanda iya gwiwa, sai hular net dake kanta itama pink. Kallo daya zakayi mata kasan littafin yayi mugun tafiya da hankalinta don sai murmushi take saki, tana jinjina kai alamun dramar da ake ciki na qayyatar daita. Ringing din wayarta ya dawo daita Daga duniyar karatu. Jawo wayar tayi taduba mai kiran. SWEET MUMMY taga na yawo a screen din wayar. Dagawa tayi ta kara a kunne tana mirginawa tsakiyar gadon. "Mamyna" "Na'am Angel" "Ina wuni mamyna?" "Lfy lau, ya aiki?" "Alhamdulilah mamyna, yaya wajensu Abdul baseet?" "Hmm Abdul baseet ko rigimmame? Sunanan dawowa jibi insha Allah" "Dagaske? Kai Amma naji dadi dama nayi missing dinsu" Tafada cikin murna "Aikau sunkusa dawowa yazo ya Dora Daga inda ya tsaya" "Kai mamy Abdul fa Beda rigima" "Ke daice bemawa" "Hhhh atoh Yamayi din in mashi Rowa" Dariya mamy itama tayi sannan tace "Daughter Wai dagaske ne abubuwan danake ji?" Gaban Saudart ne yafadi "M..me kenan?" "Wai anganki tareda A.A Wai ke budurwarshi ce" Kunya ce tadan kama Saudart sai tayi shiru "Kinyi shiru?" "Mamy.." Saikuma tayi shiru don batasan abinda zatace ba "Ba damuwa, gobe ki biyo tanan zamuyi magana" "Ok mamy" tafada a kasalance. "Saida safe to" "To mamy Allah yabamu alhairi" Kitt suka katse wayar tare. Kasa cigaba da karatun tayi takoma ta kwanta tana kallon ceiling zuciyarta fall da saqe saqe...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ya yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 022 Washegari kamar yadda mamynta ta buqata, biyawa tayi gidanta. Kamar ranan bata iske kowaba sai mamy kadai, yaran basu dawoba shikuma mijinta yana banki (dayake bank manager ne). Hira suka dan ta6a kafin mamyn ta dauko maganar jiya. "Angel, jiya munfara magana bamu idaba" "Eh mamy" Saudart tafada tana sinne kai. "Tell me Angel, dama A.A saurayinkine? Wace cinema naji yace kun hadu? Dama kina zuwa cinema ne? Me kuma yakaiki binshi wannan taron?" Shiru Saudart tayi don tama rasa da wacce tambaya zata fara, gashi bawani karya ta iya shiryawaba. "Saudart kinyi shiru, kinkau san waye A.A? Kinsan matsayinshi kuwa? How come kika fara soyayya da wanda ni dake Munsan kwata kwata baya cikin tsarin mazajen dakike so, Saudart are you hiding something from me?" Qaqaro murmushi tayi tana cewa "N..no mamy, Allah babu abunda nake boye miki, kawai hadi ne na Allah" "Naji, me yakaiki cinema at first place har kuka hadu?" 'Woo yau na banu' inji Saudart cikin zuciya. "M..mamy tareda daddy fa mukaje, w..wani film ake haskawa shine mukaje kallo" Tafada sai raba idanu take alamun rashin gaskiya. "Saudart, karya kikemin?" "A'a mamy, mezaisa inmiki qarya? I swear kallo mukaje da daddy muka hade" Ajiyar zuciya mamy tasauke dukda haryanzu bata ida yarda daitaba. "To meyasa kika bishi taron?" 'Ohh mamy pleease' tafada a zuciyarta "Ina jinki" inji mamy data tsareta da idanu. "Mamy cewa yayi nabishi" "Kuma sai kika bishi?!" Inji mamy ahasale "Mamy am sor..." "Dalla rufemin baki! Har namiji yazo yace kibishi kema kibishin? Ina tarbiyyarda nabaki? Kuma shi baban naki da saninshi yabarki kikaje? Ina hankalinki yatafi? Ehh?" "Am sorry mamy, bazan sake ba" "Kima sake din sakaran banza, yaje yawani nunaki wa mutane, idan be aureki bafa? Wannan ai sakarcine..." Nan taita fada ta inda take shiga batanan take fitaba, itadai Saudart haquri kawai take bata, nan Daga baya fadan yakoma nasiha, nasiha mai ratsa jiki tayi mata har saida zuciyar Saudart ta karye tafara hawaye. Sai wajajen 12:pm ta var gidan Tawuce bakery. A bakery ma ranan ranta a dagule yake, anya tayima kanta adalci data yarda da wannan auren, ga kuma sa6ama ubangijinta datayi. Haka tawuni ranan zuciya a cunkushe sai istigfari take akan Allah ya yafemata da ita da daddynta. Suna zaune falo suna kallo sukaji sukaji qarar doorbell. Ganin baby batada niyyar motsawa yasa Ummy cewa "Bakiji ana danna bell ne?" "Wayyo Ummy dan Allah kiyi hqr idan natashi wuceni za'ayi kuma ba damar tariyowa, please kiyi hqr" "Zaki tashi ne ko saina sa6amiki" Baki a cinne ta tashi tanufi kofar tanayi tana waigen tvn Qara danna doorbell da'akayi yasa ta qarasa wajen kofar a afusace tana cewa "Ana zuwa, haan?" Tana budewa sukayi four eyes da Ashraf sai Sadeeq bayanshi. Saurin ja dabaya tadan yi tana yaqe "Laa! Ashe kune? S..sannunku Ku shigo" Wata uwar Harara ya gallamata sannan yashigo zaiwuce tayi saurin ra6ewa ya wuce, Sadeeq na shima yashigo yana dariya ganin yadda baby ta bude azafafe tana ganin Ashraf Duk ta daburce. Harara ya wanka mashi. "Meye abin dariyar?" Sake dariyar yayi cikin tsokana yafara waqa "Taji tsoro abata ruwan mad'aci ta kuskure..." Kwa6e fuska tayi cikin shagwa6a tareda juyawa zata tafi tana cewa "Wlh yaya Sadeeq mun 6ata kuma baxamu shiryaba nan kusa" Wari idanu yayi ya biyota ganin tasa gudu. "Haba autas, tsaya mana" Amma harta haye. Dariya yayi sannan yajuyo suka hada ido da Ashraf daketa yimashi antayen Harara tundazu. Shima antayamashi nashi yayi sannan ya qaraso falon a kunyace ya zauna gefen Ashraf. Zamowa yayi Daga kujera ya tsugunna yana gaida Ummy. Amsawa tayi cikin fara'a tana tambayar Yasu mamanshi. Komawa yayi kan kujerar yana amsamata suna lfy. Nan fira ta 6arke don dama Sadeeq dan gidan Ummy ne, kusan Duk weekend dama yana zuwa gidan ya yini kamar yadda shima Ashraf ke zuwa gidansu, idan suka yini gidansu Ashraf ranar Saturday to gidansu Sadeeq zasu yini ran Sunday, idan kuma ran Saturday sun yini gidansu Sadeeq to ran Sunday gidansu Ashraf zasu yini. Wannan abota nasu na burge mutane musanmman su Ummy, don da wuya kaji Kansu, idanma sun 6ata saikiga babu mai sukuni acikinsu har saisun shirya. Hira suketayi gwanin sha'awa dama Sadeeq qaqa lafiyar giwa? Ashraf kau takaici ya rufeshi sai zungurin Sadeeq yake kan yafadi abinda yakawosu Amma yayi banza dashi kamar bejin zungurin, dariya fall ranshi. Dadai Ashraf yaga abin nashi rainin hankali ne saiyayi Fushi ya tashi yana cewa Ummy zai shigo, a fito lafiya tayimashi sannan yayi gaba kamar zai tashi sama. Dariya Sadeeq yayi yana girgiza kai saida ya sake 6ata kusan mintuna talatin sannan yacema Ummy bari shima ya haura. Izuwa yanzu saura kadan Ashraf yayi bindiga. Da sallama Sadeeq yashiga yana qumshe dariya. Ashraf dake rigingine kan gado kafaffunshi zube qasa yayi saurin tashi kamar Wanda aka tsikara, "Get out dan ubanka!" Waro idanu Sadeeq yayi sannan ya dan dafe kai "Ohni wannan uban nawa na shan zafi wajenka" "Nace out!" "Sai kazo ka fiddani din, ba'a fita yafada yana riqe qugu yana girgiza kamar dan daudu. Tasowa Ashraf yayi yana nad'e hannun Riga yana cewa " wlh koka fita ko in fiddaka" Cikin girgiza Sadeeq yace "Fiddani din" Nan suka hau kokowa, sai Ashraf takaishi bakin kofa dakyar sai yakuma zille yadawo ciki dagudu, shikuma bazai haqura ba, yana nishi yana komai zai sake maidoshi bakin kofa saikuma yasake zillewa yadawo yana kyakyatamashi dariya. Babu abinda ke tashi dakin sai nishi da dariyar Sadeeq. Ganin babu sarki sai Allah yasa Ashraf haqura yawani laftashi kan kujera yamike yana haqi "Shege.. Rusheshen banza" Dariya Sadeeq keyi sosai "Naji raggo ajeebo kawai, d'an ni dinne bazaka iya fiddawaba? Shame!!" Tsaki yaja yawuce bedroom dinshi yana gunguni. Shidai Sadeeq saida yagama dariyarshi sannan ya tashi ya shiga bedroom din yaga Ashe wanka yashiga. "Woo yaji maza dole yaje ya watsa koko juye akeyi oho?" Ashraf dake jinshi yaja tsaki kawai. Sai Bayan kusan 20mins Ashraf yafito yana tsane jiki fuska a tamke. Ganin Sadeeq na lasta mashi laptop yasa yaje ya kwace yana mashi mugun kallo "Bi sannu kar towel din ya kunce inshiga uku, ca6! Dakau Saudart saita daure ni" Tsaki yaja yana ajiye laptop din kan mirror. "Get out zan shirya" "Yo ai hikenan" inji Sadeeq shima yana Fadawa bandakin. Koda yafito Ashraf harya bar bedroom din. Bude closet din Ashraf yayi yaza6i wasu qananun kaya yasaka sannan yafito ya iske Ashraf falo yana kur6ar coffee. Shima hada coffeen yayi yazo ya zauna kusadashi yana kur6a. "Wai dude Duk hade haden rannan Duk na menene?" Banza yayi dashi "Kaji?" "Please ka kyaleni Sadeeq, please" "Haba aminin, kayi hqr ka gayamin, please" Harara ya antayamashi. "Dan ubanka ya mukayi dakai?" "Name fa?" "Bansaniba" "Wohoho, please ka gayamin mana, idan Nasani zan nuna ban sani bane" "Na nawa kuma? D'an rainin sense kawai" "Naji, yi hqr ka gayamin" "Mtcheew, batun damn contract marriage din mana, ya mukayi dakai, ba cewa nayi ka gayama Ummy ba?" "Sannu😒 niga rasa kunya kazar birni ko?" "Au bazaka fada mataba?" "Ni zan aureta? Kaji qarfin hali" "Ok, sai kaje kacema wannan tsohon banzan ya dawomin da kudina nafasa" "Wannan kuma ake kira impossible tense, ka lashe" Shaqoshi yayi "Dan ubanka ina wasa dakai?" "A'a..A'a, yi hqr, bari mufita zan gayamata, Shikenan?" Sakinshi yayi yana Harara "Idiot" Shima harararshi yayi. "Expired element". ***************************************** " Ina jinka Sadeeq" Sosa qeya yasakeyi sannan yace "Ehmm dama..dama.." Takaici kamar Ashraf yayi me? Jibeshi kamar wani na Allah. "Sadeeq Wai ya haka? Menene Wai?" "Ummy dama Ashraf ne... Ehm...yakeson..ehm.. Atura...ehm atura gidansu Saudart" Ya qarasa zancen yana susar qeya. Sunkuyar dakai Ashraf yayi cikin kunya da takaicin Sadeeq, kai Sadeeq mumu ne, haka ake magana? Aikau zaici ubanshi. Murmushi Ummy tasaki cikin jindadi "A'a Masha Allah, shine kuke wani sinne sinne Tun dazun? Kai alhamdulilah, aikau zan aika Ayi magana da kawunanka insha Allah, Allah yayi muku albarka" Sadeeq cikin qara sinne kai da sigar Neman magana yace "Amin Ummy, Wai kuma yace kar asa da nisa. In so samune..." Wani dundu Ashraf yakai mashi abaya Wanda ya hanashi qarasawa. Tashi Sadeeq yayi cikin dariya yagudu sama ganin Ashraf na niyyar kaimashi wani dukan. Shima Ashraf maramashi baya yayi sukayi sama. Dariya sosai Ummy keyimusu, abotarsu na burgeta sosai. Tashi tayi don ta dauko wayarta takira kawunnanshi don sanar dasu wannan abun farincikin...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 023 Kan kace me? Har maganar Neman auran A.A ya zagaye family, Masu murna nayi, yan baqin ciki nayi, Masu Kishi nayi. Nan da nan kawunnan sukayi bincike akan Saudart kuma suka sami gamshashen sakamako. Cikin dan qanqanin lokaci aka fidda ranar da zasuje Neman auran Saudart. Alhaji shamsu baki har kunne dayaji wannan daddadan labarin. Shirye shiryen tarbar manyan baqi yake kamar zai tarbi sarakuna. Sai rawar kafa yake, burinshi ya burge ahalin A.A Alhaji shamsu har office yaje ya tadda mijin mamy ya fadamashi abinda ake ciki don yanaso ya kasance harda dangin uwar Saudart wajen. Sosai mijin mamy yaji dadi itama mamyn haka don haka itama ta sanarda danginta aka samu mutum daya sai Abba (wato mijin mamyn). Saudart kwata kwata batasan wainar da'ake toyawaba, sai ranar Daren zuwansu wato asabar taja kamar daddy nacikin busy sosai. Koda ta tambayeshi ce matayayi baqi zaiyi gobe. Bata kawo komai aranta ba tace Allah yakawosu lfy. Ranar lahadi kamar yadda tasaba tana gama abinda take Tawuce gidan mamynta. Nan suka hade da qannenta aka bude chafter fira, sunata bata labarin Maiduguri, dakuma tsarabar dasuka samo. Itadai mamy sai binta take da kallo tanajin dadi at last Saudart zatayi aure, burin kowacce mahaifiya kenan idan diyarta takai minzalin aure to tayi. Dukda Saudart ta lura da kallon datake mata saita share tacigaba da biyewa su Abdul. A Bangaren su alhaji Shamsu kuwa, tarbar mutunci sukayima dangin A.A, sosai ahalin suka shiga ran dangin A.A saboda karamcinsu, Bayan anci ansha anyi wasa da dariya nan suka bada kudin mungani munaso, sosai adadin kudin yakusan rikitasu da farko sukaqi amsa saida aka Kai ruwa rana sannan suka amsa nan take aka tsaida ranar biki, nan da wata daya. Taro ya watse lafiya, Alhaji shamsu sai godiya yakema su Abba da abokanshi daya gayyato nan suma suka Kama gabansu kowa zuciya fall da murna. Zaune suke Saudart na karanta musu wani story book na yara. Duk sun zuba mata idanu kamar TV basusan ko motsawa tayi saboda yadda labarin ya dauko dadi, cikin nutsuwa take Masu karantun cikin lafiyayyen turancinta ga yadda take acting kamar itace don da anzo inda mayya ke magana saita qarama muryarta girma takoma naban tsoro, da anzo inda diyar sarki zatayi magana sai ta maqe murya, da anzo wajen kuka saita kwa6e fuska tana magana cikin muryar kuka. Hakan yasa labarin kemusu dadi sosai kowa ya maida hankali yana sauraronta harda mamy dake zaune kan kujera tana saqar hannu. Sallamar Abba ne ya katsesu, dukkansu dagowa sukayi suna amsa sallamar Saidai sa6anin da dasuke rugawa su rungumeshi yau kowa Daga inda yake zaune yake aikamashi sannu da zuwa don basusan abinda zai katse musu story din. "To? Yau ba tarba? Wato antynku tazo anbar yayina ko?" Dariya sukasa gabadaya harda Saudart. "Abba sannu da dawowa" inji Saudart "Yauwa daughter, ya weekend?" "Alhamdulilah Abba" "Oya kutashi mutafi sama, oya oya get up" tafada tana zungurin qeyarsu don suba su mamy waje. "Saudart idan kin kaisu kidawo muyi magana" Dukda gabanta yadan fadi saitayi murmushi tace "to Abba" Sannan ta tisasu gaba suka haye sama. Aminullah dake sama dama don acewarshi baya shiga cikin yara Wai karsu rainashi. Yana ganinsu yamiqe zaune yana hade rai. "Anty lafiya naga kun dawo nan?" Harara ta dalla mashi "Lafiyar ce takawo hakan" "Haba anty ni dan Allah Ku chanza room wadannan yaran damuna zasuyi da hayaniya" yafada yana gallama su Abdul Harara "Sannu babba, wlh Saidai kai ka chanza room. Ace mutum kwata kwata beson qannenshi su ra6eshi? Kuma wlh karka saki ka ta6asu. Ka ta6asu nida Kaine" ta gallamashi Harara sannan tafice. Afalo ta taddasu da alama suna cikin farinciki don fuskarsu Duk a washe suke. Qarasowa tayi ta zauna qasa dan nesa dasu. "Qaraso nan daughter" A kunyace ta qaraso kusadashi tana sinne kai. "Masha Allah, Alhamdulilah. Babu abinda zamuyi a wannan lokacin sai godewa Allah, dakuma fatan Allah ya sanya alhairi acikin lamarin. Allah ya tabbatar da alhairi kuma yasa abokan rayuwane Ku har mutuwa ta raba" Kan Saudart ya kulle sosai don tarasa inda batunshi ya dosa. Nasiha sosai Abba yayimata mai kashe jiki mamy ma ta Dora da nata, sai Daga baya taji Abban nacewa ansa biki, waikuma bikinta da A.A ban da wata daya kacal. Diff.. Wutar Saudart ta dauke, tashin hankali wanda bata ta6a tunanin zata shigeshiba tashiga, Aure? AUREN KWANGILA? kenan ya tabbata AUREN KWANGILA zatayi? Kenan ya tabbata A A din zata aura. Zufa yaita qetomata Daga inda take zaune. Gabanta banda bugun uku uku babu abunda yake. Sudai su mamy basu wani luraba, koda suka gama mata nasihar suka sassamata albarka sai suka sallameta. Ahankali ta nufi stairs idanunta na kawo ruwa. Haka taita takawa ahankali har takai sama dakyar tashige wani dakin da babu kowa ciki ta fada kan gado tana lumshe idanu Wanda hakan yaba hawayen idanunta damar gangarowa. Maido kallonta mamy tayi kan Abba dake kallonta itama adorably. Rungumeshi tayi cikin farinciki shima ya qanqameta. Saida ya dagota yaga Ashe hawaye take. "Subhanalillah Rahma ya haka" Share hawayen tayi tana murmushi "Abbansu. Am very happy, words can't express my happiness, Wai yau diyata aka sama biki?" "Saiki godewa Allah kuma azo afara shirye shirye don wannan biki da alama na manyane" Dariya sukasa gabadaya nan mamy taita kiran yan uwa da abokan arziqi tana fadamusu shima Abba hakan take awajenshi don Saudart yarinya ce yar gata mai shiga ran jama'a koda yini daya tayi dasu. Duk Wanda aka gayamawa sai yayi farinciki musanmman idan sukaji Wanda zata aura don aganinsu sun dace dajuna sosai. A bangaren oga Alhaji shamsu hakan take, don tuni yafara yagama shelar sa bikin ga abokan kasuwancinshi da kuma abokan arziqi. Nan suma sukaita tayashi murna suna mai fatan alhairi. A bangaren baby kau labari nakai mata ta danna wani uban ihu tana tsalle. "At last! At long last!!". Duk Wanda yaganta zaiyi zaton Murnar auren take Saidai ita Murnar nata kashi biyune na farko yayanta zai auri balarabiya kyakyawa mai kirki na biyu zai tafi yabar mata gidan ta wala ta Shana son ranta. Dagudu ta haye sama ta lalubo wayanta ta dannama Saudart kira. Saudart kau kuka take hurjanjan tana tunanin makomarta, ringing din wayarta yasata dan tsagaitawa ta kalli wayar, ganin mai kiranta yasata Jan tsaki ta kashe wayar gabadaya tayi cilli daita. Ganin bata dagaba harta tsinke yasata sake bugawa nan taji switch off. " Tofah? Halan kunyata takeji" tafada tana ta6e baki. Datarta ta bude tahau direct Tawuce group din CLASSIC LADIES tayi breaking din news din, zokuga hauka wajensu teema sai kakkafi suke suna kicihi suna fadin yadda bikin zaizama one in town, sukau team Suzy ana la6e Saidai su karanta massages dinsu Amma anrasa wacce zata fito ta tanka. Suzy kau hauka tuburan tafara dataji labarin sa auren, sai kurma ashar take dana Zage Zage. Beebah ta dannama kira tana dauka tahau masifeta, ta inda take shiga batanan take fitaba, beebah taita kwantar mata da hankali akan tabari Allah yakaisu gobe har bakery dinta zasuje su tisiyeta. Dakyar tasamu ta lalla6ata harta haqura Saidai zuciyarta uwa ana hura garwashi...✍ More comments, more post. Gaskiya aqara flow din comments sunyi kadan. Aqara ko in nad'e hannu😏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 024 Mu leqa hajji A.A😕 Kwance yake kan gadon dake dakin Sadeeq, ya wani rigingine yayi matashin kai da hannayenshi idanunshi a lumshe, Kai ka zata barci yake Amma idanunshi biyu hasalima sauraron Sadeeq daketa waya da abokanansu yana gayamusu sa biki yake. Ya kusan mintuna talatin yana Abu guda, sai bugama mutane waya yake kai kace bikinshine akasa. Ajiye wayar yayi Bayan yagama sannan yazo gefen Ashraf dake kwance haryanzu ya d'ad'a mashi bugu a cinya. Bude idanu yayi bashiri ya tashi zaune. "Kutt.. Dan ubanka ni ka daka?" Inji Ashraf yana kaimashi bugu shima. Dojewa Sadeeq yayi yana dariya. "Dan ubanka ka barni sai qone credit dina nake wajen kiran mutane Bayan Kaine ka cancanta kayi hakan" "Mtcheew, waya saka? Meye na wani shela a auren da atattashi yan wattanni? Mtcheew ni wlh ba haka naso abin ya kasance ba, banaso kowa yasan da bikin saisu Ummy, suma dan dolene Amma dayake kai dan iska ne shine ka 6atamun tsari Tun a gathering" ya qarashe zancen yana lafta mashi Harara. Ta6e baki Sadeeq yayi wanda tunda Ashraf yafara magana hankalinshi na kan waya. "Yanzu dai yaushe zamu fara hado lefe? Ga wasu kayanan an turomin sunada kyau, Kaga saimu fara dasu ko? Kalla kagani" Wani kallo Ashraf ke binshi dashi "Are you kidding me? Wa zanma lefen? You're mad" "Haba Ashraf, auren A.A sunkutukum ace babu lefe, me kakeson mutane suyi tunani akai?" "Whatever Sadeeq, whatever, I don't care, suje suce koma menene abinda Nasani shine bazanyi wasting din kudinaba akan auren da ba dorarreba" ya qarashe zancen yana juyamishi baya. Ta6e baki Sadeeq yayi kawai shima ya maida hankalinshi kan wayar hannunshi. Sai can da magriba Saudart takoma gida, Duk tayi suku suku daita, ga zazza6in dake Neman cin galaba akanta. Dakyar tayi parking tafito, tafara tafiya ahankali zuwa cikin gidan. A falo ta tadda daddy sai waya yake, saida ta saurara dakyau tagane order Kayan furniture yake badawa. Ganinta dayayi yasashi ware mata hannu daya. Dagudu ta qarasa wajenshi ta rungumeshi tana sakin kuka. "Ok, hang on, I'll call you later" Katse wayar yayi ya ajiye sannan yaqara jawota jikinshi yana rarrashi. Jin jikinta yadau zafi yasa hankalinshi tashi. "Subhanalillah, shalele? Zazza6i kike?" Cikin muryar kuka tace "Dad, dama aurena za'asa shine Baka damu da ka sanar daniba?" "Am sorry shalele, kiyi hqr kinji?" "Dad yanzu kenan dole saina aureshi? Daddy AUREN KWANGILA? Dad ni zanyi auren yan wattani?" Saikuma tafashe da kuka. Tausayinta ne Yakama Alhaji shamsu Amma daya tuna dinbin alhairin dazai samu sai ya kawar da tausayin. "Shalele ta, akwai dinbin alhairi a wannan auren, am telling you zaki godemin watarana" Kukanta kawai tacigaba dayi don ita bata wani hango alhairi a wannan lamari. Dakyar yasamu ya rarrasheta ya kaita har daki ya 6allamata magani tasha sannan ya rufeta da bargo yajamata kofa. Haka taita juyi a gado gashi tanason tayi barci Amma barcin yaqi zuwa, ganin hakan yasata miqe wa ta dauro alwalla tayi nafila raqa'a biyu ta Dora da karatun Al qur'ani mai girma har barci barawo ya saceta kan sallayar. WASHEGARI babu laifi izuwa yanzu tadanji sauqin zuciyarta. Daily routine dinta tayi sannan tayi wanka ta shirya cikin wata Arabian gown mai shigen bubu kalar maroon mai adon golden stones. Saita yafa gyalen rigar in a simple way. Yaukam an danyi kwalliya dob harda jambaki maroon aka gogama le6e. Fitowa tayi cikin nutsuwa ta tako qasa, a falo taga daddynta tsaye yana daura agogo da alama shima fita zaiyi. Murmushi tayi ta qaraso wajenshi a sanyaye. "Daddy na" tafada a shagwa6e "Na'am shalele ta, kai Amma fa kinyi kyau " Kai daddy, ina kwana? " "Lfy lau shalele, ya jikin?" "Jiki alhamdulilah daddy, as you can see, bakery ma zani" "To dakyau, yanzu muje na rakaki motarki ko?" Qara shagwa6e fuska tayi "Uhm uhm daddy, Nidai kai zaka kaini" "Tofah, yau kice rigima akeji, to muje, anything for my princess" Dariya tayi sannan suka fito hannunta cikin Nashi. Budemata kofa yayi yana dan sunkuyawa dramatically "Get in Mi princess" Dariya tayi sannan tashiga, shima ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya tada motar suka fice. Sosai Saudart taware sai fira suke suna dariya har suka iso bakeryn. Har ciki ya rakata yana zagaya bakery din yana yaba cigaban da'aka samu sannan Daga bisani yaimata sallama ya kama gabanshi. Dukda haryanzu tanajin dan damuwa a cikin zuciyarta haka ta danne ta Zage tanata aikinta kamar koda yaushe. 3:00pm Maryam ce tashigo office din fuska babu walwala tac gaida Saudart. "Lfy lau...wani Abu?" "Yes ma'am, kinyi baqi" tafada still fuskarta cunkushe. Dukda taga yanayin fuskarta saita basar don bata cika son shishigiba. "Ok ashigo dasu" Bayan yan sakonni kofar tasake budewa suka shigo. Dagowa tayi don ganin su waye baqin. Yanmata biyu tagani dukkansu babu mai shigar arziqi cikinsu. Ta farkon Suzy sanye take cikin wata armless top sky blue mai fidda sura sai baqin straight skirt wanda yasha tsaga Daga qasa har zuwa cinya kanta sanye da hula baqa Wanda Rabin kai tarufe hakan zai Baka damar hangen gashin dokin data qarama kai, ga wani qaton Google data kwamama idanu Wanda ya rufe kusan Rabin fuskar. Habeeba kau sanye take da crazy jeans sai wata Riga mai kamada shimi fara saita Dora yar ficikar jacket sama kalar wandon Itakau kan ko arziqin hular besamuba. Sunci uwar kwalliya an fente fuskar kamar aljannu. Binsu taitayi da kallo kafin Daga bisani tayi musu murmushin nan nata mai tafiya da mutane. "Sannunku please have a seat" tafada cikin faran faran. Kallon juna sukayi suna kya6e baki. "Please Ku zauna, maryam a aiko da Kayan motsa baki" "No need, ba wannan ya kawomu ba, magana ce ta fatar baki ta kawomu muyi mu fice Tun kafin numfashi ya gagaremu a wannan garbage din" inji beebah Suzy kau tunda ta Dora idanu akan Saudart jikinta yayi Sanyi sbd tama wuce yadda take ganinta a pics ga wani nutsuwa da kwarjini da Allah yaimata. Nan take kishinta yaqara ninkuwa a zuciyarta wata Wutar qiyayyarta na sake ruruwa. Dukda bataji dadin amsarsu ba sai bata nunaba ta wayance tana cewa "Ok, how may I help you?" "Help who?" Inji beebah tana aikamata kallon raini. "Baki kai matsayin da zamu nemi taimakon ki ba, we came here ne sbd muja kunnenki for your own good, ki fitar harkarmu don bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane" Shiru Saudart tayi tana kallonta don ita tunda take bata ta6ama ganin fuskoki Masu Kama da wadannan ba bare wani Abu ya hadasu, to kodai 6atan kai sukayi? On the other side kuma maryam ce Wanda dama bata fitaba, sai huci take qasa qasa don dama saida sukayi rashin mutunci kafin su shigo mafarin shigowartama kenan fuska a cunkushe. "Amm.. Excuse me, gaskiya inajin 6atan hanya kukai don ni gaskiya banma ta6a ganin fuskarku ba sai yau" Wani makirin murmushi mai sauti Suzy tayi sannan ta qaraso tana Jawo kujerar dake facing din Saudart ta zauna tana Dora kafa daya bisa daya Wanda hakan yaba cinyarta damar fitowa gabadaya. "Really? Are you sure baki ta6a ganin fuskar mu ba? More especially ni? Kenan Darling din naki be fadamiki komai akainaba" Calculation tafarayi, Darling? Darling dina? Waye kenan? "Well, am A.A's girlfriend, his babe" ta qarashe zancen tana cire Google din idanunta tana juyi da idanun tana kalkadasu a duniyance. Wani murmushi ya kufcema Saudart, lallai iska na wahalar da mai Kayan kara, tofa Ashe dama yanada budurwa, lallai aikau sunyi matching. Itama cikin duniyanci tadan Waro idanu "Wow! Ashe anty ce? You're highly welcome, Aida kinfada tunfarko, Saidai how come baby boo na beta6a bani labarin ki ba, you're welcome please maryam akawoma anty abin ta6awa" Wani qululune ya Tsayawa Suzy a wuya, baby boo? Lallai. Beebah dake tsaye haryanzu ta bata amsa. "Ba abun mammaki bane idan baby boo din naki be ta6a baki labarinta ba, kinga kenan yaudararki yake, Bayan ke yanada wata kuma 6oyemiki dayake ya nuna ba sonkiba yake, playing dinki yake" tafada cikin son cusamata Kishi. Wata yar siririyar dariya Saudart tasaki tanayin luuu da idanu sannan takuma budesu, Wanda Duk saida suka saki baki suna kallonta don abin ba qaramin kyau yaimata ba. "Dani da ita wa yake yaudara? Look" tafada tana nunamusu zoben hannunta Wanda yasamata Tun ranar datayi signing din contract din. "Shiya sakamun zube a gwiwowinsa yana roqona na aureshi, secondly ya nunani wa jama'a and am quite sure kuma labari yajemuku and lastly maganar danake muku haka akwai baikonshi akaina, yanzu wa yake yaudara? Waye main chick a cikinmu kuma waye side chick? Look it normal saurayi yayi budurwa samada goma, what matters is wa yakeso kuma yakebi Amma ba Wanda ke sonshi kuma take binshi ba, he's my fiancée kekuma he is your boyfriend ko makaho ya laluba yasan akwai banbanci a tsakanin sunayennan biyu, so zan baki shawara kafin kice ko kuce zaku yanke hukunci Ku fara auna abin a mizani Ku fara tantance matsayinku sannan kuyi bursting, ok?" Tsit kakejin office din, Wutar su gabadaya ta dauke, maryam dake baya tundazu kamar taita rawar zanku don murna. A afusace Suzy ta miqe tsaye tana bugun saman table din da karfi sannan ta nunata da yatsa "Who the fuck did you think you are? Ehh? Kinsan koni wacece? Ehh? Kinsan koni diyar wanene?!" "Ta yaya za'ayi in sani? Bayan a fuskama sai yau nafara saninki? Wacece ke din? Diyar wacece? Diyar bill gate? Ko mangal? Ko dangote? Please ki Sanar dani Atleast sai nayi keeping record kan na ta6a Kasa diyar wani shege a fagen love" tafada tana murmushi. Kutt... Nufota tayi gadan gadan beebah tayi saurin tareta. "Easy, easy Suzy, ki barta just calm down ba girmanki bane.." "Ato, gayamata dai don da alama tayi nisa batajin kira, be kamata tana irin wannan abun yaranba inhar tanaso a taimaka a karata" Wani kallo beebah ta watsa mata "You'll definitely regret this, and also ruwan kine ki fita harkar A.A ruwanki ne karki fita, Amma a shawarce zaifi miki kwanciyar hankali kifita harkarshi for your own good, if not..." Saita saki murmushi tana kada kai. "If not?.." Inji Saudart tana langwa6e kai tana wani jujjuyawa saman kujera. Matsowa beebah tayi gab da ita tana dafa table din da hannaye biyu tadan sunkuyo cikin rada tace "If not Daga ke har almajirin babanki sai kunyi danasanin zuwanku duniya.. Have a nice day" Ta qarashe zancen tana kalkadamata yatsu sannan ta kama hannun Suzy tajata suka fice. Binsu da kallo tayi har suka fice sannan ta saki wani murmushin takaici. 'Dad Kaga abinda kaja ko? Kaga abinda kwadayinka yaja mana ko?' Duk acikin zuciya take wannan zancen. Jingina tayi da kujerar tacigaba da juyawa ta maida idanunta ta lumshe, zuciyarta fall da baqinciki. Ganin haka yasa maryam lallabawa ta fice ta jamata kofa zuciyarta fall da tausayin ogansu...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu. Wayyo fans, nayi missing dinku irin totally dinnan☹, kwana biyu kunjini shiru wlh hidimace ta tisoni gaba, ban samu kainaba sai yau. Masu bugomun waya donjin ko lfy da Masu cigiyata a group, ina godiya da kulawarku agareni. Ashaanty na yinku irin totally dinnan😍 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 025 Wasa wasa ranakun sai tafiya suke, dukkan 6angarorin wato na Saudart da Ashraf sun Shiga busy. Su Ummy an dage wajen hada lefe na gani na fada, donma wannan coronar tahana fita waje da acan za'ayi sayayar Amma dukda hakan kayane ba gani na fada wanda kallo daya zakayi musu kasan anci uban naira. 6angaren daddy ma ba'a barshi abayaba don Kayan daki haddadu kayattatu yayi ordering har set biyu. Ga shima ya hada mata nashi lefen na musanmman abinka da mai irin sana'ar. Set daya na akwati wato akwati shidda maqare da kaya Nagani na fada yayima shalelenshi. Niko nace anya be manta cewa auren na dan taqaittacen lokaci bane🤔 Bangaren mamy ma ba wasa, Kayan kitchen na musanmman take hadama angel dinta, abinka da ita kadai ce diyarta mace, Duk burin duniya ta Dora akan auren diyarta, sosai naira tayi kuka wajen hada Kayan kitchen din, shima Abba wato mijin mamy ba'a barshi abaya ba don dangin electronics wato su plasma, generator, deep freezer, ovens e.t.c Duk shi yayi mata, abin dai zai😉 Su dangin mamy da Abba suma ba'a barsu abayaba don sosai suka bada gudunmawa dukda yanzu bawai kudi ke akwai sosai ba. Sosai suke son Saudart saboda kirkinta da zumunci ga uwa uba girmama na gaba da son mutane. Ataqaice dai kallo daya zakayima hidimar bikin kasan na yan gatane, yan gaban goshi kuma Duk wannan haukan da'ake Daga amaryar har angon babu wanda yasan Anayi. Kowa harkar gabanshi yake hankali kwance. Don wani sa'in har mancewa da wani aure suke. Bikin na sauran sati biyu mamy ta buqaci Saudart tadawo gurinta har zuwa bikin. Alhaji shamsu be hanaba haka itama Saudart dadi taji sosai koba komai zata rage zaman kadaici tunda ga su Abdul. Saida taje sannan tasan manufar mamyn na dawowarta nan, wato gyarata mamy zatayi ciki da bai. Da farko taso qin yarda da Gyaran Amma da mamy ta tambayeta dalili Kasa amsawa tayi Dole t hqr ba don tasoba aka fara gyarata wasan zuciyarta kuma tasan asarar kudi kawai ake, Auren da na yan wattani ne? Gyara sosai akema Saudart, abinka da yan Maiduguri. Cikin yan kwanaki Saudart tafara riqidewa, ga dama yaya lfy giwa, dama can mai kyauce kuma tana bama fatarta muhinmmanci sosai take sheqi Amma yanzu tafi sheqi sbd dilkan da'ake mata ta musanmman. Hakan a 6angaren Kayan mata da maganin Sanyi Duk ba'a barta abayaba. Ingattatun Kayan mata da aka hada da fruits ake bata, ga yawan shan farfesu da ake sata tayi, gashi yanzu batada abinsha sai tattaciyar madara ko kindirmo. Haka a bangaren lectures gameda auratayya, sosai mamy ta cire kunya ta zauna ta nusar da Saudart abubuwan da batasaniba gameda aure, tana kuma koyarda ita dubarun zama da miji, abinda wasu iyayen mata yanzu basu iyawa Wai kunya, qarshen kunya dai shine ki Tisa diyarki gaba ki bata Kayan mata, tunda itama tasan me kike bata da kuma amfaninsu tunda yanzu kai ya waye, a wajen karance karancennan ma wata Duk tasan komai. So iyaye mata ba'a maganin mata kawai yakamata mu tsaya ba, mu nusar dasu miye auren da kuma abubuwan dasuka qumsa don dayawa yanmatan mu basusan ainahin menene auren ba sundai san in anyi aure ana tarraya tsakanin miji da mata, Amma basusan yadda zasu kula da mazajensuba dadai sauransu don ba'a koyamusu ba, Abu daya kawai aka koyamusu shine shan Kayan mata sai kiji har akwai mai suna, mallake miji, bita zai zai dade sauransu. Babu abunda zaisa ki mallake miji yadawo tafin hannunki kamar biyyaya da tsantsan kyautatawa tunda zuciya tana matuqar qaunar mai kyautatamata. Duk Kayan matan dazaki dirqa a banza don wasu sai sunason harkar zasu mutuntaka daka basu sun gama nan take suna iya sufkama rashin mutunci, Amma mace mai biyyaya da kyautatawa bazata ta6a wulaqanta ba awajen mijinta. Tun Saudart najin kunyar mamy idan tafara mata ire iren lectures dinnan harta Bari don mamy ba ruwanta. Su Abdul baseet sunji dadin dawowar Saudart gidan don sosai take debe musu kewa. **************************************************** "What?! 5 million? 5million? Kam bala'i? Lallai kana wasa da wuta" Afusace ya miqe ya nufi hanyar waje ko Dora suit dinshi dake rataye beyiba. Kwankwasawa yayi a afusace ya murda ya bude batareda yajira anmashi isoba. Dagowa Sadeeq yayi yana kallonshi sai huci yake kamar mayunwacin zaki. "Toha, lfy ango kasha qamshi? Wannan dirar mikiya haka? Ai sai Kasa in arci na dog" "Sadeeq ina wasa dakai?" Yafada cikin Fushi "Ehh" yabashi amsa hankali kwance. "Dan ubanka Kalla, Kalla nace" yafada yana shaqoshi yana nunamishi screen din wayar shi. "To ai ta dauke mallam, Wai ya haka? Ka sakarmin wuya" Sake Kunna wayar Ashraf yayi sannan yaqara haska mishi "Ubanmi aka rubuta?" Injishi yana huci "Anyi withdrawing 5million" Sadeeq ya amsa yana matse idanu sbd shaqarar da Ashraf yayimashi. "Dan ubanka me kayiman da kudi har 5million? Daga cewa za'ayi project saika zaremin 5million? Dan ubanka ina project din?" "T...to ka sakeni mana in amsa" Sakinshi yayi yana galla mashi Harara. "Aradu badan Kai ango bane daka gane kurenka, mugu kawai" "Naji, ina kudina?" "Na cinyesu nikam, Haba!" "Kasan Allah saika fadamin uwar ne kayi dasu" "Mtcheew, banza to na cire naqara wajen hidimominka, Shikenan?" "Wane hidima!" "Bansaniba! Mtcheew dalla ficemin office aiki nake" Shaqoshi yaqarayi "Kasan Allah? Saika fadamin" "Mtcheew to cikani" Sakinshi yayi yana huci. "Dan ubanka nufinka su mamy zasuyi maka komai? Nabasu 3million suqara wajen hada lefe kingin kuma zan bugo I.v sai aba Amarya kingin as pocket money, saima ka qaro wata 5million din don akwai events daza'ayi kuma munada buqatar money, real money" Galala Ashraf yayi yana kallonshi tunda yafara mgn har yakai aya. "Wai tsaya, come again, kana nufin da kudadena akayi wadannan abubuwan?" "To da danawa? Bakada hankali, to Bari kaji jiya munyi mgn da qawar Amarya basu shirya wani event ba sai walima ta mata wanda zasuyi a bangarenmu kuma Ummy naji tace zasuyi mother's eve, Kaga kenan Kowanne bangare zaiyi nashi to Bayan daurin aure sai Ayi dinner gabadaya kafin ka shilla da amaryarka" Ya karasa zancen yana kashe mashi ido daya😉 "Kaga dole mu basu enough money dazasuyi hidimar walimar hankali kwance, so please we need another 5million" Kutt.. Kasama magana Ashraf yayi na wucen gadi. Sai Daga bisani ya tashi yanufi kofa "Kuma wlh kafara biyan bashi kenan Tun Daga wannan watan, saika biyani kudina don bazanyi asaraba wlh" Dariya Sadeeq ya fashe dashi yana cewa "Ba komai, yanzu yaushe za'a qaramana 5million din?" ,"kazo ka qwata don ubanka " Yafada yana ficewa cikin Fushi. *****************************""""' "Wai Ashraf meke damunka ne? Sbd kawai zakaje ganin amaryar ka saika wani dinga jamana tsaki kamar wata tsaka? Aida Tun acan kace Baka zuwa bawai kazo nan ka cikani da tsuwaba" "You know what Sadeeq, wlh idan Baka fita harkataba zan mugu mugun sa6amaka, munafiki Kasa bansan Kaine ka hada makalkashiyarba? Idiot dan sa idon kawai, wlh kaji haushi Sadeeq, banza mai zubin ifritai" "Naji mallam, hakan dai bazai hana kajeba, shure shure baya hana mutuwa, kayi sauri kana 6atamun time ko nafasa rakiyar, ehe" Takaici yaqara qume Ashraf, kwafa yayi yacigaba da shiryawarshi cikin 6ata lokaci dukdan yaba Sadeeq haushi Amma ko ajikinshi. Saida yagama feshe jikinshi da turarruka sannan ta Dora hular kube yawani kasheta a gaban goshi. "Kai kai Kai!! Kaga ango bada Lanka asare kaje gida kace yafadi, wannan gayu haka? Duk dan aaburge Amarya ne? Gaskiya Amarya saita rude idan taganka, Wai ja ganka kuwa" Tsaki yaja yafice yanacewa "Kasameni waje idan kagama haukan" "Yo ai hikenan" yafada yana maramashi baya. Saida sukayima Ummy bankwana, ta basu wata Leda Wai suba Saudart kuma tana gaisheta, Sadeeq ya amsa yayinda Ashraf harya kai waje. Binshi Sadeeq yayi da sauri yana cewa "To? Duk zumudin ganin amaryar ne haka, atleast kajirani mana tunda ko sanin gidan bakayiba, kuji qagarrare" Banza Ashraf yayi dashi ya shige mota, shima Sadeeq mazaunin driver yashiga yarufo sannan ya tada motar suka shilla...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Ka jiqan wadanda suka mutu sanadinta da dukkan musulmai da suka rigamu gidan gaskiya🤲 Ya Allah ka jabanci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 026 Zaune take ta tankwashe kafaffu sai shan farfesun da mamy tayimata take tana yatsina fuska. Murda kofar da'akayi aka shigo yasata saurin dagowa tana kallon kofar. Mamy ce tashigo tana murmushi. "Wai haryanzu baki cinyeba Angel?" Kwa6e fuska Saudart tayi tana turo baki "Mamy wlh babu dadi" "Mtcheew, shirmamma, Allah ya shiryaki yanzu tashi kidan watsa ki chanza kaya kuma kiyi sauri nabaki minti biyu" Da sauri ta tashi dama ba son sha takeba. Girgiza kai mamy tayi ta dauke bowl din farfesun ta fice. A gaggauce ta warwatsa ta fito ta saka wata yaloliyar Riga ta fada kan gado tana Jawo wayarta tana danne danne. Shigowar mamy yasake katseta. "A'a? Meye haka? Baqi fa gareki kinwani kwanta, common change to something decent kizo ki fice" "Baqi mamy? Su waye?" "Bansaniba" Tashi tayi ya chanza rigar jikinta da wata jallabiya jaa ta dora zumbulelliyar hijabi baqa akai wanda tsawonta yakai har idon qafa ta zura hannayen hijabin sannan tadan murza turare mai sanyin qamshi ta fito. A falo ta tarda mamy zaune. "Kiyi sauri dama kin 6atamusu lokaci, suna falon baqi, zan aiko Kamal da refreshment" "Tou mamy" tace tana ficewa tana tunanin ko suwaye baqin. Sallama tayi bakin kofar falon. Saida taji an amsa sannan ta sanyo kafa ahankali tashigo kai a qasa. Haka kawai taji gabanta yafadi batareda wani daliliba. Kallo daya tayimusu na second daya ta dauke kai, hakan yasa tasan su biyune Saidai bata gane kosu wayeba. "A'a? Gimbiya qaraso, lale sannu da fitowa sarauniya" Jin muryar sadeeq yasa gabanta sake faduwa, to? Dama yasan gidansu? Shida waye? Cikin nutsuwa ta isa kujerar dake facing dinsu ta zauna sai a sannan ta dago cikin nutsuwa ta kallesu. Idanunta ne suka sauka cikin ba Ashraf dake maqale da waya a Kunne alamun waya yake. Wani kallo ya watsamata wanda yasata saurin dauke idanu ta maidasu kan Sadeeq daketa yashe baki. "Sannunku dazuwa, ina wuni" Tafada cikin murmushi "Lfy qalau gimbiya, ya hidima?" Inji Sadeeq yana dan take qafar Ashraf a fakaice alamun yabar wayar hakanan mana. Yana jinshi yayi kamar besan abinda yakeba saima qara relaxing dayayi a kujera yana cigaba da amsa wayar shi cikin murya qasa qasa don ko Saudart batajin abinda yakecewa. "Alhamdulilah" tafada tana ta6e baki cikin zuciyarta tana cewa, Masu hidima dai yakamata kayima ya hidima ba niba. Kamaldeen yashigo da tray dake dauke da Kayan motsa baki da drinks da sallama a bakinsa. Amsawa sukayi suna kallonshi, Qarasowa yayi ya ajiye saman centre table din sannan ya gaidasu a ladabce Amsawa sadeeq yayi fuska asake while Ashraf yayi mashi murmushi kawai. Juyawa yayi ya fita. Shiru ne yadan ratsa falon. Ganin wayar Ashraf ta iskanci ne yasa sadeeq miqewa. "To Bari kuga yadda za'ayi"/yafada yana qarasawa centre table din ya dauki qaramin plate ya koda snacks ciki ya dauki robar hollandia daya yana cewa " Ato, bari nabaku wuri Ku soye, kunsan masoya basu cika son shishigiba" Yana kaiwanan ya fice ya koma garden ya zauna ka daya Daga cikin kujerun shaqatawa ya zauna, ya fara aika abinshi yana yi yana danne dannenshi a waya. Tsit falon yayi yasake yin wani irin shiru sai qarar ac da akeji saikuma muryar Ashraf da ake danji qasa qasa alamun haryanzu be gama wayarba. Itadai Saudart haryanzu kanta sunkuye yake don batama son sake kallonshi. Sai tambayar kanta dalilin zuwanshi gidansu take. Idan bata manta ba rabon data ganshi Tun wajen gathering, kusan wata daya kenan. Shikau dakyar yagama wayar don dama sungama maganar dasuke kawai qara Jan mutumin da magana yake don beson ko kalma daya ta hadasu da Saudart, sai gashi mutumin ya kawo excuse na zaiyi attending din wasu. Komawa yayi ya jingina da kujera yayi irin wannan shegen zaman dake bata haushi yacigaba da danne danne awaya. Tsaki taja a zuciyarta ji yadda yayi wani balancing kamar yana dakinshi. Shiru dakin ya dauka babu mai niyyar magana ita kanta qasa tana wasa da yatsunta, shima kanshi saman waya yana danne danne. Sun dade ahakan Amma babu wanda keda niyyar motsawa, dukda kowa ya gaji da zaman. Saudart Jitake kamar ta tashi tayi tafiyarta Amma ta hqr atleast gidansu ne, su kwana haka. Shima Ashraf da ba abinda yake awayar Saidai yashiga nan yashiga can jiyake kamar yabar dakin Amma jin kanshi yaqi bari don be iya ma tashi ya taka gabanta, Wai raini zai jamashi. Haka sukaita zama kowa da abinda yasha mashi kai, sunfi awa daya ahakan Amma still babu wanda jinkai yabari yayi magana. Yadda kasan kurame aka akai zaman. Sadeeq dadai yaji shirun yayi yawa kuma dare qarayi yake ya miqe yana daukar plate daya rage snacks yan kadan ya taho. Da sallama yashigo, ga mammakinshi yadda yabarsu haka ya taddasu. Ga Kayan motsa bakinda aka kawo musu ko alamar anta6asu be ganiba. Basarwa yayi ya qaraso yana murmushi "A'a romeo and Juliet, wannan soyewa haka, naga fira yayi dadi ko niyyar kirana bakuda shiyasa na dawo" Murmushi kawai Saudart tayi akunyace. "To mallam romeo mujeko? Ko anan zamu kwana?" Ta qasan idanu ya watsa mashi mugun kallo sannan ya miqe yana saka wayar shi aljihu sannan ya fiddo bundle din yan dubu dubu biyu ya ajiye saman table sannan yasa Kai yafice cikin takunshi ba qasaita. Binshi da kallo Sadeeq yayi yana qumshe dariya. 'Shege da Baka badaba dana haddasa bomb yau tsakaninka da Ummy, marowaci kawai' Duk a zuciya yayi wannan zancen. Shima tashi yayi ya Dora ledar da mamy tabasu shima da wrapper din #500 daya sannan yace "To amarsu zamu ruga qauyanmu" Da murmushi ta dago "Ayyah, to Allah ya tsare. Agaida gida" "Gida zaiji kwarai, mungode" Nan ya miqe sannan ya fice. Ajiyar zuciya tayi tana rolling dara daran idanunta. Miqewa tayi itama tafice Bayan ta daidaici sun tafi. A falo ta tarda mamy kamar dazu. Amsa sallamarta mamy tayi sannan ta Dora dacewa "Da harna fara shawarar zuwa kiranki, wannan zama haka?" Ta6e baki Saudart tadanyi sannan tace "Mamy Bari in hau" "To, asauko lfy" Ibrahim mamy tasa yaje ya kaikaye falon nan yadawo hannunshi dauke da Leda da kudaden da suka ajiye mata. Ganin kudaden yasa mamy dan zaro idanu "Wannan fa Ibrahim?" "Kan centre table nagansu" Amsa tayi tana jujjuya kudin sannan ta leqa ledar, Waro idanu tayi ganin abinda ke ciki, fiddosu tayi tana kallo, wasu haddadun turraruka ne hudu set, kallo data zakamasu kasan tsadaddune. "Kiramin Antyn taku" Da gudu ya haye sama itakuma ta cigaba da jujjuya Kayan hannunta. Bayan yan mintuna saiga Ibrahim tareda Saudart sun sauko. "Mamy gani" "Saudart wannan fa?" Sai lokacin ta tuna dasu don Duk taga sanda suka ajiye. Su suka kawo, ba ledar Wai mamansu ta aikomin. "Masha Allah, Amma kingode Amma kudin sunyi yawa da baki amsa ba" Ta6e baki tayi a fakaice sannan tace "Mamy ajiyewa fa yayi yawuce, bema saurareniba" "Dukda hakan, Amma kau kingode, ki tabbatar kin kirashi kinmashi godiya most especially mamanshin don wlh idan kikaji kudin perfumes dinnan saikin riqe baki" "Tou, zan kira" Tafada deep down tana cewa Basai inada number dinshi ba? Haka mamy taita santin Kayan kafin Daga bisani ta sallameta. Wayarta tajawo ta Kunna data tahau WhatsApp Kamar jira ake saiga message din baby na sticker din Daga hannu. 'Mayyar chatting' tafada cikin zuciyarta sannan itama ta tura mata sticker hyy. "Aunty Duk yau baki hauba" "Ni kece, kodayaushe kina online, ko wahala sub bakyaji" Sticker din dariya baby ta aikomata "Basai idan ni keyin sub dinma? Garori nake samu su cikamin waya da data" "Allah ya shiryaki to, please kiyimin godiya wajen Ummy" "Akan me?" "Ina ruwanki? Ji gulma" "Lol, kai anty Daga tambaya? Wai insan irin godiyar dazan matane" "Babu ruwanki, kawai kiyimin godiya nace" "To ko nabata kiyimata da kanki?" Sticker din kallon kin rainani ko ta turamata sannan ta tura "Ki kiyayeni baby" Sticker din dariya baby ta turamata sannan ta rubuta "Am sorry, zan gayamata, kuma Ku tanadarmin daki inanan tafe nanda kwana uku, saura sati biki kenan" "Tofah, kiyi me? Bayan ana biki gidanku" "Ai nanma gidanmu ne, idan dai ba son zuwana akeba" "A'a me yayi zafi? Allah yakawoki lfy, kice zanyi babban baquwa" "Kwarai kuwa don wlh ban zama nan lovely dinki yaita takurani babu gaida babu dalili, ya hanani rawar gaban hatsi" "Kanku akeji, nikam zan sauka" "To sauka lfy, sai kun ganni" Sauka tayi ta kashe datarta sannan takoma tayi lamo akan gado tana tunani. Wai yanzu dagaske aure za'ayi mata? Aure da wanda bataso kuma batajin zata ta6a sonshi? Auren da keda qayaddaden lokaci? Auren contract? Ajiyar zuciya tasaki nannauya tana fadin Allah gani gareka...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 027 Abu sai matsowa yake, dama Duk Nisan rana idan Kasa zuwa zayayi. Yau saura sati daya biki, gidan mamy yafara cika da Mutanen Maiduguri dama dangin Abba ma. Saudart yau tana cikin farinciki sosai saboda wasu cousin dinta dasuka zo wato Nafeesa da mardeeya. Qawayene sosai kuma yan uwa, Nafeesa diyar yayan mamy ce ita kuma mardeeya diyar kanwar mamy. Tunda suka qaraso gidan yaqara hargitsewa, ihun murna Saudart taitayi data gansu don batayi tunanin Tun yanzu zasu tahoba don ko jiya sunyi waya sunce sai ranar Daren biki zasuzo Ashe plan suka shirya dukdan subata surprise. Nanfa aka samu nayi tsokana kala kala babu wanda basuyi mataba, itama dayake bakin zaii yake kana mata fari zata maidama baqi, dama halinsu ne hakan, sunsaba. Itama mamy a bangarenta ba sauki don Mamman mardeeya wato qanwarta itama tazo da ita za'a cigaba da shirye shirye kasancewar dama su biyune mata a family dinsu kingin Duk mazane. Su shidda ne, maza hudu mata biyu. Yayyan mamy uku, kawu bala, kawu Mamman da kawu shehu, sai mamy sai maman mardeeya sai auta kawu Yusuf. Sosai suka hau hirar yaushe gamo sun wani baje a falo harda danginsu Abba don akwai kyakyawar alaqa tsakaninsu da mamy sosai, suna sonta sosai sbd kirkinta da faran faran dinta. Shigowa Saudart tayi daure da qaramin towel a qirjinta iyakarshi cinya. Ganin wayarta tayi hannun Nafeesa da alama bincike take mata. Da sauri ta qarasa ta fizge tana danqara mata Harara. "Uban me kikemin da waya?" Dariya sukayi harda mardeeya dake tsefe kitsonta don gobe zasu wankin kai. "Tofah, yaushe kika fara mana shamaki da wayarki?" Inji mardeeya tana taje inda ta tsefe "Ato, ganemin hanya sis, hegiya Dama sonike inga dame akayi saving din surukin namu, Amma da alama babu number shi a wayar don sau uku kenan ina scrolling babu suna mai kamada nashi ko a call log banga makamancin sunan masoyi ba" Harara Saudart Taqara lafta mata tana wucewa closet dinta tana cewa "Ato, an gayamaku kowama baqauyene irin Ku? Yanzu qauyancine saving din contract din masoyi, real love shine ka hardaceta aka, sbd ire irenku Masu snatching" Shewa suka dauka sannan suka kashe. "Inyee? Kunji masoya, Wai snatching, uban wa zanyi snatching Bayan inada mukhtar dina dan sardidi son kowa qin wanda ya rasa" inji Nafeesa tana harararta "Ato, wayasani Abu a duhu, wayasani ko naiman mararraba kike dashi, jira kike kiga handsome ki watsar dashi, mutum kamar dan chali chali qiris yake jira ka kalleshi ya 6arema baki Wai nan dariya yake, wannan kekam kin huta don ko Fushi yayi baki ganewa, tunda Maimakon ya hade fuska ke gani zakiyi kamar dariya yake miki. Sai kinji saukar mari sannan zaki gane Ashe ranshi a6ace yake" Mardeeya saboda dariya har saukowa qasa take tana dafe ciki, Nafeesa ancika faam tashi tayi tanufo Saudart data gama saka Riga ta bita da gudu. Zagaye dakin suka shigayi suna dariya. Mardeeya tahau yin kida da tsinken tsifarta tana kuchasu mata kuchasu, kuchasu ba mai hanaku. Suna cikin haka aka banko kofar dakin aka shigo, Duk Juyowa sukayi don ganin mai shigowa. "Yeee! Antyna!!!" Ta ruga dagudu ta rungume Saudart tana tsalle kamar wata yar yarinya, Saudart namata dariya. Sukau Nafeesa sagale sukayi suna kallonsu, musanmman baby dabasu saniba, shigartama kadai zai saka sanin yar Masu kudine ga fatarta dake sumul sumul alamun Hutu. "Wow! Antyna kinganki? Wlh kin hadu! Bari muyi selfie yau akwai status" Tsaki Saudart taja tana tureta "Kekam Allah ya shiryaki baby, ke kenan daukan pics da dorawa status. Nikam banso" "Haba aunty please" "A'a nikam" "Wayyo Ummy, wlh anty kuka zanyi" tafada tana zaman yan bori kan gadon dakin tana kwa6e fuska. Kallon juna Nafeesa da mardeeya sukai sannan suka maida kallon kanta. "Please anty* "Ok Amma kwara daya". Ihun murna tayi ta taso taciro qatuwar wayarta ta kashe Masu selfie. " wow! Wlh yaya ya iya za6e wlh kinma fishi kyau" .tafada tana Dora hoton a status da caption din *me and my cute in-law* Sai a sannan ta lura dasu mardeeya daketa kallonta, suna hada idanu suka janye idanu cikin basarwa. "Laa, anty suwaye wadannan naga kunadan yanayi" Murmushi Saudart tayi tana shafa mai tace "Cousins dinane" "Wow! Hyy" tafada tana Daga musu hannu fuska fall murmushi. "Hyy" suma suka amsa suna mata murmushi. "Kuna kama wlh Saidai Antyna tafiku kyau" Yatsina fuska Nafeesa tayi tana cewa "To kina buqatar spec sbd da alama biki kike gani, wannan ai itace hajiya munin cikinmu" Baby nasamu abinda akeso, aka wani gyara zama sannan akace "Wa? Ca6 in-law ai ta dabance, kyawunta kamar watane a Daren sha hudu, kuka jerama baza'ama lura dakuba saboda Tun Daga nesa zata dukkan daukan idanu" Mardeeya tace "Allah yasa ranace a qarfe sha biyun rana, wannan ai fari ya ceceta, da baqace da kau ba'a magana, cuss kenan" "Atleast dai farin ya ceceta, wasu kau koda farinma ba kyau sukeba kullum ana cikin yima fuska kwaskwarima" inji Saudart tana Masu gwalo. "Gayamasu dai anty, farar mace alkyabbar mata, wasu da makudan kudinsuma suke naiman farin, karshe atoye fuska a banza, Daga baya akoma multi colour" "To kinga kenan kalar mu ce mai tsada, chocolate colour wanda baya saiduwa bare asiya, shi fari ana sayanshi baqifa?" Haka sukaita cafta tsakaninsu, dayake baby batada baqunta tuni suka dinke yadda kasan dama sunsan juna. Basu suka kwantaba sai sha biyun dare saboda fira. Washegari da azahar suka fita dukkansu wankin kai, basuyi wani wahalar rabon iv ba saboda online invitation sukayi Basai anwani sha wahalar zirga zirga ba, anko ma Duk ta online aka turasu da dressing code din walima wanda Arabian gown ne baqa kowa zaisa, a dinner kuma kaya pink and blue za'asa. A saloon din aka wankema dukansu kai, akayi musu stretching dinshi. Zo Kaga santi wajen su baby da aka gamama Saudart, don hauka Wai shima gashin daukar shi hoto zatayi ta Dora status. Dariya su Nafeesa sukaita yima diramarsu don dakyar baby ta hqr bata daukanba. Nan aka musu manicure da pedicure, qunshi kuma sai saura kwana uku za'ayi. Basu dawo gidaba sai gab da magrib don Saida suka biya shopping suka jidi Kayan amfani na biki wanda Duk baby ta biya. Koda suka dawo Sallah kawai sukayi sukaci abinci suka kwanta don Duk a gajiye suke. Washegari saura kwana biyar biki, ranar kuma za'a kawo lefe, tunda safe su Saudart suka fita kitso banda baby wanda tayi zuciya saboda tace tafison Saudart tabar gashin hakanan ita kuma taqiya shine tace bata rakiyar. Da qarfe hudu na marece dangin A.A suka kawo lefe na gani na fada. Set biyu shaqare da tsadaddun kaya da wata mota da aka sako Kayan ciki fara qall qirar Prado. Sosai akayimusu tarbar mutunci da karamci kuma suka basu tukuici mai tsoka. Baby kau sana'ar aka hau yi. Hoto taita daukar Kayan da motar sai iyayi take. Sai tsokanarta danginsu suke Wai tagudo gidansu Amarya ai datayi hqr har gida zatazo tasameta, ita taita biyemusu suna raha. Yauma sai can magrib suka dawo sukaga gida haryanzu dinke da yan ganin lefe. Jikin Saudart ne yayi Sanyi ganin akwatina baje tsakar falon, batace komai ba ta haye sama batareda tayima akwatinan kallo biyu ba. Su kau mardeeya wuri suka samu suka zauna sunata duba lefen suna santi. Koda Saudart tashiga daki kuka ya kufce mata ta toshe baki da tafin hannun damanta tana kuka. Dagudu tafada kan gado tana kukan, Shikenan dagaske auren dai za'ayi mata. Wayarta taciro takira daddy taita mashi kuka. Sosai yaita rarrashinta, saida yasha wahala kafin yasamu tayi shiru. Tananan kwance su baby suka shigo dakin, kamar hadin baki suka fada Mata ajiki. Nanfa suka shiga tsokanarta baby na kareta, itadai Saudart banza tayi dasu don ba Sune gabanta ba. Sai Daga baya baby tazame dankwalin Saudart taga kitson. Nanma rudewa tayi don yau tamafi jiya rudewa. Shikku akayi mata qananu an tamkesu da qaton ribbon ya sauko har wuya. Nanma Wai hoton kitson zata dauka, dakyar ta hqr da daukar hoton don Saudart qin yarda tayi, su Nafeesa mezasuyi musu inba dariya ba suna musu ihun sunji Kansu. Yauma sai kusan dayan dare suka kwanta, yayinda Saudart bata samu barci ba sai wajajen uku sbd yadda Taita juyi tana tunane tunane...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Ramadaan Ramadaan!! Ramadaan!!! Watar alfarma Ramadaan Wata mai cike da haske da ni'imomi Ramadaan Watan da babu kamarsa Duk cikin wattani, Ramadaan. To ya? Ko kun fara yima babban baqonmu tanaji? Idan Baku faraba to Ku fara, mu dage mu kwashi gara6asar wannan wata mai albarka. Mu nemi kusanci ga ubangijinmu mu kasance Masu yawaita istigfari, mu kasance Masu yawaita tilawar Al Qur'an mai girma. Mu kwashi gara6asar wannan watan sosai don idan damar yin haka ya kufce mana ba lallai bane musake samun wata damarba domin babu mai tabbacin wani shekarar zai zagayo yanada rai. Allah kabamu ikon yin tsarkakkaken ibada agareka a wannan wata mai alfarma🤲 Allah ka amshi ibadunmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 028 Yau saura kwana hudu biki, yau Saudart na gida bataje koina ba while su Nafeesa da la'asar sunje wajen tailornsu dasukaba dinki. Zaman nata cikin kadaici yasata samun tunani da hasaso rikittaciya da 6audaddiyar rayuwar auren dazasuyi da wanda zata aura wanda a tarihin rayuwarta bata ta6a jin irin wannan auren yafaru awani wajeba. Haka ta wuni zurr kwance dama ba tsarki garetaba so bata wani damu kanta wajen tashi ba, Saidai ta mirgina nan ta mirgina can, sam tarasa meke mata dadi. Yauma da marece liss suka dawo kowa da shopping bag dinshi don shopping suka wuce Daga wajen dinki, itama Saudart sunmata nata sayayyar. Nanfa aka dasa fira, uwar kaudi kau har gwada Masu irin rawar dazatayi take, kuma ba laifi ta iya rawa don sosai rawar tayimata kyau. Nan ta zauna tana basu labarin qawayenta musanmman bestie dinta teema har tana cemasu karsu damu ai gobe zasu hadu a walima. Haka sukaita hirarsu itadai Saudart na kwance tana jinsu idanu a lumshe, don abinda ya dameta ya daketa bata tasu takeba. Washegari Tun goma nasafe mai qunshi wata yar Indonesia tazo gidan da ita da yaran aikinta biyu. Nanfa suka kama aiki. Ogan ita kema Amarya, yaran aikin kuma nama su yanmatan amaren. Sai wajajen azahar aka gama. Zokuga qunshi, ba irin jagwalgwalonmu ba🤣 Combination akayima Saudart jaa da baqi akayi mata wasu irin design kamar ba hannu yazanasuba. Sosai qunshi ya hau da farar fatarta, suma su baby ba laifi nasu ma yayi kyau Saidai fa kunsan komai na Amarya yafi kyau. Nanfa gida yafara dinkewa da jama'a yan walima dukda qarfe hudu za'a fara. Su teema sai wajajen uku suka qaraso su biyar yan gayu yan kwalisa. Nan suka hade aka fara 6arin iyayi, sai a sannan su Nafeesa suka gano dalilin kaud'in ta saboda Duk kusan haka qawayenta suke. Nanfa daki ya hargitse da hayaniya kowa qoqari yake yafadi cikinshi, babu abinda ke tashi dakin sai shewa da surutu. Da dai Saudart taga abin nasu azimun ne saita sulale tabar musu dakin takoma bedroom din mamy. Wajajen qarfe 3:30pm saigasu maryam da Duk ma'aikatan bakery dinta mata. Tafe suke da manya manyan robobi shake da snacks kama Daga cup cake, meat pie, doughnut, sausage roll, samosa, pizza, da dai sauransu. Sosai Saudart tayi mammaki ganinsu da wadannan Kayan don kwata kwata batama Masu magana kwatankwacin hakaba. Nan akayimusu maraba suma Duk sanye suke da baqar after dress wasu kuma Nada kwalliyar wasu kalolin. Sosai Saudart tanuna jindadinta akan karamcin dasukayi mata wanda hakan ba qaramin dadi yayimusu ba. 4:00pm dai dai shaharrariyar malamar nan wato mallama wasila ta iso, izuwa lokacin harabar gidan dinke yake da mutane kowa cikin Arabian gown black. Dayake harabar Nada girma sosai anan aka jera kujeru kowa ya zazzauna suna facing din inda mallamar ke zaune, itakau Saudart an tanadar mata mazaunin ta Daga gefen dama. Saida komai ya lafa sannan aka fito da Amarya. Wohoho nanfa kallo yakoma sama😳 Sanye take da atamfa Riga da skirt pieces Masu kalar jaa da fari saita Dora qatuwar alkyabba irinta ya'yan sarakuna fara qall mai aikin golden da zaiba , ta sanya hular alkyabbar wanda tarufe Rabin fuskarta. Sosai akaita santinta saboda ta hadu iya hadewa, su baby Sune Masu tattare mata wutsiyar asoya dake Jan qasa harta samu ta qarasa wajenta ta zauna. Nanfa akafara abinda ya tarasu, zikiri aka farayi mai ratsa zukata sannan aka dasa kirari mai sa jazaba don daidaikune wadanda basuyi hawaye ba Daga qarshe ta rufe musu da wa'azi mai ratsa jiki musanmman ga Amarya, tana gwada Mata nauye nauyen daya rataya akanta amatsayinta ba matar aure tana mata misali da Nana fadima da matan annabinmu Muhammad (s.a.w) Sosai jikin Saudart yayi liqis, Kanta a duqe babu abinda take sai hawaye, don sosai wa'azin matar ya ratsa ga6o66in jikinta. Sai wajajen shidda aka gama, nan aka shiga raba ledoji Masu dauke da sallaya ko doguwar hijabi da cazbaha hadeda snacks da akayi wrapping cikin irin wannan abun mai kyalkyali. Anan na hango su tawagar yan AUREN KWANGILA NOVEL GROUP sun Kasa zaune sun Kasa tsaye kowacce burinta tasamu rabonta. Can na hango ummu bilal ana ta miqa hannu za'a amshi Leda Bayan ga wata nan cikin qatuwar hijabinta sai kunbiya kunbiya take daita. Dayan gefen kau sis hajara Nagani sai bin baby take kamar bindi Wai adole sotake su zama qawaye don tasamu hallatar dinner Bayan daurin aure. Can gefe naga maman fateema da ummu arifullah suna leqa ledar juna don ganin me suka samu. Itakau umman abdullra'uff ana gefe kan kujera sai gutsirar pizza ake ana tauna ana wani lumshe idanu (ba sabban ba🤣) A can gefe kuma Mamman twins ce kamar tayi bindiga don bata samu komaiba, su twins sun hana🤣 basu tashi rikice mataba saida aka fara rabo, Maman twins fa ta kumbura, wazai kawo gudunmawar allura a saceta?🤣 Taro yayi taro inda aka hada malama wasila da shatara na arziqi, sai godiya take tana kwararowa auren albarka ana amsawa da amin. Itakau Saudart dama ana gamawa tasamu ta silale daki ta kulle kanta tafada kan gado ko alkyabbar bata cireba sai kuka. Sosai jikinta yayi Sanyi Jitake inama zata iya maida hannun agogo baya da kome daddy zaiyi da bata yarda da aurennan ba Amma inaa? Kin makara Saudart bakin alqalami ya buhe😏 Washegari kuma wato ranar Daren biki yayi daidai da ranar mother's Eve nasu Ummy. Su baby amara qahon zuciyar biki don kau wannan Tawuce qirjin biki, shirya wa sukayi dukkansu suka wuce gidansu. Babu yadda basuyi ba akan Saudart ma ta shirya sutafi tare Amma hausawa ma sunce shiru ma amsace don kwandon shara tasamu tasakasu ciki ta rufe. Tafiyar su sukai suka barta ita kadai dama haka tafiso don taji dadin yin tunanin ta. A gidansu A.A akayi mother's Eve din a garden dinsu dake can cikin gidan. Sosai partyn ya qayattar, bawani chasu akayiba kawai zazzauna ake kowane table da kujeru hudu round dinshi ana zaune ana ci anasha ana fira ga wani sanyayan kida dake tashi a background. A ataqaice sai 10:oopm su baby suka dawo gidan mamy kowacce agajiye liqis kuma kowa ce da burin data tanaddarwa gobe, wato ranar daurin auren. ******************************************* Bankado kofar akayi da wani uban force kamar za'a qilleta. "Gobene! Daga gobene fah! Gobene!! Gobene! Daga gobene haba! Gobene!" Wani uban tsaki Ashraf yaja kamar bakin zai cire yana antayamashi wata uwa uban Harara. "Waikai wane irin marar saiti ne zaka wani shigo na mutane daki bako sallama" Yafada cikin Fushi Daga hannuwa Sadeeq yayi alamun surrender yana dariya sannan yakoma bakin kofar ya kwala wata uwar sallama sannan yashigo. Tsaki Ashraf yasake ja yana maida kanshi kwance yana cigaba da shafe shafen wayar shi. "Ango! Ango!! Kaga ango wajen amaryar sa Saudatu tauraruwar mata, ango bada kanka asare kaje gida kacewa Ummy ya6ace, ango kasha qamshi, kana kuma cikin shan qamshi kuma zaka sha qamshi" ya qarashe zancen yana kashe mashi ido daya😜 Ashraf da tunda yafara 6a66atu yakeji kamar ya shaqeshi kowama ya huta ya juyamishi baya yana Jan tsaki. "Ko tsakama datayi bataci ribaba, tsaki kamar wata tsohuwar karuwa, Nidai tashi su bash na falo don iskanci kawani zo ka qunqume uwar daka kamar wata sabuwar amarya" "Bazan fitoba din! Kasan Allah Sadeeq? Wlh Allah zan mugu mugun sa6amaka, Wai ina ruwanka danine uhm? Dakai mayene dana kade har ganyena, wlh ka fita sabgata Tun kafin na shufkama rashin M" "Tun yaushe kuma allaramma ango? Rashin m dinka ai harna saba dashi Kaga babu abinda zai tadamin hankali, oya miqe" "Don ubanka miqar dani din" yafada cikin qulewa "Wlh tsab kai kanka kasan ina iyawa Amma sbd kai angone Shiyasa nake ragamaka.." "Dan ubanka karka ragamani, mtcheew dalla fita!" "Yo ai hikenan, tunda hakan kakeso" Yafada yana fita Tsaki Ashraf yasake ja sannan yakoma ya kwanta, ba laifinshi bane don yaga nazo gidansu ne. Be gama tunaninshi ba yaji ansake banko kofar, dagowar dayayi yaga su bash sunata shigowa sukai biyar da Sadeeq daya cika na shiddan. Dafe kai Ashraf yayi yana komawa yana kwanciya, yasan yau tashi ta qare. Nan kau suka hau tsokanarshi Tun yana Masu kumfar baki harya saduda don tsagerane suka hadu don wasu cikin su sunmafi Sadeeq qulluwa. Haka ya zuba Masu idanu har suka gaji suka kyaleshi, shima saida yayi barcin qarya sannan suka shafamashi lfy, nan suka juya akalar firar zuwa na dinner gobe kowa na fadin albarkacin bakinshi. Sai can wajajen dayan dare suka samu suka kwanta shikau Ashraf tuni dama barci yayi awon gaba dashi. RANA BATA QARYA....✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu. Karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 029 RANA BATA QARYA...... Yau ranar jumu'a ce mai cike da tarihi a rayuwar wasu, jumu'ar da bazasu ta6a mantawaba. Yau ne ranar daurin aurensu, AUREN KWANGILA. Tunda ta farka ko matsawa Daga inda take batayiba, dama ba Sallah takeba bare ta tashi tayi. Tana kwance ido lumshe kamar mai barci Saidai idanunta biyu tana sauraron Duk wani zirga zirga da hayaniyar mutane. *yau ne* tafada cikin zuciyarta *yau ba gobeba* *yau zan zama matar aure* *matar auren kwangila* *matar mutumin da banajin ko digon sonshi daidai da qwayar zarra acikin zuciyata* *matar aurenda nan da wani d'an lokaci zata zama baza wara* *me kika yima kanki Saudart?* *anya baki cuci kanki ba* *anya daddy beso kanshi dayawa ba* *inama ace mafarki ne* *Allah yasa mafarki ne* *Allah yasa ba gaske bane* Hawaye suka silalo mata dukda idanun a rufe yake. Wani nauyi taji zuciyarta nayi mata kamar an doramata qaton nutse a qirji. Sosai hawayen keta silalowa batareda tayi wani yunqurin taresu ko sharesu ba. Daidai nan mardeeya tashigo dama sunje amso dinkin anko dinsu ne dawowarsu kenan tabaro su baby qasa. "Subhanalillah" tafada tana Qarasowa wajenta. "Saudart" tafada tana dan jijjigata ganin idanunta haryanzu a rufe yake. Banza tayi da ita Saidai hakan besa hawayen sun tsayaba. "Sister menene? Dan Allah ki tashi, Meya faru?" Nanma shiru saima juyamata baya datayi. "Saudart kiyi hqr, nasan kukanki baya rasa nasaba da auren daza'a daura miki yau, Duk macen datasan ciwon kanta dole ta koka ranar aurenta ba don zata bar iyayenta kadaiba, don itama zata taka wani matsayi wanda bata ta6a takawaba a rayuwarta, nauye nauye zasu hau kanta wanda idan ba me dakkakiyar zuciya bace bazata iya dauke nauyin ba" Kamo hannayenta tayi tariqe sannan cikin sigar rarrashi tace "Sis kiyi hqr, Allah baya dorawa bawa abinda baya iyawa, ki kasance mai Neman tallafi a wajen Allah kuma ki kasance mai hqr, idan kinadashi ada ki Dora akai, darajar 'ya mace ke har namiji ma shine aure, ki kasance jajirttaciyar mace abun kwatance a fannin aure, ki zama abun alfahari ga mamy da daddy ke harma garemu gabaki daya, dukda aure rai gareshi idan ba'a mutu dashiba yakan mutu yabar ma'auratan don Allah aurenki yazama abin kwatance a family dinmu, babu yaji bare saki please, nafi kowa sanin yadda mamy ta kwallafa rai akan aurenki don sau ba adadi ina jinsu idan suna fira da ummina akan tanason kar aurenki yazama irin nata, tafison kiyi auren mutu-ka-raba, ya kasance yayanki duka nawajenki yadda zaki basu tarbiyya kuma su taso tare, please sister kicikama mamy wannan buri nata, ki jajirce sis, aure yanada dadi haka wani shafin idan aka bude yafi mad'aci daci, ki riqe Allah da manzonsa kuma ki riqe hqr.." Shiru tayi ganin yadda kukan nata ya tsananta, shiru tayi tana kallon yadda take kukan, abinka ga ruwa ruwa sai itama taji digg digg hawaye sunfara digomata. Nan aka rasa mai rarrashin wani cikinsu don hade kai wuri guda sukayi hannunsu cikin na juna sunata rizgar kuka. Ita kukan Saudart ya Kasu kashi kashi, ga na fargabar aure da na barin iyaye gana fargabar yadda mamy zataji idan auren ya mutu. Itakau mardeeya kukan tsantsar tausayinta take dama na mata gabadaya, wanda Daga inda kayi aure nauyi yahau kanka, gana miji, idan kuma aka hayyayafa gana 'ya'ya. Ahaka su baby suka taddasu. Turus sukayi abakin kofa suna kallonsu kowacce takasa motsi. Baby ce ta fara takawa ta qarasa wajensu itama ta zauna ta rungumosu gabadaya itama ta bude nata muryar da Allah yabata tafara raira nata kukan. Ganin hakan yasa itama Nafeesa tayi wajensu dagudu itama ta rungumosu sukaita kukan tare da wannan ya dauka sai wannan ya aje, da wannan ya aje sai wannan ya dauka. (Nima ganin haka yasa nadan kauda kaina na matso guntun hawaye na😢 sannan na share da hanki) Suna haka matar kawu bala tashigo, tana ganin yadda suka cure waje daya tafara sallalami tana tafa hannaye. "Ni asiya mezan gani?" Hakan yasasu dagowa Kowanne fuska jaga jaga da hawaye. "Wannan wane irin sabon sakarcine zakuzo Ku cure waje daya kuna kuka? Meya faru?" Nafeesa ta nunasu cikin muryar kuka tace "haka nisa baby mukazo muka tardasu suna kuka" "Mtcheew Maimakon Ku rarrashesu shine kukayi joining? Ke mardeeya Meya sakaku kuka?" "Haka nazo na isketa nima tanayi" "Mtcheew, andaiji haushi Maimakon ki rarrasheta shine kika biyemata" "Na rarrasheta taqi shiru" "Mtcheew ni matsamin dalla" Ta wuce ta kamo hannun Saudart da kanta ke duqe haryanzu tana hawaye. "Ya isa haka baby, kiyi hqr kinji? Kowa haka yaji a lokacinshi, kiyi hqr, taho muje" Tafada tana miqar daita tsaye suka nufi hanyar waje. "Saura kuma Ku zauna karku tashi Ku shirya" tafada tana ficewa da Saudart. Sun kusan mintuna goma zaune jigum jigum babu mai magana. Can kamar an tsikari baby ta wani miqe tsaye tana kallon agogon hannunta. "Guys har 11:30am yayi fa, Nidai bari kuga infada toilet, ato banmaga meye nawani kukaba Bayan ba aurena bane kuma ma aini farinciki yakamata nayi za'a rabani da dunqum" Ta qarashe zancen tana Fadawa toilet. Kallon Kansu sukayi Bayan sun rakata da kallo harta shige sai sukayi murmushi. Bedroom din mamy anty asiya ta kaita don nan kadaine babu mutane. Nan ta zaunar daita tanata yimata nasiha sannan Daga bisani ta hadamata ruwa mai dan gumi a jacuzzi tabata umarnin tashiga tayi wanka. Ba musu ta shiga Bayan ta cire kayanta ta daura towel. Ta dade sosai a toilet din sannan tafito tana tafiya kamar wanda Kwai yafashe mawa aciki. Kayan data tadda kan gado wanda anty asiya ta fiddomata ta dauka tasa. Doguwar rigace ta materials marar nauyi mai style din fish. Sannan tadan shafa powder tasa kwalli a idanun ta kwanta don sosai kanta ke sarawa. Can saiga anty asiya tasake shigowa da bowl hannunsu sai wata Leda. Tada Saudart tayi wanda dama ba barci takeba ta tilastata shan farfesun da bread. Saida tacinye Tass sannan tabarta Wai acewarta vazatabar diyarta da yunwa ba. Paracetamol ta 6alla mata tasha sannan ta kwantar daita tafita ya rufomata qofa. Dakinsu baby kau tuni yafara tashin hayaniya don su teema an iso. Kowacce tasha anko dinta kowacce da irin daurin data kashe. Baby ce tsaye gaban mirror ansha dinkin doguwar Riga mai budewa Daga qasa, dogon hannun rigarko Duk anyi raga raga ajikinshi wanda yaba farar hannunta damar fitowa cikin hudojin. Fuska kau tasha simple makeup Wai sai ga dinner zatayi heavy makeup. Ta wani kashe daurin ture Kaga tsiya. Nanfa suka fara kashe selfie, Duk inda ka wulga flasher ce kawai ke wall wall akota ina kowa burinshi ya dauki hoton dayafi kyau, style din hotuna kam harda na hauka, haka sukaita yi ana dorawa a status, dp, pp e.t.c ********************************************* "Wai Ashraf wannan wane sabon salon iskanci ne Wai, zaka wani shanya mutane waje kawani shige daki harda murza key? Ko bakasan qarfe nawa bane?" Inji Sadeeq afusace, yasha fararen dakkakiyar shadda da babban rigarta yar three quarter irindai ta gayun zamani yawani kashe hula gefen goshi. Su bash suma cikin irin shigar zazzaune suna jiran tsammani Duk sun zubama kofar idanu. "Baaam! Baaam!! Baaam!!!" Yasake bugun kofar cikin quluwa. "Dan ubanka kafito kona kira Ummy yanzu yanzunnan!" Tsaki Ashraf yaja yana daura agogon fata qirar apple a hannunshi sannan ya feffeshe turarrukanshi ya kaha hularshi akai, Duk cikin kwanciyar hankali yake hakan don yaqara qular dasu. Saida yagama shan qamshinshi sannan yabude kofar yafito fuska a tamke. Su Sadeeq dake jira ya fito sukusa cinshi danye suka Kasa motsi. Hade yake cikin dakkakiyar shaddarshi milk colour mai aikin deep brown wanda yarufe kusan duka gaban babbar rigar sai hula kalar aikin Kayan takalmi da agogo ma hakan. Ga fuskarshi datasha Gyaran fuska, dan siririn sajenshi sai walqiya yake. "Tuff tuff, kuci kanku" yafada yana tuha Masu yawu. Sai a sannan suka dawo Daga duniyar kallonshi. "Wow! Wow!! Wow!!" Haka sukaita fadi kamar wasu motocin yan sanda. Tsaki Ashraf yaja yana cewa "idan kun gama jiniyar kusameni waje" Kallon juna sukayi suka fashe da dariya "Wooo! Tofah kunji, kuna 6atamishi time shi yayi gaba, he can't wait" inji wani mai suna Abbas's. Nan suka fito sai tsokanarshi suke shikau ci kanku bece dasuba yashige wata farar motar ya danna lock yaba drivern umarni yaja. Dariya suka sake kwashe wa dashi sannan suma suka hau motocin suka Mara mashi baya. Unguwar ta cika maqil da mutane da manya manyan motoci, kallo daya zakayima taron kasan ana gudanarda gaggarumin abune. 2:30pm daidai aka daura auren ASHRAF AUWAL da SAUDATU SHAMSU KANKIYA. Daurin auren daya samu hallatar manya manyan qusoshin gomnati da yan kasuwa. Fuskar alhaji Shamsu kamar gonar auduga, yaudai burinshi yacika yazama surukin A.A Nan akaita zomashi Allah yasa alhairi, a gefema Abba ne da tawagarshi shima sai barka ake mishi. Can 6angaren angwaye ma abun ba sauqi sai Allah ya sanya alhairi ake zuwa yimashi, Shidai iyakarshi yaqe su Sadeeq ne Masu amsawa suna godiya. Maroqa kau kasuwarsu ce tabude, nan suka baje kolinsu suna wasa ango da Amarya Dama abokan angon gabadaya, sunkau sha 6arin naira don su bash kamar basusan zafin nemaba haka sukaita watsa naira. Masu daukar hotuna kau kowa burinshi ya dauka, Duk inda suka wulga Saidai sunji walai anata daukar su. Ganin abun bana qarewa bane yasa Ashraf sulalewa ya fece. Tunda taji sautin buda na tashi Duk ilahirin gidan gabanta ya tsananta bugu. Sake cusa kanta tayi cikin bargo tana sakin wani marayan kuka wanda izuwa yanzu har idanunta sun gaji da tsiya yar hawaye, tausayin kanta yakamata nankau taita kuka kamar babu gobe. Su baby anajin an daura tawani dale gado tana tsallen murna, Duk sai akaita mata dariya. Wayarta ta kwace hannun wata safeena ta Danna ma Ummy kira tana rugawa toilet. Ana dagawa tawani Danna ihu "Ummy!!!" "Ohh zaki kashe min kunne" "Ummy finally, anty tazama family dinmu, finally yaya is married!" "Yes sweetheart, mu gode wa Allah" "Alhamdulilah Ummy zan sake kiranki" Ta katse wayar ta fito waje ta tarda harsu teema sun fiddo mp dinsu sun Kunna anqure volume. Aikau tayi joining suna rawar so na amana. Sai wajajen 5na marece akazo daukar Amarya, zokaga kuka, ba Saudart ba ba mamy ba, dakyar aka samu aka 6an6aresu aka fito daita, Dama su yanmatan amare ana cikin mota an qame tundazu. Fitowa akayi daita fuska lullu6e da lifaya aka sakata mota, tanaji tana gani aka shilla daita...✍ Toya? Wakeson acigaba yau? Koko abari sai gobe? Adadin comments dinku zai bada amsa Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 030 Saida aka fara biyawa daita gidan daddy wato alhaji Shamsu, don suyi bankwana. Nan ne mutane sukaga Ashe kukan datayi acan nafila ne bisaga na nan. Sosai ta damke daddy tanata kuka, jikin daddy ne yayi Sanyi don yafi kowa sanin dalilin kukanta. Ko dan nasihar nanma Kasa yimata yayi Saidai samata albarka dayaitayi. Nanma dakyar aka 6an6areta Daga jikinshi Aka fita daita. Cikin dalleliyar motar da'aka taho daita aka maidata sannan aka tada motocin sukayo layi sai gidansu A.A Tun a harabar gidan aka fito tarbosu, sai 6uda dangin Ango suke, da wannan ta aje sai wannan ta dauka. Ahankali Saudart tafito Daga motar Bayan an bude mata bakinta dauke da addu'a. Ganin fitowar amaryar yasa budar qara yin sama. Ummy nacan cikin falo da tawagunta wani farinciki ne ke sake ratsa ta jin yadda aketa callara buda. Ahankali aka kamo hannunta aka wuto daita anata buda har suka shigo falo. Mancewa Ummy tayi dawata surukanci ta tashi ta tarbota cikin fara'a hakan yasake Tunzura Masu budar suka qara volume. Itadai Saudart kanta a qasa sbd matsananciyar kunyar datakeji. Zaunar daita Ummy tayi tana mata lale marhabin sai kashe musu hotuna ake. Haka akaita zuwa anamata sannu dazuwa itadai kanta qasa sai hawayen dake digowa diss diss saman hannunta Kiransu baby dahar an tu6e za'a shiga wanka azo afara shirin dinner akayi tazo suka dunguma da Saudart dakin Ummy. Nan akazo akafara mata shiri don dama bawani sallar dazatayi Sukuma baby aka koma daki inda ke cike dasu yanmata hardasu Nafeesa ana shirin dinner. Izuwa yanzu Duk wani fi'ili da iyayi nasu baby Nafeesa ma ta koya don idan tafara yadda kasan Dama can haka take Itadai gwara gwara mardeeya ita abin nata da dan dama Dama. Tofah gida ya kacame sai shirin dinner ake suma a 6angarensu ango hakan take. Yanzu ma saida yagama shan qamshi sannan yashiga shiri. Abokanan ango su shidda ango sukasha kamar dai dazu. Sanye suke cikin wata dakkakiyar shadda sky blue babbar Riga da tan ciki. Anyima babbar rigar aiki da zare dark blue, sun kashe hula wasu a goshi wasu a qeya. Sosai suka bada kala don kallo daya zakayimusu kasan samarine Masu ji da kyau, kudi, dakuma wayewa. Sanye suke da takalmi half cover farare Tass, saima kun gansu sun hadu👌 Yanzu ma saida ya qular dasu sannan yafito. Yanzunma jiniyar suka dauka, don haduwar ta yanzu taci uban ta dazu. Sanye yake cikin tsaddadar dakkakiyar shadda fara Tass babbar Riga da yan ciki wanda taji aikin sama na kalar sky blue, saiya kashe hula sky blue akai hannunshi daure da agogon fata qirar Gucci fara sai takalmi suma na company Gucci farare qarr. Wow! Nima nayi nawa jiniyar, watakan nama Kasa magana ne, Saidai nabaku dammar hassasoshi da kanku don ya hadu qarhe👌 Nanfa aka hau yimashi kirari, Kowanne da irin kirarin dayake mashi ba shaqiyanci. Abun nasu ya daina bashi haushi yanzu saima dariya, murmushi ya saki wanda yaqarawa kyanshi kyau. Gabadaya suka dunguma sukayi waje abun gwanin sha'awa suka nufi motocin dake fake a waje. Mota daya Sadeeq da Ashraf da bashir suka hau dayan kuma su abbass suka hau suka shilla sai gidansu A.A Su baby Angama shiri cikin anko din dinner dinMaterials pink Ayi shafi da blue glass tapita. Dukkansu anko din dinkin doguwar Riga sukayi mai wrapper 'o' a qasa, kowacce ta kashe daurin head sky blue, Duk an fente fuskoki da heavy makeup. Sunyi kyau sosai sai kashe hotuna suke. Can wajajen Bayan isha'i gida ya harmutse da buda. Hakan yasa Duk aka fito don ganin Meya Jawo hakan. Angwaye ne suka qaraso ga motocin kai mutane dinner Jere birjik waje, har mutane sunfara shiga, can Nagano maman twins Bayan wata mota tareda wata yar yarinya data taho daita wanda zatayi mata rainon su twins koda sun nemi yimata buqulu🤣 Cikin washe baki suka shiga cikin gidan Shidai ango iyakarshi murmushi dabe kai zuci ba. Nan akaita tsokanarshi su sadeeq na kareshi Shidai nashi yaqe. Har wajen Ummy aka rakoshi, da sauri ya qarasa ya rungumota yana lumshe idanu itama Ummy kankameshi tayi farinciki da kaunar danta na huda zuciyarta. Sai daukar su hoto ake tayi ahakan don sunqi sakin juna. Duk d'ari d'arin da baby keyiwa Ashraf ta daure ta qarasa itama ta rungumesu gabadaya hakan yasa akaita shewa ana daukar su hoto. Sun dade ahakan sannan suka warware rungumar Kowanne farinciki fall fuskarshi. "Yaya congratulations" inji baby tana mashi murmushi Shima murmushin ya maida mata "Thanks lil sis" Sosai tayi farincikin sakin fuskar dayayi mata. "Yaya, please selfie?... Please" Murmushin gefen baki kawai yayi hakan yasa tayi saurin Ciro wayarta har kyarma take ta matso dab dashi suka dauka sai kuma ta dauki wani tareda ummy. Ganin abun nasu bana qarewa bane yasa bash radawa Ashraf time na tafiya fa. Hakan yasa suka miqe. Yanmata Duk inda ango ya wulga saisun bishi da idanu, Nafeesa da mardeeya kau har kusan jalale sukayi Ashe dama haka angon Saudart yake? Lallai tayi dace. Shiga wasu sukayi dob fitowa da Amarya, izuwa yanzu jama'ar dakin Duk sun fita sun shige mota wasu har anfara tafiya dasu. Fitowar Amarya yasa kallo yadawo kanta. Yanzu fuskarta abude take, tasha heavy makeup wanda ya bayyana 6oyyayen kyawunta tsantsa. Masha Allah mutane sukaita fadi don ba qaramin haduwa tayiba cikin farar wedding gown dinta da akayima ado da pink colour. Sosai rigar ta amshi qirar jikinta kamar a jikinta aka dinka. Gashi anmata wani fitinannen daurin head pink kamar fanka don bazuwa. Yanzu ma Ummy ce Taqara tarbota tana fadin masha Allah saboda kyawun datayi. Itadai Saudart nata sinne kai sai murmushi datake a kunyace. Nanfa aka kuma bude wani sabon babin daukar hoto, Duk abinda ake Ashraf be ko kalli gefen Saudart ba, itama hakan saida akace Amarya da ango su jera a daukesu tare. Rasa wanda zaifara motsawa akayi cikinsu, ganin abun nasu nayine yasa wata abokiyar wasansu A.A ta kamo hannunshi ta jawoshi wajen Saudart ta Dora hannunshi a kafadar Saudart kamar irin yad'an rungumota dinnan. Hakan yasasu jin wani vaqon al'amari a jikinsu wanda hakan yasasu saurin dagowa tare suna kallon juna. Wall wall aka daukesu hoto suna kallon junan. Saurin janye idanunsu sukayi Kowanne gabanshi na faduwa. Qoqarin zame mashi take yaqara matseta yana dan harararta ta qasan ido Hakan yasata janye dara daran idanunta tana kallon qasa Duk abinda suke ananan anata daukansu hoto saida sukayi mai isarsu sannan aka fara fita zuwa mota dama saura yan kadan su kingin sun tsufa acan. Saida Ummy tayimusu nasiha mai ratsa jiki sannan tace musu sutafi Allah yayi musu albarka. Tashi Ashraf yayi itakau Saudart tama Kasa motsawa, hakan yasa Ummy tayi mashi ido akan ya tadata. Ba don yasoba ya duqa ya kamo tsintsiyar hannunta, hakan tasata dan razana ta dago ta kalleshi, kauda Kai yayi, tana shirin zame hannunta Ummy tace "Ku tashi kuje daughter" Babu yadda ta iya tamiqe still hannunta cikin nashi suka jera suka fita. Saura motarsu kadai dama, Sadeeq ke mazaunin driver. Yana ganinsu yayi saurin fitowa don budemusu kofa. Ganin sun fito waje yasa Saudart kwace hannunta tana hade rai. Ta6e pink watery lips dinshi yayi yana fadin "as if I care" Banza tayi dashi ta kauda kai, Qarasawa tayi tashiga motarda Sadeeq ya Budemata, saida Ashraf yasha qamshi sannan shima ya qarasa ya shiga yana Jawo kofar. Zagayawa Sadeeq yayi mazaunin drivern yana girgiza kai, Shidai yaso ganin irin zaman da zasuyi. Tada motar yayi ya shilla kan kwalta. Babu mai magana acikin su har suka qaraso, nanma Sadeeq ya fito ya budemusu kofa. Yanzuma saida yasha qamshi don har Sadeeq yafara hasala don dai kawai yana ganin Saudart ne da babu abinda zai hana ya balbaleshi. Saukowa yayi ahankali yana gyara babbar rigar shi. Itama Saudart fitowa tayi cikin nutsuwa ta tsaya Daga can gefe. "Ehmm... Ango dan Allah ka kama hannun Amarya Ku shiga Ku kadai ake jira" Harara ya watsa mashi ya dauke kai. "Please Ku kadai fa ake jira, please" Kamar bazaiyi ba saikuma ya matso dab da ita Saidai yakasa riqo hannun don beson yasake jin abinda yaji dazun daya riqe hannunta. "Ashraf mana" inji Sadeeq cikin qosawa. Tsaki yaja sannan ya kamo hannun ya riqe yana qara tamke fuska. "Yauwa kutaho ahankali" inji Sadeeq yana yin gaba. Cikin takun qasaita suka taho kafada da kafada dukda kowa da kalar abinda yakeji ajikinshi. Ana ganin 6ullowarsu aka saki kidan ranarku ta umar m Sharif. Nan yam rakiyar Amarya da ango aka fito aka jera bayansu Ahankali suka qarasa stage din hannunsu cikin najuna, sukau yan rakiya sai rawar waqar suke suna maramasu baya har suka kaisu mazaunin su. Sosai aka qawata mazaunin nasu da decoration sky blue and pink. Zama sukayi ahankali Ashraf na taimaka Mata ganin tana Neman missing step. Ta6e bakinta tayi don ba cika son ta6atan dayakeyi take ba. Shima Ashraf ganin idanun jama'a yasashi tarota da babu abinda zaisashi tarota Saidai ta shekara tana faduwa. Nanfa aka fara abinda ya tarasu. Kowanne kagani a dinner ji da kanshi yake don dinner ne tsararre kuma na yan gayu don haka kowa ya aure wankanshi. Bayan dan barkwanci da m.c yayi da yan surutansu dasuka saba aka kira wasu Afro dancer don su nishafadar da mutane. Yan yara ne mata wa'inda basufi shekaru takwas takwas ba su hudu sanye cikin Riga pink da crazy jeans blue Kansu yasha bands blue da pink. Nan aka kunnamasu waqar hiphop suka shiga yin rawa iri daya mai burgewa. Sosai suka burge mutane abinka da yara, man akaita yimusu 6arin kudi, sai tafi akemusu. Bayan nan abokan ango suka fito su shiddan Kowanne nasa6ar babbar rigarshi. Nan aka sakamusu waqar EBEANO. zokuga rawa wajen abokan ango, har wani baza babbar rigar suke suna shaku shaku sosai suka burge mutane sai tafi akemusu wasu harda fito don rawar tasu iri daya da alama sun dade ana training. Bayan waqar taqare aka chanza musu waqar GIDODOGO nasu p-square da diamond Nanfa Hall yadauki sowa ganin sun chanza salon rawar su. Saudart da Ashraf Kansu Saida suka murmusa don rawa suke sosai gashi sai fama suke da babbar Riga abun gwanin dariya. Waqar na qarewa suka bar stage din. Nan DJ ya chanza waqar yasa ta lokaci ne na umar m Sharif. Su baby suka fito suma su biyar Suka fara rawar waqar. Babu abinda ke tashi sai tafi su Nafeesa da badasu aka fitoba don basu iya rawar ba don musanmman baby ta hadu da qawayenta sukayi training din rawar sosai, su Nafeesa harda fito don sosai suka burge musanmman inda suka fara rawar jirgin so acikin waqar. Sun burge sosai don bawai irin girgiza jikin haukarnan sukeba ahankali suke rawar cikin yanga kuma tayimusu kyau. Nanfa suma akaita musu 6arin liqi basusan zafin kudinba. Can Bayan waqar taqare suka sauka Daga stage nan aka fara shelar Amarya da ango suma su fito su taka. Tofah nan akeyinta, ganin babu mai niyyar tashi yasa bash yaje ya tada Ashraf yana mashi rada a kunne. Kamo hannunta yayi ya dagata ta tashi suka fito stage nan aka Kunna Masu waqar Hamisu breaker ta jarumar Mata. Kama hannunta daya yayi, dayan kuma ya tallabo kuqunta. Hakan yasata saurin dagowa ta kalleshi, dan harararta yayi yana mere baki. Hakan yasa ta sadda kai. Ahankali ahankali suka fara tattakawa yayinda suka burge kowa sai daukar video ake. Ahankali ahankali akaita hawa stage din aka zagaye su ana Masu kiqi Ana dan tattakawa don waqar bata rawa bace irin ta haukannan ba. Zokuga yadda kudi ke zuba qasa, liqe akemusu kamar yayyafin kudi akeyi. Sun dade ahakan sannan aka rankaya wajen yanka cake, nanma cool music aka sakarmusu na DID YOU BELIEVE IN LOVE? Hannunsu akan na juna suka yanka cake din tare sannan sukayi feeding din juna. Daga qarshe aka saka waqa kowa yaita chashewa. Duk bidirinnan da ake su hajiya maman twins dama sauran yan AUREN KWANGILA NOVEL GROUP basusan anayiba don tunda aka fara suka Tisa abinccicika kala kala sai handama suke musanmman maman twins acewarta saitayi qara'i wasu har a Leda zubawa suke Wai akai gida musanmman ummu sadik Mayyar shinkafar biki🤣 To Allah dai yasa kar ciki ya rude, ca6 da ba kanta, wayaga su maman Fatima ana yamutse fuska kan toilet🤭 Anyi dinner lfy antashi lfy inda ango dakanshi yaja motarsu da amaryar contract dinshi agaban mota. Mutane sai dagamusu hannu suke har suka fice suka nufi sabon gidansu amatsayinsu na sabbin ma'aurata inda zasu fara gudanar da sabon rayuwa mai cike da chakwakiya...✍ Tofah fans yaya zaman nasu zai kasance? Ina Suzy? Zata dawo koko ta hqr? Zaku sami amsoshinku Bayan Sallah insha Allah. Anan zamu tsaida littafin nan harzuwa Bayan azumi insha Allah. Dan Allah ina mai Neman yafiyar Duk wanda nayima ba daidai ba acikinku, da sanina ko babu sanina,please ayafe. Nima na yafe muku gabadaya. Allah yabamu alhairin wannan wata mai alfarma. Yasa mu kwashi garabasar dake cikinta Muyi ibadunmu lfy mugama lfy. Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid 19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu karka barmu da kanmu🤲 Happy edl- Mubarak🧚‍♀ Dafatan kowa yayi sallah lafiya, Allah kasa ibadunmu da addu'o'inmu kar6a6une🤲 To kowa yazo asa layi, yau duk sai anbani barka da sallah na, idan ba haka ba muci mutum tara😏 Afara layi gajeru agaba, dogaye abaya, qwailaye agefe🤣 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 031 Garin yayi tsit, yayi duhu saboda Daren yafara nisa, ga hadarin daya hadu Wanda yaqarawa Daren duhu, iska mai dadi sai qadawa yake. Tuqi yake cikin normal speed yana sarrafa steering din gwanin burgewa. Tsit motar kamar babu kowa aciki, kowanne da abinda yasha mishi kai babu Wanda yanuna yasan da wanzuwar Dan uwanshi. Idanunshi da hankalinshi na kan kwalta ko gefenta yayinda itakuma take gefenshi lafe a kujera idanunta a lumshe. Har yanzu takasa yarda wai ita Matar aurece, wata biyu dasuka wuce idan da wani zai gayamata warhaka tanada aure babu abinda zai hanata qaryatawa, amma sai gashi cikin Dan qanqanin lokaci labarin rayuwarta ya canza, acikin wata biyu tasamu miji har anyi auren saidai ba irin auren da aka saba yiba, aure ne na takaitaccen lokaci Wanda ke shimfide akan sharrud'a da tsari. Ajiyar zuciya ta suke ahankali daidai Wanda taji ya dakatar da mortar yana horn. Can kuma taji motar tacigaba da tafiya duk abinda ake idanunta na alumshe kuma batada niyyar budesu. Direct parking space yanufa inda yake kwal babu mota ko daya kasancewar sabon gidane yau akafara amfani dashi. Parking yayi sannan yakashe motar yakoma ya jingina da bayan kujerarshi yana lumshe hazal eyes dinshi. Shiru motar ta dauka babu mai ko motsi, izuwa yanzu hadarin ya hadu sosai don iskar yaqara qarfi, sai walqiya da cida ake. Hannu yasa cikin sanyi ya balle seat belt ya bude murfin motar batareda yako kalli gefentaba ya fita ya maida kofar yarufe, sannan yafara takawa cikin takunshi na qasaita yawuce. Ajiyar zuciya ta sauke nannauya, ahankali ta bude idanunta Wanda tunda suka baro wajen dinner suke a lumshe. Tacikin mirror din gefen motar tabishi da kallo harya shige ciki. Ta6e baki tayi cikin takaici, ita tunda take bata ta6a ji ko ganin ango yabar amaryarshi amota ba ranar auren su. Koda yake auren ma gabadaya bata ta6a jin irin nasuba don haka duk abinda yabiyo bayama ba komai bane. Hannu tasa ta bude kofar itama sannan ta ziro kafaffunta ta sauko. Qanqame jikinta tayi a tsorace jin anyi wata irin tsawa da walqiya, saurin maida kofar tayi tarufe tana qanqame net din data Dora akai Wanda iska ke baraxanar fecewa dashi. Ahankali ta fara takawa itama tanufi hanyar dataga yabi hannu daya dafe da net din kanta dayan kuma ya tattaro qasan gown dinta dake sharar qasa. Dakyar tasamu ta isa main door sbd wuyar tafiya da heels din kafarta kesata. Hannu tasa a handle din kofar ta murda saigashi yabude, tura kofar tayi tashiga bakinta dauke da addu'o'i. Wani sanyi da ni'imtaccen qamshi yaimata maraba Wanda saida ta lumshe ido don dadi. Bin qayyatacen falon tayi da idanu tana jinjina 6arnar kudin da Dad yayi wajen zubamata kayan daki na gani na fada. *Lallai dad* tafada acikin zuciyarta. Haka taita bin falon da kallo tanata yan ta6e ta6en baki. Jin tsayuwar ya isheta gakuma nauyin kayan jikinta yasata fara takawa tanufi matattakalar benen datagani daga gefen dama. Ahankali taita taka mattatakalar harta kai sama. Dakuna uku ke saman ajere. Tsayawa tayi tana kallonsu tana tunanin wane ne nata. Tsaki taja cikin takaici, wai ace Amarya ke Neman dakinta, kai gaskiya dad ya cuceta, kwata kwata ba haka ta tsara aurentaba, ta Dade tana qiyasta yadda rayuwar auren ta zai kasance, ta jima tana qiyasta yadda auren ta zai zama abun koyi da burgewa ga mutane da dama, amma rana daya an rusamata tsari. Jitayi ankece da ruwan sama kamar dabakin qwarya. Ajiyar zuciya ta sauke sannan tanufi dakin farko, tana murdawa taji gamm. Tsaki tasake ja ta nufi ta tsakiyar, tana murdawa taji tabude. Tsayawa tayi tana kokwanton shiga don bata fatan ganin fuskarshi nan kusa. Fasa shiga tayi tanufi ta ukun ta murda taji itama gamm hakan yasata dawowa ta tsakiyar badon tasoba. Tura kofar tayi ahankali sannan tashiga a darare. Saida ta leqa koina ta tabbatarda babu kowa aciki sannan hankalinta yakwanta. Maida kofar tayi tarufe harda saka sakata sannan tadawo cikin dakin Nanma kamar falo an narkar da naira wajen qawatashi don Italy bed ne haddade da closet daya kusan cinye bango daya, sai mirror na bango ga saman dressing mirror din shaqe da mayyuka da turarruka kamar bana mutum dayaba. Agefe gefen gadon bedside locker ne masu daukeda lamps Daga haggu kuma koface Wanda ko ba'a fadamaka ba kasan toilet ne. Agajiye tafara rage kayan jikinta, saida yarage daga ita sai undie sannan tanufi toilet din. Nanma fadin haduwarshi 6ata time ne, dukda agajiye take hakan besata tsayawa qarewa toilet din kalloba. Tara ruwan dumi tayi a jacuzzi sannan ta hada mayyukan wanka wa'inda duk yanzu ta fasasu cikin ruwan sannan tashiga. Ta Dade cikin ruwan saboda dadinsu don harta fara gyangyadi sannan tafito ta jawo wani baby pink din towel dake gefe hange. Tadaura sannan ta FASA sabon brush ta matsa MacLean tayi brush daganan tayi alwala tafito. Wata doguwar night gown tasaka ta zura hijabi ta haye sallaya Wanda dama already a shimfide take a kusurwar dakin tayi nafila biyu. Ta Dade zaune tana kwararo addu'o'i sannan ta shafa tamike ta cire hijabin tanufi gadon don bacci ke idanunta sosai. Kashe fitilun dakin tayi ta kunna bedside lamp don bata iya kwana cikin duhu sannan tashige cikin bargo ta quddundune tana sauraron saurin saukar ruwan saman Wanda kesata nishadi. Dama ita masoyiyar damina ce, tana bala'in son ruwan sama musanmman na dare, tana jindadin yin barci ana ruwan sama. Bata wani Dade akwanceba wani nauyayyen barci mai dadi yayi gaba daita. A bangaren ango kau dama yana shiga yacire babbar rigar don ba qaramin takuramashi tayiba. Direct toilet yashige don wanka. Koda yafi to kayan barci kawai yasa ya hada coffee da coffee maker dake dakin ya zauna yana kur6a hankali kwance kamar be baro diyar mutaneba awaje. Yana cikin sha aka kece da ruwan sama sai a sannan tunaninta yafado mashi. Ta6e baki yayi yacigaba dashan coffee dinshi har yashanye. Yana gama yashige cikin bargo shima ya kwanta don shima yana son ruwan dare sosai. Shima be jimaba barci ya daukeshi Asuba tagari ma'auratan kwangila😴 Manage please🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ja yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu🤲 Karka barmu dakanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 032 Kiraye kirayen sallar asuba ya tadata, bude idanunta daketa faman rufewa dakansu tayi tana hamma da alamu dai barcin be ishetaba. Tashi tayi zaune tana miqa tana salati Dafarko taso yin dimuwa don ta mance da inda take, tashi tayi tanufi toilet don dauro alwala. Rakka'atainul fjr tafarayi sannan tayi sallar asuba. Sannan tazauna tafara laziminta nasafe. Ba ita ta tashi ba saida gari yafara haske. Komawa tayi kan gadon ta dasa barcin don rabonda tasamu cikakken barci harta manta. Sai wajajen qarfe goma ta farka dawata azabattaciyar yunwa. Rabonta da abinci tun farfesun da Matar kawunta tasata ci jiya da hantsi, bataci komai ba darana da daddarema haka. Miqewa tayi akasale ta sauko daga kan gadon tanufi bathroom. Takusan mintuna talatin saigata tafito da daurin blue towel a qirji. Dressing mirror tanufa tayi shafa Wanda daga lotion sai powder data bursinama fuska sai eyeliner datayi lining din idanu sai mascara data taje gashin idanu. Gown din data cire jiya da jallabiyar datayi sallah yau ta linke ta bude closet tasaka sannan taciro wata doguwar Riga ta atampa mai kalar dark green da yellow tayi daurin kallabin turban. Kalkade dakin tayi ta gyara zanen gadon sannan ta share dukda bawani datti tayiba sannan ta kunna burner bayan tasa turaren wuta mai qamshi. Toilet tashige nanma ta gyarashi tsaf ta goge qasan da air freshner sannan tadawo dakin. Zama tayi gefen gadon tana Dan dafa cikinta dake katsamata. Yunwa takeji amma batason sauka don batason haduwa dashi. Tadan jima kadan tana zaune taji ana danna doorbell. Kasa kunne tayi taji ansake dannawa, shiru tayi taji kozai fito yaduba amma saitaji hanata dannawa. Tashi tayi ta zari wata farar hijabi tasaka Tadan fesa turare sannan tafita. Ahankali ta sauko zuwa falon Wanda duk azatonta yana ciki. Ganin wayam yasata dakin ajiyar zuciya ta ida qarasawa ga kofar tana fadin "Ana zuwa" Koda tabude kofa wata budurwa tagani riqeda basket tanamata murmushi. Itama maidamata murmushin tayi tana cewa "sannu, kishigo please" "A'a aunty juyawa zamuyi ai, ina kwana" "Lfy lau, ya kike?" "Lfy lau dama hajiya tace akawo break" tafada tana miqamata basket din hannunta. "Allah sarki, Ummi harda dawainiya? To mungode please kice muna godiya kuma muna gaidata" "Insha Allah aunty" "Ina baby?" "Hhhh tanacan tana kumbure kumbure an hanata biyoni" Dariya tadanyi "Kai itama Ummy data barta tazo" "Cewa tayi damunku zatayi saidai nan gaba" Murmushi saudart tayi tace "to Allah yakaimu, ki gaidamana su duka" "Insha Allah sai anjima" inji yarinyar tana juyawa. Maida kofar tayi tarufe sannan tashigo da basket din falo. Dining area dake daga gefen haggu tanufa ta Dora basket din saman table din sannan ta fiddo kayan ciki. Flask ne shaqeda kunun gyada sai kulolo biyu. Daya na dankali da kwai sai dayan na farfesun yan ciki. Kallo daya tayi musu yawunta ya tsinke. Maidawa tayi tarufe sannan takoma bakin kofa ta budeta ahankali tana leqowa. Parking space ta hanga wayam Wanda hakan ke nufin yafita. Komawa tayi falon tajawo kofar sannan tacire hijabinta tanufi kitchen. Sakin baki tayi ganin dukiyar da aka narkamata a kitchen din, an cika kitchen din da kayan kitchen nagani nafada ga kayan electronic, su ovens, deep freezers, toaster dadai sauransu. Jiki a sanyaye ta qarasa inda ake ajiye su plates, cups da bowls. Wani bowl ta dauko mai kyau na tangaran da Kofi sai cokali da fork. Wajen wanke wanke taje ta daurayosu sannan ta dawo dining din. Kunun gyadan tazuba a kofin sannan tazuba farfesun cikin Dan bowl din sannan tafara ci. Sosai abincin yayimata dadi don taci sosai musanmman kunun gyadan. Koda tagama, tattara abubuwan data 6ata tayi taje ta wankesu ta maidasu ma'ajinsu sannan ta dawo falon Tadan kakka6eshi shima ta kunna burner ta hayewarta sama. Tana shiga dakin wayarta daketa faman ringing na katsewa, da sauri tanufi wayar ta dauka taga har 5missed calls Kafin ta duba masu kiran wani kiran yasake shigowa. Da sauri tadaga cikin murna "Dad.." "Shalele?" "Wayyo daddy na I missed you" tafara cikin muryar kuka "Haba shalele you know I miss you too" "Dad nidai kazo katafi dani please" tafada a shagwa6e Dariya yadanyi kafin yace "Shalele duka fa yau kwananki daya" "Nasani Dad, nidai kawai kazo katafi dani please" tafada hawaye na taruwa a idanunta "Shikenan zanzo kinji? Karki damu your dad is always with you okay?" "Dagaske zakaxo?" "Nayi alqawari, hope dai babu matsala?" "Babu komai dad" "Good, kicigaba da hqr insha Allah komai zai warware very soon okay?" "Ok dad" Nan suka Dan ta6a fira kafin suyi sallama. Sunayin sallama ta lallubo number mamy datagani cikin missed call dinta. Ringing biyu aka daga. "Mamyy!!" Tafada da qarfi tana dalle gadon Tsaki mamy taja fuskarta fall murmushi "Zaki kashemin kunne ne?" "Kai mamy bafa ihu nayi ba, kawai I miss you ne" tafada a shagwa6e "Kyaji dashi, dama su Abdul ne suka addabeni saina kiraki sunmaki mgn, gaki gasu" Nan ta miqamusu wayar, nanfa aka bude babin fira kowa da labarin dazaibata, itama tana biyemusu, daga qarshe suka cemata ta roqi mamy tabari suzo don tahanasu. Koda mamy ta amshi wayar saudart ta gwada roqon mamy din tabari suzo taqi yarda tace takuramasu zasuyi da hayaniya sai nanda sati. Sudan ta6a fira da mamyn inda a hikimance take fadamata yadda zata kula da kanta don ita a tunaninta jiya oga Ashraf ya kashe boss😂 Itadai saudart jinta kawai harta gama sannan sukayi sallama Tana katse kiran kiran baby na shigowa. Murmushi tayi ta jingina da kan gadon sannan ta dauka "Halloo" "Yee! Matar yayana!!" Tafada cikin ihu Tsaki saudart taja "Wuhh saikin dodemin kunne sannan?" "Hhhh bazaki gane bane aunty, jiya na wataya gidan nan yauma haka, gaskiya Allah yabiyaki, kin rabamu da takuratu, Allah yaqara danqon love tsakaninku" tafada cikin sigar shaqiyanci "Hmm Allah ya shiryaki baby, don kekam saida addu'a kuma ki qaddara a kunnenshi kikayi wannan maganar don saina gayamashi" Zaro idanu baby tayi daga can bangaren "Rufamin asiri aunty, karkija yace inzo inmaki zaman daki, ca6 Dana bar garin Allah" Dariya sosai saudart tayi tace "Kije ina?" "Koina ma, ai yayi can tunda dai mun rabu lfy, nahuta da muguntarshi da punishment, ingayamaki akwai ranar da don mugunta yasani share backyard da tsirin hakkin tsintsiya uku. Wlh na yini ina share wajen, quguna kamar zai cire" Dariya sosai saudart tayi kafin tace "Dagaske? Hakkin tsintsiya uku? Lallai" "Wlh kau, ai kekam Allah ya kashe yabaki, aini kadai nasan halin yaya, kana kallon yar fuskarnan tashi uwa ta mage kamar bazai iya cizon yatsarkaba idan kasamashi, mugun mugunta ke cikeda qaramin kan nan, wlh mata masu binshi suna sonshi mammaki suke bani, basusan kyan Dan maciji ke gareshi ba ga kyau ga sari, ni kinmafi bani tausayi, kidaibi asannu kar wata rana muzo ziyara mu yadda Matar yaya na sare ciyawa da reza" Dariya sosai saudart keyi harda dafe ciki don sosai tabata dariya "A'a wannan saiku, ni saidai inbashi punishment badai yabaniba" "Inyee! Kai Allah ya tsinewa love, soyyaya maida sarki bawa, mai maida mai taurin kai solo6iyo, gaskiya ina bayan ki aunty, ki murza kabunki dakyau, ki rarramamin muguntar dayayimin" "Hmm yaushe zakizo?" Tafada cikin son canza aqalar maganar Shagwa6ewa baby tayi "Ba Ummy bace tahanaba? Wai zan takuramuku?" "Kumafa hakane, Gwara karkizo yanzu takuramana zakiyi" Waro idanu baby tayi "Hakama zakice? Ba komai zan ramane" "Zaki dai rame, bari in daga kiran wadannan mayyun kafin su lasheni" "Laa su waye?" "Qawayanki mana, yawuce su mardeeya?" Dariya baby tayi tace "To anty zan kiraki anjima" "To Allah yakaimu agaidasu Ummy" "Bazata jiba, idan kin matsu ki kirata ko kizo, bayan ta hanani zuwa kuma sai kiwani aikeni wajen ta, kifadawa wadda takawo muku breakfast din ta gayamata" "Tofa? Haka akayi?" "Eh din" tafada tareda kashe wayar tana dariya. Dariya itama saudart tayi tana girgiza kai. Kiran nafeesa yasake shigowa wayar. Dagawa tayi tana cewa "Tuff tuff kuci kanku, namana daci" Ihu suka saka suna callara gud'a Wanda har saida Tadan kauda wayar daga kunnenta. "Kunga amaryar handsome bada kanki asare Kije gida kice yafadi, amarsu ta ango, kinsha madara, kina cikin shan madara, zakisha madara" inji nafeesa cikin shaqiyanci. Tsaki taja tace "Kunga idan vakuda magana mai ma'ana zan ajiye waya kun dameni da kira kamar Wanda akaba ajiyar qodarku na dauka kuma zaku toshemin kunne" "Inyee, amaryar baa? Irin anyi auren nan ba'a son wulaqanci ko?" Inji mardeeya "A to, me yafi raina? Ai kuma kanku kunsan akwai banbanci" tafada cikin sigar tsokana. "Mukau mukasan da banbanci tunda kema kinsha madarar lilo, wai yama naji muryarki garas? Ko yar shaqewarnan batayiba?" Inji nafeesa "Uban me zai shaqeta to?" "Ihu mana, jiya nasan ankira sunana wajen naiman dauki... Wayyo Allah nafeesa Dan Allah kizo ki ceceni, mardeeya! Wayyo yar uwa kizo ki kawomin dauki! Mamy! Wayyo Allah na! Kabarni haka yaya, zafi! Dan Allah kabari na tuba, akwai zafi, zan..." Diff saudart ta katse kiran cikin tsananin kunya da takaici. Lallai iskancisu nafeesa sai an hada da addu'a, kwafa tayi tana yin cilli da wayar tsakiyar gadon sannan tamiqe don dauro alwalar azahar Wanda har anfara kira. Koda tagama Dan kishingidawa tayi ta jawo wayarta ta bugama yan bakery dinta, sundan Dade suna magana sannan sukayi bankwana. Qarar doorbell miqewa, saida ta leqa ta windonta taga babu motar parking space sannan ta sauko, yanzu ma abinci aka aikomata daga wajen Ummy. Godiya tayi ta amsa ta zauna ta take cikinta sannan ta haura da sauran sama. Ataqaice haka tayini ita daya, saidai tayi game ta gyara dakin dukda ba datti tayiba don kwanciyar ta isheta, abunka da bata sababa. Sai can wajajen taran dare taji dawowarshi. Ta6e baki tayi tana cigaba da jera kayan ta a closet dukda ba'a yamutse sukeba, kawai Rashin aikinyi yasata fiddosu tasake musu sabon shiri. Ba ita ta kwantaba sai wajajen goman dare...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan cuts (covid19)🤲 Allah kabamu zaman lfy a qasarmu🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 033 Washegari ma bata fitoba saida ta tabbatar da yabar gidan, sannan tafito ta samarma kanta abinda zataci ta gyara gidan ta goge Tass ta saka turaren wuta sannan tayi hayewarta sama. Ba ita ta saukoba sai bayan azahar ta nufi kitchen ta Dora abinda zata sakama cikinta sannan ta gyare kitchen din ta tattara abincin tayi sama. Yauma sai wajajen qarfe Tara ya dawo gidan, kamar jiya beko ni takan dakintaba yayi shigewarshi dakin shi. Ataqaice dai haka sukaita wasan 6uya tsakaninsu, koko ince take wasan 6uya dashi don izuwa yanzu ta laqaici lokacin fitarshi da dawowarshi don haka ta rage zaman sama, tana saukowa qasa ta yini amma da tayi sallar isha'i kuma ita da saukowa sai Allah ya kaimu kuma. Tanada kwana biyar su mardeeya su kazo harda baby don biyamusu tayi su kazo tare. Ranar kau saudart taga ta kanta don tisata gaba sukayi da tsokana iri iri. Tun tana maida martani harta haqura, ita kau baby wani sa'in ta shigarmata wani sa'in ta koma masu Nafeesa su tararmata. Basu suka bar gidanba sai qarfe shidda da Rabi na marece bayan ta cikasu da kyauta na kayan kwalliya da snacks ta rakosu har wajenda motar baby take don aciki su kazo. Jitake kamar tabisu don zaman kadaicin ya isheta gashi tayi missing din daddynta sosai dukda kullum cikin waya suke. Ahaka sukayi bankwana cikin mararin juna saudart na musu addu'ar Allah ya tsare kasancewar su mardeeya gobe zasu koma Maiduguri. Ba ita takoma cikiba saida taga fitarsu. Bin harabar gidan tayi da kallo don yau ne karon farko data fito harabar tun zuwanta. Bin wajen taitayi da kallo don ya qayatu iya qayatuwa ga trimmed flowers daya zagaye wajen gwanin burgewa. Ta6e bakinta tayi ta jiya ta koma ciki don har anfara kiraye kirayen sallar magrib. Yauma kamar kullum tana bata sake saukowa ba bayan isha'i. Kwanci tashi yau kwananta sha bakwai a gidan. A yanayin zamantakewarsu babu wani chanji don rabonda Susa juna a idanu tun ranar auren su. Izuwa yanzu saudart tasake da gidan sosai babu inda bata saniba agidan. Akwai komai agidan kama daga abinci da kayan more rayuwa. Saidai tana cikin kadaici sosai, kullum ita kadai ke yini inba Allah yajefo mata wani baqoba, wani sa'in don debe kewa saita shiga garden dake bayan gidan don hutawa ko ta zauna falo tayi kallo. Bakery dinta kau kullum tana samun bayanai akan yadda yake tafiya kuma alhamdullilah sai bunqasa yake. Haka zalika kusan kullum sai sunyi waya da Ummy don izuwa yanzu tana Sakin jiki daita su danyi fira kasancewar Ummy batada matsala kuma tana sonta sosai don saudart badai hankali da nutsuwaba. Wani sa'in idan kadaici ya isheta saita bugama Ummy ta roqeta akan baby tazo. Duk zuwan da baby keyi bata yarda takai magrib take juyawa, saudart tasha yimata tayin kwana amma firr take qiyawa wai in taganta lahira kaita akayi. A bangaren ashraf kuwa tuni yakoma bakin aikinsa, dama hutun sati daya ya dauka, shima saboda matsawar sadeeq. Shi harga Allah wani sa'in mancewa yake da yanada mata, rabonda yasata a idanu tun awajen dinner. Yasan haqqinshine yasan yaya take ciki dakuma kula da lafiyarshi amma bejin yana iya zuwa ganinta, aganinshi ai ba normal aure bane auren su, auren kwangila ne kowa da dalilinshi nayin auren kuma kowa da abinda yake targeting. Jera abinci take bisa dining tanayi tana kada kai tana humming tana bin waqar datakeji ta earphones din kunnenta. Saida ta shirya komai a table din sannan tayi sama tana Dan hadawa da tsalle tsalle Wanda duk acikin shauqin waqar datake jine. Tana shiga tacire earphones din kunnenta ta fara tu6ewa don watsawa don yau garin badai zafiba, yadda akayi rana yau dakyar idan ba ruwan sama za'ayi ba. Tana gama ty6ewa ta dauki towel ta daura tashige toilet. Horn yayi sau daya, nan aka shiga scanning din motar, bayan angama gate din ya wangale dakanshi ya kutsa kai yashiga. A parking space yayi parking sannan yafito ya rufe kofar yayi locking din motar sannan yanufi cikin gida yana sassauta daurin necktie dinshi. Murda handle din kofar yayi yashiga da sallama, kamar kullum, yauma wannan sanyayyar qamshin da harya fara kama dakin yayi mashi maraba. Shaqa numfashi yayi ahankali sannan ya fesar, yau qamshin na dabanne don bayan na Wanda dakin yasabayi akwai wani kuma daban Wanda yakasa tantancewa. Stairs yanufa cikin takunshi na qasaita yana hawa daya bayan daya harya isa sama. Yauma kamar kodayaushe ko kallon saitin kofar beyiba ya bude kofar shi yashige. Kasancewar tana toilet tafara wanka duk bataji shigowarshi ba, hasalima tasan lokacin dawowarshi don haka bata kawoma ranta dawowarshi yanzu ba. Bayan yan mintuna tafito jikinta na digar ruwa, wucewa tayi closet direct don ga yadda ake zafinnan batajin zata iya shafama jikinta komai. Budewa tayi ta tsaya hannaye riqeda kugu tana bin kayanta dake Jere gwanin kyau da kallo tana shawarar wanne yakamata tasaka. Ta Dade tana ruwan ido kafin taciro wani three quarter din wando gari mai adon pink din zare a gefe gefen wandon sai mahadinshi wato armless pink vest mai zanen yar Tamar Barbie agaba sannan ta Parke gashinta tsakar kai tayi doughnut dashi sannan tasa wata farar hula marar nauyi. Turare kawai ta fesa sannan tazura wasu pink baby shoes ta maida earphones dinta ta dauki wayarta tafita. Harta zauna zata fara serving kanta taji tana sha'awar local lemu, tunawa tayi da lemun tamarin datagani dazu a group, ganin beda wuyar yi yasata tashi tashiga kitchen din don hadoshi. Tana shiga yafito daga dakin cikin shigar qananun kaya ba Adidas. Hannunshi daya cikin aljihu dayan kuma riqeda wayar dake kareda kunnenshi alamun waya yake. A daya daga cikin qayyatatun kujerun falon ya zauna yayi irin balancing dinnan kamar wani Dan sarki ya Dora hannunshi dake cikin aljihu bisa kan kujerar yana cigaba da amsa wayar. Cikin takunta tafito, hannunta daya riqeda wani haddaden jug, dayan kuma riqeda Glass cup. Dining tanufa batareda takawoma ranta komai ba. Serving din kanta tayi cikin plate sannan ta zuba drink din a glass cup tasaka straw aciki sannan ta zauna ta dauki spoon and fork tafara cin abincin cikin nutsuwa. Tun fitowarta ya bar gane abinda ke wakana a wayar dasuke, da ido yabita tunda tafito har ta isa dining din. Da farko kasa ganeta yayi, saida ta zauna tana facing dinshi sannan ya wayeta. Kasa dauke idanu yayi akanta, duk wani motsi nata akan idanunshi, yadda kukasan anhada magnet tsakanin idanunshi da jikinta don kallonta yake bako kyaftawa. Ita kau a bangarenta batamasan yanayiba don kwata kwata bata kawowa ranta da wani agidan bayan itaba, dukda tana jin alamun idanu akan ta amma bata maida hankali akaiba. Ringing din wayarta yasata ajiye glass cup din datake tsotsar drink din ta dauki wayar tana duba mai kiran. Ganin daddy ke kiran yasata katse kiran tana murmushi sannan tasake Kira. Ta kara a kunne fuskarta fall murmushi sannan ta dauki cup din takai baki tana kur6a. Kamar ance ta dago, sai caraf idanunshi suka hade. Wani wawan zuwa tayiwa lemun abinka da tsamiya nan take tahaumata bisa kai tafara tari cikin fitar hayyaci Wanda har tana saukowa qasa...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan cuts (covid19)🤲 Allah kabamu zaman lfy a qasarmu🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 033 Washegari ma bata fitoba saida ta tabbatar da yabar gidan, sannan tafito ta samarma kanta abinda zataci ta gyara gidan ta goge Tass ta saka turaren wuta sannan tayi hayewarta sama. Ba ita ta saukoba sai bayan azahar ta nufi kitchen ta Dora abinda zata sakama cikinta sannan ta gyare kitchen din ta tattara abincin tayi sama. Yauma sai wajajen qarfe Tara ya dawo gidan, kamar jiya beko ni takan dakintaba yayi shigewarshi dakin shi. Ataqaice dai haka sukaita wasan 6uya tsakaninsu, koko ince take wasan 6uya dashi don izuwa yanzu ta laqaici lokacin fitarshi da dawowarshi don haka ta rage zaman sama, tana saukowa qasa ta yini amma da tayi sallar isha'i kuma ita da saukowa sai Allah ya kaimu kuma. Tanada kwana biyar su mardeeya su kazo harda baby don biyamusu tayi su kazo tare. Ranar kau saudart taga ta kanta don tisata gaba sukayi da tsokana iri iri. Tun tana maida martani harta haqura, ita kau baby wani sa'in ta shigarmata wani sa'in ta koma masu Nafeesa su tararmata. Basu suka bar gidanba sai qarfe shidda da Rabi na marece bayan ta cikasu da kyauta na kayan kwalliya da snacks ta rakosu har wajenda motar baby take don aciki su kazo. Jitake kamar tabisu don zaman kadaicin ya isheta gashi tayi missing din daddynta sosai dukda kullum cikin waya suke. Ahaka sukayi bankwana cikin mararin juna saudart na musu addu'ar Allah ya tsare kasancewar su mardeeya gobe zasu koma Maiduguri. Ba ita takoma cikiba saida taga fitarsu. Bin harabar gidan tayi da kallo don yau ne karon farko data fito harabar tun zuwanta. Bin wajen taitayi da kallo don ya qayatu iya qayatuwa ga trimmed flowers daya zagaye wajen gwanin burgewa. Ta6e bakinta tayi ta jiya ta koma ciki don har anfara kiraye kirayen sallar magrib. Yauma kamar kullum tana bata sake saukowa ba bayan isha'i. Kwanci tashi yau kwananta sha bakwai a gidan. A yanayin zamantakewarsu babu wani chanji don rabonda Susa juna a idanu tun ranar auren su. Izuwa yanzu saudart tasake da gidan sosai babu inda bata saniba agidan. Akwai komai agidan kama daga abinci da kayan more rayuwa. Saidai tana cikin kadaici sosai, kullum ita kadai ke yini inba Allah yajefo mata wani baqoba, wani sa'in don debe kewa saita shiga garden dake bayan gidan don hutawa ko ta zauna falo tayi kallo. Bakery dinta kau kullum tana samun bayanai akan yadda yake tafiya kuma alhamdullilah sai bunqasa yake. Haka zalika kusan kullum sai sunyi waya da Ummy don izuwa yanzu tana Sakin jiki daita su danyi fira kasancewar Ummy batada matsala kuma tana sonta sosai don saudart badai hankali da nutsuwaba. Wani sa'in idan kadaici ya isheta saita bugama Ummy ta roqeta akan baby tazo. Duk zuwan da baby keyi bata yarda takai magrib take juyawa, saudart tasha yimata tayin kwana amma firr take qiyawa wai in taganta lahira kaita akayi. A bangaren ashraf kuwa tuni yakoma bakin aikinsa, dama hutun sati daya ya dauka, shima saboda matsawar sadeeq. Shi harga Allah wani sa'in mancewa yake da yanada mata, rabonda yasata a idanu tun awajen dinner. Yasan haqqinshine yasan yaya take ciki dakuma kula da lafiyarshi amma bejin yana iya zuwa ganinta, aganinshi ai ba normal aure bane auren su, auren kwangila ne kowa da dalilinshi nayin auren kuma kowa da abinda yake targeting. Jera abinci take bisa dining tanayi tana kada kai tana humming tana bin waqar datakeji ta earphones din kunnenta. Saida ta shirya komai a table din sannan tayi sama tana Dan hadawa da tsalle tsalle Wanda duk acikin shauqin waqar datake jine. Tana shiga tacire earphones din kunnenta ta fara tu6ewa don watsawa don yau garin badai zafiba, yadda akayi rana yau dakyar idan ba ruwan sama za'ayi ba. Tana gama ty6ewa ta dauki towel ta daura tashige toilet. Horn yayi sau daya, nan aka shiga scanning din motar, bayan angama gate din ya wangale dakanshi ya kutsa kai yashiga. A parking space yayi parking sannan yafito ya rufe kofar yayi locking din motar sannan yanufi cikin gida yana sassauta daurin necktie dinshi. Murda handle din kofar yayi yashiga da sallama, kamar kullum, yauma wannan sanyayyar qamshin da harya fara kama dakin yayi mashi maraba. Shaqa numfashi yayi ahankali sannan ya fesar, yau qamshin na dabanne don bayan na Wanda dakin yasabayi akwai wani kuma daban Wanda yakasa tantancewa. Stairs yanufa cikin takunshi na qasaita yana hawa daya bayan daya harya isa sama. Yauma kamar kodayaushe ko kallon saitin kofar beyiba ya bude kofar shi yashige. Kasancewar tana toilet tafara wanka duk bataji shigowarshi ba, hasalima tasan lokacin dawowarshi don haka bata kawoma ranta dawowarshi yanzu ba. Bayan yan mintuna tafito jikinta na digar ruwa, wucewa tayi closet direct don ga yadda ake zafinnan batajin zata iya shafama jikinta komai. Budewa tayi ta tsaya hannaye riqeda kugu tana bin kayanta dake Jere gwanin kyau da kallo tana shawarar wanne yakamata tasaka. Ta Dade tana ruwan ido kafin taciro wani three quarter din wando gari mai adon pink din zare a gefe gefen wandon sai mahadinshi wato armless pink vest mai zanen yar Tamar Barbie agaba sannan ta Parke gashinta tsakar kai tayi doughnut dashi sannan tasa wata farar hula marar nauyi. Turare kawai ta fesa sannan tazura wasu pink baby shoes ta maida earphones dinta ta dauki wayarta tafita. Harta zauna zata fara serving kanta taji tana sha'awar local lemu, tunawa tayi da lemun tamarin datagani dazu a group, ganin beda wuyar yi yasata tashi tashiga kitchen din don hadoshi. Tana shiga yafito daga dakin cikin shigar qananun kaya ba Adidas. Hannunshi daya cikin aljihu dayan kuma riqeda wayar dake kareda kunnenshi alamun waya yake. A daya daga cikin qayyatatun kujerun falon ya zauna yayi irin balancing dinnan kamar wani Dan sarki ya Dora hannunshi dake cikin aljihu bisa kan kujerar yana cigaba da amsa wayar. Cikin takunta tafito, hannunta daya riqeda wani haddaden jug, dayan kuma riqeda Glass cup. Dining tanufa batareda takawoma ranta komai ba. Serving din kanta tayi cikin plate sannan ta zuba drink din a glass cup tasaka straw aciki sannan ta zauna ta dauki spoon and fork tafara cin abincin cikin nutsuwa. Tun fitowarta ya bar gane abinda ke wakana a wayar dasuke, da ido yabita tunda tafito har ta isa dining din. Da farko kasa ganeta yayi, saida ta zauna tana facing dinshi sannan ya wayeta. Kasa dauke idanu yayi akanta, duk wani motsi nata akan idanunshi, yadda kukasan anhada magnet tsakanin idanunshi da jikinta don kallonta yake bako kyaftawa. Ita kau a bangarenta batamasan yanayiba don kwata kwata bata kawowa ranta da wani agidan bayan itaba, dukda tana jin alamun idanu akan ta amma bata maida hankali akaiba. Ringing din wayarta yasata ajiye glass cup din datake tsotsar drink din ta dauki wayar tana duba mai kiran. Ganin daddy ke kiran yasata katse kiran tana murmushi sannan tasake Kira. Ta kara a kunne fuskarta fall murmushi sannan ta dauki cup din takai baki tana kur6a. Kamar ance ta dago, sai caraf idanunshi suka hade. Wani wawan zuwa tayiwa lemun abinka da tsamiya nan take tahaumata bisa kai tafara tari cikin fitar hayyaci Wanda har tana saukowa qasa...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka wanzar da zaman lfy a qasata qasarmu Nigeria🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 033 Wani irin zabura yayi, besan yaya akayi ba kawai sai ganinshi yayi tsugunne gabanta yana riqota batareda saninshiba. Dukda yanayin datake ciki hakan be hanata jin wani Yarr daga kanta zuwa yatsan kafartaba. Ganin yana qoqarin rungumo yasata kwacewa da karfi da kingin qarfin ta, taja baya tana cigaba da tarin. Hannu tamiqa saman table din ta rarumo Goran ruwa ta 6alle murfin ta kafa Kai. Ahankali ta sauke Goran tana kallonshi da jajjayen idanunta dauka fara d'urar ruwa sanadiyar qwarewa datayi. Shikau mutuwar tsuggune yayi, ko kwakwaran motsi yakasa. Yama rasa yadda akayi yazo har gabanta harma ya ta6ata. Wani matsanancin kunya da takaici ya qumeshi kamar ya nitse a qasa. Ganin yadda take kakkare jikinta yasashi binta da wani matsiyacin kallon up and down mai nuna alamun 'mezan gani anan' sannan yaja tsaki yamiqe yajuya, fuuu yabar falon dama gidan gabadaya. Binshi da idanu tayi harya fita daga falon, zuciyarta inbanda aikin bugu babu abinda take. Ta Dade a tsugunne batareda tadawo normal ba saida taji wayarta na ringing sannan tadan farfado. Tashi tayi dakyar don haryanzu jikinta na Dan rawa rawa, ta dauki wayar a inda ta fadi qasa ta zauna saman kujera sannan ta daga. "Shalele?" "Dad.." "Kin kirani na daga kuma ta yanke, nayita bugowa kuma babu amsa" Shiru tadanyi tana qoqarin daidaita muryarta. "Dad am sorry, baqi nayi shine nayi attending dinsu" tafada muryarta still na Dan rawa rawa. "Ok, amma yanakejin muryarki wata kala? Are you okay?" "Y..yes dad, kaina ke Dan ciwo" "Subhanalillah, kinsha drugs, ko nazo nakaiki asibiti?" "No dad, am okay, nasha Dana kwanta zanji sauqi" "Ok Kije ki kwanta, zan bugo later akwai maganar dazamuyi" "Alright dad" Datse kiran tayi tana Sakin ajiyar zuciya. Haryanzu takasa yarda da abinda yafaru dazu, wai yaushe ma yadawo gidan bata saniba? Allah kadai yasan tun yaushe yake zaune yana qaremata kallo. Ashe shiyasa takejin kamar ana kallonta. *idiot* tafada cikin jin haushi da takaici. Babu abinda yafi qonamata rai kamar kallon rainin daya bits dashi. Tsaki taja ta tashi tana tattare plates din dining din don abincin ma kwata kwata yafita akanta. Saida ta dauraye plates din data 6ata ta gyare saman sannan ta haye da niyyar ita da zama qasa kuma har abada saidai ta sauko tayi abinda zatayi ta haye sama. Kwance take rigingine akan gado fuskarta na kallon ceiling saidai idanunta a lumshe suke amma ba barci take ba don duk abinda Beebah ke fadi duk a kunnenta ne. Saida takai aya sannan ta numfasa ta kalli suzyn dake kwance tundazu kamar mai barci. "Toyaya kikaji tsarin?" Kamar bazata motsaba sai can ta saki ajiyar zuciya tana bude qananun idanunta akan fuskar Beebah sannan ta motsa la66anta dakyar tace "Kenan duk wannan shirin da kike lissafowa duk inanan ina sagale da baki ina ganin su a tare za'ayi shi? You don't get me Beebah, banaso, vanason inwayi gari da tunanin my man tareda kowacce irin tsinnana, I want him for me, me alone, bazan iya jira harna tsawon lokacin da kike cewaba, na tabbata izuwa lokacin zuciya ta tariga da ta tarwatse" Zama Beebah tayi bakin gadon kusada ita tana cewa "Suzy, wannan itace kadai mafita, ya kike magana kamar batareda ke mukaje wajen ta ba, kamar bakiga yanayinta ba, yarinyar nan yar barikice, tasan takan barikanci, kalamanta ma sun nuna hakan, kawai zuru ne zaici zuru, ta hanyar data biyomana tanan muma zamu bida ita, ashraf nakine ke kadai, kisa wannan a ranki" tafada cikin qarfafa gwiwa. Haka taita lallaminta harta samu nasarar bida ita hanyar datakeso, bata bartaba har saida taga ta dorata akan abinda sukeson cimmawa. Yau kwana biyu da faruwar wannan al'amari tsakanin Ashraf da saudart. Basu sake haduwaba don kowa yasake Jan baya da Dan uwanshi fiyeda da. Ita tabar dadewa a qasa shi kuma yabar dawowa dawuri. Don haryanzu kowanne cike yake da takaicin abinda yafaru ranar. "Dad, I really need to get back to my work, I can't take it anymore, kullum ni kadai acikin gida kamar mayya? Nidai zanyi resuming on Monday, nagaji ai wannan deal din maku be shafi aikinaba, so am resuming" tafada cikin yanayin jin haushi don jitake kwata kwata ta tsani zaman gidan. "Ban qi ta takiba shalele, it's normal idan kikayi resuming amma baki tunanin yakamata kiyi advancing din profession dinki? A matsayinki na Matar A.A be kamata ace kina zuwa bakery ba da sunan aiki, it's embarrassing" Jim tayi tana sauraron daddy tana jin maganganun nashi wani bambarakwai musanmman *Matar A.A* daya ambata. "I don't get you dad" tafada cikin Rashin fahimta. Gyara zama dad yayi a bangarenshi yana murmushin samun nasara. "Abinda nake nufi shine, tunda kinada bakery kuma kina iya gudanar dashi ko kina nan ko bakya nan, why not kisamu wani aikin daban da takardunki?" Jimm tayi tana sauraron daddyn lokaci daya kuma kwakwalwarta na nazari akan maganarshi. Katsemata tunani yayi da cewa "Kinga zakifi samun kudi, ga na bakery ga salary, nima nan am trying my best, kinga saimu hadu mu hada qarfi wajen hada kudin mijinki mu biya a warware komai kowama ya huta" Shiru tayi na yan daqiqu tana nazari akan shawarar Dad. Eh hakane, wannan shawara ce, dukda bata cika son aikin office ba tana iya daurewa tayi kodan fita daga wannan vanzar deal din marar kan gado. "Ya kikace shalele?" "Deal, saidai ta ina zan fara?" "Bakida matsala sweetheart, ba ganiba? Daddy zaiyi komai wa shalelenshi" yafada cikin fara'a. "Awnn! Thanks dad, I love you" "Love you more" Tunda suka gama wayar yaketa aikin zabga murmushi. "A.A, yanzu lokacina ne" yafada yana shafa gemunshi. "Ummy please.. Zan kawota, I promised" yafada kamar zaiyi kuka "Ni dalla tashi min, haka kake cewa kullum, sai yaushe zaka kawota din? Nida diyata ace sai an Mani rowarta? To wlh kaji na rantse gobe gobenan nakeson ganinta kaji ba gayamaka" tafada tana tureshi daga kan cinyarta. Qin daga mata cinyar yayi, data tureshi saiya koma. Itakau baby na daga can gefe akan kujera tana satar kallonsu tana ta6e baki. "Wai bazaka tashi ba saika karya ni?" Inji Ummy tana qara tureshi "Ummy please mana, wai me nayi ne?" Yafada yana qara komawa "Mekayi? I told you I want to see her kana min rowa?" "To ai Ummy magana tariga ta qare tunda har kinyi rantsuwa, you'll see her tomorrow, saiki cinyeta karki barmin ko kingi" Rankwashi tabashi lafiyyaye "Eh din zan cinyeta din, dagani" Shafa kan yake yana yamutsa fuska kamar zaiyi kuka "Kai Ummy wlh yanzu kinbar so na" "Dama, ai yanzu nabar wayata yayinka, yanzu lokacin autata ce bakaiba godai godai dakai" Kallon saitin baby yayi daketa Satan kallonsu tundazu tana qumshe dariya. Ganin zai kallota yasata saurin kawar da idanu tana duba littafin hannunta a wayance. "Ke jeki hadomin coffee" yafada yana tamke fuska. "Bazata hadoba, kaje Matar ka ta hadamaka" "Kai Ummy..." "Ke tashi kiwuce sama kaima katafi gida ka baro diyar mutane ita daya" Da sauri baby ta tashi tayi sama don dama tunda yace ta hado coffee take jinta kamar saman qaya. Haka ta tisoshi gaba har wajen motarshi riqeda kunnenshi daya shikau sai qara yake saki qasa qasa, Kai kace ba A.A bane uban yan ji dakai. Haka ta turashi mota ta rufe taja baya tana dagamashi hannu harya fice yana zum6urar baki...✍ No editing, kuyita hqr da mistake please🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka bamu zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) Note: nayi mistake a page daya gabata, page 34 ne maimakon 33 Danasa. So yanzu na 35 ne zamu tashi. Ina fans din Auren kwangila? Your comments is making me go gaga💃 Ina godiya, keep it flowing💖 Ina cigiyar sis hajara, maman twins da maman fateema, fatan suna lfy. Koko babu data ne😂 gaskiya karku badamu please, kar ayimana dariya, kufito saudart na kewarku. The page is dedicated to all Auren kwangila fans, kuyi yadda kukaga dama dashi💃💃💃💃💃 035 Tana kwance tana sliding din wayarta tana shiga da fita acikin groups don yanzu itama tafara gwanancewa a chatting don shi ke debemata kewa yanzu tunda tarage zaman qasa. Tana cikin shafe shafen taga massage yashigo na baby. Shiga tayi don gani *yeee sweat Matar yaya💃* Abinda taga ta turo kenan *hmm ina sallamar kuma?* *oops na mance, am just too happy ne wlh* *ai haka kike, yar rainin sense😒* *kai aunty wani sa'in ke joy killer ce wlh😕* Sticker dariya saudart ta tura mata *😆😆 lol, seems autar tamu farinciki, am sorry to, fesamin naji👂* *anqi din😏* *haba autaras, c'mon please🤕* *anqi din, sai kinzo zakigani, bake bace kike cewa ban iya girki ba? Gobe ki sako wani extra takalmi a jakka don saikin mance na kafarki don santi😂* Dariya saudart tayi a zahiri, sosai take jin baby har cikin zuciyarta, shirmenta da barkwancinta ba qaramin sata nishadi yake ba. *Tofa, zuwa zakiyi kiyi girki ne* *laa badai be fadamaki gobe zai kawoki ba?😳* Daga gira daya saudart tayi, cikin zuciya tana cewa 'to haka akayi?' *dagaske😳💃💃💃 yee finally! Kullum saina mashi nacin zuwa yana cewa ba yanzu ba, qila surprise zaiyimin* Ta tura tana ta6e baki tana yatsine fuska. *oops🤦‍♀ ko meyasa na fadamiki? Please karkice nafada maki👏* Murmushi saudart tayi sannan ta turamata *zanyi tunani akai😎* *please anty ta ta kaina, mata a wajen sweet Ashraf dinta, an buga dake anbarki, daga ke babu qari, kiyi Kane Kane kiyi bake bake ki wala ki sarara keda kishiya saidai kiji wai, wai dinma wai😜* Sosai saudart tayi dariyar kirarin datayimata. Haka sukayita fira har goman dare sannan suka sauka. Sosai saudart taji dadin fitar daxatayi gobe, ko babu komai zata fita ta shaqi iskar rahama. Bata Dade ba sosai barci yayi gaba daita. ******************************** Tunda gari ya waye take jiran tsammani, tasan dolene yazo yayimata maganar tafiyar amma shiru kakeji wai mallam yaci shirwa. Yau Friday so sai wajajen 10:30am yafito. Kamar kullum batareda ya kalli side dinta ba ya nufi stairs, yana tafiyarshi daya saba hannu daya cikin aljihu dayan kuma riqeda briefcase. Tabbass taji fitowarshi hakan yasata gyara zamanta tayima kofar ta quri tana jiran jin yabugo tana ayyana Jan ajin dazata yimashi kafin ta budemishi. Batayi auneba taji tashin mota. Da sauri ta miqe ta nufi window dinta dagudu saidai harya fice daga gidan. Wani Abu taji ya tokareta a wuya. Kutt.. Badai playing dinta baby tayiba? Gashi tasaka ran fita sosai, a hassle ta jawo wayarta da niyyar kiran baby sai kuma tafara tunanin me zata gayamata? Ai hakan kamar tona asirin yanayin zaman su ne. Haka takoma ta zauna cikin jin haushi da mutuwar jiki. Haka ta yini a ranar tana jinta wata suku suku daita. Tana kwance wajajen qarfe dayan rana taji ana Danna doorbell. Tsaki taja ta gyara kwanciya. Jin ba'a da niyyar bari yasata tashi ta yafa gyale ta sauko fuska babu walwala don haryanzu takasa daina jin haushi. Tana budewa tayi tozali dashi. Kallon sama da qasa tayimashi tana nazarin shigarshi. Cikin girmamawa yadan russuna. "Good evening ma'am" Bejira amsarta ba ya cigaba dacewa "Sir yace inzo inkaiki anguwa" Tsayawa tayi tana kallon shi. Lallai so yafi qarfin ya kaita shi? Hmm tafi nono fari dama batada niyyar sake ganin wannan mummunar fuskar tashi. "Ok am coming" Ta koma ciki ta rufe kofar shi kuma yakoma mota. Haurawa sama tayi da sauri don kawai saita tsinci kanta cikin farinciki. Quick shower tayi sannan tafito ta shirya cikin wani dakakken lace maroon da ratsin fari anmata style din simple Zane sa half gown mai tsaga gefe da gefe sannan tadaura kallabi style din zahra buhari ta Dora farin gyale akanta ta yafa ta dauki handbag fara takalmi ma farare, hannunta na dama daure da wrist watch fari sai zobunna. Bata wani yi kwalliyar kirkiba saidai ta shafama sexy small lips dinta maroon din janbaki Wanda yasata yin kyau sosai, feshe turare mai sanyin qamshi tayi sannan ta kwashi wayoyinta da ATM sannan tafito. Back seat ta zauna, ya tada motar suka shilla. A hanya saida tasa drivern ajiye ta wani super market ta siyama Ummy turraruka ita kuma baby kayan maqulashe sannan suka wuce. Jin horn yasa baby da tundazu tana zaune tana cika tana batsewa tayi saurin leqa wa, ganin motar daya daga cikin na Ashraf ne yasata qara la6ewa tana kallo don tsoron fitowa take don duk atunaninta Ashraf ya kawota. Ganin emeka yafito daga gaban motar ya zagayo ya budewa saudart yasata qwala wata uwar qara Wanda saida Ummy dake zaune tana duba wani littafi tsoro. Dagudu tanufi kofa ta bude tayi waje tana tsalle cikin murna. Qwaqumeta tayi cikin tsananin murna tana tsalle itama saudart rungumeta tayi cikin murna. Haka suka shiga ciki kowa fuska fall farinciki karma baby taji lbr. Cikin fara'a Ummy ta tarbe saudart ita kau tayi qasa zata gaidata tayi saurin tarota tana rungumeta. "You're welcome my dear, Allah yayimaki albarka" Sinne kai tayi tana gaidata. Amsawa Ummy tayi tana zauna daita akan kujera baby tazo ta zauna kusada ita sai washe baki take. "Wai bazaki dauko mata kayan sha ba? Kinwani maqale mata" tafada tana antayamata harara. Dariya baby tayi tamiqe ta ruga kitchen din. Daidai nan emeka yashigo da kayan datayi shopping din ya gaida Ummy a girmame ya ajiye a tsakiyar falon yafita. Fitowa baby tayi fuskarta da murmushi hannunta dauke da tray mai daukeda drinks da ruwa da snacks. Doramata tayi kan stool dake kusada kujeranta daidai nan idanunta ya sauka akan ledojin qasa. "Anty wannan fa?" "Yours" Da sauri ta jawo ledar tana murna ta bude, ganin kayan maqulashe yasata yin ihu tana rungumo saudart tana murna ummy namata fadan karta karya mata daughter. Nan taware dayan ledar ta leqa taga turrarukan tace "Wannan dai ko ba'a fadaba nasan na Ummy ne, Ummy gashi" Ta miqamata. Itama leqawa Ummy tayi tana fiddowa tana santinsu itama tana godiya. Ita kau saudart kunya ma ta kamata. Haka su kadan ta6a hira ganin kamar taqi sakewa yasa tace sutafi sama dakin baby. Aikau nanfa abun nema ya samu, hira suke kamar wasu dasukayi shekaru dama dasanin Juna Wanda duk yawanci tsokana ce. Sai bayan sallar juma@ Ummy tace su shirya akaisu gidan mamy ma. Sosai saudart taji dadin haka. Nanfa baby aka dauki wanka aka cake dankwali suka tafi. Sosai mamy taji dadin zuwansu kuma taji dadin ganin chanjin Da saudart tayi don taqara yin fresh tayi kyau. Nanfa suka baje kolin fira dasu kamal Wanda mostly da baby sukeyi sai tsokanar juna suke. Sai wajajen six suka bar gidan bayan mamy tagama kashewa saudart jiki da nasiha. Direct gidan daddy suka nifa. Nanfa baby taga tsantsar soyyaya tsakanin uba da diya, fira kau sunsha shi kamar babu gobe. Koda dasu tafi kuka taitayi dakyar ya rarrasheta yasamu suka tafi. A hanya baby sai tsokanar ta take. Haka sukaita fira cikin jindadi har suka isa gidan. Sosai saudart taji dadin fitarta yau don sosai take jin wani irin nishadi data jima bata jiba. Parking sukayi suka fito suna dariya. Can dariyarsu ta tsaya gabadaya a dalilin ganin motar A.A dake fake a parking space din. "Seems sweetheart dinki nanan" inji baby cikin shaqiyanci. Harara saudart tabata tayi gaba, baby tabita tana dariya qasa qasa. Da sallama tashigo falon. Kamar hadin baki ya dago ya kalli kofar daga inda yake kwance bisa cinyar Ummy itama daidai ta kallo cikin falon sai caraf idanunsu suka gauraya...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah kabamu zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 036 Basu yiwa juna kallon second biyuba kowanne ya janye idanunshi. "A'a? Kun dawo? Dama yanzu nake tunanin kiranku naji shirun yayi yawa" inji Ummy tana ture kan Ashraf daga kafarta shikau sai sake maqalewa yake. "Wlh kau Ummy, mun dan taushe hannu" inji saudart tana zama akan wata kujera dake kallonsu. Baby ma da sallama tashigo cikin nutsuwa kamar wata saliha ta zauna kusada saudart tana gaida Ashraf "Yaya ina wuni?" "Lfy" kawai yace yana qara gyara kwanciyarshi kan cinyar Ummy. "Ya wajen su mamyn?" Inji Ummy cikin fara'a "Wlh lfy lau tana gaidaku ma" "Aikau muna amsawa, ai rananma na kirata mun gaisa" Murmushi saudart tayi tana dan wasa da zoben yatsarta tace "Allah sarki" "Oh ni, waini son meke damunka ne? C'mon get up, saika karyani tukkuna?" Tafada tana tureshi "Shhhhh Ummy mana?" Yafada cikin shagwa6a yana sake maqale mata. "Wai dukda kayi auren ma bazan tsiraba? Dama haka kike fama daughter?" Sunkuyar dakai saudart tayi cikin kunya, a bangare guda kuma tana mammakin abinda Ashraf yakeyi. Haka Ummy taita fama dashi yana wani narke mata yana zuba shagwa6a. Itadai saudart takaici na ya qumeta, don kwata kwata be burgeta ba, mata akasani da zuba shagwa6a ba qaton gardiba. Tsaki tajashi yafi cikon kwando acikin zuciyarta. Ganin abun nasu bana qarewa bane yasata tashi murmushi a fuskarta. "Ummy, Bari muke sama muyi sallah" "Ok, ai gashinan kau anata kira, muma yanzu zamu tashi" Tare suka tashi da baby da tunda tashigo bata sake cewa komai ba bayan gaisuwar datayima Ashraf. Bayan sun shiga daki baby ta fashe da dariya harda kyakyatawa. Binta da kallo saudart tayi daga bisani tace "Ke kumafa? Lafiya dai ko?" Bata amsamata ba saima fadawa datayi kan gadon ta tana mai cigaba da dariyar. Tsaki saudart taja tana cewa "To Allah yakawo sauqi" tashige toilet. Alwala ta dauro sannan tafito ta tarar har baby ta shimfida mata sallaya. Kallonta tayi ganin tayi dai daya kan gadon tana latse latse a waya. "Kefa? Ko bakiji an kabbara ba?" "An yafemin ai" Bata sake cewa komai ba ta kalli gabas ta kabbara sallar. Koda tagama magrib bata tashiba har saida akayi isha'i sannan. Nan baby uwar surutu tafara zubamata shi, itama tana biyemata har saida Ummy takira baby a waya cewa su sauko suci abinci. A dining suka iskesu, Ummy na feeding din Ashraf kamar kodayaushe. A kunyace saudart ta ja kujera daga can beda dasu ta zauna. Ajiye cokalin Ummy tayi tana cewa "Yauwa baby, Debi abincin ki ki komawarki daki nima inada abinyi" Diba baby tayi tayi gaba itama Ummy ta miqe zata tafi "Ummy banfa qoshiba" inji ashraf yana dan ware idanu "Then? Aiga Matar ka nan, tabaka" tafada tana wucewarta. Shiru wajen ya dauka na dan lokaci. Ajiyar zuciya tasaki ahankali sannan ta miqe tsaya ta dauki plate ta bude warmer din. Haddadiyar fried rice ce dataji kayan lambu tayi green shar daita. Serving spoon tayi amfani dashi ta zuba kadan a plate din, shima don kar Ummy tayi magana plus batason yin girki idan sun koma gida. Nan ta zuba banana juice din a glass cup takoma ta zauna tafara ci cikin nutsuwa da yanga. Duk abinda take yana kallonta ta qasan ido, harta gama tafara cin abincin. Shiru wajen yasake dauka idan ka dauke Qarar da cokalin da saudart take amfani dashi keyi ahankali. Shi ya maida hankali akan wayar hannunshi yana shafe shafe amma duk movement dinta yana kallo ta qasan ido. Itakau yitayi kamar batasan da mutum ba awajen maida hsnkalinta akan abincin ta dukda atakure take ga qamshinsa daya hanata saqat don duk numfashin dazatayi saita shaqeshi. Sun dan Dade a hakan, can saiya maida wayar a aljihun wandonshi ya dauki glass cup ya tsiyaya ruwan gora yasha kadan sannan ya goge bakinshi da tissue ya miqe yabar wajen. Ajiyar zuciya ta sauki harda dafa saitin zuciya "At last" tafada tana rolling din idanu. Saida tagama sannan ta tashi ta tattare abubuwan da aka 6ata takaisu kitchen ta dawo ta gyare wajen ta gogeshi kamar ba'a ci abinci ba wajen sannan takoma kitchen ta wanke abubuwan dasuka 6ata. Tana cikin kifasune Ummy tashigo da mammaki a fuskarta. "Daughter, why? Haba dakin bari baby tayi" Murmushi tayi tana tsane hannunta da hand towel. "Kai Ummy, ba komai fa, basuda yawa ai" "Dukda haka daughter, yanzu bari baby zata ida, kifito kutafi don garin naga kamar da hadari kar ruwa ya ritsa daku ahanya" Babu musu tabi bayanta Har bakin mota su Ummy suka rakosu baby harda budemata kofa tana saramata. Harara ta gallamata kafin tafita. Wata Leda Ummy ta miqomata mai dan girma tana cewa gashi babu yawa. Sosai saudart tayimata godiya cikin girmamawa sannan Ashraf ya tada motar yafara yin reverse. Dagamusu hannu Ummy da baby sukayi tayi har saida suka fice daga gidan. ******************************** Tuqi yake cikin qwarewa da burgewa, kamar kodayaushe babu Wanda ya kula wani bare ya tanka, kowa harkar gabanshi yake. Babu zato ruwan sama mai qarfi da iska ya tsuge kamar da bakin qwarya. Gashi sunyi nisa don sunfi Rabi amma da saura kuma kafin sukai gida. Duk yadda yaso ya cigaba da tuqin cikin ruwan kasawa yayi don sosai ruwan ke zuba ga iska don kwata kwata be ganin gabanshi sosai. Babu yadda ya iya don haka ya koma gefen titi yayi parking yana sauraron ikon Allah. Wani irin shiru motar ta dauka, bakajin komai sai sautin saukar ruwan saman. Kashe a.c din motar yayi ya kunna warmer don dama shi can sarkin jin sanyine, ya kwantar da kujerarshi ya jingina da ita. Itakau dama saudart jingine take da bayan kujerar ta ta lumshe idanu tana sauraron sautin saukar ruwan. Tunawa tayi da ranar dasukaje gathering dinnan ruwa ya ritsamusu a hanya kamar dai yau. Ajiyar zuciya tayi taqara lafewa a kujerar idanunta still a lumshe tanata tunane tunane har barci 6arawo ya saceta. Shikau a 6angarenshi latse latsen waya yaitayi har ruwan yadan tsagaita. Jin ruwan ya tsagaita kuma dare qarayi yake yasashi dagowa yana maida kujerar daidai. Kallon gefenta yayi ta qasan ido yaganta lafe a kujerar ta jawo gyalenta ta rufe fuska. Tada motar yayi suka cigaba da tafiya har suka kawo gida. Parking yayi a parking space sannan ya kashe motar. Izuwa lokacin ruwan yakoma yayyafi sai iska daddada dake kadawa. Qara kallon side dinta yayi Wanda yanzu tajuyo tana fuskantarshi cikin barci kuma gyallen yadan yaye. Samun kanshi yayi da kasa janye idanunshi daga sleeping face dinta. Bin fuskar yake da kallo kamar yau ya ta6a ganinta. Daga lumsassun idanunta da Zara zaran lashes dinta sukadan lankwasa saboda tsawo zuwa girarta mai dan yawa tadasha gyara ta sun kwanta luff zuwa madaidaicin qaramin hancinta mai dan tsayi zuwa kumatunta masu dan cika Wanda dukda barci take dimple dinta na haggu saida yadan lotsa sai qannanun lips dinta da sukasha maroon din lipstick sunyi dasa dasu gwanin birgewa. Kasa janye idanu akan lips dinta yayi don ba qaramin tafiya dashi yayiba. Besan iya kar lokacin daya dauka yana kallonta ba don yadda kasan yau yafara ganinta haka yakoma. Saudart kau barcinta take hankali kwance. Sai can cikin barcin tafarajin zafi, tana warmer daya kunna dazu gashi glass duk Asama suke gata batada jumurin zafi ko kadan hakan yasa barcin yafara daina yimata dadi. Ahankali tafara bude lumsassun idanunta dasukayi nauyi saboda barci, basu sauka a koina ba sai cikin nashi. Gabansu ne yafadi gabadaya kuma suka kasa janye idanunsu daga cikin najuna. Jin hasken idanunshi na Neman narkar daita yasata saurin miqewa zaune tana gyara zaman mayafinta. Shima sai a sannan ya janye idanunshi ya maidasu ya lumshe cikin takaicin kamashi datayi yana kallonta. Shiru motar ta dauka babu mai magana sai can yasa hannu ta bude murfin kofar yafita yana maida kofar da don har saida ta tsorata. Binshi da kallon takaici tayi da side mirror harya shige ciki sannan taja dogon tsakin takaici sannan itama a fusace tafito ranta a 6ace itama tayi banging din kofar ta nufi ciki. Koda tashiga bata ganshiba kuma dama bason ganinshin takeba ta hayewarta sama tana gunguni. Itadai Allah yasa dad yasamo mata aiki mai kyau tasamu asan yadda za'ayi abiyashi damn kudinshi kota huta. Haka taita gunguninta harta gama shirin barcinta ta kwanta da niyyar idanma dad besamomata aikin ba ranar Monday babu abinda zai hanata zuwa bakery...✍ Manage please Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka qaramana zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 037 The next day is Saturday, yau weekend babu aiki, tunda yaje gida ya gaida Ummy kamar yadda yasaba yawuce gidansu sadeeq. Zaune suke, Ashraf akan cushion din dake dakin abinci agabanshi yana aikawa ahankali shikuma sadeeq na kwance kan gado yana waya murya can qasa qasa don ko Ashraf dake dakin yayi qarya yace yaji kalma daya cikin maganganun dayake da alama dai da budurwa yake wayar. Juice yadauka yakai bakinshi yana kur6a yana kallon yadda sadeeq din ke dariya ciki ciki cikin salon burgewa sai wani iyayi yake saikace bashi bane idan yana dariya har Wanda ke kilometer 2 dashi najiba. Tsaki yaja ya ajiye cup din hannunshi ya dauki cokali ya cigaba dacin abincin shi. Harya gama ci begama shegiyar wayar da shi yarasa ubanme ma suke cewa. Tsaki yasake ja yana goge bakinshi da tissue sannan ya miqe ya nufeshi. Fiit.. Yaji an fige wayar Wanda hakan yasashi saurin dagowa. Harara ya 6allamashi yana kashe wayar yayi jifa daita kan gadon 6ata rai sadeeq yayi yace "To dan black stomach, meye ruwan ka da wayata? Mugun kallo yasake watsamashi sannan yace " bansaniba, na zo wajen ka kawani hadani da plate din abinci ka shareni, niga mayunwaci ko?" Shima hararar ya 6allamashi "To dama miya kawoka? Mutum da sunan yayi aurene amma qaton gaurone, shikenan dan taqamar kazo sainaqi yin waya da sweetheart dina, a'a ba dalili yanzu tunda kaci ka qoshi sai aqara gaba ko?" Tsayawa yayi yana kallonshi baki bude "Ni kake wa Rashin mutunci?" "Eh din, bakai taqamar Rashin mutunci ba? Har muce zamuzo gidanka cin taliyar Amarya kayimana baqinciki, ai kadanma kagani". Inji sadeeq yana jawo wayarshi dake tsakiyar gadon yasake dialing din number. "Hello sweetheart.. Wani yaro ne yashigo yana damuna shine nakashe na korashi..." Daidai nan kawai yaji yafita daga dakin yana ayyana mugun Rashin mutuncin dazai shufkamashi. Be zarce koinaba sai gidan gonarshi inda yawanci dama can yake zuwa a irin wannan rannakun ya huta don bejin yana iya zaman waje daya da wannan aljannar yarinyar don dole kawai tasa yake kwana gidan. Itama a bangarenta tayi duk abinda yadace tayi, ta koma sama, bata saukowa sai idan wani Abu takeda buqata kuma data dauka zata koma, hakan yasa basu hade ba har weekend din yaqare. Yau Monday, yau tunda ta farka dasafe take cikin farinciki don ko komawa barcin datake da safe ba tayiba. Shirinta kawai take na zuwa bakery. Tea kawai ta hada da electric kettle din dakinta kakkaura tasha cikin yadan warware sannan tahau shiri. Wajajen 8:25am tafito cikin shigarta ta atamfa brown da Orange Riga da skirt sannan ta zumbula hijabi har qasa brown, abinka da farar mace sai ya haskata sosai ta ratayo wata brown handbag mai kyau sai dayan hannun riqeda waya. Ahankali ta sauko daga stairs din zuciyarta fess yau zata fita tashaqi fresh air. Fita tayi tanufi parking space inda motarta (Wanda aka hadamata da lefe) take. Caraf suka hada idanu dashi shima yana niyyar bude murfin kofar. Janye idanu sukayi gabadaya suka kauda kai. Shigewa yayi cikin motar ya maido yarufe, kwata kwata be nuna damuwarshi na fitarta ba vare yadamu da ina zataje. Tada motar yayi yayi reverse ya fita daga gidan. Ta6e baki tayi itama ta maido murfin kofarta tarufe sannan ta daura seat belt sannan ta tada motar itama tayi reverse tafito akayi scanning dinta sannan gate din yabude ta fice itama. Yau saudart tana cikin farinciki sosai don sosai taji dadin zuwanta bakery din, Suma yan bakery sunji dadin zuwanta don sunyi missing dinta sosai, sai nan nan suke daita suna nunamata cigaban dasuka samu tanata yabon qwazonsu suna jindadi. A ranar saida tayi cake uku manya masu haddadun decoration sai santin cake din ake. Ataqaice dai ranar sai shidda da Rabi na marece tadawo gida agajiye don yau qara'in ayyukan data kwana biyu batayiba tayi. Shikau bedawoba sai 9:00pm kamar yadda yasaba. Ganin motar data fita dashi a parking space din yasashi sanin tadawo. Ta6e baki yayi in an I don't care manner ya fito daga motar ya shige ciki. Washegari ma yana zuwa parking space zai ya taddata tana qoqarin shiga mota. Kallo daya ta mishi ta shigewarta motar, shima beko qara kallon gefenta ba ya bude tashi motar yashiga. Ita tafara fita daga gidan sannan shima ya tada motar yafito. Yau kam kasa kawar da tunanin ina zata yayi, tunda sukazo gidan bata ta6a fitaba sai jiya da yau. Dukda yasan be kamata yadamu ba amma sai kawai ya tsinci kanshi dason sanin inda take zuwa. Acewarshi a badini ne sukasan wannan auren na tsari ne amma a zahiri matarshice ta sunna kuma haka kowa kemata kallo bazaiso tayi tarnishing din image dinshi ba ta zubdamashi da girma. Haka ya yini a office din sukuku yarasa meke damunshi dukda ba'ace besan meke damunshiba saidai bai gasgata eh saboda fitarta yashiga damuwa ba koda kuwa itace shi bawai don wani abuba yadamu saidan karta zubdamashi da mutunci (kunji fa🤔) Yana nan zaune yana operating din laptop din gabanshi sadeeq yashigo da sallama dawani file a hannu Amsa sallamar yayi batareda ya dago ya kslleshi ba. Be damuba saima file din daya Dora a saman table din yana cewa "Sir, maganar new secretary dazamu dauka ne, mutane dagawa sun kawo CV dinsu mun za6i wasu wadanda insha Allah zamuyiwa interview, gasu" ya qarshe maganar yana bude mashi file din. Beko kalli file dinba yace "Kuma ka tabbata babu arniya kodaya aciki don wannan karon I won't tolerate nonsense, ita wancan korarta nayi idan wata tayi kwatankwacin abinda tayimin saina daureta harsai igiyar tayi rara" Murmushi sadeeq yayi yace "karka samu damuwa, insha Allah nitsatsiya za'a samu, duk Muslims ne kaduba" Dan kallon file din yayi kafin yace "ba damuwa kawai proceed with the interview, I badly need the secretary kasan sati nasama zanyi tafiyar sonake kafin lokacin tasan komai" "Ok sir, insha Allah gobe za'ayi zuwa gata an fidda mai nasara, saita fara zuwa Monday" "Hakan ma yayi" yafada yana maida hankalinshi kan abinda yake. Har ya juya zai tafi yakuma dawo "Is something bothering you?" Ya tambaya cikin kulawa. Dagowa yayi ya kalleshi "Me ka gani?" "Gani nayi kamar kana cikin damuwa" "Naaah, babu komai, kana samun information wajen spy dinnan kuwa?" "Yes, ko jiya yayi updating dina" "Good, ka cigaba da keeping in touch dashi ok? Sonike komai ya kammala cikin gaggawa ko nahuta" Dariya Sadeeq yayi yace "Karka damu komai yakusan zama tarihi ai" Nan suka dan qara tattaunawa sannan sadeeq yakoma office dinshi. Yauma tasha aiki sosai saboda ba qaramin missing din aikinta tayiba. Zaune take tana shan fresh milk tana danne danne a laptop din gabanta. Ringing din wayarta yasata ajiye kofin glass cup din ta dauki wayar. Ganin mai kiran yasata dagawa ta kara a kunne "Aslm alaika sweet dad" Sautin murmushi taji daga dayan 6angaren sannan akace "Wslm habibtie" "Dad good afternoon" "Ya kike? Ya zaman gida?" Yafada yana yar dariya "Hmm Dad ina office dina ai" Cikin mammaki yace "which office?" "Bakery na mana" "Seriously shalele, kina ina?" "Allah kau dad ina bakery" Nan take ran daddy ta 6ace "Ya mukayi dake saudart? A iya sanina mun ajiye magana dake akan aiki" Jikinta ne yadanyi sanyi jin kamar yaji haushi "Dad.." "It ok, idan aikinne bakiso fine, bye" "Daddy please karka ajiye wayar, please" "Mezaki fadamin?" "Dad it's not what you think, zanyi aikin fa, kawai am bored ne shiyasa nazo bakery jiya da yau" tafada a shagwa6e Wani sanyi yaji a zuciyarshi don duk a tunaninshi ta canza ra'ayi kuma yasan halinta tana iyawa don shegen wayau ne daita. "Ok I thought kin koma bakery dinne, you see finding a better job with good salary is better" "Hakane" tafada ahankali zuciyarta na bata anya Dad beda wani shirin don ba qaramin sani tayiwa dad dinta ba tasanshi ciki da bai. "Inada daddaden labari agareki" yafada cikin zaquwa "Ok fesamin daddy" "Na Samar miki aiki!" Dukda bataji irin farincikinnan ba sai tayi pretending tace "Da gaske dad?" *yes sweetheart " "Wani irine?" "A wani company nayi miji applying, kuma suna biya sosai, an za6eki cikin wadanda za'a yiwa interview, saidai online interview ne, zasu turomiki ma ta e-mail qilama sun turo, gobe ake interview din, please don't let me down" "Insha Allah dad, wane company ne?" "Na wani aboki nane, kuma shahararrene" "To" "Are you ok?" Inji dad jin ta amsa cikin wani yanayi "Nothing Dad" tafada don haka kawai take jin aikin be kwanta mataba "Ok daughter, do your best ok? Allah yabada sa'a dukda nasan ke mai sa'ar ce" Dariya tadanyi tace "amin to Dad" Nan sukayi sallama ta yanke wayar. Ajiye wayar tayi tadanyi tagumi tana nazari. Me dad ke shiryawa? Jin yanayin maganar shi kawai datayi yasata sanin da wani Abu dayake shirya wa. Her Dad was very cunny kuma tasani. Haka taita saqa da warwarewa har suka tashi aiki ranar...✍ Manage🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ya yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka qaramana zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 038 Washegari saudart bataje bakery ba, tunda tagama aikin gida tayi breakfast ta haye sama. Bude laptop dinta tayi exactly tafara yan danne dannenta kafin lokacin interview din dazasuyi yayi. 12:00pm suka fara and alhamdullilah tana saka ran samun nasara. Ranar yini tayi a garden tana aiki a laptop dinta don tana so taqara advancing din bakery dinta ne, tana son ta bude wani qaramin shop kusada bakery din yazama wurin hada variety of ice cream. Dama ta Dade tana tunani akan hakan, ganin yanzu takeda damar yi kuma kudi ba matsala bane, yin hakan zaisa hanyar shigowar kudinta yaqaru Wanda hakan zaisa ta taimaki dad dinta ya biya duk wani bashi dake wuyanshi. She loves her Dad soo much, tunda ta taso batasan kowaba sai dad dinta, shaquwar dake tsakanin su baya faduwa, saboda shi yayi taking din both role dinshi Dana mamanta. Tun tana yarinya da gari yawaye zaimata duk abinda yakamata uwa tayiwa diyarta. Wanka, girki, yakaita school, yaje Dakota, suwuce mall dinshi su qarashe yinin tare. Weekend kuma yakaita wajajen shaqatawa suyini a can kuma yakaita gidan mamanta tayimusu yini daya Shaquwar da saudart tayi da Daddy ko kwatanta batayi da mamanta ba. Shiyasa matsayinshi ma na daban ne acikin zuciyarta. Tasan Dad dinta is not perfect, dama kuma duk dan Adam ajizine, shi ajizancinshi shine son kudi. Duk hanyar dayaga zaisamu yan gidan rana masu tsoka to saiyabi don acewarshi kudi sune komai. Anan ne ra'ayinsu ya banbanta don ita basu wani dametaba kuma tana qoqarin ganar da daddy hakan amma Wanda yayi nisa ba Lallai bane yaji kira ba. Shiyasa kullum take sakashi a addu'a don tayi imani cewa addu'a itace takobin mummunai. Haka tawuni zur a garden din sai wajajen magrib takoma cikin gida tayi hayewarta sama. Washegari ma batajeba don tunda Dad yanuna 6acin ransa akan hakan taji zuwan duk ya fita kanta. As usual tagama komai gidan sai daukar qamshi yake, tana kwance tana waya da P.A dinta akan shirye shiryen bude ice cream joint dinta . Sun dan jima kafin sugama sannan ta kashe wayar. Kafin ta ajiye wani kiran yashigo. Ganin daddy ne yasata Sakin murmushi ta kwanta tana maqalqale pillow cikin muryar shagwa6a tace "Daddy?" "Na'am shalelen daddy?" Turo baki tayi tace "daddy I miss you" "Miss you more baby, shine baki gayamin ba?" "Menene?" "Really? Bakima saniba?" "Menene to dad? Kafadamin kawai" "To albishirinki" Cikin zaquwa tace "goro fari" "You're employed!" Waro idanunta tayi cikin jindadi "Da gaske daddy?" "Eh mana, yanzu muka gama magana da P.A din companyn" "Wow dad, that's soo cool, naji dadi" tafada da murmushi a fuskarta dukda bawani farinciki takeyi canba. "And guess what?" "What?" Ta amsa tana buga tagumi da hannu daya. "A matsayin secretary aka daukeki a company din" Waro idanu tasakeyi tana cewa "Really dad?" ,"sosaima, with a sum of 250k duk wata" Sake ware idanu tayi "Wow! Wow!! Dad am speechless!" Dariya Alhaji shamsu yayi mata, I told you? Ina gwadamaki annabi kina rufe idanu. Idan kika cigaba da yimin biyyaya zakiga fin haka, zakiyi bala'in kudi" "Hmm zan daiyi kudi masu albarka dad, ba na bala'i ba" Ta6e baki yayi yace "Whatever, yanzu ki shirya zaki fara zuwa ranar Monday ne, please you have to be serious kuma kinsan I love you ko? Kuma bazan ta6a cutar dakeba" "Yes, I know" "Kuma kinsan komai nakeyi saboda ke nakeyi, banida kowa banida family bayan ke kuma banida mai farantamin bayan ke ko?" Dan daga gira tayi alamun tambaya "Eh dad, amma meya kawo wannan maganar? You know I love you so much, farincikinka shine nawa, shiyasa ma zanyi wannan aikin domin taimaka maka wajen ganin ka sauke duk wani nauyi dake kanka" "Eh nasani dear, saidai kiyimin alqawari bazakiyi disappointing dinaba, zaki qar6i aikin nan duk yadda kikaga yazo miki" Shiru tayi na dan lokaci kafin tace "Ban ganeba dad, is something wrong with the job?" "No, absolutely no, kawai I want you to accept it ne duk yadda kika ganshi" Ajiyar zuciya tayi tace "Zanyi amma sai idan be sa6ama addiniba" Cikin jindadi yace "Yes na tabbata miki be sa6ama addiniba, wlh" "To Allah yayimana jagora" "Amin my jewel, Allah ya albarkaci rayuwarki" Cikin jindadi tace "amin Abby" Kingin ranakun tashiga busy sosai wajen ganin ta ice cream joint din ya kafu. Kwana uku ana aikin kafin agama kuma alhamdullilah komai yatafi mata yadda takeso. Ranar asabar aka bude wajen kuma tadanyi taro babu laifi akayi addu'a samun sa'a akaci akasha sannan aka watse. Nanfa ta duqufa wajen ganin komai yatafi kan tsari. Ice cream babu kalar da basu saidawa, acikin su akwai na vanilla, chocolate flavour, strawberry flavour, banana flavour ddss. Alhaji shamsu kau ya dauki nauyin tallatar mata da wajen ta kafar yad'a labarai wato t.v, radio da social media. Duk wannan abun da akeyi Ashraf na sane amma ko nuna yasan sunayi beyiba, to tayama zai nuna bayan haduwarsu ma aikine. Kowa zaman kanshi yake a gidan so babu Wanda yadamu da abinda dan uwanshi ke ciki. Su Ummy kau basuda masaniya akai saida suka gani a t.v ana talla, nan baby ta kirata tana tambayar dagaske ita ta bude. Da eh saudart ta amsamata, sosai baby tayi murna wai likafarta taci gaba, dama ita mayyar ice cream ce, duk sadda taji kwadayi zatazo ta jidi son ranta. Dariya saudart tayi tana cewa babu damuwa ai kayan Allah na annabi ne. *********************************** Yau Monday, tunda wuri ta tashi tayi abubuwan data sabayi dasafe ta hada breakfast dinta taci sannan tashiga wanka. Wajajen takwas da Rabi harta gama shirinta tsabb cikin wata sky blue din Arabian gown bubu Wanda yaji duwatsu masu daukar idanu daga gaban rigar. Ta yane kanta da veil mai dan girma sky blue Wanda ya kawomata har saman ciki. Ta rataya jakka baqa sai takalmi masu dan tsini baqaqe hannunta kuma daure da agogo kamfanin Apple baqa a hannu. Fuskarta babu wata kwalliya bayan powder da kwallin data sakama idanunta sai lashes dinta data sharce da mascara, shikenan. Bata fesa turare mai uban qamshi ba, mai sanyayan qamshi tafesa Wanda saikazo kusada ita zaka jishi. Jin horn a waje yasata gane drivern da daddy yace zai turomata ya qaraso. Saka wayarta da abubuwan amfani tayi a jakkar tasake kallon kanta a madubi tana gyara daurin veil din sannan tafito. Da sauri ta sauko tana sake duba time tanufi hanyar fita. Saurin bude kofar tayi tasaka kai zatafita sai quuum! Suka qume dajuna. Ba qarya sun qumu don saida suka ja da baya suna Sosa wajen suna kallon juna. Ganin beda niyyar tankamata ko matsawa yasata ra6awa ta gefenshi zata wuce. Sai jitayi an chafki tsintsiyar hannunta an maidata baya da qarfi Wanda saida kafarta ta haggu ta murgude tayi baya baya zata fadi Allah ya taimaka ta dafe shoe shelves dake wajen. Dagowa tayi a firgice tana kallonshi don bata ta6a zaton hakaba awajenshi. Shima kallonta yake fuska a hade yana kallon direct tsakiyar kwayar idonta. "Ke makauniya ce? You hit me and you're going without saying sorry? Dole ne saikin gwada bakida manners? Well unfortunately nasani, nasan you're ill-mannered before I even get to know you" Kasa cewa komai tayi sai kallonshi datake ga wani daci datake ji cikin maqoshinta jin ya kirata marar manner. "Kina sauri zaki yawon tazubar ko? Well I don't fucking care ina zaki, kawai don't drag my good name to mud, don a matsayin Matar A'A kike ga mutane, behave yourself karki kuskure mutunci na ya ta6u a idon jama'a" Yayimata wani kallon up and down sannan yawuce ciki yabarta nan tsaye. Bata waigo ta kalleshiba dayake wucewa, zuciyarta takeji namata wani irin zafi kamar ana hura garwashi aciki. Muquut.. Ta hadiye yawu mai daci daya taru abakinta ta gyara rolling din veil dinta jin ansake yin horn. Bude kofar tayi ta fita asanyaye ranta a matuqar 6ace, tafito har wajen gate wajen drivern daya zo daukarta tabude bayan seat ta zauna. Cikin fara'a drivern yace "Sannu da isowa hajiya" Don dama akwai kyakyawar alaqa tsakanin ta da tan aikinsu don lafiya tana wasa da dariya dasu. Yaqe tayi tace "yauwa bala, ya aiki?" Da alhamdullilah ya amsa daga nan kuma babu Wanda yasake magana. Shiru tayi abaya tana sauraron tafiyar motarsu a kwalta, yayinda abinda yafaru yanzu ke dawomata. Babu abinda yafi bata haushi kamar marar manner daya kirata. Itadai tasan qumewa sukayi kuma both of them sunji zafin, why zaiyi insulting dinta? Wannan na cikin abubuwan dayasa tun farko take qauracewa ganinshi, a duniya idan akwai abinda ta tsana to cin mutunci ne amma batun yauba ta lura ya qware akan hakan shiyasa ma batason haduwarsu don bazata iya dauka ba, tafison har ta qaraci zamanta su rabu babu abinda yashiga tsakaninsu daidai da maganar fatar baki. Jin an tsaya ana horn yasata sauke ajiyar zuciya tana kauda tunaninta don yaune ranar farkonta a aiki yakamata tazama tana cikin nutsuwarta. Direct parking space yayi daita sannan yasamu wuri yayi parking. Ajiyar zuciya tasake saki tana addu'ar farawa a sa'a sannan tasa hannu ta bude murfin kofar tafito. Abinda tagani ne yasa numfashinta daukewa na wuccen gadi....✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka qaramana zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 039 Mitsitsike idanunta tayi taqara kallon wajen don tabbatar da ba idanunta kemata gizo ba amma still wajen ne, companyn ne. Juyawa tayi wajen bala dake niyyar yin reverse tace "Bala ka tabbatar nan ne inda Dad yace ka kawoni?" Cikin yashe baki yace "eh hajiya, nan ne" Sauke numfashi tayi tana dafa goshinta tareda lumshe idanu. *kiyimin alqawari bazakiyi disappointing dinaba, zaki qar6i aikin nan duk yadda kikaga yazo miki* Maganar dad na jiya yadawo mata a qwanya. "Why dad? Why?" "Hajiya? Lafiya dai ko?" Inji bala daketa kallonta tundazu. Bude idanunta dasuka fara canza launi tayi ta kalleshi tama kasa magana. "You're welcome Mrs A.A" Sukaji anfada daga bayan su. Juyawa sukayi gabadaya suna kallon mai maganar. Sadeeq ne ya qaraso yana washe baki yana cewa "You're highly welcome ma'am, mushiga ciki mana" Kallonshi tayi sannan ta daga kai tana bin company din da kallo batareda ta bayyanar da yanayin datake aciki ba a fuska ta sake maida kallonta kan sadeeq tasaki murmushin takaici sannan tajuya ta fara kiciniyar bude motar dasukazo daita. "Erm.. Mrs A.A please listen to me, atleast mufara shiga ciki inmiki bayani" Banza tayi dashi ta bude kofar zata shiga "Mrs A.A..." "A.A my foot! Karka sake dangantani da sunan nan" tafada a fusace "Amma wannan ne company din dazaki..." "Fuck the company!" Tafada tana jawo murfin motar da qarfi. Tsawa ta dakama bala akan yashigo sutafi, aikau dagudu ya bude motar yashiga ya tada suka fice. "Shit!" Sadeeq yafada yana riqeda kugu. Gudu bala keta tsulawa batareda yasan inda zashiba saidai kuma yana tsoron tambayarta don yasan idan tayi fushi akan kowama hucewa take duk yadda kau kuke daita. Can dai ya sadaqat yace "Ranki shi Dade ina zamu?" Wani kallo ta watsa mashi ta glass din gaba Wanda hakan yasashi maida hankalinshi kan tukin Can kamar bazata yi magana ba tace "Daddy.. Take me to him" Dukda besan me tace daga bayaba jin ta ambaci daddy yasashi sanin wajen shi zaya kaita. Jingina kanta tayi da kujera ta lumshe ido tana sauraron yadda zuciyarta ke zafi. Meyasa dad a duniya bayada burin da yawuce ya zubarmata da mutunci? Meyasa dad beda burin daya wuce ya quntata mata? Meyasa yacika son kanshi? Yarasa inda zai nemomata aiki sai wannan companyn? Wane irin kallo yakeson suyimata? Jin motar ta tsaya yasata bude idanu tana kallon mall din sannan tasa hannu ta bude murfin kofar tafito. Shiga mall din tayi direct tanufi office din babbanta batareda tako tankama masu yimata magana ba. Murda handle din kofar tayi ta bude tashiga batareda ko sallama ba. Wanda hakan yasa daddy da wani mutum dasuke tattaunawa tare dagowa suna kallonta. Batace komai ba ta qarasa gefen office din dake akwai cushion ta zauna ta zaro waya tana danne danne. Maida hankalinshi dad yayi kan mutumin suka cigaba da tattaunawa har suka gama suka tashi sukayi musabaha mutumin yafita. Kallon wajen saudart yayi yaga haryanzu bata dago daga kan danne dannen datakewa wayarba. Wani irin murmushin manya yayi yanufi fridge din office din ya Ciro ruwan gora da glass cup ya qaraso ya zauna kusada ita ya tsiyaya mata a cup yabata. Hannu tasa ta amsa batareda ta kalleshi ba ta kafa kai tasha kusan Rabi sannan ta ajiye. Shiru office din ya dauka, kowannensu beda niyyar magana. Kamo hannunta daya yayi yana murzawa ahankali yana kallonta itakau haryanzu idanunta na bisa wayar hannunta. "Am sorry" yafada cikin rada. Lumshe idanu tayi zuciyarta na cigaba da tafasa. "Saudart nasan a halin yanzu kin tsaneni, kuma na cancanci haka, nasan am not a good father, ina yawan 6atamiki rai, ina yawan saki a damuwa...saidai banida yadda na iya ne" Qara damke hannunta yayi cikin sigar dadin baki daya qware akai yace "Banida kowa saike, banida uwa, banida uba, banida mata, banida 'ya'ya bayan ke, ke kadai zan iya samun sassauci awajen ki, ke kadai zaki iya taimaka min, ke kadai nakedashi dazan iya dazan iya fadawa damuwa ta inkuma saka ran zaki taimaka min, wataqila da na haifi wasu da ban takuramaki dayawa ba, da nasan akwai Wanda zai tausayamin aciki, da akwai Wanda zai iya jure komai akan samun farinciki na" Haryanzu idanunta a lumshe suke saidai in banda hawaye babu abinda ke gangarowa daga cikin lumsassun idanunta.sosai maganar daddy ke shiga direct cikin zuciyarta tana narketa kamar yadda ake narke darma. Wai yau daddy yakejin inama yanada wasu yaran bayan ita? Sosai abun ya ta6amata zuciya. "It ok saudart, nasan kinzo nan ne don kice bazakiyi aiki a company din ba, babu komai, zan cigaba da Neman yadda zanyi in hada kudin, koda ban hadaba idan wa'adin yacika zan saida mall din saina bashi kudin kingin kuma saina samu wata yar Sana'a nayi... It ok kinji? Kibar kukan hakan, I love you, Allah yamiki albarka" Tashi yayi zai tafi yaji ta riqomashi hannu Wanda hakan yasashi tsayawa batareda ya juyoba. Idonta still a lumshe ta bude bakinta dakyar tace "Aiki a company din zai sakaka farinciki?" Juyawa yayi yana kallonta yace "A'a shalele, I want your happiness, don't worry" Bude idanunta tayi tana kallonshi da idanunta dasuka ida rinewa sannan ahankali tasake cewa "Zai sakaka farinciki?" Shiru yayi yana kallonta kafin yace "Eh saudart, babu company dazamu samu mai biyan albashi mai tsoka kamar wannan, kuma..." "It ok" ta katseshi da fadin haka sannan ta tashi tsaye tana gyara nadin gyalenta ta dauki Jakarta tayi hanyar kofa. Yabita da kallo Harta sa hannu zata bude kofar muryarshi ta dakatar da ita. "Shalele.." "Ina sonka, kaine silar zuwana duniya ko me nayimaka bazan biyaka, bazan so naganka cikin damuwa ba bayan inada maganinta, bazan so a dalilinaba kayi danasani ko kukan Rashin 'ya'ya dayawa ba, zan iya sadaukar da farincikina kamar yadda kasha sadaukar da naka wajen samamaka farinciki. Saidai... Saidai karka yi tunanin zaka iya sani sa6awa Allah na bayan wadda kasani nayi abaya, idan dagaske saboda na taimaka maka wajen biyan bashin kanka yasa ka nemomin aiki fine, amma idan kanada wata manufa akan haka saidai kayi haquri, wata qila anan zan Gaza sama maka farinciki" Tana kaiwa nan tabude kofar tafice. Alhaji shamsu yadade nan a tsaye yana bin inda tabi tawuce da kallo. Sai yanzu yafara tuhumar kanshi akan anya yayi mata adalci? Anya kalaman dayayi amfani dasu basuyi tsauriba, yasan saudart batada wani Wanda takeso takeson sashi a farinciki bayan shi, meyasa yayi amfani da wadannan kalaman wajen karya mata zuciya. Komawa yayi ya zauna yana jin badadi har cikin zuciyarshi. Key din motar ta amsa hannun bala ta bude motar tashiga ta tada sannan tafice daga harabar mall din. Tafiya take hawaye na gangaro mata duk kau kokarin datake na tsaidasu. Ba komai kesata hawaye ba sai kalaman dad na inama yanada wasu yaran, wannan Kalmar tafimata ciwo kuma tasan zata Dade tana cimata zuciya. Ikon Allah kawai ya kaita company din lfy. Parking tayi a parking space sannan takoma ta jingina da seat din tana lumshe idanu. "Ya Allah give me strength" Ganin zaman be yiwuwa yasata budewa ta zuro kafafunta tafito waje. Sake kallon harabar company din tayi tana tuna farkon zuwanta company din dakuma abinda yafaru a ranar. Maida murfin kofar tayi tarufe sannan tafara takawa jiki a sanyaye tanufi main entrance din. Wajen wanke hannu taje ta matsa sanitizer tafara wanke hannun yayinda komai na farkon zuwanta company din ke dawomata a qwanya. Danna botton din kofar tayi yabude tashiga sannan yakoma yarufe sannan daga can ciki kuma yabude tashiga. Daidaikun mutane taga sunata kai kawo kamar dai ranan kowa da abinda yasha mashi kai. Direct wajen elevator tanufa ta Danna number din floor din sannan tashiga. Cikin yan daqiqu sai jitayi abun ya tsaya sai kofar tabude. Shiru tayi tana kallon wajen batareda ta fitoba gabanta sai bugu yake. Ganin elevator din zai koma yarufe yasata sauke wata nannauyan ajiyar zuciya sannan ta zuro kafarta tafito. Kamar wancan karon, qamshi da sanyi yafara yimata maraba, babu abinda ya canza daga yadda yake lokacin datazo sai empty kujerar secretary data gani babu kowa akai Wanda yanzu ita zata dinga zama akai. Ta Dade tsaye tana qarewa wajen kallo batareda tayi yinkurin motsawa ba taji a bude kofa an fito. Saurin waigawa tayi suka hada ido. Washe baki yasakeyi. "There you are! Sanni dazuwa Mrs A.. I mean saudart, ga wajen ki can, muje please" Babu musu tabishi ya budemata tashiga, wajen rufe yake da glass don haka kana hangen naciki kuma koda zaka ba nawaje Abu akwai inda zaka zuge ka fidda abun batareda ka fitoba ko na wajen ya shigo. Bin office din take da kallo cikin takaici, don duk qawatuwar wajen be burgeta ba. Sadeeq sai zuba yake yana nunnunamata abubuwa yana mata bayani itakau tana gefe ta rungume hannuwa a qirjinta tana saurarenshi. Saida yakai aya sannan yace "Erm.. Yanzu wadancan files din zaki kaima boss yayi signing" yafada a darare. Jimm tayi kamar bazata motsaba saikuma can ta sauke ajiyar zuciya ta matso kan desk din dake cike da files da computoci tace "Wadanne files?" Tattaramata su yayi yabata tayi mashi godiya sannan yafice. Itama fitowa tayi daga office din tanufi office din. Daga kai tayi ta kalli abinda aka rubuta sama *the c.e.o office* Ta Dade tsaye awajen tana yunkurin shiga saikuma ta fasa. Da ace mutuwarta zatazo a lokacin koko ta 6ace 6att datafi murna. Yau zatayi facing dinshi a matsayin boss dinta, ita kuma a matsayin secretary dinshi, wannan wane irin zubarda mutunci ne? Tunawa tayi da abinda yafaru dasafe kafin tabaro gidan, kenan don yasan zatazo office dinshi yasashi yimata hakan, no wonder, dama tayi mammaki, tunda sukayi aure magana ta fatar baki bata ta6a hadasuba sai yau, kenan saboda yasan zatazo company dinshi a matsayin mai mashi aiki yasa yayi hakan? Idan hakane to ya tanadar mata cin mutuncin dayafi hakan kenan. Ca6, Lallai, zata iya jurar komai amma banda cin fuska, bazata ta6a barinshi ya maida ta abun wulanqatawa ba. Shaqar numfashi tayi da qarfi sannan ta fesar sannan ta daga hannu tafara knocking. Sai ana ukun sannan taji ance "Yes? Come in" Gabanta ne ya tsananta bugu, hannunta na dan 6ari ta murda handle din kofar ta bude...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Sorry for the late posts guys, wlh jiya nakusan awa biyu ina typing nakusan zuwa qarshe wayar tayi shut down, yadda kukasan inta😭😭 This page is for you *Ummu Muhseen* Marubuciyar littafin *GALADIMA AARIB* Allah yaqara basira da kaifin ido da zaqin hannu🤲 Ga page din nakine kiyi yadda kika gadama dashi🤷‍♀ Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 040 Tattaro sauran jarumtarta tayi ta tura kofar tashiga kamar Wanda kwai yafashe mawa aciki. Babu abinda ya canza a office din, yananan yadda ta sanshi tun farkon zuwanta. Qasa qarasawa tayi taja ta tsaya a bakin kofar zuciyarta na dukan Tara Tara. Jitake kamar qasa ta bude ta hadiyeta ta huta. Wannan zubarda mutunci dame yayi kama? Duk abinda A.A yayimata tabbass ita ta siya da kudinta, da wane ido zata kalleshi? Dawane ido zai kalleta? Yaya zai fassarata? Jin shirun yayi yawa yasata dagowa Tadan saci kallonshi taga kanshi na kan system bemada niyyar dagowa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ida tattaro kingin kuzarinta ta qarasa cikin office din. "Good morning" tafada cikin nutsuwa Cak ya tsaya da typing din dayake yakasa cigaba saboda muryarta datayi mashi dirar mikiya a kunnuwa. Dora files din tayi saman table din sannan tace "I was told to bring these files to you, your signature is needed" tafada cikin nutsuwa amma deep down she's dying. Juyawa tayi saurin yi tanufi hanyar kofa. Dagowa yayi yana kallonta, saidai harta kusa kaiwa bakin kofar, hakan yasashi dakatar daita da "Wait!" Cak ta tsaya tana runtse idanu da qarfi zuciyarta kamar zata Faso qirjinta ta fito dan bugawa. Ganin batada niyyar juyowa yasashi cewa "Who are you?" Yawun bakinta taji ya qafe jitake kamar ta 6ace 6att daga office din. Dakyar ta tattaro yawu a bakinta ta hadiye sannan cikin calm voice tace "Am your new secretary" Yes itace, tabbass muryarta ce, bazai ta6a Qin gane muryarta ba, kallon bayanta yake don still bata juyoba, dukda be cika qaremata kallo ba amma still yasan wannan jikin, jikinta ne. Ganin ta cigaba da tafiya zata fita yasashi cewa "Stop!" Da qarfi. Ja tayi ta tsaya again batareda ta juyoba. Cikin qufula yace "come back here!" Anzo wajen! Dama abinda take Gudu kenan, facing dinshi, bataji tana iya facing dinshi, her emotions won't let her. Hawaye taji suna Neman tarrarmata a idanu tayi saurin maidasu, tayiwa kanta alqawari duk rintsi bazata ta6a barinshi yaga weak point dinta ba. Juyowa tayi ahankali ta kalleshi suka hada idanu. Dumm.. Gabansu yafadi gabadaya yayinda Ashraf yayi mutuwar zaune awajen yana kallonta baki bude. Qarasowa tayi har gaban table dinshi fuska ba yabo ba fallasa tana kallonshi "What! W..what the hell are you doing here?" Fuskarta normal batareda ta bayyana yanayin datake cikiba tace "Sorry, banyi introducing kainaba, I'm miss saudart shamsu by name, your new secretary" tafada cikin mugun wayancewa yadda kasan yau dama tafara saninshi. Sagale yayi da baki yana kallonta don he's totally speechless ma. Batareda ta nuna damuwa da tsaretan dayayi da idanu ba ta cigaba dacewa "Today is my first day, guess I have a lot to handle, zanje in hada scheme of work" Tana kaiwa nan tajuya tanufi qofa cikin takunta. Kasa tsaidata yayi harta fita. What! What the hell is going on? Hannu na 6ari ya jawo landline din dake kan table dinshi ya daddana lambobin landline din office din sadeeq. Fita tayi ta rufo kofar ta jingina daita hannunta dafe da qirjinta tana numfashi sama sama. Ita kadai tasan jarumtar datayi wajen facing din Ashraf. This is the toughest time ever in her life. Saida tagama dawowa daidai sannan tamiqe daga jikin kofar ta wuce jiki a sanyaye office dinta ta bude tashiga. Tsayawa tayi tanabin tsararren office din da kallo Wanda desk din dake daga gefe cike yake da computoci ga files files da scripts agefe ajere gwanin sha'awa. Tsaki taja don babu abinda ya burgeta aciki, ta qaraso ta zauna akan kujerar dake facing din desk din. Ringing din landline din ya dakatar dashi daga rubuce rubucen dayake. Saurin toshe baki yayi yana qumshe dariya ganin boss ke kira. Saida ya daidaita nutsuwarshi sannan ya daga wayar. "Hello?" "Get the hell here! Now!" Ding.. Aka katse kiran. Murmushi sadeeq yayi don dama yasan za'a Rina. Tashi yayi ya gyara suit dinshi sannan yafito. Taga fitowarshi amma saita kauda kau ta fara plugging din socket din system din tanayi tana kallonshi qasa qasa harya shige office din. Da sallama yashiga office din. Ganin yanayin fuskar Ashraf yasashi kusan kecewa da dariya, mazewa yayi ya qaraso cikin office din. "Good morning s..." "Kaga riqe gaisuwarka Mr man, what the hell did you think you're doing?" Yafada cikin daga murya "Menene..." "Don't dare ask me menene! Kafini sanin dalilin zuwanka nan" yasake katseshi a fusace "Sir.." "Don't sir me! Ka Kirani da Ashraf dina mallam, ubanwa yasaka daukarta?!" Yafada cikin tada jijiyoyin wuya. "Ashraf..." "Just shut up! Yanzu kaje ka rubuta mata takardar sallama, she's fired!" "What! Ashraf meye haka? Atleast ka saurareni" "Nagama magana, she's fired" "Amma..." "Ammo! Get out!" "A.A..." "Out!!" Shiru sadeeq yayi yana kallonshi cikin ido da alamu shima yafara fusata. "Me kake jira? I said out!" "Bazan fitaba! Zoka fiddani idan ka isa! Why zaka dinga yimin tsawa? Who did you think you are?!" Yafada shima cikin daga murya "Atleast ka tsaya ka saurareni mana, kwana biyu da yad'a vacancy letter babanta yakirani akan na dauketa aikin, I was shocked nima a lokacin amma daga baya naga ai muma wani opportunity ne garemu na tracking dinshi Nasan yanada wata manufa bayan dalilin daya karantomin na daukarta, he thought bamu sanshi bane, he thought bamusan me yake qullawaba ne. Wannan itace the easiest and the fastest means na cimmashi. I thought kaima cunkusashen kwakwalwarka zata baka haka amma am mistaken" ya qarshe zancen yana makamashi mugun kallo "Koma menene bazan iya aiki da wannan aljanar yarinyar ba" "Ita waya ce maka dason ranta tazo? She's forced kamar yadda aka tilastamata wajen qaddararen auren ka, bayan haka ko kallo baka isheta ba kaima kasani, kuma kafin ka kira wani da aljani kafara duba mirror" "Hey watch your words! Am still your boss" "Boss my ass! Nabi boss dagudu, idiot" yafada yana nufar kofa "Kaje nayi suspending dinka saina nemeka" "Sai kazo ka fiddani din, mtcheew" ya fita yana bugo kofar da qarfi. Bin qofar yayi da kallo, yasan sadeeq yakai bango ne, shi dama be iya zuciya ba, kamar yadda yakeda wuyar zama haka yakeda wuyar sauka. Tsaki yaja yakoma ya zauna yana huci. Jin anbude kofa yasata dagowa, gani tayi sadeeq ne yafito daga office din. Ta6e baki tayi ta kauda kai. Kamar zai wuce saikuma yadawo yayi knocking akan glass door dinta ya tura yashigo. Ko dagowa batayiba bare ta kalleshi, typing kawai take cikin qwarewa. "Is everything alright? Ko akwai wata matsala?" Batareda ta kalleshi ba idanunta akan screen din computer tace "No" ataqaice Be sake cewa komai ba yajuya yafita don ya lura itama yar shan qamshice na bugawa a news. Da harara tabishi don shima haushi yake bata ba kadan ba. Cikin qwarewa ta tsara scheme din sannan tafara printing din appointment letters datagani tili guda a email har tana mammakin uwar me zaiyi musu da zasuyita bankomashi wasiqar Neman izinin ganinshi. Saida tayi printing din sha biyar tana bi according to the date, sannan tsagaita hakanan ta duba agogo taga daya saura. Tattara takardun tayi ta tashi tafita ta nufi kofarshi badan ranta yaso ba. Sau biyu tayi knocking amma babu amsa hakan yasa ta murda handle din kofar ta shiga da sallama. Yana zaune kan kujerarshi ya aza gwiwar hannun damanshi dake riqeda Biro bisa table yana taunar murfin biron ahankali. Tunda tashigo ya kafeta da idanu harta qaraso gaban table din cikin salon tafiyarta. Dukda ta taqura matuqa da tsareta da idanun dayayi hakan besa tanuna ba. Qarasowa gaban table din tayi taga ko ta6a files din dazu beyiba. Dora takardun hannunta tayi kan table din "This is the scheme" tafada tana turamashi. "And these are some of the appointment letters, the one to be attended should be indicated, naga wasu harda na last week, there are two meetings tomorrow ma, daya joint meeting ne na Adams &co. Company, dayan kuma partnership meeting, gasunan dai a wannan takardar" tafada tana turamashi takardar. Shidai tsayawa yana kallonta yadda tawani yi fuska tana kwararo zance. Batareda tasake cewa komai ba ta juya tafara tafiya. "Wow! Bravo" yafada yana tafa hannayenshi. Cakk ta tsaya bugun zuciyarta na tsananta. "So? Are you this shameless?... Nasan kunya gaba kuka bata ba bayaba amma ban ta6a tunanin Rashin kunyr harta Kai hakaba" Jitayi jinin jikinta na kafewa yayinda wani daci daci ke ziyartar maqoshinta...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar(covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Gaskiya naji dadin previous comments dinku😊 Saidai na lura kuna naiman raina mana boss, to a qiyaye fa😒 Komu sa shalelenku kuka ehe😏 This page is yours *Ummu bilal* and *sis hapsy* ngd dama sauran members na Auren kwangila💖 One love💓💓💓 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 041 Jitayi jinin jikinta na kafewa yayinda wani daci daci ke ziyartar maqoshinta. "Are you that desperate?" Yafada yana takowa inda take tsaye bata juyoba. "Idan ban mantaba a company dinnan, a office dinnan, a rana irin ta yau, kika bude baki kikace ban isheki kalloba bare abinda na mallaka, you don't care who I am and my personality. Ya akayi kuma yanzu? Abin mammaki yau the proud peacock ce a gabana amatsayin secretary na...you shouldn't have stooped so low, basai kin qasqantar da kanki ba wajen cin kudina, you have the right. Da kin tambayeni ko nawa kikeso zan baki kodan darajar wannan tsararren auren namu, amma it's a shame, an extreme shame ace diyar shamsu, the mighty Saudart herself tayi stooping low wajen zama secretary na... *koba hakaba?*" yaqarashe maganar cikin rad'a yana kafeta da hazal eyes dinshi kasancewar ya zagayo gabanta suna kallon juna. Wani siririn murmushi tasaki ta kalleshi taga shima fuskarshi dauke take da murmushin gefen baki Wanda yafi kama da na mugunta. "Isn't that obvious Mr A.A?" Tafada still murmushi a fuskarta. "Ba qasqantar dakai bane, it's called *BUSINESS*" Daga gira daya yayi still yana kallonta murmushin kuma bebar fuskarshi ba. "A tunanina a matsayinka na dan kasuwa yakamata kasan the full meaning of *BUSINESS*, wannan ba qasqantar dakai bane, *BUSINESS* ne, *HALAQ* dinane, my sweat. Me kake tunani? A matsayina na yar kasuwa, diyar yan kasuwa, babana shahararren dan kasuwa ne, mamana shahararriyar yar dealer ce, duk abinda nasan zai kawomin samu muddin halaq ne zan yishi. Am a real hustler, I hustle day and night so far it's halaq, bana depending akan wani, bana jiran abun wani, bana kwadayin abun wani saboda be dameni ba, inacin guminane, haqqina, same goes with this, aiki zanyi kuma a biyani, I don't care" tafada tana daga kafadu🤷‍♀ "Batun aure kuma Kai kema tunawa dashi har kake ganin zanci darajarshi, as far as am concerned ni ba Matar kowa bace, karka manta it's all contract, signed contract. So am here for business ne kawai, bansanka ba, baka sanniba, babu wani alaqa tsakaninmu saina boss da employee dinshi, bayan wannan kuma babu wani dangantakar... *koba hakaba?*" itama ta qarshe maganar cikin rad'a. Murmushin da beyi niyyar yi bane ya subucemashi yadan kawar dakai yanayi. Lallai wannan yarinyar, her courage, her pride da confidence dinta yayi yawa. Da watace dauko dago kai ta kalleshi bazata iyaba, da watace da yanzu tananan tanaji kamar ta nitse don kunya amma banda ita, banda shugabbar yan girman kai din duk duniya. This is an opportunity, damarshice na koyamata hankali, na koyamata yadda ake girmama na gaba. "Nice one miss Saudart, business ne ya kawoki right? Babu wani dangantaka tsakaninmu saina boss damai aikin shi, good and so be it, let the business start" Saikuma ya matso dab daita har suna shaqar numfashin juna, idanunshi cikin nata. "But are you sure you can cope with a boss like me?" Dukda yadda takeji na yanayin kusancinsu ta danne tace "is this a challenge?" Cikin rad'a yace "yes" Murmushi ta qaqaro Wanda bekai zuciba tace "Challenge.. Accepted"itama cikin rad'ar. Murmushin gefen baki yayi yana kallonta, itama samun kanta tayi da d'an rausayar da kanta gefe itama dauke da irin murmushin shi. Jada baya yadanyi still idanunsu cikin juna sannan yajuya yanufi desk dinshi. Wasu takardu dogaye ya kwaso batareda yasan adadinsu ba yadawo gabanta ya dorasu saman table kusada ita. Batace komaiba sai kallon takardun datayi sannan ta maida kallonta akanshi alamun qarin bayani. " kiyi copy dinsu, kiyi printing sannan kowane guda daya ayi photocopy dinshi waje goma...Good luck " ya qarshe zancen yana komawa mazauninshi ya zauna yayi balancing Yana binta da wani irin kallo. "With pleasure" tafada da murmushi sannan ta tattare takardun tafice. Binta yayi da kallo harta fita, wani irin haushi yakeji azuciyarshi, wai me yarinyar nan ke taqama dashi ne? Me ta dauki kanta ne? Soyayi yayimata wankin babban bargo yau amma daga qarshe shi ta cusama haushin. Qwafa yayi yana jinjina kai, zan koyamiki hankali ne. Itakau tana shiga office dinta ta ajiye takardun saman desk dinta ta shige toilet dake cikin office din. Ahankali ta qarasa gaban sink din toilet din ta bude fanfon wajen ta Tara tattausan tafin hannayenta ruwan na zuba cikinsu tana kallo. Biji biji tafara gani sanadiyar hawayen dasuka tararmata acikin idanu. Barinsu tayi suka gangaro batareda tayi yunqurin tsaidasu ba. Tun tana hawaye harta fara shesheka ahankali. Zafi takeji acikin zuciyarta kamar ana ruramata wuta, ga wata wutar Qin Ashraf dake ruruwa a zuciyarta, ga takaicin abinda daddy yayimata dazu, Abu dai yazaman mata goma da ashirin. Saida taci kukanta ta qoshi sannan ta wanke fuskarta da ruwan fanfon ta tsane fuskarta da hand towel. Dagowa tayi ta kalli kanta ta cikin mirror dake jikin sink din taga idanunta dama fuskarta sunyi jajur. Murmushin takaici tayi sannan ta daura alwala tafito. Dayake tazo da spare hijab a Jakarta dama, veil dinta ta warware ta samu qusurwa ta shinfida, dayake Allah yamata baiwar gane gabbas duk inda ta tsinci kanta, down haka shimfidawa tayi ta zura hijabi ta gabatar da sallar zuhr, tayi addu'o'inta sannan ta miqe tacire hijabin ta yafa veilbdinta qaraso gaban desk dinta. Takardun daya bata ta dauka tafara dubawa. Gabanta ne yafadi ganin uban aikinda yasata. Takardun qwara shabiyar dogaye kowanne an rubuceshi gaba da baya, tasan intayi gudun tsiya tayi copy din biyu cikin awa daya, kafin a kaiga printing ga kuma photocopy. Jitayi wasu sabbin hawaye na zuwamata, saurin maidasu tayi tana girgiza ksi 'No saudart, ba yanzu ba, you're strong, be strong' Jan kujerar gaban desk din tayi ta zauna ta zari paper daya tafara aikin. Aiki take tuquru batareda shiriritaba, babu abinda ke tadata sai sallah, tama manta dawani Abu waishi abinci, kodama ta tuna batajin tana iya sama cikinta wani Abu. Qarfe shidda saura kofar office din Ashraf ta bude ya fito hannunshi daya riqeda briefcase dayan kuma sa6e da jacket din suit dinshi. Taji fitowarshi kuma tasan shine amma ko dago kanta batayiba bare ta nuna tasan da wanzuwarshi. Shima ko gefenta be kallaba yawuce private elevator dinshi da shi kadai ke ya Danna floor din qarshe kofar ta bude yashige. Sai bakwai saudart tafito daga company din, shima bawai tagama aikin bane. Tadaiyi copy din duka tayi printing dinsu, photocopy kawai yarage Wanda ta aje da niyyar shine Abu na farko dazatayi gobe idan Allah ya kaimu. Agajiye tashiga motarta tarufe tafice daga company din, saida ta tsaya restaurant tayi takeaway taje pharmacy ta siya maganin ciwon jiki sannan tanufi gida. Agajiye ta qarasa gida, sallar magrib da isha'i tayi tadanci abinci sannan tasha magani tabi lfyar gado. Kasancewar a agajiye take bata wani Dade a kwance ba barci ya sadado ya dauke ta...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 042 Washegari tunda tayi sallar asuba bata koma barciba. Laptop dinta taja tadanyi yan dube dube da gyare gyare akan abinda yashafi bakery dinta da ice cream joint. Ciwon jikin yarage sosai saidai haryanzu yatsunta na zugi saboda typing datayi. Qarfe bakwai da Rabi ta rufe laptop din, ta tashi ta jona ruwa a electric kettle sannan tashiga wanka. Bata jimaba sosai tafito ta shirya cikin atamfa Riga da skirt ta Dora baqar after dress ta yane kanta da gyalen after dress din. Yauma bawani kwalliya tayiba tadai dan bursuna powder da kajal ta taje lashes din idanunta da mascara. Hada kakkauran shayi tayi ta zauna tasha sannan ta feshe jikinta da turare tasaka takalmi tadau Jakarta tafice. Direct parking space tanufa nan taga duka motocinshi nanan alamun be fitoba. Shigewa motarta tayi tabata wuta sannan tafice daga gidan. Qarfe 8:25am ta isa company din. Parking tayi a space din sannan tafito cikin unique shigarta ta wuce cikin company din cikin takunta mai cikeda nutsuwa. A gyare ta tarda office dinta sai tashin qamshi yake da alama ma ba'a jima da gyarashi ba. Babu 6ata lokaci ta jawo aikin da bata idaba jiya tahauyi. Cikin qanqanin lokaci tagama sannan tadawo ta zauna gaban system dinta ta bude. Sai qarfe goma Ashraf ya iso company din. Ta gaban office dinta yazo yawuce amma ko daga kai ta kalleshi batayiba hasalima nunawa tayi batama lura dashiba. Saida tagama abinda tajeyi tsaff sannan ta kwashi dukan takardun tafito daidai shima sadeeq yafito daga office dinshi. Ganin tana niyyar yin fuska tawuce yasashi saurin cewa "Good morning ma'am" Tsayawa tayi batareda ta juyoba, tasan ita yakamata ta gaidashi sbd yafita matsayi a company din amma batajin tana iya gaidashi, a halin yanzu ta tsani duk Wanda keda alaqa da A.A idan aka cire Ummy da baby. "Hyy" kawai tace zata wuce. "Yau za'ayi meeting dinnan ko?" Yaqara fada Batareda ta tsaya daga tafiyar datakeba tace "Nasani" Tayi knocking sau daya tabude kofar tashige tabarshi anan. Jin anbude kofar anshigo yasashi dago kai yana kallonta. Qarasowa tayi gabanshi batareda tabari sun hada idanu ba ta ajiye takardun kan desk din. "Good morning" tafada ciki ciki Be amsaba kuma bebar kallonta ba "Ga papers dinnan, kuma yau munada meeting biyu, daya qarfe 12:00pm dayan kuma bayan asr" Bece mata komai ba sai jawo takardun data ajiye yayi yafara dubawa. Yayi mammaki sosai na ganin ta gama aikin duka kamar yanzu, shi bemayi tunanin zata gamashi yau ba, a tunaninshi saikuma batun gobe. Be bari mammakin ya bayyana a fuskarshi ba ya cigaba da dubawa ko zaiga mistake ko dayane amma komai daidai yake kuma cikin tsari. "Ok, amshi" yafada yana miqamata takardun. Babu musu ta amsa "Ki chikwikwiyesu duka" Dum gabanta yafadi tayi saurin dagowa ta kalleshi. Dagamata gira daya yayi yace "Yes, squeeze it" Wani Abu ta hadiye a maqoshinta dakyar sannan ta ajiyesu kan table din ta fara dauka da daya daya tana chukwikwiyewa tana ajiyewa gefe. Tasan yayi hakanne don ya 6atamata rai yaganta cikin bakinciki saidai bazata bashi abinda yakeso ba don haka ko afuska bata nuna ta damuba, fuskarta nanan dai yadda take babu yabo babu fallasa amma karka bincika zuciyar. Haka taita chukwikwiyewa harta gama. "Sasu a waste basket" Babu musu ta kwashesu ta zubasu a wani emptyn kwadon shara dake daga can gefe. "Good ga wannan ki karanta" yafada yana miqamata wata paper Amsa tayi tana dubawa "Ba aciki zaki karanta ba, a bayyane" Daidaita muryarta tayi sannan tafara karantawa. " 1. Lokacin zuwa office 8:00am 2. Hada coffee 8:55am 3. Gabatarda aikin da aka kwana dasu 9:10am 4. Girmama na gaba dakai ta hanyar kiranshi sir ko ma'am 5. Kar ashigo office harsai anbada izini duk jimawarka kana knocking. 6. Another coffee 3:00pm 7. Closing time 6:30pm" Dago kai tayi daga takardar bayan tagama karantawa. Ahankali yabude bakinshi kamar beso yawani yi balancing a kujera yana dan jujjuyawa yace "Nakine.. Fatan za'a kiyaye" "Ok" tafada a ataqaice "Ok..what?" Yafada yana tsareta da idanu Banza tayi dashi don batajin tana iya kiranshi da sir din dayakeso, Kai ina? Bekaiba. "Magana Nike" Nanma tsit don ko gefenshi bata kallaba Murmushi mai dan sauti yasaki sannan yajawo wasu takardun cikin wadanda yabata jiya ya Diba da yawa Suma batareda yasan adadinsu ba ya tura a gabanta yace "Same thing da kikayi jiya" ya koma ya jingina da kujerar yana kallonta. Babu musu ta kwasa har gyara zamansu take kamar bata damuba sannan tajuya tafice. Binta da kallo yayi harta fice sannan yayi qwafa yana jinjina kai. Komawa tayi office dinta ta Dora takardun saman desk ta zauna kan kujera ta kifa kan akan desk din tana sauraron yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata fado Gawani suya na musanmman datakeyi. So take tayi kuka ko zataji sauqi amma kwata kwata kukan yaqi zuwa, ambaton sunan Allah tafarayi tana dan jujjuya kanta saman desk din. Ta jima ahakan sannan tafarajin sauqi acikin zuciyarta. Tashi tayi ta jawo papers din Suma tahau copy dinsu. 11:55am ta dakatar da aikin datake ta miqe tanufi office din A.A don 12 dot za'ayi meeting din. Kwankwasawa tayi taji shiru tasake nanma shiru, tasake nanma tsit. Murmushin takaici tasaki, wato don ya wulaqanta ta yasashi kafa dokar idan ba iziniba aka badaba kar a shiga. Komawa tayi office din ta share shi, ayi cancelling din meeting din for all she care. 12 daidai sadeeq yafito daga office dinshi da niyyar wucewa shima meeting din. Mammaki yayi ganin saudart a office tana aikin ta ta dode kunne da earphones irin Wanda ake dorawa akai dinnan. To ko batasan da ita za'ayi meeting din ba ne? Tambayar dayayiwa kanshi kenan. Qarasowa office din yayi yayi knocking. Dagowa tayi ta kalleshi batareda tace komai ba. Shigowa yayi ya tsaya daga bakin kofa yace "Are you not supposed to be in the meeting Hall?" Dan zame earphones din kunnenta tayi tana cewa "Perdon?" Ajiyar zuciya yayi yace "nace meyasa baki fito meeting din ba?" "Boss dinne ke barci" tafada tana maida earphones dinta Shiru yayi cikin mammaki. "Barci?" Bata ko dagoba bare yasamu amsa. Fita yayi ya nufi office din A.A din ya bude batareda ya kwankwasa ba. A.A daya cika faam saboda tafiyarta datayi daga tayi knocking uku be amsaba kuma gashi har sha biyun ta gota bata dawoba ya dago Kai don ganin wane isashen ke shigowa batareda knocking ba. Ganin sadeeq ne yasashi kauda kai. Shima sadeeq qara tamke fuska yayi don haryanzu be huceba ya qaraso ciki. "Yadai? The meeting is 12 gashi yanzu past 12" "Cancel it" yafada batareda ya kalleshi ba. "What?" Inji sadeeq cikin Waro idanu "Am not speaking Chinese" inji Ashraf yana wullamashi mugun kallo "Wai for goodness sake Ashraf lafiyarka qalau kuwa? Meeting din da kusan wata daya kenan da arranging dinshi zakace ayi cancel? What exactly is your problem?" Inji sadeeq ciki quluwa jiyake kamar ya rufeshi da bugu. Banza Ashraf yayi ya kyalleshi "Look Ashraf idan saboda saudart ne fine, ka sallameta din, atleast kasan badakai ta dogaraba kuma itama Kanta bada son ranta take aikinnanba ni shaidane, zanje inyi firing dinta kowama ya huta" yafada afusace yanufi kofa. "Don't dare me! Ban sakaba" "Saika sani?" "Sadeeq don't!" Hakan yasashi juyowa yana kallonshi "Menene to? Bakai kace kayi firing dinta ba?" "That was then, amma yanzu dolene tayi aikin, dolene!" "Kai ka isa kasata dolene?" "Namayi yawa so shut the hell up!" "Mtcheew yanzu zaka meeting din ne koko?" "Dole saina jera dakai?" Tsaki sadeeq yaja yafice yana fadin "kanka yakeji" Koda yafita bega saudart a office din ba hakan yasashi wucewa Hall fin meeting din inda a can yaganta sunadan tattaunawa da baqin cikin Sakin fuska. Saida ya mula yasha iska sannan yashigo Hall din fuskarshi a tamke. Saida ya zauna sannan meeting din yafara. Saudart ce ta miqe tafara gabatar da dalilin taruwar meeting din. Sosai ta burge mutane da yanayin yadda take gabatar da abin cikin nutsuwa da turancinta lafiyayye ga fuskarta a sake very friendly, hakan yasa kowa ya maida hankalinshi kacokan akanta. Bayan tagama takoma ta zauna nan P.A wato sadeeq ta Dora daga inda ta tsaya yana yimusu bayani dalla dalla akan abinda ya tarasu sannan shima boss ya Dora da nashi shima cikin bi daki daki da ganin cewa ya warware musu komai. Ataqaice dai saida sukayi awa daya a office din sannan aka gama meeting din kuma alhamdullilah ansamu abinda akeso Gawani farijinin da saudart tayi nan take don sai yabonta ake kan qwarewarta da fara'arta. Koda suka fito direct office dinta takoma tayi azahar sannan takoma kan aikinta dukda tasan shima qarshen shi basket za'a sakasu. Uku dot ta dakata ta tashi tana gyara gyalenta sannan tafito ta nufi office dinshi don hadamashi coffee din. Bugu daya, biyu, uku amma yanzu ma tsit ba'ada niyyar amsawa hakan yasata Jan tsaki ta murda kofar tashiga da sallama...✍ Manage please🙏 Ummin fasihu ce 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Wayyo fans naga cigiyarku, am sorry😢 wlh WhatsApp dina yayi expire, dama na fadamaku yakusa sai yau naturo wani, but I missed you too, soo much😘😘 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 043 Yanzuma dagowa yayi yana kallonta, batareda tabari sun hada idanu ba ta nufi coffee maker din office din tafara hadawa. Dauke Kai yayi ya maida kan rubutun dayake acikin zuciyarshi kuma yana ayyana yadda zai koyamata hankali. Wato simple instruction bazata biba, kenan she's too big tajira yabata izinin shigowa? Kwafa yayi cikin zuciyarshi, he wonder why she's so proud of herself, jin kanta yayi yawa, me take dashi? Metake taqama dashi? Idan kyau ne akwai wadanda suka dameta suka shanye a kyau suna binshi, akwai classic ladies dirarri wadanda saita raina kanta agabansu masu so ko kallo daya ne yayimasu amma basu isheshi kalloba. Mace bata ta6a rainashi ba yadda ta rainashi, mace bata ta6a nuna halin ko-in-kula dashiba kamar yadda takeyi, wasu ma dying suke dan suji ya furta koda kalma dayace garesu amma this one is as if ko ganinshi batason yi. Beta6a sanin akwai mata masu girman kai da jida kai sai akanta, yasaka shi akebi yana wulaqanci son ganshi hakan yasa yakejin wani iri yanzu idan tanuna she didn't care about his existence, gani yake it's an insult to him ace kamar wannan yarinyar na nuna batamasan da wanzuwarshi ba. Ajiye mug din coffee daketa faman tururi agabanshi ya katsemashi tunani. Dagowa yayi yana kallonta qasa qasa. "Sugar or honey?" Ta tambayeshi batareda ta kalleshi ba. Banza yayi da ita tareda cigaba da rubutunshi. Bata sake tambayarshiba ta dauki sugar cube biyu tasaka mashi ta jujjuya sannan ta maida sugarn da zuman ma'ajinsu tayi hanyar fita. "Stop!" Ta dakatar daita da hakan. Cak ta tsaya batareda ta juyoba. "Come back here" yafada still hankalinshi nakan rubutunshi Babu musu tadawo ta tsaya gabanshi not saying anything "Throw the coffee away" yafada batareda ya dagoba. Jimm tadanyi sannan ta dauki mug din tawuce toilet ta juye a sink ta dauraye mug din tadawo ta kifa, harta kusan kaiwa kofa taji yace "Make another one" Wani Abu taji ya zo daidai maqoshinta ya tsaya yaqi wucewa. Me wannan gayen ke nufi da itane? Ta hadamashi yasata zubarwa kuma yace ta hada wani? Me yakeso daita ne? 'He want you angry'_wata zuciyar ta rada mata. 'Then he should hug transformer' tafadawa zuciyar Juyowa tayi batareda nuna dumuwar komaiba a zahiri amma a badini tafasa take, kai tama fara kamu, jitake kamar ta Dora hannu aka taita ihu. Haka takoma tasake hado wani coffee din, wannan karon honey tasa teaspoon daya takawo mashi. Yanzunma be tashi yimata magana ba saida takusan kofa sannan yace ta zubar. Gani yake abin nata gaba gaba yakeci, wato she can't ask twice? Lallai Sake sata hada wani yayi, tahada again this time around sugar tasa saida ta ajiye yasake sata zubarwa. He want to show her ya isa and she must follow his instructions a matsayinshi na boss dinta. Itakuma a 6angarenta she know exactly abinda yake nufi amma ta nuna batasaniba, her ego won't let her ask again. Haka taita zaryar hadawa tana zubarwa, sosai zuciyarta ke suya kawai daurewa take ga maqoshinta har wani yaji yaji yakeyi amma taurin kai ya hanata surrender Ahakan sadeeq yashigo don ajiye wani file sannan ya wuce masjid. "Throw it away" yasake cewa batareda ya dagoba Itama bata kalleshi ba tashiga toilet tadawo da empty mug. Da mammaki sadeeq yatsaya yana kallonsu cikin son fahimtar meke faruwa. "Make another one" yasake umartarta. Babu musu tasake hada wani takawo ta ajiye. "Throw it away" "What?" Inji sadeeq cikin tsananin mammaki Wani kallo Ashraf ya wurgamashi yana kauda kai. Itakau saudart bata tsaya sauraron su ba tawuce toilet din. "Ashraf meye haka?" Banza yayi dashi. "Look Ashraf, da baban wannan yarinyar kake da case bada itaba, why zaka dinga wahalar daita? Plus almubazzarancin dakake, kasan wani nacan ba Neman Rabin wannan vesamuba amma kai kesawa a zubar?" Nanma banza yayi dashi, zai sake magana tafito riqeda mug din "Ermm.. You can go please" inji sadeeq yana kallonta. Batace komaiba ta kifa mug din tawuce zuciyarta kamar tayi bindiga. Saida tafita sannan sadeeq yasake cewa "A.A kaji tsoron Allah, sbd kaga mutum na qarqashinka zaka dinga zaluntarshi" "Dakata mallam! I have the right din sakata ko hanata, am her boss ok?! Inada right to do anything ok?! Don haka karka sake questioning dina, muddin zata cigaba dayimin girman kai to bataga komaiba ma, mtcheew!" Ya tashi yanufi toilet kamar zai tashi sama. Binshi da kallo yayi harya shige sannan ya ta6e baki yad'an daga murya yace "To zuciyatu, karka manta munada meeting bayan asr, idan kuma kaga dama cancel it, ruwanka" ya fice Tsaki yaja cikin toilet din yanufi sink din, abinda yagani yasashi tsayawa yana kallo cikin mammaki. Coffee ne ciki wani bowl yawuce rabi, kenan ba zubarwa ba take? Ya tambayi kanshi. Wata takarda yagani qarqashin bowl din tadan leqo. Dagawa yayi yazarota ta duba yaga an rubuta *ALLAH YA HANA* Wani Abu yaji har cikin zuciyarshi Wanda be ita cewa ga yadda abun yake. Tsaki yaja ya cimimiye takardar ya yadda ya dauro alwala yafito daukeda bowl din ya juye coffee din cikin flask dake office din da niyyar zaibayardashi kyauta. Itakau tana fita office dinta tawuce sannan direct tanufi toilet dagudu tana toshe bakinta saboda kukan dake Neman kufce mata. Sosai take kuka jikinta har wani rawa rawa yake, jitake ta tsani komai a rayuwarnan, rayuwar kwata kwata ta daina yimata dadi, she can't believe ita ake wulaqantawa haka, dama ance idan ka hau motar kwadayi zata ajiyeka a tashar wulaqanci, and this is all daddy's fault, koma me akayimata shi yaja mata, son kanshi da kwadayin shi yaja mata. Saida taci kukanta ta qoshi sannan ta daura alwala tafito ta gabatarda asr. Tana zaune bayan tagama sallar taji ringing din landline, kamar bazata tashiba saikuma ta tashi taje ta daga. "Miss saudart hope baki manta da meeting din ba?" Inji sadeeq daga dayan bangaren "Yes" ta amsa a gajarce. "Ok it's time" yafada sannan ya katse kiran. Gyara fuskarta tayi yakoma normal sannan ta fita. Yanzu ma alhamdullilah the meeting is successful and saudart is becoming more popular, tana wani baiwa na shiga rai farat daya don haka nan danan tasiye zuciyar mutane dayawa. Sosai suke yabonta don wasu saida suka magantu suna cema Ashraf wannan tafi wancan don Helen babu abinda ta iya sai shegen iyayi, a maqe murya ana rangwada , gata kullum a tsuke kuma irin matan nanne masu ga6a ga6an jiki, shiyasa wani sa'in idan tasa wasu kayan maimakon ta burge saima tazama abun kallo. 6:30pm tabar office din kamar yadda yafada. Yauma haka tadawo agajiye saida ta kora da maganin ciwon jiki. A ataqaice dai haka saudart taita fama, mugunta kala kala A.A kemata, duk yadda zai 6atamata rai saiya yi, haka kawai zai sata unnecessary Abu daga qarshe yasata yagewa ko lallatawa da kanta, hakan ba qaramin 6atamata rai yakeba hakannan take daurewa don shima ta gumamashi. Sai yanzu tagane dalilin dayasa baby ke kiranshi mugu don yaci sunan kuwa, don kusan kullum saita la6e toilet tasha kukanta. A bangaren daddy kuwa yashiga damuwa sosai, tun lokacin databar office dinshi yashiga damuwa, yasan be kyauta mataba Sam, yasan yaso kanshi dayawa, rabon daya ganta kosuyi waya tun ranar, ita bata kiraba shikuma kunya ta hanashi kira. Addadafe ranakun satin suka wuce aka shiga weekend. Sai a lokacin tasamu damar leqa bakery dinta da ice cream joint. Kuma babu laifi Allah yasamata albarka a harkar don tana samu sosai. Ranar lahadi kuwa qannenta sukazo suka yimata yini, sosai taji dadin zuwansu don sun debemata kewa sosai, basu suka koma gidaba sai magrib bayan ta cikasu da gift sosai. Suna tafiya itama ta hayewarta sama don batason ganinshi, rabonta dashi tun ranar Friday a office kuma batason ganinshi din sai goben shima don yazama dolene don yanzu tsanarshi qara farashi take kowacce daqiqa mai tafiya...✍ Sorry babu yawa, banda chaji🙏 Zanmaku another page da anjima insha Allah Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 044 MONDAY jiki a sanyaye take shiri.tana tunanin ya kuma haduwarsu ta yau zata kasance. Idan akwai abinda tafi tsana yanzu to bewuce ganin koda wulginshine ba, gani take kamar kullum qaramata tsanarshi ake, tasan yauma dakyar idan bazai sata kukaba. Qarfe 8:00am daidai yayimata a office, tunda kuma tashigo tashiga busy Abu guda dazai burgeka gameda ita shine duk tsanarshi da aikin datake hakan be hanata yin aikinta tsakani da Allah, she's so hardworking shima shaidane. Be shigowa company din ba sai wajajen 9:00am, kamar kullum bata nuna taganshi ba harya shige office. Can taji landline dinta na ringing, batareda ta dauke kai daga abinda takeyi ba ta daga wayar ta kara a kunne. "Come" taji ance aka katse kiran. Bin wayar tayi da kallo sannan ta saki tsaki ta ajiye ta tashi Kamar dai yadda tasaba knocking uku tayi bata jira amsaba tashiga "Good morning" be amsata ba yace "Have a seat" batareda ya kalleta ba. Jan kujerar gaban table dinshi tayi ta zauna. Shiru yadan ratsa office din nawani lokaci kanshi kasa yana yan rubuce rubuce kafin ya dago ya kalleta. Sanye take da dakkakiyar shadda dark purple sai farin gyalen data yafa stylishly fuskar kamar kullum babu tarkacen makeup. Sosai tayi kyau in her own way. Balancing yayi sosai saman kujerar yana dan jujjuyawa yana kallonta. Kamar mai ciwon baki yace "Duk sadda nashigo office you should follow me kiji ko akwai magana basai na kiraki ba, ok?" "Ok" tafada tana ta6e baki cikin zuciyarta "Good, now take a look" yafada yana miqamata wata takarda yana kafeta da mayun idanunshi Babu musu ta amsa tana dubawa "It's a business trip" yafada yana kallonta Itakuma tana kallon takardar "Tafiya ce mai matuqar muhinmmanci Wanda dole tafiyar saidake tunda you're my secretary, but am not sure of going with you don nasan akwai wata manufarki na aiki anan, tayaya zan yadda dake?" Yafada yana kallonta. Ta6e baki tayi tana daga kafadu "Then ka nemi wani, don't care" "Hmm haka kike cewa amma ni da ke munsan yo do care" Batace komai ba don izuwa yanzu gani take yawane musayar magana dashi, she so much despise him da ko magana bataso ya hadasu. Ajiye takardar tayi ta harde hannu a qirji. "Dake zani babu Wanda zan chanza so maintain" Nan ma banza tayi dashi taba iska ajiyar shi "Tafiya zamuyi qasar Spain, akwai wani contract dazamuyi signing da wani shararren company Wanda zaijama company dinnan cigaba, well meyasa nake ma fada maki, is not as if cigaban mu kikeso ba" yafada yana yatsina. Nanma ta6e baki tayi without saying a word "Wednesday zamuyi tafiyar, jibi kenan, nabaki hutun gobe saboda shirye shiryen tafiyar, flight din12:00pm zamubi, your visa and everything Will be ready by tomorrow, don't forget 12:00 flight zamubi" yafada bossily "Ok" ta amsa absentmindedly "Coffee" yafada yana sake jingina da kujerarshi Babu musu ta tashi ta hadamashi coffee din don yanzu kullum saita hadamashi. Be sake cin arziqin tambayarshi sugar yakeso ko zumaba, duk wadda taga dama shi take samashi shima beyin complain haka yake amsa. Tana gamawa ta ajiye mashi tafice. Koda takoma office tunani taitayi, business trip? Spain? What has dad got her into? Me zatacewa mamy akan tafiyar? Kullum suna waya dolene idan suka tafi zata kira taji baya shiga kuma dole idan sun isa can ta kirata da foreign number. Daddy? Tunaninshi ne yafadomata a rai, rabonta dashi tun ranar databar office dinshi, sati guda ciff kenan. Wayarta ta janyo tashiga contact ta dannama number shi kira. Harta gama ringing ta katse ba'a dagaba, taqara kira nanma shiru hakan yasata turamashi gajeren SMS *good morning dad, fatan kana lfy, kasaka mu cikin addu'a jibi insha Allah zamu Spain* Tana aikawa ta kashe wayar takoma ta jingina da bayan kujerar tana lumshe ido. Dad na ganin kiranta amma yakasa dagawa, kunyartar yakeji kamar me? Jin txt yashigo yasashi saurin dubawa. Jikinshi ne yayi sanyi bayan ya gama karantawa. He missed his dear daughter badly, kusan koda yaushe saiya dauki waya zai bugomata amma saiya rasa me zece mata sbd yasan he's not a good father to her, kullum burinta ta faranta mashi, tana mashi biyyaya daidai gwargwado amma yasaka mata da wannan amma he's regretting sosai. Kwana biyun nan dayayi beji muryarta ba jiyake kamar yayi shekaru bejitaba. Sosai yake nadaman abinda yayi, yasan ba qaramin zubda mata da mutunci yayiba Wanda shi a lokacin duk beyi tunanin hakan ba kawai shi hangenshi me zai qaru dashi be tunanin me zai ragu dashi. Danna number ta yayi ya kira amma switch off, sake kira yayi nanma haka, Qin haqura yayi yaita kira dan sosai yakeson jin muryarta, jiyake dolene ya nemi yafiyarta kuma ya warware komai. Bata kunna wayartaba har takoma gida. Saida tagama komai na aladarta ta haye gado sannan tajawo wayarta ta kunna. Massages ne sukaita shigowa babu qaqqautawa dukna daddy. Tsayawa tayi suka gama shigowa sannan tafara budewa, na farkon taga ansa *shalele na...am sorry* Na biyun kuma akasa *I know am not a good father, am ashame of myself, will you find a place in your heart and forgive your dad?* Jikinta ne yayi sanyi, a sanyaye ta bude na ukun *please switch on your phone.. Please* Zata bude na hudun kiranshi yashigo wayar A sanyaye ta daga ta kara a kunne tayi shiru "Shalele?.." Kamar yace fara kawai saita fara hawaye. "Shalele am sorry, am soo sorry" "Daddy me nayi maka da tsanani haka harka shareni na tsawon one week?" Tafada cikin kuka "Ai nayimaka abinda kakeso ko? Then why did you abandon me?" "Shalele kiyi hqr.." "No dad, kai zan ba hqr, wataqila nayimaka wani abun ne, am sorry" tafada cikin matsanancin kuka zuciyarta na zafi "Shalele please kiyi shiru,stop crying kokuma nima nayi, am soo sorry, am selfish, saboda sonkai irin nawa na zubda maki mutunci ba zubdama kaina, am sorry kinji? Daga yau no more zuwa aiki companyn, insha Allah zan yi qoqarin hada kudin a warware komai, nayi nadama, please forgive me" yafada cikin sanyin murya "No dad, ni bakayimin komaiba, infact ina iyayin komai don farincikinka, am not leaving the company now, ba yanzu ba" "No shalele, it's over" "No dad, not yet..please banaso kasamu karayar arziqi" "No shalele, I can sell the mall ma, samu da tashi duk na Allah ne, zan sayar, Zan kammala komai cikin week dinnan a biyashi" yafada sounding serious 'No dad not now, kabani lokaci" Haka sukaita ja, dakyar daddy ya haqura but har cikin zuciyarshi dagaske ne yayi nadama, akan abin duniya yana Neman salwantar da farincikinshi, akan abin duniya yana Neman rysa kanshi, yasan yayi kuskure and he's regretting kuma ya quduri aniyar gyara wa. Sun dan ta6a hira kasan sannan sukayi sallama, ranar tayi barci mai dadi don murmushi kasa barin fuskarta yayi ko acikin barcin. Washegari gidan mamy taje ta yini, sosai taji dadin zuwanta don dama tayi kewarsu, wannan karon sun hadu da Abba kasancewar ranar yadawo daga wata tafiya, nan suka hadu sunata fira gwanin sha'awa. Anan take gayamasu batun tafiyarsu Spain acewarta aiki zaije shine zai tafi daita. Addu'o'i sukayi mata sosai da shawarwari nagari sai la'asar tabar gidan tawuce mall din daddy. Dariya taita yimata daddy ganin sai kakkauda kai yake wai besan su hada ido. Tun yana kunyarta harya ware sukaita fira don saudart bata wani dauki abun dazafi ba yadda yayi tunani. Sai tambayarta yake ya A.A ke treating dinta sai tace lfy, beyimata komai. Matsamata yayi akan tayi shopping na tafiya. Dafarko taqiya amma daya matsamata saita dan tsinci gowns kadan. Ganin haka yasa Dad yimata shopping din dakanshi, gowns yan kanti ya kwasanmata kala kala kowanne da March na shoes da bag dinshi. Sosai taita complaining sunyi yawa amma shi ko a jikin shi Shidai burinshi ya faranta mata. Ba ita tadawo gidaba sai wajajen 9:00pm shima daddy ya kawota dakanshi. Fitowa tayi tana dagamashi hannu harya wuce, she's so happy, duk saita nemi baqincikinta ta rasa. Haka tashigo gidan niqi niqi da kaya, tun a parking space tagane yana gidan. Da sallama tashiga falon, hangenshi tayi kan daya daga cikin cushion din falon ,zaune sanye da baqar singlet da baqin wando ya duqufa kan laptop. Kallo daya sukayima juna suka kauda kai. Wuce shi tayi ta hayewarta sama batareda tasake kallonshi ba tashige daki Toilet tawuce tayi wanka don ta kwashi gajiya sosai. Koda tafito shirya wa tayi cikin kayan barci sannan tahau shirya kayanta. Saida ta tabbatar ta kammala komai sannan tabi lfyr gado ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya...✍ No editing🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 045 Qarfe goma daidai tafito daga dakinta sanye da wata jallabiya peach colour mai adon pink agaba tayi rolling din gyalen jallabiyar, hannunta daya riqeda handbag dayan kuma janye da qaramin trolley. Saukowa tayi janye da trolley din jikinta sai tashin qamshi yake. Tsayawa tayi a falon ta kashe komai na wuta kamar yadda tayi a kitchen da dakinta sannan tafito waje walking majestically kamar ba ita ake jiraba. Ashraf ya qulu iya quluwa, tundazu ya aika drivern dazai kaisu yakirata amma sai yanzu taga damar fitowa. Ta side mirror yake kallonta ta taho kunnenta kare da waya da alamu waya take ga wani sihirtaccen murmushi datake saki Wanda ya bayyana jerrarun haqoranta farare Tass ga dimple dinta na dama daya lo6a. Tsayawa yayi yana kallonta don tunda yasanta be ta6a ganin murmushinta ba she's always moody or expressionless. Qarasowa tayi driver yayi saurin fitowa ya zagayo ya budemata kofar baya side din dama tashiga ya rufe sannan ya zagaya baya don saka trolley din a booth. Qamshin turarenshi dataji gab daita yasa gabanta faduwa, batayi tunanin tare zasu tafiba don koda driver yazo dazu tazaci shizai kaita shi Ashraf din yariga yayi gaba. Cikin dabara ta gyara zama tanasa style tana dan matsawa daga gefenshi. "Ok sweet dad saina kira din, love yah" tafada tana blowing mashi kiss Sannan ta katse kiran tana qara dan matsawa daga gefenshi. Satan kallonshi tayi da wutsiyar ido taga hankalinshi nakan wayar hannunshi fuskar nan kamar anmashi bishara da jahannama. Ta6e baki tayi ta maida kallonta ga windown motar tana kallon waje yayinda drivern ya tada motar suka fice. Tsit motar tayi babu mai ko qwaqwaran motsi, kowanne ya maida hankalinshi ga abinda yashamashi kai. Saudart sai kalle kallenta take ta window, ganin andauki hanyar gida Ummy yasata jin wani irin farinciki har cikin zuciyarta. Horn daya yayi aka wangale musu gate din suka shiga sannan direct suka nufi parking space Bata jira akazo aka budemata ba ta 6alle murfin motar tafita da sauri tanufi su Ummy dasuma suka nufi parking space din. A tsakiyar hanya suka hadu suka rungume juna saudart da baby dake ta tsallen murna itakam saudart sai dariya take. Sakin baby tayi ta qarasa wajen Ummy daketa washe baki ta duqa da niyyar gaisheta Ummy tayi saurin tarota itama ta rungumeta cikin farinciki. Ashraf daya fito ya jingina da mota Kasa daina kallonsu yayi ganin yadda suke murna daga ganinta kawai kuma da alamu sunma mance dashi. Be ida sanin sun mance dashiba saida yaga sun juya su duka sun nufi cikin gida cikin raha da dariya. Kutt.. Yafada yana Waro idanu ganin dagaske fa mancewa dashi din sukayi, afusace yamiqe daga jikin motar shima yanufo cikin gidan kamar zai tashi sama. A falo suka yada zanyi baby sai zuba take kamar ri6a6iyar radio, sai roqonta take wai dan Allah tayiwa Ashraf magana aje daita Ummy nacewa bata isaba saidai ita ta gayamashi da kanta itakau saudart sai dariyar dramarsu take. Suna haka sukaji an banko kofa an fado ciki Wanda hakan yasasu dagowa dukansu suna kallon kofar. "Laa wai Ashe kana waje" inji Ummy Wanda hakan yaqara fusatashi ya turo baki yana ida shigowa falon Itadai saudart kauda kai tayi tana ta6e baki don ita kwata kwata shagwa6ar dayake haushi yake bata. Saurin daidaita zama baby tayi tana qaqalo murmushi tana gaidashi. Banza yayi daita yawuce ya zauna kan wata kujera nesa dasu sai cika yake yana batsewa. "Ummy ina kwana?" Yafada yana hura hanci "Lfy lau, lafiyarka kaketa hawa kamar flour da yeast yaima yawa?" Tafada cikin sigar tsokana Kallon baby dake faman danne dariyarta yayi ya gallamata harara tayi saurin sadda kai qasa sannan ya kwa6e fuska "Ummy yanzu ace nazo gidannan amma ko lura dani bakiyiba sbd wancan" yafada yana gallama saudart harara, aikau akaci sa'a shi take kallo lokacin daya watsamata hararar, hakan yasata kauda kai tana ta6e baki cikin zuciyarta. "Saika rungumi sorry, aini idan daughter na waje macewa nake da kowa" inji Ummy cikin halin ko-in-kula "Amma ai kinsan da tsohuwar Zuma ake magani ko?" Yafada yana turo baki "Waya gayamaka? Sabuwar ma tanayi, wani sa'in ma tafi guarantee" tafada tana antayamashi harara sannan ta maida hankalinta Jan saudart data sadda kai tana saurarensu tafara janta da fira tana amsawa a kunyace itakam baby anyi 6amm ankasa magantuwa. Ahaka aka gabatar musu breakfast sukadan ci sannan suka tashi zasu tafi baby sai liqewa saudart take tana mata rada Itakuma saudart na antayamata harara. Haka suka fito har wajen da motarsu take. "Anty ayimana tsarabar honeymoon, yan biyu nakeso masu kyanki" baby ta sake radamata a kunne. Tsarabar harara tasamu harda mintsini Wanda yasata Sakin qara tana dariya. "Ummy zamu wuce, ayafe" tafada a kunyace. "To Allah ya yafemana gabadaya, Allah ya tsare daughter ya kaiku lfy ya maidoku lfy kinji? Ya tsareku daga sharrin masu sharri" Baby ma tayi caraf tace "Anty Allah ya tsare kuma karki manta da tsarabata" tafada tana kashemata ido daya Harara ta bankamata tana jinjina kai alamun zata gane kurenta ne. Ashraf dake gefe yanata kumburi ya matso kusa yana cewa "To saura saniyar ware, nima a taimaka ayimani addu'an" Dariya sukayi gabadaya sannan Ummy ta rungumoshi shima tana mashi addu'o'i sai wani basarwa yake yana amsawa da amin ala dole fishi yake. Sannan shima yashiga motar driver dake ciki tundazu ya tada motar yajasu suka fice suna dagawa juna hannu. Ajiyar zuciya yayi bayan sunfita ya koma ya jingina da kujera yana mammakin irin son dasu Ummy suke mata dakuma irin girmamawar da takewa Ummy dukda shi be wani dauki nata iyayen da darajaba. Cikin yan mintuna suka isa airport din, lokacin shadaya da Rabi saura. Cikin dan qanqanin lokaci aka gama komai suka shiga jirgin suka zauna mazauninsu dake kusada juna ita daga ciki shi daga baki baki. 12 dot aka fara announcing din kowa ya maqala seat belt dinshi jirgi zai tashi. Komawa itama tayi zata daura amma duk yadda taso daurawa takasa abinka da sabon shiga😆 Tana cikin kiciniyar sawa taga an ziro an amshi belt din Wanda hakan yasa fatarsu ta gogu da tajuna. Saurin sakar mashi tayi tana qamewa kujerar idanunta a ware tana kallon spotless light hannunshi harya gama dauremata ya janye yakoma ya jingina da seat dinshi ya cigaba da danne dannenshi cikin basarwa. Ajiyar zuciya tayi ganin ya janye sannan ta gyara zamanta itama tana basarwa. Jin anfara announcing jirgi zai tashi yasata fiddo wayarta tayi plugging earpieces ta maqalama kunne don batason jin tashin jirgin, she's so nervous ga tsoro fall cikinta saidai batason bada kanta musanmman datasan wannan marar mutuncin na kusada ita. Lumshe idanu tayi tana sauraron waqarda ta kunna, Rabin hankalin kuma nakan tashin da jirgin keyi. Jikinta a qanqame yake amma saika samata ido sosai zaka gane don kallon farko zakaga kamar she's normal. Saida jirgin ya daidaita a sararin samaniya sannan taji normal tasaki jikinta. Lafewa tayi a kujera idanunta a lumshe tana jinta duk a takure musanmman datasan yana gefenta ga qamshin turarenshi daya addabi qofofin hancinta. Koda waiter din jirgin tazo tambayar abinda sukeso bata tambayeta ba don duk tunaninta barci take. Ashraf kadai ta tambaya shima yace beson komai. Tun tanajin abinda ake sama sama harwani barci mai shegen dadi yayi gaba daita. *SPAIN - MADRID* cikin barci taji kamar ana janye mata bargo, hakan yasata qanqame abinta tana yatsine fuska. Jitayi an qara ja ana cewa "hey wake up" Ahankali tafara bude lumsassun idanunta da barci be ishesuba. Dishi Dishi tafara ganinshi har ganinta yadawo daidai "Wake up sleepy head" yafada yana tashi tsaye Saurin miqewa zaune tayi har bargon na faduwa. Saurin duqawa tayi ta daukeshi zata linke sai wani tunani yafadomata arai. Daga ina wannan bargon? Tasan daga ita sai kayan jikinta tayi barci, to shi bargon daga ina yafito. Gani tayi wata waitress tazo taba Ashraf wata Leda tana murmushi. Amsa yayi sannan ya miqawa saudart yana cewa "Saiki basu bargonsu ko?" Amsa tayi batareda tasan ko menene ba sannan ta miqama waitress din bargon tabi bayan Ashraf dayayi gaba. Wani irin sanyi ya suroma saudart data fito daga jirgin, yadda kukasan tana cikin fridge Qanqame jikinta tafara yi tana bin ashraf, saida suka amshi kayan su sannan Ashraf yajuyo yaga yadda take dan qanqame jiki. Guntun tsaki yaja ya ajiye trolley din ta tako gabanta har suna musayar numfashin juna. Saurin dagowa tayi tana kallonshi da alamun tambaya a fuskarta, batayi auneba ya fizge ledar hannunta yana gallamata harara sannan ya bude yaciro abin ciki ya sunkuyo yana doramata qatuwar jacket din pink Wanda takaimata har gwiwa. Dagowa tayi tana kallonshi ganin yana antayamata mugun kallo yasata kauda kai tana yatsina baki sannan ta zura hannun rigar, ganin yana Neman ballemata buttons din yasata saurin riqewa tana cewa "Thanks ina iyawa" Saki yayi yana tsaki "Thank God at least kauyanci da sauqi tunda kin iya balle buttons" ya juya yayi gaba Rakashi tayi da harara sannan tayi sauri ta balle buttons din ta kama trolley din ta bishi kafin ya 6acemata. Haka taita binshi Rabi tafiya Rabi Gudu don karya 6ace mata don airport din bade mutane ba gashi saiwani zabga uban sauri yake. A gaban wata baqar dalleliyar mota taga ya tsaya wani da alama driver ne ya bude mashi yashiga, itama tana Qarasowa drivern yayi saurin zagayowa yabude mata yana gaidata cikin turanci, amsawa tayi tana murmushi sannan tashiga yarufe ya saka kayan a booth sannan ya zagayo dagudu gaban motar yashiga ya bata wuta sannan suka fice daga airport din...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 046 Cikin wani estate drivern yashiga dasu. Estate ne hadadde Wanda ya amsa sunanshi estate. Estate din shiru kamar babu mutane aciki. Gidajene bungalow Jere duk iri daya. Bazaka iya banbancesuba saika duba number dake liqe a kowanne kofar gidan kasancewar gidajen Jere suke according to their numbers. Kowanne gida an qewayeshi da furranni masu kyau da ban sha'awa. "Wow!" Saudart tafada cikin zuciyarta tana qara ware idanu tana kallon gidajen ta windown motar. Sosai wurin ya qawatu gashi babu mutane sosai a unguwar sai yan jefi jefi dake wucewa a qasa ko bisa abin hawa. Kowanne yasha kayan sanyinshi saboda sanyin da'ake surawa. Allah mai iko, Allah daya gari banban. Acan Nigeria ana can ana sheqa musu ruwa sukau nan sanyi ake zuba musu. Haka taita kalle kallenta hartaji tsayawar motarsu. Kallon inda suke tayi taga agaban wani bungalow irin wadanda suka baro suke babu ko banbanci harta fentin Jin an budemata kofar yasata barin kallo ta dauki handbag dinta tafito tana kallon harabar wurin. A wayence take qarewa wajen kallo. Gidane bungalow dan qarami kamar dai wadanda suka wuto. Kewaye yake da furrani that are well trimmed, butterflies (mallam bude takarda) sai kara kaina akai suke gwanin sha'awa. Ga koina tsit bakajin komai sai kukan tsintsaye masu dadin sauraro "Wow" tasake fada cikin zuciyarta tana jin wani shauqi na dibanta, the place is soo perfect. "Idan kin gama qauyancin saiki shigo" taji an fada a bayanta. Saurin juyowa tayi taga harya shige ciki. Harara tabishi dashi sannan itama tafara takowa janye da trolley tana humming din waqar wonderland na film din yar tsana barbie ahankali tanajin nishadi har cikin zuciyarta. Saida tashiga ciki sannan taga Ashe gidan daga waje yake dan qarami don cikin ba laifi akwai girma sosai. Wani makeken falo zaka fara cin karo dashi dake kewaye da wasu qayattatun guntayen kujeru sai kofofi uku dake jikin falon a different direction Wanda hakan ke nuna dakuna ne awajen sai daga haggu wani ke6anttacen wuri da akasa dining table aka zagayeshi da chairs, daga dama kuma idan kadan bi kusurwar wajen zai sada ka da kitchen. "Your room" ta tsinkayi muryarshi yana cewa haka. Kallonshi tayi taga yana gwada mata daya daga cikin dakunan Wanda dakin shi kadai ne babu wani kusa dashi sa6anin kingin biyun dake kusada juna. "Mine" ya nuna daya daga cikin biyun dake Jere. "Study room" yafada yana nuna dayan sannan batareda ya qara cewa komai ba ya juya yashiga dakin dayace nashi ne yabar ta nan tsaye tana binshi da kallo. Tsaki taja tana kwaikwayonshi "Your room... Mine... Study room, mtcheew botorami kawai" Tafigi trolley dinta tashiga dakinta. Dakin dan madaidaici ne bawani girma ke gareshi ba. Akwai dan qaramin gado a dakin shima dan dunqullale kamar kujerun falon, sai wardrobe mai dan girma sai mirror da babu komai Asama sai wani study table and chair daga gefe. Ajiye trolley din tayi ta cire jacket din saman rigarta tashiga qalqale dakin dukda ba irin dattinan yayiba, yadaiyi qura sama sama Canza bedsheet tayi ta goge wardrobe din ta fiddo yan kayanta ta jera sannan ta goge saman mirror ta jera jera mayyukan shafawanta da kayan kwalliyarta akai dukda bawasu yawa ke garesu ba sannan tabi koina ta share ta goge sannan tashiga toilet ta wanke shi Tass. Fitowa tayi falon taga babu kowa babu 6ata lokaci ta shiga gyara falon shima dayake beda wani tarkace nan da nan tagama gyaranshi takoma kitchen nanma ta gyara ta gogeshi tsab. Abinda zai burgeka gameda ita shine batada qyashin aiki gata da kazar kazar tana aikine da dukkan kuzarinta. Fitowa tayi riqeda bokiti da mopper aciki hannun rigarta a tattare zuwa gwiwa Wanda yaba siraren fararen hannunta bayyana. Dagowar dazatayi sai idanunta ya sauka akan nashi. Tsaye yake bakin dakinshi ya sauya shiga zuwa qananun kaya baqaqe sai qatuwar jacket fara daya Dora akai. Janye idanu sukayi gabadaya daga kan juna cikin basarwa. Wucewa yayi hanyar waje yana cewa "karki fita" ya fice Bin bayanshi tayi da harara harya fita sannan taja tsaki tana cewa "to ubana" Maida kayan datayi amfani dasu tayi ma'ajinsu sannan itama ta shige dakinta don yin wanka. Cikin yan mintuna tafito ta sauya kayanta zuwa wata gown din baqa sannan ta shimfida sallayar ta gabatar da sallar la'asar da aketa kira. Tana nan zaune kan sallayar taji ana bubbugo kofarta. Jimm tayi tana sauraron bubbugar kofar tana tunanin wake bubbugamata kofa. Qara bubbugawa akayi wannan karon da dan qarfi hakan yasata miqewa ta nufi kofar ta bude ahankali. Shi tagani tsaye bakin kofar ya juyawa kofar baya. Yanajin an bude yaja tsaki sannan ya miqamata ledar hannunshi batareda ya juyoba. Amsa tayi babu musu sannan batareda ta jira komai ba ta rufe kofarta cikin bugowa da qarfi. Juyowa yayi yana kallon ruffafen kofar a mammakince sannan yayi qwafa yana jinjina Kai sannan shima yawuce ya zauna falon ya bude takeaway dayayi yafaraci. Itakau tana shigewa dakin ta tsaya tana antayama kofar harara sannan tawuce ta zauna bakin gadon tana bude ledar tana yatsine fuska. Takeaway tagani na fried rice da fried plantain akai sai robar fresh milk mai sanyi. Ta6e baki tayi sannan tabude tafaraci don dama yunwar takeji rabonta da abinci tin a gidan Ummy. Koda tagama kwanciyarta tayi kan gadon tanata buga game don debe kewa. Sosai takeson yin kyau waya da yan gida amma bata chanza layi ba so it's impossible. Tananan kwance har aka fara kiran sallar magrib. Tashi tayi ta dauro alwala tayi ta zauna tana tilawa har aka kira isha'i sannan ta tashi ta kawota itama. Tana cikin linke sallayar sallar taji ana bubbugo kofar dakin. Waigawa tayi tana kallon kofar batareda tabar abinda takeba. Jin anqara bugowa yasata cewa "waye?" "Open the damn door!" Taji anfada cikin tsawa ta waje Guntun tsaki taja ta cigaba da linke sallayar sannan ta maidata ma'ajinta sannan tanufo kofar tana kumburi. Ganinshi tayi a tsaye ya tattara komai na fuskarnan ya hade waje daya. "Menene?" Ta tambaya cikin halin ko-in-kula da yanayinshi "First and last warning, karki sake barina tsaye ina knocking a kofar nan ok, gidanane ba nakiba ok?!" "Mtcheew amma ai dakin dakinane ko" tafada a zuciya a zahiri kuma tace "Ok, menene?" Tafada hannunta riqeda kofa alamun jira take yafadi meya kawoshi takoma ciki "And secondly, karki manta am still your boss, speak to me in respect, ok?" Yafada Yana hararar ta Ajiyar zuciya ta sauke tana harde hannunta a qirji don taga abin nayi ne "Ok" tafada tana kallonshi "Now jeki shirya kifito and kar qauyanci yasaki barin jacket din kizo kina bina kina kakkarwa kamar mai falfadiya" ya juya yawuce Binshi da kallo tayi sannan taja tsaki tana cewa "psycho kawai" Sannan takoma ciki. Bata dauki lokaci ba wajen shirya wa ba tafito sanye da light pink jallabiya ta yafa gyalen in a simple way ta Dora jacket din akai don ko Karen hauka ya cijeta tasan bazata iya fita hakanan ba. Awaje ta iskeshi zai shiga mota. Qarasowa tayi itama ta kama kofar baya zata bude. "Mallama who is your driver?" Ya tambaya tana binta da wani kallo Sakin kofar tayi tadawo gaba ta bude tanajan tsaki cikin zuciyarta 'kai wlh Dad ya hadata da qalli qallala wlh" tasake Jan wani tsakin Shima shiga yayi sannan yaba motar wuta suka fara tafiya. Tafiya suke cikin normal speed babu mai tankama wani kowa da inda yake kallo. Koina fayau yake da haske kamar ba dare ba kuma ga mammakinta sai gani tayi akwai mutane da dan yawa yanzu awaje sa6anin dazun da rana. Wasu zaune kan grass carpet suna fira wasu suna tafiya mostly mace da namiji hannayensu cikin juna. Haka taita kallon garin tana yabawa kyawunshi a zuciyarta har suka qaraso inda zasu. Shi yafara fita sannan itama ta bude kofar ta fito. Gani tayi supermarket ne yakawota. Ganin yayi gaba yasata binshi itama. Basket ya dauka yawuce yafara shopping dinshi yabarta nan tsaye. Da farko Qin motsawa tayi daga inda take, can kuma sai tayi wani tunanin, tabbass tana buqatar kaya most especially kayan sanyi don taga alamar sanyin garin bana irin nasu bane. Itama basket din ta dauka tafara zagaya wajen tana daukar abinda takeso kama daga kayan sanyi, turarruka, air freshener na daki Dana toilet, mayyukan wanka da dai sauransu. Saida tayi shopping son ranta sannan ta qaraso wajen biyan kudin. Matar wajen ta zazzage kayan tana listing dinsu daya bayan daya harta gama sannan ta maidasu a wata shopping bag tabata. Amsa saudart tayi sannan ta fiddo purse dinta da duk kayan amfaninta ke ciki ta fiddo ATM dinta taba Matar. "No ma'am, the fee is paid" tafada tana murmushi "By who?" Inji saudart kamar batasan wazai biya din ba "By a guy" ta amsa "Well bansanshi ba, bansan ya biyaba, abinda nasani shine nayi shopping and am paying myself" tafada cikin turanci...✍ Battery low!!! Anmani hankali ranan, idan nacigaba wayata na iya mutuwa inyi biyu babu, please kuyi manage zan fanshemaku gobe insha Allah da page biyu. Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Jinjina gareku fans din AUREN KWANGILA gaskiya naji dadi sosai da nuna qaunar dakukema book dinnan. *Ummu sadik* ta AUREN KWANGILA NOVEL GROUP ina yinki sosai, ngd da addu'o'inki agareni dama sauran yan group din gabadaya, Allah yabar qauna💖 Jiya nayimuku rushing😆 wlh banda chaji sosai ne shiyasa nace koyayane bari nadanyi yafi babu, amun afuwa🙏 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 047 "Erm.. Am sorry ma'am amma anbiya" Matar tafada. (Note duk da turanci suke magana ni zan dan sirka da Hausa saboda sauqin fahimta) "Then zan maida kayan" tafada tana qoqarin juyawa. A halin yanzu babu abinda ta tsana kamar ayimata alfarma, alfarmar ma ta rasa Wanda zaimata sai A.A? No, bata ciba yamata gori inaga taci? "Please ma'am, wait a minute" inji Matar tana yan latse latse a landline din gabanta sannan ta dauka ta kara a kunne. Magana tafara cikin yaren Spanish, itadai saudart shiru tayi tana sauraronta dukda batasan me take cewaba. Can saita ajiye wayar murmushi a fuskarta tace "ok ma'am, kawo ATM din" Babu musu ta miqamata tacire kudin sannan ta maido mata. A bangaren Ashraf kuwa duk abinda yafaru yana sane don suna tareda managern supermarket din daya kasance tsohon abokinshi ne tun primary. Agabanshi Matar takira manajan tana cemashi Matar tayi insisting kan ita zata biya kudin Jin haka yasa manajan gayama Ashraf din, nunawa yayi babu matsala amma deep down kamar yayi bindiga yaji don a gurinshi ba qaramin zubda mashi mutunci tayi most especially da manajan ke tsokanarshi wai ya canza dubara wannan batayi aiki ba don duk tunaninshi irin yaganta dinnan ne ya qyasa yana son shigar da kanshi. Shidai banza yayi dashi sukayi sallama sannan yanufi motarshi daidai itama ta qaraso. Beko kalleta ba ya bude mazaunin driver yashiga, cikin zuciyarshi yana ayyana abinda zaimata ya huce. Oho batasan yanayiba, itama budewa tayi ta zauna sannan yaja kamar zasu tashi sama sukabar wajen. Yadda sukazo haka suka koma babu mai cewa komai. So take ta tambayeshi inda ake siyarda layi amma tana gudun dizgi don taga fuskarshi babu alamun yakosan Kalmar dariya, hakan yasa tashafawa kanta lfy tayi shiru har suka iso gida. Yana parking ta bude kofar kamar dama jira take tafita hannunta riqeda ledojinta, zata wuce ya dakatar daita dacewa "Gobe 10:00am.. Be ready" yafada ataqaice. Batace komaiba tajuya tashige tana ta6e baki. Saida ajiye duk abubuwan data siyo inda ya kamata sannan ta jona ruwan shayi a heater data siyo ta shige toilet don yin wanka. Kayan barci tasa bayan ta fito ta hada kakkauran shayi da kayan tea din data siyo tasha sannan ta shige cikin bargo sai 😴 Washegari tunda wuri ta shirya don sosai take bama lokaci muhinmmanci, idan aka bata appointment bata wucewa saida dalili, batada African time ko kadan Tun tana jira adaki tana kasa kunnen jin fitowarshi harta fito falo ta zauna ta cigaba da jiranshi. Sanye take cikin wata baqar Dubai gown Wanda yad'an kamata daga sama ya bude daga qasa. Tayi rolling da gyalen rigar ta Dora qatuwar rigar sanyi baqa akai mai flowers farare jefi jefi. Kafarta sanye da baqin booth na mata Wanda yakai mata har gwiwa, fuskarta daukeda simple makeup, Jan la66anta sai walqiyar lip gloss suke, tayi kyau sosai cikin shigar abinka da farar fata. Fiddo hannunta na dama dake cikin aljihun rigar sanyin tayi ta kalli baqar agogon dake daure da tsintsiyar hannunta taga har sha daya da minti goma. Sake kallon kofar dakinshi tayi a karo na ba adadi tanajin kamar taje ta bubbuga kofar. Tsaki taja cikin jin haushi, ita ba komai yasa ta qagara yafito sutafi ba saidan sotake sufita ta siya sim card tasa kozataji muryar yan gida taji sanyi. Maida kanta tayi kan jikin kujerar, hannunta zube cikin aljihun rigar sanyin, zuciyarta ba suya. Wannan wane irin wulaqanci ne? Yace 10:00am gashi har to 12 amma ko niyyar fitowa be dashi. Shikau a bangarenshi yana sane daita kawai wulaqanci ne, acewarshi itama taji yadda yaji jiya a supermarket. Tundazu yana jin motsinta a falo yayi biris ya qyaleta. Sai 11:20 ya tashi yashiga wanka bayan yan mintuna yafito sannan yafara shiryawa don qarfe 2;00pm sukeda meeting din daya kawosu. Cikin farin suit mai Jan shirt daga ciki ya shirya, yasa necktie ja irin dan guntun nan, ya taje sumar kanshi daketa walqiya saboda gyara sannan ya feshe Jikinshi da turare sannan ya dauki briefcase dinshi ya fito. Afalo ya isketa lafe jikin kujera idanunta a lumshe Amma yasan ba barci take ba, kallo daya yayimata ya dauke kai cikin basarwa yana gyara necktie dinshi. Taji fitowarshi amma taqi bude idanu don iya shaqa ta shaqa. "Coffee" yafada in his usual husky voice Saurin bude idanu tayi tana kallonshi cikin mammaki, she was like, what the hell? Shikau babu abinda yadameshi ya duqufa sai gyara takalminshi yake. Ganin bata tashi ba yasashi dagowa yana kallonta, sai yaga itama shi take kallo fuskarnan har wani ja ja take don 6acin rai, abinda ta Dade yanaso kenan, ya 6atamata rai. "Hello??" Yafada yana waving hannu a fuskarta "Nace coffee and fried spiced egg" yafada cikin son qara qular daita "What? Ni kuku ce?" Tafada cikin tsananin fishi don yau kwata kwata takasa controlling din fushin ta "Then mecece? Am your boss kuma komai bazaki sai kinyi it's part of your job, after all biyanki zanyi ba kyauta bane" yafada Yanajin wani nishadi a zuciyarshi ganin sai qara hawa take "Yes aiki nake maka but am not a cook, am a secretary for crying out loud" tafada tana yarfa hannuwa cikin fishi. "Wannan ke ya shafa, nidai kawomin abinda nasaki, now!" Ya qarasa maganar cikin dan daga murya Shiru tayi ranta a mugun 6ace, tunda take bata ta6a shiga 6acin rai data kasa controlling irin yau ba. Ya shanyata na kusan 2hours sannan kuma yace ta hadamashi coffee harda wata shegiyar fried spiced egg? Dakyar ta iya controlling din kanta sannan ta tashi fuu tashiga kitchen. Binta yayi ta kallo harta shige sannan ya juyo yana murmushin jindadi Cikin yan mintuna saigashi ta dawo riqeda mug din coffee ta diremashi a gabanshi tanufi hanyar dakinta a fusace "Karki qara step guda anan" yafada yana dakatar daita. "Kijirani ingama mutafi" yafada yana daukar mug din batareda yayi complaining din Rashin ganin kwan ba. Nanma saida ya 6atamusu lokaci sannan ya gama sha ya miqe yayi gaba yana cewa "shall we" Binshi tayi da mugun kallo sannan itama ta biyo bayanshi zuciyarta kamar zatayi bindiga. Saida yashiga mota ya zauna sannan tafito. Tunda tafito yake kallonta tacikin motar. Ta taho sanye da fuskar angry bird yan kumatunta sun dan turo alamun she's still angry. Tunda yake beta6a ganin Wanda fushi yaima kyau ba kamarta, kamar fuskar taita zama ahakan. Ganin ta qaraso yasashi saurin kauda kai yana basarwa. Bude kofar tayi ta shigo ta zauna still fuskarta a tamke jitake kamar taita ihu don haushi. Kunna motar yayi yaja suka fita daga harabar gidan. Tsit motar tayi kowa da abinda yasha mishi kai, saudart sai cika take tana batsewa, jitake kamar tayi kuka, sosai take missing yan Niger she badly want to call them. "The meeting will hold at 2:00pm" taji yafada Yaitayi kamar bata jishiba don ko kallon gefenshi batayiba. Hakan yasashi juyowa yace "Are you deaf?" Ya tambaya cikin husky voice Juyowa tayi ta watsa mashi Lulu eyes dinta sannan ta dauke kai tana cewa "ok" Shiru yayi shima ya kauda Kai yana lumshe ido yana budewa ahankali don shikadai yasan abinda yaji data watsamashi idanun nan. Cigaba da tuqin yayi yana sauraron bugun zuciyarshi data sauya a take. Itakau cigaba da kallon waje tayi tana kumburi gashi tana son cemashi ya biya dasu wajen saida layi amma takasa. Kamar wasa sai gani tayi yayi parking gaban wani babban shagon siyarda wayoyi. Hakan yasata saurin gyara zamanta daga kishingiden datake tana kallon wajen murmushi na su6ucemata batareda tasaniba. Jin kamar ana kallonta yasata juyowa suka hada idanu, yawani basar ta hanyar gallamata harara yana ta6e baki. Kauda Kai tayi tana cewa "oho dai" cikin zuciyarta amma qasan zuciyarta fall farinciki at last zata samu kiransu daddy Saida tabari yafita sannan itama tafito lokacin harya shigewarshi, hakan yasa itama ta shiga zuciyarta fall murna Direct wajen wani saurayi taje cikin masu saida wayoyin shagon "Hi" tafada "Hello ma'am you're welcome, wane taimako zan iya yimiki?" Yafada cikin murmushi "Layi nakeso" duk a harshen turanci suke maganar Nan ya fiddomata ta sayi guda biyu tasaka nan take "Zai fara aiki bayan awa daya" yafada mata yana bata receipt "Ok thanks" tafada tana amsa fuskarta fall murna Waje tafita fuskarta a sake sa6anin dazu ta taddashi jingine da motar ya rungume hannu a qirji. Qarasowa tayi ahankali zata zagaya ya dakatar daita da "take" yana cillomata makullan motar. Cafewa tayi tana kallonshi da alamun tambaya "Drive us ai ba nikadai na iya driving ba" yafada yana zagayawa inda take zama Mere baki tayi sannan tadawo ta bude mazaunin driver tashiga ta kunna motar sannan tajasu cikin driving dinta mai burgewa. Tafiya suka fara yana gwada mata hanya har suka iso wani shahararre kuma qawattacen hotel. "Ok shiga" yafada yana danne dannenshi. Dan jimm tayi kamar zatayi magana saikuma tafasa ta shiga ta samu wuri a parking lot tayi parking. Fitowa sukayi kusan tare suna kallon environment din. Jin ana kabbara yasashi basu umarnin sufara sallah sannan. Masjid din hotel din suka shiga shi bangaren maza ita na mata don yin sallar. Koda aka gama sallar tayi addu'o'inta saita fito. Hangoshi tayi da wasu mutane uku duk cikin shigar suit, biyu farare daya baqi suna magana da alama sune zasuyi meeting din dasu. Qarasowa tayi wajen cikin Sakin fuska tana gaishesu suna amsawa Suma cikin fara'a "Meet my secretary, Miss saudart shamsu" inji Ashraf yana nunata "Nice meeting you miss" suka hada baki wajen fadin haka. "My pleasure sir(s)" tafada cikin girmamawa "Shall we?" Inji baqin cikin mutanen yana nuna hanyar ciki. "Sure" duk sukace gabadaya suka dunguma suka shiga ciki suna tafiya suna fira jefi jefi...✍ Insha Allah idan nasamu lokaci zakuga next page ko zuwa dare ne amma idan kukaji shiru kuyimin uzuri🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 048 Restaurant din hotel din sukayi reserving don gudanar da meeting din. Zauna suka kan kujerun dake zagayeda wani round table, kowanne da robar swan a gabanshi da glass cup duk sunyi shiru suna sauraron bayyañin da daga daga cikin mutanen mai suna *Hussain* keyi. Meeting ne akan wani contract na ordern gwalagwalai dazasuyi, kasancewar companyn A.A companine na dealer gwalagwalai da zinarai, yana daya daga cikin companyn dayayi fice a Nigeria dama Africa gabadaya, yana ordering din gwalagwalai a qasashe daban daban. To anan ma hakan take, zuwa yayi don yin ordern wasu latest design na gwalagwalan masu tsadan gaske don sabbin design ne don ba'a gama saninsu a duniya ba. Wani qaramin akwatin glass ne a tsakiyar table din Wanda ke dauke da sample din gold din. Saida Hussain yagama 6a66atunshi sannan ya buqaci su duba suga ingancinshi. Budewa baqin cikinsu yayi ya fiddo ya miqama saudart dake gefen Ashraf, ta amsa sannan ta miqama Ashraf. Sundan Dade suna dubawa (Ashraf & saudart) suna jujjuyawa suna dan qus qus tsakaninsu da alamun shawara suke yankewa. Sudai mutanen kallonsu suke har suka gama sannan Ashraf ya maidama saudart Itakuma ta miqama Wanda yabata. Cikin inganttaciyar turancinta tace "Yayi kyau sosai, amma kunzo mana da kala kalan designs dinsu ne, munason mu za6a" tafada tana kallonsu, Ashraf dake gefenta na kada kai alamun abinda tafada gaskiya ne Baqin Wanda yakira kanshi da *zahid* yace " sosaima, gashi Ku za6a" yafada yana bude musu laptop ya shiga hotunansu sannan ya turomusu Gabansu. Nan suka shiga dubawa suna za6an choice dinsu suna qus qus, idan ka gansu a lokacin baka ta6a tunanin tom & jerry dinnan ne don dukansu sunci serious sosai. Saida suka za6i iya Wanda sukeso sannan aka maida musu laptop din. Nan sukayi cinikin iya adadin dazasu saya Wanda za'a turomusu ta jirgin ruwa bisa yarjejeniyar zasu fara bada Rabin kudin anan, Rabin kuma sai kaya sun isa. Anan aka yanke shawarar zasu sake haduwa a companyn su Hussain din ranar Monday don biyan Rabin kudin kamar yadda suka tsara sannan suyi abun a rubuce kowa yasa hannu saboda yazama shaida. Awa daya meeting din ya dauke su sannan su saudart suka miqe don tafiya kowanne fuskarshi fall fara'a. Har mota suka rakasu, dayake makullan motar na hannun saudart sai kawai tashiga mazaunin driver ta zauna tana jiran Ashraf dahar yanzu suke magana da mutanen. Can sukayi musabaha sannan shima yashiga motar suka bar hotel din. Tunda suka hau hanya babu Wanda yacewa kowa uffan gar suka qarasa gida. Lokacin da suka iso har anfara kiraye kirayen sallar la'asar don haka bema shiga gidanba yawuce masjid din estate din Itakuma ta shigewarta ciki don gabatarda tata. Bayan tagama sallar ne taciro wayarta tafara kiran yan Niger. Da daddy tafara, sosai suka sha fira dashi Wanda Rabi shagwa6a ce take zuba mashi yana biyemata sannan takira mamy nan Suma suka gaisa da kowa na gidan kowanne nabata sabtun tsarabar dazatayi mashi sai dariya take musu. Sai bayan sunyi sallama sannan ta bugama Ummy. Sosai Ummy taji dadin kiran nata, sunsha fira sosai kafin takaima baby wayar As usual ihun nan nata na hauka taitayi da sunan murna, nan sukasha fira kamar ba gobe sai tsokanarta baby take wai ya? An samu tsarabar nata koko da saura? Itakuma tana amsa mata da zata gane kuranta ne saita gayamashi. Haka sukaita firarsu, dakyar suka ajiye wayar kowanne najin qaunar dan uwanshi har cikin zuciyarshi. *********************************** Tana cikin shirin kwanciya kasancewar har Tara tayi taji ana bubbuga kofarta. Dan jimm tayi daga gyaran zanen gadon datake ta kalli kofar. Jin ansake bugowa yasata Sakin bedsheet din ta zura hijabin sallarta akan doguwar rigar barcinta sannan tanufi kofar. Tana budewa taga shine, gyara tsayuwarta tayi tana kallonshi da alamar tambaya. "Coffee.. Kikawomin a study room" yafada yana wucewa. Galala tabishi da kallo harya shige. Mene? Coffee cikin Daren nan? Wannan wane irin wahalarwa ne? Mutum na shirin barci awani tsiromashi aikin hada coffee? Sosai ranta ya 6aci don barci ke idanunta burinta kawai ta kwanta. Babu yadda ta iya haka tawuce kitchen din ranta a jagule, tsaki kau tafishi yafi cikin kwando kafin tagama hadawa. A study room din tasameshi zaune gaban laptop sai danne danne yakeyi. Ciki ciki tayi sallama sannan ta qaraso gabanshi kamar bataso sannan ta dungure mashi mug din coffeen a kan table din gabanshi tajuya da niyyar komawa. "Come back here" yafada batareda ya dago daga kan laptop din ba. Saida tayi jimm kaman bazata juyoba sannan tajuyo tadawo gabanshi ta tsaya. Dagowa yayi yana kallon yadda taketa faman kumburi tawani tsaya mashi akai. "Da ina zaki?" Ya tambayeta "Ina bayan dakina?" Tafada cikin son danne fushinta "Na sallameki ne?" Ya fada cikin son qular daita "Ba na hada cofeen ba? Ni Am sleepy wlh" tafada tana turo baki. "Barci? Dama barci ya kawoki nan?" "Bashi ya kawoni ba, amma ai yanzu na hadamaka coffee din ko? Zan iya tafiya ko?" Tafada cikin tsiwa tsiwa Daukar mug din cofeen yayi ya kafa Kai ya shanye sannan ya diremata "Make another one" Wani Abu taji ta taso ya toshe mata maqoshi, Kutt... "Bakijiba? Nace ki hado wani" tafada yana kallon yadda fuskarta ke yin ja ja ja ja alamun tana cikin tsananin 6acin rai. Batace komai ba ta figi mug din ta fice tana bugomashi kofa har yana toshe kunne. Binta yayi da kallo sannan ya jinjina Kai yana murmushi "Shima wannan you'll pay for it" yafada yana maida hankalinshi kan laptop din. Can saigata ta dawo ta qara dungure mashi mug din har coffee din badan zubewa. Dagowa yayi yana kallonta da mammaki "Wai kwakwalki qalau kuwa?" 'Kai ka cancanci tambayar' tafada a zuciyarta Banza tayi dashi ta juyamashi qeya. Qwafa yayi ya cigaba da danne dannenshi sannan ya dauki mug din yakai baki da niyyar kur6a. Kur6a daya yayi yayi saurin furzoshi ko maqoshi be kaiba saboda wani zau dayaji a harshenshi. Kauda Kai tayi saurin yi tana son hadiye dariyarta "Kutt... Uban me kika samun a coffee? Kasheni zakiyi?" Ya tambaya yana kallonta cikin mammaki "Ni me nasa?" Ta tambaya tana dan matsawa baya. "Me kika sa ko? To wlh saikin shanyeshi yafada yana daukar mug din ya nufota. Ai a sittin tayi wani turning tana fasa qara ta bude kofar tayi waje tana tsuwa. Binta shima yayi dagudu saidai kafin ya taddota harta shige daki ta Danna sakata sama da qasa tana numfashi sama sama. Bubbuga kofar yashiga yi da karfi yana cewa tazo ta bude amma tayi banza dashi saima antayama kofar harara datake " to wlh ki tabbatar nan zaki cigaba da zama har abada don ido na idonki..." Sai yayi Kwafa yana jinjina kai sannan yayi tafiyarshi "Idan na fito karka barni da rai, mugu kawai mummuna" tafada tana murguda baki sannan ta haye gado tashige cikin bargo...✍ Kuyi manage🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) Sorry for the late post🙏 Yanzu bazaku dinga ganin post ba akai akai, munada hidima, please bear with me🙏 Washegari Friday, bata yarda tafito daga dakinta ba saida ta tabbatar yabar gidan gabadaya. Sai a sannan tasamu kwanciyar hankalin fitowa don yin aikace aikacen datasaba. Saida ta share koina, ta goge, tabi da freshener sannan tashiga kitchen don samarma kanta abin ci. Tana cikin suyar kwai taji ana bubbuga kofa. Gabanta ne yafadi jin bubbugar kofar abinka da marar gaskiya don duk a tunaninta Ashraf ne. Kwan ta kashe batareda ya ida soyuwaba ta saka a plate ta jidi kayan breakfast din tayi daki dasu sannan ta dawo cikin sanda ta qaraso kofar tana leqen wajen ta wurin nan na kofa don ganin waye. Ganin wasu yanmata biyu tsaye yasata Sakin ajiyar zuciya sannan tabude. Yanmata biyu tagani tsaye fararen fata kowacce tasha kayan sanyinta sai washe mata baki suke. Itama washe masu nata bakin tayi Tanadan matsawa don basu wuri sy shiga tana cewa "Please come in" Babu musu suka shigo suna bin falon da kallo suna murmushi. Maida kofar tayi ta rufe sannan ta qaraso ciki tana musu tayin zama cikin fara'a Babu musu duk suka zauna "Bari nakawo muku ruwa" tafada cikin turanci Dakatar daita daya tayi dacewa "A'a yar uwa, murda ga gidanmu nan kusada ku, bawani tafiya mai tsawo mukayi ba kuma ma sanyi ake ba'a cika shan ruwa ba" Murmushi saudart tayi sannan ta koma ta zauna tana cewa "Kenan Ku maqobtanmu ne?" "Eh mana, fa gidanmu nan No 35 Itakuma wannan No 37" inji Wanda tayi magana dazu "Wow, nice to meet you" tafada cikin Sakin fuska. "Thank you, sunana Loveth wannan kuma Reyna" inji mai maganar "Wow nice name, ni sunana saudart" tafada tana murmushi "Wow nice name too, amma Ku baqi ne ko?" Inji Wanda aka kira da Reyna "Eh kwananmu biyu yau" saudart tabasu amsa "Ayyah ai naganku jiya dazaku fita, banma San akwai mutane saida naganku jiya" inji Loveth "Ai saboda bamu Dade bane shiyasa" saudart ta amsa "Ok, dama zuwa mukayi muji zaki samu zuwa wajen hada kayan Good Friday?" "Good Friday?* inji saudart cikin Rashin fahimta "Eh, good Friday wani taro ne haka mukeyi duk ranar Friday, duka yan yankinan zasu hadu don zumunci, anan muke sanin baqin dasuka shigo kuma mu qulla zumunci" inji Loveth Reyna ta Dora dacewa "Akwai wata mata a block 39, doctor ce kuma duk ta fimu shekaru, a gidan ta duk muke taruwa mu hada kayan da za'a dan ta6a a gathering din, muna zuwane da marece mukama aikin ayi agama da wuri, idan zaki samu damar zuwa saiki leqo ayi dake" "Wow yayi kyau sosai, insha Allah zan leqo idan nasamu dama" inji saudart tana murmushi "To Allah yasa" suka fada suna tashi zasu tafi. Har waje ta rakasu suka nuna mata gidan doctor din daga nesa sannan sukayi sallama suka tafi. *5:00pm* Fitowa tayi cikin shigarta ta doguwar rigar atamfa mai A shape ta Dora Jan rigar sanyi mai hula akai kasancewar cikin atamfar akwai kalar ka, wannan karon ta Dora hular rigar sanyin. Hannunta daya riqeda wayarta dayan kuma riqeda makullan gidan. Direct gidan dasuka gwadamata ta nufa tana tafe tana qarewa surrounding din dayayi tsit kallo. Tun kafin ta isa gidan tafara jin hayaniya da shewa shewa na fitowa daga gidan ga qamshin girki daya fara ziyartar hancinta. Ida Qarasowa tayi tana kallon kofar gidan da akasa *39* agaban gidan Ahankali tafara bugawa amma kasancewar cikin akwai hayaniya sosai babu Wanda yajita. Ganin haka yasata fara bubbugawa da qarfi. Ta dan Dade tana bubbugawa sannan tajiyo taku alamun ana tahowa hakan yasata gyara tsayuwarta tana kallon kofar. Ana budewa tayi ido hudu da Reyna dake sanye da apron. "Yeah! Gatanan tazo" tafada tana leqa bayanta da alamu da mutanen ciki take Kan kace me? Sai gasu sunata leqowa don ganinta Murmushi tayi cikin jin kunyar yadda suka zubamata idanu "Hyy" tafada tana dagamadu hannu "Hello... Hyy...hey" duk suka amsa gabadaya suna mata murmushi Loveth ce ta leqo sanye da apron hannunta duk fulawa da alamun kwabi take. "Welcome saudart, Ku matsa tashigo mana, kunwani tare hanya" tafada tana kama hannun saudart suna shiga ciki, taja hannunta har kitchen din gidan Wanda duk tsarin gidan irin nasu saudart ne kawai banbancin kayan ciki ne Wata mata Wanda aqalla zatakai shekaru 40 suka gani da wasu yanmata suna aiki suna fira. "Dr zahra, ga baquwar nan tazo" Nan duk suka dago suna kallonta "Wow she's so cute, welcome baquwar mu" tafada tana Qarasowa wajen ta tana murmushi Itama murmushin ta maidamata tana gaidata sannan suka gaisa da duk yanmatan gidan sannan aka koma bakin aiki. "Amma daga Africa kike ko?" Inji Dr zahra "Eh daga Nigeria" "Wow, ni daga Pakistan nake amma na ta6a zuwa Nigeria, a wane state kike?" "A kano state" inji saudart tana amsar wuqar dake hannun Dr din da cabbage datake yankawa. "Ohh nikuma Abuja naje, ai Nigeria is a lovely country, har yanzu nakasa mantawa daita" inji Dr zahra din Haka sukaita fira a tsakaninsu, dayake saudart batada baqunta nan da nan ta ware duma fira kamar sun Dade da sanin juna sai tsokanar juna suke. Babu abinda ke tashi a gidan sai hayaniya da darairaku. Sosai saudart taji dadin zuwa gidan don tasamu nishadi sosai, da yanzu tana can qunqume cikin gida babu abokin fira. Abinka da aikin yawa nan da nan suka kammala komai. Tare dasu Loveth suka fito daga gidan suka Kamo hanyar gida suna tafe suna fira har suka iso gidansu saudart. Lokacin har anfara kiraye kirayen magrib. Sallama sukayi da juna akan saisun hadu anjima. ************************************* Tsaye take gaban gadonta sai kallon kayyayakin data baza kan gado take tarasa Wanda zata za6a don ruwan ido. Can dai ta dauki wata dark purple din Arabian gown din roba mai dogon hannu tareda farar jacket marar hannu mai gashi ajiki Wanda takawo har gwiwa sannan ta yane kanta da farin gyale. Kamar kullum yauma simple makeup tayi, sai kuma purple janbakin datasa abaki ta feshe jikinta da turare mai sanyin qamshi sannan ta dauki wayarta ta fito. Direct gidan Dr zahra tanufa. Nan ta tarda su Loveth da sauransu ansha gayu sai hada hadan fita da abinci suke. Suna ganinta suka ja suka tsaya baki bude suna kallonta. Qarasawa tayi tana rufemasu baki tana cewa "Kurufe kar quda yashiga" tafada tana hararsu Sai a sannan sukadan sun bude baki "Wow saudart, you look soo takeaway!" Inji Reyna "Ni banma ganetaba dafarko na rantse" inji Loveth Wata yar Korea mai suna chuchu tace "Anya are you sure you're a Nigerian? Ni idan aka fadi Nigeria the first thing dake zuwa min arai shine baqaqe, munana, gajeru..." Hararar da saudart ke antayamata ya hanata qarasawa tafara dariya "Nikuma idan akace Korea Abu na farko dake zuwa min arai shine mitsi mitsin idanu, qurmemen goshi, tsawo kamar pole sai nannanan hanci" saudart itama ta rama. Nan duk aka kwashe da dariya, nan fa aka Dora kan inda aka tsaya dazu, suna kai abinci suna cafta har suka gama, nan suka fito suka zauna. Wajen filine kamar filin kwallo qasan shimfide da Grass carpet, koina fayau kamar ba dareba. Mata na daga bangaren haggu sun hada group dinsu hakama maza a bangaren dama sai cafta suke Wanda be wuce ta kwallo ko wrestling. Sai gashi estate din dake tsit kodayaushe yau tacika da hayaniya yadda kukasan sallah ake ko wani gaggarumin Abu. Saudart na can tsakiyar yanmatan tana maida yadda akayi, yadda kukasan ta Dade da saninsu, kusan itace centre of concentration don duk Wanda yabude baki saudart yake kira. Cafta suke kan qasashe kowa na kare nashi yana kushwle na dan uwanshi, kusan duk tararmata sukayi don duk tafisu baki kuma tasan amsarda zataba mutum daidai da maganar shi kuma da wuya ta bada amsa bata Baku dariya ba, hakan yasa duk suka tararmata suna sukan Nigeria Itakuma tana karemu. Acan bangaren maza kau zaune suke kashi kashi, wasu na games irinsu ludo ko whot wasu na caftar kwallo ko wrestling. Ashraf na cikin masu buga whot, game suke mai zafi Wanda ko daga kai beson yi. A cikin mazan akwai wani dan Spain dake zaune can gefe tundazu ya zubama bangaren mata idanu kuma ba kowa yake kallo ba sai wata cute, unique babe dabe ta6a ganin mai tafiya da zuciya farat dayaba irinta. Tunda ya qyalla idanu akanta yakasa dauke ido akanta. Maganarta, murmushinta, harararta duk sun tafi da imaninshi Yana lura da yadda idan suka hada idanu take saurin kauda Kai cikin basarwa tana cigaba da surutunta. Hannu bibbiyu yasa yabuga tagumi yana kallonta babu ko kyaftawa. Jitayi an ta6oshi hakan yasashi dagowa ya kalli mutumin "Yadai amir? Bakayin komai, kawani dawo nan ka buga tagumi, lfy?" Ajiyar zuciya ya sauke sannan yasake kallon saitinta kafin yace "Ta tafi dani" yafada cikin shauqi "Wa?" Inji mutumin "Cutie... Na fada soyyayar cutie" yafada yana lumshe idanu "Wacece cutie" inji mutumin "Kalli can, duba dakyau, wacece kamar zahra acikin taurari? Haskenta na dabanne, kyawunta na dabanne, murmushinta? Wayyo! Idan tayi murmushi jiyake kamarvzan narke, ji idanun, soo perfect! Ya rabb kabani ita badon halina ba" yafada yana qara kallonta "Wai wancan mai purple and white din?" Inji mutumin "Hell yes! Itace, mii ruhi" yafada yana dafa saitin zuciyarshi "Sistern wannan baqonne, I asked him yace tareda qanwarshi yake, qanwarshi ce" Waro idanu amir yayi "Dagaske? Ina yake?" Nuna mashi Ashraf yayi dake buga whot dinshi hankali kwance. Zumbur amir ya miqe yanufi wajensu ya zauna kusada Ashraf. "Aslm alaika" yafada yana miqa mashi hannu "Wslm" Ashraf ya amsa yana shaking dinshi "Kaine baqonmu ko?" Inji amir yana murmushi "Eh nine" inji shi yana murmushi "Wow, nice to meet you, ni sunana Amir Khalid, iyayena mutanen morroco ne, amma anan suke zaune, nan suka haifeni, nan nayi karatuna har zuwa matakin PhD, yanzu ni constructional engineer ne ina aiki a company AL-DABB COMPANY LTD.." nan yaita rattafo tarihinshi, Shidai Ashraf sauraron shi yake yana tunanin shi wannan kanshi daya kuwa? Daga ganin mutum saika bugs da bashi tarihinka? Be qaseshi ba har saida yagama yadora da "Tun ina qarami nake son Africans, kuma ina mararin hada alaqa dasu.. ERM..naga qanwarka...tunda nake ban ta6ajin abinda nakeji gameda itaba..please.. Please ka bani dama in tunkareta...ina... Sonta" ya qarashe maganar cikin dar dar don ganin yadda harya daga kati zai buga amma kalamanshi sunsa hannun maqalewa a iska. Shima shiru yayi yana kallonshi a daddarce don ganin abinda zai biyo baya. Sai gani yayi ya kara waya a kunnenshi yana amsa waya ya tashi ya matsa can gefe yana cigaba da amsar kiran. Ajiyar zuciya amir ya sauke ganin Ashe waya zaiyi don shi a tunaninshi shi yasashi wannan qamewar. Saitin matan yasake kallo yaganta tsaye itada wata zasu tafi hakan yasashi saurin miqewa yabi bayan su Suna cikin tafiya da Reyna zasu qaro juice sukaji anaqwalamasu kira daga bayansu Juyawa sukai, gabanta ne yafadi ganin wannan mayen mutumin ne daya addabeta da kallo. Saurin Kamo hannun Reyna tayi don su tafi don ita tsoron shi ma take amma sai Reyna ta cije. Dagudu ya qaraso wajensu yana shesheka duqewa. "Kai matan nan saurin tsiya gareku" yafada yana shesheka "Wai ma, muda muke tfy ahankali" inji Reyna tana bin saudart datayi gaba Shima saurin bindu yayi yana cewa "Eh mana, ba kamar wannan ba qauyar" yafada cikin tsokana Harara saudart ta gallamashi Wanda saida zuciyarshi takusan barin aiki "Wacece baqauyar?" Inji Reyna tana dry Dakyar ya lalubo muryarshi yace " wannan mana, halan kurma ce?" Dariya sosai Reyna tayi tace "A'a ba kurma bace amma baqauya ce, qauyen Nigeria" tafada tana dariya ganin yadda saudart ke hararta "Nigeria Nigeria? Inanema Nigeria? Sai sunan yayi min shige da sunan zoo" inji amir cikin tsokana Harara saudart ta gallamashi for the first time tace "A'a cave ne ba zoo ba" Dariya sukayi gabadaya Amir yace "Allah na ta6a zuwa Nigeria sau daya cikin wani watan Ramadan, munje wani project, the country is damn hot, kamar da oven akayi gidajen, ataqaice muna tsakiyar yin project din nafara ganin wani hazo hazo, inajin dum dum cikin kaina kamar ana daka, ataqaice saidai farkwa nayi naganni hospital, anamin qarin ruwa" dariya su saudart suke tunda yafara lbrin don yadda yake lbrin sai kayi dry Cikin jin dadin sasu dry dayayi ya cigaba dacewa "Ataqaice ranar aka samamin visar dawowa, azumi na kau tuni yazama sheqaqqe" Nanma dariya suka fashe dashi amir na tayasu, basu ankaraba sukaga ansha Gabansu Wanda hakan yasa su saurin dagowa. Ware idanu saudart tayi cikin matsanancin faduwar gaba ganin Wanda yasha Gabansu, fuskarnan tashi babu rahma...✍ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 050 Kallonta yake da rinnanun idanunshi dasuka chanza kala bako kyaftawa, hakan yasata jin cikinta na Neman juyewa don bata ta6a ganinshi a irin wannan yanayin ba. Bata ankaraba taji ya chafko hannunta yafara janta. Amir da Reyna dasukayi mutuwar tsaye tundazu sukayi saurin binsu "Bro please don't hurt her, wlh I mean no harm, don Allah kayi hqr" inji amir dake binshi da sauri don shi duk a tunaninshi hukuntata zaiyi a matsayinshi na yayanta sbd ya ganta tsaye da wani. "Please bro listen to me" yafada Yanajin kamar ya kwaceta da qarfi don be qaunar abinda zai ta6a lu'u lu'u dinshi Ko kallon gefenshi Ashraf beyi sai Jan saudart dayake da sauri yanufi gida itakau saudart kasa magantuwa tayi sai binshi take kamar raqumi da akala Saurin shan Gabansu amir din yayi yana cewa "Please bro listen to me" "Get lost you fool!" Inji Ashraf cikin qaraji "Please kayi hqr, ni nazo na sameta, please don't hurt her" yafada pleadingly "Bazaka kauceba?!" Inji Ashraf dakeson controlling din kanshi don jiyake kamar ya shimfidar dashi yaita naushinshi a fuska "Please.." Wani wawan bangaza Ashraf yayi mashi Wanda har saida yakai qasa sannan yasake damkar hannun saudart, fuuu sai hanyar gidansu. Halbi daya yayi ma kofar ta bude yashiga yana tura saudart ciki Wanda batayi masauki a koina ba sai kan kujera. Dagowa tayi tana kallonshi da idanunta dasuka fara chanza kala taga shima kallonta yake da rinnannun idanunshi. "Waye shi?" Ya tambaya yana huci Bata amsaba kuma bata bar kallonshi ba. "Nace who the hell is he?!" Yafada cikin qaraji har jijjiyoyin wuyanshi na bayyana. Gyara zamanta tayi batareda tace komai ba zuciyarta na suya, tashi tayi tana gyara squeezing din rigarta sannan tanufi hanyar dakinta Shan gabanta yayi cikin quluwa "Magana nake maki!" Ya daka mata tsawa Watsamashi jajjayen idanunta tayi Wanda ke qoqarin Tara ruwa tace "Give way" "nace meye hadinki dashi?! Eh! Kin wani taho kina yaqe mashi baki kan hanya, abinda yakawoki nan kenan? No modesty no class, yazo yana maki magana..boom sai washe baki, wayasan what will come next? Are you that desperate?" Yafada cikin hayyayakowa "And don't forget it's me! My life! Ina ruwanka! The last time I checked babu wata alaqa a tsakaninmu, I owe you no explanation, it's none of your damn business ko me kaga munayi! Ko hugging dinshi kaga nayi banga abinda yashafeka ba" tafada cikin tsawa itama Damkar hannunta yasakeyi da qarfi don jitayi kamar zai qille dan hannun. "Ni kike fadawa haka?" Kiciniyar kwace hannunta take hawayen datake qoqarin 6oyewa na gangarowa "Ka cikani you dirty pig!" Tafada cikin cracked voice "Nace ni kike cewa you can hug him!" Yafada still damke da hannunshi, shi kanshi yasan what he's doing was wrong, amma yarasa dalilin dayasa yakasa controlling din kanshi, wani Abu mai zafi ke tasomashi daga qasan zuciya har zuwa maqoshi. "Leave me alone!" Tafada tana daga dayan free hannun da niyyar marinshi amma ya damqeshi shima ya hada ta wancan ya riqe. Fashewa tayi da kuka tana kiciniyar kwacewa don jitake kamar qarwashin wuta ke riqe hannun. Jingina ta da bango yayi still riqeda hannayenta da hannunshi guda dayan kuma ya dago fuskarta data jiqe sharkaf da hawaye yace "Don't.. Ever..let me see.. You with that.. Guy..again" yafada yana nishi sama sama kaman Wanda yayi wasan tsere. Qalato yawu tayi a bakinta ta tofamashi yayi saurin kauda fuska "I hate you! Damn you!" Tafada cikin kuka sosai Tsayawa yayi yana kallon yadda take kukan jikinta har rawa yake in the process. Sai yanzu yake wondering why yake behaving like this? Meye nashi don yaganta da wani? Ina ruwanshi? Tsayawa yayi yana kallon yadda hawayen ta ke gangarowa, duk ga gangara daya jinshi yake kamar gangarar darma acikin zuciyarshi. "I..hate..you...with passion" tafada cikin rawar muryar kuka. Sosai Kalmar ta dakeshi, wannan shine karo na biyu data ta6a furta mashi Kalmar qi. Amma wannan Karon Kalmar tafi dukanshi bisa na farko. Sakin hannayenta yayi yana kallonta. Sulalewa tayi ta zauna qasa sannan ta cusa kanta tsakiyar kaffafunta tana cigaba da kuka. Ahankali ya dinga ja baya still idanunshi akanta harya isa bakin kofarshi sannan yajuya ya budeta yashiga yarufo. Jingina yayi da kofar yana sauraron siririyar sautin kukanta. Hannu yasa cikin gashinshi yana dan harmutsawa, yarasa abinda yazo kanshi, he's too harsh on her, yarasa dalilin daukar zafin dayayi nan take. Abinda yaguda kenan shiyasa tunda amir yafara gayamashi yana Sonta dazu yayi saurin bar mashi wajen don jiyayi yana Neman kasa controlling din kanshi. Amma sai me? Sai ganinta yayi tareda shi suna fira harda dariya, be iya misalta abinda yaji a lokacin don baya misaltuwa, jiyayi kamar yayi diving wuqa acikin mutumin. Shiru yayi yana sauraron sautin kukanta daya fara raguwa Wanda yakejin kamar ana digamashi darma ne a zuciya. Jin be iya cigaba da sauraronta yasashi shigewa toilet yaje bakin sink ya bude tap din yana dauraye hannunshi "I hate you!" Maganar ta ta dawo mashi. Yasani tun ba yau ba cewa ta tsaneshi amma furtawan datayi dakuma yanayin data furta yau yasashi sanin ba qaramin tsana tayimashi ba Wanda kuma hakan ba qaramin karta mashi zuciya yakeba. "Ya rabb, take control" yafada yana kallon kanshi ta madubin toilet din. Itakau saida tasha kukanta ta qoshi sannan ta lalla6a tashige dakinta a daddafe ta kwanta sannan ta Dora daga inda ta tsaya, tunda take bata ta6a tsanar hallita kamar yadda ta tsani A.A ba kuma batajin zata iya tsanar wani kamar yadda ta tsaneshi. Ataqaice dai dukansu biyun kai harma da amir yadda sukaga rana haka sukaga dare don babu Wanda tunani yabari yayi barci. Washegari bayan sallar asuba Ashraf nakan hanyar shi ta dawowa gida yaji ana mashi sallama ta baya. Ko be juyaba yasan amir ne, da farko kamar yayi banza dashi saikuma ya tsaya ya juya yana amsa sallamarshi fuska tamke. Ganin yadda ya tamke fuska yasa amir miqamashi hannu suka gaisa cikin dar dar "Bro please kayi hqr, nayima Sistern ka magana batareda izininka ba" "It ok" inji Ashraf yana shirin wucewa Saurin binshi yayi yana cewa "Am so sorry bro, wlh tsakani da Allah nakeson sis dinka, please kabani dama please" yafada yana marairaicewa. Wani zafi yaji zuciyarshi nayi mashi kamar dai jiya, dakyar yayi controlling din kanshi yace "Ba sister ta bace... She's my *wife*" Cak amir yayi suman tsaye idanunshi a ware Shikau Ashraf be qara kallonshi ba yayi gaba zuciyarshi na suya. Binshi amir yayi da kallo baki bude cikin tsananin mammaki da kunya "Oh no! Matarshi? What have I done? Innalilahi" Ya Dade nan tsaye cikin jimami sannan can da tsayuwar ta isheshi ya nufi gida jiki a sa6ule. *********************************** Ahaka Saturday da Sunday tawuce babu Wanda yaqara saka dan uwanshi a idanu. Wasan 6uya sukeyi tsakaninsu don basu yarda su hadu. Ranar Monday ma saboda meeting din dazasu yasasu haduwa. Meeting din marece ne don haka sai large hudu da Rabi suka bar gidan. Kamar koda yaushe yauma motar tsit take babu mai ko motsin kirki. Sanye take da Riga da skirt na material ta Dora baqar after dress akai tayi rolling din gyalen after dress din. Kafafuwanta sanye da flat shoes masu igiyoyi, hannunta riqeda baqar purse. Shikau sanye yake da baqar suit mai light blue din shirr daga ciki, necktie dinshi ma blue sai takalmi cover shoes baqaqe. A harabar company din suka yi parking sannan suka fito. Ashraf yayi gaba hannunshi riqeda briefcase Itakuma ta Mara mashi baya. ******************************** Alhamdullilah komai yatafi daidai sun biya Rabin kudin kuma sunyi signing dukansu harda shaidu sannan kowa Nada copy din takardar saboda tsaro. Saida suka danyi fira sannan suka tashi suka tafi. A wani corridor da beda nisa da office din dasukayi meeting din igiyar takalmin saudart ya warware. Tsayawa tayi ta ajiye purse dinta kan wani tudunka ta duqa tafara maida daurin. Jin kamar ba'a biyoshi yasashi tsayawa ya waigo. Saurin daure takalmin tayi ganin ya zubamata wannan mayattatun idanun nashi sannan ta tashi ta taho suka wuce. Rabonda magana ta hadasu tun ranar juma'a daddare dinnan. Haka suka jera har suka isa motar, harta kama handle din motar zata bude saita tuna da purse dinta. Dan laluba jikinta tayi taji batanan sannan tajuya tana waige waige. Ya lura da ita hakan yasashi tsayawa kallonta, Dagowa itama tayi ta kalleshi taga ita yake kallo saita dauke kai. "What?" Ya tambaya ahankali abinda be ta6a yiba kenan "My purse" ta amsa qasa qasa "Ok go get it" yafada yana shiga motar. Babu musu ta juya don komawa daukowa tana mammakin yadda yake magana cikin sanyi kamar bashi ba. Ta6e baki tayi tana tsaki don hakan bazai chanza tsanar datake mashi ba. Shima binta yayi da kallo harta shige sannan ya sauke wata nannauyan ajiyar zuciya. Hannu yasa yana shafa kanshi daga gaba zuwa baya yana tunanin abinda ke damunshi kwana biyu, haryanzu beson gasgata abinda yakeji game daita amma it look real. Yakusan mintuna goma yana jiranta harya fara qosawa saigata. Da ada ne da yanzu ya dau zafi amma sai tsintar kanshi yayi da kasa yimata magana. Shiga tayi ta rufo kofar ta jingina da kujerar batareda tace komaiba. Shima bece komai ba ya tada motar suka fice. Saida suka fara tafiya sannan yajuyo ya kalleta yaga jingine da kujera take ta lumshe idanu kamar meyin barci "Jibi zamu koma 9ja" yafada kamar Wanda akayi wa dole "Ok" itama ta fada qasa qasa. Daga haka babu Wanda yasake cewa komai har suka Kai gida...✍ Ummin fasihu ce 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 051 Washegari da hantsi tafito daga gidan sanye cikin doguwar hijabi har qasa don ba'a ma hango kayan datasa aciki. Qarfe sha biyun rana ne amma sai kayi tunanin bakwai din safe ne saboda lullumi dakuma buji. Direct block *37* tanufa ta kwankwasa kofar gidan. Shiru taji hakan yasata sake bubbugawa. "Yes!" Taji anfada daga ciki saikuma taji taku na tunkaro kofar. Budewa akayi Reyna ta bayyana. Waro idanu tayi kamar Wanda tayi gamo tana rufe bakinta da tafin hannu. Harara saudart ta gallamata tana cewa "To nashigo ne ko naqara gaba?" Saurin Kamo hannunta Reyna tayi tana cewa "Oh saudart! Ki shigo, am soo sorry, wlh tun washegari naso nazo amma tsoron shi nake, ina tsoron naje na taddashi ko ya taddani gidan, we're soo sorry!" Tafada tana jawota cikin dakin cikin kulawa. "Mtcheew, wannan sorry din duk na menene to?" Inji saudart tana kwace hannunta ta nemi kujera ta zauna Dawowa Reyna tayi kusada ita ta zauna tana cewa "Wlh tun ranar muka shiga tashin hankali musanmman Amir, gani muke dukanki zaiyi, babu yadda beyi daniba nazo gidanku kona gayamashi block dinku amma tsoro ya hanani don gani nake a yanayinshi dinnan yana iya hadawa damu ya make, am so sorry, hope beyimiki komai ba?" Tafada tana dafa kafadarta. Tsaki tasake ja tace "ni babu abinda yayimin dalla, ni Abu daban yakawoni kinzo kin isheni da surutu" inji saudart don kwata kwata batason ayi maganar "Ayyah ai dole na damu ai, haryanzu amir bebar damuna ba, wai inbaki hqr besan ke Matar aure bace" Dagowa tayi da sauri ta kalleta "Waya fada miki ni Matar aurece?" Ta tambaya a mammakince "Amir mana, sun hade da mijin naki yana bashi hqr anan ya fadamashi, ai wlh yanada gaskiya dole ne yayi kishi, imagine wata tazo tace maki tana sonshi kuma the next minute ki gansu tare dole kiji haushi" inji Reyna Banza saudart tayi ta kyaleta don ita har mancewa take dawani aure dake kanta, jinta take soo free kamar ba Matar aureba. Ganin zata sake magana tayi saurin katse ta da "Look Reyna komai yawuce, ninan Abu daban yakawoni, idan kuma bazaki saurareni ba fine" Saurin riqo hannunta Reyna tayi ganin zata tashi tana cewa "Ok ok ina jinki, am sorry" Saida ta murguda mata baki cikin wasa sannan tace "Gobe zamu koma Nigeria" Dafe qirji Reyna tayi da sauri kamar Wanda akayima mugun Abu. "What? Please wasa kike? Nasan wasa kike ko?" Inji Reyna unbelieving "Hmm wlh dagaske nake, meye abun wasa aciki?" "Oh My good Lord saudart, akan wannan Abun zaku tafi? Please karku tafi zan kira amir yazo har gida yabaku hqr" Tsaki saudart taja cikin takaici "Look nifa nagayamiki nama manta da wannan babin, dama Abu yakawomu kuma mungama shiyasa zamu tafi" tafada tana kallon yadda duk Reyna tabi ta susuce "No, nasan duk saboda abinda yafaru ne, please don't leave, wlh besan ke Matar aure bace" tafada cikin marairaicewa. Tsaki saudart taja ta miqe tana cewa "Bari kiga intafi tunda bakida ganewa" Saurin shan gabanta Reyna tayi tana cewa "Ok ki rantse please, ki rantse ba saboda hakan zaku bar nan ba" Tsaki saudart taja tace "Wai nata6a yimiki qarya ne?" "Nidai please ki rantse" "To na rantse, mungama abinda yakawomu shiyasa zamu tafi, ke ke tunawa da abinda yafaru ni harna manta, yanzu haka zuwa nayi naji babu inda zaki anjima Ku rakani shopping ke da Loveth?" Sai a sannan hankalin Reyna ya kwanta har wani sauke ajiyar zuciya tayi "Better, nazaci sbd haka zaku tafi and maganar shopping? It's capital YES! ko da inda zani bazan bari wannan damar kasancewa dake na qarshe ta su6ucemin ba, waya sani ko bazamu sake ganin junaba?" Tafada tana langwa6a kai gefe "Insha Allah zamu sake hadewa ok? Koba yanzu ba" tafada itama tana langa6e kai "I'll miss you" tafada tana rungumeta "I'll miss you much" inji saudart tana murmushi Ganin batada niyyar sakinta yasata yimata chakulkuli Wanda hakan yasata saurin sakinta suna dariya tare "Ok now tafiyar nanan? Loveth zata samu zuwa?" "Yes, yaushe zamu?" "4:00pm dot zanzo nan, idan Baku shiryaba zan tafiya ta" tafada cikin kashedi "Yes ma'am" inji Reyna tana sarawa sukayi dariya gabadaya sannan suka fito tare tayi mata rakiya harta kusan kaiwa gida sannan ta koma ***************************************** *4:33pm* "Mtcheew zanyi tafiya ta fa!" Inji saudart dake kofar gidansu Loveth fuskarnan a hade. Reyna dake gefenta sanye da wando da shirt sai purple jacket ita gwiwa akai gashinta awaje ta kama hannun saudart tana cewa "Kinga zomu tafi, she's not serious" Saudart sanye take cikin lace jaa Riga da zani ta yafa gyale baqi stylishly, kallo daya zakamata kasan cikkakiyar bahausa ce. "Mtcheew mutafi" inji saudart din tana bin Reyna. Dagudu Loveth tafito daga cikin gidan takalmi a hannu tana cewa "Kujirani please!" Saida ta iso motar sannan ta ajiye takalmin tasaka tana numfarfashi wai don tayi Gudu. Sanye take cikin baqar English gown mai tsaga a baya kanta kuma daukeda hula fara sai qatuwar handbag hannunta. Haka suka shiga motar Reyna din sunama juna tsiya. Reyna ce ta zauna mazaunin driver sai saudart gefenta sai Loveth abaya, haka suka tada motar suka bar wajen suka kama hanyar fita daga estate din. Babu laifi sunyi spending din good time at are, shopping sukayi kamar babu gobe, duk abinda tagani ya burgeta saita dauka. Haka suka jero suna shopping suna fira da dariya gwanin sha'awa, saida suka gama kaff sannan fa aka bude babin selfie, wai hotunan tarihi. Sunyi hotuna harna hauka, daga qarshe rasa style din dazasuyi sukayi sai sukaita style din hauka suna dariya, it's a happy moment for them don jisuke kamar karsu dawo gida. Ataqaice dai sai gab magrib suka baro supermarket din. Nan suka sako duk kayan dasuka siya a mota suka shiga. Wannan karon saudart ce ta tuqosu, suna tafe suna tsokanar juna suna dariya. Koda suka iso gida har angama sallar magrib. Kofar gidansu saudart suka yada zango don duk tafisu kaya, saida tagama sauke kayanta kaff sannan sukayi sallama akan saisun zo bankwana gobe idan ransu yakai. Haka ta cicci6i kayan Niki Niki tashiga gidan. A falo ta ganshi zaune yana danne danne a laptop, kallo daya tamashi ta kauda Kai tawuce shi kayan na rinjayarta. Binta da kallo yayi harta kai bakin kofarta ta ajiyesu ta bude kofar sannan ta kuma kwasa tayi ciki tarufo kofar. Ajiyar zuciya ya sauke yana shafa kanshi ahankali sannan ya cigaba da abinda yake. ********************************* Washegari tunda ta tashi da asuba takasa komawa, dama jiya ba wani barcin kirki tayiba, jitake kamar tajawo lokacin don lokacin be wani yimata Gudu. Flight din 10:00am garesu amma tun 7:00am take falo zauna sai gyara zama take agogo kau ta dubashi yafi a qilga. 9:00am sai jitayi ana knocking a kofar falon. Saurin tashi tayi taje ta bude, ihu tasaki ganin Loveth da Reyna ta qanqame su cikin murna "Hmm muda ba'a ganmu ba saimu juya" inji wata dake baya. Sai a sannan saudart ta ankare dasu taga sunada yawa ma harda Dr zahra. Saurin sakinsu tayi tana yi musu iso ciki fuska washe. Nan suka shigo suka zauna taje ta kawo musu ruwan sha sai washe baki take. "Hmm sai murna ake za'a gida kamar irin can yafi nan dinnan" inji wata cikinsu Kamar jira ake nan falo ya kaure da cafta kowa na fadin albarkacin bakinshi itakau Dr sai dariya take musu. Jin hayaniya a falo yasashi cikin mammaki sosai, to gidan dai babu kayan kallo bare yace kallo aka kunna kuma ma wannan beyi kamada kallo ba yafi jin hayaniyar a zahiri. Saurin kammala shirin yayi yana duba agogonshi don har Tara da Rabi. Turus yayi daya fito yaga gugun mutane zaune a falo saudart tsakiyar su suna dariya. Ganinshi yasasu natsuwa suna gaidashi. Qarasowa yayi yana amsawa yana kuma gaida Dr. "Sai Nigeria ko?" Inji Dr zahra cikin tsokana. Dariya kawai yayi yana shafa kanshi "To Allah ya tsare, wish you safe journey, Ku gaishe da mutanen Nigeria, insha Allah zanzo watarana har gidanku, tunda duk munyi exchanging din number" tafada cikin fara'a "To Allah yasa" inji Ashraf yana satar kallon saudart daketa murmushi. Farincikin datake aciki afili yake baya 6oyuwa. At last zasu koma qasarsu. Fitowa sukayi tareda gungun mutanen sai tsokanarta suke tana biyemasu, har mota suka rakata harda budemata kofa tashiga. Sai kuma a sannan suka fara marairaicewa wai zasuyi missing juna. Haka dai suka rabu zuciya babu dadi sai dagawa juna hannu suke har suka bar hangen juna. Komawa tayi ta jingina da kujerar tana sauke ajiyar zuciya tana murmushi. Shima dayake satar kallonta tundazu murmushin yasaki ya kauda Kai yana mammakin saurin sabo irin nata, ji yadda mutane sukazo rakiyarsu kamar sunyi shekaru a qasar. Haka motar tayi tsit har suka qarasa airport din. Suna fitowa daga motar tafara bin airport din da kallo, kamar jiya ne suka shigo airport dinnan da niyyar shigowa qasar amma wai yau sune aciki da niyyar barin qasar zuwa qasarsu. "Can't wait" tafada cikin zuciyarta tana murmushi Saida aka gama komai sannan suka shiga jirgin. Kamar wancan karon kusada juna suka zauna. 10:00am dot aka fara sannarwa na kowa ya daura belt dinshi. Wannan karon ba'ayi qauyanci ba nan da nan ta daura. Jin ana sanarwa na jirgi zai tashi yasa ta koma ta lafe a kujera murmushi a fuskarta. Jin yafara tafiya yasa bugun zuciyarta qaruwa, jin ya daga yasata Sakin nannauyan ajiyar zuciya "Bye Madrid, bye Spain" tafada ahankali tana bude idanu tana yiwa qasar kallon qarshe...✍ Kuyi hqr babu yawa, haihuwa akamana ban samun zama, wannan ma dasafe nake samu nadanyi kafin infita, da babu kwata kwata Gwara kadan, bear with me har komai ya warware🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 052 Tafiyar awa biyar ne babu yan mintuna, kamar wancan tafiyar, barci ne yayi awon gaba daita ba ita ta farkaba sai gab da zasu sauka. Jin suna landing a airport yasata jin wani shauqi na dibanta. "Home, sweet home" tafada cikin zuciyarta tana murmushi. Jitake kamar tayi tsuntsuwa taganta gida. Saukowa aka farayi amma sai gani tayi Ashraf beda niyyar tashi don latse latsenshi kawai yake hankali kwance gashi dole saiya tashi itama zata samu damar fita sbd ita ke daga ciki shike waje. Shiru tayi itama taqi tankamashi amma deep down she's burning. Saida ya mula yasha iska sannan ya tashi ya kara wayar a kunne sannan yanufi hanyar fita cikin takunshi na qasaita. Binshi tayi da kallon takaici sannan taja tsaki ta miqe itama tafito. Kamar wancan karon drivern dazai kaisu gida haryazo. Shiga sukayi dukansu gidan baya sannan drivern yajasu suka fice daga airport din. A parking space yayi parking suka fito gabadaya, saudart na qarewa gidan kallo, jitake kamar tayi shekara rabonta da 9ja, komai na dabanne da nacan, hatta iskar damuke shaqa yasha banban Dana can. Driver ne ya fiddo mata kayanta na booth yakaimata har falo ita kuma tana kaisu can dakinta a sama. Saida suka gama shigar da kayan tsaff sannan drivern yatafi, shikau Ashraf tuni yasake fita don haduwa da sadeeq. Saida ta kammala komai inda yakamata sannan tayi wani juyi tana fadawa kan gadon "Bari na kira wannan chali chalin" tafada tana nemo contact din baby sannan ta Danna mata kira. A bangarensu Ummy kuwa suna zaune baby tayi matashin Kai da kafar Ummy taji wayarta na ringing. Kamar bazata dubaba saikuma ta daukota tana dubawa. Wani ihu tayi tana zabura daga kwancen datake a kafar Ummy har saida Ummy tadan firgita. "Oh my God! Wlh anty ce, itace!" Tafada tana qara ware idanu tana kallon screen din wayarta. "Wannan wane irin hauka ne baby?" Inji Ummy a qule "Sorry Ummy, kalla wlh anty ce da number Nigeria, kenan sun dawo? Bari na daga karta tsinke" tafada tana daga wayar. Ihu ta challarawa saudart cikin kunne Wanda saida saudart ta janye wayar daga kunnenta tana dariya. "Aunty? Dagaske kece? Yaushe kuka dawo? Shine ko agayamana ko? To munyi fushi" inji baby tana kallon Ummy dake kallonta itama fuskarta da murmushi "Ayyah autar mata, am soo sorry, surprise mukayi muku, kuma wlh dawowarmu kenan, ina Ummy?" "Gatanan tana jinki, abata?" "Eh bata" Nan ta miqama Ummy wayar "Aslm alaikum" inji Ummy cikin muryarta mai cikeda natsuwa da kwarjini "Wslm Ummy, barka da wuni Ummy" inji saudart cikin ladabi "Barkanki dai daughter, ya kuke? Ya hanya? Wannan surprise visit haka?" Dariya saudart tadanyi tana cewa "Ayyah Ummy, kuyi hqr, surprise mukayi muku" "Ai babu komai, surprise Nada dadi ai, amma da kun fada da na turo baby ta gyara muku gidan kafin Ku iso" "Ayyah Ummy, babu komai ai, zanyi besides gidan bawani qura yayiba sosai" "Dukda haka bari tazo ta kama maki, kunsha hanya kuma sai a Dora da wahala? Bari tazo yanzu" Nan sukadan ta6a fira, itakau baby tanajin maganar tafiya daman ta haye sama dagudu don shiryawa. Cikin dan qanqanin lokaci saigata ta sauko cikin shirinta, lokacin har sun gama wayar, ta amshi wayarta tayimata sallama sai rawar jiki take sannan ta fice. Saudart taji dadin zuwan baby sosai don tare suka gyara gidan kuma tasata nishadi sosai, surutu kau kamar an kunna radio, saida suka gama sannan tayimusu girki suka zauna sunaci tana gwadamata hotunan dasukayi dasu Reyna a supermarket, baby sai santin hotunan take. Sai wajajen isha'i driver yazo daukar baby, nan ta hadata da tsarabar datayo musu, trolley qananu biyu. Sosai baby tasaki baki tana kallon kayan don batayi zaton sunkai hakaba. Zata fara qorafi saudart ta hayewarta sama tana cewa ta gaida Ummy ta maida kofa ta rufe. Babu yadda ta iya haka ta kwashi kayan tafito suka wuce. Agida ma saida Ummy tasaki baki ganin tsarabar, trolley daya na baby daya nata. Shaqe kowanne yake da gown gown masu kyan gaske sai kayan kwalliya da mayamayai a trolley din baby Itakuma Ummy turarruka da takalmi masu kyan gaske. Suna zaune suna duba kayan Ashraf yashigo. Shima bin kayan da kallo yayi don besan dasuba. Saida ya zauna suka gaisa sannan Ummy tafara mashi qorafin kayan sunyi yawa, anan ya nunamasu shi bema San dasuba. Sosai Ummy taji dadin abinda saudart tayi kuma hakan ya linka soyyayar datake mata ada. Nan take ta kirata tana mata qorafin kayan sunyi yawa, itadai iyakarta dariya batace komaiba, sai daga baya Ummy tayimata godiya sosai kamar irin uban kayan nan akayimata amma kasancewar duk qanqantar alhairi dadi ke gareshi yasa taji dadi sosai. Ashraf kau duk wayar dasukayi yana jinsu, sai bin kayan yake da kallo yana mammakin halin saudart. Meyasa take son ahalinshi? Meyasa bata tsanesu ba kamar yadda ta tsaneshi? Meyasa take girmama ahalinshi bayan be dauki nata a bakin komaiba? Ko sau daya be ta6a takawa gidansu ba ko wajen daddy ko mamy da niyyar gaisuwa tun bayan aure, be ta6a zuwa ba bare su saba dajuna amma gashi ita tazama kusan jininsu don yana ganin zallar qaunar dasuke mata dakuma Wanda take masu. Haka yabar gidan jiki a sa6ule, kwakwalwarshi chunkushe da tunani Kala kala, yanajinshi cikin wani yanayi marar misaltuwa. Koda ya isa gida har goma takusa, be isketa a faloba kamar yadda yayi tsanmmani. Kashe wutan falon yayi ya haye sama ahankali. Kofar dakinta dake rufe ya tsaya yana kallo batareda yasan dalili ba. Ada babu ruwan shi da dakinta don gar mantawa yake tana nan, amma yanzu jiyake kamar yaje ya bubbuga ta fito yaganta. Ya Dade yana kallon kofar sannan ya sauke ajiyar zuciya ahankali ya murda handle din kofar dakinshi yashiga jiki a mace. A ranar haka yaita juye juye yana tunane tunane har barci barawo yayi awon gaba dashi. Washegari basu hadeba, lokacin data fito harya fita, office dama sai Monday zatayi resuming don haka yau gida zata ta wuni. Taji dadin zuwanta gida don murna sukayi tayi dasuka ganta kamar su maidata ciki, Suma tsarabarsu ta fiddo musu ta basu sai murna suke. Anan tayini sukasha firarsu sannan da marece as usual tawuce mall din daddy. Sosai daddy shima yayi murnar ganinta sai nan nan yake daita ya rasa inda zai sata don murna. Shima yasha tsaraba danginsu agogo, takalmi, turarruka da sauransu. Ba ita ta dawo gida ba sai bayan isha'i. Koda tadawo shi be dawoba don haka hayewarta tayi sama. Shima kamar jiya saida ya Dade yana kallon kofarta Yanajin inama ta fito daidai lokacin yaganta. Ya rasa dalilin son ganintan amma kawai jiyake yanason kallon fuskarta, rabonshi da its tun jiya amma jiyake kamar yayi wata be ganta ba. Saida yagaji da tsayuwa sannan yasa hannu yana shafa kanshi ahankali "Ya rabb, take it easy on me" yafada yana kallon kofar again, sannan yayi ajiyar zuciya ya bude nashi kofar yashige. Agurguje🙏 Yau Monday. Rabon da Ashraf yasaka saudart a idanu tun ranarda suka dawo daga Spain. Yau kwana hudu kenan, tun yana daukan abinda yakeji a wasa har abin yafara bashi tsoro. Sosai yabi ya sussuce don ma miskiline shiyasa ba'a ganewa amma shi kadai yasan abinda yakeji. Gashi gida daya suke amma miskilancinshi ya hana yaje wajen ta yaganta don gani yake hakan kamar zubda ajine. Itakau saudart har mancewa take ma dashi don a ranakun nan tashiga busy ba kadanba, shi kadai ke haukanshi don wani sa'in mancewa takeyi da wanzuwarshi. Tunda wuri ya shirya yau yawuce office badon komaiba sai don yaganta, he was glad cewa finally zai ganta tunda dole yau tazo aiki. Haka yaci gayunshi cikin grey suit Wanda yayi bala'in amsarshi sannan yafice. Saidai me? Yana zuwa company wani mummunar labari ya riskeshi Wanda yayi matuqar girgizashi. Yayi parking din motarshi ya hayo sama cikin nishadi da Farincikin zaiga muradin idanunshi. Saida ya kalli empty office dinta yaga wayam batanan sannan ya kalli agogon hannunshi yaga duka duka 7:45 Murmushi yayi yana shafa kanshi ganin uban safkon dayayi saboda ganinta. Office dinshi yashiga Wanda yake qal qal sai zuba qamshi yake. Be Dade da zamaba saijiyayi an bude kofar batareda anyi knocking ba Wanda hakan yasashi saurin dagowa don duk a tunaninshi saudart ce. Ganin sadeeq ne yasashi binshi da kallo ganin kamar fuskarshi na daukeda damuwa. Ahankali sadeeq ya qaraso gabanshi fuskarnan a dagule babu fara'ar nan babu tsokana da shaqiyanci. "Kai kuma fa lfy?" Inji Ashraf yana kallonshi Bece mashi komaiba sai wata takardar daya ajiye mashi agaba yana kallonshi. Ganin hakan yasashi dauka tareda dubawa. Abinda yagani yasashi zabura tsaye yana ware idanu "What!" Yafada cikin firgici yana sake ware idanu akan takardar "Am sorry Ashraf" inji sadeeq asanyaye "Innalilahi waina ilaihi rajiun, innalilahi waina ilaihi rajiun, innalilahi waina ilaihi rajiun" yafada cikin dimuwa...✍ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 053 Jiyayi kaffafuwanshi na Neman Gaza daukanshi yasashi komawa ragwaf akan kujera yana cigaba da maimata innalilahi "Ashraf please don't take it easy on yourself" inji sadeeq yana Qarasowa wajen shi yana dafa kafadarshi Kasa magana yayi sai kallon takardar dayakeyi "Sadeeq how come? Garin yaya hakan yafaru?" Ya tambaya cikin surewa "Destiny.. Ashraf qaddara ce, please kayi tawwakali, Allah shine me badawa kuma mai amshewa, shiya hallici riba da faduwa" inji sadeeq cikin tattausan laffazi "Sadeeq kasan millions nawa nayi asara? Why? Why me?" Yafada yana dafe kai zuciyarshi na wani irin quna "Kayi hqr Ashraf, bakai kadai kayi asara ba harda su, remember Rabin kudin ka bada, kaga kenan Suma sunyi asarar, tunda matsayin Suma Rabin kudin sukayi asara" yafada yana dan murza kafadarshi. Dafe kanshi yayi da hannu biyu ya Dora a desk zuciyarshi na tuquqi "Why? Jirgin betashi collapsing ba saida ya dauko kayana? Ya Allah wannan wace iriyar qaddara ce?" Yafada cikin matuqar surewa. "Ashraf please karkayi sa6o, ka dauki qaddara please, wannan na cikin cikar imaninka, qar6ar qaddararka aduk yadda tazo maka" inji sadeeq cikin jimami. Ringing din wayarshi ce ta katse su. Kasa dagawa yayi hakan yasaka sadeeq dagawa yasa hands free. Labari dayane, can su Hussain suka bugo suke fadamashi yadda abin yafaru har jirgin ya jirkice cikin ruwa, kuma ba'a tsira da komaiba. Ashraf na sauraron su amma yakasa cewa komai har suka gama wayar, he felt soo empty don sosai ya zuba dukiyarshi hundreds of million don aganinshi sana'ar ta samuce. Sunanan jugum jugum sukaji ana knocking din kofa. Kamar yadda ta saba knocking uku tayi sannan ta bude ta shigo. Turus tayi ganin su jigum jigum, hakan yasata Qarasowa ciki ahankali tana kallonsu. Dauke kai yayi daga kallonta zuciyarshi na tafasa don yanzu besan ganinta musanmman da zuciyarshi ke kitsima mashi wani Abu. "Good morning" tafada tana kallonsu daga wannan zuwa wannan. Sadeeq ne yayi qarfin halin qaqalo murmushi ya nunamata wajen zama yana cewa "Morning miss, please sit" Zama ta qarasa tayi tana kallon Ashraf daya kauda Kai gefe sannan ta maida kallonta kan sadeeq da alamun tambaya a fuskarta. "Mr sadeeq, hope everything is ok?" Ta tambaya innocently Murmushin yaqe yayi mata yana cewa "Yes miss, da dai sauqi za'ace" inji sadeeq yana Satan kallon Ashraf "What happened?" Inji saudart Zai bude baki yayi magana Ashraf ya katseshi da. "Look keep quiet my friend! Me zaka gayamata Wanda batasaniba? A matsayinta na secretary na ita wannan labarin zai fara riska kafin kowa, so meye na pretending? Kifito fili ki nuna Farincikin dakike aciki mallama, dama abinda kikeso kenan, my downfall, now kinsani, go and celebrate" "Ashraf..." "Kaga kyaleni mallam, don't Ashraf me ok? Ba gaskiya bane? Eh! Ki gayamin baki tsaneni ba? Da bakin ki kika fada, kullum kina cikin addu'ar taggayyarata kuma gashi Allah ya amsa, sai kiyita murna, keda kwaddayayyen babbanki, now leave! Kibarmin office dina! Get out of my life!" Yafada cikin qaraji. Daskarewa saudart tayi inda take zaune. Tarasa inda maganar shi ta dosa, sosai kanta ya kulle. "Haba Ashraf? This is wrong..." "Look mallam ban kasa dakai ba ok? Kacemata tafita before I do something stupid, taje ta gayawa Shamsu tau burinshi yacika!, kufita dukanku!!" Yafada kamar wani sabon kamu. Saurin miqewa tayi ta dufi hanyar waje cikin sassarfa. "Damn you!" Sadeeq ya fadawa Ashraf cikin fushi sannan ya maramata baya. A office ya taddata ta juyama kofa baya. Shigowa yayi da sallama Wanda hakan yasata saurin goge hawayenta da bayan hannu. "Miss saudart dan Allah kiyi hqr..." "It ok" tafada tana juyowa ta kalleshi da idanunta dasuka farayin ja "Miss saudart wlh baya cikin hankalinshi ne, he's in shock, dazu takarda yazo mana cewa..." "Jirgin gwalagwalai yayi collapsing ko?" Ta katseshi da hakan Kallon mammaki yayimata sannan yace "Kinji labari kenan?" Jan hanci tayi ahankali sannan tace "Eh nasani, tun kafin mubaro Spain, nasan jirgin zaiyi collapsing" tafada tana kallon yadda ya Waro idanu cikin kidima. "W...what! Tayaya? Kardai dasa hannunki aciki?" Ya tambaya bakinshi na 6ari Murmushi saudart tayi sannan ta fiddo wayarta ta kunna wani video ta miqamashi Amsa yayi yafara kallo . Da farko magana kawai yakeji be ganin mutanen sannan daga baya fuskarsu ta bayyana. Wadannan mutanen ne uku dasukayi meeting dasu a Spain tsaye suna magana akan yadda zasu tsara yadda jirgin zai kife a ruwan shi yadda baza'a zargi wani Abu ba Wanda a zahiri jirgin dauke yake da gwalagwalai na bogi. Sannan suka tsara yadda zasuyi kason abinda suka samu idan komai yatafi daidai, duk wannan abin da turanci suke magana. Zufa sadeeq keyi takoina har saida yagama kallon video din sannan ya dago yana kallon saudart totally speechless. Itama shi take kallo, ganin kallon dayake mata Yama kasa magana yasata cewa "Ni nayi video din.... Ranar bayan meeting din mun fito muna tafiya sai igiyoyin takalmi na suka since, shine na aza purse dina a wani dakali da duqa na daure... Cikin ikon Allah saina manta da purse din nafita saida zan shiga mota natuna nadawo domin dauka. Harna dauka zan wuce naji maganar su saikuma naji ya danganci meeting din damuke saina kasa kunne. Ahaka suka fito daga office din suna maganar cikin turanci don da alama baqin cikinsu bejin Spanish, jin abinda suke fada yasani shiga firgici, narasa yadda zanyi saina la6e ina sauraron su, anan idea ta fadomin na dayi recording, da voice naso nayi sainaga Gwara video tunda fuskarsu is showing clearly, hannuna na 6ari nafiddo wayata na dauke su har suka gama tattaunawarsu suka shige dayan office din" Dagowa tayi tana kallon sadeeq daya tsuramata idanu kamar T.v "Haka nafito rai a jagule, naso nafadama A.A saikuma nakasa, firstly at that time ya 6atamin rai ina fushi dashi, secondly dukda wannan ya isa hujja gani nake be cika hujjaba Gwara nabi a sannu inta bibbiyarsu insamu enough evidence" "Muna cikin mota yafadamin jibi zamu koma Nigeria, hakan yasani cikin rudani sosai don sonike in bincikesu sosai, haka na kwana ranar ina tunanin mafita" "Washegari mukaje shopping din tafiya dawasu qawayena biyu, daya mai suna Loveth masanar computer ce sosai, kamar wasa na tambayeta ta iya hacking din account din mutum tace eh, nace ta koyamin tace zata koyamin amma saina fadamata dalilin hakan, dafarko naqiya saikuma daga baya na gayamata, jin hakan yasata taimakamani nayi hacking din account din zahid, ya kasance duk abinda suka turamashi duk ina gani.... Gasunan" Tafada tana Ciro wasu takardu a Jakarta ta miqa mashi. Hannu na 6ari ya amsa yana dubawa. Waro idanu yayi don komai na ciki, yadda suka hada komai. Koda takardun kadai sukayi amfani saisun dauresu bare uwa uba ga video. Dagowa yayi yana kallon saudart dake kallonshi itama, sai 6ari bakinshi yake yakasa magana Murmushi tasaki sannan tace "Wannan ya isheku Ku dauresu, aciki idan ka duba sosai zakuga ba akanku suka faraba, sun yaudari mutane da Dana ta wannan hanyar, go ahead a sue them, best of luck" tafada tana fita daga office din tabarshi nan tsaye yakasa ko motsi...✍ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) Gaskiya naji dadin comments dinku na page daya gabata, sai jiya nasan AUREN KWANGILA Nada masoya dayawa. Jinjina gareku members din *AUREN KWANGILA NOVEL GROUP* *OFFICIAL MARCY NOVEL FANS* *HOME OF HAUSA NOVELS* *MATAR BAHAUSHE NOVEL FANS* *FAUZZIYA D SULEIMAN NOVEL GROUP* *KANO NOVELS* duk naga comments dinku da fatan alhairi da addu'o'inku gareni, ina godiya sisters🙏 Allah yabar zumunci🤝 Masu qorafin short page suyi haquri, yanzu ban zama sosai, dakyar nakesamu nayi muku wannan dasafe kafin na fita, nima na qagara Nagama littafin, dama aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, please bear with me, mutafi ahakan har insamu kaina, ngd da qaunar Ku agareni💝💝💝 054 Saida yaji Qarar rufewar kofa sannan yadawo hayyacinshi. A tamanin shima yafito office din amma sai gani yayi elevator din na rufewa daita aciki "Miss saudart!" Yafada da qarfi yana nufarta amma har yagama rufewa. "Shit!" Yafada yana nufan private elevator din Ashraf don cimmata. Hannu na rawa ya Danna last floor yashiga. Jiyayi kamar elevator din baya Gudu don jiyake kamar yafita yabi ta mattatakalai. Finally elevator din yatsaya a last floor, tun kafin yagama budewa ya ra6a ta gefe yafita yayi waje dagudu. Tayaya zaibari ta tafi bayan wannan abun datayi musu Wanda bazasu iya sakamata da komaiba. Fitowa yayi a harabar company din yana wurge wurgen idanu don ganinta. Can parking space yaganta tana qoqarin bude motarta. A sittin ya nufi wajen yana kiran sunanta, tana jinshi tayi banza dashi ta bude motar tashiga, ta ziro hannu don maido kofar motar taji an riqe kofar gamm. Dagowa tayi tana kallonshi da alamun tambaya batareda tayi magana ba. "Miss saudart... Please karki tafi... Kizo mu warware komai tare please" yafada yana maida numfashin gudun dayayi Murmushin nan nata tasakeyi sannan tace "Warware me? I've done my part, ko babu ni zaku iya warware komai" "Please saudart, kizo mu gwadawa A.A, yaga abinda kikayi please, don't leave just like that" Guntun murmushin takaici tayi sannan tace "Ni ba don wani nayiba, idan da danshi zanyi to believe me ya Dade be fada chakwakiyar datafi wannan ba, ni don Allah nayi, kuma wannan abun ina iya yiwa koma wanene, muddin na tsinci kaina a position na taimaka wa wani zan taimaka mashi badon komaiba saidan samun lada, duniyarnan yar qanqanuwa ce, batada tabbas bansaniba wataqila wannan shine aikina na qarshe a duniya, ina iya fita yanzu inyi clashing dawata motar in mutu, yanzu haka ina iya kai Kalmar nan tazamo itace ta qarshe a duniya, idan mutane zasu dinga tuna mutuwa dakuma nazari akan duniya da sun zage, sun nemi hanyar lada at any possible time or little opportunity, kana iyayin Abu Allah yabaka lada daya bazaka San muhinmmancin wannan ladar ba sai ranarda kake Neman ladar ruwa a jallo, lada daya yana iya hana mutum shiga aljanna yafada wuta, lada daya na iya hanaka shiga wuta kashiga aljanna, shiyasa duk abinda kasan zaka aikata kasamu lada komin qanqantarshi karka bari damar ya wuceka Ni nayi saboda Allah ne da qwadayin lada, so basai ka kaini wajen shi ba don bayada abinda zai iya biyani asalima da saboda shi zanyi da ba zanyi ba, saidai a matsayinka na aboki kuma dan uwanshi zan baka shawara, ka fahimtar dashi meye duniya, dukiya ba itace komaiba, dan Adam daraja gareshi, musanmman mahaifa, yau mahaifinka ko mashayi ne yasha yayi tatul yazo yana Marisa tsakar hanya dole nakane, dole kaji zafi idan aka sokeshi koda yana yin abinda aka sokeshi akai muddin kasan darajarshi, mahaifa ba abin wasa bane saboda bakada tamkarsu kuma bazaka samu tamkarsu ba, duk wannan zai iya zagin mahaifan wani ko yayi maganar Rashin da'a gamedasu to ka bincika, besan darajar nashi bane, ko kisan kai mahaifina yayi hakan bazai sani gudunshi ba ko w sokeshi inkasa nuna jin haushina ba, saboda bayan Allah da manzonsa wadannan hallitun biyu sune mafi daraja acikin hallitu.... Nabarka lfy". Tana kaiwa nan ta rufo kofarta ta tada motar tabata wuta. Ja yayi da baya cikin mutuwar jiki yabata hanya tayi reverse yabita da kallo harta fice daga kamfanin. Ya Dade nan tsaye yana saqawa da kwance wa sannan dakyar yasamu yajuya jiki a sanyaye yashige company din. Direct office dinta yakoma inda ya ajiye takardun da wayarta Wanda bata tsaya amsaba. "Wane irin zuciya saudart ke dashi? Gaskiya samun irin saudart acikin al'umma zaiyi wuya a irin wannan zamanin" Kwasan kayan yayi ya nufi kofar Ashraf ya bude yashiga batareda knocking ko Neman iziniba. Jin anshigo yasashi dagowa a masifance don ya balbale koma wanene. Ganin sadeeq da yanayin dayake ciki yasashi fasawa ya tsaya yana kallonshi. Qarasowa sadeeq yayi ya ajiye abubuwan gabanshi yana kallonshi. Shima kallonshi yayi sannan ya kalli takardu da wayar kan table din. "Wannan fa?" "Ka duba mana, amsarka na aciki, na barka lfy" yajuya yafita batareda yajira single word from him ba. Saida ya rakashi da kallo harya fice sannan ya dauki takardun yafara dubawa. He was in shock sai zare idanu yake yana bin takardun da kallo, kanshi ya qulle ruff yakasa gane komai. Wayar ya jawo ya kunna power dinta nan yaga ba password sai sliding din daza'ayi kawai. Sliding yayi ta bude sai yaga video ne akan screen din. Kunnawa yayi yafara ganin the shock of his life. Daskarewa yayi a zaune, he was shocked, speechless, dumbfounded, ko kwakwarran motsi yakasa. Zabura yayi ya miqe tsaye ya kwashi kayan sai office din sadeeq. Shima ko knocking be tsaya yiba ya banka ya shiga yaga sadeeq zaune yana operating din computer hankali kwance. Sadeeq yaji shigowarshi amma ko dago kai beyiba, dama yasan dolene yazo. "S..sadeeq? Kaga abinda nagani kuwa?" "Me kenan?" Inji sadeeq yana cigaba da danne dannen shi "Kamar yaya me kenan? Kai ka kawosu fa?" Inji Ashraf yana zama kusada shi, fuskarshi still in shock. "To tunda ni nakawo maka su, chunkusashen kwakwalwarka be isa yagayama naganiba" yafada in a harsh tone. "Look sadeeq, ba fada ya kawoniba, now tell me ina kasamu wannan?" Banza yayi dashi ya cigaba da aikinshi. Cikin fushi Ashraf yayi unplugging din socket din computer din "Fuck you! Am asking you!" Yafada atsakankanin haqora. "Me kake tambaya ta?" Inji sadeeq yana qaremashi kallo yana qoqarin danne 6acin ranshi. "The damn video and the damn paper! Ina kasamesu?!" "The damn girl" ya amsa yana kallonshi "Mene?" Inji Ashraf cikin Rashin fahimta "Nace the damn girl ce tabani" "Who?" "Your secretary" yafada still trying to control his anger. "W..what!!" Yafada yana ware idanu cikin tsananin mammaki "Yes... Itace ta dauki video din, takuma jajirce wajen samo evidence din dazamu iya sueing dinsu" "No.. This is unbelievable" inji Ashraf cikin tsantsan rudani Miqewa sadeeq yayi yana takowa gabanshi yayi folding din hannayenshi a qirji yana cewa "But it is Mr A.A, it is" Kallonshi Ashraf yake in Short of words, sai motsi bakinshi yake amma yakasa magana hakan yasa sadeeq cigaba dacewa "Itace, ita ta jajirce harta samo mana evidence din dazamu iya kamasu dumu dumu....." Nan yashiga bashi labari tiryan tiryan yadda saudart ta bashi shima daga farko har qarshe. Kasa ko motsi Ashraf yayi, infact jiyake kamar jinin Jikinshi sun daina gudana sai bin sadeeq yake da kallo kamar zombie Dafa kafadarshi sadeeq yayi yana cewa cikin sanyin murya "Yanzu kaje, kayi pressing charges akansu, be happy komai zai dawo, amma ina tayaka baqin cikin rasa Abu Wanda yafi duk dukiyoyinka da qadarorrinka daraja, jeka please jeka" Kasa koda motsi yayi, ganin hakan yasa sadeeq shigewa toilet yabarshi nan tsaye. Ya Dade ahakan tsaye duniyar na juyamashi. Tunawa yayi da lokacin da tacemashi ta manta da purse dinta. Tunawa yayi da dadewar datayi kafin tadawo Tunawa yayi da yanayinta data dawo Ashe v lokacin taimakonshi tayi? Tunawa yayi da abinda yayi mata a Daren ranar. Jefata dayayi a kujera, shan gabanta dayayi, damqar hannunta dayayi, hawayenta, gangarowarsu. *I hate you... With passion* kalmarta tayi mashi amsa kuwa a kunne. *I hate you! Damn you!* Kalmar ta tasake dawo mashi. Tunawa yayi da farkon haduwarsu. Abubuwan dayaymata, auren su, fara aikinta a company dinshi, wahalhalun daya bata, baqaqen maganganun daya gayamata, muguntan dayayi mata. Amma despite wadannan, ta taimakeshi? Tayi risking din life dinta da time dinta ta taimakeshi bayan muzgunawar dayake mata? Tunawa yayi da maganganun daya ya6a mata da safennan, har kiran sunan baban ta yayi gatsau, yaci mutuncin ta. "Innalilahi waina ilaihi rajiun" yafada yana zamewa ya zauna kan kujerar da sadeeq ya tashi. Jingina kanshi yayi da jikin kujera zuciyarshi zafi, cikeda danasani marar amfani. Lumshe idanunshi yayi yana hadiye yawu mai daci . Saida sadeeq yakusan mintuna talatin a toilet sannan yafito don a tunaninshi yafita. Turus yayi ganinshi zaune ta jingina da kujera idanunshi a lumshe. "Yadaiyi mallam? Mekuma kakeyi anan? Kaje ka shirya komai mana, munada enough evidence zama be ganka ba" Bude rinnanun idanunshi yayi ya kalleshi sannan ya Bude baki dakyar yace "Ina.. Take?" Kallon Rashin fahimta yayi mashi. "Wa kenan?" Shiru yayi yana maida idanunshi ya lumshe Yanajin zuciyarshi na zafi. Can kuma kamar an tsikareshi saiya miqe tsaye wayar still a hannunshi ya riqeta gamm danshi sannan yafice da sauri sadeeq yabishi da kallo. Office dinta yashiga amma wayam sai qamshin ta data bari. Ahankali ya tako ciki yana qarewa office din kallo yadda komai is soo neat and unique kamar dai mammalakiyar office din. Ahankali ya qarasa kujerar datake zama yajata baya ya zaune yana sauke ajiyar zuciya. Ya Dade ahakan sannan ya dago wayar hannunshi yana binta da kalli. Idan be manta ba kamar yana yawan ganinta da irin wannan wayar. Kunnata yasakeyi yayi sliding tadawo still kan video din. Danna home yayi nan take photon ta ya bayyana a screen din daro daro. Photon fuskarta kadai, kanta nannade da Jan gyale, fuskarta dauke da wannan killer smile din nata me bayyana dimple dinta na hannun dama da haqoranta hudu na gaba. Bin hoton yake da kallo yana kallon every noook and cranny na fuska kamar yau yafara ganinta. Wet slippery red lips dinta yabi da idanu yana kallon yadda suka dan raba sukaba haqoranta damar fitowa cikin murmushin. Hannu yakai ahankali kamar mai tsoro ya shafa fuskar kan screen din *SAUDART* ya furta ahankali cikin yanayin shauqi da bege...✍ Kuyi hqr nasan yayi kadan please bear with me🙏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) Ayyah fans naga cigiyarku, nima kuna raina, jiya throughout ban hau online ba saboda hidimar suna, jiya Daren suna yau suna, yanzu ma squeezing din time nayi nasamu posting amma insha Allah komai yakusan warwarewa. Ngd da qauna😘😘 055 A bangaren saudart tunda tafita take falfala uban Gudu a kwalta tana sa bayan hannunta tana share hawayenta akai akai. This guy is unbelievable, duk rayuwarta bata ta6a sanin tsana irin wannan ba, tsanar datake mashi baya misaltuwa, baki yayi kadan ya misalta. "It's coming to an end! Komai yazo qarshe insha Allah" tafada tana juya steering din motar tana shan corner wani junction ta dauki hanyar dazai kaita bakery dinta. Ashraf besan iya lokacin daya dauka zaune ba kanshi kife akan desk din office din saudart. Idanunshi biyu amma shi kanshi be iya cewa ga takamaimai abinda yakeji ko yakeso ba. He just feel like being like that forever, jiyake kamar ya kasance ahakan har abada. Sadeeq daya fito daga office dinshi don yin sallah yayi turus sanadiyar hangoshi dayayi ta glass din office din saudart. Tsayawa yayi yana shawara da zuciyarshi yaje wajen shi ko ya kyaleshi. Da kamar yawuce sai kuma ta sauke ajiyar zuciya sannan yanufi kofar ya budeta ahankali ya shiga da sallama. Shiru babu amsa don ko motsawa beyiba. Matsawa yayi kusada shi inda yake zaune kanshi kife a desk ya dafa kafadarshi Wanda saida yadanji ya zabura kadan alamun bemasan da shigowarshi ba saida ya ta6ashi din. "Ashraf.." Shiru yayi kuma be dagoba "A.A?....get up it's zuhr already" yafada babu yabo babu fallasa Sai a sannan ya dago ahankali ya kalleshi Kauda Kai sadeeq yayi alamun still yana cikin fushi dashi ne. "Lokacin sallah yayi" yana kaiwa nan ya fice batareda yaqara waiwayarshi ba. Binshi yayi da kallo harya fice sannan ya bar kallon inda yabi yafita, ta tashi jiki babu qwari yashiga toilet din office din ya daura alwala sannan yafita shima masjid din companyn Tare suka fito bayan sallar suka jero suka nufo cikin company din amma babu Wanda ya cewa kowa uffan. Koda suka isa floor dinsu wucewa sadeeq yayi office dinshi batareda ya ko kalleshi ba. Binshi da kallo yasakeyi sannan yadan saki murmushin dabai wuce iyakar le6enshi ba. Shima mara mashi baya yayi har office dinshin ya taddashi jingine da kujerarshi yana dan wawwanawa. Jin anshigo yasashi dagowa don ganin mai shigowa. Ganin shi yasashi dauke Kai ya cigaba da jujjuyawa a kujerar. Shima bece komai ba ya qaraso gabanshi yaja kujera ya zauna yana kallonshi saidai duk yadda yaso yadago su hada ido yaqi bashi dama don besake kallon gefenshi ba. "Sadeeq.." Yafada cikin muryarshi datayi sanyi lokaci daya. Banza yayi dashi ya cigaba da wawwanawa a kujerar "Am...am sorry, very sorry" yafada cikin muryar rada. Mammaki ne Yakama sadeeq don jin ya furta Kalmar ban haquri gareshi, abinda be ta6a yiba kenan. Sunsha susami sa6ani kuma Ashraf keda laifi amma beta6a bashi hqr ba saidai yayita Neman hanyar dazasu shirya amma beta6a furta Kalmar sorry a gareshi ba. Katse mashi tunani Ashraf yayi dacewa "I truly am... Bansan abinda yahau kaina ba har nayi blunting haka, am sorry" yafada yana kallonshi Sai a lokacin sadeeq yadago ya kalleshi yaga shima shi Yake kallo babu alamun wasa a fuskarshi "Excuse me, haqurin me kake bani? Wani Abu kayimin ne?" Inji sadeeq cikin basarwa Dan murmushi Ashraf yayi sannan yace "Komai na, nasan nayi blunting dazu kuma abin ya 6atamaka rai am sorry" Ta6e baki sadeeq yayi yana dauke kanshi daga gurinshi yana cewa "A tunanina kanaba Wanda be kamata ba haquri ne, ni bakamin komai ba, kuma blunting dakayi ai bani kayi mawa ba, kafini sanin Wanda zakaba hqr" yafada cikin son danne 6acin ranshi. Maida le6en qasa Ashraf yayi cikin bakinshi yana dan taunawa ahankali yana kallon table din gaban sadeeq. Can ya miqa hannunshi ya dauki pen din sama yana dan dukan table din da pen din still yana taunar le66anshi na qasa ahankali Har sadeeq yacire rai da zaiyi magana sai jiyayi ahankali yace " will she ever forgive me?" Yafada cikin wata kan iriyar sanyayan murya still idanunshi akan desk din yana dan dukanshi da pen. Shiru sadeeq yayi yana kallonshi batareda yasan abinda zaice mashi ba . Jin shirun yasashi dagowa yana kallonshi "Eh? Nace zata iya yafemin? She hates me" yafada cikin yanayin da kallo daya zakayi mashi kasan Yanajin ciwon abinda yafada "Yes she hate you, kaga laifinta ne don tayi hakan? Laifinta ne data tsaneka ko kawai haka kawai ta tsaneka? You...kai ka koyamata tsanarka ba kowa ba, you caused it all!" Yafada at last batareda ta sake yunqurin danne 6acin ranshi ba. "Nasha fadamaka yarinyar nan batada masaniyar abinda ke tsakaninka da mahaifinta, she has no case in this at all, amma ka saurareni? Instead kullum cikin Neman hanyar dazaka quntata mata kake, kullum cikin 6ata mata rai da cimata mutunci kake, what did you expect from her? So kake duk bayan abinda kakemata tazo tana godiya tana washe maka baki? Me zai hanata tsanar ka? Karka manta zuciya tana son mai kyautata mata ne tana kuma Qin mai muzguna mata, kai ka auna kanka a mizani kaga a wane bangare kafada kafin kayi complaining din ta tsaneka" yafada cikin bayyana fushinshi da baida kyan gani. Haryanzu Ashraf be dago kanshi ba kuma bebar dan bubbuga desk din ba da pen ba amma idanunshi sun kada sunyi jajur don kalaman sadeeq direct suke wucewa cikin zuciyarshi suna mai barazanar tarwatsata. "Ashraf, saudart mutum ce, tacika yar halak, despite abubuwan dakake mata amma ji abinda ta sakamaka dashi, ta saka alhairi ga sharri, ka tsaya kayi nazari daga farkon haduwarku zuwa yanzu me tayimaka na Rashin dacewa kai kuma me kayimata na Rashin dacewa tsahon wannan lokaci saika dorasu a mizani kaga wane zai rinjayi wani. Ashraf saudart has a good heart... Golden heart. Tanada qualities da ba kowacce mace ke dashi ba a wannan zamanin. *Biyyaya* da *sanin darajar mutum* Biyyayarta yasata Qin bijirewa mahaifinta dukda ranta besoba, sanin darajar mutane kuma yasa bata ta6a wulaqanta wani ba musanmman mai alaqa dakai dukda abinda ke tsakaninku, kaifa? A kullum bakada abin wukaqantawa kamar babanta a gabanta. Tell me, wannan be isa tsaneka ba? Tell me!" Yakai aya Yana dan huci sama sama Runtse idanunshi Ashraf yayi gamm yana sauraron yadda zuciyarshi ke bugu da qarfi ga wani zafi na musanmman data keyi. Shima shiru sadeeq yayi yana maida kanshi bisa jikin kujera yana dan sauke numfashi ahankali. Sun kusa minti daya babu Wanda yayi magana sannan sadeeq ya dago kanshi daga jikin kujerar daya jingina daita ya kalli Ashraf dake kallon desk haryanzu hannunshi still riqeda pen amma yabar bubbugawa "Ashraf kayi wa baiwar Allahn nan ba daidai ba, shigowarta arayuwarka alhairi ne, kamanta da abinda tayimaka yanzu, ko babu wannan ta kawo farinciki a ahalinka, Ummy da baby nakasancewa cikin farinciki marar misaltuwa by mere ambaton sunanta, suna Sonta kuma tana sasu farinciki duk sanda sukayi tozali daita, wannan baiwar ba kowa Allah yaba ba, ko anan aka tsaya kasan ta cancanci girmamawa" yafada cikin tattausan laffuza kamar bashi ke fada yanzu ba Zagayowa yayi kusada inda ya sunkuyar dakai ya dafa kafadarshi sannan yace "It's not too late, kai ka koyamata qinka, Kai zaka koyamata akasin haka, kawai kayi qoqarin amfani da damarka kar jin kanka ya yaudareka har damarka ta su6uce maka" Nan ma shiru bece komai ba kuma be dagoba. Sadeeq bedamu da hakan ba yakoma ya zauna yana cewa "Yanzu the major thing shine mufara gamawa da case din mutanen nan, saudart tayi fiyeda Rabin aikin, mu saura ide ide. So cheer up guy, munada aiki gaban mu" yafada trying to be carefree. Ranan dai haka Ashraf ya wuni jiki amace, yarasa abinda ke mashi dadi, duk Yama bar zancen mutanen Spain, sadeeq ne keta fafutukarshi akai shikau saidai ya zauna yayi jigum zuciyarshi fall tunani. Sai six yauma yabaro company yayo gida direct. Tun a parking space ya tabbatar da bata gidan don babu motarta a space din. Parking yayi ya fito cikin sanyi yashiga cikin gida still hannunshi damke dawayarta dake hannunshi. Da sallama yashiga falon yana dan sassafta daurin necktie dinshi yana qarewa exclusive falon kallo. Saida yagama loosening din necktie din sannan yanufi stairs yafara takawa ahankali harya haye sama. Kamar yadda tasaba yan kwanakin nan tsayawa yayi yana kallon kofar dakinta tunani kala kala na Kai komo a zuciyarshi. Ya Dade ahakan sannan yashige dakinshi. Ana kiraye kirayen sallar magrib yafito da alwala don tafiya masjid. Qara kallon kofar yayi yana ayyana tadawo tunda duk inda take bata wuce magrib. Jin ana Neman tada iqama yasashi sauka yawuce masjid. Saida yayi isha'i ma sannan yadawo. Kallon parking space yayi yaga still babu motarta, tsayawa yayi yana kallon wajen tunani kala kala namashi yawo a qwanya. Wucewa yayi yashiga falon ta zauna daya daga cikin kujerun falon ya kunna kallo yana kallo amma hankalinshi kwata kwata yana waje yana sauraron dawowarta amma shiru har 10. Tashi yayi yana wondering what keep her so long outside, waje yafita ya tsaya a balcony yana kallon hanyar shigowa gidan. Ya Dade sosai a tsaye yana tsaye yana kallon kofar shigowa amma babu alamun ta. Ganin har 12 bata dawoba yasashi juyawa asanyaye yakoma falon ya zauna kan three seater din falon yana tunanin to inatake, ko tana gidansu? No ai it's not yet over, bazata tafiba just like that, she can't. Zamewa yayi kan kujerar yana mai tausayawa kanshi don yafi kowa sanin kanshi idan ya kwallafa rai akan Abu yakuma so abun Tofa ya dinga wahala akanshi kenan yasan be iya son Abu ba kamar yadda be iya Qin Abu ba. Fiddo wayarta dake hannunshi yayi ya kunnata yayi sliding, wannan kyakyawar fuskar, ma'abociyar fara'a da kyawu ta bayyana. Tsayawa yayi yana kallonta kamar yau yafara ganinta, sannan ahankali yashiga cikin gallery dinta yafara bin hotunanta daya bayan daya yana kallo yayinda abinda yakeji gameda ita ke qara hawa, zuciyarshi na qaimi wajen zaburar dakuma rura wutar soyyayarta a zuciyarshi...✍ Tofa! Team A.A sai a tanaji handkerchief don yanzu the mighty Ashraf is in saudart mercy😆 Team S.S lokacin Ku ne💃 amma fa a tausayamana kar a wahalar damu dayawa. Insha Allah da komai ya warware zaku dinga samun update akai akai Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Am back💃💃💃 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 056 Wasa wasa tun Ashraf na zuba idon ganin dawowar saudart har yafara surewa. Yau Friday Wanda yayi daidai da ranarda akayi shara'a da mutanen Spain. Anyi bincike anga basu kadai suka yaudara ba, sun yaudari mutane da dama ta wannan hanyar don haka aka yankemasu hukuncin zaman gidan yafi na tsawon shekaru goma bayan sun biya duk wadanda suka yaudara kudadensu, qarshe ma company dinsu akasa kasuwa aka siyar sannan aka ba kowa haqqinshi cikinsu harda su Ashraf. Duk wannan bidirin da ake hankalin Ashraf be wajen sosai, duk sadeeq ne ya tsaya a komai don yakasa gane kan Ashraf, yakoma wani soo silent dashi, dama yanada dan miskilancinshi tou sai abin ya hade da damuwa sai ya kasance duk inda kaganshi zaune yake shi kadai yana qurama waje guda idanu. Kwana hudu kenan rabonshi da ita, bata zuwa office, bata gida, bata bakery don kullum ne sai yaje bakeryn yayi parking daga nesa yana kallon masu shige da fice amma ko mai kama daita begani. Har spy yasa Wanda zai zauna permanently wajen don ganin ko za'a samu akasi yana tafiya tazo amma duk amsar dayace, babu saudart. A gida ma Ummy ta lura da yanayinshi dukda idan yaje yakan fuske yaita acting normal amma dayake uwa uwace ko yaya danta ya sauya koda ya 6oyemata saita gane, tasha tuntu6anshi akan abinda ke damunshi amma saiya waske da gajiya ce ko ayyuka sukai mashi yawa. Dayake su Ummy ma sunada labarin yaudarar da akayi musu yasata ganin qila duk akan maganar ce, saidai har kawo yanzu basu ta6a sanin saudart na aiki a companyn shi a matsayin secretary ba bare Susan itace silar warwarewar wannan qulla qulla ba don ko wannan tafiyar dasukayi su a tunaninsu aiki yatafi da Matarshi don haka basuda masaniya akan komai bare su zargi komai. *********************************************** *MONDAY* Zaune yake a kujerarshi mai jujjuyawa, hannayenshi harde a Qirjinshi yayi balancing a kujerar idanu a lumshe sai jujjuyawa yake a kujerar kadan kadan. Sanye yake da suit saidai tasaman na rataye a jikin wani hanger dake daga gefen office din, sai farar shirt da baqin wandon daya bari a Jikinshi, gashin kanshi kwance luff sai sheqi yake. Kamar kullum yau ma tunaninta daya zaman mashi jiki yake, dama da ka ganshi haka shi kadai yayi zurfi a tunani to ba kowa ke maqale a zuciyarshi ba sai ita. Tunaninta ke debe mashi kewa, hotunan ta ke sashi nishadi, don kullum yana maqale da wayarta yana kallon hotunan ta. Yanzun ma tunanin inda zai ganta yake, koda yake baza'a ce besan inda take ba, hasalima yafi kowa sanin inda zai sameta saidai baya tunanin zai iya binta har wajen, bazai iya binta har can ba don aganinshi hakan ba qaramin zubda mutunci bane, hmm karkuyi tunanin soyyayar saudart ta chanza shi ko yayi laushi. A'a he's still the proud Ashraf dakuka sani, haryanzu jin kanshi na nan, badan haka ba da tuni yabita har gidan daddy ya dawo daita amma gani yake hakan ba qaramin zubda class bane. Yes yasan yana sonta amma hakan bazai sa yajawowa kanshi raini ba, shi yanzu kawai soyake tadawo, idan yasamu tadawo to komai zai tafi cikin sauqi, zaisan yadda zai cusamata soyyayar shi, yadda zai yimata mummunan kamu taji duk duniya babu Wanda take so saishi, shikuma sai yadan jamata aji sannan ya nuna yafara Sonta😒 Haka yaita wawwanawa a kujerar yana tsaka yana kwance wa akan yadda zai 6ulloma al'amarin. Jin bubbugar kofa yasashi dagowa yana kallon kofar office din. Sake bubbugawa akayi a Karo nabiyu hakan yasashi Jan guntun tsaki don ya tsani a dameshi yana cikin tunani musanmman ma irin wannan. "Yes? Come in" yafada cikin harsh voice sannan yajawo wata takarda yana kallo fuska a daure. Murda handle din kofar akayi sannan aka turota aka shigo sannan aka maida aka rufe. Jin muryar sadeeq na sallama yasashi amsawa qasa qasa sannan ya dago da niyyar tambayarshi lfy? Idanunshi basu sauka a koina ba sai cikin nata. Cak bugun zuciyarshi ya tsaya, jinin Jikinshi ya daina gudana yakuma kasa ko kyafta ido akanta. Cikin takunta Wanda nayau yafi na kullum ta qaraso gaban table dinshi. "May I?" Tafada tana Jan kujerar gaban table din baya ta zauna batareda ta jira jin ko yabata izinin zamanba ko A'a. Shidai binta kawai yake da kallo without blinking, maqoshinshi yaji ya bushe babu yawu ko kadan, be ta6a sanin yayi missing dinta har hakaba sai yanzu daya ganta, be ta6a jin abinda yakeji gameda itaba irin na yanzu, jiyake kamar Gwara lokacin da be ganinta, jiyake kamar yana narkewa ahankali, soyyayarta sai qara fuzgar zuciyarshi take. Zama tayi ta Dora kafa daya bisa daya itama ta kalleshi. Sanye take cikin doguwar rigar net baqa mai dan kamawa daga sama sai budewa daga qasa, hannun rigar dogone har qaurin hannu, kasancewar ba'a yiwa hannun lining ba yasa farar fatarta tayi reflecting tacikin raga ragan net din, kanta kuma nade da baqin gyale iya kafada sai qaton sun glass data kwamama fuska Wanda yakusan cinye Rabin fuskar, dan guntun bakinta kuma dauke da dark red lipstick Wanda yaqarama kyanta kyau. "Have a seat Alhaji" maganar sadeeq ta katse Ashraf daga kallon qurrillar dayakema saudart yajuyo dan ganin dawa yake. Alhaji shamsu yagani yana Neman zama a kujerar dake kusada ta saudart. Binshi da kallo yayi harya zauna sannan ya maida kallonshi kan saudart data hade gabass da yamma na fuskarta yana mata kallon Rashin fahimta. Tsit office din yayi babu mai niyyar motsawa kowa ya zubama dan uwanshi idanu kawai. Ganin sun kusan 5mins babu mai niyyar magana yasa sadeeq dake tsaye still agefe yadanyi gyaran murya yace "You're highly welcome Mr and Miss shamsu" yafada cikin fara'a. Dawowa yayi gefen Ashraf dahar yanzu be dauke ido akansu ba sannan yacigaba dacewa "Akawo coffee ko drinks?" Murmushi saudart tadan saki tana kallon sadeeq "No, mun gode da karramawa, amma ba zama yakawomu ba bare ayi maganar refreshment, we're here for *BUSINESS*" tafada tana maida kallonta kan Ashraf dake kallonta still, zuciyarshi sai narkewa take ahankali soyyayarta na hudata ta koina. "Business?" Inji sadeeq cikin Rashin fahimta sai kuma ya kalli Ashraf Wanda alamu sun nuna bemasan wainar da ake toyawaba. Maida kallonshi yayi akansu sannan yace "Ok, wannan wane irin business ne?" Wannan karon Alhaji shamsu yayi magana yace "Ba business bane, qarshen business ne, munzo ne mukawo qarshen business din dake tsakaninmu" yafada shima calmly Gaban sadeeq ya fadi, dama ya zargi hakan tunda yagansu, dama abinda yake Gudu kenan. Kallon Ashraf yayi da yanzu Alhaji shamsu yake kallo Wanda da alama shima yaji abinda yace din don shima wani kallo yake mashi mai wuyar fassaruwa. Maida kallonshi yakuma yi gasu saudart yace "Ban fahimceku ba, what do you mean by qarshen business" "A tunanina business daya ke tsakaninmu.." Katse ta sadeeq yayi da "Yes and that was aikin ki anan" Wani kallo ta jefeshi dashi "That was then, I thought tun wancan satin na ajiye aikin" "Da izinin wa? As far as I remember bamu sallameki ba kuma baki kawo resignation letter ba" inji sadeeq Wanda yanzu tsoron shi daya ne, rabuwarsu da Ashraf. Dan guntun murmushi tayi sannan tasaka hannu a jakka tafido wata takarda a linke ta turamasu Gabansu "Here, ga resignation letter din, nabar aiki" "But why, meye dalilin ki na hakan" inji sadeeq, Ashraf kau ba baka sai kunne "Dole saida dalili? A tunanina kamar yadda boss ke iya sallamar employee dinshi haka kawai shima employee na iya barin aiki haka kawai, yanada right din hakan" "Amma kinsan baki ida one month ba? What about your salary?" Dariya tadanyi tana sinne kai "Salary? Me zanyi dashi?" Shiru sadeeq yayi yana kallonta "I don't need your salary Mr, saboda ba don shiba nafara aiki, you can keep it, zai qaramaku wani abun, nikam.. A'a" "Bamucin gumin mutum, salary dinki guminki ne, so muma babu amfanin dazaimana" Daga kafadunta tayi in an I don't care manner Sannan ta maida kallonta kan Ashraf daya zama kurman qarfi da yaji "As I was saying, munzo nan ne don qarashe business, I mean *THE CONTRACT*" kallon daddy tayi shikuma ya doro wani akwati saman table din tareda budewa saiga kudade raw, dubu daya daya bundle bundle. Bin kudaden Ashraf da sadeeq sukayi da kallo kowanne da irin kalan bugun zuciyarshi "Mr A.A, a rana irin ta yau wata hudu dasuka wuce nazo nan don Neman taimakon ka na rancen kudade qimanin million talatin a wajen ka, kace naje nadawo bayan kwanaki biyu Ranar da nadawo kuma ka sanar dani zaka bani rancen amma kanada sharadi" Dan dakatawa yayi yana kallon Ashraf don ganin reaction dinshi, sai gani yayi still yana bin kudaden ne da kallo hakan yasashi cigaba dacewa "Sharadin shine nabaka auren diyata bisa sharadin babu abinda zai shiga tsakaninku na auratayya kan idan na maido kudinka zaka sakarmin ita." Nan ma dakatawa yayi yana kallonsu, sadeeq sai zufa yake dukda sanyin A.c din office din shikuma A.A is expressionless, baka iya gane yanayin dayake ciki. Turamasu akwatin yayi yana cewa "Yau gashi na maido maka da kudaden ka Mr A.A, dama wancan karon mu hudu ne, ni, kai, saudart sai kai Mr sadeeq" "Now here is your money, give me my daughter" yafada yana tsaresu da idanu. Itama saudart su take kallo zuciyarta na halbawa da sauri, wannan ne ranar data Dade tana dako, ranar da komai zai warware, kallo daya tayi musu ta ga mammaki da firgici dukda na Ashraf be nuna ba sosai, dama haka takeso, tayi taking dinsu in surprise, tayimusu dan baka zata, ta nunamusu ba dasu suka dogaraba. Yau dai zata rabuda qaya, tunanin hakan ya hanata barci jiya don azaune ta kwana. Tana murna amma kuma tana samun faduwar gaba Wanda batasan kota menene ba kuma bata damu tasaniba, all she know is yau zata rabu da allaqaqai and she's glad it's happening A bangaren sadeeq kuma tashin hankali ne qarara a fuskarshi. Tayaya zasu rabu yanzu, saudart is the perfect lady for Ashraf, ta dace dashi, idan ta su6uce mashi yayi babban asara. Dama abinda yake Gudu kenan, dafarko beyi tunanin abin zai zama haka ba amma gashi abun na Neman juyemusu. Kudaden yaqara kallo sannan ya kalli Ashraf da haryanzu su yake kallo fuska babu yabo babu fallasa amma shi kadai yasan badaqalar dake faruwa a zuciyarshi...✍ Ku bude next page da 200 comments, zan qilga idan baikai ba karku saka ran ganin wani page din nan kusa😏 Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) Wow! Gaskiya jiya naga ruwan comments ta koina😄 Harda yan la6el duk anfito jiya anyi sharhi, gaskiya naji dadin comments dinku na kowanne group, amma mafi yawanku duk masu Allah ya qara ne ga A.A dinmu. To afa kiyayemu ehe, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaqi🤔 To kudaibi sannu kar shalelen taku ta antayaku cikin kogin kunya🙈😆 057 Tsit kakejin office din kamar babu Abu mai rai aciki. Wani irin shiru ke ratsa office din babu mai ko motsi bare akaiga magana. Kallon kallo ake tsakanin juna kowanne na jiran dan uwanshi ya motsa. Ganin shirun yayi yawa yasa Alhaji shamsu muskutawa kadan yace "Ya kukayi shiru?" Yafada yana kallonsu Sadeeq ne yayi qarfin halin bude baki yace "Abin ne yazo mana a bazata... But.. Atleast.. Dakun fadamana munsan da zuwanka" yafada cikin kame kame. Murmushin manya Alhaji yasaki sannan yace "It's still don't make different, duk dayane, damu gayamaku kafin muzo damu gayamaku yanzu aganina duk dayane tunda a takardar contract din bamuyi yarjejeniyar sai mun fara fadamaku ba idan zamu maido, ko akwai?" Yafada yana tsareshi da idanu. Ajiyar zuciya kawai sadeeq ya sauke don besan ta cewaba kuma. Kallon Ashraf da tunda suka shigo kawo yanzu be furta Kalma dayaba yayi sannan yabude bakinshi dakyar yace "Sir, they are here for the end of the contract" yafada yana kallonshi yana son karantarshi but he's blank. Shiru office din yasake dauka duk idanu suka koma kanshi kowa na jiran reaction dinshi yayinda shi ko dago kai beyiba idanunshi haryanzu na kan akwatin gabanshi yana kallo amma a badini zuciyarshi takusan gama tarwatsewa. Komai ganinshi yake kamar a mafarki, koda wasa be ta6a kawota ranshi zasu iya biyan kudaden nan nan kusaba, komai ya juyemashi ya zomashi a baibai. Rabuwa? Rabuwa da saudart? Wannan shine Abu na qarshe dazai zomashi arai, Ada yake sanyo rabuwarsu a tunaninshi amma banda yanzu, no way, bazai ta6a yiwuwa ba. Saida suka fara qosawa da shirun sannan ya janye idanunshi akan akwatin da yayima quri tundazu sannan ya dagasu ya zubamata su. Wani kaifi taji idanun nashi sunyi mata ga wani kwarjini na musanmman dasukayi dan saida jikinta ya amsa wannan kallon, hakan yasata saurin janye idanunta tana sauraron bugun zuciyarta daya qaru farat daya Kafeta yayi da sharp eyes dinshi babu ko kyaftawa Wanda hakan yasata jin ta ataqure matuqa, sadda idanunta tayi aqasa cikin zuciyarta tana godewa Allah ta sanyo sunglass babu yadda zai iya hango kwayar idanunta bare ya fuskanci halin dasuke ciki. Ahankali ya motsa bakinshi kamar mai ciwon baki still idanunshi akanta yace "Ina son ganin ki" yafada yana kafeta da idanu. Kallon juna saudart da daddy sukayi sannan suka maido dubansu akanshi kuma "Ganina?.... You mean yanzu baka ganina ne?" Tafada tana kallonshi tacikin glass dinta Yanzun ma saida yayi kamar bazai yi magana ba sannan yasake motsa bakinshi dakyar "Alone" yafada a ataqaice Wani qululu ta tokareta, me wannan gayen ke nufi ne? Abinda ya kawosu daban abinda yake fadi daban, gashi sai wani shan qamshi yake kamar Wanda ake tilastawa yayi magana? "Alone kamar yaya?" Tafada tana qoqarin danne 6acin ranta don yau ranar farinciki ne gareta, ranar da tadade tana jiran isowarta, ranar da ta shanye wulaqanci da cin mutunci saboda ita, batason mood dinta ya 6aci don yau ranar farincikinta ne "I mean ke kadai... Zamuyi.. Magana ne" yafada yana kallonta "Ka fadi koma menene anan din, inaji babu wani baqon fuska anan, idan P.A din nakane baka yarda dashiba kana iya sashi yafita" tafada tana kauda idanunta daga piercing eyes dinshi "Eh zai fita amma tareda wannan ma" yafada yana nuna Alhaji shamsu Haushi yakamata, wai wannan, daddyn natane wannan ma "Karka damu shi wannan din is my backbone, idan bashi bani, kome kafada Mani kamar shi ka fadamawa, so feel free to say anything... Besides banga abun long story ba anan, wannan magana ce na signing da divorce, banga abun tsayawa na wasting din lokaci ba, as you can see munada ayyuka dayawa gabanmu Wanda zamuyi attending, can we please proceed with the signing Mr A.A?" Tafada tana jin kamar tayi exploding dan haushi Shiru office din yasake dauka, Shidai sadeeq na gefe yana kallon ikon Allah, bashida tacewa don haka nashi idanu. Dora hannayenshi yayi akan table din yadanyi leaning forward sannan yace "Yes miss, nima banaso na 6atamiki precious time dinki nima na 6ata nawa, all I ask is five minutes of your time and mine, minti biyar kacal then komai saiya wakana" "Wai minti biyar din me? Wace magana ce dole saimun ke6e?..." Katseta yayi dacewa "Look miss, wannan office ne ba kasuwa ba ok? Don't dare shout on me, wata hudu dasuka wuce, ke daya kikazo signing din contract din, daga ni sai ke, that's the same procedure we gonna take, five minutes kawai na tambaya and after that sai ayi koma menene" yafada shima cikin fada dukda wata zuciyar na kwa6arshi akan ba tahaka yakamata yabiba amma girman kanshi yahanashi sauraronta. Saudart iya quluwa ta qulu, bude baki tayi zatayi magana daddy ya damke hannunta Wanda hakan yasata yin shiru ta juyo tana kallonshi. Daga mata Kai yayi ahankali alamun ta amince kawai sannan ya maida kallonshi ga Ashraf dake masu wani kallo mai wuyar fassaruwa yace "Five minutes ko? Ok munbaka, muda muka jira kusan five months, five minutes bazai bada matsala ba" Yana kaiwa nan yamiqe tsaye ahankali sannan ya kalli saudart da kallo daya zakamata ka fuskanci ranta beso wannan hukuncin ba, yadan yimata murmushi sannan yafita. Binshi dawani disgusting kallo Ashraf yayi harya fita don ya tsaneshi fiyeda yadda kuke tsammani, a duniya bayajin akwai Wanda ya tsana sama da wannan mutumin. Sadeeq ma bejira komai ba ya nufi kofar fita yana addu'ar daidaito atsakaninsu, qasan zuciyarshi kuma fall take da takaicin ashraf, ya rasa irin taurin kanshi, shi a tunaninshi kwantar dakai zaiyi yabasu haquri asamu a warware komai amma gani yayi ma wani sabon wulaqanci ya tsiro dashi da girman Kai Can gefen Alhaji ya zauna yana Satan kallonshi cikin zuciyarshi yana cewa "Albasa batayi halin ruwaba" ********************************************** Shiru office din yasake dauka, babu Wanda keda niyyar magana acikin su. Ba yau suka fara ke6ancewa su biyu awaje dayaba amma yau yanayin dasukeji yasha banban Dana da. Duk sai suka zama speechless, babu mai ko motsi atsakaninsu. Sun kusan cinye mintuna biyu ahakan sannan Ashraf ya sauke ajiyar zuciya mai sauti Wanda hakan yasa tadan dago ta kalleshi, sai gani tayi yasa hannu ya dauki bundle daya cikin kudaden yana dan jujjuyawa a hannunshi. Dagowa yayi ya kalleta still yana jujjuya kudin a hannunshi itakau ta kauda idanunta tana jinta duk a takure "Sun cika?" Yafada still idanunshi kanta "Ka qilga" ta amsa ataqaice without looking at him Murmushin gefen baki yayi Wanda shi kadai yasan yayi abunshi yana maida kudin cikin sauran sannan ya kama zip din jakkar ya zuge "Why the sudden change? Meyasa baki gayaman ba" Ya tambayeta yana maido dubanshi akanta. Kallon Rashin fahimta tayi mashi Wanda shima besan tanayi ba saboda glass dinta daya kare idanun. "I said why? You should have tell me" yafada calmly "Tell you? Meyasa saina gayamaka?" Tafada tana mashi wani kallo Ajiyar zuciya yasaki sannan yace "Ok..ok..firstly inason yimiki godiya akan abinda kikayi mana, that shows you're loyal" Mere baki tayi tana yatsina fuska "Me kenan? I don't get you" Murmushin gefen bakin yasakeyi sannan yace "Kin taimaki al'umma da dama, da wadanda sukayimawa a farko damu dama wadanda zasu sake yimawa nan gaba da asirinsu be tonuba, thank you" Ta6e baki taqara yi don ita bata wannan takeba "It ok, besides ni don Allah nayi badon ayi appreciating dina ba, now back to business" tafada cikin qosawa da maganganun shi Tsayawa yayi yana kallonta yana tunanin dama har haka ta tsaneshi? A qagare take ma ya sawwaqe mata don alamu sun nuna a matse take, zaman nan ma da maganar dasukeyi kamar an matsamata ne, kallo daya zaka yimata ka hango qiyayyar datake mashi Wanda hakan yaqara sagemashi gwiwa. Jiyake kamar ya zube agabanta yaita bata hqr har ta haqura su zauna tare cikin aminci da soyayya, amma bazai iyaba, kar Allah ya gwada mashi ranarda zai zube gaban mace yana bata hqr, bazai ma ita misalta kanshi a wannan yanayin ba. "Ok.. Back to business" yafada yana komawa ya jingina da kujerarshi yana kallonta "Now me kikeso?" Ya tambaya yana bin kyakyawar fuskarta da kallo kamar yasamu mirror "Me nakeso? Kafini sanin abinda nakeso" tafada cikin 6acin rai ganin kamar Neman raina mata hankali yake "A tunani na zaku bari harsai mun cika 6months sannan mu warware komai, don't forget yanzu dududu watannin mu uku da auren, me kike tunanin duniya zata fada akanmu" yafada shima yana mammakin kanshi na maganar dayayi Kallon mammaki saudart ta tsaya tana mashi "Me duniya zatace? Ina ruwana da abinda zatace? It's my life Mr" "Yes, it's your life, babu Wanda zaiyi questioning dinki amma mamy fa? Me zaki cemata idan kin koma gida bayan watanni uku a matsayin bazawara?" Sosai maganar ta daki saudart har saida hakan yanuna a yanayinta. Ganin hakan yasashi dorawa da "Yes in so samune murabu din kowa ya kama gabanshi kowama yahuta, amma me zaki gayama mamy? Don't forget batasan komaiba gameda wannan auren ba, ya zataji idan labari ya risketa na kinfito bayan watanni uku da auren ki? Wane dalili zaki fadamata ya rabamu?" Yafada yana kallon yadda yanayinta ke qara chanza wa. "D..don't worry, nasan me zan gayamata, wannan ba damuwarka bace" tafada trying to be firm "Me zaki fadamata? Cewa dama auren contract ne auren mu?" "Wannan be shafeka ba, uwatace ba takaba, babu abinda yashafeka" "Nikau ya shafa miss, mezan fadawa Ummy idan muka rabu? Mezance shine silar rabuwarmu?" Yafada trying to convince her "Look mubar wannan maganar, contract ne ya hadamu, kuma shi zai rabamu, babu ruwan wani da abinda zai fada don gamsar da mahaifiyarshi, besides aure nawa akayi? Normal aure, amma basuyi three months dinba auren ya rabu? Mutuwar auren mu a yanzu ba wani Abu bane it's normal, kana iya gayamata duk abinda kaga dama, I don't care" tafada firmly Sa halshe yayi ya kashi qasan le66enshi ya tsaya yana kallonta ganin tarkonshi besamu danuwa ba "Amma kinsan mutuwar aure saida dalili? Wani dalili zan bayar na rabuwa dake?" "Dalili? Dama saida wani dalilin, atunanina kafi kowa sanin dalilin haduwarmu shi zai zama silar rabamu" "Amma wannan ba hujja bace dazamu rabuba haka kawai, dole sai an samu kwakwarar dalili" Tsayawa tayi sororo tana kallonshi "What are you driving at wai?" Ta tambaya tana kallonshi unbelieving Jan kujerar shi yayi dabaya sannan yamiqe tsaye ya nufi window din office din da labulen ke bude ya tsaya yana kallon waje hannunshi a aljihu itakau sai binshi da idanu take "Dukda auren mu ba normal aure bane, auren yarjejeniya ne, hakan be hana asashi a jerin aure saboda shima shafamashi fatiha akayi kuma igiyoyin nan uku akwai su tsakanin mu, dan haka shima aurene kuma yana cikin auren da Allah yafada cikin *suratul thalaq* Inda Allah (swt) yayi hani da saki batareda da qwaqwaran hujjaba, bayyananniya. Saki yana daya daga cikin abinda Allah beso, Wanda awata ruwayarma cewa ake idan aure yarabu, al'arshi girgiza take saboda girman abun koda kuwa akwai kwakwaran dalili bare wannan Wanda bekai hujjar dazamu fake daita ba mu sa6ama mahallicinmu, idan mukayi hakan me zamu cewa mahallicinmu? Dame zamu kare kanmu?" Saudart datayi mutuwar zaune tunda yafara magana kasa cewa komai tayi. Wai meke shirin faruwa ne? Meya kawo wannan maganar kuma? A tunaninta izuwa yanzu sunmance da sun wuce wurin amma sai bullowa yake da abubuwa daban daban "Look A.A ko mema kake? Meya kawo duk wannan wa'azin? Ohh dama duk kasan da wannan ka fara qirqiro maganar auren tun farko? Inajin kai ka faro komai ba wanibs, ina ilimin, ina sanin a lokacin? Koko sai daga baya duk kasan wadannan? You force me into this marriage kuma yanzu kafara gayamin story? No way! Bazan ta6a zama dakaiba a matsayin miji, are you not ashamed? Just listen to yourself, bazai ta6a yiwuwa ba kanaji? I can't even stand you, bana jure zama na tsayin lokaci wuri daya dakai, shine kakemin maganar zaman aure, are you kidding me? Look Gwara kabar wannan kwalo kwalon naka and face the reality, this is just business and zai qarene a business! So wa'azinka bazai qareni da komaiba, ka Adana abinka zaifi yimaka amfani mallam" tafada cikin huci Juyowa yayi yana kallonta tunda tafara har takai aya, Takowa yayi cikin takunshi harya iso gabanta inda take zaune yana kallonta "And who told you nima sonike na cigaba da zama dake din, I have no option ne, abinda nasani shine bazan qara tafka sa6oba kamar yadda nayi a bayaba, bazan sakeki batareda wata qwaqwarar hujjaba, final!" Miqewa tsaye saudart tayi ba shiri "What!" Tafada tana zare tabarau dinta, jikinta har rawa rawa yake saboda tashin hankali "Look are you ok? What did you mean by bazaka sakeni ba? Me kake nufi? Na zauna da Wanda duk duniya babu Wanda natsana kamarshi? No way!" Tafada cikin qaraji, tashin hankali qarara a fuskar Kalmar tsanar data ambata ba qaramin dukanshi tayi ba hakan yasa ya dago idanunshi dasuka fara chanza launi shima ya zubamata "Nikuma bazan sakekiba! No way!" Yafada cikin 6acin rai Kallo tabishi dashi na yan daqiqu sannan tasaki wata bushashiyar dariya Wanda daga ji iyakarta fatar bakin "Wlh kayi kadan Ashraf, baka isaba, dolene ka sakeni! Saika sakeni wlh!" "Nikuma bazan sakekiba! Aure yanzu aka farashi, sai kisani sakinki din!" Shima yafada a tsawace "I hate you! You brat! I hate you!!" Tafada cikin qaraji hawaye na 6alle mata. sai kuma tafara daukar files files din table din tana jifanshi dasu kamar sabuwar kamu tana nannata I hate you din cikin kuka sosai. Be kare kanshi ba haka yatsaya yana kallonta zuciyarshi na bleeding, duk Kalmar ta daya na I hate you jinshi yake kamar sukar wuqa a zuciyarshi. Saida tagama watsar da kayan table din sannan tadawo kanshi tana dukanshi da hannu tana kuka sosai sai nannata Kalmar ta tsaneshi take. Sakin Jikinshi yayi tana dukanshi yana kallonta Yanajin kamar zuciyarshi zata tarwatse. Jiyake inama zai iya yin kuka da yayi yarage rada din dayake ji a zuciya Ganin abin nata bana qarewa bane yasashi Kamo kanta, yayi locking din la66ensu waje daya yashiga bata the hottest kiss ever...✍️ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 058 Waro dukkan idanunta tayi kamar zasu fado daga socket dinsu tana kar6ar the shock of her life. Jikinta ya mutu nan take kamar Wanda aka zarewa lakka, tayi baya baya zata fadi ya sa hannu daya ya tarbota ta qugu yasake mannata da Jikinshi yana kissing dinta kamar kura tasamu nama Jikinshi har rawa rawa yake. Sun kai minti daya ahakan, saudart kam bata iya misalta yanayin datake ciki don batama cikin hayyacinta. Ashraf kam wani irin yanayi ya tsinci kanshi, having the extra soft lips of the love of his life in his mouth is undescribable. Kissing dinta yake yana licking kamar yasamu tomtom shi kanshi yafara fita ahayyacinshi Ahankali ya fara cire bakinshi daga nata yana kallon fuskarta daya koma jaa kamar tomato. Kallon juna suke suna sauke numfashi ahankali tare kamar wadanda sukayi wasan tsere. Dukansu sun kasa yarda da abinda yafaru yanzu. Kallon juna suka cigaba dayi kowa na qoqarin daidaita numfashin shi. Saudart takasa yarda da abinda yafaru yanzu, she can't believe yau tasamu first kiss dinta, kuma da Wanda duk duniya babu Wanda ta tsana kamarshi. Wani ihu tafasa mai mugun qara Wanda saida Ashraf yasaketa babu shiri. Jada baya tayi ta mannu da bango tana qara fasa wani Qarar Wanda yafi na farko, jikinta sai 6ari yake. Nufota Ashraf yayi da niyyar yimata magana amma ganin ya tunkarota yasata taqarqarewa ta fasa wata Qarar Wanda saida ya toshe kunnuwanshi. Banko kofar office din akayi, Alhaji yafado ciki kamar an jefoshi sadeeq biye dashi dukansu a giggice da alamun ihunta sukaji suka shigo. Ganin saudart sukayi manne da bango tanata ihu shikuma Ashraf na daga can gefe hannayenshi Dade da kunnuwa. Da sauri Alhaji ya nufi saudart ya riqota Jin an riqota yasata fasa wata Qarar tana qanqame jikinta cikin fitan hayyaci. "Shalele! Shalele!! Nine... Meya faru? Open your eyes and look at me.. Daddy ne..open your eyes!" Inji Alhaji yana riqeta gagaam ganin yadda take kiciniyar qwacewa. "Shalele listen to me, daddy ne..daddy, please look at me" yafada yana rungumeta Jin kamar muryar daddy yasata dagowa ta dubeshi ganin shine din yasata qara qanqame shi tana kuka kamar zata shige cikinshi "Take me out dad! Ka fiddani daga nan" tafada cikin gunjin kuka. "Shalele..." "Please dad! Take me out" tafada tana qara qanqame shi "Ok..ok" inji daddy da duk ya rikice suka nufi kofar still tana maqale dashi sannan ya bude suka fita. Binsu da kallo sukayi har suka fita sannan ahankali sadeeq yajuyo yana kallon Ashraf, kallon tuhuma. Shikau Ashraf cizon le6enshi na qasa yayi yana runtse idanunshi da qarfi zuciyarshi na mashi wani irin zafi. "Me kayi mata?" Inji sadeeq yana cigaba da jifanshi da kallon tuhuma. Bude idanunshi dasuka rine yayi yana sauke numfashi mai nauyi har kana iya ganin yadda qirjinshi ke sama da kasa tacikin rigar shi. Jiyake inama zai iya kuka kamar yadda yaga saudart nayi yasan ko babu komai zaiji dan sauqi sauqi a zuciyarshi. Yasan yanzu beda wani chance kuma, maimakon ya gyara abubuwa gashi ya ida lalatasu. "Nace what did you do to her?" Inji sadeeq yana matsowa gabanshi. Juyamashi baya Ashraf yayi tareda dafa desk dinshi da hannu biyu Yanajin kamar ya dauke sadeeq da mari don da yasan yadda yakeji da bazaima fara tanka mashi ba. Abin ne yaba sadeeq haushi ganin magana yake mashi amma yawani juyamashi baya, hakan yasashi juyoshi da qarfi yana cewa "Am talking you junk!" Be qarasa maganar ba yaji an shaqeshi, kafin yasan meke faruwa harya mannashi da bango still shaqe da wuyanshi sai huci yake. Waro idanu sadeeq yayi yana kallonshi not believing what is happening sai qoqarin kwatar kanshi yake amma yakasa. Haryanzu qirjinshi sama da qasa yake sai motsa bakinshi yake amma wani Abu daya toshe mashi maqoshi yaqi barin maganar tafito. "She is.. My.. Wife" yafada da daddaya kamar mai cutar asthma Kusantoshi yayi har yana kusan hade fuskarsu "So... Fuck off" yafada yana sakinshi sannan yaja dabaya yana dafe gefen qirjinshi daya dayake ji kamar ana hura mashi wuta awajen sannan yajuya yafita cikin sassarfa. Sulalewa sadeeq yayi yana zama qasa yana murza wuyanshi don ba qarya ya shaqu, sai jujjuya wuyanshi yake don jinshi yake kamar ba nashi ba. ************************************************ Kasa gane kan saudart daddy yayi don tunda suka fito take kuka kamar ranta zai fita duk inda suka gitta sai an bisu da kallo. Dakyar yasamu suka isa motarsu yabude bangaren mai zaman banza ya turata ta zauna sannan yarufe shima cikin sauri ya zagayo yashiga mazaunin driver ya rufo ya tada motar yayi reverse suka fita daga company din gabadaya. Akan hanyar ma bata bar kukanba muryarta harya fara shaqewa, baqincikin da take ciki bazai ta6a misaltuwa ba, bakinta sai zugi yake don ba qarya yasha tsotsa, duk zugi daya dazaiyi saiya tunamata da abinda yafaru, saiya tunamata she just kissed her worst enemy hakan ba qaramin tsimata yakeba hakan yasa takasa tsaida kukanta duk rarrashi da magiyar da daddy ke mata. Daddy kau abin ba qaramin kulle mashi kai yayi ba, me Ashraf ya fadawa shalele daya rikitata har haka? Shidai normal ya taddasu bare yayi zargin wani abun. Kukanta ba qaramin rikitashi yakeba hakan yasashi qara speed ya nufi gidan shi direct. Hannu dafe da qirji yafito yana tsoma qafarshi duk inda yaga dama harya samu yafito. Motarshi ta nufa direct ya bude ya fada ciki ya rufo da qarfi ya maida kanshi kan seat din yana numfashi ahankali still hannunshi dafe da gefen zuciya. Ya Dade ahakan, saida yafara jin sauqin abinda yakeji sannan ya miqe zaune ya kunna motar shima yabata wuta ya fice daga company din cikin wani mugun speed Wanda saida duk aka bishi da kallo. Tuqi kawai yake amma badan kariyar Allah ba da komai na iya faruwa don tuqin ganganci yake sosai, zagi kau yashashi wajen mutane amma a banza don besan suna yiba. Ahakan ya qarasa gida yayi wani irin parking a tsakar hanya ya sauko ya nufi cikin gidan yana hada hanya. A falo ya zube qasa yana wani irin haki kamar zai mutu, hannunshi dafe da zuciya sai ambaton sunan Allah yake ko zaiji sauqin abinda ke damunshi Abu daya yasani, son saudart jarabta ce daga Allah kuma wataqila cutar Sonta zaiyi ajalinshi don dukda halin dayake ciki, soyyayarta qara farashi take a zuciyarshi, wutar soyyayarta qara ruruwa take a zuciyarshi. A bangaren saudart kau suna yin parking a parking space din gidan ta 6alle murfin motar tafito tayi cikin gidan dagudu. Saurin kashe motar Alhaji shamsu yayi shima yafito ya maramata baya yana qwalamata kira. Ina? Ko sauraronshi batayi ba ta haye sama ta bude dakinta tashige sannan ta maido kofar ta rufe harda saka sakata sannan ta sulale wajen ta cusa kanta tsakankanin cinyoyinta tana cigaba da kukanta cikin shaqaqqiyar muryarta. Duk bugun kofa da magiyar da daddy yake mata akan ya bude besata ta motsa daga inda take ba, kukanta kawai take yayinda kanta ke saramata kamar zai rabe gida biyu. Dakyar ya iya tashi daga inda ya jibge tundazu, hannunshi still a wuyanshi yana murzawa. Tunda yake be ta6a ganin Ashraf acikin irin wannan yanayin ba, duk karfinshi kasa qwatar kanshi yayi Wanda yasan da zai kara minti daya be sakeshi ba da tuni ya margaya. Nufar qofa yayi ahankali still yana jujjuya wuyanshi dayake jin dole yaje ganin mai gyara don Yanajin akwai qashin daya goce😆 Fita yayi shima yanufi motarshi dafeda wuya sannan yashiga ya tada motar yanufi gidan Ashraf don yasan yadda yafita cikin wannan yanayin dole asamu matsala. Direct gidan yanufa, tun a yanayin parking din Ashraf yasashi tabbatar da hasashenshi. Saurin kashe motar yayi ya sauko sannan yanufi ciki dagudu. Afalo ya taddashi zube bisa rug din tsakiyar falon. Dasauri ya nufeshi tareda dagoshi. "Ya sallam" yafada jin jikin Ashraf rau kamar garwashi. Ahankali ya taimaka mashi ya kwantar dashi akan three seater din falon sannan ya tsuggunna gabanshi "Ashraf? Ashraf are you ok?" Yafada cikin tsananin damuwa Dakyar Ashraf ya bude idanunshi wadanda sukayi nauyi ya kalleshi. "Sorry ok? Zan kira doctor yanzu ok?" Yafada yana murza hannunshi daya Ahankali Ashraf ya motsa bakinshi alamun zaiyi magana, hakan yasa sadeeq saurin matsowa saitin bakinshi "She.. Hates me" yafada cikin wata iriyar murya Wani mugun tausayinshi sadeeq yaji ya lullubeshi "Shhhh it ok, bata tsanekaba kaji?" Yafada cikin sigar lallashi "She do... Ta tsaneni" yafada yana lumshe idanu "Shhh it ok, karka sake magana ok? Bari nakira Dr" Nan yafiddo wayarshi yakira doctor din. Cikin dan qanqanin lokaci Dr din ya qaraso, nan yashiga duba Ashraf sadeeq na gefenshi yana kallon amininshi cikin tausayawa. Saida yagama dubashi sannan ya umarci sadeeq yakamashi sukaishi daki. Haka suka kamashi su biyu suka kaishi daki suka kwantar dashi sannan aka daura mashi drip akayi mashi allurar barci sannan Dr ya rubuta ma sadeeq wasu magunguna yabashi akan su za'a bashi idan ya farka. Kiran messenger sadeeq yayi ya bashi umarnin yasiyo magugunan dazaimashi text yanzu yakawo gidan A.A Sannan yayi mishi txt din sunayen magungunan yakoma ya zauna gefen Ashraf daketa barci yana sauke numfashi ahankali ya kama hannunshi guda yana murzawa cikin tsananin tausayinshi...✍️ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 😆😆😆 gaskiya jiya kun bani dariya musanmman yan AUREN KWANGILA NOVEL GROUP. Team S.S duk kurin da cika bakin? Yada saurin karaya haka? Gaskiya bakuyiwa S.S adalci ba da kuke hijira kuna komawa A.A, tace agayamaku tana tsananin fushi daku😡 kuma zaku gane shayi ruwane biredi soso ne😠 059 Kiraye kirayen sallar azahar yasata dago kanta daga gwiwarta a inda take zaune bakin kofa tunda tashigo. Ta Dade da barin kukan saidai na zuci datake. Jiki ba kwari tamiqe tana dafa bango ciwon kanta na tsananta. Da bin bango ta isa toilet ta daura alwala sannan tafito tana takowa ahankali. Shimfida sallayarta tayi ta gabatarda sallar zuhr dinta sannan takoma ta zauna ta jingina da jikin gadon ta tareda lumshe idanu. Abubuwan dasuka faru yau tun daga zuwansu company har yanzu yashiga dawomata a kwanya. Wani murmushin takaici ya su6uce mata Lallai saita gwadawa A.A ba kowa ake takawa kuma ya takuba. Yayi kadan yayi controlling din life dinta, dolene yasake ta koda kuwa sai an hada da shari'a. Bazata iya da irinshi ba, bazatama iya misalta hakan ba ko da wasa. She hate him with passion don haka maganar zaman aure dashi ma bai tasoba kwata kwata. Bubbugar kofar dataji ya katse mata guntun tunaninta. Kallon saitin kofar tayi batareda tace komaiba "Shalele?" Taji muryar daddy a tausashe "Please open the door for daddy, ki bude kinji yar leleta?" Shiru tayi kawai tana kallon kofar tanajin kanta cikin wani yanayi "Kinga lokacin sallah yayi, please ki bude, ina cikin damuwa sosai, do you want daddy to be sad?" Yafada cikin sigar lallashi. Girgiza mashi kai tayi kamar yana ganinta sannan ta yuqura ta tashi dakyar ta nufo kofar. Jin motsinta kusada kofar yasashi dakatawa da rarrashi dayake mata yana kallon kofar. Murda handle din yaji anyi sannan aka bude kofar saudart ta bayyana fuskarnan fayau. Saurin shiga yayi yana rungumeta Itakuma kamar abinda take jira kenan saita fashe da kuka dakusashiyar muryarta. Bubbuga mata baya yafara yi cikin sigar rarrashi yana cewa "Shhhh ya isa hakanan, please stop crying kar wani ciwon yakamaki" yafada yana nufar gadonta daita sannan ya zaunar daita ahankali Itakuma ta Dora kanta a kafadarshi tana sauke ajiyar zuciya akai akai "Am so sorry shalele, duk nine silar komai" yafada asanyaye Girgiza mashi kai kawai ta iyayi hawaye na gangaro mata. "Kiyi hqr ki fada min me yayi miki, please" yafada yana shafar kanta Shiru saudart tayi tana sauke ajiyar zuciya ahankali, tasan ko giyan wake tasha bazata ta6a fadamashi abinda ya faruba. "Kinji shalele ta, tell me please" "Dad cewa yayi bazai sakeniba, wai babu hujjar yin haka, Dad I hate him, ko ganinshi banason yi" ta qarashe maganar tana matsar qwalla. "It ok kinji? Babu Wanda zai tilasta miki zama dashi, abaya na tilasta miki yin hakan saboda son kai irin nawa amma yanzu hakan bazai ta6a maimata kanshi ba kinji? Kuma munada kwakwarar hujja na warware auren nan ko agaban kuliya ne, so relax, aurenan kamar anyi angama ne kinji?" Qanqame shi tayi cikin farinciki tana kada kai cikin farinciki. Haka yaita tausarta da kalamai har zuciyarta ta ida yin sanyi sannan ya tilasta mata tadanci abinci yabata magani tasha sannan yasata ta kwanta yajamata bargo tayi pecking dinta a goshi sannan yafita yabar dakin yana jawomata kofa. A bangaren Ashraf kau bashi ya farkaba sai bayan la'asar. Ahankali yafara bude idanu, tun yana gani Dishi Dishi har ganinshi ya washe idanunshi suka sauka a fuskar sadeeq dake zauna gabanshi. Ganin ya bude idanu yasa sadeeq saurin gyara zaman shi yana mashi sannu murmushi a fuskarshi. Yunqurin tashi yayi yana yatsina fuska, dasauri sadeeq ya taimaka mashi ya zauna yasamashi pillow a bayanshi don samun comfort. "Sannu, ya jikin? Ina kema ciwo?" Inji sadeeq Girgiza mashi kai kawai yayi Alamun babu tareda lumshe idanu "Ok Bari na hadoma ko tea ne kasha sai kasha magungunan ka" yafada yana fita batareda yajira amsarshi ba. Binshi da kallo yayi harya fita sannan ta sauke nannauyan ajiyar zuciya. Kallon hannunshi yayi yaganshi da cannula da alamun saida aka qaramashi ruwa. Hannu yasa ya shafo kanshi yana furzar da huci Abinda yafaru dazu yafado mashi arai. Tunawa yayi da yadda yake sarrafa tausassan la66anta masu kamada auduga da wani scent din da bakin ke fiddawa na mint. Murmushin gefen baki yayi yana cizon le6en qasa in a naughty way. Tunawa yayi da lokacin daya cire bakinshi daga nata, irin kallon datake mashi, kallo mai cikeda shock da giggita. Fararen idanunta data ware akanshi da guntun bakinta da yadan bude in shock. Wani murmushin yasaki yanzu mai sauti yana daukar filon kusada shi tareda rungume shi aqirji Kissing her feel soo good, damn good. Tunawa yayi da yadda ta qanqame jikinta tanata rusa ihu, yar dariya yasaki yana cewa "matsoraciya" Haka yaita zabga murmushi shi kadai kamar wani shabiyu sha uku har sadeeq yashigo besaniba. "Inyee! Wannan washe haqoran duka menene?" Inji sadeeq cikin sigar tsokana Dagowa yayi yana kallonshi tareda zabga mashi harara still fuskarshi dauke da murmushi. Qarasowa yayi da tray din tea din tareda direwa a bedside locker ya zauna kusada shi yana cewa "Wato ni inacan ina faman hada maka tea harda qonewa amma kai kananan kana dariya kai kadai ko? Tell me what's funny" yafada Yanajin dadin yanayin daya ganshi "Am..in..love" yafada kamar mai koyon magana yana qara rungumar pillon Waro idanu sadeeq yayi cikin mammaki, dukda yaga alamun son saudart a idanunshi be ta6a tunanin zai furta dawuri hakaba Tsalle yayi yadawo kusada shi kan gadon "Maimata inqaraji dan uwa, kamar ban fahimci zancenkaba" yafada cikin sigar waqar sambisa. Murmushi Ashraf yasaki mai tsadan gaske yana dan mintsinin sadeeq Wanda har saida yadan saki qara. "Yes am in love......I love her" yafada cikin shauqi "Wayyo dadi kasheni! Dunkum din abokina is in love! Yeah! Oya Jo soapy soapy, tashi muyi rawar soapy, tashi muyi rawar soapy, soapy soapy!" Yafada yana miqewa Yana rawar soapy din. Wurga mashi pillow Ashraf yayi yana dariya sosai "Kai dan iska ne ko?" Yafada yanada dariya "Yan iska ba, inyee gaskiya saudart ta ciri tuta, wannan washe baki haka? Rabon da naga kana irin wannan dariyar har mantuwarma ta mance" Dariya Ashraf yasakeyi yana girgiza Kai "Kaifa dan iska ne" "Na yarda, wato shiyasa dazu aka kusan sheqeni ko? Haryanzu wuyana ciwo yake na rantse" Dariya Ashraf yayi mashi yana cewa "Maganin mai shiga sabgar mata da mijinta kenan" Bude baki yayi yana toshe wa "Inyee ni kake fadawa haka? Lallai Bari na koma gefe naita kuka" Dariya Ashraf yayi kawai sannan yadan girgiza Kai yanayinshi na chanza wa "Meye kuma?" "Ta tsaneni" yafada cikin wani yanayi "A'a bata tsaneka ba" "Ta tsaneni kaima kasani" "Amma ai kai k koyamata tsanar ka din, why not ka koyamata sonka?" "How?" "By showing her love tsantsa" Girgiza Kai yayi "Banjin zata saurareni" "Zata saurareka mana, kawai all you need to do is ka sauke wannan shegen girman kan naka dabeda amfani ka yaqo zuciyarta" Dariya Ashraf yayi yana shafa gemunshi "Nikuma banason abinda zai ta6a Mani jin kai na, yaya za'ayi kenan?" Harararshi sadeeq yayi sannan yace "To saika cika form din wahala don kai dashi kun qulla abota kenan" Dariya kawai yayi bece komai ba "Yanzu sha tea din kasha magungunan" Babu musu yaziro kaffafun kasa ya amshi tea din yana sha ahankali "Ummy fa? Yakamata ta sani" inji sadeeq Dagowa Ashraf yayi daga kofin bakinshi yana kallonshi "No" "No? Sokake taji abakin wasu?" Inji sadeeq "Fushi zatayi kasan halinta, insha Allah ni dakaina zan gayamata amma sai komai ya lafa" "Komai ya lafa kamar ya?" "Sai saudart tadawo gareni" "Amma baka gudun taji waje?" "Wazai gayamata? Saudart bazata gayamata ba I know, tsohon ta ma bazai faraba, nima bazan fadaba saidai ko kai zaka fadi" "Hmm to Allah ya kyauta, ga magungunan kasha ka rama sallolinka insamu inkoma gida." Saida yasha magungunan shi sannan ya rama sallolinshi sannan yadawo ya zauna suka dan ta6a fira sannan sadeeq yatafi bayan yagama quleshi da tsokana. Dawowa yayi ya zauna kan daya daga cikin kujerun falon yana kishingidawa murmushi kwance a fuskarshi. *I love you* *I love you so much... SAUDART*...✍️ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 060 Ranar zaune yakusan kwana, sai saqa da warwara yake na yadda zai 6ullowa saudart, wani abun har mammaki yake bashi don ko a mafarki be ta6a tunanin zai ware wani kaso cikin lokutanshi masu amfani ya asarar dasu akan tunanin mace ba amma gashi har hana idanunshi barci yake don tunanin yadda zai 6ullomata. Washegari sai 11:00am yafarka saboda Rashin samun isashen barcin dabeyiba jiya Wanda saida yayi sallar asuba sannan barcin ya daukeshi. A gaggauce ya fada toilet don yin wanka da brush. Fitowa yayi bayan wasu yan mintuna ya shirya cikin wasu ash colour suit ya feshe Jikinshi da turare. Fitowa yayi yana gyara necktie dinshi yanufi motarshi. Shiga yayi ya tadata sannan yafice daga gidan. Opposite din bakery dinta ya parka motarshi yana kallon mutanen daketa karakaina a wajen. Ya Dade cikin motar yana kallon wajen batareda yasan me ya kamata yayi ba. Can yaga wani yafito daga bakery din da alamun daya daga cikin ma'aikatan ne. Saurin bude kofar yayi ya fito ya tsaya gefen motarshi yana kallon mutumin dake qoqarin ketaro titin zuwa bangaren da Ashraf yake. Saida ya qetaro yana niyyar wucewa Ashraf yayi saurin dakatar dashi. "Ehmm barka" inji Ashraf yana dakatar dashi Juyowa mutumin yayi yana kallonshi da alamun Rashin ganeshi sannan yace "Barka dai" Hannu Ashraf yabashi sukayi musabaha sannan yace "Erm madam nanan kuwa? I mean saudart" Girgiza Kai mutumin yayi yana cewa "A'a rabonta da Bakery dinnan tun Friday, lfy?" Murmushi Ashraf ya sakarmashi "No lfy lau, dama aikoni akayi wajenta ne, amma idan babu damuwa kozan samu number ta?" Kallon Rashin yarda mutumin yashiga binshi dashi Wanda yasa Ashraf jin duk ya tsargu da kanshi. "A'a banida numberta, idan order kukeso ko wani abun kana iya shiga ciki kasamu P.A dinta amma babu mai number ta" yana kaiwa nan yawuce yana waiwayenshi don hakanan yaji be kwanta mashi ba. Shima Ashraf binshi yayi da kallo harya wuce sannan yasa hannu ya shafi kanshi yana hurar da iska. "This is gonna be tough" yafada yana saka hannayenshi a aljihu yana qara kallon bakery din. Ganin tsayuwar batada amfani yasashi shiga mota yabata wuta yabar wajen. Direct company dinshi yawuce, anan yayi assigning din wani daga cikin guards dinshi kan ya cigaba da saka idanu a bakery dinta duk sanda yaganta yayi alerting dinshi. Yakuma yi assigning din wani a unguwarsu akan yasaka idanu a gidansu saudart duk sadda yaga fitowarta yayi alerting dinshi. Komawa yayi jikin kujera yana jujjuyawa ahankali yana jinshi empty, Yanajin kamar yarasa wani 6ari nashi mai matuqar muhinmmanci. Ranar babu wani aikin dayayi bayaga tunaninta, abin har tsoro yake bashi don gani yake kamar qaramashi Sonta ake akowace daqiqa mai wucewa. Wasa wasa kwana uku kenan da assigning din masu saka ido akan saudart amma babu wani labari mai dadi. Kullum amsarsu daya ce, basuga fitowarta ba. Ashraf yashiga cikin tsananin damuwa, damuwarshi dayace anya lafiyarta qalau kuwa? Idan yayi la'akari da yadda suka rabu a haduwarsu na qarshe sai yaga kamar ba lafiya. Duk yabi ya susuce, kodayaushe wayace a hannunshi yana jiran akirashi ace anga fitowarta amma shiru, idan kuma yagaji shi yabuga amsar duk dayace, babu ita. Duk wannan budirin da'ake sadeeq na gefe ya zuba mashi idanu, don shi abun ya daina bashi mammaki yanzu saima takaici. Yaya za'ayi ace kana tsananin son ganin mutum kuma kasan inda yake amma ka kasa zuwa ganinshi saboda wani dalili naka na banza? Hakan yasashi bude kwandon shara ya sakashi ciki ya rufe ya cigaba da harkar gabanshi acewarshi idan kaji ana rakani kashi to ba zawo bane. Yau Saturday babu aiki don haka yau gidansu ya wuni yana hutawa. Kwance yake yana waya murya qasa qasa da alamu da masoyiyarshi yake wayar. Da sallama Ashraf yashigo looking so pale, kallo daya zakayi mashi kasan yana cikin damuwa don duk yazama wani iri, gashi nan dai. Dagowa sadeeq yayi ya amsa sallamar sannan ya cigaba da amsa kiranshi hankali kwance. Samun kujerar dake dakin Ashraf yayi ya zauna ya jingina da kujerar yana dafe kanshi dake dan Sara mashi. Sadeeq na ankare dashi amma ya share yacigaba da wayarshi batareda ya kulashi ba, shima Ashraf bece komai ba sai lumshe idanun dayayi hannu dafe dakai yana sauraron wayar sadeeq. Ada idan yaganshi yana waya irin haka has yake bashi yana yi mashi kallon marar aikin yi amma yanzu jiyake dama shine ke wayar da muradin ranshi, abar kaunarshi, Saudart. Haka yaita jiranshi harya gama wayar batareda ya katseshi ba ko yanuna 6acin ranshi akan shareshin dayayi hasalima kalaman sadeeq din yake sauraro yana mammakin ina ya iya wadannan kalamai haka. Dagowa sadeeq yayi yana kallonshi sannan yadan ta6e baki "Ya dai? Naga you look pale" Bude lumsassun idanunshi yayi ya kalleshi sannan ya maidasu ya rufe batareda ya tanka mashi ba. "Mtcheew dan wahala kawai" inji sadeeq yana daukar remote zai kunna kallo Bude idanunshi yasakeyi ya kalleshi sannan cikin sanyi yace "Please banson hayaniya karka kunna" Wani kallon uku saura kwata sadeeq yayi mashi sannan yace "Dalili? Dakinka ko nawa? Kaji qarfin hali" Sauke ajiyar zuciya Ashraf yayi yana dan rolling din idanu "Sadeeq dama haka kake? Dama kai maqiyina ne bansaniba? Ni atunanina idan ina cikin damuwa saika fini shiga damuwar amma am mistaken" Sadeeq da tunda yafara magana yake antayamashi harara yaja tsaki yace "To ni me zan maka? Ashraf taurin kanka yasa nafara tantamar da irin qashin da'akayi namu kan akayi naka, kana wahala zuciyarka na wahala amma kasan yadda zaka kawo qarshen wahalar ka kasa, saboda wani banzan dalili naka can" yafada cikin jin haushi "But am trying ko? Duk hanyar danasan zan ganta inabi kaima kasani" yafada kamar zaiyi kuka "Nidai tawa ta sameni, dafarko ina zaman zamana hankali kwance banida damuwar komai amma tunda tashigo rayuwata ta sauya komai, gashi yanzu ta tafi tabarni da jinya gashi kai da nake tunanin zan dan samu sauqi a wajen ka kaima ka juyamin baya" yaqarashe zancen yana dafe Kai. "Mtcheew kai ka siya ai, muddin bazaka sauke girman Kai ba bakaga komai bama, ita saudart din allurace da zata bace bakasan inda zaka ganota ba? Kasan inda zakaje ka ganta kawai baka shirya ganinta bane" yafada yana maida hankalinshi kan kallon dazai kunna "I can't, bazan iya taka gidan mutumin nanba, zan iya zuwa koma inane inganta amma banda wannan gidan" inji Ashraf yana dan huci. "Why? Ai ba wajen shi zakajeba, wajen Matar ka kaje, ni banga wani Abu aciki ba" "Ni nagani, the first and worst mistake dina shine sanyota acikin deal dina, da bansata aciki ba da ko saninta banyiba bare har wannan masifar ta hayeni" inji Ashraf yana cije le6an qasa. "Yes Ashraf, Allah ne ke nuna mana kurenmu, yakuma nuna mana aure ba abin wasa bane, dukda rama sharri da sharri ba haramun bane anfison a ramashi da alhairi, amma mu saimuka nemi ramawa fiyeda yadda akayi mana, muka kuma saka Wanda bata jiba bata ganiba kuma muka dauki abu mai martaba irin aure muka maidashi wasa shiyasa muka rufta aciki" inji sadeeq shima cikin sanyi. "And you warned me, ka gargadeni akan hakan amma ni idanuna sun rufe fansa kawai nakeson dauka gashi yanzu muntashi ba wan ba qanin saima masifar danake ciki, wlh danasan yadda zan cire Sonta a zuciyata danayi hakan ko na huta, kullum kamar qaramani Sonta akeyi, with every passing minute, second, breath jinake kamar qara huramani wutar Sonta ake, am helpless, bansan yaya zan tunkareta ba, bansan Kalmar dazan yi amfani dashiba, bansan komai ba, all I know is I love her, I so much love her" yafada cikin wani irin yanayi mai ban tausayi. Cikin tausayawa sadeeq ya dawo kusada shi ya zauna tareda dafa kafadarshi "It ok bro, insha Allah komai zaizo da sauki, ka riqe addu'a kuma kaima kayi trying best dinka, ka ajiye komai kayi fighting for your love, insha Allah saudart alhairi ce a rayuwarka shiyasa tun farko ka sakota aciki, insha Allah zakayi dariya watarana.." Ringing din wayar Ashraf ce ta katsesu. Saurin saka hannu yayi ya fiddo wayar jin ringing tone din Ummy ne Wanda contact dinta kadai yasama tone din. Janye hannunshi sadeeq yayi daga kafadarshi yana kallonshi yayinda shikuma ya daga ya kara a kunne yana sallama. Ganin yanayin fuskarshi na chanzawa yasa sadeeq kuramashi idanu da alamun tambaya "Ummy.. Lafiya?" Inji Ashraf cikin Rashin fahimta. Bansan ko me ummin tace ba sai gani nayi wayar takawo haske alamun an katseta. Ahankali ya sauke wayar daga kunnenshi fuskarshi dauke da ayar tambaya. "Lafiya?" Inji sadeeq daketa kallonshi tundazu "Ummy ke Neman mu" Ashraf ya amsa absentmindedly tunani kala kala na yawo a qwanyar shi. "Meyasa?" Inji sadeeq Miqewa Ashraf yayi "Muje amma she don't sound normal". Shima miqewan yayi ya Dora t-shirt akan singlet dinshi yasaka takalmi suka fita. Sallama sukayima umman sadeeq dake falo akan zasu dan fita su dawo sannan suka fice da motar Ashraf. A harabar gidansu Ashraf sukayi parking suka fito. " sadeeq wani Abu na faruwa, inaji a raina something bad is happening" inji Ashraf yana kallon hanyar cikin gidan "Babu komai insha Allah, mushiga nasan babu komai sai alhairi" inji sadeeq cikin qarfafa mashi gwiwa. Haka suka jero kamar yadda suka saba sadeeq ya Danna door bell sukayi jigum suna kallon kofar. Bayan yan daqiqu sai gani sukayi an murda kofar an bude. Baby ce ta bayyana fuskarta adagule alamun something is happening. Saurin qaqalo murmushi tayi tana kaucemasu tana gaishesu. Yau babu Wanda yasamu halin amsawa saboda fargaba don haka shiga sukayi atare suna sallama. A falo suka hango Ummy zaune kan one seater fuskarnan babu fara'a tadago tana amsa sallamarsu tana masu wani irin kallon daya kada hanjin cikinsu. A sanyaye suka qaraso suka zauna qasan tsadadden rug din dake tsakiyar falon suka sunkuya kai. Itama baby dawowa ciki tayi ta zauna kan kujerar dake nesa dasu ta zauna tana kallonsu Tare suka gaidata cikin sanyi kallo daya zakayi musu kasan suna cikin fargaba sosai. Kallo tashiga binsu dashi batareda ta amsaba hakan yasasu sunkuyar dakai kasa "Ina matarka?" Ummy ta jefo masu tambayar a bazata. Hakan yasa duk suka dago kai gabadaya suka kalleta sai kuma suka kalli juna. Maida kallonsu suka sakeyi kanta sannan Ashraf cikin inda inda yace "Ni?" Batace komai ba sai tsareshi da idanu datayi Wanda hakan ba qaramin sanyaya mashi jiki yayiba. Sunkuyar dakai yayi sannan ya bude baki yace "Tana gida" "Ka kirata tazo yanzu" tafada commandly Dagowa yayi yasake kallonta yanason karantar yanayinta "Ummy.. Wayarta a kashe.. Take" Dan murmushi Ummy tasaki mai kamada na takaici sannan ta kalli baby tace "Kirata" Jiki a sanyaye baby ta Ciro wayarta ta kira number saudart sai gashi tashiga suna kuma ji saboda hands free tasata. Har tayi ringing dinta tagama ba'a dagaba. Maido kallonta Ummy tayi kansu sukayi saurin sunkuyar dakai. "Ina matarka Ashraf!" Gamm ya runtse idanunshi tashin hankali qarara a fuskarshi. Tunda yake Ummy bata taba kiranshi da sunanshi ba sai yau. Nan take zuciyarshi tafara bugawa abnormally gumi na tsatsafo mashi. "Nace where is your wife!!" Ummy ta daka mashi uban tsawar da bata ta6a yi musu ba. Nan take baby tafashe da kuka tana toshe bakinta shikuma Ashraf yadago yana kallon Ummy idanunshi sunyi jajur. "Ummy.." "Shut up!" Ta katse sadeeq din a tsawace "Kabari nadawo kanka tukun" tafada a fadace "Now answer me, ina matarka?" Ta maida akalar tambayar kan Ashraf. Bakinshi yabude zaiyi magana amma yakasa sai 6ari da bakin keyi. Be Ankara ba yaji an wurga mashi takardu a fuska sun watse a gabanshi "What is this?! Nace meye wannan!" Ta tambaya a tsawace Bin takardun yayi da kallo nan take Jikinshi yadauki rawa...✍️ Ummin fasihu ce🧚‍♀ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Aslm fans🙋🏻‍♀️ sorry kunjini shiru kwana biyu, wayatace tasamu mtsl😟 amma yanzu komai yayi daidai. Masu cigiya, masu kira da masu text duk nagode da qauna😍😇 Allah yabar zumunci🤲 Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) Bin takardun yayi da kallo nan take jikinshi yadauki rawa. Shima sadeeq takardun yake kallo fuskarshi fall mammaki zuciyarshi na bugawa. "Nace meye wannan!!" Suka sakejin muryarta tsakar kansu. Kasa dagowa Ashraf yayi daga kallon takardun sai binsu yake da kallo kamar yau yafara ganinsu. "Ummy... we can explain.." inji sadeeq cikin kwantar da murya "Explain? Kenan wannan gaskiya ne?" Tafada cikin sanyin murya tana kallonsu most especially Ashraf daya kasa dagowa, idanunshi sun kada sosai "Yes ummy...amma.." "Ya sallam!" Inji ummy tana komawa dabaya ta zauna akan kujera jagwab tana dafa kai, tashin hankali qarara a fuskarta. Da sauri Ashraf ya rarrafa gabanta yana kamo hannunta data dafe kanta dashi "Ummy?.. ummy am sorry, am so sorry" "Sakarmin hannu" tafada cikin sanyin murya. Qara qanqame hannun yayi yana cewa "No ummy, Dan allah kiyi haquri ummy, please" yafada muryarshi na rawa rawa, jiyake kamar yafashe da kuka ko zai samu sauqi. Idan akwai abinda ya tsana duniyarnan to 6acin ran ummy ne, kullum cikin taka tsantsan yake wajen ganin ya faranta mata rai amma yau tashin hankali da 6acin ran dayake hangowa a idanunta yasashi jin kanshi so guilty. Baby kau na gefe tana sheshekar kukan dataci, bata ta6a ganin ummy da yaya a wannan yanayin ba, hakan yasata jin wani iri ga baqin labarin da hankalinta yakasa dauka daya riskesu. Shima sadeeq rarrafowa yayi kusada ashraf cikin sanyin jiki. "Ummy munyi kuskure amma Dan allah ki sauraremu, please" yafada shima kamar zaiyi kuka. "Let go of my hand" ummy tasake cewa in a cool mode wanda hakan yaqara tada hankalin Ashraf "Ummy.." Fizge hannunta tayi a fusace daga riqonshi sannan ta miqe tsaye tana nuna masu kofa da yatsa. Tashi baby tayi tayi sama dagudu tana toshe bakinta cikin qoqarin hana kukan daya kufto mata fitowa. "Out!!" Tafada a tsawace. Kasa ko motsawa Ashraf yayi daga kneeling position dinshi, jikinshi yayi liqis jiyake kamar babu sauran lakka ajikinshi. "Nace kufita and never come back again! Get out!" Tafada cikin qaraji. Hakan yasa sadeeq saurin tashi don yasan halin ummy idan ranta ya 6aci, dawuya kaga 6acin ranta amma idan ranta ya6aci batada kyau. Kamo ashraf dake durqushe haryanzu yayi dakyar suka miqe. Dago kai ashraf yayi ya kalleta da idanunshi dasuka yi jaa, siraren jijiyoyi jajjaye duk sunfito akan farin idanun. "Ummy am.." Daga mashi hannu tayi sannan ta nunamashi kofa. Babu musu suka juya su biyun kowanne kamar zakaran da aka tsoma cikin ruwan zafi suka fita. Komawa ummy tayi ta zauna tana dafe kai zuciyarta a jagule. Cikin mutuwar jiki kowannensu ya kama murfin motar yabude yashiga. Tada motar sadeeq yayi sannan yabata wuta suka fita daga gidan. Tafiya suke amma babu mai cewa uffan kuma babu mai niyyar maganar, kowanne da tunanin daya addabi ruhinshi. Ahaka suka isa gidan Ashraf din, ko gama daidaita parking din beyiba Ashraf ya 6alle murfin motar yafita. Binshi da kallo sadeeq yayi sannan ya ida gyara parking din shima yafito. A falo ta taddashi kwance bisa kujera two seater, kanshi akan hannun kujera daya kaffafuwanshi akan daya sun sauko qasa, hannu daya dafe da kai yayinda idanunshi ke a lumshe. Dauke kai sadeeq yayi yawuce dining area, yabude fridge din wajen taciro gorar ruwa da cups yadawo cikin falon. Zama yayi kan kujerar dake gefen ashraf sannan ya tsiyaya ruwan a cup sannan yayi tapping din kafadar ashraf. Bude idanunshi yayi dakyar ya dago ya kalleshi yaga ruwa yake miqomashi. Maida idanun yayi ya rufe batareda yako motsaba. "Kasha Ashraf, you'll feel better" inji sadeeq a tausashe. Shiru yayi kamar bazai motsaba saikuma ya bude idanu ya miqe zaune ahankali ya miqa hannu ya amsa cup din ruwan ya kafa kai. Saida yashanye sannan yasake miqama sadeeq ya amsa yasake cikawa yabashi ya amsa yaqara sha sannan ya ajiye cup din kan stool din gefen kujerarshi yakoma ya kwanta. Ajiyar zuciya sadeeq ya sauke sannan yace "Ashraf?" Banza yayi dashi "Ashraf katashi, we need to discuss this" A kwancen dayake batareda ya bude idanuba yace "Babu abun tattaunawa anan sadeeq" "Ofcourse akwai, dole musan wa ya gayawa ummy wannan abun" Murmushin gefen baki yayi wanda shikadai yasan yayi abinshi "Ni dakai munsan wanda yafada, meye na wahalarda kanmu? Bansan har haka tadauki abinba, telling my mother without my consent?" "Saudart? No bazata iyaba" inji sadeeq Shiru ashraf yayi besake cewa komaiba "Ashraf.." "Dan allah kayi haquri ka kyaleni, please.. i need to be alone..please" yafada yana dafe kanshi. Shiru sadeeq yayi yana kallonshi, yasan yadda yakeji kuma ya tausayamashi, komai sai juyemasu yake from normal to abnormal. Yasan yadda suke da ummy, yasan dole abin yayi affecting dinshi sosai. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya miqe yana cewa "Ok, zanje gida amma please take it easy on yourself" Bece komaiba kamar yadda be bude idanunshi ba. Dafa kafadarshi yayi yana dan murzawa "Be strong" yafada cikin qarfafa gwiwa sannan yajuya yafita. Ahankali ya bude idanunshi bayan yaji fitarshi ya saukesu a p.o.p din falon Yau ummy ke fushi dashi? Yau ya 6atawa ummy rai? Garin yaya be ta6a tunanin wadannan abubuwan zasu bayaba tinda farko? Yana iya jurar komai amma banda fushin ummy, bazai iya jurewaba samm. ******************************** Driving yake tunannuka kala kala na yawo akanshi. Haryanzu yakasa yarda cewa Saudart zata iya gayawa ummy komaiba, yanaji ajikinshi ba ita bace. Karya motarshi yayi awani round about ya dauki hanyar gidansu Saudart. A opposite din gidan yayi parking sannan yafito yana kallon gidan. Tsallakawa yayi yazo bakin gate din yafara bubbugawa. Saida ya bubbuga sau hudu sannan yaji motsi daga ciki. Tsayawa yayi yana kallon yadda karamar kofar gate din ke motsi alamun budewa akeyi sannan kofar ta bude fuskar maigadin ta bayyana wanda kallo daya zakamashi kasan buzune. Murmushi sadeeq yayi yana miqamashi hannu yana mashi sallama. Shima miqamashi hannun yayi yana amsawa yana mashi kallon rashin sani. "Erm.. dan allah ko madam nanan? Saudart nake nufi" "Eh yananan, lfy?" Inji buzun cikin gur6attacciyar hausanshi Murmushi sadeeq yayi "Eh lfy lau, dan allah kamin sallama daita, kace sadeeq ne, abokin mijinta" Kara karemashi kallo buzun yayi sannan daga bisani yace "To..to, amma ki tsaya nan bari na fadamashi, ki tsaya" saiya rufe kofar sannan yashige ciki don sanarda madam saudart. Zaune take a falo kan one seater ta doro kaffafunta a kan kujerar tana filing din akaifunta na hannu, kanta dauke da earphones dinnan da ake dorawa akai tana sauraron cool music cikin low volume. Kallo daya zaka mata kaga tadan fada, ga hasken data qara wanda hakan yaba fatarta damar fitowa sosai cikin blue black din roba gown din dake jikinta. Sallamar maigadin dataji yasata dagowa daga abinda take. Amsawa tayi cikin fara'a, duk kwakwarka baka iya gane damuwarta don allah yayita mai fara'a da yawan murmushi. "A'a? Sannu mallam audu, kina lfy?" Tafada cikin sigar tsokana. Washe baki yayi yace "Wlh lfy lau hajiya, barka da hutawa" "Barkanmu dai, wani abu kikeso?" Tasake tambayarshi cikin yanayin maganarshi fuskarta daukeda murmushi. "A'a hajiya, kayi baqo ne" Dan daga gira daya tayi "Baqo? Waye?" "Wai abokiyar maigidanki ne, wai saddiqu" Dan ware idanunta tayi "Sadeeq?" "Eh" "Shi dawa?" Ta tambaya still idanunta aware. "Nidai ita kadai nagani" Ajiyar zuciya ta sauke "Yana ina yanzu?" "Tana shan waje aradu, cewa nayi tajira in fadamaka" "Ok..ok, kagane? Kaje kashigo dashi ganinan tafe" "To angama" yafada yana fita don aiwatar da yadda tace. "Sadeeq? Meya kawoshi?" Tambayar datayiwa kanta kenan. Tashi tayi ta tattara tarkacenta ta haura sama tana cire earphones din kanta. Doguwar hijabi kawai tazira ta zura takalmin soso sannan ta dauki wayarta tafito tana addu'ar allah yasa takardarta yakawo mata. Tun daga nesa ta hangoshi zaune kan farar kujerar roba kusada parking space wata empty kujerar na facing dinshi. Dauke kai tayi ganin shima ya dago yana kallonta ta qaraso wajenshi ta tsaya daga dan nesa dashi tana mashi sallama. Cikin fara'a ya amsa yana cewa "Sannu da fitowa *Mrs A.A*" Jin sunan tayi wani banbarakwai amma saita basar tace "Yauwa sannu" Nunamata kujerar gabanshi yayi yana cewa "Bismillah mana" Itama kallon kujerar tayi kamar yanzu tasan daita sannan ta dauke kai tana cewa "No need, hakanma am ok" Miqewa shima yayi yana cewa "in that case nima bari na tashi yadda zamufi fuskantar juna" Kauda kai tayi batareda tace komaiba "Kin wuni lfy?" Yafada yana pocketing din hannunshi "Lfy, yes? How may i help you?" Tafada tana kallonshi Murmushi yadanyi yace "Magana nazo muyi *Mrs A.A*" Kallonshi tayi kafin tace "Idan ban manceba, ba ta6a warning dinka akan dagantani da wannan sunan" "Why? Ba sunanki bane? Ko ba matarshi bace" Guntun tsaki taja "Now get to the point, kazo da sign dinne ko da takardar?" "Takarda? Tame?" "Kafini sani" tafada tana kauda kai cikin son danne 6acin ranta "Nazone don in tambayi dalilinki na aikawa ummy da takarda don nasan bake kikajeba dakanki" Kallon rashin fahimta tayimashi. "Takarda? What are you talking about?" Ganin kamar bata ganeba yasashi cewa "Kin gayawa ummy komai, dont you? Why zaki aikamata bayan kisan wannan is between us, mu kadai" Tsayawa tayi tana kallonshi na yan sakanni sannan taja tsaki. "Look, basan akan me kake magana ba, i thought kazo da takardata ne shiyasa kaga nafito tun farko. Batun kaima ummy takarda ba aikina bane, why should I? Koda aika takardar zanyi to ta sammaci zan aiko maku ba kotu don am taking this issue down to court, it's better kaba abokin naka shawara akan mu warware komai a tsakaninmu salin alin ko kotu ta taimakamana wajen warwarewa" "Court? Kinsan me hakan ke nufi? Zaku tonama kanku asirine a idanun duniya da kanku, kinsan abinda zai biyo baya? Kinsan abinda duniya zata fada akanku?" Yafada cikin ayar tambaya "I dont care, as far as zan rabu da wannan mutumin duniyar ta dade bata fadi koma menene akaina ba" tafada in an I-don't-care manner "Amma kinsan hakan zaiyi tarnishing din image dinku ko?" "Yadaiyi tarninshing din image dinshi, am independent and not that famous, shifa? Kana ambatar A.A kowa saiya waigo don sunanshi, sunanshi zai 6ata a banza, zai shafama kanshi baqin fenti a bugamashi tambarin zalunci wanda bazai iya taimakon naqasa dashiba saiya nemi wani abu in exchange. Court zata tuhumeshi da bribery, corruption and harrassment, labari zai yadu a duniya akuma wajen abokan huldarshi, zai samu karaya fiyeda tunaninka, now tell me waya kwan aciki?" Ajiyar zuciya sadeeq yasauke sannan yace "Saudart, why did you hate him that much? Allah nason bayinsa mai gafara, ki tuna koshi Allahn daya hallicemu muna mashi laifi mu nemi yafiyarsa yakuma yafemana" yafada cikin sanyin murya "Shima Allahn dakace sai mun nemi yafiyarshi yake yafemaba, tell me.. is your friend sorry?" "He is, na rantse, you need to see yadda yakoma, yayi nadama sosai kuma yana cikin damuwa plus ga ummy na fushi dashi, idan kin ganshi dole ki tausayamashi" "Mtcheew, story for the gods, look ban damu da nadamarshi ko damuwarshi ba don banma yadda yayi din ba. All I know is yabani takardata, tun farko shiya faro komai don haka he must end it. Ka fadamashi nabashi daga nan zuwa monday ya aikomin da takardata idan ba hakaba, wlh kaji na rantse? Zan kai wannan issue din court, idan yanajin yafi qarfin kowa ai befi qarfin shara'a ba, daga yau zuwa monday inba hakaba yaga sammaci.... Have a wonderful day" Tajuya tabarshi tsaye anan. Binta yayi da kallo harta shige sannan yasa hannu yashafi kanshi cikin damuwa. "Ya allah take control" yafada ahankali sannan yajuya yanufi hanyar fita jiki a sanyaye. Da sauri ta haye sama tashige dakinta ta maido kofar ta rufe ta jingina daita tana numfashi mai nauyi "Ummy? Ummy tasan komai?" Tambayar datayiwa kanta kenan. Qarasawa gaban gadonta tayi tana cire qatuwar hijabinta tana fiffita da hannu saboda zafin dataji yana suromata takoina. Tasan idan ummy taji dolene zata kira mamy ta tambaya. Ya sallam! Bazata iya kiyasta tashin hankalin da mamy zata shigaba idan taji labari. Tasan she's doomed kawai. "Ya allah kasa barazanar danayimasu yayi tasiri akansu, allah karabani da wannan bawa naka lfy" tafada tana kallon sama tareda daga hannayenta tafukanta abude. "Allah kasa sai komai ya warware sannan mamy zataji, Allah mun tuba ka yafe mana" tashafa sannan ta dago kaffafunta saman gadon ta rungume tana dora kanta akan gwiyagunta, zuciyarta fall da fargaba...✍️ Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamurranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) Jiya na mance banyi numbering din page ba, na jiya is page 61 yau kuma 62 062 Haka yadawo gidansu jikinshi a sa6ule, duk abunda ke faruwa beyi blaming din saudart ba, tanada gaskiya ta kowane fanni, Ashraf was so rude and cruel to her, yamata abubuwa kala kala wanda dolene ya fice mata akai, mance abubuwan dayayi mata ba abu bane mai sauqi ba. Saida ya gabatar da sallar asr sannan yasake fitowa da niyyar sake leqa Ashraf, ahalin yanzu mugun tausayi yake bashi don abun duk ya hargitse mashi, tsawon lokacin dasuke tare be ta6a ganinshi acikin irin wannan yanayin ba. Saida yabiya wani restaurant dake kan hanya yayimusu takeaway don yasan haryanzu beci komaiba sannan yawuce gidan. Sa6anin dazu, yanzu a bedroom dinshi ya iskeshi zaune akan sallaya ya jingina da jikin gadonshi da alama be dade da gama sallah ba. Dagowa yayi ahankali ya zubama sadeeq daya shigo da sallama ido sannan ya amsa ciki ciki wanda ko kadan sadeeq bejishi ba yadaiga bakinshi ya motsa. Be damuba ya qaraso ciki riqeda ledar hannunshi ya dorata a mirror sannan yasake ficewa. Maida kanshi yayi ya lumshe idanu yana dorawa daga inda tunaninshi ya yanke. Jiyayi ansake bude kofar hakan yasa yasake bude idanun yadan dago yana kallon sadeeq daya dawo da plates da cups tareda cokula. Batareda yace mashi komaiba ya dauko ledar ya zauna bisa rug din dakin yana facing din Ashraf sannan yafara ciro abubuwan dake cikin ledar. Jujjuyesu yayi a plate, jollof rice ce dataji kayan lambu sai qamshi take sai gassashiyar kaza da robobin yoghurt. Saida ya zizzuba kowanne a inda yakamata sannan yasaka spoons ciki ya tura tsakiyarsu. "Oya bismillah" yafada yana gyara zama. Ganin beko motsaba yasashi dagowa ya kalleshi saiya tsinci idonshi cikin nashi wanda hakan yanuna dama shi yake kallo. Gira daya ya daga mashi alamun lfy? Dan murmushi yayi kawai still yana kallonshi. "Oya muci, favourite dinka ne" yasake fada yana kallonshi Babu musu shima ya tashi zaune shima yana takwashe kaffafunshi kamar dai sadeeq cikin zuciyarshi yana alfahari da abotarsu da sadeeq, sadeeq yacika amini kuma danuwa agareshi, duk tsanani duk wuya yana taredashi, duk cikin abokanshi sunfi shaquwa don yafi iyawa dashi, dukda wasu halayen nasu ya banbanta amma hakan yake haquri dashi suna jallaftawa a hakan. "Wai ya? Kawani yi sakale kana kallona, nufinka nizanyi feeding dinka?" Yafada yana antayamashi hararar wasa. Murmushi kawai yayi ya dauki spoon ya debi abincin yakai baki. "Atoh don ba sweetie dinka bace" inji sadeeq shima yana kai loma. Haka sukaci abincin sadeeq na janshi da fira duk na barkwanci duk don yasaki jikinshi yaci abincin sosai. Babu laifi yadanci don yaci fin rabi sannan yakora da kakkaurar yoghurt din yakoma yadan jingina bayanshi da gadon. "Daga gidansu saudart nake" inji sadeeq yana kai cup baki. Dagowa Ashraf yayi dasauri ya kalleshi saidai yakasa cewa komai, koyaya aka ambaci sunanta sai jikinshi da zuciyarshi sun amsa. Yana sane yaqi qara cewa komai ya maida hankalinshi kan abincin dukda yanajin idanun ashraf akanshi. Cigaba yayi da kallonshi yanason ya tambayi me yajeyi kuma ya ya taddata amma yakasa sai idanun daya zubamashi kawai. Saida yagama kwalailaitarshi da tsantsani sannan yarufe plate din yasha cikin zuciyarshi yana ayyana mai hali baya ta6a chanza halinshi. Yasan a qagare yake yaji komenene amma girman kai ya hanashi magana wai ahakan ne wai ya saduda. Dagowa yayi ya kalleshi yaga still shi yake kallo amma yana iya hango 6acin rai cikin idanunshi dukda be nunaba a fuska. 'Baka buguba' inji sadeeq cikin zuciyarshi sannan yamiqe da niyyar tattare kwanukan wajen wanda hakan ya tunzura Ashraf sosai. Wannan wane irin salon wulaqanci ne kafaro magana kakuma yi shiru? "Ehen? Me kajeyi wajenta bayan abinda tayimana?" Yafada cikin 6acin rai dayaga beda niyyar magana. Dariya ce takusa su6ucewa sadeeq yayi saurin dannewa sannan yadago yana kallonshi da plates a hannu. "Perdon? Me kake magana akai?" Yafada cikin waskewa Wani malulu ta tsayawa Ashraf a wuya, lallai ma sadeeq. Tsaki yaja yamiqe a fusace ya dauki sallayar ya linke ya ajiyeta a ma'ajiyarta sannan ya haye gado ya kwanta. Dariya sosai yaba sadeeq hakan yasashi saurin fita da kwanikan yana dariya marar sauti, wani sa'in Ashraf yayi wani abun kamar qaramin yaro. Saida ya kimtsa komai sannan yadawo saman ya taddashi still kwance yaba kofar baya. Murmushi yasaki sannan ya qaraso shima ya haye gadon da qarfi yana rera yar waqarshi ta beginning to fall in love yana jawo wayarshi. "Duk yau banji muryar rabin rai ba wlh" yafada yana scrolling a wayar da niyyar lalubo numberta. Fitt.. yaji an fige wayar hakan yasashi saurin dagowa. "Nan ba gidanku bane kuma ba dakinka ba, kabari saika koma gidanku sannan kayi koma me zakayi" inji Ashraf cikin jin haushi. "Ikon allah, daga kira?" Inji sadeeq yana danne dariyarshi "Koma menene, this is my house don haka inada iko dashi" yafada ahasale "To naji, yi haquri bani bari nakoma falo nayi don gaskiya bazan iya jure rashin jin muryar ruhin ba na tsawon yini daya" Haushi yaqara qumeshi "Saidai katafi gidanku kayi wlh dama va gayyatarka nayiba, now out" yafada yana nunamashi kofa "Iyee? Ni kake kora Ashraf?" "Eh gidanka ko nau?" "A'a nakane, yanzu ashraf ni kakema rashin M? Babu komai nina kawo kaina" yafada yana juya kai gefe "Rashin M har yakai naka? Marar mutunci kawai" "Ni me nayi to?" "Bansaniba!" "Dan allah gayamin, haka kawai kawani sauya lokaci daya kamar mai iskokai, dazunfa hirarmu muke" "Guguwa gareni qarewar iskokai, mtcheew" yasake juyamashi baya "To yanzu yi hqr, gayamin meya faru rigimatu" Tsaki yaja batareda yajuyoba, jiyake kamar ya shaqureshi, wai tayaya mutum zai faro magana kuma ya manta? "Kaji?" Wani tsakin yasake ja sannan yace "Don iskanci saika faro magana kuma kayi shiru?" Danne dariyar dake cinshi yayi yana kallon bayan ashraf daya juyamashi "Magana? Wace magana?" Ya tambaya kamar gaske Wani dogon tsaki yaja sannan kamar bazaiyi magana ba yace "Ta yarinyar mana, mtcheew" yafada cikeda takaici Dariyar da sadeeq keta dannewa tundazu yasaki harda bubbuga katifar. Juyowa ashraf yayi yana kallonshi sannan ta girgiza kai "Madness on point" yafada cikin borin kunya. Shidai sadeeq bece komaiba sai dariyar dayake hakan yasake tunzura ashraf yakai mashi bugu yayi saurin matsawa baya don ya kauce sai yajishi qasa kasancewar dama bakin gado yake, hakan yaba ashraf dariya sai yadan murmusa yana kada kai. Miqewa sadeeq yayi yana dan tsagaita dariyarshi don ba maganarshi damar fita. "Wace yarinya?" Jifanshi ashraf yayi da pillow yana cewa "Bansaniba dan air kawai" Dariya sadeeq yasakeyi sannan yadawo yazauna kan gadon yana cewa "Gakanan babban dan air? Wlh ka rage wannan shegen girman kan naka marar amfani, idiot nazaci bakada bakine wlh da saidai nafasa fada" "Mtcheew kanka akeji" inji ashraf yana juyamashi baya "Hmm wlh ina tausaya maka yaro, wlh ka ajiye girman kai ka yaqo soyyayarka kafin kayi asararta gabadaya, did you know she's taking this issue to court? Kuma wlh dagaske take" Juyowa yayi bashiri yana kallonshi a galale "Court?" "You heard me right ai, to wlh makaka kotu zatayi a warware komai kuma kasan zancenan yaje kotu wlh an warware angama ne don tanada evidence kuma sunanka ne zai 6aci abanza" Kasa koda motsi ashraf yayi sai idanun daya zubamashi kamar dolo "Court? Is she crazy?" Yafada unbelievingly Daga kafada yayi kawai yana jingina da kan gadon "Ni bama wannan ba, inason sanin wanda yagayawa ummy ne, don da alamu ba ita bace batama san hakan ya faruba, maganar gaskiya ashraf you have to fight, tun kafin komai ya ta6ar6are" "No, zan rabu daita kawai" yafada a sanyaye "What!" Inji sadeeq yana waro idanu "Yes she hates me, bazata iya zama daniba kuma bazan iya tilastamata ba, son kai din zaiyi yawa" "Mtcheew amma bakada hankali, meye na saurin karaya?" "Duk abinda zan mata bazata ta6a saurarata ba" "Ka gwada? Eh? Dukfa abinda ake ko sau daya baka ta6a nunamata kayi danasani ba bare akaiga ka nemi yafiyarta. Maganar gaskiya ashraf you're so annoying, durkusawa wada ba gajiyawa bane, kayi mata laifi meye aciki don ka nemi yafiyarta? Kasan wani tasiri neman yafiyarta zaiyi a rayuwarka? Mtcheew gwanin takaici wlh" yafada yana saukowa daga gadon tareda ficewa. Binshi yayi da kallo sannan ya sauke ajiyar zuciya yana shafa kanshi ahankali yana antayawa cikin kogin tunani. A bangaren saudart kuwa haka tawuni sukuku kamar marar lfy, jiran dawowar daddy kawai take. Sosai ta birkicewa daddy bayan yadawo, kuka kawai take tana tsoron maganar nan takai kunnen mamy. Sosai daddy ya damu yanajin duk shine silar faruwar komai, yanajin duk shine mai laifin. Dakyar yasamu yashawo kanta hankalinta yadan kwanta amma can qasan zuciyarta fargabace da tsoron yadda abin zai kaya. Tunda yakoma falo beqara shiga dakinba don yavashi haushi sosai. Yananan har aka fara kirar magrib. Daya daga cikin toilets din falon yashiga ya daura alwala. Fitowarshi yayi daidai da saukowar ashraf shima wanda shima da alama masjid zaya. Jerowa sukayi batareda suncema juna uffan ba suka nufi masjid din. Basu suka fitoba sai bayan isha'i Cikin gidan suka koma sadeeq yanufi parking space. Binshi da kallo ashraf ta tsaya yayi harya bude motar dazu zai shiga. Takowa ashraf yayi wajen yana cigaba da kallonshi. "Ina zaka?" Banza sadeeq yayi dashi "Look am sorry, nifa bada nufin ba 6atama rai nayi maganarba" Wani mugun kallo sadeeq ya watsamashi "And wayace ranshi ya6aci?" "Idan ba fushi kakeba meye na tafiya?" Shigewa yayi cikin motar ya rufo sannan ya kalleshi ta window yana cewa "Gidanmu zani dare yayi" "I thought nan zaka kwana" Harara ya 6allamashi "Bakada hankali, gidan auren naka zan kwana? Mtcheww" Ashraf beqara cewa komaiba sai dan jada baya dayayi ganin ya tada motar, hakanan yakejin va dadi har cikin zuciyarshi, shi kowama fushi yake dashi, saudart,ummy, yanzu shidinma dayake dan kwantar mashi da hankali yayi fushi. Bama motar wuta sadeeq yayi sannan yafice daga gidan bayan ya dage glass din motar yabar ashraf da binshi da kallo. Yadan dade anan tsaye feeling soo empty sannan yasoma takawa yakoma cikin gidan a sanyaye yanajin komai na duniyarnan namashi ba dadi. Sama ya fara haurawa ahankali hannayenshi zube cikin aljihu kanshi a qasa harya qarasa sama. Tsayawa yayi tareda dagowa ahankali ya zubama kofar dakinta ido tunani kala kala na zarya a ranshi. Ahankali ta taka yanufi kofar yana kallon kofar. Hannu yasa yakama handle din ya murda ahankali dukda yasan a kulle take. Ga mammakinshi sai yaji ta bude, hakan yasashi tura kofar yayi stepping ciki ahankali yana qarewa dakin kallo. Yaune karo na farko daya ta6a shigowa dakinta, tsarin dakin ya burgeshi sosai don komai a tsare yake in a tidy way sai dan qura qura da dakin yayi na yan kwanakin dayayi bega gyaraba. Takowa yayi ahankali cikin dakin yana bin koina da kallo kamar mai inspecting yanajin wani irin feeling gameda ita. Ahankali ya qarasa bakin gadonta dayake liss kamar ba'a hawa yadan kakka6e saman gadon ya zauna ta jingina da kan gadon yana sakin nannauyan ajiyar zuciya. Lumshe idanunshi yayi ahankali yana tariyo duk abinda yafaru dasu tun farkon haduwarsu har ixuwa yanzu. Yasan yayimata laifi kai laifukama dayawa, tsawon rayuwar dasukayi tare be iya tuna abu daya datayimashi wanda ba daidai ba, duk shi kemata. Bata ta6a bude baki da nufin yimashi rashin kunya ko zagi ba dukda abinda yake mata saidai ko tabashi amsa daidai datashi ko ta basar tanuna vataji haushi wanda shikuma hakan ke quleshi a lokacin. Gani yake jijji dakanta yayi yawa ita ba kowan kowaba amma sai shegen girman kai hakan kesa yaqara yimata wani abun dazai qonamata rai. Ajiyar zuciya yasaki yana kamo le6enshi na qasa yana dan cizawa "Will she ever forgive me?" Tambayar dayayiwa kanshi kenan *kata6a nuna danasaninka gareta bare akaiga ka nemi yafiyarta?* Maganar sadeeq na dazu ta dawo mashi. "No" yafada ahankali Duk haukan dayakeyi batasan yanayiba, batasan yayi nadama ba, batasan irin qaunar dayake mata. Duk meyasa? Ya sake tambayar kanshi *Girman kai* wani sashen zuciyarshi yabashi amsa. *is better ka ajiye wannan girman kan naka marar amfani kafin wuri ya quremaka* Maganar sadeeq ta kwanaki tasake dawo mashi. *saudart alkhairice agareka ashraf, karkayi kuskuren barinta ta su6uce maka* Maganar sadeeq tasake dawomashi *Son, ina alfahari dakai da matarka, samun suruka da mata irin saudart zaiyi wuya a wannan zamanin, ka godewa allah don samun mace tagari shine dadin zaman duniya* Maganar ummy data ta6a yimashi watarana dayaje gidan tadawomashi. Tunawa yayi da tashin hankalin daya hango qarara a fuskar ummy dazu. She's scared, tsoro take ta rasa suruka irin saudart, tana jiyemashi tsoron rasa mata kamarta, tana jiyemashi tsoron rasa abokiyar rayuwa tagari kamarta. Amma tambayar anan shine shi yanajin tsoron rasata? "Yes, am scared" ya amsa ahankali. To meyasa bazai yunqura wajen ganin ya mallaketa na har abada? Meyasa yakeson girman kanshi yakaishi yabaro? Meyasa? Haka yaita juyi shikadai yana saqa da warwarewa, ganin hakan ba mafita bane yasashi miqewa yashiga toilet dinta ya daura alwala sannan yadawo ya bude closet dinta dake a tsare sai qamshi kayan keyi ya ciro sallayarta yarufe ta shimfida yahau yashiga jera nafiloli. Akan sallayar barci ya sadado ya daukeshi...✍️ Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 063 Yau ya makara wajen tashi sakamakon rashin samun isashen barcin dayayi. Tashi yayi yashiga toilet din dakin ya daura alwala sannan ya kabbara sallar asuba kasancewar har bakwai nasafe tayi. Saida yagama yayi addu'o'inshi sannan ya fito daga dakin yakoma nashi yaqara komawa kan gado don kwata kwata barcin be isheshiva. Sai wajajen 11 saura yasake farkawa yashiga bathroom yayi wanka ya fito sannan yashirya cikin wasu qananun kaya dasuka qar6eshi sosai suka kuma qara fiddo mashi qirarshi na qarffafen namiji. Makullan motarshi kawai ya dauka sannan yafito daga dakin ya sauko qasa sannan yafita waje. Parking space yanufa ya bude daya daga cikin motocin wajen yashiga ya fita daga gidan. Direct gidan ummy yanufa cikeda fargabar abinda zai tarar. Saida yayi parking sannan yafito ya kulle motar sannan yanufi hanyar cikin gidan. Danna door bell din yayi yana kallon kofar yana tunanin yadda zai fuskanci ummy yau, sosai yakejin kunyarta dakuma shakunta. Budewa akayi fuskar mai aikinsu ta bayyana. Saurin russunawa tayi tana gaidashi a ladabce tareda kaucewa gefe don yasamu damar shiga. Da hannu ya amsa mata sannan yashigo yana qarewa falon kallo. Can ya hango baby lafe bisa kujera tanata faman danne danne awaya. Jin sallamarshi yasata saurin dagowa tana gyara zamanta tana amsawa. "Yaya sannu dazuwa" tafada cikin murmushi Saida ya zauna a kujerar dake facing daura daita sannan ya amsa yana jingina da kujrar "Ina kwana yaya?" Injita "Lfy" ya amsa a taqaice Shiru palon ya dauka nawani lokaci sannan yadago ya kalleta "Ummy fa?" "Tana sama" ta amsa a sanyaye. Be sake cewa komaiba yamiqe ya haura saman baby tabishi da kallo. Saida yayi knocking sau uku sannan yaji muryar ummy daga ciki tana cewa "Na'am, come in" Ahankali kamar marar gaskiya ya murda handle din kofar ya tura sannan shima yashiga bakinshi dauke da sallama. Dagowa tayi daga bisa sallayar datake zaune wanda alamu sun nuna bata dade da gama sallar walha ba ta dubeshi sannan ta kauda kai tana amsa sallamarshi. A darare ya qaraso ciki yana kallonta sannan yasamu can dan nesa daita ya zauna qasan rug din dakin. Shiru dakin ya dauka babu mai niyyar magana, ita tana cigaba da jan cazbin hannunta shikuma yana satar kallonta. "Ummy ina kwana?" Ya gaisheta cikin sanyi Kanta kawai ta dagamashi batareda ta ko kalleshi ba hakan yaqara sanyaya jikinshi. Hakan sukaita zaman kurame na kusan minti shabiyar. Ashraf jinshi yake so akward, sosai cold attitude din ummy ya dameshi gashi taqi bashi fuskar yayi magana. Saida tagama laziminta sannan ta miqe zata nade dardumar yayi saurin amsa yana nademata. Batace mashi komaiba ta wuce ta rataye cazbinta ta cire hijabinta itama ta adanata sannan tanufi hanyar toilet. "Ka sauka kaje kaci abinci" ta umarceshi daidai zata shige toilet din sannan tashige tarufo. Bin kofar yayi da kallo sannan ya sauke ajiyar zuciya cikin jindadin maganar datayi mashi koba komai tadamu dashi, fushinta be hana ta lurada beci komaiba. Tashi yayi ya fita yajamata kofa sannan ya sauka. A falo ya qara tadda baby wannan karon waya ke maqale a kunnenta da alamun wayatake. Tana ganin saukowarshi tayi saurin yin sallama da wanda suke wayar ta sauke wayar. Zama yayi a inda ya tashi dazu sannan yadago ya kalleta. "Serve me food" yafada yana lumshe idanu. Tashi tayi babu 6ata lokaci tawuce dining area zata kwaso kayan karin dake sama. "No bari naqaraso" yafada yana tasowa. Dining din yaqaraso yaja kujera ya zauna sannan tace "Yaya tea ko kunu?" "Kunu" ya amsa yana danna wayarshi Kunun gyadan dayaji madara tayi serving dinshi sai fried plantain kamar yadda ya buqata sannan tajuya da nufin tafiya. "Wait.." Juyowa tayi tana kallonshi "Dawo kizauna fira zamuyi" yafada yana kai kofin a baki. Dawowa tayi ta zauna tanajin abun wani banbarakwai, shi dake korata idan zaici abinci yau ita zata tayashi fira? Cigaba yayi da karyawarshi itakuma ta nutsu sai jujjuya wayar hannunta take tanajinta duk a takure. Saida ya cika cikinshi sannan yadago ya kalleta yana goge bakinshi da tissue sannan ya jefa a waste basket din dake can gefe. "Ya school?" Taji ya tamvayeta "Lfy lau yaya" ta amsa tana mammakin sudden change dinshi cikin zuciyarta. "Kinadai karatu ko? Idan naga C.O a result dinki saikin gane kurenki ne" Murmushi tadanyi "Kai yaya, tunda kake ganin result dina ka ta6a ganin C.O? Am trying hard yaya" "To try harder" yafada yana danna wayarshi. "Insha allah" tafada tanajin dadi wai yau suna fira da yaya babu tsangwama ba harara. Shiru wurin yadan dauka kasancewar babu mai wani abun dazai sake fadi, can sai ashraf ya ajiye wayar hannunshi yadago yana kallonta in a serious mode ganin hakan yasata sadda kai. "Baby" taji yakirata Hakan yasata dagowa tana kallonshi itama. "Tell me, waye yazo jiya? Waye yazo yasami ummy jiya yabata wannan takardun" yafada yana kafeta da idanu. Shiru baby tayi tana sadda kai qasa cikin tsoro. "Tell me ok? Don't get scared" yasake fada ahankali "Suzy.." Dan ware idanunshi yayi "Wanene?" Yasake tambaya cikin mammaki Hawaye taji suna taranmata a idanu "Suzy ce yaya" Shiru yayi yana kallonta don harga allah inba yanzu data kira sunanta ba harya mance da wanzuwarta a duniyarnan. "Suzy? How?" Sniffing tayi ahankali sannan tace "Muna zaune bayan mungama lunch mukaji doorbell na ringing, Asabe taje ta bude sai gashi sun shigo tareda ita tayi shigarnan nata na rashin dacewa. Nayi mammaki dana ganta har cikin falonmu amma sai banyi maganaba muka bita dakallo nida ummy hartazo tanemi wuri tazauna ta dora qafa daya bisa daya tana taunar chewing gum. Nice nace 'mallama lfy zaki shigo gidan mutane babu ko sallama and ki zauna vatareda an baki iziniba?' Kallon banza ta watsamani sannam tace 'Save it, ba wajenki nazoba wajen kakar da ko diyata nazo, so mind your damn business' Shiru mukayi muna kallonta cikin mammaki don babu wanda ya fuskanci inda ta dosa. Kallon ummy tayi tace 'barka da warhaka hajiya, fatan kina lfy?' Karfin hali ummy tayi tace 'lfy lau, wacece ke?' "Surukarki nan gaba insha allah kuma uwar jikanki nan bada dadewa ba" Kallon juna mukayi nida ummy sannan na miqe a fusace ina cewa 'Look mallama tashi kifita! Rashin ajin naki haryakai kibiyo mijin wata har gidansu don rashin zuciya..' Ummy ce ta katseni ta hanyar dagamani hannu sannan ta kalli suzy da ko ajikinta saima kallonmu sheqeqe datake. 'Baiwar allah, vamu fahimci bayananki ba' 'Ok ina nufin ni karuwar danki ce Ashraf mai dauke da danshi ko diyarshi a marata, yanzu kin gane?' Abin ya dakemu sosai dagani har ummy. Bansan sadda nakai wajenta ba sai gani nayi ummy na kiciniyar rabani daita. Dakyar ta banbareni jikinta tanamin fadan meye haka nakeyi. 'Ummy qarya takeyi, tana daya daga cikin yan iskan dakebin yayane tun kafin yayi aure, ganin be aureta ba shine zata yimashi sharri, nasanta ummy nasanta farin sani' nafada ina huci 'Kin sanni amma bakisan yayanki ba, idan ni yar iskace to yayanki dan guguwa ne don shi ya koyamin iskanci yafake da auren bogi don azaci kamili ne a zahiri bayan yana tsula tsiyarshi a 6oye' Kalamanta sunyi mugun 6atamin rai hakan yasa na nufeta again ummy tayi saurin kamo hannuna sannan takalli suzy 'Kinsan dawa kike magana? Kinsan kan wa kike magana? Kinsan abinda zaki iya jama kanki akan wannan qazafin?' Inji ummy da alamun itama ranta yafara 6aci. 'Ba qazafi bane hajiya ban taho nanba saida sheduna, ashraf auren bogi yayi, tsararren aure yayi da wannan yarinyar don wanda itama tayishi ne don tarufama kanta asiri...' Cakumota nayi wanda hakan yayi sanadiyar katsewar maganarta nafara bugunta takoina hakan ya fusata ummy ta juyoni da qarfi ta daukeni da mari wanda yasani dawowa hayyacina, nan taita man fada inda take shiga batanan take fitaba sannan tajuya kan suzy tace ta zauna ta gayamata komai dalla dalla. Zama suzy tayi sannan tacigaba dacewa 'Nida Ashraf masoyane tun a school, shine saurayina na farko kuma shine yafara kawarmin da virginity na' saita fashe da kuka. 'Shi ya lallatani nikuma saboda soyyayar danake mashi yasani biyemashi, bayan yagama karatunshi yadawo nigeria yafara aiki nikuma yabarni can ina kammala karatuna, lokacin kuka takuramashi kan batun aure shikuma ni yakeson aura nikuma family na sunce bazasu aurar daniba saina kammala karatu na. Hakan ya tada hankalina sosai..dafarko harnaso bijirewa akan saina kammala karatun don inasonshi sosai don hakanma yabashi damar yin amfani da son danake masan ya lallatani. Ana hakan yazo qasar wanda dama al'adarshine daya fita qasar waje da sunan business trip wajena yake gangarowa muyita masha'ar mu. Nan yaita rarrashina ganin yadda duk nadamu yacemin yasamo mana mafita wai akwai wata yarinyar dazasuyi auren kwangila daita. Cikin mammaki na tambayeshi Auren kwangila kamar yaya? Sai yace wai itama yar hannuce wato tasha mu'amala da maza to shine takeson yin aure amma tana tsoron kar asirinta ya tonu don a zahiri tana pretending ita kamilace kuma nitsatsiya wanda a badini kuma karuwace, shine tazo mashi da tayin ya aureta na yan wattani saisu rabu yadda zatayi aurenta a matsayin jawara babu wanda zai zargi komai, suka yanke wannan shawarar akan babu abinda zai shiga tsakaninsu har su rabu wanda lokacinda zasu rabu kuma zaiyi daidai da nagama karatu sai muyi aurenmu'" Shiru baby tayi tana sheshekan kukan da tundazu tafarashi, shikau ashraf kamar statue yakoma sai binta da kallo yake babu ko kyaftawa. "Yaya wlh bakaji yadda najiba alokacin, zuciyata kamar ta tarwatse, nasan karya take yaya, sharri take qulamaku kaida anty hakan yasa natashi nasake nufarta ina bugunta ina kuka ina cewa karya take wlh sharri take muku. Itadai ummy batace konaiba, she's shocked to death don tama kasa motsawa. Dakyar suzy ta kwaci kanta ta tureni nafadi sannan ta watsamana wasu takardu tana magana cikin qaraji wai muduba idan qarya take don harda shaidu gasunan. Duqawa ummy tayi ta tattara takardun tana dubawa nan mukaga takardar comtract ne na auren kamar yadda tafada ga sa hannunka 6aro 6aro gana aunty ga kuma na sadeeq na hudun kuma tace natane. Mun shiga rudani sosai don sosai hankalinmu yatashi. Dayar takardar kuma na gwajin juna biyu ne nata na wata biyu sai hotuna dakuke tare. Ahankali ummy ta dago ta kalleta sannan ta sake kallon hotunan taga eh ita dince tareda kai. 'Juna biyu gareki?' Ummy ta tambaya 'Eh ummy kuma nashine wlh' ta amsa tana matsar hawaye 'To meyasa kika tonaku bayan ba haka kukayi dashi ba?' Ummy tasake tambaya 'Saboda yanason tilastamin zubarwa ne kuma ni ina tsoron aikata kisan kai, dana gayamashi yace to ku in zubar ko intafi can nida cikin kar in alaqantashi dashi don ba shirya zubewar mutuncinshi ba, nikuma naji haushi nafara masifar be isaba don tun farko shiya lallatani ba wani ba, shine yayiman mugun bugu yakuma ce yafasa auren kuma karna sake nanuna nasanshi. Ganin ban iya facing din family dina da wannan abin kunyar yasani tahowa nan don a warware komai asamamin mafita' Tashi nasakeyi ina qaryata cikin kuka 'Ummy qarya take wlh, son yaya take da aure shikuma yaqi saurarenta shine tabiyo ta wannan hanyar tayaya za'ace anty saudart karuwa ce? Tayaya yaya zaiyi zina? Wannan sherrin editing ne' Dagaman hannu ummy tayi sannan tace ma suzy ta tafi zata nemeta saita tashi ta tafi. Zuwa nayi kusada ummy nayita mata rantse rantse cewa qaryane, sharri ne Batace mani komai ba sai shirun datayi na wani lokaci sannan ta umarceni na kira aunty saudart. Kira biyar nayimata lafiyayye amma bata dagaba hakan yasa ta kiraka tace kuzo. Saigashi kuna zuwa kuka gasgata abin" Ta qarashe tana kifa kanta a dining table din. Tsitt wurin ya dauka bakajin komai sai kadawar a.c dake wajen Idanunshi sun kada sosai kamar gauta yayinda numfashinshi ke fita da nauyi har kana iya hango yadda qirjinshi ke sama da qasa. Motsin dataji yasata dagowa daga kifa kan datayi taga shine ya miqe. Sosai yanayinshi ya tsoratata hakan yaqara bugun zuciyarta. Juyawa yayi batareda yace komaiba ya fice daga dining din dama falon gabadaya yanufi parking space cikin wani irin taku nashi wanda ban ta6a ganiba saiyau. Wayarshi yaciro yana dailing din number yana bude motar. Ba'a dagaba harta tsinke hakan yasa yasake bugawa lokacin harya shiga motar ya tadata. Sai a kira na uku aka daga, lokacin harya fara reverse "Fuck you! Ina kake!" Yafada cikin wani irin murya Bansan kome aka fadamashi ba saiya sake cewa "Damn you! Nace where the hell are you before I straggled you to death!" Yafada tsakankanin haqora, qirjinshi sai sama da qasa yake alamun zuciya Bansan kome akace ba sai gani nayi yayi tilli da wayar seat din baya sannan ya bama motar wuta yafice daga gidan kamar zai tashi sama...✍️ Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 064 Tsit dakin yayi bakajin komai sai qarar a.c dake aiki. "Kutt... amma anyi tsinnaniyar yarinya, ciki? How and when?" Inji sadeeq cikin tsananin 6acin rai Cize le6enshi na qasa Ashraf yayi yana kalkada kafa daga inda yake zaune, shikadai yasan abinda yakeji acikin zuciyarshi. "Lallai dolene akoyama yarinyarnan lesson, ni wlh nama manta da ita ashe tananan tana bibbiyarku, abu mafi daure kai anan shine ina tasan cewa auren contract kukayi? There is something fishy here" yafada yana zagaye dakin "I can't believe ummy kallon mazinaci takemin a jiyan nan, kallon me lallata yanmata, ni... ni Ashraf" yafada cikin wani yanayi "Dolene mu nunamata kuskurenta Ashraf wanda nan gaba ko wuqa akasamata a maqoshi bazata qara gigin yima wani qaxafi ba, qazafin zina ba qaramin abu bane musanmman ma akan Saudart kamilar mace... baiwar Allah, allah kadai yasan yadda zataji idan labarin nan ya risketa" Shiru dakin yasake dauka kowa da kalar tunanin dayake. Ringing din wayar sadeeq ne ta katse musu tunaninsu. Zaro wayar yayi ya duba sannan ya dago ta kalli Ashraf daya lumshe idanunshi. "Ashraf.. ummy ce" yafada yana maida kallon ga wayar kuma Bude idanunshi yayi yazuba mashi kawai batareda yace komaiba. Ganin kiran zai tsinke yasashi saurin dagawa yakara a kunne. Sallama yafara yimata sannan ya gaisheta a ladabce. Bansan kome tacemishi ba saiya dago ya kalli Ashraf da shima kallonshi yake yace "Eh gashinan ummy" Magana aka sakeyi tacan 6angaren sannan yace "Insha allah ummy" Katse wayar yayi ya maido kallonshi ga ashraf dake kallonshi haryanzu. "Ka tashi mutafi" "Ina?" Ya tambayeshi ahankali "Ummy ke nemanmu tace takira wayarka ba'a dagawa" inji sadeeq yana nufan closet dinshi don zaro rigar dazai daura bisa singlet din jikinshi. "Ban iyawa, bazan iya fuskantar ummy ba ahalin yanzu" yafada yana dafe kan dake saramashi "Meyasa? Yanzu ne the right time dazamu fahimtar da ita komai tun kafin abu ya girmama, yau zatasan komai so stand up dalla" inji sadeeq yana dora shirt saman singlet din. "Allah kadai yasan kallon datakemin yanzu, i swear sai suzy tayi nadamar zuwanta duniya" yaqarashe yana huci "Ai fadi ma 6ata baki, she really need to learn the lesson of her life, tashi mutafi" Jiki asanyaye ashraf yatashi, besan yadda zekuma qara facing din ummy bayan yagama sanin kallon datake mashi. ************************************* Zaune suke gabanta qasan rug kamar dai jiya kowanne kanshi sunkuye. "Ina kiranka baka dagaba" inji ummy tana kallon Ashraf daya kasa hada idanu da ita "Am..sorry, na..barota a mota ne" yafada kanshi still a qasa "Wacece wannan?" Tafada tana turomashi wani pics gabanshi. Dagowa yadanyi yana kallon pics din. Hotonshi ne da suzy tadan shige mashi ajiki tana dariya shikuma yadanyi murmushi Bazai manta ranar dasukayi hoton ba, ranar suna school ba'a dade da gama sheqa ruwan sama ba, garin yayi shar mutane sun fito waje sai daukar pics suke. Saukowa shima yayi hannunshi riqeda wani qaton littafi shima yatsaya yana kallon students din "My.." yaji an kwala mashi kira abaya. ko be juyoba yasan itace Qarasowa tayi gabanshi tana haki, binta yayi da kallo yadda kayan jikinta suka dan jiqe gashi tawani tsuqe cikin jumpsuit (biri da wando) babu ko mayafi sai yar hular datasa akai. "Please muma muyi hoton..please" tafada zata riqe hannunshi. Dan zamewa yayi yana harararta "Look at you, wai bakijin sanyi ne kam?" Ya tambaya yana binta da kallo cikin kishi Itama kallon kanta tayi sannan ta kwa6e fuska "Am sorry zan chanza yanzu, please mu dauka ko dayane" "No" yafada firmly yana juyawa zai tafi. Bunshi tayi tafara mishi magiyar ya bari ko dayane suyi, ganin bazata barshiba yasashi hqr ta tsaya ta fiddo wayarta ta matso jikinshi kadan, bece mata komaiba don aqagare yake tayi din yatafi. "Please kayi murmushi mana wannan hade ran dukna menene?" Tafada a shagwa6e Tsaki yaja sannan yadanyi yaqe ta daukesu sannan yadan tureta daga jikinshi yana cewa "Ai shikenan ko? Am going to the library, see yah" yajuya yatafi. "Nace wacece wannan?" Muryar ummy tasake maidoshi daga duniyar tunanin daya lula. Ajiyar zuciya yasaki sannan ya bude bakinshi dakyar "Tsohuwar budurwa ta ce" Shiru dakin ya sake dauka. Rintse idanunshi yayi snnan yacigaba dacewa "A school muka hadu kuma muka fara soyyaya... saidai tafiyarmu batayi wani nisaba muka rabu don kwata kwata batada kamun kai, ga shigar datakeyi anyhow dukda ina nuna mata rashin dacewar haka amma bata dauka..." Shiru yasakeyi idanunshi still rintse yana sauraron bugun zuciyarshi. "Mun..mun rabune ranar dana..." Shiru yasakeyi hoton yadda ya taddata suna musayar hot kiss dawani qaton arne a wani class na dawomashi a qwanya. "Sadda na.. naganta dawani suna.." sai yayi shiru yakasa idawa. Ummy kallonshi take tunda yafara magana kuma haryanzu bata daina kallonshi ba "Ummy na rantse ban ta6a zina ba, ko zanyi bazanyi da qazamiyar yarinyarnan ba, bansaniba.. bansan abinda aka fadamaki kenan ba, yes aurenmu da Saudart AUREN KWANGILA ne amma babu wata yarjejeniya makamanciyar wadda ta fadamaki a tsakaninmu da saudart, she's innocent.. hasalima..bada son ranta akayi auren ba, believe me ummy.. kinfi kowa sanin halin danki..." Ya qarashe maganar muryarshi nadan rawa rawa. "Ummy suzy shaidaniyace, sharri ta qullamasu saboda daga baya tadawoma ashraf yaqi sauraronta shiyasa ta buyomashi ta wannan hanyar, ummy ni aminin ashraf ne tare muke akoda yaushe, ko alokacin dasuke soyyayar ban ta6a ganin ya riqe koda dan qaramin yatsanta ba, hasalima bawani sonta yakeba duk ita taita cusa kanta gareshi" inji sadeeq "Hakane ummy, nima nasan suzy farin sani, qawayenta kawai zaki kalla kisan ko ita wacece, tasha cusa kanta gareni don tasamu shiga awajen yaya akaro na biyu, tasha tazo taita rarrashina akan nabata number yaya amma naqiya, ga sa bikin su yayama saida suka fito qarara suka nuna baqincikinsu, magangannu kala2 babu wanda basu fadaba, ummy ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba suzy qarya tashiryama yaya do n tasamu a liqamashi ita" inji baby itama fuskarta bayyane da 6acin rai. Shiru dakin yasake dauka, kan ashraf haryanzu aqasa zuciyarshi na bugawa yanason jin wane hukunci ummy zata yanke. Ajiyar zuciya ummy tasauke mai sauti sannan tace "Kalleni Ashraf" Shiru yayi yakasa dagowa, bejin zai iya dagowa su hada ido daita, wani irin nauyinta yakeji "Nace ka kalleni" Ahankali yadago ya kalleta saikuma yayi saurin kauda kai ganin ta kafeshi da ido. "Nasani, nasan qarya take kuma sharri takemuku tun alokacin datake maganar, nasan cikinku babu wanda zai iya aikata abinda tace kun aikata, nidama ban zargeka ba ban kuma zargi daughter ba cos I trust you both" Ajiyar zuciya ashraf yasauke mai sauti yanajin kamar ana lifting din wani qaton dutse a qirjinshi. "Wacece saudart? Meya hadaku? Meye silar wannan auren naku na contract?" Tambayar ummy tasauka a dodon kunnensu. Kowannensu shiru yayi zuciyarsu na bugawa. "Magana nike" tafada tana binsu da kallo. "Ummy.." "Shhhh.. barshi yayi magana, dashi nake ba kai ba, ka gayamin komai ashraf karka saki ka 6oyemin komai" tafada tana kallonshi. Shiru falon yasake dauka, sai motsi yake da baki amma yakasa magana, yarasa ta inama zai fara. "Saudart diyace ga SHAMSU KANKIYA...Tsohon aminin Abbu" yafada yana lumshe idanu. Ware idanu Ummy tayi tana kallon Ashraf unbelievably Bakinta na rawa tace "Shamsu qolo?" Kada kai yayi zuciyarshi na suya. "Nafara ganin appointment letter dinshi ne wattanin baya dasuka wuce, akan yanason rance don farfado da company dinshi dake neman collapsing... ina ganin sunan naga tabbas kamar nasanshi wani wuri, hakan yasa babi diddigin qundinshi ta internet anan naga shidinne bawani ba... nan take tsohon raunin dayaimana a zuciya ya motsa naji na tsaneshi fiyeda yadda na tsaneshi da, dafarko sai naso qin taimaka mashi amma sai wata idea ta fadomin, mezai hana inyi ramuwar gayya nima in dandana mashi abunda ya dandana mana? Saina amsa buqatarshi nabashi ranar dazamu hadu sannan nakoma naita bin diddiginshi daga kan iyalanshi zuwa abokan aikinshi dakuma abinda ya tara da abinda ake binshi bashi. Saura kwana daya mu hadu na gayawa sadeeq plan dina, dafarko yaso hanani yacemin inbarshi da allah kawai mai yiwuwa sakkayar allah ce yake gani tun yanzu amma sainaqi saurararshi don alokacin *WUTAR FANSA🔥*(littafina ba gaba insha allah) ke ruruwa azuciyata, na nunamashi bansan zancenba acewata don indauki fansa yasa allah yaturoshi wajena..dakyar nayi convincing din sadeeq ya amince min shima. Ranar farkon dayazo...." Nan yashiga bata labarin zuwan Alhaji shamsu nafarko company dinshi da yadda suka kaya sai kuma zuwanshi da biyu da yadda ya gabatarmashi da sharaddinshi dakuma amsar daya bayar na zaije ya shawarta. Yakuma gayamata zuwan da saudart tayi da abinda yafaru tsakaninsu wanda hakan yaqara 6atamashi rai dakuma qara jin lallai saiya aureta donya koyamusu hankali gabadaya. Yabata labarin yadda alhaji yaita fadi tashi har yasamu saudart ta yarda dakuma yadda aurensu yakasance har izuwa zaman aurensu ya gangaro zuwa fara aikinta a companynshi da abubuwan dayaita mata na muzgunawa ya gangaro zuwa tafiyarsu spain da zamansu acan dakuma yadda ta taimaka mashi wajen kama mayaudaran mutanen dasukaso karyashi har zuwa lokacin dasuka dawomashi da kudinshi da niyyar kawo qarshen contract din da abinda yafaru aranar dukda ya 6oyemata kissing dinta dayayi sannan ya gangaro har zuwan da sadeeq yace yayi gidansu jiya da barazanar makashi kotu datayi. Shiru yayi yana sauke numfashi ahankali saboda doguwar maganar dayayi. Dakin yayi tsit babu mai ko motsi yadda kasan babu kowa ciki. "Na aureta ne badon komaiba saidon in rama abinda yayimana ko fiyeda hakan, nabashi rancen ne bisa tsarin zanyi shige da fice yadda komai nashi zai lallace yakasance babu uwar kudi ba riba ga kuma uban bashi. Nikuma lokacin sai in nuna bansan zancenba saiya biyani inhar yanason diyarshi, sonake ya talauce shima yakoma bayada komai shima ya dandana abinda ya dandana inyaso shima zuciyarshi ta buga ya fadi mattac..." Tasss! Sautin dayaji a qunnenshi ya hanashi qarasawa. Kafin ya tantance meyake faruwa tasake daukeshi dawani zazzafan marin a dayan kumatun Dafe duka kumatun yayi ta dogo da sauri yana kallon ummy daka tsaye sai huci take idanunta sun chanza launi. Toshe baki baby tayi da hannu biyu tana ware idanu, tashin hankali qarara a fuskarta. "Da hankalinka?" Ummy ta fada tana nunashi da yatsa manuniya. "Nace da hankalinka da iliminka ka aikata wannan abin da ko jahili bazai aikataba?" Kasa koda motsi yayi daga tsugunnen dayake hannayenshi dafe da kunci yana kallonta Yakasa yara yau ummy ta dora hannu akanshi da sunan duka abinda bazai iya tuna when last tayimashi va tsawon rayuwarshi "Fansa haukane?! Aure? Aure ka maida abin wasa? Abun daukar fansa? Ka rusa rayuwar yarinya da future dinta duk akan fansa?" Ta tambaya cikin zaremashi idanu. "Ummy don alla.." katseshi tayi ta hanyar qamtsamashi nashi qason marin "Yimin shiru! Harda kai? Atunanina kafishi hankali ashe taron zamuce ta tadda muje?!" Dafe kuncinshi shima yayi yana sadda kai qasa "Kaiga sarkin zuciya? Mai zuciyar qarfe dabakasan kabar mutum da allah ba? Akan banzar daukar fansarka ka janyo wanda bata jiba bata ganiba kana neman lallatamata rayuwa?! Kana..." Kasa idawa tayi ta juya kawai ta dafe kanta kasancewar ta mai zuciya idan ranta yayi mugun 6aci maganama gagararta yake. Ganin hakan yasashi saurin rarrafowa yana riqemata qafa. "Ummy am sorry, am soo sorry" Fizge kafarta tayi da karfi taja baya. "You're not but you will be, kutashi kufita! Kutashi nace!!" Tafada tsakankanin abinda ya toshemata maqoshi. Saurin tashi sadeeq yayi amma ashraf ko gezau "Kutafi nace kuma kai.." Ta nuna ashraf "Gobe kamar yanzu inason ganinka anan gidan da takardar saudart, banaso ko igiya daya ta rage atsakaninku" Agigice ya dago yana kallonta yayinda zuciyarshi tayi wani mugun bugawa. "Kaji nagayamaka! Ke tashi kitafi dakinki!" Ta dakama baby tsawa. Dagudu ta tashi tayi sama aguje. Itama bin bayanta tayi tahaye sama batareda tasake kallonsu ba. Dafe kanshi ashraf yayi cikin tashin hankali wanda tunda yake beta6a shigaba yayinda zuciyarshi ke bada wani hucin zafi kamar a oven....✍️ *WAYE ASHRAF?* Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamurranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 065 *WANENE ASHRAF?* *AUWAL MUHAMMAD* Haifaffen garin wudil ne dake jahar kano. Su shidda ne awajen iyayensu *MUHAMMAD JARIRI* wanda akafi sani da *MAMMAN* da matarshi *AMEENATU* Yayansu shidda, maza hudu mata biyu. Auwal shine d'a nafarko, sai ibrahim dake bimishi sai Nuradeen, sai Jamila, sai Zaharadini sai auta Halimatu wanda watanta uku a duniya ta rasu. *MALLAM MAMMAN* manomine wanda ya riqe noma amatsayin sana'arshi, yanada rufin asiri daidai gwargwado don cikin noman yake samun abinci dazasuci harkuma su sayar. Duk cikin yaranshi babu wanda yayi boko don lokacin ba'a wani bama karatun boko muhinmmanci ba. Iyakarsu makarantar allo sai suwuce gona idan sun tashi don taimakawa babansu. Jamila nada shekaru sha shidda akayimata aure dawani d'an abokin Mallam Mamman dake qauyen kakumi. Auwal tun tasowarshi yakasance yaro mai hazaqa da zuciyar nema, duk yafi sauran yan uwanshi kazar kazar da qoqarin aiki. Shiyasa sukafi shaquwa da Mallam Mamman don sosai yake taimakamashi a gona. Auwal da kingin yan uwanshi sunada hadin kai ga girmama na gaba dasu suk qarantar taxarar dake tsakaninsu kau, hakan yasa zaman lfy, girmama juna da hadin kai ya wanzu a ahalin. Koda sukadan qara tasawa sai suka amshi ragamar nomar yakasance mallam mamman ya sakarmusu komai yakoma yana hutawa. Haka rayuwa tacigaba da kasancewa a wannan ahalin har watarana wani abokin mallam mamman dake zaune cikin garin kano yakawo mashi ziyara. Anan su Auwal suka taddasu lokacin sun dawo daga gona, saida suka gaishesu sannan suka shiga cikin gidan. Bayan sun shige ne abokin mallam mamman wato *MALLAM SANI* yayima mallam mamman tayin mezai hana yabashi daya daga cikin yaran yabishi kano ya hadashi da d'anshi sudinga aikin tuqin dayake. Dafarko mallam be yarda ba, dakyar mallam sani yashawo kanshi yace zai shawarta. Sai bayan isha'i sun zaune tsakar gida kamar yadda suka saba, samarin na zagaye da tray din abinci sunaci yayinda iyayen ke gefe. Anan ne mallam mamman ya tada maganar da abokinshi sani yazomashi daita. Nan take Auwal yanuna ra'ayinshi nason bin mallam sani don sosai yake sha'awar fita wani wurin nema. Da farko mallam yaqi yara don ganin duk yafisu himma da qoqarin noma gashi shine babba amma ganin babu mai ra'ayin zuwa cikin qannen yasa ya yarda shima saida Auwal yadan sha wuya wajen shawo kanshi. Cikin dan qanqanin lokaci suka shirya, ranar da mallam sani zai koma kanon yabiyo suka wuce da Auwal din. Acan kanon mallam sani ya hada auwal da danshi mai suna Lawal wanda shima tsarar Auwal dinne suna daukan kayan gwari a mota suna kaiwa garruruwa. Tun Auwal nabin Lawal a mota amatsayin karen mota har shima ya qware da tuqi shima aka bashi mota. Alhamdulillah yana samu bakin gwargwado don duk qarshen wata idan zai ziyarci wudil yana zuwa masu da alhairi bakin gwargwado. Suma su Nura suna itakar qoqarinsu a harkar nomansu idan kuma auwal yashigo garin yazo hutu wanda duk yawanci kwana hudu yakeyi haka zasu hadu sutafi gonar gabadaya. Cikin dan qanqanin lokaci Auwal yayi suna, masu bada mottoci haya suka sanshi saboda gaskiyarshi da riqon amana. Tun yana daukan kayan gwari har yakoma daukan kayan smuggeling irinsu shinkafa, man olga dadai sauransu. Sosai yake samu da wannan sana'ar dob harya gyaramasu gidansu dake wudil dukda ba rusheshiba yayi akayi saboba saidai duk ya gyagyarashi an chanza sabon rufi na kwano sa6anin ba karare saikuma shafe da akayima gidan both qasa da bango. A 6angaren qannenshi kau suma suna samun cigaba sosai don Ibrahim yabude dan shago yana siyarda kayan masarufi wanda yake hadawa da noma. Nura kuwa yakama kiwo na dabbobi daban2 wanda shima hakan be hanashi nomanba. Shikuma Zaharadini daga baya Auwal yatafi dashi kanon don sudinga aikin tare. Auwal cikim tafiye tafiyenshi ba tuqin mota watarana yaje garin yola ya hadu dawata kyakyawar bafulatana mai suna *FATIMA* wanda ke kawo tallar nono da wara a inda suke sauke kaya. Wasa wasa suka shaqu dajuna soyyaya tashiga tsakaninsu, ya kasance dik sadda yashigo garin suna tare kofar qaton shagon dasuke sauke kayan suna fira kamar karsu rabu hartakai yafison daukan kayan yola don haduwa da sahibarshi. Ahaka suka qulla shekara daya suna soyyaya . Awani dawowa hutu dasukayi wudil mallam mamman da yafara tsufa ya tarasu ya nemi kowannensu ya fidda mata yayi aure musanmman Auwal da Ibrahim kasancewar sune manya. Anan ibrahim ya bayyana cewa shi dama akwai wacce yakeso mai suna *Raliya*, yarinya nitsatsiya babu wanda besantaba a garin wudil. Sosai sukaji dadin za6in nashi nan aka maido akalar tambaya akan Auwal. Shima beyi qasa a gwiwa ba ya bayyanamasu soyyayar dake tsakaninsu da Fatima yar yola. Dafarko Aminatu (inna) taso taqiya acewarta saidai yasamu mata ansn cikin wudil ta aura amma daga baya ta amince bayan mallam mamman ya fahimtar daita shi aure rabone kuma matar mutum qabarinsa. Nanfa magana takaiga manya, suma can 6angaren fatima sunso qiyawa amma daga baya sai suka amince aka saka rana lokaci daya dana Auwal da Ibrahim din. Gaggarumin biki akayi a garin wudil. Mallam mamman baqi yaqi rufuwa ana bikin yara har biyu yan gaban goshi. Jamila itama ta halarci bikin alokacin 'ya'yanta uku. Sosai akasha shagalin biki inda anan qauyen aka kawo fatima saida sukayi sati sannan suka koma cikin garin kanon awani madaidaicin gida daya kama haya. Kwanci tashi asarar mai rai. Haka Auwal yacigaba da harkarsa ta tuqi Allah na sanyamashi albarka yana kuma qara budamashi har ya tara kudi shima yasiya mota daya dukda da second yafara don gangar jikin motar yafara siya sannan ahankali ahankali yacigaba da hadata harta zama cikkakiyar mota nan shima yabadata haya ga qanninshi Zaharadini yayinda shima yacigaba da nashi tuqin, saiya kasance ana bashi haya shima yana bayarwa kuma hakan ba qaramin budi ya qaramashi ba. Ana cikin haka suka hadu da *SHAMSU ABUBAKAR* wanda akafi kira da *SHAMSU QOLO* d'an qauyen kankiya dake jahar katsina shima yashigo kano ne cirani. Sun hadune wani zuwan da shamsu yayi zai sari jarkokin man olga sai aka hadoshi da motar Auwal suka taho alokacin shamsu na aiki ne awani qaton shagon kayan masarufi aqarqashin wani. A wannan tafiyar suka qulla abota kasancewar shamsu mutum ne mai saurin shiga rai ga iya tsara kalamai ga raha. Cikin dan qanqanin lokaci suka zama aminan juna don sosai suke qaunar juna har takaiga indai auwal nacikin gari to zakagansu jone koda wane lokaci, hakan yasa kowa yasan da abotarsu. Shekara daya da aurensu Auwal Allah yayima Mallam mamman rasuwa, mutuwae data girgiza mutane dadama don bawani jinya yayiba, amai da zawo yayi na yini daya ya sheqa. Babu shiri su Auwal suka tarkato sukayo wudil. Suna wudil har akayi sadakar bakwai. Cikin masu zuwa masu gaisuwa harda Shamsu qolo don shi tun ranar kwana biyu yazo saida akayi addu'ar uku yajuya washegari. Bayan addu'an bakwai su Auwal na shirye shiryen komawa kano Raliya matar Ibrahim ta haihu kasancewar dama da tsohon cikinta akayi rasuwar. Ta haifi danta namiji tubarkallah babu wata wata aka maida sunan margayi mallam mamman sai aka dinga kiranshi *Mallam* Sai bayan suna sannan su Auwal suka koma kano. Haka rayuwa tacigaba da tafiya, ahankali ahankali Allah yaita budama Auwal yaqara siyan mota yaqara badata haya itama wanda hakan besashi barin tuqinba. Haka yacigaba tun yana sayan tsoffafi yana hadawa harya fara siyan sabbabi dall zuwa lokacin arziqi ya zaunamashi sosai don harya ginama kanshi gida mai kyan gaske. Yakumu rushe ginin qasan gidansu ma wudil yayi na zamani ya zuba kayan more rayuwa a gidan musanmman dakin inna wanda babu yadda beyi ba daita kan yamaidota kano taqiya wai gwara ta mutu a mahaifarya. Haka zalika bebar qannenshi ba, yana taimakamasu bakin yinshi donshi mutum ne mai yawan kyautaa dukda suma basu rasa komaiba sunada rufin asiri daidai gwargwado. A 6angaren abotarsu da shamsu qolo kau sai abinda yaci gaba don izuwa lokacin shamsu shima ya bude nashi qaton supermarket wanda babu abinda mai siyar na kayan masarufi. Tun yana order a garruruwa har aka fara kawomashi daga qasashe daban daban wanda harda cotonou inda ake kawomashi shinkafa mottoci mottoci wanda duk yawanci motoccin Auwal ne, hakan yaqara danqon zumuncinsu ya kasance kansu a hade yake. Saidai matsalar Shamsu daya, had'ama da son kudi, dik inda ta qyallo zai samu saiya kutsa yabi yasamu, hakan yasa yake hadawa da ha'inci a al'amuranshi. Auwal yasha yimashi fads akan wannan halin amma yakasa dainawa don tun farko betashi ta wata isashiyar tarbiya ba na iyaye saina malamin makarantar allonsu wanda sunmashi yawa baya iya controlling dinsu duka. Ana haka wata shekara Auwal ya tilastama Shamsu dole suka tafi aikin hajji tare wanda da ason ran shamsu ne bazaijeba don shi be qaunar abinda zai zazzagarmashi da account dinshi. Bayan dawowarsu Alhaji Auwal da Alhaji shamsu, Alhaji Auwal ya tadda labarin farincikina na samuwar juna biyun Fatima wanda shekararsu ta uku kenan da aure. Farincikin da Alhaji Auwal dama makusantanshi sukayi baya misaltuwa don sadaka yaitayi yana godewa allah da kyautar dayabasu. Nanfa suka dauki son duniya da kulawa suka dorawa cikin, ba Alhajin ba ba zaharadini qannanshi ba ba fatima ba. Haka fatima taita samun kylawa ta musanmman suka raini cikin cikin tsantsan kulawa har allah ya sauketa lfy ta sum6ulo qaton d'anta mai kama daita sak masha allah. Farincikin da Alhaji Auwal yashiga alokacin 6ata bakine. Kan kace me? Mutanen wudil harsun iso lokacin har ansakama Nura mai bima Ibrahim biki. Suma yan adamawa yan ywan fatima ba'a barsu abaya ba da jamila yar kakumu haka suka garzayo kano don taya wannan ahali murnar samun qaruwa. Ranar suna d'a yaci sunan kakanshi wato Muhammad ana masa laqani da *ASHRAF*...✍️ Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 066 Ranar suna Fatima tasamu kyauttutuka dayawa wanda duk yawanci abokan huldar Auwal ne sukafi badawa, sosai suka nuna bajintarsu wajen kawo kyaututtuka na Alfarma. A 6angaren Alhaji shamsu kau abin ba'a cewa komai don shima ba qaramin kudi yakashe ba don har ragunan da aka yanka shiya siya bayan kayan jarirai da lasa lasai dayaba mai jego. Haka dai akayi sunan aka watse, kowa yakoma inda yafito. Anan Fatima tacigaba da wankanta Auwal yasamomata wata dattijuwa dake qasan unguwarsu tana zuwa kullum tana wanke jariri. Haka suka cigaba da kula da dansu cikin so da qauna, kan kace me yaron ya girma yayi bul bul kamar irin 'ya'yan turawan nan ga wayau kamar me? Yanada wata biyar suka tattara sai wudil bikin Nura. Shima babu laifi ansha shagalluluka kala kala, Ashraf kau saboda farinjini fatima har rasa hannun wa yake don beda qiwuya ko kadan da yaga saiya 6angale mashi baki yana miqo hannu alamun yanason adaukeshi, hakan yasa Fatima bata ganinshi sai ya buqaci abinci sannan za'a kawoshi ta shayar dashi akoma dashi. Saida sukayi sati sannan suka juyo kano wanda tun washegarin biki Alhaji Auwal dama yayi gaba sukuma saida suka zagaye dangi sannan suka taho. Haka rayuwa tacigaba da kasancewa. Ashraf ya taso cikin gata da soyyaya tako wane 6angare saidai duk gatan dayake samun hakan be hanashi samun inganttaciyar tarbiya ba don duk yadda suke dashi idan yayi ba daidai ba suna tsawatar mashi kuma suyimashi nasiha. A 6angaren arziqin Alhaji Auwal kuwa sai abinda yayi gaba don yanzu yabar tuqi yakoma harkar shinkafa kawai, mottocinshi basu qilguwa kullum cikin busy yake yazama babban dan kasuwa. Tun bayan haihuwar Ashraf *Ummy* kamar yadda Ashraf ke kiranta bata qara haihuwa ba sai 6arin datakeyi akai akai wanda sunyi maganin amma a banza. Da farko Alhaji Auwal (Abbu) yaso ajuya mahaifarta saboda wahalar dayaga tanasha amma saita qiya acewarta abarta ahaka haka allah ta tsara mata. Ashraf nada shekara biyar Abbu tabiyama inna, inna Raliya, ummy, inna jamila da zainab matar Nura hajji suka dunguma sukaje suka sauke faralli. Bayan dawowarsu da yan wattanni akasama Alhaji shamsu biki dawata shuwa Arab ta garin borno. Acikin wannan lokacin ciwon zuciyar Inna yatashi sosai babu wata wata Auwal ya daukota takawota asibitin kano aka cigaba da bata kulawa saidai dayake lokacinta na kusa kwana biyar tayi tana jinya ta rasu. Sosai mutuwar ta girgizasu don sunyi kuka marar iyaka. Haka suka dauki gawar suka juya wudil don Inna tabar wassiya idan tamutu koma inane a maidota wudil arufe don tafison arufeta a mahaifarta. Bayan sati biyu suka dawo kano rayuwa tacigaba da tafiya. Izuwa yanzu ansaka Ashraf makarantar primary ta private kuma allah yayimashi qwalwa da basirar daukar abu don shike ciwo nadaya a ajin duk qarshen term Ba'a dadeba bikin Alhaji shamsu ya matso nanfa sukaita shirye shirye babu kama hannun yaro. Duk tare suke komai da Alhaji Auwal don bawani dangi ke gareshiba sosai sai tarin abokan arziqi da abokan kasuwanci. Gaggarumin biki akayi nagani na fada inda babu laifi ansha shagulgula sosai sannan aka kawo amarya khadija dakin mijinta. Haka rayuwa tacigaba da tafiya Ashraf sai qara girma yake da wayau, arziqin Abbu sai qara hauhawa yake allah nasa mashi albarka hakan yasa yakeda maqiya da mahassada masu hassada dashi a6oye batareda yasaniba. Bayan shekara daya da aurensu Alhaji Shamsu sai Allah ya azurtasu da samun diya mace kyakyawa sak uwarta. Alhaji shamsu baki yaqi rufuwa don murna, ranar suna na zagayowa aka radamata sunan *SAUDATU* bayan haihuwar da 'yan wattani su Alhaji shamsu da matarshi khadija suka fara samun matsala atsakaninsu sanaddiyar sata dayayi acire mata mahaifarta wai diya daya ta ishesu acewarshi 'ya'ya talauci suke jawowa. Firr khadija taqi yarda acewarta bazai sata ta kashe kanta da rai ba, tun suna abin a tsakaninsu har yakai kunnen Abbu kasancewar Khadija tagayamashi ko zata samu yanunama Alhaji shamsu daidai. Abin yaba Abbu haushi sosai saiyaje yasamu Alhaji shamsu har company dinshi yayimashi magana shikuma sai abin ta hassalashi sosai ganin wai khadija takai qararshi wajenshi kamar wani ubanshi. Nanfa Alhaji shamsu yafara zazzaga bala'i ta inda yake shiga batanan yake fitaba, aranar dakyar Abbu yafito company din rai 6ace abinda beta6a faruwaba a tsakaninsu. Shikuma Alhaji shamsu yana komawa gida yarufe khadija da fada ta inda yake shiga batanan yake fitaba yace kuma cire mahaifa dole ayi muddin tanason cigaba da zama dashi. In taqaice muku dai saidai auren yamutu da abu yaqi dadi wanda hakan ba qaramin 6ata ran Abbu ba yayi. Wannan karon har gida Alhaji Auwal ya tadda Alhaji shamsu sukayi tatass inda daganan abotarsu ta shekara da shekaru ta watse. Ummy sam bataji dadin hakanba amma ya suka iya? Kan kace me? Har labarin 6atawarsu ya zagaye koina da aka sansu, mutane sai jimamin abun suke yayinda wasu suke farinciki akan haka. Shekara daya da faruwar wannan al'amari Ummy tasake samun juna biyu lokacin shekarar Ashraf takwas kenan. Sosai cikin yabata wahala sannan tasamu ta haifeshi bayan tasha baqar wahala tasamu diya mace sak Ashraf saidai bata ida kamoshi a haskeba. Zokaga murna wajen Ashraf don sosai yake sha'awar qane ko qanwa dama. Ranar suna na zagayowa akasamata sunan margayiya Inna wato AMINATU amma ana kiranta da *Baby* Ana haka bikin zaharadini yataso inda ya auri yar kano suka tare a gidanshi da shima yagina a unguwar. Kwanci tashi ba wuya, baby anfara girma don harta shekara biyu wanda yayi daidai da shekarun ashraf goma da wattanni. Har a lokacin Abbu basa ga maciji da Daddy, sun watsar da zumuncinsu don ko labarin juna basaji. Ana haka watarana Abbu na zaune cikin iyalanshi zaharadini ya bugo mashi waya kome yacemishi oho? Saiga Abbu ya zabura zaune har yana qwarewa da abinci Cikin sauri ummy ta bashi ruwa suna jeramashi sannu ita da yaran. Saida tarin ta lafa sannan ta tambayeshi lafiya? Yace ba lafiya bari yaje yadawo. Haka ya fice be ida qarasa abincinba wanda itama ummy kasa ci tayi sai barosu ashraf datayi a dining tadawo falo tazauna tana addu'ar allah ya jiyardasu alhairi. Acan kau Abbu yashiga tashin hankali marar misaltuwa don duka mottocinshi jami'an custom suka kame da abinda suka dauko. Babu yadda beyiba wajen ganin an sakarmashi su amma abu yaci tura kai daga baya ma har gidanshi jami'an sukazo suka watsamashi komai suka 6alle store dinshi suka kwashe shinkafa ko taci basu bariba. Wannan cin zarrafin baqaramin qonama Abbu rai yayiba don gani yake wannan cin fuskane babba. Be ida shiga tashin hankaliba saida yaji cewa tsohon abokinshi kuma amininshine ummul aba'isan faruwan wannan lamarin. Sosai abun ya dakeshi wanda har saida yakwanta ciwo. Alokacin zaharadini ne yake taimakonsu dana magani don yadda kasan daukewar ruwa hakan komai na arziqin Abbu ya qare. Magani akema Abbu amma kamar qaramashi ciwon ake. Kullum cikin ambaton sunan Shamsu qolo yake yana hawaye. Sosai su ummy dama kingin danginshi suka shiga tashin hankali akoda yaushe ummy da ashraf dashima yafara sanin komai cikin kuka suke saiya kasance Ashraf yakasa mance sunan da abbu ke yawan maimaitawa yana hawaye. Abinka da yaro saiya riqe sunan gamm a kwakwalwarshi yayinda yakema mammalakin sunan tsana wacce bata misaltuwa. Saida Abbu yayi sati biyu sannan Allah ya dauki ranshi, mutuwar da ta girgiza jama'a da dama kar ummy ma taji labari. Haka dole akamashi sutura jama'a takoina ancika unguwar danqam suka rakashi aka kaishi gidanshi na gaskiya. Su ummy basu tashi gane kurensu ba saida duk aka watse nan fa talauci ya kunnomasu kai. Gashi dama zaharadini yake dan taimakawa to shima yanzu babu mota hannunshi kuma kamar hadin baki kowa yaqi bashi dukda kau mutuncin da mutanen keyi da margayi Auwal dayake raye. Hakan yasa yakoma kasuwa yana tsaron shago wanda abinda yake samu bewani taka kara ya karya ba. Ganin haka yasa ummy ta tuntu6i zaharadini akan asiyarda gidan dasuke ciki su siya qarami kingin kudin saisu jujjuya. Saida zaharadini ya tuntu6i yayyanshi na wudil saboda hadin kai irin tasu suka kauyi maraba da hakan don suma basujin dadin halin da iyalan dan uwan nasu yake ciki kawai don basuda halin taimakawa ne. Kan kace me? Har an saka gidan kasuwa aka kau siyeshi da daraja, zaharadini ya samarmasu dan qaramin gida a unguwarsu suka zauna ya miqamata kingin kudin inda taqi amsa tace yaje yaita jujjuyawa kawai. Shima qin yarda yayi har saida magana taje gasu Kawu ibrahim nan shima kawu ibrahim yayi na'am da shawarar Ummy kan zaharadini ya juyasu tunda shima kusan beda sana'a yanzu tsayyaya albashi sai aba ummy wani kaso acikin kudin itama tafara business. Hakan kau akayi, zaharadini yaje ya sari kayan kitchen da kudaden yayi hayar shago acikin kasuwa itakuma ummy tafara sana'ar saida kayan humra da turrarukan wuta wanda Allah ya dubi maraicinsu yasamasu albarka aciki. Ashraf da tuni ancireshi daga makarantar kudi don yanzu tafi qarfinsu aka maidashi ta gomnati yazana common entrance dinshi yakau fito da result mai kyau yasamu admission awata makarantar gomnati ta secondary. Ashraf yanada hazaqa sosai kasancewar yasamu good background a makarantar primary dinsu kasancewar private ce. Ahankali yafara suna don ashraf akwai qoqari da saurin fahimta don shike topping din class dinsu duk term. Bayan haka ga baiwar kyau da Allah yabashi don kallo daya zakamashi kasan ya hada jini da fulani. Ganin yadda ake sonshi ake kuma lilliqemashi yaja ashraf tsirowa da halin jinkai da miskillanci. Yaga daman kana mashi magana saiya mula yasha iska sannan ya amsa a dage. Haka yan aji ke fama dashi musanmman masu liqemashi ya koyamasu karatu, bazaiqi koyamusu ba amma saiya wanasu son rai ya shamusu qamshi sannan ya koyamasu hakan kuma be 6atamasu rai don su shan qamshinshi ma burgesu yake don komai yake kyau yake musu. A ss1 suka hadu da *SADEEQ UMAR* the mathematician kamar yadda aka samashi suna a school din. Duk aji daya aka sasu kuma ga lokacin basusan junaba don sadeeq transfer akayi mashi yayi junior waec a school din, sai ya kasance dukkansu sun hadu a commercial class. Da farko gaba da kishi suka farayi dajuna kasancewar kowa na taqama shi genius ne. Ashraf yafishi qoqari a sauran subjects din irinsu biology, english, business studies da dai sauran subjects din da babu calculation saidai sadeeq ya dokeshi a calculation don yadda kasan aljani haka ya iya lissafi hakan baqaramin 6ata ran ashraf yakeba don yasaba shine agaba a komai. Hakan yasashi yin kishi da sadeeq musanmman idan yaga students naxuwa wajenshi solving din lissafi. Shima sadeeq lura dayayi da yadda ashraf kemashi wani gani gani yasashi kama kanshi yanuna besan da wanzuwarshi ba. Haka fa akacigaba da competition tsakaninsu kowa nason gwadawa dan uwanshi iyakarshi. Saida suka shiga ss2 suka shirya shima sadeeq ne yanemi suyi abota don harga allah ashraf na burgeshi. Kamar yadda yasaba saida yasha qamshi yana hura hanci sannan ya amince dukda can qasan ranshi murna yake don shima sadeeq na burgeshi don sadeeq badai raha da barkwanci ba, kwata kwata beda saurin fushi saidai idan aka quleshi beda kyau sa6anin ashraf da kamar akan wuya yake abu kadan ke hasalashi. Ahaka suka qulla abota mai qarfi duk inda kaga daya sai kaga dayan har takai babu wanda besan da abotarsuba a fadin makarantar. Alokacin allah yasama sana'ar kawu zaharadini albarka sosai don harya canza shago ya kama babba yana cigaba da sana'arshi ta kayan kitchen ashraf na dan kama mashi da tsaron shago duk sadda beda wani aikin yi. Ahakan suka qarashe secondary school din lokacin baby ana primary. Baby ta taso yarinya mai rigima da iyayi ga baki zai kamar parrot, rawar kanta yasa basa shiri kwata kwata da ashraf don kwa6darta yake idan tayimashi ba daidaiba babu abinda ya dameshi saidai yana sonta sosai. Bayan result dinsu yafito ne suka samu daddadan albishir na scholarship da aka bada a school dinsu na mutane biyar qasar waje wanda ciki harda ashraf da sadeeq. Farincikin ranar har rawa saida suka taka. Cikin dan qanqanin lokaci aka gama shirin komai suka lula UK karatu. Acanma bata sauya zaneba suna zuwa ba'a wani jimaba sukayi fice a school din saboda qoqarinsu ga hadin kai don kodayaushe tare suke dukda kamar kaji suke kodayaushe cikin fada suke donma sadeeq nada haquri. Nanfa akaimasu caa don lokacin sun zama samari masu jida kyau da gayu dukda sadeeq ba fari bane amma baqinshi mai kyau ne ga uwa uba fara'a dake qarawa mutum kyau dayakeda ita. Kan kace me yanmatan school din sukai musu caa dukda vasu cika tunkarar Ashraf ba don ba qaramin kwarjini yake musuba gashi fuskarshi ba wasa kullim a dinke take. Sa6anin sadeeq da ba ruwanshi idan mace ta tinqareshi saiyace yanada aure harda 'ya'ya biyu qauye idan kuma tanason yayi nabiyu daita ya kaita qauye to. Haka yake samu su rabu lfy dasu batareda ran kowa ta 6aci ba. Ana haka kwatsam yaga ashraf na soyayya da suzy wata yar nigeria wanda itama karatu yakawota qasar saidai batada kamun kai ko kadan ga shiga ta fidda tsiraici. Da farko yaso nisarda ashraf aibunta anma saiyaga kamar yana sonta sosai saiya qyaleshi saigashi basu wani yi nisaba suka rabu inda sukayi wani gaggarumin fada a filin makaranta sadda yaganta suna kissing da wani bayahude mai suna chris james Daya nuna 6acin ransa akan haka saita fara bala'i wai bawani matsiyacin da zai hanata sakewa a school donma sun samu an biyamusu scholarship da a ina zasu ganta bare har raini yashiga tsakani? Sosai abun ya6atawa ashraf rai don dakyar sadeeq ta janyeshi daga filin wanda yacika danqam da yan ganin qwam. Tun daga lokacin kowa yakama gabanshi babu mai kula dan uwanshi har suka kammala abinda yakaisu suka dawo nigeria. To anan ne zaharadini ya maidomasu dukiyarsu duka ganin ashraf ya mallaki hankalin kanshi. Nan ummy taqi yarda suka amshi kudin kawai suka barmashi ribar dayaita juyawa hakan kuma ba qaramin dadi yayimasuba kuma hakan yaqaramata qima a idanun dangin mijinta. Ahankali ahankali shima ashraf ya shiga harkar kasuwanci kasancewar shi dama ya karanta. Nan sukayi hadin gwiwa da abokinshi kuma dan uwanshi sadeeq suka fara da kadan kadan har allah yasaka masu albarka suka bude tanqamemen company dinsu wanda suka samashi suna A.A ENTERPRISES LTD wanda ahankali ahankali sukayi rassa a qasashe daban daban, talauci ya qaura a wannan ahalin suka koma kamar koma ince fiyeda yadda suke da. Ashraf shima babanshi yabiyo a kyauta shiyasa kaf family dinshi babu mai kukan babu don babu babu din. *CIGABAN LABARI* sainaga ruwan comments tukun, naga alamun kwana biyu kun danyi sanyi🙁 Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Allah ka bamu zaman lfy a qasarmu nigeria🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 067 *CIGABAN LABARIN* Wani matsanancin ciwon kai ya saukoma Ashraf nan take yayinda jikinshi har tsuma yake saboda tashin hankali. Ummy is requesting na ya datse igiyoyin dake tsakaninshi da Saudart duka kuma she mean it don ya hango dagaske take acikin qwayar idanunta. Jiyayi an dafa kafadarshi ta dama. Ko be dagoba yasan sadeeq ne hakan yasashi lumshe idanunshi dasuka chanza kala yana sauraron bugun ziciyarshi. Har lokacin sadeeq na dafe da kafadarshi saidai yarasa kalmar dazaiyi amfani dashi wajen kwantar mashi da hankali don shima hankalin nashi atashe yake don shima bega alamun wasa ko sassauci atareda ummy ba. Sun dade ahakan sannan sadeeq yayi qarfin halin jawo hannunshi sama alamun yataso sutafi. Babu musu yatashi dakyar suka juya suka bar falon sadeeq na janye da hannunshi shikuma yana biye dashi kamar raqumi da akala. Zama ummy tayi bakin gado tana dafe kanta da hannu daya. This is unbelievable, takasa yarda da abinda Ashraf ya gayamata. Saudart? Diyar shamsu? This is super shocking. Ya akayi takasa hango kammaninta dana mahaifiyarta? Dama kullum idan ta kalleta saitaga kamar ta ta6a sanin face din awani waje. Ya akayi takasa ganewa duk tsawon wannan lokacin? Kenan da khadija suke waya lokaci bayan lokaci? Ya akayi takasa gane muryarta? Ya akayi su kawu ibrahim suka kasa gane shamsu lokacinda sukaje nemama Ashraf aure? Qarar budewar kofa dataji yasata dagowa daga dafe kan datayi tana kallon mai shigowa. Baby ce tashigo idanunta jawur alamun taci kuka. Kallonta tacigaba dayi harta qaraso kusada ita ta zauna qasa. Shiru dakin ya dauka kafin baby ta dago a raunane. "Ummy?.." sai kuma tayi shiru tana hawaye. Itama ummin shiru tayi saidai batabar kallonta ba "Ummy don allah karki raba yaya da aunty..please karki 6ata komai ummy, ki gyarashi instead" tafada cikin muryar kuka. Nan ma shiru, ummy batace uffan ba. "Ummy.." "Get out" inji ummy ahankali "Ummy please..." "Out!!!" Ta daka mata tsawa wanda babu shiri ta miqe tanufi hanyar fita tana toshe baki. Komawa ummy tayi ta jingina da kan gadon, tunanika kala kala na kai kawo azuciyarta. ******************************************** Zaune saudart take a garden din gidansu ta kafe waje guda da idanu . Tunda tasamu labarin ummy tasan komai hankalinta yaqi kwanciya. Koda yaushe cikin fargaba take na kar mamy taji lbr don tasan idan taji to ta kade har ganyenta. Wayarta ce tasake daukar ringing a karo na ba adadi. Duba takai ga wayar tana kallon sunan mai kiran yayinda takejin wani iri cikin ranta. Baby ce, tun shekaran jiya take matsamata da kira da massages kala2 tana magiyar tayi picking din call dinta. Sosai takejin ba dadi har cikin zuciyarta don harga Allah tana qaunar baby fiyeda tunanin mai karatu don ta dauketa ne kamar qaramar qanwar da batadashi. Haka taita kallon kiran harya tsinke sannan tasaki ajiyar zuciya ta dauki wayar ta kasheta gabadaya don Allah yasani ko zata shekara tana kira bazata iya dagawa ba, to ta daga tace me? Komawa tayi ta jingina da resting chair din tana lumshe idanu tana tunanin hanyar daya kamata tabi don kawo qarshen wannan qaddararren auren. Kafin su iso wani zazzafan zazza6i ya lullu6eshi, jikinshi yayi rauu. Ganin haka yasa sadeeq juya akalar motar zuwa gidansu don bazai iya barinshi ta kwana shi kadaiba acikin wannan halin. Dakyar ya taimakamashi yakaishi dakinshi ta kwantar dashi sannan yafito yana amsa tambayar ummy daketa tambayarshi lfy? Amsamata yayi da zazza6i yakeyi sannan yayi saurin fita saboda gudun ta jegomashi wata tambayar. Tunani umma tafarayi to idan zazza6i yake ina matarshi dazai kawoshi nan? Hakan yasata daukar wayarta tashige daki don kiran unmy taji ko lfy? Be dadeba sai gashi yadawo hannunshi dauke da ledar magunguna yashige dakinshi. Cikin bargo ya tadda Ashraf yashige ya qudundune sai rawar sanyi yake. Remote din a.c ya dauka ya kashe a.c din dakin sannan ya haura kan gadon yana dan yaye bargon. "Ya sallam" tafada jin hucin zafin daya dakeshi, ahankali yakai hannunshi a saman goshinshi yajishi rauu. "Sorry friend" yafada cikin tausayawa "Bari na amsomaka abinci kaci kasha magani kaji ko?" Shidai be bude idaninshi ba bare ya amsa. Tashi sadeeq yayi ya bude kofar yafita don samarmasu abinci. A falo ya tadda umma zaune da alamu ma tayi zurfi a tunani, jin takunshi yasa ta dago tana kallonshi harya qaraso. Sosa qeya sadeeq yayi yanadan sinne kai alamun rashin gaskiya sannan yace "Umma akwai abinci?" Nuna mashi dining tayi batareda tayi magana ba tana tunanin to meke faruwa haka wanda Hajiya Fatima tace maganar bata waya bace saidai tazo? Fatanta dai allah yasa lfy. Wucewa yayi dining din ya dibarmusu abincin sannan yayi sama yana sauke ajiyan zuciyar sa'ar dayaci ummy bata tambayeshi komaiba. Dakyar yasamu ashraf yaci abinci don har saida umma tasa baki sannan yadanci yasha magani yakoma ya kwanta yana rufe jikinshi gabadaya da bargo. A ranar dai barci rabi da rabi yayi marar dadi saidai alhamdullilah zuwa safe jikin yadanyi sauki zafin jikin ya rage sosai saidai har lokacin kanshi nadan sarawa. Yanzu ma bawani breakfast din kirki yayiba yatashi tashiga wanka yafito yabude closet din sadeeq ya ciro wasu qanannun wanda da alamu sabbi mane ya fara shiryawa. Fitowa sadeeq yayi daga wanka shima ya tsaya yana kallon Ashraf dake taje sumarshi gaban mirror. Qarasowa yayi shima wajen mirron yana daujan wani lotion ya matsa a hannu yafara murzama jikinshi. "Ina zuwa haka?" Ya tambayi ashraf dake taje kanshi "Ummy" yabashi amsa a taqaice "Ok bari nima na shirya na rakaka" "No katafi company kawai" "Why? You need me, don't you?" "Yes, amma company yafini buqatarka, katafi kawai nima zanzo bekamata ace daga ni harkai ba wanda yajeba" yafada yana daukan turaren dudduba turarrukan sadeeq yanason ganin wanda yakamata yafesa don babu kalar nashi anan. "Ok but take care, uhm?" "Sure" yafada yana ciro daya daga cikin turrarukan ya feffesa sama sama don duk basuyi mashi ba kawai manage yayi. "Bani key" inji ashraf yana saka wayarshi a aljihu. "Kafini sanin inda suke" inji sadeeq dake cikin closet tana za6an kayan dazaisa. Guntun tsaki ashraf yaja yanufi bedside locker yaja ya dauki daya daga cikin keys din ya maida ya rufe. "Natafi" yafada yana nufar qofa. "Take care" inji sadeeq. Koda yafito babu kowa falo sai wata mai aiki dake goge centre glass table. Saurin russunawa tayi ta gaisheshi bako kalletaba yafice yanufi hanyar parking space yana danna dan botton din dake maqale a key din hannunshi motar tayi tsuwa. Yaje ya bude motar yashiga ya tada yafice daga gidan. A parking space din gidan ya tadda baby zata tafi makaranta. Jira tayi yayi parking yafito sannan ta gaisheshi ya amsa ba yabo ba fallasa yawuce. Binshi tayi da kallo cikeda fargabar ko sun rabun da saudart din, jitake kamar takoma ciki tajiyo amma saita haqura kawai tashiga bayan motar driver ya tada suka fice. Ya dade zaune a falon saidai babu ummy babu alamunta dukda ya aika wata yar aiki ta sanar daita zuwanshi. Ganin zaman yafara isarshi yasashi tashi yanufi saman. A kofar dakin ya tsaya yafara knocking ahankali. Shiru... hakan yasa yasake knocking nanma shiru. Saida takusan minti daya yana knocking sannan yaji muryarta a kausashe tana tambayar waye? Bayan yasan tasan ko waye don tasan kalan knocking dinshi. Ajiyar zuciya yayi sannan yabude baki ahankali yace "Nine ummy" yanajin wani banbarakwai don besaba ba. "Kaine wa?" Tasake tambaya in the same husky tone. Shafa kanshi yayi ahankali yana murmushi, lallai ummy kenan bata gane muryarshi ba take nufi. "Ummy Danki ne Ashraf" Tsaki yaji taja "Ehen lfy?" "Lfy lau ummy" "To ya akayi?" Shiru yadanyi yana kallon kofar da mammaki "Bakomai ummy" yafada a sanyaye. Shiru ya ratsa hakan yasashi cewa "I want to see you ummy, please ki bude" "Kazo da takadar?" Gabanshi ne yafadi hakan yasashi yin shiru yana kallon ruffafiyar kofar. "A'a" yafada ahankali "Then leave my door karka sake dawowa saida takadar kaji nagayamaka" "Ummy..." "Leave!!" Tayi mashi tsawa daga ciki. Babu yadda ya iya hakan ya juya jiki a sa6ule yabar kofar yasauko qasa yana jinshi wani iri. Komawa yayi ya zauna inda ya tashi ya zubama hanyar stairs din ido yana kallo. Ya dade ahakan amma babu alamun saukowar ummy. Sosai yakejin ba dadi har cikin zuciyarshi. Yasan yanada laifi amma saka sharri da sharri ai ba haramun bane. Kuskurenshi daya shine sako wanda bata jiba bata ganiba a abun. And now gashi abun ya rufta dashi, shi be cika burinshi na daukar fansaba, gashi allah ya jarabceshi da mugun sonta bayan mugun tsanar dayasan tayimashi ga kuma ummy na fushi dashi. Tunawa yayi da abinda suzy tayimashi, koyaya saudart zataji idan tasan qazafin da akayi mata? Sai jiyai be kyauta ba, na farko ya tilasta mata aurenshi ga wulaqanci da cin mutunci dayaita mata kala and to top it all ga mummunan qazafin zina da akayimata duk don ta dalilin shi. Daga kai yayi ya kalli agogon dake manne a bangon falon yaga har shabiyun hantsi ta wuce. Tashi yayi yagyara zaman t-shirt din jikinshi yaqara kallon hanyar stairs sannan yanufi hanyar kofar fita. Motarshi yabude yafada ciki sannan yarufe ya tada ta fita daga gidan. Tuqi yake in a normal speed har yazo ya parka bakin kofar gidansu. Tsayawa yayi yana karewa kofar gidan kallo yanajin wani iri a zuciyarshi. Ya dade ahakan sannan dakyar ya bude murfin kofar yaziro kafarshi wajen ahankali kingin gangan jikin suka fito ya maida kofar ya rufe yana qarewa gidan kallo. Ahankali ya zagayo yana zube hannunshi cikin aljihu harya qaraso bakin gate din sannan yasa hannu yana bubbugawa ahankali. Saida yayi bugu uku sannan yaji motsi daga ciki haka yasa yadanja baya yana kallon kofar. Qaramar kofar gate din aka bude sannan fuskar buzun ta bayyana. Tsayawa yayi yana qaremashi kallo shima ashraf hakan take awajenshi. "Lfy?" Inji buzun yana dan leqen motar bayan ashraf "Lfy lau, barka" "Barka dai" buzun ya amsa. Dan sa hannu ashraf yayi yana dan sosa kai "Erm s..Saudart nanan?" Qara qaremashi kallo yayi wanda har hakan yafara kule ashraf. "A'a tafita, lfy?" "Lfy" ashraf ya amsa sannan yajuya yanufi motarshi yana jan guntun tsaki. Binshi buzun yayi da kallo harya bude yashiga ya tada yatafi sannan ya ta6e baki ya maida kofar ya rufe. Tuqi yake amma yarasa inda kuma zai nufa, anya ma buzun nan gaskiya ya fadamashin batanan din? To mema ya hanashi tsayawa confirming? Tsaki yasake ja, he can't believe yau yaje kofar gidan babban maqiyinshi haryasa hannu yayi knocking din kofarshi. Karya corner yayi ya dauki hanyar bakery dinta yana addu'ar allah yasa tanacan. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Zaune take kan kujerar office dinta hannunta riqeda pen jujjuyashi take a paper. Haka kawai taji yau tana sha'awar zuwa bakery din, tagaji da zaman kadaici da yawan tunani shiyasa ta yanke shawarar zuwa bakery din ko zata samu sauqi amma tunda tazo bata iya komaiba sai zaunen datayi tana jujjuya pen tana karanta wasikar jaki. Yau ne wa'adin data dibarma sadeeq yacika, amma babu alamun nasara. Yanzu ya zatayi? Tasan ko giyar wake tasha bazata iya kai case dinnan court ba don kamar ta kwancema kanta zane a kasuwa ne. Bakowa takejiba sai mamy, koya ta tuna daita saitaji zuciyarta tayi rawa saboda fargaba. Sosai take cikin damuwa dukda tana qoqarin dannewa ko don daddy daya fita shiga damuwa yake kuma blaming din kanshi a koda yaushe. Knocking akayi a kofarta hakan yasa ta saki nannauyan ajiyar zuciya takoma ta jingina da kujerar. "Yes? Come in" Ahankali aka turo qofar aka shigo. Maryam ce sanye da apron fari hannunta riqeda da littafi da pen. "Unhun?" Inji saudart tana lumshe idanu. "Ma'am kinyi baqo" Tsaki tadanja, itafa bata cikin mood din ganawa da baqi "Ok su shigo but please duk wanda tasake zuwa ace banzoba ok?" Tafada tana dan dafe kai. "Ok ma'am" tafada tana fita daga office din. Jimm kadan aka sake bubbugo kofar. Tsaki tadanja "Come in" Maryam ce tasake shigowa da mutum biye a bayanta. Saida mutumin yashigo sannan tajuya tafita. Dagowa tayi daga rubutun datafara kafin su shigo tadan kalleshi ta maida idonta kan littafin tana cewa "You are welc..." cak maganarta ta tsaya da wani abu yazo mata a brain. Saurin dagowa tasakeyi cikin rashin gasgata da mammaki bayyananne. Dumm.. gabanta ya yanke yafadi ganin shi dinne jingine da kofa ya harde hannunshi ya zubamata piercing eyes...✍ Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka qaramana zaman lfy a qasarmu🤲 Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 068 Mutuwar zaune tayi tana kallonshi idanunta adan ware alamun mammaki qarara a fuskarta. Binshi tayi da kallo daga sama har qasa. Sanye yake cikin qananun kaya, tsadadden jeans trouser da top ash mai quntun hannu wanda ya tsaya daidai damtsenshi sai hular da rigar kedashi daya saketa baya, sosai packs dinshi suka bayyana tacikin rigan kasancewar rigar tadan kamashi. Yar sumar kanshi a kwance luff sai qyalli take, sosai yaqara mata kwarjini da haiba Shima a 6angarenshi kallonta yake yana jin wani irin shauqin dabe ta6a jiba na dibarshi yayinda qaunarta ke qara hauhawa acikin birnin zuciyarshi. Jiyake kamar ya saceta ya gudu don kwana biyun nan dayai beganta ba gani yake an chanzata. Sanye take cikin baqar Arabian gown datasha stones agaba kanta yane da gyalen rigar, fuskarta daukeda simple makeup daya qara fiddo ainahin natural beauty dinta. Ita tafara janye idanunta akanshi tana blushing sanadin tunawa da abinda yafaru tsakaninsu a haduwarsu ta qarshe. Nan take ranta yaqara dagulewa, ranta na 6aci. Maida hankalinta tayi ga rubutun datake wanda ayanzu batamasan me take rubutawa ba. Dagowa yayi daga jinginar dayayi da kofar yana kallon yadda taqara tamke fuska tana cigaba da rubutunta. Takowa yayi ahankali cikin usual takunshi na qasaita harya qaraso gaban table dinta. "May I?" Yafada yana kama kan kujerar dake facing din table dinta. Bata dagoba haka zalika bata ansaba amma hankalinta kacokan na kanshi tana sauraron duk wani motsi nashi. Murmushi yasaki sannan yaja kujerar baya ya zauna ya jingina daita hannayenshi harde a faffadan qirjinshi yana zubamata idanunshi masu mugun takurata. Jinta tayi duk atakure don sosai idanunshi ke piercing har cikin zuciyarta don har rawa rawa hannunta datake rubutunda ma bata san nami takeba keyi amma haka ta daure taqi dagowa dukda tanajin yawon idanunshi a fuskarta. Binta fuskarta yake da kallo yana inspecting every part of the face, jiyake kamar yau yafara ganinta. Baya tunanin yata6a ganin macen data kaita komai. She's just too perfect, damn perfect. Jin kallon nason yin yawa yasata dagowa at last ta kalleshi. Sarqewa idanunsu yayi waje guda wanda saida hakan ya haifarmata faduwar gaba sai tayi saurin janye idanun nata gefe tana tsuke fuska. "Yes? How may i help you Mr?" Tafada in a harsh voice. Murmushi yayi mai sauti wanda hakan yasata kalloshi takuma kauda kai. "Good Afternoon ma'am" yafada in a cool voice yana kafeta da idanu. Wani banbarakwai taji wanda hakan yasa tasake dagowa ta kalleshi. Yau ita A.A ke gaisarwa? Harda wani *ma'am*? Hmm wani sabon salon wulaqancine da izgilanci halan? Anyway koma mezaiyi ko zece bazai dameta ba itadai burinta ta rabu da alaqaqai daganan yaje ya rungumi transformer for all she care. "Yes? Get straight to the point, as you can see am busy" tafada avoiding his gaze. Guntun murmushin nan na gefen baki yayi. Bata chanza ba, she's still the proud cute princess, the angry bird. "Am sorry" ya furta ahankali. Dagowa tayi ta kalleshi again cikin mammaki. Wait kodai a make yake? Tambayar datayima kanta kenan. "Am so sorry...very sorry" yasake fada wanda kallo daya zaka mashi kasan har cikin zuciyarshi yake fadin haka. Shiru tayi tana kallonshi batareda ta iya cewa komaiba tana wondering acikin zuciyarta anya A.A data sanine wannan? The proud rude A.A? Ganin yadda ta kafeshi da idanu yasa yayi dan murmushi wanda yaqara mashi kyau sosai Ya miqa hannu ahankali ya amshi pen din hannunta yajawo file din gabanta yana dubawa. Galala tabishi da kallo kamar wata doluwa tana kallon the amaziest thing she've ever saw. Juya file din yayi baya inda ke blank babu rubutun komai akai ya dora pen asama yanadan cije qasan le6enshi. "Am sorry.. for everything" yafada yana kanshi aqasa yana rubutu itakau saudart ta maidashi t.v ko kyaftawa batayi. "For coming into your peaceful life... for not releasing how worthful you are... for the harrasment and tough time i made you went through... for everything. Words can't express how sorry I am... hope you'll find it in your heart to forgive a helpless soul... hope you'll give me another chance" ya tsayar da rubutun still idanunshi nakan file din yana kallon rubutun dayayi wanda duk maganar dayayi ne ciki. Ajiye pen din yayi saman file din sannan ya dago a tsanake ya kalli saudart dako kyaftawa batayi daga kallonshi, hankalinta yakasa daukar abinda ke faruwa. "Mafarki nake?" Tambayar datayima kanta kenan. "No" ashraf ya amsa mata don afili tafada batareda ta saniba. "Ba mafarki bane ba, dagaske ne, am here... seeking for your forgiveness *SAUDARH*, nasan ni mai laifine awajenki, inajin wani iri... wani iri idan na kalleki, am shy, am sorry" yafada yana lumshe idanu yayinda zuciyarshi ke gudu. Tabbas wani irin yakeji don tunda yasan kanshi bezai iya tuna sadda yazauna yaba mutum haquri kamar hakaba, wani abu yakeji a zuciyarshi kamar kunya kunya kamar ya6ace daga office din ya huta. Itama saudart din wani iri takeji. Wannan ba A.A din datasani bane, bawanda tasaba dashi bane, the rude, proud, wicked peacock. Sam bashi bane. Shiru office din ya dauka kowanne feeling awkward, babu wanda ya iya magana acikinsu don basusan abinda zasu sake cewa ba. Saida suka kusa mintuna biyar ahakan sannan saudart da tundazu ke kallon yatsunta tana wasa dasu ta dago ta kalleshi shima daidai ya dago sai suka hada idanu. Kauda kai tayi tareda sakin silent ajiyar zuciya sannan ta muskuta ta fara bude wani file dage daga gefen table din shikuma yabita da kallo cikin tsantsan qaunarta. Zaro wata farar takarda tayi qall wanda babu komai aciki ta turomashi a gaba ta dauki pen din gabanshi ta dora akai. Binta yayi da kallo saikuma ta kalli takardar da pen din sannan yadago yasake kallonta yaga itama shi take kallo. "Let's end this" tafada ahankali. "Ka kawo qarshen komai sai in yafemaka" tafada tana kallonshi. Shiru yayi yana kallonta batareda ya iya cewa komaiba don yadda zuciyarshi ke gudu. Kenan tana still kan bakanta? Kenan she still hate him dukda yayi stooping low yabata haquri yakuma nemi yafiyarta? "Ka rubutamin saki na then I'll forgive you Mr A.A" tafada tana dan janye ido ganin yadda ya kafeta da idanu. "Did you still hate me?" Ya tambaya cikin wani yanayi. Kallonshi tasakeyi sannan ta kauda kai "Ba maganar hatred mukeba" "Tell me, kin tsaneni ko? Kinaji kamar ki kasheni ko?" Ya tambaya mood dinshi na canzawa. "Why? Nina halliceka dazanji kamar in kasheka? Am talking about contract dake tsakaninmu ne not hatred, I want to be free again, inason jina yadda nake ada" Shiru Ashraf yayi yana kallon takardar gabanshi sannan yadauki pen din yariqe sannan ahankali yadora kan takardar yafara rubutu. Wani gauron ajiyar zuciya tasaki tana fesar da iska daga bakinta, farinciki na bayyana akan fuskarta. Bewani dadeba yagama rubutun ya linke takardar ya turamata agabanta yana dora pen din akan takardar yakoma ya jingina da kujerar yana kallon fuskarta that is litted with happiness. Ajiyar zuciya tasake saukewa sannan tasa hannu ta dauke pen din ta ajiye gefe sannan tadauki paper din tafara warware linkin fuskarta dauke da murmushin da batasanma tanayiba shikuma ashraf ya kafeta da ido yana kallon yadda fuskarta ke fitarda annuri just because yabata takarda. Dama har haka ta tsaneshi? Tambayar dayayima kanshi kenan yayinda tausayin kanshi ya lullu6eshi. Ahankali fara'ar fuskarta tafara gushewa ganin abinda aka rubuta sa6anin abinda tayi tunanun gani. Cikin tsarraren handwriting taga an rubuta: *I CAN'T LIVE WITHOUT YOU😢 PLEASE GIVE ME ANOTHER CHANCE👏SECOND CHANCE..* Qara gwala idanu tayi tana qara karantawa unbelievable Dagowa tayi tana kallonshi in shock. "Yes.. i need a second chance" yafada yana kallonta "Second what? Meye kake magana akai?" Ta tambaya still in shock plus 6acin ran daya fara tasomata daga qasan zuciya. "Second chance to prove my *love* to you" "What!" "Yes, *I love you* *I so much love you*" *************************************************** "This is unbelievable!" Inji umma cikin mammaki "Hmm kema kya gani Hajiya zainab, haryanzu nakasa dawowa daidai wlh" inji ummy tana sauke ajiyar zuciya. "Allah mai iko, ji yadda ya hadaku kuma ta hanyar baku ta6a zatoba, tabbas ashraf yayi kuskure be kamata ya saka sharri da sharri ba, amma abinda yayi bekai girman wannan hukuncin da kika yankemashi ba don yayi nadama kuma ai shima a wani 6angaren yanada gaskiya, shifa yayi sanadiyar mahaifinshi dole ya tsaneshi, idanma laifinne ai sadeeq ne me babban laifi tunda maimakon yabashi shawara ya nusardashi saiya biyemashi, zai dawo yasameni ne" inji umma tana kwafa. "A'a hajiya zainab babu laifin sadeeq, koda bebashi goyan bayaba saiyayi abinda yayi niyya nasan halinshi sarai, kuma batun aurensu dolene ya rabu don idan nabari abin ya dore banyi adalciba, kobe fadaman ba nasan ba qaramin abu yakema saudart ba, nasan halin ashraf, idan ya tsani abu yana tsanarshine da dukkannin zuciyarshi. Nasan tasha wahalarshi dukda nasan ba dukkan abinda yaimata ba yafadaman, bata sonshi tayaya nikuma zan jajirce akan dorewar auren? Ita zata cutu dole, ga wahalar datasha abaya and at the end taqare da baqinciki? No badaniba" inji ummy tana girgiza kai "Amma sai inga gwara abarsu Hajiya fatima, Allah kadai yasan dalilin dayasa ya hadasu kuma" "Hajiya zainab inason saudart, ina sonta kamar yadda nakeson baby, bazanso wani abu ya cutar daita ba. Dukda sanin diyar wanene hakan be rage son danake mataba daidai da kwayar zarra, bazan ta6a barin tayi zaman dazata cutuba" "Hmm dukda haka dai mubi sannu, tsakanin ma'aurata sai allah, kar kizo kiji kunya aqarshe" inji umma tana dariya. Murmushi ummi tadanyi sannan tace "Inason naje gidan khadija, inason ganinta" "Hakanma yakamata" "Please ki gayawa Abbansu sadeeq yabarki ki rakani gobe, i really need to see her" "Insha allah zan gayamashi amma kinsan gidanta ne?" "A'a amma baby tasani, saita kaimu" "To allah yakaimu lfy" Da ameen ta ansa sannan suka cigaba da tattaunawa akan lamarin...✍ Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Allah ka bamu zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲 Allah ka ji6anci lamurranmu, karka barmu da kanmu🤲 Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 069 Galala tayi tana kallonshi babu ko kyaftawa yayinda kalamanshi kemata amsa kuwa akunne. Shima kallonta yatsaya yi yanason ganin reaction dinta. Ga mammakinshi saiyaga tasaki murmushi mai sauti ta janye idanunta daga ksnshi tana chuckling don ita nothing make sense to her, this is total madness. Murmushi mai ciwo yayi ganin yadda take dariya qasa qasa. Wato ga mahaukaci, kodayake duk wanda yasan yanayin zamansu ada yakuma ji abinda yakecewa yanzu saiya yimashi daukan mahaukaci. "Is it funny?" Ya tambaya yana kallon yadda dimple dinta ke lo6awa. "Very funny" tafada cikin dariya. Murmushin nan nashi yasakeyi "It may sound funny amma am not joking..am serious" "Yes, it's a joke, a cheap joke" tafada murmushi akan fuskarta "Saidai yanzu ba lokacin barkwanci bane, we're discussing a serious issue, magana ta hankali" tafada tana gimtse fudskarta daga murmushin datake. Ajiyar zuciya ya sauke, dama yayi tsammaci hakan ko fin hakan ma "Am damn serious *SAUDARH*, nasan bata haka yakamata in fadamakiba, wataqila I sound straight forward or non-romantic...amma ki yarda dani, abinda nake fada yana zuwane from the bottom of my heart. Saudart I love you, I love you so much.. i can't deny it anymore" yafada emotionally. "Really? Yaushe? Kuma tayaya?" Tafada cikin izgili tana mashi wani kallon sama sama. "I don't know... bansan how and when ba.. all i know is Ina sonki" "Mtcheew, look Mr man, kamar yadda kagani ina busy lokacin daka shigo, inada aikin yi dayawa so karka nemi rainamin hankali. This damn thing should come to an end now! It ought to...nagaji!" Tafada fuskarta nayin jajaja don 6acin rai. "Saudart..." "Enough!" Ta katseshi tana numfashi ahankali ahankali, idanunta na forming din ruwa. "Kai kafaro komai, now end it!" Tafada cikin cracking voice Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda take kokowa wajen ganin ra tare hawayen dasuka cika idanunta daga zubowa. Yasan yadda takeji, she's in pain, kallo daya zaka mata kagane hakan. Cikin kwantar da murya wanda yafi kama da rad'a yace "Saudart I can't... bazan iyaba, nasan sonki jarabtace daga ubangiji, bansan sadda nafara kuma banajin akwai ranarda zan bari.... wannan hannun..." yafada yana kallon tafikan hannunshi "Bazasu iya rubutamaki abinda kikeso ba, yatsuna bazasu iya riqe pen ba dasunan datse abinda yayi bonding dinmu..am sorry" Dafe kanta tayi cikin tsananin takaici da baqinciki ta sadda kanta. "Saudart i know kin tsaneni, kibani dama...second chance don na nunamiki soyyayar danake miki, second chance don goge baqin fenti nawa acikin zuciyarki.. Let me love you" Hawayen datake dannewa ne suka kufcemata suka gangaro kan kumatunta. Jin kowanne kalma nashi take kamar digar darma a kunnuwanta. Tarasa meta tsaremashi, wane laifi tayimashi daya za6i quntatawa rayuwarta. Dagowa tayi ahankali ta kalleshi da rinnanun idanunta dake sheqin hawaye, ziciyarta na zafi. Shima kallonta yake yanajin kowanne digar hawayenta harcikin zuciyarshi, idanunshi suka fara chanza kala yanajin kamar shima yafara zubda nashi hawayen. "Why?" Ta tambaya cikin rad'a Lumshe idanu tayi taba hawayen dasuka cika idanunta damar gangarowa sannan tabude tasake kallonshi "Who are you?" Tafada muryarta na rawa. "Dama ka sanni ne? Na ta6a maka wani abu ko? You're purnishing me right?" Tafada tana lumshe idanuwanta tana shesheqan kukanta marar sauti. Kamo tender hannayenta dake kan table yayi ya riqe yana kallonta shima zuciyarshi na zafi. Bude idanunta tayi ta kalli hannayenta dake cikin nashi wanda jitake kamar rushin garwashine jikin hannun sannan tadago takalleshi batareda tayi qoqarin janye hannunta ba. "Ka tsaneni ko? Ka tsani ka ganni cikin farinciki da walwala ko? Tell me" tafada muryarta nadan siezing. "No, never! Bazan iya tsanarkiba... ban ta6a tsanarkiba" yafada almost cikin rada yana kallonta da idanunshi dasuka kada. "Then..why are you...hunting my life? Me..nayimaka?" Tafada wasu sabbin hawayen na gangarowa daga idanunta. "Babu.. babu komai, nine dai nayimaki...am sorry for coming into your life" yafada softly still hannunshi riqeda nata. Sadda kai takumayi tana dan shesheqan kukanta marar sauti tanajin duk duniya babu wanda zata yiwa tsana kwatankwacin wannan datakema ashraf. Murza hannunta yayi ahankali yana jin shesheqanta harcikin ranshi. "Saudart please stop crying, nasan you hate me, nasan kin tsaneni, please kibani dama na musanya wannan qiyyayar zuwa soyyaya..please" Dagowa tayi ta kalleshi da jiqqaqun jajjayen idanunta "Dagaske?...dama kasan na tsaneka?" Ta tambaya tana kallonshi "Yes saudart, kinsha fadamin kuma nasha hangowa acikin qwayar idanunki...dan allah kiban wata damar, please" Kada kai take ahankali tana hadiyar abinda ya tokare mata maqoshi "Zaka iya misalta adadin qiyyayar danake maka?" Tafada tana kafeshi da jajjayen idanunta. Shiru yayi yana kallo yadda ta kafeshi da idanu Girgiza kai yayi ahanksli kamar yayi kuka "A'a" yafada helplessly a raunane Itama girgiza kanta tafarayi wasu sabbin hawaye na 6allemata. "Nima haka... baxan iya misalta qiyyayar danake makaba ada.. saidai yanzu ina iya cewa...qiyyayar danake maka ada batakai kaso daya cikin kaso goma danake makaba yanzu. Ashraf I hate you! I hate you so very much! Ban ta6a tsanar wani mahalukiba yadda na tsaneka kuma banajin zan ta6a tsanar wani kamar haka... i hate you more than death itself. I hate you!!!" Taqarashe cikin kuka mai sauti sosai ta sadda kanta kan table tanayi da dukkanin zuciyarta. Lumshe idanunshi yayi ahankali wani zazzafan hawaye ya gangaro kuncinshi yanajin kamar ya cire zuciyarshi ya huta saboda radadin datake mashi. Sakin hannunta yayi ahankali jikinshi na rawa rawa yana sauraron sautin kukanta yana kallon yadda take jujjuya kanta akan table. "Leave, banason ganinka! Please leave!!" Tafada cikin ihun kuka. Rufe fuskarshi yayi da tafikan hannu yana tamke idanunshi yanajin dama shima zai iya kukan da babu abinda zai hanashi 6are nashi bakin yafara shar6a nashi. Tashi tayi da sauri ta shige toilet din office dinta aguje cikin kuka sosai ta rufo kofar. Maida kanshi yayi shima kan table din yanadan jujjuyawa yana ambaton sunan Allah acikin zuciyarshi don jiyake kamar zata tarwatse. Wajen sink ta qarasa dagudu ta dafashi tana gunjin kukanta. Ashraf yazame mata qarfen qafa, yazame mata alaqaqai, yana naiman karta lokacinta beyiba. Yazatayi dashi? Yazatayi ta rabu dashi? Wannan wace iriyar qaddarace?. Yadade ahakan yana ambaton sunan allah a zuciyarshi harya samu tayimashi dan sanyi sanyi. Tashi yayi ahankali yana dafa kanshi da ciwon kai yadawomashi sabo yajuya yanufi hanyar fita dafe dakai. Bude kofar yayi yafita batareda yama iya rufo kofarba ya ratsa tacikin mutanen daketa hidiman gabansu harya samu yafito waje. Kamar dan qwaya haka ya qaraso wajen motarshi ya bude yashiga sannan yarufo ya saka key hannunshi nadan rawa rawa ya tada motar sannan yawani figeta yabar harabar wajen da wani irin speed. Tuqi yake amma har wani biji biji yake gani sanaddiyar saran da kanshi kemashi. Wayarshi yaciro da hannu daya ya kunna yashiga contact yayi dialling din number sadeeq yana cizon le6en qasanshi da qarfi. Saida takusan tsinkewa sannan aka daga. "Hello?" Inji sadeeq daga can 6angaren "Sadeeq she hates me, ita dakanta tacemin bata iya misalta qiyyayarta agareni ba...sadeeq I want to..die" yafada cikin cracking voice. Miqewa sadeeq yayi daga zaunan dayake a office ba shiri jin yanayin maganar ashraf. "Ashraf! Menene? Ummy ce? Talk to me!" Yafada a gigice yana daukar keys din dake kan desk dinshi yana nufan kofa. "Saudart ce sadeeq, i love her...she hate me...zuciyata zafi" yafada still yana tuqin "Subhanalillah! Ashraf kuka kake? Tell me ina kake?" Inji sadeeq yana nufan elevator dagudu. Hannu ashraf yasa yashafo kumatunshi ya kalla saiyaga lema alamun kukan yake. Be amsaba sai katse wayar dayayi yajefata bayan motar yaqara speed kamar zai tashi sama. Jin wayar ta tsinke yasashi saurin qara bin jiran amma bata shiga hakan yasa hankalinshi qara tashi. Hannu na rawa ya danna last floor elevator din yabude yafada ciki yana addu'ar allah ya tsare ashraf don beta6a jinshi cikin irin wannan yanayin ba. "And nagayamashi zan rakashi amma yaqiya, ai ga irintanan" yafada restlessly yana dan zagaye zagaye a elevator din yanajin kamar va tafiya yakeba. Elevatorn ba tsayawa yayi saurin fitowa yayi parking space dagudu ya bude motarshi yashiga ya kunnata yayi reverse. Saida taci kukanta ta qoshi sannan ta dago ahankali ta kalli mirror din jikin sink din tana kallon yadda fuskarta tayi jaa ta kumbura. Kunna fanfon tayi ta tara hannunta ta debi ruwa ta wanke fuskarta sannan tajawo hand towel dake rataye awajen ta tsane fuskarta sannan tafito tana dan layi saboda yadda kuka yayi exhausting din qarfinta. Jakkarta kawai tabude ta watsa wayoyinta aciki sannan ta zage ta ratayeta tasaka sunglass dinta wanda yarufe asirin kumburan da idanunta sukayi tafito don batajin zata iya qara koda minti dayane a bakery din. Haduwa sukayi da maryam data fito daga wani office "Ma'am fita zakiyi?" Injita tana kallonta. Kanta kawai ta iya kadamata ta fice da sauri itama ta bude motarta tashiga ta kunna itama tafice daga bakery din...✍ Manage please👏 Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Happy edl-mubaraq fans🧚🏻‍♀️ Fatan anyi sallah lfy, fatan kuma ba'ayiwa nama cin rashin mutunci ba😏 Kodayake ai ko kunyima zai rama ne😆 Am back again, masu cigiyata ngd, masu kira kudos🤙🏻 Ashaanty loves you😍 070 Tuqi yake amma yarasa inda zai nufa, besan inda zai fara nemanshi ba. Fatanshi daya shine Allah yasa kar yace zaiyi driving acikin wannan halin. *saudart ce sadeeq, I love her... she hate me... zuciyata zafi* Maganar Ashraf tadawo mishi. Kenan sun hadu? Definately sun hadu, yabama kanshi tabbaci. Karya motarshi yayi yakama hanyar gidansu saudart. *wannan hannayen.... bazasu iya rubutamaki abinda kikeso ba* *yatsuna bazasu iya riqe pen ba dasunam datse abinda yayi bonding dinmu ba* Cize le6enta naqasa dasukayi jaa saboda kuka tayi tana lumshe idanu don ba hawayen dasuka qara forming a idanunta damar gangarowa. Zafi takeji a zuciyarta marar misaltuwa, she can't believe yau itace abin wasa, abin toying. Ita zai nunama isa da iko? Dama yace zai nunamata koshi wanene, dama abinda yake shiryawa kenan? Dama burinshi ya daqilemata duk wani farinciki nata? Burinshi ya ganta cikin dawwamammen qunci? Bayan hannu tasa ta sharce hawayen fuskarta ta cigaba da tuqin wanda allah allah take ta isa gida don tuqin ma yafara gagararta. Jin motsin mutum na kusanto gate din yasashi tsagaitawa da knocking din yana kallon ruffafen gate din. Qaramar kofar gate din aka bude fuskar maigadin ya bayyana. Ganin sadeeq yasashi washe baki don be manceshi ba kuma ranan dazai tafi saida yaimashi alhairi. "A'a? Kaine?" Shima sadeeq cikin fara'a yace "nine wlh, barka da warhaka" "Barkanka dai, ya aiki?" "Alhamdulillah" yafada yana gyara tsayuwarshi "Erm... tananan?" Ya tambaya "Wlh kau yau kayi rashin sa'a, yau tunda safe hajiya tafita, dazunma wani yazo nemanta saidai tafiya yayi" Dan daga gira sadeeq yayi 'Wani? Could that be Ashraf?' Uban horn din da aka danna ta bayanshi ya katse mashi guntun tunaninshi. Tare suka waiga shi da maigadin don ganin wanene ke shirin dodemasu kunnuwa. "Yar halaq gatanan" inji maigadin yana komawa ciki da sauri don budemata babban kofar gate din. Bin motar sadeeq yatsaya yi da kallo na yan daqiqu sannan yatako a nitse ya nufo motar. Gab da zai karaso ta sake tada motar ta figeta tashige cikin gidan kasancewar har anbude gate din tana badeshi da kura. Bin motar yayi da kallo yadan girgiza kai sannan shima ya maramata baya. Sadda yashigo harta fito daga motar. Kallo daya zaka mata kasan ba lafiya ba. Zuwa tayi zata giftashi ta wuce batareda tanuna tasan an dasashi awajenba "Miss saudart.." yafada ganin zata wuce Ko iskan daya kwasoshi bata kallaba tacigaba da tafiyarta. Binta yayi yana cewa "Good day miss saudart.. please listen to m..." Kasa qarasawa yayi ganin ta tsaya cak daga tafiyar datake kamar wanda aka tsaida da remote. A nitse ta juyo ta kalleshi ta cikin sunglass din idanunta sannan ta kalli saitin gate ta kwalawa maigadi kira cikin muryar da bata ta6a yimashi amfani dashi ba. Da sauri maigadin ya iso wajensu yana dan russunawa cikin girmamawa. "Wayace ka dinga shigo da kowacce shara agidan nan?" Ta jefa mashi tambayar cikin tsuke fuska. Dan dagowa maigadin yayi ya kalleta a mammakince don wulaqanci ba halin saudart bane shi shaidane. "Ayi haquri.. gani nayi.." Katseshi tayi ta hanyar daga mashi hannu. Sannan ta nunashi da car key din hannunta. "Kasake barin irin wadanan gabbages din shigowa gidannan... believe me abincinka yaqare a gidannan, now ka gwadamashi hanyar fita" "To..to hajiya insha allah" inji maigadin a sanyaye. Juyawa tayi zata wuce saikuma ta tsaya daga takunta tana dan cije le6en qasa. Juyowa tayi a nitse ta kalli sadeeq dashima ita yake kallo expressionless. Cikin sanyin murya mai shige da rada tace "Zan gwadamashi... zan gwadamashi mata ma suna suka tara, zan gwadamashi ba kowa zaka iya takawaba kuma ya taku... he's playing with fire and he'll get burns. I'll made life a living hell to him.... *mark it*" Tana kaiwa nan tajuya tawuce. Binta da kallo sadeeq yayi harta shige sannan ya dauke kai daga barin kallonta yana sauke ajiyar zuciya. Maigadi dake tsaye haryanzu yace "Kayi hqr amma wannan ba halin hajiya bane, qila 6atamata rai akayi waje" Kallon maigadin sadeeq yayi sannan yadan saki murmushi "Ba damuwa ai" yafada yana saka hannu cikin aljihu ya fiddo kudi yaba maigadin. Qin amsa maigadin yayi dafarko saida sadeeq ya 6atarai sannan ya amsa yana kwarara mashi godiya sannan yarakashi haryaga tashin motarshi sannan ya maida gate din yarufe. Ahankali take taka stairs din kanta qasa harta kai qarshe sannan ta isa bakin kofarta tasa hannu cikin sanyi ta murda yabude tashiga. Maida kofar tayi ta rufe sannan ta jingina da kofar tana sakin jakkar hannunta a wajen tareda lumshe idanunta dasuke mata yaji yaji tsabar zubda hawaye. Wannan wacce iriyar qaddarace? Ashraf qaddarartace tasani, tun shigowarshi arayuwarta tarasa walwalarta da farinciki. Tasan qar6ar kowacce iriyar qaddara yana cikin cikon imani amma bata tunanin zata iya qar6ar wannan qaddarar. Bazata iya zama cikin qunci ba tsawon rayuwarta ba, bazata iya zama da wanda ita kanta batasan iya tsanar datake mishiba. Wannan be dauki dan adam a bakin komaiba, wanda besan darajar iyaye ba. Zata iya rungumar kowacce qaddara amma banda wannan, banda wannan baqar qaddarar. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Tuqi yake amma kallo daya zaka mashi kaga damuwa qarara a fuskarshi. Wannan wacce iriyar qaddarace? Tausayi suke bashi dukkansu, yasan they are having tough time dukkansu. Kofar gate din gidan yatsaya akayi scanning dinshi sannan ya shiga. A mammakince yake kallon motar dake tsaye a passage wanda ko arxiqin a qarasa da ita parking space bata samuba. Saurin tsaida motarshi yayi yafito yanufi motar. Kasancewar tinted ne glasses din motar be hangen naciki hakan yasashi bubbuga glass din 6angaren driver ahankali. Shiru... hakan yasashi qara bubbugawa nan na tsit. Duqowa yayi yana leqe ta baqin glass din kozai iya hango mutum ciki. Hangowa yayi dishi dishi kamar mutum hakan yasashi sake bubbuga glass din. Zaune yake cikin motar kanshi kife da sterring din motar. Dakyar yasamu yakawo kanshi gida inda ko qarasawa parking space yakasa ya tsaya anan. Duk bubbugar glass din da'ake yanaji amma beda kuzarin motsawa, he's so weak har cikin zuciya, jinshi yake kamar marar lakka. "Ashraf...Ashraf open up" inji sadeeq yana bubbugawa yana leqenshi at the same time. Shiru ashraf yayi don be iyawa, da yana iyawa da be dauki tsawon lokaciba a zaune haka ba. Ganin beda niyyar motsawa yasa sadeeq miqewa yanufi cikin gidan da sauri, shi tsoronshi ma kar ace asume yake. Dakin ashraf yashiga ya nufi locker dayake aje keys dinshi. Kwasosu yayi batareda ya tsaya dubawaba yayo waje cikin sassarfa. Agefen drivern yakoma ya saki keys din qasa yashiga lalluben spare key din motar. Dakyar yagano key din sannan ya tashi ya zira a motar yabude. Gabanshi ne yafadi ganinshi zaune kanshi kife da sterring. "Subhanallilah! Ashraf?" Inji sadeeq yana dagoshi. Kamar marar lakka haka ya fadamashi ajiki yana sauke numfashi mai nauyi. "Ashraf? Are you ok?" Inji sadeeq yana nishi dakyar a dalilin nauyin da ya sakarmashi. Shiru kuma be bude lumsassun idonshi ba. Ganin haka yasashi qoqarin fiddoshi a motar. Dakyar ya fiddoshi ya ratayo hannunshi a wuyanshi yana qoqarin gyara tsayuwarshi. Sake tamke idanunshi ashraf yayi saboda ranar dake hasko saitin fuskarshi wanda hakan ke qaramashi sarar da kanshi kemashi. Dakyar sadeeq yasamu yakaishi falon ya kwantar dashi kan three seater ya dora kaffafunshi sama tareda zaremashi takalmin kafarshi sannan yadawo saitin fuskarshi ya zauna ya riqo hannunshi cikin tausayawa, ganin kamar yanajin sanyi yasashi daukar remote ya kashe A.C din dakin yadawo kusadashi yana dan murza hannunshi. "A.A are you ok?" Shiru.. "Bari nakira doctor" yafada yana zaro wayarshi. Ahankali ashraf yashiga girgiza kai idanunshi still a lumshe, shi kadai yasan abinda yakeji. "No ashraf kana buqatar doctor" inji sadeeq yana laluban number wayar Dr. Bece komaiba sai hawayen dasuka sulalo ahankali daga rufaffen idanunshi suka gangaro mashi. Babu abinda ke yawo kuma yake amo a kwanyarshi sai kalmomin saudart na daxu. Ganin hawayen ashraf yasa hankalin sadeeq ida tashi. Rungumoshi yayi sosai jikinshi cikin tausayawa "Ashraf please take it easy..insha Allah komai zaiyi daidai please" yafada cikin karyayar murya Shidai ashraf be tankaba yananan yadda yake sai hawayen dake zuba daya bayan daya. Suna haka Dr yazo. Da taimakonshi aka kamashi suka kaishi daki, izuwa yanzu jikinshi yayi rau kamar garwashi. Kwantar dashi sukayi sannan Dr yashiga dubashi sadeeq na gefe yana kallonsu cikin mutuwar jiki. Drip ya daura mashi yayimashi allurar barci sannan ya rubuta masu magunguna. Zaune sadeeq yayi gabanshi yana kallon cute face dinshi, tunda yake beta6a ganin ashraf cikin makammanciyar damuwa irin wannan ba, jiyake kamar ya daukemashi abinda yakeji ya maidoshi jikinshi. Qara kiran wayar ummy yayi karo na uku amma ba'a dagaba kamar sauran. Ajiyar zuciya yayi ya ajiye wayar ya zabga tagumi yana kallon sleeping ashraf kamar mirror. A taqaice dai ranar takasance ranar qunci garesu, damuwa qararra ya bayyana a rayuwar wadannan bayin allan, Dakyar sukaga wayewar garin. WASHEGARI Jin bubbugar bata hankali bane yasata katse lazumin nata tamiqe da sauri ta nufi kofar tabude. Baby ce ta fadomata ajiki tana kuka sosai. Saurin dagota ummy tayi tana kallonta "Meye haka? Lafiyarki kuwa?" Cikin kuka baby tace "Ummy... yaya ashraf" saikuma tafashe da kuka "Wai menene? Meya sameshi?" Inji ummy hankalinta na dan tashi "Beda lfy... yanzu haka suna hospital" tafada cikin kuka sosai. Shiru tayi saidai kallo daya zaka mata kasan hankalinta atashe yake. "Ummy please muje...karya mutu" tafada cikin kuka sosai "Jeki shirya maza" inji ummy tana komawa ciki itama don shiryawa. Hankalinta yatashi matuqa. Ita bazata iya tuna rabon ashraf da kwanciya asibiti ba. He's always healthy and energetic, ba qaramin abu zai kwantar dashi ba. "Ya rahman.. take control tafada tana daukar purse dinta tayo waje suka hade da baby suka nufi waje cikin sauri.....✍ Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 071 Zaune yake jigum ya zubamashi idanu yana kallon yadda yake sauke numfashi ahankali na barci. Sosai jiya cikin dare ya tsoratashi don giggicewa yayi da ganin yanayinshi. Tunda Dr yayimashi allurar barci be tashiba sai wajajen takwas na dare. Lafiya lau ya tashi yaci abinci ya rama sallolinshi yasha magani sannan yakoma ya kwanta. Shima sadeeq ganin hakan yasa hankalinshi kwanciya har yasamu damar kwanciya shima. Can cikin barci yaji sautin tari babu qaqqautawa wanda hakan yasashi watsakewa ba shiri. Ashraf yagani zaune yana tari tafin hannunshi dafe da qirji yanata tari babu qaqqautawa. Bashiri ya duro daga gadon ta zagayo wajenshi yana riqeshi ganin yadda jikinshi ke rawa. Sosai hankalinshi ya tashi nan yaita jeramashi sannu. Ganin tarin yaqi tsayawa yasashi sakinshi ya nufi dan qaramin fridge din dakin yaciro ruwa ya tuttula a cup yadawo da sauri ya samashi abaki yasha ko tarin zai lafa. Cikin ikon allah sai tarin ya lafa sai sauke ajiyar zuciya dayake dakyar idanunshi sun kada sun tara ruwa. "Sannu Ashraf" inji sadeeq kamar zaiyi kuka Dagowa yayi a kasalance ya kalleshi batareda yace komaiba yakoma ya jingina da kan gadon. "Sannu Allah yabaka lfy" yasake cewa cikin tausayawa. Lumshe idanu kawai ashraf yayi yana sauke ajiyar zuciya "Meke damunka yanzu?" Inji sadeeq. Bude kod'add'un idanunshi ashraf yayi ya kalleshi sannan ya dafa saitin zuciyarshi yana dan shafawa "Za..fi" yafada ahankali cikin muryarshi da baya fita sosai Kamo hannun daya dafa qirjin dashi sadeeq yayi yana dan murzawa cikin tsananin tausayinshi. Idan da wani zai ta6a gayamashi abokinshi kuma dan uwanshi zai ta6a fadawa cikin irin wannan halin saboda mace da ya qaryata amma gashi yana gani da idanunshi. Shi shaidane, iya zamanshi da rayuwarshi da ashraf yasan komai gamedashi. Ashraf mutum ne da idan yanason abu yana sonshine da dukkanin zuciyarshi haka zalika idan yaqi abu yana qinshine da dukkannin zuciyarshi ataqaice dai be iya son abu ba, be iya qallafar abuba haka allah yayishi. "She... hate..me" ashraf ya katsemashi guntun tunaninshi "Nima...na... tsani...kaina" yafada yana sake lumshe idanunshi "No ashraf, please kabar wannan maganar, you're ill" Bude jajjayen idanun yasakeyi ya kalleshi a gajiye "Na cancanci tsanarta, don't I? Kullum saina sata kuka..." "It ok ashraf, nace kabar magana" sadeeq yasake katseshi "I want..to die" yafada yana sake murza qirjinshi dake mashi zafi kamar ana hura wuta. "Ashraf please kabar magana nace, haba? Kanason..." Tarinshi ne ya katseshi wanda yasake tasomishi yacigaba dayi babu qaqqautawa wannan karon ruwa be lafarmashi dashi ba. Hankalin sadeeq yakai qololuwar tashi. Ganin abun nayine yasashi kiran Dr wanda saida yajeramashi kira biyar kafin ya daga kasancewar cikin darene don har uku ta gota. Cikin daren Dr din yafito yazo gidan suka dauki ashraf dayayi matuqar galabaita suka sakashi mota sai hospital. Dakyar suka samu suka shawo kanshi sai gab da asuba barci ya figeshi sanadiyar allurar barci da aka sake danna mashi. Sai a sannan sadeeq yasamu hankalinshi yadan kwanta yaje yayi sallar asuba, gari na ida wayewa yakira baby ya gayamata. Ringing din wayarshi yadawo dashi daga duniyar tunanin daya lula. Dauka yayi ya daga ganin ummy ke kira. Gaisheta yafarayi a girmame, saida ta amsa sannan ta fadamashi gasunan hospital din yazo yashigo dasu. Tashi yayi yafita don shigowa dasu. A reception ya taddasu tsaitsaye kallo daya yayima baby yasan tasha kuka don fuskarta ma ta isa ta baka amsa. Sake gaida ummy yayi sannan yayimasu jagora har zuwa dakin da ashraf ke kwance yana barcinshi peacefully. Dagudu baby ta qarasa bakin gadon tana toshe bakinta don hana kukanta fitowa tana kallon yadda fuskar yayan nata yayi so pale. Ahankali itama ummy ta qaraso dayan gefen gadon tana kallonshi tanajin wani abu na ta6amata zuciya. Kallon fuskarshi take datayi fayau tana hango dan fadawar dayayi na kwana biyu. Ahankali tasa hannu tashafi lallausan gashin kanshi cikin tausayi da qaunarshi. "Me Dr yace ke damunshi?" Inji ummy batareda ta daina kallonshi ba. Sadeeq dake gefe tundazu ya sauke ajiyar zuciya yace "Damuwa... cewa yayi yana stressing din zucuyarshi da damuwa ne" yafada shima yana kallon sleeping ashraf din. Kafin wani yasake magana acikinsu kofar dakin ta bude Dr yashigo. Juyowa sukayi dukkansu suna kallonshi, ganin ummy yasashi qarasowa yana murmushi. "A'a Hajiya? Yaushe kuka zo?" Janye hannu tayi daga shafamashi kan datake tana maida mashi martanin murmushin nashi tana cewa "Yanzu wlh... ya aiki?" "Alhamdullilah Hajiya antashi lfy" yafada cikin girmamawa "Lfy lau.. ya mai jiki?" "Alhamdullilah, as you can see tarin ya lafa, yasamu barci, insha allah lokacin da zai tashi everything will be ok" yafada yana qarasawa wajenshi yana dafa kanshi. Gwaje gwaje yadanyi mashi sannan ya gyaramashi drip dinshi sannan ya buqaci ummy tabiyoshi office zaiyi magana daita. Babu musu ta maramashi baya suka fita. Bayan fitarsu sadeeq ya dago ya kalli baby dake gefen ashraf tana matsar qwalla. "It ok angel... everything will be ok" yafada a tausashe cikin sigar rarrashi. Dago watery eyes dinta tayi ta kalleshi sannan ta saddasu tana saka bayan hannunta tana share hawayenta. "Hajiya gaskiya damuwace tayima danki yawa, dagani wani abune yasa aranshi har yake neman illata mashi zuciya don sosai yake stressing din zuciyar... yakamata a kula please, seems he have a tender heart wanda abu kadan zai illatata if care is not taken, yanzu munsamu komai yadawo normal, munmashi allurar barci kuma munasaka ran lokacinda zai farka zaiji sauqi zamu riqeshi a hospital mucigaba da kula dashi harya warware gabadaya insha allah" Ajiyar zuciya ummy daketa sauraronshi tundazu tayi sannan tace "To Dr mungode qwarai" "Yanzu yakamata asamarmashi abinda zai dan ci idan yatashi don zai buqaci hakan and please aguji 6atamashi rai hajiya, adinga kwantarmashi da hankali yadda zamu samu ya ida warkewa sumul" "Insha allah doctor" inji ummy tana kada kai. Dakin suka sake komawa inda suka tadda su sadeeq kamar yadda suka barsu saidai yanzu zaune baby take kan wata plastic chair kuma tabar hawayen. Umarni ummy taba baby kan taje su hadamashi break su kawo nan ta fadama sadeeq shima yaje gida ya huta hakanan ita zata zauna dashi. Da to duk suka amsa suka fita inda sadeeq yawuce da baby gida. Jawo kujera ummy tayi ta zauna kusada gadon tana kallon dan nata abubbuwa namata yawo a zuciya tana tuhumar kanta na tsauraramashi. Tasan yadda Ashraf ke taka tsantsan da gudun 6acin ranta, koyaya ra chanza fuska saiya shiga taitayinshi. Irin wadannan yaran ne da suke tsoron 6acin ran iyayensu ko yayane, basu qaunar suga 6acin rai a tattare dasu komai qanqantarshi. Wataqila she's so harsh on him, wataqila ta tsauraramashi dayawa. Amma kuma ko menene tayimashi shi yaja, tasan yanada kwakwarar hujja na daukar fansa kan Alhaji shamsu saidai bataga hujjarshi na hadawa da innocent diyarshi ba. Bataga dalilin dayasa zai jata a abinda batada masaniya akai ba, ya lallatamata rayuwa da wani banzan dalili nashi. Ta tausayawa halin daya shiga amma hakan bazaisa taso kanta dayawa ba, bazata ta6a bari sucigaba da zaman cutarwa ba, bazata tilastawa saudart zama dashiba koda kuwa hakan na nufin zai wahala fiyeda haka. Tasan yafara sonta, tun a reaction dinshi sanda ta nemi ya kawomata takardarta. Tasan be iya son abuba kuma yana matuqar wahala idan ya kwallafama abu rai besamu ba. Saidai hakan vazai sa taso kanta ba ta tauye haqqin diyar wasu. Yadda takejin son nata dan da tausayinshi haka suma iyayen nata sukeji koma fiyeda hakan. Ajiyar zuciya tasake saukewa tana qara kallon face din ashraf zuciyarta na saqa da warwara....✍ Manage🙏 Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 072 Ahankali yafara bude idanunshi dayaji sun qaramashi extra nauyi. Dishi dishi yafara gani dafarko sannan yafara ganin clearly. Bin dakin yashiga yi da kallo yanason gane a ina yake. Idanunsu suka sarke dana Ummy dake kallonshi shima. Gabanshi ne yafadi wanda hakan yasashi yunkurin tashi da sauri. Saurin tashi ummy tayi itama tana dafashi. "Easy, kabi sannu you're still weak" tafada cikin kulawa tana jingina mashi pillow abaya don ya jingina. Ahankali ya jingina da pillon yana bin ummy da kallo kamar yanason tabbatarwa kanshi ita dince. "Ya jikin?" Tafada softly Gyada kai kawai yayi yana kallonta Shafa kanshi tayi tana dan murmushi "Allah ya qara sauqi kaji? Bari nakira Dr" ta tashi tanufi waje yabita da kallo harta fice. Ajiyar zuciya ya sauke yanajin kamar anyi lifting wani qaton dutse daga saman qirjinshi. Bin dakin yashigayi da kallo wanda ya tabbatarmashi hospital yake. Ajiyar zuciya yasake saki yana komawa ya jingina sosai da pillon dake bayanshi yana tuna abinda yafaru jiya. Shi kadai yasan abinda yakeji jiyan nan don qirjinshi inbanda zafi babu abinda yake, jiyake kamar ana iza wutane a qirjinshi amma yanzu alhamdullilah yarage sosai sai dan abinda ba'a rasa ba. Bude kofar da'akayi yasashi dagowa yana kallon kofar. Baby ce tashigo riqeda basket din abinci abayanta kuma sadeeq ne cikin wasu kayan da alamun yayi wanka ne riqeda qatuwar leda dake shaqe da kayan itace. Da sauri baby ta qaraso bakin gadon ta ajiye basket din ta kamo hannun ashraf murmushi fall fuskarta. "Yaya you're awake?" Tafada cikin murna Guntun murmushi kawai yayimata yana dan lumshe idanu. Qarasowa shima sadeeq yayi yana fadin "Inyee gawa taqi rami? Ai harna fara cinikin gero shine dan baqinciki ka tashi?" Yafada shima yana ajiye ledar hannunshi kan locker dake kusada gadon ashraf. Murmushi kawai ashraf yayi don haryanzu beda kuzari sosai. "To saika fasa don yayana ko turwa ta shafa mashi lfy a taurin rai, sai yafara shan naka gumbar kafin asha tashi" inji baby tana murgudamashi baki. Dan waro idanu sadeeq yayi yana rufe bakinshi da tafin hannu "Iyee? Dama fatan dakike mani kenan? Kodayake ke zaki kwan ciki, kizama bazawara nabarki da maray..." Waro idanun da baby tayi yasashi saurin sakama zancenshi full stop yana wulwulga idanu cikin rashin gaskiya. Ashraf dai kallonsu yake kallon tuhuma, ganin haka yasa baby saurin duqawa ta ciro flask din cikin basket din tana yaqe. "Yaya bari ba hadamaka tea" tafada tana dorawa kan dayan lockern dake dayan 6aren "Nikuma na hadama fruits" inji sadeeq yana satan kallon baby dake antayamashi harara qasa qasa yana qumshe dariya. Shidai ashraf bece komaiba sai binsu kawai dayake da kallo Suna haka kofar ta bude ummy da Dr suka shigo. "A'a? Tare kuka dawone?" Inji ummy tana qarasowa "Eh wlh, zuwa nayi nai wanka na shirya nakoma na daukota" inji sadeeq yana dan sosa qeya. "To yayi, tea kike hadawa?" Ta tambayi baby dake riqe da mug din shayin tana jujjuya tea din da spoon "Eh ummy" tafada tana kallon Dr dake duba Ashraf. Saida yagama yan gwaje gwajenshi sannan ya ciromashi magungunnanshi yace abashi yasha idan ya karya sannan ya ciremashi empty drip din yafita. Bowl aka fara kawomashi yayi brush aciki don beda qarfin dazai tashi yaje toilet sannan aka bashi tea din don yasha. Kauda kai yayi kawai yana satan kallon ummy qasa qasa. Itama kauda kai tayi don tasan abinda yake nufi. Ganin haka yasa jikinshi yin sanyi ganin kamar still tana fushi dashi. Dagowa yayi yamiqa hannu zai amshi mug din ummy tarigashi amsa taja kujera ta zauna gabanshi ya debo a spoon tadan hura sannan takaimashi a baki. Dagudu ya bude bakin yana bin fuskarta da kallo, harara ta gallamashi tana sakamashi spoon din abaki, murmushi ya su6ucemashi yayi saurin sunkuyar dakai yanayi. Agefe kau baby sai antayama sadeeq harara take shikuma yana dariya marar sauti harda gwalo. Haka ummy taita feeding dinshi harya qoshi sannan ta dago dan cewa sadeeq yabata magungunnan sai gani tayi yanata dariya marar sauti kamar sabon kamu. Kallon baby tayi ganin direction dinta yake kallo taga ashraf ma ita take kallo wanda itama saida taga ummy zata waigo tayi saurin maida kallonta kan ashraf din. Maida kallonta tayi ga sadeeq daya nutsu yanzu sai muzurai yake. "Kaikuma lafiyarka?" Ta tambayeshi Dan sosa kanshi yayi a kunyace "Lfy lau ummy" yafada yana satar kallon baby dake qumshe dariyarta "To allah yasa, miqomin magungunnan kekuma miqomin ruwa" Duk juyawa sukayi su aiwatar da abinda tace baby sai danne dariyarta take. Ballar mashi magungunnan tayi tabashi yasha yanajin sanyi a zuciyarshi don abubuwan datake mashi sun nuna tabar fushi dashi. Excusing kanshi sadeeq yayi ya fita waje yana hararar baby ta gefen idanu itakuma tamashi gwalo ta gefen baki tana murmushi. Juyowa dazatayi suka hada idanu da ashraf tayi saurin kauda kai gabanta na faduwa. Ta6e baki kawai yayi shima ya janye idanunshi. Riqesu akayi asibitin ganin yanayin rashin qarfin jikin nashi. Da yamma saiga matar kawu zaharadini da shi kanshi kawun nashi sunzo ganinshi. Anan ne suka ke6e da ummy tabashi labarin komai. Yayi mammaki shima matuqa don shi rabonshi dajin ko labarin shamsu qolo tun suna mutunci da margayi Alhaji Auwal. Saida suka tattauna sosai sannan suka tafi can gab da magrib. Saudart kau a 6angarenta abin yayi affecting dinta itama sosai. Takoma wata shiru daita ranta kodayaushe a jagule. Duk yadda daddy yaso wartsakar daita yagaza don wannan karan takasa controlling din kanta. Haka zata wuni a daki ba uhm ba uhm uhm, abinci saidai abiyota dashi kuma dakyar yake samu taci. Idan ya takuramata da tambayoyi sai taita mashi kuka. A cikin kwana biyu duk ta chanza tafita hayyacinta. Saida yayi kwanaki uku sannan aka sallamashi daga asibiti, lokacin yaji sauqi sosai. Direct gidan ummy suka wuce. Sosai Ashraf ya wartsake saidai haryanzu cutarnan ta son Saudart babu abinda ya ragu saima abinda yaqaru. Kwana daya da sallamoshi Kawu ibrahim ya diro garin kano don shima tuni labari yakaimasu a wudil. Sudai su baby basusan dalilinshi nazuwa ba amma sunsan baya rasa nasaba da case din Auren Ashraf. Ranar sun hadu da Kawu zahradini da ummy da kawu ibrahim sunyi heart-to-heart discussion akan yadda zasu 6illowa al'amarin. *WASHEGARI* Bayan azahar suka shirya dukkansu wato Kawu ibrahim, Kawu zahradini, Ummy, baby da Umma suka nufi gidan *MAMY* 💖💖💖💖💖💖💖💖 Jin ringing din doorbell yasa su dagowa daga cin abincin dasuke. "Habeeb, jeka duba" inji Abba yana sipping din juice. Ajiye fork din hannunshi yayi yana goge bakinshi da tissue sannan ya sauko daga dining din yanufi kofar. Budewa yayi yayi tozali da maigadi "Baba Audu" inji habeeb yana murmushi "Na'am habibullahi" shima ya amsa yana washe baki "Kashigo" yafada yana matsawa "A'a dama baqi kukayi" "Baqi? Ina?" Yafada yana leqa bayanshi. "Suna can garage, suna neman iso ne" yabashi amsa "Ok inazuwa" yakoma ciki yafadawa su mamy. "Baqi? Jeka ka shigo dasu" inji mamy "No, kaisu falon baqi seems harda maza tunda kikaga sun fara aikowa" inji Abba. Wucewa habeeb yayi don aiwatarda yadda yace din. Tare suka tafi da maigadin har parking space din. Ganin baby cikinsu yasashi washe baki yana qarasawa wajensu da sauri "Laa aunty?" Yafada yana washe baki Shafa mashi kai tayi tana murmushi "Sheikh habibullah" tafada cikin sigar tsokana kamar yadda tasaba kiranshi a dan zamanta gidan lokacin biki. Murmushi yayi sannan yajuya gasu ummy ya duqa har qasa yana gaidasu. Amsawa duk sukayi cikin jindadi ummy na kallonshi tana hango kammaninshi da saudart sosai. Iso yayi musu suka bishi har falon baqi suna tafe baby na tsokanarshi shikuma yana murmushi don dama shi becika maganaba ko a lokacin data zauna gidan idan ta tsokaneshi saidai ya sunkuyar dakai yana murmushi hakan yasa take kiranshi sheikh ko ustaz. Saida suka zauna sannan yajuya yafita, chan saiga aminullah yashigo da kayan motsa baki. Shima yadda habeeb ya gaidasu haka shima yayi amma banda baby sai harararta dayayi yana murmushi. "Inyee lallai ka riqu, ni bazaka gaidani ba?" Tafada tana harararshi don dama shine abokin fadanta. Gwalo yaimata yafice da sauri ganin tayi kamar zata tashi. Duk dariya sukasa don sosai yaran suka burgesu. Ana haka sukaji sallamar Abba, hakan yasa suka maida kallonsu a qofar dukkansu suna amsa sallamar. Cikeda nutsuwa da dattako Abba yashigo Mamy abayanshi suka shigo suna sakeyin sallama. Amsawa duk suka sakeyi suna murmushi. Saida suka zazzauna sannan aka shiga gaishe gaishe cikin girmamawa. Sai anan Mamy ta lura da baby lokacin da itama ta zamo tana gaidasu. "Laa kamar baby" inji mamy Murmushi baby tayi "Nice mamy" "A'a wata sabon gani, yau kece gidanmu?" Tafada cikin raha tana bin kingin mutanen da kallo tana mammakin su wanene? Agefe guda kuma gabanta nadan faduwa. Ummy kau tunda Mamy tashigo take binta da kallo don sosai take hango kammaninta nada dukda ta chanza sosai, gashi kammaninta sak na saudart sai mammakin yadda takasa ganin kammanin ada tayi. Saida suka gama gaishe gaishen cikin raha da dariya sannan aka nutsu don tattauna abinda yakawosu. Ganin hakan yasa baby miqewa ta barmusu dakin tashige cikin gida....✍ Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love (Ummin fasihu) 073 "Hajiya khadija, ashe rai kan ga rai?" Inji ummy cikin murmushi. Itama Mamy murmushin take mayar mata sai kallonta take don she looked familiar "Aikaudai yaudai allah yayi mun hadu, munata saka ranar zuwa gashi kun rigamu zuwa" mamy tafada cikin fara'a Murmushi ummy taqarayi ganin haryanzu bata ganeta ba. "To yaya bayan rabuwa? Ban ta6a tunanin zamu sake hadewa ba, gashi Allah yasake hadamu a matsayin in-laws" Sai alokacin mamy tafara mata kallon rashin fahimta don bata gane abinda take nufiba, su dai du Abba nasu ido. "Erm... sorry, dama munsan juna ko?" Inji mamy tana kallonta sosai tana qoqarin gano inda ta ta6a sanin fuskar. Murmushi mai sauti ummy tayi tana kada kai "Sosaima, nasanki kema kin sanni wataqila dan an dade ba'a haduba shiyasa kika kasa ganeni, shekaru Ashirin ai ba wasaba" Kallon juna Abba da Mamy sukayi sannan suka maida kallonsu kanta "Fateema ce, matar aminin tsohon mijinki Shamsu... Matar Alhaji Auwal" Tsit dakin ya dauka, kowa yazuba masu idanu yayinda ita mamyn tazuba ummy idanu babu ko kyaftawa tanason tuna inda ta ta6a jin wannan sunan. "Auwal aminin mijinki dakika sameshi lokacin dakuka fara samun mtsl da tsohon mijinki" ummy taqara fada ganin mamy ta antaya kogin tunani. Ahankali mamy tafara ware idanu tana kallon ummy daketa murmushi yayinda take nunata da yatsa bakinta na rawa "Ummyn muhammad?!" Tafada tana ware manyan idanunta sosai Murmushi kawai ummy tayi tana kada kai. Dasauri mamy tanufi wajen ummy suka rungumi juna "Ummyn muhammad? Kece or am dreaming? This is unbelievable" tafada cikin alhini. Murmushi duk mutanen dakin sukayi suna kallonsu. Nanfa akayita firar yaushe gamo, haryanzu mamy takasa yarda ummy ce surukarta, jinjinama ikon Allah takeyi, ko a mafarki bata ta6a tunanin zata sake ganinta ba sai gashi cikin ikon allah sun sake haduwa kuma wannan karon da strong bond atsakaninsu. Sun dade suna fira suna dariya suka dan ta6a kayan motsa baki da aka kawomusu sannan suka nutsu suka dawo serious don tattauna abinda yakawosu, ummy sai kallon mamy take tana jin badadi don tasan dole hankalin mamy yatashi idan taji dalilin zuwan nasu. Ciki hikima da iya tsara zance Kawu ibrahim ya gabatarmusu abinda yakawosu wanda saida yafara basu labarin abota da amintar dake tsakanin margayi Auwal da Shamsu sannan ya gangaro zuwa yadda suka samu matsala dajuna suka koma basa ga maciji da juna zuwa yadda aka kame mottocin margayin da yadda labari ya iskesu nacewa aikin tsohon amininshi ne sanadi harzuwa jinyar dayayi wanda sanaddiyar girgizar dayayine dajin cewa tsohon abokinshi ne sanadin karayarshi wanda wannan jinyarce sanadinshi. Ya gangaro kan yadda rayuwa ta sauyamusu da yadda suka siyarda gidansu suka samu allah ta tallafamusu zuwa inda Ashraf yasamu scholarship yayi karatunshi a Uk xuwa inda yagama yabude company na A.A ENTERPRISES. Tsit falon yayi, kowa shiru kamar ruwa ya cinyesu, mamy kau idanunta sun kada sosai mood dinta ya chanza Abba kau he is expressionless, baxaka iya gane awane yanayi yake cikiba. Ajiyar zuciya kawu ibrahim ya sauke sannan yacigaba daga inda yatsaya yafara magana akan abinda ya tarasu. Tunda yafara magana mamy takafamashi idanu tana kallo babu ko kyaftawa harya kai aya. Daga mamy har Abba rasa mai kwakwarran motsi akayi, they're all dumbfounded. Kwakwalwarsu kasa daukar zancenshi sukayi. "I don't understand, i don't really understand" inji mamy tana girgiza kai hawaye na taruwa idanunta, kallo daya zaka mata kasan hankalinta yayi matuqar tashi. Kama hannunta ummy tayi kasancewar dama kusada ita take asanyaye tace "Khadija, nima i was shocked danaji wannan zancen, it's unbelievable banta6a jin makamancin wannan yafaruba ko a tatsuniya amma it's real" tafaxa asanyaye. " *AUREN KWANGILA?* contract marriage? Dama akwai irin wannan auren? Am confused" tafada kaida gani kasan she's not herself. "But how? Tayaya Saudart da hankalinta zata yarda da irin wannan shirmen? This is unbelievable" inji Abba shima cikin alhini "He forced her, bada son ranta bane, shiya tilasta mata" inji ummy "Shiya tilasta mata?! Ni meye amfanina? Why can't she come over to me and tell me! Daqiqancinta harya kai takasa confiding in me as her mother?.... dama nafada! Babu yadda banyiba akan kar amayar mashi daita tun farko akaqi saurarata, ga irinta nan, ya siyar daita akan kudi, ya musayata da kudi! Kagani ko Alhaji? Kaga abinda nake fada? Allah kadai yasan me da me yakoyamata, Allah kadai yasan tarbiyarda ya dorata akai, ya maidamani yarinya cash worm..." kuka ne ya kufce mata ta toshe bakinta tanayi sosai. Rungumota ummy tayi asanyaye tana rarrashi. "But how come tun farko baku ganeshi ba dakukazo?" Inji Abba da duk jikinshi yayi sanyi. "Alokacin nida Nura mukazo tareda yan uwan ummy, lokaci yaja gashi dama ni sau daya nata6a ganinshi lokacin rasuwar mallam, shi zahradini daya sanshi sosai bayanan lokacin yayi tafiya, kuma munyi bincike mun samu gamssashiyar shaida gamedashi tun kafinma muzo din" inji kawu ibrahim. "Innalillah waina ilaihi rajiun, wannan abu beyi dadiba samm" inji Abba yana girgiza kai. Dagowa mamy dake kuka haryanzu tayi tareda cewa "Dama nasani, that greedy man can do anything don yasamu kudi, gashi greediness dinshi yaja zai lallatama diyata future, koko ince yama lallata tunda gashi itama saboda kudin ta yarda tayi auren" "No mamy, he forced her ne" inji umma da tundazu batace komaiba. Kallon umman mamy tayi tace "bawani forcing, nasan saudart ciki da bai, idan batayi niyyar yin abuba babu wanda ya isa yasata, besides baganiba? Ni meye amfanina idan bazata iya gayamin damuwarta ba? Am her mother for goodness sake, dama i smell something fishy gameda auren nan don everything come all of a sudden ne, now yayi nasarar maida diyata kwadayyaya irinshi" tafada bitterly. Rarrashinta akai tayi don kuka take sosai, banda zafi babu abinda zuciyarta keyi. Ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan ya kalli su kawu ibrahim dakyau ya bude baki calmly yace "Now meye abin yi? Aikin gama dai yariga da yagama, sai samun solution yarage, yanxu ku me kuka yanke?" Kawu zahradini da shima tundaxu beyi maganaba yadan muskuta sannan yafara cewa "To yanxu dai two things are involved, na farko case din shamsu nabiyu kuma auren nan. Mudai bamu riqe shamsu araiba akan abinda yaima margayi, wannan tsakaninsu ne da margayi da Mahallicinsu, Allah zaima kowa sakayya daidai dashi. Batun aure kuma Ashraf yanuna yanason matarshi kuma ya janye contract din tsakaninsu, idan so samune sucigaba da zama a matsayin ma'aurata saidai wani hanzari ba gudu ba.. *saudart!*.... dole yadda tun farko auren yarjejeniya ne a tsakaninsu yanxuma yarjejeniya zamansu zai zama, ma'ana dole saida amincewar dukkansu, bazamuso mu cutar da daya ba don farantama dayan. Idan saudart ta amince zata cigaba da zama dashi to fallilahil-hamd don muma bazamu so yankewar wannan alaqar tamuba, munason saudart kamar yar cikinmu, abinda mahaifinta yayi can baya bazai ta6a shafanta ba don kwata kwata babu kamanceceniyar hallaya tsakaninsu, saudart yarinyace mai nutsuwa da tarbiya wanda samun irinta ayanzu yayi wuya, ladabi da biyyayarta yasa tunfarko ta yarda da qudurin babanta wanda ita tausayamashi tayi ganin halin dazai fada idan bata aminceba, saudart macece mai amana da zuciya mai kyau don ba don itaba da yanzu company don A.A ya fuskanci mummunar asara da karaya, muna sonta amma hakan baxaisa idan taqi yarda da cigaba da zama dashi mu tilastata tayi zaman cutuwa ba" Ummy itama ta dora da "tun farkon haduwarmu da saudart tashiga raina, nasan she's the best wife for my son, she's a girl with a pure heart, ina jinta araina fiyeda yadda nakejin baby araina, bazamu ta6a mata dole zama da Ashraf ba, haqurin datayi dashi da farko ma ya isa, i know yamata abubuwa don ni nasan waye dana idan yanaqin abu, wataqila cin zalinta dayaitayi batareda haqqintaba yasa allah ya jarabceshi da sonta lokaci guda don dama ance idan qiyyaya tayi yawa takan zama soyyaya daga baya, yana sonta fiyeda tunaninku yanzu amma hakan bazai sa a tauyema saudart haqqinta ba, cigaba da zamansu da rabuwarsu will depend on amsarta ne" Shiru dakin yasake dauka sai can Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "To yanzu abinda za'ayi shine zamu zauna dukkanmu harda Alhaji shamsu da saudart dashi kanshi mijin natan a yanke koma menene, aganina hakan zaifi? Koko?" Yaqarashe zancen yana kallonsu kawu ibrahim "Masha allah, hakanma yayi" "Yanzu zanma shi Alhaji shamsun magana inyaso duk yadda muka yanke zanyi informing dinku insha allah" "To allah ya yarda yakuma mana jagora" inji kawu ibrahim Duk amsawa da amin sukayi har lokacin mamy batabar hawaye ba. Haka dai suka tafi kowa zuciyarshi babu dadi. Mamy tayi kuka kamar me? Sai blaming din alhaji shamsu take da lallatamata rayuwar diyarta. Shidai abba inbanda rarrashi babu abinda yake don shima har zuciyarshi beji dadin abinda yafaruba don shima yanason saudart harcikin zuciyarshi kamar kingin yayan cikinshi. Aranar dai haka suka wuni cikin damuwa da bacin rai. A 6angaren Ashraf kau tunda suka dawo yakasa xaune yakasa tsaye don fargaba, jiyake zuciyarshi zata iya tarwatsewa idan yaji mummunan sakamako, dama tunda suka tafi yaketa addu'ar allah ya dorashi akansu allah yabashi nasara don rashin saudart daidai yake da rasa farincikinshi a rayuwa. Duk up and down din dayakeyi ummy na hankalce dashi tayi banza dashi kamar batasan me yakeba. Sai kai komo yake a falon yaji ko zata kirashi amma tayi banza dashi daga baya ma zama yayi a falon yana kallo yayinda dukkan hankalinshi ke kan duk wani motsi da ummy zatayi. Haka yasha zamanshi daga qarshe ummy ta tashi ta hayewarta sama tabarshi nan zaune. Babu yadda ya iya haka ya tashi shima jiki a sanyaye yakoma part dinshi zuciyarshi namashi saqe saqe. Zaune take a garden bisa wata plastic chair ta rungume hannayenta tana kallon waje guda babu ko kyaftawa wanda hakan ke nuna cewa tayi nisa cikin tunani ne Tun ranar dasuka rabu da ashraf bakery dinta wurin yazama wajen zamanta, bata qara marmarin fitaba tun ranar, kullum anan take zuwa ta zauna ba uhm bare uhm uhm sai tunani wanda yazame mata jiki. Kallo daya zaka mata ka hango fadawar datayi sosai, duk takoma shiru daita kamar ba active saudart ba. Ringing din wayarta ya maidota daga duniyar tunanin data lula. Ahankali ta kalli wayar sannan cikin rashin kuzari ta jawo wayar ta duba. Maryam ce hakan yasata yatsuna fuska sannan ta daga. Sudan jima suna magana akan abinda yashafi business dinta wanda yanzu rabonta da leqasu tun ranar nan, akasalance taita amsamata suka dan tattauna sannan sukayi sallama. Tana niyyar ajiye wayar wani kiran yashigo wayarta. Tsayawa tayi tana kallon sunan dake yawo a screen din wayar batareda ta iya dagawa ba yayinda takejin qaruwar bugun zuciyarta. Kasa dagawa tayi har kiran ya tsinke, babu 6ata lokaci wani kiran yasake shigowa again. Limshe idanu tayi ahankali tayi ta bude tana kiran sunan allah. Cikin rawar hannu tayi picking din call din ganin zai qara tsinkwa ta kara a kunne atsorace....✍ Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 074 "Aslm alaiki" tafada ahankali zuciyarta fall fargaba "Wslm Amaryar contract, ya kike?" Taji anfada daga dayan 6angaren Dumm! Gabanta ya yanke ya fadi, ahankali ta sauke wayar daga kunnenta taqara kallon screen din don qara tabbatar da mai kira din. Maidawa tayi a kunne tafara magana ad'an daburce "M...mamy? Mamy ina wuni?" Tafada bugun zuciyarta na qaruwa "Save your greetings don bana buqata, banida wannan matsayin awajenki so hang it" inji mamy Hankalinta ne yatashi wanda har saida tamiqe tsaye bakinta nadan 6ari tace "M...mamy... mmm..meya faru please" tafada yayinda wasu hawaye suka fara kawo mata. "Mefa? Just call to hear from you dukda bawani matsayi nakedashi awajenki ba" "Mamy..." saikuma tayi shiru tana toshe bakinta don kuka ne ke neman kufcemata. "Bye" mamy tafada a dayan bangaren zata tsinke kiran "No mamy please don't hang u..." Ding... taji an katse kiran. Sakin wayar tayi takoma kan kujerar tana dafe kanta da hannaye bibbiyu tafashe da wani irin kuka. "No..no" tafada tana kuka sosai. Saurin duqawa tayi tasake daukar wayar data yar qasa tana kuka tashiga re-dialling din number mamy, hannunta sai rawa suke. Takira yafi so biyar amma ba wanda aka daga. Wani kukan tasake fashewa dashi tana cillar da wayar. Dama tsoronta kenan, kullum fargabar datake kenan, shikenan tafaru taqare. "Am doomed!" Tafada tana daura hannu aka kamar wanda aka kawoma saqon rasuwar uwarta. Wayar tasake dauka tanufi cikin gida tana kuka sosai tashiga dialing din number Daddy. Kallo daya zaka mata kasan bata cikin hayyacinta. Ringing biyu daddy ya daga. Kukanta dayaji ya katsemashi sallamarshi wanda hakan yasashi zabura amiqe. "Shalele?" Zubewa tayi qasan falo don harta shigo falon tana kuka sosai wayar kare a kunnenta. "Shalele menene? Talk to me" inji daddy cikin rawar baki. "Nashiga uku daddy, daddy am doomed!" Shine abinda kawai ta iya fadamashi cikin kuka. "Subhanallilah! Shalele what happened? Meya sameki?" Yafada yana laluban car key dinshi kan table "Daddy kazo... zan mutu" tafada cikin kuka sosai Kafin yasamu damar yin wata maganar harta katse wayar. Bashiri yayo waje hankalinshi a matuqar tashe. Zaune yake jigum, yarasa meke mashi dadi. Tagumi yabuga da hannu bibbiyu yana bin screen din laptop dinshi da kallo wanda ke dauke da hotonta daya fito tarr wanda duk ya turasu akan laptop dinshi daga cikin wayar databar mashi Ahankali aka bude kofar dakinshi baby ta leqo. Ko dagowa beyiba don bemaji budewar kofarba Qarasa shigowa tayi da sallama wanda hakan ya fargar dashi yayi saurin dagowa. "Yaya?... yaya wai ka sauko muyi dinner" inji baby ahankali Komawa yayi ya jingina da kujerar dayake akai yana sauke ajiyar zuciya "Go... banajin yunwa" yafada ahankali. Jimm tadanyi kamar bazata wuceba saikuma tajuya tafita. Can saigashi tasake dawowa. Dagowa yayi yakalleta kawai batareda yace komaiba "Yaya wai kawu yace kazo" Lumshe idanunshi yayi ya bude "Ok" yafada ataqaice Saida tadan jima da tafiya sannan shima ya tashi ya dora shirt saman singlet dinshi yafito. A dining ya taddasu duka, a ladabce ya gaidasu kai a qasa. Kawu ibrahim kawai ya amsa ummy ko ko kallo be ishetaba. "Zoka zauna babana" inji kawu ibrahim yana nunamashi kujerar gefenshi A natse ya qaraso ya zauna baby tayi serving dinshi "Now eat" inji kawu ibrahim Ba musu yadauki spoon din yafara cakula abincin don bawani cin kirki yayimashi ba sai jujjuya spoon din dayake aciki. Haka suka gama in silent sannan suka fara tashi daya bayan daya yarage saura kawu ibrahim da Ashraf. Goge bakinshi kawu ibrahim yayi shima yatashi "Kasameni a garden" yafada tareda ficewa. Haka kawai yaji gabanshi yafadi ya kasa kai kofin ruwan a baki. Ajiyewa yayi yana sauke ajiyar zuciya. Tunda suka dawo yake kasa kunne yaji ki zasuyimashi magana amma shiru gashi yanzu ammashi din amma jiyake beda courage din jin sakammakon daza'a gayamashi. Ya dade zaune awajen yana saqa da warwara kafin daga baya ya miqe dakyar ya fita zuwa garden din kamar kazar da kwai yafashe mawa aciki. "Shalele kiyi hqr please, kibar kukan hakanan" inji daddy daya gaji da rarrashi Zaune take jan gadonta cure wuri guda ta hade kanta da gwiwa tana kuka cikin muryarta dabaya fita tsabar kukan datasha. "Shalele, am sorry, duk nine silar komai, ki gafarceni 'yata" yafada shima kamar zaiyi kukan Ko dagowa batayiba haka zalika batabar kukanba hakan yasashi jawota ajikinshi cikin sigar rarrashi. "Shalele kiyi hqr, nasan yadda kikeji, please kibar kukan haka, ni da kaina zanmasu bayyani kinji? Nina jawo komai kuma ni yakamata inga consequence dinshi, please kibar kuka please" Itadai batace komaiba sai kukan datakeyi qasa qasa, sosai zuciyarta kemata zafi gawani sara da kanta keyi agefe daya jitake dama tamutu ta huta. Dakyar daddy yasamu ya lalla6ata tasha tea tasha magani ta kwanta. Ya dade sosai dakin har saida yaga tayi barci sannan ya lalla6a yafita don karya tadata. Saida taji alamun yafita sannan ta bude kumburarrun idanunta ta miqe zaune ahankali, hade kai da gwiwa tayi tacigaba da hawaye tana kukan zuci. Daddy a 6angarenshi shima kasa rintsawa yayi, sosai yake danasani marar amfani. Danasani yake sosai na halinshi, yasan yanzu tuni dan kingin mutuncinshi yarigada yazibe a idanunsu mamy Sosai yakejin kunya, sai yanzu yake mammakin yadda acan baya idanunshi suka rufe yakasa hango abubuwan dazasu biyo baya. Alokacin shidai kawai abinda zai qaru dashi yake hange, be ta6a hangen abinda zai ragu dashiba. Gashi yanzu ya tsunduma 'yarshi kwaya daya, mai son farincikinshi cikin qunci da bakinciki. ********************************** Fada sosai kawu ibrahim yayimashi kan abinda ya aikata, ta inda yake shiga batanan yake fitaba. Sosai jikin ashraf yayi sanyi don tunda yake beta6a ganin kawunshi cikin irin wannam 6acin ran ba. Sai daga baya yafarayi mashi nasiha mai ratsa zuciya wanda ya ida kashe jikin ashraf. Saida yaimashi nasiha sosai sannan ya gayamashi yadda sukayi dasu Abba, ya dora dacewa "Yanzu dai dorewar aurenku ya danganta ne da amsar da yarinyarnan tabada, bazamu so kanmu dayawa ba, bazamu bari ayi zaman cutuwa ba, idan ta amince zata cigaba da zama dakai to fallilahil hamd, amma idan ta nuna akasin haka bazamu tilasta mataba, saidai muyima dukkanku fatan allah ya hada kowa da mafi alhairi" Bayan haka ya sallameshi. Tashi yayi jiki amace, yabi ta hanyar baya yashiga cikin gidan ya haye sama kamar marar lakka. Ahankali ya zauna gefen gadonshi ya jingina kanshi da jikin gadon ya lumshe idanunshi da suke a rine. Yasan shikenan, shikenan sun rabu da saudart sun gama. Tun yanzu yasan matsayar aurannan, dama mai neman kuka ne aka jefa da kashi. She hate him so much, ta tsaneshi ta tsani ganinshi burinta su rabu, meye to amsarta bayan anbata za6i yanzu na cigaba da xama dashi ko rabuwa dashi? Ofcourse rabuwa ce, yasan bazata tsaya dogon tunaniba zata za6i rabuwa dashi. Ahankali hawaye suka gangaro daga ruffafun idanunshi yanajin tausayin kanshi. Yasan rabuwarshi daita daidai yake da rabuwarshi da farincikinshi. Yasan rabuwarshi daita kamar bude sabon shafin kunci ne arayuwarshi. His last hope was gone, yanzu baida sauran wani hope, kawai yariga yarasata yagama ne. Adaren babu wanda ya rintsa acikinsu daga Ashraf da saudart har Alhaji Shamsu daya tsangwami kanshi yake ganin shine umul abaisan faruwar komai. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Washegari da zazzafan zazza6i saudart ta tashi. Sosai Alhaji shamsu ya rude don jin jiki take sosai kuma taqi yarda akaita hospital saidai aka kira family doctor dinsu yazo hargidan. Ranar wuni yayi tareda ita bekosan motsawa daga gefenta, duk motsin dazatayi saiyayi mata sannu, he's feeling guilty, yanajin duk shine silar komai, hqr kau har saudart tagaji dajinshi abakinshi. Haka ranar tazo tawuce masu dukkansu cikin qunci. A 6angaren ashraf kau sai abinda yayi gaba. Haka shima yawuni sukuku, saidai kaganshi zaune ya kafe waje daya da idanu yana tunani. Baya fita gidan sai yaga lokacin sallah yayi sannan yafita masjid, daga nan kuma sai dakinshi. Idan kuma ya sauko qasa to ankirashi ne ya sauko yaci abinci wanda ko kwata beci zai tashi wai ya qoshi daganan kuma yakoma daki ya dasa daga inda ya tsaya. Ganin tunane tunanen bazasu amfaneshi dakomai ba yasashi tashi ya daura alwala misalin shabiyu na dare yahaye sallaya yaita nafilfili yana addu'ar allah yabashi haquri da juriyar rabuwa daita yakuma yayemashi sonta kamar yadda ya doramashi don shi yarigada ya fidda rai da kasancewa tareda ita. Saida tayi kwana biyu kwance sannan tadanji sauqi. Damun daddy tayi da kuka akan ita gidan mamy zata don tasan tana fushi daita. Ganin bata ida warwarewaba yaso hanata dafarko amma ganin ta burkucemashi yasashi yarda akan tayi hqr zaikaita dakanshi washegari. Haka ta haqura badon yasoba. Washegari sukuku ta tashi, fargabar haduwarsu kawai take da mamy don tasan haduwarsu won't be funny at all. Haka ta shirya jiki amace kallo daya zaka mata kasan atsorace take. Daddy ne yaita kwantarmata da hankali ganin yadda duk ta tashi hankalinta. Haka suka fita daga gidan suka dau hanyar gidan mamy kowanne da irin fargabar dayake....✍ Sorry for the short chappy🙏 Please sai kun dinga hqr dani yanzu, wlh bansamun zamane kamar da. Da ace yadda nake samun lokaci ne kamarda da yanzu book dinnan yaqare. Yanzu typing dinma kanshi wahala yakebani don am always busy. Please bear with me, yanzu ba kullum zaku dinga jinaba, amma duk ranarda am less busy zan dinga yimuku mai yawa🙏 Nagode da qaunar dakukemani da littafin nan. Masu cigiyata da masu kirana duk nagode, Allah yabar qauna da zumunci, Allah yabarmu tare har abada💖 Ashaanty loves you so much😘💖💖💖💖💖 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 075 Fitowa duk sukayi daga cikin motar duk suna kallon qaton gate din gidan. Asanyaye saudart tajuyo ta kalli daddy kallo daya zakamata kasan a tsorace take "Kishiga sweetheart, kimin sallama da Abban nayi losing din contact dinshi" Nodding tayi a sanyaye sannan ta nufi gate din kamar wanda kwai yafashe mawa aciki. Saida tayi knocking sau uku sannan taji alamun za'a bude gate din Budewa akayi fuskar maigadin ya bayyana, yana ganinta ya washe baki yana mata maraba. "Anty kece? Yau banda mota kikazo?" Murmushi kawai tayi tace "eh bani kadai bace, Abba fah?" "Yana ciki bema dade da dawowa ba ma" "Ok" daga haka tashige ciki gabanta na faduwa. Ahankali ta danna doorbell din kofar cikin sanyin jiki. Shirun dataji yasata qara dannawa. Gani tayi an murda handle din daga ciki hakan yasata dan ja baya gabanta na faduwa. Abdul ne tagani yana turo baki, yana ganinta ya waro idanu tareda kiran sunanta da karfi ya rungumeta. Dukda bacikin nutsuwa takeba saida ta murmusa tana riqeshi itama "Aunty kece? Kitaho" yafada yana jawo hannunta zai shigar daita ciki. Saurin tirjewa tayi tareda jawoshi baya ta tsugunna daidai tsawonshi sannan tafara magana cikin muryar rada "Ina Abba?" Tafada tana dan wara manyan idanunta "He's upstairs" ya amsa shima cikin rada "Mamy?" "Tana falo" "Doing what?" "Tana tayamu homework" Ganin tana kallonshi atsorace yasashi qara qasa da murya "Aunty menene?" Furza iska tayi daga bakinta sannan tace "Nothing... mushiga" Da sallama suka shiga, Abdul agaba jaye da hannun saudart dake taka kasa kamar mai tausayinta Su kamal da tundazu suke kallon kofar don tabbatar da ita dince suka miqe aguje suka nufeta suna murna banda Aminu dake murmushi kawai daga inda yake zaune. Wara masu hannu itama tayi absentmindedly tana kallon mamy da ko dagowa daga kallon littafin habeeb batayiba fuskarnan murtuk Jiki asanyaye tayimasu habeeb murmushi ta qaraso ciki simi simi kamar marar gaskiya. Dan nesa da mamy taxauna qasa tana kallonta a sanyaye abdul sai zubamata surutu yake. Saida tagama amsamashi sannan ta dago takalli mamy a raunane "Mamy ina wuni?" Idan ku masu karatu kun amsa to itama ta amsa. Sake gaisheta tayi wannan karon ma babu amsa saima tattara littafan gabanta data shigayi tana maidamasu cikin jakka. "Mamy aunty na gaisheki" inji abdul don shi atunaninshi bataji bane. Wani kallo ta watsamashi tace "If i slap you, kutashi kuba mutane wuri!" Ta qrashe a tsawace. Simi simi suka tashi harda aminu dake kan kujera sukayi sama. Sunkuyar dakai qasa saudart tayi hawaye na kawo mata. Tashi itama mamy tayi zata wuce hakan yasata saurin dagowa "Mamy don allah kiyi haquri" tafada cikin muryarta dake dan rawa Wucewa xatayi tayi saurin riqe tip din gown dinta "Please mamy.." Fizgewa mamy tayi tajuyo tana bankamata wani mugun kallo. "Are you alright?" Sunkuyar dakai tayi hawayen dake maqale a idanuwanta na gangarowa "Am very sorry mamy, don girman allah kiyi hqr" tafada voice dinta na breaking "sorry for what? Dama wani abu kika yimin?" Kasa amsawa tayi sai matsar qwalla datake "Ni bakimin komai ba, koma menene kanki kikaimawa, so you should be sorry for yourself, Aure dai shine kuka mayar abun wasa ko? Zaku kwashi kashinku a hannu daga ke har baban naki" Jiki na rawa taqara matsota tana qoqarin riqe kafarta mamy taqara yin baya "Ni kibar matsoni, me zan miki? Dama kinsan da zamana ne? Inada wani matsayine awajenki? No, so go to your guardian dama tare kuka tone kuka binne, stop including me" tafada cikin 6acin rai. Taffukan hannu saudart tasa ta rufe fuskarta tana kuka sosai mai ban tausayi, jikinta har rawa rawa yake. "Kinga tashi ki tafi, na me zakizo kicikamin gida da hayaniya? Idan zan baki shawara ma cewa zanyi ki adana hawayen da iface ifacen zuwa gaba don zaifi yimaki amfani alokacin. Saudart kin bani kunya, am really disappointed in you, wlh ko a mafarki banta6a tunani zakiyi abinda kikayi ba. Ina tarbiyar dana baki? Ina hankalinki, ina iliminki? Ina tunaninki? Kin biyema kwadayyayen ubanki ya kaiki yabaro don ke keda kaico ba shiba, soon zaki zama bazawara kishiga layin zawarawa babanki kau babu abinda yashafeshi, iyaka yaga wani wanda zai qara tatsa ya auramiki shi shima bayan wasu lokuta ki fito kafin ya qara hango wani. Ko shi Allah kanshi dayace mubi iyayenmu cewa yayi idan basu kaucewa koyarwar musulunci bane Yanzu saudart ke bamai nusar da mahaifinki bane? Ke bame ganardashi bane ki nunamashi hanya idan yaso kaucewa? Amma kika biyemashi kega mai uba ko? And the painful thing is ina raye? Ina raye saudart kikayi wannan abin batareda shawarata ko sanina ba? Banida matsayinda zaki kawomin damuwarki? Ya huremaki kunne baki ganina da mutunci? Ace wai 'yata ce da auren contract? Auren kwadayi?.." tafada tana nuna kanta idanunta na kadawa. Kuka sosai saudart keyi tana jin duk ta tsani kanta, jitake dama tamutu kafin wannan lokacin, dama batayi witnessing din wannan lokacinba a rayuwarta. "Ku kuka sani ai, kuje can ku qarata, badai zawarci ba? Kije kiyi kiji ko akwai dadi, kikuma cigaba da biyema ubanki, watarana sai an hallakaki ta dalilinshi... yaje yayi laifi anzo andauki fansa akanki, keda bakijiba baki ganiba, go ahead Allah yabada sa'a" Tsaki taja tajuya tayi wucewarta sama zuciyarta na quna. Ahankali saudart ta dago kaffafunta ta dora kanta bisa gwiwa ta rungume kaffafun tacigaba da rera kukanta, nan take taji kanta nadan sarawa zazza6inda bagama sakinta ba na neman sake tasomata. Batasan iya dadewarta awannan yanayinba taji anyi tapping din kafadarta. Saurin dago fuskarta tayi datayi ja saboda kuka. "Saudart?" Inji abba dake sanye da jallabiya a mammakince. Sauke rinnanun idanunta tayi ahankali wasu hawayen na gangaromata ta gaidashi da muryarta dabata fita "Lfy lau, what happened? Why are you crying?" Batace komaiba sai cigaba dakukan datayi ahankali. Miqar daita yayi tsaye yana rarrashi don yasan kwanan zancen Dakyar yasamu tayi shiru sannan ya tambayeta daga ina take. Jan hanci tayi sannan dakyar tace "Gida, tare muke ma da daddy" "Alhaji shamsu? Yana ina?" "Waje" tafada tana sauke tagwayen ajiyar zuciya "Ya sallam, since when? Shine baki gayama kowaba?" Shiru tayi don ita saima yanxu ta tuna data barshi waje. Fita yayi batareda yasake cewa komaiba. Awaje kau daddy ne tsaye sai safa da marwa yake. Sai imagining din abinda ke faruwa ciki yake gashi yakira number saudart yafi aqilga amma ba'a dagaba. Jin ana bude qaramar qofar gate yasashi kafama gate din idanu sai ganin Abba yayi yafito. Murmushi suka sakarma juna, abba ya qaraso sukayi musabaha sunama juna sallama. "Alhaji shamsu, ashe kana waje? Wlh saiyanxu dana sauko saudart ke gayamin, kayi haquri please" Murmushi Daddy yayi "Bakomai Alhaji Isma'il, dama cewa nayi taimani iso, i thought baka nan ma danaji shiru" Shiga sukayi Abba agaba daddy biyedashi suna dan ta6a fira. Falon saukar baqi yakaishi sannan yajuya da niyyar sawa akawomashi abin ta6awa "Alhamdullilah Alhaji, am ok" daddy ya tsaidashi da hakan Dawowa abba yayi ya zauna yana facing din Daddy don jin abinda yakawoshi. Dan daburcewa yayi ganin yadda ya kafamashi idanu "Akan maganar auren yarannan ne.... it's was a mistake.... and... am regretting it" shiru yayi, shi kanshi yasan he sound stupid "Nasan kanada labari kou?.." Ajiyar zuciya Abba dake kallonshi tundazu yayi sannan yace "Yes, yau kwana uku kenan dazuwansu in-law dinmu nan gidan" Kallonshi daddy yayi yana dan wara idanu saikuma ya sauke idanunshi qasa feeling so humuilating "I caused it all... duk laifi nane... i forced her" Dan murmushi Abba yayi yace "yes, you made a big mistake, meyasa kayi haka Alhaji shamsu?" Shiru yayi yakasa cewa komai, jiyake kamar qasa ta tsage ya rufta ciki, wani matsanancin kunya yakeji kamar ya 6ace ya huta. "Yanzu dai faduwa ce tazo daidai da zama, dama nayi niyyar zuwa mall dinka mu tattauna, zamu hadu gidanka dasu in-laws din namu damu mu sassanta komai, saika fidda rana" Shiru Daddy yayi haryanzu yakasa hada ido da abba. Wai agaban abba kadai yakejin haka, inaga agaban in-laws din? Kokuma mai gabadaya agaban allah ranar sakamakko? "Look everything will be alright alhaji, kawai gani nayi hakan zaifi, ahadu a samama kai mafita, aurennan yayi involving su biyu ne, dole saida yarda dukkansu, we want to hear from both of them kafin a yanke hukunci, sai inga hakan zaifi" Hannu daddy yasa ya share gumin forehead dinshi sannan ya sauke ajiyar zuciya "To, yanzu... yaushe zasuzo din?" Yafada ahankali "Choose a date... duk ranarda yaimaka" Shiru daddy yayi, tayaya zaiyi facing dinsu da wannan abun kunya, kai kwadayi beyiba, gashi da mutuncinshi da komai zaizama qaramin mutum awajen ahali mai daraja irinna A.A "Gata... sunday kenan? Koko?" "Hakan yayi, zan gayamasu, insha allah komai zai warware" inji abba daya lura da uncomfortableness na daddy. Saida sukadan dade suna fira, abba na nunnunamashi abubuwan dayayi dabai kamata ba cikin hikima, dakuma illar wasa da aure. Sosai jikin daddy yayi sanyi don magangganun abba sun shigeshi sosai. Sai gab da magrib suka fito, abba yashiga yakira saudart dake inda yabarta suka fito yana sake rarrashinta yana assuring dinta mamy zata sakko ta kyaleta yanzu fushi take. Sallama sukayi da abba, daddy nata mashi godiya don sosai yaqara qima a idanunshi. Haka suka isa gida sukuku, bayan dinner daddy yashigo dakin saudart lokacin hartayi shirin barci tana zaune tabuga tagumi. Zama yayi yafara rarrashinta yana bata hqr akan duk abinda yaimata yana nunamata tsantsan nadamarshi, sannan yafadamata yadda sukayi da abba. Sosai hankalinta ya tashi don jitake bazata iya facing din ummy ba. Dakyar yasamu hankalinta yadan kwanta sannan ya lalla6ata ta kwanta sannan yafita. Kamardai kodayaushe yana fita tamiqe zaune tahada kanta da gwiwa tana tunane tunane, barci 6arawo ya sadado ya dauketa wajajen ukun safiya. *THREE DAYS LATER* Sorry ba yawa🙏 Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 076 *THREE DAYS LATER* A natse yake saukowa daga stairs hannayenshi zube cikin wandon dakkakiyar shaddarshi kalar brown. Kanshi babu hula sai sumar kanshi da tad'an taru sai shining yake don gyara Hannunshi na haggu na sanyeda agogo rolex sai baqaqen cover shoes a kaffafunshi. Dagowa duk sukayi suna kallon yadda yake saukowa qasa cikin sanyin jiki kanshi asunkuye. Cikin yan kwanakin nan sun rasa gane kanshi don yayi wani laushi kamar bashi ba, haka suka bishi da kallo harya qaraso wajenda suke zazzaune suna jiranshi. Duqawa yayi batareda ya bari sun hada ido da kowaba ya gaidasu cikin calm voice dinshi. Duk amsawa sukayi suna kallonshi cikin tausayawa. Kallo daya zaka mashi ka hango ramar dayayi cikin yan kwanakin nan, yaqara haske wanda hakan yaqaramashi kyau. "To saimu yi niyya ko?" Inji kawu ibrahim Duk tashi sukayi suka fito waje. Motocci biyu ne a harabar. Ummy da umma suka shiga seat din baya sai Ashraf da sadeeq dake gaba inda sadeeq ne matuqin. Dayar motar kuma kawu ibrahim ne da kawu zahradini sai drivern dazai jasu. Haka suka jera suka fito daga gidan suka halba titi. Shiru motarsu ummy ta dauka kowa da abinda ke kai kawo a zuciyarshi Sadeeq dake tuqi yad'an saci kallon ashraf daya jingina da seat dinshi ya lumshe idanu. Janye idanunshi yayi ya maida kan titi yana qarajin tausayin abokin nashi. *zaka ita misalta adadin qiyyayar danake maka?* maganar saudart ta ranan tadawo mashi a kwanya *A'a* *nima haka... baxan iya misalta qiyayyar danake makaba ada.... saidai yanzu ina iya cewa... qiyayyar danake maka ada batakai kaso daya cikin kaso goma danake maka yanzu ba* *ka tsaneni ko? Ka tsani ka ganni cikin farinciki da walwala ko? Tell me* *I hate you....with passion* Haka magangganun saudart sukayita mashi amsa kuwa a kunne. Yasan yau ne qarshen duk wani alaqa dake tsakaninsu. Kullum saiyayi tsayuwar dare ya roqi allah akan ya yakicemashi soyyayarta acikin zuciyarshi amma yadda kasan roqo yake aqara mashi, kowanne wucewar daqiqa da qaruwar son saudart ne a zuciyarshi. He's so weak, so broke, babu abinda ke fadar mashi da gaba sai abinda zai fito daga bakinta. Yarasa dalili, koyaya ta furta ta tsaneshi sai yaji kalmar harcikin zuciyarshi, bawai besan ta tsaneshin din bane, yasani amma furtawar datake ba qaramin tasiri yakeba azuciyarshi. Yana fargabar wannan kalmar abakinta, besaniba ko wannan karon zuciyarshi zata iya daukar kalmar ba. Da tashine dasun barshi gida, da bazai bisuba don yasan kwanan zancen, dole yauce ranar rabuwarsu kuma yasan dole ta furtamashi kalmar dake qonamashi zuciya. Jin an dafashi a kafada yasashi dawowa duniyar tunani daya fada yabude idanunshi yajuyo ya kalli sadeeq dake kallonshi shima. Sai alokacin yaga kamar ba tafiyaba suke, waigawa baya yayi yaga su ummy basa cikin motar wanda hakan ke nufin sun iso kenan "Be strong" inji sadeeq yana dan jijjiga kafadarshi cikin karfafa gwiwa. Lumshe idanu kawai yayi ya bude batareda yace komaiba. Bude murfin kofar sadeeq yayi ya fita ya maido yarufe. Shiru ashraf yayi na yan daqiqu sannan shima yasa hannu ahankali ya bude murfin motar. Saida yadanyi jim sannan ya sauko kafarshi daya sannan ahankali gangar jikinshi suka biyo baya. Wani fresh air ne ya bugeshi wanda yasashi lunshe idanu yana shaqa tareda fesarwa ahankali. Zagayowa sadeeq yayi side dinshi shima ya tsaya yana kallonsu Kawu dake gaisawa dasu Abba da daddyn saudart. Shima Ashraf su yake kallo koko ince Alhaji shamsu yake kallo wanda kallo daya zaka mashi kaga rashin nutsuwa atattare dashi. Kallonshi yake cikeda tsana da kyama marar misaltuwa. A 6angaren su kawu ibrahim kau tarba ta mutunci suka samu wajensu Abba koko ince Abban kadai don daddy bemada nutsuwar dazai tarbesu sosai. Jiyake kamar qasa ta tsage yashige don kunya, haka dai ake gaisuwan batareda ya yarda sun hada ido da daya daga cikinsu ba. Kamar ance yakallo wajensu Ashraf, idanunsu ne suka gauraya wanda hakan ya haddasama Alhaji shamsu faduwar gaba don shi kadai ya hango abinda ya hango a idanun ashraf. Ganin suna tunkarosu yasashi janye idanunshi daga kansu. Qarasowa sukayi duk suka duqa don gaidasu. "Ina wuninku?" Inji sadeeq a sanyaye. Saida suka amsa sannan ashraf shima yabude baki dakyar yace "Abba barka da wuni" Amsawa abba yayi yana murmusawa shikau daddy bece konaiba sai kauda kai dayayi. Haka suka dunguma suka nufi masaukin baqi dake gidan gabadaya. Zaune take bakin gado ta jingina da kan gadon hannayenta harde a qirjinta, ita kadai tasan abinda ke axuciyarta, tunda taji qaran mottoci tasan sun iso, hakan yasa bugun ziciyarta qaruwa, yaune damarta ta qarshe na qwatarma kanta yanci, yaune damarta na qarshe na za6arma kanta irin rayuwar dazata cigaba dayi, rayuwar farinciki ko akasin haka. Today is the D-day. Bubbuga kofar da akayi yasata dagowa ahankali tana kallon kofar. Budewa akayi daddy ya bayyana bakin kofar ya tsaya yana kallonta. Ahankali ta hadiye wani abu dake maqoshinta tareda sadda kai "Come daughter" yafada asanyaye. Qara dagowa tayi ta kalleshi da dara daran idanunta sannan ta miqe ahankali ta dauki hijab dinta dake gefenta ta warware ta zurata, saigata har tana kusan sharar qasa. Anitse ta tako har wajen daddy kanta a sunkuye, kama hannunta yayi yadan murza "Are you ok?" Yafada ahankali Kada mashi kai kawai tayi asanyaye "Ok muje" daga haka yajuya yayi gaba yana jaye da hannunta. Bugun zuciyarta yashiga karuwa duk taku daya dazasuyi na tunkarar falon baqi. Jitake kamar ta ruga don sosai zuciyarta je cikeda fargaba dakuma tsoro gakuma nauyin ummy datakeji. Haka dai suka qarasa bakin kofar falon. Sallama Alhaji shamsu yayi yashigo still jayeda hannun saudart da kanta ke qasa. Duk dagowa sukayi suna amsa sallamar saidai duk idanunsu nakan Saudart. Ahankali takebin daddy tana iya bakin qoqarinta naganin bata hardeba don tafiyarma dakyar takeyinta don tanajin yadda idanuwa ke yawo akanta. Zama Alhaji yayi kusada Abba itakuma ta zauna qasa kusada kaffafun daddy still kanta a sunkuye. Tunda suka shigo yadago yafara kallonta harta iso ta zauna batareda yako kyaftaba. Wani irin yanayi na shauqi yaji zuciyarshi nashiga by mere ganinta kawai, gani yake kamar yayi shekaru be gantaba, jiyake zuciyarshi na narkewa ahankali cikin begenta, kallonta yake ba qaqqautawa burinshi kawai tadago yayi arba da kyakyawar fuskarta dake antayashi cikin shauqi. Qoqarin tattaro sauran nutsuwarta tayi sannan cikin murya mai dan rawa rawa ta gaidasu kanta qasa. Duk amsawa sukai in chorus, kowanne da abinda kemashi yawo cikin zuciya. Ahankali Ashraf ya lumshe idanunshi yana sauke numfashi silently jin muryarta ta doki dodon kunnenshi, sai yanzu yake qara regretting din biyosu dayayi don jiyayi duk abinda yakeji can gida gameda ita ba komaibane jiyake kamar ya rarrafa daga inda yake zaune qasa yaje gabanta ya rungumeta. Shiru dakin ya dauka na wani lokaci kowa da abinda yake saqawa a zuciyarshi. Ahankali saudart tashiga dago idanunta dasuke sheqi saboda taruwa da hawaye yafara a idon, bata saukesuba a koina sai cikin na Ashraf da shima ita yakafe da idanu. Da sauri ta sadda idanun gabanta na faduwa don ba qaramin haskemata idanu idanun nashi sukayiba. Shima sadda kai yayi ahankali yana lumshe idanu yana sauraron yadda zuciyarshi ke halbawa. "Longest time Alhaji shamsu" inji kawu zahradini yana kallon daddy. Sai yanzu daddy yasamu damar hada ido da daya daga cikinsu. Tsayawa yayi yana kallon kawu zahradini sosai don he's face look familiar Ahankali yashiga bin sauran mutanen da kallo don placing finger akan inda yasansu. "Kaga ikon Allah ko? Bamu ta6a tunanin zamu sake haduwaba saigashi Allah ya hadamu again amatsayin in-laws" inji zahradini yana murmushi. Kafe zahradinin yayi da idanu yanason tuno inda yasan face din. Suma kingin mutanen falon kafeshi sukayi da idanu except Ashraf da haryanzu idanunshi ke a lumshe itakuma saudart kanta a sadde. Ganin yakasa gano inda yasanshi ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "I gave up, Sorry but i can't recall you" Murmushi kawu zahradini yayi sannan yace "zahradini ne, qani ga Auwal, *Auwal direba*" Cak komai dake motsi ajikib Alhaji shamsu yatsaya na wucin gadi, ya kafe zahradini da idanu yayinda sunan wanda ya ambata yashiga masa amsa kuwa a kunne. "Alhaji shamsu muhd na wudil.... *tsohon amininka*" Gabanshine ya yanke yafadi yawara idanu yana kallon zahradini cikin dimaucewa "Sh...shamsu? Shamsu na? Shamsu na? Kaine shamsu na?" Yafada cikin rawar murya yana nuna zahradini da yatsarshi dake 6ari. Dan dagowa itama saudart tayi tana satan kallon daddy cikin rashin fahimta ganin yadda daddy duk ya rude lokaci guda. Kafin kyaftawar ido har daddy ya qaraso gaban zahradini ya kamo hannunshi duka "Kana nan dama shamsu? Ina ka shiga? Na nemeka koina, ashe zamu sake haduwa?" Duk kallo occupant din falon suke binsu dashi cikin rashin fahimta banda ashraf dabe dagoba haryanzu. "A'a bani bane, zahradini ne qannenshi" "To yana ina? Ina yake? Ashe zamu qara haduwa dama?" Yafada yana wurwurga idanunshi dasuka kada a falon kamar mai nemanshi, kallo daya zakamashi kasan baya cikin hayyacinshi. Kawu ibrahim dake kallonsu shima tundazu shaye da mammakin ganin reaction din Alhaji ya bude baki dakyar yace "Allah yamashi rasuwa, shekaru sha takwas baya" Cak yatsaya yana kallon kawu ibrahim babu ko kyaftawa. Jiyake kamar kunnenshi ne beji daidai ba, yayi me? "Tun lokacinda kasa aka kame komai nashi akamashi terere zuciyarshi tabuga yamutu" inji kawu ibrahim da shima yanayinshi yafara canzawa. Sunkuyar dakai ummy tayi tana dauke hawayen idanunta jin an fama mata tsohon mikin dake cikin zuciyarta itakau saudart she is never confused like this in her life. Kallonsu kawai take cikin rashin fahimta, wai dama daddy yasansu ne? Tambayar datayima kanta kenan. Ahankali Alhaji shamsu ya bude baki idanunshi sunyi jajir still yana kallon kawu ibrahim "Ya rasu?" Yafada kusan cikin rada zuciyarshi na karyewa. "Innalillahi waina ilaihi rajiun" yafada ahankali yana lumshe idanu ga mammakin kowa hawaye suka gani ya silalo daga idanunshi. A mammakince saudart ke kallon daddy don tunda take bata ta6a ganin daddynta acikin wannan yanayinba. Rarrafawa tayi gabanshi da sauri ta riqo hannunshi cikin nata itama hawaye na kawomata ganin yadda yake hawaye ba kakkautawa "Daddy?" Saikuma ta toshe bakinta tana kuka. Ashraf kanshi na sadde haryanzu idanunshi a lumshe yayinda zuciyarshi kemishi zafi sosai, jiyake komai na dawomashi fresh, tsanar Alhaji shamsu na qara farashi a zuciyarshi. "Daddy menene? Why are you crying?" Tafada ahankali tana kallon daddyn Bece komaiba sai sake damqe hannunta dayayi zuciyarshi na qara raunana "Ashe bazamu sake saduwaba? Bazamu sake ganawa ba? He's gone shalele... Gone" yafada ahankali lokacin dasukayi ada nasake dawomashi fresh. Saudart batace komaiba sai kallonshi datake itama tana hawaye. "Ashe bazan samu damar neman gafararshi ba, yamutu da jin haushi na" yafada wasu hawayen na zubomashi. Zahradini ne yayi karfin halin cewa "meye na damuwa to? Ai dama burinka ya taggayara ko yabarmaka duniyar gabadaya, why making up drama" Kallonshi kawai alhaji yake batareda yasan inda magananshi yadosa ba. "Ta dalilin abinda kaimashi yasashi mutuwa, meye na kuka kuma? Bayan abinda kakeso kasamu" inji kawu zahradini yana dan huci trying to control himself Lumshe idanu Alhaji shamsu yayi zuciyarshi naqara karaya, cikin rawar murya yace "Bansaniba, b..bansan hakan zaiyi affecting dinshi sosaiba... dana sani..." saikuma yayi shiru yana rufe fuskarshi da taffukan hannunshi. "Dama tayaya zaka sani? Kayi hakanne don ka wulaqantashi, ya tozarta a idanun al'umma, jin cewa kaine sila yasashi kasa daukar haka, Auwal na sonka da zuciya daya, ya soka da dukkanin zuciyarshi amma ka rasa abinda zaka sakamashi dashi sai wannan don kawai kun samu sa6ani?" Jujjuya kai kawai Alhaji yakeyi hawaye na zubomashi sosai don ba qaramin zafi zuciyarshi ke mashi ba "Bansaniba, bansan sa6aninmu zaiyi affecting dinshi ba, nayi kuskure, nayi blunting acikin fushi ne lokacin, ya kamata yasan ba har cikin zuciyata na gayamashi magangganun ba, I was furious ne lokacin, nayi danasanin blunting agareshi tun kafinma yabar gidan" yafada cikin rawar murya sosai "Ba blunting dinka ba yasashi collapsing, sharrin dakayi mashi ne, ka hadashi da customs su kwace komai nashi? Su biyoshi har gida su wulaqantashi duk don ya nemi kwatantamaka gaskiya? Dama gyara kayanka nazama sauke mu raba ne?" Inji kawu ibrahim da idanunshi shima suka kada Cire taffikan hannayenshi yayi daga fuska yana kallon kawu ibrahim da jiqaqqun idanunshi cikin rashin fahimta "Customs? Wulaqantashi? Kamar yaya?" Yafada in confusion "Bakai bane kamashi kulla kullaba harsu customs suka kwace duka mottocinshi da abinda keciki suka biyoshi har gida suka turning gidan upside down? Ba terere dakayi mashiba yasashi kwantawa jinyar ajali sai yadda ka iya cin amanarshi ka ha'inceshi duk don ya nemi baka shawara as his amini" Sosai kan Alhaji ya kulle don shi bema gane kan labarinnan ba bare gindinshi "Ni? Sharri? When?" Yafada cikin mugun confusion....✍ Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 077 "Ni? Sharri? When?" Yafada cikin mugun confusion Sosai kanshi ya kulle don bema gane inda zancensu ya dosaba. "Must you pretend? Mu ba wannan bane gabanmu ba yanzu, abunda yakawomu shine samama yaranmu mafita a zamantakewar aurensu, bawai munzo yimaka titsiye ne akan abunda yafaruba shekara da shekaru, wannan tsakaninka da Allah ne da kuma margayi, sakkayar kowa na wajen allah, Allah ba azzalumin kowa bane" inji kawu ibrahim dake ganin kamar rainamasu hankali yakeson yi. "Please karku barni cikin duhu, ku gayamin, meye kuke nufi da namashi sharri, na wulaqantashi?" Inji Alhaji shamsu cikin kasala "Look, kamar yadda yaya ibrahim yace ba wannan yakawomu ba, munzo nan ne akan maganar auren diyarmu da danmu ne, meye na pretending? Ai what goes around comes around, gashi bayan shekaru da dama munsake hadewa da bond mai qarfi tsakaninmu wanda baxamuso ya tsinkeba akan kowane daliliba don mu munriga munbaiwa baya baya, gabanmu kawai muke duba, abinda ke tsakaninku da margayi be shafi auren 'ya'yanmu ba, ko yanzu saudart ta yarda ta xauna da danmu zamu riqeta hannu biyu bisa amana don babu abinda tayimana so stop pretending" inji kawu zahradini, kallo daya zakamashi kasan ranshi a 6ace yake. Abba da tundazu beyi maganaba yayi saurin cewa "Haba ku kuwa? Duk baikai hakaba, karku manta agaban yara muke and..." saikuma ya kalli daddy dake kallonsu in confusion sannan yace "Alhaji shamsu, kace bakasan abinda suke maganaba akai?" "I can swear to you, wlh bansan me suke nufiba" "Ok zaka iya bamu labarin abinda yafaru bayan rabuwarku da margayi Alhaji auwal?" Inji abba yana kafeshi da idanu Ajiyar xuciya ya sauke, shi koyaya akace margayin nan sai yaji abu ya ta6amashi zuciya, he can't believe amininshi ne yaxama babu. Ahankali ya bude baki dakyar yafara cewa "Auwal ba a aboki kawai na daukeshi ba ko amini, duk yawuce nan, auwal ya mayemani gurbin danuwan da bandashi, auwal komai ne agareni, masoyi, aboki, yaya. Duk damuwata shi nake kaimawa muhadu cikin ikon allah musamu mafita, shike kwa6ata idan nayi ba daidai ba batareda yin la'akari da yadda zanjiba, shike bani shawarwaru wanda suke matuqar yimin amfani. Nasan bani acikin jerin mutane masu hallayen kirki, inada son kudi, ina nemansu at every narrow way, wanda hakan yasamo asaline tun kuruciyata da ban saka komai agabanaba sai neman kudi don atunani sune jindadin rayuwa, sune komai. Auwal yasha mani fada akan hakan amma ban dauka, saidai in nuna ba gamsu kuma bazan sakeba amma hakan be hanani fasawa" Shiru yadanyi yana sauke ajiyar zuciya sannan yacigaba dacewa "Mun samu sa6anine dashi bayan haihuwar shalele, na buqaci muje tacire mahaifarta don aganina diya daya ta ishemu, tara 'ya'ya najawo talauci da wahala. Nan take tanuna rashin amincewarta da hakan, na buga na raya amma taqiya acewarta baxata kashe kanta da kanta ba. Hakan yasani fita harkarta na qaurace mata, ban yarda auwal yasan da hakanba don nasan bazai ta6a bani goyon bayaba. Kawai ranan saigashi har shagona lokacin ban gina mall dinaba, fada sosai yaimani kamar zai cinyeni don sosai ranshi ya6aci ashe khadijah taje tasameshi ta fadamashi da abun ya isheta. Ban tankamashiba harya gama banbaminshi yakuma ce bazata cire mahaifaba saidai ni inje a ciremin kwayakwan haihuwa idan dagaske haihuwarce banso aiba dole sai ita zata cire mahaifaba. Raina yayi mugun 6aci a ranar kuma bawai fadan auwal yafi 6atamin raiba, A'a qarata da khadijah takai wajenshi yafi 6atamin rai. Ina komawa gida nima najuyemata nawa kwandon masifar, ataqaice dai munfi sati ana abu guda, har allah yakawo qarshen aurenmu asanaddiyar hakan. Bayan mutuwar aurenmu da kwana biyu Auwal ya ritsani gida, ashe labari ne yakaimashi. Ranar naga 6acin ran auwal da ban ta6a ganiba don sosai ya wankeni tass sai akayi rashin sa'a nima lokacin awuya nake don tun bayan rabuwarmu komai yaqi yimin dadi arayuwa. Bazanso tuna magangganun dana fasamashi ba a ranar... idona yarufe... nakasa gane kuskuren danake tafkawa.... ataqaice dai aranar abotarmu ta watse don kowa alokacin zuciyarshi awuya take ankasa samun daya daga cikinmu dazai ankare da 6arnar damuke shirin aikatawa. Korar wulaqanci nayi mashi.... nakuma yimishi iyaka da gidana da ni kaina, shima yayimin alqawarin babu shi babu ni. Tun fitarshi a falona kafin ma yakai gate nafara danasani saidai girman kai ya hanani aikata abinda zuciyata ke rayamin wato inbishi mu sasanta. Haka na kwana cikin baqinciki da 6acin rai, abu ya hademin goma da ishirin, na farko na rabu da matata da shalelen diyata ga asarar babban jigo danayi. Ganin garin ya daina yimin dadi kullum ina cikin damuwa yasani barin kasar gabadaya. Ban tashi dawowaba sai bayan shekaru uku wanda alokacin allah ya budamin sosai naqara arziqi saidai zuciyata naga Auwal dina ina matuqar kewanshi don a daddafe nayi wannan shekarun a can qasar. Bayan dawowata nigeria na shiga nemanshi saidai tashin farko nakasa gane gidanshi, gadaini a unguwar amma gidanshi ya 6acemin haka nagama bulayi na nakoma gida. Ahankali ahankali nacigaba da naimanshi amma shiru, ga inda yake aikinshi babu alamun masu irin aikinshi duk ancanzama wurin fasali. Ataqaice nakusan wata uku sannan allah ya hadani dawani abokin aikinshi Mallam yunusa wanda irin sana'arsu daya dama shima motoci gareshi don yama fi auwal jimawa a harkar. Sosai nayi farinciki alokacin don aganina nasameshi nagama saidai abinda yafadamin yasa murnata komawa ciki, baqinciki ya maye gurbinta. Cemin yayi shekararsu daya kenan da barin qasar wai ya saida gidanshi da mottocinshi sun koma turai dazama dashi da duk family dinshi Haka nakoma gida jiki a mace, ban daddaraba na shirya naje garinsu wudil dukda zuwana daya lokacin rasuwar mahaifinshi. A wudil ma haka naita galbaro na nagaji don garin ya canza sosai jama'a su qara yawaita, kwanana biyu nabaro wudil jiki a sanyaye nadawo gida. Haka nakusan cinye sati ina jimami sosai sannan dakyar nacigaba da al'amurrorin gabana saidai auwal nanan maqale a zuciyata ina kuma roqon allah kowanne sallah ya hada fuskokinmu duk daran dadewa. Ganin kadaici yamin yawa yasa na nemi a maidomin saudart jin mamarta aure zatayi. Dakyar suka bani ita, sai alokacin nadan samu sauqi don sosai take debemin kewa. Haka nacigaba da rayuwata daga ni sai yata, nakasa qara aure don mata tsoro suke bani, bana fatan auro wanda zata cutarmin da yata wanda nakejinta kamar tsokar jikina. Haka naita zama dagani sai yata ina kulada ita agefe kuma nacigaba da business dina inda daga baya na bude mall dina mai suna A.S MALL INTERNATIONAL LTD. *A.S* din na nufin *AUWAL.SHAMSU* don har alokacin nakasa mantawa dashi, haryanzu... har gobe" Shiru yayi yana kallon mutanen falon wanda sukayi tsitt banda kallonshi babu abinda suke, ummy idanunta sunyi jajur don tayi hawayen tayi hawayen harta gaji itama umma sosai jikinta yayi sanyi don kallo daya zaka mata kagane hakan. 6angaren su kawu ibrahim ma kallonshi suke suma da alama jikinsu duk yayi sanyi. Sadeeq dake zaune qasan rug kusada ashraf shima kallo daya zakamashi kasan shima jikinshi amace yake don sai kallon daddy yake da expression din tausayi a fuskarshi, shikau goga Ashraf baka iya gane yanayin dayake ciki don haryanzu kanshi na qasa idanunshi kuma a lumshe saidai daga nesa kana iya hango jijjiyar data fittomashi rado rado a gefen wuya. Saudart kau kanta na kife akan cinyar daddy tana hawaye silently. Ahankali yakai hannu ya shafa kanta yana dan murmushi "Saudart kadai ke gareni, ita kadai ta ragemin duniya da lahira, itace farincikina nine nata, she can do anything just to make me happy amma kwadayina da son kudi yasa nayi tampering da nata happiness din... i forced her, taso nunamin kuskuren haka amma naqiji, na fake da ciwon qarya duk don ta yarda don nasan bazata ta6a jurar ganina cikin damuwaba takasa yimin maganinta muddin tanada ikon yin hakan, haka na tilastamata ba don komaiba saidon nasan zan qaru, itama haka amma dayake allah allah ne saigashi yajuyemana komai ba kaman yadda na tsaraba, ya gwadamin ban isa inyima kaina abinda beyi niyyar yiminba saigashi i end up hurting my one and only child, sanyin idaniyata" Shasheka saudart keyi ahankali kanta kife da cinyarshi tanajin wani abu na ta6amata zuciyarta. "Kuyi haquri, words can't express how sorry i am, just find a place in your heart and forgive this greedy man" yafada yana lumshe idanu. Shiru falon ya dauka, bakajin komai sai sheshekar saudart shima can qasa, anrasa wanda zai magantu cikinsu. Dakyar kawu ibrahim yabude baki vayan wani lokaci yace "Kenan vakai kasa aka kamama auwal kayaba?" Bude idanunshi yayi ya kalleshi yace "Wane kaya? Ni nakasa gane abinda kuke nufi" "Bayan rabuwarku da Alhaji da shekaru biyu bakai ka hada baki da customs ba suka kama mashi mottocinshi ba da kayyayakinshi? Har suka biyoshi gida suka burkice gidan?" Inji kawu ibrahim Girgiza kai Alhaji shamsu yayi cikin confusion "Customs kuma? Ni alokacin ina dubai" Abba ne ya sake cewa "Please ko zaku gayamana abinda yafaru bayan rabuwar margayi alhaji auwal din da Alhaji shamsun?" Shiru dakin ya dauka sannan ahankali shima kawu ibrahim yashiga bada labarin abinda yafaru bayan rabuwarsu zuwa kama mottocin margayi da akayi zuwa yadda aka gayamasu sa hannun alhaji shamsu ne zuwa jinyarshi zuwa rasuwarshi zuwa wahalhallun da iyalansa sukasha har kawo yanzu. Sosai Alhaji shamsu tashiga tashin hankali, banda innallilahi babu abinda yake maimaitawa hawaye na zubar mashi. Kasa cewa komai yayi don he's speechless ma. "Amma waya fadamaku Alhaji shamsun ne keda sa hannu akan hakan?" Inji abba "Abokan aikinshi ne" "Can you specified?" "Yes, tsohon ubangidanshi ne mallam tukur sai wani abokin aikinshi mallam yunusa" "Alhaji shamsu waya cemaka margayi shamsu yabar qasarnan gabadaya?" Inji abba yana kallon daddy Shiru yayi don he is still shock Dakyar yabude baki bayan wani lokaci yace "Mallam yunusa" "Then... akwai wata qullala anan, lokacin da abun yafaru alhaji shamsu ma be qasar koko kuna ganinshi ko jin labarinshi?" "A'a, tun bayan rabuwarsu da margayi ko labarinshi bamu sake jiba" inji zahradini "Gaskiya to something is fishy here" inji Abba "Yes, ni saima yanzu nafara tuna wasu abubbuwan da hankalina be karkata gareshi ba alokacin" inji kawu zahradini "Kamar?" Inji abba cikin alamun tambaya "Mallam tukur, farko farkon da margayi yafara hada motarshi yadan chanzamashi kullum shine yayyatashi ga mutane wai beda godiyar allah wai dan qauye yashigo qauye yanason fin ubangidanshi, alokacin banwani dauki abin serious ba don naga lafiya lau suke mu'amallarsu kamar da saidai idan benan ne zaita sukarshi, da allah ya ida budamashi kuma shi dakanshi mallam tukur din yanemi ya ajiyemashi motarshi tunda shima yazama ogan kanshi, mafari kenan dayabar tuqi, shikuma mallam yunusa dama aminin tukur kansu ahade yake. Bayan rasuwarshi kuma sune nafarkon juyaman baya sukaqi bani mota acewarsu basuda empty mota bayan nasan akwai kawai qin badawane sukai, gaskiya nima i smell something fishy" "Kenan sune suka hada baki aka cuceshi?" Inji kawu ibrahim cikin wani yanayi "Bama ceba, amma definiately zasusan wani abu gameda hakan" inji abba. Shiru falon yasake dauka, shidai daddy besake cewa komaiba don abinda ya dameshi ma ya dameshi, he's soo lost in thoughts Ashraf kau haryanzu be dagoba saidai jikinshi yayi mugun sanyi, jinshi yake so guilty, bugawa sosai zuciyarshi take kanshi na harbawa. Tsoronshi daya shine kar ace he's taking revenge on the wrong person....✍ Please fans asani acikin addu'a, i really need your prayers, allah yacikamani da kowama burikanmu na alhairi👏 Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 078 Ba Ashraf ba su kansu kawu dasu ummy jikinsu saida yayi sanyi, they never thought Alhaji shamsu was innocent, sanin halinshi na greediness yasasu yarda cewa zai iya aikata hakan, basu ta6a kawoma ransu bashi bane. "Hasbunallahu wani'imal wakeel! Alhaji shamsu kenan all these years damuke riqe dakai azuciya you're innocent? Ta ina zamu fara baka hqr?" Inji kawu ibrahim a sanyaye. Shiru falon yasake dauka kowa da abinda ke ranshi, saudart kau haryanzu bata dagoba daga kifa kan datayi a lap din daddy "Alhaji shamsu we're so sorry, mun makance mun kasa tuna shaquwa da zumuncin dake tsakaninku har muka yarda da magangganun mutanen nan, alokacin gani muke zaka iya dubada yadda abotarku ta watse kukayi baranbaran atunaninmu fansa ka dauka ta wannan hanyar don quntatawa margayi.... will you please find a place in your heart to forgive us" inji kawu zahradini shima asanyaye "Shiyasa akace zato zunubi koda yazama gaskiya, da wane ido zamu kalleka shamsu?" Inji ummy tana share hawaye. Ajiyar zuciya daddy ya sauke zuciyarshi na quna, shikau me yayima su mallam tukur zasu jamashi wannan sharrin? Yana iya tuna lokacin da suke aminta da margayi yadda mallam yunusa ke zuwamashi da maganar margayi cewa yaceme kaza yace kaxa duk don yaji haushi amma beta6a biyemashi ba saidai yanuna mashi bakomai ai shima yasan da zancen, bejin zai iya yafemasu, sune sanadin margayi auwal, sunsa ya mutu da baqincikinshi. "Dan allah ku daina neman yafiya awajena, ni bakumin komaiba, ko nine a matsayinku alokacin dolene in yarda da hakan, idan ma batun yafiyane saidai in nemi naku, wataqila da banso kaina dayawaba na nuna banson haihuwa da bamu samu sa6ani da margayi ba bare har akaiga haka, kuyi haquri mu yafi juna, tabbass na koyi darasi, ko ince darussa, na gane kwadayi mabudin wahalane kuma zafin nema baya kawo samu, please forgive me too" "Mune xamu nemi yafiyarka shamsu, ka yafemana" inji kawu ibrahim "Allah ya yafemana bakidaya, yajiqan Auwalu na yasa ya huta yakai rahma a qabarinsa yakuma hada fuskokinmu gabadaya a aljannatul firddaus" Da amin duk mutanen falon suka amsa cikin sanyi "To alhamdullilah, dama komai dake wakana a rayuwarnan rubuttacene jikin lau'un mahfuz, gashi cikin ikon Allah komai ya warware mana cikin sauqi, naji dadi sosai da warwarewar wannan matsalar nakuma yi farinciki da bayyanar gaskiya adaidai wannan lokacin, Allah kenan! Kunga ikon Allah ko, bayan shekaru kusan ashirin saigashi yasake hadaku don warwaremuku gaskiya, wannan ba qaramin abun farinciki bane, fatanmu anan shine allah ya jikan margayi dama kullihin musulmai yakuma tona asirin masu sa hannu a sanadin ajalinshi, allah yacigaba da karemu daga sharrin mahassada da maqiya na zahiri da 6uya" inji Abba Duk da amin suka amsa wanda hakan yai daidai da kwala kiran sallar azahar. Anan duk akayi haramar tashi yin sallar zuhr din. Daddy ya umarci saudart takaisu ummy sama su gabatar da sallar. A kunyace ta tashi tana masu iso sukabi bayanta. Haka duk aka fita daga falon aka bar daga Ashraf sai sadeeq. Matsawa sadeeq yayi kusada ashraf da kanshi ke sunkuye haryanzu yakira sunanshi ahankali. Shiru ashraf yayi kuma yakasa dagowa. "Ka tashi mallam muje muyi sallah ko sai munrasa jam'i?" Sai a sannan yadago ahankali ya kalleshi "Muje" inji sadeeq yana qoqarin miqewa. "Sadeeq how will I face this man? Tayaya zan iya fuskantarshi after all i did to him? Ya sallam" yafada yana dafe kai "Hmm i told you ai, ba'a yanke hukunci akan abinda bakada tabbaci akai now see what happen" "What am i suppose to do? I can't face him, i want to varnish" ya qarashe kamar zaiyi kuka "Haba varnish to where? Dole kayi facing dinshi ka nemi yafiyarshi and his daughter, afterall qaddarace da baka nemi daukar fansan ba da ba'a kaiga haka ba, da haryanzu zarginshi kuke" "Can't face him wlh, ka manta da rashin mutuncin da naita mashi? Wayyo kunya" Muryar kawu zahradini ya dawo dasu "Wai bazaku fitoba sai an kabbara?" Juyowa duk sukayi, tashi ashraf yayi shima yya jera da sadeeq kanshi qasa suka fito suma. Haka suka dunguma suka nufi massalaci dake kusada gidan don gabatar da zuhr. A 6angaren saudart ma kasa hada ido tayi dasu, haka dai ta kaisu sama ta nunamusu toilet don daura alwalla kafin su fito kau ta shimfidamasu sallaya. Suna fitowa itama tashiga ta dauro nata alwallar ta fito itama ta shimfida wata sallayar abaya ta tada nata sallar. Koda tagama suma tuni sun gama saidai ta kasa dagowa daga sunkuyen da kanta yake don ba qaramin kunyarsu takejiba sai mutsu mutsu take cikin hijab. Duk sun lura da yanayin datake ciki amma suka basar suka shiga janta da fira. A kunyace take amsa masu wanda yawanci amsar murmushi ne don jitake kamar ta nutse don kunya. Ahankali ummy ta dauko maganar aurensu inda take nusar daita cewa karta yarda ta cuci kanta, karta yarda tayi za6in da zai cutar daita, tasan komai kuma bazata ta6a ganin baqinta ba idan suka rabu da ashraf, hakan bazai chanza kasancewarta diyarta ba. Itadai saudart bata iya dago kanta ba bare ta amsa, jitake kamar ta nutse don kunya. Bayan sallar duk suka fito daga massalacin suna tafe suna fira cikin raha da jindadi. "I can't still believe A.A dana ne, d'an aminina kuma my in-law" Duk murmushi sukayi yayinda ashraf yaqara sunkuyar da kanshi qasa yanajin kunyar yadda daddy ke riqe da hannunshi. Tunda akace shine dan Alhaji auwal yaketa nan nan dashi don kusadashi ma ya tsaya wurin sahun sallah. Shikau ashraf jinshi yake so uncomfortable, yakasa koda hada idanu dashi jiyake kamar ya 6ace ya huta. "Kai alhaji yaushe ka ta6a ganin father-in-law da son-in-law na haka? Ina kunyar?" Inji abba yana dariya. "Ku kuka santa, ni nan dana ne kuma aboki ko son?" Yafada yana kallon ashraf dake sinne kai kamar wata amaryar qauye Jiyayi kamar ya nutse hakan yasashi qara sunkuye kai Dariya duk aka dauka kawu ibrahim yace "Atoh da alama shi bemanta da ita kunyarba" "Hmm bawani jinin fulanawa ne dake yawo ajikinshi kawai ba komai ba" Haka dai suka shigo gidan suna hira cikin raha da dariya shikau ashraf kanshi a qasa yake biye dasu sadeeq abayanshi sai faman danne dariyarshi. Wannan karon saida duk suka dan ta6a abin motsa baki ana fira cikin raha da dariya idan ka cire ashraf da saudart da suka kasa dago kansu sai sadeeq dake gefen ashraf shima yanna tsokanar ashraf qasa qasa. Sau biyu idanun saudart na hadewa dana ashraf duk dagowarta hakan yasa bata qara dagowaba. Saida komai ya lafa sannan suka fara gabatar da abinda ya tarasu tun farko, anan kawu ibrahim yafara bada labarin asalin aurensu A.A da dalilinshi na qirqirar auren duk don ya dau fansa akan abinda yake zargin daddy dashi be 6oyemasu komaiba har zuwa yanzu dasuke zaune. Shiru falon ya dauka, mammaki ne sosai yacika saudart don ko da wasa bata ta6a kawowa ranta Ashraf nada wata manufa gameda aurensu ba, she thought kawai irin mutanen nan ne da basu yarda suyi taimako batareda wani abu in exchange ba don ko rashin mutuncin dayakema daddy gani take kawai saboda giyar kudi dake dibanshi ne don tasan wasu mutanen kudi na maidasu rude brats. Ashe shi revenge yake taking. Ahankali tad'an dago idanu ta saci kallonshi taga kanshi na akasa don tunda akafara maganar yakasa kwakwarar motsi, jiyake kamar ya 6ace ya huta. Sauke idanunta tayi ahankali abinda takeji gamedashi naqara hauhawa yayinda kwakwalwarta tashiga tariyomata cin mutunci dayaimata ita da daddy. Daddy kau a 6angarenshi shima yayi mammaki amma daga baya kuma saiya saki murmushi yana kallon ashraf daya wani raku6e waje daya kamar wanda ruwa ya cinye. "Allah sarki son, ba laifinka bane, rashin sanine kuma rashin sani yafi dare duhu, konine a matsayinka idan banyi fin hakaba to iya abinda zanyi kenan, besides nima da nawa laifin da banda kwadayi da bazan yarda da hakanba da na hango wani abu makamancin haka amma lokaxin idanuwana sun rufe nakasa hango komai, Am sorry for putting you through pain son" Qara yin qasa ashraf yayi dakai yana jin wani matsanancin kunya jiyake kamar ya ruga aguje yabar gidan gabadaya. "Muhammad?" Daddy yakirashi da ainahin sunanshi Kasa dagowa ashraf yayi "Look at me son, ko baka yafemin bane?" Girgiza kai yayi ahankali still be dagoba. "Come closer son" Shiru yayi yakasa motsawa, kowa na falon shi yake kallo harda saudart dake kallonshi ta qasan ido tanajin wani daci daci a maqoshinta. Ahankali ya rarrafo gefen daddy ya zauna kanshi sunkuye "Ashraf?" "Am...sorry daddy, please forgive...me" yafada ahankali still kanshi qasa. "Ni bakamin komai ba,if am in your shoe i'll behave exactly the way you did, am sorry too, forgive me too" Shiru dai kawai yayi still kanshi qasa. Ganin babu mai niyyar sake magana acikinsu yasa kawu ibrahim gyaran murya ahankali sannan yace "To alhamdullilah, godiya ga allah subhanahu wata'ala daya sa muka fuskanci juna sosai ayau wanda idan kukayi duba ga wannan abu zakuga tsararrene wanda ubangiji ya tsara domin koyarda kowanne cikinmu darasi. Nafarko da Alhaji shamsu be nemi taimako a kamfanin A.A ba da haryanzu muna cikin duhu gameda abinda muke zarginshi akai na sanadin margayi. Nabiyu da Ashraf be dage akan daukar fansaba da bamuyi wannan zaman ba na yau Da alhaji bai aminta da aurennan ba da haryanzu muna acikin duhu Saigashi abun kamar a film, abinda yafaru shekara da shekaru anzo an warwareshi yanzu bayan babu wanda yata6a kawowa ko a mafarki zamu sake haduwa a duniyarnan. Dama ance kana naka Allah na nashi gashi sanaddiyar auren nan na contract tsohon zumuncinmu zai cigaba daga inda ya tsaya insha allah. Don koda auren nan ko babu auren nan bazamu ta6a watsar da zumuncinmu ba a karo na biyu kuma muna fatan insha allah zumuncinmu yacigaba da dorewa har qarshen rayuwarmu har izuwa cikin aljanna insha allah" Juyowa yayi yakalli saudart da kanta ke qasa yace "Haqiqa 'yata kin kasance diya abar alfahari ga kowa'anne iyaye, abun kwatance ga alumma, ki kasance mai biyyaya da tarbiya ga girmama na gaba dake. Da watace taga yadda Ashraf ke wulaqanta mata iyaye da ko kallo nashi iyayen bazasu ishetaba amma ke kin kauda kai kin rungumi iyayenshi da danginshi kamar naki, kin kawo haske a rayuwarsu gabadaya kin ajiye komai kin taimakeshi a lokacin da yake buqatar taimako kuma ke kadaice keda ikon yin haka alokacin batareda kinyi la'akari da abubbuwan dayaimiki kuma yake kan yimaki alokacin, gaskiya you have a good heart kuma allah ne kadai zai iya saka maki, kin jure abubuwa dayawa saboda farantama mahaifinki rai haqiqa ke yar aljanna ce insha allah" Dan dakatawa yayi yana kallonta kafin kuma ya cigaba dacewa "Saudart you've endure enough, kin juri abubuwa dadama akan wannan auren bazamu tilastaki da cigaba da zaman cutuwa ba. You have a choice, aurennan zai dorene bisa ga kalar amsar da kika bada, karki cuci kanki daughter, ada kin amince ne saboda daddynki yanzu kuma nobody is forcing you, your fate is in your hand kuma munaso ki sane ko da aurennan ko babushi babu abinda zai canza alaqarmu daku don haka choose wisely daughter" Shiru dakin ya dauka all eyes on Saudart while ashraf kanshi a sunkuye zuciyarshi na bugu abnormally. "Daughter? Ni mahaifiyar ashraf ce amma dana ji abinda yafaru the first thing dayazo bakina shine yabani takardarki don nasan you've suffered enough, ba don su kawu ibrahim sunsa bakiba akan abari aji ta bakinki da wlh bazamuzo nan ba saida takardarki, ni na haifi ashraf kuma nasan halinshi idan ya tsani abu don haka karki cuci kanki don farantawa kowa saudart, ki tuna this is your life bana kowaba, idan kin cigaba da zama dashi don wani to kanki kika cuta, just pour what's in your heart daughter, fear nothing" Shiru dakin yasake dauka saudart ko motsawa batayiba shima ashraf haka saidai kowanne bugun zuciyarshi ya chanza sosai. "Saudart?" Kawu ibrahim ya kira sunanta ahankali. Ahankali ta dago kanta ta kalleshi saikuma ta maida kanta qasa "Zaki cigaba da zama da Ashraf a matsayinshi na mijinki daga auren contract zuwa auren gaske na har abada koko ya sawwaqe maki Allah ya hada kowa da abinda yafimishi alhairi? Remember your fate is in your hand" yaqarashe a tausashe. Tsit falon ya dauka kowa idanunshi akanta, zuciyoyin kowa na qara bugu musanmman na goganku😄 sadeeq kau harda share zufar daya tsatsafo mashi a goshi😆 Motsi tafara yi da baki amma maganar taki fitowa kallo daya zakamata kasan bata cikin nutsuwa. Dafa kafadarta ummy tayi ahankali tace "keep calm daughter, just pour your mind" Lumshe idanu tayi tana sauke ajiyar zuciya yayinda komai daya faru daga haduwarsu da ashraf har kawo yanzu yashiga yawo a kwanyarta. Ahankali ta rufe idanunta ta bude bakinta dakyar tace...✍ Kusani a prayers fans👏 Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 079 Ahankali ta rufe idanunta ta bude bakinta dakyar tace "Allah yasa hakan shiyafi alkhairi" tafada cikin sanyi sosai Tsiit falon ya dauka na wucin gadi don kasa gane inda maganarta ta dosa sukayi. Kawu ibrahim ne yayi karfin halin cewa "Me hakan ke nufi daughter?" Shiru tayi kanta aqasa takasa cewa komai. "Kinga saudart ki bude baki kiyi magana, this is something serious" inji Abba Shiru tayi har lokacin kanta aqasa sai idanunta dake forming din hawaye. "Saudart kin yarda xaki cigaba da zama da Ashraf a matsayin matarshi ta sunna na har abada?" Inji daddy yana kallonta keenly trying very hard to read her mind Gyada kai tayi ahankali batareda ta dagoba. "Ba maganar kurame zakiyi ba, open your mouth" inji abba Ahankali ta bude bakinta trying very hard to control her emotion "Eh abba, na....amince" Shiru falon yadauka kowa na kallonta unbelievable Babu wanda amsarta beyi shocking ba don basu ta6a tsammanin wannan amsarba. Ashraf kau kasa gasgata kunnuwanshi yayi, amsarta kawai ke eoching a kunnuwanshi jiyake kamar amafarki. "Karya kike saudart! This is not coming direct from your heart" inji ummy cikin dan daga murya Kasa dagowa saudart tayi bare ta lalubo amsarda zata bata. Yes, amsarnan is not directly from her heart don babu abinda zuciyarta ke muradi kamar rabuwa da ashraf, she hate him and today she hate him more, jin cewa duk abubuwan dayake musu fansa ne yaqara dagula mata lissafi yasata jin bazata ta6a yafemashi ba, yasata jin qara tsanarshi a zuciyarta. Ta tsaneshi ta tsaneshi saidai wannan kalmar saidai ta tsaya a cikin zuciyarta, jitake inama tana iya furtawa, tasan furtawan kawai zai rabata dashi har abada amma kash! Bazata iyaba. Ada babu abinda take buqata irin wannan damar, damarda xata rabata dashi na har abada, kullum cikin addu'a take allah ya kawo rabuwarsu, yarabata da wannan mutumin da babu digon sonshi ko diss a zuciyarta, saigashi damar tazo amma wani abu yayimata katanga da samun cikar burinta, tana ji tana gani zata amince da abinda xuciyarta bataso, xata zauna zanan cutuwa, xata za6i rayuwar qunci da baqinciki. "Saudart look at me!" Ummy ta umarceta. Saida tayi iyakar qoqarinta na ganin ta maida hawayen dake maqale a idanunta tundaxu taqi basu damar sauka don tasan sune zasu fallasa asirin zuciyarta sannan ta dago tana kallon ummin "Tell me, wake tilastaki yanzu? Ni da ke munsan ba gaskiya kike fadi ba" Ahankali tashiga girgiza kanta trying so hard to control herself "Ummy babu mai tilastani, this is coming directly from my heart.." "Karya kike" ummy ta katseta "Saudart kinsan abinda kike shirin yi kuwa? You are depriving yourself your right" tafada wholeheartedly "No ummy, inayin abinda kuka sanine, kunce infadi ra'ayina batareda nayi considering din komai ba and that's exactly what am doing, it's my choice ummy" tafada calmly yayinda zuciyarta ke fadin akasin haka Shiru ummy tayi tana kallonta kawai, kallo ne na mammaki chakude da tausayi, tasan karya take, gashinan tana hango hakan acikin idanunta, meyasa zata za6i quntatawa kanta, meyasa xata za6i zaman cutuwa? Zaman da babu digon so aciki? Shidai ashraf haryanzu yakasa dagowa kuma haryanzu jinshi yake kamar a mafarki, kai mafarki ma ne, yarinyar da ta tsaneshi, batada wani buri daya wuce rabuwa dashi zata amincewa cigaba da zama dashi na har abada? This is a dream, mafarkin da bazaiso ya farkaba yanzu. Sadeeq ma was totally shocked, kallonta kawai shima yake yana son hango bakin gaskiyarta ta cikin idanuwanta. "Saudart?" Kawu ibrahim ya kirata. Ahankali ta dago kanta daga sunkuyen dayake ta kalleshi sai kuma ta maida kan qasa. Daddy kau sai kallon diyar tashi yake yana karantarta "Meyasa kika amince da cigaba da zama da Ashraf?" Ya jefa mata tambayar yana kallonta. Shiru tadanyi na yan daqiqu sannan ahankali tafara cewa "Saboda aganina dakuma tunanina wannan auren hadine na Allah, akwai manufofi da dama acikin wannan auren, ta dalilinshi abubuwa da dama sun warware, zumuncinda ya dade da watsewa yana neman cigaba ta dalilinshi, wannan ba komai bane face ikon allah" ta qarashe maganar asanyaye "To amma Ashraf fa? Kina sonshi? Shifa aure ba'a zamanshi akan wani dalili kuma baya dorewa idan babu soyayya, wadanda akayi na soyyayama yaya aka cika bare wannan wanda dalilinshi bekai hujja ba, gashi shi da kanshi yafadi abubuwa dadama dayamiki marar dadi a dan zamanku, kina ganin baxaki dinga tunawa ba duk in kin ganshi?" Hadiye yawun daya tararmata a maqoshi tayi sannan tabude baki dakyar, allah ma yasan dauriya kawai take amma ita kadai tasan me takeji acikin zuciyarta. "Kawu kamar yadda nafada, qaddara dakuma ikon allah ne ya hadamu, Ashraf... ya bijiro da wannan abun ta dalilin fansar dayakeson daukane, da ba'ayi auren ba akazo har yanzu da haryanzu yana ciki da daddy, yakuma yimana abubuwane bisa rashin sani, da yasan gaskiya nasan baxaiyi hakaba, so kuma allah kesawa azuciyar mutum ya musanya qiyyaya da so alokaci daya kuma... hakan na iya faruwa" ta qarashe zancen taba lumshe idanu, maganarnan datake ita kadai tasan yadda takeji, sosai zuciyarta ke zafi yayinda ita kanta tasan qarya take shirgamasu don batajin akwai ranarda zata ta6a kallon ashraf da sunan so. Tunda tafara magana dama ashraf ya dago yana kallonta, he can't believe she's saying all these. Atunaninshi yanzu zata qara tsanarshi ne dataji cewa yana amfani daita ne dan daukar fansa, atunaninshi tsanarshi zata qara hauhawa ne acikin zuciyarta, ashe zata fahimceshi? Ashe zata bashi second chance? She look soo real that yakasa gane she's just framing up ne. Kallonta kawai yake wani sabon kaunarta nasake huda zuciyarshi. "To alhamdullilahi, yanzu dai kowa yaji amsarta data bada da bakinta da kuma dalilanta, me zakuce?" Inji kawu ibrahim yana kallonsu. Ajiyar zuciya abba ya sauke yace "Masha allah, haqiqa dalilanta abin dubawane kuma babu abinda ke ciki sai gaskiya, fatanmu anan shine allah yasa hakan shiyafi alhairi kamar yadda tafada da farko" Daddy ma yace "To alhamdullilah, gaskiya naji dadi sosai da faruwar hakan fatanmu allah yabada zaman lfy ya kauda fitina kuma yaqara danqon zumuncinmu" Kawu zahradini shima yace "Amin amin, nima nayi farinciki qwarai da hakan allah ya tabbatarda alhairi" Umma da bata cika magana sosai tun sadda sukazo tace "masha allah allah yabada zaman lfy, ya tabbatar da alhairi" Kallonsu suka maida gabadaya gun ummy datayi zugum cikin damuwa kawu ibrahim yace "Kefa? Bakice komaiba" Ajiyar zuciya ta sauke ahankali sannan ta kalli saudart da kanta ke qasa sai kokowa take da hawayen dake neman tonamata asiri sannan ta maida dubanta kan ashraf dashima kanshi ke qasa sannan tace "To allah ya tabbatar da alhairi yakuma sanya albarka aciki" Duk aka ansa da amin cikin farinciki. "Kaifa oga gauro? Baxaka tofa naka albarkacin bakin ba?" Inji kawu zahradini yana kallon sadeeq. Murmushi yayi a kunyace sannan yace "Allah yabada zaman lafiya, ya kauda fitina" Duk aka amsa da amin. Itadai saudart kanta na qasa amma zuciyarta inbanda suya babu abinda take, tasan tayi wauta sosai, wautar da har ta mutu bazata bar ganin sakamakonta ba, ta ida wargaje rayuwarta da hannunta, ta ida tabbatar wa kanta bazata ta6a yin rayuwar auren da ta dade tana tsarawa kanta ba. Shikenan bakin alqalami ya bushe, there is no going back. "To alhamdullilah yanzu sai ayi maganar tarewa ko? Koko sai munsake shagalin biki tunda wancan na contract ne wannan kuma na gaskiya?" Inji kawu ibrahim cikin sigar tsokana. Duk dariya sukayi inka cire saudart da ashraf sai ummy data murmusa, shikau sadeeq duka 36 dinshi suna waje don dariya. "Duk yadda kukayi ai daidai ne" inji daddy cikin fara'a "A'a badai yanzu ba, abari amarya tagama shirye shiryenta sannan, su da kansu zasu bamu lokaci" inji umman sadeeq tana murmushi. Haka dai suka gama tattaunawarsu wanda saudart kawai jinsu take, aqagare take awatse ko tasamu ta ke6e taci kukan dake cinta yadda ya kamata, lumshe idanu tayi jin kanta na dan sara don hayaniyartmsu ma kanta bataso. Sadeeq kau a 6angarenshi sai mintsinin ashraf dako kwakwarar motsi beyiba tundaxu yana mashi rada saidai ko kadan be nuna yasan yana yiba, farincikin dake ranshi kawai ya isheshi. Yanajin yadda mutanen falon suke tashi suna barin falon har yarage saura sadeeq kadai sai shi da saudart, wani mintsini mai uban zafi yaqara mashi sannan shima ya tashi yafita. Murmushi yadan saki wanda saika lura zakasan yayishi sannan ya daga kai yabishi da kallo harya fice yaja musu kofa. Ajiyar zuciya yasaki marar sauti sannan ahankali ya maido dubanshi kanta. Tana dai yadda take, zaune lullu6e cikin makekiyar hijabinta kanta a qasa. Kallonta yake babu ko kyaftawa yanajin wani shauqi acikin zuciyarshi, be ta6a tunanin abubuwan zasu zo da sauki ba haka, a tunaninshi idan tasan gaskiya komai dagulewa zaiyi ashe ba haka bane, ashe zata yafemashi, ashe zata fahimceshi, ashe zata bashi dama. Motsi yake da baki amma yakasa fadin komai, yarasa ta ina zai fara, yarasa da wacce kalma zaiyi amfani, kallo daya zaka mashi kasan a diririce yake. Soyake tadago ya kalleta, ya kalli fuskar dake sashi cikin shauqi, fuskarda be gajiya da kallonta, fuskar da ke sashi cikin nishadi. Ahankali yayi parting din pink lips dinshi cikin muryar rada yace " *SAUDARH*"...✍ Ngd qwarai da addu'o'inku gareni, allah yasaka ma kowa da mafificin alhairi (amin) Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 080 Bata ko motsaba bare asaka ran xata dago daga sunkuyar da kan datayi. Shiru yayi yana kallonta, he can't believe yanzu tashi ce har abada, atunaninshi izuwa yanzu alaqar dake tsakaninsu tagama yankewa, yariga yacire rai da samunta don atunaninshi abune marar yiwuwa amma dayake allah me yin yadda yaso ne, gashi ya maida impossible zuwa possible. Kallonta yake wata iriyar soyayyarta na fizgar zuciyarshi, jiyake kamar ya rungumeta a qirjinshi yaita fallasa mata sirrin zuciyarshi gameda ita. "Thank you" yafada ahankali idanunshi akanta "Words... can't express how am feeling right now, i feel i am the luckiest person in this world... thanks for choosing to stay with me...forever, thanks for forgiving me, thanks for.... everything" yafada cikin romantic tone. "I promise... saudarh i promise to make you happy, i'll make sure you'll never regret your choice" yasake fada, kallo daya zaka mashi kasan he meant what he's saying. Ahankali ta dago idanunta harta saukesu cikin nashi. Janye idanun tayi tana sakin wani slight murmushin takaici kafun tace "Regret? Dana sani yanzu nafara shi and babu ranar gamashi, farinciki kuma banasa ran zan qara dandanashi saidai inga wasu nayi, rabona dashi tunda kashigo rayuwata kuma muddin kana cikinta bazan ta6a qara dandanashi ba, kar kayi tunanin wani abu ya chanza gameda yadda nakeji akanka, koda yake ya chanza din, ya qara hauhawa, hawan da baxai ta6a saukaba, dole kaji you're the luckiest man in the world don ka mallakeni saidai point of correction anan shine bani ka mallaka ba *gangar jikina* ka mallaka, kuma dashi zaka rayu har sadda sila zai rabamu walau mutuwa ko wani abun. Kaci nasarar samuna amma bazaka ta6a cin nasarar samun zuciyataba, bazaka ta6a samun kofa azuciyataba komin qanqantarta bare kakai ga shiga, remember bakada quality din mallakar zuciyata na ta6a fadamaka haka, you've not reached that standard and you'll never reach it, zaka rayu da gangar jikina ne... har abada" **************************************************** Lumshe idanunshi yayi ya bude ganin sadeeq na horn abakin gate dinsu. Haryanzu magangganunta sunqi daina yawo a kunnenshi, sunqi daina mashi zafi azuciya. Me zaiyi? Me zaiyi ta dena tsanarshi? Meyayi da zafi haka da bazata iya bashi second chance ba? Atunaninshi komai yazama tarihi ashe da sauran rina a kaba? She still hate him har tana ikirarin bazai ta6a samun zuciyarta ba? Wai gangar jikinta kadai ya mallaka? Meyasa ta yarda tacigaba da zama dashi bayan tasan babu abinda ya chanza daga tsanar datake mashi? Meye dalilinta na yarda? Waya tilastamata? Ya zaiyi? Ya zaiyi da sonta daya nacemashi yaqi fita a zuciyarshi? Ya zaiyi? Dafa kafadarshi sadeeq yayi don ya dade da parking su ummy har sun fita. Ahankali ya dago ya kalleshi a sanyaye. "Are you ok?" Inji sadeeq softly Ajiyar zuciya ya sauke sannan yasa hannu ya bude murfin kofar batareda yace komaiba yafita yarufo kofar yanufi cikin gida. Da kallo sadeeq yabishi sannan shima yafito daga cikin motar yarufe ya maramashi baya. A falo ya iskesu duka baby sai tsallen murna take tana ihun murna cikin siririyar muryarta da alamu dai an fesamata abinda ya faru. Ganin sadeeq yasa tabar tsalle tsallen ta kauda kai still murna fall fuskarta. Tashi ashraf da babu abinda yakeso awannan lokacin kamar kadaicewa yayi yana cewa zai hau sama. Da to suka bishi dashi suna kallonshi don yanayinshi is something else dukda kai tsaye bazaka ce yana cikin damuwa ba, kawai dai ba yabo ba fallasa saidai kallo daya zakamashi kasan asanyaye yake. Cigaba da zubamasu surutu baby tayi tana masu tambayoyi uwa yar jarida duk na saudart kamar ya takoma yanxu? Yaushe zata dawo ddss. Itadai ummy ko kallonta batayiba umma ce mai biyemata sai sadeeq daya tisata gaba da tsokana tana ramawa. Hakadai suka kasance cikin raha kowa kagani yana cikin farinciki don fuskarsu ma takasa 6oye hakan, jisuke yau rana ce ta musanmman agaresu, ranar farinciki. Knocking din kofar akayi ahankali, ko ba'ayi magana ba tasan daddy ne hakan yasa tayi saurin gyara zamanta tana goge hawayen fuskarta. Murda handle din kofar akayi yashigo da sallama. Amsawa tayi ahankali tana qirqiro murmushi. Qarasowa yayi cikin dakin idanunshi kafe da ita harya iso gaban gadonta ya zauna daga dayan gefen yana kallonta. Ganin irin kallon dayake mata yasata sakin murmushi cikin basarwa tace "Daddy na" tafada a shagwa6e tana matsowa kusadashi tayi pillor da kafadarshi "Shalele ta" yafada yana dan rungumo kafadarta Lumshe idanu tayi tana jin qaunar daddyn nata sosai acikin zuciyarta "Shalele, meyasa kika yarda da abinda zuciyarki bataso? Meyasa kika za6i zama da abinda zuciyarki bata muradi? Hmm?" Ya tambaya softly. Tasan 6ata lokaci ne kawai jayaya dashi akan ba haka bane don tasan idan tana iya yiwa kowa basaja to banda daddy don yasanta ciki da bai, kallo daya zaiyi mata yagano gaskiyarta ko akasin haka. "Daddy ka tayani da addu'a kawai, Allah yakawomin komai da sauqi" "Baki amsa tambaya ta ba" "Daddy, na amsa tambayoyinka tun agaban su ummy, am giving him another chance don wancan lokacin komai yafarune abisa rashin sani, shiyasa nayi mashi uzuri kuma atunanina allah kadai yasan dalilin hadamu tun farko kuma bamuda wata qwaqwarar hujjar rabuwa" Ajiyar zuciya daddy ya sauke sannan yace "To shalele allah yasa hakan shiyafi alhairi, shalele am so happy today na hadu da wadanda na shafe shekaru aru aru ina nema dukda narasa wanda nafi muradin sanyawa a idanu shekara da shekaru" yafada in mixed feeling "Allah ya jiqansa daddy yakuma yimashi rahma ka kuma yawaita sakashi a addu'a don yanxu babu abinda yafi buqata sama da ita, allah kuma ya dorar da zumuncinmu" inji saudart "Amin amin shalele, Allah yayimiki albarka, yasa kigama da duniya lfy yabaki 'ya'ya masu biyyaya kamar yadda kikemana, Allah ya qara daukakaki ya tsareki daga sharrin masu sharri" inji daddy Qara qanqameshi tayi tana murmushin jindadi don sosau taji dadin addu'o'in "Amin sweet daddy na, i love you" tafada cikin murna Dariya daddy yayi cikin farinciki shima yace "Love you more my jewel" "Daddy?" Takira sunanshi a shagwa6e "Na'am shalelen daddy" "Alfarma nakeson kamin daddy, please don't say no" taqarashe maganar kamar zatayi kuka tana qara lafewa a kafadarshi Murmushi daddy yayi sannan yace "I won't, ki fadamin" "Daddy sonike nakoma gidan mamy for a while please" tafada ahankali Shiru yadanyi sannan ya dago fuskarta cikin taffukan hannayenshi yana kallonta yace "Why?" "Hakanan, ba dadewaba zanyi sosai ba, just a week or two" tafada asanyaye Shiru yayi yana kallonta bece komaiba. "Pleeeeease" tafada kamar zatayi kuka. "Ok, anything for you" yafada yana mata murmushi. Qanqameshi tayi cikin jindadi "Yeah! That's my sweet dad!" Tafada cikin murna Shima dariyar farinciki yake, ganin shalelenshi cikin farinciki shima ba qaramin sashi cikin farinciki hakan yayi ba. Haka sukaita fira cikin raha da jindadi wanda rabon da suyi irinshi har mantuwar ta mance, haka sukaita firarsu cikin tsananin so da shaquwa yayinda hakan ya gusarmata kaso 60 na 6acin rai da kuncin datake aciki. Qarshe ma tare suka hau hada yan kayyayakinta dazata dasu gidan mamyn, daddy na mitar zata tafi ta barshi shi kadai, zaiyi missing dinta sosai. Itadai sai dariya take mashi tana fadin abinda duka yan kwansji zatayi tadawo kuma itama ai zatayi missing dinshi. Haka dai suka qarashe yinin cikin farinciki da jindadi. A bangaren ashraf kau tunda yashiga daki be saukoba sai wajajen magrub yafito suka hadu da kawu ibrahim da shima gobe insha allah zai koma suka wuce massalaci. Koda aka gama sallar basu dawoba can suka xauna jiran isha'i inda a dan wannan lokacin kawu ibrahim yaita yimashi nasiha da shawarwaru masu amfani wanda sosai ashraf yaji dadinsu don sun taimaka mashi wajen dan ragemashi abinda yakeji a zuciya. Saida suka gama isha'i sannan suka shigo gida inda direct dining suka nufa. Saida yaci ya qoshi sannan ya miqe yaima kowa saida safe sannan yayi hayewarshi sama. Koda yakoma dakinshi cigaba yayi da tunanin daya katse dazun yana nazarin shawarwarun da sadeeq da kawu ibrahim suka bashi ayau. *Ashraf nasan saudart bawai ta yarda zata zauna dakai bane don son ranta, ta yarda ne don batada za6i, ashraf wannan damace allah ya aramaka don ba kowanne mutum allah ke sake bashi damaba, ashraf take your time, don't play with your opportunity, yanzu damarkace na koyawa saudart sonka, ta mato akanka, ka tsundumata tsundum acikin kogin sonka, don't play with your chance, opportunity come but once* Maganar da sadeeq yafadamashi daxun kafin yatafi ya dawo mashi a qwanya. *Babana Allah ya azurtaka da mace tagari mai tarbiyya, kayi kokarin riqeta dakyau, karka bari tasake kufcemaka a karo na biyu don ba lallai bane allah yabaka irin wannan damar ma, ita zuciya tana muradin mai kyautata mata ne, ka kasance mai kyautatawa iyalinka zakasha mammaki* maganar kawu ibrahim yadawomashi. Ya dauki lokaci mai tsawo yana tunani wanda kuma ke qaramashi qarfin gwiwar samun saudart. Tabbas dafarko yayi kuskure ya bari girman kanshi yakusan kaishi yabaro amma ayanzu ya shirya damarar yaqo zuciyar saudart, saiya koyamata sonshi yadda duk numfashinta saita shaqa da sonshi ne, zai ajiye komai ya gyara abinda ya 6ata da kanshi. Fatanshi dai allah ya tallafamashi yakawomashi komai cikin sauqi. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Washegari wajajen 12:00pm saudart ta isa gidan mamy. Saida ta tsaya suka gaisa da maigadi kamar yadda suka saba sannan ta shige ciki janye da dan qaramin trolley dinta. Gidan shiru kuma tasan hakan be rasa nasaba da saboda yaran na makaranta ne, tasan mamy kadai ke gida, koyaya zata tarbeta? Tambayarda taiwa kanta kenan. Danna doorbell tayi tana jinginar da trolley din gefenta. Saida ta danna sau uku sannan taji muryar mamy na amsawa daga ciki sannan tajiyo takunta na nufo kofar wanda hakan yaqara mata fargaba. Budewa akayi fuskar mamy ta bayyana. Turus mamy tayi tana kallonta daita da trolley dinta da ayar tambaya a fuskarta. "Mamy barka da rana" inji saudart tana dan murmushi Kaucewa mamy tayi tana bata hanya don tashigo tana amsa gaisuwarta. Kama trolley din tayi tashigo tana jaye dashi mamy tarufe kofar tabiyota tana kallonta still da ayar tambaya. Zama saudart tayi kan daya daga cikin kujerun falon feeling uncomfortable da kallon da mamy ke binta dashi. Itama mamy zama tayi dan nesa daita tana kallonta. Zamowa tayi tashiga gaidata cikin girmamawa. Amsawa mamy tayi babu yabo ba fallasa. "Su abdul basu dawo makaranta ba?" Injita trying to sound free "Eh basu dawoba" inji mamy a taqaice. "Ayyah shiyasa gidan yai wani shiru" tafada tana murmushi. Shiru yadan ratsa falon can sai mamy tace "Ya naganki da trolley?" Dan murmushi tayi shyly sannan tace "Zan dan tayaku zamane mamy" Dan ta6e baki mamy tayi tace "ok saiki kai kayan sama ki huta, bari nakoma kitchen" daga haka ta miqe tai wucewarta kitchen din. Tashi tayi itama ta haura sama kamar yadda mamyn tace ta ajiye kayanta a dakin datake sauka anytime idan taxo kwana gidan sannan ta warware nadin gyalen jallabiyarta tabar hula kawai akanta ta sauko qasa ta wuce kitchen itama. Sau daya mamy ta waigo ta kalleta takuma juya ta cigaba da abinda take. Qarasowa saudart tayi ta amshi wuqar hannun mamyn, ba musu ta sakarmata ta koma wajen tukunyar dake saman gas cooker tana budewa itakuma saudart tacigaba da chopping din carbbage din a chopping board. Haka dai sukai aikin kamar kurame babu mai magaba cikinsu gwara gwara saudart tana dan tambayar wani abin idan zatayi itakuma ta amsa a taqaice da alamu dai bata huce ba. Cikin qanqanin lokaci suka gama saudart taita kawosu dining area itakuma mamy ta haye sama. Saida saudart ta gyare kitchen din kamar ba'ayi girkiba ciki sannan itama ta haye sama don watsawa. Wajajen biyu tana zaune kan sallaya bata dade da ida sallah ba taji hayaniyarsu abdul alamun sun dawo kenan. Shafa addu'o'inta tayi sannan tamiqe ta linke sallayarta ta ajiye samsn bedside locker ta cire hijabinta ta adanata sannan tayi hanyar waje. Su abdul nata gwadama mamy sums dinsu dasukayi a school sukaji tafiyarta. Duk dagowa sukayi suna kaĺlonta a mammakince don basusan tana gidanba. Dagudu sukayo wajenta har suna rige rige. Fasa yar qara tayi tana dan qanqame jiki ganin yadda suka nufota don yadda suka taho dinnan tsab su zibe dukkansu. Illai kuwa saigashi suna qanqameta suka tafi gabadaya suka zube. Su aminullah da kamal me zasuyi banda dariya don kamal harda riqe ciki. Mamy ma saida ta murmusa sannan ta dauke kai. Tashi saudart tayi tana turo baki tana dungurinsu ganin sun kadata kuma suna mata dariya. Haka suka taho suka w qaraso falon suna ta dariyar. Nan suka shiga gaidata tana amsawa tana tambayarsu ya school. Tuni abdul yaje ya amshe littafinshi daga hannun mamy yakawoma saudart sai washe baki yake yau yace duka sums dinshi Yabonshi saudart tashigayi tana fasa mashi kai shikau kan sai kumbura yake yana washe baki. Ganin hakan yasa su kamal fara tsokanarshi saudart na kareshi. Ganin abin nasu bana qarewa bane yasa mamy umartarsu suje su chanza su sauko suci abinci. Babu musu duk suka haye sama harda saudart dake goye da jakkar abdul da habeeb. Ita ta taimakawa qanannun suka chanza sannan suka sauko qasa suka wuce dining. Saudart ce tayi serving dinsu suka zauna suka faraci silently bayan kowa yayi basmalah...✍ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) 081 Da suka gama cin abincin duk sama suka haye don shirin islamiyya while saudart ta tsaya gyara inda suka 6ata ta tattara abinda suka 6ata tayi kitchen dasu don wankewa. Tana gamawa itama tabisu saman don taimaka masu wajen shiryawa, anan ne suke tambayarta yaushe zata koma tace musu tananan sai tayimusu sattitika. Zo kuga murna wajensu don sosai suke qaunar yar uwar tasu, haka dai suka kammala shirinsu suka fito gabadaya har wajen motarsu. Shiga duk sukayi driver ma yashiga maxauninshi ya tada motar yaja su Abdul na dagama saudart hannu. Saida suka fice sannan ta sauke ajiyar zuciya murmushi a fuskarta, dan lokacin nan datayi dasu ba qaramin tasiri yayi ba wajen gusar da damuwarta, sosai take jinta cikin nishadi. Juyawa tayi takoma ciki, bata iske kowa falo ba hakan yasata hayewa sama don gabatarda sallar asr don wasu massalatan ma harsun gama. Tana zaune kan sallayarta taji knocking din kofa, shafa addu'ar tayi sannan ta miqe ta dauke sallayar ta dora saman bedside locker sannan tanufi kofar. Tana budewa taga mamy tsaye bakin kofar tana kallonta. Murmushi tasaki sannan ta matsa don bata damar shigowa. Shigowa mamy tayi dakin itakuma ta maida kofar tarufe sannan itama ta shigo. Samun wuri mamy tayi a gefen gadon dakin ta zauna sannan ta nunama saudart dake tsaye gefenta alamun itama tazo ta zauna. Babu musu ta tako ta zauna inda mamyn ta gwadamata ta zauna ta sauke kanta kasa. Shiru ne yadan ratsa dakin kafin mamy ta kawar da shirun ta hanyar cewa "Saudart..." Dagowa saudart tayi ta kalleta batareda ta amsaba "Gayamin gaskiya, meyasa kika amince da cigaba da zama da mijinki?" Ta tambayeta tana tsareta da idanu. Dan murmushi saudart tasaki tana sauke idanunta sannan ta girgiza kai ahankali. "Look, ba maganar kurame zakiyimin ba, ki bude baki kiyimin magana" inji mamy "Babu komai mamy, kawai gani nayi hakan yafi, tunda allah yakawo fahimtar juna atsakani bekamata kuma mu butulcemashi ta wannan hanyar ba, afterall kowa nada laifi a wannan case din this will serve as a lesson to us" tafada vatareda ta yarda sun hada idanu da mamyn ba. Shiru mamy tayi tana nazarinta don kwata kwata bata gamsu da dalilantaba "Saudart kin amincene....saboda ni?" Ta tambayeta ahankali idanunta kafe a kanta. Dagowa saudart tayi ta kalleta saidai kuma takasa cewa komai sai hawayen da ke qoqarin taruwa a idanunta. Sadda kai tayi qasa tashiga girgiza kai ahankali alamun A'a "Saudart look at me.. nace kin amincene ki cigaba da zama da wanda bakiso ne saboda ni?" Bata kalletan ba sai amsa mata datayi asanyaye da "Mamy nariga na fadamaki dalilina" Kamo hannunta duka mamy tayi tana matsowa kusada ita sosai "Then look into my eyes and say it" tafada tana kallonta Kasa dagowan tayi sai hawayen dasuka silalo mata suka digomasu a hannu. "Kenan saboda ni kika yarda?" Inji mamy asanyaye. Kasa amsawa saudart tayi sai hawayen dasuke saukomata ahankali. Tasan wannan ne karo dabiyu ta zata cuci kanta arayuwa, nafarko tayine saboda daddy, mahaifi kuma jajirttace akanta yanzu kuma saboda mahaifiyarta mai qaunar cigabanta. Bazata iya jure ganin mamy cikin damuwa da 6acin rai ba bayan tasan tanada hanyar magancesu, bazata ta6a bari mamy taji kamar batada wani matsayi awajenta kamar yadda tafada kwanaki, tana iya sadaukar da farincikinta ga mutanen nan biyu muddin su zasu samu farincikin don tasan suma sun sadaukar da fiyeda hakan akanta. Ta yarda zata cigaba da zama da ashraf ne don gujewa 6acin ran mamy, ta yarda ne don mamy ta daina tunanin batada matsayi a wajenta bane. She sacrifice her happiness for her and she's ready to do more sacrifices for her muddin hakan zai sata farinciki. "Saudart why? Kinsan abinda kikayi kuwa? Kin yarda ki zauna da wanda bakiso na tsawon rayuwarki? Saboda me? Saboda nayi blunting ranan cikin fushi? You should have know i don't mean all i've said, 6acin rai ne kawai yasani fadin wadansu abubuwan amma shine zaki tafka kuskuren dakikayi a farko?" Itadai shiru tayi sai hawayen da haryaunzu be bar gangarowa ba. "To bazai yiwuba, indai saboda ni zakiyi zaman cutuwa to tun wuri a warware wannan abun, cos baxan iya jurar ganinki kina rayuwar qunci ba" Sai a sannan ta dago kanta jin yadda mamy ke magana seriously. "Mamy.." tafada ahankali saikuma tayi sniffing tasa hannu ta share fuskarta sannan tasake cewa "Mamy duk ba wannan ba nake buqata ba yanzu, addu'arki nafi buqata, bamu saniba wataqila hakan shiyafi alhairi, na yarda da farko saboda daddy dukda banaso amma a sakamakon hakan daddy ya sake re-uniting da mutanenda zumuncinsu ya dade da watsewa, yanxu kuma na yarda saboda ke saboda farincikin ki nasan bazan ta6a danasaniba, insha allah alhairi zai biyo bayan wannan ma kamar koma fiyeda wancan. So mamy batin tada magana bata tasoba, addu'arki kawai zata zama gata agareni" Kallonta kawai mamy keyi cikin tausayawa, tasan saudart diyace mai biyyaya tasan abinda ya faru ba laifinta bane maiyasa 6acin rai ya rufemata idanu ta gayamata irin magangganun data gayamata? Tasan bata qaunar 6acin ranta kuma kullum cikin taka tsantsan take don gudun 6acin ranta meyasa takasa tunawa da hakan alokacin? Jawota tayi vatareda tace komaiba ta rungume. Luff saudart tayi a kafadar mamy tanajin wani dumin dadi na ratsata wanda har hakan saida ya wanzar da murmushi a fuskarta. "Allah yayimiki albarka saudatu, allah kema yabaki 'ya'ya masu biyayya masu gudun 6acin ranki wadanda zakiyi alfahari dasu duniya da lahira" Qara lafewa saudart tayi jikinta cikin jindadin addu'ointa tana amsawa da amin "Allah yasa hakan shizai fiyemaki alhairi allah yasa kici ribar haqurinki" "Amin mamy na" inji saudart murmushi fall fuskarta. Ahankali ahankali mamy kemata nasiha gameda haquri da zamantakewar aure tana nusar daita nauye nauyen dake kanta na haqqin abokin zamantakewar auren nata. Itadai saudart batace komaiba sai lafewa datayi jikinta tana sauraronta magangganun kuma nasamun matsuggunni a can qasan zuciyarta. Ta dauki lokaci mai tsayi tana mata nasiha da shawarwarru inganttatu wanda hakan yayi nasarar kashe jikin saudart murus. Daga qarshe tace "yanzu meyasa kika dawo nan harda uwar trolley? Sokike baban naki yaga kamar ni na huremiki kunne?" Murmushi saudart tayi tace "To mamy dama waya huremin kunnen?" Dunguremata kai mamy tayi tana tashi tsaye tace "Oho dai nidai babu ruwana is better kizo ki koma" "Mamy shifa yace inzo" tafada a shagwa6e Ta6e baki mamy tayi ta bude kofa tana cewa "Kanku dai akeji bari naje nasan yanzu wadancan lasfikokin zasu dawo daga islamiyya su kuma rikita gidan da hayaniyarsu" ta fice. Ajiyar zuciya saudart ta sauke bayan fitar mamy takoma ta jingina da kan gado. Sosai takejin wani irin dadi da nishadi a zuciyarta tasan muddin iyayen nata zasu cigaba dayimata addu'a to bazata ta6a ganin ba daidai ba a rayuwarta. Komawa tayi ta kwanta tana hasaso yadda zamansu zai kaya da wanda bata ta6a jin ko digon sonshi a zuciyarta ba, saidai ta qudura a ranta koma menene bazata ta6a barin tsanarshi ya hanata neman aljannarta ba awajenshi, zatayimashi biyyaya bakin gwargwado don neman aljannarta amma bazata ta6a budemashi kofar zuciyarta ba bare sonshi yashiga. Kusan tare Abba dasu Abdul suka dawo da marece, shima abba yayi mammakin ganinta kuma yaji dadi sosai dayaji tazo tayasu yan kwanaki ne. Da daddare haka suka baje a falo sunata kwasan fira suna dariya wanda firar yau tafi ta kullum dadi saboda kasancewar saudart acikinsu, saudart nada baiwar da idan tana waje sai an gane kuma komin qanqantar lokacin dakukayi tareda ita idan ta tafi saita barku da kewarta, that's her vibe. Sai da lokacin kwanciya yayi sannan kowa ya haqura akaje aka kwanta. Tana komawa daki kuma suka dasa da daddy dake can cikin kewarta sai qorafi yakemata wai ta tafi ta barshi, saida barci yafara cin qarfinta sannan sukayi sallama ta kwanta. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Yau kwana uku kenan da dawowar saudart gidan mamy. Zaune take kan kujera, kaffafunta a saman kujerar ta takure waje daya idanunta kafe da wani english novel dake hannunta mai taken *ice and fire*. Ta shagala sosai a karatun novel din don sosai labarin ya qayatar daita don sai sakin murmushi take akai akai. Ringing din wayarta ne ya katse mata karatun tasa hannu ta daukota batareda ta janye idanunta daga kan novel din ba. Dagawa tayi ta kara a kunne batareda ta kalli screen din ba tayi sallama. Lumshe idanu yayi a dayan 6angaren ya bude cikin wani irin yanayi sadda muryarta ta dakar mashi dodon kunne. Batareda yace komaiba. Jin shiru yasata duba screen din taga baquwar number ce hakan yasata dan yamutse fuska ta maida wayar a kunnenta tace "Hello?...hello?" Amma shiru ba amsa "Mtcheew network problem" tafada tana katse kiran ta ajiye wayar tacigaba da karatunta. Furzar da iska yayi daga bakinshi yana dan murmushi sannan yasake dailing din number. Wani dogon tsaki taja wanda har saida su habeeb suka juyo daga kallon dasuke suna kallonta. "Kema ki koma ciki mana ki daga wayar dama tayaya zakiji ana kallo?" Inji mamy da itama tana falon tana danna wayarta. Miqewa tayi batace komaiba ta nufi sama tana daga kiran da harya kusan tsinkewa. "Hello?..." tafada tana shigewa dakinta. Shiru! "Look nifa banjin komai, idan ansan baza'ayi magana ba adaina bugowa mana idan kuma network ne kindly send sms dukda banga alamun network dinne ba" tana kaiwa nan ta tsinke kiran ta maida wayar silent tanajan tsaki ta fada kan gado tana cigaba da karatunta. Sauke wayar yayi daga kunnenshi yana murmushi jin ta tsinke wayar. Jin muryarta kadai ba qaramin nishadi yasashi ba. Komawa yayi ya jingina da kujerar office dinshi yana kallon number tata wanda dakyar yasameta a wayar baby daya sace jiya da daddare. Shiga yayi wurin saving din contact yayi saving din number da *other half* yana murmushi. Bude kofar office din da'akayi yasashi dagowa ya kalli kofar still murmushi a fuskarshi. Sadeeq ne yashigo looking so tired don kallo daya zakamashi kasan ya kwaso gajiya don tie dinshima a safsafce yake. Dan hade rai A.A yayi yana kallonshi harya je wajen qaramin fridge din office din ya dauko ruwa mai shegen sanyi yadawo ya zauna ya 6alle murfin yashiga kwankwada. Tsaki ashraf dake binshi da harara tundazu yayi yace "Nifa na rasa gane kanka kwana biyun nan, saidai kazo office da safe bayan azahar you are nowhere to be found sai gab da za'a tashi sannan ka lalla6o kadawo, gidan uban wa kake zuwa on duty" yafada yana hararanshi. Banza sadeeq yayi ya kyaleshi har saida yaga bayan ruwan sannan yayi cilli da goran yana komawa yana balancing akan kujerar dayake akai. "Kutt.. wlh kaje ka dauke kasa a waste basket wannan wane irin wulaqanci ne?" Yafada yana ajiye wayar hannunshi. "Mtcheew headache ne kai wlh" inji sadeeq yana tashi zaibar office din. Saurin tashi ashraf shima yayi ya nufi inda yayimashi jifa da goran ya dauka yadawo ya cusamashi a hannu yace "Tafi da abinka kuma kayi gaggawar rubutomin note akan inda kake zuwa yawon gantalinka na yan kwanakin nan ko kaga takardar sallama wlh" Kya6e baki sadeeq yayi yanufi kofa hannunshi maqale da goran ruwan da ashraf ya cusamashi yana cewa "mad oo" "Zakasan mad oo idan banga note dinba first thing tomorrow morning" inji ashraf yana kwafa. Bude kofar yayi yafita yamaidota da karfi ya rufe. Girgiza kai ashraf yayi kawai yana murmushi sannan yakoma wajen desk dinshi yana kaikaye stuff dinshi don lokacin tashin nasu yayi cikin zuciyarshi kuma yana wondering ina sadeeq ke zuwa yan kwanakinnan da rana don abin yafara damunshi, mutum kamar tsinke saidai ka nemeshi ka rasa? Haka ya ida kammala kayanshi ya fito daga office din yanajin wani nishadi a zuciyarshi duk sadda yatuno muryar saudart dayaji dazu acikin kwanyarshi. Shigewa yayi cikin motarshi ya tada yafice daga company din feeling very lively...✍ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 082 Washegari jumua't babbar rana. Ashraf ne da sadeeq cikin mota suna kan hanyarsu ta dawowa daga sallar jumu'a. Sadeeq ne ke tuqi while ashraf na danne danne a waya. Sosai ya shagala da abinda yake a wayar don bema lura da sadeeq ya dauki wata hanyar ba saida sukayi nisa sosai sannan ya ankara. Kallon waje yayi yana yatsine fuska sannan yajuyo ga sadeeq yace "And where are you taking us to?" Ta6e baki yayi yace "sai yanzu ka lura" "That's not the answer to my question" ashraf ya ansamashi yana harararshi "Inda kake complaining ina zuwa zan kaika kaima" sadeeq ya amsa mashi yana shan wata corner "Ina kenan?" Inji ashraf "Gani ya kori ji" inji sadeeq batareda ya kalleshi ba. Be sake cemashi komaiba sai maida hankalinshi dayayi kan wayarshi yana scrolling information on *how to make a girl fall for you* dayayi browsing. Jin tsayuwar motarsu ya dawo dashi daga duniyar karatun daya lula, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dago idanunshi daga kan phone din yashiga bin inda suke da kallo cikin mammaki. "Ina ne nan?" Yafada still yana bin harabar da kallo cikin mammaki "Idanunka sun fara ciwone halan?" Inji sadeeq yana bude murfin kofar sannan yafita. Shima fitowa yayi yana qara bin environment din da kallo. "Waye be lafiya?" Inji ashraf yana kallon sadeeq "Kaidai muje" inji sadeeq yana yin gaba. Maida wayarshi a aljihu yayi sannan shima ya maramashi baya yana wondering waye be lafiya aka kwantar dashi asibiti. Saida suka biya office din wani Dr sannan suka fito gabadaya da Dr din suka nufi wani ward, shidai ashraf binsu kawai yake batareda yasan wazasu je ganowaba. A bakin wani ward suka tsaya Dr din yabude kofar yashiga sadeeq yabishi sai lastly ashraf da shima ya maramasu baya very eager to know what's happening. Daga farko be dago wacece ba saida yakusan kaiwa bakin gadon sannan ya ganeta wanda hakan yasashi tsayawa cak daga tafiyar dayakeyi yana kallonta. Itama kallonshi take agalabaice da alamu dai tana jin jiki ga wasu hawaye dasukayi forming a idanunta dasuka fada ciki. Juyawa yayi batareda 6ata lokaciba ya nufi hanyar fita don baxai juri ganintaba don zuciyarshi wani irin suya take. "My.... my please don't leave...please" tafada cikin muryar kuka. Beko saurareta ba ya cigaba da tafiya harya isa bakin kofa yakama handle zai bude yaji tace "Please don't leave without forgiving me, nasan mutuwa zanyi, please forgive me" tafada cikin kuka sosai. Tsayawa yayi hannunshi kan handle din kofar batareda yajuyo ba. Ganin hakan yasata cigaba dacewa "Am so sorry my... na cuci kaina, beebah ta cuceni, nabiyewa son zuciya da hudubar muguwar qawa nafada hallaka, please forgive me" Shiru yayi yana sauraronta zuciyarshi na zafi, duk ya tuna kazafin dataje tayimusu wajen ummy saiyaji kamar yaje ya shakureta a inda take. Cikin sheshekar kukan dabai fita tacigaba dacewa "Ashe beebah ba masoyiyata bace? Ta kaini ta baro, A.A nasan bani cikin mata masu kyawun hali, nasan bana cikin masu isashiyar tarbiyya. Ashraf nasan kasoni ada, kasha yunkurin nunamini hanyar gaskiya amma nayi wasa da damata na 6ata wayauna na biyewa rudin qawaye da rayuwar turai na lallata alaqar dake tsakaninmu. Ashraf tunda nafara ganinka a uk nakamu da matsanancin sonka wanda hakan yasa naji idan ba kaiba babu wanda zan iya rayuwa dashi amatsayin mijina. Hakan yasani tattalin kaina da mutuncina don kai ganin kai kamili ne. Duk iskancina ban ta6a wuce romance don nasa a raina kai kadai zanba kaina saboda na samama kaina mutunci awajenka bayan aurenmu. Ranar daka ganni da chris muna kissing har hakan yayi sanadin rabuwarmu, aranar nashiga tashin hankali sosai kuma nadama tashigeni amma na nade tabarmar kunyata da hauka don ganin zan wulaqanta a idanun jama'a. Daga lokacin natuba daga romance life saidai kaqi kabani wani damar. Nabi duk hanyar danasan zanbi inshawo kanka amma kaqi saurarata. Alokacin da labarin aurenka ya riskeni na shiga tashin hankali sosai. Tun a lokacin naso tada bori amma beebah ta hanani acewarta asannu zamu warware komai. Na biyemata nakuma yarda daita saboda duk duniya banida qawa kuma aminiya data fita. Ita tayi convincing dina takaini wajen wani boka da nufin shiga tsakaninku kai da matarka yakuma cusa maka tsananin sona yadda zakaji bazaka iya rayuwaba batareda niba" Shiru tayi sakamakon kukan dayaci qarfinta. Izuwa yanzu ashraf yajuyo yana kallonta ya jingina da kofa hannayenshi harde da qirji shima sadeeq ita yake kallo shima jingine da bango. Babu wanda yacemata uffan har taci kukanta mai isarta sannan ta tsagaita don kanta sannan tacigaba dacewa "Bansan wannan ne hanyar lallacewar rayuwata ba, bansan kaini zatayi ta baro ba. Ataqaice dai the man demand for my virginity domin samun biyan buqata ta. Dafarko naqi yarda don banga amfanin auren ba bayan nayi loosing din abinda zai kankaromin mutunci awajenka ba amma sai sukayi convincing dina dashi da beebah cewa aikin da za'ayimaka bazai baka damar tantance am virgin or not ba, kawai dai burinka a lokacin ka mallakenine kuma bazaka ta6a barinaba har abada. Ina sonka kuma banida burin daya wuce in mallakeka na har abada hakan yasa magangannunsu sukayi tasiri azuciyata nabada kai" Sniffing tayi ahankali sannan tacigaba "ranar nayi loosing pride dina ga dirty tsohon nan, nayi kukan takaici sosai saidai beebah na kwantarmin da hankali cewa yanzu you're mine forever. Shiru shiru har aka kwashe wata banji alamun nasaraba saima canjin danakeji ajikina cos am always sick. Hakan yasa na tsare beebah da qorafi nan ta kwantarmin da hankali tareda cemin akwaima hanya mafi sauqi dazamu warware aurenku batareda munjira bokanmu ba. Nan tagayamin tasamu information awajen helen cewa aurenku is based on contract. I was shocked alokacin don abin yazomun a bazata, nan na buqaci evidence tace tasa helen tasamo mana akan yarjejeniyar huge amount of money. Hakan yasa nadanji dama dama saidai me? Bayan kwana biyu jikina yayi worsening. Dakyar na iya kai kaina hospital inda aka gwadani aka bani result din daya giggita rayuwata. Result ne na juna biyu wanda ya nuna inada jaririn ciki sai kuma cutar nan mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS. Ina gama karantawa na yanke jiki nafadi saidai nasake bude idanuna naganni akan gadon hospital. Nayi kuka sosai nayi baqinciki marar misaltuwa. Qarshe dai na lalla6a dakyar nakai kaina gidan beebah. Sosai na burkuce mata don gani nake tawa tazo qarshe kawai. Dakyar ta rarrasheni ta nuna haryanzu is not too late wajen mallakarka, ta fiddomin takardun datasamu wajen helen na yarjejeniyar aurenku takuma kitsamin yadda zan maku makirci wanda dolene umminka tasa ka aureni Banida za6i, a lokacin banida kingin burin daya wuce in mallakeka kafin inmutu hakan yasa nazo har gidanku nayi maka kazafin danayimaka. Bayan wannan ranar kuma zazzafan zazza6i yakuma lullu6eni ga laulayi daga qarshe beebah tabani shawarar terminating din cikin. I dont have choice don alokacin inajin jiki sosai haka takawoni wannan asibitin don zubda cikin. Wanda garin zubda ciki akasamu matsala mahaifata ta ta6u. Tunda takawoni hospital yau kwana goma kenan ban sake ganinta ba, ina cikin matsanancin hali gashi tagudu tabarni, banida kowa, bansan ta ina zanfara contacting din yan uwana ba. Beebah ta cuceni A.A, taci amana ta, tasani tafka kuskuren da bazan ta6a iya gyarawa ba. Please forgive me ashraf, ka yafemin kona dan ji sauqin abinda ke damuna, ka yafemin ko allah zai sassautamin halin danake ciki" ta qarashe maganar cikin kuka sosai. Shiru dakin yayi sai sheshekar kukanta kadai da akeji qasa qasa. Sosai magangganunta suka ta6a ashraf, sosai tabashi tausayi kuma yaji har aranshi ya yafemata don bega amfanin rashin yafemata dinba. Allah yasani ada yasota kuma yaso ya taimakamata wajen ganin ta gyara hallayenta amma the deed is done and it can never be undone. Kallon Dr dake tsaye shima tundazu yayi sannan yace "A minute please" Sannan yajuya yafita Dr din ya maramashi baya. Hada kai da gwiwa tayi taqara fashewa da kuka mai cikeda danasani. "Ehrm... please kibar kukan haka it's not good for your health, everything will be alright ok?" Inji sadeeq ahankali. Saida yayi making sure tabar kukan sannan shima yafita waje yarufo kofar. A corridor ya tadda ashraf tsaye hannayenshi zube a aljihu yana fuskantar Dr dake mashi bayyanin status din suzy. Qarasowa yayi shima yana cigaba da sauraranshi har yakai aya. Furzar da iska A.A yayi ahankali sannan yace "So sad.. yanzu i think the best option here shine a sanar da familyn ta, koko?" Ya maida akalar tambayar ga sadeeq daya rungume hannaye a qirji. "Yes abinda yakamata kenan" inji Dr "Yanzu ya maganar bill?" "Sir yayi settling din komai" dr yafada yana nuna sadeeq da beyi mgn ba haryanzu "Alright please take good care of her, zamuyi qoqarin contacting din family dinta as soon as possible" yafada yana gyara tsayuwarshi "Ok insha allah" inji dr din. Nan sukayi sallama suka fita daga hospital din batareda sun sake komawa dakintaba. Shiru motar ta dauka tunda suka baro asibitin. "Tayaya kasan tana asibitin" ashraf ya jefoma sadeeq dake tuqin tambayar. Dan kallonshi sadeeq yayi sannan ya ta6e baki yace "I've been looking for her tun bayan faruwar abinnan don koyamata hankali, dakyar naganota nan din da taimakon wani neighbour dinta" "And ina beeba ko mema take kiran friend din nata?" "Babu inda ban nemeta ba, yanzu hakama nasa anaimomin ita duk fadin garinnan itakuma helen ta dade da barin garinma takoma qauyensu" sadeeq ya amsa idanunshi akan titi. Ajiyar zuciya ashraf ya sauke yace "To allah ya kyauta, yanzu ina zamu nemi familyn nata?" "Suna jos, phone dinta ta 6atane kuma she doesnt wanna give any of her family number, guess tanajin kunyar suganta a wannan halin ne" "Wannan ba hujja bace just look for a way to find their contact, is better susan halin datake ciki" Harararshi sadeeq yayi yace "Look for a way... kenan ni zanma nemosu ko?" Daga kafadu yayi yace "You started it all ai, saika ida ladarka" Daga hakan basu sake cewa komaiba har suka isa company. Ashraf na sauka sadeeq yasake tada motar yafice daga company din. Ta6e baki ashraf yayi yanufi cikin company din yana cewa "Aifa, aiki ya ganka" Haka yanufi ciki walking majestically ma'aikata nata miqo gaisuwa yana dagamusu hannu harya isa sama. Harya wuce yasake dawowa dabaya yana kallon kofar office dinta. Dawowa yayi yanufi kofar office din ya bude ahankali yashiga. Office din very neat don kullum sai an gyarashi ga qamshin freshner dayakeyi mai dadin gaske. Ahankali ya qarasa gaban desk dinta yaja kujerar baya ya zauna yana lumshe idanu tareda sauke ajiyar zuciya. Bude idanun yayi yana bin files files din dake jere neatly akan desk din sannan yamiqa hannu ya dauki guda. Budewa yayi daga qarshe qarshen file din inda yakeda tabbacin rubutunta ne yana kallon neat and unique handwriting dinta. 6ata lokaci sosai yayi yana dudduba abubuwan office din wanda duk yawanci aikintane yayinda sonta ke qara hauhawa a zuciyarshi ganin yadda tayi ayyukan ba ha'inci kuma cikin tsari wanda shi a lokacin hauka ya hanashi ganin hakan don shi alokacin burinshi daya shine quntata mata. Saida yagaji don kanshi sannan ya zaro wayarshi yakoma ya jingina da kujera ya lalibo numberta dayayi saving da *other half* ya danna kira. Kamar dai yadda yayi zato qin shiga tayi don tuni tasa number a blacklist don idan ta daga baya magana saidai taita 6a66atu ita kadai. Hakan yasa tasashi a blacklist kawai. Komawa yayi ya jingina da kujera yashiga sms don rubuta saqo kamar yadda yagani dazu dayayi browsing din hanyoyin da mace zata falla ma namiji, love txt na cikinsu saidai shi empty-headed ne a wannan fannin besan me zai rubutaba don beta6a ba, dama be ta6a soyayya ba sai akan suzy kuma yawanci ita ke liqe mashi so besan wani abu ba waishi love massage. Rubutu yafara haryayi nisa kuma yaga beyiba ya goge yasake wani shima saida yakusan gamawa yaga rubbish ne ya goge. Haka yaitayi yana gogewa, be ankaraba saidai jiyayi ana kwada kiran sallar magrub. A mammakince ya miqe yana kallon time don lokacin yayimashi saurin tafiya. Fasa rubuta text din yayi yafita yafarayin sallar magrub din sannan yadawo ya dauki briefcase din yafita. A gidama bayan yagama duk abinda yake yana kwance kan gadonshi sanye da fararen sleeping robe, wayarce a hannunshi yana jujjuyawa yarasa me yakamata ya rubuta mata gashi beson using idea din wani ko yayi browsing, yanaso ne yafadamata what's in his heart, yanasone ya fadamata kalamanshi bana wani ba. Daga qarshe dai ya sadaqat yafara rubutamata akaro na ba adadi, be tsayaba saida yakai aya sannan ya sauke wani nannauya ajiyar zuciya yana kallon text din yana qara karantawa, gani yayi kamar beyiba don it doesn't sound romantic amma allah ma yasan qarshe qurewarshi kenan. Yatsarshi yakai wajen send botton yana tunanin ya danna koko? Kamar an kwa6e hannunshi sai gani yayi ya danna send botton din. Waro idanunshi yayi yana cewa "No!" Amma harya shiga. "Shit!" Yafada yana dafe kai don besoba. Sake karanta text din yayi again cikin takaici, shi sai yanzuma yaga text din beyiba kwata kwata, wannan ai se tayi zaton dan primary ya rubutata. Tsaki yaja cikin takaici yana kallon wayar yaga ko za'ayi replying. Jin shiru har kusan minti talatin yasashi haqura yayi tilli da wayar qarshen gado ya kwanta takaici fall zuciyarshi na sending din wannan message din dayayi saikace idan yagoge be turaba wani wanda yafi wannan yake iya rubutawa😒 Itakau saudart a lokacin tana ma qasa suna fira kamar yadda ya zamarmasu al'ada a gidan. Ba ita tashigo dakin ba saida 10:30pm yayi. Saida ta canza kayanta zuwa na barci sannan ta fada kan gado ta jawo wayarta don kiran daddy tayimishi good night kamar yadda tasaba. Ganin text da wata special baquwar number datayi yasata dan yin jim tana kallon number don it's very special, kallo data tayima number ta haddace don simpliness dinshi. Bude text din tayi don ganin abinda aka turo mata, sai gani tayi ansa *helloo, how are you? Hope kinci abinci? And hope baki cika cikinkiba sosai so as not to feel uncomfortable, good night, sleep like a baby* Wara idanu tayi tana sake maimaita text din wondering who the sender is. Tsaki taja ta goge text din sannan tafita tashiga call log takira daddy. Saida suka dan ta6a fira kadan sannan sukayi sallama kowa ya ajiye waya, tayi addu'ar barci ta shafa sannan ta kwanta. Sharp sharp barci yayi awon gaba daita don dama tagaji sosai...✍ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [9/1, 11:13 PM] Hayat: 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) 083 Washegari yana tashi first thing daya farayi shine duba phone dinshi ko zaiga reply don har mafarki yayi jiya tayi mashi reply din. Ganin babu komai yasashi ajiye wayar dissapointedly ya tashi ya nufi bayi don daura alwala. Bayan yan mintuna yafito daure da alwala yana dan yarfe ruwan hannunshi. Wayar ya dauka yana kallo na yan seconds sannan ya sauke ajiyar zuciya yafara typing din short good morning text yayi sending sannan yajefa wayar a aljihu yafita. Tana zaune tagama raqa'atainul fajr tana jiran a kabbarta sallar asuba taji ringing din shigowar txt a wayarta dake jikin socket. Bata bita kanta ba tacigaba da danna counter din hannunta. Saida tayi sallar asuba tadanyi tilawa sannan ta tashi daga sallayar ta linketa ta ajiye sannan tabi lfyar gado don yau weekend ba batun shirya su abdul makaranta. Ba ita ta farkaba sai wajajen takwas nasafe. Brush tashiga bayi tayi sannan tafito ta yafa dan qaramin veil akan rigar jikinta ta zare wayarta gindin chaji ta fita da nufin shiga kitchen. Tana tafe ta danna power botton din wayarta taci karo da message agaban screen din. Kallo daya tama number din ta ganeta don the number is too special to forget. Sliding din wayar tayi wayar ta bude sannan tashiga message din taga ansa *it is very important to start our day with a positive affirmation, we are the greatest gift of the universe, we are loved and appreciated. I prayed this day will bring you alot of happiness and muslim ummah altogether...SABAHAL KHAIR* Tsayawa tayi daga tafiyar datake tana qara maimaita saqon again and again wondering waya turomata. Kamar tayi replying da wanene? Saikuma ta fasa ta goge text din ta qarasa kitchen din. Mamy ta tadda ciki tana peeling din irish. "sabahal khair mamy" tafada tana dan rungumota daga baya. Fizgewa mamy tayi takaimata bugu tai saurin kaucewa tana dariya. "Ja'ira" inji mamy tana kwafa. Murmushi saudart tayi tace "yau irish zamuci? I thought abdul yace indomie yakeso" Harara mamy ta 6allamata "Don yace ita yakeso shikenan kowama ita yakeso? Idan biyemashi za'ayi kullum ita zamu dinga ci kamar yan yari, idan bazaiciba yabarshi" Kwa6e fiska saudart tayi "Kai mamy autan naki?" Ta6e baki mamy tayi batace komaiba. "Ni bari to na dafa mashi" inji saudart tanufi inda kwallin indomien yake "Dadai yafi, dama ke ke qara 6atashi" inji mamy. Haka suka hada breakfast din tare suna dan fira jefi jefi har suka kammala sannan sukakai dining saudart tawuce sama don watsawa. Da rana ma saida ashraf yasake turamata text, dukda be iya love text ba but yana qoqari wajen ganin ya rubuta something meaniful and educative, sai text din yake shige da irin quotes dinnan na encouragement. Shima shiru babh reply, bejin dadin rashin ganin reply dinta amma hakan be saremashi gwiwa ba cos he's determined to fight for her love. Ataqaice dai kullum da kalan text din dazaiyi mata. Safe, rana da dare. Kuma duk babu wanda yata6a samun reply dinshi amma hakan be dameshi ba kuma be hanashi sake yimata ba. Saudart ma a 6angarenta kullum saita karanta text dinnan na wannan special number din. Kuma kodayaushe kamar tayi replying ta tambayeshi wanene ko wacece sai kuma tafasa acewarta idan mai turowar yagaji ko tagaji da 6oye 6oyen zata bayyana kanta. A 6angaren sadeeq kuwa yasamu nasarar persauding din suzy tabada number uncle dinta. Babu 6ata lokaci ya sanar dasu yarsu fa na hospital. Washegari saigasu, abin dai ba dadin ji don koke koke akaitayi ranar a ward din don labarin daya riskesu gameda diyarsu ba qaramin giggitasu yayiba. Babu 6ata lokaci suka nemi transfer aka maidasu hospital din garinsu suka tarkata suka koma can. A 6angaren saudart kau zaune take gidan mamy hankali kwance don har mancewa take dawani aure dake kanta. Jin duk anyi shiru da batun yasa hankalinta kwanciya sosai tana addu'ar allah yasa a tafi ahakan don itakam tama kasa picturing din yadda zaman aurensu zai kasance a karo nabiyu aranta, gani take this will be worst than wancan zaman. Mamy kau biris tayi daita dafarko amma ganin kamar abin bewani dameta ba yasa tafara yimata hade hadenta irin wanda tayimata wancan karon Chanzamata sabbulan wanka tayi ta siyamata masu kyan gaske masu gyara fata takuma sa aka hadamata man shafawa mai hade hade kala kala don kamshin man ma kanshi ya isa kasan ba qaramin hadi aka mashiba sai turarrukan sawa a ruwan wanka data siyamata suma ba'a magana. Sadda taba saudart su, tsayawa tayi tana kallonsu baki sake don ita ba yarinya bace tasan duk hade haden na menene. Ganin kallon datake musu yasa mamy hade rai tabata umarnin takwashe tawuce dasu kuma daga yanzu suzama na amfaninta. Babu musu takwasa tafita tana turo baki don ba haka tasoba. Babu yadda ta iya haka tafara amfani dasu, saidai tun amfani na farko datayi dasu taji sun bala'in yimata don idan tagama wani cool qamshi takeyi mai sanyin gaske wanda hakan yasa taji takamu da qaunar kayyayakin don dama ita ma'abociyar son qamshice. Can kuma mamy ta tsiri yimata ferfesu duk daren allah bazata bari ta kwantaba saita sha farfesu da pure milk sannan ta kwanta sai kuma fruit datake yawan tilasatata ci don duk ba'a son rantaba take ci dondai bata iya yiwa mamy musune sai jitayi dama zamanta tayi can wajen daddy da duk hakan be faruba. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Yau thursday, suna zaune a falo dukkansu mamy na waya, saudart kuma da abdul da habeeb na baje qasa suna buga game, su aminu kau basu gidan suna gidan granny (mamansu Abba) Dan ihu habeeb yayi ahankali gudun kar mamy dake waya taji yayiwa saudart gwalo yana maida fuskarshi puppy face. Kallon juna saudart da abdul sukayi suka 6ata fuska tare. Dauke papern game din abdul yayi ya cikwikwiyeta yana cewa "Dama don kaga kai kadai ka iya shiyasa ka nace ayi to munfasa mu buga ludo" Dariya habeeb yafashe daita yace "Nadaiyi winning dinku, taar! Imagine ku biyu akan ni daya amma naciku 5:0 shame!!" "Don dai bamu iya bane yaro da shi kadai ya isheka" inji saudart tana harararshi "Me wannan ajebon ya iya banda shirme?" Inji habeeb yana fashewa da dariya don ya qule abdul 6ata fuska abdul yayi ya kalli saudart kamar zaiyi kuka. "Habeeb banson wulaqanci, mind yourself" tayi warning din habeeb tana gallamashi harara. Sunkuyar dakai yayi yana dariya qasa qasa ganin yadda abdul din keta rau rau da idanu hawaye harsun taru a idanun. Sallamar megadi ne ya katsesu. Duk kallon kofar sukayi harda mamy da tagama wayar sai danne danne datakeyi. "Habeeb get the door" inji mamy tana maida kallonta akan wayarta. Tashi yayi yawuce yayinda saudart ta ciro wayarta zata shiganma abdul game din ludo kamar yadda yace. Adan jima kadan saiga habeeb yadawo dakin. "Mamy baqine" inji habeeb "Who?" "Don't know sundaice inzo ince zasu shigo gaidaki" Kallon juna saudart da mamy sukayi sannan mamy tace "ok saudart jeki daukomin mayafi na, abdul tattara rubbish takardun nan kayi sama" Tashi saudart tayi tanufi upstairs dakin mamy while abdul ya tattara takardun games din hannunshi riqeda wayar saudart dayake game daita. Can saiga saudart da mayafin mamy ta bata tajuya takoma sama abinta. Kallon habeeb tayi dake tsaye tundazu bayan tagama yafa mayafin tace "Jeka shigo dasu" "Tou" yafada yajuya don shigowa dasu din. Ajikin motarsu ya taddasu tsaitsaye, qarasowa yayi yana murmushi yace "Mamy tace kushigo" Shafa kanshi sadeeq yayi yace "alright good boy muje" Habeeb yayi gaba sadeeq yabishi. Saurin kamo hannunshi A.A yayi yana wiqi wiqi da idanu kamar marar gaskiya. "What" inji sadeeq daya juyo yana kallonshi cikin takaici. "Please sadeeq, am shy" yafada cikin marairaicewa Tsaki sadeeq yaja cikin takaici yace "You know what? Idan najuya nabar gidannan natafi kenan wlh, wannan wane irin wulaqancine, ka tilastamani rakoka kuma kazo kana behaving annoyingly? Haka kabani kunya wajen daddy agidanshi dazu, kasan bazaka iya zuwaba ka jiji6oni?" Yafada yana harararshi "Mtcheew yanzu am sorry muje, wai maimakon ya kwantar ma mutum hankali saiya rufe mutum dafada" "Hankalin ya dade be tashiba, yafi rocket tashi" inji sadeeq. Wuceshi ashraf yayi cikin fushi yanufi habeeb da harya kai bakin kofa. Binshi shima sadeeq din yayi yana harararshi yana gunguni qasa qasa. Koda yakai bakin kofar kasa shiga yayi saida yajira sadeeq ya iso sannan. Harara sadeeq ya gallamashi sannan yasa hannu yatura kofar ahankali yana sallama. Shima ashraf daduk yake very nervous ya maramashi baya shima yana sallamar. Akan kujera suka tadda mamy zaune fuskarta asake tana amsa sallamarsu tareda yimusu sannu dazuwa. Ahankali suka qaraso cikin falon kansu a sunkuye suka zauna kan carpet suna fuskantar mamy. "A'a? Ku zauna kan kujera mana" Duk murmushi sukayi kansu a sunkuye suka shiga gaidata batareda sunyi yadda tace dinba. Amsa musu tashigayi tana kallonsu most especially ashraf don kallo daya tayimusu tagane kosu waye. "Ya mutanen gida? Ya aiki?" Inji mamy "Alhamdulillah, yasu Abba" inji sadeeq yana murmushi shikau ashraf kunya ta hanashi cewa komai sai sunkuye kai dayayi kawai yana sauraronsu. Amsamasu tayi da yana wajen aiki be dawoba. Saida suka gama gaishe gaishen sannan mamy ta tashi tsaye ta kalli habeeb dake zaune can gefe yana qoqarin chanza channel ta 6allamashi harara a fakaice tace "Zoka kaisu falon baqi" Tasowa yayi yazo wajensu ya tsaya, tashi duk sukayi suna yimata sallama tana amsawa cikin fara'a tanacewa su gaidamata Hajiya fateema idan sun koma sannan itama tajuya tahau sama bayan sunfita. Wani gauron ajiyar zuciya ashraf ya sauke bayan sun fito yana dafa chest. Harararshi sadeeq yayi yace "matsoraci kawai" Shima hararar ya rama batareda yace komaiba sukabi habeeb dake gaba don kaisu falon baqin. Kwankwasa kofarta da akayi yasa tadago daga linkin kayan datake, kafin tace komai har mamy ta bude kofar tashigo. Murmushi saudart tayi mata tace "Har baqin sun tafi?" Tafada tana ajiye zanen data linke. Fuska ba yabo ba fallasa mamy tace "A'a kije suna falon baqi and kitafi da refreshment" Dan waro idanu saudart tayi tace "Nikuma mamy?" Tana nuna kanta da yatsa. Wata harara mamy ta gallamata tace "no ni, zakiyi abinda nacene ko kuwa? And change into something more decent kuma karkiyi wasting dib time" tana kaiwa nan tafice tabarta sake da baki. Asanyaye ta maida kayan data linke cikin sip dinta sannan taciro wata dark blue din hijab doguwa ta dora kan kayan jikinta tadan gyara fuskarta ta fesa cool turare sannan tafita. Bata tadda kowaba falo hakan yasa tanufi kitchen tadauki tray ta bude fridge tafiddo drinks uku ta daura akai da cups ma uku don batasan adadin baqinba ta debi snacks ma sannan tafito kitchen din tanufi falon baqi. Tafiya take tana tunani nason gano su wanene, haka kawai taji beating din zuciyarta na chanzawa. She feels very nervous and uncomfortable. Koda takai bakin kofar saida tadanyi jimm na yan daqiqu sannan ta daga hannu ahankali tayi knocking sannan ta tura kofar bakinta dauke da sallama. Sadeeq kadai ya amsa sallamar while ashraf da muryarta ta saukar mashu da wata iriyar kasala ya kafe kofar da idanu cikin son ganin ta inda zata 6illo. Anitse tashigo dakin kanta qasa tana sake maimaita sallamar datayi hannunta riqeda tray. Lumshe idanu ashraf yayi akanta ya bude jin wani sanyi na ratsa zuciyarshi by the mere sight of her...✍ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [9/1, 11:13 PM] Hayat: 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 084 Wannan karon ma sadeeq yasake amsa mata sallamar cikin fara'a. Dumm.. gabanta yafadi jin muryar sadeeq wanda hakan yasata dago idanunta don ganin ko kunnenta ke decieving dinta. Caraff suka hada idanu dashi wanda dama tunda tashigo idanunshi ke kafe daita. Saurin janye idanunta tayi gabanta beating sosai don ba qaramin kashemata idanu idanunshi sukayi ba, there is something about his eyes dake sata jin takasa kallonsu na lokaci mai tsayi. Ahankali tashiga takowa falon kamar mai kirgan steps making extra sure bata harde ba don sosai take jinta a takure jin piercing idanunshi akanta. Saida tafara ajiye tray din hannunta akan centre table din dakin sannan takoma can kujerar dake fuskantarsu ta zauna ta sauke kai qasa tana wasa da zira ziran yatsun hannunta. "Good afternoon ranki shi dade" inji sadeeq cikin barkwanci. Dan murmushi tayi na kunya don sosai takejin kunyar sadeeq yanzu musanmman idan ta tuna abinda yafaru haduwarsu ta qarshe "Ina wuni?" Tafada ahankali batareda ta dagoba. "Lfy lau, ya gida ya hutu?" Yafada yana satar kallon ashraf daya maidata mirror tsabar kallo "Alhamdullilah" ta amsa a taqaice Dan shiru falon ya dauka ganin hakan yasa sadeeq miqewa ya nufi centre table din yana cewa "Bari kuga" Dan daga idanu tayi qasa qasa tana kallonshi taga ya dauki drink daya ya debi snacks din kadan a wani dan plate sannan ya miqe. "Tohm ni nayi nan" yafada yana nufan kofar fita ya fice. Dakin ne yadauki wani deadly silent, bakajin ko kwakwaran motsi aciki. Kanta haryanzu na aqasa tana fidgeting din yatsunta duk jinta take atakure kamar tasa kuka takeji. Shikau maidata t.v yayi yana kallo, Allah knows yayi missing dinta, jiyake kamar yayi shekaru be gantaba, jiyake kamar su dawwama ahakan tana gabanshi yana kallonta, yarasa dalili kawai shidai yanajin wani irin farinciki ne idan yana kallonta. Everything about her is different, fuskarta, shigarta, qamshinta, muryarya, everything! He's in love with everything about her. Muskutawa tayi ahankali tadan gyara xama uncomfortably, allah ma yasan a mugun takure take, jitake kamar ta tashi ta fita, me yake nufi da yazo ya tusata gaba kamar mirror yana kallo? Meya kawoshi ma at the first place? Ahankali ta dago idanunta da niyyar satan kallonshi Gaurayewa idanunsu suka sakeyi a karo nabiyu ya sakarmata one of the coolest smile dinshi. Saurin sauke idanunta tayi qasa tana dan runtsesu cikin kunyar hada idanun dasukayi. Ita dayasan yadda takeji idan yana kallonta da wannan idanun da ya bari, kwata kwata bata sonsu, suna sata jin wani iri. Wannan zaman nasu ya tina mata da zuwan dayayi gab da bikinsu, exactly kamar irin wannan saidai wancan bemata irin wannan kallon hasalima hankalinshi nakan waya while yanzu yawani tsareta da idanu kamar tsohon maye. "Good afternoon" yafada cikin wani irin cool voice wanda hakan yasata dan dagowa da nufin satan kallonshi. Hada idanu sukayi again tayi saurin janyesu ta kalli gefe sannan ahankali almost in rada tace "Same" Murmushi yayi sannan ya miqe yafara takowa wajenta. Bugun zuciyarta ne yafara qaruwa jin kamar takunshi na kusantota. Daidai centre table din ya tsaya ya dora hannu akan drink daya yana kallonta, sannan ahankali yace "Should I?" Qin dago kanta tayi ta kalleshi don batason qara hada idanu dashi ta daga kai ahankali tanajinta duk a takure. Murmushi yayi ya bude drink din idanunshi a kanta ta tsiyaya kadan a glass cup din sannan yamaida ya rufe ya dauki glass cup din. Maimakon yakoma mazauninshi saiya dawo kujerar dake gefenta ya zauna irin zaman balancing dinnan daya riga ya bi jikinshi ya kai cup din abaki yana kur6a idanunshi akanta. Ji saudart tayi kamar ta dora hannu aka taita ihu, jitayi tafi dazu takura dukda akwai dan tazara tsakanin kujerun nashi. Wani haushi takeji na kafeta da idanun dayakeyi, wannan kallon ko maye albarka, why zai tisata gaba kamar t.v ya takurata da wadannan mayun idanun nashi? Dan kawar da kai tayi dayan gefen fuskarta a hade tanajin kamar ta tashi tabar dakin. Haka suka qaraci zaman nasu in silent kowa da saqe saqen dayake a zuciya. Basu san iya lokacin dasuka daukaba ahakan sai jisukayi anyi knocking din kofa wanda hakan yayi sanadiyyar dawowar dukansu daga dogon tunanin dasuka lula. Da sallama sadeeq yashigo riqeda bottle din drink dinshi dayasha rabi. Dan ware idanu sadeeq yayi ganin ashraf yayi changing din wurin zama sannan yadan saki murmushi ya ida qarasowa. "To love birds, time up. Naga alamar idan aka biyemuku kuna iya kwana anan" yafada cikin barkwanci. Dan ta6e baki saudart tayi batareda ta dagoba don dama a qagare take sutafi ko tajita normal. "To ai saika tashi mallam, ranki ya dade zamu ruga kauyenmu" Dan dagowa tayi ta kalleshi sannan ta sadda kai tana cewa "allah ya tsare" Amsawa yayi da amin ya kalli ashraf dashima daidai ya kalleshi ya daga mashi gira alamun yatashi su tafi ko? Harara ya gallamashi sannan ya miqe daga xaunen dayake hakan yasa sadeeq ficewa daga dakin. Takowa yayi har gabanta yana kallonta. Bugun zuciyarta yaqarayin saman jin tsayuwarshi akanta ga kaffafuwanshi datake gani agabanta kasancewa qasa take kallo. Ahankali ya duqa gabanta yana kallonta, saurin ja da baya tayi ta shige ma kujerar tana ware manyan idanunta akan fuskarshi a mammakince don kusancin nasu yayi yawa don har tanajin saukar numfashinshi. Daga glass cup din hannunshi yayi ya miqomata yana murmushi. Kasa ko motsi tayi sai kallonshi datake cikin mammaki tana tunanin anya lafiyarshi lau? Kamo hannunta yayi ya sakamata cup din aciki ya hada yariqe tenderly yana mata wani irin kallo mai tsayawa a zuciya. Saurin sauke idanunta tayi qasa tana qoqarin zame hannunta acikin nashi amma takasa hakan yasata lumshe idanu don wani iri takeji har cikin 6argonta "Thank you" yafada cikin rada yana kallon yadda ta limshe idanu taqi budesu ga zara zara lashes dinta dasuka hade waje daya kamar na fixing Matso da hannun yayi saitin bakinta wanda hakan yasata saurin bude idanu tana kallonshi kamar zuciyarta xata fado tana qoqarin janye hannun. Ahankali yayi placing din light kiss kan yatsunta dake riqeda cup din batareda ya janye idanunshi daga fuskarta ba wanda hakan yasata saurin maida idanun ta rufe gabanta na faduwa sosai. "I love you" yayi wishpering cikin wata iriyar cool voice. Sake tamke idanunta tayi zuciyarta na bugu sosai tanajin kanta na juyamata ahankali. Ganin kamar hannunta nadan 6ari yasashi zare glass cup din hannun nata ya ajiye sannan ya saki hannun nata tayi saurin maida hannun cikin hijab still idanunta arufe. "Take care of yourself... for me" yafada cikin rada in an extra cool voice wanda saida taji tasirin hakan har cikin kwanyarta. Miqewa yayi ahankali yafara tafiya da baya baya yana kallonta. Jiyake beson tafiya, jiyake kamar yatafi daita, jiyake be gaji da ganinta ba amma he have no choice, dolene yabi komai ahankali if he really want her, zai jira, zai jure harzuwa lokacinda zayayi nasarar mallakar zuciyarta, zai cigaba da hqr har lokacinda zata koyi sonshi, so mai tsanani irin wanda yake mata. "Bye" yafada ahankali daidai yakai kofa sannan yajuya yafita. Ta dade ahalin datake ciki, takasa koda bude idanunta ne bare tayi wani kwakwarrar motsi. Jitake kamar haryanzu yana gabanta, jitake kamar haryanzu yana riqeda hannunta, jitake kamar haryanzu watery lips dinshi na kan hannunta. Jikinta haryanzu yakasa dawowa daidai, abinda yafaru yakasa barin brain dinta. Jin an dafa kafadarta yasata saurin bude idanu a zabure. Ganin habeeb ne yasata sauke ajiyar xuciya tana dan waige waige. "Mamy tace what are you still doing here" inji habeeb yana kallonta. Sauke numfashi tayi sannan ta miqe trying to be normal again "Muje" tafada tana kama hannunshi Haka suka fito suna tafe yana bata labarin chocolates dasu sadeeq suka bashi, itadai jinshi kawai take amma haryanzu bata ida dawowa daidai ba. Koda suka shiga falon wucewa upstairs tayi batareda ta tsayaba. Binta da kallo mamy tayi ta ta6e baki sannan tacigaba da kallonta. Tunda suka kamo hanya yaketa sakin murmushi akai akai, allah kadai yasan farincikin dayakeji azuciyarshi a wannan lokaci. "Uhmm am i really safe? Karfa inji saukar bugu, wannan dariyar dakake kai kadai anya lafiya?" Inji sadeeq daketa satan kallonshi tun dazu. Komawa ashraf yayi ya jingina da kujerar dayake xaune yasake sakin wani broad smile kamar wanda akawa babban albishir Murmushi shima sadeeq yayi ya maida hankalinshi kan tuqin dayake yana fadin "ba sabon ba" 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Zaune take adaki sanye cikin kayan barci idanunta a lumshe. Duk yadda su abdul suka so ta tsaya suyi firar dasuka saba da daddare qiyawa tayi tace kanta ke ciwo don har lokacin bata gama dawowa daidai ba kuma babu abinda tafi buqata alokacin kamar kadaici. Tayi nisa sosai cikin tunaninta taji ringing din wayarta alamun shigowar text. Sauke ajiyar zuciya tayi ahankali sannan ta bude idanunta ta kalli wayar dake gefenta sannan ta dauka ta bude. Wannan special number dince, bude message din tayi a sanyaye don jinta take too weak tarasa meke mata dadi. Gani tayi an rubuta *the best kind of friend is the one you sit with, not saying a word and leave feeling it's the best conversation you've ever had* *being with you today made my day and i know the smile you left on my face won't fade even in my sleep... sleep without worries JHAN* Shiru tayi tana kallon message din, qara karantawa tayi for the second time trying to figure out something. *Being with you today* kenan the special number is Ashraf's? Shine mai turomata all these messages dama? Goge message din tayi tana cilli da wayar gefen gado tana jan tsaki. "Hakan bazai chanza komaiba, nothing can change my hatred towards you, bazan ta6a bama wanda besan darajar mutane dama ba, you're wasting your time ne kawai wlh" tafada ita kadai cikin jin haushi. So wannan sabon salon duk don ta soshi yakeyi kome? Lallai iska na wahalar da mai kayan kara. Idan ma mafarki yake to yadaina, dadin bakinshi bazai amfaneshi da komaiba, wama yasani ko kawai lust yakeji gameda ita, the first time yayi stolen kiss from her yanzu ma daga zuwa yayi wani grabbing din hannunta yayi kissing. Me hakan ke nufi? Haka ta kusan raba dare cikin takaici da haushin abinda yaimata don gani take this is not love, it's lust, pure lust. Ashraf kau a 6angarenshi ranar kwanan farinciki yayi, sosai ganinta dayayi yayi tasiri a zuciyarshi, he can't just take away her picture from his thoughts. Kosu ummy saida suka lura da sauyin yanayinshi. Washegari ma haka ya tashi da ragowar farincikin jiya, last night was filled with her dreams, mafarkan dayayi daita basu qirguwa jiya, jinshi yake so un top...✍ Sorry for the short chappy. Aski yazo gaban goshi. Masu complaining saudart ta riqe wuta dayawa kuyi hqr, everything will be alright insha allah, lokaci guda ake jima mutum ciwo a zuciya, warkewarshi sai ahankali. Banason rushing din komai ne, hope zaku fahimceni🙏 Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) 085 Tun daga wannan zuwan ashraf yasamu ticket din zarya gidan mamy. Every two days saiya biya gidan duk don ya ganta yaji sanyi, wani lokacin ma daga office zai biya gidan yaganta sannan yawuce gida. Shaquwa sosai tashiga tsakaninshi da qannen saudart musanmman abdul don mafi yawancin lokuta dashi take zuwa falon baqin tasameshi susha firarsu itakau daga gaisuwa bata qara uhm bare uhm uhm. Zaryar da ashraf keyi gidan ba qaramin haushi yakebata ba don gani take duk salon takura ce, babu abinda yafi bata haushi kamar maidata t.v dayakeyi tsabar kallo shiyasa daga baya ta tsiri fita da abdul don taji sauqin kallon ko yaya ne. Messages kau tun yana turowa tana gogewa har ta haqura ta share don wasu bata ma budesu, bataga amfaninsu ba don basa qarar daita da komai, shikau a 6angarenshi be ta6a sarewa ba ya maida abun dialy route dinshi dukda be ta6a samun reply ko sau daya ba. *** Yau saturday, tunda ta tashi ta yanke shawarar yau saitaje saloon ayimata retouch daga nan tawuce supermarket tadanyi sayayya. Tunda tadawo gidan mamy bata qara fitaba sosai takeson fitan nayau koba komai zata dan motsa kafa. Fitowa tayi daga bathroom qirjinta daure da farin towel iya gwiwa kanta sanye da net cap. Kallo daya zaka mata kasan wanka tafito duba da yadda glowing jikinta ke jiqe da ruwa. Gashin hannunta gaban goshinta duk sun kwanta luff sanadiyyar ruwan daya jiqasu. Gaban mirror ta nufa tana gyara daurin towel din qirjinta. Tsayawa tayi tana kallon kanta a mirror ganin yadda skin dinta ya chanza sai glowing yake. Murmushi tadanyi sannan ta dauki man shafanta ta shafa tadanyi simple makeup sannan ta saka riga da skirt na atamfa ta yafa veil tafita. Direct dakin mamy tanufa don tasan tana ciki, su abdul kau ana islamiyya kasancewar weekend idan suka tafi tun safe sai shidda na marece suke dawowa. Tadda mamy tayi tana gyara gadonta hakan yasa ta ida shigowa tana sallama. Amsawa mamy tayi batareda ta dagoba har tagama gyaran gadon sannan ta juyo ta zauna tana kallonta. Zama itama saudart tayi kan bedside locker tana shagwa6e fuska. "Menene?" Inji mamy tana kallonta "Mamy my hair, yayi dirty dayawa" tafada tana dan turo baki. "Ehen? Ni mezan miki?" Inji mamy tana dan harararta "Zanje saloon please" tafada a marairaice "Yaushe?" "Yanzu, this is five, i promised kafinma su habeeb sudawo nadawo kawai wanki kai ne" tafada a marairaice. "Ok kin gayawa mijinki?" Inji mamy. Jimm saudart tayi tana kallonta batareda tace komaiba "I said kin gayawa mijinki?" Inji mamy tana dan waremata idanu. Kauda kai saudart tayi tana dan turo baki. "kinzo wajena wai zaki saloon, ni ke aurenki? Ko kin manta ke matar aurece? Duk abinda kike ina sane samaki idanu kawai nake don ganin gudun ruwanki, yanzu duk nasihohin danake miki shiga suke a kunnen dama su fita ta haggu ko? Gaki kamar kinsan abinda yake maki ciwo amma ba haka bane, cigaba to allah yabada sa'a and if you really want to go to saloon ki nemi izinin mijinki ni ba ruwana, duk laifinsu abbanki ne dasuka wani zubamaki ido ahakan, i wonder why za'a kyaleki anan da igiyoyinki uku akai, wannan bayi bane is better ki tarkata ki koma gidanki inhuta da kayan haushi" inji mamy cikin fada don sosai zamanta ahakan ke damunta tayima abba magana yace zata koma lokaci suke jira tarasa wane lokaci suke jira. Shiru saudart tayi tana kallon mamy tun sadda tafara fadan nata. Kwana biyun nan talura abu kadan zatayi mamy zata rufeta da fada kamar dama a wuya take. Shiyasa ma tun da can sunfi shaquwa da daddy don be cika saurin fushi ba unlike mamy dakeda fada sosai, abu kadan fada. "Am sorry to" saudart tafada ahankali sannan tajuya zata fita. "Kiranshi din zakiyi ki gayamashi?" Mamy ta dakatar daita da hakan. Batareda ta juyoba ta turo baki tace "Nafasa, zan wanke dakaina" "Eh ki wanke da kanki tunda ke kinfi qarfin ayimaki gyara, ficemin daga daki shashasha" taqarashe maganar cikin dan daga murya. Juyowa tayi tana kallon mamyn kamar tayi kuka, ita rabon ayi ma yasa tazomata maganar tun farko da bari tayi ta wanke abinta dakanta jejely da hakan be faruba. "I'll call him" tafada kamar zatayi kuka "Mtcheew kanki akeji ni ficemin da gani" Asanyaye tafice tanajin tsautsayi ma yasata dawowa gidan da yanzu tanacan wajeb daddy yana petting dinta kamar kwai. Daki takoma tana kumburi, ita tayayama zata fara kiranshi, mutumin da be ta6a kiranta ba sai texts din dayake mata kawai. Tayaya ma zata gayamashi? Me zata cemashi? Zani saloon? Daukar wayarta tayi tana kallo not knowing what to do, yanzu idan bata kiraba mamy fushi xatayi tace taqi bin umarninta. Shiga wajen rubuta sms tayi tayi shiru tana tunanin me yakamata ta rubuta mashi don bata tunanin zata iya kiranshi. Ta dade tana daurawa da kwancewa daga qarshe ta sadaqat tayi typing din. *Good afternoon, zanje saloon, permitted?* Tsayawa tayi tana kallon abinda ta rubuta tanaji kamar tagoge but she has no choice haka ta danna send botton ta senda mashi. Zama tayi wayar ahannunta tana kallonta tana jiran jin shigowar reply amma shiru. Haka tazauna kusan 30mins amma ba reply. Ranta ya 6aci sosai jitake me ma yakaita yimishi text at the first place? Jitake kamar ta dora hannu aka. Qin fitowa tayi don haushi har saida taji hayaniyansu abdul alamun sun dawo. Dagowa tayi ta kalli wayar dake can gefen gado ta jawota ta kunna taga babu reply. Kwafa tayi rai 6ace ta ajiye wayar tafita dakin ranta na suya. Aqasa ta tadda su abdul wanda dawowarsu kenan zasu hau sama su chanza uniform. Sannu da gida duk sukayi mata ta amsa ba yabo ba fallasa sannan suka haye sama don chanza kayan. Zama tayi tana kallon t.vn dake kunne fuskarta ba walwala. Mamy dake zaune falon ta kalleta sannan tace "Yanzu saudart banida ikon gayamaki gaskiya sai ki tsiri kumbure kumbure? Wacce uwar arziqi zata bar diyarta tafita yawo da aurenta batareda izinin mijinta ba? Nabaki shawara as a good mother shine kike fushi kika ma fasa tafiyar? Dakyau" taqarashe zancen tana jinjina kai. Saudart da dama kamar a wuya take sai kawai tafashe da kuka. Sakin baki mamy tayi tana kallonta a mammakince don bataga abinda tayimataba da zata samata kuka. Kuka saudart take sosai kamar wanda aka daka don harda shesheka. "Ikon Allah, me akamiki kike kuka?" Inji mamy tana kallon yadda take kukan bilhaqi "Mamy nifa baqin bin umarninki nayiba, na gayamashi yayi banza dani, ya zanyi?" Takuma fashe dawani kukan, dama me neman kukane akaima dariya. "To shine saiki 6are baki kamar yar 5yrs kina kuka? Lallai wannan sangarta tayi yawa, allah ya shiryaki" inji mamy tana girgiza kai. Itadai batace komaiba sai hade kanta datayi da gwiwa tana cigaba da kukanta qasa qasa. "To nidai kimin shiru, kuma yanzu su abdul zasu sauko suganki kina kuka godai godai dake, kitashi kishiga dakinki kije kiyitayi hankali kwance babu mai takuraki" Shiru tayi ta kyaleta batace komaiba tana sniffing ahankali. Jin saukowarsu abdul yasata share hawayen a6oye tayi fuska tacigaba da kallonta saidai haryanzu ranta a6ace yake sosai. Zama su abdul sukayi suna bata labarin abinda yafaru a school yau. Sama sama take amsamasu don batajin yin magana ma kwata kwata, suna haka sukaji knocking a kofa. Dagudu abdul yanufi kofar dagudu don duba wanene. Ba'a dadeba yadawo falon yana dan tsallen murna. "Aunty, uncle is here!" Yafada cikin murna. Juyowa tayi tana kallonshi kawai not saying a word. "Wane uncle?" Inji mamy "Uncle A'A wai inkirata" inji abdul Kallon saudart din mamy tayi tayi saurin kauda kai. "Saiki tashi ko?" Inji mamy Turo baki tayi sannan ta tashi tayi sama cikin jin haushi. Ba'a dauki lokaci ba ta sauko sanye da doguwar hijab akan kayan jikinta. Bata tadda mamy ba a falon hakan yasa tafice kawai. Koda tafita bataga motarshi ba a inda yasaba parking ba hakan yasata nufar falon baqin tana tunanin yau bezo da mota bane. Maigadi ya nufota yana gaisheta, amsawa tayi cikin fara'a kamar yadda tasaba tanufi bangarwn bakin. "Hajiya ai yana waje" inji maigadin. Hakan yasata chanza akalar tafiyar tata zuwa waje tanajin haushi dikya cika mata zuciya. A gaban gidansu gefen hanya taga wata dalleliyar baqar mota parke wanda ko ba tambaya tasan tashi ce. Ahankali kamar mai tausayin qasa tanufo motar kanta a sunkuye. Tunda tafito yaketa kallonta, yarasa dalilin da kullum take chanza mashi, gani yake kamar kullum chanzata ake, she looks soo adorable. Ja tayi ta tsaya bakin motar batareda ta dagoba. Gani tayi anbude kofar 6angaren datake tsayen. Dagowa tayi ta kalleshi suka hada idanu tayi saurin kauda kai tana sake tamke fuska. "Get in please" yafada ahankali. Shiru tayi kamar bazata shigaba saikuma ta qaraso ta shiga ta zauna batareda ta maido kafafun cikiba ta sadda kanta jin idanunshu na yawo akanta, ga qamshin turarenshi dasuka fara addabar kofofin hancinta. "Good evening?" Yafada ahankali yana kallonta "Uhmm evening" tafada kamar wanda aka tilastamawa "Zaki saloon right?" Ya tambaya yana kallonta "No, that was then" ta amsa tana kauda kai "Yanzu fa?" Yasake tambayarta still yana kallonta "Nafasa" ta amsa mashi a taqaice. "Why?" Yasake tambaya Cikin qosawa da maganar tace "kawai" tana kauda kai Ajiyar zuciya ya sauke sannan yayi starting din motarshi yace "get your legs in muje" Kallonshi tayi taga ita yake kallo saita dauke kai tace "nifa nafasa" Shiru taji yayi hakan yasata sake juyowa ta kalleshi Gani tayi ya kafeta da idanu wanda yasata jin wani iri cikin jikinta hakan yasata janye idanu ta sannan ahankali tace "Ok bari nadauko purse dina" "Ok" ya amsa yana kallonta Sauka tayi daga motar tanufi hanyar shiga gidan yabita da kallo harta shiga. Ajiyar zuciya yayi yakoma ya jingina da kujerar motar yana jiranta. Tadan jima da shiga cen saigata tasake fitowa wannan karon sanyeda maroon abaya tayafa madaidaicin gyalenta. Iskeshi tayi kamar yadda tabarshi don ki kashe motar beyiba. Babu yadda ta iya haka ta shiga motar tanajin dama tun farko bata tattagi fitarba, ita a tunaninta ma idan takoma ta gayawa mamy yadda sukayi dashi zata hana fitar saitaga akasin haka don addu'ar allah ya kiyaye kawai tamata. Maida kofar tayi tarufe tana gyara zamanta, saida yayi making sure tashirya sannan yaja motar sukabar kofar gidan. Tafe suke babu maicewa kowa uffan, saudart dama tunda tashigo tajuya kanta tana kallon waje ta window kamar yadda tasaba while shi hankalinshi rabi na kan tuqi rabi akanta. Jinshi yake so happy having her next to him. Dama yana gidansu sadeeq saqonta yashigo wayarshi. Da farko kasa believing idanunshi yayi dayaga message from *other half* saida ya murza idanunshi yaqara kallo yaga dagaske ita dince. Cikeda zumudi ya bude saqon ya karanta. It's just three words amma yajisu har cikin ranshi most especially na qarshen nan wato *permitted?* Yaji dadin ganin tana neman izininshi ne, hakan yasashi jin kamar ta nuna yanada matsayi awajenta. Babu shiri ya miqe yadauki car keys dinshi ya nufi kofa. Yanajin sadeeq nata tambayarshi ina zaya yai banza dashi yafice, this is a chance of being with her nawani lokaci and he dont want to lose it. Saida yakoma gida yayi wanka ya dauki wanka sannan yanufo gidan nasu don kaita dakanshi. Jin motar tadauki shiru sosai yasashi miqa hannunshi nadama ya kunna disc din motar yasa waqar *sorry* na justin biebier Ahankali waqar tafara tashi acikin motar in a very emotional mode. Cigaba yayi da tuqin yanabin waqar acikin zuciyarshi yanajin waqar tayi daidai da yanayin dayake ciki kuma yanajin kamar waqar na isar da saqonshine gareta. Itama a 6angarenta tunda waqar tafara ta nutsu tana sauraronta, tarasa dalili amma saijitayi waqar na tasiri a zuciyarta, tanasa jin wani sense of emotion a tattare daita. Haka duk sukayi shiru suna sauraron waqar kowa da abinda yake saqawa azuciyarshi harsuka qaraso saloon din...✍ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [9/11, 10:59 PM] +234 803 841 5695: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 087 Itakau dakyar tasamu tashige gidan tana tafiya tanajin kafaffuwanta na dan harhardewa. Wani irin abu takeji wanda batasan taqamaimen menene ba, sosai magangganun ashraf suka shigeta ga dumin da hannunta keyi haryanzu kamar yana cikin nashi. Tsayawa tayi bakin kofar falo tana qoqarin daidaita nutsuwanta, danna power botton din wayarta tayi takawo haske. Wara manyan idanunta tayi ganin har 9:27 yayi. Yanxu me zata cema mamy ya tsaidata har wannan lokacin? Ganin qara 6ata lokaci take yasa tayi taking din deep breath sannan ta danna doorbell ahankali. Ba'a wani dau lokaci ba aka bude kofar Ido hudun dasukayi da mamy yasa qirjinta bugawa tayi saurin sunkuyar dakai cikin diriricewa. Wucewa ciki mamy tayi batareda ta kulata ba hakan yasa itama tabiyota ciki kamar kazar da kwai yafashemawa aciki Saida ta ida qarasowa ciki taga ashe harda Abba a falon. Gabadaya taji ta daburce don tafiyarma saida ta nemi gagararta. Abdul ne yarugo dagudu ya rungumeta yana tsalle yana mata oyoyo. Saurin riqeshi tayi itama ganin yana neman kayar daita tana murmushin yaqe sannan suka qarasa cikin falon gabadaya. Zama tayi qasan carpet tana murmushi ta gaida abba. Amsawa yayi cikin fara'a yana tsokanar abdul wai ya tadata yafiye son jiki kamar mage. Turo baki abdul yayi yana qara matsawa jikin saudart yana cewa "Aunty kinji Abba ko?" Dan murmushi tayi tana shafa kanshi kawai. "Aunty what took you and uncle so long? Tundazu naketa jiranki kidawo in gwadamaki wani abu amma kikaqi dawowa" yaqarashe maganar yana turo baki. Wata iriyar kunya ce ta kamata tadan sadda kai tana dan rintse idanu. "Kinji aunty? Ina ke da uncle kukaje kuka dade" ya sake tambaya yana dan leqa fuskarta. Kasa dagowa tayi don sosai taqara nutsewa cikin kunya musanmman datasan Abba na wajen kuma yana jinsu jitayi kamar ta zubamashi rankwashi akai don takaici. Abba yayi gyaran murya yace "To yafa kamata kowa yaje ya kwanta, dare yayi akashe t.vn hakanan" Babu musu aka kashe kallon duk sukaima juna saida safe sannan suka wuce sama su Abba suka bisu da kallo har suka kule. Ajiyar Zuciya mamy ta sauke ta kalli Abba tace "Yanzu Alhaji aganinka yakamata azubama yarinyarnan ido haka? Da aurenta tana zaune gida? Bama wannan ba, baku ganin anshiga haqqin yaronnan? Sai inga kamar hakan be daceba" tafada atausashe damuwa a fuskarta. "Hakane khadija, yauma daga wajen alhaji shamsu nayonan, insha allah zata koma dakinta very soon" Dadi sosai mamy taji tace "To allah ya amince" Amsawa yayi da amin yana tashi shima yayi part dinshi. Saida mamy ta kashe komai na falon sannan tashiga dakinta ta shirya tafito. Saida ta leqa dakunan yaran don tabbatarda kowa ya kwanta kamar yadda tasaba sannan ta fito tanufi part din Abba. Tanajin alamun ta tafi ta bude idanunta don dama tanajin takunta tayi saurin kwanciya tayi pretending barci takeyi. Tashi tayi xaune ta jingina da kan gado ta dora tunaninda take daga inda ta tsaya. Ita tama rasa taqamaimen meke damunta, kawai dai jinta take wani iri badadi ga tunanin magangganun ashraf dayaqi barin brain dinta. Takusan raba dare ahakan kafin barci ya sadado ya saceta. Tun daga ranar bata sake bari sun qara haduwa ba, duk randa tasan zaizo saita qirqiri ciwon kan qarya ko tace batajin dadi, zuwanshi uku tana haka. Be ta6a damuwaba saima sayayyar dayakeyi mata yaba su abdul sukai mata donshi baqaramin kunyar shiga ciki yakeba. Duk zuwanshi sau uku ya ta6a shiga suka gaisa da mamy shima a darare, kunyar matar yakeji sosai kamar ya nitse dukda sakin fuskar dayake samu awajenta. Abba ma sun hadu dashi sau daya, wani zuwan daya ta6a yi shima daidai abba yadawo daga aiki. Shima a kunyacen yabishi falonshi suka gaisa sannan yafito. Kunyarsu yakeji sosai gani yake suna kallonshi da abinda ya aikata shiyasa duk yadda sukaso yasaki jiki dasu yakasa don duk lokacin dayake tareda su yanajin sense of guilt a jikinshi musanmman daddy don ko hada ido be yarda suyi don sosai yakejin nauyinshi. Shikau daddy yadda kasan d'a haka ya daukeshi, yana qoqarin janshi jiki don ganin ya sake dashi amma yaqiya don the more yake janshi jiki the more yakejin nauyinshi. *** Yau laraba, tunda ya dawo daga office yake shiri don zuwa ganin tauraruwar tashi dukda beda tabbacin yauma zai ganta. Wanka sosai ya dauka cikin manyan kaya kalar milk wanda akaima aikin brown colour, kanshi sanyeda hula brown mai ratsi ratsin milk colour. Hannunshi daure da agogon fata brown sai kaffafuwanshi dake sanye da brown half cover shoes. Sosai yayi kyau kuma kamalarshi taqara bayyana, saida yafeshe jikinshi da turarrukanshi sannan ya dauki car keys dinshi da waya yafita. A falo ya tadda ummy zaune baby tayi matashin kai da cinyarta tana mata tsifa. Saurin tashi zaune baby tayi hangoshi datayi yana saukowa qasa. Duk binshi sukayi da kallo harya qaraso falon don ba qaramin haduwa yayiba kuma ko basu tambayaba sunsan inda zashi. Hararar gefen ido ya jefama baby ganin tawani kafeshi da ido, hakan yasata kauda kai tana qumshe dariyarta. Zuwa yayi ya zauna dayan gefen ummy sai ya kasance sun sata tsakiya ya dora kanshi bisa kafadarta. Ta6e baki tadanyi tace "Sai ina kuma daga dawowanka?" Turo baki yadanyi sannan yace "Unguwa" "To Allah ya tsare ni tadamin kafada ajebo kawai" tafada tana ture kanshi. Tashi yayi zaune yana kallonta fuska adan kwa6e. "Yaya in rakaka unguwar?" Inji baby cikin neman magana Wata uwar harara ya gallamata sannan yace "Eh rakani din tunda ni sa'anki ne" "Sorry" tafada tana toshe bakinta don dariya keson kufce mata Kwafa yayi sannan ya tashi tsaye ya kalli ummy "Ummy saina dawo" "To adawo lfy" inji ummy "Yaya allah ya kiyaye agaidasu" Juyowa yayi ya kalleta tayi saurin sadda kai qasa tana shigewa jikin ummy. Kwafa yayi sannan yafice daga dakin. Tureta ummy tayi tana cewa "Ni dagani ga tsoro ga jan fada" Dariya baby ta kyalkyale dashi tace "Wlh ummy wajen aunty zaya, oh su yaya manya! Kinji yadda yaketa qamshi kuwa?" "Mtcheew saiya kamaki sannan ido ya raina fata kizo ki dameni da raki ko? Cigaba" Dariya tasakeyi tace "Ai yanzu naga yayi sanyi, yabarmin wannan muguntar ko saboda aunty ne oho? Ni ummy yaushe zata koma ne? Kullum shikenan yaita zaryar xance kamar saurayi?" "Ni tadani kiga magrib takusa, kikuma qulle kan nan hakanan kin ida tsefeshi gobe idan munada rabon ganinta, kuma kema kitashi kiyi haramar sallar" "Toh ummy" inji baby tana daukar hularta zata rufe kan itakuma ummy tayi gaba. Saida yatsaya ahanya yasiyama su abdul chocolates da kayan malaqi kamar yadda yasaba sannan yanufi gidan. Lokacin daya isa har anfara kiraye kirayen sallar magrib. Parking yayi inda yasaba parkawa yayi saurin fitowa sanadin g hango Abba dayayi. Qarasawa wajenshi yayi yana dan murmushi kanshi qasa, shima abba fara'a fall fuskarshi yake kallonshi. Koda ya qaraso, hannu abba yabashi suyi musabaha, amsar hannun yayi a kunyace ya duqa still hannunshi ana abban ya gaidashi cikin girmamawa. Amsamashi shima yayi cikin fara'a yana tambayarshi ya mutan gida shikuma yana amsamashi da duk suna lfy. Haka suka jera tare suka fita don dama massalaci abba yanufa don har ankusa kabbara sallar. Koda aka gama ma tare suka fito suna tafe suna fira dikda ashraf bawani sakin jikinshiba yayi sosai. Tare suka wuce part din abba sakamakon cemashi da abba yayi yanason magana dashi. Haka kawai yaji gabanshi na faduwa yana addu'ar allah yasadai lafiya cikin zuciyarshi. Zama abba yayi kan daya daga cikin kujerun dakin ashraf ya xauna kan centre carpet ta tankwashe kaffafunshi dake sanye da baqaqqen safa don yariga yacire takalminshi abakin kofa ya sadda kai yana sauraron abinda abba zaice. Gyaran murya abba yadanyi sannan yace "To alhamdulillah, dama ba komai yasa nace kazoba saidan na sanar dakai idan ka shirya kana iya zuwa ka dauki matarka kutafi jibi idan allah yakaimu, fatanmu akanku shine allah yabaku xaman lafiya ya kuma albarkaci zaman daku baki daya" Wani farinciki nan take ya lullu6e ashraf, jiyake kamar yatashi ya taka rawa don murna. Godiya yashiga zubama abba kamar wani maroqi kallo daya zakamashi kasan he's soo happy. Shima abba yaji dadin reaction dinshi don haka yashiga yimishi nasihohi masu shiga xuciya sosai. Saida suka kusan rabin awa ahaka sannan abba ya sallameshi. Fitowa yayi feeling soo happy, jiyake babu wanda yakaishi farinciki yau a duniyan nan. He can't wait yaganshi da ita agida su kadai just like before. Koda yafito harsu abdul sunfito don tuni maigadi ya sanar dasu zuwanshi. Dagudu suka nufoshi suka rungume kaffafunshi suna murna. Nan suka shiga gaidashi yana amsawa cikin murmushi, yacema habeeb yaje yacewa mamy zaishigo su gaisa. Can saiga habeeb yafito yana cewa sutaho. Kama hannayensu yayi suka nufi main door din suna tafe abdul na xubamashi surutu. Da sallama suka shiga falon mamy dake zaune sanye da hijab ta amsa fuskarta asake. Qarasowa dakin yayi akunyace ya zauna inda yasaba zama qasa yashiga gaidata kanshi kasa tana amsawa cikin fara'a. Tashi tayi ta haye sama don kiran saudart da tunda taji labarin yaxo ta ruga sama. Shima ashraf fita yayi tareda su habeeb don jiran fitowarta yana masu habeeb tambayoyi gameda karatunsu. Qudundune ta isketa cikin bargo don har kai ta lullu6e. Girgiza kai mamy tayi ta qaraso cikin dakin fuska daure tace "Zaki tashi ne ko saina zubamiki dundu abaya?" Jin haka yasata saurin tashi bashiri don tasan halin mamy "Saiki shirya kije ki sameshi, allah dai ya shiryaki kekam don abin naki naga sai ana hadawa da addu'a" Turo baki tadanyi tace "Ummy am not feeling well fa" Harara mamy ta aikamata sannan tafita batareda tasake cemata komaiba. Sake turo baki take tana gunguni don ita allah yasani batason fitarnan dazatayi, yanzu data fita zai maidata mirror yana kallonta da mayun idanun nan dasuke sata jin wani iri. Haka ta tashi tana kumburi ta canza kayanta daga doguwar armless gown zuwa doguwar rigar atamfa mai kalar baqi da jaa ta dora jan three quater hijab tadan fesa turare tafita tanajin an takurawa rayuwarta. Tun daga nesa ta hangosu gefen parking space shi dasu habeeb zazzaune kan plastic chair sun sashi a tsakiya sunata zubamashi surutu. Sauke idanunta tayi ganin shima ya dago yana kallonta ta cigaba da nufosu kanta qasa tana jujjuya phone din hannunta. Da sallama ta qaraso wajen duk suka kalleta suna amsawa. Jan wata kujera tayi ta zauna tana bada dan tazara a tsakaninsu sannan ta gaidashi ahankali. Ansawa yayi yana kallonta kamar zai hadiyeta don sosai tayimashi kyau kuma daya tuna cewa jibi warhaka tana gidanshi sai yaji ranshi yaqarayin fess. Habeeb yazo tafiya don ba laifi yana hankali sosai ashraf ya riqo hannunshi yana cewa ina zashi? Murmushi yayi yace ciki ashraf yace A'a su tsaya ai basu gama firarba don yasan kosun tafi bawani hira zasuyiba da saudart saidai suyita zaman kuramen dasuka saba don koyayi niyyar janta da fira bata bashi hadin kai sai taita amsamashi a taqaice ko tamayi shiru. Haka sukaita firarsu tana jinsu ko dagowa batayiba shikau ashraf suna fira yana kallonta qasa qasa don sosai take qara chanza mashi gawani kyau datake qarawa kullum. Haka akayi firar ranar tsakaninshi dasu habeeb while saudart tun maganarsu tafarko ko tari bata qaraba burinta kawai yatafi don atakure take sosai. Saida akafara kiraye kirayen isha'i sannan yatashi da nufin tafiya. Sallama sukayi sama sama tajuya tashige ciki kamar dama akan qaya take, binta yayi da kallo har saida ta shige sannan ya girgiza kai yana dan murmushi ya tafi dasu habeeb wajen motarshi yaciro kayan daya siyomusu suka amsa suna godiya sannan yashiga motarshi ya tadda yafita suna dagamashi hannu. Tuqi yake amma sai sakin murmushi yake from time to time. Jiyake babu wanda yakaishi farinciki yau aduniya, he can't wait jibi tayi yaxo yatafi da abinshi. Da daddare bayan kowa ya kwanta Abba ke sanar daita yadda sukayi da Ashraf. Sosai taji dadi don har saida hakan ya bayyana sosai a fuskarta. Dariya abba yayi yace "Dole ai kiyi murna tunda wanda ta tsaremiki wuri zata tafi, ai ina lura daku kwanan nan bakida abun hantara kamar ita" Murmushi mamy tayi tace "Wlh ba haka bane, saudart din ce sai ahankali gashi banajin dadin ganunta tana zaune haka da aure kanta" "Ai hakan shine daidai don yanzu shi kanshi ashraf din bazai wahala ba kamar yadda zaiyi da tun farkon faruwar abun takoma, yanzu nasan zuciyarta tayi sanyi sosai kuma bazai sha wahala wajen shawo kanta ba don naga alamun ke tabiyo wajen taurin kai, kinga da ana gaba abin takoma ba qaramin wahala zaishaba wajenta amma kinga yanzu lokacin yadanja kuma yana yawan zuwa suna ganawa so sai inga yanzu it will be more easier for him" "To allah yasa alhaji, kuma wlh kunyi dubara don saudart halinta sai ita idan ta nacewa abu ta nacemashi kenan, allah ya basu zaman lfy yakuma hada kansu" Amsawa abba yayi da amin cikin jindadi da qaunar matar tashi dayakejinta daya tamkar dubu...✍ Sorry for jina shiru kwana 2. Kusamu a addu'a anyi kidnapping din wani brother namu😭 Allah ya ku6uto dasu cikin qoshin lfy🤲 Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [9/14, 11:12 AM] +234 902 212 2569: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 088 Yana komawa gida yafadawa ummy yadda sukayi da abba cikin farinciki. Itama ummy tayi farinciki sosai nan ta shiga yimashi fada da nasihohi masu matuqar amfani, bashi yakoma dakinshiba har sai wajajen shadayan dare. Shima barcin qin daukarshi yayi dawuri haka yaita juyi yana ta saqe saqe har barcin ya sadado ya daukeshi. Washegari tunda yatashi yashiga busy, be nan be can kamar jigida. Shirye shirye yake sosai na tarar saudart wanda bemayi wannan doqin ba lokacin daurin aurensu, shi sai yanzu yake jin irin doqin nan na angwaye, jiyake kamar yajawo ranar taxo don beda burin daya wuce ace gashi ga saudart a muhalli daya amatsayin tashi halak malak. Itakau saudart batasan wainar da ake toyawaba don babu wanda yace mata komai. Ranar mamy da kanta tacemata ta shirya ta rakata unguwa. Dadi taji sosai don tunda taxo gidan sau daya ta ta6a fita wanda tayi da A.A, sosai take cikin kewa da kadaici musanmman idansu habeeb basanan gashi batason tambayar fita wajen mamy don tasan tana iya sawa kuma ta gayawa ashraf. Da harta ma fara shawarar komawa gidan daddy ganin batajin dadin zaman nan sosai amma kwata kwata mamy taqima bata fuska bare tayi yunqurin tunkararta da zancen. Cikeda doqi ta shirya cikin wata milk colour roll silk gown mai adon flowers brown ta sanya brown madaidaiciyar hijabi dayai mugun mata kyau ta dan yi simple makeup sannan tafesa cool turarenta. Koda tafito itama mamy tafito ashirye itama don haka batareda 6ata lokaci ba suka garzaya parking space saudart tashiga mazaunin driver kasancewar ita zata tuqasu itakuma mamy tazauna dayan gefen suka fice daga gidan. Sosai saudart taji dadin fitarsu ta yau don yawo sukayi sosai gashi mamy is so free today babu fadan nan nata haka sukaita labari gwanin sha'awa. Saloon suka fara biyawa aka wankemasu kai aka kitsesu, sosai shukku din saudart yayi kyau yazubo har wuyanta gasu qananu ne sosai. Bayan haka aka mata qunshi mai shegen kyau na baqi da jaa kamar ba hannu ya zanaba. Bayan haka suka biya supermarket sukayi shopping kala kala don ranar saida saudart ta jidi duk abinda take buqata bata samu damar fita siye ba. Itadai mamy batace mata komaiba itama tashiga daukar mata english wears na nightie masu kyan gaske. Haka suka gama shopping din suka fito sannan direct suka yi gidan wata qawar mamy. Sundan dade gidan sannan suka taho bayan ta amshi turarrukan wuta dana jiki da su humra data bada sautun akawomata sannan suka baro gidan sukayo gida. Koda suka dawo mamy bata zaunaba tayi kitchen ta hada mata wani shegen farfesun kayan ciki dasuka ji kayan hade hade kala kala da kunun aya dayaji madara da kwakwa sosai ta kawomata ta tisata gaba ta shanyesu tass. Sannan ta hada mata kujerar garwashi yazuba turare aciki tasata tsugunno akai. Itadai saudart yin abinda mamy tasata kawai take tana wondering meke faruwa, dukda tunda tazo gidan takemata wannan abin amma na yanzu yafi nada. Sharewa tayi kawai ta shashantar da zancen don gani tayi it doesn't worth 6ata lokaci wajen tunani akanshi. Washegari tinda su abdul suka tafi makaranta takoma daki ta kwanta tana hutawa kafin lokacin girkin rana yayi. Tana tsaka da waya da P.A dinta na bakery mamy tashigo dakin da sallama. Murmushi tayima mamyn sannan tayima maryam din sallama akan zata kirata later. Dagowa tayi ta kalli mamy da itama ita tazuba ma idanu tana kallo. Murmushi tayi tace "mamy na?" Ajiyar zuciya mamy tayi sannan ta qaraso ta zauna gefenta tana kallon yadda cikin yan kwanakin nan taqara wani kyau da cika. "Angel?" Inji mamy cikin tattausar murya Kallonta saudart keyi cikin jin dadin sunan data kirata wanda rabon da takirata dashi hartama manta. "na'am sweet mamy na" tafada tana kwantowa kafadar mamyn a shagwa6e. Hannu mamy tasa tana shafamata kanta dayaji qananun kitso sai daukar ido suke tafara cewa "Saudart a rayuwa idan ba'a yafewa akuma mance komai baza'a ta6a samun cigaba ba. Shikanshi ubangiji muna mashi laifi da saninmu, da gangan mudawo mu nemi yafiyarshi kuma ya yafemana mu su waye da baxamu yafema wanda sukayimana laifi ba? Saudart nobody is above mistake, idan mutum yayi maka abu bisa kuskure kuma daga baya yagane kuskurenshi yadawo yatuba, bashi wata damar ake domin gyara kuskuren dayayi afarko bawai a qullaceshi aqi sauraronshi wanda hakan na iya sawa yakoma yasake tafka wani kuskuren makamancin wannan ko wanda ma yafi wannan. Saudart Ashraf mijinki ne no matter what, aljannarki na qarqashin kafarshi, karki bari wani dalili naki na banza yarufemaki ido kikasa neman aljannarki. Ina lura da yadda yake binki kina shareshi saudart, why? Koni dakika yiwa laifi na dauki lokaci mai tsawo ina fushi dake? Keda kikayi dagangan bare shi dayayi bisa mistake? Wlh kizo kiyi karatun ta nutsu, aji idan aka jashi dayawa tsinkewa yake, idan yacigaba da binki kina mashi wulaqanci gajiya zaiyi, dole wata rana ya gaji ya kyaleki, ya fita harkarki. Bare shi namiji ne mijin mace hudu yana iya kyaleki ya auro wata wanda tasan qimarshi da darajarshi, shikenan idan mai wayauce saita janyeshi kwata kwata kizama borar gidan kuma koda kin dawo daga baya kina mashi biyyaya bazaki wani burgeshi ba don lokacin dayakeso bakiyi mishiba. Ina fadamiki hakane amatsayina na uwarki, bari ganin ina matsamaki ne ko wani abu, A'a iyakar gaskiya kenan da duk mai qaunarki zai gayamiki. Kiyi haquri komai yawuce aranki ki ajiye wannan shegen riqon naki ki fuskanci me kike ciki, duniyarnan inbakayi kau ban wuri ake, ga yan mata can bila adadin suna neman slight opportunity dazasu qwacema sakarai miji, da kinyi sanya saidai ki shafa kiji babushi, bare ke mai irin wannan mijin daya hada komai da yanmata ke buri, to wlh ki nutsu kisan abinda kike. Bakuma cewa nayi baxai miki kishiya ba, A'a namiji nada damar zama da mace fiyeda daya muddin zai iyayin adalci atsakaninsu, saidai inason ya kasance koma auren zai qaromiki ya kasance kema danaki power ku goga atsakaninku. Dan haka ki ajiye komai ki fuskanci rayuwa, idan kina ganin ashraf da laifi to babanki yafishi kuma tunda kika iya yafewa baban naki shima yakamata kiyafemashi komai yawuce hakanan, Allah yamiki albarka kinji 'yata mai biyayya? Yabaku zaman lafiya ya albarkaceku da zuri'a dayyiba" Amin saudart da duk jikinta yayi laushi tace tana qara narkewa a kafadar mamy don sosai magangganun mamy suka shigeta. "Yanzu tashi kifara packing din abubuwan dazaki buqata anjima dadaddare insha allah mijinki zaizo yatafi dake" inji mamy Dumm gabanta yafadi sosai bashiri ta daga kanta daga kafadarta tana kallonta in a shock state. "M...mene?" Tafada cikin shock Hade rai mamy tayi tace "I said anjima zaki koma gidanki so start preparing" "M..mamy but it's too...too" saikuma tayi shiru takasa qarasa maganar "It's too me?" Inji mamy tana harararta Shiru tayi kawai gabanta na faduwa sosai don bata ta6a kawowa nan kusa zata komaba don ita har mantawa ma take cewa wai zata koma gidanshi. Mamy ma kallonta take ganin yadda hawaye ke taruwa a idanunta tayi wani rau rau dasu. Girgiza kanta tayi cikin takaici tace "What are those tears for?" Inji mamy tana kallonta Sauke idanunta tayi ahankali wanda hakan yaba hawayenta damar saukowa. "Mtcheew, i don't have your time, yanxu kiyi yadda nace don kizama cikin shiri dayazo kutafi, ke da atunaninki nan zakiyita zama? Bakida aikin yi" tana kaiwa nan tafice daga dakin tabarta nan zaune tana matsar kwalla. Hada kanta da gwiwa tayi tana hawayen sosai, ita yanzu wane irin zama zasu sakeyi da wannan mutumin? Tayaya zata iya zaman aure da wanda bataso, wane irin rayuwa zasuyi wannan karon?. Wunin ranan haka tayishi sukuku zuciyarta cikeda damuwa da fargaba tama kasa tashi ta hada kayyayakinta da mamy tace. Da ranama kasa cin abincin kirki tayi sai tsakura da tadanyi don jitayi batada appetite kwata kwata. Mamy na ankare daita amma taqi tanka mata, daga qarshe ma ita taje ta harhadamata kayyayakin nata tareda sayyayar datayimata jiya na turarruka tayi packaging din komai da kyau. Su abdul dasukaga saudart ta chanza sosai suka shiga tambayar mamy meyasameta don ko kulasu saudart batayiba. Nan mamy tafadamasu komawa zatayi yau, sosai suma jikinsu yayi sanyi don sun saba daita sosai basu qaunar abinda zai rabasu. Tana zaune bisa sallaya bayan tagama sallar magrib mamy tashigo dakin. Riqe kugu daya mamy tayi tana kallonta cikeda takaici. Dagowa tayi asanyaye ta kalli mamy dake binta da mugun kallo. Sunkuyar da kanta tayi tana matsar kwalla ganin kallon da mamyn ke binta dashi. Tsaki mamy taja kafin tace "Wai saudart ke yarinyace koko? Ko ga aurenki bakiyi wannan sakarcinba sai yanxu? Cemiki fa nayi kiyi wanka kishirya this is to 8 ko ahaka zaki?" Ta tambayeta cikeda takaici Shiru saudart tayi batace komaiba "Wai bada ke nakeba?" Fashewa tayi da kukan dake cinta tundazu ta kifa kai da gwiwa tana raira kukan ahankali. Sakin baki mamy tayi tana kallonta na wani lokaci kafin tace "Wai saudart lafiyarki lau kuwa?" Cikin kuka mai cikeda shagwa6a tace "Ni shikenan mamy baki sona, bakison ganina, sai korata kike don baki sona, you're eager intafi inbarmiki gidan don bakisona" taqarashe maganar tana sake rushewa da wani kukan Riqe ha6a mamy tayi tana kallon yadda take kukan bilhaqqi, murmushi tayi sannan ta qaraso ciki ta zauna gefen gado ta jawo kan saudart ta dora a cinyarta sannan cikin lallami tace "Haba anmata na? Ni na iya ince bansonki? Kefa kadaice baby girl dina, abin alfaharina. Ni ba koranki nakeba, kema kinsan darajar ya mace shine dakinta na aure, amma ba koranki nake ba, kema kinsan it's not proper kiyita zama nan da aure akanki ko?" Ta fada tana shafa kanta. Turo baki saudart tayi tace "Amma mamy meyasa baki fadamin tunfarko ba, it's too sudden" "Ok mamy tayi laifi, kuma tana neman afuwa, forgiven?" Tafada tana leqa fuskarta. Kauda kai tayi tana tura baki. Murmushi mamy tayi mai sauti tana cewa "Allah ya shiryaminke, yanzu tashi kishiga wanka saiki fito da alwala kiyi isha'i sannan ki shirya, kinji yar maminta?" Kada kai tayi ahankali bakinta a so6are sannan ta tashi tacire hijab din jikinta ta fiddo towel tawuce bathroom. Girgiza kai mamy tayi tana murmushi sannan ta tashi tafita daga dakin itama don zuwa gabatarda isha'i. Bayan tagama takoma dakin ta isketa itama gamawarta kenan. Wucewa tayi sip dinta ta ciromata wata dakkakiyar pupple shadda dinkin doguwar riga mai wrapper 'o' shape taji paint work tareda farin gyale mai stones ajiki. Ita dakanta ta shiryata tana yi tana fadamata kalamai masu kwantar da hankali cikin tattausan murya wanda hakan ya kwantar da hankalinta sosai. Tana cikin dauramata dankwalin kayan phone dinta yayi ringing. Dagawa tayi ganin abba ne, nan yake gayamata ta taho da saudart falonshi ga ashraf dinma nan yazo, da to ta amsa sannan ta katse kiran. Bata cewa saudart komaiba ta ida dauramata dan kwalin tayimata simple cool makeup sannan ta fesheta da turare mai shegen qamshi mai dadi sannan ta doramata gyalenta saman kai ta ajiyemata fararren takalminta saitin kaffafunta. Tashi saudart tayi asanyaye ta zira takalmin ta dauki purse dinta dake kan mirrorn sannan tabi bayan mamy data kama hannunta. Zaune ashraf yake kan centre carpet ya tankwashe kaffafunshi kanshi dayasha baqar hular dara akasa. Sanye yake da dakakkiyar farar shadda dataji aikin boda kalar baqi, wrist dinshi sanyeda agogon rolex kaffafunshi sanyeda baqaqqen safa sai tashin qamshi yake. Sallamarsu ce ta katsesu suka dan dago suna amsa sallama. Tare suka shigo saudart kanta aqasa tayi wani mugun kyau cikin shigarta sai zuba qamshi take. Tuna suka shigo qamshinta ya dabaibaye mashi hanci, alokacin babu abinda yakeso alokacin kamar ya dago ya kalleta amma kunya ta hanashi saima qara duqe kan dayayi don sosai yake kunyar mamy. Jin motsi yayi kusadashi yadan saci kallon gefenshi ta qasa yaga itace ta zauna dan nesa dashi, kallo yabi hannunta dayasha henna baqi da ja data dora kan cinyarta kamar yakamo hannun don sosai qunshin yatafi dashi. Jin mamy namashi magana yasashi saurin janye idanun daga hannun nata yashiga gaisheta cikin girmamawa. Amsawa tayi tana tambayarshi ya mutan gida ya amsa da duk suna lafy. Gyaran murya abba yayi yafara masu nasiha mai ratsa jiki gameda zaman aure da haquri dajuna. Sosai nasihar tashigesu don har saida saudart ta zubda kwalla. Yana gamawa mamy ma tadora da nata sannan sukasamusu albarka da addu'o'i sosai. Bayan haka abba ya umarci ashraf yatashi yatafi da matarshi. Kuka sosai saudart keyi kamar yaune ranar aurenta, haka su mamy suka rakota har bakin dalleliyar farar motar dayazo daita tashiga gaba gefen driver tana kuka sosai shikuma yashiga mazaunin driver. Nan ya tada motar yana satan kallon saudart data rufe fuskarta da mayafi tana kuka sosai sannan ya ja motar su abdul nata dagamusu hannu a sanyaye suka bar gidan...✍ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [9/14, 12:51 PM] +234 902 212 2569: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 089 Tuqi yake cikin normal speed gwanin burgewa, motar ta gauraye da both qamshin turarenshi da nata wanda suka hadu suka bada wani scent mai mugun dadi ga sanyin a.c din motar daya qarasa cikin motar extra cool. Ahankali yaqara juyowa ya kalleta, kanta kifeda da cinyoyinta tana sheshekar kuka ahankali wanda yakejinshi har cikin ranshi. Dauke kai yayi ya maida ga tuqin dayake yana jin badadi, duk zumudinshi da dokinshi duk sun kau dalilin kukan datakeyi. Jiyayi shima yadamu sosai, meyasa take kuka? Kenan haryanzu she hate him? Yasan bata sonshi amma ai yaci ace ixuwa yanzu ta yafemashi koda bazata bashi zuciyarta ba. Qara kallonta yayi asanyaye yasake maida idanunshi a kan titi yanajin badadi don sosai kukan nata ke ta6amashi zuciya, jiyake kamar ya rungumota ajikinshi yaita patting dinta hartayi shiru. Horn yayi a bakin tangamemen gate din gidansu, ko minti biyu ba'a qaraba gate din ya wangale, Jan hand brake din yayi baya sannan yaja motar yashiga cikin gidan dayake tarr da haske kamar ba dareba. Parking yayi abaki bakin parking space don yasan yanzu zasu fito. Dan satan kallonta yayi yaga haryanzu bata dagoba kuma bata bar kukan ba. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yasa hannu ya bude murfin kofar yafita ya zagayo side dinta yabude mata kofar. Qin dagowa tayi dukda taji tsayuwar motar dakuma bude murfin 6angarenta. Sosai take cikin fargaba, fargaban irin zaman dazasu sakeyi dashi, tama kasa misalta zaman nasu a zuciyarta. Kallonta kawai shima yake, da ba a wannan gidan bane da babu abinda zai hana ya dauketa kamar baby doll yakaita har dakinta amma that must wait, bazai iyayin haka ananba. Hannunshi yakai yakamo tsintsiyar hannunta dayasha qunshi ya riqo softly. Hakan yasa kukan nata ya tsaya cak kamar anyi ruwa an dauke, gabanta yashiga faduwa kadan kadan. Qoqarin amsar hannunta yake amma takasa don ya riqe sosai. "Ki sauko don allah, yi haquri" yafada cikin sigar rarrashi Shiru tayi still bata dagoba, tanajin wani iri sakamakon riqemata hannu dayayi. Ahankali yadan jawo hannun kamar zai dagota. Haka yasa ta dago saidai kanta aqasa, ta ziro kafa daya ahankali sannan ta ida fitowa asanyaye feeling so awkward and weak. Besaki hannunba dukda tafito din saima sake damqe hannun dayayi yafara tafiya. Dole tabi bayanshi badon tasoba fargabarta na qara qaruwa. Tafiya suke hannunsu acikin na juna, jinshi yake so on top, jerawa da ita haka hannu cikin hannu ba qaramin shauqi abin yasashi ba. Wani abu ma saima sunyi settling, yayi alqawarin saiya kasheta da salo salo na love, saiya tsundumata a kogin soyayyarshi tasha tayi tatul. Murmushi yadan saki daidai sun qaraso bakin kofa. Dayan hannun dake free yasa ya danna doorbell din yana satan kallonta. Shiru saudart tayi wondering meyasa yake danna doorbell, dama basu kadaine agidanba? Budewar kofar ya katse mata tunani. "Oyoyo my daughter! Maraba lale, marhaba biki" taji muryar ummy ana rungumota. Saurin dagowa tayi takalleta taga ita dince tana qoqarin shiga daita ciki. Saurin sunkuyar da kai tayi cikin tsananin kunya suka shiga ciki tana jikinta. Murmushi ashraf yayi ganin ummy batama bi takanshi ba shima yashiga cikin ranshi yana cewa "Saukin abin matata ce ba taki ba" Saida suka shiga falo sannan saudart ta ida tantance inda suke, gidansu ashraf. Haka ummy taqarasa daita ciki tana mata marhaban cikin fara'a harta kaita kan wani kujera ta zaunar daita kamar tana zaunar da kwai, itakau saudart tsabar kunya ko dago kai takasa. Shima qarasowa yayi ciki yana kallon yadda umminshi ke wani binta ahankali cikin so da qauna, murmushi yayi yana jindadin yadda ake tarairayar gimbiyar tashi. Da dane da yanzu yana nan yanata kumburi anfi nunamata qauna, amma yanzu he's happy don masoyanta masoyinshine. Ahankali tazamo daga kujerar ta zauna qasa tana gaida ummy da itama zamanta kenan cikin girmamawa kai aqasa. Amsawa ummy tayi cikin fara'a tana cewa takoma kan kujera ta zauna amma taqi tashi saima sadda kai datayi tana wasa da fingers dinta. Qarasowa ashraf shima yayi ya zauna yana facing dinsu, kallo daya zakamashi kasan zuciyarshi fess take, don sosai yakejin wani sabon farinciki a zuciyarshi kamar yaune aka dauramusu auren. "Wai ummy hayaniyar me nakeji n.." baby dake saukowa qasa tafara fadi, ganin kamar saudart azaune kan carfet yasa kingin maganar maqalewa a iska. "Aunty!!" Tafada da karfi sannan tayo qasa dagudu tana skipping din stairs bama ta lura da akwai A.A a falon ba. Wani irin fadawa kan saudart tayi ta qanqameta cikin farinciki don ita batamasan da zancen tarewarta ba. "Hey are you mad!" Inji ashraf cikin qaraji ganin tawani fadawa matarshi Saurin zabura tayi tasaki saudart dahar yanzu kanta ke qasa ta kalli gefen dataji tsawan don ita harga allah batama lura dashiba. "Karyata zakiyi koko? Zaki tashi daganan ko saina sassa6a miki!" Yafada cikin daga murya. Saurin miqewa tayi kafinma ya qarasa maganar tadawo gefen ummy ta zauna tana shigewa jikinta tana turo baki. "To sannu, hanata zakayi su gaisa da auntyn tata?" Inji ummy tana gallamashi harara. Dan sosa qeya yayi yace "ummy kingafa fadamata tayi, karta karyata" "Eh tunda ga pencil ba dole ta karye ba?" Tafada tana harararshi Sunkuyar dakai yayi kawai bece komaiba yana kwafa acikin zuciyarshi, shidai suyi sugama yatafi da matarshi basai sun qara ganinshi ba? Dama ciki yake dasu yadda suka sashi wahala musanmman ummy data kusan samashi heart attack lokacin data buqaci takardarta, dama yadau alwashin duk sadda ya dauki saudart yatafi sai baba ta gani, sai sunyi missing dinshi sosai don yaga alamar dan zaman nan dayayi sun wani rainashi, musanmman waccan tsinken sakacen (baby😂) "Aunty ina wuni?" Inji baby dake maqale da ummy haryanzu cikin zumudi. Dan dago kai tayi ta kalleta ta sakarmata murmushi sannan ta maida kan qasa don sosai takejin kunyansu gabadaya. "Baby kaita sama dakina, bari na hadomata abinci" inji ummy Saurin tashi baby tayi kamar dama kan qaya take tadan saci kallon ashraf daketa antayamata harara ta qasan ido, tai saurin dauke kai taqaraso wajen saudart ta kamota tana mata rada a kunne "Welcome back" Batace komaiba sai tashi datayi suka wuce stairs tare, ummy da ashraf na binsu da kallo. Saida suka shige sannan ummy ta maido kallonta kan ashraf da har yanzu be bar kallon inda sukabi ba tayi gyaran murya. Saurin dauke kai yayi daga kallon dayake ya sunkuyar dakai cikin dan jin kunya. "Saika tashi kaje kaima ga abincin can dining in zakaci" tafada cikin daurw fuska. Dan ta6e baki yayi yace "No ummy am ok" Azuciyarshi kau cewa yayi "Abincin yasha zamansa, Idan naci ina zan saka kazar dazan siyamana?" "Kai kasani" tafada tana tashi tabi bayansu baby. Binta da kallo yayi harta haye sannan ya ta6e baki yana wondering meyasa kwananan ummy ke dauremashi fuska, gashi yanzu tagama washema saudart baki amma shi tawani hade mashi fuska. Ta6e baki yayi yakoma ya kishingida a kujerar yayi balancing yaciro wayarshi yana daddanawa yana jiran tagamaci ta sauko su tafi😒 Sosai yakejin zuciyarshi fess, sai practicing din abinda zai faramata yake a zuciya, soyake ya koyamata darussan sonshi dalla dalla, zai maidata queen dinshi, sarauniya, yalla6iya, ko tsinke bazai bari ta dagaba, shizai mata breakfast, yazo ya tadata daga barci romanticly ya rakata har bathroom dama yariga ya hadamata ruwan wanka mai dumi da qamshin gaske, yajirata kofar bayin harta gama tana fitowa ya sunkuceta yakaita kan gado, ya zaunar daita, ya shafamata mai ya ciromata kaya tasa sannan yakaita dining, A'a sama zaikawo abincin, zaifi bada kala, ya bude yayi serving dinta ya saka cokali ko fock yafara feeding dinta, da ana iya taunamata ma dashi zai taunamata, tagama yabata ruwa tasha sannan yayo clearing din wajen yadawo ya sungumeta yakaita falo ya kunnamasu kallo ya kwantar da kanta bisa cinyarshi suna kallo yana massaging din kanta.. wooh soyayya dadi! Saiyafi sharukh khan ma iya zuba love, saiya rudata da salon soyayya ya tsundumata tsundum cikin kogin soyayyarshi yadda duk numfashinta saita shaqane da sonshi. Haka yaita lisafe lissafenshi shikadai sai sakin murmushi yake, jin yafara gajiya dazama babu su babu alamar su yasashi daga kai yaduba agogo. Waro idanunshi yayi ganin har goma ta gota. Wannan cin abincin na lafiya ne kuwa? Almost two hours? Shiga contact yayi ya dannawa number baby kira ya kara a kunne yana tamke fuska kamar tana gabanshi. Saida takusan tsinkewa sannan aka daga "Hello?" Yaji tafada cikin muryar barci "Ke! Ya akayine? Haryanzu bata gamacin abincin bane?" Yafada cikin husky voice Zaune tamiqe tana murza idanu don ita tama dan dade da kwanciya "Wacece?" Ta tambaya tana hamma "bansaniba! Nace ina saudart" yafada a fusace Turo baki tayi sannan cikin marairaicewa tace "Nifa tunda ummy tahau sama ta korani daki wai karna takuramata" Tsaki yaja ya katse wayar kawai. Bin wayar tayi da kallo cikeda takaici sannan ta kasheta gabadaya tayi tilli daita kan gadon ta kwanta taja bargo. Yana gunguni yashiga neman number ummy. "Yanzu this is 10 sai dayan dare nufinta zamu tafi?" Yafada yana danna mata kira. Itama saida takusan katsewa sannan ta daga "Uhum?" Tafada daga dayan 6angaren Turo baki yayi cikeda jin haushi yace "Ummy this is past ten fa" "Sai akayi yaya?" Inji ummy tana daure fuska daga dayan 6angaren. Haushi ne yasake qumeshi "Ummy sai midnight zamu tafi? Bata gama cin abincin bane haryanzu?" "Wa kenan?" Taqara tambaya Shiru yayi gabanshi nadan faduwa. Wani tunani ne yazo mashi, saurin kauda tunanin yayi yana cewa no..no..no ummy bazakiyimin hakaba. "Look idan bakada abin cewa zan kashe wayata, dama barci nike ka tadani" ta katsemashi zancen zuci da hakan. Cikin dan rawar murya yace "To kiyi haquri ummy, wai gani nayi dare nayine ga securities, idan nahau hanya yanzu suna iya tareni""yafada cikin zuciyarshi yana addu'ar allah yasa ba abinda yake tunani bane zai faru "Ehen? Katafi mana, dama wani ya tsaidaka?" Shiru yayi yanajin yawun bakinshi na qafewa, besan sadda ta zame hular kanshi ba yana fiffita kanshi "ummy dan allah kiyi haquri, kibani saudart mutafi dare yayi" yafada cikin mugun surewa yana ganin yadda budget dinshu ke rushewa agaban idanunshi "Wace saudart?" "Ummy don allah, don allah kiyi haquri, please ummy, don allah" yafada duk ya rude yayinda danasanin biyowa tanan ya dirarmashi nan take. "Mtcheew meye nawani tisani gaba kana begging? Me kayimin?" "Wlh nima bansaniba ummy amma don allah kome nayi karki hukuntani da wannan, please sweet ummyna kinji?" Yafada cikin sigar rarrashi still yana yima kanshi fifita. "Mtcheew saida safe, ka kashe duk kayan wuta dake falon sannan ka kullemin kofa idan zaka tafi" tana kaiwa nan ta katse kiran tama kashe wayar gabadaya. Sakin baki yayi jin abinda tace, me kenan? Oh no! Wlh bazata sa6uba. Saurin ciro wayar yayi daga kunne yasake re-dialing din wayar amma wayar akashe. Ca6! Yau ake yinta, idan ya yarda yatafi tsaye😡 Tilli yayi da hular hannunshi ya nufi sama kamar zaiyi fiffike yatashi sama yanajin kanshi na daukan zafi. Beci burkiba akoina sai a kofar dakin ummy. Bubbugawa yake yana huci, jin shiru yasashi qara bubbugawa wannan karon da qarfi don sosai zuciyarshi ke tafarfasa. Jin kamar za'a 6alla kofar yasa ummy tasowa don ita guduma take kar ya tada saudart datayi barci tundazu wanda azahirin gaskiya ba barci saudart keyiba duk abinda ake harta wayar da ummy tagama yanzu duk a kunnenta ne. Ganin ummy ta bude kofar tafita yasata dan dagowa ta yaye bargon kanta ta kalli sannan tasaki murmushin jindadi tajuya tagyara kwanciyarta tana dariya qasa qasa. Shiru ashraf yayi yana kallon ummy kamar zai fashe da kuka, jiyake kamar yaita ihu ko zaiji sauqi. "Nace menene! 6allemin kofar zakayi?!" Inji ummy tana binshi da harara Qoqari yayi wajen sassauta muryarshi sannan ahankali cikin kwantar da murya yace "Haba ummy, haba ummy? Dan allah ki tausayamin mana, dan allah kiyi haquri ki fiddota mutafi dare yayi" Wani kallon uku saura kwabo take binshi dashi harya kai aya sannan tace "Ka gama? To wlh ka fita idona in rufe ashraf, katafi kabani wuri tun muna mu biyu wlh, tun kafin in sassa6amaka" Kallonta yake kamar zaiyi kuka, ahankali yace "Ummi yanzu ina zani ni kadai?" "Ohon maka amma wlh nakarajinka kusada kofarnan saika yabawa aya zaqinta" tana kaiwanan tajuya takoma dakin tareda bugo kofar. Tsayawa yayi yana kallon kofar cikin rashin sanin abinyi, wai wane tsautsayima yasashi zuwa gidan ma tun farko, wannan shi ake kira rabon ayi, (nikuma nace ga qoshi ga kwanan yunwa😝) Ya dade sosai tsaye a bakin kofar kamar mai jiran tasake fitowa har saida yaji kaffafunshi sunfara sanyi sannan yajuya afusace ya sauka qasa feeling so mad in anger, jiyake kamar yadora hannu aka yaita ihu. Motarshi yashiga afusace ya kunna yayi reverse, wani uban horn ya danna kamar ana yaqi sannan ya fice a tsiyace bayan an bude gate din. Tuqi yake yana huci ga idanunshi dasukayi jajir, jiyake kamar yaita kuka don takaici, kai amma ummy tagama dashi wlh, duk wannan tsare tsaren nashi duk ta rusheshi kenan abanza? Kwafa yayi yana danna kan motar cikin gidanshi bayan anyi scanning dinshi. Ko parking din kirki beyiba ya sauko daga motar ya maidata ya rufe da qarfi sannan yayi cikin gida fuuu. Jiyake kamar ya hadiyi zuciya kawai, he can't believe duk zumudin da zakwadin shi kadai zai kwana gidan at the end of the day, kai ummy tagama dashi. Direct dakinshi yashige yawani bugo kofar da qarfi, baiwar allah yadda kasan ita tamashi laifin😕 Kokowa yashigayi da rigar jikinshi don cireta yadda kasan yasamu qaton gardi. Dakyar yasamu ya cireta yana huci dukta cikwikwiye itama yayi cilli daita tana huci. "Wlh ummy kin gama dani!" Yafada yana dafe kai cikeda takaici. Tsaki yaja yafara safa da marwa dakin cikin tsananin 6acin rai, jiyake kamar yaita hauka. Wayarshi yazaro daga aljihun rigarshi dayayi cilli daita ya lalubi number sadeeq ya dannamashi kira yana huci. Kira har hudu amma ba'a dagaba da alamu dai ya dade dayin barci Tsaki yaja yana cilli da wayar kan gado yana cewa "Shege sleeping head kawai" Ataqaice ranar ashraf kasa runtsawa yayi don baqinciki, tsaki kau yakashi yafi cikin kwando dama tusa hali bare anci wake😆 Yadda yaga rana haka yaga dare don azaune ya kwana don bakinciki...✍ Please kucigaba dasa brother na a addu'a🙏 Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [9/14, 7:23 PM] +234 902 212 2569: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 090 Yauma da 6acin ran jiya ya tashi, dakyar ya iya tashi yayi alwala yafita masjid bashi yadawo ba saida gari yadan fara haske. Tunda yadawo yashige daki ya kwanta shiru zuciyarshi fall takaici. Ringing din wayarshi yasashi bude idanunshi daya lumshe sannan yadauki wayar ahankali yana duba mai kira, tsaki yaja kamar bakin zai tsinke ya maida wayar ya ajiye batareda ya dagaba. Saida aka mashi 4 missed calls be dagaba sai a ba biyar sannan ya daga yawani tamke fuska kamar mai kiran na gabanshi. "Amma A.A kaci uwar rainani, inta kiranka kaqi dagawa don iskanci?" Inji sadeeq a dayan 6angaren. "Qodarka aka ban ajiya halan dazaka addabeni da kira kamar wanda yayi maka sata, ni nace ka kirani ne?" Yafada cikin 6acin rai "Sai kace in kiraka dama? Mtcheew dama don naga missed calls dinkane har hudu yasa na kira inji lafiya ashe iskancinka ne ya motsa" "Eh shi ya motsa, and batun missed calls ai tun jiya namaka don iskanci sai yanzu zaka wani kirani kaji lafiya? Don ka maidani maloho?" "To allah yabaka haquri, ba laifinka bane, laifi nane dana kira at the first place, bye" Qiit.. ya katse kiran. Wani haushi yakuma qume ashraf, ciro wayar yayi daga kunnenshi afusace yasake dannamashi kira yana huci. Saida takusan katsewa sannan ya daga yana cewa "Menene kuma?" "How dear you hang up on me? Kai wanene dazaka katsemin kira?" Yafada afusace, dama neman wanda zai juyewa kwandon bala'i yake "Tofa? Meyasa nayi hanging? Mezai hana inyi hanging? Na tashi naga missed calls dinka wajajen 12 ba dole hankalina ya tashiba? Nakira kuma inyi comfirming ka balbaleni mezai hana inyi hanging up?" Yafada shima da alama yafara qulewa "Eh din, an balbaleka din! Mezakayi? Nace anje an balbaleka din, ko dukana zakayi?" Yafada cikin tada jijjiyoyin wuya abinda ummy tayimashi nasake dawomashi a qwanya, da yanzu suna tareda abar qaunarshi, nurul qalbi dinshi. Shiru sadeeq yayi kawai baki sake, lallai ma ashraf da alama rigima yakeji, tsawon kasancewarsu tare yasa yasan komai nashi, yasan halinshi ciki da bai, babu tantama 6atamashi rai akayi wataqila shiyasa ma yakira jiya din and da alama haryanzu yana cikin 6acin ran. "Alright...alright am sorry to, allah ya huci zuciyar the boss himself" yafada yana murmushi Tsaki ashraf yaja yakoma ya jingina da kan gado yana kalkada kafa ahankali sai muzurai yake. "Yanzu gayamun waye yata6amana boss dinmu, the whole A.A himself" Tsaki yasake ja batareda yace komaiba, shi komaima haushi yake bashi wlh. Ta6e baki sadeeq yadanyi cikin zuciyarshi yace "Kaji dashi, mutum abu kadan tsaki kamar tsaka" Azahiri kuma yace "Ko inzo ne?" Tsaki yasake ja kafin ahankali kamar mai koyon magana yace "Idan kaga dama" Dan murmushi sadeeq yasaki sannan yace "To ai hikenan, amma ka tanadarmin wani abu please ban karya ba" Wani tsakin yaja cikeda haushi yace "Ubanwa zai tanadarma? To kama cika cikinka don ba gidanmu ba nike, inanan gidana" "Gidanka? Me kakeyi gidan?" "Sainaji matsa sannan zan fadi, mtcheew" Yana kaiwa nan ya katse wayar yayi tilli daita kan gado ya maida hannayenshi ya harde a qirji yana cigaba da kalkada kaffafu. Sosai yaji dadin kiranshi da sadeeq yayi don dama ko be kiraba yanada niyyar kiranshi don a duniya babu wanda yake sharing din damuwarshi dashi kamar sadeeq, dukda wani sa'in he's so annoying amma he's the best kind of friend ever, haka yaita kalkada kaffafun yana tsumayin jiranshi, yazo yafadamashi ko zaiji sauqin abinda yakeji aranshi. Sauke wayar sadeeq yayi daga kunnenshi yana girgiza kai, Allah ya shiyaka A.A da wannan shegiyar zuciyar, zuciya kamar kuturu. Yamiqe ya ajiye wayar sannan yawuce bathroom don freshen up. Dago kai tayi daga littafin addu'o'in datake karantawa na ummy ta kalli kofar tana amsa sallamar da akayi. Baby ce tashigo, haqoran nan awaje don murna ta qaraso dakin tana kallon saudart. Itama saudart kallonta take murmushi a fuskarta harta qaraso inda take zaune akan sallaya itama ta zauna kusada ita baki awashe tace "Good morning sweet aunty!" Murmushi mai sauti tayi tace "How was your night?" "Cool... wai aunty nan dama kika kwana?" Harara ta gallamata ta maida kanta bisa littafin hannunta tana cewa "Shafa kiji" Wani irin dariya baby ta qyalqyale dashi harda dafe ciki, dagowa saudart tayi tana kallonta da alamar tambaya itama dariya nason kufcemata amma tana mazewa. "Like seriously, you mean... nan kika kwana? Whoo no wonder jiya yaya ya addabeni dakira yana balbaleni, ashe kwalele akayimashi, kai amma ummy bomb ce" tafada tana qara kecewa da dariya. Waro idanu saudart tayi jin abinda tace a qarshe sannan ta tallabe mata qeya tana cewa "Ummin ce bomb, qaddara taji tagama" Wata dariyar baby tasa kafin tace "Ai gaskiya ne aunty, a kwacema matarka a very first night dinka? Ai angama dakai wlh" "To ya isheki, tashi kifita kingama kinja na manta inda na tsaya" tafada tana maida dubanta ga littafin. "Ni aunty naga ma kamar abin be wani damekiba, naga bashi kadai akaima buqulu ba harda ke" Rolling din idanunta saudart tayi cikin qosawa da magangannunta sannan cewa "Kinsan Allah? Zan hadaki da ummy wlh, tom" Dariya baby tayi tana tashi tsaye "A'a bani na kar zomon ba, ratayar ma ba'a banba, kai amma ummy ma ta iya, naso inga idon yaya jiyan nan" tafada tana fita daga dakin. Binta da kallo saudart tayi sannan ta girgiza kai tana dan murmushi. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Tsayawa yayi yana binshi da kallon takaici yanajin kamar ya rufeshi da duka ko yaji sauqin abinda yakeji. Don iskanci an 6atamai rai yakirashi don yasamu sassaucin abinda yakeji shine zai bige da yimashi dariya? Ahankali sadeeq yafara tsagaita dariyar dayakeyi tundazu yana wani irin shesheqa don har cikinshi yafara ciwo saboda dariya. "Are you kidding me?" Yafada dakyar cikin sheshekar dariya yana kallon ashraf da fuskarshi ke dinke tsab kamar wanda aka aikowa saqon mutuwa. Hankerchief yasa ya tsane hawayen dasuka tararmashi a idanu saboda dariya yace "You mean ummy ta riqe matarka? Hhhhhhhh to wai dama tarewa zatayi shine banji labari ba? Hhhhh amma ummy ta iya, ita haka ake? Saiki riqema mutum matarshi a ranar farko? Gaskiya ummy bata kyauta manaba" yakuma kece dawata dariyar. Ashraf rasa inda zaisa kanshi yayi don baqinciki, wai yama akayi yakira wannan chali chalin dasunan ya gayamashi damuwarshi, gashi he is adding salt into his injury don dariyarshi ba qaramin tunzurashiba take. "Gaskiya ummy bata kyautaba... muje musameta muji dalilin ta na yimana wannan ta-leqo-ta-koman?" Yafada cikin rawar murya irin ta masu dariyarnan sannan yakuma kwashewa da wata dariyar harda buga kafa qasa. Tashi ashraf yayi a mugun fusace yana nunamashi kofa "Don ubanka zoka fita" yafada cikin quluwa Dakyar sadeeq ya danne dariyarshi sannan yace "Ni? Menayi kuma?" "Wlh koka fita ko in 6a66alaka acikin gidan nan kuma na 6alla banza na 6alla wofi, nace out!" Yafada cikin hargowa, jiyake kamar yaita kuka don takaici. "Haba ashraf... nifa bani nayimaka ba, saika huce kaina?" Yafada yana faman danne dariyarshi saidai kallo daya zakamashi kasan dariya na cinshi sosai "Wai bazaka fita ba!!" Inji ashraf cikin daga murya idanunshi sunyi jajur. "To..to..to yanzu am sorry kaji? Am so sorry ok? I don't mean to hurt you, kawai abin ne daban dariya" yafada yana yin serious face ganin yadda ashraf ya kunnu "Yanzu laifi ne don na kiraka na gayamaka damuwata? Saika tusani gaba kanamin dariya?" Yafada cikin jin ciwon abun. Sosai sadeeq yayi qoqari wajen danne dariyar dake cinshi yace "Haba bestie? Meyai zafi? Wlh i don't mean to hurt you, am sorry if i did" Komawa ashraf yayi jagwab a kujera yana dafe kai, sosai zuciyarshi ke tafasa, jiyake kamar yaita kurma ihu ko zaiji sassauci. "Sorry kaji insha allah matarka zata dawo gareka, i assure you" sadeeq yafada cikin sigar lallashi dukda yadda yakeson bursting to laughter amma beson yasake tunzurashi shiyasa yake dannewa. Janye hannu yayi daga dafe kan dayayi ya kalleshi da idanunshi dasuka kada yace "Yanzu idan kaine aka qwacewa mata at the very first day dazaku tare ya xakaji? Tell me" ya tambaya cikin yanayinda dole yabaka dariya. Kasa amsawa sadeeq yayi don yasan muddin ya bude baki da niyyar amsawa to tabbass dariyace zata fito, non-stop laughter. "Tambayarka nike, idan kaine zakaji dadi?" Yasake fada yana tsareshi da ido Girgiza kai kawai ya iyayi don saura kadan yayi exploding. Kuramashi idanu ashraf yayi sannan ya girgiza kai yace "Kayi dariyarka mallam ban hanaka ba" Dariyarce ta kufce mashi batareda ya shirya ba yayi saurin sa tafin hannu ya toshe baki yana yi sosai. Sosai ashraf yaqara hawa hakan yasashi fara jifanshi da pillows din kijeru yana cewa "Get out! Get out! Get out idiot!" Tashi sadeeq yayi yana dariya sosai yana kakkare jifan. Ganin abin nashi bana qarewa bane yasashi nufar waje dagudu yana dariya shima ashraf yabishi still yana jifanshi. Haka suka fito har harabar gidan yana jifanshi da pillows din yana sake tsintarsu yaba jifanshi "A.A please listen to me" yafada yana chafe wani pillow da ashraf ya jefomashi. "Listen your head! Get out!" Yafada yana turashi. Taga taga yayi kamar zai fadi yayi saurin maintaining din balance dinshi yana dariya sosai yace "Wlh shawara zan baka listen to me" Turashi yacigaba dayi harsuka qaraso wajen motarshi yana cewa "Shawara my ass! Banso! Ka dau akwalar motarka kabarmin gida" Haka ya tasa qeyarshi harya shiga mota yarufe sannan yaja baya yana huci kamar zaki. Wining din glass din sadeeq yayi qasa yace "Wlh ba zama zakayiba, kaje ka tisata gaba ta baka matarka idan ka zauna kuma zakaga zama" Wani kallon 'au bazaka tafiba?' A.A yayi mashi sannan yanufi wurin wani dutsi zai dauko, hakan yasa sadeeq saurin bama motarshi wuta yafice aguje yana qyalqyalar dariya. Kwafa ashraf yayi yana yadda dutsen hannunshi yana cewa "Daka tsaya ai" Sannan yajuya yayi cikin gida yana tsince pilluluwan daya watsar tsakar gidan. Dawowa yayi ya zauna falon ya harde kaffafunshi yana dan girgizawa irin yanajin bala'in nan. Shi wlh bazai jeba, badai saudart ba? To yabar mata ta jiqa ta shanye. Haka yaita zama ranshi a 6ace daga baya kuma yafita yawuce wani restaurant don sama cikinshi wani abu jin yadda cikin ke kiran ciroma. Koda yagama gidanshi yadawo yawuce sama ya rufe kanshi adaki, jiyake komai ma bemishi dadi, jiyake kamar yaita rotsa anything rotsable a dakin. Haka yaita daurewa har zuwa bayan azahar, ganin dai yana neman kashe kanshi cikin gida batareda wanda yakeyi dansuba sun sani yasashi shiryawa ya dauki makullan mota yafita. Hanyar gidansu ya dauka don bazai iya jurewa ba, yakasa yin zuciyar, gwara yaje duk yadda za'ayi ayi shidai abashi matarshi...✍ Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillahi kasiran! Ina farincikin sanardaku an sako brother na yau, nagode qwarai da addu'o'inku, nasan hardasu suka bada gudunmawa har komai yazo cikin sauki. Allah ya saka da alhairi💖 Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [9/16, 12:11 PM] +234 909 007 1867: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 091 Shiru yayi hannunshi kan sterring yana tunanin hanyar dazaibi yayi convincing din ummy tabashi matarshi. Shi bemaga dalilin yin hakaba, wannan ai daukan alhaki ne, shi bema ganin laifin kowa sama da nashi, da beyi kicihin biyawa ta gidanba tun farko da yanzu wani labarin ake. Shi wai irin ya kawota dinnan ayimasu nasiha ganin haka akayi wancan lokacin ashe ruwan dafa kanshi ya debo da kanshi. Ajiyar zuciya ya sauke nannauya sannan ya cire seat belt dinshi ya bude murfin kofar yafito ahankali yana shakar fresh breeze din dake kadawa. Ahankali cikin tafiyarshi ta qasaita yanufi cikin gidan yana ayyana yadda zaiyi yasamu yashawo kan ummy. Danna doorbell yayi yamaida hannayenshi cikin aljihu ya zubama kofar idanu. Jim kadan aka murda kofar aka bude. Saurin sunkuyar da kai maid din tayi tana gaisheshi cikin girmamawa. Amsawa yayi yana shiga cikin falon dauke da sallama a bakinshi. Juyowa duk sukayi daga inda suke zaune a dining suna kallon cikin falon. Dumm.. gabanta ya fadi sanadiyyar gaurayar da idanunta sukayi da nashi, sosai taji effect din idanun nashi anata wanda hakn yasata saurin sadda kai zuciyarta na chanza bugu. Shima tsayawa yayi yana kallonta, jiyayi wata iriyar kasala ta sauko mashi nan take, sosai yaji yayi missing dinta daga jiya zuwa yau. Ahankali yanufo wajensu idanunta akanta yana kallon yadda take jujjuya cokali a plate din gabanta. Satan kallon saudart baby tayi ganin irin kallon dayake mata taga kanta na qasa sannan ta saci kallon ummy taga itama hankalinta nakan abincinta saima qara tamke fuskar datayi hakan yasata sunkuyar dakai tana danne dariyar karfin halin ummy, mutum da matarshi? Jin ya qaraso wajensu yasata dagowa ta kalleshi taga tsaye yake yana kallonsu gabadaya. "Oyoyo yaya! Please have a seat" inji baby cikin iyayi. Wani tsarabar harara daya bata yasata yin tsit ta maida kanta kan abincinta tana turo baki. Jan kujerar dake kusada ummy yayi ya zauna yana kallon saudart dake tsakurar abincinta atakure ta qasan ido sannan ya maida kallonshi ga ummy datayi kini kini da rai yace "Good afternoon ummy" Batareda ta dago kai daga abincin datake ciba tace "Afternoon" Shiru yayi yana kallonta ganin yadda tawani hada gabass sa yamma daga ganinshi, shi yarasa meyasa ummy kemashi haka. "Yaya ina wuni" inji baby tana dan hura hanci adole an6ata mata rai. Ko kallon gefenta beyiba bare tasa ran amsa saima maida kallonshi dayayi kan saudart dakejin kamar ta narke saboda yadda takeji. Jin idanunshi akanta yasata qarajinta uncomfortable, allah yasani batason kallon nan ko kadan, yanasata jin wani iri sosai. Ahankali ta cije ta dago, hada idanu sukayi tayi saurin janyesu sannan cikin calm voice tace "Ina wuni?" Wani irin farinciki yaji ya ziyarci zuciyarshi nan take, farincikin da rabonshi dashi tun jiya kafin yaje daukota. Sakarmata cool smile dinshi yayi yace "How are you?" Batareda ta kalleshi ba tace "Alhamdulillah" a takaice. "Baby serve your brother" inji ummy dahar yanzu taki dagowa daga abincinta. Tashi baby tayi ta zari plate tashiga zubama ashraf abincin tana satan kallon yadda yake kallon saudart ta qasan ido. Sosai tayimashi kyau cikin doguwar rigar atamfa mai manyan flawowi yellow and dark green dake jikinta dinkin pieces taji stone works agaba, ta kamata cif cif kamar ajikinta aka dinka sai dankwalin data daura zahra buhari style, fuskarta has usual dauke da simple makeup don yau ko kwalli batasa a idanu ba sai lining din datayiwa saman idanun mai kyau. Beta6a ganinta acikin shigar atamfa ba sai yau, yafi ganinta cikin arabian gowns ko shadda hakan yasa yaga ta chanzamashi sosai kamar ba itaba. Dan ture plate din gabanta tayi ba don ta koshi ba sai don takasa kai komai abakinta saboda yadda takejin piercing eyes dinshi akanta ta zari tissue tana dan goge baki. Dagowa ummy tayi tana kallonta ciki kulawa tace "Ya dai?" Murmushi tasakar mata tadan yamutse fuska tace "Am full ummy" Wani irin binta yayi da kallo ganin yadda ta shagwa6e fuska kamar wata baby doll yanajin kamar ya cinyeta don so. "Hmm keda baby bansan gwani ba wurin rashin cin abinci, ku kuka sani ai" tafada tana sipping din ruwa. Murmushi kawai tayi sannan tadanja kujerarta baya ta tashi tana cewa "Ina zuwa" Ta juya batareda jiran amsar kowaba tashiga takawa cikin takunta mai cikeda da nutsuwa tabar wajen. Binta yayi da kallo qasa qasa yanajin badadi don beso ta tashi ba, begaji da kallonta ba da shaqar qamshinta. Maida hankalinshi yayi kan abincin yanaci yana tunanin ta ina zai 6illowa ummy ta taimaka tabashi matarshi. Ba'a jimaba baby ma ta ture plate dinta tana goge bakinta da tissue itama tayimusu sallama tabar dining din. Shiru wurin ya dauka sai qarar cokala dazakaji suna haduwa da plate. Shidai ashraf tsakurar abincin kawai yake, soyake ya dauko maganan amma yarasa ta inda zai fara. Can dai ya nisa ya dago ya kalli ummy da kanta ke bisa abincinta tanaci fuska daure. Ajiye spoon dinshi yayi sannan yayi interlocking din yatsun hannayenshi ya dora kan table yana kallonta. "Ummy.." yafada ahankali yana zubamata hazal eyes dinshi daya gado wajenta. Dagowa tayi itama ta zubamashi nata batareda tace mashi komaiba. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yaqara yin qasa da murya yace "Ummy don Allah laifin me nayimiki ne kiketa fushi dani? Dan allah kiyi haquri ki gayamin ummy, wlh bansan me nayiba" yafada yana langwa6a kai kamar wani maraya. Dauke kai tayi daga kanshi ta maida a abincinta tana cewa "Cema nayi kayimin wani abu?" "Ko bakice ba ummy ai fuskarki ta nuna, don allah ki taimaka ki gayamin ummyna" yafada cikin sigar rarrashi. Ta6e baki tayi tace "To ni bakamin komaiba, idan ma kayimin kasan ba tsoronka ba nake dazan tsaya 6oye 6oye, fitowa zanyi infadama inkuma dauki matakin daya dace akai, so stop bothering me" tafada tana kai abincin data debo abaki. Shiru yayi yana kallonta nawani lokaci sannan ya sauke ajiyar zuciya ahankali "To amma ummy meyasa kika hanani tafiya da saudart jiya?" Ya tambaya ahankali "Saboda na isa daku duka, daga kai har saudart din, idan kuma nunamin zakayi ban isa dinba to" tafada tana binshi da harara. Shiru yayi yana kallonta zuciyarshi namai zafi. Wai meyasa ummy kemashi haka? Meyayi mata take son ganinshi cikin 6acin rai da kunci. "Ummy kin isa damu mana amma gani nayi wannan..." Dakatar dashi tayi ta hanyar dagamashi hannu. Shiru yayi yana kallonta da idanunshi dasuka fara kadawa, yanajin zafi sosai azuciyarshi "Idan maganar dazaka cigaba dayimin kenan kindly leave, kokuma ni inbarma wurin":tafada tana kallonshi strictly. Sadda kanshi kawai yayi bece komaiba zuciyarshi na suya sosai, jiyake kamar yaita kuka ko zaiji sassauci. Ko gefenshi bata qara kallo ba harta gama cin abincinta ta tashi takoma falo tabarshi awajen. Haka ya zauna shiru a dining din, shikadai yasan yadda yakeji azuciyarshi, jiyake kamar yaita watsa kayan kan dining table din ko zaiji sauqi. Jin ana kiraye kirayen sallar asr yasashi tattaro kingin kuzarinshi yatashi yana qoqarin wajen ganin yayi controlling din kanshi. Falon shima yadawo inda ya tadda ummy zaune remote a hannunta. Zama yayi kan wata kujera dan nesa da ita batareda ya dagoba yace "Ummy zan tafi masjid" Itama batareda ta kalleshi ba tace "To allah ya tsare" Tashi yayi yana cewa amin sannan ya nufi kofar fita yana ayyana shida gidan nan kuma sai baba tagani tunda babu mai sonshi agidan. Direct motarshi yanufa yashige ya tada yabar gidan. Tanajin fitar motar ta ta6e baki tana cewa "Kafi ruwa gudu" itama ta tashi ta haura sama don haramar sallah. Masjid yafara biyawa yayi sallah sannan yawuce gida. Ranar dai haka yawuni rai adagule gashi fushi yake da sadeeq bare yakirashi yadanji sanyi, kodayake yanama iya kiranshi yafara 6a66akamashi wannan dariyar tashi ta mahaukata gwara ya rarrashi kanshi da kanshi amma yadauki alwashin bazai qara zuwa gidanba da sunan abashi saudart, yabarmasu su cinyeta. Washegari ma haka ya tashi rai adagule, sadeeq tunjiya yake kiranshi amma yaqi dagawa don haryanzu fushi yake dashi, ummy kau saidai yakirata suka gaisa kawai don yariga ya qudura aranshi yayima gidan yaji bazasu qara ganinshiba saisun nemeshi dakansu. Ranarma haka yawuni cikin kunci, ganin abin yayimashi yawa yasashi fita bayan asr yaita zagaye gari bashi yadawo ba sai wajajen 9 din dare. Ranar ma kamar kingin ranakun haka ya kwana cikin kewar abar kaunar tashi. Washegari monday tunda wuri ya tashi yafara shirin fita company don jiyayi duk zaman gidan ya fice mashi akai, gwara yafita aikin ko ya deba mashi kewa. Wajajen 8:30am sadeeq ya iso company din. Sosai mammaki ya cikashi dayaga wani staff yafito daga office din ashraf don beyi tunanin zaizo ba. Gaidashi staff din yayi a girmame, amsawa yayi cikin fara'a yana tambayarshi ya iyali. Fasa shiga office din nashi yayi yanufi na ashraf din ya kwankwasa ya murda handle din yashiga da sallama. Ko dago kai daga typing din dayake beyiba bare yasaka ran zai amsa mashi sallamar, be damu da hakan ba saima qarasowa dayayi cikin office din yaja kujera ya zauna yana kallon yadda yawani hade rai yana sarrafa system din gabanshi. Ganin beda niyyar kulashi yasashi jan tsaki yace "Kaifa dan air ne, ji yadda kawani yi banza dani kamar ba wajenkaba nazo" Dago kai ashraf yayi ya yimashi kallon up & down sannan ya maida kanshi kan abinda yake. Ta6e baki sadeeq yayi yace "Shine naketa kiranka kaqi picking ko?" Shima ta6e bakin yayi batareda ya tankashi ba. "Allah dai ya yayemaka wannan baqar zuciyar taka kona huta wlh, kaikam matarka tabani... wai yama naganka a office yau, kaida yakamata ace kanacan kuna honeymoon da sweetien taka?" Wani mugun kallon yadago ya watsa mashi sannan ya kauda kai Dariya sadeeq yafashe dashi yana cewa "Au na manta ashe an kwace matar, hhhhh wannan shi ake kira ga qoshi ga kwanan yunwa, wai ya kuka qare da ummyn? Kashawo kanta din?" Banza yayi dashi don koyace yayi magana yasan bamai dadi zaiyi ba. "Kaji? Dakaifa nake" Nan ma ko kallonshi beyiba bare ya tanka "Karfa ace kayi surrender ne, lallai ma, to wlh ka zauna kaga zama na rantse, ni i thought ma tun ranar zaka dawo da matarka, ca6! Wlh idan nine idan na yarda intafi tsaye, matar tawa wanda dakyar nasamu bata kufcemin ba azo kuma sake nisantamu salon komai yaqara dagulewa? Ta6!" Kallonshi ashraf dahar mood dinshi ya chanza yayi yanajin zafin abun aranshi sosai yace "Na barmata ita, i've promised bazan qara samunta akan wannan case dinba, nabarmata tayi yadda taga dama daita nikam na haqura" Wani kallon uku saura kwabo sadeeq ke binshi dashi haryakai aya sannan yaja wani dogon tsaki yace "Ban ta6a sanin rashin hankalin naka yakai hakaba sai yau, sannu zuciyatu, ai gwara kayi zuciyar kabarmata din, tunda gaka sarkin masu zuciya, to wlh kayi zuciyar angayama tanada asara ne, kai an da asara, abanza ciwon zuciya zai kamaka, kuma wlh babu ruwana bazanyi jinyar kowaba. Lallai ma, wai na barmata to kabarmata din, abanza ciwo zai kamaka bamuda asara, dama gashi cikin kwanaki biyu harka fara qarmashewa, lokacin da kake ikirarin ummy zata baka ita dakanta kakoma 1, dama yaya lafiyar giwa? Kadawo anbaka itan amma tsoronka take kakoma kifin gpanla, mtcheew so annoying" yafada yana girgiza kai cikeda takaici "To ya kakeson inyi da rayuwata uhm? I begged and begged and begged taqi ta saurareni, ya zanyi?" Ya qarashe zancen kamar zaiyi kuka "Kuma shine akace don you begged and begged and begged taqi sauraronka saikayi giving up? Dama yaya lafiyar giwa? Allah ne kawai ya dubeka yaji qanka badon halinka ba yabaka ita akaro na biyu, maimakon kayi grabbing din opportunity dinka ka gyara kuskurenka kajawota jiki ka dasa sonka azuciyarta ta hanyar wanzar da shakuwa atsakaninku shine zakayi nisa da ita har kana ikirarin ka haqura? Mtcheew amma a gaisheka" yafada yana girgixa kai. Shiru ashraf yayi yana auna magangganun sadeeq don bakomai aciki sai gaskiya. Yasan halin ummy idan ta nace kan abu dakyar take chanza ra'ayi gashi dukda yayi zuciyan abun na maqale aranshi don sosai abin ke damunshi kuma yasan ba qaramin aikin ummy bane tashareshi tayi kamar batasan yana yiba harsai ya jigata sosai "To yanzu meye mafita?" Yafada yana kallon sadeeq. Harara sadeeq ya watsa mashi sannan yaja tsaki yana cewa "Kayan takaici kawai" Shidai bece komaiba don yasan shike nema don haka dole yayi haquri "Ni nazaci wlh tun ranar zaka magance abin amma dayake kai solo6iyo ne kodayake harda wauta irinta yan fari..." "Look yafa isheka, wai yaya don zaka bani shawara zaka tisani gaba kanata debemin albarka tundazu, wlh kashiga hankalinka ina ganin girmanka" inji ashraf yana makamashi mugun kallo. "Au dama yaushe kafara ganin girman nawa? Da kana ganin girman nawa da duk rashin m din dakake shufkamin bazakamin ba" "Naji please let's talk like two matured people, please let's be serious" yafada cikin dan kwantar dakai Tsaki sadeeq yaja yana yamutse fuska irin ana nema wurinshi dinnan sannan agadarance yace "Yanzu abinda zakayi shine ka tattara yanaka yanaka kabi matarka wlh, idan ka zauna zakaga zama ne na rantse, follow her there and pretend ku kadaine agidan, ka nuna bakasan da zaman kowaba gidan, abin nufi duk kulawa da tarairayar dazakayimata kuna ku biyu kayimata acan ba ruwanka dasu, ka cire kunya ka nunawa matarka love agaban koma wanene, am telling you su zasu koma sunajin kunya idan kuma abin ya ishesu bashiri zasu hadoka da matarka su watsoku waje, koya kace?" Ya qarashe zancen yana dagamashi gira daya "Kenan in koma gidan?,but how sure are you ba zata bani ita din?" "Mtcheew kai hamago ne wlh, kai ai zakasa tabaka din kotaqi ko taso, cire kunya zakayi kana abubuwan da dole zasuji kunya da gangan, pretend ku kadai ne agidan, afterall matarkace ai, kazama bita zaizai, duk inda take ka bita, kaita maqalemata kana baje kolin love dinka babu abinda yashamaka kai, idan taga rashin kunyar tayi yawa da kanta zata baka matarka. Ca6 ai anbar sanya yanzu, ni har umma zata riqemin mata tayi kwana uku wajenta? Lallai na rantse idanba aranar idan naga damar kasancewa da matata saina kasance daitaba intafi tsaye, ko dakinta ta 6oyeta saina lalla6a nabita wlh. Ka duba kaga fa, yau 5months kenan da aurenku amma babu abinda kuka tsinana, sai yanzu komai ya warware shine kuma za'a tsiro wani sabon case? Ca6! Kodayake harda laifin ka ai, Allah ma yaqara, tun farko kaine ummul'abaisan faruwar komai, shegen girman kanka yajamaka tun farko kaqi bada kai bori yahau shiyasa ai aketa garaka takoina, dama ai ance idan bakayi sharar massalaci ba zakayi na kasuwa, da..." "Yanxu dai ya isheka, nagode da shawararka, zan duba ingani don haka atashi abarmin office hakanan, thanks for the concern" yafada yana 6allamashi harara. Sakin baki sadeeq yayi yana kallonshi a mammakince sannan yace "Kutt.. hakama zakace bayan kasamu na nemomaka mafita?" Yatsine fuska ashraf yayi yace "Kuma cema akayi amfani da crooked shawarar taka zanyi? Idanma kaga nayi amfani daita to dama can nayi niyyar yin haka tunkafin kafada don haka atashi abarmin office nace, gauro kawai" yafada cikin son qular dashi "Kutt.. amma kau wlh kayi da dan halaq, zaka gane bakada wayau wlh" yafada yana miqewa cikin fushi "Eh, agayas, gauro kawai" yafada yana qyalqyalewa da dariya ganin yadda ya kunnu "Gakanan jibgegen gauro, ai gwara ni dakai wlh tunda ni banida matar ne amma kai gashi kanada matar amma baka tashi a layin gaurayen ba kuma insha allahu ummy bazata baka matarkaba sainan da shekara daya, insha allahu saina rigaka angwancewa" yafada cikin kumfar baki Qara kecewa da dariya ashraf yayi yace "Oho dai, a duk lalacewar goma tafi biyar albarka kuma dai dolene ko a suna ne akirani da mai iyali don wlh nafi qarfin akirani da gauro kuma ko shekaru nawa ummy zata dauka kafin tabani ita bazai ta6a chanza batun narigaka aure ba bare insha allah saina rigaka angwancewa, kai in taqaicemaka da d'ana zamuje daurin aurenka insha allahu, so jeka rungumi transformer" yafada yana dariya sosai kamar ba A.A dinnan ba mai saurin hayaqa. "Allah ya kiyaye wlh, bakinka ya sari danyen kashi, wazai zauna harku gama wannan shirmen naku har kusamu d'a beyi aure ba? Bakada hankali kuma wlh munanan dakai zaka sake zuwamin da matsalarka, zakaga yadda ake ainihin rashin mutunci" yana kaiwa nan yabude kofa yafita ya maidota da qarfi. Dariya ashraf yasake fashewa dashi yana komawa kan kujera yana jujjuyawa, sadeeq is just the best, sadeeq ba qaramin kyauta bane da allah yabashi, bazai iya misalta yadda rayuwa zata kaya batareda shiba, gashi cikin dan qanqanin lokaci yakawomashi mafita yakuma sauya mashi mood daga baqinciki zuwa farinciki. Jujjuyawa yacigaba dayi kan kujerar yana qara tunanin magangganun sadeeq yana ayyana yadda zai gudanar dasu a zahirance...✍ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [9/22, 8:32 PM] +234 909 007 1867: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (ummin fasihu) 092 Haka ya wuni ranar yanata jujjuya magangganun sadeeq, koda suka tashi daga company ko kallon gefen ashraf sadeeq beyiba shi ala dole fushi yake, shikau ashraf ganin hakan yasashi tisashi gaba da tsokana yana mashi dariya, haka yadawo gida feeling so excited yanajin kamar yayi tsinsuwa yaganshi gidan ummy. Bayan yagama komai nashi yayi shirin kwanciya yahau shirya kayanshi cikin wata qatuwar trolley, kaya sosai ya loda don ya quduri aniyar duk rintsi bazai dawo hannu biyu ba, duk dadewar dazaiyi ya shirya idanma takama ayi zaman auren can sai ayi ai ba akansu aka fara ba. Ataqaice dai shine har wajajen 12 yana shirin kaya, dakyar yasamu yagama ya lalla6a ya kwanta cikeda zumudin gobe, jiyake kamar yajawo daren gari ya waye hakanan. *** Washegari as usual qarfe 9 saura ya isa company, kamar yawuce office dinshi saikuma yajuya yanufi office dinshi. Murda handle din yayi yajishi gaam alamun babu kowa ciki. Wani malalacin murmushi yasaki yana wurwura keys dinshi yanufi office dinshi. Saida yayi settling sannan ya zaro phone dinshi ya danna mashi kira ya kara a kunne yawani murtuke kamar yana gabanshi. Ringing taitayi harta katse ba'a dagaba hakan yasashi sakin tsaki yasake danna mashi wani kiran yana ta6e baki wondering ko ina yashiga? Saida kiran yakusan tsinkewa sannan aka daga. "Heelloo?.." yaji anfada cikin muryar barci Dan waro idanu sadeeq yayi sannan ya kalli agogon bango yaga 9 saura minti 2 hakan yasashi cewa "Inyee? Wato barcima kake haryanzu, don ubanka qarfe nawa?" Cikin muryar barcin yasake cewa "Yes... am...coming" "Coming din gidanku? Mtcheew wlh danazo naga baka zoba i thought ka dauki shawarata ce yanzu haka kana gidan ummy, amma kai kasani ai, scallywag kawai" ya katse wayar yanajan tsaki. Wani mugun tumble ashraf yayi daga kan gado sai jinshi yayi qasa kasancewar dama baki bakin gadon yake. Wawware idanu yashigayi don shapp ya mance dawanu zuwa gidan ummy, wai tayama wani barcin ya daukeshi, abu na qarshe dazai iya tunawa shine ya zauna gefen gado ya dan kishingida da kan gado yana lazimi yana jiran garin yadanyi haske yatashi yafara shiri. Kai amma a gaisheshi. Saurin miqewa yayi tsaye yana cire brown jallabiyar jikinshi. Agaggauce ya tu6e ya rage saura boxer kawai ajikinshi ya rataya towel a wuya yashige bathroom. Saida yakusan awa daya sannan yafito don yau wanka na musanmman ne😉 ba irin na kullum bane. Koda yafito direct yawuce gaban mirror dinshi yaja kujera ya zauna kamar irin mace ta zauna zatayi kwalliya. Sosai ya 6ata lokaci wajen shafe shafenshi don yau komai saida aka qara akan nada, sumar kanshi banda kyalli babu abinda take, dan siririn sajenshi sun kwanta luff sai shining suke, roll on ma saida ya murza kala uku duk masu shegen sanyin dadi. Saida yagama kwalailaitar sannan yawuce gaban closet dinshi yabude yaciro kayan da dama tun jiya aka riga aka waresu akan su za'asa yau. Cikin dan qanqanin lokaci ya gama shirin. Wow! As-in WOW! duk inda haduwa takai to ya kureta, sosai ya hade cikin qannanun kaya wando fari mai layi biyu a gefe gefe kalar royal blue, rigar kuma kalar royal blue mai hula daya saketa abaya, a bayan rigar akwai logo da akayi printing kalar fari mai taken *MONARCH* kaffafuwanshi sanye da fararen shoes hannunshi na dama daureda agogon kirar Apple fari sai wani qwamemmen shade daya qwamama fuska shima fari amma glass din baqine wulik don bakama hango kwayar idanunshi. Turarruka saida yafeshe kusan biyar sannan ya gamsu, wayoyinshi ya kwasa ya saka daya a aljihu ya riqe daya sannan ya sauko qaton trolley din jiya ya fiddo qarfen yashiga ja yanufi kofar yana duba agogon hannu shi. Ganin har 12 ta gota yasashi qara azama ya fita daga dakin ya kulle sannan ya sauka qasa janye da trolley din. Saida yakashe komai na wuta agidan sannan finally yafita ya kulle kifar yanufi parking space yana wani tafiyar taqama wanda kallo daya zakamashi kasan akwai abinda ya taka. Haka ya qarasa wajen wata baqar mota wulik ya danna key tun kafin ya qarasa yana wani yamutse fuska. Yana qarasawa ya bude booth ya kinkimi trolley din yasaka aciki sannan yamaida yarufe ya zagaya mazaunin driver ya bude ya shiga yana kada kai. Maido kofar yayi ya rufe sannan yajawo seat belt ya daura yayi connecting din wayarshi da mp3 din motar yasanya waqar jaruma ta hamisu breaker yawani qure volume sannan ya tada motar ya figeta gwanin burgewa ya harba kwalta. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Parking yayi a parking space yana sauke ajiyar zuciya. Bin gidan yake da kallo yana ayyana abubuwa da dama a ranshi. Kashe kidan motar yayi ya bude kofar ya sauko. Sake bun gidan yayi da kallo tacikin google din idanunshi yana qarasawa bayan booth. Budewa yayi ya ciro trolley dinshi sannan ya maida yarufe ya kulle motar sannan yafara jan trolley din yanufi cikin gidan yana jindadin yadda gidan is so silent and peacefull. Danna doorbell yayi sau biyu, jin shiru yasashi murda kofar yabude yashiga da sallama. Kamar yadda yayi tsammani babu kowa a falon sai t.vn daketa 6a66atunta ita kadai, dakin sai zuba qamshi yake mai sanyin dadi. Qarasowa falon yayi yana jan trolley din daya fara gajiyar dashi. Ajiyeshi yayi a gefe sannan yafada kan daya daga cikin kujerun falon yana lumshe idanu. Yadauki kusan mintina uku ahakan batareda wani ya sauko ba hakan yasashi miqewa zaune ya zare shade din idanunshi ya maqala agaban riga yana kallon sama. Tashi yayi ganin babu mai niyyar saukowa harzai nufi sama yaji kamar motsi a kitchen. Kamar yawuce saikuma yaji zuciyarshi na kwadaitamashi zuwa kitchen din hakan yasashi juya akalar tafiyar tashi zuwa kitchen din hannayenshi zube a aljihu. Cak ya tsaya abakin kofar a dalilin hango wata baby doll tsaye tabama kofar baya tana girki. Kallo yafara binta dashi daga kafarta zuwa kai. Sanye take da straight skirt baqi mai tsaga a baya wanda ya bayyana straight sexy fair legs dinta wanda yake very smooth dasu, skirt din roba ne don haka ya kwanta ajikinta sosai wanda hakan ya bayyana perking and arousing hips dinta sai wata jar half shoulder blouse wanda itama ta kwanta mata ajiki sosai sai kanta dake sanye da hula wanda dga gaban goshinta zuwa farko farkon kitsonta abude suke kasancewar ta nannade jelar kitsonta tayi doughnut dashi hakan yasa hular takasa rufe kan sai tayi kamar tayi acuci. Sai baqin headphones dake bisa kanta wanda kusan hakan ajininta yake muddin tana aiki ko wani abu to saita dode da headphones hakan kesa taga saurin aikin kuma bazatayi saurin gajiya ba. Binta da kallo yafarayi daga kafaffunta dake sanye da takalmin soso baqaqe wanda suka matuqar qawata yan qannanun shaped feets dinta zuwa dogayen kaffafunta sake glowing zuwa round pecking shaped hips dinta zuwa tiny waist dinta zuwa straight bayanta zuwa straight wuyanta zuwa kanta dake daukeda headphones. Nan take yaji wata iriyar kasala ta saukarmashi yakoma ya jingina da kofa yana lumshe idanunshi yana sake budesu akanta. She's just perfect! Gaskiya dolene ya godema Allah yakuma cigaba da godemashi daya mallaka mashi ita a matsayin matarshi halak malak, gaskiya da ya rasata da yayi babban rashi a rayuwarshi. Cigaba yayi da binta da ido duk motsin dazatayi, yanajin wani abu na tasomashi sanadin yadda take dan motsawa wanda kesa hips dinta moving in a sexy way. Saudart kau batasan wainar da ake toyawa ba, she's super happy yau ummy tabari tashiga kitchen, tun washegarin ranar da tadawo gidan take nacin zata shiga kitchen ummy na hanawa acewarta tayi zamanta ta huta batason ta huta, itakau aduniya babu abinda ke burgeta kuma kebata nishadi idan tanayi kamar girki shiyasa kullum saita tisata gaba kamar zatayi kuka akan tabari tashiga, to yau dai allah ya daurata kanta tasamu ta yarda amma da sharadin baby zata tayata, dagudu ta amince don she missed cooking dan kwana biyun nan dabatayi ba. Koda taje tasamu baby ta tadda barci take hakan yasa ta lalla6a tafito don dama tafison tayi ita kadai don baby bawani abun kirki zata iya tayata dashi ba inbanda cikata da surutun dazatayi. Ta dan dauki lokaci tana tunanin me yakamata ta dafa musu sannan ta yanke shawaran yimusu fried rice da pepper chicken sai tayi baking din cup cakes sai ta hada banana smoothie. Saboda aikin yayimata dadi yasata dodewa da headphones tana sauraron cool music ta hau aiki. Tun dazu take jinta somehow tanajin kamar ana kallonta ga wani sabon qamshi wanda bazata iya cewa na menene ba datakeji amma dayake hankalinta be wajen bata kawo komai aranta ba, ita burinta kafin ummy tasauko tagama komai don saida ummy ta kashemata warning kan cewa ta girka light simple food wai karta wahalar dakanta kuma tasan tana saukowa taga abinda take tofa saita sata bari don haka hankalinta gabadaya naga abinda take tana gudanar da aikinta cikin qwarewa da kuzari. Ahankali tahau bin waqar datake ji acikin headphones dinta na mawaqiyar nan *simi* mai taken *chemistry* cikin melodious muryarta "But i don't even know if am your spec oh I don't even know if i'll take you grantful ehh You don't even know my widest dream Maybe it will just be chemistry But i knoww ooo Kind of maybe you really do like me Maybe me and you we can try to Do this love something Maybe there's something there. And i know ohhh Kind of maybe you really do like me Maybe i can be your baby We should start fronting Maybe there's something else" Shidewa ne kawai ashraf beyiba alokacin Sosai zuciyarshi ta kumburo don shauki, jiyake kamar ya ruga dagudu ya chakumota yashiga bata the hot kiss ever. Ahankali yake sauke numfashi yana kallonta yanajin kanshi na qara girma don shauqi. Sosai waqar tayi affecting dinshi don jiyake kamar yana narkewa ne ahankali. Ahankali ya dago daga jikin kofar dayake jingine daita yanufota ahankali yana kallonta yana sauraron yadda take bin waqar. Zuba bananas din data yanyanka tayi a blender ta zuba cubes din qanqara sai madarar ruwa datasa bada yawaba ta rufe da marfin blender din tana waqarta cikeda nishadi tayi plugging din waqar blender din jikin socket ta kunna tasa hannu ta danne murfin don kar ya bude. Jinta take very uncomfortable jikinta harwani tsima yake hakan yasa tadan saci kallon bayanta ahankali. Ganin kamar inuwar mutum abayanta yasata saurin sakin murfin blender din atsorace ta juyo. Ganin mutum daff daita yasata ware manyan idanunta ta bude baki don sakin ihu tana ja da baya Saurin janyota yayi yasa hannu yayi saurin toshemata baki don kar ihunta yafito. Jikinta ne ya dauki rawa nan take tanajin kamar ta sume don firgici amma suman yaqi zuwa, ashe idan ma aka suma to firgicin bekai firgici bane. Jiki na rawa take qoqarin kwacewa daga riqon dayayimata, idanunta sun rufe don ko ganeshi batayi ba ma saboda tsabar yadda ta tsorata. Ganin haka yasashi qara riqota batareda ya saki bakinba yace "Shiiish it's me, nine... calm down... look at me" Ganin kamar taki nutsuwa yasashi sake cewa "Nine.. A.A.. mijinki, open your eyes" yafada wannan karon cikin dan daga murya hakan yasa ta shiga bin fuskarshi da kallo kamar meson gano eh shi din ne? Kada mata kai yayi cikin tabbatarwa yace "Eh nine... am sorry i scared you, bansan zaki tsorata bane" Ahankali take sauke numfashi tana kallonshi nutsuwarta na dawomata ahankali. Shima kallonta yake batareda ya saketa ba ko ya budemata baki ba yana jin yadda zuciyarta haryanzu ke bugawa abnormally. Haka sukaita kallon juna har ta ida dawowa nutsuwarta, mitsiniya tafarayi alamun ya saketa. "No please don't, it's me... nine" yafada don shi duk atunaninshi har lokacin firgicin ne alhalin ba haka bane kawai sotake yasaketa saboda yadda takeji. Kada mashi kai tayi alamun eh ta ganeshi. "Nine..Ashraf.. A.A?" Yafada yana kallonta sosai Janye idanunta tayi jin yadda nashi suka haskemata nata ta kada kai ahankali "Am sorry.. na tsorataki, i don't mean to" yasake fada yana kallonta Batareda ta kalleshi ba tasake kadamashi kai Ganin yacigaba da kallonta bataresa niyyar sakintaba tasata qara yin motsi uncomfortably "Ok...ok zan sakeki amma promise bazakiyi ihu ba, pleease" yaja please din a shagwa6e. Saurin sauke idanunta tayi jin yadda taji shagwa6ar tashi a cikin zuciyarta ta kada kai ahankali "Promise?" Yafada yana kallonta Nanma kada mashi kai tayi idanunta aqasa. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya saketa tareda janye hannunshi daga bakinta. Wani nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tana hadiye miyaun dasuka tararmata abaki. Dan jada baya tayi don matsawa daga kusadashi. Jin bayan kafanta iska yadan bugeshi yasata dan waro idanu don shaff ita tama manta da kalar shigar dake jikinta. Saurin sake jada baya tayi cikin tsananin kunya da nauyi tanajin kamar ta nitse ta huta. Shikau bema luraba saima wucewa dayayi wajen blender da haryanzu tanayi amma duk kusan rabi ya watse don tuni murfin yayi tsalle yayi nashi wajen. Kashe blender yayi sannan yajuyo ya kalleta inda take tsaye sai faman mitsiniya take cikin rashin sanin abunyi jitake kamar ta arta dagudu tafice daga kitchen din. Hade rai yadanyi yana kallonta yace "What is this?" Jin yanayin dayayi maganar yasata dan dagowa ta kalleshi taga yawani hada rai yana nuna abubuwan datakeyi na girki. "Dama ummy ta riqemin mata ne don tasata aikin bauta?" Yafada yana huro hanci Tsayawa tayi tana kallonshi kawai batareda tace komaiba. Bubbude pots din wajen yake yana dudduba abubuwan datakeyi, binshi da ido kawai take tana kallon ikon allah. "Ca6! Lallaima, so dama dalilin kwaceki datayi kenan? Tazo taita saki aikin bauta? Salan kiyi fading ki tottoye? No wonder, wato ga yar aiki tasamu a bulus ko? Harda wani saki girki fin daya wato ga cooking engine" yafada yana rurrufe tukannen Itadai kallon ikon allah kawai take tama rasa abin cewa. Kallonta yayi yana qara tamke fuska yadawo sak A.A dinshi yace "Yanzu fisabillilah hakan ya dace? Kema why not ki kirani ki fadamin? Allah kadai yasan abubuwan datake saki kinayi, amtsayinki na mrs A.A, mrs A.A a kitchen? Ina maid din gidan nan tukunna? Ba aikinta bane? Uban me take zata barmin ke a kitchen? Ina wannan picking stick din itama? Duk sun nade sun barminke anan kina wahala don basusan ciwonki ba ko?" Itadai sakin baki tayi kawai tana kallonshi don tama rasa me zatace mashi ganin yadda ya haqiqance yanata fada. "To wlh baxai yiwuba, muje yau sainaji dalilin mayarmin mata baiwa agidannan.. muje" yafada yana kamo tsintsiyar hannunta yayi gaba Ganin dagaske yake yasata saurin kwacewa tana dan komawa baya. Juyowa yayi ya kalleta yace "Come mana, babu abinda zasu miki, ba ganiba?" Janye idanunta tayi daga kanshi ta kauda kai tana turo baki Dawowa yayi kusada ita yace "Menene? Are you scared?" Dan kallonshi tayi taqara janye idanunta sannan kamar mai ciwon baki tace "Ni babu wanda yayi forcing dina, it's my choice, ni nace zanyi" taqarashe zancen tana kauda kai tana murguda baki "then why? Sokike ki qone?" Yafada yana kallonta Sake kallonshi tayi sannan ta kauda kai tana sake turo baki, duk ya 6atamata aikinta, mema yakawoshi gidan a daidai wannab lokacin. Wucewa tayi wajen smoothie dinta da duk rabi sun zube blender tayi faca faca tana kallonshi kamar zatayi kuka. "Kizo mutafi, let someone finish it, ina baby ma tukunna" Banza tayi dashi tafara qoqarin juye kingin smoothie din Kamar daga sama taji muryar ummy a falo tana cewa "Daughter! Daughter!! Wai haryanzu girkin ne?" Ware idanu tayi tayi saurin juyowa. "Yauwa gatanan tama sauko, bari inje inji dalilin sa matata aiki" inji ashraf yana nufar kofa. Batasan ya akayiba sai gani tayi tasha gabanshi gabanta na mugun faduwa, cak ya tsaya yana kallonta kawai Girgiza mashi kai tashigayi tana waiwayen kofa. "Please ka rufamini asiri karta ganka anan, na bani" tafada tana zare idanunta a tsorace Tsayawa yayi yana kallonta kawai ganin yadda tawani tare hanya tana leqen baya "Wannan trolleyn fa? Daughter! Daughter!!" Suka sakejin muryarta tana nufo kitchen din. Qara ware manyan eyes dinta tayi tayi saurin kamo hannunshi batareda tasan tayiba tana cewa "Innalillahi, wayyo banso tazo taganka, please hide" Tafada tana riqeshi sosai. Wutar ashraf ne ta dauke diff jin yadda ta kama mashi hannu sosai kamar her life depend on it. Bude baki yayi zaiyi magana tayi saurin saka dayan hannunta ta dode mashi baki tana girgixa mashi kai a mugun tsorave tana jin takun ummy daff da kofa...✍ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [10/11, 4:50 PM] +234 803 827 0792: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (ummin fasihu) kumun hkuri najina kwan biyu da bakuba zashinan hadda bashi nabiya🤧 093& 94& 95 A.A dogon nunfashi ya sauki tare da kallan hannunta da ke kan bakinsa san nan ya kalli fuskar ta kafin yay niyar maga yaga ta kara hade jikinta da nasa dasana diyar tafiyar ummma dataji tana yowa wanja mutuwar tsayee yayayi da kar yake iya jan yo nunfashin sa dake bara zanar daukewakdnmkllnbbbbnkkkkjjnjjikkkmjvhllllllbfjkllll Bayan yagama komai nashi yayi shirin kwanciya yahau shirya kayanshi cikin wata qatuwar trolley, kaya sosai ya loda don ya quduri aniyar duk rintsi bazai dawo hannu biyu ba, duk dadewar dazaiyi ya shirya idanma takama ayi zaman auren can sai ayi ai ba akansu aka fara ba. Ataqaice dai shine har wajajen 12 yana shirin kaya, dakyar yasamu yagama ya lalla6a ya kwanta cikeda zumudin gobe, jiyake kamar yajawo daren gari ya waye hakanan. *** Washegari as usual qarfe 9 saura ya isa company, kamar yawuce office dinshi saikuma yajuya yanufi office dinshi. Murda handle din yayi yajishi gaam alamun babu kowa ciki. Wani malalacin murmushi yasaki yana wurwura keys dinshi yanufi office dinshi. Saida yayi settling sannan ya zaro phone dinshi ya danna mashi kira ya kara a kunne yawani murtuke kamar yana gabanshi. Ringing taitayi harta katse ba'a dagaba hakan yasashi sakin tsaki yasake danna mashi wani kiran yana ta6e baki wondering ko ina yashiga? Saida kiran yakusan tsinkewa sannan aka daga. "Heelloo?.." yaji anfada cikin muryar barci Dan waro idanu sadeeq yayi sannan ya kalli agogon bango yaga 9 saura minti 2 hakan yasashi cewa "Inyee? Wato barcima kake haryanzu, don ubanka qarfe nawa?" Cikin muryar barcin yasake cewa "Yes... am...coming" "Coming din gidanku? Mtcheew wlh danazo naga baka zoba i thought ka dauki shawarata ce yanzu haka kana gidan ummy, amma kai kasani ai, scallywag kawai" ya katse wayar yanajan tsaki. Wani mugun tumble ashraf yayi daga kan gado sai jinshi yayi qasa kasancewar dama baki bakin gadon yake. Wawware idanu yashigayi don shapp ya mance dawanu zuwa gidan ummy, wai tayama wani barcin ya daukeshi, abu na qarshe dazai iya tunawa shine ya zauna gefen gado ya dan kishingida da kan gado yana lazimi yana jiran garin yadanyi haske yatashi yafara shiri. Kai amma a gaisheshi. Saurin miqewa yayi tsaye yana cire brown jallabiyar jikinshi. Agaggauce ya tu6e ya rage saura boxer kawai ajikinshi ya rataya towel a wuya yashige bathroom. Saida yakusan awa daya sannan yafito don yau wanka na musanmman ne😉 ba irin na kullum bane. Koda yafito direct yawuce gaban mirror dinshi yaja kujera ya zauna kamar irin mace ta zauna zatayi kwalliya. Sosai ya 6ata lokaci wajen shafe shafenshi don yau komai saida aka qara akan nada, sumar kanshi banda kyalli babu abinda take, dan siririn sajenshi sun kwanta luff sai shining suke, roll on ma saida ya murza kala uku duk masu shegen sanyin dadi. Saida yagama kwalailaitar sannan yawuce gaban closet dinshi yabude yaciro kayan da dama tun jiya aka riga aka waresu akan su za'asa yau. Cikin dan qanqanin lokaci ya gama shirin. Wow! As-in WOW! duk inda haduwa takai to ya kureta, sosai ya hade cikin qannanun kaya wando fari mai layi biyu a gefe gefe kalar royal blue, rigar kuma kalar royal blue mai hula daya saketa abaya, a bayan rigar akwai logo da akayi printing kalar fari mai taken *MONARCH* kaffafuwanshi sanye da fararen shoes hannunshi na dama daureda agogon kirar Apple fari sai wani qwamemmen shade daya qwamama fuska shima fari amma glass din baqine wulik don bakama hango kwayar idanunshi. Turarruka saida yafeshe kusan biyar sannan ya gamsu, wayoyinshi ya kwasa ya saka daya a aljihu ya riqe daya sannan ya sauko qaton trolley din jiya ya fiddo qarfen yashiga ja yanufi kofar yana duba agogon hannu shi. Ganin har 12 ta gota yasashi qara azama ya fita daga dakin ya kulle sannan ya sauka qasa janye da trolley din. Saida yakashe komai na wuta agidan sannan finally yafita ya kulle kifar yanufi parking space yana wani tafiyar taqama wanda kallo daya zakamashi kasan akwai abinda ya taka. Haka ya qarasa wajen wata baqar mota wulik ya danna key tun kafin ya qarasa yana wani yamutse fuska. Yana qarasawa ya bude booth ya kinkimi trolley din yasaka aciki sannan yamaida yarufe ya zagaya mazaunin driver ya bude ya shiga yana kada kai. Maido kofar yayi ya rufe sannan yajawo seat belt ya daura yayi connecting din wayarshi da mp3 din motar yasanya waqar jaruma ta hamisu breaker yawani qure volume sannan ya tada motar ya figeta gwanin burgewa ya harba kwalta. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Parking yayi a parking space yana sauke ajiyar zuciya. Bin gidan yake da kallo yana ayyana abubuwa da dama a ranshi. Kashe kidan motar yayi ya bude kofar ya sauko. Sake bun gidan yayi da kallo tacikin google din idanunshi yana qarasawa bayan booth. Budewa yayi ya ciro trolley dinshi sannan ya maida yarufe ya kulle motar sannan yafara jan trolley din yanufi cikin gidan yana jindadin yadda gidan is so silent and peacefull. Danna doorbell yayi sau biyu, jin shiru yasashi murda kofar yabude yashiga da sallama. Kamar yadda yayi tsammani babu kowa a falon sai t.vn daketa 6a66atunta ita kadai, dakin sai zuba qamshi yake mai sanyin dadi. Qarasowa falon yayi yana jan trolley din daya fara gajiyar dashi. Ajiyeshi yayi a gefe sannan yafada kan daya daga cikin kujerun falon yana lumshe idanu. Yadauki kusan mintina uku ahakan batareda wani ya sauko ba hakan yasashi miqewa zaune ya zare shade din idanunshi ya maqala agaban riga yana kallon sama. Tashi yayi ganin babu mai niyyar saukowa harzai nufi sama yaji kamar motsi a kitchen. Kamar yawuce saikuma yaji zuciyarshi na kwadaitamashi zuwa kitchen din hakan yasashi juya akalar tafiyar tashi zuwa kitchen din hannayenshi zube a aljihu. Cak ya tsaya abakin kofar a dalilin hango wata baby doll tsaye tabama kofar baya tana girki. Kallo yafara binta dashi daga kafarta zuwa kai. Sanye take da straight skirt baqi mai tsaga a baya wanda ya bayyana straight sexy fair legs dinta wanda yake very smooth dasu, skirt din roba ne don haka ya kwanta ajikinta sosai wanda hakan ya bayyana perking and arousing hips dinta sai wata jar half shoulder blouse wanda itama ta kwanta mata ajiki sosai sai kanta dake sanye da hula wanda dga gaban goshinta zuwa farko farkon kitsonta abude suke kasancewar ta nannade jelar kitsonta tayi doughnut dashi hakan yasa hular takasa rufe kan sai tayi kamar tayi acuci. Sai baqin headphones dake bisa kanta wanda kusan hakan ajininta yake muddin tana aiki ko wani abu to saita dode da headphones hakan kesa taga saurin aikin kuma bazatayi saurin gajiya ba. Binta da kallo yafarayi daga kafaffunta dake sanye da takalmin soso baqaqe wanda suka matuqar qawata yan qannanun shaped feets dinta zuwa dogayen kaffafunta sake glowing zuwa round pecking shaped hips dinta zuwa tiny waist dinta zuwa straight bayanta zuwa straight wuyanta zuwa kanta dake daukeda headphones. Nan take yaji wata iriyar kasala ta saukarmashi yakoma ya jingina da kofa yana lumshe idanunshi yana sake budesu akanta. She's just perfect! Gaskiya dolene ya godema Allah yakuma cigaba da godemashi daya mallaka mashi ita a matsayin matarshi halak malak, gaskiya da ya rasata da yayi babban rashi a rayuwarshi. Cigaba yayi da binta da ido duk motsin dazatayi, yanajin wani abu na tasomashi sanadin yadda take dan motsawa wanda kesa hips dinta moving in a sexy way. Saudart kau batasan wainar da ake toyawa ba, she's super happy yau ummy tabari tashiga kitchen, tun washegarin ranar da tadawo gidan take nacin zata shiga kitchen ummy na hanawa acewarta tayi zamanta ta huta batason ta huta, itakau aduniya babu abinda ke burgeta kuma kebata nishadi idan tanayi kamar girki shiyasa kullum saita tisata gaba kamar zatayi kuka akan tabari tashiga, to yau dai allah ya daurata kanta tasamu ta yarda amma da sharadin baby zata tayata, dagudu ta amince don she missed cooking dan kwana biyun nan dabatayi ba. Koda taje tasamu baby ta tadda barci take hakan yasa ta lalla6a tafito don dama tafison tayi ita kadai don baby bawani abun kirki zata iya tayata dashi ba inbanda cikata da surutun dazatayi. Ta dan dauki lokaci tana tunanin me yakamata ta dafa musu sannan ta yanke shawaran yimusu fried rice da pepper chicken sai tayi baking din cup cakes sai ta hada banana smoothie. Saboda aikin yayimata dadi yasata dodewa da headphones tana sauraron cool music ta hau aiki. Tun dazu take jinta somehow tanajin kamar ana kallonta ga wani sabon qamshi wanda bazata iya cewa na menene ba datakeji amma dayake hankalinta be wajen bata kawo komai aranta ba, ita burinta kafin ummy tasauko tagama komai don saida ummy ta kashemata warning kan cewa ta girka light simple food wai karta wahalar dakanta kuma tasan tana saukowa taga abinda take tofa saita sata bari don haka hankalinta gabadaya naga abinda take tana gudanar da aikinta cikin qwarewa da kuzari. Ahankali tahau bin waqar datake ji acikin headphones dinta na mawaqiyar nan *simi* mai taken *chemistry* cikin melodious muryarta "But i don't even know if am your spec oh I don't even know if i'll take you grantful ehh You don't even know my widest dream Maybe it will just be chemistry But i knoww ooo Kind of maybe you really do like me Maybe me and you we can try to Do this love something Maybe there's something there. And i know ohhh Kind of maybe you really do like me Maybe i can be your baby We should start fronting Maybe there's something else" Shidewa ne kawai ashraf beyiba alokacin Sosai zuciyarshi ta kumburo don shauki, jiyake kamar ya ruga dagudu ya chakumota yashiga bata the hot kiss ever. Ahankali yake sauke numfashi yana kallonta yanajin kanshi na qara girma don shauqi. Sosai waqar tayi affecting dinshi don jiyake kamar yana narkewa ne ahankali. Ahankali ya dago daga jikin kofar dayake jingine daita yanufota ahankali yana kallonta yana sauraron yadda take bin waqar. Zuba bananas din data yanyanka tayi a blender ta zuba cubes din qanqara sai madarar ruwa datasa bada yawaba ta rufe da marfin blender din tana waqarta cikeda nishadi tayi plugging din waqar blender din jikin socket ta kunna tasa hannu ta danne murfin don kar ya bude. Jinta take very uncomfortable jikinta harwani tsima yake hakan yasa tadan saci kallon bayanta ahankali. Ganin kamar inuwar mutum abayanta yasata saurin sakin murfin blender din atsorace ta juyo. Ganin mutum daff daita yasata ware manyan idanunta ta bude baki don sakin ihu tana ja da baya Saurin janyota yayi yasa hannu yayi saurin toshemata baki don kar ihunta yafito. Jikinta ne ya dauki rawa nan take tanajin kamar ta sume don firgici amma suman yaqi zuwa, ashe idan ma aka suma to firgicin bekai firgici bane. Jiki na rawa take qoqarin kwacewa daga riqon dayayimata, idanunta sun rufe don ko ganeshi batayi ba ma saboda tsabar yadda ta tsorata. Ganin haka yasashi qara riqota batareda ya saki bakinba yace "Shiiish it's me, nine... calm down... look at me" Ganin kamar taki nutsuwa yasashi sake cewa "Nine.. A.A.. mijinki, open your eyes" yafada wannan karon cikin dan daga murya hakan yasa ta shiga bin fuskarshi da kallo kamar meson gano eh shi din ne? Kada mata kai yayi cikin tabbatarwa yace "Eh nine... am sorry i scared you, bansan zaki tsorata bane" Ahankali take sauke numfashi tana kallonshi nutsuwarta na dawomata ahankali. Shima kallonta yake batareda ya saketa ba ko ya budemata baki ba yana jin yadda zuciyarta haryanzu ke bugawa abnormally. Haka sukaita kallon juna har ta ida dawowa nutsuwarta, mitsiniya tafarayi alamun ya saketa. "No please don't, it's me... nine" yafada don shi duk atunaninshi har lokacin firgicin ne alhalin ba haka bane kawai sotake yasaketa saboda yadda takeji. Kada mashi kai tayi alamun eh ta ganeshi. "Nine..Ashraf.. A.A?" Yafada yana kallonta sosai Janye idanunta tayi jin yadda nashi suka haskemata nata ta kada kai ahankali "Am sorry.. na tsorataki, i don't mean to" yasake fada yana kallonta Batareda ta kalleshi ba tasake kadamashi kai Ganin yacigaba da kallonta bataresa niyyar sakintaba tasata qara yin motsi uncomfortably "Ok...ok zan sakeki amma promise bazakiyi ihu ba, pleease" yaja please din a shagwa6e. Saurin sauke idanunta tayi jin yadda taji shagwa6ar tashi a cikin zuciyarta ta kada kai ahankali "Promise?" Yafada yana kallonta Nanma kada mashi kai tayi idanunta aqasa. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya saketa tareda janye hannunshi daga bakinta. Wani nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tana hadiye miyaun dasuka tararmata abaki. Dan jada baya tayi don matsawa daga kusadashi. Jin bayan kafanta iska yadan bugeshi yasata dan waro idanu don shaff ita tama manta da kalar shigar dake jikinta. Saurin sake jada baya tayi cikin tsananin kunya da nauyi tanajin kamar ta nitse ta huta. Shikau bema luraba saima wucewa dayayi wajen blender da haryanzu tanayi amma duk kusan rabi ya watse don tuni murfin yayi tsalle yayi nashi wajen. Kashe blender yayi sannan yajuyo ya kalleta inda take tsaye sai faman mitsiniya take cikin rashin sanin abunyi jitake kamar ta arta dagudu tafice daga kitchen din. Hade rai yadanyi yana kallonta yace "What is this?" Jin yanayin dayayi maganar yasata dan dagowa ta kalleshi taga yawani hada rai yana nuna abubuwan datakeyi na girki. "Dama ummy ta riqemin mata ne don tasata aikin bauta?" Yafada yana huro hanci Tsayawa tayi tana kallonshi kawai batareda tace komaiba. Bubbude pots din wajen yake yana dudduba abubuwan datakeyi, binshi da ido kawai take tana kallon ikon allah. "Ca6! Lallaima, so dama dalilin kwaceki datayi kenan? Tazo taita saki aikin bauta? Salan kiyi fading ki tottoye? No wonder, wato ga yar aiki tasamu a bulus ko? Harda wani saki girki fin daya wato ga cooking engine" yafada yana rurrufe tukannen Itadai kallon ikon allah kawai take tama rasa abin cewa. Kallonta yayi yana qara tamke fuska yadawo sak A.A dinshi yace "Yanzu fisabillilah hakan ya dace? Kema why not ki kirani ki fadamin? Allah kadai yasan abubuwan datake saki kinayi, amtsayinki na mrs A.A, mrs A.A a kitchen? Ina maid din gidan nan tukunna? Ba aikinta bane? Uban me take zata barmin ke a kitchen? Ina wannan picking stick din itama? Duk sun nade sun barminke anan kina wahala don basusan ciwonki ba ko?" Itadai sakin baki tayi kawai tana kallonshi don tama rasa me zatace mashi ganin yadda ya haqiqance yanata fada. "To wlh baxai yiwuba, muje yau sainaji dalilin mayarmin mata baiwa agidannan.. muje" yafada yana kamo tsintsiyar hannunta yayi gaba Ganin dagaske yake yasata saurin kwacewa tana dan komawa baya. Juyowa yayi ya kalleta yace "Come mana, babu abinda zasu miki, ba ganiba?" Janye idanunta tayi daga kanshi ta kauda kai tana turo baki Dawowa yayi kusada ita yace "Menene? Are you scared?" Dan kallonshi tayi taqara janye idanunta sannan kamar mai ciwon baki tace "Ni babu wanda yayi forcing dina, it's my choice, ni nace zanyi" taqarashe zancen tana kauda kai tana murguda baki "then why? Sokike ki qone?" Yafada yana kallonta Sake kallonshi tayi sannan ta kauda kai tana sake turo baki, duk ya 6atamata aikinta, mema yakawoshi gidan a daidai wannab lokacin. Wucewa tayi wajen smoothie dinta da duk rabi sun zube blender tayi faca faca tana kallonshi kamar zatayi kuka. "Kizo mutafi, let someone finish it, ina baby ma tukunna" Banza tayi dashi tafara qoqarin juye kingin smoothie din Kamar daga sama taji muryar ummy a falo tana cewa "Daughter! Daughter!! Wai haryanzu girkin ne?" Ware idanu tayi tayi saurin juyowa. "Yauwa gatanan tama sauko, bari inje inji dalilin sa matata aiki" inji ashraf yana nufar kofa. Batasan ya akayiba sai gani tayi tasha gabanshi gabanta na mugun faduwa, cak ya tsaya yana kallonta kawai Girgiza mashi kai tashigayi tana waiwayen kofa. "Please ka rufamini asiri karta ganka anan, na bani" tafada tana zare idanunta a tsorace Tsayawa yayi yana kallonta kawai ganin yadda tawani tare hanya tana leqen baya "Wannan trolleyn fa? Daughter! Daughter!!" Suka sakejin muryarta tana nufo kitchen din. Qara ware manyan eyes dinta tayi tayi saurin kamo hannunshi batareda tasan tayiba tana cewa "Innalillahi, wayyo banso tazo taganka, please hide" Tafada tana riqeshi sosai. Wutar ashraf ne ta dauke diff jin yadda ta kama mashi hannu sosai kamar her life depend on it. Bude baki yayi zaiyi magana tayi saurin saka dayan hannunta ta dode mashi baki tana girgixa mashi kai a mugun tsorave tana jin takun ummy daff da kofa...✍ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Alhamdullilah am back after almost two Months of vacations, fatan duk nasameku lfy, thank you all for your concern, wani sa'in tsoronma hawa whatsapp nake saboda jaje, amma that's all signs of love you guys got for me, nagode da qauna, Allah ya dorar da zumuncinmu har a aljannatul firddaus (Amin) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 093 Bude baki yayi zaiyi magana tayi saurin saka dayan hannunta ta dode mashi baki tana girgiza mashi kai a mugun tsorace tana jin takun ummy daff da kofa. Ganin yadda take a tsorace don hannunta dake a bakinshi har rawa rawa yake yasashi janye hannun yace "Look, I'll hide but on one condition" Saurin kada mashi kai tayi idanunta na kawo ruwa, idan ummy ta taddashi anan Ai ta banu, Ina zata sa kanta don kunya? "Zakimin coffee anjima kikawo apartment dina, promise?" Yafada yana dago qaramin yatsar hannunshi alamun su qula "Yes, promise... Please go" tafada tana turashi a kidime. Wuff kamar iska haka ya ruga ya la6e a bayan kofar kitchen din yayinda saudart tayi saurin juyawa tana tatta6a abinda ke kan wuta batareda tasan abinda takeyiba. "Daughter?" Inji ummy data shigo kitchen din Saurin juyowa tayi tana washe baki cikin yaqe tana fadin "Na'am ummy" yayinda take yawo da idanunta cikin kitchen din a fake tana son gano inda ya 6uya. Ganin shi bayan kofa yana dagamata hannu yasa gabanta faduwa tayi saurin janye idanunta ta maida kan ummy dake bubbude pots din "What?" Inji ummy ganin abinda take girkawa. Qara Satan kallon kofar saudart tayi a tsorace don tasan da ummy ta juyo dolene ta ganshi. Ganinshi tayi yafita sai leqo kai dayake kamar kusu mai shirin sata. Narke fuska tayi tana kallonshi pleadingly alamun please ya fita. Kashe mata ido yayi sannan yayimata alamun karki manta da deal dinmu Ganin ummy na niyyar juyowa yasashi saurin ficewa Saida Ummy tabi kofar da kallo jin kamar taji motsi awajen sannan ta maido kallonta kan saudart daketa raba idanu kamar marar gaskiya. "Dole kiyita zare idanu Ai, I told you kiyi light food shine kika tarki wannan uban girkin ko? Besides Ina baby danace ta tayaki?" Shagwa6e fiska saudart tayi tana cewa "Ummy barci fa take and na tadata taqi tashi shiyasa na kyaleta" "Ai kinyi daidai, zanga Wanda zai sake bari gobe ki shiga kitchen, yanzu kwashe naga duk sunyi Bari naje ni na tadata narasa wane lalaci ke damun Baby kwanan, mutum kullum ba abinda ya iya sai kwanciya kamar mai?" Tafada tana nufar hanyar fita Ajiyar zuciya saudart ta sauke da qarfi bayan fitarta sannan ta juya tana kashe gas din tana hamdala a zuciyarta Jin takun ummy na tunkaro falon yasashi saurin gyara zama ya maida hankalinshi kan wayar hannunshi yana dannawa. Sosai ummy tayi mammakin ganinshi amma sai ta basar tanufo cikin falon tana tsuke fuska Dagowa ashraf yayi daga wayarshi ya kalli saitin ummy dake tahowa ya Dan sakarmata murmushi yana maida wayar a aljihu. Zama ummy tayi tana kallonshi tana qara nazarinshi ganin yadda fuskarshi ke fayau bawani alamun damuwa unlike jiya ranan dayabar gidan rai 6ace. Zamewa yayi qasa ya gaidata cikin girmamawa kamar yadda yasaba. Amsawa tayi ba yabo ba fallasa tana dauke kai don tayi tunanin maganar ranan zai sake dauko Mata Ganin yakoma ya zauna batareda yace komaiba saima maida hankalinshi dayayi a t.v yasata cewa "Yaushe kashigo?" "Ban dadeba" ya amsa a gajarce "Wannan fa? Na wanene?" Tafada tana nuna trolley din dake tsakar falon "Oh.. Nawane, yanzu zan wuce dashi ciki" yafada batareda yanuna yaga kallon datake Mashi ba. "Naka? Tafiya zakayi?" Dan murmushi yasaki ya girgiza kai yace "A'a kayana anjima zan kaisu apartment dina" Sai yanzu tagane inda ya dosa. Lallai kenen shima yadawo nan da zama yake nufi ko me? Aikau in yasan wata besan wata ba. Bata qara cemashi komaiba itama ta maida kallonta kan t.v don Tama fasa zuwa tado baby din tinda saudart na kitchen Haka suka cigaba da zaman kurame har saida sukaji motsin saudart ta fito daga kitchen din hannunta dauke da warmers. Caraff suka hada ido tayi saurin dauke kai tanufi dining tana doddorawa akai Binta da kallo yake harta gama doddorawa takoma kitchen din Janye idanunshi yayi daga binta da kallon dayayi ya maida kan ummy, cikin taushin murya yace "Ummy ina maid dinmu ne?" Batareda ta kalleshi ba tace "Ta tafi kasuwa" "Baby fa?" "Tana sama" ta amsa a taqaice "Doing what ummy?" Dagowa tayi ta gallamashi harara tace "Bansàniba" Dauke kai yayi yana dan turo baki sannan qasa qasa yadda yasan zataji yace "Kowa nata hutawa sai matata akabari da aiki" Dan dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta janye idanunta ta cigaba da kallonta Haka saudart taita fitowa tana jera dishes din dukda duk acikin qarfin hali takeyi saboda yadda take junta very uncomfortable saboda kallon dayake binta dashi Saida tagama komai sannan ta qaraso falon adarare Dagowa ummy tayi ta kalleta cikin fara'a tace "Yauwa Yar albarka, kin gama ko?" Murmushi tadan Saki tana sinne kai "Sannu to, kije kiyi haramar zuhr naji anata Kira" Kada kai tayi kawai, kamar zata wuce saikuma tadan juyo saitin ashraf daya maidata mirror tundazu. Janye idanu tayi sanaddiyar hada idon da sukayi, cikin calm voice dinta tace "ina yini" tana dan russunawa Wani farinciki ya ziyarci zuciyarshi nan take hakan yasakashi sakarmata murmushi yana cewa "Lfy.. Sannu da aiki" Bata amsa ba sai wucewa datayi tana jinta so uncomfortable saboda shigar dake jikinta dukda yanzu ta yafa gyalle Wanda dama aiki yasata cireshi a kitchen. Saida ta haye sama sannan ummy ma ta tashi itama ta haura saman batareda tace mashi komaiba Murmushi yayi sannan shima ya tashi ya nufi trolley dinshi yaja yafice yanufi apartment dinshi yana tafe yana cilla keys dinshi sama yana cafewa zuciyarshi fess. Da sallama yashiga dakin jaye da trolley dinshi Dakin bawani datti don ana gyarashi koda bayanan bare dama yan kwanaki yayi rabonshi da dakin. Ajiye trolley din yayi kawai yanufi bathroom ya dauro alwalla a gurguje yafito don har Ana shirin kabbara sallar Koda aka gama sallar yadan jima be dawoba. Lokacin daya dawo duk suna dinning da alamu abinci sukeci. Qarasowa yayi cikin takunshi na qasaita idanunshi kafe da saudart da kanta ke qasa tana jujjuya spoon dinta a abinci Zuwa yanzu ta chanza shigarta zuwa deep blue Arabian gown buba wadda hannun yadan tsuke a daidai gwiyagun hannayenta, sai adon fararen tutar flowers da aka jera round din wuyan rigan, sai veil din rigar data yafa simply akanta. Tayi kyau sosai dukda bawani kwalliya tayiba amma glowing din fatarta kadai abin kallone da sha'awa. Saida ya qaraso sannan ya janye idanunshi akanta yana jan kujerar dake facing din saudart baya sannan ya zauna. Dagowa yayi suka hada ido da baby dake shirin kai spoon abaki, wata uwar harara ya gallamata yana kada kai Sadda kai tayi tana kumburo fuska "Anan kikafi afki ai, a girka kici" yafada yana ziran plate at the same time yana cigaba da hararanta. Qara turo baki tayi tadan saci kallon ummy taga abincinta kawai takeci hakama saudart dako dagowa bataiba Hakan yasa itama maida kanta ga abincin tanaci a sanyaye don saitaji duk ya ficemata akai duk dadinshi. Itadai saudart tin shigowarshi bata yarda taqara dagowa ba don tanajin yadda idanunshi ke yawo akanta abin har mammaki yake bata, kodai ya manta ummy na a dinning din ne. Bata ida tsinkewa da al'almarinshi saida yaji yace "dear serve me mana, yunwa" Shiru dining din ya dauka don they're all confused sun rasa dawa yake Gaban saudart yafadi jin yasake cewa "Kinji wifey? Am hungry" ya qarashe maganar a shagwa6e kamar yadda yakema ummy Daburcewa saudart tayi yayinda wata matsananciyar kunya ta lullu6eta. Dagowa tayi ta saci kallon ummy taga kamar ma batasan dasuba don abincinta kawai takeci. Hakan yasata maida kallon akanshi, kashe mata ido daya yayi sannan yace "kinji?" Rasa inda zata sa kanta don kunya tayi, tashi tayi kamar wanda aka zarewa lakka tana Satan kallon baby Wanda ta sadda kai tana qumshe dariya da wutsiyar ido sannan ta bude warmern fried rice din kamar zatayi kuka Turo mata plate din daya zara yayi yana qoqarin danne dariyarshi ganin yadda tayi da fuska da yadda take zuba abincin a daburce "Yauwa ya Isa hakan" yafada yana janyo plate din sannan ya turamata glass cup daya yana cewa "Saura drink" Bata kalleshi ba ta dauki glass din ta bulbula smoothie din dayayi gwanin kyau aciki sannan ta zari wani glass din ta zubamaahi ruwan gora masu sanyi. Duk tanayin wadannan ne a nonnoqe don wani irin kunyar ummy takeji wanda bata ta6a jiba. Komawa tayi ta zauna tanajin kamar ta nitse don kunya Shikau ko ajikinshi saima spoon daya saka a plate din ya debi spoon guda yakai baki. Lumshe idanu yayi sakamakon karon da abincin yakaimashi harcikin qwalwa, abincin is so delicious kamar yadda look dinshi is so salivating. "Hummm" yafada yana chewing din abincin ahankali ido a lumshe irin yakaimashi Karo dinnan. Kasa qumshe dariyarta baby tayi wannan karon saida tafito tayi saurin dafe baki tanayi Atare suka wurga mata harara ta gefen ido, fuskar saudart kamar mai shirin kuka, jitake kamar taita ihu don takaici Itakau ummy ko alamun tasan abinda ke faruwa bata nunaba saidai can qasan ranta mammakin rashin kunyarshi take. Cigaba da cin abincin shi yake hankali kwance yana wani lumlumshe idanu yana humming alamun yana enjoying din abincin Baby kau dakyar take cin abincin saboda dariyar dake cikinta, musanmman idan takalli fuskar saudart dake blushing don kunya, Allah Allah take su ke6e ta amayar da dariyar cikinta Saudart kau jitake kamar ta tashi tabar dining din saidai babu dama don tun farko saida ummy ta bigemata warning akan saita cinye wanda ta zuba, gashi ko Rabi bata ciba don tinda yashigo sai cin abincin yazama shiririta Haka taita tsakurar abincin kanta a qasa feeling very uncomfortable kafin daga bisani ummy ta dauki ruwan gabanta tasha ta goge baki da tissue sannan ta miqe batareda tacema kowa komaiba. Dan murmushi ashraf yasaki ganin tabar wajen tama hayewarta sama. Sannan ya maido kallonshi kan baby data nutsu sosai yanzu tana cin abincinta. Tamke fuska yayi sosai yana kallonta, hakan yasata sauke spoon din hannunta tana kallonshi idanunta rau rau "Get lost" yafada fiska ba alamun wasa Tashi tayi da sauri tana daukar plate din abincinta tafice daga dinning area din kamar zatayi kuka. Saida yagama rakata da mugun kallo sannan yamaido dubanshi kanta. Haryanzu kanta sadda yake sai jujjuya spoon take acikin abincin Dora hannayenshi yayi saman table din ya buga tagumi tareda zubamata hazal eyes dinshi kamar yasamu mirror....✍️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [11/30, 7:06 PM] +234 909 007 1867: 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 094 Qin dagowa tayi dukda yadda takejinta a tsananin takure da kallon qurillarshi ya haifarmata. Qurawa spoon din hannunta idanu tayi tana sauraron zuciyarta data sauya bugu. "Saudart..." Lumshe idanunta tayi ta budesu ahankali don taji kiran har tsakiyar kanta Kallonta yacigaba dayi yanajin wani irin feelings akanta, jiyake kamar su dawwama a hakan "Saudart..." Yasake kiranta saidai wannan karonma bata ko motsa ba saima hawayen dataji suna taruwa a idanunta wanda ta rasa ko namenene "Kinyi kyau... Sosai" yafada yana dan murmushi still idanunshi kafe akanta Still bata motsaba saima battling datake wajen maida hawayen dake neman zubomata wanda haryanzu batasan dalilin zuwansu ba. Dan matsowa yayi jikin table din wanda hakan yaqara basu kusanci Cikin muryar rada yace "Shin wani yata6a fadamiki ke kyakyawace ta qarshe?" Bejira amsarta ba sai kamo hannunta dake riqe da spoon dayayi ya riqe da hannunshi na dama ya dafe natan dana haggu yana binta da romantic kallo Lumshe idanu tayi tanajin tsigar jikinta na tashi sosai Sake qasa yayi da murya yana cewa "You're the most beautiful creature that ever exist, and am the luckiest man that ever exist for having such glowing dem as my other half" Dan matsa hannunta dake cikin hannayenshi yayi wanda saida ta sake tamke idanunta saboda yadda zuciyarta tayi zillo "And I'll continue to thank Allah for granting me such rare, pure damsel with golden heart..." Gyaran muryar dayaji daga bayansu ya dakatar dashi daga abinda zai sake cewa ya dan waiwayo don ganin waye Saurin dauke kai tayi daga kallonsu tace "Ehm.. Dama ummy ke kiran aunty" Ganin kallon dayake binta dashi yasata saurin juyawa tabar wajen. Tashi itama saudart tayi kamar wanda dama ke kan qaya ta zame hannunta daga cikin nashi ta gittashi tawuce batareda ta yarda ta dagoba. Binta yayi da kallo yayi harta haye sama sannan ya saki slight smile ya maida kanshi akan abincin shi yanaci cikin nishadi. Saudart kau tafiya take amma jinta take kamar ba a hayyacinta ba take don saida tayi dagaske don kartayi missing din steps tasamu ta ida haurawa sama Direct dakin baby tashige don bazata iya facing din ummy ba ayanzu. Taddata tayi zaune gefen gado ta jingina da jikin gadon waya kare a kunnenta. Ganinta yasata katse wayar tareda sakin ihu mai tafe da dariya. Saudart ko gefenta bata kalla ba ta zagaya ta dayan 6arin gadon ta kwanta tareda juyamata baya. Dariya baby tasake fashewa dashi tana matsowa kusada ita tace "Wuuuu! Love birds, gaskiya abin fa yabada show, wannan soyewa haka? I never knew yaya sharukhan ne sai yau, ca6 gaskiya ne da akace fear silent people, ca6!" Itadai saudart ko iskar daya kwasota bata kulaba don ko juyowa batayi ba saima lumshe idanu datayi tana sauraron bugun zuciyarta wanda be dawo normal ba Haka baby ta tisata gaba da tsokana iri iri harta gaji don kanta ta shafamata lafiya. Saudart bata tashiba saida taji ana kiran sallar la'asar sannan ta lalla6a ta tashi ta dauro alwalla tazo ta sauke farali sannan tasake komawa kan gadon. Itadai bazata iya fadin taqamaimai abinda takeji ba saidai tana jinta haryanzu ba daidai ba ga magangganunshi daketa eoching a kunnenta plus qamshin turarenshi daya kasa barin hancinta, wadannan suka taru suka haifarmata kasala tayi lamo a gado bata ko son tashi. Haka ta qarasa wuninta a daki don kunyar fitowa ta hadu da Ummy take plus batason haduwa da ashraf dukda batada tabbacin haryanzu yana gidan don ita batasan da zancen dawowarshi gidan ba Zaune take kan sallaya wanda tagama sallar isha'i akai wayarta a hannu tana yan danne dannenta. Jitayi an bude kofa amma taqi juyowa don atunaninta baby ce "Daughter" Saurin juyowa tayi jin muryar ummy saikuma ta maida kanta qasa tana gaidata a kunyace. Amsawa tayi fiska a sake tana cewa "Ya baki fito dinner ba?" Tashi saudart tayi daga kan sallayar tana cewa "Yanzu zan fito ummy" "Ok" ta amsa a taqaice tana fita Ninke sallayar tayi ta maidata ma'ajinta sannan ta zira takalmin soso ta fito. Ahankali take taka stairs din tana tunanin yadda zata iya zama taci abinci cikin sakewa agaban ummy don haryanzu kunyarta takeji sosai, jitake kamar tace aqoshe take saidai tasan ba dama. Qarasa saukowa tayi ta nufi dining din kanta qasa Jin masculine scent din turarenshi yasa gabanta faduwa don she didn't expect it Dagowa tayi ta kalli saitinshi saita hangi bayanshi kasancewar yaba hanyar shigowa bayane Maida kanta tayi qasa tana mammakin why yau ya Dade betafiba, koko dawowa yayi? Tabbas dawowa yayi duba da chanza shigar dayayi don kayan jikinshi bana dazun bane. Ida qarasowa tayi daukeda sallama a bakinta Duk dagowa sukayi suna amsamata tareda zubamata idanu. Jan kujerar dake kusada baby tayi ta zauna tana dan murmushin yaqe. Sannu tayi ummy tareda amsa sannu da baby ke mata sannan ta cije ta dago dakyar ta kalleshi Kamar kau yadda tayi tsammani idanunta suka fada cikin nashi don dama ita yake kallo Janye idanunta tayi sannan ahankali ta gaidashi Amsawa yayi yana sakarmata murmushin shi mai tsada, ba qaramin dadi yakejiba idan ta gaidashi, jinshi yake so uptop Serving din kanta tayi sannan takoma ta zauna tafaracin abincin a hankali Shiru dining din ya dauka idan ka dauke qarar cokalan daketa haduwa da plate Yanzun ma kamar dazun atakure takecin abincin don duk motsin dazatayi saitaji alamun idanunshi akanta, ga yawan hada idanun dasuke wanda duk sadda suka hada ido saiya sakarmata wannan cool murmushin nashi, haka dai take tura abincin badon tanajin dadinshi ba don duk a darare takejin kanta. Ganin taci fin rabi dakyar yasata dagowa ta kalli ummy Itama ummyn dagowa tayi daga abincinta tana kallonta batareda tace komaiba Marairaice fiska tayi sannan tace "Ummy am full" cikin sanyin murya Ga mammakin ta sai jitayi tace "Ok daughter you can go" Dadi taji wanda saida hakan ma ya nuna a fuskarta, daukar glass cup tayi ta sha ruwa kadan sannan ta goge bakimta da tissue ta miqe tareda dan satar kallonshi. Gani tayi fuskarshi ta nuna alamun rashin jin dadin tashinta Kauda Kai tayi tabar wajen tana sauke Ajiyar zuciya don Allah yasani a matuqar takure take awajen Bata jima ba da komawa dakin ba itama baby ta shigo. Sun dan ta6a fira da baby kafin barci yayi awon gaba da baby Ganin haka yasata jawo wayarta takoma ta jingina da pillow data kara da jikin gado tashiga danne dannenta. Sosai tayi missing din laptop dinta don wasu abubbuwan dole saida ita zatayi. Tana cikin danne dannenta kira yashigo wayar Qurawa number idanu tayi batareda ta dagaba yayinda bugun zuciyarta yafara sama Haka taita kallon wayar harta yanke, ko seconds biyu ba'a qaraba wani kiran yasake shigowa. Saida takusan tsinkewa sannan tayi qarfin halin daga wayar ta kara a kunnenta batareda tace komaiba "Beauty.." Taji anfada daga dayan bangaren Shiru tayi batace komaiba "Hello? Are you there?" Yasake cewa Qarfin halin bude baki tayi tace "Yes? Who's this?" Sautin murmushin shi taji kafin yace "You know better" Shiru tayi bata sake cewa komaiba "Shine kika tashi dazun without my consent?" Yasake fada bayan wasu daqiqu Dan wara idanu tayi tace "Your consent?" "You heard me" ya amsa a gajarce Ta6e baki tadanyi batareda tasake cewa komaiba "Bakice komaiba" "Me zance?" Tafada tana Zamewa ta kwanta "You tell me why you leave without my consent ko kiyi apologising for that" yabata amsa Dage giranta tayi alamun 'dagaske?' Sannan tace "Bye.. Am sleepy" "Are you kidding me" yafada da sauri jin alamun zata katse wayar Dakatawa tayi don jin abinda kuma zai sake cewa "Don't tell me kin manta da deal dinmu" "Deal?" "Kinji kenan, am waiting" "Waiting for what?" "Our deal, you promised zaki hadamin coffee kikawo apartment dina dazun, don't you?" Yafada yana lumshe idanu don sosai yakejin dadin wannan little conversation din nasu Itakau saudart mammaki nema ya kamata, ita sai yanzu ma ta tuna dawani deal, lallai ma "Kinyi shiru" "Hmm wane coffee kake magana akai? Ni bànsan abinda kake magana akai ba" Murmushi yasaki yana shafa kwanttacen sajenshi yace "Really? Ko kinsan promise is a debt? Musanmman ma nawa promise din cos bana yafe bashi" Daga kafadu tadanyi sannan tace "Bye" Bata jira cewarshi ba ta katse kiran Maganar da ashraf ke shirin yine ta maqale jin an yanke kiran. Sauko wayar yayi yabita da kallo cikin mammaki sannan ya kada kai. Kashe wayar gabadaya tayi sannan ta aza kan bedside locker ta kashe wutan dakin tabar dim light don bata iya barci cikin duhu sannan ta janyo bargon da baby ta lullu6e dashi itama tashige ciki tana sauke Ajiyar zuciya Addu'ar kwanciya ta karanta ta tottofa sannan ta qara qudundunewa a bargo tana lumshe ido Cikin barci taji kamar kofa na motsi, ahankali ta bude idanunta dasukayi nauyi don barci ta kalli saitin kofar a kasale. Ganin tayi kamar inuwar mutum hakan yasa taji gabanta ya fadi. Qara bude idanuwanta tayi don tabbatarda abinda tagani din gaske ne. Ganin shadow din na nufo gadonsu yasata qara lahewa a gadon zuciyarta na racing sai qoqarin karanto addu'o'i take amma takasa saboda yadda ta tsorata Baby kau batasan wainar da'ake toyawa ba saboda she's fast asleep gashi Allah ya horemata nauyin barci Zufa ke tsatsafo mata takoina gashi tana tsoron yin kwakwarar motsi don kar 6arawon yaganta kamar yadda ta dauka Saida yazo gaban gadon sannan taga yaja ya tsaya kamar mai tunani saikuma taga ya nufo 6aran datake kwance Rawa jikinta ya dauka yayinda tashiga karanto duk addu'ar dayazo zuciyarta, abin mammaki kuma takasa ihu sai mazari kawai datake daga kwance Ganin yazo dab da ita yasata tamke idanunta tana sauke numfashi sama sama cikin tsananin kidima Jitayi an matso dab da ita sosai har tana iya jiyo saukan numfashin mutumin akanta hakan yasata dauke numfashi cikin sadaqatwa "My coffee.." Taji anyi wishpering a kunnenta Bata motsa ba bata kuma saki numfashin ba "Nasan kina jina, fulfill your promise" yasake fada yana hurama fuskarta iska kamar wanda aka tsikara tayi saurin miqewa zaune tareda danna plug din kwayakwan wutan dakin, take dakin ya gauraye da haske Karo idanunta sukayi dashi zaune a bedside lockern dake gefenta hakan ya haifarmata da mummunan faduwar gaba don ko kadan bata tsammacci ganinshi ba don ita duk atunaninta yana can gidanshi Jada da baya zatayi yayi saurin cafko hannunta, bude baki tayi zatayi ihu yayi saurin dora yatsarshi manuniya akan lips dinshi alamun tayi shiru Kasamcewar a mugun tsorace take yasata saurin hadiye ihun tana kallonshi a tsorace "Bani coffee dina sai intafi" yafada still riqe da hannunta "A.A?.." Tayi wishpering cikin son gasgata shi dinne Daga mata gira daya yayi yace "Yes?... I told you Ai bana yafe bashi, you promised zaki kawomin coffee idan na 6uya , so nacikamaki alqawarinki kema ki cika nawa" Yanzu kau ta tabbatar da shine don har qamshin turaren nashine wanda dazu tsoro yahanata jinshi, amma me yakeyi agidan nan at this hour of the night? Huremata idanu yayi tayi saurin lumshe su "Kallon fa?" Ya tambaya yana daga mata gira daya Dan Satan kallon baby tayi dake qudundune cikin bargo batasan me duniyar take ciki ba sannan ta dago ta kalleshi tana dan frowning face dinta "Ka cikani please, am sleepy" "My coffee" yabata amsa batareda ya saketanba "Zan Maka ihu ummy tazo and you know she won't take it slightly with you" tafada threateningly "Go ahead, zanfi kowa jindadin tazo ta iskemu hakan maybe hakan sesa tasan I need my wife" Dan wara idanu tayi kafin takuma maida fuskar puppy face "Please ka kyaleni, this is not right" tafada tana qoqarin kwace hannunta "Menene ba daidai ba?" Yafada still riqe da hannun "Everything, please leave me alone am sleepy" tafada kamar zatayi kuka "Idan kinaso in kyaleki ki hadamin coffee dina kikaimin apartment dina" "But dare yayi for crying out loud" tafada tana yarfe hannuwa "And I won't leave without my coffee for crying out loud" yafada shima cikin yanayin data fada Sauke Ajiyar zuciya tayi tace "Ok kasaki hannuna tukunna" "Ki gudu?" "Zuwa ina?" "Oho but I assure you kina yunkurin guduwa zan daukeki cak wlh bazan direki koina ba sai cikin mota and direct gida zan kaiki saidai ummy ta farka taga babu ke, kuma try me and see" yafada in a very serious tone Tsayawa tayi tana kallonshi a mammakince, ganin zai iya yasata sauke Ajiyar zuciya tace "Alright naji sakeni" Babu musu ya sakarmata hannu yana kallonta without blinking Dan murza ankle din hannunta tayi sannan ta bude baki dakyar tace "Yanzu me kakeso nayimaka?" "Simple.. Just make my coffee ki kaimin apartment dina shikenan" "Ok zanyi maka gobe i promised" Wani kallo yayi mata "Are you kidding me?" "Please.. Kaga yanzu dare yayi and ummy na iya jiyomu ta tashi and you know what the result will be, I promised gobe insha Allah zai zama first thing tomorrow morning, I promised" "Hmm, I need my coffee now not tomorrow miss, idan ma ummy kikeji yanzu am sure she's fast asleep kuma aiba hayaniya zamuyiba... You know what? Da wannan 6ata lokacin damuke da yanzu kin manta da kin hada kin dawo kin kwanta, all I know is yau bazan kwanta ba saina sha coffee dina" yafada firmly yayinda cikin zuciyarshi Dariya kawai yakemata ganin yadda take kallonta in confusion Dafe kanta tadanyi cikin rasa abin yi ga takaicin baby dake kwance kamar gawa wai ace duk abinda ake bataiba saikace mai barcin mutuwa? Dagowa tayi ta kalleshi taga shi dinma ita yake kallo yawani jingina da bango ya harde hannayenshi a qirji yana kallonta kamar ya samu mirror Sauke Ajiyar zuciya tayi nannauya sannan ahankali tace "Ok" Murmushi yasaki sannan yamiqe tsaye yace "Let's go Badan ranta yasoba ta ziro qaffafunta qasa ta sauko. Sleeping gown baqa ce a jikinta mai kauri wanda takaimata har qasa sai hular net ja dake kanta wanda ta cusa duka gashinta aciki. Gwada mata hanya yayi ganin batada niyyar wucewa hakan yasata gittashi ta wuce ya bita abaya Maimakon tanufi qofa saita maida akalar tafiyarta ga wardrobe din dakin ta bude taciro long milk colour hijab dinta tazira sannan ta nufi qofar fuskarnan hade kamar zatayi bindiga, binta yayi yana murmushi yanajin kamar ya rungumota ta baya ya dauketa in a bridal style yakaita har kitchen din. Kamar munafukai haka suke sanda wurin sauka stairs din, saudart agaba hannunta tattare da gaban hijab dinta dake jan qasa shikuma biye a baya suna tafiya sadaf sadaf. Suna gab da sauka qasa hijab dinta ya tadeta tayi gaba zata fadi. Saurin riqo hannunta yayi ya janyota jikinshi ya tallabe Ajiyar zuciya ta sauke don ta sadaqar faduwa zatayi Dagowa tayi daga jikinshi ta sakarmashi harara mai cike da jin haushi sannan taqara sa hannu ta tattaro hijab din ashraf na tayata sannan suka cigaba da tafiya sadaf sadaf kamar qwarrarun 6arayi dasuka qware wajen sanda...✍️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [12/2, 8:33 PM] +234 701 416 6830: 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 096 Cikin gida yanufa cikin tafiyarshi ta qasaita. Koda yashiga falo be tarar da kowaba hakan yasashi haurawa sama domin gaisawa da ummy Tsayawa yayi yana kallon kofar dakin baby kamar mai shawara can kuma ya janye idanunshi yashiga knocking din kofar ummy Saida yasake knocking sannan yaji muryar ummy daga ciki tana bashi izinin shigowa. Murda kofar yayi ya bude yashiga bakinshi dauke da sallama Caraff suka hada idanu da saudart dake zaune saman bedside locker din ummy tana ninke mata kaya Sauke idanunta tayi qasa gabanta na faduwa yayinda mafarkinta na dazu yashiga dawomata a qwanya Kanta a duqe tana cigaba da ninkin kayan hannunta tana sauraron gaisawar dasuke cikin soyayya da nuna kulawa da juna dukda haryanzu ummy bata sakarmashi fuska sosai Saida suka gama gaisawar sannan itama saudart ta gaidashi batareda ta yarda sun hada idanu ba Amsawa yayi yana kallonta cikin so da qauna ko kunyar yimata irin wannan kallon agaban ummy beji. "Kayi breakfast?" Inji ummy batareda ta kalleshi ba "No, saukowata kenan Ai" ya amsa batareda yabar kallon saudart din ba "Ok sai kaje kaci" tafada tana janyo wayarta tana dan dubawa Kallonshi yamaida akan ummy sannan ya yamutse fuska yana yin alamun gajiya yace "Ummy akawomin nan, am very tired" Dan kallonshi ummy tayi sannan tadan ta6e baki tace "Aikin me kayi harka gaji?" "Ummy jiya fa sai wajajen two na kwanta, am busy working with my secretary" Jin hakan yasa saudart Satan kallonshi suka hada ido ya kashemata ido daya yana smirking Janye idanunta tayi tacigaba da abinda take Ta6e baki ummy kawai tayi bata qara cewa komaiba, can ta dago ta kalli saudart dake ninke kayan wanda ba abinda yasamesu kawai son aikine irin nata da rashin son zama hakanan yasata takuramata saida tabarta tayi din "Daughter" Dagowa saudart tayi ta kalleta tana murmushi tace "Na'am ummy?" "Jeki ki kawomashi breakfast dinshi kinji?" Sadda kai tayi tace "To ummy" Ajiye veil din hannunta tayi ta tashi ta nufi kofa a kunyace Binta da kallo yayi harta fita ta rufo kofa sannan ya maida kallonshi ga ummy da ke kallonshi itama Harara ta gallamashi ta dauke kai hakan yasashi sunkuyar dakai yana Sosa gefen wuya murmushi a fuskarshi "Meya hanaka zuwa aiki?" Inji ummy batareda ta kalleshi ba "Nayi taking leave ne" ya amsa a taqaice Bata sake cewa komaiba saima maida kallonta datayi a wayar hannunta Suna haka aka bude kofa ta shigo da sallama hannunta dauke da tray data hado kayan Karin akai Qarasowa gabanshi tayi a kunyace ta ajiye mashi tafara niyyar tashi Riqo hannunta yayi yana wishpering "Wazai maki serving din?" Saurin kwace hannunta tayi daga nashi tana satar kallon ummy a rude sai gani tayi hankalinta ma be wajen su Hararar shi tayi da wutsiyar ido cikin jin haushi sannan tafara qoqarin hada mashi breakfast din Ta rasa dalilin dayasa yakeson kunyatata agaban ummy, da tagansu fa? Gaskiya beda kunya ko kadan Tana cikin hada mashi tea yadan sunkuyo saitin kunnenta ya rada mata "Fatan baki manta da deal dinmu ba" Saurin dagowa tayi tana kallonshi sannan taqara satar kallon ummy taga still basu take kalloba Wai me ke damun wannan gayen ne? Abinda ta tambayi kanta kenan Dan matsawa tayi daga kusadashi tana cigaba da hadawa a gaggauce don ta qagara ta tashi tabar wajen Murmushi yasaki na gefen baki wanda shikadai yasan yayi abinshi. Besake cemata komaiba harta gama hada mashi komai ta tashi takoma wajen kayan datake ninkewa Jitake kamar ta tafi amma sai gani tayi bedace tabar kingin kayan ba hakanan Cigaba tayi da ninkin wannan lokacin cikin sauri don jinta take a matuqar taqure Tana cikin ninkin taji wayarta tayi beeping alamun shigowar massage Bata damu da ta dubaba tacigaba da abinda takeyi kawai Wani massage din ya shigo followed by another one duk atare Hakan yasata dakyar wayar don ganin massage din dukna menene haka jejjere Number data ganine yasata dagowa ta kalleshi Kashe mata ido daya yayi yana smirking Dauke kanta tayi yacigaba da abinda take taji wani text din yasake shigowa Rolling din idanunta tayi sannan tasa hannu tayi sliding wayar ta bude lock din tashiga massages din Samun kanta tayi da sakin murmushi ganin abinda ya turamata, kamar bazatayi reply ba saikuma tayimashi replying da emoji din *I don't care🤷🏻‍♀️* Yana ganin haka shima yasaki murmushinshi yasake tura *I'll make sure you do babe, it's better ki cika alqawari for your own good amma* Ganin abinda yaturo yasata ta6e baki sannan ta turamashi emoji din *oho dai💁🏻‍♀️* Murmushi yasakeyi yasake mata text da *hmm don't take it as a joke, am deadly serious, Zan baki mammaki idan kikayi tunanin playing dina cos there will be no mercy* Data karanta nanma sake ta6e baki tayi tayimashi reply da emoji din🙄🙄🙄 *we shall see* yaturamata yana kwafa afili wanda yasa ummy dagowa ta kalleshi da alamun tambaya Basarwa yayi yacigaba dacin abincin shi Bata dadeba tagama ninkin duk ta maidasu cikin closet ta jerasu gwanin sha'awa sannan tacema ummy zata tafi Cikin fara'a ummy ke mata godiya tana qarajin qaunarta acikin zuciyarta don saudart mutum ce data iya zama da mutane kuma tasan takan yadda zata sace zuciyar mutane da hallayenta kyawawa. Shidai A.A be dagoba hartayimata sallama tafita Bata dade da fita ba shima yamiqe ya kwashe kayan yafita dasu Saida yakai kitchen, maid dinsu dake kitchen din tana qoqarin Dora girkin rana ta amsa cikin girmamawa sannan yadawo yaqara haurowa saman Wannan karon kofarsu baby ya nufa Kwankwasawa yayi har sau uku sannan aka bude Mammaki yakama baby ganin shine don rabonda yazo kofar dakinta har mantuwar ta mance idanma wani abun yake buqata saidai ya kirata a waya ko ya aika a kirata "Yaya? Good morning" "Morning" ya amsa cikin basarwa yace "Tana ciki?" Tasan wanda yake nufi don haka tabada amsa da "A'a yanzu yanzun nan tafita wai ta tafi wajen ummy" "Ok" kawai yace yajuya Binshi da kallo baby tayi tana gulmarshi acikin zuciya ta shige ciki tana kada kai Bebi takan dakin ummy ba ya sauka yafita yanufi parking lot Yashiga motarshi yafice daga gidan Koda yadawo ma be gantaba, haka yasha zamanshi a falo duk don yaganta amma ko wulginta be ganiba. Da zasuyi dinner ma bata saukoba saisu ummy shikuma yakasa tambaya Haka yaita zuba ido ko zai ganta amma shiru Da daddare ma saida ya lalla6a yaje dakinsu saidai wayam baby kawai ke dakin wanda hakan ke nuni da yau dakin ummy saudart ta kwana Haka yakoma part dinshi yana cizon yatsa tareda ayyana yadda haduwarsu zata kaya. Wasa wasa kwana uku kenan suna wasan yan 6uya tsakaninsu Basu haduwa sai a lunch da dinner don yanzu abinda ke sauko da ita kenan tinda taji yadawo gidan shima da zama, da angama zata haye sama tashige dakin ummy Kwata Kwata bata yarda su hade a inuwa daya su biyu kacal, kullum tana maqale dakin ummy. Saidai hakan be hanasu magana through text massage, koda yaushe cikin warning dinta na karta yarda su hade don with every passing day tana adding salt into injury ne Itadai bata bashi amsa sai emoji da take turamashi na rainin wayau wanda tasan zasu quleshi. Wasa wasa yau kwana biyar kenan suna wannan wasan 6uyan, izuwa yanzu sun saba fira via text massage don kullum saisun kusa raba dare sunayi Kullum cikin threatening dinta yake na karta yarda su hade, itakuma taita yimashi reply da emojis na rainin hankali tana Dariya ita kadai Hakan saiya wanzar da shaquwa tsakaninsu batareda sun farga ba Da daddare su kusan raba dare suna cafta washegari kuma dasun hadu wajen cin abinci inda anan kawai yake ganinta don inbanda cin abinci babu abinda ke fiddata dakin ummy sai idan ta tabbatar baya gidan. Haka zasu hadu a dinning inda zasu dinga musayar magana da ido suna murmushi Duk abinda suke uwar sa ido (baby) tana ankare dasu don tsabar sa idonta har qagara take su sauko cin abinci Yauma kamar kullum suna zazzaune suna dinner Vibrating wayar saudart tayi hakan yasata dan satar kallonshi tayi taga shima kallon nata yake ta qasan ido Dan ta6e baki tayi taqi duba wayar Ba dadewa taqara vibrating, qin motsawa tayi bare ta duba wayan Qara vibrating tayi akaro na uku, murguda baki tayi takuma qi dagowa Baby dake ankare dasu cikin zuciyarta tace "Yau naga dan anace, tace yau batayi batayi dolene?" Itakau saudart tana sane taqi kulashi duk don ta yayinda take mashi Dariya cikin zuciya Tana cikin taunar lomar bakinta taji an zunguro qafarta daya ta qasan table din Furzar da abincin bakinta tayi ba shiri saboda shocking dataji ya zirgamata daga dan yatsa har saqar kai "Subhanalillah, lfy daughter?" Inji ummy tana kallonta cikin kulawa "Am..am ok, kawai kwarewa..." Jin an riqemata babban yatsar kafarta ta qasa yasata kasa qarasa maganarta taja baya da sauri tana sakin qara "Subhanallilah! Daughter are you ok?" Inji ummy tana miqewa tsaye, itakau baby harta bar wajen tadawo bayan kujerar ummy Itama saudart miqew,a tayi tana tura kujerarta baya tana kallon qasan table din atsorace "Daughter lfy wai?" Inji ummy itama tana leqa qasan table din "Wlh ummy wani abune mai shocking ya ta6a min kafa" tafada tana kallon qasan table din har lokacin "Shock kuma? Son please dubamana kasan table din" Ashraf dashima tinda aka fara drama din ya tsaida cin abincinshi yana kallonsu ya duqa don dubawa yayinda yake danne dariyarshi dake neman tonamashi asiri Saida yagama leqe leqenshi sannan yadago yace "There's nothing here nidai maybe imagination ne kawai" Ganin irin kallon dayake mata qasa qasa da smirk din gefen bakinshi yasata gano abinda yafaru Janye idanunta tayi cikeda takaicin tsoratata dayi. "It ok daughter, maybe imagination dinne, relax babu komai OK?" Inji ummy cikin son kwantar mata da hankali Gyada mata kai tayi takoma ta zauna tana qara Jin takaicin yadda ya tsoratata don ba qarya ta razanu. Sai a lokacin itama baby ta dawo itama ta zauna adarare suka cigaba dacin abincin su inda suke hada ido da ashraf akai akai inda duk hada idon dazasuyi sai yayi jesting dinta itakuma ta qara fumming fiska ta kauda Haka dai suka gama lunch din in silent sannan kowa ya tashi saudart ta haye sama as usual cikeda jin haushin abinda A.A yamata Koda take daki tanajin yadda massages keta shigowa amma taqi bi takansu tayi banza da wayar taqi budewa Yau Kwata Kwata bata biyemashi ba sunyi text din dasuka sabarma Kansu a yan kwanakin nan. Tun yana turamata text din tsokana harya koma turamata apologizing text amma shiru taqi amsawa harya gaji ya kyaleta ganin dgaske ba kulashi zatayi ba, haka ya haqura ya kwanta yanajin ba dadi A bangaren saudart kau duk text din dayake turamata saita bude ta karanta reply dinne kawai batayi Jin shiru daga baya be qara turowa ba yasata jin badadi itama, ta dade tana kallon wayar kozai sake mata magana amma shiru hakan yasa itama ta haqura ta rintse ido ba dadewa barci ya dauketa. Washegari duk sukuku suka tashi barin saudart data saba acikin yan kwanakin nan data tashi da text dinshi take fara karo saidai yau shiru kakeji Haka ta zauna tana azkar din safe wayarta agefenta tana kallonta akai akai cikin saka ran ganin tayi beeping Har tagama tayi tilawa dinta shiru kakeji, haka ta tashi jiki asanyaye tahau gyaran dakin ummy da yanzu yazama aikinta cikin sanyin jiki. Sanin cewa kullum saiya shigo ya gaida ummy yasata zaman jiran shigowarshi saidai har 12 shiru be shigo ba, abinda bata saniba shine yau tunda safe yayi shirin zuwa office kuma koda yashigo, saiya tararda ummy kitchen anan suka gaisa, yaso yasameta daki ko don ganin hasken idaniyarshi amma haka ya haqura yafice daga gidan. Wasa wasa har lokacin lunch babu shi ba text dinshi Sosai saudart ta tsure, yayinda fargaba tacika zuciyarta musanmman data tabbatar da yau bema yini agidan ba Kwata Kwata kamar yadda yasaba a yan kwanakin nan Fargabanta guda kardai ace maganar Mamy ta tabbata qila yagaji da wulaqancinta ya haqura zai nemi wata Wani irin abu takeji a zuciyarta tokare wanda tarasa menene Kwata Kwata ba abinda ke mata dadi, yawun bakinta ma dakyar take hadesu saboda abinda ke tsaye a maqoshinta Sai gashi itada bata zama falo yau yini tayi cikinsa tana kallo wanda a zahiri batamasan me akeyi a film dinba hankalinta nacan wani waje...✍️ Kuyi hqr ba editing👏 Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 095 Ahaka suka samu suka ida saukowa falon wanda yake dirim sai dan dim light blue colour dayadan haska falon Direct kitchen suka nufa, ashraf ya bude kofar ya matsamata ta shiga sannan yabi bayanta tareda maido kofar ya rufe. Kunna kwan wutan kitchen din yayi ya hangota daga can nesa tana kallonshi Daga mata gira daya yayi alamun kallon fa? Janye idanu tayi ta kalli wani 6arin kafin tace "I think basai an rufe kofar ba" Daga gira daya yayi kafin yace "Kinaso tsautsayi yasa ummy ta sauko ta hango kitchen din da haske? Inkuma bakiso dan sai a bude kofar a kashe wutan saina haska phone dina" yafada yana yunqurin kashe wutan kitchen din "No, ka barshi kawai" tayi saurin dakatar dashi da hakan sannan ta juya tanufi inda qaramin electric kettle yake ta fiddoshi ta dauraye sannan ta zuba ruwa ciki tayi plugging dinshi jikin socket Duk abinda take yana nan zaune kan fridge yana binta da kallo duk inda tayi yanajin wani nishadi a zuciyarshi Haka saudart taita kiciniyar hada coffee din saidai duk abinda take fuskarnan a kumbure take kamar mai shirin yin bindiga yayinda can qasan ranta take danasanin nacewa datayima ummy akan tabarta tayi girkin In less than 10mins tagama hada black coffee din ta juye a mug ta Dora a saucer ta azasu bisa wani qaramin tray sannan ta dauka tajuyo tanufoshi dasu. Kallon dai dayake mata ya cigaba dayi harta qaraso wajenshi ta Dora dan tray din saman fridge din kusadashi sannan ta juya zata wuce Cafke hannunta yayi hakan yasata tsayawa batareda ta juyoba "Ina zaki bayan baki gamaba?" Juyowa tayi ta gallamashi harara batareda tasan sadda tayi hakan ba tace "Menene kuma? Kace na hadamaka coffee na hada, what again?" "Menene deal dinmu? Zaki hada coffee kikaimin apartment dina ko ba hakaba? Nan yayimaki kama da apartment dina?" Wani malolo ya taso ya tokarewa saudart maqoshi, fizge hannunta tayi afusace tasake juyawa zata wuce Shan gabanta yayi saurin yi yana cewa "Where did you think you're going?" "Look mallam wai what's wrong with you ne? You said I should make you a cup of coffee, nayi kuma yanzu saika qirqiro wani abin? What exactly did you want from me?" Tafada atsakankanin haqoranta cikin fushi fuskarta na dayi jaja jaja "I want you to fulfill our deal, meyasa kika amince bayan kinsan you can't do it? Ni ba ruwana, I want my coffee in my room, final" Tsayawa tayi tana kallonshi tinda yafara harya kai aya sannan tayi Ajiyar zuciya tace "If not?" Matsowa yaqara yi dab da ita sannan yace "If not mu kwana anan" Kallonshi takeyi, a yanayin dayake bataga alamun wasa ba a tattare dashi kuma taga alamun zai iya din besides ita zata kwan aciki don bashida asara Sam Juya idanuwanta tayi tana cije lips kafin tace "Ok I promised zan kawomaka amma gobe, kaga yanzu dare yayi and ummy can wake up at any moment ta leqomu, please let me go I promised zan kawomaka wani gobe, ok?" Tafada cikin rarrashi kamar irin tanama yaro wayau Daga idanu yayi sama yana kallon saman ceiling kamar mai shawara hakan yasata qara cewa "You see yau da gobe duk dayane, it's just some hours to go, I promised zan kawomaka har dakin" tafada a tausashe burinta kawai tayi convincing dinshi ya yarda kota huta Yatsarshi manuniya yasa a baki yana cizonshi still idanunshi sama yana tunani, itadai saudart kallonshi take tana addu'ar Allah yadorata kanshi Sauke hannun yayi ya kalleta yana dan yamutse fiska sannan yace "Promise?" Har tarar numfashinshi take wajen fadin "Yes..yes promise" tana dan wara dara daran idanunta "Ok amma remember promise bashi ne and I don't forgive debt" "Yes I know" tabashi amsa "Good, now give me the coffee" Abinka ga mai nema babu musu ta qarasa fridge din ta dauko mug din tadawo ta bashi Amsa yayi yana kallonta, juyawa tayi ta nufi kofa da sauri don a qagare take taganta daki Jin kamar ana binta yasata tsayawa tareda juyowa "Zan rakaki ne" yafada yana dan daga hannuwa Batace komaiba tajuya taci gaba da tafiya shima yabiyota saida yakashe wutar kitchen din sannan yafito ya rufe kofar sannan yabiyo bayanta don hartayi Rabin stairs don sa6anin dazu yanzu da sauri take tafiya jitake kamar ummy zata fito su hade ne. Dakyar tasamu ta ida hayewa tayi saurin nufar kofar su ta bude tq maida ta rufe batareda ta tsaya sake mashi kallo biyu ba ta danna sakata sannan takoma ta jingina da kofar tana sauke wata wawuyar Ajiyar zuciya. Murmushi yasaki sannan ya kada kai ya juya yafara sauka qasa yana sipping din coffee dinshi Sosai yayi missing din coffee dinta hakan yasashi gamawa dashi cikin dan qanqanin lokaci ya maida mug din kitchen ya rufo ya fito ya nufi apartment dinshi cikin nishadi. Tashi tayi daga jinginar datayi a qofar tana sake sauke wata Ajiyar zuciyar sannan ta nufi gadon tana kallon baby data kanannade acikin bargo tanata shar6ar barcinta hankali kwance Girgiza kai tayi tana mammakin irin wannan barcin nata, wannan tasan har asace bazata saniba Cire zumbuleliyar hijab dinta tayi ta ninke ta maida wardrobe sannan ta zagaya dayan gefen ta haye gadon tajawo bargon dakyar ta lullu6e kasamcewar duk baby ta kanannade ciki sannan ta lumshe idanu Ga mammakin ta jitayi barcin yaqi zuwa, saima abubbuwan sasuka faru dazun keta dawomata a kwanya Tunawa tayi da yadda yasa yatsa baki dazun yana kallon sama alamun tunani saikace wani yaro da yadda yawani yamutse fiska yana ta6ula baki Girgiza kai tayi, tun ba yau ba tasan shi da wannan sakatar amma tana mammakin yadda shagwa6a kemishi kyau bayan shi namijine. Wait... Kyau? Yaushe ma tafara tantance kyaunshi? Tambayar datayi ma kanta kenan No, su6utar tunani ne, bazai ta6a yimata kyau a idanu ba bare harya burgeta, taqarasa zancen zucin tana murguda baki ita kadai *remember promise bashi ne and I don't forgive debt* Maganarshi ta dazun ta dawomata Murmushi tadan saki na gefen tana dan daga gira tace "Then I'll break your record" Ta jima ahaka tanata tunane tunane wanda duk na abubbuwan dasuka faru yaune kafin barci ya sadado ya figeta batareda ta saniba Can cikin barci taji kamar ana tashinta, yamutse fuska tayi tana qara damkar bargon jin kamar za'a janye "Wohoho aunty wai wannan wane irin barci ne haka?" Inji baby tana qara janye bargon Dakyar saudart ta bude idanunta dasukayi mata nauyi ta kalleta "Haba aunty wannan barci kamar na mutuwa? Lallai yaya zaisha fama, kinsan ko tun yaushe nake tadaki?" Harara saudart ta gallamata tana miqewa zaune, wai nacikin Masai ne zai cewa na waje ka taka kashi. Miqa tayi tanajin kamar tasake komawa ta kwanta don kwata kwata barcin be isheta ba jitake kamar yanzu ta kwanta aka sake tadata Saukowa tayi daga kan gadon tanufi toilet jin wasu wuraren har an fara assalatu. Alwalla ta dauro sannan tadawo dakin ta saka hijab tazo ta tsaya kusada baby data fara sallarta itama ta kabbarta nata tashiga yi. Yau bata tsaya azkar din safe data saba ba tana gamawa tayi yan addu'o'i ta shafa ta miqe ta cire hijab dinta ta koma kan gado Girgiza kai baby dake zaune kan sallaya tana azkar tayi tana mammakin irin wannan barcin nata Ba ita ta sake farkawa ba sai wajajen 10 na safe Tashi tayi zaune tana karanto addu'ar tashi tana miqa at the same time. Kallon gefe tayi taga baby ce kwance itama tana shar6ar barcinta. Komawa tayi ta jingina da jikin gado tana mammakin mafarkin datayi yanzu. Wai ashraf ne ke nemanta akan tazo ta kawomashi coffee dinshi as promised shine ta shigo daki aguje ta boye gefen gado tsakanin bedside locker da gadon tareda rufe bakinta da hannu bibbiyu donma kartayi kwakwarrar motsi Batafi seconds biyu ba da buya sai gashi shima ya shigo dakin yana waige waigen nemanta Qara lafewa tayi tareda qara toshe bakinta ganin yadda yakebin lungu da saqo yana nemanta. Saida yagama hange hangenshi be gantaba ya haqura yanufi kofa Ganin haka yasata sauke Ajiyar zuciya 6oyyaya cikin jindadin rashin ganinta Saida Yakama handle din kofar zai bude kamar ance ya waigo sai suka hada ido da ita a inda take Hakan yasata saurin miqewa tsaye tana sakin qara wanda yayi daidai da farkawarta. Ajiyar zuciya ta sauke bayan tagama tuno mafarkin tana mammakin yadda abinda yafadi jiya ya tsaya mata arai har tayi mafarkinshi don dama ita idan Abu ya tsayamata arai sosai saitayi mafarkinshi Tashi tayi ta sauko daga gadon tanufi toilet don tayi freshen up *** Ringing din wayarshi ya sashi dakatawa daga tsane jikinshi dayake da qaramin towel din hannunshi Nufar mirror yayi yajawo wayar yaduba, ta6e baki yayi ganin mai kiran Saida takusan katsewa sannan ya daga ya kara a kunne yace "Uhum?" "Ango! Ango!! Ango!!! Ango kasha qamshin ne koko dasaura?" Inji sadeeq cikin shaqiyanci Tsaki ashraf yaja yace "Fadi abinda zaka fadi am busy right now" "Inyee? Ka fadi hakan Ai amma wajen neman taimako ka iya marairaicewa kana qanqan da kai kamar dan maula" "Mtcheew, kamar yadda nafada maka dazu am busy so idan bakada abin fada kindly hang the call" "You're busy doing what?" Sadeeq ya tambaya in a naughty way "Bansàniba" "Kar Allah yasa kasani, dullie kawai wanda besan arziqiba" inji sadeeq cikin son qular dashi "Naji nagode, Ai kai kasan shi ko? Hakan Ai ya wadatar" ya amsa in an i-dont-care mannar "Mtcheew ba laifinka bane, laifinane Dana kiraka" "Gwara daka gane hakan, gwauro kawai" "Gwauraye dai" "Kana hauka, waye gauron, kai bakama ji kunyar fadin haka ba" "Kunyar me? Ba gaskiya bane?" "Oho dai, idan zaka ajiye shiririta kayi aure ka aje kayi don na kusan Barin mu'amala da gwauro" yafada yana taje kanshi "Hmm wai kura zatacema kare maye, kai har kanada bakin yima wani gori? Aikin banza kawai bansan abinda yasama na kirakaba at the first place, mtcheew mood spoiler kawai" yana kaiwa nan ya katse wayar I 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 (Ummin fasihu) 095 Ahaka suka samu suka ida saukowa falon wanda yake dirim sai dan dim light blue colour dayadan haska falon Direct kitchen suka nufa, ashraf ya bude kofar ya matsamata ta shiga sannan yabi bayanta tareda maido kofar ya rufe. Kunna kwan wutan kitchen din yayi ya hangota daga can nesa tana kallonshi Daga mata gira daya yayi alamun kallon fa? Janye idanu tayi ta kalli wani 6arin kafin tace "I think basai an rufe kofar ba" Daga gira daya yayi kafin yace "Kinaso tsautsayi yasa ummy ta sauko ta hango kitchen din da haske? Inkuma bakiso dan sai a bude kofar a kashe wutan saina haska phone dina" yafada yana yunqurin kashe wutan kitchen din "No, ka barshi kawai" tayi saurin dakatar dashi da hakan sannan ta juya tanufi inda qaramin electric kettle yake ta fiddoshi ta dauraye sannan ta zuba ruwa ciki tayi plugging dinshi jikin socket Duk abinda take yana nan zaune kan fridge yana binta da kallo duk inda tayi yanajin wani nishadi a zuciyarshi Haka saudart taita kiciniyar hada coffee din saidai duk abinda take fuskarnan a kumbure take kamar mai shirin yin bindiga yayinda can qasan ranta take danasanin nacewa datayima ummy akan tabarta tayi girkin In less than 10mins tagama hada black coffee din ta juye a mug ta Dora a saucer ta azasu bisa wani qaramin tray sannan ta dauka tajuyo tanufoshi dasu. Kallon dai dayake mata ya cigaba dayi harta qaraso wajenshi ta Dora dan tray din saman fridge din kusadashi sannan ta juya zata wuce Cafke hannunta yayi hakan yasata tsayawa batareda ta juyoba "Ina zaki bayan baki gamaba?" Juyowa tayi ta gallamashi harara batareda tasan sadda tayi hakan ba tace "Menene kuma? Kace na hadamaka coffee na hada, what again?" "Menene deal dinmu? Zaki hada coffee kikaimin apartment dina ko ba hakaba? Nan yayimaki kama da apartment dina?" Wani malolo ya taso ya tokarewa saudart maqoshi, fizge hannunta tayi afusace tasake juyawa zata wuce Shan gabanta yayi saurin yi yana cewa "Where did you think you're going?" "Look mallam wai what's wrong with you ne? You said I should make you a cup of coffee, nayi kuma yanzu saika qirqiro wani abin? What exactly did you want from me?" Tafada atsakankanin haqoranta cikin fushi fuskarta na dayi jaja jaja "I want you to fulfill our deal, meyasa kika amince bayan kinsan you can't do it? Ni ba ruwana, I want my coffee in my room, final" Tsayawa tayi tana kallonshi tinda yafara harya kai aya sannan tayi Ajiyar zuciya tace "If not?" Matsowa yaqara yi dab da ita sannan yace "If not mu kwana anan" Kallonshi takeyi, a yanayin dayake bataga alamun wasa ba a tattare dashi kuma taga alamun zai iya din besides ita zata kwan aciki don bashida asara Sam Juya idanuwanta tayi tana cije lips kafin tace "Ok I promised zan kawomaka amma gobe, kaga yanzu dare yayi and ummy can wake up at any moment ta leqomu, please let me go I promised zan kawomaka wani gobe, ok?" Tafada cikin rarrashi kamar irin tanama yaro wayau Daga idanu yayi sama yana kallon saman ceiling kamar mai shawara hakan yasata qara cewa "You see yau da gobe duk dayane, it's just some hours to go, I promised zan kawomaka har dakin" tafada a tausashe burinta kawai tayi convincing dinshi ya yarda kota huta Yatsarshi manuniya yasa a baki yana cizonshi still idanunshi sama yana tunani, itadai saudart kallonshi take tana addu'ar Allah yadorata kanshi Sauke hannun yayi ya kalleta yana dan yamutse fiska sannan yace "Promise?" Har tarar numfashinshi take wajen fadin "Yes..yes promise" tana dan wara dara daran idanunta "Ok amma remember promise bashi ne and I don't forgive debt" "Yes I know" tabashi amsa "Good, now give me the coffee" Abinka ga mai nema babu musu ta qarasa fridge din ta dauko mug din tadawo ta bashi Amsa yayi yana kallonta, juyawa tayi ta nufi kofa da sauri don a qagare take taganta daki Jin kamar ana binta yasata tsayawa tareda juyowa "Zan rakaki ne" yafada yana dan daga hannuwa Batace komaiba tajuya taci gaba da tafiya shima yabiyota saida yakashe wutar kitchen din sannan yafito ya rufe kofar sannan yabiyo bayanta don hartayi Rabin stairs don sa6anin dazu yanzu da sauri take tafiya jitake kamar ummy zata fito su hade ne. Dakyar tasamu ta ida hayewa tayi saurin nufar kofar su ta bude tq maida ta rufe batareda ta tsaya sake mashi kallo biyu ba ta danna sakata sannan takoma ta jingina da kofar tana sauke wata wawuyar Ajiyar zuciya. Murmushi yasaki sannan ya kada kai ya juya yafara sauka qasa yana sipping din coffee dinshi Sosai yayi missing din coffee dinta hakan yasashi gamawa dashi cikin dan qanqanin lokaci ya maida mug din kitchen ya rufo ya fito ya nufi apartment dinshi cikin nishadi. Tashi tayi daga jinginar datayi a qofar tana sake sauke wata Ajiyar zuciyar sannan ta nufi gadon tana kallon baby data kanannade acikin bargo tanata shar6ar barcinta hankali kwance Girgiza kai tayi tana mammakin irin wannan barcin nata, wannan tasan har asace bazata saniba Cire zumbuleliyar hijab dinta tayi ta ninke ta maida wardrobe sannan ta zagaya dayan gefen ta haye gadon tajawo bargon dakyar ta lullu6e kasamcewar duk baby ta kanannade ciki sannan ta lumshe idanu Ga mammakin ta jitayi barcin yaqi zuwa, saima abubbuwan sasuka faru dazun keta dawomata a kwanya Tunawa tayi da yadda yasa yatsa baki dazun yana kallon sama alamun tunani saikace wani yaro da yadda yawani yamutse fiska yana ta6ula baki Girgiza kai tayi, tun ba yau ba tasan shi da wannan sakatar amma tana mammakin yadda shagwa6a kemishi kyau bayan shi namijine. Wait... Kyau? Yaushe ma tafara tantance kyaunshi? Tambayar datayi ma kanta kenan No, su6utar tunani ne, bazai ta6a yimata kyau a idanu ba bare harya burgeta, taqarasa zancen zucin tana murguda baki ita kadai *remember promise bashi ne and I don't forgive debt* Maganarshi ta dazun ta dawomata Murmushi tadan saki na gefen tana dan daga gira tace "Then I'll break your record" Ta jima ahaka tanata tunane tunane wanda duk na abubbuwan dasuka faru yaune kafin barci ya sadado ya figeta batareda ta saniba Can cikin barci taji kamar ana tashinta, yamutse fuska tayi tana qara damkar bargon jin kamar za'a janye "Wohoho aunty wai wannan wane irin barci ne haka?" Inji baby tana qara janye bargon Dakyar saudart ta bude idanunta dasukayi mata nauyi ta kalleta "Haba aunty wannan barci kamar na mutuwa? Lallai yaya zaisha fama, kinsan ko tun yaushe nake tadaki?" Harara saudart ta gallamata tana miqewa zaune, wai nacikin Masai ne zai cewa na waje ka taka kashi. Miqa tayi tanajin kamar tasake komawa ta kwanta don kwata kwata barcin be isheta ba jitake kamar yanzu ta kwanta aka sake tadata Saukowa tayi daga kan gadon tanufi toilet jin wasu wuraren har an fara assalatu. Alwalla ta dauro sannan tadawo dakin ta saka hijab tazo ta tsaya kusada baby data fara sallarta itama ta kabbarta nata tashiga yi. Yau bata tsaya azkar din safe data saba ba tana gamawa tayi yan addu'o'i ta shafa ta miqe ta cire hijab dinta ta koma kan gado Girgiza kai baby dake zaune kan sallaya tana azkar tayi tana mammakin irin wannan barcin nata Ba ita ta sake farkawa ba sai wajajen 10 na safe Tashi tayi zaune tana karanto addu'ar tashi tana miqa at the same time. Kallon gefe tayi taga baby ce kwance itama tana shar6ar barcinta. Komawa tayi ta jingina da jikin gado tana mammakin mafarkin datayi yanzu. Wai ashraf ne ke nemanta akan tazo ta kawomashi coffee dinshi as promised shine ta shigo daki aguje ta boye gefen gado tsakanin bedside locker da gadon tareda rufe bakinta da hannu bibbiyu donma kartayi kwakwarrar motsi Batafi seconds biyu ba da buya sai gashi shima ya shigo dakin yana waige waigen nemanta Qara lafewa tayi tareda qara toshe bakinta ganin yadda yakebin lungu da saqo yana nemanta. Saida yagama hange hangenshi be gantaba ya haqura yanufi kofa Ganin haka yasata sauke Ajiyar zuciya 6oyyaya cikin jindadin rashin ganinta Saida Yakama handle din kofar zai bude kamar ance ya waigo sai suka hada ido da ita a inda take Hakan yasata saurin miqewa tsaye tana sakin qara wanda yayi daidai da farkawarta. Ajiyar zuciya ta sauke bayan tagama tuno mafarkin tana mammakin yadda abinda yafadi jiya ya tsaya mata arai har tayi mafarkinshi don dama ita idan Abu ya tsayamata arai sosai saitayi mafarkinshi Tashi tayi ta sauko daga gadon tanufi toilet don tayi freshen up *** Ringing din wayarshi ya sashi dakatawa daga tsane jikinshi dayake da qaramin towel din hannunshi Nufar mirror yayi yajawo wayar yaduba, ta6e baki yayi ganin mai kiran Saida takusan katsewa sannan ya daga ya kara a kunne yace "Uhum?" "Ango! Ango!! Ango!!! Ango kasha qamshin ne koko dasaura?" Inji sadeeq cikin shaqiyanci Tsaki ashraf yaja yace "Fadi abinda zaka fadi am busy right now" "Inyee? Ka fadi hakan Ai amma wajen neman taimako ka iya marairaicewa kana qanqan da kai kamar dan maula" "Mtcheew, kamar yadda nafada maka dazu am busy so idan bakada abin fada kindly hang the call" "You're busy doing what?" Sadeeq ya tambaya in a naughty way "Bansàniba" "Kar Allah yasa kasani, dullie kawai wanda besan arziqiba" inji sadeeq cikin son qular dashi "Naji nagode, Ai kai kasan shi ko? Hakan Ai ya wadatar" ya amsa in an i-dont-care mannar "Mtcheew ba laifinka bane, laifinane Dana kiraka" "Gwara daka gane hakan, gwauro kawai" "Gwauraye dai" "Kana hauka, waye gauron, kai bakama ji kunyar fadin haka ba" "Kunyar me? Ba gaskiya bane?" "Oho dai, idan zaka ajiye shiririta kayi aure ka aje kayi don na kusan Barin mu'amala da gwauro" yafada yana taje kanshi "Hmm wai kura zatacema kare maye, kai har kanada bakin yima wani gori? Aikin banza kawai bansan abinda yasama na kirakaba at the first place, mtcheew mood spoiler kawai" yana kaiwa nan ya katse wayar Dariya ashraf yayi yana ajiye wayar kan mirrorn yanufi closet dinshi Agurguje ya shirya cikin wasu qanannun kaya wando da T-shirt baqaqqe tareda feshe jikinshi da turarenshi mai dadin qamshi ya dauki wayoyinshi ya fice daga dakin...✍️ Manage pls👏 Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 097 Dole ta tashi tabar falon jin ana kiraye kirayen sallar magrib Alwala ta dauro tazo ta gabatar da sallar magrib ta zauna bayan ta ida ta zabga uban tagumi Tunani kala kala na kai kawo a kwakwalwarta "To ko fushi yayi? Amma Ai ita yayima laifi meyasa shi ke fushin kuma?" Tambayar datake tayi ma kanta kenan Tarasa dalilin dayasa rashin kulawarshi agareta na yini daya yayi affecting dinta sosai har haka Gashi ego dinta ya hana ta lalubeshi ta waya koda ta text dinne, gani take hakan zubda mutunci ne agareta. Tana nan zaune tana karatun jaki har aka fara kiraye kirayen isha'i, saida ta chanzo alwallarta sannan tazo ta gabatar da ita itama Zaune suke a dining sunayin dinner Ummy tun dazu take nazartar saudart ganin yadda take tsakurar abincin kamar bataso dama tana lura da ita duk yau kamar bata cikin walwalarta don takoma wata sukuku daita "Daughter?" Dagowa saudart tayi ahankali ta kalleta "Meke damunki ne? Is anything bothering you?" Ta tambaya cikin kulawa Itama baby tsayar da cin abincinta tayi tana kallonta don itama tun dasafe ta lura yau Auntyn tata bata cikin walwala don ko magana bata cika son yiba Murmushin yaqe saudart tayi tace "Am fine ummy, kawai am not feeling well ne" "Me yasameki to, is it fever?" Tafada tana ta6a wuyanta donjin temperature dinta "No ummy kawai slight headache ne kuma banida appetite" ta amsa asanyaye Cikin jimami ummy tace "Eyyah, now ki daure kiqara cin abincin ko yayane saina baki medicine, ok?" Gyada mata Kai tayi ta dauki spoon dinta "Sorry aunty" inji baby Itama kadamata Kai tayi tashiga cigaba da tura abincin badon dadi ba She's just missing him so very much Ayyanawa take aranta da yananan da yanzu yananan ya takurata da wannan mayen kallonshi, da yanzu duk hada idon dazasuyi sauya kashe mata ido, da yanzu yakusan cika mata waya da texts Haka dai tasamu tadan qaracin abincin, ummy ta rakata sama ta 6allamata maggunguna tasha ta kwanta bisa umarnin ummy Tana cikin bargo taji ummy na waya da ashraf Shiru tayi cikin bargon tana sauraronta harsukayi bankwana Dago wayar dake hannunta tayi tacikin bargon tana kunnata tana kallonta Gani take kamar daya gama wayar da ummy zai kirata or yaturo text amma har aka kusa shafe awa ba kodaya daga ciki dayayi *why are you angry?* ta tambayi kanta still tana kallon wayar *Are you fed up with me already?* *am I too harsh?* duk wadannan zantukan acikin zuciya takeyinsu Lumshe idanu tayi tanajin zuciyarta na daci sosai *am missing you.... So much* tafada under her breath tana dora wayarta akan qirjinta tareda rungumeta Ahakan barci ya dauketa batareda ta saniba A bangaren A.A kau dama tun jiya sukayi arranging meeting da wani company mai muhinmmanci Koda saudart taqi kulashi kyaleta yayi ya kwanta saidai Sam barcin yaqi zuwa hakan yasashi tashi yajawo laptop yadan rage ayyuka wanda hakan yasashi raba dare sai can wajajen uku yasamu ya kwanta Da asuba bayan yagama sallah kawai yahau shirin office dukda zuciyarshi na azalzalarshi akan yakira saudart ko yamata text yadda yasaba saikuma ya fasa acewar gwara yabata space tahuce ganin yadda tahau sosai jiya inda shi harga Allah besan hakan zai 6atamata rai ba Koda yafito don gaida ummy sai yaci karo daita a kitchen hakan yasa besamu Damar haurawa sama ba Dayake sauri yake ko break be tsaya yayi ba yawuce zuciyarshi cikeda son ganinta A office kau tunda yaje yashiga busy don aiki ne sosai a desk dinshi kasancewar yayi sati rabonshi da office din kuma be samun damar ragewa a gida sanaddiyar shiriricewa dayake da saudart ta waya Ga kuma meeting din dazasuyi wannan yasa be dawo gidaba sai wajajen 10 don sosai aikin ya riqesu gashi ba secretary bare adan samu saukin aikin Koda yadawo a matuqar gajiye yake hakan yasa yanufi part dinshi kai tsaye yayi wanka yayi shirin barci don dama yayi dinner awaje, hakan yasashi kiran ummy yayimata saida safe don a yadda yake agajiyen nan be iya sake fitowa Koda suka gama waya saida yashiga contact dinta yanaji kamar ya kirata sai kuma wata zuciya tace mashi ya kyaleta kawai yadan bata space yadda zata huce sosai hakan yasashi ajiye wayar ya shige cikin duvet nan da nan barcin gajiya yayi awon gaba dashi 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 Washegari ma tun bayan sallar asuba yayi shirin office don yau dinma sunada aiyuka da meeting masu muhinmmanci dazasuyi. Wajajen 7:30am yafito daga part dinshi yashigo cikin gida saida suka gaisa da maid dinsu dake falo tana mopping sannan ya haura sama dakin ummy Saida ya kwankwasa sau biyu sannan ummy tabashi izinin shigowa Da sallamarshi yashiga yaci adonshi cikin blue suit da farar inner yayi kyau sosai sai baza qamshi yake Amsawa ummy dake zaune akan sallaya hannunta riqe da hisnul Muslim tayi tana dagowa daga littafin Zaunawa yayi shima qasa kusada ita yana satar kallon saudart dake qudundune a bargo da alamu ma barci take Gaida ummy yayi cikin girmamawa yana dora kanshi kan kafadarta Shafa kanshi tayi tana amsawa tana tambayarshi ya gajiyar jiya Amarairaice yake amsamata da alhamdullilah Maganar breakfast tayi mashi yace A'a zaiyi acan yanzu sauri yake Haka yatashi sukayi sallama da ummy yana qara satar kallon saudart da batasan wainar da akeyi ba ya fita Abakin kofa yaci karo da baby itama zata shigo Gaidashi tayi ya amsa yayi gaba Binshi tayi saurin yi tana fadin "Please yaya inzo ka ragemin hanya?" Banza yayi daita kamar bazai amsaba saikuma yace "Don't waste my time" Da sauri tajuya tashiga dakin ummy tayimata sallama a tsaitsaye ta fito tana gyara zaman jakkarta dake dauke da few books ta sauka da sauri gudun karya wuce yabarta A parking space ta ganshi yana niyyar shiga mota hakan yasata saurin qarasowa itama ta bude dayan side din ta shiga ya kunna motar yaja suka fice daga gidan Sai wajajen 9:30 saudart ta tashi barcin da ummy tasata dole takoma Dama tana gama sallah da azkar dinta ta tashi zata gyara dakin ummy tasata takoma ta kwanta ganin haryanzu komai sukuku take yinshi kamar marar lakka Tana kwanciya ba dadewa wani barci mai shegen dadi yayi gaba daita kasancewar dama jiya bawani barcin kirki tayiba Batafi minti 15 da barci ba ashraf shikuma yashigo Addu'ar tashi ta karanto tana yaye bargon jikinta Dumm gabanta ya bada jin qamshin da mutum daya tasani dashi waige waige tashigayi a dakin kafin ta sauko qasa tana qara shaqar qamshin Tabbas qamshinshi ne, hakan na nufin yashigo dakin? When? Bude kofar da akayi yasata dagowa ta kalli saitin kofar Ummy ce tashigo cikin fara'a tana cewa "Daughter kin tashi? Ya jikin?" Murmushi tayi tana cewa "Da sauki ummy" "To masha Allah, maza kiyi brush ki sauko ki karya" Da to ta amsa tashige toilet domin yin yadda ummin tace Koda ta sauko har an ajiye mata abincin, abakin maid dinsu takejin baby ta tafi makaranta tarema suka fita da Ashraf Sosai ranta ya dagule fiyeda jiya ma, jitake komai yabar mata dadi, jitake kamar ta shekara bata ganshi, she's missing everything about him Yauma haka ta wuni sukuku saidai she's trying her best wajen nunama ummy she's normal don sosai ummy ke nuna damuwarta akanta. Wajajen two baby tadawo gidan hakan yasa tadanji sauqi sauqi saboda surutu da ban dariyar baby yadan rage mata damuwarta *6:15pm* Saukowa tayi daga sama hannunta riqe da qaramin bowl data gama shan farfesun cow leg da ummy tabata wanda yaji kayan qamshi da maggunguna masu inganci Shiga tayi kitchen ta dauraye bowl din ta maidashi ma'ajinshi sannan tafito daga kitchen din tana dan yarfe hannayenta Cak ta tsaya da abinda take tana kallonshi zuciyarta na chanza bugu Ashraf da dawowarshi kenan yana zaune akan kujera ya duqa yana zare socks din kafarshi ya dago shima idanunsu suka gauraya Kasa janye idanunta tayi akanshi tacigaba da kallonshi wani emotional feeling na tasomata daga Chan qasan zuciyarta Shima hakan take agareshi, kafeta yayi da idanunshi kamar zaiyi devouring dinta yana sake jin kewarta acikin zuciyarshi Sun kai kusan two minutes suna kallon juna kafin ashraf ya tashi ahankali ya nufota Kallonshi tacigaba dayi idanunta na kawo kwallar da batasan dalilinta ba harya qaraso gabanta Sai a lokacin ta sauke idanunsu qasa wanda yayi daidai da digar hawayen idanunta Dago ha6arta yayi yana kallon fuskarta hakan yasata saurin lumshe idanunta wanda hakan yaba sauran hawayen damar gangarowa Da mammaki yake kallonta don besan dalilin wadannan hawayen ba "Saudart..." Saurin juyamashi baya tayi gabanta na bugawa sosai yayinda hawayen ta yaqi tsayawa Ganin haka yasashi zagayowa ta gabanta yasake fuskantarta Saurin rufe fuskarta tayi da tafukan hannu don batason yaga hawayen gashi ita ta kasa tsaidasu Shiru yayi yana kallonta na wani lokaci kafin yace "Saudart.." Nanma shiru kuma bata sauke hannunta ba daga kan fuskar "Are you still angry?" Ya tambayeta a tausashe Nanma bata motsaba saima qara gudu da hawayenta sukayi "Am sorry uhm? I don't mean to scared you" yafada almost in wishper Nanma batace komaiba "Please open your face"yasake fada amma bata bude ba "Are you still angry?" Yasake tambayarta cikin damuwa Shiru tayi bata kuma janye hannun daga fuskarta ba "My presence is irritating you ko? Intafi?" Yaqara tambayarta cikin sanyi Samun kanta tayi da girgiza mashi kai ahankali "Then ki bude fuskarki please" yafada yana janye hannunta hakan yasa tayi saurin Zamewa ta zauna qasa tana cusa fuskarta a tsakankanin qaffafunta Murmushi ya su6uce mashi shima yabita qasan ya zauna yana kallonta na wasu daqiqu yace "Wai 6oye fuskar dikna menene?" Banza tayi dashi takuma qi dagowa Murmushi yasake saki sannan ya matso da fuskarshi dab da tata yace "Did you miss me too?" Sai a sannan ta dago fuska sha6e2 da hawaye ta gallamashi harara ta maida fuskar a inda ta dagota Dariya sosai tabashi hakan yasashi yin kayanshi Sake dagowa tayi ta kalleshi ta 6ata fuska ganin yadda yake mata Dariya Yunqurawa tayi zata tashi yayi saurin kama hannunta yana Dariya yace "It ok, it ok na daina" yafada yana dan toshe baki da dayan hannun fuskarshi dauke da murmushi Dan kawar da kai tayi tana dan murmushi, aabin mammaki jitayi zuciyarta wasai babu digon damuwa ko kadan saima farincikin daya maye gurbinshi Tankwashe kaffafu yayi ya buga tagumi da hannu bibbiyu yace "Now tell me, wadannan hawayen na menene?" Harara taqara gallamashi tana saka bayan hannu tana goge fuskar Wani white handkerchief yafiddo daga aljihunshi yabata Saida tadago ta kalleshi sannan ta amsa ta ida goge fuskar tanayi tana shaqar qamshin handkerchief din "Inaji, why those tears?" Yasake tambaya yana kallonta Qin dagowa tayi bare tabashi amsa "Oho? Nagane, saboda Karna tambayi coffee Dina ko? Hard luck👎🏻 don wannan bazai ceceki ba" Qara dagowa tayi ta dan harareshi "That also won't save you miss emoji, I'll make sure you learn a lesson" Sinne kai tayi tana Dariya marar sauti jin yace mata miss emoji Qara kusanto da fuskarshi yayi da nata yace "Yanzu gayamin, did you miss me?" Dagowa tayi ta kalleshi tadan yamutse fuska tace "No?" Kamar a sigar tambaya Wara idanu yayi harda dan bude baki yace "Really?" "Ni kau kinga you're sticked to my brain, ina aiki amma ke nake hange, because of you saida nayi mistakes dayawa wanda saboda cancelling da retyping kalli yadda yatsuna sukayi swelling ga wancan annoying fringe daya tasani gaba da ban haushi, Abu ya hademin goma da ishirin kamar inyi hauka shine zaki ce bakiyi missing dinaba nima? Kai amma kin gama dani" yaqarashe zancen yana dafe Kai🤦🏻‍♂️ Dariya yabata sosai hakan yasata sadda kai tanayi ahankali ga wani farinciki dake sake lullu6e zuciyarta Zai sake magana yaji gyaran murya a bayanshi hakan yasasu juyowa gabadaya Baby ce tsaye tadan Sosa qeya tace "Erm... Dama ummy tace na gayamuku Ku tashi kuyi sallah" Waro idanu saudart tayi tayi saurin miqewa tsaye don ita tama manta inda suke saboda shagala Shima miqewa yayi yana kallon wristwatch din hannunshi yaga bakwai da kusan rabi, tuni aka gama magrib sai batun isha'i kuma Saurin bin bayan baby da tuni tayi gaba Dariya fall cikinta tayi yayinda shikuma yabita da kallo Saida takai bakin stairs zata taka saikuma tajuyo Hada idanu sukayi ya kashe mata ido daya, saurin juyawa tayi ta haurawarta tana smiling itama Saida ta 6acema ganinshi sannan ya kauda kai yana murmushi hadi da shafa kanshi Zira takalminshi yayi yafice shima yanufi part dinshi dauke da murmushi a fuska...✍️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 098 Koda saudart ta haye saman kasa shiga dakin ummy tayi, tayaya zata iya facing din ummy? Wataqila ma ta gansu Ta dade a bakin kofar tana shawarar shiga, ganin dai bata iyawa din yasata chanza akalarta zuwa dakin baby Jin an bude kofa yasa baby dagowa tana kallon kofar Tana ganin itace ta fashe da Dariya tana toshe baki Ko gefenta saudart bata Kalla ba tanufi toilet Alwala ta dauro tadawo ta zari hijab cikin wardrobe tahau sallayar da baby ta shimfida mata ta kabbara sallah Koda ta ida har wasu massallatan sun fara isha'i don haka itama tashi tayi ta jona da ita *DINNER* zaune suke su uku suna cin abincin dare in silent Tun saudart na dari dari da ummy harta dan saki jiki ganin ummy bata wani nunamata komai ba Abincin takeci saidai rabin hankalinta naga kofar shigowa, she's wondering why haryanzu be shigo yin dinner ba Haka kawai saita samu kanta da damuwa da hakan tanajin abincin ma na fita kanta Sunyi nisa acin abincin taji screeching din handle din kofa hakan yasata saurin dagowa tana kallon saitin Bayyanarshi yasata jin wani sanyi na ratsa zuciyarta yana maye gurbin damuwarta Janye idanunta tayi cikin jin kunyar kamata dayayi tana kallonshi ta maida kan abincin ta tana tsakura Da sallama yashigo dining area din ya chanza shiga zuwa blue three quarter da farar T-shirt Duk amsa mashi sallamarshi sukayi yaja kujerar dake facing din saudart ya zauna yana kallonta ta qasan ido Baby ce ta gaidashi ya amsa yana janye idanunshi daga kanta sannan ya dago ya kalli ummy yana gaidata Amsawa itama tayi agajarce tana cigaba da cin abincinta Dago idanu tayi da niyyar Satan kallonshi sai kawai suka fada cikin nashi kasancewar dama ita yake kallo Kashe Mata ido yayi kamar yadda yasaba idan suka hada ido Janye idanunta tayi dan murmushi na su6uce mata itama ta gaidashi asanyaye Amsawa yayi in joy sannan yasa hannu ya janye plate din abincinta ya maido gabanshi yahau ci batareda ya damu da kallon reaction dinta ba Dagowa tayi ta kalleshi tana 6ata fuska ganin beko dagoba bare yasan tanayi ba yasa tadan saci kallon ummy taga ita abincinta ma takeci da alama ma batasan abinda sukeba Hakan yasata satar kallon baby itama, kashe mata ido baby tayi tana sunkuyar dakai don 6oye dariyarta Janye idanunta tayi daga kanta ta zari wani plate din taqara serving kanta wani abincin Gamawarta keda wiya taga anqara janye plate din an turomata wancan na dazu wanda yanzu babu komai ciki don dama abincin ciki bawani mai yawa bane Sagale tayi tana kallon plate din leftover din sannan ta dago ta kalleshi Daga mata gira daya yayi tareda sakin murmushin gefen baki na mugunta yacigaba dacin abincin shi yana kada Kai Janye idanunta tayi tareda sadda kai cikin rashin sanin abin yi Jin qarar jan kujera baya yasata dagowa taga Ashe ummy ce ta tashi tana goge bakinta da tissue Batace komaiba tabar dining din tahayewarta sama Ganin haka yasa itama baby shan ruwa ta tashi tun kafin akoreta itama tabar wajen cikeda jin haushin buqulun da ummy tayimata na ganin qarashen show dinsu Barin baby wurin keda wuya itama saita matsar da kujerarta baya zata tashi yayi saurin dafe hannunta yana dagowa tareda sakarmata idanunshi Dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta maida kanta qasa sanaddiyar kwarjinin dayayi mata Tashi yayi ya dauki plate din abincinshi ya zagayowa wajenta yajawo wata kujera ya maidota gefenta ya zauna ya ajiye plate din gaban su yaqara spoon daya aciki ya tura plate din gabanta yana cewa "Oya eat" Bata dagoba saima wasa datakeyi da zoben yatsarta tanajinta amatuqar takure a dalilin kusancinsu ga qamshin turarenshi daya addabi qoffofin hancinta Ganin taqi kulashi yasashi debo abincin a spoon yakai saitin bakinta Dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta kauda kai "Open up mana" yafada yana sake binta da cokalin abincin qara kauda kai tayi tana cewa "am full" "You're not, idan dagaske kin qoshi meyasa kika zubo wannan?" Qara janye fuska tayi ganin yana qara nufota da spoon din tana cewa "Allah na qoshi" "Baki isaba" yafada yana qara matsowa zaibata da tsiya hakan yasata yunqurawa zata tashi yayi saurin maidota ya zagayo hannunshi ta tiny curvy waist dinta yayi pulling dinta ajikinshi Waro manyan idanuwanta tayi in shock tayi saurin sa tafukan hannu ta dafe broad chest dinshi ganin jikin su na neman hadewa Wani yanayi ashraf yajishi aciki don sosai contact dinsu yakawo effect agareshi "Now open up" yafada cikin muryarshi data fara chanzawa Atsorace take kallonshi ga kuma yadda tsigar jikinta ke tashi sosai Saurin kauda kai tayi again ganin yaqara nufota da spoon din Yatsunshi biyu ya luma mata a kwarin kugunta wanda yasata saurin zabura ta fada jikinshi tana gasping. Lumshe idanuwa yayi jinta ajikinshi yasaki cokalin hannunshi ya maida hannuwanshi ata bayanta ya rungumeta yana sauke nannauyar Ajiyar zuciya Itama lafewa tayi a jikinshi idanuwanta a lumshe tana qara shaqar qamshin turarenshi mai sanyin dadi Ga wani sense of security datake ji jinta acikin warm broad chest dinshi Shima lumshe idanunshi yayi yana inhaling qamshinta yanajin kamar su dawwama ahakan Sun dauki tsawon lokaci ahakan batareda sun Ankara ba don gabadayansu sun gama lulawa wata duniyar daban Jin saukar numfashin shi a gefen wuyanta yasata bude lumssasun idanunta da sauri, ganinta acikin qirjinshi yana sake qoqarin cusa kanshi a wuyanta yasata saurin dagawa daga jikinshi tana ja baya Kasancewar a kasalance yake yasashi kasa riqeta sai komawa dayayi da baya ya jingina da kujera ya sakarmata idanunshi dasuka fara chanza launi Tashi tayi da sauri ta nufi hanyar barin dining din Binta da kallo yayi a kasalance harta bar wajen sannan ya maida kanshi jikin kujera ya lumshe idanu yana sauke numfashi ahankali Ya dade sosai ahakan kafin yafarajin dan daidai, dakyar yatashi yafice daga part din yanufi part dinshi cikin jan kafa Saudart ma dakyar takai sama saboda harhardewa dataitayi Tana kaiwa sama dakin baby kawai ta nufa ta bude kofa tashiga Hango baby tayi tayi daidaya agadon tanata sharar barcinta hankali kwance Qarasowa tayi ciki a kasalance ta fada gadon itama tayi ruff da ciki tareda lumshe idanuwa A bangaren ashraf kau abin juyemashi yasoyi don ya tadowa kanshi 6alli, shima ruff da ciki yayi hannunshi dafe da mara Shikanshi yasan yau sai Allah dama ya lafiyar giwa? Gashi shi Bashan maggungunan nan yakeba tun can acewarshi bazai cutar da kanshi ba don sha'awa sign din lafiya ne rashinta shine cuta don me zai cutar da kanshi da kanshi? Ya dade ahakan idanunshi lumshe yana daddana wajen daya qulle tamau har can wani wahallalen barci yayi gaba dashi WASHEGARI Tun ana kiran farko ta tashi ta tada baby suka dauro alwalla tare suka gabatar da sallah. Baby bata zauna ba ta tashi tahau shirin makaranta kasancewar sunfara exams Tana nan zaune har baby tagama shirinta saita tashi suka fita tare zuwa dakin ummy domin gaidata Koda suka shiga isketa sukayi tana qoqarin gyara gadonta Shigowarsu yasata juyowa tana amsa sallamarsu tare suka gaidata cikin girmamawa ummy ta amsa cikin jindadi tana tambayar baby badai harta shirya ba Amsamata tayi da eh yau exams din safe garesu nan ummy tace sutafi qasa tayi mata package din breakfast idan ta Isa can saitaci Saida baby tayima saudart sallama sannan suka fita tare da ummy Ganin haka yasa ta ida gyarama ummy gadonta tahau kalkale dakin kamar yadda tasaba Shigansu ummy kitchen keda wuya ashraf yashigo falon shima cikin shirin office saidai fuskarnan a murtuke take ta koma ta ainahin A.A marar M Yau dama da 6acin ran jiya ya tashi, idan yatuna da badan ummy ta mashi buqulu ba da yanzu wannan lalular tashi yazama tarihi sai ranshi yasake 6aci shiyasa yau yashirya dawuri don zuwa office ko zai danji dama dama Haurawa sama yayi yayi knocking a kofar ummy, bejira ayimashi isoba ya bude yashiga bakinshi dauke da sallama Saudart da fitowarta kenan daga wankin toilet ta dago sukayi ido hudu Sanye take cikin doguwar cotton gown dark green, hannun rigar attatare iya gwiwa hannayen ajike alamun tayi amfani da ruwa Gabanta ne yafadi ganin mutum tsaye a bakin kofa ya tsareta da idanu Sauke idanunta tayi qasa yayinda abinda yafaru jiya yayi flashing a kwalwarta Dagowa yayi daga jinginen dayake jikin kofa yafara takowa gareta Jin takunshi yasata dagowa itama tana kallonshi Qarasowa yayi gabanta sosai sannan ya tsaya yana cigaba da tsareta da idanu Kasa jure kallon nashi tayi hakan yasata sauke kanta qasa Hannu yasa ya dago habarta ahankali suka tsurama juna yayinda kibiyoyin qauna ke fita a idanun kowannensu yana shiga najuna Ahankali yafara kusanto fuskarshi gareta batareda ya janye eye contact dinsu ba Itama samun kanta tayi da kasa ko motsawa sai kallon cikin idanuwanshi datake tana kar6ar saqonsu izuwa nata Hada goshinsu yayi still idanunsu ana juna Bugun zuciyarta yaqaru sosai yayinda jikinta yadan fara tsima Hannayenshi yadora a waist dinta yajawota jikinshi yana neman hade bakinsu Sosai jikinta yashiga rawa hakan yasa tafara tafiya da baya baya Shima binta yashigayi batareda ya saketa ba har suka dangana da kofar toilet Sake sunkuyowa yayi tsinin hancinsu na ta6a najuna, suka shiga musayar numfashi Ahankali yafara kusanto bakinshi anata hakan yasata saurin rintse ido gamm Lower lip dinta yafara kamowa da lips dinsu yajasu ahankali sannan ya sakesu Jan numfashi tayi ta qarfi tana kwantowa jikinshi Qara rungumo waist dinta ya hade bakinsu yashiga bata the romantic kiss ever Sosai jikinta yayi lakwas kamar an zaremata lakka, jinta take kamar tana yawo agajimare, wani irin feeling da batasan tanadashiba yashiga tasomata yana sake tsumata Shima a 6angarenshi yariga yagama fita hayyacinshi kissing din extra soft lips dinta yake kamar yasamu alawa, Kwata Kwata sun fita hayyacinsu bare sufarga Susan a ina suke. Ummy ce data gama sallamar baby hartama tafi ta hauro sama tana amsa kiran waya daya shigomata yanzu Hannu ta Dora akan handle din kofar ta murda tareda tura kofar 😱😱😱 Nayi nan🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 099 Hannu ta dora akan handle din kofar ta murda tareda tura kofar Tura kai tayi ciki tana amsa waya fuskarta dauke da murmushi Dago idon datayi bata saukesu akoina ba sai akansu Gabantane yabada damm tayi saurin juyawa tana zare idanu Saurin sake bude kofar tayi tafita cikin sassarfa Sukau gwanayen basumasan tanayiba don sunyi nisa awata duniyar datasha banban da tamu Kissing dinta yake so passionately yana kalkada harshenshi da nata yana sucking tenderly Tuni lantarkin jikinta yaqara hawa jikinta yaqara yin laqwas badan kofar data taresu ba da tuni sun zube qasa Saudart idanuwanta na alumshe tanajinta tana yawo a gajimare tama manta awace duniyar take ga yadda qasanta ke qara tsumuwa feelings na fizgarta takoina dama yaya lafiyar giwa? Qiris dama take jira dama an tsumu tun a gida Bata dawo hayyacintaba saida taji hannunshi daya cikin rigarta a bare boob dinta guda Hakan yasata zabura ta kwace bakinta tana bude idanunta ba shiri Sai a sannan tunaninta yafara dawomata tafara qoqarin tureshi daga jikinta Qara qanqameta yayi cikin fitan hayyaci "No...please" yafada cikin muryarshi dabata fita sosai "Please... stop A'A" tafada dakyar saboda yadda ya matseta kamar zai shige jikinta Qanqameta yaqara yi yana sauke wani wahallalen numfashi yana qara cusa kanshi a wuyanta "A.A.... Ummy, nashiga uku...ummy" tafada tana fashewa da kuka jikinta na rawa sosai Jin sautin kukanta yasashi dan sassauta riqon dayayi mata yana sauke numfashi ahankali Ganin tsayuwar na neman gaggararsu yasashi Zamewa qasa still tana wrapped a hannayenshi Lumshe idanu yayi yana dora gefen fuskarshi bisa kanta yana cigaba da sauke numfashi Shikadai yasan abinda yakeji, jiyake kamar zai shide saboda yadda mararshi ta qulle gamm Qara turata yayi a qirjinshi yana sauraron sautin kukanta dake fita ahankali ga yadda yakejin bugun zuciyarta a qirjinshi Hadiye wasu yawu dasuka tararmashi a maqoshi yayi ya dago yayi kissing din kanta ya dago fuskarta dake a qirjinshi yafara binta da kisses takoina "It ok uhm? Stop crying" yafada yana kissing soft kumatunta na dama Zaro hanki dake gaban aljihun suit dinshi yayi yashiga tsanemata hawayen fuskarta Saida yagama sannan yaqara kissing din goshinta dake qawace da qanannun gashi dake kwankwance "Am sorry uhm? I don't know what came over me, it just that... I... love you" Fadawa tasakeyi ajikinshi tana sauke numfashi ahankali tanajin yadda zuciyarta ke swelling in emotions Shima zagaye hannayenshi yayi abayanta yana kwantar da kanshi akan nata *** Ummy kau cikin harde qaffafu ta Isa qasa, kitchen ta zarce don ahalin yanzu bata buqatar ta hadu da daya daga cikinsu Maid dinsu tajuyo ganin yadda tafado kitchen din kamar wanda aka jefo Hakan yasata fara tambayarta lfy ganin yadda duk take a burkuce Saurin saita kanta tayi tawani sha murr cikin basarwa tace mata bakomai ta tafi bari ta ida breakfast din Bin umarninta tayi ganin ba wasa a fuskarta ta wuce sumi sumi tabar kitchen din Dafe kanta ummy tayi bayan fitarta tana mammakin irin wannan rashin kunyar ta 'ya'yan zamani Yanzu su rasa inda zasu baje kolin iskancinsu sai a dakinta? Dama tun dawowarshi gidan tana lure da take takenshi Ko tsiramata idanun dayake a dining duk lokacin cin abinci tana sane shiyasa wani sa'in idan abun yaso yin yawa saita tashi tabarmasu dining din Su ke abinsu amma ita ke jimasu kunyar Jiya jiyan nan tazo ta taddasu zaune afalo qasa kamar su shige jikin juna saidai tajuya tafasa yin abinda ya sauko daita, daga baya ma saidai ta aika baby takirata ganin har isha'i na niyyaryi bata dawoba. Hakan be isaba sai gashi the same day da daddare ganin har kusan 10 bata shigoba kamar yadda tasaba yasata fitowa ta leqa dakin baby taga wayam sai babyn kadai daketa sharar barcinta Fitowa tayi tana wondering ina take Ganin kwayakwan falo a kunne yasata Saukowa taga ko tana anan saidai me kafin ta qarasa ta hangosu manne dajuna a dining hakan yasata juyawa bashiri takoma inda tafito Yanzu kuma wulaqancin nasu harya kai yanzu su rasa inda zasu baje kolin rashin kunyarsu sai a dakinta? Kai gaskiya tana ganin rayuwa, dolene ma ta tarkatasu ta korasu kafin sujamata abin kunyar dayafi wannan Wasa wasa tun tana tsumayen fitowarshi har abin yafara bata tsoro jin shirun yayi over Jan stool tayi ta zauna ta zabga tagumi tana jiran taji koda motsin daya daga cikin su ne Ita sai yanzu ma take danasanin riqe saudart, dama ummar sadeeq taja mata kunne akan haka tace tsakanin miji da mata sai Allah qarshenta tazo taji kunya gashi hakan kau yafaru Ita wai nan riqeta tayi don ta garashi yasan muhinmmancin ta Ashe ja'irar 6ulamata qasa a ido zatayi Aiko tunda abin hakane gwara suzo Susan inda dare yayi masu, bata iyawa Jin qauri ya turnuke kitchen din yasata saurin tashi ta kashe gas cooker din tana bude tukunyar dake akai Ganin abin ciki yafara kamu yasata jan tsaki ta dauko wurin kwashewa ta kwashe tana ayyana dolene ma suzo su kama gabansu bazasu maidata uwar banza ba Tana cikin jiqa tukunyar datayi kamun a sink taji motsi abakin kofa Waigowa tayi suka hada ido da ashraf da saika rantse da Allah ba shi ta kamaba ya saka Yar mutane a corner don yawani maze kamar babu abinda yafaru Dauke kai tayi tacigaba da abinda take Qarasowa ciki yana cewa "Ummy yau ke ke breakfast din? Ina maid din?" Bata ko dagoba tace "Na aiketa" a gajarce "Ayyah nashiga dakine naga ban gankiba shine nace bari nazonan Ashe kina ciki ma" "Hmm" kawai tace don ita bawai son firar takeba ita in so samune ma yatafi yabata wuri "Ummy to nidai zan wuce office munada aiyuka masu yawa baxan iya tsayawa yin break ba, nayi a office" Cikin zuciyarta tace "Jikayi nace katsaya dama?" Amma a zahiri tace "To Allah ya tsare, take care" batareda ta juyoba Da amin ya amsa yafice yana mammakin wannan tsare gidan na ummy, watsar da tunanin yayi tinawa dayayi aidama haks take yan kwanakin nan dukdan saudart amma yasan maganinta Ai idan tasan wata Ai batasan wataba Koda yafita saida ta jima sosai a kitchen din kafin tafito tayi shahadar komawa saman Kamar yadda tazata bata taddataba dakin hakan yasa ta maido dakinta ta rufe tana sauke Ajiyar zuciya Bin dakin tayi da kallo taganshi tsab tsab. Kada kanta tayi ta wuce toilet tana ayyana dolene ma su tattara subarmata gida😆 A bangaren saudart tana samu ashraf yafita tayi sauri ta ida gyara dakin, batajin tana iya hada ido da ummy dukda batasan meya faruba amma gani take data kalleta zata gano abinda yafaru, hakan yasa tana gamawa ta lalla6a tabar dakin takoma na baby Ummy kau maid dinsu takira akan taje tasamu saudart dakinsu tayimata maganar breakfast don ahalin yanzu batajin zata iya facing dinta Saudart kau bata kawo komai aranta ba ta sauka tayi break dinta abubbuwan dasuka faru dazun naqara dawomata a qwanya, dolene tadan ja dabaya da ashraf idan ba hakaba watarana kunya za'aji, yanzu ace dazu ummy tashigo ta gansu ahakan ina zatasa kanta? Dolene ta takamashi birki tunda taga kamar kunya be isheshiba (ruwa kike yarinya😒) Yinin ranar ummy bata fitoba bare su hade, gwara gwara ma da baby tadawo sun shigo tareda saudart dakinta akan lunch sai cemasu tayi suje suci kawai she's busy Ba wanda yakawo komai aranshi suka fita don zuwa suci, baby na bata labarin yadda exam din yau yayi zafi. *** Zaune take a dakinta tana dudduba wasu kaya da za'a kawomata sari daga China aka bubbugo kofa Saida tadanyi jimm sannan tabada izinin shigowa Ashraf ne yashigo cikin shigarshi ta jallabiya ash colour da alama daga massallaci yake don dama ba'a dade da idarda isha'i ba Kallo daya tayimashi ta dauke kai tana amsa sallamarshi Qarasowa yayi ciki ya zauna qasa kusada qaffafunta yadora kanshi à cinyarta Saurin ture kanshi tayi afusace tana cewa "Meye haka?" Shagwa6a fuska yayi kamar zaiyi kuka yace "Kai ummy" Tsaki taja tacigaba da abinda take Kumbura fuska yayi yana hura hanci wai nan yayi fushi besan dama ciki take dashi ba Tsaki tasake ja ta dago daga abinda take tace "Kana jina? Jibi ka dauke matarka kabarmin gidana na gaji da ganinku fatan kajini dakyau? Jibi jibin nan kaji na gayamaka, tom" tafada tanajan kunnenta daya alamun yajita dakyau sannan tayi kwafa tacigaba da abinda take Wara idanu ashraf yayi cikin tsagwaron mammakin kalamanta "Ummy jibi?" Cikeda masifa ta zaburomashi tace "Eh jibin! Dan wlh karma ka kuskura kuwuce..." Kasa ida maganar tayi jin ya qanqameta yana ihun murna "Kai ummy amma Allah ya tsundumaki a aljannar fiddausi, insha Allah ga kofar gidanki gana annabi (s.a.w), Allah ya baki duk abinda kikeso, Allah ya hadaki kema da Abba a aljanna" Wani dundu takai mashi abaya tana tureshi ajikinta "Dan gidanku zoka fitarmin a daki, marar kunyar banza kawai" Dariya yake yana Sosa baya inda tazuba mashi qulli yace "Babu komai ummy, dukda haka Allah ya saka da alhairi ya kuma farantamaki yadda kika faranta Mani" Pillow din gefenta ta dauka ta jefeshi dashi tana cewa "Bazaka fitaba nace?" Saurin ficewa yayi yana Dariya harda dafe ciki Kwafa ummy tayi tana kada kai, can kuma tayi murmushi tana girgiza kai tana fadin Allah ya shirya Shikau qasa ya sauka yana cigaba da kaka6a dariyarshi don har kwarewa yake tsabar Dariya Aqasa suka hade da saudart datayo hanyar sama itada da baby Tsayawa sukayi kallon ikon Allah ganin yadda yake dariyar kamar sabon kamu Ganin saudart yasa ya tattakura ya fashe dawata dariyar yana nunata yana tafi Sororo sukayi suna kallonshi suka kalli juna sannan suka qara maida kallonsu kanshi Dakyar ya iya hadiye dariyarshi yace "Congrat *MRS ASHRAF AUWAL*" saikuma yaqara fashewa da Dariya yana tafi yawucesu yana cewa "Well play momma, well play" Daga saudart har baby binshi da kallo sukayi baki bude har saida yafice daga falon sai a sannan suka kalli juna Fashewa da wata mahaukaciyar Dariya baby tayi harda rintse idanu Sororo saudart take kallonta itama tanajin gabanta na dan faduwa, kodai sun haukace ne? Qarfin halin cewa "Kekuma lafiya?" Tayi tana danja baya kartaji saukar bugu Qara kecewa da Dariya baby tayi kafin tace "Wlh mijinki ya haukace, Allah ya zare, shikenan Yaya ya zare" Takuma fashewa dawata dariyar tanayin sama dagudu Binta da kallo saudart tayi adan tsorace zuciyarta na ayyana mata kodai dagaske basuda lafiyar ne? Ita bataga abin Dariya ba anan, shi ya sauko yana Dariya marar dalili itakuma tana Dariya wai ya haukace, idanma haukacewar yayi aiba Dariya ya kamaceta ba, kuka ya kamaceta. Ta jima atsaye tana jujjuya abin aranta sannan ta fara hawan saman jiki a sanyaye Asama kau dakin ummy baby tafada tana cigaba da dariyarta mai kamada ta mahaukata Kafin ummy ta dago harta fado Kanta tana cigaba da dariyarta Tureta ummy tayi tana cewa "Lafiyar ki lau kuwa?" Cikin Dariya baby tace "Wlh ummy yanzu muka hadu da yaya qasa yana gagga6a Dariya kamar sabon kamu, wlh harda tafi" takuma fashewa dawata dariyar Wani dogon tsaki ummy taja bayan tagama binta da kallon takaici Kofa ta nunamata tana cewa get out Ba musu ta tashi tafita tana cigaba da dariyarta Saudart na zaune a dosane gefen gado tana tunane tunane tajiyo dariyar baby na tunkaro dakin Saurin dago Kai tayi tana kallon kofar. Shigowa tayi tana cigaba da dariyarta saidai yanzu tadan rage saboda cikinta daya fara amsawa Bata ko kalli saudart ba ta fada kan gado tana qara dafe cikinta daya fara mata ciwo Dom Dariya Itadai saudart na zaune tana kallon ikon Allah tana ayyana duk yadda akai baby bata rasa ingilmu akanta Saida ta huta sannan ta tashi ta wuce toilet saudart tabita da kallo Bata dade ba tafito daure da towel da alamu wanka tayi Kallon saudart datayi zugum tana kallonta tayi tace "Aunty ke ba yanzu zakiyi wankan ba?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "A'a yanzu zanyi" Daga haka ta tashi ta wuce itama toilet din tana qara mammakin abinda yasamesu Koda tafito har baby tayi barci Chanza kaya zuwa na barci tayi tazo ta kwanta gefen baby tana kallonta Saida ta tottofamata addu'o'i sannan itama tayi addu'ar barci ta rintse idanu Ta dade tana jujjuya abinda yafaru dazun kafin wani barci mai dadi yazo yayi awon gaba da ita...✍️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 100 A bangaren ashraf kau he is super happy, shi bema wani lura da baby ba daya sauko qasa kodayake ga yadda yakeji alokacin koda ya gantan hakan ba zai hanashi bayyana farincikinshi ba. Yau ummy ta sashi farincikin da be ta6a yiba arayuwarshi, haryanzu ganin abin yake kamar wasa Koda yashiga dakinshi, saiti yayi kamar a wasan tsere ya falfala da gudu yayi wani qundunbala akan gado yana Dariya, jiyake kamar yayi hauka don farinciki. Harya dauko wayarshi zai kira amininshi saikuma yayi tsaki ya jefar da wayar can gefen gado yakoma ya kwanta rigingine yana qiyasta yadda zasu shimfida sabuwar rayuwarsu su biyu a matsayin ma'aurata Ranar dakyar barci yasaceshi can tsakiyar dare wanda ke cikeda da mafarkan saudart Yau tunda yatashi da asuba be komaba, gari na danyin haske yafice daga gidan ko shiga gaida ummy beyiba A bangaren su baby kau yauma da wuri ta shirya don yauma sunada exam na safe saidai dawuri zasu dawo don paper daya garesu Tare suka shiga gaida ummy wanda ta amsamusu as usual cikin fara'arta ko kadan bata nunama saudart komaiba shiyasa itama bata kawo komai araiba Baby tayimusu sallama ta tafi while saudart tahau gyara dakin ummy kamar yadda tasaba Sai wajajen 10 tagama gyare gyaren dakunnan nasu sannan ta sauko qasa tayi break tana gamawa ta hayewarta sama don hutawa 1:30pm baby tadawo daga school, saida tayi wanka sukayi sallar zuhr sannan suka sauko yin lunch Anan ne ummy kecewa idan sungama zata basu kudi suje saloon suyi gyaran kai da Kunshi Zokaga murna wajensu, musanmman saudart da tunda tazo gidan bata sake leqa wajeba Cikin zumudi suka qarashe cin abincin sannan suka haye sama don shiryawa baby sai tsokanar saudart take wai ba sabon ba yau akuyar daure tasamu sake, itadai saudart bata biyemata ba don a qagare take sutafi kafin ummy ta chanza shawara Wajajen uku suka fito cikin shirin su ta kamala don duk hijabai sukasha har qasa, da baby gyale taso sawa amma ganin saudart ta zumbula hijab yasata fasawa itama ta zira tata har qasa Tare sukaje suka amshi kudin ummy sai yaba kyawun su take sannan sukayi mata sallama suka fita zuwa parking space inda driver ne zai kaisu. A wani qayattacen saloon driver ya ajiyesu, koda ganin yanayin wajen kasan na masu dashi ne Shiga sukayi cikin sa'a kuma ba jira kasancewar yau alhamis ba mutane sosai ba kamar weekend ba Cikin dan qanqanin lokaci aka fara musu gyaran kan wanda saida sukayi zaman tsefeshi sannan aka hau gyaran A taqaice dai basu suka dawo gidaba wajajen six na marece saboda harda qunshi akayi musu duk jaa both kaffafu da hannaye, sosai qunshin ya fito a fararen fatarsu gwanin sha'awa Agajiye suka dawo gidan, saida suka fara biyawa dakin ummy dake zaune robobin fresheners da turaren qamshi kala kala da humrori agabanta tana packaging dinsu Sosai ta yaba kyawun dasukayi tana santin qunshinsu sannan ta umarcesu suje suyi sallah kasancewar anfara kiraye kiraye alokacin Saida sukayi har isha'i sannan suka sauko sukaci abinci suka koma saman A dakin ma hira suka dasa wanda duk baby ce mai surutun itakau saudart dakyar take amsamata don a matuqar gajiye take burinta kawai takai kaffadunta qasa kewar ashraf dake maqale a qasan zuciyarta, rabonta dashi tun jiya, duk yau bata sashi a ido ba saidai hakan yamata daidai don yanzu tsoron haduwarsu take don ta lura bashida self control, idan sun hade duk abinda yazomashi akai yi yake beko la'akari da inda suke Tunawa tayi da kissing dinshi na jiya hakan yasata jin tsigar jikinta na dan tashi, ganin hakan yasata yakice wannan tunanin a zuciyarta ta maida hankalinta akan baby dake zuba kamar Yar tsanar da aka sawa battery Ashraf kau tunda yafita be dawo gidan ba sai wajajen 10, amatuqar gajiye yadawo hakan yasashi wucewa part dinshi kawai Yana shiga ya rage kayan jikinshi ya kwanta ko minti goma beyiba barci yayi awon gaba dashi *WASHEGARI* Juma'atu babbar rana! Yau kowannensu cikin nishadi ya tashi, kowannensu najin farinciki wanda basusan dalilinshi ba kodayake saudart ce za'ace batasan dalilin farincikin ba amma Oga A.A yasan abinda yataka dama Yauma kamar jiya tunda safe yafita saidai sa6anin jiya yau saida yashiga ya gaida ummy kafin yafita dukda bata amsamashi ba da kyau amma hakan be dameshi ba don bayajin ga yadda yakejin kanshi akwai abinda zai 6atamashi mood dinshi Koda yafita saida yaje ya qarasa settling din aikinshi na jiya sannan yawuce saloon shima aka dan saisaye Mashi suma dukda bawani yawa gareta ba akaimashi trimming din sajenshi yafito gwanin kyau, sannan akaimashi gyaran farce da filing nails sannan akaimashi foot bath Bashi yafito daga qayattacen saloon din maza dinba saida aka kusan shiga sallar Juma'a Gidanshi yawuce daga nan ya shirya cikin sabbabin shaddarshi Yar gaske mai shegen maiko kalar golden ya kashe hula kamar wani sabon ango yafice massalaci a gaggauce don karya rasa sallar juma'a A bangaren saudart kau tunda tashiga gyara dakin ummy, ummy ta riqeta don abinci ma saidai takawomata nan dakin, ga cimmar datake bata taci ayau din na musanmman don duk dangin fruits ne da farfesu da pure madara dasukaji hadi Wankama kanshi yau ruwa musanmman tayi amfani dasu wanda yasha hadin turarrukan wanka masu shegen qamshin dadi To tun anan saudart tafara shan jinin jikinta don ita ba qaramar yarinya bace tasan ko me akebata, kanta ya kulle sosai yayinda zuciyarta tashiga fargabar Allah yasa ba abinda zuciyarta ke rayamata bane zai faru Hakan yasa tanemi dan kuzarinta data tashi dashi ta rasa saita koma wata sukuku daita gashi ummy bata bata fuskar tambaya ba kodayake kota bata me zata cemata? Hakan yasa takoma wata sukuku daita tanayin duk abinda ummy tasata. A bangaren ummy kau tana lure da yanayinta amma tayi kamar bata ganiba Saida tasata tayi wanka tayi sallah sannan ta fiddomata wani jan danqareren lace mai touches din baqi tabata akan tasa Ba yadda ta iya haka ta amsa tasaka dinkin riga da skirt sunmata ciff kamar ajikinta aka dinkasu Ko ita kanta ummy saida tayaba da kyawun datayi don sosai kalar kayan suka fitoda glowing skin dinta Saida tagama shiryawa sannan ummy ta zaunar daita don suyi magana Tunda tafara magana saudart ta tsinci kanta cikin faduwar gaba Da nasiha ummy tafara mata, nasiha mai kashe jiki da sage gwiyagu Tun anan saudart ta sadaqat don ko makaho ya laluba yasan mezai faru Saida tagama mata nasihar sannan tacemata tazama cikin shiri anjima mijinta zaizo yatafi da ita Kasa tsaida hawayenta tayi hakan yasa tabarsu suna digowa kanta aqasa, dukda tasan koba dade koba jima saita koma dakinta hakan besata jin wani iri ba, saida ummy ta rarrasheta sosai ta sassamata albarka sannan tabarta ta sauka qasa don ida shirye shiryen datake tun safe Haka saudart takoma ta kwanta zuciyarta namata nauyi Koda baby tadawo a wannan halin ta sameta, tambayar duniyar nan tayimata amma tayi banza daita don bata tata takeba Ganin hakan yasa baby maida akalar tambayarta ga ummy inda ummy ta gayamata yau zasu koma gidansu Sosai itama baby taji ba dadi don yan kwanakin nan ba qaramin dadinsu tajiba tareda ita saboda tana debemata kewa sosai haka itama tadawo dakin ta zauna kusada ita ta zabga tagumi tanajin kewarta tunma kafin ta tafi Haka dai suka qarasa wunin ranar jiki asanyaye *8:00pm* Wata sabuwar mota baqa wulik mai sheqi tafara horn a bakin gate din gidan motar qawace take da decorations masu qyalqyali both gaba da bayan motar Saida aka gama scanning din motar sannan gate din ya wangale motar tashigo ciki Maimakon motar tayi parking space saita wuce har gaban entrance din gidan ta tsaya Saida aka kusan shafe minti daya da tsayuwar motar sannan aka bude driver seat, nanma saida aka ja daqiqu 20 sannan aka ziro qafa daya mai sanye da half cover farare tass sannan gangar jikin mammalakin kafar yabiyo Tsarki ya tabbata ga mahallincin wannan kyakyawar hallitar mai cikeda kwarjini da haiba Wato fadin haduwar A.A a wannan Daren 6ata bakine don duk yadda zan misaltamuku shi ya wuce nan Sanye yake cikin baqar shadda yan ubansu wanda akaiwa aiki kalar fari Dinkin Riga da wando ne na samarin zamani rigar da kadan tawuce cinya Kanshi sanye da hula fara an wani kasheta a gefen kai, hannunshi na dama sanye da tsaddadiyar agogon fata itama fara sai takalmin shi half cover suka farare Sosai yabada kala cikin shigarshi ta black and White ga wani daddaden qamshi dake fita daga jikinshi Maida kofar yayi yarufe sannan ya zagayo yanufi kofa fuskarshi na fitar da annuri irinna angwaye Knocking yayi a kofar falo yasa hannu ya murda handle din kofar batareda ya tsaya jiran isoba Tura kofar yayi yashiga da sallama. Babu kowa a falon sai t.v daketa haukanta ita kadai Hakan yasashi nufar sama direct cikin takunsa na qasaita Suna zazzaune ummy na ida packing din kayyakin da tasaimata dangin kayan qamshi itakuma baby na yima saudart simple makeup wanda dakyar tasamu ta yarda ayimata Knocking din kofar da akayi yasasu danyin Jim da baby da ummy yayinda zuciyar saudart tabada damm har saida tadan dafe saitin zuciyar "Baby get the door" inji ummy jin ansake kwankwasawa Ida shafamata janbakin tayi sannan ta ajiye ta nufi kofar da sauri yayinda saudart taja lifayar dake nade ajikinta ta rufe fuskarta Harzai qara knocking sai yaji alamun za'a bude kofar hakan yasashi fasawa ya zubawa kofar ido Cak baby ta tsaya tana kallonshi from head to toe baki sake ganin yayan nata ya wani transforming kamar bashi ba Harara ya gallamata ganin yadda tawani bake hanyar ita bata barshi yashiga ba sai kallon datake binshi dashi kamar yau tafara ganinshi "Jira kike inyi ball dake sannan?" Yafada yana harararta Sai a sannan ta wara idanu tace "Kai yaya! You look soo takeaway👌" tafada cikin murna Dan yatsine fuska yayi sannan yace "I know" Ganin yanufota yasata saurin komawa baya ta ra6e gefe yashige sannan tabashi abaya tana kumburi Da sallama yashiga wanda yayi daidai da faduwar gaban saudart Qara sunkuyar dakai tayi tana jin ummy na amsa sallamarshi Koda ya shigo dakin da saudart yafara yin tozali wanda ke can gefen gado kanta a qasa Kasa janye idanunshi yayi akanta ganin yadda tayi mugun kyau cikin baqar lafaya dake nannade a jikinta, ba qaramin kyau tayimashi ba dukda ba gannin fuskarta ba yake Tanaji suna gaisawa da ummy, haka kawai ta tsinci kanta da matsananciyar fargaba da tsoro, yanzu fa tafiya zaiyi daita, shikenan daga ita saishi, hakan data tuna yasata jin hawaye na tararmata a idanu na tsananin fargaba Shikau gogan zama yayi qasa yana gaida ummy kanshi a sunkuye don haka kawai yaji yau yana kunyarta sosai Itadai ummy amsawa tayi sannan ta umarci baby dake tsaye tundazu akan tabasu waje Ba don tasoba ta juya tafita tana tura baki acikin zuciyarta tana cewa 'mumafa wataranan auren zamuyi, abinda ba'aso muji din Dole afadamana' Sudai basusan tanayi ba Sawa ummy tayi saudart ta sauko itama ta zauna kusada ashraf sannan tashiga yimasu nasiha mai ratsa zukata inda acikinta tafi jaddadamasu Kalmar haquri don duk zaman dakaga ya dore kuma yayi qarko to haquri yayi tasiri sosai a wannan zaman Sosai nasihar tashige su don har saida takawo kwalla a idanun saudart Saida tagama musu nasihar sannan tasama auren albarka dasu kansu sannan ta dago saudart daketa hawaye yayinda ashraf yadauki tilin kayan da ummy tayi packing a qaramin trolley suka nufi qofa Baby na zaune a falo taga su ummy na Saukowa, ummy riqeda da saudart Hakan yasata tasowa itama takama hannun saudart din suka rankaya waje Awaje kau ba qaramin mammakin ganin wannan sabuwar dalleliyar motar sukayi ba gashi tasha decoration sai qyalli take Baby da bakinta yaqi rufuwa ta bude front seat gefen mai zaman banza Ganin hakan yasa ummy ida qarasowa da ita Gab da zasu shiga saudart ta juyo zata duqa ummy tayi saurin tarota Cikin muryar kuka saudart kecewa ta yafemata duk abinda tayimata a iya zamansu Sosai ummy taqara jin qaunarta na linkuwa a zuciyarta hakan yasata rungumarta tana saka mata albarka tareda cewa babu abinda tayimata sai alhairi itama baby dake gefe tana shedding crocodile tears ta qaraso ta rungume saudart tana wai itama ta yafemata Duk abinda suke ashraf na gefe yana kallonsu har sukayi suka gama sannan aka sakata a galleliyar motar da cikinta keda sanyi kamar fridge Sannan suka rufo qofar Ganin hakan yasa shima shiga mazaunin driver yana dan Sosa qeya ganin mugun kallon da ummy ke watsa mashi Shi besan me ta tarewa ummy ba duniyar nan tasamashi ido, haka yashiga yajawo kofar yarufe yanadan murmushin gefen baki, saida yasaci kallon yadda tawani makure scan gefe guda yayi murmushi yana kada kai sannan ya tada motar yayi reverse yana hango yadda baby keta dagamusu hannu baki a washe yayinda ummy ke kallon motar kawai harya juya yanufi gate dake wangale yafice daga gidan zuwa matrimonial home dinsu a karo na biyu....✍️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 101 Tuqi yake ahankali cikin normal speed, motar is so silent inka cire cool music dake tashi ahankali cikin motar Satan kallonta yayi akaro na ba adadi yana qara jin wani shauqi a zuciyarshi wai yau gashi ga sahibarshi zasu matrimonial home dinsu akaro na biyu Wanda wannan tafiyar tasha banban da wancan Wancan sun tafine da bada niyyar zama na dindindin ba, sun tafi ne sa niyyar zama ba dan taqaittacen lokaci, suntafi ne kowa da nashi manufar dayake son cimmawa wanda da hakan ta samu kowa zai kama gabanshi Amma wannan tafiyar tako ina tasha banban da wancan Wannan tafiyar bata taqaittacen lokaci bane Zasu tafine da niyyar zama tare na har abada Zasu tafine batareda wata manufa ba sai ta zama irinna ma'aurata Zasu tafine amatsayin masoya dukda ita haryanzu baida tabbacin tana sonshi amma yanada tabbacin babu tsanarshi ko digo a zuciyarshi Ko ahaka aka tsaya he's happy Qara satan kallonta yayi yaga tawani lafe a kujera ta makure can gefe kanta a qasa Murmushi yadanyi sannan ya dora hannunshi na dama saman nata dake bisa cinyarta Ahankali ta dago ta kalleshi wanda dama abinda yakeso kenan Kashe mata ido daya yayi fuskarshi still da murmushi Sauke idanunta tayi tareda qoqarin zame hannunta daga qarqashin nashi Qara riqe hannun yayi gamm yacigaba da tuqi da dayan hannun Ganin yaqi bari ta janye hannun yasata kyaleshi tasake lafewa a kujerar tana lumshe ido Basu wani jimaba suka iso gidan Direct parking space yanufa da motar yayi parking Sake juyowa yayi gareta yaga haryanzu kanta na qasa rabin fuskarta a rufe don be iya hango komai sai cute red bakin dayasha janbaki Dan murza hannunta yayi tenderly sannan ya saki hannun ya bude murfin bangarenshi ya sauka Tana jinshi amma ko motsawa batayi ba hartaji an bude murfin bangarenta Ahankali ta dago ta kalleshi taganshi tsaye yana miqomata hannu alamun ta taho Tunawa tayi da wancan zuwan nasu wanda ko arziqin kallo bata isheshi ba saima barinta dayayi a mota yayi wucewarsa saidai tagaji ta fito don kanta Jin an kamo hannunta yasata sake dagowa ta kalleshi Pulling din hannun nata yayi hakan yasata ziro qaffafunta ta sauko a motar still hannunta acikin nashi Rufe kofar motar yayi sannan yajuyo wajenta Batayi auneba taji ya cirata daga qasa ya dauketa in a bridal style Waro idanu tayi tana qara qanqameshi ganin kamar zai yadata Zatayi magana ya katseta da "shhhh" hakan yasa maganar maqalewa Fara tafiya yayi daita hanyar main entrance din gidan kamar ya dauki Yar tsana ko nauyi beji Itadai saudart is very uncomfortable, jitake kamar zai kadota hakan yasa tariqeshi matakam tana raba idanu, Allah Allah kawai take ya direta Koda suka qarasa bakin kofa hannu daya yasa ya bude kofar sannan yajuya yasa baya ya turata ta bude Matso da bakinshi yayi saitin kunnenta kamar zaiyi rada hakan yasa tayi saurin rintse idanu jin saukar numfashinshi akan kuncinta "Kiyi mana addu'a zaman lfy da albarkar aure while ni nashiganmana da qafar dama" yafada in wishper Shiga yayi da qafar dama still tana ahannunshi while ita tayi addu'ar acikin zuciyarta still idanunta a rufe Wani irin qamshi mai tafeda sanyi ya kadomata wanda hakan yasata bude idanunta ahankali Sake wara idanunta tayi ganin falon dirim cikin dim light sai yan kwayakwan disco light dake bata haske kala kala suna walainiya Cigaba da tafiya yayi da ita cikin dakin da bata iya hangen komai saboda dan hasken dakin hakan yasata qara riqeshi tana wurwurga idanunta a falon tana wondering yadda akai yake gane hanya Saida suka iso tsakiyar falon sannan falon yayi fau da haske mai tafeda wani romantic music a background din falon Saudart da dafarko hasken ya kashemata idanu ta rintse su tashiga budewa ahankali kamar mai tsoron wani Abu Qara wara idanunta tayi in amazement tana sake bin falon da kallo Mutsu mutsun saukowarta yasashi direta qasa ahankali yana kallonta Bin falon da kallo tashiga tana takowa tsakiyar cikin falon sosai while shi yana tsaye inda yake yayi pocketing din hannayenshi yana kallonta cikeda farinciki "Wow!!" Tayi exclaiming ahankali tana dan wara idanunta ganin yadda akayi decorating din falon an chanza mashi fasali kamar bashiba don komai Sabone hatta kayan furniture din sabbine danqarraru wadanda suka amsa sunansu Zame takalmin qaffafunta tayi ta taka lumtsetsen red centre carpet din tsakiyar falon ta qarasa ga wani centre table na glass wanda tun shigowarsu shi yafara daukar hankalinta Qarasawa tayi gaban table din ta durqusa tana kallon qaton framed photo dinta ita da Ashraf da aka jingina da table din aka zagayeshi da coloured candles masu ci ahankali sai tarin cards dake Jere a table din Qurawa Pics din idanu tayi tana mammakin yaushe sukayi wannan pics din Subiyu ne acikin hoton tana jingine dashi suna Dariya su biyu Ba qaramin kyau hoton yayi ba don kallo daya zakamasu ka hango dacewarsu da juna Ganin yadda ta durqusa ta tsurawa hoton ido yasashi sakin murmushi yatako gareta yana murmushin jindadi Tana durqushen taji an rungumota ta baya an zuro kai ta gefen wuyanta anyi mata rada a kunne da "Welcome back *MRS A.A")* lumshe idanu tayi jin saukar wet lips dinshi a gefen wuyanta bakinta na fidda wani sihirttacen murmushi Juyota yayi suna fuskantar juna hakan yasata bude idanunta tana kallonshi still fuskarta dauke da annuri Huramata iska yayi a idanu tayi saurin lumshe su tana murmushi "How did you see that?" Yafada yana sa dan yatsarshi a ramin kumatunta daya lo6a sanaddiyar murmushin datayi "It soo...amazing" tafada tana qara fadada murmushin ta Sosai yaji dadin comment dinta hakan yasashi fadada murmushin shi shima yana hada goshinsu tareda sakin light kiss akan lips dinta yace "Anything for mi-lady" Itama murmushin tayi tadan janye jikinta tajuya ta kalli pics dinsu sannan ta kalleshi "When mukayi pics dinnan?" Yar qaramar Dariya yasaki sannan ya miqe tsaye yana dagota yace "Abin wani sirri ne" Be bata zarafin sake wata magana ba yasake cirata sama yayi hanyar stairs daita yanabin cool music dake tashi haryanzu a falon Jin yana waqa yasata jin kunya ta sinne kanta a qirjinshi tana Dariya jin yadda ya wani maqe murya ala dole waqa yake Ahaka suka qarasa sama dashima yasha decorations masu ban sha'awa Bude kofar dakinta yayi yatura suka shiga yana qara sautin muryarshi cikin bin waqar wanda hakan yaqara volume din dariyar saudart don she found it so hilarious À bedroom din wani sabon kallon tayi don shima kamar falon an chanza mashi fasalinshi Komai sabone ga makeken gadonta wanda yafi mafarko yasha shimfida ta alfarma gasu tiny tiny red flowers warwatse a gadon abin gwanin sha'awa A kan gadon ya zaunar daita sannan ya maido qaffafunta saman gadon Bin dakin tashiga yi da kallo daga zaune cikin mammakin uban kudin daya kashe wajen yin wadannan abubbuwan don tasan ko ba'a tambaya ba an kashe kudi sosai ma kuwa Saida tagama kalle kallenta sannan ta maido kallonta kanshi Hada ido sukayi hakan yasata sunkuyar dakai tana murmushi Dan jan hancinta yayi sannan ya miqe tsaye yace yana zuwa Binshi tayi da kallo harya fita sannan ta maida hankalinta akan kalle kallen datake Ba'a jimaba ya dawo hannayenshi riqe da ledoji manya manya Tana kallonshi ya ajiyesu saman carpet dake gaban gadon sannan yaqara fita can saigashi yadawo da tray mai daukeda plate da spoons, forks da cups Ajiyesu yayi qasa suma sannan ya tattare hannun rigarshi kamar me shirin yin wani uban aiki ya jawo wata Leda ya fiddo banqarrarun kaji dasukasha gashi😋 Ya dorasu a tray din sannan ya dauki ledar fruits ya fiddosu ya daurayosu sannan yadawo yashiga yanyankasu Duk abinda yake saudart na zaune kan gado tana wasa da zoben tanayi tana Satan kallonshi ta qasan ido tana mammakin yadda yake abin expertly kamar mace Saida yagama sannan ya bulbulamasu fresh milk a koffufukan ya jejjera komai ya kwashe abubbuwan dabasuda amfani yafita dasu Be jimaba yasake dawowa beyi wata wata ba ya dauke saudart ya maidota kan carpet gaban abubbuwan daya gama shiryawa Sunkuyar dakai tayi tana mammakin yadda yake daukarta every now and then kamar bejin nauyinta "Now da me zaki fara mi-lady?" Yafada yana bowing dramatically Dan dagowa tayi ta harareshi sannan tayi saurin sunkuyar dakai Dan wara idanu yayi sannan ya kada kai "Zanyi maganin wannan ne very soon" yafada yana kada kai Itadai bata dagoba bare ta tanka mashi Cinyar kaza yaciro yanufo bakinta dashi, ganin hakan yasata kauda kai Binta yayi dashi nanma ta maida kan wani 6aran "Kinsan Allah? Zanmiki dura" yafada yana sake tunkararta da naman Sake kauda kai tayi tana cewa "Allah am full" adan shagwa6e "You're not" yafada yana qara nufarta dashi Yunqurawa tayi zata gudu yayi saurin kamota ta waist yayi pulling dinta ajikinshi Luu tafada a qirjinshi tana rintse idanu sanaddiyar shock dayabi ilahirin jikinta asanaddiyar waist dinta daya ta6a Luma yatsunshi biyu yayi a kwarin waist dinta hakan yasata zabura bashiri tana riqeshi "Oh my God, please stop" Murmushin gefen baki yayi don tun ranan yagano nan na daya daga cikin weak point dinta "Then eat" yafada yanayi kamar zai qara sa yatsa awajen Hakan yasata saurin kada mashi Kai alamun ta yarda zataci Kaimata yayi abaki, babu yadda ta iya hakan yasa ta bude bakin tadan cira tahau taunawa ahankali Duk yadda taso ya saketa taci dakanta yaqiya dole ta haqura yacigaba da bata tana jikinshi Saida taci sosai don qin kyaleta yayi saida ya tabbatarda ta qoshi sannan ya kyaleta ta sauka daga jikinshi tana sauke Ajiyar zuciya Sai a sannan shima yasamu zarafin cin kayan, saida yayi nak sannan ya kora da milk din mai sanyi Duk abinda yake saudart na zaune kai a sadde Tattara kayan yayi sannan yaba saudart umarnin tayi wanka ta chanza yana zuwa Saida taji alamun yafita sannan ta sauke Ajiyar zuciya Tashi tayi kamar yadda yace tashige toilet donyin wankan don itama tana buqatar hakan Tadan jima a toilet din sannan tafito daure da towel qarami tana yan ra6e ra6e Ganin be dawo ba yasa tayi saurin nufar closet dinta ta bude taciro wata long hijab tazura sannan tashiga shiryawa ata cikin hijab din Saida tagama shirinta harta yi yana shafe shafenta na mai da humrori masu qamshi ta zauna a gefen gado sannan yashigo Dagowa tayi ta kalleshi sannan ta sunkuyar dakai tana amsa sallamarshi Da alama shima wankan yayi don harya chanza shiga zuwa farar jallabiya "Kinyi alwalla?" Ya tambayeta yana kallonta Girgiza kai tayi batareda ta dagoba "To jekiyi" Tashi tayi ahankali tanufi toilet din kamar wanda kwai yafashemawa aciki Koda tadawo harya shimfida sallaya yana zaune akai Ganinta yasashi miqewa itakuma ta qaraso bayan shi ya kabbara sallah yajasu sallar raka'a biyu ta nuna godiya ga Allah (s.w.t) daya nunamusu wannan ranar Saida suka gama sannan yajuyo ya dafe kanta yashiga kwararo musu addu'o'i wanda ita kanta saida tayi mammaki don batayi tunanin yanada ilimin addini irin haka ba Saida yagama sannan yasake daga hannayenshi sama yashiga roqamusu zaman lfy da zuri'a masu albarka Sai a sannan yafara mata tambayoyi gameda addini itakuma tana amsawa calmly, sosai yaji dadin hakan harsaida hakan ta nuna a fuskarshi Bayan wannan suka tashi suka nade sallayoyin ya amsa ya maidasu a closet Ganin yana neman cire jallabiyar agabanta yasata kauda Kai da sauri Shiko ko ajikinshi, cire jallabiyar yayi yarage daga shi sai short nicker da singlet ya haye gado yana sauke qayyataccen net din dake maqale na gadon qasa wanda ya sauko yarufe koina ya qara qawata gadon Saudart wayancewa tayi da shiga toilet saida ta dade sosai sannan tafito tana tafiya ahankali Dayan side din gadon tawuce ta daga net din tashiga ta zauna a darare Ganin beko motsaba yasata kwantawa tana qudundunewa cikin hijabinta She's feeling so nervous ga tarin fargabanta dake ranta, komai ganinshi take kamar a mafarki, tunda take bata ta6a kwana same daki, same bed da namiji ba saigashi yau gata fa namiji a gado daya, namijin ma mijinta, mijintan wai ashraf, Ashraf da ada batada maqiyi sama dashi, shine mijinta wanda ahalin yanzu idan tace bata sonshi to tayi qarya. Ita kanta batasan sanda tafara sonshi ba saidai tagano hakan ne alokacinda yadanyi nesa daita na kwana biyu agidan ummy Alokacin tagane ainahin me takeji gameda shi don wani matsanancin kewa da kishinshi taji tanaji a lokacin har... Zancen zucinta ya katse jin mutum ya kwanto bayanta ta ziro hannunshi ta cikinta ya rungumeta Tsit tayi tana qara qanqame jikinta gabanta na tsananta faduwa Jitayi yana neman cire hijab dinta hakan yasa taqara riqeta "Shhh I mean no harm, kawai sonake kisha iska ne" taji yayi wishpering a kunnenta Haka yaita lalla6ata harya samu ya rabata da hijab din Ahankali yafara romancing dinta romance mai birkice lissafiñ mace Kan kace me lantarkin ta yaja sosai, koina na jikinta yadau chaji Saida yaga yagama birkitama diyar mutane lissafi sannan yanemi shiga the main the main😜 Ganin hakan yasani jan doyoyin qaffafuna na fice masu adaki tunkafin suyi disvirgin din idanuna🤪 No editing👏 Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 102 Cikin barci Abu mai dan gumi na kai kawo a kumatunta Dan yatsine fuska tayi tana dan motsawa alamun bataso amma hakan be hana jin shafarba Ahankali tafara bude nannauyan idanunta da suka dan kumbura Caraff ta hada idanu dashi zaune gefen kanta yana cigaba da shafamata kumatunta murmushi a fuskarshi Saurin maida idanun tayi ta rufe gamm cikin wata matsananciyar kunya dabata ta6a jinta ba yayinda abubbuwan dasuka faru adaren jiya suka shiga flashing a kwakwalwarta Daren jiya dare ne na tarihi agareta, daren da bazata ta6a mantawa dashi ba, daren da ta cika burinta na mallakawa wanda ya cancanta kanta Wato mijin aurenta na sunna Dukda ba qaramar wuyaba tasha amma taji dadi, taji dadi Allah yabata ikon bama mijinta kyautar da ba zai ta6a gogewa a kwakwalwarshi ba, taji dadi da Allah ya kareta tsawon rayuwarta har zuwa rana irinta jiya, don wannan bakomai bane face kariyar Allah domin yanmata ire irenta da dama bai basu damar haka ba, wasu sun rasa nasu mutuncin sanadin rudin shedan wasu kuma an Kwata da qarfin tsiya, ita da Allah ya tseratar mezai hanata gode mashi? *Budurci* mutuncin mace ne, duk macen da ta rasa nata ga wani ba mijinta tayi asara, domin babu babbar kyauta dazata sa kizama mai qima a idon miji na har abada kamar yasameki dall a leda ya kasance shi zai 6areki Yanmata akula, adage da neman kariyar Allah kuma a riqe mutuncin kai don budurci idan ka rasashi ka rasashi kenan bazai ta6a dawowa ba ko me zakiyi, Allah yacigaba da tsaremana mutuncin mu dama kanmu baki daya (amin) Ganin hawaye na gangarowa ta ruffafun idanunta yasashi rudewa yayi saurin dagota jikinshi "Oh my... Am so sorry, nine ko? Am sorry, inane kemiki ciwo?" yafada cikin sigar lallashi Bata ce komaiba sai lafewa datayi a broad chest dinshi hannunta dafe da blanket din jikinta don she's still naked Kissing din kanta yayi ya dago fuskarta yashiga bin every nook and cranny din fuskar da kisses cikin tsananin shauqin so da qauna Sake maidata yayi qirjinshi ya rungume gamm kamar wanda za'a kwacemawa "Allah ya albarkaci rayuwarki mi-lady, Allah ya daukakaki yacigaba da kasamcewa tare dake, haqiqa nayi sa'ar mata ta gari wanda zata zama uwa ta gari ga yayana, wanda zata dora yayana bisa tarbiyya inganttaciya. Saudart... Bansan me zance mikiba, tabbas ke kyauta ce agareni daga Allah, Dana rasaki da ba qaramar asara nayiba Na nufeki da sharri ke kin sakamin da alhairi, bansan me zan cemiki ba, bankuma San dawace kalma zan baki haquri ba akan abubbuwan danayimiki abaya, am ashamed of myself, please do forgive me" ya qarashe cikin sanyi Saudart dake lafe a qirjinshi tana sauraranshi ga wani sanyi dake ratsa zuciyarta saboda kalamanshi ta lumshe idanu ta bude cikin jindadi Dago fuskarta taji anyi hakan yasa ta kalleshi saikuma ta sauke idanunta qasa "Please forgive me" yafada yana shafa kumatunta tenderly Murmushi tadanyi sannan ta dago ta kalleshi "I've done that, nariga na yafema tun lokacin da naji kayi hakan ne a rashin Sani, nima ka yafemin abinda nayi mak..." Katseta yayi ta hanyar rungumeta matakam cikin tsananin farinciki yace "I love you so very muuuuch" yafada yana showering dinta da kisses ata koina ganin abin nashi yawuce makadi da rawa yasata fara neman sauka ajikinshi tana qara qanqame bargonta Dariya yayi mata ya lakace mata hanci sannan yatashi yacire jallabiyarshi yana kallon yadda tawani saurin kauda Kai, murmushi yayi cikin zuciyarshi yana cewa dolene ma yaciremata wannan kunyar Toilet yanufa ya hadamata ruwan dumi sosai sannan yadawo wajenta Saida akasha daga sosai sannan ta yarda ya dauketa shima saidai ya hada daita da blanket din wai be gananmata jiki Shidai banda Dariya babu abinda yakemata Cikin toilet dinma saida yasha fama kafin ta zauna ruwan sai kukan shagwa6a takemishi dukta rikita dan mutane Saida ya canzamata ruwa sau uku sannan yabarta tayi wankan tsarki sannan ya nadota a towel kamar jaririya ya maidota daki ya dorata kan gado Fiddomata jallabiyar mata yayi tareda hijab ya ajiyemata sannan ya fita Ganin yafita yasata tashi tana dan cije qasan lips ta zira kayan sannan ta tada sallah Koda tagama ta dade tana kwararo addu'o'i ga aurensu sannan tashafa Tana zaune tana danna counter ashraf yashigo dakin dauke da tray Kallo daya tayimashi ta dauke kai don sosai take kunyar kallonshi babu kayan kirki ajikinshi, daga shi sai boxer da singlet, ita da don tatace daya maida jallabiyarshi Ajiye tray din yayi a gefenta ya tashi ya dauki sabbin toothbrush biyu ya cirosu ya matsa toothpaste sannan yabata daya Tare sukaje sukayi brush din sannan suka dawo suka zauna Bubbude abubbuwan daya kawo yayi yana tambayarta me takeso Da mammaki take kallon kayan, tea ne a flask sai Irish da kwai yayi gwanin kyau sai rolled fried egg Dagowa tayi ta kalleshi ya kashe mata ido daya yana dagamata gira daya Murmushi tayi kawai ta sauke idanunta qasa Hada masu tea din yayi niyyar yi ganin hakan yasa ta kar6a zatayi ya hanata acewarshi beson ta wahala Kakkauran tea ya hadamasu sannan ya subamasu Irish din a plate daya ya dora rolled egg din gefe da gefe Itadai kallonshi take wani abin nashi na bata Dariya ganin yadda yazage yana aiki kamar mace Wannan karonma saida ya tilastata taci sosai sannan sukasha ruwa suka koma suka kwanta don haryanzu akwai barci a idanunsu Basu jima da kwanciya ba barci mai dadi yayi awon gaba dasu 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 A yan kwanakin nan saudart taga gata, wanda bata ta6a hasasoma kantaba awajen ashraf, jiyake da its kamar me? Koda yaushe cikin tarairayarta yake yana bata kulawa, be bari tayi komai don sai daga baya ganin abin naso yayi yawa tafarayi dukda beso hakan ta haqura Saidai duk abinda takeyi yana maqale daita kamar bindi tun tana kunyarshi harta daina don ashraf marar kunya ne na bugawa a news ammafa injita Harka kau tunda yadaga mata qafa na kwana biyu tadan huta ya koma mata, sai a sannan tagane tanada aiki ja agabanta don ta lura don son harka ne sosai hakan yasa itama bata wasa ta wannan fannin gyara kanta take sosai shiyasa gatanan kullum zaiii Kuma tana qoqarin ganin duk lokacin da yazo da buqatar shi bata gwasaleshi ba, she's always ready to make her husband happy hakan ke qara sa qaunarta na qara linkuwa a zuciyarshi *** Tsaye take tana motsa dambun naman dake cikin kasko while shikuma yana gefen kitchen din zaune bisa freezer ya rungume hannayenshi a qirji yana kumburi wai da bala'i fushi yake ta hanashi ya tayata aiki wanda da taya aikinne da dasauki don maqale mata yake yama hanata aikin gabadaya, shine don tace yau batason taikon shine yake fushi Qara Satan kallonshi tayi tana qumshe dariyarta ganin yadda yake cika yana batsewa, girgiza kai tadanyi acikin zuciyarta tana cewa A.A rigima "Sweet yanaji kayi shiru?" Tafada tana dan waigowa Harararta yayi sannan ya dauke kai still hannayenshi rungume a qirji Dariya yabata hakan yasata darawa sannan tace "Haba gogana waya ta6amin zumana?" Dukda yaji dadin zumar data kirashi don duk sanda takeson sashi Dariya haka takecemashi don hakan na sa kanshi fasuwa sosai Kauda Kai yayi don karta ga murmushin shi tama dauka ya huce "Kaji honey?" Tafada a shagwa6e Juyowa yayi ta watsa mata harara sannan yace "Ni kibar damuna, ba ke kikace nima intafi inbaki wuri ba wai ina damunki?" Waro idanunta tayi harda dafe baki "Yaushe nace hakan?" Tafada tana qara wara manyan idanunta Harararta yasake yi sannan yace "Bansàniba" "Haba Zuma, cewafa nayi kaje ka huta" "Ai shine nike hutawan ko?" Yafada yana hura hanci "To saikuma kayi shiru ba labari ba komai kamar kurma gakuma hannayen daka runguma aqirji ko nauyi bakaji" tafada tana qumshe Dariya ganin yadda yake kallonta yana muzurai "Ina ruwanki? Aidai hannu nawane kuma qirjin nawane kibari saina axa anaki saikiyi qorafin kuma bakin nawane banga damar maganar bane, shima hutawa yake" yaqarashe yana marmar da idanu wanda saida hakan yasa tafashe da dariya. Saida tayi mai isarta sannan tace "To? Allah yabaka haquri, yanzu dai zoka tayani da yankan cabbage na salad" Tun kafin tagama ya watso mata wani kallo, jin tagama yasashi gyara zama yana qara rungume hannu irinna yarannan yace "Ca6! Ai dan ba qari, nida kika kora?" Waro idanu tayi saikuma ta marairaice tana dafe zuciya tace "Wayyo! Kabar cewa na koreka, bakaji yadda nakeji ba, jinake kamar ana sukana anan" taqarashe tana qara dafe saitin zuciyar Waro idanu yayi ya diro daga freezer din yazo wajenta "Dagaske?" Yafada yana qara wara idanu Kada kai tayi tana qara 6ata fuska "A ina? Anan?" Yafada tana ta6a qirjinta Saurin buge hannunshi tayi tana harararshi Dariya ya fashe daita sosai yanufi dan fridge din dasuke aje kayan veggies yafiddo cabbage din yana cewa "Draw kenan" Tura baki tayi gaba tajuya tacigaba da abinda take Anan gefenta ya dawo yafara yankan cabbage din yana tsokanarta tun bata biyemashi harta fara ramawa Ana haka kira yashigo wayarshi, dan karkacewa yayi ya zaro wayar yaduba mai kira Ganin mai kiran yasashi jan tsaki yaqi dagawa Dan kallonshi saudart saikuma ta maida hankalinta ga abinda take batareda tace komaiba Sake kira akayi bayan wancan ta tsinke Dafe Kai yayi yana rolling din idanu "Ka daga mana sweet" inji saudart tana kwashe dambunta "Wlh mutuminnan yasama rayuwata ido" yafada yana yatsine fuska Murmushi tayi don tasan ko wa yake nufi "Dukda haka ka daga babu kyau" Ganin zata tsinke yasashi saurin dagawa ya kara s kunne yana 6ata rai Banji kome akace acan bangaren ba sai gani nayi yaja tsaki yace "To meyafi raina? Dan sa ido kawai" Shiru yaqarayi alamun ana magana ta dayan a 6angaren sannan yace "Sosai ma, gatanan ma tana jinka" Jin hakan yasata dagowa ta kalleshi tana dagamashi alamun me yace? Murmushi kawai yayi mata sannan yaqara cewa "Cewa tayi kana takurama rayuwarmu fa, cema akai yadda kake gwauro haka kowama yake?" Wara idanu saudart tayi jin qiri qiri yana shatata mata qarya Ko me akace a wancan bangaren oho? Sai cewa yayi "Cewa tayi ahakan? Kaida..." Ganin tanufoshi zata fizge wayar yasashi Jada baya yana Dariya Zagaye kitchen din suka shigayi saudart na mashi kukan shagwa6a akan ita bata yarda shikuma yana mata Dariya Jin hakan yasa sadeeq katse wayar tacan yana cizon yatsa Lallai yau ashraf yamashi gori kuma zai gwadamashi yaji gorin Kwafa yayi yacigaba da aikinshi yana kada kai...✍️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [12/10, 6:57 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 103 *A WEEK AFTER* Zaune yake bakin gado, jikinshi sanye da farar singlet wanda ta fiddo muscles dinshi sai wando baqin three quarter Laptop ke gabanshi yana operating sai mug din coffee dake gefenshi yana tururi, aiki yake a laptop din yanayi yana daukar mug din gefenshi yana kur6a akai akai Jin qarar budewar kofa yasashi dagowa daga laptop din Tsayawa sukayi suka kafe juna da kallo nawani lokaci kafin tasaki wani kafirin murmushi na gefen baki ta qaraso cikin catwalk dinta Tana zuwa ta dauke laptop din cinyarshi ta maye gurbinta ta tareda saqalo hannunta around wuyanshi Cusa kanshi yayi aqijinta yana shaqar qamshinta yana moaning ahankali Ture kanshi tayi tana Dariya ahankali tana cewa "Naughty boy" Saurin maidota yayi a cinyarshi ganin tana neman tashi ya rungumeta gamm yace "And where did you think you're going?" Dan bude idanu tayi tace "Kwantawa zanyi, ga laptop dinka kacigaba da aikinka nizan kwanta, sleepy" tafada tana hamma saikuma ta daga hannaye sama tana miqa wanda ko ba'a fadaba kasan ta tsokana ce Rungumeta yayi sukayi rolling zuwa tsakiyar gadon ya dawo samanta ita tana qarqashinshi "Are you trying to seduce me? Tell me" yafada yana dan cizon kunnenta in a sexy way 6ata fuska tayi tace "Seduce kuma? Nidai kaje kacigaba da aikinka am sleepy" "Bakiso inyi aikinba Ai" Kafin tace wani abu ya hade bakinsu waje guda suka Lula duniyar ma'aurata Kwance suke bayan komai ya lafa, sunja bargo ajikinsu tana kwance ajikinshi tana wasa da gashin qirjinshi "Mi-lady wai meye sirrin ne?" Dagowa tayi ta kalleshi sannan tace "Sirrin me?" Saida yayi kissing din forehead dinta sannan yafada cikin rada "You're always sweet, kullum qara dadi kike? What's the secret behind this?" jan gashin qirjin nashi tayi da dan qarfi hakan yasashi sakin qara "Ouch! It hurt" yafada yana Sosa wajen Saudart data tashi zaune tun sadda tayi mashi muguntan ta fashe da Dariya tace "I know, dan wulaqancin saikace ina dadi?, ni abinci ce" "A'a ke abin ci ce" yafada yana kashe mata ido in a naughty way Fashewa da kukan shagwa6a ta fada jikinshi tana kaimashi dukan wasa a qirji Rungumota yayi yana Dariya sosai sannan yashiga mata chakulkuli itama fashewa tayi da Dariya tana zillo tana bashi haquri Saida ya jigatata sosai sannan ya kyaleta ta fada jikinshi suna sauke Ajiyar zuciya tare Tana sauke numfashi ahankali tace "Ammafa kai mugune, wlh cikina harya fara amsawa" Dariya yayi yace "Gakinan babbar muguwa, kiri kiri kin hanani aiki Kwata Kwata" Waro idanu tayi tace "Yaushe na hanaka?" "Kin fini Sani ai Yar rainin sense kawai, kin hanani zuwa office nan dinma kin hanani kata6us, wancan anacen tun yana takuramin haryayi fushi ya qyaleni" Dariya tasake yi kafin tace "Ni na hanaka zuwa office?" "Eh mana, inba keba waye? Wlh kiji tsoron Allah" yafada yana 6ata fuska kamar zaiyi kuka Dariya tasake yi tace "Kodai kaji tsoron Allah, halan da igiya na daureka nave bazaka fitaba?" "Ai yamafi igiya, please saudart let's be serious ya kamata kiyi considering zancena, bekamata kinamin hakaba wlh, please jan ajin ya isa hakan" Dan hade fuska tayi tace "What are you talking about?" "Kinfini Sani saudart, wai meyasa tana tado wannan maganar saiki chanza mood dinki?" "Then kabar tadowa, final" tafada tana juyamashi baya Kwantowa yayi kan bayanta ya zuro hannayenshi ta cikinta yaqara jawota jikinshi yace "Saudart meyasa bazaki zama secretary dina ba akaro nabiyu? Ko haryanzu komai be wuceba awajenki?" Lumshe idanu tayi ta bude kafin tace "Idan komai be wuceba awajena bazanyi qaryar cewa ya wuceba, ina son kasani wancan karonma da dalilin yin hakan, ni Kwata Kwata banida ra'ayin white collar job ko aiki a qarqashin wani, plus banida burin aiki da aurena, nafison in zauna gida as a house wife inyaso bakery dina ya isheni, I can run my business anan gida" Shiru taji yayi bece komaiba hakan yasata juyowa Ganin ya kafeta da ido yasata itama tsayawa kallonshi don a iya zamanta dashi tasan kàso mai yawa koda ba duka bane a hallayenshi Tasanshi da saurin hawa, yanzu hakan 6acin ran dayake qoqarin 6oyewa take hangowa a idanunshi Lumshe idanu yayi yana hadiye yawu dakyar sannan yabude ya kalleta yaga still ita yake kallo "Bakison aiki a qarqashin wani? Nine *wani?*" yafada ahankali yana kallonta da piercing idanunshi Girgiza mashi kai tayi cikin inda inda tace "N..no, ba haka nake nufi b.." Katseta yayi ta hanyar manna mata light kiss a baki ya dan shafa kanta yace "It ok uhm? Bari nayi wanka" Bejira cewarta ba yatashi yawuce toilet tabishi da kallo jiki a sanyaye Tashi itama tayi zaune ta jingina da gadon tana kallon kofar toilet din Ita harga Allah badon ta 6atamashi raiba tayi wannan maganar Ita bakin gaskiyarta ta fadamashi, shiyasa tun sadda yafara tadomata wannan maganar taketa zillemashi saboda gudun irin wannan Ita harga Allah batason aikin office, don babban burinta tazama full house wife wanda zata kula da ragamar gidanta batareda wani abu ya raba hankalinta biyu Tun tana yarinya aure ke burgeta kuma take tsara yadda take burin aurenta ya kasance Shiyasa bata ta6a ra'ayin aiki ba don aganinta duk silar raba hankali biyu ne shiyasa tun farko taqi aikin office ta za6i tabude nata business din wanda ki tana a gida zata iya running din abinta batareda ya shigarmata a hidimar gidantaba, shiyasa duk nacin daddy saidai yagaji ya kyaleta Ita bata ta6a tunanin zai dauki wannan abin dazafi ba, dukda ya waske yanuna kamar beji haushi ba ita tasan he's boiling inside Tasan Ashraf kuma tafishi sanin wannan bangaren nashi saboda shi yafara gwadamata Tasanshi da saurin fushi kuma tunda ta yanke shawarar zama dashi na har abada tasan tanada aiki gabanta, dole saitayi haquri da wannan halin nashi na saurin fushi amma batayi tunanin tun yanzu zasu fara samun matsala dashi ba, this is just three weeks da tarewarsu, be kamata ace sun fara samun sa6ani ba Buga tagumi tayi da hannu daya tana tunanin mafita Jin qarar budewar kofar toilet yasata dagowa Shine yafito cikin bathing robe yanufi mirror batareda ya kalli side dinta ba Binshi da kallo tayi harya jawo stool ta zauna gaban mirror din Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sauko itama hannunta riqe da bargon data siturta jikinta dashi ta qaraso bayanshi Yana kallonta ta madubi ta qasan ido harta qaraso wajenshi ta amshe brush din hannunshi tana cigaba da sharce mashi gashin Bece mata komaiba sai jawo lotion dinshi dayayi zai shafa "Are you angry?" Ta tambaya a tausashe Saida ya kalleta ta madubi sannan ya janye ido yana matsa lotion din a hannunshi yace "No" a taqaice Zuro kanta tayi ya gefen wuyanshi tana kallonshi ta mirror tace "You are, am sorry bansan zakayi fushi ba" Dan ta6e baki yayi yace "Meyasa zanyi fushi? Ra'ayin ki fa kika fada, bakison aiki under *wani*" yafada yana stressing din Kalmar *WANI* din Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "Ba yadda ka daukaba nake nufi, you misunderstood me, Kwata Kwata bana ra'ayin aikinne" "Shine nace fine ko? Tunda baki ra'ayi ai baxan maki doleba" yafada yana ajiye lotion dayagama shafawa "You still don't understand me" "Meye ban fahimtaba? Da Hausa muke magana, why zakice ban fahimta ba?" "Saboda baka fahimta ba, daka fahimta da bakayi fushi ba" tafada tana danja baya ganin yana niyyar tashi Closet yanufa yabude yace "Eh nayi fushi ne dazu saboda ban fahimta ba amma yanzu na fahimta" "Haryanzu baka fahimta ba tunda ba barin fushin kayiba" Juyowa yayi ya kalleta hannunshi dauke da kayanda yaciro "Waya gayamaki am still angry?" Nuna idanuwanshi tayi tace "These" Yar Dariya yayi yana barin gabanta yace "Then idanunki sun nuna maki ba daidai ba don ni am not angry" yafada yana warware kayan zaisa "Then musu na burgeka" tafada tana qarasowa gabanshi Da taimakonta yasaka kayan ya feshe jikinshi da turarrukan shi yasa takalmi "Where are you going?" Tafada tana kallonshi Dan kallonta yayi kafin ya kauda kai yace "Waje" Dan murmushi tayi ta qaraso wajenshi tace "Ahakan? Zaka fita kana fushi dani?" Tafada tanadan langwa6e Kai "Injiki ba" "A.A bekamata wannan abin yazama wani abu daban ba, ka tsaya my fahimci juna" Tallabo fuskarta yayi yamata light kiss a kumatu yace "Ni na fahimceki saidai idan kece baki fahimceni ba, bakison aiki a qarqashin wani, fine.. I won't force you" Zata sake magana ya dora yatsarshi a la66anta yace "Shhh please muyi dropping wannan topic din ok? Please... Zan tafi mezan siyamiki" Girgiza kanta tayi ahankali tana kallonshi "Bakison komai?" Ya tambaya a tausashe still yana riqe da fuskarta Kadamashi kai tayi kawai Kiss ya doramata a lips sannan yace "To natafi, kije kiyi wanka uhm?" Kada mashi kai tayi sannan tace "Allah ya tsare" a sanyaye Amsawa yayi da amin yana sakin fuskarta sannan yafita tabishi da kallo Ta dade nan tsaye tana kallon ruffafiyar kofar kafin tasaki Ajiyar zuciya ta wuce toilet donyin wanka Wunin ranar haka ta idashi a sanyaye batajin dadin komai, komai yinshi take kamar marar lakka gashi yaqi dawowa har magrib Hakan yasanya ranta ida jagulewa tana jin kamar taita ihu ko zataji sauqi Shikau a 6angaren ashraf koda yafita rasa inda zaya yayi, he's angry, very angry shiyasa yaza6i yafice daga gidan don beson yayi pouring din anger acan Karo na farko kenan daya ta6a shanye 6acin ranshi, ada idan yayi fushi yana bursting ne nan take amma yau sai tsintar kanshi yayi da son qin nunawa, shiyasa ma yayi saurin barin gidan saboda yadda yakejin zuciyarshi don qiris yake jira yayi bursting Awani eatery ya tsaya yashiga, soft drinks kawai yayi ordering aka kawo mashi Zubawa yayi a cup yafara kur6a ahankali *wani?* wai *wani*, wai shi take referring da *wani* Sake kur6ar drink din yayi yana lumshe idanu Shi a yadda ya dauketa yanzu be kamata ta kirashi da *wani* ba, ya dauka Ai yanzu sun zama daya, komai nashi natane natama nashi ne amma ga yadda ya fahimceta yanzu ita ba haka ta dauka ba Tana mashi kallon A.A din da, haryanzu mu'amalantarshi take irin na da, idan ha haka ba why zata kirashi da *wani?* Yasan she's proud amma yayi tunanin wancan karonma don basu shiri shiyasa take nunamashi hakan Ashe a jininta yake Idan bahaka ba me take nufi da hakan? Wato tafi qarfin tayi aiki qarqashinshi ko? Haka ya zauna awajen yanata saqa da warwarewa shi daya, Karon farko da yaji be sha'awar sharing damuwarshi da kowa, ciki harda babban amininshi sadeeq Gani yake wannan matsalar a tsakaninsu ne kuma a tsakaninsu yakamata suyi solving dinta Bashi yabar wajenba saida akafara kiraye kirayen magrib Tashi yayi yawuce masjid din kusada wajen yayi magrib yatsaya akayi isha'i dashi sannan yanufo gida...✍️ Meye shawararku ga saudart? Ta yarda koko ta zauna kan bakanta? Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [12/12, 7:47 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 104 A parking space yayi parking din motarshi yafito yana wurwura makullan hannunshi Bayan seat ya bude yaciro ledojin dake ciki sannan ya kulle motar yanufi cikin gida Da sallama yashiga falon, qamshin daya riga ya kama falon tafara mashi maraba gawani sanyi mai dadi da A.C ke badawa Shiga yayi falon ya nemi wuri a kujera mai daukar mutum daya ya zauna Jingina da kujerar yayi yana sauke Ajiyar zuciya sannan yadago kafarshi daya ya doro a dayan yana qoqarin zame safarshi Jin qarar taku yasashi dan dakatawa sannan yadago calmly Murmushin nan nata mai bayyana beauty point dinta tayi tana cigaba da tunkaroshi cikin salon takunta Nan take kaso mai yawa daga fushinshi ya yaye yayinda yaji wani sanyi na ratsa zuciyarshi Lumshe idanu yayi yasake budewa akanta Sanye take cikin skinny red trouser sai farar top mai fadadden kafada wanda yaba smooth kafaddunta damar fitowa Kanta sanye da jan hula hakama qaffafunta sanye suke da jan takalmi sai tashin qamshi mai fitinnanen dadi take Tana kusan isowa wajenshi ta shagwa6e fuska Sauke kafarshi yayi ya waremata hannu, ganin haka yasa ta qarasa da sauri ta fada jikinshi ta qanqameshi ga mammakinta saiji tayi idanunta sun kawo ruwa Shima rungumeta yayi yana cusa kanshi a gefen wuyanta yana shaqar daddadan qamshin dake tashi ajikinta Sundan jima ahakan sannan ya dagota yayi cupping din fuskarta ya hade goshinsu yana kallon cikin kwayar idanunta dake kyalli saboda ruwan dasuka taru ciki Manna ma jan lips dinta dake maiko don lipgloss kiss yayi yace "What are this for?" Yafada yana huremata idanu hakan yasata saurin lumshesu wanda hakan yaba hawayen damar gangarowa Komawa tayi jikinshi ta maqaleshi ta turo baki cikin shagwa6a tace "I miss you" Murmushi yasaki sannan yasa hannu yana shafan bayanta yace "Miss you too" Sundan jima ahakan sannan ta tashi zaune a cinyarshi ta manna mashi kiss a kumatu tace "Welcome back, hope baka gajiba?" Cikin jindadin tattalinshi datake da tarairaya yawani lumshe idanu ya bude yana wani narkewa yace "Am so tired" "Oh sorry" tafada tana Zamewa qasa ta ida ciremashi safar sannan ta 6allemashi boturan riganshi ta zaremashi ita yarage saura singlet a upper part dinshi Wucewa tayi a dining area ta bude fridge ta dauko mashi ruwan gora masu sanyi ta doro a tray da cup tazo ta zubamashi tabashi Amsa yayi yace "Thank you" Murmushi kawai tayimashi tana kallon yadda ya kafa kai ya shanye yasake miqomata ta zubamashi ya sha fin rabi sannan ya ajiye yana komawa jikin kujerar Dauke kayan tayi tace "Wanna bath before eating?" "No fara kawo abincin sai muyi wankan daga baya, ga wadannan ma kiwuce dasu" yafada yana nuna mata ledojin daya shigo dasu Amsawa tayi da to sannan tayi yadda yace Binta da kallo yayi yanajin wani qaunarta acikin zuciyarshi Be ta6a tunanin zatayi saukin kai kamar hakaba, bakin gwargwado tana mashi biyyaya tana kuma nuna kulawa agareshi sosai wanda hakan kesashi qarajin be iya nesa daita Shi dama can dan son tarairaya ne kodayake kowane namiji yanason a dinga nunamashi kulawa da tarairaya, idan mace ta ajiye girman kai tajawo mijinta ajiki ta nuna duk duniya batason abinda zai ta6ashi ba qaramin samunshi zatayi a tafin hannunta ba Ki kama mijinki ki shagwa6a shi ya kasance komai ke kemashi harta da Kai ruwan buta a bayi ya kasance yana mashi wuya don yasaba ke kemashi to wlh hakan babban sirrine don zaki zama 6arin jikinshi, ko nan da can kika matsa zasu shiga cikin matsanancin kewarki, irinsu ne ko tafiya ta kamaki na kwana saikiga kafin ki dawo kewarki takusan kasheshi yaji babu abinda kemashi dadi duniya, sai kiga shikadai yana sambatunshi 'da tananan da tamin kaza tamin kaza' Akwai mazajen da duk abinda zakimusu basa yabamaki agaban ki ko su nuna sunajin dadin hakan, saidai a qasan ransu tarin yabone da begenki wanda sai bakinan kinyimashi nisa walau tafiya ko rabuwa ta har abada (mutuwa) sannan zaita amayosu yana jin kewarki na nuqurqusar ruhinshi Hakama idan kuka samu sa6ani da miji kar hakan yasa ki fasa yimashi abinda kika saba yimashi koda kuwa shine da laifi. Kiyi harkokinki yadda kika saba koma fiyeda hakan, idan ke keda laifi zafin zuciyarshi zai rage ganin yadda kika hidimta mashi idan kuma shi keda laifi jikinshi zaiyi sanyi ganin yamaki laifi amma baki qullaceshi ba saima alhairin dakika sakamashi dashi Aduk abinda kike ki tuna bautar Allah kike kuma neman aljannarki kike, neman aljanna Nada wuya amma mu mata sai inga kamar Allah ya saukaka mana, mijinmu aljannanarmu, mu kyautata musu musamu aljannarmu, so simple but hard to many of us saboda girman kai irin namu Wasu gani suke yawan kyautatawa miji raini yake kawowa, wasu kuma kyashin yin wani abin suke saboda gani suke daya suke dashi, wasu kuma raini dama yariga yashiga tsakaninsu gani suke mutuminda tsirara yakeyi gabansu ai bawani batun girmamawa To annabi s.a.w yace 'da anama wani sujjada bayan Allah subhanahu wata'ala to da an umarci mata dasuyima mazajensu sujjada' Idan zaki kalli mijinki karki kalleshi a matsayin miji kawai, ki kalleshi a matsayin wanda zai Kama hannunki ya shigar dake aljanna, ki kalleshi amatsayin tsaninki zuwa aljanna Bayan wannan kuma akwai yanmata yanzu birjik masu neman damar auren mijin sakarya Mijin wacce batasan inda kemata ciwoba, damunsan yadda wasu yanmatan goggagun yan bariki ke neman irin wannan damar damun qara tamqe belt dinmu don wasu yanmatan ko zawarawa sunfison ire iren wadannan mazan wanda matayenshi basusan komaiba gameda damqe miji ahannu sai shashanci daya cikamasu kwalwa, yadda sukuma zasu shigo su murza kanbunsu yadda sukaga dama, kina hangame da baki kiga miji yamaki Nisan da saida tantado zaki iya hangenshi yadda daga baya kokin dawo kina abinda yadace abaya kiyi bakiyiba bazaki isheshi kallo ba don bazaki burgeshi ba don ihu bayan hari kikayi kuma bazai ta6a yarda don Allah kikayi ba gani zaiyi dan kinga Amarya nayi shiyasa kema kikafara hakan ba qaramin zubarmiki da mutunci zaiyiba a idanunshi. A word is enough for a wise💁🏻‍♀️ Now back to business😎 A falon ta kawo abincin kamar yadda ya buqata Sauka sukayi a centre carpet suka zauna tashiga serving dinsu Saida tagama sannan ta dago ta kalleshi taga ita yake kallo hakan yasata kashe mashi ido daya tana dagamashi gira daya alamun xupp? Murmushi yayi mata kawai ya maida hankalinshi akan abincin yafaraci suna dan ta6a fira Can saita sarqaho hannunta cikin nashi ta kwantar da kanta bisa kafadarshi Hakan yasa yadan juyo ya kalleta Itama kallonshi tayi saita marairaice fuska tana turo baki tace "Am sorry" Murmushi yadanyi yace "For what?" "For everything, bansan kalamaina zasu 6atama raiba dazu I wouldn't have use the words, am sorry" tafada tana kama kunnuwanta Murmushi yasake yimata sannan yadan sunkuyo kanshi yayimata kiss a goshi yace "Apology accepted" Wara idanu tayi ta qanqame hannunshi dake cikin nata tana murna tace "Oh thanks my Zuma" taqarashe tana kissing din damtsenshi Murmushi yayi shima yayi kissing din forehead dinta yace "Thanks also my sweet, and nima forgive me" "Ni bakayimin komaiba" "Nayi mana, am trying to force you against your wish" "No your wish is my command, I shouldn't have argue with you amma gani nayi as a wife kamata yayi ace ina gida always taking care of you and our home" "Yes amma nidin dazaki kula dani wuni nake a office, idan na fita tun safe sai da marece sometimes sai dare, kinga saina dawo zaki kuladani while ina buqatar kulawarki duk yinin ranar, saudart bansan daliliba banason matsawa ko nan da can daga wajen ki, I always miss you, ina kewar firarki, your smile, your face, your scent, everything Idan ina nesa dake I always feel lonely, hankalina saiya kasu biyu, mafi rinjaye na awajen ki, nasan kona koma office bazan iya abin kirkiba saboda kewarki, zanso ace kina kusadani koda yaushe, mu tashi tare muyi break tare mu shirya tare mu fito tare, yazama kullum ke zaki dinga driving dina zuwa office, nikuma inmaido mu gida vice versa Besides kinada qualification din zama secretary dina wanda samun mai cancanta irin naki zaiyi wiya, aiki tareda ke wancan karon ba qaramin nasara yakawoba a company din dukda alokacin ba shiri mukeba, to inaga yanzu? Kuma kowa zai zama secretary dina anan gaba baxan iya trusting dinshi ba kamar yadda zanyi trusting dinki don kingama winning din trust dina, baki ha'inceniba sadda muna maqiya ya za'ayi kiyi yanzu muna amatsayin ma'aurata kuma masoya? Amma ba komai tunda bakida ra'ayin hakan baxan takura miki ba, zan samu wata, zansa a liqa vacancy letter nasan insha Allah zan samu wanda itama zata cancanta" Yaqarashe yana daukar spoon don cigaba dacin abinci Saudart da tunda tafara magana takejin wani sanyi na sanyaya mata zuciya ta hade rai jin kalamanshi na qarshe Binshi da kallo tayi ganin yama maida hankalinshi ga abincin yanaci hankalinshi kwance, nan take taji wani abu yazo ya tokare mata zuciya Sunkuyar da kanta tayi tana hadiye abinda ya tsayamata wuya yayinda takejin wani mahaukacin kishinshi na tasomata Wato zai samu wata, duk abinda ya lissafa suyi, yaita ganinta koda yaushe, suyita magana kuma koda wane lokaci suna tare ita kuma tana gida sake da baki saiya dawo sannan zata ganshi Tunawa tayi da haduwarsu tafarko da tsohuwar secretary dinshi, tunawa tayi da shigarta, yanzu haka zaisamo wata tayita shigar dataga dama ta janye mata shi? Nan take taji ranta ya jagule, ranta ya 6aci, abincin Kwata Kwata yafita ranta Ganin kamar bataci yasashi dagowa ya kalleta "Why are you not eating?" Yafada yana kallonta Kallonshi tayi fuska a kumbure saikuma ta juyamashi baya Dan lekota yayi ta bayanta yace "Menene?" Matsawa tayi daga gefenshi takoma can dan nesa dashi tace "Ni ka kyaleni" Galala yayi yana kallonta yace "Ni menayi kuma?" "Oho? Bacewa kayi zaka samu wata ba? Saikaje kasamu" tafada idanunta nakawo Shiru yayi na wani lokaci yana kallonta saikuma yafashe da Dariya sosai yana nunata To dama mai neman kukane aka jefa da ledar kashi Ganin hakan yasata 6ata fuska ta maida kanta tsakankanin gwiwa tafara hawaye Da farko ya dauka wasa take amma jin sheshekar kamar ta gaske yasashi dago fuskar Mammaki yakamashi ganin fuskar jage jage da hawaye "Subhanallilah, wai dagaske kuka kike?" Ture hannunshi tayi ta maida kanta bisa gwiwa tana cigaba da kukanta Dariyar dake neman kufcemashi ya danne ya rungumota jikinshi yace "Oh am so sorry, wlh bansan kinji haushi ba" Fizge kanta tayi daga jikinshi tana cewa "Leave me alone, kaje kasamu watan saime?" Tafada cikin muryar kuka Riqe baki yayi saikuma yasake kamota ya maidata jikinshi yace "Haba my princess, meyayi zafi? Kefa kikace bakiyi?" Qara fizgewa tayi tace "Ni yaushe nace hakan?" Wara idanu yayi yace "Kefa kikace bakya ra'ayi" "Yanzu kuma nace inayi" tafada tana murguda mashi baki Dariya yafashe da ita harda tafi yace "Someone is jealous here oh" Fadawa tayi jikinshi tana dukan qirjinshi tana kukan shagwa6a shikau sai Dariya yake Ganin bazata bariba yasashi kamo hannayenta ya riqe yana qara rungumeta "It ok..it ok, yanzu kin yarda zakiyi?" Turo baki tayi ta qara sinne Kai ajikinshi Dariya yayi ya dagota yayi cupping din fuskarta "Uhmm?" Saida ta harareshi sannan tace "On one condition" Dariya yayi yace "Harda sharadi?" Bata amsamashi ba sai hura hancin datake "To inaji meye sharadin" Sniffing tayi sannan tace "Saika gayawa ummy sannan" Dan kafeta da idanu yayi sannan yace "Why?" "Saboda yin shawara da nagaba dakai musanmman mahaifa yanada kyau domin sunfimu hangen nesa" Sosai yaji dadin abinda tace sai cewa yayi "Naga dai alamar sokike ki nuna kinfini son ummy, to ummin nan dai tawace naga alamu qwace kikeson yimin tuntuni, to kin makaro" yafada yana mata gwalo "Kwace tun yaushe nayimaka? Kaidaine baka farga ba" tafada tana mashi hararar wasa "Eh din kidau ummin dama ta isheni ni zan komawa Mamy" yafada shima yana hararta "Oho dai, idan Mamy ce gaka gata" "Jealousy kawai" yafada yana Dariya yayinda itakuma ta hade rai tacigaba dacin abincinta Haka suka qare cin abincin cikin raha da tsokana sannan yatashi ya dauketa kamar Yar tsana ya haye daita sama...✍️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [12/10, 6:57 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 103 *A WEEK AFTER* Zaune yake bakin gado, jikinshi sanye da farar singlet wanda ta fiddo muscles dinshi sai wando baqin three quarter Laptop ke gabanshi yana operating sai mug din coffee dake gefenshi yana tururi, aiki yake a laptop din yanayi yana daukar mug din gefenshi yana kur6a akai akai Jin qarar budewar kofa yasashi dagowa daga laptop din Tsayawa sukayi suka kafe juna da kallo nawani lokaci kafin tasaki wani kafirin murmushi na gefen baki ta qaraso cikin catwalk dinta Tana zuwa ta dauke laptop din cinyarshi ta maye gurbinta ta tareda saqalo hannunta around wuyanshi Cusa kanshi yayi aqijinta yana shaqar qamshinta yana moaning ahankali Ture kanshi tayi tana Dariya ahankali tana cewa "Naughty boy" Saurin maidota yayi a cinyarshi ganin tana neman tashi ya rungumeta gamm yace "And where did you think you're going?" Dan bude idanu tayi tace "Kwantawa zanyi, ga laptop dinka kacigaba da aikinka nizan kwanta, sleepy" tafada tana hamma saikuma ta daga hannaye sama tana miqa wanda ko ba'a fadaba kasan ta tsokana ce Rungumeta yayi sukayi rolling zuwa tsakiyar gadon ya dawo samanta ita tana qarqashinshi "Are you trying to seduce me? Tell me" yafada yana dan cizon kunnenta in a sexy way 6ata fuska tayi tace "Seduce kuma? Nidai kaje kacigaba da aikinka am sleepy" "Bakiso inyi aikinba Ai" Kafin tace wani abu ya hade bakinsu waje guda suka Lula duniyar ma'aurata Kwance suke bayan komai ya lafa, sunja bargo ajikinsu tana kwance ajikinshi tana wasa da gashin qirjinshi "Mi-lady wai meye sirrin ne?" Dagowa tayi ta kalleshi sannan tace "Sirrin me?" Saida yayi kissing din forehead dinta sannan yafada cikin rada "You're always sweet, kullum qara dadi kike? What's the secret behind this?" jan gashin qirjin nashi tayi da dan qarfi hakan yasashi sakin qara "Ouch! It hurt" yafada yana Sosa wajen Saudart data tashi zaune tun sadda tayi mashi muguntan ta fashe da Dariya tace "I know, dan wulaqancin saikace ina dadi?, ni abinci ce" "A'a ke abin ci ce" yafada yana kashe mata ido in a naughty way Fashewa da kukan shagwa6a ta fada jikinshi tana kaimashi dukan wasa a qirji Rungumota yayi yana Dariya sosai sannan yashiga mata chakulkuli itama fashewa tayi da Dariya tana zillo tana bashi haquri Saida ya jigatata sosai sannan ya kyaleta ta fada jikinshi suna sauke Ajiyar zuciya tare Tana sauke numfashi ahankali tace "Ammafa kai mugune, wlh cikina harya fara amsawa" Dariya yayi yace "Gakinan babbar muguwa, kiri kiri kin hanani aiki Kwata Kwata" Waro idanu tayi tace "Yaushe na hanaka?" "Kin fini Sani ai Yar rainin sense kawai, kin hanani zuwa office nan dinma kin hanani kata6us, wancan anacen tun yana takuramin haryayi fushi ya qyaleni" Dariya tasake yi kafin tace "Ni na hanaka zuwa office?" "Eh mana, inba keba waye? Wlh kiji tsoron Allah" yafada yana 6ata fuska kamar zaiyi kuka Dariya tasake yi tace "Kodai kaji tsoron Allah, halan da igiya na daureka nave bazaka fitaba?" "Ai yamafi igiya, please saudart let's be serious ya kamata kiyi considering zancena, bekamata kinamin hakaba wlh, please jan ajin ya isa hakan" Dan hade fuska tayi tace "What are you talking about?" "Kinfini Sani saudart, wai meyasa tana tado wannan maganar saiki chanza mood dinki?" "Then kabar tadowa, final" tafada tana juyamashi baya Kwantowa yayi kan bayanta ya zuro hannayenshi ta cikinta yaqara jawota jikinshi yace "Saudart meyasa bazaki zama secretary dina ba akaro nabiyu? Ko haryanzu komai be wuceba awajenki?" Lumshe idanu tayi ta bude kafin tace "Idan komai be wuceba awajena bazanyi qaryar cewa ya wuceba, ina son kasani wancan karonma da dalilin yin hakan, ni Kwata Kwata banida ra'ayin white collar job ko aiki a qarqashin wani, plus banida burin aiki da aurena, nafison in zauna gida as a house wife inyaso bakery dina ya isheni, I can run my business anan gida" Shiru taji yayi bece komaiba hakan yasata juyowa Ganin ya kafeta da ido yasata itama tsayawa kallonshi don a iya zamanta dashi tasan kàso mai yawa koda ba duka bane a hallayenshi Tasanshi da saurin hawa, yanzu hakan 6acin ran dayake qoqarin 6oyewa take hangowa a idanunshi Lumshe idanu yayi yana hadiye yawu dakyar sannan yabude ya kalleta yaga still ita yake kallo "Bakison aiki a qarqashin wani? Nine *wani?*" yafada ahankali yana kallonta da piercing idanunshi Girgiza mashi kai tayi cikin inda inda tace "N..no, ba haka nake nufi b.." Katseta yayi ta hanyar manna mata light kiss a baki ya dan shafa kanta yace "It ok uhm? Bari nayi wanka" Bejira cewarta ba yatashi yawuce toilet tabishi da kallo jiki a sanyaye Tashi itama tayi zaune ta jingina da gadon tana kallon kofar toilet din Ita harga Allah badon ta 6atamashi raiba tayi wannan maganar Ita bakin gaskiyarta ta fadamashi, shiyasa tun sadda yafara tadomata wannan maganar taketa zillemashi saboda gudun irin wannan Ita harga Allah batason aikin office, don babban burinta tazama full house wife wanda zata kula da ragamar gidanta batareda wani abu ya raba hankalinta biyu Tun tana yarinya aure ke burgeta kuma take tsara yadda take burin aurenta ya kasance Shiyasa bata ta6a ra'ayin aiki ba don aganinta duk silar raba hankali biyu ne shiyasa tun farko taqi aikin office ta za6i tabude nata business din wanda ki tana a gida zata iya running din abinta batareda ya shigarmata a hidimar gidantaba, shiyasa duk nacin daddy saidai yagaji ya kyaleta Ita bata ta6a tunanin zai dauki wannan abin dazafi ba, dukda ya waske yanuna kamar beji haushi ba ita tasan he's boiling inside Tasan Ashraf kuma tafishi sanin wannan bangaren nashi saboda shi yafara gwadamata Tasanshi da saurin fushi kuma tunda ta yanke shawarar zama dashi na har abada tasan tanada aiki gabanta, dole saitayi haquri da wannan halin nashi na saurin fushi amma batayi tunanin tun yanzu zasu fara samun matsala dashi ba, this is just three weeks da tarewarsu, be kamata ace sun fara samun sa6ani ba Buga tagumi tayi da hannu daya tana tunanin mafita Jin qarar budewar kofar toilet yasata dagowa Shine yafito cikin bathing robe yanufi mirror batareda ya kalli side dinta ba Binshi da kallo tayi harya jawo stool ta zauna gaban mirror din Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sauko itama hannunta riqe da bargon data siturta jikinta dashi ta qaraso bayanshi Yana kallonta ta madubi ta qasan ido harta qaraso wajenshi ta amshe brush din hannunshi tana cigaba da sharce mashi gashin Bece mata komaiba sai jawo lotion dinshi dayayi zai shafa "Are you angry?" Ta tambaya a tausashe Saida ya kalleta ta madubi sannan ya janye ido yana matsa lotion din a hannunshi yace "No" a taqaice Zuro kanta tayi ya gefen wuyanshi tana kallonshi ta mirror tace "You are, am sorry bansan zakayi fushi ba" Dan ta6e baki yayi yace "Meyasa zanyi fushi? Ra'ayin ki fa kika fada, bakison aiki under *wani*" yafada yana stressing din Kalmar *WANI* din Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "Ba yadda ka daukaba nake nufi, you misunderstood me, Kwata Kwata bana ra'ayin aikinne" "Shine nace fine ko? Tunda baki ra'ayi ai baxan maki doleba" yafada yana ajiye lotion dayagama shafawa "You still don't understand me" "Meye ban fahimtaba? Da Hausa muke magana, why zakice ban fahimta ba?" "Saboda baka fahimta ba, daka fahimta da bakayi fushi ba" tafada tana danja baya ganin yana niyyar tashi Closet yanufa yabude yace "Eh nayi fushi ne dazu saboda ban fahimta ba amma yanzu na fahimta" "Haryanzu baka fahimta ba tunda ba barin fushin kayiba" Juyowa yayi ya kalleta hannunshi dauke da kayanda yaciro "Waya gayamaki am still angry?" Nuna idanuwanshi tayi tace "These" Yar Dariya yayi yana barin gabanta yace "Then idanunki sun nuna maki ba daidai ba don ni am not angry" yafada yana warware kayan zaisa "Then musu na burgeka" tafada tana qarasowa gabanshi Da taimakonta yasaka kayan ya feshe jikinshi da turarrukan shi yasa takalmi "Where are you going?" Tafada tana kallonshi Dan kallonta yayi kafin ya kauda kai yace "Waje" Dan murmushi tayi ta qaraso wajenshi tace "Ahakan? Zaka fita kana fushi dani?" Tafada tanadan langwa6e Kai "Injiki ba" "A.A bekamata wannan abin yazama wani abu daban ba, ka tsaya my fahimci juna" Tallabo fuskarta yayi yamata light kiss a kumatu yace "Ni na fahimceki saidai idan kece baki fahimceni ba, bakison aiki a qarqashin wani, fine.. I won't force you" Zata sake magana ya dora yatsarshi a la66anta yace "Shhh please muyi dropping wannan topic din ok? Please... Zan tafi mezan siyamiki" Girgiza kanta tayi ahankali tana kallonshi "Bakison komai?" Ya tambaya a tausashe still yana riqe da fuskarta Kadamashi kai tayi kawai Kiss ya doramata a lips sannan yace "To natafi, kije kiyi wanka uhm?" Kada mashi kai tayi sannan tace "Allah ya tsare" a sanyaye Amsawa yayi da amin yana sakin fuskarta sannan yafita tabishi da kallo Ta dade nan tsaye tana kallon ruffafiyar kofar kafin tasaki Ajiyar zuciya ta wuce toilet donyin wanka Wunin ranar haka ta idashi a sanyaye batajin dadin komai, komai yinshi take kamar marar lakka gashi yaqi dawowa har magrib Hakan yasanya ranta ida jagulewa tana jin kamar taita ihu ko zataji sauqi Shikau a 6angaren ashraf koda yafita rasa inda zaya yayi, he's angry, very angry shiyasa yaza6i yafice daga gidan don beson yayi pouring din anger acan Karo na farko kenan daya ta6a shanye 6acin ranshi, ada idan yayi fushi yana bursting ne nan take amma yau sai tsintar kanshi yayi da son qin nunawa, shiyasa ma yayi saurin barin gidan saboda yadda yakejin zuciyarshi don qiris yake jira yayi bursting Awani eatery ya tsaya yashiga, soft drinks kawai yayi ordering aka kawo mashi Zubawa yayi a cup yafara kur6a ahankali *wani?* wai *wani*, wai shi take referring da *wani* Sake kur6ar drink din yayi yana lumshe idanu Shi a yadda ya dauketa yanzu be kamata ta kirashi da *wani* ba, ya dauka Ai yanzu sun zama daya, komai nashi natane natama nashi ne amma ga yadda ya fahimceta yanzu ita ba haka ta dauka ba Tana mashi kallon A.A din da, haryanzu mu'amalantarshi take irin na da, idan ha haka ba why zata kirashi da *wani?* Yasan she's proud amma yayi tunanin wancan karonma don basu shiri shiyasa take nunamashi hakan Ashe a jininta yake Idan bahaka ba me take nufi da hakan? Wato tafi qarfin tayi aiki qarqashinshi ko? Haka ya zauna awajen yanata saqa da warwarewa shi daya, Karon farko da yaji be sha'awar sharing damuwarshi da kowa, ciki harda babban amininshi sadeeq Gani yake wannan matsalar a tsakaninsu ne kuma a tsakaninsu yakamata suyi solving dinta Bashi yabar wajenba saida akafara kiraye kirayen magrib Tashi yayi yawuce masjid din kusada wajen yayi magrib yatsaya akayi isha'i dashi sannan yanufo gida...✍️ Meye shawararku ga saudart? Ta yarda koko ta zauna kan bakanta? Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [12/12, 7:47 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 104 A parking space yayi parking din motarshi yafito yana wurwura makullan hannunshi Bayan seat ya bude yaciro ledojin dake ciki sannan ya kulle motar yanufi cikin gida Da sallama yashiga falon, qamshin daya riga ya kama falon tafara mashi maraba gawani sanyi mai dadi da A.C ke badawa Shiga yayi falon ya nemi wuri a kujera mai daukar mutum daya ya zauna Jingina da kujerar yayi yana sauke Ajiyar zuciya sannan yadago kafarshi daya ya doro a dayan yana qoqarin zame safarshi Jin qarar taku yasashi dan dakatawa sannan yadago calmly Murmushin nan nata mai bayyana beauty point dinta tayi tana cigaba da tunkaroshi cikin salon takunta Nan take kaso mai yawa daga fushinshi ya yaye yayinda yaji wani sanyi na ratsa zuciyarshi Lumshe idanu yayi yasake budewa akanta Sanye take cikin skinny red trouser sai farar top mai fadadden kafada wanda yaba smooth kafaddunta damar fitowa Kanta sanye da jan hula hakama qaffafunta sanye suke da jan takalmi sai tashin qamshi mai fitinnanen dadi take Tana kusan isowa wajenshi ta shagwa6e fuska Sauke kafarshi yayi ya waremata hannu, ganin haka yasa ta qarasa da sauri ta fada jikinshi ta qanqameshi ga mammakinta saiji tayi idanunta sun kawo ruwa Shima rungumeta yayi yana cusa kanshi a gefen wuyanta yana shaqar daddadan qamshin dake tashi ajikinta Sundan jima ahakan sannan ya dagota yayi cupping din fuskarta ya hade goshinsu yana kallon cikin kwayar idanunta dake kyalli saboda ruwan dasuka taru ciki Manna ma jan lips dinta dake maiko don lipgloss kiss yayi yace "What are this for?" Yafada yana huremata idanu hakan yasata saurin lumshesu wanda hakan yaba hawayen damar gangarowa Komawa tayi jikinshi ta maqaleshi ta turo baki cikin shagwa6a tace "I miss you" Murmushi yasaki sannan yasa hannu yana shafan bayanta yace "Miss you too" Sundan jima ahakan sannan ta tashi zaune a cinyarshi ta manna mashi kiss a kumatu tace "Welcome back, hope baka gajiba?" Cikin jindadin tattalinshi datake da tarairaya yawani lumshe idanu ya bude yana wani narkewa yace "Am so tired" "Oh sorry" tafada tana Zamewa qasa ta ida ciremashi safar sannan ta 6allemashi boturan riganshi ta zaremashi ita yarage saura singlet a upper part dinshi Wucewa tayi a dining area ta bude fridge ta dauko mashi ruwan gora masu sanyi ta doro a tray da cup tazo ta zubamashi tabashi Amsa yayi yace "Thank you" Murmushi kawai tayimashi tana kallon yadda ya kafa kai ya shanye yasake miqomata ta zubamashi ya sha fin rabi sannan ya ajiye yana komawa jikin kujerar Dauke kayan tayi tace "Wanna bath before eating?" "No fara kawo abincin sai muyi wankan daga baya, ga wadannan ma kiwuce dasu" yafada yana nuna mata ledojin daya shigo dasu Amsawa tayi da to sannan tayi yadda yace Binta da kallo yayi yanajin wani qaunarta acikin zuciyarshi Be ta6a tunanin zatayi saukin kai kamar hakaba, bakin gwargwado tana mashi biyyaya tana kuma nuna kulawa agareshi sosai wanda hakan kesashi qarajin be iya nesa daita Shi dama can dan son tarairaya ne kodayake kowane namiji yanason a dinga nunamashi kulawa da tarairaya, idan mace ta ajiye girman kai tajawo mijinta ajiki ta nuna duk duniya batason abinda zai ta6ashi ba qaramin samunshi zatayi a tafin hannunta ba Ki kama mijinki ki shagwa6a shi ya kasance komai ke kemashi harta da Kai ruwan buta a bayi ya kasance yana mashi wuya don yasaba ke kemashi to wlh hakan babban sirrine don zaki zama 6arin jikinshi, ko nan da can kika matsa zasu shiga cikin matsanancin kewarki, irinsu ne ko tafiya ta kamaki na kwana saikiga kafin ki dawo kewarki takusan kasheshi yaji babu abinda kemashi dadi duniya, sai kiga shikadai yana sambatunshi 'da tananan da tamin kaza tamin kaza' Akwai mazajen da duk abinda zakimusu basa yabamaki agaban ki ko su nuna sunajin dadin hakan, saidai a qasan ransu tarin yabone da begenki wanda sai bakinan kinyimashi nisa walau tafiya ko rabuwa ta har abada (mutuwa) sannan zaita amayosu yana jin kewarki na nuqurqusar ruhinshi Hakama idan kuka samu sa6ani da miji kar hakan yasa ki fasa yimashi abinda kika saba yimashi koda kuwa shine da laifi. Kiyi harkokinki yadda kika saba koma fiyeda hakan, idan ke keda laifi zafin zuciyarshi zai rage ganin yadda kika hidimta mashi idan kuma shi keda laifi jikinshi zaiyi sanyi ganin yamaki laifi amma baki qullaceshi ba saima alhairin dakika sakamashi dashi Aduk abinda kike ki tuna bautar Allah kike kuma neman aljannarki kike, neman aljanna Nada wuya amma mu mata sai inga kamar Allah ya saukaka mana, mijinmu aljannanarmu, mu kyautata musu musamu aljannarmu, so simple but hard to many of us saboda girman kai irin namu Wasu gani suke yawan kyautatawa miji raini yake kawowa, wasu kuma kyashin yin wani abin suke saboda gani suke daya suke dashi, wasu kuma raini dama yariga yashiga tsakaninsu gani suke mutuminda tsirara yakeyi gabansu ai bawani batun girmamawa To annabi s.a.w yace 'da anama wani sujjada bayan Allah subhanahu wata'ala to da an umarci mata dasuyima mazajensu sujjada' Idan zaki kalli mijinki karki kalleshi a matsayin miji kawai, ki kalleshi a matsayin wanda zai Kama hannunki ya shigar dake aljanna, ki kalleshi amatsayin tsaninki zuwa aljanna Bayan wannan kuma akwai yanmata yanzu birjik masu neman damar auren mijin sakarya Mijin wacce batasan inda kemata ciwoba, damunsan yadda wasu yanmatan goggagun yan bariki ke neman irin wannan damar damun qara tamqe belt dinmu don wasu yanmatan ko zawarawa sunfison ire iren wadannan mazan wanda matayenshi basusan komaiba gameda damqe miji ahannu sai shashanci daya cikamasu kwalwa, yadda sukuma zasu shigo su murza kanbunsu yadda sukaga dama, kina hangame da baki kiga miji yamaki Nisan da saida tantado zaki iya hangenshi yadda daga baya kokin dawo kina abinda yadace abaya kiyi bakiyiba bazaki isheshi kallo ba don bazaki burgeshi ba don ihu bayan hari kikayi kuma bazai ta6a yarda don Allah kikayi ba gani zaiyi dan kinga Amarya nayi shiyasa kema kikafara hakan ba qaramin zubarmiki da mutunci zaiyiba a idanunshi. A word is enough for a wise💁🏻‍♀️ Now back to business😎 A falon ta kawo abincin kamar yadda ya buqata Sauka sukayi a centre carpet suka zauna tashiga serving dinsu Saida tagama sannan ta dago ta kalleshi taga ita yake kallo hakan yasata kashe mashi ido daya tana dagamashi gira daya alamun xupp? Murmushi yayi mata kawai ya maida hankalinshi akan abincin yafaraci suna dan ta6a fira Can saita sarqaho hannunta cikin nashi ta kwantar da kanta bisa kafadarshi Hakan yasa yadan juyo ya kalleta Itama kallonshi tayi saita marairaice fuska tana turo baki tace "Am sorry" Murmushi yadanyi yace "For what?" "For everything, bansan kalamaina zasu 6atama raiba dazu I wouldn't have use the words, am sorry" tafada tana kama kunnuwanta Murmushi yasake yimata sannan yadan sunkuyo kanshi yayimata kiss a goshi yace "Apology accepted" Wara idanu tayi ta qanqame hannunshi dake cikin nata tana murna tace "Oh thanks my Zuma" taqarashe tana kissing din damtsenshi Murmushi yayi shima yayi kissing din forehead dinta yace "Thanks also my sweet, and nima forgive me" "Ni bakayimin komaiba" "Nayi mana, am trying to force you against your wish" "No your wish is my command, I shouldn't have argue with you amma gani nayi as a wife kamata yayi ace ina gida always taking care of you and our home" "Yes amma nidin dazaki kula dani wuni nake a office, idan na fita tun safe sai da marece sometimes sai dare, kinga saina dawo zaki kuladani while ina buqatar kulawarki duk yinin ranar, saudart bansan daliliba banason matsawa ko nan da can daga wajen ki, I always miss you, ina kewar firarki, your smile, your face, your scent, everything Idan ina nesa dake I always feel lonely, hankalina saiya kasu biyu, mafi rinjaye na awajen ki, nasan kona koma office bazan iya abin kirkiba saboda kewarki, zanso ace kina kusadani koda yaushe, mu tashi tare muyi break tare mu shirya tare mu fito tare, yazama kullum ke zaki dinga driving dina zuwa office, nikuma inmaido mu gida vice versa Besides kinada qualification din zama secretary dina wanda samun mai cancanta irin naki zaiyi wiya, aiki tareda ke wancan karon ba qaramin nasara yakawoba a company din dukda alokacin ba shiri mukeba, to inaga yanzu? Kuma kowa zai zama secretary dina anan gaba baxan iya trusting dinshi ba kamar yadda zanyi trusting dinki don kingama winning din trust dina, baki ha'inceniba sadda muna maqiya ya za'ayi kiyi yanzu muna amatsayin ma'aurata kuma masoya? Amma ba komai tunda bakida ra'ayin hakan baxan takura miki ba, zan samu wata, zansa a liqa vacancy letter nasan insha Allah zan samu wanda itama zata cancanta" Yaqarashe yana daukar spoon don cigaba dacin abinci Saudart da tunda tafara magana takejin wani sanyi na sanyaya mata zuciya ta hade rai jin kalamanshi na qarshe Binshi da kallo tayi ganin yama maida hankalinshi ga abincin yanaci hankalinshi kwance, nan take taji wani abu yazo ya tokare mata zuciya Sunkuyar da kanta tayi tana hadiye abinda ya tsayamata wuya yayinda takejin wani mahaukacin kishinshi na tasomata Wato zai samu wata, duk abinda ya lissafa suyi, yaita ganinta koda yaushe, suyita magana kuma koda wane lokaci suna tare ita kuma tana gida sake da baki saiya dawo sannan zata ganshi Tunawa tayi da haduwarsu tafarko da tsohuwar secretary dinshi, tunawa tayi da shigarta, yanzu haka zaisamo wata tayita shigar dataga dama ta janye mata shi? Nan take taji ranta ya jagule, ranta ya 6aci, abincin Kwata Kwata yafita ranta Ganin kamar bataci yasashi dagowa ya kalleta "Why are you not eating?" Yafada yana kallonta Kallonshi tayi fuska a kumbure saikuma ta juyamashi baya Dan lekota yayi ta bayanta yace "Menene?" Matsawa tayi daga gefenshi takoma can dan nesa dashi tace "Ni ka kyaleni" Galala yayi yana kallonta yace "Ni menayi kuma?" "Oho? Bacewa kayi zaka samu wata ba? Saikaje kasamu" tafada idanunta nakawo Shiru yayi na wani lokaci yana kallonta saikuma yafashe da Dariya sosai yana nunata To dama mai neman kukane aka jefa da ledar kashi Ganin hakan yasata 6ata fuska ta maida kanta tsakankanin gwiwa tafara hawaye Da farko ya dauka wasa take amma jin sheshekar kamar ta gaske yasashi dago fuskar Mammaki yakamashi ganin fuskar jage jage da hawaye "Subhanallilah, wai dagaske kuka kike?" Ture hannunshi tayi ta maida kanta bisa gwiwa tana cigaba da kukanta Dariyar dake neman kufcemashi ya danne ya rungumota jikinshi yace "Oh am so sorry, wlh bansan kinji haushi ba" Fizge kanta tayi daga jikinshi tana cewa "Leave me alone, kaje kasamu watan saime?" Tafada cikin muryar kuka Riqe baki yayi saikuma yasake kamota ya maidata jikinshi yace "Haba my princess, meyayi zafi? Kefa kikace bakiyi?" Qara fizgewa tayi tace "Ni yaushe nace hakan?" Wara idanu yayi yace "Kefa kikace bakya ra'ayi" "Yanzu kuma nace inayi" tafada tana murguda mashi baki Dariya yafashe da ita harda tafi yace "Someone is jealous here oh" Fadawa tayi jikinshi tana dukan qirjinshi tana kukan shagwa6a shikau sai Dariya yake Ganin bazata bariba yasashi kamo hannayenta ya riqe yana qara rungumeta "It ok..it ok, yanzu kin yarda zakiyi?" Turo baki tayi ta qara sinne Kai ajikinshi Dariya yayi ya dagota yayi cupping din fuskarta "Uhmm?" Saida ta harareshi sannan tace "On one condition" Dariya yayi yace "Harda sharadi?" Bata amsamashi ba sai hura hancin datake "To inaji meye sharadin" Sniffing tayi sannan tace "Saika gayawa ummy sannan" Dan kafeta da idanu yayi sannan yace "Why?" "Saboda yin shawara da nagaba dakai musanmman mahaifa yanada kyau domin sunfimu hangen nesa" Sosai yaji dadin abinda tace sai cewa yayi "Naga dai alamar sokike ki nuna kinfini son ummy, to ummin nan dai tawace naga alamu qwace kikeson yimin tuntuni, to kin makaro" yafada yana mata gwalo "Kwace tun yaushe nayimaka? Kaidaine baka farga ba" tafada tana mashi hararar wasa "Eh din kidau ummin dama ta isheni ni zan komawa Mamy" yafada shima yana hararta "Oho dai, idan Mamy ce gaka gata" "Jealousy kawai" yafada yana Dariya yayinda itakuma ta hade rai tacigaba dacin abincinta Haka suka qare cin abincin cikin raha da tsokana sannan yatashi ya dauketa kamar Yar tsana ya haye daita sama...✍️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [12/13, 7:16 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 105 *WASHEGARI* Hannun su sarqahe Dana juna suka fito suka nufi parking suna tafe suna hira qasa qasa suna dariya Kallo daya zakayi musu kaga sunyi bala'in dacewa dajuna Sanye yake cikin buggagiyar shadda dark blue mai baqin aiki agaban rigar sai takalmi baqaqe da baqar agogon fata dake sanye a hannunshi na dama sai baqar hula zannah bukar dake riqe a hannun saudart wanda ke sanye da Atamfa dinkin zane simple da half gown wanda ya kawomata har gwiwa tayi daurin Zahra buhari, sosai atamfar tahau jikinta kasancewar black and pink colour ce hakan yasa ta haskata sosai Koda suka Isa jikin motar dazai hau saida suka tsaya nanma suna cigaba da firarsu wadda da alama tayimasu dadi don sai kwasar dariya suke Kallon wristwatch din hannunshi yayi ya wara idanu "Kingani ko? Ni bani hulata idan na biyemiki saina rasa sallar juma'ar gabadaya" Dan turo baki tayi sannan ta doramashi hular akai tana gyarawa saida tagama sannan tadan Jada baya tana kallonshi Dan wara hannu yayi yana dan jujjuya yace "To ya?" Dariya tayi tahada yatsarta manuniya da babban👌tace "Fabulous!" Murmushi yayi yayi mata nuni datazo tahowa tayi da sauri suka rungumi juna sannan yasakarmata kiss a kumatu ya bude kofar motar yashiga yana cewa "Saina dawo, zan dawo maki da babban baqo" "To Allah ya maidoku lfy" tafada tana tura murfin kofar yarufe sannan taja dabaya tana dagamashi hannu harya fice daga gidan Ajiyar zuciya ta sauke sannan tajuya takoma ciki **** A parking space motar tayi parking sannan aka bude murafen motar ta kowane gefe suka fito gabadaya Rufe kofar 6angarenshi ashraf yayi sannan ya zagayo wajen sadeeq dashima yasha manyan kayanshi milk saidai kanshi babu hula sai yar sumanshi daya Tara dake walqiya saboda gyara Shima rufe murfin kofar side dinshi yayi yana cefa wayarshi a aljihu "Ya? Muje ko?" Inji ashraf yana danna ma motar remote Harararshi sadeeq yayi yace "Ko baka fadaba, mtcheew sai wani rawar kafa yake anzo gidanshi",yaqarashe yana yatsina Dariya ashraf yayi yace "Ba doleba, idan haqori banzane kaza ma tayi mana" "Saka ranka a ruwan sanyi, me kakeci nabaka na pouring, wlh albarkacin madam kaci harna zo gidannan, wlh badon itaba ba abinda zaisa naqara taka cikin gidannan tunda nalura kai bakasan arziqi ba, nan nan kazo fuska sha6e2 da hawaye da majina an kwace maka mata, nayi ruwa nayi tsaki wajen nemomaka hanyar dawowar matarka amma don rashin mutunci saidai inji labarin tarewarta abakin wani" Ashraf daketa dariya tunda yafara magana yace "To Ai banga amfanin gayamaka bane, amfaninka yaqare tun lokacin dakayi ruwa kayi tsakin wajen nemo mafitan, kaga meye nawani gayamaka?" Saboda quluwa sadeeq beqara cewa komaiba don yasan ranshi ne kawai zai 6aci Knocking ashraf yayi a kofar sannan ya murda kofar yasa hannu daya ya tare sadeeq dake baya ya zuro kai yana leqen falon Shidai sadeeq tsayawa yayi yana kallon ikon Allah harya gama leqe leqenshi kamar tsohon 6arawo sannan ya dago ya juyo yace "Yauwa mushiga bata ciki da alamu tana sama" Cije lip din qasa sadeeq yayi yana kada kai yana ayyana irin wulaqancin dazaiyiwa ashraf shima idan yayi aure sannan yabi bayanshi suka shiga cikin falon dake tashin qamshin turaren wuta mai dadin qamshi Direct sama ashraf yawuce yana kwala kiran 'princess' Shidai sadeeq samun kujera yayi ya zauna yana ayyana da zuciyarshi marar qwari ce da tuni ta buga saboda wulaqancin ashraf amma bakomai lokaci ne kuma wlh saiya gane kurenshi Kwafa yayi yana girgiza kaffafunshi daya hade waje daya yanabin falon da tsarinshi yaburgeshi da kallo Saudart dataji kiran ashraf ta taso da sauri ta bude kofar sukaci karo dashi shima yasawo kai Jada baya sukayi tare suna Sosa goshi suna tura baki "Wannan kai naki masha Allah kamar na kwakwa? Aisaiki fasa nau" yafada yana harararta 6ata fuska tayi tace "Nice mai kan kwakwa?" Dariya yayi yayi saurin riqo hannunta ganin tajuya cikin fushi "A'a.. Haba ina? Bake bace" Juyowa tayi ta kalleshi tana tura baki tace "To waye?" "Na qasa ne" yabata amsa Dan waro idanu tayi tace "Yana qasa? Waye please" "Guess" "Sadeeq?" Dunqule hannu yayi yaimata jinjina yace "Kwaret! Yanachan yana fama da ciwon zuciya" yaqarashe yana dariya sosai Wara idanu tayi atsorace tace "Ciwon zuciya kuma?" Dariya yasake fashewa dashi yace "Eh mana, badai shi dan rainin wayau ba? Tundazu naketa hadamashi zafi nasan qiris zuciyarshi ta buga" yasake fashewa da dariya Tsayawa tayi tana kallon yadda yake dariya, ita wlh idan yayi wani abin saitaga kamar ba A.A din data Sani bane don bata ta6a tunanin hakan wannan side din nashi yakeba, ita idan yayi wani abun saitaga kamar baby ce Huremata idanuwa yayi yace "Kallon fa?" Lumshesu tayi tana murmushi tace "Muje kabar bawan Allah qasa shi kadai" Dariya yayi sannan yace "Hmm bawan kanya dai, kisa hijab don bamai kallonmin mata" Wara idanu tayi tace "Hijab kuma? Ina laifin gyale" Hade rai yayi yana kallonta bece komaiba hakan yasata sauke Ajiyar zuciya tace "To naji karka hanani barci dawannan fuskar taga da daddare" Murmushi yayi while itakuma tazaro wata farar hijab iya gwiwa tasa sannan ya kama hannunta suka fito. Sadeeq na zaune yana typing din wayarshi yaji motsin su hakan yasashi dagowa ya kallosu Ganin yadago yasa saudart qoqarin zame hannunta daga cikin nashi amma yaqi bata damar hakan dan qara riqewa yayi gamm Janye idanunshi yayi shima yana murmushi ya jefa wayarshi a aljihun gaba acikin zuciyarshi yana gulmar dacewarsu "Allah yaja da daran gimbiyarmu kuma madam dinmu Mrs A... au Miss saudart" yafada yana dan dafe baki Kunya saudart taji don tasan tunamata yayi hakan yasata sunkuyar dakai tana dariya sannan ta zauna a kujera dake facing din nata shima ashraf ya zauna gefenta "Ina wuni" tafada a kunyace don harga allah kunyarshi takeji sosai dubada rashin m datayi mashi abaya "Lfy ma'am, kuma shikenan ko ànememu kunjimu shiru ko ajikinku" Dariya tadanyi tace "Aikau muna cigiyarku, kullum saina yi cigiyarka awajenshi" tafada tana Satan kallon ashraf dake wani shan qamshi shi adole ga mai mata Kallonshi shima sadeeq yayi yace "Wa? Wannan? Ai dabaki faraba don nima kaina kwanan nan ba gane kanshi ba nake, shikenan kuma daga tarewa sai kulle? Dan Allah ataimaka asakar mana shi yadawo company don wlh muna buqatar shi" Kunya sosai taji hakan yasata dan murmusawa sannan ta miqe tana cewa "Ina zuwa" Saida tawuce sannan ashraf ya kalli sadeeq yace "Kai wayace maka ana fira da matata" Wani kallon up & down sadeeq yayi mashi ya watsar ya zaro wayarshi yacigaba da abinda yake dazu Kwafa ashraf yayi sannan ya miqe ya marama saudart dake kitchen baya Can saigasu sun fito tare shi dauke da warmers itakuma eating utensils A falon suka kawo kamar yadda ashraf ta buqata don talura yafison cin abinci a qasa Saida suka ajiye sannan takoma takawo local juice data hada da ruwa ta ajiye. Tana shirin serving dinsu ashraf ya dakatar daita yace ta tafi kawai zasu qarasa dakansu Dik abunda suke Shidai sadeeq na zaune yana kallonsu ta qasan ido yana mammakin yadda cikin kankanin lokaci ashraf yashawo kan saudart don idan baka saniba bazaka ta6a cewa ada basa shiri ba Ganin tawuce yasashi mayar da wayarshi a aljihu ya sauko qasa yafara bubbude kulolin Ashraf nata mashi shaqiyanci amma ko kallo be isheshi ba Haka suka zauna suka kwashi girki sadeeq sai santi yake yana cewa shima idan yayi aure irin wannan za'a dinga yimashi shikau ashraf inbanda dariya babu abinda yakemashi Saida sukayi nak sannan suka sha ruwa suka koma suka zauna suna maida yadda akayi wanda yawanci labarin company ne da yadda abubbuwa ke tafiya Sai wajajen la'asar sannan sukayi haramar tafiya, ashraf yaje ya kirawota Don suyi bankwana Godiya sosai sadeeq yayiwa saudart yana yabon dadin abincinta yakuma dora da dan allah asakar masu boss yadawo aiki Itadai dariya kawai ne nata sannan sukayi bankwana suka fita tareda ashraf Dawowa tayi ta tattare kwanikan anan taci karo da bundle din yana #500 qasan tray Ko ba'a fadaba tasan sadeeq ne ya ajiyesu Kwashe kayan tayi ta dauke kudaden ta gyara wajen fess kamar ba'ayi komai ba awajen sannan ta haye sama donyin sallah Su ashraf kau yawonsu suka wuce bayan sunyi sallar la'asar awani massalaci, sai wajajen magrib kana suka rabu Direct gidan ummy yanufa inda acan yayi magrib dinshi da isha'i Sai bayan yadawo yasami ummy har daki da maganar cigaba da aikin saudart a company dinshi Ga mammakin shi sai yaji ta amince farat daya damasu addu'ar Allah yasa hakan shiyafi alhairi Sosai yaji dadin hakan ya amsa da ameen suka cigaba da firarsu kafin yayimata sallama yawuce gida Agida cike da farinciki yafadama saudart amsar ummy, itama taji dadi sosai hakan yasa itama tashiga murna Saida sukaci abinci suka haye sama sannan ta gwadawa ashraf kudin dazu Cewa yayi ta ajiye kawai tunda kyautarta ce Godiya tayimashi sannan tace yayi extending din godiyarta ga sadeeq Washegari saturday da marece suka wuce shopping din kayan aikin saudart Itadai binshi kawai tayi amma zuciyarta fall mammakin wane irin kayan aiki kuma? Saida sukaje tagane abinda yake nufi Gown gowns kala kala ya jiddarmata kowacce da irin kalar zumbuleliyar hijabinta sai saffofin qafa tuli guda Itadai binshi kawai take da basket din turawa mammaki ma ya hanata magana Saida yagama sannan ya biya aka saka a ledoji aka jibgemasu a booth Akan hanyar komawarsu take tambayarshi gameda kayan nan yake fadamata natane wanda zata dinga sakawa idan zasu office Mammaki yakamata ganin ina zata da wadannan jibga jibgan kayan ko zafi baya tunanin ya kasheta Akan hakan saida sukaso samun sa6ani don ta nuna ita bazata iyaba shikuma yace bazai bari tafita ba kowane Tom and jerry na ganemashi mata Ranar haka suka kwanta kowa rai a 6ace Washegari ma haka suka tashi amma ba wanda yanuna a fuska don lafiya lau suke mu'amalantar juna kamar babu abinda yafaru Fadan nasu bewani dadeba suka shirya don bayan zuhr suna zaune sunacin abincin rana ashraf yatado maganar inda yake nusar daita dalilin dayasa yayi hakan, kishin matarshi yake kuma amatsayin ta na matarshi kamata yayi ta tayashi kishin kanta Sai a sannan ta sauko takuma amince don tayi nazari cewa sai da so ake kishi kuma abin alfaharinki ne mijinki ya nuna kishi akan wata shiga taki don kar wani yagani har ya yaba Nan take sukaba juna haquri suka koma yadda suke Anan yake gayamata gobe insha Allah zasu fara zuwa companyn Da daddare bayan isha'i yace ta shirya sufita Cikin murna tayi hakan suka fice Ga mammakinta dakuma farincikinta gidan Mamy sukaje Taji dadin zuwa gidan sosai don sunsha hira da qannenta damasu Mamy bakidaya inda tayita mammakin shaquwar da qannenta sukayi da ashraf yadda kasan dan gida Anan suke gayamasu gobe insha allah zasu fara zuwa aikin Dayake dama sunada masaniya akai sai suka bisu da addu'a da fatan alhairi Daga nan sai suka wuce gidan daddy Zokuga murna wajen saudart yadda kukasan ta shekara bata ganshi ba ko jin muryarshi Shagwa6a Kala Kala taita yamashi suna mata dariya ashraf na qara jingina soyayyar dake tsakaninsu don yadda tasake haka da daddy batayi hakaba da Mamy Shima fatan alhairi yaimasu sadda suka fadamashi dakuma fatan nasara Sundan jima a gidan sannan suka fito daddy ya rakosu har mota yana masu bankwana suka tafi Direct bakery dinta suka nufa Ganin hakan yasashi danneshi cikin tsantsar farinciki don yau ya faranta mata bako kadanba Haka suka fito suka shiga bakery din wanda wannan shine karon farko da ashraf zai shiga cikinshi Sosai wajen da tsarin wajen ya burgeshi Haka sukaita gaisawa da ma'aikatan wajen masu aikin dare wanda bakinsu har kunne ganin madam dinsu da mijinta sunkawo musu ziyara sai rawar jiki suke wajen welcoming dinsu Saida suka zazzagaya bakery din sosai sannan suka yada zango a office dinta inda cikin qanqanin lokaci aka cikamasu gaba da kayan snacks da kayan sanyi kala kala Sun jima office din suna ciye ciye da fira sannan suka tashi da niyyar tafiya Basu suka dawo gidaba sai wajajen 12, kowannensu agajiye yake liqis, haka suka shige ciki suna hada hanya kamar yan maye...✍️ Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [12/14, 9:43 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 106 Washegari tunda suka tashi sallar asuba basu komaba, tare suka tsaftace gidan sannan suka fada kitchen suka samarma Kansu abinda zasu karya dashi Saida sukayi wanka suka shirya tsab sannan suka karya cikeda nishadi da raha 08:15am suka fito daga gidan ashraf sanye da brown American suit mai farar inner sai dan necktie dinshi daya matse wuya dashi takalmunshi brown hakama wristwatch Itakuma saudart sanye take cikin English gown peach colour wanda yadan matseta daga sama ya bude daga kugu zuwa qasa, hannun rigar net ne dogo har zuwa wuyan hannu, anma rigar kwalliya da manyan tuttoci pink a gabanta saita dora zumbuleliyar hijabinta pink colour wanda badon tasa heels ba da saita ja qasa kafadarta rataye da pink side bag dayan hannunta riqe da faskekiyar wayarta Tare suka jero suna tafe suna hira gwanin sha'awa "Wa zaiyi driving?" Inji ashraf "Kai mana, ni da wadannan zumbula zumbulan kayan zanji ko da driving?" "A'a munriga mun ajiye deal ke zaki kaimu ni na maidomu" "Uhn uhn? Allah nidai bana iya driving da wadannan kayan" tafada a shagwa6e tana folding hannayenta a qirji "To muyi deal, wanda yafara kaiwa ga motar shizai zauna a 6angaren mai zaman..." Be idaba yaga ta ruga cikin dan gudunta ta nufi motar, ganin hakan yasashi saurin maramata baya saidai ina? Harta rigashi qarasawa Dariya ta fashe dashi ganin yadda ya 6ata fuska kamar zaiyi kuka Yi yayi kamar zaiyi mata rankwashi tayi saurin noqewa tana karewa da hannu "If I knock you ehn? Wannan ojoro ne wlh baki bari na ida magana ba kika ruga" yafada yana harararta Fiddo harshenta tayi tana talemashi fuska tace "Eh din, c'mon zokayi driving dina" Kwafa yayi yana jinjina kai sannan ta zagaya bangaren driver ya danna remote ya bude itama ta bude sannan suka shiga Rufo motar sukayi atare sannan yayi starting din motar yayi reverse suka fice daga gidan Tafiyar minti sha biyar sukayi suka isa company din Tun acikin motar take bin company din da kallo tana tuna wasu abubbuwa dasuka shude Jin shiru be motsaba bare ya fita yasata kallonshi taga shima ita yake kallo yawani 6ata rai "Yadai?" Tafada tana daga gira "Mtcheew jinake wama ya hanani hadowa da nikab? yanzu haka zamu fita aita kallon min ke" yaqarashe yana so6are baki Tsaya tayi kawai tana kallonshi, lallai tana da aiki yau Allah ya hadata da murdadden mutum, dama yasan yanada wannan kishin ya buqaci tayi aikin "Kinyi shiru" yafada yana kallonta "To me zance? Sokake ka maidani masquerade koina arufe abun tsoro kamar ninja?" Tsaki yaja wanda ta lura habit dinshi ne yace "Ni wlh sainaga ma kamar wannan shigar tafi yimiki kyau" Ajiyar zuciya kawai tayi bata ce komaiba don itakam batada tacewa kuma Sundan dade ahakan sannan yaja tsaki ya bude motar yafita, binshi da kallo tayi tacikin motar harya zagayo side dinta ya budemata Murmushi tadanyi ganin yadda yake ta wani hura hanci ta dauki jakkarta ta ziro qaffafunta ta sauko ya maida yarufe Kamo hannunta yayi ya riqe tightly kamar wanda akace za'a kwacemawa suka nufi cikin company din Duk wanda yayi musu kallo daya saiya sake kallonsu don they looked soo breathtaking Haka suke wuce ma'aikata suna kaimasu gaisuwa saudart na dagamusu hannu tana dan murmushi while gogan ko kallonsu beyi yawani hada rai kamar hadari Ahaka suka shiga main door din company, maimakon su shiga da daddaya kamar yadda ya kamata sai yajawo hannunta suka shiga tare ganin tana neman tsayawa Haka kofar takoma tarufe tasake budewa daga ciki sannan sukayi stepping out Yadda wurin yake a sadda tasanshi haka yake so silent and cool ma'aikata kowa a post dinshi sai masu kai kawo jefi jefi, wurin sai tashin qamshi mai hade da sanyin dadi yake Basu tsaya wata wataba suka nufi lifter inda duk inda suka gifta sai ma'aikata sun kwashi gaisuwa wanda saudart ce kadai mai amsawa itama ta hanyar murmushi Direct private lifter dinshi suka fita wanda shikadai ke shiga ta cikinshi, saikau sadeeq idan takama Daddana code yayi kofar ta bude sannan suka shiga Satar kallonshi tayi suna atsaye a elevator din suka hada ido kasancewar shima ita yake kallo Yi yayi kamar zai bangajeta yana cewa "Naa.... Amebo kawai" Dariya tayi tace "Amebos dai, kaima Ai kallona kake" Dan budemata idanuwanshi yayi yace "Ni kike cewa haka? Kin manta ni boss dinki ne?" Daga gira tayi saikuma ta juya idanu🙄 tace "Boss indeed" Hade face yayi yace "To bani haquri" Kallonshi tayi tana yatsina sannan tayimashi puppy face🥴 Wara idanu yayi yace "Ni din" Murguda baki tayi tace "Eh din😏" Kamo hannunta daya yayi ya jawota jikinshi yace "Sake yin abinda kikayi yanzu" Qoqarin kwace kanta tayi tana turo baki Dama abinda yakeso kenan kan kace me? Harya hada bakinsu waje guda yashiga sarrafa lips dinta Riqe waist dinshi tayi idanunta a lumshe tana amsar saqonshi while shi yana riqe da fuskarta da dukkan hannun yana kissing dinta passionately Elevator din ya dade da tsayawa batareda sun farga ba sai can suka saki juna suna mayar da numfashi Dago idanunshi dasuka fara chanza Kala yayi ya kalleta yaga itama shi take kallo tana numfashi ahankali Wani naughty look yayi mata tareda cije lip dinshi naqasa sannan ya danna wani botton kofar ta bude ya miqomata hannu babu musu ta saka hannunta cikin nashi tana turo baki Haka suka fito kofar elevator din takoma ta rufe Bin wajen take da kallo tana tuna lokacin datake aiki anan Kallon office dinta dake rufe tayi tana tuna rayuwar datayi acikinsa abaya Jin anja hannunta yasata dawowa daga duniyar tunanin data Lula "Ya dai?" Daga kafada tayi alamun ba komai sannan tabishi Office dinshi ya bude suka shiga, shima yananan yadda yake sai tashin qamshi yake Suna Isa tsakiyar office din yasaki hannunta yadanyi gaba yana wara hannu yace "You're welcome back to our beloved company *MRS ASHRAF AUWAL*" murmushi tayi sannan tasa hannu ta dafe ciki ta sunkuya dramatically tace "Thanks sir" Matsawa yayi gefe yana nuna kujerar dake facing din inda yake zama yace "Have a seat ma'am" Sake yin yadda tayi dazu tayi tace "My pleasure" Sannan tawuce ta zauna, murmushi yayi shima ya zagaya ya zauna a kan kujerarshi yayi irin balancing dinnan nashi sannan ya hade rai yace *"Kinzone domin kimin godiya saboda na za6i yin hakan dake?"* Dagowa tayi ta kalleshi yayinda farkon zuwanta office din yashiga flashing a kwanyarta Dagowa yayi daga balancing dayayi still fuska tsuke ya dora hannayenshi a table din yace *"koko kinzo muyi selfie kisamu abin dorawa a status?"* Fashewa da Dariya sukayi gabadaya harda kyalkyalawa tunawa da bayan dasukayi, idan da yanzu ka shigo ka tarda suna wannan dariyar saikayi tunanin ko ciwon mental garesu "Yeah, nazo daukar selfie ne my arrogant A.A" tafada tana dariya Shima dariyar yayi ya yafito ta da hannu yace "Oya zokiyi my proud peacock" Tashi tayi tana Dariya ta zagayo wajenshi ya Kama hannunta ta zaunar daita laps dinshi ya amshi wayar hannunta yafara kashemasu selfie suna Dariya, daga bayama zurmuqeqiyar hijabin ya ciremata suka cigaba da hotonsu, saida suka gaji don Kansu yabata wayar yace "Hope wadannan sun isheki?" "Sosai ma Mr rudie" Zagayo hannunshi yayi ta cikinta ya matseta da jikinshi sosai har saida tadanyi Yar qara yace "Waye rudie din?" "Kafini Sani"tabashi amsa tana lumshe idanu jin yana sissina wuyanta "Bawani" yafada cikin mumble yana qara cusa kanshi a wuyanta Ganin hakan yasata yunkurin kiqewa yayi saurin qara qanqameta "Sweet meye haka? Nanfa office ne aiki yakamata muyi" "Ai shi muke yi" yayi mumbling yana kissing din gefen wuyanta "Nidai uhm uhn, kabari" tafada kamar zatayi kuka "Nima uhm uhm" yafada shima yana dora hannunshi saman boobs dinta ta saman (Tofah🤔 dama abinda yake nufi kenan da kawo diyar motane office, nidai ina ganin rayuwa ni shatu🤦‍♀️ aradu nakusan barin bibbiyar mutanen nan don naga dagaske dai disvirgining din idanuna zasuyi, ina dalili?😠) Har nayi zuciya zan tattara takarduna akayi knocking din kofa Jarabbabun basuji ba sai ana uku sannan sukayi saurin releasing juna ta zira hijabinta ta koma wajenta da sauri ta zauna sai a sannan yabada umarnin shigowa Sadeeq ne yashigo da niyyar balbaleshi da bala'i sai ganin saudart yasashi Fasawa yashiga gaidata Ita kunya ma taji, gashi jitake kamar ya dago abinda suke hakan yasa ta amsa akunyace sannan ta tashi ta kwashi wasu files da batamasan na menene ba tawuce tafita Saida tafita sannan sadeeq ya zauna yana mashi shaqiyanci wai to karfa zuwan saudart yasashi shiririta zagewa zaiyi ya kwashi aiki don yasan halinshi Shidai ashraf be tanka mashi ba, saida ya tabbatar ya quleshi sosai da shaqiyancinshi sannan yabaro office din yana dariya Ba'a jimaba shima yafita yawuce office din saudart inda duk nan ya shiritar daita shi beyi aiki ba be bari itama tayi na kirkiba Haka suka tashi lokacin closing batareda sun tsinana wani abin kirkiba inda wannan karon saudart ta maidosu gida Haka suka cigaba da rayuwar su cikin tsantsar soyayya da girmama juna Koda wasa basa qaunar 6acin ran juna koda yaushe cikin taka tsantsan suke wajen gujema abinda zai jawo 6acin rai ga dayansu Kullum suna manne dajuna ba gidanba ba company ba donma saudart wani sa'in botsarewa take idan taga alamun shiriritar na neman yawa, koda yaushe haka zaka gansu cikin farinciki da annushuwa basa qaunar abinda zai nisantasu daidai da minti daya A cikin sati na biyu dafara zuwansu aiki ashraf ya shirya musu business trip zuwa Dubai wanda acan qasan ranshi ba business kawai zai kaisu canba harda honeymoon Cikin dan qanqanin lokaci suka gama shirye shiryensu na tafiya sannan sukabi gidajen iyayensu sukaje bankwana inda sukuma suka bisu da addu'ar dawowa lfy Ranar Talata da qarfe 12 na hantsi jirginsu ya daga zuwa shaharariyar qasarnan Wato Dubai...✍️ Manage👏 Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ [12/15, 7:49 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (Contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 107 (Semi final) *DUBAI* Sai can da marece liqis jirginsu ya sauka a airport din babbar Birnin tarayyar Dubai Kai tsaye a wani kataffaren hotel mai suna *AN-NUR INTERNATIONAL HOTEL* suka yada zango Daki mai ciki da falo da toilet suka kama wanda aka zuba kayan alatu da more rayuwa aciki Kasancewar agajiye suke, wanka duk suka fara yowa suka sauke sallolin Kansu sannan sukaci abincin dasukayi ordering Bayan sunci abincin ashraf ya fita itakuma tadan gyagyara wajen tareda shirya kayansu a closet Tun kafin tagama aka fara kiraye kirayen sallar magrib hakan yasa tana gamawa ta dauro alwalla tayita ta zauna lazimi kafin ayi isha'i ta tashi ta yita itama. Tana gamawa ta tashi ta linke sallayar ta maida a closet din sannan ta tu6e ta daura towel tashige wanka Koda ta fito sama sama tayi shafa saboda gajiyar dake nukurkusarta ga barci dake idanuwanta, tasamu ta chanza zuwa kayan barci ta lalla6a ta kwanta Batasan dawowarshi ba saidai ta tashi cikin dare tajita ajikinshi ya qanqameta Jin hakan yasata qara shigewa jikinshi wani dadadden barcin na sake daukarta Kwana biyu sukayi suna abinda yakaisu dangane da aikinsu suka kamalla suka tura reports wa sadeeq ta e-mail sannan suka shiga honeymoon dinsu gadan gadan Kwanaki biyar suka qara a Dubai suna yawon shaqatawa da bude ido agefe guda kuma suna gwangwaje amarcinsu Duk wani wuri na shaqatawa da bude ido dake Dubai saida sukajeshi ciki harda tourist centres da zoos ddss Satinsu daya a Dubai suka sake cirawa basu dira a koinaba sai Philippines Ananma saida sukayi sati suna kwasar amarcinsu a wani dan qaramin island(gida a tsakiyar ruwa) dasuka sauka wanda dan wurine zagaye da ruwa, a wurin akwai ginin dan qaramin bukka wanda ita kanta abin kalloce don dukda bukkace ba qaramin tsaruwa tayiba Zagaye suke da ruwa don ko fita zasuyi cikin gari saidai su hau kwale kwale akai su hakama idan zasu dawo Sosai saudart taji dadin rayuwar wajen it's so quiet and has a romantic atmosphere Tsakaninsu da wata bukkar akwai dan tazara don haka island din yake bukkokine jefi jefi hakan yasa wajen yacika shiru dayawa, da marece haka zasu fito su zauna bakin ruwan suna shan sanyayyar iskar wajen suna fira wani lokacin kuma suhau kwale kwale ayawata dasu cikin ruwan Satinsu daya aqasar suka cira kuma, basu dira koina ba sai SPAIN Fadin murnar da saudart tayi 6ata bakine don ko a jirgi ma sai mutsu mutsu take jitake kamar tayi tsuntsuwa taganta can Bata ta6a tunanin zata sake zuwa wannan qasar ba, tayi missing din mutanen qasar especially Reyna da Loveth Gwara gwara Loveth suna waya suna kuma chatting via media amma Reyna kwata kwata bata samunta A estate din dasuka sauka wancan karon sukayi dasauki wannan karon ma saidai ba wancan gidan bane, wani ne kuma daban kasancewar dama gidajen na haya ga ire irensu matafiya dabasu son sauka hotel dama tsirarun yan qasar dasuke sha'awar zama wajen Murnar saudart takoma ciki bayan ta iske duk yawancin qawayenta na wancan zuwan duk basunan ciki harda Reyna data koma qasar haihuwarta Wato Italy Saidai tayi murna sosai da iske Loveth nan aka zauna anata firan yaushe gamo, anan ne Loveth ke bata sabuwar number Reyna suka kirata video call Hauka ne kadai Reyna batayi ba don murnar sake ganin saudart tana cizon yatsan takaicin rashin haduwarsu Ananma saida sukayi sati daya inda a ranar daren da zasu daga wato juma'a ranar Good Friday dasuka saba haduwa awajen don zumunci da sanin juna ashraf ya hadu da gayen da yaso shiga gonarshi wancan karon😆 Sunyi mammakin ganin juna don basu ta6a tunanin zasu sake hadewa ba Gaisawa sukayi cikin mutuncin kamar ba abinda ya ta6a hadasu, suka zauna kusada juna suka shiga cafta irin tasu ta maxa dukda ashraf be cika tofawa ba Saudart kau a 6angarensu wannan karon ma nan da nan tayi qawaye, can zaka hangota tsamo2 cikin mutane ana maida yadda Washegari suka cira daga qasar suka shilla Saudia don yin umra Sosai saudart tashiga shauqi ganinta gata ga dakin Allah Ibada sukeyi ba dare ba rana suna addu'o'i da neman kusanci awurin Allah. Bata ida shiga shauqi ba saida sukaje madina, gata ga qabarin Annabi Muhammad (S.A.W) Ranar taci kuka kamar ba gobe tana yima fiyayyen hallita kirari (muma Allah ya gwadamana irin wannan rana, amin🤲🏻) Satinsu biyu anan sannan suka fara shirye shiryen komawa gida Nigeria *NIGERIA* Anan kau tun bayan tafiyar su ashraf da yan kwanaki sadeeq yayima ummanshi magana akan wadda yakeso. Sosai umma taji dadin wannan hadin don haka batareda 6ata lokaci ba ta sanarda danginta Dana margayi babanshi (baban sadeeq yarasu tun sadeeq na shekaru 5 sanaddiyar hatsarin mota) Suma sosai dangin sukayi murna don dama sadeeq ya Isa aure masha Allah kuma sun jima suna Mashi magana akan haka Cikin qanqanin lokaci aka tura kudin mungani munaso inda aka tsayar za'a tsaida ranar aurenne idan babban yayan yarinyar yadawo daga tafiya. *SAUDI ARABIA* Tun saura kwana biyu sudawo Nigeria suka fara shopping din kayan tsaraba Kaya suka jida sosai kamar basujin zafin kudinba kowanne zuciyarshi cikeda dokin komawa gida *NIGERIA* Qarfe 5:00pm sukayi landing a filin jirgin sama na Aminu kano Baby da sadeeq dasuka zo tarbansu suka shiga baza ido don ganin ta ina zasu 6ullo Acikin mutanen masu Saukowa suka hangosu suma hannunsu sarqahe ana juna Baby tafara hangosu hakan yasata qara gwala idanu don tabbatar da eh su dinne "Ya sadeeq kalla" tafada tana nuna satinsu da yatsa hakan yasa shima yabi inda ta nuna din da kallo Shima hangame baki yayi cikeda mammaki don shima a kallon farko be ganesuba Sun chanza sosai sun wani yi fresh especially saudart ga kumatun da kowanne ya ajiye ku6ul2😆 Sunyi kyau sosai cikin shigar ankon dasukayi black and white sun taho hannunsu sarqahe dana juna gwanin sha'awa Baby jitake kamar ta ruga taje ta taryosu saidai tanajin nauyin yin hakan gaban sadeeq hakan yasata tsayawa tana kallonsu fuska awashe Sai daga su saudart ma suka hangosu nan take dadi yakama saudart tasaki hannun ashraf tayi saurin qarasawa ga baby daketa washe baki suka rungume juna baby harda dan ihun murna tana cewa "Sweet auntyyy" Shikau ashraf yana qarasowa suka gallama juna harara shida sadeeq kamar irin basuji dadin ganin junaba amma karka bincika zuciyarsu don cike take da murnar sake ganin juna bayan fin wata basusa juna a ido ba "Hmm sai yanzu kuka gama business trip din?" Inji sadeeq yana watsa mashi harara Yatsina fuska ashraf yayi yace "Shafa kaji" Tsaki sadeeq yaja yace "Kaji dashi, zonan ba don halinka ba" yafada yana jawoshi ya rungumeshi Shima ashraf hugging dinshi yayi yana murmushin daya bayyana haqoranshi don ba qarya yayi missing dinshi sosai A bangaren su baby kau sakin saudart tayi daga rungume juna dasukayi tadan ja baya tana kallonta tace "Ehhh? Wai aunty kin ganki kuwa? Wannan murjewa haka? Meye sirrin" Yitayi kamar zata bata rankwashi hakan yasata saurin noqewa tace "Sirro, ni ina ummy na?" "Hajiya ummy ana gida, cewa nayi nice first din ganinku tunfa 4 something Muke nan muna jiranku, ammafa wlh hajiyata kin wanku, halan dakukaje chan cikin injin din wanke fata aka saki? Wannan murjewa haka?" Itadai saudart bata sake bi takanta ba don idan da sabo tasaba da halin baby Juyawa tayi suna gaisawa da sadeeq dake mata shaqiyancin wai daga business trip shikenan sai baba tagani? Itadai dariya kawai tayi daidai lokacin kuma baby ke gaida ashraf tana mashi ya hanya amsawa yayi sannan suka dunguma suka shiga motar, su baby na baya su ashraf na gaba inda sadeeq ne mai tuqi suka fice daga airport din. A qofar gidansu suka ajiyesu babu yadda basuyi dasuba akan su shiga amma suka qiya suka juya suka bar wajen Haka su saudart suka shiga gida cikeda gajiya hade da farincikin dawowa qasarsu lfy. Sai washegarin ranar suka bude tsaraba kowa aka ware mashi tashi sannan suka gama hanyar gidajen iyayensu Gidan Mamy suka fara zuwa, sosai Mamy tayi farincikin ganinsu ta tarbesu cikin jindadi tana nan nan dasu Su habeeb basusan hakan ma Abba hakan yasa gidan yayi shiru Tun a kallon farko da Mamy tayiwa saudart tagane ba ita kadai bace, duk yadda akayi akwai abinda ke lafe a mararta Hakan yasata farinciki sosai nan taita jide masu kayan ciye2 kala2 Ashraf beji ba dayawa sai saudart data barraraje ta kwashi girkin don dama kwanakin nan haka take, ashraf har mammaki take bashi saboda cinta, kome tasamu ciki Sun dan jima anan sannan suka wuce gidan ummy Ananma tarba suka samu sosai daga uummy, su baby ba'a nan Itama ummy a kallon farko asirin saudart ya tonu, itama tayi murna sosai don tamafi Mamy murna da hakan Anan itama suka jidemasu nasu tsarabar ummy nata murna dasa albarka Sai anan take gayamasu kawo kudin neman auren baby da akayi Sosai saudart taji mammakin wanda akace ya turo while shi ashraf beji irin mammakin nan ba don dama yasan za'a rina Sosai suka nuna farincikin su akan hakan balle saudart dataga dacewar hadin Anan suka qarasa wunin ranar inda saudart tasamu baby bayan tadawo ta tisata gaba da tsokana itakau sai rufe fuska take tana Dariya *** Saida wata Monday din ta zagayo sannan suka koma aiki Saidai wannan karon shiriritar tafi yawa ta 6angaren saudart Batada aiki sai ciye ciye, Kwata Kwata batajin dadin bakinta ya zauna hakanan don kasa hade miyau take shiyasa koda yaushe cikin ciye2 take Haka zatazo ta zauna a office din ashraf ta tusa kayan ciye2 agaba wanda duk yawanci malaqi ne, taita jidama ciki babu ko gajiya Ashraf tun abin na bashi mammaki harya fara damunshi don ko hanata yayi saita tusashi gaba da kuka Ya lura ba ciwon ciye2 kadai ke damunta ba harda na kuka don yanzu tazama wata ruwa ruwa, qiris take jira ta 6arema baki Yauma zaune yake a office dinshi yana typing a system dinshi yanason qarasa wani aiki da ake buqatarshi cikin gaggawa Dagowa yayi a karo na ba adadi ya kalli saudart dake zaune kan wata sofa dake gefen office din ta tankwashe kaffafu bowl din soyayyar gyada mai 6awo a gabanta sai wani bowl din a gefe tana zuba 6awon aciki Cin gyadar ta takeyi tana lumlumshe idanu kamar mai cin soye Tunawa yayi da darun dasuka sha kafin asiya gyadar Daga ganin mai tallar gyada a hanyarsu ta tahowa ta tibure dole saiya tsaya ta saya Daya qiya tasamashi kuka wurjanjan kamar wacce akayi was dukan tsiya, babu arziqi yajuya ya saimata nan ne fa yasamu lfy Girgiza kanshi yayi ya maida kanshi a system din gabanshi yana ayyana dolene ma suje asibiti yau idan sun tashi don abin yafara yawa kar ace wata cutace basu Sani ba sai ta girmama tafi qarfin magani sannan Da wannan tunanin yacigaba da aikinshi wanda ita yakamata ta kama mashi amma yasan idan ya matsa mata shi zai kwashi kayan haushi don kamar asiri datahau system da niyyar aiki saita bingire da barci, kai dolene ma yau ayita ta qare, dole yakaita aduba lfyarta don shi abin yafara bashi tsoro (Wayaga first enter🤣🤭) Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻 (contract marriage) Story written by Ashaanty love💖 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 *FINAL🤸🏻‍♀️* Koda suka tashi daga aikin asibiti yawuce daita straight Yanajin tanata mitar ita lfyarta qalau yayi banza daita don shi yasan ba lafiya ba Koda suka Isa asibitin haka suka fito suka nufi ciki saudart bakinnan a ture ita Allah Dole fushi take wai ya kawota hospital on no purpose Shidai be kulata ba saima kama hannunta dayayi suka shiga cikin qayattaciyar asibitin Cikin qanqanin lokaci sukaga likita kasancewar sunada family doctor a asibitin Saida ashraf yagama koramashi bayanin abinda ke damunta fuskarshi dauke da damuwa sannan yace dan Allah a gwadata kar ace wani ciwon ne Shidai doctor murmushi yayi sannan yakira nurse ya umarceta da diban jinin saudart Dakyar tabari aka diba don saudart daman mugun tsoron allura take Saida aka diba sannan doctorn yafita zuwa lab dakanshi don aunawa yabar ashraf da aikin rarrashinta don hawaye take sosai dama tusa hali bare anci wake Saida doctor yakwashe fin 30mins sannan yadawo fuskarshi washe Congratulating dinsu yafarayi sannan ya miqa mashi result din yana fada musu abinda ke ciki Mutuwar zaune duk sukayi suna kwalalo idanu waje sannan suka kalli juna Saurin fizge takarda tayi daga hannunshi ta duba tana qara wara manyan idanunta Ciki? Ciki fa? Kuma na haihuwa, how come bata ta6a kawoma ranta hakaba? Dama haka ake samun cikin a 6agas ba ciwo ba wahalar komai? Ita harga Allah bata ta6a kawo hakan a ranta ba don tasan yawanci masu ciki suna shan wahala sosai a farkon samun cikin fa yawan amaye amaye, itakau ki ciwon kai bata ta6a ba gashi period dinta dama duk wata biyu takeyi shiyasa bata damu da rashin ganinshi ba wancan watan ba don it's something normal to her Zokaga murna wajensu musanmman Ashraf, bakinan ko sayuwa beyi, sujjadar shukur yayi cikin farinciki sannan ya kama hannun doctor cikin yin musabaha yana kwarara mashi godiya sannan yakoma wajen saudart da itama takasa 6oye murnarta yayi hugging dinta batareda yasani ba yashiga kwararamata godiya kamar maroqin da aka biyama hajji Itadai saudart kunya ma ta rufeta ganin yadda yake irin wannan 6arin jikin agaban doctor sai dariya doctor kemasu Saida doctor ya gindaya mashi abubbuwan daya kamata ta baryi har cikin yayi kwari kamar daukar abu mai nauyi da ayyukan wahala kuma ciye ciyenta da yawan barcinta is normal ya kyaleta kuma yadinga siyanmata abubbuwan data nuna tanaso except kayan sanyi da zaqi sannan ya sallamesu Ranar saudart taga rawar jiki takuma qara tabbatarda namiji kunya be isheshi ba don a daren babu wanda be kiraba ya gayamawa, wai harda surukanshi da rashin ta ido To su dama su ummy da mamy sun sani sunede da basuda man kai suka kasa gano hakan, sosai sukayi murna akan hakan most especially Daddy, ranar saida ya shige daki yaci kukanshi na farincikin diyarshi daya tilo zata samar mashi jika kuma tsatson babban amininshi margayi Auwal Tofa daga ranar ashraf yakoma bayada aiki sai kulada saudart da unborn dinshi Duk motsinta akan idonshi saiya tambayeta meke damunta, ko me take buqata Saida yayi kwana uku agida yana kula daita sannan ya koma aiki shima koda yaushe suna maqale a waya da kuma zuhr tayi zai dawo gida ya duba lfyar matarshi sai bayan asr zai koma Saudart likafa taci gaba, yanzu dai babu zuwa aiki babu aikin komai saina ci, koda yaushe ka ganta to bakinta yana motsi don irin cikin nanne mai tara yawu, sosai takeba ashraf tausayi musanmman idan yaga tana barcin nan nata na fama, wani irin sonta yakeji a zuciyarshi da tausayinta yana addu'ar Allah ya rabata da abinda ke cikinta lfy A bangaren maganarsu sadeeq kau tuni akasa rana, nan da wata hudu Wato bayan graduation dinsu baby Zokaga murna wajen sadeeq, nanfa yafara yima ashraf wani gani gani wai shima yakusan zama angon yaga ta gori Shidai ashraf dariya yakemashi yace Ai kuma na gaba yayi gaba kuma dole akira mijin iya baba, wai yabishi ahankali don shi surukinshi ne idan yakawo mashi raini saiyayi mashi buqulu yaga ta tsiya, Dariya sadeeq keyimashi yace wannan labari ne Haka akaita rarrafawa inda saudart da ashraf suka cigaba da rainon cikin dasuke ma so marar misaltuwa while su baby da sadeeq ana gefe ana shirye shiryen biki wanda saudart tayima laqabi da *Auren zafafa biyu* don a tsakanin sadeeq da baby ba'a San gwani ba don hallayarsu daya daga zafin dumin har rawar kan, tasan dai gidansu dandalin drama zai zama don zani ce ta tarda muje *** Biki fa ta matso inda ake shirye shirye tako wanne bangare Kallo daya zakayiwa shirye shiryen bikin ka tabbatar da na yana gaban goshi ne bana bayan qeya ba Ashraf shi ya dauke nauyin komai da za'ayiwa baby both kayan daki da kitchen Sosai ya narka kudinshi wajen hidimar tilon qanwarshi da duk duniya baida kamarta Saudart itace jagaba amara qahon qirjin biki don duk da ita ake zuwa siyayyar kayan kitchen, agefe kuma tana koyawa baby nau'ikan girke girke iri2 don shiririta yasa bata wani iya girkin kirki ba Ummy kuma anata 6angaren zagewa tayi ta gyara diyarta kuma autarta ciki da bai, abin dai chakwai👌 Basu wani tsara bidi'o'i ba a bikin sai kauyawa party da za'ayi ranar Daren biki sai walima ranar biki Abin yaba kowa mammaki don babu wanda beyi tunanin za'asha shagulgulaba a bikin dubada yadda yanayin amaryar mai jiran gado da angon suke Qawayen baby dasuka shirya ma bikin sosai suna dokin shi suka shiga mita wai ta za'ayi bikin *mhiz meebie* guda ace event daya za'ayi wai kuma qauyawa? Bude kwandon shara baby tayi tasakasu aciki ta rufe acewarta batada lokacin su Biki ba saura 1 week su nafeesa da mardeeya (cousins din saudart) suka antayo daga Maiduguri don tun bayan bikin su ashraf suke zumunci sosai da baby Sosai baby taji dadin zuwansu, babu 6ata lokaci suka tare dakinta aka shiga maida yadda akayi Lokacin da su nafeesa suka hade da saudart sosai suka shiga yimata dariya don alokacin ta chanza sosai, ciki ya hurata dukda bawani girman ciki gareta ba saidai ta chanza tawani ajiye wasu tayani muni a fuska nanfa suka shiga saida halin dasuka saba na tsokanar juna irin na abokan wasa Biki na saura kwana uku wasu qawaye uku ba baby suka qara zuwa gidan cikinsu harda teema aminiyarta Alokacin daka shigo gidan zaka tabbatar da kashigo gidan biki don yafara cika da yan biki kama daga dangin ummy na yola har dangin abbansu ashraf na wudil Aranar kayan lefen baby suka duro gidan Masha Allah, ko hasiddin ida hasada yagani saiya yaba don sosai sadeeq yataka rawar gani a kayan Su saudart sune gaba gaba wajen ganin lefe sai yabawa ake Saudart anshiga busy, Ku kau bikin autares kuma qanwar miji guda? Duk hidindimun da akeyi agidan da ita akeyi donma ummy na dan hana wani abin saboda condition dinta Duk kayan snacks da drinks da ake amfani kuma ake kan amfani a bikin daga bakery dinta suke tana gaba akan wannan Shima ashraf a bangaren shi yashiga busy, gashi babban aminin ango gashi babban yaya ga amarya Sosai kanshi yadau chaji don sosai yanuna shi dan halak ne don komai tare sukeyi da sadeeq yayinda ya dauke mashi abubbuwa da dama yayimashi da aljihunshi Ranar Daren biki wanda yayi daidai da kauyawa day A wani gidan gona na ashraf aka yishi Cä6 duk wanda beje party dinnan ba yayi missing Watakan ya qayatu kamar me, dukan jama'ar wajen sanye suke cikin kayan ainahin kauyawa wadanda suka amsa sunansu kauyawa don bazaka ta6a tunanin akwai daya daga cikin su daya ta6a taka gate din makaranta ba don kowannensu da irin shigar ban dariyar dayayi Shidai ango sanye yake da wata kodaddiyar malun malun mai jirwaye jirwaye don asalinta blue shadda ce aka jiqata a hypo dukta 6aci, babbar rigar har tadeshi take saboda girma da tsawo yasa wani dan iskan three quarter aciki wanda ba'ama hangoshi don malun malun din ta rufeshi sai rawanin daya Nada akai da wani blue din soson wanka abin gwanin dariya Itakau baby sanye ake cikin riga daban, zane daban kallabi daban tawani tamke kai fuskarta kau tasha makeup din qauyawa da dige dige Ashraf sanye yake cikin wata kodaddiyar Yar shara sai baqin three quarter shima wanda shine shigar manyan abokan ango sunsha irin wannan cover shoes din na Fulani Saudart itama sanye take da kaya duk daban2 ga dan tumbinta daya qara qawata abun itama fuskarta tasha makeup din kauyawa kamar wata aljana hakama sauran qawayen wasuma abin nasu harda hauka Ranar masu rake sunyi ciniki don kowanne da Yar sandar rakenshi a hannu Waqa aka samasu ta qauyawa akafara shiga kamar a dandali ana rawa Can aka saka waqar Naira Marley da cblvck mai taken *baby kingsway* Duka manyan abokan ango idan ka cire ashraf da aka nemeshi ko sama ki qasa suka shiga Tareda mai girma ango daketa fama da malun malun dinshi ta fama Suka shiga yin rawar waqar iri daya wanda da alama sunsha training kafin su iyata Nan take wajen ya dauki tafi da sowa, abinda zaifi baka dariya shine rawar sadeeq don kafin sugama ya jigata sakammokon shan qasan dayake idan babbar rigarshi ta tadoshi kuma haka Yake tashi ya cigaba da rawanshi ko ajikinshi Ansha dariya har saida cikin wasu ya kulle don wani abin da gangan sukeyi duk dan suba mutane dry Saida suka gama sannan akaba Amarya da ango fili don su danse, aka saka masu waqar macukule suka shiga maming yadda kasan su suka yita dama Kai fadin abubbuwan da akayi awajen 6ata bakine don sosai wajen yazama dandalin barkwanci don wasu saboda dariya cikinsu harya qulle Can na hango yan group din *AUREN KWANGILA 1&2* da yan group din *OFFICIAL MARCY NOVEL* da yan group din *HOME OF NOVELS* Can na hango *Maman naseer* na kallon *ayiya baby* dake qoqarin kwaikwayon rawar tingarangajam da wasu maxa keyi a filin wasan yayinda *beebat* da *Fatima haruna* ke tsamo2 cikin qawayen baby da alamun dai ansamu shiga Awani bangaren kuwa *Maman Zainab* inkiya *nifa na nutsu😆* tana gefen ta nutsu tana kallon yadda wata kwaila daya daga cikin qawayen baby ke rawa kamar zata lauye Akusada ita naga *Umma aliyu* da *malaash* suna tunsura dariya ganin kwalliyar wata wanda sak ya maidata wata ifrituwa Agefensu kuma *Rahila Abba* ce tana rawar tambola har wani zaro harshe ake alamun rawa tayi dadi Acan tsakiyar taro na hango *Maman Hassan* da ita da tawagarta su *ummukulthum*, *Dr halima* da *ummu sabira* tsaye kowa da Yar sandar rakenta ana wazga ana rausaya kai alamun abin na antayasu cikin shauqi sosai *Ummu Muhseen* kau ana maqale bayan wasu yanmata yangayu masu selfie sai tantado take ita da tsiya sai an dauka daita (lol😆) A bangaren ashraf kau dama fili na hargitsewa a rawar farko ya faki idon abokan shi ya lalla6a ya janye matarshi suka gudu Dama jinsu bash yake lokacin dasuke cewa babu abinda zai hanashi dansewa ranar partyn ko training din rawan dasuka yi kallonsu kawai yake don bega lalacewar da zata sashi yin rawa a bikin koda kuwa ya iya bare shi zero over kunnuwa ne a fannin rawa, bega dalilin da zaisa yayi embarrassing din kanshi da kanshi ba Saudart kau ta cika tayi famm don taji haushin gudowar dayayi da ita batareda taga komai ba a partyn hakan yasa ko kallonshi batayi saima kauda kai datayi tana kallon window din motar Acan kau sai wajajen 10 na dare suka tashi kowa ya watse bakinshi dauke da labarin partyn Washegari saudart taqara jin zafin tafiya daita da ashraf yayi sakammokon lbrin da yan biki ke badawa na partyn dama vidiyoyin da akayi, ta ciji yatsa sosai na missing datayi bama ita kadai ba harda wadanda suma basu samu hallata ba Aranar gida ya ida kacamewa da jama'a kasancewar ranar daurin auren ne Amarya ana can daki ita da zugar qawayenta masu halinta Wato duk yan iyayi ne, babu abinda ke tashi a dakin sai shewa da hirraraku, Amarya an qame akan gado taci adonta cikin wani danqareren pink lace mai touches din fari, fuskarnan tasha makeup ga kannan dashima yasha dauri Babu ruwanta tana tsakiyar qawayenta suna shewa suna maida yadda akayi kamar ba ita za'a daurawa aure anjima ba A bangaren saudart kau tana cikin jama'a komai da ita akeyi sosai dangin su ummy da Abba suka yaba qoqarinta don taxage komai daita akeyi. Sai bayan an sauko sallar juma'a aka daura auren *ABUBAKAR SADEEQ UMAR* da *AMEENATU AUWAL (BABY)* akan sadaki mai daraja Zokuga bakin ango, kasa rufe baki yayi don farinciki, mutane sai bashi hannu suke suna masu fatan zama lfy Shima ashraf anci gayu cikin milk din yan ciki da babban riga kana ganinshi kaga aminin ango yayinda shikuma ango ke sanye da all white Wato komai nashi farine kama daga babbar rigarshi da yanciki zuwa takalmi zuwa hula kai komai nashi farine acewarshi yau farar ranace dole yayi shigar nuna hakan Daga wajen daurin auren suka wuce reception inda akaci akasha cikin farinciki da aminci Nanfa aka bude babin tsokana atsakanin angon da abokan ango, to dayake angon A ne shima sai caftar tayi dadi don duk abinda ka fada saiya samomaka amsarshi Ashraf kau Kwata Kwata hankalinshi baya Kansu yakoma ga sarkin fushi Wato saudart da tun jiya tayimashi fushi don ya dauketa daga party, shi yanzu wani abin nata Dariya yake bashi don yanzu tazama wata rigimmamiyar qarfi da yaji, abu kadan sai kumburi Tun dazu yake kiranta taqi dagawa, ganin bazata amsa dinba yasashi qyaleta yana cije lower lip dinshi A bangaren saudart kau batama San yanayi ba don wayarta na cikin jakarta dake dakin ummy itakuma tana wajen Amarya da izuwa yanzu tayi laqwas, haka kawai taji jikinta yayi sanyi tun lokacin da labarin daurin aurenta ya risketa Nanfa akazo aka zagayeta anata callara mata guda a kunne ana mata wakar tazama dauko riga Tun baby na cijewa harta kasa riqe kukanta tashiga yin kayanta wurjanjan Saudart ita abinma dariya yabata don bata manta yadda baby ke cika bakin babu abinda zaisata kuka ranar aurenta, ca6 kamar wani auren dole? Sai gashi tana kuka bilhaqqi da gaskiya Dayake mutane duk sunsan shaqiyancinta babu wanda ya tausaya mata alokacin don kowa dariya yake mata yana qara tunzurata, saida akazo daukarta sannan tafara bawa mutane tausayi don kuka take sosai ta maqale umminta wai babu inda zata ita tafasa auren. Dayawa sun tausayamata yayinda wasu irin su abokan wasanta sai qara tunzurata suke da waqar 'ke kikace kinaso' Acikin masu tausaya mata harda saudart don sosai abin ya tuna mata da itama ranar aurenta hakan yasa take dauke hawayenta akai akai Dakyar aka 6am6are Amarya jikin ummy da itama ke hawayen mixed feeling tana godewa Allah daya nunamata auren autarta lfy dakuma jimamin rabuwa da yarta wanda kowacce uwa mai aurar da diya keji Haka aka fito daita akasata cikin galleliyar motar daaka tanadar ta daukar Amarya, cikin motar harda saudart don qin sakin hannunta baby tayi ta wani maqalemata dole saida ita aka shiga motar saudart na ayyana darun da za'asha idan zata taho A wani qanqararren gida suka shiga, ba qarya gidan yabada don ya qawatu iya qawatuwa Tarbar mutunci danginsu sadeeq sukayiwa su Amarya, gidan babu abinda ke tashi sai guda Itade baby kanta na qasa fuskarta lullu6e da mayafi yayinda haryanzu take riqe da hannun saudart gamm Saida aka rakasu hat dakinta dake sama yasha kayan alatu sannan ala barsu don suyi shirin walima Chanza shiga duk sukayi inda Amarya taci adonta cikin maroon materials riga da skirt aka doramata alkyabba milk colour asama wanda hular ta rufe mata rabin fuska Saudart dai shadda purple tasa riga da zane pieces sannan ta dora zumbuleliyar hijabinta wanda yanzu ya zamemata jiki don rabon datasa gyale harta manta don baban kishi be bari idanma zatasa saidai tasa cikin gida tayimashi kwalliya amma bawai tafita dashi ba Sosai walimar ta qayatar, ango da Amarya sunfito sharr dasu kamar ka sace, ango shima dakkakiyar shadda milk yasha wanda sukayi ango shida dukan abokanshi, fuskarshi sai fidda annuri take Ansha wa'azuzuka masu ratsa jiki sannan aka dora da zikiri mai antaya mutane shauqi sannan aka rufe da addu'a Saida aka gama sannan aka maida Amarya dakinta dama kuma magrib tayi Sosai baby ta tashi hankalinta ganin bata ga wulgin saudart ba, koina an duba ko sama ko qasa babu ita hakan yasa baby kuka sosai dukta tada hankalin mutane Itakau saudart dama tun fitowarsu taga ashraf cikin zugan abokanshi, to tun kafin taron ya watse tabishi suka gudu bayan sun gama sassanta tsakaninsu Baby kau taci kuka dakyar aka samu aka rarrasheta, qawayenta kau saida aka rako ango sannan suka samu suma suka fece tareda abokan ango, akabar daga Amarya sai ango (zakici ubanki ne😎) *Agurguje* Akwana atashi lokaci yacigaba da tafiya, kwanaki na zama sati, sattitika na zama watanni Watan haihuwar saudart Yakama yayinda izuwa yanzu dukta chanza kammani saboda yadda cikin ya hurata Ranar wata laraba ta tashi da naquda aka garzaya da ita asibiti Saida ta wahala sosai sannan ta sulli6o danta masha Allah mai kamada ubanshi Zokaga murna wajen wannan ahalin Ashraf baki har qeya anyi da, anzama daddy Sosai akayi hidima ga haihuwar wanda baby bata wani yi abin kirkiba awurin saboda qaramin cikinta dake bata wahala don mai laulayine sosai Ranar suna baby boy yaci sunan kakanshi, Wato *AUWAL ASHRAF AUWAL (A.A.A)* sai ake Mashi laqabi da *Junior* Ansha shagulgula a sunan inda sadeeq shima yayi bajinta donshi yabada abin yanka yakuma jidema baby kayyayaki masu tsada da yawa Daddy ma yayi farinciki sosai kuma shima ya taka rawar gani a hidimar sunan inda shikuma yake kiran d'an da *Aminin* *FIVE YEARS LATER* Aguje wasu yara suka rugo suka nufi kitchen, ta gaban na qara tana kiran "mummy!" Da qarfi Saurin juyowa saudart dake kiciniyar hadama Dad (ashraf) coffee tayi daidai yarinyar dabata fi shekaru uku ba ta fadomata ta rungume qaffafunta tana sakin qara Burki yaron daya buyota yaja sanadin mugun kallon da mummy ke watsamashi, yaron bazai wuce 5 years ba, kallo daya zakaimashi kaga tsantsar kamarshi da babanshi "Junior wai meke damunka ne? Kai kenan idan kana nan yarinya bazata walaba? What exactly is your problem?" Inji saudart rai 6ace "Mummy wlh ita ta zubarmin da paint fa" yafada yana kumburi Caraff yarinyar dake maqale still daita tayi tace "Mummy wlh its not intentionally" "Yimin shiru! Kin iya zuwa kijawo fada sannan ki rugo kina neman 6uya ko? Tom kacigaba, will apologize to him now ko saina makeki?" Tafada cikin zaromata idanu Turo guntun bakinta yarinyar tayi sannan ta kalli Junior dake antayamata harara tace "Am sorry" "To zuciyatu kaji dai she's sorry, kuma kaima ka dinga sanin inda zaka ajiye abinka yadda baza"ayimaka barna ba kuma nasha fadamaka idan tayi maka abu kazo kayi reporting bawai kadau hukunci ahannunka ba amma bakaji ko?" Sadda kai yayi qasa yace "am sorry" "To oya kuwuce upstairs ganinan" Juyawa duk sukayi ganin wanda ke bakin kofar yasasu sakin ihu tare sukaje suka rungumeshi Duqawa yayi yana Shafa Kansu tareda jan kumatunsu "Junior and zahra, Tom and jerry kunanan kuna sa mummy magana ko?" Tare suka nuna juna zahra nacewa "it's him" junior na cewa"it's her" Dariya yayi masu yajawosu ajiki yace "It ok amma idan kuka sake bazan sake kaiku gidansu *Jidda* ba (diyarsu baby) "Daddy mun daina!" Suka fada tare "Ok now go upstairs Ku ida homework dinku ok?" Jijjiga kai sukayi sannan suka juya sukayi waje aguje Binsu da kallo sukayi saudart na girgiza kai sannan tajuya tacigaba da abinda take Qarasowa yayi wajenta ya rungumota ta baya ya ziro kanshi ta wuyanta yana kallon abinda take yace "Yadai matar contract" "Ba lau ba mijin contract" ta amsa Huramata iska yayi akunne yace "Menene ba lau ba" "Contract dinnan yayi due, yakamata akawo qarshanshi" Juyo daita yayi suka fuskanci juna yace "Ko?" Yana sissinar wuyanta "Yes" tafada tana lumshe ido fuskarta dauke da murmushi "Ok then, Ai alqawarinmu be cika ba, karki manta da deal din, sai munyi jikoki biyar, kinga ko yayan baki gamaba bare ayi maganar jikoki" 6ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace "To yanzu ya zamuyi?" "Kawai Samar dasu zamuyi awuce wurin" "How?" Tafada tana kallonshi seductively Hade goshinsu yayi waje guda ta zura hannu tabayanta ya kashe gas din dakeci sannan cikin muryar rada yace "By doing the do" Kafin tasamu zarafin magana ya hade bakinsu wajen daya...✍️ Alhamdullilah! Alhamdullilah!! Alhamdullilahi rabbil alameen!!! Godiya ta tabbata ga Allah s.w.t daya bani ikon kammala wannan littafin lfy Kurakuren damukayi ciki Allah ya yafemana Godiya gareku fans wadanda kuka jajirce kuna bibbiyar littafinnan har kawo yanzu da muka gamashi cikin qoshin lfy, Allah yabar zumunci yakuma dorar da zumuncin mu har a aljanna (insha Allah) Taku akoda yaushe Ummin fasihu🧚🏻‍♀️ Saikuma mun sake hadewa awani littafin Ma'asallama🤝🏻