[01/08 3:32 PM] Sumayya Takori: *SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar Gobe kiyama* AUREN KWANGILA- Page1 January, 1996 K yakkyawan gidan ginin zamani na nan a tsakiyar hamshakiyar unguwar Asokoro cikin babban birnin tarayya, Abuja. Ba shi da girman da ya wuce kima, amma fasahar da aka zuba wajen gina shi abar kwatance ce, sannan hawa daya ne babu hawan bene (flat house). Ainahin ginin gidan a tsakiyar gidan aka yi shi, inda furanni suka zagayeshi suka yi masa rumfa har samansa, rufin da aka yiwa gidan brown ne ire-iren rufunan gidajen kasashen ketare. Kamar yadda rufin gidan yake brown haka fentin gidan ma yake ruwan madara da ruwan kasa (milk&brown). Daga can gefen dama na gidan an gina guest rooms wato dakunan saukar baki wadanda maigidan yayi su ne musamman don saukar ‘yan uwansa dake Kanon Dabo idan sun zo. Gidan ya kawatu da furanni kala-kala dogaye da gajeru masu sanyi da kamshi da kyawun gani hadi da kayatarwa a harabar gidan da kewayensa. A kasa kuwa ‘grass carpet’ ne sun kwanta sun yi lumm, masu taushi da sanyi hadi da sanya nishadi a zuciyar mamallaka gidan. Da ka shigo get din gidan dakin maigadi za ka tadda a baryar dama, daf da get din. In ka kara yo gaba kadan rumfar adana motoci ce, ga su na a jere sai numfashi da sheki suke yi, mulmulallu kuma kosassu rufe cikin tamfol, adane reras cikin rumfar ba tareda kowacce ta gogi ‘yar uwarta ba, samfur din kowacce daban dana ‘yar uwarta, motoci ne da wadanda suka ci suka tada kai ke yayi a wancan zamanin. Wannan kayataccen gida dana bata lokaci wajen wassafo muku, mallaki ne na Professor Dr. Hamza Dakata, wanda ke rike da mukamin (parmanent secretary) na ofishin shugaban kasa mai ci a wancan lokacin, shekara ta alif dari tara da casa’in da shidda wato (1996). Matar gidan, Hajiya Maryam Hamza Dakata, na zaune cikin daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun da suka kawata falon. Saboda girmansa kujeru saiti uku ya ci ba tare da kowanne seti ya san da zaman dan uwansa ba. Wato a kowacce kusurwa ta falon akwai setin kujeru kala daban da ‘yan uwansu, haka kilishin da ke shimfide a kasansu (carpet) kala daya yake da setin kowanne setin kujera. Sai aka yi labulaye mai ratsi da kalar dukkan kujerun falon. Idan ka dubi Hajiya Maryam sai ka ji kamar ka sace ta ka gudu sabida kyau da iya ado. Kai ba za ka ce ita ta haifi yara maza guda hudu da ke zagaye da ita tana koya musu aikin makaranta na yi a gida ba (homework). Kallo daya za ka yi wa yaran ya ishe ka kimanta irin hutun rayuwar da suke ciki su da iyayensu, domin dukkaninsu girmansu ya haura shekarunsu. Babban, wanda ke amsa sunan Abdul’azeez shekarunsa goma sha uku. Yana amsa sunan “Yaya Azeez” daga bakin kannensa. Sai mai bi masa Isma’el da kannen sa biyu ke kira “Ishma” shekarunsa tara. Daga Isma’el sai Usman shi kuma shekarunsa bakwai a duniya tsiransu babu yawa. Hajiya Maryam ta jima bata kara haihuwa ba bayan haihuwar Usman, sannan ta haifi autan ta Haleem wanda har yanzu bai kai ga shiga makaranta ba, dan shekaru uku. Lokaci zuwa lokaci Hajiya Maryam kan daga kai ta dubi agogon bango, sai kuma ta sauke ta ci gaba da nunawa Azeez aikin makarantarsa (home work), da gani za ka fahimci dakon wani abu take (jira); tana tsammanin shigowar maigidanta ne daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Ya ci a ce ya shigo gida tun dazu shi da ba ya kai wa magriba a (office) in ba da wani kwakkwaran dalili ba. Idan hakan ta faru ma zai yi waya ya gaya mata. Amma yau shiru. Usman ya sosa mata inda ke mata kaikayi da cewa. “Wai Mammah ina Daddy ya je ne har yanzu bai dawo ba? It’s almost past eight fa (takwas har ta wuce)”. Hajiya Maryam ta yi ajiyar zuciya, “Kada ku damu. Bari in lalubo shi a waya, watakila aiki ne ya tsare shi”. Ta shiga latsa wayar hannunta, wadda a lokacin (mobile) ake kiranta, rike ta sai masu kambun susa, ta kai a kunnenta, amma har ta yi burarinta ta gama Daddyn bai dauka ba. Ta kira ya kai sau goma ba amsa. Cikin danne tashin hankalinta ta dubi ‘ya’yan nata wadanda suka tsura mata ido kamar a kwayar idonta suke son gano mahaifin nasu. Sai ta rasa me za ta ce musu, duk suka yi shiru. Daidai sanda aka murda kofar falon aka shigo, duk suka maida hankalinsu ga kofar don a zatonsu Daddy din ne. Maimakon shi din, mai aikinsu ce, Jamila. Ta shigo cikin ladabi ta tsuguna a gaban uwargijiyarta. “Mammah abincin dare ya kammala, na shirya komai a (dining)”. Mammah ta nisa, “To sannu da aiki Jamila, muna jiran shigowar Daddy ne kafin mu ci abincin”. Jamila ta ci gaba da durkuson bata tashi ba kanta a sunkuye. Mammah ta lura akwai magana a bakin Jamila. Cikin kulawa ta ce “Ya aka yi ne kuma Jamila?” Jamila ta muskuta cikin matsanancin ladabi, kanta a kasa. “Na zo in yi muku sallama ne, gobe zan koma gida kauye”. Gaban Hajiya Maryam ya fadi, don tana jin dadin zama da Jamila, yarinyar na da hankali, tsabta da ladabi. Ta yi masu aiki kala-kala daga garuruwa daban-daban, amma ba ta taba yin mai aikin da ta ke jin dadinta irin Jamila ba. Shekarunsu uku kenan tare tun haihuwar Halim aka samo mata ita daga kauyen Kura. A tsayin shekarun nan ba ta taba yi mata wani abu da ba ta ji dadinshi ba. Yi-na-yi-bari-na-bari da alheri da kyautatawa ke shiga tsakaninsu. Ta daure ta ce. “Lafiya za ki tafi gida? A sanina lokacin zuwanki gida bai yi ba? Cewa nake yau watanki daya da dawowa?” Jamila cikin matsananciyar kunya ta ke magana. “Ki yi hakuri Mammah (yadda take ji ‘ya’yan ta na kiranta), ni ma ba da son raina zan barku ba. Domin hakika ku mutane ne na kwarai wadanda suka san hakkin dan Adam da darajar da Allah ya yi masa komai kaskancinsa. A wannan zuwan nawa gida na samu miji da muka daidaita, iyayenmu suka yi magana da juna. Na yi wa iyayena alkawarin bayan wata daya zan dawo a daura mana aure. Tunda na dawo nake so na fada miki kunya ta hanani sai yanzu da lokacin ya zo”. Jikin Hajiya Maryam ya yi sanyi. Tabbas duk son da ta ke mata ba za ta hana ta yin aure ba kam a kan neman duniya. Murya a sanyaye ta ce. “Toh Jamila. Na yi miki murna. Allah ya sanya alkhairi, Ya kuma hada mu da alheri. Jira ni ina zuwa”. Ta mike ta yi dakinta ta dauko rafar kudi a jakarta, turamen atamfofi Holland guda uku da mayafai da takalma da jaka uku-uku ta zo ta zubewa Jamila. “Ga kudin aikinki na wata uku a gaba, wannan kuma gudumawata ce Allah ya sanya alkhairi, Ya bada zaman lafiya”. Idanun Jamila suka cicciko da kwallah, ta sa hannu biyu ta karba tana godiya. Ta tashi ta koma sassansu na ma’aikatan gidan. AbdulAzeez ya dago kai daga kan littafinsa, duk maganganun da suke yana jinsu amma bai dago ba sai yanzu da Jamila ta bar falon, yace, “Mammah garinsu za ta koma?” “Eh, aure za a yi mata Abdul’aziz”. Usman ya ce, “Ba za ta dawo ba?” Nan ma ta daga musu kai, ta ce, “Eh”. Damuwa ta nuna sosai a fuskar yaran, don sun shaku da Jamila. Tana kula da su sosai, tana jansu a jiki. Haleem ya ce, “To Mammah, wa zai dinga goya ni?” Ta yi murmushi, “ai ka wuce goyo yanzu Haleem. Kada ku damu, za mu samu wata. Addu’a za ku yi Allah ya sa mu samu mai irin halayenta”. Suka daga hannu duka suka ce, “Ameen”. Isma’el da bai yi magana ba, sai yanzu yayi dogon nazari irin na yara masu tsinkaye sannan ya ce. “To yanzu Mammah wa zai dinga yi miki wanke-wanke da sauran ayyukan data ke yi?” Ta yi murmushi, “Ni zan yi da kaina Isma’el, kuma ba da jimawa ba za mu samu wata...........” Ba ta kai ga rufe bakinta ba suka ji horn din motar Daddy. Ai a guje, in ba ka yi ba ni wuri, Maryam da yaranta ba ga uwar ba, ba ga ‘ya’yan ba, kowanne so yake ya fara isa ga Daddyn. A tare suka isa daidai lokacin da direbansa ya yi fakin a babbar kofar shiga falon, wadda ta kasance ta gilashi (sliding door) suka taro shi zuwa cikin falon don ta nan yake shiga, sauran mutane kuwa sai dai su zagaya su shiga ta kofar kicin. Bakinsa kamar zai tsage don fara’a, ya bude hannuwa suka shige ciki har uwar. Da alama cikin farin ciki yake mara misaltuwa. Da alama akwai soyayya da shakuwa mai yawa a tsakanin wannan family. A haka suka shiga falon yana dauke da Haleem. Sai jero masa tambayoyi Isma’eel da Usman suke yi na ina ya je yau bai dawo da wuri ba? Shi da ma babban wato Abdul’aziz magana ba ta dame shi ba, uban ya kamo hannunsa suka zauna tare cikin kujera, “Come on Babban Yaya. Wa ya taba min kai na ga kamar kana fushi?” Abdul’aziz ya kwantar da kai a kirjin Babansa cikin damuwa. “Daddy ka yi dare ne duk mun damu. You know we care for you too much (ka san mun damu da kai sosai)”. Yana shafa lallausar sumar kan yaron, yana murmushi ya ce, “In ka ji shiru alheri kenan. Amma ba zan fadi wannan albishir din da ke bakina ba sai dukkanmu mun ci abinci mun koshi kada farin ciki ya hana ku cin abinci”. Ya fada tare da mikewa rike da hannun Abdul’aziz din. Da, mafi soyuwa a zuciyarsa, cikin ‘ya’ya maza hudu da Allah ya ba shi. Gabadaya suka hau kujerunsu na cin abinci suka fara ci cikin nutsuwa. Sai da suka kammala suka yi hamdala suka koma bisa kujerun falon, sannan Daddy ya dubesu daya bayan daya yana murmushi ya ce. “Tun safe muna dakin (meeting) da (President), Ambassadan kasar Saudiyya ne ya yi (retire) kuma cikin ikon Allah ni aka baiwa kujerarsa. So ku soma shiri, nan da sati biyu kacal za mu koma birnin Jeddah da zama”. Usman da Isma’el suka soma tsalle, amma abin mamaki ban da Abdul’aziz. Shi kamar ma damuwa ya shiga. Daddy na lura da shi ya kara jawo shi jikinsa, “Ya ya dai Azeez? Kai ban ga kana murna ba”. Ya yamutsa fuska kadan, kana a hankali ya ce, “Daddy I love Nigeria. Bana son matsawa daga cikinta zuwa kowacce kasa. Na fi son in girma, in rayu, in yi karatu a cikinta in tallafe ta watarana. Kowa ya samu ci gaba, sai ya gudu daga cikinta. (I want to be exempted) daga masu yin hakan”. Daddyn ya tsura masa ido yana al’ajabi, wai yaro dan shekaru goma sha uku ke wannan maganar. Shi ne da wannan ‘patriotism’ din (kishin kasa). Ya san kuma abin da ya fada haka yake har zuciyarsa. Shi din kuma ya kasance wani mutum mai girmama ra’ayin ‘ya’yansa. Ya tattara hankalinsa waje guda wajen baiwa yaron amsa. “Ba za ka iya taimaka wa kasarmu ba Abdul’azeez sai ka karantu ka gogu kayi koyi da kasashen da suka riga suka gyara nasu kasashen suka ci gaba. Sannan komawarmu kasar Saudiyyah falala ce mai yawa Azeez. Ga ka kullum kusa da dakin Allah ka je ka roki duk abinda kake so. Ga makarantu na musulunci ba irin namu ba. Ga abinci mai albarka ga kwanciyar hankali. Abubuwan alherin suna da yawa, kuma ai ba dauwama za mu yi ba a can zama ne na kayyadadden lokaci. Ka saki ranka ka ji? Mu je mu gina sabuwar rayuwa”. Ya fada yana bubbuga kafadun yaron. Ga mamakinsa budar bakin Abdul’azeez sai cewa ya yi, “Daddy I’m okey with my life here (ina jin dadin rayuwa ta a nan). Ina son school dina (Regent). Bana so in rabu da ita da abokaina, tunda dama (boarding) nake yi sai in dinga zuwa muku hutu in an yi hutu karshen kowanne ‘term’. Hajiya Maryam da tun dazu ba ta saka musu baki ba, sai yanzu ta ce, “Abdul’aziz kafiyarka ta yi yawa, duk abin da Daddy ya gaya maka ba ka amince ba ko me?” “Na amince Mammah. Abin da ya fada, haka ne. Babu kasa irin Saudiyyah. But I love my country, Nigeria (ina son kasa ta Najeriya) anan nake so in rayu”. Iyayen duka suka dube shi baki a sake. Daddy ya sanyaya murya, “Za ka iya rayuwa babu mu Abdul’azeez?” “Zan iya Daddy, na ce maka ai duk hutu ina tare da ku ko in tafi Kano. I just want to live and study in Nigeria (kawai ina so in rayu, in yi karatu a Nigeria ne).” Ya gyada kai cikin girmama ra’ayin yaron nasa. “Shi kenan Abdul’azeez tunda haka ka zaba. Mu ma mun amince”. Sai a lokacin suka ga murmushin Abdul’azeez. **** Tun a cikin satin Hajiya Maryam ta soma shirin tafiyarsu Jeddah. Damuwarta daya rashin mai aiki. Jamila ta tafi tun a washegarin ranar da suka yi magana. Ta so a ce da Jamila za su yi wannan hijira mai albarka, ita ma ta samu sauyin rayuwa. Ga shi aure ya raba su yadda ba ta da damar sake zama da ita har abada. Tana zaune a falonta ta kira aminiyarta a nan cikin Abuja, Hajiya Halima. Mijinta (controller) ne na (Custom) ita ta samo mata Jamila. Ta gaya mata tana son mai aiki da gaggawa za ta tafi da ita Saudiyyah an yi wa Baban Halim Ambassada. Hajiya Halima ta taya ta murna, ta kuma ce babu lokacin da za a je kauye a nemo, amma ga tata nan Habiba jiya-jiyannan aka kawo mata ita. Su tafi ita za ta nemi wata, ta turo direba ya dauke ta. Hajiya Maryam ta yi wa kawar tata godiya sosai suka yi sallama, ta ce ga direban nan tafe yanzun nan. Alkasim direban Hajiya ya je ya dauko Habiba. Matashiya ce kyakkyawa, amma ba yarinya ba ce, za ta yi shekaru ashirin da tara Haka. Sosai ta yi wa Hajiya Maryam, don da alamu za ta yi tsafta da kuzari. Tun a ranar ko ta soma birge Hajiya Maryam da aiki kamar janareta. Ta gayawa Habiban maganar tafiya da zatayi da ita Saudiyyah ko zata je gida ta fada ta kuma yi sallama amma sai Habiba tace ita bata da kowa, ko sunan garin su ta omanta. Daga nan har birnin Sin su tafi ita bata da matsala. Yakamata ace Hajiya Maryam tayi dogon nazari akan hakan amma da yake a bukace take da neman mai aikin sai bata zurfafa maganar ba, tayi tunanin wani bacin ran ne ya fito da ita daga gida shiyasa tace hakan, tasa aka kai ta aka yi mata fasfo aka hada da nasu Daddy ya karba. Dr. Hamza bai fiya son wadannan ‘yan aiki da maidakinsa ke kwasa ba, ta kan gaya masa ba yadda za ta yi ne ayyukan gidan sun fi karfinta bazata iya rayuwa babu su ba, amma ba sa yi mata girkin da zai ci ita ta ke yin abunta. Hajiya Maryam ta yi murna da samun Habiba sosai da alama tasu za ta zo daya, don duk halayen Jamila tana da su har ma ta zartata wasu abubuwan. **** [01/08 3:33 PM] Sumayya Takori: *SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI* 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* *Auren kwangila* page2 ASALINSU Gidan marigayi Malam Abdullahi Dakata ba boyayye ba ne a unguwar Dakata da ke cikin jihar Kano. Gida ne da ake yi wa kallon babban gida sabida yadda ya wadata ‘ya’yansa maza da mata da ilim addini da na zamani. Sana’ar Malam Abdullahi har ya bar duniya sayar da manya da kananan shaddoji wadanda yake shigo da su daga Cotano ya zuba a babban shagonsa da ke kantin Kwari. Da wannan sana’a ya riki iyalansa, ya ba su tarbiyya mai inganci da ilmin da ake alfahari da su a yanzu. Malam Abdullahi ya dade da rasuwa a lokacin da ‘ya’yansa suka kawo karfi. Allah bai yi zai ci gajiyar ilmin ‘ya’yansa ba, wadanda duk sun fito daga cikin mace daya ne, Inna Rabi. Ya rasu ya bar ‘ya’ya hudu, maza uku da mace daya. Babban dan Malam Abdullahi shi ne Atiku, wanda ahalin gidan ke kira Baffa Attiku, mai bin sa Adda Hafsatu, sai Abdulkarim Dakata, da autansu Idris Abdullahi Dakata. Allah ya karbi ran Inna Rabi Idris na da shekaru ashirin da biyar. Baffa Atiku wanda ya zamo shi ne babba a zuri’ar Malam Abdullahi shi ne mahaifi ga Dr. Hamza da suka haifa da maidakinsa Inna Ramatu. Sun manyanta, amma ba za a kira su tsofaffi ba. Dr. Hamza kadai suka haifa, mai bin Baffa Atiku a maza wato Abdulkarim Dakata a yanzu haka Sanata ne mai wakiltar Kano ta tsakiya, yana Abuja da iyalansa, Adda Hafsatu ‘ya ta biyu ga Malam Abdullahi ita ce, mahaifiya ga Hajiya Maryam, Hajiya Maryam din ce babbar ‘yarta sai kannenta hudu mata Anty Luba, Anty Furairah, Anty Mariya, Aunty Murja da autan Adda Ibrahima wanda ke karatunsa yanzu a jami’ar Ahmadu Bello mataki na farko, yana karantar tsimi da tanadi. Lubabatu, Furairah, Mariya da Murja duk an aurar da su bayan kammala karatun sakandire, su da nasu iyalin duk a Kano suke zaune. Autan Malam Abdullahi wato Idris Dakata, yana karatun likitanci ne a jami’ar Maiduguri, bai kai ga yin auren fari ba, yana amsa sunan Uncle Idris daga bakin yara da manyan wannan zuri’a mai albarka. Adda Hafsatu mahaifiyarsu Hajiya Maryam ta yi aikin gwamnati na tsayin shekaru talatin. A yanzu ta yi ritaya bayan rasuwar mijinta ta zauna a gida ta rungume ‘ya’yanta kasancewar maigidanta Alhaji Hassan ya jima da rasuwa. Kenan Hajiya Maryam da Dr. Hamza ‘yan uwan juna ne, ‘yar mace da Dan namiji suke. Sun tashi gida daya, sun samu tarbiyya iri daya. Aurensu ba na hadin zumunci ba ne, shi ya ce yana sonta tun tana karama. Amma ba wanda suka yi wa auren zumunci bayansu cikin zuri’arsu, kowanne daga waje yake kawo abokin rayuwarsa in ka cire Hamza da Maryam. An yi musu aure tun kafin ta kammala digirinta na farko, shi kuma yana koyarwa a jami’ar Bayero. Ya samu muqamin Farfesa a shekarun kuruciyarsa saboda hazaqarsa wajen rubuce-rubuce da wallafe-wallafe a fanninsa na (political science). Ya rike muqaman gwamnati guda uku a Federal Government kafin Allah ya kai shi ga samun matsayin (parmanent secretary) na ofishin shugaban kasa. Wanda abokin mahaifinsa ne tun na kuruciya ya dauki mukamin ya bashi. Suka tattara suka koma Abuja da iyalinsa. Gidan Mal. Abdullahi ya kara yin fice a unguwar Dakata ko don mukaman dan sa da babban jikansa; Parmanent Secretary Hamza da babban dan siyasa Abdulkarim, wadanda ba dare ba rana duk sanda suka zo garin Kano taimako suke yi wa al’ummar unguwar su da kewayenta ba na wasa ba. A yanzu haka ciki gidan marigayi Malam Abdullahi babban dansa Baffa Atiku da maidakinsa Hajiya Ramatu mahaifan Dr. Hamza ne a ciki, sai Idris wanda in ya zo hutu gida a karshen kowanne zangon karatu dakinsa yana nan a soro na biyu. Adda Hafsatu ma bayan an sayar da gidan gadon ‘ya’yanta su Hajiya Maryam an raba musu gadon mahaifinsu, nan gidan ta dawo ta share dakin mahaifiyarsu marigayiya Inna Rabi ta yi zamanta kusa da dan uwanta Baffa Atiku da maidakinsa Ramatu, suna zamansu lafiya. Babu yaro gabansu sai autan Adda Ibrahim wanda ya fara karatun jami’a. Duk da haka ba ka raba dakin Adda da yara haka dakin Inna Ramatu sabida ‘ya’yan su Luba, Mariya, Furairah da Murja duk hutu suna gidan ko ranar da ba makaranta. Adda Hafsatu na baiwa Inna Ramatu girma yadda ya kamata kasancewarta matar Yayanta kuma suruka a gare ta. Amma wani zubin sukan manta surkuntar su yi ta harkar arzikinsu da kula da jikokinsu. Inna Ramatu ta rike girmanta ta hada shi da kyautatawa. Don haka ake zama na aminci da kwanciyar hankali da wadata a gidan marigayi Abdullahi Dakata. ‘Ya’yansu sun wadata su da komi na rayuwa, sun dauke duk wani nauyi na rayuwar iyayen nan nasu bakidaya. Dr. Hamza ke dauke da nauyin karatun Uncle Idris da Ibrahima don ya fi Sanata Abdulkarim sakin hannu. **** An gama komai na shirin hijirar Ambasada Hamza Atiku Dakata, da iyalinsa kasar Saudiyyah. Washegari suka wuto gida Kano. Babban gidan ya kacame da murnar zuwansu. Ga shi ya kama lahadi ce, su Luba da yaransu duk sun zo kamar yadda suka saba duk lahadin karshen mako. Uncle Idris ma ya zo daga Maiduguri yana (housemanship) a asibitin Malam. Iyalin Sanata Abdulkarim ne kawai babu suna Abuja kuma dama dai akwai matsala ta fanninsa domin abin a zahiri yake, babu iyalin da zai yiwu ace babu baraka ko yaya take a cikin su, hakika Sanata Abdulkarim Abdullahi Dakata, bai yi sa’ar mata ba. Ko kusa Anty Zuwaira (matarsa) ba ta so ya rabi danginsa ko ya wahalta musu, ba kuma ta so suma su rabe shi. Da wuya ka gansu a Kano sai dai ya yiwo waya ko aike, kowa a cikin zuri’ar ya kwana da sanin wannan. ‘Ya’yansa ba su saba da ‘yan uwansa ba, sai na mamarsu da yake ita ma diyar wani kusa ce a Abuja. Ta kan dan yi zumuncin da Hajiya Maryam tunda ita ma mijinta mai matsayi ne kamar su koma fiye da su. Akwai sanayya tsakanin yaranta uku Farhan, Ramadhan da Sha’aban da su Abdul’azeez, amma ban da na sauran dangi da ke Kano. Gidan ya cika sosai da zuri’ar Malam Abdullahi mazansu da matansu da ‘ya’yansu. Adda Hafsatu da mai aikin gidan nata zirga-zirga tsakanin madafi (kicin) da tsakar gida don hada abin da za a ci da rana. Kuma da ma kafin su zo labarin abin alkhairin da ya samu Dr. Hamza ya riga su isa. Don haka ana zaune ne a babban falon marigayi ana sallama da juna, da hirar zumunci. Dr. Hamza ke tambayar kawunsa Idris (autan su Baffa Atiku) wanda malam Abdullahi ya haifa a shekarun girmansa matakin karatunsa, ya sanar da shi yana (housemanship) ne yanzun a nan Kano. Ya koma kan su Lubabatu kannen Hajiya Maryam, Luba koyarwa ta ke a karamar sakandire da yake NCE kadai gare ta. Ya ba ta shawarar ya kamata ta tafi karo karatu (in-service), haka nan zai dauki nauyin karatun. Luba ta ce, insha Allah zatayi amfani da shawarar sa. Furairah ba ta aiki da yake maigidanta ba ya so. Dr. Hamza ya dade da ba ta jari tana kasuwanci yanzun ma kara mata ya yi don ta fadada kasuwancin nata. Murja na yin (masters) ta ce a barta ta kammala kafin a nema mata aikin ba ta son hada taura biyu a baka. Ya gaya wa Gyatumarsa Inna Ramatu da surakuwarsa kuma uwarsa Adda Hafsatu su zamo cikin shiri tunda duk suna da (passport) na Hajj da Umrah da yake kai su duk shekara, da sun yi (settling) a sabon muhallinsu zai aiko musu su tafi su ga sabon matsugunninsu. Da dare a dakin Adda Hafsatu, ita da babbar diyarta Hajiya Maryam suna hirar sallama irin ta Da da mahaifi, Adda ke tambayar dan gaban goshinta, wato Abdul’azeez ba ta ganshi tare da su ba. Hajiya Maryam ta fada mata duk yadda suka yi da shi, da amincewa da Babansa ya yi ya maida shi makarantarsu ta kwana (Regent, Abuja) kafin su taho Kano. Adda ta yi dariya, ta ce, “Dan baiwa kenan, mai ra’ayi da akida ba irin na kowa ba kamar Kakansa. Ni ina ki ka samo sabuwar mai aiki ne, ina Jamilar? Kyakkyawa da ita kamar ba mai aiki ba. Da ganinta bafullatana ce. Ke kam ba kya gajiya da canza masu aiki”. “Adda, Jamila ta yi aure. Kuma Adda masu aiki ba sa zama ne, kowacce sai an saba da ita, sai ta ce ga uzurinta za ta koma gida”. “Ita wannan din tare za ku tafi har Jeddan?” “Eh Adda, gara na dau ta gida da in je can in neman mai aiki Takari, da yawansu basu da amana kuma yawancinsu ba mutanen kirki bane kuma basu da takardar shaidar zama (igama)”. “Har yanzu kina nan da halinki na saurin yarda da mutane Maryama? Da za ki dauki wadda ba ki san asalinta ba ki tafi da ita inda ke ma ba ki da kowa? Ba kya fada a nema miki cikin dangi tunda babu wanda zai samu wannan damar ya ce a’ah?” Hajiya Maryam ta girgiza kai da sauri tareda gyara zama, “Adda, bana so jinina su yi min aiki, sabida hali irin na dan Adam. Dan uwanka in ya zama mai aikinka ba ka da sirri a dangi, kuma ko me za ka yi masa ba zai gode ba. Bar ni dai da baren. Ki kwantar da hankalinki a kan Habiba Adda. Wallahi haka nan na ji ta kwanta mani a rai tun ganina da ita na farko. Ba ki ga yadda ta ke kula da yara ba bilhaqqi ga zafin nama da tsafta”. Adda ta gaji da koda Habiba da Maryam ke ta yi ta tare ta da cewa, “Allah ya zaunar da ku lafiya da juna, Ya kade sharri, Ya hada ku da alherin da ke tare da ita”. “Ameen, da addu’o’inku gare mu Adda ba za’a cutar da mu ba,1- insha Allahu”. Adda ta janyo katuwar (Ghana Must Go) ta ajiye mata a gabanta. Tanadin tafiya ne ta yi mata na kayan girki, yaji, daddawa, kubewa busasshiya, busasshen kifi, kayan kamshi na gargajiya, kuka da sauransu. Ba karamin dadi Hajiya Maryam ta ji ba, wani abu sai mahaifiya. Ta yi ta godiya tana kara son Addar tata a zuciyarta. Washegari suka kamo hanyar Abuja cike da kewar gida, iyaye da ‘yan uwansu. Ranar Asabar, biyu ga watan biyu, na shekarar alif dari tara da casa’in da shidda (2/2/1996). Ambassador Dr. Hamza Atiku Dakata da iyalinsa suka daga kasar Saudiyyah. Ko da jirgi ya sauke su a birnin Jeddah ba su shiga gidansu ba, wucewa suka yi Madinah suka fara aikin umrah. Habiba ta kasa gasgata abin da idanunta suke gane mata, wai yau ita ce a kabarin Manzo sallallahu alaihi wasallam. Ko da wannan ta tsira kadai ta san Allah ya fara yi mata sakayyah ne akan abin da ya rabo ta da gida. Ta faki idon Hajiya Maryam ta share hawayen da suka zubo mata data tuno kananan ‘ya’yanta. Kwanansu biyar a Madinah suka nufo Makkah suka cika umararsu, sannan suka wuce Jeddah inda gidansu yake a unguwar (Albasatin). Ambasada ya shiga sabon ofishinsa a ranar Litinin. **** Aikin Habiba a gidan Ambasada kullum shi ne, kafin Daddy da Hajiya su fito ta shirya yara shirin zuwa makaranta, sunan makarantar da suke zuwa (Hala International School). Direba ya debe su zuwa makaranta har Halim shi ma an sanya shi ajin rainon yara. Daga nan ta dora wa Hajiya sanwar safe kafin ta fito ta karasa, ta share ko’ina na kayataccen gidan duk da yana da girma, Habiba ba ta raki. In ta tashi da asuba ba ta komawa barci, ta yi (mopping) ko’ina, in Mama ta sakko kasa ta kama mata su hada (breakfast) na Daddy, na yaran ita Habiban ce ke yi. Ta kwashe ta jera a tebirin cin abinci, ta gyara dakin yara ta tattare kayansu da suka wargaza. Ta wanke duka bayin gidan (toilet, ban da na Daddy, wannan Mammah ce ke yi da kanta. Sannan ne za ta wuce dakinta ta yi wanka ta kintsa kafin Mama da Daddy su gama karyawa ya tafi office. Daga Daddy har ‘ya’yansa da mota uku suke amfani, direbansa daban na yara daban, wata babbar (Limousine) ce baka wuluk ta kai yaran makaranta, shikuma wadda yake shiga karama ce (Hyundai). Bayan ita akwai babbar cherokee jeep duk na hawansa ne shi kadai. Yaran na riga shi fita kullum. Basu rufa watanni uku ba Hajiya Maryam ma ta shiga makarantar islamiyyah ta karfe sha dayan rana zuwa azahar, don haka ya zamo duk al’ummar gidan ba sa zama sai Habiba. Cikin watanni hudu sai ga Habiba ta soma canzawa, sakamakon cima mai kyau da muhalli mai kyau. Kyawunta na fulanin usli ya bayyana muraran, duk da ba kwalliya ta ke ba, kullum cikin bakaken jallabiyoyi ta ke, wadanda Mammah ke sai musu ita da Habiban don fita waje da zuwa Harami. Duk juma’ah suke shiga harami su yi Dawafi da sallar juma’ah, sai yamma lis suke dawowa Jeddah. Watanninsu hudu kenan a Saudiyyah, Habiba ta dade tana samun wasu sauyuka a tattare da ita. Amma jarumtarta ba ta bari ko ya ya Mammah ta ga gazawarta ba. Inna Ramatu da Adda Hafsatu sun zo sun yi sati biyu sun shiga Makka da Madinah sun yi umrah sun koma. Yawan kasala, zazzabin dare, da tashin zuciya suke damun Habiba. In gari ya waye kuma sai ta yi garau. Duk da haka ba ta gaza komai a ayyukanta ba, tana daurewa tana yi don ba za ta iya barin Mammah da aiki ba, kuma in ta hadiyi (Paracetamol) da suke da shi a kicin tana samun karfin jikinta. Yau da gobe Habiba ta gane cikin jikinta ne ke girma. Wanda ta dade da manta yana tare da ita. Don dai ita doguwa ce, shiyasa bai fito sosai ba. Ba ta yi wani mamaki ba, don tun a gida ta san da hakan, soyayyar abin da ke cikin nata ya lullube ta. Ta kara kaimi wajen lullube jikinta ruf da manyan bakaken abayoyinta. Wani lokacin Hajiya Maryam kan ce da ita ta dinga cirewa tana shan iska mana, sai in za su fita. Ba ta cewa komai sai dai kawai ta yi mumushi. Haka Habiba ta ci gaba da rainon cikinta har tsayin watanni takwas wanda yabi tsayin jikinta da fadin jikinta ya yi kwanciyarsa ba tare da sanin uwargijiyarta ba. **** Abdul’azeez ne ya zo hutu, zuwansa na uku kenan tun dawowarsu Jeddah, don haka gaba daya iyayen da ‘ya’yansu cikin farin ciki suke. Duk da shan kamshinsa yana son Habiba, sabida yadda ta ke haba-haba da shi idan ya zo. Duk wata hidimarsa a wuyanta take, kulawar data ke masa daban ce da wadda take yiwa kowa a gidan, yaron ya shiga ranta sabida kyawunsa da sanyin halinsa. Shima AbdulAziz yana son Habiba ne saboda a cewarsa yana son girkinta, ta iya girki. Sannan ita din mai tsafa ce yadda yake so fiye da duk masu aikin da Mammah ke yi. A kicin Abdul’azeez ya tadda Habiba tana aikin abincin rana. Lokacin Mammah tana makaranta, iyakacin shi bakin kofa ya dube ta da murmushi a ransa yana cewa, ta yi kiba, ta zama katuwa kamar ana hura ta. “Anty Habiba abin nan da ki ka yi wa Mammah jiya nake so in kara ci”. Ya fada da tattausar muryarsa. Habiba ta juyo da murmushi, “Dan gidana wanne a ciki? Jiya girki uku na yi wa Mammah, akwai dan wake, akwai burabusko akwai kuma faten acca”. Ya dan kanne ido alamar tunani, har ya ba ta dariya, “Mai ruwa-ruwan, ba mai duwatsun ba”. Habiba ta yi dariya ta ce, “Faten acca ba burabusko ba?” Ya ce, “Ehh, ba mai kwaya-kwayan ba”. Abdul’azeez ba zai daina ba ta dariya ba, ta sake murmusawa, “Ba ni minti goma sha biyar toh”. Ya shigo kicin din ya ja kujera a gefe ya zauna, “Bari to in jira ki a nan, kina yi kina yi min hirar garinku, ina son labarin kauye. Duk masu aikin Mammah daga kauye suke, suna yi min tatsuniya irin ta garinsu”. Murmushin fuskar Habiba ya dauke nan take, kafin ta ce. “Ni ba daga kauye nake ba Abdul’azeez, daga cikin birni nake. Halin rayuwa ya sa na zabi in yi nisa da gida”. Abdul’azeez ya tattara hankalinsa ya bai wa Habiba, “Na sha yin tunanin ba daga kauye ki ke ba Anty Habiba. Sam ba ki yi kama da kauyawa ba, sannan ba ki da kauyanci. Anty Habiba ya sunan garinku?” Haka kawai ranta ke son yaron, saboda yaro ne mai tarin baiwar hankali da nutsuwa. Ba shi da sakin jiki da mutane, amma ita yana sonta. Alkawari ta yi wa zuciyarta babu wanda za ta fada wa daga inda ta fito ko abin da ya rabo ta da gida, don kada a ce za a maida ita. Yin nisanta da mijinta da ‘ya’yanta shi ne babban abin da ya fi mata kwanciyar hankali. Yanzu ji ta ke kamar tana rayuwa a kan gajimare don dadi da kwanciyar hankali, tunda ta rabu dasu, duk da lokaci-lokaci tana tuna su ta ji kewarsu. Wani dan guntun hawaye ya tsattsafo cikin fararen idanunta, Abdulaziz na lura da ita ya kara tattara hankalinsa a kanta, “Ki yi hakuri in don na ce ya sunan garinku ne ki ke kuka Anti Habiba....... insha Allah bazan kara tambayar ki ba”. Ta juyo ta dube shi cikin girgiza kai, “Sunan garinmu JIMETA cikin jihar Adamawa”. “To Anty Habiba ina mijinki? Ba ki da ‘ya’ya?” Ta tsura wa AbdulAziz ido, kaunar yaron na shiga ranta. Shi ne mutum na farko da ya tambaye ta wani abu da ya shafi rayuwarta tun fitowarta gida. Duk wadanda ta hadu da su a gaba suna duba amfanin da za ta yi musu ne kawai, ba ruwansu da (personal life) dinta. Ta yi masa murmushi, ta ce, “Abdul’aziz duk ina da su”. Cikin mamaki ya ce, “Kuma mijinki ya yarda ki tafi aikatau ki barshi da yaran?” Ta kura wa yaron ido cikin tunanin abin da za ta ce masa, amma ta rasa. Sai idanu da ta zuba masa, irin yaran nan ne masu son bin kwakkwafin abu da ake kira (inquisitive), wayonsa da nisan tunaninsa ya wuce shekarunsa. Da ya tabbatar Habiba ba ta da amsar da za ta ba shi, sai ya ce, “Ya’yanki nawa ne Anty Habiba?” Yatsunta uku ta daga masa, wato su uku ne. Ba ta kara ce masa komai ba, sai hawaye da ta ke sharewa. Hankalinsa ne ya gaya masa cewa ya kyale ta, ga dukkan alamu ba ta son zancen mijin da ‘ya’yan da yake yi mata kamar yana yi mata fami a kan wani gyambo ne. Mikewa ya yi ya nufi hanyar fita daga madafin, ita kuma ta ce, “Ai ya kusa nuna faten, bari in juye maka”. Ya ce, “Miko min library, wani littafi zan duba ina da ‘holiday assignment”. Da haka ya karasa ficewa daga kicin din yana jin tausayinta, ta ko’ina ba ta yi kama da ‘yan aiki ba, and she has her own family (tana da nata iyalin), amma ta zabi ta bauta wa wasu iyalin ta bar nata a kan dalilin da ya tabbata ba kudi ba ne (talauci) kamar sauran masu aikin Mammah. Habiba ta juye kyakkyawan faten accan da ta kammala a karamin (foodflask) ta hada da plate da cokali ta nufi dakin karatun yaran gidan, wanda ke kan wata matattakala guda uku a cikin babban falo. Sai an bi ta kan matattakalar ne za a shiga (study room) din. Ta hau matattakala ta farko ta hau ta biyu, santsin (marbles) da silifan kafarta dan madina ya kwashe ta, ji ka ke timm! Ta yi wata mummunar faduwa rub-da-ciki a kan cikinta. Ta saki wata irin kara mai amo, wadda ta ratsa har kwanyar Abdul’azeez da ke zakulo littattafai daga kan kantarsu. Da gudu ya jefar da littafin ya nufo falon. Habiba ce ta fadi a kasa ga ta nan tana murkususu male-male cikin jini. Fate-faten ya watse a kasa, plate din tangaran din ya tarwatse ba abin da yake ambato saboda gigicewa sai “Subhnallah, zamewa ki ka yi?” Babban abin da ya ruda shi wannan jinin da ke malelekuwa daga kafafunta. Ya rasa me zai yi ya taimaka mata, ba a kiran Mammah a waya in tana islamiyya, bari kawai ya kira asibiti kai tsaye, don Daddy ma ba ya gari yana garin ‘ABHA’. Kan wayar falo ya nufa da sauri ya duba ‘code’ na kiran (Accident & Emergency) na asibitin su ya kira, a takaice ya yi musu bayani suka ce suna tafe da ambulance. Isowar jiniyar motar asibitin gate din gidan ya yi daidai da dawowar Mammah, direba ya dauko ta daga islamiyya ta ga an fito da mutum kwance bisa gadon daukar marasa lafiya, jini kaca-kaca an shiga ambulance an ja motar an tafi. A sukwane ta fada cikin gidan suka gabza karo da danta Abdul’azeez shi ma a firgicen yake, gabadaya ya gigice ya kamata ya rukunkume ya ce, “Mammah Habiba ce, faduwa ta yi”. Kamo hannunsa ta yi suka fito, direban nasu ba bahaushe ba ne, dan Sudan ne sunanshi Salah, motar suka fada Mammah ta ce da Salah su bi bayan ambulance din. Likitoci ne rankatakaf a kan Habiba, abinki da kasar da aka san darajar rayuwar dan Adam fiye da ko’ina. Mammah da Abdul’azeez na bakin kofar dakin da aka shigar da Habiba suna ta safah da marwah, bakin Hajiya Maryam dauke da addu’o’i iri-iri. Tana rokon Allah ya tada kafadun Habiba, ta rabo baiwar Allah da kasar haihuwarta ba tare da ta san komai a kanta ba, ko inda ta fito. Allah ya gani duk masu aikin da ta ke yi ta san asalinsu da yawansu har kauyensu tana zuwa, amma Habiba ta karbe ta (while she was desperate) a neman mai aikin ba tare da wani bincike ba, kuma tunda suka zo ba ta bincike ta a kan komai nata ba, idan ta mutu a ina za ta nemo danginta? Sannan me za ta ce musu ya kashe ta? Hawayen tausayi da tashin hankali ya zubo mata, ta kai bakin hijabinta tana sharewa. Abdul’azeez ya yi tagumi a zaune kan wata kujera ta silver. Rokon Allah yake cikin zuciyarsa, Ya sa ba wani mummunan lahani ya samu Habiba a dalilin yi masa girki ba. Ya dauki alhakin hakan kacokam ya dora a kansa. Tana cikin aikinta yazo ya sata aiki. Duk da haka bai yi hawaye kamar Mammah ba, idanunsa ne suka kada suka yi jazir, hankalinsa na kara tashi in ya tuna sanda ta ce masa ai ta gama, ya zauna ya ci a kicin din, ya ce shi a’ah sai dai a biyo shi da shi library. Wajen mintuna talatin suka kwashe a haka kafin daya daga likitocin ta fito, likiciyar Balarabiya ce mutuniyar Egypt, ta ce da Mamma ta biyo ta ofishinta. Mammah jiki na rawa ta bi ta. Wayar Mamma na hannun Abdul’azeez ya ga shigowar kiran Daddy. Da sauri ya amsa, ya ce, “Daddy ka dawo?” Ya ce, “A’ah Azeez ina bisa hanyar dawowar, ina Mamarku ba ni ita, jikina na ba ni wani abu na faruwa shi ya sa na kira ta”. Abdul’azeez ya ce, “Eh Daddy, muna asibiti ma yanzun Doctor ta yi kiranta”. “Waye ba lafiya?” Ambasador ya furta cikin faduwar gaba, sannan cikin sanyin murya. Abdul’azeez ya gaya masa duk abin da ya faru, a karshe cikin rawar murya ya ce, “Ni na jawo ko Daddy? Da ban sa ta aikin ba da ba ta fadi har ta ji ciwo jini na zuba daga jikinta ba ko Daddy?” Daddy ya ce, “Cool down my son, kwantar da hankalinka ba kai ka jawo ba, tsautsayi ne wanda ba ya wuce ranarsa. Ko ba ka sa ta girki ba in Allah ya yi za ta fadi a yau ta ji ciwo za ta fadi ne. So kwantar da hankalinka za ta warware insha Allahu, kai wa Maman wayar har ofishin likitar a gaya min ko me ke nan”. Hajiya Maryam, uwargidan Ambassada Hamza Dakata na can ta daskare a zaune ta zama mutum-mutuma a kujerar da ke fuskantar likitar mata Dr. Unaisa Jamaal da takardu a hannu. Ta fi yarda da ba daidai likitocin suka dubo ba dai, wai Habiba za a cire wa baby (CS) dan wata takwas saboda ba za ta iya haihuwa da kanta ba, ta zubda jini, sannan ta bugu ta inda har mahaifarta ta samu lahani, idan kuma ba a gaggauta raba ta da babyn ba za a iya rasa su bakidayansu. Rayuwarsu cikin hatsari ta ke. “Ciki! ?” Hajiya Maryam ta tambaya tana zaro wa likiciyar manyan fararen firgitattun idanunta. Dr. Unaisa ta gyada kai cikin tabbatar mata. “Kuma bai kai lokacin haihuwa ba, za mu cire shi ne don tserar da rayuwarta da ta abin da ta haifa. Ku yi gaggawar sanya hannu don a shiga da ita dakin tiyata. Tsananin rudewa Hajiya Maryam ta gama fita hayyacinta, shin da ma da ciki ta dauko Habiba, ko a nan Jeddah ta samu abinta? Tsananin rudewa ya sa ta kasa lissafa iya watannin da ta yi da Habiban. Yau watansu shida tare a birnin Jeddah in haka ne Habiba da abinta ta zo yana dan watanni biyu. Jikinta yana karkarwa ta zura hannu a jaka don dauko wayarta ta kira Ambasada, tsabar rudewa ta ma manta wayar na hannun Abdul’azeez. Daidai lokacin yaron ya murdo kofar bayan likita ta bashi iznin shigowa ya mika mata wayar. Ta kira Ambassador da sauri, bai bata lokaci ba ya amsa don a lokacin ya gama magana da Abdul’azeez, wayar tana hannunsa. “Daddy zo ka sa hannu don Allah a yi wa Habiba tiyata, baby za a cire mata. Wai ashe duk tsawon lokacin nan Habiba ciki ne da ita ba ta fada min ba, ni kuma ban taba ganewa ba, ni wawuyar ina ce Daddy?” Dariya Ambassada ya yi, “Ah toh! Wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho. Garin kwashe-kwashenki watarana fin haka za ki kwaso. Ina cikin Jeddah ku ba ni minti goma zan karaso, ba ni likitan”. Ta mika wa Dr. Unaisa wayarta jikinta yana ta mar-mar, “Ungo maigidana zai yi magana da ke”. Ta karba suka yi magana kadan, ta mayar mata. Mammah ta kara a kunnenta, Daddy ya ce, “Ke da ki ka kwaso abinki sai ki sa hannu, sun ce ba za su iya jirana ba, babu lokaci”. Ya kashe wayarsa. Jiki na rawa ta karbi takardun ta rattaba hannu suka mike tare ita da likitar suka fito. Nan inda ta bar Azeez ta tadda shi suka hadu suka zauna jigum-jigum ta kasa gaya masa ko me ke akwai. Ita kuma Doctor ta wuce su suka shigar da Habiba dakin tiyata. **** An dauki awanni biyu kenan, daidai lokacin da aka kira sallar la’asar. A lokacin ne Abdul’azeez ya tuna ko sallar azahar ba su yi ba shi da Mammah. Yana mamakin yanayin da ya ga Mammah a ciki na gigita fiye da sanda suka zo tun lokacin da likita ta kira ta ofishinta. Ya zarce na ace ciwon Habiba ne kadai ya sanya ta a wannan hali. “Mammah mu je mu yi sallah”. Ya fada har sau biyu, kafin Hajiya Maryam ta ji me yake cewa, da yake tana cikin lalura sai ta ce, “Je ka kayi, zan zo daga baya”. Ya mike ya bar reception din zuwa masallacin cikin asibitin. Tashinsa da fitarsa ya yi daidai da fitowar likitoci biyu daga dakin da aka shigar da Habiba daya daga cikinsu rungume da jariri sai kyanyara kuka yake nannade cikin shawul fari kal, wanda ta san ita dai ba ita ta ba su ba. Mikewa ta yi tsaye cikin hailala ta tare su tun kamin su iso ta mika hannu ta karbi jaririn da ba ta san mace ne ko namiji ba. Ta maida dubanta ga likitar cikin zakuwa, “Habiban fa?” Sai a lokacin ta lura da fuskokinsu dukkaninsu babu mai walwala. “We are sorry...”. Dr. Unaisa ta fada cikin turanci. Ba tare da damuwa da yadda Hajiya Maryam ta fiddo ido cikin dimaucewa ba ta ci gaba da yi mata bayani cikin lallashi. “Mun yi duk iya kokarinmu mu yi saving dinta Allah bai ba mu nasara ba. Ta zubar da jini da yawa, kuma tana da hawan jinin da ba ya samun kulawa, ta hadu da jijjiga (pre-eclampsia) hakoranta sun datse harshenta da muka sa mata ruwan nakuda ba tare da sanin cewa tana da hawan jini ba (induced labour). Dole muka yi fida don ceton ranta bama ta abinda ke cikinta ba, ko kafin mu gama, ta cika”. Hawaye suka ziraro daga idanun Mammah masu zafi na kewa, sabo, tausayi da kauna. Ta rungume jaririn tsam a kirjinta. Daidai lokacin da Abdul’azeez da Daddynsa suka shigo, Dr. Unaisa ta ce ta ba su jaririn za su binciki lafiyarsa don ba ya numfashi yadda ya kamata. Kasa mika mata ta yi don gani ta ke in ta ba su za su kara dawowa hannu rabbana su ce jaririn ma ya cika. Kaunar da ta ke yi wa Habiba daga Allah ne saboda kyawawan halayenta. Daddy ne ya kwakulo jaririn daga hannunta ya ba su suka juya wani daki na musamman da ake kira (day-old). Shi kuma ya kama hannunta ya ja ta har kan kujerun reception din ya rungumo ta yana lallashi. “Kullu nafsin za’ikatul maut Maryama, cool yourself...” Ya fada yana bubbuga bayanta, sai ta fashe da kuka. Abdul’azeez ya ce, “Daddy Habiba ta rasu?” Ya daga masa kai. “To wannan Baby din fa? Haifarsa ta yi?” Ya kara daga masa kai. Bai san sanda shi ma ya fashe da kuka ba. Haka Daddy ya zama dan lallashi, ya lallashi uwar ya lallashi dan. Daga karshe su duka biyun ya hada ya rungume. A haka aka turo gawar Habiba ta gabansu aka saka a ambulance duk suka mike suka bi bayan motar a tasu motar zuwa gida. Tun a mota Ambasada ke waya da abokan aikinsa na Embassy Of Nigeria da makotansa yana fada musu akwai janaza a gidansa, don haka kafin su isa har mutane sun fara cika get dinsa. Hajiya Maryam da matar makocinsu Hajiya Sugrah su suka wanke Habiba suka shirya ta, mutane sama da hamsin duk ‘yan Nigeria ne suka sallace ta suka yi mata rakiya zuwa gidanta na gaskiya. RAI ba a bakin komai ba! Duk haka za mu tafi daya bayan daya. Ya Allah ka sa mu cika da kyau da imani (hawaye). Sai dare mutane suka daina shigowa, ya rage daga Hajiya Maryam sai yaranta. Sun hadu su biyar har ita sun yi jigum-jigum a babban falo. Da gani cikinsu duka babu wanda gushewar Habiba ba ta doka ba. Musamman Abdulazeez. Hatta Halim da yake karami ya yi sanyi ya daina walwala, ya fi kowa sabawa da Habiba, ya fi kowa hawa bayanta ta goya shi. Sai ta yi awanni biyu da shi goye a bayanta tana ayyukanta ba tare da ta gaji ba. Suna yi suna hira tana biyewa shirmensa babu kosawa. Tun safe bai ganta ba, ya kuma ga sanda aka fita da ita kwance kan wani gado ya tambayi Mammah ina za a kai Habiba sai ta sa mishi kuka, tun daga nan bai kara tambaya ba, sai dai kuzarinsa ya zube, ya yi shiru a kwance saman kujera kamar yadda ya ga kowa ya yi shirun. A lokacin Hajiya ta tuna da babyn da suka baro a asibiti. Zumbur ta mike ta tadda Daddy a (bedroom) dinsa. Yana zaune a bakin tankareren gadonsa yana waya, shi fa da alama mutuwar nan ba ta doke shi ba, harkokin gabansa yake yi tunda ya tsaya ya yi wa gawar Habiba gata, ya yi duk abin da musulunci ya umarce shi tuni ya koma sabgoginsa.Dukkansu tun karin kumallon safe ba abin da ya kara shiga bakinsu, amma tana kallonsa ya je kicin ya dafa shayi da kansa ya aika direba ya sayo masa Dajaj (KFC) ya shige daki ba ta kara jin duriyarsa ba. Da sallama ta shiga dakin, bai fasa wayar da yake yi ba. Ya daga ido ya dube ta, ta zauna gefensa tana kallon yadda ya ci kaza ya bar kasusuwa haushinsa ya kama ta, wato ba ya taya su makokin da suke ciki balle ya je ya lallashe su ita da ‘yan samarin ‘ya’yanta. Ya sanya hannunsa cikin tafukanta ya matse da karfi, a lokaci guda yana ci gaba da wayarsa inda ta fahimci da kawunsa Sanata Abdulkarim yake yi. Kawun da ya zame masa kamar aboki sabida shekarunsu daya kuma tare sukayi karatu tun daga sakandire har jami’a. Sai da ya kammala ya ba ta (attention) dinsa. A sanyaye ta ce, “Zan koma asibiti ne in ji halin da Baby ke ciki”. Sosai ya kalle ta, yini guda duk ta zuge, ta fige. Yana mamakin wannan kauna ta ‘yan aiki da Allah ya dora wa maidakinsa. “A dawo lafiya, Allah ya jikanta, Ya ba ku hakuri”. Ta ce, “Amin”. Tare da mikewa za ta fita. “Maryama!” Ambassada ya ambata cikin sanyin murya. Ta dakata ba tare da ta juyo ba. Ya miqe ya tako zuwa jikin kofar, har inda ta ke tsaye rike da (handle) din kofar. Hannayensa ya kai ya zagayo da su cikinta, wato ya rungume ta ta baya. Ya dora kansa saman kafadunta. “Yau ko sumba daya ban samu daga Maryam dina ba. I’m sure kina son Habiba. Ko kanwarki ce ta ciki daya sai haka! My condolence dear, Allah ya yi mata rahma”. Sosai hawaye suke sauka a kan kumatunta. Ta juyo ta rungume shi ta sumbaci goshinsa, “Na gode Daddy”. Ta sake shi da sauri ta fita. Bayan fitarta Ambassador zancen zuci ya shiga yi, “Allah ya sa kada ta ce ita za ta riqe abin da mai aikinta ta bari. Abin da ba zai taba yiwuwa ba ne, ko ‘ya’yan ‘yan uwansa ba ya dauka riko balle ‘yar mai aiki, duk wani taimako zai yi maka, amma ban da dauko ka ya tsoma cikin iyalinsa. Yana da kakkarfan ra’ayi a kan ‘single nuclear family life’, ta yadda ko bako ne ya zo zai kwana daya ba ya sakewa cikin iyalinsa har sai bakon nan ya tafi. Ji yake kamar a kansa yake zaune. Ya girgiza kai, ya ci gaba da kiraye-kirayen wayoyinsa. Hajiya Maryam a gaban tebirin likita Unaisa, “Jaririyar mace ce, an haife ta da cutar pneumonia, numfashinta ba ya fita yadda ya kamata. Da alama uwarta na yawan ta’ammali da ruwa, da shan ruwan sanyi ko? Za mu rike ta cikin kwalba (incubator) har sai ta cika watanni tara”. Hajiya Maryam ta ce, “An gode Doctor, Allah ya raya ta. Zan iya ganinta?” “Sosai kuwa. Zo mu je, don yanzu za a cire (oxygen cylinder) din a sanya ta a kwalba. In ta cika watanni tara sai ki zo ki tafi da ita”. Hajiya Maryam ta tsura wa jaririyar ido, ta dade ba ta ga kyakkyawar halitta ta fulanin usul irin wannan ba. Komai nata na Habiba ne. A very cute baby. Ta kai bakinta ta sumbaci goshinta, kumatunta da bakinta wata irin kauna ta UWA ga DA na ratsa zuciyarta daga Ubangiji subhana. Allah bai taba nufarta da haihuwar diya mace ba, abin da kullum ta ke wa addu’a, amma tun daga kan Halim haihuwar ma ta dakata mata ko batan wata ba ta kara yi ba. Ba ta jin ko dangin Habiba da uban yarinyar nan za ta yarda su raba ta da wannan jaririya da ta sanya wani irin sanyi a idanu da zuciyarta. Da kyar Dr. Unaisa ta karbe jaririyar ta shiga wani daki na musamman da ita. Direba ya dauko Hajiya Maryam suka dawo gida. Bayan kwana bakwai da rasuwar Habiba, Hajiya Maryam tana zaune a falo ta kira Hajiya Halima aminiyarta. Wato wadda ta samo mata Habiba. Bayan sun gaisa da tambayar lafiyar iyali, Hajiya Maryam ta ce, “Halima, ko kin san asalin inda Habiba ta fito? Ina nufin garinsu na ainihi, miji da iyayenta?” Hajiya Halima ta ce, “Tabdijam! Wallahi ba ni da sani a kan ko daya. Ni ma wata mai aikin Rabi’a ce (kanwarta) mai suna Asabe ta kawo min ita, kuma ta ce haduwa suka yi a motar haya sabo ya shiga tsakaninsu, duk da lokacin Habiban ba ta cikin hayyacinta ta ganta kamar wata mai iskoki. Saida ta kwana uku a wurinta tana yi mata addu’a sannan ta warware. Ta ce tana son ta samar mata gidan aiki ta fito neman aikatau ne. Asaben ta ce, ita ma aikatau ta ke a Abuja, su wuce can za ta samo mata. Suka zauna tare a gidan Rabi’a na tsayin watanni biyu tana bincika mata gidan aiki, shi ne da na ce ina so ta kawo min ita, washegari kuma na ba ki da na lura kin fi ni bukatarta. Ita kanta Asaben yanzu sun dade da rabuwa da Rabi’a ta koma kasar su Ghana. Ba mu yi wani zama mai tsawo ba da har zan binciki wani abu nata”. Hajiya Maryam ta nisa, “Halima Allah ya yi wa Habiba rasuwa”. Hajiya Halima ta ce, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un...” Mama ta katse wayar, ba ta so Hajiya Halima ta sa ta kukan da ta samu ya tsaya mata tun kwana uku da rasuwar Habiba. Kullum cikin kirga kwanaki ta ke na ranar da za ta amso jaririyarta. Haka duk sati tana tafe ganin baby a cikin kwalba daga nesa cikin rakiyar Dr. Unaisa. Tana gaya wa Halim kwanan nan za ta kawo masa kanwa, ya samu abokiyar wasa da zuwa makaranta. Hutun Abdul’azeez na wata uku ne, don haka Daddy bai barshi ya zauna a gida ba ya komai ba har watanni uku, ya dauke shi ya sanya a Tahfiz inda yake daukar haddar Alqur’ani mai tsarki daga islamiyyar wasu Larabawan Madinah da sauran littattafan addini shi da sauran ‘yan uwansa a ranakun karshen sati, wato Alhamis da Juma’ah, in sun tafi tun safe sai karfe shidda na yamma, don haka Hajiya Maryam ba ta cikin matsalar rashin mai aiki sosai a dan tsukin, kafin kowannensu ya tafi tahfiz ta raba musu aikin cikin gida da za su yi a tsakaninsu don ita sam bata son harka da Takari. Abdul’azeez shara, Isma’eel wanke-wanke, Usman (mopping), Halim kara bata wuri, sauran ayyukan gidan na waje maza masu aiki ke yi, kamar wanki da guga, gyaran furanni da ba su ruwa. Rayuwar gidan Ambassador Hamza Atiku abar sha’awa ce abar koyi. Ba su da abin da ya fi tarbiyyar ‘ya’yansu da nema musu ilimi muhimmanci a gare su. Yaransu nitsattsu masu hankali da sanin yakamata. Uwar da uban kuma soyayya da shakuwa mai karfi ce a tare da su, ta yadda in ka lura za ka fahimci ba soyayyar aure ce kadai a tsakaninsu ba, akwai ta jini mai gudana a cikin jiki da jijiyoyi. Kaunar da suke yi wa yaran ba ta hanawa su ba su ingantacciyar tarbiyya, su kwabe su in sun yi ba daidai ba cikin nasiha da jansu a jiki. Sai dai fa kaunar Abdul’azeez daban ta ke da ta kowa a zuciyar Ambasada. Idan da abin da Abdul’azeez ya tsana shi ne a yi masa tsawa, ya fi son ko ya yi ba daidai ba ka fada masa a hankali shi ya sa ya fi son Daddy, ya fi sakin jiki da shi tunda Mammah tana yin tsawa. Rannan ya yi laifin yin kwallo (ball) da Magenta (qiddah) inji larabawa, sabida ta sa masa baki a abinci, Mammah ta yi tsawa. Yatsunsa biyu ya sa ya toshe kunnuwansa ya rufe ido jikinsa yana bari da karkarwa, cikin karkarwar jiki data murya ya ce. “Mammah please... tell me what you want to me to do, but please don’t shout.......”. Sai ga hawaye sun shimfido a guje. Jikin Mammah ya yi sanyi, daga ranar ba ta kara daga masa murya ba sai lallashi da nasiha, don Abdul’azeez ko dukansa aka yi ba ya hawaye. Amma in kayi masa tsawa zai yi abinda yafi kuka. Hutunsa ya kare ranar wata lahadi, suka kai shi airport ya daga Abuja, gidan karamin Kakansa Sanata Abdulkarim ya sauka. Washegari ya koma makaranta. Ya yi daidai da ranar da Mammah ta karbo baby daga asibiti, bayan likitoci sun tabbatar da koshin lafiyarta. Dr. Unaisa zaunar da Hajiya Maryam ta yi, ta yi mata lacca ta lokaci mai tsawo kan yadda ake kula da mai lalurar nimoniya, da shawarwari kan abincinta. Ta bada shawarar madarar da za a dinga ba ta (SMA) tana buqatar dumi (heat) a kowanne lokaci, kasancewa cikin kaya masu kauri a lokacin zafi, kasancewa cikin kayan sanyi sosai a lokacin sanyi. Ta kasance jikin uwa a kodayaushe don samun dumin jikin uwa, kasancewa a daki mai dumi da shan madara mai dumi sosai. Wannan zai taimaka ta murmure sosai cikin watanni kalilan. Hajiya Maryam ta yi wa Dr. Unaisa godiya sosai, ta karbi lambar wayarta ita ma ta karbi tata. Duka ‘bill’ din da asibitin ya caje su ta file din iyalin Ambasada aka biya. [01/08 3:34 PM] Sumayya Takori: SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Auren kwangila Page 3 Karfe shidda daidai na yamma Salah direba ya yi (parking) a cikin (gate) din gidan Ambasadan Najeriya a kasar Saudiyyah Professor Dr. Hamza Atiku Dakata, Hajiya Maryam ta fito rungume tsam da kyakkyawar bakwainin jaririyarta cikin farin shawul mai tsananin taushi. Salah ya biyo ta da jakar ‘shopping’ din kayan jarirai da abubuwan bukatar su da ta yo a kasuwar (Baaba Sheriff), ta karasa cikin falon bayan ta ture kofar gilashin (sliding door) da ta raba harabar gidan da tangamemen falon wanda ya ji kayan alatu da ababen more rayuwa iri-iri. Daddy ne zaune a kan kilishi cikin ‘ya’yansa uku yana duba littattafansu na makaranta, don ganin halin da kwakwalwar kowannensu ke ciki. Halim yana kan cinyarsa da nashi (drawing book) din, a yadda ya fahimta Isma’el shi ne mai matsala, yana da rauni kwarai a kan darasin lissafi (mathematics). Nasiha yake masa sosai cikin hikima kan ya maida hankali ya iya lissafi domin shi ne kashin bayan ilimin boko. Mammah ta yi sallama suka mike da gudu suka yi kanta. Fadi ta ke, “Ku yi a sannu kada ku kada kanwarku, kun ga ba ta da lafiya”. A sannu Daddy ya daga ido ya dube su, ya soma dan yamutse fuska, suka hada ido da matar tasa. Ta fahimci ya canza fuska, gwiwoyinta suka yi sanyi, amma a haka ta karasa gare shi ta zauna dab da shi ta miqa masa jaririyar, kamar ba zai karba ba ko me ya tuna kuma ya karba, ganin Usman ya danne Isma’el duk a kokarinsu na kowanne so yake a bashi jaririyar ya dauka, sai ya karba don ya raba fadan, amma ba cikin dadin rai ba. Sama-sama ya kalli ‘yar sai kuma ya mika mata, ya tambaye ta, “To yanzu ya za ki yi da ita? Bana jin gidan marayu na Saudi-Arabia za su amshe ta, tunda mu ba ‘yan kasa ba ne”. Mammah cikin mamakin sauyin da ta gani a tare da Daddy farad daya, ta ce da shi cikin kwantaccen sauti. “Wai da so nake ka yi min izini in sha magani in samu ruwan nono in shayar da ita”. Girgiza kai ya shiga yi, “Wasa ne wannan, ki shayar da dan da ba nawa ba?” Kamar za ta fashe da kuka ta ce, “Daddy........” Ya dakatar da ita, “Please don’t argue with me Maryama. Ki maida ita wajen dangin mahaifiyarta, ba zan iya riqon dan da ba nawa ba balle in kasa yin adalci tsakaninsa da ‘ya’yana Allah ya tuhume ni, musamman rikon maraya. Na yi miki alkawarin zan dauki nauyin iliminta har zuwa digiri na kololuwa idan tana so a ko’ina ta ke cikin duniya. Amma ba zan hada ta da ‘ya’yana in rike ba”. Hajiya maryam ta fashe da kuka, “Don Allah Daddy kada ka yi min haka... ina sonta, ina son uwarta ina son diya mace... Allah bai ba ni ba... don Allah Daddy ka yi min alfarma ka barni in rike ta koda wannan itace alfarma ta karshe da zaka yimin a rayuwa”. Ta daga hannuwanta biyu gare shi tana kuka tana roko. Dukkan yaran ma kuka suka sa suna rokonsa har Halim, “Daddy ka bar mana don Allah, muna so, kada a kai ta wani waje ta mutu kamar yadda Mamanta ta mutu, do us a favour”. Inji Usman. Suka kama babyn duka suka kankame, ita kuma da ta ji matsa ta canyara kuka da muryarta kamar gyare don zaki. Su biyar din duka kuka da hawaye share-share. Sakin baki Ambasada ya yi yana kallonsu, kafin ya ce “Na shiga ukuna. Ku dakata, mu yi magana ta maslaha”. Ya fada yana daga hannu irin na saranda. Duk suka dakata suna share hawaye suna hadiyar zucci. “Zan bi ra’ayinku tunda kun rinjaye ni, amma da sharadin ban yarda Mammah ta yi (breast-feeding) dinta ba, a nemi ‘alternative”. Sai duk suka juya suna kallon Mammah don jin ta bakinta. Kowannensu fuskarsa na nuna “Mammah ki yarda da hakan”. Hajiya Maryam ta sa habar zaninta ta goge fuska da majina, “Daddy ba ta da lafiya ne, tana da pneumonia, tana bukatar ruwan nono da dumin jikin uwa, in ban shayar da ita ba bani da kulawar da zan ba ta fiye da hakan”. Mikewa ya yi yana dakile fuska. Ya kakkabe rigarsa ya nufi matattakalar da za ta sada shi da dakinsa. Yana tafe yana fadin, “Shawara ta rage ga mai shiga rijiya, na ba ku daga yau zuwa gobe ku yi shawara, har madara zan dauki nauyin saye sadaqah fisabilillahi. Amma in ba haka ba gobe zan sa a buga mata fasfo ku kai ta inda ku ka dauko uwarta”. Ya yi wucewarsa ya shige daki ya rufo kofa. Usman ya matso sosai jikin mammanshi, idonsa a kan babyn da ta zuba fararen yatsunta cikin baki tana tsotso alamun yunwa. “Mammah ki yarda don Allah mana? Tunda mun samu ya bar mana?” Isma’el ya ce, “Mammah don Allah ki yarda ta sha madaran, rayuwa da ciwo duka na Allah ne, idan mai tsawon rai ce sai ki ga Allah ya raya mana ita. Take heart Mammah...”. Ya fada tare da kai hannu santar kirjinta yana shafawa alamun ta yi hakuri ta bi abin da Babansu ke so. Hajiya Maryam ta tsura wa ‘ya’yan nata ido, yara masu hankali da tunani tun a qananan shekaru irin nasu. Har sun fi ta tawakkali da hangen nesa. Da gaske Allah shi ne mai rayawa ba nonon uwa ba. Ta rungumo su gefe da gefenta, jaririyar na bisa cinyarta, ta sumbaci kowannensu a goshinsa, “Na amince. Gobe zan gaya wa Daddy. Yanzu zan fara ba ta madara kun ji ana kiran sallah, maza kowa ya je ya yi alwala yanzu Daddy zai sauko ku wuce masallaci”. Duk suka mike cike da murna har da tsalle suka nufi toilet don dauro alwalar. Ita kuma ta dauki ledar shopping dinta da babyn ta nufi dakinta. A take ta tafasa ruwan zafi ta hada madarar ta soma ba ta. Wata irin kauna tana mamaye zuciyarta na ‘yar da ba ta san daga ina uwarta ta ke ba balle ubanta. Sai dai kaso 90% na zuciyarta ya amince yarinyar nan ba shegiya ba ce, da ubanta. Habiba ba ta yi kama da mutanen banza ba, sannan ba yarinya ba ce balle a ce shege ta yi ta gudu. Ta fi amincewa da cewa wani nau’i ne na kaddarar rayuwa ya rabo ta da gidan mijinta da iyaye da ‘yan uwanta. Ba ta yi gigin zuwa turakar Daddy a yau ba kwata-kwata, shi ma bai neme ta ba. Duk abubuwan da ta saba yi masa kafin su kwanta da kansa ya yi, zuciyarsa fal haushin Maryam, tunda daga samun ‘ya har ta fara watsar da shi, da ma a ce ita ta haifa da sauki ba zai damu ba. Ya yi tsaki yana shan ‘gahwah’ (coffee) ya fi sau shurin masaki. A haka ya kwana cikin bacin rai, ita kuma tana can tana ceton rayuwar ‘yar marainiyar Allah. Ta kashe A.C ta kunna (room heater), ta ciro kayan sanyi masu kyau cikin sayayyar da ta yi ta sunke ta a ciki, da pampers. Ta cika mata ciki da madarar da Dr. Unaisa ta yi umarni. Nan da nan ta hau baccinta cikin kwanciyar hankali. A lokacin ne ta tuno da Daddy, ta yi ajiyar zuciya ta yi shirin bacci ta manna jaririyar a jikinta, ta rufe su ruf cikin lallausar bargo, suka yi bacci abinsu. Tun asuba kukan baby ya tashe ta, ta tashi zaune ta dauke ta ta yi toilet da ita. Wanka ta yi mata da ruwa mai dumi sosai, ta nado ta cikin shawul. Shafe ta ta yi da man zaitun ta canza mata (diaper), ta shirya ta cikin (overall) farare tas! Da hula mai kauri. Sannan ta hado madararta ta shiga ba ta. Ta kura mata ido ba ta ko kiftawa. Habiba ta ke tunawa da karamcinta, da yanzu ta fara jiyo sukurniyarta tana shara da goge-goge kafin ta fada kicin ta hada mata kayan girki kafin ta sauko. Hawaye suka ciko a idonta, me ya sa Habiba ta yaudare ta? Me ya sa ta boye mata asalinta da cikin da ta ke dauke da shi? Rayuwar yarinyar a gaba ta ke kokawa idan Allah ya raya ta ta fahimci ita din ba uwarta ce mahaifiya ba, ba a san kowa nata ba, ba a san daga inda ta fito ba. Ta ajiye ajiyar zuciya mai nauyi, ta share hawayen idanunta. A hankali ta sanya babyn cikin gadon da ta hada yanzu, sai bacci ta ke sadidan cikin koshin lafiya. Wanka ta yi, ta ci gayunta kamar yadda ta saba, kai ba za ka ce ta yi shekaru talatin da biyarba. Ta san sirrin gyara na diya mace kala-kala. Ta lakanci ado da kwalisa tun tana budurwa, haka yanzu da shekaru suka fara turawa ba abin da ya canza Maryam Dakata. Farar mace mai farar aniya, uwar gidan Professor kuma Ambassador Hamza Atiku Sakata. Kicin ta fada ta soma hada wa iyalinta abin kari. Sosai ta yi latti, domin har gari ya waye. Sanin Daddyn a sama-sama yake da ita ta ce bari ta yi masa abincin da ya fi so, don ta dan faranta ransa. Kunun gyada ta hada ya ji madara yadda ya kamata. Ta hau suyar sinasir din da ta kwaba tun daren jiya. A gurguje ta ke yin komai, miyar ta ji ganyen alayyahu sosai da tsokar kaji. Sun dahu sun yi lugub. Yaran kuma (quaker oat) ta dama musu, ta soya musu ‘pancake’ ta shirya wa kowanne a sundukin abincinsa. Da hanzari ta shirya wa Daddy tebur jin baby ta fara kuka. Su Isma’el suka fito daga dakinsu cikin shirin makaranta kowanne goye da dirkekiyar (school bag) dinsa. “Mammah sabahul khair”. Duk suka fadi a tare bayan sun shigo kichin din cikin russunawa. Kansu ta shafa daya bayan daya tana murmushi, “Sabahul khair, ‘yan albarka, kun tashi lafiya?”. Isma’el ya ce, “Karasa aikinki Mammah, I will help you with the baby”. Ta yi murmushi ta daga masa kanta. “Madararta na nan a kan (side drawer) ba ta ina zuwa”. Da hanzarinshi ya juya zuwa dakin nata. Tun a kan Halim Isma’el ya iya raino, shi ke taimaka mata da rainon Halim har ya yi wayau. Yanzun ma baby ya ciro daga gadonta ya aza a kafadunshi yana rirriga ta har ta yi shiru. Ya zauna gefen gadon Mammah ya ba ta ruwan zam-zam ta sha sosai, sannan ya sanya mata madarar a baki. A ranshi yana cewa, duk da dai an ce ba a gane kamannin jariri, amma wannan da ganinta Habibah ce sak! Mammah turakar Daddy ta nufa da saurinta, suka ci karo a matattakalar bene ya yo shirin office tsaf, rike da (briefcase) dinsa. Ta karba suka sauko tare, sai faman dauke mata kai yake yi. Ta yi murmushi a ranta ta ce, “Insha Allahu watarana sai ka yi alfahari da ‘yar da ba ka son rikewa din”. Su Isma’el ya kwala wa kira yana kokarin ficewa daga falon ba tare da ya dubi (dining) din ba. Ba ta yi fushi ba, ta ce, “Daddy break fast fa?” “I’m ok”. Ya fada yana duba agogo. Ta ji ba dadi yadda mata ke ji in sun takarkare sun zabga wa maigida girki ya ki ci. Usman da Halim suka wuce tare da shi, Isma’el ya fito dauke da baby ya mika wa Mammah, sannan ya dau jakarsa da kwandon abincinsa ya bi bayansu da gudu. Ta yi ajiyar zuciya ta goya baby jikinta a sanyaye. Da gaske Hamzanta ya canza daga halin da ta sanshi da shi. Ta san shi mutum ne mai tausayi da taimakon na kasa da shi, ba ta san me wannan yarinyar ta tare masa cikin gidan nan ba, da alama za ta fuskanci barazana mai yawa a rayuwar aurenta a kan rikon yarinyar daga mijinta, abin kaunarta. Ta kuma shirya karbar kowanne kalubale in har zai bari su rayu tare. Ba za ta kai ta Nigeria ba, inda ko sun je babu inda za ta kai ta a karba in ba gidan marayu ba. Ta shirya yin jihadin rikon ‘yar Habibah ko da Daddy zai kara aure ya kora ta Nigeria a dalilin haka. Ta watsar da tunanin ta shiga harkokinta. Islamiyyar ma ta daina zuwa sai ‘yarta ta isa bari a makarantar rainon yara (creche). Amma dole ta nemi ‘yar aiki don ayyukan gidan sun fi karfinta. Karshen ta dai Takarin da bata so. A nan unguwarsu Albasaatin ta yi kawaye biyu ‘yan Nigeria matan ma’aikatan Embassy, daya matar mataimakin Daddy ce Safiyya sun fi su dadewa a Saudiyyah sosai, bayan ta gama girkin rana ta kira Anty Safiyya ta ce ta cigita mata mai aiki don Allah Takari, ta ce ta bari sai Juma’ah za ta shiga Misfalah in ta je Harami za ta taho mata da ita. Ta yi godiya suka aje wayan. A daren ranar, Hajiya Maryam ta yi shiri kamar yadda ta saba ta nufi turakar maigidanta, aiki yake yi a tsakiyar gadonsa cikin na’ura mai kwakwalwa. Ciki-ciki ya amsa sallamarta ba tare da ya dago daga abin da yake yi ba. Kokarin sauke baby ta ke daga bayanta don ta koma ta dauko gadonta. Da hanzari ya dago ido ya dube su. Ya zare farin gilashin kara karfin gani da ke idanunsa, cikin kaushin murya yake magana. “Ban gane ba? Kina nufin tare zan kwana da yarinyar nan? Ta ya ya ki ke tunanin zan iya jure kukan jaririn da ba nawa ba? Excuse me please,Maryam! It’s enough wallahi, abin da ki ke min a kan yarinyar nan ya ishe ni. You are forcing me to be a father of your adopted daughter while i’m not. To bari ki ji in gaya miki, wannan ya zamo na farko kuma na karshe. Daga yau sai yau, kada ki kara kawo min ita dakin barcina. Ke kanki na hakura da ke in har za ki hada hidima ta da tata, ko za ki hada mana makwanci. Idan duk alfarmar da na yi mata ba ki gode min ba zan ba ki mamaki wallahi, don aure zan kara ki ji dadin kula da ‘yarki......” Tana kuka sosai ta juya da ‘yarta a kafada jikinta har rawa yake, domin Daddy fada yake sosai. Cikin babban sauti wanda ba ta taba sanin yana da shi ba. Tana fita ya banke kofarsa yana sakin tsaki. Haka suka kwana kamar jiya zukata babu dadi. Washegari bayan yara sun tafi makaranta, shi kuma ya tafi office, kamar jiya yau ma bai kula abincin da ta bata lokaci ta shirya masa ba. Tun asuba ta tashi ta soya masa waina (masa) don ta san yana matukar sonta, haka ya tsallake ya bar mata kayanta kamar jiya ya sa ‘ya’yansa a gaba suka tafi. Su kansu yaran ba sa cikin walwala ganin halin da iyayensu ke ciki na rashin walwalar suma, yanayi ne da ba su taba ganinsu a ciki ba tun tashinsu. Daddy da Mammah suna matukar kaunar junansu, sun fahimci juna, ra’ayinsu daya kusan a kan komai na rayuwa, sai yau a kan ‘yar Habiba, kowanne gani yake shi ne a kan gaskiya. Shi Dr. Hamza ba muguwar zuciya ce da shi ba, ba rashin tausayi gare shi ba, ba kin taimako gare shi ba, a’ah, ra’ayi ne na rikau irin na Malam Bature, duk wani taimako da zai wa mutum ko jininsa ne ya fi yarda ya yi masa shi daga nesa komin girmansa, amma ban da ya dauko shi ya kawo cikin family dinsa. Ita kuma Hajiya Maryam tana matukar son Habibah, son ne ya shafi abin da ta haifa, sannan tana tunanin in ba ta rike yarinyar nan ba ina za ta kai ta? Ba ta san komai da ya dangaci Habibah ba ba ta san daga inda ta fito ba, sannan in ta kai ta gidan marayu tana tausayin rayuwar da za ta taso a ciki. Za ta taso ne a shegance, a shegantata bayan ita ta yarda yarinyar nan ba shegiya ba ce da ubanta, akwai abin da ya rabo Habiba da mahaifinta. Me ya sa Daddy ba zai yi mata alfarma ba? Hantsi na dagawa ta samu wayar Anti Safiyyah ta daga suka gaisa da tambayar lafiyar yara. Anti Safiyya ta ce, “Mai aikin babba ki ke so ko yarinya, ko budurwa?” “Babba dai, wadda ta san ciwon kanta. Ban da wadda ba ta kai shekaru hamsin ba”. Safiyyah ta ce, “To alhamdu lillahi an samu. Sunanta Azumi, ‘yar Sakoto ce, zan kawo ta ranar juma’a insha Allahu. Za a dinga biyanta Riyal dari biyu duk wata, duk irin hidimar da ki ke so ta yi miki za ta yi miki, ku dai tattauna a tsakaninku”. “Na gode Safiyyah sosai. Na gode Allah ya kara zumunci”. In ji Mammah. Da haka suka ajiye wayar. A cikin wannan hali na zaman doya da manja, zuciya ba dadi, Hajiya Maryam ta ci gaba da zama da mijinta a dalilin ‘yar mai aikinta. Ana i’gobe za su cika kwana bakwai da baro asibiti tunanin ragon suna (haqiqa) ya dame ta. A yadda Daddy ke kumbure-kumburen nan za ta doshe shi da zancen yanka ragon suna? Ta yi tunanin ta bai wa Salah ya sayo da kudinta kamar yadda ta yi amfani da kudinta wajen siya mata suttura, madara kam ya saya katan-katan kamar yadda ya furta, sai dai wani (positive) tunani ya shige ta. Bai kamata tun yanzu ta soma yin gaban kanta a kan yarinyar ba, dole ta ba shi hakkin da yake cewa tana ‘forcing’ dinshi na zaman uban yarinyar yana so ko ba ya so, in ta sayi rago ta yanka mata ya tabbata ita ce uwarta, ita ce ubanta kenan, “You must be the father you don’t want to be Daddy!”. Ta fada a fili. A daren ranar ta cancada kwalliya, turare kala-kala ta feshe jikinta da shi, a gobe ta ke sa ran za a kawo mata sabuwar mai aikin. Ba za ta iya barin Baby ita kadai ba, don haka ta kira Usman da Isma’eel da Halim ta jere su a gadonta ta ce su kwana a nan. “Isma’el ba ka da nauyin barci, ka kula da baby in ta motsa. Ga madararta, ga ruwan zam-zam dinta ka duba pampers akai-akai”. “Dont worry Mammah, je ki lallasar mana Daddy ya daina fushi da ke. Mammah tausayinki nake ji, ya ce wai wata sabuwar mata zai kawo mana ke kin daina sonsa sabida jaririya”. Murmushi ta yi, ta ce, “Isma’el Allah ne ya halatta masa auren mata har hudu in yana da iko. Ba saboda jaririyarmu ba ne. Kuma ba saboda ita yake fushin da yake yi ba, ni ce na yi masa laifi”. Ta fadi hakan ne don kada su fassara mahaifin nasu a matsayin mutum mara tausayi da adalci. Wanda tuni hakan ya fara darsuwa a zuciyar Isma’el tunda ya fi Usman da Halim wayo. Amma yanzun ya yarda da abin da Mammah ta ce, sai dai ko kusa ba ya son Daddy da wata macen bayan mahaifiyarsu. Akwai abokinsa a makaranta a Abuja da yake ba shi labarin cewa Mamansa ta rasu wajen haihuwarsa a hannun (step-mother) dinsa yake, kullum sai ta dake shi ta sa babansa ya dake shi, kuma ba ta bashi abinci sai mai aikinsu ce ta ke ba shi. Wannan labari da Salim ya ba shi ya tsaya masa a zuci, ba ya so ya ji an ce za a kara aure. Da haka Mammah ta wuce ta barshi yana tunani, yana kallon Baby da ke barcinta cikin kwanciyar hankali a cikin kyakkyawan gadonta da ke gefensu. Usman da Halim tuni sun yi barci. Mammah ta yi sallama a kasaitaccen (bedroom) na Ambassador Hamza Dakata, tuni ya kashe fitila ya rufe kwamfuta yana azkar din barci, dole ya amsa sallamar don bai zaci ganinta a lokacin ba. Kwana shida kenan rabon da su hada makwanci, in ya ce ba ya kewar Maryam ya san ya yi babbar karya ya kwana da yunwa. Mace daya tamkar da dubu wadda ta mamaye filin mata goma a zuciya da ruhinsa, ta haifa masa sanyin idaniya ABDUL’AZEEZ HAMZAH ATIKU, in ya ce zai hada matsayinta da na wata mace da sunan aure ya san ya fada ne kawai don ya ji dadin bakinsa ko ya huce haushi amma Maryam ta wuce nan a zuciyarsa. Jin ta ya yi ta kwanta a gadon bayansa ta sanya tausasan hannuwanta ta rungume shi, hawayenta na sauka saf-saf a kan kafadunsa. Runtse ido ya yi wani sanyi na ratsa zuciyarsa. Ta ja bargon da yake kokarin rufawa ta ajiye a gefe. “Ka yi hakuri Daddy don Allah ka yi hakuri, na yarda laifina ne, na kasa hakura da tsarinka in yi maka biyayya. Na yi ne don neman lada a wurin Ubangiji ba don in bata maka rai ba Daddy”. Ta fadi cikin shesshekar kuka mai motsa zuciya balle zuciyar masoyi. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya dago ta ya juyo suka fuskanci juna. “Why Maryam? Me ya sa ki ka zabi farin cikin wasu bare da ba ki hada alakar komai da su ba a kan nawa? Na dade ina mamaki, ina tambayar kaina anya Maryam dina ce? Ta bar ni kwana shidda ba tare da ta san halin da nake ciki ba? Ya ya nake rayuwa? Me nake ci nake rayuwar? Anya Maryam ke ce???” Hawaye ta ke sharewa sosai, “Tunda ka gaza fahimtata Daddy, ka kasa mara min baya mu ceci rai, mu yi jihadin rikon maraya tare, mu yi domin neman lada a wurin Ubangiji na amince ka fadi duk yadda ka ke so a yi da jaririyar nan na maka alkawarin zan bi, in har za mu koma rayuwarmu ta baya ka kuma fasa auren da ka ke cewa yara za ka yi. Ba zan iya hada ka da kowacce mace ba Daddy ‘depression’ zai kama ni”. Bai san sanda dariya ta kwace masa ba, ya yi sosai sannan ya gintse fuska, “Ina nan fa ina jiyo laccar da ki ke wa Isma’el yaushe ki ka juya ta a baibai? Kin ce Allah ya ba ni iko, yanzu kuma kin ce ‘depression’ zai kama ki, dole in yi aure Maryam don in samu mai kula da ni, ke kuma ki ji da ‘yar da ki ka fi so a kaina. Me ye laifina a nan?” Ta share hawaye da tishu ta ce. “Ai na ce ka fadi yadda ka ke so a yi, ko cewa ka yi in jefa ta a kwatami zan jefa tunda ba ka sonta”. Ya hade fuska, “Ni na ce miki bana sonta? Me ta min? Kawai kin kasa fahimtata ne ke ma, amma a bar zancen haka, kowa ya zauna a kan ra’ayinsa. Amma abubuwan da ki ka dauko hanyar yinsu ba zan lamunce su ba, dole ki ba ni dukkan kulawar da ki ke ba ni a baya. Ban amince ki canza ko kwaya daya ba, bana son zama da masu aiki amma na amince ki daukar mata Nanny zan biya ko nawa ne. Ki daina hada lamarina da nata, daga sanda na dawo office karfe shidda na yamma har zuwa wayewar gari in fita (office) lokacinki nawa ne da yarana ki bar ‘yarki can wajen mai rainonta. Kuma ki ci gaba da bincike a kan danginta, duk ranar da suka bayyana za ki mayar musu da ‘yarsu”. Gyada kai ta yi cikin hadiyar zuciya, “Na amince Daddy, wallahi na amince. Na gode, Allah ya kara rufa maka asiri duniya da lahira. Alfarma ta karshe da nake nema ka yi mata haqiqa, ka sanya mata sunan duk da ka zaba, ka yi mata khutbah gobe da safe kafin ka wuce office, already na nemi Nanny din wallahi, gobe Safiyyah za ta kawo ta........”. Ta cika shi da surutu, bayan shi kuma cike yake da wata irin kewarta, janyo ta ya yi kawai ya sanya cikin kirjinsa, ya rufe su ruf da bargon mai tsananin taushi da kamshi. Can kusan makoshinsa ya ce, “Ke don Allah ya ishe ni haka, gobe zan yanka mata ragon...” Da haka hirar ta kare, ta koma mai ma’ana da kara dankon kauna. Hakika ta yi kewar mijinta, shi ma Daddyn ya yi kewarta yadda harshensa ba zai iya fassarawa ba, sai dai ‘emotions’ dinsa a daren ranar bakidayanta sun nuna mata hakan. “Daddy kenan! Zuma, ga zaki ga harbi”. Maryam Dakata ta fadi cikin zuciyarta cike da shaukin mijinnata, dan uwanta, uban ‘ya’yanta. ***** Washegari da Salah ya sauke shi a office ya ba shi umarnin ya sayo babban rago a yanka da sunan ‘yar Mammah, da ta ce ta ba shi zabin sunan da za a saka wa jaririyar, cewa ya yi shi fa babu ruwansa. Ta sa wa ‘yarta sunan da ta ke so idan kuma haqiqar da ya yi mata ma ba ta gode ba, to don Allah ta kyale shi haka. Da yake lallaba shi ta ke, sai ba ta ja da nisa ba. Ta mika masa bebin tana marairaicewa. “To don Allah amshe ta ka yi mata khutbah da sunan Addah, wato Hafsatu”. Harara ya dalla mata, “A dalilin me? Ga sunan uwarta za a ce na uwata zan saka? Ba gara ki sa mata Habiban ba don a gane danginta da sauri?” A ranta ta ce, “Bakinka ya sari danyen kashi. Hmmm! Ko an gane ba wanda zan bawa, ‘ya ce Allah ya riga ya ba ni, iyayena da ‘yan uwana sun isa su zame mata dangin”. Ta sake kwantar da murya, “Daddy, ba zan taba mance sunan uwarta ba, don Allah ka sa mata Addah, don ta biyo kyawawan halayenta”. Yana cin magani ya amsa, ya zauna a bakin kujera ya kai bakinsa saitin kunnenta yana yi mata khutbar. Dadi ya kashe Mammah a zuci. Bayan ya fita da awanni uku Anti Safiyya ta yi sallama, matar biye da ita. Kyakkyawar tarba Hajiya Maryam ta yi musu. Bayan sun ci abincin rana suka soma tattaunawa. Azumi ta amince za ta taya Hajiya Maryam ayyukan gida, za ta yi rainon Hafsat da amana. Shekarunta arba’in da biyar, nitsattsiyar mace sosai. Mamma ta miqa mata Hafsat din da ta yi wa lakabi da SUHAANAH kasancewar sunan mahaifiyarta ne, a take Azumi ta karbe ta ta goye. A gaban Anti Safiyyah Hajiya Maryam ta zaunar da Azumi a kan kilishi, ita da Anty Safiyya suna kan kujera ta soma magana cikin nutsuwar da Allah ya halicce ta da ita. “Azumi ga ni ga wadda ta kawo min ke, kawata Hajiya Safiyya, na daina zama da ‘yan aikin da ban san asalinsu ba. Tsakani da Allah ki gaya min daga ina ki ka fito a Nigeria, da inda iyalinki suke. Zan kuma yi bincike idan kin yi min karya”. Anty Safiyya ta gyada mata kai, “Haka ne kwarai. Azumi muna sauraronki”. Dattijiyar ta gyara zama cikin hankali ta ke magana. “Daga jihar Sokoto na zo Saudiyyah, idan na yi miki karya Allah ya hukunta ni daidai da abin da na aikata na yaudara”. Mammah ta ce, “Sokoto wace unguwa? Gidan wa?” “Unguwar Mabera, gidan Malam Isuhu Maishanu, mun zo Saudiyyah ni da mijina muna neman na kanmu a Shari Mansur shekara biyar a baya, muna kawo goro da sauran abubuwan da mutanenmu ke bukata, an sha kama mu har sau biyu ana mayar da mu Najeriya muna dawowa, kamar yadda ki ka sani in ka dandani zaman saudiyyah ba ka iya bari da sauki, to hakan ce ta faru da mu ni da maigidana. Shekarar baya ya rasu ya bar ni da ‘ya’ya biyar namiji daya hudu mata. Namijin Yusha’u ya jima da yin aure a Maishanu. Na aurar da mata biyu a can gida Sokoto, ta ukun wato Harira da autar Ladidi kuma suna hannun kanwata a Talata Mafara. Idan akwai karya cikin abin da na fada Allah ya hukunta ni da laifin yaudara da cin amana”. Anty Safiyya ta dafa kirjinta da hannunta na dama ta dan fiddo mata ido ta ce, “Ni ‘yar Sokoto ce gaba da baya, Iyayena da kakannina, don haka zan bincika abin da ki ka ce daga yau zuwa gobe. A unguwar Nakasari da unguwar rogo iyayena suke na san Mabera sosai”. Azumi ta gyada kai alamar amincewa. Hajiya Maryam ta nisa, sannan ta dubi Azumi, “Abin da ya sa na yi miki wannan titsiyen ba rashin yarda bane, mai aikina ta baya ce...........” Tiryan-tiryan ta ba su labarin tun kawo mata Habiba Abuja zuwa yau. Azumi ta sakko Hafsat ta kara rungume ta a jikinta, ta sa mayafinta ta kara rufe ta sosai daga ita har Anty Safiyya sai da suka yi hawaye. Safiyyah ta karbi Hafsat ita ma ta rungume tana kallon kyakkyawar fuskarta, ta ce da Hajiya Maryam. “Na rantse da Allah na dauka haihuwa ki kai, ganin yarinyar nan fara tas kamar ‘ya’yanki. Kina da tsayi, kina da dan jiki ba a fiya ganewa ba idan irinku nada ciki. Allah ya ba ki ladan wannan jihadi na ceton ran maraya da sadaukarwa saboda Allah”. Murmushi ta yi, ta ce, “Amin”. Amma ba ta gaya musu halin da ta ke ciki da maigidanta a kan lamarin ba. Ciki ba don tuwo kawai aka halicce shi ba, wani abun yana bukatar sirri. Bayan tafiyar Safiyya, Azumi ta goye Hafsat wadda Mammah ta kira (Suhaana) suka ci gaba da ayyukan gida tana nuna wa Azumi kan komai na gidan. Ta nuna mata dakinta. Kwarai dattijuwar mai hikima da azanci ce, har girkin dare ita ta yi, kuma Hajiya Maryam ta yaba, tuwon shinkafa da miyar busasshiyar kubewa da ta ji naman ragon sunan Hafsatu. Sai Mammah ta yi na Daddy kawai, su Isma’el suna ta santin girkin Baba Azumi, yadda Mammah ta koya musu su dinga kiranta.SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Auren kwangila Page 3 Karfe shidda daidai na yamma Salah direba ya yi (parking) a cikin (gate) din gidan Ambasadan Najeriya a kasar Saudiyyah Professor Dr. Hamza Atiku Dakata, Hajiya Maryam ta fito rungume tsam da kyakkyawar bakwainin jaririyarta cikin farin shawul mai tsananin taushi. Salah ya biyo ta da jakar ‘shopping’ din kayan jarirai da abubuwan bukatar su da ta yo a kasuwar (Baaba Sheriff), ta karasa cikin falon bayan ta ture kofar gilashin (sliding door) da ta raba harabar gidan da tangamemen falon wanda ya ji kayan alatu da ababen more rayuwa iri-iri. Daddy ne zaune a kan kilishi cikin ‘ya’yansa uku yana duba littattafansu na makaranta, don ganin halin da kwakwalwar kowannensu ke ciki. Halim yana kan cinyarsa da nashi (drawing book) din, a yadda ya fahimta Isma’el shi ne mai matsala, yana da rauni kwarai a kan darasin lissafi (mathematics). Nasiha yake masa sosai cikin hikima kan ya maida hankali ya iya lissafi domin shi ne kashin bayan ilimin boko. Mammah ta yi sallama suka mike da gudu suka yi kanta. Fadi ta ke, “Ku yi a sannu kada ku kada kanwarku, kun ga ba ta da lafiya”. A sannu Daddy ya daga ido ya dube su, ya soma dan yamutse fuska, suka hada ido da matar tasa. Ta fahimci ya canza fuska, gwiwoyinta suka yi sanyi, amma a haka ta karasa gare shi ta zauna dab da shi ta miqa masa jaririyar, kamar ba zai karba ba ko me ya tuna kuma ya karba, ganin Usman ya danne Isma’el duk a kokarinsu na kowanne so yake a bashi jaririyar ya dauka, sai ya karba don ya raba fadan, amma ba cikin dadin rai ba. Sama-sama ya kalli ‘yar sai kuma ya mika mata, ya tambaye ta, “To yanzu ya za ki yi da ita? Bana jin gidan marayu na Saudi-Arabia za su amshe ta, tunda mu ba ‘yan kasa ba ne”. Mammah cikin mamakin sauyin da ta gani a tare da Daddy farad daya, ta ce da shi cikin kwantaccen sauti. “Wai da so nake ka yi min izini in sha magani in samu ruwan nono in shayar da ita”. Girgiza kai ya shiga yi, “Wasa ne wannan, ki shayar da dan da ba nawa ba?” Kamar za ta fashe da kuka ta ce, “Daddy........” Ya dakatar da ita, “Please don’t argue with me Maryama. Ki maida ita wajen dangin mahaifiyarta, ba zan iya riqon dan da ba nawa ba balle in kasa yin adalci tsakaninsa da ‘ya’yana Allah ya tuhume ni, musamman rikon maraya. Na yi miki alkawarin zan dauki nauyin iliminta har zuwa digiri na kololuwa idan tana so a ko’ina ta ke cikin duniya. Amma ba zan hada ta da ‘ya’yana in rike ba”. Hajiya maryam ta fashe da kuka, “Don Allah Daddy kada ka yi min haka... ina sonta, ina son uwarta ina son diya mace... Allah bai ba ni ba... don Allah Daddy ka yi min alfarma ka barni in rike ta koda wannan itace alfarma ta karshe da zaka yimin a rayuwa”. Ta daga hannuwanta biyu gare shi tana kuka tana roko. Dukkan yaran ma kuka suka sa suna rokonsa har Halim, “Daddy ka bar mana don Allah, muna so, kada a kai ta wani waje ta mutu kamar yadda Mamanta ta mutu, do us a favour”. Inji Usman. Suka kama babyn duka suka kankame, ita kuma da ta ji matsa ta canyara kuka da muryarta kamar gyare don zaki. Su biyar din duka kuka da hawaye share-share. Sakin baki Ambasada ya yi yana kallonsu, kafin ya ce “Na shiga ukuna. Ku dakata, mu yi magana ta maslaha”. Ya fada yana daga hannu irin na saranda. Duk suka dakata suna share hawaye suna hadiyar zucci. “Zan bi ra’ayinku tunda kun rinjaye ni, amma da sharadin ban yarda Mammah ta yi (breast-feeding) dinta ba, a nemi ‘alternative”. Sai duk suka juya suna kallon Mammah don jin ta bakinta. Kowannensu fuskarsa na nuna “Mammah ki yarda da hakan”. Hajiya Maryam ta sa habar zaninta ta goge fuska da majina, “Daddy ba ta da lafiya ne, tana da pneumonia, tana bukatar ruwan nono da dumin jikin uwa, in ban shayar da ita ba bani da kulawar da zan ba ta fiye da hakan”. Mikewa ya yi yana dakile fuska. Ya kakkabe rigarsa ya nufi matattakalar da za ta sada shi da dakinsa. Yana tafe yana fadin, “Shawara ta rage ga mai shiga rijiya, na ba ku daga yau zuwa gobe ku yi shawara, har madara zan dauki nauyin saye sadaqah fisabilillahi. Amma in ba haka ba gobe zan sa a buga mata fasfo ku kai ta inda ku ka dauko uwarta”. Ya yi wucewarsa ya shige daki ya rufo kofa. Usman ya matso sosai jikin mammanshi, idonsa a kan babyn da ta zuba fararen yatsunta cikin baki tana tsotso alamun yunwa. “Mammah ki yarda don Allah mana? Tunda mun samu ya bar mana?” Isma’el ya ce, “Mammah don Allah ki yarda ta sha madaran, rayuwa da ciwo duka na Allah ne, idan mai tsawon rai ce sai ki ga Allah ya raya mana ita. Take heart Mammah...”. Ya fada tare da kai hannu santar kirjinta yana shafawa alamun ta yi hakuri ta bi abin da Babansu ke so. Hajiya Maryam ta tsura wa ‘ya’yan nata ido, yara masu hankali da tunani tun a qananan shekaru irin nasu. Har sun fi ta tawakkali da hangen nesa. Da gaske Allah shi ne mai rayawa ba nonon uwa ba. Ta rungumo su gefe da gefenta, jaririyar na bisa cinyarta, ta sumbaci kowannensu a goshinsa, “Na amince. Gobe zan gaya wa Daddy. Yanzu zan fara ba ta madara kun ji ana kiran sallah, maza kowa ya je ya yi alwala yanzu Daddy zai sauko ku wuce masallaci”. Duk suka mike cike da murna har da tsalle suka nufi toilet don dauro alwalar. Ita kuma ta dauki ledar shopping dinta da babyn ta nufi dakinta. A take ta tafasa ruwan zafi ta hada madarar ta soma ba ta. Wata irin kauna tana mamaye zuciyarta na ‘yar da ba ta san daga ina uwarta ta ke ba balle ubanta. Sai dai kaso 90% na zuciyarta ya amince yarinyar nan ba shegiya ba ce, da ubanta. Habiba ba ta yi kama da mutanen banza ba, sannan ba yarinya ba ce balle a ce shege ta yi ta gudu. Ta fi amincewa da cewa wani nau’i ne na kaddarar rayuwa ya rabo ta da gidan mijinta da iyaye da ‘yan uwanta. Ba ta yi gigin zuwa turakar Daddy a yau ba kwata-kwata, shi ma bai neme ta ba. Duk abubuwan da ta saba yi masa kafin su kwanta da kansa ya yi, zuciyarsa fal haushin Maryam, tunda daga samun ‘ya har ta fara watsar da shi, da ma a ce ita ta haifa da sauki ba zai damu ba. Ya yi tsaki yana shan ‘gahwah’ (coffee) ya fi sau shurin masaki. A haka ya kwana cikin bacin rai, ita kuma tana can tana ceton rayuwar ‘yar marainiyar Allah. Ta kashe A.C ta kunna (room heater), ta ciro kayan sanyi masu kyau cikin sayayyar da ta yi ta sunke ta a ciki, da pampers. Ta cika mata ciki da madarar da Dr. Unaisa ta yi umarni. Nan da nan ta hau baccinta cikin kwanciyar hankali. A lokacin ne ta tuno da Daddy, ta yi ajiyar zuciya ta yi shirin bacci ta manna jaririyar a jikinta, ta rufe su ruf cikin lallausar bargo, suka yi bacci abinsu. Tun asuba kukan baby ya tashe ta, ta tashi zaune ta dauke ta ta yi toilet da ita. Wanka ta yi mata da ruwa mai dumi sosai, ta nado ta cikin shawul. Shafe ta ta yi da man zaitun ta canza mata (diaper), ta shirya ta cikin (overall) farare tas! Da hula mai kauri. Sannan ta hado madararta ta shiga ba ta. Ta kura mata ido ba ta ko kiftawa. Habiba ta ke tunawa da karamcinta, da yanzu ta fara jiyo sukurniyarta tana shara da goge-goge kafin ta fada kicin ta hada mata kayan girki kafin ta sauko. Hawaye suka ciko a idonta, me ya sa Habiba ta yaudare ta? Me ya sa ta boye mata asalinta da cikin da ta ke dauke da shi? Rayuwar yarinyar a gaba ta ke kokawa idan Allah ya raya ta ta fahimci ita din ba uwarta ce mahaifiya ba, ba a san kowa nata ba, ba a san daga inda ta fito ba. Ta ajiye ajiyar zuciya mai nauyi, ta share hawayen idanunta. A hankali ta sanya babyn cikin gadon da ta hada yanzu, sai bacci ta ke sadidan cikin koshin lafiya. Wanka ta yi, ta ci gayunta kamar yadda ta saba, kai ba za ka ce ta yi shekaru talatin da biyarba. Ta san sirrin gyara na diya mace kala-kala. Ta lakanci ado da kwalisa tun tana budurwa, haka yanzu da shekaru suka fara turawa ba abin da ya canza Maryam Dakata. Farar mace mai farar aniya, uwar gidan Professor kuma Ambassador Hamza Atiku Sakata. Kicin ta fada ta soma hada wa iyalinta abin kari. Sosai ta yi latti, domin har gari ya waye. Sanin Daddyn a sama-sama yake da ita ta ce bari ta yi masa abincin da ya fi so, don ta dan faranta ransa. Kunun gyada ta hada ya ji madara yadda ya kamata. Ta hau suyar sinasir din da ta kwaba tun daren jiya. A gurguje ta ke yin komai, miyar ta ji ganyen alayyahu sosai da tsokar kaji. Sun dahu sun yi lugub. Yaran kuma (quaker oat) ta dama musu, ta soya musu ‘pancake’ ta shirya wa kowanne a sundukin abincinsa. Da hanzari ta shirya wa Daddy tebur jin baby ta fara kuka. Su Isma’el suka fito daga dakinsu cikin shirin makaranta kowanne goye da dirkekiyar (school bag) dinsa. “Mammah sabahul khair”. Duk suka fadi a tare bayan sun shigo kichin din cikin russunawa. Kansu ta shafa daya bayan daya tana murmushi, “Sabahul khair, ‘yan albarka, kun tashi lafiya?”. Isma’el ya ce, “Karasa aikinki Mammah, I will help you with the baby”. Ta yi murmushi ta daga masa kanta. “Madararta na nan a kan (side drawer) ba ta ina zuwa”. Da hanzarinshi ya juya zuwa dakin nata. Tun a kan Halim Isma’el ya iya raino, shi ke taimaka mata da rainon Halim har ya yi wayau. Yanzun ma baby ya ciro daga gadonta ya aza a kafadunshi yana rirriga ta har ta yi shiru. Ya zauna gefen gadon Mammah ya ba ta ruwan zam-zam ta sha sosai, sannan ya sanya mata madarar a baki. A ranshi yana cewa, duk da dai an ce ba a gane kamannin jariri, amma wannan da ganinta Habibah ce sak! Mammah turakar Daddy ta nufa da saurinta, suka ci karo a matattakalar bene ya yo shirin office tsaf, rike da (briefcase) dinsa. Ta karba suka sauko tare, sai faman dauke mata kai yake yi. Ta yi murmushi a ranta ta ce, “Insha Allahu watarana sai ka yi alfahari da ‘yar da ba ka son rikewa din”. Su Isma’el ya kwala wa kira yana kokarin ficewa daga falon ba tare da ya dubi (dining) din ba. Ba ta yi fushi ba, ta ce, “Daddy break fast fa?” “I’m ok”. Ya fada yana duba agogo. Ta ji ba dadi yadda mata ke ji in sun takarkare sun zabga wa maigida girki ya ki ci. Usman da Halim suka wuce tare da shi, Isma’el ya fito dauke da baby ya mika wa Mammah, sannan ya dau jakarsa da kwandon abincinsa ya bi bayansu da gudu. Ta yi ajiyar zuciya ta goya baby jikinta a sanyaye. Da gaske Hamzanta ya canza daga halin da ta sanshi da shi. Ta san shi mutum ne mai tausayi da taimakon na kasa da shi, ba ta san me wannan yarinyar ta tare masa cikin gidan nan ba, da alama za ta fuskanci barazana mai yawa a rayuwar aurenta a kan rikon yarinyar daga mijinta, abin kaunarta. Ta kuma shirya karbar kowanne kalubale in har zai bari su rayu tare. Ba za ta kai ta Nigeria ba, inda ko sun je babu inda za ta kai ta a karba in ba gidan marayu ba. Ta shirya yin jihadin rikon ‘yar Habibah ko da Daddy zai kara aure ya kora ta Nigeria a dalilin haka. Ta watsar da tunanin ta shiga harkokinta. Islamiyyar ma ta daina zuwa sai ‘yarta ta isa bari a makarantar rainon yara (creche). Amma dole ta nemi ‘yar aiki don ayyukan gidan sun fi karfinta. Karshen ta dai Takarin da bata so. A nan unguwarsu Albasaatin ta yi kawaye biyu ‘yan Nigeria matan ma’aikatan Embassy, daya matar mataimakin Daddy ce Safiyya sun fi su dadewa a Saudiyyah sosai, bayan ta gama girkin rana ta kira Anty Safiyya ta ce ta cigita mata mai aiki don Allah Takari, ta ce ta bari sai Juma’ah za ta shiga Misfalah in ta je Harami za ta taho mata da ita. Ta yi godiya suka aje wayan. A daren ranar, Hajiya Maryam ta yi shiri kamar yadda ta saba ta nufi turakar maigidanta, aiki yake yi a tsakiyar gadonsa cikin na’ura mai kwakwalwa. Ciki-ciki ya amsa sallamarta ba tare da ya dago daga abin da yake yi ba. Kokarin sauke baby ta ke daga bayanta don ta koma ta dauko gadonta. Da hanzari ya dago ido ya dube su. Ya zare farin gilashin kara karfin gani da ke idanunsa, cikin kaushin murya yake magana. “Ban gane ba? Kina nufin tare zan kwana da yarinyar nan? Ta ya ya ki ke tunanin zan iya jure kukan jaririn da ba nawa ba? Excuse me please,Maryam! It’s enough wallahi, abin da ki ke min a kan yarinyar nan ya ishe ni. You are forcing me to be a father of your adopted daughter while i’m not. To bari ki ji in gaya miki, wannan ya zamo na farko kuma na karshe. Daga yau sai yau, kada ki kara kawo min ita dakin barcina. Ke kanki na hakura da ke in har za ki hada hidima ta da tata, ko za ki hada mana makwanci. Idan duk alfarmar da na yi mata ba ki gode min ba zan ba ki mamaki wallahi, don aure zan kara ki ji dadin kula da ‘yarki......” Tana kuka sosai ta juya da ‘yarta a kafada jikinta har rawa yake, domin Daddy fada yake sosai. Cikin babban sauti wanda ba ta taba sanin yana da shi ba. Tana fita ya banke kofarsa yana sakin tsaki. Haka suka kwana kamar jiya zukata babu dadi. Washegari bayan yara sun tafi makaranta, shi kuma ya tafi office, kamar jiya yau ma bai kula abincin da ta bata lokaci ta shirya masa ba. Tun asuba ta tashi ta soya masa waina (masa) don ta san yana matukar sonta, haka ya tsallake ya bar mata kayanta kamar jiya ya sa ‘ya’yansa a gaba suka tafi. Su kansu yaran ba sa cikin walwala ganin halin da iyayensu ke ciki na rashin walwalar suma, yanayi ne da ba su taba ganinsu a ciki ba tun tashinsu. Daddy da Mammah suna matukar kaunar junansu, sun fahimci juna, ra’ayinsu daya kusan a kan komai na rayuwa, sai yau a kan ‘yar Habiba, kowanne gani yake shi ne a kan gaskiya. Shi Dr. Hamza ba muguwar zuciya ce da shi ba, ba rashin tausayi gare shi ba, ba kin taimako gare shi ba, a’ah, ra’ayi ne na rikau irin na Malam Bature, duk wani taimako da zai wa mutum ko jininsa ne ya fi yarda ya yi masa shi daga nesa komin girmansa, amma ban da ya dauko shi ya kawo cikin family dinsa. Ita kuma Hajiya Maryam tana matukar son Habibah, son ne ya shafi abin da ta haifa, sannan tana tunanin in ba ta rike yarinyar nan ba ina za ta kai ta? Ba ta san komai da ya dangaci Habibah ba ba ta san daga inda ta fito ba, sannan in ta kai ta gidan marayu tana tausayin rayuwar da za ta taso a ciki. Za ta taso ne a shegance, a shegantata bayan ita ta yarda yarinyar nan ba shegiya ba ce da ubanta, akwai abin da ya rabo Habiba da mahaifinta. Me ya sa Daddy ba zai yi mata alfarma ba? Hantsi na dagawa ta samu wayar Anti Safiyyah ta daga suka gaisa da tambayar lafiyar yara. Anti Safiyya ta ce, “Mai aikin babba ki ke so ko yarinya, ko budurwa?” “Babba dai, wadda ta san ciwon kanta. Ban da wadda ba ta kai shekaru hamsin ba”. Safiyyah ta ce, “To alhamdu lillahi an samu. Sunanta Azumi, ‘yar Sakoto ce, zan kawo ta ranar juma’a insha Allahu. Za a dinga biyanta Riyal dari biyu duk wata, duk irin hidimar da ki ke so ta yi miki za ta yi miki, ku dai tattauna a tsakaninku”. “Na gode Safiyyah sosai. Na gode Allah ya kara zumunci”. In ji Mammah. Da haka suka ajiye wayar. A cikin wannan hali na zaman doya da manja, zuciya ba dadi, Hajiya Maryam ta ci gaba da zama da mijinta a dalilin ‘yar mai aikinta. Ana i’gobe za su cika kwana bakwai da baro asibiti tunanin ragon suna (haqiqa) ya dame ta. A yadda Daddy ke kumbure-kumburen nan za ta doshe shi da zancen yanka ragon suna? Ta yi tunanin ta bai wa Salah ya sayo da kudinta kamar yadda ta yi amfani da kudinta wajen siya mata suttura, madara kam ya saya katan-katan kamar yadda ya furta, sai dai wani (positive) tunani ya shige ta. Bai kamata tun yanzu ta soma yin gaban kanta a kan yarinyar ba, dole ta ba shi hakkin da yake cewa tana ‘forcing’ dinshi na zaman uban yarinyar yana so ko ba ya so, in ta sayi rago ta yanka mata ya tabbata ita ce uwarta, ita ce ubanta kenan, “You must be the father you don’t want to be Daddy!”. Ta fada a fili. A daren ranar ta cancada kwalliya, turare kala-kala ta feshe jikinta da shi, a gobe ta ke sa ran za a kawo mata sabuwar mai aikin. Ba za ta iya barin Baby ita kadai ba, don haka ta kira Usman da Isma’eel da Halim ta jere su a gadonta ta ce su kwana a nan. “Isma’el ba ka da nauyin barci, ka kula da baby in ta motsa. Ga madararta, ga ruwan zam-zam dinta ka duba pampers akai-akai”. “Dont worry Mammah, je ki lallasar mana Daddy ya daina fushi da ke. Mammah tausayinki nake ji, ya ce wai wata sabuwar mata zai kawo mana ke kin daina sonsa sabida jaririya”. Murmushi ta yi, ta ce, “Isma’el Allah ne ya halatta masa auren mata har hudu in yana da iko. Ba saboda jaririyarmu ba ne. Kuma ba saboda ita yake fushin da yake yi ba, ni ce na yi masa laifi”. Ta fadi hakan ne don kada su fassara mahaifin nasu a matsayin mutum mara tausayi da adalci. Wanda tuni hakan ya fara darsuwa a zuciyar Isma’el tunda ya fi Usman da Halim wayo. Amma yanzun ya yarda da abin da Mammah ta ce, sai dai ko kusa ba ya son Daddy da wata macen bayan mahaifiyarsu. Akwai abokinsa a makaranta a Abuja da yake ba shi labarin cewa Mamansa ta rasu wajen haihuwarsa a hannun (step-mother) dinsa yake, kullum sai ta dake shi ta sa babansa ya dake shi, kuma ba ta bashi abinci sai mai aikinsu ce ta ke ba shi. Wannan labari da Salim ya ba shi ya tsaya masa a zuci, ba ya so ya ji an ce za a kara aure. Da haka Mammah ta wuce ta barshi yana tunani, yana kallon Baby da ke barcinta cikin kwanciyar hankali a cikin kyakkyawan gadonta da ke gefensu. Usman da Halim tuni sun yi barci. Mammah ta yi sallama a kasaitaccen (bedroom) na Ambassador Hamza Dakata, tuni ya kashe fitila ya rufe kwamfuta yana azkar din barci, dole ya amsa sallamar don bai zaci ganinta a lokacin ba. Kwana shida kenan rabon da su hada makwanci, in ya ce ba ya kewar Maryam ya san ya yi babbar karya ya kwana da yunwa. Mace daya tamkar da dubu wadda ta mamaye filin mata goma a zuciya da ruhinsa, ta haifa masa sanyin idaniya ABDUL’AZEEZ HAMZAH ATIKU, in ya ce zai hada matsayinta da na wata mace da sunan aure ya san ya fada ne kawai don ya ji dadin bakinsa ko ya huce haushi amma Maryam ta wuce nan a zuciyarsa. Jin ta ya yi ta kwanta a gadon bayansa ta sanya tausasan hannuwanta ta rungume shi, hawayenta na sauka saf-saf a kan kafadunsa. Runtse ido ya yi wani sanyi na ratsa zuciyarsa. Ta ja bargon da yake kokarin rufawa ta ajiye a gefe. “Ka yi hakuri Daddy don Allah ka yi hakuri, na yarda laifina ne, na kasa hakura da tsarinka in yi maka biyayya. Na yi ne don neman lada a wurin Ubangiji ba don in bata maka rai ba Daddy”. Ta fadi cikin shesshekar kuka mai motsa zuciya balle zuciyar masoyi. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya dago ta ya juyo suka fuskanci juna. “Why Maryam? Me ya sa ki ka zabi farin cikin wasu bare da ba ki hada alakar komai da su ba a kan nawa? Na dade ina mamaki, ina tambayar kaina anya Maryam dina ce? Ta bar ni kwana shidda ba tare da ta san halin da nake ciki ba? Ya ya nake rayuwa? Me nake ci nake rayuwar? Anya Maryam ke ce???” Hawaye ta ke sharewa sosai, “Tunda ka gaza fahimtata Daddy, ka kasa mara min baya mu ceci rai, mu yi jihadin rikon maraya tare, mu yi domin neman lada a wurin Ubangiji na amince ka fadi duk yadda ka ke so a yi da jaririyar nan na maka alkawarin zan bi, in har za mu koma rayuwarmu ta baya ka kuma fasa auren da ka ke cewa yara za ka yi. Ba zan iya hada ka da kowacce mace ba Daddy ‘depression’ zai kama ni”. Bai san sanda dariya ta kwace masa ba, ya yi sosai sannan ya gintse fuska, “Ina nan fa ina jiyo laccar da ki ke wa Isma’el yaushe ki ka juya ta a baibai? Kin ce Allah ya ba ni iko, yanzu kuma kin ce ‘depression’ zai kama ki, dole in yi aure Maryam don in samu mai kula da ni, ke kuma ki ji da ‘yar da ki ka fi so a kaina. Me ye laifina a nan?” Ta share hawaye da tishu ta ce. “Ai na ce ka fadi yadda ka ke so a yi, ko cewa ka yi in jefa ta a kwatami zan jefa tunda ba ka sonta”. Ya hade fuska, “Ni na ce miki bana sonta? Me ta min? Kawai kin kasa fahimtata ne ke ma, amma a bar zancen haka, kowa ya zauna a kan ra’ayinsa. Amma abubuwan da ki ka dauko hanyar yinsu ba zan lamunce su ba, dole ki ba ni dukkan kulawar da ki ke ba ni a baya. Ban amince ki canza ko kwaya daya ba, bana son zama da masu aiki amma na amince ki daukar mata Nanny zan biya ko nawa ne. Ki daina hada lamarina da nata, daga sanda na dawo office karfe shidda na yamma har zuwa wayewar gari in fita (office) lokacinki nawa ne da yarana ki bar ‘yarki can wajen mai rainonta. Kuma ki ci gaba da bincike a kan danginta, duk ranar da suka bayyana za ki mayar musu da ‘yarsu”. Gyada kai ta yi cikin hadiyar zuciya, “Na amince Daddy, wallahi na amince. Na gode, Allah ya kara rufa maka asiri duniya da lahira. Alfarma ta karshe da nake nema ka yi mata haqiqa, ka sanya mata sunan duk da ka zaba, ka yi mata khutbah gobe da safe kafin ka wuce office, already na nemi Nanny din wallahi, gobe Safiyyah za ta kawo ta........”. Ta cika shi da surutu, bayan shi kuma cike yake da wata irin kewarta, janyo ta ya yi kawai ya sanya cikin kirjinsa, ya rufe su ruf da bargon mai tsananin taushi da kamshi. Can kusan makoshinsa ya ce, “Ke don Allah ya ishe ni haka, gobe zan yanka mata ragon...” Da haka hirar ta kare, ta koma mai ma’ana da kara dankon kauna. Hakika ta yi kewar mijinta, shi ma Daddyn ya yi kewarta yadda harshensa ba zai iya fassarawa ba, sai dai ‘emotions’ dinsa a daren ranar bakidayanta sun nuna mata hakan. “Daddy kenan! Zuma, ga zaki ga harbi”. Maryam Dakata ta fadi cikin zuciyarta cike da shaukin mijinnata, dan uwanta, uban ‘ya’yanta. ***** Washegari da Salah ya sauke shi a office ya ba shi umarnin ya sayo babban rago a yanka da sunan ‘yar Mammah, da ta ce ta ba shi zabin sunan da za a saka wa jaririyar, cewa ya yi shi fa babu ruwansa. Ta sa wa ‘yarta sunan da ta ke so idan kuma haqiqar da ya yi mata ma ba ta gode ba, to don Allah ta kyale shi haka. Da yake lallaba shi ta ke, sai ba ta ja da nisa ba. Ta mika masa bebin tana marairaicewa. “To don Allah amshe ta ka yi mata khutbah da sunan Addah, wato Hafsatu”. Harara ya dalla mata, “A dalilin me? Ga sunan uwarta za a ce na uwata zan saka? Ba gara ki sa mata Habiban ba don a gane danginta da sauri?” A ranta ta ce, “Bakinka ya sari danyen kashi. Hmmm! Ko an gane ba wanda zan bawa, ‘ya ce Allah ya riga ya ba ni, iyayena da ‘yan uwana sun isa su zame mata dangin”. Ta sake kwantar da murya, “Daddy, ba zan taba mance sunan uwarta ba, don Allah ka sa mata Addah, don ta biyo kyawawan halayenta”. Yana cin magani ya amsa, ya zauna a bakin kujera ya kai bakinsa saitin kunnenta yana yi mata khutbar. Dadi ya kashe Mammah a zuci. Bayan ya fita da awanni uku Anti Safiyya ta yi sallama, matar biye da ita. Kyakkyawar tarba Hajiya Maryam ta yi musu. Bayan sun ci abincin rana suka soma tattaunawa. Azumi ta amince za ta taya Hajiya Maryam ayyukan gida, za ta yi rainon Hafsat da amana. Shekarunta arba’in da biyar, nitsattsiyar mace sosai. Mamma ta miqa mata Hafsat din da ta yi wa lakabi da SUHAANAH kasancewar sunan mahaifiyarta ne, a take Azumi ta karbe ta ta goye. A gaban Anti Safiyyah Hajiya Maryam ta zaunar da Azumi a kan kilishi, ita da Anty Safiyya suna kan kujera ta soma magana cikin nutsuwar da Allah ya halicce ta da ita. “Azumi ga ni ga wadda ta kawo min ke, kawata Hajiya Safiyya, na daina zama da ‘yan aikin da ban san asalinsu ba. Tsakani da Allah ki gaya min daga ina ki ka fito a Nigeria, da inda iyalinki suke. Zan kuma yi bincike idan kin yi min karya”. Anty Safiyya ta gyada mata kai, “Haka ne kwarai. Azumi muna sauraronki”. Dattijiyar ta gyara zama cikin hankali ta ke magana. “Daga jihar Sokoto na zo Saudiyyah, idan na yi miki karya Allah ya hukunta ni daidai da abin da na aikata na yaudara”. Mammah ta ce, “Sokoto wace unguwa? Gidan wa?” “Unguwar Mabera, gidan Malam Isuhu Maishanu, mun zo Saudiyyah ni da mijina muna neman na kanmu a Shari Mansur shekara biyar a baya, muna kawo goro da sauran abubuwan da mutanenmu ke bukata, an sha kama mu har sau biyu ana mayar da mu Najeriya muna dawowa, kamar yadda ki ka sani in ka dandani zaman saudiyyah ba ka iya bari da sauki, to hakan ce ta faru da mu ni da maigidana. Shekarar baya ya rasu ya bar ni da ‘ya’ya biyar namiji daya hudu mata. Namijin Yusha’u ya jima da yin aure a Maishanu. Na aurar da mata biyu a can gida Sokoto, ta ukun wato Harira da autar Ladidi kuma suna hannun kanwata a Talata Mafara. Idan akwai karya cikin abin da na fada Allah ya hukunta ni da laifin yaudara da cin amana”. Anty Safiyya ta dafa kirjinta da hannunta na dama ta dan fiddo mata ido ta ce, “Ni ‘yar Sokoto ce gaba da baya, Iyayena da kakannina, don haka zan bincika abin da ki ka ce daga yau zuwa gobe. A unguwar Nakasari da unguwar rogo iyayena suke na san Mabera sosai”. Azumi ta gyada kai alamar amincewa. Hajiya Maryam ta nisa, sannan ta dubi Azumi, “Abin da ya sa na yi miki wannan titsiyen ba rashin yarda bane, mai aikina ta baya ce...........” Tiryan-tiryan ta ba su labarin tun kawo mata Habiba Abuja zuwa yau. Azumi ta sakko Hafsat ta kara rungume ta a jikinta, ta sa mayafinta ta kara rufe ta sosai daga ita har Anty Safiyya sai da suka yi hawaye. Safiyyah ta karbi Hafsat ita ma ta rungume tana kallon kyakkyawar fuskarta, ta ce da Hajiya Maryam. “Na rantse da Allah na dauka haihuwa ki kai, ganin yarinyar nan fara tas kamar ‘ya’yanki. Kina da tsayi, kina da dan jiki ba a fiya ganewa ba idan irinku nada ciki. Allah ya ba ki ladan wannan jihadi na ceton ran maraya da sadaukarwa saboda Allah”. Murmushi ta yi, ta ce, “Amin”. Amma ba ta gaya musu halin da ta ke ciki da maigidanta a kan lamarin ba. Ciki ba don tuwo kawai aka halicce shi ba, wani abun yana bukatar sirri. Bayan tafiyar Safiyya, Azumi ta goye Hafsat wadda Mammah ta kira (Suhaana) suka ci gaba da ayyukan gida tana nuna wa Azumi kan komai na gidan. Ta nuna mata dakinta. Kwarai dattijuwar mai hikima da azanci ce, har girkin dare ita ta yi, kuma Hajiya Maryam ta yaba, tuwon shinkafa da miyar busasshiyar kubewa da ta ji naman ragon sunan Hafsatu. Sai Mammah ta yi na Daddy kawai, su Isma’el suna ta santin girkin Baba Azumi, yadda Mammah ta koya musu su dinga kiranta. [01/08 3:33 PM] Sumayya Takori: SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* AUREN KWANGILA 1 Page 4 Kyakkyawar kulawa Suhaana ke samu a hannun Mammah da Baba Azumi. Tuni ta murmure ta yi kubul-kubul abin sha’awa cikin watanni uku kacal ta iya zama, har tana karya kafa tana so ta fara rarrafe. Yarinya mai kyau da ban sha’awa ga gashi fal kanta duk da an yi mata askin suna. Mammah ba ta gajiya da yi wa gashin ado da ribbons kala-kala da yi masa style iri-iri. Duk sharuddan da Daddy ya gindaya mata a kan rayuwar Suhaana a gidansa tana kokari wajen kiyayewa. Daga karfe shidda in suka shige daki ita da uwargoyonta Azumi ba sa kara fitowa sai lokacin da Azumi za ta dora sanwar safe, za ta goye ta ta shiga kicin bayan ta cika mata ciki yadda ba za ta yi kuka ba. Dakin da Habiba ta zauna a nan Mamma ta sanya Azumi, yana daga can gefe suna da nisa sosai da bangaren Daddy. Cikin watanni ukun nan bai fi sau biyu Ambasada ya dora ido a kan Suhaana ba. Na farko Isma’eel ne ya sanya ta cikin keken koyon zamanta ya tura ta harabar gidan, inda suke wasan kwallo shi da wasu yaran makotansu larabawa. Usman da nasa abokan suna wasan tseren keke a layin, Halim na tsaye jikin keken nata yana yi mata wasa. Hancin motar Daddy ya sako kai, yana hakimce a gidan baya na galleliyar Hummer-Jeep, Salah ke tukawa. Da sauri mai kula da shukoki da wanki da gugarsu mai suna Habibullah ya zo ya bude wa Daddy kofar bangaren da yake zaune ya fito. Da gudu Haleem ya turo keken Suhaana zuwa gare shi yana, “Daddy oyoyo”. Daga shi ya yi sama ya girgiza ya dire, daidai idanunsa suka sauka a kan yarinyar. Kyakkyawa ta kin karawa kamar larabawan Jiddan suka haife ta. Tsafta ta kama jikinta sosai. Ya kalle ta na minti biyu ya dauke kansa ya yi cikin gida, Haleem ya tura ta suka ci gaba da wasansu. Ganinsa na biyu da ita ranar ‘open day’ na su Usman ne, an bukaci iyayen yara duka su zo don sanin halin da yaransu ke ciki a makaranta da karatunsu. Mota daya suka yi amfani da ita shi da iyalin nasa, ya ganta a hannun Azumi wadda ta sha hijab bakikirin ta shigo bayan motar, ai bai san sanda ya bude wuta ya fara fada ba, “Me jaririya kamar wannan za ta je yi makarantar yara? Maza ku koma gida, ai ba gidan biki ba ne”. Sum-sum-sum Azumi ta fito daga motar jikinta a salube. Ba tun yau ba ta fahimci uwar dakin nata na fuskantar kalubale daga mijinta a kan rikon yarinyar in ta yi la’akari da yadda ta ke faman cewa su zauna a daki in Daddy yana gida, kada ta bar Suhaana ta yi kuka. A lokutta da dama kuma da ta ji dirin motarsa ya dawo za ta zabura ta sunkuci ‘yar ta yi daki da ita tana cewa Azumin, “Ku shige, sai Allah ya kai mu gobe”. Duk me ya yi zafi? Me ye laifin wannan ‘yar yarinya abin son ganin kowa? Duk inda suka shiga sai an yaba ta, ana nuna sha’awa a gare ta, to shi Ambassada saboda Allah wane irin mutum ne kenan? Ta kasa fassara shi, domin kuwa mutum ne mai yawan taimako da faram-faram da jama’a, ko dai shi ya yi wa Habiban cikin ta haife ta shi yasa ba ya son ganinta? Ta yi saurin yin istigfari tana rokon Allah ya yafe mata wannan mummunan zato da ya ziyarci zuciyarta. Mutum ne na gari, mai rikon addini da kaunar iyalinsa, da kula da matsalolin al’ummar Najeriya mazauna Saudiyyah matuka da lafiyarsa, jiki da aljihunsa da matsayin kujerarsa. Ita kanta shi ya yi mata takardar zama tare da su a matsayin family dinsa. Ta watsar da tunanin ta shiga hidimar Suhaana. Watannin Suhaana hudu kenan ta fara rarrafe, Mamma ta yi tunanin komawa islamiyyarta tunda Hafsat ta yi wayo, hidimarta ta ragu, ga Azumi na taimakonta bilhakki da zuciyarta daya. Tsakaninta da Ambasada lafiya lau, tunda tana kiyaye duk abin da ya ce mata ba ya so din. Ba ta kuma damuwa ta yi masa uzuri da ajizanci irin na dan Adam, dukkanmu masu nakasu ne ‘in one way or the other’, sannan tunani da halayya kowa da irin nasa. Lokacin Hajji ya zagayo, su Adda Hafsatu, Baffa Atiku, Inna Ramatu dasu Luba na shirin zuwa, duk Ambassador ya ba su kujerar hajji, tare za su taho da Abdul’azeez ya samu hutun karshen shekarashi ma ya wuce Kano tun satin da ya wuce. Anty Zuwaira ma ta yi mata waya za su zo aikin Hajji ita da su Farhan ban da Sanata. Don haka suna ta shirye-shiryen zuwan bakin ita da Daddy da Azumi, duk da ba jimawa za su yi a Jeddah ba kwana uku za su yi su tattara su wuce Makkah har masu gidan. Amma tarba sosai suke shirya wa iyayen nasu da ‘yan uwansu. Ranar laraba jirginsu ya sauka, suka je ita da Daddy da yara suka dauko su a filin jirgin saman sarki Abdul’azeez. Azumi da Suhaana na gida, ko da suka iso Azumi na hidimar jera abinci a ‘dining’ goye da Suhaana har hada baki suke wajen tambaya, “Maryama haihuwa ki ka yi?” Har da masu zaro ido. Murmushi ta yi, ta karbo ‘yar daga bayan Azumi ta dora a cinyar Adda Hafsatu, “Karbi takwararki Addah”. Da matsanancin mamaki Adda Hafsatu ta karbi ‘yar da ita da sauran duka suka zuba mata ido, ba ta kama da kowa a gidan kawai farar fatarta ce irin tasu. A hankali Adda Hafsatu ke tunanin ina ta san wannan fuskar? Tabbas ta taba ganin mai irin wannan fuska har digon tawwadar Allah a goshi irin na wata fuska da ta dade da gani ne. Sun damu ta gaya musu inda ta samo ‘yar, ta ce sai sun ci abinci, in son samu ne su yi mata hakuri zuwa gobe su Zuwaira ma su iso sai ta gaya musu tare. Dole haka suka kwana cikin tararrabi da tunani, sai dai kowannensu yarinyar ta shiga ransa, musamman Anty Luba. Washegari iyalin Sanata Abdulkarim su ma suka iso, suka dauko su a airport ita da Abdul’azeez da Salah direba, don ba jituwa ce sosai tsakaninta da dangin mijin nata ba cikinsu babu wanda ya damu da harkarta, haka ake rayuwar. Don ‘ya’yanta ma ta koya musu irin halinta na raina mutane in ba wanda suke (under the same social class) ba. Da Hajiya Zainab da nata iyalin kawai ta ke mu’amala, tunda su masu farcen susa da mukami ne. Ita Mammah ba damuwa ta yi da harkarta ba, ita ta ke shige mata duk da haka babu wanda ya nuna mata wani hali mara dadi, an yi mata barka da zuwa kamar kowa, yaranta sun shige cikin su Usman suna ta harkokinsu, Abdu’azeez tun zuwansa washegari ya wuce Tahfiz dinsa bayan sun dauko Anty Zuwaira. A daren ranar bayan an gama cin abincin dare, Mammah ta kwance musu zare da abawa na rayuwar Hafsat, Daddy ba ya nan lokacin kuma su ma ba ta gaya musu halin da ta ke ciki da shi ba a kan rikon yarinyar. Ta sani idan ta fada Baffa Atiku ba zai yi masa ta dadi ba, don sau tari shi yake ‘correcting’ dinsa kan halayensa na masu jajayen kunnuwa da suka yi masa katutu. Kowa shiru ya yi cikin tausayawa, Baffa Atiku ya ce, a miko masa ita ya yi mata addu’o’i na neman tsari daga sharrin mutum da aljan, irin wadda yake yi wa duk dan da aka haifa a zuri’arsu, mace ko namiji. Baffa Atiku malami ne sosai masanin addinin muslunci. Alherin Daddy a kan yarinyar ta fada ba other dark side din ba, ta ce ya yi mata khutbah da sunan Inna Hafsatu, ya yi mata haqiqa, ya dau nauyin madararta da iliminta in Allah ya raya ta. Daddy ya gama mata komai da wannan alfarmar ba za ta tozarta shi ba a kan dan kankanin gazawarsa. Sosai haka abin yake har zuciyarta. Anty Zuwaira ce kawai ta dan nuna hali. Yamutsa fuska ta yi, ta ce, “Adda Maryam anya ba ki yi wauta ba? Zamani fa ya canza, ba ka rikon dan da ba kai ka haifa ba saboda gudun abin da gobe za ta haifar da butulci na al’umma a yanzu”. Hajiya Maryam ta harare ta, kafin ta ba ta amsa, “Me nake so ta rama min da shi in Allah ya raya ta?” Ta tsattare ta da ido. Zuwaira ta yi shiru, don ta rasa amsar ba ta gaskiya. Ba abin da ba ta da shi a rayuwa, me ta ke bukata jaririya ta biya ta da shi na rikonta in ta girma? Jin ta yi shiru Hajiya Maryam ta kara jefo mata tambaya. “Idan don Allah ka yi rikon a wajen wa ka ke neman sakamako?” Gabadaya suka hada baki wajen fadin, “A wajen Allah. Allah ya ba ki lada”. Zuwairan Abdulkarim ba ta kara magana ba. Kwanansu uku cif, Zuwaira biyu suka dunguma har ‘ya’yansu suka wuce cikin Makkah don gabatar da aikin hajji. Hotel din Hilton Ambassador ya kama musu dukkanninsu. Azumi da Suhaana su kadai aka bari a Jeddah, sai maza ma’aikata. Mammah ce ta ce su zauna a gida har su dawo, duk don ta zauna lafiya da Daddy ya sake cikin iyayensa da ‘yan uwansa, babu wadda ba ya son gani din. Allah shi ne mai rayawa. Aka ce ko jinjiri ya san mai kaunarsa, ba karamin sabo Suhaana ta yi da Mamma ba. Mai ba ta abinci, mai yi mata wanka, mai yi mata komai, mai lullube idanunta da murmushin kauna irin na UWA. Mai bata dumin jikin da uwa ke ba wa danta. Mai lallashinta in tana kuka, mai bata abinci akai-akai, mai kula da lafiyarta da kai ta check up asibiti akai-akai don treating lalurar ta. Mai saya mata duk wani abu na jin dadin rayuwa da yaro dan gata ke bukata. Daina ganin Mammah da ta yi cikin gidan sai ya sabbaba mata rashin kuzari da rashin walwala. Azumi ba ta san Hafsat- Suhaana na da nimoniya ba, saboda da ta zo babu A.C a dakin da ta ke, amma don samun wuri irin wanda masu aiki suka gada, da jama’ar gidan suka yi kaura, sai ta ke yi musu shimfida a falo ta kure musu A.C abinta. A lokacin ana zabga bala’in zafin nan da rana mai shiga kwakwalwa na kasar Saudiyyah, ta ce a ranta, “bari mu dana A.C kamin masu gidan su dawo”. In tana shan ruwan sanyi Suhaana ta nuna tana jin ki shi, shi ta ke ba ta. Ta barta da ‘yar shimi tsakiyar AC wai ta sha iska, rannan da ruwan sanyi ma tayi mata wanka tana fadin “zafi yayi yawa kada kiyi kuraje”. A kwana uku da tafiyar su Mammah, ranar cikin dare tana bacci ta ji numfarfashi irin mai fita ta baka ba ta hanci ba. Ta bude ido a hankali, ta ga yarinya na girgiza da sankarewa. Tuni ta bude ido gabadaya, ta mike zaune ta kamata tana girgizawa, tana fadin, “Na shiga uku ni Azumi. Wayyo Allah na!”. Ta rarumo wayarta a caji bayan ta kankame ‘yar a jikinta, ta danna wa Mammah kira. An yi sa’a Mamma ba sa barci da wuri, tana tare da su Luba, Furairah da Mariya da Murja wadanda suka iske su a can jiya. Hira suke yi a kayataccen falonsu na hotel. Addah da Inna Ramatu da Anty Zuwaira sun shige daka sun yi barci, shi kuwa Daddy da ma ba sa tare, dakinsa daban shi da Baffa Atiku da Abdul’azeez da su Farhan yaran dan uwansa, Halim ne kawai tare da Mammah, ya dade da yin bacci. Wayar Mamma ta yi kara, ta daga ta duba kamin ta amsa, Azumi ce. Haka kawai ta ji gabanta ya fadi, kiran me Azumi ke mata cikin dare haka, karfe goma sha biyu da rabi? Da sauri ta amsa, “Azumi ya ya? In ce ko lafiya?” Cikin makyarkyatar murya ta ce, “Ina fa lafiya Mammah? Suhaana ta sassankare min, numfashi ma ta baki ta ke yinsa, idonta ba ya buduwa”. Mikewa tsaye Hajiya Maryam ta yi tana dafe kirjinta cikin matsananciyar faduwar gaban da ya fi na baya. Ta daure a hankali ta ce da ita. “Wanka ki ka yi mata da ruwan sanyi?” Da sauri Azumi ta ce, “A’ah”. “Ruwan firij ki ke ba ta bana filas dinta ba?” “Gaskiya na ba ta sau daya da ta sa kuka sanda nake sha tana so ta sha, amma dan kadan”. “A.C ki ka kunna mata?” Hajiya Maryam ta fada cikin son kecewa da kuka, da a kusa suke sai ta manta da yawan shekarunta ta kantsa mata mari. “Eh, toh mukan zauna a falo, kin san zafi ya yi zafi a nan Jeddah”. Mamma haushi da takaici suka rufe ta, amma kokari ta yi ta danne fushinta, tana fada wa zuciyarta laifinta ne ba na Azumi ba, domin ba ta gaya mata ba, bai kamata ta tuhume ta a kan laifin da ba ta da masaniya a kan faruwarsa ba. Cikin gaggawa ta ce, “Ba ki san ba ta da lafiya ba? Da nimoniya aka haife ta, ku fito get yanzu zan turo asibiti su dauke ku”. Ta katse kiran, ta sake kiran Dr. Unaisa. A gurguje ta gaya mata, ta ce ba matsala za ta turo ambulance a dauko su yanzu. Hankalin Hajiya Maryam bai kwanta ba sai da Dr. Unaisa ta tabbatar mata an ba ta duk taimakon gaggawar da ta ke bukata. Bacci ya dauke ta, ta kara da cewa, “She’s now breathing normally, kwantar da hankalinki”. Ta yi ajiyar zuciya suka yi sallama. Ajiye wayar tata ke da wuya ta hango idanun ‘yan uwanta a kanta, duk suna mata kallon me ke faruwa? Ta gaya musu, Luba ta ce, “Me ya sa ki ka ce su zauna a gida tunda kin san tana da lalura?” Ta yi ajiyar zuciya cikin damuwa, “Bana so ta sha wahala ne, kin dai ga yadda aikin hajji yake”. Duk suka yarda da hujjarta. Su Murja da basu da labari duk aka gaya musu. Tun daga ranar bayan an sallamo su daga asibiti, Azumi ba ta kara kunna A.C ba, ba ta kara ba ta ruwan sanyi ba. Tana kiyayewa wajen yi mata wanka, wato da an gama wankan a nade ta cikin shawul a sa mata suttura kafin iska ta shige ta, koyaushe tana manne a jikinta. Kullum sai Mammah ta kira don jin lafiyarta da yadda suka kwana. Tana gaya mata inda matsala komi kankantarta ta kira ta gaya mata. Cikin sati hudu cif suka kammala sauke faralinsu suka dawo Jeddah. Mammah ta ga ‘yarta ta kara girma, ta kara zama buleliya, jazur da ita wanke hannu ka taba. Ta dauke ta ta rungume tana sunsunarta, ita ma Suhaana sai kyalkyala dariya ta ke. Sunan mahaifiyarta da ta sanya mata ya kara mata kaunar yarinyar, don bayan SUHAANA da ta sanya mata, wani zubin sai ta ce ADDAH TA. Kwana uku su Adda suka kara a Jeddah jirgi ya kwashe su dukkansu, ya mayar gida Najeriya ana cike da shaukin juna, kamar kada a rabu. Abdul’azeez binsu ya yi, ya ce zai karasa hutun nasa a gidan Kawunsa Abdulkarim tunda Tahfiz din ma da yake daukar haddar sun yi hutun aikin hajji. **** Haka rayuwar gidan ta koma yadda ta ke, yau da dadi, gobe babu tsakanin Ambasada Hamza da matarsa Maryam a kan Suhaana. Yarinya tana girma shakuwa na kara karfi tsakaninta da ‘yan uwanta uku; Usman, Isma’eel da Halim. Kaunarta ga matar da ta dauka matsayin mahaifiya, wato Maryam Dakata na kara karfi. Haka nan ta saba da uwar goyonta Azumi, Daddy kuwa ko hanya ba ta hada su sai guri ya kure. A haka Hafsat ke girma, tana tashi da kwazon son karatu wanda ta tashi ta ga ‘yan uwanta ukku a kan turbarsa. Tun ba ta isa shiga makaranta ba ta haddace alifun, Ba’un har zuwa karshe. Ta haddace ABCD har zuwa karshe, ta kuma iya rubuta su. Duk kuma ta koya ne a wurin Isma’eel, Usman da Halim. Lokacin da bakinta ya fara budewa da sunan Mammah ya fara budewa ‘MOMMAH!’. Ta dauki tsawon lokaci kafin bakinta ya iya furta Ishma’el, Usman da Haleem tare da Baba Azumi. Bayan wadannan mutanen guda biyar ba ta san kowa ba, ba ta saba da kowa ba. Ba ta da wani abu mai muhimmanci da ya wuce su, sai karatunta. Ba ta taba sanya DADDY a jerin mutane ba. Ya fi mata kama da wata halitta daban, wadda in ta ganta ta ke neman maboya, ta ke zurawa da gudu wajen uwar goyonta saboda gizagon da muzuran da yake mata. Shi kuwa Abdul’azeez ko ya zo ba ta cikin shirginsa. Bai dauke ta a bakin komai ba bayan wata mutum ‘YAR KARO mai zaman cin arziki a gidansu. Sam ba ta cikin shirginsa, ko kyakkyawan kallo ba ta samu daga gare shi, halayensa sak! Na ubansa. Shekaru na mirginawa, rayuwa na juyawa dauke da ci gaba da nasarorin rayuwa iri-iri a gidan Hamza Dakata da sauran ‘yan uwansa da ke Najeriya, Sanata Abdulkarim ya samu nasarar hayewa kujerar ministan huldar Najeriya da kasashen ketare, Ibrahim autan Adda ya gama karatunsa a jami’ar Ahmadu Bello ya samu aiki a Federal Inland Revenue Service (FIRS) da taimakon Dr. Hamza, yarinyar da yake nema ma Sa’adiyya an ba shi an yi bikinsa, suna zaune unguwar Jambulo a Kano. Minister Abdulkarim ne ya gina masa gida. Uncle Idris autan su Ambassador ya kammala karatun likitancin da yake yi a jami’ar Maiduguri ya dawo Kano, ya kama aiki da asibitin Malam Aminu Kano. Yayi aure da wata likita Tauheeda suna zaune a gidajen likitoci na asibitin. Kowa a gidan marigayi Malam Abdullahi Dakata ya tsaya da kafafunsa, ya kafa iyali ba mazan ba, ba matan da ke gidajen aurensu ba, babu mai jiran dan uwansa ya zo ya ba shi, Ambassador Hamza da kawunsa Minster Abdulkarim sun tsaya musu, sun kafa su yadda ya kamata, zuri’arsu bakidaya sai sam-barka. Shekarar Hafsat hudu ta gama Raudha (nursery), kuma a shekarar ta wuce firamare aji biyu aka sanya ta maimakon daya (double promotion) a ‘Halah International School’ da ke birnin Jeddah, Isma’eel ya gama firamare ya shiga sakandire yana aji biyu, Usman na ajin karshe a firamare a shekarar nan zai fita, Halim na aji hudu, ‘yar Momma ko kuwa ‘yar karo in ji Abdul’azeez tana aji biyu. Sau tari in ya kalle ta daga nesa yakan tuno mahaifiyarta, musamman in ya ganta ta gifta ta gabansa, hatta tafiyarsu iri daya ce, idanunta da bakinta duk na Habiba ne. Amma fa hali ya bambanta, tun a kananun shekarunta ya lura ba ta da sakin jiki da mutane kamar Habiba, ita dai Mammah da Baba Azumi, koyaushe tana jikinsu kamar ‘yar mussa (mage), sannan su kadai ne masu jin muryarta, bako irinsa sai dai ta bi su da ido daga nesa, ko gaisuwa albarka, sai in Mammah ta ce ta gaishe shi. Sam ba ta cikin ‘yan kayansa, ba ta dame shi ba amma har gobe uwarta tana ransa. Bai damu da ita ba kamar su Ishma, haka abin yake a wajenta ita ma, ganinsa ta ke wani bako mai zuwa gidan lokaci zuwa lokaci, mai irin idanun Daddy masu gizago da muzurai kamar dodanni. Su Usman su ce ‘Mammah’, Hafsat ta ce, ‘MOMMAH’. Hausarta ba ta fita sosai. A shekarar da Abdul’azeez ya kammala karatunsa na sakandire a (Regent-Abuja) ya zana jamb, ya nemi gurbi a jami’ar Ibadan (University of Ibadan) a shekarar ne wani abin alhini ya samu wannan family. Abin alhinin kuwa shi ne, an yi wa Ambassador Dakata sauyin wajen aiki da karin girma, daga Saudi-Arabia zuwa kasar Belgium. **** BELGIUM Kasar Belgium na daga cikin manyan kasashen Europe, ita ce headuquater ta dukkan (European Union and Nato). Babbar kasa ce mai tarin albarkatun kasa. An kirkire ta a shekara ta (1830), tana makwabtaka da kasashen Neitherland da Luxemburg. Belgium sautari a kan kira ta da ‘Battle field of Europe’, ko kuma ‘cockpit of Europe’ saboda karfin rundunar sojojinta. Sunan Belgium ya samo asali ne daga ‘Gallia Belgica (Roman province) a (100BC). Ana kiran mutanen kasar Belgium da ‘Belgians’. Belgium ta samu ‘yancin kanta a shekara ta (1830) 4th October. Manyan yaren kasar guda biyu ne; Dutch; wadanda ake kira (Flemish) da kuma French-speakers; (walloons). Kadan daga cikinsu kuma suna amfani da harshen Jamus musamman jama’ar Brussels babban birnin kasar Belgium. Brussels City, a matsayinsa na Capital Territory ya fi kowanne state na kasar girma da fadi, da hada al’ummatai daga ethnicities daban-daban. Don haka birnin Brussels shi ne inda hukumomin jakadancinsu yake, kuma a nan ne Ambasadodin kowacce kasa ke zaune. **** Maimakon su yi murna da wannan sauyi da karin girman da Daddy ya samu sai suka shiga alhini mai dumbin yawa, suka soma tunanin yadda za su iya barin birnin Jeddah da kasar Saudiyyah bakidayanta, sun yi mugun saboda rayuwar Jeddah, shiga Harami, makarantunsu, makotansu, abokanansu da komai na garin Jeddah, ba yadda suka iya, aikin jakadanci ya gaji hakan. An sanya musu ranar tashi sati biyu masu zuwa, gida Nigeria za su fara sauka su huta na wata guda, kafin su tattara zuwa Brussels. Suhaanah, ba ta san me ake yi ba, ta ga dai Mamma nata parking kayayyaki, tana zirga-zirgar shiga kasuwanni. Siyayya ta ke kamar me a Baaba Sheriff. su Ishma kullum cikin damuwa suke. Ba ta da sha’awar wai ta tambaya ta ji me ake yi, jikinta ya ba ta ko mene ne ba mai dadi ba ne a gare su. Sai ita ma ta dauki damuwar ta sanya wa ranta. Ana igobe za su tashi zuwa gida Najeriya Mammah ta zaunar da ita tana yi mata bayani. “Adda ta kina ta ganin abubuwa ba za ki tambaye ni ba? Ni wannan shirun naki yana damuna wallahi, a ce mutum ya yini zungur babu umh bare umh-umh sai karatu? Ko Mungo Park in yayi karatu ya gaji yana ajiyewa ya shiga cikin ‘yan uwansa a yi mu’amala mai dadi da shi, in ya ga abin da bai sani ba ya tambaya. Addah ki dinga sakin jiki da al’umma don Allah, watarana babu ni, na mutu, in kin ki yin sabo da kowa sai ni ranar da babu ni yaya zaki yi? In kin ga abin da ya kamata ki nemi sani akai, ki dinga tambaya”. Turbune fuska tayi kamar zata yi kuka “don Allah Mommah ki daina zancen mutuwa. Insha Allahu tare zamu mutu. Ban ga abin da zan tambayan ba ne, na fahimci kamar za mu yi tafiya ne, na ji kina gaya wa Anty Safiyyah ranar litinin (gobe) za mu tafi. Na ji kina zancen tsaraba da su Addah, inda za mu je ne ban sani ba”. Murmushi Mammah ta yi, ta janyo ta gefenta na dama, “Na bari Addah, ni na so na mutu yanzu ban goya ‘ya’yanki ba? Ban shirya miki kasaitaccen dakin aure ba? Gida za mu je, kasar haihuwarmu, inda tunda aka haife ki ba ki taba zuwa ba sai dai su su zo”. Suhaana ta ce, “Nigeria?” Mammah ta ce, “Ashe kin san sunan kasarmu?” “Na sani mana, ba inda Yayan su lshma yake karatu ba? Garinsu Adda Hafsatu da Baffa Atiku”. Dariya Mammah ta yi tana bubbuga bayanta, “Ke ba garinku ba ne? Wato na su Addah ne da Yayan Isma’el?” “Jeddah ne garinmu Mommah, da Makkah da Madinah don Allah mu ci gaba da zamanmu......” Sai ta sa kuka. Kuka sosai Hafsat ke yi Mammah da Baba Azumi suna lallashinta, Mammah na fadin, “Mutum ya taba gudun asalinsa Addata? Ba fa kasarmu ba ce Saudiyyah, aiki ne ya kawo Daddy, Najeriya ma na da dadi...” “Mommah za mu dawo? Ina son makarantarmu bana son barinta”. “A ko’ina akwai makarantu, makaranta sai wacce ki ka zaba zan kai ki a duniya Suhaana, daga Najeriya gaba za mu kara zuwa nahiyar kasashen Turai”. Da sauri Suhaana ta katse Mammanta, “Wadanda ba sa sallah?” Mammah ta ce, “Ba duka ne ba sa sallah ba, kowacce kasar duniya akwai musulmi akwai wadanda ba musulmi ba”. Suhaana ta share hawaye da tafukanta, haka suka yi ta bata baki da lallashi daidai lokacin da Daddy ya leko dakin zai ma Mammah magana, ya tsinkayi kadan daga zantuttukansu. Tsaki ya yi ya dubi Mammah da ta kwantar da kan Hafsat a cinyoyinta, ya soma sakin sababi irin wanda ya saba muddin zai ga Hafsat a wuri na babu gaira babu dalili. “Yanzu wannan gansamemiyar yarinyar ki ke dorawa a kan cinya? Gata mugun abu, to kar ki je garin da ba’a sallar ki tafi inda ki ka fito mana? Mtsw! Ni ina ki ka ajiye min takardun da na ba ki dazu da safe? Shi ne abin da ya kawo ni”. Tuni Hafsat ta hau mayarkyata irin wanda ta ke yi in Daddy na mata sababinsa wanda ta fahimci ita kadai yake yi wa a cikin gidan nan, hatta Baba Azumi gaisuwar mutunci ke shiga tsakaninsa da ita. Mammah ta bata rai sosai, ba ta ce masa ko kanzil ba, ta mike ta dauko takardun a (bedside drawer) dinta ta ba shi ya juya ya fita yana ci gaba da fadansa. Ba ya son sangartar da ake yi wa yarinyar nan a gidan nan, shi ya sa ta raina shi, ko gaishe shi ba ta yi in ta ganshi kamar ta ga mala’ikan daukar ranta. A karshe suna jin sa yana fadin. “Maryam kin kusa kawo ni bango. Ai gida Nigeria za mu je sai kin san yadda za ki yi kin nemo dangin mahaifiyarta, ba zan sake kwasarta zuwa wata kasa ba, balle watarana ta ce ni ne ubanta, rayuwar Turai ba irin ta Saudi-Arabia ba ce”. Da haka ya wuce. Hafsat ta shige bandakin Mammah da gudu ta rufo kofar ta murda mukulli, ta durkushe a jikin kofar tana wani irin kuka sosai. **** [01/08 3:33 PM] Sumayya Takori: SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* AUREN KWANGILA 1 Page 5 HAFSAT-SUHAANAH Wato tunda ta taso, ta soma wayon fahimtar abubuwa yadda suke a zahirinsu, ta fahimci Daddy ba Babanta ba ne, ba tare da kowa ya zaunar da ita ya gaya mata ba. Ganin irin yadda yake mu’amalantarta, ba ta da soyayya ko kankani a kwayar idanunsa, idan ta hada da yadda yake mu’amalantar Ishma (Isma’el), Haleem da Usman da wannan babban nasu mai zuwa duk bayan watanni uku da ya fi kowa rashin sakin fuska a gidan in ya zo, wanda su Usman ke kira Yaya Azeez ko Yaya Abdul’azeez, duk wanda ya zo bakinsu shi suke kiransa da shi. Abin da har gobe ba ta sani ba, ba kuma ta ke son ta sanin shi ne; Mommah mahaifiyarta ce da ta dauke ta cikin mahaifarta, ko Baba Azumi ce da wannan alhakin? Babu wanda ya taba tararta gaba da gaba ya gaya mata amsoshin wadannan tambayoyin da suka dade da suna yi mata katutu a zuciya da kwakwalwa. Duk wani gibi na uwa da uba da dangi Mommah ta cike mata shi, ‘yan uwanta sun cike mata da kauna sahihiya, Daddy ne kawai matsalarta a duniya, ba ta san me ta yi masa ko ta ke yi masa wanda ya haifar da kiyayyarta a zuciyarsa ba. Kiri-kiri yake nuna bambanci tsakaninta da ‘yan uwanta, wanda hakan ya fassara mata ita din ba ‘yarsa ba ce, ba za ka taba tsanar ko kyarar abin da ka haifa ba. Ba ta taba sanya Yaya Azeez cikin jerin mutanen da ke cikin rayuwarta ba. Ta dauke shi wani ‘total stranger’ (bako ba dan gidan ba), ta hada su shi da al’amarinsa ta aza a muhalli na daban, muhalli iri daya shi da Daddy; muhallin wasu mutane biyu da ke ji mata ciwo a zuciya. Ba ta taba yin wani abu don ta kyautata wa Daddy ya nuna ‘appreciation’ (jin dadin) hakan ba, komi ta yi laifi ne, abin fada ne. In ba ta gaishe shi ba don ta gane ba ya son kowacce mu’amala ta hada su, ya sauke wa Mammah kwandon bala’in ta janyo ta raina shi. In ta gaishe shi ya ce ba ya son hayaniya alhalin ba haka ta ga yana mu’amala da sauran mutane ba. Ta kan tambayi kanta. “Ni din to su waye suka haife ni? Idan Mammah ce ko Baba Azumi ina Babana? Ko da gaske akwai wanda ke da uwa ba tare da uba ba? Shin uwa ita kadai kan samar da dan adam cikin mahaifarta? Ko ni din daga sama na fado dakin Mommah?” Tambayoyi ne da amonsu ba ya rabo da yi mata amsa-kuwwa cikin kunnuwanta kullum ranar Allah. Ta ci gaba da kuka mai sosa zuciya tunda ba ta da wanda zai amsa mata tambayoyin da suka addabe tan, balle ta ji sanyi-sanyi. Baba Azumi ce ke dukan kofar sosai, tana fadin, “Hafsatu bude, bude kin ji Hafsatuna, kin ga Mammanki ma kuka ta ke yi, idan ba ki daina ba kin bude kofar kin fito ba itama bazata daina ba.....” . Bude kofar ta yi da sauri ta karasa da gudu ta fada jikin Mammah. Ta rungume ta tsam tana fadin, “Addata ki yi hakuri da Babanki kin ji? Ki yi masa uzuri, uzuri sau saba’in Allah ya ce ki yi masa kafin ki tuhume shi da rashin adalci a gare ki”. “Na yi masa Mommah, kullum kuma cikin yi masa nake, cewa da yake ba shi ne Babana ba Mommah shi ne abin da ke sa ni kuka. Idan ba shi ba ne wane ne? Mommah ko ke kadai ki ka haife ni? Ko Baba Azumi ce?” Mammah ta kara matse yatsun hannunta, “Na gaya miki ni ce uwarki. Ni ce ubanki, nice komai naki, ki daina sanya tambaye-tambayen nan marasa ma’ana a zuciyarki balle su dame ki. Ni na gaya miki watarana Daddy zai so ki, yanzu akwai dalilin da ya sanya yake yawan yi miki fada in kin shekara goma sha takwas na yi alkawarin zan gaya miki komai”. Da haka suka ci gaba da harhada kayansu. Karfe goma na daren washegari jirgin KLM ya kwaso Ambasada da iyalinsa daga birnin Jeddah bayan sun je sun yi dawafin bankwana a dakin Allah mai alfarma. Bai dire su ko’ina ba sai garinsu na haihuwa (Kano) inda suka tadda kafatanin zuri’arsu manya da yara a filin jirgin saman Malam Aminu kano sun zo tarensu, aka rurrungume juna sannan suka rankaya (main house) dinsu da ke Unguwar Dakata. Gidan Malam Abdullahi Dakata, a yau komawa ya yi kamar gidan biki, bikin ma irin gagarumin nan, kwansu da kwarkwatarsu suna tare da mutanen Jeddah, ana ta hirar yaushe gamo na abin da ya shafi junansu. Sun samu Inna Ramatu, wato mahaifiyar Ambasada babu lafiya sosai, ta kuma ki yarda a kai ta asibiti sai Uncle Idris ke duba ta a gida. Ba yadda Dr. Hamza bai yi ba Inna ta yarda ya kai ta asibiti, ta ki amincewa, ta ce, “Kun raina kulawar da Idrisu ke ba ni ne? Asibitin me alhalin muna da malamin asibitin a gida?” Cikin tausasawa ya ce, “Inna duk da haka gara a je asibiti, su ke da kayan aiki, Idris taimakon farko (first aid) yake yi muku don Allah ki amince mu je”. Lallashin duniya Dr. Hamza ya yi, amma baiwar Allahn nan ta ki. Allahu akbar! Kwanansu uku a Kano Allah ya karbi ran Inna Ramatu, ranar litinin a kan sallayarta, bayan ta idar da sallar isha’i tana lazumi. Adda ce ta shigo mata da abincin darenta, sai ta yi tsammanin bacci ne ya dauke ta a kan sallayar. Ta ajiye abincin ta matsa ta dauko filo don ta gyara mata kwanciya, nan ta tarar Inna Allah ya amshi abinSa. Salatin Adda cikin fadin, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Shi ya janyo hankalin jama’ar gidan da ke tsakar gida an shimfida manyan tabarmi suna jam’in sallar isha, wadda Daddy ke limanta. Fadin irin gigicewar da Ambasada hamza ya yi na rashin nagartacciyar mahaifiyarsa abin ba a cewa komai, sai dai a yi gumm! Zuciyar maza ta girgiza ta azabtu. Ba abin da yake so a duniya in ka cire Baffa da iyalinsa kamar tsohuwar nan tasa. Inna Ramatu uwa ce abin koyi, abar alfahari a gare shi. Ba ta haifi kowa ba sai shi, don haka ba karamin so ta ke yi masa ba. Kamar wani abokinta haka ta dauke shi. Duk damuwar da yake ciki da ya yi tozali da Innar nan ta yi masa murmushin nan nata, zai neme ta ya rasa. Bare in ya zauna a gabanta tana yi masa nasihohi a kan rayuwa da yadda ake maganin kalubalenta don samun nasara cikin rayuwa. Inna kan ce, “Hamza kada ka bari duniya da daukakar da Allah ya ba ka su sa ka wulakanta dan Adam, ko ya ya yake wallahi watarana zai yi maka rana. Ka ji tsoron Allah, ka rike sallah, ka taimaki na kasa da kai. Ka rike addininka su ne sirrin zama lafiya da cimma nasarar komai a rayuwa”. Gaskiya tun bayan rasuwar kakansa Malam Abdullahi Dakata ba a kara yi masa mutuwa ba. Don haka mutuwar Inna ta doke shi yadda ba’a zato. Da safe aka yi janazarta, lokacin da suka kama gawar ta shi da mahaifinsa suka sa a kabari, sai ya yanke jiki ya fadi. Haka Baffa Atiku ya taro shi, aka kwashe shi aka sa a mota aka yi asibiti da shi. Ya sha dirif ba adadi, kwanansa uku sannan ya dawo hayyacinsa. Dakin asibitin cika yake makil da ‘yan uwansa, ‘ya’ya da iyaye, duk wanda ya zo wucewa sai ya tabbatar wannan majinyacin dan dangi ne. Ko da ya dawo gida ranar sadakar uku ya zauna wajen karbar gaisuwa ba shi da kuzari, tsoron duniya yake da abin da ke cikinta. Ya yarda ba komi ba ce komin daukakar da Allah ya yi maka, rana daya za ka fadi, kuma ba ka san ranar ba, ka je ka girbi abin da ka shuka. Ya kan tuno ‘memories’ na rayuwarsa da mahaifiyarsa da yadda ta yi ta hidima da shi tun yana yaro, ya samu gatan uwa har girmansa. Wani bai samu ko nononta ya sha ba, hakika gatan UWA ya fi komai dadi ga dan adam a duniya. Gabansa ya yi wata mummunar faduwa da wata fuska ta zo ta gilma ta gabansa. A sanda yake zaune yana wannan tunanin, ba wata ba ce yarinyar gidansa ce Suhaana (Hafsat) ta wuce ta gabansa ba tare da ta kula da shi ba, kasancewar ba shi kadai ba ne zaune a kan katuwar tabarmar da aka shimfida ba a kofar gidansu, shi da abokansa ne biyu da suka zo masa ta’aziyya daga Abuja, Ambassadan Najeriya a kasar Senegal Dr. Yahya Garba, da Ministan huldar kasuwanci da kamfanoni na kasa baki daya (minister of commerce and industry) John Akure, a gefe kawunsa Minister Abdulkarim Dakata ne da nashi jama’an suna ta karbar gaisuwa. Ido ya bi ta da shi har ta tsaya a inda aka aike ta, wata (kiosk) ce nan kusa da su mai fentin gidan wayar MTN (yellow), da alama shagon waya ne. Ta mika kudi aka ba ta katin waya na dubu da dari biyar ta juyo. Fuskar uwarta ta gilma masa saboda yadda suke bala’in kama, hatta tafiyarsu iri daya ce don yakan ganta a kai-akai in tana hidima da yaransa a falo ko tana shirya abinci a (dining) kafin Allah ya dau ranta. Ya hanga ya duba a fadin wajen nan duka ‘yan uwansa ne na jini, da aminan arziki. Ita wannan yarinyar ba ta da ko mutum daya da za ta nuna ta ce nata ne, ba ta da wanda za ta yi tinkaho da shi a duniya da sunan ‘IDENTITY’ dinta. Ya hana a bata nono, ga shi rai da alkawari, Allah ya raya ta har ta soma balaga. Kalmar ‘sannu’ wannan ba ta taba hada shi da ita ba alhalin ta rayu a gidansa cikin iyalinsa tsayin shekaru goma sha uku. Anya abin da yake yi a kan marainiyar Allahn nan Allah ba zai tambaye shi ba? A kan wata akida ta kafurai wadanda suka samar da ilimin BOKO? Mahaifinsa ya ba shi ilimin addini yadda ya kamata, mahaifiyarsa ta hore shi da zama mutum mai tausayi, da jin kan na kasa da shi ba tare da tunanin abin da gobe za ta haifar ba, ko abin da za a saka masa da shi ba. Ya tuno ayoyi na alqur’ani mai tsarki da suka yi umarni da babbar murya da a kyautata wa maraya. ‘Wa ammal yatima falaa taqhar’ (DHUHA; 9). ‘Wa yas’alunaka anil yatamaa, qul islahul lahum khair, fa’in tukhaalidu hum fa ikhwanikum.... Wallahu ya’alamul mufsidu minal muslih, walau sha’Allahu la’a’anatakum, innallaha azizun hakim (Baqrah; 220) ‘Wa’abudullah walaa tushriku bihi shai’an wa bil walidaini ihsanan, wa bi zilqurbaa wal yataamaa wal masaakin...” Har zuwa karshen ayar (Nisa’i; 36). A karshen ayar Ubangiji subhanahu wata’ala ya kara da cewa. “Innallaha laa ya hibbu kulla mukhtalin fakhoor”. Fassara; - “Amma maraya kada ku cutar dashi/cinye gadonsa” - Suna tambayar ka (Yaa Muhammadu) akan lamarin maraya, ka fada musu cewa abin da Allah yake umarni shine kyautata musu, idan kunyi cudanya dasu to ‘yan uwanku ne. Allah ya san mai gyarawa daga mai batawa a cikinku,da Allah ya so da ya shiryar da ku. Hakika Allah mai iko ne mai hikima cikin lamuransa. - Ku bautawa allah shi kadai kada kuyi shirka da shi, ku kyautatawa iyayenku da ma’abota kusancin zumunci, da marayu da miskinai da makotan ku na gidaje da matafiyi da kwarkwarorinku/bayinku. Hakika Allah baya kaunar wanda yake marowaci mai fariya. Tunaninsa bai gushe ba ya ci gaba da tuna masa yadda ya wanzu yana kuntatawa maidakinsa ‘yar uwarsa, abar kaunarsa, matar rufin asirinsa don kawai ta yi jihadin yin ceton rai don Allah da neman sakamako a wurin Ubangiji. Ya muzguna musu tsayin shekaru goma sha uku ba tare da sun yi masa laifin komai ba, ba tare da zaman yarinyar tare da su ya rage shi da komai ba. Zai iya rantsewa tun daga ranar da yarinyar nan ta shigo gidansa yake ganin albarka da ci gaba iri-iri a rayuwarsa. Maryam ko uwarta ba ta taba gaya wa cuzgunawar da yake yi mata a kan yarinyar nan ba, balle tashi uwar har Allah ya dauki ranta... Hawaye masu dumi suka biyo idanun Ambasada Hamza, bai damu da ya kai hannu ya share ba, haka ya barsu suna ta malala a kan kundukukinsa. Abokan nasa suka ci gaba da ba shi baki, ba su san kuka biyu yake yi ba, kukan rashin mahaifiya da kukan nadama. Rayuwa kenan. Hafsatu ba ta san bidirin da Daddy ke yi da zuciya da kwakwalwarsa ba, ta sayo wa Mammah katin wayar da ta aike ta ta kamo hanyar dawowa, kanta na sunkuye ta ke tafiya don ba za ta iya daga ido ta dubi taron mazan nan da ke zazzaune a kofar gida ba. Kamar an ce da ita ‘dago kanki’ gab da za ta shiga gida ta dan daga kai saboda jikinta ya ba ta ana kallonta sosai, ai kuwa karaf sai idanunta cikin na Daddy. Ta ganshi yana shatatar hawaye kamar karamin yaro suka yi ido hudu da shi. Tuni ta gigice ta ci uban tuntube da wani dutse dake gefe ta fadi kiff! A kasa. Don ta tsammaci a cikin taron mutanen nan balbale ta zai yi da bala’in da ya saba. Ji ta yi an sa hannu biyu an dago ta. Ta ji zafin faduwar sosai da sosai, gwiwoyinta duk sun kukkuje lebenta ya fashe jini ya wanke bakin. Ta cira ido a sannu cikin dauriya ta dubi wanda ya daga ta; Hamza Atiku Dakata ne. “Wace irin tafiya ki ke yi haka Adda? Ba kya kallon abin da ke gabanki? Adda in don ni ki ka rude haka don Allah ki yi hakuri, kar ki sake firgita in kin gan ni, ba dodo ba ne ni, BABANKI ne”. Hafsat-Suhaana, ba abinda ta iya yi banda ta runtse idanunta, mafarki ne kawai ire-iren mafarkan da ta saba yi a kan Daddyn, saboda yadda ta sa damuwa da lamarinsa a ranta. Ta ki bude idon don ba ta so ta farka daga wannan daddadan mafarki. Daddy ya sa hannu ya dauko hankicinsa daga aljihu fari tas ya shiga goge jinin da ke zuba daga bakinta. Tuni mutane wajen biyar suka taso suka isko su cikin girmamawa wani likita abokin Uncle Idris ya kama hannunta ya rusuna ya ce da Daddy zai tafi da ita asibiti, ya koma ya zauna ba komai. Dr. Isah ya kama hannunta tana tafiya da kyar saboda azabar da gwiwoyinta ke mata. A gaban motarsa ya sanya ta, ya shiga motar ya ja zuwa wani (private hospital) da yake aiki, ya gyara mata ciwuwwukan ya sa magani ya nade da plasta. Ya ba ta wasu ‘yan magungunan a leda ya dawo da ita gida. Tuni labari ya isa ga Mammah daga bakin dan Anty Mariya, wai Adda ta fadi a waje, Daddy ya sa a tafi da ita asibiti. Sai ta ji maganar banbarakwai, ina ruwan Daddy da Suhaana har da zai ce a kai ta wani waje? Kar dai fa ya aika da ita gidan marayun da yake ikirari! Ai sai ta zabura ta mike da gudunta zaninta na kwancewa tayi sa’ar riko shi kafin ya kai kasa, ko mayafi babu a jikinta ta yi hanyar soro. Luba ce ta dau mayafi ta bi ta da shi ita ma da gudun. Uban karo suka yi ita da Daddy da ke kokarin shigowa, saura kadan ita ma ta fadi. Jikinta na bari, muryarta na karkarwa cikin son fashewa da kuka ta kama shi tana girgizawa. “Ina ka tura a kai ta? Ina ‘yata, ina marainiya ta, ina ‘yar amanata?” Gani da ta yi yana hawaye ya sa jikinta ya yi matukar sanyi. Ta fada jikinsa ta fashe da kuka. “Don Allah kada ka raba ni da Addata, na roke ka Daddy duk abin da ka ke so zan ci gaba da yi, in har za ka barmu mu rayu tare. In ka ce ma ba za ta bi mu ba na yarda mu zauna a nan, ka kara aure ka tafi da matar, wallahi na amince”. Girgiza kai yake yi, ya raba ta da jikin sa, ya ce, “Cool down Maryam, I have realized my shortcomings and I promised to become a changed person. Zan taya ki son ‘yarki da kula da ita har karshen rayuwarmu. Trust me!” Ya fada cikin sanyin murya yana share mata hawaye da tafukansa. “Maryam faduwa ta yi, na ce a kai ta asibiti. Na rantse miki da Allah bayan wannan babu wani abu”. Maryam Dakata ta bi shi da kallo, irin kallon kurillar nan na son karanto zuciyar mutum. Kamar Hafsat ita ma ta dauka mafarki ta ke yi. Ta sanshi, ta san halinshi ba ya fadar abin da ba haka yake a zuciyarsa ba, wani irin frank person ne shi, saboda ba ya shakkar kowa, ko ya fadi abu don ya faranta maka bayan ba shi ne a zuciyarsa ba. Kwayar idanunsa masu haske da sheki sun gaya mata komai, saboda ba yau ta sanshi ba. Hakika ta yi hakuri da shi shekaru rututu, yau ga ribar hakurinta ta girba. Da ma an ce mahakurci mawadaci, kuma komai ya yi farko zai yi karshe da ikon Allah. Sosai ta rungume mijinta tana kukan da a yanzu ya san na farin ciki ne. Luba da ta biyo ta da mayafi ta dade a soron farko rike da mayafin tana jiranta. Da ta ji kamar tattaunawar sirri suke sai ba ta labe ba ta koma cikin gida, wannan ba tarbiyyar da Adda Hafsatu ta yi musu ba ce, (wato labe). Ibrahima autan Adda ne ya taho cikin gidan don kiran Daddy ya gaya masa ya yi wasu manyan bakin daga lagos, sai ya tadda su a haka a soro. Da sauri ya juya zai koma, suka saki juna Daddy ya kira shi. Ya dawo kansa a sunkuye ya fadi sakonsa, Mammah ta koma cikin gida, shi kuma ya fita. Hafsat ta shigo tana dingishi ta sha plasta a baki da kafafu. Tun kafin ta zauna Mammah ta taso ta taro ta tana tambayarta, “Garin ya ya ki ka fadi?” Kowa sai sannu yake yi mata, bakin ya haye ya yi suntum. Halim ya dube ta, sai ya kyalkyace da dariya. Ta harare shi da kumburarrun idanunta, ya yunkura zai fice yana ta dariya yana yi mata sannu, sannan yace “Ina ruwan alkubus! Ya hau ya yi fam!” Baba Azumi ta kai masa duka ya fice da gudu. Ta ce, “Mommah tuntube na yi da dutse. Ga katin wayar ga canjinki”. Ta mika mata abin da ta kudundune a hannunta na dama. Duk azabar da ta sha bai sa ta zubar dasu ba. Tsabar girmama komai na Maman ta. Mammah ta karba tana fadin, “Ni wannan katin waya da ba a je siyansa ba!”. Wata zuciyar ta ce da ita. “Gara da aka je siyansa, watakila shi ne silar dawowar Daddy kan kyakkyawar turba”. Da aka yi sadakar bakwai Mammah ta sa direba ya dauki Baba Azumi suka kama hanyar Sokoto, domin ta ga ‘ya’ya da danginta kafin lokacin wucewarsu Brussels (Belgium). ***** Haka suka ci gaba da rayuwarsu cikin ‘yan uwa cike da alhinin rashin Inna Ramatu. Sati biyu a tsakani suka wuce Abuja. Abdul’azeez bai san da rasuwar Inna Ramatu ba, ya samu gurbin da ya nema a jami’ar Ibadan, sun ba shi kwas din da yake matukar so, wato LAW, inda zai karanci LLB tsayin shekaru biyar. Kafin isorwar mutanen Jeddah ya fara jarrabawar zangonsa na farko, Daddy na sane da hakan shi ya sa ya kyale shi kawai don kada ya raba masa hankali. Inna ta riga ta tafi, babu wanda ya isa ya dawo da ita. Azumi ta samu ‘ya’yanta da jikokinta lafiya a gida Sokkoto, ta sauke musu sha tara ta arzikin da ta tara musu. Maimaikon su ga tsufa mai yawa tare da ita, sai suka ganta ras! Kamar an kwashe mata shekaru goma an zubar, da ma kuma aike ba ya yankewa tsakaninta da su, duk shekara in an zo aikin hajji daga Sokoto. Sun riga sun san a gidan Ambasada ta ke cikin kwanciyar hankali. Ba ta dawo Abuja ba, sai a satin da za su tashi zuwa Brussels, dukkan shirye-shiryen tafiyar tasu ya kammala. Hankalin Mammah da na ‘yarta ya kwanta sun zama cikin nutsuwa da kwanciyar hankali domin da gaske Daddy ya canza a kan Addar Mammah ya cure ta cikin su Isma’el, Usman da Halim. Babu nuna bambanci, babu duk wannan hayagagar. Sau da yawa sai ya yi mata abu su bai yi musu ba. Ya bude mata (account) a Brussels kamar yadda ya bude wa gabadaya ‘ya’yansa duk wata yana sanya musu kudi daga albashinsa saboda lalurar rayuwa mai zuwar ma dan Adam watarana ba tare da ya shirya ba. Daddy na shiga office dinsa da sati daya ya sanya ‘ya’yansa duka a makaranta, bayan ya karbo musu (transfer) daga makarantunsu na Jeddah. Amma kasancewar ba su iya Dutch, Wallonian ko German languages ba daga Larabci sai Turanci, dole ya sanya su a wata makarantar daban inda ake koyar da wadannan harsunan, don da su suke amfani (as formal language) a kasar bakidaya. ‘ST. John Berchmans Collage’ ita ce makarantar su Hafsat Dakata a Brussels. A nan din ma an bai wa Ambassador gida a jerin gidajen jakadodinsu, mota da direbobi kamar a Jeddah, direbobi su kai shi office, su kai ‘ya’yanshi makaranta su dauko su. An sanya Hafsat aji daya na sakandire, Halim aji hudu, Usman da Isma’eel an sanya su cikin masu zana jarrabawar shiga jami’a na shekarar gabadayansu dama tsiran aji daya ne tsakaninsu, Ismael ya kammala sakandirensa a Jeddah har ya yi jarrabawar shiga jami’a. Amma da suka zo nan Brussels tsarin jarrabawar nasu ba iri daya ba ne da na Saudiyyah, suka ce dole ya jira zuwa shekara mai zuwa ya maimaita irin tasu don haka zasu zana lokaci daya da Usman kafinnan shi Usman ya kammala. Babban burinsa ya samu gurbi a jami’ar ‘Harvard’, jami’ar nan mai tsohon tarihi a Amurka, don haka ya dage da karatu baya wasa kafin lokacin jarabawar ya zo tareda malami Belgian da Daddy ya daukar masa, Usman ma in yana gida yana zama a yi dashi, ba ya wasa ko kadan don ganin cikar mafarkin sa na zuwa Harvard. Yau da gobe aka ce ba ta bar komai ba. Hafsat na girma tana kwankwadar ilimi mai tsada, kwakwalwarta na kara budewa da ilimin zamani. Burinta na zurfafa shi na kara karuwa a zuciyarta. Ta samu kanta da wani mayataccen ‘determination’ na son yin ilimi mai zurfi domin ta zama wani abu a rayuwa ta dogara da kanta. Tana ganin yadda Daddy ke wahala da su, shekaru na kara tura musu shi da Mammah, sun karar da kuruciyarsu bakidaya wajen hidimarsu, cinsu, shansu, sutturarsu da iliminsu. Tana so ta zama uwa kamar Mammah, ta yi wa ‘ya’yanta abin da Mammah ke musu ko ta kwatanta. Tana sha’awar Daddy da zurfin iliminsa wanda ta tabbata shi ne silar matakin da yake kai a yau. Don haka hafsat ta kudiri aniyar yin ilimi har sai ta kure shi in ana kurewa, za ta iya yin komai a kan a barta ta yi karatun zamani mai zurfi. Tun a Jeddah sun yi haddar Alqur’ani mai girma, sun yi ilimin addini sosai, shi ma tana so ta fadada shi har fiye da ilimin bokon in ta samu dama. Mammah da kanta ta yi tunanin daukar musu shehin malami da zai ci gaba da ba su karatun addinin musulunci a gida, a ranakun karshen mako. Ta gaya wa Daddy, ya samo wani Malami Basudane ya ci gaba da ba su karatun littattafan addini. A gefe daya suna tisa haddar su. Yadda suke fahimtar boko haka suke fahimtar addinin musulunci fiye dashi, sabida foundation dinsa da suka ginu akai tun suna kankana. A tsayin shekarun da suka yi a Belgium sun je gida sau uku, su Baffa Atiku, Adda da sauran dangi sun zo Brussels sau biyu, Baffansa Abdulkarim duk sanda ya samu sarari yana zuwa da iyalinsa su yi hutu. Abdul’azeez bai zo ko sau daya ba. Ba shi da sha’awar Belgium, wani irin mutum ne murdadde mai ra’ayi da akida, babu abin da ya isa ya sauya shi daga kan perceptions dinsa (beliefs), burinsa ya zama babban attorney wanda kasarshi za ta yi alfahari da shi. Yana so ya zama lawyer na farko da zai kawo sauyi cikin tsarin shari’ar da kasarmu ke tafiya a kai ta son zuciya da danne mara karfi. Yana so ya kauda cin hanci da rashawa da suka yi wa kotunan kasarsmu katutu. A kauda karya a tsayar da gaskiya, ba shi da burin zama lauya mai zaman kansa; lauyan gwamnati yake son zama. Ta haka ne zai samu damar taimakon al’umma marasa karfin kwatar hakkinsu. Hakan ba zai kasance ba sai ya kai kololuwa a karatunsa na lauya, sannan sai in ya zabi ‘CIVIL LAW’ ya zama gawurtacce a cikinta. In haka ne kuwa ashe yawon hutawa a kasashen Turai ba nashi ba ne. Lokacin hutunshi shi ya kamata ya zame masa lokacin jajircewa don cimma burin rayuwarsa. Daddy ya dade da kama masa dan kyakkyawan muhalli daura da makaranta a garin na Ibadan tun lokacin da ya ce ba zai samu dinga zuwar musu hutu ba saboda yanayin karatunsa. A waya suke jin lafiyarsa, ita din ma sai karshen mako yake kunnata. Minister Abdulkarim da ‘ya’yansa su Farhan sa’o’insa kan yi tattaki lokaci zuwa lokaci su ziyarce shi har Ibadan, idan ka ganshi ba za ka ce dan Ambassador ba ne, sabida irin rayuwar (typical Nigerian) da yake ciki, gwagwarmayar neman ilimi yake yi yadda sauran masu rangwamen gata ke yi a jami’o’inmu na kudu dana arewa. Ba shi da wanda za a kira abokinsa na jiki sai ko abokin karatu. Ba ya tambayar Babansa kudi shi da kansa yake sanya masa duk wata. A ganin Abdul’azeez Hamzah Attikou, jin dadi da rayuwar jin dadi, za su biyo baya ne sa’ilin da dan Adam ya samu cikar burinsa. Amma gwamutsa seeking goal attainment (neman cimma buri) da rayuwar hutu da jin dadi irin ta gidansu is a barrier to goal achievement (shinge ne ga cikar buri). Saudiyyah ma da ya yarda yake zuwa sabida ita dole ce ga kowanne musulmi, kuma yana koyon karatun Alqur’ani da sauran karatun addini, yana Ibadah a Makkah da Madinah. [01/08 3:33 PM] Sumayya Takori: SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137880 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* AUREN KWNGILA 1 Page 6 **** A wannan shekarar da ake ciki ya fito da (LLB) mai daraja ta farko. Duk wani masoyin Dr. Hamza ya taya shi murnar wannan hazikanci na Abdul’azeez, gabadayansu sun zo gida don yin bikin sallah karama. Sun yi sati daya a Kano suna cin bikin sallah su Hafsat na zuwa cikin gari kallon hawan sarkin Kano (Durbar) kullum ita da su Haleem da ‘ya’yan su Furerah, Hafsat abin ya burge ta saboda ba ta taba gani ba sai wannan karon. Ta shige cikin sa’anninta ta saki jiki yadda Mammah ke so. In tana gwara hausarta su Halima ‘yar Anty Mariya da su Saimasu yi ta cin dariya. Wani zubin ma sai Haleem ya maimaita musu abin da ta fada suke ganewa, yaren Dutch (Flemish) ya mamaye bakinta ko turanci ba sosai ta iya ba, larabcin ma ta dade da manta yadda ake yi sai ‘yan kananan kalmomi saboda rashin abokinyi. Mammah ta bula mata hanci gefen dama da ‘yar barima ta danyen ‘gold’ wadda ba karamin kara mata kyau ya yi ba. Har suka koma Abuja Abdul’azeez bai zo Kano ba yana Ibadan, sati biyu dama yaran za su yi dan hutun nasu ba mai yawa ba ne. Za su koma tare da Baba Azumi su yaran saboda makaranta. Daddy da Mammah za su tsaya ‘convocation’ din Abdul’azeez a Ibadan wanda za a yi sati na sama. Su Hafsat suka tafi cike da kewar iyayen nasu. Hajiya Maryam ta daga ido tana kallon babban dan nata, wanda ta kwashe lokaci mai tsawo ba ta sanya shi a idonta ba. Yana cikin kayansa na barin jami’a kamar sauran dalibai ‘graduates’ ‘yan uwansa, a cikin jami’ar Ibadan-Nigeria. Ya zama babban matashi fiye da tunaninta. Wasu irin ilhamomi sun bayyana a tare da shi da ba duk maza Allah ya halitta da su ba. Ga wani siririn saje da ya kwanta gefe da gefen fuskarsa. Sauran ‘ya’yanta duk sun fi shi haske, amma kalar fatarsa ta fi ta kowa ban sha’awa. Ya fi kama da mutanen Qatar din Misra ko ko larabawan Habasha da aka fi sani da Ethiopians. A yau ne ya cika shekara ashirin da biyar idan har lissafin da ta ke yi daidai ne. Ga tabon sujoud nan ya bayyana a saman goshinsa. Alamu ne na ba ya wasa da sallolinsa biyar kamar yadda ta hore su bakidaya. Wani matsanancin farin ciki ya ziyarci zuciyarta. Ta daga hannayenta biyu sama tana kara rokon Ubangijin sammai da kassai; “Rabbi ja’alni muqimassalata wa min zurriyyaty, Rabbana wataqabbal du’a!” Fassara; “Ya Ubangiji ka sanya na zamo mai tsaida sallah ni da zurriyata, Ubangiji ka amshi addu’ata”. Daga Ibadan Kano suka wuce, Baban su Sha’aban ya hada get-together-party a Dakata na taya yaran nasu murnar kammala digirin, Farhan da Sha’aban ma sun gama duka da sakamako mai kyawu, daga jami’ar Nsukka. Su-ya-su suka yi abinsu, babu wani bare a ciki. Daga ‘ya’yansu sai jikokinsu, sai iyayensu da Kakanninsu. Walimar ta kayatar. An yi vedio, an yi hotuna don tarihi. Daddy ya nemi jin ta bakin Azeez ko zai bi su Brussels kafin tafiyarsu Law school? Abdul’azeez ya ce, “Daddy, akwai wani course na shekara daya da zan je a kan kwamfuta a Kazaure (informatics) ina so na samu wadataccen ilimin na’ura mai kwakwalwa kafin zuwan lokacin tafiya ta hidimar kasa, in na gama NYSC zan taho, na yi maka alkawarin ranar da na zama cikakken lauya, wanda ya yi dukkan karatunsa a kasarsa ta haihuwa zan zauna tare da ku a duk inda ku ke”. Ambassador ya dan daga kafada alamar ba shi da matsala a kan hakan, “Do as you wish Abdul’azeez, ina girmama ra’ayinka, babu laifi a cikinsa, dukkaninku na ba ku ‘yancin gudanar da rayuwarku yadda ku ke so in har ba zaku karkace daga kan tarbiyyar da muke dora ku a kai ba. Ku ji tsoron Allah a duk inda kuke ku kasance masu tsaida sallah a duk inda kuka samu kanku. Itace tushen kasancewa cikin nutsuwa da kowacce nasarar rayuwa (sallah)!”. Bai bar Najeriya ba sai da ya gama masa komai na shiga institute din ya wuce Kazaure ya fara shiga aji, sannan suka taho Brussels shi da Mammah. **** Ba su dade da dawowa ba ciwon Hafsat ya tashi, wai sun je Beach kawarta Aalimah ta ce su shiga su yi wanka, ta ce a’a ita ba ta shiga ruwa mai sanyi, Mammah ta hana ta. Aalimah ta dauka tsoro ta ke ji shi ya sa ta ce hakan. Can ta iso inda take tana swimming ta ce, “Suhaana miko min float din can”. Ta kuwa juya don ta miko mata, kawai sai ta jata ta baya cikin ruwan ji ka ke “tsundum!” Ita dai Aalimah tana dariya tana karawa sai gani ta yi Suhaana ta sassankare idanunta na kakkafewa. Da sauri ta fito ta janyo ta waje, ta maida kayan jikinta, jikinta yana rawa ta zura da gudu neman taimako. Kwanansu biyu a asibiti kamin da a sallame su. Tun daga ranar Mamma ta raba ta da kawaye ta ce ko me ta ke so a aboki ta yi da ita, ba ta yarda wata alaka ta shiga tsakaninta da kowa ba bayan bangaren karatu. Isma’eel ya dade da samun gurbi a Jami’ar Harvard, shekarunsa uku kenan a Amurka, yana karantar (Sofware Engineering). Usman na babbar jami’ar Brussels, kai daya suke tafiya a karatun shi da Ishma. Halim na shekarar farko a wata jami’a a Sweden. Shi kansa Usman da ke cikin Brusseels suna dadewa ba su sanya shi a ido ba, ya tattara kayansa gaba daya ya yi kaura zuwa cikin hostel wai an fi karatu in mutum yana makaranta. (Ina ruwan ‘ya’yan Farfesa). Don haka gidan daga Mammah sai autarta, wadda ke shirin zana jarrabawar karshe a high school din ST. John Berchmans College’, fitacciyar sakandiren birnin Brussels. Sai ko Baba Azumi. Haka Hafsat ke rayuwarta cikin kwanciyar hankali da soyayyar iyayenta uku, Daddy, Mammah da Baba Azumi. Sune duniyarta data budi ido dasu, sune farin cikin ta. Bata san wata rayuwa ba a duniya bayan wacce suke ciki. Don haka ta taso cikin wata irin nutsuwa da nutsuwar zuciya. Bata san kowanne irin kalubale na rayuwa ba. A shekarar da ta kammala karatun sakandire a shekarar ne suka samu wani sauyin rayuwa mai taba zuciya. ***** AUREN KWANGILA! Sabuwar gwamnati ce ta hau, daga sabuwar jam’iyya mai farin jini NRC (Northern Region Congress) a kasar mu ta gado, Nigeria. Bayan an rantsar da ita ta shiga ofis, abu na farko da ta fara yi shi ne; sauke Ambassadodi na dukkan kasashen duniya tana dora sababbi masu jini a jika. Cikin Ambassadodin da aka sauke har da Ambassador Hamzah Atiku Dakata. ***** “To komai na duniya ai ba shi da tabbas ko? Haka ita kanta rayuwar, komai na cikinta fararre ne kuma kararre. Shekaruna goma sha takwas ina jakadanci, don yanzu an sauke ni bai kamata ku damu ba. Ai mun sha miya, don an bai wa matasan kasarmu kujerunmu ba abin damuwa ba ne, ku kwantar da hankalinku, ku maida hankali a kan karatunku, ku kawo min sakamakon da zan yi farin ciki irin na Yayanku, shi ne kawai abin da za ku yi min in ji dadi”. Daddy kenan, ke lallashin samarin ‘ya’yansa, wadanda hankalinsu ya tashi da wannan sabon al’amari da ya tunkaro su. Wayar safe daban, ta dare daban suke bugowa don jin halin da mahaifinsu ke ciki. Isma’el ya yi ajiyar zuciya cikin karyayyar murya yake magana. “Daddy ba barin Europe da za mu yi ba ne yake damuna ba, don kamar yadda bata dada Ya Azeez da kasa ba haka ni ma bata dada ni ba. Ina zaune ne don ta zama muhallin iyayena, amma nafi son zama a Nigeria. Ko yau ka ce in bar Harvard in taho mu taho gida tare zan barta in taho. Damuwa ta Daddy in ka koma gida me za ka yi? Shekarunka ba su kai a ce ka yi ritaya ba, me za ka yi Daddy ka ci gaba da daukar nauyinmu?” Murmushi Prof. Dr. Hamza ya yi, don yanzun mun cire masa lakanin Ambassador, jiya ba yau ba! Shi ya sa aka ce dan Adam taka a sannu, kada ka bari mulkin duniya ya rude ka, domin komai na duniya mai karewa ne. Mai tunani kadai ke yarda da wannan a lokacin da yake kan ganiyar mulki ko mukami ko kololuwar jin dadin rayuwa. “Classroom zan koma mana Isma’el? A karkade ‘duster’ a dauki alli (marker) a koma yadda ake a baya, (duniya rawar ‘yammata, wai na gaba ya koma baya.) President Na-Dabo ya dade da rasuwa (wanda Daddy yayiwa Parmanent Secretary kuma abokin mahaifinsa na kuruciya wanda ya bashi Ambassadorship). Classroom din shi ne tushen duk wani mataki da na taka a rayuwa ta, ya ya yau zan guje shi don na yi aikin jakadanci na lokaci mai tsawo? Ku kwantar da hankalinku, ku yi addu’a Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare mu bakidaya”. Da wadannan kalaman ya samu ya taushi dukkan ‘ya’yan nasa, ita kam Suhaana kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha don dadi. Allah ya gani ba son kasar Belgium din nan ta ke ba, tana zaune ne sabida iyayenta, in ta barsu ina zata? Har gobe bata manta Jeddah ba da memories din cikinta. Tafi son kasar Saudiyyah fiyeda kowacce kasa a duniya. Tana kuma son Nigeria. Tunda suke zuwa Nigeria ta ke matukar son garin Kano yana matukar burge ta saboda cikowar jama’arsa da hada-hadar kasuwancinsa, wuraren tarihi da hawan (Durbar) na duk shekara. Tana son Adda Hafsatu da Baffa Atiku, tana son girkin Addar mai miyar taushe da miyar kuka, kubewa da kalkashi wanda in ba zuwa suka yi Mammah ta yi guzurinsu ba ba sa samu. Da a ce za ta iya barin Mammah da ta roke ta in sun koma Najeriya a barta a Kano, ba ta son Abuja. Sau daya taje gidansu na Asokoro suka sauka suka kwana bakwai bata ji dadin garin ba ko kadan. To ba za ta iya barin Mammah ba ko na sati guda, sai dai in tare za su zauna Daddy ya sai musu gida ko su zauna a Dakata dakin marigayiya Inna, tunda babu kowa. “Ina ruwan Hafsatu?” In ji Baba Azumi a lokacin da ta ke gaya mata abin da ke ranta game da Kano da Abuja. Baba Azumi ta ce, “To shi kuma Daddy fa? A hannun wa ku ka barshi a Abuja in anyi yadda kike tunani din?” Hafsat ta ce, “Sai ya dinga zuwa mana weekend”. Baba Azumi ta ce, “Wa zai dinga ba shi abinci to? Sai dai in kin yarda ya kara auren wata matar bayan Mamanki”. Hafsat ta girgiza kai da karfi, “In haka ne gara in yarda mu zauna a Abuja tare”. Baba Azumi ta kyalkyale da dariya, ta ce, “Na lura Hansai kishi za ki yi”. Hafsat ta ce, “Mene ne kishi?” “Dadina da ke Hausa ba ta ishe ki ba, kishi shi ne ka ji ba ka son hada abin da ka ke so da wani, ku amfana dashi tare, kin gane?” “Na gane, to dama wa zai so ya yi sharing abinda yake so? Ai abin da ka ke so ba ka son shi da kishiya”. Mammah na kicin tana jinsu tana murmushi. Baba Azumi ta dafe haba, “Ke nan ba za ki auri mai mata ba ko ke a karo miki Hafsatu? Ni kin ga kishiyoyi uku na zauna da su a aurena na fari. Ranar da mijinki zai kara aure ki ce sai mun zo da katafila danne kirji?” Hafsat ta yi mata zuru da ido, kafin cikin sanyin murya tace. “Wane ne mijin? Baba Azumi an gaya miki zan iya matsawa daga kusa da Mammah ne balle inyi aure?” Baba Azumi ta yi shiru, cikin zuciyarta ta ce. “Bari dai in yi shiru haka, kada Mammah ta ji mu ta ce zan gurbata mata tunanin ‘ya, ‘yarta ba irin ‘ya’yanmu ba ce, rainon Turai ce”. Ta mika mata wayarta, “Ungo latso min Isma’eela mu gaisa, na kwana biyu ban ji shi ba”. Ta yi hakan ne don kawar da waccan hirar tasu. Maryam Dakata da ke kicin tana saurarensu ba tareda sun sani ba, juya ludayi kawai ta ke a miya sakamakon wani sabon tunani da ya shige ta mai nauyi a zuciya. Yadda Hafsat ta girma lafiya, ta rayu cikin aminci babu tabarbarewar tarbiyyar zamani da ta kafofin sadarwa ko kawayen banza, yarinya ta gari mai karancin budewar idanu na masifofin zamani, yaddatake jin labarin Nigeria da yadda mutanen cikinta suka koma muddin ta bar Hafsat ta shiga jami’a a Najeriya ba abu ne mai wuya ba kawaye ko samarin banza su sauya mata Hafsatunta ba. Su rusa mata ginin nan da ta yi shekara da shekaru tana yi a rana daya. Tana da labarin duk abubuwan da ke faruwa a jami’o’in Najeriya da wajenta, wanda tabarbarewar zamani hadi da shigowar tafi-da -gidanka da watsar da fadar Allah da Manzo (S.A.W) da kyawawan al’adunmu na iyaye da kakanni ya haifar. Wallahi-wallahi aure za ta yi wa Hafsat da sun koma Nigeria a shekarunta goma sha bakwai, ba za ta barta ta je jami’a babu aure ba. Wannan ne kadai kwanciyar hankalinta. Ta runtse idonta da karfi ta bude, sa’ilin da wani tunani ya ziyarce ta, wanene MIJIN? Kamar yadda Hafsat ta ce. Wa ya ce yana sonta? Wa zai aure ta bai san ubanta ba? Wa zai aure ta koda yana son ta ba tare da watarana ya yi mata gori ko ya tozartata ba? Wa zai aure ta idan ya ji cewa ita da Dr. Hamza ba su ne iyayenta na haihuwa ba? “Babu!” Zuciyarta ta ba ta amsa, “Ko da an samu babu wanda zai yi mata riko na gaskiya da amana irin yadda ki ke so ta samu a gidan aure in ba wanda ki ke da iko da shi ba... abin nufi, wanda kika haifa daga mahaifarki, wanda za ki sa shi ya yi, ya yi. Ki hana, ya hanu, ya yi mata ba daidai ba ki tsawatar da dukkan ikon ki. Su hudun nan duk kina da iko da su... amman guda ukun ‘yan uwan jini ta dauke su, abokan shawara. Idan wata mu’amala bayan wannan ta billa a tsakaninsu ba za ta gasgata ta ba, za ta kalle ta amafarki ba reality ba. Wancan din dai da ba ta sani ba, wanda yake matsayin stranger a gareta ba ta san komai a kansa ba, ya fi dukkaninsu yin biyayya a gare ki. Ya fi su rashin shakuwa da ke wanda hakan ya haifar da ganin kimarki da jin nauyi cikin idanunsa fiye da dukkanninsu. In ki ka yi umarni ba zai tsallake ba, in kika sa kara ba zai gitta ba, yana so ko ba ya so. Wata zuciyar tace. “balle ma wane lafiyayyen matashi zan wanke Hafsat in baiwa ya ce min ba ya so???” Sai murmushi ta ke yi ita kadai tana juya miya a kan wuta, zuciyarta jinta ta ke kamar an wanke ta da ruwan alkausara. Ta soma kidayar kwanakin da suka rage musu komawa gida Najeriya. ***** A yau ake yaye su daga ‘Law School’ a jihar Lagos (call to bar ceremony). Bayan kwashe shekara daya cikin gwagwarmayar wannan makaranta,sadaukar da kai da juriya, wadda rayuwar cikinta tafi kama data secondary school boarding, ya sake fito da kwalin (BL) wanda ya bashi shaidar zama cikakken Lawyer. Barrister Abdul’azeez Hamzah Atiku, sanye cikin (black robe) da (WIG) dinsa. Ya yi kyau har fiye da yadda ya kamata a ce ya yi kyan, domin da gaske ya yi kyan babu karya. Gefensa iyayensa ne Hamza da Maryam, daya gefen Baba Azumi ce rike da hannun kyakkyawar budurwar zubin fulanin Yola. Kallo daya ya yi mata ya gane ta, ya ce cikin zuciyarsa, “Yar Habiba ce ta girma haka. To shi girman yara mata bashi da wuya ne? Haka ya ga ‘yammatan Dakata duk sunyi irin wannan girman su Saima dasu Khalisa sa’anninta cikin dan kankanin lokaci. Yanzu ta ma rikide gabadaya ta koma Habiban, sai dai ita a goge ta ke sumul kamar tarwada. Kai ka ce ba ta taka kasa”. Fuskarta da yanayin zubin halittar ta baiyi kama dana cikakkun ‘yammatan Nigeria ba, tafi kama da ruwa biyu, wadanda a turance ake kira halfcast. Daga yanayin rashin sakewarta a wajen mutum zai gane bata saba shiga taron mutane irin haka ba, watakila shi ya sa dattijuwa Azumi ta rike hannunta. Sanye take da wata tsadaddiyar doguwar riga da mayafin ta ruwan bula mai turuwa sakar kasar Oman da takalmi mara tudun dunduniya dan shafal samfurin vincci. Shima ruwan bulan ne mai turuwa. Duk iyalin Abdullahi Dakata sun bakunci ‘Law School’ ta jihar Lagos a yau. “The Barrister was now call to the Bar......” Inji Abdulkarim Dakata, ya fada tareda rungume jikan nasa cikin dariya. Haka Dr Idris da matarsa Dr. Tauheeda suka karaso wurin Uncle Idris ya rungume shi yana fadin “congratulations my grandson”. Shi dai murmushi yake yi, cikinsa kuma sai kartawa yake, weakness dinsa kenan ba ya jure yunwa, rabonsa da abinci tun jiya. In ka lura sosai za ka ga yana dan kalle-kalle kamar yana jiran wani. Ta yi masa alkawarin kawo musu lunch shi da bakinsa. Amma har yanzu bai ganta ba. Ga Baba Abdulkarim ya fara cewa a tafi a nemi restaurant mafi kusa su ci abinci su wuce ba za su kwana a Lagos ba. A hankali ta ke tuko kankanuwar motarta tana nema mata matsugunni a parking lot. Kallo daya ta yi wa ‘yan Dakata ta gane su domin duk suna kama da juna mazansu da matansu. Ta fito cikin shiga ta alfarma, sanye cikin wani tattausan (swiss lace) kalar kore me haske da ratsin kore mai duhu, ta murza daurin kai ya zauna tsaf a kanta cikin kwarewa da gogewa da yin hakan. Siririn mayafin da ta yafo kore ne me haske kalar dogon takalmin kafarta. Wadanda ke bayan motarta su ma suka fito suka bude ‘booth’ suka shiga fito da sundukan abinci dirka-dirka na alfarma suka doso iyalin Dakata. Sakin baki suka yi suna kallo ana jere musu abinci na alfarma a kan kilishin da suka shimfida, kamin kyakkyawar budurwar ta soma gaishe su kanta a sunkuye cikin nuna kunya. Su dai amsawa suke fuska a sake, shi kuma ya dauke kai yana waya bai bada fuskar da za a fahimci wani bayani daga gare shi ba, har ta zo ta gifta shi za ta wuce. Suka hada ido suka jefi juna da murmushi, sannan ta wuce ta tada motarta, hadimanta suka shiga suka tafi. ‘Mu’azatu’ sunanta, diyar tsohon ‘Attorney General of the Federation’. A baya ya rike mukamin zababben shugaba na ‘Nigerian Bar Association (NBA), sannan kuma ‘Senior Advocate of Nigeria (SAN) Habibu Rufa’i. A yanzu haka shi ke da mukamin (Director General of the Nigerian Law School) ta jihar Lagos daya daga cikin manyan malamansa a ‘Law school’ duk da shi baya koyarwa amma jininsa da Abdul’azeez ya hadu, yana zuwa neman karin ilmi wajensa. Haduwarsu ta farko da Mu’azatu tun farkon shigowarsa ‘Law school’ ne. Gidan mahaifinta cikin ‘Law school’ din ne a matsayinsa na (DG), asalinsu ‘yan Jigawa ne. Ta fara ganinsa a ofishin mahaifinta ya zo neman wani haske daga gare shi. Haduwarsu ta biyu a falon mahaifinta ne ya gayyato shi cin abincin rana. Mu’azatu ta rasa nutsuwarta tun ganinta na farko da dan Hamza Dakata, shi ma dai bai san me ya sa ba ya ji yarinyar ta dan kwanta masa da farko suka fara gaisuwar mutunci saboda Babanta, amma ba’a jima ba Mu’azatu ta fiddo soyayyarta gare shi a fili. Da farko ya nuna rashin amincewarsa don yana da abin da ya sa a gaba fiye da soyayyar a lokacin, sannan soyayyar wani abu ne da baya cikin lissafinsa nan kusa, amma abin mamaki ba a jima ba ta rinjaye shi ya fara sonta. Itama Mu’azatu law ta ke karantawa a LASU (Lagos state university). Yarinya ce ‘yar kwalisa, kuma ‘yar gata domin ita kenan ga iyayenta. Ana ji da Mu’azatu kamar tsoka daya a miya. Duk da haka tana da tarbiyyarta daidai gwargwado, sai kuma idanunta da suka bude sosai da rayuwar Lagos wadda babu tsarin al’adun mu a ciki, matsalarta kadai girman kai da ji da kai, amma ai ta san a inda ta ke yin shi, banda ga wanda zuciya da ruhinta ke so. Don haka Abdul’azeez bai san wannan side din nata ba. Abdul’azeez bai taba kawowa ransa soyayya ba nan kusa, balle aure. Gani yake a lokacin har gobe ba’a haifi macen da zai so ba. He’s very selective and choosy when it comes to matar aure. Amma da shigowar Mu’azatu rayuwarsa ta rusa komai, duk da cewa da farko ta sha wahala kafin ya amincewa soyayyar ta. Mu’azatu ta fahimci matsalar Abdul’azeez da zaman ‘law school’ abinci ne. Ba ya son abincin sayarwa har ya gwammace ya yi ta cin snacks da kayan gwangwani a dakinsa in bai samu lokaci ya dafa da kansa ba. Tun haduwarsu ta fahimci hakan, tuni ta dauke nauyin cikinsa sau uku a rana da abincin gidansu. Da farko bai yarda ba don sanin cewa yau da gobe sai Allah, amma ta dage kan na gida ne, ba musamman ta ke yi ba. Balle ya ce tana shan wahala. Daga karshe ma da ya ki yarda dangana maganar ta yi da mahaifinta, wanda Abdul’azeez din ke matukar girmamawa, baki da baki ya kira shi ya ce da shi daga ranar kwanon abincinsa uku a rana ya koma gidansa. Da wannan damar Mu’azatu ta samu kasancewa da Abdul’azeez koyaushe in ba ta makaranta, har sabo mai karfi da makauniyar soyayya ta shiga tsakaninsu. In daya bai ga daya ba a rana sai ya gaza sukuni. Tsohon Attorney General Habib ya fi ‘yarsa farin cikin samun Abdul’azeez a matsayin mijin da ta tsayar za ta aura sabida ya gane yaron dan baiwa ne kuma ya san daga inda ya fito, ya san wanene mahaifinsa daga jin sunansa, sannan Abdul’azeez din ya tabbatar musu babu matsala daga iyayensa don su ba ma a kasar suke ba. Da wannan suka ci gaba da murza tsaftattacciyar soyayyarsu wadda ba sa bari ta shafi lokutan karatunsu, an ce wai sai hali ya zo daya ake tafiya tare. Ita ma Mu’azatu kwaruwa ce a karatun Law don kuwa tsotsa ta yi daga uwa da uba. Abdul’azeez kuma na son babbar yarinyar mai manyan kwalaye irin nasa, wadda ba sai ya sha wahala wajen sarrafata ba, gogaggiya, kilalliya. Don haka Mu’azatu ta yi daidai da tsarin da yake son matarsa da shi ta kowanne fanni, ya sa ta kori duk wasu masu sonta ya yi mata alkawarin aure duk lokacin da ya shirya yin aure. A yadda ya kudurta a baya, bayan kwalin BL zai wuce ne ya yi Masters (L.LM ko MBCL) kafin ya yi aure, amma zuwan Mu’azatu zuciya da ruhinsa, ya sa ba abinda ya sa a gaba yanzu irin na ya shiga kotu ya fara aiki ya aure Mu’azatu ko hankalinsu ya kwanta bakidayansu. Abdul’azeez bai taba zina ba, bai taba sha’awar ta ba, kullum kuma yana kara rokon Allah ya kare shi, don haka ya ga cewa yin aurensa da Mu’azatu a yanzu shi ne abu mafi a’alah a gare shi, domin kwarai yake yaki da shaidan da zuciyarsa yadda Mu’azatu ke nanike mishi, ta ke shiga har inda yake a duk lokacin da ta so. Sun yi alkawurruka masu yawa a daren jiya shi da Mu’azatu, duka na aure ne komai runtsi, ko da Daddynsa ya ce sai ya yi L.LM zai yi aure ya yi mata alkawarin zai aure ta komai daren dadewa. Shi ne yau Mu’azatu ta kawowa iyayensa da ‘yan uwansa abinci. Ba tare da sun tambaya ba suka gane komai; suruka suka kusan yi. Adda Hafsatu ce kawai ta ce yarinyar ba ta yi mata ba, idanunta a tsaitsaye kamar na kurege, sannan ba ta sonshi da auren bariki, ya je Kano ya samo yarinya ‘yar usuli, babu irin matan da ba a kyankyashe a Kanon Dabo ba, Jalla babbar hausa, yaro ko da me ka zo an fi ka. Murmushi kawai ya yi a ransa yana fadin, irin kazaman yaran nan da ko alwala ba su iya ba, Adda ta ke so in je in auro? To da aikina zan ji ko da rainon karamar yarinya? Mammah dai babu wanda ya gane halin da ta ke ciki a kan Mu’azatu, ta yi kokari ta boye bacin ranta da kaduwarta. Ita a yadda ma ta dauki Abdul’azeez ba shi da zabi in dai a kan mace ne, ganin yadda neman ilimi ya zama priority dinsa fiye da komai. Ashe duk namiji komai tsaurin halinsa sunansa namiji in dai a kan mace ne. Har murmushin da suka yi wa juna shi da Mu’azatu ta gani. Mammah ta yi ajiyar zuciya a cikin jirgin Azman da suka hawo zai maida su Abuja. A fili ta ce. “Humm! Tabdi! Ashe za mu sabunta yakin duniya na biyu (world warII) ni da Abdul’azeez idan ya ce wannan mai tsayayyun idanun zai kwaso mini”. Daddy da ke gefenta da jaridar ‘daily Nigerian’ a hannu ya juyo ya dube ta. “Ke da wa ki ke magana?” “Ni da zuciyata. Ban ji ka ce komai a kan wannan yarinyar da Abdul’azeez ya kwaso ba”. “Me zan ce to? Bai isa auren ba ne ko me?” Mammah ta shiga girgiza kai, (showing resentment), “Ni ban ce bai isa aure ba. Amma na riga na yi mishi mata tun ina Brussels”. “Wace ce?” In ji Daddy cikin mamaki. “Addata!!!” Ta fada kai tsaye, tun kafin ya gama rufe bakinsa. Duk da ya gane wadda ta ke nufi, amma yana so ya kara tabbatarwa, “Kina nufin Hafsatu?” “Ita fa Daddy...” Ta warware masa daga hirarsu da Baba Azumi da ta ji wadda ta haifar mata da wannan tunanin, har tunaninnikan da ta samu kanta da yi a lokacin. Ta kare da cewa. “Daddy ina ganin wannan shi ne gata na karshe da zan yi wa Hafsat in san cewa na cike ladana, shi ma Abdul’azeez hankali na zai kwanta ko bayan raina saboda na san na hada shi da matar rufin asiri, nagartacciya wadda zai yi alfahari da ni a kanta a nan gaba”. Gyada kai Prof. Hamza ke yi yana murmushi, “Mammah the match-maker...!” Suka kyalkyale da dariya gabadaya. Ta tsayar da dariyar tana dubanshi cikin ido. “Ka bar maganar wasa Daddy, mene ne ra’ayinka?” “Ra’ayina? Ra’ayina shi ne ko kusa ba sai an yi yakin duniya na biyu ba, in kin yi masa umarni zai yi miki biyayya ko ba ya so. Amma ki sa a ranki ba a taba sanya wannan dan naki ya so abin da ba ra’ayinsa ba. Kin kwana da sanin wannan”. Jikinta ko kadan baiyi sanyi ba da wannan tuna tarwada ta Daddy. Yana rufe baki ta dora. “Su yi zaman aure cikin aminci shi ne ya dame ni ba su so juna ba. Soyayya ba lallai ta faru a sanda ake son faruwarta ba, ni in za su zauna lafiya to su tsufa babu soyayyar”. [01/08 3:34 PM] Sumayya Takori: SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* AUREN KWANGILA 1 Page 7 Sun dade a Abuja Daddy yana cuku-cukun komawa aikinsa na koyarwa a jami’a, kafin jami’ar Abuja ta dauke shi a matsayinsa na Farfesa. Sauyin rayuwar ba kadan ba ne, sai dai ga mutum wanda ya san mece ce rayuwa ya kuma yarda samu da rashi duk na Allah ne irin Hamza Atiku hakan ba zai sa su kasance cikin damuwa ba. Zuciyarsa a sake ta ke, yana ci gaba da harkokinsa cikin karbar canjin rayuwar da ya same shi rana daya, shi da iyalinsa. Ba karamin hikima da dabara ya yi ba wajen bude wa ‘ya’yansa account a lokacin da duniya ke gara masa. Hakika ya tara musu abin da zai dauki nauyin karatunsu a ko’ina suke cikin duniya, har su gama su kama aiki, su dogara da kansu. Sati daya bayan ‘call to Bar ceremony’ Abdul’azeez ya dawo gida cikin iyayensa da ‘yan uwansa. An tura shi Federal High Courtta Abuja, inda zai fara aiki sati biyu masu zuwa. A zaman Abdul’azeez cikin satin Mamma ta kasa sukuni, tana hankalce da mu’amalarsa da kowa na gidan, inda ta gane abubuwa da dama a tare da dan nata, wadanda a da ba ta sansu ba. Nisan muhalli na lokaci mai tsawo ya yi mata shamaki da shi. Ta fahimci ya yi nisa a soyayyar Mu’azatu Rufa’i, gab yake da ya bayyana hakan gare su. Gaisuwa kadai ke hada shi da Suhaana, bayan wannan ba wani abu. A kokarin Hajiya Maryam na son sanya sabo da shakuwa a tsakanin ‘ya’yan nata biyu, sai ta maida Suhaana mai hidimar Abdul’azeez; gyaran dakinshi kullum in ya fita motsa jiki da safe; kai masa karin kumallo in ya gama ya koma daki. Haka lokacin cin abincin rana da dare, ita Mamman ke aike ta kirawo shi dining, har a gama cin abincin kallo wannan Hafsat ba ta samu. Ba abin da ya damu Suhaana, kullum cikin walwalarta ta ke, tunda ba ya kyararta, ba ya yi mata kallon banza, kusan kullum yana kwance cikin doguwar kujerar hutawa da ke gefe guda a falon gidan, yana waya da Mu’azatu. Sati biyu suka cika, Barrister Abdul’azeez Hamza Atiku ya shiga Federal High Court a matsayin lauyan gwamnati na kasa mai rajin kare hakkin ‘yan kasa. Idan ya fito fully robed (dressed in black gown and wig) sai ka yi masa kallo na biyu sabida yadda kayan suka amshe shi, suka zauna cif a jikinsa, suka fito da ilhama da cikar halittarsa. Mammah ta dago ido daga talabijin ta dube shi a sanda ya shigo falon yana daura agogon hannunsa, cikin shirinsa tsaf na shiga office. Daddadan kamshin turarensa (creed aventus) ya cika mata hanci. Hawayen farin ciki suka ciko a idanunta. A yau ga babban dan da ta haifa ya zama babbban mutum wani abin amfani ga al’umma, wahalar da suka sha a kansa wajen tarbiyya da neman iliminsa ba su fadi a banza ba. A cikin zuciyarta wannan addu’ar ta ke yi, wadda ba ta rabo da bakinta a duk lokacin da ta ga ‘ya’yanta za su fita; “Rabbi ja’alni muqimas-salaata wa min zurriyyaty, Rabbana wataqabbal du’a”. Idan har iyaye za su kama wannan addu’ar a bakinsu a kan ‘ya’yansu, hakika za su zamo masu tsaida sallah, a idonsu ko a bayan idonsu. Sallah ita ce babban jigon kasancewa cikin nutsuwa da tsoron Allah ga matasa. Kuma ita ce abin da ke ba su wahala a yanzu shi ya sa zina ta yawaita, musifun rayuwa suka addabi matasanmu. In ka tsaida sallah hakika ka ribaci gabadayan rayuwarka, domin ita din garkuwa ce daga aikata alfasha da aikin munkari, shi ya sa Hajiya Maryam ba ta wasa da yi wa ‘ya’yanta wannan addu’ar. Rolex yake daurawa a damtsen hannunsa na hagu, ya yi fes! Ya yi wani irin fresh da shi. Duk kodewar da ya yi sabida wahalar karatu, yanzu ta bace. Kyawunsa da kwarjininsa sun kara fitowa fili. Sosai Mammah ta ke kallonsa tana marmasa wannan addu’ar a zuciyarta, har da addu’o’in nema masa tsari daga duk wani abin ki,makiya da mahassada, domin kwarai yaron nata ya burge ta, ya kuma ba ta sha’awa, ta ji wani wata sabuwar kauna sosai a kansa a zuciyarta. “Mammah na fito, na makara fa, yau ko karin kumallon wannan ‘yar taki ba ta ba ni ba”. Mammah ta yi murmushi “Ga shi nan a kan tebir, ba ta jin dadi ne shi ya sa ban tashe ta ba. Mararta ke ciwo”. Cikin rashin damuwa ya ce “To ba sai a kai ta asibiti ba? Ni na tafi Mammah babu time din da zan tsaya karyawar ma fa, ana jirana”. Mammah ta ce “bari in sa Azumi ta sanya a basket ta sa maka a mota”. Ya wuce yana fadin. “Toh, ta hanzarta”. Da ya dawo office bai samu Mammah a gida ba, Daddy ma bai dawo ba. Azumi ce kadai a gidan. Yana tafe yana waya da Mu’azatu kamar masifa. Yarinyar ta gama kame zuciyarsa da dadadan maganganunta na soyayya. Tana da baiwar sarrafa harshe da iya zance mai sace zuciyar masoyi, ba mamaki tunda lauya ce. Hakika ya yi nisa a son Mu’azatu da kyar in burin Mammah zai cika a kan kudirinta. Baba Azumi ya tarar tana mopping a babban falo “Mutanen gidan ba sa nan ne Mama Azumi?” “Sun je asibiti, amma yanzu za su dawo”. “Waye ba lafiya?” Ya fadi yana bude warmers din abinci da ke jere saman dining-tabledin falon cikin rashin baiwa zancen muhimmanci. . “Addah ce”. In ji Azumi. “Wace ce Addah?” Ya tambaya, don shi bilhaqqi bai san wata Addah ba bayan Kakarshi ta Kano. “Ina nufin Hafsat”. “Suhaana?” “Ita fa”. “Da ma sunan Adda aka sa mata ba HABIBA ba?” “Eh”. In ji Baba Azumi.Cikin ranta tana mai mamakin yadda akayi bai san hakan ba shekaru dai-dai har goma sha bakwai. Amma da tayi tunanin yadda baya zama tare dasu a duk tsayin lokacin sai ta kore mamakin. Ya zauna a kujera ya fara cin abincinsa cikin kwanciyar hankali. Bai tambayi me ya same ta ba, don a ganinsa ba abin da ya shafe shi ba ne. Itama tsohuwar cigaba tayi da ayyukanta cikin falon bata kara ce dashi komai ba, saboda babu sabo tsakanin su sosai kamar su Ishma da suka karasa girma a hannu ta, kuma sosai yake mata wani irin kwarjini kamar maigidan gashi da wani irin tsare gida. Mammah da diyarta Hafsat a teburin likitar mata Dr. Hajara Bello a hamshakin asibitin (Diff Hospital) dake nan Asokoro. “Jinin al’ada ne za ta fara, ta dade bata fara ba, wasu yaran daga shekaru sha uku ma suke fara al’ada, ki kwantar da hankalinki. Da ya zubo shi kenan, (pain reliever) kadai za mu ba ta. Wasu matan kan yi fama da hakan idan za su fara al’ada. Wasu yana ci gaba har sai sun yi aure za su samu saukinsa, wasu har su haihu. Yanzu in za ta sake yin wani zai zo da sauki ba kamar wannan ba. Da ta fara irinsa a ba ta wadannan kwayoyin da na rubuta mata”. Mammah ta yi godiya ta karbi takardar maganin, suka fito. Ta tsaya a (Pharmacy) ta saya suka taho gida. Don azaba Hafsat ba ta san inda kanta yake ba. Suna tafe a hanya Mammah na mata sannu, tana shafa mata bayanta. Ta hada gumi kashirban. Hajiya Maryam na fadi a ranta, “Hafsatu an girma, daga yanzu zuwa kowanne lokaci za ki iya daukar ciki. Ki yi hakuri, kina so ko ba kya so, AURE zan yi miki”. Sanda suka iso falo Abdul’azeez ya gama cin abincinsa, yana kokarin mikewa daga dining din. Idonsa ya sauka a kan Hafsat, wadda rabin jikinta ke rungume jikin Mammah, sai cije lebe take yi. Idanunta ko bata iya bude su, Mammah na rike da ita. Ya wuce hanyar dakinsa yana fadin, “Mammah sannu da zuwa”. Cikin bacin rai Haj. Maryam ta kira sunansa. “Abdul’azeez!” Cak! Ya tsaya, don in ka ji Mammah ta kira sunansa to ranta ya baci ne. Bai juyo ba, amma ya dakata. Cikin fushi ta ce, “Baka ganina tareda mara lafiya ne? Is this a way to address a patient?” “Yi hakuri Mammah”. Kawai ya ce. Tareda dukar da kansa kasa. Wannan halin nasa na ko’in’kula da al’amarin mutane yana bala’in bata haushi. Ta yi tsaki ta ja Hafsat suka wuce jin wayarsa na kara da wani lafiyayyen tune mai sanyaya zuciya da ta dade da fahimtar na Mu’azatu ne. Domin duk sanda ya ji shi zai tashi ya kebe, in kuma daya tune din ne zai amsa shi a gaban kowa. Saida suka kai kofar dakin Hafsat ta juyo ta dube shi. “Za mu yi muhimmiyar magana ni da kai da Daddy, karfe goma na dare”. “Ok, Mammah”. Ya wuce dakinsa, su ma suka yi ciki. Hafsat ta sha magungunan ta ta kwanta, Mammah ta nufi dakin Daddy. Ba ta dade da hadiyar magungunan ba bacci mai nauyi ya dauke ta. Karfe goma daidai Daddy da Mammah suka fito karamin falonsa, bayan sun shirya komai cikin sirri a tsakaninsu. Abdul’azeez suke jira. Ba su dade da zama ba shi m ya shigo cikin kaftani na danyar farar shadda mai gautsi, sai maiko ta ke. Dawowarsa kenan daga gidan wata Antin Mu’azatu a Apo, Mu’azatun ta zo Abuja ta sauka a can don kawai ta ganshi, ta yi kewarsa da yawa, ya yi kewarta shi ma har yadda ba zai iya kwatantawa ba. Shi kansa bai san adadin soyayyar da yake yi wa Mu’azatu ba, ta shiga ransa da yawa, yana shaukinta. Yana son karar da lokuta tare da ita don hakan na sanya shi nishadi. Yana sonta, ba ya gajiya da tausasan kalamanta masu kara masa kaunarta, yana son komai nata, ba shi da buri a halin yanzu sai na aurenta, su zama abokan rayuwar juna na har abada. Ya kudurce a ransa ba za’a tashi daga wannan zaman ba, ba tare da ya gabatar da maganar Mu’azatu ga iyayensa ba, su je su nema masa aurenta. Yana wannan tunanin yana murmushi cikin ransa, hango ranar da ya mallaki Mu’azatu yake yana kissima abubuwa iri-iri masu muhimmanci cikin rayuwarsa da za su gudana a ranar. Ya tsinkayi muryar Daddy can tsakar kansa. “In ka gama murmushin, sai ka arawa mahaifiyarka hankalinka”. Da sauri ya dago kai ya dube su su biyun, sun masa kyau a idanunsa. Babu alamun tsufa ko kadan a tare da su, saboda tsabar kula da lafiya da samun hutu. Babu mai yarda sun ajiye Da kamarsa mai shekaru (29). Su ma kallonsa suke da murmushin cikin alfahari da shi a nasu zuciyoyin. Hakika ko ba su fada ba babu Da kamarsa a zukatansu. Sun dade suna ba shi ‘yancin kansa kan dukkan al’amuran rayuwarsa, amma a yau? Su ma suna son su motsa kwanjinsu na iyaye a kansa, ya yi musu alfarmar da ba su taba nema ba. Mintuna biyu suka share suna yi wa juna murmushin, kafin ya sadda kansa kasa. “Mammah, ina fatan lafiya? Na shiga fargaba kan maganar da ki ka ce za mu yi muhimmiya, tun dazu ina babban falo sai yanzu da na ji saukowarku na shigo”. Mammah ta muskuta kadan, sannan ta ce “Maganar aure ne. Me ka shirya wa rayuwarka yanzu tunda gwagwarmayar neman ilimi da aikin yi sun kare?” Ya dago ya dubi Mammah, she’s talking now on behalf of Daddy, why? Daddy da ke zaune ne ya kamata ya yi masa wannan tambayar ba ita ba, kasancewar ba ta yin hukunci a kan komai na rayuwarsu sai shi. Amma yanzu ya yi shiru yana duba jarida, kamar bai san me suke yi ba. “Ai Mammah a kan gabar maganar nake”. Ya fada cikin nutsuwa. “Kamar ya ya?” Mammah ta tambaya kamar ba ta san me yake ciki ba. “Na samu mata a Lagos”. “Ga shi kuma ni ma na yi maka, tun shekaru masu yawa”. Da hanzari ya cira kai ya dube ta, sai kuma ya sunkuyar. Mammah ta ci gaba da fadin. “Ban san za ka iya ganin mace ka ce kana so ba ne shi ya sa na yi kan gaban kaina, saboda ni kullum kallon wani ustaz nake maka, wanda baida idon kallon mata, da sanin cewa ba za ka watsa min kasa a ido ba, kasancewar na san ban taba neman alfarma a gare ka ba a kafatanin rayuwarmu, shi ya sa na yi tunanin in na nema sau daya za ka yi min (alfarmar). Na dauka ba ka da buri a rayuwa sai na zama lauya, ban san kana da lokacin matan bariki ba a yadda ka ke tafiyar da rayuwarka”. “Ba matar bariki ba ce”. Ya fada cikin gigicewa da karkarwar murya. Shi kansa bai san yaushe kalaman suka subuto daga bakinsa ba. “Ban damu in santa ba, ko inda ta fito. Tunda ba abin da zan iya kulla mata a kanka. Bayan in ce mata ‘sorry’. Tunda ba’a yi shawara da ni ba kafin a soma ‘dating’ dinta. Ban san da ita ba, don haka don an ba ta hakuri ba zai zama laifi ba. Kai in ma na sani tuntuni birki zan taka akanta tun kan abin ya yi nisa, tunda kuwa ni ma ina da budurwar da na dade da tanadarma lauyan. Abdul’azeez ba shi kadai ne namiji ba, za ta samu wani a gaba, harma wanda ya fi shi, amma wannan Abdul’azeez din has a wife since”. Wani irin gumi ke barko masa tun daga tsakiyar sumar kansa har zuwa yatsar kafarsa. Me Mammah ke nufi ne a kan Mu’azatu? Ba fa duka kalamanta yake fahimta ba. Tun daga lokacin da ta ce “..... Ga shi kuma ni ma na yi maka mata tun shekaru masu yawa”.Sauran sama-sama ya ji su. Ai abin da ba zai taba yiwuwa ba ne a ce wata zai aura ba Mu’azatu ba. “Ka yi shiru, sai zufa ka ke sharewa, me ye abin tashin hankali cikin maganganun mahaifiyarka?” Daddy ya yi magana lokaci na farko, bayan ya ajiye jaridar hannunsa a gefe. Tuni wani zazzabi-zazzabi ya rufe shi, idanunsa sun rufe ruf! Harshensa ya bushe karaf, babu digon yawu a bakinsa. Ya lashi busassun labbansa ya daure ya yi magana a sanyaye. “Ai Daddy ban gane abin da Mammah ta ke fada ba ne sosai, ta yi maganar ya kamata inyi aure, na ce na samu matar da zan aura mun daidaita kanmu, ina gab da gabatar muku da ita ne”. “Ahh lallai”. In ji Daddy. “Wato duk dogon bayanin da ta yi maka ba ka fahima ba? To yaushe ka kurumce? Sai mu kai ka kasar da ba ka so a yo maka (hearing-aid)”. Ya fada a harzuke. “I’m sorry Daddy, tunanina ne ya tafi nesa, amma wallahi da gaske ban fahimta ba”. “To bari in yi maka dalla-dalla”. Hajiya Maryam ta fada cikin hadiye fushi.“Na yi maka mata tun tuni, ita waccan din da ka ce kun daidaita ta yi hakuri ba za’a aure ta ba. Da kaina zan kira ta in ba ta hakuri. Mun dade muna bin ra’ayin, wannan karon alfarma ne na ce ka yi min, ka yi min biyayya a kan nawa ra’ayin sau daya tak! A rayuwa, ka auri zabina”. Abdul’azeez ya kama kansa da hannuwansa biyu yana juyawa, “Wallahi Mamma ina son Mu’azatu.......” Duk suka kama baki suka bi shi da kallo. Abdul’azeez ya ci gaba da cewa cikin gigicewa, “Mammah zan miki kowacce alfarma amma ki kauda wannan, in na yi haka na yaudari Mu’azatu, na karya alkawari. Na karya zuciyarta na yi cin amanar kauna......” Babu wanda bai fusata ba a cikin iyayen. Cikin fushi Hajiya Maryam ta ce, “An ci amanar, an yi yaudarar, an karya zuciyar. Ta zo ta rufe mu da duka, wayar kuma da zan yi in ba ta hakurin na fasa. Soyayyar ta ci abu kazan-kazan ubanta! Wallahi in ka ga ba a yi auren nan cikin watan nan ba, daya daga cikinku ne ya rasu, ko kai ko ADDAH! Mun ba ka kwana uku ka yi shawara da zuciyarka, da duk wanda ka yarda da shi na ka zabe mu, ko mace a kanmu. Tashi ka ba ni wuri”. Ya dade bai tashi a wurin ba, yana zaune a inda yake. Zufar na kara kwarara fiye da farko. Dazu aka fahimtar dashi wacece da suna Addah a cikin gidansu, ba wata ba ce Hafsat-Suhaana ake nufi, wannan kankanuwar yarinyar data tashi gaban mahaifiyarsa, wadda aka haifa akan idonsa a Jeddah, ‘yar mai aikinsu Habibah, mara asali, ‘yar sakandire, shagwababbiya, wadda shi kwata-kwata ko kyakkyawan kallo bai taba yi mata ba, bai taba daukarta a matsayin mutum ba. Cikin tashin hankali ya mike, ya isa gabansu ya tsugunna a kan gwiwoyinsa. “Ku yi hakuri Mammah, na yi sa’insa da ku, ni ma ban so na yi ba. Na yi kuskure Mammah ki yafe min”. Sai hawaye a kan kafafunta. Zuciyar UWA, a take ta ji sanyi a zuciyarta. Ko da ma can fushin nata ba mai yawa ba ne, saboda ta san za a yi hakan. Ta kuma shirya karbar kowanne abomination dinsa. Yanzu an wuce wurin, tunda ta fada ya ji, ya yi reaction, lallashi yake bukata yanzu. Hannu ta kai ta dago kansa, “Ya wuce Abdul’azeez. Ni dai in kana so ka faranta min, mu zauna lafiya ni da kai, to ka karbi zabina, ka yi min alfarma a kan hakan, ka yi min biyayya. Za ka samu duk abin da ka ke so a mace a tare da Addah, in ka yi hakuri zuwa gaba kadan. Duk da haka na ba ka kwana uku ka je ka yi shawara da zuciyarka ko da wanda ka yarda da shi, ka zo min da abin da ka yanke, ba ni lambar iyayen Mu’azatun”. Girgiza kai ya yi cikin sabon tashin hankali “Don Allah Mammah kar ki kira su, na roke ki da Allah. Suna da girma a idona, malamaina ne, sun yi min alheri mai yawa. Ni da kaina zan gaya musu a lokacin da ya dace, don Allah Mammah...” Hannu biyu ya daga alamar roko. Mamaki ya kara kashe iyayen a zaune. Wane irin so yake yi wa yarinyar haka? Anya Abdul’azeez ne? This stubborn child of her’s? Duk ya sukurkurce sabida wata banzar yarinya? “Umh!” Mama ta ce, tare da daga kafadu da dan bude hannu har da kyabe baki (nuna alamu ne na ba ta da matsala da hakan, kuma ba ta takura ba, ba ta damu ba). Ya yi ta rike lambarsa, ita dai matsalarta a cika mata burinta, a auri Addarta, a rike mata ita cikin aminci. Cikin ‘ya’yanta hudu kuma shi ne zabinta, don ta san shi ne ya fi kowa nagarta, shi ne extraordinary. ‘As a mother (a matsayinta na uwa) wadda ta raine su dukkaninsu a tafin hannunta, tana da kyakkyawan yakinin an halicce su ne domin junansu, za su zauna lafiya cikin amana da juna. Za su gode mata watarana da wannan hadin da ta yi musu, za su yi alfahari da auren alherin da ta ke nufinsu da shi. Za su fahimci juna a hankali, su kaunaci juna, su zauna lafiya. Haka Abdul’azeez ya baro gaban iyayensa yana cikin rudu da tashin hankali da neman mafita cikin kwakwalwarsa. Mammah da Daddy sabgoginsu suka shiga cikin yin addu’a a zuciyarsu a kan Allah ya zaba masa mafi alkhairi a cikinsu. In wa’adin da suka dibar masa ya cika, ya zo ya ce ya amince shi kenan, in ya shafa wa idonsa toka ya ce zabins1a ya ke so ba za su takura shi ba, za su kyale shi ya auri wadda ya ke so, babu komai rayuwa ce, ka haifi Da a cikinka in ya girma ya yi ilmi ya ce, ya fi ka sanin abin da ya ke alkhairi a gare shi. Kwance yake rigingine yana fuskantar ceiling, tunanin mafita ga auren da iyayensa suka bijiro a gare shi yake yi, neman hanyar gujewa al’amarin yake ko ta halin kaka, saboda a gare shi abu ne da ba zai taba yiwuwa ba rabuwa da Mu’azatu, kuma wai wannan kwailar da aka haifa a kan idonsa ita ce matarsa. To me za ta ba shi? Me za ta yi masa? Aurenta ko child abuse? Me zai dauka a jikinta? A yadda ya ci burin yin aure a dan tsukin nan, ya mori rayuwar aure kamar kowanne lafiyayyen matashi mai jini a jika kamarsa, wanda babu zina a tsarin rayuwarsa... a zo a ce wai wannan jaririyar ce matarsa? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un...... ita ya kama yana maimaitawa har nutsuwa ta zo masa. Me ya shiga kan Mammah ne? In ‘ya’yanta kawai ta ke so ta aura wa ‘yar tata ai ba shi kadai ne danta ba, akwai kanana daidai da ita, wannan ko jambaki bai taba ganin ta shafa ba balle hoda, kullum haka ta ke a kojale, ido ko kwalli babu. Ita Mammah ke ganin ya dace ta zame masa uwargida cikon farin ciki? Mahadin rayuwa abar hutawarsa? Ya san halin Mammah kwarai, tunda ta yi wannan furucin ba abin da zai sa/ba wanda zai sa ta canza. Sunansa sorry cikin farin cikin da ake samu a aure. Tunda ba za a aura masa wadda zuciya, ruhi da gangar jikinsa ke so ba. Sun manta da cewa kiyayyar namiji a kan mace ba karamin al’amari ba ne. Mace akewa auren dole a wanye lafiya amma ba cikakken namiji wanda ya san ‘yancinsa kamarsa ba. Zuciyarsa ta yi duhu, idanunsa sun yi masa bakikkirin, har wani hayaki-hayaki yake gani yana fita daga idonsa, yana ji kuma yana gani wayarsa na haske da ruri da tune din Mu’azatu, ya yi ya tsinke ya sake ci gaba, amma ko dan yatsansa ya kasa motsawa. Me zai ce wa Mu’azatu? Yarinyar da ta dauki soyayyar duniya da amanar duniya ta dora a kansa? Suka gama tsara rayuwarsu yadda suke so? Ya san yadda Mu’azatu ke da kishi a kansa, ta sha gaya masa ba za ta iya sharing dinsa da kowacce mace ba, don ma in yana da burin polygamy ya rushe, za ta iya rasa ranta a kan su mallake shi ita da wata. Duk kuma ya gaya mata cewa ya amince, shi da ma a tsarin rayuwarsa mace daya ce har bayan ransa. Duk wannan ya zama tarihi kenan? Zai rasa Mu’azatu cikin dan lokaci kalilan? Dole ya yi wani abu, dole ya yi wata hikimar ta yadda ba zai samu matsala da iyayensa ba, ba kuma zai rasa mu’azatu ba. Mammah ba uwa ce irin sauran iyaye ba, ita ko a cikin iyaye mata ta daban ce. Ta cancanci a yi mata biyayya kowacce iri ta ke so. Zai yi kokarin kada ya bata mata, kuma shi ma ya faranta wa nasa ran ya samu abin da yake so cikin sauki. Akwai mafita biyu da yake ganin zai gwada, in ba su yiwu ba, sai ya yi wanda zuciyarsa ta fi kwanciya da shi. Mu’azatu ta gaya masa ko an zo neman aurensu, sai dai a yi baiko, amma biki Daddynta ya ce sai ta je ‘Law school’ ta dawo zai yarda a yi. Tana shekaarta ta karshe a jami’a yanzun haka. A lokacin da ta fada masa yadda suka yi da Daddyn nata ya fada mata cewa shi ba zai iya jira ba, amma ya yi mata alkawarin zai barta ta je gaba da ‘Law school’ ma a gidansa in har tana so. Yanzu zai yi amfani da wannan damar ya aiwatar da kudirinsa, yadda zai faranta wa kansa, ya kuma faranta wa iyayensa. Don ko jiya da ya tambaye ta ya suka yi da mahaifin nata a kan maganar da suka yi, saboda yana so ya turo magabatansa a yi tambaya, ta gaya masa cewa, ita ba za ta iya dosar Attorney din da wannan maganar ba, don ba zai taba amincewa ba tunda ya riga ya zartar da hakan, gara ma in shi zai je ya fadi hakan da kansa zai fi jin kunyarsa, ya yarda ko da da ta kare LLB ne. Ya ajiye ajiyar zuciya mai nauyi, a kasalance ya mika hannu ya dauko wayarsa, ya nemo lambar da yake nema, ya yi text ya tura. Jikinsa gabadaya ya yi sanyi, ba shi da kuzari ko kankani, hango yadda zai jure rasa Mu’azatu kawai yake yi. Muguwar tsanar Addah da kyamarta nata kurdawa kowanne sako da lungu na zuciyarsa. “Haka kawai? Why me?” Ya furta a fili. Fitowarsa kenan daga dakin karatu, rungume da littattafai. Ya doshi hanyar fita daga cikin jami’ar Harvard, yunwa yake ji sosai. Bai dade da shiga commercial bus don ko awa gida ba ya ji alamar shigowar sako cikin wayarsa. Zaro wayar ya yi daga aljihunsa ya duba, ‘If you are free ka kira ni, za mu yi magana ta sirri, kuma very important’. Ajiye wayar ya yi cikin aljihu, “Wallahi sai na ci abinci, kada ka fada min abin da zai kori yunwar nan da ta addabe ni”. Sai da ya iso gidan da Daddy ya kama masa ya yi wanka, ya ci abinci. Ya sallaci la’asar, ya samu nutsuwa sannan ya zauna a ‘balcony’ ya kira Yayan nasa. ISMA’EL DAKATA ne. “Yauwa Ishma are you o.k? Za mu iya yin maganar babu kowa tare da kai?” Isma’eel cikin mamakin yadda husky voice din yayan nasa ta zaftare ta koma rabi, ya ce, “I’m alone Yaya”. Nisawa Abdul’azeez ya yi, ya sauke numfashi mai nauyi. “Ishma, wata musiba ce ta tunkaro ni, nake so ka taimaka mini. Ni kuma na yi maka alkawarin yi maka duk abin da ka ke so a duniya, zan kuma dinga raba albashina biyu ina turo maka duk wata har ka gama karatu ka kama aiki ka tsaya da kafafunka”. Maganganun (sounds funny) a kwakwalwar Isma’eel, daga ji ba abin alheri Yayan zai nema ba, tunda har sai ya biya shi lada. Ladan ma wai na rabin albashinsa duk wata. “Ni kuwa me zan yi maka da har sai ka biya ni Yaya Azeez? Gaya min ko me ka ke so in yi maka, in har na alkhairi ne. Zan iya fansar da raina don in cece ka, amma wace irin musiba ce wannan da iyayenmu ba za su iya yi maka maganinta ba sai ni?” “Su suke son jefa ni a ciki Isma’eel”. “Subhanallahi, please Yaya, don’t say this again. Na yi amanna ba za su taba jefa ka a musiba ba, sai alkhairi ga rayuwarka. Yanzu dai me ka ke so in yi? A shirye nake da in taimaka in har abin alkhairi ne, kuma zai tafi da damuwarka, don Allah me ka ke so in yi? Wallahi ba sai ka ba ni komai ba zan yi. You sound worried. Ni ma na shiga cikin damuwa.......” Abdul’azeez ya canza rikon wayarsa daga kunnen dama zuwa hagu, ya juya ya tabbatar babu kowa a cikin dakin, kuma babu motsin kowa daga waje. “So nake ka bugo waya wa Mammah, ka ce mata ka dade kana son Hafsat, don Allah a ba ka aurenta, saboda ka kasa maida hankali kan karatunka saboda soyayyarta. Ka ce sonta ka ke tun tana yarinya. Ka nuna mata irin wani abu zai iya samunka din nan in ba ka samu aurenta verysoon ba, sauran kalaman ka tsara abinka, ai kai ba yaro ba ne tunda na ba ka topic din, ka gane?” Mamaki ya gama kashe Isma’eel a tsaye. Sai da ya lalubi kujera ya zauna, “Yaya wace Hafsat din?” “Ta gidanku mana”. “Kana nufin Suhaana?” “Ni wallahi sunannakin nata ba duka na rike ba, kuna kiranta da sunaye barkatai. I don’t actually know, ta wajen Mammah dai”. “Don Allah Yaya mu yi magana ta fahimta, Hafsat-Suhaana Addar Mammah?” A ginshire Abdul’azeez ya rausaya kai ya ce, “Eh, ita! Don na ji Baba Azumi ma ta ce mata Addar”. Dariya ta kama Isma’eel amma ya gintse, yanzu ya gano bakin zaren duk da bai gaya masa ba. Mamakin Yayan nasa ya kama shi, amma tunda bai fito fili ya gaya masa dalilin bukatar tasa gare shi ba bari ya bi shi a hakan. “Yaya a kan me to? A kan me zan yi hakan, a kan me zan yaudari Mammah in yi wasa da hankalinta a kan abin da ba haka yake ba a zuciyata? Yaya Hafsat mai martaba ce a wajen Mammah da mu bakidaya da muka rayu tare, muka san wace ce ita, wace irin martaba Allah ya yi mata. Kasancewarta ba jininmu ba ba ya nufin ba ma kaunarta ko don kaunar da mahaifiyarmu ke mata. Yarinya ce ta gari, amana a wajen mahaifiyarmu, ta ya ya ka ke tunanin zan iya playing game a kanta? To a kan me ma?” Abdul’azeez ya hadiyi miyau, jin makoshinsa ya bushe kyamas da jin alamun ba zai samu nasara a plan dinsa na farko ba. Amma dai bari ya ci gaba da turzawa tunda Isma’eel dai a kasansa yake. “A kan duk kaunar da ku ke mata, ba ta kai wadda ke tsakanina da ku ba”. Ya fada cikin kwantar da murya, jin kamar Isma’eel ya fusata. “Haka ne Yaya, to amma a kan me zan yi karyar ina son nata? Ni ban taba sonta ba! So na soyayyar aure, amma ina mata dukkanin kaunar da Yaya ke wa kanwarsa. Har tsarkin kashi na yi wa Suhaana, ban taba yi mata wani kallo bayan wanda nake yi wa Halim ba. Sannan ba zan iya wasa da hankalin Mammah har haka ba, me ta yi mana da ta cancanci haka? Ka yi hakuri Yaya, ba zan iya ba. Kuma kaima na rokeka ka bari, ka yi mata abin da ta yi maka umarni da kyakkyawar zuciya, kar ka sake tunanin yi mata (trick). Yaya, Allah yana kallonka, duniya da kyale-kyalen cikinta aikin banza ne. Mammah ita ce kofar shigarka aljanna, matsayin da Allah ya ba ta a gare ka ya wuce duk yadda ka ke zato. Na yi maka alkawarin wannan maganar da muka yi ni da kai an barta a nan, ba za ta taba fita daga bakina ba. Mu wuni lafiya”. Ya kashe wayarsa. Duba wayarsa ya yi sosai, yana mamaki. Shi Ishma ya kashe wa waya??? “Ba dole ya kashe maka waya ba, tunda ka kawo raini ga mahaifiyarsa?” Zuciyarsa ta yi hanzarin halarto masa da amsa, “Da kyar ma in girmanka bai zube a idanunsa ba!”. Ta kara ankarar da shi. Jikinsa ya yi matukar sanyi, kansa ya yi masa nauyi. Babu nasara a ‘plan 1’, bari Allah ya kai mu gobe ya aiwatar da ‘plan 2’. In shi ma babu nasara sai ya amince da babban, wanda zuciyarsa ta fi kwanciya da shi. So, ya rufe masa ido, ta yadda har ya kasa ganin muhimmancin nasihohin kanin bayansa Ismael. Washegari ya kira tsohon minista, kawun mahaifinsa Abdulkarim Dakata. Ya gaya masa yana son ganinsa, ya ba shi lokaci ya tadda shi a gida ko ofis (yana aiki da ofishin jam’iyyar NPC a yanzu, a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyah). Akwai shakuwa ta musamman a tsakaninsu. Abdulkarim na son Abdul’azeez kamar ko ma fiye da yadda yake son su Farhan. Ya zabi ya same shi a office. Don haka washegari, kwana biyu kenan da yin maganar da iyayensa, a gobe ne za su zauna da shi don jin abin da ya yanke. Ya wani rame tun daga jiki har fuska a kwana biyu kacal saboda daura wa kansa masifar da Allah bai dora masa ba. Mammah na kallon duk motsinsa a kwanaki biyun nan tana shan mamaki, anya yarinyar nan da iyayenta haka suka kyale Abdul’azeez? Ko dama shiyasa suke bashi abinci? Uban wa ma ce ya aike shi cin abincinsu? Wannan wace irin masifa ce? A ce wai ita Abdul’azeez ke jayayya da ita a kan mace? To su zuba ita da shi ta ga iya gudun ruwansa dan halas ka fasa! Sun kulle kansu a office shi da tsohon Sanata kuma tsohon minista, kawu ga mahaifinsa. Ya kwashe komai ya gaya masa tun haduwarsa da Mu’azatu a (Law school) da hidimar abincinsa da ta rika yi ita da iyayenta har ya gama. Da alkawuran da kakkarfar soyayyar da ke tsakaninsu. Da kuma abin da iyayensa suka bijiro da shi shekaran jiya na auren Addah. Da amsarsa da suke jira a gobe. Sosai Abdulkarim ya tsaya ya saurare shi da kunnuwan basira, kafin ya hadiye fushinsa ya soma zubo masa wasu irin tambayoyi da duk hikimarsa ta lauya bai san yadda zai yi ya amsa masa su ba. “Yanzu me ka ke so in yi?” Ya yi shiru, gabansa ya soma faduwa ganin yadda yanayin kawun Baban nasa ya canza gabadaya. Abdulkarim kuwa cikin mamaki yake, wai ashe sun haifi wani Da cikin zuri’ar Abdullahi Dakata da za su yi wa umarni ya tsallake ya yi gaba yana neman hanyar kubucewa daga yi musu biyayya a kan wata aba soyayyar banza? Akwai dan da suka so, suka wahala a kanshi irin Abdul’azeez? Akwai dan da tsohon Ambassadaya nuna wa soyayya a zuci da fili irin Abdul’azeez? Yanzu Abdul’azeez ya yi girman da ya yi ilmin neman hanyar kubucewa umarninsa? Yake ganin ya fi su sanin abinda ya dace da shi da wanda bai daceda shi ba? Shin uwa irin Maryam ta cancanci ‘ya’yan da ta wahalta wa haka su ki yi mata biyayya a girmansu? Sosai ya boye fushinsa, yake kallonsa da idanun rahma. Cikin kwanciyar hankali yake magana. “Na ce me ka ke so in yi?” Ya sake yin shiru duk plans din da ya tsaro ya kasa furta ko daya. Wani irin kwarjini kawun Daddyn ya yi masa. Abdulkarim ya jeho masa tambaya ta biyu, ganin ya kasa amsa masa ta farko. “Abincin da gidan su yarinyar suka ba ka na shekara daya kai ka roke su? Ko ko ba ka da kudin sayen abinci da hakan zai sanya auren diyarsu ya zama dole? Ita Maryam abincin shekara nawa ta ba ka?” Shiru Abdul’azeez ya yi yana da na sainin kawo kansa kotun shiga ba biya, fita da Allah ya isa. “Mu ture ta maganar abinci, wata nawa ta dauke ka cikin wahala da kaka-ni-ka-yi a karkashin mahaifarta? Ka san me ta jure a yayin fitowarka duniya? Wace irin dawainiya ta yi da kashi da fitsarinka? Me ta yi ta koya maka zama, rarrafe da tafiya a kan doron kasa? Wane irin jele ta yi zuwa asibiti a duk lokacin da ba ka lafiya? Bari in gaya maka abin da ba ka sani ba, ka kasance yaro mai yawan zubar da jini ta hanci (Nasal bleeding) wato ‘habo’, Maryam kullum tana asibiti don nema maka waraka. A duk sanda ka ke wannan ‘nasal bleeding’ din Maryam kuka ta ke yi tana share maka a gaban kowa da mayafinta da dankwalinta, don haka ina tunasar da kai da kakkausar murya da ka shiga hankalinka. Ka ba ni mamaki Abdul’azeez yanda ban taba zato ba, a tunanina duk cikin yaranmu babu mai hankalinka da kaifin basirarka, kullum kwatance nake wa su Sha’aban da kai ina cewa su yi koyi da kai, tukunna ma wai shin ni don Allah don Annabi da ka zo wajena ka gaya min, a matsayin ka kawo karar iyayenka,saboda Allah me ka ke so in yi maka a kan wannan umarnin da suka yi maka?Suke so ka rufa musu asiri ka yi musu biyayya kan abinda suke so?” Zufa ya rika sharewa irin wadda ta rika addabarsa a lokacin da yake gaban iyayen nasa suka yi masa nasu umarnin na auren Suhaana, yanzun ma da wannan masifaffen Kawun ya tsatstsare shi da manyanidonsayana jiran amsar bakinsa ita ta rika tsattsafo masa ta kowacce mabubbugar gumi ta jikinsa. Da ya sani da bai zo ba!Ya dauki lamarin da zafi fiye da iyayensa ma. Shi bai taba sanin Minister Abdulkarim ya iya fada haka ba, ga kisan mummuke mai kashe gwiwoyin mutum. Abdulkarim Dakata ya katse tunaninsa da lallashi. “Yi wa Allah ka gaya min me ka ke so in yi a kai Abdul’azeez, na yi kuskure da na tari hanzarinka, bayanin bakinka kawai na ji ban tsaya na ji role din da ka ke so in taka a kai ba”. Abdul’azeez ya dan nisa cikin jin sassauci. “Ba burina in ki yi wa Mammah biyayya ba Uncle, amma ni ma ta duba hanzarina”. Ya fada cikin yankewar buri da sagewar gwiwa. “Mene ne hanzarin naka?” “Ta bar ni in auri Mu’azatu, ta ba wa Usman yarinyar in Isma’el baya so, shi ma danta ne. Kuma ya fi daidai da ita, bai girmeta da yawa ba, ba ta isa aure ba, ta yi kankanta da yawa, sannan ba ta da asali, har gobe ba’a san ubanta ba. Wannan abun shi ya fi damuna, kyankyaminta nake yi Kawu, kamar yadda nake kyamatar zina”. Abdulkarim ya yi shiru. Hanzarin nasa ya dan taba shi. Da gaske ba su san ubanta ba, ba su san asalinta ba. Wannan abin dubawa ne, to amma su suka raine ta, sun san halinta sun san komai nata. Maryam ita ce uwa mafi kusanci da ita, inda tana da wata illa ko wani gibi ba za ta ce sai ya aura ba, if she is harmful ba za ta so hada jini da ita ba duk son da ta ke mata. Babu yadda za a yi a ce ta fi sonta a kansa. Ya san halin Prof. Bai da takurawa ‘ya’yansa, idan Abdul’azeez ya ce bai so ba zai taba takura masa ba, amma Maryam kaifi daya ce. Asali da dangi abin dubawa ne a aure tabbas. Amma nasa case din akwai bambaci tunda iyayensa su suka raine ta. Ya nisa a hankali cikin sassauci. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* AUREN KWANGILA 1 Page8 “Na fahimce ka Abdul’azeez, amma kada ka manta iyayenka su suka raine ta, in tana da wata illa sun fi ka sani. Sannan Ubangiji ba ruwansa da kana da hujja, biyayya ya ce dole ka yi musu, ka na so ko ba ka so. Don haka ka watsar da komai ka yi musu biyayya na tabbatar maka ba za ka yi da na sani ba. Za ka ga da kyau a rayuwa. Kada ma ka sake kawo zancen Usman ko Isma’el, sun fi ka sanin da zamansu suka ce kai suke so ka aura. Abdul’azeez ni gani nake wani gata ne Maryam ke son yi maka, kasancewarka mafi soyuwa a zuciyarta, kuma tana ganin ta isa da kai. Idan ta ba ka amana za ka rike, idan ta yi umarni za ka yi biyayyah, haba Abdul’azeez kada ka watsa mata kasa a ido, ake dauko Da daga gidan marayu a aura balle wadda mahaifiyarka ta raina tun cikin jinin haihuwa? Me ye amfanin karatunka na lauya in ba za ka yi amfani da shi wajen binciken abin da ya shige maka duhu ba? Za ka iya bin diddigi ka nemo mahaifin yarinyar nan daga inda mahaifiyarta ta shigo hannunku. Bayan wannan sai me ye matsalarka da mai sunan Addar?” Shiru ya sake yi, bai ga amfanin ya sake magana akai ba, tunda babu wanda zai fahimce shi. Magana ce ta SO; love... feelings.... devotions...... emotions.... to ba ya jin ko daya a kanta. Ba ya sonta ba ya kaunarta, bata da abinda zai kaunata. Bai da wani feeling a kanta ko da na kanwa, (sai ko na dan gida da ‘yar aikin gidansu). Don haka daga yanzu ya dinke bakinsa, ya daina wahalar da kansaneman taimakon kowa, they will never understand him; cewa yana cikin soyayya wadda ta hana shi gane kome suke son ya gane. They only want to excercise their power ta iyaye a kansa, su dakushe masa farin cikin rayuwa, zai yi abin da ya ga dama, zai nema wa kansa mafitar da za ta raba shi da wannan bakar kaddara da ake neman daura masa. Ya samu abin da zuciya da ruhinsa ke so (Mu’azatu) ba tare da ya batawa iyayensa ba, ba tare da ya bata wa kowa ba har ita yarinyar. A matsayinsa na wanda ya san hakkin dan Adam da ‘yancin da Allah ya ba shi ya san ita ma mutum ce kamar kowa, ba zai zama azzalumi a kanta ba. Ba zai bata wa iyayensa saboda ita ba, shawarar da zuciyarsa ta yanke masa ta karshe shi ne daidai. Mikewa tsaye ya yi, kansa a sunkuye ya zuba dukkan hannayensa a aljihu, “Ku yi hakuri Kawu, na yi alkawarin yi muku biyayya. Na yi kuskuren yin jayayya da ku, na amince zan aure ta Kawu, ku yi hakuri, ku sa min albarka”. “Allah ya yi maka albarkar duniya da lahira. Allah Ya shige maka gaba a kan duk abin da ka sa gaba, ko kai fa Abdul’azeez? Na ji dadi kwarai, that’s my grandson!” Ya fada yana bubbuga kafadunsa. Shi kuma ya yi murmushi. Har mota ya rako shi, bai koma office ba sai da ya ga hawansa kan kwalta da bacewarsa. ***** Washegari daidai wancan lokacin da suka zauna wato karfe goma na dare, yau din ma tun kafin cikar karfe goman Mammah da Daddy ke zaune a falon suna dakon shigowarsa. Goma na bugawa da minti biyar Barrister Abdul’azeez ya yi sallama ga iyayensa. Sosai Mamma ta bi shi da kallo, so ta ke ta karanto yanayin da yake ciki, fuskarsa kadaran-kadahan ta kasa karantar komai, sai dai ta fahimci ba ya cikin damuwa kamar wancan lokacin. Kyakkyawan sajen nan ya kara kwanciya a kan fuskarsa kamar wani bako daga Qatar. Shadda ce (Getzner) ruwan kasa a jikinsa, kansa da hula mai launin ruwan kasa mai haske. Dole duk macen da ta san ciwon kanta ta yi wa kanta sha’awar hada rayuwa da Abdul’azeez Dakata, domin baiwarwakin da Allah ya yi masa suna da yawa, don haka bata ga laifin wannan yarinyar ‘yar Lagos data yi masa kamun kazar kuku ba, gata take so ta yiwa kanta. Mammah ta fada a zuciyarta. Gefen kafafunta ya karasa ya zauna. Daddy ya dube shi yana murmushi. “Yau tun safe ban ganka ba”. Ya dan muskuta, “Na fita ne Daddy, ban jima da dawowa ba”. Sautin muryarsa kadai suka ji suka fahimci babu sauran damuwa a tare shi. A tare Daddy da Mammah suka sauke ajiyar zuciya. “To ya ya? Ina maganarmu ta kwana?” Prof. Dr. Hamzah Dakata ya tambaya cikin raha. Mammah ba ta tsoma baki ba. Ya sunkuyar da kai, “Mammah na amince ki aura min duk wadda ki ke so ko da sun kai goma, na hakura da Mu’azatu na karbi zabinki Mammah, ki yi hakuri da jayayyar da na yi da ke ranar bana cikin hayyacina. Mammah na amince, ku sa min albarka”. Kura masa ido ta yi cikin kallo na kurilla, ita dole so ta ke ta karanto zuciyarsa, da ta kasa fahimtar komai sai ta furta abin da ke zuciyarta. “Amma ya aka yi ka canza ra’ayinka haka da sauri Abdul’azeez? Na fa sanka farin sani, na sanka a kan ra’ayi da akidarka, anya babu wata makarkashiya a zuciyarka? Ba fa zan yarda a cutar min da Adda ba, daidai da kwayar zarrah!” Ya hadiye wani miyau ji kake, mukut. Mammansa sau tari haka ta ke kamar psychologist, she reads their minds easily, duk wani motsinsu ta sani. Ya kara zama serious ya sunkuyar da kansa. “Mammah dole ne in yi muku biyayya kowanne ra’ayi nake da shi. Na bi Allah, na bi umarninku. Zancen Mu’azatu na ajiye shi a gefe ba don na daina sonta ba, da ma iyayenta ba so suke su aurar da ita yanzu ba sai ta gama (Law School). Amma Mammah ita din ta yarda ta amince za ta aure ni?” Har yanzu kansa a sunkuye yake, bai dago ba yake yin maganar cikin tsanaki. Hajiya maryam ta ce, “Sunanta ne ba ka sani ba?” Murmushi ya yi, ya ce, “To Mammah sunayen nata ne sai mutum ya rasa na kamawa...” Dariya ya ba su sosai. “Zabi guda daya wanda ya fi kwanta maka a ciki ka dinga kiranta da shi, kai kadai”. Inji Daddy. Cikin alamun jin kunya ya sadda kai bai ce komai ba. Hajiya Maryam ta rufe zaman nasu da cewa. “Sai ka koya mata amincewa da auren naka, tunda ka fita hankali, daga ranar da aka daura muku aure”. ***** A daki ta samu Suhaana tana ninke fararen (innerwears) dinta da ta wanke tana jerawa a sif din da ta ware musu. Tunani ta ke yi a zuciyarta tun dawowarsu Nigeria Mommah ba ta kara yin zancen karatunta ba. Bayan ta san babban burinta shi ne ci gaba da karatun, tana matukar burin yau a ce ta zama wani abu a dalilin karatu, ta tsaya da kafafunta ta fuskanci rayuwa mai cike da kalubale da ke gabanta. Tun ba ta kawo haka ba ta san ita ba ‘yar Prof. Hamzah ba ce, ba ta san ubanta ba, ba ta san ta inda ta shigo hannunsu ba. Ba ta son yarda da gaskiyar da ke a bude “ita ba ‘yar Mommah ba ce”, amma dole ta yarda, rashin zama ‘yar Prof. Dakata na nufin rashin zama ‘yar Maryam Dakata, iyakar gaskiyar kenan. Ta share hawayen da suka cika mata ido da bayan hannunta, Mammah ta ce sai ta cika shekara goma sha takwas za ta gaya mata komai da ya kunshi rayuwarta. Tana so ta nemo uban nan da uwar nan nata ko ta samu cikakken farin ciki irin na kowa. Hakan kuma ba zai zama mai sauki ba sai ta yi ilimin zamani mai zurfi, ta yadda ba sai ta nemi taimakon kowa ba a sanda ta tashi aiwatar da wannan jan kalubale da ke gabanta. Cikin wannan halin na zurfin tunani Hajiya Maryam ta same ta, har ta zauna kusa da ita ba ta sani ba, sai da ta kai hannu ta kama nata ta rike gam cikin nata. A sanyaye ta sauke idanunta a kan Mammah kwalla cike da idanunta. Hankalin Hajiya Maryam ya tashi, ta ce. “Addah tunanin me ki ke yi haka har da hawaye? Har na shigo na zauna ba ki sani ba”. Ta kai hannu ta dauke hawayen ta kakalo murmushi. “Mammah ina tunanin yaushe zan ci gaba da karatu ne?” Hajiya Maryam ta yi jimm! Sannan ta girgiza kai, “Shi ne kuma har da hawaye? Kayya, in kuwa shi ne ki yi hakuri, rana ta farko da zan gaza wajen yi miki abin da ki ke so, sai dai hakan ba yana nufin ba za ki yi ba kwata-kwata a rayuwarki. Za ki yi idan mijin aurenki na so, kuma ya amince ki yi a dakin aurenki, ki yi hakuri Addahta, ina da dalilai na masu yawa da ba zan iya barinki karatun jami’a a gabana ba, na fi gane in bi umarnin Ubangiji in yi miki AURE sai hankalina ya kwanta ya tsumma a randa. Abin da kuma na zo in nemi amincewarki a kai kenan. Hafsatu aure zan yi miki”. “Aure Mommah?” Ta tambaya cikin mamaki, da alamun kuma cikin sautinta da fuskarta ba ta gama fahimtar me Mammah ke nufi ba. “Eh, aure irin nawa ni da Daddy, ki bar gidan nan ki koma gidan mijinki, ku rayu tare ki haifo min jikoki in yi ta raino. Ku yi zamanku lafiya ke da mijinki, mu da ke sai ziyara, haka Allah da manzonsa suka ce a yi wa kowacce ‘ya mace idan ta kai munzali, kuma kin kai, kin fahimce ni?” Idanunta suka yi rau-rau, gab ta ke da ta saki kuka, muryarta na rawa ta ce, “Mommah karatuna fa? Mommah in na rabu da ke da Baba Azumi ni da wa zan zauna?” Murmushin kwantar da hankali Hajiya Maryam ta yi mata tare da dafa kafadunta, cikin idanu ta ke kallonta. Kwayar idanuwanta na nuna zahirin kaunar da ta ke mata. “Kwantar da hankalinki Addah, aure abu ne da kowacce ‘ya mace ta gada, kuma gaba yake da kowanne burinta. Shi fa wannan karatun na zamani ba Allah ne ya ce a yi shi kafin a yi aure ba. Duka da haka shi ma abu ne mai amfani, amma ko kusa amfaninsa bai kai aure ba. Ki fahimci abin da na fada miki a baya dalla-dalla, za ki yi karatun jami’a idan mijinki na so, kuma ya amince a gidanki. Amma yanzu aure zan yi miki, za ki bar mu ni da Baba Azumi ki zauna a gidan mijinki yadda kowacce mace da ki ka sani ke zaune a gidan miji. Amma na yi miki alkawarin duk sanda ki ka so ki ganmu za ki ganmu, zan zo gidanki ko cikin dare ne kin ji Addahta?” Ta gyada kai alamar ta fahimta, sai kuma ta fada jikinta ta saka kuka. Bayanta Hajiya Maryam ke shafawa tana lallashinta. “Yi hakuri kin ji Addahna? Ba zan kai ki inda za ki cutu ba, ba zan bari a bata miki rai da gangan ba sai in ba na raye. Ki yi hakuri ki yi min biyayya yadda shi ma da ya fi ki shekaru ya yi mini. Na yi miki alkawarin insha Allahu dukkanku ba za ku yi da na sani ba, sai kun yi alfahari da wannan aure naku, sai kun gode min watarana”. Baba Azumi daga falo tana shara ta ke jin tashin muryar Mammah da alamun kukan ‘yar gidanta. Ta ajiye tsintsiyar ta taho. A bakin kofa ta tsaya tana kallon ikon Allah. “Kukan me ta ke yi? Ke fa abin kuka ba ya miki wuya, don Mamarki na shagwaba ki?” Murmushi Hajiya Maryam ta yi, “Wannan kukan mai dalili ne. Yau Mommah ta yi laifi dole ta ke lallashi, kukan aure ne na rabuwa da Mammah da Baba Azumi, ko Suhaana?” Ta daga kai ta ce, “Eh”. Duk sai ta ba su dariya. Mammah ta share mata hawaye, Azumi ta ce “To ai mijin na gida ne, ba za ki yi nisa da mu ba. Ni na taba ganin auren gata ma irin naki Hansai? Babban Yaya gabadaya fa, uban gida magajin gida, lauya na al’ummah na Hansatu bada kanka a sare, Yayan Isma’ila, Yayan Usmanu, Da daya tamkar da goma Mammah ta zabo miki duk cikinsu. Daina kuka kin ji? Yi farin ciki ki gode wa Mamarki, ita mai sonki ce”. Nan fa Hafsat ta hau zazzare ido tsakanin Mammah da Baba Azumi tana so su yi mata karin bayani, wane Babban Yayan Baba Azumi ke nufi? Sai dai ba ta samu komai daga karin bayanin da ta ke son jin ba don Mammah ficewa ta yi kawai tana murmushin wannan kirari da Azumi ta yiwa Abdul’azeez.Da yake tayi maganar da ita tun jiya. Inda ta bada goyon bayanta dari bisa dari da kyakkyawar addu’a. Baba Azumi kuma ta wuce ta ci gaba da shararta suka barta cikin ci-da-zuci, sakar zucci da tunanin zuci mai nauyi. Ba dai wannan ‘baren’ (total stranger) na cikin ‘ya’yan gidan nan ba? Ba dai wannan wanda ya fi kowa odd hali cikin gidansu ne ake nufin zai zama mijin nata ba???? ***** “Kina ina Mu’azatu?” “Har yanzu ina Apo, sai gobe zan bar abuja, mene ne? You sound worried?” “A ina zan same ki? Magana ce mai muhimmanci da ba ta bukatar distraction, gidan Anty kuma ba ya rabo da jama’a”. “To ko in zo office dinka yanzu? Sai direba ya kawo ni, ina ganin za mu iya tattauna kowacce irin magana a can”. Ta fada cikin faduwar gaba, jin muryar Abdul’azeez na rawa, abin da ba ta taba ji daga gare shi ba. “Alright” Kawai ya ce ya kashe wayarsa. Mota kirar matrix ta sauke Mu’azatu Rufa’i a Federal High Court da ke kan titin (OAU Quaters, Kashim Ibrahim Way Maitama, Abuja), cikin tafiyarta mai kama da tana taku a kan kwai ta karasa zuwa ofishoshinsu. Daya bayan daya ta ke wucewa tana duba sunayen da ke rubuce jikin wani dan karfe a saman kowacce kofa har ta zo inda ta ke nema. ‘Barr. Abdul’azeez H. Dakata’. Shi ke rubuce a saman ofishi mai lamba (24). Ta kwankwasa daga ciki ya amsa, ta murda ta shiga. A kan doguwar kujerar leather ruwan kasa yake zaune cikin daya daga kujerun tattaunawa da baki da ke ofishin. Sanyin air-condition ya ratsa ta kamar yadda ya mamaye ofishin da kamshin turaren mamallakinsa. Mu’azatu na mamakin son sanyi irin na Abdul’azeez a gida ne, a mota ne, a ofis ko yaushe za ka same shi ya kure A.C shi ba wanda ya yi rayuwa a kasar sanyi ba. “Koma ki yi sallama malama, sannan ki shigo”. Ya fada cikin sanyin murya. “Ai na yi knocking ka ce in shigo”. “To ni bana son knocking saboda ni ba arne ba ne, sau nawa zan gaya miki?” Ta zumbura baki, ta koma ta yi sallamar ya amsa. A ranta tana fadin “yana cikin damuwar ma ba ya fasa ba da order, order dai! Da kyar nan gaba in bai zama Alkali ba”. Kusa da shi ta zauna suka zuba ma juna ido, idanunsa sun kada sun yi jajir. Ba ta taba ganinsa cikin rashin nutsuwa irin na yau ba. Duk ya birkice kamar ba shi ba (smart-guy) mai tafiya da imaninta, yau har wani cukurkudewa gashin kansa ya yi ga wani gashin fuska ya karu na babu gaira babu dalili. “Wai me ke faruwa ne Abdul’azeez? You look worried. You sound worried, ni ma ka dugunzumar min da hankali, da ina da hawan jini na tabbata da yanzu kafin na iso ofishinnan ya hau”. Ta fada a jere ko numfashi ba ta tsaya ta shaka ba. Tana rufe baki ya ba ta amsa. “Duk a dalilinki ne Mu’azatu”. “A dalilina? To me ya faru?” “Kin yarda ina sonki Mu’azatu?” “Na yarda, amma me ya kawo wannan tambayar?” Ta fada da hanzari. “Na tambaye ki ne saboda ki yarda da ni, ki yarda da abin da zan gaya miki babu karya ko yaudara. Ba ni da nufin su gare ki shi ya sa na yanke shawarar gaya miki gaskiyar halin da nake ciki da iyayena a yanzu, kada ki ji a wani wuri daban ki yi wa zancen fassara a baibai ko ki yi tunanin na yaudare ki, amma in muka hada kai muka amince da juna za mu shawo kan mastalar, mu samu cikar burinmu a lokacin da ya dace da burin iyayenki. Kin yarda da ni Mu’azatu?” Jikinta a sanyaye ta ce, “I trust you ka sani, ko mene ne ka gaya mini zan fahimta. Amma don Allah kada ka ce Mu’azatu ba zan aure ki ba...!!!” Sai hawaye. Karo na farko da ya yi kuskuren kai hannu ya rungumo Mu’azatu a jikinsa. Nasa idanun na fidda kwalla. How he wish Mammah za ta fahimci karfin wannan soyayyar? Ba zai iya barin Mu’azatu saboda wata mace ‘yar uwarta ba, wadda ya tabbata ba ta da abin da ya fi na Mu’azatun, ba ta fita da komai ba. Sai ma dai ace bata kaita ba. Ko ma ta fitan shi son da yake wa Mu’azatu (has no reason), wato babu dalili. Abin da ya sani kawai yana sonta, ita ma tana sonshi, ba don uwa-uwa ba ce sai ya ce wannan abun da da ta yi masa zalunci ne. Ba ruwanta da feeling dinsa, ita dai kawai a biya mata tata bukatar. Kwalla mai zafi ta gangaro masa, ya yi saurin dauke ta kafin Mu’azatu ta gani. A lokaci guda kuma ya sake ta ya janyo ta suka kalli juna. “Ba zan taba cewa ba zan aure ki ba, it’s a promise. Zan aure ki komi runtsi, yanzu dai ki ba ni hadin kai ki ji damuwar tawa, kina kara min damuwa da fitar hawayenki Mu’azatu, bayan na kira ki ne don mu fahimci ta yadda za mu billowa matsalar, ba fa wata gagaruma ba ce (we can overcome it)”. Mu’azatu ta share hawayenta, ta ba shi hankalinta. “Mu’azatu, kin san girman iyaye, kin san karfin ikonsu a kanmu, kin san tsattsauran umarnin Ubangiji a kanmu na mu yi musu biyayya, Ya ce (Ubangiji)‘Wa qada rabbuka alla ta’abudu illa iyyahu Wa bil walidayni ihsaana’, Ya kara da cewa, ‘Wala taqul-lahuma uffin walaa tanhar humaa wa qul-lahumaa qaulan-kareema’(Isra’i). A wata ayar ya kara cewa, ‘Daga bautarsa sai kyautayi ga iyaye.......’ Allah (SWA) ya kara cewa ma mu dinga nema musu gafara ko suna raye, kamar yadda suka ji kanmu muna kanana. ‘Wakhfidh lahuma janahazzilli minar rahmati Wa qul rabbir-hamhumaa kama rabba yaani saghira... (Isra’i). Mu’azatu duka wannan kadan ne daga ayoyin Ubangiji da suka yi umarnin mu zamo masu kyautayi da biyayya a gare su, wallahi Mu’azatu duk da wannan sanin sai da na sa kafa na take, na yi PROTEST (tawaye). Na yi jayayya da su a kanki, na shiga na fita ta wasu hanyoyin duk don in kaucewa umarninsu in tsira da ke.......” Mu’azatu ta shiga girgiza masa kai alamar, “A’ah”. Ya ce, “Yes, ban yi nasara ba ai, don haka na amsa wa bukatarsu. AURE za su yi min Mu’azatu da wata macen ba ke ba.....!!!”. Girgiza kai kawai Mu’azatu ke yi, numfashi na neman dauke mata, tana neman shidewa. Tallafo ta ya yi ya rungume suna amfani da nasa numfashin. Kawai sai ga kira a wayarsa da ke gefe, juyawa yayi a hankali yana kallon sunan da ke yawo a fuskar wayar ‘Precious Mammah’. Da sauri ya saki Mu’azatudon gani ya yi kamar itace tsaye a kansa ta kama shi rike da macen da ba tashi ba, rike da macen da ba su halatta mashi ba. Bayan ture Mu’azatu da ya yi daga jikinsa har dada ja baya ya yi ya sanya rata sosai a tsakaninsu. Hannunsa na kyarma ya amsa wayar Mammah. “Kana ina?” Ta tambaya cikin muryarta mai sanyi. Kunuwanta na zuko mata kukan Mu’azatu. “Ina... ina... office Mam....mah...” “Idan ka gama da ita, to ka zo ka gana da ita wannan ita ma. I think is high time ku fara fahimtar juna lokaci yana kurewa”. Ta kashe wayarta tare da sakin tsaki, “Me ake da matan bariki? Bin namiji har ofis don rashin mafadi?” Ta fadi cikin bacin rai da tafasar zuciya. Anya wannan yarinyar ba za ta zame wa Hafsat barazana ba in an yi auren nan? Anya da gaske Abdul’azeez yake zai iya rabuwa da ita? Tunanin da ya cunkushe zuciyar Hajiya Maryam kenan. Shi kuwa Abdul’azeez a sanyaye ya ajiye wayar, kalaman Mammah tas! A kunnen Mu’azatu, kamar da gayya ma Maman nashi ta fada don ta ji, kamar ta bugo da gayya ne don sanin cewa suna tare a lokacin, ta tabbatar mata da abin da ya gaya mata. Kafin ya ankara sai ganin Mu’azatu ya yi ta kai bakin kofa ta kama ‘handle’ za ta murda. Yunkurawa daya ya yi, Mu’azatu ta ganshi gabanta ya kare kofar, ya sha gabanta. Kokari yake su hada idanu, amma ta ki. Kuka kawai ta ke yi. Ta gama gane irin auren da ake son yi masa, irin na yarinya (sweet 16) din nan da (Proffessional) wanda ya gama mallakar hankalin kansa, to ita zai rainawa hankali? Kamar shi za a yi wa auren dole idan ba yana so ba? Ko macen da ta yi karatu irin nasa ana yi wa auren dole balle shi namiji? Shi ne ya zauna yana tsarata yana jawo mata ayoyi shi ga Ustazu? Da wata makirar Mammansa mai muryar karuwai. Cikin tsananin fusata ta dube shi, “Ka ba ni hanya in wuce Malam, lest you regret knowing me (don kada ka yi nadamar sanina”. “Minti goma za ki kara min kacal, zan ba ki hanyar...” Cikin gunjin kuka ta ce, “Bana son kara jin kowacce kalma daga gare ka, Allah ya hada kowa da rabonsa.....” Ya runtse ido. Ji ya yi saukar kalaman tamkar digar dalma a zuciyarsa. “Duk kokarin da na yi da wanda nake yi da wanda zan yi DOMINKI abin da za ki ce min kenan Mu’azatu? A halaka fa zan saka kaina don in tsira da ke Mu’azatu...” Ta zame kasa, kan gwiwoyinta ta kifa kai tana kuka. Shi ma ya bi ta ya durkushe. “Wallahi zan aure ki Mu’azatu komai rintsi. Ki barni in yi auren don in zauna lafiya da iyayena. Na yi miki alkawarin na SHEKARA DAYA ne da wasu watanni, lokacin kin kammala BL dinki”. Ta dago rinannun idanunta jike da hawaye, ta dube shi. Bai iya karya don ya burge ba! Wannan halinsa ne da ta dade da sani. Ba ya yi maka karya don ya faranta maka, kai shi kwata-kwata a halayyarsa babu karya, yana fadin abin da ke zuciyarsa ne kawai ba tare da tunanin zai yi maka dadi ko akasinsa ba. Tana son Abdul’azeez, tana son komai nasa, in ta ce za ta iya barinsa ga wata mace ‘yar uwarta, mai halitta irin tata data tabbata da cewa ba ta fita da komai ba ta fadi ba nauyi. Abin da ba za ta iya ba shi ne, tarayya da wata a son nasa, ko mallakarshi tare da wata. Sai ta yi shiru da kukan tana goge hawaye, tana hadiyar zuciya. “Kin amince da abin da na fada Mu’azatu? Zan yi auren, zan rabu da ita a lokacin da iyayenki suka shirya aura min ke, zan aure ki”. Kallonsa ta yi cikin ido, tana kara jin wutar sonsa na fizgarta, losing him easily is not easy (rasa shi cikin sauki ba abu ne mai sauki ba). Ta samu muryarta na fita cikin tangardar harshe, “Amma... amma..... ka san ba zan iya hada ka da wata ba ko? Ba zan iya zama da kishiya ba...!” Girgiza kai ya yi, “Ni ma ba zan iya zama da mata biyu ba. I know... na ce miki rabuwa da ita zan yi in lokaci ya yi, ki yarda da ni, ki amince da kalamaina. Bana magana don in bata lokacin ki da nawa. Ungo hannuna mu kulla alkawari...”. Ya mika mata karamin yatsansa, yana kallon cikin idanunta da yanayin da ta ke masifar so. Wani tattausan murmushi ya subuce mata. Ta mika nata karamin yatsan, suka sarke su suna jifan juna da wani mayataccen murmushin SO. Sun amince an halicce su ne domin junansu. Don su zama abokan rayuwar juna, babu wata SUHAANAH da ta isa ta shiga tsakanin wannan soyayyar. ***** To mai karatu, kai ka yarda da hakan? Anya kaddarorin rayuwa suna tafiya yadda muka tsara su ne? Anya Abdul’azeez bai yi kuskure ba? Abin da yake shirin yi me sunansa? Bravity ga Mu’azatu? Dishonestness ga Mammah? Unfairness ga Suhaanah? Ko ko me yake nufi??? **** Mu karasa a littafi na 2, kada ku damu, tare suke. Taku har abada Sumayyah Abdulkadir Buk 2 SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Sanin cewa Mammah na jiransa a gida ya sa ya ki shiga gidan da wuri. Bayan rabuwarsa da Muazatu ya tuko mota a hankali kamar wanda kwai ya fashewa a ciki, ya taho gida. Da ya zo kofar gidan bai karaso ba ya kashe motar daga nesa, ya kifa kai a kan sitiyarin motar ya rufe idonsa. A wannan dan lokacin ya tsara komai, ya tsara kalaman da zai yi wa Suhaana amfani da su. Ya yayyafa wa zuciyarsa ruwan sanyi a kan ta rage tsanar yarinyar, ta sake da ita yadda za ta fahimci duk abin da yake nufi. A kananan shekarunta yana da tabbacin shawo kanta ta yarda da tsarinsa ba zai yi masa wuya ba. Sai da ya tabbatar ya shirya kalaman a kan harshensa ya yi bitarsu sun zauna sosai, sannan ya tashi motar a hankali ya karasa gida. Mammah da ke dokon shigowarsa tana jin sanda maigadi ya bude masa get ya shigo ya adana motar a mazauninta. Ya tattaro wayoyinsa da brief-case hadi da kamfutar laptop ya fito. Yana rataye da falmaran din bakar suit din jikinsa a kafadunsa. Bai yi tsammanin ganinta a falon ba, don ya san karfe tara ta ke shiga barci, yanzu kuma tara har da rabi. Ya sanya a ransa Baba Azumi zai sa ta yi masa magana da Addar, don haka ya shigo kansa tsaye. Ta cika ta yi fam a kan kushin din falon, ya ja ya yi turus! Da suka hada ido, ta sassauta fushin da ke kan fuskarta, cikin sanyin murya ta ce, Na dauka ba ka kai wa magriba a waje in ba da wani muhimmin case a hannunka ba? Ya nisa a hankali, Yi hakuri Mammah wallahi baki na yi suka tsayar da ni, sai yanzun na samu kaina. Ta so ta ce da shi, Baki ko budurwar banzarka? Ta ga cewa shiga personal-lifedinshi ba girmanta ba ne, sai kawai ta mike ta nufi hanyar turakar maigidanta tana fadin, Ka je study room Addar za ta zo yanzu. A ransa ya ce, Ai a bari na ajiye kayan hannuna, na ba wa cikina hakkinsa, na dan yi freshen up kada ta ganni a jigace haka ta san cewa ta shigo rayuwata, ta takura ta da yawa. Ita dai Mamma ta yi wucewarta, shi kuma ya nufi dakinsa. Sai da ya gama duk abin da zai yi, ya yi wanka ya shirya cikin T. Shirt mara nauyi (black colour), an yi rubutu da farin fenti dara-dara (ARMANI). Ya hada da bakin wandon (jeans), ya taje sumar kansa, ya feshe jikinsa da turaren Eternity Moment.Zuciyarsa ma na hango masa EternityMoment dinsa da Muazatu kamar yau ne, in har yarinyar nan ta yarda su rufa wa juna asiri. Ganin karfe goma na dare ya sa shi yin saurin fitowa ya janyo kofar dakin. Ya karasa cikin gidan ya shiga dakin Baba Azumi da zummar ya tura ta ta kira Suhaanar. Ya yi sallama daga bakin kofar, ta amsa tare da yi masa izinin shigowa. Lekawa ya yi kadan yana fadin, Ba ki yi bacci ba? Sai ya ga Suhaanar kwance bisa cinyoyinta tana lallabe mata sassalkan gashin kanta. Ba mu yi ba, muna dakon dawowarka ne, sai kuma Adda ta ce in yi mata kalba kafin ka dawo. To ga ni na dawo, kuma ina jin barci. Ku yi hakuri da kalbar nan haka. Suhaanah ta mike ta lalubi dankwalinta ta daura. Ya wuce study room din da Mamma ta yi umarni, ya zauna yana jiranta yana kuma duba agogon hannunsa. Hafsat ta dubi Baba Azumi cikin damuwa, Idan na je bayan ina wuni sai me zan ce masa? Baba Azumi ta juya kai cikin murmushi, Ni ma ban sani ba. Haba Baba Azumi, ba ku koya min abin da zan ce ba za ku tura ni in yi hira da shi? Ta fada kamar za ta yi kuka. Baba Azumi ta kafe ta da ido, Ni da wa kenan? Ta yi shiru, ta sunkuyar da kai. Jikinta ya bata tayi rashin kunya. Ita me ya sa ba ki yi mata wannan tambayar ba, sai ni marainiyar wayonki ko? Yi hakuri. Toh, tashi ki je yana jiranki, kin ji ya ce bacci yake ji. Ta mike a kasalce ta yafa mayafin abayar Oman ruwan makuba da ke jikinta, kusan shigarta kenan dogayen riguna kala kala da wuya ka ganta da atamfa ko leshi sai in zasu Kano, a cewarta zani yana mata wahalar daurawa shikuma lace nauyi yake mata, ta nufi dakin karatun nasu. Kanta a kasa ta yi sallama ta shiga. Ya dago a hankali yana kare ma sigarta kallo. Doguwa ce, siririya, kamannin Habiba sun kara fitowa a jikinta, sai dai zaa kira ta mai kuruciya da gogaggen jiki fiye da Habiba sanda ta ke raye. Kuma Habiba ta fita kaurin jiki. Kwakwalwarsa ta soma daukan caji tana tuno masa wata hira ta karshe da ya yi da mahaifiyarta..... Rai-rai-rai hirar ke dawo masa... anya tunaninsa a kan Addah gaskiya ne? Hafsat BA SHEGIYA BA CE... Inda amana shi zai gaya wa kowa cewa da ubanta. Sai dai me? He is not after that (ba wannan ne a gabansa ba), tashi rayuwar ce, ba ruwanshi da rayuwarta. Ta dade da zama, ta gaishe shi bai ji ba. Ko ya ji bai amsa ba, ba za ta iya tantancewa ba. Ba ki iya gaisuwa ba? Ya tambaye ta bayan ya dawo daga duniyar tunaninsa. Na ce ina wuni tun dazu ba ka amsa ni ba. Ta fada fa accent dinta mai nuna har yanzu Hausar ba ta gama daidaito a bakinta ba, yaren Dutch (flemish) ya riga ya daddatsa harshenta. Taushin muryarta kawai ya kara masa kwarin gwiwar za ta amince da duk abin da ya zo da shi, akwai innocence intonationa cikin muryarta. Sake gaisuwar zan amsa yanzu. Ta dan saci kallonsa don tabbatar da shi din ne Yayan su Halim din nan, ko ba shi din ba ne? Wancan ko a murya ba shi da kirki, wannan a cikin muryarsa akwai sassauci. Ina wuni? Lafiya lau, kun wuni lafiya? lafiya alhamdulillah. Ya yi dan jim kafin ya ce, Mammah ta sanar da ke aure za ta yi mana ko? Ta sanar da ni. Ta amsa kamar cikin rada, ba don ya kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da ba zai ji ta ba. To ke me ye raayinki? Ba tare da ta dago ta dube shi ba, ta amsa. Hawaye nuna son ci kowa a idanunta. Ni ba ni da wani raayi sai nata, ni abin ikonta ce, ni mai biyayya ce ga dukkan umarninta. Sai ya ji yar kunyar kansa ta kama shi. Ba ta haife ta ba, shi ta haifa, ita a shirye ta ke da ta yi mata biyayyar, shi da ta haifa ya gaza. Shiru ya ratsa, kafin ya kira ta a hankali, Hafsah! Wani irin sauti ne mai taushi da ba wanda ya taba kiran sunanta da shi a duniya, don haka ta dago don ganin wanda ya kira ta da shi din. Abdulazeez Hamzah Dakata ne. Like father like son. Ta fada a zuciyarta. He looks so much like his Dad. Ba ta zurfafa kallon nasa ba, ta sunkuyar da kanta, ba ta zaci yana da sassauci haka ba a yadda ta sanshi a baya, duk da dai ta fahimci a kanta ne kawai yake zama tough din a kan sauran kannenshi ba haka yake ba, shin ko hakan na da nasaba da cewa don ita ba jininsa ba ce, ba ta da mahaifi? Za ta so watarana ya amsa mata wannan tambayar. Mene ne babban burinki a rayuwa? Ina nufin bayan auren da Mammanki ke son ki da shi, me ki ka fi so a rayuwarki? Ta dan daga kanta sama alamar tunani, kafin kalaman su fito a nitse daga bakinta. In ci gaba da karatuna, karatu mai yawa har PhD. Ya tsaida idanunsa a kan ta. Sai kuma me? Ta dan yi nuku-nuku ta kasa fada sai motsa baki ta ke yi. “Hafsah feel free with me, bayan matsayina na Yayanki ni din kuma yanzu mijinki ne in Allah ya yarda. Ina so ki saki jiki da ni ki gaya min me ki ke so a rayuwarki komai wahalarsa ko tsaurinsa? Ta dan samu nutsuwa kadan, ta waiga ta tabbatar babu kowa cikin dakin karatun, daga su sai Allah! Ta saci kallonsa kadan, sannan ta ce, Ina so....inaso in nemo mahaifina a duk inda yake, na san mahaifiyata ta rasu, Halim ya taba gaya min ta rasu ne wajen haihuwata, amma shi baa sanshi ba, ba a san inda yake ba. Na sha tambayar Mommah sai ta ce in bar zancen sai na yi shekara goma sha takwas, yanzu kuma shekaru na sha bakwai. Abdulazeez ya nutsu yana saurarenta, da ta gama, ya sarke yatsunsa cikin junansu, yana kallonta kanta a sunkuye. Da kyar yake gane abin da ta ke cewa da Belgian harshenta, amma duk da haka yana ganewa, ya ce. Hafsa, na ji dukkan bayaninki, na kuma fahimta. Na farko na amince zan barki ki ci gaba da karatu, da kaina zan cike miki JAMB da ake yi a nan Nigeria, am sure za ki haye daga nan zan kai ki jamia ki zabi duk abin da ki ke so ki karanta. Burinki na biyu ganin mahaifinki ko? Ta daga kanta a hankali tana wasa da yatsun hannunta. Na yi miki alkawari ni da kaina zan nemo miki shi insha Allahu. Na san garin da yake. Ta dago kanta da sauri, ta ware manyan idanunta a kansa. Amma ta kasa magana. Da gaske nake Hafsah. Har yayye ne da ke guda uku, amma ban san maza ne ko mata ne ba. Kawai sai ya ga hawaye ya gangaro kan kundukukinta, masu dumi, wasu na korar wasu. Mamaki ya kama shi ainun, amma bai bar hakan ya nuna a kan fuskarsa ba. Na yi tunanin abin da za ki ji dadi ne, amma sai in ga kina kuka? Ta sunkuyar da kanta, sannan ta share ambaliyar hawayen da bayan hannunta. Ni ma ban san me ya sa ni kukan ba, amma watakila kukan farin ciki ne. Ya ce, Yadda zan zama sanadin farin cikin nan naki, nake rokon ke ma ki zama sanadin nawa farin cikin da ba mai samar da shi gare ni sai KE! Ta dago jikakkun idanunta ta kalle shi. Ni me nake da shi da zan saka maka wannan farin cikin da za ka ba ni? Iya tunanina ba ni da komai. Ya sauko daga kujerar da yake kai, ya zauna dabas a gabanta. Idonsa ya kai ga yatsun hannunta da suka sha adon jan lalle yan sirara da su. Ya dawo da kallonsa kan fuskarta cikin nutsuwa, ya ce. Ba abin da za ki ba ni Hafsah, kawai amincewarki nake nema mu yi planning contract marriage (AUREN KWANGILA) tsakanina dake na tsawon shekara daya da wasuwatanni kadan. Contract Marriage? Kana nufin auren da Mommah ke nufi mu yi, da ma (contract marriage) ne? Ta tambaye shi cikin yamutsa fuska na rashin fahimta. Ba haka nake nufi ba. Bana so ko kadan Mammah ta san wannan zancen. Zai tsaya ne a tsakanina da ke kawai, zan cika miki manyan burikanki na rayuwa da izinin Allah kafin cikar waadin nan. Ke ma kuma za ki taimaka min wajen cikar nawa burin, ki samu farin cikinki, ni ma a karshe in samu nawa ba tare da kowa ya san me muke ciki ba har zuwa karshen waadin. Ban gane ba har yanzu, mene ne waadin? Sannan ta ya ya za a yi hakan ba tare da wani ya sani ba? Mene ne ma naka burin? Meyasa Mammah bata gaya min hakan ba? Ta fada cikin tsananin shiga duhu, fuskarta da yanayinta gabadaya sun nuna hakan, sun bayyana tsananin rudun da kalamansa suka jefa ta. Gaskiya hausarta da shekarunta sun yi kadan su fahimci abin da yake nufi kai tsaye. Tana bukatar ayi mata gwari-gwari. Hafsah ina da wadda nake so in aura ne, sunanta Muazatu. Mahaifinta Malamina ne shekarunmu biyu tare kenan, mun fahimci juna mun amincewa juna. Sannan mun yi wa juna alkawarin aure komai runtsi to the very end. Amma Mammah ta ce ba ta amince ba, Daddy ya mara mata baya sun ce ke zan aura ba ita ba. Hafsah kamar yadda ki ka fada min burikanki a yanzu, da yadda ki ke matukar sonsu, da burin ganin cikarsu. Ni Muazatu ce burina a yanzu. Bayan ita duk wasu burirrikana na rayuwa zan iya ce miki Allah ya cika min su (Alhamdu lillah). Za a yi mana aure kamar yadda Mammah ke so, mu zauna gida daya in sanya ki a makaranta, ki yi ta karatunki. Aurenmu babu takura, domin kowa zaman kansa zai yi kamar yadda dai ki ke zaune yanzu a gaban Mammah, gida kawai za mu canza bayan shi ina tabbatar miki ba abin da zai canja. A cikin wannan lokacin zan nemo miki inda mahaifinki da yan uwanki suke. Da gaske ne mahaifiyarki ta rasu a kan idona, ba zan taba mantawa ba. Ba zan ce miki komai a kai ba, ki jira Mammah ta gaya miki kamar yadda ta yi alkawari. Idan na yi miki hakan ina ga na gama cika burikanki ko? Sai ni ma ki cika min nawa burin wanda ba shi da wahala, abu ne mai sauki Hafsah, shi ne ki amince in lokacin da na dibar wa Muazatu na aurenta ya cika za mu rabu, wato ZAN SAKE KI. Mu hadu mu bai wa Mammah uzuri da cewa halinmu bai daidaita ba, ko kuma haka kaddara ta tanadar mana. Mun rabu ne ba don ba ma son juna ba, sai don kowannenmu ya kasa jure halin dan uwansa. A wannan lokacin na san ba su da wani zabi sai su barni in auri Muazatu, ke ma ki auri wanda ki ke so. Ga mahaifinki da yan uwanki a gefe da kuma karatunki, ina fatan kin fahimce ni? Ta yi shiru na tsawon lokaci, idanunta na hango mata ranar da za ta kammala karatunta ga mahaifinta da danginsa a gefe, dasu Mammah kamar yadda aka yi wa Abdulazeez a (Law school). Hakika ranar za ta zamo ranar madaukakin farin ciki a gare ta wadda babu irinta... Me ki ka ce Hafsah? Ta tsinkayi muryar Abdulazeez mara amo kuma mai taushi a can tsakar kanta. Ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi mai nisan zango. Ta yi ajiyar zuciya, sannan ta daga kanta a hankali ba tareda wani dogon tsinkaye ba ta ce, Na amince. Ya gyada kansa shi ma, Haka nake son ji, idan da amincewarki to komai zai tafi daidai babu tangarda har zuwa lokacin da (contract) din zai kare. Mammah ba za ta yi irin fushin da ki ke tunani da mu ba, za ta fahimce mu, in har ki ka gaya mata da amincewarki aka yi komai, kika nuna mata ke ki ka zabi sakin don ba za ki iya da halina ba. Ni ma na fada mata na kasa jure halinki ne. Sai dai ina so wannan ya zama babban sirri a tsakaninmu Hafsah. Sirrin da babu wanda za ki fada wa mun yi shi duk duniyar nan. Sannan bayan rabuwarmu insha Allahu zan zamo mai taimaka miki ta kowacce fuska a rayuwarki, na yi wannan alkawarin, I promised. Sai da ta daga kanta alamun ta fahimce shi, sannan ya mike yana sanya wayoyinshi a aljihu. Ina ga iyaka abin da za mu tattauna din kenan, dare ya yi. Ki je ki kwanta. Ya mike ya nufi kofar fita daga dakin karatun kai tsaye without giving her a second look(ba tareda ya kara kallontaba). Yaa Azeez! Ya ji ta kira shi a hankali. Sai ya ja birki ya tsaya a inda yake dab da kofar, hannunshi na kan handle din kofar. Cike da mamakin kiran sunansa da ta yi. Ba ta taba yin hakan ba ko da wasa a kafatanin rayuwarsu. Duk da cewa ta kira sunan ne kamar yadda sauran kannenshi ke fada amma a kunnenshi sai ya ji kamar wani abu daban ta fada ba sunan nasa ba. Ya juyo ya fuskanceta daga inda yake tsaye ba tare da ya dawo ba. Ba ta ko motsa daga inda ya barta ba, har zuwa lokacin kuma tana ta cakuda kyawawan yatsunta cikin junansu. Kanta a sunkuye. Na gode!. Ta furta tana mai dago kai ta kalle shi. Ji ya yi kamar zuciyarsa ta yi tsalle ta fice daga kirjinsa ta dawo, da gaske ne (shes so innocent) in ba haka ba me ya yi da har zaa gode masa? Shi a nasa tunanin ma in zaa dubi lamarin da idon basira ai babban laifi zai aikata a gare ta (saki a wajen diya mace). A gefe guda ga kuma tsallake maganar mahaifiyarsa da zai yi, ai kuwa bai cancanci godiya ba ta kowanne bangare. Sai dai ko ta wajen Muazatu wadda zai tsallake umarnin iyayensa a kanta saboda farin cikinsu shi da ita. Bai san me zai ce mata ba, saboda haka kawai ya daga kai sannan ya juya ya fita daga dakin karatun. Ya koma dakinsa idonsa cike da bacci da gajiya. Ko da Muazatu ta kira shi don su yi hirar daren da suka saba (midnight call) cewa ya yi da ita, ta yi hakuri bacci yake ji. Kuma ya yi magana mai yawa saboda ita a daren nan. Ya yi alwala ya yi nafila rakaa biyu, ya roki Allah ya rufe bakin Hafsah kar ta tona masa asiri a wajen Mammah komai runtsi. Duk da dai ya lura yadda ta ke son cika burikanta, zai iya danne komai, wanda haka yake har zuciyar Suhaanan. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* ***** Kwana ta yi tana juya maganganun da suka yi na karatunta da nemo mahaifinta a zuciya da kwakwalwarta. Su kadai ta ke tunani a matsayin matsalolinta yanzu a rayuwa, ga shi ta samu wanda ya yi alkawarin dauke mata su. A kan me kuwa ba za ta yi masa yadda yake so ba ita ma? Auren ko kadan ba ya kanta dama, bata da wani hopea kansa ko experience kan abin da ya kunsa sosai balle har ta sa shi a lissafinta. Ta amince ne dama saboda Mammah don ta amince wa ranta babu abin da Mammah za ta nema a wajenta ta kasa yi mata, amma sam ba ya gabanta. Sai ga shi a yanzu ya juye ya zama sanadin alkhairi a gare ta, sanadin da zai kai ga cikar burikan rayuwarta (karatu da mahaifinta). Ta faranta wa Mammah, sannan ita ma ta samu farin cikinta. Har ila yau, shi ma ya samu nasa cikar burin. A iyaka dan kankanintunaninta, me ya fi wannan kwangilar sauki da riba kuwa??????? ***** Gadan-gadan Tsohon ambasada Hamza Atiku da maidakinsa Hajiya Maryam suke shirye-shiryen auren yayansu, auren da suke so ya bar tarihi a dangi don haka ba karamin shiri suke masa ba. Soyayyar Abdulazeez da Muazatu sai abin da ya karu, kullum suna tare a waya, ko ta biyo shi office ko shi in ya tashi ya je can inda ta sauka gidan Antinta har ta koma gida Lagos ba abin da ya sauya. Ba ya yi mata zancen komai game da aurensa, ita ma ba ta tambaya, ba ta taba neman sanin yarinyar da za a aura masa din ba, shi ma bai taba yin wannan gwanintar ba. Zai iya cewa daga ranar da suka yi magana ta farko shi da Suhaana ko a hanya ba su kara haduwa ba, duk da cewa gida daya suke kwana. Yana riga kowa fita a gidan, sannan ba ya dawowa da wuri. Mammah ma ba ta kara damuwa da su kebe din ba don su kara fahimtar juna, shirye-shiryen biki kawai ta ke, hankalinta kwance, don ta lura yar damuwar da Suhaana ta ke ciki bayan ta yi mata zancen auren tun daga ranar da suka yi magana ita da Abdulazeez ta rabu da ita, ta saki ranta tana ba ta hadin kai a kan komai. Biki ya rage saura sati uku tuni an bugo I.V an fara rabo cikin dangi. A yadda Mammah ta tsara za su taho Kano ne, a nan za a yi komai, liyafar cin abincin dare (dinner) kawai za a yi a Abuja washegarin daurin aure. Kullum za ka ganta tana waya da mutanen Dakata ana ta shirye-shirye. Ta fannin Daddy kokari yake ya kammala ginin da yake yi wa Abdulazeez a Estate din (Sun-City). Wani kyakkyawan Mansion mai hawa daya da ya dauki shekaru yana gininsa yana dakatawa tun yana Ambasada, yanzu ya maida hankali yana so a kammala komai cikin lokaci. Mammah zaune a kayataccen falonta cikin kwalliya ta kece raini kamar kullum. Waya ta ke yi da aminiyarta ta cikin Abuja, Hajiya Halima matar Controller, magana suke yi a kan babarbariya mai gyaran jiki da Hajiya Haliman za ta turo ta fara gyara amarya daga yau har ranar da za a kai ta dakinta. Wannan shi ne gudunmawarta. Sosai Mammah ta yi godiya, ta daga murya ta kira Hafsa wadda ke dakinta tana gyaran kayanta da aka kawo daga wanki da guga. Ta ajiye rigar hannunta ta fito ta tadda Mammah a falo, tun kafin ta zauna Mammah ta ce. Ki yi shiri gobe za mu wuce Kano, kuma Hajiya Halima ta turo mai gyaran jiki za ta zo ta fara miki daga yau, tare da ita za mu tafi kano. Suhaana ta ce, Mommah me jikina ya yi da za a gyara shi? Na yi dauda ne? Dariya Hajiya Maryam ta yi, ta rike hannunta cikin nata. Kullum Adda ta tsaf ta ke, kal-kal kamar tarwada saboda wanka. Shi gyaran aure daban yake, ba irin wanda ki ka saba yi ba. Hafsat har tausayin Mammah ta ke ji a ranta in ta yi duba da yadda ta dora ranta a kai ta ke kuma zumudin auren nasu. Ba ta taba ganin abin da Mammah ke farin ciki da shi a duniya irin auren nan nasu ba. Ya ya za ta ji a ranta idan ta gaya mata na wucin gadi ne ba mai dorewa ba ne, ta kyale wata mai gyaran jiki? Ai ko Ya Azeex bai ce ta boye ba, ita a karan-kanta ba za ta iya fada ba. Karfe shida na yammacin washegari suka isa birnin Kano, ta Dabo ci gari, jallabiyya babbar hausa, yaro ko da me ka zo an fi ka, mai Dala da gwauron Dutse, Kano tumbin Giwa, ta sarki Ado Allah ya yi maka rahma. Abdulazeez bai taho tare da su ba, yana Abuja sai ana saura kwana daya daurin aure zai taho tare da tawagar lauyoyin chambarsu. Mai gyaran jiki mai suna Fannah ta shiga aikinta a kan Suhaana. Eh, lallai, ta yarda da abin da Mammah ta ce, shi gyaran auren daban yake, kuma wannan da ake mata ba karami ba ne. Ganin yadda cikin kwana uku fatar jikinta ke wani irin salki da sheki. Ga Addar babu kawaye sai yayan dangi ne suka zama kawayen nata su Halima yar Anty Luba, Saima da Khalisa yayan Anti Mariya da Anty Furairah duk da ta dan girme su don cikinsu ba wadda tayi candy. Gayya sosai Hajiya Maryam da kannenta suka yi. Ta bangaren maza ma ba karamar gayya Dr. Hamza ya yi ba shi da sauran yan uwansa. Baa maganar Minister Abdulkareem Dakata ya yo babbar gayyata ta manya zuwa daurin auren jikan nasa. An yi kamu ranar alhamis, jumaa aka yi wunin biki a nan mainhouse nasu. A yammacin ranar wato ana I gobe daurin aure Abdulazeez da abokan aikinsa suka iso. Tsohon Minista Abdulkareem Dakata mai masaukin baki ya yi musu masauki a gidan saukar baki na Tahir Guest Palace. Washegari asabar karfe goma daidai na safe daruruwan jamaa suka shaida daurin auren Abdulazeez da Hafsat a kan sadaki naira dubu hamsin lakadan, wanda ya fito daga aljihun Abdulkarim Dakata. Aka yi adduoi masu yawa aka shafa. Daga nan maza suka wuce liyafar cin abinci acan Tahir wadda Dr. Hamza ya shirya, mata kuma suna shirin tafiya Mothers Nighta daren ranar a (FABS EVENT CENTRE) wanda Hajiya Maryam ta shirya. Rana ta farko da fuskar Hafsat-Suhaana ta soma daukan make-upna zamani a rayuwarta. Ta koma tamkar wata sabuwar kyakkyawar halitta ta daban wadda aka baro daga cikin kwai don kyau da ban shaawa. Hatta Anty Zuwaira da ke adawa da auren a zuciyarta sakin baki ta yi tana kallon Hafsat, ta kuma yarda har ranta yarinyar kyakkyawa ce tun asali, kawai ta raina asalinta ne har gobe tana ganin wautar Hajiya Maryam na hada wannan auren, yaro irin Abdulazeez yarinya yar asali, yar gata, yar babban gida ta dace da shi ba yar mai aiki ba. A raayinta fa. Amma tunda ita ta haifi abinta wa ya isa ya yi magana? Ta yi tsaki ta dauke kanta daga kallon yarinyar. Wadda Hajiya Maryam ta shirya cikin wani rantsattsen leshi baki mai ratsin silver, goggoron kanta silver, dankunne da sarka, takalmi da purse duka silver. Duk wanda ya daga kai ya dube ta sai ya ce, Masha Allah. Hannunta cikin na Mammah wadda ita ma ta sha nata adon cikin koreni tattausan leshi, kawayenta su Anty Halima na take mata baya cikin tasu shigar ta alfarma suka shiga motoci zuwa (Fabs Event Centre). Taron na mata ne zalla, don haka babu bukatar zuwan ango da abokansa. Sai dinnerta gobe da za a yi a Abuja ne zasu halarta, washegari lahadi za a yi ta (by- couple), wato kowa da mijinta. Iyakar (programmes) din da suka tsara kenan, kuma alhamdu lillah komai ya kayatar. An ci an sha, an yi hotuna da vedio don tarihi aka watse. Suna fitowa daga mota za su shiga gida Abdulazeez da wasu abokansa biyu, Barrister Abdallah da Barrister Adebayo na tsaye a dakalin kofar gidan suna magana. Yana cikin farar shadda kal (hilton) da babbar rigar rataye a kafadunsa. Hasken fitilar kofar gidan ya haske masa yaran yammatan dake fitowa daga mota, fuskar Hafsat tarwai a tsakiyar yammatan. Ya gyara tsayuwa yana kallonsu suna shige shi daya bayan daya zuwa cikin gida. A ransa ya ce, ina ruwan (sweet sixteens), gaba daya kawayen ma wadanda duk ya sansu a dangi yara ne kamarta. Abin ya ba shi dariya sosai, sai da ya yi murmushi. Adebayo ya ce Wow! Abdulazeez you have a beautiful wife, looking gourgeous. Abdulazeez ya galla masa harara, ita ma ya juya ya galla mata tata, ya dauke kai suka ci gaba da maganarsu da Abdallah. Ta ga hararar da ya yi mata sosai, don wajen akwai wadatar haske duk da dare ne. Jikinta ya yi sanyi da ma a sanyayen yake. Tun lokacin da aka tabbatar mata an daura mata aure jikinta ya mutu, bakinta ya mutu. Mammah ta lura da hakan, amma ba ta ce mata komai ba. Is normal ai, mace ta canza sanda aka daura mata aure. Nauyi ne babba ya hau kanta, ta zama karkashin mulkin wani, ta zama UWA, ai kuwa nauyin ba karami ba ne. Washegari da safe kowa na gidan ya tashi ne da shirin wucewa Abuja. Karfe tara daidai motocinsu suka tashi zuwa Abuja dauke da amarya shi ma angon da tashi tawagar sun kama hanya, zuwa azhar suna cikin Asokoro gidan tsohon Ambasada Hamza Atiku. Nan kowa ya ci abinci aka huta. Su Anty Halima suka wuce gidan amarya don kara gyaggyara komai, wato jeren da suka tsaya maaikatan kamfanoni suka yi. Sai shirin tafiya dinner wadda za a yi a (A-class). Ana yi mata kwalliya, amma gabanta faduwa yake yi jin ana fadin har da angon da abokansa za a yi dinar, idan ta tuno da muguwar hararar da ya zabga mata a Kano ba laifin tsaye babu na zaune. Amma sai Abdulazeez ya bada mamaki, har aka yi dinnar aka kare bai ba da wata matsala ba. Ko nuna wata kafa da zaa gane baya maraba da auren Hafsat. Da aka tashi ne dai ya bi abokansa bai tsaya bi ta kanta ba ko motar da ta kawo su tare, sai ita kadai aka dauko a motar aka dawo da ita gida. Sai shirin tafiya kai amarya. Nan fa ake yinta. Yau zaa raba Suhaana da Mommah, Suhaana da Baba Azumi. Kuka ta ke kamar na fitar rai, ko Mammah ta ji tausayinta ta barta su ci gaba da rayuwarsu tare. Ita kanta Hajiya Maryam dauriya kawai ta ke yi, amma zuciyarta ta gama karyewa. Baba Azumi dai sai kewaye ta shige ta kulle, sannan aka iya fitar da Hafsat zuwa falon Daddy. Albarka kawai ya sa mata ya ce su je da ita, zai biyo ta gidanta ya yi mata fadan. Kawai sai aka ga Mammah ta dauko mayafi ta yafa ta kama hannun Hafsat zuwa mota ta ce da ita zaa je. Su Hajiya Halima na tsokanarta wai surukar sabon qarni. Murmushi kawai tayi tana shanye hawayenta. Sannan ne Hafsat ta rage kukan motoci suka kama hanyar Sun-city. A daidai wannan lokacin Abdulazeez yana dakinsa na gidansu. Ya kulle kansa yana waya da Muazatu, kuka ta ke yi masa sosai cikin matsanancin tashin hankali. Gani ta ke ta rasa Abdulazeez ta gama, yau zai shiga dakin amaryarsa shi ke nan fa! Shi kuma lallashinta yake yana kara tabbatar mata da alkawarinsu. Amma ina! Muazatu jinsa kawai ta ke, ta kasa yarda duk da ta san har zuciyarsa yake nufin alkawarin, amma tunda ta ga hotunan bikin da yarinyar da yake cewa ba ya so din a wayoyin abokansa hankalinta ya yi mugun tashi. Ta dauka wata bakauya aka aura masa da farko, ko wata wadda ba ta amsa sunan mace ba, amma idonta ya gane mata Hafsat-Suhaana kwance a kafadun mahaifiyarsa, ta kuma gansu tare a hotunan sun sha anko sun durkako (A-class) inda aka yi dinar kamar don su aka halicci juna. Tuni ta daina yarda da kalaman bakinsa duk da cewa duk cikin hotunan da aka nuna mata din babu inda ta ga ya kama Hafsat ko ya mannu da ita don nuna soyayya. Da ya gaji da lallashinta, amma ta ki daina kukan, sai ya yi shiru. Amma bai kashe wayar ba, bai san kuma da kalaman da zai yi amfani da su Muazatu ta yarda da shi ba. A ganinsa duk wasu kalamai da yake da su sun kare. Ta sanshi ai, ta san halinsa, ta san babu karya cikin halayensa. Ya yarda ya auri Hafsat ne don ya samu hanyar aurenta, kuma babu soyayyarta ko kankani cikin zuciyarsa. Me ya sa ba za ta yarda ba? Shirun nasa sai ya kara tunzura ta, ta ci gaba da gursheken kuka. Zuciyarsa ta dinga bugawa fat-fat-fat, tsigar jikinsa ta dinga tashi. Enough, is enough Muazatu, ki gaya min yanzu me ki ke so na yi? An zo gabar da ta ke so don haka ta sassauta kukan.Abdul na dade ina yi maka tanadin kaina, ina tattala maka budurcina, ban taba wasa da shi ba. Ban taba shaawar bada shi ga waninka ba, kullum burina ya zamo kai ne za ka karbe shi cikin girma da daraja. A yau wata ta riga ni samunka, da ka kusance ta ta gama janye min kai, komai rashin son da ka ke mata. Wallahi in ka kusance ta na hakura da kai har abada ko kai ne autan maza. Zan roki Allah ya cire min sonka ko ya zama ajali na a kan in yi sharingdinka da wata, ni wannan ne kawai damuwa ta. Shiru ya yi kamar ruwa ya cinye shi. Shi kansa bai san me ya sa ya yi shirun ba. Muazatu ta baro zance wanda shi kansa ya girmi kwakwalwarsa. A ganinsa bai kamata ta shiga wannan hurumin ba duk da akan-kansa bai taba kawo yiwuwar hakan cikin rayuwar auren kwangilar da zai yi da Hafsat ba, amma ai matarsa ce, koda yace da Hafsat kayyadadden zama zasu yi iyayensuda suka daura auren da tsarkakakkiyar niyya suka daura shi kamar yadda addinin muslunci yayi umarni, ba su san da wani abu bayan wannan ba, don haka ko ta ina aka je aka dawo sunan Hafsat matarsa, an taba gindaya wa miji hukuncin kada ya kusanci matarsa? Koda yake son Muazatu shi fa ba sakarai ba ne da zai zauna mace ta gindaya masa abin da ta ke so ta ce dole sai ya bi ba. Don haka ransa ya baci sosai da maganar Muazatu kawai sai ji ta yi ya kashe wayar. Matsanancin tsoro da mamaki suka taru suka lullube Muazatu. Ta ciro wayar daga kunnenta ta duba sosai, ya kashe. Tunda suke tare bai taba kashe mata waya ba, me hakan ke nufi?? SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama ***** Yan kawo amarya sun ajiye ta sun juya, Mammah kuwa da dabara ta samu ta fice. Aka barta daga ita sai Harira yar Baba Azumi a dakin da aka tanada don mai aiki a gidan. Harira matar aure ce da yaya hudu, lokacin da Baba Azumi ta gayyato su biki daga Sokoto Mammah ta yaba da hankalinta da kazar-kazar dinta don su suka yi ta tsaftace gidan lokacin biki da rabon abinci, ta roki Baba Azumi ta barta ta zauna da Adda ta debe mata kewa zuwa sati biyu kacal. Kafin lokacin ta saba da sabuwar rayuwarta ta saki ranta. Baba Azumi ta amince don haka aka bar Harira a gidan tare da Hafsat. Tunda Harira ta shige dakinta ta rufe kofa ba ta sake fitowa ba. Hafsat-Suhaana ta ci kukanta ta gaji har ta gode Allah, hawayen suka tsaya don kansu. Kanta ya sara, ya soma ciwo ta kwanta lamo! A kan filo ta rufe jikinta da mayafinta, ta takure a can gefen gadon ta soma ajiyar zuciya. Ko da ya kashe wayar da suke yi da Muazatu komawa ya yi ya jingina bayansa da kofar dakin nasa. Ya lumshe ido zuwa dan lokaci ya bude ya zura wayarsa a aljihunsa. Lokacin ya tuna su Abdallah suna kofar gida suna jiransa su raka shi gidansa. Toilet ya shiga ya yi wanka ya canja kayan jikinsa da wani sassalkan ya din filtex (milk colour) ya taje sumar kansa, ya sanya hular da ta dace da kayan nasa, ya daura agogon (swatch) a damtsen hannunsa ya fesa turare har kala uku. Ya janyo manyan jakunkunan da ya hada kayansa na dakin nasa ya sanya takalmi sabo dal! Ya fito da jakunkunan sannan ya janyo kofar dakin nasa ya fita. Gidan babu kowa a falo, duk sun dawo daga kai amarya sun gaji sun kwanta, gobe kowa zai kama gabansa. Har ya fice bai hadu da kowa ba, ya tadda abokansa a waje zaune kan fararen kujerun da ke harabar gidan suna hira. Yana fitowa suka mike suka karbe shi jakunkunan suka shiga motocinsu suka wuce (Sun-city). Kofar gidan akwai maigadi wani Danfulani da Daddy ya samar musu, ya bude musu (gate) suka shigo da motocinsu, suka yi parking suka firfito. Dukkaninsu Lauyoyi ne na gwamnati da masu zaman kansu. Shi ya bude kofar falon suka shiga, kowa ya nemi inda ya yi masa ya zauna a lafiyayyen (European parlor) da Mammah ta shirya, in ka wuce shi za ka tadda (African parlor) wanda bai kai shi girma ba, wanda ya ji shimfidun gargajiya da adon carpet din fata na jikin bango da su tum-tum abin gwanin ban shaawa kai kace sun hada jini da sarauta ne. A cikin wannan (African parlour) kofofi ne guda biyu wadanda suka kunshi dakunan barci biyu, daya nasa, daya na matar gidan. Daddy ya kawo shi ya ga gidan tun sanda ake gininsa don haka ya san kansa. A kowanne dakin barci akwai makewayi, kicin (madafi) yana gab da shiga kofar falon farko, wato ba a cikin falon aka yi shi ba. Akwai yar doguwar baranda a kofar shigowa falon, wadda aka aje fararen tukwanen fulawoyi masu kyawun gani da fararen kujerun roba. Harabar gidan za ta iya cin motoci uku ba tare da kowacce ta gogi yar uwarta ba. Dakin maigadi na jikin gate, dakin mai aiki yana daga bayan ginin falon, wato sai an fito daga main building din an zagaya ta baya za a tadda dakin mai aiki. Yadda su ESQ Abdallah suka nemi wuri suka zauna cikin tausasan kujerun falon haka shi ma ya nema ya zauna. Barrister Taufeeq shi ne karshen shigowa yana janye da jakunkunansa yana daga tsaye ya ce, Dare fa ya yi, ka shigar da kayan Malam ka fito mana da amarya mu saya maka bakinta, mu yi muku addua mu koma namu gidajen. Harararsa ya yi ya mike ya karbi jakunkunan ya yi ciki. A ransa ya ce, wai su saya min bakinta, to in yi me da shi? Tsakanin dakunan biyu zai yi rantsuwa bai san wanne aka ba ta ba, wato ba zai iya cewa ga nasa ga nata ba. Tsayawa ya yi yana kallon kofofin guda biyu da kallo mai kama da harara. Ba wata amarya da ya yi niyyar kai musu su yi abin da za su yi, kawai su tafi. Ya ce ta zo cikin abokansa ma ai sai ta raina shi. Ya yi kundunbala ya murda handle din kofar dama ya tura jakunkunansa. Cikin ikon Allah shi ne nasa, ya jefar da jakunkunan ya fito ya tadda su. Yaya ina amarya ka fito kai kadai? Taufeeq ya tambaya, sauran kuma suka bi shi da ido kamar sa cinyeshi. Ta yi barci. Ya samu bakinsa da fadin hakan ba tare da ya shirya ba. Duk suka mike, To sai mu wuce, randa muka zo idonta biyu mun yi muku adduar dare ya yi. Ni na yafe adduar taku in ba za ku yi min ni kadai ba. Dariya suka yi, Taufeeq na fadin, Ka fadi gaskiya Malam. Suka wuce Ahmad na fadin, Da gaskiyarsa fa, wannan aladar babu kyau ko kadan. Mai kishin iyalinsa ba zai yarda da ita ba. Baki ya kama yana kallon Ahmad cikin takaici, Kishi? Ya ambata cikin sigar tambaya da nauyin baki. ESQ Ahmad bai ba shi amsa ba, ya daga masa gira ya yi murmushi, ya ba shi hannu. Amma Abdulazeez ya noke ya hana shi nasa. Ka yi min sharri, sannan ka ba ni hannu? Wuce ka tafi. Na gode zan rama. Suka yi tafiyarsu kowannensu da irin dariyar da yake yi masa. Da wannan haushin ya dawo ciki. Ya rasa abin da zai yi. Har ga Allah bai yi niyyar shiga inda ta ke a daren nan ba, sai kawai ya shige dakinsa ya rufo, ya dauki (remote) ya kunna naurar sanyaya daki ya hau shirya kayansa, daga jakunkuna zuwa sif din jikin bango. Sai karfe biyu na dare ya gama, ya yi sallar nafila ya kashe wuta ya kwanta. Wayarshi da ya bari a kunne a gefen kansa ita ta tashe shi da kiran Muazatu da assalatun fari. Kansa ya yi masa gingirin sabida bacci da gajiya ba zai iya magana ba don haka ya matsar da ita gefe ya koma ya ci gaba da barcinsa. Wannan ya kara daga hankalin Muazatu wadda yadda ta ga rana haka ta ga dare, cikin matsanancin tashin hankali. Sai karfe biyar da rabi alarm din da ya saita ya tashe shi, ya dauro alwala ya gabatar da (rakaatainil fajr), sannan ya bada farali. Haka kawai ya ji ya kamata ya tashe ta ta yi sallah in ba ta tashi ba, ko ransa na so ko ba ya so. Dan karamin tsaki ya yi, sannan ya mike daga inda ya yi sallah. Haka kawai an dora masa nauyin mutum yana zaman-zaman sa. Har zuwa lokacin wayarsa na ci gaba da ruri, jinjinawa naci irin na Muazatu ya yi, in ya tuno yadda suka yi sai haushinta ya sake kama shi, ya kasa amsa wayar. Da ya ga ba ta da niyyar daina kiran sai ya kashe wayar gabadaya ya mike ya nufi dakin Hafsat. Kwankwasawa ya yi sau biyu ya saurara babu amsa, ya sake (knocking) har yanzu babu motsinta, sai kawai ya murda kofar ya shiga a sike, ba tare da tunanin komai ba. Tana lullube cikin bargo bakidayanta, zazzabi, masassara da ciwon kai sun taru sun rufe ta tun daren jiya. Allah kadai ya san yadda ta yi ta kawo yanzu. Gabadaya ta rufu ko don yatsanta babu a waje, sai karkarwa ta ke. Shi kansa bargon da filon da ta ke kai karkarwa suke. Ya lura da hakan, ya dan yamutsa fuska. Ba ki da lafiya ne? Daga cikin bargon ta daga kai, bai san ta yi ba, haushi ya soma kama shi, ba ya son shiga shirginta ko kankani, kuma ba ya son yana magana a kyale shi. To kuma ta dukunkune cikin bargo bai san halin da ta ke ciki ba, tana ta faman karkarwa wanda ke nuna bata da lafiya. What could he do? He actually dont know. Yana wannan sake-saken ya jiyo motsin mutum a falo. Da sauri ya juya ya fito. Da farko har ya so ya tsorata don bai yi zaton akwai wani mahaluki a gidan bayan su ba, kawai sai ya ga mace a tsakiyar falo da tsintsiya a hannu. Gari ya dan soma haske wanda ya ratso daga fararen curtains din falon ya haska masa matar sosai. Da mamaki ya ce. Daga ina? Harira ta zube tana gaishe shi da sakkwatancinta. Da sauri ya amsa, so yake ya ji daga ina ta billo. Sunana Harira, yar Baba Azumi ce. Ya yi ajiyar zuciya, a take ya ji kamar an yi masa rahama. Ya wuce dakinsa yana mata magana ciki-ciki. Ki shiga ki duba ta, nake jin ba ta da lafiya idan akwai bukatar taimako na zan fito anjima ki sanar da ni. A cikin ransa in ban da godewa Mammah ba abinda yake yi da ta samar da third party a tsakaninsa da Hafsat, da ina zai sa ransa? Zuciyarsa ba za ta juri shiga harkarta ba, sannan zai je koina hankalinsa kwance ya dawo sanda yake so ba tare da tunanin ya ajiye wani ba. Kowa ya ci gashin kansa. Harira ta shiga da sallama, amma Hafsat ta kasa amsawa, ta daure dai ta yi motsi daga cikin bargonta. Harira ta isa gaban gadon ta yaye bargon, sai Hafsat ta kara dunkule jikinta. Karkarwa ta ke sosai, wadda ta bai wa Harira tsoro. Abinda tayi zato ba shi ta gani ba. Tun kayan data zo dasu ne a jikinta har sarka da dan kunne suna nan a muhalli su. Ta hau gadon ta ciccibo ta, ta taimaka mata ta shiga bayi ta yi fitsari, ita ta yi mata alwala ta ce, ko a zaune ne ta yi sallah sai ta gaya wa maigida su je asibiti, ya ce inda matsalar rashin lafiya a sanar da shi. Ta ba ta katon mayafi ta yafa, ta shimfida mata darduma. Daga zaune ta yi sallar. Harira ta taimaka mata tana daga zaune ta canza su zuwa doguwar riga yellow da mayafinta ta kamo ta suka fito falo, ta zaunar da ita a (three seater), tana dunkule jikinta cikin karkarwar jiki kanta cikin cinyoyinta. Tun Harira tana kallon kofar dakinsa da tunanin zai fito, har ta hakura da kallon kofar tasa ta mayar kan baiwar Allah wadda ke cikin wani hali na neman taimako na masassara da zazzabi mai zafi da matsanancin ciwon kai. Ita ba abun ta je ta buga masa kofa ba tunda bai ba ta umarnin hakan ba. Haka ta zauna shiru, ta tallafo Hafsat jikinta. A daidai lokacin ya murdo kofar dakin nasa ya fito, lokacin gari ya idasa wayewa sosai. Kallo daya ya yi musu ya dauke kansa wayar da ke hannunsa ta fara ruri. Ba ta da lafiya ne? Ya tambayi Harira. Zazzabi ne ya rufe ta, ina ga gajiyar biki ne. Ya wuce gaba yana amsa wayarsa, bayan ya ce da ita, Ku biyo ni mu je asibiti. Harira ta kamata, ta taimaka mata suka bi bayansa. Baya suka shiga duk su biyun. Ya tada motar a ransa yana fadin, Lallai direba ya samu. Ya ja dan karamin tsaki. Yarinyar ta faya langwai, shes not strong anymore kamar lagwanin risho. How could he be the husband of such a fragile and delicate woman? Hes bold and energetic,yana son jarumar mace kamarsa ba dangin ta-kitse-ta-narke ba. Asibitin da file din gidansu yake ya kai ta wato DIFF. Nan da nan likitoci suka karbe ta, ashe tana ma da file da su bai sani ba. Yadda Mama ba ta sakaci da lafiyarta tun dawowarsu Abuja ta ke kawo ta check up lokaci zuwa lokaci na nimoniyarta. Kulawa ta musamman suka shiga ba ta a daki na musamman. Ya nuna wa Harira inda za ta zauna ya yi tafiyarsa gida, ya manta da su. Wanka ya yi, tare da yin shirin (office) don shi ba wani hutu da ya dauka don bai dauki kansa ango ko sabon aure ba. Yana nan a (single Abdulazeez) dinsa, he will never answer the namemarried sai ranar da Muazatu ta zamo matarsa. A office ya tadda sabon case mai tsauri, don haka ya zama (occupied) bai kara tunawa da wata Suhaana ba. Aiki ya dukufa yi kain da nain kamar yadda ya saba a kullum. Sai da Suhaana ta samu barci zazzabin da ciwon kan suka sauka, likitocin suka fito suka kyale ta. Suka ba wa Harira izinin shiga da umarnin kada ta yi wani kwakkwaran motsin da zai tashe ta, sai ta tashi don kanta. Tun Harira na kallon kofa tana tsammanin shigowar Abdulazeez har ta gaji ita ma barci ya yi awon gaba da ita a kan kujerar da ta ke zaun a gaban Hafsat. Ba ita ta farka ba sai ana kiran sallar azahar. Ta bude ido ta kalli Hafsat da ke barci ta ga ta tashi itama tana kwance ne kawai lamo a kan filo. Ta ce, Hafsatu kin tashi? Kai ta daga mata. Nurse ta turo kofa ta shigo da keken magunguna, ta dubi Hafsat ta yi mata murmushi, Kin tashi? Ita ma kai aka gyada mata. Ta dubi Harira ta ce, Ki hada tea ki bata mai kauri, sannan in ba ta magungunanta. Harira ta ware ido tana kallon dakin, babu komai na ci a dakin. Ta rausayar da kai ta ce da Nos din, Don Allah ko za ki taimako da shayin? Maigidan nata bai dawo ba tunda ya kawo mu. Nos din cikin mamaki ta ce, Ya zai kawo matarsa ba lafiya ya tafi bai ajiye muku komai ba? Harira ta yi shiru, don ita ma abin ya ba ta mamaki. Amarya ce fa, amarya guda! Da aka kai masa jiya-jiya? Za ta iya tunawa ko sallama bai yi mata ba da zai tafi. Ta ce da Nos din, Wattakila uzziri yarrike shi, kiddai taimakko mata da shayin. Nos din ta fita a harzuke, can ta dawo da shayin a kofin. A wajen wasu marasa lafiyan ta karbo. Harira za ta kama Hafsat ta tashi, ta dakatar da ita ta tashi da kanta. Nos ta ba ta shayin ta karba tana sha a hankali, kamar ba ta so. Sai da ta shanye ta ba ta magungunan da ruwa, ta ce ta koma ta huta. Ta sa hannu a wuyanta da goshinta, zazzabin ya sauka sai zufa ta ke. Ta ce, Good, ki kara hutawa zuwa yamma in Doctor ya zo ya kara ganinki za ku iya tafiya gida. Ta amsa daga can kasan makoshinta, Toh. Karfe shidda na yamma Abdulazeez ya tashi aiki. A matukar gajiye ga yunwa, coffee kawai ya sha tun safe. Ya harhada komatsansa da system zuwa black robe dinsa da wig ya zuba a kujerar gaban motarsa. A hankali yake tuki idanunsa na lumshe sabida gajiya, a kan hanyarsa ya gifta ta asibitin da ya zube su Hafsat. A take ta fado masa a rai, ya tuno da su. Da hanzari ya yi reverseya shiga asibitin yana fadi a zuciyarsa. Haka kawai an dora wa mutum nauyi, yana fama da kansa. Ni kaina kulawar nake bukata. A yadda na kwaso gajiyar nan kulawar mace nake bukata, ba ni in yi ta fama da ita ba. Sosai ya yi dogon tsaki, amma a take ya yi istigfari cikin zuciyarsa a lokacin da zuciyarsa ta tambaye shi, Wa ka ke wa tsakin? Daga shi sai bakaken suit din jikinsa ya fito kansa babu hula. Cikin takunsa na nutsuwa ya nufi cikin asibitin. Ya murda kofar dakin ya shiga da sallamarsa can kasan makoshi. Doctor da Nos din nan ya tarar a dakin suna kan Hafsat. A fusace Nos Hindatu ta dago ta dube shi don ta kudure a zuciyarta sai ta kare wa mijin yarinyar nan Hafsat tanadi idan ya zo, don hatta abincin rana ita ta ba su. Amma me? Kwarjini da kamalar Abdulazeez Hamzah Dakata sai ya disashe ganinta ya kashe kuzarinta, ya warware mata duk wasu kalami da ta shirya na cin mutuncinsa. Fuskarsa a daure ta ke tamau, ya ba wa likitan hannu suka yi musabiha. Likitan ya ce, za su iya tafiya gida ya rubuta musu sallama yanzun nan, don ta warware, stressne kawai wanda ba ta saba da shi ba. Ba sai ya biya bill ba, yana cikin billdin gidansu. A takaice ya yi masa godiya ya juya zai fita, sai kuma ya kalli Harira a fizge, Ina jiranku a mota. Da sauri ta mike tana yafa mayafi, sosai ta ke jin shakkarsa ba ta san me ya sa ba. Yana da tsare gida sosai kuma da alama ba ya son wargi. Hafsat da kanta ta mike ta yafa mayafin doguwar rigarta ta sauko daga gadon ta zura takalminta suka bi shi a baya. Tunda ya shigo idanunta suka sauka a kansa sau daya, ta ga yadda ya yi murtuk da fuskar nan ba ta kara marmarin kallon inda yake ba, kuma da ma ita ba gwana ba ce a kan kallon nasa ba, ba tun yau ba. Abu ne da ta horu da shi tun tana karama; ta ganshi ta sunkuyar da kai. Da ma ya tula shirginsa a kan kujerar gaban motar don haka baya suka shiga dukkansu, kuma ko kujerar (empty) ce babu fuskar zamanta kusa da shi. Ko da wasa ita ma ba za ta fara ba. Ko da suka iso gida ya kwashi shirginsa ya kule a dakinsa, ba su kara ganinsa ba. Zama suka yi zugum-zugum a falo daga ita har Harira, kowacce ta yi tagumi cikinta na kugi. Zuwa yanzu Harira ta fahimci wannan auren da matsala, ba auren SO ba ne. Don ta lura ita ma amaryar ba ya gabanta. Amma dai ko ya ya ne a shekarunsa ya kamata a ce ya san cewa, akwai hakkin ciyarwa a kansa. Ta dubi hafsat sai ta ji tausayinta ya kamata. A ganinta wannan salihar yarinyar mai kyau da kamala ta wuce auren RASHIN SO! To ba ta san wace irin kaddara ke tare da ita ba. Mikewa ta yi ta nufi kicin don ta ga ko za su samu abin da za su ci. A daidai wannan lokacin Abdulazeez ya fito. Ya yi wanka ya sauya kayan jikinsa zuwa kananan kaya. Rike yake da mukullin motarsa da wayarsa ya wuce Hafsat a falon ba tare da ya ce mata uffan ba. Ba ta tsammanin ma ya kalle ta ya fice. Wata irin ajiyar zuciya ta saki ta sauke tagumin da ta yi ta mike ta nufi dakinta, ta ajiye mayafinta ta fada toilet ta sakar wa kanta showerna ruwa mai dumi. Ruwan na sauka a jikinta a hankali, sai ta ke ji kamar yana wanke mata zuciya, yana tafiya da yar damuwar da ta samu kanta a ciki tun shigowarta gidan. Rashin kulawar Abdulazeez gare ta bai dame ta ba ko kadan, tunda ta fi kowa sanin wane irin aure ke tsakaninsu. Horon yunwa da ta soma cin karo da shi a cikin auren shi ya so ya taba zuciyarta, musamman da yake ga mutum a tsakaninsu ko don ita ai ya rufa asirin rashin son nasa gare ta. Tana zaune a gaban madubi tana shafa ta ji ana dan kwankwasa mata kofa. Rigar wanka ce a jikinta ta tawul ta kame gashin kanta a tsakiya da katon (hair-bound). Shigo. Kawai ta ce, don ta san Harira ce. Murda kofar ya yi ya shiga, ya tsaya daga jikin kofa hannayensa duka biyu rike da fararen ledoji guda biyu. Ta cikin madubi ta ga wanda ya shigo din, sai ta kasa juyowa ta yi kasa da kwayar idanunta. Ajiye ledojin ya yi ya juya ya fita tare da rufo mata kofar. Sun kusa gwabza karo da Harira wadda ta taho rike da plate shake da jallop din taliya, ta ja gefe da sauri ta ba shi hanya ya wuce. A ransa yana fadin, Abincin ma sai an dafa mata, gata mugun abu. To da babu wannan matar ni zan dafa kenan? Ko kuwa ana nufin kullum in je restaurant in sayo abinci sau uku a rana? Mtsew! SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Yau yana (office) da laasar ya samu wayar Mammah, ta ce da ya dawo ya dauko Harira da kayanta ya kawo mata ita za ta koma Sokoto. Mijinta yayi waya ta koma. Muryarsa ta nuna damuwa a sailin da yake cewa. Mammah da kin bashi hakuri zuwa gaba kadan, na ga alama suna jin dadin zama da junansu, kin ga ni in na fita tun safe sai karfe shida nake komawa gidan, tana debe mata kewa. Mammah a dan hasale ta ce, Sanda na kawo ta kai ka ba ni shawara? Ko kuwa mace da aurenta sai ta dawo gidanku da zama? Ya yi murmushi, Aah, ba ni ba ne, kuma ai dama ba nufina ta dawo kwatakwata ba kamar two months haka, lokacin ta saba. To yanzu ma ban nemi shawararka ba, ka dauko ta ka kawo min ita na ce, in ka ga dama ka kwana ba ka koma gidan ba, ai zaman aure ne mu ma da haka muka saba a namu gidajen. Za a yi yadda ki ka ce Mammah. Ta kashe wayarta, ya ajiye tashi a gefe cikin zuciyarsa yana jinjina rigima kala-kala irin ta mahaifiyarsu. A nata bangaren Hajiya Maryam Hamza Dakata murmushi ta yi tana rike da wayar a hannunta, ta dubi Daddy da ke gefenta ta gaya masa yadda suka yi da Abdulazeez. Ya ajiye takardun dalibansa da yake (marking) ya dube ta sosai. To ke me ya sa za ki raba su da mai aikin?Na san ba wata waya da mijinta yayi don naji Azumin na gaya miki ya tafi fatauci ne Shagamu Ta gyara zamanta tana fuskantarsa ta ce, Daddy, daga baya ne na fahimci na yi kuskure da na tura ta. Ba aure irin na Adda da Abdulazeez ake sanyawa third-party ba, in hakan ta kasance ba za su yi irin shakuwar da nake so su yi ba. Miji na tausaya wa matarsa in ya ga hidimar gida da ta abincinsa ta yi mata yawa, har ya yi marmarin dauke mata wasu hidindimun idan ya san cewa ya barta a gida tun safe har yamma ita kadai, zai fi damuwa da komawa gida cikin lokaci ya ga halin da ta ke ciki, ko ya dinga kiranta a waya sabanin in ya san akwai wani tare da ita. Jinjina kai Daddy ya yi, ya ci gaba marking dinsa yana mamakin Maryam, ya ce, To sai yaushe kuma za ki barmu mu je mu gansu, nace in bazaki ba ni zani kin hana, ko ki kira ta a waya ki ji lafiyarta? Allah kadai ya san yadda ta ke cikin damuwa da wannan takunkumin naki. A nan kuma dariya ta yi, ta kafe shi da kyawawan idanunta, Manta da su Daddy. Sai ranar da Abdulazeez a kan karan-karansa ya ga ya dace ya saya wa Suhaana waya. Mu kuwa sai ta shekara zamuje. ***** Zaune ta ke a kan sallayarta bayan idar da sallar isha tana jan cazbaharta cikin istigfari, ta jiyo sallamar Harira daga bakin kofa. Juyawa ta yi suka hada ido, ta ganta ta sha lullubi dauke da katuwar (Ghana must go) dinta. Da sauri ta karashe lazimin ta shafa adduar cikin kulawa ta ce, Aunty Harira ya ya dai? Tana mata kallon mamaki. Harira ta rausayar da kai, Hansatu Allah ya sada mu da alkhairi, zan koma gidan Mammanku ta turo a dauke ni. Gaban Hafsat ne ya bada wani irin damm! Zuciyarta wadda da ma a karye ta ke kullum ta sake karyewa. Rasa me za ta ce ta yi, Harira na ta yi mata adduar fatan alheri, da zaman lafiya ita da mijinta ba ta iya ta amsa ba, sai jin (horn) din Abdulazeez suka yi, wanda ya sa Harira sungumar jakarta ta wuce. Wani kuzari ya shige ta da ta tuna watakila rabuwarsu kenan har abada ya kamata ta yi mata alheri ko ya ya ne, domin hakika ta ji dadin zama da Harira, mace mai saukin kai da sanin yakamata, mara shisshigi da saido. Ta dade da fahimtar zaman da ta ke yi da mijinta ba zama ne na soyayya ba, amma ko da wasa ba ta taba tambayarta wani abu a kai ba. Kokari ta ke ta sanya ta a hanyar yadda za ta kyautatawa Abdulazeez ko ba zai kula ta ba. Kullum sai ta tsaya ta ga sun shirya masa abinci sau uku a rana, mai rai da lafiya. In zai fita sai ta ce, ta raka shi da (basket) din karin kumallonsa, haka in ya dawo za ta ce ta fita ta kwaso kwanukan daga bayan motarsa, ta yi masa sannu da zuwa ko ranta ba ya so. Girki kawai ta sani, sai wanka da tsaftar jikinta, amma gyaran gida Harira ce. In ta ce ba za ta yi kewarta ba, ko ba ta ji dadin zama da ita ba, to tabbas ta yi karya ta kwana da yunwa. Idanunta babu dalili ma kawo kwalla suke yi, balle yau ta yi dalili. Da hanzari ta mike ta bude (wardrove) dinta. Manyan turamen atamfofin (Vlisco) ta kwaso har guda biyar da sinkin sabulai guda goma ta watsa a katuwar leda ta bi ta da su da sauri. Har ya tada motar ya yi reverse ya hango fitowarta da gudu-gudu ta madubi. Ya dan dakata har ta cimmasu. Bude kofar motar ta yi ta azawa Harira a cinya, sai ga hawayen sun zubo. Harira kanta daurewa ta ke yi, amma idanunta sun kada sun yi jazir. Ta daure ta kama hannun Hafsat ta ce, To me ye na kuka Hansatu na? Ai ana tare, Baba Azumi ta riga ta hada mu. Na yi miki alkawarin in ki ka haihu ni zan zo in yi miki jego, ke dai ki yi kokari kafin shekara mai zuwa ki haiho min santalelen ango ko kawa mai kirki kamarki, kin ji? Kokarin jan motarsa ya soma don sun soma ba shi haushi. Maganganun Harira sun yi masa wani iri, sai ya ji kamar da shi ta ke. Hafsat ta ja baya ta rufe mata kofar ya fizgi motar da gudu. La-shakka da cikin kasa ne da ya bule ta da kura, sai aka yi saa kananan fararen duwatsu ne shimfide da harabar gidan bakidayanta. Ciki ta koma ta fada gadonta tana kuka riris, kuka mai dalilai da yawa. Mammah ta daina sonta ne? Ismaeel, Usman da Halim ma? Baba Azumi ma? Tunda Mammah ta yi mata aure kuma shi kenan ta rabu da ita? Auren da ta tabbatar ba dadinsa ta ke ji ba. Yar Harirar da ta bata tana debe mata kewa ta dauke abarta duk don a takura ta a nuna mata yanzu ba mai sonta? Ya ya za ta yi rayuwa a gidan nan daga ita sai Abdulazeez din da shara ta fita daraja a idonsa? Ya Allah ka kawo min sauki ni Hafsatu, idan kuma mutuwa za ta fi min sauki ka gaggauta daukar raina in huta da zaman gidan nan. **** Kusan kwanan da ta yi tana kuka shi ya sa washegari ta makara, don bayan ta idar da sallar asubah a nan kan sallayar barci ya sake yin awon gaba da ita. Ba ita ta farka ba sai bakwai da rabi, kuma lokacin ne Abdulazeez ya ke tafiya aiki. Salati ta yi ta mike da ta dubi agogo ta fada toilet ta rage mararta ta wanko bakinta ta fio falo don wucewa kicin ta gani ko akwai abin da za ta iya ba shi na gaggawa duk da ta san da kyar ne in bai fice ba. Amma ga mamakinta yana tsaye jikin dining yana daura agogo, ya shirya tsaf cikin suit bakake da farin tie a wuyansa kamar kullum yana kurbar tea din da ya hada cikin cup a gurguje. Karfe tara daidai zai shiga kotu a kan case din wasu yara da kanin mahaifinsu ya cinye musu gado, tun daren jiya ya gama (compiling) duk wasu hujjoji da ya tara, amma ya manta da wani (recording) da ya yi saving dinsa a kan desktopdinsa ta ofis dole ya yi sauri ya je ya yi burning dinsa zuwa discyadda in ta kama zaa iya playing dinsa a kotun saboda haka kusan a gurguje ya kammala shirinsa yau ya fito. Ya samu ya hada shayin don ba ya jin yau yana bukatar abinci daga safe har dare, sai ya ga abin da ya turewa buzu nadi a kan wannan case din kamar yadda ya saba, musamman case na marayu ba ya daukarsa da sauki. Jiya saboda wannan aikin bai samu ya kwanta da wuri ba don haka a dan makare ya tashi ya shirya ya fito falon. Sanyin A.C da ya ratsa shi a falon ya ba shi mamaki, don ya lura duk lokacin da ta fito da asuba sai ta kashe ta, amma yanzu ya tabbatar yadda ya barta jiya da daddare ya shiga daki ya kwanta haka ta kwana tana aiki. Talbijin a kunne, wutar falo a kunne, wadanda kullum sai ta kashe su ta ke kwanciya. Ya kafa wa kofar dakinta ido kamar hakan ne zai tabbatar masa tun shigarta daki jiya tana kukan tafiyar Harira ba ta kara fitowa ba. Sai ya matsa ya kashe A.Cn da sauran kayan wutar gabadaya ya tsaya nan jikin dining ya hada teadin da yake sha wanda ya dafa da butar ruwan zafi (kettle) yana sha daga tsayen da yake yana daura agogo. A daidai lokacin Hafsat-Suhaana ta murdo kofar dakinta ta fito. Sanye ta ke cikin riga da wando na barci masu kauri, kanta cikin hular wanka (shower-cap), bai juyo ya dube ta ba da yake ya bata baya, tunda har ta fito to lafiya ta ke kenan. Ya karasa shanye shayinsa ya ajiye kofin a kan (table) ya dora (wig) dinsa a kansa ya suri rigar lauyoyinsa da (briefcase) ya fice zuwa harabar gidan. Ya bude motarsa ya shiga, ya ajiye kayan hannunsa a kujerar gefensa ya yi wa motarsa key Danfulani ya bude masa get ya murza kan motarsa ya nufi (office). Barin Harira gidan maimakon ya kawo shakuwa kamar yadda Hajiya Maryam ta yi zato, sai ya kara lalata zaman gidan. Hafsat sai ta yi kwana biyu ba ta sanya Abdulazeez a idanunta ba. Da safe ya daina bi ta kan abincinta, da ma Harira ke cewa ta dauka ta bishi ta sanya mishi a mota, shi kuma ba ya musantawa in ta kawo ko in ta ce masa Ga breakfast yanzu kuwa da babu Harira ba ta da wannan kwarin gwiwar, shi ma ba ya nuna yana bukata, in ya fito zai hada tea ko coffee ya sha ya fice, ita kuma ta kama kanta sosai, ba ta yi masa shisshigi ta tsaya a matsayin da ya ajiye ta na mai yi masa gadin gida. Ya daina turo direbansa daukar abincin rana tun tafiyar Harira ko me ye dalili ba za ta iya cewa ba. Da ya dawo karfe shida wanka yake yi ya shiga kicin ya kama girkinsa ya yi ta bare-barensa duk ya baba mata kicin ya tara mata kayan wanke-wanke. Tunda ta lura ya daina cin abincinta ta daina dafawa da shi, iya cikinta ta ke dafawa don duk ranar da ta ajiye masa na dare, a ganinta lokacin yana gida. To yadda ta ajiye shi haka za ta dawo ta samu abinta, ta dauka ta sa a firji washegari da safe ta yi steaming dinsa ta cinye don uwarta ba ta koya mata almubazzaranci da abinci ba, ko ta dumama ta mika wa maigadinsu. Yana ganin abincinta wanda ya san don shi ta ajiye, amma tunda ta daina ce masa ga abinci zai tsallake shi ya yi abinsa. Girki ba bakonsa ba ne, don kuwa shi ya raini kansa ba wani ne ya raine shi ba. Da ya gama ya zai zauna a dining din kicin din ya ci abinsa don ba ta wasa da tsaftar madafin nasu. Yana gamawa zai shige daki ya hau aiki, in kuma ba ta a falon to zai yi zamansa ne a nan ya baje takardunsa da systems dinsa ya yi aikinsa. Shi kadai ya san yaushe yake shiga daki ya kwanta. Hafsat ba ta kara shiga shirginsa, wanka ta ke yi ta dauro alwala ta gurfana a side din da ta ware ta yi shimfida cikin dakin ya zama muhallin ibadarta, ta gurfana gaban mahaliccinta tana kai masa bukatunta. **** Haka kwanakin ke mirgina musu har tsayin watanni ukku, rayuwar tasu ba wani abu mai dadi da za a dorar, connection dinsa da Muazatu ya yi rauni saboda ta samu tafiya (Law School) a jihar Adamawa (Yola) dole ta maida kai ta ajiye soyayyar a gefe, shi ma cikin lokacin nan fama yake da cases iri-iri masu zafi saboda a hankali fasaharsa da kwarewarsa a kan aikinsa ke fitowa sarari. Ya shiga sahun lauyoyi yan gaban-goshin gwamnati wadanda ake damkawa duk wani case na marassa galihu, (private individuals) sun fara son janye Abduazeez Dakata, amma ya tsaya a raayinsa na kasancewa lauyan gwamnatin tarayya mai rajin kare hakkin yan kasa. Wanda babban burinsa a gaba shi ne, barin Bar zuwa Bench. Wato daga lauya zuwa mai shariah (justice). Yau yana zaune a office wata abokiyar aikinsa Barrister Surayyah Tanko ta isko shi rike da wasu files a hannunta. Tana zuwa ta dire masa su. Aiki yake yi, amma ya dago ya dube ta, Taimaka ka duba min su Barrister Abdulazeez ka gani ko akwai abin da ya kamata mu kara ni da Adebayo. Zan je (Jamb Office) na dawo yanzu, zan sayo wa Suhaima jamb form, saura kwana uku a rufe. In aka rufe kuma sai wata shekarar. Idonsa ya dan kafa mata, matar aure ce amma tana son shiga shaaninsa da yawa bai san dalili ba. Sai kuma ya ji kamar ta yi masa tuni game da wani nauyi da ke kansa. Hafsat!. Sunan ya fado masa a rai (with a low tune). Surayyah ta gyara tsayuwa ganin sai kallonta yake yi, amma in ka dubi tsakiyar idonsa za ka lura ba ita yake kallo ba, tunani yake yi. Ta kada masa yatsunta a fuska, ya dauke kai daga kallonta ya mayar bisa (computer). Tunanin me ka ke ta yi haka Barrister ina ta magana ba ka jina? Ina jinki. To amma ka yi shiru? Ki yi hakuri ba zan iya duba miki files din nan ba, amma zan bai wa Abdallah. Ni ma in zan samu mai rage min nawa ayyukan zan so. Surayyah ta dan bata rai, Ka ce dai kana tunanin budurwarka, amma ba ka da ayyuka da yawa, tunda jiya ku ka gama shariar da ka ke yi. Murmushi ya yi har dimple dinsa ya lotsa gashin saman idonsa ya kwanta sosai a kan lumsassun idanunsa. Ba tare da ya dube ta ba, hannunsa a kan (system) dinsa ya ce, Budurwa kuma? Ai an dade da wuce wurin Surayyah. Im married. Sai bayan ya fada zuciyarsa ta jefo masa tambaya. Are you really married? Ya girgiza kai da sauri, a fili ya ce. No, not really. Ita dai Barrister Surayyah ta saki ido da baki da kunne duka tana kallonsa tana saurarensa, shaidaniyar zuciyarta na kara kawata mata shi ta kowacce fuska, shikadai ke burgeta duk fadin kotun, akan sa mantawa take ita matar aure ce, ba ta ma fahimci me yake fada ba. Ya kashe system din ya dube ta. Ki wuce gaba a motarki zan bi ki a baya, sai dai bana gudu a titi ni kada ki bace mini. Ni ma zan sayi Jamb form. To mu yi amfani da mota ta mana? Haram, in shiga motar matar mutane. Ni zan shiga taka. Allah ya kiyashe ni daukar mace a gaban mota ba Muazatu ba. Sosai abin da ya fada din ya yi mata ciwo, ta ce. Ai sai ka tafi kai kadai, ni ban iya tafiya a hankali ba. Ta juya, ya bi bayanta yana fadin, Ga shi kuma bana niyyar yin abu in fasa. Ta zumburo baki suka fice tare, kowa ya shiga tasa motar a haka suka tafi. Da gayya Surayyah ke sharara gudu shi kuma bai yi kasa a gwiwa ba wajen binta, har suka isa. Suka nemi wuri suka yi parking ita ta shige gaba suka sayi forms din, babbar yarta ta sayawa, shi kuma ya saya da sunan Hafsat Hamza Atiku Dakata. A hanyarsu ta dawowa ya yi mata signal ya dauke kan motarsa ya nufi gida, bai koma (office) ba duk da lokacin tashinsa bai yi ba. Yana so ya cike mata da sauri tunda ya ji cewa babu isasshen lokaci. Yaushe rabon duniya da ayyaraye! Suhaana ta ce a ranta, lokacin da ta tsinkayi muryar mijinta Abdulazeez na yi mata sallama a kofar kicin, ta bada baya tana soya miya a kan gass wadda za ta sanya a firji ta yi mata kwana biyu tana amfani da ita, don kayan abincin da ke cike da firji da freezer da nama da kifi duk sun kamo hanyar karewa, girke-girken da ta saba dole ta hakura ta koma cin fara da miya. Su kansu kayan miyar daga wadannan da ta ke soyawa babu wasu, cancana abinta za ta yi tunda ba ta san ina za ta nemo wasu ba. Kayan abinci kam suna nan a shake a buhunhuna da katon-katon ta san har gaba da shekara ba za su kare ba. Yau kwananta hudu ba ta sanya Abdulazeez a idonta ba, ta kan dai jiyo bare-barensa a kicin in ya dawo kafin magriba, lokacin kam ita ta kammala abin da ta ke yi ta shige daki don ta lura yana jin dadin yin aiki a falon in tana nan kuma sai ya kuke a daki, shi ya sa ta haramta wa kanta zaman falon don ya sake a gidansa. Amma abin mamaki yau ga shi a gidan karfe hudu na yamma, wai yana yi mata sallama. Amsawa ta yi ciki-ciki ba tare da ta juyo ba. Sosai ta ke jin kiyayyarsa a ranta don ta lura bayan rashin so ba shi da imani ko kankani, ba shi da kirki, ba shi da adalci. Wasu tawagar hawaye suka shimfido a kan kundukukinta, ba ta yi wani hobbasa na hana su zuba ko share su ba. Zubar tasu ne kawai zai sa ta ji sanyi a zuciyarta. Ko da ya ce za su yi AUREN KWANGILA, auren cin gashin kai ba ta zaci har da rashin sanin halin da junansu ke ciki ba, yanzu in mutuwa ta yi haka gawarta za ta rube ta lalace a daki sai ta fara doyi zai sani. In ciwo ta ke sai ya ci ya cinye ta zai sa ni. Tun tana tunanin Mammah da mutanen gidansu, har ta hakura ta daina, ta yarda Mammah ta aurar da ita ga azzalumin danta ne don ta gaji da ita, ya kashe ta da bakin cikinsa duk su huta. Hawayen suka fara gudu suna sauka a kan kirjinta, hakoranta na karkarwa suna haduwa da junansu saboda kuka mai cin rai, amma ta sa hannu ta toshe bakinta ba ta son amon kukan nata ya fito fili. Abdulazeez ransa ya so ya baci da yadda ta yi watsin Allah-tsine da shi a bakin kofa, ta kuma amsa sallamarsa kamar ba ta so. Sannan ta ki juyowa. Kwafa ya yi ya zuro jikinsa ya idasa shigowa cikin kicin din yana kallon abin da ta ke yi. A matsayinsa na wanda rabonsa da abinci tun daren jiya, sosai miyansa ya tsinke da wannan hadaddiyar miyar wadda ta ji naman saniya zuku-zuku sai tashin kamshin spices da mushroom curryta ke yi. Ya hadiye miyau mukut! Ya bi ta da harara duk kuwa da ance aikin banza harara cikin duhu don kuwa bayanta kawai yake iya gani. Sallama fa nake yi amma ki ka yi banza da ni? Haushi ya ba ta sosai, kamar ta juyo ta dalla masa mari amma ina! Ko tsakiyar idanunsa ba za ta iya kalla ba balle mummunar magana ta hada su har akai ga abin da zuciyarta ke kissima mata. Na amsa ai. Ta sake amsawa ciki-cikin. Cikin hadiye kukanta gabadaya. Kwafa ya sake yi ya juya ya fice yana fadin, In kin ga dama ki zo ki yi min bayani in cike form dinki ne na jamb. Ai ba ta san lokacin da ta saki ludayin miyar a kasa ba ta biyo bayansa. Jin karar faduwar ludayin ne ya sa Abdulazeez ya juyo sai ganinta ya yi har ta kusa cimmasa, fuskarta jage-jage da hawaye. Wani abu mai kama da tausayi ya so ya tsirga masa, yana mamakin son karatu irin nata, wato fushi ta ke da shi sosai a kan laifin da bai sani ba, amma jin zancen jamb ta manta komai ta biyo shi har ta manta ta bar wuta a kunne. Dakatawa ya yi, ta zo ta shige shi ta yi falo ya dawo ya kashe gass cooker din da kansa, ya rufe mata miyar sannan ya bar kicin din. A falon ya same ta a tsaye, zama ya yi cikin (3 seater) ya jawo briefcase dinsa ya fito da scratch card din da receipt ya daga lumsassun idanunsa ya dube ta, Kawo takardunki, sai ki zauna mu cike. Zan iya cikewa da kaina. Kina da system ne? Akwai tawa ta gida, amma babu internet connection. Ga mamakinta sai ya tura mata jakar laptop dinsa. Dauki wannan ki yi da ita, ki hanzarta ki gama zuwa gobe sun kusa rufewa. Dauka ta yi ta matsa gabansa ta karbi scratch din da sauran takardun ta tsugunna a gabansa ta yi shiru. Tunanin me ya tsayar da ita yake yi, sai ji ya yi can a tsakar kansa tana fadin, Na gode sosai. Ya bude idanunsa sosai a kanta daga lumshewar da suke yi da kansu, You dont need to thank me. Its part of our contract, kin manta ne? Girgiza kai ta yi, a sanyaye ta ce, Ban manta ba, duk da haka na gode. Sai ya kasa ba ta amsa ya bi ta da ido har ta mike ta shige daki dauke da system din cikin nutsuwa. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* A yadda ransa yake a jagule din nan, ya san Muazatu ce kawai za ta iya tafiyar da damuwarsa, ga shi ya mata laifi, ya bata mata rai tun jiya yake ignoring call dinta. Tun kafin ya karasa dakinsa ya kira ta. Ya manna wayar a kunnensa ya murda kofar dakinsa, ya shige ya mayar ya rufe, har da murza key. Kamar a mafarki Muazatu Rufai wadda ta fita hayyacinta cikin kwana biyu ta yi firgai-firgai saboda tashin hankalin da ta samu kanta a ciki, ta ga sunan Habeeb-qalby da ta sanya wa Abdulazeez Dakata na yawo a screen din wayarta. Sai ta dauka gizo ne idanunta ke mata kamar yadda suke mata tun jiya, don haka har kiran ya kare bata taba wayar ba, sai ma wasu azababbun hawaye masu dan banzan yaji da ta ji sun kwaranyo mata. A karo na biyu wayar ta ci gaba da ba da ruri da Habeeb-qalby, ta kai hannunta ta damke gashin kanta tana ta cije labbanta na kasa da hakoranta tana rokon Allah in mafarki ta ke ta farka. A nasa bangaren Abdulazeez jikinsa ne ya yi sanyi, ya tabbatar bai kyauta wa masoyiyarsa ba, kamar wani wanda ya yi auren soyayya da zai janye jiki daga gare ta don kawai an kawo masa amrya? To me ye gaminsa da amaryar da ya janye wa Muazatu dominta? Wata zuciyar ta ce da shi, Ba don amarya ba ne, kalamin bakinta ne. Ba ta iya magana ba. Ba ya so kowa ya shiga (personal life) dinshi hatta iyayensa haka Allah ya halicce shi, don haka yake kara kyamatar wannan auren, don a ganinsa Mammah ta shiga rayuwarsa da yawa ta rushe masa future ta hanyar aura masa yarinyar da ba ta yi daidai da tsarin rayuwarsa ba. Zai kuma bi duk hanyar da zai bi ya gyara rayuwarsa yadda ya riga ya tsara tun lokacin da ya mallaki hankalin kansa. Ya yi fushi da Muazatu amma ya huce, ya kuma kara tabbatarwa kansa ba zai iya rayuwa ba tare da ita ba, dole ya lallashe ta. Ki yi hakuri Muazatu. Abin da ya rubutakenan ya tura mata. Muazatu ta karanta abin da Abdulazeez ya turo mata. Lumshe idanunta ta yi, wata rahma ta sauka a zuciyarta. Kalaman (are short, yet they mean alot to her) girmansu ya yi na ruwan kogi ya wanke zuciyarta. Duk da haka ba ta mayar da amsa ba, ba ta kuma kira shi ba sai da ya kara ragaita. Ya turo mata sako na biyu. Muazatu please, Im sorry. Sannan ya sake kira. Wannan karon ta amsa kiran, amma maimakon ta ce komai, kuka ta sanya masa. Kyale ta ya yi ta yi har ta gaji. Ta share hawayenta sannan ta ce, Na huce. Murmushi ya yi, ya gyara kwanciyarsa cikin niimtaccen gadonsa, ya ja quilt ya rufe rabin jikinsa, ya canza rikon wayar daga dama zuwa hagu. So soon haka? Murmushi ta yi kamar yana ganinta. Tunda ka san ka yi min laifin, ka kuma amsa ka yi, ci gaba da fushin nawa na mene ne? Au, ni ba ki san kin yi min laifi ba? Ki dubi tsabar idona ki ce wai..... In ana sulhu ba a tone-tone. Ta katse shi. Ki yarda to ba ni kadai na yi laifi ba, dukkanmu mun yi wa juna. Muazatu bana son raini, ko da aure tsakaninmu bai kamata ki ce min kada in kusanci matata ba. Ina ruwanki? This is my personal world, mind your own business. Im sorry once again for not picking your calls. In na ce ban yi kewarki ba na yi babbar karya. I love you Muazatu, you are the goal I want to achieve now, believe me or not. Wata doguwar ajiyar zuciya Muazatu ta sauke, duk da kalamansa na farko sun yi radadi a zuciyarta, to na karshen sun wanke radadin. Haka yake, haka Allah ya halicce shi, ba ya boye gaskiyar abin da ke zuciyarsa don ya faranta maka, ba ya karya don a so shi, in za ka so shi ka so shi a yadda ka same shi. Ta dade da fahimtar hakan. Im sorry too... ...and I love you more... Dariya ta saki har da wata irin shesshekar shauki. Suka ci gaba da hirarsu yadda suka saba, amma ta yau ta fi ta kullum gardi. Bayan fitarsa da rufo kofarsa Hafsat tasowa ta yi ta dauki ledojin da ya aje ya fice ta bude. Sunkin gasassun kaji ne suyar (YAHUZA) da juice da fresh milk da daurin (shawarma) har guda biyar. Harira ta yi sallama ta yi mata izinin shigowa. Ta aje mata abincin da ta dafo (express). Cikin sanyin muryarta ta ce da ita, Ga shi kuma ya sayo da baki dafa ba. Ba komai, gobe sai in dumama in ci. Ta mika mata leda daya ta karba, ta yi godiya ta dau abincin da ta kawo ta fita tana fadin, Allah ya tashe mu lafiya, in kin ci ki sha magungunan naki. Hafsat ta ce, Insha Allah. Ta fita ta rufo mata kofar. Zama ta yi a tsakar dakinta ta ci kazar nan ta koshi, ta sha magani sannan ta yi sallolin nafila kamar yadda ta saba. Ta sanya kayan barci masu laushi, ta yi addua ta kashe wuta mai haske, ta bar dim-lightta kwanta. Asuba ta gari Hafsat-Suhaana. ****** Washegari da safe bayan ta yi sallar asubah ta yi wanka. Ta shirya tsaf cikin wata lallausar atamfar (holland) koriya shar, ta yi daurin kai sosai ya zauna mata a kai cif-cif gwanin ban shaawa. Dressing din da bai dameta ba amma Mammah tace dole ta dinga yin shi yanzu ta rage zama da dogayen rigunan nan nata, ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi, wadanda Mammah ta cika mata gaban madubi da su. Ta zura kyawawan kafafunta cikin (flat shoe light green) samfurin polota fito falo. Motsin Harira ta ji a inda ta fahimci kitchen ne, sai ta bi ta can. Daga bakin kofa ta tsaya tana dan murmushi, Anty Harira ina kwana, mun tashi lafiya? Harira ta saki dariya jin an kira ta da Aunty, ta juyo, Lafiya kalau Hansatu, ya karfin jikin? Na warware, ba inda ke min ciwo. Haka ake so, na kammala abincin kari ina zanik-kai muku? Me ya sa ba ki jira ni na zo mun yi tare ba? Jiya ma haka ki ki yi girki ke kadai. Murmushi Harira ta yi, a ranta ta ce, Mene ne amfanina? A fili kuma ta ce, Kina fama da rashin lafiya zanis-sa ki aiki Hansatu? To na warke. Yanzu tare za mu dinga yi, ki yi shara, wanke-wanke da sauran ayyuka, ki bar min girki. Shi kenan Hansatu, tunda haka kinka bida. Zo ki gani, ashe gidan cike yake da kayan abinci, firinji cikke da nama da kihi har da markadadden kayan miya bokiti guda. Hafsat ta idasa shiga kicin din suna dubawa tana sanya wa Mammah albarka cikin zuciyarta. Ita ta kwashe tangarayen da harira ta zuba soyayyen dankali da Agada (plaintain) da farfesun kayan ciki ta kai kan kyakkyawan dining table wanda aka yi wa muhalli a can wata kusurwa ta falon. Ta dawo ta dauki flask din shayi da tea cupsda kayan hadin shayin duka ta jera su a diningta samu wuri a daya daga jerin kujerun falon ta zauna. T.V ta ke son kunnawa, ba ta san ya za ta jona ta ba, sai ga shi ya fito rike da gown dinshi a hannu (bakar rigar lauyoyi) da wiga kansa (hular lauyoyi) yana tsuke tie din wuyansa. Gabadaya falon ya gauraye da kamshinmasculineturarensa (Creed Aventus) har Hafsat ta ji turaren jikinta ba kamshi yake ba. Kafafunsa cikin (black covers) kirar Italy yana takun nan nasa gab-gab-gab shi ba sauri ba, shi ba tafiya a hankali ba. Idanu suka hada sosai, dukkansu sai suka dauke kai cikin koinkula. Ita ta fara dauke idonta ta mayar wani gefen, wata hudubar Mammah ta fado mata tun tana karama, Duk inda ki ka ga babba ki gaishe shi ko da da shekara ya girme miki. Sakamakon hakan sai ta samu kanta da zamowa daga cikin kujerar da ta ke zaune cikin nutsuwa bakinta ya ambato kalmar, Sabahul khair. Da accentdinta mai taushi. Barrister Abdulazeez Dakata ya mirgina kai ya amsa a ginshire, Lafiya lau. Ya ci gaba da tafiya a falon zai fice. Hafsat ta samu kanta da cewa, Ga abincin karin kumallo. Cikin harshenta na Brussels. Sai bayan ta fada ta shiga cikin nadama da juyayin wa ya aike ta? Bai ce ta shiga rayuwarsa ba a rayuwar auren da ya shirya musu. Amma ga mamakinta sai ya ba ta amsa da turanci, don shi ba wai ya kware a yaren nasu ba ne, amma yana ji. Na makara, amma a sanya a basket a sa min a mota. Cikin nutsuwa ta mike ta shiga madafin ta dauko (food-basket) sabo fil ta dauko kanan food flasksmasu kyau ta fito ta juye kowanne a flask daya. Ta dauki filas din ruwan zafi zata saka cikin basket din sai ya ce, Bar wannan, inada kettle ina shan (coffee) a office. Kanta a kasa ta ce, Toh.Ya fice, ta bi bayansa tana dauke da kwandon. A jikin kofar motar ta tsaya ya bude ya shiga, sannan ya mika hannu ya bude (lock) din kujerar baya ta sanya basket din. Sai ya ce mata, Thank you. Ya rufo kofar. Juyawa ta yi ta koma, shi kuma ya murza kan motarsa kirar (GMC) ya yi reverse Danfulani ya bude masa kofa ya fice. Kicin ta leka ta tadda Harira a dining din kicin din tana karyawa, ta gyare koina tsaf. Sannu da aiki Anty Harira, ki dinga zuba wa maigadan gidan nan abinci don Allah. Harira ta ce, Ba sai kin fada ba, na ba shi tun dazu. Ta ce, Ok. Falo ta koma wajen kayan wuta ta yi ta kokari har ta jona T.V ta zauna da remote a hannunta, har ta nemo wata tashar Larabawa suna girke-girken kasar Turkiya da yadda ake sarrafa su. Sosai abin ya dauki hankalinta. Sai ta ji shaawar gwada abin da suke koyarwa don haka ta shiga dakinta ta samo jotter da biro ta soma (jotting-down) daki-daki yadda za ta gane. Wani irin tsire suke nuna yadda ake yi na nikakken nama mai suna adana kebabi da recipe din, a zuciyarta tana fadin ta samu abin yi za ta gwada su ci ita da Anty Harira. Sai wajen sha daya na safe ta kashe T.Vn ta leka kicin, Harira ba ta nan ta wuce dakinta. Nan ta hau hada kayan girkin da za ta bukata. Kafin karfe biyu na rana gidan ya gauraye da niimtaccen kamshin tsiren mutanen Turkiya. Ta kwashe shi daga oven ta zauna a nan dining din cikin kicin tana ci. Bayan ta dibarwa Harira. Kwana biyu ta sake yi don na farko yayi mata dadi,Harira ma wuni tayi tana santin tsiren, tana zaune a kicin tanaci tana tunani. Tunda ta zo yau kwana biyu ba ta yi magana da Mammah da su Ismaeel ba, sosai ta ke cikin kewarsu. Ga shi ba ta da waya, ko sanda ta ke gida ba ta rike waya ko da wa za ta yi magana da wayar Mammah ta ke yi. Tana wannan tunanin tana kai lomar adana kebab dinta ba ta ankara ba sai ganin giftawar mutum ta yi har ta so ta tsorata. Da sauri ta waiwaya, Abdulazeez ne. Kai tsaye ya wuce ga firji ya bude ya dauko gorar ruwan Faromai sanyi ya bincire murfin ya kafa a bakinsa ya ringa kwankwada, sanyi da gardin ruwan na ratsawa har cikin kwakwalwarsa yana wanke gajiya da zafin da kwakwalwar ta kwaso. Ta dauke kai daga kallonsa yayin da ta sauke wata siririyar ajiyar zuciya, ina ma za ta iya? Da ta roke shi ya ara mata wayarsa ta kira Mammah da Baba Azumi da Yayanta Ismael Dakata mazaunin kasar Amurka ko ta ji dadin zuciyarta daga matsewar da ta yi mata wuri guda sabida kewarsu. Wannan aure jinsa ta ke tamkar an kawo ta kurkuku, ya yanke alakarta da kowa nata, Mamanta ba ta kara bi ta kanta ba, miji kamar malaika kullum fuska babu walwala, in yasa kafa ya fice sai goshin maghriba yake shigowa gidan daga nan bata karaganinsa sai wayewar gari in ya fito don tafiya office, in sun bashi abinci yana karba, in ta gaishe shi zai amsa, bayan wannan ba wata kalma dake kara hadasu, da alama ba ya son bude ido ya ga fuskarta, watakila bayan rashin so ita mummuna ce. Ita ma ba so ta ke ya so ta ba, amma akalla ya bude kofar da aurensa ya rufe mata na datse alaka tsakaninta da kowa nata. Ji ta yi idanunta sun cicciko da kwalla kafin ta yi aune kwallar ta zubo, sharr! Da sauri ta sa bayan hannunta tana sharewa. Har ya wuce ya bar kicin din yana mamakin me ya yi mata ya sanya ta kuka? Daga kawai ya shigo kitchen? Watakila ba ta son ganinsa ne, in ba haka ba shi bai ga laifin da ya yi mata ba. Alkawururrukan da ya daukar mata tun a yau har ya fara kokarin cika su. Ci gaba ta yi da cin abincinta tana hawaye, a haka Harira ta cimmata. Wai Abdulazeez ya ce a sanya mishi abinci a mota zai koma ofis. Nuna mata inda ta zuba masa abincin ta yi da hannunta, har tsiren ta zuba masa mai yawa, ba ta so ta yi magana Harira ta gane kuka ta ke yi. Ta manta cewa gaba take da ita. Murmushi Harira ta yi, ta ce. Ki kai masa da kanki Hansatu, ki yi hakuri kin ji? Wannan Hansatun da Harira ke kiranta da shi dariya yake bata, amma yau haushi ya ba ta. Ba ta ce komai ba ta mike ta dauki basket din ta fita. Yana cikin motar har ya kunnata ya rufe kofar da alama ita yake jira, ba ta yi masa magana ba ta bude kujerar gaba ta ajiye kwandon ta rufe kofar. Ya ja motarsa da hanzari ya bar harabar gidan, daman mantuwa ya yi ya dawo, amma ba aladarsa ba ce dawowa gida cin abincin rana ba. Abin da ya tarar tana ci ne ya ba shi shaawa har ya ce a ba shi abincin. Rayuwar amarya Hafsat-Suhaana da Abdulazeez kenan a gidan aurensu har tsayin sati biyu. Za ta yi girki sau uku a rana, kuma babu wanda ba ya ci, na safe zai fita da shi, na rana da ba ya samun sukunin dawowa zai turo direban ofishinsu ya daukar masa, na dare kuma in ya dawo masallacin unguwarsu sallar ishai zai ganshi a diningya zauna ya ci. Weakness dinsa kenan (abinci) kuma da a ce Hafsat na da wayo da ta dade da gane hakan. Ba ya son abincin sayarwa sai ta kama dole. Sanda yake (schooling) shi yake dafawa kansa. Da ya tafi Law-school daga gidansu Muazatu ake ba shi. Da ya gama ya dawo gida mahaifiyarshi ta sangarce shi da dadadan girke-girkenta wadanda dandanonsu yanzu ya yi masa daidai da wanda Addarta ke ba shi, wanda ke nuna ko dai ta koya ne a wajenta, ko kuma tare suke yi. Kallon farko da yake yi mata na sangartacciya, ya soma gogewa. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Ta dago ta dube shi kamar za ta ce, aah, ya tsare gida sosai. Ya sanya layin etisalat a ciki ya yi charging wayar sosai. Kamar yadda ta haddace karatun sallahr farillarta haka ta haddace lambobin uwarta da na Baba Azumi. Da sauri ta shigar da lambobin ta kasa danna call don ba ta san karbar da Mammah za ta yi wa kiran nata ba, sai gani ta yi Abdulazeez ya danna mata. Runtse idanunta ta yi lokacin da ta ji tattausar muryar Hajiya Maryam na fadin, Assalamu alaikum. Wasu hawayen dadi suka sauko mata, ta kasa amsawa. Daga can bangaren Mammah ta ji shiru, ta ce, Wa ke magana ne? Bude idonta ta yi suka sauka cikin na Abdulazeez, ya daga mata gira cikin karfafawa. Muryarta ta yi rauni sosai, ta ce, Mommah. Sai kuka. Duk duniya babu mai kiranta haka sai Addarta, murmushi ta yi, ta ce, At last ya sayi wayar? Abdulazeez juyawa ya yi ya fita don ya basu dama suyi maganarsu, ya dauki jakar system,wig da gown dinsa ya bar gidan yana mamakin irin wannan soyayya da ke tsakanin mahaifiyarsa da Suhaana. Zai iya rantsuwa shi bai samu rabin-rabinta ba. Ya ya za ta ji ranar da ya dawo mata da Suhaana da takardar saki? Zuciyarsa ya ji ta birkice, kwakwalwarsa ta daina aiki. Sai dai no matter what ba zai iya jure rashin Muazatu ba. Uwarsa ce dole watarana za ta yafe masa. Kuma zai san yadda ya yi Suhaana ta wanke shi tunda ita ce (apple of her eyes),his love to Muazatu is estimable, and hence; inevitable. Tunda ya yi biyayya ya yi abin da suke so, shi ma sai a ba shi hakkinsa. Fisabilillahi ya yi kokari da ya kawo wannan lokacin bai mallaki abar sonsa ba. Amma a kwanakin nan sosai yake jin tausayin Hafsah image dinta kuma na yawan gilmawa a idanunsa. Ya kara samun kwarin gwiwar son taimakon rayuwarta ta kowanne fanni. Mammah da yarta a waya ana shan hira. Tunda ya yi hankalin saya miki wayar alhamdu lillahi. Na sa masa ido ne ai in ga kamun ludayinsa. Waadin da na diba na zuwa gidanku ya kusa cika ai ko ba ki kira ba Adda... Amma Mommah wata hudu... babu ke babu Daddy ko Baba Azumi, babu ko su Haleem? Momma me na yi miki da zafi haka? Kada ki sa in ci gaba da yarda da kaina cewa; kin daina sona... Sai kuka. Murmushi Hajiya Maryam ta yi, irin murmushin nan na UWA maabociyar kawaici da yakanah. Me ya yi zafi na wannan kukan Addah? Ashe uwa na daina son danta? Akwai dalilai da yawa da suka sanya babu wayata kuma babu kafata a gidanku. Amma tunda kin dauka haka da zafi zan gaya miki wasu don in wanke kaina daga wannan zargin naki Addah. Aurenku ba aure ne na soyayya irin sauran aurarraki ba. Ina da karfin iko a cikinsa, wanda in na sa za a yi, in na hana za a bari. Bana son wannan karfin ikon nawa ya ci gaba da tasiri a cikinsa. So nake ku shaku da juna, ku so junanku ba tare da sa hannuna ba. Idan na zo na ganki cikin wani hali, ko ki ka gaya min wani abu wanda zuciyata ba ta gamsu da shi ba, ba zan jure ba sai na murza wannan kambun nawa. Ki fahimce ni Addah, bana son ji ko ganin komai da ya shafe ku ba so da kaunar junanku ba. Kuma na fara samun abin da nake so alhamdulillah. A jiya na fahimta. Duk da haka kuna bukatar karin lokaci ki gafarce ni, ki kara min watanni biyu a gaba kafin in tako kafafuna gidanku. Amma daga yanzu na amince ki kira ni duk yadda ki ke so, ko sau dari ne a rana. Dariya ta yi, dadi har cikin ranta. Duk da in Hausa mai tsauri ce ba ta fahimtarta. Yanzun ma ba ta fahimci wani muhimmin abu cikin zantukan Mamarta ba. Ta dai fahimci ba daina sonta ta yi ba, tana da dalilinta na rashin zuwan da rashin kiran. Tana so sai sun shirya sun saba da juna sun kaunaci juna don kansu. Tausayin Hajiya Maryam ya tsirga a zuciyarta, shin ya ya za ta ji ranar da ta fahimci duk wannan hakilon nata a tutar babu zai tashi? Abdulazeez ba fara sonta zai yi ba? Kuma ba zai taba son nata ba, yana da wadda zuciyarsa ta riga ta mutu ta rube a kanta? Hawayen tausayin Mammah suka zubo mata, don ta kawar da tunanin da ya addabi zuciyarta sai ta ce, Mommah ya cike min JAMB. Fassara farin cikin zuciyar Hajiya Maryam ba zai rubutu ba, Na ji dadi sosai Hafsat, wane course ya sa ma ki? Ban sani ba Mommah, kuma ba ni da zabi. Na bar mishi wuka da nama. Ni dai in yi karatu kowanne iri ne Mommah. Murmushi Hajiya Maryam ta yi ta sanya wa Abdulazeez albarka cikin zuciyarta. Ni na san me zai sa miki, tunda shi karatu in ba shariah ba (Bar and the Bench) to ba karatu ba ne. Dariya Hafsat ta yi, Kuma Mommah duk sai mu taru mu tare a kotu? Mammah ta ce, Eh toh!! Ku haifi yaya ma ku maka su a kotu. Kunya ce ta lullube ta don haka ta sauya zancen. Mommah ba ni Baba Azumi. Ba ta nan, ta je Sokkoto auren babbar yar Harira, ta samu miji. Murna sosai ta yi wa Harira, Kuma Mommah sai ki ka dandana mana Harira ki ka zo kuma ki ka kwace? Ta yi dariya ta ce. Dandani haukaci kenan. Gani na yi gara ke ma ki dage kamar sauran mata ki nemo aljannarki da kanki ba tare da mataimaki ba. Ki zama (total housewife), ranar da ki ka haihu na yi miki alkawarin mai aiki don haka ki dage...... Rufe ido ta yi cikin jin kunya kamar Mommah din na kallonta. Mommah ki daina kira min haihuwa, Im still your baby! You are still my baby Addah! Na daina. Dariya suka yi tare. Ki ka ce in kira ki sau dari a rana Mommah? Ai sai Daddy ya ce ba lafiya ba. To ai ke ce Addah kin bi kin daga min hankali a kan abin da bai kai ya kawo ba, don na aurar da ke sai in yi ta zarya a gidanki? Kina so mijin ya ce surukar ba ta kwarai ba ce? Dariya ta ke yi sosai wadda rabon da ta yi irinta har ta manta. Kwanaki da watanni sun shude sun tafiyar da farin cikinta na gida, sun dasa wata sabuwar rayuwa a gare ta a gidan Abdulazeez Dakata. Rayuwa mara dadi da ba ta ko son tunawa. Amma yau ta zo mata da farin ciki mai yawa a dalilai masu yawa;Theres compassion in him today (Abdulazeez), Mommahs love... Abu daya ya rage da zai cika wannan farin cikin... brothers love...! Mommah ina Amerikawa? Ina Belgians? Murmushi Mammah ta yi, Duk za su samu hutu lokaci daya. Watan April. Na yi miki alkawari ranar da zan zo gidanki, Usman da Ismaeel sune masu take min baya. Haleem ba yanzu ba. Wani dan ihu ta saki, sai da Mammah ta toshe kunnenta ta kashe wayar tana murmushi. Daddy ya shigo, fuskarta kawai ya kalla ya ga annurin da ta ke ciki, zuciyarsa ta gaya masa ta gaji da takunkumin da ta sanya wa kan nata ta yi magana da yarta. Dariya ya yi ya zauna yana fadin. Har an shekara ne? Cikin rashin fahimta ta ce, Da me fa? Da kai Hafsa gidan aure. Abin ya ba ta dariya sosai, ta ce, Ai da ma ban ce shekara ba, cewa na yi sai sun shirya kansu. Kuma ita ta kirawo ni tana ta kuka wai na daina sonta. Cikinsa kamar ya fashe don dariya ya dora, Ke kuma dama a kan gwiwa ki ke, tana kira ki ka haife? Harararsa ta yi, harara irin tasu ta manya, Aah ka manta nakudurta nake yi. To ai da alama Hausa ba ta ishe ki ba, in aka ce mace na kan gwiwa ai nakuda ake nufi. Yau kin haihu kowa ya huta. Dakin ta bar masa don ta lura yau zolaya yake ji, ta ce, In ka fito wanka table is ready Ba fa abincin da zan ci sai kin ba ni labarin wayar nan. Dakatawa ta yi a bakin kofa, ta juyo ta dube shi hannunta biyu harde a kirjinta. To Daddy me ka ke so ka ji? Sun shirya? Su wa? Ta yi kamar ba ta gane ba. Yayanki mana. Danka dai, ni ba ni da wasu yaya bayan Suhaana. To na ji, ina nufin da na da yarki, sun shirya? Har ya saya mata waya da jamb form ya cike mata. Ta fada tana kada masa ido. Tausayi ta ba shi sosai, don shi ya fi kowa sanin Abdulazeez da kyar in babu yaudarar mahaifiyarsa cikin alamarinsa. In zai so abu ba ya sonsa a lokaci guda sai ya gane yana da matukar amfani a gare shi. Tun sanda ya zo babu damuwa ya ce ya amince da auren Suhaana bayan da fari ya yi tawaye he didnt believe him! Ko zai so Hafsat not that soon, watakila har sai ta haifa masa yaya. Kuma shi a satin nan Attorney General Habib Rufai ya kai masa ziyara har Gwags karkashin rakiyar attorneys da yawa, bayan sun gaisa yake gaya masa shi ne Baban Muazatu yarinyar da yaron wajensa ke nema ya ce sai ta kare (Law-school), yanzu ta ci karfin karatun nata su zauna su tsayar da lokaci da ta kare sai a yi biki ba sai an kuma jan lokaci ba. Bai ce komai ba saboda kwarjinin mutumin da mutuncinsa hakan kuma ya ganar da shi cewa, Abdulazeez bai bar neman Muazatu ba. Tun ranar yake jin tausayin Hajiya Maryam, yake kirkiro duk abin da zai sa ta farin ciki, ba abin da ya fi ka kasa juya Dan da ka haifa muni a zuciya. Ya kuma yi alkawarin ba zai yi mata zancen ba Abdulazeez din zai zuba wa ido ya ga iya gudun ruwansa. Tun a ranar da hakan ta faru yake cewa su je su ga Suhaana tana cewa aah da sauran lokaci. Wayar da ta ce ya saya wa Suhaana da makaranta da zai maida ta, ya tabbata akwai dalilinsa amma ba SO ba, kamar yadda ita Maryam ta ke tsammani. Ajiyar zuciya ya yi yana kallonta tana ta jera mishi abinci a dining ya mike ya isa gare ta ya rike hannunta. Dakatawa ta yi ta juyo ta dube shi, murmushin tausayi ya yi mata. Ki bar abincin nan bana jin yunwa, mu je ki cuda ni a wanka. A sanyaye ta ce, Toh. Don ta ga Daddyn shi ma a sanyaye yake. Haka kawai sai ta ji nata jikin ma ya yi sanyi. Saboda murnar maganar da ta yi da Mammah yau ko abinci ba ta girka ba (quaker oat) ta dauko ta dama cikin sayayyar da ya yo musu. Ta sha ta koshi ta shige daki sai barci cikin kwanciyar hankali. Ba shi ya dawo gidan ba sai dare, akwai abin da yake yi wanda ya rike shi.Wani abun alajabi ne ya faru cikin kudurah da Iradar Ubangiji, yana shirin tafiya garin Adamawa a washegari don fara binciken alamarin Hafsat duk da cewa bai san kowa a garin ba. Wani sabon Lawyer ne aka kawo ofishinsu wanda haka kawai yake yi masa yanayi damatarsa, Barrister Sagir Babba. Ba halinsa ba ne shisshigi, amma sai da ya san yadda ya yi ya shigewa Sagir a bisa dalilai masu yawa. Da suka tashi suka fito ya tadda Sagir ya bude bannet din motarshi yana ta tabe-tabe. Kusa da shi ya yi parking ya bude motarsa ya watsa shirginsa ya rufe ya iso gare shi, ya ce, Ya ya dai Barrister? Magriba ta kawo kai muna nan. Ya girgiza kai cikin takaici, Kai dai bari, karfen nasara ne da ba shi da tabbas. Jiya na karbo motar nan daga gareji, amma har ta kara kwafsa mani. Akwai (Mechanics) a nan kusa ne? Ka san ni bako ne a garin naku duka-duka yau satina biyu a cikin Abuja. Garejin da aka duba min ita can ne kusa da gidana a Kubwa. Dadi ne ya kama Abdulazeez, ba abin da yake nema yanzu sai kusanci da bakon Barrister wanda ke sanya shi ayyana abubuwa da yawa a kansa a zuciyarsa tun ganinsa na farko da shi. Ina ganin mu je yanzu na sauke ka a gida, Kubwa ba nan ba ce, in dare ya rufa maka a nan da kyar za ka samu abin hawa. Gobe sai in yi wa (mechanic) dina waya ya zo nan ya duba maka ita. Sagir ya rufe bannet din yana fadin, Ai kuwa na gode da wannan taimako. Na gode sosai. Ba damuwa. In ji Abdulazeez, ya fada yana bude masa gaban motarsa ya shiga suka tafi. Suna tafe suna hira. Abdulazeez da mawuyaci ne ko shekara ku ka yi ya tsaya yana gaya maka abin da ba ka tambaye shi ba, yau sai ya bude ciki yana ta yi wa Sagir hira rututu, ya gaya amsa shi dan Kano ne yan unguwar Dakata, amma a nan aka haife su a nan suka girma. Last year ya yi aure. Lawyer ake yi wa lauyanci, amma bai gane ba. Bai kware da hausa ba, bafullatani ne don haka rabin hirarsa da Turanci yake yi wa Abdulazeez. Ya ce shi dan asalin Adamawa ne, ya yi dukkan karatunshi a FUTY, ya yi (Law School) a Lagos. Ya dade da fara aiki, kasancewar gwamnatin tarayya yake wa aiki sau biyu ana canza masa wajen aiki. Ya zauna a Kaduna, ya zauna a Jigawa yanzu kuma aka dawo da shi nan. Yana da mata yar uwarsa da yara biyu. Daidai lokacin da suka shigo Kubwa yana nuna masa hanya har kofar gidan da ya kama a Kubwa. Abdulazeez ya sauke shi, ya yi nufin juyawa amma Sagir ya dage sai ya shigo sun gaisa da matarsa Rabia, ya ce da shi ya yi dare, amma Sagir ya nace saboda ya ji dadin taimakon da ya yi masa sosai. Suna shiga falon zuciyar Abdulazeez ta yi wani irin harbawa, wata yarinya ya gani mai yawan sumar kai fara sol, an kame mata gashin a tsakiyar kanta da ribbon. Ba za ta wuce shekaru biyar ba, idan har ba warkewa ya yi daga makanta ba wannan Suhaana ce tana karama, lokacin da suke Jeddah yana ganinta in ya je hutu. Da gudu ta sheko ta rungume mahaifinta, shi kuma ya daga ta sama suna ta magana cikin fulatanci da ba ya ji. Sai ga Mamanta ta billo daga kicin dauke da yaro a hannunta, fara kyakkaywa amma babu wayewar matan zamani sosai a tare da ita, ta gaishe su, mijin na mata bayanin Abdulazeez da taimakon da ya yi masa cikin fulatanci. Kara rusunawa ta yi tana kara gaishe shi, ta ce cikin yar hausarta mara amo. Don Allah ka zauna ku ci abincin dare a nan. Murmushi ya yi, ya ce, Na baro Madam ita kadai. Babu damuwa, ka ba ni waya in yi mata magana. Dariya ya yi, Ba za ta fahimci hausarki ba. Ta dan turbune fuska, Duk gidanmu na fi su iya hausa saboda ni na zauna a cikin Hausawa a Kaduna da Jigawa. Sagir ya gaya mini. Jan hannunsa Sagir ya yi ya ba shi ruwan alwala ya nuna masa bayin da ke cikin falon, yana gaya masa Rabia bata gajiya da magana, ya shiga ya yi alwala, alajabin zuciyarsa na kara ninkuwa. Tabbas in ya rantse ba zai yi kaffara ba yana tare da jinin Hafsat. Idan a da yana kokwanton kamanninta da Sagir kamanni ne kawai ganin wannan yarinyar ya kara tabbatar masa da zarginsa, sannan Adamawa ai Yola kenan. Kuma a cikin Yola JIMETA take. Last week da yayi browsing garin a kokarin sa na soma binciken ya gano Jimetan a cikin Yola ne, itace (Yola North).Idan har bai manta ba shi ne garin da mahaifiyar Suhaana ta gaya masa nan ne garinsu. Allah mai karfin iko! Buwayi gagara misali. Shi da Sagir suka yi sallar magriba, ya ja shi dining suka ci abinci, tuwon shinkafa ne miyar taushe, ta ji tantakwashi da man shanu. Yaushe rabon da ya ci tuwon shinkafa! Sosai ya ji dadin abincin ya yi musu godiya. Naira dubu biyar ya ba wa yarsu, ya ce ta sha (choculate). Uwar ta yi godiya suka rako shi har bakin motarsa ya ja ya tafi suna daga masa hannu. Yana tafe a kan titi yana tunani, sanyin A.Cn motarshi na ratsa kasusuwa da bargonsa. Allah ya dube shi ya kusa yanke masa wahala insha Allahu. Zai cika wa Hafsat alkawurrurukan da ya daukar mata a kan lokaci, zai ci gaba da manne wa Sagir tare da bincikarsa har ya tabbatar da zarginsa, amma ba zai hada su da Hafsat ba in har ya zamanto da gaske sune yan uwanta, sai waadin aurensu ya cika. Don haka ko da ya shigo ta dade da yin bacci. Bai damu da ya neme ta ba ya wuce dakinsa don ya san yau ba ta da damuwa tunda ta yi magana da Mammanta, hankalinta ya kwanta. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Barrister Abdulazeez Dakata ya koma da bayansa ya jingina a jikin kujerar da yake zaune. Kewar Muazatu ta sauko masa, yau kwana uku ba su yi magana ba, ya san kuma bai isa ya kira ta a wannan lokacin ba (as a law-school student). Fassara reactions din Suhaana yake so ya yi, wadanda ta yi yau a gabansa ya gane inda ta sa gaba, ya kasa. Idan haushinsa ta ke ji me ya yi mata? Da ma can ya yi mata alkawarin samun kulawa irin ta maaurata ne da yanzu ya saba alkawari ya bata mata rai? Ya yi zaton ya fada mata kowa zai yi zaman kansa ne ba tare da shiga rayuwar dan uwansa ba? In ta manta ne zai iya sake zaunar da ita ya sake yi mata rehearsal na rayuwar da za su yi har zuwa waadin auren. Idan bukata gare ta na wani abu, ko kayan abinci ta bude baki ta ce babu kaza mana, shi yake hana ayi zalinci balle shi a kan-karan-kansa ya zalunci na kasa da shi. Ya ci gaba da lalubawa cikin kwakwalwarsa yana nemo ta inda ya kuskure mata. Wata zuciyar ta ce, Kicin... waya... audugar mata...!!! Kansa ya sara, wadannan ma bukatu ne masu muhimmanci a wajen mace tunda ya san ba zai iya bukatar da ta fi kowacce din ba. Mikewa ya yi ya nufi kicin yana dube-dube, abubuwa da yawa irin su dankali, albasa, doya, kayan miya duk babu. Ya bude freezer da sauri ya mayar ya rufe. Babu komai! Ya bude firji nan ma babu komai na kayan girki, irinsu (Veggies), babu lemuka, babu ruwan sha komai na kayan masarufin gida babu a kicin din. Ya so ya fahimci hakan tun da jimawa abubuwan da ke kansa suka mantar dashi. To don me ba za ta bude baki ta gaya masa ba? Ko bata da baki ne? Zuciya mai gaskiya da adalci a tsakiyar kirjinsa ta ce da shi. A ina ta ganka? In ka dawo ba ka nemanta, in za ka fita ba ka gaya mata. Kowanne irin aure akwai bincikar lafiyar iyali a cikinsa, banda naka. Kikkifta ido ya shiga yi, irin na guilty conscience, ya fito daga kicin din. Ya sa a ransa zai dinga bincikar lafiyarta ko da bayan kwana dai-daya ne. Dakinsa ya shige ya yi wanka, ya yi sallar laasar ya sanya kananan kaya marassa nauyi ya dauki makullin motarsa ya fice. Kasuwa da supermarkets ya shiga, duk abin da ya kamata maigida ya ajiye a gidansa ya sayo, wanda zai jima bai kare ba. Hatta pad katon guda ya saya. Waya ce dai har yanzu zuciyarsa ta ki amince masa da ya sai mata a kan dalilai masu dama. Ya juyo kan motarsa ya nufo gida, booth dinsa da kujerar bayansa shake taf da kaya. Danfulani ya sa ya kwaso kayan ya shiga da su kicin ya tsaya yana nuna masa inda zai adana kowanne. ****** Sanda Hafsat ta dauki computer din Abdulazeez ta shiga daki tsakiyar gadonta ta ajiye ta, tana cike da doki ta nemo takardun karatunta cikin lockers din da ta adana wasu muhimman takardunta da littattafai na makarantarsu ta (St. John Berchamans College). Lokacin da Mammahta hadasu cikin kayanta don ta san watarana za ta bukace su. A dokance ta ke komai, amma me? Tana kunna system din fuskar wata kyakkyawar mace ne a home-screen din tana kwance a kan hannayenta tana sakin wani irin tattausan murmushi. An ce ko ba SO aure daban yake, Allah (Subhanahu wataala) shi kadai ya san iyakacin karfin izzarSa a cikinsa. Ji ta yi ranta ya wani irin jagule, zuciyarta ta matse, idanunta sun rufe da kansu. Ko bai gaya mata ba wannan ce Muazatu kenan. Wadda Abdulazeez ya yarda ya saba wa iyayensa a kanta, ya jefa Mammah cikin dawwamammen bakin ciki da bacin rai a kanta. Ta ji ta tsani Muazatu, wata irin tsana da ba ta taba yi wa dan-Adam dan uwanta ba. Bacin ran da ya sanya ta kasa yin abin da ta ke dokance da yi, zuciyarta ta yi duhu matsananci. Kawai sai ta kashe komai ta ture gefe ta koma ta kwanta, ta lumshe idanunta. Sai da suka gama kimtsa komai ya sallami Danfulani, ya zuba ruwa a karamar tukunya ya dora a gass ya kunna. Nan da nan ya yi zafi, ya dauko ledar cous-cous cikin katon dinsa ya farke ya juye rabi. Ya kashe gass din. Ya kwashe gabadaya a (food-warmer) ya diba a plate. Miyar da ransa ya biya da ita tun dazu ya diba ya zuba a kai ya sanya mata sauran a firji yadda ya ganta, ya ja gefe kan karamin dining din cikin kitchen din ya ci ya koshi. Ya kora da ruwa mai sanyi ya fito ya yi dakinsa. Karo ya ci da katon din (sanitary pad) da macleans din (beverly hills formula) da ya saya mata a falo har da shampoo din (pert-plus) a cikin katuwar leda don haka ya dawo da baya ya dauka ya fasa shiga nasa dakin ya nufi nata. Daga kwanciyar da ta yi barci ya dauke ta, ga ciwon kai. Ya yi sallama har sau uku bai ji ta amsa ba, ya yi niyyar ajiyewa a nan bakin kofa ya tafi sai ya tuna da systemdinsa, kuma zai yi amfani da ita yanzun. Babu tunanin komai a ransa ya murda kofar dakin ya shiga don a tsammaninsa ma ko tana toilet ne. Barci ta ke yi, ta saki jikinta sosai tana bacci bilhaqqi. Gashin kanta ya wargaje a kan filo bakikirin da shi mai sulbi da sheki, amma tsayinsa bai wuce dokin wuyanta ba. Abin da bai taba gani a matan da ya taba sani ba sai na kanti, musamman Muazatu kullum cikin adon gashin kanti ta ke shi ya sa ya fahimci ba ta da gashin ne, kuma ba ta son a gane. Ga wata irin tattausar fata mai hasken da babu surki da mayukan kanti (natural), bakinta jazur dan mitsitsi gwanin ban shaawa. Gashin idonta mai tsayi ya bi fatar idon ya kwanta a kan matsakaitan idanunta. Doguwar riga ce a jikinta mara hannu irin ta robar nan ta bi fatar jikinta ta kwanta a koina, kalarta (orange). Kirjinta bai cika sosai ba, amma cikar kugunta ya nuna Allah ya ajiye mace nan da wani dan lokaci. Bai san tsayin mintunan da ya kwashe a tsaye yana kare mata kallo ba har sai da ta motsa ta juya, ta ji kamar inuwar mutum a kanta. Da sauri ta bude idanunta da suka sauya kala saboda bacci ta sauke su a kan Abdulazeez Dakata, wanda ya yi hanzarin sunkuyawa zai dauki system dinsa. Nata hannun ta kai ta dafe system din. Wani gefen yake kallo bai yarda ya juyo ba balle ta ga kwayan idanunsa. Zan dauki laptop din ne. Ban yi ba. Ta fada da murya irin ta wanda ya tashi daga barci. Tuni ya manta da komai, ya juyo ya dube ta da mamaki. Ba ki yi ba? Amma na gaya miki ki hanzarta ko? Za su rufe kuma ni ma ina amfani da shi. Tura baki ta yi gaba ta kyabe shi abin dariya. Na kunna zan yi, hoton yammata ya hana ni ganin icons din. Ta sakar masa abarsa ta shiga tattare takardunta da suka watse a kan gadon. Kasa dauka ya yi, mamaki kamar zai kashe shi. Shi yarinyar nan ta ke kyabewa baki? Ya girgiza kai ya dauki abarsa, bai ga laifin kowa ba sai kanshi, shi ya bada kafa har ta soma raina shi. Sanda ba ta ganinsa ta isa ta cuno masa baki ne har ta ce ya zuba yammata a computer? Kwafa ya yi wadda ta zame masa alada in abu ya ba shi haushi. Yanzu haka hoton Muazatu ta gani shi ne za ta yi masa sharri wai yammata. Kamar irin ya zuba hotunan mata kala-kala din nan. Har ya kai bakin kofa ya rasa abin da ya saukar da haushin da ta ba shi, sai ya dakata ya juyo ya mika mata hannun damansa na hagun na rike da laptop. Ba ni takardun ni in yi miki. Ba musu ta tattara ta mika masa, idanunta na kallon taga. Dawowa ya yi ya amsa, ya fice yana murmushi. Aladar maza ne jin dadi in matansu na gida sun nuna suna kishinsu ko me? Ita din yarinya ce karama da ya tabbata ba ta san mene ne so ba, amma ta samu zuciyarta da kishinsa. Bai san me ya sa hakan ya darsa abin da ya ji a zuciyarsa ba. Bayan ya gama cike mata takardun cike da mamakin hazakarta a dukkan makarantun da ta yi a Jeddah da Brussels ya yi submitting sai ya dauko tangamemen hoton Muazatu da ke dakinsa ya dawo da shi falo ya kafa. Kana shigowa falon da shi za ka fara tozali. Ba ita ta fito daga daki ba, sai da yunwar cikinta ta hana ta jin dadin kwanciyar da ta ke ta yi tunda ta yi sallar ishai. A hankali ta sauko daga gadon ta nufi kitchen. Nan ta tadda plate da cokalin da ya ci abinci da warmer a kan dining. Da sauri ta bude inda ta tadda farin cous-cous, a plate din da ya ci ta zuba, ba tareda ta tsaya wankewa ba saboda yunwa, ta bude firji ta zuba miya ko dumamawa ba ta tsaya yi ba ta zauna ta hau zubi. Sai da ta yi kat! Ta yi gyatsa ta yi hamdala ta sha ruwa sosai, ta wanke kayan da suka bata, sannan ta bar kicin din. Ba ta yi tozali da hoton Muazatu ba sai washegari. Sai da ta gwammace da ta sani ba ta yi magana a kai ba. Dauke kai ta yi daga kan hoton ta ci gaba da sabgoginta kamar yadda ta saba. Amma abin ya yi mata ciwo sosai, da ma an ce mutum shi yake bada dama a gane abin da ba ya so. Za kuwa ta ba shi mamaki, ko a fuska ba zai kuma gane ba ta son Muazatu ba. A daki ta tadda wata katuwar leda da ta lura tun jiya ya ajiye ta, zama ta yi a gefen gado ta jawo ta ta bude. Kunya ce sosai ta kama ta ganin abin da ya sayo mata, sai dai ta ji dadin macleans din sosai, kuma wanda ta ke so ko a Brussels tunda suka dawo ba ta same shi ba (beverlyhills formula). Da kuma Harpic da parazones na wanke toilet sannan air wicks har kala uku. Ta ji dadi sosai a ranta, wannan ya nuna yana daga cikin mutane masu gano laifukansu da kansu su gyara, ba zalunci da rashin adalci ba ne da ta yi inkari da su. Musamman da ta shiga kitchen ta bude firij da freezer sosai ta yi istigfari na kuskuren fahimtar da ta yi masa a farko. Shi kadai ya san yadda daren jiya ya kasance masa a tarihin rayuwarsa. Wani sabon alamari da ya bakunci gangar jikinsa don ba zai ce da zuciya ba. Ita zuciya so ne a cikinta, gangar jiki kuma ba ka iya katange shi daga abin da ya ga dama. A shekarunsa a duniya talatin kuma cikakken musulmi, mai tsantseni wanda bai taba yin zina ba, yake rokon Allah kullum ya tserar da shi daga aikatata, Ubangiji subhana ya amshi duainsa bai taba aikatawar ba har zuwa yau da aka dauko wata mace da bai so aka mallaka masa da igiyoyin aure. A tunaninsa yadda ta shigo, haka za ta koma inda ta fito, saboda bai yi tanadin hada rayuwa da ita ba ta kowacce fuska. Sannan a perception dinsa ba ka shaawar mace sai kana sonta. Ya yarda ya amince har zuciyarsa ba ya son Suhaana, babu soyayyarta ko rabin cokali a zuciyarsa, amma ganin da ya yi mata jiya tana bacci ya tunatar da shi cewa shi ma namiji ne, yana bukatar mace for now. Ba sai ana son mace kadai ake shaawarta ba. A cire duk wata maganar gangar jikinsa, so ko rashinsa, (he need a wife). Gane hakan da ya yi bai hana (criticsms) iri-iri zuwa cikin kansa ba... Wannan alamari da gangar jikinsa ke bukata a yanzu baa farawa don a daina... what of idan ta yi ciki? Ya ya rabuwar za ta kasance mai sauki idan da Da a tsakani? Wane uzuri zai kawowa Mammah idan ya mayar mata yarinya da ciki? Runtse idanunsa ya yi da karfi ya ci gaba da juyi a makeken gadonsa cikin wani hali na kaka-ni-kayi! Wata zuciyarsa ta kawo shawarar ya kai ta asibiti a yi mata (family planning), da gaggawa wata zuciyarta hana ta ce, hakan zalunci ne, babban zalunci!!! Ba ta taba haihuwa ba, idan ka lalata mata mahaifa sannan ka sake ta, Allah ba zai barka ba. Cikin halin da ya kwana kenan, ya rasa inda zai sa kansa. Duk shawarar da ya kama in ya zurfafa tunani, sai ya ga ba mafita ba ce. Mafita guda biyu ce, ya sa mata ido ta koma a yadda ta zo. Ya auro Muazatu su shimfida rayuwa mai maana da soyayya mara yankewa. Ko kuma ya maida Hafsat cikakkiyar matarsa, amma babu rabuwa, kuma babu Muazatu... sosai yake girgiza kai inresentment..... zan iya jure komi in dai zan same ki Muazatu!!! Ya fada a fili cikin rashin sanin abin yi, da ciwon mara mai tsanani ya kwana. Bai taba ganin dare mai tsayin na yau ba a kafatanin rayuwarsa. Idan haka sauran watannin da suka rage musu za su kare, ashe ba zai kai su da sauran numfashi ba. Mataki biyu Abdulazeez ya dauka don kare auren kwangilarsa lafiya ba tare da ya kara fadawa halin da ya samu kansa jiya ba. Na farko ya daina shiga dakin Hafsat, in ganin lafiyar tata ya zama dole, zai dinga jiranta a falo. Mataki na biyu, zai sai mata waya ya dinga kiranta yana jin lafiyar tata don rage kusanci a tsakaninsu. Zai ci gaba da kin dawowa gida sai ta kure. Rashin Muazatu ma ya taimaka wajen samun sararinsa da har wata mace za ta yi kokarin kutsowa cikin rayuwarsa. Muazatu ba ta barinsa haka nan ba sa tare, sai in yana bakin aiki, in tana gari suna tare, in ba sa gari daya koyaushe suna manne a waya. Don haka washegari Hafsat ba ta sanya Abdulazeez a idanunta ba ya fice ofis da sassafe. Da ya tashi office gidansu ya wuce, a can ya ci abinci. Sai da Mammah ta ga karfe tara ta yi ba shi da niyyar komawa gida ta ce ya tashi ya tafi. A nan yake gaya wa Mammah zai saya wa Hafsat waya tunda ta ki zuwa gidansu, kuma ta hana shi kawo ta. Ta yi murmushi cikin ranta ta ce, Mu je zuwa... wai mahaukaci ya hau Kura. A (Bannex) da ke Wuse 2 ya tsaya ya yi cinikin wata karamar (Iphone) ya saya da sunan Hafsat. Har jikin (receipt) Hafsat Dakata aka rubuta. Sanda ya iso gida ta dade da kulewa a daki. Ya so ya tadda ita a falon ya ba ta wayar, hakan bai yiwu ba. Ga shi kuma ya sa wa kansa takunkumin daina shiga dakinta. Sai washegari zai fita ita kuma ta fito daga kicin suka hada ido, rabon da ta ganshi tun shekaranjiya. Shi ya fara dauke idonsa, zuciyarsa na harbawa. Akwai wani maganadisu mai kama da magnet a cikin kwayar idanunta, wanda duk lokacin da ya yi kuskuren hada ido da ita sai ya ji shi a jikinsa. Neman kujera ya yi ya zauna, ya dafe kansa ya kasa ce mata komai. A sanyaye ta zagaye kujerar bayansa, ta tsugunna a gabansa, ta ce. Good morning. Da ka ya amsa ta hanyar daga kansa da ke cikin hannayensa, amma ba ta yi nasarar samun kallo daga gare shi ba. Inda sabo ya ci a ce ta saba, don haka ba ta wani damu ba ta mike za ta wuce. A sanyaye ya cira kai daga cikin hannayensa ya ce, Hafsah? Dakatawa ta yi ba tare da ta juyo ba. Cikin mamakin wai ashe ya san sunanta? Dauki wayar nan taki ce. Dawowa ta yi ta dauki wayar ta duba, sai kuma ta mayar ta ajiye ta a inda ta dauke ta tana girgiza kai. Ba abin da zan yi da ita Yaya Azeez. Cikin mamaki ya ce, Ba za ki dinga kiran Mamanki ba? Ni ma zan dinga kiranki in ina office. Ga mamakinsa, sai hawaye suka balle mata. Ta ya ya za ta gaya masa cewa, mahaifiyarsa ta daina sonta? Tunda ta kawo ta nan ta aje yau kusan watanni hudu ba ta kara waiwayarta ba. Sai ta mike kawai tana share hawaye ta nufi dakinta. Haushi, takaici, mamaki su suka taru suka rufe Abdulazeez. Bai san lokacin da ya bi ta dakin ba a fusace. Tana zaune a kujerar gaban mirrow ta kifa kanta a kan madubin tana kuka. Hannunta ya fizga ya mikar da ita tsaye suna fuskantar juna. Kafadunta biyu ya rike ya girgiza ta. Na yi kama da saanki Haleem da za ki dinga kawo min raini? Ta fiddo jajayen idanunta tana dubansa cikin firgici. Ya sassauta rikon da ya yi mata ganin ta tsorata sosai yadda yake so, ya ja hannunta ya zaunar da ita a gefen gado, ya ci gaba da tsayuwa a kanta. Muryarsa akwai sassauci a sailin da yake cewa. Jiya na yi miki abin arziki na ba ki system dina, ki ka saka min da rashin kunya. Ban daddara ba yau na sake yi miki abin arziki na sayo miki waya don ki dinga magana da Mamanki da yan uwanki ni ma in dinga jin lafiyarki, in daina tunanin na jima a office ban san halin da ki ke ciki ba, shi ne za ki yi min rashin kunya again wai ba kya so? Cikin girgiza kai hawaye na ci gaba da fita ta ce, Ba rashin kunya ba ne. Yanzu misali in ba ka system dina, kana kunnawa ka ga hoton namiji ya ya za ka ji? Waya kuma abin da ya sa na ce maka bana bukatarta saboda da ma don Mammah nake sonta, kuma Mamma ta dade da mantawa da ni, ta daina sona... tunda ta kawo ni ba ta kara nemana ba alhalin ta san ba ni da kowa sai ita... Ta kifa kanta cikin cinyoyinta, ta ci gaba da kuka sosai mai taba zuciya. Hannun Abdulazeez ta ji a saman kafadunta ya cira ta tsaye, kokari yake ya raba tafukan hannayenta da fuskarta, amma ta ki bari. Ya ce, Suhaana, in kin yarda ni Yayanki ne Azeez kamar yadda ki ka fada dazu ki dube ni... Sosai ta rage kukan domin abin da ba ta zata ba ne. Hannunsa ya kai habarta ya dago fuskarta daidai tashi, ya shiga share mata hawayen da yatsun hannunshi. Runtse idanunta ta yi sakamakon jin wani sabon alamari na bin illahirin gangar jikinta. Bude idonki Suhaana ki dube ni, magana za mu yi. A hankali ta ke bude idon, amma ta kasa bude su gaba daya ta dube shi cikin ido, kamar yadda yake nufi. Yana da wani irin girma na musamman a idanunta ba tun yau ba. Burinta ya daina kai hannu saman fuskarta don haka ta bude idon. Janta ya yi suka zauna a gefen gadonta yana kallon agogo, da mamaki yau shi ne har karfe tara na safe a gida saboda diyar Mammah. Sai da ya ga ta nutsu sosai ya ce, Ashe mutum yana fushi da iyayensa Hafsat Kai ta girgiza masa. Amma ke ki ke fushi da Mamanki? Sunkuyar da kai ta yi tana kallon yatsun kafarta. Mikewa ya yi ya koma falo, ya dauko wayar ya dawo ya dora mata a saman cinyarta, Common, call your Mammah.... SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* ****** Kiran lambobi masu tsayi ne ya tashe ta daga barci bayan ta yi sallar asubah ta koma. Code ne na kasar Amurka. Barcin idonta ya wartsake nan da nan sai dai kafin ta amsa kiran, ya katse. Ta ciji yatsa za ta kira, kiran ya sake shigowa. Wannan karon ta yi nasarar amsawa. Bride of the year. In ji (Brothern) da babu kamarsa a wajenta. Illaila... Ta amsa tana dariya. Sunan da ta ke kiransa kenan tana yarinya, ba ta iya cewa Ismaeela ba. Mammahs doll (yar tsanar Mammah). Shi ma ya rama, kafin ya rufe baki ta rama, Bachelors of the century... “Brides of the moment. Ismaeel ya amsa cooly, muryarsa cike da kulawa ga yar uwar tasa wadda ya shafe watanni bai yi magana da ita ba. Ya yi-ya yi Mammah ta ba shi lambarta ta ce ba ta da waya, Yayan nasa kuwa tunda ya bada masa kasa a ido a kan bukatarsa na a hada baki da shi a yaudari Mammah a kan sistern da bai da kamarta ya kulla gaba da shi. Jiya kamar daga sama kawai sai ga lamba Mammah ta turo masa, wai ta Suhaanah ce. Tun a lokacin ya so kiranta ya yi tunanin dare ne sosai a wajensu, haka ya yi ta daurewa har gari ya waye. He so much missed her, she so much missed him. Akwai wata irin shakuwa a tsakaninsu wadda ta samo asali tun lokacin da suke taya Mammah rainon ta a Jeddah.Ta san da suna tare da ba ta shiga damuwar da ta shiga a baya ba. Hira suka shiga yi, amma ko kadan ban da zancen aurenta ko halin da auren ke ciki, hirarsu suke irin wadda suka saba tun ta yarinta. Ta tambaye shi ina labarin Usman, ya ce yazo America daga Brussels suna tare, ya je excursion birnin Orlando. Tana jin fitar motar Abdulazeez wajejen karfe takwas na safe, ba su yi sallama ba sai da cajin wayarta ya kare, wayar ta kashe kanta. Ta sauko daga gadon ta sanya wayar a caji. Ta duba agogo, karfe takwas na safe. Bandaki ta shiga ta yi wanka, wanke baki, alwala sannan ta fito. Ta samu kanta da yin kwalliya sosai da (lace) mai tsananin taushi, kalar pusher pink da ratsin baki. Sosai kalar da leshin suka karbeta suka kwanta a sassalkar fatar jikinta. Ta fesa turare (christian dior) ta fada kitchen ta daura apronta hau girki. Wata zuciyar na cewa, ta dafa da Abdulazeez, wata na cewa aa, ko kin dafa da shi ba ci zai yi ba, ina ma ki ka ganshi? Motsi ta ji ana zura mukulli a jikin kofar falon, ko kadan ba ta ji karar shigowar motarshi ba, domin ta kure qiraar Abdurrahman Sudaith a gidan gabadaya cikin Suratul Maidah, ko ba don haka ba motar Abduazeez GMC Terrain ba ta kara, sai in shi ya yi horn. Ba ta fito ba ci gaba ta yi da abin da ta ke yi, tana mamakin me ya dawo da shi a wannan lokacin? Misalin karfe goma sha daya na safe. Zama ta yi ta ci dankali na turawa da agadan data soya da farfesun kaza, ta wanke hannunta da liquid soap ta cire apron din ta adana a mazauninsa ta kora da gwangwaninfantasannan ta fito zuwa falon. Ya watsar da gown dinsa da wig a tsakar falon, hatta briefcase din ta yi nata wurin. Kwance yake a kujerar da ta fi kowacce tsayi a falon, ko takalmin kafarsa da socksbai cire ba,he dont even loose his tie, kwanciyar da daga gani za ka fahimci ba ta lafiya ba ce ya yi. Ji ta yi gabanta ya yi mummunan faduwa, ta rabe ta bayan kujerar da yake kwance ta wuce dakinta ta rufo kofa a hankali. Amma ga mamakinta ta kasa zaune ta kasa tsaye, so ta ke ta san me ya same shi, sai dai ta san ba ta da wannan matsayin. To amma ai ko babu aure Abdulazeez dan uwanta ne kamar Ismaeel, tunda Mammah ce ta haife shi, ba za ta taba son wani mummunan abu ya faru da shi ba, ko rashin lafiya. A haka lokacin sallar azahar ya yi mata, da ma tana da alwala ta matsa wajen ibadarta ta tada sallah. Samun kanta ta yi a cikin sujjadarta tana yi wa Abdulazeez addua har da hawayenta, a kan ko ma me ye ke damunshi, Allah ya sa ya zo masa da sauki. Da ta idar tana so ta fito falo ta ga halin da yake ciki, amma ta kasa. Zama ta yi ta hada kai da gwiwa sai a lokacin ta tuna da wayarta, ko Mammah za ta kira ta gaya mata ya dawo a cikin wani irin yanayi ba lokacin da ya saba dawowa ba? Wata zuciyar ta ce. Akul! Ki je ki tabbatar da abin da ya same shi din tukunna, yanzu haka ma ya bar gidan. Mikewa ta yi cikin sanda kamar marar gaskiya ta bude kofa ta fito falon. Yana nan yadda ta barshi awanni uku da suka wuce, ko juyawa bai yi ba. Ya yi rub-da-ciki a kan hannayensa. Is touching him a crime? (Taba shi zai zama laifi?) Ta tambayi kanta. Ba ta sani ba, don haka ta je ta tsaya a kansa tana tunanin abin yi. Lokacin sallah ya yi. Ta fada muryarta na karkarwa. Ko motsi bai yi ba, sai ta tsugunna ta kai hannunta kan goshinsa. Zafi rau! Ta taba wuyansa shi ma kamar garwashi don zafi. Kawai sai ta durkushe a wurin ta sanya kuka. Da kyar ya cira kansa daga kwancen ya bude idanunsa da suka kankance suka yi jawur yana kallonta. Ta dago fuskarta suka yi wa juna kuri da ido. Wane taimako zan iya ba ka? Abinda ta iya tambayarsa kawai kenan cikin karkarwar murya. Duk halin da yake ciki sai da ya yi murmushi,shes very soft-hearted. Ki duba lokar jikin gadona akwai paracetamol ki dauko min. Dakin a bude yake? Ya lumshe ido tare da daga kai, shi bai ma taba rufe kofar dakinsa ba wai don zai fita, ashe ba ta taba shiga ba? Mikewa ta yi da hanzarinta har tana tuntube zuwa dakin. A tsayin rayuwarta ba ta taba ganin dakin barci mai ban shaawa irin wannan ba. Yafi nata tsaruwa ninkin ba ninkin. Ko kuma idonta ne ya ga hakan? Bazata iya cewa ba. (English Bedroom) komai fari da ruwan toka (white and ash), hatta labulayen. Ba ta wannan ta ke ba, drower din ta nufa kai tsaye ta debo kwayar maganin ta fito. Kicin ta koma ta samo gorar ruwa mara sanyi ta dawo. Taimaka mishi ta yi ya tashi zaune, ta sa mai kwayar maganin a hannunsa ya watsa su a baki ta kafa mai robar ruwan a bakinsa. Komawa ya yi zai kwanta ta rike masa hannu, dan dago ido ya yi da kyar ya dube ta da idanun tambaya. Kada ka kwanta a nan, ka koma daki. Ba zan iya ba. Ya ce da ita a wahalce. Ill help. Ta ba shi amsa. Ciwo ya ci karfinsa, amma a ransa ta ba shi dariya sosai. Dube ta yar ficika da ita, ko ya za ta iya daga kato irinsa? Da zai iya doguwar magana da ya tambaye ta hakan. Ki bari in kwanta kadan forsome minutes tunda na sha magani zan koma. Ba ta ce komai ba ta koma ta zauna a gabansa, zuciyarta a jagule. Ya maida idonsa ya rufe sai bacci. Da ta ji yana sauke numfashi irin na bacci, sai ta samu kwanciyar hankali, ta koma daki ta yi sallar laasar. Kicin ta koma ta hado duk abin da ta soya a kan tray ta dafa shayi baki da lipton din tetly tea, ta zuba kayan kamshi su kani fari da citta kadan ta tace ta dauko ta dawo falon da su, ta ajiye a gefensa. Baccinsa ya yi nisa sosai, don haka sai ta koma daki ta kwanta tana ci gaba da yi masa adduar samun sauki. Cikin dan barcin da ya soma figarta ta ji kamar ana kiran sunanta. Ta bude ido sosai, daga falo ne Abdulazeez ke kiranta. Da sauri ta fito, ya tashi yana zaune dafe da kansa da hannun damansa. Zama ta yi a gefensa ta hau zuba masa shayi ta zuba zuma, ta juya ta mika masa. Bai yi musu ba ya karba ya soma sipping a hankali. Tana kokarin zuba agada da chipsya ce. Bar wannan. Ba ni farfesun kawai. Ta zuba a dan bowl na tangaran ta tura gabansa. Tana so ta ce ya cire suitdin mana saboda sai zufa yake yi, amma ta yi shiru, kada ta wuce makadi da rawa. Kafafunsa ya mika mata bayan ya ajiye bowl din a gefe ba don ya gama ba.Cire min. Dago ido ta yi cikin wata irin siga ta kalle shi. Kwayar idanunsu suka sarke da na juna. Ta ya ya za ta iya kama kafafunsa ta cire masa takalmi da safa? Aikin ya so ya yi mata tsauri. Shi kuma ba da wata manufa ya fadi hakan ba, zazzabin jikinsa ya sauka ne, zafi yake ji sosai. Ganin umarninsa ya jefa ta a gajeren tunani, sai ya fara kokarin cirewa da kansa. “Sorry, you can go (za ki iya tafiya). Sai ta ji ba dadi, mene ne a cikin cire safa da takalmi da ta kasa? Bashi da lafiya shine dalili. Bayan wannan ba wani abu.Mikewa ta yi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi daki zuciyarta babu dadi. Da ya cire takalman ci gaba ya yi da shan farfesun kadan-kadan. Girkinta yana da wani sinadarin dandano irin na Mammansa. Ya fahimci hakan tun sanda yake cin abincinta, lokacin da tana amarya. Ganin cin abincin nata da yake yi zai haifar da wani bond na daban a tsakaninsu shi ya sa ya daina, ba don ba ya so ba. Auren da ba mai dorewa ba bai kamata ya bari ya yi tasiri mai yawa a zuciyarsa ba. A nan ya bar bowl da spoon din da ya sha farfesun ya tattara shirginsa ya koma daki. Bai kara fitowa ba, wanka ya yi, sannan ya yi sallolin azahar da laasar da ke kansa, ya bi lafiyar gadonsa ya kwanta bayan ya kashe wayoyinsa. Tufka da warwara yake, na yadda rayuwarsu ta gaba za ta kasance tsakaninshi da ita. ****** Ta ci abincin dare ta yi shirin kwanciya, amma anya za ta iya barcin nan mijinta na gefe ba shi da lafiya? “Ki daina kiranshi mijinki fa, mijin Mu’azatu dai”. Wata zuciyar ta gyara mata.ď Har yanzu hotonta da ya kafa musu a falo yana nan. Ta shafa wa kanta lafiya ne ta daina kallon bangaren da hoton yake. Abdulazeez bai cancanci ki tausaya masa ba, saboda ba sonki yake ba, ko yau din ma da ya kula ki don ba shi da yadda zai yi ne, ba shi da mai taimaka masa. Manta da shi ki yi barcinki. Amma abin mamaki ta kasa bin wannan shawarar ta zuciya mai gaskiya. Ko ba ya sona Dan Mommah ne, duk wani jininta amana ne a gare ni, ba za ta ga Da na ba lafiya ta kauda kai ba. Ni ma ba so nake ya so ni ba, amma tunda ya fara kyautata min, dole in kyautata masa ko da ba zai gode ba. Saukowa ta yi daga gadon ta bude wardrove dinta, ta dauko wadataccen mayafi ta lulluba. Kicin ta nufa ta gasa masa karamar kazar gidan gona data yiwa hadin kayan kamshi dana dandano sosai ta yayyanka akan farantita hada da gwangwanin maltinata kinkima a kan tray ta yi dakin nasa. Tsayawa ta yi a bakin kofar ta yi sallama, kirjinta na dukan uku-uku. Tana jin sautin muryarsa kasa-kasa kamar yana waya, Come in. Ya fada yadda za ta jiyo ci gaba da wayarsa. Murda kofar ta yi ta shiga, sanyin A.C har ya yi yawa, kamshin turaren da yake yawan amfani da shi (creedaventus) ya gauraye da sanyi da kamshin A.Cn ya bada wani atmosphere mai dadi da sanyaya zuciya. Karasawa ta yi ta janyo wani dan teburin gilashi karami ta dora tray din hannunta, ta matso da shi gabansa. Wayarsa ya ci gaba da yi, bai ce mata komai ba. Cikin hirarsa ta ji yana fadin, Iv never lost a case, but I lose it today Muazatu. (Ban taba faduwa a shariah ba amma na fadi yau Muazatu). Yanzu haka a kwance nake ba ni da lafiya tun safe..... Tsaki ta yi ta juya za ta fice, sai jin hannunta ta yi cikin na Abdulazeez, ya riko hannunta ta baya. Kasa juyowa ta yi, zuciyarta na wani irin tafasa, ita ba ta taba ganin irin wannan masifar ba, Muazatu dai! Komai Muazatu! Tana jin ranar da suka yi aure sai ya maida ita cikinsa don so. To ke ina ruwanki? Wani bangare na zuciyarta ya tambaya. Zuciyarta ta bada amsa nan take. “Ni ma mace ce, ko da baa sona ina da zuciya irin ta yaya mata tunda muna tare, har zuwa ranar da za mu rabu. Watakila ranar ne zan daina damuwa da lamarinta. Ba ta ankara ba ta ji hawaye sun shimfido mata. Sauri ta yi ta kai daya hannun ta share su. Bacin ranta na ninkuwa, ya hana ta tafiya kuma bai fasa wayarsa ba. Kalaman da ake fada a cikin wayar ba ta taba jinsu ba. Idan ta fizge hannunta ya ce ta yi masa rashin kunya. Sun yi a kalla mintuna biyar a haka, sannan ya yi sallama da Muazatu. ...missed you Habeeb Qalby... ... missed you more habeebty... Ya jefa wayar kan gado ya juyo ta suka yi facing juna. Duk da babu hawaye a kan kundukukinta idanunta sun yi jazur, kuma ya gane kuka ta ke yi. Kukan farin mutum ba ya buya,gabadaya fuskarta ta kada ta yi jazur. Ban san abin da yake yawan sanya ki kuka ba. Fitar hawaye abu ne mai matukar sauki a wurinki na fahimta, cmmon zo mu zauna, ki gaya min ni ne nake sa ki kuka, ko kina yi kawai don ki ji dadi ne? Janyo ta yayi ya zaunar a kusa da shi, jikinsu na gugar na juna. Shiru ta yi masa kamar ba da ita yake magana ba. Ko ransa ya baci, to wannan karon bai nuna ba, ya yi appreciating kulawar da ta nuna masa a yau, a lokacin da yake tsananin bukatar hakan. Ya tuno kukan da ta rika yi ganinsa cikin halin rashin lafiya, wannan ya nuna yana da wani matsayi ko ya ya ne a zuciyarta, wanda bai san a wane rukuni yake ba tsakanin na miji da na dan uwa. Kusa da ita ya jawo tabledin da ta dora masa abinci. “Lets eat, mu ci tare. Na tabbata ke ma ba ki ci ba. Girgiza kai ta yi ranta a jagule, Ni ba na jin yunwa. “Space din cikina zai ishe mu mu biyu, ki ci. I assure you cikina zai shigo. Murmushi ta yi ta sunkuyar da kanta, ko ba komai yayi nasara ya fiddo murmushi akan fuskartahow could this be possible? Ta fada cikin raunin murya. A duniyar yan uwantaka everthing is possible Hafsah, just eat, muna ci muna hira. Dauke kai ta yi cikin mamakinsa, da ma haka yake? Haka yake Hafsat, in ki ka yi laakari da yadda yake tadi da Muazatunsa ke yake yi wa (horrowface), ke da ba ya so. Ta saci kallonsa ta gefen idonta, cin kazarsa yake da forka tsanake. Sajen fuskarsa ya kwanta a kan kyakkyawar fuskarsa sai sheki yake kamar gashin kansa. Ta yi rayuwa a cikin larabawa da turawa ba ta taba ganin wanda saje ya yi wa kyau irin Abdulazeez ba, hancinsa gwanin kyau, idonsa abin shaawa, bakinsa..... dole wannan Muazatun ta nace masa tunda ta san ya fi ta komai. Ba ta ankara ba ya juyo sai idonsa cikin nata, ya kama kwayar idonta red-handed tana yi masa kallon kurillah na babu gaira babu dalili, kallo mai zurfi mai cike da magana wadda bakinta ba zai iya furtawa ba. Da sauri ta sunkuyar da kanta, shi ma ya shiga kallonta. Kafin ya yi murmushi ya juya ya ci gaba da cin abincin. Tunda ta ce ba za ta ci ba, bai takura ta ba. Karamin firjin cikin dakin ya mike ya nufa, gwangwanin coca-cola ya dauko ya dawo gefenta ya sake zama.Maltinar data kawo masa ya ture gefe. (Hes a Coca-Cola addict). Budewa ya yi ya sha sosai, ya rike ragowar a hannunsa. Hafsat me ya sa sanya ki kuka? Ya tambaya (in subdued). Shiru ta yi ba ta ba shi amsa ba, to ta ce masa me? Abubuwa da yawa suna sanya ta kuka. Tana da tausayi, tana da raunin zuciya, ba ta son ji ko ganin alamarin Muazatu, shi kuma yana yi mata abubuwa da gayya tunda ya fahimci ba ta so din. Don haka yi masa shirun shi ne abu mafi alkhairi a gare ta. Barin zancen ya yi don ya yarda ba za ta amsa ba. Wani sabon zancen ya kawo har mamakin kansa yake yi. Tana basar da shi, tana komai amma kamar dole sai an yi hirar? So yake ya debe mata damuwar da ya ganta a ciki bayan kuma shi ne sanadinta. “Who thought you how to take care of a patient? (Wa ya koyar da ke kula da maras lafiya?) Girgiza kai ta yi, kafin ta amsa cikin kankanuwar murya, Nobody! Wato babu kowa. Abdulazeez ya dube ta na yan sakanni, Sagir da yarsa na kara fado masa a rai, hatta yadda ta ke basarwa haka Sagir ke basarwa in yana ba da amsa. Ajiyar zuciya ya yi yana lissafi cikin zuciyarsa. Hafsah. Ya kira ta da bayyanannen sauti. Dagowa ta yi a hankali ta dube shi, ya fi kowa iya kiran Hafsah, yana da wani irin taushin murya da dole in yana magana ka saurare shi, balle kuma in a kotu ne, jerarrun kalaman bakinsa na da daukar hankali da kowanne harshe yake yinsu tsakanin Hausa da Turanci. Yana da lafuzza nasa na kansa masu sanya mai saurarensa nutsuwa. Sosai ta ji wata irin nutsuwa ta shige ta, ta ba shi dukkan hankalinta don da alama magana mai maana yake so su yi ba wasan da yake ta janta da shi tun dazu ba, don gusar da bacin ranta. Kafin a yi mana aure mun zauna, mun yi maganganu masu yawa ko? Wadanda suka shafi rayuwar auren da za mu yi, da lokacin da za mu yi (terminating) auren. Na fada miki cikin zamanmu babu takura, babu munanawa juna, babu zalunci. Kowa zai yi zaman kansa ne ya ci gashin kansa. Sannan ya cika alkawarin da ya daukarwa dan uwansa. Don haka yanzu da ki ka yi waya hankalina ya gaza kwanciya, don haka nake kara rokonki ki rike amanar da ke tsakaninmu ki san abin da za ki dinga gaya wa Mammah da su Ismaeel. Ta fannina ina nan ina ta kokarin cika alkawurra na, wane alkawari ne onyour side? Sake gaya min don in tabbatar ba ki manta ba. Ga mamakin Hafsat ba ta farin ciki da zuwan ranar rabuwar nan yanzu. Amma ta fahimci rabuwar ita ce babban abin da ya sa gaba a yanzu tunda ga shi yana kara jaddada mata. Kara sunkuyar da kai ta yi, ta soma karanto masa alkawuran wadanda suke kwance luf a cikin kanta. Mun rabu ne ba don ba ma son juna ba, sai don kowannenmu ya kasa jure hali da dabiun dan uwansa. Haka kaddara ta tanadar mana Mommah. Kwanciyar sautinta yake bi da tasa zuciyar. A lokacin da ta ke furta kalaman. Ta fade su ne cikin kwantaccen sauti kamar da Mammah din ta ke magana. Je ki kwanta Hafsat, na gode da kulawarki ta yau. Allah ya ba mu alkhairi. Cikin nutsuwa ta mike ta bar dakin, ba tare da ta sake waiwayowa ba. Insha Allahu, daga rana irin ta yau za ta koya wa zuciyarta jarumta, ta daina hango komai sai ranar rabuwa. Bacin ran da ta ke sa wa kanta a kan Muazatu aikin banza ne Abdulazeez bai fa san tana yi ba. Ya yi nisa a kan Muazatu, nisan da ko uwar da ta haife shi ba ta isa tabuka komai a kai ba balle wata ita Hafsat da bai dauke ta cikakkiyar mutum ba, face wani tsani da zai bi ya taka ya kai ga cikar burinsa. Don haka barcinta ta yi cikin nutsuwa har da munshari. Washegari da ta yi sallar asubah ba ta koma gado ba, kicin ta fada ta shirya masa break fast mai rai da motsi. Ko kafin karfe bakwai ta shirya komai tsaf a cikin food basket don ta dade da sanin ba ya karya kumallo a gida sai ya je office. Daki ta koma ta yi wanka, doguwar riga ta saka kirar Dammam ruwan dorawa. Ta sharce kanta ta kame da katon bound shima (yellow). Turarrukanta ta feshe jikinta da su, sannan ta fito falo. A tsakiyar falon ta tadda shi yana shirya wasu takardu a briefcase dinsa. Morning Suhaana. Ya fada ba tare da ya dago ya dube ta ba yana ci gaba da abin da yake yi. Gefensa ta karasa ta russuna tana gaishe shi. Yaya jikin naka Yaya Azeez? Wannan karon ne ya juyo ya dube ta, ta yi wani irin kyau da (fresh) kamar jinsin Somali. Hannun damanshi ya mika mata, Gara mu yi irin wannan gaisuwar za ta fi gamsarwa. Kunya ta ji sosai ta sunne fuskarta cikin tafukanta tana murmushi. Tun a Brussels Mommah ta hana ni yin hannu da maza. Idanunsa biyu ya fiddo mata, Kuma ta ce har mijin da ta daura miki aure da shi? Mikewa ta yi, ta nufi daki da gudunta ta rufe kofa. Ba ta taba jin kunyar Da namiji a rayuwarta irin ta yau ba. Kamar wani abu daban ya bukaci su yi ba gaisuwa ba. Ana fadin kalmar Miji sosai a cikin magana ba tare da mace ta ji komai a kai ba. To amma gare ta yadda ya fada din da tunedin da ya yi amfani ya zo mata da sabon salo, ga wani irin launi da kwayar idanunsa ta bayar na rikida a sanda yake fadin maganar kamar ba Yayansu Azeez ba. Wani kwayan mutum guda daya da ta ke wa fassarori masu yawa a baya tun daga shekarunta na kuruciya har girma zuwa dangantakar AURE da ya hada su yanzu. Kullum kuma daga sanin da ta yi masa zuwa yau sake rikida yake yana fitar da sababbin halaye da kamanni masu ban mamaki na yau daban da na gobe da ke sanyawa ta rasa gane inda ya sa gaba. Wato gaskiya ne da aka ce, kada ka yi judging halin mutum sai ka zauna da shi. Idan ka ce za ka yi hukunci da fassarar zuciyarka a kan mutum, za ka fadi gaibu kuma Ubangiji subhana ya hana amfani da zato, domin zunubi ne. Zaman tare shi kadai yake proving who that person is (wane ne wannan mutum din).Abdulazeez kishiyar yadda ta dauke shi yake a bangarori da dama, barshi dai da raayin rikau irin nasa, amma mutum ne mai matukar kirki, kuma mai sanin yakamata. Masanin sirrin zamantakewa. Kokari yake daga jiya zuwa yau ya sa ta sake da shi ta daina wannan dari-darin da ta ke yi da shi. Sai dai ya manta cewa, duk wani abu da aka san yana da karshe to ba za a zira jiki a cikinsa ba. In yau sun yi musabaha gobe kuma sai Yayan musabaha ko babanta? Jingine ta ke da kofa idanunta a rufe tana wannan tunanin. Ta tuno da abincin da ta shirya masa. Da gudu ta bude kofar ta fito ta sungumo basket din ta bi bayansa. Shi har ya isa ga motar ya bude zai shiga. Yaya Azeez. Ta kira sunansa. Waiwayowa ya yi ya kuma dakata da shiga motar har ta karaso. Kujerar baya ta bude ta sanya basket din, ya shiga motar ya tashe ta. Kanta ta zura ta window din side din da ya ke ta soma magana cikin sanyin muryarta. Na san ka dade da daina tafiya da abincina ofis. Ban sani ba ko abokanka ne suka ce babu dadi? Amma yau ka yi min alfarma ka ci ko babu dadin, saboda ba ka da lafiya. Bai kamata ka zauna da yunwa bahar sai ka dawo. Idanu ya zuba mata, ya kasa cewa komai. Ta ja da baya tana waving dinsa. Ya ja motar tare da daga mata hannu ya fita daga get din gidan nasa. Sai zamansu ya dauki wani sabon salo mai ban shaawa. Kowanne kokari yake ya kyautatawa dan uwansa iyakar iyawarsa. Tun daga ranar Abdulazeez bai kara girki da kansa ba, girkin matarsa Hafsat yake ci safe da rana da daddare. Da safe zai tafi da shi, da rana zai turo a daukar masa, da daddare za su zauna su ci tare a dining ko a dakinsa. In ba shi da ayyuka da yawa su yi hirar mutanen gidansu ko ya ba ta labarin shariu iri-iri da suke yi a kotu. Ya kan gaya mata cewa, rape case wato lamarin fyade ya fi yawa yanzu a kotunan Nigeria. Rannan yana bata labarin wata shariah ta fyade da suka yisai wani abu ya fado mata a rai, ta gyara zama ta hau bashi labari inda tace. Ka ga sanda muke Brussels, akwai wani malamin mu Belgianya kan gaya mana each kind of sexual act is not a crime in their countryexcept rapeindai mutumya girma, yawuce shekara sha takwas.They teach this as sex education. Dana dawo Nigeria na kara hankali sai na fahimci cewa karya suke yi, every sexual act is prohibited, not only rape. Ba tare da kowa ya fahimtar da ni ba. Abdulazeez rubutu yake yi, amma abin da ta ke fada sai ya dauki hankalinsa. Me ake da makarantun nasara?Hasbunallahu waniimal wakeelya ce cikin ransa. Dakatawa ya yi da rubutun ba tare da ya dago ya dube ta ba. How do you came to know that? (Ta ya ya ki ka fahimci hakan)? Ya tambaye ta, cikin kokarin danne kaduwarsa. Sake gyara zama ta yi, ta soma bashi labari. A secondary school dinmu ta ST. Barchmans College a ajinmu akwai wani yaro Bature Fayol da wata yarinya Jessica, a gaban kowa suke kissing. Ban saba ganin wannan aladar ba a inda na baro (Jeddah) don haka hankalina ya tashi na gaya class masterdinmu don ya hana su. Sai ya tara mu duka ya ce, They are not committing a crime, since its not a rape. Amma yanzu shekarunsu sun yi kadan su dinga aikata hakan su bari sai sun gama high-school. Na so in gaya wa Mommah a lokacin na ji tsoro sanin cewamuddin taji sai ta cire ni daga makarantar nikuma inason makarantar saboda na saba da ita. Amma na sa a raina abin da malamin nan ya fada ba gaskiya ba ne, wannan aiki ne na arna marassa addini. Turawa ba wani abu ba ne a wurinsu ko a hanya za ka iya ganin suna kissing, masu aure da marasa aure. Da muka dawo Nigeria sosai na ga bambanci mai yawa. Ban ga mata na rungumar maza ba wai don ana goodbye, ban ga ana kissing a kan titi ba. Abubuwan da na saba gani duk bana ganinsu a nan. Ko masu aure ban ga suna yi ba. I then concluded that; things like that are not accepted here in Nigeria and hence, its a crime in Islam and culturedaga manya har yara, masu aure da marassa aure. Abdulazeez gumm! Ya yi, ya ki ba ta amsa. Haka ne ko ba haka ne ba? Ta tambayeshi curiously. Ban sani ba Suhaana, tunda dai kin ga ni ba ni da mata. Ya amsa a gajarce, cikin son a bar zancen. Da sauri ta ce. Ba ga ni ba? Dariya ce ta kama shi, amma ya gintse, saboda yadda ta fadi maganar kanta tsaye kuma innocently. Suhaanah matar wucin gadi ce ke. Mene ne wucin gadi? Ina nufin.......temporary. Ok, na fahimta. Mu matan wucin-gadi ba a kiranmu matan aure? This is beyond my knowledge Hafsa. Da na san kina da baki da Law na zabar miki. An tabo hirar da ta ke so (karatu) tuni ta manta da waccan.Au, ba law ka zabar min ba? Mommah ta yi tsammanin hakan. Girgiza kai ya yi, Ba law na cike miki ba, career din da ya fi dacewa da ke ne. Tashi ki je ki kwanta kin dame ni da surutu, kada gobe ki makara a kicin, kuma ki hana ni fita sai kin gama. Yau saura kadan ki sa a zane ni Dariya ta saka ta mike tana fadin, Zan so ganinka Justice yana zane ka. Murmushi ya yi, ya ce mata, Sai dai in tafi da ke a zane mu tare, tunda ke ki ke makarar da ni. Night! Ya kada mata yatsu. Ya maida kai kan aikinsa lokaci zuwa lokaci yana tariyo hirarsu a ransa. ...Sex is a crime in Nigeria...all kind of sexual acts are prohibited in Islam and culture daga manya har yara, masu aure da marassa aure....... sai dariya ta kama shi ya yi murmushi, cikin ransa yana fadinIn mun rabu kin sake aure za a sha kallo a gidanku ke da future husband dinki. A wannan dan tsukin sun zama abokan juna, ko ciwon kai ta ke sai ta gaya masa ya ba ta magani. In sharia ya yi, sai ya gaya mata yadda ta kaya. In zai shiga kotu sai ya kira ta ya gaya mata ta yi masa addua, he dont want to be a loser! In ya yi nasara sai ya gaya mata adduarta ta karbu. Ta shirya in ya dawo su je Dominicta ci Pizza ta sha ice-cream ladan adduarta. Fitarsu ta biyar kenan zuwa (Dominic) hakan ba karamin faranta ran Hafsa yake ba. In ba ya nan tana tare da su Mammah a waya. Ko ta dauko Alqurani tayi ta tilawa da sauran littattafanta. Baba Azumi ma ta dawo daga Sokoto duk sanda Mammah ta kira ta, ko ita ta kira ta za ta hada su su sha hira. Haka kawai zai ce kada ta yi abincin dare in ya dawo za su fita su ci a Chinese restaurantko KFC. Don haka a wannan dan tsukin Hafsat ba ta da damuwa ko cikin cokali. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Ranar wata alhamis ya shigo mata da (past quastions and answers) na Jamb ya ce ta duba ranar asabar zai kai ta ta zana. An tura ta wata makarantar sakandire ta gwamnati a nan Abuja inda za ta zana jarrabawar. Ta dukufa karatu ba ji ba gani duk da a wurinta da matsayinta na dalibar (ST. John Barchmans College) wannan ba wani karatu ne na a zo a gani ba. Da yake asabar ce ba aiki, tun bakwai da rabi ta shirya ta fito tana tsumayinsa. Da ya fito ya ganta idonta luhu-luhu ya tabbatar masa ko isasshen barci ba ta yi ba. Tausayi ta ba shi sosai, kowanne dan Adam da abin da yake so, shi Muazatu yake so, Hafsat kuma karatu ta ke so. Yana rokon Allah ya cika mata burinta, shi kuma Ya ba shi ikon zama tsanin cikar wannan burin. Da suka isa ya nuna mata inda za ta fito ta zauna ta jira shi idan sun gama. Sai da ta shiga ajin zana takardar ya ga shigar invigilators sannan ya bar makarantar zuwa gidansu. A can ya karya kumallo ya tadda Mammah da Baba Azumi na shirye-shiryen tarbar Ismaeel, Usman da Haleem. Sun kasa zaune sun kasa tsaye. Ya tambayi Mammah karfe nawa za su sauka? Ta ce, Nan da awanni biyu. Ya kudure a ransa zai ba da mamaki ba tare da ya yi shawara da Mammah ba. Kafin azahar ya koma, ta gama papers dinta tsaf ta fito. Inda ya nuna mata ta jira shi ta nufa kai tsaye, ta samu wani benci ta zauna. Tana nan zaune tana kallon shige da ficen mutane wasu a kafa, wasu a motoci. Kamar daga sama ta ji muryar namiji yana yi mata sallama. Da sauri ta juyo, kallo daya ta yi masa ta gane fuskarsa, a kusa da ita ya zana papers dinsa, zai girme mata sosai don zai yi shekaru ashirin da uku. Dauke kanta ta yi ta amsa sallamarsa. Karshen bencin da ta ke zaune ya zauna, Kin riga kowa submitting wannan ya nuna kin shirya wa jarrabawar nan sosai. In magana fa ta karatu ce Hafsat ba ta shariya. OBJ questionsdin ne sai an yi wani shiri? Murmushi ya yi, ya ce, A wajenmu yan Nigeria sai an yi, don ke da ganinki Afro-Arabian ce. A nan kuma shiru ta yi masa. Wace Uni za ki? Ban sani ba wallahi, ba ni na cike ba. Haka ya yi ta janta da hira, wani ta amsa wani ta share shi don ba ta ga dalili ba, kuma ba ta iya wulakanta mutane ba. Tun daga nesa ya hango Hafsat a inda ya ce ta zauna, amma abin mamaki tare ta ke da wani a benci daya. Hafsat murmushi ta ke yi wani irin murmushi da ya ba shi mamaki, kuma saurayin yana magana, wani irin kyau ta yi masa da handbagdinta a kan cinya. Amma tsaya... wane ne wannan saurayin na kusa da ita? Me ye alakarsu da har ta ke sakar masa wannan murmushin a matsayinta na matar aure? Ba ya tsammanin ko su Ismaeel tana yi wa wannan murmushin (A idonsa fa). Girarsa ta tattare ta hade wuri guda, cike da mamakin yadda yake tsaye a gefensu zaune cikin mota, amma ba ta ma ganshi ba. Wayarsa ya dauka ya kira numbarta don ga dukkan alamu ba su da niyyar rabuwa ko zai kwashe awanni yana jira. Yana kallon sanda ta bude jakarta ta dauko wayar ta kara a kunnenta. Muryarta mara amo mai tsananin taushi ta fito tar-tar ta speaker don wayar a jone ta ke da aux na motar. Bai amsa sallamarta ba ya yi shiru kawai yana jinta. Yaya ka iso? Ban ganka ba. Kana ina? Sai kuma ta fara juye-juye alamun tana nemansa. Tana ganin motar ta ce da matashin wani abu, sai gani ya yi ta tashi, shi ma ya biyo ta sun nufo motar tare, amma ba ta sake cewa komai ba. Daga inda yake ya fahimci saurayin ne yake ta magana ta yi shiru, inda ya fahimci ta gane shi ne ya zo, kuma shirun da ya yi mata yana da maana. Har suka karaso idanunsa a kanta bai dauke ba, ta bude kofar tare da sallama ta shiga ta zauna. Zai iya rantsuwa ko shopping mall yarinyar nan za ta shiga sai ta yi sallama, daya daga cikin kyawawan dabiunta da ke burge shi kenan. Amma yadda ta jefa shi cikin matsanancin bacin rai yau bai jin ko kallon fuskarta zai iya yi balle amsa sallamarta. Ba ta dauke hannunta daga rufe kofar motar da ta yi ba ya yi mata giya ya fizge ta da wani irin gudu kamar zai tashi sama da su. Sun hau titi sosai sun kama hanyar cikin gari, so ta ke ta ce ya rage gudun babu fuska, hasalima ba ta taba ganin fuskarsa haka kamar hadari ba, takurewa ta yi a kujerarta ta hade jikinta wuri guda ta yi shiru. Abin kirkin da ya yi niyyar yi mata yau yake so ya fasa, wata zuciyar na tausarsa. Ya karya kan motar ya hau titin da zai kai shi unguwarsu Asokoro. Kamar daga sama Hafsat ta tsinkayi muryar Abdulazeez a cikin kanta, cikin yanayi mai boye halin da zuciyar mutum ke ciki. Waye shi? Ya tambaya a matukar gajarce. Ba tare da ya dauke kansa daga titi ba, kuma ba tare da ya dube ta ba. Ta murza yatsun hannunta cikin junansu, sannan ta ce, Ni ma ban sanshi ba. Muryarta ta nuna zullumin da ta ke ciki irin na guilty conscious. Bai sauya daga yanayin da yake ciki ba ya ci gaba da tambaya. Ba ki sanshi ba ki ke hira da shi kina matar aure? Ba ki sanshi ba murmushinki ya zama mai arha a gare shi? For Allahs sake me ya hada ki da saurayi Suhaana? Wace irin hira zai miki har ya samu murmushinki haka? Dagowa ta yi ta kalle shi. Har zuwa wannan lokacin idonsa na kan titi. Ya ci gaba da magana cikin bacin rai ammawannan karon kamar cikin lallashi. Aure kowanne iri ne yana da martaba da mutuncinsa. Kuma kin sani wannan auren yana da limit kina da enough timeda in maza dari ki ke son kulawa a nan gaba za ki yi. So please kar ki kara bana so, I repeat it, bana so! Kada ki ba da kofar da za a fahimci irin zaman auren da muke yi. Sai ta yi shiru tana kallon hanya cikin mamakinsa. Ta yi rantsuwa ta daina sanya alamarin Muazatu a ranta, amma da ta ce ashe babu dadi. Maganarsa ta karshe ta yi mata ciwo wai ta bari sai aurensu ya kare ta kula maza dari in tana so. Ita da a rayuwar da ta yi cikin turawa ma ba ta sanya kanta cikin shaanin maza ko ya ya yake saboda yadda Mammah ke kwabarta a kullum, sai yanzu da ta ke da sunan matar aure? Aurensa da ta ke tare da shi yanzun kawai yake karewa, ba ruwanshi da duk irin rayuwar da za ta yi a gaba, koda kuwa ta karuwanci ce, to kula maza dari a yana nufin karuwanci. Ji ta yi idanunta sun cicciko da kwallah. Amma ta yi kokarin maida ita. Ta koma ta jingina da kujera ta rufe idonta ba tare da ta ce da shi komai ba. Ba ta bude idonta ba lokaci mai tsawo, sai da ta ji ya ja birki ya kashe motar. Sai dai da ta bude idon maimakon ta ganta kofar gidanta, sai ganinta ta yi a kofar gidan iyayensu (gidansu). Duk wani bacin rai nemansa ta yi ta rasa. Da sauri ta dube shi kamar ta rungume shi. Ya wani hade rai ya matse gira ya dauke kai daga kallonta. Murmushi ta yi ta soma kicin-kicin bude kofa amma ta kasa. A marairaice ta dube shi kamar za ta yi kuka. Wallahi in ki ka fito da hawaye juyawa za mu yi. Mu shiga a tare, in mun je falo ki zauna kusa da ni, kada ki yi hannu da Haleem balle Ismaeel. In na kula ki, ki ba ni attention, kin san Mammah proffessional ce wajen karanto psychological movesdin kowa cikin yayanta, don haka ki nutsu. Ita dai burinta ya bude mata kofa ta ganta a falon gidansu, don haka da gaggawa ta amsa. Sai da ya gama yangarsa da noke-noke da neme-neme cikin motar na babu gaira babu dalili, zuciyarta kamar ta fito ta bakinta don takaici, sannan ya bude kofofin motar. A tare suka fito tana so ta shiga da sauri, amma dole ta jira shi ya zagayo suka jera, What a perfect match? Abin da Ismaeel ya fada kenan wanda suka fara tozali da shi a cikin falon yana cin abinci a dandaryar kasa. Haleem, Usman, Mammah, Daddy, Ramadan da Shaaban da Farhan yayan Uncle Abdulkareem wadanda su ma gidansu a nan Abuja ne unguwar Maitama, suna hade a makeken family diningdin gidan suna cin nasu abincin. Tare da su aka je aka dauko su Ismaeel daga filin jirgi. Hafsat kasa jure wannan tafiyar da Abdulazeez ke so su yi ta yi, ana shigowa falon taku daya-biyu ta sheka da gudu ta rungume uwarta, uwar da babu kamarta a duniyarta, wadda ta fi dutsen sapphire daraja a gare ta. Hajiya Maryam Hamza Atiku. Lallai ma, wato duk cikar mu nan Mammah kadai ki ka yi kewa? Inji Auta Haleem. Kyale ta Brother, ni sau daya ta taba kirana a waya, ni in na kira ta a ce na aje voicemail. Cewar Usman wanda ba su cika shiri ba, shi halinsa ma daban ne da na kowa a gidan, bai cika shiga shirgin mutane ba hatta iyayensa sai dai su neme shi, irin mutanen nan ne masu kamewa, shi dai bar shi ya fuskanci karatunsa ya fiddo (CGPA) mai daraja. Wai ni yarinyar nan ta ke kira bachelor saboda ta riga ni aure kamar ba a hannuna ta soma ta-ta-ta ba. Cewar Ismaeel. Haka kowannensu ke jifanta da korafinsa, ita dai ta yi shiru ta dora kanta a kafadar Mammah sai murmushi ta ke yi. Tana binsu da idanun kauna daya bayan daya. Mammah wadda farin cikinta ya kasa boyuwa ta ce, Kai ku kyale min yarinya ina dalili? Daga jarabawa ta dawo ko hutawa ba ta yi ba. Ta ja mata kujerar kusa da ita ta zauna, ta tsugunna ta gaida Daddy wanda ke magana da Abdulazeez tun shigowarsu. Sosai ya amsa yana kara jin yarinyar har cikin ransa da matsayi iri-iri na ya, na suruka, na rabin jiki ga Abdulazeez dan da bai da kamarsa. Hatta sauran yayan sun san haka, sai dai su yi hakuri, duk wani Da ya biyo bayan Abdulazeez a wajen tsohon Ambassada Hamza Atiku. Sai ga Baba Azumi ta billo daga corridor din kicin tana dauke da katon din ruwan sha mai sanyi na FARO. Da Hafsat ta fara tozali fuskarta ta washe, bakinta ya fadada, ta rasa dalilin wannan gashin kuma na Hajiya Maryam, wai ba za su je wajen Hafsat ba sai ta shekara a gidan miji, ga shi ai su sun kasa jurewa sun zabi mai fishshe su. Tunda sun zo ai ba za ta kore su ba. Oyoyo da yar Baba, oyoyo da yar Mammah, lale da amarya mai abin mamaki. Turbunewa Hafsat ta yi tana cuno baki, Da na zo da kaina Baba Azumi? Wai ke ma har da ke, ba kya nemana... kin manta da ni... Ina kaka za ta manta da jikanyarta? Wane mutum!!! Gabadaya aka yi dariya, sabida irin yadda ta jinjina girman alamarin. Hafsat ta karasa gare ta ta rungume ta. I missed you so much Baba... Baba Azumi na jin turanci sama-sama ta ji abin da Hafsat ta ce. Kin yi fari, kin yi kiba, Babban Yaya ya iya kiwo. Mu ma mun yi kewarki yar Mammah, kullum ma muna yi (kewar). Ta fada tana bubbuga bayanta. Da kyar Baba Azumi ta samu Adda ta sake ta. Hafsat na ji Mammah na tambayar Abdulazeez ko ciwon Hafsat ya taba tashi? Dago kai ya yi ya dubi mahaifiyarsa cikin mamaki, dama tana da wani ciwo ne? Mantawa ka yi tun haihuwarta tana da pneumonia? Habiba na shan ruwan sanyi sosai da yin taammali dashi Tsit falon ya yi, kowannensu na tuno Habiban da rayuwarta ta dan gajeren lokaci tare da su, wadda ba za su taba mantawa ba. Hafsat ji ta yi kamar an yi mata shocking a lokutta da dama mantawa ta ke tana da wata uwar bayan Mammah, tunda ita dai ba ta santa ba ko a hoto. Ga shi Mammah ba ta so a yi zancen. Yau tunda ita ta tado shi ba wani ya sa ta ba, sai ta gaya mata cikakken asalinta. Shesshekar kukanta kawai aka ji ya ratsa shirun da aka yi, Don Allah don Annabi Mommah ki gaya min wace ce ni a cikinku? Na san ba ki yi min haihuwa ta jini ba da ba ki hada aurena da Yaya Abdulazeez ba. Na dade da sanin wannan, ina da wata uwar daban bayan ke. To amma uba fa? Ko shege ne ta yi ta kawo muku... Sunkuyar da kai suka yi bakidayansu, saboda su ma ba su da wannan amsar. Abdulazeez ne ya katse shirun da shesshekar kukanta ya ce, Suhaana, Hafsat Suhaana. Har sau biyu. Ta amsa cikin rishin kuka, Dago ki dube ni. Dagowar ta yi ta dube shi, in lissafin da ta ke yi daidai ne shekarunta goma sha takwas jiya, su gaya mata ko ma wane iri ne asalinta za ta iya dauka. Don hakawith eager( da zakuwa) ta ke kallon mijin nata, tsakiyar iyaye da yan uwansa idanunta cike da hawaye. Ba shegenki ta yi ba, ni ta gaya min kina da uba kamar kowa da yan uwa na ciki daya har ukku, kuma ba ta yi kama da mutuniyar banza ba. Mace ce mai cikar mutunci, mai kirkin gaske. Da yardar Allah sai na nemo mahaifinki da yan uwanki Hafsat na sadar da ke gare su. Ki ba ni wata uku, I promised. Daga kai ta yi cikin amincewa, Wipe-off the tears... (goge hawayen). Ya fada cikin kankanuwar murya. Kunya ya ba ta sosai, tasa gyalen abayarta ta rufe fuskar bakidaya. Dariya kowa yake mata, zuciyar Hajiya Maryam kamar koramar madara da zuma don dadi na kulawar da Abdulazeez ya nuna akan Hafsat a gaban kowa. Ita dai haka ta ke so, Abdulazeez ya so Suhaana da zuciya daya, in ya yi hakan ya gama mata komai, kuma albarkarta gare shi ba za ta taba yankewa ba. A yau Hafsat-Suhaana ta san ko wace ce ita a cikin iyalin gidannan, daga bakin uwarta/surukarta Maryam Dakata. Labarin da ya tsaya mata a zuciya ya kasa wucewa;yar mai aikinta ce ita! Babu wata alakar jini ko ta yaya! Her mum is her servant, her maid. Ba ta san daga inda ta ke ba, amma ta raine ta, raino irin na fisabilillahi, wanda dan cikinka kawai za ka iya yi mawa, duk hakan bai isa ba Abdulazeez ta zaba mata a matsayin miji. Dan gatan da bai rasa komai ba, mai asali da ilimi. Mutane irinta nawa ne a cikin alumma?? Yanzu ta gano dalilin da ya sa Abdulazeez ya kasa sonta! Allah sarki!! Ai ya yi kokari ma, kokarin da maza irinsa da yawa ba za su iya ba. A yau ta karbi uzurinsa da hannu bibbiyu, na son rabuwa da ita a gaba, za ta taimaka masa ya cika burin rayuwarsa ya yi auren da maza masu gata irinsa ke yi, wanda hankalinsa zai kwanta da shi. Ba don Mammah ce ta haife shi ba, da ta ce ta zalunce shi da ta hada shi aure da ita don kawai tana sonta. Wannan bai isa hujja ba a ganinta. Ta gyara mata rayuwa shi ta gurgunta tashi, ta hanyar aura masa yarinya irinta mara galihu mara asali mai kaskantaccen matsayin a gidansu. Amma faruwar wannan alamarin a yau da abin da Abdulazeez ya yi mata na karamci a gaban iyaye da yan uwansa sai ya kawo wani SABON ALAMARI mai girma a zuciyarta a kansa. Wani bakon feeling da ba ta san daga ina yake fitowa ba tsakanin zuciya, ruhi da gangar jikinta. Ya dasa wata katotuwar bishiya mai yawan ganyayyaki, sai yabanya (yado) suke a rassan jikinta. Babu wani bangare na wadannan halittu guda uku tsakanin zuciya, ruhi da gangar jiki da ba ya ambaton sunansa a wannan lokacin da murya mai tsananin amo da amsa kuwwa.......ABDULAZEEZ HAMZAH ATTIKOU... cikin sauti maabocin amo da karsashi. Jinsa ta ke yi a koina na sassan jikinta da wannan sabon alamari mai ban mamaki da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba. Kowa ya dubi Hafsat ya san ta zama cool a kan yadda ta zo a farko. Da faraa da faram-faram, da dokin kowa nata. Sai babu wanda ya bai wa canzawarta hankalinsa. Hatta Mammah kuwa, sun alakanta hakan da sabon labarin rayuwarta da ta ji. Abdulazeez ne kawai ya lura da canzawarta mai harshen damo ce (mai maana biyu), kasancewarsa wanda yake kwana ya tashi gida daya da ita a halin yanzu, kuma a irin shakuwar da suka yi a wannan lokacin zai iya cewa ko Mammah ba za ta gaya masa wace ce Hafsat ba, sai dai ta gaya masa (little Hafsat) amma ba baligar ba. Hafsat-Suhaana mai sanyin hali ce, ba ta da daukar duniya da fadi, mai kirki ce, mai girmama na gaba da ita. Mai gudun zuciya da karbar rayuwa a duk yadda ta zo mata ba tare da ta yi jayayya da ita ba. Yanayinta ba ya iya boye abin da ke zuciyarta. Wadannan sune manyan halayenta da ya fahimta a tsayin zamansa tareda ita. Sosai ya fahimci hayaniyar gidan ta daina burge ta, tana bukatar privacy na yin nazarin sabon labarin da ta ji da kuma yadda zuciyarta za ta karbe shi, ta saba da shi, tana bukatar kadaicewa ta yi jinyar zuciyarta. Mammah dai duk abin da ta san Hafsat na so shi ta ke kokarin yi mata yau. Ta kawo wannan ta kawo wancan. Duk don ta kawar mata da damuwar. Baba Azumi na can kitchen tana yi mata awara kwano guda da za ta sanya a firji ta dinga soyawa in ta ji marmari kasancewar tana sonta. Ishma ya yi mata tsaraba sosai na (English wears) da takalma da jaka leda guda. Ta idar da sallar magriba a dakin Mammah, ta ci gaba da zama shiru a kan sallayar ita ba lazimi ba ita ba addua ba; deep in thought. Abdulazeez ya shigo dakin ya isa har inda ta ke zaune ya tsaya a kanta, Mammah na gefe tana shirya mata kayan girki da ta siya mata a Bacco. Bai ma lura Mammah tana gefe ba yake magana. Hafsat, mu tafi gida. Dagowa ta yi ta dube shi da kwayan idanunta da suka kankance. Wani irin kallo ta ke masa a yau withutmost respect da ita kanta ba ta san irinsa ba. Samun kanta kawai ta yi da mikewa ta hau ninke sallayar. Ita ma za ta fi son hakan, kadaicin kawai ta ke so. Ta yi jinyar sabon alamarin nan da ke faruwa da zuciyarta. Harararsa Mammah ta yi, amma fuskarta annuri ta ke fitarwa. To Alhaji, ai ka bari ku ci abinci ko? Were having a get-to-gether dinner today in honour of Hafsats eighteenth birthday. Za a yi hotuna da vedio a aje don tarihi. Za mu dawo. Ya fada tare da kama hannun Hafsat ya mika da ita tsaye, ita kuma ta kwace cikin jin kunya. “Shes not in the mood Mammah, za mu dawo in an kwana biyu. Daure fuska Hajiya Maryam ta yi, ganin yadda yasaHafsat ke jin kunya kamar ta shige cikin kasa da abinda yakeyi din a gabanta. Na fi ka sanin shes not in the mood din ai, a haka nake so a yi hotunan da vedion. Na so in yi mata ne tun jiya ranar da ta cika shekara sha takwas Allah bai yi ba. Ko hawaye ta ke a haka za a yi, ka je ka sauko da Daddy. Murmushi ya yi ya saki hannun Hafsat ya juya ya fita, sosai Mammah ta ba shi dariya, wai ya je ya sauko da Daddy sai ka ce wani dan karamin yaro? Kawai tana neman hanyar da zata kore shi ya bar musu dakin ne. Tare suka ci abinci gabadaya a makeken family dining din gidan, uwar da uban da yayan su biyar, Abdulazeez kusa da Hafsat, Ismaeel ne ya dauko digital camera dinsa ya dinga daukar hotuna da vedio. Duk abin da wannan family suka san zai faranta wa Hafsat yau shi suke mata har Daddy. Ko ita butulu ce dole ta manta komai ta saki jikinta ta koma cikin walwala. Hotuna sun yi kyau sosai, Ismaeel ya ce zai wanko ya kawo musu gida. Mammah ta gama hada mata komai suka rako su har bakin mota suka shiga suka nufo gida. Ba wanda ya yi magana a tsakaninsu har suka shigo gida. Kowa ya nemi dakinsa, wanka ta yi don ta ji dadin jikinta tayi brush yadda ta saba duk dare sannan ta fito ta sanya kayan barci. Ta shafa turaren (Rihanna Rogue) sama-sama ta bi lafiyar gado. Ya jawo (files) din da ya dawo dasu daga officebayan ya fito daga wanka, ya daura wasu tausasan pajamasruwan makuba na(Neiman Marcus)ya yi amfani da turarukan da yake amfani da su da daddare (beforemidnight, da midnight oud)wai zai yi aiki don kore wa kansa tensiondin da yake ciki, amma abin mamaki ba ya fahimtar komai a cikin takardun, dole ya mayar ya rufe saboda Hafsat kawai yake gani tana gilmawa a cikinsu, da yanayin da ta ke ciki a yau. Tana bukatar mai kaunarta a kusa da ita, kada kadaicin rayuwar ya yi mata yawa. To amma ya yi wa kansa alkawarin ba shi ba sake shiga turakarta tun lokacin da ya tsallake rijiya da baya, me zai iya yi na nuna mata yana tare da ita cikin kowanne hali da ta samu kanta a ciki? “Be with her today, the whole night. (Ka kasance tare da ita yau, a tsayin daren bakidayansa). Kaso tamanin na zuciyarsa ya amince da hakan, kaso ashirin yana kalubalanta. Ba don komai ba sai don gudun abin da hakan zai haifar, sai dai yana da tabbacin ya yarda da kansa ba zai iya cutar da Hafsat ba, rayuwarta bakidaya amana ce yanzu a hannunsa. Faruwar wani abu da ya danganci auratayya a tsakaninsu ko ya ya yake don kankanta zalunci ne da cutarwa a gare ta. Yana da yakinin zai rike amanar Hafsat kamar yadda zai rike Haleem, ko da shi zai cutu, albarkacin mahaifiyarsa da halayen kwarai na yarinyar, wadanda suka ba ta matsayi na musamman a zuciyarsa. Wayarsa ya mika hannu ya dauko, sai kuma ga kiran Muazatu ya shigo. Ga mamakinsa sai bai ji dadin kiran da ta yi masa a wannan lokacin ba. Ko bai fada ba muryarsa ta nuna hakan a sanda ya amsa wayar. Muazatu ya aka yi? Ta yi dan jim, don ba haka ya saba amsa mata waya ba, muryarsa a dusashe. Ba abin da ba ta kissima a zuciyarta ba da cewa shi ke faruwa, wato tare yake da matar da yake cewa ba ya so. Ta yi magana a kai cibi ya zama kari. Makoshinta da lebban bakinta suka bushe rayas, ta kasa ce masa komai saboda wani bakin ciki da wutar kishi da ya zo ya tokare ta, sai ji ya yi ta kashe wayarta. Ya duba sosai ya tabbatar kashewa ta yi, sai yake tambayar kansa laifin da ya yi mata? Iyaka hangensa bai gani ba don haka ya rabu da ita, ya kira Hafsat. Kwance ta ke kawai tsakiyar niimtaccen gadonta, barci ya ki zuwa, ta rufe rabin jikinta da duvet da wayarta a hannunta tana duba hotunan da Ismael ya turo mata da suka dauka dazu, ta tsayar a kan wanda ya dauke su ita da Abdulazeez ya rankwafo ta bayanta kamar tare aka halicce su. Duk sun yi murmushi. Zooming hoton ta sake yi tana hango abubuwa da dama. In dai ba yaudararta zuciyarta ke yi ba, to kuwa tana gaya mata sun dace da juna. Ya fi ta tsayi, ya fi ta fadi (physique chest) gare shi. Komai na halittarsa abin mace ta tsaya ta kare wa kallo ne. Ko shi ya sa Muazatu ta kasa hakura da shi ta bar mata duk da ya aure ta? Ta ke jira ayo waje da ita domin ita ta shigo? Ko ita mene ne aibunta da Abdulazeez ya kasa sonta? Tambayoyin da zuciyarta ke mata da abubuwan da ta ke darsa mata a yau sun fara ba ta tsoro saboda ba ta ga dalilinsu ba. Tunda bai boye ba ya fada mata ita ba matar aurensa ba ce, matar wucin gadi ce, ta samu kanta da tambayar zuciyarta; mene ne bambancin matar aure da matar wucin-gadi? Ina ma tana da karfin zuciyar da za ta iya yi masa wannan tambayar?? Daidai wannan lokacin kiransa ya shigo cikin wayar da sunan da ta yi saving dinsa da sai a yanzu ta ke kalubalantar kanta kan dalilin ajiye lambarsa da wannan sunan Hussy wato Husband, amma ta kasa gogewa. Ai shi ma ya fada; Aure kowanne iri ne yana da martaba da mutuncinsa. Aurenku ma aure ne tunda ana tare ba a rabu ba, thus,hesindeed your husband wanda kowa ya shaida, ku kadai kuka san kun bashi waadi. Amma wadanda suka daura shi da kyakkyawar niyya suka daura da sadaki da waliyyyai da shaidu kamar kowanne auren sunnah. Amma ga mamakinta ta kasa amsa wayar tasa, a kan dalilin da ba za ta ce mene ne shi ba. Ta yi har ta katse, ya sake kira a karo na biyu. Hafsat ta ce cikin ranta, Ko sau dari za ka kira ba zan amsa ba Yaya Azeez, me ya kai matar wucin-gadi zuwa turakar maigida a daidai wannan lokacin? Gara in rage shige maka, in tsaya a matsayina kafin zuciya ta ta kumbura a kanka da alamuranka masu ban mamaki. Na kasa gane inda ka sa gaba, na kasa gane inda ni kaina nake heading a kan alamarinmu. Yau kadaicin kawai nake bukata. I want to be alone!. Ta mike hannu ta yi (light up) daga makunnin da ke jikin gadonta. Fitilu masu sassaucin haske suka maye gurbin masu hasken. Hoton nasu ta ci gaba da kallo tana ta ci gaba da zooming dinsa kamar ta zuko Abdulazeez din daga cikinsa ta mayar jikinta su zama abu guda saboda wani irin intense feelingdake bakuntarta, zuwa lokacin ya gaji da kiran ta ya kyale ta. Tana cikin wannan halin ta ji an zura mukulli a jikin kofarta ana budewa. Sosai ta razana, sai dai kuma ta san ba mai yin hakan sai mamallakin gidan. Don haka tsoron nata ya ragu, ta bai wa kofar attention dinta tare da boye wayarta da sauri cikin quilt har ya bude ya shigo. Rufe ido ta yi ita a dole ga wadda ta yi nisa a barci. Ta yi zaton zai koma ne daga bakin kofa kamar yadda ya saba, amma sharia sabanin hankali. Kai tsaye gadon ya nufo, ya hawo shi bakidaya ya bude duvet din ya shige ciki ya kwanta a gefenta. Ji ya yi kafarsa ta shuri abu ya sa hannu ya dauko, wayar Hafsat ce, wadda ta suma a kwance sabida kaduwa da mamaki, Abdulazeez a kan gadon barcinta? Ba ta son ta yi motsin da zai fahimci idonta biyu, tunda dai bai rabe ta ba, ya yi amfani da daya filon ne ya kwanta kusa da ita, don haka ta ci gaba da tamke idonta. Sai dai zuciyarta harbawa ta ke yi kamar ta faso allon kirjinta ta fito saboda gigicewa. Ba ta sani ba wayarta na hannunsa, kuma tana nan a yadda ta boye ta. Kyakkyawar fuskarsa ce a hoton ta cika screen din da alama zooming ake ta yi. Da ya matse shi sai ya ga ashe ma ita da shi ne wanda Ismael ya dauke su dazu, amma ba kanta ta ke kallo ba, shi kawai ta ke kallo. Sosai mamaki da alajabi suka taru suka lullube shi, ya kuma tabbatar idonta biyu ba barci ta ke yi ba, abin da ta ke yi kenan kafin ya shigo. Ba ya so ya yarda da abin da zuciyarsa ke gaya masa, don haka shi ma ya boye wayar a kasan filo a zuwan bai gani ba yana karyata zargin da zuciyarsa ke nanatawa. Mene ne a cikin kallon hoto? Babu komai. Kawai tana gani ne ba da wata manufa ba. Shes very young... hakan ba zai kasance da ita ba at this tender age... in ji wani bangare na zuciyarsa. Sai kuma wani irin tausayi da bai san dalilinsa ba ya tsirga masa. Duk yadda yake gudun yin zalunci a cikin tafiyar nan anya zai tsira daga aikatashin? Hafsat ba mutum ba ce? Ko kuwa babu zuciya a cikin kirjinta? Ko kuwa halittar ta daban ce da ta sauran yaya mata? In babu so babu shaawa? Idan ya katange kansa daga soyayyar kowacce diya mace bayan Muazatu zai iya katange Hafsat daga hakan a kansa a matsayinsa na mijin aurenta da ba ta da wani makusanci da ya wuce shi a yanzu? Su kwana gida daya su wayi gari tare su wuni gida daya? Abin da ya faru dazu tsakaninta da saurayi ya fado masa. Wani irin yanayi ya shiga mai wuyar fassarawa fiye da tsammaninsa. Dakin ya dauki shiru ga zafi ya dameshi kasancewar Hafsat bata amfani da AC, ta saba da rayuwar ta a haka don tsira da lafiyarta. Ba ka jin komai sai bugun zuciyoyinsu, saukar numfashin kowannensu ya sauyaya koma akai-akai yake sauka. Hafsat ta rasa a duniyar da ta tsinci kanta a yau kasantuwar Abdulazeez tare da ita, a gado daya, cikin mayafi daya. Wata irin nutsuwa ta ji na sauka a zuciya da ruhinta. Zuciyarta ta shiga wani irin kai-kawo tsakanin kirjinta da kwakwalwarta. Anya kuwa kadaici ta ke so kamar yadda ta yi tsammani a farko ko kadaicewa da Abdulazeez? Idan haka mata ke samun nutsuwa in suna tare da mazansu na halal a gado daya, ashe kuwa babu wadda zata so a sake ta, ashe kuwa babu wadda za ta so wata mace ta rabi mijinta. Ina kuma a ce da baby kwance a tsakani yana kicking (in between) a tsakaninsu? Ba ta san sanda ta yi motsi ba don ta gaji da kwanciya a kan barinta na dama. Tana so ta sauya barin kwanciya ba ta so ya san idonta biyu, kuma ba ta sani ba ko babu space mai yawa a tsakaninsu ta goge shi? Ta takura sosai, ga wannan abin da ke tsakiyar kirjinta yana yawo shi ma ya takura mata.... Abubuwa kawai yake gaya mata kala-kala wadanda suka faru, da wadanda za su faru ranar da ta rabu da Abdulazeez ya auri Muazatu...... shin wai ita wace irin shashasha ce da ta yarda ta zauna ya gindaya mata abin da ya ga dama ta hau kai ta zauna don kawai tana so ta yi karatu ta ga danginta? Me ta rasa na dangi? Da me Daddy ya rage ta na mahaifi? Me ta rasa a uwa? Su Ismaeel arent enough? IsntBaba Azumi a great Grandma?Iyalin Abdullahi Dakata bakidaya ba su ishe ta rayuwa ba? KARATU! Zuciyarta ta ambato. Ko da ace Abdulazeez bai kai ta makaranta ba, ba ta da ilimin da zai isheta ta rayu da shi har karshen rayuwarta? Nasa ba zai ishe su ba? Gabadaya kwangilar na nufin za ta samu wadannan abubuwan, amma shi za ta rasa shi!!! Hafsat-Suhaana ji ta yi zuciyarta ta yi wani matsanancin duhu kamar hadadden hadari mai tafe da guguwa da cida mai gigitarwa. Mai barazanar tafiya da mutum dungurugum in ya zauna a cikin wannan guguwa. To haka ta samu kanta kwatankwacin a cikin guguwa wadda in ta ci gaba da yin wannan zazzafan tunanin guguwar nan da ke tarnaki a zuciyarta za ta tafi da ruhinta ta mutu, Abdulazeez ya huta da wannan kayan nadama da ya jefa ta a ciki. Zan amince in rasa komai, in dai zan tsira da shi...!!! Conclusion na zuciyarta kenan. Amma ai kin riga kin yi alkawari, sannan yadda ki ka amince da hakan shi ma abin da ya yarda da shi kenan a kan Muazatu, har kuwa fushin iyayensa. Zuciyarta ta yi wani bakikirin, ga wani irin tukuki na fita daga cikinta. In ba ta yi kuskure ba za ta iya cewa, har tururi ta ke yi... ba ta ankara ba ta ji hawaye masu dumi suna sauka suna jika filon da ta ke kwance a kai. Motsi ta sake yi kadan har ga Allah ta gaji da wannan azabtacciyar kwanciya wadda ko motsi ba ta isa ta yi ba. A na me? Ita da gadonta da dakinta? Tsaki ta saki, tsuuu! Abdulazeez, wanda zuwa wannan lokacin shi ma a nasa bangaren kwakwalwarsa neman tarwatsewa ta ke yi da tuno abin da ya faru dazu, ya janye duvet din daga jikinsu bakidayaya yi gefe da shi. Ya tashi ya zauna. Cikin shakakkiyar murya ya ce. Ni ki ke yi wa tsaki Hafsat? So ta ke ta ce, wanda ya tsargu da shinake ta tuna abin da hakan zai janyo. Ta fahimci abu na karshe da ya ki jini kenan(a kawo masa raini), amma fisabilillahi ya takura mata, ya hana ta barci, ya muzguna wa zuciya da kwanyarta. Ya zo dakinta har gadonta ya hana ta sukuni. Tashi ta yi zaune ta dafe kanta da hannuwanta bibbiyu. Shi ma mikewa ya yi ya zauna ya jingina da filonsa. Da kallonsa ta ke da ta ga yadda yake kallonta da kyawawan idanunsa. Me ye dalilinki na kin daukan waya ta? Yadda ya yi maganar cikin kwantaccen sauti sosai ya kara lugwigwita zuciyarta. Da farko shiru ta yi sai da ya kara nanatawa. Fuskarta ta kifa cikin tafukanta ta ba shi amsa cikin raunin murya. Barci nake yi. Wayarta ya zaro daga inda ya tura ta ya boye a bayan filonsa ya rike a hannunsa ba tareda saninta ba. Barci ko kallon mijinki? Muryar da ya yi amfani da ita wajen fadin hakan ba ya tsammanin ya taba magana da irinta a tsayin rayuwarsa. Duk da muryar ta karasa kassara ta,hakan bai hana ta yin jarumtakar kare kanta ba. A bayanta yake a kishingide, tana gabansa da kadan azaune ta mike kafafunta a kan gadon. Baya ganin fuskarta sai bayanta da kwantaccen gashin kanta wanda ke ta sheki da kyalli cikin dim-light din. Girgiza kanta ta yi cikin musanta zancensa. Ni ba ni da miji. Hasalima ban san da kasancewar kowa cikin dakin nan ba bayan ni Hafsat. Murmushi ya yi, karfin gwiwarta ya kayatar da shi, ko da kuwa kalamanta sun masa ciwo. Wayar ya dora mata a kan cinyarta, Wannan da ki ke kallo fa? Sosai ta razana, don ba ta taba tsammanin wayar nan tana hannunsa ba. Dauke wayar ta yi ta rike a hannunta, ta ba shi amsa. Mijin wucin-gadi ne. Sai ga hawaye suna safka dai-daya a kan kundukukinta. Zuciyarta na yi mata wani irin ciwo da tsanar Abdulazeez da duk abin da ya shafe shi. Da bai shiga rayuwarta ba, da yanzu duk haka ba ta faru ba. Da ba a aura mata shi ba, da yanzu tana gidansu tare da Mammanta, da yan uwanta cikin sukunin zuciya. Gabadaya ya shiga zuciyarta ya kekketata, ta rasa abu guda daya da kwakwalwa da zuciyarta ke nufi da wannan walagigin da ta ke yi da ruhinta a kan Abdulazeez Dakata, wanda bai san kowa ba sai kansa. Kowa ya mutu da hurtings in dai shi zai tsira da wata banza Muazatu har mahaifiyarsa kuwa. Hafsah! Abdulazeez ya kira ta muryarshi na rawa. Shi ya fadi kalmar wucin-gadi yanzu da ta ba shi irinta ji ya yi kamar ta huda masa hanji. Ya rasa abin da ke masa dadi. Hannunta ya jawo da karfi ta fado jikinsa karo na farko a rayuwar aurensu. Kuka ta saki mara amo bare sauti, wannan kuka yana fitar da zafin da ke zuciyarta ne kawai, amma ba shi da sauti sai shessheka. Rungume ta ya yi a tsakiyar kirjinsa da wata irin runguma mai tsananin karfi, kamar zai tsaga tsakiyar kirjinsa ya sanya ta har ta soma tunanin kashin bayanta zai karye. Kokarin kwace kanta ta ke yi, amma ko gezau ta kasa ture wannan giant wanda ya riga ya gama kekketa zuciyarta, yake shirin dumping dinta nan ba da dadewa ba. Ina ruwansa da ita? Ina ruwansa da rayuwarta?Meye dalilin sa na zuwa dakinta yanzu? Yadda ta yi alkawari za ta cika da izinin Allah, ta san ba ta da matsayin samar wa zuciyarta abin da ta ke so a yanzu, wato ci gaba da rayuwa da shi har karshen rayuwarsu, fitina ce kawai da giggiwa irin na zuciya. Idan Abdulazeez mai son kai ne (selfish) hakika ya kwatanta adalci a cikin (selfishness) dinsa. Ya kamata ita ma ta kwatanta,ba a biye wa zuciya sai ta kai mutum ta baro. Ya ci gaba da rayuwa da ita alhalin babu soyayyarta ko digo a zuciyarsa? Ta ruguza masa farin ciki don amfanin kanta? Ko wannan shi ne kokari na karshe da za ta yi a rayuwarta sai ta tabbatar ABDULAZEEZ ya auri MUAZATU...... sai ta tabbatar ya cika burinsa... sai ta yi hobbasar da mahaifiyarsa ba ta yi fushi da shi ba a kan hakan. Daina mutsu-mutsun kwatar kannata ta yiganin cewa wahalar da kanta kawai take yi, bai yi mata sassaukan riko ba, bai rike tada sauki don ta kwace a sanda ta so ba, ta kwantar da kanta kawai a kirjinsa kukanta na raguwa a hankali har ta daina shi bakidaya. Hannunsa na dama ya sanya cikin yatsunta ya sarke su sosai na hagun na rungume da ita tsakiyar kirjinsa. A wannan lokacin ta tabbata da zaa tsaga jikinta ba za a samu digon jini ba ya hau ya yi sama saboda duniyar gajimaren da ta tsinci kanta. Balle kuma data tsinci tattausan bakinsa cikin nata. Dukkaninsu idanunsu sun rufe sun manta da kowanne irin nauin aure suke yi. Abin da suka sani kawai shi ne, su maaurata ne, kuma suna tsananin bukatar junansu. Alamarin ya fi karfi daga Abdulazeez a matsayinsa na namiji wanda ya kawo wadannan shekarun bai taba kusantar mace da irin wannan kusancin ba. Idanunsa sun rufe, hankalinsa ya gushe, ya soma sumbatarta da sumba mai tsayi da zurfi a duk inda bakinsa ya kai daga kan fuskarta da masangalin wuyanta, cikin wata siga mai nuna tsananin bukatar miji zuwa ga matarsa....... Abubuwa da yawa ke yawo a kan Hafsat suna ankarar da ita rayuwar da Abdulazeez zai jefa ta idan ya samu wannan nasarar a kanta, kuma ya sallame ta kamar yadda ya kudurta; bazawara... second hand... ko mai ciki da goyo babu aure, babu martabar zama a dakin aure...... ! Sai gantali a jamia, amma ba ta da martabar da za a kira ta matar aure, ko matar Barrister Abdulazeez Hamzah Attikou!Wannan sai MUAZATU. Ita sunanta sauta ga wawa..... bazawara under twenty years!!! Don haka a take ta soma protest. Zuciyarta ba ta afu ga Abdulazeez a yau don wannan rayuwar ba ne kawai, sai don ci gaba da rayuwa tare da shi har karshen rayuwarta. Protest ta ke sosai da dukkan karfinta da iyawarta, wanda hakan ya tayar da hankalin Abdulazeez fiye da zatonsa. Lallashi ya koma, duk da ba cikin hayyacinsa yake lallashin ba ya san kalaman sun yi tsauri a ce Suhaana yake gayawa su. Wannan jaririyar kanwar tasa da aka haifa akan idonsa ta girma a gaban mahaifiyarsa. Kalaman da yake gaya mata ta ki yarda ko kadan su yi tasiri a tare da ita, don ta amince na yaudara ne da neman cimma buri, ba ta hango komai a wannan lokacin sai zawarci babu budurci. Wani mai matar za ta aura ba ta da damar gina family nata na kanta irin na gidansu sai na gidan wasu. Ko kishiyar Muazatu ba ta isa ta zama ba sai kanwar mijinta. Wani kuka ne ya taho tun daga kololuwar zuciyarta ta rusa masa shi tunda karfinta ya yi kadan ya raba ta da Abdulazeez a daren yau. Sosai ya tsorata da kukan mai kama da na an yanki naman jikinta, ya koma gefe ya dafe kansa a gefen gado da dukkan hannuwansa. Wannan damar ta samu ta ja duvet ta lullube jikinta tana ci gaba da gabza kuka kamar wadda aka aiko wa sakon mutuwa. Haushi da bakin ciki ne ya sanya shi maida Pajamas dinshi ya bar mata dakinta. Da sauri ta sauko ta murza wa dakin key ta bar mukullin a jiki. Ba ta sani ba ko ta bar dakin a bude a yadda ya zuciyan nan ba dawowa zai yi ba. Shi kadai ya san cikin halin da ya kwana. Amma ga Hafsat abin ba haka ya ke ba. Bayan ta goge ido daga kukan kwantar kan data rakito barci ta yi har da munshari da saleba, cikin mafarkinta kalaman Abdulazeez ne wadanda ya fada mata a lokacin da ya tashi daga Barrister Abdulazeez zuwa MIJIN HAFSAT! Sunan da ba za ta fada a fili kowa ya ji shi ba saboda har gobe tana tantama a kansa. Su ke nanata kansu cikin barcinta suna kara armasa mata shi. Sosai ta makara sallar asuba don a rayuwarta ba ta taba ganin dare mai tsayin na yau ba. Wanda ta sanya shi cikin darare masu dumbin tarihi a gare ta. Wani dare daga cikin dararen da ba za ta taba mantawa da su ba. Ko da ta yi sallah ta shiga kitchen don sama musu abin da za su ci duk da ta makara, alamu ta gani na an yi girkin taliyar indomie da dafaffen kwai. Duk da lahadi ce yau ya ki zama a gidan, ba ta san inda ya tafi ba. Yadda ta yi girkin rana haka na dare ya tadda shi a dining Abdulazeez bai taba ba, kuma ta tabbatar ya dawo gidan, don ta ji motsinsa sake fita ya yi ba tare da ya neme ta ba. Murmushi ta yi ta kwashe ta ajiye a kofar shigowa babban falonsu inda ta ke ajiyewa Danfulani abinci ya zo ya dauka da kansa. Fushi Yaya Azeez ya ke yi da ni? Ta fada a hankali. Ya fi mini. Ta fada a fili. Wannan alamari ya fi karfina, sai Yayata abar sonka Muazatu, tunda na gane shi ne muhimmi a cikin auren ba kamar yadda na zata ba. (Its not a crime) idan akwai aure, kuma sai an kai zuciya nesa zaa iya bijirewa. Balle daga Abdulazeez din da ta yarda zuciyarta daban ta ke daukar kowanne alamarinsa. Lumshe idonta ta yi tana tuno yadda ya ke kissing idanun kansu ba su tsira ba. Labban bakinta ta cije don ji ta yi kamar yana bayanta yana sake kissing din su. Ya Ilahi. Suhaana ta fada a fili, tare da kwashe kwanukan daren ma ta koma kicin da su ta adana abincin a firji, ta rufo kitchen din da sauri jin horn din motarsa ya dawo gidan misalin karfe tara na dare. Gidan Barrister Sagir ya tafi, a can ya ci abincin dare, Hafsat ta jika nata ta cinye. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Daki ta shige da gudu ta rufe kofarta. Ba ta kara fitowa ba sai washegari bayan ta idar da sallar asubah ta fito kitchen don hada masa abincin kari da zai fita shi, tunda ranar (office) ce. Da wuri ya shirya don ya ba ta haushi, duk saurin da ta yi ta gama tana fitowa daga kitchen din ta ga ficewarsa daga falon. Da sauri ta koma kitchen ta dauko basket din, amma tana fitowa yana yin reverse zai fice daga gidan ga Danfulani ya wangale masa get. Yana hango fitowarta ta madubin motar har tana tuntube don sauri, ya fizgi motar da gudu ya fice daga gidan. Allah ne ya so ta kananan duwatsu ne shimfide da harabar gidan bakidaya, la-shakka da ta sha kura. Kasa daurewa ta yi sai da ta yi hawaye, sabon salon da zamansu ya dauka ke nan. A ganinta laifin da ta yi bai yi kamarin da zai yi wannan fushin ba. A kan gaskiyarta ta ke. Yaushe ta tashi daga matar wucin-gadi zuwa parmanent wife? A cikin ajandarsu babu auratayya. Ba kowa ya fahimtar da ita wannan shi ne aure ba, shekarunta da kwakwalwarta ne. Abin da ta ke ji a kan Abdulazeez ma zuciyarta na son fahimtar da ita maanarsa da gangan ta ke kin karba. Idan wannan alamari da Abdulazeez ya bijiro a gare ta shi ne aure, hakika auren abu ne mai matukar nauyi kwarai, kuma zai iya ruguza duk wasu tubala da suka gina auren nasu a kai, tunda ba zaa fara don a daina ba. Ga shi ta sha alwashin taimakawa Abdulazeez ya samu abin da yake so ya cika burin rayuwarsa. ***** Kwanaki sun shura ana wani irin zama mara dadi tsakanin Abdulazeez Dakata da matarsa Hafsat-Suhaana. Shi yake fushi da ita ba ita ke fushi da shi ba, fushin da in zaa daura masa wuka a makoshi a tambaye shi dalilinsa ba zai iya fada ba. Hafsat ta fi shi gaskiya in gaskiyar yake so. He attempted to cross the limit, ita kuma ta ankarar da shi. Me ye laifinta fisabilillahi? Ya daina cin abinci da ita, ya daina hira da ita. Ya daina zaman gidan. Shakuwarsu da Sagir da iyalinsa ta karu a dalilin yawan zuwa gidan da yake yi yanzu don debe kewa, ko gidan iyayensa. A ganinsa janyewa Hafsat shi zai ceto shi daga katoton ramin da zuciyarsa ke son jefa shi, ramin da in ya kuskura ya fada sai ya yi tsalle dubu bai iya fitowa daga cikinsa ba. Dole ya lallashi Muazatunsa suka shirya domin ya yarda har da nisa da ita cikin dalilan shakuwarsa da Hafsat, shakuwar da ba za ta haifar da Da mai ido ba, sai tarin nadama. Sau-tari ya kan samu kansa cikin zurfi a tunani, Hafsat matarsa ce da addini ya halasta mishi iyaye da duniya bakidaya suka shaida. Yana da damar kusantarta no matter what, rashin samun damar hakan na iya jefa shi cikin wani hali a yanzu da yake tsananin bukatar mace a tare da shi. Ya ture komai ya karbi hakkinsa, shi ya ga abin da ya gani, ba yarinya ce kankanuwa ba irin daukar da yake yi mata. Ko protest din da ta yi masa ya nuna Hafsat na da wayonta, ta san abin da ta ke hangowa a cikin aurensu duk da tana da feeling a kansa wanda in ya yi rantsuwa ba zai yi kaffara a kan hakan ba. Tana da wani feeling na daban a kansa a yanzu bayan aurensu da zamansu tare na tsayin watanni, zuciyarsa ce ke karyatawa da gangan. Da hujjar cewa; yarinya ce, shekarunta ba su kai ta bambance da abin da zuciyarta ke so ba, sai wanda aka karkatata a kai. (Anya kuwa Abdulazeez?). Shi da kansa ya soma saukowa daga dokin fushin nasa ba tare da kowa ya lallashe shi ba. Ganin halin da fushin nasa ya jefa Hafsat. Ta shiga cikin matsananciyar damuwa da rashin walwala, in bai yi kuskure ba zai ce har ramewa ta yi jiya da ya saci kallonta tana gyaran falon, a lokacin yana zaune tsakiyar 3-seater ya mike kafafunsa da system a kan cinyarsa yana duba wani aiki. Amma duk da haka ya sa a ransa zai rage kusancinsu don tserar da kwangilarsa. Daga jibi Alhamis zai soma azumin tadauwai don samun lafiyarsa. Washegari suka wayi gari da baki na ba-zata. Mammah da Baba Azumi, Ismael ya tuko su ya kawo su. Shi bai fito ba ma. Fitowarsa daga wanka kenan Danfulani ya kira shi ya sanar da shi, wai suna da baki ga su zaune a cikin mota sun ce daga Asokoro ne. Bai tsaya goge ruwan jikinsa ba ya sanya kaya, bakin wandon Jeans da shudiyar T.Shirt yar gidan Nordstrom. A gurguje ya fito don ya san babu wasu da ya sani a Asokoro sai iyayensa. Ilai-kuwa, Mammah da mai aikinta Azumi da kaninsa Ismael ke fitowa daga mota. Mammah! Ya fada cikin bayanannen farin ciki. Karasawa ya yi da sauri, shi ba abin ya rungume ta ba ta ce ya yi girma, shi kuma a yau ban da rungumar bai san me zai yi mata don nuna mata jin dadinsa ba da tako kafarta muhallinsu. Hannayenta biyu ya kama, You arehighly welcome to our home Mammah. Murmushi ta yi ta kwace hannunta tayi gaba, ya russuna ya gaida Azumi, ya ba wa Ismael hannu, ya karbi handbag din Mammah ya shige cikin gidan da sauri yana kwala wa Hafsat kira, Hafsa! Hafsa!! Mammah ta ce, Wannan kira haka ai sai ka ba ta tsoro. In ka kyale ta har dakin zan isko ta. Kwance ta ke lamo a cikin quilt kasancewarta mai yawan son dumi ko da gari babu zafi, kanta a kan filo ta cure gashin kanta a gefe, kwance ta ke kawai ko wanka ta kasa tashi ta yi saboda nauyin zuciya. Ba tunanin kowa ta ke ba sai na Abdulazeez din da ya hana zuciyarta zama lafiya a duk kwanakin nan, da tunanin hanyar da za ta bi ya daina fushi da ita. Kamar daga sama ta ji yana kwala mata kira da wata murya kamar ba tasa ba. Kasa amsawa ta yi, amma ta mike zaune cikin faduwar gaba. Sai ga shi ya shigo dakin, da sauri ya iso gare ta, har gadon ya isko ta ya zauna a bakin gadon. Hannunsa daya ya nutsa cikin sumar kansa ya iko hannunta da dayan ya dube ta cikin ido. Mammah ce. Don Allah Hafsat ki rufa min asiri, mu koma shirinmu na dade da hucewa wallahi. Yadda ya marairaice yana mata maganar ya yi balain ba ta dariya. Sosai ta dake ta dauke idonta daga kansa jin wani abu na fizgar zuciyarta daga cikin kwayan idanunsa. Ta rasa dalilin da ba ta iya jure kallon idanun Abdulazeez masu dauke da wani maganadisu da ba ta taba ganinshi a idon kowa ba. Hannayenta biyu ya kamo ya matse su sosai cikin nasa. Kina jina Hafsa? Don Allah ki manta komai, babu lokacin magana save it, za mu yi ta in sun tafi. Duk wani punishment ki tanadar min zan dauka, amma ki saki ranki don Allah. Daga kanta ta yi alamar ta ji, kuma ta amince. Sai jin sallamar Mammah sukai a bakin kofa, da sauri Hafsat ta janye hannayenta daga cikin nasa. Mammah ta yi kamar ba ta gani ba. Ba dai sai yanzu ki ka tashi daga barci ba? Saukowa ta yi daga gadon da gudu ta yi kan Mammah ta rungume ta kankam. Abdulazeez ya ce, Ba ta jin dadi ne. Tun jiya ta ke fama da zazzabi, amma na ji yanzu ya sauka. Ni ki cika ni kada ki kada ni. Da kyar Mammah ta samu Hafsat ta cika ta suka zauna tare. Dakin ta ke bi da kallo, komai tsaf a gyare ban da gadon. Ta ce, Zazzabi? Ba sai a je asibiti ba? Ana raina zazzabi ne? Ta kafe Abdulazeez da ido. Sunkuyar da kai ya yi don gudun haduwar kwayar idanunsu. Ya san halinta sarai, kallo daya za ta yi masa ta karanto karya, ko gaskiya a kalamansa. Ba shi kadai ba har sauran yayanta. Hafsat tuni ta yi kitchen ta soma tattaro abin saukar baki, kusan duk abin motsa baki da lemukan da suke da su a firji ta kwaso, Ismael na tsokanarta, Baba Azumi na tare mata. Su matar gida manya, sai dai kuma babu wanka babu kwalliya. Baba Azumi ta ce, Eh din, ta dai fi budurwarka mai kama da shamuwa da wasu kafafunta a bubbude kamar tayar mota, ko ba ta yi wanka da kwalliyar ba. Dariya ya yi, ya ce, Wallahi Wasila ta fi Adda kyau, ga gayu, ga class, amma wannan tsami gayen sai Yaya ya hada da hakuri don bana jin ko girki ta iya. Kumburi sosai ta yi tana hararar Ismael, Mammah da Abdulazeez suka fito. Mommah, kin ga Illaila ko? Wai ni ce tsami-gaye? Mammah ta ce, Ba dole ya ce miki tsami-gaye ba? Karfe goma na safe amma ba ki wanka ba, ba ki dafa wa mijinki abin kari ba, ba ki gyara gadonki ba balle ki yi masa kwalliya. Kamar za ta fashe da kuka ta ce, Wallahi Mammah ina yi yau ne kawai. Abdulazeez ya harari Ismael kasa-kasa. Mammah na fa gaya miki ba ta jin dadi. Kana kare ta ne kawai amma ba zan yi miki uzuri ba Addah, shi ya sa ban gaya muku zan zo ba, zuwana na farko ga yadda na tadda ke. Hafsat ta soma kuka kamar ta ce da Mammah in ta dafa abincin ba ya ci, ya daina kula ta dalilin hautsinewarta kenan, ta tuna rokon da ya yi mata yanzun nan na ta rufa masa asiri. Amma Abdulazeez ya cuce ta. Duk yadda ta ke hana idonta barci ta hada masa (verities) na abinci mai rai da motsi kullum sai dai ta zubar, ko ta bai wa maigadi, yadda ta ke kalkale gidan nan da kwalliyar da ta ke dandasawa ko kallo ba ta ishe shi ba yau daya sun tashi a banza! Ganin tana kuka zuciyar Hajiya Maryam ta tabu. Abdulazeez cikin damuwa ya ce, Ishma, me ya sa ba ka iya wasa ba ne? Ni na ce da kai ba ta girki? Ismael fa ba ya gajiya da tsokana, sai dai in bai ga abin fada ba, ya ce, To Yaya a zubo mana man tunda an dafa? Mammah ta janyo Hafsat jikinta. Rabu da Ismael Addah, ni na dafo mana abincin saboda bana so ki sha wahala. Ta dubi Baba Azumi, Karbi mukullin boot a shigo da coolers din nan gabadaya. Ismaeel ya yi mata gwalo ya mike suka fita shi da Baba Azumi. Ta sake bara baki tana kuka, wai ya yi mata gwalo. Abdulazeez abin ya ba shi dariya, ya ce, Me ya sa ki ka zo da shi ne Mammah? Da Usman ki ka dauko. Ka san Usman da gudu a titi, ni kuma bana son gudu shi ya sa na dauko shi. Na manta takura miki zai yi Addah. Allah ba zan je gidansa ba, kuma ba zan je bikinsa ba. In ji Hafsat. Karaf! A kunnensa yana shigowa dauke da food-warmers din Mammah masu kyau,ya ajiyesu tsakiyar falon ya ce, Ai gara kada ki zo din, balle ki koya wa Wasilata kazanta, rashin girki da rashin gyara. Abdulazeez ya dau filon kujera ya jefa shi da shi. Filon ya cafe da hannayensa yana fadin, In ba za ki koyi gayu ba na rantse sai na yi wa Yaya budurwa yar gayu ko cikin kannenWasila. Sosai Abdulazeez ya fusata, ya ce, Fita daga gidan nan Ismael, tunda babu gadonka a cikinsa. Hannayensa biyu ya hada irin na rokon afuwa yana kallon Hafsat, Im so sorry uwargidan Ya Azeez. Amma kafata kafar uwata. Mammah ta girgiza kai, Ni ma ba za mu jera ba, tunda kana fatan a yi wa Addata kishiya. Na tuba na bi Allah na bi ku dukkanku. Baba Azumi ki gaya musu wasa nake, amma ai ita Adda ta sani ko a cikin kanne ita ta musamman din Illaila ce. Zumburo masa baki Hafsat ta yi, Aah, yanzu ka daina sona. Dariya ya yi wadda ta fiddo fararen hakoransa bakidayansu, Ke me ya sa ba wuya ne ki ce an daina sonki? An gaya miki ana fara son mutum don a daina ne? Youre special sis, ke da Yaya Azeez mutu-ka-raba takalmin kaza, ba yar gayu ba, ko yar sarkin Istanbul haka za ta ganku ta barku. Na tsaya miki sister, ko Mammah? Mammah ta shimfida ledar cin abinci a tsakiyar falon gargajiyansu (African parlour) ta soma shirya plates da cokula ba ta kula shi ba. Can kuma ta ce, In mutum ya ce shiga abin da ba ruwansa shi ne sanaarsa, ai sai kowa ya ja baki ya yi shiru ya zuba masa ido ya yi ta yi har Allah ya gajisshe shi. Hafsa ta ce, Sosai kuwa Mammah. Ta faki idon Mammah ta yi masa gwalo. Abdulazeez bai kara kula su ba, wayar hannunsa yake daddannawa yana duba sakonni. Funkason fulawa ne da sinasir da miyar agushi wada ta ji alayyahu da ganyen ugu da naman saniya, mammah ta dafo musu. Ita ta yi serving kowa. Daga Abdulazeez har Hafsat sun ji dadin abincin, sun bude ciki sosai sai ci suke don rabon kowannensu da cin kwakkwaran abinci cikin sukunin zuciya, tun fadansu. Babu wanda ya kara samun nutsuwar zuciya irin wanda ya samu a yau. Lallai UWA rahma ce, kuma komai girman Dan Adam yana bukatarta. Allah ka kara wa iyayenmu lafiya da nisan kwana mai albarka. Mammah sarkin saido ta yi mamakin irin yadda suke ta narkar abincin nan. Ga shi da alama kowannensu ya rame idonsa ya fada, sai satar kallon junansu suke. Ko dai gaskiyar Ismael ne Hafsat ba ta girki? Amma da wuya hakan ta kasance don da ita dai ta san ba sakaran kiwo ta yi wa Addarta ba. Kusan koyaushe tare suke girki in tana gida, musamman da suka dawo Nigeria inda ba ta zuwa makaranta. Ta yi ajiyar zuciya har sai da kowa ya dago ya dube ta. Ta kudurce a ranta za ta binciki Hafsat ta tabbatar tana dafawa mijinta abinci ko ba ta dafawa. Garin kalle-kallen Hajiya Maryam idonta ya fada kan kasaitaccen hoton Muazatu kafe a bangon gabas maso kudu na falon. Idonta ta kafa wa hoton tana son tuno inda ta san fuskar, kamar ta taba ganinta a wani wuri amma duk kokarinta ta kasa tuno inda ta gantan. Adda wace ce wannan? Ta tambaya cikin mamaki tana mai nuna hoton da dan alinta. A lokaci guda ita da Abdulazeez suka kai idonsu ga inda Mammah ke nunawa. Gudun jini ne ya katse a jikin Abdulazeez zuciyarsa ta yi wani irin bugu, wani rugugi ya ratsa a cikin kansa. Tun sanda ya kafa hoton don ya bakanta wa Hafsat bai kara tunanin zaman nasa kuskure ba ne, ko tunanin wani zai iya zuwa ya gani ya tambaya balle Mammah, mutum ta karshe da bai taba kawowa ba cikin masu ziyartar gidansa sabida fillancinta na alkunya. Hafsat ya duba da sauri suka hada ido, ta yi saurin dauke kanta ganin ragaita da muzantar da ke cikin kwayar idanunsa. Saura kadan dariya ta kufce mata, amma ta hadiye. Da ma an ce in za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, ba ka sani ba ko kai za ka rufta. Halacci da yawa ya yi mata a rayuwar aurensu ta tsayin watanni shidda, ko da ya bata mata alherinsa ya rinjayi kuskurensa. Ta tuno ranar da ta san ko ita wace ce a cikinsu Abdulazeez bai kyamace ta ba, ya ce da ita; ita ba shegiya ba ce da ubanta a gaban iyaye da yan uwansa. Ya ce, uwar da ta haife ta ba ta yi kama da mutuniyar banza ba. Mace ce mai cikar mutunci, mai kirkin gaske. Ya sha alwashin nemo mata uban da ya haife ta da nemo mata yan uwanta na jini ya sadar da ita gare su cikin dan lokaci kalilan. Kafin a yi haka Abdulazeez ya yi mata alheri da kyautayi mai yawa a cikin gidan nan... she adores him much... she respectshim alot... duk wata kulawa da ya kamata a baiwa mace a gidan aure yana bata kafin suyi fada. Samunbakinta ta yi da budewa yana bai wa mahaifiyarsa amsa ba tare da ta shirya kalaman a kan harshenta kafin ta furta su ba. Kawata ce Mammah... sunanta Faizah. Abdulazeez ya yi baya ya lumshe idonsa yana maida numfashi, ya dauki mintuna bai bude ba. Ya yi kasa da kansa, Hajiya Maryam mamaki ya kashe ta a zaune. Kawa Addah? Shi ne ki ka makala ta a bangon dakinki? Kullum mijinki na tozali da ita? To bakya kishin mijin ne? Da gani ma wannan ai ta girme ki kuma da kyar in ba ta da aure? Ni yaushe ma ki ka canza hali har ki ka saki jiki da kawaye? Maza-maza sauke shi tun kafin in sabar miki. Jiki na rawa Hafsat ta mike ta hau kici-kicin sauke hoton, amma ta kasa. Mammah ta juya akalar fadanta kan Abdulazeez. Ban so zuwa gidan nan ba, ashe rashin zuwan nawa kuskure ne babba, kana ina Addah ta yi kawance da wannan mai soyayyen idon kamar an soya gyada marau-marau ba ka tsawatar ba? Dubi kirjinta duk rabi a waje bakinta kamar na karuwai an kafe ta a falonka wai matsayin kawar matar gida, kai kuma ka bari. Za ki sauke hoton nan ko sai na kwankwatsa shi a tsakiyar dakin nan? Hafsat ta soma hawaye, duk ta bi ta gigice, ba ta taba jin Mammah na fada haka ba. Hannunta sai rawa yake haka hoton, ga shi ta kasa cire shi. Tasowa ya yi ya iso gare ta, gabadaya jikinsa ya mutu, Lemme help. Ya fada mata cikin kunnuwanta da tattausan lafazi. Zagaye ta ya yi cikin hannayensa kamar ya rungume ta, a haka ya ciro hoton ya sauke shi kasa. Mammah ta bi su da kallo, duk su biyun sun sunkuyar da kai, sai ta kasa ci gaba da fadan. Suka koma inda suka tashi suka zazzauna. Ismael ya ce, Ni wallahi ma kamar na santa. Abdulazeez ya galla masa harara, Mammah ma ta ce, Ah toh, ni ma kaina kallon sani nake mata. A ina ta santa? Ta jefa tambayar ga Abdulazeez. Shiru ya yi kamar ba da shi ake ba, sai da Mammah ta kara maimaitawa. Cikin sanyin murya Hafsat ta ce, makwabciyata ce. Tana da aure? Girgiza kai ta yi a hankali alamar babu. Hajiya Maryam ta ji kamar ta rufe Adda da duka don haushi, wane irin kwantaccen kai ne da ita? A yi mutum kamar sakarai bai san halin da duniya ke ciki ba sam? Ko dai ba ta kishin mijin ne? Watakila don ba sonsa ta ke ba, amma ko yaron goye ai ya san kishi. Zuciyarta ta zo wuya da yawa, in ta ci gaba da kallon Hafsat dukanta za ta yi. Mikewa ta yi tana gyara daurin zaninta da mayafi alamar tafiya. Baba Azumi ma ta mike, Ismael tattara kwanukan nan ka kai mota, mu za mu wuce, sai gani na biyu. Idanun Hafsat suka kawo ruwa, ta tabbatar ba karamin bata wa Mammah rai ta yi ba. Zuwanta gidan kenan na farko tunda ta aurar da ita, amma ba ta tsinci komai cikinsa ba sai bacin rai. A kan laifin da ba nata ba. Hasalima wanda ya yi laifin ya yi ne don ya wulakantata ya nuna mata ita ba wata tsiya ba ce a gare shi. Ga shi ta juye komai a kanta don shi ya tsira daga fushin mahaifiyarsa. Ga mamakinta ta kasa yin nadamar abin da ta yi, gara ranta ya baci da na Abdulazeez dinta! Duk yadda ya so su hada ido don nuna mata godiyar da ke cikin idanunsa ta ki yarda. Ba ta yi don ya gode mata ba, tunaninta yanzu na yadda za ta shawo kan Mammah ne ta daina fushi da ita. Har mota suka rako su, ta bude wa Mammah kofar mazaunin baya ta zauna, Azumi da Ismael direba na gaba. Kasa rufe murfin motar ta yi ta tsugunna a kan gwiwoyinta a kan cinyar Mommah ta soma kuka. Baba Azumi ta ce, Me ya yi zafi Addar Mamanta? Ba za ki yi ba daidai a yi miki fada ba? Kin san shagwababbu ba su yarda sun yi kuskure, Mammah da kin kyale mata hoton ta har Yaya Azeez ya ji yana son Faizar ya auro ta mu ga karshen kawance. Cewar Ismael. Ciro kai ta yi fuskar nan jage-jage da hawaye ta ke harararsa. Dariya yake sosai, ya ce, Ni ki matsa in ja mota za ni zance wajen Wasilata. Duk yadda ta so Mammah ta sakar mata fuska ta ki yin hakan, har Ismael ya ja motar Danfulani ya bude musu suka hau kwalta don barin shiyyar rukunin gidajen (Sun-City). Shi dai Abdulazeez ba baki sai ido, hannun damansa ya sanya cikin tarin sumar kansa yana cakudawa. Daya daga cikin aladunsa in ya san yayi ba daidai ba. Yau ba don wasu dalilai masu yawa ba tsugunnawa zai yi ya goya Hafsat-Suhaana, ya kai ta har tsakiyar gadonsa. Duk da haka zai gaya mata ya gode da irin godiyar da ta dace. Su Mammah na ficewa ta yi cikin gida da sauri ko kallonsa bata yi ba. Da hoton Muazatu da suka sauke ta fara cin karo. Tsaki ta yi ta bi ta kansa da takalmi ta wuce dakinta. Ta turo kofar za ta rufe ya sa hannayensa ya tare. Karfi ta sa wajen son rufe kofar ya nuna mata nata karfin rabin cokali ne, domin turowa daya ya yi ya shigo dakin ya maida kofar ya rufe. Jingina ta yi da kofar ta rufe idonta hawaye na zuba. Habarta ya kama da hannun damansa ya dago fuskarta, ji yake kamar ya sanya halshensa ya dauke hawayen da ke zuba kamar an sunce famfo, wata zuciyar na hana shi. Maimakon hakan, yatsunsa biyu Hafsat ta ji a saman fuskarta suna share hawayen. Sosai ta kara tamke idonta sakamakon jin wani abu mai kama da jan wutar lantarki na bin jikinta. Yi min komai da zuciyarki ta ga Ideserve as a punishment Suhaana, amma ki kwantar da hankalinki, ina mai tabbatar miki Mammah ba za ta iya dogon fushi da ke ba, so kawai ta ke ta nuna miki kin yi wauta, amma ba fushi ta ke da ke ba. Magana Abdulazeez ke yi kasa-kasa, ta yadda ba don ta kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da ba za ta ji shi ba. Wata irin kasala ta ji tana saukar mata, bude idonta ta yi a hankali ta dube shi. Damuwarsa kadan ce a kan abin da ya faru. Ji ta yi ya janyo ta jikinsa a hankali ya hade su sun zama mutum daya. Sosai ta ji nutsuwa na shigarta hawayen idonta na daukewa. Kamshin jikinsa na jefa ta cikin wani irin shauki mai wuyar fassarawa. Dankwalin kanta ya zame ya fadi kasa gashin kanta ya wargaje ya rufe hannayen Abdulazeez da ke zagaye da ita. Ba ta iya aune ba ta ji hannayensa cikin gashin kanta, bakinsa kuma cikin nata. Kissing dinta yake yi tun daga kololuwar zuciyarsa. Alamarin da ya jefa su cikin wani irin yanayi dukkaninsu da ba su taba ji ba a rayuwarsu. Daga can tsakiyar unguwa aka kwada kiran sallar laasar. A yau duk jarumtar Hafsat ta kasa yin protest din, ta kuma kasa yin kowanne kokari na juya wa Abdulazeez baya, ta nemi duk wani kyakkyawan tunani da ke cikin kanta ta rasa. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Ladanin ya ci gaba da kwada kiran sallah har tsakiyar kwanyar Hafsat. Tana cikin mutane masu matukar kiyaye lokacin sallah. Zame jikinta ta yi, an yi saa rikon da ya yi mata ba mai karfi ba ne sabida shi kansa ba shi da karfin, dukkansu zubewa sukai a kan marbleskowanne na kokawar nemo consciousness dinsa. Kafin kunya matsananciya ta zo ta lullube Hafsat, ta sanya kanta cikin kafafunta ta kasa dagowa. Abdulazeez ta ji ya kwantar da kai a bayanta ya yi shiru kamar ba ya jin kiran sallar da ake ta yi. Muskutawa ta yi cikin jin nauyi ta yi masa magana. Yaya Azeez ana kiran sallah? Ina ji Hafsat, na kasa tashi ne. Ko in daga ka?. Ya jinjina kai, dariya na son kama shiduk da halin da yake ciki,wai ta daga shi kamar wani dan ta, har yanzu bai sauke kai daga gadon bayanta ba, Its not easy daga kato iri na. Amma tunda kince zaki iya zo ki gwada. Above all (fiye da komai) a yau, kuma a yanzu, ina so in ce miki NA GODE! Murmushi ta yi duk da ta san ba kallonta yake ba. NAGODE din ta me ce ce? Dagowa ya yi daga kwanciyar da ya yi a bayanta ya juyo da ita gabansa suka fuskanci juna, kwayan idanunsa ya kalmashe a cikin nata ta yadda ba za ta iya dauke su ba in ba shi ya aminta da hakan ba. For everything!. Ya ba ta amsa da murya mai cike da mazantaka. Tana so ta dauke idonta amma ta kasa sabida bai ba ta damar hakan ba. Ban yi don ka gode min ba Yaya Azeez, yi wa kai ne. Amma ni ma ka yi min alfarma ka maida hoton Aunty Muazatu dakinka, tunda ban fiya shiga ba. Abdulazeez bai taba jin ya ji nauyin mace a rayuwarsa irin wadda ya ji yau na matarsa Hafsat ba. Ko ba ta fada ba bai yi niyyar maida hoton Muazatu falo again ba don mahaifiya ba wasa ba ce. Ba ya son tuna kalaman da Mammah ta yi amfani da su a kan Muazatu wadanda sun kara farkar da shi ya san cewa akwai babban aiki a gabansa. Mammah ba za ta taba son Muazatu ba komin sauyin da lokaci zai kawo. Shi ma kuma ba zai daina sonta ba komin sauyin da lokacin zai kawo. Babban kuskuren Abdulazeez tunda ya fara soyayya da Muazatu bai taba bai wa Allah zabi a kai ba. Abin da ya sani kawai yana sonta, dole ya samar wa zuciyarsa abin da ta ke so don bai iya jure zama loser a komai. Not even in the court of justice. In aka kada shi (wanda da wuya ake samun hakan) har ciwo yake yi. Allah ya halicce shi mutum mai nasara a dukkan abin da ya sa gaba. Yana da yakinin a gaba ma zai yi nasara, zai samu Muazatu kuma zai daidaita da mahaifiyarsa a kanta. Ita dai Hafsat tunda ta samu kalamanta suka jefa shi a tunani ta sulale ta yi bandaki. Sanda ta fito babu shi a dakin, sai kamshin turarensa. Ajiyar zuciya ta yi ta matsa gefen ibadarta ta tayar da sallah. Bayan ta idar da sallah ta yi nafilfilinta sunkuyawa ta yi ta fada a tunani, abin da ya faru tsakaninsu yan mintuna kalilan ta ke tunawa da shauki mai yawa.Fondest thought! Wato tunani mafi soyuwa a zuciya. Ko ba a gaya mata ba, wannan shi ne romance na tsakanin miji da mata da a shekarunta da rayuwar da ta yi ta tsayin lokaci a cikin masu jajayen kunnuwa ya kamata a ce ta sani. To amma ai kuma masoya ke yinsa kuma ba ya faruwa sai da soyayya. Wannan na nufin..... wannan na nufin... tsakaninta da Abdulazeez Dakata akwai SOYAYYAH??? Tambaya ce da ta yi tsananin zurfi a kwakwalwarta har barin kanta ya soma ciwo. Wata murya ce daga can kasan ranta ta ke cautioning din ta. Ki yi a hankali Hafsat! Be very careful!! Wannan rayuwar da Abdulazeez ya soma jefa ki a ciki kuma zuciyarki da gangar jikinki suka karbe ta da hannu bibbiyuwill ruin your entire future.tunda ya ce MATAR WUCIN-GADI ce ke, wani abu da Hausawa ke kira dandani haukaci, ya maida ke emotional, kuma ya yi dumping dinki ya dauki wadda yake yi wa so na hakika. Da ma dai a ce zai dauke ki da irin matsayin da zuciyarki ta dauke shi a yanzu ne, amma ki ja babban layi a kan wannan alamarin kowa ya tsaya a limit dinsa har zuwa karshen tafiyar. Wani karfin zuciya ne ya shigi Hafsa a wannan lokacin. Ta yarda gaskiya ce zallah super ego side dinta ke gaya mata psychologically. Ta ci gaba da karfafawa kanta gwiwa da cewa, gara Abdulazeez ya yi ta fushi da ita, amma za ta tserar da martabarta no matter what! Yana son kansa da yawa duk da akwai adalci a cikin (selfishness) dinsa. Ya kamata ita ma ta so kanta, ta tanadarwa mai sonta na hakika abin da zai yi alfahari da ita. Wanda ba komai ba ne sai cikakkiyar Addah Hafsatu...... Haka kawai ta ji kuka ya zo mata, wanda ba na komai ba ne sai na tausayin kanta. A masallacin unguwarsu irin fadan da Abdulazeez ke yi wa kansa kenan. To amma ya ya zai yi ne? Shi kansa yana mamakin alamarinsa da Hafsat, yadda yake zama ba shi ba muddin za su kadaice. Yana bukatar amini da zai gaya wa damuwarsa, ya ba shi shawara. Sai dai kuma Allah ya halicce shi wani mutum mai son rike duk wani sirri da ya shafi iyalinsa. Hatta Muazatu ba ta san tsakaninsa da Hafsat ba. A tunaninta rayuwa suke kamar kowadanne maaurata in ta yi laakari da yadda ta kusa rasa shi a kan kalamanta a kan aurensa. Gabadaya manyan abokansa Abdallah, Taufeeq, Esq Ahmad and co. Kalamansu na alkhairi ne a kan Hafsat tun lokacin aurensu. Yarinyar da komai nata da kamalarta sun kayatar da kowannensu, duk da sun lura kamar Abdulazeez ba ya sonta. Ba tare ya yi karatu da su ba, wajen aiki ne ya hada su, don haka ba su da labarin Muazatu kowani abu da ya shafe ta. Abdallah ya taba gaya masa ko bai son yarinyar nan wani lokaci zai zo da zai so ta, ko da zai mata kishiya. A lokacin ya ce da shi, Allah ya kiyashe ni zama da mata biyu. Kuma haka yake har kokon ransa. Bai taba mafarkin zama da mace sama da daya ba a burikan rayuwarsa. Yana kuma rokon Allah kada ya jarabce shi. Ga shi lokaci sai gudu yake yi yana tunatar da shi manyan alamuran da ke gabansa. Tafe yake daga masallaci zuwa gida yana tuki a hankali yana tunani cikin neman mafita ga rayuwarsa. Yadda yake tafiyar da motar tsammani za ka yi tayoyinta sun lalace ne. A haka dai har Allah ya nufa ya zo gida. Yadda ya bar gidan haka ya dawo ya same shi. Ya fahimci Hafsat ba ta fito ba. Dakin nata ya leka duk jikinsa a sanyaye yake, tana durkushe a kan sallaya ita ba sallah ba, ita ba barci ba. Ya dade rike da murfin kofar yana kallonta, abubuwan da suka far a dakin mintuna kalilan da suka gabata na dawo masa. Wani gajeren lokaci ne da ya kasa gushewa a cikin rai da zuciyarsa. Ajiyar zuciya mai nauyi ta subuce masa, wadda ta ankarar da Addah wanzuwarsa a dakin, duk da kafin hakan kamshin jikinsa ya ziyarci hancinta. Ba ta kawo shi ba ne, saboda yadda suka cakuda da juna a yau sosai ita kanta kamshin creed aventus ta koma yi bakidayanta. Kasa dagowa ta yi ta dube shi sabida nauyinsa da ta samu kanta a ciki tun faruwar alamarin. Kamar wannan shi ne karo na farko, sai da ya kira sunanta. Dagowa ta yi ta zauna sosai ta dafe gado da hannunta na dama, amma ga mamakinta ta kasa kallonshi. Murmushi ya yi ya shigo har tsakiyar dakin ya tsaya, hannayensa duka biyu zube cikin aljihun bakin jeans din da ke jikinsa. Yau da wuri zan kwanta, saboda gobe lahadi ina so zan yi sammako, za mu je jihar Adamawa daurin auren kanin wani abokin aikina a Yola, zan samu abokiyar kwana a dakina? Bana jin dadin jikina, ina tsoron kada cikin dare zazzabi ya rufe ni. Kunkuni ta hau yi tana zumburo baki,kaji wani sabon batu, ya kasa jin me ta ke cewa. Sake matsowa ya yi ya zauna a gefen gadon daidai hannunta. Da sauri ta janye hannun, Aah Hafsah na fara cizo ne? Ta yi masa shiru. To zan samu yar tayin kwanan? Sunkuyar da kai ta yi tana magana ciki-ciki, sauka ya yi daga gefen gadon ya zauna a gabanta sosai ko ya fahimci me take cewa. Ta yi saurin ja da baya. Da mamaki yake kallonta, ta sunkuyar da kai ta ki yarda su hada ido. Wani abu ya faru ne bayan na fita? Ya tambaya da murya ta nutsuwa. Girgiza kai ta yi, Ba abin da ya faru. Ya ce, Na ga kina ta guduna ne, Hafsat yaushe ta kaimu da haka? Kwalla ya hango ta taru a gefen idonta tana ta kokarin maida ita. Kafin ta ankara ya dago fuskarta sai kawai ta sake su ta ba su damar silalowa. “Yaa Sattaru Sutrukal jameel. A fitata da dawowata na yi wani abu da ya bata miki rai? Girgiza kai ta yi. To tashi mu je na ce ki taya ni kwana, ina da tafiya gobe da asuba saboda a yammacin gobe za mu dawo. Mikewa ta yi ba don ranta na so ba sai don a dan zamanta da shi ta fahimci shi mutum ne mai naci a kan abin da ya sa kansa, ba ya niyyar abu ya fasa. Wardrove dinta ta bude ta dauko kayan barci masu kauri ta shige toilet, brush ta fara yi sannan ta yi wanka ta sanya su. Kanta cikin shower-cap ta fito sai digar ruwa ta ke. Fatar jikinta ta kara yin fresh, ga mamakinta har zuwa wannan lokacin yana zaune a gefen gadonta, wayarta da ta sanya a caji ce rike a hannunsa, gallery din wayar ya shiga. Hotunansa ne duk a ciki wadanda Ismael ya turo mata da wadanda bai san a ina ta same su ba. Ga kuma na dinner dinsu da aka yi a A-Class. Dagowa ya yi da zummar tambayarta inda ta same su, amma sai ya ji harshensa ya sarke. Kai ka ce ta fito ne daga jinsin Somali. Wayar ta subuce daga hannunsa ta fadi kasa. Turo baki ta yi tana tambayarsa don me yake mata bincike a waya? Budar bakinsa sai cewa ya yi, Don na isa! Ta sake cuno bakin ta tsugunna a gabansa za ta dauki wayarta, ya ce, Wallahi ki ka sake cuno min baki I will kiss it... Yadda ya ja lafazin kiiiiiissss din ya sanya ta ba shiri maida bakinta daidai. Za ta mike ya take hannunta mai rike da wayar. Wata yar kara ta saki, Yayan Haleem za ka ji min ciwo. Ki gaya min abin da ki ke fadi don na ce ki taya ni kwana. Ta runtse ido don zafi don sosai yake murje mata yatsu da yatsun kafarsa. Da sauri ta ce, Ba fa wani abu na ce ba, cewa na yi sai dai in a kwanta kai da kafa. Me ye kwanciya kai da kafa? Don Allah ka daga min hannu, sai in maka bayani. Tausayi ta ba shi sosai ganin yadda idonta har ya tara hawaye. Hannun ya kamo ya rike cikin nasa yana murza mata, abinki da farin mutum har ya yi jajawur. Ta matse kwalla da hannun hagunta, So sorry! Ya ce, sake zumburo baki ta yi. Amma data tuna abinda ya fada yanzunnan tayi maza ta gyara shi. Yi min bayani ina jinki, mene ne kwanciya kai da kafa? Ka sanya kanka inda na ajiye kafata, ko ni in sanya inda ka ajiye kafarka. Dariya Abdulazeez ya yi, Saboda me to? Ta yi shiru tare da kwace hannunta ganin ya fara canza yanayin murza mata yatsun, wayarta ta dauka ta yi gaba. Ya bi bayanta. Sai da ya rufe koina na gidan ya kashe wuta da kayan wuta, sannan ya same ta a dakin. Ta jefa filo a kan resting chair ta yi kwanciyarta ta rufa da zanin atamfarta. Yana shigowa ya ce, Me ya yi zafi na kwana a kujera Hansatuwa Addar Mammanta? Na yarda a yi kwanciyar kai da kafa. Tashi ta yi tana murmushi jin sunan da ya kira ta da shi, Ka yi alkawari? Alkawarin me? Ba za ka canza position din kwanciyar ba. Na yi alkawari Hafsat, amma in kafata ta tsokale miki ido ba ruwana. Kana juye-juye ne in kana barci? Juye-juye kai! Har da mirgine-mirgine. To ni zan je karshen gado, kai kuma ka zauna a farko, kuma still kai da kafa. In aka yi hakan bargon ba zai ishe mu ba. Dauko wani, kowa ya rufa da guda daya. Ya marairaice fuska, Ga shi kuma guda daya ne Babana ya sai min, ke ce Mammanki ta saya miki da yawa. To bari in je in dauko nawa. Ok, go. Ta mike ta nufi kofa ta murda ta fita. Da dan banzan gudu ta dawo ganin wani uban duhu. Gabadaya fitilun gidan ya kashe bai bar ko guda daya ba. Dariya sosai Abdulazeez yake yi. Ya mike ya isa ga dan firjinsa, madarar oldenburger fresh milk ya zubo a kofi ya kawo mata. Zama ta yi a gefen gadon tana ta fushin dariyar da yake mata. Mika mata ya yi, Karbi ki sha, ba kyau kwana da yunwa, daga ni har ke ba mu yi dinner ba. Ba musu ta karba ta kwankwade, ya kara mata ta shanye ta ba shi kofin ta haye can karshen gadon ta nufa da zanin atamfarta. Zama ya yi a farkon gadon yana shan madarar a hankali. Dauki duvet din ki rufa ke daya na bar miki. Ta kuwa janye ta kudundune a cikinsa. Shi ina zai iya rufa da wani quiltbayan zai kwana cikin zafi babu AC sabida ita? Dama tsokanar ta yakeyi. Sai da ya gama abin da zai yi, ya yi addua, sannan ya yi (light off) ya kwanta. Shi ya tashe ta da asubah suka yi sallah tare. Cikin sauri ya yi wanka ya shirya cikin farar shaddah kal yar ciki da babban riga, ya kafa hula zanna-bukar ya daura agogon rolex a damtsen hannunsa duk Hafsat na kallonsa. Lokar jikin gadonsa ya janyo ya dauko wani tsohon envelope da yake ta boyonsa ya sa a aljihunsa. Turare ya dauka yana fesawa sai ganin Hafsat ya yi a gabansa, ta mika hannu ta karbi turaren daga hannunsa ta shiga fesa mashi. Daga shi har ita murmushi suka kama yi, wanda ba su san dalilinsa ba. Sai da ya rike hannunta mai turaren don ya yi masa yawa. Kallon juna suka yi na yan sakanni kafin Hafsat ta sunkuyar da kanta. Horn din mota suka ji diiiit-diiit! daga bakin gate Sagir na jira. Da sauri ya saki hannun Hafsat ya sumbaci goshinta ya juya da sauri ya fita. Shafo wajen ta yi, ta sa wa yatsun ido tana kallo. Ba ta san dalilin murmushinta ba. A fili ta ke yi musu adduar dawowa lafiya. Gadon Abdulazeez ta koma ta haye ta yi kwanciyarta tare da nannadewa cikin duvet dinsa wadanda ba sa komai sai tashin kamshinsa. A yinin ranar bakidaya kasa tsinana komai ta yi, kewarsa ta ke yadda harshenta ba zai iya bayyanawa ba. ***** To fah! Ga AUREN KWANGILA ya dauko wani sabon salo, ko yaya zaa kare??? Ni kaina ban sani ba!!! Nayi muku alkawarin cigaban bazai jima ba. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* *** A JIMETA Jirgin Arik ya sauke Abdulazeez da Sagir a Jihar Adamawa (Yola), karon Abdulazeez na farko da zuwa Adamawa a rayuwarsa. Kai shi a jihohin Nigeria bakidaya zai iya kirga wadanda kafarsa ta taka, wadanda karatu ya kai shi (Ibadan, Lagos), sai ko mahaifar iyayensa (Kanon Dabo) sai kuma yau da ya taka kafarsa a Adamawa a dalilai guda biyu. Na farko abokinsa Sagir wanda yake abokantaka da shi da zuciya biyu; kyakkyawan tsammaninsa na cewa yana da alaka da Hafsat da kuma aiki da ya hada su wuri guda. A yau kuma ya zo Adamawa ne don amsa gayyatar Sagir da ya yi masa na daurin auren dan Yayarshi Modibbo da kuma son yin kyakkyawan bincike a kan Sagir da ahalinsa don tabbatar da wannan zargi da zuciyarsa ta riga ta mika wuya da shi. Daga filin jirgin saman (Yola Airport) shatar taxi suka yi (drop) har garin JIMETA kofar gidan iyayen Sagir da ke unguwar DEMSAWO. Demsawo unguwa ce mai tsohon tarihi a Jimeta. Babban gida ne irin na extended family (gidan Gandu) wanda ya tuna masa da nasa gidan kakannin da ke Kano. Tun isowarsu wajejen karfe goma na safe suka tadda jamaa sun fara taruwa a kofar gidan wanda dakali guda biyu suka sanya shi a tsakiya. Karfe goma sha daya na safe za a tafi gidan su yarinyar inda za a daura auren, nan gidan su Sagir shi ne wurin haduwa (meeting point). Sai yi musu barka da zuwa yan uwan Sagir ke yi har suka samu damar shiga cikin gidan. Wuce wannan lungu, shiga wannan sashe har suka tadda bangaren iyayen Sagir wanda ke can karshen gidan. Abdulazeez zai iya rantsewa ya ga fuskoki na mata da maza masu yanayin zubin halitta ko kamanni na fuska da matarsa Hafsat sun kai guda goma. Tazbihi kawai yake yi wa Allah Sarkin kaga halitta wanda ya halicci wannan family ya kuma sanya kamanceceniya mai tsanani a tsakaninsu da Hafsat wadda idan har ba ta jini ba ce, to hakika imaninsa ya karu da Ubangijinsa.Mai yin halitta yadda ya so a tsakanin alummar Annabinsa Muhammadu (SAW). Alamarin ya kara rikirkita shi a lokacin da suka kuke ga isowa kuryar gidan zuwa dakin dattijuwar da ake ta kira da Daada a bakin manya da yara. “Daada adon nderna (Dada kina ciki)? Sagir ya tambaya a kofar dakin, yana mai zura rabin jikinsa ciki. “Mido nder Sagir, yottu nder (ina cikiSagiru, karaso ciki). Bismillah Barrister mu shiga daga ciki. Ya gusa ya bai wa Abdulazeez hanya. Tare suka shiga dakin suka zazzauna a kan tabarmar kaba da ke shimfide, suka fara gaida Daadan, wadda ko kusa Hausa ba ta zauna a kan halshenta ba. Shi ne abokina da nake gaya miki Barrister Abdulazeez Dakata. “Jabbama-jabbama Abdulazeez, Allah ya kara albarka a gare ku da iyalanku, barka da zuwa garin Jimeta. In ji dattijuwa Daada, cikin tattausar muryarta mai cike da nutsuwa. Irin dattijan nan ne da yawan ibada da kula da sallah ya sanya musu kamala, dattaku da nutsuwa ta musamman a rayuwar girmansu. Abdulazeez dago ido ya yi yana kallon Daada, wannan karon zuciyarsa neman hantsilowa waje ta yi. Hakika baa mutuwa a dawo, kuma har da shi aka binne Habibah a birnin Jeddah, idan kuma aka hada shekarun Habiba a sanda ta ke raye tare da su zuwa yanzu shekaru goma sha takwas ko kusa ba za ta yi shekarun wannan dattijuwar ba. Ba don haka ba da ya ce Habiba ce ba mutuwa ta yi ba, Nigeria ta dawo. Hatta wata tawwadar Allah da ke gefen hancin Habiba ga ta nan a gefen hancin Maman Sageer. Bai gama farfadowa daga tunanin da ya lula ba ya lura da wani enlargment na wani hoto a gabas maso kudu na dakin, wanda ya gama warware duk wani tunani da zargi da ya saura masa. Wani farin Dattijo ne tare da Daada, da yaya maza da mata sun kai goma har da Sagir tun bai wuce shekaru sha takwas ba, a cikin jerin matan ga wadda zai iya kira HABIBAH ko daga barcin mutuwa aka taso shi Habiba ce wannan. Jikinsa har rawa yake yi, yana kallon Sagir da Dada na magana yana kallon hoton. Kafin ya sauke idonsa an cika gabansu da akusan abinci kala-kala. Muryar Sagir ya tsinkaya a tsakar kansa, Tunanin me ka ke haka ina ta magana ba ka jina? Mu ci abinci maza mu tafi lokaci na tafiya Abdulazeez. A hankali ya sauke idonsa a kan Sagir ya sake daga su ya kalli hoton sannan ya kalli mahaifiyar Sagir. Tunani ya yi gara ya bar komai a cikinsa kada ya bata musu rana, bayan suna da abin farin cikin da suka shirya yi. Wannan tunanin ya sa shi daidaita fuskarsa ya maido hankalinsa ga Sagir, wanda ya ciko kofi da farin kunun gyada mai kyawun gani a ido ya miko masa, ya kuma dauki plate ya cika musu da wainar shinkafa da kuli (maasa) ya sanya a tsakiyarsu suka fara ci. Dada na tambayarsa ko yaransa nawa? Murmushi ya yi. Dada auren nawa ko shekara bai yi ba. To Allah ya kawo masu albarka. Amin Dada. Sosai ya ji dadin abincin nan, don ya jima bai ci irinsa ba. Kuma basu karya ba suka fito. Da suka gama Dadan ta miko masa kwanon sha cike da sabuwar madarar shanu mai dumi. Ya karba ya sha sosai, da doki mai yawa. A lokacin angon ya shigo wanda Sagir ya kira da suna Modibbo, ya sha manyan kaya sai kamshin turare yake. Sai Abdulazeez ya kara tsinkewa, tsinkewar da bai yi a baya ba na zaton da dangin Hafsat ya ke tare. Yanzun ne ya karasa mika wuya. Wannan saurayin bafillace wanda alamu sun nuna ya samu ilmin boko mai zurfi bai bar komi na Habibar da ya sani ba. Mika musu hannu ya yi suka yi musabaha, ya ce da kawun nashi, wato Sagir ya tashi su wuce unguwar su amaryar inda za a daura auren. Bayan an daura aure sun dawo aka yi liyafar cin abinci a wani babban falo da ke gidan na mahaifin su Sagir. Suisu ne family din gidan maza zallah. Ko abokan ango ba su da yawa, daga nan jamaa suka soma watsewa. Booking dinsu na komawa Abuja na karfe biyar na yammacin ranar ne, don haka cikin gidan Sagir ya ja shi suka koma. A lokacin mahaifin su Sagir da suke kira da Malam Babbah ya dawo yana shigifarsa wadda ke kusa da dakin Dada, can Sagir ya ja shi suka gaisa da Malam. Ya gabatar da shi a matsayin amininsa a wajen aiki. Malam Babba malami ne na sosai, malamin Alkurani masanin addini wanda gwamnatin jihar ta Adamawa ta san da zamansa, ta ke kuma damawa da shi a kan alamuran da suka shafi addini a jihar. Kamalarsa da kwarjininsa a bayyane suke na malaman kwarai maabota dimbin ilimi. Sosai yake jan Abdulazeez a jiki don ya sake su yi hira, kasancewar Abdulazeez bai saba shiga irin wadannan wuraren ba sosai yake nuna bakunta, ga kuma nauyin da zuciyarsa ta yi. Amma duk da haka ya saki jiki da Malam Babba sun yi hirar iyayensa da kakanninsa da ke Kano. Ba karamin dadi Abdulazeez ya ji ba lokacin da Sagir ya ce su koma dakin Dada su yi mata sallama, su yi haramar wucewa airport. “On warti na (kun dawo)? Dada ta tambaya. Ai tun dazu muka shigo muna tare da Malam Babba. Sagir ya ba ta amsa cikin fulatanci shima. Wasu abubuwa cikin jarka ta turo gaban Abdulazeez. Ga man shanu da kindirmo ka kaiwa maidakinka. Ga kuma masa sabuwa an yi muku ita ma ka tafida ita, na lura kana sonta sosai. Murmushi ya yi, ya ja jarkokin gabansa yana godiya, Sagir na taya shi. Idonsa ya mayar kan hoton nan da ke kafe ya ci gaba da kallonsa. Har Dada ta lura ya kurawa bangare guda ido, ta juya don ganin abin da yake kallo. Kana kallon yan uwanka ne? Ta fada da hausarta mai rauni, fulatanci shine harshen da ya kama harshenbakinta, tsilli-tsilli take jefa hausar wadda ma dalilin Abdulazeez din take yin ta. Mikewa ya yi ya isa ga hoton ya bambaro shi daga bangon ya dawo ya zauna kusa da Dada da shi a hannunsa. Dada yanzu duk ke ki ka haife su? Murmushi ta yi, amma saboda alkunya irin ta Fulani sai ba ta ce masa komai ba. Sagir ya matso kusa da shi ya soma yi masa bayanin jamaar cikin hoton. Wannan shi ne babban yayanmu Yaya Tijjani, wannan Yaya Yushau, wannan kuma Yaya Habiba... sai Maiwada, Saade, Fusam, Haladu, ni Sagir da autan Dada Nuru. Duka mu tara ne yayan cikin Dadanmu. Yatsansa (ibham) ya dora a kan fuskar Habibah ya ki daukewa, har Sagir ya lura ya ki dauke yatsansa daga kan fuskar ta. Kamar yana bukatar karin bayani a kanta, amma bai furta hakan da bakinsa ba. Sagir ya kara matsowa kusa da shi sosai. Ita wannan da ka ke gani a yanzu ba ma tare da ita. Ita ce Yaya Habiba mahaifiyar Modibbo da aka daura wa aure yau. Mun rabu da ita shekaru goma sha tara kenan, har gobe zukatanmu cikin taraddadi suke da tarin alhini. A duk halin da muke ciki farin cikinmu ragagge ne a dalilin rashinta, da rashin sanin wane hali ta ke ciki tunda kuwa ba mutuwa ta yi ba, bacewa ta yi sama ko kasa muka rasa ta. Sai bayan shekaru masu yawa da muka tsananta addua komai ya bayyana gare mu na sanadin barinta gida, labarin mai tsaho ne Abdulazeez. Sannan ba mai dadin ji ba. Kuma mai taba zuciya. Mun yi duk wani nema na duniya har gobe babu Yaya Habiba babu labarinta. Musabbabin fara ciwon hawan jinin Dada kenan, wanda ta ke fama da shi har gobe. Malam kuwa a duk istikharar da zai yi a kan Habiba ya ce ba ya ganin komai sai duhu, Allah ya rufe masa komai, mun kasa sanin komai a kanta. Tun muna cikin tashin hankali har a hankali muka soma sabawa da rashin Yaya Habiba. A yanzu sai dai mu tuno ta mu yi mata addua, amma mun saba da rashinta, shekaru goma sha tara ba kwana tara ba ne. A yau babban danta Ridhwan (Modibbo) ya yi aure, kaninsa Abdurrahman na ajin karshe a jamia, sai autanta Imaamu yana aji uku a FUTY, to ka ji. Ajiyar zuciya mai nauyi Abdulazeez ya sauke, a lokacin da Sagir ya saka aya na takaitaccen labarin da yake ba shi. Ya tambayeshi ina mijnta? Sagir ya ce Yana nan a raye. Da ka kula da wani farin mutum mai hula ruwan kasa da farar shadda a wurin daurin auren nan yanata gaisawa da jamaa shine mahaifin su Modibbo. Malami ne a tsangayar harshen turanci a FUTY. Duk wanda ya kwana ya tashi a Federal University of Technology Yola, ya san da zaman Farfesa Bashar Maijamaa sabida rubuce-rubucensa a kan koyar da harshen turanci a jamiar FUTY. Abdulazeez na son sake tambayarsa ko me suka gano sanadin barin Habiban gida bayan watanni da batan nata?Sai shesshekar kukan Dada suka ji, wadda tun sanda Sagir ya fara bada labarin ta soma kuka. Duk cikin yayana ta fi kowannensu taimaka mini, kafin a yi mata aure ban san shiga madafi don yin girki ba, data tafi gidan miji ma bata fasa dafowa ta kawomin ba, ta fi dukkansu kyautayi a gare ni. Zuciyarta mai kyau ce, mai kaunar UWA, mai nufin alkhairi ga kowa. Samun mace mai kyautayi da jin kan UWA kamarta a wannan zamanin abu ne mai wuya. Ta so mijinta da zuciya daya, ta zauna da shi tsakani da Allah tun ba shi da komai. Rana daya Hajara ta raba su, ta shiga tsakaninta da yayanta. Ta bar su sun girma babu dumin Uwa. Ta raba ni da nagartacciyar diyata! Ba zan taba yafewa Hajara ba har duniya ta nade....... Ta ci gaba da kuka sosai mai taba zuciyar duk mai imani. Ki ba ni watanni hudu Dada, as alawyer(a matsayina na lauya) na yi alkawarin binciko miki labarin yarki Habiba, domin kamar na santa, kamar na taba ganinta a wani wuri. Abdulazeez ya samu kansa da fada ba tareda ya shirya kalaman akan harshensa ba, sun fito ne kai tsaye ba tareda karbar umarni daga zuciyarsa ba sakamakon tausayin wannan UWA mai tsananin begen diyarta. Daga Sagir har Dada zabura suka yi suka mike tsaye. Hannu dafe da kirji, baki a bude. Da gaske Abdulazeez? Suka hada baki wajen fadar hakan. Gyada kansa yayi cikin tabbatar musu da sahihancin furucin sa. Tun ranar da na fara ganinka zuciyata ta gaya min kana da alaka da Habiban da na sani. Rokona daya mu bar zancen nan a matsayin sirri a tsakaninmu zuwa dawowata. Na yi muku alkawarin da kafata zan dawo da cikakken bayani a kan Habiba, da shaidu kwarara. Da ya zo nan, ya kuma tuna Habiban ba ta duniya sai ya ji kwalla ta cika masa idanu. Kabar ni in gaya wa Malam na samu wanda ya taba ce min ya ga Habiba bayan shekaru sha tara kafin mu tadda kushewa ko na ji dadi a zuciyata. Dada ta fada tana kukan farin ciki. Za ki iya gaya wa Malam, amma daga shi babu kari har in dawo. Bana so ku kasance cikin zullumi har tsayin wannan lokacin ne shi ya sa. Zullumi ko kwanciyar hankali? A kalla dai mun san tana nan ba mutuwa ta yi ba....... Sai ya kauda ido, ya share ambaliyar hawayen da suka cika masa ido da yatsun hannunsa. Karfe biyar daidai na yamma jirginsu ya taso daga Adamawa zuwa FCT Abuja. ***** Hafsat ta ji dadin tsarabar kindirmo, man shanu, masa da kuli da Abdulazeez ya kawo mata daga Jimeta. Sosai ta ci ta koshi ta sanya ragowar a firji za ta dinga dumama musu a microwave har ta kare, nonon ma da man shanun duk a (fridge) ta adana su. Washegarin ranar ya kai ta ta baiwa Mammah hakurin fushin da ta ke yi da ita, ta ce ita ba fushi ta yi ba, tana so ne ta yi hankali da kawayen zamani, Nigeria ba Brussels ba ce ta kama kanta, ta rungume mijinta ta fita sabgar kowacce tarkacen kawa in ba haka ba za su kai ta su baro. Hafsat dai hakuri ta ke bayarwa a kan laifin da ba nata ba. Ita da Abdulazeez yanzu wani irin kyakkyawan zama ne a tsakaninsu. Kowanne gani yake ba mai kirki a duniya irin dan uwansa. Ya wadata ta da duk wani abu da dan Adam ke bukata na abinci da suttura da na amfani. Bai kara (attempting) neman komai daga gare ta ba, ganin iyayenta da kakanninta da irin gidan da ta fito da ya yi, ya kara mata kima da martaba a idanunsa. Ya yarda Hafsat ba gangar da zai ci amfaninta ya yar da kwaurenta ba ce. Gara ya maida ita ga iyayenta da yan uwanta cikin mutuncinta, ta samu miji na gari mai nagartattun halaye irin nata ta aura. In yaso ya zame mata bango abin jingina a duk sanda ta bukaci hakan. Don haka soyayyarsa da Muazatu ta kara karfi a wannan dan tsukin wadda saura kadan ta kammala (Law-school) dinta. Jarrabawar su Hafsat ta fito, ta kwaso pointsmasu yawa har (300). Ba da jimawa baya samar mata gurbi a NILE jamiar nan mai zaman kanta dake birnin tarayyah, Abuja. Duk wani shige da fice da dalibi zai yi don zama cikakken dan makaranta Hafsat tare da Abdulazeez suka yi shi. Ta zama cikakkiyar dalibar Nile University a tsangayar ilimi da koyarwa (education) inda za ta gwanance a fannin koyar da ilimin halicce haliccen duniya Geography (Education/Geography). Ba sa kwana a daki daya, Abdulazeez ya haramtawa kansa wannan. Kullum kuma shi yake kai ta makaranta da kansa sannan ya wuce office. Don haka basa bata lokaci da safe suna fita da wuri, in ta riga shi tashi ya tura direban office dinsu ya maida ta gida, in sun tashi lokaci daya shi zai biya ya dauke ta su tafi gida. Wannan ma ya taka wata rawa ta musamman wajen sanya shakuwa mai tsananin karfi a tsakaninsu. ****** Sosai Hafsat ke jin dadin abin da ta ke karanta. Darasin (Geography) da ma na cikin darussan da ta ke so tun a sakandire. Shi ma Abdulazeez ganin ta samu A1 a darasin ya sanya shi zabar mata shi, sannan halayenta za su yi kyau da na malamin makaranta saboda tana da hakuri, sanyin rai da juriya. Hafsat na jin dadin karatunta a NILE fiye da tsammani, ta yi kawa wata mutuniyar Zamfara mai suna Mami, aiki ne ya kawo mijinta Abubakar Sadik Abuja, Mami za ta girme mata da wajen shekaru hudu don shekarunta ashirin da biyu. Komai na Hafsat da yanayin shigarta na kamala da tsantseni na burge Mami wadda ainahin sunanta Rabia Sada. Mijin Mami maaikacin Etisalat ne, duk ajinsu babu wanda Rabia ta ga ya kamata ta yi abota da shi sai Hafsat Dakata, ko don ta amfana da ita saboda cikin dan lokaci hazakarta ta (good foundation) din da ta samu ta fito fili, kowa ya fahimci talented ce. Daga assignment har test ita ce zakaran gwajin dafi. Ita dai Hafsat ba ta zura jiki a kawancensu da Mami sosai, saboda yadda Mammah ta tsoratar da ita a kan kawayen Abuja, amma yadda Mamin ke nace mata ya sa dole ta ke kula ta, amma a abin da ya shafi harkar karatu kadai. Ba ta taba yarda wata magana bayan ta karatu ta hada su ba. Har ga shi watanni sun gangara suna shirin fara jarrabawar (first semister) wanda ya zo daidai da kammala (Law-school) din Muazatu wadda ta shafe watanni goma a jihar Yola. ***** Yau a kan idon Mami da mijinta Abubakar Abdulazeez ya dauki Hafsat, da ta bude motar ta shiga ta zauna, sunkuyawa ya yita saman kanta yana gyara mata sarkar wuyanta da ta harde cikin gashin kanta ta baya,gashin yake zarewa daga cikin sarkar a hankalihannayensa zagaye da ita. Yayin da kanta ke kusa da kafadunsa. Sosai Mami ta saki baki da hanci da ido daga nesa ta ke kallonsu da mamaki, don ba ta taba sanin Hafsat na da aure ba ganinta yarinya karama danya shataf. Couple din sun zauna mata a zuciya sun kasa bacewa, sai zancensu ta ke yi wa mijinta a hanya. Ba ta taba ganin matar da ta dace da miji irin Hafsat Dakata ba, har kishi ya sike Sadik ya ce. Wallahi zai ajiye ta a gefen titi, ina ruwanta da kallon mijin kawarta har ta ke yaba shi a gabansa sabida jahilci? Sosai Mami ta kama kanta don ta san halinsa sarai zai iya ajiye ta a titin a kan kishinsa, amma ta sa a ranta za ta tirke Hafsat sai ta ba ta labarin rayuwarta da inda ta hadu da wannan handsome da ta dade ba ta ga namiji mai tarin abubuwan da ya mallaka ba.Duk da itama ta san ba abune mai sauki samun hakan daga Hafsat din ba yadda take ji da class dinnan da zata tsaya tana wani bata labarin rayuwarta ko na mijinta. Amma ance a rashin tayi akan bar arha. Zata gwada saarta. A washegari da ta turke Hafsat da tambaya, nan da nan tayi fuska, ta ce ita ba mijinta ba ne, Yayanta ne. Amma irin Yaya a dangi ko familyfriends din nan ko? Saboda ita dai ta ga abin da ta gani wanda ya sanya ta shakka a kan zancen Hafsat. Murmushi Hafsat ta yi har kuncin nan ya lotsa ciki sosai. Murmushin da Mami ta kara dorawa a sikeli. Ke me ye damuwarki Mami a kan hakan? Daga ganin mutum ba ki san ko wane ne ba sai ki ce mijina ne? To babu ko daya. Mami ta ajiye biron hannunta tana murmushi ta ke kallon Hafsat. Ni na ga abin da ya sa na tambaya ko kin ki gaya min Hafsat, a sanda ya bude miki murfin mota ki ka shiga ki ka zauna, ya sunkuya yana gyara miki sarkar wuyanki. Akwai wani babban alamari cikin kwayar idanunsa a kanki. In kin sani kina boye min ne ban ga laifinki ba, don na dade da sanin kawance na da ke bai dadaki da kasa ba. In kuma ba ki sani ba, ina mai sanar da ke wannan. Idan kuma da gaske Yayanki ne kamar yadda kika dage im telling you wannan Yayancin will turn to something very special nan ba da dadewa ba. Bin labban Mami Sada ta yi da kallo, a lokacin da ta ke furta kalamanta. A ranta tana mamakin me ta gani da ya sa ta fadar hakan?Ko jiya Abdulazeez kwana ya yi da wadda yake so a kan waya, tsakaninta da shi ya kai ta makaranta ya dauko ta, ta dafa masa abinci ya ci. Ba ta da sauran buri a kan Abdulazeez yanzu, ta dade da yi wa zuciyarta fada, kuma zuciyar ta dade da shiga taitayinta. Ba ta sanya mata komai sai tunanintahowar ranar karewar KWANGILA wadda ta tabbata tana tafe nan bada jimawa ba. Bai gaya mata ba, amma tana lissafe da watanni, kuma ta ji yana fadin zai tafi Lagos (call to Bar Ceremony) din masoyiyarsa, ba ita ya gayawa ba, abokinsa Abdallah ta ji yana gayawa a waya. Ga mamakin Mami gani ta yi idanun Hafsat sun cicciko da wata zazzafar kwallah. Ta kuma dade da barin jihar da suke ciki, ta lula wata jihar daban ta tunani mai zurfi. Wannan ya tabbatar mata akwai wani alamari mai girma tsakanin Hafsat da handsome din da ta kira Yayanta kamar yadda ta ke ikirari. Amma tunda Hafsat mutum ce da ba ta son a yi mata shisshigi cikin (personal life) dinta zai fi kyau ta kyale ta. Ni dai shawarata ita ce, duk runtsi kada ki bari ya kubuce miki, nasan mijinki ne ba saurayi ba, irin wadannan daban ne Hafsat, alamu sun nuna yana daga cikin mazan da matan waje ba za su kyale wa matansu na gida kadai ba. In wannan ce matsalarki Hafsat ki cire kunya da kawaici ki damke mijinki da hannu bibbiyu, in ba haka ba za ki sha mamaki cikin garinnan. Sosai Hafsat ta yi mamakin yadda Mami ta gane Abdulazeez mijinta ne. Maganganunta kuma kamar ta san me take ciki a rayuwarta da shi din. Bata ce komai ba sai binta da kallo. A wannan ranar direban office dinsu ya sa ya maida ita gida sabida ayyuka da suka yi masa yawa. Don haka a hanyarsu ta dawowa ta kifa kanta jikin murfin motar ta yi kukanta mai isarta ta koshi. Kukan tausayin kanta... kukan rashin sanin mene ne aibunta da Abdulazeez ya kasa sonta har duniya ta fara gane tana da matsala makamanciyar wannan a tare da shi? Aibubbuka da yawa Hafsat. Babban cikinsu rasin asali, don haka ki ci gaba da yi masa uzuri kamar yadda ki ka faro, watarana sai labari. In ji zuciyarta. ****** Sai da ya bari Hafsat ta kammala jarrabawar karshen zango da ta ke zanawa sannan ya je gida a wata ranar lahadi tunda ba ranar aiki ba ce, ya tabbatar Daddy yana gida a lokacin Ismael ya koma America, Haleem da Usman ne kawai ya rage ba su koma inda suka fito ba. Ya samu Mammah da Azumi uwar goyon Suhaana wadda a yanzu za a iya ce mata kaka a gare su, ya ce ya zo ne da muhimmiyar magana, yana bukatar su zauna a falo dukkanninsu. Mammah ta je ta fito da Daddy ya same su a falon har Haleem. Barrister da sanyin safiyar nan, ya aka yi? Murmushi ya yi ya sadda kansa kasa. Har gobe Dr. Hamza bai bar jan yayansa a jiki ba duk da dukkanninsu a yanzu babu wanda bai isa a yi masa aure ba banda Haleem, shi ma da a kauye ne ba irin rayuwarsu ba, da tuni ya jima da yin auren. Sai da kowa ya nutsu ya ba shi hankalinsa, sannan ya fara ba su labari tiryan-tiryan tun hirar da yayi da Habiba aranar da alamarin zai faru, da bincike da ya soma a boye akan garin Jimeta, haduwarsa da Barrister Sagir Hashim Jimeta. Yadda ya rika nace masa duk da kasancewarshi ba mai son harka da jamaa ba, sai dalilin kamanninshi da Suhaana. Yadda suka zama abokai na jiki a watannin da suka gabata da yadda har yake zuwa gidansa cin abincin dare duk don ya shiga jikinsa, ya tabbatar da abin da yake son tabbatarwa. Gayyatarshi daurin auren dan Yayarshi da Sagir yayi, da abin da ya faru zuwansu Jimeta ya kwashe duk ya gaya musu. Mammah da Baba Azumi sai kabbara suke yi zukatansu fal farin ciki. Dr. Hamza Atiku sunkuyar da kai ya yi yana tuna tarin wautar da ya yi a baya, yana kara istigfari cikin zuciyarsa. Ka yi maganar da Addah? Mammah ta tambaya. Girgiza kai ya yi, Ban taba yi mata zancen ba har bayan da na tabbatar, saboda bana son abin da zai dagula karatunta. Masha Allahu. In ji Mammah. Tafiya Jimeta ta same mu, tunda ai ta kare jarrabawar ko? Ta gama jiya. Bari in yi wa mutanen Kano waya su shirya don gabadayanmu za a yi wannan tafiya. Kan ka ce me ye wannan Mammah ta hau bugawa su Adda Hafsatu waya, su Luba, Mariya, Furera da Murja, har Aunty Zuwaira da ke nan Abuja ba ta bari ba. Matar Uncle Idris da matar Ibrahima da sauransu. Cewa su yi shiri za su tafi Yola an gano iyayen Addarta. Tsofaffin hotunansu da suka sha yi da Habiba a Jeddah ta hau bincikowa, Abdulazeez ma yana da wasu daga ciki, ya sanya a aljihu ya tafi da su har Jimeta da zummar in bukatar hakan ta taso ya fiddo su, to kuma da ya canza shawarar rashin tada maganar a lokacin daurin auren ya dawo da abinsa ya boye inda Hafsat ba za ta gani ba. Shiri sosai wannan family ke yi na tafiya Jimeta (Yola North), wanda za su yi kwanaki uku masu zuwa. Mammah ta kasa bari har zuwa karshen mako don haka ta sanya tafiyar ranar Laraba, masu aiki su dauki uzuri. Washegari a ofis dinsu ya tadda Sagir yana rubutu cikin wasu files. Gaisawa suka yi kamar yadda suka saba, tun kafin ya yi magana Sagir ya riga shi, ya gaya masa Dada ta ce a yi masa tuni kan maganar nan ko tana da rabon ganin yarta a sauran numfashinta. Ta fara kasa jurewa jiran. Sadda kai Abdulazeez ya yi yana jin wani iri a zuciyarsa. Daga bisani ya ce da Sagir, abin da ya kawo shi kenan. Iyayensa sun yi shirin tafiya Jimeta a kan maganar Habiba ranar Larabar nan ya sanar da su Dada. Iyayenka??? Sagir ya tambaya cikin mamaki. Daga masa kai Abdulazeez ya yi da siririn murmushi a fatar bakinsa, ya ce, Dogon labari ne Sagir, amma a gidanmu Yayarka ta zauna. Sauran bayani sai mun isa can. Daskarewa Sagir ya yi a zaune, yana tazbihi yana kadaita Allah. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* ***** WASHEGARI An tara maza da mata, babba da yaro na nesa da na kusa, na zuriar Malam Hashim Babba Jimeta. Da zuriar Dr. Bashar Mai-jamaa Numan, wanda shi ma dan nan asalin Yola ne daga karamar hukumar NUMAN. Kamar yadda Malam Babba da Dada suka bada umarni; duk wani jininsu ya hallara an ga Habibah. Tunda Sagir ya shigo da bakin falon ganawar wannan family kowa yake raba ido ya ga ta inda Habiba za ta billo, tunda an gaya musu wadanda suka rike ta ne suka kawo ta. Tun fitowarsu Mammah ta ja mayafin Hafsat ta rufe mata rabin fuska, ta ce ta rufe fuskarta ta kalli gabanta, sai ta ce ta bude za ta bude. Ita dai Addah mamaki ya hana ta cewa komai, saboda ita dai tun tasowarta ba ta san suna da yan uwa a Yola ba. Jikin tsohuwa Dada da Malam Babba ya yi sanyi ganin har wadannan baki suka gama shigowa suka zazzauna babu Habiba babu alamunta. Gaggaisawa aka fara yi, sannan Malam ya bude taron da addua. Daddy ya gabatar da kansu su ma suka gabatar da kansu a matsayin iyayen Habiba da yan uwanta, ga kuma mijin aurenta Prof. Bashar Mai-jamaa, karshe Malam ya tambaye su wane labari suke dauke da shi game da yarsa Habiba? Sannan ina ta ke yanzu? Dr. Bashar ya kara da cewa, Lafiya nake zaune da maidakina Habiba tun ina matsayin Malamin makarantar sakandire. Rana daya na tsiri karo aure sakamakon kowa da rubutacciyar kaddararsa ta aure, amma ba don Habiba ta gaza da ni ta kowanne bangare ba. Yaranmu uku, Modibbo (Ridhwan), da Abdurrahman sai auta Imamu a lokacin da na auro Hajara. Tun zuwan Hajara gidan ya ki zama lafiya, fitintinu iri-iri kullum da tashin hankalin da zan dawo na taras. Amma duk sanda na yi bincike a kan rikicin zan tadda Hajara ce ta tado shi. Zaman lafiyan ya kara tabarbarewa a gidan lokacin da Habiba ta samu ciki na hudu, Hajara kuma ta kwashe shekaru uku a gidan kenan babu ciki ba dalilinsa. Wannan ciki ya kara daga hankalin Hajara ta fiddo ainahin kalarta a fili, ta mace mai tsananin hassada akan abinda Allah bai bata ba. Na sha ji tana fadi wa Habiba wannan cikin ba dai ki haife shi a gidan nan ba, ko dai ya bi rariya ko ki haife shi akan titi.Sai in tsawatar da kakkausan harshe, in kuma gaya mata Allah ya fi ta. Mugun bakinta ya kare a kanta. Saboda Habiba ba ta da fus, bata iya tashin hankali ba,rashin katabus dinta yayi yawa, shi ya sa Hajara ke mata duk cin kashin da ta ga dama. Ido wannan Habiba bazata daga ta dube ta ba. A karshe ni na koma kishiyar, saboda ni nake tare wa Habiba fadan in ina nan, in bana nan kuwa tana shan ukuba a hannun Hajara. Sabida haka ne na ga gara in sauwakewa Hajara auren nan ko ma samu kwanciyar hankali ni da iyalina. Na saki Hajara saki daya, amma ta ki tafiya, ta ce gara ma in barta ta zauna a dakinta, don in ta tafi biyu-babu zan yi, don kuwa ta sha alwashin Habiba ba za ta haife cikinta cikin gidan nan ba. A karshe ta karfi na fidda Hajara daga gidana, na watso mata kayanta waje, wannan shi ne dalilin rabuwata da Hajara na farko. Na maida hankali ga kula da Habiba duk da cikin ba mai matsala bane sam kamar haihuwarta na baya, ji nakeyi kamar wannan ne karo na farko da zaa yimin haihuwa bansan dalili ba. Muka ci gaba da kula da yaranmu da zamanmu cikin rufin asiri da kwanciyar hankali. Wata rana cikin Habiba nada wata biyu ba kadan na wayi gari na tafi wajen aiki inda nake koyarwa a makarantar yammata ta (GGSS YOLA). Na dawo na tadda su Abdurrahman zugum-zugum a gida su kadai. Na kama Imamu da ke ta kuka na aza bisa cinyana ina tambayarsu ina Mamansu ta je ba ta gaya min ba, ba ta kuma tafi da Imamu ba? Suka ce ai ta tafi unguwa tun kan su dawo makaranta, shi ma Imamu shi kadai suka same shi a kofar gida. Haka na shiga kicin na shiga nema musu abin da za su ci, muka ci gaba da zaman jiran dawowar Habiba, ina cike da mamakin abinda tayi don bata taba yin haka ba koda wasa, ba inda take zuwa bata nemi izni na ba, sannan wai ta bar karamin yaro kamar Imamu a kofar gida. Har rana ta fadi ba ta dawo ba. Ban kawo komai a raina ba na sanya a raina cewa, babbar lalura ce ta fidda ita tunda ba ta taba yin hakan ba. Da na ga dare ya yi ne hankalina ya soma tashi, ga Abdurrahman da Imamu sun ishe ni da kuka. Don haka na sako su a gaba muka taho gidan Dada nan Demsawo, mu muna (Upper Luggere) a lokacin. Tafiyar da har yau ba ta dawo ba kenan, ga yayanta duk sun zama maza, ban da Modibbo babu wanda zai iya tuna ta sai a hoto. Mun dukufa addua muna rokon Allah ya bayyana ta ba dare ba rana, mahaifinta kun ganshi nan ya yi shekaru ba ya bacci, ya kuma ce a duk istikharar da yake yi a kan Habiba Allah ba ya nuna masa komai a kanta. Dada ce ta ci gaba da rainon su Imamu ta ki bai wa kowa a gidannan su ko nawa dangin. Rana daya na tsinci kaina ba abinda nake so sai dawo da Hajara gidana, na dawo da ita muka ci gaba da zama, amma Dada ta hana ta jikokinta. Watanni shidda da bacewar Habiba malamai babu adadi Malam Babba ya baza, shima baa barshi a baya ba, suka mike suna addua dare da rana a kan kowanne boyayyen alamari ne tattare da Habiba Allah ya bayyana mana, Ya kuma maido ta gida lafiya cikin iyalinta. Rannan na dawo aiki na tadda cincirindon mutane a kofar gidana. Ana hango ni aka shiga darewa ana bani hanya. Hajara ce ta ke hauka tuburan a tsakiyar unguwa, ta kekketa sutturar jikinta duk da yadda matan makwabta ke kokarin rufe mata tsiraici abu ya ci tura, da an saka za ta yage su, tana fadin duk irin sharrin da ta rinka shukawa a zamanta da Habiba. Wallahi wasu ko da wasa ban sansu ba, Habiba ba ta taba fada min ba. A karshe ta ke fadin, ita ta yi wa Habiba kurciya ta bar Yola, kuma ko za ta mutu a haukace Habiba ta tafi kenan ba za ta dawo ba. Gidana ma da ta dawo asiri ta yi min ta dawo, kuma ban isa in karya shi ba saboda a kogin Niger-Delta ta jefa. A sanda ya zo nan hawaye sun jika fuskarsa, ya sanya gefen babbar rigarsa yana sharewa. Hafsat-Suhaanah, wadda zuwa yanzu ta fahimci ko a ina suke, da kuma dalilin zuwansu, da ko wane ne wannan farin bafillacen maabocin zati da kamala. Jikinta tsuma ya hau yi, tsigogin jikinta suka shiga tashi, ta kura masa ido ba ta ko kiftawa. Wani irin feeling ta ke ji yana fizgar zuciyarta irin wanda ba ta taba ji a kan kowa ba. Ci gaba ta yi da kallonsa, wannan feeling na kara cika kowanne sako na zuciyarta. Shin ko wannan shi ne abin da kowanne Da ya ke ji a kan mahaifansa, su ma mahaifan suke ji a kan yayansu wanda Daddy ya kasa ji a kanta a baya??? Mammah ta lura da jikin Hafsat rawa yake yi, kuma ta bude idonta daga lullubin dolen da ta saka ta tana ta kallon Dr. Bashar Mai-jamaa Numan. Jawo ta jikinta ta yi, ta kwantar da kanta a cinyoyinta. Hafsat ta rufe idanunta hawayen farin ciki suka shiga kwaranyo mata. Farfesa Bashar ya ci gaba da bada labarinsa bayan ya tsane hawayen idanunsa da hannun babbar rigarsa. Cuta ta karshe Hajara ta yi min, ba ni kadai ba, har iyayen da suka tsugunna suka haifi Habiba. Tunda duk son da nake mata ban kai su ba. A lokacin na damka ta hannun iyayenta na sake ta saki uku. Ni da su, (Malam Babba da Dada) da sauran yan uwanta na ciki daya da yayan da ta haifa muka rungumi kaddara. Domin a shekarar farko in Malam ya yi istikhara yana gaya mana ya ganta lafiya cikin kwanciyar hankali a duk inda ta ke. Amma a shekaru na gaba sai ya ce ba ya ganin komai a kanta sai duhu. Allah ya rufe masa alamarinta. Yaya Tijjani babban Yayansu, kasancewar maaikacin gidan talabijin ne na jihar Yola, ya yi hobbasa iri-iri wajen neman Habiba a kafafen yada labarai har yau ba amo ba labari, babu ko wanda ya ce ya taba ganinta sai a wannan shekarar da dan wajenku, abokin Sagir ya zo daurin auren Modibbo ya ce mana yana da labarinta, ya san inda ta ke, zai dawo mana da cikakken bayani a kanta bayan watanni hudu. Ya gaya musu cewa, shekaru takwas ya kwashe bai kara aure ba, kasancewar matan bakidaya tsoro suke ba shi, kuma yana sanya ran zai ga Habiba komai daren dadewa bai taba fidda rai ba. Kuka Hafsat ta fara yi cikin mayafinta lokacin da Dr. Bashar ya dasa ayah. Mammah ma kukan ne ya ci karfinta. Da fari tausayin iyayen Habiba ta ke ji, amma yanzu Dr. Bashar yafi bata tausayi. Da ace Habiba ta yi tsawon rai zai fi kowa bukatarta a yanzu ko mata ukku gare shi. A hankali ta ke jijjiga Hafsat da ke kuka a kan cinyarta. Daddy da Abdulazeez hankalinsu na kan Mammah da Addah wadanda kukansu ya soma fitowa fili har aka soma maida hankali gare su duk da dai fuskar Hafsat na rufe cikin mayafinta. Wani iri Abdulazeez ke ji a ransa da kukan Hafsat, yadda shi kansa ba zai iya fassarawa ba. Mammah ta share hawayenta cikin murya mai sanyi ta soma ba su labari. Tun daga sanda aminiyarta Hajiya Halima matar Controller ta kawo mata Habiba da kuma bayanin da Haliman ta yi mata a kan Habiban na yadda ta same ta, zuwa yi mata fasfo da visa da tafiyarsu Jeddah, yadda ta gane Habiba na da ciki bayan tsautsayi ya sameta sun je asibitihaihuwar gaggawa ta sameta. A nan ne ta dago ido ta dubi ahalin Habiba sun zubo mata na mujiya caaa! Kamar idanunsu sa fado. Russunar da kwayar idonta ta yi kasa, muryarta cike da alhini ta ce. Im sorry, ina mai baku hakurin sanar da ku cewa, Habibah ta rasu a wurin haihuwar diyarta Hafsat-Suhaanah...!!! Ta yaye lullubin kan Hafsat ta ce, Je ki ga mahaifinki Hafsat!. Hawaye ne suke bulbula daga idanunsu bakidaya, in ka dauke yara-yaran matasa da aka haifa a bayan batan Habiban. Hatta Yaya Tijjani kuka yake yi, Fusam, Saade mai binta da Haladu, sun ko kasa kallon Hafsat din. Fuskar Dr. Bashar cikin tafukansa yana ta gunjin kuka, amma hakan bai hana shi dagowa ya mikowa Hafsat hannu ba. Wadda ita ma nata kukan ya tsananta, kanta ko kallabi babu. Wani ignition Abdulazeez ya samu zuciyarsa na yi da kallon Hafsat cikin wannan hali. Shi ba abun ya je ya mikar da ita tsaye ya rungume ta ba, komai ya kare a tsakaninsu. Ya riga ya yanke hukuncin da tun baa je koina ba ya soma shiga halin haulai akan ingancinsa. Kasa jure ganin wannan abin tausayin ya yi, ya tashi ya fice zuciyarsa na wani irin zabalbala. Ga shi ya riga ya aiwatar da komai, tun a Abuja ya sanyawa Hafsat takardar sakin cikin handbag dinta a lokacin da ya sanyata ta koma daki wai ta canzo mayafi, tsabar shikansa yana jin kunyar bata takardar sakin a hannunta. Saboda shi ma ya san ko giyar wake ya sha ba zai iya fuskantarta ido cikin ido ya ba ta wannan takardar sakin ba, duk da abu ne da ta kwana da sanin kasancewarsa, to amma akwai KARAMCI da KYAUTATAWA a cikin zamansu, wanda ba zai taba gogewa daga tarihin rayuwarsa ba, kuma ba zai gushe yana kallon Hafsatu da su ba. Da sassarfa ya isa ga motarsu ya bude ya shige ya maida kofar ya rufe, ya kwantar da kai a kan sitiyarin ya kai hannu ya dafe kirjinsa daidai saitin da ke azabtar da shi. ME NA AIKATA??? Yake fadi a fili. ***** Da rarrafe Hafsat ta rarrafa ta isa ga Dr. Bashar kafin ta karaso ya taso ya cimmata, ya sanya ta tsakiyar hannayensa ya rungume. Yanayin da Hafsat ta samu kanta a wannan lokacin ba ta taba tsintar kanta a kololuwar dadin irinsa ba. A tsaye suke tsakiyar taron nan kusan minti goma kafin Dada ta mike ta rabo ta da uban ta kamo hannunta. War hadosabajoam Hafsatu (Zo nan kawata Hafsatu). In ji tsohuwa Dada. “Sobirawo na malla launirawo? (Kawalli ce ko kishiya ce?) Daada ta sake fadi tana hawaye. Duk da Hafsat ba ta san me ta ke fadi ba ta isa gare ta, ta rungume ta don ta fahimci ita ce mahaifiya ga Habiban, wato Kaka a gare ta. Malam Hashim Babbah ya share nasa hawayen ya shiga baiwa kowa baki. Ya ce, Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Alhadulillahi har sau uku. Sannan ya cigaba da cewa Allah bai yi lamunin za mu sake ganawa da Habiba ba, amma bai barmu da kewarta mai yawa ba tunda ta ajiye Hafsu. Zuciyoyinmu yanzu sun samu nutsuwa daga taraddadin da kullum suke ciki. Baiwar Allah!Ya dubi Hajiya Maryam. Alkhairinki ya bi ki har yaya da jikokinki. Ba mu da kalaman da za mu furta godiya a gare ki. Muna rokon Ubangiji Ya fi mu godewa. Ba sai kin fadi irin rikon da ki ka yi wa yarinyar nan ba, ido ba mudu ba amma ya san kima, kowa ya dube ta ya san ta fi karfin komai na rayuwa. Allah ya zama gatanku ke da mijinki da zuriarku bakidaya. Kowa ya amsa da, Amin-amin. Hafsatu matso kusa da ni, ko ba kya aure da tsoho? Dube ni sosai, gemuna bai gama kodewa ba. Murmushi ta yi ta matsa kusa da shi. Ya kama hannayenta biyu ya rike cikin nasa. Adda Hafsatu babar Hajiya maryam ta ce da shi. Anya takwara tana auren nan da kai Malam? Dubi sardidin mijinta a gefe, gara ka rike Dadanka kada ka yi ba-wan-ba-kanin. Ido ya koma ga inda Adda Hafsatu ta nuna, kowa na son ganin wane ne mijin dalleliyar baturiya Hafsat? Wayam! Babu kowa, babu wanda ya ankara da fitarsa saboda a lokacin sun rude da koke-koke. Modibbo ya fiddo ido cikin mamaki ya tambayi Adda Hafsatu, Ba dai Barrister abokin Kawu Sagir ba? Shi kuwa. Jiya aurensu shekara guda da watanni uku. Aunty Luba ta ba da amsa. Kuma Da yake a gare su, shi ne babba dansu. Aunty Mariya ta kara bayani. Allahu akbar! Allahu Akbar!! Abinda Malam Babba da iyalinsa ke fadi kenan cikin jinjina halin GIRMA da karamci irin na Hajiya Maryam da mijinta tsohon Ambassador Hamza Atiku. Daddy ya ciro waya yana kiran Abdulazeez. Yana dagawa ya ce da shi, Ina ka tafi? Ka shigo yanzun nan. Ba tare da ya saurari amsa daga gare shi ba ya kashe wayarsa ya maida aljihu. Falon ya rikice da tofin albarka da fatan alkhairi ga Hajiya Maryam Hamza Atiku. Sai da kowa ya gaji ya bari sannan ta gyara zama, ta ce. Na yi zama da Habiba zama na amana, domin ta so yarana ta kaunace su, ta kula da su tsakani da Allah, musamman Abdulazeez na hannun damanta. A kan idonsa aka haifi Hafsat a asibiti can Jeddah. A tasowarsu kuma sai na fahimci yana shiri da uwa ba ya shiri da yarta, tun a wannan lokacin nake nazarinsu na fahimci sam ba sa ga maciji. Ni kuma na sa a raina tun a lokacin Abdulazeez ba shi da mata sai Suhaana. Mun yi musu aure ba tare da son ran kowannensu ba, su suka san yadda sukai suka shirya kansu. Kalaman da ya tsinta kenan a shigowarsa falon wadanda suka kara tsinka masa zuciya. Wata juwa-juwa ya ji tana kwasarshi tana neman fyada shi da kasa jin kowa a falon na kiran sunansa cike da kauna da tsananinbegensa a zukata da fuskokinsu, Angon Hansatu!.Shine mijin nata? Wasucikinsu suka ceAbdulazeez na Hafsu. Allah ya yi albarka!. Kowanne da abin da yake cewa na nuna kauna da kulawa a gare shi. Kusa da mahaifinsa ya lallaba ya zauna, amma sai Malam Babba ya ce ya taso ya zo kusa da shi. Da rarrafe ya yi hakan, sabida gwiwoyinsa sun kasa daukar sa. Malam ya yafito Addah da hannayensa. Cikin matsananciyar kunya ta tashi daga kusa da Dada ta tafi ta zube a gabansa. Hannun Abdulazeez ya dauka ya sanya cikin na Hafsat ya cure wuri guda. Daga Abdulazeez har Hafsat bugun zuciyarsu ya tsananta a wannan lokacin, sun kuma kasa duban junansu idanun kowannensu na kan kyawawan yatsun da Malam Hashim ya cure ya dunkule wuri guda,siraran zobunan danyen gold na hannunta guda biyu sun kawata yatsun. Yatsun kawai suke kallo sarke cikin najunansu da tunanuka masu nauyi a zukatansu. Abdulazeez na ji a ransa sallama yake yi da Hafsat, sallama irin ta SAI WATARANA...... Hafsat na tunani a zuciyarta, mene ne muhimmin aibunta da Abdulazeez ya kasa sonta??? In a da rashin asali ne, yanzu fa? Zai dubi Allah da girman UWA ya kaunace ta su ci gaba da kyakkyawar rayuwarsu ko kuwa? Ko kuwa zai rufe ido a karo na biyu ya zabi Muazatu a kan su su biyu ita da mahaifiyarsa? Yau ta tsayar da zuciyarta wuri guda ta fahimci kauna ce sak! Mai lullube da soyayya ta ke yi wa mijinta Abdulazeez Dakata ba wani abu daban ba. Ba za ta taba sonsa da abin Allah wadai ba. Fushin iyaye kuwa abin Allah wadai ne, tana rokon Allah ko ba zai so ta ba ya ci gaba da zama da ita don tsira daga fushin UWA-MAHAIFIYA, ta amince ya auro Muazatu ya karo cikin gidan za ta zauna lafiya da ita, koda kuwa bazai iya adalci a tsakanin su ba zata jure ta zauna. Ta sa a ranta muddin ta samu damar kebewa da shi kafin barinsu Jimeta za ta shawarce shi a kan wannan hangen na zuciyarta. Za ta iya jure komai ban da rasa shi a yanzu. Yana da matsayi iri-iri cikin rayuwarta. Ya cika mata dukkan burirrikanta. Ya kawo dawwamammen farin ciki da kwanciyar hankali gare ta. Za ta so shi da makamancin hakan shi ma (Allah sarki Hafsat). Kawunansu Malam Babba ya kama ya shiga kwararo musu addua. A karshe ya ce, Miji ake baiwa amanar matarshi, amma ni Hashim Babba Jimeta, ke Hafsu na baima amanar jikana Abdulazeez, ki kula min da shi, ki rike shi amana, Allah ya yi muku albarka bakidaya. Abdulazeez ji ya yi idanunsa sun cicciko da kwalla. A haka ya dago su ya kalli Hafsat wadda kanta ke sunkuye, mayafinta ya zame ta baya. Manyan kitson kanta sai kyalli suke suna daukar idonsa. Da a ce bai yi azarbabin kuskuren sanya takardar nan a jakarta ba ya bari sai za su koma Kano ya bata hannu da hannu kamar yadda zuciyarsa ta shawarce shi da farko, da yayyagawa zai yi yanzu ba wanda ya ji ba wanda ya gani, ya yi fatali da wasu alkawurruka da ya san ya daukarwa Muazatu tunda ita ba Allah ba ce. In ya so ya yi kaffara ya ci gaba da zama da Hafsat har karshen rayuwarsa. An ce ana barin halas ko don kunya! Ya tabbata zai iya mantawa da Muazatu cikin rayuwarsa, amma ba zai taba iya mantawa da Hafsat ba. Alamarinsa da ita ya fi gaban a kira shi soyayya irin tashi da Muazatu. Wani alamari ne daban beyondhis expectations. Wasu igiyoyi ties sun bi sun daddaure zuciyarsa tamau sun hanashi sukuni da jin dadin rayuwar ko ta yaya, daga jiya zuwa yau da bai kwana wuri guda da Hafsat ba. Ya tabbata za su ci gaba da bibiyarsa suna kassara shi har karshen rayuwarsa in bai yi gaggawa ya gyara kuskurensa ba. Kamar an ce da Hafsat dago. A hankali ta cira idonta suka sauka cikin na Abdulazeez. Sababbin alamura masu ban mamaki ta gani a cikinsu wadanda bata taba gani ba. Ji ta yi ba za ta iya jure kallon tsakiyar idanunsa ba domin sosai ta fahimci yana cikin wani hali da ta kasa ganewa. Sunkuyar da kanta ta yi ta zame hannunta daga cikin nasa ta koma jikin Dada ta zauna. A kusa da Malam ya ci gaba da zama ya kasa tashi. Don ya san muddin ya mike kafafunsa ba za su iya daukar nauyin gangar jikinsa ba. Ya tafka gundumemen kuskure wanda bai san ya ya zai yi ya gyara shi ba. Hotunansu da Habiba a Jeddah Mammah ta fiddo kala-kala a ke ta gani. Duk cikin bakar abaya ta ke irin ta matan Saudiyya amma fuskarta a waje ta ke ta dage himar din sama dauke da murmushi mai keta zuciya da hakorin makkah na gwal a bakinta, yawanci duk tare ta ke da su Ismael a wuraren wasan yarababu Abdulazeez yana Nigeria a lokacin. Adduoi na musamman aka yi aka rufe taron, sannan jamaar gidan suka shiga fiddo da garar abinci kala-kala wanda aka tanada musamman dominsu. Rago guda aka kyafe aka gashe musu ko daddatsa shi baa yi ba. Abinciccikan na fulanin Jimeta ne irin su tuwon Alabo (nyiri gurka)da miyar kubewa, tuwon masara da miyar yakuwa da gyada wato (hako lauto), tuwon dawa da miyar zogale (hako kabije) tuwon shinkafa da miyar karkashi (hako gubudo). A fannin abin sha kunu ne guda uku; ga kunun shinkafa (garibasise), kunun gyada (gari biriji), kunun tsamiya (garijabberi) sannan ga soyayyar rama (saande). Kowa yaci abincin nan da matukar marmari yayi hanian hade da gasashshen naman rago. Har dare suna gidan sai magriba maza suka fita sallah, suma matan suka yi a cikin gida. Bayan sallar ishai suka yi sallama da kowa za su wuce masauki. Mammah ta dubi Hafsat wadda ita ma ta mike tana son ta bi su saboda rashin sabo, ta ce ta zauna da Dada, gobe kafin su wuce Kano za su biyo su yi sallama, kuma ta sanya wayarta a caji za ta kira ta anjima. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Ta zura hannu cikin jakartatana lalubo wayar, sai ta ji farar takardar cikin ambulan. Zaro ta ta yi ta juya ta a hannunta ganin an rubuta sunanta HAFSAT a jikin ambulan din. Sai dai abu daya ya ja hankalinta, handwriting din Abdulazeez ne wanda ya riga ya zauna a memory din ta sabida yawan duba takardunsa data ke yi in ya bari a falo. Ta maida ita inda ta dauko ta don ta ga bai kamata ta bude agaban Mammah ba batasan ko menene a ciki ba. Mammah ta ce. Wasikar mene ne wannan kamar rubutun mijinki? Cikin jin kunya irin nata ta sunkuyar da kai, ta ce, Ina jin shi ya saka. Mammahbata ce komai ba ta yi musu sallama ta bi bayan su Adda Hafsatu, Suhaanah ta koma dakin Dada rike da jakarta. Har karfe goma sha daya na dare Hafsat da kakarta Dada ba su kwanta ba. Hira suke yi tana ba ta labarin rayuwar mahaifiyarta. Da duk abin da ya kamata ta sani na zuriarsu. Ita kuma Hafsat na ba ta nata labarin rayuwar a gidan tsohon Ambasada Hamza Atiku har zuwa aurenta. Dada ta ce, A duniya da ma akwai sauran mutane irin wadannan? Alherinsu ya bi su har yaya da jikoki. A cikin labaran da ta ke baiwa Dada ba ta taba kuskuren cewa Daddy bai karbe ta a baya ba, ta riga ta shafe wannan daga tarihin rayuwarta, ko Daddy bai yi repenting kuskurensa ba ba za ta gushe tana mai yi masa uzuri ba da kallonsa matsayin uban da ya haife ta. Suna shirin kwanciya tana kakkabe gadon bonon Dada da gefen zaninta don ta kwanta, Dada ta shimfida sallaya za ta dasa sallar daren da ta ke cinye rabin dare tana yi sannan ta kwanta. Ta bawa Dada baya tana ta kakkabe gadon, ta ji muryar Dada na zolayarta. Tun ganina da shi na farko na ji ya kwanta min a zuciya kamar autana Nuru. Da Hajiya Mairamu ta sani ta barki kin bi mijinki kun yi kwanan sallama, tunda za ki kwana biyu a nan a kai ki ki ga sauran dangi da ba ki gani ba, kuma Babanki ya ce za ku je Numan ya kai ki wajen nashi yan uwan. Murmushi ta yi ba tare da ta juyo ba, a ranta ta ce, Maaurata na hakika su suka damu da juna har in za su rabu na wani dan lokaci su damu da su yi sallama da juna ban da mu Dada! Mu namu auren suna ne kawai. Ta shiga tunanin ita yaushe rabon ma ta kwana daki daya da Abdulazeez Dakata? Tun wani zamani can da suke cikin zama na aminci kafin ya rikide mata ya canza kamar wahainiya, har gobe in za a kashe ta ba ta san ina Abdulazeez ya sa gaba a aurenta ba. Idan ta yi kokarin fassarawa sai ya rikide ya canja wanda ya nuna shi kansa ba shi da direction. Tunowa ta yi da takardar dazu da ta ciro a jakarta har Mammah ta gani, ta yi mamakin yaushe ya sa takardar a jakarta ba ta sani ba? Ta kuma cika da dokin son ganin me takardar ta kunsa? Don haka da ta gama gyaran gadon, kayan barci ta sanya ta jona wayarta a caji, sannan ta dauko takardar ta bi lafiyar gadon audugar kakarta, ta rufe rabin jikinta da bargon Dadan ta bude takardar ta soma karantawa. Ga abin da Abdulazeez Dakata ya rubuta wa matarsa Hafsat-Suhaana. ‘A zaman da muka yi na tsawon watanni goma sha biyar, in na ce akwai wata rana da ki ka bata min ko kika yi min abin da raina ba ya so ba bisa kuskure ba, na zalunce ki. Ta nawa bangaren ne akwai babban gibi da ya sa ni kasa ci gaba da zama da ke Hafsah, amma ba don ba ki cancanci a so ki ba, ko a ci gaba da zaman aure da ke ba. You are a darling (ke abar so ce) ga duk wanda Allah ya yi wa alfarmar samunki a matsayin mahadin rayuwa. Rauni na guda daya ne; INA SON MUAZATU! Na yi duk iya tunanina don nema wa aurenmu mafita na rasa Hafsat don shinge ne (barrier) a gare ni ga samun Muazatu, amma ba don ina kin ki ba. A bisa hakan, da wasu dalilai da dama na yanke igiyar aurenmu guda daya kamar yadda muka yi YARJEJENIYA. Allah ya ba mu mafita ta alkhairi ni da ke bakidaya. Sa-hannu ESQ Abdulazeez Dakata. A hankali Hafsat ta lumshe idanunta, zuciyarta ta yi wani irin bugu sau uku; fat-fat-fat, a jere a lokaci daya. Ta shaki iska don ta fesar amma iskar ta makale ta ki fitowa daga huhunta. Kokawa ta shiga yi da numfashinta daga huhu zuwa makogaro amma iskar ta ki fita wanda hakan ya maida ita unconscious na lokaci mai tsawo. Sai numfarfashi ta ke ta baka kamar mai ciwon asthma da ta samu attack. Dada ta yi sallama kenan daga sallar da ta idar ta ji numfarfashin Hafsa kamar na fitar rai. Da sauri ta yaye mayafinta ta wurgar ta yo kanta. Bakinta ta sanya cikin bakinta ta shiga ba ta taimakon farko irin wanda ake badawa mouth-to-mouth idan numfashi ya yi gardama. Sun dauki mintuna biyar a haka kafin ta ji numfashin Hafsan na daidaita. Dago ta ta yi ta kwantar a kan kirjinta ta rungume ta. Ko da Hafsat ta samu kanta runtse idanunta ta yi hawaye suka soma sauka wani na bin wani. A ganinta bai kamata sakin ya fitar da ita hayyacinta har haka ba tunda akalla ta san da wanzuwarsa. Lokacin karbarsa ne ba ta sani ba. Ya zo mata ne awkwardly(bagatatan) kamar fadowar aradu. Abdulazeez ya shammace ta, ya kuma tafi da dukkan farin cikin da ta ke ciki a yau wanda shi ne silarsa. Bai kamata ta ce ya karya zuciyarta ba, amma ya karya din. Rokon Allah ta ke ya sa mafarki ta ke yi, ire-iren mafarkanta na ranakun KWANGILA sun cika Abdulazeez ya sake ta. Ta farka ta ganshi yana shirin (office) a gefenta ko yana kumbing kanshi yana feso mata ruwan jikakkiyar sumar sa a fuska, amma ta yi duk wani kokari da za ta iya don ta farka daga mafarkin yau, wasu hujjoji masu yawa sun tabbatar mata na yaureality ne. Hujja ta farko jinta jikin dattijuwa Dadanta, tana shafa kwantaccen gashin kanta tana tambayarta, shin tana da ciwon asthma? Da hausarta da ba ta fita sosai, amma kwarai ta ke gane duk abin da ta ke fada. Ba ni da asthmaDada, amma ina da nimoniya (pneumonia). Ta amsa cikin dusashshiyyar murya. Amma abin da ki ka yi dazu, ya fi kama da na mai ciwon asthma. Hannu ta kai tana share hawayen da ke yin ambaliya suna bulbulowa daga idanunta. In ma ba ni da Asthma Abdulazeez ya saka mini. Abinda ta fadi kenan cikin zuciyarta. Baccin da ba su yi ba ke nan, sai da aka yi kiran assalatu a kunnuwansu. Hafsat ta ga kuka da ciwon zuciya ba za su kare ta da komai ba tunda dai (he finally made his decision) ba ya bukatarta cikin rayuwarsa, bai boye ba ya gaya mata, ya kamata ta bude zuciyarta ta rungumi kaddararta da hannu bibbiyu...Ta karbi rayuwar a yadda tazo mata. Ko wani bai fada mata ba ta fahimci zuciyarta ta dade da kamuwa da so da kaunar Abdulazeez... to idan so cuta ne ya kamata hakuri ya zamo maganin cutar nan tunda an ce babu cutar da ba ta da magani a duniya. Da wannan tunanin Hafsat ta kwarara zuciyarta, ta karbi butar da Dada ta cika mata da ruwa ta zaga ta kuma dauro alwala. Kafin ta yi sallah sai da ta tabbatar ta yi wa takardar sakinta kyakkyawan boyo, ta yi alkawarin kame bakinta ba dai wani ya ji wannan maganar daga bakinta ba, shi da ya aikata ya yi musu bayani in sun nemi baasin rashin dawowarta. Ta zo Jimeta kenan! Ita da Abuja sai da ziyara, ziyarar ma daga shekara sai shekara. Ta dauki rayuwar da ta yi da Abdulazeez Dakata ta sanya cikin wani kundi (littafi) mai dadin karantawa. A yau ta kawo karshen karatun wannan KUNDI wato littafi ta rufe shi ta adana cikin tsohon akwatin karfe ta tura karkashin gado tare da duk wani alamari da ya shafe shi. Tana tausayin kanta da sabon sunan da alumma za ta laka mata na bazawara(before the age of 20), amma ta fi tausaya wa Mammah.Wadda ta dauki duk wani buri ta dora a kan aurenta da danta. Dan da a wurinta ba nata ba ne, ita ce yarta. Idan kalaman Abdulazeez sun so su yi mata ciwo sai ta yi maza ta kawo uzuri... iyakar gaskiyarsa ya fada... ya fadi zahirin abin da ke zuciyarsa ne. Yana daga cikin halayensa da ta ke so; fadar gaskiya komai dacinta... Bata da abubuwan da Muazatu ke da su, shi ya sa ya kasa ba ta gurbin matar aure!!! Sallah ta ke, amma kuka ta ke yi, hawayenta na bilbila a cikin sujjadarta. Rokon Allah ta ke ya ba ta juriya ta karbi sabuwar rayuwar nan da ta zo mata!!! ****** Da dai a ce ba daki daya ya kwana da kakansa Baffa Atiku ba da Allah kadai ya san irin halin da zai kasance. To Baffan kamar ya gane yana cikin wani hali, ya kasa ya tsare ya hana shi tunanin komai. Idan Allah ya yi maka alfarmar rayuwa da kakanninka, to ka gode masa duk girmanka. Suna da wani feeling a kan jikokinsu da son farin cikinsu wani lokacin fiye da iyayen da suka haife su. Bai titsiye shi a kan sai ya gaya masa damuwarsa ba, amma ya lura ana ta kiransa a waya ba ya dauka, karshe ma da aka ci gaba da kiran wayar ya kashe ta bakidaya ya sanya ta a caji. Baffa bai bar kunnuwansa sun huta ba sai da bacci ya soma fizgarsa. Wani azababben barci da babu komai sai mafarkin Hafsat-Suhaanah, da halin da ta ke ciki a daidai wannan lokacin domin ya tabbata zuwa yanzu kyakkyawan sakonsa ya isa gare ta. Kowa ya kalle shi a washegari sai ya tambaye shi ko ba shi da lafiya ne? Musamman Daddy wanda ya fi kowa shiga damuwar halin da ya ga Abdulazeez din a ciki. Ya zabge ya fyade a dare daya kamarwanda ya yi wata yana jinya, ya ce in ya san bashi da lafiya ba zai iya tuki ba su je Airport su hau jirgi ragowar su taho a mota, ya ce zai iya, kuma lafiyarshi kalau bacci ne bai samu ba. Wani irin kallo Daddy ke binsa da shi na rashin yarda. Demsawo suka nufo suka yi sallama da kowa na gidan, Mammah ta ce da Hafsat tunda hutu bai kare ba ta yi zamanta sai hutu ya kare Abdulazeez ya zo ya taho da ita. A karshe ta ce, ta je yana dakin Malam su yi sallama. Ta yi sallama da Dada da matan su Yaya Tijjani, da sauran kannenHabiba da basu koma gidajensu ba tun jiya, an hada musu tsarabar Jimeta rankatakaf! Yara suka yi ta kwasa suna kaiwa mota. Mammah ta fita ta shiga mota suna jiran Abdulazeez. Kusa da dakin Malam dakin Nuru ne autan Dada, yana makarantar da yake koyarwa a lokacin da yake ranar aiki ce jumaa da safe. Hafsat ta tafi don cika umarnin Mammah, amma sai ta ratse ta shige dakin Nuru ta rufe har da saka sakata. Ba ta son ganinsa, ba ta son wata alaka ko ta gaisuwa ce ta sake shiga tsakaninsu. Me ya saura a tsakaninsu? Babu for now! Sai yan uwantakar musulunci da zumuncin haihuwarsa da Maryam Dakata ta yi ya riga ya hada. Da ta san haka zafin saki yake a zuciyar diya mace da ba ta yarda da wannan yarjejeniyar ba. Da ta san haka zafin so yake, da ba ta yarda ko kusa Abdulazeez ya shiga rayuwarta ba. A sanda suke tare, the feeling is so sweet a yanzu da rabuwa ta zo, itspainful, very painful. Zuciya ta yi duhu, babu komai cikinta sai kunci mai azabtar da ruhi. Hawaye ke zuba daga idanunta suna sauka a kan tafukan hannayenta. Abdulazeez Dakata zaune a dakin Malam Babba, Mammah ta ce da shi, ga Hafsat nan zuwa. Ji ya yi kamar ta dauke masa wani nannauyan dutse da ya danne zuciyarsa. Kokari zai yi ya karbe takardar daga hannunta tun wani bai ji ba bai gani ba, ya yi repenting. Ya san Hafsat na da sanyin zuciya, sannan tana girmamashi, tana yawan yi masa uzuri, kalamai kadan za su wanke wannan gundumemen laifin nasa (kamar yadda yake tsammani). Daga shekaranjiya zuwa yau ya nutsu ya tantance aya da tsakuwa, ya yarda rayuwarsa ba za ta taba komawa daidai ba, ba tare da dawowar Hafsat cikinta ba. He can do without Muazatu, but he cannot do without Hafsat, wannan wani abu ne da ya yarda da shi daga jiya zuwa yau kadai ganin yadda rayuwar ta birkice shi (upside-down) ta maida shi wani birkitacce susutacce. Rokon Allah yake ya sa Hafsat ba ta yi zancen wasikar nan da Mammah ba. Kai ba ta yi ba... babu wani canji a tare da Mamman har ta shiga mota. Don haka ya ci gaba da taraddadin jiran fitowar Hafsat ya maida hannun agogo baya. Amma har ya kwashe mintuna talatin a zaune babu Hafsat balle kamshin sanyayyan turarenta. Hankalinsa ya soma tashi ne lokacin da Daddy da Mammah suka shiga kiran wayoyinsa da ke aljihun rigarsa, da fari kamar ba zai amsa ba amma suka ci gaba da kiran. Dole ya amsawa Daddy. Har yanzu sallamar ba ta kare ba ne Yayansu? Akwai tafiya fa a gabanmu rana tana yi. Ga ni nan Daddy. Kawai ya ce a sanyaye. Ya tabbata Hafsat ba za ta fito ba kenan. Da za ta fito da tsawon mintuna talatin din da ya share a zaune sun isa su fito da ita, daga dai cikin gida zuwa dakin Mallam. Wannan ma shaida ce mai tabbatar masa da cewa Hafsat ta karbi sakonsa;(And she acts accordingly). Cikin sagewar gwiwa da debe tsammani ya fito daga gidan Malam Hashim Babbah Jimeta, ya ja motar da iyayensa da kakanninsa ke ciki, suka soma fita daga shiyyar Demsawo. Tafiya sannu-sannu har suka hau titi dodar suka bar garin Jimeta. Ji yake tamkar ya bar wani bari na gangar jikinsa cikin Jimeta, barin da bai san yadda zai yi ya dawo da shi jikinsa ba. Anya bai tafka kuskure ba? Ta yaya ya tabbatar rabuwa da Hafsat shi ne babban tsanin da zai samo masa Muazatu daga wajen mahaifiyarsa? Anya hakan ba shi ne kuskure ba maimakon ya zamo MAFITA a gare shi? Da wadannan tunanukan masu nauyi Abdulazeez yake tuki yana wuce dazuzzuka da bishiyoyi, garuruwa da kauyuka yana mai jin tamkar karshen rayuwarsa ya zo! Da wacce kalma zai kare kansa ranar da Mammah ta karbi sakin da ya yi wa Hafsat don ya samu Muazatu??? ******* Sai da ta ji tashin motocinsu sannan ta koma cikin gida. Dada ta tambaye ta sun tafi? Ta ce sun kama hanya. Kwananta uku ba inda ba a kai ta ba gidajen yan uwa da dangi. Ranar da ta cika sati gidan Yayanta Modibbo ta wuni a Use-Demsawo tare da matarshi Kaltum. Washegari kuma gidan mahaifinta wanda ke cikin gidajen malamai na jamiar Yola. Matarshi Aunty Kubra maaikaciyar gwamnati ce a hukumar haraji ta jiha, mace ce da ta san ciwon kanta, ta ke kuma rungume da su Imamu da zuciya daya. Cikin sati daya da Hafsat ta yi a gidan mahaifinta Dr. Bashar tare da shi da yan uwanta na ciki daya Imamu da Abdurrahman tunda Modibbo da suke kira Hamma Modibbo yana nasa gidan, Modibbomaaikacin (Immigration Office) ne. Sabo mai tsanani ya shiga tsakaninsu musamman Imamu, wanda ke karatunsa a (American University Yola) a kan tsimi da tanadi. Shikuma Abdurrahman yana aiki da gidan wayar Etisalat. Rayuwar gidan abar koyi ce domin kowanne na da abun yi, sun fahimci juna kuma ilmi ya ratsa kowa. Tsakanin Imamu da Abdurrahman da Dr. Bashar din kansa har rige-rige ake wajen farantawa Hafsat da suke kira (GAAJI) wato auta da harshen fulatanci. Wannan ya taimaka kwarai wajen mantar da ita Abdulazeez da duniyarsa. A karshen satin Daddy ya shirya musu tafiya zuwa NUMAN ainahin asalinsa don su kai Hafsat ta ga sauran yan uwansa tunda iyaye babu sun kare. A motar Dacta Bashar kirar Sienna suka yi tafiyar har Hamma Modibbo da maidakinsa Kaltum. Ita da Kaltum na kujerar can baya, Abdurrahman, Modibbo da Imamu na kujerar gabansu, Daddy ke tukin motar, Aunty Kubra na gefensa. Tafiya ce mai dadi da sanya nishadi a gare su, suna tafe suna hira har suka isa garin Numan. Yan uwan haihuwar Dacta Bashar su uku ne ke raye, Baffa Saadu, Malam Zakari da Surajo duk tare suke da iyalinsu a can Numan kowanne na da kwakkwarar sanaarsa. Su Malam Zakari sun ga yar dan uwansu sun kuma ji duk abin da ya faru da Habiba. Addua kan Habiba ta sha ta kamar yadda Hajiya Maryam ta sha tofin albarka da fatan alkhairi. Bayan dawowarsu daga Numan da kwana daya Dada ta aiko Nuru ya zo ya dawo mata da Hafsat ta yi shirin komawa gidan mijinta, Mammah ta yi mata waya cewa hutun su Hafsat ya kare za su koma makaranta ranar litinin kwana uku masu zuwa. Tun barin su Mammah Jimeta Hafsat ba ta kara kunna wayarta ba. A ganinta wayar ba ta da sauran amfani a gare ta. Ba ta da sauran alaka da wanda ya mallaka mata wayar amfanin me zata yi mata? Mammah kuwa da Baba Azumi in ta samu nutsuwa za ta dinga kiransu ko ta wayar Dada ne tana gaishe su. Da ta dawo Demsawo ta tadda sakon Mammah daga bakin Dada, rasa me za ta ce ta yi. Ta fito fili ta ce da Dada ba ita ba Abuja, mijinta ya sake ta ko me? Kwata-kwata ba ta son tuna cewa an sake ta kalmar tana yi mata maqaqi a zuciya. Wa za ta gaya wa tsakanin Malam, Mammah da Daada ba tare da hankalinsa ya tashi ba? Ko dai shiru za ta yi ta koma Abujan ta ci gaba da zama gidan Mammah ta cigaba da zuwa makaranta tunda ba za ta iya barin karatunta ba? To amma Yayan Haleem ya sake ki, kuma ki koma ki ci gaba da zama gidan mahaifinsa? Alhalin ba rasa muhallin zama ki ka yi ba? Wata zuciyar ta ce. Haba Hafsatu? Kada ki zam-makaho warke ka karya sandarka! Har abada ba ki da gidan da ya fi na su Abdulazeez din in har duniya da halacci da amana. Koma gaban Mammah ki ci gaba da karatunki in har za ta barki, ki kuma cika alkawarinki na taimaka wa Abdulazeez ya cimma burinsa...... Wani hanin ga Allah baiwa ne!. Da wannan shawarar Hafsat ta soma shiri kamar yadda Dada ke ta yi mata itama don komawa Abuja. Sai dai irin hakukuwa da sauyoyin da Dada ke damawa kala-kala tana ba ta, ta ce ta shanye a kan idanunta kasa gane kansu ta yi. Da ta tambaye ta ko magungunan me ta ke bata? Cewa ta yi na gyaran aure ne. Bakinta ta ja ta yi shiru ta ci gaba da shirya yan kayan da ta zo da su wadanda duk sun ji jiki saboda maimaita su da ta yi ta yi tana wankewa kasancewar ba ta debo kaya da yawa ba. Ana i-gobe Hafsat za ta koma Abuja, Mammah ta kira ta a wayar Dada, ko gaisawa ba su yi ba ta soma yi mata fadan rashin amfani da wayarta da ta ke yi. Hakuri ta yi ta ba ta, ta gaya mata sun yi tafiya zuwa Numan kuma tun zuwanta ba ta zama. Ziyarce-ziyarcen dangi ake raka ta nesa da kusa. Mammah ta karbi uzurinta, ta kuma gaya mata goben jirgi za ta hawo ta dawo. Abdulazeez ba ya kasar, ya je America graduation convocation na Ismael daga jamiar Harvard, daga can za su wuce na Usman a Brussels sai nan da sati biyu za su dawo shi da Ismael da Usman din. Don haka nan Asokoro za ta taho in ya dawo sai su koma gidan nasu. Wata ajiyar zuciya Hafsat ta yi cikin sanyin murya irin nata ta ce, Toh Mommah, sai Allah ya kawo ni lafiya. A gaida Baba Azumi da Daddy. Za su ji, ki gaida Dada da Malam da duk mutanen gidan. Da wannan suka yi sallama. Washegari Dr. Bashar da kansa da Imamu suka kai Hafsat da kayanta filin jirgin saman Yola, jirgin Azman ta bi zuwa Abuja. Babanta ne ya biya kudin tikitin duk da Mammah ta aiko mata da kudi ta account dinta, ita a wajenta har gobe nauyin Hafsat yana wuyansu ba abin da ya canza. *SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* ***** Ta sauka a Abuja da misalin karfe shidda na yamma, a reception suka hadu da Salisu direban gidansu ya zo daukanta. Ya karbi kayanta ya sanya a boot ya bude mata murfin motar ta shiga ta zauna ya rufe suka nufo Asokoro. Suna shigowa tangamemen getdin gidan ta hango Mammah a kofar shiga babban falo tana jiran isowar su. Ta kara kyau, kullum kamar ana kara mata kuruciya, za ka rantse ba ta haifi Haleem ba balle uwa-uba Abdulazeez. Wasu zafafan hawaye na tausayin Hajiya Maryam da ita kanta suka cicciko idanunta. Ta san tana son aurenta da dukkan zuciya da ruhinta, amma ta yi amanna Mammah ta fi ta son wannan auren da dorewarsa. To ya za su yi? Tunda wanda ke da iko da igiyoyin auren ya tsittsinka su? Ba ya sonta! Ba ya bukatar hada rayuwa da ita, dole ita da Mammah su dau dangana su hakurkurtar da zukantansu. Allah ya sa hakan ya zama alkhairi ga rayuwar kowannensu. Ta sa gefen mayafinta a fakaice ta share hawayenta. Mammah na tsaye aka fito da kayanta na boot ta kasa jiranta ta karaso inda ta ke ta tako ta iso jikin motar ta bude mata kofa. Salisu ya roke ta ta bar masa kayan zai shiga da su. Ta kama hannun Hafsat abinda ta lura da shi jikin Hafsat a matukar sanyaye yake tamkar wadda aka yiwa duka. Idanunta sun kode da alamun ta jima bata sanya musu kwalli ba. Kai in ba ta yi kuskure ba, za ta iya cewa Hafsat ta rame. Ta dai bar komai a cikinta Hafsat din ta samu ta huta. Dakinta na yammatanci aka shigar da komai nata, a can ta yi wanka ta yi sallah kuma har can Baba Azumi ta kai mata abincinta ba su ce ta zo ta ci a dining ba kamar yadda yake a aladar gidan duk don ta samu nutsuwa. Ta nemi wata doguwar riga mara nauyi cikin kayanta ta sanya, ta zauna da zummar ta ci abincin, amma duk yadda ta kai da kokarin ganin ta ci din abin ya faskara. Zuciyarta ta yi nisa wajen tunanin yadda za ta nunawa Mammah takardar sakinta! Haka ta saka abincin a gabanta tana kallo kwata-kwata hankalinta ba ya jikinta. Sau biyu Mammah na shigowa jin shirun nata ya yi yawa tana ganinta cikin wannan halin. Azumi ma shigowarta biyu, har suka fita ba ta san sun shigo ba balle fitarsu. Mammah dakinta ta koma ta yi shiru, daga bisani ta yi kiran Baba Azumi, ta shigo ta zauna gefen uwargijiyarta a kan center carpet, Mammah na gefen gadonta. Ba ki fahimci Adda na cikin damuwa ba? Azumi ta gyara zama ta ce, Ni kuwa na fahimci hakan. Har magana na yi mata sau uku ba ta san ina yi ba. To a ganinki me ke damunta? Ko a da Hafsat da ta san ba ta da kowa sai mu ba ta sanya kanta cikin damuwa ba sai yanzu? Ba kya tunanin tafiyar mijin ce? Inji Baba Azumi. Ba ta magana da shi a waya. Ya gaya min rabon da ya yi magana da ita tun a Jimeta. Ta kashe wayarta kwata-kwata tsayin kwanakin nan data yi acan. Da na yi mata fadan kashe wayar cewa ta yi ba ta samun zama, kuma ta je kauye. Shin a wannan zamanin duk inda ka je za ka kasa yin muamala da waya? Balle ka kasa magana da mijin aurenka tsayin sati biyu? Duk sai suka yi shiru. Daga bisani Azumi ta ce Ina tunanin matsala ce suka samu a tsakaninsu. Mammah ta runtse ido kadan ba ta ce komai ba, amma ta yarda da abin da ta ce din. Ki zuba musu ido Maman Haleem, kada ki tambaya, kada ki bi baasi. Tsakanin mace da miji sai Allah. Sanda za su shirya kansu ba za ki sani ba. Zuciyar Hajiya Maryam babu dadi, ta ce, Haka ne. Amma can a karkashin zuciyarta tana jin ba dadi, sanin cewa auren Abdulazeez da Suhaana ba normal auren so ba ne. Sai dai ya taho da nasara fiye da yadda ta tsammatar masa. Tana tsoron duk wata matsala da ka iya tasowa a cikinsa. “Ya Rabbi Sallim! Ta furta a fili bayan fitar Azumi daga dakinta. ****** Kwanan Hafsat biyu kenan da dawowa daga Jimeta. Mammah na lure da ita, ba abin da ya canza cikin yanayin da ta dawo da shi, sannan ko sau daya ba ta ga ta jona wayarta a caji ba balle ta kunna. Washegarin ranar suka koma makaranta. Hafsat ta sani, amma ko alama ba ta yi wa Mammah zancen ba. Ji ta yi karatun kansa ya fita a ranta, duk wani buri da ta ci masa ya zagwanye. Ashe karatu ba shi ne farin cikin rayuwa ba? Ashe akwai abin da yamace ta fi bukata a rayuwarta fiye da karatun boko? Ashe ba abin da ya fi muni ga rayuwar diya mace fiye da sakin da ada ta ke ganin ba komai ba ne? Ashe tsakanin zuciyarta da Abdulazeez soyayyah ce kuma kauna ce mai tsananin da zuciyarta ta kasa karbar rabuwa da shi da sauki??? Duka a bandaki (toilet) ta ke wannan tunanin, ta shiga da zummar wanka, amma sai ta bige da zama a kan (soak-away) ta shiga shesshekar kuka, kukan da a baya ba ta yi ba tun ganin takardar sakinta. Koyaushe cikin mutane ta ke a Jimeta ko gaban kakanninta, suna yi mata hirarrakin uwarta da ke debe mata kaso 80% na tunanin Abdulazeez da karewar KWANGILARsu. Yanzu ne komai ya rufto mata take jin kanta cikin wata irin kewa mara misaltuwa. Tamkar ta rasa komai na jin dadin duniya, tamkar ta rasa komai data taba mallaka a rayuwarta.Zamanta cikin gidansu da kasancewarta kusa da wadda ta fi kowa kusanci da shi a duniya ya maido komai sabo kuma danye a zuciyarta, ya maido mata komai baya na rayuwarda ta yi da shi ta shekara da watanni.Yadda shekarar ta kasance dalla-dalla a kan tafin hannunta....... Daga rayuwar DUHU zuwa rayuwa mai HASKE kafin ta karkare ta koma DUHU dudum a halin yanzu kenan da wannan rayuwar taduhu da haske ta kare bakidaya. Sai dai duk ta inda zuciyarta ta karkata don baiwa Abdulazeez laifi Hafsat ta ki karba, zuciyar mai so da kaunar Abdulazeez kare shi ta ke yi. A bisa dalili da dama da hujjojinta kwarara! Muhimmi cikin hujjojinta shine;Abdulazeez bai taba yaudararta da cewa za su dore da rayuwar aurensu ba! Bai taba yaudararta da kalmar SO ba. Zuciyarta ce ta zarme zuwa ga son abinda yafi karfinta.... ta zamo out of her controlta jefa ta cikin matsananciyar soyayya da kaunar Abdulazeez din data ke da tabbacin baya son ta. Ba ta yarda da hakan ba sai yau da suka rabu, auren kwangilar ya kare! A yau ta yarda cewa ta dauki lokaci mai tsawo cikin soyayyar Abdulazeez Dakata ba tare da saninta ba. Wani kwantaccen so mai bin jiki da jijiya. Ba ta fahimci hakan ba sai a kurarren lokaci, lokacin da ya zamo haramiyarta...!!! Fuskarta ta sanya cikin tafukanta ta dinga kuka wanda ke fitowa tun daga karkashin zuciyarta. Shigowar Hajiya Maryam na uku kenan dakin tana komawa ta fita da sauri, saboda zuciyarta da ta kasa jure sauraron irin kukan da Hafsat din ke yi. Ta koma dakinta jikinta har rawa yake yi. Babu wanda zai tada hankalin Hafsat, ya jefa ta cikin wannan halin in ba mijinta Abdulazeez ba, tunda wa ta ke da shi bayan iyayenta da su in ba shi ba? Babu wanda zai bata mata rai a Jimeta! Zuciyarta na son daukar waya ta kira shi, wata zuciyar na hana ta.So ta ke ta ce da shi da ka bata min ran marainiyar Allah Addah yar amana ta, gara ni ka bata nawa ran. Ta tuna shawarar da Baba Azumi ta bata; Kada ta shiga, kada tatambaya, kada ta bi baasi. Baba Azumi ba yar aiki ce kawai agareta ba yanzu, uwa ce a gareta, kuma wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi. Bataso ta yarda da kaso mafi rinjaye na zuciyarta da ke cewa, Abdulazeez ba ya son Hafsat har yanzu....... damuwar Hafsat kenan. Shigowar Daddy dakin nata yana tambayar wasu mukullansa ya sa ta farfadowa daga zazzafan tunanin da ta fada, wanda zuwa yanzu ya fara tafarfasa zuciyarta. Dagowa ta yi a hankali ta dube shi idanunta jazir. Da sauri Dr. Hamza ya karasa shigowa dakin, Lafiya Maryama? Me ya faru? Mutuwa aka yi? Ya kama dukkan hannayenta biyu ya rike cikin nasa. Ganin yadda hankalinsa ya tashi da ganin yanayinta ya sa ta nemo wa kanta murmushi wanda bai wuce iya fatar bakinta ba. Bai kamata ta ce masa komai ba, tunda itama ba ta san me ke faruwa din ba. Ga shi Baba Azumi ta ce ta ba su lokaci, watakila da ya dawo sun koma gidansu komai zai wuce, ko harshe da hakori ai ana sabawa. Ita da ta yi auren soyayya da Prof. Hamza wane irin bacin rai ne bai jefa ta a ciki ba, kuma ta jure sun zauna a haka har aka zo gejin da bacin ran nata shi ne abu na karshe da yake guje mawa? Hafsat ce ba ta jin dadi. Ta fada a hankali yadda zai kwantar da hankalinsa. Ya ce, Ai sai ku je asibiti a duba ta, ba ki zauna kina tagumi da jan ido ba. Ya dauki mukullayensa a kan lokar gadonta, ya juya. Har ya kai bakin kofa ya kama marikin kofar sai ya juyo da murmushi a kan fuskarsa. Ko amarya zan samu ne kwanan nan aka gaya min indirectly? Duk yanayin da ta ke ciki sai da ta yi murmushi, a zuciyarta ta ce, Ina ma hakan ne! Sai dai a matsayinta na mace, kuma babba ba ta ga wani alamu na juna biyu a tare da Hafsan ba. Jin ba ta ce komai ba ya lura kuma ba ta son magana sai ya fita, zuciyarsa na gaya masa kamar ta sakaya masa wani abu, amma ko ma mene ne in ta yi wari da bakinta za ta fada mishi. Haka suka zauna a gidan su uku tsayin sati biyun, ba sa ummm ba sa umm-umm. Baba Azumi ce kadai ke yi musu hira. Ita ma idan tayi-tayi ta rasa mai tayata sai ta yi shiru. Ana i-gobe Abdulazeez da su Ismael za su dawo Hajiya Maryam ta ce wa Hafsat ta shirya ta koma gidanta, su tafi da Baba Azumi don ta taya ta su yi tiding gidan ta kwana, za ta turo Salisu ya dauke ta in Abdulazeez ya sauka a Abuja. Hajiya Maryam na ganin yadda Hafsat ta kidime ta rikice, ta gigice, a karshe ma kasa zaman wurin ta yi ganin yadda ita da Azumi suka zubo mata ido. Mikewa ta yi ta nufi daki, kafin ta isa da gudu-gudu ta karasa ta shige, kuka ya kufce mata, karshen tika-tika-tik! Me kuma za ta ce wa uwar tasu? Za ta ci gaba da boye sakin ne kuma? A dauke ta a maida ita gidanta bayan kuma auren babu shi, ya mutu? Tambayoyin da ta ke ta jero wa kanta kenan ta rasa amsar ko daya. Bayan tashinta da kulewarta Hajiya Maryam da Baba Azumi suka bi bayanta da kallo sannan suka dubi juna, an rasa mai magana a cikinsu. ****** ABDULAZEEZ DAKATA Shi kadai ya san yadda rayuwar ta kasance masa a tsayin sati biyun nan da Hafsat tayi a Jimeta. Zai iya kiransu kwana goma sha hudu mafiya tsayi da fadi a renakun rayuwarsa. Abin da ya sani kawai shi ne; ba ya iya zaman gidan, barci kadai ke kawo shi cikinsa. Da safe zai yi wanka ya tafi office babu tunanin karin kumallo, sai ya je can dinhanjin cikinsa ya hana shi sukuni yake samu ya sha coffee ya cika wa kansa aiki duk don ya hana kansa tunanin komai. Haka zai zauna babu ko tunanin abinci sai lodawa kansa aiki, sallah kadai ke tayar da shi.Ba shi zai baro office ba sai karfe shidda na yamma. Daga nan kuma kai tsaye gidansu zai wuce, a can zai yi sallar maghriba da isha tare da Daddy, su ci abinci tare har Mammah ya zauna ya ki tashi har sai Daddy ya ce da shi dare ya yi, watarana har ya tsokane shi ko zai koma Jimeta ne a yi sati biyun tare da shi? Daga Daddy har Hajiya Maryam sun fahimci yana cikin damuwa wadda cikinsu babu wanda tunaninsa bai ce da shi ta rashin maidakinsa a kusa ba ce. Don haka babu wanda ya bashi hankalinsa. Babu daren da zai zo ya wuce a tsayin kwanaki goma sha hudun nan da bai gwada kiran wayar Hafsat ba sama da sau hamsin a rana, amsar dai a kullum iri daya ce; wayar a kashe ta ke. Ya kasa amsa wayar Muazatu ko guda daya daga ranar da ya saki Hafsat! Abinda shi kansa bai san dalili ba; wadda ke can gidan su a birnin Lagos hakan ya dugunzuma nata hankalin. A ganinta yanzu lokacin farin cikinsu ne, lokacin cikar burinsu, me yake nufi da kin amsa wayarta idan shi ya kasa kiranta? Kwanansa bakwai da baro Hafsat a Jimeta ya yanke wa zuciyarsa komawa. Wannan ne kadai mafita a gare shi, ya koma ya samu Hafsat ya gyara dingimemen kuskurensa ko rayuwarshi ta koma daidai, zai lallaba ta ya karbe takardar... ya yayyagata kafin kowa ya gani, zai maida ita dakinta kafin kowa ya ji. Ya godewa Allah ya yi sakin da addini ke so zuciya bata kaishi ta baro bakidaya ba! Idan ya samu ya dawo da Hafsat sai kuma ya san ya zai yi da Muazatu. A wannan gejin yana jin zai iya karya alkadarinsa ya zauna da su su biyun. Ya fahimci abin da yake kin fahimta da gangan; Hafsat ba ta shigo rayuwarsa don ta fita ba, ba ta shigo zuciyarsa don ta yi KWANGILA ta wuce ba... Ba mata irinta ne ake aura a saki a lokacin da ake so ba. Ba mata irinta ake saki don a samo wasu ba. Ba mata irinta ke barin gidan auren su na farko zuwa wani, ba tareda kwakkwaran dalili ba. Irin Hafsat saidai wata kaddararta daban mai karfi ta raba su da gidansu na farko (mutuwa) amma ba common saki irin wannan ba. Ya yarda ya amince a cikin mata akwai virtuousones;Their prices is per above rubies! Baa amfani da su don cimma wata manufa sai don biyan bukatar rai kadai! Ya yarda ya amince zuciyarsa SOYAYYAh ta ke wa Hafsat ba irin wadda ta ke yi wa Muazatu ba... Idan abinda yake ji a kan Hafsat shi ne soyayyah zai so wani masanin ilmin zuciya ya taimaka mishi, ya fada mishi wanda yake ji a kan Muazatu kuma mene ne shi??? Ya tsaya, ya nutsu, ya kintata, ya yi estimating, sai ya samu cewa the feeling is totally different....Ba soyayyah kadai yake yi wa Hafsat-Suhaanah ba, har da wata boyayyar kauna yar usuli mai yawan kintace. Yana begen sake ganinta ko da sau daya ne, yana kewarta cikin gidansa... Har ila yau yana nadamar yin AUREN KWANGILA da ita... yana nadamar yin amfani da halitta mafi soyuwa a zuciyar mahaifiyarsa don son cimma wata manufa. Watakila Ubangiji ya canza zuciyarsa a kanta ne don Ya ganar da shi kuskurensa. Duk ilmin addinin da yake da shi bai yi amfani da shi ba, ya sa kafa ya take saninsa saboda soyayyar Muazatu data rufe masa idanu. Sanin kansa ne babu wani aure na kwangila a cikin addini, kai duk wani aure da za a kafa shi a kan wasu sharudda ko a deba masa waadi bai inganta ba a addinin musulunci. Duk wani aure da za a yi shi ba ka kusanci iyalinka ba har tsayin watanni ukku ba tare da dalili ba, shi ma ba cikakken aure ba ne! Ya zauna ya cutar da Hafsat watanni goma sha biyar bai taba sauke nauyin auratayya da Allah ya dora a wuyansa ba ba tare da hujja wadda addini ne ya tsara ta ba. Babu mamaki don Allah ya hukunta shi da soyayyar Hafsat da ta hana shi nutsuwa a lokacin da ya haramtawa kansa ita. Ta tsayar da duk wasu daily activities na rayuwar cikakken mutum a gare shi. A tsayin kwanakin nan bakidaya a dakin Hafsat yake kwana a kan gadonta. Barci gwanin iya sata kadai shi ke sace shi, shi ma duk inda assalatun fari ta ke zai bar idanunshi. Zuciyarshi ta dora daga inda ta tsaya na tunanin hanyar da zai bi ya maido Hafsat cikin rayuwarsa ba tare da kowa ya ji ya gani ba. Babu mafita ban da komawa ya cimmata a Jimeta. Bai kara fahimtar cewa ya fita daga saiti ba, sai da ESQ Ahmad Kutama ya kawo wasu manyan files ya ajiye a gabansa. Da mamaki yake dubansa kafin ya janyo kujera ya zauna a gabansa. “Check these files for me properly,please. Janyo su ya yi gabansa yana dubawa, shi ya rubuta clues na shariar da za su yi sati uku masu zuwa, amma me? Clues din ba su da alaka da wannan shariar na wadda za su yi kafin waccan ce. Lumshe idonsa ya yi ya bude a hankali, Im so sorry. Kawai ya iya cewa. Ahmad ya bi shi da kallon tsaf! Ga shi dai ya yi shigarsa tsaf cikin suit kalar grey da ratsin fari ta ciki kamar yadda ya saba,but its obvious that he is definitely upset... alamu ma sun nuna kwana biyun nan he didnt shave his face, sannan gashin kan ya cukurkude alamar ba ya samun extra kulawar da yake samu a baya duk da shi ba maabocin yawan askin bane amma kula yake da sumar sa sosai. Ya san yana da aure don har da shi aka raka shi dakin matarsa balle ya ce rikicin soyayyah ya fada. To me aure ba ya iya fadawa soyayya for the second time? Ahmad ya tambayi kansa. Bayan wannan shi dai ya san Abdulazeez bai da matsala, dan gata ne na karshe, gatan da ya sa duk ya riga su aure. Saboda Babansa ne ya gina masa gida. Su kuwa sai haya suka kama cikin Abuja. Shi nasa wata biyu kenan, na Abdallah wata hudu. To ko kuma ta gidan ce ta ke birkita shi haka? Duk zai iya yiwuwa. Ya san Abdulazeez da shegen zurfin ciki a kan abin da ya shafi matarsa. Bai taba zama yayi hirarta da wani a cikin su ba. Ko suna hirar yammatansu kafin suyi aure shi baya magana. Haka bayan sunyi aure suna zancen amaren nasu a gabansa irin sun makarar dasu ko makamancin haka ko kai baya dagawa balle ya tofa. Amma duk da haka ya samu kansa da son taimaka masa koda da shawara ne don bai taba ganinsa cikin wannan halin ba. Ga shi alamarin har yana so ya shafi aikinsa. Abdulazeez din da ba ya barinsu su yi kuskure ko kankani yau shi ake yi wa gyara mai girma haka. Gyara zamansa ya yi ya fuskance shi sosai. Me ye matsalarka Barrister? Yau karo na farko a rayuwarsa neman wanda zai budawa cikinsa yake yi, ko zai samu wata shawara wadda ta fi tasa inganci. Ya yarda ya gama lalata rayuwarsa in bai je Jimeta a gobe ba har takardarsa ta je hannun mahaifiyarsa. Ba hukuncin da zata yi masa yake tsoro ba; bazata taba yarda da dawowar Suhaanah gareshi ba! Ta sha gaya musuopportunity comes only once in life (dama tana zuwarwa dan adam sau daya ne a rayuwa) kuyi amfani da ita a sanda kuka sameta. Yau ba yana son Hafsat-Suhaanah don Mammah ba ne, sonta yake a karan-kansa da soyayya mai azabtarwa. Bai san sanda ya buda baki ya ce da Ahmad. In an yi saki, ya ake a gyara? In an yi alkawari aka kasa cikawa daga baya ya ake a yi kaffara? Gaban Ahmad sai da ya fadi, bai san sanda ya ce a tsorace, You mean ka saki Hafsat? Auren shekara daya kacal?Kai kuwa me tayi maka haka da zafi? Kamar zai kife shi da mari ya ce, Ya zan tambaye ka, kuma ka bi ni da tambaya? Ai ban san sakin wane iri ba ne. Ya fada cikin sanyin jiki. Abdulazeez ya kwantar da kansa a kan teburinsa. Murya a raunane ya ce. Thisis the deadly mistake ive ever made, na sake ta Ahmad, amma ina so in dawo da ita. Dubi yadda na zama cikin sati daya kacal da yin sakin. Da farko na yi zaton Muazatu nake so a kanta, yanzu da babu ita cikin gidan na gane Muazatun ba ta da matsayi mai yawa a tare da ni. Ka taimake ni Ahmad ba ni da idea. So yake ya ce da shi. Ai mun gaya maka, watarana za ka so yarinyar nan ko da za ka yi mata kishiya. To amma tausayin Abdulazeez din ya hana shi fadin hakan, yanzu ba lokacin raddi ba ne. Lokacin neman mafita ne. Kuskure ne ya riga ya yi shi sai a nemi hanyar gyarawa in mai gyaruwar yayi. Bai nemi baasi ba, cike da fargaba ya ce. Sakin guda nawa ne? Ba tare da ya dago ba ya ce, I think daya ne. A gurguje ma na rubuta ina tsoron ta zo ta ganni ina rubutawa. Ahmad proffession dina bai kare ni da komai ba da na kasa gane ba hanyar samo Muazatu na bi ba, hanyar kara tsanarta a zuciyar mahaifiya ta na bi. Hanyar kara nesanta kaina da ita na bi. A karshe in kare da babu ko dayansu muddin zancen sakin ya je kunnen Mammah. Ahmad ya dafe kai. Yanzu ina Hafsat din? Tana garinsu Jimeta. Just call her now (kira ta yanzu) ka ce da ita na maida ke dakinki, shi ne muhimmi kafin komai. Ko ta yarda ko bata yarda ba; ta maidu. Wayar ya janyo cikin kasala duk da ya san ba samun nata zai yi ba, amma haka ya yi ta gwada jera kiran yana katsewa. Ya dubi Ahmad cikin rauni. Ta dade da yanke communication da ni, na tabbata ta dade da ganin takardar, da kyar in bata canza layin waya ba. Ahmad dai haushin Abdulazeez kamar ya kashe shi. Wai a kan wata da yake hange a waje ya saki ta gida, ba dole hakki ya rikide masa zuwa soyayya ba? Tunda gobe weekend ne za ka iya zuwa Jimetan, make sure ka kwace takardar ka kuma gaya mata ka maida ita ta ji da kunnenta. Ita kuma wannan Muazatun ajiye zancenta a gefe sai ka dawo da zabin mahaifiyarka. Abdulazeez kana tune da hakkin mahaifiya kuwa da karfin ikon da Allah ya ba ta cikin rayuwarka? Allah (S.W.A) Ya ce a bi ta, a bi ta, a bi ta kafin ya ce a bi uba. Amma budurwa??? Kana son ganin albarka cikin rayuwarka? Ta aura maka mace har mace mai daraja irin wannan ka saki? Inda hali mu tafi tare, mu hau jirgi don mu yi sauri. Ireallywant to help. Daga office din kai tsaye gida ya wuce, ya samu Mammah da Daddy a falo suna cin abinci. Sun masa tayi, amma yau sam ya kasa cin abinci. Jiransu ya yi har suka kammala, Daddy ya dawo tsakiyar falo ya zauna a kujerun falon na alfarma. Budar bakin Daddy sai cewa ya yi. Za ka wakilce ni a graduation din Ismael da Usman a America da Brussels jibi, zaka fara halartar na Ismael first,sai ku wuce Brussels na Usman tare dashi, ni ayyuka sun min yawa, passport dinka daka bani na sabunta maka watannin baya ya jima a wajena don haka tuni na gama maka shirin komai, thumb print kawai zakaje kayi da safe namaka bookingma, sai ka zaba tsakanin jirgin safe ko na dare. Na gayawa shugabanku dazu ya baka leave na sati daya na tura ka wakilci kuma ya amince, zakayi sati daya sai ku dawo tare da su duka. In an kwana biyu kuma ni sai in je wa Haleem visit a Sweden. Dukkansu babu wanda bai lura da yanayin canzawar fuskarshi ba. Wata irin canzawa kamar an aiko masa da sakon mutuwa, fuskar har wani brown ta koma. Da kyar ya iya hadiyar miyau, cikin damuwa ya ce. Daddy Jimeta za ni gobe. Mammah ta ceJimeta kuma? Cikin mamaki sosai, ta cigaba da cewa. Dan zaman da za ta yi cikin yan uwanta na sati biyu kacal za ka haramta mata karashe shi? Ina ce next week za ta dawo? To ban yarda ba, wannan rashin hakuri da rashin kawaici har ina?. Daddy ma yana bayan Mammah, ya ce, Ba za ka je Jimeta ba sai ka dawo daga graduation din nan sai kaje ku taho tare. Ya amsa a ladabce,kansa na kasa, kasancewar yasa a ransa bazai kara jayayya da iyayensa ba har karshen rayuwarsa! Amma kallo daya za ka yi masa ka fahimci bai so wannan tafiya ba. Tamkar wata obstacle ce ga isa ga Hafsat da gyara gundumemen kuskurensa da wuri. Zuciyarsa na lallashinsa da cewa, Hafsat-Suhaanahwill not expose his shortcomings, za ta yi masa uzuri kamar yadda ta saba, za ta rufa masa asiri kamar yadda ta saba, zata jira shi har ya dawo kafin ta dawo Abuja bazata dawo ita kadai ba komai dadewar da zai yi balle sati daya kacal, tunda ma ai shi zai je ya dauko ta wanda dole a jira ya dawo. Abin da Abdulazeez Dakata ya manta shi ne duk yadda muka kai ga tsara wa kanmu alamura sai Allah ya nufa. Bai yiwuwa mu yi ta tafka kuskure yadda muke so mu ce zamu gyara komai a lokacin da muka ga dama. Allah yana ara mana dama mai dumbin yawa a rayuwa mu yi ta yin abin da muka ga dama, rana daya in Ya tashi kama mu ba Zai ba mu damarrepentingna minti daya ba. Wasu alamuran na zuwa cikin rayuwarmu don su zama iznah a gare mu. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* ***** A falo ya tadda Hafsat, ta yi daidai da takardu irin na zane manya-manyan nan tana zana World Atlas. Wani assignment ne na cikin hutu (holiday assignment) aka basu akan wani kwas map analysis. Zane ta ke yi na kwallon duniya world map ta maida hankalinta kacokam kan abinda ta ke yi. Idan ka kalle ta a zuciyar ka abinda zaka fara cewa shine; (A Geographer withdetermination and enthusiasm). Ko shigowar motarsa ba ta ji ba balle takun sawunsa. Tsayawa ya yi a bakin kofar shigowa falon ya jingina da kofar hannunshi na hagu na dogare da kofar dayan na cikin aljihun wandonsa. Langabar da kansa ya yi gefe yana kallonta. Watanni goma sha biyar kenan cif da aurensu, wanda ya yi daidai da SHEKARA DAYA da watanni uku. Abubuwa da yawa sun faru cikin wadannan watanni goma sha biyar din wadanda ba za su taba shafewa daga kwakwalwarsa ba! Masu dadi da marassa dadi, na ban dariya dana ban haushi. A cikin wadannan watanni, Muazatu ta gama LLB tayi karatu a Law-school ta gama ta fito a matsayin cikakkiyar lauya daidai da burinsa na matar da zai aura. Ya zauna da Hafsat-Suhaana cikin wadannan watanni zama wanda aka tsara yadda zai kasance tun farko, amma abin mamaki ya rikide ya jirkice zuwa ba yadda aka tsara shi ba. Ya zo da abubuwa masu yawa beyond his mere or casual assumption...... Awata rana irin ta yau daidai wannan lokacin yana rungume da Muazatu a ofis dinsa yana daukar mata alkawurran da baa so musulmi ya dauka saboda ba shi ke iko da rayuwarsa ba. Gabadaya rayuwarmu rubutacciya ce tun haihuwarmu a Allon Lauhul-Mahfuz. Manzon Rahma (S.A.W) ya ce, yana daga cikin alamomin munafuki in ya yi alkawari sai ya saba, in aka amince masa sai ya yi hainci, idan ya yi zance sai ya yi karya (Bukhari). Ya yi wa Muazatu alkawari, in ya saba sunansa MUNAFIKI. Ya yi wa Muazatu zance tun daga karkashin zuciyarsa, in ya canza shi ya yi KARYA. Muazatu ta amince masa, in ya zabi Hafsat ya barta ya yi HAINCI. Ta rabu da kowanne Da namiji saboda shi. Shekaru ukku kenan cif tana dakon soyayyarsa mai wahala a zuci. Lokaci ya zo da zai aiwatar da kalaman bakinsa yana so ko ba ya so. To amma anya babu babban kuskure a cikin alamarin nan? Yaya rayuwar Hafsat za ta kasance in ya rabu da ita? Karatunta zai dore? Mammah za ta barta ta ci gaba da makaranta babu aure? Zuciyarsa wadda har yau ba ta baiwa Hafsat matsugunni guda daya a cikinta ba ta ce da shi. Tun farko ba ka yi wa Hafsat alkawarin rayuwa mai dorewa da ita ba, kuma ta san wannan. Abu daya ka ke yi wa shi ne SABO! Ba mutuwa ake yi wa kuka ba sabo ne, da sannu zai gushe tamkar ba a yi shi ba. Babu mai mara maka baya ka auri Muazatu kana tare da Hafsat. Matsayin da Hafsat ke da shi babu soyayyah sai emotion. Wani irin emotion na can karkashin zuciya. Wanda a kullum yake da nauyi kamar ansababban dutse an danne shi. Zuciya mugun nama.. ta ci gaba da angiza shi da cewa... Muazatu na jiranka Abdulazeez da tarin soyayyah mara algus..... za ku shimfida rayuwa mai maana irin wadda ka ke buri..... soyayyah irin wadda ka ke mafarki... yadda ta yi maka tanadin kanta tsawon shekarun nan ta tsayar da soyayyarta a kanka kai kadai, ta cancanci ka watsar da komai ka cika alkawarin da ka daukar mata... sai ka rabu da Hafsat ne za su dubi alamarinka da Muazatu da idanun basira. Hafsat duk wasu alkawururruka da ka daukar mata a yau Allah ya nufa ka cika mata su. Abu daya ya rage ka damka ta a hannun MAHAIFINTA, wanda in Allah ya so Ya yarda wannan ya zama tarihi. Zuciyar ta ci gaba da qawata masa komai na Muazatu ya fi na Hafsat sau dubun dubata. Hafsat har gobe kamata ya yi a ce tana gaban iyayenta suna ci gaba da rainonta... yadda ka shirya rayuwa da matarka ta aure da tarin bukatar gangar jiki da zuciya,me Hafsat za ta iya dauka a ciki? Wane martanin soyayya kake tunanin samu daga gare ta? Muazatun dai! Ita ce daidai da rayuwarka, wadda za ta zage ta nuna maka soyayya dakwanji, da jiki da zuciya. Haka zuciyarsa ta yi ta kawo wahayi iri-iri na kyakkyawar rayuwar da zai shimfida da Muazatu in ya same ta. Bangaren kyakkyawan tunani ya toshe, idan ma akwai, to son cika alkawarin da ya dauka ya rinjayi komai... A ganinsa in ya cika wannan alkawarin ne zai kubuta daga sahun munafukai, makaryata, mahaintakuma rayuwarsa ta zauna lafiya. Duk sanda zuciyarsa ta kawo masalaha ga rayuwar ita Hafsat din, daya zuciyar sai ta hambare. Da hujjarta na cewa, ita yar gata ce yanzu... mai iyaye, yan uwa da kakanni babu abin da zai dame ta don ta rabu da kai... Mammah kuwa in za ta yi adalci ai ka yi mata biyayya, lokaci ya zo da za ta karbi naka zabin ta ba ka yancin da Ubangiji ya ce ta baka. A zaman da ka yi da yarta ba ka taba cutar da ita ba... ba ka taba bata mata ba sai ko bisa ajizanci irin na dan adam, ko ka yi kuskuren ma kana kokarin gano kuskurenka da kanka ka yi repenting. Idan ba a gode maka ba a rikon da ka yi wa Hafsat, to a kalla ba za a yi maka tofin Allah tsine ba......!!! Da wannan kwarin gwiwar Abdulazeez Hamza Atiku ya dauke ido daga kallon Hafsat, ya karasa shiga cikin falon. A lokacin ne Hafsat ta ankara da shigowarsa. Wani irin dadi ta ji a ranta domin sosai ta yi kewarsa a gidan tun fitarsa. Rashin abin yi ne ya sanya ta yin assignment din kuma map din ya yi kyau sosai kamar ba ita ta yi ba. Ga mamakinsa ya kasa hada ido da Suhaanah a yau, kai tsaye ya nufi dakinsa ba tare da ya ce da ita komai ba. Hafsat ta yi dan jimm! Me ke damun Yayanta Abdulazeez? Ko wani ne ya bato masa rai a waje? Mikewa ta yi da niyyar binshi dakin, amma sai ta dakata. Sun dade da daina shiga dakin junansu. Sannan a lokacin da miji yake cikin fushi matarsa nesa-nesa ya kamata ta yi da shi. Damuwarta shi ne, ta shirya masa abinci mai rai da motsi da za ta so ya ci kafin ya shiga barci. Amma haka ta hakura ta soma tattara kayan zanenta don barin wajen. A wannan daren mai cike da rudani ga Abdulazeez Dakata daga shi har Hafsat kowanne ya kasa barci. Cikin sulusin dare ya samu takarda ya yi rubutu ya ninke ya adana a lokar gefen gadonsa. Wata irin ajiyar zuciya ya saki ya maida kansa ya jingina a kan filo. Amma ga mamakinsa ya kasa runtsawa. Ya rasa takamaiman abu guda da kwakwalwarsa za ta kama, gabadaya ta hargitse, ta cukwikwiye, duk kuwa da ya yanke hukuncin da zuciyarsa ta fi amincewa da shi din. Kamata yayi ace ya samu (peace of mind) bayan zartas da hukuncin amma kamar ya kara hargitsa kwakwalwar sa fiye da baya. Hafsat kuma damuwarta me ke damun Abdulazeez ne? Ba ta taba ganinsa cikin wannan yanayin ba. Ko ba ya jin yin magana zai gaya mata ba ya son magana ta yi harkarta ta kyale shi. Amma a yau ko alfarmar hakan ta kasa samu balle ta ga kwayar idanunsa. Ga shi da alama yana cikin rudani irin wanda ba ta taba ganinsa a ciki ba. Ta samu kanta da mikewa ta dauro alwala ta dasa sallar nafila cikin daren. Addua ta ke ko mene ne matsalar Abdulazeez Allah Ya ba shi kyakkyawar mafita, Ya iya masa abin da ba zai iya ba, Ya shige masa a gaba a kan alamuransa (Allah sarki Hafsat). ****** Wani barci ne mai nauyi ya sure ta gabanin asubahi, bayan ta idar da sallar asubah. Ba ita ta farka ba sai wayewar gari tangararan. Lokacin tuni Abdulazeez ya tsufa a office. Takaicin kanta ne mai tsanani ya kamata. Haka ta mike ta yi wanka ta shiga kicin don sama wa cikinta abin da zai ci. Abdulazeez bai dawo gidan ba har ta yi shirin barci, gidansu ya tafi a can ya ci abinci. Hatta Mammah ta lura cikin damuwa yake, amma da bai furta ba sai ta kyale shi. Yana gidan har karfe goma, Mammah ke tambayarsa ko ya gaya wa Hafsat maganar tafiyarsu Yola? Ya ce, abubuwa sun masa yawa, ya manta. Amma da ya koma zai gaya mata. Fada sosai Mammah ta hau yi masa na ba ya daukan abubuwan kowa da muhimmanci sai nasa. Hakuri ya ba ta ya kuma tabbatar mata yau zai gaya mata. Da ya dawo ta dade da shigewa daki ta kashe wuta ta kwanta. Ko ta yi barci ko ba ta yi ba, ba zai iya cewa ba. Text ya yi mata a ciki ya ce ta shirya kayanta da na bukata wanda zai yi mata sati biyu za su tafi jihar Adamawa jibi dukkansu, har su Mammah. Washegari tana kunna waya abin da ta fara gani kenan. Sai kawai ta ji gabanta ya fadi, me za su je yo wa a Yola? Wa suka sani a can? Har kuma sati biyu? Allah ya so ta hutunsu na sati hudu ne. A hakan dai cike da zullumi ta soma shiri tun a lokacin. Karin kumallo mai kyau ta shirya ma Abdulazeez a safiyar ranar. Amma sai tsintar bude masa get da fitarsa ta yi tun kafin lokacin da ya saba tafiya office ya yi. Jikinta ya kara yin sanyi fiye da yadda yake a mace tun daren jiya. Haka ta kare wunin sukuku tana shirya kayanta cikin travelling bag. Haka ya yi ta zillewa haduwarsu har zuwa ranar tafiya. Ba su hadu ba sai asubahin ranar da ya fito cikin shiri da nashi jakar kayan marasa yawa. A falo ya same ta a shirye don kusan kwanan zaune ta yi saboda zuciyarta ta kasa sukuni balle ta yi barci. Jikinta ne kawai yake ba ta canjin Abdulazeez yana da nasaba da wannan tafiyar.Ya kalle ta kasa-kasa yace ta koma daki ta canza mayafi wannan yayi shara-shara, nan ta ajiye hand-bagdinta ta koma dakin don bin umarninsa. Mamaki fal ranta don ita bata ga laifin mayafin data yafa ba, yanada kauri ba laifi kuma yanada girma, ita data fi amfani da abaya ma da dan mayafinsu bai taba cewa komai ba sai yau akan babban gyale. Tunda suka shiga mota ta gaishe shi, ya amsa bai kara ce mata komai ba. Nauyin da zuciyarsa ta yi kawai ya ishe shi. A Asokoro ma ba su bata lokaci ba kowa a shirye yake. A motoci za su yi tafiyar. Manyan jifa-jifai uku na Dr. Hamza, sun biya sun dauki Uncle Abdulkarim da yaransa, za su tsaya a Kano su dauki su Adda Hafsatu don Anty Zuwaira ta ce ita kam ba za ta samu zuwa ba. Sanin halinta mijin bai takura ta ba. Wajejen karfe sha daya na rana suna cikin Kano. Babu bata lokaci su Adda ma sun shirya su kawai ake jira su iso. Motar farko Abdulazeez ke ja, Hafsat da Mammah, Baba Azumi da Adda Hafsatu da Daddy ne a ciki, ta biyu Baffa Atiku, Dr. Idris Dakata, matarsa Dr. Tawheedah, matar Ibrahimada Minister Abdulkareem da dansa Ramadan ne a ciki, Ibrahima ke jan su, ta karshe su Aunty Luba, Murja, Mariya, Furerah, Usman da Haleem dasu Farhan, direban Daddy Salisu ke janye da ita suka kama hanyar Adamawa. Daddy ya ce, ba za su daura musu nauyi ba, Hotel zai kama musu gabadaya in sun isa. Ana ta hirarraki a motar banda Hafsat da Abdulazeez, wanda ke tuki cikin nutsuwa da kwarewar tuki. Daddy ne a gefensa, a kujerar baya ta farko ita da Mammah ne, a ta biyu Baba Azumi da Adda Hafsatu. Hafsat kwantar da kanta ta yi a kujerar gabanta tun tana tunane-tunane har ta rasa na kamawa, barcin da ta ci bashinsa ya yi awon gaba da ita. In lokacin sallah ya yi suna tsayawa a gidan mai su yi sallah su ci abincin da Mammah ta yo musu guzuri sannan su ci gaba. Akai-akai suna waya shi da Sagir har Allah ya kai su Jimeta lafiya, misalin goma na dare. Don haka ya gaya wa Sagir ba za su samu shigowa a daren ba sai gobe da safe sun wuce masauki. Sagir ya yi korafin cewa, don me ba za su karaso su sauka gidansu ba? Ya ce, suna da yyawa ne, sannan shi ma ba tsarinsa ba ne tsarin Daddy ne su yi hakuri. Sagir ya ce ya fada masa sunan hotel din da suke, zai kawo abincin da aka tanadar musu. Ya gaya masa sunan (Jireh Suites). A reception din hotel din ya tarbi Sagir, ya karbi kabakin abincin ya kakkai musu, Mammah da Daddy daki daya suke, Baffa Atiku shi kadai. AbdulkarimDakata shikadai a dakinsa, Dr.Idris da matarsa Dr. Tawheedah daki daya, Usman, Uncle Ibrahim,Haleem dasu Farhan daki daya, Sauran yan tafiya duka mata ne daki guda suka hada. Daga reception Sagir ya koma. Sun ci sun sha daga abincin fulanin usli, sun sha fura da nono kindirmo har sun gode Allah, sannan kowannen ya nemi makwanci don huta gajiya. Abdulazeez na tare da Baffa Atiku, Hafsat na tare da su Aunty Luba, Daddy dai ya dauka daki daya Abdulazeez din ya kama musu shi da Hafsat din tunda shi ya kakkama dakunan,ko kusa ba wanda ya gaya mata abin da ya kawo su wannan gari mai dumbin albarka. Shi da Baffa Atiku suka kwana, wannan kadai ya debe masa kaso hamsin na daga damuwar da ke nukurkusar zuciyarsa. Domin dai Baffan kusan kwana suka yi yana ba shi labarin kuruciyarsa, ya gaya masa hesbrave, genius, and patriotictun yana yaro, babu abin da ke girgiza shi a kan raayinsa da determinations dinsa na son zama babban lauyan gwamnati. Yana so ya ci gaba da zama hakan a yanzu da ya zama cikakken mutum mamallakin iyali. Ya cigaba da amfani da wadannan qualities din akan aikinsa da iyalinsa. Ji ya yi gwiwoyinsa sun yi wani irin sagewa... Does these qualities are still with him? Da sauri ya girgiza kai cikin musanta hakan da cewaNo,they areabsolutely not. Hes only brave on Muazatu yanzu, but not on anybody and anything else. Juyar da kai ya yi ya ci gaba da sauraron labaran da Kakansa ke ba shi na rayuwarsa ta baya, yana diba yana zuba su a sikeli yana auna su da rayuwarsa ta yanzu.Sai ya ga cewa; ratar da ke a tsakani mai tsananin fadi da girma ce tunda ya kasa yi wa kowa bravity da patriotic din sai Muazatu!!! A dakin iyayen, Mammah na shirin kwanciya ta ce da mijinta Dr. Hamza. Ko ka lura da sauyin yanayi a tare da Abdulazeez da Addah? Tunda muka taho ba sa magana da junansu har muka iso. Sannan da ya zo kama daki bai kama musu tare ba ina lura. Haka kawai sai in ji gabana yana yankewa ya fadi in na kalle su tun tahowarmu. Daddy ya ja bargo ya rufa ya kashe fitila mai haske. Tsohuwar nan kin fiya sa ido, ina ruwanki da tsakanin miji da mata? In kuma fadan masoya ne suka yi a tsakaninsu fa? Ko harshe da hakori ai ana sabawa. Don Allah kada ki bata min daren yau da Psychological Investigations dinki. Kanwar Haleem nake so mu samo tunda gobe za a kwace Hafsat.... Ya fada yana murmushi don son gusar mata da damuwarta. Fuska ta yi sosai jin fatan da yake mata (gobe zaa kwace Hafsat), sannan ta isa gare shi tana fadin, Mai raba ni da yata ko girgizar kasa albarka. Mu je dai su ganta su san da zamanta, su san labarin tasu diyar, in koma da abata. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* ****** Tafe suke cikin kwazazzabo cikin farar mota hilux mai hawa kowanne irin tudu da kwari cikin wani kauye wai shi Kufana a Southern Kaduna. Muazatu na ta korafi, Regina ta ce, Dadina da ke wutar ciki Muazatu, garaje da rashin hakuri. Tunda na ce miki matsala aka samu kuma zai gyara ki adana min wannan rashin hakurin naki har mu isa. Dole Muazatu ta yi shiru ba don ta so ba. A ganinta Regina tana daukar alamarinta da wasa don ba ita ta fada cikin abin da ta fada ba. Har suka iso karkashin wata bishiyar kanya nesa da wani hawan dutse. Regina ta faka motar. Tare suka fito ta sa mukulli ta rufe motar, fili ne fetal ba gida gaba ba gida baya, sai wani dogon dutse a tsakiyar filin. Wannan dutsen Regina da Muazatu suka nufa har suka iso gabansa, kowacce ta tattare zani suka fara hawa dutsen nan kamar kadangaru daya na zamowa daya na tallafo ta har suka iso bakin wani dogon kogo na rarakakken dutse, Muazatu takalmi, dankwali da mayafi duk a hannu saboda wahala, har hawaye ta ke yi. Zuwanta wannan wajen na biyu kenan bayan Regina ta ce in ka zo sau daya ba ka kara dawowa bukatarka ta gama biya. Haduwarta ta farko da Abdulazeez Dakata a ofishin mahaifinta ta fara sonsa kamar ta ciro rai ta ba shi. Ba irin kyautata masa da ba ta yi ba don ya so ta, bata taba tunanin neman soyayyarsa ta wata hanya bayan kyautatawa ba. Amma sai ya bada mata kasa a ido, ta hanyar nuna mata shi babu wannan a gabansa, yana da abin da ya kawo shi Law School ta yi hakuri ya ci gaba da bata girman da yake ba ta na kasancewar ta yar malaminsa. Duk wasu dabarunta sun kare, ta kasa canza wannan murdadden lauyan data fahimci ba abinda ke canza masa wani irin raayin rikau irin nasa. Regina abokiyar karatunta ce wadda ta fito daga jihar Benue. Hira ta yi hira a tsakaninsu irin ta shaqiqan aminairannan sai ta ke gaya mata yadda ta samu kanta a kan Abdulazeez da raddin sa gare ta, da kuma matsanancin halin data ke ciki akan hakan. Ba da wata manufa ta fadawa Regina ba sai don ta rage radadin dake ranta, irin wanda dan adam ke samu idan ya raba damuwarsa da wani nasa. Wani sakaran kallo Regina ta yi mata ta ce. Ke wa ya gaya miki yanzu ana tarar namiji haka zikau, a ce ana sonsa ba tare da an tabbatar an kama shi a hannu ba? Muazatu ta ce, ita ba za ta iya biye-biyen malamai ba, saboda in aka fara baa dainawa, ta ga Mamanta na yi amma ita ta hane ta, ta sha ce da itaadashi ne wanda baa dauka. Regina ta ce, Ina da inda zan kai ki a yi miki aiki a kansa, in aka je sau daya babu komawa, kuma aikinsa na har kabari ne (har wanda aka yi wa ya mutu). Idan kuma na ce ki kara komawa kada ki kara kallon inda nake. (Mafarin zuwan Muazatu Rufai wajen boka Chiwonzhu a Kaduna-South, kauyen Kufana). A kan idonsu ya kamo tunkiya ya kalli kudu ya farke mata ciki, zuciyar tunkiyar ya tsigo tana yararin jini ya dora ta a kan wani kasko ya zuba hayaki a kai ta hau tiriri har sai da jinin jikinta ya kone. Bata zuciyar ya yi a tafin hannunta ya ce ta gutsire ta sau goma sha biyu, duk gutsira daya ta ambaci sunansa har ta cinye. Duk kyankyamin da Muazatu ke ji haka ta cinye danyar zuciyar tunkiyar nan. Ya hada ta da wani garin magani ya ce a ciyar da shi a abinci tsayin kwana talatin ba tsallakewa. Wanda ta nufa da wannan asiri ba zai taba samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba har sai ya aure ta. Zai iya ja da kowa a kanta, in yace kowa yana nufin kowahar sai ya aure ta. Wannan shi ne makasudin Muazatu na fara ciyar da Abdulazeez abincin gidansu, daidai da rana daya ba ta taba kuskurewa ba, har zuwa cikar waadin da boka ya debar mata. Dawowarsu a yau tsibirin boka Chiwonzhu ga su a gabansa, tun shigowarsu yake dawurwura a kansu yana zagaye su. Yana bugun kan Muazatu da wani gashi yana wasu maganganu da ba sa fahinta kafin ya yi zaman yan bori a gabansu. Idan ya yi hakan, yana jira ka fadi abin da ya kawo ka ne, ya gama duba matsalolinka. Ya daina damuwa da ni, ya ki zuwa mu yi aure, ya daina kirana, ya daina amsa nawa kiran. Nema yake ya fasa aurena daga dukkan alamu. Kakansa ya lalata komai yarinya!. Gabadaya suka dago a firgice suka dube shi. Wani farin dattijo mai farin gemanya, mai tarin shekaru rututu. Yana can Arewacin Najeriya yana karya duk wani sammu da ke jikinsu ba tare da su kansu sun sani ba!!!. Idanun Muazatu suka firfito cikin tashin hankali. Yanzu ba wani taimako da za ka yi min ya aure ni? Ta fada cikin son kecewa da kuka. Ko mun yi zai sake lalatawa, amma akwai aiki guda daya wanda ba yadda zai yi da shi sai dai daga gare ki amincewar take. Fadi ko mene ne wallahi zan iya in dai ba zan rasa Abdulazeez ba. Muazatu ta fada tana kuka tare da zubewa a gaban Chiwonzhu. Zai iya zama mai tsauri a gare ki, amma ina tabbatar miki kamar yankar wuka yake. Kuma ba a jikin jikansa zai zauna ba balle ya karya, a jikinki zai zauna har gaban abada.In ba ni ba babu mai iya karya shi. Rokonsa Muazatu ta shiga yi ya yi mata wannan aikin, ko nawa ne za ta biya. Ita dai burinta ta auri Abdulazeez ko ta halin kaka. Chiwonzhu ya ce, Aikin ba ya bukatar ko sisinki. Magani ne zan shafa a jikina in sadu da ke, idan ba a yi auren nan cikin sati biyu ba, kada ki kara dawowa inda nake. A hankali Muazatu ta soma ja da baya, Regina ta soma harararta, Me ye a ciki? Ba kanki aka soma ba, na kwanta da shi ya fi sau goma, me ya ragu a jikina? Girgiza kai Muazatu ta shiga yi tana kara ja da baya, Im a virgin Regina, aladarshi ba daya ta ke da tamu ba. Idan na je masa babu budurci ba zan taba yin daraja a idonsa ba.... Kuma aka ce miki haka za mu kyale shi bayan an yi auren? Kamar ta ce da ita, An zo gurin, maganar Mamana ta tabbata;in aka farabinsu ba za a daina ba. Nikuma ba zan iya jura ba, ko zuwa wajen nan kadai balai ne balle hada jiki da wannan kazamin mutumin. Shi dai boka wasu harkokinsa ya shiga yi a cikin kogon ya manta da su ita da kawarta suna ta jayayya. Da suka fara isarsa ya ce, idan ba ta amince ba su tattara su bar gabansa. Muazatu ta wawuri jakarta ta mike kan su ce me ye wannan har ta kai kofar kogon. Chiwonzhu ya dube ta cikin takaici, Ki sa a ranki ke da wannan mutumin har abada! Ba zai taba aurenki ba. Kina iya gwada wani bayan ni, don ki tabbatar da abin da na fada. Da kuka wiwi Muazatu ta fito daga kogon Chiwonzhu, ta soma kokarin saukowa daga dutsen, ga rashin nutsuwa ga tashin hankalin abin da ya fada. Santsin dutsen da ta ke kokarin bi a hankali ya kwashi sassalkar kafarta ta yo suuuufa tun daga sama har kasa ta fadi a kan kwankwasonta. Wata azababbiyar kara ta saki Regina na kallonta daga saman dutsen ta yi tsaki ta ci gaba da saukowa a hankali har ta sauko tsaf, ta kama ta ta mikar tana zuba ihu a haka suka karasa motarsu. Regina ta watsa ta kujerar baya ta tuka motar suka tafi. Kwananta uku tana jinyar Muazatu wadda ko zama ba ta iya yi sai kwanciya, amma Regina don mugunta ta ki kai ta asibiti. Kwana ta ke kuka tana gaya mata pelvic-girdle dinta (kashin kugu) ya karye. Da ta gaji ta tattara ta ta sa a jirgin Lagos ta koma gida. A wheel-chair maaikatan jirgin suka turo Muazatu zuwa reception. Nan ta fiddo waya ta kira Babanta ya turo a dauke ta tana filin jirgi ta karye. Da kansa ya zo cikin tashin hankali har da Mamanta suka kwashe ta sai wani babban asibitin kashi. Likitoci suka duba ta sosai, nan suka gayawa Babanta ta samu tsagewar kashi a kashin kugunta za a yi mata aiki. Ya yi addua kada abin ya taba lakarta (spine). Hankalin Attorney General ya yi mummunan tashi, Mamanta sai kuka. Bayan an yi aikin an fiddo ta Babanta da Mamanta suka sanya ta a gaba ta gaya musu inda ta je ba da saninsu ba kwana hudu ta karye. Tana kuka cikin zafin ciwo ta gaya musu tun zuwansu na farko wajen Chiwonzhu da Regina a kan Abdulazeez har kawo na wannan karon da abin da ya rikitata har ta sulmiyo. Ran Attorney ya yi mummunan baci, idanunsa ya yi jazir ya ce. Wato duk tsawon lokacin nan charming din Abdulazeez ki ka yi don ya so ki? Na raine ki kan ki zamo mai son kanki ki zama heartless Muazatu? Ina ki ka kai darajar da Allah ya yi miki ta diya mace? Shin daga kan Abdulazeez aka ce maza sun kare a duniya? Mene ne farin cikinki na zama da wanda ki ka san ba don Allah yake sonki ba? Kina tsammanin akwai abin da ba kararre ba a wannan duniyar? Muazatu kin san azabar da ki ka gana wa zuciyarsa tsayin wannan lokacin? Kin san ya ya zuciyar tunkiya ta ke? Haka ake nufin ki maida zuciyar mijin aurenki. To ina batun samun aljannan kuma tunda kin maida zuciyarsa ta tunkiya? Yau da kin ba wa bokan nan kanki da na yi tirr da haihuwar ki. Afuwar da zan miki kenan tunda ki ka tsira da wannan hankalin. Kin san halin da ki ka jefa zuciyarsa tsayin wannan lokacin Muazatu? Gaskiya na ga iyayensa na yin baya-baya da maganar aurenki, ashe su suka san abin da suke gani daga gare shi a kanki. To bari ki ji in gaya miki aure zan yi miki karshen watan nan. Ba irin maneman da Allah bai baki ba kina wulakanta su kike tsaye nacin wanda baya son ki. Jinina yafi karfin irin wannan auren. Ko a waya ki ka kara kiran Abdulazeez ban yafe miki ba duniya da lahira! Kuka Muazatu ta sa, Daddy kada ka yi min haka, wallahi tun kafin hakan yana sona, tun kafin in je Kadunan muke tare. Mamanta ta kai hannu ta buge bakinta. Ban ce kada ki taba bin bokaye ba a rayuwarki? Ban gaya miki adashin da babu dauka ba ne? Ban gaya miki in aka fara baa dainawa ba? Kin biyewa arnan kawayenki kafirai wadanda su basu san Allah shi ke sawa Yake hanawa ba? To wallahi ni ma na fada ko shi ya saura namiji a duniya ba za ki aure shi ba! Abin da ba ki sani ba ma iyayensa sun dade da yi masa aure, jiya wata kawar Mamansa ta gaya min mun hadu a wajen conference, ke ya mayar sakarai, shashasha. Kuka Muazatu ke yi har ta ji babu dadi, Mummy na sani fa! Ya yi min alkawarin zai sake ta in na gama law-school mu yi aure. Ga mamakinta daga uwar har uban sai suka bushe da dariya, So he is playingwith your senses duk da asirin naki? Ya dauke ki mai kwakwalwar yar tsana. Tunda ki ke kin taba jin wannan almarar? In ji Maman. Attorney ficewa ya yi don takaici bai kara dawowa asibitin ba har bayan kwana biyu. Shi kadai ya san me yake shirya mata. Akwai wani Grand Khadi abokinsa tun na karatu, dansa Barrister Muntada ya dade yana son Muazatu ba ta ma sani ba. Yana aiki a court of appeal ta jihar Lagos. Mahaifinsa ya biyo ta kan Daddynta yana nema wa dan nasa izinin a bashi dama ya fara nemanta. Attorney ya ce ya dakata saboda akwai maganar wani studentdinsa a yanzu a hannunsu, amma bai san me Allah zai zaba mata ba. A lokacin ya fadi hakan ne ganin tsohon Ambassador Hamza na yin baya-baya da zancen. To a ranar da ya bar asibitin bai kwanta ba sai da ya nemi Grand Khadi Akilu Lawal ya ce ya baiwa Muntada Muazatu, ko yaushe suka shirya su fito. Alkalan sun shirya komai a tsakaninsu ba tare da Attorney ya kara bi ta kan Muazatu ba a wannan lokacin, don ya fara tunanin bayan buguwar tata a kwankwaso kanta ma ya bugu ta fara fita daga seti a kan Abdulazeez. Wannan kenan. ****** Kwanan Hajiya maryam biyar a asibitin DIFF sannan ne aka samu jikinta ya sauka taji sauki sosai likita ya ba su sallama tare da kaidojinsa cikin buhu, hatta abincinta ya canza shi ya mayar da shi zuwa na masu lalurar hawan jini. Duka jamaar gidan Dr. Ya hana su zuwa tun zuwansu na farko ya ce hutu ta ke bukata, don ranar da suka zo sai da jininta ya kara hawa. Hafsat ce kawai tare da ita, ita ma ba wata hira suke ba don mafiya yawan lokuta ma tana barci. Shi kadai ya san cikin yanayin da ya kwana a wannan rana, zai iya rantsuwa cewa idanunsa ba su runtsa ba. Yana da tabbacin Mammah za ta yi fushi duk ranar da ya karar da auren kwangilarsa amma bai yi zaton alamarin zai yi girman da har zai taba lafiyarta ba. Their Mum is always healthy and vibrant, always busy taking care of them and their Dad, yau bakin cikinsa ya jaza mata cuta ya kwantar da ita a kan kafafunta. Ba ta sani ba, ya fi ta shiga damuwar abin da ya aikata. Ya runtse ido ya aikata ne don ya tserar da kansa daga tozarta alkawari. Zan yi repenting Mammah... Ki ba ni dama! One last chance! Ya fada a fili ya fi sau shurin masaki. Washegari har ofishin Ahmad ya tadda shi, kallo daya ESQ Ahmad Kutama ya yi masa ya tabbatar alamarin bai tafi yadda suka so ba. “Be a man. Abin da ya fara ce da shi kenan. Komai ya cabe Ahmad,yadda bazan iya gyara shi ba. Mammah ta ji. Shes now on admission. Na tabbata ni ne sanadi. Ga mamakin Ahmad sai ga hawaye sun sauko a fuskar Abdulazeez shar-shar! Hannunsa Abdulazeez ya kama ya ce, What will I do now? In Muazatu ce na fasa aurenta, ba ni da wani sauran buri a kanta. I need my wife back, and my Mums forgiveness. Ahmad ya jinjina kai kafin ya ce Daga yau ka daina jayayya da iyaye, ka kasance mai godiya da abin da Allah ya baka ko baka sonshi komai kankantarsa, ka daina zurfafawa a soyayya ko kiyayya, komai mai iya canzawa ne a duniya banda mulkin Allah da ikonSa a kanmu. Ba duka abin da muka kallafawa rai muna so bane alkhairi a garemu. Wasu alkahairan na rayuwar mu a lullube suke bamu san dasu ba amma Ubangijin da ya halicce mu ya yi mana tanadinsu in munyi hakuri mun bi iyayenmu zasu tadda mu har inda muke. Mu daina cewa lallai sai mun mallaki abinda muke so ko ta halin kaka. Mu roki Allah zabinsa ba zabin zuciyarmu ba. Abdulazeez ina mai fada maka da babbar murya ka yi kuskure! Ba Mamanka kawai ka sabawa ba har da Ubangijin da ya halicce ka. Aure ba abin wasa ba ne, umarni ne na Ubangiji. Amma ka yi shi ba da tsarkakkiyar niyya ba, duk auren da aka yi shi babu ikhlasi kuma aka kayyade masa waadi bai inganta ba a shariah. Bana tunanin ko ka rufe zancen nan ka karbe takardarka daga hannun Hafsat ka ci gaba da zama da ita auren ku ya gyaru duk da dai ni ba malami bane. Ka kwashe fiyeda shekara ba ka sauke hakkin aure da Allah ya rataya a wuyanka ba, wanda shi ne gundarin auren. Wasu malaman ma sun ce watanni uku babu saduwa tsakanin maaurata kuma babu hujja ta rashin lafiya ko tafiya, auren ya lalace. Don haka sanin da iyayenku suka yi ina ganin shi ne daidai. Su zasu nemi yadda zasu gyara muku auren idan sun huce. Ka roki Allah gafarar wannan zunubin da tuba nasuuhan. In aka ce tuba nasuuhan wato a yi shi da niyyar ba za a sake maimaita laifin ba. A yanzu kam, ai kada ma ka doshe su da bukatar su maida maka Hafsat, hakan zai zamo tamkar zubawa wuta fetur ne. Suna kan tsinin fushinsu, kuskure ne ka riga ka tafka, sun maka zabin da suke ganin shi ne daidai da rayuwarka da raayin su ka ce ba su iya ba, kai ne ka iya. Saboda sun tsaya maka kayi karatun zamani har kana ganin ka fisu sanin zamanin. Sai ka jure duk wani punishment da za ka fuskanta daga gare su, ka kwantar da kai kawai ka amshi laifinka da hannu bibbiyu, duk wani bayani da zaka yi musu bazai gamsar dasu ba a yanzu, amma ga wata shawara... ka nemi hadin kan matarka. A sanyaye Abdulazeez ya dago, cikin ransa yarda yake da duk kalaman da ke fita bakin Ahmad, ya ce. Kutama, Suhaana ta yanke duk wani communication gap da ke tsakaninmu. Daga ranar da muka rabu ba ta kara amfani da wayarta ba. Ina jin kunya in je gidanmu in ce zan ganta, ban da nan din kuma ban san inda zan ganta ba, ba ta zuwa koina Ahmad, ko da makaranta. Dariya Ahmad ya yiya ce Haba Abdulazeez kaman ba namiji ba? Kada ka bada maza, mazan ma mafiya hikima da sarrafa fasaha (lauyoyi). Kai za ka nemo hanyoyin communicating da ita. Kada ka manta weakness din mata daya ne (soyayyah). Balle kai dinnan (brainlliant and handsome hunk Abdulazeez) wanda na tabbata Hafsat ta dade da macewa akan ka. Ka fi Romeo iya soyayyah, ka fi (William Shakespeare) iya sarrafa harshe wallahi za ka sha mamaki. Sai da ya sa Abdulazeez murmushin da bai shirya ba amma bai ce masa komai ba. Damuwar dake cin sa a zuci ta hana shi bawa zancen nasa muhimmanci. **SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* **** Tunda suka dawo gida daga asibiti Hafsa ke hidima da Mammah, ta hana ta yin komai na gidan, girki ita ke yi, nasu daban na Mammah daban. Baba Azumi na taya ta da gyaran gida da tsabtarsa, wanke-wanke da shara. Ga Ismael na debe mata kewa da hirarrakin budurwarsa da yake matukar so Wasila, in ya je zance ya dawo duk hirar da aka yi a kunnenta za ta kare. Duk da baa gama hirar ba tareda sunyi fada ba saboda wasan kanin miji irin na Ismael mai ban takaici. Su ba yara ba ne daga shi har Usman, ganinta a gida da halin da Mammah ke ciki lokacin da suka dawo ya fahimtar da su abin da ya faru ba tare da kowa ya zaunar da su ya gaya musu ba. A zuciyar Ismael bai yi mamaki ba in ya tuno abin da ya faru tsakaninsa da Yayan nasa kafin auren. Ya tuno zuwansu na farko gidan nasu, da yadda aka yi kan hoton budurwar falo wadda ya tabbata budurwar Abdulazeez ce don ya tuna inda ya ganta bai fada bane a lokacin saboda Mammah. Ranar call tothe bar ceremoney ne na Yayan nasu. Ita ce ta kawo musu abinci. Ba tun yau ba ya san Yayansa is very selective and ideal a kan macen aure. Amma bai ga inda wadannan halaye suka yi proving kansu a gare shi ba in dai a Muazatu ya kare. Ko ta ina ba su daidaita ba, tarbiyyah, aladu, dabiu da halayya. Daga ganinta girman kudu ce, kuma sakakka, ba kunya ba kamun kai, ba aladun Malam Bahaushe ko daya a tare da ita. Da ya kalle ta sosai ma sai ya ga kamar ba bahaushiya bace. Suhaanah kuwa ai matar manya ce ko shi ba zai gaya mata komai ba banda zurfin ilmi wanda in yayi hakuri nata na tafe yanzu take nemansa. Sun samu labarin ganin dangin Suhaanah da aka yi kafin dawowarsu. An ce fadan da babu ruwanka dadin kallo gare shi. A kwayar idon Yayansa ya ga alamari mai girma a kan Suhaanah ranar da ya sanya ta gaba da tsokana a gidansu. Don haka ya san ko ma mene ne wannan ba shi ne karshen auren Yaya Azeez da Hafsat-Suhaanah ba. Shi Usman dama dan ba ruwana ne, bai kawo komai a ransa ba kuma bai tambaya ba, shi ya ma dauka zaman da ta ke yi a gidan din jinyar Mammah ta ke yi. Yau kwanansu biyar da dawowa daga asibiti Hajiya Maryam ta dan fara sakin ranta, har suna hira da ita. A daren ranar ta shiga ta tadda Hafsatun a dakinta tana shirin bacci. Irin zaman da ta yi a gefen gadonta da yanayin fuskarta ya tabbatar mata muhimmiyar magana ta kawo ta. Barin komai ta yi ta zo ta zauna a gefen kafafunta. Hajiya Maryam ta daga ido ta dube ta, kullum kara ramewa ta ke a tsaye kamar kudin guzuri. Ta juyar da kai cikin takaici ta ce, Zuwa na yi mu yi magana Addah. Kanta ta sunkuyar tana sauraronta. Kina da iddarshi a kanki? Dagowa ta yi ta dubi Mammah cikin rashin fahimtar Hausarta, har gobe Hausa mai tsauri na yi wa Hafsat wuyar ganewa. Hajiya Maryam ta fahimce ta sai ta maida bayanin nata gwari-gwari. Na ce ya taba kwanciya da ke? Kasa ta kara yi da kanta kamar tace da kasar ta hadiyeta ta huta, kunya, daburcewa da kidimewa babu wanda babuwannan lokacin a tareda ita. How could she say to his mother something like that (ta ya ya za ta iya fadawa mahaifiyarsa wani abu kamar wannan)? Da za ta iya da ta ce da ita, sam ita ba ta sani ba. Ya sha kai hannunshi gare ta,he even kissed her, but they had never have it. In wannan shi ne abin da ta ke son ji. Maimakon hakan sai ta soma shesshekar kuka. Ba ta son tuna komai da ya dangance shi, zuciyarta ba ta da karfin dauka. Haushi ya kama Hajiya Maryam, da babbar murya ta ce Addah! Ta dago kai idanunta jage-jage da hawaye, ta ce. Tambayarki nake yi don in soma lissafa kwanakin iddarki, na ce ya taba ki? Girgiza kai ta yi alamar aah. Wani bacin rai ya kara mamayar Hajiya Maryam, kiyayyar har ta kai da haka? Shekara daya da watanni rututu ba kwana daya ba. Mikewa ta yi a azama ta bar dakin ta yi dakin Dr. Hamza. Kallon news yake lokacin da ta shiga, sallama ma a cikinta ta yi ta. Gefensa ta zauna ta dafe kanta tana jujjuyawa. Remote ya sanya ya rage sautin talabijin din ya fuskance ta. Daddy ni wawuyar ina ce yaron nan ya yi wasa da hankalina har haka? Ko hakkin aure bai taba bata ba. Allah shi ne shaida ban hada wannan aure don in zalunci wani a cikinsu ba. But for the betterment of all of them. Ya wahalar da ni a banza! Ya bata min lokaci da aljihu da zuciyata duk a banza! Ba zan yi masa baki ba, amma ka zama shaida ko ya dawo daga baya ya ce in maida masa Hafsatu ko bayan raina aka maida ban yafe ba! Yau da yawun bakina ka aura wa Abdulazeez duk macen da yake so. Tun dawowarta daga asibiti ba su zauna sun yi maganar ba, ko ta taso da ita katse ta yake ya ce sai ta samu lafiya. Murmushi ya yi irin nasu na manya, maabota wayewar kai da tsinkaye ya kira sunanta a tausashe. Maryama, ni fa na dade da sanin Abdulazeez bai bar neman auren yarinyar nan ba ko bayan aurensa da Hafsatu. Cikin madaukakin mamaki ta saki baki tana kallonsa. Nan ya gaya mata tattakin da mahaifin Muazatu ya yi har ofishinsa ya ce Muazatu ta gama Law-school in sun shirya su fito a yi aure. Amsar da ya ba shi cewa yanzun akwai wani uzuri a gaban yaron in ya gama da shi zai yi magana. Ya ce da ita. Ta inda za ki gane ba da zuciya daya ya yi auren nan ba shi ne, saurin amincewarsa. Bayan a fili ya nuna kuma ya fada ba ya sonta, ga wadda yake so. In kin ci gaba da bincikarsu za ki gano bakinsu daya, akwai abin da suka shirya a boye ko daga wasikarsa da yadda ta dage wajen kare shi, da son na aura masa Muazatun. They have their own target, so ina so ki kwantar da hankalinki, ki bar sanya wa kanki ciwo a banza. Tarkonki ya riga ya yi kamu cikin shekara dayan da sukayi taren. Ki gode wa Allah ki kara binsu da addua, kuma ki fita daga sabgarsu. Kare shi da ta ke yi alamomi ne na kauna da soyayya, ko shi kin ji ya zo ya doshe ni da zancen tsohuwar budurwarsa? Ni kuma zan ba shi mamaki, sai na aura masa ita!!! ****** Washegari da magriba da ya taso aiki gidan ya zarto. Kallo daya Mammah ta yi masa sai da gabanta ya fadi. Allah kadai ya san rabonsa da kwakkwaran abinci, a kwayar idanunsa ta ke gane yunwar cikinsa. Ya yi baki ya rame da ma jikin ba wani jiki ba. Dogon hancin ya kara zama pointed a tsakiyar fuskarsa. Lumsassun idanun sun kara fadawa ciki sun zurma ciki sosai sai suka kara zama oily sabida shekin da suke fitarwa, sun canza launi daga farare zuwa grey-greyhaka. Yana shigowa falon inda Mamman ta ke zaune ya nufo, a gefen kafafunta ya zauna ya gaishe ta. Abu daya ya sa ta amsawa ganin Ismael da Usman sun bi ta da appealinglook, sun marairaice idanu suna dubanta kamar su suka yi laifin. Hafsat na can kusa da T.V da zurmemen hijabinta da carbi a hannunta, idar da sallarsu ta magriba kenan. Ya samu kujerar darare gefen Usman ya zauna ganin yadda Mammah ke cika tana batsewa. Tunda Hafsat ta ji muryanshi a falon da scent dinsa ba ta kara wani kwakkwaran motsi ba, ba ta juyo ba balle ta kalle shi. Ta ji yadda muryarshi ta kara sirancewa. Zuciyarta ta soma wani irin harbawa tana fama da kai-kawonta cikin kirjinta. Daddy ya shigo falon rike da brief-case dinsa ya mike ya karba kowa ya yi masa sannu da zuwa, ya wuce part dinsa kai tsaye. Abdulazeez na biye da shi. Mammah ta nufi kitchen wajen Baba Azumi ta ce ta hada wa wancan mutumin abinci, amma ba in ji ta ba. Murmushi Azumi ta yi, ta ce. Ya ci albarkacin ya taba auren yarki ma ai wani abu ne Mammah. Hararar Azumin ta yi, ta yi wucewarta daki. Azumi ta yi murmushi tana girmama hali na dattaku da karimci irin na uwargijiyarta, nata ba nata ba ne, na wani shi ne nata. Irinsu kuwa yayansu ba sa tozarta a rayuwa. Ta san Abdulazeez ya yi laifi da ya cancanci kowanne irin hukunci daga gare ta, amma ba ta jin dadin yadda ta yi watsi da shi gabadaya da duk wani alamarinshi. Ta tabbata ko bai fada ba yana can yana tunanin yadda zai yi ya gyara kuskurensa. Ta roke ta ta bashi dama ko da ita ce ta karshe. Ba wanda yake sama da aikata kuskure a wannan duniyar tamu? Wasu lokutan daga kurakuranmu muke gane yadda za mu tari rayuwa a gaba. Amma Mammah ta fito fili tace da ita kada ta kara yi mata maganar Abdulazeez. Wannan ya zamo na farko kuma na karshe. Don haka yau ba karamin dadi ta ji ba ganin ta ce a bashi abinci.Duk da tace ba in ji ta ba. Duk fushin uwa bata iya jure yunwar cikin dan ta. Azumi ta fada a fili cikin madafin (kitcen) a lokacin da takezubawa Abdulazeez abinci mai rai da motsi. Daddy ya dube shi cikin nutsuwa, fuskarsa fayau babu alamun wata damuwa ko bacin raiya ce. Mun gama magana da Kawu Abdulkarim zai je nema maka auren a Lagos din, gobe in Allah ya kaimu zai tafi ta jirgi, kuma insha Allah abin ba zai dauki lokaci ba, ko don ka samu nutsuwa. Daga ganinka ko abinci ba ka samu. Mun yarda da kaddara kuma mun karbe ta da hannu bibbiyu. Ka yi hakuri mun takura rayuwarka da auren da ba ka so, we never know rashin son ka da Hafsat mai zafi ne har haka. Allah ya sanya albarka a auren da zaka yi. Ita kuma Hafsan Allah ya musanya mata da mafi alkhairi. Ga mamakin Daddy hawaye ya kama yi. Hawaye sosai kamar an bude famfo. Wani abu da bazai iya tuna lokaci na karshe da ya gani daga idanun Abdulazeez ba, har a lokacin yarintarsa. Dr. Hamza ya yi biris da shi kamar bai san yana yi ba ya shiga tattara wasu takardu a kan center-table yana zuba su cikin files. Muryar Abdulazeez cikin rauni ya tsinkaya a tsakar kansa. Daddy, ni na ce ka nema min aure? Ba tare da ya juyo ya dube shi ba ya amsa. Hafsat ta nemi ayi mata wannan alfarmar, roko mai dimbin yawa.A yanzu kam ba abinda zata roka mu kasa yi mata don mun gurgunta mata rayuwa. Mun kuma fahimci har gobe kana son yarinyar nan yar Attorney-General Habibu Rufai dalilin rabuwarku kenan. Ko ba don haka ba sai in barka kai kadai a gida bayan ka saki matarka? Yadda Abuja ta lalace din nan zan zuba maka ido ka zauna kai kadai bayan ka dandana auren ka san dadinsa da rashin dadinsa? Cikin dusashshiyar murya da kuka ya karar da karsashinta ya ce. Daddy ni fa tun washegarin da na yi sakin na maida aurena, ban ganta ba ne balle in gaya mata, sannan ba ta rike waya balle in kira ta. Wani sakaran kallo Dr. Hamza ya yi masa. Da ma auren yarjejeniya aure ne? Wani busasshen miyau ya hadiye mai azabar daci, Daddy ka fahimce ni don Allah, its a mistake, ka gaya wa Mammah na tuba na bi Allah na bi ku. I want my wife back. Daddy ya ce, Aaha! Ni me ye nawa a ciki? Can muku kai da uwarka, ni dan daura aure ne in biya sadaki, kuma na damkawa waliyinka Abdulkarim ya kai Legas. Na sauke duty na as a fathera karo na biyu ban barka ba aure ba. Na yi maka abin da ranka ke so, in ba ka gode min ba akalla kada ka sa ni ciwon kai. Na dauka makaman yakinmu muka zubar muka yi maka abin da ka ke so don a zauna lafiya? Me ya sa dan Adam baa iya masa? Ko kana nufin ka ce ka fasa auren Muazatun bayan ka yi mata alkawarin za ka saki matarka ka aure ta? Kai tsaye ya ce Daddy na fasa, wallahi Hafsat na ke so. Ku yi min alfarma Daddy one last chance!. Zama sosai Dr. Hamza ya yi, ya ce, Kuma? To ba ka isa ba. Ba za ka maida ni karamin mutum ba. Ka sa a ranka ka auri yar Attorney ka gama, kai da wadda ba ka so kuma kun yi sallama ta har abada. Ya shige bedroom dinsa ya barshi anan. Ya dade a zaune ya rasa ta inda zai fara tunanin rayuwa da wata mace cikin gidansa ba wannan mamallakiyar gidan ba, wadda aka gina gidan da sunanta ta tsara abunta yadda ta ke so, uwarta ta shirya mata shi daidai da burin ta, ta ke kwana ta ke wuni tana tsaftace shi da kamsasa shi, ta zauna da shi cikin kyautatawa da karimci. Ta sayo wa kanta kauna da soyayya ba tare da kowa ya koyar da ita ba. Ya shiga tunano abubuwan da yake hangowa a Muazatu; ba wani abu ba ne banda zaton she will be very good in bed. A zamansa da Hafsat da dan physical releationship din da ya shiga tsakaninsu ya gane ba abu mafi dadi da ban shaawa ga Da namijin da ya san ciwon kansa, irin ya mallaki mace innocentwadda bata san komai a wannan fannin ba, mai asalin YAKANAH (sunan wani littafin Takori)maabociyar alkunya ga mijin aurenta, take kuma tsananin kaunarsa a karkashin zuciyarta ba tareda ta fito da hakan a sarari ba saida ya fahimta cikn reactions dinta, emotions dinta da kwayar idanunta. Inyaso shi da kansa ya koyar da ita yadda yake so ta zama ba wadda ta shigo da iyawarta tun daga waje ba.... he cursed his previous perception (Ya tsinewa tunaninsa na baya). Haka ya mike cikin matsanancin sanyin jiki da na gwiwa. Ganin cewa Tsohon Ambasadan ba zai kuma sauraron komai daga gareshi ba, ya shiga ratsa falullukan gidansu yana wucewa. Bai tadda kowa a falon farko ba inda nan alummar gidan suka fi zama. Yana kallon abincin da Azumi ta ajiye masa amma ba ya jin ko ruwa zai iya kurba a gidan nan. Har zai fice ya ji kamar an fizgo shi an dawo da shi baya. Zai ga Hafsat a yau kuma a gidannanno matter whatya jaddada mata ya maidata dakin ta tana so ko bata so tunda don haka taki kunna wayarta, ya kuma ji daga bakinta; shin ta amince da hukuncin Daddy da Mammah? Ya auri Muazatu akan dole a raba su har abada??? Kai tsaye dakinta ya nufa ko gabansa ba ya gani sosai. Wata mahaukaciyar soyayya ke dawainiya da shi. Wannan kuma alkawarin Allah ne, duk namijin da ya saki matarsa babu kwakkwaran dalili sai Ubangiji ya hukunta shi da soyayyarta. Fitowarta daga wanka kenan, ta zauna gaban mirrow tana shafa lotion na (cocoa butter) a jikinta, daure da faffadan towel har gwiwarta. Da ta gama kuma kayan barci za ta sanya ta kwanta. Ji ta yi an murdo kofar a hankali an shigo. Ta yi zaton ganin daya daga cikin mutum biyu; Mammah ko Baba Azumi, tunda su ne kadai masu shigowa dakinnata.Amma su kam suna sallama ai har su jira a basu izni. Saidai me? Dagowar nan da zata yida wa zata yi arba? Abdulazeez ne; Her Ex- Abdulazeez, Eh... ta kira shi Ex don kalmar da ta dace da su yanzu kenan. Takaitaccen kallo daya ta yi masa ta dauke kanta. A cikin takaitaccen kallon data yi masan wasu rikitattun alamura da dama ta gano a tare da shi irin wadanda bata taba gani ba cikin kwayan idanunsa. Amma wannan ba shi ne a gabanta ba, yanayin da ya shigo ya same ta ne sanin cewa yanzun ba muharraminta ba ne, kuma tsakaninta da wardrove da nisa, idan kuma ta mike tamkar ta yi hakan da gayya ne har gara ma ta ci gaba da zamanta a yadda take kuma a inda take. Sunkuyar da kanta ta yi tana tuno yadda Yaya Azeez ya iya rufe ido ya rubuta mata saki, duk irin zaman amincin da suka yi.Ai ko da yarjejeniya akwai wani abu da bahaushe ke mutuntawa in relationship da ya kira da suna sabo turken wawa kuma dai ma ai haram baya haramta halaal, kawai saboda wata banzar budurwarsa. Ta tuno bakin cikin Muazatu da ta dinga kwankwada daga gare shi launi-launi kamar wadda bata da tsokar zuciya a cikin kirjinta.Ko ita mayya ce ta hakura da Abdulazeez Dakata! Za ta cika wa Daddy duk alkawurrukan da ta daukar masa, Allah ya hada kowa da rabonsa na alheri.......!!! Ji ta yi kawai kuka ya zo mata,kukan da bata shurya yinsa ba bata kuma so zuwansa ba, domin zai nuna rauninta wanda a yanzu take jin bata da shi indai akan Abdulazeez ne, kokari take ta maida hawayen kada ta barsu su zubo har yayi zaton tana da damuwa akansa. Abdulazeez jingine kawai yake a jikin kofa ya zuba mata shanyayyun idanunsa da suka kara kankancewa. Wani dunkulallen abu da ya tsaya masa a makogaro tun rabuwarsuyaki wucewa ya ji yana narkewa yana (dissolving gradually). Hafsat ba ta ankara da yaushe Abdulazeez ya tako har ya iso gabanta ba. Abin da ta fahimta kawai shi neta ji sanda ya mikar da ita tsaye a lokacin da bata zata ba, sai kuma ta tsinci kanta gabadayanannade cikin jikinsa ya zagayeta da dukkan hannayensa yayi mata kyakkyawan masauki a physique chestdinsa. Wani bigire da ba za ta iya mance duniyar da yake jefa ta ba duk da hakan ya faru ne sau bai fi ta kirga ba. The familiar scent of ‘Creed Aventus, his heart beats and hers...suka taru suka maida itadevastated suka soma yakar duk wani alwashi da ta ci a kansa cikin dan kankanin lokaci. Ba ta gama farfadowa daga wannan duniyar ba ta ji Abdulazeez ya soma sumbatar duk inda bakinsa ke iya kaiwa daga dogon wuyanta zuwa fuskarta,a karshe bakinta ya zama final destinationdinsa sai da ta nemi numfashinta da hayyacinta na wucin-gadi ta rasa. Can tsakar kanta kalaman nan nasa suka soma amsa-kuwwa..... Na sake ki ba don bana sonki ba...... rauni na guda daya ne; ina son MUAZATU! Kokarin kwatar kai ta soma yi, ganin alamarin na neman shallake karfi da iyawarta sai ta sa kuka.Kukan da ta san, shi kadai ke kwatarta daga hannun Abdulazeez a duk lokacin da irin haka ta faru.Tamkar wanda aka yi wa allurar kashe kuzari sai ya dakata amma ba tare da ya raba ta da jikinsa ba, hot kisses din da yake blusteringaggressively ya daina. Ya maida kanta kan kafadunsa.Ga mamakinta samun kanta tayi da kwanciya sosai a kafadun nasa..kamar dama canjiran wannan damar take yi.Kasancewar ya kere ta a tsawo sai da ya rankwafa, hakan sai ya zamanto tamkar ya boye ta ne gabadaya cikin jikinsa. Cikin kunnenta da muryarsa mai tsananin taushi da yawan kashe mata jiki yace da ita. “Are we still friends? Shiru Hafsat ta yi kamar ruwa ya cinye ta, ruwan hawayenta sai ya kara yawa da jin kalamansa yana sauka a gadon bayansa. Janye jikinta ta yi a hankali ta durkushe a kan kafafunta, shi ma sai ya bi ta ya tsugunna a gabanta irin tsugunnon neman afuwa. Fuskarta ta sanya a tsakanin cinyoyinta ta ki dagowa ta kalle shi. Sake tausasa muryarshi ya yi ya rankwafa saitin kunnenta. “Hafsat and Abdulazeez are meant to be together forever! Auren kwangilar, ya kare ne don ya gyara auren,ya tsaftace shi daga kuskuren da aka tafka wajen gina shi, ki sa wannan a ranki. So please ki kyale zuciyarki ta huta ta samu abinda ta ke so, ki daina takura mata a banza. I know it will hurt, but you donno how much it deeply hurtthe culprit.(Nasan laifin nawa da ciwo, amma baki san yadda yake azabtar da mai laifin ba). Yadda tawa zuciyar ta kasa zama lafiya kema taki ba za ta taba zama ba sai ta dawo ga mamallakinta. Zan barki ki kwanta Hafsat, sai da safe. Amma ki yi min alfarma ki kunna wayarki, I just want to be saying good night. Zan samu Hafsah??? Nan ma shiru, kamar da dutse yake magana, kuma ta ki dagowa. A wurin Hafsat in ma da gaske Abdulazeez yake maganganun da yake yi ya zo a matukar makare (very late) lokacin da zuciyarta ta riga ta kangare da karbar rayuwa a duk yadda tazo mata. Ta riga ta koya mata hakura dashi da duk dadi duk wuya daga lokacin da ya gaya matain written (a rubuce) ya zabi Muazatu akan ta. Cikin damuwa ya ce. Hafsat in ba ki dago kin amsa ni ba, ki tabbata zan kwana a dakinki. I will make sure na yi abin da Mammanki za ta maida min ke a gobe. Zan yi abin da na shekara ban taba yia nawa gidan bayau a gidanta. Wallahi Hafsat da gaske nake, za mu yi first night dinmu yau a dakin nan idan ba ki dago kin min magana ba. Daga intonation din muryarshi ta fahimci babu wasa cikin alamarinsa, wani irin tsoro ya shige ta da tashin hankali. Ta cira kai daga tsakankanin cinyoyinta ta dago, amma ba ta dube shi ba, fuskar nan murtuk kamar hadarin gabas idanunta sun yi jazir sabida kukan da ta ci. Cikin ranta ta riga ta ci alwashin yaki da zuciyarta in dai a kan Abdulazeez ne, bata jin yanada sauran kalaman da zai kassara ta dasu. Bashi da ragowar kowanneremnant(small remaining) birbishin soyayyaa tareda ita da zai sake tasiri akanta. Wai shin ba ta basu fili ba shi da Muazatun tasa, ta bar musu gidansu kamar yadda ya bukata, ta fita daga cikin rayuwarsa da yace bata da gurbi? Me ya kawo shi inda ta ke yanzu? Abdulazeez bai yi kama da mayaudara ba, bashi da attributes dinsu ko daya, bai taba yaudararta ba ko da kuwa da kalmarI love you ne, ba ta so ya fara yanzu don kawai yana son ya farantawa iyayensa, ko don ya tsira da sauran mutuncinsa da kekwayaridanunta wanda har gobe ninkuwa yake yi akan dalilin da bata sani ba duk da ya furta saki a gareta. Ido ya zuba mata yayin da ta kawar da kai gefe taki yarda ta kalli sashen da yake, wani irin sassanyan kyau ne da ita natural wanda bai taba tsayawa ya tantance shi ba, ko kuma giyar son da ke dibansa a yanzu ce take nuna masa hakan? Ba zai iya ganewa ba. Shi dai ya san ta masa kyau a idanunsa irin yadda bai taba gani ba. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki wadda ba ta sa Hafsat ta kalle shi ba. Gefen hagunta ta ke kallo, yayin da yake zaune a damanta. Wani irin kwarjini ta yi masa a yau, ya ji yana shakkar furta abin da yake son furtawa. Zuciyar mazantakarsa ta karfafe shi da cewa, Matar ka ce fa! Mace ba ta taba yi wa mijinta kwarjini sai in ya tabbatar shi din mai tarin laifi ne a gare ta. Yes.He admit shi mai laifi ne da yafiyarta kawai yake nema a yanzu. He is dying to haveeven a single word from her amma ga dukkan alamu ba zai samu daga Hafsat din ba. She is no longer the Hafsat he know mai son kyautata masa da neman kulawarsa ta kowacce fuska. Har in bata samu hakan ba ta shiga wani hali. Wannan kallo daya zaka yi mata ka fahimci so kawai ta ke ya tashi a wurinnan ya rabu da ita, ya kyale ta ya fita daga rayuwarta, zamansa tare da ita a yau ya takura ta (ba kamar wancan zamanin ba da babu abinda take so irin ta ganshi a kusa da itaby her side koda ba hira suke yi ba).Ko bata furta hakan ba an ce labarin zuciya a tambayi fuska. Idanuwan ta sun fada, yanayin ta bakidaya ya nuna. Wani abu da shi kuma bai shirya wa a yanzun ba, daga nan har gaban abada (wato fita daga sabgar tata). Gyara zamansa ya yi ya kamo habarta da hannunsa na dama, a kokarinsa na son su dubi junafor the first time don yana tantamar anya Hafsat din da ya sani ce wannan? Amma maimakon hakan Hafsat sai ta rufe idanunta gabadaya, the long eye-lashes suka bi idon suka kwanta duk da a jike suke da hawaye. Rufe idon da ya birkita shi sai jin saukar harshensa ta yi saman fuskarta yana dauke hawayen da ke zuba, alamarin da ya rikita Hafsat ya soma kwace duk wasu makaman yakinta, amma a hakan kokari ta ke ta nuna bijirewarta, hankalinta in ya yi dubu ya tashi da ta tuna babu aure ko na kwangilar a tsakaninsu, ta kuma bude dukkan idanunta ta dube shi. Sai da ta gwammace ba ta bude idon ba don gaba daya kwayar idon Abdulazeez tsoro ta bata, bata taba ganin sa cikin wannan halin ba(lasciviousness) zallah a cikinsu irin wadda bata taba gani daga gare shi ba. Baya ta yi da karfi ya riko ta.Kada ki bari ta kai mu da haka Hafsah...., kada ki bari in sa miki karfi. Na ce na maida ke, ba tun yau ba Hafsah... kina nan a matsayin matata da amincewar kowa ko babu, and I need my wife NOW!” ”SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Sarai ta fahimci manufar Abdulazeez cikin kwayan idanunsa kadai koda bai janye duk wani hijabi dake tsakaninsu a yau ya furta da bakinsa ba.Hafsat ta fahimci kukatactic dinta, ko karfinta bai isa ya raba ta da Abdulazeez a yau ba, ko daga irin rikon da yayi mata, ta soma tunano abin da zai iya faruwa in ta barshi ya rinjaye ta.The worst thingkusancinsu ga iyayensu, ga ta ga Mammah, sannan auren ma duk da yace ya mayar ita bata yarda da sahihanci da ingancinsa ba, ta fi yadda da gurbatacce ne tun waazin data ji a rediyo shekaranjiya akan yin yarjejeniya a cikin aure.Sai ta soma roko muryarta na shaking ba tare dasanin hakan kara triggeringdin shi yake yi ba. Ta kankame jikinta wuri guda ganin kamar baisan ma tana yi ba lamarin kara girmama yake yi, kafin da azama ta mike tsaye, muryarta na karkarwa hadi da jikinta gabadaya ta soma maganar da ba ta yi niyya ba tana hawaye. Yaya Azeez me ya sa haka don Allah? Im no longer your wife. Kuma a gidanmu? Na hada ka da Allah ka tafi, ka yi hakuri na yi maka alkawarin zan saurare ka da duk abin da ka zo da shi, amma ba yau ba........ Daga inda ta barshi zaune a kasa ba sauran kuzari ko na cikin cokali a tare da shi ya daga jikakkun idanunsa ya dube ta, tayi azamar sunkuyar da kanta. Then let me hug you properly Hafsah..... Ba zan yi wani abun bayan hakan baI promised.I just want to be closer to you again, in tabbatar Im not that far from you..... Ba yadda ta iya, tana ji kumatana gani ya mike, da wani irin rawar jiki ya rungume tan.Wata irin tight runguma tamkar zai tsaga zuciyarsa ya sanyata ciki don tsoron kada wani abu wai shi rabuwa ya sakegittawa a tsakanin su. Wanda ya tabbatar target din iyayensa kenan bazasu taba sauraron sa ba. Babu wani uzri da zai kawo da zai yi tasiri a zukatansu. Hafsat din dama ita ce hope dinsa gata itama yau ta bashi mamaki, alamu sun nuna ko a da tana son sa kamar yadda ya dade da fahimta to yanzu ta daina son sa.Kanta na tsakiyar kirjinsa duk suka yi shiru, basa komai sai sauraron bugun zuciyar junansu. Kowanne tunanin da yake daban ne amma akan dan uwansa ne. Ita dai Hafsat a nata bangaren, Muazatu ce a kahon zuciyarta, ta tsaya mata a makogaro ta ki wucewa da wani irin kishi mai tsanani wanda ya sababba mata tsanar Abdulazeezdin bakidayadon sanin irin zurfin son da ya ke mata. How could she live with a husband like him zuciyarsa na ga watanta? Abinda ta jura a baya ko kusa bazata iya jurar rabin-rabin sa yanzu ba saboda ta fara sanin ciwon kanta, don haka maganar su mayar da wannan gallababben auren a gareta ma bata taso ba ta je ta cigaba da kwankwadar bakin cikin Muazatu.Sai dai a yadda ya zo yau ya soma sanya shakku a zuciyarta;could all these be fake? Ana karya da emotionna zuciya da gangar jiki kuwa? Bai taba zama irin yau a gare ta ba. Jikinsa kansa wani irin rawa yake da ya samu ya rungumetan yadda ya bukata. To ina ya kai Muazatun? Fatanta dai a yanzu ya tafi, kada wani ya ji motsinsu a gidan nan ina za ta sanya kanta? Ina alkawarin da ta yi wa Daddy? Zamewa ta yi daga jikinsa ta isa ga wardrove ta fiddo doguwar riga da sauri ta sanya, saboda rikicewa a baibai ta sanya rigar. Ta dade da manta cewatawul ne kawai a jikinta. Koda suke auren ai bai taba kare mata kallo haka ba sai yau da batasan sunan auren nasu ba? Gashin kanta tarwatse a kafadunta duk ya hargitse, duk yana tsayeinda ta barshi yana kallonta daga ya koma bisa gadonta ya kishingide.Yadda ta ke yin komai a gaggauce ga hawaye na bulbula duk sai ta bashi tausayi. “Please go Yaya Azeez... help me and go. Ya kalli cikin idanunta ya lumshe mata lumsassun idanuwansa. I will go Hafsah, but on one condition; switch on your phone. Ta sa bayan hannunta ta share idonta, a kagare ta ce. Tana hannun Daddy!. Hannu ya zura cikin aljihun sassalkarmakubar shaddagetzner da ke jikinsa wadda zuwa yanzu duk tayi squeezing ya fiddo babbar wayarsa ya mika mata. Use mine, I will call you tonight. (Yi amfani da tawa, zan kiraki cikin dare). Karasowa ta yi tsakiyar dakin inda yake zaune a kan rug ta mika hannu don ta karba ba wai don ta amince wa zuciyarta za ta yi abin da ya ce din ba, aah sai don ta samu ya tafi. Amma sai ya hada hannun nata da wayar ya janyo ta ta fado bisa cinyoyinsa. Hannayensa ya sa ya zagaye ta ya kwantar da kai bisa kafadarta, da muryar da a yanzu shi kansa ya ke tantamar kasantuwarta mallakinsa ya sake maimaita tambayar da yayi mata tun farkon shigowarsa dakin bata bashi amsa ba. Hafsah are we still friends? Rufe idanunta ta yi, cikin kokawa da numfashi hadi datsokar naman da ke cikin kirjinta (zuciya), wadda ke yi mata wani irin kai-kawo da sabon son Abdulazeez data binne da ransa ya taso bakidaya ya soma yabanya. Girgiza kai ta yi kai tsaye cikin rawar murya ta ce. No, we are not. Ko da na ce Im sorry Hafsah? Mikewa ta yi da niyyar gudu ya sake fizgo ta, ya kankame ta cikin jikinsa. Dubi yadda na zama Hafsah saboda rashinki, ko abinci ba na ci, bana iya aiki a ofis, bana iya shiga court, ba na barci Hafsah, ban san na aikata kuskure mafi muni ga rayuwa ta ba sai na ranar da na dawo daga Jimeta babu ke a gidan Hafsah! Sometimes our mistakes serves as an instrument of improving our imperfections and shortcomings. Daddy da Mammah sun shirya azabtar da ni a kan kuskurena Hafsah, amma in muka hada kai muka nuna musu muna son juna dole su kyalemu mu koma aurenmu. In sun ki Hafsat zan basu mamaki; sai dai nima in dawo nan mu zauna tare, amma komai mai sauki ne in kina bayana. Na rantse miki ba irin rayuwar da mukayi zamu maimaita ba ki daina tunanin komai ki dauke shi bygone. Ki tausayawa Abdulazeez dinki, ba shi da kowa yanzu a gidan nan daga Allah sai ke....!!!. Duk wasu kalamai na namiji mai hikima Abdulazeez ya yi amfani da su yau a kunnen Hafsat don ya wanke laifinsa, tare da jaddada mata babu wata mace a zuciyarsa sai ita. Mace mai rauni da saurin karaya, hadi da kasancewar zuciyar ta riga tanarke tayi raga-raga a soyayya na lokaci mai tsawo ba tareda ta samu martani ba. Yau har abinda mafarkinta bai taba bata ba Abdulazeez ya gaya mata. Tuni ta mance da wata Muazatu, kashedin Daddy da duk batancin da Abdulazeez ya yi mata.Ta nemi duka makaman yakinta ta rasa duk kuwa da yadda tayi musu kyakkyawan riko a baya.Wadannan kalaman na Abdulazeez na yan mintoci sun wanke duk wasu kasurgumanlaifukan sa da ta dade tana kallonsa dasu. A karshe ya ce mata aurensu yana nan ba abinda ya same shi tunda dama saki daya yayi,kuma tun tana Jimeta ya maida ta. Ta kashe waya saboda shi da tuni ya gaya mata. Amma zai kara bincike a wurin malamai shima. Wadannan sauran igiyoyin biyu kuma zai kiyaye su yadda zai kiyaye ransatill eternity! Tana so ta tambaye shi zancen Muazatu ba ta so ta bata wannan mooddin da suke ciki. Wanda tsayin a shekara guda da watanninda suka yi gida daya basu taba kasancewa a cikin kwatankwacin irinsa ba. Kuma bata so ta bude baki tayi magana yaji kalaman bakinta kada ya ga hucewarta da yawa.Don haka ba ta dai ce komai ba, amma labarin zuciya a tambayi fuska. A fuskarta ya ga sassauci,kuma a kwayar idanunta yaga soyayyardake zuciyarta da yayi zaton tayi expirena regaininggradually (farfadowa a hankali). Tashi ta yi daga jikinsa ta koma gefen gado ta zauna. Mikewa ya yi ya kawo mata wayar har inda ta koma tazauna din. Ta karba ta ajiye a gefe ba tare da ta dube shi ba, ta ce. Please go, its almost past twelve Yaya Azeez. Za ka iya karanto damuwar da zamansa har wannan lokacin a dakin ya jefa ta a sautin muryarta kuma zaka iya gani akan kyakkyawar fuskarta karara. Kanta ya zo ya tsaya ya zuba hannayensa duka cikin aljihun kaftaninsa ya ce. I will. Amma me zan samu daga amaryata Hafsah da zai sa in yi barci mai dadi a yau? Tsuke baki ta yi, sannan ta yi kicin-kicin da fuska, ta soma kunkuninta. Bakomai take cewa cikin kunkunin nata ba banda (nidai don Allah ka tafi)ya kasa jin me take cewa. Lebunanta biyu ya kama na sama dana kasa da yatsunsa biyu da babban yatsan sa ibham da dan ali sabbab ya matse da karfi. Hannu ta kai ta doke hannunsa. Da mamaki yace. Hafsah!!! Ta ce a kumbure. Naam. Ni ki ke bugewa? Bata yi niyyar magana ba amma ta san halin sa saraiabu kadan zai ce ta masa rashin kunya koda shine bashi da gaskiya. Idonta ya cicciko da kwallah tace. To ba kai ne ba? Gashi ka kumbura min lebe.I just want you to go. Kugunsa ya kama da dukkan hannayensa daga tsaye yana dubanta da wata irin siga. Idan na ki fa? I will not use your phone.Ta amsa da sauri. “Ok, lemme go now!. Ya ci gaba da tsayuwar kuma, yana kallon ta kamar ya hadiye ta. Dafe kanta ta yi, sabida tsayuwar tasa a kanta na making dinta unease. Kanta har ya fara sarawa. Hafsah! Ya sake kiranta, wannan karon sigar kiran da tasirinsa tun daga kwakwalwarta har yatsun kafarta. Dagowa ta yi a hankali ta dube shi da rinannun idanunta.Sai dai kuma bata jima ba da dagowar da sauri ta maida kanta kasa. Bai taba yi mata wannan deep and lingering look din ba. Kamar yadda ya ce din ne, he just need his wife ta ga hakan a kwayar idanunsa. Hafsat ta yarda in ba ta lallaba Yaya Azeez ya tafi ba yau zai kwanan mata a daki, ya hada ta da abin kunyar da ba ta da inda za ta kai nauyinsa. Yaya Azeez don Allah ka tafi, call me as soon ka isa gida, we will talk about it. Ta fada cikin sanyin murya, wadda ke nuna babu fushinsa a zuciyarta. Tsugunnawa ya yi ya dafa gwiwoyinta da hannayensa biyu. Tunani nake Hafsah ko na je gidan wahala zan sha. Damuwa bazata barni inyi barci ba. Yau so nake na zama mijin Hafsah na haqiqah, ta yadda zan bar ma Mammah tabon da ba za ta iya raba mu ba. ButIm not sure and Im afraid ko auren ya maidu ko bai maidu ba, wannan shine damuwata Hafsah. Yanzu za ta iya raba mu easily (asaukake)tunda ban tabbatar da aurena ba, babu iddata akanki. Magana yake da muryar da bai taba yi wa wata diya mace magana da irinta ba. Ita kanta Hafsan da ake yi wa maganar kunya ta jefa ta kuma ba sosai take jin ta ba. Abdulazeez ya kai hannu ya dago habarta, runtse idanunta ta yi saboda har gobe wannan respect din da ta ke ganin Abdulazeez da shi na babban Yayansu yana nan ba abinda ya canza, aka zo aka kara nauyin aure akan wancan. Yau kuma ga shi ya sanya ta a gaba yana gaya mata maganganun da suka fi karfin hankalinta. Kwantar da kanshi ya yi a cinyoyinta abin da ya kara ninka kunyar tata.Please Hafsah tell Mammah you love your husband ko da ba kya sona. I will make sure I made it realistic, I will teach you how to, balle ma na san kina sona tuntuni ko Hafsah? Ba za ki hukunta Yayanki a kan kuskurensa ba, bazaki duba baya ba gaba kawai zaki kalla ko? Kin min uzuri mai yawa a cikin zamanmu, ina rokon ki kara min da wannan ko da shi ne zai zama na karshe. Ki kula da wayar, ki barta a jikinki, a vibration. Ta ce. Toh!. Dasauri, don dai ta samu ya tafi. Ya mike a kasalance, ya zura hannayensa cikin aljihun wandonsa. Ya soma takawa zai fice, sai kuma ya juyo. Ba zan samu komai ba Hafsah? Not even a single good night kiss??? Rufe fuskarta ta yi da dukkan tafukanta. Me kuma yayi saura? Abdulazeez ya amayar da komai dake cikinsa wata da watanni da bata taba zaton ma irinmaganganun zasu iya fitowa daga bakinsa ba. Cikin rawar murya tace. Yaya Azeez ka je don Allah... I want to be alone!. Jikinsa ba lakka, cikin wani irin yanayi ya bar gidan. ********* A sassan Daddy suna hirar tsakar dareshi da Mammah, sun yi barci sun farka suna hirar alamuran yayansu, masu sakin da masu karatuabroad, suka ji alamun fitar mota daga gidansu. Ba karamin kaduwa sukai ba. Da gudu suka isa ga taga suka daga labule. (GMC Terrain) din Abdulazeez suka gani tana fita a hankali, bayan ya fita maigadi ya maida gate din ya rufe. Azeez a gidan nan at this time? Mammah ta fada cikin mamaki tana kallon agogo. Karfe biyu daidai na dare. Dariya Daddy ya yi ciki-ciki ya koma gadonsa ya kwanta ya harde kafafunsa, amma bai yi magana ba. Sababi ta kama yi ita kadai kamar ta ci babu, kamar da uban nashi ta ke tunda dai shi ai baya nan bai san tana yi ba. Zancen da tafi nanatawa;zai zo gobe ya tadda ni. Me Abdulazeez ke yi mata cikin gida a wannan tsakar daren? Har ta yi ta gama Daddy bai ce uffan ba. Dankwalinta ta dauka tana shirin barin dakin zuwa na Hafsahita ta bata amsar tambayarta tunda Daddy ya mata banza. A fusace Ambassador Hamza ya fizgo ta. Saura kadan ta sha kasa, Allah ya taimake ta ta fada gefen jikinsa. A kausashe ya ce Maryama!Sau nawa zan gaya miki ki fita harkar yaran nan? Wallahi za ki sha kunya in ba ki kama girmanki ba. Tsakanin mace da miji sai Allah, ki zuba musu ido. Ta hakura da fita wajen Hafsat ne kawai ba don ta yarda da abin da ya fada ba, a wurin ta babu komai tsakanin Abdulazeez da Hafsat sai kiyayyah! Kiyayyar sa gareta a fili take in har Daddy zaiyi adalci, wata yaudarar dai yake son sake shirya mata ko wata kwangilar irin wadda ya kware akai.Ta hakura ne ba don amincewa da kalaman Daddy ba sai don ta samu damar yin tunanin matakin da za ta dauka a kansugobe. Washegarin ranar Uncle Abdulkarim ya tafi Lagos neman auren Muazatu Rufai wa AbdulazeezDakata. Hafsat kuwa tun fitar sadaga dakinta ta kashe wayarsa da ya bata. Ba don ba ta son yin magana da shi ba, sai don tana ganin yin hakan zai zamo tamkar hainci da cin amanaga Daddy. ****** Labarin da tsohon minista Abdulkarim Dakata ya zo wa da dan sa tsohon Ambassador Hamza Atikuda mai dakinsa bai musu dadi ba, ya karya duk wani budgetdinsu na gallazawa Abdulazeez da suka yi niyyar yi da auren masoyiyarsa da a yanzu suka gama fahimtar baya muradi. Attorney General Habib Rufai, ya ce Abdulazeez ya yi hakuri ya gaji da rashin tabbas dinsa da rashin tsayayyar magana daga shi har iyayensa, ya bada auren yarsa ga Barrister Muntada Akilu Lawal sun gama komai, jira suke a sallame ta daga asibiti a daura aure. Duk da haka Daddy bai yi niyyar gaya masa ba, ya kudire a ransa sai ya gwada shi again a kan Muazatu don tabbatar da zancenta ya mutu a zuciyarsa ko kuwa tana kasa tana dabo ne??? Da safe Hafsat ta shiga gaida Mammah a dakinta kamar yadda ta saba bayan fitar Daddy office. Ciki-ciki ta amsa mata, ko darajar kallo bata samu ba. Hafsat ba ta lura ba, don dama cikin kwanakin Mamman nasu ba fiye walwala ta yi ba. Ta juya zuwa closet din Mammah din tana gyara mata, kayan wankinta da aka kawo daga wanki da guga ta ke shirya kowanne a bangarensa. Maryam Dakata yar kwalisa ce ta karshe. Bangaren Vlisco daban, na laces, na atamfofi, na material, na shadda kowanne da inda Hafsah ke masa matsugunni, ba za ka lalace da kallo ba sai ka je shoe rackdinta, ga bags ahangerdesign daban - daban. Ba ta san cewa daga bayanta Mammah binta ta ke da kallo ba. Hatta tafiyarta sai da ta yi observing (duba ta filla-filla) ba ta ga komai ya sauya ba, kai! Mammah kenan!Wata ajiyar zuciya ta saki wadda ta shiga kunnen Hafsah, ta kuwa juyo ta dube ta tayi maza ta daure fuska. Tana gamawa ta fito daga closet din za ta koma daki ta kafa sanaar tata (tunanin Abdulazeez) Mammah ta kira sunanta. Dawowa ta yi ta zauna a kasan kafafunta, don ta lura magana ce a bakin Mammah. A nitse Maryam Dakata ta dubeta ta soma magana. Sabida miji ya sake ki kin daina karatu ko? Za ki yi asarar komai ba auren ba future? Saboda shi ne autan maza wanda aka ce daga kanshi maza sun kare an daina haihuwarsu? Nutsar da kanta kasa ta yi sosai tana jin faduwar gaba. Mammah ta ci gaba. To bude kunnuwanki da kyau ki jini. Sakin aure ba kanki farau ba, ba shi ne karshen rayuwar diya mace ba! It just means wannan mijin ba ya yi da ita, watanta wadda ta fi ta wani abuyake so. Me ya kamata ita wannan mace ta yi in ita mai hankali ce? Tuni idanuwanta suka kawo ruwa, a bisa dalilin da ba ta tantance shi ba. Da ke nake magaan Addah, idan macen da miji ya ce ba ya yi da ita, watanta yake so mai zurfin ilmi, ta matsa ta ba shi wuri ya kawo wadda tayi daidai da raayin sa, in ita mai hankali ce da sanin ciwon kaime ya kamata ta yi? A wannan gabar,wannan matakin, ta riga ta gama fahimtar abin da Mammanta ke ankarar da ita. Sai dai zuciyarta da soyayya ta riga ta gama illatawa ta lullube ruf,har babu masaka tsinke jin zafin kalaman Mammah ta ke a kan Dan ta, wanda ita ta tsugunna ta haifi abintaballe tace bata kaunarsa, amma cikin kalamanta kaf babu uzuri ko sanayyaa gareshi ko daya, indirectly she want her to do away with him kawai don yayi kuskuren da babu wanda yake sama da aikata shi a matsayin mu na yan adam,don haka ta kama mamakinta a can karkashin zuciyarta; tambayar kanta take ita din (Maryam Dakata) shin wace irin uwa ce? Ashe gaskiyar Abdulazeez da ya ce ba shi da kowa yanzu a gidan nan daga ita Hafsat sai Allah! Sun dauka da zafi har fiye da ita da aka yi wa sakin. Shin Mammah na tunanin akwai wata halitta da za ta aje a doron duniya daga jinin jikinta da za ta yi mata laifin da za ta kasa yafewa? Ran Hajiya Maryam in yayi dubu to ya kai kololuwar baci da reaction din Hafsat, mai nuna babu jin zafin Abdulazeez a ranta, bata ji zafin komai da Abdulazeez yayi gareta ba. Kada dai tana can wajen miji tana shan AC ta yi sakacin da dare daya kacal Abdulazeez ya juye mata kwanya? Da salon yaudararsa dacontracts din da ya kware akai? Tsawa ta daka mata, Answer me I said...!. (Nace ki bani amsa). Hafsat ta soma kuka, cikin rishin kukan ta ce, She has to forget him and move forward... (sai ta manta da shi ta fuskanci gaba), Ta gyada kai cikin gamsuwa da abin da ta furta da bakinta, sannan ta nunata da dan yatsa(abinda bata taba yi ba). Kin fadi amsa daidai da abin da ya kamace ki. Forget him... move forward...thinkbig for your future!Ki je ki karkade takardunki gobe ki koma makaranta. Ni da kaina zan dinga kai ki ina dauko ki ba direba ba. Hafsat ta gyada kai. Umartarta ta yi da ta tashi ta ba ta wuri, mai nuna har yanzu ranta a bace yake. Sum-sum-sum ta mike kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, har ta kai bakin kofa ta tsinto muryar Mammah a tsakiyar kanta. Ina wayar da ya baki? Bani ita nan! Saura kadan Hafsat ta saki fitsari a wando don kaduwa da mamaki hadi da tsoro. Amma ba ta ce komai ba, a sanyaye ta murda kofar ta fita, ba ta yi mintuna biyu ba ta dawo da galleliyar wayar Abdulazeez ta russuna ta mika mata. Mammah ta jinjina kai sannan ta karba ta yi jifa da wayar can karshen gadonta. Ko da Hafsat ta koma daki toilet ta shige ta kulle kanta, guilty conscienceya bi ya dabaibaye ta, ta shiga tunanin da wane ido zata kara kallon idanun Mammah, ga kuma son mijin da tausayinsawanda shi yafi komai yawa a daidai wannan lokacin. Da ta san Mammah za ta kwace wayar da jiya ba ta kashe ta ba, da ta barta sun yi sallama da juna, da ta gaya masa how much she love and missed him, da ta gaya masa ta yafe masa baki da baki. Da ta yi masa goodnight kiss din da ya nema ta ki yi masa ta kore shi dole.Yanzu kam ta san da wuya su kara kadaicewa nan kusa tunda Mammah ta gano me ya faru jiya. Kuka ta dinga yi wanda ba ya mata wahala. Ita yanzu wane karatu za ta iya? Ta dade da tsanar karatun. Babu komai a zuciya da kwakwalwarta sai Abdulazeez Hamzah Atiku!!! Aiki yake a office Barrister Surayyah ta shigo, ransa ya yi mummunan baci, ta zo ne kawai ta kara masa damuwa kan wacce yake ciki. Da surutanta na banza na rashin kamun kai. Ya tattare girar sama da ta kasa ya maida fuskar kamar hadarin gabas. Wani irin kwarjini ya yi mata, hakan yasa ta hau inda-inda na abin da ya kawo ta, wai photocopy za ta yi a ofishinsa nasu injin ya samu matsala. Nuni kawai ya yi mata da machine din ya mike ya soma tattare takardunsa da systemdinsa ya cire wayarsa daga caji ya bar mata ofishin. Ya bawa masinjansa umarnin in ta fito ya rufe masa ofishin. Ba tun yau ba hakan ta sha faruwa, Barrister Surayyah Saidu ya kwana da sanin sonsa ta ke yi a matsayinta na matar aure kuma. Rashin samun fuska ya hana ta fitowa gaba da gaba ta gaya masa. Tafe yake a kan hanyar Asokoro yana tunanin abin yana Allah wadai da wannan rikitaccen zamani da Allah ya kawo mu. Saboda takurar Surayya da ire-irenta cikin Abuja ya soma tunanin komawa karo karatunsa (L.LM) ya fara gajiya da Federal High Court. Bai samu wannan matsalar a Ibadan ba zamanin karatunsa. Bari dai ya gama da kalubalen da ke fuskantarsa yanzu. He wanted to move forward... Har ya iso gidansu tunani yake yi, tunanin abin da ya sa Hafsat kin yarda ta yi amfani da wayar da ya bata jiya. Wane irin lallashi ko ban baki ko ban hakuri kuma zai yi mata bayan wanda ya kwashe awanni biyar cur yana yi mata jiya ta fahimce shi? Ita ce kadai hope dinsa a gidan nan. Kusan tare suka shigo gidan shi da Daddy da ke kwance a bayan mota hyundai Salisu ya dawo da shi daga ofis. Shi ya karba ma Daddyn tarkacen hannunshi, ya bude sliding doorta shiga falon farko, Ismael ya fara hanga yana kallon tashar Sunnah T.V, babu Mammah da Hafsat suna kitchen suna aikin abincin dare. Ismael ya yi musu sannu da zuwa suka wuce shi zuwa sassan Daddy. Har gaban Daddy ya isa ya mika mishi kayan, sannan ya samu waje ya zauna ya tankwashe kafafunsa yadda ya saba in yana gabansu cikin tsantsan ladabi. Daddy ya ajiye hularsa ya ce, Yanzu da ma zan kira ka, kakanka ya dawo daga Lagos. Wani irin bugawa kirjinsa ya yi ya sunkuyar da kansa kasa. Daidai lokacin da Mammah ta shigo dauke da Jug da cups da bowldata shako da dambun naman kaza ta jero a kan karamin tray zuwa gaban Daddyn. Dambun naman ya soma ci wanda ya zame masa alada, Abdulazeez ya gaida Mammah ta kauda kai kafin ta amsa kamar ba ta so, zuciyarsa ta yi masa ba dadi jikinsa ya kara yin laasar. Daddy ya yi kamar bai ga halin da yake ciki ba ya dora bayani. Sun ba ka aure. Sati mai zuwa kakan naka ya tsayar za su koma a daura aure. Na bada sadaki dubu dari biyu amma kawun yaki karba ya dawo min da su ya biya daga aljihunsa. Sai ka je ka fara shirin daurin aure da abokanka da gyaran gida ko fenti ne ka sake, ke kuma Maryama ku shirya ku wuce Kano a can zaa yi komai. Da sauri ta ce. Ai ba sai na je ba, auren dan fari? Inna Hafsatu da su Zuwaira zasu yi duk abin da ya kamata, ga iyayensa su Furairah duk sun isa gabatar da komai. In an kawo amarya na je in ga dakin yar masu kudi da mulki. Allah ya sanya alkhairi. Tsam ta mike ta bar musu falon. Zuciyarta na wani irin zafi. Kafin ta kai kicin ta share hawaye sau uku. Saboda ita bata san minister Abdulkarim yazo da bayanin baza su bawa Abdulazeez Muazatu ba, sun mata miji. Bata san duk bayanin Daddy ne ya shirya abinsa ba. Tanashiga ta tadda Hafsat ta takarkare tana ta suyar dankali, tun jiya ta lura saboda fadan da ta yi mata ta daina walwala kwata-kwata, yau ta kai ta shoppinga Sahad na komawa makaranta da laasar har suka zo gida uffan ba ta ce mata ba. Ita ma sai ta basar da ita. A ranta mamaki ta ke yi tana fadin ta yaro kyau ta ke......Yau ni Hafsat kewa fushi sabida da namiji. Amma mu zuba ni da ku. Yadda na hada wannan auren cikin mutunci kuka hada baki kuka tozarta ni ya kare har abada! Zan ga karshen soyayyah. Ta ce. Yi a hankali kada ki kone hannu. Ta ce a hankali ba tareda ta juyo ba. Ai na gama, kwashewa nake sai in je in yi sallah. Ta ce, To jira ni in kwashe abincin duka, mu je sallar tare. Hafsat ta ce, Toh. Ta jingina da kitchen cabinet tana jiranta bayan ta gama nata. Sai ga Abdulazeez har cikin kitchen din. Suna hada ido gaban Hafsat ya yi mummunan faduwa. Wata irin rama ta gano a jikinsa da fuskarsa, idanunsa sun kada yadda suke yi in yana tsananin jin yunwa ya dawo daga ofis. Ta yi hanzarin sunkuyar da kanta, tana karbar sakon bugun zuciyarta. Mammah ta juyo ta dube shi ta ci gaba da kwashe abincinta a warmers, a cikin ranta mamaki ta ke yau Abdulazeez ne a kitchen? Ba ta yi zaton ko hanyar kitchen din ya sani ba komai saidai yace a dauko masa kafin ya bar gidan. Ita ma zuciyarta ta tabu da ganin yadda ya sauya, ta ce. Ko lafiya? Hafsat ya dan kalla ya russunar da idanunsa. Ajiya na bata zan karba. Kai tsaye Mammah ta ce, Wayarka? Ya yi shiru. Ta ce. To in ita ce tana hannun Usman na bashi tun safe ya baka. A sanyaye ya juya ya fita daga corridor din kitchen din ya dakata yana kallon Hafsat daga nesa wadda ke fuskantar kofar shiga kitchen din. Ta dago suka hada ido, kallonta yake kallon Me ya sa ki ka yi min haka? Ita kuma ta rausayar da kai, kallonI have no idea. Ta ke yi masa. Sai ji ta yi Mammah ta buga mata ludayin miya a tsakar kanta tana fadin. Za ki wuce mu je ko sai na tsokale miki idanun munafurcin? Shashasha. Wawuya kawai! Wadda ba ta san ciwon kanta ba. Da sauri Abdulazeez ya bar wajen, yana jin sababin da ake matan har kokon ransa. Maitama ya nufa kai tsaye gidan tsohon Minister Abdulkarim Dakata, he has to cancel it all. Daddy na shirin kashe shi da ransa! Shi bai ce musu yana bukatar Muazatu yanzu ba. Ya dage sai ya aura masa harda biya masa sadaki na makudan kudi. Ko auren Hafsat da kansa aka ce ya biya, amma wannan da yake na mugunta ne an ce fenti kawai ake bukata yayi. He have a lot to tackle a gabansa ba karin aure ba. Shi ina zai kai mata biyu? Idan har igiyoyin aure uku ne daya ya ce ya saki, kuma ya ce ya mayar tun abun bai je koina ba. Ya same su complete happy familykamar yadda suke koyaushe. Tare da samarin yayansu; Shaaban da Farhan saannin Ismael da Usman ne. Ramadan ne saansa. Nan ya yi sallahr Isha, sai ya zauna a kan sajjadar ya yi shiru ya rasa abin da zai fara roka ma kansa. Wargajewar zancen aurensa da Muazatu ko dawowar Hafsat gidansa? Daga karshe sai ya daga hannu ya ce. Na bar maKa alamarina Ya Ubangiji, Ka zaba min abin da ya fi alkhairi, Ka sassauto da zuciyar Mammanah, Ka sanyaya mata, Ka sa ta afuwanta min. Abin da yake ta fada cikin adduar sa ta yau kenan. Uncle Abdulkarim ya aiko Farhan ya kira shi jin shirunsa ya yi yawa, ga shi ya ce wajensa ya zo. Sai da Farhan ya jira shi ya kammala adduoinsa, sannan ya gaya masa Daddy na jiransa. Kallo daya ya yi masa ya dubi Aunty Zuwaira ya ce. Je ki hado mindinner. Ko ba ta daraja dangin mijinta ban da iyalin Dr. Hamza Atiku.Dinner mai rai da motsi ta hado har da zazzafan black tea. Sanya shi ya yi a gaba ya ce ya cinye abincin nan a gabansa in yana so ya saurare shi. Haka ya zauna ya yi ta turawa kamar yana cin dusa. Ya bude masa gwangwanin coke yasan yana sonta sosai tun yana yaro ya bashi ya shanye, ya zuba masa ruwa ya sha. Abdulazeez ya samu ya soma regaining consciousnessdinsa. Idanun karamin Kakan na kansa ya san dai ba zai wuce damuwar auren nan da aka hana shi a Lagos ba. Sanda uban ya kira shi da maganar auren ya yi mamaki, ya ce duka-duka yaushe aka yi aurensa, how could he cope with two wives a shekarunsa? Daddy ya ce rabu da Abdulazeez, ka je ka nemo masa auren nan shi ne kawai maganinsa, ba ka sanin muhimmancin abunka sai ranar da ya kubuce maka. Ya saki mai sunan Addah, bayan ya nemo mata iyayenta. Musabbabin sakin ne har yau ba mu sani ba, ta ki fada, ya ki fada. A lokacin ne Minister Abdulkarim ya tuno yadda suka yi da Abdulazeez a kan auren Hafsat. Idan a da ya ce rashin asali ne, to ba ga shi ya bi shawarar da ya bashi a baya ya nemo mata asalin ba? Dole akwai abin da suke boyewa dukkansu,wanda ya tabbatar ya zu ba rashin asali bane, ya kuma sa a ransa yau sai ya ji shi. Sai da ya tabbatar ya samu nutsuwa ya ce da shi. “Whats wrong my grandson? (Me ya faru jika na) Sunkuyar da kai ya yi, ya kara tankwashe kafafunsa cikin matsanancin ladabi, cikin damuwa ya ce Uncle ba da yawuna Daddy yake nema min aure ba. In factwannan tsohuwar magana ce tsakanina da yarinyar na kuma dade rabona da ita. Alkawarin da na yi mata na cika shi, daya alkawarin zan yi masa rafkanuwa (wato na aurenta). Koda kuwa na azumi dari (100) ne Uncle. Alamarin ba daga ni ba ne daga Allah ne,alamari ne irin na zuciya da mutum baida iko a kanta. Ka taimake ni ka bashi hakuri ya mayar min da matata, ban san wani hakikanin so ba sai a kanta. Kuskure ne na yi,ina neman afuwa da yafiyarsu, don Allah Uncle ka taimaka mini. Cikin idanu Abdulkarim Dakata ke kallon jikan nasa, yana karanto zahirin abin da ke zuciyarshi ne zallah yake amayarwa. Ya amince gaskiyar zuciyarsa kawai yake gaya masa kuma Dr. Hamza bai gaya masa gaskiyar yadda ta kaya zuwansa Lagos wajen Attorney General ba. A matsayinsa na babba, tuni ya gano dalilin Dr. Hamza. Ya ce. A kan me ka saki matarka? Abdulazeez bai zaci wannan tambayar ba, don haka sosai ta ruda shi, ya hau kame-kame, abin da Abdulkarim Dakata ya tsinta cikin kame-kamen nasa kawai shi ne; ......Wallahi ba don bana sonta ba ne!!! Ya tausasa murya ya ce. Abdulazeez, sai na san matsalarka gabadaya zan iya dosar mahaifinka. Ka tuna ba ni na haifar masa kai ba balle in tursasa shi kan duk hukuncin da ya yiwa rayuwarka.Feel free to discuss your problem with your junior grandpa. Im at a door to help. Hakan ne ya sanya wata irin nutsuwa da aminci cikin zuciyarsa. Ya samu kansa da warware wa Abdulkarim Dakata komai tun haduwarsa da Muazatu, fitinannen son da ya samu zuciyarsa da yi mata rana daya bayan da in the first place mutuncin Babanta ya sa yake kula ta. Amma shi a a ransa ya san da farko ba son ta yake ba. Yanada buri mai yawa akan karatu da ya shafe masa tunanin soyayya ko yin aure a lokacin.Kuma ya sanar da Muazatu hakan amma rana daya ya samu kansa in ba aurenta yayi ba bazai taba nutsuwa ba. Kawo zancen Hafsat da Mammah ta yi masa rana daya, tunanin hanyoyin gujewa auren da ya yi ta yi ya rasa, don tsira da Muazatu. A karshe ya ga babu mafita (don Mammah ba da wasa ta dauki alamarin ba) ban da ya nemi Hafsat su yi auren a kan yarjejeniya na zaman auren shekara daya da watanni daidai da lokacin da Muazatu zata gama law-school. Ya gaya masa tubalan da aka gina yarjejeniyar akai daidai da burin kowannensu. Ya dan yi shiru, kansa na kasa (feeling guilty). Tsohonminista Abdulkarim ya saki baki, hanci da ido yana jin wauta da kuruciya zallarta hadi da shiga hurumin Ubangiji duk saboda soyayyah. Ya ce a ransato ita Muazatun da diamond aka kerata da dole sai an aure ta ko ta halin kaka? Abdulazeez ya kara sunkuyar da kansa cikin jin nauyin abin da zai fada. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Abdulazeez ya ja wani gwauron numfashi, sannan ya sauke shi a wahalce. Ya ba su tausayi sosai. Amma ba wanda ya nuna duk don su kara tsoratar da shi bisa kuskurensa. Baffah ya ce, Daddy ya kira Maryama ta hada shi da Hafsat. An yi saa suna tare ta dauko ta daga makaranta kan hanyarsu ta komawa gida. Hafsat na russuna murya tana gaishe da Baffa ya ki amsawa, ya bude mata nata rabon a kan don me bata gaya wa uwarta ba lokacin da Abdulazeez ya ce su yi yarjejeniya? Fada yake mata ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Fadan da bata taba zaton ya iya ba. Kullum shi mai tausasawa ne a gareta. Ya gaya mata hukuncin abin da suka aikata. Hafsat da gari banza ma kuka ta ke yi balle yau? Baffa fa! Mahaifin Daddy gabadaya. Bai bata damar cewa komai ba ya mikawa Abdulazeez wayar, Sake maimaita mata a gabana ka mayar da ita dakinta. Abdulazeez da ya hau maimaitawa sai da ya fada mata ya kai sau goma. Abdulkarim ne ya kwace wayar ya zuba masa rankwashi a tsakar ka. Ya bawa Daddy wayarsa. Adda Hafsatu ta ce, yau abin da yake so ta girka, amma wallahi ba za ta zuba masa ba. Hakuri ya dinga ba ta, amma ta kafe ba zai ci ba. Ta ce, Ai ko don albarkacin sunana da yarinyar nan ta ci ta fi karfin kalmar saki daga bakinka. Tukunna ma wace ce Muazatun? Ku hada ku aura masa mana ya san bambancin mai suna HAFSAH da sauran sunaye? Uncle Abdulkarim ya kwance musu labarin zuwansa neman auren Muazatu da yadda aka sallamo shi, ya ce har gobe ita yarinyar tana sonsa, mahaifinta ne ya ki, bai san dalilinsa ba, kuma ya yi gaggawar yi mata aure. Shi bai taba ganin mahaukacin so irin wannan ba, wanda Abdulazeez ke wa Muazatu, son da zai ja ka ka saba wa Ubangiji don ka faranta wa budurwa, ka gwammace bacin ran iyayenka a kan farin cikinta? Allah ya yi mana katanga da yayanmu da irin wannan son, yau da Abdulazeez ya auri yarinyar nan watakila ko gaida iyayensa sai ta ba shi izni. Baffa ya yi tsai! Da ransa, yana sauraron labarin da Abdulkarim ke baiwa Addah. Bai ce komai ba, amma ya gane wannan yarinyar ita ce mai farautar jikan nasa. Ya kudure a ransa nemawa Abdulazeez kariya fiye da dukkan jikokinsa don shi ko yanayin aikinsa ma hatsari gare shi. Ba su baro Kano ba sai da ya sa Abdulazeez ya yi wanka da ganyen magarya har sau uku, ya ba shi rubutu kala-kala, ya ba shi adduoi da nafilolin da zai rika yi duk daren jumaa da litinin. Ya ce kuma idan ya ki yi Allah Ya isansa. Dariya ya yi, sannan ya alkawarta masa zai yi. Ya ba shi na sauran yan uwansa ya tafi musu da shi. Tunda suka dawo gida Abuja, Mammah ta kara tsananta matakanta na tsaro a kan Hafsat da Abdulazeez, da kara toshe duk wani communication gap a tsakaninsu. Ba abin da ya dame ta da wani aurensu da aka mayar kamar ma ba ta san an yi ba, bai wani wani damu ba ya ci gaba da ayyukan gabansa cikin kwanciyar hankali. A ganinsa ba shi da damuwa yanzu a rayuwa tunda kuwa koma nisan jifa kasa zai fado,sannan hausawa suka ce wai karshen alewa kasa!. ****** Yau watan Hafsat guda da komawa makaranta, karatun session din ya kankama sosai. A watan gabadaya wani abu bai kara hada ta da Abdulazeez ba ko da gaisuwa, Mammah ta bi kowacce hanya ta sadarwa tsakaninsu ta toshe. Haka suka zauna tsayin wata biyu a gidan ba ruwan kowa da zaman dan uwansa. Idan ya taso aiki gidan yake zartowa, amma sai dai ya tsaya iya falon farko da wajen Daddy don Mammah ta hana ta fitowa ma in dai yana gidan, har sai ya gama cin abinci da hirar da suke yi tsakaninsa da Daddy da su Ismael ya bar gidan, ko giftawar Hafsat ba ya gani. Sai dai ta shige toilet ta yi kukanta mai isarta, kukan tausayin Abdulazeez dinta! Sau biyar ta ji shi a dakin Mammah ya je bata hakuri, amma ba ta tankawa. Azumi ba ta gari ta je ganin gida can Sokoto, ya tabbata da ta taimaka masa wajen tausar Mammah. Ko gaisawa za ta yi da Dr. Bashar da su Dada sai ta wayar Mammah, kuma a gabanta. Ta gama ta karbe. Time-table ta ke bi wajen kai ta makaranta, ita kanta ta gaji da wannan zirga-zirgar da ta sanya kanta babu gaira babu dalili don abu ne da bata saba ba (tukin mota), amma tsabar kada Abdulazeez ya samu damar kebewa da Hafsat ya sa ta hana Salisu kai ta da daukotan. Ranar yau ta kasance asabar, sai suka wayi gari da bako a gidansu; Abdulazeez ne da jakunkunansa, ya bude dakinsa na samartaka na gidan ya ce Salisu ya shigar masa da jakunkunan ya shirya masa kayan a wardrove ya share masa dakin ya goge koina ya wanke masa bayi. Ismael ya shige nasa dakin wanda ke daura dana Abdulazeez din banda dariya ba abinda yake yi. Usman ya zo ya tadda shi yace. Kana zaton Mammah za ta barshi ya zauna ne? Ya sassauta dariyar ya ce. To ya zata yi dashi? Za ta kore shi ne shi da gidansu? Ai ni ya kyauta min, Mammah ba ta jin lallashi, an mayar da aure kuma meye na cigaba da rike masa mata?Attimes she behaves like AddaHafsatu; tough and disciplined. Tun tashinta daga barci ta ke jin scent din Abdulazeez a gidanta. Bata kawo komai ba tunda ta san yana zuwa gidan amma ba irin wannan lokacin ba sai yamma can in ya tashi ofis. Da ta yi wanka ta shiga kitchen don ta ga me za ta dafa, shi ta gani ya jona kettle yana dafa black tea dinsa wanda shi ne abin shan sa duk wayewar garin Allah, daga shi sai threequater da farar singilet. Daga bakin kofa ta tsaya tana kallon ikon Allah. Juyowa ya yi jin alamun mutum, addua yake Allah ya sa Hafsat ce ta fito ya samu ya ganta ko daga nesa ne kafin fitowar Mammah, amma sai ya ga Mamman da kanta ba sako ba. Russunnawa ya yi ya soma gaishe ta, bata amsa ba ta wuce ciki ta kunna gass ta dora ruwa. Sai ya tuna mata da shekarun yarintarsa, haka yake ba ya son a dafa masa shayi, ya fi so ya yi shi da kansa. Hafsat ta shigo tana mutstsike idonta da alama tashinta kenan daga barci, riga da wando ne na barci farare sol a jikinta marasa kauri sosai amma ba su kama jikinta ba, kanta ba kallabi ta kame tulin gashin kanta a tsakiyar kan da black hair bound. Kwata-kwata ba ta lura da shi ba ta shigo kitchen din. Kai tsaye gefen Gass-cooker ta nufa inda Mammah ke tsaye tana cika tana batsewa, ba ta lura da yanayinta ba saboda idonta ma bai gama washewa ba. Mammah ba ni aron waya zan kira Yaya Imamu, mafarkinsa na yi yanzun nan. Ba tare da ta dube ta ba, ta ce. Tana kan bed-side. Juyawar nan da za ta yi da zummar fita sai ta yi arba da Dan Ambassador Hamzah Atiku, tsaye yake jikin kitchen-cabinet ya harde hannayensa a kirji. Lumsassun idanun dake dimauta ta ke kallonta admiringly daga can kasan idanun. Zuciyarta ta ji ta harba da karfi.Yaushe rabon duniya da ayyaraye! Yaya Azeez ashe tana da rabon sake ganinsa nan kusa??? Watanni biyu masu kama da two decades. Hajiya Maryam haushi ya ishe ta ganin sun manta da ita a wurin ta tsaya ta ki ficewa, sai kallon juna suke yi da wani irin yanayi cikin kwayan idanunsu.The excessive emotions for seeing each other continue to linger in their eyes(shaukin su na ganin juna ya cigaba datsayuwa na lokaci mai tsaho cikin idanunsu). Wani uban dundu ta zuba mata sauran kadan ta fada kansa. Da sauri ya taro ta, ita kuma sai ta yi maza ta zame saboda kunyar da ta kamata. Mammah ta dube shi ta ce fitar min daga kitchen, in ji dai nan din ba gidanka ba ne? Me ma ya kawo ka da sassafen nan? Sunkuyar da kai ya yi yana shafa kansa. Mammah ai na dawo nan, the house is very wide for me (gidan yayimin fadi da yawa). Hafsat ta dafe bakin ta da hannayenta biyu ganin yadda Mammah ta fusata, cikin damuwa kuma a marairaice ta ce. Mammah we didnt talk, ni ban san ma yana kitchen din ba da ban shigo ba. Ki yi hakuri. Shi kuma ya ce. Ni ruwan zafi nake dafawa. Allah Mammah I didnt give her a second look, ki yi hakuri. Ya juye tea dinsa a mug (kofin tangaran mai zurfi) ya zuba zuma kadan a ciki ya fita. Hafsat ta ja gefe tana jin wani irin radadi a zuciyarta. Mutum da gatanshi ya koma kamar wani maraya a gidan ubansa! Shayin ma ba zaa bashi ba sai ya dafa da kansa. Da kuka wiwi ta bar kitchen din. Hajiya Maryam ta bi ta da kallo bakinta a bude, sai kuma ta girgiza kai ta yi murmushi ta juya ta ci gaba da abin da ta ke yi. Ta yi rub-da-ciki tsakiyar gadonta tana kuka ta ji an murda kofar dakinta da alamar shigowar mutum, a zatonta Mammah ce ta biyo bayanta don ta lallashe ta tasan bata iya jure ganin ta cikin bacin rai, don haka ko dagowa ta ki yi. A kan bed-side drawer na gadonta ya zauna kafarsa ta dama na bisa gadon daya na kasa. Tashi ki sha tea. Muryar Abdulazeez ta ji kamar a cikin mafarki. A firgice ta dago da hawayenta shabe-shabe suka hada ido. Hankalinsa kwance yake, da alama yanzu kam ba shi da damuwa. Waiwayawa ta yi bakin kofa a kidime kuma ta juyo ta dube shi a rikice. Na shiga uku! Ta furta a fili muryarta na rawa har ta so ta bashi dariya, mug cupdin hannunsa ya mika mata har ya sha rabin shayin. Karbi, ko sai na baki a baki? Harara ta maka masa tamkar idanun zasu fadokasa. Da kai ka ke ba ni shayi? Girarsa ya daga mata. Just taste it, mine is special....just beyond comment(ki dandana ki ji, nawa na musamman ne, fiye da yadda zaki iya sharhi. Mikewa ta yi tsakiyar gadon ta dirgo da sauri, gara ta fice daga dakin nan in ba haka bata lura bashi da matsala in Mammah ta sanya ta a turmi ta kirba tunda shi yana da Muazatu. Ita kuwa ba ta da mai damuwa da ita ta wannan fannin wanda zai tsaya ya lallasheta in ta sha dukan. Kafin ta kai kofar Abdulazeez ya riga ta, ya kuma murza key din da ke jiki. Hannu ta dora a ka za ta zuba ihuya toshe mata baki da hannun daman sa ya janyo ta tana tirjewa har gefen gadonta. A jikinsa ya zaunar da ita, ya dauko shayin ya kai bakinta. Turewa ta yida karfi tana kokarin mikewa har da zabura,da haka duk suka zubar da ragowar shayin a jikkunansu. Ga shayin da sauran zafin sa sosai amma ba ta wannan take ba. Ta yi wuf ta mike jin Mammah na buga mata kofa, iyakar rikicewa Hafsat ta rikice, iyakar rudewa ta gama rudewa, tashin hankali baro-baro ya bayyana a fuskarta. Ta soma kyarma daga tsaye tana masa kallon ka cuce ni. Murmushin mugunta ya yi mata ya karasa a nitse ya bude kofar. Hajiya Maryam ta bi shi da kallo, sannan ta shigo ciki sosai ta dubi Hafsat wadda ke tsaye fararen kayanta jike tsamo-tsamo da bakin shayi. Ido ta dan kafa mata, Hafsat ta rasa me za ta ce mata, kafin ta tattaro kalaman kare kanta Mammah ta juya ta bar musu dakin. Kuka ta saka ta yi kanshi da duka, tana isowa bata ankara da ya bude hannuwa bata fada ciki dawata itin azama ya rungume ta. Ya wani irin lumshe ido kamar bazai bude ba. Kokawar kwace kanta ta koma maimakon dukan huce haushin data yi niyya, cikin hakanya samu saar cafko bakinta ya soma kissin cikin wata irin siga mai nuna tsananinkewarsa da kishirwarsa da hakan, alamarin da ya tafiyar da ragowar kuzarin ta gabadaya jikinta ya saki bakidaya. Sai da ya tabbatar ba ta da sauran karfin fada da shi sannan ya saketa ya ja da baya ya zauna a dandaryar kasa ya rufe idanunsa yana maida numfashi, kallo daya zaka yi masa ka tabbatar ya shiga damuwar da bai taba shiga a rayuwarsa ba,cikindusashshiyar muryayace. Hafsah ya ki ke so in yi mata? Ba ta jin lallashi ko kadan, ba ta jin ban hakuri, zuciyarta kamar ta dutse.I can handle her(zan iya da ita) ki daina damun kanki. Mammah ta sanni ni ma na santa, daga ni har itaba mai iya canza wani, don haka ki koma gefe kawai kiyi kallo. Ta koma gefen gadonta ta zauna ta dafe gefen kanta dake balain sara mata. Kawai sai ta sa kuka ta kifa kai cikin cinyoyinta. Gefenta ya dawo ya zauna ta yi saurin matsawa. Wallahi ita nake so sau dubu ba kai ba, kuma wallahi na fi ka saninta, har yaushe ka zauna da ita? Kullum gudunta ka ke, sai yanzu rana tsaka bayan ka gama wulakanta ni ka zo ka ce za ka shiga tsakaninmu? Ka tafi ka auri Muazatunka tunda tace bazata hakura ba ka kyale ni da Mammah nah. Babu damuwa ko kadan a tattare da shi ya ce. Duk na ji, kuma na yarda kin fi ni saninta.Amma maganar na wulakanta ki ni ban santa ba.Idan kuma akwai wata rana da hakan ta faru a zamanmu ki gaya min ita, na yi kuskure na yi saki, kuma na ce na mayar a gaban kowa in ga wanda ya isa ya ce bai maidu ba. Sannan ta wani bangaren I might not call it a mistake; da yardarki aka yi shi (sakin) saboda ba ki san daraja ta ba, kin fi son boko a kaina. Na ba ki bokonki nace ki tsufa kina yi karewa, yanzu kuma ki fi kowa daukar zafi wai an sake ki? To an sake kin, kuma an ce an mayar da ke sau sabain in kin isa ki ce babu auren kwata-kwata damuwar ki ce. Na ba ki minti talatin ki yi wanka ki yi min kwalliya, you are looking shabby, ki sama min abin da zan citunda kin zubar min da tea kuma Mammanki ba bani za ta yi ba tunda Azumi ba ta nan. Ya mike ya yi ficewarsa ya barta nan a zaune kamar an kafe ta. Ashe gaskiya ne da ta ke ji ana fadinwai maza ba su da kunya? Sai dai wasu daga cikin kalamansa sun tsaya mata a rai, ta nutsu tana analysing(duba su filla-filla) tana dora su a sikeli na hankali da adalci.... Ba ta san darajarsa ba! She is afterstudies morethan the marriage itself. Da yardarta aka yi saki, aka yi contract, aka shirya komai aka tsara shi daidai da burin kowannensu. Kamata ya yi yanzun da ya yi nadama ya yi damarar gyara kuskurensa ta ba shi goyon baya su hadu su gyara kuskurensu tare, su nemi afuwar iyayensu game da yaudarar da suka yi musu a sirrance hadi da yafiyar Allah na saba masa da suka yi da gangan. Adashin karkacewa daga umarnin Ubangiji da suka yi ne saboda son zuciyoyinsu suke kwasa gabadayansu a yanzu. Ko wannan soyayyar dake cin zukatansu azaba ce mai zaman kanta. Sannan takunkumin Mammah ma kadai punishment ne mai cin zuciya. To amma anya zabar farin cikinsu ita da shi a kan biyayyar Mammah abu ne da ya kamata daga gare ta?Butulcewa umarnin ta wani abu ne da ya kamata ta aikata cikin hankalin ta? Ta tabbata ta kuma amince duk abin da Mammah ke yi tana yi ne don ta daidaita rayuwarta, tana yi ne for her own well-being da kwato mata darajarta. Tana yi ne don ta samu eternalfarin cikin aure da rayuwa mai inganci har karshen rayuwar ta. Hakika takasance mai matukar rauni kwarai a kan Abdulazeez da soyayyar sa. Kada ta manta Mammah ta yi musu aure cikin mutunci, ta so su zauna da juna cikin aminci su kaunaci juna da zuciya daya, amma suka hadu ita da shi suka yaudare ta, Eh, yaudara mana? They blackmailed her! She didnt deserve such a betrayal! Dagakowannensu. Kuka sosai ta soma yi, ta mike ta isa ga closet dinta tana canza kaya, ko dankwali ba ta tsaya dauka ba ta nufi dakin Hajiya Maryam. Da rabe-rabe a jikin bango ta shiga dakin, guilty conscience na abinda ya faru na dibanta duk da ta san ba laifin ta bane amma ita Mammah ai bata san haka ba, fuskarta fal hawaye ta shiga dakin. A gefen gadonta ta same ta tana waya, kallo daya Mammah ta yi mata ta dauke kanta, ta ci gaba da maganar da ta ke yi. Ta lallaba ta isa ga gefen kafarta ta zauna tana ta share hawaye. Ta fi minti goma sha biyar tana magana a waya inda ta fahimci da Auta Haleem ne, tana shirya masa zuwa hutu daga Sweden karshen watan nan. Da ta kammala tana ji suka yi sallama, ta ce Love you too Haleem. Ta ajiye wayar tana shirin mikewa don ta bar mata dakin Hafsat tayi maza ta rike kafarta tana kuka. Don Allah Mammah ki yi hakuri ki saurare ni, ba ni na kira shi ba, bansan sanda ya shigo ba, kawai ganinsa na yi a kaina na zo zan fita ya rufe kofar. Mammah in kin yi fushi da ni ina zan sanya rayuwata in samu irin sanyin da nake samu a tare da ke? Janye kafafunta ta yi, amma ta koma ta zauna, ta ce. Za ki samu a wurin mijinki,wanda ba kya son bacin ransa, mijin da ya yanke igiyar aurenki ya watsar, ya ce wata mai aji yake so ba ke ba. Yar masu kudi mai zurfin ilimi. You are unbelievable Hafsat! Sau nawa za mu yi wannan maganar? For the first time na fara shakkarki, don kin canza daga Addah ta da na sani, tunda har zaa iya hada baki da ke a yi wasa da hankalina. Naji komai na abin da kuka kulla kada don ban yi miki zancen ba ki dauka ban ji ba. Karshen tashin hankali Hafsat ta shige shi, kukan ma ta neme shi ta rasa. Ba ta taba zaton alamarin zai yi girma haka a zuciyar Mammah ba, da ko kusa ba ta sanya kanta a ciki ba. Ba ta san sakin wani abu ne special ba, a lokacin tana ganin all a woman wants is knowledge(abinda diya mace ke bukata shine kawai ilmi), kuma Mammah ta hana ta, ta ce AURE shine gaba. Tana so ta ga yan uwanta na jini,tanaso ta ga wanda ya diga jini ya haifeta, Mammah ba ta taba damuwa da hakan ba. Bata so ma ayi mata zancen. Ba ta so ta takura mata da ta nemo mata danginta za ta ga kamar ta raina kulawar da suke bata ne. Abdulazeez ya zo kamar daga sama ya ce zai yi mata duk wadannan abubuwan cikin sirri, kuma cikin dan lokaci kalilan. All he need in return shi ne ta amince za su rabu bayan shekara daya! Dokinta ga hakan,enthusiasm dinta ga son zuzzurfan ilmi, rashin sanin me auren kansa ya kunsa, da rashin sanin cewa SAKI shi ne babban koma baya ga rayuwar diya mace, da rashin sanin cewa babu mai iko da zuciyarsa sai Ubangijin da ya halitta masa ita, su suka taru suka kai ta ga amincewa ga bukatar Abdulazeez Hamza Atiku,ba wasa da hankalin Hajiya Maryam ba, ko nufin yaudara a gare ta. Maryam din data rayu shekaru goma sha takwas da doriyaagainst all odds don tserar da rayuwarta tun tana cikin kwalba (incubator).Ta zabi Da mai sunan Da a cikin yayan ta ta aura mata,ba tareda laakari da nata matsayin ba, duk don ta samar da kyakkyawar rayuwa a gareta a shekarun girma bayan wadanda ta samar a shekarun kuruciya. Hafsat ta ga ba ta da mafita a yau ban da warware wa Mammah komai, wannan Mammah din da ba ta da kamarta, yadda komai ya faru da dalilin amincewarta. “It happened on 31st september a studyroom da ki ka ce in je mu ganafor the first time........... Tiryan-tiryan ta gaya mata komai, har irin zaman da suka yi a gidansu a Sun-City. Amma da ta zo inda suka soma having physical contact sai ta ke kaucewa. Ta kare da cewa. Ban taba sanin yana da kirki ba sai da na zauna da shi, abubuwa da yawa da na girma ina gani a tare da shi, sai na tadda su akasi ga tunanina. Ko a cikin mutane shi na daban ne. Yana da qualities da za a so shi a kansu ba tare da amincewar zuciya ba; he is genius, he is unique. Ya tabbatar da kasancewarsa mai gaskiya da rikon amana a kan Muazatu. Ya tabbatar shi mai muhimmanta alkawari ne akaina da Muazatu. Duk alkawuran da ya daukar min ya cika min. Sai na ga bari ni ma in taimake shi ya kai ga samun wannan burin nasa guda daya. He used to say;he has only one weakness... shi ne soyayyar Muazatu. Mommah in na ce sai ya ci gaba da zama da ni bayan duk wannan halarcin da ya yi min, shi kada ya auri wadda yake soya samu farin ciki na zamo cikin masu son kansu da yawa. Bayan Annabi SAW yace imanin mu baya cika har sai mun so wa yan uwanmu abinda muke so wa kanmu. Nima ba da son raina ne aka yi sakin ba,but a iyaka tunaninsa a lokacin (its the only solution), kuma na ji ciwo sosai a zuciyata yadda bazan iya kwatantawa ba Mammah. Ki tambayi Dada I became unconsciousna lokaci mai tsawo lokacin da na tsinci takardarsa cikin jakata. A lokacin ne na gane yanzu ba karatun nake bukata bawhile it is too late, akwai wani abu wanda ya fi shi muhimmanci ga diya mace wanda ni na rasa a halin yanzu..... (Sai bayan ta fadi hakan kuma ta ji kunya sosai, watairin kunyar Mammah da bata taba ji ba tsayin rayuwar ta, ta ga kamar ta ce ne da Mamansa tana sonsa indirectly) bayan ba haka take nufin fada ba. Mammah ba ta nuna a kage ta ke da son jin karshen bayanin nata ba. Amma jin ta yi shiru ta kasa ci gaba sai ta fahimci kalmomin bakinta sun kare. Kallonta ta ke tana jin tausayinta da jin son ta sosai yana karuwa a ranta. Hafsat din kanta na kasa. Maryam Dakata ta kira sunanta cike da kulawa. A hankali ta dago amma ta kasa kallon kwayar idanunta, sai yanzu ne ta ankara da irin kalaman da ta ke bulbularwa ba tare da tunanin wa ta ke gaya wa su ba. Ta gama fallasa asirin zuciyarta ba da saninta ba. Ta gaya wa UWA tana cikin soyayyar Danta a fakaice, wannan abin kunya da me ya yi kama??? Kanta ta kara sunkuyarwa tana jin tamkar ta ce da kasar ta tsage ta shige. Mammah ta fahimci halin da ta ke ciki, murmushi ta yi ta ce. Ni na nutsu na saurare ki, amma ni kin ki saurara ta. Tambaya biyu kawai nake son in yi miki, in ki ka amsa min su genuinely na daina shiga tsakaninki da mijinki kuma a yau dinnan zan tattaraki in maida ke dakinki don na lura kun fi kusa, kun wuce da tunanina....... Mommah ba haka ba ne, ni wallahi..... Ta fada kamar za ta yi kuka, amma ta kasa karasawa. Mammah ta riga ta gama fahimtar tana son Abdulazeez yanzu, ina za ta kai wannan kunyar? Addah yau suruka na zame miki? To idan na koma suruka ina za ki nemo uwa? Ke ki ka zauna da ni a lokacin da shi yake nesanta kansa da ni. Ke na sani a matsayin ya ba shi ba. Ban zaci aurenki da shi zai sa ki canza min matsayi ba. Tashi ki je in kin shirya magana da ni a matsayin UWA kya dawo, amma yau suruka ki ke kallona. Murmushi ta yi har sai da kumatunta suka lotsa ciki sosai. An-ti Ummeeee.... Wato Ke uwata ce.(Yau aka tuno larabcin Jeddah). Kallonta Hajiya Maryam ta yi a tsanake, ta tabbatar ta samu nutsuwa sosai sannan ta ce. Naji duk bayaninki kuma na fahimce ki. Tambayoyi biyun da zaki amsa min properly sune;How sure are you (ta ya ya ki ka tabbatar) yanzu yana sonki so na haqiqa? How sure are you ya daina son ita waccan din ko ya fasa aurenta acan gaba, idan kika koma gidansa? Shiru ta yi don ita kanta ba ta sani ba. Abin da ta sanin shi ne zamanta da shi a yadda suke a gidansu ko babu soyayyar ya fiye mata wannan zaman gashin kumar da ake musu a yanzu. She cant get into his mind(bazata iya shiga zuciyarsa ba balle ta gano wadannan amsoshin). Zuciya abin sirri ce. Sai dai abu guda da ta ke da tabbaci shi ne, ba zai taba yi mata karya ba. Karya is out of his vocab bank (vocabulary bank). Sannan kuma ita zuciyar ai tana canzawa Mammah, kamar yadda komai na duniya ke iya canzawa. Nima ai da ba son nashi nake ba. Lokaci daya na tsinci kaina dumu-dumu a duniyar da in ba shi ba zan iya rayuwa ba. Sannan yana da damarkarin mata biyu ma bayan ni da Muazatu. Mammah ta duba wannan mana ta yi masa uzuri. Sai dai ko giyar wake ta sha ta san itama ba za ta iya yi wa Mammah wannan bayanin ba. Zai bayyana gare ta cewa ta makance a son mijinta, wanda a zahiri hakan ne. Ta yadda bata ji bata kuma hango komai sai na yadda zata koma rayuwa da shi.Saidai fa bazata taba zabar sa akan Mammah ba koda son ne zai yi ajalinta. Gara ta zuba ido ta bar wa Allah alamarinsa, ta bar Mammah ta yi hukuncin da ta ke ganin shi ne daidai. Duk son da ta ke masa ta san bai yi na wanda ita da ta haife shi take masa ba. Idan so cuta ne, to hakuri da biyayyar iyaye maganin komai ne. Kina iya tashi ki je ki yi wanka mu yi shirin dora lunch. Ranar da ki ka samu amsa ga tambayoyina ki zo ki goya mijinki ku koma gidanku. Kuma ki tabbatar kin nemi wani abu kin ci. Silly girl kawai. Sum-sum-sum ta fice kanta a kasa. Mammah ba ta bi ta kanta ba, ta fito falon. Abdulazeez ne da Usman, Ismael ya fita. Hira suke amma tana shigowa falon suka yi shiru. Fuska dinke ta wuce su zuwa part din Daddy. Ta same shi yana ta aiki cikin projects din dalibansa na PhD, kasancewar yau ba zai shiga jamia ba. Tana shigowa ta soma korafi ko gaisawa ba ta bari sun yi ba. Ya kasa fahimtar daya kwakkwara cikin complains din nata. Abu daya ya fahimta; Abdulazeezya bar mata gida! Ya zo ne kawai don ya takura wa Hafsat ya zuge ta ta ki yi mata biyayya. Kansa ya mayar kan abin da yake yi ya ci gaba, amma ya kasa fahimtar komai saboda ta dame shi da korafin ta. Dakatawa ya yi ya cire medicated lensesdinsa, ya dau waya ya kira Abdulazeez ba tareda sanin yana cikin gidan ba, ko mintuna uku bai yi ba ya shigo, wannan karon ya sauya kayan jikinsa da alama wanka yayi a lokacin da itada Hafsat suke heart-to-heart talk dinsu. Shirt ce fara sol long-sleeved mai rubutun Nordstorm da ruwan tokar trouserajikinsa. Ya yi kyau sosai kuruciyarsa ta fito fili. Yana ganin yanayin Mammah ya san kararsa ta kawo. Daddy tun kafin ya zauna ya ce dashi. Me ka yi mata? Sunkuyar da kansa ya yi ya ce Daddy a sanina babu komai. Na dai kwaso kayana ne kawai na dawo nan, saboda matsalolin da nake fuskanta na zama ni kadai da na abinci da tsabtar gidan kansa. Sanda nake dawowa daga office na gaji, abinci kawai nake bukata kuma babu. Sai dai in kara bata lokaci in yi expressda kaina shi ma kuma wani lokacin gajiya ba ta barina sai dai insha coke in kwanta. In na ce sai na tsaya na biya na saya sallar magriba za ta wuce ni. Ka san kuma mutum da ya saba komai a yi masa, sannan the house is somehow dirtyalways. Ya fada cikin muryar da dole a ji tausayinsa amma banda Hajiya Maryam. Dr. Hamza ya ce. Ki barshi ya zauna mana? A kanki yake zaune? Ga mari ga tsinka jaka? Cikin mamakin abin da ya fada ta ce, Haka ma za ka ce? Wace jakar na tsinka masa? To in dai gidana ne na ce ya zauna, ki gode Allah da ya ba ki shiryayyun yaya a wannan zamanin, wasu da yawa irin damar da ya samu suke nema su tambade. Kai kuma na ba ka wata daya ka kawo min matar aure.Attorney ya bada auren yarsa har katin gayyata ya kawo min duk da ban samu na je ba, tunda ita Hafsat din uwarta tace bata yarda ta koma ba ka barta tabi abinda uwarta ke so. Idan watan nan ya wuce ba ka kawo min mata ba zan je Kano in nemo maka duk wadda na ga dama saboda kai din na dade da gane cewa namamajo ne akan mata, in banda haka ta yaya ga wata an halatta maka a cikin gida da igiyoyin aure na halali,amma hankalinka da soyayyar ka bakidaya suna ga wata a waje, don haka gara in cika maka gida dasu ko ka nutsu dana gidan aure. Ban amince zamanka ya zama zaman shiga sabgar Hafsat a gidannan ba ko ka dinga shigar mata daki, kowa yayi zaman kansa. Is that ok with you two? Mammah kamar ta goya Daddy yadda ya wanke mata shi tas! Ta ji dadin wannan hukunci har fiye da zaton ta, itata fara fita ranta ya yi wasai daga takaicin da ya cusa mata yau. Dama abin da ya fi ci mata tuwo a kwarya kenan; shiga dakin Hafsat da yake yi. Ban da haka ya yi ta zama a gidan mana ita ina ruwanta? Bayan fitarta Abdulazeez ji ya yi kamar an sauke masa wani gingimemen dutse daga kansa maimakon wankin babban bargon da akai masa ya bata masa rai. Attorney ya ba da auren yarsa! Whichmeansbai karya alkawari ba! An je nema masa auren kamar yadda ya alkawarta, dissappointment din daga iyayenta ne. Babu kaffara a kansa, babu tunanin ya ci amanar wata halitta da ta ba shi dukkan yarda da aminci. Karasawa ya yi gefen kafafun mahaifin nasa, wanda ya maida gilashin idonsa ya ci gaba da abin da yake yi alamar ya gama magana da su. Don Allah Daddy ka taimaka min ta huce, ka taya ni ba ta hakuri, ta yi fushi da ni mai tsanani, na amsa na yi laifi ku dubi girman Allah ku yafe min. Daddy ko gaisuwa ta ba ta amsawa, na janyo mata cuta, Daddy in na mutu yanzu wuta zan tafi babu tantama... Ta yi min alkhairi na saka mata da butulci. Ban san darajar abinda ta ba ni ba sai da lokaci ya kure mini, kuskuren ya riga ya afku. Ni babu wata mata da zan iya kawowa cikin sati hudu daga nan har gaban abada sai HAFSAH! Ko ba za ta mayar min da ita ba atleast ta furta yafiyarta gare ni in samu sauki a zuciyata.... Na ji. I will talk to her.Abin da tsohon Ambassador Hamzah Atiku ya ce da shi kawai ke nan a matukar gajarce. Jiki ba kwari ya baro falon nasa ya koma main parlour. A can ya yi kyakkyawan gani, Hafsat ce ta yi wanka ta canza kayan jikinta da wasu riga da skirt yan kanti na calvin klien jajaye da ratsin baki. Ta gyare gashin kanta ta kalmashe shi cikin bound kalar kayan jikinta. Ko ba komai dai anbi umarninsa anyi masa kwalliya. Ta zubo soyayyen chips tubus dashi da saucedin hanta da koda a faranti tana ci da cokali mai yatsu, ga coffeemai zafi a karamin kofi a gefe. Wani abu ya hadiye da ya tokare a makoshinsa ya koma can kujerar karshe ya harde dogayen kafafunsa. Kallonta kawai yake kamar ya samu T.V, ai a cikin sharuddan da aka kafa masa din ba a ce kada ya kalle ta ba.Kuma kallon babu zunubi. Ta yi kamar ba ta san da shi a falon ba, ta ci gaba da cin abincinta a tsanake. Usman ya ce, Shi mijin ba zaa ba shi ba? Ta ce, Na karfi ne!. Ya kama baki. Rashin kunya ne abin? Ta yi masa shiru. Mikewa ya yi har inda ta ke ya dauke farantin ya kwace kofin ya kai masa. Karba ya yi da murmushi ya ce. Na gode Usman, you are the best. Ya dora a center-table ya soma cin abinsa. Tashi ta yi cikin fushi ta yi kitchen wajen Mammah. Mommah kin ga Ya Usman ya kwace min abinci ya bashi? Zuba wani. Kawai ta ce don ba ta son surutu. Usman ya shigo kitchen din yana fadin, Mammah yarinyar nan ba ta da imani na lura. Ya Azeez tun safe ba abin da ya ci sai ruwan shayi, amma ta shako faranti ta zauna tana cin abinta a gabansa babu ko tayi. Hajiya Maryam ta juyo ta watsa masa harara, ai ba ta san kan zancen ba. Ta nuna shi da yatsa ta ce Usman, ka kiyaye ni, kada ka shiga hancina don in na tashi fyato ka ba za ka ji dadi ba. Allah ya ba ku hakuri. Ya ce yana hada hannuwa irin na indiyawa. Hafsat ta yi masa gwalo da ta ga Mammah ta juya. Ya yi mata alamar, za mu gamu ne ya bar kitchen din. Da rana gabadayansu suka ci abincin rana har Daddy da Abdulazeez a kan tebir. Shi da ita sai satar kallon juna babu ko kwakkwaran motsi daga Hafsat. Daga Mammah har daddy babu mai walwala a fuska. Shi ya fara jin zafin matar tasa ne kan hukuncinta a kan Abdulazeez, ba karamin karya mishi zuciya ya yi ba dazun daurewa kawai ya yi. An ce so-so ne, amma son kai ya fi. Yana son dansa fa, na Hafsat karah ne. Ita kuwa Maryama na wani shi ne nata kullum nata ba nata ba ne, ba tun yau ba haka ta ke. Ita kuma Mammah dalilin rashin walwalarta shi ne kada Abdulazeez ya ga fuskarta ya dame ta da wannan nataccen ban hakurin nashi. Har aka gama cin abincin daga shi har Hafsat babu wanda ya ci wani abin kirki. .SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* A yammacin ranar Azumi ta dawo. Kusan Abdulazeez ya fi kowa farin cikin dawowar Baba Azumi, mai sonsa da jin kansa. Ya tabbata za ta taimaka masa sosai wajen shawo kan Mammansa. Tun dawowarta ta fahimci yadda ta tafi ta barsu haka ta dawo ta tadda su, ba wani ci gaba daga bangaren uwargijiyarta. Ita ta ci gaba da kula da komai na Abdulazeez, tsaftar dakinsa da toilet dinsa da cikinsa. Ba tun yau ba ta san ba komai yake ci ba. Su sun yi rayuwa cikin turawa don haka suna amfani da ire-iren abincinsu sosai-sosai musamman kayan gwangwani. Abdulazeez kuwa na son Nigerian Food musamman na Yarbawa su Amala, sakwara, miyar ganye;su Ugu alayyahu, egusi, water leaf, da kifi da ganda saboda zamansa a kudu (Ibadan da Lagos gidansu Muazatu), su ta himmatu wurin yi masa nasa daban, wani lokacin su Hafsat rai na biyawa ta ce kuma ba mai ci har Maman nasu. Mammah kan kyabe baki ta ce, Ina ruwan oduduwa dangin Yarbawa. Shi ya sa duk halinsu na naci kun diba. Ban da haka na ce a bar min gidana, a bar min ya ta, a je a auro yar Yarbawa kun ki, har asalin uwarta na jiyo ba yar Jigawa ba ce yar Ogun ce. Uban ne dan Jigawa. Baba Azumi kan rausayar da kai ta ce, Kin san wani ba ya auren matar wani, jiya mun ga aurenta a obashin (ovasion magazine) Ismaeela ya kawo mana. Mammah ba ta kara bi ta kansu ba. Su Hafsat sun fara C.A don haka a dan tsukin ba ta da sukuni, test-test da assignment kawai suke yi. Yau litinin, Mammah za ta je ganin likita kuma ya yi daidai da lokacin shigar Hafsat test. Ba yadda ta iya ta ce Salisu ya kai ta, in ya ajiye ta sai ya dawo ya same ta a Diff Hospital. Ita ya fara ajiyewa a asibitin, sannan ya karya kan motar suka nufi NILE shi da Hafsat. Danja ce ta tsaida su a wani shatale-tale. Barrister Abdulazeez Dakata a nashi motar, cikin shirin office yake (fully robed). Ya yi tsakin bata masa lokacin da danja tayi don ya makara, ya dan juya gefen damansa sai ya hango Salisu da motar Mammah, a kujerar baya Hafsat ce ta warware handout tana ta karatu. Magana ya yi masa ba ta san suna yi ba, sai ji ta yi Salisu ya gangara ya faka a gefen titi. Ta dago don ta tambaye shi me ya tsaya yi zai makarar da ita, sai ji ta yi an bude kofar side din da ta ke. Mutum na karshe da ba ta zaci gani ba, suna yin kwana uku a gidan ba su hadu da juna ba sabida yanayin aikinsa da lokacin dawowarsa very late gefen maghriba. Lokacin ita ta shiga sallah, sai wajen cin abincin dare kawai suke haduwa, ita kuma ta tsame kanta. Don ko ta zauna ba iya ci ta ke ba saboda idanun Abdulazeez da na Mammah, kowanne na kokarin ganin cewa idonsa ya hana abin da ba ya so. Mammah ba ta son wadannan idanun na Abdulazeez su yi tasiri wajen karya lagonta, tunda ta bi kowacce kafa ta communication ta toshe. Shi kuma nasa idon so suke su fahimtar da ita how miserable and helpless they aresaboda rashin ta cikin rayuwarsa yanzu. Don haka ko da ta daina zaman cin abincin Mammah ba ta ce don me ba, ta ma fi son hakan. Amma tana tabbatarwa Azumi ta kai mata nata daki kuma ta ci. Da safe kuma Azumi a basket ta ke sanya masa karin kumallo ya tafi da shi office ba ya son abin da zai makarar da shi, mutum ne mai tsantseni a kan aikinsa da muhimmancin lokaci. Ajiyar zuciya ta yi sakamakon tunanin da ya tafi da ita kawai saboda arba da Abdulazeez a inda bata zata ba. Fuskarsa babu wasa ya ce. Fito, ni zan karasa da ke. Cikin damuwa ta ce, Ni ba zan fito ba, Mammah..... Wallahi kin ji na rantse ko ki fito ko in dauke ki na fiddo ki, a kan me wani gardi zai fita da matata ni me ye amfanina? Kawaicin da nake yi ne ba ki san ina yi ba sai na fito da true colour dina? Daga amon muryarsa ta fahimci a matukar fusace yake, Mammah ta gwammace Salisu ya kai Hafsat makaranta a kansa, Salisu ne trusted dinta, shi kuma dan taadda mai cutar mata da ya. Jikinta har bari yake ta cizgo jakarta ta fito daga motar, ba tun yau ba ta san duk abin da ya fada zai iya aikatawa. Shi ya bude mata kofar gaba ta zauna ya rufe. Ya zagaya ya shiga bangarensa. Da matsanancin gudu ya fizgi motar. Ban da faduwa ba abin da gabanta ke yi, tunanin Mammah kawai ta ke yi. Me Salisu zai je ya gaya mata? Ta shiga ukunta! A wannan dan tsukin burinta kawai ta ci gaba da yi wa Mammah biyayya a kan duk abin da ta ke so. Ta fahimci duk abin da Mammah ta ke so ta fahimta. Ta kamma kanta, ta bi abin a sannu. Kada tayi garaje, kada tayi gaggawa wajen komawa cikin rayuwarsa. Namiji ba abin yarda ba ne. Sannan ba dan goyo bane. Balle mai wayo da wayewar kai irin Abdulazeez Dakata, the smartest person she have ever know. Ba ya fadin sirrikansa sai dai reactions dinsa su nuna. Kamar yadda Mammah ta kafe a kai ne, how sure she is yanzun yana sonta? How sure she is ya daina son Muazatu? Duk da ko yana sonta ko ba ya sonta yanzun doesnt mattertunda ta yi aure ta barshi. Amma Mammah a kan gaskiyarta ta ke, shekara daya da watanni da suka kwashe tare karkashin inuwar aure me ya hana ya so ta? Sai bayan ya yanke ta daga cikin rayuwarshi ta dawo gaban wadda take sonta da kauna ta har abada? Wata zuciyar mai tsananin so da kare Abdulazeez ta ce. Ke ma me ya hana ki so shi da farko, sai bayan kin zauna da shi? Wanda ke nufin dukkaninku abu daya ku ke bautawa;You didnt get to know each other well sai bayan zaman.You are not close to each other sai bayan zaman. Soyayya kuma bata faruwa sai da kusanci. Soyayyar bata huda kowannenku ba sai a cikin zaman. Give him a chance Hafsat, reason with him. Zuciyarta ta ji tana yin wani irin laushi wanda ya sa ko da ta ga ya bar hanyar Nile ba ta damu sosai ba. Sai dai ta sa a ranta cikin kowanne hali shell not betray her mother! Shellstand by her not by him (ba za ta ci amanar Mammansu ba, za ta tsaya a bayanta baa bayanshi ba). Ginin da ya nufa da su ya tabbatar mata ofishinsa ya kawo ta, (Federal High Court of Nigeria). Ya yi parking a parking lot ya cire wayoyinsa daga cajin da ya sanya su a motar. Ya dauko suit-case da jakar system dinsa, wig dinshi a hannu ya fita daga motar. Tsayawa ya yi yana jiran ta fito ya rufe motar. Hafsat ta ki ko da motsi. Kyale ta ya yi ya je office din ya ajiye kayan hannunshi ya dawo, da ya shigo cikin motar juya masa keya ta yi tana duban taga. Murmushi ya yi ya ce, Me ki ke nufi da ni ne yarinyar nan? Ba tare da ta juyo ba ta turo baki, Laifin me na yi da za ka kawo ni kotu? Test zan yi amma already ka sa ta subuce mini. Za ka iya jin damuwar hakan sosai a amon muryarta, domin ta shirya wa gwajin sosai ta kwana tana karatu. Hannunta ya fizgo ta yi juyowar da ba shiri, a fusace ya ce. To hell with your test, duniya kawai ki ka sa a ranki ba kya tunanin lahirarki. Da kin san yawan zunubin da Mammah ke sanya ki kina kwasa da kin tausaya wa kanki Hafsat. Tana tare da mijinta kullum tana gyara aljannarta, ta nesanta ki da naki kina ta kusanta kanki da wuta. Shin ni ba mutum ba ne, ba ni da feeling? Shekaruna talatin da uku har yau ban san ya ya aure yake ba. Hafsat ko ba kya sona dole ne ni ma ki yi min biyayya yadda ki ke mata. Ko kuwa shi kenan saboda na yi laifi ni rayuwata ta kare? Kuka ta soma yi a hankali, ta rasa inda za ta tsoma zuciyarta, shi da Mamansa sun sa ta a kwana, kowanne gani yake shi ya kamata ta yi wa biyayya, a wannan lokacin ba ta san me ya kamata ta yi ko ta ce masa ba banda; Me ka ke so in yi maka yaya Azeez? Hannunta da ke cikin nasa ya janyo a hakali ya hade ratar da ke tsakaninsu. Ajiyar zuciya kawai suke yi dukkanninsu cikin motar. Wata irin nutsuwa da suka dade rabonsu da ita ke overwhelmingdinsu tun daga kwakwalwa har babban yatsar kafarsu. Tsawon mintuna ba wanda ya iya yin magana a cikinsu. Hafsat ce ta ankara mutane na gilmawa jefi-jefi suna aje motocinsu. A hankali ta zame jikinta daga nashi ta koma cikin kujerarta sosai ta zauna, ta lumshe idanunta, karfin scent dinsa da na air-freshner din motar suka hade da sanyin A.C suka bada wata atmospheremai dadi a cikin motar. Kansa ya kwantar a kan sitiyarin yana regaining hargitsewar bugun zuciyarshi. Sun jima a haka kafin cikin raunin murya ya ce. Gidanmu nake so mu koma Hafsat direct daga wajen nan. Na roke ki kada ki ce min aah... Kai ta shiga girgizawa da sauri showing resentment (cikin nuna rashin yarda) I cannot do this to Mommah (bazan iya yin haka ga Mammah ba). Dagowa ya yi daga kan sitiyarin ya dube ta sosai cikin tsakiyar idanunta, duk da ta ki yarda su hada idanu ta san idonsa akanta yake. Then blame yourself kan duk abin da na zaba mana!. Ya tada motar ya fita daga harabar kotun kasa, ya hau kan titin da zai kai shi titin Aguiyi Ironsi. Hafsat dai ikon Allah ta ke kallo, gabanta na tsananta faduwa don bata san me yake nufi ko ina zai kai su ba, sai dai zuciyarta na gaya mata... ko me Abdulazeez zai zaba musun nan ba alheri ba ne gare su.........!!!Mu karasa a littafi na hudu kuma na karshe. Kada ku damu, tare suke. Taku har abada Sumayyah Abdulkadir Takori Buk 4 SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* A ganinta hakuri da biyayya shi ne abin da ya kamace su daga ita har shi. Duk abinda hakuri bai bayar ba rashinsa ma bazai taba bayarwa ba! Hafsat dai sai dago kanta ta yi daga tunaninta ta gansu a harabarRockviewHotelAbuja. Kallon tsoro ta fara yi masa, amma ya ki ko ya dubi inda ta ke. Tana nan zaune ya je ya dawo ya bude kofar side dinta, jakarta ya fara daukowa sannan ya ce, Mu je daga ciki. A raunane ta ce Yayan Haleem,Hotel? Hasken fararen idanunta kadai da yadda ta wargazasu a kansa, suka gusar da duk wani tension da yake ciki. Yadda ta yi maganar ya kwaikwaya. To ko mu ma yan abin nan dinne ne? Tsoron zuciyarta ya ninka na farko ganin Abdulazeez na nade hannun suit dinsa da zummar daukanta a gaban mutanen da ke shige da fice. Sauri ta yi ta fito, kiris ya rage ta fashe da kuka ta wuce gaba ta barshi a baya. Sai da suka shiga reception ta dakata har ya cimmata don batasan ina zata nufa ba, hannunta ya rike suka wuce cikin lifter. Suna shiga lifterta kwace hannunta ta harare shi ta gefen ido. Jinjina kai yayi, ya ce. Ki harareni yadda kike so. Za ki yi bayani ne Hafsah. A ranta ta ce Allah na kowa ne, tuni ya riga ya zame min gata. Katin kofar ya sa a jikin kofar kawai ta bude,ya bata hanya ta wuce tukunna ya mayar ya rufe sai faman cin magani take yi. Fuskar nan kamar kunun kanwa sabida kirnewa. In ma ya lura to ba abinda zai iya tasiri bane akansa a wannan lokacin. Tun daga bakin kofar Hafsat ta gane yau ta shigo wata koma da taimakon Allah ne kadai zai fitar da ita. Ta san dai ya yar da jakarta da ke hannunsa a muhallin da bata tantance ba. Ya kuma raba ta da mayafi da dankwalin kanta cikin wata irinnutsuwa. Idanunsa na fidda wani chemistry zuwa cikin nata mai bayyana intent and in depth sorrow din da ya kasance ciki na rashinta lokaci mai tsawo. Sauran alamuran da suka biyo baya sun fi karfin ta iya bayyana su; Is a kind of gentle romance wanda ba ta taba sanin akwai irinsa a duniya ba. Tashin hankalinta ragagge ne sanin cewa she is safe a yau kam. Kwananta biyu da karbar bakonta kuma a iya saninta na addini da na boko mace mai alada miji ba ya kusantarta. A yadda ya santa da tsoron ta shiga hannunsa ya yi mamaki da yau ba ta tsorata sosai ba, karewa ma she contributed a lotdonganin ya samu nutsuwar da bai da ita,wanda hakan ya zo masa kamar a mafarki. Don haka duniyar da suka fada mai nisan zango ceda ta shallake tunanin su. Sai da komai ya kankama ya gane Hafsat shigo-shigo ba zurfi ta yi masa (abun mata ce a jikinta). Alamarin da ya jefa shi cikin wani hali wanda ita kanta sai da ta tausaya. Gefen gadon ya koma ya zauna ya dafe kansa da ke tsananin ciwo hade da ciwon mara mai tsanani da ya bakunce shi, kodayake ya dade yana damunsa a kwanakin nan tun dawowarsa gidansu da Hafsat din da yake yawan gani kodayaushe tana gilmawa ta gabansa. Itama Hafsat din shiru ta yi, tayi tsuruu a gefensa kamar wadda ta yiwa sarki karya. Tana farin ciki da kubutarta, amma hakika tausayin Abdulazeez ya mamaye farin cikin. Ya cancanci samun farin ciki komai kankantarsa a yau daga gare ta. Duk da tana da tabbacin ko lafiyarta kalau ba za ta amince ba. A hankali ta iso inda yake zaune a gefen gadon kafafunsa a kasa, ta kwantar da kai a bayansa. Cikin sanyin murya ta ce, Im sorry. Bai ce mata komai ba, wayarsa da ke ta kuwwa a kan bedside din ya dauka. Ya yi sliding kiran ya amsa. Tunda ka san ba halina ba ne in zo in kuma fitan, kasan ina da uzuri ne. Ya jefar da wayar ya janyota ta dawo jikinsa. Wani irin kallo yake binta da shi da sai da ta kasa jurewa ta rufe fuskarta da hannunta daya. Dole ki rufe fuska tunda kin san kin yi nasara a kaina, Mammah ta san haka ki ka girma kuwa Hafsah? Ita kullum tana miki kallon babynta a Jeddah acikin incubator? Anyway I appreciate, and I must thank Hafsah for this great moment. Wata irin kunya da ba ta taba ji ba a rayuwarta ita ta lullube ta a wannan lokacin. Mikewa ta yi tana kumburi irin na nade tabarmar kunya. Please Yaya Azeez mu bar wajen nan, ba mutuncinmu ba ne. Ni mutunci na ne. Ya fada bai da alamar tashi sai wani lafiyayyen kallo da yake ta binta da shi. Abubuwanta ta soma tsincewa a dakin wadanda yayiwa fatalin Allah-tsine, ta daura kallabinta ta yafa mayafi ta juya masa baya. Dariya ce ta kama shi ganin zip din rigarta ta baya bakidayaa bude, ya ce. InnaHafsatu saura zip din. Hannu ta kai ta shafo wajen. YaIlahi! Wata harara ta juyo ta zuba masa tamkar idanun sa fado.Tasowa ya yi cikin takun nutsuwaya iso gabanta, idonsa kan bakin data ke ta turowa gaba. “Lemme help.....(bari in taimaka). Ta zumburo baki tareda ja baya. Bana so, ka bari!. Ya daga hannuwa sama daga taimako? Da na sani na yi shiru Mammanki ta gyara miki da kanta. Ya fada yana ja da baya cikin hadiye dariya. Kansa ta yi da wani sabon kuka da ya zo mata nan take kamar mai shirin rufeshi da duka, data tuno rashin kyautawar data yiwa Mammah. Ya kuwa yi mata wata irin kyakkyawar runguma ya hade bakunansuin no space measure.Hawayen ya shiga daukewa..., ko kadan bai barsu sun sauko kan kundukukinta ba.... Komai ya dawo sabo kamar baa yi shi ba. Hafsat ta tausayawa kanta a wannan rana don har azahar Abdulazeez bai barta ta huta ba,amarcinsa yake yiiri-iri kamar babu gobe. Sai da ya samu relief daga tsofaffin damuwoyin sa da suka dade yana fama da su a kan Hafsah sannan da magiya da roko har da hawayenta ta samu ya amince zai maida ita makaranta. Test dai har biyu ta yi asararsu, amma Abdulazeez ya ce mata ladan da ta samu ya ishe ta shiga aljannah. In dai miji ke wa matarsa sanadin shiga aljannah, yau ya daga mata ta shiga cikin aminci Ud-khuluhaabissalaam!. Ya fada da larabcin da har yau bai manta ba. Wanda yasa Hafsat tuno birnin Jeddah with nostalgia. Suna hanyar NILE ya na tuki, batareda ya juyo ya dube ta ba yace, Karfe nawa za a dauke ki? Ciki-ciki tace. Sai 5pm Mommah za ta zo. A gaban department dinsu ya ajiye ta, kafin ta fita ya rike hannunta. Ta juyo ta dube shi idanunta narai-narai, sunyi wani irin maiko da kyalli, wani yanayi da yake matukar son gani cikin idanunta,a zuciyarta ta ce, “Oh ni! Me kuma ya saura? “Take a look into my eyes Hafsah! Will you now believe it if I say I really love you?(kalli cikin idanuna Hafsah, yanzu zaki yarda dani idan nace ina matukar sonki? Daga masa kai ta yida sauri sabida a kagare take data fita, sama-sama ma taji me yake cewa, hankalin yayi gaba, bata son a ja zancen da tsawokada wani tsautsayi ya gifta Mammah ta zo da wuri, ya cika hannun nata don ya fahimci yanayin da take ciki. A zuciyarsa yana jinjina kaunarta da uwarta da gudun zuciya irin nata, wani alamari da shi yanzu anzo gejin da bazai iya ba.Mammah ta kure duk wani hakuri da kawaicinsa. Na gode Hafsatu, me ki ke so in ba ki? Ban taba ba ki komai ba. Murmushi ta yi har hakoranta suka bayyana, Zo in rada maka. Ya kuwa sunkuyo da kunnensa daidai bakinta. Keep loving me till eternity!. Kafin ya farfado daga duniyar shaukin da kalamanta suka jefa shi ta dauke jakarta ta fice. Rufo masa kofar ta yi, ta yi waving dinsa sannan ta juya da dan gudu-gudunta ta barshi da murmushi. Ya dade bai iya tuka motar ba, sabida wata irin kasala da ta bakunce shi. Tana cikin rukunin matan da yake fatan samu a rayuwarsa, har fiye da yadda yake burin samun. Ashe baa judging mace a fannin auratayya da zurfin ilmi, yawan shekaru da wayewa? Halitta ce kawai ta ubangiji. A yau ya kara cursing perceptiondinsa. Sai laasar ya koma office. A nan ne ya tadda dalilin kiran da su Barrister Abdallah ke ta masa yana kashe musu waya. Abin alkhairi ne ya same su su goma a ofishin. Takarda ce ta fito ta tura su karo karatu (L.LM) daga (Federal Government) zuwa Amurka wanda zai dauki tsayin shekara daya kacal. Kowa a cikinsu murna yake, ban da Abdulazeez Dakata, sannan tafiyar za ta kasance wata mai zuwa, lokacin da suke da shi na shirye-shirye kadan ne. Shi tun tali-tali kasashen turawa ba sa cikin yan kayansa. Baida shaawa a kansu. Yana da burin tafiya (L.LM) ko ba su tura su ba amma accross Nigeria. Duk wani pride dinshi yana kasar haihuwar shi. Ko zuwa graduation din Ismael da Usman a kan dole ya je saida Daddy ya nuna bacin rai. Don haka su ESQ Ahmad sun yi mamakin ganin babu wani farin cikin abin a tare da shi, da suka dame shi da tambayar dalili ya ce ba damuwar kowannensu ba ne. Karfe biyar na yamma Hafsat ta fito daga dakin karatu ta doshi inda Mammah ta yi parking tana jiranta. Ta bude ta shiga suka yi wa juna dan murmushi kafin Hafsat ta ce. Yaya B.P din Mommah? Hope doctor bai ce yana sama ba? Ta tuka motar suka fita daga parkinglot ta hau kwalta sosai, sannan ta juyo ta dubi Hafsat fuska ba walwala. Yaya test din? Shaf! Ta manta da zancen wata test duk da Mami ta gaya mata an yi, kuma ba ta samu halin taimaka mata da ko attendance ba, lecturer din ya kasa ya tsare. Inda-inda ta hau yi saboda a rayuwarta bata saba karya ba. Karya wani abu ce da Mammah ta rayu tana gaya mata mai yin ta dan wuta ne. Amma hakika yau zatayi karya ga Mammah, a inda bata da mafita. Au... am, Eh....test din.. test din ba wuya sosai. Ta samu kanta da fada cikin daburcewa. Wanda ko daga yanayin data yi maganar ya gama fallasa ta. Sabida abune da baa raine ta da shi ba take kuma feeling guilty na yinsa tun kan a gane ba gaskiyar ta fada ba. Abin da ba ta sani ba tunda ta shigo motar jikinta kamshin Abdulazeez yake yi. Duk cikin yayanta ba mai amfani da wannan turaren sai shi, ya dade da kame komai nasa, sannan ita Hafsan bata fesa turare in za ta fita. Bayan haka Salisu ya koma ya tadda ta a asibiti da wuri, ta ce ya aka yi ya yi sauri haka? Ya ce ai sun hadu da Barrister ne ya ce ya koma shi zai kai ta. Ta rasa me za ta yi wa Salisu ta huce don haushi da takaicinsa, don haka uffan ba ta ce masa ba. Wani abun personal ne, kuma shi Salisu ya kwana da sanin waye Abdulazeez a gidan, kuma ya san Hafsat wace ce a gare shi. Ko babu aure ya isa ya hana Abdulazeez tuka Hafsat? Don haka ta kowanne bangare ta mishi uzri, amma za ta yi maganinsu. Kanta na bisa titi tana tuki. A ajandar AUREN KWANGILAr naku, har da cewa bayan ya maida ke makarntar, ya kuma kore kin, zai dawo kuma dagabayaya hana ki karatun? Hafsat ta ji numfashi ya dauke mata na dakika biyu. Tayi kokarin hadiyar miyau amma makoshinta taji ya bushe kyamas. Wannan test din guda biyu, kin rubuta su ko ba ki rubuta su ba? Ta sake fada cikin son controllingtsananin fushin da yake yunkuro mata. Wani tashin hankali ya ziyarci Hafsat, sai ta ke ganin ai kamar Mammah ta ga komai ma a kan idonta. Sunkuyar da kai ta yi, wata matsananciyar kunya da guiltyconscience na lullube ta. Mammah ta yi kwafa, bata kara magana ba haka Hafsat din, har suka isa gida. Ta kasa daga kai balle ta dubi Mammah. Suna zuwa gida Mammah sassan Daddy ta wuce ita kuma ta yi dakinta, bakin gado ta nema ta zauna a kasalance ta yi tagumi, ba ta da kalmar kare kanta yau a wurin Mammah, a kan-kanta ba ta da bayanin da za ta yi mata don ta yarda da ita, ta yarda ba da son ranta ba ne ta bi Abdulazeez, tana kan biyayyarta, ya fi karfinta ne da duk wani kokarinta na tsayawa a bangaren Mammah, sannan zuciyarta mai tsananin laushi ce a kansa sai dai idan ba su kebe ba. Ba ta dade da shiga falon Daddy din ba Dr. Hamza ya fito daga bedroom dinsa ya ganta a falon a zaune. Kallo daya ya yi mata ya fahimci ranta a matukar bace yake, kuma ba abin da ke bata ranta a dan tsukin sai lamarin Abdulazeez da Hafsah! He is tired of all these yau zai kawo karshen komai. Tun kafin ya zauna a kujera ta soma. ....Daddy ni fa na gaji da zaman Abdulazeez a gidan nan, ina tufka yana min warwara, sabida ya mayar da ni marainiyar wayonsa. Na samu matsala ban samu kai Addah makaranta da kaina ba, na tura Salisu ya kai ta, ya tare su a hanya ya dauke ta tun safe har yamma ban san inda suka je ba. Tana da test har biyu bai barta tayi ba. Ya sake ta kamar yadda ya yi wa kansa alkawari, kun mayar da aure ban hana ba don an fi karfina,nace kome sai sanda na ga dama kun amince.To binbinin na menene?Karatun ma marufar asirin diya mace ba za ta tsira da shi ba tunda bata da soyayyarsa? Bana zalunci, bana goyon bayan yinsa! Ka ja masa kunne wannan ya zama na karshe da zai kara shiga harkar Hafsat. Iyakar bacin rai ran Dr. Hamza ya baci, amma ya yi kokari matuka ya daidaita muryarsa yadda bacin ran bai fito a cikinta ba. Ya lalubi kujera ya zauna. Da izinin wa ki ke zirga-zirgar tukin mota kai Hafsa makaranta da dauko ta? A kan karan-kanki kina tuka mota ki je unguwa? Ta yi shiru ba amsa. Wani irin nutsatstsen murmushi ya yi ya dube ta sosai. Akwai mai zalunci ma irinki a duniya? Zaro idanunta ta bakidaya tayi a kansa, bai damu ba da yadda tayin ya gyada kai cikin karfafa ingancin furucinsa,ba tare da ya bata damar cewa komai ba ya cigaba. Yara na son junansu kin dage sai kin raba su. Ba kya tukin mota amma saboda kiyi zalunci kin jureshi yanzu. Ita Hafsan ki tambaye ta mana da wadanne kafafun ta fita daga motar ta bi shi? Ko aka ya dauke ta ya canza mata mota? Ita da bakinta ta gaya miki sun je wani waje ba makarantar ba ko kuwa kwakkwafinki na balai? Kin san Allah Maryama! Ki fita daga idona in rufe. Daga yau ban yarda ki kara tuka mota ba. Ban yarda ki kara kawo min zancen Hafsat da Abdulazeez ba in ba na alheri ba. Tunda ke ba kya afuwa. Shin da Allah ba ya afuwa a gare mu ga tarin laifukanmu, da mun kawo yau ne? Shin ke ba za ki yi afuwa ga dan cikinki ba ko don kwadayin rahmar Allah a gare shi? Ya biki, ya biki, ya biki har kin kai shi gejin da zai soma fandare miki. In bai saci matarsa daga wajenki ba, da ki ka bi ki ka kankane masa, zina ki ke so ya je ya yi ko me? Please ina son kadaici, hayaniyarki ciwon kai ta ke sa mini, ba don na tsufa ba da na dauko budurwa sabida tension dinki a kwanakin nan da ke neman nima ya hauhawar da jinina. Ko ba komai na san in na dawo zan samu mai yi min sannu da zuwa. Saboda auren yayanki duk kin lalata kyautatawar da ki ke yi wa naki auren. Don Allah je ki daga cikikiyi hayaniyarki ke kadai. Rai bace ta wuce ta bar dakin, ta sanya kai za ta fita, Abdulazeez na sanyo dogayen kafafunsa zai shigo saura kadan su yi karo. Da sauri ya ja baya ya ba ta hanya. Mugun kallon da ta jefa masa sai da gabadaya hanjin cikinsa suka hautsina. Ya tabbatar ta bare da shi ne, amma da wuya in Hafsat ce ta fada mata laifin nan da ya yi mata. Salisu ya fado masa a rai. Ya yi catching breath dinshi sharplysannan yayi saranda ya shiga falon Daddy. Yana shiga shi ma bai barshi ya zauna ba ya soma karbar nasa rabon don bai gama hucewa ba. Kai da uwarka so ku ke ku kwantar da ni ko? Ina lallaba tsufana cikin koshin lafiya shi ne abin da ba kwa so ko? Tunda ta fada maka abin da ba ta so ka bari mana har sai ta sauko? Ka san dai ba za ta dauki matarka ta aura wa wani ba ko tunda ka maida ta? To gajen hakurin na mene ne? Ka ba ta lokaci mana tunda ka san yadda zuciyarta ta ke kamar ta kuturwa ba mai sa ta ba mai hana ta? Not even her mother! Idan ka kawo ni bango ni ma korarka zan yi daga gidan nan.... Shi dai ya zauna a kan kafafunsa ya nutsu yana sauraro. Sai da ya gama tsaf sannan ya kwantar da kai da murya ya soma ba shi hakuri. A karshen ban hakurin nasa yace. Kuma Daddy ba wani waje na kaita ba banda makaranta....... Dr. Hamza ya kara harzukowa cikin hargagi ya ce. Na tambaye ka? Na ce tambayarka na yi? Ko bangon duniya ka kai ta ina ruwana ba matarka ba ce? Im talking about your mother, dole ka guji bacin ranta idan kana so ka wanye lafiya. Hakuri ya ci gaba da bayarwa sai da Daddyn ya ce ya ishe shi, ya tashi ya ba shi wuri sannan ya mike. Sai kuma ya dawo ya zauna ya fiddo takardun sponsorship dinsu na tafiya karo karatu ya karasa a hankali ya aje masa a kan tebir. Ya shiga yi masa bayanin komai. A karshe ya ce. Amma Daddy ni na yanke shawarar ba zan je ba, zan koma Ibadan na yi. Wata harara Dr. Hamza ya watsa masa, Ibadan? Aah ODUDUWA! Wallahi ka ji na rantse ka tafi karatun nan ka gama, salon ka je ka kara lakewa wata yar Attorneys din ko dangin Yarbawa? Su baka surkullensu cikin abinci kazo ka daga mana hankali? To ka sa a ranka cewa, in ka ga ba ka tafi karatun nan ba, bana numfashi ne. Jikinsa ya yi sanyi kalau, ya kasa tashi. Bakinsa ya shiga motsawa alamar akwai sauran magana a bakinsa. Daddy ya harare shi. Me ya rage kuma? Sunkuyar da kai ya yi, cikin fargaba ya ce, Dama wai cewa zanyi wai.... ko in yi visa da Hafsat? A nitse Ambassador Hamza ya dube shi, can kasan zuciyarsa tausayi ne fal! A hankali ya furta. Ita kuma nata karatun fa? Abdulazeez ya ji duniyar kanta ta tsaya masa cak! Da ya san abin da karatun nan zai zame masa kenan da baa fara shi ba. Shi ba abin ya ce zai nema mata wani a can ba shekara daya kacal zai yi. Ci gaba ya yi da zama ba shi da niyyar tashi. Tausayi ya cika zuciyar Dr. Hamza, daurewa kawai yake yi. Ganin Abdulazeez ba shi da niyyar tashi, kuma ana ta kiraye-kirayen sallar magriba ya ce da shi. Idan zuwa lokacin uwarta ta sauko, zan duba possibility na zuwanta wajenka hutu har ka kammala, ka fada musu su fito mu yi sallah. Godiya ya yi sosai, sannan ya bar dakin. Tare suke yin sallar magriba da isha wani lokacin in har dukkansu suna gida. Saboda kunyar Mammah yau Hafsat kasa fitowa ta yi daga daki tun shigewarta. Abincin dare ma Baba Azumi ce ta kai mata. Washegari Hafsat ta shirya tana jiran fitowar Mammah ta sauke ta. Shiru-shiru ta ji babu ko motsinta a gidan. Dole ta yi gammon kunyarta ta fito zuwa kicin. Baba Azumi ce kadai tana ta aikace-aikace, ta gaishe ta sannan ta tambaye ta Mammah, ta ce ita ma yau tun safe bata ganta ba kuma Daddy ya jima da fita. Juyawa ta yi zuwa dakin Mammah, a darare ta yi sallama ta shiga. Fitowarta daga wanka kenan tana shiryawa. Gaishetata yi, ta amsa ba yabo ba fallasa, wannan ya ba ta karfin gwiwar cewa. Mammah, dama na jiki shiru ne, na leka kicin Baba Azumi tace ba ki fito ba. Ki je ku tafi da mijinki, nawa mijin ya hana ni kai ki. Dan jimm! Ta yi, jin kamar cikin gatse ta fada, ta yi kasa da kanta, Ki yi hakuri Mammah abin da ya faru jiya wallahi.... Addah! Did I ask anything? Ta girgiza kai tare da hadiyar miyau, mukut!Mommah to ai na ga kamar....kamar kin yi fushi ne? Murmushin takaicinsu su duka biyun ta yi, sannan ta dube ta. In ba so ki ke yau ma ki bata min rai ba to ki wuce ki neme shi ku tafi. In kun ga dama ku wuce gidanku daga can. Im just trying my best to protect your dignity,in kuma kwato miki darajar ki da ya bi ya wulakanta sabida wata mace yar uwar ki da bata fi ki komai ba, amma na lura aikin banza nake yi. Adda kina da wayonki dana ke ganin baki da shi, tunda har kinsan ki yimin karya sabida Abdulazeez. Don haka bana cikin shaaninku, ku barni in yi alamuran gabana. Kukan da ba ya yi mata wuya ta soma, Mammah ko ta kula, ta ratseta ta wuce zuwa closet dinta, kaya ta saka ta fito ta wuce ta gabanta ta bar mata dakin. Makarantar da ba ta je ba kenan saboda rashin dadin zuciya. Inda Allah ya taimake ta ma ba su da gwaji, kuma lacca daya gare su. A yinin ranar bakidaya Mammah ba ta shiga harkarta ba, Azumi kadai ke kula ta, ita ma ta lura yau ta yi tsami tsakanin Mammah da yar gaban goshinta. Amma an ce fadan da babu ruwanka dadin kallo gare shi balle irin nasu, da in ka sake ka shiga koda da ba da hakuri ne kai ne da shan kunya. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Washegari bayan ta shirya ko breakfast ta kasa, labewa ta yi jikin tagarta sai da ta ga ficewar Abdulazeez daga parking space na gidan. As usual cikin shigarshi da ke tafi da imaninta;dark grey suit da farin tie a wuyansa rike da black robe dinsa da wig a hannu, ya bude mota ya shige. Ya ajiye su a kujerar gefensa ya gyara tie din wuyansa ta hanyar sassauta shi, sannan ya kunna motar.Har ya bar gidan a kan idonta. Ajiyar zuciya ce ta subuce mata, ba ta da idea na yadda ta yi kewarsa cikin kwanaki biyun nan. Mayafi ta yafa kalar atamfar jikinta ta dauko handbag dinta ta fito. A kicin ta tadda Mammah da Azumi ta gaida su. Azumi ta amsa, amma Mammah ciki-ciki ta amsa. Cikin marainiyar murya don Mamman ta ji tausayinta, ta ce, Mammah ko Illaila yana nan? Zan je na roke shi ya kai ni makaranta. Kamar ta rabu da ita, sai kuma ta ce, Ke ma kin san bacci yake, amma ai kina ji shi wannan din mai sammakon ya fita ko? Me ya sa ba ki fito da wuri kin bi shi ba? Shiru ta yi, a ranta ta ce. Don kar in kara laifi. Sai ga Usman ya shigo, Mammah yake nema. Ya dube ta ya dubi Mammah da ke cin magani. Ya aka yi ne senior Sis? Mammah ta ce, Ka sauke ta makaranta in hanyar za ka yi. Ya fada mata sakon da ya kawo shi, ya ce su je ya kai ta. Kwana uku Usman ke kai ta makaranta ya dauko ta, ta ki yarda ta hadu da Abdulazeez ma, duk dai don kada ta kara laifi a wurin Mammah. Shi din kuma isvery busy shirin tafiyarsu kain da nain shi da colleaguesdinsa, wataran har tara na dare yake kaiwa bai dawo ba sabida cuku cukun visar su. Mammah ta san da zancen tafiyar, sai dai ba wanda ya ji ta bakinta a kai, ta ce da Daddy da ya gaya mata zancen Allah ya bada saa. A cikin ranta damuwa ce tsantsa, kada kuma wannan karon ya je ya kwaso mata soyayyar baturiya. Zuwa wannan lokacin ta sallama, ta hakura ta yi niyyar amincewa ta maida Hafsat gidanta bayan ta gama jarrabawar karshen semesterda za ta fara sati mai zuwa, sai kuma ga wannan zancen tafiyar ya taso. Sati daya bayan haka suka wayi gari da baki na ba-zata, Malam Hashim Babbah Jimeta, uwargidansa Daada Zainabu da kafatanin iyalinsa maza da mata, masu aure da marassa aure. Wannan tafiya takakkiya ce ta godiya daga wannan zuria mai albarka zuwa zuriar Maryam Dakata da maigidanta tsohon Ambassador Hamza Atiku. Daga nan Abuja, Kano za su wuce gidan marigayi Malam Abdullahi Dakata. Daddy ya san da zuwansu don yana office Malam ya kira shi ya gaya masa tahowarsu, ya kuma kira Mammah a take ya gaya mata. Nan da nan ta sa maaikatan gidan maza na waje su bude sashen baki su gyara duk da kusan koyaushe a gyare yake. Ita da Baba Azumi kuma suka shiga kitchen. Hafsat tana makaranta sai gefen maghriba ta dawo. Tun daga gate ta fahimci gidansu a cike yake, motocin buses(Yola Express) har ukku, tana kuma iya shaida motar Babanta Sienna da motocinsu Uncle Sagir data Modibbo. Tun Usman bai gama daidaita parking ba ta fice saura kadan ta fadi. Shi ya biyo ta da jakar hannunta cikin gidan. Tana shiga falon farko ta yi arba da DAADA da gudu ta runtuma ta rungume tsohuwar, daga nan ta shiga bin matan daya bayan daya tana runguma bakin nan har kunne. A gaban Dr. Bashar ta dakata sai yashe baki ta ke. Cikin dan fillancin da ta koya wajen Dada ta ce da shi, Abba mi nani beldun larugo ma, noi lawol? (Abba na ji dadin ganinka, ya ya hanya?) “Minma minani beldun larugo ma Ghaaji, on don jambe jaumu sare ma be saro ma(ni ma na ji dadin ganinki auta, ina fatan kina lafiya ke da mijinki da iyayenki)? Mindon jam do hairu Abba (lafiya muke cikin alheri Abba). Imamu ta kalla ta ce, Na yi mafarkinka Hamma Imamu, ashe ba da jimawa ba za ka zo. Murmushi ya yi, ya ce, Gaji abeddi vodugo (kin kara kyau). Barrister ya iya kiwo. Kunya ta ji ganin Mammah ta kalle ta. Ta ce masa Ya Futy? Are you done with your project? Ya ce, Na gama, ina jiran su kira ni defence. Barrister ya gaya min you are studying Geography, yana so ki zama malamar makaranta sabida sanyin halinki, teachingsai mai hakuri. I told him that is how our mother was, she is very cool. Kin san kusan koyaushe muna waya da shi. Shekaranjiya ya ce zai zo Jimeta in the nexttwo weeks sallama, zai tafi karo karatu. Maganganunsa sun jefa ta a kogin mamaki, sun yi nitso da ita a kara son Abdulazeez, sai dai magana ta karshe ta kidima ta, karo karatu? Yaushe aka yi wannan maganar? Kasancewar falon ya gauraye da hirarraki tsakanin bakin da jamaar gidan kasancewar har Daddy ya dawo ya zauna cikinsu ba mai jin hirarta da Yayanta Imamu, Yayan da ya fi sauran (Modibbo da Abdurrahman) shiga zuciyarta saboda kulawarsa gare ta da personality dinsa na son karatu irin nata. Imamu rikakken dan boko ne, wanda son zurfafa ilimin bokon ne ya hana shi aure da neman aiki har yanzu, tun bayan kammala digirinshi na farko. Ba tare da ya lura da yanayin kidima da labarinshi ya jefa ta ba ya shiga ba ta labarin kyakkyawar alakar da ke akwai tsakanin mahaifinsu da Abdulazeez a yanzu. Da kuma su kansu ba tare da saninta ba. Ya kare zancensa da tambayarta ko tare za su tafi? In tare za su tafi ya ya nata karatun? Ajiyar zuciya mai nauyi Hafsat ta sauke ta dubi Yayanta Imamu, gaskiya ta gaya masa ita ba ta san da maganar ba. Rokonta ya yitunda ba ta sani din ba, kada ta ce ta ji ta a bakinsa. Da ya san ba ta sani ba da bai fada ba. Dariya ta yi, ta ce, Wallahi babu komai. An yi hira ta zumunci iri-iri, an ci abinci an sha ababen sha daban-daban. Sai wajen karfe tara Abdulazeez ya dawo ya tadda su duk da dai ya san da zuwan nasu, suna hanya Dr. Bashar ya gaya masa da suka iso ma Daddy ya kira shi ya sanar da shi ya ce yana office yana cike-ciken takardu kasancewar tafiyar tasu saura sati daya. Sai yanzu ya gama ya dawo. Hannu Dr. Bashar ya bude masa tun shigowarsa yana fadin, Come here my son. Kunya ya ji sosai, ya so ya fara isa gurin Malam Babbah, amma Dr. Bashar ya makale shi. Ismael dariya abin ya ba shi ganin reaction dinsa kamar mace a gaban suruki, wai Yaya Azeez ne da jin kunyar wani. Har karfe goma na dare suna falon, sannan kowa ya fara neman makwanci, mazan a hoteldin (Berkshire, Asokoro) Daddy ya yi musu masauki, matan suna guest rooms wasu suna cikin gidan. Hafsat ta ceDada bakuwarta ce gado daya za su kwana. Mammah kuma Aunty Kubra da Kaltum matar Modibbo ta kai nata dakin. A dakin Baba Azumi ma akwai su matan Yaya Tijjani, matan sauran yayyen marigayiya Habiba su biyar, sauran kuma suna guest rooms din gidan. Malam Babbah an ba shi daki daya a dakin bakin saboda ya ce ba zai iya kwanan hotel ba. Da manyan jifa-jifan Daddy Ismael, Usman da Salisu suka yi ta jigilarsu zuwa hotel. Abdulazeez yana dakin Malam Babba, sabuwar hira suka bude, Malam Babba na son jin labarin rayuwar yarsa Habeebah a Jeddah da kuruciyar Hafsat.In ya tambayi Abdulazeez dayan wannan, murmushi yake yi ya ceMalam Habeeba ispious (mai ibada ce) as far as I know. Ba abin da ta ke so irin jumaah ta zagayo mu shiga cikin Haraam, mu yi umrah (dawaf, safah da marwah) ta yi ta sallah a maqama Ibrahim. Na dade da lura da hakan a tare da ita, sannan tana son karatun alkurani. Akwai islamiyyah da Daddy ya sanya ni ta Larabawa a can Jeddeh idan na je musu hutu, idan na dawo sai ta ce in karanta mata inda aka kara min. As for Hafsat ba zan iya karar da komai a kan kuruciyarta ba. Saboda sun yi dukkan kuruciyarsu a wata kasar TuraiBelgium yayin da ni nake nan Nigeria. Dan sanin da na yi mata sanda suke Saudiyyah ne. An haife ta bakwaini, ta dade a cikin incubator;wata kwalba ce da ake saka jariran da aka haifa ba su isa lokacin haihuwa ba. Ban taba yi mata kallon rayayya ba; dalili na shine an haife ta bakwaini, kuma uwa bata mike ba, sannan ga pneumonia. Amma buwayar Allah da ta wuce misali. Tunda ta taso shakka ta ta ke, ban san dalili ba. Ya dan yi shiru cikin jin kunyar abin da zai fada a gaba. Kodayake laifina ne Malam, ban ja ta a jiki yadda ya kamata ba, na so Habeeba kamar Yayata, amma abin mamaki Hafsat ba ta shiga raina ba, shagwabarta ta yi yawa. It doesnt sound good ko Malam? Malam Hashim na jin turanci, saboda ya sha gwagwarmaya a rayuwarsa, kuma ya yi alaka da masu ilimin boko. Furtawa a kan harshensa ne ba ya yi, don haka tsaf ya ji abin da Abdulazeez ya ce. Murmushi ya yi, ya ce, Ga shi kuma an ce a so kare har jelarsa.. Dariya ya yi cikin jin nauyi. Tsorona ta ke ji sosai kamar dodo Saboda ba ka sakar mata fuska. Inji Malam. Ya tura hannunsa cikin tarin sumar kansa, wani murmushi ya subuce masa. Sai kuma Mammah ta zo ta hada aure ba? Saboda ta yi maganinka. Dariya ya yi, ya ce. Na yi protest fa kala-kala Malam, ni da kai aminai ne, can we make a very tight secret? Jinjina kai tsoho Hashim Babbah Jimeta ya yi, ya ce, Fadi da Hausa ko fullata. Ya zama serious ganin yadda dattijon ma ya dauki seriousnessya dora a kamilalliyar fuskar dattijantakarsa, mai cike da farin gemanya. Na ce za mu iya yin sirri ba tare da kowa ya ji ba? Sai don ka roka min Mammah alfarma da afuwarta? A shirya nake da yin hakan Abdulazeez. Malam kowa yana kuskure ko? Gyada kai Malam ya yi, Har Annabawa da sahabbai. Ban da Khatimul Anbiyae wa Imamul Mursaleena. Wata nutsuwa Abdulazeez ya ji ta saukar masa, kaunar dattijon ta kara ratsa shi. Ya ji zai iya gaya masa komai tsakaninsa da Hafsat ko da ba zai yi masa uzuri ba. Komai ya farke masa tun daga ranar da Mammah ta bijiro masa da maganar bukatarta na ya auri Hafsat har gabar da suke kai a yanzu. Ya kare zancensa da cewa, Shi ne kuskure mafi girma da na san na taba yi a rayuwata da girmana Malam. Ban san ya ya SO na hakika yake ba sai a kan Hafsat! Ban san cewa soyayyar aure daban ta ke da soyayyar matan waje ba sai da Mammah ta aura min Hafsat! Ban san wani abu mafi azabtarwa a rayuwata ba sai da ta kwace min Hafsat. Ban san ladabtarwa mafi wahala ba sai raba ni da Hafsah da Mammah ta yi a halin yanzu. Ta hana ni Hafsat tun bayan maida aurenmu da su Baffa suka yi, ko ganinta ba ta bari in yi Malam duk da ta san auren ya maidu. Malam babu wani nauin ban hakuri da ban baki da ban yi mata ba ta ki saurarena. Na hada ta da Adda Hafsatu (mahaifiyarta) ko ta ga girmanta ta mayar min Hafsat, amma Adda ta ce ta yi mata daidai, ba za ta ko sanya baki ba. Malam sun kasa yi min uzuri su karbi kuskurena kamar yadda na tabbatar ni mai laifi ne, kuma na karbi laifina. Ka taimaka ka roka min ita don na ga tana ganin girmanka, ko ba za ta ba ni Hafsat in tafi da ita ba, ta dinga amsa gaisuwata yadda ya kamata, ta daina fushi da ni, kuma ta yafe min laifin da na yi mata. Kasancewarsa mutum mai tarin ilimin addini da sani a fannonin zamantakewar yau da kullum, ya fahimci duk labarin da Abdulazeez ya ba shi, da abin da yake so ya fahimta indirectly (yana matukar son Hafsat daga baya bayan da ya zauna da ita na tsawon shekara daya da wasu watanni). Mammanshi kuma ta ki yarda da shi a karo na biyu, bata yarda da sauyin zuciyar tasa bata ki maida masa Hafsat don ta sayo mata mutunci da martaba a idanunsa. Wannan wace irin mutum ce maabociyar kawaici da karah? Mai maida nata ba nata ba ne, na waninta shi ne nata? Mai rufe ido ta hukunta dan cikinta da mafi azabtarwar hukunci a gare shi akan yar wani? Ai ko Abdulazeez ba ya son Hafsat kuma ya ce yana son karo mata uku bayan ita in har yana raye ya samu ya gama. Hannunsa ya kama ya rike cikin nasa yana dubanshi cike da kauna. Yayin da shi ya sunkuyar da kansa guilty concience na sakin Hafsat na lullube shi. Malam Babba ya ce. Ina Muazatu yanzu? Bayan ita akwai wata wadda ka ke so? Jin zancen ya yi kamar daga sama kasancewar ba shi ya tsammaci ji ba. Girgiza kai ya yi da sauri, Babu wannan zancen fa Malam. Na ba ka cikakken labarin ne don ka fahimci komai ba don a tado wannan zancen ba mara fasali. Wani alamari ne da ya riga ya shude, babu ko birbishinsa a zuciyata yanzu. Soyayya ce ta shekarun kuruciya kuma ta dade da gushewa. Malam ya ce, Tana ina yanzu? Da sauri ya ce, Ta yi aure Malam, ko ba ta yi aure ba bari in maka a fili tunda hakan ka ke so, bana son ta yanzu, ban kuma san me ya kai ni ga son nata ba a wancan lokacin saboda bata dace dani ba ta kowanne bangare. Na lissafa lamarina da ita cikin kaddarori masu zuwa su wuce a rayuwar dan Adam. Malam ya fahimce shi sosai, amma don ya kara kore shakku ya kuma tabbatar Hajiya Maryam ba ta shiga hakkin Abdulazeez saboda Hafsat ba, sai ya ce, An taba son mace a daina Abdulazeez? Da sauri ya ce, Wasu kaddarorin na shigowa rayuwarmu ba don su tabbata ba, ana haduwa da su a kan hanya a kuma rabu kafin a iso gida. (Dreams are conceived, but not all dreams are born alive. Some are aborted. Others are stillborn. -Zainab Alkali).Wannan ne zahirin tsakanina da Muazatu. Malam ya gamsu da bayaninsa, sannan ya yi murmushi ya dube shi, bari in in kara yi maka nawa bayanin akan masalar aurenku. Duk da BaffaAtiku yayi nasa. Tunda ka yi kome na gaggawa kafin kammala iddah kuma saki guda daya ne aurenka da Hafsatu yana nan ba abin da ya same shi. Niyyar farkodama sharia ba ta yarda da ita ba tunda an gina ta ne a kan muta, komen da ka yi wa sakin da kyakkyawar niyya da tsaftar zuciya shi ne ya gyara auren. Abdulazeez ya san Baffa ya fadi hakan, amma da Malam ya kara maimaitawa sai ya ji hankalinsa ya kara kwanciya. Murmushi yake ta yi, sai da Malam ya yi masa dariya. Fada ya koma yi masa kan abin da ya yi (yarjejeniya a cikin aure), ya ce aure ba abin wasa ba ne, ibadah ce wadda ake neman dacewar Ubangiji a cikinta. Cikin kowacce ibada sai an sa taqwa wajen biyayya ga mahalicci. Ba abu ne da ake yinshi kara-zube don biyan bukatar rai ba; abu ne da ke gine kan tsari da dokoki na shariah ba a hada shi da son cimma wata manufa. Ya gargade shi da yin istigfari da tuba nasuuhan. Wato tuba da zummar ba za a sake maimaita wannan kuskuren ba. A karshe ya ce. Ka sani Hafsat yar Hajiya Maryama ce babu wani mai iko da ita sama da ita. Har kuwa Dr. Bashar, don haka lallashi da ban-baki da kamun kafa za mu yi shi har sai ta hakura. Za a iya yi mata dole, amma abin da zai biyo bayan yin dolen shi ne abin gudu, wato tsaurara mata fushi a zuciyarta. A shirye nake da in tsugunna a gabanta gobe in yo mana bikon Hafsat ka ji ko? Je ka ka yi baccinka har da minshari. Amma ni ma ina rokon alfarmar ka zo Jimeta in karo maka kyawawan fulani guda biyu, Hafsatu ta yi maka kadan. Dariya ya yi, ya ce, Malam! Bari mu fara kama dahir tukunna,ma yi wannan zancen daga baya, watakila nan da shekaru ashirin! ****** WASHEGARI Assalamu alaikum. Mammah ta fada daga bakin kofar dakin da aka sauki Malam Babba. Gyaran murya ya yi, ya ce, Ameen walaikumussalam, shigo daga ciki Hajiya Maryama. Ta tura kofar ta shiga, Azumi ta biyo bayanta dauke da tray mai girma. Gaban Malam din ta isa ta ajiye wanda ya yi wanka ya shirya cikin farar shaddah, ya sha farin rawani da babbar riga, farin gemunsa ya kwanta sosai. Azumi ta gaishe shi a nan ne Hajiya maryam ta gabatar da ita wajensa matsayin uwa ta biyu ga Hafsa tun a Birnin Jeddah. Kujuba-kujubar rayuwa a kasashen ketare duk tare aka yi ta har yau da aka dawo gida. Ta gaya masa mutuniyar Sokoto ce, yayanta da jikoki duk suna can. Zaman Hafsat takeyi yau shekara sha takwas. Malam Hashim ya kara gaisawa da Azumi, ya yi mata adduar alkhairi. Mammah ta matsa gabansa, ta ce. Wanne zan zuba wa Malam? Kunun Acca, na Alkama ko na gyada? Murmushi ya yi, ya ce, Sannunku da hidima, muna rokon Ubangiji ya fi mu godewa. Zuba na Acca. Ta tsiyaya masa a kofin tangaran, ta zuba masa kosai da aka yi shi luba-luba ya ji albasa da kwai, a gefe ta zuba dankalin hausa (sweet potatoe) da na Turawa. Sai farfesun bindin Saniya a kwanon tangaram. Suka mike don su ba shi wuri ya ci abinci. Ya ce, Hajiya Maryama in ba abin da ki ke yi ki zauna in gama akwai abin da nake so mu tattauna. To babu komai Malam, bari in je in sallami su Dada sai in dawo kafin nan ka kammala. Babu laifi. In ji shi. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Sai dai kowa a gidan ya karya aka fidda kwanukan wanke-wanke kafin a dora abincin rana, sannan Mammah ta samu nutsuwa, ta dawo ta tadda Malam. Sai da suka sake sabuwar gaisuwa ya ce da ita, Akwai shanu da tumaki da marigayiya ta ke kiwo guda biyar a cikin garkena kafin barinta gida. An ci gaba da kiwatawa a bayanta. A yanzu haka sun bunkasa da albarka mai yawa, kafin in taho na sa an tattara su wuri guda an raba su ga magadantayadda Ubangiji ya yi umarni. Na Hafsatu ban san ya zan yi da su ba na ce in mun zo zan ji ta bakinki. Ajiyar zuciya Mammah ta yi ta gyara zamanta, sannan ta ce, Ni ma a hannuna akwai kudin aikinta na tsayin lokacin da ta yi tare da mu, na so in ba ta a karshen kowanne wata ta ce in dinga tara mata, tun a wancan lokacin na zuba su a wani account a kasar Saudiyyah ban kara waiwayarsu ba, sai dai details din komai yana hannuna, zuwa yanzu Allah kadai ya san hauhawar da suka yi. Zan sa Babansu ya dawo da su account dinsa da yake har yanzu yana da ajiya da su, sai ya ba ni in ba ku a sake rabawa magadanta. Sannan ita Hafsat akwai wasu kudaden masu yawa a account dinta wanda Babansu ya bude musu ita da sauran yan uwanta a kasar Belgium, kowannensu na amfani da nashi ban da ita don haka ni yanzu Hafsat ta fi ni kudi, ta koma Hajiya Hafsatu. Ta karashe da dariya. Shiru Malam Hashim ya yi yana magana da zuciyarsa, wace irin mutum ce Maryam Dakata? Anya akwai sauran mutane irinta a duniya? Yanzu har wani kudin aikin Habeebah ta ke ajje da shi bayan dawainiyar abin da ta haifa ta bar mata? Da kyar ya iya yin magana, amma hawaye cike da idanunsa. Duk da wannan hakki ne na magada, amma na ari bakinsu dukkansu na ce mun yafe! Ya taso daga inda yake zaune a kan center carpet ya iso gabanta ya durkusa tana zaune a kan kujera. Alfarma muke nema wadda daga ita babu saura cikin dimbin alfarmominki Hajiya Maryama. Cikin wannan kyautayi naki mai yawa, cikin wannan adalci naki abin kwatance, da wannan zuciya mai taimako irin taki wadda babu irinta, ki bar waiwaye da hango komai na baya da ya riga ya wuce, ko wanda zai faru a gaba, ki maida wa yaron nan matarsa! Mun yi kuskure kuma mun gane mun yi, mun ladabtu da ladabtarwarki, muna masu farin cikin sanar da ke cewa, makamancin wannan ba zai sake faruwa ba, insha Allahu. Shi ne har sai ka durkusa min Malam? Don Allah ka yi hakuri, abin bai yi girman haka ba, don Allah ka bar durkuson na, zan maida ita insha Allahu. Malam ya koma ya zauna, Na gode sosai Hajiya Maryama. Ai ita kuruciya ba abin da ba ta sa wa. A ranta ta ce, A lokacin da ya shirya kwangilarsa shekarunsa talatin da daya, shi ne za a kira wa kuruciya? Maganar dukiyar Hafsat suka koma yi, ta ce a ci gaba da yi mata kiwo a Jimeta, kudadenta za a saya mata hannun jari ta dinga karbar share duk wata zuwa asusunta, sannan za ta saya mata motar hawa tata ta kanta. Malam ya ce, duk yadda ta yi shi ne daidai. Ta ce, Ya kamata ku je ku ga muhallinta duk da dai an kwana biyu ba a shiga ba. Suna haka Abdulazeez ya shigo, ya yi shirin office, kamshin daddadan turarensa ya sanyaya dakin. Yau suit din da ya sanya dark green ce haka wandonta, da farin neck tie kamar kullum. Kafin ta jefo harara ya yi maza ya durkusa ya gaishe ta, Malam kuma ya kafe ta da fararen idanunsa ya ga yadda za ta amsa don haka ta amsa kadaran-kadahan a zuciyarta tana jinjina rashin ta idon Abdulazeez da ya iya dosar Kakan Hafsat da wannan maganar. Ubangijin da ya halicce shi Ya halicce shi frank mara boye gaskiyar abu don a so shi, ko mai fuska biyu. Yadda fuskarsa ta ke sak, kamilalliya haka zuciyarsa ta ke. Ya juya ga Malam din yana masa barka da tashi ya ce, Ya ya bakuntar birnin tarayyah? Kwana biyu ka huta zafin Yola, ko mu rike ka a nan na shekara uku? Murmushi ya yi, ya ce, Barni in mutu a mahaifata, zafin Yola ai gyara fata yake yi ban da haka ai da ba ka gan ni haka ba. Dariya ya yi, ya ce, Ni kuwa duk zuwana garinku bana iya kwana da riga, sannan kafin na taho bana duba madubi sabida yadda baqina da muni na yake nunkuwa. Ni kuwa da na ce amaryarka ta Yola can za ka bar muna ita, ko ma ke ganinka a kai-akai ashe ita ma barikin za ka taho da ita? Mammah ta dago da sauri ta dube shi, ya gintse fuska ya ce, Malam! Kada ka ballo min ruwa mana! Ka ga uwarta tana hararata, yaushe muka yi haka da kai? Ka ji min dan albarka, ba jiya ka ce in aje maka ita sai bayan shekaru ashirin ba? Mammah ta fiddo idanu sosai tana kallonsa. Ya dafe kai, ya ce, Malam, shekara ashirin irin ta Bahaushe nake nufi, kuma kai fa ka kawo zancenka, ka fada yadda Mammah za ta gane ba ta cika fahimtar abubuwa a yadda suke ba. Mikewa ta yi ta bar musu dakin bayan ta yi wa Malam sallama za ta je wajen sauran baki. Da sauri Abdulazeez ya bi bayanta, a corridor din dakunan ya sha gabanta ya kamo hannunta ya marairaice idanu, Mammah ni fa ban san zancen da yake yi ba. Kwace hannunta ta yi, Matsa ni ka ba ni hanya, a daura maka dari ma mana ya ga kana so ne. Ya sake tare ta, shi lallai ta yarda zancen na Malam Babbah ne. ta ce, Wallahi Abdulazeez kana shiga hancina da yawa, ka kai karata ban ce maka komai ba, wani ya ce bayan Hafsat kada ka kara aure? Gashin kansa ya shafo, ya ce. Balle ma shes o.k for me, as you are o.k for Daddy. Harara ta manna masa ta lura yau nishadi yake ji, tunda ya ci ta da yaki. Wata irin kaunarshi ke kara ratsa ta. Duk yayanta ya fi su kama da ita, hasken fata kawai ta fi shi, Za ka ba ni hanya ko sai wani ya zo ya ganmu a nan? Ya ce, Zan matsa, amma sai na ji yaushe ne?. Yaushe ne me? Za ta koma saboda tsoronki nake ji kada Malam ya tafi ki ce ba ki san zancen ba. Dariya ce ta kamata, amma ta shanye, ko za ta maida Hafsat ai sai ta gyara ta ba haka lokaci daya ba yadda ta fahimci take-takensa, in Hafsat ta shiga hannunsa sai gyaran Allah, dole ta dasa ta a zuciyar mijinta, ya daina hango kowacce ya mace. Duk gyaran amarcin da ta yi mata ta tabbata iska ya bi. Juyawa ta yi ta koma dakin Malam yana duba wani littafi, ta ce. Malam, ka gaya masa kada ya takura min a kan komen Hafsat, tunda na ce maka za ta koma to tabbas za ta koma, amma sai na shirya. Malam ya ce, Abdulazeez mu kara hakuri ta yi mata lalle tukun. Gabadaya suka bushe da dariya har ita. Ta ce, Lalle da kitso kuwa. Ya ce, To ai ka ji, aikinsu kenan. Mammah ta ce, Malam ko za ku je ya kai ku can gidan nasu ku gani? Wata unguwa ce nan a gabanmu Sun-City. Girgiza kai Malam ya yi, Ba sai mun je ba. In ta haihu mun zo suna. Duk rashin kunyarsa yanzu kam ya ji ta, ya fice da sauri ita ma ta wuce sauran dakunan. Dada ta tambayi Malam ya ta ga Hafsatu da Abdulazeez a gidan tun zuwansu ya ce gyaran gida ake musu. Mazan ma debo su aka yi daga hotel suka dawo gidan a nan suka karya kumallo. Haka wannan family suka wuni cikin aminci, suka shaku da juna cikin dan lokaci. Da Usman zai maida Dr. Bashar, Modibbo, Abdurrahman, Imamu masauki da daddare Hafsat ta bi su. Dakin da aka kama musu babba ne ciki biyu da falo, su suna ciki daya, Dr. da suke kira Abba na daya. Usman tafiya ya yi ya barsu ya ce zai dawo karfe goma ya dauke ta. Wata irin hira aka yi yau tsakanin Hafsat da mahaifinta, da yan uwanta. Hira mai shiga rai da sanyaya zuciya. Rabin hirar labarin mahaifiyarsu suke ba ta da yadda ta kula da rayuwarsu da tattalinsu. Ta ji halin da kowannensu ya shiga ranar da suka neme ta suka rasa. Ta ji tsayin lokacin da mahaifinsu ya dauka bai kara aure ba. Rayuwarsu a hannun Dada har zuwa girmansu. Har gobe kewarta muke Gaaji (Auta), ba mu fita daga cikin kewar ba. In ji Imamu, Har gobe gani nake kamar zan rufe ido in bude in ganta ta dawo ga ki a gabanta. In ji Modibbo. Ni har gobe gani nake kamar unguwa ta tafi, ko ta je Demsawo ne ta dawo . In ji Abdurrahman. Hafsat sai ta sa kuka. Ba ta santa ba, ba ta taba ganinta ba sai a hoto! A hoton ma a dakin Dada, Mammah ba ta taba nuna mata ba sai zuwansu Jimeta, Abbah da ke kallonsu cikin tausayi da kauna bai yi magana ba sai wannan karon, ya ce, Kun sa ta a gaba don ku yi hira ne, ko don ku sanya ta kuka? Ba ku yi murna da uwar rikon da Allah ya bata ba? Ba ku yi murna da kyakkyawar rayuwar da ku ka ganta a ciki ba? Ko ku ba ku gode wa Allah da mijin nuna wa saa da ya yi mata baiwa da shi ba? Tunda nake ban taba ganin mutane masu karamcin wadanda na gani tare da ita ba. Kada ku manta fa matsayin yar aikinsu uwarta ta zauna da su, suka dauka suka rike duk da ba su da tabbacin halaccinta. Sannan ba su yi tunanin hakan ba suka aura wa gudan jininsu. A yadda alumma ta koma yanzu dan aikinka kamar ba cikakken mutum ba ne, masu kudi ba su dauki masu hidimarsu komai ba face tsumman takawarsu. Don haka kada mu kasance masu butulci ga Allah mu gode maSa a bisa wannan jarrabawa da Ya yi mana. Usman bai dawo daukarta ba sai sha daya na dare, shi da Ismael ne. Sun yi hira da su Imamu sannan suka yi sallama suka tafi. Suna fitowa daga mota Abdulazeez na bullowa daga guest house wajen Malam, zai shiga gida. Cikin mamaki yake dubansu su duka ukun, har suka iso inda yake tsaye. Kugunshi ya kama Ku kuma daga ina a daren nan? Yana zabga musu harara daya bayan daya har ita Hafsat din. Ismael na son yin dariya, amma ya san bai isa ba. Mun dauko Addah daga wajen Abbanta ne. Da izinin wa? Ya fada yana hararar Hafsat din, rabon da ya ganta tun ranar rockview, ba ta kara yarda ko da kuskure sun hadu ba. Shi kuma ya san bai isa ya je inda ta ke ba. Haka ya yi ta daurewa yana hakurkurtar da zuciyarsa, sai kuma hidimar tafiyarshi ta kwashe kaso hamsin na lokutan da yake samu a gidan ma, ko yana nan akwai abubuwan da yake yi na cike-ciken takardu ko processing visa dinshi a system bai cika damuwa ba duk da ko me yake yi tana makale cikin zuciyarshi.Dariyar da Ismael ke yi cewa yake a ransa, kada dai Yaya Azeez kishinmu yake yi? Mammah ce ta ce a kai ta. In ji Usman. Hanya ya ba su bai ce komai ba, suka wuce babu ko waiwaye. Za ta wuce ya sarko hannun ta cikin nasa, dagowa ta yi fuska a turbune. Wani irin kallo yayi matakafin yace. Wai tsakanin ni da Mammah wa ke aurenki ne yarinyar nan? Ta turo baki cikin kunkuni irin wanda ta saba yi masa ta ce. “...Sai an shafa za’a ji!.Ba don ya kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, kuma ta saba magana irin hakan in ya mata abinda bai gamsheta ba, da bazai ji ta ba. So yake su hada ido amma ta ki, kawai sai ya finciki hannunta zuwa ciki, ta studyroom ya ratsa dasukasancewar ta cikinsa zaa iya bullewa dakunansu. Hafsat ta kalli study-roomdinnan with lingering look!Dakin daya tuna mata watarana da bazata taba mantawa a tarihinrayuwarsu ba wato ranar.... kuma dakin da aka assasa AUREN KWANGILA a cikinsa......(Wanda a yanzu ya juye ya rikide zuwa wani aure mai ban mamaki),ya bi ta can ne don kada ya hadu da kowa shiyasa bai bi ta main parlour ba zuwa inda dakunansu suke. Nashi ne a farko sannan na Ismael sai na Usman da na Haleem suna kallon nasun. Tura kofar ya yi ya fisgo ta ciki ya rufe kofar har da key. A jikin kofa ta tsaya idanunta sun raina fata, ta ce. Haba don Allah Yaya Azeez dare fa ya yi, Mammah ta san mun shigo gida tun dazu. Wani irin kallo yake mata, wanda ya kara kada hantar cikinta. Maimaita abin da ki ka fada dazun? Tukunna ma guduna da ki ke duka a kwanakin nan na mene ne? Hafsat ta yi shiru, ya ci gaba da matsowa gabanta. Har ya zamanto space din da ke tsakaninsu taki biyu ne kacal. Yatsunshi biyu ya sanya ya dago habarta cikin kankanuwar murya ya ce, Hafsah! Ta bude fararen idanunta tarrr! Ta dube shi, da wani irin kallon so da ya tsirga har babban yatsar kafarsa wanda ita bata san ta yi ba. Umarni ne na zuciyarta kawai zuwa idanunsa. Da azama ya rungume ta, ya soma magana cikin kunnenta da sauti mafi tsananin taushi da ya mallaka. Kin ce in shafa in ji ko? Ni da Mammah wa ke aurenki?Ok Hafsat lets find out......”. Dago kantayayi daga rungumar da yayi mataya sanya fuskarta cikin tafukansa ya somasumbatarta cikin wata irin siga (wani abu data lura ya fi kwarewa a kai muddin ya samu damar hakan tun a gidansu wato sumba. Ta fahimci wannan shine abinda cikin kowanne hali yake ciki (bacin rai ko akasinsa) baya iya fasawa a kantawato dai baya gajiya da sumbatarta). A yanzun kuma yana yi ne cikin yanayin da ke nuna tsananin kewar ta da yayi, da matukar son sa da hakan. A wannan lokacin ita kanta Hafsat bata da banbanci da shi na jin cewa tayi kewar tasa don dai ita mace ce, kuma maabociyar kawaici da alkunya. Saidai ita ta san bata wannan fannin kadai tayi kewar Abdulazeez ba. Ita in general komai da ya dangance shi take kewar;fadansu, jayayyar su, kalamansa, murmushinsa da komai nasa... Daga shi har Hafsat sun fita a duniyar su sun afka wata sabuwar duniyarda dawowa daga cikinta abu ne da zaidauke su lokaci. “.....Ina son in nuna miki bambancina da ita ne, da abin da ta ke sanyawa kina missing...!!!. Abin da ta iya fahimta kawai kenan cikin tarin tausasan kalamansa cikinkunnuwanta.Hafsatta fahimci abin da Abdulazeez ke kokarin yi nextshi ne raba ta da sittirun jikinta. Idan hakan ta faru kuma bata san me zai biyo baya ba; bata san iya ina alamarin zai tsaya ba. Ta tuna a inda suke, a gidan waye, kuma a tsakanin wadanda za ta kwana. Wani karfin zuciya ne ya zo mata ba don ta cancanci mallakarsa ba, sai don tunanin rashin dacewar abin da suke shirin yi cikin gidannan ya rinjayi halin da ta tsinci kanta. Daman kuma a tsaye suke don haka ta tattara dukkan karfin da ya saura mata ta tura shi baya ya fada gadonsa. Ta yi mamaki da ta ji kamar ta hankade karamin yaro, ba wani sauran karfi a tare da shi. Da azama ta isa ga kofa ta murza key din ta fice. Sai da ta tabbatar she is safe sannan ta tsaya jikin hudar kofar ta ce, Imsorry Yaya Azeez!. Ta gyara tsayuwarta, ta yi lullubinta sannan ta daidaita numfashinta, ta lallaba kamar mara gaskiya ta shige ciki. Cikin saa ba ta gamu da kowa ba, ta murda kofar dakinta a hankali ta shige. Dada ta kashe fitila sai jan rago ta ke (munshari). Hamdala ta yi ta fada bandaki don ta yi wanka. Amma me? Ba ta son ta wanke scent din Abdulazeez daga jikinta, wani kamshi da ta fi so fiye da kowanne a rayuwarta. Fasa cire kayan tayi. Tajingina da kofar bandakin ta lumshe idonta komai da ya faru a yan daqiqan da suka gabata ta ke tunowa daki-daki tana sakin murmushi. “...Ina so in nuna miki bambancina da ita ne, da abinda ta ke sawa kina missing....!!!. Ta tuno kalamansa,wadanda suka sanya ta kara zurfafa murmushinta kamar wata sabuwar mentally retarded.Wato ta fahimci wani aji na musamman Abdulazeez ya gina, ya dauki Mammah ya ajiye ta cikimai kama dana kishiyar sa. Kai Yayan Haleem sai a barshi. Daga karshe dole ta yi wankan don ta san in bata yi ba bazata iya barci ba sabida dawainiyar jamaa data sha yau.Ko da ta yi nafilolin da ta saba ta hau gado, kasa baccin ta yi. Yau ne ranar da ta yi dakacen kwace wayarta da Mammah ta yi. Muryarsa kawai ta ke so ta ji, da halin da yake ciki. Ji ta yi kamar ta yi kuka saboda tausayinsa, amma can a karkashin zuciyarta ana gaya mata hakan da ta yi shi ne daidai, su maza babu ruwansu ita kadai za ta kwana a ciki. Ta tuno halin da ta kasance a ciki ranar da suka je Rockview ko ruwan sha da kyar yake wucewa a makogaronta a gidannan sabida kunyar Mammah. Ta dauki kwanaki ba ta iya hada ido da ita. Balle yau a cikin gidanta? Ta sani ko ya yi fushi zai huce, duk da ta san fushinsa a kan irin haka ba mai sauki ba ne. Ta tuno sanda suka yi irin haka a gidansu ba ta ji da dadi ba na kwanaki masu yawa. Muguwar gaba ya kulla da ita sai ranar da Allah ya kawo Mammah gidan suka shirya dole.Abdulazeez bai iya fushi ba, kuma in ya tashi yi mara dalili yake yinsa wanda kuma in an bi salsala shi ne at fault. Da kyar bacci barawo ya iya sace ta. Zuciyarta fal da so da kaunar mijinta, wanda watanni goma sha shidda irin wadannan a baya ba ta taba tsammanin wai wata rana irin haka na zuwa da za ta so shi ba. Bata taba daga ido tayi masa wani kallo bayan na Yayansu ba; Yayan ma irin wanda baa so! Wanda da da hali da an canza shi daga yayan cikin Mammah!Ba ta san ma mene ne son ba, amma yau a kansa ta koye shi ba tare da wani ya koyar da ita ba. Shi kansa bata zaton ya taba attemptingyin wani abu da gangan ba don ta so shi! Bai taba yin wani abu da sunan ya ja hankalinta kansa ba. Ta so shi ne don radin kanta bisa umarnin zuciya, ruhi da gangar jiki. Don haka ta rattaba soyayyah a matsayin wani abu da turawa suka kira naturalisticphonemenon; wani alamari da ke faruwa bisa kudurar Ubangiji, da hikimarSa. Wanda karfinsa tamkar chemistrydin gravity. ***** Washegari mutanen Jimeta suka yi harama aka yi sallama cike da begen juna. Sun tafi tare da Ismael da Usman wadanda za su yi musu jagora zuwa gidan Malam Abdullahi Dakata. Su Inna Hafsatu tuni sun san da zuwansu, don haka tarba aka yi musu ta girma, irin wadda wannan family suka gada, su din maabota karamci ne kwansu da kwarkwatarsu. Sai suka samu iyalin Hashim Babba Jimeta suma da nasu nauin karamcin. Godiya ce dai da adduaoin alkhairi suke ta yi babu iyaka duk a kan rikon Hafsat da inganta rayuwarta da suka yi, suna rokon Allah subhana ya saka musu da mafificin alherinSa. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Sun so su wuce Jimeta a ranar yamma ta yi, dole sai da suka kwana. Kasancewar gidan babban gida mai sassa daban-daban ya kwashe su tsaf, maza sun kwana a dakunan maza, haka mata. Washegari asubanci suka yi suka koma Jimeta. Su Ismael suka juyo Abuja dauke da sakonnin Mammah daga jamaar gidan da abubuwan da Inna Hafsatu ta saba aika mata wanda ke musu wuyar samu a Abuja. Duk da ma dai lokacin zuwansu Kanon ya kusa, suna zuwa a kowanne bikin sallah karama ko sanda Daddy ba shi da ayyuka. Bayan tafiyarsu gidan ya yi tsit! Ya koma yadda yake, sai Hafsat da ke kewarsu. To ita ma ba ta samun zama ba a satin bakidaya. An kafe musu exams time-table nan da kwana hudu za su fara, wanda ya yi daidai da ranar tashin Abdulazeez zuwa kasar Amurka. In ba ta dakin lacca tana dakin karatu na makaranta ita da Mami Sada, Mami ta lura yanzun ba ta ganin Abdulazeez na kawo Suhaanah makaranta ko zuwa daukarta, wani saurayin matashi ne mai tsananin kama da shi. Saidai shi fari ne tas. Kallo daya za ka yi masa ka gane kaninsa ne, ko dai waniimmediate relationdinsa. Hafsat-Suhaanah tana ba ta mamaki, zurfin cikinta ya yi yawa, a sabon da suka yi yanzu kamata a ce ta san wani abu da ya shafe ta, amma ina! Ko lambar wayarta ba ta da ita. Ba ta da sakewa da bare, hudubar Mamanta ke nukurkusarta kullum, cewa 80% babu aminci tsakanin kawaye yanzu ta kiyaye su. Duk da ta san Mami is good kuma matar aure ce ita ba ta iya surutu ba, har gobe zaman da ta yi tun daga haihuwa har girma a kasashen ketare na tasiri a cikin rayuwarta ta yanzu da yanayin muamalarta da mutane. Rayuwa ta kowa ya yi ta kansa, kowa tasa ta fissheshe shi. Akwai sanda Rabia ta yi fushi da yadda Hafsat ta ki gaya mata tsakaninta da Abdulazeez ta fita shaaninta wajen sati guda, sai ta fahimci Hafsat din ko a kwalarta ta ci gaba da harkokin karatunta ba tare da ta kara bi ta kanta ba. Da kanta ta warware suka ci gaba da alaka don ita kam Allah ya sanya mata kaunarta. Abin da ta fahimta game da ita shi ne, a yi abin da ya hada, amma banda personal life. Abdulazeez ya je Kano sallama ya kwana biyu. Ko sallama bai yi mata ba, ita da kanta abin ya dame ta. Ta fahimci fushi yake yi da ita, abin da ya hana ta sukuni kwana biyun nan. Ko karatun da ta ke yi na first exam dinta ba sosai ta ke fahimta ba. A bakin Usman ta ji yana Kano sai gobe da yamma zai dawo. Da ya dawo ma bai shigo gida ba, Maitama ya wuce gidan Uncle Abdulkarim, a can ya yi sallar maghriba da isha. Tana lissafe da kwanaki daga lokacin da Imamu ya ce mata saura kwana bakwai ya tafi har zuwa yau. In lissafinta daidai ne gobe ne tafiyarsa. Mammah ba ta yi mata zancen ba a tunaninta tunda ta sakar musu mara ba ta shiga shaaninsu ya gaya mata da kansa, sai dai ta lura ko hanya ba sa hadawa tun tafiyar mutanen Jimeta. Wannan ba damuwarta ba ce, shirin da ta ke na komen Hafsat din shi ta sanya a gaba. Tafiyar Abdulazeez ta yi mata dadi za ta yi komai a tsanake, ita kadai ta san shirin da ke ranta. Sai karfe tara ya shigo gidan, kai tsaye wajen Daddy ya wuce sun dade suna magana a kan yadda tafiyar za ta kasance, da inda zai zauna a can. Daddy ya ce ya dauki nauyin gidan da zai zauna a garin da jamiar su ta ke, zai kama masa kusa da makaranta a matsayin gudunmawarsa. Kudin accomodation da aka basu ya rike abinsa. Abdulazeez ya ce ya fi so ya zauna a cikin makaranta zai fi maida hankali sosai, ba ya so wani abu ya raba masa hankali. Daddy ya ce. Kai da ka ke da iyali? Idan uwarta ta barta ta zo fa? Kansa ya shafa ya shiga murmushi nan da nan, kafin ya ce. Ai abin ne da kamar wuya Daddy!. Murmushi ya yi shi ma ya dau waya ya kira Mammah, suna kitchen tare da Hafsat ta sakar mata komai ta wanke hannu ta tafi. Tana shiga ta ce. Yaushe ka dawo? Ya hau gaisheta ta amsa kafin ya ce, Tun karfe shidda ina cikin Abuja, na je Maitama ne. Ga sakonki ma in ji Anty Zuwaira. Ya mika mata wata leda. Ta samu waje gefen Daddy ta zauna ya dube ta da gefen ido, idanunsa a yau basu boye tausayin dansa bada tsananin haushin ta da yake ji yana sakaya mata, a dan kausasheya ce. “Shin wai Maryama ku ba kwa afuwa ne a rayuwarku? Tun faruwar alamarin da maida auren, sai yanzu ne ya furta kalma makamanciyar wannan (nemawa Abdulazeez afuwa indirectly) daga gare ta.Cikin nuna soyayyar sa ga dan sa. Yi ta yi kamar ba ta gane ba, sabida a cikin maganar sa yayi amfani da kawaici kwarai wanda ya nuna yau an kure shi, ta ce. Afuwar meye ba ma yi? Kuma ni da wa? Idanunsa ya tsare ta da su masu kidima ta tun tana (sweet 16) har gobe kuma in ana bukatar abu daga gare ta komai tsaurinsa da su ake lallashinta. Ya ce a hankali. Biko muke yi!!!. Da farko dauke kanta ta yi wani gefen, sannan ta juyo ta dube shi da nata lumsassun idanun wadanda su ne Abdulazeez ya gado. A kara min lokaci. Ta ce a takaice.Sannan ta mike tsaye. Shi kenan zan iya tafiya? Tsohon Ambassador bai ce komai ba sai Abdulazeez ne ya ga gara ya yi amfani da wannan damar, watakila kaifin idanun mahaifinsa su yi mata tasiri. Sannan da alama yau cikin lamarinta akwai sassauci. Dagowa ya yi ya dube ta da idanun bidar afuwa. Ina neman afuwarki Mammah!For all the inconveniences!!. I promised you something like that will not happen again!!!”. Daga tsayen da ta ke ajiyar zuciya ce ta kwace mata, ta dubi mijinta Prof. Dr. Hamzah Dakata, sannan babban dansa BARR. ABDULAZEEZ HAMZAHATIKU; wasu mazaje guda biyu da cikinsu har yau ba ta san wanne ta fi so ba! Sune farin cikin rayuwarta, sune komai nata;they made her realised how a dream come true....The dream of being a mother, a wife and a brave mother in-law. Abu daya ya rage shi ne su taimaka mata ta yi actualizing the dream of becoming a grand mother daga ADDARTA ....., wanda kuma ta san a halin yanzu a shirye suke da yin hakan. Murmushi ta yi mai zurfi idonta saitin Abdulazeez amma bata kalli kwayar idanunsa ba. “Allah ya yi mana gafara bakidaya. Sai yau ya ji wata irin nutsuwa wadda ya san ya dade da rasawa. Ya ji cewa, zai iya bata lokaci, zai iya ci gaba da jiranta ta ci gaba da hucewa a hankali har nan gaba dashekara kafin ta dawo masa da Hafsat! Ba son Hafsat yake don ya karbi hakkin aure ba, sai don ya ci gaba da rayuwa da itaa gefensa till eternity. Ta zama uwa ga yayansa, kaka ga jikokinsa, cikamakon farin cikin rayuwar da zai yi anan gaba bakidayanta. ****** HAFSAT Ko wanda ke fama da lalurar bugun zuciya ya fi ta nutsuwar zucia daren yau. Sabida shi nasa heart-beatsdin is treatablewato wanda zaa iya controlling dinsa, amma ita nata ba shi a fannonin medical sciences bakidaya balle a san kalar treatment dinsa. Faruwa yake akai-akai daga umarnin zuciya da kwakwalwa. So ta ke kawai ta ganshi, a kalla su yi bankwana ko da na kalma biyu ne amma ya ki ba ta damar hakan. Bai neme ta a gidan ba har karfe goma sha daya na dare. Tana da tabbacin morning flight zai bi a safiyar gobe zuwa Amurka. In laifin da ta yi masa ne ba ta zaci ya yi girman da zai cancanci wannan hukuncin ba, ya tafi wata uwa duniya ba tare da sun yi sallama ba. Tafiyar da ba ta san ranar da zai dawo ba. Mikewa ta yi daga kan katafaren gadonta ta leka harabar gidan a karo na takwas kenan ko za ta ga gilmawarsa, akalla ko daga nesa ne ta ganshi, ko ta ji sanyi a zuciyarta. Babu shi, amma motarsa tana nan, wanda ke nuni da yana cikin gidan. Sabida shi ta riga kowa halartar dining-table yau, amma Usman din da ya je kiransa ganin shiru-shiru bai fito ba ya dawo ya ce da Mamma, hes o.kya ci a Maitama. Babu wanda ya kara damuwa a cikinsu sai ita, kowa ya shiga cin abincinsa. Mammah na lura da ita ko cokali uku kwarara ta kasa, ta tausaya mata a zuciyarta don ta san tafiyar Abdulazeez ke damunta, shi ya sa ta yi saurin bin Daddy part dinsa yau don ta ba ta dama ta yi sallama da mijinta. Ta dade a falon cikin kyakkyawar kwalliya mai sanyi, wadda kallo daya Mammah ta yi mata ta san wannan kwalliyar ta musamman ce, amma har ta ci awanni biyu a falon babu ko kamshinsa, dole ta koma daki ta shiga kulla wa kanta mai yiwuwa, tunda leken taga ma ba shi da wani amfani a gare ta. Mafitar guda daya ce, takawa zuwa dakinsa na gidan, abinda ba ta taba yi a zamansu cikin gidan ba. Take kuma kallonshi a matsayin mafi darajar rashin kunya daga gare ta. To amma banda shi babu wata hanyar sake sanya shi a idanunta kafin ya tafi, sai dai ta wayi gari babu shi a gidan, ba ta da hanyar sake dora idanu a kanshi na tsayin lokacin da ba ta sani ba. Mantawa ta yi da komai (tunanin Mammah, Baba Azumi, Ismael ko Usman wani na iya ganinta) musamman su Usman din da dakunansu ke daura da na juna. Idan ta mutu kafin gobe iyaka su rufe ta su binne su bi ta da addua babu mai dakon zunubanta da ba ta gama istigfarinsu ba kafin mutuwa ta riske ta. Shi wancan din shine kadai yardarsa zata kaita aljannah. Sanda ta hau jefa kafafunta don isa ga dakin nasa bata gama yiwa zuciyarta umarni ba. Ga mamakinta ma har ta isa dakin ba ta ga kowa ba, tana dai jiyo karar talabijin daga dakin Ismael alamar shi din bai kwanta ba. Dakunan guda hudu ne a jere, biyu na kallon biyu cikin wata doguwar baranda in ka fito daga main parlour. Nashi da na Ismael na kallon na Usmanda na Haleem. Sallama ya kamata ta yi, amma tsoron kada Ismael ko Usman su ji muryarta ya sa ta yi knockingkadan sau biyu, daga ciki ya amsaa hankali. “Yes. Ba tareda tsammanin itace ko kadan ba, yafi zaton Ishma ne,sai ta murda kofar ta shiga. Dakin ba shi da girma sosai, amma an kawata shi da abubuwa masu ban shaawa daidai da bukatar matasa yan boko kuma yayan gata ire-irensa. Daga can gefe akwai study-table da fitilar karatu dauke da manya-manyan littattafai da suka shafi aikinsa, kuma a gefensu ya dora kwanfutar kan tebir (desktop), dakin dai ba neat yake ba amma a tsaftace yake, Baba Azumin da ke sharewa ba ta san inda za ta aje masa wasu abubuwan ba don haka ta ke dagawa ta share ta mayar ta aje. Parmanent kamshin Creed-Aventus shi ya sanyaya dakin. Sannan sanyin da volt-care(air condition) ke fitarwa a speed na karshe ne. Ta san zai iya zama illa a gare ta a matsayinta na mai nimoniya, amma wannan ba shi ne gabanta ba; kallon hadarin kajin da ta karba daga Abdulazeez ne. Tsaye yake jikin wardrove ta jikin bangon dakin yana fidda kayansa yana jerawa a trolley din matafiya. Da farko ta ci gaba da tsayuwa a jikin kofa bayan ta maida ita ta rufe. Amma ganin ba shi da niyyar ce mata komai kamar ma bai yi noticingshigowar mutum ba sai ta ji gwiwoyinta sun yi sanyi. Da gaske fushi yake da ita har yau, fushin da ba ta ga dalilin yinsa ba. Takowa ta shiga yi har gaban gadon ta zauna ta jawo trolley din ta shiga gyara masa kayan ganin dannawa kawai yake ya daina jera su yadda yake yi da farko tun shigowarta. Dakatawa ya yi rike da trouser dinsa ya fasa jefawa. Malama na sa ki ne? Ko na ce ina neman agaji? Ba ta kalle shi ba, tana mai cigaba da kimtsa kayan ta ce. Its my duty!. Cikin mamakinsu ita da karfin halinta yace. Cikin thousandsof duties din gaya min wanne da wanne ki ka sani? Ke nan har kina da guts na bugun kirji ki ce kina da wani duty na matar aure? Ba ta ce komai ba, kayan ta ci gaba da fiddowa tana jerawa, ta lura rigima yake so su yi, ita kuma ba abin da ya kawo ta kenan ba. Ba irin sallamar da ta ke so su yi kenan ba. Jinta ta ke kamar a kan gajimare, tana shawagi a cikin sky-blue rainbow.At least dai ga shi a gabanta.Fada yake yi kamar ba shi bada kakkausar murya da bai taba yi mata magana da ita baamma a kunnenta ji ta ke kamar sarewa yake busa mata. Duk da haka ba ta kallonshi aikin shirya kayan kawai ta ke yi. Tsayawa yayi akanta hannayensa biyu bisa kugu. Malama. Nace ki bari ban sa ki ba, afterall ba ki san wadanda nake da raayin diba ba, sai faman danna min kaya kike.Cigaba ta yi ba ta fasa ba.Hakannan bata dago ta dube shi ba. Kafin kuma insubdued(cikin karayar murya) tace. Sunana Hafsatu ba Malama ba!!!. Tsaki ya yi. Ki fita don Allah akwai abubuwan da ke gabana ban gama dasu ba,kada ki kara min tension”. Kyawawan idanunta ta dago gabadaya ta zube su a kanshi cikin wani irin slowmotion. Abdulazeez korata ka ke yi???” Cikin ido suke duban juna, da wani irin yanayi cikin idanun su, wannan karon shi ya fara kawar da kansa kada ta hango weakness dinsa. Yana kallon wani gefen daban yace. “Im not sending you out, kawai ina gaya miki kin sa dakin ya yi min kadan. Kiran sunansa na asaliin full(cikakke) ta yi a yau ya fi komai kassara shi.She spells the name correctlyfiyeda kowa a duniya.Ci gaba ta yi da shirya kayan, sai da jakar ta cika taf! Sannan ta zuge ta. Mikewa ta yi ta tsaya a gabansa, bai fi taki biyu ne ratar dake tsakaninsu ba, idonta fal hawaye. Tunda nasa dakin ya maka kadan, zan tafi, dama sato jiki na yi na zo duk da risk din da hakan ke da shi in Mammah ta gane na zohar nan,don kawai in ganka, (in yi bankwana da kai), in nemi afuwarka ko na yi maka wani laifi ina sane ko bana sane. Yaya Azeez na ji za ka yi tafiya ne shiyasa na zo, wadda ban san ta mece ce ko zuwa ina ne ba(ko ta tsayin wane lokaci ce). All Icometo say is; all the best. Allah ya yi jagora. Ta juya za ta fice daga dakin, sai da ta kama handle din kofar dakin ya kira sunanta muryarsa na sarkewa. Kafin ta yi aune hawayen data ke ta makalewa sun zubo, sharr!. Gefen mayafinta ta sanya ta tare su, sannan ta murda kofar ta fice ta rufo masa kofar silently. Gadonta ta fada ta soma kuka, ba kukan gwasalen da ya yi mata ta ke yi ba, kukan rashin sanin ina za ta sanya kanta in ya tafi ne. Wani irin so ke bin jikinta tun daga ranar da ya furta saki a gare ta, zuwa rana irin ta yau zuciyarta bata taba hutawa ba.Watakila Allah ke hukuntasu su duka kan kuskurensu, da wannan azabtacciyar soyayyar. Ga jarrabawa a gabanta. Ta yi zaton zai biyo bayanta su sasanta, amma har wayewar gari babu ko mai kama da shi balle scent dinsa cikin dakinta. Ko dai wannan na nufin..... wannan na nufin... son da ta ke zaton ya fara yi mata ya daina??? Wannan tunanin ba karamin tashin hankali ya zame mata ba, saboda in ya daina son nata ita yanzu zuciyarta ta sa damba a sonsa da kaunarsa! Idan kuma hakan jarrabawarta ce tana rokon Allah ya ba ta ikon cinye ta da A1s, amma hakika za ta bashi sarari kamar yadda ya bukata. Washegari ita ce farkon fitowa. Tun shidda ta yi wanka ta shirya, takwas na safe za ta shiga dakin jarrabawa ta fito goma na safe. Ta shirya tsaf ta fito kitchen cike da tunanin wa zai kai ta makaranta yau? Dole Usman zai kasance tare da Yayansa a airport. Salisu shi ne last hope dinta, amma ba za ta iya tuna rabon da ya kaita wani waje ba, Mammah ba ta sanya shi, amma dole yau shi din za ta nema. Burinta ta riga Abdulazeez fita daga gidan nan. Cikin ikon Allah ta tadda Usman a kicin ko me yake yi? Oho! Kayan barci ne a jikinsa yana tsaye jikin firji yana shan ruwa. Ido ya gwalalo,yana mata duban tsoro. Hey! Mrs Mungo park! Ba dai har kin shirya ba? Ba sai 8am za ki shiga paper din ba?. Marairaice fuska ta yi yadda zai ji tausayinta. Ban karanta komai ba ne jiya shi ya sa nake so in je da wuri in nutsu in durawa kaina wani abu kafin lokacin ya cika, don Allah ka taimaka. Ba ta taba nadamar rashin koyon tukin mota ba sai yau. Mammah ta yi-tayi da ita sai ta ce tsoro ta ke ji. Ya rufe firjin ya ce. Kin yi sallama da mijinki? A gajarce ta ce. Na yi. “Wouldnt you take him to airport? “You are too inquisitive. Ta ce a gundure. Kada kafada ya yi irin na (bai shafe ni ba), sannan ya ce. Mu je. A kofar(library) ta zauna ta bude handouts dinta. Ita a dole ba ta da damuwa banda ta yadda za ta tsarge course din. Amma sai me? Shafi bayan shafi, layi bayan layi fuskar Abdulazeez Dakata ne yana murmushin nan nasa. A karshe rufewa ta yi ta sanya kanta cikin cinyoyinta ta baiwa tunanin nasa da soyayyar tasa fili su sha sharafinsu, ta bar wa Allah komai. Idan tana da rabon cin wannan course (Introduction toHuman Geographies) Allah ya yi kudurarsa a kanta. A kan idonta masu kula da labirare suka bude. Ita ce farkon shiga, a can ta cinye lokacinta, ban da tunani da bege babu komai a cikin kanta. Tunanin ko za ta sake ganinsa nan kusa? Ko zai sake tunawa da ita, ko kuma wata sabuwar Muazatun zai je ya samo? Ko suna da rabon sake zama tare? Ko Mammah ta datse auren kenan har abada? Tunaninnika ne ga su nan fal wadanda ba ta da amsar ko daya. Ban da zafin zuciya da azabtar da kwakwalwa ba abin da suke sanya mata. Agogon hannunta na bakar fata samfurinpolo ta duba sai ta ga saura mintuna talatin a shiga paper. Wani irin kuzari ya shige ta da taimakon Allah ta soma fahimtar bugaggen rubutun takardar da wanda ta yi jotting da hannunta. Kafin karfe takwas ta cika ta samu abin da ta samu da yake shes born gifted. Sau uku in ta bi topic kawai komai yawansa ya zauna mata. Sai takwas ta tattara ta fito daga dakin karatun. A kofar lecture hall ta hango Rabia Sada, daga nesa suka daga wa juna hannu, sannan kowacce ta shige. Usman bai zo daukarta ba sai karfe goma sha biyu na rana. Daga airport suka zarto bayan sun ga tashin Abdulazeez. Abin mamaki ta gansu (full house) duk a cikin motar. Motar da Daddy ya fi ji da ita duk cikin motocinsa. Wata ash-colour (Hyundai 2018 model) mai cin mutum takwas. Mami ba ta kara tsinkewa da lamarin Hafsat Dakata ba sai yau. Daddy ne a gaba, sai Ismael direba. A kujerun baya Usman ne da Mammah. Tare da Rabia suka iso jikin motar ta gaida su Mammah, ta amsa da faraa haka Daddy ya sa mata albarka. Ta ce, Mommah ita ce ta yi covering dina duk abubuwan da suka wuce ni lokacin da na dawo daga Jimeta. Madallah-madallah Mami Sada, Allah ya saka da khairan. Daga nan suka yi sallama, sun ce ta zo su sauke ta, ta ce mijinta yana hanya, Mammah ta ce a ina suke zaune? Ta ce a Kubwa. Insha Allah watarana Hafsat za ta zo gidanki, Allah ya yi albarka. Sosai Maami ta ji dadi, a yadda ta gansu high class haka ba ta zaci za su yi wannan saukin kan ba. Daga ganin Baban nasu ba karamin mutum ba ne. Ta fadi a zuciyarta. Suna tafe a hanya Daddy ke tambayarta ya jarrabawa? In ce ko ta rubutata da kyau? Murmushi ta yi, wannan jarrabawa ai sai taimakon Allah, in ta samo C she deserves a medal! Mammah ke gaya mata Haleem na zuwa gobe. A ranta ta ce, Wani na zuwa wani na tafiya, wanda Allah ya baiwa yaya da yawa nagartattu ya gama masa komai a rayuwa. Ko ba komai ta ji dadin albishir din zuwan Haleem din. Ta tabbata zai debe mata kewa, abokin kokawa, abokin wasan tseren keke, abokin kowacce dabdalar kuruciya. Washegari Haleem Dakata ya iso, har da ita aka je filin jirgin saman Abuja dauko shi. Ya kara tsayi sosai, sai dai yaan nan da lange-langen jikinsa. A da tana ganin Usman ya fi kowa kama da Abdulazeez, ashe akwai wanda ya dame shi ya shanye cikin yayan gidan. Wannan har tsayuwarsa har tafiyarsa, har murmushinsa Abdulazeez Dakata ne. Yana saukowa daga jirgi ya cimmasu, babu Daddy tare da su yana office, su Ismael ya hau rungumewa, ya rungume Mammah har da kwanciya a kafadunta, ita ce ta ji kunya ta ture shi. Ya ce, Mammah ki bar ni in ji duminki, wa ya yi dadewa irin tawa ba tare da ke ba? Ta ce masa, Ka girma. You are no more a child now. You are Arch. HaleemDakata. Lumshe ido ya yi, sannan ya iso ga Hafsat, Addar Mammah, an kara tsufa, kin haihu? Harararsa ta yi, ta ce.Da na san abin da za ka yi min kenan da ban zo tarenka ba. Yi hakuri, kada ku kai ni kotu, whereis he? “I dont know!”. Ta sha kunu sosai ta zumburo masa baki. Dariya ya yi, ya ce, Mammah ina mijinta? “In the U.S. Ta fada a gajarce, sannan suka rankaya suka nufi mota. Sai hira yake saki kamar rariya. Anyi girke-girke na musamman don tarbar Haleem. A raayin Hajiya maryam ba ta da son yan aiki barkatai su cika mata gida. Tun tana amarya yar aiki daya ta ke dauka a cikin gida, sai maza na waje don kula da harabar gida da aike,guest house da sauransu. Sai ko maigadi, hatta wanki da guga dry-cleaning suke kaiwa duk don kada ta cika gida da hadimai. Tana da kwazo, juriya da himmar hidimtawa iyalinta. Da wuya a yi mata girkin mijinta da yayanta sai bisa lalurori irin wanda dan adamya gada, kamar rashin lafiya ko tafiya. A tasowar Hafsat-Suhaanah sai suka hada hannu musamman da suka dawo Nigeria inda Hafsat din bata zuwa makaranta. Ayyukan Baba Azumi sun fi karfi ga wanke-wanke da share-share, goge-goge da wankin bayan gida. Sai sauran hidimar kicin. A yanzu Azumi shekaru sun tura karfinta ya ragu sosai, tana so ta samu lokaci ta gaya mata ta samo mata wata cikin iyalinta mai kuruciya ba don ta sallame ta ba, sai don yanzu abubuwa da yawa nauyin shekaru ba ya barinta ta yi mata su yadda ya kamata. So throughout ranar saboda zuwan Haleem ta zama busy ba ta samu lokacin zama ita kadai ba balle tunani ya aure ta, kuma ba ta da paper, inda duk ta gifta don kawowa Haleem abin da yake bukata sai ya tsokane ta, kiranta yake Senior Aunt. Shi yanzu ya daina kokawa da ita. Shes lookingolder and older saboda aure. Mammah kadai ke tare mata, ta ce su din ma watanni uku ta ba su su fiddo matan aure, ban da shi tunda bai gama ba. Ismael sai ya shafo kai ya ce, Mammah mu ai mun dade da wuce wurin. Na gaya miki kullum zance nake zuwa a Apo gidan su Wasila. Ke kawai muke jira ki ce kule mu ce casss. Usman sai ya yi tsaki, ya ce, Kai wallahi ban ga me ka gani a Wasilar nan ba, yarinya baka kirin mai kirar samudawa? Ni Mammah ai irin auren Yaya Azeez za ki min, ki je Kano cikin yaran nan ki dubo min kawai. Mammah ta dinga shi masa albarka. Ismael ba ta hana shi ba, amma har ranta ba ta son auren bariki, balle irin wadda Ismael ya kallafawa rai, ba ta zaton za a samu yadda ake so daga gare su a gidan aure saboda budadden ido da gata da yayi musu yawa. Sannan su zo su janye dan daga jikin uwarsa da yan uwansa. Ta sha wahala a kan soyayyar Abdulazeez da Muazatu, ba ta fatan a sake maimaitawa. Da daddare bayan sun yi dinner, Haleem ya ce da Suhaana yana son kunun gyada, Mammah ta ce Azumi ta yi masa ya ce shi sam na Suhaanah yake so ba na tsohuwa ba, ko ita Mammah da kanta ta yi masa. Ta ce ita ta gaji da tsirfarsa tunda ya zo bai barsu sun huta ba. Hafsat ta ce, Mommah, bari in yi masa mana? Bakonka Annabinka. Ta mike ta shiga kitchen. Tana cikin aikinta ta jiyo ihun Haleem cikin murna yana fada wa Mammah Yaya Azeez na kira, a sailin wayar Mamman ce a hannunsa yana daukar lambobin yan uwa da abokan arziki da ba ya da su don ya kirasu ya gaishesu, kawai yaga kiran lambobin U.S. Hafsat na jin yadda rigima ta kaure a kan wanda zai fara magana da shi. Daga karshe dole sai a handsfree aka saka kiran suka taru har Mammah. Kafin ya ba wa daya amsa daya ya jefo tasa tambayar. Duk dai a kan yadda ya sauka ne da yadda ya tadda wajen, how much suka yi kewarsa da sauransu. Runtse idanunta ta yi tana jin wani irin fili fetal a zuciyarta. It was like babu komai a birnin zuciyar sabida kewa. Kamar an yashe komai da ke cikinta. Birnin zuciyar is just empty! Wanda ya yi gininnika a cikinta ya yi kaura tare da komai da ke cikinta. The feeling is emotional mai ratsa zuciya da ruhi. Ba ta kara gane me ta ke yi a cikin kitchen din ba ko me ya kawo ta. Ta ga dai shigowar Mammah da sauri ta nufi gass da azama ta kashe wuta na tashi daga cikin karamar tukunya. Ta dauke tukunyar da karamin towel ta jefa ta a sink ta kunna mata famfo. Ta dubi Hafsat da ta yi tsuru-tsuru ta ce, Addah are you alright?” Daga mata kai ta yi, To tunanin me ki ke yi haka na ji shirunki ya yi yawa? Daga dama kunun gyada, I then decided to check on you, sai ganin wuta na yi na tashi daga tukunya, in ce ko lafiya ki ke? Kai ta daga mata cikin sanyin jiki ta gaza cewa komai. To ta ce me? Your son is drivingme crazy? Ba ni da tunanin komai sai nasa, ya maida ni emotional ya gudu ya bar ni? Da ta tabbatar ba za ta yi magana ba sai ta ce, Ki je daki zan yi masa. At least ta gode Allah Hafsat din ba ta kone ba. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Ba ta da bakin musu ita ma ta fi son ta gusa daga gaban nata, don ta santa kamar mai gani har hanji ta ke a kan dukkan alamuransu. Ba ta sani ba in dai Mammah ce an riga an yi walkiya ta ganta. Karfe goma na dare ta gama komai na shirin kwanciya, tana so ta tashi karfe ukku daidai na dare don mika kukanta ga Sarki Allah, ba ta da wani buri yanzu a rayuwa bayan shi, bayan neman sauki cikin alamarinsa, bayan neman soyayyarsa da kuma samun tasa soyayyar. Ta sani ba abin da ya fi karfin Rabbi, Shi mai kawo sauki ne cikin kowannen alamari muddin ka amince zai ba ka dukkan abin da ka roka yanzu ko anjima, ko ya jinkirta maka zuwa lokacin da yake ganin ya fi dacewa da kai. Tana neman sauki cikin soyayyar da ta yiscattering(yin dai-dai) da ruhinta, ta yi mata katutu a zuci, ta ke addabarta a kirji, ta ke dawainiya da duk fitar numfashinta.Ta ke neman maida ita wata tababbiya-tababbiya-mai-hankali-mai-hankali. Abdulazeez didnt deserve all these, zuciyar da ta damu da kai ta kuma san kana yi ita ta cancanci a yi wa irin wannan mahaukacin son don za ta karbi response in return. Wanda zai sanyaya ta tasan ba aikin kawai ta ke yi ba, amma banda ta Yaya Azeez din da ba shi da damuwa a kan komai nata. Ba a kanta kawai ba, it seems like komai na duniya bai fiya damunsa ba ban da lauyancinsa, da tunanin hanyar da zai bi ya kara gogewa da kwarewa a cikinsa, ta hanyar karbar cases na marassa galihu masu tsauri da ko a manyan lauyoyin gwamnati ba kowa ke yarda ya karba ba, musamman idan suka lura client din babu mamora. Tunanin da ta ke yi kenan ta ji an murdo kofarta an shigo. Daga kan filo ta dago ta dubi mai shigowar, Mammah ce. Waya ce a hannunta, tana shigowa ta iso har inda ta ke. Wayar ta mika mata, Ungo wayarki, Daddy ya dawo miki da ita. A sha soyayya lafiya. Zuciyar Hafsat ce ta yi wani tsalle ta fita daga kirjinta tayi shawagi sannan ta dawo. Kafin ta gama farfadowa Hajiya Maryam ta yi ficewarta. Wayarta ta kalla da dumbin shauki. Wani farin ciki ya rufe ta. Ba ta yi zaton da charge a ciki ba amma tana kunnawa ta ga Mammah ta shake mata ita da lantarki. Da sauri ta duba kudi, naira dubu goma cas! Sweet Mommah. Ta fada a fili. Abbanta ta soma kira. “Ghaaji, yau ke ce a waya? Wani dadi mara misaltuwa ya ratsa zuciyarta, wato soyayyar ma kala-kala ce, kuma ta iyaye daban ta ke. Ina ma! Ina ma!! Ina ma ta rayu da wannan Habiban? Ina ma Habiban tana tare da Abba? A hakan ma ta gode Allah da tarin niimomin da ya yi mata. Na bar mata wadannan dimbin masoya zagaye da ita. His blessings upon her are countless, endless, limitless. Alhamdu lillah!. Abin da ta furta kenan a fili, kuma Abban ya ji. Shi ma wani abu ya taba zuciyarsa, kusan tunani daya suke yi (Habiba) a dai-dai wannan lokacin. Daga bisani kowanne ya ware suka shiga hira. Suna yin sallama ta kira Daada, daga ita sai Malam Babba, Imamu, Abdurrahman da Yaya Modibbo. Ta yi musu ya suka je gida, ta ji lafiyar kowannensu. Sannan ta kira Kawunta Sagir shima ta gaisheshi. Cikinsu babu wanda bai nuna yabawarsa da karimci irin na iyayenta kuma surukanta ba. A zuciyarta ta ce. “Sun wuce da tunaninku, ba ku ga komai ba daga zuriar Malam Abdullahi Dakata. Sai a lokacin ta bar wayar ta huta. Ta kashe fitila, so ta ke ta yi bacci, don kada ta kasa tashi qiyamul-layl da adduaoin ta kamar yadda ta kudurta. Ba ta jima ba bacci barawo ya sace ta. Uku daidai na sulusin dare alarm din wayar da ta saita ya tada ta. Alwalah ta shiga ta dauro ta fuskanci alkibla. A yau adduoI da dama ta yi, ta yi wa uwarta da ke kabari, ta yi wa Mammah ta fatan gamawa da duniya lafiya, ta yi wa Daddy na yalwatar arziki da lafiya, ta yi wa kanta adduoI masu yawa. Ta yi wa Daada da Malam na nisan kwana da lafiya madauwamiya. Sai dai me? Instead(maimakon) ta yi adduar da ta tashi don ta yi, wato rokon Allah ya rage mata son Abdulazeez, ya sa masa soyayyarta shima, sai ta samu kanta da yi masa addua. In tace addua to tana nufin addua a kan komai; a ciki ta roki Allah Ya kare shi a duk inda ya shiga, Ya shige masa gaba a kan duk abin da ya sa gaba. Ya cika masa burikansa na alkhairi, Ya ba shi dukkan alkhairin rayuwa Ya bashi nisan kwana...... Sannan Ya kare mata shi daga ZINA da sauran ayyukan sabo masu kamanceceniya da ita. Hannunta a sama ba ta kai ga shafawa ba ta ji wayarta na kira da tune din takbeer da ta saita kiran wayarta da shi. A nutse ta kammala adduarta ta shafa ba tareda damuwa da kiran ba, zuwa lokacin wayar ta katse har sau biyu ta sake ci gaba da ruri. Sai da ta koma gado ta kwanta, sannan ta jawo ta. Lambobi ne rututu da suka fara da (+917) da ba ta shaida code din ko ina ne ba. Da farko ta yanke shawarar kin dagawa, amma ganin ba a da niyyar fasa kiran sai ta daure ta yi sliding answer button’ din. Assalamu alaikum. Ta fada a nitse. Jin mai kiran ba shi da niyyar yin magana. Cike take da mamakin wanene zai kirata da sulusin dare irin haka? Sai da ya ja fasali har tana tunanin kashe wayarta don ta fara tsorata da yi wa kanta fadan me ya kai ta amsawa ma, kira cikin talatainin dare da international number. Sai ji ta yi murya a ciki, kamar wanda aka yiwa dole yayi magana, ya ce. Ba dole ba ne na amsa sallamarki a fili ba ai, tunda na amsa cikin raina. Wani numfashi mai tsayi ta zuqa ta furzar daga huhunta. Mutum na karshe da ba ta kawo zai kara bi ta kanta ba, she feels like smilingamma ta hana kanta, ita ce mace ba shi ba, ita ya kamata ta yi jan ajin da yake yi mata. Amma anya za ta iya? In ma ba ki iya ba ki koya, Abdulazeez sai an bi hankali. Ja zarenki a sannuAddar Mommanta!Bi shi a yadda yazo. Zuciya mafi hankali da nutsuwa ta shawartar. Don haka sai ta yi shiru, ba ta ga dalilin da za a kira ta ba, kuma ya yi mata kasaita da iko ba. Kiran wayata ma sai kin ga dama za ki dauka ko? Tunda ke bazaki kira ni ba bayan an gayamin an baki waya. Wannan duk a cikin rashin tausayinki ne da kika kware akai, ko a cikin fannonin rashin so irin naki? Murmushi ta yiwa kanta mai ciwo, ita Abdulazeez yake yi wa korafin rashin so! To ita wanne za ta yi masa? Ya yi tafiya bai gaya mata ba, bai neme ta ba sai da ta neme shi. Ta je ya yi mata wulakanci, sannan yanzu yana fadin ba ta sonshi, ba ta tausayinshi. Shiru ta kara yi masa wanda ya fi komai fusata shi. Da zai iya da ya kyale ta, amma ina! Ba zai iya nutsuwa ba sai ya ji muryarta ko da kuwa abin da za ta fada mishi din ba mai dadi ba ne. Ya tabbatar Hafsat bazata ce masa komai ba, kuma bata da niyyar hakan, sannan ya tabbata tana jin sa. Don yana iya jin saukar numfashinta wanda ke fita akai-akai. “Shi ke nan Hafsah, zan barki ki yi rayuwarki the way you want it (yadda ki ke sonta), amma ki ke sanya wa a ranki akwai wani mutum far away (a nesa) da ya damu da ke da yawa, yake fatan jin ko da kalma guda daga gare ki a yau to keep him companyhar wayewar gari amma ya kasa samu. Wannan mutumin ba wani bane face mijinki Abdulazeez Dakata.Stayblessed. Ya yi maganar ne da wata murya data nuna rauninsa a yau, ba tareda ya san raunin ya bayyana kansa ba cikin intonation din sa, mai tasirin kashe jiki da gabban kowaccediya mace, balle ga macen aure ga mijin da ta ke matukar so. Macen ma mai rauni irin Hafsat-Suhaanah. Mijin kuma ba kowa bane Abdulazeez din ne data hana idonta bacci saboda shi, saboda ta roki Allah ta samu kwatankwacin wannan soyayyar da wannan kulawar daga gareshi. Kafin ta yi wani yunkuri, ya kashe. Shefeels like calling him back..amma wata zuciyar ta hana. Barshi shima ya ji in rashin kulawar da dadi. Zuciyarta ta ciko ta yi tantsan da farin cikin jin kalamansa, daga wannan emptinessdin da ta ke ji a baya, wani irin nishadi ya lullube ta. Da haka ta samu barci mai nauyi da dadi ya yi awon gaba da ita. Wanda ta dade ba ta yi irinsa ba. Washegari paper har biyu ta zana (Regional Geography and Rural Geography). Tana fitowa daga dakin jarabawar ta kunna wayarta, sakon sms ne ya fara shigowa. Yau Haleem ne ya zo tafiya da ita. Tana tafe zuwa motar ta bude sakon saboda ta gane lambar da Abdulazeez ya kira ta jiya ce. Hannunta har rawa yake yi, ko me ya rubuto? Ga mamakinta, fatan alkhairi ne a kan jarrabawarta. As you strive hard to achieve this goal, heres hoping that you excel in every course,with hope in yourself and this strong determination of yours,with me In mind.. and the assurance of my inexpressible love to you I believed that success will surely come your way. -Abdulazeez. Ita kadai ta hau blushingtun daga baki har kunne. Sakon waya mafi daraja data taba karba a rayuwarta. Sakon waya da ya sata farin cikin da wani sako bai taba sata ba. Ya goge gabadaya memories na wancan black sakon data taba karba a rubuce. Ta kusa yin tuntube da za ta shiga motar. Haleem ya ce. Tsohuwa yi a hankali, doguwa, hankalinki a gwiwa!. Ta harareshi, amma farin cikin data ke ciki ya hanata ramawa. Suna hanya banda maimaita karanta sakon ba abin da ta ke yi. Haleem na ta mata hira bata san me yake cewa ba. Hatta Mammah ta lura Hafsat yau cikin farin ciki take. Ta san ta canka daidai in ta ce waya na aiki. Addua ta ke yi a zuciyarta wadda ita kadai ta san me ta ke roka musu, wanda ba zai wuce zaman lafiya da zuria mai albarka, da soyayya mai dorewa har abada ba. Ta riga kowa shigewa daki bayan cin abincin dare, manne ta ke da wayarta tana jiran Abdulazeez ko zai kira? Ko karatun paper din gobe ta ki yi, ba ta da nutsuwar yinsa. Haka ta yi ta zaman jiran gawon shanu amma hudubar jan ajinmu na mata da zuciyarta ke ta yi mata ya hana ta yin sadaukantaka ita ta kira shi. Sai karfe hudu na asubah kamar jiya tana bisa sallayarta ta ga shigowar kiransa kamar a mafarki. Ba ta iya ta jinkirta ba ko na minti daya wannan karon wajen amsawa. Tana iya jiyo ajiyar zuciyarsa, ita ma ajiyar zuciyar ta yi ba da saninta ba. Hafsat bazaki kira ni ba, in ni ban kira ki ba? Ya fada da dukkan concern da muryarshi ke iya badawa, haka kawai yake ji a zuciyarsa abubuwan da yake mata bai kyauta ba, shi kuma yana yi ne don ya nuna mata fushinsa na abin da ta yi masa rannan duk da ya san ta fi shi gaskiya. Yaya Azeez na ga text, na gode!. Abin da ta iya furtawa kenan cikin kankanuwar murya,cike da tsoron kada yau ma ya katse maganar tasu irin jiya, ya barta da shaukin da ita kadai tasan adadinsa. Ba tare da ta bashi amsar tambayarsa ba, don ita kanta bata da amsarta. Fadan namu ya kare ne? Ya tambaya da yanayin da ke nuna yana tsananin son jin amsarta wannan karon. Murmushi ta yi ta kwanta sosai a kan sallayarta maimakon zaman sallar da ta yi akan kafafunta. Sannan tace. Its inconclusive!”. Dariya ta ba shi sosai. What made itinconclusive bayan gashi na karbi laifin bakidayansa yanzu? Saboda ni har gobe ban san laifin da na yi maka ba ka ke hora ni haka Yaya Azeez,zuciya ta a kanka mai rauni ce, idan nace rauni ina nufin rauni; ba komai ta ke iya dauka ba musamman fushin ka, tun daga ranar da ta soma son k........ Hannu ta kai ta toshe bakinta jin sakin layin da ta keyi. How sure she is yanzun yana sonta baka da zuci kamar yadda Mammah ta ce da za ta fara gaya masa sirrin zuciyarta? Wanda daga ita sai Ubangijin ta suka sani duk da cewa ya furta mata kalmomin dake nuna soyayyar? Ta ji kamar ta dawo da abin da ta fada cikin bakinta, inda hali ta bi bakin da zare da allura. A can bangaren Abdulazeez wayar ya canza wa position daga dama zuwa hagu yana jin wani kududu da ya dade da tsayawa a makogaronsa na melting gradually (narkewaahankali). Zuciyarsa ta shigaimaginatingHafsat a gabansa, da shi kadai ya san da me zai yi tukwicin wannan kalaman da bai taba jin mafi gardinsu daga gare ta ba. Ina jinki Hafsah, ki karasa don Allah... Ya fada da wata kankanuwar murya, muryar sa har rawa takeyi. Yaya Azeez, alamarin na zuci ne, sirri ne irin na zuciyar mutum, da ba lallai a zahiri ya zama hakan ba. Zuciyar mutum,Birnin sa.(Sunan wani littafin TAKORI ). Ina so in san wannan alamarin sosai, don in tantance ko irin wanda na ke fama da shi ne? Ni tawa zuciyar wani irin radadi ta ke mini in na tuno bana tare da HAFSAT-SUHAANAH, in na shafa na ji babu ita a gadon barci na. Daga sanda ta tafi Jimeta na koma gidan ni kadai, ni da zararre ba mu da maraba. A dakinta nake kwana a kan gadonta in lulluba da duvets dinta. Wadannan lausasan duvets din nata kala-kala. A kan Hafsah na san so na hakika, a kan Hafsah na san mutum na iya bada komai da ya mallaka don ya dawo da abin da ya rasa guda daya! Hafsah youare special. I love that your tender heart and everything of you, and be rest assured that Abdulazeez lovesyou so much, to an extent Hafsah ......Nayi rantsuwa ki yarda da ni!Kada ki tambaye ni yaushe hakan ta faru, ni kaina ban sani ba. Wannan fushin da ki ka ce ina yi kuwa Hafsah? Let me put it in concret and tangible example for you; fushi ne irin wanda yaron da ke tsananin jin yunwa ke yi in an raba shi da jikin uwarsa ba tare da ya koshi ba. Kina tunanin wannan yaron zai karbi wani uzuri ne a kan uwar da ya riga ya san cewa tasa ce,bai da wata uwar sai ita,bai taba samun sukunin rabarta ba ne da niimomin da Allah ya mallaka masa tattare da ita? Abdulazeez ya mance Hafsat ba ta gane wahalalliyar Hausa, she didnt get him right to where he wants to, cewa ta yi. Ni bana jin hausain disguise, kuma ni ban haihu ba. Ya ce Za ma ki ji ne. Kuma zaki haihun. Dole ki bude kwanyarki ki gane abunda nake nufi yau. Ni ma bana jin Dutch, not even Flemishballe in yi miki bayanin dana ke so ki fahimta.Shiyasa na yi miki da yaren dana iya kuma dole ki gane. Girl,bari in miki dallah-dallah toh. Ni Abdulazeez mijinki ne, miji kuma na aure, wanda Ubangiji ya dora miki nauyin dukkan hakkokinsa,amma Hafsat guduna kikeyi, a dalilin ki da ban sani ba, kina min rowar abin da ya zam halalina. Hafsat banda wata matar sai ke, ban iya neman mata ba kullum kuma ina rokon Allah kada ya dora mini. Tun a Sun-city ki ke min wannan azabar. Hafsah in ban zo wajenki ba ki gayamin wajen wa zan je? Shekaruna kusan talatin da hudu ban taba hutawa daga wannan ukubar ba. Ko babu soyayya ina da wannan hakkin a kanki. Hafsa ko kina so in kara kallo wata yar kwalisar in makale mata, in ce ina so in ba ita ba sai rijiya? Yadda yake maganar yanzun cikin wani irin lallashi ne da shi kansa bai taba zaton ya iya ba. A rayiwarsa bai taba lallashin Muazatu ba sai dai ya cedo and donts.To ko wannan shi ne bambancin matar sunnah da budurwar waje? Shi kansa bai sani ba. Hafsat ta yi shiru, ilahirin jikinta ya mutu, wani irin chemistry na bin gabban jikinta. Ta tabbatar yau da Abdulazeez a gabanta yake zai samu abin nan da ya dade yana burin samu daga gare ta whatever their contract! Saboda ya gama samun duk wani weakness dinta.Kawarda zancen ta yi saboda sosai ta ke jin kunya, wata irin kunya da bata taba ji ta Abdulazeez ba, ko sanda yake gabanta. Kuma ba ta son zancen wata din nan da ya soko suna cikin hirarsu mai dadi. Yaya Azeez bari zancen watayar gayuka ji? Ka gaya min duk irin gayun da kake so I will be doing.Mammah ta hakura ne? A muryarta akwai trembling (gargada) sannan akwai kuruciya, sokonci da kishi a fili duka a lokaci daya. Dadi ne ya kashe Abdulazeez a kwancen da yake.Dadin Hafsat na kishinsa, ko da yake da dade da sanin hakan tun ma kafin ita ta san soyayyar tasa na farautar ranta.Amma bai nuna ba don kada ta ji kunya ta fasa hirar. Rikon wayar ya canza daga kunnen damansa zuwa na hagu. Yana yawan yin hakan in yana waya. Na bari Hafsah tunda ba kya so, kuma nima fa na fada ne wai in miki misali. Banda haka ma ni idona ai ya dade da dusashewa akan ki Hafsah, in ya ga mata ma rufewa yake yi.Da ba ta hakura ba za ta sakar miki mara ne har ta baki waya? Wannan over-discplinedMaman taki! Hummm! Keni fa yau hirar mata da miji nake so mu yi Hafsah, irin wadda bamu taba yi ba, hirar realAbdulazeez dareal Hafsatin theirreal self! Ki bude baki ki ba ni amsa. Are you feeling what Iam feeling? Hafsat ta daburce, wata irin daburcewa mai cakudeda jin kunya, ta wara ido sosai daga lumshe sun data yi tana kallon dama da hagunta da bakin kofa ko wani yana jin abin da Yaya Azeez ke cewa??? Hijabinta ta janyo ta rufe fuskarta tana ji masa kunyar. A take ta tuno abubuwa da yawa, wasu da suka faru a ‘Sun-City’, wasu a Rockview da halin da ta ke samun kanta a irin wadannan ranakun. In haka ne kuwa ita ma tana da wani extraordinary feeling a kan Abdulazeez wanda daga ita sai Ubangijinta suka sani, amma wani alamarin tsakanin mutum da zuciyarsa ne, ta ya ya zai ce sai ya ji? Hafsah!. Ya kira sunanta. Kafin ta samu sukunin amsawa ya dora. In ba ki ba ni amsa ba na rantse gobe zan dawo Nigeria!. Gabanta ya fadi, in Abdulazeez ya dawo ya ce da iyayensa me ya dawo da shi? Ya fasa karatun? Bayan makudan kudaden da aka narkar a kan tafiyar daga iyayensa har gwamnatin tarayya?After all ba ta bukatar dawowarsa a yanzu bata gama planningda fuskar da za ta karbe shi ba a matsayin tabbataccenmiji a karo na biyu, wanda babu yarjejeniyar komai a tsakaninsu sai auren sunnah tsurarsa. Aure na har abada! Rayayye wanda babu ranar macewarsa sai ranar da rayuwar dayan su ta kare. In haka ne ta yi abin da yake so don a zauna lafiya. Don Allahkayi hakuri Yaya Azeez,ba sai ka dawo ba zan fada Allah.Ina jinki Ya fada a gajarce exhaustedly. Hafsat ta ja numfashi sannan ta runtse ido tace. “I really have it for you alsoI mean the feelings.... and its just..just unexpressable!. Ta fadi kowacce kalma dallah-dallah, daban daga jikin yar uwarta kamar mai koyon vocabulary. Murmushi ya yi cikin mamakin yau Hafsat ke magana haka. “Then let me come, and make itvivid to me, sai a banbance na wanda yafi tsanani tsakanin Abdulazeez da Suhaanah!. Ya fada cikin wata murya da ta kasa yarda ta Yaya Azeez ce. Na yi alkawarin bayyanawar a duk ranar da muka hadu. Hafsat ta fada cikin jin kunya. Yaushe ce wannan ranar Hafsa idan ba ki yarda na zo ba? Shekara daya ba nan kusa ba ce, Ive one year aheada gabana kafin na kammala. Jiranta zai zama kamar jiran ranar busa kaho a gare ni. Gaskiya bazan iya ba!. Dauke wayar ta yi daga kunnenta na dan lokaci, tana mai karbar tasirin kalaman a cikin kowacce gaba ta gangar jikinta. Isthis what is calledLOVE? And the feeling of having it in return? In hakanshine soyayya ta hakika, to hakika ba abin da ya fi ta dadi da sanya nutsuwa a zuciyar dan Adam. Allah ya sani tana son Abdulazeez! Wayar ta mayar kunnenta, abin mamaki he is still onthe call. Ya ce, Hafsa bude kunnenki ki ji Kalaman da yake fada mata sun yi mata nauyi a cikin kwanyarta, wanda ya kai ta ga janyo hijabinta ta rufe fuskarta bakidaya kamar yana ganinta. Mammah ta ba ta waya ne dama don Danta Abdulazeez ya kashe ta da dadadan kalamansa, ko don ya hana ta bacci da manyan maganganun sa? Ya yi formatting brain dinta ya zuba sababbin abubuwa da ba ta san da su ba a duniyarta? Kin yi alkawarin duk ranar da muka hadu babu kunya? Kin yi alkawari it will bea day in history? In kin yi wannan alkawarin zan barki ki kwanta Hafsah kuma zan yarda in zauna!. A yadda ta matsu da ta samu shakar numfashi yadda ya kamata, ba alkawarin da ba za ta iya yi masa ba yanzu. Don haka ta ce ta amince. Ya ce, Then a good night kiss, irin na Rockview. Wannan karon Hafsat ba ta da mafita banda ta kashe wayarta jin numfashi na neman fin karfinta. The Rockview memories overwhelmed her!Ita kadai ta ke murmushi mai zurfi bayan kashe wayar. ***** Washegari sai da ta makara, makara ba yar kadan ba. Ana gab da rufe exam hall. Yau kam ta sa a ranta za ta kashe wayarta kafin ta kwanta. Abdulazeez a shirye yake da ya jawo mata dako (carry over) wanda ba zai taya ta wajen sauke shi ba. He is already what he wants to be in life! Ba ta tsammanin don ta zama mai (spill over) yana da damuwa. She is a goal oriented like him. After all zai iya jiranta ta gama su dora a inda suka tsaya tunda an sakar musu mara yanzu babu tunani da fargabar ranar karewar KWANGILA! Kin kunna wayarta ta yi har bayan kwana biyu. Dawowarta kenan yau ta shiga dakin Mammah don ta sanar da ita ta dawo. Tana shiga ta ce. Kin ga Allah ki kunna wayarki ko wannan dan Anacen ya shafa man lafiya. Ina dalili zaabi a uzzire ni? Ni kuma ba zan ba ki tawa ba kamar yadda ya bukata, don ban ga dalili ba. Murmushi ta yi ta juya ta fita a ranta tana fadin, Mammah kyale Yaya Azeez kawai. He just want to me to score zero, ko in cika musu answersheet da ABDULAZEEZ DAKATA . Alhamdulillah! Yau Hafsat-Suhaana ta zana last paper dinta. Ta gama zangon farko na year 2, sun samu hutu na tsayin sati hudu, idan sun dawo za su shiga zango na biyu na (level two). Ta yi baccinta yau ta hantse har da munshari. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Gaisawa suka fara yi ita da Hajiya Halima matar Controller, sannan Mammah ta fadi makasudin kiran nata, Ki turo min babarbariyar da ki ka turo ta yi wa Hafsat gyaran amarci Fannah takeko wa? Daga gobe zuwa jibi don Allah Maman Saadiyyah. Toh!Tantabara sarkin soyyyah! Tsohuwar zuma ce ta tashi za a yi wa formerAmbasada gyara?Ko kuwa Hafsat ce ta haihu har zata koma babu gayyatar suna? Ko daya. Addar nake so a kara gyara min kawai, ta koma masha Allah fiye da gyaran farko. Dariya sosai Anty Halima ta yi. Ka ji uwa, kuma surukar zamani, wato a gyare miki yarki Abdulazeez ya sha shagalinsa!” Salati Mammah ta saka tare da runtse ido. Ni Hajiya Halima yaushe za ki girma ne? Yau in da ni na ce zan yi ki ce na addabi tsoho, na ce a yi wa yara shi ma ya zama abin magana? Sosai Halima ke dariya, To ita Hafsat har yau ba bayani ne? Ana neman shekara ta biyu fa. Ki sanya su a addua komai sai Allah ya nufa. Haka ne. Inj Hajiya Halima, Kada ki damu, Hafsat sai ta koma tamkar jiya aka kai ta. Zan yi magana da wadda ta yi mata na aure goben nan zan sa a kawo ta, ta zo Abuja yi wa yar Captain Bakari, kin san auren ya zo. Au abin ya zo? Zumunci na da Haj. Munira ya yi rauni ne, tun dawowarmu nan ban samu na ziyarce ta ba, kuma ba ni da lambar wayarta, bana jin ta san mun dawo ma, ta zo wajena a Belgium da suka kai dansu karatu can. Tun daga nan ba mu kara haduwa ba. Haka suka yi ta hira irin tasu ta aminai, sai da Hafsat ta shigo ta gaya mata ta yi baki, sannan suka yi sallama. Mammah ta yi shiri kamar yadda ta saba duk dare ta nufi turakar maigidanta. Prof. Dr. Hamzah Dakata, agogo sarkin aiki wanda a gida ma ba ya hutawa. Bautawa aikinsa yake da karfinsa, lafiyarsa da lokutansa har zuwa lokacin marking takardun dalibansa yake yi. Hajiya Maryam ta zauna a gefensa, sassanyan turarenta ya bugi hancinsa, dole ya aje biro ya dube ta da sassanyan kallo, Maryama Amarya, kuma uwargidan Hamza Atiku ya aka yi ne? Dariya ta yi ta juya masa idanu, Zuwa na yi neman alfarma, a yi wa Addah visa ta tafi America. Hannayenta biyu ya riko cikin jin dadi domin hakika ta yi masa ba-zata. Bai zaci za ta barta haka da wuri ba duk da ya san za ta barta din, Sun samu hutun ne? Eh, na sati hudu. A yi da gaggawa don ta samu ta yi ko sati uku ne. Jikinshi ya janyo ta yana fadin, Mairo yar albarka, na gode, nagode!. Hajiya Maryam ta san Ambassador yana son Abdulazeez tun yana karami, amma ba ta kara sakankancewa da kaunar ba sai yau. Tukwicin soyayya mai yawa ta karba, har da kujerar makkah. Ya ce dukkansu su je su yi umrah, Suhaana ta tafi wajen mijinta sun dade rabonsu da Saudiyyah. Don haka gabadaya gidan ba wanda ba a hada da passport dinsa ba. Haleem ne ya kai Hafsat yin tata visar babu wani cikakken bayani, shi Daddy yasa yayi processing visa din kagin su mika, duk da shima bai san me iyayen nasu suke shiryawa ba, an umarce shi ne kawai da ya ciccikeapplication din ya hada da informations din Abdulazeez wandaDaddy ya shi ya kuma ya kaitathumbprint. Daga nan ya mika nasu wajen yin na Saudiyyah. A ranar mai gyaran jikin ta zo da yamma ta fara yi mata. Ta soma ba ta wasu abubuwa na ci da sha, a take ta tuno farkon aurenta, ta kuma tuno Daada, the same da abubuwan da ta dinga ba ta da za ta dawo daga Jimeta tana zubawa a shara a boye. Zuwa yanzu kuma ta yi wayon fahimtar mene ne su da amfaninsu ba kamar lokacin aurenta ba. To ita da ba ta da mijin amfanin me za su yi mata? Daada ta ce na gyaran aure ne. Kwanaki hudu ta diba tana zuwa ta ce ta gama, sai wanda ta ba ta ta ce ta ci gaba da sha da kanta da turare na tsugunno. A washegari Mammah ta ce ta shirya za ta je Yola ta kwana biyu tana dawowa za su yi tafiya. Ta yi murna sosai, she cant wait to see Daada , Malam Babba, Abba, Imamu and co. Usman ne ya kai ta filin jirgi ya yankar mata ticket-to Yola da yar kankanuwar trolley dinta, wadda ta zuba kaya saiti uku kacal, tana rataye da matsakaiciyar handbag(vintage) da takalmin ta mai tsayin dunduniya.Sanye da wani tattausan leshi ruwan zuma da aka yiwa dinki (fitted gown)ta rufe jikinta da yalwataccen mayafi kalar kayan jikinta. Idan ka kalle ta ba za ka iya jurewa ba sai ka waiwayo ka kara sabida kyan da ta yi. Kwarjini na zuba, haiba da kamala na magana da kansu. Hafsat Hamza Atiku Dakata kenan. Wadda bullowar iyaye da kakanni na jini bai sa ta sauya identity dinta ba. Wanda kowa ya santa da shi yake kuma tubuce a takardun karatu dana haihuwarta. Ba zai ma sauyu ba, ko zai sauyu babu mai canzawa, (not even Dr. Bashar), ga kuma AURE da ya kara tiding dinta ga wannan identity din na wannan family mai albarka. A cewar Dr. Bashar.Su din a cikin rayuwarta ba komai bane facestrangers. Ta kara rike su, ta kaunace su cikin amana, ta zauna da su saboda Allah, mutane irinsu tsiraru ne a cikin alumma. Imamu ne ya zo daukarta a filin jirgi. Murna kamar su hadiye juna. A kind of brother-and sisters love mai karfi ne a tsakaninsu, fiye da Abdurrahman da Yaya Modibbo. Kai tsaye DEMSAWO suka nufa. Malam Babba na lazumi yana hadawa da gyangyadi a falonsa, Hafsat ta lallaba ta zauna ta jawo tarin gemunsa. Firgigit ya bude ido sai ganinta ya yi a gabansa kamar a mafarki. Mutsittsika ido ya yi ya tashi zaune, Hansatu an onbo (ke ce kuwa)? Ba wai don ta ji fulatancin ba fahimtar abin da ya ce kawai ta yi, Ni ce nan, ko ba ka soganina ba in koma? Hannunta ya riko ta ga alamun rauni a tare da shi ba kamar zuwansu Abuja ba. Ya ce, Wane ni in ce ki koma? Murna na yi sosai da ganinki, kwanan nan ban cika lafiya ba, bana iya cin abinci, sau uku ana yi min karin ruwa, amma yau jikin da dan dama-dama. Jabbama-jabbama! (lale-marhabin), ya ya iyayen naki da Abdulazizua Turai? Dazun nan muka gama waya da shi, yau kwana uku a jere kullum sai ya bugo ya ji ya jikin nawa, dan arziki irin albarka. Hafsat ta ji jikinta ya yi sanyi. Ita yau ta mance kwana nawa rabon da ta yi magana da shi balle common gaisuwa, ta ji shi din wane hali yake ciki saboda bokonta. Sai dai fa yana manne cikin kowanne bugun zuciyarta. Ta sa a ranta yau da kanta za ta kira shi ta wanke laifukanta, ba ta samu nutsuwa ba sai yanzu, zuwanta Jimeta ya kara jefa ta cikin nishadi. Ta san ita yau mai tarin laifuka ce a wajen Abdulazeez, wanda ba shi da gaskiya ma yana fushi a kai, balle wanda ya san an aikata masa shi ne da gangan? Daada ce ta daga labule ta shigo da sallama tana dauke da karamar kwarya an rufe da faifai, ga ludayin duma bisa, da alama fura ce ko farau-farau ta kawo wa Malam din. Nuru a bayanta, ta kusa tsorata da ganin Hafsat, wadda a yau ta rikide mata Habibanta sak! Babu wanda ya gaya musu zuwanta, Imamu kawai ta yi wa waya, shi ma don ya dauko ta filin jirgi ne. Yana ajiye ta a nan babban gida ya juya ya ce zai kai ma Abba motar ne, su koma gida tare. Hafsatu an on (ke ce?), ko kuwa Habibana ce ta dawo? Ta fada cikin raunin murya. Hafsat ta mike ta karbo furar daga hannunta ta ajiye wa Malam, sannan ta kamo ta suka zauna. Gaishe ta ta soma yi sannan ta ce, Yi hakuri Dada, ban gaya muku zan zo ba, Mommah ma na hana ta gaya muku. Ina so in muku ba-zata, za mu yi tafiya ne duk gidan shi ne ta ce in zo in muku sallama. Wurin Abdulazeez? Malam ya yi saurin tambaya. Dan jimm! Ta yi kafin ta ce, Gaskiya Mommah ba ta gaya min ba, kuma bana jin wajensa ne, don bai dade da tafiya ba ai. Suka shiga hirarrakinsu, Nuru na fadin, an je Abuja ba da shi ba yana makaranta, shi yana so ya je ya ga gidanta. Ta ce masa insha Allahu idan sun dawo za ta shirya masa zuwa Abuja. Nan da nan labarin zuwan Hafsat ya isa kowane sako na gidan, aka soma aiko mata da akusan abinci daga sassan matan su Yaya Tijjani, daga nan suka koma dakin Dada. Sai da ta yi sallah ta sake wanka sannan ta ci abinci. Cikin tarin abinciccikan kala-kala dashishi da miyar taushe wadda ta ji manshanu da naman rago ta zaba, wanda Sahura matar mai bin Habiba a haihuwa ta aiko. Sosai ta ji dadinshi sai santi ta ke zuba wa Daada. Ba ta tashi a wurin ba Mammah ta kira Daada tana ji tana fada mata ta iso lafiya. Suka yi magana wadda ba ta jin me Mamman ke cewa ta ga dai Daada na dubanta, sannan suka yi sallama. Da ta gama cin abincin daki-daki ta shiga ta gaishe su, kowa a gidannan kamar ya hadiye ta, ta dawo suka ci gaba da hira da Daada wadda nan da nan ta ga ta shiga hada saiwoyi da hakukuwa iri-iri tana damawa da nono ta gama ta bata, ta kuma kasa ta tsare sai ta sha a gabanta. Amma dai Daada kina ganin yadda na ci abinci na koshi ko? Idan na shanye wadannan abubuwan har kofi uku ai sai in yi amai ko? Daada ta daure fuska ta ce, O yara reta yahugo jemma a yara reta (To shanye rabi, zuwa dare ki sha rabi). Yadda ta ga tsohuwar ta tsume fuska ta san ko ta kara musawa ba yarda za ta yi ba, haka ta daure ta sha rabin. Duk da ranta ba ya son bauri, ga na Daada ya fi na Mammah rashin dadi.Da daddaren kuma wasu kananan yan shila guda biyu ta dafa mata kafin ta ci abincin dare. Hafsat kamar ta yi kuka, ta ce. Da na sani ma ban zo ba, ni tunda nake a rayuwata ban taba cin yayan kaji ba! Daada ta ce. Ni kuma in bi ki da su har gidanku ba! Tana cikin ci Abbanta ya yi sallama, har kofar dakin Daada, kamshin turarensa har ciki. Ya sha farar shadda, ya dora hula zanna bukar.Sardidin bafillace maabocin kwarjini da kamala. Nan ta samu hanyar gujewa yan shillan Daada don kuwa mikewa ta yi tana Abba-Jabbama. Dariya ya yi ya ce, Fulfulde sai dan gado! Daada kina kokari fa waje koyawa Gaaji gida Ya shigo daga ciki. Daada na shimfida masa darduma. Ture kwanon Daada ta yi ta koma wurinsa kamar ta shige cikinsa don So. Hira suke yi a kan karatunta da mutanen Abuja. Ya ce ta tashi su tafi gidansa gobe ta dawo. Daada ta ce. Aah. Rokon Daada ta shiga yi ta barta ta je, Aunty Kubra ba za ta ji dadi ba ta zo garin ba ta je gidanta ba, amma Daada ta ki. Ita haka kawai ba ta son Kubran ta ankare da kakkarfar soyayyar da Dr. Bashar ke yi wa Hafsat, zuciya ba ta da kashi, duk da Kubran ba ta da aibu amma an ce ido guba ne. Tashi ta yi ta bar musu dakin, ta kuma ce da Abban akwai magani da Hafsan ke sha shi ya sa ta ce ba za ta samu zuwa yau ba. Amma gobe Imamu ya zo da yamma in Abban ya koma gida ya kaitata dawo da daddare tunda jibi da safe za ta koma. Abban ya gamsu da bayaninta. Duk da ya so su raba dare suna hira ne. Komai nata irin na Habibah ne, hatta muryarta wanda shi kadai ya san abin da hakan ke darsawa a zuciyarsa, sannan wata irin kauna yake yi wa yarinyar fiye da ta dukkan yayan da ya rayu da su har girmansu. Abban na yin sallama da su ya fita, Daada ta janyo akushin da ta ture na yan shillah ta dangwara mata, Ya mu pat (cinye du). Sai da ta cinye ta bar mata kasusuwan sannan ta shafa mata lafiya. Da ta yi shirin kwanciya ta yi ta kiran layin Abdulazeez ba ta same shi ba, wayar ba ta shiga sam. Ko dai a kashe ta ke, ko kuma ya daina amfani da layin. Ta shiga damuwa ba yar kadan ba, ta dauki rashin kyautawar duniya ta dora wa kanta. Da za ta iya da ta tambayi Mammah, amma ko kusa ta san ba za ta iya ba. Ismaeel ne last hope dinta. Shi kuma ta san ta sake ta tambaye shi lambar Yaya Azeez sai ta gwammace kida da karatu. Sai ya shekara yana kasa ta a faifai. Haleem bako ne, a wajenshi ya kamata ta nemi lambar mijinta? Ai sai ya ga rashin hankalinta. Gara-gara Usman ba shi da matsala. Shi din ta kira, amma cikin rashin saa ya kashe wayarsa ya kwanta, dole ta hakura sai dai fa kafin wayewar gari har wata yar rama ta yi saboda damuwa. Da safe ta je gidajen yan uwa tare da Nuru autan Daada, har gidan Yaya Modibbo, daga can suka wuce gidan Abbanta, Imamu na shirin zuwa dauko ta sai ga su sun shigo. Da mamaki ya ce Nuru wa ya kawo ku? Dariya ta yi ta ceDan sahu, keke-napep mai dadin hawa fiye da mota. Tana gwada dadin ta hanyar kada yatsunta kusa dakunnuwanta, ya gane yau dai cike take da farin ciki mara misaltuwa. Dariya ya yi, ya ce. Ok, how do you feel it? Ta ce, Dadi sosai-sosai, ko ta ina iska na buga ka. Ai ina hawa a Kano idan muka je kallon hawan sarki da sallah tare da yayan Aunty Murja. Ta shiga ba shi labarin yadda suke zuwa Kano kallon durbar tun suna kanana. A nan falon suna ta hira Abba da Anty Kubra suka dawo suka tadda su. Abdurrahman a bayansu. Aunty Kubra ta yi ta ina ta-ka-sa-ka da ita, Imamu ya ce, Abba yau Kawu Nuru a dan sahu ya yi ta yawo da Ghaaji a Jimeta. Abba ya ce. Nuru me ya sa? Nuru ya ce. Ita ce ta dage, Daada ta ce ta jira Imamu ya zo ya kaita koina ta ki, zan maka waya ma ta kwace wayar. Hafsat ta cuno baki irin na karshen shagwaba. Kuma shi ke nan ni ba zan dana ba Abba? A Kano ma in mun je Mommah ba ta barina, ni kuma ina so Abba. Da sauri ya ce. Shi kenan Ghaaji, itsok, dama ina tsoron kar ki fado ne tunda baki saba ba, da anan ki ke ko kuma da ba a hana amfani da shi a tsakiyar Abuja ba da na saya miki wallahi. Ta ce Ka saya min ka ajiye min a gidan nan, in na zo a dinga kai ni unguwa. Imamu ya harare taAmma dai ba ni ne direban ba ko? Waye kuwa in ba kai ba? Haka suka yi ta hira cike da kaunar juna har dare. Aunty Kubra da mai aikinta suna kitchen suna shirya musu abincin dare. Abdurrahman ya ce, “I will call Abdulazeez and tell him ya koyi tukin dan sahu da zarar ya dawo. Dariya aka saka har Abban, sai wajen goma na dare Imamu da Abdurrahman suka maida ita Demsawo, Nuru a can ya baro ta tun magriba ya koma gida. Dakin Mallam ta nufa suka sake sabuwar hira, a daren kuma suka yi sallama ya kawo adduoI masu yawa ya bata, ya ce ta rage barci ta yi amfani da rabinsa wajen neman kusanci ga Ubangiji da neman yardarsa da rokon soyayyar Ubangiji daga mijin aurenta. Duk son da miji ke miki ki hada da neman soyayyarsa wurin Ubangiji. Ta Ubangijin ita ce wadda ba ta da karshe, lokaci, yanayi, tsawon zamani ko yawan shekaru ba ya canza ta. Kullum sabuwa dal take komawa. Kada ki kwanta ki ce ai ke mijinki na sonki shi kenan, wannan kuskure ne babba. Kada ki nemi soyayyar miji a wuin kowa ki nema a wurin Allah, a cikin sujjadah da tahiyarki. Tashi ki je ki kwanta, Allah ya hada mu da alkhairi. Kamar jiya, yau ma ta yi trying wayar Abdulazeez (not reachable). Haka ta hakura ta kwanta zuciya na zugi. Ta tabbata lafiya yake, har ta soma tunanin ko ya yi barring number dinta ne, don kuwa in har ta ji daidai dazu Malam ya ce sun yi magana, kamar ta ce ka ba ni lambar, amma ta yi kawaici ta kuma rufa wa kanta asiri ta yi shiru. Ta san halin tsohon nan sai ya binciki dalili. To ta ce masa me? Ni ce na daina magana da shi don ina jarabawa shi ne shi ma ya daina kirana ko me? Ita a kan kanta ta ji uzurin nata invalid wanda zai lalata shirin da ke tsakaninta da Malam Babbah har ta bar Jimeta. Ta yi shirin tafiya, ta yi sallama da kowa. An fidda jakarta mota, Imamu na mota yana jiranta. Ta shiga turakar Malam su yi sallama ta karshe. Dattijon na kishingide a kan buzunsa ya tada kai da tum-tum ya yafitota da hannu. Ta karasa gefensa ta zauna, wani qoqo ya janyo da ke rufe a gefe da fai-fai ya bata, ya ce ta shanye. Rubutu ne an barbada wani koren magani a kai (ganyen magarya). Sai da ta shanye ya ce mata, Tsari ne, ba mutum ba ba aljan ba, insha Allahu. Sannan ya kira sunantada nasabar jikinsa yadda bai taba yi ba. “Hafsatu yar Habibah jikar Hashim Babbah!!! Dagowa ta yi da sauri jin wadannan tarin sunaye da yau Malam ya kira ta da su. Murmushi ya yi ya karbi qoqon hannunta ya ajiye, sannan ya ce. Kin san me ya sa na kira ki yau ta bangaren mahaifiyarki? Girgiza kai ta yi, ya ci gaba, Saboda in tunasar da ke wani abu wanda ya kamata ki ke tunawa. Ambassador Hamza da maidakinsa Maryama ba su diga miki jinin haihuwa ba, amma tunda ki ke kin taba jin labarin ko katari da mutane irinsu? Da sauri ta sake girgiza kai, Ko a labarin hikaya, musamman yadda zamani ya koma yanzu rikon dan wani naka ma ya koma sai yadda hali ya yi balle Da irinta a gare su. Duk da tana tune da yadda shi kansa Daddy ya kasa karbarta cikin ahalinsa a shekarun kuruciyarta sai daga baya, amma duk da haka dole a sara masa. Ya yi abin a jinjina masa cikin rayuwarta, musamman sunansa da ta ke bearing har gobe. Mammah kuwa ai fadin karimcinta wani abu ne da ba zai taba yiwuwa ba. Malam ya yarda ta ankara da abin da yake so ta ankara da shi a lokacin, sai ya warware gundarin abin da yake dunkulewa. A ganinki da me za ki saka wa wadannan mutanen Hafsatu? Ko da da kwatantawa ne? Girgiza kai ta yi cikin sanyin jiki alamar ba ta sani ba. Ya ce, Sun dauki Dansu mafi darajar girma da kima a gare su sun aura miki. A lokacin da suke da tabbacin ba ki da kowa. Ba su da tabbacin halaccin samuwarki.Kin kasance mai kaskantaccen matsayi a garesuIn ke mai halacci ce da me za ki saka musu a halin yanzu da wannan Da tsaya tsayin daka ya nemo miki jininki a duniya ya damka ki gare su? Mahaifiyarshi ta yi fito-na-fito da shi don ya rike ki da daraja? Hawaye Hafsat ta soma yi tana girgiza kanta, tana da amsar amma ji ta ke in ta fade ta ta yi kadan, gara ta bari Mallam din ya bata da fadi...Sai dai da za ta iya da ta ce da kakan nata... In zan iya zan goya shi kullum! In zan iya zan daukaka darajarsa fiye da ta kowa cikin rayuwata In zan iya zan yi ta yi masa biyayya daga fitowar rana zuwa faduwarta a kan dukkan umarninsa. Zan yi ta yi masa addua a bayan dukkan sallar farillah ta In yi ta rokon Allah Ya yarda da shi, Ya buda masa, Ya kare shi daga duk wani abin ki,Ya sanya shi ya zamo miji a gareni har a aljannah!!!”. Amma ji ta ke in ta fadi hakan Malam zai ce ya yi kadan, don haka ta ba shi dama ta hanyar cewa ba ta da idea a kan hakan. Hawayen wata sabuwar kaunar ABDULAZEEZda bata taba ji bana malala a kan kundukukinta. Sai ki rike musu shi da amana, ki so shi da tsarkakkiyar zuciya. Ki ba shi soyayya fiye da wadda suka ba ki. Ki zama garkuwa a gare shi daga aikata ZINA da sauran ayyukan alfasha. Ki zame masa sanyin idaniya ki kawo madauwamin farin ciki a rayuwarsa ki zamo masa bango, a lokacin da yake bukatar jingina. Ki yi masa biyayyah a kan kowanne umarninsa muddin bai saba wa iyakokin Ubangiji ba. Hafsatu ki nuna musu ke yar halal ce wadda ta san halacci da alherin da anka yi mata. Ba kuma ki da hanyar nuna hakan sai ta hanyar aurenki da Dansu, da irin rikon da za ki yi wa auren da mai shi. Na barki da wannan, ki kara fadada shi, haske kawai na ba ki, ki yi amfani da ilmin da Allah ya ba ki ki yi su a aikace. Tashi je ki. Allah Ya yi wa rayuwa albarka!. Har suka zo filin jirgi Hafsat kuka ta ke yi, kukan da Imamu bai san dalilinsa ba. Ya dauka na kewar mutanen Jimetan ne, ya rarrashe ta har ya gaji ya rabu da ita. Ita kadai ta san me ta ke ji a zuciyarta, Abdulazeez kawai ta ke son gani, da wata irin soyayyamai yawa. She only wants to see him beside her at every blink of an eye (so kawai take ta ganshi a gefenta, cikin kowanne kiftawar ido) she wants to feel herself in his arms like before,and tell him how much she love him abubuwan da ta ke ji a lokacin masu yawa ne da harshe ba zai iya bayyanawa ba. Babban tashin hankalinta ba ta san yaushe za ta ganshi ba ya ce zai zo ta ce aah ya ce su yi magana su debe wa juna kewa, shi ma ta ce aah. Har ya gaji da bibiyarta ya yi barring dinta. Me ya sa wasu lokutan mu ke yin mistakes wanda bamu daukesu komai ba, kuma ba ma sanin kuskure ne sai daga baya??? Cikin wannan halin Hafsat ta sauka a Abuja. Zuciyarta ta kara raunata da ta hango Maryam Dakata da kanta ba sako ba! Haleem ya kawo ta filin jirgin Nmadi Azikwe tana jiran isowarta kamar wadda ta dawo daga wata kasa. Ai tana isa gare ta cikin reception(she cannot control her tears). Fuskarta Mammah din ta saka cikin tafukan hannayenta tana tambayarta ko lafiya?, Kukan da ba ta san dalilinsa ba. To ko a sake yankar tikiti a koma Jimeta ne? Ta fada cike da damuwa. Hafsat sai ta rungume ta cikin kuka ta ce. Ba fa Jimeta zan koma ba Dariya ta yi ta riko hannayenta suka nufi mota, To ko in bude ciki ki koma???” Haleem dake bayansu haushin maganganun su da shagwabar Hafsat ya ishe shi, ya karaso ya sha gabansu. Mammah, kin san Allah yarinyar nan don ta ga ba ki da babya gabanki ne ta ke miki shagwaba, she better brings you a baby soon ko yaya Azeez ya kara aure. Yayi maza ya koma bayan Mammah. Wata harara ta juya ta galla masa, kuma har zuciyarta zancen ya mintsine ta. Gwalo ya yi mata ta bayan Mammah wadda ta hau shi da fada tana fadin ita ba ta son expensive joke haihuwa kuma ta Allah ce. Ita ma ta faki idon Mamman ta yi masa gwalo ga hawaye shabe-shabe a idonta,maimakon ta ba shi haushi sai ta ba shi dariya. Ba zai iya tuno yanayin kwayar idanunta ba sanda ya ce “Yaya Azeez ya kara aure!. Azumi na ta oyoyo da dawowar Hafsat, ta cika ta da abinci kala-kala. Ismael ya ce, Ina tsaraba? Tulin kayan da Daada ta hado wa Mammah ta nuna masa. Da kanshi ya hau budewa yana ware komai gefe, akwai kindirmo sabo fari sol a cikin sabuwar farar jarka, akwai sabuwar ‘maasa da kuli’ fal a leda, su ya kinkima ya yi kitchen da su ya bar sauran tarkacen a nan, sai Azumi ce ta kauda su ta kai wa Mammah komai inda ya dace, Ismael ya ciko plate da maasa da kuli ya zo falo yana ci kenan Usman ya shigo, Shagali! Yar fillo ina nawa? Yamutsa fuska ta yi, Ni ba yar fillo ba ce. Ya ce, O.k Toh Lemme say Jimeta Lady a zamanance. Yayi???. Kafin ya rufe baki Baba Azumi ta kawo masa nasa Masan shake taf da plate.Bayan kulin ta yanka cabbage da cucumber akai. Da godiya ya karba ya ce. Baba Azumi, Allah ya nuna min aurenki! Me za su yi ba dariya ba har ita din. Azumi ta rangwadar da kai ta ce, Mujaddadi (Usmanu) mai babban suna, burina in ga naka kafin in ga nawa. Ya ce, Insha Allahu har liki zan miki wajen dinner. Mammah ta shigo falon tana fadin Hafsat ta je ta kwanta ta huta, kuma su daina kwarzabar mata Azumi. Baba Azumi ta ce, Jin dadina da farin cikina in gansu haka dukkaninsu a gabana muna hirarmu, ina tuno kuruciyarsu ta Jeddah da Beljiyan.Rai ne, watarana babu shi!. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* ***** Bayan sallar isha Mammah ta tadda Hafsat a dakinta, kayanta ta ke gyarawa cikin wardrove wadanda ta dawo da su. Janye ta ke da akwatuna biyu masu matukar kyau. A tsakar dakin ta zube su ta ce ta bude ta duba wanda bai mata ba ta aje a bayar a Kano. Dinkuna ne yan uban-ubansu daga atamfa, leshi, material zuwa ready made na voils din zamani da mayafansu. Hafsat ta hau dagawa cike da shaawa ba wanda ba ta ji ba ta so ba, amma don kada ta yi hadama sai ta ce a raba biyu a bayar din. Mammah ta ce. Dama mace tana kyautar da manyan kayan lefenta?? Cikin kayan lefen da kuka tsibe a Sun-City’ ne nasa aka dauko min na tsince manyan na bayar aka dinka miki. Kunya ta ji, ta rage murnarta a kan kayan, ita ta manta da wasu kayan lefe. Mammah ta juya ta fita tana fadin ta je Daddy na kiranta. Tsallake komai ta yi ta yafa yalwataccen mayafi ta nufi sassan Daddyn. Da sallama ta shiga, Yau wace rana Daddy ba ya aiki a takardu, News yake kallo? Hafsat ta ce a zuciyarta. Amsa sallamarta ya yi, ya kuma umarce ta da ta zo gefensa ta zauna. Abin da ya kara mata jin nauyinsa don ba za ta iya tuna rana ta karshe da ya ce ta zo kusa da shi ta zauna ba. Cikin matsanancin ladabi ta bi umarninsa, sannan ta gaishe shi. Ta lura yau Daddy cikin faraa yake sosai, ya ce, Suhaanah an gama jarabawa lafiya, sai hutu ko? Murmushi ta yi, ta ce, Ai hutun ba yawa Daddy, har mun ci sati daya. Gyada kai ya yi, ya ce, Mammanki ta gaya miki za ki bi mijinki ki karasa hutun tare da shi? Da sauri ta dago sai kuma ta tuna da wa ta ke magana, ta yi maza ta sunkuyar. Mafarki ta ke ko idonta biyu? Ko dai cikin mafarkanta ne masu nuna mata Abdulazeez a dan tsukin wadanda suka zame mata jiki a yanzu? Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, kafin ta girgiza kai ta ce masa. Aah, ba ta yi min zancen ba. Cikin kulawa ya ce, To sai ki je ki hada abin da za ki bukata, Im sorry you areto fly alone (ke kadai zaki tafi), na san za ki iya. A rage cost din dan rakiya, mu ma kuma za mu tafi umrah gabadaya duka a goben, amma za ki riga mu tashi. Za mu tashi Saudiyyah karfe biyu na rana, ke kuma za ki tashi zuwa America sha biyu na rana. Ungo nan. Ya miko mata passport dinta da tickets a tsakiyarsa. Jiki a sanyaye Hafsat ta karba ta yi godiya, za ta mike ya ce, Kada ki damu direct flight na nema miki har can babu (transit) kina sauka kuma zai dauke ki, ya san lokacin tasowarki da sauka. Duk da haka ki kunna wayarki da zarar kin sauka. Hafsat ta rasa a wane yanayi ta ke jin kanta, farin ciki ko taradaddi? A haka ta isa dakin Mammah. Daga bakin kofa ta rabe kamar mara gaskiya. Mammah ta yi kamar ba ta ganta ba, ta ci gaba da gyara kayanta cikin closet dinta. A ranta ta ce, Gulmar banza, bayan ji ta ke kamar ta goya ni. Hafsat ta gaji da tsayuwa don kanta ta karaso ciki, a gefen gadon Mammah ta zauna ta dukar da kai. Ba ta ce mata komai ba yau za ta ga karshen fillanci. Ita da kanta shirun ya dame ta, ta motsa bakinta amma ta rasa jumlar da za ta hada wadda za ta bada maana. Tausayinta da kaunarta suka cika zuciyar Hajiya Maryam, irin macen da ta ke yi wa yayanta fata da buri kenan, mace mai kawaici, addini da alkunya. Yanzu fatanta yana kan Ismael da Usman Abdulazeez ya gama dacewa.Sai dai ga dukkan alamu burinta a kan Usman da Haleem zai cika, Ismael kam ya ce sai irin wadda yake raayi shi ba Yaya Azeez ba ne. A wannan karon ta sanya a ranta ba za ta takura wani a cikinsu ba kada a zo a samu irin matsalolin da aka samu a na farko ba don Allah ya nufa auren rayayye ba ne, kuma aka yi saa suka kaunaci abin daga baya. Da saki uku Abdulazeez ya yi kuskuren yi ba ta san ya za ta yi da kayan nadama ba, da kallon Hafsat a gabanta matsayin bazawara a shekarunta da ko ashirin ba su kai ba. Don haka tsakaninta da yan baya addua ce da fatan alkhairi babu tursasawa. Yanzu kam hankalinta ya kwanta, zuciyarta cikin farin ciki ta ke da wannan buri da Allah ya cika mata na sanya Hafsat-Suhaana cikin ahalinta, tsatsonta, jininta, kuma uwa ga jikokinta na farko. Su Ismael su yi yadda suke so za ta bi su da addua. Karasowa ta yi gabanta ta cire mata tagumin da ta yi. Hafsat ta dago ta dubi Mammah, sai ta ji hawaye sun ciko idanunta. Ba ta san ta ina za ta fara cewa za ta yi kewarta ba. Ji ta ke kamar yanzu ne karo na farko da za ta bar gida zuwa gidan miji kamar ba a yi hakan a baya ba, kamar ba yan satittika aka ce ta je ta yi ba! Kamar idan ta tafi ba za ta dawo ba take ji!!! Ba ta yi aune ba sai hawayen suka balle. Salati Mammah ta yi duk da a hankali ne, ta ce, Ko ba kya son zuwa ne Addah? In ba kya son zuwa babu komai, ki yi zamanki har ya dawo, amma sai dai ki tafi Kano tunda ba a yi visar Saudiyyah da ke ba, Azumi ma Sokoto za ta. Hawayen ta share da sauri, Aa, Mommah. Murmushi ta yi, da ma tsokanarta ta ke yi don ta ji cikinta ne. Ta ce To ai kukan da ki ka zo ki ka tasa ni a gaba kina min sai ki tada min hankali, in ba hakan ba ne mene ne? Hawayen ta ke ta gogewa da gefen mayafinta. Mommah, ina tunanin yadda zan zauna a wani wuri babu ke ne. Dariya ta yi. Da ki ka zauna a gidanki tsayin shekara da watanni ni na taya ki zama? Ki sa a ranki kamar unguwa ki ka je ki ka dawo, za ki dora daga inda ki ka tsaya. Sai dai wannan zaman zai kasance ba irin na baya ba. Shi wannan akwai focus, kuma komai ki ka yi a cikinsa kin yi ne don neman aljannah. Wancan kuwa na sabo ne babu lada a cikinsa sai alhaki. Ku rike istigfari koyaushe ki bi mijinki ku zauna lafiya. Gidana babu space na yaji tunda wannan karon ba ni na tursasa ku zama da juna ba,don haka bazan yi tolarating kowanne nonesense daga dayanku ba. Ku yi hakuri da juna tunda kun ce kun ji kun gani kuna son zama da junanku, sai a yi zama na soyayya da amana. Tashi ki je ki hada abubuwan amfaninki. Kayan da ki ke amfani da su duk ki barsu ki yi amfani da sababbin da na baki. Mu kwana lafiya. Hafsat na shirya kayanta cikin babbar jaka tana hawaye. Haka kawai maganganun Mammah ke shawagi a kanta. Wadanda ke nufin wannan karon za su yi zama ne ita da Abdulazeez irin na kowadanne maaurata babu interference na iyaye. An ce kuma cikin zaman aure akwai kalubale mai yawa wanda duk son da ake wa juna sai an yi hakuri. Daya zai iya bata wa daya rai kuma dole ya yi hakuri. Ga Abdulazeez mutum mai wuyar shaani, abu kadan zai nuna ransa ya baci. Tana rokon Allah ya ba ta nasara cikin zama da shi ya dinga sassauta zuciyarsa a kanta. Salisu direban Daddy shi ya kwashi dukkan jamaar gidan da kayayyakinsu a washegari zuwa filin jirgin saman Nmadi Azikwe. Ismael da Usman ne suka yi ta yi mata shige da fice na awo da immigrationcheck har ta shiga jirgi da kayanta bayan sun yi bankwana da juna.Ba ta dade da shiga jirgi ba su ma aka fara screening din kayansu. A kan idonsu jirginta ya keta hazo ya lula cikin sararin samaniya. A lokacin ne Daddy ya fiddo waya ya kira Abdulazeez ya gaya masa tasowar Hafsat da lokacin da za ta sauka. Yadda ta ji maganar bagatatan haka shima ya ji. Amma ya yi kokari ainun ya rike kansa da reaction dinsa, ta yadda Daddyn bai gane yadda ya karbi zancen ba. Ya ce masa dai insha Allah zai je ya dauke ta a kan lokaci, sannan ya kara da godiya. Daddy ya juya ya ce da matarsa. Kamar bai yi murna ba!. Mammah ta ce. Itama ai ba ta yi murnar ba, har da kuka, Oho su suka sani!. ****** HADUWAR AMARYAR DA ANGON! Jirgin Egypt Air ya sauke Hafsat-Suhaanah a birnin NewHaven din Connecticut da misalin karfe bakwai na dare agogon kasar Amurka. Jamiar da Abdulazeez ya zo, wato (YALE UNIVERSITY) tana cikin New-Haven din jihar Connecticut. A sannu ta biyo bayan jerin gwanon fasinjojin da ke saukowa daga matattakalar jirgi rataye da jakarta louisVuitton a kafadarta ta dama. Bakar abaya ce a jikinta ta nade kanta da dan mayafinta. Fuskarta ce kawai a waje, ta yi fayau sabida baccin da ta sha a jirgi. Takalmin kafarta mai tsayin dunduniya ne siririya wadda ta daure igiyoyinsa a idon sawunta. Saukarta a sararin airport din Bradely International Airport ya tuna mata da abubuwa da dama; rayuwarsu a Belgium da kewayenta, bambancin ba mai yawa ba ne da nan.Amma in ka dubi tsakiyar idanunta za ka hango yar kankanuwar damuwa makale cikin kyawawan idanunta wadanda bacci ya canza musu launi. Shin Abdulazeez ya san da zuwanta? In ya sani da yardarsa aka turo ta? Shin wace irin tarba za ta samu daga gare shi? Ta yi masa wani alkawari mai girma da yau ce ranar cika shi Alkawarin cewa duk ranar da suka hadu; babu kunya a tsakaninsu..... And It will be a day in history! Yau ga ranar ta zo, amma ta zo a wani irin jirkice; Abdulazeez din yana fushi da ita. A yayin da tata zuciyar ke cike taf da alamura masu wuyar fassaruwa;so much love, so much affection, so much devotion, so much emotion, so much respect for him and so much many more things!!!Ina ma ana dawo da hannun agogo baya? Da ta yi rewinding ta goge duk wani laifi da Abdulazeez ke ganin ta yi masa! Bata yi da gangan don ta bata mishi rai ba. Bata dauki hakan laifi bane sai da ya nuna bacin rai akai. Ina ma ya kasance cikin mutane masu saurin yi wa abokan rayuwarsu uzuri kamar yadda kullum ita ta ke yi masa? Da Allah kadai ya san muhimmancin ranar yau a gare su. Duk da dare ne amma koina haske yake da fitilu masu tsananin haske wadanda ko allurarka ce ta fadi za ka duka ka dauki abarka ba da wuya ba. Kanta tsaye ta ke tafiya janye da jakarta bayan ta dauko ta daga kayan da jirgi ya sauke. Kujerun da matafiya ke zama don jiran masu daukarsu ko hutawa ta nufa ta zauna da jakarta a gabanta. Alal hakika ta gaji tibis, kwanciya kawai ta ke son yi a lallausar katifa, ba ta tare da yunwa don ta ci abinci a jirgi, abincin ma na mukami domin kuwa a first class seats ta zo. Tunanin ta inda za ta ga Abdulazeez ta ke yi cikin dubban mutanen nan farare, jajaye da bakake. In bata yi kuskure ba tace har da shudaye da koraye. Ta tuna Daddy ya ce ta kunna wayarta. Tana laluben wayar cikin jakarta ta ji an zauna a gefenta. Kafin ta dago Creed Aventus ya ziyarci hancinta da karfinsa. Kafin ta farfado ta ji muryarsa mai amo da karsashi (husky) cikin kunnuwanta.A yayin da ya rankwafo sosai daidai kunnen nata har tana jin sanyin numfashinsa. Welcome to New Haven!!!”. Abinda Ya rada mata kenan. Muryar ta kara gardi da dadin sauraro fiye da koyaushe. Ko kuwa ita kadai ta ji hakan? Bazata iya cewa ba! Lumshe idanunta ta yi, kafin a hankali ta bude su tarr a kanshi. Dauke kansa ya yi ya dubi wani gefen daban, We can go (zamu iya tafiya). Wani irin kallo ta bi shi da shi kasa-kasa, zuciyarta na melting. Ya kara tsawo fiyeda wanda ta san shi da shi, ya yi wani irin freshya saje da black-Americansdin da ke giftawa jefi-jefi. Sai dai kuma ya yi musu zarrah kasancewar shi akwai hasken addinin musulunci a tare da shi da cikar zati da kamala. Wadanda suka samar da wani irin kwarjini a tareda shi. Sanye yake da dogon wando da riga Long-sleeved(Burberry Hartford) ruwan makuba. In ta ce;he is handsome is not enough to convey thehandsomeness, ta san hakan tun tana karama da ta ke ganinsa a gidansu a Jeddah. Ta kuma sha fadin hakan a zuciyarta cewa ya fi duk yan gidan kyau mai daukar hankali, sai dai kuma duk sun fi shi kirki. Har gobe hakan ne a wurinta, sun fi shi saukin kai da dadin muamala, ya fi su Psychological Charisma. A haka ta mike cikin sanyin jiki, za ta ja jakarta ya sanya hannu ya dauka, suka jera zuwa harabar airport din inda motocin haya suke jiran fasinja. Tun kamin su karasa wani siririn bature ya iso gare su ya karbi trolley din daga hannunsa yana tambayarsu inda za su je. Hannunta ya kama ya rike cikin nasa suka shiga farar taxi din mai matukar lafiya da sabunta. Sai da suka fara tafiya Abdulazeez ya ce da shi. NewHaven Towers!. NewHaven TOWERS, gidan bene ne mai kunshe da gidaje masu yawa(apartments)da mafi yawan daliban Yale ke zama, ana kiran daliban Yale University da (Yalies).Apartmentsdin ba iri daya ba ne, ya danganta da yadda ka ke so, single room, onebedroom, two bedrooms ko three bedrooms. Suffofin New Haven TOWERS sun hada da proximity ga jamiar Yale, wuraren siyayya, wuraren cin abinci, libraries, museums, parks da duk wasu ababen dabe kewa da dalibin Yale zai buka. (New Haven Towers) yana nan a Downtown na birnin NewHaven County. Idan aka ce Downtown ana nufin mahada ko cibiya ta kasuwanci, aladu da tarihi, siyasa da Geographical heart. Sau tari downtown’ synoymous ne da (CBD) na kowanne gari, wato Central Business District ko kuma a kira downtown da city-center ya fi saukin fahimta. Abdulazeez Dakata na zaune a two bedrooms apartment a cikin New Haven Towers’. Daga (New Haven Towers) a kafa yake takawa zuwa makaranta kullum sabida bauchi nisa (trackable distance) ne. Da taxidin ta sauke su a daidai kofar shiga ginin TOWERS din shi ya dauki jakar ta har handbag dake hannunta suka hau ta lifter. A kofar apartment dinsa ya ciro makulli a aljihunsa ya bude, jakarta ya fara shigarwa sannan ya ba ta hanya. Sai wani dauke kai yake yi ya ki yarda su hada ido. Wucewa ta yi ciki ta samu lallausar kujerar wadataccen falon ta zauna, sannan ta warware lullubin kanta ta shiga karewa falon kallo. Matuka tsarinsa ya ba ta shaawa, komai neatandclassycikin tsari irin na bature, a can gefe study-table ne, manya-manyan littattafan law sun cinye filin tebirin sai inda zaa aje littafi ayi rubutu kadai suka bari. Ga study light mai ban shaawa komai na falon har labulaye brown da milk ne (ruwan kasa da ruwan madara). Akwai talabijin ta jikin bango, amma da alama ba’a kunnata sam. Kujerun wasu yan gujib-gujib na leathermasu tsananin taushi kalar su ruwan madara zallah. Daya daga cikin dakunan barcin guda biyu ya shiga bata kara ganinsa ba. Ranta ya soma baci da wannan tarba da Abdulazeez ke mata, a kalla ya nuna mata dakin da za ta shiga ta sauke lalurorinta, ko ba zai yi mata magana ba. Idonta ta ji ya kawo ruwa da ta tuna salloli uku ne a kanta, ta taho tun daga Nigeria har America saboda shi, amma daga sannu da zuwa ko sannu ba ta kara samu ba. Tana wannan tunanin ya fito daga dakin da alama wanka ya yi, ya yi sallar magriba da isha a gefe duk tana zaune. Sannan ya sake komawa dakin ya sauya kaya ya fitohar da takalmi a kafarsa alamar fita zai yi. Kallonta ya yi da mamakin har yanzu tana a inda ya barta? Kamar ya wuce ta, sai kuma ya iso gabanta ya tsaya, sanyin turaren wankan sa na dunhillduk ya cika mata hanci. Dakin ma sai na ce ki shiga za ki shige shi? Ai kuwa kina da aiki kuma zaki kwana anan wajen tunda ba ni na gayyato ki ba. Ya sa kai ya fice abinsa. Ci gaba da zaman ta yi tana shaqar bacin rai, daga bisani ta ji fitsari na neman kwace mata. Dole ta mike ta suri jakarta ta murda dakin da ke daura da wanda ya fito. A nan ta lura ya ajiye mata trolley da tun shigowarsu ba ta ga inda ta yi ba. Kofa daya ce tal a cikin dan kyakkyawan dakin barcin wadda ta san toilet ce. Can ta nufa da hanzarinta, fitsari na barazanar zubo mata. Sai da ta yi shi ta samu saida. A gurguje ta daura alwala ta fito ta kintaci gabas ta nada mayafinta ta tada sallah. Sai da ta rama sallolinta a nutse sannan ta kara da shafaI da wutiri ta mike ta soma rage kayan jikinta don ta shiga wanka. Wanka ta yi sosai da ruwa mai dumi don garin akwai sanyi duk da bai yi nisa ba, nisan da zai soma zubar da kankara. Tana wankan ta ji motsinsa a dakin da rufe kofarsa. Da ta gama wankan sai da ta leko da kanta ta tabbatar ba ya dakin, sannan ta fito gaba-gadi. Ledoji ta gani ya ajiye mata guda biyu wanda ko ba ta bude ba bata raba daya biyun abinci ne. Ga lafiyayyen kamshi na tashi. Kwalliya ta tsaya ta yi sosai da daya daga cikin dinkunan da Mammah ta yi mata na wani material light bluemai santsi, an yi masa doguwar riga fitted gownda aikin duwatsu a gaban rigar sosai, ta murza daurin kai kamar mai shirin zuwa dinnerparty. Ta sa dankunne da sarka deep colour na material din na dutsen (cubic zirconia). Ba ta shafa jambaki ba, sai ta yi amfani da wet-lips mai taushi da kamshi. Har za ta zauna ta ci abincin ta ga gara ta je falo ta ci a can?Na me za ta kunshe kanta a daki don maigidan ba ya maraba da ita? Ai gara ta je ya yi ta ganinta tana harkokinta, in zamanta ya takura masa ya maida ita gaban iyayenta. Falon ta fito rike da ledojinta, akwai dining table a gefe mai cin kananan kujeru uku, amma ba ta hau ba, tsakiyar rug ta baje ta fiddo kazar Kentucky Fried Chicken da chips da gwangwanin pepsi mai sanyi har guda biyu ta hau cin kayanta hankali kwance. Zaune yake a study-table yana rubutu, wando ne three quarter a jikinsa da farar singlet ko sanyi ba ya ji. Tun fitowarta yana hankalce da ita ta gefen idanunsa, yana kuma ci gaba da hada assignment dinsa duk a lokaci daya. Ganin alamarin yake kamar a mafarki, yau ga shi ga Hafsat matsayin cikakkun maaurata a KARO NA BIYU! Its indeed a day in history wadda ba zai taba mantawa ba. Godiyarsa ga Ubangijin halitta wanda ya halatta AURE ya kuma halicci SOYAYAYAH ba za ta taba gushewa ba. Sosai yake enjoyingsharetan da yake yi musamman ganinyadda damuwarta a kan hakan ta fito karara. Dazu yana kallonta har kananan hawaye ta yi saboda bai nuna mata dakin kwana ba. A ransa ya ce. Ashe babu dadi? Da ta gama cin abincin ta nufi kofar da ta gane kitchen za ta kai ta, murmushi ta yi tana bin madafin da kallo. He still cooks. Ta fadi in a whisper (cikin rada).A shara ta zuba ledoji da kasusuwan kazar da ta ci ta wanke hannunta a sink da sabulun wanke hannu.Kawai sai ta hau gyara kitchen din. Kitchen ne na zamani, amma ya hadu da girkin namiji. Komaiout of order sai dai babu kofi ko kwanon da bai wanke ya killace ba ya rufa farin tawul akansu. Ta bude firji da freezer yana da kayan abinci daidai cikinsa. Da gani ba kullum yake yi ba, sai a (leisure time) dinsa. Falon ta dawo ta nemi kujera ta zauna ta zuba tagumi. Wannan karon ya gama rubutun ya koma typing dinsa cikin laptop dinsa. Kamar bai san da zaman mutum a falon ba, zuciya ta soma zo wa Hafsat wuya duk kuwa da cewa ba halinta ne fushi ba. Ta ga in ta ce kuka za ta yi ta yi kan wulakancin Abdulazeez ta fadi ba nauyi. Gara ta dinga damunsa yadda zai yi gaggawar maida ita gaban masu kaunarta. Mikewa ta yi ta isa ga T.V ta hau kokarin jona ta, ko banza ta samu abokin hira kada bakinta ya soma ciwo. Cikin saa kuwa ta hada ta, ta dauki remote tana neman tashoshi, ta dire a bollywood wato tashar fina-finan India ta saka murya sosai suna ta raye-rayensu. Duk yadda ya kai da son ci gaba da abin da yake yi, hakan ya faskara. Hayaniyar ta dame shi, shi tunda ya zo bai taba jona T.V ba. Tsaki ya yi ya daga murya yadda za ta ji ya ce. Please ki kashe. Banza ta yi amsa kamar ba ta ji ba. Tasowa ya yi a fusace ya je ya kashe ya koma ya ci gaba. Mikewa ta yi ta je ta sake kunnawa ta dawo ta zauna. Ba ta gama zaman ba ta ganshi a gabanta, cikin bacin rai ya ce. “Are you here to disturb me (kin zo ne don ki dame ni)? Hafsat ba ta taso ta ga ana tsiwa a gidansu ba, sannan ba ta cikin halayenta, amma yau ta yadda komai hali yake yi, kuma in ka ce ba za ka iya abu ba, to tabbata condition din bai same ka ba. Domin samun kanta ta yi da mayarwa Abdulazeez martani cikin launin nata bacin ran. Kana iya mayar da ni inda na fito, tunda zama na takura ne a gare ka!. Da sauri ya amsa. Da ni na kawo ki? And I think you have your return tickets in your handbag?(Na yi zaton kina da tikitin komawarki a jakar ki?)” Duk dauriyarta sai da hawaye suka silalo ta mike ta nufi daki. Kayanta ta jawo ta soma dannawa da ma ba ta jera su a wardrove ba suna cikin trolley din. Wadanda ta fitar da ta yi wanka ta ke dannawa, ta zuge ta saka hijabin sallarta. Keeeeeeeyyyy! Haka ta janyo jakarta ta tadda shi a falon yana ci gaba da aikinsa. Gabansa ta isa ta tsaya fuskarta babu ko digon hawaye ta goge su tsaf a daki. Na fito Yaya Azeez, kai ni airport. Da farko ko dagowa bai yi ba. Shi kansa ya san yanzu kam ba daidai yake typing dinsa ba. Yana yi ne kawai kada tasan ta birkita nutsuwarsa. Dagowa ya yi ya dube ta cikin ido da shanyayyun idanunsa. Ki ka taho tun daga Nigeria ke kadai sai zuwa Airport ne zai gagare ki???” Dauke idanunta ta yi daga kallon cikin idonsa sakamakon wani maganadisu da ke fita daga tsakiyar idonsa, yana shiga natamiraculously. Ba abin da za ta iya karantawa cikinsu a wannan lokacin ban da rashin damuwa da lamarinta. Gefen hijabinta ta kai ta rufe fuskarta ta soma kuka. Tashi ya yi tsam da takardunsa da laptop dinsa ya shige dakin kwanansa. Sai da ta yi mai isarta sannan ta bai wa kanta hakuri ta koma dakin da kayanta. Ba ta da kudi a hannu, amma tana da credit cards’ har biyu. To amma ta koma gida ta ce wa Mammah me bayan ta gama gargadinta gidanta ba space na yaji? Babu kawo kara, su je su zauna su yi HAKURI da juna, to ko wannan shi ne hakurin da ta ke ikirari? Haka ta kwana bacin rai da sake-sake. Amma da yake akwai gajiya sosai a tare da ita ba ta san yaushe wani wahalallen bacci ya yi awon gaba da ita ba, har sai da ta makara sallar asubahi. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Washegari ba ta tashi ta tadda shi a gidan ba, ya wuce makaranta tun bakwai na safe. A gefen filonta ta ji motsin takarda. Zarota ta yi ta duba, “You can use thekitchen. Jefar da takardar ta yi a fusace ta mike ta yi toilet. Ba ta shiga kitchen din ba sai wajen sha daya na safe. Bakin shayi kawai ta dafa don ba ta jin za ta iya sanya wani abu a cikinta saboda haushin mai apartment din nan. Da rana ma kwai ta dafa guda biyu da indomie noodle guda daya ta ci jin hanjin cikinta na rawa da karkarwa. Ta yi niyyar dafa masa abinci ta tuna Abdulazeez fa in yana wannan fushin nasa maras dalili ba ya cin abincinta, wahalar banza za ta yi ya zo a kan idonta ya tsallake nata ya nemi abin da zai ci. Ba shi ya dawo gidan ba sai da yamma niki-niki da ledoji. A kitchen ya zube su ya wuce ta a falo tana kallo ya shige dakinsa. Kwanan Hafsat uku kenan a America amma ba abin da ta gani sai bacin rai da damuwa. Abdulazeez ya zube mata komai na ci da na amfani, amma ban da kulawarsa wadda ita ta fi bukata fiye da komai. Duk ta wani rame sabida damuwa da rashin cin abincin kirki. Shi da kansa ya soma damuwa da ramar da ta ke yi din, wanda ya san shi ne sila. Ya soma saukowa ko ba komai ya san ya rama, ta dandani irin abin da ya ji a lokacin da ta yanke communication a tsakaninsu a lokacin da ba ya bukatar komai sai kulawarta. A sanda ya soma saukowa a sannan ne ya lura ita ta hau ingarman dokin fushi. Sai ya janye saukowar suka ci gaba da zama a haka. Sai dai wannan karon in ta yi girki yana ci, ko ba komai ya yi kewar abincinta yadda ba zai iya bayyanawa ba. A haka suka share sati daya, a karshen satin tafiya ta kama shi kan wani assignment dinsa zuwa Texas (The Supreme Court of Texas), ga shi ba ya so ya shiga sabgarta ganin yadda ta ke a kan tsininta. Abincin ma yau ba ta dafa da shi ba, daidai cikinta ta dafa ta shige daki. Ba zai kuma iya tafiya ba tare da ya sanar da ita ba, haka ya wuni da wannan damuwar. Tunda ta zo kuma bai hada mata layin waya ba, amma shi yana magana da su Mammah a Saudiyyah. Ya gaya musu ta zo lafiya bai san me ya sa ba ta kira waya ba tunda ta zo, amma lafiyarta lau. To su ma they are busy da ibadah ba wanda ya damu da rashin kiran nata tunda shi suna jinsa. A daren ranar bayan ya hada yan kayan da zai yi amfani da su na kwana biyu, wato asabar da lahadi sai ya fito ya nufi dakin nata. Sanda ya murda kofar ya shiga tana kwance a gadonta tana lazumi. Sosai ya tsaya yana kallonta, abu biyu ne ya dauki hankalinsa, ramar da ta yi da hawayen da ta ke zubarwa. Jikinsa ya ji ya yi wani irin sanyi, ya shigo dakin gabadayansa ba tare da ya zo da niyyar hakan ba. Lokaci na farko da ya soma zargin kansa da rashin kyautawa kan abin da yake yi tun zuwanta.An rabo ta da kowa nata an turo ta wajenshi, amma tukwicin da zai yi wa iyayensa kenan?Wadanda ba su bukaci ko kwandalarsa cikin tafiyarta ba sai don su faranta masa. Amma ita har yau ba ta yi hankalin ta yi wa mutum laifi ta san ta yi ba, har ta nemi sulhu kan laifinta? Sai ma nasa laifin ta ke gani, wannan shi ne a doke ka a hana ka kuka. Haka ya daure duk wani bacin ransa da laifin da ta ke ganin nasa ne ya ya zauna a gefen gadon daura da kafafunta. Rana ta farko da ya shigo dakin har ya zauna tun zuwanta. Dauke idonta ta yi daga kansa ta juya bakidaya daya barin ta ci gaba da sharar hawayenta. Ya ji haushin abin da ta yin, amma ya hadiye ya ce. Ki juyo mu yi magana, tafiya zan yi ta kwana biyu Imgoing for some assingments to Texas. Ai ba ta san lokacin da ta juyo ba ta mike zaune. Ni kuma in zauna da wa??” Cikin tsakiyar idanunta ya dube ta kai tsaye. Da da wa ki ke zaune a gidan nan? Ban yi zaton kin san da mutum a cikin gidan ba? Mikewa ta yi ta diro daga gadon ta nufi wardrove ta soma kwaso kayanta, cikin rishin kuka ta ce. Wallahi ba zan zauna ba, ko dai kafata kafarka, ko ka sa ni a jirgi in koma gida. Yanzu ne na yarda da duk abin da Mammah ta ke fada. How sure am I yanzun kana sona? Zuciyata ta zarme na ki yarda da ita, bayan na san duk duniya ba wanda ya kai ta sona! Na yarda da dadin bakinka, da kalaman ka na yaudara, na yarda duk abin da ka ke fada da zuciya daya. Da na san haka kake da ban zo ba.Kaicona! Da na yarda aka maida auren nan!! ..…Auren da tun fil azal nasan bani da gurbi a cikinsa..!!!”. Ta sulale a kan gwiwoyinta rungume da rigarta a hannu, ta sa kuka mai cin rai. Ba ta san yaushe ya taso daga gefen gadon da yake zaune ba. Ta dai ganshi yana ciro wasu daga cikin kayanta wadanda ta ke watsawa a jaka. Fita ya yi da su bai ce mata komai ba. Wannan ya fi komai kara bakanta mata rai; shirun da ya yi mata. Zama ta yi a wurin ta saki kukan gabadaya. A can dakinsa shi kuma da ya hada kayanta da ya debo da nasa ya rufe jakar ci gaba ya yi da sabgoginsa, amma duk sai ya ji ya kasa sukuni, maganganunta sun taba shi, ya kuma yardar wa kansa hukuncin nasa ya yi tsauri fiye da laifin da yake ikirarin ta yi masa. Ga wata irin soyayya da ke cinsa a zuci. Yau Hafsat din ce matsayin matarsa ta hakika a dakin aurensa babu zancen yarjejeniya, amma ya tsaya yana wahalar da su dukkansu a banza. Ita ta kasa ganewa lallashi yake so. So yake ta lallashe shi, ta yi admittingda kanta ta yi masa laifi, amma ta ki yin hakan. She only insist on ba ya sonta. Murmushin takaici ya yi, ya tabbata in zai iya buda mata son ta gani ba ta da fadin zuciyar da za ta dauki nauyin rabin sa. Duk yadda ya so ya yi bacci a wannan daren ya kasa. Hafsat ce a cikin apartment dinsa, amma wai ya raba daki ba ma makwanci da ita ba. Tana can tana kukan bakin cikinsa, yana nan soyayyarta na neman hallaka shi. Abin da ya dade yana jiran samun yancinsa shi ne a hannunsa amma ya jefar. Ya tuna yadda yake hana idonsa barci yana rokon Allah ya dawo da ita cikin rayuwarsa ya gyara kuskuren da ya yi, Ubangiji maji rokon bayinSa Ya amsa masa a lokacin da bai zata ba. Anya wannan gabar da ya kulla da ita don kawai ta kashe masa waya tana so ta yi jarrabawa ba butulci ya yi wa Ubangiji ba? Wani irin tausayi da kauna suka taru suka dabaibaye shi. Soyayyar da ke dankare a zuciyarsa ta yi ta kawata su. Tsohuwar ajiya ta soma bankadowa tana fiddo kanta. Tsayawa ya yi yana karbar isowarsu daya bayan daya cikin zuciya da ruhinsa. Yayin da gangar jikinsa ke musu masauki a muhallin da ya dace da kowannensu. Kafin ya mike ya shiga toilet dinsa da zummar yin wankan da ya zame masa jiki kafin ya kwanta, ya sanya Pajamas samfurin‘FENDI ya soma cumbing kanshi, gashin ya yi tudu kadan don ya kwana biyu bai yi saisaye ba. A yau bayan CreedAventus da ya lura Hafsat na matukar so, ya samu kansa da fesa wasu turarukan da bai taba fesawa ba. Ya kalubalanci zuciyarsa dalilin yin hakan?Dalilin fesa turaren da bai taba amfani da shi ba?Wanda ya tabbatar ya fi Creed aminta zuciya da sanyayata.Sai zuciyar ta ce. Because you want to please her. Kuma dai ai yau kake Abdulazeez angon Hafsah in an bi salsala; wadancan watannin da kwanakin har sama da shekara sun shude a banza ne. Ita kuwa Addar bayan ta gama kukanta ta gaji sai ta mike kanta na sarawa saboda kukan da ta yi. Wanka ta yi ta dauro alwala. Abayar sallarta ta sanya da hijabi ta feshe su da turaren ibadarta wanda ta tanada kawai don sallah. Nafilfili ta ke yi tana kai karar Abdulazeez a wurin Allah. Ba muguwar addua ta ke masa ba, ita kadai ta san me ta ke roka, wani sirrin na zuciya ne. Ashe da gaske wasu tun kan su tashi daga sujjadarsu Allah yake amsa musu bukata??? Hafsat ba ta san hakan ba sai yau, domin kuwa cikin sujjadarta ta ji budewar kofarshi da shigowarshi. Hasken da ta bari ya fara ragewa ya sanya dim-light ba ta kara jin motsinshi ba. Ta dauka ma fita ya yi, ashe cikin duvet dinta ya shige bai kara motsin da za ta san yana dakin ba. Har wajen biyun dare agogonsu na can Hafsat na nafilfilunta. Abdulazeez bai katse ta ba, yana fama da zuciyarsa. Amma da ya hangota ta cikin kankanin hasken fitilar ta daga hannuwa biyu tana addua, tashi ya yi da sauri ya sauko daga gadon ya sunkuce ta suka koma tare. Kinsan Allahyarinyar nan ki bar ni haka! In ba kuma rokon Allah ki ke ya zauta ni ba. Inna zauce kin fi kowa asara.In kuma wuta ki ke roka min to ki sani ni ne mai kai ki wuta ko aljannah, ba ki isa ki kai ni ba!. Hijabin ya zare cikin nutsuwa ya yi gefe da shi, amma ya rasa yadda zai yi ya zare abayar bai san ta ina ta bi ta zarga ta ba. Sumbatarta ya soma yi ta hanyar da yake ganin shi ne kadai samun rangwamensa watointenselykamar wannan ne karo na farko da ya taba samun damar hakan.Hafsat ta zama mutewuta da gudun jini suka dauke mata, saboda kusan a cikin shock ta ke da wannan sudden reactiondin nasa ba ta gama tantance a halin da dukkaninsu suke ciki ba, ganin alamarin ta ke kamar gizo irin na mafarkanta. Abdulazeez ya zame mata hawainiya mai rikidewa duk kalar da yake so a gareta, a kuma lokacin da ya ga dama. Haka za ta bari ya yi ta tamaula da emotion dinta duk yadda yake so? Wata zuciyar ta ce Kada ki zama mai butulci ga Ubangijinki Hafsah! Wanda ya amsa duainki tun kafin ki dago daga sujjadah, Ya kawo miki Abdulazeez din har makwancinki a tafin hannunki. A lokacin da ki ka riga ki ka fidda rai. Yau dai for the first time, let your hearts have the freedom it wants. Lokacin ya zo daidai da sanda Abdulazeez ya samu nasarar amshe abayar bakidaya daga jikinta. Hafsat ta runtse idanunta lokacin da ta fahimci yau babu sauran hijabi tsakaninta da Abdulazeez, ita ce ranar da yake gaya mata cewa “it will be a day inhistory.Ranar da za ta zama shi ya zama ita, ranar da zata zamanto babu sauran kunya ko shamaki a tsakaninsu. Hawayen da ta ji suna fita a idonta ita ta san na farin ciki ne, kuma na tsoro da fargaba duk a lokaci daya. Daga ita har shi sababbi ne a cikin alamarin wanda hakan ya janyo wa dukkaninsu rawar jiki na ban mamaki da neman taimakon dan uwansa. Lokacin da mai faruwar ta faru Hafsat ta san ba ita kadai ba, shi ma Abdulazeez din ya sha wahala. Duk da sanyin garin amma gumi suke. Shi kansa ya yi mamakin dauriyar da ta yi domin ba ta yi kukan nan nata wanda gari banza yinsa ta ke kamar ba gobe ba. Bai juya mata baya ba kamar yadda maza da yawa ke yi a irin wannan lokacin, shi a lokacin ne ma ya sanya ta a jikinsa sosai, physique-chestdinsa ya zame mata mahuta, wurin maida numfashi da sauke ajiyar zuciya. Cikin daruruwan kalaman da ya gaya mata a wannan ranar ban da albarka da ya sanya mata ba ta rike ko daya ba. Saboda ta yi amanna da cewa, shi kansa ba’a hayyacinsa yake fadarsu ba, to don me za ta kama su? Ai gara ta bari a gaya mata wadanda za ta iya yarda da su a lokacin da ya dace. Duk wani taimako da mace ke bukata a wannan ranar Abdulazeez ya yi wa matarsaHafsat, wankan ma shi ya yi mata tana kunkunin ta data saba tana ba ta so amma bai saurare ta ba. Shi ya gyara gadon da komai na dakin ya ba ta kayan da ya ga dama ta saka. T.Shirt dinsa ce da wandonsathree quater wai haka yake son ganinta, in ka ganta cikin kayan sai ka yi dariya duk da dai shi ma ba kauri ne da shi har can ba, amma ya fi ta girma da tsayi sosai. Ya ciccibota ya aza a kan ruwan cikinsa ya dora kanta a kan kirjinsa ya ja quilt ya rufe su iya kafada. Sai rufe idanunta take wani abu da ake kira (ta baya ta rago) kunyar bata zo wa Hafsat ba sai wannan lokacin.A lokacin da Abdulazeez ya karbe komai da ya saura a tsakaninsu, ta dawo cikakkiyar Mrs Barrister Abdulazeez Hamzah Atiku. Wani matsayi, wani da-kace, wani buri, wani fata, wani kintace, wani mafarki data dade tana yi.Fuskarta ya tallabo da tafukansa ya dube ta ya ce complains time wato (lokacin korafi). Samun kanta ta yi da jin kunyar Yayan nasu fiye da kowacce rana a tsayin rayuwarsu. Yo wane complains gare ni bayan ka karyata komai? Zancen zuci Hafsat ke yi ba ta san cewa a fili ta ke yi ba!. Murmushi ya yi ya kankame ta sosai yana dariya mara sauti. Hafsat ni ban karyata ki ba!. Rufe idonta ta yi da hannayenta tana shirin guduwa daga saman ruwan cikin sa ya damko ta. Ya juya kwanciyarya koma shine a sama, dogon karan hancinsa na gugar nata ya soma magana cikin sanyin murya. Cikin korafinki ban karyata ko daya ba, amma ina so ki maimaita min su yanzu, zan iya ba ki amsa. A dazun na rasa amsar ba ki, saboda ni kaina ban yarda da kaina ba da hukuncin da na dauka a kanmu tun zuwanki. Amma yanzu Im ready to answer you daya bayan daya. Hannunta ya ji cikin sumar kanshi, cikin jin kunyar kalaman da ta fada masa dazun ta ce. Ni fa abin da ya wuce bana iya dawo da shi Yaya Azeez, bacin rai ne. Saboda ke ma ba ki yarda da kanki kan abin da ki ka fada din bane Hafsah”. “Na roke ka don Allah a bar maganar nan sosai take cakude yatsunta cikin sumar kansa duk dai don ta samu ta mantar dashi munanan kalaman data san ta yi amfani dasu gareshi cikin bacin rai. Ta ya ya zan bar wadannan zafafan korafin naki ban ba ki amsar da ta dace da ke ba?Capital NO Addah Hafsat. Kin ce bana sonki, Mammanki ta gaya miki bana sonki. Hafsat Mammanki ba ta yi min adalci ko kankani, me ya sa ba ki gaya mata ke ma kin fi son bokonki a kaina ba? Saboda wannan banzan bokon ki ka kashe min waya mai nuna ba ki da lokacina sai kin gama da abin da ya fi miki ni muhimmanci, sannan za ki saurare ni. Ni da yake ke ce a gabana nawa karatun nake ajewa gefe in samawa zuciyata salama in ji muryarki;it doesnt change the fact that you are not with me but ithelp me a little to feel youbesideme.(Hakan baya canza gaskiyar cewa bama tare, amma yana taimakamin in ji ki a kusa da ni ko yaya ne). Hafsat ki ka yanke min wannan jin dadin ki ka sanya ni cikin ukuba. Ita Maman naki da nake roko ta hada mu ta ce ba dai da wayarta ba tunda ta ba ki wayarki. Hafsat wannan bai ishe ta ta gane ni na damu da ke ba, ke ba ki da lokacina sai na abin da ba zai amfane ki ranar gobe kiyama ba? Along the way kuma ta ke fada miki bana sonki? Ko kuwa baya ba ta taba canzawa ku a gurinku? Hafsat bari in gaya miki wani abu wanda na lura har yau baki sani ba. Ban taba kin ki a zuciyata ba dai-dai da rana daya, saboda ina son Mamanki (Habibah), ta so ni, ta kula da ni kamar dan cikinta. A garin hidimta min ta fadi har hakan yayi sanadin nakudar haihuwarki lokaci bai yi ba. Kullum na tuna wannan ranar zuciyata tana raurawa. Mammah ta yi min tayin aurenki ne at a very wrong time bayan na yi wa Muazatu alkawarin aure. Wani irin so na yi wa Muazatu mara tushe don ni kaina in za a kashe ni kan in fadi dalilin son da nake mata ba zan iya fada ba. Daga baya bayan na zauna da ke na kuma rabu da ke na gane ba son Muazatu nake ba infatuation ne. Ke din dai dana ki kwantar da hankalina a kan ki ke zuciyata ke yi wa so na hakika. Kin ce zuciyarki ta zarme, ta zarme da yawa akaina, ta yarda da duk abinda na fada bayan ba gaskiya na fada ba. To Hafsat letthis heart know thatAbdulazeez bashi da kalaman sake maimaitawa don ta yarda dashi but he is morethan zarmewa a kanta. And I thank her (the heart) for this abundance love for me. And I promised eternal love for her alone. Zan kasance mai yi mata uzurin da ban iya yi mata ba, zan so ta fiye da yadda ta so ni, zan kula da ita fiye da yadda zan kula da kaina. Zan ci gaba da ba ta farin ciki fiye da wanda ta bani a daren yau Jumaah ashirin gawatan Fabrairu a birnin NewHaven din Connecticut. A yau ina rokonki Hafsat ki yafe min sabon Ubangijin da na ja ki muka aikata a matsayina na mai hankali da sani fiye da ke (yarjejeniyar aure) wanda haramun ne kuma ta wata fuskar yaudara ne a shariance . Bayan Mammah ta hana ki komawa aurena na na sha wahala kafin Baffa Atiku ya yarda su maida aurenmu. Sai da ya zaunar da ni ya ba ni fatawa ta ilmi inda na fahimci ba karamin shirme muka aikata ba. Godiya ta daya ga Allah da na yi gaggawar maida ke dakinki kafin ki gama iddah, yau da ban san makomar rayuwata ba in Mammah ta aura miki wani. Wanda na tabbata da na yi wannan kuskuren hukuncina gareta kenan. Suhaanah Im sure da hakan ta faru zan iya haukacewa. Ya mannata a kirjinsa sosai tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri-da-sauri. Tsigar jikinsa na tashi, cikin sanyin murya ta ce. Ni fa tun a lokacin duk da ba wanda ya gaya mini zuciyata ta gaya min ba abin kirki muka kulla ba, kuma ya zama yaudara ga Mammah. .Daina tuna min Suhaanah kin ji? Ihate myself ranar da na dawo na tadda Mammah a gadon asibiti. Ya Allah kada ka maimaita min wannan ranar, ke ma ki yi ta istighfari kamar yadda har gobe ban daina ba. ****** Washegari sun gama shirinsu tsaf na tafiya Texas. A jaka guda suka hada kayansu kala bibbiyu. Tare suka yi breakfast wanda Abdulazeez ne ya girka, ya kuma ba ta magani (pain reliever) da Panadol,ko kitchen din ya hana ta shiga. Tafiyar ma ba don ta zame masa dole ba ya ce da ya fasa, sabida duk da tana dauriya don kada ya barta ita kadai ya gane bata jin dadin jikinta, duk da ta gasa jikinta yadda ya kamata da taimakon sa. A cewar Abdulazeezyana son honeymoon-time dinsu ya kasance cikin New Haven Towers kawai. Ita kuma ta ce tana so ta je Texas din, ko ba komai za ta bude ido. Ta kuma labartawa Mammah garuruwan da ta gani a kan hanya. Ko kuma don ki samo mata dan Texas ba? Mammah is eager to grab hergrandson from you shi ya sa ta kasa hakuri in dawo ta turo min ke nan. Wata uwar harara ta suburbuda masa tamkar idanun sa fado. Dariya ya yi ya fizgi jakar kayansu ya janyo hannunta yana fadin. Ni da wannan kallon da ake kashe ni da shi ma za a barni in hada assignment din nan?Anya ba a daki za a kulle ni ba sai na samar da baby din nan? Fisge hannunta ta yi, ta yi gaba cikin fushi. Ya sake riko ta a bakin kofa ya kankame ta. Neman bakinta yake tana kaucewa, amma sai da ya yi nasarar samun shi ya biyar da shi yadda yake so. Daga zaman da ya yi da ita zuwa jiya ya fahimci wannan shi ne weaknessdinta. She enjoys it ko cikin fushi take.... Amma ita kam duk yadda ta so ta fahimci nasa har yau ba ta yi nasara ba. A da ta dauka kissing dinne, a jiya kuma ta ga ba haka bane. Its beyond that.... Abdulazeez is indescribable! Ga saurin fushi, ga wahalar saukowa, in yana yi da kai ya fi kowa saukin kai, in ba ya yi da kai ya fi kuturu ban haushi. Gwani ne kuma sadauki a fannin nunawa matarsa soyayyah!!! Sun bata lokaci sosai kafin su bar gidan, duk kwalliyar da aka yi sai da aka bata ta aka sake wanka da sabon (dressing). Wanan karon sauri ta yi kafin ya gama abin da yake yi ta sauka kasan gininsu tana jiransa don kada ya kara bata musu lokaci. Ta lura shi soyayyar ta fi masa komai muhimmanci a halin yanzu, duk wani abin da zai yi ya biyo bayanta (soyayyar). He had achieved a lot in life itace kawai bai samu ba. Don haka yanzu da ya same ta bai dauketa da sauki ba. Bata taba ganin mutum serious a kan abin da ya sa gaba irinsa ba. Itama soyayyar seriousness yake bata na gasketare da bata dukkan hakkokinta. Tana wannan tunanin ta ji hannunsa cikin nata. Ta daga fararen idanunta ta dube shi, ya yi kyau cikin sabon dressing din da ya sake fiye da na dazu. Riga ce short-sleeve fara tas an yi rubutun kamfanin Nike a jikinta, trouser dinsa baki sidik shi ma ya fito ne daga Nike’. Farin cambas ya daura a kafarsa shi ma dan gidan Nike, sumar kansa ta kwanta luf sai sheki ta ke, he looks so much like his father. Ta ce a ranta, sai dai shi din cike yake da tarin kuruciya cikin thirtieth dinshi. Ba ta da maaunin da za ta iya dora kiyasin matsayinsa a zuciyarta wanda ya rubanya ya hauhawa sau sabain daga jiya zuwa yau. “Lets go Mrs. Thinking. Tukunna ma tunanin me ki ke yi na dade a gabanki ba ki sani ba? Tunanin ina ma zan iya in gaya wa Mommah abin da ka ce, ta san cewa ba ta yi maka gwaninta ba. Dariya ya yi, ya sha gabanta. Kada ki jawo abin da zan rungume matata a bainar jamaa Hafsah!A duniya akwai Uwa mai tausayi da jin qai irin tawa?She is like mother Terasa!(A humanitarian). Ta kawo min matata a lokacin da ya fi dacewa in a very silent and tranquil environment free from all worries andstresses. Salute to your Mommah! Just tell her I love you and Im making this to you practically and you are responding to the practice tooyadda ya kamata!. Ta zaro ido, sannan ta kai hannu ta rufe idanunta, ta mayar dasu ta toshe kunnuwanta biyu. Yaya Azeez zan koma gida ka tafi kai kadai. Zaka dode min kunnuwa. To ki koma mana? Nan garin mata da yawa sai wadda na zaba daga farare zuwa bakake, kuma yadda ki ka maida ni yanzu ba zan iya kwana ni kadai baHafsat. Sai yanzu na san na yi asara mai yawa, wai har shekara da rabi abinda nayi tamissing kenan! Oh me!!!. Ya fada cikin jinjina lamarin da takaicinsa a fili with exclamation.Yana so ya kallo tsakiyar idanuntadon gano reaction dinta amma ta ki hakan, tafiyarta kawai takekanta tsaye kamar ta fishi sanin hanya. Wani dan kishin-kishin abunda ya fada a sama na sukarta, kalamansa na gaba kuma suka danne kishin suka suka sanya mata jin kunya, don haka kishi da kunya ne suka taru suka lullube ta suka hanata magana taki yarda ta kalleshi. A gefen titi suke tafiya suna zantukan nan. Abinki da inda ba ruwan kowa da kowa. Ya sakeshan gabanta ya baro jakarsu a baya. Hafsat haka mukai ta asara??? Duk yadda ta so daurewa tare da boye fuskarta sai da ta yi dariya mara sauti, sannan ta juya ta janyo jakarsu da ya bari abayata yi gaba ta barshi. Da sassarfa ya cimmata ya riko hannun damanta har sai da jakar hannunta ta sabule ta kusa faduwa kasa. Sake maimaita tambayarsa yayi shi lallai sai ta bashi amsa zaa cigaba da tafiyar. Dakatawa tayi tana russunar da gazing dinta daga duban kwayan idanunsa,sannan cikin jin nauyi da sanyin muryarta tace. “Yanzu dai a kan titi muke Yaya Azeez, kaga an fara kallonmu, reserve your quations sai mun je Texas. Suka hau taxi zuwa filin jirgin kasan Amtrak. Train suka bi mai zuwa Texas (Dallas) kai tsaye daga NewHaven County, duk station din garin da aka tsaya don daukar fasinja da saukewa sai Hafsat ta tambaye shi sunan garin ya gaya mata. Sun wuce garuruwa daban daban kafin daga karshe jirgin ya tsaya a Dallas(Texas), fasinjoji suka fita, hatta handbag dinta shi ya karba ganin alamun gajiya da ji ga tarin zaman jirgin kasaa tare da ita. A cikin filin jirgin ya saya mata lemo Pepsi mai sanyi da ta ce tana so. Yana fadin wannan shin last timeda zaki sha pepsi dinnan naga kina son ta, tunda kika zo kike shanta kullumbayan cutarwa suke yi. Ba don a jigace take ba har bata son magana da ta ce dashi ba gara ni ba? Kaima ka daina shan Coca-Cola duk uwarsu daya ubansu daya. Kamar ya ji ta, ko da yake Abdulazeez reads her mind easily ta dade gane hakan, wisdom dinshi har tsoro yake bata. Sai cewa yayi nasan motsin da kikeyi da baki ai, ko ni da kika ga ina shan Coca-Cola tozero sugar ce. Sukazauna a karkashin wata rumfaya jirata ta sha, sannan suka fito inda za su samu abin hawa. Da wayarsa ya yi amfani wajen samo hotel mafi kusa da kotun da zai yi abin da ya kawo shi. Ya gaya wa mai motar inda zai kaisu suka shiga suka tafi. Karamin daki ya kama musu ciki daya (falle daya) kwana biyu, ya sa katin a kofar ta bude ya shigar da jakarsu. Ta bi shi a baya ya maida kofar ya rufe. Hafsat tsaye ta yi a jikin kofar tana kakabin yadda za ta rayu daga ita sai Abdulazeez a wannan dan karamin dakin, shi kansa gadon bai fi mutum daya ya kwanta a kanshi ba. Da ta sani ta hakura ta zauna a NewHaven kamar yadda ya ce da farko, to in za ta canza kaya ko shi zai canza ya za a yi kenan? In za su yi wanka fa? Ta kasan ido ya dube ta yana zaune gefen gadon yana warware igiyar cambas dinsa, abinki da Lawyer nan da nan ya gano abin da ta ke tunani. Murmushi ya yi ya ci gaba da cire takalminya zare socks, sai da ya gama tsaf sannan ya dago ya dube ta a kaikaice. Akwai wani dare da ya saura ne da Jemage bai gani ba???” Ban gane abin da ka ce ba, waye jemage? Ta amsa innocently. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Mikewa ya yi ya tako har inda ta ke kyawawan tafukansa na mannnewa akan marblesya tsaya a gabanta, space din da ke tsakaninsu ba shi da tazara, hannayensa biyu ya dora a kafadunta, daya a kafadar hagu daya a ta dama. Ya rage tsawonsa suka yi kai daya sannan ya dube ta cikin idanunta da shanyayyun idanunsa,fitarnumfashinsu na sarkewa dana juna. Da na sani Hausa na nema miki a jamia Hafsah. Murmushi ta yi kumatunta suka lotsa sosai. Itama Hausar karantarta ake yi?? Kwarai kuwa, yadda ake karanta Geography. Ya sa hannu ya soma warware mata lullubin dake kanta, ya saki mayafin a kasa, ya kai hannu kan hudar karan hancinta da barimar danyen gold yar kankanuwa ta dade da samun muhalli yana mai zagaye barimar da dan alinsa.Yana daga abinda yake so a kawatacciyar fuskarta maabociyar zati da kamala wannan hular hancin,sai kuma ya zarce da hannun damansa saman kanta ya shafo kwantaccen gashinta mai santsi da sheki tun daga farkonsa har karshensa.Sannan ya hada mikakken karan hancinsu wuri guda ya soma magana cikin wata irin kasalalliyar murya. Mommanki ba ta gaya miki daga ranar da ta aura min ke mun zama sirrin juna ba? Ba ta gaya miki mun zama marufar asirin juna ba? Ba ta gaya miki mun zama abu guda ba babu sauran boye-boye ko kunya a tsakaninmu? Na dauka kunyar ta kare daga jiya Hafsah?Amma na gani cikin kwayar idanunki kina kokonton zama da ni Abdulazeez a dan tsukukun daki???” Dariya ta yi ta somakokarin sunne kanta cikin jikinshi. Ba dama tayi magana cikin ranta sai Abdulazeez dinnan ya karanta? Bai bata damar hakan ba (buyan) ya dago fuskarta yana so su hada ido ta rufe idon da azama.Thelong eye lashes.... suka bi idon suka kwanta luf; wani abu da ya dade da lura da cewa yana tsananin fizgar zuciyarsa zuwa gare ta ya sumbaci idanunta ko bai niyya ba. Fuskarta ya saka cikin tafukansa ya ce. Kina min wannan lumshe idon Hafsat, za ki bari in yi assignmentdinnan kuwa? Babu kuzari a cikin muryarsa a lokacin da yake fadin hakan. Bude idanun nata ta yi da sauri. Ni fa ba lumshe ido nake ba,ido ne bana so mu hada. Saboda me toh? Hafsah in ba ki kalle ni ba wa za ki kalla? Ko ni in ban kalle ki ba wace pretty face zan kalla haka? Murmushi ta yi sosai da jin kalamansa. Don Allah ka je ka yi assignment dinka.Ina so ka ci maki da yawa kafi duk abokan aikin ka cinyewa. Dariya ta ba shi sosai, wai cinyewa kamar wani abinci.Ya janyo ta sannu a hankaliya rungume tsantsan a jikinsa, ya ce. Ashe kina sona haka da yawa Hafsat? Me ya sa ba ki gaya min ba tun muna gidanmu? Saidai ki dinga ga kallon hoto na a waya a cikin duvet? Hannuwanta ya ji ta zagaya a bayansa ta rike shi gam-gam itama. Saboda na san ba ka sona lokacin Yaya Azeez, kaga fadar ba abinda zata sauya sai ma dai ta lalata komai,kuma ko na fada babu amfani tunda sakina za ka yi ka auro Muazatu. Lumshe idanunsa ya yi, kansa a kafadunta, idanunsa a rufe yana shakar daddadan scent din gashinta, ya ce. Kin san wani abu? Aah. Ban yi wa Muazatu irin son da nake miki ba Hafsat. Ko kusa da juna basu je ba. Ni dai kawai in aure ta shine babbar damuwata, wata damuwa data tsaya ta tokare a raina. Abin da nake ji kawai shi ne sai na aure ta ne zan samu kwanciyar hankali da nutsuwa, ko hannunta ban taba shaawar in kama haka kawai ba. Hirarrakinmu babubondbabu tiesirin wanda nake ji in ina hira dake kamar zan zauce.Hirarrakinmu sun fi yawa a kan karatunta, rayuwarta da alamuranta. And I respect her Dad (ina girmama Babanta), wannan shi ne tsakanina da Muazatu Rufai which is totally opposite to your case. Hafsat tun daga ranar da ki ka sa ni a gaba kina tambayata wai ‘sex is not allowed in Nigeria na fahimci you are very very innocent, your heart is soft and freshbabu komai a cikinta sai tarin tsabta da kuruciya. Ranar da na yi rashin lafiya ki ka kula da ni na kara fahimtar zuciyarki mai kyau ce, kuma kin san hakkin abokin zamanki duk da kuruciyarki ko da bana dadada miki. I cannont recall when I started touching you and how,but your protest....???Hummm! Ya fahimtar da ni kin kulle wani abu a ranki a kan zamanmu, kin fara sanin ciwon kanki wanda a da ba ki sani ba. Kina kullace da ni akan wasa da rayuwar ki, kuma a shirye kike da ki yi fighting dina for your rightda na danne a kan wata. Tun daga lokacin Hafsat na soma tsoronki, na fara shiga taitayi na, na kuma fara sansano wata rana na zuwa da ke din nan da nake rainawa za ki juya duniyata idan ban yi da gaske ba. Ban fita daga wannan taraddadin ba na soma hada jiki da ke ba tare da zuciyata ta yi shawara da ni akan hakan ba . Hafsah ba zan iya hakan da macen da bana so ba. Inada kyama inada tsantseni.Im very sensitive and cautious ga inda zan kai hannu na balle jiki na. Your protest brought a number of sleepless nights to me!!! Ba zan iya gaya miki halin da na shiga ba saboda a lokacin na yi zargin kin fara sona kamar yadda na samu zuciyata da hakan ina karyatawa da gangan, za ki bari mu mori auren ko ya ya ne, soyayya ta sa a manta da kwangilar har sai lokacin ta ya zo. Sai kika nuna min kin san abin da ki ke yi, wanda hakan ya sa ni jin kunyarki, ya kara miki kimaa idanuna. Ya tattaro miki daraja mai yawa, na zo ina tababar yiwuwar rabuwar nan. Na shiga tsaka mai wuya, ga alkawari ga soyayyar gaskiya ta huda ni. A lokacin na yardar wa kaina na zalunce ki da wannan contract da na jefa mu a ciki, amma na rasa hanyar fita. I then concluded in fita daga sarkakiyar da na jefa kaina daga baya in dawo da ke mu gyara aurenmu ba tare da kowa ya ji ba. Lokaci ya yi min halinsa ko in ce Allah bai barni na yi yadda na ga dama da rayuwarki ba, sai da Ya hukunta ni, Ya dandana min azabar subucewarki daga hannuna. A karo na biyu ina rokonki ki yafe mini domin hakika na zalunce mu bakidayanmu.. Dumi ya ji a bayansa wanda ba ya ko tantama hawayen Hafsat ne. ba tun yau ya lura ba abu kankani ke sanya ta kuka. Abu kankani ke karya zuciyarta. To yanzu sabida Allah cikin labarin zuciyarsa da yake ba ta me ye abin kuka? Dago ta ya yi daga jikinsa ya soma dauke mata hawayen da bakinsa. Alfarma ta karshe da na ke nema ki yi min Suhaanahdont ever talk about Muazatu again, shes a bygone in our life,sheexists only in our past; our destiny to be tormented by.Lets create our peaceful present and abright futuretunda ita din ta zame mana ciwo. Yo ciwo mana? Duk wani abu da zai sa ka fita hankalinka ka kasa gane abu mai kyau da mara kyau kuma ka kasa bin iyayenka akansa ai ya zama ciwo. I dont want to recall the moment I put you in trouble with your mother (bana son tuna lokacinda na sanya ki a matsala da Mamanki ) saboda hoton Muazatu a falonki. Ranar nan na ji kunyarki mai yawa na muzanta, na kirga ta cikin tarin uzururrukan da ki ke yi mun. Imsorry Hafsah once again, ni na kasa yi miki uzuri ko daya. You received a weird welcome from me. Dariya ta yi ta zame daga jikinsa ta zauna a gefen dan tsurut din gadon don kafafunta sun gaji da tsayuwa, da alama shi Yaya Azeez tsayuwa ba ta gajiyar da shi sai kace soja. A kalla sun kwaso mintuna sittin a yadda suke. Cikin shagwabar da ba ta san ta yi ba ta ce. Kuma sannan ka yi barringdina ba, na kasa kiranka.. na kusa mutuwa sabida damuwa da rashin jin muryarka!”. Kusa da ita ya zo ya zauna kafada-da-kafada, ya juyo yana kallonta da kyawawan idanunsa.Fuskar sa kawai ta bayyana dadin da kalaman ta suka yi masa baka da zuci. She loves him to such an extent amma tahadiye. Ta iya controlling kanta a kullum. Hannayenta ya kama ya rike gam! Cikin nasa. Saboda ki dandana abin da ake dandanawa in mutum na son magana da matarsa ta hana shi. A duniya ina da rival irin karatunki Hafsah? Im very-veryjealousof it. Ya fada yana kaurara very-very din wanda ya fito tun daga karkashin zuciyarsa. Hafsat me za ta yi in ba dariya ba? Ban da an an kashe deal din Muazatu kuma ta yi masa alkawarin ba za ta kara zancenta ba, da ta ce wani abu akai. Kafafunsa ya mayar kan tafukan kafarta ya sarkesu cikin na juna ya kumatake susosai da yatsunsa, ya fiddo fararen idanunsa a kanta cikin damuwa. “Tell me please. Ni da bokon nan naki wa ki ka fi so? Na san da Allah ya ba ku damar aure fiye da daya da mu biyu za ki aura ni da shiIm sure. Ya karashe kalaman da karyayyen sauti. Ta sunkuyar da kai ya dago fuskar ta. “You are to look directly into my eyes and answer me Hafsah(cikin idanuna za ki kalla ki amsa mini). A yadda Hafsat ke jin zuciyarta tun daga lokacin da ta fara hankali a gidan Abdulazeez, ta fara bambance me zuciyarta ke ji a kansa, ta fara sanin darajar aure da martabarsa; to tun a lokacin ta riga ta mika wuya ga cewa; za ta iya hakura da komai in dai za ta tsira da shi!!! Idan ta ce komai tana nufin KOMAI!!! Ciki kuwa har da nemo mata biological parentsdinta. Ta ji cewa za ta iya rayuwa a doron kasa ko babu kowa in dai yana tare da ita. Yau da ya yi mata wannan tambayar sai ta samu kanta da kasa cewa komai. A ganinta kalaman will not be enoughto express her inner feelings wani lokacin shiru ya fi faida a inda babu gamsasshiyar amsa. Maimakon hakan, sai ta fada jikinsa da karfi ta wani irin cukwikwiye shi tamkar zata shige cikin tsokar jikinsa. Yana iya jin karfin matsar da ta yi masa da iyakacin karfinta kamar zata balla shi. Har sai da ta kai shi ga fadawa saman dan gadonsu akan bayansa sabida bai zata ba jinta kawai yayi. Ta bishi ta turmushe tana tumurmusa ta koina. Dariyar da bai shirya yi ba ce ta kufce masa. Meye haka Hafsat? Karya ni zaki yi? Nasa rukon da ya yi mata in returnya kuma jirkita ya maida ta upside-down(is beyond herwords to express the tightness). Hakannanya sanya ta yin nadamar gwada masa karfi don nuna innerexpressionsdinta. Bata da idea na yadda zata nuna din kuma tana so ya fahimta. Wani riko ne da ko jiya bai yi mata kwatankwacinsa ba. Amma can kasan zuciyarta ta sa a ranta za ta jure goman wannan a kowacce rana...... in dai hakan zai sa Abdulazeez ya rayu da ita ita kadai! Cikin kunnenta ya rada mata, a lokacin da ya dawoABDULAZEEZ dinsa maimakon mijin HAFSAH! . “Addah Hafsatuh,kin kusa balla ni fah! Yarinyar nan karfi gareki dama??In shi ki ka aura, ai ba za ki so ki balla shi ba;Imvery surelallaba abinki za ki yi ta yi ku tsufa kuna morar juna cikin lallaba tsufanku da tsohuwar soyayyar ku. Ta dubeshi cikin takaicin abinda yake fadidaga cikin duvet dinta data cukwikwiye ita kadai ta hana shi (dama ta saba) ta bata fuskatace. Bokon? Bokon zan aura Yaya Azeez?” Ya dago fuskarta cikin tafukansa yana jan tsinin karan hancin ta da yatsun sa biyu,wata halitta guda daya da tafi komai burgeshi da jan hankalinsa a fuskar matarsa Hafsat (dogon karan hancinta). Kallonta yake deeplytamkar ya hadiye ta bakidaya don SO. Cikin imitating(kwaikwayon) yanayin da ta yi maganar yace. “To ni Abdulazeez damainada wani rival dina duniya bayan shi ne? Kar fa ki manta har kwana kike raba mana ni da shi, kada wani ya shiga na wani, ke ga mai maza biyu, in ban yi kishi da Bokon ki ba Hafsah da wa zan yi a duniya???” Hannu ta kai ta dafe goshinta. Na rantse Yaya Azeez da kai mace ne da mun shiga uku sabodamita. Oh ni Hafsatu yar Habibah jikar Hashim Babbah! Da na san abinda kashe wayar nan zai jawo min kenan da banyi shi ba. Juya mata baya yayi yana so yayi dariya. Amma ya hadiye don ya san ta tsani hakan, ta sake jawo shi da karfi ta baya jikin ta yana dan rawa. Yaya Azeez babu wani duvet din? Na rufa da wannan amma kamar da zanin atamfa na rufa ban daina jin sanyin ba. Ta fada kamar zatayi kuka kuma sosai da gaske bilhaqqisanyin take ji,tsigar jikinta har tashi take yi duk da ta rufa din ta kuma handame abin rufar ita kadai ta hana shi. Juyowa yayi ya kama duvet din yana kokarin janyewa ta rike gam-gam. I cant do without It, don Allah ka bar min nikadai. Rausayar da kai yayi yana mata wani irin kallo wanda daga jiya zuwa yau ta gama sanin maanar sa tsaf!Idanunta sukayi kwalkwal amma ta riga tayi alkawarin juriya ga alamarin nan no matter what in dai zata tsira da shi!!! Ga mamakinta bayan ya raba ta da duvet din maye gurbin sa yayi a hankali in a way that is unusual to her.Hakan yasa rawar da jikin nata ke yi da tashin tsigar jikintaya ragu. Relax Addahh,ni ba na jin sanyi,balle in kwace miki abin rufar ki. Andits not what you are anticipating Baby.... Sabuwarhanyar samar da HEAT kenan wadda tafi dukkan duvets dinki. Youhave me now......no need of your quilts daga rana irin ta yau. Ya hade bakunansu wuri guda kamar yadda ya hade jikkunansu, hannunsa cikin sumar kanta yana fadin. Jaruma, kuma matsoraciya Hafsatu matar Barrister Abdulazeez Hamzah Atiku!. Murmushi ta hau yi irinna karkashin zuciya. Tana mai kara nitsewa a cikin jikinsa. Wani identity data dade tana kwadaitawa zuciyarta a farke ko a mafarki. Yau gashi ya fito kai tsaye daga bakin mamallakin sa. “The heat is unique, so its provider! Magana take a zuci cikin lumshe idanu tana kara rungumeshi tsam, batasan cewa a fili take yi ba.Shima murmushin yayi yace mata a cikin kunnuwanta. “TheMammahs patient is also unique too. I love herso much Hafsah! And the word LOVE is not enough!It can only make a comparison. Allah ya kara miki lafiya!!! ****** Wannan assignmentdai da kyar aka yi shisharp-sharp a washegari, sai dai su kansu sun san ba za su ci makin yadda Hafsat ta yi fata ba. In aka ce ya samu C to sunyi kokari. To duka an cinye lokacin a soyayya da wani irin honeymooning mai ban mamaki a dan tsukukun dakin (ta bakin Abdulazeez) dake cikin hoteldin WyndhamDallas Suitescikin birnin Texas. Tunda suka shigo hotel din nan sau biyu ya fita ya je kotun, daga safe zuwa yamma, ya harhada abinda ya kawo shi ya rubuta yayi typing acan.Abinci daga hotel din suke order a shigo musu da shi. Ranar litinin suka koma NewHaven suka ci gaba da rayuwarsu mai tsafta da ban shaawa, wadda soyayya da kauna yar usulisune jigonta.Hafsat tarairayar Abdulazeez ta ke kamar ta maida shi cikin kirjinta, tareda kinkimar duk wasu bukatun rayuwarsa da dukkan iyawa da jarumtar da bai taba zato ba. Abdulazeez kula yake da Hafsat kamar yadda yake kula da bugun zuciyarsa. Duk wani abin bukatar diya mace ya kaita ya saya mata. Ya sayawa Mammah tsaraba sosai. Akwai sanda suka shiga wani shagon kayan sawa ya ga tana diban T.Shirts da Trousers masu kyau na maza tana faman gwadawa da jikinsa tana jefawa a kwando, ya ce. Ban gaya miki bana bukata ba ne? Tsaraba kawai nace kiyi ba ruwan ki da ni. Da na zo na sayi kaya masu yawa wasu ko taba su ban yi ba har yau. Ba tare da ta kalle shi ba ta ce. Ba fa kai nake sayawa ba Malam . Haleem nake daukarwa!. Dariya ya yi da ya tuno wani zuwa da ya yi Jeddah Haleem din ya faki idon Mammah da Baba Azumi ya danne ta yana kirbarta tana ta zabga ihu, shi ya daga shi daga ruwan cikinta. Ta sha wahala iri-iri a hannun Haleem, amma duk gidan har gobe ba wanda ta ke so kamar shi. “Shine kuma kike gwadawa da ni? Ai na fishi tsaho? Kuma shi mai kiba ne. Ki hada da Usman ko banza ya sha jigilar kai ki makaranta ya dauko ki, a lokacin da aka sanya ni a makarantar Mammah,kuma dai yana son ki kullum mukayi waya sai ya tambayi lafiyarki. Dariya ta yi jin abinda yace wai (makarantar Mammah) ta ce, He is the first in the list, na saya mashi a Texas, shi da Hamma Imamu. Ya ce, Abba fa? Kai ma ka san ba ya saka kananan kaya. Ki saya masa wani abun to, ga agoguna ga takalma? Waya ta fiddo ta kira Imamu ta tambaye shi lambar kafar Abbansu, sannan ta dauka mishi takalma kafa uku da tsadadden agogon POLO. Ya ce hatta Malam da Daada sai an yi musu tsaraba. Dariya ta yi ta ce, ita ba ta ga abin da ya dace da su a nan ba, ya bari in ta koma gida za ta saya masu. Ya ce, Wallahi ko ki ma Ismael tsaraba ko na gaya masa kin ware shi, kin maida shi saniyar ware. Ta zumburo baki, tace ba abinda zan saya da sunansa, ina kaiwa zai gayamin bakar maganar da sai tayi shekara tana damuna.Ka manta sanda yace nikazama ce, don kawai ya rako Mammah ban yi wankan safe ba, zai aura maka yar gayu. Murmushi Abdulazeez yayi yana tuno ranar shima, abubuwa da yawa sun faru a ranar very bitter and sweeteralso,ya kada ya raya ta ki, sai ya fiddo waya ya kira Ismael. Ishma, Hafsat ta yi wa kowa tsaraba ban da kai saboda laifuffukanka masu yawa ne. Ismael yayi dariya ya ce ya ba ta wayar. Da farko tace bazata karba ba sai ta ga rashin kirkinta, shi Abdulazeez Ishma ne nasa yafi shiri dashi a kan sauran duk da shine sakonsa. Karba tayi tana hura hanci, ita ga wadda zaa bawa hakuri. Ismael yayi gyaran murya sannan yace, “Addahmeye na daukar zafi da ni haka? Da zaki yiwa kowa tsaraba banda ni?Ni fa ko da na ce zan aura wa Yaya yar gayu, in kin mutu nake nufi!. “......Insha Allahu Wasila ce za ta fara mutuwa kafin ni..... Abdulazeez ya fizge wayar jin ana zancen mutuwa ga Hafsat ta fara hawaye a tsakiyar shago. Ba ta hango komai sai ranar da za ta mutu ta bar Abdulazeez kamar yadda Ishma yayi mata fata, ya manta da ita ya auri watanta. Ta karbe duk wannan soyayyar da yake gwada mata wadda daga ita sai Allah sai shi suka san yadda take. Hannunta ya kama suka bar shagon bayan ya biya su kudin kayan da suka dauka. Sannan ya kira Ismael suna cikin taxi don komawa gidaya soma sauke masa fada da bacin rai mai tsanani, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. “Daga yi maka abin arziki Ishma, wai ni babba inaso in gyara muamalar ku dana lura bata da dadi duk da na san kai ne ba ka da gaskiya? Ashe girma na bai isa yayi amfani ba Ismael?” Ya karasa cikin kwantar da sauti. Ismael dariya yake yiko a kwalarsa ya ce, Ai ba za mu taba shiryawa ba sai ranar da ta daina shagwaba da kazanta a gidan miji. A karshe gajiya ya yi ya rabu da shi, saboda ya fara sa masa ciwon kai. Haka Allah ya yi shi(very annoying). Hafsat kuma ba ta daina kuka ba har suka je gida, kayan ma duk shi ya kai mata daki. A kujerar falo ta zube tana ta sharar ido. Sunkuyawa ya yi a gabanta bayan ya fito daga dakinta ya juyo mata bayansa.... She wonder what he is going to dohaka sunkuye a gabanta duk da hawayen da ta ke yi. Haubayan nan Hafsat in goya ki, yi maza ki riga yayan Abdulazeez hawa, in mutuwar da ya ke ambato ta zo ta ganki a bayana za ta ji kunyar dauke ki ke kadaita barni. Sai ta hada mu mu biyun ta dauka. Da gudu ta haye bayan nasa ta kwanta, ta sarkafo hannayenta a wuyansa ta rungume shi tsantsan,kukan ya rikide ya koma dariya. Sosai ya bata dariya. Ba mutuwa nake gudu ba Yaya Azeez, yadda za ka manta da ni ne idan na mutun kayi aurenka. Shi ne na ce mu makale juna kawai mu zama kamar alkaki, yadda za ta ji kunyar dauke ki ta bar ni. Har a lahira ina rokon Allah ya zaba min HAFSAT-SUHAANAH matsayin matata a gidan aljanna, na yi miki alkawarin ko Hurul-eeni ba zan roka ba!. Sosai ta manne a bayan nasa tana wani irin blushing da bata jin ta taba yin irinsa a rayuwarta, wanda ke fitowa tun daga karkashin zuciyarta. Hakika kalamansa sun ratsa har tsakiyar ruhinta sun haifar da farin ciki da annashuwa marar misali. Tuni ta mance da shirmen Ishma ta rungume mijinta. Rokon Allah ta ke cikin zuciyarta ya biye bakin Abdulazeez Dakata. Ya sa in mutuwa ta zo ta dauke su tare, in ya so su bar ma Mammah yayansu ta goya. Cikin wannan nishadin suka shige bedroomdinsu ba sa ganin kowa da komai a gabansu da bayansu sai junansu SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Tun Hajiya Maryam na kidayar kwanakin dawowar Hafsat tana jiran Abdulazeez ya kira ta ya ce rana kaza za ta taso, har lissafin ya subuce mata. Hafsat dai tunda ta saka kafa kasar America Abdulazeez ya raba ta da wayarta. A cewarsa gabadaya lokacin nasa ne, sai ya yi covering shekarar da ya yi asara har da doriyar watanni biyar a banza,cikin yan satittikan da suka zamo nasa. Sati uku suka cika, aka shiga na hudu, shi ma ya kare aka shiga na biyar Abdulazeez bai da niyyar maido mata Hafsat ta koma makaranta. Ta yi fadan har ta gaji kullum da uzurin da zai bayar. Uzuri na karshe da ya ba ta shi ne, Hafsat ba ta jin dadi yana tsoron sako ta a jirgi ita kadai, a bari zuwa wata mai kamawa sai ya yi kokari ya kawo ta da kansa, ko kwana biyu ne ya yi ya koma. Dan jim! Mammah ta yi kafin ta ce, Me ya same ta? Cikin damuwa ya ce, Ni ma ban sani ba, ba dama ta dora girki dai sai ta yi amai, wai ba ta son kamshin abinci. Idan na siyo ma bata ci ba tare da ya dawo ba. Snacks kadai da Pepsi ke zama a cikinta... Bai karasa ba ya ji Mammah ta kashe wayar, sai da gabansa ya fadi, cike da tsoron ko wata mummunar cutar ce da bai sani ba ya fadi symptoms dinta? Ya juya ya dubi Hafsat din wadda ke kwance a dandaryar marbles kamar wadda tayi wata uku tana jinya, damuwarsa ta kara nunkuwa. Ya ce, Don Allah Hafsat ki yarda mu je asibiti, na yi miki alkawarin ba zan yarda su yi miki allurar ba, kuma ki tashi daga tayal din nan sanyinsa zai cutar da ke. Kukan da ta kwana tana yi ta ci gaba, da kyar in ba mutuwar da Ismael ya yi mata fata ce ta iso ba, ba tare da ta ga Danta da Abdulazeez ba. Yau kwananta biyar cikin wannan halin ta ki yarda su je asibiti, honeymoon ya guntile ya koma jinya. Ta yi-ta yi ya sa ta a jirgi ta tafi ya ki, shi a wahale ita a wahale, yana cutuwa ta fannin karatunsa sosai, ita kuma ba abin da ta ke tsoro a duniya irin a huda jikinta da allura, ta san yadda ta ke vomiting din nan abu na farko da asibiti za su yi mata shi ne, saka drip. Ya taso daga inda yake rubutu cikin system dinsa ya dago ta daga tiles din ya hada da jikinsa. Sai kawai ta fasa kuka tana fiffizgewa, ita dai ya kyaleta ta fi jin dadin can. Zama ya yi a kasa ya rungume ta kamar shi ma zai yi kukan. To ni ki kwanta a kaina duk yadda ki ke so, kiyi birgima kiyi ta kukan yadda yayi miki, amma ba zan iya kallonki kwance a kasa ba sanyin nan na huda jikin ki. Zamewa ta yi ta koma inda ya dauko ta ta yi kwanciyarta ta juya masa baya. Abdulazeez ya rafka tagumi ya soma tunanin ko dai ya yi musu yadda suke so ne ita da Mammah ya maida ita gida? Duk da cewa zamanta tare da shi as a patient nauyi ta zame masa, musamman yadda karatunshi ya dau zafi a wannan dan tsakanin, ya fiye masa rashinta cikin gidan sau dubun dubata duk da yanzu babu abin da ta ke tsinana masa sai aikin kwashe amai da gogewa da ya hau kansa. Wanka ma shi yake mata, abinci sai dai ya sayo ita kuma ya sayo mata snacksda pepsi amma wallahi hes enjoying this new life fiye da farkon zamansa a gidan shi kadai. Sai dare ya samu wayar Mammah, da sauri ya amsa a lokacin yana kan hanyar komawa gida ya fita sayo harpic na wankin toilet dinsu. Muryoyinsu su biyu ya ji ita da Daddy, da alama a handsfree suke magana, Daddy ya ce, Kana jina ko Abdulazeez? Ya ce, Ina jinka Daddy. Mammah ta ce, Kai kadai ne? Ya ce, Eh, a titi ma nake. Daddy ya ce, Ka je ka kira hospital din su zo su tafi da ita da kansu, kada ma ka tsaya a wajen ta ganka. Idan ta samu karfin jikinta ka sako ta jirgi ba abin da zai faru insha Allah. Cikin damuwa ya ce, To Daddy. A tare suka hada baki, Yauwa Abdulazeez Allah ya yi muku albarka. Ji ya yi damuwarsa ta tafi gabadaya, ya amsa da karsashi, Ameen-ameen Daddy, ameen Mammah. Hafsat na kwance ya shigo ya ce, Tashi ki shirya za mu yi baki yanzu. Bata fuska ta yi zai katse mata kwanciyar jin dadinta ta kan marbles wanda ya fi komai dadi a gare ta yanzu. Da ya ga tana bata masa lokaci ya shiga ya dauko mata doguwar abaya da mayafinta kawai ya ciccibo ta ya hau saka mata, sai cin fushi ta ke tana mita. Wadanne irin baki ne tun ina da lafiyata ba su zo ba sai yanzu da na koma gawa ta ki rami? Dariya ya yi, ya ce, Ashe kin iya Hausa kike cewa baki iya ba? Ta zumburo baki ya kama lebunan da yatsunsa biyu, Ki yi a hankali da ni kada na karasa gawar, kin ga ina tausaya miki kwana biyu, to ki lallaba ni in ci gaba da daga miki kafa har ki warware in koma angwancina. Rufe idonta ta yi da tafukanta, Yaya Azeez ka dinga jin kunyata mana, ni fa kanwarka ce. Hannayen da ta rufe idon da su ya dauke, ya dube ta cikin ido ya dage girarshi sama ya ce, Really? Neman wajen boyo ta koma a jikinsa, shi kuma ya ki yarda da hakan, wai lallai ta dube shi cikin ido ta maimaita ita kanwarshi ce ba matarshi ba. Suna wannan diramar suka ji kararrawa. Mayafin ya dauko ya nannada mata a ka ya taimaka mata ta mike, Mu je mu bude musu, ga su nan sun iso. Har takalami ya dauko mata. Cikin mamaki ta ce, To ka je ka bude musu mana? Na sani ko da maza? Hannunta ya ja zuwa bakin kofar yana fadin, Aah mata ne. Mata! Ta fada in exclamation! Tuni ya gano inda ta nufa, kawai ya yi dariya ya bude kofar. Hafsat ta yi arba da kyawawan matan turawa guda biyu, amma dai da fararen kayan maaikatan jinya a jikinsu. Wani murmushi suka kashe ta da shi, kowacce ta kama hannunta daya suka yi gaba da ita zuwa farar ambulance din da suka zo a cikinta. Ta waiwaya hagu da dama babu Abdulazeez babu alamarsa, ya gudu ta inda ba ta sani ba. Ta so yi musu gardamar kin shiga motar, ta ga za su gwada mata karfi duk da dai lallashinta suke yi, amma fa ba ta ga za su yarda da abin da ta ke so ba. Sai tsintar kanta ta yi a wani kyakkyawan asibiti. Abin da ta ke gudun shi aka fara yi mata, tana kuka tana komai. Ta sha allurai kala-kala, kulawa dai zallah kamar tana gaban Mammanta. Zuwa washegari dai kam da kanta ta nemi abinci white rice and stew, haka suka kawo mata. Lallabata suke kamar kwai in ta tambayi mijinta su ce sai ta daina kukan allura za su barshi ya zo. Kwananta uku ta samu karfin jikinta sosai, haraswar ta tsaya, sai mugun cin abinci kamar tashin hankali. Magungunan da za su kara mata karfi da lafiya suka bata suna kara jadda mata ta dinga sha kullum kuma ta dinga kula da kanta. A daren ranar suka sallame ta, ba ta ga Abdulazeez ba sai lokacin. Bai ce komai ba ya kamo hannunta yana sakar mata wani irin murmushi, suka shiga taxi ta kai su gida. Suna shigowa falo ya wani irin juyo ya sure ta bai dire ta a koina ba sai dakin barcinsu. Ba don kar ya saukar mata da hajijiya ba juyi yake so ya yi ta yi da ita. Idanu ya zuba mata kamar zai cinye ta. Kafin ya mirginota ta dawo samansa, ya ce, Kin san wani abu? Hafsat wadda duk ta bi ta tsorace da abubuwan da yake yi masu kama da na sabon kamu, ta ce, Aa, ban sani ba. Har na soma hango ki kina breastfeeding Hafsat. Oh me! Ya rungume ta. Hafsat wadda ta ji zancen a baibai ba ta fahimce shi sosai ba. Rokonsa ta ke ya gaya mata abin da yake nufi da hakan amma ya ki, hanyar faranta ran junansu yake bi kala-kala, lungu da sako kusufa-kusufa. Ranar yau ta kasance cikin jerin ranakun farin cikinsa a rayuwa, ba zai taba mantawa da ita ba. Its a SECOND day in historybayan ranar dawowar ta cikin rayuwarsa. Abin da ya ce mata kawai kenan. A karshe da suka koma cikin consciousness ya damka mata passport dinta da tikitinta. Muryarsa abin tausayi ya ce. Na amsa wa Daddy da Mammah za ki koma gobe. Hafsat na ba ki amanar kanki da kanki da ta abin da ke cikinki. Ban yarda ki jigata shi saboda bokon nan naki ba. Ni ko third class ki ka fiddo in dai BABY na zai zo cikin koshin lafiya Allah ya sanya albarka. Aclass of degree ba shi ne matsayin ilmi ko kokarin dalibi ba. It determines the condition da dalibin yake ciki a yayin karatun, duk da kokarin ma yana taka muhimmiyar rawa. Iwill come soon... and I will miss you soon. Ya kwantar da kai a kafadunta. Yayi shiru. Hafsat is speechless. Cikin tarin zantukansa masu kama da wasiyyar bankwana sentencedaya ta tsaya mata a rai, Amanar kanki da ta abin da ke cikinki. Which means ......an gaya wa Yaya Azeez she is pregnant a asibiti, dalilin farin cikinsa haka kenan. To shi cikin haka ake samunsa cikin dan lokaci kalilan? Kamar kiftawar ido? Kamar a majigi? Shekara daya da doriya ba a same shi ba sai yanzu? Zancen zucinta ya subuce ya fito fili. Dariya sosai ta baiwa Abdulazeez ya dago kansa daga kafadunta ya dube ta cikin ido da idanunsa da ke sanyaya mata zuciya. Saboda wancan lokacin its a crime in Nigeria. Yanzu kuwa baa Nigeria muke ba,it is allowed here in the U.S. Ita ma sai abin ya ba ta dariya, ta tuno lokacin da ta zauna tana zancen da shi babu ko kunya. Kai ta rafka wauta a baya, kada Allah ya maimaita. A daren ya hada mata kayanta da tsarabar da ta dade tana jida. Har Baba Azumi ta samu dogayen riguna biyu masu kyau na masu jini a jika. A daren gabadayansa cikinsu ba wanda ya runtsa..., The farewell is very very emotional (bankwanan ma taba zuciya ne). Soyayyar cikinsa is an extraordinary (babu kamarta a tarihin rayuwarsu). Alkawururruka suke daukarwa juna kamar ba za su kara haduwa ba sai a Darussalam. Duk da bakin Hafsat ya mutu, tun daga jin labarin ta kusan zama UWA, uwar ma ta jikokin Hamzah Atiku da Maryam Dakata; mutane mafiya darajar girma da kima a gare ta fiye da kowa a duniya in ka cire wadanda suka yi silar zuwanta duniya. Shin ko adadi nawa za ta so wannan Dan? Mai cin tudun soyayya uku a zuciyarta??? Na farko na kasancewarsa Dan da ya fito daga mahaifarta, na biyu na kasancewarsa daga jinin jikin ABDULAZEEZ Hamzah Atiku; wani kwayan mutum guda daya da ta ke so da dukkan ruhi da zuciyarta da soyayyah marar misali. Na uku kasancewarshi jikan Mammah. Jikan ma na farko da bata taba dauka ba sai a kansa. Sai da aka sanar cewa za a rufe jirgin sannan Abdulazeez ya raba Hafsat da jikinsa. Suna daga tsaye ya kowa ya shige ya barta. Ita ce karshen shiga ta zauna a (first class seat) dinta yadda tazo daga barin dama ta barshi tsaye ya zuba hannayenshi cikin aljihun bakin wandonNordstrom da ke jikinsa da farar T/shirt Tommy Hilfiger. Har ta bace wa ganinsa murmushi ne a kan fatar bakinsa, image din wannan yanayin da wannan ranar ya zauna mata a zuciya. Lokacin da jirgi ya karci kasa ya lula sama cikin hazo sai ta sa hannayenta biyu ta dafe cikinta. Wata amana da ta karba da hannu bibbiyu ta ke rokon Allah ya taya ta rikonta. Ta zame musu sanyin idaniya dukkaninsu, kuma nauin farin ciki ga iyayensu. ****** Hafsat ta sauka lafiya a Abuja. Kwananta biyu ta huta gajiya, sannan ta koma makaranta. Ta tarar Haleem ya koma makaranta, Ismael da Usman na shirin tafiya hidimar kasa. Baba Azumi jikin girma ya motsa ba ta da lafiya, yarta Harira ta zo daga Sokoto wadda ta zauna da ita a gidanta tana amarya tana taya Mammah kula da ita, Mammah ta yi sabuwar mai aiki Jummai daga Minna ta ke. Ita da Harira suke zaune da Mammah kafin Harira ta koma Sokoto, saboda ta baro mijinta da yaranta. Jummai na da kirki sosai da faram-faram nan da nan suka saba. Ta ji dadin ganin Harira matuqa, Mammah ta gaya mata kullum sai ta yi zancenta. Nan da nan suka taru suka debe mata kewar Abdulazeez kasancewar daga Harira har Jummai masu son barkwanci ne na a buga a jarida. Mammah kula ta ke da Hafsat da mugun cin abincinta yadda ya kamata da duk abin da mace mai juna biyu ke bukata. Salisu ke kai ta makaranta ya dauko ta, da daddare in za ta kwanta sai ta girke mata (food flask) a gefen gadonta saboda tashinta cikin dare cin abinci. Bayan wannan ba ta fuskanatar wata matsala, ko kwana biyu ba ta yi ba daga Jummai har Harira sun gane matsalar Hafsat din duk da Mammah bata fada musu ba. Sai suka kara zage damtse wajen taya ta kulawa da surukuwarta ko kofi ba sa bari ta wanke. Baba Azumi na jin jiki sosai, ciwon kafa da ciwon baya daga karshe sai kwantar da ita aka yi a asibiti gabadaya. Kullum da daddare suna midnight call dinsu don lokacin ne kadai Abdulazeez yake free, komai ta yi a rana sai ta sanar da shi, shi ma duk abin da yake ciki sai ta ji. Harira ce ta ke kwana da mahaifiyarta Azumi, Mammah da Jummai na jigilar abinci, Hafsat ma kullum ta taso makaranta can ta ke fara biyawa sai dare suke komawa gida tare da Mammah. Asibitin yana da kyau sosai wanda iyalan gidan ke zuwa ne (Diff hospital) Hafsat ma anan take ganin likita, tana samun kulawa sosai. Kullum sai Hafsat ta gaya wa Abdulazeez damuwarta a kan ciwon uwar goyonta, ko tafiya ba ta iya yikuma Mammah ba ta bari ta kwana. Hakuri yake bata, ya ce. Ke ma patient ce. Insha Allah za ta tashi, girma ne. Washegari Mammah ta tura Salisu da babbar mota har Sokoto ya debo yayan Azumi gabadaya su zo su duba ta, suka kuwa taho kwansu da kwarkwatarsu da yayansu sai da Salisu ya biya kudin motar haya bus guda daya suka taho tare, saboda motar ta gagara kwashe su. Baba Azumi sai budar ido ta yi ta ga yayanta maza da matan zagaye da gadonta kamar a mafarki. Sai da ta yi kuka don dadi, ta yi ta yi wa hajiya Maryam adduar alkhairi. A tsakiyarsu ta hango Hafsat rungume da daya daga cikin jikokinta ta saje a cikinsu sai hira suke yi. Hawaye ya kara zubo mata ta ce a kirawo mata ita, hannunta ta kama tana ta yi mata addua tana fadin Allah ya sauke ki lafiya, Allah ya ba ki dan albarka irinki. Allah ya zaunar da ku lafiya ke da mijinki. Allah ya cika miki burikanki na duniya da lahira. Tabbas ke yar halak ce wadda ta san halacci, kin so ni kamar ni na haife ki, mijinki ya kaunace ni kamar ni na haife shi. Allah ya hada kawunnanku ku rayu tare, rayuwa mai tsayi da albarka. Duk dakin amsawa suke yi da, Ameen-ameen. Ban da Hafsat da haka kawai jikinta ya yi sanyi da wannan doguwar addua da Baba Azumi ke kwarara mata a yau a bainar jamaa. Zamewa ta yi ta koma can karshen dakin ta zauna kanta yana sarawa, don ko ya ya ta yi doguwar tsayuwa sai ta ji hajijiya da ciwon kai. Hirar ta koma tsakanin Azumi da yayanta da jikokinta har Mammah ta iso kawo abincin dare. Ta kuma ce da su su yi sallama ta tafi da su gida su huta gajiyar hanya, su ci abinci. A guest house dinsu aka sauke su duka, Jummai da Harira na ta shigar musu da abinci na alfarma. Suka kwana cikin jinjina mutunci irin na Maryam Dakata. Uwarsu kam ta zauna da mutanen kirki babu irin alherin da ba ta samu a jikinsu ba, su ma kansu sun huta da su ba wanda bai ci arzikinsu ba. Da safe bayan sun karya kumallo kowa ya yi wanka aka yi shirin komawa asibiti. Sai aka bugo wa Hajiya Maryam waya, Azumi rai ya yi halinsa da asubahin ranar. Iyakar kidimewa Maryam ta rude, Innalillahi wainna ilaihi rajiun. Kawai ta ke ambata, wayar ta sulale ta fadi daga hannunta. Ta zame ta zauna a gefen gadonta tana ci gaba da salati da dayanta Allah. Ina za ta nemo karfin gwiwar kallon idanun yayan Azumi da jikokinta ta gaya musu gushewarta a doron kasa? Ga Hafsat mai yaron ciki... kawai sai ta fashe da kuka. A haka Jummai ta same ta, jinta shiru-shiru kowa ya shirya ita ake jira a tafi asibiti. Hafsat ba ta nan tana makaranta. Jummai ta samu Mammah tana gursheken kuka. Tuni jikinta ya ba ta, Mammah ta ce ta hada wayar da ta tarwatse ta miqo mata. Kuka ta ke hawaye sun hade da majina. Jummai ta yi yadda ta ce, ta kira Daddy shi a lokacin ya isa office. Ta gaya amsa, shi da yake namiji ne cewa ya yi, ga shi nan zuwa. Asibitin ya nufa ya karbo gawar don yau Harira ma ba ta kwana wajenta ba, ta ga yan uwa kuma jikin nata ya fi na kowacce rana samun sauqi. Sai ta biyo su. Da nufin a dawo tare gabadaya da safe. Suna tsaitsaye a harabar gidan duk sun sha wanka sun ci kwalliya, masu goyo sun goya yayansu sai gani suka yi get ya bude, motar asibiti zungureriya ta shigo. Kofofinta suka bude, malaman asibiti biyu suka sauko da gawar a kan gado. Babban danta Yushau shi ne mai karfin halin karasawa ya bude fuskarta da aka lullube. Ai kuwa ya fasa kuka wanda ya tabbatar wa sauran yan uwansa da zatonsu. Daidai lokacin da motar Daddy ta biyo baya, sannan ta su Ismael. Gida ya rikice ta koina hatta Ismael da Usman kuka suke yi. Yushau ya matsa kusa da Daddy ya yi kuka ya koshi, Daddy na bashi baki, ya roke shi suna so su tafi da Azumi gida Sokoto su yi janaizarta a can. Daddy bai musa ba, nan ya shirya motoci har da shi da yayansa suka dauki hanyar Sokoto, Mammah ta ce za ta biyo bayansu daga baya saboda Hafsat ba kowa a gidan. A kan hanyarsu ta dawowa gida ta ga Salisu ya dauki hanyar gida maimakon ta asibiti, ta ce, Salisu mu fara zuwa asibiti in ga Baba tukun. Bai juyo ba ya ce, An sallame ta. Kamar yadda Mama ta tsara masa. Hajiya Maryam kokari ta yi sosai ta danne alhinin da ta ke ciki, amma ba ta yarda sun yi tsayuwar minti biyar tare ba. Ta tambaye ta Salisu ya ce an sallame ta, kuma na zo gida ban gansu ba daga ita har bakin. Ba tare da ta dube ta ba, ta ce, Sun wuce gida Sokoto da ita, sun ce a can za su karasa jinyarta tunda ta samu sauki. Ni ma gobe zan bi su in kara tabbatar da samun saukin nata. Ta ce, Mu tafi tare Mommah, na san ba za ki wuce kwana daya ba. Kai ta girgiza, Kwana uku zan yi, ki zauna saboda makaranta, ko in kai ki gidan Hajiya Halima ko gidan Kawunku? Ta girgiza kai don ba ta son harkar gidan Anty Zuwaira ba tun yau ba. Zan yi zamana ni kadai, ni da ba wuni nake a gidan ba? Mammah ta ce, ba zan iya barinki ke kadai ba zan dauko Saadiyya yar hajiya Halima ta taya ki zama. Ba tare da damuwa ba ta amince. A daren direban Hajiya Halima ya kawo Saadiyya, budurwa ce ita ma a Nile ta ke karatu. Da suka gane yan makaranta daya ne, sai suka saki jiki da juna suke ta hirarsu. Mammah ta jaddadawa Saadiyyah yadda za ta kula da abincin Hafsat ita abin har kunya yake ba ta, yadda Mammah ke treating dinta ko a gaban waye kamar wata karamar yarinya. Ta ce, Kai Mommah ita kadai za ta dinga girkin? Tunda mu biyu ne mu yi tare mana. Ta ce, Ban yarda ba, kin ji na gaya miki. Saadiyyah ko ferar dankali kada ki bata. Tana dariya ta ce, Toh Mammah. Hafsat akwai shagwaba, Mammarta ta daure mata kugun yinta. Da safe Salisu ya kama hanyar airport da Mammah, bayan sun sauke su Hafsat a makaranta, suka wuce zuwa Sokoto. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* Bayan sadakar ukun Azumi mutanen gidan suka dawo gabadaya duk jikkunansu a sanyaye cike da kewar tsohuwa Azumi. Abdulazeez ya san da rasuwar, shi ma kuma ya fi kowa jin dadin hukuncin da Mammah ta dauka na rashin sanar da Hafsat. Adduar da ba ta yi mata ba ya hada yake yi musu su biyu. Har Azumi ta yi arbain da rasuwa Hafsat ba ta sani ba. Ranar sadakar arbain Daddy ya aika wa iyalinta kudi masu yawa a sayi duk abin da ya kamata a yi sadaka, da ma kuma sun tafi da komai nata da ke gidan. Rayuwa kenan, Azumi kamar ba a yi ta ba a gidan tsohon Ambassador Hamza Atiku. Allah ka sa mu cika da kyau da imani, mu gama lafiya da kowa, amin. ****** Hafsat ta ci gaba da rainon cikinta karkashin kulawar uwa/suruka ta gari Hajiya Maryam Hamza Atiku. A gefe tana ci gaba da karatunta cike da kwazo. Semester ta kare suka yi jarrabawa amma hutun na sati biyu kacal. Wannan karon ko Yola ba ta je ba balle ace America, Mammah ta ce ita da hawa jirgi sai ta haihu kuma. Ga hutun daman ba yawa, shi ma a nasa bangaren da ya gama semester din farko ya so ya zo gida, amma yana da dissertation da zai rubuta a cikin hutun, dole ya hakura tunda kullum suna tare a waya da daddare. Sai da cikin Hafsat ya cika watanni bakwai Mammah ta gaya mata gaskiyar rasuwar Babarta Azumi. Hafsat ta sha kuka kamar ranta zai fita, kamar a lokacin aka yi mutuwar, hatta Abdulazeez ta yi fushi da shi kan shi ma bai gaya mata ba, Mammah ma an yi fushi da ita na kwana biyu tana ta lallashi tana bada hakuri. Abdulazeez ya ce. We want to save lives, wasu na tafiya wasu na zuwa! Haka rayuwar ta gada, take heart sweetheart. ****** Ranar wata litinin Hafsat ta sankato katon danta a asibitin (DIFF) mai tsananin kama da ubansa. Lokacin watanni biyu suka rage wa Abdulazeez ya gama L.LM dinsa. Fadin farin cikin da wannan family suka samu kansu a ciki ba daga su ba, ba daga mutanen Yola ba, ba zai misaltu ba. Zo ki hango jika a hannun tsohon Ambassador Dr. Hamza Atiku Dakata yana ta tofe shi da addua ya hana Maryam dauka wai in ta ga ya fi shi kyau sakinshi za ta yi. Gefe ta koma tana bai wa Hafsat tea a baki tana fadin. Ka yi ka gama Daddy, ga sabon jini ba abin da zan yi da tsoho mai furfura. Duk da Hafsat cikin hajijiyar haihuwa ta ke sai da ta yi wa maganarsu dariya a fili. Daddy ya haskawa Baby camera da galleliyar wayarshi ya dana masa hoto ya tura wa ubansa. Wannan ya faru tun a asibiti kafin su dawo gida. Kwanansu hudu suka tattaro bakidaya suka yo Kano inda Mammah ta ce a can za a yi taron suna. Adda Hafsatu ta girka garwa a murhu ta soma wanke Hafsat da ganyen dalbejiya da runhu. Babyn ma ita ta ke masa wanka safe da yamma. A dakin Addar suke kwana ita da Mammah suna gado ita da jaririnta, Mammah na bisa carpet ta jefa filo bisa. Duk kukan darensa ba ya hana ta barcinta domin kuwa sun san yadda suke yi masa ya yi shiru. Azababben jego Addah ke mata har kuka ta ke yi in ana wankan nan na runhu da gashi da zaman ruwan zafi. Ana i-gobe suna gidan ya kacame da shirye-shiryen abincin gobe, duk kannen Hajiya Maryam sun zo da yayansu gidan ba masaka tsinke, Aunty Mariya ta goye babyn ta rufe shi ta fita da shi dakin da suke. Hafsat ta fito daga wankan yamma ta shirya cikin atamfa (Vlisco) ruwan goro da ratsin blue ta daura dankwalin sama-sama ta kwanta tana hutawa. Tunanin Abdulazeez ta ke yi, rabonta da shi tun ana i-gobe za ta haihu, zafin nakuda ya sa ba ta tuna da wayarta ba sai bayan ta haihu. Da aka sallamo su ta neme ta a dakinta ta rasa har suka taho Kano ba ta tambayi Mammah ba saboda kunya, ta san da ta ji tana cigiyar waya ta san wanda ta ke so ta kira shi ya sa ta biyo gida (fillanci) ta yi shiru kawai. Tana kwance tana wannan tunanin ta ji iskar da ta ke shaka tana sauyawa da wani atmosphere mai dadi da kwantar da zuciya;the familiar scent of creed aventus, idan mafarki ta ke yi tana rokon Allah kada ya tada ita daga wannan daddadan mafarki. Tattausan hannunsa ta ji cikin nata ya matsa shi sosai yatsunsa sarkafe da nata. A hankali ta ke bude idonta don tsoro ta ke ji kada ta bude idon gabadaya ta ga ba haka ba, gradually idanuwan suka washe a dakin hasken kwan fitila ya haska mata shi sosai. The last person da ba ta yi tsammanin gani nan kusa ba. Taimaka mata ya yi ta mike daga kwanciyar, abinka da danyen jiki koina ya yi taushi tubus ya yi wani irin fresh kamar da ka taba ta jini zai yi tsartuwa, ta zama kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba. Gefenta ya dawo ya zauna kafafunsa na zube a kasa ya ciccibo ta gabadayanta ya aza bisa cinyoyinsa. Kallonta yake cikin ido da wani irin yanayi cikin kwayar idonsa. Kunya ta kamata sai kokarin guduwa ta ke yi, sai ji ta yi ya fara kissing dinta gabagadi ta inda duk ya samu a matukar dokance. Aunty Mariya da ta shigo kawo yaro ta yi kyakkyawan gani ai ba shiri ta juya sai ta ci uban tuntube da robar wankan baby da ba a dauke ba saura kadan ta fadi, ta dafe babyn da ke bayanta da iyakacin karfinta. Da sauri Hafsat ta dire kasa, shi kuma ya hau yi mata. Sannu Aunty Mariya, dan waye a bayanki? Wata uwar harara ta zuba masa, ta ce, Danka ne! Ina ma na fadi mun fadi ni da shi in ga ta karshen soyayya a cikin mutane? Da ya yi wata zabura sai ga shi a gabanta, What? Jaririn kwana shiddan ki ke goyawa? Idan kafarsa ta lankwashe fa? Sauko shi, maza sauko shi. Ya soma kokarin kwanto goyon daga jikinta da kansa. Kunya ta lullube Hafsat shaf! Ya manta da wa yake magana, kanwar mahaifiyarsa ce ba yar mace da dan namiji suke ba balle ya ce abokiyar wasansa ce. Shi yake abin kunyan, amma ita ke jin kunyar a jikinta. Mariya ta kwance masa dansa tana harararsa bai ko san tana yi ba ya tafi duniyar kallon kyautar da Allah ya yi masa kamar ya yi khaki ya tofar. Aunty Mariya ta fice tana ta fadace-fadace wai Abdulazeez ya yi mata rashin kunya saboda ta goya dansa. Zo ki gani Hafsat yana tsotson bakinsa yana murmushi, may be he is saying welcome to me. Tuntsirewa ta yi da dariya. Ai tun jiya yake tambayarka. Da gaske? Shi ne ba ki min waya kin gaya min ba? Abin sai ya koma bai wa Hafsat tausayi, saboda shi tsakaninsa da Allah ya yarda. Fathers love. Ta fada a hankali har ya shiga kunnuwansa. Which is like no other. Ya ba ta amsa, sannan ya sanya hannun hagunsa ya janyo ta barin hagunsa ya hada su ita da jaririn ya rungume ya lumshe idanunsa. Allah ya yi muku albarka, Allah ya taya ni kulawa da ku. Idan bana nan Allah ya kula min da ku. Allah ya sa mahaddacin Alqurani ne, sanyin idaniya ga iyayensa da kakanninsa, abin alfahari ga alummah.... Hafsat na ta amsawa da Ameen-ameen. Cikin jin kunya. Karkata kunnensa ya yi zuwa bakinsa yana masa kalmar shahada, ya yi masa khutbah da sunan da ba ta sani ba. Ya ciro dabinon da ya yo guzuri na (ajwa) daga aljihunsa ya tauna ya sanya masa a baki, yaro ya kama lashe baki, cike da annashuwa ya ce, Hafsat zo ki gani, ya san zaki. Ta waiwaya ta sake waiwayawa bakin kofa da window. Yaya Azeez, don Allah ka bari kada a jiyo mu, za a ce kana rashin kunya, ko ba ka ji me Aunty Mariya ta fita tana fada dazun ba? Wata banzar harara ya yi mata, ya ce, To hell with the kunyar, in samu Dan kaina na farko ba zan gode wa Allah ba? Ba zan yi farin ciki ba? Saboda kada ace banida kunya? Sassauta murya ta yi cikin lallashi, Ba haka nake nufi ba, nufina ka boye kada ka bari a ji sai in kuna ku biyu kai da shi. Nan kuwa gidan iyaye ne kowa na iya ji. Babban yatsansa ya sa na tsakiya da na farko ya dalle mata baki, ta dafe bakinta don azaba nan da nan ya kumbura. Idanunta sai da suka yi ja. Ya ce, Gobe ki kara gaya mini traditional folkloresirin wadannan goya shi zan yi in fita tsakar gida kunyar ta makanta ki. Ta ja baya tana kumburi dafe dda bakinta, bata kara magana ba don lebenta ya yi mata nauyi sai ga Adda Hafsatu ta shigo kawo mata gasasshen nama sai tiriri yake ya ji albasa da yajin daddawa, ta mika mata, Cinye maza kafin a kwashe tuwon. Ta kalli jaririn da yake ta tsotson baki da hannu, ta ce. Shin yaushe rabonki da ba shi abinci? Zumburo kumburarren bakinta ta yi, Adda wallahi da zafi, da karfi yake zukowa sai na yi hawaye. Adda ta dube shi sai juya yaron yake a hannunsa yana kare masa kallo kamar bazai daina ba. Kai bata shi ta ba shi abincinsa, tun azahar rabon da ta shayar da shi, yaro mai hakuri amma sai kin kure hakurinsa, yau kwana shidda ana abu daya, haka za ki daure nan da kwana goma zai daina zafin. Kallon Adda ya yi cikin mamaki. Nonon ne sai an roke ta take bayarwa? Addah Hafsatu ta ce Wallahi haka ake fama da ita kullum. Idanuwa ya watso mata. Mugunta ki ka koma? Ta kawar da kai nan ya yi nasarar ganin yadda bakinta ya kumbura daga dalli daya. Dariya ta kama shi amma ya dake, Adda kin ga matso ki rike min yaron nan, danneta zan yi wallahi sai ya sha ya koshi. Adda kuwa ta karbi yaro ganin ya mike ya nufo ta da karfi ta ce. Adda kawo shi!. Ta yi dariya ta dora mata shi a cinya, juya masa baya ta yi ta janyo katon hijabi suka shige ciki ita da jaririn, ta bayanta ya leka, Adda za ta toshe masa hanci fa? Adda ta harare shi, ta ce, Abin da ka yi wa Mariya za ka yi min ni ma? To ta toshe din, ko ka taya ta nakudarsa? Da sauri ya tare ta tun kafin ta kai ga rufe baki. Amma ba don ni ba ai da ba a samu cikinsa ba... Salati Hafsat ta saki daga cikin hijabinta, Addah ta tattara kwanuka ta bar dakin kunya kamar ta nitse. Mariya ba karya ta ke ba, Abdulazeez haihuwa ta sa ya zama fitsararre. Tana fita ya sassauta murya. Don Allah, don Annabi ki cire hijabin nan in ganku, Hafsat don Allah. Itssomething Im always dreaming oftundawowarki. Kamar za ta yi kuka ta ce Idan ka takura ni yin haka a gidan nan ka shiga hakkina Yaya Azeez. To shi ke nan na hakura, amma in mun koma gidanmu ba za ki dinga rufewa ba ko? Shiru ta yi ta kyale shi, inda Allah ya cece ta shi ne isowar mutanen Jimeta da aka zo aka fada wadanda suka wuni a hanya, dole ya tashi ya bar dakin ba don ransa ya so ba don sun soma tuttudowa dakin. An yi suna na gani na fada a washegari a gidan marigayi Malam Abdullahi Dakata. Fulanin Jimeta sun hade da kanawan Dabo. Tafe suke da motocin gara mai ban mamaki ta aure daban, ta haihuwa daban har da manyan bajimai da ransu guda biyar a motar shanu. Aka dinga saukewa a tsakar gidan don dakin da Inna Hafsatu ta ce a zuba ya cika. Gidan suna sai ya koma gidan wani gagarumin biki don su kam kamar yanzu suke ji sun zo auren Hafsat. Baffa Atiku fada ya hau yi a kan garar nan a cewarsa an riga an wuce gurin kuma su Hafsat ba surukarsu ba ce yarsu ce. Daada ta ce sun san da hakan su ma ba su ce yarsu ba ce, abin da alada ta gadar ne suke son a yi musu alfarma su yi ko yaya ne. Shi kansa Abdulazeez ya sha bandiran shaddoji manya-manya, hatta Daddy da Mammah nasu daban, jariri akwati biyu fal da kayan sawa masu kyau da tsada, haka mai jego akwati guda na turamen zannuwa da lesuka. Kakanni ma ba a barsu a baya ba. An ce wai ko kogi ba ya kin yayyafi wannan gaara ta yi wa iyalin Dakata dadi duk da ba su taba kawo hakan a ransu ba. Na Baffa Atiku daban, na Adda Hafsatu daban. Aunty Zuwaira ta zo suna don Uncle Abdulkarim ya bude mata wuta wannan karon kuma a kan idonta aka yi komai. Tana zaune a gefen gadon da Hafsat ta ke lokacin da Ibrahima autan su Mammah ya shigo ya ce mahaifin Hafsat zai shigo ganin jariri, sosai ta muskuta ta baza ido a kofa. Prof. Bashar Mai-Jamaa Numan ya daga labulen dakin da sallama, zaratan matasan yayansa uku na biye da shi. Kwarjini da kamala da tantagaryar boko ya dallare idanunta. Ita da kanta ta dauki jaririn ta kai masa a kujerar da ya zauna daga can farkon dakin. Hafsat baki ya ki rufo, ga kunya tana ji wai ita ce ta haihu Abba ya dau jika. Imaamu na ta tsokanarta wai ta zama Maama, Abdurrahman ya ce jariri bai dauko su ba da ya fi haka kyau. Aunty Zuwaira yau har da cewa da Abdurrahman. A gabana? Ai kuwa Abdulazeez ya fi Addah kyau, fari kawai ta fi shi. Hafsat na kallonta a ranta tana mamakinta. Tunda ta taso ta san Aunty Zuwaira, ba ta taba yi mata kallon arziki ba, kalma mai dadi bata taba shiga tsakaninsu ba. Iyakaci ta gaisheta ta amsa a wulakance. Yau ita ce da yin wasa da dariya da yan uwanta don ta ga idon mahaifi. (Ya Allah ka barmu da iyayenmu ba don halinmu ba, ka kara musu tsawon rai da lafiya. Wadanda nasu suka rigaye mu Allah Ka sabunta rahma a gare su, ka jikansu ka yi musu gafara kama Rabbayaany saghirah). Dr. Bashar ya dago ido ya dubi yarsa Hafsah cike da kauna. Kina ina ki ka bari Abdulazeez ya kwashe komai shikadai bai sammana ko kadan ba? Dariya ta yi ta rufe fuska, ya karanto adduoi ya tofawa baby. A bakinsa ne ma ta ji sunan yaro Abubakar-Sadiq (Khalipha) sunan da mahaifinsa ya zaba masa kenan. Suna da kwana biyu yan Jimeta suka koma, yan Abuja suka soma nasu shirin. Adda Hafsatu ta yi tsalle ta dire ta ce nan za a bar mata masu jego ba za a lalata mata aiki ba. Mammah ta je tana mata wanka da ruwan (gass-cooker). Su tafi in ta yi arbain su zo su dauka. Mammah ba ta yi musu ba don ba ta jayayya da mahaifiyarta a kan komai, kuma ta yarda sai sun fi samun kulawa a nan fiye da wajenta. Abdulazeez dama kwana uku zai yi ya koma U.S sai nan da watanni biyu zai dawo gabadaya. A daren da su Mammah ke shirin komawa Abuja a washegari, shi ma a daren yake nasa shirin komawar. Jirgin da zai bi na asubah ne daga Kano, zai yi transit a Ethiopia. A dakin Uncle Idris na da yake kwana a soron gidan na farko. Wanda shi yanzu gidansa yana nan cikin gidajen likitoci na asibitin Malam, iyalinsa da su aka yi sunan Khalipha. Mammah da kannenta mata hudu Luba, Mariya, Furairah, Murja da Hafsat dake can saman gado tana shayar da jaririnta. Sun saka mahaifiyarsu a tsakiya ana hirar bankwana kasancewar gobe ita Mammah za ta koma Abuja ita da Jummai mai aikinta, Abdulkarim da iyalinsa sun koma tun jiya. A cikin hirar ne Mammah ta sako zancen da ya dade yana cinta a zuci, ya kuma fi karfin a yi shi a waya sai yau da Allah ya hada su ido da ido. Ta dubi mahaifiyarsu ta ce. Addah! Ta ce, Naam. Ki tambayi Mariya da Luba shin ko Saima da Halima sun tsayar da mazajen aure ne? Addah ta ce, Ai da kunnuwansu, kuma sun ji ki. Mariya ta ce. Halima sarkin ruwan ido? Tana nan tana ruwan idon nata wai mijinta ma ba a haife shi ba. Ni abin da ya sa ban damu ba ganin bana ne ta kammala secondary tana da sauran lokaci a gaba, amma Babanta ya fi so ya yi mata aure. Luba ta ce, Saima dai akwai wani yaro da ta ke so, sai dai bana jin auren nan zai yiwu? Mammah ta ce. Saboda me? Yo, Yaya Maryamu tsiransu a haihuwa shekara uku, yanzu ne yake shekararsa ta farko a jamia ita kuma tana ajin karshe a secondary, sannan iyayensa sun ce ba za su yi masa aure ba sai ya gama degree ya yi hidimar kasa ya samu aikin da zai iya rike iyali. A matsayin Saima na mace yaushe za ta tsaya jiran wannan mijin? Wata ajiyar zuciya Mammah ta yi cikin jin dadi, ta maida akalar zancen ga mahaifiyarsu. Adda ki roka min Mariya da Luba, su baiwa yayansu Usman da Haleem auren Halima da Saima, shi Ismael ya zabo wadda ta yi masa tuni, su kuma sun bani zabi da yake sun fi shi son kwanciyar hankalina. Ni kuma na hanga na ga gida ba ta koshi ba baa kai dawa ba. Yayan nan ina da su yammata har ukku, ban da Ismael ya kawo wata Wasila da sai a hada har Khalisa (yar Furera). Hajiya maryam sai gani ta yi kannen nata sun fashe da kuka. Da fari ta tsorata kafin Mariya ta soma bayani. Yaya Maryama anya akwai sauran mutane irinki a duniya? Yadda zumuncin zamani ya koma mutum ko ciki daya ku ka fito in shi ba shi da shi kai kana da shi ba ka jawo shi jikinka, neman yadda za ka nesanta kanka da shi ka ke, amma ke yayanmu za ki aura wa yayanki yan gata irin haka? Ta ci gaba da kuka. Aunty Furera ta ce, Tunda Ismael ya kawo wadda yake so kada ki kara zancen Khalisa, da Saima da Halima da Khalisa duka daya ne. Yaya Maryama mu da yayanmu naki ne ba sai kin roke mu ba. Iyakaci mu gaya wa iyayensu maza saboda hakkin haihuwa. Allah ya tabbatar mana da wannan abin alkhairin. Ya sa zumuncinki shi ne silar shigarki aljannah. Adda ma albarka ta yi ta sa mata, ta ce, Maryam har gobe ina alfahari da haihuwarki, daya tamkar da goma. Allah ya albarkaci gabanki da bayanki. Sun tsayar za a fara yin bikin Ismael da Wasila, Usman da Haleema in sun kammala hidimar kasar da suke yi. Zaa jinkirta na Haleem da Saima sai ya gama karatunsa nan da shekara biyu lokacin ita ma ta gama secondary watakila har ta fara tertiary. Hafsat na gefe tana jinsu tana shayar da danta Khalipha ita ma abin ya gamsar da ita. A ranta ta ce Fitinanne ya je ya nemo yar Abuja haka za ta zo ta fitine su kamar yadda ya fitine su. Suna haka suka ji sallamar Abdulazeez, dare ya yi sosai don sun soma jin barci ma. Aunty Murja ce ta amsa masa Mariya sai harara. Kai kuma lafiya da tsohon daren nan? Kai da ke da tafiya a gabanka da asubahi ya kamata a ce yanzu ka kwanta. Hafsat na ganin shigowarsa ta yi maza ta cire yaron ta gyara rigarta. Ya dubi Aunty Mariya cikin lallashi. Wai don kawai na ce bai isa goyo ba ki ka dauki gaba da ni haka? Ta ce, Au, wato haka ka ce ko? Wallahi sai in fallasa abinda idona ya gane min.... Da sauri ya ce, Mammah ki bata hakuri, kuma ni ba da wani nufi na ce Khalipha bai isa goyo ba, don kada ya samu gocewar kashi ne kasancewar kashinsa bai yi kwari ba. Mariya ta ce. Ita Addar har a bakwaininta mun goya ta a Saudiyyah, nata kashin ya goce? Balle wannan shekararre a ciki? Wani irin bata fuska ya yi. Ni Dana bai shekara a ciki ba. Mammah ta kalle shi, sai da ya ji kunyar da yake jin ba shi da ita yanzu. Ya hau shafa kai ya ce. Wai sallama na zo muku. Mariya ta ce. Ka zo mana ko ka zo musu? Dukkanku. Ta ce To, mun karbi tamu. Allah ya kiyaye hanya. Ke Addah ku je daga falo ku yi sallamar mu muna magana. Ya kuwa juya ya fita yana ce da Anty Mariya. Dadina da ke zuma ce, ga zaki ga harbi. Ta ce, Ka ce min kunama ma duk daidai da kai ne. Ci gaba suka yi da maganganunsu, Murja ta lura Hafsat ba ta da niyyar tashi ta dube ta ta ce Addah ba jiranki yake yi ba ne? Anty Mariya ta ce, Bar munafuka jira ta ke sai an maimaita don a ce mata saliha, ni yau a tafin hannuna suke. Da sauri Hafsat ta zura hijab ta sauko daga gadon ta doshi kofa saura kadan su yi dariya amma ban da Mammah, magana suke ita da Adda Hafsatu. A falo ta tadda shi a zaune da alama a kagare yake da zaman jiran da ta sa shi. Yana ganinta ita daya ta ce. Koma ki dauko shi. Kamar za ta yi kuka ta ce Ni wallahi ba zan iya dauko shi a gabansu ba. Mikewa ya yi ya koma dakin, sai ga shi ya dawo da yaron a hannunsa ya zauna yana ta aikin kallonsa. Can ya lura har yanzu a tsaye ta ke kamar a ce Kyat ta arta a na kare. Ya ce, Kin min kerere a ka!. Ta dosana can nesa da shi ta zaune a dofane. Wani haushi ya kama shi ya zube shanyayyun idanunshi a kanta. Is that the kind of farewell you choose for Us(wannan ce irin bankwanar da ki ka zabar mana)? Ya yi maganar ne cikin kwantaccen sauti yana danne bacin ransa. To wace iri za mu yi? Ita ma ta tambaya cikin irin yanayin da ya yi tasa tambayar. Au tambaya ta ma ki ke yi? Ta mirgina kai, Yaya Azeez we are not alone. Muna tsakiyar iyayenmu ne, please ka tuna wannan. Su suka ce ba za mu yi sallama ba saboda suna nan? Ba su ce ba,we are to make use of our senses, mu yi abinda ba zaa ga rashin kawaicinmu ba. Muryarsa a sanyaye ya ce. Madame! Yanzu ni me na yi na rashin kawaici? Ko dakin da nake ban ce ki je ba, ko soro ban ce ki je ba. Im going thausand miles away, amma ko kusa da ni ba za ki zauna ba. Ba za ki zo mu kalli Khalipha tare ba. Ba za ki gaya min abin da zan ji dadi ba in dinga tuna shi yana debe min kewarku ba. Guduna ki ke yi kamar zan sace ki, in wannan ita ce kunya, toh Allah wadaranta! Wuce ki ba ni waje, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi. Kasa tafiyar ta yi duk da kafin a yi hakan ita ce abin da ta fi so ta yi, sai hawaye da ta soma sharewa. Bai kara bi ta kanta ba ya ci gaba da kallon Dansa yana sumbatarsa. Daga karshe ya mike ya shiga da shi ciki ya kwantar ya zo ya wuce ta ya fice. Ji ta ke kamar ta bi bayansa ta bashi hakuri, amma ta san ba za ta iya ba. Hawayenta ta share da gefen hijabinta, sannan ta shiga dakin. Daga ita sai Mammah suka kwana a dakin, tana daga kasa kan carpet. Dukkansu a daya bedroom din suka kwana, Addah Hafsatu da ma (kwana sallah) ce kaman Dadanta. Washegari gida ya watse kowa ya koma inda ya fito. An nemi wayarta kafin a gano Abuja aka baro ta, Mammah ta ce za ta bayar a kawo mata ko za ta sayi sabuwa? Ta ce a barta, yanzu kam ba ta da bukatarta, in za ta yi kira za ta yi amfani da ta Adda. In za a kira ta a kira Addan ta ba ta. Ta fadi hakan ne sanin halin kayanta, in ya yi fushi da ita punishment dinta a yi barring dinta zuwa sanda aka ga dama. ****** Alhamdulillah! Yau Abubakar (Khalipha) ya cika kwana arbain a duniya. Sun yada wanka. A washegarin ranar gidajen yan uwa suka wuni. Uncle Ibrahim ya kakkaisu har AKTH gidan Dr. Idris Dakata. Mammah ta ce da Adda Hafsatu Hafsat ta shirya ta wuce Jimeta daga Kano ta yi sati daya sannan ta koma Abuja. Ibrahim autan Addah shi ya kai su filin jirgi ya yankar musu tickets ita da Zulai mai sa mata ruwan wanka wadda tsohuwar mai aikin gidan Malam Abdullahi Dakata ce. Ita Adda ta sa ta rakata Jimeta don ta taimaka mata da hidimar Khalipha. Sun samu Imamu na jiran saukarsu ya dauke su zuwa Demsawo. Dangi sun ga Khalipha sun more. Haka ake kwantar da shi a gefen buzun Mallam a kan yar katifarsa mai laushi wai ya je taya shi hira. Su ne har Numan, daga karshe a gidan Abbanta ta kwana biyu. Suka dawo babban gida Daada ta soma yi musu shirin komawa. Gyaran haihuwa ta ke mata bana wasa ba irin na fulanin usli da nono da madara da tukudi da hakukuwansu na gado. Ta kuma yo mata guzurinsu. Ranar Lahdi Abba da kansa ya kai su filin jirgi shida su Modibbo. Aka sa Zulai a jirgin Kano, Hafsat da danta a jirgin AZMAN mai zuwa Abuja. SUMAYYA ABDULQADIR TAKORI 07030137870 *Littafi na farko shine kawai free. 234 na sayarwa ne. Idan ka fidda 234 ba sai na hada ka da Allah ba zai isar min insha Allahu. Ku biya Ku karanta a nitse cikin farin ciki yafi maka kayan zunubi ranar gobe kiyama* ***** Hafsat ta iso Abuja lafiya ta tadda dalleliyar kankanuwar motarta tana jiranta. Tafiyayya tun daga General Motors din Amurka, sakon Baban Khalipha matsayin gift dinsa na haifa masa Abubakar Sadik. Usman ne mai wannan bayanin ganin ta tsaya tana shafa motar tana tambaya ko Daddy ya yi sabuwar mota ne? Maimakon ta yi murna, kunya ta yi ta ji ba ta kara zancen motar ba. Ismael ya ce, in ba ta so ta ba shi ya samu ta kai Wasila shopping. Harara ta dalla masa, Mammah na bada baya ta sassauta murya ta ce da shi. Ashe ba sonta ka ke ba, tunda ba za ka iya saya mata mota ba. Tafi ya yi har sau uku. Cikin ransa yace haihuwa ta bude idon Addar su. A fili kuma a yace Sannu matar so! Ki bari in samu aiki ki sha kallo, Wasila ta fi karfin mota wallahi, private jet zan gwangwaje ta da shi in ta haihu. Ki ma daina murna wai SO ne ya sa aka siya miki, wallahi arzikin Sadik ki ka ci, da can me ya hana a saya miki aka bar mu muna jigilar kai ki makaranta da dauko ki?. Ismaeel ya kunnata yadda yake so, ya tashi ya bar gidan yana mata dariyar keta. Hafsat sai ta koma gefe ta zama yar kallo tana kallon yadda ake soyayyar jika da kaka tsakanin Daddy da Mammah da jikansu Khalipha Abubakar As-siddiq. Ita dai ta san ta haifi Abubakar ne, amma wadannan bayin Allah sun fi ta kaunarsa. Daddy in ya dawo kafin ya ci abinci sai ya ga Khalipha cikin gadonsa a gefensa, yana wutsilniya da kyawawan kafafu da hannayensa cikin koshin lafiya. Mammah kuwa goyo, ko umh ya ce za a jefa shi a baya a daure. Ita da shi tsakaninsu shan nono, ko Jummai ba ta taba musu jika sai dai ta yi wankin kayansa. A wannan lokacin sai ta ga ba abin da ya kamace ta irin ta ba da kaimi wajen ibadah da gode wa Mahaliccinta. Ya yi mata komai a rayuwa, burinta a yanzu shi ne cikawa da imani da ganin dawowar mijinta kasar haihuwarsa lafiya. A wannan satin suka koma makaranta, bayan dogon hutu da suka sha na gama zangon farko na shekara ta uku. Sun fara (second semester) na level three Usman ya soma koya mata driving. Dole ta ajiye tsoron don tana so ta koya din ko don ta ragewa Abdulazeez hidima, ta lura da yadda yake takura kansa sosai wajen kaita makaranta da dauko ta sanda suke gidansu. Cikin sati biyu da farawarsu ta soma ganewa, shi kuma zai koma Edo inda yake hidimar kasa. Don haka ya makala mata katuwar L ta ke tuka kanta. A gida ta ke barin Khalipha kasancewar ya fara shan madara. Cikin satin nan suke sa ran dawowar Abdulazeez gida bakidaya. Daddy ya sa an fidda komai na gidansu an zuba sabo na yayi, hatta fenti an sake. Gida ya koma kamar ba a taba zama a cikinsa ba. Mammah ta yi wa Daada magana a nema wa Hafsat rikon ya a dangi, wadda ba ta haura shekara goma ba saboda ta taya ta da Khalipha, Daada ta ce gara babba wadda ba sai ta bi su makarantar ba, akwai Lantana kanwarta da ke aure a Girei mijin ya mutu shekarar baya, kuma ba ta taba haihuwa ba, za ta yi mata magana in ta amince za ta koma wajensu. Sosai Hafsat ta ji dadi, don kuwa mammah ta sangartata da rainon Khalipha ba wani iyawa ta yi ba. Ta fara tunanin yadda za su karke in sun koma gidan nasu da wannan kukan daren nasa da goyo kadai ke rufe bakinsa, ita ba ma iyawa ta yi ba, ji ta ke kamar zai fado ko kafarsa ta goce kamar yadda Abdulazeez ya ce. Saura kwana biyu Abdulazeez ya dawo Lamtana ta iso Abuja. A washegari Daddy da kansa tare da maidakinsa suka zuba su a mota suka maida su gidansu. Salisu ya biyo su da motarta. Sun dade suna tofe gidan da adduoi. Mammah ta jaddadawa Baba Lamtana yadda za ta dinga kula da Khalipha sannan suka shake musu store da kayan garar Hafsat da aka kawo daga Jimeta. Na freezer ma ba abin da Mammah ba ta ajiye musu ba. Danfulani dan amana, har yanzu shi ke kula da gidan bai je koina ba don Abdulazeez ba ya wasa da hakkinsa. Daga Mammah har Daddy sun kasa sakin Abubakar su tafi, shi kuma kamar ya gane sai kuka yake yi. Sai da Mammah ta goya shi ta yi ta jijjigawa ya yi bacci, sannan ta je ta shimfidar da shi a gadonsa suka bar gidan kamar kar su tafi. Ina ruwan abin cikin kwai ya fi kwai dadi!. Haka Lamtana ta ce bayan fitarsu. Hafsat ta ce. Ai sauri zan yi in yaye shi in kai musu abinsu. ****** A zaton Hafsat da aka ce washageri Abdulazeez zai dawo ta sa a ranta irin da yamma ko da rana ko da daddare. Tunda dai ita ba waya suke yi ba. Karfe biyar da rabi na Asubahi ta idar da sallah, tana so ta yi lazimi amma wani irin mayataccen barci ke cin idanunta, kasancewar Khalipha bai barta ta runtsa ba daren jiya saboda kuka, ba ya bude jiniyarsa sai tsakiyar dare, Lamtana ta zo ta buga mata kofa don ta taimaka mata ta ce ta je ta kwanta ba komai za ta iya da shi. Goya shi ta yi, ta yi ta yawo da shi a dakin ba dama ta zauna. Ta ba shi ruwa, ta ba shi nono duk a banza kuma ta san lafiyarshi kalau. Haka yake yi a gidan Mammah ba ta san yana yi ba baccinta ta ke shaka komai a kan Mammah yake karewa. Sai jiya ta san yaya Mammah ke shan wannan hidima. Ba ta samu ya yi bacci ba sai goshin asubahi, ita ma da ta idar da sallar a nan kan dardumar ta bingire tana bacci. Wani bacci mai tsananin nauyi da ta dade rabonta da irinsa. Har Abdulazeez ya shigo ya shiga toilet dinta ya yi alwala ya fito, ya yi sallah a gefenta ba ta sani ba. Ya dade yana addua yana gode wa Allah da ya dawo da shi cikin iyalinsa lafiya. Zuwa ya yi ya ciro Khalipha daga gadonsa ya maida shi tsakiyar gadonta. A ransa yana fadin.This is punishment. Ta jefa yaro a gado shikadai tana can tana bacci ba ta san me yake ciki ba. Kamar ya tashe ta sai ya lura tana jin dadin baccinta. A hankali ya dauke ta ya maida ita gadon ya sanya Khalipha a tsakiyarsu ya ja quilt din ya rufe su iya wuya. Shi ma da gajiyar zaman jirgi ya dawo, don haka bai dade yana kallonsu admiringlyba shi ma ya yi bacci. Yunwa ce ta tashe ta, kasancewar ba ta ci abincin dare ba ta yi baccin. Ta sha mamaki da ta ji ta a kan gadonta, ba ta fita daga wannan mamakin ba ta yi arba da danta a gefenta. Kusa da shi mahaifinsa ne Barrister Abdulazeez Hamzah Attikou, yana ta barcinsa freely irin baccin warware gajiyar zaman jirgi. Wani dakace (INAMA A CE!) Da ta taba yi a can a baya... Ita da Abdulazeez matsayin maaurata na din-din-din da BABY (in between) yana kicking kwance a tsakaninsu. Yau Allah ya cika mata wannan dakace da ba ta taba mafarkin zamansa reality ba. Ci gaba ta yi da kwanciya a yadda take a kan pillow tana kallonsu; her heartSWELLING with love and pride (zuciyarta na kumburi da soyayyah da alfahari). Ba ta jin in za su shekara a haka za ta gajiya da kallonsu. Wani naushi da Khalipha ya sa kafa ya kirba wa ubanshi ba shiri ya soma bude idonshi a hankali. A kanta ya sauke su, suka yi wa juna kuriiii da ido. Babu wanka, ko kwalliya,ko wani special artificial abu a tare da ita sai kayan barci masu tsananin taushi, amma a haka ta kawatu a zuciya da idanunsa fiye da duk matan duniya da ya taba cin karo da su a rayuwarsa. Sannu da zuwa!. Ta fada cikin nutsuwa da farin cikin da ya gaza boyuwa a cikin muryarta. He is kicking me. Ya yi complaining.Ba tareda ya amsa sannu da zuwan nata ba. Me ya sa ka rabo shi da gadonsa toh? Because I want him to do so. (Saboda ina son shi da yin hakan). Murmushi ta yi.Then why are you complaining? (Me yasa kuma kake korafi?) Because Im appreciating (Sabida ina jin dadin hakan). Ya ba ta amsa. To Allah ya raya maka shi rayuwa mai tsayi da albarka. Ke ban da ke? Ke ba kya son shi ko Hafsat? Murmushi ta yi. Ta ya ya zan ki son dan Abdulazeez dina? Lumshe ido ya yi kalmar karshe ta yi masa dadi. Ban ga alamar hakan ko daya daga gare ki ba. In fact a gabana sai an roke ki ki yi breast-feeding dinshi. Wannan abu ya dade yana mun ciwo. Ka yi hakuri, lokacin ban saba ba ne, ina jin zafi sosai. To ba za ki daure saboda shi ba? Na san dai duk zafin bai kai na labour ba, horon yunwa ga Dana Hafsah! Girgiza kai ta yi, ta san Abdulazeez da mita akan hakkin sa. Ta dade da sawa a ranta zancen nan bai wuce ba idan ya tuna sai ya dawo dashi sabo. Ka bar abin da ya wuce ya wuce don Allah, na ji na yi laifi, ina ba ku hakuri dukkanku. Sosai ya ji tausayinta, domin tuni har kwallah ta taru a idanunta. Ba za mu hakura ba, sai in kin yarda ki samo mana kani ko Babata Habibah a yau. Zaro idanu ta yi, Haba-haba Abban Khalipha! Ku ji tausayina mana! Sosai ya ga tsoro da fargaba cikin fararen idanunta, duk kuwa da dadin da ta ji na jin cewa da ya yi zai yi wa Habibah marigayiya takwara. Mikewa ya yi ya dauke yaron daga tsakaninsu ya maida shi gadonsa. Dawowa ya yi ya daga duvet din ya shige jikinta sosai. Ni, da ke, da shi, wa ya fi cancanta a fi tausaya wa? Ni da na shekara babu mata,a gabadayaya shekarun kusan uku da aure baifi sati biyar kacal na mallaki matar ba, da ke da ki ke tsoron wani cikin bayan kina cikin koshin lafiya, ko kuwa shi da ko yau aka haifi wani zan taya ki mu yi ta rainonsu? Hafsat ba ta iya ta yi magana ba sakamakon sakonnin da ya soma aikawa cikin illahirin gangar jikinta. Ga son mijin, ga kewarsa, ga kuma matsanancin tsoron rainon ciki da gumurzun nakuda. Su suka taru suka hana mata nutsuwar da Abdulazeez ke so ta yi. Ya fahimci halin da ta ke ciki, kuzarinsa ya ragu kashi talatin cikin dari, ya rungume ta sosai cikin rawar murya ya ce I will not to anything without your consent (bazan yi komai ba sai da amincewarki), ko da hakan na nufin ni zan cutu, sai dai na yi alkawarin zan taya ki da hidimarsu ko kullum za ki haifo min dozen.Ina da yadda zan kula da ku Hafsah, da zan iya zan cire miki ciwon nakudarsu, amma da ba zan iya ba zan yi wanda zan iya. Its a promise. Hawayen tausayi da kauna suka kwaranyo mata. Ba ta yi magana ba, amma martanin da ya soma karba daga gare ta shi ya tabbatar da amincewarta. Ita din mai kunya ce ya sani, amma yau ta ajiye ta a gefe. Burinta daya ta faranta amsa da iyakar iyawarta ko da hakan na nufin duk bayan wata daya za ta haihu. Idan za ta haife kasuwar Kwari duk shekara in dai da Abdulazeez ne, tana maraba da ita.......!!! A wannan ranar, sai ya zamanto kamar dukkaninsu are new to the system..... Kamar koyar da juna suke yi... Kamar kuma directing juna suke yi..... Kamar kuma wani abu makamancin hakan bai taba faruwa a tsakaninsu ba!!! Kowannensu tsoro yake ji, tsoron kada ya bude ido ya tarar mafarki yake yi, mafarkin cewa haka za su rayu da juna har karewar numfashinsu. MURFI BAYAN SHEKARU GOMA Abubuwa da yawa sun faru a wadannan shekarun guda goma masu kama da kiftawar ido. Auren Ismael da masoyiyarsa Waseela Faruk, Usman da Halima diyar Anty Luba, Arch. Haleem Dakata da amaryarsa Saima diyar Anty Mariya. Wadannan dukkaninsu manyan maaikata ne yanzu, Haleem na aiki da kamfanin gine-gine na Julius Berger, Ismael software Engineer ne da kamfanin Microsoft Corproration reshen birnin Honk-Kong din China, Usman maaikacin kamfanin oil and gass na Oriental Energy mallakin Muhammed Indimi. Yayin da mai gayya Yayan kowa Uban Abubakar ke ta taka matakai na nasara kala-kala a aikinsa (as a Civil Lawyer) mai tsayawa alummar kasarshi Nigeria masu rangwamen gata da aka zalinta ko aka dannewa hakki dadukkan karfinsa,ilmin sa har ma da aljihunsa,da jerin hulunan nan masu wuyar samu guda uku; LLB (Civil Law), BL, L.LM (Civil Law), tare kuma da jerin yayansa guda biyar, maza hudu mace daya; Abubakar, Umar, Usman da Aliyu, ga kuma auta Habibatu (Hibbah). Bayan kwashe shekaru goma yana (practicing Bar), yayi applying a (Judicial Service Commission),bada jimawa ba aka yi shortlisting dinsa cikin masu yin jarrabawar (conversion from Bar to Bench)yayi interview. Kamar koyaushe Abdulazeez mai nasara ne balle akan aikinsa da wannan enthusiasm din nasa na komawa Mai shariah daga Bar. A wannan lokacin Hafsat-Suhaanah Allah ya cika buri; B.A ED, M.ED, PhD in Geography.Dr. Hafsat Hamza Atiku kenan uwargida ga Justice Abdulazeez Hamza Atiku. Ta fito da kwalin doctorate ne a wannan Shekarar. The tsruggle contineous as an educational researcher....... Yau an kawo hula ta karshe komai ya zama tarihi. Bayan kammala Doctoral dinta da shekara daya a yanzu haka shirin bude makarantarta ta kanta iyayenta da mijinta Justice Dakata ke yi wadda za a bude a garin Jimeta/Yola. Makarantar sakandire ce mai hade da Primary da Nursery. Ba da jimawa ba aka yi luncheon din bude makarantar mai suna HABIBAH BABBAH MODEL SCHOOL. Wannan makaranta private school ce, amma ba mai tsadar da mai karamin karfi bazai iya biya ba. Yan uwanta maza uku Modibbo, Imaamu, Abdurrahman da kawunta Nuru autan Daada wanda dama tsohon malamin makaranta ne su suka kama mata komai. Don haka yanzu tana yawan zuwa mahaifarta Jimeta a matsayinta na principal. Abbanta wanda yanzu ya yi ritaya shi ya maida ita ta maye kujerarsa a FUTY (as a part-time lecturer). Duka yayanta maza suna hannun Mammah, Hibbah ce kawai tare da ita, wadda ta zame mata cingam a duk inda ta shiga, ita ma don ba ta isa shiga makaranta ba ne Mammah ta kyale mata. A cewarta mutanen da ba sa wuni a gida ba za ta bar musu yaya a hannun su ba da ranta da lafiyarta tunda ita bata aikin. Ko basa wannan jigilar ayyukan nasu butin Mammah ne rike dukkan jikokin ta. Abdulaziz din ne dama mai kulaficinsu ban da Hafsat wadda ke jin ko yaya dari ta haifa Mammah ta ce ita za ta rike a shirye ta ke da yin hakan wholeheartedly, sai dai shakuwar Abubakar (Khalipha) da mahaifinsa wata irin shakuwa ce ta daban data sauran yayan da kowa ya san Abdulazeez ba zai iya barwa Mammah shi gabadaya ba. Duk Jumaah in ya taso aiki yake sa wa a dauko shi tunda a weekend suna gida shi da Addah sai lahadi da dare ake maida shi Asokoro. Sun dade da tashi daga gidansu na Sun-City, Abdulazeez ya yi gini da kansa a Apo. A cewarsa gidan Sun City mallakin Abubakar Sadik Khalipha ne. Amintarsa da abokan aikinsa, Ahmad, ESQ Abdallah da Taufeeq sai abin da ya yi gaba, wanda zumuncin ya shafi matansu da yayansu, Sagir kuwa wannan mai dungurugum ne matsayinsa na kawun Hafsat. Duk da yanzu kowannensu ya bar Abuja da tarin ci gaba; Ahmad na Lagos, Taufeeq na Court of Appeal ta jihar Oyo, Abdallah na garinsa na haihuwa Taraba da kotun jihar (Magistrate Court) matsayin Judge, surukinsa Sagir kuwa an maida shi Porthercourt. Hafsat ba ta yada Rabia Sada ba, bayan sun gama degree a Nile aka yi wa mijinta Sadik sauyin wajen aiki suka koma Kaduna. Har kaduna Abdulazeez ya kai Hafsat wajen Mami saboda ta gaya masa irin taimakon da ta ke yi mata in ta kara hutu, haka da laulayin cikin Khalipha Mami ta taimaka mata sosai. Hafsat ta gane cewa, kawaye da ta ke gudu ba duka ne bara gurbi ba a kan Rabia Sada, tsakani da Allah Mami ta ke kaunarta, tuni ta sallama suke zumunci ta waya har gobe. Mammah ma na bayan wannan kawancen, don haka ko hanya ce ta bi da su Kaduna in za su Kano sai sun tsaya wajen Mami. Mammah ta samu surukarta Wasila matar Ismael ba yadda ta ke tsammani ba, ta gane ba duka yayan masu kudi ba ne marasa tarbiyyah. Ba duka girman Abuja ba ne marassa kunya ba. Ya danganta da tarbiyyyar cikin gida da yammatan suka samu. Wasila dai a Abuja aka haife ta, ta kuma girma a can ta yi karatu a kasar Russia amma yadda ta ke bin Ismael sau da kafa ta ke karrama ta kamar sauran ya sa Mammah ta yi saranda. Ba a gane mutum mai tarbiyya by social status, abin a zuciya ne. Mutum na gari Allah daban yake halittar sa. Duka surukan nata ba ta da mastala da su, don Saima da Halima ita ta karasa rikonsu a gidan mazajen a hannunta suka bude ido da rayuwar aure. Ko gobe suka hadu da Ismael sai sun yi ta sun kasa jituwa har gobe. Wasan kanin miji mai shegen zafi (sunan wani littafin TAKORI). A wata sharia da Abdulazeez ke jagoranta a Federal High Court Abuja, rannan cikin lauyoyin shariar ya ci karo da Muazatu Rufai matsayin lawyer mai kare wanda ake tuhuma. Ya gane ta, ita ba ta gane shi ba saboda canzawar da kowannensu ya kara yi. Dadin dadawa ba ta yi tsammanin ganinsa a wannan matakin ba. Bayan gama shariar ita ta yi winning. Kamar yadda yake mai sharia shi ke fara tashi bayan kammala shariah. Muazatu tana tattare takardunta lokacin da Justice ya mike zai wuce ta hanyar da ya shigo, karaf! Suka hada ido. Murmushi ya yi ya dan dakata ya ce da ita, Congratulations Barrister Muazatu, I know you can make it tunda na hangoki. Itama murmushin ta yi cikin kore shakku da dimbin mamaki.Thank you My Lord. I Absolutely believed you will come to Bench someday, but I never ever thought it will be so soon like that. A gaida SUHAANAH. Jinjina kai ya yi, tare da yi mata godiya da fatan alkhairi. Ta bi shi da kallo har ya kulewa ganinta, wani abu na dan taba zuciyarta mai kama da tasowar tsohon miki, amma da ta tuna Barrister Muntada da irin rayuwar farin cikin da ta ke samu tare da shi, ga albarkar zuria har shidda, a take ta daga hannu ta godewa Allah. Ta ce a ranta, Ba duka abin da muke so a rayuwa muke samu ba, in mun yi tawakkali mun bi iyayenmu, sai mu zauna lafiya. ****** Lokacin da zaayi bikin baiwa Abdulazeez (Chief of the Justices of the Federal High Court) ma sun sake haduwa, wannan karon Hafsat da yayanta suna tare da shi itama tareda mijinta Muntada da nata yayan. Kallo daya Hafsat tayi mata ta gane ta, ko don hotonta da ya shekare mata a falo. Ko taji wani abu a ranta yau kam tafi karfin kishin ta. Duba da cewa Muazatun bata nuna komai ba sai kauna da kulawa ga yayanta. Itama sai ta ja nata a jiki har sukayi hotuna tare.Sun zo ne musamman tun daga jihar Lagos don halartar wann kasaitaccen bikin karin girma da kasar Nigeria ta baiwa Justice Abdulazeez Dakata sakamakon jajircewa da sadaukar da kai irin nasa na tsahon shekaru ga kotunan Nigeria, ba kuma karkashin gayyatar kowa ba sai kasancewar su karkashin umbrella guda na aiki da proffession. Justice ABDULAZEEZ HAMZAH ATIKU da HAFSAT-SUHAANAH nima ina fatan alkhairi. -Takori June, 2019 Masha Allah laquwwata illa billah. Nan na kawo karshen littafin AUREN KWANGILA. Kuskuren da ke ciki ku taya ni rokon Allah Ya yafe mini. Darussan alkhairin da ke ciki Allah Ubangiji ya hada mu cikin ladan ni da ku baki daya. Sai mun hadu a sabon littafina AALIMAH nan ba da jimawa ba insha Allah. AALIMAH sabon salon rubutu ne a cikin jerin littattafan Takori. Idan nace yafi min sauran ko nayi kuskure to kadan ne don ina ji da shi (on its own). Mu hadu da Aalimah Mansour Raazee a cikin littafin AALIMAHdon jin irin nata kaddarorin and her journey to diaspora.. Taku har abada, Takori.