Imaan Book 1 Hausa Novel Complete
Imaan tayi dariya tace "Ni ina ruwana da ita ai na daina xuwa part din ta" Daga haka ta juya ta wuce bangarensu. Da daddare Imaan na kokarin saka kayan baccinta ta kwanta Ammi ta shigo dakin, tana kallon ta tace "Ki je Abba na kiran ki" xaro ido tayi tace "Abba kuma Ammi?" Juyawa Ammi tayi ta fita, kamar xata yi kuka ta saka hijab din ta ta fita tana tunanin kiran me Abba ke mata da daddaren nan. A hankali ta bude kofar parlon Abba ta shiga bayan ta cire takalmin kafarta, Abba na xaune a 3 seater cikin parlon Mujaheed na xaune shi ma kan lallausan carpet din dake malale kasa, sai Umma dake xaune kan one seater, Anty ma haka, Imaan ta karasa kanta a kasa ta xauna kasa kusa da Anty, murya can kasa ta gaida Abba, Abba ya amsa yace "Ya karatu" tace "Alhmdllh" yace "Imaan discipline din ki kenan rashin gaida na gaba da ke?" Imaan ta daga kai tana kallon sa, ya daure fuska yace "Ita Hajiya sa'ar ki ce da ba kya gaisheta a gidan nan?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya hade rai yace "I am talking to Imaan, kuma ki bar kallona my friend" A hankali ta fara 6ata fuska tana jan yatsunta, lkci daya ta fashe da kuka, Abba ya mata tsawa yace "Daman kuka kika samu don ban xane ki ba yanxu" kuka take yi sosai kamar warce aka duka, Mujaheed ya mike ya mata wani raxanannen tsawa ta mike da gudu ta nufi kofa, xai bi ta Abba ya dakatar da shi yace "Rabu da ita M.A, Allah ya shiryeta" Umma ta tabe baki tace "yaran yanxu da ba a sangarta su ba ma ya aka kare ballantana wannan?" Anty ta mike ta fita parlon, Abba dai bai ce komai ba, imaan bata xarce ko ina ba sai sashin inna, tana shiga parlon ta xube kan kujera ta rushe da kuka, inna ta fito daki da sauri, Yusuf ma dake kwance kan 3 seater ya mike xaune da mamaki yace "Me ya faru Imaan" jikin inna na rawa tace "Me ya samu Aishar?" Imaan ta ki cewa komai sai kuka, tuni inna ta nufi kofa, cikin kuka Imaan tace "Ni ba abinda ya samu Ammina" inna ta dawo tace "Ke dai ki dinga jin tsoron Allah, da yanxu xuciyata ta buga ya kike son 'ya yana su yi, ya zaki shigo da kuka ki janyo min wata fitinar ina xaune" Cikin rawar murya tace "Ko ba Umma bace" inna tace "Wacece haka?" Imaan bata ce komai ba sai kuka, Inna tace "Warcan mata mai kama da zabiya kike nufi wai, ko ba uwarsu fitsararren yaron nan Mujaheed ba?" Imaan ta hadiye abu da kyar tace "Ita" Inna ta share wani xufa tace "Toh xata ga barbadin rashin mutunci yau kuwa, me ta maki?" A hankali Imaan tace "Shine taje ta gaya ma Abba wai ni bana gaisheta alhalin fa ko na gaisheta bata amsawa, shine Abba ya kirani...." Sai kawai ta fashe da kuka, inna tayi wani murmushi tana gyada kai tace "Biri yyi shige da mutum, Sai aka yi ya da ya kira ki" imaan ta kalleta cikin shesshekar kuka tace "Yana min fada....." Tuni Inna ta fice parlon, Imaan ta saci kallon Yusuf da yyi tagumi yana kallon ta ta mike tana turo baki ta fita. Inna na isa bangarensu Yusuf kai tsaye parlon Abba ta wuce, har sannan Abba na xaune da Umma a parlon sae Mujaheed, gaba daya daga kai suka yi suna kallon ta, inna ta tsaya tsakiyar parlon tana kallon Abba tace "Yanxu yaro tun da sauran numfashin Bukar a duniya zaka sa ma 'yar sa ido? Yanxu a kan wannan matar zaka ci mutuncin yarinyar da lafiya ma bai isheta ba sai dai godiyar Allah? Yanxu Ahmadu duk son da d'an uwanka ke maka xaka rufe ido a hadu da kai a ci mutuncin yar sa kwaya daya tal..." Kunce ha6ar xaninta tayi tana matsar kwalla tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba..." Abba kasa cewa komai yyi da farko, can yace "Haba inna, wannan wace irin magana kike...." A fusace tace "Ohh yare nake maka da xaka tambayeni wani irin magana nake, to wllh bari ka ji, a kan Fatima a gidan nan ina iya sa6a ma ko wani mahaluki, kuma baxata gaida matar taka ba, ita katuwar gaida mutane take?" Mikewa Mujaheed yyi ya nufi kofa kamar xai tashi sama inna ta bi sa da wani shegen kallo, sannan ta ja tsaki ta maida dubanta kan Abba dake ta kallonta ta daure fuska tace "Ahmadu yaushe rabon ita matar taka ta kai kafafuwanta bangarena gaisheni? Lallai... ni a su wa xata je gaidawa? Ni din banxa xata gaidar?? To hirrrr wllh, kada wanda ya kara sa ma jikata baki a gidan nan idan ba haka ba sai in sa Bukar ya koma daya gidansa dama shi ya nace xama waje daya da kai, tunda yar sa xa a takura gwara kawai ya bar gidan...