Dr Mukhtar yace
"Ina kinji ko Na'ima kawar ki tafi karfi na sai dai mugani kawai mu latse baki, ko za'a ?an taimaka min na?an lallasa ne basai ciki ba iya waje kawai". yakarasher maganar da dariya ha?e da tsigar zolaya.
baki Raliya ta ta?e tana fa?in
"Yanzu dai muyi abun da yakawo mu, Dr muna da damuwa fa".
Na'ima ta kar?i zancen da fa?in
"Kwarai kuwa Dr akwai matsala".
yace "Wani damuwa kuma ai ni a tunani na yanzu bakuda wata sauran ragowar damuwa ke Na'ima da kike da SALEEM a hannun ki".
"A'a Dr gaskiya da saura nasame shi kam amma da saura munaso mukuma samin shi sosai yazamo nawan da gasken gaske".
zaman ta ta gyara da kyau ta da?a fuskantar shi kana tace
"Dr yau nazo haihuwa".
ido yawaro yace
"Haihuwa kuma anta?a haihuwar da ba ciki?". yafa da dariya
sai kuma yakuma sakin dariyar shakiyyanci
yace "To ai cikin naki baikai na haihuwa ba tukun".
wani goron numfashi ta sauke kana ta da?a gyara zaman ta da kyau tace "Dr tunani na kenan ranar da cikin nan zaikai na haihuwa, ace ciki yayi wata tara yaya zanyi narasa yanda zanyi,
rabon da naji wani abu yasani shiga damuwa irin haka na mance, Dr taya zanyi nasami ?a kune manya aikin kune kunfimu sanin yadda za'ayi".
jakar hannunta ta aje gefe kana ta?aura hannayenta biyu kan teburin gaban su sannan tacigaba da fa?in.
"Ko nawa ne zan biya har idan nima bukatata zata biya".
?an shiru yayi yayin da yake ?an juyawa kan kujerar da yake kai, sannan yasauke numfashi kana yace
"Gaskiya wannan buka taki babbace a gaskiya yanzu samin ?a a cikin asibitin nan da kamar wuya, yanzu an saka matakan tsaro iri-iri, kinsan kwanaki fa munyi ta shari'a da wasu mutane wan da mukayi musu canjen ?a,munyi ta samin matsala dan ma allah ya rufa asiri,
amma mezai hana tun da kince kinason ?an cikin gaggawa kije gidan marayu, gidan marayu yakamata kije, akwai wan da suka haifi ?a?a zaki iya samin wan da yau ma ta haifa ta yar aka samu aka kai shi gidan marayun,
to inaga kije ki ?auka a can ?in zaifi".
kai Raliya ta jinjina alamun gamsuwa da shawarin nasa tace
"Eh gaskiya hakan ma kawai za'ayi gidan marayun zamuje mu samo ?an acan kagama babu wanda ya isa ya zarge mu, sukuma hukumar gidan marayun zamusan yadda zamuyi da su tun da akwai ?a?an banki".
Shiru Na'ima tayi yayin da ta zurma cikin tunani na?an wani lokaci kana ta ce
"To shike nan amma kuna ganin baza'a sami wata matsala ba ko?, dan nifa bana so maganar tafita naso ace munyi shi anan sakanin mu basai ansako wasu ciki ba".
Dr Mukhtar yace "Ai samun ?a a gidan marayu shine kawai mafita kuma rufin asiri, tun da jakar ku na cike da makullin kulle bakin wasu ai an gama,
idan mukace a nan ne zamu samu to za'a iya samin matsala dan har yanzu asibitin nan idon hukuma yana kansa sun saka ido sosai suna jiran suji wani abun yakuma fita su sami mafakar hujjojin da suka tara, wan da naki bada damar hujjar tasu tayi aiki idan da ku?i meye bazamuyi ba".
ido Raliya ta kanne tace "Wai wan da kayiwa ai kin nan nawa ne yabaka haka?".
wani munafukar dariya yayi kana yace
"Miliyan 10 tabani kuma ko wani wata ina ?aukar albashi daga gurin ta".
"Bayan 10 million tana kan baka wani ku?in kuma?".
Na'ima tayi maganar da fuskar mamaki.
yace "To ai kin wasa nayi mata ka?an fa yarage yata?a nawa aikin dan ma Dad yatsaya da gaske kan lamarin, canjin ?a ai bakaramin kasada bane, jigo na canza mata da shi ?a na miji na musan ya mata da mace, to ku?in wasa suke samu a kasar nan 10 million wani ku?i ne agurin su,
duk wata 300k nake ?au ka a gurin ta tukuicin godiya."
dariya suka sheke da shi cikin muryar dariya Na'ima tace
“Kai Mukhtar wlh bakada dama shine ko ?an salalan nan babu.”
"Haba wani salala ke me zakiyi da ku?i yanzu kinada jakar ku?i a gefen ki, kinada ABDALLAH IDRIS ABDALLAH me kuma zakiyi da ku?i, ai nine abun a taimaka dan ko Raliya ku?in da take samu bani samun irin sa".
mikewa Na'ima tayi tana fa?in
"Kace dai bazaka bamu ba kawai musan in da muka ajiye ka, aminiya tashi mutafi gidan marayun nan yanzu ba'a bori da sanyin jiki".
zai yi magana sai kuma yayi shiru sakamakon hayaniyar da yaji ke ?an tashi daga can waje da alama a cikin parlou'n asibitin ne in da mutane ke zama dan jiran ganin likita.
wata nurse ce ta shigo bayan tayi knocking an bata izinin shigowa,