Showing 126001 words to 127901 words out of 127901 words

Chapter 43 - Karfe A Wuta 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

491

ba zan sake ba in sha Allah, dan Allah ka janye korar da ka yi mini daga gidanka, nayi kuskure ka yi haƙuri "

Sai dai mai unguwa yayi tsit, dan kuwa Al'amin ya gama kwaikwaye shi a gaban mutane, yayi mamakin maganganun da suka fito daga bakin Al'amin ɗin.

"Officer, zan kawo yaron da yake sayar da wannan capsule ɗin, a riƙe shi a matsa shi, ya faɗi ina yake samota" ya sake kallon guduma ya ce "Ka shelanta, cikin unguwar nan, duk wanda na kama da sayar da irin wannan nau'in kayan, sai na lahira ya fi shi jin daɗi"

Ya jinjinawa Al'amin kai.

"Yanzu dai ina nema masa afuwa, yayi nadama in sha Allah ba zai sake ba".

"Idan ya sake fa, ni fa gaskiya rayuwata tana cikin hatsari"

"Ayi rubutu, duk abun da ya yi zan ɗauki laifin"

Ba mai unguwa ba, har Guduma Nura sai da ya kalli Al'amin.

Aka yi sulhu da rubuce-rubuce, suka fito, guduma ya risuna yana yi wa Al'amin godiya.

"Manta, mu je ka rakani asibiti, kan waccan uwar mitar ta sakani a gaba"

Guduma ya ce "Antynmu ayi mata godiya, abinci yayi daɗi na gode master" bai ce komai ba, suka tafi asibiti.

Ko da suka je emergency, Al'amin har gaban gadon yaron da ya karya ya je, ya tarar da shi a kwance, ana saka masa ruwa.
Yana ganin Al'amin ya rikice, ya yinƙura zai ɗago, Viper ya mayar da shi, ya kalle shi ya ce "Na ji babarka na kururuwa na nakasta ka, a ɗaukar mata mataki, kai ba ka gaya mata babu mai iya ɗaukar mata mataki ba? Yanzu ka dawo hayyacinka ka tuna abun da ka yi ko? Ba ka sanni ba ko? Saboda ka sha ta gaya maka ƙarya, ni ka tunkara zaka sara ko? Wai ba kai ne ɗan mama ba, da aka rufe kwanaki madaki ya saka ka kashe wani yaro a dabarku ba? Ya shiga ya fita an sake ka, yanzu kuma da ka nakasa ya kasa taimakon ka ko?".
Ya sunkuyar da kai ya yi shiru.

"Za a zo a biya kuɗin maganinka, nan gaba ka sake zuwa ka tari gaban tirela, ta kanka zan bi"

Ya kalli guduma ya ce "Tashi mu ware"

Ya tashi suka tafi.



Bayan fitar su Al'amin, jauhar ta kaiwa telar da take yi wa aiki kaya, ta rage mata wani abu a cikin kuɗin, amma ba ta bata duka ba.

Ta tarar da yaran matan layin, suna ta bajekolin magungunan mata, ana ta shewa.

"Jauhara ba za ki sayi abun arziki ba, ga kaya nan sai wanda ki ke so, kuɗi kuɗi iya kuɗinki iya shagalinki"

Kawai tayi murmushi ta basar da su.

Wasila ta ce "Wai sai an yi magana sai ki wani din ga mazewa kamar baki san komai ba? Ke an daina irin wannan abun kamar a zamanin da, idan baki zanzare kin fitsare ƙafafuwanki ba,bar ganin mijinki a haka ba ruwansa da kowa, wallahi sai ki ga ya fara 'yan leƙe-leƙe, ki zo ki ɗauki gyara hajiyata, ita mace sai d gyara, wannan kyan fuskar ta ki ba shi kawai yake so ba"

Jauhar ta ce "Hmm Anty wasila kenan"

"Ba wani anty wasila, malama ki rage maƙo dan Allah, kin iya neman kuɗi sai aukin saka turaren wuta a gida, da goge goge, amma ba zaki sai kayan gyara ba, ina ta tallata miki kayan maman neehal ɗin nan, baki ga kyan su ba, amma sai ki yi burus".

Suwaiba tela ta ce "Wai wasila ki ƙyaleta mana, ki ka sani ko tana abun ta, idan tana yi gaya miki zata yi?"

"Ba wani, ni fa jauhar ƙanwata ce, ƙanwa na ɗauketa, kunyarta tayi yawa Allah ya sa ba haka ki ke yi masa ba, babu yadda za ayi ki je ki ganta da shirt da wando, sai uban hijjabi da dogwayen riguna kamar zata yi ɗawafi. Ki tsuke ki ci zamaninki tun da ƙuruciyarki, ni ga wani tsumi nan na baki, na maman neehal ne, tested and trusted, ki gwada zaki bani labari.
(0706 677 4630 ga lambar da zaku samu maman neehal, domin samun kayanta)

Kamar sokuwa haka Jauhar ta karɓa, kasancewar ta san ba wani amfani da zai yi mata.

A gurguje ta kammala abun da za ta yi a gidan, ta fito saboda irin manyan karatun da ta ji suna yi, da suka fi ƙarfin kanta.

Ta koma gida, ta din ga kallon robar abun da anty wasila ta bata, na wurin Anty lubabatu ma suna nan, ko kallonsu ma ba ta yi.

Aka fara kiraye-kirayen  sallar magariba, tana salla, ƙarar wani babur ya cika mata kunne, bayan ta idar tana cikin lazumi, ta ji ana kokowar shigowa da abu, ta tashi ta fito tsakar gida, ta tarar da Al'amin yana shigowa da wani tsohon babur jincheng, hannunsa riƙe da salansar babur ɗin.

"Master, wannan kuma fa?"

"Jaki ne" ya bata amsa.

"Wai sai ka yi ta gaya mini baƙar magana, wai ko shi ne ya cika layin nan da ƙara?"

"Eh"

"To meyasa ka cire masa salansa? Ka ji ƙarar kuwa ba daɗi, kamar ya shekara ba a kunna ba".

Ya jingine salansar, duk ya ɓata jikinsa da baƙin mai, ya ce "Na fi son sa a haka"

"To wai a ina ka samo babur?"

"Sata na fara" yayi maganar zai shigar mata falo.

Ta ce "Allah ya baka haƙuri, amma tsaya na kai maka ruwa banɗakin tsakar gida ka yi wanka, idan ba haka ba zaka ɓata carfet ɗin da baƙin mai"..

"Naɗe abun ki na wuce, ba zan yi wanka a tsakar gida ba"

Ta shagwaɓe ta ce "Ba fa a tsakar gida ba, toilet ɗin tsakar gida".

"Ƙoƙarin shiga falon yake, tayi sauri ta ɗaukko tsumma, ta durƙusa ta ce "Bari na goge maka, kar ka ɓata mini carfet" ta gogge masa, sannan ya shiga.

Warin sigarin da yake yi ya sanya ta bin sa da ruwan zafi, ta matsa masa toothpaste a kan brush, ta ajiye masa.

Allah ya taimake ta, babu musu yayi wanka yayi brush, ya fito yana goge jikinsa, ya buɗe wardrobe ta shigo da sauri ta ce "Saura ka watso mini kaya ƙasa, na sake gyarawa, nuna mini wanne zaka saka na ɗaukko maka?"

Ya nuna mata, ta ciro masa su, kafin ya karɓa ta miƙo masa kwalbar turare ta ce "Ka shafa turaren, sai ka saka"

Haɗin da take amfani da shi ne, ta daka alumun, da farin muski na gari, da kanumfari, da lalle, ta dafa su suka tsumu ta ta ce, ta zuba madarar turare a ciki.

Ya karɓa ya shafa, ya miƙa mata, ta karɓa ta ce "Ai naka ne, na bar maka"

Ya karɓa zai ajiye, ta ce "Baka ce ka gode ba" sai ya miƙo mata abun ta, da ya ce ya gode gara ya dawo mata da abun ta.

Tayi dariya ta ce "Hukuma sai da rarrashi, na janye ba sai an yi godiyar ba"

Ya ajiye, ya fara ƙoƙarin saka kayan, ta fita ta bashi wuri, shi kansa ya ji daɗin jikinsa sosai da sosai, ga ƙamshin yayi masa daɗi sosai da sosai.

Ya fita ya kame a falo, ƙamshin turare sai ɗibarsa yake yi.

Akwai English wears a cikin kayanta, sai dai ba ta taɓa gwada sakawa ba, dan kunya ma take ji, domin kuwa sai kwanan nan ta daina yawo da hijjabi a cikin gidan.

Da ƙyar ta iya fitowa da doguwar rigar atamfa, da ta ɗan kamata cif jikinta, ta zo ta zauna a falon, ta ce "Master ya ku ka yi a police station kuwa?"

"Labari zan baki ko yaya?"

Ta ce "Eh mana"

"Kunna radiyonki, ki ji labarai idan shi ki ke son ji".

Cikin shagwaɓa ta ce "Ni naka nake so"

Ya ce "To ni ban san me zan ce ba"

Ta ce "Ai shikenan"

"Yauwwa, na ce ba ka ga azumi saura 'yan kwanaki, yakamata ace ko sugar da lemo mu saya mu je mu gaida su Abba"

"Sai kin dawo" ya faɗa yana shan kunu.

"Master meyasa?"

"Kawai".

"Na san akwai dalili, amma koma menene ka yi haƙuri, ba a fushi da iyaye, kai fa ka gama yi wa wani nasiha ɗazu, meyasa ba zaka yi amfani da ita a kanka ba?"

Juya mata baya ya yi, irin idan kin gama kya yi shiru.

Zuciyarta cike da fargaba, ta taka ta je kusa da shi ta zauna ta ce "Masu sunanka manyan mutane ne, dattawa, ba sa haka, dan Allah kar ka saka mu shiga fushin Allah, iyaye ba abun watsarwa bane ba, ranar da babu su da kuɗi ba zamu gansu ba, mun rasa iyaye mata, mazan sai mu nemi albarkar su"

Ya ɗaga hannunsa ya ɗora a kan kunnensa, ta kalli dogwayen yatsunsa, faratansa sun yi tsayi.

"Gobe in Allah ya kaimu friday ce, a yanke farce, sumar nan ma tayi yawa yakamata a rage ta, ayi maka gyaran fuska kafi kyau idan aka aka rageta"

Juyowa yayi gaba ɗaya, ya ƙureta da idonsa.

Sai jikinta yayi sanyi, tsigar jikinta ta tashi yarrr.

"Kin fa dame ni" yayi maganar a hankali, amma muryar da yayi amfani da ita, har cikin zuciyarta.

"To me nayi maka na takura?" Shiru yayi bai yi mata magana ba, ya cigaba da ƙare mata kallo.

Ja tayi da baya, ta ce "Dama wainar fulawa zan yi mana mu sha da tea, bari na ɗora"

Ta fita tsakar gida, ta hura kurfoti, ya biyo ta gaban kaskon ya zauna, sai dai kallon da yake yi mata duk ta takura.

"Master, kamar fa akwai ɓera a gidan nan, dan Allah ka sayo maganin ɓera"

"Shi m tsoron nasa ki ke ji kenan?"

Tayi murmushi ta ce "Eh, amma ba sosai ba"

"Ya haɗa nasa shayin, tana soyawa yana cinyewa"

"Master ban gane ba, idan ka cinye ni fa?"

"Sai ki soya wata"

"Ko kuma ka soya mini ba, ƙullin fa bashi da yawa, ka ƙoshi gaskiya" ta janye plate ɗin.

Ta gama ta haɗa nata tea ɗin, ta fara ci.

Ya zuba mata ido, cin abincin ma yanga take yi masa.

Yana zaune yana kallonta, ta gama ta haɗa wanke-wanke ta yi.

Ta gaka komai, zata shiga ɗaki ta ce "Na gama taso mu tafi, kar sauro ya saka maka zazzaɓi".

"Dama na ce miki ke nake jira ne?"

Jauhar ta ce "Eh dole ka ce haka, tun da na cika maka cikinka, aishikenan sai da safe, dan Allah kar ka sha komai ka ji master".

Yayi mata shiru, ta ce "Master, magana nake fa, na san kana ji na, dan Allah kar ka sha komai ka ji Mai zamani"

Ɗagowa yayi ya kalleta, tayi masa murmushi, tasowa ya yi, ya biyo bayanta. Tsayawa tayi ta ga me zai yi mata.

Yana zuwa ya riƙe kunnenta ya ce "Me ki ka ce?"

"Master na ce"

"In kuma jin kin faɗi wannan sunan" sai dai duk wannan abun fuskarsa ba fara'a.

Cikin shagwaɓa ta ce "Kunnena zai cire fa" ya tura ƙeyarta, har ƙofar ɗakinta, ta ce "Kar in sake ganinki sai gobe in Allah ya kaimu".

"To na ji, amma dai kar ka sha komai dan Allah" wucewa yayi ɗakinsa, ta ƙarasa gaban gadonta tana murmushi.

Ta yi wanka, ta shirya ta shafa turarukan ta, ta nemi wuri ta kwanta. Sai murmushi take yi, tana jin daɗin cigaban da ake samu a kan zaman su.

Ta kalli pillown da take rungume da shi, ta shafi pillown a hankali, tana tuna hirarrakin da aka yi ɗazu da su Anty wasila.

Tabbas abun da take ji game da aure ya sha banban da abun da ta tarar, to ko ba haka abun yake ba? Sai kuma ta tuna har a littatafan addini ta karanta.

Hakan yana nufin Al'amin ba shi da lafiya ne? Ko kuma ita ɗin ce ba ta gabansa, sai dai ya ci, yayi shaye-shayensa ya je yawonsa, ko kallon kirki ba ta ishe shi ba.

Tunani take yi ko dai tana da wani naƙasu ne, da ya sanya ba ta gabansa, ko da wasa


Ayshercool
08081012143

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login