Showing 3001 words to 3777 words out of 3777 words

Chapter 2 - Auren Jinsi Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

31 Dec 2024

119

tace amin..... Salmah mikewa tayi cike da kunya..... Amma tana jin dadin irin adu'ar da mom ke musu....




Hajiyata ina jin dadin irin adu'oe naki.... Amma meyasa bakya musu adu'a Allah yabasu maza nagari tace alhaji ni ina tunanin yarannan baza'a taba bari suyi aure ba baka ga yadda abubuwa suke ta faruwa.... Ni ina tausayin yarinyar wallahi gaskiya salmah tacika yar halak.... Data iya kame kanta daga sharrin shedan dubi shekarunta fa amma ka yi dubi da wannan lokacin da muke ciki sai kaga Yara kanana suna zinace zinace ga kuma babbar masifa mace ta nemi yar uwarta mace ko su nemi hanyar biya MA kansu bukata ta hanyar masbution da sauran su..... Sai dai Allah ya shirya kawai..... Amin yace kawai.....

Salmah kwance ta tarar da nasmat a gado idonta a lumshe matsawa kusa da ita tayi tace my little kiyi hakuri ban san akan abinda kike fushi ba Kenan.... Ki sani wallahi ni kaina inda zan kama wani daga cikin family na da irin wannan aiki zan dau hukunci da yafi naki tsauri..... Nasmat da sauri ta taso tace kamar wa Kenan..... Tace ko ke ko kuma wani daga cikin family mu.... Tace indan mom kika kama da irin wannan aiki fa Zaki iya daukan hukunci tace sosai Allah ma yatsere mom bazata yi wannan aikin ba amma nasmat ina tabbatar miki da cewa indai kuwa nakamata to gaskiya basan yadda zanyi ba kuma zan tsanenta na kuma nisanta kaina da ita...... Nasmat wannan kalmar ta lesbianism da ita aka rusa mun duk wani plan na rayuwata kuma aka rabani da farinciki na...... Wanda zan sanar dake yanzu duk da kin San wani Abu akan Kamal ko...... To bari kiji waye Kamal agareni......


** ** WAYE KAMAL ****

watarana mun tashi daga school ranar wensday 15 /3/2010 ina tsaye a cikin makaranta ina jiran driver yazo.... Driver bai zo ba har nagaji da tsayu naje jikin wata bishiya dake cikin makaranta na zauna angama daukan kowa sai ni kadai..... Wata malamar mu me mana Islamic studies tafito zata tafi.... Motar ta nakusa da inda nake zaune kallona tayi tace dayyib salmah kabir dake haka take kira na mekikeyi ne har yanzu baki tafi ba..... Lokacin na riga nagama cika kuka ne kawai ban fara ba..... Nace MA driver na bai zo ba har yanzu I don't know what's wrong with him...... Kuma ba wanda yazo dad ya hanani Hawa abun haya....... Tace ayyah to muje in kaiki gida ko... Watakila akwai matsala ne..... Haka nashiga muka tafi..... A hanyarmu na komawa ne wata Motar kawai tazo ta bigi motrmu da karfin gaske wanda yasa motocin cin Karo.... Mallama fateemah nata sallati nikuma ina ihu kafin ta taka birki duk mun Sha wahala.....fitowa mukayi daga Motar hannu Mallama fateemah nake jini sosai...... Hijab dina na cire na kama hannu na daure shi..... Dayan na cikin Motar ne ya Bude Bayan Motar wani saurayi matashi ya fito cike da rashin mutunci ya nuna Mallama fateemah da hannun yana shirin zaginta..... Bai karasa fadan abinda yake shirin fada ba na mare shi...... Bodyguard din shi ne ya nufo ni da sauri tsawa ya daka me..... Nace kaima giyar hauka kasha ko to zo ka dakeni..... Kai kuma da baka da kunya bakasan darajar mutane ba.... Yasa ka yin kuskure amma baka ganin ba har zaka sa rufafen bakinka zaka yiwa mutane rashin kunya....... Ganin tayi ya kura MA kirjinta ido..... Yana lashe baki..... Bunsuru kawai...... Hannun Mallama fateemah takama suka shiga mota Dan tafiya asibiti......... Nasmat Mallama kasa tuki tayi nikuma lokacin ban iya driving ba...... Zaunar da ita nayi na fito nace Dan waye ya iya tuki anan...... Nasmat abun mamaki wannan saurayin ne yace wa security shi yaje ya yi driving din....... Kowa mamaki yakeyi haka...... Ni ban tsaya jin magangunsu ba muka tafi asibiti da Mallama...... Anyi mata dressing din gun yadda ya kamata.... Dakuma injection saboda tsoron tortonois..... Haka yakai Mallama gida..... Nima agidanta na sauka....... Bodyguard din yatafi..... Bayan yatafi ne naba Mallama fateemah number mom..... Ta mata bayani..... Gidanta na kofar na isa....... Bandade a gidan ba mom ta zo ta dauke ni da kanta....... Nasmat abun mamaki ashe Kamal yayi afani da security shi ne Dan cimma wata...............







Typing.......
By:H. @.S🔵🔴

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login