Showing 1 words to 3000 words out of 5521 words

Chapter 1 - Amanata Ce Book 1 Hausa Novel Complete

💥 *AMANATA CE* 💥

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/OUD2pf7LpH1gw7

17/4/2024

💫LAFAZI WRITTER'S ASSOCIATION💫.
{L A W A}
==Kyakkyawan lafazi acikin rubutu nadanfare dabin 'ka'idojin adabin hausa===


💥AMANATA CE💥
<< BY AYSHERTY>>

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah
Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, wanda shine yabani iko da daman fara rubuta wannan littafi.👏🥰

Ina miqa dunbin godiyata agareku masoyanaa,tare da fatan alkhairin da kukemin,Allah yasaka da alkhairi,Allah yabar zumunci, nagode maku.🫂

*I dedicated this book to u my AMRATY much love Allah yabar qaunaa🫂🌹*
---------------------------------------------------

*....FREE PAGE...*

PAGE 1_2
Tunda tatashi yau take acikin fargaba, sanin cewa yau zae dawo,domin baqaramin mugunta yake mataba, ita wallahi batasonma yadawo qasannan gwanda yayita zama can UKn, don tasan indae yadawo shikenan hutunta yaqare acikin gidannan,tsaki taja tana turo baki gaba,shi wannan miskilin dan rainin wayon sae masifar bala'i ba abinda ya iya sae sa mutane aiki da mugunta.
SABIYYA! SABIYYA!!
Zumbur tamiqe daga kwancen da take tana fadin na,am MAMII! ganinan tanadan daga muryanta,saeda tatashi tsaye nace wowww ma sha Allah domin duk wannan tunanin nata tana kwance cikin blancke ta rufe jikinta har wuya, kyakkyawace ajin farko,doguwace amma ba sosaiba dan kuwa ita baza,acemata gajeriyaba,farace sollll tanada shape mae kyau irin dae shape din da ake cewa 8,tanada dara dara idanu masu dauke da zara zaran eyelashes, tanada dogon hanci da kuma matsakaicin baki pink lips wanda yai daidai da zubin fiskarta, amma kana ganinta kaga shagwababbiya tagaban kwatance, kai tsayawa fadan kyan SABIYYA ma bata bakine nidae kawai nace ma sha Allah.
Dasauri tayi palourn jin mamii naqara kiranta, ahankali take tafiya kamar bataso amma ita ahakan sauri take har tazo daedae kan sopa inda mami take,gani mamii, yade daughterna naganki wani so cool,baki tatura tace toh mami aikinsan dae yaya zae dawo, zae fara takuramun, murmushi mamin tayi tace hmmm keda yayan naki ai ba,a shiga tsakaninku idanma anshiga za,aji kunya, yanzunma muka gama waya yace kije ki gyara masa part insa anjima zai sauqa,diddira qafafu tafara tan cewa yanzu shi yayannan tun kafin yadawo zai fara sani aiki duk masu aikin gidannan? Allah ni bazan gyara masaba,bayan kona gyara cemin yake ba,abinda na iya?tafada tana kawo hawaye idonta, ya,isa SABIYYA kyaleahi bari nasa samira tagyara mishi inkuma bae masaba inyadawo yagyara abinshi, gyada kai tayi tana ficew daga palourn,wani part naga tashiga dayake gidan part ukune, part din gefen naga tashige,tana shiga ko sallama batayiba tawuce tayi cikin palour kai tsaye kan cushion dake falon tazauna 3seater tajuya baya,bata dadeba da kwanciya wata mata dattijuwa sosai tafito,kawai sae ganin mutum tayi salati tayi tace meye kuma wannan haka da za,a somin palour akwanta,sai ansamin datti,tun safe nake tsaye,saboda yau dan lelena zae dawo, wani irin kallo SABIYYA tayiwa matar tana turo qaramin bakinta na tsiwa tace tab wannan mugunne dan lele? Wallahi dakankima zaki koreshi baridae yadawo zamu ganii,mutun sae miskilancii, bude baki ANNA tayi tace ehh lallai SABUYA 😂 wallahi kamar agabansa akai, ni ficemin daganan karki batamin gurii,kinsansa badae tsaftaba,tabe baki tayi tace dama ko bakiceba tafiya zanyi, oho dai aje can aiwa AISHA rashin kunya badae ananba,ficewa sabiyya tayi kamar zata tashi sama.


Page 3_4

Bangaren tsakiya tashige tana zuwa wata kyakkyawan mata na fitowa daga kitchen da alama aiki take,fadawa jikinta sabiyya tayi tana cewa wasshhh AMMIna nagaji,tureta tayi tana cewa matsa can!! aikin dana saki kenan ko sabiyya kuma dama bakije taro yayan nakuba? Baki taturo tace tohfa Ammi kince yaya kikewa abinci,kowa sae yawanice yaya yaya!!! Mutun sai mugunta kuma aitaimasa wahala, kumani Allah bazanje tarisaba,hakana naga ANNA wai sae gyara ake saboda ga gold zae dawo,walkahi shiyasa mamii take burgenii ita baruwanta dashi ko harkansama bata shiga tafi sonama tafada tana tana hawa stape.(nikam nace mutum da danshi ace ba,a tatasa) girgiza kai AMMI tayi tace Allah yashiryeki SABIYYA.
Tana hawa saman tashige wani daki daga ganu dakintane,wowww ma sha Allah yayi kyau sisai,wata qofa tashiga da alama bathroom ne wanka tayi da sabulanta masu matuqar tsada da qamshi, tadauro towel tafito. Mai kawai tashafa tadu Wata hadaddiya black abaya tasaka tagyara kanta palour tafito tayi kwanciyarta akan three seater tadau wayarta tana dannawa.

Sae wajen 4:30 naga anbude tangamemiyar gate din gidan ,sae ga wata dankareriyar jib tashigo wasu motoci biyu na biye da ita,kai tsaye a parking space sukaiwa motocinsu masauqi, dasauri drivern yafito ya bude back seat dib jib din,saeda akadau kusan 5mints kafi yaziro zara zaran qafafunshi,mae dauke da black cover shoe,candae yafito gaba daya,wowwwww ma sha Allah wannan kamar ba dan NIGERIA ba,kyakkywane aji farko shekarunsa bazasu wuce 35 dogone sosai,bashida haske sosai yanada faffadan qirji, bakinsa zagayayye madaidaicii,yanada hanci kamar anzana,ga saje gashin kansa baki wulik, ammafa idan akace kyau toh * KHUBAIB *yakai kai tsaye kina kallon KHUBAIB zaki gane cikakken bafilatanine gaba da baya, ragowan nasauran motanne suka fito gaba daya sukai compound en gidan kallonsu yayi daya bayan daya baega SABIYYA ba jinjina kai yayi aransa yana fadin hmmmm uwar tsiwa,zama ki fitone.😂

Wani saurayine yadaebi trollynsa yakai Part din Mamii,shikuwa yahuce bangarenshi ya watsa ruwa,kai tsaye part en AMMI ya nufa yana shiga ammi na fitowa daga kitchen da munna tatareshi a,a my SON ashe kun qaraso shiyasa naketajin hayaniyarsu juhaifa awaje kenan,ehh wallahi Ammi na sameku lafiya,lafiya kalau Alhamdulillah ya hanya?zauna mana, cikin palourn yaqaraso dan baema kula da itaba,ita kuwa tunda yashigo qamshinsa yatabbatar mata da shidinne, Ammi ce tace yauwa SABIYYA tashi kiyi saving nashi zanje sama daddynku yadawo abun yaquremin ban qarasaba tafada tana hayewa upstair, tura baki tayi tana sako sabbin kwallah tana diddira qafafu nata qunquni tayi dining, kallon saman yayi yaga Ammi ta wuce biyo bayan SABIYYA yayi ita batasanma ya biyotaba tanata qunquninta, tagama saving nasa,tajuyo zatayi mishi tsiwa kawai taji tayi karo da abu.......


BY AYSHERTY....✍🏻


LAFAZI WRITTERS ASSOCIATION

AMANATA CE
(By Aysherty)


Page 5_6


Dagowan dazatai sukayi ido hudu dashi, Dan Allah Yaya karkamin komi ohh kinsan me kikai kenan? kai tashiga girgizawa Dan ita batasa yajitaba,rabawa tayi ta gefenshi zata wuce fizgota yayi tafada qirjinshi kunnenta yamurde ihu tasa Dan jitai kamarma kunnen zaecire .wayyooo Ammiey dasauri yacikata yana turata yace out mara kunya.

Dagudu tafita kai tsaye part en Anna tayi tana zuwa tagada jikin Anna tana kuka, toh kekuma keda wa haka zakizo ki nemi ki karyamin qasusuwa haka? cikin shagwaba tace koh ba yaaya bane? toh waye haka kuma Ina wannan mutumin mae kamada samudawa?cikin kuka tace shii. Anna tace toh daga dawowarsa har kin tsokano shi kenan zaku fara tallahn hali,cikin kuka tace bashineba ba.abinda nai masaba yakama dukana da belt kuma wallahi Anna da zafiii, tafada tana turo baki, duka ?Anna tafada cikin mamaki gyada kai tayi. Anna tace yoo banda shi shashashane inashi Ina dukan mata. hardasa su balt, kamar yasamu doki? ni wallahi har ya gundureni kwata kwata barni dashi shiga ciki ki kwanta. dasauri tashige bedroom en Anna ta haye gado ta lullube har wuya tana dariya Dan tasan zaesha masifa gurin Anna.

Bayan yagama cin abincin Ammiey tasauko tareda daddy tace har kagama son? ehh Ammiey nagama, Ina sabiyyanfa batai saving naka bako? uhm bakomai Ammiey nama gama ai, Allah yashirya sabiyya Ammiey tagada. Barka dadare Abba,yafada tareda Dan rissinawa ga Abban wanda yake riqe da hannun Aaufaa barka dae son ya aikin? Alhamdulillah Abba, ma sha Allah, Allah yayi jagora AMIN Abba, yafada tareda barin part en.


PAGE 7_8


WACECE SABIYYA!WANENE KHUBAIB!


Alhaji Ahmad da Alhaji Mus,ab manyan yan kasuwane,tun suna yara kansu aahade yake suna tare da maihaifiyarsu FATIMA wato 《Anna》tun suna qanana mahaifinsu ya rasu,sun taso cikin kulawar mahaifiyarsu dan sunsamu tarbiyya.tunda mahaifinsu yarasu suka shiga cikin quncin rayuwa.sunsha Wahala mahaifiyar tassu tasha wahala duk dangin baban suka karbe kadarorinsa sukace nasune, bayanda suka iya sbd basuda qarfi sunaji suna gani bazasu iya komiba sbd lokacin suna yara sae qanwaru daya Amina,

wannan dalilin yasa suka tashi da neman nakansu inda suka dinga samun nasarori suna habbaka kasuwancinsu bisa gaskiya amana atsajaninsu,bayan Ahmad yakai shekara 38 shikuma mus,ab 36 alokacin Anna ta matsa musu kan suyi aure anan dae aka samu Ahmad din yayi ya auri matarsa kykkyawa Hafsa《Mamii》suna yaya biyar KHUBAIB shine babba inda yagama karatun doctor dinshi a uk kuma yana aiki tsakanin qasashe yanada hospitals nashi nakanshi,ayanzun yanada shekara 35 sae mae binsa Umar,sae Maryam,khadeeja,sae autaa Mubeen.

saeda KHUBAIB yashekara biyar sannan mus,ab yayi aure da matarshi shima kykkyawa AISHA 《Ammiey》 saeda tai shekara biyar bata haihuba, har suna tunanin ko na lafiyaba? sunje asibiti antabbatar musu suna lafiya kawai lokacine baeyiba anan yan uwanshi suka matsa mada yaqara aure,yace abarshi da matarshi lokacine.nandae KUBAIB yadawo hannun Ammiey itace komanshi, kwatsam itama tasama ciki murna kam ba,a magana, har ta haifi yarta mace aka samata sunan ANNA wato fatima suna kiranta SABIYYA,gata kam sabiyya nasamu amma duk gatan bai hana sun tsaya sun bata tarbiyyaba,inda ayanzu takeda shekara19 kuma tagama secondry highet institution zataje,saeda sabiyya tayi shekara 15 sannan Ammin taqara haifan namiji mae suna Aayaan,sae qaramarsu Aaufaa. sabiyya tataso cikin shagwaba da tsiwa ga tsojana shiyasama basa jituwa da yayannata KHUBAIB.

CIGABAN LABARI 😊

Part ensu yanufa yaje suka gaisada mamii da daddy,sannan yawuce part dinshi yawatsa ruwa,jallabiyya yasa ashh color yafesa perfformance dinshi da yake using da dare,masallaci ya huce bayan anyi issah yashigo gidan, part din Anna yawuce tareda sallama amsawa tai ciki ciki,yadae mutuniyar naga kin wani hade rai kobakya murna dadawowana ne inkoma yafada tareda zama saman sofa,ehh kakoma tunda dae kai sallamammene MAE dukan mata bakada hali daga dawowa kasa wannan mitsitsiyar yarinyar kana duka da balt kamar an aikoka, tafada tana matsar qwalla.nikuma Anna wana duka daga dawowana?

wannan yarinya SABUYA 😂 haba Anna kema kinsan halin SABIYYA da tsiwa da rashin kunya,nan yafada mata duk yanda akai,sakati tafara tana cewa yau naga shedaniyar yarinya wallahi ba halina kikayiba, bansaniba kocan dangin bafilatanar uwarki ki dauko wannan haliba, har da zuwa kikwantamin afaka.toh wallahi tun wuri fitomin daga dak....kaikuma zauna dan albarka inkawo maka ferfesun da naimaka na kaji mae romo romo,ina cikin dokin ganinka wannan mae kamada tsinken jiki ba auki tazo ta batamin shiri, kasan irin kudin da na kashe gurin hada maka wannan lafiyauyan ferfesun? tun safe ban zaunaba ina abu daya, murmushi kawai yayi yace toh Allah dae yasa kin iya girkin? galala tayi da baki tace hmmm lallai.amma banabi ta halinkuba kaida waccan fingin kawai tashige kitchen din flask din tadauko mishi dan qarami takawo mishi hade da ruwa masu sanyi,ta ajiye batace komaiba,sabiyya kuwa tunda taji maganar nama take abakin qofa tana leqowa tana ganin an ajiye masa tanannade riganta tazo da gudu tadauke flask din ta gudu sae part din mamiij tabar Anna da sakin baki😂, kuka Anna tafasheda tace nashiga uku ni pateee wannan wace irin aljanar yarinyace datasan irin kudin da na kashe gurin hada wannan ferfesun da saeta tausayamin tun safe ban tsugunaba Ina aikinshi.😂😂 shikuwa gogan naku ido ya lumshe ya jingina jikin kujera.......



Follow the AYSHERTY READERS HUB 😘♥ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VabieVQ5Ejy0dPcySR1h


https://chat.whatsapp.com/HrLqaKJbOUD2pf7LpH1gw7


PAGE 9_10


Bata tsaya ko inaba sae part en mamii kallonta mami tayi tace kedawa Daughter wannan irin gudu haka da flask?mami daga gun Ammiey nake shine naga Yaya zae qwaceminn shine nagudo gurinki, nan tazuna tacinye abinta,

Bayan Anna tagama koke kokenta takalleshi taga yama rufe ido tasaki baki tace yo aikai sallamammen ma baka damuba dagowa yayi ya kalleta yace badae ni kikayiwaba tace ehh fa yo wanake dashi in ban makaba? Toh kiqyaleni da ita,inkuma baki bataba insiyo miki wani,kwafa tayi tace kaidin kaidinne taci albarkacinka.murmushi yayi yace toh koh kefa da kya tsaya kina biyewa shirmenta? Yafada tareda ficewa a palourn, part dinshi yaje yakwanta.

Nan suma su daddy da Abba sukazo sukaiwa Anna sallama kowa yanufi part enshiii.



*Ban mance dakuba mutanen arziqi yan AMANATA CE FANS GROUP luv uhh oll 😘*

*Kuma ban mance dakuba yan AYSHERTY READERS HUBB 😘😘 qaunarku ajinina take ALLAH yabar qauna nagode da fatan alkhairynku gareni masoyana*


<<<>>>>>>>

Tundaga ranan bata sake bari sun haduba indai tajishi guri toh zata san yanda zatai bazai gantaba,

Yau yakama sunday da yamma suka shirya itada maryam driver yakaisu wani qaton super market zasuyi siyayya,dama ita SABIYYAn siyayyan kayan bikin ummi qawarta kawai tace zatai,ita kuma maryam driver zae kaita gidansu mamii,

Bayan sungama siyayyanne tace kawai driver yakai maryam ita tahau ko napep ne taqarasa gida,haka kuwa sukai maryam tahau driver yaja suka tafi, tadade bakin titi ko kyallin napep babu dayake manyan gurarannanne bakasafai napep suka fiye shigowa gurinba, har tazo tagaji ga garin hadari yafara hada hadariu, nanfa jikinta yafara rawa dan tunda take bata taba kaiwa haka wajeba ita kadai, wani guy ne yafito daga gurin yazo zae shiga motanshi, iskane yataso sosai tarda qura, mayafintane yacire yabi iska saekan wannan guy din,saejin abu yayi mae qamshi kan fuskanshi, qoqarin motsawa take amma takasa sbd gaba daya jitake kamarma bakomi jikinta, durqusawa tayi tasaki kuka,tana fadin wayyooo Ammina, harya juya sae ganinta yayi duqushe tana kuka,dasauri yadawo tareda mayafinnata ya durqusa gabanta yace yadae babe,sorry ga mayafin naki karba tayi jiki na rawa tasa, sannan tamiqe ahankali tace nagode, murmushi yayi yace bakomai babe amma. Ina zaki haka naga kamar siyayya kikaiko? Ehh tabashi amsa ataqaice,ayya inba damuwa muje inyi dropping naki gida,dasauri tace a,a nagode, haba bae kiyarda dani kinga hadarinema agarin kar ruwa yasauko yataba wannan kykkyawan jikinnaki,gefe taqara matsawa tace a,a, zanje dakaina,hakadae yadunga mata naci har ta yarda dasauri yabude mata front seat tashiga,yasa mata lugagges dinta back seat, sannan yadawo driver seat yayiwa mitan key suka bar wajen, saeda suka hau road sannan yadan kalleta yace babe wani unguwa? Nan dae tafada mishi sukadau hanya, suna tafiya yana mata fira daga uhmm sae a,a shine answernta, har yakawota bakin gate din gidansu yayi perking, ahankali tadago takalleshi zatamai godiya taga ya kafeta da idi, turo baki tayi, murmushi yayi yace woww beautiful, rufe fiskarta tayi tana murmushi tace nagode sosai,, uhmm please zanso insan sunan wannan kykkyawan, sadda kanta qasa tayi kafin tace sunana SABIYYA woww nice name,nikum sunana Aaryan, please babe wallahi tunda naganki naji ina matuqar sonki,please kibani dama in gabatarda kaina gareki,murmushi tayi dan itama tunda taga guy din yay mata, amma sae tai shiru,,uhmmm please beauty please kibani numbernki inyasao sae inzo har gida muyi magana ko, qasa tasadda kanta tace ni banida waya ai,haba beauty kamarki ace bakifa waya wannan ta hannunkifa??? Daqyar dae yashawo kanta tayadda tabashi numbern,dakanshi yazagayo ya bude mata mota tafito sannan ya kwaso mata lugagges enta,yarakota har gate, suna qarasawa khubaib na fitowa zaije masjid ganinsa datai saida yayan cikinta suka hautsina, dakewa tayi amma kana ganinta kasan atsorace take,beauty waye wannan dan da yaganshi saeda gabanshi yafadi,yayane tafada ataqaice tareda karban kayan tai masa godiya tashige, shikuma yajuya yaiwa motanshi key yabar wajen.....


PAGE 11_12

Tana shiga tayi part dinsutayiwa Ammi sannu da gida,sannan tanuna mata siyayyan tabata wa,enda za,akai dinki,
Taawuce upstair tana zuwa ta dora wayanta kan mirrow tafada bathroom tayi wanka tafito tasa sleeping dress tafito tadauko Aaufaa takwantarda ita,itama tahau gado,Ammi ce taturo qofan tace kebazaki sauqo kici abinciba? A,a Ammi naqoshi wallahi,toh mae kikaci da kika qoshi kinsanfa banason wannan rashin cin abincinnaki common kinsakko kokuwa? Turo baki tayi tana kawo hawaye idonta ta sauqo tayi palourn wajen dinning tabufa taje spagetti kawai taci with soup tayi brush takoma,harta fara bacci wayanta yahau ringing tsaki tayi tajawo wayan,bakuwan number tagani bata dagaba har yakatse,can aka kuma kira dagawa tayi tai shiru, hello beauty taji sassanyar murya,shiru tayi saeda aka qara fadin hello are u on the line? Uhmm helloo kawai tace, murmushi yayi yace sunanan Aaryan kinganeni? Ohhina yini? Lafiya qalau beauty ya daren? Alhamdulillah......

pls atayani sharing *Aysherty ce*



_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️



Alhamdulillah tace, yauwa ma sha Allah beauty koh kin fara baccine?uhmm ehh nakusan dae farawa, hmmm beautyna kinsan me? a,a yafada ahankalii, wallahi tun dazun dana gankii naji ina matuqar qaunarki, lokaci daya naji qaunarki azuciyata, please kibani dama inzo in ganki? Yafada yana marairaicewa, uhmm toh aini yanzu karatu zanyi,nayi qarama da aureni tafada cikin yar shagwabar da tasa yanayinshi canjawa, haba my beauty ai aure lokacine ko kin gana ko baki gamaba in lokacin yazo saikiga kinyi,kuma indae karatune nidakaina zan barki kici gaba da karatunki agidana.... Nan dae yadinga janta da fira mae adadii har suka gama wayan takwanta bayan tasanarda shi randa zaizo......

Washe garii da yamma..
Gate din gidan aka bude nan motar Khubaib ta shigo gidan kai tsaye parking lot ya wuce, breaf case inshi ya dauka ya wuce, ta garden yazagaya yazo daedae kujerun dake garden yahango SABIYYA kwance a qudundune,kamar zae huce saedae yatsaya ya qaraso inda take, kallonta yayi itama ta kalleshi yaga yanda take rawan sanyi ga bakinta duk abushe, alaman batada lafiya.tsugunawa yayi kee me kike anan dasauri takamo hannunsa jiyayi jikinta zafii rauu,yaya banida lafiya nakasa tashi,kaina ciwo zazzabi nakeyi,yunwa nakeji,,tafada cikin raki, hade fuska yayi dukda tabashi tausayi kuma yayi niyyar duk sanda suka hadu saeta gane kuranta, amma dayake miskiline yamaze yace toh mae yakawoki nan??? Itadae sae qoqarin shigewa jikinsa take domin

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login