Showing 3001 words to 5521 words out of 5521 words
Chapter 2 - Amanata Ce Book 1 Hausa Novel Complete
baqaramin sanyi takejiba tundazu takasa tashi saboda jirin da takeji, kallonta yayi yadda ta cukuikuyeshi tana rawan sanyi,fuskanta na qirjinshi,, toh tashi muje ciki, kuka tasa mashi tace yayan bazan iyaba jiri nakeji,rasa yanda zae mata yayi kawai yasa hannu yadauketa sukai part din Ammi lokacin da yashiga Ammi na zaune itada Aayaan da Aaufaa sunata mata fira sama sama suna ganin anturo qofan Aayaan yace laaa yaya mae yasamu antyy Ammi anty,dasauri Ammi tataso tace son lafiya mae yasameta? Kaita dakinta nan yayi stair yakaita bedroom dinta yakwantar kan bed Ammi ce taqara tambayansa nan yamata bayanin kimai, Ohhj Allah yagyara halin sabiyya saeda tacemin kanta na ciwo zataje garden duba wasu takardu nace tabarshi akwai sanyi,ashe can din tatafi?
Abba ne yashigo dakin yace yade son batada lafiya ne? Eh Abba nan Ammi tamasa bayani, toh kadubata kawai nizanje mutattauna kan tafiya makarantarta ukn gun yaya toh Abba, Amminma fita tayi taje kitchen dafa mata light abinda zatadanci.
Bude lumsassun idanunta tayi tadorasu kan fuskanshi,shima ita yake kallo,sannan yamatso bakin bed din yadan hau yace meke damunki ? Fuska adaure,, turo baki tayi tana sakin sabbin kwallah tace,ni yaya karkamin allura please,, firgitattun idanunsa ya watsa mata wanda yasata sadda kai qasa
dasauri tana turo baki hadeda shagwabe fuska, kallonda yayi matane yasata fadin tohh nii zazzabii nakeyi da ciwon kai ai,tafada tana hawaye, aikuwa yazama dole inmiki alkura kuka tasa mishi ni wallahi banasi tohh abanmin ciwona, bae kukataba qara tasa,wayyo yayaa zafiiii ahankali yada murza mata wajan sannan yakwantarda ita kan bed, yajuya yabar dakin tabishi da harara tana turo baki ahankali tace,wallahi yana sani yamin da zaf, ahankali kuma ba,a dadeba bacci yay awon gaba da ita.
PAGE 13_14
Banayan Abba yaje sun hadu part din Anna tareda daddy duk suka tattauna kan tafiyar SABIYYA dan ita maryam tace ita a india takeso tayi karatunta gurin uncle dinta (Yayan mami) ita kuma sabiyya dama tun farko UKn takeso, saekuma gashi khubaib nacan,sae suka yanke shawaran tunda khubaib din zaeyi aure sae sutafi tare tayi karatunnata can.haka dae suka tattauna kan lamarin yayan nasu har dae sukai sallama kowa yayi part insa.
Khubaib kuwa Part dinsa yaje ya watsa ruwa,bayan ya fitone yaga miss calls 3quater yasa da T-shartt sannan yadau wayan tsaki yadanja ganin mae kiran kamar ba dazu suka gama wayanba harta sake qira,call din yabi 2rings tadaga tan yanga hello babe ina kasaka wayan ne inata qira baka picking? Murmushi yadanyi yace haba babe dazufa muka gama waya kwata kwata sati nawane? Hmmm babe bazaka ganeba naqagu naga anyi aurennen wallahi, hmmm Banan kenan kamarma kin fini zumudi, hmm haba babe kasan fa yanda nakejinka araina, hmm dagaske?ehh mana babe aikaima kasani,,toh amma ko an daura ba,asatin zamu tafiba sbd zamu tafi da SABIYYA zaa dunga zuwa skul acan sin, DUMMMM haka gaban Banan yafadi sbd ita wallahi tunda taga SABIYYA taji ta tsaneta kwatakwata ko ganinta batasonyi, dan indae taganta ko tajita sae gabanta yafadi, yanaji kinyi shiru babe,,murmushin dole ta qaqalo tace uhmm bakomai ai qanwar muce,har ransa yaji dadin abinda banan din tafada, ahaka dae suka dan taba fira sannan suka kashe wayan, kwanciya yayi yana tunani wannan auran nasa shifa kwata kwata bai tabajin yanson banan ba hasalima bai tabajin komi akantaba, kawai zai auretane kodan maganan da ake yawan yimishi kan aurennan, amman badan yana soba,gashi kuma za,a hadasa da wannan yar rigimar,tsaki yaja hade da lumshe lulu eyes dinshi.
*WACECE BANAN???*
Banan yar shahararren mae kudice wadda akalla zatakai shekara 25,kyakkyawace ba laifi, yar gata agurin iyayenta,su biyu iyayensu suka haifa Banan, da Aayrah,yan gatane na gaban kwatance, ammafa yan duniyane bakadanba, basuda kamun kai ko kadan domin kuwa tsabagen gata da sangartar da suke samu indae kaga banan toh itace hotel wajan alhazai da masu kudi, itace gidan rawa, club, dasauran gurare irin wadannan wanda babu tarbiyya cikinsu, amma kwata kwata daddynsu bayason wannan dabi,ar mummyn tasuce take goya musu baya,tace ai baza,a takure mata yayaba abarsu su shaqata, ahaka yake haquri domin shima baya iya komai akansu,duk ammallakeshi.
Tunda suka hadu da Khubaib lokacin yaje company siyan mota itama taje, tunda taganshi taji tana matuqar qaunarshi har zuciyanta, nan tafadawa mummyn tata itadai saeshi gaba daya ta susuce musu, dahaka ta dinga bibiyansa, har tagane shi likitane nan tasamo bayanansa, haka itada qawarta ishma da mummynta suka dunga bibiyansa har suka tsara plan din za,akai Banan din hospitals dinsu amatsayin batada lafiya emergency haka kuwa suka tsara, bayan tasa wani bakin kwalli idonta, qawarta ishma tataho mata dashi, wanda suna hada ido da khubaib zaejishi atarkonta, dariya sukayi ganin alamun samun nasara yazo,haka kuwa suka dauketa ranga ranga suka kaita,lokacin da suka kaita akai emergency da ita, nan suka nemi khubaib din yadubata daqyar suka samu yazo dan sunci sa,a ranan yashigo, nan yace su fita zae dubata yayi iya dubansa baiga wata matsalaba, ita kuma sae wani fizge fizge take, nan yafita zuwa office dinsa,dasauri tadau phone enshi ta kunna tayi sa,a babu password, nan taduna taga numbernsa, dasauri tadauko phone dinta tadau numbern, dasauri tafita ta,ajiye jin ana murda handle din qofan, takoma takwanta, marairaicewa tayi tana hawaye, please doctor kadubani tafada agalabaice, tausayi tabashi domin shi bayason ganin mace cikin wahala, kuka tasaka masa tana riqe handa dinshi, kallonta yaqarayi yaga yanda take wahala, ahankali yace juya zan miki injection kuka taqara samasa tana juyi,sitake kawai su hada ido ko haqanta ya cimma ruwa, hii you are wastinh my time,yafada yana kallonta tareda jan injection en juyowa tayi suka hada ido,wani irin faduwa gabansa yayi sakamakon haduwar qwayoyin idanuwansu guri daya, injection din da ba,aiba kenan, kawai sae gani tayi ya fice daga room din don wani iri yadingaji awannan lokacin daqyar ya iya kaiwa office dinshi yasa key, ita kuwa su isma suna ganin fitarshi awannan yanayin suka shiga dakin shewa sukasa suna dariya, nam suka tattare kayansu sukai gaba ganin haqansu ya cimma ruwa.....
kwanciya yayi kan sopa dake office din ya lumshe idanuwansa dayakejin sun masa nauyi, gaba daya tunaninta yahanashi sukuni,, tunani yayi kawai yaje yasameta, romm din yakoma amma wayam bakowa. Gaba daya hankalinshi nakanta,ahaka lokacin tashinsa baeyiba kawai yatattare takardun yarufe office din yaja mitarsa yayi gida.
PAGE 15_16
..........Bayan sun koma gida dadare taqirashi ganin bakuwan number baeyi picking ba sae da aka qira sau uku, sannan yayi picking gabansane yafadii dummmm jin muryanta tana fadin yafe doctor, shiru yayi taqara cewa hello doctor i,m your patient some hours back, jiyay hannunsa yagara rawa jin itance, sannan yace where are you going all of you? hmmm bawannanba doctor ainama warke, at first tun lokacin danafara ganinka agurin Hameem motors.......nan tafada mishi irin son da take mishi,shima tsintan kanshi yayi da fada mata irin yanayin da yashiga tun farkon ganinta......
Alokacin da tamatsa mishi da zancen auren, yakai maganan wajansu Abba,sunyi farin ciki jin zaeyi aure, amma daga baya da akai bimciken wacece yarinyar fada sukayi masaa sosai,akan wace irin yarinyace wannan nan yace yaji yagani ita yakeso dasukai qoqarin hanashi, har cuta yayi kamar zae mutu,ganin hakan yasa sukace
Allah yasa hakan ne yafi alkhairy,nan aka tura akai musu baiko aka tsaida ranan biki wata uku ayanzu bikin nasu saura sati biyu.....
*muje zuwa*
taku har kullum Aysherty....
🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌
*Yawan comment react dinku yawan typing* *Sannan kar amanta da sharing please*
*By Ayherty*
*PAGE 17_18
*CIGABAN LABARI*
Bayan sun gama wayan tatashi dagudu tana kuka taje gurin mummy, tafada jikinta mummmy kinji wani rainin hankalii wai da wannan mae kamada aljanun zae tafi idan anyi auren,, whatttt !!! Mummy tafada cikin qarajii, meyake nufi da ita zae tafii, ehh haka yace wai karatu zatai, miqewa mummy tayi tace, ya isa daughter rabudashi kallonta Banan tayi tace inrabudashi fa kikace? Wallahi nasan bawani karatu iskanci dae, ya isah nace, zokiji kunnenta tamiqa mata tarada mata magana,qara tayi tace dagaske mummy, yes kedai kikwantarda hankalinki. Shikenan mum nagane, futa tayi ranta fess, nan tashirya tadau key din motorn ta tayi gidansi ishma domin tattauna yanda events din bikin zae kasance.......
Lokacin da tafada mishi cewa yayi shifa inma za,ai wani ecent to iya dinner kawai za,ai rana daya, kuja tasa masa tace duk qawayena kowa abikinsa ana kece raini amma ni rana daya za,ai ganin zata daga mada hankali yasa yace taturo account dinta sufadi nawa suke buqata yatura musu, su suje suyi, shi badaban friends dinsa da zasuzoba, shi baiyi niyan yin kowani events ba.
Haka rayuwa taci gaba da juyawa,kwanci tashi asarar mae rai!!!
Yau yakama thursday iya yau zasu kawai zasuyi event dinsu coz khubaib yace yafison daurin auren friday, don sunday zaeyi resuming work, kuma bayason bidi,oeh a bikinsa,dan wadannan event dinma dazasuyi daqyar yayarda, da cewa yayima bazaejeba amma tunawa da yayi friend dinsama zasuje haja yahaqura, daqyar ta kalallameshi yayardan zaije.
Tun safe suke shirye shirye, gidan har yacika da yan uwa, su Amina ma qanwar su daddy (anty meena) duk sunzo da yayanta, su uku, dangin babansuma wasu sunzo sunata borin kunya ganin yanzu suma sunada abin duniya. Yan uwan mamii kuwa ba,a magana dan bikin dan gatan famiky ake.
Da dare around 8:30 duk sunci ado dan yau kamu zasuyi kuma a friends and family event center za,ai, sunata hidima Ango yasha wata dakakkiyar shadda skyblue yar ciki da babbar riga, yasa wata tsadaddiyar hula dark blue,yasa wani black covershoe, yadaura watch dinsa mae masifar kyau yafito shar dashi ga kannan nashi da face nashi sunsha gyara yanata qyalli kaii ma sha Allah kawai nace, motocine maqil qofar gidan anata daukan mutane zuwa friends and family event center gurin da za,ai Dinner.
Daga wanka tafito tana tsane jikinta da towel, dan tun dazu tazo part din mamii dan kayansu yanacan itada maryam adakin maryam din, maryam tuni taqosa da jiranta, dan da cewatai kanta na ciwo bazataba, nan mami tace tayi zauniyarta, maryam kuwa taje tafadawa Ammi, nanfa Ammin tarufeta da fada kan cewa setaje, nandai tagama zumbure zumburenta tashiga wanka,da maryam tagaji dajiranta kuma da Ahsan dinta zata tafi amotarsa ( dan gidan uncle Jaid inda zataje karatu india suma aikine yamaidashi can).
Tunda bikin yayan yatashi gaba daya takejin badadi, itadai tasan ba farin cikine batayiba amma tarasa dalilin faduwar gabanta,gashi za,a hadata da wannan matartasa, da kowa yasan duniyancinta.
Daqyar dae tashafa mayujanta masu qamshi tayi dan light make-up dan uta bason tafiyan takeba, sannan tasa jewelries dinta na gold masu kyau, sannan tadau diguwan fitted gown dinta tasa dark blue, tayi dan simple steps akanta, tadauko takalminta dark blue maedan tsini tasa, sannan tayafa dan mayafinta blue maedan duhu kadan amma yanda dan haske, ga hannayenta sunsha lalle kaii ma sha Allah kawai nace danaga tafito, dakin mamii tashiga tayi sallama, wowww ma sha Allah daughterna kinyi kyau sosai, amma ya,akai kikai late haka dun kiwa yatafi? Sadda kanta qasa tayi tace shiryawa nai mamii, toh daughtena yanzu wazan samu yakaimin kee, kowa yatafi tunda dinner dib yana dayane, shiyasa kowa yatafin, toh mami nahau napep kawai, zaro ido mami tayi tace daughtena napep fa kikace rufamin asiri, kidau wannan wankan kicemin kyahau napep??🙊 uhmmm kawai sabiyya tace,
Mamin ce tace bari inkira wannan miskilin muji in basu tafiba su ajiyeminke, dummm haka taji gabanta yaqara faduwa, mae yakeson faruwa danine tafada cikin ranta. Muryan mami ne takatseta daga tunanin datake jin tana cewa, kun tafine!? Bataji mae yaceba, mami taqara cewa bari daughtena tafito kuyimin dropping nata okay? Toh kawai yace, dan yasan rigina kawai za,a hadasada.
Yauwa daughter maza kije suna parking space zasuyi dropping dinki zuwa waje,okay mami saena dawo, kidafamin hallop cius cous, dan yau anan zan kwana sannan tafice bata jira cewan maminba, murmushi mami tayi tace uhmm daughter rigima yau kuma nan za,a kwana kenan, nandai tacigaba da harkokinta da aiyukanta dan tace baza taje wajan shashancinnanba.
Kar amanta da Comment, reac, share.
PAGE 19_20
Gaba daya ranshi yagama baci, sabida jiran dasuke mata bayason jira kokadan,tafiya take amma kamar bazata takaba,daqyar taqaraso gurin moton, back seat yabude nan tahangoshi ciki gaba tabude zata shiga sanin cewa back seat na Amaryane,amma saetaga kaya aciki, rufewa tayi tashiga back din tarufe tazauna, wani irin sayi da qamshine ya ziyarci hancinta mae dankaran dadi, tazauna yanda kasan itace amaryan tsabar dacewan dasukai, harara ya dalla mata sannan yace ubanwa yahanaki bin mutanen da sae yanzu zaki batawa mutane lokaci!?? Dan bakinta na tsiwa taturo gaba tace toh badae mami ce tace kutsayani ba!? Kuma ni ai shiryawa nak.... Tsaki yaja yace shhhhh bansan jin komi, tura baki tayi takauda kanta gefe tana kallon window, nan wani friend dinshi jameel yajasu suka tafi tareda kunna musu kida. Kadan kadan yana tashi sukai gidan su isma don daukota.
<<<<<<,Idan ran Banan yai dubu yabaci sbd jira tun dazu take kiranshi baya picking,shi baimasan tana kiranba wayan na silent, suna zuwa ana fito da ita itama tasha kyau ba kadanb tasa street gown pinck color mae uba tattara tayi kayu da anmata dauri dark pinck net din da tayafa kuma light ne sae hill shoe light pinck. da jakanta, tayi kyau ma sha Allah,