Showing 21001 words to 24000 words out of 45625 words

Chapter 8 - Hamdah Book Three Complete Hausa Novel

Rasheeda   

17 Oct 2025

200

basu san komai ba, amma nasan akwan atashi idan hakan yaci gaba da faru zasu tashi da abun a ransu,
nasan ɗaci da kunar dake tattare da kuncin ganin UWA cikin damuwa game da ɗan ta, dan kuwa shike hanani sukuni a koda yaushe.
wasu hawaye ne masu zafi da kuna suka cigaba da wanke min fuska cikin jan sheshsheka nashiga faɗin
"Ummi na kizauna gidan Abba Ummi bazan taɓa yafewa kai na ba har idan nayi sana diyyar barin ki gidan Abba, Ummi na zancigaba da yin nesa dake har idan hakan zai sa ki cigaba da zama gidan Abba."
kuka sosai ya kwace min cikin muryar kukan nacigaba da faɗin
"Abba wlh ban ai kata zina ba ban taɓa ai kata zina ba, Abba zan cigaba da yin nesa daku har idan hakan zaisa Ummi na tacigaba da zama agidan mu, bana so nayi maraicin uwa batare da tabar duniya ba,
Abbu Mamie Ya Masa'ud Auny Rafee'at Aunty Jaleela Nusaiba Fauzaun, kewan ku da begen ku yana hanani sukuni,kullum da ku nake kwana cikin raina, shin haka kuma kuke kewata ina son ku ko da yaushe ina tare da ku a cikin zuciya ta,
ku yar da dani wlh ƴaƴana ba shegu bane, wlh Allah ban taɓa zina ba,
Allah sarki Inna ta da kina nan da kin faɗa musu kalar tarbiyyar da kikayi min wan da ko da agidan karuwai zan zauna bazan yi iskanci ba, bazan yi ba, bazanyi ba,
Ya SALEEM Ya SALEEM Ya SALEEM me na tare muku kai da matar ka meyasa zaka rabari da *MAHAIFIYA TA* karabani da ahalina me nayi muku, me yasa zaka sheganta min ƴaƴana tsaftatattu ka dan ganta su da wani uba wan da bansan ko waye shiba,
duk hakan na menene da har sai ka kazanta min ƴaƴa? ƴaƴa na ba kazan ta bane kamar yadda ka faɗa ƴaƴana tsaftatattu ne bazan taɓa yafe maka Ya SALEEM bazan yafe maka b...."

Kuka ne yaci karfi na nakifa kaina da guiwa na nayi ta kuka kamar raina zai fita.
najima sosai zaune a gurin ina ai kin kuka, mai cike da kuna da bakin ciki. da kanshi hawayen ya tsaya badun na tsai da shi ba, sai dai kukan zuci danake, a hankali na mike cikin matsananciyar ciwon kai wan da dakyar nake iya buɗe idona duka sabo da zafin ciwon kan, na nufi ciki.
direct bedroom na shige kana shiga bathroom wanka nayi nafito na sauya kaya na zo na kwanta bakin gado,
karatun Alkur'ani na kunna cikin wayata a hankali nake bin karatun, a sannu narika jin zuciya ta tana samin salama da nutsuwa, a hankali narika jin bacci na fizgata ta, na lumshe idanuna.
can cikin baccin da ya ɗauke ni da nisan ta baifi na minti 20 ba.
najiyo muryar su Nasmah, da gudu suka haye gadon suna faɗin
"Mommy mun dawo Mommy mun dawo."
ida nuna na rumtse da ɗan karfi dan har lokacin kai na bai bar yimin ciwo ba,
mike wa zaune nayi jin sun zube a jikina na ɗago su ina faɗin
"Wai har kun dawo? amma dai ba'a tashi ba ko."
nayi maganar ina duban agogo, karfe 12 har da rabi,nayi mamakin gani in da lokaci yatafi har haka, ranar yau karfe 12 saura suke dawowa har sun dawo anyi musu wanka an sauya musu kaya.
lallai najima ina kuka har ban san lokaci yatafi har haka ba, tausayin kaina ya kamani, ɗan guntun kwallar da ke kokarin sauka a idona ɗaya nayi saurin kai yatsata na tare shi kana na gyara zama ta ina faɗin
"Ashe dai lokacin tashin naku yayi, to yaya karatu yau ansha wasa ko."
nayi maganar ina shafa kansu.
baki Nasmah ta washe ta mike tsaye a kangadon tace
"Mommy yau Aunty'n mu tayi mana haka."
tarike kugu tare da girgizawa, dariya nayi ina faɗin
"Au kice yau Aunty rawa tayi muku."
"Ba haka bane haka ne".
Naseem yafaɗa tare da mike wa yarike kugu yasoma tsalle.
ido na ware nace "Kai kuce yau kunsha rawa." cikin tsallen yace "Eh ai hadda chocolate ma."
tsai da tsallen da yake yayi sai kuma ya dira a godon da gudu yafita sai gashi ya dawo da School bag ɗin sa, a tsakiyar gadon ya zazzage School bag ɗin sai ga Chocolate masu yawa haɗe da littattafan sa sun zubo,
da mamaki nace
"Yau kuma Talatu kayan zaki tacika muku a jakar."
nakai hannu na ɗibo chocolate dasuka kai guda biyar kala daban daban, ga kuma wasu a gaban sa, da ɗan mamaki nake kallon su dan asanina babu kalar waɗannan chocolate ɗin acikin kayan cime-cimen su kalar nasu ba irin wannan bane.
"Kai Naseem a ina ka samo waɗan nan chocolate ɗin?."
nayi maganar ina duban sa, da sauri Nasmah tace
"Nima akwai nawa." ta dira agadon da gudu tayi waje, Naseem ko bai bani amsa ba sai kokawar buɗe laidar chocolate ɗin yake.
ta shigo da school bag ɗin ta itama ta zazzage, nace
"Kai wai waya baku wannan abun haka, Talatu Talatu."
nashiga kwaɗawa Talatu kira dan na fara tunanin ko rikici sukayi mata gun shirya su tabuɗe wani katon ɗin chocolate ɗin daban.
Naseem da yakai Chocolate ɗin baki ya kutsura yana ɗaga kafaɗa alamun yana jin daɗin abun yace
"Daddy yace mucinye wannan duka dai kaya mana wani."
"Ai yace idan ka kaiɓa min baye kaya maka ba ni de bani da yawa."
cewar Nasmah tana kai wan da ta ɓare baki.

Ido da baki na waro da mamaki tuno wan da suka taɓa kiran sa da Daddy a makarantar su nace "Wani Daddy mutumin nan ko?, a ina kuka san shi dan gidan ku da har zaku rika ce masa wani Daddy."
Naseem daya cika chocolate a bakin sa yace
"Ai Daddy yace kuma dai jo ya auke mu ya kai mu can guyin kifi babba."
cikin tsawa nace "Bana ce muku kada wani yasake baku abu ku karɓa ba? ashe bakuji ba so kuke nazane ku ko?, bana ce muku nice Daddyn ku nice Mommy'n ku ba, shi ba Daddy'n ku bane, baku san shiba shima bai sanku ba, bakuda Daddy nice Daddy'n ku, kuna jina dai ko?."
nariko kunnuwan su ina jijjigawa a hankali, suka gyaɗa kai.
shiru nayi tare da komawa na jingina bayana da jikin gado jiki a sanyaye nashiga maganar zuci
"Kuhi hakuri ƴaƴana ni zan cigaba da zame muku uwa kuma uba a duniyar na."
jin kwalla nakokarin zubomin nayi saurin dakatar dashi...

A ranar nasa aka kawo musu chocolate dawsu kayan makulashe aka kara kan wan da yake gida.
washegari ranar asabar bamu wuni a gida ba yawon guraren shakatawa muka tafi, ni Faty Naseem Nasmah da kuma Talatu, sai direba. sai yamma muka dawo niki niki da kayan makulashe, washegari ranar Lahadi ma muka kuma fita, shima sai yamman muka dawo a part ɗin su Inna wuro muka yada zango sai bayan isha muko koma side ɗin mu, ai ko muna shiga su Nasmah suka ɓingire da bacci.
koda gari ya waye dakyar nata da su Talatu ta tafi da su dan yimusu wan ka da shirin makaranta, dan tare jiya muka kwana da su.
kamar kullum na rakosu muna ɗagawa juna hannu suka fita.
ina komawa ciki wanka nayi nashirya cikin les copie colour da ɗan ratsin gold ajiki,
da misalin karfe 10 da rabi nasauko kasa da mayafi akai na sai ƴar karamar jaka mai ɗauke da wayoyina da wasu ƴan kuɗi dana saka ciki,
dinning area na nufa, in da na tadda Zulai tagama shirya komai na breakfast, a ɗan gaggauce nayi breakfast ɗin, ina yi ina duba agogo, dan fita zamuyi da Bappa zuwa asibitin da ake ginawa dasunan Inna ganin yan da ai kin ke tafiya, ina saurin ne dan jiya nace mishi karfi goma da rabi zamu tafi nasan kuma yanzu haka yagama shiri ni yake jira.
koda na fita a kofar masallaci dake ta nan cikin gida na taddashi zaune, na karaso in da yake tare da gaida shi, daga nan muka shige mota muka nufi asibitin.
masha Allah asibiti yayi kyau saura kaɗan a kammala aiki, bamu bar asibitin ba sai wajen karfe 12:20pm nacewa Yakubu muwuce makarantar su Nasmah mu ɗauko su.

Abakin get ɗin makarantar Yakubu ya faka mota yafita da sauri yana faɗin
"Bari naje na fito da su". yayi cikin makarantar da sauri, muna nan zaune can yafito da sauri kamar zai kife kasa yakaraso gefen da nake yace
"Hajiya wai an zo an ɗauke su."
ido na waro da mamaki nace "Wa yazo ya ɗau kesun bayan kai muna tare da kai ina ce kai ne me zuwa ɗaukar su."
Bappa yace "Zancen banza kai wani direban akayi musu sabo ne da zaizo ɗaukar su? ko dai bakaji abun da suka faɗa da kyau bane?."
yace "Wlh haka mai gadin yafaɗa Bappa."
da sauri Bappa ta buɗe motar yafita ai ko nima da sauri nafita narufa masa baya har ina haɗawa da sassarfa.
babu kowa cikin makarantar sai mai gadi da masu kula da tsaftar makarantar sai shara da goge-goge suke, hankali tashe Bappa ke tambayar mai gadi, mai gadin yace
"Ai ko minti goma basu da tafiya ba duk ɗazu muna tare da su anan da wasu ɗaliban mota tazo tafaka nan bakin get suna ganin motar suka zuba a guje zuwa gurin motar suna murna, da naso hanasu dan ganin ba ɗaya daga cikin irin motocin da ake zuwa ɗaukar su da shi bane, to ganin yan da suke ta murna sukayi gun motar a guje yasa nayi tunanin ɗaukar su a kazo, dama badaga gida akazo ɗaukar su ba!."
maigadi yakarashe maganar yana buga kirji.
Yakubu da gumi yafara keto mishi kamar zai fashe da kuka yace
"Ina ni ke zuwa ɗaukar su kuma gani a gaban ka sai kuma hajiya wata rana,ko mutumin yasako irin fuskata ce ya zo."

Bappa yace "Amma kuwa abun da mamaki amma ya kamata lokacin da kaga ba ɗaya daga cikin motocin da ake zuwa ɗaukar su da shi bane yazo kama yayi kaje kaga ko waye ne,amma wani abun mamakin da kace wai sun je gurin motar da gudu kuma suna murna to ko wani ne daga gida yazo ɗaukar su tun da sun san mun fita har da direba?."
ni dai kasa magana nayi sai ɓari da jikina yake cikin matukar tashin hankali tuni idanuna suka kawo ruwa kan kace me hawayen suka fara sauka.
murya na rawa Yakubu yashiga tafa hannu da salati yana faɗin
"Dama ance yanzu masu garkuwa da mutane sun canza salo akwai wani abun da suke yi sai dai kaga mutum na ta binsu kamar ya sansu harsu tafi da shi, wayyo Allah Naseem da Nasmah ko dai sune."
cikin gwalalo ido mai gadi yace
"Wayyo Allah nashiga uku wayyo ai kina shikenan dama ance idan aka sami matsala to abakin ai kina, ashe dama tsarin da masu garkuwa da mutane suka fito dashi kenan? shi yasa yarannan sukayi ta tsalle kamar doki suka ruga in da motar take, ashe jansu ake taciki kamar kuran karfe."
ɓarin jikina ne yakaru yayin da zuciya ta ke bugawa da karfi gudun hawaye na yakaru.
Bappa yace "Kai ya isa haka Falyakum khairan au yasmuq, in sha allahu babu abun da zai faruku muje gidan mugani wata kila daga gida ne akazo aka ɗauke su tun da sunsan bama gidan."
yadube ni yana cigaba da faɗin
"Kice Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un."
kalmar nashiga nanatawa kana muka juya gun mota, muka bar maigadin nan tsaye yana ta rafka salati dafaɗin shikam yau yasan ai kin sa yazo karshe har in sace yaran akayi.
acikin mota Bappa yarika zuba addu'o'i yakuma hanani kukan danake shirin yi yace nayi ta faɗin
Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un.
a haka muka isa gida.

Muna isa Yakubu yayi hon maigadi ya wangale get yana kokarin wucewa parking lot nace
"Ka sauke mu anan."
dan gani nake kamar motar bata tafiya da sauri tsabar tashin hankali.
tun kan ya dai-dai ta parking muka fito daga motar maigadi yakaraso yana mana sannu batare da dukkanmu mun amsa ba Bappa yayi saurin cewa
"Wayaje ya ɗauko su Naseem a makaranta a cikin ku?."
maigadi yace "Gaskiya babu wan da yaje ɗauko su dan tun da kuka fita ma babu wan da yafita, yau kam sunsha zama a makaranta Yakubu yayi hanzarin zuwa ɗauko su."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un an ce anzo an ɗauke su kuma kace ba wan da yafi tun fitar mu an sace su kenan."
nayi maganar tare da fashewa da kukan da Bappa ketasa ni danneshi, nacigaba da faɗin
"Ina suke ina suka shiga waya ɗauke su.".
maigadi ya walalo ido tare da faɗin
"Iye! ansace su!."
Bappa yace "Ka tabbatar da babu wan da yafita."
yace "Wlh babu wan da yafita tun fitar ku ina bakin get ɗin nan........!





Mommyn Twins ce







7



HMD WASA FARIN GIRKI!



Littafin na siyar wa ne kibiya ki karan ta my no 08034690723




Mai gadi yashiga jan hanci yanaci gaba da faɗin "Sam babu wan yafita ai da nasani dana shiga ciki naje na karɓi makullin mota naje na ɗauko su ai, na ɗan iya mota ba sosai ba amma da wasu su ɗauke su gara ni naje a haka na ɗauko sun, wasu matsiya tane masu niman jaraba suka ɗauke su, duk tai makon da akewa mutane baiyi musuba har sai sun haɗa da sata, wayyo Allah Naseem wayyo Nasmah, ashe da rabon ragowar shayi da nama gobe bazan shaba, kullum sai sun kawo min na haɗa da nawa duk na kallame."
zuwa yanzu tashin hankalin Bappa yafara bayyana yashiga faɗin
"Kanu innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un Allahumma ahjirni fi musibati²."
bakina na toshe da tafin hannuna jin kuka mai sauti yana son suɓuce min najuya ina kokarin barin gurin Bappa yakira sunana najuyo ina hawaye yace
"Je ki zauna kada ki ɗaga hankali sosai na tabbata zasu kira kuma bazasu cutar da su ba dan kuɗi suke bukata za'a kuma basu babu komai."
kai kawai na gwaɗa najuya nasoma tafiya, maigadi yabiyo ni yana cigaba da jan hanci yace
"Anyi bako Hajiya."
ban iya juyowa ba bare nabashi amsa Bappa ne yace "Ina bakon?." yace "Gashi can a mota yana shigowa kuma kuka shigo,"
"Wanene?." cewar Bappa, yace
"Gashi can cikin mota ai da naso hanashi shiga ganin baiyi kama da irin waɗan da za'a dakatar ba shine na barshi ya shigo."
yayi maganar yana nuna wata mota dake fake gefe a farfajiyar gidan.
Bappa ya girgiza kai kana ya soma tafiya yana faɗin.
"Ana cikin wani hali ta ya za'ayi a saurari wani bako."
Cikin matukar da muwa da tashin hankali nake tafiya, "Me zaisa su ɗauke su in dai kuɗi ne akan su ɗauke su ni da sun faɗa min ko nawa ne zan basu, me yasa suka zaɓi su cutar da yaran da basujiba basu gani ba.
wlh Allah sai yabi musu kadin su tun suna ciki ake cutar dasu da zaluntar su, har suka fito duniya."
wasu zafafan kwalla ne suka rika wanke min fuska bana ko iya ganin gabana, tunani na ɗaya awani hali suke yanzu..
Bappa har ya wuce motar da mai gadi yace masa bako ne ciki, sai kuma ya dawo sanin da yayi kan cewa bako rahama ne,
gilashin motar ya kwankwasa, a hankali aka zuge glass ɗin.
cikin matukar mamaki Bappa ke lallon mutumin da waɗan da ke tare da shi, yana zaune a mazaunin direba waya na rike a hannunsa yana ta faman latsawa, Nasmah na zaune a gefen sa tasaka kanta jikin kafaɗar sa tana ta cin chocolate, Naseem kuwa na zaune a gefen mai zaman banza rike da waya a hannunsa yana buga game yana kuma taunar chocolate.
cikin tsananin matukar mamaki Bappa ke cigaba da kallon mutumin da mamakin ganin sa tare da su Naseem,
tabbas bazai taɓa mance wannan fuskar ba, mutumin daya samar musu da ingantaccen ilimi a rugar su,mutumin da ya yayi ruwa yayi tsaki wajen ganin an cafke ƴan ta'addan da suke shiga rugar su suna kaɗa musu shanukai su kashe musu makiyaya.
cikin girmamawa mutumin yashiga gai da Bappa, Bappa ya amsa fuska ɗauke da annuri yana yi masa kallon sani, shiko mutumin ga duk kan alamu bai gane shiba, cike da al'ajabin ganin su tare da su Nasmah Bappa yace,
"Ikon Allah kai ne nan tare da su Naseem da muke zaton ko ƴan garkuwa da mutane ne suka ɗauke su."
da sauri Bappa ya juya yana faɗin
"HAMDAH taho gasu nan."
cak naja na tsaya dai-dai lokacin dana ke kokarin ɗaura hannuna jikin kofar side ɗina, najuyo da sauri, magana Bappa yaci gaba dayi yana nuna cikin motar.
"Gasu nan cikin mota Allah yayi ikon sa."
dagudu na nufo gun motar ina share hawaye na da bakin mayafi na,
ina isa gun motar nawuce gaban Bappa da sauri batare da duban cikin motar ba duk da glass ɗin motar a sauke take, hankali na nakan murfin motar dana saka hannu ina kokarin buɗe motar sai jin ta nayi a rufe, da sauri na ɗago karaf idanun mu ya haɗu da juna, da mamaki nake kallon sa sai kuma nan take naji raina ya ɓaci,
mutumin da yace wai arika turo mai wayo yarika ɗaukar su Naseem a school ba ni ba, wan da kuma suke kiran sa da Daddy yayi ta tara musu chocolate kamar sun zama shazumame sar kin shan zaki.
fuska na ɗaure tamau ina duban su Nasmah nace
"Ku sauko nan!." nayi maganar cikin tsawa da zare idanuna.
Bappa yaɗan matso yana faɗin
"Wlh mun shiga tashin hankali sosai da akace wani mota daban yazo ya ɗauke su ba ɗaya daga cikin motocin gidan nan ba, mungama zaton masu garkuwa da mutane ne, suka ɗau ke su."
kai ya jinjina tare da yin murmushi wan da yayi sana diyyar bayyanar kyakkyawar dimple ɗin fuskar sa, batare da yayi magana ba ya kai hannu ya buɗe marfin motar, baya na ɗan ja kaɗan ya buɗo marfin, ya zuro kafafun sa waje, Nasmah dake gefen sa yaɗago ta cak yafito da ita ya aje ta kasa, kana asannu yafito daga cikin motar,tsayuwar sa ya gyara kana yaɗan sunkuya jikin kofar yamika hannu cikin motar Naseem ya rike hannun nasa yaɗago shi cak yafito da shi, sai da ya ajiye Naseem kasa kana ya ɗago da murmushi yace.
"Idan za'a cigaba da barin su har kowa ya watse a makaranta ba'a je ana ɗaukar su kan lokaci ba to kuwa zasu iya fuskantar hakan,domin su masu garkuwa da mutanen babu ta in da basa nan."
kai Bappa ya jinjina cike da gamsuwa da maganar sa kana yace
"Tabbas kuwa, Allah yashiga sakanin nagari da mugu."
a kufule nace
"Babu ranar da ba'a zuwa ɗaukar su kan lokaci in ban da ranar da nayi ta kiran Yakubu bai ɗaga ba, sai kuma yau, yau ɗin ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login