Showing 21001 words to 22137 words out of 22137 words
. Ba tare da ya zare Alƙalamin nasa ba ya kai hannun sa yana Ɗaga kiran . "Hello Daddy" .
Ya furta in a lower Voice , a kasalance tamkar mara laka da kuzari a jikin sa .
Cike da Rashin jin daɗin ɗabi'ar Maleek Daddy yace " Maleek are you Okay ? What happened to your manners? Is that the way to approach your elders or parents you see ? Tarbiyyar da Muka baka kenan ? Ka daga Waya na ba Gaisuwa ba komai yau kwana nawa... Daddy I'm very sorry . "Good Day Dad" . Ya katse Mahafin nasa cike da ƙasa da Muryar sa da ladabi kaman ba shine mai Baɗalar nan ba.
Ka taho gida yanzu ina son ganin ka Maleek . Abun da ka dade kana Aikatawa a America ya biyo ka har ƙasar ka ya cimmaka .
Wani irin sarawa kan Maleek yayi Zuciyar sa na masa tunani iri iri nan take . Motsa laɓɓan sa yayi tare da kiran sunan mahaifin nasa "Dad..."
Cike da fushi Daddy ya katse Sa yana cewa " baturiyar da ka yaudara yar ƙasar London yau ta sauka har gida , don haka mintuna talatin na baka ka taho yanzu . "Ƙit " Dad ya katse kiran yana barin Maleek da waya a hannu . A hankali ya furta "Jenny" . Jenny ce ta biyo Ni har nan? Wani irin gumi ne ya karyo masa , zafi da raɗaɗi gami da tashin hankali na shigar sa . Wani mataki Daddy zai Ɗauka yanzu ? Dole da matsala babba .
**
Tun da Suka isa Gidan Billy Hasile ke rarraba ido komai bin sa take da kallo a ƙauyance , gani take tamkar ba a duniyar da ta sani take ba . Wayyo Aradu Wannan Nine....Nine fa....Hasile ce wannan Ko Adda .? Tayi maganan da ƙarfi tare da nuna kan ta a jikin wani tanfatsetsen Glass dake hasko masu komai na falon .
Murmushi Billy tayi tana kai hannun ta tare da kama Hasile kana tace " Kwarai Wannan Hasile ce ɗiyar Fulani . Sabuwar Rayuwa kenan Miki , inda zaki yafi wannan ma .
Cike da rashin Fahimtar gundariyar Hausan na Billy Hasile ta cigaba da kallon kanta tana Washe baki tare da Ƙara faɗaɗa fara'ar ta. Muryar Billy taji tana cewa " Hafsat Ga Baraka itace zata gyara mini ke yanzu ku haura sama ina zuwa .
Kallon Wacce aka kira da Baraka Hasile tayi kana ta gyaɗa kan ta tana bin bayan Baraka dake bin Hasile da kallon tausayi tare da tunanin Kin shigo cikin baƙar rayuwa ba tare da Sanin Ki ba dana iyayen ki . Yanzu Hajiya Abun nata ya koma Har da yara Wanda basu san komai ba ? . Haka Baraka tayi ta saƙa magana a zuciyar ta tana riƙe da hannun Hasile suka haye Saman benen falourn Bilkisu Billy .
"Hummm" Ajiyar zuciya Billy ta sauke tana sakin Murmushi tare da tunanin An fara cin rabin aikin , yanzu saura kaɗan . Wayar ta ta fiddo tana Fara latsa kiran Aminiyar ta Nihla don da ita ne zata iya cimma burin ta na ganin Bayan Maleek .
Ƙwance Nihla take a ƙayataccen bedroom din ta , idanun ta a kunshe hawaye na gangaro mata . Sosai ta tsorata da ganin Jenny a rana guda a kuma lokaci irin haka ? Wannan Kyaƙyƙyawar ya wulakanta wacce ta fini kaman sama da ƙasa ,to ina ga Ni Nihla? Kuka take yi sosai a wannan sa'ilin dai dai nan kiran Billy na shigo mata .
A hankali takai hannun ta tana Daukar kiran , kana. Muryar Billy ya katse ta tana cewa " Nihla ya kk ya kayan Dadi kuma ? . Kamin Nihla ta bata amsa ne Billy ta cigaba da cewa " Ga sabuwar Wata baƙauyiya da na samun Miki wacce zata nado Miki komai na Maleek zan kawo Miki ita a matsayin yar Aiki daga nan sai ki kaita Part ɗin Mahaifiyar sa , Bayan zamu san yanda zamu sadata dashi ...... mtswwwww " . Tsakin Nihla ya katse Billy kana ta fara cewa " Wacce baƙauyiya? Kin san halin da ake ciki yanzu ? Akwai matsala babba .
Matsala ? Billy tayi maganan tana mikewa daga tsaye kana ya cigaba da cewa " Meke faruwa ? . Cikin kuka Nihla ta kwashe mata labarin komai tana sanar mata ,kana ta cigaba da cewa " Wannan fa baturiyar ba zata tafi ba, kuma Ni naga tausayawa a idon su Ammie akan labarin da ta zaiyana masu na rayuwar ta da Maleek. Kai Maleek mugu ne , mayaudari me zai yi dani dama , yana da irin Wa'annan .
Kai Nihla amma na raina tunanin ki. Ki yarda dani Maleek zai So ki ya kuma kaunace ki . Amma sai a yau kin amince da shugiwar Hasile RAYUWAR sa....!
Dan shiru Nihla tayi kana tace " Tayaya.? . Wani murmushi tayi kana tace natsu zan Miki bayani .
Indai zan samu Maleek komai zan iya yi . Yanzu ki fara zuwa da yarinyar sai mu shirya komai . Alright , Muna hanya .Billy ta furta tana sakin Murmushi tare da datse kiran .
**
Habawa Baiwar Allah , mai companin ne ba zaki barni na gansa ba ,tsawon kwana takwas ina zuwa amma kin ƙiya ?.
Juyowa Sectaryn tayi tana watsa mata harara kana tace " Ke ana daukar masu digiri da masters ke babu ɗaya kizo Kice kina son magana da mai Company ? To a matsayin ki na secondary certificate me kike so a baki , sharan kamfani ko goge goge?. Takaici ne ya kama Zuciyar Matashiyar kana a hankali tayi baya tana kokarin komawa ne , nan take manager ta fito daga Office din Ogan nasu . Hello young lady...! Baiwar Allah. Ta kuma kiran matar da sunan a karo na biyu . A hankali ta juyo kana tace " yace ta shiga , miss Laurat ki barta wuce Oga sir yana son ganin ta .
Cike da mamaki Sectaryn ta bata wuri tana cewa managern wato Madam Ayawa" Ok ma".
Buɗe mata kofa tayi tana shiga da tsumman jikin ta . Wani irin haske ne tagani yana haskaka idanun ta , tsoro da mamaki suna rufa mata a lokaci guda . Wani irin gizo gizo take gani tamkar shi tamkar bashi ba . Cikin wani irin Rawar murya ta ambato sunan sa hannun ta dafe a ƙirjin ta " Rayyanu......! Rayyanu kaine dai nake gani da ido na ? Kaine tsohon mijina Rayyanu dana sani.............?
*To masu karatu anan na kawo karshen Free page ga masu buƙatar cigaba da karanta littafin mr romantic Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409*
MAMAN TEDDY.