Showing 57001 words to 60000 words out of 81054 words

Chapter 20 - Buri Daya Book One Complete Hausa Novel

nake tuno kamannin wancan hoton wlh itace....

Daga Palo Ina cikin kalle kalle saigashi ya fito palon daureda towel fitowarsa wanka kenan yafito daukar wayarsa daya Bari nan.

Cikeda mamaki da takaici yake kallona nikuma cikeda mamakin da qaunar tsananin kyawun fuskarsan nake kallonsa sbd Sam ban gane cewar shi bane Saida yayi mgn na ganesa take na rikice masa sbd tsoro da fargabar mutum daya da fuska biyu.

Ganin haka yasa ya zaunar Dani yamin bayanin Wai qonewa yayi Kuma baason iska na hawan gurin saiya warke shiyasa ake rufe gurin to idan aka rufe nan kawai saiyanayin wani iri shine ake sauya fuskar gabaki daya Amma yasa na masa alqawarin bazan taba fadawa kowaba ciki har iyayena nikuma na masa alqawarin bazan taba fadaba sbd Ina sonsa......

Wani wawan Mari am ya dauketa dashi a haukace yace"

Kinsan waye wannan???
Fatalwace ba mutum din gaske ba ya Dade da mutuwa da hannuna na kashesa shekaru sama da biyar dasuka wuce,
Wannan balai ne,shi masifa ne, marainiya zai maidaki gaba da bayanki Dan kuwa daga dad,mum harni wlh kinramu shikenan maraici zakiyi wannan alqawarinsa....

Jijjigasa fammah tayi da qarfi tana kuka sbd ganin ya haukace lokaci daya sai surutai yakeyi jikinsa na mazari tace"

Am pls stop all this Ni bana gane komai all I want is wannan tashin hankalin ya wuce muyi rayuwa kamar kowa cikin kwanciyan hankali,

My haydar bazai taba cutatarda familyna ba,
Shi ba mugu bane bazai muna komaiba,Yana Sona bazai cutatardaniba...

Tureta am yayi ya fice a dakin ko gani bayayi sbd tsananin tashin hankali,

Meye hadin nadeeyarsa da zanen hoton zaki?
Bazai iya rayuwa Babu nadey ba Koda ita din jinin Zaki ce,

Shin wannan da fammah ke fada zakin ne kuwa kokuwa shine yake qoqarin kasa fahimta
Gabaki daya qwaqwalwarsa ta toshe baya gane komai....

Kwalbar alcohol ya daga ya kwankwada kozaiji sauki Amma saijin yayi qwaqwalwarsa tasake hautsinewa ya daga kwalbar ya shanye
Atake yaji kansa ya kasa daukar nauyin balainta yafara ihu Yana wurgi ta komai.

Fammah dake rakube tasake fashewa da wani kukan kamar zata shide
Tabbas ko Basu mutuba tasan ita ko yanxu tana cikin tsananin maraici
Dad na kwance sai antayar,mum na prison ga am kamar ya haukace.

Sunan nadey yake Kira Yana ihu tareda farfasa Kaya duk yajiwa kansa ciwo qarshe nan ya zube cikin fasassun kayan da kwalba yafara wani irin kuka ahankali sbd duk qarfinsa ya qare itama ahankali tadawo kusadashi ta rungemesa tana cigaba da kukanta itama.


***
_6:36 am_

Ahankali ta bude idanuwanta da??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sukai Mata wani irin nauyi ga kanta da shima yayi Mata wani irin nauyi..

Ahankali tafara qoqarin tashi tana qoqarin tuna abinda yafaru jiyan,

Kallon dakin tahau Yi tana dafe kanta tareda saukowa gadon ta miqe tsaye tana sake qarewa dakin kallo sbd yanayin tsarinsa da haduwarsa tasan cewa ba qaramin wurine takeba.

Kan qaramin frame 'din dake aje gefen bedside lamp idanuwanta suka sauka taga zanen hotonta tayi saurin daukar frame din taga tabbas itace take tasan cewa am ne ya daukota
Ta aje cikin tsananin baqin ciki tahau dudduba kanta gabanta na tsananin bugawa tana tsoron idan ba wani abin yamataba.

Ajiyar zuciya tasake data ganta lafiya kalau Amma yanda zuciyarta ta kasa daina bugawa da sauri da qarfi yasa hankalinta tashi ta nufi qofa cikin sanda ta fito ahankali tana lalleqawa cikin faduwar gaba.

Wani dakin dake kallon inda ta fito yajiyo faduwar Abu tayi saurin kallon qofar tareda dafe zuciyarta dake bugawa da qarfi ta nufi qofar ta daga hannunta dake rawa ta tura ahankali tana Shiga.

Cak ta tsaya bakin qofar dakin tareda waro idanuwa tana dafe qirjinta da numfashinta na sarqewa sbd abinda tagani.

Tsaye yake gaban mirror daureda towel alamar wanka yafito,

Bayansa zuwa qwandar hannunsa dake daureda abinda a duniya tafi kowa sanin na mijintane Dan baitaba ciresa daga hannunsaba,

Ahankali idanuwanta suka sauka kan tabon cizon datasan itace tayi masashi haryazama tambo a hannunsa duk da tasan Idan yaso zaiyi amfani da magani ya goge tabon Amma yaqi qoqewa sbd Yana buqatar ganin tabon...

Girgiza Kai tayi da qarfi tafara ja da baya tana dukan kanta da qarfi tace"

Oh my God I'm loosing it...ciwona na hauka yadawo,,,why am I seeing tinz....

Faduwa tayi tana neman fita hayyacinta...

da sauri ya juyo Jin faduwar mutum da mgn abayansa
Yana juyowa Suka hada idanu

Atake ta zaro ido tana kure fuskarsa da kallo saikuma idanuwanta suka fara rufewa ta zube kwance a sume.

Cikin tsananin tashin hankali yayo kanta Bai tsaya komaiba ya dauketa yayi gado da ita ya kwantar Yana Kiran sunanta.

Fuskarsa ya hanga cikin mirror yaga asalin fuskarsace cikin tashin hankali yace"

Darn it..tariga ta ganni.
#MAMUH.

*_Mamuhgee36_*
Sake dafe kansa yayi cikeda damuwar yanda zata fuskanci zancensa idan ta farka sbd ta riga ta gansa Babu wata kwaskwarima a fuskarsa takuma tabbarda shine ba fatalwa to Yaya zata karbi alamarin??yaso shine yafara bayyana mata kansa batareda itace ta fara ganowa ba.

Ruwa ya dauko a fridge ya dawo bakin gadon ya zauna ya xuba ruwan a hannunsa ya shafa a fuskarta Yana Jin wata irin kasala na saukar masa.

Sake shafa Mata ruwan yayi tafara bude idanuwanta ahankali ta waresu akansa ta qurawa fuskarsa ido hawaye na cikowa cikinsu gabaki daya,
Tsoro,fargaba tareda tashin hankali sun daddaure jikinta sai wani irin rawa da jikinta keyi hawayen idanuwanta na gangarowa,

Batasan mezatayiba sbd sbd dai ba qaramin alamari bane take fuskanta yanxu na ganin Wanda Suka San ya mutu shekaru biyar baya a gabanta ace bazata sake somewa ko gama wannan tunanin batayiba idanuwanta suka sake lumshewa zata sume yayi saurin girgizata Yana cewa"

No no Not again please....

Ware idanuwanta tayi murya na rawa jikinta na daukar sabon mazarin tsoro da tashin hankali daqyar ta bude baki tace"

Ya...ya...yya yaaa...

Daga Mata Kai yayi tareda sake girgizata sbd ganin alamar Bata hayyacinta sbd tsoro Kuma kamar Bata Gama tabbarwa da shi din bane cikin wani irin yanayi yace"

It's me,nine I'm real ba fatalwa bane ban mutuba da Raina,
Ki dawo hayyacinki karki illata kanki nine da gaske ba wani gixo ba Ni din daine a gabanki......

Wani mugun yunquri tayi ta turasa baya tareda yin baya tana masa wani irin kallo idanuwanta jajir da fargaba tace"

Kana cewa baka mutuba Kaine Kaine,
Kana tunanin gwaninta kayi ko dadi zaka sani da fadar hakan??
Qwalqwalwata bazata iya daukaba,
Ciwon haukana dawowa zaiyi I'm only imagining this,,,,ya Allah karka Bari na sake dandanar ciwo da radadinda ke cikin hauka....

Ya Allah ka tayardani daga wannan mafarkin danakeyi....wlh I'm going insane....

Da qarfi ya damqota tareda girgiza ta da qarfi ya Kira sunanta sbd ganin yanda jikinta ke rawa sosai tana surutai da qarfi....

Qwacewa take sakeyi tana neman ihu da fixgewa ya sake riqeta Yana Kiran sunanta hankalinsa na tashi Saidai Sam batamasan yanayiba gabaki daya ta fice hayyacinta..

Jin zuciyarsa na neman karyewa da halinda tashiga yasashi rungumeta da qarfi cikin jikinsa tareda kwantarda kansa cikin wuyanta Yana Kiran sunanta da wata irin muryar sanyin jiki kamar zaiyi kuka sbd gab yakeda zaucewar shima matuqar wani Abu yasake samunta.

Tabbas yasan Dole zata gigita da ganinsa sbd ana maganar mutuwane,
Tasan ya rasu shekaru sama da biyar saikuma tagansa yanzu Kai tsaye Dole hankalinta zai tashi.

Yanda ya matseta a jikinsa Yana Kiran sunanta ahankali tun tana fixge fixge hartayi sanyi jikinta ya saki gabaki daya alamar ta sake somewa.

Lumshe ido yayi tareda girgiza kansa Yana tallafota gaba daya yasake maidata ya kwantar Yana mamakin yanda take somewa ita tunda can.

Wasu ruwan yasake shafa Mata
Tareda tsayawa bakin gadon yayi folding hannuwansa zuciyarsa duk a hargitse.

Ahankali tasake bude idanuwanta ta kafesa dasu wannan karon ko motsi kasawa tayi ta lumshe ido tasake budewa ta sauke masa
Take taji zuciyarta ta karye sbd yanzu Kam tabbas tasan shi din ne Babu maganar fatalwa kokuma hauka..

Wasu hawayen dataso ruqewane Suka gangaro ta gefen idonta sbd tasake tabbatarda da dai shi dinne Yana raye.


Kasa cewa komai tayi sbd wani mugun nauyi da dukkanin gabban jikinta suka dauka sbd mutuwar jikin data sameta,
Wani irin sanyi qasusuwan jikinta suke sake dauka akaro na farko a rayuwarta dataji zuciyarta ta toshe da wani irin nauyin gaske Wanda ya Hana bakinta budewa bare magana.

Fuskarsa take sake qarewa kallo,
Haskensa da kyawunsa na nan saima qaruwa dasukayi sbd hutu da Jin dadin daya samu,

Ahankali ta sauke kallonta a gefen wuyansa zuwa kunnensa na dama dasukayi duku tareda alamar qonuwa Wanda tabonta yakusa bacewa gabaki daya wasu sabbin hawaye suka silalo Mata.

Ahankali ta dafa ta tashi zaune tareda dauke idanuwanta daga kansa ta sauko gadon yanabin jikinta dake wani irin rawa a boye Wanda ya tabbatarda na ganinsane.

Fuskarta ya kalla yaga yanda yanayinta ya sauya sosai Babu wata rahama a fuskar tata saima hawayenta data share tana miqewa tsaye daidai agabansa.

Am in trouble""yafada tareda sake ajiyar zuciya ya matso zai kamo hannunta tayi baya ahankali batareda ta dago ta kallesaba ta juya zata fice ya riqe hannunta tareda dawo da ita baya zaiyi magana ta rigasa da qwace jikinta cikin qoqarin danne halinda take ciki tace"

Please Ina buqatan komawa inda ka daukoni.

Kallonta yayi da fararen idanuwansa tareda dawowa gabanta ya kalli fuskarta dake sunkuye yace"

Ina kike maganar komawa kenan???

Inda ka dauko ni Dilla's.

Sakinta yayi tareda mayarda fuskarsa yanda yasaba wato a tamke shima ba sauqi Kai tsaye yace"

Bazaki koma can ba infact ko Ina bazaki komaba Ni nasan inda zan kaiki.

Dagowa tayi wannan karon takasa riqe tarin baqin cikin dake cin zuciyarta kamar zata mutu tace"

Nace gida zankoma so inaga Banga wani dalili ko iko dakake dashiba na hanani besides karka manta satoni kayi Wanda Ni bansan manufarka akan hakan ba and inada damar dazansa a Kamaka akan hakan.

Idanuwansa ya zuba Mata cikeda yanayi na tsananin mamakinta akaro na farko dayaga zallar fushi Mai qarfi atareda ita.

Kina tunanin banda wani ikon hanaki kokuma kina tunanin Zaki iya sakawa a kamani din sbd kina taqama da me????

Cikin fushi tace"

Koma Dame nake taqama it's none of your business,
Kai me kake taqama dashi dazakazo bayan shekaru ka tsaya gabana bakaji kunyar Allah da tsoronsa ba na barin matarka dakayi da 'yan uwanka tsawon shekaru kana raye baka nemesu ba,baka dawo garesu ba,
Bakasan irin halinda suka shigaba sbd rashinka,
Bakasan ya rayuwa tayi musu tsanani ba sbd Babu kai....rawa muryarta tafara Yi hawaye na ciko idanuwanta tace"

Dama basuda mahimmanci da wani matsayi a rayuwarkane daka zabi barinsu Babu waiwaye kokuwa dama lokacine ka dibar musu a rayuwarka,

Meye laifina Dana mahaifina daya bakani ko kuwa munzama takurane a rayuwarka????

Meye laifin babana Dani kaina???
Idan duk munada laifi damuka zabeka fiyeda kowa meye laifin baby z ita????

Sai alokacin ya matsota sosai Yana kallonta da idanuwansa dasuka rikide ja sosai ya daga hannu zai kamota tasake ja Baya cikin daga murya tace"

Enough..enough Mr haydar,,,ka daina kusantoni da yawa sbd haryanzu ban manta da darajataba ta 'ya mace Kuma musulma....

Ba zato ya jawoto jikinsa ya matse tareda zuba Mata jajayen idanuwansa jikinsa na rawa sbd bacin ran zancenta yace"

Shi wancan da kike tare dashi a gidansu shi musuluncin Bai hau kansa bane????
Wlh bazaki sake zama a gidanba idan Kuma kinason kwada qarfin ikon danake dashi ne akanki da rayuwarki ki gwada zakisha mamakina sbd inanan bawai canzawa nayiba.....


Fixgewa tayi itama cikin Hana kukanta zuwa tace"

Bana magana akan rayuwar kowa da canzawar kowa anan Ina magana akan rayuwatane da abinda Naga damar Yi da Wanda Naga damar bari,
Idan kana maganar baka canza ba to Ni na canza ba Nadiya bace wannan ND NOAH ce...and stay the hell out of my life.....

And bana buqatar ganin qarfin iko ko dukiyan dakake dashi sbd dama Abu ne nasa kaina sbd tunanin anrabani da abinda nakeso fiyeda tawa rayuwar Ashe bansaniba shine ya rabu Dani Dan haka Ni kaina daga yau na fita daga fadanda Babu ruwana zanje na fuskanci Wainda suka cancanci qaunata da lokacina.

Tana Gama fadar hakan ta fice da gudu sbd wani irin kuka Mai tsananin nauyi da qarfi dakeson zuwan Mata tana dannesa numfashinta har sarkewa yakeyi jikinta Babu inda baya rawa.

Kasa motsi yayi sbd duk jijiyoyin jikinsa sun daure da mamakinta da fargabar tashin hankalin maganganunta dake bayyanarda tsantsar radadin baqin cikin barinta datake ganin yayi.

Securities Basu wani hanata fitaba tana fita ta tari wata taxi data kawo ta fada kawai sai alokacin tasake wani irin kuka Mai tsananin cin Rai da damuwa tareda ciwon abin datake ji cikin ranta.

Har Sukayi nisa Bata saniba Saida yasake tambayar inda zai kaita ta bude baki daqyar tareda fada masa tana share hawayenta tareda qoqarin barin kukan duk da tasan bazata iya barinba.

Yana Isa qofar mansion din ta fito ahankali tareda ce masa ya jirata tafito.

Ciki tayi tana qoqarin maida kukan dayake sake taso Mata sbd fammah data hango tsaye jikin qofa tana knocking qofar side din am tana kuka sosai kamar zata shide.

Kasa riqe nata itama tayi tasakesa tareda wucewa ciki da gudu tanajin inama duk shekarun nan a gaban babanta ta zauna tayisu da tabbas bazata cutatu yanda takejin ta cutatu yanzu ba.

Sama ta haye tahau hada duk wasu kayanta tafara jawo luggage dinta tana share hawayenta dasuka qi tsayawa a Palo taci Karo da am da fammah tsaye dukkaninsu Babu Wanda baibata tausayiba take zuciyarta tasake karyewa ta silalo hawaye masu radadi ta rintse idanuwanta ta bude saitaji takasa kallon fammah ga am da zuba Mata idanuwansa dasuka shanye sukai jajir a dare guda ya lalace yakoma tamkar asalin Dan giyar dayayi shekaru ashirin Yana sha,
Hawaye ne cike da idanuwansa Saidai Basu saukoba sbd muguwar karayarda zuciyarsa da gangar jikinsa suke ciki,

bude baki tayi daqyar ta furta"

I'm leaving......

Ba zato qafafuwansa Suka sare ya zube gabanta tareda riqo qafafuwanta cikin wani irin yanayi na kuka da tausayi yace"

Baby Dan allah karki barni wlh bazan iya rayuwa Babu keba,
I can't live or survive without you,
Karki tafi kibarni a wannan halin I will die if you leave me.... please baby idan na Miki wani laifi ne forgive me Dan Allah please baby don't leave.....

Kuka tasake sbd akaro na farko daya fara Bata tausayi musamman yanda fammah ke jansa tanason tayar dashi cikin tsananin kuka Yana kwacewa Yana surutai da kuka sosai..

Cikin tsananin kuka itama ta janye qafafuwanta ta ja Baya yayi saurin rarrafowa Yana wata irin magiya gabaki daya baya cikin hayyacinsa.

Cikin tsananin kuka fammah itama ta zube gefen Dan uwanta ta dago ta kalli nadey din tana kuka tace"

Dan Allah Ina roqonki daki rausayawa rayuwata ki tallafi Dan uwana dashine kadai ya ragemin a yanxu,

Bansan wane sirrine yake boye a tattareda saninki da familynaba Amma Dan Allah kiji tausayin maraicina ki tallafi Wanda zai tallafi tawa rayuwar.....

Girgiza Mata Kai nadey tayi hawayenta na sake gudu ahankali ta furta"

I'm really sorry fammah...

Tana fadar haka ta fice da sauri tana sakin siririn kuka tana jiyo ihun fammah na Kiran sunansa Amma Bata tsayaba sbd zuciyarta data fara karyewa alhalin itama tallafin take buqata a tata kuncin Wanda zuwanta gaban mahaifintane kawai zai yaye matashi.


Taxi din tashiga sukabar gurin.
Direct gidansu Annah yakaita canma Basu gane kantaba tana Shiga ta tattara sauran kayanta suna tayata hada kayanta data kasa hakuri anan ne tasaki kukanta Mai qarfi datake riqewa mum din Annah da Annah na gefenta Suka Bata damar tayi kukan duk dake cikin ranta kozataji sauqin zuciyarta.

Sosai tayi kukanta saidataji sauqin nauyin datakeji a qirjinta kafin ta shiga toilet tayo wanka tana fitowa takira JJ da wayan annah ta shirya cikin skinny jeans fari da farar loose chiffon top ta Dora black full-length jacket da black scarf ta fito da kayanta daidai isowar JJ kallo daya yamata yaji nauyin zuciyarsa ya qaru sbd idanuwanta dasuke a kumbure musamman data gansa sai idanuwanta suka sake cikowa da hawaye tun kafin yayi magana ahankali da rawar murya ta furta"

Dady j I can't handle this anymore,,,inason ganin babana Dan haka it's time for me to go home....

Da sauri ya qaraso gabanta cikeda kulawa Yana cewa"

Baby please karki dagamin hankali tell me yafaru?
Meya sameki?
Waye ya daukeki?
Ina ya kaiki?
Meya Miki?

And....and..fuskar Wanda ya daukeki Dana gani was it re.....

Yes dady j shine,Yana nan da ransa Bai mutu ba Muna wahalarda rayuwarmune akan Wanda baisan munayi ba....

Da manyan idanuwansa yake kallonta ko qyaftawa yakasa Yi shima duk jarumtarsa zuciyarsa bugawa takeyi sosai sbd kukuwar yarda da zancen,

Girgiza kansa yakeyi tareda juyawa da qarfi ya daki iska Yana sake girgiza Kai sbd wannan zancen ya girmi tunaninsa Kai tsaye Rana tsaka ace Wai sarki Bai mutu ba,
To meyesa ya boye musu kansa???
Idanma Bai nemi kowaba shi Bai kamata yakasa nemansaba qarin abin tashin hankalin shine suna taredashi Bai sanarmusuba Kai this is so confusing.

Wani murmushin takaici tasaki tace"

Shall we???

Dago jajayen idanuwansa yayi ya kalleta yaga yanda fuskarta tayi jajir ta kumbura take yaji ransa yaqara baci Saidai shikam yau zasuyi face to face da sarki yau zasuyi magana as man to man.

Direct airport yakaita Babu me magana acikinsu harsuka karbi tickets ta juyo ta kallesa zatayi magana shima daqyar yarigata da cewa"

Karki damu yau zuwa gobe zamu Gama claiming komai a gobe zaa buga sunayen Noah's a kamfaninsu da mansion dinsu da angama zandawo jibi insha Allah.

Jinjina masa Kai tayi tareda juyawa ta shige shikuma ya koma.

Bata fi mintuna ashirin ba aka Kira flight dinsu ta tashi ta shige.

Yamma sosai ta Isa starling city dad da kansa yazo daukarta sbd yayi wata da JJ yafada masa komai dake faruwa gameda haydar.

Ji yayi duk duniya farin cikinsa yadawo Sam kasa boye farin cikinsa yakeyi tuni labarin yafara yaduwa a cikin abokanan mu'amalarsu ta business har zancen yafara fita.

Duk murnarsa raguwa tayi dayaga halinda nadey ke ciki yafara qoqarin danne murnarsa da farin cikinsa Yana duba yanayinta itama sbd tabbas wannan abin abun dubawa ne ga miji yabar matarsa tsawon shekaru Babu waiwaye.

Da gudu baby z tazo ta rungumeta itama cikin tsananin kewa da soyayyar 'yarta ta rungumeta tareda rintse ido hawaye na silalo Mata.

Nanny Nancy ma rungumeta tayi cikin kewarta dasukayi suka shige har dakinta har lokacin baby z na maqale a jikinta itama Sam takasa sakin 'yarta.

Wanka tayi tayi sallah tana qoqarin danne komai tasake dasu Suka hau labarai dad ma sakewa tayi taqara masa bayanin halinda ake ciki gameda mansion dinsu Dilla data siye harda na Nigeria and dad Insha Allah I will be going back to Nigeria next week zanji da maganar claiming takardunsu na can da muka karba.

Kallonta yayi cikin farin cikin ganin Bata wani dauki abin da zafi ba yace"

Ok allah yakaimu Saidai idan kinje ku zauna gidan Dr sayyid tunda nasan za'ayi renovating gidan Yaya dattiya ne sbd nasan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login