Showing 9001 words to 12000 words out of 30903 words
nayi, nayi shiru ban iya
cewa Ado komai ba, iyaka dai ranar mun kwana
lafiya amma ko kusa da ni bai zo ba, balle ya ce zai
taba ni, ina wurina yana nashi.
Washegari da Asuba yana idar da Sallah Asuba
ya shigo ya tashe ni ya wuce ya fita, sai dai
maimakon sai Azahar in ga ya dawo, wajen sha
daya naga shigowarshi. Ya koma gefe yana cire
ranbut din kafarshi da hand glove din hannunshi
mahadin ranbut din.
50
Naji Baba Tanimu daga daki yana ce mishi "Ka
dawo ne Adamu?" Ya ce mishi "Eh Baba, na
dawo." Ya ce "Sannu da kokari ka ji? Ubangiji ya
yiwa kokarin ka albarka." Yayi murmushi ya ce
Amin Baba." Ya shigo cikin dakin namu ya same
ni ma Zaune.
Ya kakalle ni yayi murmushi, ya ce to ko ke fa?
Kin yi wankanki kinyi fes da ke, na sani ba kya jin
dadin mu'amalla da kayan da ki ke amfani da su
tunda sunyi miki karanci da yawa dogayen riguna
biyu ne kawai, sai zanin da ki ka zo da shi a jikinki.
Kiyi min hakuri a yanzu, na katse shi ta hanyar
fara gaishe shi, yana gama arnsa gaisuwar ya kalle
ni cikin natsuwa ya ce, samo min dumamen tuwo
wurin Goggo Ayalle, na ce to, na tashi na tafi cikin
zuciyata ina tunanin tun zuwanmu gidan kwanaki
ashirin da daya da suka wuce ban taba lura da cin
shi ko shanshi ba, ban kuma taba dora tukunya a
murhu don yin girkin rana ba, tunda kowa yana
abincin ranarshi.
Ni dai nasan duk abin da Goggo Ayalle zata ci
zata bai haka nan ma Yaya Ruwailah tunda nima
yanzu yayan nake kiranta.
Na dawo da kwano mai dauke da tuwon da aka
dumama shi tare da miyar shi a wuri daya na ajiye
51
mishi na koma gefe na zauna sai ya sake kallona
cikin natsuwa ya ce min baki bani cokali ba, nayí
maza na kalle shi saboda sanin shi ba mai cin tuwo
da cokali ba ne.
"Da cokali za ka ci?" Ya ce, "Eh, dashi na ke ci
yanzu saboda hannun nawa ba na jin dadin cin
tuwon da su." "Me ya same su? mu gani." Bai yi
magana ba ya ware min tafin hannayen nashi.
Tsigar jikina tayi matukar tashi tayi wani
yarrrr! hankalina yayi matukar tashi da yanda naga
hannun Ado gaba daya hannun nashi bororo ne ya.
duru ruwa, wani wurin ma ya fashe ya zamą miki
babu dadin gani.
Fuskarta a yamutse saboda yanda hankalina
yayi matukar tashi na tambaye shi me ka ke yi
hannunka yayi haka? Shirun da yayi bai ban amsa
ba yasa na sake tambayarshi Noma? cikin nutsuwa
ya kalle ni ya ce min, in nayi noma menene
Humaira?
Ni ba namiji ba ne? Ni fa ba wannan ne wahala
a wurina ba, wahala a wurina bai wuce ki ki yarda
mu zauna lafiya ba, amma in za ki yarda mu zåunna
lafiya ki gamsu da kokarina ki yarda da cewar in
ban yi miki ba, ba ni da shi ne.
Kiyi min hakuri ai ba zan gane ina wahala ba
52
sai in rinka ganin tanfar abin da ya dani a
matsayina na namiji kawai nake yi in kuwa haka ne
kin ga bai zamo min wahala ba.
Ban iya cewa Ado komai ba saboda kukan da
soma yi ban taba hira na gane matsananciyar
ramar da yayi ba sai a yau, na dai san nai Goggo
Ayalle tana yawan fadin yaron nan Adamu ya
zube. Amma ban lura na gane irin zubewar ba, sai a
yanzu.
Tashi yayi yaje ya dauko cokalin ya dawo ya
zauna ya soma cin tuwon, ni in don ni ki ke kuka to
ki share hawayenki, in kina so in san kina tausayina
to in ina tare da ke ki bar ni in samu kwanciyar
hankalin da nake bukata.
Yaua gamawa ya tashi ya sake fita, nima na
share hawayena na tashi naje sasan Baba Halliru
wurin Goggo Jaku na gaisheta, na ce mata Goggo
yau zan karbi furar da kullum ki ke cewa bana
zuwa ina karba, tayi murmushi ta ce, kai ai kuwa
dai kin kyauta yar nan, gata kuwa an gama
mulmulata.
Ta miko min tayi shar gwanin sha'awa, sai
Kamshi take yi, gata nan debi maza yanda zai ishe
ki nasa hannu na debi guda hudu ta ce ke tafi can
da kwauro, za ki yi wa kanki, ta sake watso min
53
guda shida a cikin kwaryar da ke hannuna nayi
mata godiya na tafi.
Nura na kira ko Zulai yaya, Yaya Ruwaila ne
gaba daya suka taho na ce to ke Zulai je ki ki huta
kai Nura yi sauri kaje bakin kasuwa ka sayo min
nono, ya ce to.
Ina zaune ina dama furar ina tunanin kai! Dabai
akwai fura, amma babu nono. nono ruwa-ruwa? Na
jawo robar yougort din da ke dakin na bude shi na
juye a cikin damammiyar furar na gaurayata na
rufe.
Ana yin Azahar Ado ya sake shigowa nayi
mishi sannu da zuwa, ya amsa. Na jawo kwanonon
fura na mika mishi ya kalle ni da walwala a
fuskarshi ya ce to ke fa? Na ce ai na sha, ya ce eh,
amma ba zai taya ni musha tare ba ai.
Na zauna muna shan furar tare har muka gama,
muka dan yi hira kadan sai na kalle shi na ce mishi,
"To ka dan kwanta mana ka huta." Ya ce in kwanta
Humaira? Nayi maza na ce mishi eh, ya ce to za ki
yi min tausa ne? Na gyda mishi kaina nuna alamar
eh.
Yayi maza ya mike akan katifar nima na bi
bayan shi na soma yi mishi tausa ina yi mishi danna
ina bin gabobin jikinshi ina matsawa cikin hikima,
54
shi kuma yayi lamo ya lumshe idanunshi nuna
alamar jin dadi.
A hankali kuma yana furta wasu kalmomi da ni
kadai ke iya jin su, bacci mai nauyi Ado yayi bai
farka ba har sai da na tashe shi, wajen karfe hudu
da rabi na yamma abin da bai taba yi ba tunda
muka zo, ya kwanta da rana yayi bacci.
Da daddare rannan muna hira ni dashi ya kalle
ni cikin natsuwa ya ce min ni kuwa Aisha in ban da
kar in yi ta takura miki har in yi ta kai ki bango ban
sani ba da na roke ki kiyi min wata alfarma, na ce
ta menene? Ya ce dakin nan da muke zaune a ciki
ne bana son shi, duk da nawa ne.
Na ce, ni na gane saboda gininsu ma ya
banbanta da na sauran dakunan gidan shi da na
Baba da na Goggo Ayalle.
Bai bani amsa ba sai ya ce min nan din a takure
nake, ba zan iya sakewa nayi kusa da Baba da yawa
ba zan iya zama dashi duk wani motsina yana ji ba,
shi ne nace da za ki yarda da mun fita daga ciki
mun koma wasu tsofaffin dakuna da ke ta can baya,
babu kowa a wurin sa muyi zamanmu zuwa
lokacin da zan samu halin samar miki wurin da zai
dace da ke."
A hankali cikin natsuwa na ce mishi, to mu
55
koma mana. Ya zuba min ido yana kallona, babu
damuwa? Na ce to ai ba daki na biyo ba, ba kuma
shi nazo nema ba, ni a wurina kai ne muhimmin
abu, kai na biyo kai ne mijina a yanzu kuma zan iya
zama da kai a duk in da ya kama.
Kwana uku kawai da yin wannan maganar
tamu Ado ya gama gyaran dakunan da da shara ake
zubarwa a wurin ya kwasheta fes ya gyara wurin ya
tsabtace shi ya gyara dakunan gyara na musamman
ya sai buhun siminti ya toshe duk in da yake
bukatar a toshe shi.
Ina jin Baba Tanimu yana yabon kyan aikin da
Adon yayi, amma ban san kyan wurin ya kai haka
ba sai da Adon ya kira ni naje na gani, dakuna uku
ne a wurin gaba daya yayi musu gyara na sosai,
kowane daki ya maida shi abin da yake son ganin
ya zama guda daya, ya gyara shi a matsayin dakin
kwana daya dakin dahuwa, wato kicin daya kuma
bayan gida na sosai da za'ayi amfani da shi akan
komai sannan ya killace wurin da wata yar
katanga.
Yayi mata kofar shiga dan karamin tsakar
gidan kafin ka shiga 'yan kananan dakunan ni dai
wurin ya ban sha'awa, yayi murmushi ya ce to
yaushe za ki dawo ciki? Na ce ko yanzu, ya yi
56
murmushi ya ce, to shi kenan.
Baba ne yasa Ado daukan katuwar katifar da
ke dakin da muke din, don haka ya sayo mishi 'yar
karama.
Randa na tare a sabon dakin namu tsaf na same
shi ya malale shi da leda yasa katifar yayi mata
shimfida ga akwatinshi a gefe sai Jakar da yazo da
ita da 'yan tarkace kadan, dakin dahuwa kuwa yasa
risho har da tukwane guda biyu da yan tarkacen
kayan aiki kadan, food flask da dinner set da kuma
wasu kwanuka.
Ga bokitaye da randa da dai wasu tarkace, ga
kuma kayan abinci dan daidai gwargwado ko a ina
yaké samun kudin da yake kashewa? oho!
tambayar da na.yi wa kaina kenan, a zuciyata dai
nasan babu abin da yafi min ban dakin nan dadi,
don na samu kebabben wuri har da bayan gidan
hadakan da ban saba da shi ba yake sani jin kiyan
yin wanka.
Nayi maza na kammala abubuwan da zan yi
nayi wanka saboda jin dadin ganin bandakin na
zauna na shafa mai nayi gyara irin yanda na saba yi
a gida, gaba daya dakin ya gauraye da kamshin
kayan shafan da nayi amfani da su.
Ado bai shigo ba sai da yayi sallár Isha'i shima
57
yana shigowa bandakin naji ya shiga yana wankan,
Cikin zuciyata na ce ashe shima da kwiyan wankan
yake ji, don tunda muka zo ban gan shi yana
wankan dare ba, yana shigowa dakin ya sanya
hannayenshi duka biyu ya sure ni.
"Kina lissafin kwanakin aiko? Kina lissafin
kwanakin da nayi ina hakuri ina fama da shan jar
kanwa da lemon tsami? Tuni na langabe mishi na
sa shi ya mance duk wata damuwa in har yana da
ita da kuma wahalar da yake wuni cikinta, wanda
nasan ya manta rabon da yayi irinta, duk wani abin
da nasan zan yi wa Ado rannan da zai sa shi jin
dadi ko farin ciki nayi mishi.
Na kuma yi matukar yin hakuri da shi, ban
Duna mishi gajiyawata ko korafi kan al'amuranshi
ba, ba don komai ba sai don zuciyata ta riga ta
yarda ta amince da cewar Ado mijina da na kuduri
aniyar zama dashi a kowane hali yake ciki in
taimake shi, in ba shi hadin kan da da yake nema a
tare da ni, in jiyar da shi dadi gwargwadon abin da
zan iya yi.
Saboda na yarda na amince sona yake yi da
zuciyarshi guda daya dawo da ni kauyensu da yayi
kuma ba laifi ba ne gurinshi na asali yazo da ni
mafi yawancin wahalar da yake yi kuma na yarda
58
mati yawancinta tawa ce.
Sallar Asuba ya fita yayi ya dawo ya same ni
nima ina sallar, nayi zaton komawa zai yi ya dan
kwanta kafin ya fita tunda ni dai nasan kashi uku
bisa hudun daren idonshi biyu ne, amma sai naji ya
ce min ni na tafi bai ma jira amsawata ba.
Na idar da sallata na koma na kwanta, sai da na
dan yi bacci kafin na tashi na duba abin da muke da
shi na abinci na gama gyaran wuri da tsabtace shi,
nayi wanka nazo na shirya abin karyawa, na karya
na gyara jikina na jawo kofar wurina na rufe don
kar kaji su shiga suyi mana ta'adi.
Na fita naje na gaida manyan gidan duka kafin
na wuce can tsakar gida wurin haduwar matan
gidan. inda ake da babban fili sosai da ke dauke da
wurin girki a can nesa ga runbuna a can wani gefen
ga in da ake aikace-aikacen wanki ko wanke-
wanke, wani gefen can kuma daka ake yi da nika
ga kuma wata katuwar rumfa da ke tsakanin wasu
manyan bishiyoyi in da ake zama ana yin hira.
Zaman tsakar gidan nan yafi komai dadi, don
wuni ake yi ana raha ana barkwanci ana kwashewa
da dariya, shagala nayi a cikinsu ana tayi ina kallo
har ina taimakon masu daka da yin tankade, ban
ankara ba sai naji ana kiran sallar azahar.
59
Gaba daya aka watse kowa ya nufi wurinshi
don yin sallah, kofata tana rufe kamar yanda na
barta a zuciyata na ce yau ma Ado bai dawo ba
kenan, na idar da sallah naje na karbo fura nazo na
dama na ajiye mishi na koma wurin matan gida, na
ce ba zan iya zaman kadaici ba, in ya dawo ya kira
ni ko kuma ya sha furarshi ya tafi.
Ado bai shigo ba sai bayan 'sallar magariba, ban
taba ganin tashin hankali da bacin ranshi irin na
rannan ba, kina nufin ba za ki iya zaman wurinki
ba? To me yasa ki ka yarda ki ka dawo? Kina nufin
ai ba zan dawo gida in same ki a wannan dan
tsukakken dakin namu kina zaman jiran dawowana
ba?
Sai in ina son ganinki in biki cikin mata ina
kwala miki kira? Ke ba ki san hakkina ba? Ba ki
san abin da za ki taimake ni da shi ba? Fura ce zan
rayu a kanta Humaira? ba ki ga kamar dandanon
abincinki a bakina zai yi matukar yin amfani a gare
ni ba?
To bari in gaya miki dama kin bi a hankali
wannan taron nasu da ki ke gani-randa suka tashi
tambayar junansu gulma suka sa dake a ciki abin
zai baki mamaki, ke baki taba zaman gidan yawa
ba duk fitinar da ki ka sani a gidanku wasan yara
60
ne.
Gabana ya yanke ya fadi, jin da nayi Ado ya
kira fitinar gidanmu wasan yara na ce to ai gara ka
maida ni gidan namu, abin da kawai na fada kenan
Ado yasa hannu ya make ni, kina hauka ne? Na ce
kina hauka ne da kullum za ki rinka kallona kina
cewa in maida ke gidan naku ke kina da gidan
zuwa ne?
Ko ba ki ji abin da maigidan ya fada ba sanda
ki ka zabi biyo ni? Ya ce kar ki sake taka gidanshi
saboda ya yafe min ke bai da sauran bukatarki."
Dukan da Ado ya yi min bai 6ata min rai ya
daga min hankali irin wannan maganar da ya soka
min ba saboda gaskiyar abin da Babana ya gaya
min ya gaya min. Nayi kukan bakin ciki har na gaji
a kasa da kwanaki talatin na barin iyayena da nayi
na biyo shi har ya fara goranta min abin da ya
farun.
Tabbas Ado namiji ne dama kuma nasha jin
Mama tana cewa shi namijin ba dan goyo ba ne, a
gabanshi kuma ma ta fada ta ce namijin ai ga ki
nan gashi nan.
Rannan dai kam kwanan da muka yin ba mai
dadi bane, don haka yana fita sallar Asuba na duba
inda 'yan kudina da nake tarawa suke, don yau kam
61
nayi niyya ko ba za su kai ni gida ba in dai za su
raba ni da garin Dabai, to zan tafi in yaso nasan
yanda nayi na karasa gida.
Ban ga komai a wiirin ba sai nera hamsin saura.
ya kwashe kwana biyu muna cikin wani hali ni
dashi, rannan ya dawo da yamma ya same ni, kin
gani Humairah mu biyu ne ni da ke a nan, ya
kamata in wani abu ya faru a tsakaninmu na rashir
jin dadi in na ba ki hakuri ki hakura, ba zai yiwu
ace kullum sai na kai wa Inna maganar za ki hakura
ba, in dai ba so ki ke mu rinka tayar mata da
hankali ba.
Kuka na soa yi sosai da sosai, kiyi hakur na
sani ban kyauta ba da nayi miki gori, to amma ke
kin ga yayi miki daidai kan maganar da ba ta taka
kara ta karya ba ki rinka cewa in maida ke
gidanku? Ai ya kamata ace ni da ke mun fahimci
wani abu a tsakaninmnu, shi ne zaman namu bana
rabuwa ba ne ba kuma na wulakanta juna ba.
Tsawon lokaci yana yi min maganarsu na
rarrashi da ban baki har dai ya samu ya gawo
kaina na hakura, muka shirya.
Tun daga wannan lokacin na rage shiga can
cikin gida don yin hira da matan gidan sai dai kawai
in gari ya waye in shiga in gaishe su dukan su in
62
dawo wurina in gama aikina in gyara komai in yi
wanka in gyara jikina, duk da 'yan kayan nawa har
yanzu guda uku ne sai lodin rigunan baccin da babu
damar in sanya su da rana sai da daddare in yi
mana abin karyawa irin wanda naga ina, so don
komai na abinci Ado kawowa yake yi, komai
tsadarshi kuwa.
Agada, Doya, Dankali, Wake, Kuskus,
Indomie, kwai, manja, Mangyada, Manshanu,
Shinkafar tuwo saboda masa da kuma ta wara duk
ina da su ina kuma da kayan tea zan kuma tashi da
safe in je in kar6o kunu da kosai, don ko ban je ba
za a biyo ni da shi, don haka nake girmama su in je
da kaina.
Shi kuwa Ado ka'ida ne kome nayi na karyawa
to sai na karbo mishi dumame wurin Goggo Ayalle
ya fara dashi kafin ya ci wani abin.
Kullum zai baro gonarshi sha daya ya dawo
gida, yana dawowa zai tube kayan jikinshi ya shiga
bandaki yayi wanka, ni kuma sai in tsoma su a
ruwa in wanke su in shanya in wanke mishi ranbut
din nashi na hannu da na kafan in jefa su kan rufin
dakin namu su sha rana, sai da yamma in kwashe
su.
Yana fitowa daga wankan zan sanya mishi
63
tabarma a inuwan dakina ya hau kai ya zauna in
gabatar mishi da abin da na tanadar mishi.
Yana ci muna hira yana bani labarin gonar
tashi, mafi yawancin lokaci in muka zauna a wurin
zai yi wuya mu tashi bai nanata gaya min maganar
da ya saba gaya min ba, ina so in samu damar dda
zan nuna miki halarcina Humaira, ina so in samu
damar da zan nuna miki cewar ni din da namiji ne.
In ya gama abin da zai yi ya kama hanya ya fita
sai kuma in sake zama in shirya mana abinda zai
dawo da azahar ya ci, hakan kuma bai hana ni
tanadar mishi furar da zai sha bayan yaci abincin."
Da daddare kuwa food flaks din mu nake
dauka in kai wurin da ake kwashe tuwon darea
zuba mana namu in yi musu sannu da aiki in dauka
in kawo mana in zuba mana manshanu da yaj1 muci
ba tunda ya hana ni cin abincin hadaka da su ba,
ban dai kara tsinkewa na lamarin gidan yawa na
kara tsorata da zaman gidan yawa ba irin ranar da
aka wayi gari a gidan ana tuhumar Ade 'yar dakin
Yaya Furera wai tayi gulma.
Ade kuwa kishiyar, Ruwailah ce ranar ne na
gane su matan gidan ba shugabancin matan sasansu
suke yi ba, a'a group ne kawai daga kowane sasa ka
ke in kana so zaka shiga kan hakan ne ma nake
64
ganin tanfar gaba dayansu kowacce kokari take ta
janye ni in shiga nata group din.
Ni kuwa kashedin da Ado ya yi min da kuma
ganin abinda ya faru a ranar don ma anyi sa'a Yaya
Baidu yana gida, shi ne ya fito yayi tsawar da
kowacce ta shiga taitayinta da ba a san abin da zai
faru ba, yasa na kara tsorata na kara kama kaina.
Sannu a hankali ma sai na daina zuwa karbo
mana tuwon daren, ina yi mana namu saboda
kullum Ado yana yi. min maganar ke ba taya su
aikin komai ki ke yi ba, amma sai kin je kin karbo
musu tuwon su, in nayi abincin daren dai ban sawa
kowa, amma na rana gaba daya tsofaffin gidan
nake sanya musu, su kuma yaran matan wacce ta
aiko danta ko tazo ta ce in zuba mata in zuba mata,
wacce