Showing 27001 words to 30000 words out of 39976 words

Chapter 10 - Gidan Uncle Return Book 1 Complete Hausa Novel

07 Feb 2025

248

ya fita kasancewar Allah ya jarabceni da laulayi kamar masifa.




Ranar wata lahadi data zamo baqar rana mafi muni a rayuwata 12/8/2003 fadan qabilanci ya barke a yankin da muke tsakanin Hausawanmu yan kara masu harkar shanu, cikin dare muna kwance nida mijina sai mukaga hayaqi ya turnuke sararin samaniya na tashi da sauri na tureshi daga jikina nace “Abban Hudah tashi kagani yanda gari yayi baqi" haka nake Kiransa tun lkcn da nasamu ciki saboda yanason sunan kamar me, shima ya miqe na janyo qaton cikina na fito tsakar gidan daidai lkcn da aka buga qofarmu na kalleshi da sauri ya matso gabana ya riqe hannuna yace.
“Ina tunanin maqotanane Amba bari naje kamar wutace ta Kama a wani gidan" Jinjina masa kai nayi har ya fita ya dawo ya shafa cikina yace “ki kulamin da kanki" daga haka bai sake cemin komai ba sai sanyin jiki daya fice yabarni dashi naja qafata daqyar na shiga daki na zauna gabana yana faduwa, bayan kamar wuccewar awa daya sai naji matan unguwarmu Hausawa sunata ihu na zabura da sauri na fita nima ashe mugun gani zanyi Abba a gabana akayiwa mijina yankan rago Ina kuka yana miqomin hannu nima Ina miqa masa ya har yakai ga durqushewa ya bude bakinsa jini na zuba a maqogwaronsa yace “ki...gudu Khadija kada su cutarmin dake da dana...."




Yana fadin haka ya fadi yana ambaton kalimattusshahada take mala'ikan mutuwa ya zare rayuwar Bukar inaji Ina gani yana kwance kamar na kirashi ya amsa yan ta'addan nan suka fara yayyafa mana fetur matan da aka kashe mazajensu masu yaya na daukan yayansu suna gudu nikuwa na tsaya qyam sai kallon mijina nakeyi na kasa furta ko kalma daya, matar limamin unguwarmu ne ta riqo hanuna tajani da qarfi Ina cijewa Ina kuka me ban tausayi ina kiran sunan mijina Ina gudu daqyar mutanen nan suna binmu har Allah ya taimakemu muka tsallake shingen da suka gicciya.
Tsayawa sukayi suna tattaunawa tsakaninsu kafin su fara sakar mana alburusai Abba munkai mu dari Amma daqyar tara muka tsallake muka ratsa daji me dogayen bishin robber muna gudun wucce sa'a kwana muke muna gudu babu ruwa babu abinci idan qarfin mutum ya qare saidai kaga ya yanke jiki ya fadi anan zamu tafi mubarshi a haka a dajinnan Saida muka shafe sati guda ya kasance saura mu hudu ranar da muka shiga sati na biyu ne muna tsaka da gudu qafata ta riqe na durqushe ciwo ya fara daganan Matar liman ta dubi sauran matan tace musu “kuje mu zamu taho daga baya Ina zaton haihuwa ce"




Kamar masu jiran tsammani suka cigaba da gudunsu mukuma muka wanzu anan tsayin dare inata fama babu wani me taimaka mana dako paracetamol saidai matar liman tayi min addu'a ta tofamin wajen asuba ciwo ya kamani ganga ganga cikin ikon Allah na haifo yata mace kyakkyawa sosai saidai kash kuka daya tayi a duniya ta mutu itama miqewar da matar liman zatayi kawai saijin saukar harsashi mukayi a bayanta ta yanke jiki ta fadi take nima na kifa kan jaririyar cikin halin Dana kasa bambamce mutuwa nayi ko Suma koko idona biyu,
Inaji sukazo kanmu suka rinqa turamu da qafa harda me kwanciya yana kara kunnensa a qirjinmu yaji babu numfashi sannan suka sake harbin matar liman suka taka qirjina suka wucce suna cewa Nonsense Hausa, da wannan azabar takanin da sukayi suka tafi suka barni sun dauki 30 minutes da wuccewa sannan na samu na miqe daqyar na kalli Matar liman da jikinta ya saki na kalli jaririyar yata da take kwance babu numfashi sai na fashe da kuka na juya naci gaba da tafiya inabin sawun wadannan yan ta'addan a gaba na ishe gawar matannan biyu da muke tafe tare dasu na tsallakesu na wucce,
Wata hanyar na yanka saboda gudun tsautsayi Ina tafe Ina rike ciki ni kadai a baya bana samun komai saidai idan yunwa tacini na yagi ganyayen bishiya naci anan ma na shafe kwanaki biyu nazo wuccewa ta wani guri me duhun gaske na rinqa jiyo nishin mace tanata kiran sunan Allah, gabana ya fadi nayi kamar na tafi sai Kuma naji bazan iyaba take na juya na nufi gurin da nake jiyo nishin,




Hankalina ya qara tashi ganin wata kyakkyawar bafulatana ce kwance cikin halin naquda ga kan dan ya danno amma babu Wanda zai taimaka ya janyo matashi gashi qarfinta ya qare take naji wata juriya tazomin na matsa na budata na rintse idona na janyo Mata babynta mace kyakkyawar gaske yarinyar ta rinqa kukan neman agaji na kama hannunta nasa mata a bakinta na kalli uwar ashe itama ni take kallo ta lumshe idonta tare da yafitone cikin muryar galabaita tace “Adamawa Maybalwa Moddibo Almud" daga haka bata qara furta kalma daya ba saida tayi nishinta me wahala da firgitarwa jikina yanata rawa tace “amanarta nabarmiki ki riqeta tamkar yarki ta cikinki Allah yasan abinda yake nufi ya aikoki cikin rayuwarta Sunana Ummuh Salma Adamawa Maybalwa Moddibo Almud" daga haka bata qara furta komai ba sai shaquwa da tayi idanunta suka kakkafe,




Najima Ina kuka da kallon wannan tashin hankali kafin hankalina ya dawo jikina na cire dankwalina na nade yarinyar dashi mukaci gaba da tafiya duk yanda naso babyn ta Kama nonona taqi saidai idan naji tana kuka na bata ruwa a haka har Allah ya fito dani titi nayi saa motar kano ta cika saura gurin mutum daya na shige abina inata rarrashin jaririyar, lkcn da akazo karbar kudin mutanen nayi wuqi wuqi domin banida ko sisi drivern da kondostan suka rinqa fada har suna iqirarin zasu saukeni,
Wani mutum ne a motar da tunda na shigo yaketa kallona ya dauki kudina ya basu na kalleshi kawai sai hawaye ya qara wankemin fuska ya dauko wani youghurt dake gefensa yabani na karba jikina na rawa na dago kan wannan jaririyar na fara bata, Allah sarki baiwar Allah ashe yunwa takeji itama aikuwa tasha da yawa kamar ba jaririya ba na sabata a kafadata tayi gyatsa sannan na dauki sauran madarar nasha kadan na rage Mata ta anjima tunda taqi Kama nonona,
Sai a lkcn naji wata nutsuwa tazomin na zubawa yata ido inata kallonta Ina murmushi qaunarta tana ratsani inajin kamar yata data mutu minti uku bayan haihuwarta a hankali na furta “kece madadin Hudattu na Hudah ta tafi Hudah ta dawo" nidai bansan tsayin lkcn da muka dauka ba muka sauka a tashar unguwa uku kaina ya juye na kasa gane komai hakan yasani neman guri na zauna,




Wannan mutumin ya matso gabana ya tsugunna yace “baiwar Allah darene Kuma alamunki sun nuna baki cikin nutsuwa dagake har yarki idan zai yuwu kibini gidana ki kwana da saff sai musan ya zaayi" banida zabi hakanan nabi mutumin nashiga motarsa muka tafi Sulaiman crescent wani babban gida Alh Ibrahim yabani daki daya ya fita ya siyomin abinci da kayan sha yace naji nayi wanka, banyi masa musu ba saboda babban mutum ne duk da bashida yawan shekaru amma yanada kamala, na dade a bandakin Ina gasa jikina da yayi tsami ni naga haihuwar rashin gata babu gyara ashe har qaruwa nayi bansani ba,
Ina fitowa naga wata nurse tana duba yarinyar tabata magunguna nima tace muje ta dubani, aikuwa a daren nan Saida akayimin dinki nasha wuya Amma naji dadi, abin mamaki muna dawowa naga Alh Ibrahim ya gwaggwafe yana yiwa Hudah wanka sai abin ya birgeni naji qaunar mutumin ta ratsa zuciyata tunda nake bantaba gani ba kojin labari sai akansa hatta nurse din abin yabata sha'awa ya dago yaga munata kallonsa ya share hawayensa yace “na saba yiwa jarirai wanka Ummuh tanashan wahala wajen haihuwa saidai yaran basa zama yanzu itama narasata ta mutu da tsohon cikina a jikinta Ummuh mace me biyayya sun qonemin ita Allah ya Isa....."




Duk da kasancewata abar tausayi amma sai naji tausayin Alh Ibrahim yafi taba zuciyata hatta mai shine ya shafawa Hudah yasa mata Pampers yasa mata wata kyakkyawar riga yayi kissing nata ya miqomin ita yace “kibata abincinta" a sanyaye nace “bata kamawa" a kidime ya dubeni yace “meye yasa?" Girgiza masa Kai nayi na karbeta na rungume ya miqe lkcn 11:30pm ya fita saijin tashin mota nayi bansan Ina yajeba harna fara bacci naji ya dauketa ya fita da ita na miqe nabishi sai naga ashe madarar jarirai ya siyo ya hada da ruwan zafi yaje bata yana hawaye na rakube ina kallonsa damuwa tace ta fito fili amma yanayin yanda yake kallon Hudah yana hawaye har hawayensa na diga akan fuskarta ya nunamin lallai yafini shiga damuwa fitowa nayi ya dago ya kalleni ya kasa jurewa kawai saiya qanqame Hudah a qirjinsa yace “agabana suka yima yarana biyu yankan rago sukayiwa matata fyade sannan suka fice dani suka bamkawa gidan wuta dama ace wannan yatace da Ummuh tabbas data zaftaremin wani kaso cikin damuwar da zan dawwama a cikinta.........
# *UMMUH HAIRAN*
[9/22, 8:28 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: *🌱F.T G.U RETURN🌱*
*19*



*_Pls paid before read, account Fauziyya Tasi'u 0255526235 GTB ko hoton card MTN ta wagga number 09013718241 or VTU for this number 09031307566 regular 200 VIP 500_*




Jikinane yayi matuqar sanyi na juya na zauna daqyar Ina Jinjina abubuwa tabbas duka damuwarmu iri dayace saidai tashi ta ninka tawa, ya jima yana zaune a parlourn bansan sanda ya tashi ba ya shiga wani dakin ya kwanta Ina jiyo karatun qur'anin sa har bacci ya daukeni da asuba na tashi inaji ya tafi masallaci saida haske ya hudo sannan ya dawo ya dauko Huddatu ya kawomin muka gaisa ya tambayeni jiki nace da sauqi ya tsaya kamar zaiyi mgn saikuma ya fice nabisa da kallo kusan ssakanni bayan fitarsa sannan na sauke idona akan yarinyata da taketa baccinta cikin kwanciyar hankali na kwantar da ita nima na kwanta.
Goma mutsu²n Hud ya tasheni gashi ban iya komai na jarirai ba, da dabara na cirenta Pampers Ina Shirin sanya Mata ruwa ya shigo yace “kakkai kada kisa Mata ruwan sanyi" wipper ya dauko ya miqomin na karba na gogenta jikinta shikuma ya fita bai jima ba ya dawo da madarar daya hado Mata yasa a cikin ruwan sanyi ya dauketa ya shafeta da zaitun ya sanya Mata kaya a dakin da nake naga ya bude wani akwati ya dauko kayan nan ma saida ya share qwalla yana sanya Mata yace “tanadin haihuwar Ummuh ne kullum idan tasamu ciki kayan Mata take siye Allah kuma sai yake bata maza"




Da wannan ya gama shirya Hud ya miqomin ita ya fita ashe kitchen ya shiga ya sama mani abinda zanci ya kawo min bayan naci ya tambayeni unguwar mu na fada masa yace to na shirya yana zuwa, fita yayi yadan jima sannan ya dawo yace na fito mu tafi na fita Ina rungume da yata ya budemin mota na shiga ya koma duk kayannan na baby ya daukosu akwati biyu yasamin a but muka tafi.
Daga Sulaiman crescent zuwa Zoo road da yar tafiya a hankali yake tuqin yana satar kallon Hud har mukaje ya fita yayima megadi magana shikuma yaje yayiwa Abba magana suka fito tare ya miqa masa hannu sukayi musabiha sun jima a tsaye naga Abba ya nufo motar da sauri ya bude ya janyoni ya rungumeni yana gdy ga Allah yacemin “Khadijatou Ina Bukar badai sun kasheshi ba?" Sai lkcn abin ya dawomin danye na sake fashewa da kuka me taba zuciya. Alh Ibrahim yace.
“Ai baa bincike Alh yanayin da na ganta kadai ya Isa ya tabbatar da cewa ta rasa bangon rayuwarta kamar yanda na rasa duk wani farin cikina tabbas sun kashe Mata mijinta ko Khadijatu?" Daga Kai nayi Ina kuka nace “a gabana sukayi mashi yankan rago Abba" rungumeni Abba ya sakeyi yana hawaye yace “wannan itace yar da kika Haifa?" Shiru nayi inason fadin gsky amma qaunar da nakewa amanata yasa naji bazan iyaba jana Abba yayi muka shiga gda yayiwa Alh Ibrahim gdy yace yau shima zai wucce Adamawa duk ranar da Allah ya dawo dashi zaizo yaga Huddatu




Koda naji ya ambaci Adamawa saida gabana yayi kwance kwance ya fadi hakanan dai na daure mukayi sallama nayi masa gdyr kayan babyn daya bamu muka shiga gda muna shiga Shattima dake zaune yana karatun exams da sukeyi a lkcn ta gama secondary ya taso ya matso gabana ya miqa hannu ya karbi Huddatu ya kalleta ya kalleni sai yayi murmushi yace “dukkanku daga ke har Uncle Bukar bata kama daku dani take kama" kowa dake parlourn saida yayi dariya nace “kakai me qarfin hali kuwa batayi kama damu ba Amma tayi kama dakai" dariya aka kumayi shikuwa ya qanqame Hudah tun daga wannan ranar shine ke rainonta komai shine yakeyi Mata duk wani tanadinsa akanta ya qare hakan ya qaramin qaunar dan'uwannawa ganin yanda yake qaunar yata.
Abinda ya rinqa bawa kowa mamaki yanda duk wani maganin duniya da ake nema iyayena suka tsaya suke nemansa domin Hudah ta Kama nonona amma fir taqi idan aka matsa Mata ma sai tayita shidewa dole aka qyaleta ake siyanta madara akaci gaba da bata, watanni uku da dawowarmu Kano Alh Ibrahim yazo gdanmu da shatara ta arzikinsa yawanci tsarabar duk ta Huddatu ce bai wani jima ba saboda yace “German zai wucce zai koma can da zama" ya jima yana kallon Hudah sannan mukayi sallama tare dayi masa fatan alkhairi ya tafi har airport Abba ya rakashi tun daga wannan ranar bamu sakejin duriyarsa ba ko yana raye ko ya mutu Allah masani, wannan shine asalin abinda yake boye Abba bani na haifi Huddatu ba"



*_ASALIN LABARI_*



Shiru ce ta gauraye parlourn bakajin komai sai qarar A.C kowa inda hankalinsa ya tafi daban Ammi ce ta katse shirun da cewa “amma tabbas kin munafurcemu Khadija meye ya hana ki fadi mana gaskiya tun farko?" Hudah da tunda Amba ta fara bada labarin take kuka ta miqe ta nufi qofa ta fice daga parlourn suka bita da kallo babu Wanda ya iya yi mata mgn, dakinta ta shiga ta zauna a qasa ta saki sabon kuka me sauti cikin qunar zuciya da tunanin abubuwa da yawa, babban abinda yafi damun ranta shine son sanin wacece ita Adamawa Maybalwa Moddibo Almud “to waye Moddibo Almud” meye alaqarta dashi? Abinda taketa tambayar kanta kenan tana cigaba da rera kukanta,
Ji tayi an bude qofar an shigo ta dago ta sauke idonta cikin nasa yana dafe da qirjinsa idanunsa sunyi zuru² ya zauna a qasan shima kusa da ita ya dora hannunsa daya a saman kanta yanason yin magana amma ya kasa ji yakeyi idan yayi mgn kamar zuciyarsa zata fado, shigewa tayi jikinsa tana kuka ta qanqameshi tace “ashe ba uwata bace Uncle meyesa kuka boyemin tun farko?" Cikin sarqewar murya yace “wh...what?" Kukanta taci gaba dayi tana cewa “banida wani jibi da zuri'arku hasali ma munyi hannun riga ta wasu bangarori Uncle ku kun kasance Kanuri nikuma na kasance Bafulatanace Uncle inane Adamawa Maybalwa waye Moddibo Almud? Ina zangansa naji waceceni.




Wani numfashi ya sauke me zafi yace “Alhmdllh ni dama na dade inajin hakan a raina amma meyesa Aunty Khadija tayi mana haka meyasa bata bayyana mana gsky tun farko ba saida me afkuwa ta afku?" Kukanta kawai takeyi yana shafa bayanta, shigowar Ammi ne yasashi daga kansa ta dubesa tace “meye ya dawo dakai daga asibiti Faruqu yace baisan ka fitoba" numfashi ya sauke yace “jikina ne ya bani Life bata cikin nutsuwa Ammi duk abinda ya shafeta a ruhina nake jinsa don Allah kada ki koreni ki barni na rarrasheta mu nemawa rayuwarmu mafita"
Tunda ya fara mgnr take harararsa har ya gama tace “tashi ka fita kan na saba maka yo kai har mutumin arziqine da zakace zaka rarrasheta ka rarrasheta ko ka rarrashi kanka" dagowa yayi zaiyi mgn ta rintse idonta tace “fice nace daqiqi mara kamun Kai...." Kalmar ta sokeshi sosai ya miqe yana hada hanya ya fice daga dakin daqyar yakai kansa waje ya shiga dakinsa don bazai iya driving ba zuwa gdansa, Juyawa Ammi tayi ta kalleta tace “da kika fada masa din dadin me kikaji shashasha dake kidaici gaba da biye masa yayita kaiki yana baroki saura kwanaki ashirin da daya bikinki idan ya rarakeki kyasan me zaki fadawa mijinki" zaro ido tayi gabanta na faduwa Ammi tace “koda yake mema ya rage Miki komai ya tsotse dake ke sakarya ce wannan yaron har abin sone? Inda nice ke ko kallon tsiyama zai samu a gurina ne balle na arziqi to ki kiyayeni insha Allahu bazai taba samun ki ba yo ubanme ma zaayi dashi"




Tunda Ammi ta fara mgnr take kuka har saida takai qarshe sannan tace “ni koma ya yake inasonsa Ammi don Allah kada ku rabamu bansan halin dazai kasance ba idan kuka rabamu...." Gwabe mata baki Ammi tayi tace “dacan ya yake kasancewa ko an fada miki zai mutu saboda ke kinga ki kiyayeni Hudah zanci qaniyarki ke dan ubanki ma barin gidannan zakiyi gara na rabaku kada ku jamana abin tur ki qyalemu ma da tunanin yanda zamu tunkari mijinki"
Bata qara mgn ba kuma batayi Shiru da kukanba Ammi ta tashi zata fita tace “saboda banida kowane bakisan asalina ba shiyasa bazaki barni na rayu da farin cikina ba wlh Ammi matuqar baku barni na rayu da Abdulfatah ba nikuma saina gudu bazan taba zama da wani namiji matsayin miji bashi ba, haba Ammi yama zakuyi haka ya zaayi dan'uwana yana sona inasonsa kukaini inda baasan ciwona ba"




sosai kalamanta suka sanyaya jikin Ammi ta fice da sauri tana haki saboda bata taba tunanin haka daga Hudah ba ita kullum abinda yake bata mamaki yaushe Hudah tayi baki haka da bata iya jure magana indai akan Shattima ne saita mayar, tajima tana jinjina kalaman nata kafin ta miqe ta tarar da Abba yanata kaiwa da komowa a parlourn saman ya juyo yace “meye ya hadaki da Autane naga ya tafi dakin baqi yana layi naje na tarar dashi a kwance yanata kuka na tambayesa meye yake damunsa yacemin kece" zama tayi tace “gsky ce bayaso yaje zai sake hurewa yarinyar nan kunne shine nace ya fita daga dakin" matsowa yayi gabanta ya tsugunna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login