Showing 63001 words to 66000 words out of 67143 words

Chapter 22 - Uwa Ko Ukuba Book 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

26 Sep 2025

804

hannunta daya rike, he just hates her sabida yanda tasan waye Fawaz ta aika Asmeey dashi, dayayi raping nata fa? Dawazai auri Asmeey? Tazama bazawara kenan fa, yakai kusan 4min abayin yatashi ya wanke fuskansa yafito sai kawai yaji baimason fitan daman fidan wani friend nashi zaije sai kawai yakarasa yasamak kofansa key yahau gadonsa ya kwanta.
[06/01, 15:27] +234 806 229 2100: =ث?UWA KO UKUBA=ث?



'
EPISODE 2?? 0??



Ramla ce tashigo dakin Mamie da kayan Asma u na salla, Ya Aya takarasa shafa mata mai dakuma magungunan da Ya Mustapa yabada adinga samata ajiki wajen duk wani tabo na duka dake jikinta, jikinta duk ciwo fuskanta bai sabe ba, tayi ja tana zaune da towel da hannunta karyayye, Aya tadauki jakan taga kayan salla ne tace  Ramla simple kaya zaki kawo or even better dauko jakan dana ijiye mata agaban wardrobe naku na jiya wannan ledan dasauri Ramla tace  toh tajuya tafice, Aya ta kalleta tace  kinkicin komi you have to eat kona miki noodles ? Gyadama Ya Aya kai tayi alamun eh, Aya tace  ohh har yanzu baki dena son indomie ba toh shikenan, meyake miki ciwo yanzu ? Ahankali tanuna hannunta, Aya tace  zai dena sannu ko, Aysha ma zatai magana dake takira dazu bari na kirata gyadamata kai tayi, Mamie tashigo dakin da tray na shayi mai kamshi tace  kisha shayin nan Asmeey yana helping da healing kashi sosai Aya tace  Mamie wai baki gajiya by now bai kamata kina all this work serving namu abinci ba dan dariya Mamie tayi tace  Wlh I m use to it, to yara maza gareni Aya dole nine zanyi serving nasu abinci, da Allah yabani mace da tuni duk bana abubuwan nan, Ma u ya hannun yarage zafi ? Gyadama Mamie kai Asmeey tayi, Mamie tace  sannu kinji wai ina kayanta sanyi na shiganta Aya tace  Ramla taje takawo Mamie tace  toh bari naje naba yayyinku abinci dasauri Aya tace  Mamie kibarshi bari naje na basu dasauri Mamie tace  no zauna da Asmeey tana fita Ramla na shigowa taba Aya ledan tace  ina zuwa tafice Aya tabude kayan wani simple english gown taciro black ne tawuce wajen kofan ta rufe da key sannan tadawo tadagata pant tafara bata akunyace tashiga sawa Aya ta taimaka mata sannan tabata gown din tasaka yamata kyau gown din Aya tai murmushi tace  kinga yanda gown din yamiki kyau tadauki tea tabata a right hand nata dakeda lpy tace  zauna toh bari naje makiki indomie Ya Aya tafice yarage saura ita kadai adakin, dakin tabi da kallo hakanan kawai taji tsoro yakamata dasauri ta mike hannun data rike tea dashi na rawa kaman zata kabar da tea ta shiga tafiya dasauri da kyar tabude kofan daidai Ya Mustapa na shirin shigowa ta tsaya chak tana numfashi yace  Asmeey menene give me the tea yasa hannu ya karbi tea yana kallonta yace  bakowa adakin ne? Gyadamai kai tayi tace  Ya Aya taje kitchen gyadamata kai yayi yace  muje juyawa tayi ahankali ta shiga ciki ta zauna bakin gadon hannunta ya dauka yarike yace  yana hurting sosai ? Girgizamai kai tayi daidai Ramla na dawowa dakin yace  stay with her Ramla bayan kinyi breakfast I will come back namiki fixing drip ta gyadamai kai dakinsu Hameed ya leka yaga dukansu sunyi wanka suna bacci maida musu kofan yayi yarufe yawuce dakin Abba inda nan Mamie take yanzu yayi knocking tareda sallama ya shiga.

Around 1 Abba yafito yana sanye da tufafi mai kyau da babban riga da hula yataho dakinsu Hamad bude kofa yayi Hameed yagani zaune kan gado yayi alwala yace  bazakaje masallaci bane adan kunyace tuna abinda yama Abba dazu yace  Hamad nake jira yana alwala a bandaki daidai nan Hamad yafito Abba yace  kumuje turare Hamad yawuce ya fesa yana sauke hannun rigansa sannan yataho Hameed biye dashi suka fito sauka sukayi suka fito tsakar gida Baba suka hango shima yasha manyan kaya masu kyau ya kafa hula yana gaisawa da Yayan Mom da aminansa guda biyu dake wajen sai kuwa ustazun yaran gidan dan babban malamin bai sami daman zuwa ba.

Masallaci suka shiga aka tada salla sukayi ana sallamewa da 2mins Hameed yatashi zai fice Abba yace  koma ka zauna zama yayi kusa da Munir dake gefensa, Abba yakalli Hamad dake zaune kusada Ya Mustapa dake azkar sannan Ustaz yacire Mic daga wuyanshi yakashe duka, babban aminin Baba yafara bude wajen da addu a kowa ya kallesa yace  tom babban aminina ya gayyace ni dan nazo nan nabada auren diyarsa Asma u atare gaban Hamad da Hameed da Munir da sauran yayinsu suka buga, rawa hannun Hamad yafara gently yaji saukan hannun Ya Mustapa akan hannunsa dasauri Hamad yadago kansa yakali Ya Mustapa hawaye harsun taru aciki yasauke kansa da sauri kasa, Baba ya kalli Ustaz yace  Bismillah Akaramakallahu gyaran murya Ustaz yayi yace  Masha Allah ayau mun taru anan domin muzama shaida akan auren daza a daura tsakanin Hussain Abubakar wato Hamad dawani irin sauri Hamad yadago kansa kirjinsa ya buga shima Hameed dudda he felt relieved but he was shocked dayaji sunan Hamad, Munir yawani irin jin dadi harda wani motsi kaman zai kwaso shoki Hameed yamai wani annoying look ya natsu yana murmushi, Ustaz yace  da yarmu Asma u Muhammad Sani, anyi duban jini da sauransu? Ya Mustapa yace  Hamad AA ne, blood group O negative zai iya auren kowa Ustaz yace  Masha Allah nan yacigaba da daurin aure tsakanin Hamad da Asmeey akan sadaki dubu dari Baba ya fiddo da kudin yabiya duk su Abdullahi da Faisal dasu Hameed are in shock cus basu san da maganan ba kawai aka shafe, Abba yace  kawo goron da sweet Doctor tashi Ya Mustapa yayi sai alokacin ya saki hannun Hamad da kawai ya sauke kansa kasa kirjinsa sai bugawa yake, baimasan wat he is feeling ba, Ya Mustapa yashigo da goro one bag da sweet aka bude aka rarraba Aminnan Baba suka amsa suka sa albarka sukai sallama suka tafi, Yayan Mom Alhaji Mahmood yace  toh ni ku nunamin sirikin nawa ba gane yan biyun nake ba wanne ne Hussein wannene Hassan? Baba yayi dariya yanuna Hamad yace  gasa nan sai kawai Hamad yaboye fuskansa a guiwa gwanin kunya sai kace wata Amarya mace, zokaji dariya a masallaci hatta Ustaz saida yayi dariya da su Ya Faisal ma haka shima Hameed saida abin yabasa dariya dudda he s in shock, Munir harda rike ciki dan wlh Ya Hamad kaman wata mace abinda yayi sosai fa ya kife fuska a knees.
Baba yakame tasa dariyan yace  surukinka akwai kunya Alhaji Mahmood Yayan Mom yace  ahh ai nagani to Masha Allah, Allah yasa albarka, ga Asma u dai mun baka amana, mun yarda dakai cus nasan waye mahaifinka tun muna yan samari kafin ya koma kano Baba yace  kwarai Abba ya jinjina kai, Alhaji Mahmood yace  zama da mata sai hakuri saikuma anakai zuciya nesa dan haka ina maka fatan alkhairi bari naje Alhaji ma assalam yamika musu hannu yana gaisawa da kowa Baba ya bisa dan yanaso yayi magana dashi yajuyo yakalli Munir dake dariya yana washe baki uwa Aj 1 aka daurama aure yace  kai zonan tashi Munir yayi yabisa da sauri.
Ustaz yamike yayi sallama da Abba yafice, Abba yatashi yadan kalli Hameed daya sunnar da kansa yana sosakai na rashin gaskiya Abba yace  muna komawa gida za akai kudin aurenka gidansu ita wacce kakeso din tijararre yawuce yafita, Ya Abdullahi yatashi yana kallon Hamad dahar lokacin yakifa kansa kan guiwansa yace  ango, ango, ango Hamad Faisal yace  wuhuhuuuu sai amarci ina gayamaka Ya Abdallah zokaga dariya harshi Ya Mustapa saida yadan kyakyata amman a fuske, Hameed yataso shima yace  ku tsaya kuje Yaya duk suka tsaya suna kallosa yace  yanzu kowannenmu zai dauki topic ne dazai koyamai kan zaman aure, ni Hameed his twin brother i will take him kiss and hug zokaga dariya, Ya Faisal dan sune sako dagashi sai su yace  as yayan ango I will teach him tarayya wani kalan tashi Hamad yayi tsaye da duka hannunsa a fuska zai fice suka rikeshi suna ihu.  Angooo Angooo kaman zai fashe da kuka Ya Hamad har lokacin hannayensa nakan fuska yace  Yayaaaaa Ya Mustapa na dan dariya ciki ciki yazo ya karbesa yace  dalla ku cikasa wai mehaka kuna abu kaman yara Hameed yace  damafa yadan kyasa harda siyamata ice cream kaman Hamad zaiyi kuka yace  ni banso yajuya yafita daga masallaci zasu bisa Ya Mustapa yataresu yace  wai sai kun sakashi kuka zaku huta? He s in shock let him be Ya Abdullahi yace  Ya Doctor wai ya akayi Abba ya chanza ? Ya Mustapa ya harari Hameed yace  wannan mara kunyan yanada babe so karya wahalan da Asmeey that is already going through alot shine aka hada da Hamad, once we get to kano zamu mai gini a compound a flat da zasu zauna Ya Faisal yace  but Ya Doctor tayaya Hamad zai fara rayuwa da mace ku baku gansa ba? I m still worried for Asmeey fa, cus can heeeeeee? Suka wani bushe da dariya, Ya Mustapa yayi shiru but duk sun gane maganan sa, Ya Mustapa yace  well all I know is he s a man, komujima komu dade zamuga yaransa Hameed yayi wani ihun iskanci yace  Yaya kaga dan Allah nima muna komawa kano washe garin rannan kuje gidansu Zee wlh Yaya nakai 2more months banyi aure ba zaku iya rasani washhh kunnensa Ya Mustapa yakama yace  kaiko naughty boy ihu Hameed yayi yana dariya yace  sorry Yaya Sorry Ya Mustapa yace  lemme warn you tundaga yanzu naga ka takurama Hamad koka samai ido ranka sai ya baci and that goes for dukanku yasaki kunen Hameed yanuna Faisal da Abdallah da duk ke gimtse dariya, yace  allow him to get close to matarsa, banda sa ido you know yanda Hamad yake wlh na kamaku in anyway ranku zai baci Faisal yace  Yaya bazan samai ido ba but wlh Yaya curiosity wan kee me I just want to see yanda Hamad zaiyi coitus Zokaga dariya Hameed harda faduwa akan dadduma cus ya dauka shi kadaine dan iskan ashe Ya Faisal ma dan iska ne, infact yama fishi iya iskanci is the way he said coitus that killed him finish, duk kawai yanda Hamad zaiyi abu akeso agani, Ya Mustapa yakallesu da Faisal da Hameed sai kuma ya kalli Abdullahi dayaga shima rike dariya yake da kyar hannuwansa har zabura suke sabida yanaso ya tuntsure da dariya yace  ohhh hardakai Yayansu akeso aga coitus ? Ya Abdallah yawani bushe da dariya yana kama cikinsa yace  Ya Musty sorry, sorry, is not my fault, to Hamad din namune wlh ko mace bata isa tanuna mai kunya ba, ni I can t wait to see his wife with belly maybe aruwa zatasha, yaron da a bayi yake chanza kaya yayi wanka how he go do the thing now? With clothes on or off ? Zokaga dariya su ukun kaman mahaukata, ganin suna nema susa shima yayi dariyan babba dashi 40 something years kawai Ya Mustapa yajuya yafice daga masallacin yace  yan iskan yara sunma manta duk a masallaci suke zama sukayi ciki suna gulma suna bude babin Hamadi.
[06/01, 15:27] +234 806 229 2100: =ث?UWA KO UKUBA=ث?



'

EPISODE 2?? 1??




Tsaf Baba ya sanar da Yayan Mom Alhaji Mahmood abinda ke faruwa tundaga kan zancen fyade, wanda already tun jiya ya sanar dashi awaya dakuma zancen karbe gidan gadonsu datayi, ran Alhaji Mahmood yabaci yanaso yaje yasameta Baba ya hanasa yace  yabarta tayi yanda taga dama da gidan sundanyi magana kafin yawuce shima, Baba yawuce yatafi.

Baba na zaune dakin Gwaggo, Ammi ta shigo, Aya ta shigo, Gwaggo na zaune daketa washe baki, Mamie ma haka, Baba yace  Aya na aurar da Asmeey! Dasauri Aya ta kalli Baba tace  Baba Asmeey ? Gyadamata kai yayi yace  ba a dade da daura aurenta ba anan masallaci sabida inaso jibi su Yaya da Gwaggo suka tashi wucewa su tafi da ita ahankali Aya da gabanta ke fadi tace  waye mijin Baba ? Murmushi Baba yayi yace  Hamadi! Murmushi Aya tayi saikuma tayi wata cute dariya sanin Hamadi sarkin kunya takalli Mamie tasake murmushi Mamie ma haka, Baba yakalli Gwaggo yace  Gwaggo bance ki fitar da zancen nan ba Asmeey y ata ne nakuma aurar da ita na sanar da Baffan ku Aya Alhaji Mahmood hardashi wajen daurin aure, zuwa gobe idan Asmeey tadan sami karfi da kyau zan sanar da ita, kafin kitafi inaso keda su Ramla ku hadamin kayanta tsaf da credentials nata da komi nata zaku iya ciremata kaya kala biyu da zata saka gobe da shi jibin tayi tafiya, sauran zansa akai mota yau din nan dasauri Aya tace  toh Baba Ammi tayi murmushi tace  Allah sanya alheri Mamie Mamie tace  Ameen Ameen nagode dan hira sukayi Aya sai wani dadi takeji.

Ranan sai yamma Ya Aya tatafi sai alokacin Asmeey tafara jin damuwa bataga Mom ba tana nan saita fara tunane tunane Ya Hamad ma tadanyi shiru saita kalli kofa shima bata gansa ba duk saita farajin ba dadin Munir ya shigo yana wani murmushi yahayo gadon yace  Asmeeeyyyyy dan hararansa tayi tana turo baki tace  sunana kake kira kai tsaye dariya yasake yi yace  I am just happy sabida ke  ni? Asmeey tadan tambayashi dasauri yace  wai Nana dan murmushi Asmeey tayi bata kara magana ba tadaura kanta kan pillow tana kallon yanda yake taba wayansa yana Instagram sai kawai Mom tasake fadomata arai tace  Munir Mom na side dinta? Yana jinta Munir yayi banza da ita hannunta mai lafiya tamika ta taba Munir tace  Munir Mom fa ? Batare daya kalleta ba yace  kije takarasa karya dayan hannunki duka kinga saiki huta shiru tayi bata sake cewa komiba kanta na kan pillow tana kallon wayansa tashiga lumshe idanu ahaka bacci yayi awon gaba da ita.

Sai wajajen 11 nadare yashigo gidan kawai dan kar ace this and that ne da yau yakoma Kano sabida kunya shigowa gidan yayi yahayo sama zai shiga dakinsu Abba yace  Hamad dago kansa yayi yasauke yace  na am wucewa yayi gaban dakin Abba daya shiga yabisa abaya Mamie na zaune tana kallon wani shiri da akeyi a tv takalli Hamad din daya kasa kallonta kasa akasa yace  Mamie ina yini  sannu da dawowa Mamie ta fadi, Baba yadauki bandir na 1k din yadago yace  gashi dazu Baba yazo nemanka yabaka bakanan, sadakin Asmeey ne karike mata idan tadan sami lpy saika bata lokacin muna kano kallon kudin yayi saiya kasa karba yasake sauke kansa kasa Abba yace  ha a wai ba sako nake baka ba koko cewa nayi kudin naka ne? Kudin matarka ne karba kaje ka ijiye yana ahaka kansa akasa kaman mai tsoro yadaga hannuwansa yamikama Abba duka biyun yakasa dagokai saura kadan Abba yayi dariya yasamai kudin a hannu Hamad ya karba kaman flash yajuya dasauri yafita daga dakin, dakinsu yawuce ahankali yabude kofan bakaramin dadi yaji dayaga Hameed na bacci ba shigowa yayi yamaida kofan yarufe yatafi wajen akwatinsa yaduka yasaka kudin achan kasa sannan yatashi yafada bayi yafito yahau kan dadduma sannan yadawo gadon ya kwanta yayi shituuuu ahaka bacci am yayi awon gaba dashi.

Surutun Gwaggo ma yau yasake tadata daga bacci bude idanu tayi ahankali Gwaggo na saman kanta tana tafamata uban yawu a hannu wai addu a take dauke hannunta tayi tana turo baki Gwaggo tace  bazaki bari nagama miki addu a ba bakiga kin denajin zafi ba ahankali tace  ni har yanzu zafi yakemin baki Gwaggo tasaki tace  ahhhh lallai kin dace da Hamad dan bakin halinku daya Asama, ohh ni Allah baya amsan adduata kenan ko bakina baida tsarki tashi tashigayi Gwaggo tace  wai bazaki zauna najarasa ba ahankali tace  ni fitsari nakeji tawuce bayi Gwaggo tabita da kallo tace  hartadan fara kumari zaki iya tsarkin da hannu daya konazo namikin tsarkin? Juyowa Asmeey tayi ta kalli Gwaggo tace  huu um Gwaggo ta kwashe da dariya tace  ai shikenan jeki abinki nima daman nayi maganan ne amman ina tunanin warin dazan shaka idan kin hada da kashi maida kofan tayi dasauri ta rufe tafito da alwala tazo tahau dadduma ahankali take salla da hannun.

Yauma haka aka wuni agidan Hamad baya nan only God yasan ina yake zuwa ansan he will definitely do that so babu wani cikin bothers dinsa daya nemesa.
Yau all through Gwaggo na dakinta hakan yasa Asmeey takasa zuwa wajen Mom but zuciyanta na zuci zucin tunanin Mom, sai bayan Isha i Gwaggo tasa Mamie takamata ta kaita kasa dantai bacci da asusuba zata tashi tahada kaya tunda Allah baiyi zuwansu kauye ba sabida ciwon yarnan Asama.
Sallama Baba yayi hakan yasa Asmeey tadago kanta ganinsa yasa tashiga kokarin tashi dasauri Baba yakarasa wajen gadon yakai hannunsa yadagata yana saka mata pillow abaya yace  sannu ya jikin ? Ahankali tace  dasauki Baba zama yayi bakin gadon yana facing nata yakai hannunshi ahankali yadauki hannun nata da aka kulle yana kallo yayi shiru fuskanshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login