Showing 6001 words to 9000 words out of 67143 words

Chapter 3 - Uwa Ko Ukuba Book 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

26 Sep 2025

795

sai kawai tadan turo baki kadan, kaman tai bacci itama haka takeji amman ba hali, wani black Zara cover shoe tadauka tasaka tai rolling gyalen da kyau sannan tai backing bagpack dinta abaya, she looks very smart and elegant kaman wata yar secondary school dan bata da wani tsayin kirki 55/56 ne length nata har a abaya ma, tadauki wayanta kiran iPhone 11 normal tafito, duk kudin Baba kwata kwata bai bata yaransa ba cus shi bai taso cikin kudi ba, dayan flat na left tawuce tabude shima dakin na kamshi an kunna turaren wuta bakowa a falo hakan yasa tawuce bedroom din tai knocking tace  Ammi bude kofan da sauri Ammi tayi cikeda fara a tace  za a tafi kotun ne our fresh Lawyer murmushi tayi dake kawatar da fuskanta sosai tace  eh natafi gyalenta datai rolling Ammi takai hannu ta shiga gyara mata shi da kyau tace  toh adawo lpy Allah bada sa a, ki kiyaye kada ki batama Mamanki rai koda wasa kinji Husna gyadama Ammi kai tayi tareda dan murmushi tajuya tafice Ammi tabita da kallo tai murmushi.
Sauka kasa tayi tafice waje, Mom tagani na kokarin bude wani black jeep mai kyau da sauri tayi wajen motan Mom ta kalleta tadauke kai tashiga ciki abinta ta zauna, baya tabude ta ijiye jakanta sannan tadawo gaba tazauna tasaka seat belt dan baka shiga motan Mom bakasa seat belt ba, Mom taja motan daidai ana kiranta tashiga magana da client nata itakuma tajuya tana danna wayanta da babu anything fun aciki, Mom tahanata tiktok, instagram, the only application takeda shi is watsapp shima sabida family da irin class group na school, Mom is very strict she watch them closely, tiktok saidai ta kalla awayan Ramla kuwa, wayan ma akwai hours datake amfani dashi, for example yanzu suna kaiwa kotu that is the end of taba waya sai kuma idan an koma gida zata taba kadan su yi aiki Mom can call her anytime for a case hakadai so in a way bata taba waya for good 3hours wlh saidai tsakar dare, tana cikin daddana wayan Mom tace  drop that phone and pick the case file dana baki ahankali tace  to jakanta tajawo dake baya ta saka wayan tadauki case file din tashiga dubawa har sukakai court Mom tai parking takashe motan suka fito ta goya jakanta tana rike da case file din, Mom tafito tasaka gown nata duk Asmeey na kallonta, Mom is so elegant and charismatic and very intelligent, she really wants to make Mom happy and be like her but tana ganin kaman bazata iyaba even though she s trying but she is not as brilliant as Mom, she s not as smart as Mom, gama saka gown din Mom tayi tajuyo ta kalleta ba rahama tace  me kika tasani a gaba kina kallo dan murmushi tayi gabanta na faduwa ahankali jikinta da dan sanyi tace  wlh Mom ina sonki dan kallonta Mom tayi sai kawai takara tamke fuska tace  I don t want your dumb love, make me proud that s how you show Mahaifiyarka kana sonta, that s all I require from you, not your nonsense love words wawiya kawai sauke kanta kasa tayi ahankali ga few people here and there na wucewa, Mom tadauki handbag nata tarike tace  kwaso files a back seat bude bayan mota tayi ta kwaso files dayawa tarike Mom tarufe motan tana rike da hadadden jakanta na Hermes suka shiga cikin court din, nan da nan client nata suka taso former controller general ne yace  barka da zuwa Mrs Saraki gyadamai kai Mom tayi majestically tana murmushi yadan kalli Asmeey dake biyeda Mom hakan yasa ahankali Asmeey tace  good morning Sir murmushi yayi yace  wowww wat a voice, wannan Mrs Saraki junior ce Masha Allah, you are so lucky to have this woman as your mother young lady, mahaifiyarki itace real definition na beauty and brains itadai Asmeey na kallonshi bataso tai magana Mom tai fushi, Mom tai magana dashi kafin su shiga court room aka fara case Mom tafito Asmeey tadauki pen da jotter tana kallon mahaifiyarta. Mom is just great, Mommy is just who she thinks she s like the woman dominate the courtroom, Mom tafara magana u must listen dole ne kawai, anya zata taba iya zama kaman Mom kuwa? Mom wants her ta gajeta she s scared cus tasan bazata iyaba. Almost 1hour akai a kotun bayan kowani party ya bada evidence alkali yayi ruling client na Mom as not guilty yasa other party su biyashi sum na 500000 charges sai murmushi Mom keyi, Asmeey sai kallon Mom take cus hardly Mom ke kallan murmushin nan da ita, dan jotter ta dake kan cinyanta ne ya fadi kasa bata sani ba, alkali yawuce yafita aka tattashi a kotu ana, fita Mom tashiga magana da client dinta itakuma Asmeey tashiga hada abubuwan su, tana kokarin sa komi ajaka taga an miko mata jotter ta, wani black hand dake sanye da Rolex chak ta tsaya tanabin hannun da kallo dake sanye da suit black saikuma ahankali tadago kanta ta kalli gabanta, wani dogon matashi ne yana sanye da suit black kyakkyawa gaske yanada yawan gashi akai da dan karamin gemu yana kallonta gently yace  u dropped this Asma u dan zaro idanu tayi jin yanda yakira sunanta kuma bata sanshi ba daidai lokacin Mom tajuyo takallesu anatse tace  Fawaz dasauri matashin yakalli Mom hakan yasa itama Asmeey tajuyo ta kalli Mom dataji takirashi tasa hannu ta amsa jotter batare data sake kallonshi ba, saikuma ta sauke kanta tacigaba da hada kayan shikuma matashin yawuce wajen Mom datai sallama da client nata Fawaz yakarasa gaban Mom cikeda girmamawa yace  Mom ina yini murmushi Mom tamai cikakke tace  your Mom told kadawo you will come and see me today, I told her I will be in this court, muje let s go Son takalli Asmeey dahar lokacin nahada files tace  let s go uwar kwainani common hada files kaman kina hada nation gyadama Mom kai tayi da sauri ta goya jakanta abaya takai hannu zata dauki files din Fawaz yarigata yace  allow me to help dasauri Asmeey takalli Mom data dauke kai abinta tace  muje Son binta Fawaz yayi sukai gaba Asmeey na binsu abaya suka fice wani office Mom tabude tace  kushiga nan kujirani, i have a meeting with the judge Fawaz yafara shiga office din, Asmeey zata shiga Mom tamata wani kallo tace  review those two yellow files gyadama Mom kai tayi tace  toh tashiga office din tana tafiya ahankali, Fawaz na zaune kan couch dake office din yana danna wayanshi iPhone 16 pro max Asmeey tawuce tazauna kan wata single chair dake wajen dake facing dinshi, tasa hannu tadauki yellow files din tabude tafara dubawa, ahankali yajaye idanunshi daga kan wayanshi yadaurasu akan Asmeey dake dube dube, pink lips dinta suna motsi alamun karatu take, kana ganin yarinyar kasan irin yaran nanne da iyayensu did a good job bringing them up sannan an killace su sosai, tundaga kan takalmin kafafunta yake kallo har zuwa fuskanta gadan gyalenta daya zame baya yana hango gaba gaban gashinta dake nan a kwance yayi kyau. Jin kaman ana kallonta yasa tadan dago kanta sama karaf suka hada idanu dasauri ta sauke kanta kasa, gently Fawaz yace  whats with the case Asmeey? Murya chan kasa kaman mai tsoron magana tace  it s confidential murya chan kasa yace  give me ur number dan kallonshi tayi saikuma ta sauke kanta tace  Mom forbid me, I m in school ba aure zan yi ba yanzu the way she talks sincerely shows she s just a Mommy s gurl, like she went straight to point, murmushi yayi yace  baki sanni ba ko? Tun kina jaririya nasanki dan kallonshi tayi da manyan idanunta sai kuma ta sauke kanta kasa tace  but I don t know you, I ve never seen you murmushi yamata yace  do you want to know me? Girgizamai kai tayi alamun no yace  why tace  Mom tace I have no business with men that are not my family ahankali yace  but I m technically your family, I m Mom s best friend son bakisan Maryam kawar Aya ba dasauri tace  Ya Miemie? Gyadamata kai yayi yace  yes ni yayansu Miemie ne sosai mamaki ya kasheta saikuma tasake maida kanta kan abinda take karantawa yadinga kallonta kusan 20min saiga Mom tashigo office din Asmeey ta dago kanta da sauri Mom tamika mata key mota tace  je mota kijirani I am coming karba tayi tawuce tafita daga office din, Mom takalli Fawaz tace  I believe Mommy dinka told you everything Fawaz, like I told her right from the first time kace kanason Asma u zan baka aurenta but kabari tagama Law school, kaga babban salla saura 2weeks immediately bayan salla list zai fito, inaso taje law school, I don t want any distraction na maza kona soyayya in her life, I refuse to give her room for that cus she s a small girl, batasan komiba, everyday tana taredani, I m training her, bawani kokarin kirki Asmeey kedashi ba soyayya at this junction can mess with her IQ, I will send her number to you but can I trust you bazaka sa tai deviating ba? Murmushi Fawaz yayi akunyace yace  Mom I promise you in sha Allah  good Mom tafadi tace  nima I trust you, I know you want wats best for Asmeey, beside kaima Barrister ne, you are in the same profession da ita, so you will help her and guide her through and through gyadama Mom kai yayi akunyace, Mom ta yagi paper tarubuta number Asmeey tamikamai tace  gashinan tashi muje ahankali yasa hannu ya karba yace  thank you Mom murmushi tamai tace  you are welcome Son muje tamike, atare suka fito Asmeey na zaune a mota taga sun fito tareda Mom ita batasan ya akayi ba dudda sunsha zuwa gidansu Ya Miemie bata taba ganinshi ba sai yau, no wonder taga Mom namai murmushi ashe yaron Besty ta ne, har wajen motan ya karaso sannan yama Mom sallama yawuce yashiga cikin wata 2024 mad Benz ya kunna yabar wajen Mom tashigo motan ta tada taja sukabar wajen.
Around 3 suka shigo gidan Mom tai parking gateman yazo yana gaisheta yashiga kwashe kaya sannan suka wuce ciki suna shiga yaran dake falo suna video game dukansu suka taso wajen Mom suna gaisheta.  Mommy welcome welcome Mom murmushi tamusu kadan tace  ya school an dawo jakanta tabude taciro packet na chocholate data sayo musu tabude taba kowa bibbiyu, yaran Ammi ne dukansu su bakwai Ramla ce farko, sai Yusra, Amina, sai Maza four Areef, Ahmad, Kamal sai autan giran Ibraheem, sai karba suke suna godiya Ammi tashiga saukowa daga staircase da murmushi kan fuskanta tace  an dawo ahankali Asmeey tace  ina yini Ammi  lafiya lau sannu ku da zuwa for the second time takara kallon Mom tace  sannu da dawowa Maman Aya ba yabo ba fallasa Mom tace  yauwa sannan tawuce sama Asmeey ma tawuce sama, dakinsu ta shiga kaya tacire ta daura towel tafada bayi dantai wanka tai salla tasan yanzun nan Mom zata kirata kitchen cus Baba na dakinta yau.

KANO
Wuraren 3 nadare yabude idanunshi, gently yatashi zaune yana yaye bargo he feels great and strong duk zazzabi yatafi hannunshi ya tattaba yadauki wayanshi yataba screen din yayi haske ya haska yatashi yana tafiya ahankali yawuce wajen wardrobe nasu yabude shima ahankali yaciro wani farin jallabiya mai kyau da new singlet and boxer da hula yawuce yatafi bayinsu tareda kunna wutan bayin, yakai kusan 30min aciki dan da dabara yayi wankan bai bari ruwa yataba wajen ba sannan yafito ashirye tsaf ya ijiye kayanshi cikin laundry basket yazo ya feffesa turare dakin yadauki kamshi sannan yahau kan dadduma yayi sallan ish i sannan yatashi yafara kiyamun Layl.
Gentle and very soft kira an shi kasa kasa yatada Hameed duk gidansu babu wanda yakai Hamad ilimin addini ya haddace Al Qur ani kawai shi baiyi choosing rayuwan jama malamai baki da sauransu bane cus baison shiga mutane sabida yanayin shi ne but babu wani book dazaka kawoma Hamadi dabazai koyarda kai ba, gashi he loves novels but only Arabic novels yake karantawa. Tashi yayi shima ahankali yawuce bayi alwala yadauro yazo ya shimfida dadduma kusada shi ya tsaya yabishi sallan around 4:30 suka idar. Hameed yatashi yakunna wutan dakin yadawo kan dadduman yana kallon Hamad yace  yajiki?  I m not sick Hamad yafada ciki ciki, hararanshi Hameed yayi yace  kaida ke kuka jiya pretender kawai hade fuska Hamadi yayi, cikeda tsokana dan kawai yasashi yayi magana yace  ohh bakasan sanda kayi kuka ba ko wen u were having pains saiga hawaye sharrr a idanun yaron Mamie tashi daga dadduman Hamadi ya yunkura zaiyi da sauri Hameed yarikeshi yace  yakuri yakuri toh! Zauna lemme go and make coffee for you dauke kai yayi yay banza dashi Hameed yawuce yafita yasauka kasa ya shiga kitchen yasa ruwa a heater yadauko musu cups guda biyu ya zuzxuba instant coffeee ruwan na yafasa ya tsayaya yasamusu sugar da spoon yadauko yahayo sama yashigo dakin ya ijiye agabansa shima ya zauna, gently Hamad yasa hannu yadauki coffee yakai bakinshi ya kurbi kadan Hameed ma haka ahankali yace  an biyamu jiya nasama kudi a account dasauri yakalleshi hade fuska yayi sosai bana wasaba, Hameed yayi murmushi yace  ni wlh bantaba ganin mutum abaibai irinka ba Allah idan da nine bana aiki kai kana aiki I swear ATM card dinka ma dani zai dinga zama tsabagen yanda zanci kudinka kaiko u hate nabaka kudi, you hate kaci kudina why eh Hamadi? Am I not your twin? Why do you hate taking money from me ?Kaman bazaiyi magana ba saikuma murya chan kasa yace  save your money kayi aure da Zainab wani irin zaro idanu Hameed yayi, wlh, wlh Hamad baitabamai magana hakaba sai yau, dauke kai Hamad yayi kaman bashi yayi magana ba yakai tea bakinshi, Hameed yawani kwashe da dariya yace  Hamadi daman kasan ina soyayya da Zee? Duk wayan damukeyi kana pretending kaman bakasan komiba dama kasani? Iyye ikon Allah har wani so kake nayi saving kudi for aurenmu dariya Hameed yahauyi sosai yana kallon Hamad da kaman bashi yayi maganan ba coffee yake kurba abinsa kuma yaki kallonsa, dan tsagaita dariya Hameed yayi yace  jiya I don t know what got over me I almost kissed her ijiye mug na coffeee Hamad yayi kawai ya yunkura zai mike da sauri Hameed yarikeshi yace  Hamadi wai I can t gist with u, if I don t tell you wats going on in my life wazan gayamawa? Besides ma idan baka koyi all this ba how will you get married? Tayaya zaka raya sunnan ma aiki da iyalinka ? Fizge hannunshi Hamad yayi dasauri yayi hanyar kofa, Hameed ya kwashe da dariya yace  wlh matarka ba kunya zataci ba atoh banza kawai bugomai kofan Hamad yayi da karfi, habawa me Hameed zaiyi inba dariya ba abun Hamad is too much shifa Hamad ko kallon mata baya iyayi, you will never see Hamad with any friend aduniya, you will never see Hamad a inda ake maganan banza, ko abu zaiyi on google idan irin advert din banzan nan yayi popping up yahakura kenan wlh, just look at yanzu because of conversation na kiss yagudu yatafi masallaci, Wlh he s not sure Hamad yamasan yanda ake sex taraya da iyali, he remembers suna yara a fiqhu duk ranan da za ayi wani baabi na wani abun kunya he will leave the class, Allah yama Hamad kunya da jin nauyin anything raw and bad he just can t stand it, he just wants to see ranan da Hamad zaiso wata ko ranan aurenshi kai he will love to see matan Hamad da ciki cus yanaso yasan tayaya zaima matanshi ciki ko a ruwa zata sha Hamad fa ko kaya baya iya cirewa gabansa hmm, Allah ya kyauta.

Bayan sallan asuba kowa yadawo banda Hamad daya tsaya muraji a sai wajejen 9 ya shigo gidan the way yake tafiya ka kalleshi saika kara kallonshi, yana taku cike da izza da natsuwa da haiba da kuma kwarjini, farin jallabiyan jikinsa nawani irin sheki, yau Saturday ko maybe saisa yaga motocin yayyinshi agidan dan yawanci on a Saturday sukanzo suyi breakfast tareda Abba ayi catching up rannan ba aiki.
Gently yayi sallama yashiga falon dukansu suka amsa Abba ne zaune akasa kan lallausan carpet dinsu yana sanye da jallabiya da yar hula akansa ga charbi a hannunsa yana kallon Hamad din, sai Ya Mustapha dake zaune kan kujera kusada Abba, sai Ya Abdullahi shima sanye da jallabiya zaune kan 2 sitter, ya Faisal na zaune kusada shi, sai Hameed dake zaune akasa kusada Abba, ga upan atampopi da lace sunkai kusan 50, each da shaddodi anan tsakiyan dakin, ahankali yakarasa cikin falon har zuwan gaban Abba anatse yace  ina kwana Abba kanshi Abba yashafa yace  yaya karfin jikin? Kanshi akasa yace  dasauki tashi yayi yabama Ya Faisal hannu cikeda girmamawa yace  ina kwana murmushi yamai cikeda so yace  ya jikin gyadamai kai yayi yabama Ya Abdullahi shima yacemai  ya karfin jiki hannu yabama Ya Mustapha kanshi akasa yace  good morning Ya Mustapha anatse yana kallonshi yace  how are you? Wat time katashi? Ahankali yace  3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login