Showing 12001 words to 15000 words out of 67143 words

Chapter 5 - Uwa Ko Ukuba Book 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

26 Sep 2025

796

book nata datai jotting komi, tabude zata karanta, Mom tamata wani kallon uku saura kwata tace  kikaje law school haka zaki dingayi? Reading from book? how many days nabaki case din nan nace kiyi reviewing? Murya chan kasa irin na mara gaskiya tace  7days Mom tahada fuska tana karkada kafa tace  idan kikamin shirme awajen nan ranki zaiyi masifan baci Asma u, drop that book I m listening gyadama Mom kai tayi saita ijiye book din gently and calmly tafara briefing Mom voice nata narawa, tun tana yi Mom na aikinta harta juyo ta natsu tana kallonta she really tried, saida takai procedural issues ne takakare Mom tamata wani kallo hakan yasa hawaye yafado daga idanunta tace  sorry Mom Mom tace  okay wat is procedural issues? Anatse tace  Procedural issues shine irin wat is the appealing party claiming the lower court did wrong example kaman ruling on evidence, jury instructions, granting of summary judgment, etc Mom ta gyadakai cikeda gamsuwa tace  okay if you know this then a case file dana baki menene Procedural issues na wajen shiru tasakeyi cus bata karanta yakai wajen ba, Mom na karkada kafafu tace  7days but bakiyi going through this case file dana baki ba sabida kwana biyu nadan daga miki kafa! This should be the last time you will try this wlh kika kara ranki zaiyi masifan baci! I want you to be the best lawyer in this entire Nigeria, I want you to pass bar exam naki, you re my daughter no body a Bauchi can mention law ba akira sunana ba Mrs Turaki and kece magajiyata my successor, you just have to work hard you have no option, you must study Asma u dole ne ba negotiation am I clear? Ahankali Asmeey tace  yes Mom Mom zata sake magana aka bude kofan tareda sallama Baba ne ya shigo yana sanye da wata lafiyayyan gizna datasha aiki yabi Asmeey da kallo dake zaune akasa kan carpet gaban mahaifiyarta idanunta sunyi ja kaman ma tai kuka yace  kinyi breakfast Ma u? Girgizama Baba kai tayi ahankali tace  a a agogon hannunshi ya kalla sannan yazo wajen yasa hannu yadagota yace  wuce kije kiyi kari, je Ammi tabaki abinci Ma u na murmushi tayi sosai Baba daban ne kawai he s very sweet, caring, and very affectionate, ahankali tace  toh Baba wucewa kofa tayi yabita da kallo tafice shikuma yakaraso wajen ya zauna gefen Mom, cikeda nuna rashin jin dadi yace  why are you so hard on this girl? Jibeta kaman ba Hamda na yar bakutu ba duk ta rame haba! Kin addabeta, finally tagama makarantan at least let her rest, all this damuwa yanzu na menene ita da ko list nasu bai fito ba rufe iPad nata Mom tayi tadauki Hermes bag nata tanasa iPad din ciki tace  Alhaji I don t know why you are saying all this now! I ve always been like this to all yarana and Alhamdulillah kai karan kanka you are proud of my upbringing, Asma u is my daughter, no one loves her better than I do anatse Baba yace  of course I know that Barrister and ina alfahari da tarbiyan da kika bama yaranmu Aya is a Nurse, Aisha is a journalist working with BBC, ga Asma u kice dole saitazama lawyer irinki while Munir na MBBS, my point is all yaran nan baki samusu pressure dakike sama Ma u ba, kwata kwata baki la akari da she s still a small gurl, burin dakikasa akanta yasa I don t even know wat you did dahar Asma u tayi WAEC at 14yrs tafara university at 15yrs she s 21 yanzu wai harta gama LLB, please go easy on her, stop pressuring her, karatu is a gradual process all this things dakike forcing nata takoya yanzu she will learn it gradually a law school, karatun dakike sata da menene menene sukesa idan tayi bacci da kyar take tashi da asuba, batada lokacin kanta, bata da lokacin kula da kanta kowace yarinya a gidan nan da kitso akanta banda Asma u sabida rashin time, please and please I don t want this! Kibimin y a ahankali, boko ba dole bane, ba dole Asma u saita gajeki ba we have other kids agidan ai, allow this girl to be herself please Baba yafada calmly yana kallon Mom, Mom takalleshi sai kawai ta dauke kai tace  naji tamike zata tashi yasa hannu yarikota tadawo takalleshi tace  menene kuma ? Murmushi yamata yace  yau ina side naki baki tambayeni mexanci ba dan lumshe idanu tayi tabude tace  mezakaci Baban Aya ? Murmushi yayi yasa hannu a aljihu yaciro bandir na yan 1k guda uku yabata yace  make anything, gashi this is for you takalli kudin he s mutum da baya kallon kudin matansa he always gives them money, murmushi tayi tace  thank you manna mata kiss yayi a goshi yace  natafi, kibimin yarinya ahankali a kotu ahankali tace  to adawo lafiya me y a. Dan dariya Baba yayi yafice daga dakin.
[03/01, 07:38] +234 806 292 7511: =ث?UWA KO UKUBA?=ث?





'

https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn


EPISODE 5??
Abba yace  Abdallah saikai tashi yayi yadauki 5yard yace  Allah amfana Abba Allah kara budi Abba yace  Faisal tasowa Faisal yayi yadauki 5yrd shima yace  Abba Allah saka da allhairi Abba yace  Hassan sai kai tashi yayi ahankali yadauki 5yard Abba yace  zabi another one ku baku da iyali so kala bibbiyu zan muku murmushi Hameed yayi yakara another color daya yace  nagode Abba Abba yajuya yakalli Hamad dake zaune kusada Ya Mustapa yace  saikai Hussaini tashi yayi ahankali yadaura hannunshi yadauki the first two shadda dake in line Mamie tace  iri dayane duka change color cikin calm voice nashi yace  Mami zaban mini Hameed yace  toh yaron Mamie Abba yace  ina ruwanka hararansa Mamie tayi tasa hannu ta zaba masa irin na Hameed ya karba kanshi akasa yace  Jazakallah Abba murmushi kawai Abba yayi yace  to cire mata naku Hajjaju ina Gwaggo ? Mamie tace  taje makota anyi haihuwa wai an mata takwara Abba yadanyi murmushi kawai tadauki atampa daya lace daya tace  gana Ramla tasake ciro wasu biyu tace  gana Asma u  Yusra da Amina Abba yace  to kwasan ma mazan ma Shadan su su Munir haka Mamie tacirema duk wani yara na danginsu kayan salla sai mai aikinsu Lami da yaranta Faisal yahada kayan a babban gana masgo yafita yakai mota yadawo Abba yakalli Mustapa yace  yau salla saura sati biyu ko Abdalla yace  saura 13days Abba Abba yace  okay ina ganin ana gobe salla zamu wuce Bauchin akwai abinda zanyi yakalli Abdallah yace  next week sai akai duka motoci ayi musu service ko Abdallah yace  toh Abba Abba yace  Masha Allah yataba aljihunshi yaciro 50k guda biyu yabama Hameed daya yace  gashi kudin dinki da kudin takalmin salla dasauri Mustapha yace  Abba don t worry about that zan basu please dawainiyan yayi yawa dasauri Hameed ya karbi nashi 50k yace  Ya Mustapha kudi baya yawa Abba ya girgiza kai yakalli Hamad yace  Hamad zo ga naka kin motsi yayi tausayin Abba yakeji sosai baida arziki kaman da kuma sai kashe kudi yake anatse yace  Abba kabarshi inada takalmin salla atare dukansu sukace wanne? Dan kallon Abba yayi kadan yace  Ya Mustapa bought sabon takalmi last week for me dashi zanyi amfani Abba yace  dudda haka amsa wannan nina baku nace kusaya take it kasa tashi yayi yadan kalli Ya Mustapa dayamai alamu da idanu ya amsa hakan yasa yatashi yasa hannu biyu ya amshi kudin ahankali yace  nagode Abba Abdallah yace  zansa mai dinki na yazo ya amshi kayan ya aunaku I will pay for the 2 of you Mamie tawuce aka kawo breakfast kunu ne lafiyayye da kosai Abba kuma aka dumamai tuwo cus he can t do without tuwo, ko half cup na kunnun bai iya sha ba yawuce yatafi sama kowa ya kalleshi but aka barshi gamaci Ya Mustapa yayi yawuce sama Hamad na zauna kan gadonshi yana taba laptop dinshi Ya Mustapa yashigo gently ya ijiye laptop din, Ya Mustapa yakarasa wajen yace  too much sitting is not good for you allow system dinka to rest okay, da lafiya ake komi zama yayi yaduba ciwon is looking very good magani kawai yabashi da allura sannan ahankali yace  do you need anything? Girgizamai kai yayi
Ya Mustapha yace  zamuyi tafiya next week going to family house for salla you know how you get so tell me idan kana bukatan anything for traveling din ahankali yace  bakomi gyadamai kai yayi yace  okay zanje hospital yanzu anjima i will call you sai muje tare na siya maka desktop dinka tunda na da ya lalace Dasauri ya kalli Ya Mustapha hancins a Mustapha yaja yace  dudda you will never say it out loud I know how much all this su system and desktop dinka daya lalace means to you, my tech little bro so we will get it today anyone kakeso baki yabude zaiyi magana Ya Mustapha ya harareshi yace  yimin shiru just complete project din daka fara and send it to Microsoft muga abinda Allah zaiyi, in sha Allah you will win, I also speak to wani friend dina za a nema maka aiki idan an samu any slot, idan kuma babu I think I will just enroll you kafara phd muga abinda Allah zaiyi kafin aiki yazo saikai aure dawani irin sauri Hamad ya sunnar da kanshi kasa abin saida yasa Mustapa yayi dan dariya sannan yawuce zai fita, harya taba handle gently Hamad yace  Yaya juyowa Mustapha yayi yakalleshi batare daya amsaba, sauke kanshi kasa yayi ahankali yace  thank you Yaya murmushi Mustapa yayi yajuya yabude kofan yafice, daukan laptop din yayi yasa ajikinshi yashiga site dinshi yana duba message da mutane sukamai he s into creating website, building application, prototype, software development and maintenance and so much more anything tech he just knows it, banda haka yana program daban daban a online yana karban certificate, kwanan nan nema baya iya aiki sosai sabida operation din nan, aiki kadan yayi ya ijiye laptop din akan gadon Hameed yana lumshe idanu bacci na neman kwashesa.
Shigowa dakin Hameed yayi ganin yana bacci yasa yafada bayi yayi wanka yashiga shiryawa cus one of his colleague na aure yau zasuje daurin auren tsaf ya shirya cikin wani lafiyayyen shadda ya kafa hula aka tareda fesa turare saikuma yajuyo ya kalli Hamad kafin yasa hannu yadauki turarukanshi wajen kayanshi dake nan a gyare, yarasa yaya Hamad ke selecting oil perfumes dinshi cus turarenshi smells out of this world shafawa yayi ya maida ya ijiyesu hargitse sannan yarufe wardrobe din nasu yasaka takalminshi Hermes yadauki key motarshi ya wayanshi yawuce yafito Mami ne kadai a falo tana magana da Lami dazata kasuwa tana ganinshi tace  sai ina yan samari kai ya sosa yace  colleague dina a bank ke aure yau Mamie shine zamuje mai daurin aure Mamie tace  mesa bakaje da dan Uwanka ba ? Kallon Mami yayi yace  Mamie are you seriously asking this question kema kinsan ko sama da kasa zata hade bazaije ba besides ma he s sleeping I think magungunan shi na sashi bacci Mamie tace  to adawo lafiya drive safe wucewa yayi yafice yashiga motarshi Camry ta 2010 yabar gidan.
Around zuhur ya farka yatashi zaune ahankali yana kallon dakin he hates dirt, Hameed ya bata ko ina, sauka yayi ya shiga gyara dakin ya gyara gadajen su ya kwashe kayan Hameed daya cire yasaka a laundry basket yadauki broom ya share dakin ya kwashe a Parker yazuba a leda yabari awajen yashiga bayi yadauro alwala yafito yadauki leda yawuce yasauka kasa bakowa falo yatafi mosque yay1 salla yadawo afalo yaga Mamie tana zaune tace  zokaci abinci ahankali yace  anjima .

Around 4 yadawo daga masallaci wayanshi yafara ringing, screen din yakalla ganin Ya Mustapa ne yasa yadauka Ya Mustapha yace  start coming ina hospital gyadamai kai yayi tareda katse wayan yafada bayi wanka yasakeyi batare daya bari ruwa yashiga ciwon ba sannin babu kowa yasa yafito yazo wajen kofansu yasa key sannan ya tsaya gaban wardobe nasu yana budewa yaga aikin Hameed kawai yazaro wani dark blue jean da t-shirt fari ya shirya tsaf kayan sunmai bala in kyau turare ya fesa yadauki p-cap dark blue yasa akanshi, he loves wearing p-cap sabida iska sannan yadauki wani black shade, he always put on shade idan zai fita cus idanunshi somehow makes people to be looking at him both men and women kuma he hates that, wayanshi yadauka yasa a aljihu yadauki wani key dake saman side drawer shi yasa wani easy pam yafito yana tafiya ahankali looking expensive and classy kaman wasu designers yasaka, Mamie na zaune tana sauraron wani wa azi a Sunna tv taji kamshinsa hakan yasa tadago sai kawai ta tsareshi da ido Masha Allah! Hamad is simply handsome kawai karasowa falon yayi tace  zaka fita? Gyadamata kai yayi tace  ina zaka?  wajen Doctor a asibiti gyadamai kai tayi tace  jekadauki key mota na kaje dashi girgiza mata kai yayi yace  da machine dina zani shiru Mamie tayi tace  Tom saika dawo ayi gudu ahankali gyadamata kai yayi yafice wajen lipan dake tsakar gidan fari yaje yadaga katsa yadauki tsuma ya goggoge yadade bai fita ba he hardly go out baida wajen zuwa idan yafita kawai da dalili, tass ya goge machine din dayayi kura sannan ya warware glass din yasaka ya kara gyara p-cap dinshi yahaukan machine din yayi wani irin kyau ya kunna machine din mai gadinsu yabudemai gate yafice.
Kusan 30min yabata cus saida ya tsaya yashamai sannan yakai hospital din yayi parking yaki shiga yaciro wayanshi yakira yayanshi, Mustapa na zaune yaga kiranshi kawai ya girgiza kai yatashi batare daya daga ba yadauki key yafito yaganshi yace  let s go to my car ya wurgamai key yace  drive nagaji karba yayi suka wuce shiya jasu har zuwa computer village wani shago na slot Mustapa yace  you know wat u want pick up shiru yadanyi Ya Mustapa yace  muje wucewa sukayi direct wajen wani desktop yafara zuwa na dell yana duba spec din, HP EliteOne 800, 200 G45420 All-inOne G3Touchscreen... AiO - 6th Gen....CORE 13 11. This is the perfect desktop dayake bukata for his kind of work but ganin kudin #1,600,500.00 kawai saiya wuce da sauri yana duba wasu saiya juyo yakalli yayanshi yanunamai na wani 700k yace  this Mustapa yakalla sai kawai yawuce yakalli mai shagon yanunamai na farkon yace  wannan mukeso dasauri Hamad yazo kusada shi murya chan kasa yace  Yaya the money is too much anatse Ya Mustapa yace  but this is the spec your kind of job needs, don t think about the money think about abubuwan dazakayi dasu kasan how worried I was da desktop dinka ya lalace, you are stuck a software da kake developing sabida rashin desktop, I know Abba baida karfi sosai zamu karamai burden ne bayan responsibility na kanshi da yan uwansa, look at kudin daya kashe na kayan salla dudda baida shi kaman da but bazai taba dena abun nan ba cus it s something daya saba yi batun yauba, even if it s all my salary I will use it to get this for you, kai kadaine cikinmu da har yanzu baka kama wani takamaiman aiki ba and ka kama hanya desktop ya lalace just let me do my duty daidai yaciro katinshi Hamad ya kalli katin na UBA dinshi ne which is salary account nashi maybe ma all his savings ne zaiyi using cus duka duka salary Doctor nawane, he has family ga dawainiyan su Abba, gashi ba a dade damai operation ba duk sun kashe kudi duk sai jikinshi yayi wani iri, zare kudin akayi aka bashi ATM dinshi back mai shagon ya dauko kwalin brand new desktop din yaba sales boy nashi yace  take it to their car suka bishi suka fita ana kokari sawa a both kaman ance Musty yajuyo yaga wata yar matashiya tana kokarin bude motanta tashiga amman sai kallon Hamad da hankali shi ke kan abinda ake sawa a booth yake, dan murmushi yayi da gangan yadan taba Hamad yace  Hamadi ana magana dakai look over there juyowa Hamad yayi yakalli yayanshi ya kalli inda yake nunamai cus yadauka wani abune ganin wata ke kallonshi dawani irin sauri yadauke kai yarufe booth yawuce yakoma driver seat ya zauna yajawo kofa yarufe itakuma yarinyar ta taho harda dan gudunta sai kawai tai knocking gaban motan Hamad yadago kai yakalleta dan glass din motar tinted ne bata iya ganoshi yaki bude kofan yajuya yana jiran Ya Mustapa yashigo subar wajen, ganin Hamad yaki bude kofan yasa Ya Mustapa yazagayo yabude kofan dasauri Hamad ya kalleshi, Ya Mustapa yace  ana magana dakai sauke glass kaman zai mutu dan haushi ya sauke glass din, da sauri yarinyar cikin turenci tace  you are Mr Hamad ko? The Tech genius Hamad ya dauke kanshi yaki magana yaki kallonta, yarinyar tai murmushi takalli Ya Mustapa tace  it s him I know him, he developed wani EHR software for

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login