Showing 18001 words to 21000 words out of 24325 words

Chapter 7 - Afnan Book 1 Complete Hausa Novel

09 Oct 2025

217

sutura da wanka sannan aka fito da gawarsu, lokacin da aka fito da gawawwakin su KU zo kuga tashin hankali agurin mutane ,ga kamal ya takarkare sai hauka yake Yana faman kuka kamar Wanda besan komai ba akai, mutane kuwa an d'芒ge sa茂 faman rarrashin sa ake ,ahaka dai akayi musu sallah Aka daukesu zuwa inda kowane bawa sai yaje, wato makabarta, innalillahi wa'inna ilaihirraju un wayyo allanmu yanzu shikkenan katafi kabarmu, munyi rashin aboki n'a gari, kamar yafada tare da juyowa ta biyo BAYAN mutanen dasuka kawo su AREEF suka bunne, abin da zai Baku mamaki tun alokacin da aka Haka kabarin AREEF wani danshine na ruwa wan da yake kwance acikin Ramin ,ga wani haske dake fitowa abin dai ba a magana Kai kana kallon wannan lamarin kasan duk mutumin da ke cikin wannan kabarin ta dace, ma,ana dai alkairin AREEF da kaunarsa da mutane da keutata musu da yake basa yatafi abanza ba, shiyasa MALAMAI suke cewa" idan katashi rayuwa kazabi rayuwa daidai da yadda kaga ubangijinmu ya koyar akai, kada kace Dan kana da tarin dukiyar ki wata nasaba kace zakana kyarar mutane kokuma ka nuna Kai kafi karfina kakula mutum,to abin da Baku sani ba kekkewar shaida itace wadda idan kamutu mutane zasu shaideka Akan halinka me kyau Allah yasa mu dace.

*FILIN GIRGI DAKE SAUDEE AREBIYAA*

. Wasu da karai da masu fa da aji da mulki da kasaita da barori da matan sarki da sarakai dadama na hango a jere a airport suna zaune suna jiran isowar me gayya me ayki uban tawaga gagara gasa Dan sarki jikan sarki Zaki me taurwatsa dukkannin wa ta gayya mutumin da kowa acikin garin yake ji dashi da Kuma alfahari da ikonsa.

Cikin takun kasaita take sakkowa daga mattakalar jirgin Yana tafiya cikin Isa da alfarma irin na yayan sarakuna, sanye yake da farar alkebba wadda Tasha aykin fari da Baki,Haka zalika takalmin dake sanye a kafarsa farine da baki me dauke da zanen ado irinna tambarin sarauta, hular dake jikin alkebbar Bata iya rufe kan sa sabi da yawan gashin dake kwance a kansa baya iya kamasa sa茂 da yadda ya zubo a kafadunsa kamar wata mace, idanunsa kuwa sanye suke da bakin glass me Kelli da ado bake inya gano cikin idon sa sa茂 dai in shi dayake kallonka, fuskannan tasa ADAURE take ran Babu alamun annuri a cikinta ballema kasaka ran zaimaka dariya ko murmushi,Amma duk da wannan hadaran da yayi be Hana asalin kywunsa bayyanaba ,kywunda ya tsokane dubbunnan "yayan sarakunan garin kowacce acikinsu so take tamalleki wannan gwarzon.

Tun kafin ya karaso gurin dakarai da sauran kana nun sarakai suka karaso suna Masa sannu dazuwa tare da take Masa baya har zuwa inda sauran iyayensa da kannensa suke, AYAAN kuwa dake gefansa kallon kowa yake Kar domin ya fahimci sauran matan dake gurin Basu so dasowar yarima awanan lokacin ba sun so ace yayi Zan sa da dai tashin hankalin dayake hada yaya su fada akansa,duk da shi baisan sunayi ba yadaisan mutum daya wadda take haukanta itama tadalilin takuramasa da akai sai ya aureta ,Kuma yasan har abada bazata taba samun kan yayan Saba , murmushi kawai yayi acikin zuciyarsa yace" uhm nidai Naga wace sarauniyar ce wadda zata samu nasarar sace zuciyar yaya AREEYAAN.

Tun da yakarasa gurin AREEYAAN ya durkusa harkasa gaban dattijawar dake gabansa Yana gayshesu daya BAYAN daya ,sukuma sai faman murmushi suke suna faman samasa albarka, BAYAN antarbi yarimane kowa ya watse tare da Shiga mota ragowar hadiman suka taho a doki.

Acan gidan *SARAUTAR MANAMI* kuwa sarauniya ZAKIYYA taci ado da kunshi irin nasu n'a sarakai da wata arniyar alkebba wadda kafara Sara ranar domin AREEYAAN kawai ya kalla ya yaba, murmushi take itakadai kekkewar budurwar wadda bazata huce shekara 26 ba takure wanka sabo da AREEYAAN ,zaune take a kusa da wata budurwar da alama dai kanwar AREEYAAN ce Kai da Kana kallonta kaga jinninsa sabida tsananin kamar da sukeyi, murmushi take sakarwa sarauniya ZAKIYYA tana cewa" uhm su anty ZAKIYYA duk wanan wankan na tarbar yayane?" Hmm bazaku gane ba yarinya tun da aka cemin yau yarima zai dawo kasarnan nake shiryashiryan dawowarsa ,me bakiyi mamakin zuwana masarautar Nan tun safe ba?" Eh kuwa na Yi mamaki gaskiya lalai anty ZAKIYYA kina son yayana Kuma insha Allah kece Zaki zama mata agurin Yaya AREEYAAN" ameen summa ameen *HAYAAM* kinsan yayan naki bashi da tabbas haryanzu Ni nake kidana Kuma ninake rawana nakasa gane kansa kwatakwata narasa kalar macen da yakeso waishi Anya mutumne kuwa?" Uhm kema kenan balleni danake kanwarsa wallahi har so nake Yaya AREEYAAN yayi magana ko nazauna Ina kallonsa sainaga kamar aduniyar nan Anya za a samu mutum me kyau da kwarjini irin yaya AREEYAAN kuwa" suna tsaka da wanan zancenne sukaji Busa tana tashi Nan take HAYAAM Tace" anty ZAKIYYA gafa Yaya yakaraso " murmushi zakiya tayi Tace" Nabaki kyautar dinare da zoben gold guda biyu" woww anty duk Ni kadai " wanna kadanne HAYAAM daga cikin abin da na shirya Miki domin nafahimci kina Sona da yayyanki 馃挴.

Tom a asbiti kuwa Kamal ne zaune a dakin da AFNAN take ya kura mata ido Yana kallon ta cike da mamakin yadda duk ta rame lokaci daya ,dai dai lokacin tashin ta daga bacci kenan bude ido tasoma yi a hankula har tagama budeshi tar a kan Kamal, Babu laifi tadanji dadi ajikinta domin duk yawan furgitar da takeyi yanzu ta rage domin yanzu tana iya tuno abubuwa dayawa har ta iya zubar da hawaye Amma Babu bakin magana sai dai kawai kallo da hawaye, Kamal ne ta kalleta yace"AFNAN" kallonsa kawai tayi ta gefan ido daya batare da Tace Masa komai ba, ganin hakan yasa Kamal yacega ba dacewa" kiyi hakuri kinji kada kice bazaki iya daukar wanan kaddarar ba Allah dayabaki Yaya AREEF ya Baki su momy shine ya karbi abinsa,Dan Allah ki daina kukannan domin har cikin zuciyata nake Jinsa banason ganin hawayenki nazu ba kada kisakawa kanki ciwan kai, Ni kaina naji mutuwar Nan amma Babu yadda na iya dolene nayi hakuri da abin da rayuwa ta zo Mana dashi," Yana magana yana share kwallar karya da majina.

_ 馃拫 *AFNAN* 馃拫______

*Chptar 14*

馃拑馃拑*TO!! TO!! TO!! Shhhh*馃槍 *KUNA INA MASOYA LITTAFIN*馃拫*AFNAN*馃拫WANAN LITTAFIN DABAN YAKE DA SAURAN AFNAN FA AKA FADA MUKU KUNSAN YADDA KUKAJI WANNAN LITTAFIN ZA A KWASHI ROMON DADI ACIKINSA AFNAN LITTAFINE MECIKE DA TARIN ABIN BAN AL,AJANI FADAKARWA NISHADAN TARWA DUK ACIKIN WANNAN LITTAFIN ME SUNA 馃拫 *AFNAN* 馃拫.

*NICE TAKU HAR KULLUM MARUBUCIYAR *鉁嶏笍

馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

_*AFNAN*_

_*BY*_

_*HAFSAT UMAR 茒AN GORO*_

馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

_*JARUMAI馃挭馃徎WRITER'S ASSOCIATION馃摎*_

_*Marubuciyar*_

1- Burina Mu'azzam

2- Ba Mahaifiyata bace

3- Babana ne sila

4- Ummu Amani

5- Amatullah

6- Zuciyarta

7- Mace Rayuwa

8- Rayuwar 茦as茩anci

9- Mar'atussaliha

10-Babbar sakayya

_And now_

馃拫_*AFNAN*_馃拫

*BOOK one*

*Chapter 14*

_______ kallon da tayi ceke da damuwa da bacin Rai ,duk da idan taganshi a zaune akusa da ita sai taga kamar Yaya AREEF zai shigo daga baya, idon da ta kura masa ne yasa Kamal yace" AFNAN " naam Yaya Kamal" meyake damunki ne Naga duk yanayinki ya canza ,banace kiyi hakuri da kaddarar da ta fada akanku ba"? Hmm bazaka ganeba ni yanzu babban BURINA asallameni daga asbitin nan sonake n'a koma gida nazauna, idan Ina kwance anan Babu abin da nake tunani da tsammani illa zuwan Yaya AREEF" meyasa mutuwa zatamin Haka me na aykata ne naketa fuskantar wadannan abubuwan " yi hakuri share hawayenki AFNAN bazaki koma gida ba idan kika koma can Zaki na tunawa dasu domin gidan zai xamar Miki tamkar kango ko makabarta bazai yuwu ke kadai ki zauna a wannan gidan ba" to idan ban zauna a gidan muba Ina zanje gashi shima doctor yaki yanememu wallahi na Kara tsanarsa duk ta dalilin sa narasa komai nawa, narasa gata naraha ahali narasa mebani abin da nakeso ,Babu momy Babu Abba sannan Babu Yaya AREEF to idan ban tsani doctor ba wa Zan tsana ,yayana yadade Yana fadamin cewa Babu kyau kace ka tsani mutum sai dai kace ka tsani halayyarsa, Toni abin da yamin babban zunubine da b茅 cancanci n'a yafe Masa ba,kawai sabi da a shirya gida Dan tarbarsa narasa kowa Allah ya Isa tsakanina da shi mugu azzalumi, Daman sai da nafa dawa Yaya wannan mutumin ba zai taba taimaka Mana ba ya kyaleshi Amma yaki gashinan abin da yajamin" takarasa maganar muryar ta na sarkewa Sabi da kuka, murmushin gefan fuska Kamal yayi acikin zuciyarsa Kuma yace" tab gwari kenan gaskiya naji dadi da mukayi hanzarin hallaka su AREEF kace da munyi jinkiri sai dai muji anyiwa yarinyar Nan ayki, da shikkenan mafarkin da nadade Ina Yi domin samun kudi da ita ya kusa lakacewa sai Kuma Allah ya dubeni Sabi da ba Sara zanyi ba" afili kuma yace" AFNAN to mezai Hana asaka gidanku a kasuwa musayar idan yaso sai mu koma wata anguwar musai wani hakanne kawai zai sa ki rage tunanin su a ranki, ma,aykatun A.R kuma naci gaba da kula da guraren ina ajiye Miki kudaden ko Yakika gani" Kai ta wadannan kake wallahi da ace za a bani za bi akan ba zabi kudi ko Yaya AREEF ,wallahi Yaya Zan za ba Sabi da nasan ko da ajeji muke zaune bazan ji komai ba Sabi da nasan zai kula dani fiye da rayuwarsa "AFNAN baza dai ki daina maganar AREEF d'in ba ko !? Ni yanzu ga maganar Dana ke muki kin amince" uhm eh Yaya Kamal na amince muddum hakan shine mafita a rayuwa ta nayar da asayar da gidan domin yazamar min kamar Dani", tom shikkenan yanzu dai Bari na Kira doctor ya salla meki ko tun da Naga jikin da sauki ko"? Eh dasauki Amma yanzu idan aka sallameni Ina Zaka kaini" uhm zamuje gidan mu Mana sai na kaiki gurin mahaifiyata kafin ki Kara samun sauki sai a saya Miki gida" Allah sarki yarinyar Babu wayo Tace " tom shikkenan Allah sarki momyna Allah ya jikanku da rahama yasa aljanna itace nakoma.

Fita daga dakin Kamal yayi jikinsa har Bari yake wajen futa daga dakin yashiga office d'in doctor, sallama yayi Masa tare da neman izinin shiga , daga ciki doctor yayi magana" yes shigo Mana Kamal" shiga Kamal yayi ya nemi kujera ya zauna ,gysawa sukayi tukunna kafin yace," doctor Daman nazone Akan sallamar da za ayiwa AFNAN yau" sallama Kuma to Amma itace Tace ko Kaine?" Ni na Isa bani bane itace da kanta tanemi sallama" mamakine yakama doctor Dan Haka yace" hm Amma idan mun sallameta inane zataje,?" Doctor yafada tare da tsare Kamal da Ido, " am uhm Daman gurin mahaifiya ta Zan kaita nasan ita zatafi iya rikonta yadda yakamata" okay Babu damuwa kaje zuwa Nan da minti kalilan Zan sa a sallameku insha .

Tom ba a fi minti 5 ba doctor ya rubuta ma AFNAN ta kardar sallama tare da yimata addu,ar Allah ta Kara lafiya, ko kulashi batayiba ta Kama hanya tayi Gaba Kamal Yana binta a baya har suka karasa inda taga motar Kamal take, bude motar Kamal yayi yashiga sanan itama tashiga Babu ko uhm suka fara tafiya, abin da ya fara bawa AFNAN tsoro shine yadda yake tafiya ya bar cikin mutane zuwa wani jeji Wanda batasan inane gurinba, Ada batai niyyar yimasa magana ba Amma yanzu sai yace "Yaya Kamal Ina Kuma zamuje BAYAN kace gurin mamanku zaka kaini?" Murmushi Kamal yayi yace " ay Daman mamana anan take rayuwa ita aduniya batasan mutane da yawan takura shiyasa take rayuwarta ita kadai, Kuma ma kinsan me ita kadaice a gidan take aykinta Kinga tasamu wadda zata dinga tayata" shiru AFNAN tayi batare da tasake cewa komai ba,Bata son musu dashi shiyasa ma tayi masa shiru har suka karasa wani gida Wanda shi kadaine kwallin kwal acikin jejin , da alamun yadda taga gidan kamar Babu mutane aciki ko ba ataba yin rayuwa acikiba sai bace komai ba kamar yadda ya Shiga ta bishi ABAYA" itadai Tun da tafara kallon ciki suka Shiga Bata ga alamar KO ruwa anzubar ba balle girki ballantana kuma ace mutum Yana rayuwa aciki" kallon sa AFNAN t'ai Tace" Yaya kamal Ina umman?" Kije tana wancen dakin " Babu musu AFNAN tanufi inda Kamal ya nunamata ,dauke da sallama abakinta ta Shiga tare da cewa.... Abin da taganine yasa maganar kasa fitowa daga bakinta ta makale,wani mugun yawu ta hadiye ji kake kukukut tare da zaro Ido tan girgiza Kai tana ja dabaya, Fadeela dake kwance a kan makeken gadon saurin dagawa AFNAN gira tayi tare da kashe mata ido daya Tace" kinyi mamakin ganina ko" hmmm banyi mamaki ba anty fadeela ina umman su Kamal?" Au waike tsammaninki anan Zaki samu umma to ay nice umman ,AFNAN kenan ke yarinyace bakisan komai ba atinaninki Zan bari ayi Miki aykine BAYAN nasan Ina karuwa da abar !! Kuma wanan abar itakai ce nake iya gamsuwa da ita sanan kice Zan rabu dake" Baku da hankali daga ke har wancan shashashan yayan naki" a,a anty fadeela kidai na zaginsa Dan Allah yayana yamutu kina zagarmin shi?" Anzageshi da ban duramasa asharba ma wallahi duk abin da yayimin saina ramashi akanki" nashiga uku anty fadeela me Yaya AREEF yayi Miki"? Au Baki sani ba hargidan mu yaje gaban iyayena da kannena ya ci zarafina ya kunya Tani adalilinke dinan wallahi kadan yagani naso ace namansa fatafata yayi BAYAN ya mutu Ashe mutuwar tayi Masa da kyau" zaro Ido AFNAN tayi tare da share hawaye Tace" kenan kece kikayi sanadiyyar mutuwar iyayaena" confirm!! " Kuka AFNAN ta fashe dashi tare da cewa" Wallahi natsaneki sayyanzu nagane cewar abin da Yaya AREEF fake fadamin gaskiya ne kuma wallahi sa茂 n'a tona asirinki sai na gayawa Yaya Kamal kece kika kashe Masa abokinsa Kuma yanzu zanje na tona Miki asiri" tafashe dakuka me ban tausayi, jitai an tsaya a bayanta ana cewa" wane Kamal din to ay nine jigon mutuwar tasa " arazane AFNAN ta juyo ga mamaki sai taga kuwa dagaske kamal dinne" nunasa Tai da yatsa tana jijjiga Kai tana kokarin magana Amma takasa sai dai hawaye masu zafi dake fita daga idon yarinyar, hannun da take nunasa dashi ya Kama ya murdeshi tare da tsinka mata mari hagu da dama yace" ni sa ankine Zaki nunani da yatsa " sa,a kikace da haryanzu kike Raye har kike iya nunani da yatsa "Yaya Kamal Ni kamara Wai shin dagaske ne ko mafarki nake Dan Allah kuce mafarki nake, idanko har dagaske ne wannan zancen dan Allah kukasheni nima dan Allah" dariya Kamal ya kwashe da ita yace " kiji shashasha idan da badan akwai aykin da zamuyi dake musamu kudadeba ay tuni kema kinbisu , Kuma Kari kadan kika gani tun daga ranar da AREEF ya daga hannu ya mareni Akan ki daga lokacin nafara irga ranar Nan Kuma gashi tazo, akullum zanmiki sauki kina da maruka guda hudu".

Kallon fadeela Kamal yayi yace" Bea kina da wanin abin da zakiyi da ita ayanzu?" Uhm a,a abarta sai zuwa anjima yanzu akai ta makwancin ta " okay angama ranki yadade "ya tunkuda keyar AFNAN Gaba har zuwa wani daki da bashi da maraba da gidan Dan kande ma,ana gidan yari" Babu ko da gado sai wata yaloliluwar tabarma, shikkenan abin da ke cikin dakin, tunkuda ta yayi ciki tare da janyo kofar ya saka mukulli sanan yace" duk abin da Zaki bukata ko ruwa ko wanka akwai bathroom aciki abin ci Kuma bakullum zakina ciba sabi da mu ba bayinki bane shima Sabi da Kar kirasa ruwa ajikinki da karfi shiyasa zamuna Baki" daga Haka ya bar gurin yakoma dakin da fadeela take.

Akwance yasameta inda yafita ya barta ,zama yayi tare dacewa" wash, Amma fa wanan yarinyar Bata da wayo Daman Haka abin zai zomana da sauki bansani ba tab yanzu abin da ya kamata shine yadda zamu iya samun dukiyar AREEF Kuma kinsan Dole sai munsan inda takaddun gida je da filayensa sukeko, sanan Dole ne nazama nine shugaba a ma aykatunsa ,Kuma idan munason samun wadanan abubuwan Dole sai AFNAN tasaka hannu Kuma tasanar damu inda suke, domin tasan komai game da AREEF"tabbas hakane Amma Taya kenan zamu samu?" Idan taki fa," uhm saikace baki sanni ba ay Yana cewa zata mana taurin Kai zanci ubanta wallahi sa茂 namata Dukan da zata kasa tashi" hhhh a,a banda Wanda zata kasa tashi idan kamata irin wanan Dukan ay ka cuceni domin Babu yadda za,ai AFNAN ta iya biyan bukata " okay tom shikkenan Ni yanzu Zan tafi domin inje na karbi mukullin gidan " agurin wa idan aka hanakafa?" Uhm Zan kirawoki video call ki sata Dole saita yi magana " okay tom shikkenan adawo lafiya kafin kadawo na BIYA bukatata Tun kan kafara kawo mana costumes" ah wato ke me wayo gwara kifara tun yanzu tom Babu laifi ga kee din idan kin Gama saiki rufota" okay sai kadawo Allah ya tsaremin kai" ameen my bea.daga Haka ya fita daga dakin ta nufi hanyar fita.

AFNAN nazauna a dakin ta saka kanta a tsakankanin cinyoyinta tana zubar da hawaye tana tuno irin fatan da tasamu alokacin da AREEF yake Raye ,komai sai dai ayi mata hatta gado sai angyramata take kwanciya Haka bacci idan zatayi sai a kirjin Yaya AREEF sai gashi yanzu gurin da zata kwanta ko me aykin gidansu baza a Bata wanan dakin ta kwanta ba " tasake fashewa da kuka, Fadela ce ta shigo cikin takun Kasa茂 ta tana tafe ko Ina na jikinta rawa yake cikin takun kasaita, ta karaso kusa da AFNAN ,durkusawa tayi ta dafa kafadar ta Tace" my love Bea yakike?" Banza AFNAN tayi mata tare da cigaba da kukan da take" hmm

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login