Showing 3001 words to 6000 words out of 37713 words
dagata na wanke mata, kaimadai kasan Princess bataji taki yarda tahau pooo, nikuma gaskiya banson saka musu pampers, yaran suncikacin pampers saikace abinci gashi huggies kake siyamusu mai shegen tsada, kudinshi yakai kudin Rabin buhun shinkafa, saisa nake maneji wanan zamanin ba kudi
"
ayanda ranshi ke suya idan shi miji mai dukane zai iya kassara Asiya kasa hakura yayi yace
"
for God sake ke wace irin mace ce Asiya? Keke siyan pampers din? Kudinki ko nawa? Badan asaka musu nasaya ba? Look at my kids babu wanda yay wanka cikinsu, jibi Hydar? Look at you Asiya, look at yanda kika maidamin da gida, jibi yanda falona ke doyi? Ke wace irin jakan mace ce
"
? Sosai zagin yamata ciwo ahankali tace
"
nice jaka baban Hydar
"
? Cikin bacinrai yace
"
kinmafi jaka barikiji, macen da batada tsafta, kazamiya ce ta karshe ai jakace, inajin ciwon kai nabaro office dannazo gida na kwanta ina tuki tunanin gidan na, deep down nasan bazan taba zuwa na ganshi agayre ba, you are a disgrace to womenhood, to all married women ma, where is Mimi
"
? Yamata tambayan ranshi abace, cikin kunan rai tai fari da ido tana turo baki tace
"
oho ni ina kallo bansan inda
tayi ba
"
wani irin kallo yamata sanan yakada kai kawai yama kasa cewa komi ya tsugunna yadauki princess data washe baki ganin mahaifinta yay bedroom dinshi da ita, saida ya wanke mata kashin sanan yafito rikeda ita yana neman Mimi, dakin Asiya ya shiga, dakin gaja gaja ga zarnin fitsarin yara, ganin Mimi yayi gaban madubi tadauko janbakin mamanta tabude tana gutsura tana dariya tana shafawa tana ganin Babanta tayar tana murna cikin muryanta na yara tace
"
Dady
"
murmushi yayi yadauta yace
"
Hello Mimi
"
fita dasu yayi daga dakin ya shiga dakin yaran shima kaman bola bude drawer su yayi ya kwasan musu kaya masu kyau da takalman sanan yafito yawuce dakinshi, ruwa yahada na zafi yamusu wanka ya nadosu a towel ya ijiyesu kan gadonshi shida kanshi ke mugun ciwo amman saiyaji ciwon kan ya washe, falo yayi yaga har lokacin tana zaune inda ya barta tacigaba da kallonta nema ganinshi yasa tadan firgita, Hydar yadauka dake bacci yay dakinshi dashi bayi yakai yaron yamai brush da wanka sanan yafito ya shiryasu yaran sukai kyau dan dukansu kyawawa ne masha Allah suna kama da mahaifinsu, Hydarne babba, sai Princess da Mimi yan biyu, bayan ya shiryasu ya kunna musu game a pad dinsu yabarusu kan gadonshi shima ya shiga wanka yafito ya shirya cikin native yay kyau sanan yadau key ya sauke Hydar daga kan gadon yana daukan Mimi yace
"
who wants to go out with Dady?
"
atare dukansu sukace
"
mii Dady
"
murmushi yayi yadauki Princess ya kama musu hannu suka rirrikeshi sai kamshi suke suka fita, ko kallon mahaifiyarsu baiyiba yabude kofar falo yafita bayan mota yabude yasasu ciki sanan ya shiga gaba ya kunna motar sukabar gidan.
Kasancewa yasan best friend dinshi Abdul na gida Navy neshi yana leave yasa kawai yay gidan, yana horn mai gadi yafito ganin Dr Bashir ne yasa da gudu yabude gate yana mika gaisuwa.
"
Barka da zuwa Likita bokan turai, ah
'
aha yau manyan baki garemu harda su yan biyu da ubangidana Hydar
"
bude mota Bash yayi yafito yabude ma yaran da dagudu sukai cikin gidan Bash yabisu da kallo, mai gadi yace
"
ai shikenan yanzu zasu hade dasu Amima ahau hayaniya kana ganin tara haka sunsan gidan kawayen su
"
kudi Bash yaciro ya mikamai daidai lokacin wani namiji wanda bazai wuce tsaran Bash dinba yafito yadauki princess yana sanye da native yana murmushi yamikama Bash din hannu suka kashe.
"
aidani yau nazo inda baka rigani ba kaga yanda su Amima ke damuna nakaisu wajen twins kuwa suyi wasa
"
dariya Bash yayi yace
"
gashinan nakawo su ai
"
sukai ciki, falo suka shiga yabi falon da kallo ko
'
ina tsaf tsaf gawani kamshin turaren wuta dake tashi da dadad zuciya, da gudu Amima datake mate din Hydar tazo yarinyar looking so neat and fine tagaida Bash.
"
Dady good morning and welcome, princess come let
'
s go
"
kallonshi Abdul yayi yace
"
kagani ko kiri kiri yara suzo gidana wajena amman yarana su hanani zama dasu kaman wajensu sukazo
"
dariya Bash yayi yace
"
ni wajen su Amima na kawosu not you
"
kama hannun princess tayi sukai dakinsu daidai lokacin matar Abdul dataci gayu sosai tana sanye dawata vilisco gown takafa uban dauri kaman bata haifi yara biyuba takaraso gabansu dauke da tray tana murmushi tace
"
Barka da zuwa Dr, wato ni za
'
ama sonkai ko, zakazo da yara ina Maman su
"
wata yar murmushin dole ya kakalo yace
"
tana wasu yan abubuwa ne amman tace ba gaidaki
"
murmushi tayi tace
"
shikenan, akwai fried rice, moi-moi da gizzard souce, jellof rice, akwai coselow, akwai salad wanne za
'
a kawo
"
dan murmushi yayi yashafa cikinshi yace
"
nagode madam but am full yanzu, anjima naci
"
gyadamai kai tayi sanan takalli mijin nata in a very loving way tace
"
Baby kai me zan kawoma? Do you need anything
"
wani dirty look yamata ko kunyan abokinshi baijiba yace
"
yes
"
sanan yanuna mata kumatun shi yace
"
a peck
"
sosai take jin kunyan Bash hakan yasa tai kaman batajiba tajuya zata tafi shima bash yay kasada kanshi, ganin ta tafi yasa ya daga murya yace
"
na biki bashi, you know me very well, anjima zaki biya in excess
"
sanan yajuya ya kalli Bashir dayaga hankalinshi yay nisa yay tagumi, ahankali yakira sunanshi.
"
Bash, Bash
"
amman shiru yay nisa, hannunshi yakai yataba kafadarshi ya jijigashi sanan yasauke ajiyan zuciya. Da sauri Abdul yace
"
Hey Bash, are you okay? Meke damunka? Tunanin me kake haka?
"
shigewa yayi cikin kujera da kyau yana kallon saman dakin yama kasa magana dan baimasan ta inda zai faraba.
Ganin haka yasa Abdul yatashi, tray kayan kwalaman shi da matarshi ta kawo yadauka yace
"
tashi muje study dina, stand up
"
tashi yayi ahankali yabishi har zuwa study, shiga ciki sukayi Abdul yamaida kofan yarufe da key sanan yazauna gefenshi kan dogon kujeran yay facing dinshi tareda rungume hannu a kirji anatse yace
"
Bash
"
dagokai ahankali Bash yayi ya kallai da idanunshi da nanda nan suka kada sukai jaaa kaman hawaye zasu zubo daga ciki take Abdul yakaraya, hannunshi yadaura kan kafadarshi ya bubbuga yace
"
man up, man up dude, ya isa, is normal at a point in life kowa nada obstacle din dayake encountering, but whatever it is karka bari yakaika kasa kaji, I understand maganan namaka girma u don
'
t wanna tell me is.......
"
kafin ya karasa maganan Bash yatari numfashi shi yace
"
is not like I don
'
t wanna tell you Buddy banmasan ta ina zan faraba
"
da sauri Abdul yace
"
kafara kota ina, am listening and I will understand
"
shiru yadanyi kafin yasauke ijiyan zuciya yace
"
is about Asiya, Abdul banmasan tayaya zan maka bayanin Asiya ba, but tunda nake I
'
ve never seen kazaman mace irinta ba, kazama ce ajikinta, agidanta, ako
'
inama kazama ce, gata very lazy, ko ruwa kyaman sha nake agidana, my house is smelling, takori duka yan aikinta wai kallona suke bla bla bla bazata karayin yan aiki ba yanzu house dinmu is a mess
"
yaydan shiru sanan yace
"
dude I miss sex, I can
'
t remember the last time I had a great sex, ina ganin tun muna newly wed yanzu all this subsequent ones sabida kawai babu yanda zanyi ne
"
yasake yin shiru yace
"
yawanci ana cewa maza ke wahalar da mata ke cutan mata a aure but wlh is a lie not all are like that, I provide Asiya with everything da yakamata ace matar aure nasawa, ina saimata manya manyan atampopi su sharaton, codivoire, english, super whatever you know sometimes tarema muke zuwa nidakai muma matanmu shopping, you know what I buy, ina saima this woman lingerie, kayan bacci, english wears su bomb short, tight, jean, dukdan tasamin but wlh bazata samin ba, kayan zamanta agida sune daurin zanin kirji, idan zakaje gidana sau dari arana zakaga Asiya da daurin zani a kirji sau dari, kaga tai wanka to zata biki ko suna kokuma gidansu shine zataci gayu
"
yasake yin shiru, sanan ahankali yace
"
is not like ina tonama matana asiri wajen abokina, kasan bantaba maka complain din Asiya ba yau kusan 7yrs da auren mu but I
'
ve heard enough, Asiya bata kula da kanta, she
'
s so bushy down there like the last time I had sex with her I had to treat my P dan duk ta yanyankeni, ina saitamata perfumes, bodyspray, rollon duk bata amfani dasu sai zata fita she smells and stink, bansan mata biyu, I want to live my life with one woman, one woman means one peace, but you know I can
'
t keep living like this, bazan iya cigaba da rayuwa ba ban samun maccen danake saduwa da ita, for fuck sake am a Doc I know the implications of that, bankumasan nafara ne
man mata, but this woman is pushing me to, I need sex badly wlh, am starving, am starving Abdul, am star......ving.....
"
yay shiru sabida muryanshi tafara rawa bubbugamai kafada Abdul yayi yana fuzar da iska yasan abokinshi tun suna yara, yama jinjina mishi da har yanzu bai kara aureba ko fara neman mataba dan Bash namiji ne mabukaci, kuma yasan yanason Asiya sosai saisa yaki karamata kullum with the hope zata chanza.
EPISODE 4️⃣
Anatse Abdul yace
"
listen here Bash, have you tried talking to her, explaining everything to her? Kasan communication is everything a aure
"
Tabe baki yayi yace
"
talking, I
'
ve talked and talked and talked, nagayamata namata expaning komi ta kwanciyar hankali, namata ta tsiya, yan uwan ta sunmata amman ina ajininta yake, the worse part is bata tsorona, halin I don
'
t care take nunamin, irin ko oho dinan, could you believe yanzun nan dana shiga gida I met Princess na pupu akasa Asiya na kwance kan kujera tana kallo, cewa tayi tafara akasa ne saisa tabarta kawai ta karasa, kasan harnama yaran nan wanka nafito bata share kashin ba yana kasa ita tana kallo
"
girgiza kai Abdul yayi yace
"
I need you to calm down, matan mu can be our test from Allah, nasan kanason Asiya
"
cikin wata irin raunanniyan murya yace
"
alot Buddy, I love Asiya sosai, akwai karin maganan da akeyi da at this stage ina karyatashi cewan in kanason mutum no matter yanda yake u will love him regardless, but wlh is a lie, inason Asiya but ban jure warin jiki dana bakinta ko sha
'
awanta nakeji dazaran tazo kusadani sha
'
awa zai kwanta, I want her to change but taki, I
'
ve bought heaven on earth for her danta chanza taki, kawai ta kwanta kan wanan dogon kujeran taita kallo shikadai ta iya, I am feed up Abdul, nagaji da halinta
"
dafashi Abdul yayi yace
"
is okay, ina ganin abinda zamuyi gobe zansa wife taje gidan un announce intaga yanayin gidan saita mata fada, takoya mata wasu abubuwan
"
girgiza kai Bash yayi yana tabe baki yace
"
idan kaga Asiya ta chanza it must be a miracle dan abin ajininta yake am telling u
"
bugamai cinya Abdul yayi yace
"
Common kaidai bakasan inda za
'
a dace ba, just chill okay, I wouldn
'
t want you to be sex starving yourself za
'
amata fada, inma yakai wife tafita da ita takaita Spa ne a aske komi amata su sauna bath duk sai amata kasamu gobe kadanje ka juye ruwan kasaki mara koba hakaba
"
ajiyan zuciya yasauke yace
"
Allah sa taje
"
binshi da kallo Abdul yayi yamugun bashi tausayi amman baiso yanunamai dan zai karaya da yawa, but Asiya na wahalar da bawan Allah nan sosai, tashi yayi ganin yay shiru yace
"
how about muyi game, you know sai jiya na amshi ps6 danai order daga Ali express fa
"
washe baki yayi yace
"
really
"
hanyar kofa Abdul yayi yace
"
bari na dauko muyi connecting to this TV, while d children are there da mamansu having fun we the Dadies should have to, wat do you think
"
dan murmushi Bash yayi cute dimples dinshi suka losa yace
"
I concur
"
fita Abdul yayi shikuma yay shiru yana kallon book shelve dake Wall din study room din.
Wuni sukayi agidan, yaran bama sukara neman babansu ba sai wasa sukeyi, matar Abdul tabasu abinci sunyi sunyi nak, da daddare bayan magrib tamusu wanka tasamu su new pj bayan ta shafa musu hoda awuya, sai bayan sallan isha suka dawo gidan yanda yaga yaran nashi sunyi kyau an sakamusu pyjamas na bacci an shafamusu farin hoda awuya da fuska saiyaji inama haka maman su ke tsaftacemai yara, sallama sukayi bayan anhada musu kayan ciye ciye Abdul yabasu kudi sanan suka taho gida.
Falon suka shiga tagoge kanshin but still falon wasn
'
t in a goodshape, ga wari dake tashi na rug irin rug din da ruwa yazube akai dinan, ka kayayyakin sawan yaran dasuka cire, harda soaked pampers, girgiza kai kawai yayi yay dakinsu dasu dan princess tariga tai bacci, ganin dakin nasu ba
'
a gyaraba kaya kan gadonsu, hydar zaihau kan gadon yace
"
let
'
s go to my room ku kwana achan Hydar
"
hannun yaron yakama daidai zasu fita Asiya tabude kofa tashigo tana daure da zanin atampa akirji, ganin yaran yasa ta washe baki cikeda murmushi dakuma son yaranta tace
"
iyye yaran Mama an dawo, kunyi kyau waya samuku kayan baccin nan
"
? Hydar ne yace
"
is Mummy Amima
"
magana daya tayi Bash yadauke kai dan wari bakinta yake irin sosai dinan ta gefenta yabi yafita da yaran tabishi da kallo yay dakinshi dasu, tabe baki tayi cikin kunkuni tace
"
dukdai mezakayi yaranane nina haifosu baka isa ka rabani dasuba, mutum kawai sai jaraba inba kullum shigowa gidan nan kayi kaga ina aiki kaman jakaba bakajin dadi, yo ina dalili hakanan, nai aure danna huta kuma sainaita aiki, kowa dai yasan duk gidan da akwai yara ai baya gyaruwa wlh basaikaita fushin ba
"
tabe baki tabi tabude kofa tafita tabude kofar dakinta ta shiga.
Saida ya tabbatar da yasaka yaran bacci yay musu addu
'
a yafito bayan ya chanza kaya, falon yakoma ya nannade katon rug din dake wari yafito dashi gateman yakaimawa yabashi kudi yace a wanke gobe, sanan yadawo falon bayan ya dauko tsintsiya ya shiga shara dan baison kazanta, baison yanda falon ke wari randa wani nashi zaizo kunya zai kamashi.
Jin karan tsintsiya ana shara yafa ta diro daga gadon tafito falon tanajan kafa, kallo daya yamata yacigaba da aikin dayake, tsayawa tayi ta bayan kujera ahankali tace
"
Baban Hydar yanzu danso kake duniya ta tsinemin ace na maida mijina boyi-boyi sai kawani hau gyare gyare kana shara, nafa share dakin dazu, yanzu daka dawo bakaga babu kashin dazuba
"
ko kallonta baiyiba ya kwace duka tilin kayansu dake kan kujera da kasa yazuba a basket yay bakin kofa, ya bude kofa ya kwalama mai gadi, da gudu mai gadi yazo, basket din yabashi yace
"
ai Sadaka da kayan nan gobe Bala
"
da sauri ta taho daidai ya maida kofar ya rufe ta tsaya a gabanshi tace
"
akanme zakace mai gadi yay kyauta da kayana dana yarana eh Baban Hydar? Wai me aka makame kake wanijin bala
'
i, mesa kake min hakane
"
? Taushe hancinshi yayi da hannu yace
"
for crying out loud Asiya wai kokarin maida kanki jaka kike ne? Fisabilillahi bakijin warin da bakin ki keyi da hammatan ki, kina doyi bazaki aske wanan gashin hammatan ba bakisan shike saki wari ba? Look at your teeth kaman kubewan da aka daka ya kwana so irritating Godddd!
"
tabe baki tayi tace
"
tunda kana neman bala
'
i harda bunsuru na zaka iya kwatantani ba kubewa kadai ba, babu randa bazanyi wanka ba da safe ba warin danike hancinka ne, bakina kuma bai wari bana brush ne sabida matsalan danake dashi na gingivitis, gums dina ciwo sukeyi nai brush
amman dudda haka babu randa bancin kanunfari kuma kanunfari yana hana baki wari dan haka kome zakace kace ninasan kaina, kuma nidai ko Allah yasan bansanka sharaba sabida ai inayi inkaga dama ka ijiye tsintsiyan inkaga dama kaitayi kanka akeji
"
tana maganan tai gaba abinta, binta kawai yayi da kallo yama rasa mezai ce mata, harta rufo kofa bai cemata komiba kodan yaga tana sonshi ne yasa takemai haka karasa gyara falon kawai yayi yay mopping ya gyara kujeran ya goge, sanan yaje showglass din turaren wuta na falon ya jona burner yasa turaren wuta dakin yadau kamshi yay kitchen akofar ya tsaya yataushe hanci sabida hango tukwanen abinci dayayi ga abinci aciki am wulakanta tsutsa na yawo da flies ga hadadden kitchen amman kazanta ya batashi, ganin tsigan jikinshi yafara