Showing 45001 words to 48000 words out of 64985 words

Chapter 16 - Abban Sojojin Bokk 3 Hausa Novel Complete

zaune asaman Stool dake agaban mirror,
   "Mommy wannan abun kunyar har ina?taya zaki ce abra tadawo gidan nan da zama?bayan ga hayaam kuma!Nan fa gidan surukanku ne ba gidan ƙanin mahaifinku ba...." a fusace Aunty babba ta jefa ma hafsat wayar hannunta cikin sa'a tasamu gefen goshinta,dafe wurin hafsat tayi saboda zafin da taji,
  Rai a6ace tace"Hafsat ki fita daga idona in rufe!kina yimun shisshigi acikin lamurrana,Ina ruwanki da zaman su Abra acikin gidan nan?ke zaki ciyar dasu ne?ko saman kanki zasu zauna ne"?
  Shiru hafsat tayi batare da ta tanka mata ba,hayaam dae bata sanya masu baki ba,saboda gudun rashin kunyar hafsat don bata raga ma kowa acikinsu,

Wuraren ƙarfe tara,Azmee da Saude suka kammala girke girken breakfast na gidan,yanzu ta samu sauƙi wurin yin aiki don Saude ba ƙaramin taimaka mata takeyi ba,dayake itama kwararriyace wurin iya girki tana son yin girki,bayan sun kammala,Azmee ta shiga jera mata Warmers acikin tray tana kaiwa saman dining table,cikin lokaci ƙanƙani suka kammala jera abincin,

ɗaya bayan ɗaya matasan gidan suka shiga fitowa daga bedroom ɗinsu,su Kanal yousouf,Irfan jabeer khaleed twins,fawan,sune waɗanda suka fara hallara daga baya,Abbansu tare da Mommynsu junaid suka fito,kafin wani lokaci kowa ya fito,hadasu Dr haris su Captain adam,najeeb talal da kuma junaid,da sauransu duka dai,Mutun ɗaya ne bai fito ba,bakowa bane fa ce Surgeon general Rafayet,

Bayan matasan sun hallara Azmee taje ɗakinsu Sehrish ta taso su daga bacci,atare suka fito bayan sunyi brush su uku kowacce sanye da hijabi ajikinta,tun ta sallar asuba ce da suka sanya ajikinsu basu cireta ba,bacci yayi awon gaba dasu,
  Gaishe dasu Abba suka fara yi,fuskar kowannansu ɗauke da murmushi haka suka shiga amsa masu gaisuwar,daga bisani suka shiga gaisar da yayyensu,kowa da irin yadda yake amsa masu gaisuwar cike da zolaya,don wasu ma hada kwaikwayon Muryarsu,hakan ba ƙaramin nishaɗi ya sanyasu ba,

Komawa su kayi tare da samun wuri suka zauna a dining chairs ɗin da Abusufyan ke zaune,atare suka haɗa baki wurin cewa"Daddy ina kwana?ka tashi lafiya,"
ɗagowa yayi tare da kallon fuskokinsu ɗaya bayan ɗaya kafin yace"Lafiyalou Alhamdulillah!"

Natsuwa kowa yayi,yayin da Azmee da saude suka shiga zuzzuba masu abincin,kowa na faɗin abunda yake so yaci,
  Gyaran murya Abba yayi tare da kallon azmee yace"An kai ma Ammi nata breakfast ɗin"!?
  azmee tace"Eh nakai masu,a ɗakin gwaggo don acan tace mun zatayi kalacinta,ita da ƴar uwarta,"
  Murmushi ya ɗan yi don ba ƙaramin daɗi yaji ba,
  "Azeema fa"? Ya kuma tambayarta,
"Itama tana atare dasu,can ɗakin gwaggon,"
Jinjina kai abba yayi kafin ya kuma cewa"Aunty saratu fa?da ƴanmatan ta suma ankai masu nasu"?
  Saude ce ta kar6e da cewa"Ni nakai masu a ɗakinsu,"
  Abba yace"Aikin ku yayi kyau,"ya ƙarasa maganar tare da kai hannu ya ɗauki plate ɗin dake hannunsa yaci gaba da cin abincinsa da azmee ta zuba mashi,
  Abbas yace"Azmee banga su Amal ba?ko ankai masu nasu ne"?yayi maganar ayayin da yake ƙoƙarin ajiye spoon ɗin dake hannunshi,?
      "Na kai masu a bedroom ɗinsu," ta bashi amsa,
  Ganin Abbas ya tambayi iyalinsa ne yasa Ishaq yin gyaran murya yace"Azmee wai ni ina ƴata hafsat ne?ko an manta dasu ne?naga ban gansu ba!?
  "Ni kaina inata so in tambayesu,tun shekaran jiya rabon da in Sanya su a cikin idona,tamkar basa a cikin gidan nan"!Acewar Abbansu,
  "Bari na kirasu,"Azmee ta faɗi hakan tare da juyawa ta nufi ɗakinsu laila,
  abinci take ci,amma hankalinta ba akwance yake ba,Yau tunda ta tashi daga bacci gabanta ke ta faɗuwa rasss!rasss!mafi yawancin lokutta in taji gabanta na yawan faɗuwa to tabbas wani abune zai faru da ita!mai kyau ko mara kyau,sam takasa cin abincinta,sae faman jujjuya cokalin hannunta takeyi acikin plate ɗin dake agabanta,
   A hankali ta ɗago da idanunta tare da azasu akan Hosana dake ta faman cunkusa Burger acikin bakinta,yadda kasan zata 6ara bakin ko gajiya da Ci ba tayi,Allah sarki rayuwa kenan,Allah mai yadda yaso,kamar basu bane waɗannan yaran ba,masu yawo babu takalmi a ƙafafunsu,kawunansu babu ɗan kwali,Kayan jikinsu duk a yayyage,babu mai son su,rayuwarsu a wulaƙance kowa gudunsu yakeyi,Amma yanzu komai ya canza!Yanzu gasu acikin danginsu,kowa sonsu yakeyi,suci mai kyau su sha mai kyau,su kwana a mai kyau,suturar sawa ma sai sun za6i wadda suke so su sanya ajikinsu,duk mai yajawo wannan, haƙuri!sun rungumi ƙaddararsu sun cinye jarabawar da Allah yayi masu,basuyi gajan haƙuri ba,kullum cikin kai kukan su wurin Allah suke,saboda sun san cewa shi kaɗai ne zai iya share masu hawayensu,duk irin ƙuncin rayuwar dasu Sehrish suka shiga,basu ta6a ƙasƙantar da kansu ba don suyi bara,ko su siyar da mutuncinsu don su samu kuɗi,kamar yadda wasu mutanen keyi,

Janye idanunta tayi daga kan hosana ta mayar dasu kan jahad,wadda ke ruƙe da bread a hannunta,tana goga mashi butter,abun ya ɗaure mata kai kowa sai cin abinci yake yi hankali kwance,amma ita takasa Cin nata,to ko dai bata da lafiya ne? ta ƙarasa zancen zucin tare da juyawa,karaf idanunta suka sauka akan Fuskar Abusufyan wanda ke kallonta,har sai da ta ɗan razana kaɗan,sunanshi ta ambata abakinta a hankali"daddy,"
..murmushi ya ɗan sakar mata tare da cewa"Daughter,tun ɗazu ina kallonki,kin ƙi cin abincinki,kin tasa ƴan uwanki gaba kinata kallonsu ɗaya bayan ɗaya,faɗamun meke damunki ne'?
  "Daddy am not feeling well,gabana sai faɗuwa yakeyi,bansan meyasa ba,shiyasa ma nagaza cin abincin"muryarta akasalance tayi maganar,
  Jahad tace"Daddy,jiya ma batayi wani isasshen bacci ba,"
  "Saboda me"?yayi tambayar yana kallonta,
  "Nikaina bansan meyasa ba,kawai bana jin daɗi ne,"
  Jinjina kai yayi tare da cewa"Kada ki damu in sha Allah wannan faɗuwar gaban da kikeji Alkhairi ne zai faru dake,"
  "Allah yasa haka ne daddy" ta ƙarasa maganar tare da kai hannu ta ɗauki cup of tea ɗin dake agabanta,ta shiga kur6arsa a hankali,ba don tana jin daɗinsa ba,

Suna cikin cin abincin nan,sae ga Azmee tare da hafsat,sun shigo dining area ɗin,Aunty babba na a bayansu ta sanya Niqab a fuskarta,hayaam dai bata fito ba,saboda gudun karsu haɗu da Sgr a wurin,da hannu Azmee tayi masu nuni da su zauna a inda su Jahad suke,saboda nan ke akwai empty chairs guda biyu da suka rage,da yake table ɗin mai mazaunin mutun Shida ne,
  Tunda suka zo wurin,idon kowa ya koma akan Aunty babba dake sanye da niqabi,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,sai da suka fara gaishe dasu Abba,sannan suka samu wuri suka zauna,hankalin Aunty babba sam ba'a kwance yake ba,bata so fitowa ba,Azmee ce ta sanar da ita cewa Ishaq yace su fito dining suci abinci,tayi mata hakan ne saboda ta rama Wulaƙancin da sukayi mata,

Daƙyar ta iya gaishe da Abusufyan,batare daya ɗago ya kalleta ba ya amsa mata,hafsat tace"Uncle ina kwana,"?
"Lafiya lou hafsat,ashe kuna acikin gidan,ae nayi tunanin kun koma Kaduna ne,"
Murmushin yaƙe tayi,sae faman zazzare ido takeyi,duk sunbi sun tsargu,ita da mommynta,ita dai Sehrish ta zuba ma sarautar Allah ido,so take taga ta yadda Aunty babba zataci abinci da niqabi a fuskarta,ba ita kaɗae ba hatta jahad abunda take jira kenan,Ishaq kuwa tuni ranshi yayi mugun 6aci,sarai yasan cewa da gangan ta zura niqabi a fuskarta bayan tasan cewar abinci zata ci,alamun rashin gaskiya duk sun bayyana atattare dasu,ita da hafsat,
Serving ɗinsu Aunty azmee tayi,ta tura masu plate ɗin abincin agabansu,hafsat dai tayi kokarin cin abincin,kaɗan kaɗan take tura chips abakinta,Aunty babba kuwa kamar gunki haka ta ƙame saman kujerar taƙi motsi,fargabarta kada hosana ta gane cewa itace,
Murmushin mugunta sehrish ta saki,tare da yin gyaran Murya tace"Aunty,ki cire niqabin mana,in ba haka ba,bazaki ji daɗin cin abincin ba,gashi yana ta hucewa,bazaiyi maki daɗin ci ba inya salafce,"
Mazurai Aunty babba tashiga yi ta cikin niqabin,ƙululun baƙin ciki kamar ta shaqo sehrish ta rufe ta da bugu,ƙin magana tayi saboda gudun kar Hosana taji Muryarta,ta kara tona mata asiri,hakan yasa Jahad cewa"Na ji tayi shiru,kodai bacci ne bai isheta ba"?tayi maganar tana faman ƙumshe dariya abakinta,sehrish tace"inaji tayi bacci ne a zaune,bari na cire mata niqabin don tasha iska kada numfashinta ya sarƙe," yunƙurawa Sehrish tayi tare da kai hannu zata zame niqabin dake a fuskar Aunty babba,ae kuwa a firgice Aunty babba ta zabura ta miƙe tsaye tana faɗin"Karki kuskura ki ta6amun niqabi na," rai a6ace tayi maganar,aikuwa Hosana najin Muryarta,ta daddage ta fasa uwar ƙara,tare da yin wurgi da kofin dake a hannunta,a gigice ta miƙe tana ƙokarin guduwa,gaba daya hankalin kowa ya dawo kanta,Omar ne ya miƙe da sauri ya ruƙo hannunta yana tambayarta lafiya,
A tsorace tashiga fadin"Banason ta!na tsane ta!wlh ya Omar muguwace matar nan,tazo nan ne don ta kashe mu,dan Allah ku koreta daga gidan nan,wayyo Allah na....."ta fashe da matsanancin kuka,tashin hankalin da ba'a samashi date!nan fa kowa ya miƙe tsaye yana bin Aunty babba da kallo,saboda tsabar ruɗu muryarta na kerma tashiga cewa"wa...wallahi Billahil azimu Ni bansanta ba!bansan laifin me na aikata mata ba,yarinyar nan fa mahaukaciya ce tana da ta6in hankali,shiyasa take wannan sambatun...."tunkan ta ƙarasa maganar Abusufyan ya daka mata tsawa tare da cewa"karki kuskura ki ƙara kiran ƴata da sunan mahaukaciya!in ba haka ba ranki zai 6aci a wurin nan ne!hosana bazata ta6a tsangwamar mutun hakanan ba batare daya aikata mata wani mugun abun ba," ya karasa maganar tare da jan dogon tsoki,
"Ya Omar dan Allah ku sakar mata karnuka su fiddata daga cikin gidan nan,wlh babu Allah aranta!so take takashe maka hosanarka,"cikin shesshekar kuka take maganar,Marshal sai ƙokarin rufe mata bakinta yakeyi don ta daina amma ina hosana taƙi rufe bakin,don har cizon hannunshi takeyi,in yayi ƙoƙarin toshe mata baki,Aunty babba kuwa sae faman zabga salati takeyi,jikinta sae kerma yakeyi,tuni zufa ta jika ta sharkaf,ƴan hanjin cikinta kuwa sae faman kaɗawa sukeyi,hankalin General ishaq ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoranshi kada ace wani mugun abunne laila ta aikata ma yarinyar da har take tsoron ganinta,
Lalla6awa Aunty babba tayi da gudu tabar dining area ɗin ta koma cikin dakinsu,tana shiga ciki ta aza hannayenta asaman kanta tana faɗin"Na shiga uku!Na bani!na lalace!Waccen mahaukaciyar yarinyar tana son taja mun bala'e ina zaman zaman lafiyata,"tana magana tana cizon yatsan hannunta,"Aunty laila meya faru,"hayaam ce tayi mata tambayar,
"Hayaam ta faru ta ƙare!yarinyar can ta gama dani!"muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,hannu tasa tare da zame niqabin fuskarta,tayi wurgi dashi ƙasa,sannan tashiga zagaye ɗakin tana faman cizon yatsanta,

"Dan Allah kowa yayi haƙuri ya koma ya zauna,ina tunanin ciwon hosana ne ya motsa,ba wani abu ba shiyasa take ta sambatu,"Omar ne yayi maganar don ya kwantar masu da hankalinsu,
Fashewa da wani sabon kukan hosana tayi tana faɗin "Wlh ya Omar Ni da hankalina,da tunani na!nasan me nakeyi,wannan matar itace ta...."kasa ƙarasa maganar tayi saboda tsawar da Omar ya daka mata "Shut up hosana!bana son na ƙara jin maganarki a wurin nan!in ba haka ba saina sa6a maki," tafin hannunta tasa tare da toshe bakinta,tana yin kuka ƙasa kasa,
"Ka daina yi mata tsawa Omar,tabbas akwai abunda akayi ma yarinyar nan,wanda ya ƙona mata zuciya shiyasa take wannan sambatun,ya kamata mu lallasheta,muji menene matsalarta"? Acewar Abba,
Ishaq yace"hakane,In ba damuwa Inason ganinka Omar tare kuma da yaran,"
Ya ƙarasa maganar tare da shigewa gaba,Omar yabi bayansa hannunshi ruƙe dana hosana,jahad kuma na abayansu,

Bayan tafiyarsu,kowa ya koma ya zauna,wasu suka cigaba da cin abincinsu,wasu kuma suka bar dining ɗin waɗanda suka ƙoshi da abincin kenan,wurin yayi tsit kowa da abunda yake saƙawa aranshi,

A 6angarensu General ishaq kuwa,a farfajiyar gidan suka zauna saman wasu ƙayatattun kujeru na shakatawa,kowa ya zauna,Hosana da jahad suna fuskantar Ya Omar da kuma ya ishaq,
Gyaran murya ya ɗan yi tare da kallonsu yace"dalilin dayasa na buƙaci ganinku,saboda inason jin menene alaƙar dake atsakaninku da Laila matata?shin taya akai hosana ta santa da har take tsoran ganinta"?
Kafin su bashi amsa Omar yayi hanzarin cewa"Ae farko sun ta6a zama a wurinta,Ni na kaisu gidanka,a lokacin kayi tafiya,na damƙa amanarsu a wurin laila,saboda ina da tabbacin cewar zasu samu kyakkyawar kulawa a wurinta,tun da ita mace ce,zasu fi sakewa a wurinta,"
Tunda ishaq yaji hakan gabanshi ya fadi,saboda yasan halin laila sarai,bata da mutunci,saboda mugun halinta yasa masu aiki suke gudun gidan,duk ƴar aikin da sukayi ƙarshe guduwa takeyi daga gidan saboda masifarta,
janye idonshi yayi daga kan Omar dake magana,ya mayar dasu kansu jahad da hosana,yace"Ina sauraronku?A zaman da kukayi tare da laila me ya faru?
Jahad tace"babu komai,munyi zaman lafiya tare da ita,"tana rufe bakinta hosana tace"wlh ƙaryane!jahad ƙarya takeyi maku,batason ta faɗi gaskiya ne,"ta ƙarasa maganar tana matse kwallar data zubo mata a idanunta,
"Jahad!kinsan banason wasa!faɗamun gaskiyar abunda ya faru acikin gidan,bayan na barku," Marshal ne yayi maganar fuskarshi a ɗaure babu alamun wasa tattare dashi,hakan ne yasa jahad ta natsu ta shiga kora masu bayani,
"Ya Omar,tun lokacin da ka tafi kabarmu a gidan,Aunty laila ta rufe mu acikin wani tsohon store,babu ci babu sha,iska kanta daƙyar muke shaƙarta saboda wurin a ƙuntace yake,babu window,ga ƙwari dake yawo acikin store ɗin,ranar acikinsa muka kwana,hosana ko bacci bata samu ba......"gaba ɗaya jahad ta kwashe duk abunda ya faru dasu agidan Aunty babba,tun daga A har Z ta sanar masu,a ƙarshe ta fashe da kuka,
Ishaq kuwa ba abunda ke fitowa daga bakinshi sai kalmar innalillahi'wa inna ilaihirraji'un,'Muryarshi har kerma takeyi wurin cewa"Omar meyasa ka kaisu gidana ne?wlh da ace ka sanar dani tunda farko,da banbari ka kaisu wurin laila ba,saboda nasan halinta,hakanan nake zaune da ita,matar nan bata da imani!muguwace!yanzu ni bansan ya zanyi ba!da wani ido zan kalli Abusufyan da sauran ƴan uwana idan sukaji wannan Zaluncin da laila ta aikata ma Yaran nan!!
Yana magana,huci na fitowa daga bakinshi,ranshi yayi mugun 6aci idanuwanshi sunyi jawur,
Marshal Omar kuwa saboda tsabar 6acin rai,ya gaza buɗe baki yayi magana,tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu saboda takaicin abunda laila ta aikata ma su jahad,yaran da ya damƙa mata amanarsu,sai yanzu ya gane dalilin da yasa duk in yaje gidan a lokacin da suke wurinta,sai yaga fuskokinsu babu walwala ashe bayin Allah azabtar dasu takeyi,
Daƙyar ya iya buɗe baki yace"Amma Laila ta cuce Ni!ban ta6a tunanin zatayi mun haka ba,Meyasa zatayi mun haka?laifin me kuka aikata mata?kawai saboda taga baku da gata ne,don nace mata marayu ne ku shine ta ƙuntata rayuwarku?Ashe itace ta sanya wannan fasiƙin mutumin ya ɗauke ku acikin motarshi don ya zubar mata daku acikin dajin,har yayi ƙoƙarin Yima hosana fyaɗe acikin gidan gonarshi.... " sai yanzu ya gane dalilin da yasa Major yaƙi sanar dashi gaskiyar lamarin daya afku,koda ya tambayeshi a lokacin baya sai cewa yayi yalla6ai banso in shiga tsakaninka da Matar yayanka ne,Ashe mugun abu ta aikata masu,
A fusace Ishaq ya daki table ɗin dake agabansu,ya miƙe azabure yana ƙokarin zame belt ɗin wandonshi,a ƙoƙarinshi na ya shiga cikin gidan yayi ma Aunty babba bugun tsiya,
Da sauri Omar ya ruƙo hannunshi,"Ya ishaq,ba anan yakamata ka yanke mata hukunci ba,koba komai ita uwar ƴa'ƴanka ce,mutuncinta zai zube agaban kannenmu,da sauran mutanen gidan,inaso taci albarkacin wannan,"
Runtse ido ishaq yayi wani irin huci ke fita daga bakinsa,damƙar hannun Omar yayi tare da janye shi daga ruƙon da yayi mashi,ko waiwayenshi baiyi ba ya shige cikin gidan,

Jiki ansayaye Omar ya mayar da idanunshi kan su hosana dake tsaye,wani irin tausayinsu ne ya lullu6eshi,matsawa yayi tare da janyosu ya rungumesu ajikinshi,tamkar ya zubar masu da hawaye haka yake ji,Yayi danasanin kaisu wurin laila,bakomai ne yaja hakan ba fa ce rashin sani,cikin sanyin Murya yace"kuyi haƙuri ku yafe mun,duk laifina ne dana kaiku wurinta,wlh danasani kai tsaye Abuja na kawoku gidanmu,Ni duk atunanina zaku fi samun kulawa a wurinta,ƙaddarace kawai ta riga fata,Amma wlh da ace kun sanar dani tun lokacin da nake zuwa gidan,da saita ɗanɗani kuɗarta," ya ƙarasa maganar a lokacin da yake ƙoƙarin raba jikinshi daga nasu,
Jahad tace"Ya Omar kadaina ɗaura ma kanka laifi,dama can Allah ya ruga da ya ƙaddara faruwar hakan,kuma yanzu ae komai ya wuce,ni wlh ba don hosana ta fara tona mata asiri ba,da babu wanda zaiji wannan maganar abakina,don har gargaɗin hosana nayi akan kada ta sanarma kowa amma bataji ba,"
Murmushi Omar ya ɗan yi tare da kallon hosana dake ta faman sauke ajiyar zuciya,ruƙo hannunta yayi cikin nashi sannan yace"Hosana tayi mun dai dai jahad!idan har aka biye ta taki,bazaki ta6a bari a hukunta mara gaskiya ba,saboda tausayinki,abunda nakeso ki gane jahad,Irin waɗannan mutanen masu baƙar zuciya,idan har ba'a dinga hukunta su ba,to basu ta6a gane kuskurensu,balle har suyi nadamar abunda suke aikatawa su daina," jinjina kai jahad tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace"Hakane ya Omar,kayi gaskiya,Sehrish ma ta ta6a fadamun hakan,lokacin da nayi ƙokarin hukunta hosana akan tonan asirin da taso tayi ma matar Ya ishaq,' sun jima atsaye suna magana kafin daga bisani Omar ya ruƙo hannayensu tare da shigowa dasu cikin gidan,


Hankalin aunty babba fa yaƙi kwanciya,babban abunda takeyi ma fargaba shine kada Hosana ta tona mata asiri agaban surukansu,kusan sau uku tana shiga toilet saboda cikinta daya katsa,har wurin ƙarfe 2:30,bata daina safa da marwar nan ba,acikin ɗakin,ƙafafunta har sai da suka fara yi mata raɗaɗi sannan ta samu wuri ta zauna daga gefen gadon tana faman sakin huci,shigowa hafsat tayi cikin ɗakin,fuskarta jawur sae faman kuka takeyi,aunty babba na ganinta ta miƙe hankalinta a matuƙar tashe ta shiga tambayarta Meya faru,Cikin shessheƙar kuka hafsat tace"daddy ne,Yayi mun faɗa sosai akan abunda muka aikata masu hosana,har mari na sai da yayi,kuma yace daga yanzu babu ni babu shi,In nemi wani uban,!"
Hannu aunty babba ta aza asaman kanta tana ambaton"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un!wayyo!nashiga uku!shikenan Hosana ta gama dani ta tona mun asiri wurinsu ishaq,Wayyo Ni laila,Zawarci ba fashi," tana magana tana cizon yatsanta,
  Fitowar hayaam kenan daga cikin toilet taji suna wannan maganar,jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,babban abunda take ji ma tsoro shine Ishaq ya saki Laila,saboda tasan cewa muddin ya saki aunty babba,to zamanta a gidan ya qare!!tunda bata da wata aƙala dasu,!Tashin hankali,ishaq bai ta6a gigin ta6a jikin hafsat ba,duk irin girman laifin da take aikatawa,amma yau akansu hosana Tasha mari,idan har hakane menene hukuncin aunty babba?ita da ta ɗauki nauyin shirin gaba daya,OMG!! Rungumota hayaam tayi ajikinta tana lallashinta,daƙyar ta samu hafsat tayi shiru,

*Boss Bature*

  ❤🤍❤
*💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*




Saman Gadon ta haye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login