Showing 12001 words to 15000 words out of 64985 words
Chapter 5 - Abban Sojojin Bokk 3 Hausa Novel Complete
manna mata kiss kafin ya rungumeta,fuskarta asake tace"My romeo,"Amsa mata yayi da mommy,a lokacin daya koma wurinsu twins suna gaisawa,Jahan yace"Ina zuwa naga key ɗin mota a hannunka,"
"Zanbi su uncle ne," ayaan yace"Kada ka bari Mommy taji to,in ba haka ba bazata bari kabi su ba,"
"Saboda me"?ya tambaya yana kallonshi,Jahan ne ya bashi amsa da cewa"Saboda bazata barka ba,idan ta tambayeka ina zaka je,sae kace mata gidan abokinka zakaje,"duk wannan maganar da sukeyi a kunnan abbansu saboda yana kusa dasu,kallonsu kawai yakeyi,juyawa junaid ya ɗanyi tare da satar kallon mommyn,idonta na akanshi hakan ya tabbatar mashi da cewar so take taji me suke cewa,'
"Ka tafi kawai,"acewar ayaan,
harya juya zai tafi ya tuna da Abbansu,dawowa yayi tare da zuƙunnawa agabanshi yace"Abba,"ɗaure fuska abba yayi batare da ya tanka mashi ba,
"dan Allah kayi haƙuri abba in na 6ata maka rai,bazan ƙara ba,"
Ta6e baki abba yayi tare da cewa"Junaid kenan,ae ni yanzu babu ruwana dakai,kafi ƙarfi na,"_
Ashagwa6e ya kuma cewa"pls abba,kayi hakuri,ka manta da abunda ya faru jiya,bazan ƙara ba,"
"Naji,tashi ka tafi,ka kulamun da kanka,"
Murmushi junaid ya saki tare da mikewa ya manna mashi kiss a fuskarshi,sannan cikin sauri ya kama hanyar fita,
"Junaid ina zuwa"? Jin muryar Momnynsu yasa shi dakatawa da tafiyar da yake yi,
tsayawa yayi tare da juyawo ya kalleta,
"Mommy gidansu abokina zani je,"
"Kai da wa?waye zai kai ka?
Nuna mata key ɗin motarshi yayi kafin yace"Ni zan kai kaina,"
Jinjina kai tayi tare da cewa"Okey,u can go," da sauri ya fuce daga cikin gidan,
Mayar da idanunta tayi akan abbansu tace"Dama inaso inyi magana dakai,wai meyasa kuka bar romeo yana Driving da kanshi?Also babu wani security guard dake tsaronsa,Shi kadae yake yawonshi,"
Abba yace"Allah xai tsare mana shi,"
Alexandra tace"Nasan da wannan,Amma wannan babban ganganci ne,koda ace kowanne daga cikinsu zaiyi yawonshi batare da security guards ba,amma bai kamata ace kamar junaid ƙaramin yaro yana yawo shi kaɗae ba,ba wani tsaro atare dashi,Especially yadda kowa ya sanya mashi ido,gaskiya ni hakan bai kwanta mun araina ba!!"
shiru abbansu yayi yana nazarin maganarta,
Jahan yace"Gaskiya Abba,maganar mommy gaskiya ne,yakamata ace junaid akwai security guards dake tsaronsa duk inda zaije,musamman a wannan yanayin da muke ciki,bibiyar rayuwarmu akeyi don kawai acutar damu,junaid kuma yafi kowa ƙaranta acikinmu,yana buƙatar security,"
"Abunda nake ƙoƙarin fahimtar dashi kenan,"acewar mommnynsu,
jinjina kai Abba yayi tare da cewa"hakane,zanyi wani abu akai',
daga nan suka cigaba da tattauna a tsakaninsu,
*Boss Bature*
Tun bayan da Hayaam ta tura ma Aunty babba hotonsu hosana,bata samu damar duba hoton nasu ba,ko whatsapp ɗinta bata shiga ba,wayarma tana ajiye cikin bedroom ɗinta,Shirye shiryen zuwa walima kawai sukeyi,atare da hafsat suka fita saloon daga nan za'ayi masu ƙunshi,bayan nan kuma zasu biya Shopping mall,saboda siyayyar da tace zatayi ma Ƴa'ƴan uncle ɗinsu,basu suka dawo gidan ba sai wuraren karfe shida na yamma agajiye suka dawo,kowa ya wuce bedroom ɗinshi,Aunty babba na shiga ɗakinta,kai tsaye ta faɗa saman gadonta ta shiga sharar bacci,Hafsa kuwa saida ta fara yin wanka,ta canza kayan jikinta izuwa riga da skirt marasa nauyi,sannan ta fito falo ta kwashe shopping bags ɗin da suka bari a falo,takaisu ɗakinta,tana cikin dudduba kayan wayarta dake ajiye gaban mirror ta shiga ringing,hannu takai tare da ɗaukar wayar tana kallon screen ɗinta,ganin Sunan Aunty Hayaam ya bayyana akan secreen ɗin wayar,yasa ta ɗaga kiran tare da karawa a kunnanta,
"Assalamu Alaikum aunty hayaam,'
Ko amsa mata sallamar batayi ba tace"Hafsat ina Aunty laila take ne?tun da sassafe na tura mata hoton bata duba ba,har nagaji da jira,"
Hafsat tace"yanzu muka dawo daga kasuwa agajiye,tana a bedroom ɗinta ina jin bacci ne ya dauketa,ko inyi mata magana ne"?
Hayaam tace"A'a,kawai idan ta tashi ki sanar da ita cewa na tura mata hoton ƴa'ƴan abusufyan ɗin,ta duba ta whatsapp ɗinta,"
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hafsat,muryarta na rawa tace"hoton ƴa'ƴan Abusufyan dinmu!zan sanar mata kuwa,"
Rejecting call ɗin tayi,da gudu ta fito daga bedroom ɗinta,kai tsaye ta haye upstairs ɗakin aunty babba,tura kopar ɗakin tayi tare da shigewa ciki,a kwance ta samu aunty babba saman gadonta sai sharar bacci takeyi,ga wayarta ajiye agefenta,
Cikin sanɗa takai hannu tare da ɗaukar wayar,ta danna power ɗinta ta kawo haske,ganin akwai password yasa ta ɗan bubbuga kafarta tana cewa"Kai mommy,yanzu dole sae kin tashi sannan zan samu damar ganin hoton babies ɗinmu!gaskiya ni a ƙagare nake,"
Tana cikin maganar,ta tuna da finger print ɗin dake akwai ajikin wayar,nan take zuciyarta ta bata shawarar cewar me zai hana,ta lalla6a ta hau saman gadon,ta dangwalo yatsan aunty babba,kota samu wayar ta buɗe,Good idea,ta furta hakan tare da lalla6awa ta hau saman gadon,cikin sanɗa ta ƙarasa inda aunty babbar take,hannunta ta ruƙo tare da sanya yatsan hannunta a wurin,ya rubuta mata wrong,haka ta dinga bin yatsun hannun aunty babba tana jarabawa,har sai da taci nasarar buɗe wayar,saukowa tayi daga saman gadon,ta tsaya atsaye,hannunta har kerma sukeyi wurin daddana wayar,tsoranta kar Aunty babba tafarka saboda tasan halin Mommyn nata,ta tsani wani ya ɗaukar mata wayarta,kamar mara gaskiya,
Tana shiga whatsapp ɗinta,sai ga wani security ɗin,rai a6ace tace"Mommy kamar mara gaskiya,duk tabi waya ta garƙame da security,"
Allah yaso shima finger print ne,komawa tayi tare da dangwalo yatsan aunty babba,whatsapp ɗin ya buɗe,
Kaitsaye ta shiga chat ɗinsu da Hayaam,anan taga hoton da Hayaam ta tura mata,bai buɗe ba hoton saboda data a kashe take,cikin sauri hafsat ta kunna data ɗin,nan take yashiga loading yana ƙoƙarin budewa,a hankali hoton ya soma bayyana,ƙura ido hafsat tayi tana jiran hoton ya kammala buɗewa,
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu ji kake Daram!!Dararam!!tamkar ana buga ganga,Waro ido waje hafsat tayi agigice a matukar razane,tamkar wadda taga Zombie,hankali a matuƙar tashe tace"Kai!!!"
Hannunta har kerma yakeyi wurin yin zooming ɗin hoton nasu ta matso dashi kusa don tagani dakyau,gaba ɗaya tagama kiɗima,wata irin zufa ce ta soma tsattsafo mata agefen fuskarta,daƙyar take iya haɗiye yawun bakinta saboda maƙoshinta daya bushe ƙamas,juyawa tayi ta kalli Aunty baba dake ta faman mutsu-mutsu alamar zata farka daga baccin da takeyi,aikuwa cikin sauri tayi deleting ɗin hoton gaba daya,sannan ta rufe wayar,tayi wurgi da ita asaman gadon,jikinta na kerma ta fuce daga dakin,gudu gudu sauri sauri haka take tattaka stairs ɗin ƙiris ya rage ma tayi tuntu6e saboda yadda jikinta ke rawa kafkaf kamar wadda sanyi ya kama,
Bedroom ɗinta ta koma,tana shiga ta aza hannu akai tana faɗin"Tashin hankali!In har dagaske ne abunda idanuna suka gane mun acikin hoton nan kenan hakan na nufin cewa HOSANA DA JAHAD Suna araye kuma suna a gidansu daddy!taya hakan ya faru?Kenan Ya Omar shine ya ɗaukesu?Ina wannan tsohon mutumin da mommy tasa ya kwashe su da nufin ya zubar dasu?Taya akai hosana da jahad suka kasance ƴa'ƴan uncle ɗinmu!?wacece ita ɗayar yarinyar mai kama dasu sak!dama su ƴan uku ne?Tabɗijancan,akwai matsala,
Komawa tayi gefen gadonta ta zauna tare da kifa hannunta asaman fuskarta,hosana da jahad suna raye,suna gidan abban mu,wayyo Allah na,ina farin ciki sosai,duk da ina tsoran abunda zai biyo baya,Ashe jinina ne su!shiyasa akace rashin sani yafi dare duhu,mun cutar dasu sosai,mun zalunce su bayin Allah,mutuwa ce kawai batazo ta daukesu ba acikin gidan nan amma sunsha wahala,sun ƙuntata,tabbas Mommy mun shiga uku,idan Abba yaji,daga ni harke ba wanda zai tsira,kwara ni hukuncina mai sauƙi ne tunda na nuna masu soyayya daga baya amma ita mommy itace silar fitar dasu daga gidan nan don azubar dasu,Wayyo Allah na!,
Yatsun hannunta sae faman kerma sukeyi,jiki na rawa ta ɗauki wayarta tare da lalubar numbar junaid ta danna mashi kira,
A lokacin junaid yana tare dasu Uncle abusufyan,dama sai daya fara kiranshi a waya ya tambayi address ɗin inda suke ya bashi,har an kammala yi masu saloon tuntuni,anyi masu ƙunshin jan lalle a hannuwansu,daga can suka wuce shoprite siyayya,bayan sun kammala siyayyar,suka biya gidan Uncle ɗin nasu wuraren 6,saboda su kwaso wasu daga cikin kayansu Jahad da hosana wanda zasuyi kwalliyar walima dasu,
A bayan motar junaid aka sanya trolley ɗin kayan nasu,sannan Sehrish da hosana suka shige motar abusufyan,jahad kuma ta shiga motar junaid,atare motocinsu suka fita daga cikin gidan,
Tunda jahad ta shiga motarshi,ya ɗaure fuskarshi,dama tun wurin siyayyar yake ta shan mur yana murtuke mata fuska,amma hakan bai hana tayi masa magana ba,duk in ta ɗauko abu sai ta gwada mashi ta tambayeshi zaiyi mata kyau,daƙyar yake amsa mata da eh,ko a'a,sai dae kawai tayi murmushi ta girgiza kai,
Kiran Hafsat na shigowa a wayarshi,yace"ki ɗauki wayar,ki amsa wayar sai ki sanyata a handsfree,"
hannu jahad tasa tare da ciro wayar daga aljihun gaban rigarshi,picking call ɗin tayi bayan ta sanyata handsfree sannan tayi Mata sallama,
Muryar hafsat ce ta karaɗe kunnansu"Junaid!kana ina ne"? Gaban jahad ne ya faɗi rass saboda jin muryar hafsat,duk da bata tabbatar da cewar ita bace,amma muryar tayi mata kama da ta sister hafsat,
"Ina akan hanyar komawa gida ne yanzu hakan,"
Hafsat tace"junaid dan Allah so nake in tambayeka,waɗannan yaran ƴa'ƴan uncle abusufyan Ƴan uku ne"?
"Of course they are triplet,"ya bata amsa a yayin da yake ƙoƙarin juya sitiyarin motar,ya karya kwana,
Hafsat tace"Ya sunan su"!
Juyowa yayi ya ɗan kalli jahad da idanunta ke akan shi,kafin ya mayar da idanunshi kan driving din da yakeyi,a jere ya ambaci sunayensu"Hosana Sehrish Jahad"!hafsat na jin haka,a gigice ta kashe wayar,
"kiran ya katse,"Jahad ta faɗi tana ƙare ma wayar kallo,
"May be network ne,idan na koma gidan zan kirata,"
"In mayar maka da wayar"?
"A'a ki ruƙe a wurinki,idan mun isa gida zan kar6a,"
ta amsa mashi da toh,
Gallery ɗinshi ta shiga tana kallon kyawawan hotunanshi da yayi,tare da videos,yawanci duk na ban dariya ne,wasu yana a kwance,wasu ya zullo harshe waje,wasu hotunan ya kashe idanunshi,
Dariya ta dinga yi a yayin da take kallon videos ɗinshi na tiktok,duk yana sauraron sautin dariyarta,wani lokacin har satar kallon fuskarta yakeyi,ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,musamman inta tuntsire da dariya,wani sa'in hada kifa kanta saman laps dinta saboda tsabar dariya,murmushi kawai yayi tare da mayar da hankalinshi akan driving ɗin da yake yi,a haka har suka ƙarasa gida,
Bayan hafsat ta katse kiran,ta Kifa kanta asaman pillow ɗinta,tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka,dama ance dana sani ƙeya ce,
Farkawa Aunty babba tayi da wata irin matsiyaciyar yunwa,sae faman hamma takeyi,tashi tayi daga zaune tare da kai hannu ta ɗauki wayarta tana cewa"Ko hayam ta tura mun da hoton?bari na duba na gani,Allah yasa dai bata manta ba,"
shiga cikin whatsapp ɗinta tayi tare da duba chat ɗinsu da hayaam,rai a6ace taja dogon tsoki tare da cewa"Wai dama bata turamun hoton ba!harfa ƙara nanata mata nayi akan ta tura mun hoton amma bata turo ba," ta ƙarasa maganar tare da yin wurgi da wayar saman gadon,
Saukowa tayi daga saman gadon,fita tayi daga cikin bedroom din ta sauko ƙasa,kai tsaye ta nufi kitchen,
Batare da 6ata lokaci ba,ta shiga harhaɗa kayan da zatayi amfani dasu,bayan ta ɗaura girkin,ta ɗebo snacks a plate ta haɗo da coke mai sanyi ta dawo falo,ta zauna,tana ci tana kallo a plasma hankalinta kwance,
jin motsin mutun a gefenta yasa tayi firgit tare da juyawa don taga wanene,ashe hafsat ce atsaye yanayinta kamar na wadda tayi amai da zawo,fuskar nan tayi gwanin ban tausayi,idanunta sun ƙankance saboda kukan da tasha,
"Hafsat!lafiya naga fuskarki tayi jawur?kinyi kuka ne"?
Girgiza kai hafsat tayi tare da cewa"Babu komai mommy,wani film nake kallo acikin wayata,shine ya sanya ni kuka,"
Tsoki Aunty babba taja"shirmen banza,kawai daga kallon film saiki kama kuka kamar wata sakarya,"
murmushin takaici hafsat tayi tare da samun wuri daga gefen aunty babba ta zauna,batare da tace komai ba,
Aunty babba taci gaba da cewa"gaskiya kowane film ne wannan ya ciri tuta tunda har ya iya sanyaki zubar da hawayenki,yadda kike da shegen taurin kai,
"Mommy ba zaki gane bane,"
"Taya za'ae in gane?tunda bakiyi mun bayanin meya faru ,acikin film ɗin ba,ki ɗan bani labari mana,"
Gyara zama hafsat tayi kafin ta soma bata labarin kamar haka"wata matace fa,mijinta ya kawo mata wasu marayun yara donta rainesu a wurinta,tun ranar da mijin ya kawosu gidan shi kuma yayi tafiya,ae kuwa matar nan,ta shiga gana masu azaba,ta hanasu abinci yunwa kamar zata kashesu,har bugunsu takeyi,sannan kuma ta dinga sanyasu aikin wahala,har saida suka kusa rasa rayuwarsu,mommy kinsan meya faru"?
Dakatawa Aunty babba tayi daga shan lemun hannunta da takeyi tace"a'a saikin faɗa,"
"Hmmm,Mommy ƙarshe fa matar nan,tasa aka kwashe yaran nan,aka 6atar dasu saboda kawai kar asirinta ya tonu a wurin mijinta...'
"Hakan da tayi yayi mun dai dai,"Acewar aunty babba,
Murmushi hafsa tayi kamin tace"Ae ban ƙarasa maki labarin film ɗin ba,bayan tasa an zubar da yaran nan,ita duk a tunaninta sun mutu ma,Ashe can wurin gararin rayuwar da sukeyi a daji Allah ya haɗasu da kanin mijinta har ya taimakesu ya kaisu gidansu mijin,da akayi bincike aka gano cewar yaran ƴa'ƴan kawunsu ne wato ƙanin mahaifinsu,"
Aunty babba tace"tashin hankali!ita ko wannan ya zatayi da kanta?
Dariya hafsat tayi tare da cewa"Nima abunda nake tunani kenan!amma Mommy idan kece ya zakiyi,"
shiru Aunty babba tayi tana tunani kafin daga bisani tace"Ae kawai tunkan asirina ya tonu zan gudu ne,a neme ni arasa,amma nikam hafsat wai ya sunan Film ɗin nan ne?tayi tambayar tare da kallon hafsat ɗin wadda itama kallonta takeyi,mikewa hafsat tayi tsaye tare da cewa"An fara kiran sallar magriba,bari naje nayi salla,"
"Amma baki faɗamun sunan film ɗin ba!"Aunty babba ce ta sake nanata mata tambayar da tayi mata,
*AN YANKA TA TASHI* shine sunan film ɗin mommy,yanzu na kalleshi a tashar youtube,tana kai ƙarshen maganarta,ta juya da sauri ta wuce bedroom ɗinta,
Zugudum Aunty babba tayi tana maimaita sunan film ɗin da hafsat ta faɗa mata,wato An yanka ta tashi,
Aranta tace"gaskiya ya kamata in kalli film ɗin nan,Inaso inga yadda matar nan zata ƙare,ko ya mijinta zaiyi da ita?tabɗijancan,akwai badaƙala,"tayi maganar tare da mikewa ta wuce kitchen domin ta duba girkin da ta ɗaura,
Bayan ta kuma fitowa daga kitchen ɗin,upstairs ta wuce bedroom ɗinta,gefen gadon ta zauna tare da miƙa hannunta ajikin drawer chest ta janyo gidan farko,sabon sim ne ta ɗauko tare da daukar wayarta dake ajiye saman gadon,zura sim card ɗin tayi aciki,sannan ta lalubo lambar wayar Ammi wadda tayi copying kan phone,danna mata kira tayi,nan take kiran ya shiga,kusan sau uku kiran na katsewa batare da anyi picking ɗinsa ba,tana kira a karo na hutu Ammi ta ɗaga kiran 😳
ɗan zaro ido Aunty babba tayi kafin ta gyara natsuwarta tare da zabga sallama"Assalamu Alaikum Ammi barka da warhaka,"ta maƙe muryarta yadda ammi bazata iya gane muryar wacece ba,
on the other hand Ammi ta amsa mata da cewa"Wa'alaikumus salam,barkanki dai,zan iya sanin dawa nake magana"a dake take magana,
Aunty babba tace"Nasan bakisan dawa kike magana ba,saboda baki sanni ba,Ni matar abokin Abusufyan ce,wadda ke zaune a ƙasar turkey,"
Shiru ammi tayi tana sauraran me magana,
Aunty babba taci gaba da cewa"akwai wani mummunan abu da abusufyan ya aikata a 6oye baison kowa ya sani,shiyasa na kira don in sanar dake,don banason abunda zai ta6a mutuncin family ɗinku,wannan abun kunya ne,muddin ya fita waje mutane sukaji to fa,zaku rasa duk wata ƙima da martaba da kuke da ita....'
tana cikin magana Ammi ta dakatar da ita"Ya isa haka!banason wata kwanana,ki faɗamun abunda kikeson sanar dani!me Abusufyan ya aikata?wani laifi ne wannan da har kike ikirarin zai ta6a ƙimar family ɗinmu a idon jama'a,"?
Wani irin wahalallen yawu aunty babba ta haɗiye kafin daƙyar ta soma kora mata jawabi kamar haka
"Shekarun baya da dadewa,Abusufyan yayi ma wata fyaɗe,harta samu ciki....."
Wata irin tsawa da Ammi ta daka mata har sae da takusa sakin fitsari a wando,a tsiwace tace"Dakata!ki iya bakinki!kinaso ki shiga tsakanina da ɗana ne!wacece ke,kada kiyi tunanin kin kirani da 6oyayyiyar number,zan iya sa agano munke duk inda kike,"
Muryar Aunty babba na kerma tashiga faɗin"wlh dagaske nake ammi ba ƙarya nake ba,gobe idan kinzo abuja wurin walima,zaki ga yaran,ae suna nan gidan Abba,Sun jima suna 6oye maki gaskiya,saboda tsoron hukuncin da zaki yanke ma Abusufyan,yanzu haka maganar da nake maki,sun gama shirya yi maki ƙaryar cewar yaran ba shaggu bane ta hanyar aure aka haife su bayan ba haka bane,suna nan yaran ƴan uku ne mata,sun girma sosai,' tana kai ƙarshen maganar Ammi tace"Kin gama"?
Shiru Aunty babba tayi tana faman mazurai aranta tace"Wannan tsohuwa badae taurin kai ba,bansan ya zanyi na fahimtar da ita ba,ta cika jaraba,"
tana cikin wannan zancen zucin Ammi ta katse kiran,
Wurgi Aunty babba tayi da wayarta,tare da mikewa tana cewa"Ae shikenan,nasan cewa gobe tana ganin yaran zata tuna da kalamai na,daga nan saita ɗauki hukuncin daya dace,"
❤🤍❤
*Boss Bature*
Zaune yake asaman Sofa mai mazaunin mutun uku,gaba ɗaya ya tattara hankalinshi akan Laptop ɗinshi da yake daddawana anatse,jikin shi na sanye da linen tank top,blue colour tabi shape din jikinsa,sick pack din nan nasa ya bayyana ajikin rigar,trouser ɗin jikinsa kuma white colour ne,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga kowani sashe na jikinsa,
Shigowa Azmee tayi part ɗin nasa da sallama a bakinta,yayin da hannunta ke ruke da tray,amsa mata sallamar yayi batare daya ɗago ya kalleta ba,ƙarasawa azmee tayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman empty table din dake a gefenshi,hannu takai tare da ciro plate ta daukko serving spoon tana ƙokarin buɗe warmer,muryarshi ta katse mata hanzarinta da cewa"ɗazu da safe meyasa kika kawomin breakfast?kuma kika gyaramun bedroom ɗina,dama kece ke gyara mun part ɗina ne"?
gabanta ne taji ya faɗi rass,muryarta na kerma tace"A'a bani bace,Sehrish ce,"
"Meya hanata yi mun aiki,"?yana magana yana danna laptop dinsa har time ɗin bai ɗago da idonshi ba ya kalle ta,
Azmee tace"Am...um...dama..."bata ƙarasa maganar ba,ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannunshi,cikin sauri ta shiga taitayinta,
Cike da bada Umarni yace"Call her right now,"
Jiki na rawa azmee ta juya tare da fucewa daga part dinsa,downstairs ta saukko,babu kowa a falon duk suna a bedroom ɗinsu,wasu ma sunyi bacci,
Kai tsaye ɗakinsu Sehrish taje,tsayawa tayi abakin ƙopar ɗakin tana kwankwasawa,sai faman knocking takeyi amma ba'a buɗe mata kopar ba,da alama sun jima da yin bacci,
Har sae da ta fidda rai da za'a buɗe mata kopar,tana kokarin juyawa tabar wurin,taji alamun za'a buɗe kopar,Jahad ce ta buɗe ɗakin tana tambayar wanene,
Ganin