Showing 9001 words to 12000 words out of 185502 words
Chapter 4 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete
a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:50 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*5*
Tana shiga kusa da mamanta ta zauna tana fad'in "Mama lafiya? Ya naga baki d'ora girki ba har yanzu?"
Kallonta tayi tana sauke ajiyar zuciya, juyawa tayi ta kalli su Yaseen dake duba littafinsu suna karatu, girgiza mata kai tayi tace "Ba komai Mimi, zan d'ora yanzu."
Da alamar tuhuma ta kalleta tace "Mama, ko dai babu abinda za'a dafa ne?"
Da sauri ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kan ta, cikin k'aguwa Mimi tace "Mama ki min magana mana, idan baki fad'a min damuwarki ba wa zaki fad'a ma?"
Kallonta ta sake yi a hankali tace "Hakane, Mimi ba tunani na abin da zamu ci yanzu bane, tunanin yanda zamuyi da dare nake, har malam ya bar gidan nan babu tabbacin zai samo mana wani abu, saidai abu na ubangiji kawai."
K'ura mata ido tayi tana kallo, dafa kafad'arta tayi tace "Amma mama shi ne ba zaki fad'a min ba, har yanzu ina da canji a hannu na na kud'in da Mas'ud ya bani a ranar dana siyi kayan makaranta, bari na d'auko."
Da kallo ta bita har ta shige d'akin, jim kad'an ta fito ta tsuguna gabanta ta nuna mata jaka guda tace "Kin gani mama, yanzu me za'a siyo sai naje da kaina."
Girgiza mata kai tayi tace "A'a Mimi ba sai kinje da kan ki ba, kawo sai na ba Yaseen ya je."
Ita ma girgiza kai tayi tace "A'a mama zan je, kinsan aikensu yanzu ba zasu dawo da wuri ba."
Jinjina kai tayi alamar gamsuwa, dan haka tace "Mimi ko garin tuwo babu shi bare shinkafa, ki siyo mana wani abun da zamu iya sarrafawa da wuri kafin lokacin tafiyarku islamiyya."
Jinjina kai tayi ta mik'e tace "To mama, bari na siyo mana ko ledar macca guda biyu."
Bata jira me zata fad'a ba ta koma d'akin ta d'auko hijab ta saka ta fita, gungun yan matan unguwarsu ta wuce suna zaune a kan dakali suna hira, babu wacce ta kalla a ciki bare ta musu ko da sannu, hakan yasa suka kafa dandalin yi da ita dan dama haushinta dayawa ke ji. Tana zuwa ta siyo abinda tasan zasu buk'ata ta juyo ta dawo, tana kawowa daidai su suka bushe da dariya har da tapa hannu zabayar ciki na fad'in "Sarauniyar kuri, ji da kai da nuna isa, ka ganta a hanya tsabal tsabal gidansu kamar rudun tamtabaru."
Cak ta tsaya tare da juyowa ta kallesu, gyara tsayuwa tayi ta tofar da yawu ta bisu da harara tace "Idan mutum ya na da k'arancin abun yi dama ya kan zama mai neman fitina, ni kuma a halin da nake ciki yanzu ban da lokacin masu abun yi ba bare marasa shi."
Yatsina fuska tayi tare da takawa zata wuce, tsaki wata tayi tace "K'aryar banza da wofi, da bamu san asalin balbela bane da sai tace mana daga masar take."
Wata ce tayi saurin cewa "Dan kawai Allah bai miki hallita irin ta iyayenki ba, shikenan kin d'auki girman kai da raina mutane kin d'ora a kan ki, sai ka ce wata 'yar shugaban k'asa."
Sama da k'asa ta juyo ta hararesu taja dogon tsaki ta wuce ta barsu, hakan kuma zafi ya musu sosai dan sun so ta kulasu yanda zasu k'addamar da abinda suka tsara mata, da dukan tsiya zasu mata su mata baja-baja sai fatar nan ta canza kala, dan su har yau sun rasa gano dalilin da yasa fatar jikinta da surarta suka zama kala daban, idan ka dubi Mimi da gidansu da iyayenta, dole ka tuna da ayar da Allah mad'aukakin sarki yace *ya na fitar da duhu a cikin rana, kuma yana fitar da rana a cikin duhu, sannan yana fitar da rayayye a jikin matacce, kuma yana fitar da matacce a jikin rayayye, sannan yana azurta wanda ya so ba tare da hisabi ba*.
*Sheikh*
Tagumi ya buga yana kallonta yanda take ta cika mishi plate d'in gabanshi wanda tasan ba zai iya cinye abincin ciki ba, saidai har k'asan ranshi dad'i yake ji yanda Hafsat bata wasa da abincin shi, tunda ya aureta shi dai yayi hannu riga da yunwa, saidai ko baya gari amma yana gari kam yafi k'arfin nan. Zaune tayi tare da matso kujerarta kusa da shi ta d'auki cokali ta d'ebo ta nufi bakinshi, murmushi ya sakar mata tare da yin bismillah ya karb'a, sake d'ebowa tayi saiya nuna mata had'in kokombre da tayi da hannu alammar shi yafi so, yar harara ta cilla mishi ta d'ebo tana fad'in "Allah dai yayi walk'iya na ga mutum, domin kuwa nima nayi bincike na gano sirrin kokombre nan."
Yar dariya yayi ya kanne mata ido d'aya yace "Kuma ai kinji dad'i da mijinki ya zama mai son kula miki da kanshi ko?"
Cikin jin kunya ta sunkuyar da kan ta, d'ago hab'arta yayi yace "Bana so ki fara kallona a matsayin *tsoho*, shiyasa nake bin duk wata hanya data inganta dan na inganta miki lafiyata."
Dariya tayi mai birgewa tace "Na ji dad'i, amma a baya na damu sosai da son sanin sirrin nan amma ka k'i fad'a min."
Murmushi yayi yace "Ina rok'on Allah ya ma rayuwarki albarka, tunda na nuna miki ina son kokombre sosai da kabewa da kuma miyar albasa, baki tab'a gazawa ba wajen sarrafa min su, wasu lokuta abu daban kike dafawa dan ku ci, amma ni saikin d'ora min wanda na fi so."
Murmushi tayi tace "To ai dan hidimarka nake zaune a gidan, idan ba zanyi ba miye anfani na?"
Da sauri ya rik'o hannunta yace "Kina da, *Hassy* ko babu wannan ni zan iya zama da ke, karki manta ke fa 'yar uwata ce, mahaifinki da mahaifina ciki d'aya suka fito, kinga kuwa ko babu aure tsakaninmu zan iya rik'eki."
Murmushi ta kuma yi tana sunkuyar da kan ta, karb'an cokalin yayi ya fara cin abincin yana bata ita ma yana fad'in "Ki shirya k'arshen wata zamu fita hutu insha'Allah."
D'aga manyan idonta tayi ta kalleshi sai kuma tayi k'asa da idonta, ba sabon abu bane wannan kam a wurinsu, idan har kaga bai fita da ita k'arshen wata ba to baya gari ko kuma sabgogi sun mishi yawa, amma ya kan ware k'arshen wata ya d'auketa su keta hazo wani lokacina ita ke zab'ar inda zasu tafi, ba dan komai ba sai dan ita ma ta huta na kwana uku kawai ba tare da aikin gida ko kula da yara ba.
Jinjina kai tayi tace "Insha'Allah, Allah ya saka da alkairi, Allah ya k'ara bud'i."
Da murmushi yace "Madalla da *mata ta gari*."
Da sauri ta d'ago tace "Ga *miji na gari*."
A tare suka lak'aci hancin juna suna had'a baki wajen fad'in "Bisa koyarwa *addinin islama*."
Cin abincinsu suka ci gaba da yi har ya kammala ya shiga dan shiryawa dan ana daf da kiran sallah la'asar ne.
*Madarasatul darul tauhid*
_(04:35 na yamma)_
Duk girman unguwar nan cike yake da mutane sakamakon sabkar nan, bak'i ta ko ina sun halarta bisa gayyatarsu da akayi, har yan makaranta sun zo kowane da kalar nasu uniforme, kusan makarantarsu Mimi sun zo a makare, dan ko da suka zo tuni an fara gabatar da karatu, gashi kuma ajin da aka ware dan sauke bak'i 'yan makarantar sai ta tsakiyar filin dole zasu bi su wuce.
Mai kula da bak'in na ganinsu mata da fararen hijabai da siket bleue maza kuma farar hula da farar riga ya tarbesu, da 'yar bulalarshi a hannu ya shiga gaba yana bud'e musu hanya suna wucewa, ta tsakiyar filin suka bi suka wuce ta bayan babbar rufar alfarma dake d'auke da manyan bak'i. Sam Mimi bata kalli wajen ba dan daga nesa ta hango duk manya ne a wurin, daga kujerun da aka aza musu zuwa babban carpet d'in dake shinfid'e zaka gane haka.
*Kamar tsautsayi* idonshi suka sauka a kan ta, kuma wani hukunci na ubangiji bai kalli kowa ba sanda kallonshi ya juyo a lokacin da 'yan makarantar ke wucewa, saida ta zo d'an nesa dashi wanda da a lokacin ta juyo zasu fuskanci juna ne ya kalleta da kyau, nutsatsiyar fuskarta ta kamala wacce babu d'igon kwalli a kai, tafiyarta ta wahainiya cikin sand'a da ladabi, hannunta jimk'e dana Asma'u suna takawa a hankali. Baisan lokacin daya furta " *Tabarakallah, masha'Allah, tabarakallah ahsanul kalik'in*."
Wata nannauyan ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idonshi, a hankali ya d'ago hannunshi ya d'ora daidai zuciyarshi ya dafe sosai, wani k'ayataccen murmushi ya saki yana bud'e idonshi, a k'asan zuciyarshi ya furta "Hak'ik'a nan ya amsa da k'arfi, da fatan zaki zama *alkairi a gareni*."
Mayar da hankalinshi yayi kan karatu amma ta wani b'angare tunanin yanda zai yi da sabo kuma bak'on lamarin yake, shin ya tuntub'i malamin makarantar a game da lamarinta? Ko kuma dai 'yan barandarshi kawai zai sa su nemo mishi gidansu ya gabatar da kan shi? Ko kuma dai ya fara shiga jikin yarinyar har ya fahimci *wacece* ita? Miye halayenta? Ya d'abi'arta take? Daga wane gida ta fito? Shin zata so shi ta zauna da shi? To amma ko zai san wacece ita dole sai ya fara sanin inda take rayuwa, dan haka yanzu wannan ne yafi mahimmanci a gareshi sanin *gidansu*.
Sam bai samu halin da zai ci gaba da wulk'ita idonshi dan sake ganinta saboda tururuwar da jama'a sukayi a kan shi, kowa son yake su gaisa wasu daga nesa suna d'aukar hoto, da k'yar jami'anshi guda biyu da tallafawar 'yan agaji suka taimaka har ya shiga mota suka bar wurin.
Tare da k'awayensu suka taho, amma sannu sannu duk suka rabu ya rage daga ita sai Asma'u kowace rik'e da ledar wainar da aka basu ta sadaka, suna karyo layin gidan taja wani birki ta tsaya tare da rik'e Asma'u suka koma baya, yanda ta zaro ido kamar an tsorata ta ne yasa Asma'u d'an juyawa sannan ta kalleta tace "Mimi lafiya? Me kika gani?"
Cikin rashin gaskiya tace "Ke baki ganshi bane? D'an wahala ne fa."
Da mamaki Asma'u tace "D'an wahala? Waye haka kuma?"
Tsaki tayi tace "Ki gane mana, *Muttak'a* ne."
Zaro ido tayi tace "Muttak'an ne d'an wahala?" Murmushi tayi tare da fad'in "Ya ci sunansa kam, dan kati ma na kud'i dayawa yake turo miki."
Cikin rad'a tace "Asma'u ki bar wasa mana, bai san gidanmu ba fa, ya akayi ya zo nan?"
Da alamar tuhuma tace "Idan ba ke kika fad'a masa ba ya akayi ya zo?"
Hararanta tayi tace "Idan ni na fad'a masa kuma saina tambayeki?"
Dafe k'ugu tayi tana feso iska a bakinta tace "Matsala kenan."
Tab'e baki Asma'u tayi tace "Ke kika jawota da kan ki, duk da kin bawa Mas'ud dama ya kawo kayanki shikenan."
Wata harara ta cilla mata ta jin haushi tace "Ana maganar arziki zaki sako min ta tsiya, Mas'ud d'in dana gama rufe babinshi ne zaki wani tado min zancenshi."
Da maamaki tace "Ban gane kin rufe babinshi ba? Me kika masa Mimi?"
Kallon idonta tayi tace "Abinda kike so mana, ba ke kika fad'a min idan nasan bana son mutum na fad'a masa gaskiya ba? To gaskiyar na fad'a masa."
Girgiza kai tayi cike da jimami da rashin jin dad'i tace "Gaskiya Mimi baki kyauta ba, haba dan Allah."
A k'ufule ta kalleta tace "Kinga ba wannan ba, fad'a min yanda zanyi na shiga gidanmu ba tare da mutumin can ya ganni ba?"
Tab'e baki tayi tace "To shi banga aibunsa ba, ki tsayar dashi mana tunda kin kori Mas'ud."
A hassale tace "Ke Mas'ud d'in banza, idan kina son shi ki fad'a min saina had'aku, shi kuma waccen lek'a kiga yanda yake mana, sam baya da tsari da iya ado wani sakarai da shi, kud'i ne Allah ya bashi amma babu aji."
Da mamaki Asma'u tayi murmushi tace "Wasu ko mahaukaci ne suna so indai yana da kud'i, amma ke ko kana da kud'in sai ka iya d'aukar wanka, sannan ka zama mai k'ananan shekaru, dan na gama fahimtar kina gaba da duk wanda yake d'auke da shekaru arba'in da sama."
Dariya ce ta kubce mata ta kalli Asma'u tace "Ba haka bane, ba gaba nake da masu shekarun ba tunda ubana ba shekarunsa kenan, kawai dai nasan a wannan shekarun babu abinda zan samu na soyayya a gurin mamallakinsu, mafi aksarinsu kuma zaki ga suna fama da shirgegen tunbi da nonuwa, sannan in k'ara tuna miki *sa'an babana ne*, ni kuwa me zai sa na auri sa'an babana a shekaru? Ai da kunya ma."
Girgiza kai Asma'u tayi tace "Mimi ina jin tsoron ranar da zata zo kiyi nadama a kan wannan fariya da kike."
Farr tayi da ido tace "Ba fariya bace."
Jujjuyawa tayi da sauri ta k'arasa kusan dakalin dake k'ofar wani gida, zaune tayi tare da yaye hijabinta ta baya ta dawo dashi a gaba, Asma'u data k'araso ne tace "Ba zaki shiga gida bane?"
Yatsina fuska tayi tace "Sai ya tafi."
Da mamaki Asma'u tace "Mimi ko dai ba kya so yaga gidanku ne?"
Da sauri ta kalleta tace "Saboda me? Ke tunda muke dake kin tab'a ji ko ganin na nunawa wani gidan da ba namu ba?"
Kawar da kai tayi tace "Asma'u duk iskancina wallahi bana jin kunyar a ga gidan, hasalima alfahari nake a ga daga ina na fito, haka-zalika bana jin kunya nuna iyayena duk da zubin hallitarsu, ina son kayana a haka kuma duk wanda ya nemi raina min su wallahi zamu saka k'afar wando d'aya da mutum."
Ajiyar zuciya Asma'u ta sauke tace "To in hakane ki shiga gida mana kar dare ya miki a nan."
Tab'e baki tayi tace "Nasan waye Muttak'a, dan magriba ba zata sa ya bar k'ofar gidanmu ba, ni kuma haka kawai na tsani na ganshi kusa da ni."
Ita ma tab'e baki tayi tace "To kinga ni tafiya zanyi, dan bana tsaya na biye miki ba har magriba ta mana a waje."
K'ala ba tace mata ba sai binta da kallo tana d'an jujjuya ledar wainarta, wucewar su Yaseen yasa ta cewa "Kai ku zo nan."
Da kallo ta bi gajerun k'fafunsu har suka k'araso, ledar hannunta ta mik'a musu tace "Ku kai wa mama ta ci ta baku sauran."
Yaseen dake babba ne ya karb'a yace "Mimi ina kika samu waina dayawa haka? Mu fa hak'uri aka bamu aka ce bamu samu."
Wani murmushin gefen labb'a tayi tare da girgiza kai, ita fa tana zaune aka biyota da wainar ma tare da Asma'u da ta ci albarkacin ta, wanda ya bata wainar abokin d'an ajinsu ne dake ikrarin wai yana son ta, kallo d'aya ta mishi ta d'auke kanta daga gareshi bata sake kulashi ba har yau, amma ko yanzu da zai ganta tsaye zata siyi pure water zaiyi tsal ne ya biya kud'i, ko da ba ita kad'ai bace yawansu ya kai dubunnai. D'an kallonsu tayi tace "Ku tafi gida."
Juyawa sukayi sai kuma tace "Ku zo." Dawowa sukayi suna kallonta, cikin gargad'i ta kama kunnenta tace "Akwai wani mutum a k'ofar gida, idan ya tambayeku ina nake ku ce an rik'emu a aji muna hadda, sannan idan kun shiga gida ku fad'awa Mama na tafi duba jikin Iya Delu."
Saida ta sake zaro ido tace "Kun ji ko?" Da sauri suka jinjina mata kai alamar to tare da juyawa suka wuce.
*Alhamdulillah* munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.
Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:50 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�