Showing 183001 words to 185502 words out of 185502 words
Chapter 62 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete
kai shi yasan da walakin goro a miya, tabbas akwai abinda take da buk'ata, amma sau nawa suke samun sab'ani saidai shi ya d'auki da dangana da girma ya nemi sulhu, amma ita ta dinga botsarewa kenan tana fusata tana hawa da sauka.
Ita ma kallonshi take ganin yana ta kallonta sai kawai ta fad'a jikinshi ta fashe da kukan shagwab'a tana fad'in "Kayi hak'uri yallab'ai ka yafe min ka ji."
Wani munafikin murmushi ya saki a ran shi yace "Na-san a rina dama, mata da kurb'e kurb'e musamman idan sun haihu."
Dariyar mugunta ya dinga saki ya shiga shafa jikinta yana zura hannayenshi cikin rigarta, tsam tsigar jikinta ta fara tashi tana rage sautin kukanta sai kuma ta d'ora hannunta na dama kan nonon shi tana shafawa tana rufe ido.
Biye mata yayi shi ma sosai saida yaji suna buk'atar kwanciya kawai ya janyeta a jikinshi ya sake nuna mata k'ofa da idonshi da shi ma ya kamu da jarabar yace "Fi...ta a nan."
Da mamaki ta kalleshi sai kuma ta sake langab'ewa ta matso zata rik'e hannunshi ya sake nuna mata k'ofar alamar ta fita, duk k'ok'arinta saida hawaye suka fito mata dan sosai take jin yanayi marar dad'i a jikinta, juyawa tayi a fusace ta bar d'akin zuwa d'akinta ta cire hijabinta ta kwanta gefen 'yarta dake baccinta ta k'ura mata ido.
Tun tana d'an lumshe ido tana matse k'afafunta har bacci ya d'auketa ita ma marar dad'i. A hankali ya shigo d'akin ya zuba mata ido, murmushi ya saki yana godewa Allah daya nuna mishi lagon yarinyar nan, kamar kowa'e d'an adam yana da rauninshi, haka shi ma yanzun ya hango na ta raunin, ba zai cutar da ita ta haka ba dan cituwar zata iya shafarshi, saidai shi ya d'an samu sauk'in wani abun daga gareta, abu d'aya da zaiyi shi ne ya sake dagewa wajen inganta lafiyarshi dan samun sauke mata hakk'inta, ya sani har ga Allah wasu lokutan idan ya zurfafa tunani ya kan ji kamar ya tauyeta, dan a lokacin da tsufa zai riskeshi ya kai k'adamin da baya buk'atar mace, ita kuma a lokacin ne zata kai ganiyar shekarunta da dole wutar sha'awa ke ruruwa a jikinta, tambayar anan ita ce shin ya zaiyi idan lokacin nan ya zo? Shin zai saketa dan kar ta fad'a halaka? Ko kuma idan ya rik'eta zata fad'a wata mummunar hanya ce?
Nauyayyen numfashi ya sauke yace "Hasbunallahu wani'imal wakil."
A hankali ya k'arasa kusanta tare da sunkuyawa yasa hannayenshi cak ya d'agata gaba d'aya, bud'a ido tayi da sauri tace "Waye?"
Sai kuma suka had'a ido, rufe idonta tayi jin yace "Waye kuwa ban da na ki."
Turo baki tayi tana wuntsila k'afafu tace "Sauke ni k'asa malam, bayan yanzu ka koroni a d'akinka."
Dariya yayi yace "Na gane ban kyauta ba ai, shiyasa na zo bada hak'uri."
"Ni kawai ka saukeni ba zan hak'ura ba." Ta fad'a tana kumbura, cikin fara'a yace "Muje kan gado tukuna na bada hak'urin, sannan ne zan tantance an hak'ura ko ba'a hak'uran ba."
D'akinshi ya shiga da ita ya rufe ya kaita kan gadon ya sauke, rumfa ya mata ya nemi had'a bakinsu sai kuma tayi zurum ta had'a bakinshi da na ta, waro idon da yayi ya kalleta yasa ta jin kunya ta cire bakinta a na shi ta sunkuyar da kai, tallabo hab'arta yayi yana kallonta da tausayi yace "Ryam, ni ne ko? Ni ake da buk'ata a wannan lokacin ko?"
A hankali ta jinjina kan ta sai kuma ta sunkuyar da kai cikin muryar kuka tace "Abdul k'aik'ayi nake ji a jikina, sai na dinga ji kai kawai nake so na ji kana tab'ani, ko k'amshin turarenka kad'ai na ji saina ji wani irin abu da bana gane ko miye, Abdul tsoro hakan yake bani, wasu lokuta ma idan kana d'akin Aunty Hafsat haka nake jin zuciyata na bugawa da sauri, sai na dinga jin haushin komai sai nayi ta kuka ni kad'ai a d'akina, amma ban tab'a fad'a maka ba dan bana so ka d'auka zan raina Aunty Hafsat ne."
Wuf yayi da bakinta a na shi ya shiga tsutsa dan kad'an ya rage ta saka shi kuka wallahi, ta bashi tausayi sosai yarinyar, hakan na nufin tana jin kishin shi kenan, amma bata nunawa ko kad'an ko da daga ita sa茂 shi ne saboda kar tayi laifi.
*Asa-Ma'u*
Sagala yaron yayi a gabanshi irin goyon nan na zamani hannunshi rik'e da bulunbotin yaron yana d'an jijjiga madarar da ake bashi wasu lokutan. Da sauri ta fito a d'akin tana fad'in "Yasha ne?"
Kallonta yayi yace "Yanzu dai zan bashi, kin shirya ne?"
K'arasowa tayi tana gyara hijab d'inta tace "Na shirya Baby, to wai me ya tsayar da kai da har yanzu bai sha ba?"
Turo baki yayi yace "To ni na iya ne, dan Allah ki bashi da kan ki."
Dariya tayi tace "Nima ban iya ba, yanzu dai muje Baby, kaga fa an kusa sallah la'asar yanzu."
Nufa hanyar fita yayi tayi saurin fad'in "Kawo shi to, so kake ka fita a haka a ce kai ke goyonshi?"
A hankali ya shiga since yaron daga jikinshi, saida ya kalli fuskarshi yana ta baccin shi ya mik'a mata ta karb'eshi, fita sukayi a gidan yana rufe k'ofar take fad'in "Yau nasan sai na ci d'an banzan duka a wurin Salma, bikin sunanta a ce sai yanzu nake fita a gida."
Juyowa yayi ya kalleta yace "A'a fa Hajia ba dole, idan ana ganin kinyi rana a warhaka ma wallahi sai mu koma ciki, ai kinsan duka kwananki uku yau da yin arba'in, babban jarumta fa na yi ta barinki fitar nan."
Dariya tayi tana kallonshi tace "Nagode to jarumi na, amma idan ka hanani ai kuka zanyi."
D'ora yatsarshi yayi a baki yace "Dan haka to a min shiru, kuma a je a dawo mu d'ora inda muka tsaya."
Bud'e mata k'ofar mota yayi zata shiga ta kalleshi ta ja kunnenshi tace "Wai kai abun nan baya isarka ne?"
Girgizz kai yayi ya rintse ido cikin shagwab'a yace "Wayyo Hajia zata cire miki kunnen yaro."
Sakinshi tayi tana dariya ta shiga ta zauna, saida ya shiga shi ma yayi oda mai gadi ya bud'e musu k'ofar sannan ya kalleta yace "Ko kad'an ba kya isata Ma'u na, ni kaina ina mamakin yanda bana gajiya dake kamar wani maye."
Dariy ta fashe da ita tace "Mayen Ma'u kenan?"
Jinjina kai yayi yana dariya ya bata hannu suka buge yana fad'in "Ashe kin gane, mayen Ma'u ne ni."
Isowar motarsu tayi daidai da isowar jibgegiyar motar sheikh, Asma'u na ganin motar tayi dariya tace "Shegiyar k'awa kenan, na d'auka ni kad'ai nayi maraice, ashe harda kayan gidan sheikh."
Dariya Asas yayi shi dai bai ce komai ba dan kan abinda ya shafi Mimi bai cika zak'ewa ba yanzu, karbar *Mujaheed* yayi ta fita sannan ta zagayo ta karb'eshi, k'aramar sumba ya aika mata tare da fad'in "Ki kula da kan ki Ma'u na, sannan ki kula min da zakina, ina sonku."
Murmushi tayi tace "Kai ma ka kula da kan ka, sai ka dawo."
Shiga gidan Salma ta nufa inda Mimi ma ta fito d'auke da Ama ta mata wani irin shiri na ban mamaki ga hijab d'un da aka saka mata yarinyar mai d'aukar hankali ta ci uwar kwalliya a fuskarta, murmushi Asma'u tayi ta nufesu a ran ta tana fad'in "Da alama shirin Ama kad'ai zai d'auketa awa uku."
Tana k'arasowa da ladabi ta d'an lek'a ta gaishe da sheikh Mimi na k'ok'arin karb'ar Mujaheed tana masa wasa, ita ma Asma'u karb'ar Ama tayi sukayi musaye. A mutumce sheikh ya amsa mata tare da mik'awa Mimi hannayenshi ta bashi yaron, sumbatarshi yayi kafin ya mik'o musu shi, zasu wuce ya sake kallonta yace "Ryam."
"Na'am." Ta fad'a tana juyowa, cike da gargad'i yace "Kin dai san aikina na baro na zo dan na kawoki nan, ki koma gida a kan lokaci kinji?"
"To tsohon yan matanshi." Ta fad'a tana wucewa ta bi bayan Asma'u data wuce da Ama, cike da zolaya Asma'u ke fad'in "Mimi irin wannan shiga haka kamar wata 'yar mafiya, wallahi babu mai ganeki sa茂 wanda ya sanki."
Banza ta mata har suka shige ciki suna ta ratsa taron matan suna shiga inda d'akin Salma yake, suna shiga da sallama Asma'u dai da ba nik'ab gareta ba an ganeta, amma dayawa basu gane Mimi ba, dan ruf take k'afafunta da safar k'afa d'auke da takalmi mai tsini, hijabinta dogo har k'asa ga kuma nik'ab, saida ta d'aga nik'ab d'in suka gane wacece, ai tuni suka kwashe da shewa ba ma kamar Jamila da ita ma ba'a jima da aurenta ba tace "Iyee! Ashe kayan gidan sheikh ne."
Salma kuma dak'uwa ta ma Mimi tace "Shegiyar matar malam, Mimi ke ce."
A hankali ta mik'awa Jamila Mujaheed ita kuma ta cire nik'ab d'in tasa a jakarta ta tattaro hijabin shi ma ta jefawa Jamila data fashe da ihu tana fad'in "Wai wai wai! Ke Mimi me kika ci haka a gidan sheikh wai? Kin ganki kuwa?"
A sanyaye kamar ba Mimi ba ta haura kan gadon ta samu wuri ta zauna tana gaisawa da sauren k'awayensu wanda ta sani da ma wanda bata sani ba, suna had'a ido da Asma'u dake kallonta da mamakin yanda ta ga bata kula da tsiyar da su Jamila ke mata ba, a sanin data ma k'awarta ta d'auka zata juya musu manyan d'uwawun nan na ta ne data k'ara masha'Allah sannan tayi fari da ido ta kwankwatsa musu magana, amma sai bata ga hakan ba ta ma fita a harkarsu.
Mimi ma murmushi ta sakar mata tace "Asma'u nayi hankali fa yanzu, ta y'a zan tsaya ina shiririta a gaban 'yata."
Dariya su Jamila suka fashe da ita inda Mimi ta kalleta taja tsaki, hararanta Jamila tayi tace "Mimi an matan tsohonta, wai dan Allah me kike sha ne."
Cikin jin haushi tace "Ke madarar mijina nake sha, ina dalilin wannan jaraba haka, na ji tsohon ne amma ai dan ubanki ke gaki nan har yanzu baki da ciki, ni kuma zuwa d'aya tak ya min na d'aukeshi."
Sauke numfashi tayi ta nunata da yatsa tace "Kinga ki rabu dani ko na ji da abinda ke damuna."
Salma dake ta k'yalk'yala dariya ce tace "To fa! Me ke damunki ne?"
Jamila ce tace "Watak'ila wani cikin ya mata."
"To sai me?" Cewar Asma'u, a raunane Mimi ta kalli Salma tace "Wallahi jiya kusan kwana mukayi a asibiti Mamar malam ba lafiya."
Da sauri Asma'u tace "Mamar malam kuma? Wane malam d'in?"
Nuna Ama tayi tace "Ama nake nufi dan Allah."
Cike da tausayawa Salma tace "Me ya sameta?"
Cike da jimami tace "Wallahi asma (athim)."
"Take da?" Cewar Jamila a tausashe, jinjina mata kai tayi tace "E, kamar da wasa fa yanzu gashi abun sai girma yake."
Addu'a sukayi ta jera mata kafin su ci gaba da hirarsu irin ta k'awayen zamani.
Sanda aka fara shigo da abinci ne Mimi ta hangi Aisha na shigowa d'auke da *Ahmad* yaronta ita ma, da sauri ta kalli Salma tace "Ke dan ubanki ba dai k'awance kike da d'iyata ba?"
Kallonta Salma tayi ta kalli inda ta nuna sai kuma tace "To miye a ciki? Ke 'yarki ce ni kuma k'awata."
Duka ta kai mata tana fad'in "Ke tsir!"
Dariya Salma tayi tace "Ke wallahi ba wani k'awance bane muke, kawai irin gaisawar nan ce ta yanar gizo."
Shigowar Aisha yasa Mimi d'auke wuta ta kama jikinta irin ba wasan nan, da farin ciki Aisha ta k'arasa kusanta tana mik'a mata Ahmad ita kuma ta d'auki Ama tana mata dariya da fad'in "Aman Abie, kina lafiya?"
Mimi ma wasa take ma Ahmad dan ko gida Aisha ta tafi da shi Hafsat ce ke mishi tsiya, amma ita Mimi tace tana son abun ta, hakan yasa wata rana ma sheikh yace ta daina kawo masa shi gida tun kafin ya hanashi kwanciyar hankali a gida.
*10:30*
Fitowarshi kenan daga d'akin Hafsat ya mata saida safe ya shigo d'akin, ganin wuta kashe yasa shi lalubawa ya kunna, dau! Idanshi suka sauka a kan ta tana tsaya bakin gado ta dafe k'ugu da hannayenta duka biyu, daga k'asa ya fara kallon irin guma guman takalmin data saka, takalmi ne fa irin na 'yan matan zamani k'afa ciki wanda har maza na sakawa, wando dogo na mata wanda ya matse daga k'asa sama kuma a bud'e a wajen gwiwan da cinyoyi duk a yage irin dai na 'yan gayu, sai rigar mai botira a gaba amma duk ta b'allesu saita d'aure daga k'asa sosai, sai bras d'inta fara tas data d'an bayyana kad'an ita ma. Hula ta d'ora da ake kira hana sallah ga wani uban gilashi tartsetse a fuskarta da ta ci uwar kwalliya, sai bakinta dake d'auke da lolipop tana tsutsa.
D'an k'asa tayi da gilashin ta kalleshi da idonta da suka sha eyeshadow ta kashe mishi ido d'aya, a saukake ya had'a yawu murya can k'asan mak'oshi yace "A'uzu billahi mina shaid'anin rajim."
A hankali ta shiga takowa cikin takon birgewa har ta tsaya gabanshi hannunta dafe da k'ugu, sauke gilashin ta sake yi ta d'ora hannunta a kafad'arshi tace "Sheikh ni ce shaid'aniyar kuma?"
D'an zabura yayi dan wallahi sai yaji kamar mafarki ne yake, tar ya sauke idonshi a kan ta yana mata wani kallo kamar wacce ta gaura masa mari yace "Ryam yau kuma wane fitsararren ne a jikinki haka? Na ga kayan bacci kala kala a jikinki har da wad'anda kamar babu, amma wannan fa? Baturen wace k'asar ce?"
Bushewa tayi da dariya kamar zararra sai kuma ta had'e rai tana kallonshi tace "Abdul, ni ce mai iskokai a kai? Haka kake nufi ko? Nagode."
Sake d'ora hannunta tayi a kafad'arshi cikin rad'a tace "Abdul ka manta ne, yau muka shekara cif da aure, shiyasa na maka wannan shigar, kuma kai na ji ka fad'a a wa'azinka cewa babu laifi mace ta wa mijinta gayu na d'aukar bakin duniya indai daga ita sa茂 shi ne, to shi ne nawa sai ya zama abun fad'a har an tofe ni da a'uziyya."
Kallon k'wayar idonta yayi shi ma yace "Da gaske? Yau ne aka d'aura aurenmu."
D'aukarta yayi cak ya shiga lalubar k'irjinta yana fad'in "Lallai yau zan baki mamaki, wannan gayu ai sai na biya ma zuwa safiyar gobe, amma kafin goben mu fara ban ruwa wa gonarmu ko yan matan tsohonta."
Cire hular kan ta tayi ta jefar haka ma alewar bakinta tana fad'in "Hakane tsohon yan matanshi."
Fad'awa sukayi kan gadon inda suka shiga tallafawa junansu cike da so da k'auna da kuma...馃ぃ
_Allah nagode maka daka nuna min ranar nan, yau gani a k'arshen *matar mutum*, Allah ka bani ladar fad'akarwa kasa a anfana da hakan, kuskuren da nayi Allah ka yafe min tare da makaranta na._
*Kamar yanda na fad'a muku ina son yin dogon hutu insha'Allah a k'alla na tsawon watanni, a wannan lokacin zan samu damar nazari da bincike akan labarin da nake son tab'owa insha'Allah wanda ni ce zan k'irk'iri k'asata da kuma sunayen mutane na dan kaucewa cin zarafin kowa, watak'ila kafin nan mu had'u daku a labaren dake riskata na gaskiya, akwai yiyuwar hakan akwai kuma yiyuwar barin hakan, fatana dai Allah ya sake sadamu da alkirinsa.*
*Alhamdulillah*