Showing 171001 words to 174000 words out of 185502 words

Chapter 58 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

daina. Kuma har yau idan ta je gidan bata wani sakin fuska da jikinta ga Mimin, hasalima daga gaisuwa bata k'ara ce mata komai ba, amma yanzu da ta ji abinda Anas ya fad'a mata sai kawai ta ji wata kunya ma ta kamata, sai taji tana buk'atar b芒 wa Mimi hak'uri sannan su koma kamar yanda suke a baya kafin ta tare gidan uabnsu.





*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*56*



Rayuwa kenan, yau Mimi da kan ta ce tasa a tuk'a mata tuwo dan ta ci, tunda ta kira Aunty Shapi'a ta fad'a mata haka sheikh ya tsura mata ido yana kallo da mamaki, tunda ta fahimci kallon me yake mata ta d'auke kai tana basarwa, murmushi yayi ya mik'e tsaye yana fad'in "Allah ya raba lafiya."

Kallonshi tayi cikin turo baki tace "Ni fa babu abinda nake da, a fa daina alak'antani da ciki."

Bai juyo ba sai ma wucewa da ya ci gaba da yi zai fita yana fad'in "Yo mutum idan masifa yake ji ya fita waje yayi mana, ni a wani tsatsareni nan dan an ga ba ruwana bana duka."

Fashewa tayi da kukan shagwab'a tace "Sheikh ni ko? Ni kake fad'a ma magana? Ba komai ka ci gaba da yi cizgani, kuma ai ko dan cikin jikinka ga dinga lallab'ani kana lelena."

Juyowa yayi yana gimtse dariyarshi yace "Toh! Dama ciki ne da ke?"

Da sauri ta girgiza kai hakan yasa shi sakin mirmushi ya juya ya fita a d'akin yana fad'in "Na tafi tafsir sai na dawo."

D'aga masa hannu tayi alamar bye bye tace "A dawo lafiya tsohon yan matanshi."

Shi ma hannun ya d'ago mata sanda yake fita a d'akin zuwa falonta kafin yake ficewa, saida ta tabbatar ya isa falon ta mik'e da gudu tana hangen bayanshi tayi tsalle ta hayeshi wanda hakan ya zo mishi a bazata saida yayi gaba da k'arfi yana tangal tangal sai kuma ya tsaya da k'afafunshi yana juyo da kan shi yana son kallonta yace "Oh Allah! Oh Allah ka ga baiwar nan taka ka shirya min ita."

Dariya ta kyalkyale da ita tare da saukowa a bayanshi tana fad'in "Ni ma na rama abinda ka min a ranar."

Da fara'a ya kalleta yace "Amma Ryam ke ai yanzu ba ke kad'ai bace, ciki ne da ke fa, ko kina ki zubar mana da shi ne? Kinsan dai ina son ku aje min yara ko?"

Bubbuga k'afafun ta shiga yi a k'asa tana fad'in "Um um fa! Idan fa kana kirana mai ciki zai daina yi maka shokin ma, kasan dai kai ka ce tana birgeka idan ina yi ko?"

Cikin fad'ad'a dariya yace "Idan kika daina sai ki koya min ni na dinga yi miki."

Da sauri ta zaro ido tace "Lahhh! Astagfirullah, Allah ya tsareni da koyawa shehi na rawa, ai sai mala'iku su tsine min."

K'yalk'yalewa yayi da dariya yana fad'in "Wato dai so ake na makara a tafsir ne ko?"

Matsowa tayi daf da shi ta shiga gyara masa zaman hularsa da rigarsa tana fad'in "Kaga dai yau babban tafsir zakayi kuma haskawa kai tsaye ne, ka kula sannan ka nutsu ka aje hankalinka wuri d'aya ko Allah ya sa ka dace da fad'arsa."

Sumbatar kuncinta yayi yace "Nagode Ryam, ina k'aunarki sosai, ina alfahari dake."

Murmushi tayi tace "Baka buk'atar komai?"

Girgiza kai yayi alamar a'a yace "Babu, sai abu biyu kawai, bansan ko zan samu ba?"

Da kulawa ta kalleshi tace "Me fa? Yallab'ai ka d'auka ma angama."

Suna kallon cikin idon juna yace "Na farko ina so ki bani damar sumbatar k'aramin Abdul Waheed d'in dake kwance cikin mararki, hakan zai k'aramin karkashi. Na biyu kuma ina so na ji kin fad'a min kina so na."

Murmushi ta saki tare da d'aga rigarta tace "Na baka izini tsohona, idan ma kana buk'ata zan iya ara maka shi ku tafi tare ai."

Tintserewa yayi da dariya yace "Taya zan tsinana wata tsiya a tafsir ina da k'aramin cikin nan, ai zan zauna nayi ta shafarshi ne."

Dariya ita ma ta dinga yi har saida yace "To na biyun fa."

Wulwula idonta tayi sai kuma ta d'aga k'afafunta ta cimma tsayinta ta manna masa sumbata a kuncinshi da ke zagaye da yalwataccen gemu, da gudu ta nufi shiga d'aki inda ya bita da kallo yana dariya, girgiza kai yayi ya sa kai ya fita zuciyarshi wasai yana jin wani nishad'i.

Babban masallacin Gaddafi suka sauka inda yake d'auke da manyan mutane, masallacin cike yake da dubbanin jama'a sun kasa kunne suna sauraren nutsatsen wa'azin, inda yake nusar dasu da raha yanda zasu fahimta tare da kafa musu misalai, gabanshi cike yake da wayoyi ga kuma kamarori dake d'auka da babban gidan telebejin t茅l茅 sahel dake d'auka su ma suna haskawa kai tsaye.

K'aramar wayarshi daya bari kunne ne mai d'auke da lambobi masu mahimmanci tayi haske alamar sak'o ya shigo, sanin ko ma waye yasan yana tsaka da mahimmin abu yasa sheikh d'aukar wayar dake gabanshi, duk da haka kuma bai daina fad'an abinda yake fad'a ba a bakinshi, saidai yana sauke idonshi a kan gajeren sak'on da Mimi ta turo masa mai d'auke da tsirarun kalmomi kamar haka _"Ina sonka."_

Sai ya samu kanshi da yin shiru na 'yan tsirarun sakanni, aje wayar yayi a ranshi ya fad'i "Nagode Ryam." A zahiri kuma d'an saita nutsuwarshi yayi ya kalli gabanshi yana d'an gyaran muryar da zummar ci gaba sai kawai suka had'a ido da Abba dake zaune sahun gaba kuma a kullum ya ga sheikh d'in shi dai fatanshi bai wuce "Allah ka tsayar da hankalin yarinyar nan wuri d'aya, Allah ka cire mata duk wasu tsutsotsi dake kan ta kar ta tarwatsawa bawan Allah nutsuwarshi." Ba yasa yanzu ma tar yake kallonshi, dan shi a kowane lokaci gani yake za'a ce ga abinda Mimi tayi marar kyau.


*Washe gari*


Ana addu'ar kaffaratul majalis aka fara mik'ewa, da sauri ita ma ta mik'e tana kallon Hafsat d'in data kasance malamarta a aji ta nufi wurin, tana zuwa sunkuyawa tayi tana d'an mamatse k'afafu tace "Aunty Hafsat ba zan jiraki mu tafi tare ba yau, da gudu zan tafi wallahi saboda..."

Sai kuma tayi shiru suna kallon juna, da fara'a Hafsat tace "Saboda me?"

Matse k'afafu tayi gam har tana d'ora hannunta a mararta tace "Aunty fitsari, fitsari nake ji sosai..."

Da sauri ta juya ta nufi k'ofar fita inda Hafsat ta bushe da dariya tana fad'in "Kar dai ki b'ata mana aji malama."

Ko juyowa ba tayi ba ta d'auki takalminta a hannu da gudu tayi b'angarensu, sauren yan ajin da suke d'aukar hadda da basu fita bane suka dinga dariyar Mimin da kuma k'iyasta yanda zamansu da Hafsat ke birgesu, kawai rayuwa ce suke irin ta yaya da k'anwarta, ko da suna kishin juna to saidai sun b'oye a zuk'atansu, amma a zahirinsu kam babu wannan alamar.

Tana shiga falon da gudu d'akinta tayi hari dan tunda ta tare bata tab'a shiga ban d'akin Hafsat ba dake falon, tana cikin gudunta zata shiga d'akinta ta ji muryar Aisha tace "Aunty Mimi."

Cak ta tsaya tare da juyawa ta b'angaren k'ofar d'akin Hafsat d'in da mamaki, ganin tabbas Aisha ce yasa ta sake fad'ad'a mamakinta dan tun kafin ta tare gidan nan rabon da taji ta kirata da aunty, a zahiri kuma sai ta d'an d'aure fuska dan kar ta kawo mata wargi tace "Umm."

Da fara'a a fuskarta ba kamar da ba tace "Auntyna gudun me kike haka?"

Ba yabo ba fallasa tace "Zan shiga ciki ne."

K'arasowa Aisha tayi wacce ta d'an jima da zuwa bata samesu ba hannunta rik'e da plate da biscuits a ciki tana ci, gaban Mimi ta tsaya tace "Auntyna kuma shi ne sai ki dinga gudu cikin gida, idan fa kika wahalar mana da k'ane."

Bud'e baki Mimi tayi ta zaro ido bata san sanda tace "Ke kuma wa ya fad'a miki?"

Murmushi Aisha tayi tana sunkuyar da kai tace "Ai kwanan baya da mukayi waya da Hajia ta fad'a min baki ji dad'i ba, sai kuma akayi sa'a ciwo iri d'aya mukayi da ke, shiyasa na gane."

Sunkuyar da kai Mimi tayi ta bushe da dariya haka ita ma Aisha, suna cikin k'yalk'yala dariyarsu Aisha tace "Aunty Mimi wajenki na zo dama."

Da kulawa ta kalleta tace "To, ina jinki, lafiya dai ko?"

Jinjina kai tayi tana wasa da biscuit d'in cikin plate d'in tana fad'in "Lafiya lau Aunty, dama hak'uri na zo baki akan abubuwan da suka faru a baya, dan Allah ki yafe min insha'Allahu ba zan k'ara ba."

Da murmushi a fuskarta tace "Aisha na yafe miki da jimawa, taya kike tunanin na rik'e a zuciyata har haka, wallahi ba komai na yafe miki, nima ki yafe min kinji?"

Da sauri Aisha ta fad'a jikinta ta rumgumeta tana fad'in "Nagode auntyna, Allah ya saka da alkairi."

D'an shafa bayanta tayi tace "Ba komai Aisha, ya wuce har abada."

Da wata fara'ar tace "Nagode."

D'an sake shafa bayanta tayi tace "Aisha."

A sanyaye ta amsa da "Na'am."

A hankali ita ma tace "Fitsari nake ji, kar ya fara b'ata min jikina."

Da sauri ta janye daga jikinta tana dariya tace "Haba Aunty, ashe shiyasa kika shigo a guje."

Ai bata tsaya cewa komai ba ta kwasa da gudu tayi falonta, a ban d'akin nan ta shiga tayi fitsari har wani rufe ido take saboda yanda yake fita tana jin mararta na yin wani sakai, tana fitowa Aisha ta samu ta zauna kan kujerar dake kusa da fridge ta bud'a alamar zata d'auki wani abu, cire k'aton hijabinta tayi ta aje tana fad'in "Wai kin jima a nan ne?"

Kallonta tayi tace "E aunty ba sosai ba, dama nasan kuna aji shiyasa na zauna jiranku."

Ita ma fridge d'inta nufa ta d'auki ruwa ta bud'e zata sha ta zauna kan kujera, ganin Aisha ta d'auko bud'on had'in dabinonta da madara mao had'e da kankana yasa ta saurin fad'in "Karki sha wannan, magani ne."

Kallonta Aisha tayi ta kuma kalli bidon, ita dai tana ganin alamun madara a ciki, cikin yatsina fuska tace "Aunty maganin me?"

Ita ma yatsina fuskar tayi tace "Mama ta aiko min da shi jiya, na kasa sha ne ma da naji babu dad'i."

Da sauri Aisha tace "Halan na ciki ne? Haka ni ma Hajia ta ce zata kai min magani na dinga sha wai yana wanke dattin yaro, amma ba yanzu ba sai cikin ya girma."

Cike da dagiya da son b'atar da ita Mimi tace "E su ne, amma wannan d'in Mama ta ce na sha ne."

Mayarwa Aisha tayi ta d'auki maltina ta bud'e tana sha tana korawa da biscuit d'inta, Mimi ma tana shan ruwan ta cire safar k'afarta ta mik'e da kayan da jakarta mai d'auke da kayan makaranta ta nufi ciki, tana shiga siket d'in yadin na uniforme ta cire ta cire riga ta d'aura towel ta shiga wanka.


Sanda Hafsat ta dawo gidan ta samesu ta ji dad'in ganinsu a tare, ko ba komai alamu ya nuna sun manta da komai kenan zasu rumgumi junansu, hakan yasa ita kan ta a nan falon Mimin suka dinga hirarsu ta rayuwa tunda akwai 'yarsu ba zasu yarda su saki layi ba, sai sallah azahar ce ta tashesu Mimi tayi a nan d'akinta Hafsat da Aisha suka fita, a can ne kad'ai suka samu damar tattaunawa na 'ya da uwa tare da k'ara mata da shawarwari na zaman aure.

Mimi na idar da sallah Aisha ta shigo tace "Aunty Mimi inji Amie ki zo mu ci abinci."

Mik'ewa tayi akan sallayar tace "To."

Cire hijab tayi ta nad'e sallayar ta wuce tana fad'in "Muje."

Da kallo Aisha ta bi bayanta, a gaskiya ita ma dake mace kuma tsararta wannan sura da halitta ta Mimi abar kallo ce, musamman yanzu ma da kwanciyar hankali da jin dad'i suka tilasta mata k'ara zama rusheshiya tubarkallah, tayi k'iba ta cika mulmul ko ina mazaunanta sun sake fitowa, kuma sa'ar ta d'aya tana da tsayi amma fa a haka ma ta fara gajarcewa, saidai duk k'ibarta bata da wawan tumbin nan, gashi dai tana da ciki amma kuma dake k'arami zaka rantse bata da shi har yanzu mararta ce kawai ta taso.


*Zaune* suke yana tsakiyarsu yana kallon kowace duk sun zubawa takardun gabansu ido suna kallo, Mimi a ranta addu'a take "Allah kasa Hafsat ce zata ci zab'en nan, ba zan iya tafiya na bar k'asata a wannan halin ba."

Inda ita ma Hafsat addu'arta ita ce "Allah kasa Mimi ce zata d'auka, ni na tafi so ba adadi ya kamata ita ma na bata 'yar damarta, Allah ka sani nayi iya k'ok'arina wajen ganin ba sai ya bi ta hanyar nan ba, amma ya nuna min hakan ne adalcin da zai iya yi."

Sheikh dake ta kallonsu ganin kowace sai mi-mi take da bakinta yasa shi fad'in "Ku fa nake jira, kowace ta d'auki d'aya."

Kallonshi Hafsat tayi ta marairaice tace "Sheikh na fad'..."

Bai bari ta fad'a ba ya d'aga mata hannu alamar tayi shiru, shiru tayi cikin sand'a ta kai hannunta ta d'auki d'aya a cikin takardun, Mimi ma a hankali ta kai hannu ta d'auka, jikinsu duk a mace suka shiga warwarewa, Hafsat na ganin babu komai a ta ta takardar ta daka tsalle kamar yarinya tana fashewa da dariya da fad'in "Woooo! Mimi tafiyarki ce, dan haka a tashi a shirye, ni dai a taho min da tsaraba."

Juyawa tayi ta nufi d'akinta tana fad'in "Allah ya kiyaye hanya oga, a dawo lafiya."

Da kallo suka bita saida suka ga shigewarta Mimi ta kalleshi tana matsar k'walla tace "Sheikh bana son tafiyar nan, a tsorace nake sosai wallahi, ji nake kamar ajalina ne ke kirana."

D'ora yatsarshi yayi a labb'anta yace "Shiiiii! Babu abinda zai faru dake Mimi, ki had'a kayanki kinji, muna tare insha'Allah."

Marairaicewa tayi tace "Amma kuma fa ciki ne da ni."

Jinjina mata kai yayi yace "Ba wani abu bane wannan, na gama da matsalar nan tun tuni."

Shiru tayi tana kallonshi sai kuma ta saki murmushi tace "Wow! Yau ni ce burina zai cika ta hanyar keta hazo."

Rik'o hannunshi tayi tace "Kuma ka ga fa zan samu damar rainon cikina ba tare da kowa ya ganni ba, dan ni dama kunya nake ji wallahi."

Dungure mata kai yayi yace "Kina jin kunyar a kalleki a ce cikin tsoho ne jikinki ko?"

Dariya tayi ta kwanta a k'irjinshi tana fad'in "Tsoho, humm! Ni kad'ai nasan waye wannan tsohon, tsohona jarumi ne, ingarman doki ne ko kuma na ce matashin doki ne."

K'amk'ameta yayi yana dariya yace "Ki ce dai na ciri tuta?"

Ita ma cikin dariya tace "Tun a waccen ranar."

D'ago hab'arta yayi yace "Wace rana?"

Kallon idonshi tayi tace "Waccen ranar mana, ranar daka kusa sumar dani."

Tintserewa sukayi da dariya ya mik'e da ita a jikinshi yana fad'in "Mu shiga daga ciki sai ki rama to."

D'an shak'o wuyan rigarshi tayi tace "Da gaske? Zaka bani dama na rama?"

"Um." Ya fad'a yana d'aga mata kai, jinjina kai tayi tace "Kuma karka rama, ka barni ni kad'ai nayi komai na."

Cak ya d'auketa suka nufi d'akin yana fad'in "Na yarda yan matana, zan baki dama ki more ke ma."

Cike da kunya ta rufe idonta har suka shiga ciki ya direta, cike da farin ciki da k'aunar juna suka shiga farantawa junansu rai musamman Mimi ma data zage damtse ta nemi susuta shi da yammacin da har saida jam'in sallah la'asar ya sub'uce musu dukansu.




*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:59 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�

*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA*


_GA DUKA_

*'YAN AMANA TA*


馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃

鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


*57*




Sun jima wajen Hajia suna ta hira tunda suka zo mata ban kwana, Mimi na gefensu tana saurarensu tana sinne kai tana ta b'oye cikinta a cikin hijabi duk da ba fitowa yayi ba sosai, saida suka tashi zasu tafi duk suka mik'e tare Hajia na sake jaddada "Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare, ku kula dan Allah."

Da fara'a suka amsa da "Ameen." Dafa kafaf'ar Mimi tayi tace "Ki kula da kanki kinji ko, duk abinda kika ji a jikinki kar kiyi k'auron baki ki fad'a masa."

Sunkuyar da kai ta sake yi tana jinjina kai alamar to, takawa sukayi zata rakasu saidai daf da fita k'ofar Asas ya turo k'ofar da dama a bud'e take yana fad'in "Assalama alaikum."

A tare suka amsa da "Wa'alaika salam." Ban da Mimi da ta amsa k'asa k'asa tana kakkawar da kan ta, dan ita fa yanzu kunyar Asas take ji, shiyasa duk lokacin nan da aka d'auka sau biyu kawai taje gidan Asma'u.

Da fara'a kamar yanda suka saba sukayi musabaha Asas na fad'in "Hajia bak'i kikayi ashe?"

Dak'uwa ta masa tace "Su waye bak'in a gidan nan?"

Sheikh ne ya tab'e baki yace "Watak'ila shi Hajiarmu, ya manta mu 'yan gidan nan ne."

Dariya Hajjia tayi tace "Da alama kam."

Kallon sheikh yayi yana turo baki gaba yace "Ni fa ba bak'o bane, ni da gidan Hajiata d'in."

Harara sheikh ya dalla masa yace "Kai bana da lokacinka, tafiya zanyi sai na dawo."

Murmushi yayi ya d'an saci kallon Mimi dake bayan Hajia kad'an yace "Matar yaya ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login