Showing 21001 words to 24000 words out of 185502 words
Chapter 8 - Matar Mutum Book 1 Hausa Novel Complete
tsawa har ma su kirashi da *Abdul Waheed*, hatta Hajia sarakuwarshi wacce yake kallo kamar uwa bai tab'a jin ta kirashi da sunan da ba sheikh ba, uwa uba kuma Hafsat ko Ashraf, kowa dai sheikh sheikh ko gafarta malam ko ustaz ko ranka shi dad'e, a ko ina kallon wanda zaiyi alfarma ake masa, girmama shi ake kamar za'a masa sujada. Shine yanzu aka kira da Abdul, lallai ko ba komai yarinyar ta ciri wata tuta da ba kowa ya cira ba, watak'ila a dalilinta zai iya gano wasu abubuwa da suka jima da shige masa duhu.
Saida ya gama tsareta da ido ya kuma d'aureta da su kafin yace "Kin sanni ne?"
A hankali ta jinjina kai tace "Waye bai san fuskar nan ba, ai sai dai makaho."
A dak'ile yace "Kenan ke ma makauniya ce?"
Da sauri ta girgiza kai alamar a'a, numfashi ya sauke ya gyara tsayuwarsa yace "Ina son magana da iyayenki mai mahimmanci, zaki lamunce min na je."
Da sauri ta kalleshi tace "Abbana baya nan." Da sauri ta rintse ido tana danne harshenta daya sakata yin k'arya, sai kuma ta ji ai hakanne zai rabasu lafiya kar ya sake tunanin neman gidansu. Ba tare daya d'auke idonshi ba yace "Ina ya tafi?"
Murya k'asa k'asa tace "Ya je k'auye."
Jinjina kai yayi yace "Kenan zaki iya bani lambarki dan na samu labari idan ya dawo."
Tsuru tayi tana kallon k'afafunshi masu kyawun fasali, hummm! A zuciyarta take jin idan fa ta ciro IPhone d'inta ya gani misali zai bayar da ita wajen wa'azi, sai kawai ta girgiza kai tace "Bana da waya ni, dama data mamana nake kiran k'awaye na, shi ma ba kullum take bari na ba."
Wani sanyayyan murmushi yayi saboda jin dad'in abinda ta fad'a, dan gaskiya kai tsaye ya fad'i hakane saboda yaga kalar ta ta k'awar (wayar), cikin farin ciki yace "Ki bani lambar mamar, kafin ki isa gida zanyi kira dan kiga lambar, idan kinje ki saka suna."
Da mamaki ta d'an kalli gefen fuskarshi sai ta jinjina kai alamar to, murmushi ya sak茅 yi yace "Idan Abba ya dawo saiki fad'a min idan na kiraki."
Sake jinjina kai tayi alamar to, gyara tsayuwa yayi yace "Saida safe Ryam."
A nutse tace "Saida safe." Takawa tayi d'aya biyu uku taji yace "Wane suna zaki saka a lambar?"
Juyowa tayi taga ya hard'e hannayenshi a k'irji ya zuba mata ido, cike da kunya tace "Ku fad'i wanda kuke so to."
Murmushi yayi da a lokacin ta kalli fuskarshi wanda ya birgeta sosai, saida ya lumshe ido yace "Ki saka *Abdul*."
Da sauri ta bud'a baki irin zatayi mamakin nan sai kuma cak ta tsaya ta shkga tariyo kalamanta na d'azu, sunan Abdul na fitowa ta ji kunya ta kamata kawai ta juya da d'an sauri tana murmushi ta bar gurin. Shi ma murmushin ya shiga sakar mata har ya ga ta shiga kwanar hannun hagu, girgiza kai yayi ya bud'e motar ya shiga yana bud'e ruwan hannunshi, saida ya d'aga kai ya tsiyaya a mak'ogwaronshi yasha sosai kafin ya rufe ya aje, wani murmushi ya sake yi y'a shiga juyawa yana fad'in "Abdul, hmmm! K'uruciya kenan, ni ne Abdul ko Ryam?"
Kamar jiran gusawarta yake daga gaban sheikh sai kuwa ya kirata, da rawar jiki ta shiga lalubo wayar a k'ugunta da tunanin guy nan ne, amma ganin sunan d'an wahala saiya sakata jan wani dogon tsaki, saida wayar tayi daf da tsinkewa kafin ta d'auka tana sake yin k'asa da tafiyarta a sannu sannu, shiru dukansu sukayi saida ya tabbatar ba zatayi magana ba sannan yace "Mimi, kina ji na?"
A dak'ile ta amsa da "Um! Ina aji."
Numfashi ya sauke mai sauti yace "Mimi me yasa kike son wulak'antani?"
Yatsina baki tayi ta harari wayar tace "Me yasa ka ce haka?"
Ba alamar fara'a yace "Saboda na ga take-takenki ne, Mimi ki fad'a min gaskiya idan kinsan ba kya so na, bana so duk abinda nake a kan ki ya zama wahalar banza ce."
Cikin jin haushi da rashin bawa abun mahimmanci tace "Ba komai, ka daina tunanin haka."
"Kin tabbata Mimi?" Ya tambaya kamar yana gabanta, ba tare da shakkun komai ba tace "Umm."
Daga inda yake y'a jinjina kai yace "Mimi, ina da karamci ga wanda ya min karamci, ina da alkairi da kuma b芒 wa abubuwa baya, saidai Mimi bana son yaudara da k'arya, na so ki fad'a min ba kya so na dana barki na nemi wata, amma tunda kika ce babu komai shikenan, saidai fa Mimi kiji da kyau, wallahi duk randa na fuskanci akwai cin amana a tafiyar nan ta mu wallahi zaki sha mamaki na, indai har kina so na Mimi ni mai iya jure duk wani wulak'anci ne saboda ke, amma ki wulak'anta ni akan wani? Wannan abu ne da ba zan d'auka ba ko kad'an, akan kuma haka zan iya komai wallahi."
Tunda ya fara magana ban da gwalo da marmad'a masa ido babu abinda take yi tana turo baki da jan tsaki, saida ya kai k'arshe tace "Me zaka iya yi to? Ba zaka hak'ura ba kenan? Amma ai kasan ance *matar mutum* k'abarinsa ko?"
Cike da tabbaci yace "Haka aka ce, iya gaskiya na gad'a miki Mimi, wallahi saidai duk mu rasaki daga ni har masu son na ki."
Da d'an k'arfi tace "Kamar ya duk ku rasani? Kasheni zakayi?"
Tab'e baki yayi yace "Kusan haka." Wani murmushi kuma ya saki yace "Mimi ina da zuciya da bana so ki san kalarta, saida safe kawai ki kula min da kan ki."
Datse kiran yayi ta bi wayar da kallo, sai kawai ta tab'e baki tace "Baka da wuta, baka da aljanna, ba a hannunka arzikina yake ba, dan haka baka da rayuwa ko mutuwa, banza jahili mummana kawai."
Da haka ta k'arasa gida, da sallamarta mamanta ce ta fara kllonta tace "Sai yanzu daga siyan maganin?"
Saida ta sunkuya ta mik'a mata tace "Mama da k'yar fa na tsallaka titi, kinsan dare baiyi ba sosai?"
Shigewa tayi d'aki ta cire hijabi ta haye gadon k'arfen mai rumfa da knarfi hakan yasa ya shiga d'an yin k'asa da sama da ita tana lilawa, wayar ta ciro bayan ta rage haskenta duka ta shiga chat da k'awayenta, ta wani b'angare kuma tunanin sheikh take yi, sai kawai ta tab'e baki tace "Watak'ila ma ko taimako ne zaiyi wa Abbana."
D'aga kafad'a tayi alamar ohon d'in nan, hakan yayi daidai da shigowar kira a wayarta na bak'uwar lamba, wani sharme ta saki ganin wata k'asaitacciyar lamba mai tsari da sauk'in hardacewa a kai, saida ta gyara kwancinta ta kashe murya sosai ta d'auka tayi shiru, daga wajenshi ne ya fara fad'in "Amincin Allah su tabbata a gareki *maah*."
Wani sanyayyen murmushi ta saki tayi shiru kamar ba zata amsa ba, sai kuma ta lusmhe idonta tana tsinkayo amon muryarta tana fad'in "Kai ma haka, *bak'o*."
Murmushi yayi har tana jin sautinshi kafin yace "Ba sunana bak'o ba, sunana *Ashraf Sabi'u Aliyu Sharif*, amma dai dayawa daga cikin mutane sun fi kirana da *Asas*."
Jim tayi tana sauke numfashi tana jin yanda muryarshi ke ratsata, a sanyaye ta sake maimaita "Asas?"
Da fara'a yace "Eh, amma fa ba sunan gaskiya bane, gaba d'aya sunana dana iyayena ne aka had'a akayi abr茅g茅 suka tayar da Asas, lokacin ina makaranta ne aka lak'aba min shi."
D'an murmushi tayi tace "Asas."
Murmushi yayi yace "Da alama sunan ya miki dad'i ko? To nawa zaki siya sai ki d'auka gaba d'aya na bar miki."
Murmushi tayi tace "Ban siya ba, idan na siya ai b芒 zan samu alfarmar kiranka da shi ba."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Maah, ina *sonki*, ke ma kina so na? Zaki iya bani dama na zama abokin rayuwarki."
Lumshe ido tayi ta sauke wani numfashi, haka kawai taji wata k'walla kamar yau aka fara fad'a mata kalmar nan, bud'a ido tayi ta sauke numfashi tace "Zanyi tunani a kai."
Waro idonshi yayi yana sake kallon shukokin da iska ke d'an kad'asu, kai duk yanda aka yi yarinyar nan yar sarkin abzin ce, dan wannan shan k'amshin nata da ajin abun ba'a cewa komai. Wani numfashi ya sauke yace "Maah ki taimake ni, ina sonki da zuciya ta, ina son aure sosai a rayuwata, ki amince min na zo gidanku ta yanda ba zan sha wahala ba kafin dogaren gidanku su barni shiga."
Da mamaki tace "Dogarai? Wane iri?"
Da d'an sauri yace "Oh! To ina nufin jami'an gidanku?"
Tashi tayi zaune ta gyara zamanta da kyau tana k'arewa d'akinsu kallo tace "Ni ba 'yar kowa bace, k'yalek'yale ne kawai na zamani ya haskani, mahaifina talaka ne da a kullum saiya fita yake samo mana abinda zamu ci, mahaifiyata ba 'yar kowa bace ita ma, duka iyaye na suna da wata baiwa da Allah ya hallicesu da ita, watak'ila kai ma idan ka gansu ka tuna cewa su suka haifeni zaka iya gano wannan baiwar, karatu na ba wani mai zurfi bane, a matakin bac kawai na tsaya, islamiyya ce har yanzu nake kai kuma ina ci gaba da nema har gobe, a tak'aice ni ce *Maryam Adam Shehu*."
Wani basaraken murmushi ne ya kubce mishi ba dan komai ba saidan jin dad'in yanda ta fad'a masa gaskiyar wacece ita, kai lallai ta dabance wannan, saidai wace irin baiwa ce take magana a kai? Ajiyar zuciya kawai ya sauke yace "Maah, naji dad'i sosai yanda kika fad'a min wacece ke? Na yarda dake d'ari bisa d'ari, kuma ni dama nasan bakiyi kama da wacce zata iya cutar da kowa ba, Naana ki min alfarma d'aya dan Allah?"
A hankali tace "Wace irin alfarma?"
Cikin zumud'i yace "Ki min alfarma na zo gidanku, a gaban mahaifinki zan durk'usa na nemi ya taimaka ya bani aurenki, wallahi zan kula dake Mimi, zan tallafi rayuwarki data iyayenki da dama duka yan uwanki, dan Allah na rok'eki kinji."
Shiru tayi tana sakin murmushi mai tsadar gaske, jin bata amsa ba yasa shi saurin cewa "Dan Allahhhh! Kada ki ce a'a mana mai sunan mamana, Hajiata tana da tausayi da kawaici, sannan ga ta da magana d'aya tak, dan Allah ki kasance mai irin halinta kema."
Yanda yake mata magiyar yasa ta cewa "Shikenan na ji, a karon farko na ji kaine mutum na farko daya shiga zuciyata, na amince Asas."
Da wata irin k'ara ya saki ihu a kunnenta yana fad'in "Yess! Yess! Ta amince, kai naji dad'i sosai, maah, insha'Allah gobe zan zo gidanku na ga Abbanki, idan ya amince ya bani ke saina turo mgabata na, amma fa maah ni maraya ne uwa kawai gareni, amma ina da wanda ya zame min kamar uba, sheikh."
Murmushi tayi tace "Daga gobe zamu yanke kai maraya ne ko akasin haka, idan Abba na ya amince zaka zama kana da mahaifi kai ma."
Murmushi yayi yace "Nagode da wannan karramawar Mimi, sai kin ji ni gobe."
Jinjina kai tayi tace "Saida safe."
Shi ma a nutse yace "Saida safe *beaut茅* (beauty)."
Lumshe ido tayi har taji ya datse kiran, wani farin ciki ne ya mamayeta ta shiga murna sai kawai ta kashe wayar gaba d'aya ta gyara kwancinta jin mamanta na fad'in "Amir shi ga ka ga wai Mimi tana ciki kuwa?"
Tan jin shi ya shigo ya fita yana fad'in "Mama bacci take."
"Bacci?" Ta maimaita da mamaki.
Bata sake fitowa a d'akin ba har baccin na gaskiya ya d'auketa, saida mamansu ta mik'e ta shiga d'akin ta daddab'ata, tana bud'a ido tace mata "Nan kike kwana ne?"
Saukowa tayi daga kan gadon tana murza ido tace "Mama an gama shinfid'ar ne?"
Dak'uwa ta mata tana fad'in "Ni ce zan miki shinfidar?"
Hanyar fita ta nufa cikin sumalin bacci mamanta tace "Ke zo nan?"
Dawowa tayi ta zube durk'ushe dan a tsaye take ita, da hannu ta mata alama tace "Mik'e tsaye."
Mik'ewa tayi amma duk da haka saida ta d'an rank'wafa sabida nauyi take ji sosai ta tsaya a kansu kamar zata ci tuwo a kawunansu, matsawa maman tayi ta jawo rigarta tare da zura hannunta a k'asan rigarta, a tsiyace taja baya tana fad'in "Mama?"
Wani kallo ta mata tace "Ba ki da gaskiya kenan?"
Girgiza kai tayi tace "A'a mama, ba abinda nayi fa."
Da d'an gajeran hannunta tace "To zo nan." Sunkuyawa tayi cikin dubara ta yaran zamani ta zage wayar dake k'ugunta tayi baya da ita ta b'oye, tana ji ta shiga zura hannunta a cikin rigarta saida ta kai kan mamanta, dama rigar t-shirt ce dan haka ta fizge bras d'inta da k'arfi tana fad'in "Wannan jarabar ba zaki dinga cirewa kina hutawa ba."
Tsaki tayi tare da damk'ar nononta na dama da k'arfi, cije leb'e tayi ta rintse ido tace "Washhhhhh!"
Zage hannunta tayi tana mata kallon tuhuma tace "Me yasa nonuwanki keta cika suna batsewa Mimi?"
Girgiza kai tayi tana sunkuyewa tace "Ba komai Mama."
Sama da k'asa ta kalleta tace "Kin tabbata?"
Jinjina kai tayi, k'ofa ta nuna mata alamar ta wuce, saida ta b'oye hannayenta a cikin riga kafin ta fice a d'akin, ganin har su Yaseen ba'a musu shinfid'a ba yasa ta jan tsaki tace "Yanzu nan duk sai nayi shinfid'ar nan?"
Cikin hushi ta shiga shinfid'a musu tabarmarsu da ta ta wacce suke kwana da mama, duk da wani lokacin ta kan farka a tsakiyar dare ta nemi maman ta rasa, amma kuma idan aka wayi asuba zata ganta a gefenta (馃槑 Yo mamana ina Abba yake? Caskalewa ake).
*Alhamdulillah*
06/08/2021 脿 11:51 - Mme Ishaq馃拑馃グ: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*MATAR MUTUM*
_(K'abarinsa)_
馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈�
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*'YAN AMANA TA*
Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.
Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage* da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)馃憣 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.馃グ
馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃
鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔�
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*9*
Washe gari ta tafi makaranta kuma kamar kullum ana shiga hutun minti talatin duk suka had'e wuri d'aya dan ayi hirar duniya, saida ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta kalli Jamila dake kallon IPhone d'inta tana fad'in "Wai Mimi da gaske jiya ya baki wayar nan? Kai ina ma ni ce wallahi ta birgeni sosai."
Wani malalacin murmushi tayi tace "Kinga ban fad'a miki ba, jiya fa mutuminki na had'e dashi har mukayi magana baki da baki."
Da sauri ta kalleta tace "Shapi'u?" Harara ta dalla mata tace "Mayyar Shapi'u, to uban Shapi'u."
Dariya su Asma'u suka saka duk da dai basu gama shiryawa da ita ba, turo baki Jamila tayi tace "Mimi ban son cin zarafi, surukin nawa?"
Tab'e baki tayi tace "Kinga ni sheikh na had'u dashi nake son fad'a miki."
Da farin ciki tace "Lah! Sheikh Bala?"
Cikin jin haushi tace "Ke sheikh Balan wa? Sheikh Abdul Waheed nake fad'a miki, haba."
Ta k'arashe da d'auke kanta, duk zaro ido sukayi Jamila tace "Sheikh Abdul Waheed?"
Asma'u kuma kallonta tayi tace "Mimi ban sonki da k'arya ba fa, a ina kika ganshi ke kuma?"
Hararanta tayi tace "Tunda kinsan haka me yasa zanyi muku yanzu? Da wacce nake jin tsoro a nan?"
Jamila ce tayi saurin cewa "To ina kika ganshi?"
Gyara zama tayi tace "Jiya da dare ne na je siyowa Yaseen maganin zazzab'i, kawai na ganshi zai tsallaka titi har ya min magana..."
Yanda ta fad'a musu duk abinda ya faru yasa Jamila cewa "Tabb'! Mimi sheikh Abdul waheed ne fa aka ce mai bawa gwamna shawara akan harkar ilimi, sannan an ce shi kad'ai mahaifinshi ya haifa, kuma mahaukatan bilyoyi ya gada fa, uwa uba ga ilimin addini da Allah ya bashi, a hakane zaki ce kin ganshi a kan titi har ya shiga mota ya tuk'a? Mutumin da a wa'azi ma mutum biyu ne a bayanshi."
Cikin jin haushi ta kallesu su ukun tace "Yanzu mak'aryaci kuka d'aukeni ko me? Kun dai kunsan mutumin nan ba birgeni yake ba bare na yi k'aryar had'uwa da shi, tayiwu fa kawai sun san juna da Abbana ne."
Duk wani shek'ek'e suka kalleta alamar sam zancenta bai samu karb'uwa a wajensu ba, dan haka cike da alfahari tace "Ban wayata ke na nuna miki sanfiri."
Mik'o mata wayar Jamila tayi tana sake tab'e bakinta, karb'a tayi ta shiga jerin t茅l茅phone d'inta, lambar data gani mai jan rubutu data nuna an kira ba'a d'aga b芒 ta danna wacce ta mata kama sosai data Asas wacce ta sakawa sunan *d'an beauty*. Tana jin wayar ta fara k'ara tayi saurin sakawa a amsakuwa tana nuna musu su mayar da hankali kan wayar, duk zubawa wayar ido sukayi kamar zai fito daga ciki.
Ana d'agawa ta sake nutsuwa ta