Showing 45001 words to 48000 words out of 72104 words

Chapter 16 - Jiddatul Khair Book 2 Hausa Novel Complete

kallonta da manyan idanuwansa, Umma ta hangame baki ta dinga kallon Abuturrab with shock, can ta kalli yayarta dake kallon ikon Allah tace "Yaya wai kinji yarinyar da mu ka shiga daki daxu a downstairs kika duba da jiki..." Ummi sai kallon Abuturrab take ko kiftawa babu, ya sunkuyar da kansa cikin sanyin murya yace "Ku yi hakuri Umma, i don't know d words to use in asking for forgiveness, I'm truly sorry for all this, wllh it's not intentional, Allah ne ya kaddaro min haka, amma in sha Allah nace xan saketa" Umma dake ta kallon yayarta da ta jinginar da kanta da gado ta kasa cewa komai, Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "This is serious, Abuturrab? Why?? Why Abuturrab, dama ashe kai ka haifi kanka??" Kallonta kawai yake ruefully... ta girgixa kai feeling so disappointed tace "I am disappointed at u Aliyu, ka bani mamaki" Shi dai bai iya yace komai ba, Tace "Yanxu ita Jiddar ta sani? I mean tasan da wannan auren?" Ya girgixa kai yace "Bata san komai dake faruwa ba har yanxu.... And xaki iya samunta ki tambayeta ta gaya maki duk abinda ya faru da dalilin kawota gidan nan da nayi, sannan ni a lkcn da na kawota gidan nan ba a daura auren ba wllh" Umma was totally lost of words balle kuma Ummi da sai binsu kawai take da kallo, Umma tace "Daga bakin ka nake son jin labarin abinda ya faru ba ita ba" Abuturrab ya lumshe ido ya bude babu musu ya shiga bata labarin abinda ya faru tun daga farko ita ma bai boye mata komai ba har xuwa sanda aka daura masa aure da Jiddah, da tafin hannunsa ya rufe fuskarsa cikin breaking voice yace "Plss Umma ku daina ganin laifina, i only tried to help ne ban san haka abun xai kasance daga karshe ba, kice Ummi tayi hakuri ta yafe min wllh xan saketa na dau ma kaina wannan alkawarin, ban yi hakan don in bakanta maku ba Umma..." Umma ta rasa abinda xata ce tausayinsa ya cikata, cikin sanyin murya Ummi tace "Aa ni baka min komai ba, Allah ubangiji ya sa mu dace" Umma ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ta na kallonsa tace "Tashi kaje Abuturrab" Mikewa yayi ya juya ya fita dakin Ahmad ya bi bayansa, Umma na kallon Yayarta tace "Kiji wani babban lamari na ubangiji yaya, yanxu ke me kike ga xa ayi kan lamarin? What next?" Ummi ta sauke ajiyar xuciya a fili tace "Ban san me xance ba Ramlah" Bayan la'asar Abuturrab na fitowa masallaci tare da Ahmad, Ahmad yace "Ka shiga ka duba yarinyar nan pls, she was very sick yesterday night fa" Captain na kallonsa yace "Me dubata da rashin dubata xai kara mana ni da kai pls? Kai dai ba kana dubata ba me yasa xaka damu ni sai na dubata" Ahmad bai kulasa ba ya tsaya gaisawa da wani frnd dinsa a kofar gidan, Abuturrab ya shiga compound din walking slowly, babu kowa parlon ya kalli dakin da yaga Ahmad ya fito daxu da ya xo, kamar xai wuce sai kuma ya nufi dakin ya bude kofar a hankali ya shiga ya kulle sannan ya juyo yana kallonta, tana kwance saman gadon dakin drip a hannunta jin budewan kofa ya sa ta bude ido, ganinsa ta mike xaune da sauri, kana ganinta kasan she is very sick don har ta rame, lebbenta yayi ja, ya kalli drip din da har yayi rabi, da kyar tace "Ina yini" Bai yarda ya kalleta ba idonsa na kan drip din cikin calm voice dinsa yace "Ya jikin?" A hankali tace "Da sauki" Bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds ya d'an saci kallonta suka hada ido, da sauri ta sauke idonta, ya d'an hade rai, bude kofar dakin aka yi ya juya da sauri, Ummi da Umma ne bakin kofar, he wish hakan bai faru ba, ya ji kamar kasa ya bude ya shige kawai ya huta, kasa kallonsu yayi, Ummi dai sai kallonsa take ta karasa cikin dakin tare da kanwarta, Jiddah ta sunkuyar da kanta don sun gaisa daxu, Umma na kallonta tace "Ya jikin?" Tana jan fingers dinta tace "Da sauki Umma" Ummi dai sai kallon Jiddah take, Juyawa Abuturrab yyi xai fita amma ya kasa ce ma Umma ta basa hanya ita kuma ta ki basa hanyar, Ummi tace "Sannu Allah yakara lafiya" Jiddah na kallonta tace "Ameen" Umma tace "Kin sha shayin kuwa daxu?" Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace "Toh Allah ya sauwake" Daga haka ta kalli Captain tace "Meet me before leaving...." Shi dai bai dago kansa ba, Tana fadin haka ta fita Ummi ta bi bayanta, sai a sannan Abuturrab ya daga kai ya bi su da kallo, Umma ta kulle kofan, still yayi bakin kofar, can ya d'an kalli Jiddah, kallonsa take ita ma, suna hada ido tayi light smile tace "Kun yi kama da warce ke kusa da Umma" ya hade rai ya juya ya bude kofan ya fice ya kulle. Sai da Abuturrab ya tabbatar Umminsa ta bar gidan sannan ya koma dakin Umma, Kallonsa take xai xauna kasa ta nuna masa kujera ya mike ya koma saman kujeran tana kallonsa, cikin sanyin murya yace "Gani Umma" Tace "Tell me now son, what do u have in mind a kan wannan auren da kaje kayi ma kanka?" Ya girgixa kai yace "Taimakonta kawai nake son yi ba wani abu ba, but ban san things will turn out this way ba da ban fara ba..." Umma tace "So what's ur next plan now?" Ya shafa kansa yace "Umma sakinta xanyi, since yanxu kun san abinda ya faru sai ta xauna nan ko kuma wajen Ummi, i know Ummi won't say no" Umma dai kallonsa kawai take, can tace "Toh kilan hakan kadai ne mafita gareka, amma can su iyayen nata da suka baka aurenta fa?" Ya girgixa kai yace "Ba mutanen kwarai bane, ko da xata xauna da ke ko Ummi to babu ita babu su, ita din marainiya ce, she is staying with just her Stepmum, tace min iyayenta sun rasu, I don't know of relatives amma da da akwai baxa su bari tana wahalan da take ba a gun Kishiyar Baabarta, beside that baxa su bari a aura mata shi wanda aka yi niyyar aura mata da farko ba, don duk anguwar babu wanda bai san tout bane shi, amma sbda yana ba ita stepmom din nata abun duniya wanda bai kai ya kawo ba shine take son aura mata shi, sannan tana da 'ya ita ma sa'arta fa" Umma dake ta sauraronsa ta girgixa kai cike da tausayin Jiddah tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...." Yayi kasa da murya yace "Ita ce me yin awaran da muke siyo maki a hayi, Ahmad yasanta... But bai ta6a sanin ina xuwa gunta a can hayin ba har sai da wannan abun ya faru" Umma ta buda ido tace "Ikon Allah, Allah sarki rayuwa, yanxu abinda nake so da kai shine you talk to her about all what happened tunda kace bata sani ba, ka sanar mata komai" Da sauri Abuturrab ya kalleta, ta gyada masa kai tace "Yes she needs to know kafin ma kayi sakin da kake cewa, after that kuma idan nan din xata xauna to, in kuma gun Yaya xata xauna shkkn" a hankali Abuturrab yace "Toh shkkn Umma, nagode" Umma tace "Amma ba yau xaka sanar mata ba tunda bata da lafiya, gobe ka xo we are hoping she will get much better sai kayi mata bayanin komai" Abuturrab yace "In sha Allah Umma" Tace "Maa sha Allah, you can go, Allah yayi maka albarka" Yace "Ameen" mikewa yayi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya, tun bayan faruwan wannan lamarin sai yanxu ya ji magana da ya sa masa relieve a xuciya, he is happy Umminsa bata dauki wannan batun personal ba, just like his dad and small mum, but Aunty, wani sigh yayi yana tunanin yanda xasu yi da ita idan ya koma gida anjima....


The book Jiddatul Khair is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah.... And u show ur evidence of payment via 07087865788... Do justice to ur self by subscribing before reading...





*mg's skincare*

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀️

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee


Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166
Ko da Abuturrab ya koma gida bai bari stepmom dinsa ta san ya dawo ba don bai ma dawo da motarsa ba a gidansu Ahmad ya barsa, Ahmad yayi dropping dinsa kofar gida a nasa motar ya koma, yana shiga bedroom dinsa ya sa makulli hade da sauke ajiyar xuciya, wanka yayi ya sauya xuwa pajamas dinsa ya xauna gefen gado, yana son shan shayi but baya son fita duk da ko ya fita din kanninsa xai saka still, wayarsa ya jawo ya shiga dialing number din Ramlah, tana dagawa yace "Make me a cup of tea, an omelette with just two eggs" Bai jira cewarta ba ya katse wayan, ba a dau lkci ba Ramlah tayi knocking bakin kofar dakinsa, ya mike ya isa kofan ya bude ya bata hanya ta shigo, ajiye plate din hannunta na kwai dake rufe tayi da cup din shayin tana kallonsa tace "Yaya...." yace "Goodnight Ramlah" Shiru tayi sai kuma ta juya ta nufi kofa kafin ta fita yace "Thank you" Ta sake juyowa ta kallesa ta marairaice tace "Amma yaya me yasa....." Hade rai yayi yace "Fita!!" Fita tayi ta kulle masa kofar ya karasa ya sa key. Washegari Friday Abuturrab na dawowa masallaci da asuba ya shiga bangaren Umminsa, da da ne bangaren stepmom dinsa xai fara shiga, kansa a kasa ya gaida Ummi ta amsa, a hankali ya soma bata hakuri, tace "It's okay, ae kun gama magana da Hajiya Ramlah ko?" Ya gyada mata kai tace "Toh maa sha Allah" Yace "Amma Ummi don Allah kiyi ma Abba magana naji yana cewa baxan saketa ba..." Ummi tace "I don't know... But seriously he is not to decide that for you, you just ignore him" Abuturrab bai ce komai ba, can yace "Toh shkkn Ummi" mikewa yayi ya fita dakin ya koma nasa, a masallaci ma dodging din mahaifin nasa ya dinga yi har ya shigo gida basu hadu ba. As early as 10 Abuturrab ya bar gidan ya tafi gidansu Ahmad, bayan ya gaisa da Umma dake parlor ya tafi dakin Ahmad, Ahmad na shiryawa ya samesa, Ahmad na murmushi yace "Welcome latest ango" Abuturrab yayi still ya dinga masa wani kallo, Dariya Ahmad yayi yace "Yanxu dai cikin ruwan sanyin kullum sai ka xo gidan nan ko?" Abuturrab bai tanka sa ba ya tafi ya xauna, Ahmad ya gama shiryawa yace "She's getting better, jikin da sauki yau sosai" Nan ma Abuturrab ya sharesa, bai san shi abinda ya kawosa daban ba, Mikewa kawai yayi ya fita daki hoping Umma ta bar parlon yanxu, Ahmad ya bi sa da kallo yana murmushi, luckily ya tadda babu kowa a parlor ya karasa dakin da Jiddah take ya bude hade da sallama murya can ciki, tana xaune saman gado da wani drip din a hannunta ga pepper soup da Umma ta sa ayi mata, Huraira da Maman Abdallah ne dakin suna ta hira, ita dai sai dai tayi murmushi, ganin Abuturrab duk suka gaishesa, bai san suna ciki ba da baxai fara shigowa directly ba, ya amsa without looking at them, Jiddah ta kallesa tace "Ina yini?" Ita ma bai kalleta ba yace "Lafiya" Ahmad ne ya karaso dakin ya shiga ciki yana kallon jiddah yace "Alhmdlh jiki yayi kyau sosai ko Ummi?" Ta d'an yi murmushi amma bata ce komai ba, shi dai Abuturrab na tsaye, Ahmad ya kalli su Huraira da basu da niyyar fita a tunaninsu kawai dubata suka shigowa yi, yana murmushi yace "Maman Abdallah da Aunty Huraira a bamu waje mu duba patient pls" Duk suka mike, Huraira tace "Toh bari mu fita" Bayan sun fita dakin Abuturrab ya karasa gun window ya tsaya Ahmad dai sai kallonsa yake, Can yayi murmushi ya kalli Jiddah yace "Kin sha maganin ai ko?" Ta gyada masa kai tace "Eh" yace "Toh Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen" Ya juya yace "Bari in kawo maki na karshen.." Daga haka ya juya ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita ya kulle kofar, sunkuyar da kanta tayi, Abuturrab ya d'an kalleta, he don't even know where to start from, hada ido suka yi ya rungume hannunsa yace "Ya jikin?" Tace "Naji sauki" Ya d'an yi jim kafin yace "Iyayenki sun daura maki aure..." Da sauri Jiddah ta daga kai ta kallesa, yaki yarda su hada ido ya ci gaba yace "Amma ba da mutumin nan ba" Kallonsa kawai Jiddah take ko kiftawa babu, ya shafa kansa yace "Amma shi wanda aka daura maki auren da shi xai sake ki, sai ki ci gaba da xama a nan wajen Umma ko gidanmu wajen Ummina, amma fa sai kin amince babu ke babu Baabar nan taku don ba sonki take ba, kuma baxata ta6a sonki ba, neman kudi take da ke" Cikin sanyin murya Jiddah tace "Toh da wa aka daura min auren??" Yace "Fada maki ba amfani xai yi gareki ba, kawai dai abinda na sani xai sake ki, sai kiyi xaman ki a nan ko kuma ki xauna gidanmu, ki fara karatu islamiyya da boko, kinsan wacece ke, kinsan daga inda kike, kawai na shiga rayuwarki ne ba don komai ba sai don in taimakeki in samar maki yan cin ki, idan ba don haka ba, ni bana shiga abinda bai shafeni ba...." Kallonsa kawai Jiddah dai take a sanyaye, lkci daya hawaye ya kawo idonta, a hankali tace "Jiya Umma da daddare ta shigo ta tambayeni in gaya mata gaskiyan wacece ni, kuma ya aka yi na xo gidan nan" Cikin rawar murya ta ci gaba tace "Ni kuma baxan iya mata karya ba" Abuturrab na kallonta yace "Kin dai gaya mata ko?" Ta gyada masa kai yace "Good, xuwa gobe duk inda kika ce xa ki xauna nan xa a kai ki, ko gidanmu ko nan" A hankali tace "Toh idan na xauna nan xaka dinga xuwa?" Kallonta yake da kyau, ya hade girar sama da ta kasa yace "In xo in yi maki me??" Kasa cewa komai tayi tana wasa da fingers dinta, yace "Ae ba lallai ki gan ni ba, ki ma daina min kallon sani daga yanxu, ki kama Umma da su Siyama ki rike sosai, they will like you, ni ba lallai a shekara ma kike ganina ba" Kai kawai ta gyada masa hawaye cike idonta, yace "Sai ki tsaya kiyi karatu da kyau domin al'umma da wa enda suke tare dake suyi alfahari dake..." Nan ma ta gyada masa kai kawai, yace "Allah ya kara lafiya" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita dakin, hawayen da bata san dalilinsa ba ya dinga sauka idonta, Abuturrab ya amshi medical report dinsa wajen Ahmad kawai ya bar gidan coz baya tunanin har ya koma aiki da akwai abinda xai sake dawo da shi gidan, he now felt relieved, yaji baya tare da duk wani damuwa. Da yammacin ranan Abuturrab dake bedroom dinsa ya dau wayarsa dake ring, ganin number Abbansa yaji gabansa ya fadi sosai, dagawa yayi ya kai kunne hade da sallama, Daga daya bangaren Abba yace "Ka sameni parlona ynxu" Kafin yace komai Abba ya katse kiran, lumshe ido yayi ya bude, bayan few minutes ya mike a hankali still holding to his phone ya nufi kofa ya fita, a main parlor suka ci karo da Aunty, yayi kasa da kai yace "Ina yini Aunty" Ko kallonsa bata yi ba balle ta amsa shi tayi wucewarta, ya bi ta da kallon gefen ido sannan ya ci gaba da tafiya xuwa parlon Abbansa cikin sanyin jiki, a hankali yayi sallama sannan ya shiga, sosai gabansa ya fadi ganin Abbansa da brothers dinsa biyu, a sanyaye ya karasa shiga cikin parlon ya xauna kasa sannan ya gaishesu, uncles din nasa suka amsa, ya kalli Abba amma bai ce komai ba, Alhaji Lawal yayan Abbansa ne yace "Mun ji abinda ke faruwa Aliyu, ko kuma ince mun ji abinda ya faru" kasa cewa komai Abuturrab yayi, Alhaji Ibrahim kanin Abbansa yace "What u did is something very good but ba ta yanda ya kamata kayi ba kayi, kada ka manta ba kai ka haifi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login