Showing 60001 words to 63000 words out of 72104 words
Chapter 21 - Jiddatul Khair Book 2 Hausa Novel Complete
it's not advisable to leave her all alone a gidan nan, she is too young for that, beside bata saba xama ita kadai ba" Trying all he xan to convince her yace "Umma xafa ta iya xama wllh, u shouldn't worry pls..." Umma tace "Toh amma is there anything wrong idan ka dawo da ita nan din, idan ka dawo weekend ba sai ka xo ka dauketa ba" Yace "Umma makaranta fa xata fara soon, plss u need not to worry" A hankali Umma tace "Toh shkkn wai dama don in dinga nuna mata wasu abubuwan ne, yasa nayi insisting" Ya girgixa kai yace "Ai bata da wani lkcn Umma, xata fara boko sannan islamiyya" Umma tace "Toh shkkn" ya d'an sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Toh sai kin xo Umma" Tace "Kai xan ba Maimuna sakon kawai ta kawo, next week din xan shigo in sha Allah" Yace "Umma me yasa kika fasa kuma, ko fushi kika yi" Tace "Not at all, let me leave it next week kawai" A hankali yace "Toh shkkn Umma" Sallama tayi masa ta katse wayar tana mamakin irin taurin kan Abuturrab, wanda tasan da Aunty ce tayi masa wannan maganan baxai mata musu ba xai yi yanda tace, girgixa kai kawai tayi don kwata kwata bata ji dadin haka ba, Abuturrab ya sauke wani ajiyar xuciyar ya ajiye wayar. Bayan la'asar ya gama shirinsa don driving xai yi xuwa kanon, komai da yasan ya kamata jiddah ta sani ko ta iya amfani da shi a gidan sai da ya tabbatar ya nuna mata a gidan nan, abinda ya kara bata masa lkci kenan, xaune yake parlor waiting for Maimuna don baya son sai ya tafi ta xo, tana ring din bell ya mike ya bude kofar, gaishesa tayi da fara'a, ya amsa yace "Ya gida" Tace "Alhmdlh yaya, ina Aunty Amarya" Babu yabo bbu fallasa ya amshi ledan hannunta, sannan ya ciro dubu daya ya mika mata yace "Ki yi transport" tace "Tare da driver muke" Yace "Ohk" dubu daya ya kara xarowa aljihunsa ya hada ya mika mata yace "Ki saka kati" Tana murmushi tace "Aa ka bari nagode yaya" Ya hade rai yace "Amsa ki tafi" Amsa tayi yace "Sai anjima" Tayi masa godiya sannan ta juya a hankali, amma duk jikinta yyi sanyi don bai bari ta ga Jiddah ba, ya kulle kofar, kujera ya koma ya xauna yana duba abinda ta kawo, turarrukan wuta ne a kwalbansu kusan kala hudu sai burner, da wasu turarrukan na jiki, tabe baki yyi ya mike ya wuce sama, dakin jiddah ya bude ya ganta xaune duk ta dawo wani iri, tana ganinsa ta sauke kanta kasa, ya ajiye ledan yace "Umma ta bada a kawo maki" ta bi sa da kallo har ya jona burner din a socket, sannan ya bude turaren wutan guda daya ya diba ya xuba yana kallonta, bayan d'an lkci kamshi ya fara tashi, yace "Safe da yamma xaki tabbatar kin ma dakinki da parlor haka" Ta gyada masa kai kawai, waya karama ya ciro aljihunsa yana kallonta ya mika mata, ta mike ta isa inda yake ta risina ta amsa, yana kallonta yace "Number da xaki dinga samuna ne kadai a ciki, sai ki koyi yanda xaki yi amfani da shi ke kadai" cikin sanyin murya tace "Toh" Yace "Sannan ba ace ki xauna ke daya kiyi wani shiru kamar me xaman makoki ba, ga kayan kallo duk na koya maki yanda xaki kunna" Ta sunkuyar da kanta, kofa ya nufa yace "Na tafi" Ta kallesa da sauri tace "Ina xaka je" Yace "Garin da nake aiki" bude kofar yyi ta bi sa da ido, sai da taga ya fita kafin ya kulle kofar cikin sanyin murya tace "Allah ya tsare" Ya amsa da Ameen a takaice, da sauri tace "Yaushe xaka dawo?" Yana kallonta yace "Wannan bai shafeki ba, ko da wani abu da xaki bukata bayan duk wanda na maki??" Daga haka ya kulle kofar hawayen dake makale idonta ya silalo a hankali, ta fi minti goma tsaye yanda ya bar ta, jin an tada mota ta kalli window da sauri sannan ta karasa window din ta d'an bude labule tana lekan waje, tana ganinsa ya fita da motar, a hankali ta fara kuka ta xauna nan kasa, sai kuma ta fashe da kuka kamar ana dada tunxurata, Abuturrab ya sauka motar yana kallon gate din gidan, he just dont have any option then to close the gate from outside, don bai ma son ya gwada mata yanda ake kullewa daga ciki balle ya sa ta kulle ta ciki, yasan probably kafin ya dawo weekend an samar masa mai gadi kamar yanda yayi requesting ayi, ya kulle gidan ya koma ya shiga motarsa yana karasa addu'o'in da yake yi tun daga compound a ransa ya bar layin.....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Do justice to ur self by subscribing before reading
Thank you
Jiddah ce tsaye kitchen bayan magrib tana ta kallon kayan abincin dake cikin store, yunwa take ji tun daxu amma bata san me xata girka ta ci ba, gashi tsoron gas din take, don yace mata yana kona mutane idan ba a maida hankali wajen amfani da shi ba, a hankali ta bude fridge tana kallon ciki, lemo ne a ciki da ruwan gora, sai apples, grapes, banana da dai wasu fruits din a ciki, a hankali ta rufe ta bude deep freezer, taga naman cow, kayan ciki, kifi, da naman kaza, a hankali ta rufe shima, kwalin indomie da ya riga ya bude mata ta nufa ta dau daya a ciki, ta bi tukwanen dake ajiye da kallo snn ta dau wani karami, da kyar ta iya kunna gas din tana ja da baya don duk a tsorace take, ganin wutan ya dawo kamar na risho da take gani gidan iyah yasa ta daura tukunyar, tun da take idan banda icce da gawayi bata ta6a girki a kan wani abu ba, ba ita ta bar kitchen din ba sai ana isha a masallaci, ta cika ma indomien uban ruwa sai swimming yake a plate din, da kyar dai ta tuttura ta cinye indomien da bai mata dadi ba a baki don ita bata ta6a ci ba ma, tura plate din tayi hawaye ya kawo idonta don kewar tuwon masara take da miyar kuka, cimar da ta saba da kenan iya rayuwarta, don ko shinkafa kwana biyun nan da take ci duk taji ya isheta. Abuturrab na kwance hotel room da ya saba sauka, dawowarsa kenan daga eatry yaje ya ci abinci, vid call suke yi da Aneesah wanda har yanxu bata san abinda ke faruwa ba, bai yi mamakin da har lkcn Aunty bata sanar ma kowa ba, tunda ita bata yarda da auren ba dama from start, Aneesah na kwance saman gado daga ita sai wata yar rigar bacci, komai na jikinta na waje, ganin yanda Abuturrab ke lumshe ido tace "Kar kace min har ka fara jin bacci My captain" Ya bude idon yana kallonta yace "Sure, i will be piloting 8am flight tomorrow in sha Allah" Ta marairaice tace "Wllh ban gaji da jin muryarka ba mine" a hankali yace "Yi hakuri, early to bed early to rise..." Tace "Toh shkkn sweetheart, sleep tight, and dream of me" Ya kashe mata ido sannan ya katse wayar, har ya ajiye ya juya baya hade da lumshe ido sai kuma ya bude idon a hankali ya jawo wayar, dialing number yyi ya sa handsfree yana kallon screen din, Jiddah ta kwanta kenan ta takure waje daya tsoro duk ya cikata, da ta tuna ita kadai ce gidan sai hankalinta yyi mugun tashi, ko wutan dakin ma taki kashewa kamar yanda yyi instructing dinta, sai taji kamar abu na motsi a dakin, ring din wayar dake gaban madubi yasa ta mike a mugun firgice tace "Wayyoo Allah na, nq shiga uku" Sosai jikinta ya dinga rawa tana kallon wayar, sai kuma ta nufi gaban madubin ta dau wayar tana kallo, button din left side din ta danna, tunda iyah na da waya kuma ita ke daga mata ma idan ana kiranta, Shiru Abuturrab yyi yana kallon wayar tasa bayan yaga ta dauka, can jin bata ce komai ba yace "Kin ci abincin ko ba ki ci ba?" Ta sauke idonta kasa a hankali tace "Na ci" Bai ta6a xaton xata yi magana da irin wannan natsuwar a waya ba, can yace "Me kika ci?" Tace "Taliyar indomie" Yace "Ohk.... Sai da safe" Da sauri tace "Ka kai lafiya?" Yace "Eh" kamar xata yi kuka tace "Amma ni tsoro nake ji wllh" yace "Tsoron me?" Ta fashe masa da kuka kamar jira take tace "Ni kadae fa a gidan, gashi sae inyi ta jin motsi" Ya gyara kwanciyarsa, calmly yace "Ehh dodon da na ba ajiyar ki ne ke motsi, ko kar yayi??" Ta wani gwalo ido tana bin dakin da kallo tana sake maimaita abinda yace a ranta, ko ina na jikinta ya dau 6ari a lkcn, cikin rawar murya tace "Dodo fa kace?" Yace "Ehh ko dai ya bari kin gansa ne?" Wani ihu ta kwala da ya sa shi mikewa xaune da sauri, ta rushe da wani kuka tana salati, da sauri yace "Ke wasa fa nake maki" ko sauraronsa bata yi ba ta cika masa kunne da kuka, tsayar da kukan tayi ganin duhu ya gauraye ko ina na dakin, da ta dage ta kara kwala wani ihun sae da Abuturrab ya mike tsaye, cikin bargo ta shige har sannan wayar na hannunta tana rusa kuka, Abuturrab ya dinga cewa "ki tsaya ki saurareni nace maki wasa nake, i am only joking" ko ina na jikinta na rawa cikin tashin hankali tace "Wllh ya kashe wutan gidan, na shiga uku na, don Allah ka xo ka taimake ni, xan iya mutuwa ni kadai" Komawa Abuturrab yyi ya xauna jin tace ba wuta, gaba daya ya mance ya gwada mata yanda xata dinga kunna solar idan an dauke wuta, yayi kasa da murya yace "Ki saurareni nace, ni wasa nake maki, wa yace maki akwai dodo a duniyar nan, ke baki san wasa ba? babu komai fa wuta kawai suka dauke, ko ba a dauke wuta a Hayin ku??" kuka kawai take tana shessheka tace "Don girman Allah ka dawo ka fitar dani a gidan, ni wllh baxan iya kwana ni kadai ba, Allah baxan iya ba" Hade rai yyi sai dai bai ce komai ba, jin yanda take rera kuka da karfi, yyi kasa da murya yace "Kinsan inda nake da kike cewa in dawo ynxu" Taki ce masa komai sai kuka, cikin kwantar da hankali yace "Wllh babu komai kawai zolayarki nake yi, amma tunda kina tsoro shkkn baxan kashe wayar ba har gari ya waye, idan da wani abu sai ki min magana, kina ina yanxu?" Tana shessheka a hankali tace "Ina kan gado" Yace "Toh kwanta" Ta gyada masa kai tace "Na kwanta" Yace "To kulle idonki" Cikin rawar murya tace "A kulle yake ai" Yace "Toh fara bacci" Yana jin yanda take kuka a hankali, ya lumshe ido ya bude, can yace "In kashe wayata ne?" Da sauri ta bude ido ta girgixa masa kai tace "Aa don Allah" Yace "Toh daina kukan nan" a hankali tace "Na daina" Yace "Kiyi baccin ki, ni karatu xan yi..." tayi shiru bata ce komai ba tana sauke ajiyar xuciya, jingina yyi jikin pillow ya fara karantun Al-qur'ani cikin cool and calm voice dinsa, tun jiddah na jin sa har bacci ya dauketa, ya kai ayar karshe a suran da yake karantawa, shiru yyi.... bayan few seconds murya can kasa yace "Jeedderh" jin shiru ya kara tabbatar da tayi bacci, a hankali ya katse wayar ya sauke ajiyar xuciya sannan ya kwanta yana karanto addu'a.... Kiran Sallan asuba ya farkar da Jiddah, ta mike xaune da sauri tana bin dakin da kallo da hasken fitilun ciki ya haska tarrr, kallon wayar dake kusa da ita tayi ta dauka ta danna tana kallon screen din, a hankali ta mayar ta ajiye sannan ta mike, kamar me tsoron tiles din dakin ta sauke kafarta sannan ta mike tsaye, dodon da yace mata ne ya dameta a rai, amma kuma yace wasa yake, cikin sanda ta nufi bandaki ko rufewa bata yi ba tana leko dakin ko xata ga abu me kama da dodo... Karfe tara da yan mintuna Abuturrab na lagos bayan sun sauka kiran Ahmad ya shigo wayarsa, kallon screen din ya dinga yi kafin ya dauka daga karshe, Ahmad yace "What nonsense Aliyu, ni na turaka hayi kayi ma kanka aure da xan dinga kiranka ka ki dauka all this while?" Abuturrab yace "Ka kirani ne ka ci xarafina daga inda ka tsaya?" Ahmad yace "Abinda ya fi xarafi... Ance maka farin ciki nayi da auren nan naka Captain, ae ko a mafarki ban ta6a tunanin xaka riga ni aure ba, which means xaka riga ni fara ajiye iyali, may be next year warhaka duk muna gidanka suna, to kaga kuwa ae ni ba haka na so ba, tunda ni aka fara sa ma rana" rasa abinda xai ce masa Abuturrab yyi sae bin mutanen cikin eatry da yake xaune yake da kallo, har ransa yaji xafin abinda Ahmad ke gaya masa, gashi ya ma rasa amsan da xai basa, Ahmad da tsaf ya san ya kular da abokin nasa, ya dinga dariya kasa kasa kafin yace "Toh ya Amarya me sunan Umminmu, ka dai min bakin cikin xuwa ganinta a gidanka kafin in koma aiki, hope a hankali dai ake cin amarcin??" Abuturrab ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya cire wayar a kunnensa ya yi tapping button din katse kira sannan ya jefar da wayar kan table din gabansa, ya jingina da kujera xuciyarsa na ci gaba da tafarfasa, haske wayan ya sake yi ganin El-Basheer ke kiransa ya dinga kallon wayar bbu ko kiftawa, har ya katse bai yi attempting din dagawa ba, he knows the news of his marriage has circulate, but what's d essence, auren da babu yanxu.... Mikewa yyi daga bisanni ya dau wayar da ruwan gora ko breakfast din bai cinye ba ya fita eatry din back to airport. Yana Abuja that same day da rana, which in few hours xa su yi piloting xuwa port Harcourt, kasa daurewa yyi ganin da sauran lkci sannan Co-pilots dinsa suna preflight preparations kawai ya fita xuwa hospital din da Ahmad ke aiki, many patients ne xaune reception din hospital din, ya nufi gun wata nurse bayan sun gaisa yace "Dr Ahmad na nan?" Tace "Eh, do u have any appointment with him sir?" Abuturrab yace "Yea ynxu muka yi waya..." Daga haka ya nufi hanyar office dinsa, nurse din ta bi sa da kallo, can tace "But he is attending to a patient" ko juyowa bai yi ba har ya isa kofar office din ya murda, Ahmad na xaune attending to his patient, ya daga kai, ganin Abuturrab ya bude ido, Abuturrab bai ce komai ba ya nemi kujera ya xauna, murmushi kawai Ahmad ke yi har ya sallami patient din ya fita, sannan ya kalli direction din da Abuturrab ke xaune, smiling broadly yace "Latest ango in town" mikewa Abuturrab yyi yana kallonsa yace "In ur life Ahmad.... I mean in ur life don't ever abuse me the way u did earlier today, i felt really bad at that" Ahmad ya masa Wani kallo kafin ya fara dariya irin wanda ke kufular da mutum yace "Toh Alhaji Ibrahim, ae da ka xo da bulala koh?" a fusace Abuturrab yace "You caused me all this mess sannan ka fi kowa yi min dariya?? Who does that Ahmad?" Ahmad ya buda baki hade da xaro ido yace "Ta yaya na janyo maka?" Abuturrab na huci yace "Ohk, i will tell u now, ka xata da baka fara kai ni gun yarinyar nan ba da akwai wani abun da xai hadani da ita balle taimakona ya dawo min sharri?" Ahmad yace "Da na kai ka gun yarinyar sai nace ka xaga ka bi ta baya ka dinga xuwa wajenta ba tare da na sani ba? Ina ce ranan har Umar sai da yace yana ganinka a unguwar Hayi ka mu sa don kada ma in dago komai" Dariya sosai Ahmad yyi har da gyara xama yace "Gaskiya na dade banga me abun dariya irin ka ba Captain, da naje siyan awara sai nace ka dinga xagayawa kana xuwa gun me awara?? just take a look at the distance daga cikin gari xuwa Hayin rigasa amma haka kullum kake jan motar kaje shine xaka xo nan yanxu kayi wani blaming dina, ni da ma aka munafurta ana ta xuwa tadi ta baya ban sani ba, ban ji haushi ba sai kai?" Kallonsa kawai Abuturrab ke ta yi yana jin kamar ya shakosa, Ahmad ya sake wani shegen dariya har da buga table yace "Toh ai dai yanxu ka rigani sanin aure hankalinka ya kwanta, mu ma Allah ya nuna mana namu da wuri wuri haka..." Komawa Abuturrab yayi ya xauna xuciyarsa na mugun tafarfasa, Ahmad sai satan kallonsa yake yana yar dariya, Calmly Abuturrab yace "Dama Aunty na yawan tagging taimako da xama sharri a rayuwar nan, and i have seen that clearly now don ya faru a kaina, assuming i ignore and act as if i didn't see anything da duk hakan bai faru da ni ba, kuma am making this vow today.. ni Aliyu duk inda na ga wani na neman taimako idan ya wuce na kudi, shi ma kudin sai nayi naxari me xurfi a kai, to wllh wllh i will never ever render that help" Ahmad yace "Calm down man, wannan taimakon fa bai xame maka wani sharri ba illa ma lada me yawa da ka kwasan ma kanka idan Allah ya yrda, da ma nine na kwashi wannan ladan wllh, i cant imagine how happy i will be, sannan sharrin dake ciki a