Showing 36001 words to 39000 words out of 72104 words
Chapter 13 - Jiddatul Khair Book 2 Hausa Novel Complete
wllh xai aika abinda ya fada, kwakwalwarsa ya ta6u da dadewa mu kuma bamu da halin kai sa ko ina a dubasa, har cewa aka yi mu kai sa dawanau a kano to ina kudin?" Wani mutumi a wajen yace "Alhmdlh abinda xan fada kenan ka riga ni Malam kabiru, gwara kawai a aura mata wani tunda uwar ma tace ba ji take ba yarinyar, kun ga tana dawowa sai a kai ta dakinta kawai..." Abuturrab yace "Akwai wani yaro na, ina son nema masa aurenta yanxu" Kallonsa duk suka yi, Mai Anguwa yace "Toh in dai kasan halinsa ina ga wannan ba matsala bace amma kafin nan ya kamata ka gabatar mana da kanka..." Abuturrab ya shafa kansa a hankali yace "Ni sunana Aliyu Usman Umar... An haifeni nan cikin garin kaduna, ni matukin jirgin sama ne" Sake baki duk suka yi suna kallonsa kamar ranan suka ta6a ganin me tukin jirgin sama, yace "Gidan iyayena na nan Malali..." Mai Anguwa yace "Maa sha Allah Aliyu, to amma a ina kasan ita wannan yarinya da ake magana a kai?" Hansai ta amshe tace "Wllh daga siyan awara muka sa6a da shi, customer na ne shi da dadewa, da motarsa yake xuwa yyi parking ya siya har na dubu biyar dubu goma yana siya, toh shine jin rasuwar mai gidana sai ya kawo mana kudi dubi hamsin dubu dari, ta haka muka saba muna mutunci sosai da shi" Mai Anguwa yace "Ikon Allah" Abuturrab dai bai ce komai ba, Mai Anguwa yace "Toh amma shi wannan yaron da kake son hada yarinyar da shi wanene, sannan a ina yake?" Abuturrab yace "A kano yake, yana aikace aikace ne a airport din kano..." Hansai tace "Shi ma jirgin yake tukawa?" Ya girgixa kai yace "Aa..." Wani datijo dake xaune wajen da baxai wuce shekara sittin da takwas ba yayi gyaran murya yana taunan goransa yace "Amma fa wata kusan ya fi wata kusan nake ji ai... Tunda haka ne ni yanxu xan bada sadaki sai a daura min aure da ita wannan yarinyar...." Da mamaki Abuturrab ke kallonsa, can ya girgixa kai yace "Haba Baba ai addininmu ma bai ce haka ba, da taxara sosai tsakaninku da yarinyar nan...." Dattijon ya hade rai ya katse sa yace "Toh kai idan taimako kake son yi ka aureta mana kai da babu taxara me yawa tsakanin ku, shi fa wannan yaron da kake son hadata da shi nasan ba kowa bane d'an goge gogen iyapot ne, ni kuwa kowa yasan babu rashin ci babu rashin sha a gidana, matana uku ko wacce kuma tana da yara shidda shidda, shi me anguwan ai yasan wanene ni, auren yarinyar nan da xan yi tamkar jihadi xanyi don ance bin maza take" Kallonsa kawai Abuturrab ke yi with disgust, Dattijon ya ja tsaki yana ci gaba da taunan goronsa da jajayen hakoransa yace "Idan tsakani da Allah ne kai ka aureta mana yaro xaka wani kawo ma mutane fi'ili a nan, kaga mai anguwa a yanke min sadaki yanxu in bada a wuce wajen dama ina da niyyar auren kwanan nan" Yana fadin haka ya fiddo yan dari biyar biyar a aljihunsa, lokaci daya tunanin Abuturrab ya kwance, Hansai ganin 'yan dari biyar biyar tana d'an kame kame tace "Ai wllh tamkar taimako xaka yi Alhaji, wannan babban taimako ne, ni kaina da na haifeta bana shaidarta, kawai dai Allah ya shirya mana xuri'a" Alhajin ya murmusa yace "Babu komai ai tamkar jihadi xan yi, Ni mai anguwa ne waliyi na, ita kuma sai a samu wani...." Abuturrab ya rufe ido ya bude, yaji kansa ya fara juya masa ya dinga kallon tsohon nan da ya fara kirga kudin da ya ciro, rasa tunanin da xai yi yayi, he was totally lost, Hansai dake ta kallon kudin hannun tsohon tace "Kawai a daura tunda ga sadakin a kusa" Jibril yace "Wannan taimako ne me girma xaka yi Alhaji, Allah ya saka da alkhairi, tana dawowa daga gantalin da ta tafi sai a wanketa a kai maka gida kawai" Abuturrab ya kalli mai unguwa after gathering much courage yace "Ni xan aureta, sai ka xama waliyi na" Ba Hansai ba kowa na wajen sai da yayi mamaki, mai Anguwa wanda da alama dama bai yi na'am da daurin auren da wannan tsoho me suna Alhaji Saleh ba yace "Toh Madallah Aliyu" Tsohon ya d'an ja tsaki ya mayar da kudinsa aljihu, A nan take kuma aka daura auren Abuturrab da Jiddah a kan sadaki dubu arba'in, su kenan kudin jikinsa da ya ciro daxu bayan ya siya ma Umma drugs, Xaune kawai Abuturrab yake a wajen amma gaba daya he is absentminded and lost ga wani sanyi da yaji yana shigarsa kamar xai yi xaxxabi, har aka gama komai aka raba dabino da alawan da aka siya a nan cikin layi, Hansai dai ta kasa gane ko murna xata yi ko akasin haka, Ya xa ayi babban mutum kamar wannan gashi har yace jirgin da bata ta6a gani ba duk tsawon rayuwarta yake tukawa ace wai ya auri Jiddah maimakon Bibalo, tunanin hakan yasa taji wani bakin ciki ya tokareta a kirji, lkci daya hankalinta ya tashi sosai ba kadan ba ta dinga xufa daga inda take xaune, yanda take xufa haka Abuturrab ke xufan shi ma, tunda yake bai ta6a shiga rudani da confusion lkci guda irin wannan ba, wait!!! what did he just do now??? What have he done to his life?? A cikin lkci ba me tsawo ba aka gama komai, sama sama ya dinga jin albarkan da dattijan wajen ke sa masa na cewar ya rufa ma jiddah asiri duk da ga abinda aka ce tana yi amma hakan bai sa ya kyamaceta ba gashi ya taimaketa ya aureta domin nisantata daga cutarwan iliya, Abuturrab ya mika ma mutumin karshe hannu sannan ya mike a hankali ya nufi motarsa walking slowly kamar mara lafiya, yana shiga motarsa ya tada motar ya kashe Ac don sanyi yake ji sosai ya fara driving ya bar layin, ikon Allah ne kawai ya kai sa gida lafiya cause blurry ya dinga gani ga kansa dake juya masa ya dinga ganin komai double, ko parking din kirki bai iya yayi ma motar ba ya sauka ba tare da ya rufe ba ya shiga ciki mai gadi ya bi sa da kallo, direct dakinsa ya nufa ba tare da ya kalli kowa na parlon ba, duk suka bi sa da kallo, Aunty ta kalli Ummi, Ummi dai bata ce komai ba, Aunty ta mike ta bi bayansa da sauri, cikin bargo ta gansa ya lullube har kansa, da mamaki tace "Are you okay Aliyu???" Bai iya ya bata amsa ba, ta sauke bargon a hankali ganin he is shivering so much, da mamaki tace "Baka jin dadi ne?" Ya gyada mata kai kawai, tace "Subhanallah, let me switch off the Ac"
Nan na kawo karshen free pages na *Jiddatul Khair* in sha Allah, and the paid book is 500 Via
👇🏻
3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah.....
And u show ur evidence of payment via my WhatsApp Number 👉🏻 07087865788.....
Plss just WhatsApp ban fiye son phone call ba, and i am begging you don't come to my DM without any concrete reason, it's tiring wllh....😓😰 just come, patronize, i save ur number, and i add u to my groups... Shikenan
Thanks and i love you all as u patronize.💖
Kashe Ac din dakin Aunty tayi ta sauke curtains ta dawo ta xauna kusa da shi tace "Sannu, ko dai a kira Dr? amma daga ina kake haka?" Girgixa mata kai kawai yayi don bai jin ma xai iya magana, ta mike ta fita don daukan wayarta ta kira Dr din, Tana cikin dialing number likitan ta kalli Ummi tace "Baya jin dadi ne wllh" Ummi tace "Ikon Allah, to Allah ya sauwake" Aunty na gama kiran likitan ta koma daki..... Abu kamar wasa Abuturrab har da karin ruwa, he was so weak and sick, sae bayan isha family Dr din nasu ya bar gidan. Karfe goma da yan mintuna wayar Abuturrab dake gaban mirror din dakin Aunty ya fara ring Aunty ta dau wayar ganin Ahmad ne ta kyabe baki ta dauka don tun daxu yake kira, bayan ya gaisheta yace "Ya tashi Aunty?" A takaice tace "Aa..... ko minti sha biyar ban yi da fitowa daga dakin ba" Ahmad ya d'an yi shiru sannan yace "Amma jikin da sauki?" Tace "Eh toh amma har yanxu his temperature is high" Yace "Toh Allah ya sauwake, likitan ya tafi?" Aunty tace "Ehh" Yace "Toh Allah ya bashi lafiya" Aunty tace "Ameen" daga yayi mata sallama ya katse wayar, Aunty ta ajiye wayar ta koma bangaren Abuturrab ta bude kofar dakinsa, tsaye taga Ummi a dakin kusa da shi tana kallonsa, Aunty tace "Ya tashi ne?" Ummi ta juyo tace "Aa" Aunty ta karasa kusa da shi ta xauna ta sauke duvet din tana kallonsa ta kai hannu goshinsa, taji har sannan da xafi, juyawa Ummi tayi ta fita daga dakin... a hankali Abuturrab ya bude idonsa da yayi masa nauyi sbda ciwon kai, ji yake kamar ana sara masa goshinsa, Aunty tace "Sannu son, ya jikin?" Bai iya ya bata amsa ba ya sake lumshe ido, tace "Baka ci komai ba, in hado maka shayi?" Girgixa mata kai yayi, bai sake bude idonsa ba har ta ga alamar ya koma bacci, ta mike ta fita daga dakin ta kulle masa kofar. Can cikin dare Abuturrab ya farka, da kyar ya mike xaune coz he was pressed, ko hasken fitilan dakin bai so don kara masa ciwon kai yake yi, ya kalli drip din hannunsa da ya kusa rabi, ya mike tsaye da kyar yana jin jiri ya kashe ruwan ya bar cannula din kadai a hannunsa bayan yyi disconnecting dinsa daga jikin ruwan, kamar me counting steps dinsa ya nufi bandaki ya shiga duk da jirin da yake ji, da alwalansa ya fito ya xauna gefen gado ya dafe kansa, ko kadan bai son tuna komai da ya faru yau, it's making him down and weak, Bude kofar dakin aka yi Aunty ta shigo ya daga kai da sauri, tace "Ka tashi Abuturrab, sannu ya jikin" A hankali yace "Alhmdlh" Ta karasa kusa da shi tana dialing number Ahmad don kiransa ne ma ya tasheta yana fara ring tace "Duk abokinka ya takurani gashi nan ni dai" Tana fadin haka ta mika ma Abuturrab wayar, ya amsa ya kai kunne yyi shiru, daga daya bangaren Ahmad yace "How are you feeling captain?" Cikin sanyin murya yace "Alhmdlh" Ahmad yace "Ka samu ka ci wani abun kuwa?" Abuturrab yace "I will take tea now" Ahmad yace "Do so plss, Dr Shariff din ya baka drugs ne?" Abuturrab yace "I just woke up ban sani ba" Ahmad yace "Ohk, ruwan yayi rabi yanxu?" Abuturrab ya kalli drip din sannan yace "Almost" Ahmad yace "Toh Allah ya sauwake" Abuturrab yace "Ameen" sallama Ahmad yyi masa ya katse wayar, ba a dau lkci ba Aunty ta dawo dakin rike da cup din tea ta mika ma Abuturrab tace "Gashi ka samu ka sha" Ba musu ya amsa, tana nan tsaye sai da ta tabbatar ya sha shayin sannan ta amshi cup din ta fita, Mikewa yayi ya koma bathroom ya wanke bakinsa ya fito ya dau pray mat ya shimfida ya hau sannan ya tada sllh, ko da Aunty ta dawo dakin ganin yana sallah ta koma dakinta, ya jima xaune kan darduma daga bisanni ya mike a hankali ya dauke darduman ya koma kan gado, mayar da ruwan yyi ya kashe wuta ya kwanta ya lullube jikinsa yana jin kamar wani sabon xaxxabin xai sake rufesa. Da asuba duk yanda Abuturrab ya so tashi yin sllh kasawa yyi, Karfe shidda da yan mintuna Aunty ta shigo dakin, ta kunna wuta ta karasa gun gadon ta cire duvet din da ya rufe har kansa da shi, bude ido yyi a hankali, tace "Ka samu kayi sallah kuwa?" Girgixa mata kai yayi, tace "Da ka daure ka tashi, amma how are you feeling now?" A hankali yace "Alhamdulillah" mikewa yyi xaune, tace "Let me get u something to take sai ka sha magungunan idan ka idar da sallahn" Fita tayi dakin, yayi karfin halin tashi ya cire ruwan da ya rage kiris ya kare sannan ya shiga bandaki, yana sallah ta dawo dakin, ta ajiye masa cup din shayi da ledan drugs din ta nemi waje ta xauna har ya idar da sallahn sannan ta sa ya dau shayin da ta hada masa ya sha.... Karfe goma na safen Abuturrab na bedroom dinsa hannunsa rike da bowl din pepper soup, Ummi ce tsaye dakin tana kallonsa, ko minti biyar ba ayi da fitan family Dr dinsu daga dakin ba, bayan few minutes ya d'an kalli Ummin tasa, ji yayi gabansa ya fadi sosai, a hankali yace "Why don't u sit Ummi?" Ummi tace "Am okay here" Ba tare da ya kalleta ba yace "Aunty fa?" Tace "She is in the kitchen" Bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da shan pepper soup din hannunsa a hankali, Ummi tace "Kun yi magana da Abban naka? Ya kira kana bacci daxu" Ya gyada kai yace "Ehh Aunty ta bani mun yi waya" Tace "Ohk" Juyawa tayi ta fita dakin ya bi ta da kallo, lkci daya jikinsa yyi sanyi, ya ajiye bowl din hannunsa ya jingina da gadon da yake xaune, he needs someone to talk to about this unfavorable issue, he needs to share this with someone that's understandable, who will this be, rike kansa yayi yana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.... Xuwa yamma Abuturrab ya d'an samu saukin ciwon kan dake damunsa, ya fito wanka kenan yana goge kansa da karamin towel din hannunsa aka bude kofar dakin, Ahmad ne ya shigo dakin hade da sallama, ganin Abuturrab a tsaye, ya tsaya daga bakin kofar ya rike waist dinsa yace "This is better, and I'm glad i saw u this way" Abuturrab bai ce masa komai ba, Ahmad ya d'an yi murmushi yace "Medical report dae ya xama na gaske yanxu kenan" Abuturrab ya kallesa yace "Ka taho min dashi?" Ahmad ya karasa ya xauna gefen gado yace "How are you feeling now?" Abuturrab ya nufi gaban mirror a hankali yace "Alhamdulillah" Ahmad yace "But dama baka jin dadi ne, coz naga sickness din yyi striking dinka so hard, you look lean...." Ta madubi Abuturrab ke kallonsa bai ce komai ba, Ahmad yace "Ba shiru xaka min ba, i left my work for ur sake na biyo train" Abuturrab yace "Da baka dawo ba ma ni xan kiraka ka dawo, i have been expecting you" Ahmad yace "Hope you are feeling much better now?" A hankali Abuturrab yace "Not at all.... We need to talk Ahmad" Keenly Ahmad ke kallonsa cause he can see how worried and confuse he looks, Mikewa Ahmad yyi ya karasa kusa da shi yace "Tell me what's wrong Captain?" Kasa ce masa komai Abuturrab yayi, Ahmad ya koma ya xauna yace "To ka gama shiryawa mu yi magana" Yana kallon Abuturrab har ya gama shiryawa ya dawo ya xauna gefen gadon shi ma, Ahmad yace "Me ke faruwa tell me" Abuturrab ya shafa kansa a hankali kamar me tunanin ta inda xai fara, bude kofar dakin aka yi Aunty ta shigo rike da bowl din fruit salad biyu, murmushi tayi ganin Abuturrab tace "Alhmdlh, son jiki yayi kyau, you are looking much much better and healthier now" Abuturrab yyi murmushin karfin hali bai dai ce komai ba, ta karasa ta mika masa Bowl daya na fruit salad din tace "I made this for u" Amsa yayi yace "Thank you Aunty" Kujeran dakin ta xauna tana shan fruit salad din daya bowl din hannunta tace "Abbanku ma ya kara kira yanxu nace da sauki, shi ma duk ya damu" Ahmad da ya d'an hade rai yace "Ina yini..." Ba tare da ta kallesa ba tace "Lafiya lau" magana ta ci gaba da yi da Abuturrab dake shan fruit din hannunsa, Ahmad ya mike yace "Alright Captain, sai ka xo can gidan namu, i will be leaving now" Abuturrab ya kallesa da sauri, ta gefen ido Aunty ta harari Ahmad tana ci gaba da shan fruits salad dinta, Abuturrab yace "Ai nace maka nima xan fita Ina son in sha iskan waje" Ahmad yace "Okay ka sameni mota idan ka gama, i will wait" daga haka yace ma Aunty "Sai anjima" ko tankasa bata yi ba har ya fita ya kulle kofar dakin, Aunty tace "Yaushe har ka farfado xaka wani fita Abuturrab? Shi Ahmad din bashi da hankali ne ko don ya xo lkcn da jikinka yayi kyau, kana fama da kanka ina wani fita idan ba neman magana ba?" Abuturrab ya shafa kansa yace "Aunty na gaji da xaman gidan ne, ni nace masa mu fita, ba shi ba" Ta tabe baki tace "Toh ai shkkn...." Bayan kusan minti ashirin Abuturrab ya fita xuwa gun Ahmad bayan ya sanar ma Ummi xai je gidansu Ahmad din, Sbda yanda idonsa ya fada yasa shi saka bak'in spec dinsa, kananun kaya ne jikinsa wani sanyayyen kamshi na tashi jikinsa, kana ganinsa kasan he is still recovering, he still looks weak, Kallonsa kawai Ahmad yake yi har ya karaso ya shiga front seat, Ahmad na kallonsa da d'an damuwa yace "Wai malaria ne ya kamaka haka Captain, ka rame fa, kamar wanda yayi sati a kwance" Captain bai ce masa komai ba, Ahmad ya tada motar suka bar layin. Karfe biyar da few minutes suka isa gidansu Ahmad, Abuturrab yace "Ka bar motar a waje ba dadewa xan yi ba xaka maida ni gida ynxu" Hakan yasa Ahmad yyi parking a waje, Abuturrab ya bude motar ya sauka ya nufi cikin compound din, Ahmad ma ya sauka ya rufe motarsa ya bi bayansa, sosai gaban Abuturrab ya fadi bayan ya shiga compound din sun yi ido hudu da Jiddah dake tsaye ta jingina da bango a bakin tap din dake cikin compound din ta tara bucket.....
Abuturrab